Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 HALACCIN SARAUTA 1  benaxir  September 18, 2015  Hausa Novels  167 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya yar kimanin shekara ashirin da daya zaune adakinta wanda yasha kaya,duk abinda ya’mace budurwa zata bukata toh akwai shi acikin dakin aliya takardune agabanta dakuma hotunan mutane wanda take bi daya bayan daya daga dan zaman da ni benaxir nayi ina lekenta nasamu labarin cewa Aliya yar asalin garin yombi ne wata babbar masarauta da ake darajar mulkin sarauta,tanada shekara sha biyar sarkin yombi ya bukaci akashe duk masu hannu da reshawa wanda acewarta sarkin yabada sakon akashe mahaifinta mussaman acikin wannan hargowan don mahaifinta yakasance shine galadima kuma yana kawo musu matsala a fadan garin, duk wani abu marar kyau mahaifin aliya hassan adamu yana kokarin yafidda hakkin musulunci dakuma hakkin mutane, hakan yasa sarkin garin yabukaci da akasheshi cikin saa aka kashe hassan adamu da matarsa alokacin aliya tana makarantan kwana na yan’mata dawowarta ta tarar da mai aikinsu wanda yabata wani karamin akwati acewarsa ana gobe mahaifin zai rasu yace abata, tayi kuka sosai harta bude akwatin anan tasamu takaranta tarihin komi mahaifinta dama yasan zaa kasheshin donhaka yamata bayanin komi, dawannan aliya tayi alkawarin saita rama wa iyayenta abunda aka musu, barin garin tayi ta tafi abuja gurin yar mamanta inda ta kammala secondry dinta a shekara sha shida, sannan tasamu admsn a g.s.u ta takaranta sociology na shekara hudu sannan taje tayi service dinta,ta kammala komi tanada shekara ashirin da daya, duk wannan tsawon lokacin aliya bata saurayi namiji da sunan soyayya ba acewarta zaibata mata duk wani plans din ta, yar mamanta wacce tazauna agunta tasan da maganan ramakon da aliya takesonyi kuma tagoya mata baya duk da tana tsoro anma taga ita aliyan bata tsoro, aliya agun bautar kasanta wanda tayi a benue tasamu nasaran samun wani mai suna ikem zama tayi tayu training agunsa, yakoya mata fada, yakuma koya mata duk dabaru da abubuwan dake faruwa acikin gidan sarauta, ya ilmantar da ita da basira dakuma dabaru dazata kare kanta takuma yi ramakonta cikin kwanciyan hankali, yabata littafan tarihi dakuma littafan koyan basira da littafan daya shafi sarautan hausawa harna yare aliya takaranta tsaf takoya, saan da aka samu shine aliya macece mai hazaka da basira, batada mantuwa ko kadan, kallon abu sau daya yakansa ta haddaje abu batare da ta mantaba, sai abun yasamu daidai sanadin karanta sociologyn datayi, saita zamto mai nutsuwa gurin karanta mai dan adam yake ciki yake kuma sonyi, saidata kammala komi sannan ta tattara takoma gidan antynta inda tafara shiri antynta tamata waazi anma aliya tanuna tafiyan shikadai zaisa tamutu lafiya, tabarta aranan aliya ta tattara tatafi yombi inda tasamu daki tajera kayan alatu dakomi. Dakin yana wani lungu ne wanda bakowa bane zaikawo akwai abun duniya aciki, aciki tazauna tagama hargowanta agarin yombi tana tara labarai gameda fadan sarki. Tahado kan matarsa,da yaransa daduk wani abu daya shafi sarkin, sannan tadau niiyan shiga fada, Dafarko taje tasamu matar dake kwasan bayi takai fada,taroketa datanason zama afada akan acewa ita yar kwarkwara ce anma batasan wacece ba,tanason tazauna as baiwa don tagane ahankali dafarko taki yarda anma da aliya tacire dubu goma tabata bashiri tace “kije kisaka kaya irin nasu na bayi mushiga” aliya ta amince da hakan takoma gyda tashirya tsaf tanemo wasu tsoffin kaya tasaka, sannan tanufota, matar tace “muje kishiga cikinsu karki fadawa kowa komi, kina gama nemo mahaifiyarki karki manta dani” aliya ta amince dahakan ita burinta tashiga fadan sarki takashe sarki, dahaka suka shige kafanta na dama tafara shiga fadan tare da adduan Allah yabata saa, gefen fannin bayi aka kaisu anan aka bukaci da su zazzauna, akasa suka zauna aliya tajuya tana kallon wurin dakyau takuma kalli bayin dake gefenta kowannensu kuka yake don basuda niyyan zuwa ita kuwa ko ajikinta, acan saiga matar tashigo tareda wata wacce taji tana kira da “umma uwar soro” umma uwar soro tace duk sumike acewarta zata rabasu ne zata zabi masu aiki a fada, da masuyi a kicin, da na bandaki, dakuma sauran kwarkwaraye dafarko ta umurci kowacce taje tayi wanka aka basu wani farin riga susaka, aliya tayi wankan tsaf sannan tafito tajera layin ana dubiya ne daga fatan jikinsu, sai kuma kyansu, da yanayin tsayinsu, tafara bi daya bayan daya inta yanke awani gu zakiyi aiki zaabaki uniform din aikin gurin kodata iso kan aliya takare mata kallo , aliya doguwa ce bawanda zaice guntuwa ce, saidai bakace , bakinta mai kyau, tanada hanci dan daidai da karamin bakinta sai manyan ido, hakika black beauty ce don yanayin fatarta baacika samun irin shiba, hannun hajjo tarike dasauri takalleta tareda cewa “anya ke baiwa ce?” Aliya tayi murmushi don dama tashirya wa tambayan tace “fatana na gado ne” umma uwar soro tacigaba da dubata gashin hajjo acunkushe cikin ribbon ta cire ribbon dim saiga gashi yazubo har gadon baya, ta girgixa kai sannan tace kumika mata uniform din fada, anan aka bata blue yard ne anyi dogon riga fittet, sai dankwalin dan karami hajjo daure kanta tayi duk kokarim ta cunkushe gashin abun ya gagara. Aka kaita masaukin bayi aka nuna mata katifanta, dakin ko na karnuka albarka don baida fasali ko kadan anma yata iya? Tadau niyya, tana zaune ta gefenta tafara hararanta aliya bata kulata ba can dai tamiko tareda cewa “keeh zoki wankemim kafa ga dutsen ce” aliya takalleta sannan tajuya tacigaba da abunda take yarinyan ta tashi kamo gashin aliya tayi tasake mata mari wanda ya nutsar da sauran bayin yakuma janyo hankalinsu tace “nace ki gogemin kafa” wata dake gefe tacewa aliya kiyi fa. Itace shugabanmu anan aliya bata musa ba ta tsugunna ta goge sannan tamike. Azuciyanta tace duk zansami lokacinku bata kanku nake ba yanzu,ananne umma uwar soro tashigo dakin sannan tace tunda munsamu sabbin bayi aikin naku zai canju,keh meye sunanki? Aliya tace “aliya” tohm dake aliya dake bilki zakuna isa gun yarima yusuf, sauran kuma duk kunsan wurin zuwa” ficewa tayi alokacin ita bilkin taja aliya tareda cewa “baki taki saa ba daga zuwa sai gun yarima yusuf? Bama yarima abdullahi ba. Tafdi zakisha wulakanci dan wulakancine anma yaka iya kana talaka dakai,” aliya bata furta komiba don ko bilki bata fada mataba tasan waye yarima yusuf bashi kadai ba kowa afadan saidatasani takumasam mezasu iya aikatawa donhaka tashirya wa yusuf, bilki ce tace tashi muje sunmike tsum suka nufi kicin kowacce tadauki tray sannan suka nufi fannin yariman aliya tana hankalce dakomi duk tafiyan dasukeyi,sun nufi kofan inda dogarai biyu suke tsaye akofan bilki kai akasa tace “mun isowa da yarima abinci” daga ciki yace ” kushigo” dogaran ne suka basu wuri suka shiga falone babba yasha duk wani kayan alatu dayakamata ace saurayi dan sarki yasamu. Yana kwance akan kujera, suka sunkuyar dakai suka mika abincin kan dinning sannan sukaja gefe suka tsaya, wannan ma aladace bazasu bar falon ba harsai yarima yagama cinye abincin, mikewa yayi yanufi kan dinning din yana kallon abincin daya bayan daya,bilki tana rike da serving spoon tazuba mishi friedrice din sai yamballs da ferfesun kayan ciki, zobo ma tazuba mar akofin yana danne wayarsa wacce aliya takare masa kallo, dogo ne wankan tarwada yanada faffadan kirji,manyan idanuwa wanda taga alamun kaman shine gadon gydansu dogaye ne masu manyan idanu,yanada dan dimple saidai baya murmushi wannan dama tasani tundaga farko, ayadda ta karanceshi akwai alamun damuwa atattare dashi wanda yaboye babu wanda yasani, wannan damuwan itace ke hanashi sakewa har yake matsifa da fadace fadace don baida abunyine ,loneliness yamar yawa, harya gama ci baiyi magana ba yamike yakoma kan kujera dama tashan bbc yake kalla, har alokacin yana danna waya sun tattara abincin sannan suka fito dakinsu suka nufa, aliya tadanci abincin kadan wanda su bayi suke samu dama asalinta bamai ci bane hakan yasa tazama sirir[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 2  benaxir  September 19, 2015  Hausa Novels  122 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Tazauna tana nazarin fadan da yadda komi take, takalli bilki sannan tace “inane hanyar fadar sarki?” Bilki tajata tareda cewa “zomuje” kaf saidata nuna mata hanyan fannin kowa tundaga kan sarkin isa, zuwa ga matansa gimbiya falmata da gimbiya yakolo, tace “sauran matansa biyun gimbiya ainau da gimbiya atika sun rasu, kwarkwaransa sunkai hudu wanda ni kaina bansan sunayensu ba,umma uwar soro itace tasan kome dake cikin fada ta fannin mata, Aliya tace “toh fannin yara fa? Bilki tace “yaran sarki su sha takwas ne, bakwai suna karatu akasan waje, sauran suna zaune anan,suma don su sukaki tafiya,anan munada yarima yusuf,yarima abdullahi,yarima shehu,sai fulani hauwa, fulani hafsat, fulani zainab, sauran kananun yarane, ihsan,isham,ilham,ashfaq,,ashraf, manyan daga kan abdullahi, yusuf shehu,zainab ,hauwa hafsat,kowanne nada bayinsa dakuma fanninsa. Kananun ma sunada fanninsu agefen na iyayensu, in batun hali ne kuma yarima abdullahi shine ya gado halin ubansa na dattako, yarima yusuf yanada wulakanci bar ganin yau yamana shiru gobe zai iya watsa mana wulakanci, amata kuma zainab itace ta kirki saidai tacika fada, hafsat da hauwa kuwa girman kai, a tsakaninsu ma rikici suke, saboda iyayensu daban ne, da hafsat, zainab da yusuf , ilham , ashfat uwarsu daya wato falmata, yayinda abdullahi, shehu, hauwa,ashfaq,ihsan,isham uwarsu daya, wato yakolo, sauran na kasan wajen yayan atika, da ainau ne bansan sunayensu ba dai, anma babban dan sarkin shine yusuf, sai abdullahi, sai wani akasan wajen Tana bayaninta aliya tana kallonta can tacigaba dacewa kuma kinga anan falmata da yayanta su suke mulki donhaka kinsan kowa yafi bin inda akwai tsoka nafi ladabi wa yan dakin falmata kuma nafi samu” aliya tace “anma ai kinashan wulakanci” bilki tace wannan dole musha. Haka sukayi ta tadi har dare sannan suka koma kai abinci sunsameshi zaune yana waya suka jera abincin akan table sannan suka ja suka tsaya, aliya najinshi ya idar da wayansa tsaf sannan yataho kan dinning din bude abincin yayi cikin rashin damuwa yanuna aliya “ke zonan!” Ta matso ahankali kanta akasa daukan abincin yayi ya watsa mata!, saiga miyan egusi. Wanda yasha kamshi tas ajikin aliya, bata dago kanta ba bata kuma furta komi ba, bilki ce dasauri tanufo gun ta sunkuyar dakanta akasa tana bashi hakuri itama daukan sakwaran yayi ya watsa mata, sannan yaja tsaki yabar musu gun, abinda aliya ta tsana arayuwarta wulakanci, lalle yanaso taci kaniyanshi, baya cikin lissafinta anma karya bari tasashi aciki don zaiga ba daidai ba, daukan tray din tayi tafice, bilki kuma ta tsaya bada hakuri, cikin zafin rai yace takoma takira aliya, shi acewarsa akan me zata tafi bazata rokeshi ba,akan me bazatayi ladabi agareshiba,bilki dasauri tashigo dakin inda tasami aliya tacanja uniform tasaka wani, dankwalin kanta take daurawa,tace “yarima yana nemanki meyasa zaki tafi baki bashi hakuri ba?” Aliya cikin rashin damuwa tace “saboda bazan tsaya jikina a bace agunba” toh dai kizo muje kibashi hakuri” aliya tayi shiru tabita suka koma wanda yana zaune akan laussasan kujerarsa yahade kafa daya kan daya, gashin kansa ya kwanta luf luf sunkuyar dakai sukayi akasa, bilki tafara bada hakuri anma aliya bakinta tsit” bilki tafara tunkude aliya domin itama tayi magana anma aliya kam taki cewa komi, can dai yace “ke dago kanki naganki”aliya bata dago ba bashiri bilki taja kanta wanda saida dankwalinta yafadi akasa gashin kanta yaxubo yarufo mata kai, cikin rashin damuwa yakalli bilki tareda cewa “aina kuka samo wannan bakan? Kije ki aske mata gashi banison ganin gashi, balle yazubemin a abinci, aliya wani murmushi tayi wanda itakanta sai Allah sukadai sukasan meke ranta, ni kaina benaxir na tausaya mashi sosai,ficewa sukayi bilki jikinta na bari, suna shiga dakin tace don Allah yazamuyi?” Aliya tacire kanta tareda cewa “aske zuwa yanda yakeso”bilki taji. Hauahi har ranta anma babu yadda ta iya tarage gashin aliya yadawo dan daidai yanda sauran nasu yake, sannan suka zauna, bilki tayi mamakin ganin aliya bata damuba,anma aliya tace mata “ke indai gashin kainane kibashi sati biyu zakiga yadda zai dawo” tadai bari aranta dahaka suka kwanta bacci, washegari dassasafe suka nufi fannin sa yana bacci donhaka saida suka jirashi ya idda baccinsa,sannan suka shiga yayi wanka abincinsa suka basa, sannan suka hau gyran dakin, suka share sukayi goge goge sannan suka gyra mishi lallausan gadonsa dakin tuni yagume da kamshi alokacin harya fice da dogaransa, sunfito kenan aliya rike da roban dasukayi goge goge kanta akasa tanadan sauri, sai jitayi tabugi mutum, tuni wani dogari yayo kanta zai maka mata sandanshi anma cikin zafin murya taji ance “rabu da ita” bai juyo yakalleta ba yaci gaba da tafiyansa bilki cikin tsoro tace “waike meye matsalanki? Yarima abdullahi nefa wannan kinci saa ba yayan bane da yau saikinyi tsallen kwado” aliya taja numfashi tabi yadda yabi dakallo sannan suka fice, Umma uwar soro ce tabukaci dukkan bayi masu aiki dasu hallara wanda aliya tashiga cikinsu tana sauraro, cikin izza tace ” munsamu labarin akwai wanda basa aikinsu dakyau, yau yarima yusuf yamin bayani akan yanason canjin masu masa aiki, donhaka kuzo kudauki hukuncinku kafin naci gaba da magana bilki da aliya ne suka fita inda suka mike akabasu bulala hamsin hamsin, gwara bilki tasaba anma aliya tunda uwarta ta haifeta zunguri bata taba sha mai lafiya ba, nan da nan jikinta ya kumbura fatanta yattatashi, dakyar akayi daki da ita, zazzabi ne mai zafi yarufeta wanda saida umma tanufota tareda cewa duka hamsin kacal shine kike mana ciwo? Kimike yanzu a kicin zakina aiki, agun zaki dauwama, bilki har hawaye tayiwa aliya anma babu yadda ta iya , aranar saida aliya tanufi kicin yadda taga girman tukwanen saida cikinta yakada saura kadan ta tsure, wasu manyan tukane ne. Dasu ake girkin gydan, ga kicin din uban zafi, haka dai aliya tadaure, iyakacinta kicin sushiga dasafe sushiga darana suzo kuma sushiga daredare ciwon baya da ciwon jiki yasaka aliya takar ramewa, takara dawowa baka, idonta yakara fitowa, tuntana shan wahala har tasaba, Watarana tana zaune a kicin babu tunanin da batayiba, yakamata tabar kicin dinnan takoma wani gu daban inbahakaba zuwanta yazama na banza, jakadiyan gimbiya falmata ce tanufo kicin din bashiri kowa yamike yanuna ladabinsa, tabi su daya bayan daya sannan ta je wa aliya “kizonan” aliya tabita basu nufi ko ina ba sai fannin falmata, macece wacce bata wuci arbain ba,fara ce kyakyawa saidai daga kallonta kasan ba karamar makira bace,cikin kissa ,kissisina da izza take rayuwanta, zuwan aliya yasa takalleta sama da kasa sannan tacewa jakadiya wannan kika samo? Jakadiya tace “itace tayi saura a masu ilmin bayin” falmata takalli aliya sannan tace “da alamu kingaji da kicin din?” Aliya wacce ta durkusa kanta akasa tace “ae ranki shi dade” falmata tace “zan aikeki karki bude aikan inkinkai lafiya toh zaki dawo gefena da aiki” aliya tace “komi kikace ranki shidade” jakadiya ce tamika mata takarda tareda cewa” zaki kaiwa umma uwar soro” takarbi takardan sannan tafice harta kusa isa zuciyanta yaraya mata data bude takaranta budewanta taga anrubuta “ki kasheta” abun ya tsorata aliya, metayi wa gimbiya? Babu! Toh gimbiya na gwadata ne duk yadda akayi, tunda taji tace “itace tayi saura a masu ilmin bayin” gwajine! Donhaka ta nannade takardan tanufi gun umma uwr soro wacce tabude takaranta cikin izza tamike ranta abace tace kinsan mekika kawomin kuwa? Kinfa kawomin cewa za’aje akashe gimbiya falmata ne, aliya aranta tace “bahaka bane tabbas gwajine” waya baki ? ” babu bansan wayeba” babu yadda umma batayiba har kiran dogarai tayi suka dirke aliya taji jiki sosai anma taki magana, candai saiga jakadiya tazo takarbeta fannin falmata takaita, falmata tayi murmushi sannan tace “kinwuce gwaji” donhaka na amince dake zan ci gaba da aiki dake, zakibar kicin kidawo fannina, sannan ungo wannan tamika mata wani kullin magani, inaso kije kisaka a abincin da zaakai fannin abdullahi naji labarin ke kike zubawa”aliya tace “komi kikeso rabki shidade shizanyi” dahaka tamike tafice dakinsu tanufa tana tunani, lalle makirci da duk wani kissa da izza yakare a maitan son mulki wato tasan danta yusuf baida hankali tunda shaye shaye yake bazaa bashi mulkin garinba gwara takashe abdullahi ahankali sai shehu, oh Allah, dahaka har yamma tayi tafita da kullin jakadiya nabiye da ita tana leka ta, ahadin abincin yamballs ne saita zuba, tana zubawa jakadiya tafice, bashiri taxubar da wannan kwabin sannan takarayin wani, tashirya tsaf aka kaimishi, sannan tanufi fannin falmata tana durkushe kanta akasa sannan tace “na zubo ranki shi dade” falmata tayi murmushi sannan tace “kullum zakina sakamishi, maganin tsotse jinine, zaisamishi karamin hauka, kinga idan yahaukace bawanda zai karbi mahaukacin sarki gwara dan shaye shaye,” aliya tayi murmushi sannan tace ” gidan shikenan har abada yazama naki gimbiya, mata mai ran karfe, wanda yatabaki yataba zakanyan jeji mai cutar hauka, sai ke mata kadai azuciyan sarki, daga mulkinki babu nakowa yayinki bamai karewa bane, takawa lafiya gimbiyan sarki, uwar sarki kakan sarki,” falmata takalleta sannan tace “kkigama aikin ki na kicin daganan kindaw[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 3  benaxir  September 20, 2015  Hausa Novels  135 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya tayi murnushi irin na wanda yadade yana begen abu yazo yasamu daga baya,tamike tsum tafice kicin,kullum haka take saita kulla maganin inta kulla jakadiya na kallonta tana komawa sai tajuye tahada wani, ahaka zuwa ran da tacika sati daya tadauko gyadan suya tana sane cewa yarima abdullahi bayason waken suya,yakan kwantar dashi ciwo tasan hakane a binciken datayi tun kafin isowanta fada,tasan matsalan kowa da kowa, donhaka acikin hadin alale tasaka garin waken suya ,aka kaimishi ,ta isa fannin falmata adaidai lokacin jakadiyar ta tashigo da gudu tana murmushi, ta sunkuya kanta akasa tace “gimbiya ga yarima abdullahi acan rai agurin Allah” falmata takalli aliya sannan tace “aikinki na kyau sosai dahaka zamu cigaba ciwo dai takamashi yanzu” mikewa tayi don kissa ta nufi sashen yarima abdullahi inda ake dubashi,tasamu yakolo na gun itama tayi tagumi duk tadamu, likitan yagama dune dubensa sannan yakalli yakolo wacce tamai alamu dayayi shiru karyafadi ko ma menene, falmata dasauri tace “meya sameshi? Dan masoyina?” Likitan yayi murmushi sannan yacev”zazzabi me kawai ba tsanani” falmata takalli idonsa tabbas tasan karya yake donhaka tayi murmushi sannan tace “toh Allah bashi lafiya barin koma anjima zan dawo” fitanta tawuce fanninta anan ta kalli jakadiya tareda cewa ” kema kingane karyane ko?” Jakadiya tace “ae wlh gimbiya boye miki sukeyi basuso kisani” falmata tayi dariya sannan tace “makirai dukkanku saina kaiku kasa” Aliya na durkushe a gefe itadai kanta na kasa tana sauraren mesuke fada, can jakadiya ta dan muskuta sannan tace “yazakiyi da wazirin toh?kinsan shiyake saka sarki yayi dole,abu kaman asiri,magananshi kadai sarkin yakeji,” falmata taja tsaki sannan tace “bar wawan mutum,gashi yanata janyo wa mutane balai, mutane nawa wazirin yakashe anma kowa naganin laifin sarki, tundaga kan galadima hashim, har kan barade yusuf, ” aliya wacce kanta ke kasa saida gabanta yayi mummunan fadi, owwh dama ba sarki bane ya kashw babanta? Waziri ne? Lalle tana bukatan karin bayani kuma tasan jakadiya ce kadai zata gaya mata donhaka ta nutsu dai har lokacin da falmata zata kwanta sannan suka fito suna tafiya jakadiya nagaba ita tana baya, sannan tace “ranki ya dade inada tambaya” jakadiya tace “mu isa sashinmu tukum”, sashin jakadiya da yanuwanta yafi na bayin dan fasalin gani da kyau,tana durkushe akasa jakadiya tace inajinki, aliya ta numfasa sannan tace “bayanin kisan da waziri yakeyi, inaso kidan karamin bayani, inada masaniya akan yadda zaayi” jakadiyan ta kalleta sannan tace “bakida kai, kina baiwa mezaki iyayiwa wazirin garinnan? Ko shi sarki ya yakare? Anma tunda kinason ji shikenan, akwai lokacin da yafara hakan, yasamu saran kashe duk wanda yabata masa rai, hakan yasa sarki hada meeting akan zaa saukeshi abawa galadima waziri tunda yafishi adalci da gaskiya, anma wazirin yayi hada hadansa yasa aka kashe galadiman, anzo zaa daura barade ma nan yakara kashe barade toh kinga bawanda zaice mutuwa daga Allah kowa yasan akwsi dalili” aliya gabanta na tsananta fadi. Tace “nagode insha Allah zannemo mana hanyan tsira” jakadiya dai jinta take don bata yardaba, ta girgiza kai sannan tace “munajira” Fitan aliya fanninsu tanufa, lalle yakamata tabar fada duk tsanani saidai anya zaa barta? Baridai ta saci hanya, shigan kamala tayi kaman bakuwa ce tazo tasami kayan agun bilki wacce tamata kashedi kala kala, sannan tafice gydanta tanufa tabude dakinta har gurin yayi kura, wanka tafara shiga tagoge jikinta sosai sannan tanemi riga da skirt na atamfa yakamsta sosai,tayi sallah sannan tuni tajawo littafanta da abubuwan zane zanenta tafara tunanin yadda zatayi da waziri toh ashe inhakane zaman fada baikamata ba, yakamata tafice takashe waziri tukun, saidai baridai taga mezai faru, tana zaune har bacci me nauyi ya kwasheta tayi bacci sosai sannan tashinta tacigaba da zane zanenta tayadda zata ci karo da waziri. Gani tayi dare yayi bata damuba dama tariga data yiwa jakadiya bayanin zataje ganin wata kakanta, inbaa gantaba, kuma ta amince bilki ce dai hankalinta yatashi sosai.l, karfe tara na dare zaman dakin ya isheta tuni tanemi dogon abaaya tasa sannan tafice tana tafiya tana danna wayanta wani hotel ne wanda akwai restaurant aciki tunda tazo garin kafin ta isa fada agun takecin abinci,shiganta tazauna tayi ordering indomie kawai,tanajira don saisun dafa kafin sukawo agefen gun taji hayaniya a hall mikewa tayi tanufi gurin ga mamakinta ganin yarima yusuf tayi, wanda kwalban giya ne ahannunsa babu dogari, gashi yafara layi aliya taja tsaki tareda cewa “useless” harzata tafi taga mutumin dake aiki a hotel din yana jan yusuf akan yafice yusuf sai zuba hauka yakeyi yana surutai, abun yaci mata rai. Tanufi gun shi sannan tace “yarima yusuf ne don Allah kubarshi” mutumin baice komi ba yatafi tajuya zata tafi yusuf yakamo hannunta ta mugun tsorata anma dai tadanne azatonta yaganeta ne, anma tunanin yana cikin maye hala ne inyaganen yaki saketa donhaka ta fizgeshi suka bar hotel din ,abincin da bataci ba kenan, fitowansu tasakashi akan hanya takare masa kallo, asalin dolo ne, no wonder dan fari ne ashe dole yayi wawanci tace cikin rashin kulawa da rashin damuwa ” kawuce katafi gida, wani dolonci ne yasa kafito ba dogarai?yakalleta baice komi ba can kawai yafara yunkurin amai, amai yakwara mata haushi taji kaman takamashi da duka. Taja wani tsaki sannan tace saikayi ai , juyawa tayi tana tafiya harta isa kofan gidanta juyowan dazatayi taga mutum ashe biyota yayi babu yadda batayiba yaki,tashigar dashi tareda cewa “wlh ba yarima ba ko sarki kake inkamin amai anan duka zaka sha” saiyace “nifa dan sarki ne kuma sarki!” Bata kulashiba ganin baya hayyacinsa toilet tashiga tacanja kayan jikinta takara wani wankan sannan tace “kashige kayi wankan kaima, abun haushi bacci tasamu yafarayi wani salati tayi tared[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 4  benaxir  September 21, 2015  Hausa Novels  122 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR ruwa ta debo ta watsa mishi,tuni yafarka sannan tace “wuce muje” har toilet takaishi tazuba mar ruwan zafi sannan tarufo tafito, bayan minti goma saigashi yafito yana bin bango sanye da jallabiyan mata, abun yaso yabata dariya saikawai yafada kan gadon, wani matsanancin bacci ne ya kwasheshi yadda taga rana haka taga dare tsoronta karya farka yamata wani abu, saida asuba bacci barawo yakwasheta, karfe goma daidai yafarka ga mamakinsa yaganshi akan gado lullube da bargo, tunanin meya faru yafarayi, yatuna wani abun yamanta wani anma yamike ganin jallabiya ajikinshi ya tsorata kodai yazo daki da karuwa ne baisaniba?” Bashiri yafara neman kayansa anma baiganiba nan yahango aliya akan kujera saidai baiga fuskarba saboda gashinta yazubo tagaban fuskan, yaje ahankali yabude bakace sedai bakinta mai kyau ne, yabayyana kalan fatarta da kyan fuskanta, yakare mata kallo gabanshi na tsananta faduwa numfashinsa ne yahade danata hakan yasa ta farka dasauri ganinshi akanta yasa tace “meye haka? ” yadan bata rai sannan yace ” kinsan da yarima kike magana ko, akanme zaki kawoni nan, ko nina kawo kaina ? Bani kayana nasaka, takalleshi ta tabbata yadawo hayyacinsa sannan tamike tsakar gyda tanufa ta tattaro masa tareda cewa “kayi amai ajikinsu na wankema, sannan nan gaba in zakace shaye shayenka ka tattari dogaranka,my plan is not saving some kind of soul” abun ya harzukashi anma yashare toilet yashiga yasaka kayan sannan yafito baiko cemata uffan ba balle nagode yafice, taja tsaki tareda cewa “halinsa sak uwarsa” nan ta harhada abunda zata hada sannan tamaida kayan bayinta tarufo gidan saboda tassn yagane gidan karyace zaimata wani mugunta. Fada takoma inda ta tsinci bilki cikin tashin hankali tana cewa ina kikaje? Aliya tace “gaysuwa” bilki taja tsuka tareda cewa “yanzu da umma uwar soro tazo ta yi kirge fa?” Ganin bilki zata dameta yasa aliya tafice tabarta, fannin falmata ta isa bayan anmata iso tagayamata tadawo, dawowanta daki taji bilki nafada itada wata baiwa agefe. Ai yarima bai kwana agyda ba, jiya anata nemenshi harta wayoyinsa yaki dauka,ko yakoma shan giyansa da neman mata, sunata surutai anan aliya tatuna ashefa yaga fuskanta, donhaka dole tayu kaffa kaffa da shi acikin gidan, hakan kuwa tayi suka koma yin wasan boye boye duk inda taganshi canja hanya take Watarana dasafe abisa aladan gidan matan sarkin zasu hadu suje gaida sarki dasu da yaransu insun dawo kuma, sai suma maaikatan sumika nasu gaysuwan gun matan sarki, ahanyan dawowa falmata tace anemo mata yarima yusuf, shiganta bayan wasu mintinai saigashi yashigo yazauna akan kujerar dake kallon nata, “inaso ka kasa kunne kasaurareni” tafada cikin rashin faraa, “shaye shayenka yafara yawa, jiya abuge aka kawoka. So kake kasakani a magana? Wazaiba wa dan giya sarki? Yakamata ka nutsu wlh tun kafin lokaci yakurema,” baice komi ba yana kallon hanyan kofa wanda jakadiya ta aiki aliya tashigo da tray, ganinta dayayi yatuna ta cak, itama tana ganinshi saidata tsorata anma tayi kaman ba ita bane ya ce “KE! Zonan,” ta iso kanta akasa “dago fuskanki” tadago yatabbatar itane anma yagane mahaifiyarsa donhaka yace “jeki” falmata tace “meyene?” “Tamin kama da watane” alokacin aliya ta ajiye tray din tajuya tafice, saida falmata ta tugeshi baice uffan ba yafice, jakadiya tabada shawaran amasa aure dawuri ko mace zata nutsarshi, namiji mai gagara ai macece mai nutsar dashi, anma falmata tace itakam sam bazaa kawo wacce zata kwace mata danta ba, anma tana ganin karshe abunda zatayi kenan, acan fannin kuwa yanashiga falonsa, yakira bilki wacce itace take masa hidimansa. Yabukaci yasan sunan baiwar datake fannin uwarsa, anan bilki ta tsorata sosai duk da tagane bayaninsa anma tayi kaman bataganeba, daya watsa mata wani tsawa bashiri tace masa aliya sunanta. Kuma tataba bauta agunsa yace acanjata, anan yashiga tunani yazaiyi toh da ita? Yakamata tadawo shiyanason ganinta donhaka ya aika aka kira umma uwar soro, yace mata yaduba yayi nazari akan baiwar dayasa aka kora, ayi hakuri adawo masa da ita suna aiki da bilki yafi gane aikinsu. Ta amsa masa da toh, adaren ranar umma takira aliya tasanar mata bataji dadiba dontasan meyakesonyi, zaibata mata plans dinta, anma haka bayadda ta iya, daredare bilki takai masa shayi ya juye mata akaya yace ta aiko dayan baiwan, tana isowa tafadawa aliya duk jikinta yabaci donma Allah yasa ba tafashashe bane balle yakoneta, aliya cikin dacin rai tanufi fanninsa bayan anmata iso sannan tashiga yana zaune akan kujera ta tsuguna tamika masa sannan yace dama ke baiwa ce kika fita? Da izinin waye? Kanta agefe tace “gimbiya falmata” yaja tsaki sannan yace “da mummyna kike aiki?” Yanzu zantona miki asiri kasheki zaayi baiwa dake kinfita kinje kina tonamana asirin gyda ko?” Batace komi ba, jiyayi kaman jikinsa na mararin jikinta, gashi yadan sha giyansa kadan, kanta yanufa tamike tana matsawa haka yakomota duk karfin datake jidashi yahadata yadama wurgata kan gado yayi yafara sumbatu, tana kokarin tashi yana kokarin danneta. Ganin zata masa taurin kai gashi ji yake zuciyarsa na masa zogi, na masa radadi kaman yarasa wani abu a fannin jikinsa yanzu yasamu baisan lokacin daya rinka naushinta ba tuni tayi laushi yakwanta luff ajikinta, tareda cewa nafiso injini haka. Aliya tagama galabaita batasan lokacin data gantsara masa cijo ba bashiri ya tsala kara tu[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 5  benaxir  September 22, 2015  Hausa Novels  123 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR dogari ne yaleko nan da nan yusuf yace “kaita cell” wani wawan damka yamata tana fizgewa anma haka yafice da ita , rufeta sukayi a gun ,ko da falmata tayi cikiyanta domin taje tasawa abdullahi maganinshi anan tasamu labarin yusuf yarufeta, donhaka tuni ta nufi fanninsa fuska a murtuke tace “anma dai kasan cewa wannan baiwata ce ko?” Batareda yadamu ba yace “anma laifi tayi donhaka dole na hukunta ta” yana fada ya sunkuyar dakai” falmata tamike tareda cewa dogari “ciromin ita yanzunnan tazo tasamen” aikuwa ana cirota wanka tayi sanmam tanufi gun falmata wacce take kunshe da wasu kaya agabanta, laya ne dawasu kullin magani, jakadiya tamikawa aliya wacce bata tsorata ba, don duk takaranta a littafai salo salo na makirci da kishi, jakadiya tamika mata sannan falmata tacigaba da magana ” zaki san yadda xakiyi kikai dakin yakolo, guda biyune naraba ko da zaasamu matsala da naki, gida biyu maganin gobara” aliya tamike tareda cewa toh, fitanta tanufi daki tana tunanin yadda zatayi saida tabari daredare sannan taje baya tagida tabinnesu, mikewanta dasafe tanufi fannin falmata tareda cewa “gimbiya bansan tayaya zanshiga fannin ta ba” falmata tace “nasan yadda zaayi kixo nan gobe dasafe” Washegari dasafe tajeta alokacin dukkansu daga falmatan har yakolo suna zaune suna karban gaysuwa saiga aliya, falmata na ganin aliya ta umurci jakadiya data kamota, duk sauran bayin dakatawa sukayi suna kallon ikon Allah don sunsan halin falmata sarai, jakadiya narikota falmata tahau fada wa aliya ” baki da hankali ne? Tun karfe nawa nace kizo na aikeki? Ku bata jikinta!” Bashiri suka hau dirkanta yakolo ce tabata hakuri anma falmata taki saurarawa tunda aliya take bata taba shan duka irin wannan ba , ana gama dukantan falmata tace sukoreta, alokacin yakolo uwar tausayi kamar yadda mutane suke mata laakaci, tasa aka kawo aliya tabata uniform dinsu nacan sannan tace tadauketa aikin, shikenan plan din falmata yayi daidai, alokacin hauwa yarinyar yakolo ta tausayawa aliya sosai donhaka ta ce yakamata tana aiki acikin gurin ko da zamane agefe tadan taimaka dawasu abun, yakolo kuwa ta amince, fitowar aliya zuwa dakinsu tuni jakadiyar falmata tanufota tareda cewa “kinsam yanzu baza ana ganinki damu ba, donhaka kisan yadda zakiyi kibada maganin, akwai wacce muka bata sauran baizama dole kisantaba” dahaka aliya ta amince aanma akasan ramta tariga datasan tabirne maganin, saidai batasan wane aka bawa sauran maganin ba dazata san yadda zatayi tahana, anma duk dahaka bata cire hope ba, suna zaune watarana kawai saiga gimbiya tamike daga kan gado, tacire laqqabinta ta fizge gashin kanta, tuni tafara jan jikinta tana jan fatanta, hankalin kowa yatashi tuni aka isar da sako ga sarki, ya umurce da ariketa, sannan ayi addua ya iso gun dakanshi, yakolo tayi luf sai surutai takeyi ” bakuga bera bane suke bin jikina? Duk dakina kananun bera, kutashi kuciremin ina jakadiya? Kiyi sauri kiciremin” aliya dake gefe kuka take kallon idon falmata tana ta kuka, oh ! Mata da kissa ita adole kishiyanta ba lafiya, can dai dataga sarkin yazauna agefe sannan tafara tafara magana “Allah sarki yakolo ta kiyi hakuri Allallah zai kawomiki dauki, Allah karemin ke,”daga ita har jakadiyan sai hawaye suke, abin yabawa aliya haushi yayin yakolo malamin yafara mata adduoi, wani zobe yagani a hannunta sannan yace tacire sarki dakansa yacire mata yamika masa, yakalli sarkin sannan yace “wannan zoben mai girma na tsafi ne, yawo ake da kurwanta asama,aina tasamo?” Sarki yakalli jakadiya maanan yana neman karin bayani jikinta nabari tace “nima haka nagani tana sawa bansan aina bane” dasauri hauwa tace “kawowa akayi alokacin gaysuwan sarakuna umma falmata tabata”falmata cikin kuka da kissa tace nima inadashi bantaba sawa bane. Acikin kayan sarakuna aka kawo(kayan sarakuna kyauta ne da matan sauran sarakunnan garin suke kawowa don hada zumunci kowa yakan hada nashi) sarki cikin zafin rai yace malam gama aikinka zamu binciko wayayi wannan danyen aikin,aliya taji dadin haka Koba komi zatasamu daman ganin matan waziri, [9/22, 7:45 PM] Adda Bena: Ahaka aka watse don barin yakolo tayi bacci, aliya tagaji sosai anma duk tana tunanin yazatayi don tasan tsafin da falmata tayine yake aiki, bata idda tunaninta ba taji hayaniya mikewa tayi tafice tafannin yakolo ne, dogaran basu bari ashigaa anma kasancewar sun wayeta suka barta, yakolo ce itakadai tanata hada kanta da bango, tana kuka duk jikinta jina jina, jakadiya dasauri tariko aliya tareda cewa kitsaya da ita barin yi magana da umma uwar soro, ficewanta aliya tanufi gimbiya yakolo wacce ganin aliya take cewa “aliya kirike matannan tadena rikemin kai, ” aliya duk tarude dagudu abdullahi da hawa suka shiga hauwa tana zubar da hawaye, aliya cikin zafin nama take cewa “kina lailalaha illahala, auxubikallimatti lahi tammat min sharri ma kalaq” dasauri hauwa tafara fada aliya ma nafada abdullahi nafada, kara yakolo tasake tanacewa takamani sunayi dakarfi ahakan har tayi shiru tana nishi mai karfi, can tace ” ga matan can tana kuka wai ina konata, kuma zata dawo takasheni” aliya tadebo ruwa ta tofa adduoi sannan ta watsa mata suka shafa mata ajiki, nan da nan bacci mai nauyi ya kwasheta, juyowan dazasuyi sukaga umma uwar soro tana labe agefe. Tana kallo ta tsorata sosai anma tace mutum biyu suzauna anan sauran sufice, hauwa da jakadiya ne suka zauna, alokacin aliya tafito domin tawuce dakinsu tana tafiya abdullah dake bayanta yace “baiwar Allah” tajuyo a hankali tareda sunkuyar dakai yace “nagode da taimakon mahaifiyata dakikayi, Allah bar zumunci,” aliya tace ameen yarabb,tana tafiya yabita da kallo shidai yasan kaman yasanta awani guri anma dai yawuce dakinsa. Tana isa daki takwanta luff sai bacci Dasafe tafito dontaje mika gaysuwanta agun yakolo, dogarai ne suka tsaya akanta tareda nuna mata hanya tabisu baki alaikum har fannin yusuf, yana zaune akan kujera dagashi sai singlet ko a jikinta don ko lokacin training dinta mazan da singlet suke training ganin bata damuba yasan yana dealing da babbar yar bariki, cewa yayi danna zakimin!, zaro ido tayi anma ya katseta dacewa “kiy[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 6  benaxir  September 25, 2015  Hausa Novels  134 Views [9/25, 2:21 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya ta runtsa sannan tace “mekakeso dani?!” Cikin rashin damuwa yace “kenake so” bata kalleshiba tadauko towel, tashiga toilet tajiko da ruwan sanyi, tana zuwa ta maka masa dasauri yace “awhsh meye haka?” Fuska a murtuke tace “danna kace kana so!” Tana fada tana danna masa kafan lumshe ido yake cikin dadi don shikam har ransa yadda yakejin sanyin haka yakeji aransa, sonta yake don jiya dakyar yayi bacci tun taimaka masa datayi take idda mishi gizo, mintsinansa tayi bashiri yabude ido, “meye haka?” Yadda yabata rai, saikace meshirin kashe barawo, bata kulasa ba tamike tareda cewa “nagama” tajuya zata fita , samata kafa yayi tuni ta tuntsire tayi kasa, cikin tausayi yace “wayyo kiyi hakuri ” bata kulashiba tamike tafice, dadi yaji aransa. Itakuwa inbanda kwashe masa albarka ba abunda take a zuciyanta, fannin yakolo tanufa, jiki dasauki hamdallah, shima don sarkin yadauko malamai sukayi saukan qurani, sannan malamin yayita bayani ” wannan adduan dakuke rainawa ance kunayi kunaga kaman wasane,kuyi zikirin safe dana yamma ,Allah yana kareku, fatiha,falaq da nas , ayatul kursiy,ga lailaha illa anta subhanaka inni quntum minal zalimin, lailaha illalahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shay in qadr, akwai su dayawa kunemi hisnul muslim shine makamin mumini, duk sharri da asiri da jinn Allah zai kareku, inhar kanayi kuma kaga wani abu yasameka toh kadauka wannan kaddara ce kuma jarabawa, don annabi SAW anyi masa asiri kuma takamashi, anma kuma yakarya. Don haka dole kuyi imani da kaddara, ku yarda Allah shiyake komi, babu yadda zaayi dan wani abu yasameki saiki bude baki kice wacce ce tayimin haka, a a nikam anmin asiri, zato zunubi, Allah bayason haka, duk abinda yasamu mumini anaso kayi imani kakuma fuskanceshi, zama kace anmaka asiri kana biye biye ba daidai bane, safe da yamma ko yaushe ka kasance da adduanka,” yakalli jakadiya tare dacewa “abasa qur’an” tamika masa yakalli qur’anin gashinan dai anma sai kura alamun cewa andade ba a budeba, yace “toh kunga wani matsalan meye amfanin fansar quranin da zaa ajiye don ado?,ba gwara kubayar sadaqa a masallatai ba?,sai kuga agyda ansiya qur’an sama da goma, an ajiye wato acemuku musulmai kuba arna bane, ina amfanin haka baka karanta qurani, anma kullum zaa kunna tv, zaa hau whatsapp, facebook, wata inbatahau ba kaman zatayi zazzabi, zaatashi tsakar dare ayita waya kuma sai akwanta goshin asuba, anmanta da Allah waiyazubillah, yakamata duk mu tsarkake ranmu, bature yazo mana dawani cuta mai wuyan magani,duk wannan social media din cutane, Allah ya tsaremu, yakuma kara mana imani, anma dole mucanja inhar munaso muga mai kyau, rashin bin Allah da dokiknsa shike sawa muke ganin jarabawa kala kala, ” duk kowa jikinsa yayi sanyi sarki kansa yaji wannan waazin don yamanta wen last yabude qurani, gwara sallah yanayi dukka a masallaci anma baya farilla, falmata kuwa wacce tazo daga baya , bindin shedan tamanta wen last tayi sallah, donkuwa a maganin da akabata an umurceta da kartayi sallah na kwana arbain, donhaka take zuane, yakolo kuwa baiwar Allah wacce tayi imanin jarabawa take fuskanta agun ubangiji taji dadin jawabin malam ko ba komi zai kara mata tuni da mutuwa dakuma kwanciyan kabari, bayan anwatse aliya tanufi dakinsu tasamu bilki wacce ita tana kwance tana hutawa tamike tareda cemata “matan sarakuna yaushe zasu kara zuwa?” Bilki tace “ran laraba menene?”aliya tace ” babu kawai inason sanine” dadi taji ganin plans dinta yana tafiya daidai, Ran laraba dasafe tanufi gun dogari isa, shine wanda tasaba dashi sosai kuma tarokeshi alfarmar yanema mata kayan dogorai set daya, duk da yaso yakawo mata taurin kai. Dubi goman ta mint tahada tabashi,ba bata lokaci ya amince, donhaka ta karba tanufi baya tasaka tarufe kanta, tadauko fatar gemu wanda tayo guziurin kayanta tun daga kudu, tsayawa tayi a babban gate gurin da dole kayan sarakunnan sushigo, a tsayawanta tafara gadi, dogari isa ne agefenta abun mamaki dukka dogaran bawanda yace komi asalima basu nuna sunsan bakon fuska bane, hakan yatabbatar mata dacewa dogari isa yatoshe bakinsu, oh kudi samunka mutunci, rashinka balai, karfe daya daidai suka iso, matan sun shige yayinda kayansu dole aduba kamar yadda sarki ya umurta, ahaka aliya tagama cuse cusenta takulla komi sannan tacire kaya tabawa dogari isa, wanda tuni ya ajiye a boyeyyen gu don kar asiri yatonu, anshiga anyi iso ma matan sarautan harda mazajen nasu, lami lafiya anci abinci anyi tadi, anan aka fara fitar da kayan kowa ana dubawa, matan sarkin sun nua farincikinsu musammamn ma yakolo wanda don ita akadawo dazuwan laraba musababbin ciwonta, sarkoki ne, sai laces,shadoddi. Da kayan kwalama, can kasan wani shadda gezner jakadiya tana budewa sai ga laya da zobe, gaba daya hankalinsu yayi kan gun don sun mugun tsorata , jakadiya wacce ada take gudan farin ciki tana kirari saigashi tafara salati, tuni hankalim kowa yayi gun, umma uwar soro ce tanufi gun tareda cewa “kayan waye” jakadiya tace “na matan waziri” falmata wacce ta harzuka sosai tace “ku kamata” bashiri dogaran suka nufo kanta tareda bata hanyan fita, magana kaman iska tuni fada tadauki hayaniya waziri wanda ke fadar sarki jin abunda yafaru yasashi rudewa, bashiri ya roki da abarshi yashiga daga ciki, anma sarki yace mai ” uwar soro zata mata hukuncin daya dace, babu ruwan fada ko sarki aciki”. Falmata kuwa abunnema yasamu duka sosai matar waziri eshallo tasha, [9/25, 6:36 PM] Adda Bena: Yakolo bataji dadiba acewarta yakamata ko darajan sarautan mijinta a lamunta mata, anma falmata taki , dadi takeji tasamu naman fansa akai, bakin ciki kaman zai kashe waziri anma babu yadda ya iya, uwar gayyan kuwa aliya taji dadi acewarta yanzu tafara daukan fansa, tunda yarabata da kowa nata saita rabashi dakowa nashi da duk wani wanda yasa hannu a kashe iyayenta, tana zaune bilki tashigo tareda cewa kizo inji yarima yusuf, shiganta tasameshi yana zaune da kwalban giyansa, da alamun maye, tuni tadaure fuska, yakalleta tare dacewa “kinga ko ni yarima ne, kuma kome nakeso ina samu, ina sonki kinji? “Aliya bata furta komi ba, kwace kwalban tayi tareda ajiyewa agefe. Kallonsa take sosai, yusuf namiji iya namiji saidai yasaka shaye shaye agabansa duk yayi baki yadawo wani iri, wannan wani irin rayuwa ne, itama zata iya amincewa kanta cewa tana sonsa saidai soyayya yanzu bashine solution dinba, gwara tadanne ranta tabi hakkinta tukunna, tajuya zata fice taji yana sumbatu, kwance akan kujera, zuwa tayi tagyra masa kwanciyan tadauko bargo tarufesa sannan tazura mishi ido gashin girarsa acike yake ga gashin akwance tamike zata fita taji yaruko hannunta, Kufara turowa adda [truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 7  benaxir  September 27, 2015  Hausa Novels  138 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR cikin numfashi yace ina zakije? Aibanyi baccinba” tadan musguna gefe sannan tace “toh meruwana?” Ficewarta tayi gabanta nafadi daki tanufa ta kwanta tana tunani, alokacin bilki tashigo take mawa aliya bayanin cewa dakyar waziri yaroki alfarma yanzu dai anrufe matarsa harsai ran asabar ayi hukunci, bayan aliya ta idar da sallahn isha tanufi fannin yakolo wacce tasamu sauki kaman ba ita bace a kwance kwanaki, abdullahi na gefenta suna magana koda aliya ta tambayeta ko akwai abinda take bukata tace babu tafito kenan tana tafiya taji ankirata “baiwar Allah” tajuyo tareda sunkuyawa yamika mata glass hannunsa alamun takarba, tamika hannu zata karba sai yafado shiyasake itakuma bata karba ba, tuni ta sunkuya tafara kwashewa jikinta na bari karya mata wani abu,sunkuyawa shima yayi yafara kwashewa , jikin kwalban ne yadan shiga yatsanta, wani kara tasaka, tuni yariko hannun yana dubawa yayi mamaki kwarai dayaji hannunta da balain laushi, don asaninsa bayi dai kam adan wahalan dasukesha jikinsu tauri gareshi kaman ma icce, cire kwalban yayi wanda saidatayi dan kara. Hakan yakara bashi mamaki domin wannan dan ciwon bawani abu bane inhar cikakkiyar baiwa ce, yanaso yatambayeta tarihinta tun farkon xuwa gydan yake mata kama da yasanta awani guri anma yarasa ainane, mikewa tayi tareda bashi hakuri yace bakomi, anan tasaka kai zata wuce fanninsu ga mamakinta saitaga yusuf a tsaye kaman tsohon zakanya daya fi shekara baici abinci ba, batace komiba tawuceshi shima komawa yayi, dama asali gunta zaije saikuma yaci karo da ita tare da kaninsa, wanda bayaso, lallaima yarinyannan zataga tsiya, ranan baiyi bacciba yanata tunani kodai soyayya suke? Yanzi haka hala ya rungumeta kafin yazo? Toh meye suka rike hannun juna? Kanshi ne zata fara ciwo tuni yajawo giyansa ya kwankwada sannan yacigaba da hidimarsa domin kuwa ya manta shagaf da bakin cikinsa, Bilkisu ce tafarka tsakar dare saikuwa taga aliya akan salllaya tace “kekam kullum ne saikinyi sallahn nan?kowacce dare inna farka saina ganki akan sallaya baccin awa nawa kike? Gashi bakya baccin rana sai jifa jifa,” aliya tayi shiru sannan tace “akullum dan adam mai neman biyan bukata ne, akullum yakan so wani abu, koda wannan bukatar tabiyu toh zai samu wata tafito. Don haka meyesa bazan juya alkiblata agun mai amsa adduoi ba? Mai Jinkai? Mai Buwayi? Mai Girma? komi shine, duk wanda yarike Allah da manzonsa bazai taba wulakanta ba, bazaiga wulakancin duniyaba, duk kuma mai sallahn dare akwai wani haske da yakesamu agun Allah, akwai daukaka da daraja da Allah yake basa a idon duniya, yana hani da mummunan aiki, donhaka ni inada bukatu na Allah yakareni, yajikan iyayena yakuma biyamin bukatata don nacimma burina kema dakin fara haka bazaki taba tozartaba!” Bilki tayi tunani sosai maganan aliya gaskiya ne bata taba shiga wani tashin hankalin dazaa wulakantataba, asalima tafi shekara 10 agydan anma aliya datazo a watanni kadan tafita farinjini, kwarjini, kima da mutunci agun mutanen gydan har masu aikin gydan, gaskiya dole tafara itama dahaka tamike tayo alwala itama tafara sallahn,gari na wayewa aliya tanufi fannin falmata wacce ta watsake sosai tadanyi aikacen da bazaa rasaba, sannan tafito ahanyarta taga abdullahi yana ganinta yafara murmushi “yakike? Ya hannunki?” Ta amsa da ” lafiya lao” yayi mumushi sannan yawuce,isanta dakin ta tarar da bilki tana jiranta , tace ina kuma zamuje?” Bilki tace “gun yarima yusuf don yin aiki” tamike akan gado takwanta tareda cewa “atunannina niba baiwar sa bane yanzu, a fannin gimbiya nake” bilki arude tace “anma dai kinsan inbanje dakeba wulakanci zansha ko? Don Allah kiyi hakuri muje!” Aliya ganin bilki zatafara mata kuka tamike suka nufi fanninsa, yana kwance yaki tashi jin muryan bilki ya daka mata tsawa tareda cewa tafice tabashi gu!” Aliya ce tace “kayi hakuri yarima” shiru yayi hakan yabata daman bude kofan suka shiga, tuni suka kimtsa gun, yanakan gado bai motsaba, sukayi sharansu da goge goge, sungama alokacin yamike bilki tadauko abincinsa, ta ajiye, harsun fice suna tsaye suna jira yasauko daga kan gadon tareda nuni ma bilko na tafita, ficewa tayi aliya bataji dadiba anma babu yadda ta iya, tazuba mishi yaci duk shi kallonta yake sosai, yaki yakyafta ido yadda take servn dakomi yabashi mamaki, cikakken wayayyiyar macece tasan yadda ake handling fork, da yadda ake servn duk da cewa bayin gydan anyi training dinsu na alada anma yadda aliya take nata dabanne, ganin kallon yayi yawa ta tashi takoma inda suke tsayuwa tana jira yagama, , yagama ci a nutse sannan tazo kwashewa cewa yayi tazauna, hankali akwance tazauna abunta, shikam tana bashi mamaki irin tsoron da bayi mata suke if aka musu haka saboda ana sani koransu ake, anma aliya hankalinta akwance yace “zan iya jura idan kikace baki sona, anma bazan iya jura naga kina soyayya dawaniba, yafi ciwo!” Takaleshi fuskarshi asalin alaman tausayi ne, kana ganinsa kaga wanda ya tsume a soyyayya, abun tausayi duk fadin ransa da mulkinsa ji yadda yake ladab agaban mace, nimadai benaxir abun yaban mamaki, aliya tace “nifa karka jawomin akoreni, banda hanyan ci da sha sai agydannan,!” Wani kallo daya saka mata sai datayi shiru, yace “kigayamin waye ke ko inyi maganinki bakiyi kama da talaka ba, babu komi naki mai kama da talaka , takalli jikinta sannan tace meka gani ajikina, ko dankunne babu, sai wannan azurfan,” yakalli azurfan sannan yace. Talaka bazai taba saka azurfam dubu arbain ba, tayi shiru lalle yusuf yawuce tunaninta dole tanemo wani karya don azauna lafiya, donhaka tafara kuka, shiru yayi yana kallonta, zuciyarsa na tafasa, meye kuma na kuka? Don kawai namiki magana? Haba aliya !” Haka yata lallabi cikin kukan tace, “ni bansan iyayena ba, natashi agun wata antyna a abj, anma iyayena yan garinnan ne. Toh antyn tamutu suka koreni yan gydan shine nadawo wannan gydan banawa bane, nata ne babu hanyar ci da sha shine kawai naje nima aka kamani” har cikin ransa yaji tausayinta yakuma tausayinta tuni yace “zan yantaki, kuma zan aureki” ido ta zaro sannan tace ” kanaso ka kara tadamun hankali kasan cewa bazaa barka ba, dan sarki dole sai yar sarauta, baba na manomi ne ta ina muke da sarauta, dariya yayi sannan yace “ni mai ruwana , inasonki abunda nasani kenan, kuma bawanda zai hanani aurenki, balle jikina nabani ke matata ce,” aliya tace “toh nidai kayi hakuri kabarni nasamu naci, kuma ba sonka nakeba donhaka kayi hakuri” dariya yayi yasan tafada ne, hartamike zata fita yace. Tsaya!, yakaraso gefenta tana tsaye tana tunanin mezaice don hankalinta bai kwanta dashiba, “jiya me abdullahi yamiki? Inace bai rungumekiba? Daure fuska tayi tareda cewa “meya kawo runguma?* kamanta yanada wacce yakeso har anyi tambaya?, meye na zargin?” Yayi murmushi “toh ai All men cheat, saidai kawai girmanki da darajarki zai gwada, inhar yabari kikasan yana neman wata, toh bai daraja kiba, anma mai sonki ko zaki mutu bazaki saniba, so bawani abubane don yaganki yace yanaso,” bata kulashiba zata fice saiyacigaba ” kinga kaman ni ko ina neman wasu ba damuwa tunda kece major share holder aiba damuwa, ” tasan har ranshi yafada, sabida yusuf nada neme neme, hakan yake tsorata ta kodai itama jikinta yakeso! Namiji ba a iya. masa, gashi tafara sonsa, kyaunsa da takurinshi ya sa tafara sonsa, son da bata tabayiwa wani da namijiba, wanda inhar tana tare dashi takan manta duk wani bakin cikinta shiyasa take taka tsantsan dashi domin kuwa yusuf zai iya ruguza mata plan dinta, matsalan shine yusuf ne namiji data fara so take kauna, har daki tunani takeyi ina mafita? Yazatayi? Kodai zata gudu tabar fadane? Toh gashi tanason ta gyra zaman yakolo da falmata don yakolo tana cikin hatsari, toh itadai yazatayi?? Gashi batada abokin shawara, tayi missing iyayenta sosai kuka tayi sosai kaman ranta zaifita har aka kira azahar alokacin tayi sallah anma idonta ya kumbura bilki ta bukaci sukai abincin rana inyaso inta dawo taje gun yakolo, anma aliya taki, koda bilki taje haka tadawo bayadda ta iya tanufi fannin, yana zaune haka tagama zubawa yana kallonta ganin idonta ya kumbura tuni ya ce meya samekk? Bata amsa ba wanda hakan yasashi kara birkicewa, aliya meya sameki?” Bata bashi amsaba sai taji wani sabon kuka, hannunta a fuskanta tuni yaga hannunta a kumbure ma, nan da nan yarude first aid box yadauko yayi dressing hannun, yasa bandage har lokacin hawayen ne ke zuba, yayita rarrashinta hartayi shiru, wani irin sonta ne ke tsuma shi, yace mezanmiki kiji dadi kidena wannan kukan?” Tayi shiru sannan taja numfashi sannan tace “karka yantani, karabu d[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 8  benaxir  September 28, 2015  Hausa Novels  130 Views [9/28, 8:19 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR kallonta yayi tareda mikewa yana cewa “kinsan hakan baamai yiwuwa bane, donhaka kibari kawai” kukan takara sake mishi bashiri ya dawo tare da nuna amincewarsa, dakyar dai yabarta tafice tanufi fannin yakolo wacce tasamu suna muhawaran kayan azumi da zaa raba wanda saura kwanaki ne kadan, yakolo macece mai kima, mutunci da daraja kowacce ya zataso ace tasameta a matsayin uwa ko suruka, daga kan kayan azumi suka koma bayanin auren abdullahi, nanfa ashe yarinyan yar gidan waziri ce, hankalin aliya yatashi, itadatake shirin daukan fansa meyakai abdullahi? Wani zuciyar tace “keda kike harin uba, meya hadaki da ya” dahaka tabar zancen Yusuf kuwa hankalinsa ya gagara kwanciya da aliya dogarai uku yadiba suka fice daga fadan, gidan aliya suka nufa anma gidan arufe gam, donhaka kawai yusuf ya umurcesu dasu balla mishi kofan, sunsha wahala kafin suka samu suka cire kofan, yana shiga yakarewa idon kallo babu wani abu dazai iyacewa zai cire masa kokontonta aransa, yagama bincikenshi haryafito saiyakoma kasan gado anan yaga wata yar box kamar asusu, yacirota yakira daga cikin dogaransa suka balla masa,sannan yabude. Littatafai ne sai hotuna guda uku, dayana galadima daya kuma na wata wacce da alamu matan galadiman ne, saikuma hoton yarinya da galadiman, daya zura mata ido tabbas aliya ce kammaninta bai canja ba, yafara bude takardun daya bayan daya, tunda yake baitaba shiga tashin hankali irin na wannanba, ya mugun tsorata, tabbas yasan harda sarki a hannun kashe galadima toh anma gashi fansa tazo dauka, yaduba takardun kaf, kwalin degree dinta ne, harda certificate din nysc, ya tsorata da aliya anma yaji nutsuwa aransa, yasan duk dadewa zai aureta tunda itama yar sarauta ce, kuma tanada ilminta, toh anma yazaiyi yaceci mahaifinsa,? Dasauri yamayar da komi sannan yafito alokacin har ankawo wani kofan yasa suka saka sannan aka jingina mata mukullin a kasan kofan, sauran mukullin yatafi dashi, dakyar ya iya takowa yazo fada, jiki a sanyaye yanufi fanninsa, kwanciya yayi akam gado yana juyi babu irin tunanin dabaiyiba aransa, yagagara bacci yakuma gagara tashi yagagara motsi duk tashin hankali na bidansa, sallarhn magrib ce tasashi tashi ko dayaje masallacinma a gefe ya kudundunu, for the first time tunda mahaifiyarsa ta auresa daya mike yayi nafila rakaa biyu yana rokon Allah yabude masa haske a lamarin daya danno masa, Allah yasa abunda yake zargi bahakaba, yayi kuka sosai wanda kowa a masallacin yaji mamaki, abdullahi ne yadafa kafadarsa tareda cewa “zanyi mamakin abunda zai kawoka masallaci harkayi nafila, nasan bakaramin abune, Allah yashige mana gaba, sannan wannan yarinyar aliya!,” dasauri yusuf yakalleshi jin ya ambaci aliya , yace ” bata taba maka kama ba? Kaman kasanta abaya?, tanamin kama da nasanta anma na manta,” dasauri yusuf yace ba itabace wannan daga wata duniya tazo” abdullahi ganin yusuf ya amsa da zafin nama yatabbatar da maganansa don tuni yana zargin yayan nasa da son aliya, shidai babu keta balle hassada adduanshi tazama sanadin shiryuwan yusuf, Yusuf nakomawa fada yashiga daki baifi minti goma ba saiga bilki da aliya sunshigo rike da tire dinsu suka ajiye akan dinning sannan suka koma gefe, yatashi yazo yazauna abincin yake kalla anma baya shaawan ci, asalima baiyi niyyan saukowa daga kan gadonba saidon yakalli aliya dakyau hakan yasa yazo yazauna, kare mata kallo yayi wacce itakuma kanta a sunkuye ne batasan yanayiba, tabbas duk wanda ya tsura mata ido yasan batayi kama da baiwa ba, kuma duk mai ilmi da wayewa yasan cewa aliya wayayyiyar macece, ba daga kayaba kome tasaka wayayyen mutum baya buya , zuciyarsa tayi nauyi jiyake kaman yayi hauka, zaitona mata asirine don yaceci mahafinsa? Kokuma zai rufa mata asiri don yana sonta,duniya tamasa zafi, kansa ya sunkuyar akan table din tareda cewa “kufita” sunfice saidai aliya jikinta yabata ba lfy ba, tadai share suka dawo daki, * bilki tana jaje tareda cewa shekarana goma agydannan bantaba ganinshi haka ba, toh ko kinmasa wani abune?? Aliya bata kulataba alokacin shikuwa yarike kansa wacce take matsanancin ciwo, tunaninsa yarude, bude fridge yayi sannan yaciro giyansa kwalba guda saidaya shanye a lokaci guda, yakara ciro wani yakafa kai saidaya shanye, fadi yayi agun sai bacci, can karfe takwas bayan aliya tagama sallolinta tafito tayi magana shiru jin baimata isoba tasan meyake ayyanawa, donhaka tashiga tareda dubawa ga mamakinta taganshi a kasa kaman matacce, kanshi tanufa tana girgizashi sai dai yana numfashi hakan yasa ta tabbatar bacci yake, pillow tadauko masa sannan tasaka masa, tarufa masa bargon domin a.c na dakin akunnene, tana zaune ta zura masa ido tana tunani “yarima! Meyake damunka? Meya sameka kashiga damuwa? Bantaba ganinka hakaba!” Fuskarshi ta dishe ,zuciyanta na mata radadi jitayi kaman andaura mata dutse akirji, batasan hawaye nazuba a idontaba, dawuri tasa hannu tana gogewa, abun yabata mamaki daga ganinshi haka shine tafara kuka? “Yooo ni aliya wani irin so nake maka? Innalilahi, karnazo nagagara cimma burina, zuciya batada kashi” wasa wasa hawaye nazuba saigashi tanata kuka, oh ni benaxir abun mamaki dama haka first love din take?, Tun karfe takwas aliya take zaune akan yusuf bata runtsaba har karfe uku nadare tana gadinsa, lokaci lokaci dogaran suna lekowa don tabbatar da babu abinda yasami yariman, karfe uku tamike tayo alwala tahau sallah, a sujjadda ta tsinci kanta da rokon Allah ya shiryi yusuf, Allah yabashi lafiya ya yaye masa damuwansa sannan yanema masa mafita, sai asuba tahakura bayan sallahn asuba tacigaba da gadinsa, yusuf bai farkaba sai karfe goma nasafe tana ganin yabude ido tafara tambayanshi ko lafiyansa lao, yayi matukar jin kunya bayajin kunyan [9/28, 8:25 PM] Adda Bena: Mahaifiyarsa bayajin kunyan mahaifinsa anma ya tsinci kansa da jin kunyan aliya, ta taimaka mishi yaje bandaki sannan tafito. Wanka taje tayi sannan tacanja uniform dinta tamike kan gado, bacci mai nauyine ya kwasheta, Yusuf kuwa fitowarsa yaga babu ita dasauri yakira dogarinsa daya tareda cewa “ina aliya? Kiramun ita ai batagama aikin ba” ya amsa da toh, bilkisu ce ta tasheta anma haka tamike sukaje fannin, tea yasa tahada mishi yana kare mata kallo, tayi iya kokarints ganin ta danne baccin datakeji, tahadamai yaci da cake sannan yakoma kan gado, zata dita yace “dawo ki tsaya harsainayi bacci” tana tsaye haryafara bacci sannan tafito bacci takomayi, har azahar alokacin yatashi yaga bilki ransa ba karamin baci yayiba tareda cewa ina aliya? Kikiramin ita, ta sunkuyar dakai gami dacewa “bataji dadibane yarima tana bacci yanzu haka” yazaro ido mai yasameta?” “Babu baccin dabatayibane yajawo mata, tun shekaranjiya rabonta da bacci, ” shiru yayi yana tunawa tabbass yatashi yaganta kenan azaune ta kwana, tsanar kansa yayi yanajin haushin kansa oh aliya, kiyimini hakuri, shikadanshi kaman yakashe kanshi, mikewa [truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 9  benaxir  September 30, 2015  Hausa Novels  115 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Budewa yayi yashiga wanda yabawa bayin mamaki domin yaran sarakunan har matan basu zuwa gun, umma uwar soro ce kadai me shiga da fice agun, gaba dayansu kowa ya sunkuyar dakai domin sun gama tsorata, ayadda suka sanshi sunsan sarai cewa ba lafiya ba, bayada mutunci ko kadan , yakare musu kallo yaga wani gado ne akwai mutum kan gadon yanufa, aliya ce tana bacci , yazura mata ido sosai. Yasa hannu yasa ajikinta yaji yayi zafi sosai, bayin sunyi mamaki nan da nan kowacce tafara tsegumi, yafice fanninsa yanufa yadau wayarsa yakira likitan gydan, bashiri yazo anan yasa bilkisu suka kamo aliya suka kawota fanninsa aka dubata, likitan yace rashin hutu ne da wahala, da rashin sabo da wahalan, yabata pain reliever, da maganin bacci, haka dai yatafi hankakin yusuf atashe baiyi motsi agefenta ba, yanata kallonta yarasa wani yanayi zai fassara kansa, Maganan yusuf yashiga fannin bayi tuni tabaza cikin fada, falmata ranta yabaci sosai, data bukaci bayani agun jakadiya nan jakadiya ta ce mata “bayin sunce kwana biyu yana nuna alamun damuwa wa aliya” falmata tazaro idanu domin ta mugun tsorata, yanzu yarasa wacce zaice zai kula sai baiwa? Duk neman matanshi bai kare awaje ba harsai yazo gun bayi?” Jakadiya tadanyi gyran murya sannan tace ” gimbiya wannan fa inaga nufinsa daban, don sundade tare, inhar biyan bukata ne kinsan yarima yanayi sau daya zai shareta” falmata takara tsumuwa, batasan lokacin data mike tanufi fanninsa ba, dogarai suna kokarin yimata iso anma ko jiransu batayiba tafice tashigo, gabanta ne yayi mummunan fadi ganin yusuf yana zaune agefen aliya, da alamu yayi nisan tunani tunda baisan tashigo dakin ba, wani tsawa ta daka masa wanda saidaya firgita ganinta yasa yadan rusuna, bai idda ba tace “wani rashin hankali ne wannan? Jakadiya fita da ita!” Jakadiya taje ta tashi aliya wacce jikinta yayi zafi sosai tarasa yadda zatayi, donhaka taruketa zasu fice falmata tace “saketa!” Aikuwa aliya tajita akasa dasauri yusuf yanufeta yadagota zaifice da ita budan bakin falmata tace “zandaga maka nono yusuf, wlh inka kuskura kabita zandaga maka nono” cak ya tsaya ji yake kaman yayi hauka. Alokacin aliya tajanye jikinta tareda cewa “zan iya tafiya badamuwa karka damu” fitanta sashimsu tanufa inda kowa kallonta yake alamun tausayi bata kulasu ba takwanta, alokacin jakadiyar yakolo tazo ta dubata, acewarta yakolo na gaysheta da jiki, fitanta kenan alokacin yusuf yabar gydan don baiga amfanin zamansa ba, gydan aliya yanufa anan yakwanta yasha giyansa, barci ta kwasheshi, falmata kuwa tarasa yazatayi gwara tun wuri takauda aliya donhaka ta umurci azo da aliya, dakarfi aka kamo aliya tana kallonta aliya duk tacanja kamanni, falmata ta umurci da adauko bulali nan aka baza aliya ta kwashi dari masu karfi da zafi, tunda mahaifiyarta tahaifeta bata taba shan wannan azaban ba, aka kwara mata ruwan sanyi, falmata tace “sakamakon da ake samu kenan idan mutum yashiga hurumina,” suma aliya tayi anma haka falmata ta umurci a watsa mata ruwan sanyi tana farkawa aka daure hannayenta tabaya da kafafunta aka kwantar da ita akasa,tasa aka dauko kankara aka jera mata a cinyoyinta,kakkarwa take, duk tafita hayyacinta burinta baisamu yacika ba zata mutu, dukka wanda yakegun dole yatausaya mata. Bilki ce taruga da gudu fannin yakolo tasanar da ita abunda ke faruwa, bashiri yakolo tafito isowanta gun tace akunceta falmata takalleta sama da kasa tareda cewa “a matsayinki na wacece?” Yakolo tace “a matsayinta na baiwa ta!, inbaki manta ba ai kinkoreta nadauketa!” Faalmata taji kaman ta makuro wuyan yakolo tsaki taja tare dacewa “zanga wanda zai daina abunda nasashi,inku jahilai ne takoma tazauna a kujera; yakolo tayi murmushi dakanta tanufi kan aliya ta kunceta. Tarungumota sannan tanufi fanninta da ita, falmata tsaki taja tabar gun tareda zagin bayin, A fannin yakolo ta aika aka kira likita yaxo yamata dressing jikin yabata magunguna, abdullahi ne yashigo ya tsorata ganin yanayin datake ciki, tana bacci anan sukayi shawara da mahaifiyarsa a[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 10  benaxir  September 30, 2015  Hausa Novels  122 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Tana farkawa tayi mamakin ganinta afannin yakolo anma yakolo ta gwada mata bakomi, sallolinta tayi a zaune don bata iya tashiba, abdullahi duk tausayinta yacika sa gashi haryafara tsanar kansa yasan tabbas yasan aliya anma yamanta aina ne? Wannan wacce irin mantuwa ne, Yusuf bayan farkawanshi wanka yayi yacanja kaya sannan yarufo gydan yadawo fada, atake yafara neman bilki cikin kuka tasanar mishi da abunda yafaru, ranshi abace yanufi fannin mahaifiyarsa donjin baasi kamar kullum cemasa tayi “inzaka shekarana kana neman yanmatan da basu daceba baxan gaji da koransu ba, kanemo mai tushe mai asali, ” baice komi ba yafice , fannin yakolo yanufa wanda kowa saidayayi mamaki yagaysheta sannan yace “nazo daukan baiwa tace ” tagane meyake nufi anma tace “wacce baiwar fa?, ” yayi shiru sannan yace “marar lafiyannan aliya” tace “au! Aibansaniba kamanta mahaifiyarka ta koreta ne? Ni na karbeta, kuma daga yau na yantata donhaka daga kai har mahaifiyarka bakuda dama akanta!”. Zaro ido yayi yayin daya tuna kalmomin aliya na “karka yantani, karabu dani kuma ka manta dani” subhannalahi ai ta tona mishi asiri aliya batason a yantata, anma shiyasan yantata shine kadai hanyan dazai iya soyayya da ita, baice komi ba yabar gun A haka aliya taringa jinya kullum yusuf na hanyan gaysheta wani lokacin suhadu da abdullahi wani lokacin kuma da shehu, wanda baya zama agydan saboda makaranta wasa wasa saida aliya tayi sati sannan tawarke, aranan yakolo tabukaci tagayamata gaskiya, Tagayamata cewa ta yantata , aliya batasoba anma yanzu kam shine kadai hanyan dazatabi donta rama abunda falmata tamata, dole tarama saitaji zafi ninkin abunda taji, zataga itako falmatan wazai juya yusuf, uwace ita tafita daraja anma namiji kam inkika tsuguna kika haifeshi aikinsan wa ya mace kika haifawa, domin kuwa komi mace zaifara yiwa, dadday ne masu fara tuna uwayensu. Shiyasa bahaushe yace da ki haifi gwamna gwara kinhaifi matar gwamna domin gwamna matansa zaituna kafin ke, itakuwa komi uwarta da danginta, sungama magana da yakolo inda yakolo tabata kayyaki da kudade tace tatafi garinsu don hakan kadai ne zai tsirar da ita daga gun falmata, abdullahi ne yazo alokacin yazaunar da ita yace “dani da mahaifiyata muna tunanin akwai wani igiyan dangantaka a tsakaninmu dake inbahaka ba kuwa babu yadda zaayi ni kullum ina tunanin nasanki awani guri yayin da itakuma take tunanin cewa tana kaunarki haka kawai, toh ko dai babu mudai iyakacin gatan dazamu iyamiki kenan!” Aliya tayi godiya sosai tabbas baxata manta da hallacinsu ba, ko agun bayin kuwa su bilki nata kuka kowa yasaba musamman bilki tafijin jiki, da kuka suka rabu tafice tanufi gydanta ga mamakinta taga makullimta baya shiga kuma ba kofanta bane, tuni tasan aikin yusuf ne don if barawone bazai gyra kofan ba, tazauna agefen kofan tana tunanin yadda zatayi saitaji alamun key a gefenta tuni tadauka tabude taga yabude, dakin warin giya da kwalaben giya hakan yatabbar mata da cewa yusuf ne yake zuwa dakin, abubuwanta ta tattars sannan tarufo kofan, tarar machine tayi taje takama hotel kafin tasamu gida dondai tasan batagama aikintaba babu abinda zaisa tabar garin, wanka taje tayi tanayi tana kallon tabon cinyoyinta na dukan da falmata tayi tasake shower yana zubo mata, tuni tafara tunanin iyayenta kuka tayu sosai wanda saida yasamata ciwon kai tafito tayi sallah sannan takwanta wayanta takunna, msgs tagani dayawa na auntynta kusan kullum saita kirata taji yatake, tajero mata txt tareda mata adduan samun nasara, saikuma malaminta yana tambayanta yaya aikin datasa agaba? Sai daidaikum yan makarantansu dakuma invitation na bikukunan frnds dinta, bacci ne yakwasheta, bata tashiba sai bayan magrib donhaka tayi magrib tasanyo dogon abayanta tafita reception don cin abinci, tayi ordern fried rice da grilled fish, game take awayanta saikawai taga mutum yazo yazauna, bata kulashi ba shikuwa sai kallonta can data gaji da kallon tadauki wayanta tacanja sit yakara binta tuni taji abincin yafita mata akai hanyar dakinta tanufa yakuwa bita saidata fakaici mutane tarikoshi dakarfi hannayensa tawullosu tabaya tarike kara yasaka. Cikin zafin nama tace “meye kake bina?” Karan yakeyi babu daman magana anma yadaure tareda cewa “inason zama abokinki” danna hannun tayi dakarfi tare dacewa “ni ba saarka bace! Not interested!” Sakeshi tayi tareda nufa dakinta nan yafara tunani oh mace dakarfi kaman doki,dahaka yakoma shima Yusuf kuwa shigowanshi gyda yadan siyo kayan kwalamansa yashigo fannin yakolo don gayda aliya, ga mamakinsa tace ” na yantata tunda kasan hakan aikasan cewa zata tafi duk lokacin dataga dama, toh itama tatafi,” zaro ido yayi yasake kayan dagudu yafice mukullin mota yadauko yatuka wani wawan tuki dayakeyi saida ya tsorata mutane gydan aliya yanufa ya bude yaga bata ciki, yaleka kasan gado yaga ta tattare kayanta, wani tsaki yaja bakin ciki nacinsa hannunsa yabude da bango yana magana shikadai “aliya wlh inasonki, meyasa kikatafi? I[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 11  benaxir  October 1, 2015  Hausa Novels  144 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR zama yayi dirsham babu irin tunanin dabaiyiba aransa, yasan dai kome yasameta. Bazata taba barin garin batare data cimma burinta ba a dan sanin daya mata, macece mai tsayuwa akan raayinta, nan kuma takara bashi tsoro domin kuwa yasan tabbas bazata bar mahaifiyarsa ba, gida yakoma yatara dogarai yabasu cikiyanta, har cikiya da hotonta idan amsamu wanda yaganta zai samu kaso na dukiya mai soka Aliya kuwa tuni tasamu tanemi hayan gida ciki da falo, taje tasiya sabbin furnitures, da kayan kallo da duk wani abu datasan yana wancan gydan tabari, saidata koma gaba daya sannan hankalinta yakoma kan yadda zatasamu daman juya fada batareda sungantaba, tayi iya tunaninta anan ta tuna da bilki, toh tayaya zatayi magana da bilki babu yusuf? Dole shikadai zai iya dauko mata ita, inbahaka bilki bazatabar fada ba, ko acikin matan sarkin bawacce tafi kusanta balle tanemi alfarma, tsaki taja tasako dan riganta iya gwiwa da jeans, tadaura dankwalin akanta batayi kama da yaran hausawa ba ko kadan wanda tayi hakanne donta batar da kammani, yanayin garin yamata dadi sosai yadda take tafiya duk wanda zai ganta zai tabbatar da macece marar son damuwa da tashin hankali, masara tagani ta ciro gudan dubu daya a aljihunta tamikawa matan, matan tamika mata guda daya da canji aliya taki karba haka tabar mata canjin, matan tabita da godiya, hankalinta a kwance tanaci tana tafiya can taga taro andan cika dasauri tanufi gun, wasu ne suke fada ana kokarin rabasu ganin mazane ba yadda ta iya tajuya tatafi, har gyda taje sannan ta kwanta akan kujera taji dadin dan zaga garin datayi koba komi tayi exercise din kafa, buga kofa taji anyi batareda tunanin komi ba tamike tabude ga mamakinta saitaga ysuf, mayar da kofan tayi zata rufe atake yasako hannunsa bahali dole tabari, tana juyawa takama kanta tareda cewa “mekazoyi?” Cikin murna da farinciki ji yakeyi kaman ya rungumota yace “yazaayi bazanzo ba. Naxo gaysheki ne” tana zama tadauko wani takarda tana dubawa tareda cewa “mutanen garinnan munafukai ne, har anje anfadamaka inda nake, fitan danayi ko awa biyar banyiba” bai amsa ta ba illa zama dayayi yana kallonta, ta ajiye littafin tareda cewa “taimakona zakayi, inaso kadaukomin bilkisu akwai maganan dazamuyi” ganin tadage yace “maganan yadda zaki kashe babana da mamana?” Ta mugun tsorata anma tadanne tareda yin murmushi tanacewa “mesukamin? Babu , donhaka ni tambayan bilki kawai zanyi!” Yamike tareda cewa bazaki ganta ba nasan menakeyi, so kike kiyi amfani dani wurin ramakon ki ko?” Ganin datayi tamkar yasan komi ta tabbatar dacewa lallai yakaranta littafinnan donhaka tabata rai tareda cewa “ae!” Baiyi mamaki ba, dama yasan dole zaa rina, abunda zatace kenan, yamike tareda cewa “kinemi wani hanyan ramakonki badaniba, sannan kiyi adduan Allah yarufe bakina akanki” yana fada yabar gydan, ko ajikinta don tasan bazai fadaba, dazai fada tun tana baiwarta zaifada, tayi zama tana tunanin hanyan dazatabi duk iya tunaninta dole yusuf ne hanyan, inbai taimaka mataba babu yadda zatayi, gashi yariga dayasani tasan zaibi duk wani hanya domin yaga ya tsayar da ita, wanda aganinta bazai taba faruwa ba, donhaka dole tabi hanya daya, wato ta ajiye komi tajanyo yusuf ajikinta har yasota wanda bazai iya mata musu ba, wani zuciyan tace toh yanzumman ya aka kare? Donhaka bari tagwada tagani Kwanansa uku bai lekota ba, tana hankalce anma tana adduan Allah yasa yazo din, domin zuwanshi ne kadai mafita agareta, cikin ikon Allah dayamma kamar yadda takeyi, yau kuma dogon rigane ajikinta tadaura dankwalin taje cin masara, harta karbi masaran taji murya abayanta yanacewa shima abashi, juyawan dazayi taganshi, bata kulashi ba takarba tafara tafiya wanda yana binta abaya sanye yake da kannanun kaya sunyi asalim yimasa kyau, kowa kallonsu yake domin ba karamin kyau sukayiba, tayi kaman batasan akwai mutum agunba har sukaje kofan gydan tabude tashiga yabiyota, bata kulashiba tacire dankwalin gashin yazubo tazauna tamike kafafunta alamun tagaji, tanaji yana kiran sunanta tashareshi tamkar bada ita yake ba, ganin ta mayar dashi mahaukaci yanufi kanta kwalban coke dake hannta yakarba yawurga akasa tas tafashe, aliya bata dago ta kalleshiba balle ta tambayeshi, ganin zata haukatar dashi yasa yanufi kanta ganin zai mata hauka tasa kafa ta tokareshi hawaye ne a idonsa ” don Allah kiyi hakuri duk zuciyan dakikayi dani kiyi hkr, baxan iya rayuwa ba keba, wlh inasonki aliya kefe madafar zuciyata, na yadda ko meye zakiyi dani kiyi, kiyi amfani dani zanyi biyayya inhar zaki gwadamin so, komi kikeso zanmiki in bilkisu ce barin aika akirata” yamike zai fita tace “yarima!” Yajuyo yakaleta sannan tace ” kainake son kaje kadaukota dakanka” ba musu yace “toh (Kuyi hkr nayau bayawa, nayu latti ne,[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 12  benaxir  October 2, 2015  Hausa Novels  122 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Fitanshi baikai awa daya ba saigashi da bilkisu, tana shigowa aliya tajata suka shiga daki tabarshi a falo, shigansu bilkisu tayi mamaki kwarai, kallon gidan takeyi dakuma aliya wacce taga wautanta na rashin gane aliya tunfarko, tabbas aliya batayu kama da baiwa ba idan tayi laakari da yanayinta, aliya ta numfasa sannan tace ” kiyi hakuri bilkisu ke kadai na yarda inaso kitaimakeni, anma saikinmin alkwari cewa har mutuwarki babu wanda zaki fadawa” bilki tayi shiru,azaman duniya idan ana kirga masu sonta tasan dole aliya tazo aciki, domin ta taimaketa sosai donhaka batareda wani tunani ba tanuna amincewarta anan aliya ta fara kissa mata labarinta daga farko har karshe akan waccece ita, dakuma dalilinta nazuwa fada!, bilkisu ta tsorata sosai don bata taba kawo haka arantaba, anan taroki bilki datazama idonta acikin fada, bilki babu gardama ta amince aikuwa aliya ta mata alfarman komeye takeso zata mata, dawannan suka fito yusuf na falo har bacci yafara kwasansa domin sun dade adakin, bilki tafito haka yamayar da ita kamar yadda ya fito da ita, dawowansa yasami aliya na kallo shi abun na damunsa toh batada yanuwane suka barta take wannan garajen? Kayan kasada? Hakadai yazauna akujera yadurkusa dakanshi takaleshi ganin yadda yayi tace “meye ka sunkuyar dakanka kaman shege a rabon gado” abun yabashi dariya anma yadaure fuska bai tanka ba, ganin haka yasa itama ta tsuke tareda cewa “alakarmu bazata yiwuba inhar bakadena shaye shaye ba, daga yau kadena!” Yayi shiru yana kallonta ko falmata datace yabar shaye shaye tana masa fada baitabajin yadena ba sai ranan, yasa aranshi bazaikara shan wani abuba, “insha Allah nadena” jinhaka yasa tasake masa sukadanyi tadi duk maitarsa nason sanin meye plans dinta taki fadamishi, anan yake cemata auren abdullahi bayan sallah, ta ce “ni yakamata nashiga kasuwa ma saboda banda kayan azumi ko kadan, muje karakani” aikuwa suka fice tsum dogon riga iya gwiwa dakuma wando takara sawa sannan sukafito yakalleta dakyau azucinyanshi yace “wannan yarinyar yar bariki ne wlh” kaman tashiga zuciyansa tace “karkayi tunanin ni yar bariki ce, nayi rayuwar kudu” yayi murmushi tareda cewa “kinyi kyau” dakafa suka taka har kasuwa shikam har kafofinsa sunfara ciwo yasan yau sai yayi jinyansu amma itakuwa ko ajikinta tasaba , suka siya komi don inhar zata mika kudi shiyake mikawa, ganin zai rainata tace “nifa ba irin yanmatanku bane na zamani dazakuna kashewa kudi donku siya zuciyarsu” yayi murmushi sannan yace “oh mata dai, yanzu da bansayaba zakije kice yarima guda dan sarki anma haka yabarni nasa kudi nasiya tsabar rowa” abun yabata dariya tace ” toh aiku mazanne hannunku kaman kuna ajiyeshi agyda kafin inbanda haka ai kasan shi kyauta yana kara dankon zumunci, zuciya tanason mai taimaka mata, ko mata da mijine wlh inkana kyautata mata darajanka dabanne, aanma wasunku sai balain rowan tsiya, wani lokacin kunsan mace tafi karfin abu duk dahaka kumata mana, ko bazata karba ba. Anma wai saikuce kuna gwadata ne, waxaku rainawa hankali, gwara kanayi kana ihsani,” tabashi dariya nan yakara tabbatarwa macece mai experience na rayuwa, anma yadanne ransa yace ” samarin g.s.u marowata ne kenan?” Kut wlh a a, mukam yan gombe akwai kyauta” “Ta ina kika zama yar gombe????” “Oho dai gwaramu kaida kagama a.t.b.u samarin atbu ne da rowa” “Allah kije kiga mu har mota muna saya” “Ae naji wannan zubairun” Ganin me masara sukayi ta tsaya tana dubawa tadauko daya tabashi tareda cewa “Ci” yakarba ya gutsura ” hmmm dadi” Suna tafiya sunaci baisaba ba duk saiyajishi a tsarge anma yahadu da yar tasha yazaiyi da rayuwansa?” Gyda suka nufa kicin suka ajiye na ajiyewa sannan suka fito, yamata sallama yanufi gyda Tun ranan suka soma shakuwarsu har azumi ta shigo shine yarage zuwa don yana wuni bacci ne, aliya kuwa alokacin takafa ibadunta, tanajin labari lokaci lokaci agun bilki idan tasa yusuf yadaukota, falmata bata canjaba, donhaka aliya ma bata ajiye kudirinta ba, aliya tayiwa bilki kayan sallah, yayinda shima yusuf haka yasiyo akwati guda yaciko da kaya yakawo mata, taki karba anma ya ajiye yafice yabarta, taji dadi koba komi her first love worth it, ayanzu son datakewa yusuf yawuce duk wani tunaninta, akullum addua take Allah yabarsu tare, Yusuf kuwa satin farko shiru baisha giyaba , ana shiga nabiyu yafara canjawa, kana ganinsa kaga marar lafiya watarana ansha ruwa yashigo gun aliya anan yazauna kaman zaimutu tayi tambayan duniya anma yace mata bakomi, bata rabu dashiba harsai da ya rike cikinsa yana cewa “aliya ki gafarceni, kishi nakeji ” dasauri tadauko masa ruwa yasha anma ya girgiza kai alamun bashibane alokacin tagane meyake nufi, babu giya agidan duk tarude “karka mutu bazaka mutuba, Allah yaga zuciyarka kaci gaba da danneea” idonsa yayi jajur, duk yafita hayyacinsa batasan lokacin data fitaba, giyan taje tasiyo takawo mai tareda cewa gashi kasha kadan, ahaka harka bari” yakalleta idon jajur yace “nariga nayi alkawari bazan kara shaba, kibari kawai” hakan yasa ta je toilet tajuye gaba daya tafito sai karfe goman dare sannan yasamu kanshi yakoma gyda nanma yaje yakara tarar dawani tashin hankalin don falmata cewa tayi yaje shan giya baikulata ba hartagama hargowanta tafice anan kuma labari ya iso mata cewa kullum ana ganinsa tareda wata, nan ta bukaci a dubo mata wayene! Dukkan sarakunan gari ancika makil a fada, donyin council meeting wanda akeyi kowani laraba, masu sarautan duk kowa yazauna don a tattauna matsalolin al umma dake faruwa, inda anan aka shigo musu da kayan sha da ciye ciye, sungama lafiya inda waziri yasanar da auren abdullahi dazaayi a sati mai xuw, sannan yamusu barka da sallah, zaikoma yazauna sai yafara rike wuya yana muzurai, duk hankalin kowa yayi kanshi anan yakwanta yana muzurai, farin yawu yafara fitarwa, tuni aka nemo likita anma kafin ya iso, waziri yace ga garinku Labari tuni yazaga gari aliya wacce ta idar da karatun quraninta taga yusuf yashigo a birkice idonss jajur yana cewa “aliya nasan kinzo daukan fansa ne anma kina mace meya hadaki da kisa?” Takalleshi tareda cewa “wana kashe? Sannan meyasa zanyi kisan?” “Karki rainamin hankali waya kashe waziri?” Mikewa tayi zummur tareda dafa kirji “yarasu? Alhndlh? Amma waye haka yataimaken? Kenan bani kadai bace me harinsa” “Abunda zakice kenan? Ke wato kin kwashe kayanki agaban manzo” “Bawani kwashe kaya. Wlh bani bane, anma inaso nasan waye, burinmu daya, ni nayi niyan kashe waziri anma bada hannuna ba, naso nabi hanyar da hukuma zata hukuntashi, nawa tona masa asiri ne kawai” Ficewa yayi yabarta “Aliya tuni tafara tunani, azumi na garata anma haka tamike taji wayam batajin yunwa, duk ta kagu tasan waye mai tayata aikinnan, Wayarta ce tayi kara daukan dazatayi taga antynta ne “Aliya ki saurareni kiji yayanki yazo yadamu ingayamasa inda kike naki fada jin kince kar infada kowa, anma kuma yanemoki donhaka kizama ashiri zai iya samunki kibi ahankali don yadau alwashin kashe su ne acewarsa kina bata lokaci” Aliya tayi kufum kafin tace “wani yaya? Dama imada yayane? Yaushe aka haifes[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 13 & 14  benaxir  October 4, 2015  Hausa Novels  119 Views [10/4, 5:37 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Bata amsa ta ba saidai cewa datayi “ina kasuwa zankiraki idan nakoma gida saimuyi magana kedai kiduba dakyau zai iyayin wani abu daban, nibansan gurinki yazo ba sai yanzu dayake kirana” kashe wayan tayi aliya ta tsaya kallon wayan, bataci ta zamaba gwara tamike dakyau tanemi mafita duk da tasan cewa yusuf baxai taba fadawa kowaba, dole tafita neman danuwanta!, dole tabi diddigin kisan kafin sarki yarigata yasa akamoshi. Murna zatayu ko bakin ciki? Anma dai koba komi its a relief tanada danuwa ba ita kadai aka bari ba, tuni tafara tunanun yadda zataga bilkisu din abakin bilki ne kadai zata sami lbr, kayanta tacanja tadauko wani katon roba tafita shago takarbi pure water tajuye aciki ta tusa wayanta acikin zanin sannan tanufi hanyar fada, ahanya mutane su tsareta don siyan pure water abun yafara batamata rai ita tasaka ne don bukatunta daban akan meyasa zaana tareta don asiya? Dahaka dai tanufi fadan inda ta fara survey din gurin duk rashin hankalinta da kuma basiranta babu hanyan bi, katangan ma dogo ne irin dogon da babu dan adam dazai gwada shiga haka, agun aka siya pure watern dukka don yanada sanyi sosai roban da kudin tamikawa wani almajiri tadawo gyda, kwanciya tayi akan gado itakam zatayi hauka gashi ankusan shan ruwa haryanzu batasami hanyan shiga fadaba. Tasan dole tabi hanyan daya kamata tabi wato yusuf,bayan asha ruwa saigashi yazo ganinta yayi akan sallaya yaga batamasan yazoba hakan yatabbatar masa dacewa tunani take, shi gani yake kaman ita takashe waxiri anma yadda tayi dazu tasashi kokonto, kuma dayaje fada yasami lbrn duk abunda aka kawo aci daga kicin bilki tana fanninsa a lokacin toh kodai aliya tanada wani ne bayan bilki? Kokuma gaskiya ne ba ita takashe shiba? Hakadai yazauna agabanta ganin tadamu batasan yazo gunba yabuga kanta kadan tuni takaleshi yayi murmushi tareda cewa “waya taba minke yanzu na ajiye tarbiya ta da rawani na Nazuba mai farillai da mustahabban rashin mutunci” kallonsa tayi tareda cewa “kaifa asalim dan tasha ne ko baa taba gayamaka ba?” Yayi dariya tareda cewa “gashi kinfadamin? Bazaki kira bilki kiji daga gareta ba?” Jin yafadi haka ta tabbatar gwadata yake donhaka Allah ma yataimaketa bata fara fadaba, donhaka tace “a a bani da abun fada mata”* tuni yaji sanyi aransa don yatabbatar da ita tasata zata bukaci taji wani abu tadin mutuwan suka farayi inda tabugi cikinsa taji abunda takesonji , tabbas wanda yasa maganin daga kicin yafito tadaisan yayanta bazai je as bawa ba don bawanda zaiyi tunanin haka , toh yazama kenan yana da mai taimaka masa bata idar da tunaninta ba yacigaba dacewa “yanzu inaga bikin abdullahi zaa daga saboda rasuwannan, ” “Wacece budurwarsan nan?” “Yar galadiman yanzu” “Ni naganshi ma dazu dawani da na tambaya akacemin dan galadima marigayi ne” “Toh bantambaya ba wani galadiman ba, tunda san ke kadaice agun wanda yarau da ko?” Gabanta yayi mummunan fadi anma tadaure takirkiro murmushi zuciyanta na bugawa dakarfi tace “ae! Nikadai suka haifa saidai dayan galadiman, wat a bad luck duk sauran masu sarautan basu mutuwa sai galadima!” Ya jinjina kadan sannan yace “yanzu gashi wazirin yarasu shima ai Allah dai ya dakatar ahaka” “Ameen” “Sarki yasa ayi bincike sosai you have to be careful sosai, don nasan wannan bazai dauka dasaukiba acikin fadansa akashe mutum” Duk ta kagu yabar mata dakin tayi tunani donhaka tafara baccin karya, ganin haka yasa yace “opps! Harkinyi bacci barin koma ” Yana fita yarufo mata kofan tawaje tuni tamike tazauna dakyau, yayanta yaje as mutumin arziki yana shuka tsiya daga kasa, lalle toh ai babu marabansu da ita, gashi batama san sunan yayan ba, yanzu yazatayi? Tunani yazo mata tunda yusuf yace suna yawan zama tare dole ta ziyarci fada, Taci wanka tasha kyau sosai abaya ne bski ajikinta tafice tsum tanufi fada ganin fadawan suka fara tsareta tanuna musu cewa tazo gaysheda gimbiya yakolo, dolenta tajira aka tambayo gimbiya sukace ai aliya ce. Nan tabada dama aka shiga da ita, Tagama survey dinta kafin tanufi fannin yakolo tana isa yakolo tagwada farincikinta sosai takuma ja ta ajiki, aliya tagwada mata yau tazo gari don tagaydata nan da nan yakolo tace “toh dole nabaki masauki, zaki zauna a fada harsai lokacin dakika ga daman tafiya” [10/4, 6:11 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya tanuna jin dadinta tareda cewa “barinjr hotel din dana ajiye kayanna nadebo tukuna” dahaka suka danyi tadi aliya ta musu taaziya inda yakolo ta amsa, fitowa tayi tanufi fannin da aka kaita taroki bayin da su kira mata bilki don Allah sunji dadin ganinta suma dahaka suka kira bilki itama magana ce acike a bakinta, nan ta zayyana ma aliya cewa bawanda yasan waye , aliya ta tambayeta waye abokin da abdullahi ke shigowa dashi tace ” awh dan gidan galadima marigayi ne , sunanshi sufyan, tun wancan satin yazo” “Kisa masa ido! Sosai fa” “Toh” Suna rabuwa tafito tanufi gydanta tadibi kayanta na sati biyu hade da kayan sallahnta sannan tadawo fadan, tuni ta makale wa fannin yakolo tunda taji labari cewa sufyan da abdullahi suna yawan shigowa” tuni shakuwa tashiga tsakaninsu domma duk yaranta mata sunkoma makaranta saura abdullahi ne shehu ma bayanan, aikuwa an idar da sallah sai gasu sunshigo tana zaune akan kujera suma suka shigo abdullahi na ganinta yafara murmushi “aliya ce yau agydannan?” “Yarima na gaydaka” nan tajuyya takalli sufyan saida gabanta yafadi shima kallonta yake, kammaninsa daya da babanta, tabbas yayanta ne babu tantama ta amince, Allah mai iko anma yadda yayi ta tabbata bai ganeta ba, taji dadin haka donhaka sai suka gaysa sunadan tadi, yakolo tashige daki tabarsu inda sukasha hiransu sosai anan tadansan wasu abubuwan akanshi, nacewa ashe kasar waje aka tafi dashi tun primary yaje gun kanin babansu a cyprus anan yafara makaranta harya gama, jitakeyi kaman taje ta rungumi yayanta anma babu dama,koba komi tanada danuwan dazata kishingida ajikinsa idan tashiga damuwa, basu tafi ba sai karfe 10 sun sake sosai abdullahi ma baida matsala har cewa yayi washegari zasuje gun matar dazai aura takuma amince, , donhaka washegari dasuka shirya tashiga mota abdullahi na gefe sufyan na tukawa, suka isa yarinyan tanada kyau ga kamala da mutunci da dattako, tana kallom aliya da sufyan tace “anma kai yayanta ne ko? Kuna kaman sosai” gabanta yayi mummunan fadi bashiri taji sufyan yayi dariya yana cewa “tsabar soyayya ne muka dawo kama, budurwa tace fa” tace “awhh gaskiya kam, Allah bar soyayya” Yabar aliya da tunani tuni shima abdullahi yafara tsokansu Yusuf yaje gidan aliya yaji shiru yabude da extra key dinsa anma duk dahaka baiganta ba, akwai kayanta donhaka saiyayi tsammani kotaje wani gurine ganin har karfe sha daya yatabbatar masa da bazata kwana a gida ba, aduk zamansa da ita baitaba jin takira sunan wani ko taje gun wani ba balle yayi tsammanin zataje, tuni yafara tunani lallema tayi sabon saurayi, tafita dashi kishi duk yabi ya turnukeshi dahaka yadawo, washegaru ma yakoma shiru bata dawi ba dayagaji yakoma shigowansa gida kenan yaganta tafito a mota tareda abdullahi dakuma sufyan, tunaninsa tadaure kayan jikinta yatabbatar masa da ba baiwa bace tadawo, toh metazo yi? Wannan yarinya da kwainane. Suna tafiya yakamota tabaya tajuyo tareda fuzge hannunta menene! “Mekikazo yi anan? “Meruwanka?” “Bazaki fadaba?” “Ziyara nazo na sati biyu, kuma karka kuskura kanuna muna tare don zan dizga ka” Yayi mugun tsorata lalle yarinyannan munafuncinta ko sallah bayayi, Aliya da sufyan da abdullahi sun shaku sosai don ran sallah saidata fita tagansu suna hawa, duk da ta kalli masoyin nata wanda bakin ciki yasa yanzu yake shareta yakoma ruwa tsundum ba shan giyansa, Satinta biyu cif tasamu tahada duk wani info din dazata hada, ayadda taga sufyan bai ganetaba ita aganinta tagama dashi duk wani hanyoyinsa zata toshe, sunmata goma na arziki kafin ta tafi gydanta takoma ta zauna tana tunani tabbas yakammata tamike tsaye jin datayi abdullahi da sufyan suna magana a mota ya tsaya mata arai tagagara ganewa kuma ” toh wanda bashida laifi ya mutu dalaifin wani” Sallah tayi takwanta acikin barci taji kaman ana shafa kafanta bude ido tayi mugun figita tayi don ganin wanda ke gabanta, sufyan ne sanye da kananun kaya, tajuya takalli dakin ta tabbatar dacewa ae gydanta nefa sannan ta kalleshi “sufyan mekazo yi anan?” “” hello little sister! Long [truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 15  benaxir  October 5, 2015  Hausa Novels  103 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR “So am d fool here” yadanyi murmushi sannan yace “Kinda” zama yayi agefen gadon yayinda itama tamike tazauna, “meyasa kika kasheshi? Kinsan hukuncin kisa?” Kallonshi tayi a harzuke sannan tace “meye zakawani ce nakasheshi? Sharri zakamin?” “If bake kika kasheshiba toh waye?, yayi daidai ma domin kuwa bashi yakashe baba ba!, bakuma sarki bane” zare ido tayi jin yace bashi yakasheshiba , sannan jin kuma bashi yakashe mahaifinsu ba toh waye? , “keda kike zaune anan fiye da watanni ni acikin sati naxo nasamu lbrn dakika garara samowa,” “Yoo toh ai kai namiji ne ka manta? Zaka iya shiga ka fita duk inda kakeso, nikuwa mace inada limits,” “ba abunda ke tafe dani ba kenan, gidannan zaki tattara kibarshi acikin satinnan, kikoma gydan inna nagayamata zaki koma,kina ya’mace kina zaune ke kadai, in wani abu yafaru fa, kinje kin koyo halin yahudawa,” “Nifa zaka takuramin wlh, kaida kaje can wani bariki ne baka koyo ba, angayamaka bana lura dakai da abdullahi ne? Kuma akanme zanje gun inna? Nasan da ita ai naki zuwa” “So kike kizauna saboda wannan katon yusuf din yana zuwa kuna rufe daki kubiyu ko? Mekuke ayyanawa?” “Awhhhsh yayah kanada zato, nifa ba abunda yataba hadani dashi!” “Ki rantse baitaba rike yatsanki ba” “Ae baitaba ba” tana fada tana murkuda baki, hannu yasa ya riko kunnenta tareda cewa “ko ki tattara ko namiki duka” “Wayyo yayah sakemin kunne zafi,” yasake tacigaba da murguda masa baki tana tattare wayoyinta “nikam ka fita wlh, duk kazo ka takurani” “Ba inda zanje, ki zauna ki sauraren, waziri baya gari lokacin da akayi kisan baba, wanda hakan yana nuna baisan da labari ba, alokacin yaje taaziyan mahaifin matarsa, dole mukara tsananta bincike,” “Toh naji katafi sai anjima”mikewa yayi yafice tareda murmushi rufo kofan tayi, tazauna tana tunani tasan yadda yafara maganan nan bazai barta ba saiyasamu biyan bukata, duk yana nema yatakurata tana zaman lafiyata, yusuf ne yashigo fuska a murtuke ganin yazauna bai kulataba tace “meye kashigomin kaman gunki” Bai kulataba sai haki dayakeyi ganin zai bata mata lokaci tadauko jakanta sannan tafito harzata wuceshi yamike yarufo kofar, ganin yatsaya kaman gunkin gasken, ta harzuka sosai tabugeshi da zummar tawuce hannu daya yasa ya bangeta, saigata a kan gado, yakoma yazauna akan kujera sannan yafara “Aliya kinsan inasonki, kuma bana danganta soyayyanki dakomi, aliya meyasa kike min haka? Meye tsakaninki da sufyan yanzu naga yafito daga gydannan? Dama dalilinki nazama a fada kenan don ku shaku dashi? Meyasa kike haka aliya? Kina wahalar min da zuciya” Dariya tayi tareda cewa “sufyan fa kace,” Mikewa yayi yabuga table din dake gabansa dakarfi sannan yafice binshi tayi da kallo don mamaki take harta mike tafito saigashi yadawo rike kanta yayi dakarfi, yaki sakewa, gashinta nazafi tanacewa “yarima ka saken, dazafi nace kasaken HALACCIN SARAUTA 16  benaxir  October 6, 2015  Hausa Novels  110 Views [10/6, 7:05 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Bai saketa ba baikuma kulataba, kan kujera yakaita tazauna zuciyanshi na kuna yaja tsaki yafice, duk da zafin datake ji bashi zaisa tagagara yin dariya ba, tadauko ribbon ta tace kan sannan tafara hada akwatinta,wayanta taji yana kara tadauko tareda dubawa antynta bashiri ta dauka tasa a kunnenta “Anty ina wuni inashirin kiranki” “Bakomi yakike? Kinhadu da yayankin?” ‘Ae yatakurani wlh” “Hehe amfaanin yayan kenan “Cewa fa yayi intattara inkoma gun anty kuma wlh banaso, don bazan sake nayi abunda ke gabana ba,” “Ai yafi kina ya mace ba daidai bane kizauna a gyda ke kadai, shiyasa tunda nake gayamiki banaso ai bayadda na iyane dake da taurin kanki “Kai anty ni yanzu mene ne lbr?” “Lbr shine ki lallaba danuwanki kimasa biyayya, shikadai gareki shine gatanki, maganan ramakon nan kibarshi haka, kifito da mijin aure” “Hahahahaha anty zakisa cikina yayi ciwo, cewafa kikayi aure, nida ko mashinshini bandashi” “Kedai kikaki sauraransu, bari zantura miki adduoin dazaki nayi kingane?” “Toh anty sai anjima” Kallon wayan ta tsayayi tana daria, ita sai yanzu tunanin aure yazo mata, bayan tadan kimtsa kayan ta tattara tafito don zuwa siyayyan dan abunda baa rasaba, tsintar tsohuwa tayi ahanya sukayi ta tadi ta shagala sosai, komawanta gyda tasamu dakinta fanko sufyan yasa an tattara dakin tsum, haushi taji kaman ta tashi sama anma babu yadda ta iya, wayanta tadauka da zumman kiranshi saita tuna batada numbanshi, tsaki taja rike da ledodin hannunta tanufi gydan inna tashiga da sallama inda innar taketa murna kaman ta hadiyeta, ga kayannan kwartaye sunfi goma suna shigarwa hakan yasa tadaina mamaki domin kuwa ita tasan cewa Dan zuwanta kasuwa da bata wuce awa uku ba baikai ace an tattara mata kayanta ba, wato ya nemo kwartaye don su samu suyi sauri kartahanasu kwashewa, tana tsaye tana gantsaran goruban data saya tana kallonsu harsuka kimtsa mata kayanta tsaf, harzasu tafi tace “ai baku gama ba” takarbi tsumma da tsintsiya agun inna tabasu suka share suka goge, taciro musu zanin gado suka gyra, sannan tayi murmushi tareda cewa nagode! Koba komi sunji jiki, tashiga dakin yaji komi tsaf kunna a.c tayi tasaka turaren wuta sannan tashiga wanka, fitowarta tasamu inna ta aiko mata da abinci ,tabude taga tuwon shinkafa ne da miyan agushi yasha kasusuwa, bude ciki tayi sosai don bata cika girki ba, inzatayima bata yin tuwo Bude ciki kawai tayi taci tayi nak tayi gyatsa sannan ta mike akan gado, Yusuf kuwa hanyan gydanta yanufa yaga babu kowa, hankalinsa tayi kololuwan tashi,domin kuwa duk a tsammaninshi abunda yamata ne yasa tacanja gydan yasan bakaramin wahala zaisha ba kafin yakara samota, haushin sufyan da takaicinsa yamasa yawa, gashi a ranar anfara bikin abdullahi wanda da har andaga saboda mutuwan waziri anma sarakunnan suka nuna badamuwa adaura kawai don matan makaranta zata wuce daganan, fada tacika makil yana tunanin ta ima zaiga sufyan don yatambayeshi, saanshi daya zaaje dinner duk da baiyi niyyan zuwa dinnern ba anma haka yashirya tsum yaja mota yanufi gun, duk iya kokarinsa na son ganin sufyan bai ganshiba, haka yahakura yazauna kanshi akasa, matan dake gun duk hankalinsu yayo kanshi dn yusuf bana zubarwa bane saidai shiyana ta tunanin masoyiyarsa ba, sufyan ne yafito manni wa amarya da ango [10/6, 8:35 PM] Adda Bena: Yusuf na ganinshi yamike yanufi kansa cikin bakin ciki da takaici har wani duhu duhu yake gani, yana isowa ya damko sufyan dakarfi sufyan yajiyo tareda matsowa yana dan taka rawan shakiti bobo, yusuf yace “Ina taje?” “Bangane ina tajeba?” “Bata gayamaka inda zatajeba?” “Tafadamim, baikamata kasaniba, inaso kafita harkanta, kafita hidimanta, ba saar yinka bane,” Yusuf daya kara damkoshi sai tunkudr shi yayi akasa dakarfi wanda saida hankalin mutane yadawo kansu HALACCIN SARAUTA 17  benaxir  October 7, 2015  Hausa Novels  100 Views [10/7, 9:02 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR sufyan yamike yana karkade kayan jikinsa tareda kallon yusuf, yusuf baiji kunyan wani abuba yakara nufa kanshi ya damko shi dakarfi abdullahi wanda ke filin yanufi kansu don rabasu, anma yayi latti domin sufyan yasha naushi, yusuf tsakaninsa da Allah ya mammaujeshi alokacin dakyar abdullahi yasamu ya kufce sufyan sannan yashiga tsakaninsu, wasu ne sukaja yusuf don yadena abun kunyan dayakeyi wanda magana tuni ta yadu, yarima yana fada ,sufyan mota aka nufa dashi don yawuce masaukinsa gogan naku kuwa fada aka wuce dashi alokacin zuciyarshi tafasa take duk ya rikici a gigice aka kaishi fanninshi falmata ce tanufo kanshi don labari ya isota cewa fada yake akan liya, cikin fushi wanda bai taba ganinta aciki ba ta umurci kowa ya watse yabarta da danta “yusuf mekakeso namaka? Kai ba karamin yaro ba yusuf, wani irin rayuwa ne haka yusuf? So kake ka kasheni?daga yau acemin kasha giya, jibi mata, yau kuma akan baiwa kake fada? “Kidena cemata baiwa saboda a yanta ta, rabon dakiji anganni da wata tun yaushe? Tun ran da nahadu da aliya!, giya fa? Tun yaushe???” “Da Allah min shiru da bakinka da rimi rimi abun arziki kadena sha, meyasa kadawo sha?” “Saboda narasa wacce tahanani sha” “Kana nufin kacemin ba don Allah kabari ba sai don ita?” “Dazan bari dana bari tuntuni, anma don ita nabari Allah nagani donhaka karkiga laifina. Kinaso in nutsu kema ya kamata kidena musgunawa yaran wasu, kidena neman batanci da yaran wasu” Hannu tasa ta gaura masa mari, wanda saidayaga walkiya a fuskansa.”ina magana kana magana?; yaushe nahaifeka? Kai wato mace dadi ko, kaje ta tusaka kasan pant dinta,” “Nifa ko tabata bantabayiba” “Yimin shiru munafiki, duk duniya bawanda karaina kaman ni, nagaji zangayawa sarkin saimugani ko shi zaka ji maganansa!” [10/7, 9:09 PM] Adda Bena: Bata saurari mezai ce ba tafice, fanninta tanufa, gaskiya yakamata tadauki babban mataki akan aliya, jakadiya takira tareda cewa ” kinemomin duk inda aliya tashiga ki kawomin ita nan” Aliya kuwa tana zaune akan gado tana game din candy crush bacci yaki daukanta, sufyan ne yakirata awaya tadauka “Kekuma kina tareda mahaukaci ne bansaniba?” “Waye mahaukacim?” “Mahaukacin saurayinki mana, zaimin hauka a bainar jamaa, total yarinta?” Tana kwance ne saidata mike, ita duk tunaninta hala yusuf yasha wani abune yaje da zafin kishinsa yayi wani yarintar, “Yaya meyasameshi? Yana ina? “Anma zanmiki rashin mutunci, bazaki tambayi jikina ba saina wani kato? Nidana sha duka?mtsw” “Kayi hakuri bazai karaba, anma don Allah yana ina?” “Gidan ubansa” “Shikenan don Allah kana hakuri dashi” Bai saurareta ba yakashe wayansa don yaga itama giyan soyayyan ke dibanta [10/7, 9:29 PM] Adda Bena: Ta kashe wayan takira wayan yusuf wanda ke kashe ahaka taketa tryn har bacci ya kwasheta, bata juyaba sai asuba, Har rana tana tryn numbansa baya shiga ta tattara sallayanta tanufi tsohon gidanta a kofar gydan taja kujera tana zaune tayi hakane dan yusuf ko zadu hadu, wasu yanmata ne guda biyu kana ganinsu kaga yan biyu don inka cire kayan jikinsu dasuka saka daban daban kominsu na siffar jikinsu iri daya ne, suka nufo kanta daya sanye da abaya daya kuma sanye da atamfa Mai abayar takarewa aliya kallo bisani tayi tsaki sannan tace “yanzu wannan jaka dabbar ce daman? Baka mummuna kaman kasam takashi na!? Shikuwa yarima meyagani anan? Mai atamfan itama takare mata kallo sannan tace “bar munafiki nema yake yajamin raini da kaskanci, ta ina zaahadani dawannan gidahumar? Banza talaka!” Aliya zuciyanta na tafasa musamman datagano maganansu cewa mai atamfar ce budurwar yusuf. Bata kulasu ba tadanne zuciyanta tanufi sgiga gidan, coke din hannunta tasaka ta watsawa aliya a jiki, wani juyowa da aliya tayi ta damko makokoronta “KE WLH TLH NI KARAMAR MAHAUKACIYA CE!!!ZAN ZUBAMIKI RASHIN MUTUNCI!!! Kuyi hkr daga yau har zuwa saturday zakuna samun kadan kadan due to am a little bit busy, HALACCIN SARAUTA 18  benaxir  October 8, 2015  Hausa Novels  109 Views [10/8, 8:34 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR mai hijabin wacce itace hussienan takalli aliya cikin rashin tsoro tasa hannu itama tariko wuyanta, tareda cewa “ke angayamiki tsoron ki akeji?banza karuwa jaka dabba!” Aliya tasa hannu ta make bakinta tareda cewa “ki iya bakinki don banda mutunci” “Dama ina kikeda mutunci banza” Aliya fuzgan jikinta tayi tareda tattare komatsanta tafice tabarsu agun, gyda tanufa ta zauna akan kujera cike da bakin ciki da takaici, yusuf tasan zainemeta, anma wasu irin dabbobine wannan? Lalle zasugani shikuma yusuf zaixo yabata labarin suwaye, Sufyan [10/8, 8:59 PM] Adda Bena: Ne yashigo kafanta yatare hanya ya mauje kafan yawuce hakan yasa ta tashi, tareda kallonsa “haba yaya dame zanji bakin cikin wancan yanmatan komeye?” “Wasu yanmata?” “Yanmatan yusuf bansansuba, kuma baitaba ban lbr ba” “Wannan saurayinkin baiyi kama da mutum ba, nima haka yamin hauka, bawannan bane takawoni, angama binciken wanda yayi kissan waziri ansamu cewa wata baiwa ce tashigo fadan itada mahaifinta waziri ya kwace gydansu da duk wani abu dasuka mallaka. Sannan yayi hanyan sanadin mutuwar matarsa, yanzu dai zaayi hukunci jibi, [10/8, 9:35 PM] Adda Bena: Kuma abincike na nasamo cewa akwai wani alh.hamidu shine kanin galadima na yanzu suna tare da baba randa zai rasu donhaka dole munemi hanyan dazamu sameshi donjin bayaninsa,” “anma yaya fisabillilah” Bai saurareta ba yafice don yunwa ne ta isheshi cikin gyda yanufa yatarar da inna yaci yakoshi sannan yafice, fitansa kenan saiga yusuf wanda CID dayasaka su suka masa kwatance ya iso gydan, sallama yayi yashigo suka gaysa da inna wacce take zaune yadda yamata ladabi taji tana kaunarshi yatambayi ko aliya tananan, tace akaishi fanninta, aliya tamike kafafu batasan da shigowanshi ba hannu yasaka ya mintsineta, “innalilalh ” tamike a razane wanda hakan yasa yayi murmushi, bata rai tayi kaman tunda aka halliceta batayi dariyaba tuni yasha jinin jikinsa, “meya faru don Allah?” Bata kulasa ba tamike tagyra jikinta tajawo gyale sannan ta yafa sannan tace “meye haka kashigowa mutane ba sallama, ko kamanta dakin mace ne?” Yayi mamakin magananta zaiyi magana tace “kafitamin kuma karka kara dawowa” baice komi ba kuma bai tashiba hakan yasa ta kwalawa idi kira, almajiri ne idi kato jibgege, hakan yasa yusuf naganinshi yamike jiki a sanyaye HALACCIN SARAUTA 19  benaxir  October 10, 2015  Hausa Novels  115 Views [10/10, 8:04 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Yana fita tarike kanta domin ciwo yake mata, itakanta tasan matsananinci so dakuma kishin datakeyiwa yusuf bana wasa bane,gashi yaje yadauko maganan yanmata yazatayi da rayuwarta inhar hakanne dagaske? Shikenan zaidaina sonta? Kawai tazauna tafashe da kuka, kuka takeyi nanma ta tuno da iyayenta tafara wani sabon babin kukan, inna ce tashigo ganin tana kuka tafara lallabinta dakyar tayi shiru. Itakanta tasan cewa aliya tayi rashin iyaye, saidai batason ta tada mata hankali ne anma ganin tadamu da ramako gakuma kukan datakeyi, don itadai tasan cewa dakyar rana yazo yafadi, aliya batayi kuka ba,a fuska akwai karfi anma zuciyanta mai rauni ne, saidata tabbatar cewa aliya tayi shiru sannan tace “inaso ki goge hawayenki ki saurareni, yau zanfadamiki tarihin iyayenki, tarihin rayuwarki, na boye da wanda ke kanki bakisaniba hatta yayanki baisaniba” jin haka yasa aliya ta gyaro zama tashare hawaye sannan tace “inajinki inna” “Mahaifinki hassan adamu shine galadima na 55 a garin yombi, kuma ya gada ne kaka da kakkani, sunyi auren soyayya da mahaifiyarki aisha, wacce tahaife ku rai biyu dake da sufyan, mahaifinki dan biyu ne haryau baki taba tunanin kitambaya ba?” Alokacin aliya ta tabbatar batayi wayo ba, tunaninta yayi nisa a yin ramako har bata hango kananun matsalan dake gabanta wanda matsalan da ake samu yanzu kenan, abu yasami mutum maimakon kazauna kabincika daya bayan daya zuciyanmu sai tayita ta mana raye raye muje har ga aikata zunubi,anan inna tacigaba “kekam ko ni kin gujewa kinki zama kinsanni, bayan ni ce gambon su mahaifinki su yan biyu ne hassan da hussieni, saini gambonsu, mu uku ne, hussienin mahaifinki yanzu haka yana raye anma baa garinnan ba, yana can senegal yana zaune da matarsa, kuma musabbabin tafiya shine mahaifinki dashi an bukaci abawa dayansu sarauta, sai shi hussien yagwada yanaso kuma mahaifinki bayaso, donhaka saiyake taimakawa don abashi bayan rasuwar galadima na 54 cikin ikon Allah sai mutanen fada sukaki yadda acewarsu hussieni na da aladun bature. Dawasu halaye wanda ni bansaniba anma sunfada anyi rikici sosai a kafin aka yanke bawa mahaifinki, randa akabawa mahaifinki aranan shi hussieni yabar garinnan bayan dogon magaanam dasukayi adaki dagashi sai hassan, haryau bawanda yasan mesuka fada, kuma tunranar hussieni ya tsani hassan dinsa, yakuma tsaneku, donhaka son yusuf shiga gydan sarauta inason gayamiki sai me shiryi, wacce kikeda kyakywan niyya, mace mai ilmi hazaka da karamci, don sarauta dakike gani yana raba uba da da, balle wa da kani Bayan tafiyan hussieni munyi jimami sosai, don mahaifinki har a asibiti ya kwanta don kewar danuwansa, munyi rashi sosai saidai ya gwadamana baya sonmu, yagwada mana abun duniya tafi masa mu, dakyar mahaifinki ya taso daga ciwo, sannan bayan haka yazo yanuna rashim amincewarsa na karban sarautan, nanma anyi daga kafin yakarba don inhar sarautar tabar hannunmu zata koma wani gida ne bazata dawoba, kaka da kakkani sarautar tamu ce, bayan mahaifinki yahau tundaga ranan yafara samun barazana, mafarkai kala kala, gashi ke kanki nasan zaki tuna lokacim da ummanki tayi barim yanbiyu sau uku, sufyan yazo yafara abu kaman tababbe bayason makaranta yafara bin almajirai babban dalilin dayasa hassan yadaukeshi yakai kasan waje kenan donhaka malamai suka bashi shawaram yadagashi a garin yombi, dalilin dayasa kenan kikaga anrabaki da danuwanki, kekuma ba abunda yasameki, wanda hakam yasa mutanen gari suka fara surutun cewa lallai lallai asiri akayi muku wanda bayaso babanki yasami magaji, ummanki tadamu sosai musamman da aka rabata dashi [10/10, 9:06 PM] Adda Bena: Ana haka shikanshi hassan yafara samun matsala da yan fada, kinsan ance baasamun mugun sarki sai mugun bafade, donhaka yalura duk munafukai ne agefen sarkim saiyazama shikadai mutum dayake kin yadda da maganganunsu, donhaka tuni tsana da keta, da hassada yakara shiga tsakani, donhaka rayuwarku gaba daya tadawo abin hatsari, hakam yasa ya kwasheki yakai makarantan kwana don kar wani mummunan abu yasameki, ran mutuwan mahaifinki kuwa ina asibiti mai gidana yana jinya, aka turomin labarin mutuwarsa, nayi jimami sosai nabukaci adauko ki daga makaranta akacemin a a abarki don kuna jarabawa, da sati daya surukata tarasu munje kaue taaziya kafin nadawo kika dawo kika tattara kika tafi abuja koda nadawo nayi bakin ciki anma dana gane gun wa kikaje saina bari kawai nasam zata rikeki amana, mukan yi waya da ita lokaci lokaci Tana gayamim awani hali kike ciki, saidai bantaba yarda tahadamu ba, aganina guduna kike zanbaki wuri, kinji takaiccecen tarihinki nasan bakisan da hakaba, iya abinda zan iya sanar dake ayanzu ne, saikuma ina gargadinki da duk wani magana dakikeyi nacewa zaki dau fansa, kidenashi na gargadeki daki daina, karkije ki janyo abunda zai dameki dakuma tashin hankali agareki, abinda yawuce yawuce, inkuma kinki yadda zaki girbe abunda kika shuka, domin bishiya kikeso ki tumbuke, dafatan kinjini? (Insha Allah daga gobe zaku fara ganin dayawa, nagode da sauraramim dakukayi so[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 20  benaxir  October 11, 2015  Hausa Novels  116 Views [10/11, 7:33 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya ta gyada kai wanda itakanta inna tasan cewa baikai har zuci ba, tana tantama dakyar ta amince anma tana tsoron abunda zaije yadawo idan aliya tayo bincike, bata cika son bincike ba itakam, tadai mike tabarta, tana fita aliya ta watsa ruwa tasako dogon riga tadaura dankwalin sannan tafito, inna ta kalleta “ina zuwa?” “Kasuwa” ta amsa, inna takare mata kallo , saidai batace komi ba saikin dawo, aliya tasan mezatace donhaka ne ma tagodewa Allah datayi shiru, Allah yagani batason takuri rayuwarta ba tsanani, tafice saidai itakanta tasan tafita ne don taji gydan ya isheta batada dalilin fita, ganin me awara tayi tanemi gu tazauna tasiya ta murmuzashi a cikin ledan yadawo kaman kwado sannan ta tusa a jakarta, gydanta nada taje haryanzu baa shiga gydan ba, tashiga tazauna taci awararta ta koshi dama tana yawo da coke dinta, takora da coke sannan tafito da zummar takara gaba, hanyan fada tanufa kai tsaye batareda wani tunani ba, harta yanki kwana taga sufyan agabanta bai saurari mezatace ba ya damko hannunta ya wuce da ita basu tsaya ba sai awani lungu, “Meye kuma yaya?” “Bakida hankali ko? Ina zakije?” “Fada zanje” “Kimusu meye” “Na ga yusuf” “Mahaukaciya,wuce mutafi” Fizgan hannunta yayi suka isa bakim titi ya tsari keke napep suka hau sannan yayi kwatancem gun, “Da kafana nazo, dakayi hakuri zankoma da kafana!” Bai amsata ba har suka isa yamikawa mai keken kudinsa sannan suka shige inna tana tsakar gyda taga yazo yawuce da aliya donhaka ta dauraye hannunta dama tana wanke kayan miya ne, tabisu don ganin meke faruwa, “Bakida hankali ne? Sau nawa zangayamiki aliya sau nawa zangayamiki ki fita hidimar fada!, kifita rayuwarsu, mutanennen baruwanki dasu, yusuf dinnan nagayamiki mahaukaci ne ki hakura dashi kinki yadda wato ga karamin dan iska” Inna tashiga dakin ganin yana matsifa yaki shiru tace “meyene yake faruwa? “Inna kiga shigan jikinta, yarinya gaba daya tadawo inyamura, aladan yarbawa, kinmanta akasan hausa kike? Kinje kin dauko dabian wasu kina mana anan!” “Yau nashiga uku zaku kasheni, meye zaka wani ce yarbawa, agarin yarbawa nazauna? Kaidai inzakayi matsifanka kayi ai gwara ni kai fa? Wayasan mekake aikawata, dogon riga ne ajikina meye aibunsa, ?” “Dakikasa dogon rigan shine zaki cire dankwalin?kin yafashi a gefe ,kokuma kisaka gajeren wando kina yawo a kasuwa, zanga ta inda zaki auru a garinnan, dawannan halin tashan kikeson auren dan sarki? Wazai baki? ” Haushi suka bata itadai tasan ba laifi tayiba sunbi sunsa mata ido, wacce tasa atamfa ta rataye gyale awuyanta tarufo jikinta baaga laifinta ba? Saita datasaka abaya dayarufe jikinta don kawai tayafa gyalen?”nikuma nce maka zan auri yusuf ne? Ko na ce maka zanyi aurene? Basai ku aurar dani nagani ba” bai kulata ba yace “inna karta kara fita dawani shigan daya sabawa addini, wannan ai karamin hauka ne!” Yana fita tamike aranta tana cewa inga karamin beran dazai takurani , da tuntuni bakasan daniba saidana girma nasan darajana da mutuncina, tsaki tayi tamike akan kujera baccine mai nauyi ya kwasheta bata farka ba sai magrib tamike tadauro alwala tayi sallah sannan takunna tv duk da batagane mesukeyi don wani indian film ne tadai zurawa tvn ido sallama taji anyi anshigo tagane muryan anma tarufe idonta kaman tana bacci, yashigo yazauna ganin tana bacci yazura mata ido, yarasa yazaiiyi yanason aliya baikuma san meyasa takeson juya masa baya ba, saiyanzu yasan dalili da hussiena takirashi awaya yatabbata tazo tasami aliya ne, yadda yasan kishin aliya yasan saiyayi dagaske, ganin tanata runtse ido yaki ya tafi yasa tadanyi juyi [10/11, 8:01 PM] Adda Bena: Tuni ya tallafota bashiri tamike “meye haka zaka rikeni” saketa yayi awh dama idonta biyu dakyar takoma don taji kunyan abunda tayi. Cikin borin kunya tace “mekazomin anan, ilya yana nan baiyi nisa ba” “Ki kira ilyan ko kasheni yayi ba inda zanje yau saikin gayamin menamiki,aliya hussiena ba budurwa ta bace so ake ahadamu da ita naki babanta abokin babana ne alh.hamidu, tuni tazauna tareda zaro ido, don ta tuna cewa sufyan yace mata alh.hamidu shine wanda suke tare da mahaifinta ran ajalinsa, dasauri ta sake fuska donkar ya fuskan komi “to ni meruwana?” “Nidai don Allah kiyi hkr. Kezan aura kenakeso ke zuciyata take bida “nan yagama sumbatunsa anma aliya ko cikanka batace ba, yana fita tajawo wayanta sufyan takira yana dauka yace “menenee? “Kazo gida nasamu labarin alh.hamidu” bata saurayi mezaice ba ta kashe wayan cikin minti talatin saigashi ya iso “Aina kika samu labarin? Keda kike nanike a daki?” “Meruwanka? Yusuf yazo yana ban hakuri akan yan biyun dasuka min hauka ranan, wai yaran aminin sarki ne alh.hamidu” “Allahu akbar, duk bincikena banje kansa ba, don naga baida sarauta anma tazo gidan sauki, yaran yanbiyu ne? “Ae! Bazaka gane wanne bace hassana ko hussiena” “Tazo daidai zanyi soyayya da daya, kozan sami kusanci da mahaifinsu ko yakikace?” “Kayi da hussiena” “Munafuka don kihadani fada da yaronnan ko?” “Oho dai kaikasani” “Kedai ki tabbata babu wanda yasan alakanmu don anasani shikenan ansan kema yar galadima ce plans dinki duk zasu rushe” Ficewa yayi yabarta bai nufi ko ina ba sai fada fanni abdullahi da matansa, yasamu tarba sosai anan yagwada sa cewa yaga yar alh.hamidu kuma yanaso, abdullahi yayi farinciki inda yace wacce aciki? Sufyan yagwada cewa hassana yakeson aura, aikuwa nan da nan yafara murna yara masu hankali kayi saan mace dawannan yace su shirya daredare zasuje gun mahaifinta, Daredare suka sha manyan kaya suka nufi gydan alh. Hamidu wanda yakarbesu hannu biyu biyu, abdullahi yayi bayanin kudirin sufyan a matsayinsa na dan marigayi galadima, nan da nan alh.hamidu yace “hassan adamu? ” Abdullahi ya gyada kai tareda cewa “ae shi” “Masha Allah ashe zankara ganinka? Mahaifina aminina ne sosai, Allah yajikan rai” Dukkansu suka amsa da “ameen” “Ban isa naci amanar abotana da mahaifinka ba, donhaka in hassana ce nabaka!” Sufyan yanuna farincikinsa yakuma yi godiya ayayinda akace suzo washegari don ganin yarinya Ranan sufyan yayi bacci mai dadi ganin cewa yadauko hanyar bayyanar gaskiyan mutuwan iyayensa, Washegari yashirya cikin janfa ya sha turare sai kamshi yake suka nufi gydan shida abdullahi ayayinda aka musu iso, yana zaune kanshi a kasa gabanshi na fadi wanda shikanshi yarasa dalili tayi sallama ahankali muryanta cikin sanyi sannan tashigo, alokacin yadago yakalleta, tanada haske saidai bata da tsayi, kananun ido gareta anma tanada karan hanci, kyaunta dan daidai masha Allah, dama shi bai fiyeson bakaken mata ba, musamman wanda yafisu haske, abdullahi ne yatabashi tuni yadawo daga duniyan tunaninsa yafara amsa gaysuwarta, kanta a kasa a zuciyanshi yace “anma aliya munafuka ne, yanzu wannan salihan yarinyan zatace taje tamata fada?wannan ai daga gani ba ruwanta salihar macece, suka gaysa sannan abdullahi yafara neman sasantasu itakanta hassanan tana fara ganinshi taji ya kwanta mata arai, domin kuwa sufyan yahadu namiji ne awaye, mai kyau da kwarjini taji ta narke da sonsa awansu biyu suka fito tarako su har gate sannan yakarbi numban wayanta, suna fita daga gidan tashiga dagudu gun hussiena wacce take labe take kallonsu tsaf suka hau tsalle da murna , su hassana anyi mijin aure, Sufyan kuwa yaki daina murmushi shikam sonta yake, karfa yagagara cika aikinsa harya ajiyeshi a gydansa sannan yakara fitowa yataho gydan inna, yayi hakanne donkar abdullahi yasan gydan saboda bacin rana, aliya tana kwance yashigo “Adarennan yaya meza kacemin?” “Ke. Tashi! Sharri zakiyima hassana ko? Yarinyannan yar salaha da ita ba ruwanta, “Ko dai taje ta nutsu don kissa irin na mata nikam kabarni bacci zanyi” fannin inna yaje yaci yakoshi sannsn yafice” Washegari aliya taci wanka tsaf tashirya cikin atamfa dinkin yakarbeta sosai ba kadan ba, tana zaune, sallama akayi wasu dogarai ne sukace wa inna ana neman aliya a fada Hankalin inna yayi dubu yatashi tazo fannin aliya “mekika yi musu?” “Babu , suwaye?” “Daga fada ana nemanki” tayi tunani iya tunani tarasa meya hadata dagun, tafito a sanyaye s[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 21  benaxir  October 12, 2015  Hausa Novels  104 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Gabanta fadi yake don babu irin tunanin dabatayi ko wanene ba, dahaka suka isa fada taga bayanda tasaba ganin mutane ba, andan cika sosai, fannin falmata aka nufa da ita inda taana ganinta ta taso ta wanka mata mari umma uwar soro ne tayi sauri taja aliya wacce tarike kuncinta cike da takaicin abunda yasameta batasan metayi ba ankafamata mari, falmata cikin fushi take cewa “duk wanda ke da hannu acikin wannan aikin kuhado min dashi,” ahanyan fita da itane taga sufyan da abdullahi suna tsaye ganinta da yayi yasa ya tsure anma bai gwadaba don kar wani ya tsammace wani abu, yaja abdulllahi gefe tare da tambayanshi meya faru? “Kasan harkan mata da matsala, nagayawa yusuf yabar yarinyannan saboda abunda zai jawo mata, mahaifiyarsa batada shariya, yaki yadda, yanzu yazo yakwanta ciwo tun ast week, anma ciwon yayi tsanani ne shekaranjiya wanda dogaransa sunce daya dawo daga gidan aliya ne yakwanta. Kuma sumbatu yake yana kiran sunanta, hakan yasa mahaifiyar tace ko aliya tamishi wani abune, wai mayya ce tanason cinye mata da, ” “Subhanallah” “Yanzu dole munemi hanyar fidda aliya daga wannan matsifan narasa meya dawo da ita garinnan” “Muje muga gimbiya” Suka nufi fannin gimbiya yakolo inda suka mata bayanin abunda ke faruwa hankalinta yatashi sosai, anma babu yadda ta iya bata isa tasaka baki aciki ba, don baa haka, yazama dole tanemi mai ceton aliya hakan yasa tafito don zuwa ganin aliya wanda akasa a cage, aliya idonta ya kumbura yayi bul don tasha kuka, ita badamuwanta abunda suke mataba damuwanta shine yusuf yawarke ko zata gwada masa irin son datake mar, kodataga gimbiya tuni kukan yakaru,gimbiya ta yi umurni wa masu gadin dasu fice zatayi magana da ita suna fita tariko hannunta “Aliya meya faru? Kigayamin gaskiyan abunda kika sani” Cikin kuka aliya tabata labarin abunda yafara faruwa tundaga tsohon gidanta, zuwa haduwanta dasu hassana da hussiena dazuwamshi data koreshi da ilya, dakuma zuwanshi na biyu shekaranjiya kenan sannan tacigaba dacewa “wlh ranki shi dade ni ba mayya bace,jinina a tsarkake yake,” Gimbiya yakolo taji tausayinta anma babu yadda ta iya donhaka tace “bazai yiwu naceceki ba, dole dole shi zai ceceki idan yamike akan gado, inhar bai mike ba, zata iyasakawa a illata ki”hankalin aliya yakara tashi bata taba jin mutuwa zamzam haka ba, tagama tsorata tarasa ina zata saka ranta, gimbiya tasamu tadan lallabata kafin takoma fanninta ta ai akira bilki, ta umurceta datana kai mata abinci tace injita, takira abdullahi da sufyan ta bukaci suje suga jikin yusuf din ko zaagane meke damunsa sun nufi fannin sa, suka tarar da likita ne sai bayi guda biyu, sufyan yazauna yadan duddubashi kasancewar yanada dan ilmi akan lafiya,yakuma tambayi likitan shidai likita yace jininsa tahau abinda yagani kenan, sufyan yadanyi dube dubensa sannan yaja gefe yazauna kusa da abdullahi yana cewa “nifa inaga akwai abunda ke damunsa yana boyena, its lyk akwai weak heart, mezai hana akaishi asibiti agani, abdullahi ya amince da shawaran, nan da nan ya umurci da azo akai yusuf asibiti , falmata wacce take fanninta tuni tafaso dakin hankali a tashe tana cewa ” iiiiiina kuma zaku kaishi?” Daga yanda take jan maganan sufyan yagane cewa tabbas batada gaskiya, abdullahi yadaure fuska sannan yace “asibiti zamuje suduba jikin dakyau” “Babu inda zaku kaishi!” Cikin tsawa tafadi haka don saida hankalin bayin yakoma gun kowa ya tsaya jungum jungum, ganin basuda niyya yasa abdullahi yariko yusuf din dasauri sufyan yarikoshi alamun yabari karya rikoshi haka suka barshi akan gado suka fito domin kuwa falmata ta kasa ta tsare Bilki kuwa dataje kai abincin basu barta tashiga ba dole takoma tasanarwa yakolo abun yaci mata rai anma babu yadda ta iya dole ta san yadda zaayi a farkar yusuf kamin wani abu yasami aliya, sufyan kuma samu yayi ya lallabi abdullahi suka shiga gari babban asibiti suka dauko likita yazo da kayan aikinsa a fannin abdullahi yasauka wani daki da aka ware masa, suna jira dare tayi donsu cika aikinsu inhar basu magance matsalan adaren ba washegari zaa iya zartarwa aliya hukunci domin falmata tasa annemo hujjoji nacewa aliya mayyace kuma ita take illatashi inhar baakasheta ba yusuf bazai tashi daga sumbatun dayake ba,saida suka bari kafa yadauke sukaja likitan suka kaishi fannin yusuf suka rufo kofan, yayi bincike sosai yagano cewa kwaya aka bashi wacce tafi karfin kwalkwalwarshi hade da allura, saboda kasanceear aliya ce aransa yasa yake sumbatar sunanta, yadanyi dube dubensa sannan yace zaiyi alluran dazaiyi reversing dinshi, anmishi allurai kwaya biyu anma likitan yanuna musu cewa sai bayan awa hudu ko biyar yatashi hakan yasa dole suzauna agun, dukkansu babu wanda ya runtsa yusuf baitashiba sai hudu na asuba nan da nan suka lallaboshi yazauna suka watsa mai ruwa zai fara matsifa abdullahi yatoshe mai baki sannan yace yayi shiru yaji, cikin basira suka mai bayanin abunda ke faruwa sannan sukace hanya dayane don ceton aliya idan safiya tayi yacigaba da yadda yake inyaso idan antashi hukunta ta yafito yafadi gaskiya shikam tuni hankalinsa yatashi jin cewa aliya na cage saboda shi, zuciyarshi na radadi mikewa yayi waizaice yadaukota suka danneshi dakyar suka lallabashi ya yarda, kafinnan suka wuce fannin abdullahi don yin alwala sutafi masallaci alokacin ankira sallah Dasafe aliya idonta yacika ya kumbura ganin cewa yau komi zai iya faruwa da ita, taci kuka harta koshi ta godewa Allah,karfe goma saiga dogarai inda akaje da ita mahukunta, gurin da ake hukunta duk wanda yayi laifi acikin fada, ta sunkuyar dakanta ayayinda umma uwar soro taketa bayanin abubuwan da aliyan tadauka daga karshe tace “zaki fadi gaskiya ko ki fuskanci hukunci, ke ba baiwa bace da an miki hukunci mafi tsanani, sannan kinsan cewa hukuncin maita a masarautannan shine akashe mutum, donhaka kifadi gaskiya kisake yarima kisake kurwansa,donkar ki fuskanci tashin hankali, ” Aliya kuka take sosai yayinda take kallon sufyan wanda ke mata alamun tayi shiru anma tagagara ganewa shikenan itakam yau mutuwa tazo mata, ta ina zata sake yusuf, gashi mintuna kadan aka bata tasakeshi, kukan datake harya hade zuciyanta alokacin. Kawai saiga yusuf yashigo filin falmata it[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 22  benaxir  October 13, 2015  Hausa Novels  129 Views [10/13, 8:13 PM] Benaxir omar: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR cikin wani yanayi na fargaba tace “yarima?” Dasauri tanufeshi shikuwa yanufi inda aliya take ya kunce igiyan da aka daureta dashi, ji yayi kaman ya rungumota ko zatasan halin da zuciyanta take ciki anma babu yadda ya iya, tuni kuwa abdullahi yashigo filin shima riketa yayi suka dagota wanda kowa saida yayi mamaki kenan aliya tasan dukkansu? Bilki ce tanufesu don riko aliya, sufyan ma gun yanufa nan da nan akasata a mota yanufi asibiti da ita, yayinda falmata ta yi umurni da a watse nan da nan yusuf yace baigama ba yanada magana, hankalin falmata yatashi tasan cewa asirinta zai tonu donhaka takara daure fuska anma yusuf bai saurareta ba, yakira likitan dasu abdullahi suka kawo mishi da likitan da falmata takawo, yacewa likitan falmatan yamasa bayanin meke damunsa cikin tsoro yace “zazzabi ne da rashin bacci,”, yakalli likitan da sufyan suka kawo masa sannan yace masa “meka samu yake damuna?” “Allurai ne akayi ranka shidade da dan kwayoyi ” Yusuf yamike yahade rai tamkar sarkin dayake shirin yanke hukunci “kukama minshi harsai yafadi dawa yahada baki aka sashi abunda yayi,” nan da nan dogarai suka kamashi, anan yahado da tsohon da aka kama wanda yake cewa tabbas shi mai kama mayune kuma aliya ma mayyace ita tacinye iyayenta, dukka yasa aka kamasu sannan yanufi fanninsa wanka yayi da zummar yabi aliya asibiti saidai fitowarsa yatarar da mahaifiyarsa tana jiransa, bai kalletaba balle yanuna yasan tana gun harta gaji donkanta sannan tace “in nina haifeka kasakesu” Wani kallo daya mata itakanta saidata tsure bai kulata ba don tunda yake itakanta bata taba ganin bacin ranshi irin na ranan ba, kaya yasa yafito don ji yayi yatsani munanan halayyan mahaifiyarsa don batada hali ko kadan tabari son mulki da son zuciya yarufe mata ido, bayason halin mahaifiyarsa ko kadan yasan shima da halinsu daya anma haduwarsa da aliya yacanja, yadawo cikakken mutum yadawo mai tausayi yakuma san darajan dan adam, yanzu yasan meya keyi kuma ya gode Allah daya hadasa da aliya akullum yana kara kaunanta sonta daban ne, dasauri yakunna motan sannan yafice daga fadan, asibiti yanufa wanda aka kwantar da aliya wacce ta gigice, sufyan duk tunaninsa karya rasata, haushin duk yancikin gydan yakeji don gani yake aliya zata iya rasa ranta, Allah kadai yasan kukan dayake a zuciyansa, tunaninsa Aliya ce kadai tarage masa yazaiyi insun rabashi da [10/13, 8:50 PM] Benaxir omar: Aliya , donhaka duk tunaninsa ta tsaya cak yusuf ne yashigo a rude yana tambayan ina aliya, abdullahi ne yamasa bayanin cewa sunbata gado suna dubata,numfashi yaja yazauna yadafa kansa nauyi yaji kanshi yanayi, don shikanshi wankan dayayi ne ta taimaka masa yaji karfin jiki, sunfi awa azaune kafin likitan yafito nan da nan suka mike inda yace musu tasamu kidney problem don kaman anmata wawan bugi agun, kuma gaskiya dukka biyun sun lalace ana son acire kuma abata guda daya, bayan haka anason jini sannan kuma tabugu sosai akanta dole ajira aga farkwanta suyi adduan Allah sa tatashi lfy kar asamu wani matsala,sufyan dafa kai yayi ya tsuguna agun saiga hawaye suna zubowa, abdullahi da yusuf wanda shima ya rikice kallomsa suke, kishine yashiga ran yusuf akanme sufyan zai damu? Meye hadinshi da aliya? Atake yace likitan yacire nasa inyazo daya, anma sufyan nan da nan yamike tareda cewa muje aduba kidney din, da jinin , yusuf wani harara yasakar mishi domshikam ji yayi hankalinsa yatashi har bari hannunsa yake, likitan saiyaga kaman abumsun gasane, donhaka yace waye yafi kusa da ita? Yusuf yayi caraf yace “nine masoyinta” Sufyan bai kalleshiba sannan yacema likitan “muje ! Ni yayanta ne uwa daya uba daya!” Ba yusuf ba hatta abdullahi dake kallon su sai daya tsorata wayan hanninsa yasake a kasa, tunaninsa ya tsaya cak, ya cukumo sufyan “kai dabban wani gari ne? Don kawai kana sonta zakace kai danuwanta ne?” Inna wacce tashigo asibitin a rude taga sufyan wanda yakirata yamata bayani tanufo kansu dasauri tanacewa “sufyan ina kanwarkan take? Yau munshiga uku innalilahi” yusuf sakeshi yayi don ya mugun tsorata, azatonsa yasan wacece aliya ashe yaudaran kansa yake baisan komi akantaba, jan jiki yayi gefe tareda zama akan kujera yayinda sufyan yanufi dakin likitan don samun karin bayani gameda kidney dazai bayar inda likitan yasanar dashi cewa dukka biyu sunsami matsala sun lalace donhaka dole acire asamata wani ko guda daya tasamu tayi surviving, tunda har kumbura tanayi wanda sai alokacin shi sufyan yalura dahakan shidai yasan yaga tacanja baiyi tunanin wani abuba tunda baidade da ganintaba anan yace shi yayanta ne uwa daya uba daya aka bashi duk wani fike dazai cika, yasa hannu sannan yace afara duba jinin , jininsu yazo daya atake aka diba , leda biyu yabayar yakwanta don yahuta bayan kwana uku zaa cire kidney dinshi daya abawa aliya, har kuka saidayayi akan gadon, yanason yar kanwarsa Bangaren yusif kuwa yarasa mezaiyi murna? haushi?takaici? Dole dai yayi dukka dole yayi farincikin cewa sufyan yayanta ne ba aure a tsakaninsu balle yadamu , nabiyi kuma dole yaji takaici da aliya taboye masa asalin cewa sufyan yayanta, tabbas hakane abdullahi yasanar mishi sufyan dan marigayi galadima ne anma baitaba kawowa aliya ba, lallai shi soko ne, meyasa aliya taboye mishi wannan bayan yasan babban sirrin ta balle wannan, shidai yanzu duk yarude damuwansa tafarka Inna kuwa duk ta tsure duk yanuwa na nesa saidata kira tasanar musu, antynsa ta abj ma tace zata biyo jirgi ta taho washegari, anan yusuf yasan cewa lallai aliya tanada gata, anma meyasa suka barta take bulayi agari? Abdullahi kuwa ayanzu yatabbatar da inda yasan aliya. Tun randa yafara kallonta yasan cewa yasanta awani gu!, tabbas itace kanwar sufyan wacce suke wasa da ita ya kyalla yace yana sonta, wacce yanemeta yarasata, akacemasa tatafi abuja dazama, wacce itace first love dinshi, ba shakka itace shiyasa duk lokacin dayaganta cikin wani hali baya sharewa saiya taimaketa, tabbas itace innalilahi yazaiyi? Yanzu yafarajin sonta danye, ruwa tsundum yadawo, yazaiyi da yusuf? Yazaiyi yatabb[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 23  benaxir  October 15, 2015  Hausa Novels  105 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Tunaninsa duk yajuya, alokacin suka nufi fannin da aka kwantar da sufyan abdullahi ne ke zaune agefensa inda yake zura masa ido sufyan yayi murmushi sannan yace “karka damu, zageni kawai raina baxai baci ba,” hakan yasa abdullahi ya makeshi dakarfi tareda cewa “soko, wawa!ka cuceni wlh, kacemin harda ita a rasuwa meyasa ka boyemin tana raye?”sufyan bai damu da zagin ba yace “yazama dole ne,dole in boye wa duniya wacece ita, ko so kakeyi itama abimin ita akashe?” Shidai abdullahi baice komi ba yasan cewa abun yanaciwa sufyan rai shiyasa baiyi wani rikici ba har suka sallameshi daga bed rest din dasuka bashi alokacin sukaje dubata, tafarka anma ta jigata sosai, har ranta taji haushi asalin haushi taji don tabbas tasan cewa tanada matsalan kidney tanemi nasayarwa ko zata siya asaka mata tafasa daga baya acewanta kar tazo tafara ciwo bata cika burinta ba, gwara tagama idda cika burinta kafin ta kwakulo wani ciwo gashi yanzu sun nemo, kuma sunaso sucire tasan duk yadda zatayi suhakura bazasu hakura ba dole tabari su saka, fatanta Allah yatada kafadunta don ta cimma burinta Sufyan ne da abdullahi suka shigo dakin ta tsaya ne taga ko zataga yusuf bata ganshiba nan da nan zuciyanta ya sosu sosai, abdullahi kuwa saiyake ganinshi kaman bakon mutum agareta, kaman bakon fuska, tayaya zaifara fuskantarta? Shikam yadawo ruwa tsundum!, zama sukayi agefe sufyan yariko hannunta cikin tausayi, yanason kanwarsa gani yake itace sauran bangaren jikinsa, ganin basuda niyya magana ta bude baki da kyar sannan tace “meye haka kaman na mutu!” Sufyan yayi murmushi tareda cewa “bazaki mutuba ko raina zan iya cirewa nabaki don na sadaukar dakaina agareki”abdullahi hawaye ne ke zuba masa a ido anma yanata kokarin yaga yadanne yashare saboda kar agane, duk lokutan dasuka kasance tare suna yara yatuna, yatuna lokacin daya mata alkawarin zama da ita ko wani hali na rashi ko samu, yamata alkawarin taimakonta cikin kowani hali ko da kuwa zai rasa ransa ne, cikin sanyin murya yace “yajikinki?” “Dasauki ranka shi dade” a karo na farko kenan dayaji wani iri data kirashi haka yasan ada takan ce masa “yayana” bazai iya zama ba bai amsata ba yafice yabar dakin waje yafita yashiga motarsa kuka yafarayi sosai, tunda yataso yayi wayo baiyi kukan dayayiba, nadama duk ta isheshi, toh ni benaxir damuwan meyakeyi? Aiba laifinsa bane, yusuf ne yashiga dakin alokacin inna tagama jimaminta tana zaune itama agefe shidai sufyan yaki motsawa, yusuf yazauna agefe tareda cewa “yajikin?” Bata amsa shiba anma ta gyada masa kai, hakan yasa yaja gefe yazauna duk yadamu, likitan ne yashigo don dubata bayan dube dube yace sufyan yazo su gwada kidney dinshi, yabi likitan inda sukaje akayi scanning aka duba kidney dinshi da lafiyansu sannan ko shima zai iya badawa wani bayan dogon bincike likitan yakirashi kanshi a sunkuye yana cewa “kayi hakuri sufyan, bazaka iya bawa aliya kidney dinkaba saboda kaima naka basuda isheshen lafiya,” wani dogon salati inna tayi sufyan kam daskarewa yayi agun, yagagara motsi shikan hankalinsa yatashi, yazaiyi da rayuwansa? Anan yafara rokon likitan yakawo dabara ataimakawa yar kanwarsa anan likitan yakawo shawarar akira yusuf, nan da nan suka kirashi atake ya amince zaibayar inda akace yashiga don amasa scanning shima, bayan ankammala likitan yace washegari zasuji result tunda dare yayi, hankalinsu duk yatashi innace ta kwana a asibitin abdulahi da yusuf suka koma gyda, ko yusuf dayaga falmata zata dameshi fitowa yayi yabar masu gidan, Washegari karfe tara anty ta iso asibitin yusuf, abdullahi da sufyan suma duk suna gun, likitan yakirasu inda yabawa yusuf hakuri cewa “yusuf you are not a donor donhaka bazaka iya bataba, kidney dinta bazai karbi naka ba” tunda sufyan yake baitaba fuskantar tashin hankali irin wannan ba baisan sanda yafara fidda hawaye da gumi ba, yusuf kam kuka yake wiwi, yarasa yazaiyi anan duk suka fito abdullahi yagagara tafiya, hankalinsa yatashi office din yakoma tareda cewa “dr. Kidney dina guda dayace tayi saura, ko akwai hanyan dazan iyabata ? Tunda kunce agobe kukeso!,” Likitan yakalleshi alaman mai tababben hankali sannan yace “kayi hakuri kanaso ka mutu ne?” Cikin tsawa abdullahi yace “meruwanka da mutuwa ko rayuwata! Kagayamin hanyan dazanyi”cikin tsoro likitan yajawo files dinsa sannan yace “Inhar zaka bada sauran kidney dinka zakadawo bakadashi ko daya, toh munada dialysis machine wanda yake aikin da kidney yakeyi, dashi zakana amfani har lokacin da jikinki zatayi resistn ,” abdullahi yayi hamdallah sannan yace duba kagani ko zan iyabata inyaso kacire ayau dinnan kanemo danwanka zanbiya ko nawane, kusamu kusamata kozata sami lafiya, sannan karka yadda kafadawa kowa!” Likitan ya tsorata shikam yakasa gane kansu, gashi dai danuwanta bazai iya bada nashiba, yusuf kuma falmata ce ta aiko wa asibitin wasika cewa karsu yadda su dauka nashi susawa wata banzar bawa ko dukkansu zasu rasa aikinsu, hakan yasa duk suka tsorata suka cemasa nasa bazai karbu ba, ga abdullahi mai mata anma ya yanke shawaran yahakura da duniya, dahaka yaduba yaga komi daidai atake yayi magana da likitan dazasu cire, adaren ranan suka cire masa kidney dinshi kwaya daya, masha Allah sadaukarwar soyayyaya da cika alkawari tabbas abdullahi yanuna nagarta da hallacin sarauta, yanuna cewa inhar baicika alkawari a matsayinsa na masoyinta ba albarkar sarautar gydansu zaisa yacika, yagwada mata cewa agydansu yatashi da nagarta, baimanta da alkawarin tun suna yara ba yau yacika. Yacika mata alkawarinsa nacewa zai tsaya agefenta, zai taimaketa koda kuwa zaizama ajalin rayuwarsa, acikinmu mutane nawane suke cika alkawari????????? Sufyan kuwa yana wata duniya daban don neman kidney dazaasa wa aliya shida yusuf sai kiransu akayi aka sanar dasu abdullahi yabayar yusuf dayake tuki saidayayi wawan reverse yatsaya sanin cewa abdullahi kidney dinshi dayace tarage suna nufin yabada wannan? Lalle kam akwai rikici, abdullahi nason al[truncated by WhatsApp] HALLACIN SARAUTA 24 & 25  benaxir  October 16, 2015  Hausa Novels  137 Views [10/16, 7:54 PM] Benaxir omar: HALLACIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR sufyan ne yarikeshi tareda cewa “wuce muje” bai iya tuka motan ba hakan yasa sufyan yafito dashi yakoma yafara tukawa asibitin suka koma dasauri suka shiga, alocin matan abdullahi kuka take sosai hankalinta yatashi nan da nan magana yazaga gari, har fada tunda yakolo take hankalinta baitaba mummunan tashi irn na wannan karon ba, a gigice tabar fadan ta umurceta da akawota asibitn, kuka take sosai alokacin data iso asibitin yacika tam, mutane saisukaja gefe kawai suna kallon ikon Allah, yakolo ne ta bukaci tashiga dakin anan likitan yasa aka shigar da ita, don yace mata dan nata yanada jiki mai kyau tun awa biyu dasuka wuce idonsa biyu, hankalinsa akwance duk da zafin ciwo dake damunsa, cikin zafin murya da raunin zuciya tace “meyasa zakayi haka abdullahi? Baizama dole don zaka gwada mata kana sonta kasa rayuwarka a hatsari, haba abdullahi yanzufa kai rayuwa batada amfani agareka zaka iya mutuwa akoda yaushe aduk lokacin da jikinka tagaji da wannan injin, haba abdullahi!!” Tunda yake baitaba jin mahaifiyarshi takira sunanshiba yasan cewa ta tabu matuka, donhaka yamika mata hannunsa tarikoshi gam kaman bazata sakeba “tun ina karami kin koyamin muhimmanci rikon alkawari da cika alkawari, a tarbiyan gidanmu na sarauta natashi naga mahaifina yana cika duk wani alkawari daya dauka , meyasa nima bazan kwatanta hakaba? Shin bakimin kwadayin aljanna? Shin bakimin kwadayin rahaman Allah? Don Allah ki kwantar da hankalinki, nasan ina son aliya anma cika alkawari shine musababbin bata sauran kidney dina, inban bataba duk nan babu mai bayarwa, sufyan nashi ba lafiya, yusuf kuma nazo wucewa naji gimbiya falmata ta aiko ace mishi karsu yarda subada na yusuf ko abakin aikinsu, kuma nasan cewa ko batayi magana ba bazaitaba yiwuwa yusuf yabada nashiba, tunda kinga yana shaye shaye bazai yiwu ace kidney dinshi lafiya lao ba, annemi nasayarwa baasamu daidai nataba, dole nacika alkawarin dana mata nacewa koda raina zanbayar don naceci rayuwarta, kitaimaka ki bano kwarin gwiwa don insamu inwarke, mutuwa kuwa inna mutu lokaci nane babu wanda yake mutuwa ba lokacinsa ba, ” yakolo kuka take sosai tareda hamdala azuciyanta tana godewa Allah dayabata yaro mai ingantarcen tarbiya, mai kyan hali tunda take bata taba ganin abdullahi yayi alkawari yasaba ba, mutum ne mai daraja dan adam, taja numfashi sannan tace “nagode sosai daka fahimtar dani, Allah yarayamin kai yabaka tsawon rai yataimakeka,Allah yadaga kafadunka” anan tamike tabar dakin kuka yacita sosai balle matarsa karshe gado aka bata anan likitan yasamu tanada ciki ga murna ga bakin ciki, yusuf kuwa yana makale a gefen dakin tiyatan dazaayiwa aliya, yaki motsawa azamansa agun falmata tasa akirashi yakai sau biyar daga karshe tashi yayi yawanke dogarin da mari saida aka fita dashi yace karsu dameshi, sufyan kuwa zuwa yayi yasiyo abubuwan dazaa bukata na abdullahi da matarsa, Mai martaba sarki yaji bakin ciki sosai musamman da falmata tace masa wa baiwa yabada kidney dinsa, shikadai a fada yarinka fada, daga baya ne da yakolo ta koma gida dakyar a kukan nata sai ganin mai martaba tayi akanta yana shigowa yafara fada akanme zatabarshi yafita haryaje yabada jikinsa ganin yadda yake fadan tasan cewa falmata ta shuka wani makircin anma yazatay? Dole tamai bayani hakan yasa tazaunar dashi tamai bayani dalla dalla tana kuka yaji tausayinta sosai yakuma ji son dansa yakaru, rungumarta yayi yana lallashi [10/16, 8:21 PM] Benaxir omar: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Yusuf kuwa tun yana jira yaji bazai iyaba, kuka yake wiwi sufyan yafara lallashinsa anma duk dahaka yusuf yagaza yana kuka yana cewa “aliya kitashi, namiki alkawari bazan kara shan wani abuba, aliya na nutsu nadaina duk abunda nakeyi, aliya wlh inasonki, dukkan kai nason dukkan ki, “jin abun yadawo sumbatu yasa sufyan yabashi gu, antyn abuja da inna dakuma yanuwa kakkani duk suna zaune ana jira likita yafito yace ansaka mata lafiya nima benaxir ina tsaye agefe inata adduan Allah yasa ayi aiki lafiya Bayan awanni kadan sai gashi likitan yafito sun bazama kanshi kaman zasu cinyeshi, anan yabukaci sufyan yazo nan da nan yusuf yabisu likitan zaiyi magana sufyan yace “badamuwa ana tare” binsa sukayi office suka zauna sannan yafara bayani “anyi aiki lafiya alhamdulilah jikinta kuma yakarba, yanzu bata tashiba don Allah duk wani abu na tashin hankali kar ayi agabanta, sannan inaga kar agayamata wa yabata kidney dinshi yanzu harsai ta warke,” anan sufyan da yusuf suka mishi godiya sannan yamusu bayani akan akwai nurse dazatazo tamusu magana, suka fito ahaka sannan inna tamike tareda tambayan sufyan yace anyi lafiya, dakin abdullahi yanufa don suyi magana anan yace masa ai anyi aiki lafiya anma bata farka ba, yayi murmushi sannan yace “ina rokon alfarmarka” “Na mefa?” “Don Allah kasamu kayiwa yusuf magana da duk wanda yasan maganan nan wanda kasan zai iya fadawa aliya, don Allah kar afada mata nina bata kidney acemata siya akayi, ” “Anma kasan dole tasani ko? Tunda yanzu bakamn da ba, dole kana yawan zuwa asibiti maganan gari baya buya” “Nidai kamin wannan alfarma abari sai bayan raina afada mata, don fada mata yanzu zaisa tafara diddigi banaso tagane cewa nine masoyinta dana guje mata,” “Ba gudu mata kayiba, ita tagudu maka kadena fadan haka” “A a nidai don Allah kar afadawa kowa maganan nan tawuce, karta sani” Dahaka sufyan ya yarda bayan fitowarsa yakira yusuf yamasa bayani anma yaboye masa dalilin dayasa abdullahi yayi haka shidai yusuf yasan cewa abdullahi na son aliya ne inbahakaba bazai taba bada wani fanni na jikinshi yazabi mutuwa akan rayuwa ba, dahaka sufyan yabarshi harzai fita yaci karo wani likita wanda haushinsu yakeji alokacin akan meyasa zasu yadda abdullahi yabada jikinsa, ba gaira a dlili ya makuro likitan tareda tambayansa dalili, likitan yana neman hanyan kwacewa karya mutu don numfashinsa daukewa takeyi, dayaga zai wahala yace “gimbiya falmata ce tahana mu yarda kabayar” ahankali yasake wuyan tareda cewa “mekace?” “Gimbiya falmata ce ta aiko da wasika akan duk wanda yacire wani bangare na jikinka abakin aikinsa” Sakeshi yayi yabar corridor din mota yanufa yayi wani wawan[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 26  benaxir  October 17, 2015  Hausa Novels  122 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Ayadda ya isa kofan gate din sukansu dogaran saida suka matsamishi sunga yadda yashigo da motan, abude yabar motan da mukullin ajiki yashige cikin gidan a birkice fannin falmata yanufa a harzuke dogarai dasuke kofan gun suna ganinshi suka matsa masa don ayadda yazo kaman guguwa ne ta tunkudoshi tana zaune a falo rike da waya a kunnenta yashigo fuskarshi a daure bata taba ganinshi haka ba, tuni tasha jinin jikinta ta tabbata angaya masa, ajiye wayan tayi tana kallonsa,cikin hushi da zafin murya yace “inaso kibani hujjanki nashiga rayuwata, kibani hujjanki na takurani,” dakewa tayi duk da ta tsorata “bakayi girman da zaka yanke wani hukunci dakanka ba!, inbanda dolonci irin naka nadan fari tayaya zaka cire wani fannin jikinka a matsayinka na dan sarki, sannan kuma sarki anan gaba kace zaka bawa baiwa?!” Murmushi yayi wanda tafi kuka ciwo yace “yanzu na fahimci inda kika dosa, toh inaso yau kisa aranki bakida da , sarki kuma kike can kinemi wanda zai cika miki burinki, baiwa???? Itace ta nutsar dani, takuma ladabtar dani abunda ke kika gagara yi!” Yana fadan haka yajuya yafice, ji tayi kaman ya watsa mata ruwan zafi, salati tayi tana rike kirjinta, yau dan cikinta shine ke mata gori,haryazo corridor yaga jakadiya yasan ita aka aika tafadi sakon, daya makuro wuyanta wani kara tasaka domin a tsammaninta zata leka lahira ne, dakyar dogarai suka karbeta suma yakoma kansu akarshe rikeshi akayi don abunsan yafara dawo karamin hauka, kuka yakwanta wiwi yanayi a daki tunda tahaifeshi baitaba tur da halayenta irin na ranan ba, yayi wadaran da halin mahaifiyarsa akan meyasa bazata koyi nagari ba don itama nata suzama nagari, Matar abdullahi tafarka jikin nata da dan sauki gashi cikin mai laulayi ne, duk tadamu kishin mijinta yashiga ranta duk da yamata bayanin cewa arashin na mutane ne yabada nasa, toh ita tambayan anan shine yasan guda daya ne yasaura mishi akan meyasa zai bayar? Yana nufin zai mayar da ita karamar bazawara! Lallema duk tabi tadamu jira take yawarke don tasauke masa farillai da mustahabban rashin mutunci,aliya sai sha daya na dare tafarka da salatinta tafarka tuni sufyan ya kirkira su kowa yanufo gun dama abdullahi na asibitin, sai inna, yusuf kuwa yanacan shima bakanshi, bude idonta taga sufyan akanta duk tarame tayi kashin wuya, lebenta ya bushe idonta ya kumbura yayi jaa yariko hannunta yana murzawa idonsa fir akanta, dakyar tadan murmusa sannan tabude baki zatayi magana anma takasa, yace mata tayi shiru kartayi magana Allah yabata lfy. Inna ma sai faman tofa mata addua take taki motsawa daga baya kuma tamike ta dauro alwala tafara sallah tana addua Allah yadaga kafadun aliya, baccine yakara kwasan aliyan sannan yazauna agefe shima ya gyangyada sai asuba dayaji kiran sallah sai ya mike yafita dauro alwala yanufi masallacin asibitin, inna kuma a dakin tayi sallah, aliya sai karfe goma ta farka yusuf shima yashigo anma kana ganinshi kassan yana cikin damuwa,idonsa radau radau ya kumbura, yazauna agefenta itama kallonsa take yariko hannunta jikinsa yayi sanyi lao itakuma zafi kaman wuta, batayi magana ba har lokacin tagagara magana, yusuf kuwa shi dazaa cire zafin yakoma kansa dayafi kowa farin ciki, yazura mata ido alokacin likitan yazo dubata donhaka suka fita bashi wuri. Dawowansu dakin bayan likitan yagama yusuf yazauna agefe. Can dai aliya ta daure sannan tace “wayaban kidney dinshi? HALACCIN SARAUTA 27  benaxir  October 18, 2015  Hausa Novels  126 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Bai amsa tambayanta ba yace “yajikin naki? karki kara magana” bata kara cewa komi ba, tana tunani ne taga waye yabata, taga yusuf garau donhaka tasan bashi bane, sufyan ma taganshi tasan bashi bane, taga inna taga antyn abuja duk sauran tsofi ne donhaka taciresu a lissafi, saikawai tasa aranta na siyarwa aka saka mata, nan tafara adduan Allah yasaka da alheri wa duk wanda aka samata kidney dinshi, yusuf yaki motsawa agefenta itakuma idonta zur akansa shima hakan jiyake kaman ya hadiyeta, inna ne suka shigo anma duk dahaka yusuf yaki matsawa saidai kowa yagaidata daga nesa, sufyan daya shigo yaganshi yasan meyakeji donhaka yajashi dakyar yace yaje yahuta ganin sufyan yadage yasa yusuf yanufi dakin likitan ranshi abace yatuna da tsohon bacin ransa, likitan yazaro ido don yaji labarin yusuf yasan mesuka aikata donhaka tuni yashirya dazuwansa , zama yayi akan kujera sannan yace masa “inaso infarajin bayani daga farko meyasameni , me kuma kuka shuka da gimbiya kuka min karya!, ” yayi gyran murya sannan yace “yarima duk abinda yafaru kadaukeshi kaddara tun asali dana dubaka kai kanka bakada ishesshen lafiya, abubuwan dakake sha sundan maka lahani kadan, kidney dinka basu da lafiyan dazaka bawa wani, ana cikin haka kuma mahaifiyarka ta isar da sakon karmu cire, dafatan zaka fahimceni” yusuf bai ce komi ba yatashi yanufi kanshi fitsarine likitan baiyi a wando ba domin ya mugun tsorata yusuf yariko kwalan rigansa sannan yace “daga yau duk abunda yashafi aliya, babu wasa aciki inaso kasan dahakan” Juyawa yayi yabar office din dakin da aka kwantar da abdullahi yanufa idonsa biyu yanaso asallameshi anma likitan yace bayanzu ba saiya kara samun sauki donhaka duk asibitin tahau masa kai, Yan biyu ne hassana da hussiena suka shigo kowacce taci kwalliya dakin da abdullahi yake aka nuna masa suka gaysheshi da jiki sannan suka ajiye ledan hannunsu yusuf yafita alokacin, harzasu wuce abdullahi yace kucika ladanku mana ku gayda aliya, hussiena kaman tace a a anma tana kunyan abdullahi donhaka tace masa toh, dakin da aka kwantar da aliya suka nufa, idonta biyu bakowa a dakin sai inna suka gaysheta kamar abun arziki sannan suka nufi gadon aliya hassana tagaidata yayinda hussiena ke mika mata sakon harara, aliya murmushi tayi don tasan dalili, can dai hussiena takalli tareda cewa “anma kinsan yarima yayi asaran kudin tara? Ace wannan zaicire sauran kodan shi kwaya daya yamika mata? Dasunan soyayya? Mayya duk yaran sarkin kin mamaye” inna ce tanufo kansu tareda katseta tanacewa “kuyi hakuri baason daga mata hankali” aliya ce ta katse ta tareda cewa “wani yarima?” Hassana taja tsaki tareda cewa “wanne kuwa abdullahin dakika nakike wa” wani nauyi taji akanta kaman ansauke mata dutse (Kuyi hkr kumin uzuri for today , ciwon ido ya matsoni kar na muku typing shirme lols, and plx masu tambaya ko benazir macece ko namiji letz make it these way , ni Macece, a 20yr old single lady, nd plx masu dropping numbansu a blog dina kudena plz HALACCIN SARAUTA 28  benaxir  October 21, 2015  Hausa Novels  111 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Fita sukayi adakin suka barta da bugun zuciya har cikin ranta ta tsorata kwanyanta yafara caji, tasan haka kawai mutum bazai cire koda yabayar ba, wani zuciyan tace yanzu haka tsabar zumuncin dake tsakaninku ne, harta bar maganan ahaka saikuma ta tsorata data kara tunawa sunce guda dayan data rage masa yabayar, inna ce tariketa ta kwantar da ita anma aliya ta gagara kwanciya duk ta tsure hankalinta yatashi tuni tamike a tsaye tana cewa “inna nikam ko dai zanfita ne? Ina yaya?” Duk a gigice take hakan yasa inna tarikota tareda cewa “kwanta, barin kira miki yayankin” fita tayi don tanemo sufyan bata ganshi ba donhaka saitayi magana da nurse daya don su samu sudubata a lokacin shigowansu jikin ya rikice aliya duk ta tsorata sosai nurse dinne ta rikota itakuwa duk ta gigice dakyar aka kwantar da ita wani irin kuka take mai shiga zuciya tana kama jikin inna, “inna kitaimaka kinemomin yayana” batasan meye matsalarta na, anma ta tsorata bashiri tafita duk da batada tabbacin ko zataga sufyan din filin asibitin tanufa tazaga bataganshiba donhaka takoma ta dakin abdullahi tanufa ganinshi azaune a rikice tace “yarima ina sufyan? Kataimaka ka nemoshi munshiga uku aliya” agigice yamike yacire kalulan hannunsa sannan yace “muje” dagudu gudu suka nufi dakin alokacin aliya ta bankade nurse din tana cewa akaita gun sufyan, abdullahi ne yakomota yariko hannunta sannan yace “aliya kikalleni” kallonsa tayi agigice tarude anma yadda ya zura mata ido tuni taji wani nutsuwa yashigo mata, ya kwanto mata, hannunta na bari tace “yariiiiiim” “Shhhhh karkiyi magana kiyi shiru” Shirun tayi kaman yadda yace addua yatofa mata sannan yace wa inna insha Allah bazata kara firgita ba, zama yayi dirsham agefenta acewarsa sai sufyan yazo zaitafi, wata nurse ce tashigo tareda rokonsa yakoma daure fuska yayi kaman yaga malaikar mutuwa yana cewa ba inda zanje kuma karta nima takurashi, hakan yasata fita don tasanar da manyanta, inna tayi tayi dashi yamike yafice anma yaki yarda, tuni tafara nadamar kiransa anma abdullahi yakafe, aliya kuwa tana jingine a kwance tana ta tunani, tarasa tayaya zata tambayeshi inkuma yabata da zuciya daya ne fa? Yazatayi? Wani irin nauyinsa takeji yanzu fa duk gadaranta akwai kidney dinshi ajikinta, ita damuwanta sufyan yazo ta tambayeshi gaskiyan alamarin, Sunfi minti talatin ahaka kafin yashigo, shigowarsa yasamu aliya tayi bacci abdullahi na gefenta, tuni yanufo kansa, “kaida bakada lafiya kazo gadin wata marar lafiyan?” “Kai nake jira kadawo, firgita takeyi shiyasa nayi hakan” sufyan ne yajashi suka nufi dakin da aka kwantar dashi, sannan yadawo dakin da aka kwantar da aliya sannan yazauna cikin mintuna kadan saiga bilkisu dama sufyan yaroka abarta tafito don sunfi sabawa da aliyan yakolo ta amince, shigowan bilkisu dole tajira aliya ta tashi bayan farkwanta alokacin sufyan yanufi gun abdullahi , aliya naganin bilki ta wangale baki sanin cewa zuwanta bana banza bane bayan bilki tamata jajen yajikin sannan tamika mata wani takarda tare da cewa duk abunda kikeson sani yana cikin nan, Allah yabaki saa, bashiri tafice don tsoro takeji Aliya ta paki idon inna tasaka tacikin bargo taboye sannan takoma ta kwanta, can dai tamike tasaka akasan katifan tamayar ta kwanta, Bayan sun watse daredare anbarta da inna wacce tabude baki sai bacci take, taciro takardun tabude hotuna ne tsoffi dakuma wani enlarger karami, mahaifinta ne da alh.hamidu mahaifinsu yan biyu saikuma sauran biyun su uku, da mahaifinta dawani wanda take kyautata zaton cewa shine dan biyun mahaifinta hussieni sai alh.hamidu gabanta ne ya tsananta fadi, ta mugun tsorata asaninta tace bilki ta bincika mata alakan alh.hamidu da fadan gidan kusancinsu ta bakin tsoffin bayin dasuka san kan gydan, karshe kuma ga abunda bilki takawo mata, tasan bilki batayi makaranta ko ilmin dazatayi wannan binciken ba, dole akwai wanda yasan sirrinta, waye toh? Sufyan? Inhar shine toh bazai bawa bilki ba dakanshi zaiboye. Abdullahi? Tasan abdullahi bazai taba kawo aikinta ba, don baigama sanin alakarta da sufyan ba balle abunda yakawota(a tunaninta abdullhi baisan cewa ita kanwar sufyan bane), yusuf? Salati tayi tabbas yusuf ne shine kadai namijin da yasan sirrinta , amma meyasa yataimaketa? Nanma dai tagodewa Allah damuwanta burinta yakusan cika, yanzu dole tasami hanya da alh.hamidu don taji daga bakinshi meya sani, tunda duk shine mafi kusa acikinsu Batayi bacci ba har asuba nurses sunzo sun dubata suka fice ana idar da asuba bacci ya kwasheta, abdullahi ne yashigo dakin don ganinta inna tana wuridi yadan zauna agefe, idonsa ce tahango mai takarda, jaa yayi don yaga menene (Salam, akwai batu jiya dayayi ta zagawa akan na rasu, ba ni bace wata benazir muhd ce yar nasarrawa, nagode ga dumbin masoyana dasuka kira donjin lafiyata, duk wanda aka tayar ma hankali ko yashiga wani damuwa ina rokon afuwa don Allah nidai ina raye, Alla[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 29  benaxir  October 22, 2015  Hausa Novels  106 Views HALACCIN SARAUTA NA BENNAXIR OMAR Jawowan dayayi yaga bangon envelope ne donhaka sai ya ajiye agefen pillow, yana zaune har yusuf yazo mikewa yayi yafice don tun randa yusuf yaje yacemar yagode baikara mishi magana ba. Har abdullahi zaifita yusuf yace “tsohonka na memanka” gabanshi ne yafadi dum donyasan ba maganan dazaamishi saina maganar bayar da kisney dayayi shiyanzu matarsa yake jin tausayi karya mutu su gaza kulawa da ita da dan cikinta, dakin yanufa yatatara abunda zai dauka yafice gyda yanufa yayi wankarsa matarsa duk ta tsorats don tasan baa sallameshiba yadawo, ta so tabashi abun karyawa baikulata ba yafice don ganin sarki mai ran karfe baisameshi ba don yana bacci dole yahakura yakoma Yusuf kuwa zama yayi dirshan agefenta ya tsura mata ido. Tadawo gangar jikinsa tadawo wani gurbi arayuwansa itace tsoka da jininsa, tadawo tamkar bugun zuciyanta domin duk numfashin datayi sai yaji kaman daga jikinsa ne, bata farkaba sai takwas na safe likitan yaga warkewanta dawuri yakuma ce taci abinci sosai wanda ada ruwan lipton suke bata da abu mai ruwa hankalin kowa ya fara kwanciya banda na aliya damuwanta su sallameta awannan asibitin don tasamu tafita ta cimma burinta, sufyan ne yashigo alokacin yusuf yashiga gari anan ta mai bayani sannan tabada takardun daya karanta shima ya yarda da magananta nacewa saita gun alh.hamidu, donhaka yace zai danne damtse don yasamu kusanci da mahaifin hassana, alokacin kuma ta tambayeshi ko yasan dalilin dayasa abdullahi yabata wani bangare ajikinsa, bayaso yatada mata hankali donhaka yace “kinsan abokina ne, amintan dake tsakaninmu yabi,” bata gamsu da bayaninshi dama yasan bazata yarda ba, zatamai wani tambayan ya tallafota tare da cewa ta kwanta tayi bacci, hakan yakara tabbatar mata akwai dalili yusuf ne zaigayamata, saidai tatuna guntun kishin shi donhaka ta share, tuni ta gargade zuciyanta da kartayi binciken dalili balle yadawo mata tashin hankali, Dagari yama wayewa abdullahi yakoma gun sarki inda a tunaninsa fada zaimasa. Yamasa fadan kuwa sosai tareda cewa inhar kanaso ka gwada hallacinka kamata yayi kasiya, yanzu kai zaka iya mutuwa duk lokacin da jikinka ta gaji da wannan injin, nan dai abdullah yasha fada anma daidai da second daya baitaba nadamar abunda yayi ba, Satin aliya daya aka sallameta tuni takoma gida ankara gyra fanninta tasan aikin sufyan ne da antyn abuja wacce aranar tawuce abj, duk da tadawo gida mutane basu dauke kafa ba. Don gaydata alokacin sufyan yasami kusanci da nahaifin hassana tuni yashirya randa zaimasa tambayoyin hotunan yadiba sannan yaje gydan, hassana ta tarbeshi sannan tamasa iso bayan sun gaysa sai sufyan yayi bayanin meya kawosa tareda hotunan ya ajiye mai,alh. Hamidu yayi murmushi sannan yace “dama nakai shekara sha biyu inajiran rana irin ta yau, ranan da yayan cikinsa zasuxo don jin bayani saidai nasan ku biyune, ina kanwarka? Kaje kadaukota itama tanada hakkin tasan meyasami mahaifinta” sufyan yace toh tareda ficewa gyda yaje ya kinkimo aliya a mota yamata bayani tuni jikinta yayi sanyi domun ta tsorata sosai, suka koma inda suka sameshi kamar yadda sufyan yabarshi yafara dacewa “iyayenku yan biyu ne masu son juna dakuma matukar kama, hakan yasa shakuwa a tsakaninsa, sarauta da son mulki shiya shiga ransubwanda shaidan yazo yashiga tsakani , bazan taba fada muku waya kashe iyayenku ba saidai ina rokonku dakuyi hakuri, ku yafewa kowaye ne, ku manta, don tsananta bincike baya jawo komi sai bacin rai,” sufyan da aliya duk sun kagu suji bayani anma sai waazi yake akarshe yace “ranar karshe da mahaifinku da hussieni suka gana adaki kafin hussieni yabar gari, bawanda yake gun sai ni danake falo suna daki abunda naji kuwa shine hussieni yace ko duniya zata juya saiya mulka garrinnan, yayinda hassan ya musanta , hussieni kuwa yace su zuba sugani” donhaka kuhakura da binciken haka” sufyan da aliya sunyi sunyi anma mutum kam ya gunshe baki a bacin rai suka fito suka fice, hassana wacce tashirya don soyewa da masoyinta sai karar mota taji yafice, .gyda suka isa inda akarshe suka yanke shawarar dole mutum dayane yazama ansansu[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 30  benaxir  October 23, 2015  Hausa Novels  99 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR tuni suka fara tunanin hanyar dazasu je su sameshi ko shi yazo, Washegari sufyan yaje gun alh.hamid tareda rokonsa ko akwai hanyar dazaayi asamu hussieni yazo, yace mishi hanya daya ne kadai zaisa hussieni yazo, in ance mishi anga ajiyan mahaifinsa, ajiya ne wanda kakanku yayi wa hussieni haryau baasamu ba, donhaka dole kusamo wannan hajiyan don hussieni yazo, sufyan ya amsa da toh anma shi tuni ya shuka dabararsa, wasikar jaki yayi yasa aka tura inda yake fadawa hussienin shine dan hassan kuma ga ajiyarsa a hannunsa, yayi hakkanne don baida kudin dazaice zaije bayan haka baisan yadda kanin mahaifin nasa zai karbe sa ba, gwara yajawo shi yazoshi duk da taimakon alh.hamdiu yanemi address din yatura Aliya ta warke garau haka ma abdullahi rayuwa tacigaba da gudana musu, duk da aliya ta dan ja baya da yusuf anma tana sonsa , daidai da kankanin lokaci sonsa baitaba raguwa mata ba, abdullahi kuwa yanzu da taimakon injin bature yake rayuwa, yariga daya cire rai wa duniya don yasan wahalarshi tazo karshe, Acikin wata biyu wata rana sai labari ta iso sufyan cewa ga hussieni yazo gari, ya tare ne agydan alh.hamidu hakan yasa aliya da sufyan suka shirya tareda inna don zuwa gayda shi, kasancewar sunsaba da gydan shigansu sunyi mamaki don kammanin mahaifinsu ne sak a fuskan hussieni sai yanmata guda biyu wanda duk daga kallonsu ansan yan biyune, zasuyi saan aliya, kyawawa dasu suma kammanin mahaifin suka dauko, hussieni ya tarbesu sosai a matsayin yayansa, aliya taji dadi ganin cewa itama gata da yanuwa tuni suka saba da yanbiyun, sunsha tadi sosai sai can dare sannan su aliya suka dawo gyda Washegari sufyan ne ya koma anma wannan karon duk acikin gyda suke, alh.hamidu da hussieni suna falo donhaka sufyan yashirya don yaje yatambayeshi yarike hannun kofan zaishiga yakasa kunne donjin mesuke fada, Alh.hamidu yace “kasan cewa yarannan sundameni maganan mahaifinsu sai tsananta bincike suke, ni bansan mezance musuba, kasan dai bazan bude baki nace musu hussienin mahaifinsu shiyasa akashe mahaifinsu don samun sarauta” “Nagode daka rufe maganan baka furta ba, ni bansan tayaya zanyiba, nayi nadaman abunda na aikata gashi idan ina kallon yaransa duk sai naji na tsargu mussaman macen, itace na cuta da maraici, hakika son zuciya da zugin shaidan su suka sani na aikata abunda nayi,yanzu kunsamamin ajiyan ne? Don da wannan ajiyan zan iya karban sarautar sarki bana galadima kawai ba, nadawo gida bazan koma ba,” Sufyan dake rike da hannun kofan yasake jiki a sanyaye yafice batareda kowa yasaniba, gyda gun aliya yanufa yashiga tana bacci don tace mai haka kawai takejin faduwar gaba da ciwon kai yace tayi bacci inta tashi tasameshi agydan alh.hamidu, zura mata ido yayi hannunsa na bari yana shafa gefen fuskanta, farkawa tayi tazauna tareda cewa “yayah” bai amsataba yafara kokarin share hawayensa, tunda take bata taba ganinshi awannan yanayun ba, tuni jikinta itama yahau bari “yayah! Meya faru? Waye ba lafiya?” Hannunsa na bari yariko nata yarungumota kuka yake sosai mai tsananta zuciya, tuni tafara itama duk da batasan dalili ba, cikin yanayin tausayi yace “aliya hakika agarin bincikenmu yau mun bincikawa kanmu tashin hankali, aliya alh.hussieni shiya sa aka kashe mahaifinmu” tsak ta tsaya tana kokarin daidaita numfashinta anan wayan sufyan tayi kara cikin yanayin tausayi yadauki wayan, “hello, naam” Salati taji yafarayi yamike cak “abdullahi? Innalilahi!! Innalilahi wainnailaihirajiun!! Gamunan zuwa! Innalilahi!” Fitsari tasake awando wani kuka yaci fuskanta, gabanta ya tsananta fadi, “yayah meya sameshi?” Baikulata ba yace “shirya mutafi” dankwali kawai tadauka tabishi, nima benaxir gabana yana fadi nabishi don ganin meya faru! HALACCIN SARAUTA 31  benaxir  October 24, 2015  Hausa Novels  132 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Mota ya fizga dakarfi sai alokacin aliya taga jikinta ajike anan ta tabbatar da aefa fitsari tayi anma wayake tanan yanzu, tunda kayan jikinta ba nunawa zaiyi ba goran ruwa tagani a motan tabude ta watsa ajikinta, fada yanufa dasu suka sami gurin acike, dakayar yasamu gun parking yana tafiya aliya tabi sahunshi fannin yakolo suka nufa wacce babu matsaka sinke ancika, tundaganan jikin aliya yayi sanyi komawa tayi tazauna, agefe wasu hawaye masu zafi suka fara bin kumatunta sufyan ne yakamo hannuta suka shiga shima dataimakon hauwau. Wacce tanuna cewa su yan gida ne suna shiga dakin acike agefe aliya ta tsaya sufyan yakarasa gun, abdullhi ne akwance agun macecce, duniya inazakije damu, mun aikata alheri mun mutu munbarta, dole kowani rai mamace ne, sufyan durkusawa yayi agun tuni dogarai sukayi gefe dashi don baabarin kowa kusa da gawan. Yakolo ma ba kanta dakyar aka danneta, aliya kuwa wani kyalli kyallu take gani a idonta tuni ta fizge dankwalin kanta tajuya dagudu zata nufi kan gawan rikota akayi, tuni sufyan shima yamike yarikota yusuf wanda ke can kuryan daki tuni yafito ganin aliya tuni ya nufa kanta rikota akayi anma yadda kukasan karfin aljannu gareta wani fizga datayi bashiri suka fada tabaya kan abdullahi tanufa zata budeshi anma nanma dogarai suka kara rikota, tuni umma uwar soro tace a fice da ita, daukanta cak akayi akafice da ita, wani irin kuka takeyi wanda duk mai kallonta sai ya tausaya mata, itakanta tadawo abun tausayi , sumbatu takeyi “yarima meyasa zakamin haka? Yarima meyasa zaka tafi baka amsamin tambayoyin dake raina ba? Kasan cewa sanadina kamutu anma baka gayamin hujjanka ba! Innalilahi wainna ilaihi rajiun!” Kuka takara fashewa da, yusuf ne yajata, yasa aka nemo bilkisu tarikota suka koma gefe acewarsa akaita fanninshi harsaitayi shiru kafin tashigo cikin jamaa, Anyiwa abdullahi wanka yadda ake kowani mamaci, abdullahi kuwa yasha fatan alheri agun alumma, iyayensa sun sakamishi sunkuma nema mishi aljanna, hatta mtanem gydan dsuke karkashinsa suna aiki kowa alheri yake fada akan abdullahi, duk wanda yazauna da abdullahi yasan mutum ne mai tausayi, marar son fada, mai son gaskiya, mai adalci mai kuma bin hakkin dan adam, matarsa da mahaifiyarsa sunbada kyawawan shaidu suma akansu, a inda sarki dakanshi yake jawabi amfanin zuwa duniya kenan, kazamto nai kyautatawa mutane , kazamto mai tausayi karkace don kafi karfin wane, ko wane yana aiki akasanka ka wulakantashi , kasani cewa shaidun duniya shine shaidan lahiranka, muguji duniya muzamto masu shiri akowani lokaci don ziyartar kabari, musani cewa aikin damukayi duk yana cikin littafanmu, yakuma yi jawabin cewa kar mutane suce don abdullahi yabada kidney dinshi shiyasa yamutu, wannan bahaka bane lokacinsa yayi, daya bada da bai bayarba dukka Allah yayi zaimutu yau, kuma mutane susani cewa akullum idan aka tambayi abdullahi maganan kidney dinshi da dalilin bayarwa yanada hujjojinsa anma babbar hujjarsa itace yayi alkawari kuma a matsayinshi na dan musulmi, na wanda yataso cikin mutunci da daraja a matsayinsa na balagagge wanda yasan hukuncin marar cika alkawari hakan yasa yacika alkawarin, kuma shi sarki yana alfahari dashi hakkika abdullahi abun koyi ne, Allah ya sa mucika da imani Ansamu ankaishi makabarta kafin sudawo aliya tasuma yakai sau uku, haka kawai takejin haushin kanta gani takeyi kaman itace musabbabin dalilin dayasa abdullahi yarasu, dakyar aka mata alluran bacci tasamu ta kwanta Sufyan kuwa abun duniya tamasa yawa dawanne zaiji, mutuwan amininsa kokuma bincikowan dayayi cewa hussieni shiya kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa, dawani ido zai kalleshi duk yaga missed call dinsu anma bai dauki ko daya ba, atunaninsa basuda abin fada mashi gun inna yanufa yatarar tana kan sallaya tana ganinshi tashafa addua tareda cewa “sufyan ya akaji da hakuri?” “Alhmdlh” “Allah yajikanshi yamishi rahama” “Amin inna, dama nazo muyi maganane akan alh.hussieni” “Inajinka” “Kinsan shiya kashe iyayena shiyasa kika boyemin ko?” “Hmnm abdullahi kenan, rasuwa fa aka maka yakamata kayi hakuri ai yanzu ko” “Yanzu nakeson kifadamin amsata” “Nasani. Sannan alh.hamidu ma yasani, munga babu amfanin gayamuku ne,kuma nagayamaka anan nagayamaka, sufyan kadaina bincike, addininmu ma batason irin wannan binciken, tasar da kwantaccen magana,ana zaman lafiya kunje kun binciko abunda zai hanaku zaman lfy, yanzu dakasan cewa shine mezakayi?” “Lallai inna kinban mamaki, tambaya kikayi mezanyi? Kotu zamu shiga!, bazan hakura ba harsai anyiwa iyayena adalci, kina nufin muna ji muna gani ankashe iyayenmu a banza kenan? Da ke! Da duk wani wanda yakeda hannu aciki wanda yasani da komi duk sainakaiku kotu, zaku fuskanci hukunci ” Baikulataba yafice duk da ta tsorata tana kokarin yimasa bayani, fada yakoma har lokacin ance aliya bata tashiba ganin yusuf yayi donhaka yaje shima yazauna agefensa, yusuf na zubarda hawaye yace “kasan dalilin da yabata kodan shi?” “Nasani” “Menene” “Don yamata alkawari zai kareta koda ranshi zai cire yabata” “Bayan haka” “Yana sonta!! Itace mace tafarko daya fara so a duniya” Yusuf dama yasan dahakan yana son ya tabbatar dinne, ajiyan zuciya yayi wanda shi sufyan yagagara ganewa ko na farinciki ne ko na bakinciki Acan cikin fada kuwa fannin falmata jakadiya ce tashigo tana murmushi, falmata ta kalleta itama murmushin take, jakadiya tafada kasa tana kirari Sai ke Jaruma a cikin jarumai, jaruma acikin jagororin ma jagoranta Idan akaji ance kasaita in anduba kin cancanta taimako dare zuwa rana kin sabayi wa al’umma mai dukiya mai ran karfe Mai kudi uban matsiyata baki fushi ko anzage ki Baki zagi ko anzageki ja muje kece gimbiyar magimbiyata kara masu kece babbar su Mai girma agidan girma sannan kuma matar mai girma,uwar gida a gidan mai girma,Mai hidima a gidan hidima sannan kuma matar mai hidima, farin cikin mai hidima, zuciya hasken annurin mai hidima, zakanya saidai aganki anesa badai a matso kusa ba,” Wani irin murmushi da dariya falmata tayi cikin jin dadi, ta daga giranta sama sannan tace “kinga na kashe da’ saura uwarsa sannan uban gayyan uban gidan, yusuf[truncated by WhatsApp] HALACCON SARAUTA 32  benaxir  October 26, 2015  Hausa Novels  145 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR jakadiya tana rusune harta mike ta fice. Bawanda yakai falmata farin ciki aranan saboda tana ganin wanda zai tare mata sarautar danta yafadi kasa yamutu, shehu kuwa baiyi hankalin dazata sashi a sahun masu karban sarautan ba. Donhaka tuni tafara tunanin hanyan dashi kanshi sarkin zai mutu, babu tsoron Allah babu tunanin lahira, tunaninta shine takashe duk wanda tasan zaishiga tsakaninta da mulkin garin, Sai dare sannan aliya tafarka atake sufyan ya tallabota yadawo da ita gida yana ganin inna baikulataba yashige da aliya ciki, saida yatabbatar takwanta ya rufo kofan sannan yafito inna tana tsaye tana jira yafito, baikulata ba tana kiransa, inba don babu gun da zaikai aliya ba da gidan nata saisu tattara subar mata shi, Cikin dare aliya tayita firgit tana wasu mafarkai, dolenta tamike,alwala tadauro tafara sallah har asuba tana yiwa abdullahi addua, tausayin matanshi da abunda zasu haifa yacikata, Dasafe sufyan nazaune wayansa tayi kara alh.hamidu ne yake cemasa yazo suna jiransa, baiyi bacciba tsabar yana tunanin hanyan dazsi bullowa maganan, motansa yaja yafice gydan alh.hamidu yanufa suna zaune a tsakar gydan suna jiranshi, sun gaysa yabasu girmansu sannan yazauna, inda hussieni yake tambayansa alkawarinsa, sufyan yayi murmushi sannan yace “komi zaizama naka idan kabani tarihin yadda akayi ka kashe mahaifina!” Ba hussieni ba har alh.hamidu saida yabude baki don mamaki,hussieni yagagara cewa komi,hakan yakara tunzura sufyan, hawaye ne suka fara zubo mishi yafara magana cikin sanyin jiki “Ashe karshen duniya zatazo dahar danuwa zaisa hannu yakashe danuwansa saboda dukiya?saboda mulki?” Bawanda ya amsa mishi kaman tsoffin barayi da aka kamasu hussieni kanshi akasa yafara magana “kai mahaifinka ne. Nikuma danuwana , wlh tlh ba abunda nashirya yafaru ba kenan, Allah dai yayi zanzama sanadi, tabbas munyi musu da shi batun mulki anma ban kwallafa raina ba. Nasan na umurta da amai dukka anma bance sukasheshi ba, bankuma ce suhada da mahaifiyarka ba. Allah yayine lokaci yayi don Allah kayi hakuri, karkuma kabari kanwarka taji alokacin sufyan yayi kukan zuci daya tuna da iyayensa anma tuni ya watsake saboda ayanzu zucuyarsa tabushe yana tunanun daukar fansa, recordern dayake recordn yasawa stop sannan yamike yafice batare da ya ce musu komi ba dama yakira lawyernsa awaya tuni yadamka masa shaidansa tareda basa go ahead nashigar da kara kotu, koba komi yanzu yaji sanyi aransa Aliya kuwa tacanja gabadaya ba abinci sai ruwan lipton, sufyan yayi lallamin harya gaji yusuf ma yayi nass Bayan sati biyu alokacin anwatse a gun rasuwa. Sannan alh.hamidu da alh.hussieni sun shiga kotu inda zaa fara sauraren karansu Aliya tadan sake, yanzu hankalinta ya kwanta maganan rama mutuwan iyayenta anmma abunda yafi bata ciwo shine danuwan mahaifinta shi yakashe mahaifinta. Abunda ciwo,saidai yanzu tabar komi agun Allah har lokacin sufyan baya magana da inna , aliya tayi iya kokarinta anma yafaskara yusuf na iya kokarinsa ganin ya farantawa aliya yayinda soyayya mai karfi tashiga tsakaninsu, tuni yafara maganan aurenta yasamu falmata da zance atake tace batasan zance ba, nan yakoma kan yakolo ta yadda takuma sa albarka inda anan yasako waziri da sarki, dafarko waziri yaki amincewa acewarsa dole yusuf yadauko yarinya mai asali, nan fa yusuf yazayyana masa rayuwar aliya tundaga farko dakuma wahalhalun datasha waziri yayi mamaki sarai anma yace zai gwada tunkarar sarki, sarki yanajin magana yatambayi wacece atake waxiri yace yar marigayi galadima,sarki yaji dadi sosai tuni yafara murna, wannan yarinyan ai ita keda asali, nan waziri yace “anma akwai matsala mai martaba, yarinyan tashin hannun mace tayi dakuma tashin gari” Sarkin yayi shiru don tantance me wazirin ke nufi donhaka yace “yi bincike mai tsanani muji”dahaka waziri yabar maganan, falmata taji labarin abunda ke faruwa donhaka ta nufi sarki da maganan anma yanuna mata shi ba ruwansa,don shikanshi yanaso yusuf yayi aure, baitaba tsammani kuma yusuf zaikawo yarinya yace yanaso ba donhaka tuni tarikice duk tana tunanin hanyoyin dazata hanashi wanda shi yusuf har daina zuwa gaysheta yayi tsabar yasan kalan mitanta, Aliya kuwa tasan bakaramin rikici bane zai afku donhaka tuni tafara lura da takunta, ga masu nufinta da sharri, ita anata taso ta tattara tabar garin bata da dsmuwa da gun anma dole tajira a idar da case din iyayenta a kotu, Waziri yayi iya bincikenansa akan aliya tuni yakira yusuf “Kana sane da tayi bauta agydannan?” “Tayine alokacin batasan kowa ba” “Kasan dai yanayin rayuwarta bai shiga danaka ba” “Nasani shiyasa nake rokonka daka sa baki, kaikadai ne inka yabeta sarki zsi yadda, don Allah kataimaka” “Zan yi iya kokarina, anma kai kasan halin mahaifiyarka” Dawannan suka rabu inda yaje yagabatar da zancen da duk wani tarihin aliya agaban sarki, sarki yadannan approve makake, nima dai benaxir na dannan approve duk da munsan amincewan mezai jawo, ansa rayuwar aliya cikin hatsari da damuwa, anma munsan cewa aliya ce kadai zata iya gyrawa falmata duwawun zama, muje zuwa gobe[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 33  benaxir  October 27, 2015  Hausa Novels  106 Views HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR falmata kashe kanta ne batayiba domin amincewar da sarki yayi, ta tura duk wanda take ganin zai iya magana wa sarki anma taci tura, waliyyim aliya shine alh.hussieni anma sufyan yayi kif da ido akan bai san zance ba, dole akarshe aka bukaci alh.hamidu yazama waliyyi, duk soyayyan dayakewa hassana yayine domin yasamu hankakinta anma daga karshe yaga sone na gaskiya , hussiena ma tasha alwashin zaman lafiya kam aliya da yusuf bazasu sameshiba agydan Anyi zama a kotu inda lawyernsu sufyan yaci karan, kotu tabawa alh.hussieni zaman prison na shekara ashirin da daya sannan ta bukaci daya fidda gadonsu ko kuma kotu taci tararsa, a ranan aliya tayi kukan farim ciki tunda take bata tabajin kwanciyan hankali irinna ranan ba, jitayi kaman ansauke mata dutsen badr akirjinta, tuni ta maida hankalinta kan batun aurenta duk da tasan tashin hankalin dazata shiga, antyn abuja ne ta bukaci taje don su samu ayi siyayyanta, ta tattara dan komatsanta duk da yusuf bai so ba, shi yanzu babban damuwansa yaga ya aureta, Sunyi sallama tatafi yayinda yakoma fada, shigansa yatarar da bilkisu da abincinsa, zama yayi yarike kai yana tunani kansa yamasa nauyi har yanzu falmata taki yarda da auren, yasan son zuciyanta ne anata tunanin wai saidai ya auri hussiena, shi haryau hussiena bata kwanta masa arai ba , bilkisu ce tayi tari hakan yadawo dashi daga tunaninsa yakalleta sannan yace “meke faruwa acikin gyda gameda aurena” kanta a kasa tace “Gimbiya yakolo tafara shiri, yayinda gimbiya falmata bata fara ba, ita shirinta da hussiena takeyi” Baice komi ba yatashi yafice sannan yanufi fannin falmata anma sa iso sannan yashiga daga ciki tana zaune akan kujera yazauna akasa abinda bayayi, hakan yatabbatar mata da bukata yazo dashi, bata kulashiba yasa kanshi akasa sannan yace “Ina neman amincewarki na auren aliya” “Ban bayarba, kuma ko bayan raina ban sa baki ba” “Inaso kibani hujjanki wanda addini ta haramta min auren aliya” “Yar kan titi!! Yarinya tagama gantalinta agari! Kowani dan iska ya kwasa! Kainan tayi fitsari tabaka kasha ba dole kabiya kaman agwagwa ba!” Ga mamakinta taga yamike yafice , baikuma cewa komiba, tunda shi mahaifinsa yasa albarka hujjanta ba kwakkwara bane dazatace masa kar ya auri aliya, fannin yakolo yaje, yasami hauwa tana ganinsa tafice don haryanzu tsoronsa takeji, yakolo tayi murmushi tareda masa iso, bayan karasowarsa yazauna dum a kasa, nan da nan tagano alfarma yazo nema, yagaysheta ta amsa masa sannan yace “Naje gun gimbiya na nemi ta amince min auren aliya taki yarda, kuma hujjojinta ba ingantattu bane, kitaimaka ko zakisa baki” “Bakomi yusuf, kasan mahaifinka inta sa rai akan abu, kai yakamata ka lallabata anma zan gwada kokarina kaji” “Nagodr Allah yasaka da alheri” Ficewa tayi, tuni abdullahinta ya fado mata arai, tasan yarinyar dayakeso aketa rikici akai, gashi cikin mata yafara fitowa duk da sunriketa tana fadan akan saita haihu tukun zasu barta tafita, Yakolo tayi iya kokarinta don fahimtar da falmata anma falmata kaman ana zuba mata man fetur, dahaka biki ya matso kusa aliya tadawo gari saidai tagagara zama, rokon yusuf tayi akan ko zai taimaka yabata aron bilkisu, haka kuwa akayi , tuni bilki tafara taimaka mata, jin aliya zata auri dan sarki tuni dangin nesa da wanda aka manta dasu suka fara bayyana kowa saiyace yazo auren marainiyan Allah, Ran jumaa aka daura auren aliya da yusuf, inda akayi dinner daredare nagani nafada, munsha gwaggori munsha rawa,yusuf na makale da matarsa, hannunsa gam anata shi yanzu gani yake duk duniya bawanda yakaishi hakuri da juriyan dayayi, angama dinner inda aka kai amarya fanninta side guda aka ware mata a fada, dakuna uku da falo biyu,tabbas tasamu kaya tasha gata, sufyan yashare mata hawaye tayi kukan rashin iyaye anma batayi maraici ba, kowa yayi mamakin ganin yadda falmata tasake ranta da maganan biki, harwani jan aliya take ajiki, acewarta komi yawuce,anma aliya tagagara sakewa da ita, randa aka kaita an watse aliya tana kunshe jikin gyalen kyabban da aka rufata dashi duk ta kagu tana jiran angon nata,don tsoro takeji dakin ya mata girma sosai, kukan kare tafaraji, dafarko bai dametaba anma datayi tunanin gydan babu inda aka ajiye kare, tuni tafara tsorata kodai yusuf yasiya ya ajiye a fanninta ne? Toh anma matsalanta shine jin kukan take kaman agabanta yakeyi, hannunta ne yafara bari tafara salati da dan karfi sannan taji shiru, can kuma takarajin kukan karen daga nesa saikuma karan kofa, saura kadan tasake fitsari awandonta taji anbude kofan, yusuf ne batasan lokacin data rungumoshiba, jikinta na bari jinhaka yasa shima ya kamata, sunfi mintoti ahaka kafin yajawota yazaunar da ita akan lallausan gadon, “leeya meya sameki?” Bata bashi amsaba, tafarajin wani kukan karen wannan karon harda kulya, salati takeyi jikinta na bari, tuni jikinsa yayi sanyi domin bata cikin hayyacinta, alwala yadauro yace itama tayi anma dole saida yarakata toilet din don tsoron datakeji. Tafito yajasu sallah yakamo kanta yatofa mata addua, sannan yafara tambayanta akan littafai daga kan fiqhu, hadiths da dan tauhid, yayi mamaki sosai dayaga tanada sani, baitaba zaton tasani sosaiba, daganan ne yace “mezakici?” “Babu kabarshi” Cire mata kallabin yayi, sannan yarikota naman ya yaga kadan yafara bata tana tauna ahankali yabata da soya milk haka taci takoshi sannan yace tadan kwanta, tana kwanciya taji kukan karen zumbur tamike kaman an tsira mata allura, rikota yayi yana tofa mata addua, atakaice haka suka kwana a zaune har asuba, dazaran zata kwanta sai kukan kare ko qulya, asuba nayi sukaji shiru, hakan yabashi daman fita masallaci, tana sallah bata fitoba saboda baccin daya kwasheta, karfe shida daidai saiga umma uwar tsoro falmata ta turota buga mata kofan tayi can dai tabude, bata tasheta ba ta nufi kan gadon taja bedshit din tafice, kaiwa falmata tayi wanda tana zaune tana jira ganin babu komi akan bedshit din yasa ta salati, tana cewa “saida na gayawa yusuf wannan yarinyan tagama gantalinta, yaki yarda, kue kudauko min ita,” Dauko aliya cak akayi aka wurgata akasa. Jiri ne yake dibanta anma tuni ta warsake don ruwan sanyi tas falmata tasa aka watsa mata, alokacin yakolo tazo ranta yayi mummunan baci, inba raina darajan dan adam ba yazaayi matar danki dan cikinki zakina wulakantawa? Tuni fa gyda ya hargitse, nima benaxiratu idona na rufewa anma dole nabude[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA 34,35  benaxir  October 29, 2015  Hausa Novels  110 Views [10/29, 7:11 PM] Adda Bena: [10/29, 6:45 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya bata iya daga kai ba, tarasa meyake mata dadi, ayayinda falmata da yakolo ke magana, anma falmata tayi kif da ido tareda “cewa tunda ba danki bane saikiyi hakuri” yakolo taji zafin kalman dakinta takoma don abun yafi karfinta, Yusuf nafitowa daga masallaci yaga shehu wanda yayi latti, donsai alokacin zaishiga masalaccin [10/29, 7:10 PM] Adda Bena: Ganin yusuf yasa ya tarbesa tareda cewa “kayi sauri kashiga ciki kaga ikon Allah hakan yasa yadada sauri jikinshi nabashi wani abu yafaru ne,aikuwa idonsa kan aliya yayi tana zaune a kasa , Allah sarki marainiyar Allah dasauri yaje yadauketa falmata nakiranshi bai kulataba fanninsu yanufa da aliya daki yakaita yaga babu bedshit nan da nan yagane me akayi mata ajiyeta yayi yaje yadauko kettle yahada mata ruwan zafi sannan yace “tashi kishiga,” da taimakonsa tashiga bandakin tarufo, jin ta dade baikuma ji motsin ruwa ba yasa yabude bandakin tana zaune acikin bathtub din tana kuka, tausayinsa yakamata bata rai yayi sannan yace “zanmiki wankan” kallonshi tayi adan tsorace anma bai kulata ba, yarufo bayan gidan yakamota, tagara yimasa gaddama, haka yacire kayan yakunna showern kunya duk yarufeta, tagagara motsi haka yacudeta kaman jaririya sannan yadaukota ya ajiye, ya shafa mata mai yaciro mata kaya marar nauyi wani dogon riga ne haka, daya ciro yasamata, yahada mata tea a falo yazo yazauna ya lallabata tasha, itakam sai ganin ikon Allah take, mutumin datake masa kallon soko yau gashi soko na aikinsa,saida ya tabbatar batada matsala sannan yashiga yadau wanka, yafito fannin bayi yanufa, yasa akira masa wanda suka dauki aliya , sannan yafara fada akan me zasu taba mishi matarsa nemo dogarai yayi yasa aka basu jikinsu, saidaya tabbatar kowacce taji jiki sannan yanufi fannin yakolo yagaysheta anan tadada basa hakuri yanuna bakomi , yanufi gun falmata wacce tacika fam tana jiransa, zuwansa tafara masa fada akan me zai hukunta bayi sannan yafara gayda kishiyanta kafin ita, tunda tafara magana baice mata uffan ba harta gama,hakan yakara tunzurata tuni ta kullace aliya aranta, gani takeyi ta mallaka mata da, fitowarsa yanufi gun mahaifinsa suka fara gaysawa, kafin yakoma fanninsa, tare suka wuni har dare alokacin aliya tafarajin wannan kukan kuma, tuni tafara tsorata [10/29, 7:39 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR haka suka kara zama adaren basu runtsa ba, tuni aliya tafede rashin bacci yafara takurata. Ga ciwon kai ita saitana jinta asama itabaa kasa ba, baa sama ba, kaman jira kaman ana yawo da ita, Ga rashin kwanciyan hankali haka suka jera sati ahaka bata bacci daredare dasafe kuma inta kwanta saitahau mafarki,ganin abun banayi bane yasa yusuf yakira sufyan suka gayamasa abunda yafaru tunda yake baitaba shiga tashin hankalin ba, nan yafara dana sanin amince mata ta auri yusuf, bai kawo kowa aransa ba anma yasan akwai wanda basuson aliya da yusuf, akwai wani malamin da sufyan yasani donhaka ya umurci yusuf da aliya suje gunshi, Babban malami ne yanada almajirai nan yusuf yabukaci ganinsa, aka musu iso a zaure, malamin yashigo , aliya sanye takeda babban gyale yarufe fuskanta hannunta ne kawai awaje, malamin nazama, yace “subhanallah, ciro abun hannunki” dasauri tafara ciro zobunan, yace “a a. Na azurfan” cirowa tayi tamika masa, yakarba dasauri ya kira almajiri daya yamika masa sannan yace yaje ya sa awuta, sannan yajuyo yakalli aliya tareda cewa “baiwar Allah kinata yawo da tsafi ajikinki, ai kurwanki ake yawo dashi asama, ” tuni jikinta yafara bari, yusuf yakalleta tareda cewa “waya baki zoben?” “Acikin kayan aurena nagani” baice komi ba inda malamin yace sutafi meke tafe dasu, tamishi bayani zalla zallah Yace “dafarko jirin dakikeji wannan zoben ne, shiyake jawo haka yawo ake da kurwanki asama,, nabiyu kuma asiri ne akamaki mai suna janduks, shi wannan sihiri anayine wa mutum inda mutum zaisa ranshi a tsaka,” daga yusuf har aliya gyra zama sukayi don kowannensu yagama tsorata jikinsu na bari, musamman aliya, duk dabarun sihiri data karanta bata karanto dawannan ba, “Sihiri ne akewa mutum na kwana ashirin, dafarko akan dauki hoton mutum kowani abu dakika mallaka a yi amfani dashi, sannan wannan sihiri shine zakina jin kukan dabobbin dakikafi tsoro, inkin kwanta kuma zakina mafarkin kura, shiwannan kura zaina binki ne,har kwana ashirin idan kuran ta yakeki zaki mutu acikin kwana ashirin, idan kuma ke kika yaketa zata koma kan wnda yayi sihirin, kinada wani tabo ajikinki dakika samu a mafarkin?” Ta gyada kai tareda cewa “kuran danake mafarkinsa kullum inna tashi sainaga cizon ajikina yayi baki”. Yace “haka sihirin take, yanzu zanbaki dabarun karyawa, inbaki karyaba zaki iya rasa ranki Allah ya sauwaka” aliya da yusuf jikinsu na bari sukace to inda yaci gaba da bayani yana cewa “Akofar dakinki ko kuma tsakar gydanki kinemi rami akwai inda aka birne laya kiduba, dole sai an birne laya medauke dasunan wanda akeso ya mutu din, kinemo acire, sannan inzakiyi bacci kikaranta yasin, fatiha, falaq, nas, da suratul jinni, kikaranta kikwanta zakiyi mafarki anma zakisamu karfin yakanta, donhaka kisamu ki kashe wannan kuran hakan kadai zaisa kizauna lafiya, sannan dalilin ganin wannan kuran wanda yayi asirin kowani dare yana kona laya da takarda me dauke da sunanki donhaka saiki dage da addua wani lokacin mune bama nemawa kanmu tsari, munsan sihiri nakama mutum anma zamu iya karyawa,ki kasance kina bacci da alwala, ki kasance kin rike hisnul muslim,ki guji zama cikin najasa, Allah yana taimakawa wanda ya taimakawa kansa ne” Sunmasa godiya sosai sannan suka mike sukafito dakyar aliya take tafiya jin ance kwana ashirin, acikin kwana ashirin taci bakwai, ashe dama haka abdullahi yaji daya bata kodanta yasan zai iya mutuwa kowani lokaci, ashe haka yaji? Innalilah kuka tafarayi yusuf harya tukata gyda. Sannan yafara lallabinta, dakyar tashanye kukan tafito bilkisu takira tareda cewa tanemo dogarai, suna isowa tafito itama tace sufara tone gun duk inda sukaga laya kowani abu na alajabi su kawo, tana tsaye akansu tana jira nima benaxiratu nadau gatari daya nafara dube du[truncated by WhatsApp] HALACCIN SARAUTA (THE END)  benaxir  November 1, 2015  Hausa Novels  126 Views [11/1, 7:04 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR (First of all, m sooo sorry kunjini shiru kwana biyu nd i couldnt explain myself, y’all should find a place in ur hrts to forgive me,bikin one of my closest frnds nayi. Sunyi kokarinsu don ganin sunsamu laya kowani abu makamancin haka don samun babban kyauta kamar yadda aliya tamusu alkawari, basu sami komi ba haka suka hakura har dare ana abu daya, aliya duk tashiga damuwa da tashin hankali, anki abarta tahuta da mijinta ankuma ki abarta tazauna lafiya, Daredare takaranta surorin kamar yadda akace tayi takwanta zuciyanta cike da son kama kowacece, acan tafarajin kukan kulya da kare nan da nan tafara Allahumma ajirni fi musibati waakrijhi khailriha, tanayi tana hadawa da auxubillah, ahaka tazauna yusuf na gefenta yana tayata addua yagagara bacci duk da taso yayi anma yaki, hakan yasa suka zauna suna ta addua ahaka har asuba, asuba nayi yafice masallaci itama tayi sallolinta sannan tawuce kan gado , tana addua harta jira bacci ya kwasheta Tayi dan mafarkan Allah kuma yabata nasara ta jiwa kuran ciwo, itama ta ji ciwo bata tashiba sai karfe daya. Inda tayiwa yusuf bayani yace tacigaba dahaka har na sati kamar yadda malamin yace zata kashe kuran inhar tana kokarin fada dashi, [11/1, 7:35 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR kullum tana fada dashi kuran yadawo baida ishashen karfi, aranan tafito tana son zuwa fannin yakolo ko zasu gaysa, wani bakin abu tagani rana ya hasko mata, harta wuce takoma tadauka ga mamakinta laya ne, hannunta na bari tadauka tana addua, harta isa dakinta tana isa tanemi babban container tazuba sannan tarufe, wayanta tadauka takira yusuf yana dauka muryanta na rawa tace “kayi sauri kazo gyda, don Allah kayi sauri” yadda yaji magananta tuni ya tsure dama yashiga kasuwa ne babu shiri yadawo fada, tana zaune a falo yashigo anan tanuna masa shima ya mugun tsorata anma dole yadanne nasa don karta rude, wurin malamin suka nufa dashi, yadauki layan sannan yace tayi addua ta tofa ajikinta ta kona layan agun, aikuwa tana haka yace toh yanzu saura takarasa nakasa kuran inhar tayi haka toh ba tabbas wacce tamata wannan sihirin, asiranta zai tonu dahaka sukayi sallama dashi. Sunkoma gida sukaga fannin falmata a cike arude yusuf yashige aliya na biye dashi abayanta, falmata ce adaki tana kwance sai kuyangu akanta, dakuma yakolo su umma uwar soro, mutane dayawa dai haka, hankalinshi tuni yafara tashi, yaleka ta dakyau ga mamakinsa ganinta yayi kaman ba itaba, kamanninta duk yacanja, tacanja wasu manyan kuraje ne suka fito mata, ga doyi kuma, kowa hannu na hanci tuni yakai nashi hannun , anan akace kowa ya watse aka barsu kadai adakin umma uwar soro tace takai awa daya ahaka, don tunda jakadiya tazo tamusu bayani akan falmata nakwance kawai saiga kurajen sunfara fitowa abun kuma bai tsayaba, shiru yayi zuciyarsa na masa zargi, anma duk dahaka yazauna, duk iya kokarin da akayi dawasu likitoti abu yaki tafiya wari yaki tsayawa, falmata acikin dakikai kadan tadawo abun tausayi, wanda hakan tuni yafara yawo a fada, falmata tayi sihiri yadawo kanta acewarsu kenan, kowa sai Allah kara yake, dama ta addabi kowa acikin fadan, kowa yanata farinciki, yayan cikinta ne kawai suke kukan abun, suma ni benaxir na tabbata don ita tahaifesu shiyasa, inbahaka ba babu yadda zaayi suji haushin abunda yake samunta, yusuf dai zama yayi agefenta yana kallonta yarasa ma yazaiyi sannan kuma mezaice mata, [11/1, 8:01 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR dahaka tana kallonshi tana zubda hawaye, aliya ma tana daga gefe tayi tagumi duk tsanar falmata datayi yaukuma tausayinta taji, tamike tadauko ruwa sannan tabata, tana jingine a kujera, tana kallon aliya yusuf ma nagefe, Wani abun mamaki shine tun ranan aliya tadena jin kukan kare da kulya, sannan tafara baccinta abun ya matukar bata mamaki hamdallah tarinkayi wa Allah tana godiya, tayi salollinta, Falmata ankaita asibiti anma sunbada shawaran ayi maganin gida nan da nan aka nemo mai maganin gargajiya, yusuf kuwa yahado da wannan malamin bayan dan magana dasukayi sai malamin yace mishi tabbas itace, yusuf jikinshi yayi sanyi donhaka dakyar yakira aliya malamin itama yamata bayani kuka tayi sosai jikinta yayi sanyi, tanata tunani duniyan shinawa yake? Da girmanka da mutuncinka zaka nemi gun boka , me boka zaimaka wanda Allah baimaka ba? Mezaka tanadar wa kanka agun boka? Daya wuci wulakanci da dizgi, duniyar kanta nawa take da mutum zai sa rayuwarshi ta kaskance, ta zama wulakantacce, Takoma gun falmata anma bata canja mata fuska ba, tacigaba da zama tana jinyarta da bayin dasukenan, Wannan hali na aliya yasaka falmata jin kunya, taji inama tunfarko bata kullaceta ba, bata mata asiriba, sannan bata musguna mata ba, tana kuka taroki gafaran aliya takuma nuna nadamarta a fili, aliya tanuna mata bakomi hakan yasa tacire komi aranta, mijinta kuwa tuni tasamu kanshi duk da dafarko yana fushi da halin mahaifiyarsa aliya tayi iya kokarinta ta gwada masa muhimmancin mahaifiyarsa dakuma hatsarin fushi da ita, tabbas yayi alfahari da aliya domin kuwa tazamto masa garkuwa, itace macen da annabi yace a aura wacce zata gyra maka yayinda kashiga hatsari wacce zata zamo maka garkuwa,yana alfahari da aliya yana kuma tausayinta a matsayin marainiya, Falmata ahankali tafara samun sauki da yusuf yahado malamai anata addua da saukan qurani, domin sarkin yayi tashi harya gaji, Allah cikin ikonsa tasamu sauki duniya takoya mata hankali ta nutsu tazama mutumiyar arziki domin kuwa hatta bayi darajasu take, kansu yazama ahade da yakolo Yayinda aliya tahade da mijinta, abun alfahirinta,garkuwan jikinta sannan sanyin idaniyanta Sufyan yazo ya auri hassana wacce ta tare a gydan da sufyan ya kare mata,zaman lafiya alhmdlh nima benaxir omar ina jinjina muku dakukayi hakuri dani duk da matsalan dana rinka samu bansamu na karasa muku da wuriba dakuma rashin cigaba akan lokaci, nagode sosai Allah yabar zumunci Ina gayda rukayya bayero for helping out, yu really made me do dix, Kausar nd ummi aisha na sadaukar da littafinnan agareku don nuna godiyata agareku, Tom ni benaxir omar nagode muku saikunjini asabon labarina dazanyi anan gaba HANNU[truncated by WhatsApp] Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239