x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

YANZU YANZU : Yan Najeriya za su sake fita zanga zangar tsadar rayuwa da yunwa ranar 1 ga watan Ogustan 2025.

  • Blog
  • DAILY NIGERIA
  • YANZU YANZU : Yan Najeriya za su sake fita zanga zangar tsadar rayuwa da yunwa ranar 1 ga watan Ogustan 2025.
Start ads

YANZU YANZU : Yan Najeriya za su sake fita zanga zangar tsadar rayuwa da yunwa ranar 1 ga watan Ogustan 2025.

04 Jul 2025 YANZU YANZU : Yan Najeriya za su sake fita zanga zangar tsadar rayuwa da yunwa ranar 1 ga watan Ogustan 2025.
After Image Ads

YANZU YANZU : Yan Najeriya za su sake fita zanga zangar tsadar rayuwa da yunwa ranar 1 ga watan Ogustan 2025.     

 

       Kungiyoyin fararen hula a Najeriya sun sake shirya zanga zangar lumana domin yaki da tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.

A wata sanarwa da Sakataren gamayyar kungiyoyin fararen hula masu kishin Najeriya Kwamared Amin Al- Aminu ya fitar a daren Juma’a a Abuja ,yace za’a fita zanga zangar ne a ranar 1 ga watan Ogusta na shekarar 2025.

Arewa  Novels ta rawaito cewa a shekarar da gabata ta 2024,a ranar 1 ga watan Ogusta, yan Najeriya suka fita zanga zangar tsadar rayuwa,da rajin tabbatar da shugabanci na gari, a tsawon kwana 10 saidai ba’a cika kwanakin ba zanga zangar ta rikide ta koma tarzoma da sace sace keyan gwamnati da na jama’a da lalata dukiyoyi.                         

           Zanga zangar ta 2024 ta kuma janyo rasa rayuka da dama da jikkatar wasu.

Saidai Sanarwar ta kungiyoyin fararen hula masu kishin Najeriya sunce a wannan karon sunyi tsari mai kyau,yadda za’a kaucewa abinda ya faru a shekarar ta 2024.

Arewa Novels ta rawaito cewa kungiyoyin fararen hular sun fara raba wasu takardu ga yan Najeriya dake nuna cewa zanga zangar babu fashi.

A cikin takardar sun rubuta cewa babu Komai a Najeriya sai YUNWA,da RASHIN AIKIN YI da  RASHIN MAKOMA MAI KYAU.

Sannan suka kara dacewa ,a yayin Zanga zangar zasu nusar da gwamnatin Bola Tinubu da gwamnonin Najeriya cewa yan Najeriya na rayuwa ne karahin mulkin yan Jari hujja da Kuma Iko na yan ta’adda.                 

           Haka zalika sun nemi da lalle Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo da tallafin man fetur da Darajar naira da yaki da cin hanci da  rashawa sannan ya bude iyakokin Najeriya da aka rufe tun watan Ogusta na shekarar 2017 da gyara tattalin arzikin kasa da sauransu.

Har yanzu hukumomin tsaro ko bangaren gwamnatin tarayya basu ce Komai ba kan yunkurin sake fita zanga zangar.         

End Ads

0 Comments

Leave a comment

Your email will be kept private.