COMPILED BY ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS WASAAPP 08066360176 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 1 and 2 Ina mika g0diya ta wa ALLAh (swa) daya bani ik0n rubuta wannan littafin. Sannan wannan littafin kageggen labari ne ban yi d0n cin zarafin wata k0 wani ba dan haka idan yayi dai dai da rayuwar ka/ki ayi hakuri. Na sadaukar da wannan littafinne ma Aunty na Aysha biciki (AysM) ALLAh ya kara basira da daukaka... Masoya zaku iya fadan ra'ay0yin ku ta wannan numbern 090649847980 . Nagode. A fusace ya shig0 gidan yana faman kwalla mata kira kamar gidan zai tarwatse saboda tsabar ihun da yake yi, ke saude! Ke saude! Cikin hanzari ta fito daga daki tana amsa kiran da yake mata. Gani mallam ta fada tana karasowa ya kalleta cikin daure fuska sannan yace se yanxu kikaga damar amsawa? Cike da ladabi tace kayi hakuri mallam wallahi sallah nakeyi shiyasa. Dan ta6e baki yayi sannan yace ina salma take? Ki gaya mata zatayi bako anjuma kuma saura yazo taki fita wallahi ranta seya baci dan nagaji da ganinta a gabana ba miji. Inna saude ta kalleshi sannan tace haba mallam aure ai lokaci ne idan lokacinta yayi ko tana s0 ko bata so xatayi ai... Cikin jin haushi ya katse ta ke saude na dade da sanin ke kike zugata to bari na fada miki a wannan karon na tsaida magana. Na riga nayima salma miji ke baki isa na canja maganata ba kuma ki ja mata kunne k0 tana s0 k0 bata s0 se anyi aurennan. Inna saude tayi kasa da muryanta tace dan Allah mallam kayi hakuri ni ban isa na zuga salma akan ta bijire ma umurninka ba sbd ni da ita duk a karkashin ik0nka muke, kuma insha Allahu salma bazata watsa maka kasa a ido ba kayi hakuri. Jin abinda saude tace ne yasa mallam amadi sassautawa sannan yace ai kene saude da wata irin magana ya zango ina miki maganar nayi mata miji amma kina cewa aure lokaci ne, ai lokacin yayi kenan tunda har na zabo mata mijin daya dace da ita. Gidan da zata je ta huta k0mai se anyi mata ba tare da tasha wuya va. Inna saude ta matso tana cewa mallam irin wannan k0dawa se kace wanda zata auri govenor Murmushi mallam Amadi yayi saboda jin ta s0sa masa inda yake masa kaikayi, ai saude mijin da salma zata aura kamar g0venor yake a wajen mu dubi ciki gidannan k0 dan tiles babu balle aje kan abin sanyinnan A.c ake ce masa k0 me ai kuma kinga duk wanda yake da irin wannan a gidansa se dai mu kirasa da govenor a gidannan. Cikin mamaki inna saude take kallonsa k0da yake ba abin mamaki bane awajenta tunda tasan halin mijin nata. 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 2.I dedicate this page 2 my l0vely sis maimuna dauda guda (ummi) Allah ya bar qauna... Zaku iya fadan ra'ayoyin ku ta wannan numbern 09064984798 ngd Tunda tasan halin mijinnata mutum ne mara godiyan Allah, wanda k0mai ya samu baya isarshi, a kullum shidai hangen na wani yake yi. Murmushi tayi sannan tace wai ni mallam waye kake ta zuzutawa ne haka? har yanzu banji ka fada min sunan shi ba. ALH. ABDUL ME DALA ya fada yana zama akan taburman dake shinfide a tsakar gidan... Cikin fΓ­rgici inna ta dafe kirji badai Alh. Abdul dana sani ba? Dan murmushi yayi sannan yace shidin dai nake nupi. INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI'UN. Abinda inna saude take ta maimaitawa kenan. Yanxu malam ka rasa gidan da zaka kai yarinyar nan se wannan gidan? Gidan da kowa yasan ba gidan zama bane, amma saboda s0n abin duniya kake so ka maida 'yarka bazawara. Kai inma zawarcinne ai da sauki indai baza'a kassarawa mutum rayuwa ba. Inna ta fada tana goge zufan da ke zubowa daga fuskarta wanda yake sauko mata tun lokacin da taji an ambaci sunan ALH. Abdul me dala. Duk kawaici irin na inna saude wanda ko wani irin hukunci mallam amadi zai yanke a gidan zeyi matukar wuya kaji tayi magana koda kuwa hukuncin beyi mata dadi ba. Amma yau sanadin jin sunan ALH. Abdul da tayi ta tanka. Wanda shi kansa mallam amadi saida yayi mamakin hakan. Shiru yayi yayi mata dan besan me zaice mata ba. Shidai yasan ya riga ya gama yanke hukunci kuma ba wanda ya isa ya canja masa ra'ayi [1:34PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 3.Cikin sanyin jiki inna saude ta zauna kusa dashi.sannan tace mallam wannan maganar fa abin dubawa ne don Allah kabar salma ta zabi wanda take so, har nawa salmar take? da za'a ce an gaji da zamanta ba miji. Kwata kwata fa bata fi 18yrs ba. Dan Allah kabar maganar hadata da ALH. Abdul dinnan. A hargitse ya dago yana mata wani mugun kallo, sannan yace ke saude wallahi fita daga cikin maganar nan idan har kina son mu shirya dake, nan gidana ne salma kuma 'yata ce inada iko da ita da da duk abinda yake cikin gidannan. Ina da ikon aura mata duk wanda nake so. Ke koda kuturu naso ta aura dole tayi min biyayya balle cikekken mutum me tarin dukiya. Kuma bari kiji billahillazi ko mallam dattine ya dawo duniya kinga dai shiya haifeni ko? To be isa ya hana na daurawa salma aure ba. Sake baki inna tayi tana kallon shi ba tare da ta'iya cewa k0mai ba. Jin maganar na shi har iyayen shi yake sawa aciki. Arziki na bin mu kinamana bakin ciki to ta Allah ba taki ba. Ya fada yana miqewa daga kan taburmar da suke zaune. Ya saka takalman sa ya fice daga gidan yana banbamin masifa. Bin bayansa da kallo tayi kana tace mallam ina guje maka ranar nadama dan nasan tananan zuwa wallahi se kayi nadamar abinda kake shirin aikatawa. Mikewa tayi ta fara aikace-aikacenta d0n yamma tayi gashi bata gama abincin dare ba. [1:34PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 4.matashiyar budurwa ce kyakkyawa doguwace amma ba sosai ba, fara ce kar jikin ta dan daidai kirar coca cola. tana da faffadan fuska me dauke da manyan idanu tare da madaidaicin hanci da faffadan baki,. tana da beauty point a gepen kumatunta hagu da dama. haqoranta farare wanda suke dauke da siririn wushirya a tsakanin su , tana sanye da dogon hijab har kasa ruwan kasa hannun ta yana dauke da al-qur'ani me girma.!!! da sallama ta shigo gidan tana cewa inna na dawo, inna saude dake kitchen tana tuka tuwo ta amsa mata sallamarta tana cewa salma kin dawo? cikin nutsuwa ta amsa mata da eh nadawo, sannan tace inna bari nazo na taimaka miki kafin a kira sallah. A'a salma yi zamanki ki huta,keda yanxu kika dawo. ai harna gama daman tuwo ne ya rage ban tuka ba. To inna salma ta amsa tana cire hijab din makarantar hadda da take zuwa dashi,.sannan ta shige daki ta ajiye Al-qur'anin dake hanunta,ta fito ta nemi waje ta zauna tace inna har yanzu baba be dawo bane? inna saude ta amsa da cewa ya dawo ya sake fita ne, amma yanzu zaki ganshi ya shigo tunda magariba tayi. Inna bata gama rufe baki ba mallam Amadi yayi sallama ya shigo gidan. sannu da zuwa baba cewar salma, yawwa sannu 'yar albarka. Da mamaki take kallon mahaifin nata rabon da taji irin haka a bakinsa har ta manta. Da Sauri ta tashi ta debo masa ruwa a buta,domin yayi alwalan sallar magriba. sannan itama ta dauki buta tayi ta shiga daki domin tayi sallah itama. [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 5 Bayan mallam Amadi ya dawo daga sallah, ya nemi waje ya zauna inna saude ta kawo masa abincin shi. Bayan ya gama cine ya dubeta yace ina fatan kin fadama salma sakon da na baki??? inna tace ban fada mata ba mallam, amma yanzu zan fada mata insha ALLAhu Da harara ya bita dashi,sannan yace kira min ita nina fada mata tunda ke baza ki iya ba.kayi hakuri mallam yanzu zan fada mata. Tsawa ya daka mata yana cewa ki kiramin ita nace, da hanzari inna ta tashi ta shige daki tana me kwalama salma kira. Amsawa salma tayi sannan tace inna wani abu xan yi miki? girgiza kai tayi tace mahaifinki ne yake kiranki. Gaban salma ne ya fadi ta shiga maimaita INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI,UN!a cikin zuciyarta dan tasan idan taji kira daga wajen mahaifinta, tofa ranar da bakin ciki zata kwana Inna ta juya ta fice daga dakin tana cewa ki fito yanxu karki bata lokaci. Da hanzari ta biyo bayan mahaifiyar nata,can gepe ta tsuguna cikin girmamawj tace baba gani.Ya dubeta yace dama ba wani magana bane maganar auren kine nagajr da ganinki a haka ba miji,saboda haka na zaba miki miji kuma anjumj zezo saura naji kin masa wani abu. Wallahi jikinki zai gaya miki, yanzu ki tashi kije ki shirya kafin yazo. a hankali salma ta mike tana hada hanya ta nufi daki,jin irin hukuncin da mahaifinta ya yanke ba tare daya tuntubeta yaji ra'ayinta kona mahaifiyarta ba. tana shiga daki ta fashe da kuka 😭 tana me cewa ya ALLAh ina rokonka kasa hakan ya zamomin alkhairi a rayuwataπŸ™πŸ™πŸ™ kuyi hakuri da wannan. [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Masoya makaranta novel dina ina jin dadin yanda kuke nuna kaunar littafina. Nagode sosai ALLAh ya bar kauna. Page 6 WANENE MALLAM AMADI??? Mallam Amadi dan asalin garin Bauchi ne, a karamar hukumar Ningi. kasuwanci ne ya kawo mahaifinsa cikin garin bauchi Mahaifinsa yana da rufin asiri daidai gwargwado, su 2 ne a wajen iyanyen su. shi da kanwar sa hadiza wanda take aure a cikia anguwar nassarawa jahun. Bayan rasuwar iyayen su shiyaci gaba da kula da kasuwancin da mahaifin su yakeyi, yana sayar da kayan yara a kasuwan central. Mallam Amadi mutum ne me son abin duniya, ko kadan baida godiyan ALLAh. Matarsa daya inna saude tun auren saurayi da budurwa be sake wani auren ba. macece me kawaici da hakuri. ko kadan bata da tashin hankali shiyasa suke zaune lafiya da mallam Amadi dan bata ketare umurnin sa.suna zaune ne a unguwar liman.'yarsu daya ce ummu salmawanda baza ta wuce 18years ba. yarinya ce me hankali dan duk halin inna saude ba abinda ta bari. Tayi karatunta har zuwa matakin secondary, taso taci gaba amma mallam Amadi yace ba'a gidansa ba se dai ta fitar da mijin aure. Hakane ma yasa ta shiga makarantar hadda dake kan tudu. salma yarinya ce me farin jini kowa sonta yakeyi se dai ita ko kadan bata kula su. Gashi duk wanda zezo wajenta zaka samu me kudine.Hakane yasa mallam Amadi yake jin haushinta, acewar sa tana masa bakin ciki ne. A hakane watarana ta dawo daga makarantar hadda Alh.Abdul-Razak me dala ya ganta. Tunda ya ganta yaji ta kwanta masa arai, hakane yasa yayi bincike akanta kuma ya yaba da tarbiyanta. Wannan ne dalilin dayasa yazo wajen Mallam Amadi domin ya nemawa tilon dansa namiji aurenta. Daman me neman kukane aka jefe shi da kashin awaki,nan take mallam Amadi ya amince ba tare daya tuntubi salma da mahaifiyar ta ba. Acewar sa koda tana da wanda take so to se dai yayi hakuri. [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 7 and 8 Readers naji korafin ku akan a kara yawan page kuyi hakuri yaronah ne baida lafiya,amma insha ALLAhu idan ya samu sauki za'a kara yawan pages din. ina godiya a bisa comment din da kuke yi ALLAh yabar kauna. BACK TO STORY Salma tana cikin kukanne inna ta shigo ta same ta, samun waje tayi ta zauna sa'annan ta dubeta tace salma kiyi hakuri ki dena kukan haka dan ba'abin da kukan ze miki se dai ya jawo miki wani ciwon. Nasan ki yarinya ce me biyayya, a wannan karon ma ina son kibi umurnin mahaifin ki. Insha Allah zai zamo alkhairi a gareki. cikin sheshshekar kuka salma tace inna ni damuwata bansan wanda za'a aura min ba, bansan halinshi ba, kuma ma inna nawa nake da za'ace angaji da ganina ba miji? Dan murmushi inna tayi wanda daga gani bai kai ciki ba,iya fatan bakin ta ya tsaya. Salma addu'a zakici gaba dayi,dan kinsan halin mahaifin ki indai ya fadi magana tofa ba wanda ya isa yasa shi canjawa. to inna wa za'a aura min? salma ta tambaya tana me share hawayen ta. ALH. ABDUL-AZEEZ ME DALA. Cikin mamaki salma take kallon inna, wai inna kina nufin A-Azeez me dala da nasani? shidin dai nake nupi inna ta tabbatar mata. cikin gigicewa salma ta fashe da kuka tace inna yanzu a rasa wanda za'a aura min se A.A? Mutumin da kowa yasan halin matarsa,ko iyayen shi fa bata bari yaje wajen su balle 'yan uwansa. Duk wacce ya aura fa seta raba su ko kuma ta haukatar da ita. gaskiya inna nikam bazan iya auran A.A ba. se kije ki fada ma mahaifin naki cewa kefa baza ki iya auran wanda ya za6a miki ba. Kafin salma tace wani abu suka jiyo muryan yaro a tsakar gida yana sallama,inna ce ta amsa. Yaron yace wai ana sallama da salma,kace tana zuwa. Inna ta dubi salma tace ki tashi ki fita tun kafin mahaifin ki ya fito yazo ya same ki. Cikin sanyin jiki salma ta tashi ta dauki hijabin ta ta fita. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 9 and 10 Readers nagode da addu'o'in da kuke min ALLAh ya saka da alkhairi. AMEEN A jingine yake a jikin wata mota ruwan toka kirar marcedez benz c-class 2018. Matashin saurayine wanda bazai wuce 35yrs ba, fari dogo kyakykyawa ne ajin farko daka kalle shi zakaga yana maka yanayi da jarumin film dinnan na indi'a wato sharukh-khan. yana da faffadan fuska da kwantaccen saje, idanuwansa madaidaita ne, yana da dogon hanci da madaidaicin baki wanda ke zagaye da siririn gashin baki, wanda ya dada kawata fuskar shi. yana da faffadan kirji wanda yake cike da gashi, baida kiba sosai. Mekaratu zanso ka ganshi gayen ya hadu iyakan haduwa ko a kasar india iyakaci😜😜😜 yana sanye da shadda skye blue be saka hula ba, se kwantaccen gashin kansa dayasha gyara atakaice duk yanda ake neman hadadden saurayi to ABDUL-AZEEZ Yakai. Ba wanda zai ganshi yayi zaton yanada aure. Sallama tayi cikin zazzakar muryarta ASSALAMU ALAIKUM. cike da kasaita da jin kai ya amsa mata, ina wuni? ta fada kanta yana kallon kasa. saida yaja aji dan har tayi tunanin bazai amsa ba sannan yace lafiya. kamar wanda akayi masa dole,shiru ne yadan ratsa wajen kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa. ita tana tunanin wani irin zama zasuyi da shi, yayin dashi kuma yake tunanin an takura masa da akasa yazo wajenta. A ganinsa tayi masa karama, sunkai wajen 15mnt ba tare da dayansu yace uffan ba. Cikin izza ya fara magana, ina fatan anyi miki bayanin zuwana? be jira abinda zata ce ba yaci gaba. inason ki sani a tsarina bani da niyan auren mace fiye da guda daya matata kadai ta isheni rayuwa ban damu da tana haihuwa ko batayi ba, dan ita haihuwa nufin ALLAh ce duk lokacin daya so zai bamu kisani takura min akayi akan sena aure ki, i love my wife, i dont think zan iya hada sonta da wata 'ya mace a duniya bayan mahaifiya ta. Mahaifina shi ya zaba min ke, saboda haka ke ZABIN MAHAIFINA ce. ina fatan kin fahimta? shiru tayi masa batace komaiba. tabe baki yayi sannan yaci gaba nazo nan ne saboda umurnin mahaifina, yace na sanar daku baya son aja dogon lokaci. Zaizo ya samu mahaifinki zasuyi magana, kuma bana bukatar a cika min gida da tarkace dan haka ba se an kawo ki da komai ba hope u understand??? Cikin jin haushi salma ta dago tana binshi da wani mugun kallo, cikin kumar rai ta fara magana. Nima ai kai ba zabina bane kai ZABIN MAHAIFINA ne. kuma da kake cewa kar a cika maka gida da tarkace ai dai kasan komai talaucin mu dole za'a kaini da abinda ALLAh ya hore mana, dan haka maganar kar a cika maka gida da tarkace ma bai tasa ba, we do what ever we want. iyaka bacin rai Abdul yakai 😑😑😑😑😑shi mutum ne wanda baya son raini. tunda yake a rayuwar sa ba macen data taba fada masa magana makamanciyar wacce salma ta fada masa. wacece ita? da zata ce shiba zabinta bane. har akwai macen da zata kalle shi ta nuna masa bata kaunar sa?? ke wacece dazan fadi magana kice baza kibiba??? TO wallahi bari kiji kar wanda yazo min da tarkace gidana this is an order. ya karashe maganar yana huci. kuma kisan irin maganar da zaki dinga fada min idan kuma ba haka ba wallahi saina koya miki hankali. yana gama magana ya shige motar sa yabar wajen. kada kai salma tayi itama ta shige gida tana jinjina rashin mutunci irin na A.A. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 11 A tsakar gida ta samu mahaifinta yana jiran dawowarta. Sannu baba ta fada tana kokarin wuce shi ta shige daki. ke zonan ya kirata dawowa tayi ta tsuguna a gefensa. Ya kukayi dashi?? ina fatan baki masa rashin kunya ba? Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tayi mishi bayanin yanda sukayi,sannan ta daura da cewa baba ni inaga be kamata ace an kaini gidansa ba komaiba dan zai iya zamamin abin gori watarana. Kinci kaniyar ki wani irin gori? to bari kiji koda ma beyi wannan maganar ba ni bani da kudin da zan saya miki kayan daki. dan haka ko cokali bazan saya va, kuma wallahi daga yau na sake jin kin fada masa maganar data bata masa rai zaki gamu dani kinji na gaya miki. Tashi ki ban waje ya daka mata tsawa shashan yarinya mutum yana nema mana sauki kina son ki mana bakin ciki. Cike da sanyin jiki salma ta tashi ta shige daki. inna ta gani zaune akan sallaya ta idar da sallan isha'i da alama ta gama jin maganganun da sukayi da mahaifinta. sallaya ta shimfida itama tayi sallah bayan ta idar ne take sake yima inna bayanin yanda sukayi da A.A inna tace salma kiyi hakuri tunda yace baya bukatar a kaiki da komai to kibar maganar a haka tunda kinsan mahaifinki bazai saya ba. Akwai kudin da nake tarawa saboda zuwan irin wannan ranar ko vaxa a miki komaiba zan hada kudin ko kayan kitchen a saya miki da gara komai kankantar sa saboda gudun gorin kishiya. Rungumeta salma tayi cike da jin dadi nagode inna ALLAh ya bar min ke.πŸ™πŸ™πŸ™. ai duk avinda nayi miki nayima kainane salma tunda ke kadai ALLAh ya bani. yanzu ki tashi kije ki kwanta, saketa tayi taje ta kwanta inna se da safe, to salma kiyi addu'a kafin ki kwanta. to inna ta amsa sannan tayi addu'a ta shafa ta gyara kwanciyarta. ASUBA TA GARI 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 11 A tsakar gida ta samu mahaifinta yana jiran dawowarta. Sannu baba ta fada tana kokarin wuce shi ta shige daki. ke zonan ya kirata dawowa tayi ta tsuguna a gefensa. Ya kukayi dashi?? ina fatan baki masa rashin kunya ba? Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tayi mishi bayanin yanda sukayi,sannan ta daura da cewa baba ni inaga be kamata ace an kaini gidansa ba komaiba dan zai iya zamamin abin gori watarana. Kinci kaniyar ki wani irin gori? to bari kiji koda ma beyi wannan maganar ba ni bani da kudin da zan saya miki kayan daki. dan haka ko cokali bazan saya va, kuma wallahi daga yau na sake jin kin fada masa maganar data bata masa rai zaki gamu dani kinji na gaya miki. Tashi ki ban waje ya daka mata tsawa shashan yarinya mutum yana nema mana sauki kina son ki mana bakin ciki. Cike da sanyin jiki salma ta tashi ta shige daki. inna ta gani zaune akan sallaya ta idar da sallan isha'i da alama ta gama jin maganganun da sukayi da mahaifinta. sallaya ta shimfida itama tayi sallah bayan ta idar ne take sake yima inna bayanin yanda sukayi da A.A inna tace salma kiyi hakuri tunda yace baya bukatar a kaiki da komai to kibar maganar a haka tunda kinsan mahaifinki bazai saya ba. Akwai kudin da nake tarawa saboda zuwan irin wannan ranar ko vaxa a miki komaiba zan hada kudin ko kayan kitchen a saya miki da gara komai kankantar sa saboda gudun gorin kishiya. Rungumeta salma tayi cike da jin dadi nagode inna ALLAh ya bar min ke.πŸ™πŸ™πŸ™. ai duk avinda nayi miki nayima kainane salma tunda ke kadai ALLAh ya bani. yanzu ki tashi kije ki kwanta, saketa tayi taje ta kwanta inna se da safe, to salma kiyi addu'a kafin ki kwanta. to inna ta amsa sannan tayi addu'a ta shafa ta gyara kwanciyarta. ASUBA TA GARI 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 12 Kuyi hakuri na jina shiru da kukayi kwana 2 hakan ta farune dalilin abubuwa da suka yimin yawa amma insha ALLAhu zaku dinga jina yanzu akan lokaci. masoya littafin ZABIN MAHAIFINA nagode a bisa kaunar da kuke nuna ma litta fina. masu min magana ta whatsapp,facebook, da masu kiran waya kai harma da wanda basu samu damar min magana va duk ina godiya a gareku. Washe gari da safe bayan sun gama karin kumallo. Mallam Amadi ya wuce kasuwa, salma ta tattara kwanuka ta fara wanke-wanke, sallama akayi aka shigo, wata matace wanda daka ganta kasan kanwar mallam Amadi ce saboda kamar da sukeyi. Da hanzari salma ta mike, sannu da zuwa aunty hadiza ta fada fuskarta dauke da murmushi. Cikin fara'a matar ta amsa mata, yawwa sannu salma aiki akeyi ne? eh aunty. Ina innar taki? tana cikin daki salma ta amsa mata. Sallama aunty hadiza tayi inna ta amsa mata, sannan ta shiga dakin, A'a hadiza ne yau a gidan namu? wallahi ni ce yaya, da yake haka take kiranta dashi kasancewarta matar yayanta. ta nemi waje ta zauna, gaisawa sukayi, sannan inna tace hadiza kwana 2 shiru kamar bakyanan. wallahi yaya inanan kawai fitanne se a hankali kafita kabar yara su kadai suyita maka barna. Yanzu ma yaya Ahmad ne ya aika nazo. Ina fatan dai lafiya? Hmm inna tayi ajiyar zuciya,sannan tace Hadiza ina fa lafiya, mallam ya dage wai aure zaima salma,harma ya za6a mata miji. Wani irin aure kuma yaya? nawa salma take da za'a dage se an mata aure? yanzu pa zamani ya canja, yarinya se takai 25years to above ba'ayi mata aure ba. Gaskiya yaya Ahmad be kyauta ba. Bari ya dawo ni zanyi masa magana, A'a hadiza ki rufa min asiri karkiyi wa mallam maganar nan dan cewa zeyi nakai karar sa wajenki. Kin dai san halinsa. to shikenan bazan yi masa maganar ba ALLAh yasa hakan shine alkhairi Amin inna ta amsa mata. sannan suka ci gaba da tattaunawa game da yanda bikin zai kasance. Salma ce ta shigo ta gaishe da AUNTY hadiza. Amsawa tayi tace salma kiyi hakuri komai na rayuwa mukaddari ne, haka taki jarabawan take badon ALLAh baya sonki bane yasa yayi miki haka A'a yayi ne domin ya gwada imanin ki. kiyi kokari ki cinye jarabawan ki kinji 'yata? Gyada kai kawai salma tayi dan idan tace zatayi magana zata iya fashewa da kuka. tashi kije aunty hadiza tace mata, mikewa tayi ta fita,ta fara shirye-shiryen daura abincin rana. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 13 Da yamma bayan mallam Amadi ya dawo daga kasuwa, inna ta kawo masa abincinsa yaci sannan ta kira masa Aunty hadiza. gaisawa sukayi suka dan taba hiransu xa 'yan uwan taka. Mallam Amadine ya fara mata bayani akan auren salma,bata ce komai ba se sanya alkhairi da tayima auren. yaji dadi sosai da yaga bata daga hankalinta ba. kamar yanda inna tayi,hakanne yasa ya daura da cewa dazu ALH. Abdul-Razak yazo kasuwa ya same ni, akan suna so a sa musu auren da wuri, dan haka na yanke musu nan da wata 1. se ku fara shirye-shirye. Ita dai Aunty hadiza bata ce komai ba tunda inna ta hanata magana amma abin ya bata mamaki ace aure wata daya, seka ce ana neman kai da yarinya koda yake aure lokacine idan lokacin yazo dole se anyi shi. Tashi tayi tayi musu sallama akan zata dawo washe gari su tsara yanda bikin zai kasance. 。 。 。 。 Lokaci yanata karatowa biki ya rage saura , salma tana shan gyara a wajen Aunty hadiza. Magunguna masu amfani take bata ba wanda zai mata illa a jiki ba. Gyara kam salma tasha shi, dan ita kanta tana jin canji ajikinta sosai. Dilka da halawa kullum se anzo anyi mata shi, bata fita ko ina, makarantar hadda ma ta dena zuwa. Tayi kyau tayi jajir abinka da farar mace duk inda tayi kamshine yake tashi, indai ta zauna a waje kamshinta yana dadewa kafin yabar wajen. Tun ranar da Abdul yazo be sake zuwa ba, har yau daya rage saura 2weeks biki. An kawo lefe na gani a fada. Akwati 12. kayan cikima kawai abin kallo ne. kai komai hassadan mutum idan yaga wannan lefen dole da rude. Aunty hadiza ne ta zaba mata wanda zatayi fitar biki dashi aka kai dinki. inna ta fidda kudin da take tarawa saboda auren salma. an siyo mata kayan kitchen da gara. anyi cincin din biki da dubulan,tawaita,alkaki,tsatstsafa,nakiya. An siya mata duk avinda akasan zata bukata.komai dai sunyi dai-dai karfinsu. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Yau dai nayi k'ok'ari nad'anyi muku da dan yawa kuyi hakuri da wannan. Nagode da addu'o'in ku gareni. Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 16 Yau asabar 11/12/2017 aka daura auren UMMU SALMA AHMAD DA ABDUL-AZEEZ ME DALA. Akan sadaki 100k.Daurin auren daya tara dubban mutane da manyan masu kudi da mukamai na NIGERIA. ba abinda kakeji se busan algaita da karan ganguna ana yima ango kirari. Ango kam yayi kyau ya hade cikin wani yadi milk kyau me tsadar gaske,fuskar sa sai fidda annuri take yi baza ka fahimci halin da yake ciki ba dan fuskar sa ba yabo ba fallasa. A can na hango HASSAN ATK yana gaisawa da ango yasha babban riga da 'yar ciki kai kace shine ma angon😁😁😁 Acikin gida kuwa ana daurawa anty hadiza ta sake guda, salma tana zaune a bakin gado tayi tagumi,tayi kwalliyarta cikin swiss lace red colour da ratsin blue and white.tasha sarkan gold da awarwaro ba karya tayi kyau sosai. Abokan wasanta sa'anninta suna gefe se tsokanarta sukeyi, da yake salma ita ba ma'abociyar kawaye bane indai ka ganta da kawa to 'yar uwanta ne. Yanzu ma su suka zame mata kawaye kowa a cikin su tasha ado se zuba kamshi suke yi. Aunty hadiza ne ta shigo tana fada musu akan sunce yanzu zasu zo su dauki amaryan su, saboda mahaifiyar A.A ta hada walima a gidanta. salma tana jin haka ta fashe da kuka. Rarrashinta aunty hadiza ta shigayi, inna ce ta shigo dakin ta zauna a gefen salma ta ruk'o hannunta ta fara mata nasiha. Salma nasan ke yarinya ce me biyayya da hakuri "ina so ki rik'e wannan a zaman auren ki" ki kasance me tsabta da rik'o da addini karki yadda mijinki ya shinshino wari a jikinki, ki kasance kullum cikin k'amshi. karki zamo me sa'insa da miji karki raina abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wanda ta girme ki, karki shiga harkan ta koda ta nemiki da fada. tsakaninki da kowa girmamawa, ki kasance me hak'uri a gidan mijinki, kiji kik'i ji, ki gani kik'i gani wannan ne zesa ki zauna lafiya a gidanki. ki zama me girmama 'yan uwan mijinki, karki yarda mijinki ya fahimci bakya son 'yan uwansa. ki kasance me gyara SHIMFIDAR MIJINKI (princess eyshat Aysm) A karshe ina miki nasiha da ki zama mace me yima mijinta Addu'a da rike sirrin mijinta, ki yawaita addu'a da kaima ALLAh kukanki, ki rik'e azkar safe da yamma insha ALLAhu zai zamo kariya a gareki. ALLAh yayi miki albarka, ALLAh yasa gidan zamanki ne πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™ AMEEN aunty hadiza ta amsa.Inna tadan goge kwallan daya taru mata, tace hadiza rakata wajen malam kafin su k'araso. Aunty hadiza ta ruko hannun salma da tunda aka fara mata nasiha take kuka harda sheshsheka suka fita. Kofar dakin mallam Amadi sukaje sukayi sallama ya amsa musu ya basu umurnin su shiga. Suka shiga suka nemi waje suka zauna. "Aunty hadiza tace yaya ga salma nan kayi mata nasiha sunce yanzu zasuzo daukan amaryan"Duban salma yayi wacce take kuka k'asa-k'asa yace "to salma menene abin kukan? keda za'a kaiki gidan da zaki huta" ba ruwanki da aikin wahala, to nidai abinda zance miki kawai shine kiyima mijinki biyayya, duk abinda yace miki karki yadda kiyi masa gardama. Karki sake ya kawo min k'aranki. in kuma kika bari ya kawo min k'aranki to wallahi ba abinda zai hana naje har gidan nayi miki shegen duka. Dan baza kiyi min bak'in cikin zuwa hajji wannan shekaran ba. Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu)Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu) Hadiza kamata kuje gashican naji ana neman amarya may be masu daukanta ne sukazo kar suyita jira. Maganar shice ta dawo da ita daga duniyar thinking data fada, kama salma salma tayi suka fice daga dakin ba tare da tace masa wani abu ba. Dakin inna saude ta maida ita,ta dauko mata make-up kit tace ta sake gyara fuskarta. Bayan tadan gyara, Aunty hadiza tadan yi mata nata nasihan sannan tace karki yadda ki zama bora a gidan mijinki, kuma karki sake kishiya ta raina ki duk yanda za'ayi kiyi domin juyo da hankalin mijinki gareki kuma ki dage da addu'a. insha ALLAhu se kinfi k'arfinta. ba abinda ta isa tayi miki. kuma................ bata kai ga fadan abinda take soba sukaji sallamar masu daukan amaryan har sun k'araso. Bayan sun shigo an gaggaisa Aunty hadiza ta rik'e hannun salma ta kaita wajen innarta sukayi sallama, sannan suka fito suka shishshiga motoci. salma se aikin kuka takeyi😭😭😭😭 tana bak'in cikin rabuwa da innarta😑😑😑. Gidan su A.A dake unguwar tambari estate suka nufa. Babban Gidane ya hadu iya haduwa tun daga get zakasan nera tayi kuka. dan ko a layin yafi ko wani gida kyau da tsaruwa. A haraban gidan motocin sukayi parking, fito da salma akayi wanda kanta yake lullube cikin mayafi aka nufi cikin gidan da ita. Wani hadadden falo naga an shiga wanda ban taba ganin irinsa a k'asar mu ta NIGERIA ba. se dai kasashen turawa. falo ne dayaji kujeru ash da baki ga chanise carpet da labulaye duk arsh da baki. ga k'atuwar plasma da home tiatre se aiki sukeyi kai gaskiya falon ya hudu. Daga kan da zanyi na hango wata hamshak'iyar mata daga ganinta jin dad'i da hutu sun samu zama a jikinta. Kyakykawa ce doguwa fara tana da d'an k'iba amma ba sosaiba. baza ta wuce 55years ba amma idan ka ganta zakayi zaton batafi 45years ba saboda yanayin hutu da take ciki. Hajiya Halimat me dala kenan uwargida a wajen Alh. Abdul razak me dala kuma mahaifiya Awajen A.A. Tana zaune tare da k'awayenta se murmushi take zubawa. Tasowa tayi cikin takunta na manyan mata ta k'araso ta rungume salma daka kalleta zakasan tana cikin farin ciki."well come to our family my daughter" ta fada tana murmushi, sannan ta jata suka zauna akan daya daga cikin kujerun da suke falon. Duk mutanen wajen ba wanda bata burgesu ba. wanda suka santa kam basuyi mamaki ba dan sun santa macece me son mutane bata da girman kai ko kadan. Su aunty hadiza waje suka nema suma suka zauna, bayan 'yan gaishe-gaishe suka damk'a musu amanar salma, suka ce sun kar6a da fatan Allah ya tayasu ruk'o. Agurguje Salma na hango an fito da ita daga wani daki tasha lufaya milk colour fuskarta tasha make-up, tayi kyau sosai. Haraban gidan suka nupa wanda aka k'awata su da kujeru saboda gudanar da walimah. Batare da bata lokaci ba malama juwairiyya ta fara gudanar da lecture bayan ta bude taro da addu'a. Tayi bayani akan hakkokin miji akan matar sa da kuma yanda mace zata tafiyar da rayuwar aurenta da dai sauran su. Bayan ta kammala ne aka rarraba bags wanda suke dauke da hoton ango da amarya a ciki akwai hankacif,memo,key holder,calender da juice kala-kala wanda suma suna dauke ne da pics din ango da amarya. se take away wanda akasa rabin kaza,donnut da meat pie. Ba'a tashi daga waliman ba se 5:00pm. Wani daki na musamman aka kai salma,wata budurwa naga ta shigo dakin wanda batafi 21years ba,kyakykyawa doguwa bata da jiki sosai black beauty sadiya Abubakar kenan (my namecy😜) wanda aka daukota tun daga sokoto domin tazo ta shirya salma zuwa wajen dinner. Toilet ta shiga ta hada ruwan wanka wanda yasha turaruka masu kamshi,ta fito ta umurci salma da ta shiga tayi wanka ta dauro alwala saboda lokacin sallar magriba ta k'arato.Bayan salma ta fito ta shafa mai se sady ta dauko make-up kit dinta ta fara tsantsara ma salma kwalliya. Wanda ya dauke su tsawan awa daya da rabi. MASHA ALLAH abinda ya fito daga bakina kenan lokacin danayi arba da fuskar salma. A gaskiya me karatu zanso kaga salma a lokacin.Indai ba farin sani kayi mata ba zeyi wuya ka shedata. nima dan na lab'e a lungun gado ne shiyasa har na ganeta.😜 Azuciyata kuwa nace anya A.A zai gane salma kuwa shida ko gama saninta ma beyi ba. muje zuwa 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Yau dai nayi k'ok'ari nad'anyi muku da dan yawa kuyi hakuri da wannan. Nagode da addu'o'in ku gareni. Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 16 Yau asabar 11/12/2017 aka daura auren UMMU SALMA AHMAD DA ABDUL-AZEEZ ME DALA. Akan sadaki 100k.Daurin auren daya tara dubban mutane da manyan masu kudi da mukamai na NIGERIA. ba abinda kakeji se busan algaita da karan ganguna ana yima ango kirari. Ango kam yayi kyau ya hade cikin wani yadi milk kyau me tsadar gaske,fuskar sa sai fidda annuri take yi baza ka fahimci halin da yake ciki ba dan fuskar sa ba yabo ba fallasa. A can na hango HASSAN ATK yana gaisawa da ango yasha babban riga da 'yar ciki kai kace shine ma angon😁😁😁 Acikin gida kuwa ana daurawa anty hadiza ta sake guda, salma tana zaune a bakin gado tayi tagumi,tayi kwalliyarta cikin swiss lace red colour da ratsin blue and white.tasha sarkan gold da awarwaro ba karya tayi kyau sosai. Abokan wasanta sa'anninta suna gefe se tsokanarta sukeyi, da yake salma ita ba ma'abociyar kawaye bane indai ka ganta da kawa to 'yar uwanta ne. Yanzu ma su suka zame mata kawaye kowa a cikin su tasha ado se zuba kamshi suke yi. Aunty hadiza ne ta shigo tana fada musu akan sunce yanzu zasu zo su dauki amaryan su, saboda mahaifiyar A.A ta hada walima a gidanta. salma tana jin haka ta fashe da kuka. Rarrashinta aunty hadiza ta shigayi, inna ce ta shigo dakin ta zauna a gefen salma ta ruk'o hannunta ta fara mata nasiha. Salma nasan ke yarinya ce me biyayya da hakuri "ina so ki rik'e wannan a zaman auren ki" ki kasance me tsabta da rik'o da addini karki yadda mijinki ya shinshino wari a jikinki, ki kasance kullum cikin k'amshi. karki zamo me sa'insa da miji karki raina abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wanda ta girme ki, karki shiga harkan ta koda ta nemiki da fada. tsakaninki da kowa girmamawa, ki kasance me hak'uri a gidan mijinki, kiji kik'i ji, ki gani kik'i gani wannan ne zesa ki zauna lafiya a gidanki. ki zama me girmama 'yan uwan mijinki, karki yarda mijinki ya fahimci bakya son 'yan uwansa. ki kasance me gyara SHIMFIDAR MIJINKI (princess eyshat Aysm) A karshe ina miki nasiha da ki zama mace me yima mijinta Addu'a da rike sirrin mijinta, ki yawaita addu'a da kaima ALLAh kukanki, ki rik'e azkar safe da yamma insha ALLAhu zai zamo kariya a gareki. ALLAh yayi miki albarka, ALLAh yasa gidan zamanki ne πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™ AMEEN aunty hadiza ta amsa.Inna tadan goge kwallan daya taru mata, tace hadiza rakata wajen malam kafin su k'araso. Aunty hadiza ta ruko hannun salma da tunda aka fara mata nasiha take kuka harda sheshsheka suka fita. Kofar dakin mallam Amadi sukaje sukayi sallama ya amsa musu ya basu umurnin su shiga. Suka shiga suka nemi waje suka zauna. "Aunty hadiza tace yaya ga salma nan kayi mata nasiha sunce yanzu zasuzo daukan amaryan"Duban salma yayi wacce take kuka k'asa-k'asa yace "to salma menene abin kukan? keda za'a kaiki gidan da zaki huta" ba ruwanki da aikin wahala, to nidai abinda zance miki kawai shine kiyima mijinki biyayya, duk abinda yace miki karki yadda kiyi masa gardama. Karki sake ya kawo min k'aranki. in kuma kika bari ya kawo min k'aranki to wallahi ba abinda zai hana naje har gidan nayi miki shegen duka. Dan baza kiyi min bak'in cikin zuwa hajji wannan shekaran ba. Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu)Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu) Hadiza kamata kuje gashican naji ana neman amarya may be masu daukanta ne sukazo kar suyita jira. Maganar shice ta dawo da ita daga duniyar thinking data fada, kama salma salma tayi suka fice daga dakin ba tare da tace masa wani abu ba. Dakin inna saude ta maida ita,ta dauko mata make-up kit tace ta sake gyara fuskarta. Bayan tadan gyara, Aunty hadiza tadan yi mata nata nasihan sannan tace karki yadda ki zama bora a gidan mijinki, kuma karki sake kishiya ta raina ki duk yanda za'ayi kiyi domin juyo da hankalin mijinki gareki kuma ki dage da addu'a. insha ALLAhu se kinfi k'arfinta. ba abinda ta isa tayi miki. kuma................ bata kai ga fadan abinda take soba sukaji sallamar masu daukan amaryan har sun k'araso. Bayan sun shigo an gaggaisa Aunty hadiza ta rik'e hannun salma ta kaita wajen innarta sukayi sallama, sannan suka fito suka shishshiga motoci. salma se aikin kuka takeyi😭😭😭😭 tana bak'in cikin rabuwa da innarta😑😑😑. Gidan su A.A dake unguwar tambari estate suka nufa. Babban Gidane ya hadu iya haduwa tun daga get zakasan nera tayi kuka. dan ko a layin yafi ko wani gida kyau da tsaruwa. A haraban gidan motocin sukayi parking, fito da salma akayi wanda kanta yake lullube cikin mayafi aka nufi cikin gidan da ita. Wani hadadden falo naga an shiga wanda ban taba ganin irinsa a k'asar mu ta NIGERIA ba. se dai kasashen turawa. falo ne dayaji kujeru ash da baki ga chanise carpet da labulaye duk arsh da baki. ga k'atuwar plasma da home tiatre se aiki sukeyi kai gaskiya falon ya hudu. Daga kan da zanyi na hango wata hamshak'iyar mata daga ganinta jin dad'i da hutu sun samu zama a jikinta. Kyakykawa ce doguwa fara tana da d'an k'iba amma ba sosaiba. baza ta wuce 55years ba amma idan ka ganta zakayi zaton batafi 45years ba saboda yanayin hutu da take ciki. Hajiya Halimat me dala kenan uwargida a wajen Alh. Abdul razak me dala kuma mahaifiya Awajen A.A. Tana zaune tare da k'awayenta se murmushi take zubawa. Tasowa tayi cikin takunta na manyan mata ta k'araso ta rungume salma daka kalleta zakasan tana cikin farin ciki."well come to our family my daughter" ta fada tana murmushi, sannan ta jata suka zauna akan daya daga cikin kujerun da suke falon. Duk mutanen wajen ba wanda bata burgesu ba. wanda suka santa kam basuyi mamaki ba dan sun santa macece me son mutane bata da girman kai ko kadan. Su aunty hadiza waje suka nema suma suka zauna, bayan 'yan gaishe-gaishe suka damk'a musu amanar salma, suka ce sun kar6a da fatan Allah ya tayasu ruk'o. Agurguje Salma na hango an fito da ita daga wani daki tasha lufaya milk colour fuskarta tasha make-up, tayi kyau sosai. Haraban gidan suka nupa wanda aka k'awata su da kujeru saboda gudanar da walimah. Batare da bata lokaci ba malama juwairiyya ta fara gudanar da lecture bayan ta bude taro da addu'a. Tayi bayani akan hakkokin miji akan matar sa da kuma yanda mace zata tafiyar da rayuwar aurenta da dai sauran su. Bayan ta kammala ne aka rarraba bags wanda suke dauke da hoton ango da amarya a ciki akwai hankacif,memo,key holder,calender da juice kala-kala wanda suma suna dauke ne da pics din ango da amarya. se take away wanda akasa rabin kaza,donnut da meat pie. Ba'a tashi daga waliman ba se 5:00pm. Wani daki na musamman aka kai salma,wata budurwa naga ta shigo dakin wanda batafi 21years ba,kyakykyawa doguwa bata da jiki sosai black beauty sadiya Abubakar kenan (my namecy😜) wanda aka daukota tun daga sokoto domin tazo ta shirya salma zuwa wajen dinner. Toilet ta shiga ta hada ruwan wanka wanda yasha turaruka masu kamshi,ta fito ta umurci salma da ta shiga tayi wanka ta dauro alwala saboda lokacin sallar magriba ta k'arato.Bayan salma ta fito ta shafa mai se sady ta dauko make-up kit dinta ta fara tsantsara ma salma kwalliya. Wanda ya dauke su tsawan awa daya da rabi. MASHA ALLAH abinda ya fito daga bakina kenan lokacin danayi arba da fuskar salma. A gaskiya me karatu zanso kaga salma a lokacin.Indai ba farin sani kayi mata ba zeyi wuya ka shedata. nima dan na lab'e a lungun gado ne shiyasa har na ganeta.😜 Azuciyata kuwa nace anya A.A zai gane salma kuwa shida ko gama saninta ma beyi ba. muje zuwa 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 14 Yau ya rage saura sati 1 biki gida ya fara cika da 'yan uwa na kusa da na nesa. sallama akayi aka ce wai ana sallama da salma. Aunty hadiza ce ta cema yaron kace tana zuwa, da yake yanzu kusan kullum se tazo saboda hidiman biki. salma kije ana sallama dake a waje aunty hadiza tace, tashi salma tayi ta dauki hijabinta tayi hanyar waje,kiranta aunty hadiza tayi, kina nufin haka zaki fita wai? ko kwalliya bakiyi ba bare ki fesa turare? maza jeki shafa ko hoda ce ki goga jan baki ki fesa turare. tura baki salma tayi sannan ta koma daki ta danyi make up ta fesa turare ta fito. Har lokacin aunty hadiza tana tsaye a wajen data barta, to ko kefa ta fada tana murmushi da zaki fita kamar ba amarya ba,zakije wajen miji fuska farau-farau ba kwalliya. ko kulata salma batayi ba ta fita ta barta tana ci gaba da maganar ta. A jingine a jikin mota ta hango su, wannan karon su 2 suka zo, shida wani saurayi kamar shi black beauty dagani zeyi saukin kai dan fuskar shi cike take da murmushi. ba kamar A A ba daya hada rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa. Tun da ta fito yake kallonta yana kare mata kallo, ba lefi tayi mishi kyau se dai fa shi kowacce mace bata burge shi inba matarsa humaira ba. Sallamarta ne ya dawo dashi daga tunanin daya fada. kauda kai yayi se abokin sane ya amsa sallamar. Gaisawa sukayi sannan yace hajiya salma nasan baki sanni ba, sunana SALEEM nine babban abokin Abdul. Munzo ne domin muji irin shirye-shiryen da kuke yi. seki fada mana event nawa zakiyi da yawan kudin dazai isheki se mu baki. cikin sanyin muryanta ta ce ba abinda zanyi kuma bana bukatar komai.tokai kaji abokina, ta yaya za'ace amarya bata bukatar komai? ai bazai yuwuba. ko kallon shi A A beyi ba balle ya nuna yaji abinda yake fada. dan tsaki saleem yaja sannan ya maida kallon shi gun salma yace to mu ta bangaren mu akwai dinner da muka shirya bayan ankai amarya karfe 8:30pm. Ina fatan ba matsala? Gyada mishi kai kawai tayi duk da a ranta bata so hakan ba, bude mota saleem yayi ya fito da wani leda tare da emvelop ga wannan kayan shi zaki sa a wajen dinner. wannan kuma ki rike a wajenki saboda hidiman biki duk da kince bazakiyi komai ba 500k ne ba yawa. dan rusunawa salma tayi ta karba sannan tayi masa godiya. Murmushi saleem yayi mata dan ba karamin burgeshi tayi ba, bakomai amaryar mu ya fada sannan ya dubi A A ko akwai wani abin da ban fada ba? kauda kansa yayi cike da jinkai yace idan ka gama surutun zamu iya tafiya. ya fada tare da shigewa mota Murmushi saleem yayi danshi ya saba da halin Abdul,mutum ne wanda baya son hayaniya se kayi magana goma be amsa maka daya ba. shiyasa baya damuwa da duk abinda zeyi masa saboda yasan halinsa in and out. Tun suna yara suke tare kasan cewar iyayen su aminan juna ne. ko sunyi fada a lokacin suke shiryawa To amaryar mu, mu zamu tafi se munzo daukan ki nan da sati. godiya salma tayi masa tare da juyawa ta shiga gida suma sukaja motar su suka tafi. salma tana shiga ta mikawa aunty hadiza ledan da kuma emvelop din, bude ledan tayi taga kayane a ciki. wani hadadden material ne purple colour da ratsin fari anyi masa dinkin doguwar riga. se farin takalmi hill da farin poss, se head purple da kuma sarka da dan kunne fashion purple da fari. wannan kayan fa? aunty hadiza ta tambaya, bayani salma tayi mata. aikuwa kudinnan se dai a bude miki account a saka miki. bari na kaima innarki ta ajiye zuwa a gama biki se akai banki. WAI WAYE A A ne??? ku biyo ni a next page domin muji cikekken tarihin A A me dala 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 *ZAB'IN MAHAIFINA* 🌳🌳🌳🌳🌳 Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)* Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM* _AYSHA BICHIKI_ Page 15 Ina jin dadin yawan comment dinku da nake gani, nagode sosai ALLah ya bar kauna. WANENE AA ME DALA?? ABDUL-AZEEZ ABDUL-RAZAK ME DALA shine cikekken sunanshi, mahaifinsa Alh. Abdul-razak me kudine na gaske yana da kamfanin saida motoci har guda uku bayan haka kuma dan kasuwa ne sosai. Abdul saurayine meji da kansa ga kyau ga nera uwa uba ilimin boko da arabic. yayi karatunsa har zuwa matakin masters akan business. Abdul mutum ne miskilin gaske, danshi mutum ne da baya son hayaniya. Idan kaga yanda mata suke binshi abin zai baka mamaki,amma ko kallo basu isheshi ba. Shikadai ne da namiji agun iyayensa,shine first born sai kannen shi mata guda uku Hafsat,Amina da ummul khairi. Sun samu tarbiyya a gurin iyayen su, kasancewar su masu arziki hakan besa sun sangarta su ba. Abdul sun hadu da matar sa humaira ne a wani super market,sunje shopping shida abokinsa Saleem. tunda ta ganshi ta rikice akansa amma shi ko kallo bata ishe shi ba. hakanne yasa tabi duk hanyar da tasan zata jawo hankalin shi gareta kasan cewarta mace me budadden ido dan gidansu 'yan boko ne ita kadaice 'ya awajen iyayenta. ko kadan iyayenta ba ruwansu da irin rayuwar da take yi dan ko zata kwana a wajene ba wanda zai tambayeta dalili. wannan ne ya bata damar sheke ayanta yanda take so. dan gidan malamai ba wanda bata sani ba, idan dai taga kayi mata yanzu zata kai sunanka gun malaminta a mallake mata zuciyar ka. Hakanne ta kasance lokacin da taga A A. tunda taga alamun dan jin kaine taje ta sanar da malaminta akayi mata aiki a kansa. Aikuwa aiki yayi kyau dan a hakane ta samu har ta aure shi. iyayensa basuso auren ba kasancewar ta me karancin tarbiyya, amma ba yanda suka iya tunda ya dage akan yana sonta a haka, se dai kawai suka ci gaba dayi masa addu'a. Bayan anyi auren ne ta fara fiddo da asalin halayyarta, ko sau 1 bata taba daga waya ta kira iyayen mijinta ba domin ta gaishe su,ballantana ta taka da kafarta taje har gida. koda kannensa sunzo bata bari su ganshi,se dai tace musu bayanan. daga karshe ma zuwa tayi ta samu me gadi akan ko sunzo kar ya yadda ya barsu su shigo gidan, duk randa ya barsu to abakin aikinsa. Abdul mutum ne me son iyayensa da 'yan uwansa, hakan ne tasa suka fara samun sabani da ita. Wata rana da yayi mata maganar ta shirya suje su gaida iyayensa aikuwa ta rufe ido tace ba inda zataje. ranar taga bacin ran da bata taba gani tare da shi ba dan ce mata yayi indai bata je ba to saidai ta tafi gidansu. Badan ranta yaso ba ta bishi suka tafi. Ganin hakan da yayi mata yasa ta koma gun malaminta aka hana shi zuwa wajen iyayen shi, a cewarta tunda akansu ne yace taje gidansu to suma seta rabashi da su. Indai kaga yaje wajen su to se dai ya saci hanya ba tare da tasani ba Wani zuwa da yayi ne mahaifiyar sa take yi masa maganar karin aure,tunda shekaransu 5 da matar sa amma bata taba koda batan wata ba. ce mata yayi baida matar da zai aura se dai su zaba mishi kasan cewar sa mutum ne me biyayya, abinda basu sani ba humaira bawai haihuwa ne batayi ba, ta samu ciki har sau 2 tana zubarwa dan tace bata shirya haihuwa yanzu ba. Aikuwa yasha albarka a wajen iyayensa. hakanne yasa suka aura masa 'yar kanwar Alh. Abdul-razak. kwata-kwata auren be wuce 2 month ba ya rabu da ita. Bayan ita seda suka aura masa mata har guda 3,duk yana rabuwa da su. ta karshen kamma da hauka tabar gidan. saboda taso ta basu wahala kasancewarta ma'abociyar karatun al-qur'ani me girma. hakanne yasa tace kawai a haukatar da ita bokan yace gaskiya shi bazai iya ba, se dai a bari lokacin da bata da tsarki, Wannan ne dalilin dayasa ta samu galaba akanta. Tun daga lokacin basu sake aura masa wata ba dan ko sunje ba'a basu. To a wannan karonne aka dace da mahaifinsa yazo wajen mallam Amadi nema masa auren salma,shikuma ya amince, saboda son abin duniya yajefa rayuwar 'yarsa a halaka. yanzu labarin zai fara kudai ku biyo ni domin jin abinda zai faru nan gaba 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI page 17 Bayan sady ta gama mata make-up din salma ta saka hijab d'inta tayi sallar magriba dan lokacinsa harya kusa fita, tana idarwa aka kira isha'i. Tashi tayi ta yi sallar isha'i. Bayan ta idar tayi addu'o'inta aka shiryata cikin doguwar rigan material fitted gawn, wanda A.A suka kawo mata akan tasa ranar dinner. tasaka mahadin kayan ta fesa turare. Gaskiya salma tayi kyau dan kuwa my namecy taci kudinta, inso samune ayi mata k'ari😜.dan ta'iya shirya amare. Hajiya halimat ce tayi sallama ta shigo dakin. waw! my daughter kinyi kyau sosai,ta kai dubanta ga sady tace gaskiya takwara kin iya tsara kwalliya,ai wannan indai baka santa ba baza ka iya ganeta bama. Lallai kina da kyauta me tsoka tunda kika sa daughter tayi kyau haka. Ita kuma sady jin an yabeta ne yasa ta fara magana cike da iyayi,ai hajiya inayi fiye da hakama. murmushi Hajiya halimat tayi ta kama hannun salma suka nufi falo. Kawayen amarya na zaune sunyi kwalliyar su cikin lace orange da touch din blue a jiki, se suka saka head blue suma sunyi kyau ba lefi. Har bakin mota hajiya halimat takai salma, wata had'ad'd'iyar mota naga ta bud'e ta saka salma a ciki, galases din motar tint ne baka iya hango wanda yake ciki. ta dubi saleem dake zaune a gaban motar tace ga amanar 'yata,kar ku bari wani abu ya tab'a min ita dan kunsan bazan bari ba. Sake juyowa tayi ta kalli A.A wanda ke zaune a bayan motar. yana sanye da shadda purple colour anyi design fari a gaban rigan, ya saka farin hula da farin takalmi se agogo silver colour. Shima yayi kyau sosai a takaice dai sunyi anko ne da salma. Ya hade fuskarnan kanshi yana kasa yana daddana waya be ko nuna alamun yasan da zaman mutane a wajen ba. Girgiza kai kawai tayi ta rufe motar ta juya ta koma cikin gida. Bayan k'awaye da sauran mutane sun shishshiga mota ne, motoci suka fara tafiya suka nufi hanyar da zata kaisu "ME SANDA GREEN GARDEN" sbd acan zasu gudanar da dinner. Tafiya akeyi amma ba wanda yayima dan uwansa magana. Salma kanta yana k'asa tana wasa da zoben azurfan dake hannunta shikuma ya maida hankali wajen danna waya ko me yake dannawa oho. Da saleem yaji shirun yayi yawa ne yayi magana"amaryan mu yau ba gaisuwa ne?" murmushi salma tayi ta dago kanta ta kalle shi ta cikin mirro tace ina wuni yaya saleem. Lafiya lau ya amsa mata cike da jindadin girmama shi da tayi. Ya hidiman biki? Alhmdlh! ta amsa. Duk abinda sukeyi A.A be ko d'ago kanshi ba balle ya tanka musu. Ba wanda ya sake magana har aka k'arasa wajen. Bayan motocin sun gama parking mutane suka fiffito suka nufi cikin hall din. Juyowa salim yayi ya kalli A.A yace Friend dan ALLAh karka fita ku d'an jira ayi arranging din k'awayen,πŸ™πŸ™πŸ™ be d'ago ba balle ya amsa masa. Bayan fitan saleem ne ya d'an juyo da kansa ya kalli salma da kanta yake k'asa, zuba mata ido yayi gabansa yana faduwa ya rasa dalilin dayasa idan ya kalli yarinyar se yaji faduwan gaba. A gaskiya tayi mishi kyau sosai, daman haka take da kyau? duk da mata basa gabansa amma ya tabbatar wa kansa wannan ta dabance. dan tana da wani sirrin kyau wanda mutum bazai saniba d idan yana tare da ita ga wani kwarjini da tayi masa. Besan lokacin daya saki murmushi ba, adai-dai lokacinne salma ta d'ago da kanta dan taji a jikinta kamar ana kallonta. Suna had'a ido ya d'auke kansa ya murtuk'e fuska kamar be tab'a dariya ba. Kallonsa kawai salma takeyi tana mamakin halinsa mutum se miskilancin tsiya, gashi dai ta kama shi yana kallonta amma ya kauda kai kamar bashi ba. Dani kake zance zakama dawo kan hanya indai nice ta fad'a a zuciyar ta. muje zuwa 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:35PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI page 17 Bayan sady ta gama mata make-up din salma ta saka hijab d'inta tayi sallar magriba dan lokacinsa harya kusa fita, tana idarwa aka kira isha'i. Tashi tayi ta yi sallar isha'i. Bayan ta idar tayi addu'o'inta aka shiryata cikin doguwar rigan material fitted gawn, wanda A.A suka kawo mata akan tasa ranar dinner. tasaka mahadin kayan ta fesa turare. Gaskiya salma tayi kyau dan kuwa my namecy taci kudinta, inso samune ayi mata k'ari😜.dan ta'iya shirya amare. Hajiya halimat ce tayi sallama ta shigo dakin. waw! my daughter kinyi kyau sosai,ta kai dubanta ga sady tace gaskiya takwara kin iya tsara kwalliya,ai wannan indai baka santa ba baza ka iya ganeta bama. Lallai kina da kyauta me tsoka tunda kika sa daughter tayi kyau haka. Ita kuma sady jin an yabeta ne yasa ta fara magana cike da iyayi,ai hajiya inayi fiye da hakama. murmushi Hajiya halimat tayi ta kama hannun salma suka nufi falo. Kawayen amarya na zaune sunyi kwalliyar su cikin lace orange da touch din blue a jiki, se suka saka head blue suma sunyi kyau ba lefi. Har bakin mota hajiya halimat takai salma, wata had'ad'd'iyar mota naga ta bud'e ta saka salma a ciki, galases din motar tint ne baka iya hango wanda yake ciki. ta dubi saleem dake zaune a gaban motar tace ga amanar 'yata,kar ku bari wani abu ya tab'a min ita dan kunsan bazan bari ba. Sake juyowa tayi ta kalli A.A wanda ke zaune a bayan motar. yana sanye da shadda purple colour anyi design fari a gaban rigan, ya saka farin hula da farin takalmi se agogo silver colour. Shima yayi kyau sosai a takaice dai sunyi anko ne da salma. Ya hade fuskarnan kanshi yana kasa yana daddana waya be ko nuna alamun yasan da zaman mutane a wajen ba. Girgiza kai kawai tayi ta rufe motar ta juya ta koma cikin gida. Bayan k'awaye da sauran mutane sun shishshiga mota ne, motoci suka fara tafiya suka nufi hanyar da zata kaisu "ME SANDA GREEN GARDEN" sbd acan zasu gudanar da dinner. Tafiya akeyi amma ba wanda yayima dan uwansa magana. Salma kanta yana k'asa tana wasa da zoben azurfan dake hannunta shikuma ya maida hankali wajen danna waya ko me yake dannawa oho. Da saleem yaji shirun yayi yawa ne yayi magana"amaryan mu yau ba gaisuwa ne?" murmushi salma tayi ta dago kanta ta kalle shi ta cikin mirro tace ina wuni yaya saleem. Lafiya lau ya amsa mata cike da jindadin girmama shi da tayi. Ya hidiman biki? Alhmdlh! ta amsa. Duk abinda sukeyi A.A be ko d'ago kanshi ba balle ya tanka musu. Ba wanda ya sake magana har aka k'arasa wajen. Bayan motocin sun gama parking mutane suka fiffito suka nufi cikin hall din. Juyowa salim yayi ya kalli A.A yace Friend dan ALLAh karka fita ku d'an jira ayi arranging din k'awayen,πŸ™πŸ™πŸ™ be d'ago ba balle ya amsa masa. Bayan fitan saleem ne ya d'an juyo da kansa ya kalli salma da kanta yake k'asa, zuba mata ido yayi gabansa yana faduwa ya rasa dalilin dayasa idan ya kalli yarinyar se yaji faduwan gaba. A gaskiya tayi mishi kyau sosai, daman haka take da kyau? duk da mata basa gabansa amma ya tabbatar wa kansa wannan ta dabance. dan tana da wani sirrin kyau wanda mutum bazai saniba d idan yana tare da ita ga wani kwarjini da tayi masa. Besan lokacin daya saki murmushi ba, adai-dai lokacinne salma ta d'ago da kanta dan taji a jikinta kamar ana kallonta. Suna had'a ido ya d'auke kansa ya murtuk'e fuska kamar be tab'a dariya ba. Kallonsa kawai salma takeyi tana mamakin halinsa mutum se miskilancin tsiya, gashi dai ta kama shi yana kallonta amma ya kauda kai kamar bashi ba. Dani kake zance zakama dawo kan hanya indai nice ta fad'a a zuciyar ta. muje zuwa 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 18 Wannan shafin nakine ke kadai UMMU LAILA. kiyi yanda kike so dashi, Nagode da k'aunar ki gareni ALLAh ya bar Zumunci🀝 Bude murfin motan akayi ta gefen salma,aunty hadiza ce ta fito da ita. Shima A.A ya bud'e ya fito K'awayen amarya ne da abokanan ango suna tsatstsaye. Salma da A.A suka shiga tsakiya aka nufi cikin hall din abokai da k'awaye suna watsa musu flower. Tun daga wajen hall din kake jin kid'a yana tashi. D.J ya bada sanarwan shigowan ango da amarya, duk wanda suke cikin hall din suka mimmik'e. Saida sukaje suka zauna sannan mutanen suka zazzauna. Bayannan D.J ya tashi yayima ango da amarya barka da zuwa. Aka nemi abokin ango da k'awar amarya suzo su bada tarihin ango dana amarya. Saleem ne ya tashi ya bada na ango, wata 'yar uwar salma tazo itama ta bayar. Bayan sun koma sun zauna aka umurci ango yazo ya yanka cake shida amaryar sa. Ruk'o hannun salma A.A yayi,da sauri ta dube shi ko kallonta beyi ba ya mik'e tsaye,dole tasa itama ta tashi suka je wajen da zasu yanka cake din. kid'a aka sake cikin wak'ar nura m inuwa wanda yayi musu na bikin. Cake d'in me hawa uku ne, an rubuta sunayesu a jiki. hannunta da nashi suka had'a suka yanka, nan hall d'in yad'au tafi. ya d'auka yasa mata a baki cikin jin kunya ta karb'a itama ta yanka ta bashi. Bawanda zai gansu yayi zaton ba masoya bane se dai idan ka sani, juyawa sukayi suka koma wajen zansu. Nan akaci gaba da gudanar da taron yanda ya kamata, anci ansha an goge wuya. Wajen diban abinci ne na hango 'yan group d'in just hausa novels da 'yan group din princess eyshat Aysm da 'yan group d'in ummun sadiq novels se ture-ture sukeyi kowa yana son ya cika timbinsa.πŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ˜ƒ Bayan an tashi daga taron aka maida salma gidansu A.A ita da k'awayenta dan acan zata zauna har agama bikin. Washe gari ya kama yini tun safe sady tasa salma tayi wanka dan tanason tayi mata kwalliyar datafi ta jiya. Aikuwa ta tsara mata dan har taso tafi jiya kyau, tayi shigar jan atamfar sufer wax da ratsin green a jiki. ta saka sark'an diamond da abin hannunsa. Anyi wunin biki lafiya sunyi hotuna se fatan ALLAh ya bada zaman lafiya. Da daddare bayan mutane sun watse angwaye sun sallami k'awaye kowa ta tafi. Salma tana zaune a kan kujera a dakin hajiya halimat, Aunty hadiza ta shigo ta sameta, to salma nizan tafi tunda ance ba yau za'a kaiki ba,in yaso gobe zan dawo ina fatan babu matsala??? girgiza kai salma tayi idonta ya cuko da hawaye tace bakomai aunty ki gaida min da innata. murmushi Aunty hadiza kawai tayi sannan tayi mata sallama ta tafi. A gurguje mahaifiyar A.A ce ta shigo ta sami salma a zaune tayi tagumi. zama tayi kusa da ita ta janye hannun tace, ki dena damuwa daughter ki daukeni kamar mahaifiyar ki, duk abinda yake damunki ki sanar dani karkiji kunyata kinji? gyada mata kai salma tayi, yanzu ki tashi kije ki kwanta kinga dare yayi. Ta ruk'o hannun salma ta kaita bakin gado tace ta kwanta, ta lullub'a mata bargo kasancewar lokacin sanyi ne, ta kashe mata wuta ta fita ta nufi d'akin me gidanta. ASUBA TA GARI SAL-AZEEZ. Washe gari bayan sunyi breakfast, salma tayi wanka sady tayi mata make-up kasancewar itama a ranar zata koma garinsu sokoto dan aikinta ya k'are. Salma ta shirya cikin shadda light brown d'inkin doguwar riga yasha aiki, ta yapa gyale dark brown tasa takalminta flat shima dark brown. k'arfe 11:00am Aunty hadiza ta iso ita da wata k'anwar inna saude Aunty Asma'u. Bayan an gaggaisa hajiya halimat takai salma falon Alh. Abdul-razak me dala domin su gaisa dan tunda tazo basu had'u ba saboda sha'anin biki. Kanta a k'asa ta durk'usa a gefe cikin jin kunya ta gaida shi, fuskar sa d'auke da murmushi ya amsa mata, sannan ya d'anyi mata nasiha. Ya mik'a ma hajiya halimata emvelop ki bata wannan ATM ne dana bud'e mata account saboda idan tana buk'atar kud'i ba saita tambaya ba, yanzu haka akwai kudin dana zuba a ciki 1million naira, zan dunga tura mata 500k duk wata insha ALLAhu. Godiya sosai salma tayi mishi tana jinjina karamci irin nasu. Hajia halimat ta ruk'o hannun salma suka fito daga falon, suka iske su Aunty hadiza suna jiransu, gyalenta ta d'auko dan tace harda ita za'a raka salma gidanta 'ya'yanta mata se tsokananta sukeyi, kowacce tana rataye da jakanta kowa zata koma gidan mijinta tunda an gama bikin. Motoci suka shishshiga Aunty hadiza da Aunty asma'u suna cikin mota d'aya, se hajiya halimat da salma suma suna 1 dukkansu driver ne yake jansu. Wanr had'ad'd'en gida naga sun nufa dake cikin G.R.A(sir kashim) bud'e musu get me gadi yayi saboda besan amarya bane, dan tun jiya matar gidan tayi masa warning akan karya yadda ya barsu su shiga. Bayan motocin sunyi parking a haraban gidan, suka fiffito salma bakinta d'auke da addu'an neman tsari ta fito da k'afar dama, gabanta se calugude yakeyi. da gudu me gadi ya k'araso daya fahimci su wanene su. dan Allah hajia kuyi hakuri wallahi tace min karna barku ku shigo,in kuma na barku to a bakin aikina ya fad'a yana durk'usawa. kallonsa hajia halimat tayi tace ka kwantar da hankalinka mallam musa ba wanda ya isa ya rabaka da aikinka, Nan take ya fara murmushi dan yaga kamanninta da me gidan ya tabbatar mahaifiyasa ce, godiya yayi mata sannan ya koma bakin aikinsa. Ita kuwa hajiya halimat dama dalilin zuwanta gidan kenan, dan ta tabbatar za'ayi hakan. Cikin gidan suka shiga, gidan flat ne baida girma sosai amma ya tsaru. idan ka shiga zaka tarar da babban falo wanda yasha had'ad'd'un kujeru seti 2, brown da milk, se labulaye da chanise carpe da t.v plasma babba. a can gefe kuma dining room ne an k'awata shi da dining table da kujeru. Akwai k'ofofi guda 2 a cikin falon left and right. kowani kofa yana d'auke falo madaidaici da 2 bedroom da toilet, se kuma kitchen wanda yake d'auke da store aciki. Akwai babban kitchen ta baya wanda yake kusa da BQ da alama a ciki masu aiki suke girki. D'aki 1 na uwargida humaira ce, d'ayan kuma na A.A ne wanda yanzu ya barma salma shikuma ya koma d'akin gimbiya humaira. Gidan dai-dai zaman mata d'ayane ita da mijinta, dan basu dad'e da komawa gidan ba. Basu samu kowa a falon ba da alama masu gidan har lokacin basu tashi ba. Aunty hadiza ce ta ska key ta bud'e dakin dake mazaunin na salma suka shiga. Gaskiya d'akin ya tsaru readers na barku ku wassafo yanda d'akin yake basai nayi muku bayani ba. Dad'a gyara ko ina sukayi sannan Aunty hadiza taja hannun salma d'aki suka d'anyi maganganunsu ta bata shawaran yanda zata zauna da kishiyarta, karta yarda taji tsoronta, ta fiddo da hisnul muslim a jakarta ta bata, tace ta dage da addu'a. ta kuma yi k'ok'arin juyo da hankalin mijinta gareta. suka fito sukayi musu sallama dan ita hajia halimat tace ba yanzu zata tafiba se tayima matarsa warning akan salma. to kunji pa readers koya zata kasance ko biyo ni. Bayan su Aunty hadiza sun tafine suma suka fito babban falo suka zaunag Hajiya ta dubi salma tace daughter ki dage da addu'a pa da kuma azumin litinin da alhamis, kin riga kinsan komai ba sena fad'a miki ba. K'arar bud'e k'ofa sukaji A.A ne ya fara fitowa bayansa humaira ce tasha riga da skirt na lace golden sun matseta kanta ba d'ankwali se kitson attach da ya zubo mata har baya, ba lefi tana da kyau amma bata kama k'afar salma ba. Ido hud'u sukayi da mahaifiyar sa da sauri ya k'araso cikin falon yana murmushi. Zama yayi akan kujera sannan yace "Gud morning cwt Mom ai bansan kinzo ba" itama murmushin tayi dan taji dad'in ganin d'an nata dan rabonta dashi tun ranar dinner. Gud mornin son da fatan na same ku lafiya?? ko kad'an bata nuna masa b'acin ranta ba dan tasan bayin kansa bane. lafiya lau ya amsa mata. Se alokacin humaira ta k'arasa shigowa falon dan mutuwar tsaye tayi da ta gansu, batayi tsammanin ganin hajiyar ba saboda bata tab'a zuwa gidan su ba, bayan hakama ai tayi wa get man warning,wato bejiba seda ya bud'e musu aikuwa yayima aikinsa. ta fad'a a cikin zuciyarta. Akan kujera ta zauna 1 seater ta gaida hajiyar ta amsa mata ba yabo ba fallasa. idonta ta kai kan salma wanda ko kallo basu isheta ba balle ta gaishe su. Gabantane yayi mugun fad'uwa ganin tsantsar kyau irin na salma tunda ake mata kishiya ba'a tab'a mata me kyau da kwarjini kamar salma ba. Hajia halimat tayi musu nasiha sannan tace "Abdul ga salma nida kaina na kawo maka ita inaso kayi adalci ban yarda ko bayan raina ka rabu da ita ba, kasani duk randa kasake ta to wallahi seka saki wannan matar taka" kuma ina so yanzu ka raba musu kwana. idan ka gama 7days dinka a dakin salma se su fara raba kwanakin. Ba tare daya kalli humaira ba yace ya raba kwana bibbiyu. Iyakan b'acin rai humaira takai, lallai wannan matar wato tanan ta b'ullo ai kuwa intasan wata batasan wata ba. Matsalan da take samu 1 ne duk yanda takai ga son ta raba Abdul da iyayensa ta kasa. danta kasa cire masa sonsu a zuciyar sa, ta waje d'aya ta samu nasara data hanashi zuwa gidan se dai yaje a b'oye ba tare data sani ba. Kuma indai zasu bashi umurni to seya aikata ko ita bata isa hanashi yi ba. Amma ta mallake shi yanda take so, duk abinda taga dama shi za'ayi. mik'ewa hajia tayi ta ruk'o hannun salma tace toni zan tafi. Mik'ewa A.A yayi dan ya rakata amma ta dakatar dashi,kayi zamanka nagode. Jiki a sanyaye ya koma ya zauna ALLAh yasa badai fushi Momynsa tayi dashi ba. Har takai bakin k'ofa zata fita ta juyo tace maganar malam musa me gadi ban yarda a canja shi ba. Da hanzari ya amsa mata, duk miskilancin A.A baya yima iyayenshi saboda baya k'aunar b'acin ransu. Aikuwa nan humaira ta dad'a cika dan tasan bata isa tayi masa komai ba tunda wannan tsohuwar ta hana. Fuuuu... ta mik'e ta shige daki cikin tsanin b'acin rai. da kallo kawai ya bita ba tare da yace mata komai ba. Kai aradu nagaji wanga typing ya ban wuya, har ya cinye min chaji kowa wamin karo-karo. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 19 Wannan page d'in nakine takwarata Sadiya Abubakar ina yinki irin sosai d'innan ALLAh ya barmu tare k'awataβ€πŸ’“β£πŸ’•πŸ’ž Suna isa bakin mota hajiya ta mik'ama salma emvelop d'in da Alh. Abdul-razak ya bata, sannan tace ki dinga yin girkin ki da kanki karki yadda akawo miki wani abu kici,zuwa gobe zan turo miki da yarinya wanda zata rik'a yi miki aiki, Cikin girmamawa salma ta amsa sukayi sallama hajia halimat ta shiga mota driver yaja suka tafi,salma kuma ta juya ta shiga ciki tana shiga ta wuce d'akinta ko kallon A.A dake zaune a falon batayi ba. Ita kuma humaira tana shiga d'akinta ta fashe da kuka tana tsinema hajia halimat. "Wlh bazai tab'a yuwuwa ba koda zanyi yawo tsirara se yarinyarnan tabar gidannan, wata zuciyar tace kin manta tace idan har ya saketa kema zakibar gidan. tsaki tayi tace aikuwa da alama ajalinta yazo dan kuwa bazan tab'a bari ta zauna min a cikin gidana ba. (kuji fa jama'a kamar ita ta gina gidan da kud'intaπŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ˜ƒ) Waya ta d'auko tayi dialing wani number, can aka d'auka hellow humy kina lafiya? aka fad'a daga d'aya b'angaren, ina fa lafiya lina wancan shegiyar tsohuwan yanzunnan tabar gidannan, wata tsohuwa? lina ta tambaya. Mahaifiyar Abdul mana, to me tazoyi? lina ta sake tambaya. Waita kawo masa amarya, wani uban ashar lina ta sake sannan tace ki jirani ganinan zuwa wallahi seta raina kanta. To kiyi sauri dan ALLAh humaira tace sannan ta kashe wayarta. ta nemi bakin gado ta zauna, bata dad'e dazama ba lina ta shigo cikin d'amammun kaya riga da wando, kanta ba ko d'an kwali se wani siririn gyale data yafa a kafad'a. tana shiga suka rungume juna, ke ina amaryan take? lina ta tambaya, tana d'akinta, to tashi muje muci uwarta, zatasan ta shigo gidan bala'i. Basu sami A.A a falon ba da alama ya bar gidan. ko neman izini basuyi ba suka cusa kai cikin falon salma, salma tana zaune ta sake wanka ta had'e cikin riga da skert na atamfa, d'inkin ya kamata ya fiddo da shape d'inta, kanta ba d'an kwali se gashinta da tayi parking wanda yasha gyara ya sauk'o mata har gadon bayanta. Plat ne a hannunta tana cin abinci da alama girki tayi. ba humaira ba hatta da lina se da ta raina kwalliyarta dan humaira irin siraran matannan ne wanda basu da k'iba ko kad'an se dai kyau a fuska, dama dama lina tana k'iba se dai bata da shape ko kad'an, sukub take kamar namiji. kallo d'aya tayi musu ta d'auke kanta kamar bata san da mutane a wajenba. Kallon juna su humaira sukayi da alama wannan ba kamar wanda aka saba kawo musu bane. Lina ce tayi k'arfin halin zuwa ta tsaya akan salma tace ke inason yanzu-yanzu ki tattara kayanki kibar gidannan, in har kina son tsira da ranki da kuma lafiyar ki. Kallonta salma tayi up and dawn sannan tace a matsayinki nawa kike bani umurni? mijina ko iyayena ne kad'ai suke da ikon bani umurni nabi amma ba ke ba. ke barima kiji ko megidannan duk da zaman shi nakeyi to shima be isa yace nabar gidannan ba. shi me gidan be fad'a miki cewa nice nake da iko da gidan da abinda yake cikinta ba? ko shi a k'ark'ashin ikona yake kinga kuwa se yanda nayi dashi, humaira ta fad'a tana k'arasowa cikin falon. Murmushi salma tayi tace idan su kina iko dasu to nikam baki isa kiyi iko dani ba wallahi dan nafi k'arfinki. Nunata humaira tayi da yatsa tace wallahi ke baki isa kizo har gidana kice zaki yimin rashin kunya ba, kodan kinga tun farko na k'yaleki banyi maganin ki ba, to ki kiyaye harshen ki tun kafin ki had'u da mummunan sakamako. Mik'ewa salma tayi tace don't point your pinger at me or else... "me zaki iyayi? humaira ta katseta tana huci" Duk randa kika sake nuna min yatsa wallahi sena karyashi, kuma da kike cewa ina miki rashin kunya ai kece baki rik'e girman ki ba. kuma baki isa kiyimin komaiba se abinda ALLAh ya k'addaro min. sannan ta nuna musu kofa, ku fice min daga falo yanzu ko kuma na nuna miki abinda zan'iyayi yanzu. Tsaki humaira tayi tace wallahi salma se naga bayanki ki rubuta ki ajiye dan ni kad'ai akayi Abdul kuma dani kad'ai zeyi tarayya babu wata 'ya macen da ta isa ta zauna a matsayin matar sa bayan ni, sannan ta ruk'o hannun lina wanda ta kasa magana suka bar falon dan taga alamar salma bata da mutunci. suna fita salma taje tasama kofarta key ta dawo ta zauna taci gaba dacin abincinta,tana mamakin kanta yanda ta iya sa'insa da humaira ba tare da taji tsoronta ba abinda bata tab'ayi ba. lallai idan kaga mutum baya magana to ba'a tab'o shi bane ta fad'a a fili. Daki suka koma lina ta kalli humaira tace lallai humy wallahi sekin tashi tsaye,dan naga yarinyar nan ba kamar wad'ancan bane dan bata da tsoro da alama ta taki wani abu. Ajiyar zuciya humaira tayi, tace lina banci ta zama ba, yanzu zamu tafi wajen boka me gani har hanji, idan nayi sake yarinyar nan zata rusamin budget, kin dai san dalilin da yasa na auri Abdul bawai dan tsananin k'aunar sa bane kawai dan dukiyar sa ce.Wannan ne dalilin da yasa nake zubar da ciki idan na samu, k'arshe zuwa nayi aka fitar da mahaifar saboda bana buk'atar haihuwa balle idan ya mutu d'an ya gajeshi. shiyasa nake son nasashi ya rubuta sunana a dukkan kadarorinsa kafin na aikashi zuwa lahira. ihu lina tasa irin nasu na 'yan bariki tace shiyasa kike burgeni k'awata, dan bakya wasa da hanyar samun kud'i. yanzu ki tashi mu tafi wajen bokannan dan kinsan masu iya magana sunce da zafl-zafi akan bugi k'arfe,kuma ba'a bori da sanyin jiki. tashi humaira tayi ta d'auko gyalenta ta yafa ba wanda zai ganta yayi zaton matan aure ce. Wata benz arsh colour naga sun shiga, da k'arfi ta danna horn cikin hanzari me gadi yazo ya bud'e mata get da mugun gudu ta fita dan kad'an ya rage ta take masa k'afa, girgiza kai yayi yana yi masu fatan shiriya. Jin fitan motane yasa salma ta fito ta kawowa me gadi sauran abincin data dafa, har k'asa mallam musa ya durk'usa yana yi mata godiya, dan tunda ya fara aiki a gidan ba'a tab'a bashi abinci ba se dai a kawo masa daga gida. readers ina son na dena posting har sena gama typing nayi muku gaba d'aya amma menene ra'ayin ku???? ina jiran amsoshin ku. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 20 Wannan page d'in nakine ne my daughter(hapsert bnt hassan Ameen) kinfi kowa son novel d'innanπŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ˜ƒ ina yinki irin sosai d'innan❀ Wani k'ungurmin jeji naga humaira sun shiga, ba gida ko daya a wajen, tun a bakin jejin suka ajiye motarsu, da k'afa suke takawa ga uban nisa. A can na hango wani bukka wanda shi kad'aine a wajen, suna k'arasawa sukaji an daka musu tsawa, saida suka firgita, karku yadda ku k'araso ku tsaya daga wajen da kuke, saboda sarkin aljanu da mutanensa suna zaune a wajen, meke tafe daku??? Cikin rawan murya humaira ta fara magana, dama akan maganar kishiyar da aka min ne. Me kike so ayi mata?? bokan ya tambayeta wanda basa ganin shi sai dai suji muryar sa. Ina so a bani maganin da zai zamo ajalinta. Bushewa yayi da dariya wanda saida jejin ya amsa, yace ke humaira lallai yanzu na tabbatar baki da iyami, tabbas irinku muke buk'ata. Amma zan fad'a miki gaskiya wannan yarinyar idan bakiyi da gaske ba ita ce silar tonuwar asirinki. Aljanun mu baza su iya zuwa kusa da ita ba, saboda jikinta akwai tsari, kuma tana yawan addu'a bata zama babu alwala, aikinki akwai tsada. Cikin sauri tace boka kasan kud'i ba matsalata ba ce,ko nawa ne zan biya. Zaki bada dubu d'ari biyar,aciki za'a siyama sarkin aljanu bak'ar saniya da bak'ar tinkiya, da bakin bunsuru da bakin zakara, za'a yanka mishi saboda jinin yake buk'ata. Da hanzari humaira ta ciro kud'in ta ajiye a wajen. tana ajiyewa aka wurgo musu k'ullin magani. Ki d'auki wannan maganin kisa mata a abinci, ki tabbatar taci, dan iya abinda zamu iya yi miki kenan, danko kusa da ita bazamu iya zuwa ba, wannan ne temakon da zamu iya baki. sunkuyawa humaira tayi ta d'auka, sannan suka fara tafiya da baya da baya, har saida suka dena hango bukkar tukunna suka juya, dan haka dokar bokan take. K'arasawa sukayi wajen motar su suka shiga suka tafi. A hanya humaira ta kalli lina tace, nifa bansan ta yaya zan saka mata maganin nan a cikin abinci ba, dan nasan ko na bata abu baci zatayi ba. Amma humy har yanzu kwakwalwar ki bata ja wallahi. ina ce mijin a hannun ki yake? kuma kinsan se abinda kika tsara masa yake yi, gyad'a kai humaira tayi. to yanzuma haka zakiyi, kawo kunnen ki kiji,gani nayi lina ta fad'a mata wani magana sukayi dariya suka tafa, ko me tace mata oho. Bayan sun koma gida suka shige bedroom suka rufo k'ofar, direct kan bed suka nufa tun kafin su k'arasa naga sun fara shafa junansu. A'UZUBILLAHI. Abinda na furta kenan, dama su 'yan lesbian ne? A guje na juya na bar musu d'akin ina nema musu shiriya, Bayan sun gama watsewar su, lina ta fito ta tafi tana jaddadawa humaira akan tasan yanda zatayi ta bata maganin taci MENENE DANGANTAKAR LINA DA HUMAIRA??? Humaira sun had'u da lina ne a wajen party, asalin lina bayarbiya ce amma ba musulma ba ce. tun tashin lina yarinya ce hatsabibiya tun wana k'aramar ta take bin maza, data girma ta zama budurwa ne idanunta suka dad'a bud'ewa, daga k'arshe tattarawa tayi tabar garinsu OYO ta biyo saurayinta suka zo BAUCHI. Tunda tazo ta bud'e bariki kala-kala ba iya bin maza ta tsaya ba, hatta hajiyoyi d'aukanta sukeyi sun had'u da humaira ne a wajen birthday partyn da saurayinta ya had'a mata, tun daga lokacin suka k'ulla k'awance, ita ta koyama humaira lesbian da bin bokaye,(ALLAh ka had'amu da k'awaye nagari AMEENπŸ™πŸ™) Da daddare bayan A.A ya dawo yana zaune a falo, humaira ta fito cikin shigar riga da skert english wears, sun kamata se dai ko kadan basuyi mata kyauba, kasancewarta siririyar mace da bata da shape ko kad'an, se tayi kamar an d'aura wa muciya zani.😜😜 Kusa dashi tazo ta zauna tana mishi barka da dawowa kamar ba abinda ya faru(duk plan d'in lina ne). Ya amsa mata cikin jin dad'i, saboda shima fargaba ce ta hana shi dawowa gidan tun da ya fita da safe. tace mishi su tashi suje suci abinci, wanda me aikinta blessing ta girka ta jera akan dining table. mik'ewa yayi suka nufi kan dining d'in, bayan sun kammala cin abincin suka dawo falon suka ci gaba da hiransu suna kallo kamar yanda suka saba. Humaira ne ta dubi A.A tace babyna daman akwai maganar da nake son muyi dakai, ina jinki ya amsa mata ba tare daya kalle ta ba.('yan mulkin sun juyo kanta kenan). Naga har yanzu baka kirata ka fada mata yanda tsarin gidan nan yake ba. Kallonta yayi sannan yace wani tsari kenan??? had'e rai tayi tace ina so ne ka fad'a mata duk wacce take da girki ta fito a dinga cin abinci tare da ita, ban yarda kowa ta dinga yin nata ba. kauda kanshi yayi cikin jinkai yace kije ki kirata, tashi humaira tayi ta nufi part d'in salma. k'wank'wasa k'ofar tayi, salma dake zaune tana kallon tashar Arewa 24 ta taso ta bud'e k'ofar, tana ganin humaira ta b'ata fuska tace lafiya? murmushin mugunta humaira tayi, tace "kizo mijina yana kiranki" ta juya tayi tafiyarta. d'an tsaki salma taja tace da wayace ba mijinki bane? (ina fatan salma ba haushi kikaji baπŸ˜ƒπŸ˜ƒ) juyawa tayi ta Koma cikin daki ta dad'a gyara fuskarta ta fesa turare me dad'in k'amshi, ko hijab bata d'auka ba ta nufi falon da suke. Tunda ta doso wajen yake binta da kallo, kasancewar kayan baccine a jikinta riga da wando cotton, sun kamata tsam rigan me hannun shimi ne, wandon a iya guiwa ya tsaya mata, ta saka hulan turban kalan kayan pink. tana zuwa ta nemi waje ta zauna ba tare data ce musu komai ba, humaira da tun fitowar salma tayi dana sanin kiranta da tace ayi ganin irin kallon da A.A yake mata. Gashi ba daman tayi magana kar plan d'inta yargaje🀣🀣🀣🀣 Ta wurga ma salma harara sannan ta juya ta kalli A.A daya maida hankalinsa ga kallon t.v ta daure tace "babyna gatanan ta fito ka fad'a mata" beko kalle ta ba yace ki fad'a mata mana tunda tsarinki ne hakan. Da sauri ta dube shi jin tana mishi magana yana bata amsa wani iri. wai meke faruwa ne kodai asirin da namishi ya fara warwarewa ne? daga zuwan ta komai ya fara warware wa, aikuwa zanyi saurin aikata lahira tun kafin komai ya kmab'e min, tayi maganar cikin zuciyarta. duban salma tayi dakanta yake kallon wani gefe na falon tace "to amarya dama maganar girki ne, kinsan hajiya tace yayi miki kwana 7 d'inki kafin araba kwana bibbiyu. saboda haka yanzu duk wacce take da girki zata fito a had'u a dinga cin abinci tare. Akwai wacce take yi mana girki, ina fatan ba matsala?" ta k'arasa tana murmushin yak'e mamaki ne ya kama salma,tabbas akwai abinda take shiryawa dan tasan ruma baya tsami banza, ita zata nuna ma kirsa? wato dan tana gaban mijinta shine zata nuna ita na ALLAh ne, aikuma zata nuna mata itama macece tana da irin nata salon. Murmushi salma tayi tace "haba Aunty ai duk abinda kika yanke dai-dai ne, amma ni inso samune nafison na dinga yima mijina abinci, dan banason masu aiki su dinga yima mijina hidima..... Tun kan salma ta k'arasa humaira tayi saurin katseta, ganin tana neman wargaza mata plan. tace"haba k'anwata kamar ke kina auren Alh. A.A me dala ace kina girki da kanki. ai wannan abin kunya ne a gare mu. girgiza kai salma tayi tace ba abin kunya bane Aunty tunda aikin ladane kuma wa mijina zan yima, ni inaga ai ba lefi aciki. A.A da yake kallon news a t.v amma hankalinsa yana wajensu,yana jin maganganun da sukeyi, ya juyo ya kalli humaira yace "tunda tace zata iya ki rabu da ita mana, kun cika min kunne da surutunku, kun hana na fahimci abinda ake fad'a a news d'in. Yana maganar yana satan kallon salma da take jifansa da murmushi duk dan ta k'ular da humaira. humaira da ranta ya gama b'aci ta kalle shi ta fara magana ta ma manta da batun wani plan tace "wallahi duk abinda na tsara shi za'abi, koka manta haka akeyi aduk lokacin da kayi aure? kaine ka bani damar tsara duk yanda nake so dan haka yanzuma haka nake buk'atar ayi. kallonta salma tayi tana murmushi tace "Aunty menene abin d'aga hankali anan? kawai dan zan dinga yima mijina hidima ai ba wani abu bane.... Keee!... Badake nake yiba da wanda ya ajiyeki nake magana. humaira ta fad'a tana huci kamar kububuwa Look humaira kinsan fa ban cika son hayaniya ba, please kowa ta tafi d'akinta banson tashin hankali. Mik'ewa salma tayi fuskarta cike da murmushi ta wuce d'akinta. itama humaira tashi tayi ta dube shi tace, "Abdul nika wulak'anta a gaban wancan banzan ko? to wallahi se nayi maganinku daga kai har ita. ta wuce shi ta shige d'aki" Tsaki yaja ya kashe kallon ya nufi d'akin salma, hakanan yake jin ya rage tsoron humaira yana ganin yanzu bazai d'auki rashin mutuncin ta ba. kuyi hakuri da wannan wallahi har nayi ya goge. Readers naji k'orafin ku zan dingayi kullum insha ALLAhu, wanda ba'abi ra'ayin ku ba ina me baku hak'uri. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 21 Sistr eyshert Aysm ina miki murna da fara sabon novel d'inki (WAZAN SO) ALLAh ya k'ara d'aukaka,yanda kika fara lafiya ALLAh yasa ki gama lafiya. Inayin ki sistr irin sosai d'innan.😘 Akashe ya samu wutan falon amma yana iya hango d'an haske ta cikin bedroom d'in. Sallama yayi sannan ya shiga d'akin a kwance ya sameta ta bama k'ofar baya, tayi nisa a tunani da alama batasan mutum ya shigo d'akin ba. Gefenta yaje ya kwanta ya juya mata baya,sannan yaja bargo ya lullube jikinsa. ya kashe bedsite lamp dake gefenshi, se a lokacin salma tasan ya shigo d'akin. Cikin sauri ta mik'e zaune ta ce mallam lafiya zaka shigo min d'aki ba ko sallama, Ko juyowa beyiba bare ya nuna yasan tana magana. duk da haka batayi shiru ba, gaskiya ka tashi ka koma d'ayan d'akin dan ni bansa ba kwana da wani namiji a cikin d'aki d'aya ba. Batare daya juyo ba ya fara magana "Nan gidana ne ina da ikon shiga duk inda naso a kowani lokaci, kuma ya kamata kisan banbancin dake tsakanin da da kuma yanzu, ki iya bakinki saboda yanzu a k'ark'ashin iko na kike, ba k'ark'ashin ikon iyayenki ba. Agidana kike ba gidanku naje ba. Shiru salma tayi batare da ta sake cewa komai ba ta mik'e domin ta koma d'ayan d'akin. Muryar shi taji yana bata umurni koma ki kwanta, dan ni bana raba makwanci da matata ki kiyaye ko saboda gaba, komawa salma tayi ta kwanta amma ta gagara runtsawa saboda fargaba da rashin sabo, ga sanyi da takeji. Shima ba baccin yakeyi ba, tunani ne ya cika kwakwalwar sa, ya rasa me yake damunsa ga wani feeling dayake ji wanda be tab'a jin irinsa akan wata 'ya mace ba. Sauk'ar numfashinta yaji abayansa alamar bacci ya d'auketa, juyowa yayi yana kallonta tana baccinta cikin kwanciyar hankali, ta dunk'ule jikinta waje d'aya. Tsintar kansa yayi da rungumota zuwa jikin sa, a tare suka sauk'e ajiyar zuciya, itakam cikin bacci ne ba tare datasani ba, yayin dashi kuma najin dad'in jinta dayayi ajikinsa ne. Kallonta yakeyi be tab'a sanin tana da kyau sosai haka ba, tayi mishi kyau datake bacci, sleeping beauty ya furta a hankali. Jawo bargon yayi ya lullub'a musu gaba d'aya, yayi addua ya shafa musu. abinda ya juma beyi ba wato addu'an kwanciya. Cikin dare salma ta farka tajita a jikin mutum, hannu takai ta kunna lamp d'in dake gepenta, zuba mishi ido tayi tana kallon fuskarshi ga kwantaccen sajen shi wanda ya kwanta a fuskar shi, ya k'arama fuskar shi kyau da kamala gaskiya ta yarda Abdul me kyau ne. Hannun shi ta kalla wanda ya zagayeta dashi tunani takeyi ta yanda zata cire hannun batare data tashe shi, gashi so take yi ta tashi ta d'auro alwala tayi sallan nafila. A hankali ta zare jikinta a cikin nashi ta nufi toilet domin ta d'auro alwala, k'aran bud'e kofar toilet d'inne ya tashe shi. Yana kallonta ta cikin hasken dayake d'akin, ta fito ta d'auki hijab d'inta ta tada kabbara. Raka'a hud'u tayi tadad'e a sujjadarta ta k'arshe tana kaima ALLAh kukanta kafin ta d'ago ta sallame. bayan tayi zikiri tayima annabi salati,ta d'auko alqur'ani ta fara karatu cikin sanyin muryanta. Duk abinda takeyi A.A yana kallonta nan take farin ciki ya rufeshi, Salma itace irin matar dayake burin ya aura tun farko. Haka kawai shima yaji yana sha'awar yin nafilan koda raka'a 2 ne, idan be manta ba rabonshi da ya tashi sallah da daddare tun kafin yayi aure. mik'ewa yayi ya shiga toilet d'in ya d'aura alwala,ya fito ya shimfid'a sallaya ya tada kabbara. Bayan ya idar yayi addu'o'inshi, sannan shima ya d'auko alqur'ani daya gani a gefe ya fara karantawa. Salma tabar karatun da takeyi ta juyo tana kallon shi jin yanda yake k'ira'ar sa kamar sudes, A.A daya kammala karatun shi ya juyo ya kalleta jin dayayi tayi shiru da barin karatun. Gani yayi ta zuba mishi ido da alama hankainta baya wajen. hure mata ido yayi, yace "yadai 'yan mata kallon fa?" cikin sauri ta kauda kanta cike dajin kunyar kamata da yayi tana kallon shi. Rufe qur'anin tayi ta mik'e ta cire hijabin ta ninke ta adana shi, sannan taje ta kwanta, Shima tashi yayi yaje ya kwanta ya jawota jikinsa, ya lullub'a musu bargo suka koma bacci. ASUBA TA GARI SAL-AZEEZ. Humaira kuwa tana shiga d'akinta ta d'auki waya ta kira lina ta fad'a mata duk abinda ya faru, masifa lina tahauta dashi,tace bakiji abinda boka ya fad'a bane? yace fa idan kikayi wasa ita ce silar tonuwar asirinki. gashi kin jawo har yana miki musu a gabanta. humaira tace "wallahi lina rainane ya b'aci shiyasa" humy sefa kinyi hakuri kin daure zuciyar ki kafin komai ya tafi yanda muke so. dad'a bata shawari lina tayi sannan sukayi sallama Shiru-shiru humaira bataga A.A ya biyo bayanta ba kamar yanda ya saba, tashi tayi ta leka falon gani tayi bakowa da alama d'akin salma ya tafi. dawowa tayi d'aki ta kasa zama duk tunanin kar wani abu ya shiga tsakanin su, gashi ba daman taje d'akin Saboda kar plan d'insu ya wargaje. A tak'aice ranar haka humaira takwana tsabar kishi kamar zatayi hauka. Da asuba ya riga salma tashi, saida yayi alwala sannan yazo ya tasheta ya shimfida sallaya yayi raka'atainil fajri. Bayan salma ta d'auro alwala yaja su sallar asuba, bayan sun idar sukaci gaba da karatun alqur'ani har gari ya k'arasa wayewa. Salma ce ta gaishe shi ya amsa fuskar shi d'auke da murmushi, dan jinshi yake cikin farin ciki. Mik'ewa tayi tashiga toilet ta had'a mishi ruwan wanka ta fito ta fad'a masa, binta yayi da kallon mamaki da tunda suke da humaira bata tab'a had'a masa ruwan wanka ba dan komai da kansa yake yi. thanks yace sannan ya tashi ya nufi toilet d'in ita kuma ta nufi kitchen dan ta d'aura musu breakfast dankali ta soya musu da kwai, tayi musu farfesun kayan ciki, se ruwan lipton dayaji kayan k'amshi. bayan ta kammala ta debi kayan breakfast d'in takai babban falo dan tana da tabbacin humaira bata tashiba a lokacin. d'ayan bedroom d'in ta shiga do tayi wanka. A.A ya fito daga wanka daga shi se towel a daure a k'ugunsa, se k'arami a hannunsa yana goge sumar kanshi. gaban mirror yaje yana k'arewa mayukanta dake kan mirron kallo. hannu yasa ya d'auko wani lotion me k'amshi ya shafa. Fitowa yayi yanufi d'ayan d'akin dan ya shirya, saboda akwai sauran kayanshi daya manta be kwashe ba a d'akin. shigarsa tayi dai-dai da fitowar salma daga wanka, tana d'aure da towel wanda ko cinyoyinta be gama rufewa ba. Daskarewa yayi a wajen, ganinta d'aure da towel ya d'aga masa hankali, takowa ya farayi zuwa inda take tsaye, salma data kasa yin gaba bare baya tsabar kunya daya rufeta kamar k'asa ta tsage ta shiga haka takeji. Ganin yana nufota ne yasa ta juya a guje ta koma toilet d'in ta rufo kofa. murmushi kawai yayi ya girgiza kai. kan mirron d'akin ya nufa ya shafa ma sumar sa mayuka ya fesa hairsprayer. sannan ya nufi wall drop ya ciro kayan da zai saka. Black jeans ya ciro da farar t-shirt me guntun hannu, a gaban rigan an rubuta HANDSOME da bak'ak'en harufa. Ya saka farin takalmi cover shoe se bak'in jacket daya d'aura akan kayan kasancewa lokacin hunturu ne. turaruka ya d'auka ya fesa san ya bar d'akin ya nufi part d'in humaira Salma saida taji fitar shi ta fito ta koma d'ayan bedroom d'in ta shirya cikin doguwar rigar material fitted gawn bata d'aura d'ankwali ba se tayi rolling da siririn mayafi kalan kayan, ta fesa turarukanta ta fito ta nufi falo. Bata tarar da kowa ba, zama tayi akan kujeran dining d'in ta fara had'a tea dan baza ta iya zaman jiran su ba. bata dad'e da zama ba A.A ya fito da alama har yanzu humaira bata tashi ba, hanyar fita taga ya nufa ta d'an d'aga murya tace "ga breakfast d'inka fa" Juyowa yayi yana kallon ta shi abin natama ya dena bashi mamaki se burgeshi da takeyi. Yaushe rabon da yayi breakfast a gidansa ai harya manta, se dai kullum idan yaje office ya aika a siyo mishi a restaurant, indai kaga ya karya a gidansa to ranar weekend ne shima se 11:00am. shi harya ma saba, duk lokacin da zai tafi office harya shirya humaira bata farka daga bacci ba bare ta bama mai aiki umurnin abinda za'a girka(mata dan ALLAh mu gyara) K'arasowa yayi ya zauna, cup ta d'auka ta had'a mishi tea ta d'auki plate ta zuba mishi dankalin da farfesun. be wani ci da yawa ba ya tashi duk da abincin yayi masa dad'i. briefcase d'insa ya d'auka ya nufi hanyar fita daga falon, "A dawo lafiya ALLAh ya tsare ya bada sa'a" salma ta fada tana bin bayansa da kallo. Juyo wa yayi, yayi mata k'ayataccen murmushi dan har a ransa yaji dadin adduar datayi masa, sannan ya juya ya fita, muje zuwa 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 22 Tattara wajen salma tayi, sannan ta dauki plate ta d'ebama me gadi ta hada masa tea ta fita domin takai masa. A zaune ta tarar dashi yanajin radio, bayan sun gaisa ta mik'amishi, karb'a yayi yanata zuba mata godiya. Salma ta kalle shi tace "Baba dan ALLAh za'a samu ganyen magarya anan kusa?" eh baza a rasa ba, akwai anan baya bari naje natsunko miki. Godiya salma tayi masa sannan ta koma ciki. Tana zaune a falo taji ana sallama tashi tayi ta lek'a, taga me gadin ne ya dawo hannunsa d'auke da bak'in leda, mik'amata ledan yayi "hajiya gashi ansamu amma d'anye ne" karb'a tayi tana murmushi bakomai baba daman nafi buk'atar d'anyen, godiya ta sake mishi. part d'inta ta koma ta tsinki ganyen magaryan guda 7 ta zuba a wani roba ta jik'a da ruwa, ta tofa ayoyin shifa aciki da wasu adduo'i ta barshi ya jik'a. Zob'onta ta hada me dadin gaske,da ruwan addu'an ta saka a fridge. Falon ta koma ta tattara kayan da sukayi breakfast wanda suka bata, ta wanke ta maida komai yanda yake. Ta gyara part d'inta ta fesa room fresh, ta kunna turaren wuta a burner, ko ina ya dau kamshi. Humaira ta fito tayi wankan ta tayi kyau ba lefi se dai idanunta sun kumbura da alama taci kuka ta k'oshi. dining taje tayi breakfast sannan takoma kan kujeran falon ta zauna. k'arfe 11:00 salma ta d'aura abincin rana, shinkafa da miya tayi wanda yaji naman kaza, tayi had'in coslow. ta zuba shinkafar a cooler, coslow d'in ta zuba awani d'an tangaran ta rufe da farin leda ta saka a fridge Tunanin wanda zata samu yakaima A.A office takeyi, knocking taji anayi mata, zuwa tayi ta bud'e humaira tagani a tsaye " malama kizo kinyi bak'i, ta juya abinta fitowa salma tayi tabi bayanta. Ita dai bataga kowa a falon ba, waje ta lek'a ta tarar da drivern gidansu A.A tare da wata yarinya wanda baza tafi 14years ba. Bayan sun gaisa yake fad'a mata hajiya ne ta aiko shi ya kawo mata 'YAR AIKIN. Ya mik'o mata wani leda yace "ga wannan tace zakiga bayanin komai a ciki. karb'a tayi tace yace ta gode, harya juya zai tafi ta tsayar dashi "dan Allah ko kasan wajen aikin Alh. Abdul?"Alh. gidan nan? ya tambaye ta "eh shi nake nufi" salma ta bashi amsa. Nasani ranki ya dad'e, dan Allah aika zan baka ka kai mishi idan bazan takura ka ba.salma ta fad'a, A'a hajiya bakomai ki kawo sena kai mishi. Hannun yarinyar salma ta kama suka shiga ciki bata tarar da humaira a falonta ba, Abincin ta had'a acikin basket ta d'auko had'in zob'onta wanda yayi sanyi ta zuba a jug, ta d'eba ma yarinyar abinci a plate ta bata sannan ja d'auki basket d'in takaima drivern. Manage with this 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 23 Ledan da aka kawo mata tadauko ta bude,turaruka ne masu kamshi na jiki, se hadin zuma ,dabino da ridi, se mad'i da sauran kayan mata masu inganci. Kowanne an rubuta yanda zatayi amfani dashi ajikin takarda. Mayarwa tayi cikin ledar aranta tana raya mezatayi dashi, ita tagaji dashan irin wadannan abubuwae, dan tun tana gida Aunty hadiza take d'ura mata su. gwanda ma turaren xata iya amfani dasu. dauka tayi takai cikin dakinta, ta bude wall drop dinta tasa a ciki ta rufe. ta dawo falon ta tarar da yarinyar ta gama cin abinci. zama tayi akan kujera ta kalli yarinyar tace "menene sunanki?" sunana jamila, yarinyar ta amsa mata. To jamila zaki dinga yimin wanke-wanke da shara se mopping, iya kacin ki falo da kitchen banda cikin d'aki wannan zan gyara da kaina. ina fatan zakiyi aikin ki ba tare dakin bani matsala ba? Insha Allahu aunty zan kiyaye, zaki sameni mebin umurninki. to shykenan yanzu kije kitchen akwai wanke-wanke se kiyi, amsawa tayi sannan ta mike ta shiga kitchen din domin ta aiwatar da aikin da aka sata. tananan zaune har yarinyar tagama ta fito, mik'ewa tayi tace"dauko kayanki muje na nuna miki yanda zaki zauna. B.Q takaita dakunane guda 2 kowanne da toilet a ciki se falo a tsakiya, se k'aton kitchen a gefe da alama shine manda ake girki a ciki. daki daya blessing ne a ciki, d'ayan d'akin wanda ba kowa salma tace ta shiga, ta juya ta koma part d'inta. Toilet ta shiga ta d'auro alwala tayi sallar azahar. ta dawo falo ta zauna ta kunna tashar arewa24, ta samu suna hasko film din dawo-dawo. Tana zaune taji an turo k'ofarta an shigo ba neman izini, d'aga kai tayi dan taga waye me k'arfin halin shigo mata d'aki haka. Blessing ta gani 'yar aikin humaira, cikin b'acin rai salma ta daka mata tsawa "Ke!.. baki da hankali ne? da zaki shigo min d'aki ba neman izini, haka aka koya miki a gidanku?" Jikinta yana b'ari ta durk'usa tana bawa salma hakuri. Fuska ba fara'a salma tace "me kikazo yimin a d'aki?" cikin girmamawa ta amsa hajia babba ce ta aiko ni nazo na karb'a mata abinci a wajenki. shek'ek'e salma take kallonta tace kije kice mata ban girka da ita ba. cikin sauri ta mik'e ta fita Bugo kofar akayi aka shigo, humaira ce cikin masifa ta fara magana " ke salma ina abincina?" ban girka dake ba salma ta fad'a. kutman uba..πŸ™Š ina cikin gidannan kiyi abinci kice baki girka dani ba? to wallahi baki isa ba, da wani tsugudidin ne yasa kikace zaki dingayi da kanki? kallonta salma tayi tace "ai da nace zan dingayi da kaina bance hardake zan dinga girkawa ba, wa mijina nace zan girka. Alfarma d'aya zan iya miki, shine zan dinga yi dake safe da dare, da rana kuma seki nemi abinda zakici. Hakan ma albarkacin mijina kikaci, dan haka karki sake zuwa kice na baki abinci danni ba 'yar aikinki bane. Dubanta humaira takeyi cike da mamakinta,yarinya k'arama ta tsaya tana fad'a mata magana , wanda inda tana da k'anne tayi k'anwa ta 2 da ita, lalle ta samu waje da yawa tace " wallahi salma ina tausaya miki, ni humaira nayi alk'awarin sena LALATA (littafin sad-naf) miki rayuwa, se kinyi nadamar shiga gonata da kikayi. Tab'e baki salma tayi tace " ni nafi k'arfinki wallahi, idan kina takama dabin malamai ne to ni kuma na rike addu'aπŸ™πŸ™ kuma da yardan Allah ba abinda kika isa kiyi min. Mu zuba ni dake aga wanda zeyi nasara,humaira ta fad'a kafin ta juya ta fita daga falon. tsaki salma tayi, taci gaba da kallonta. Driver ya kai abinci office d'in A.A masinja yayi masa izinin shiga bayan yaje ya fad'a masa yayi bak'o, tura k'ofar yayi ya shiga da sallama. Duban shi A.A yakeyi cikin mamakin ganinshi, yace lafiya kuwa mallam haladu? lapia lau Alh. k'arami(dayake haka suke fad'a masa) gaishe shi yayi kafin yace "daman hajiya karama ce tace na kawo maka wannanπŸ‘‰ . duban basket din A.A yayi yana yamutsa fuska kafin yace wacece kuma hajia karama? Amaryanka nake nufi ranka ya dad'e. kallon basket d'in ya sakeyi cikin mamaki yace "gidan kaje"? eh ranka ya dad'e hajia ce ta aikeni nakai mata 'YAR AIKI. Gyada kai yayi ya nuna masa kan centre table yace ya ajiye a wajen. 5000k ya mik'a masa, karb'a drivern yayi yana zuba godiya kafin ya fece daga office d'in. basket d'in ya d'auko ya ciro cooler da jug d'in. Ya bud'e ya zuba abincin tare da had'in coslow, sannan ya fara ci. yana ci yana lumshe ido rabon daya ci abinci me dadin wannan harya manta, ko abincin restaurant dayake aikawa asiyo masa ba yanda ya iya ne kawai, gidan hajiyar sa ne idan yaje yake cin abinci kamar wannan. to shikuma yanzu ba zuwa yakeyi sosai ba. dan ko yaje baya dad'ewa bare har yaci girkinta me dad'i. sosai yaci abincin yasha zob'on, a ransa yana jinjina ma yarinyar dan komai nata dabanne, gaskiya yanzu yana farin ciki da ZAB'IN MAHAIFINSA. kiran masinja yayi ya bashi saurae abincin, zob'on kuma ya saka a fridge, zuwa anjuma zai sha dan yayi masa dad'i sosai. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 24 Da daddare salma ta tuka tuwon shinkafa miyar egusi wanda yaji ganda, da jallop din taliya da kifi, ta hada da sauran zob'onta na cikin fridge. bata kai abincin dining ba saboda bata yarda da humaira ba. Me aikinta ta kira ta bata abincin su dana megadi. Kwalliyarta tayi cikin riga da skert na jan leshi, babban falon taje ta zauna tana jiran dawowar A.A. tana zaune humaira ta fito waje ta nema ta zauna se zabga ma salma harara takeyi. Da sallam ya shigo falon cikin husky voice d'insa, mik'ewa salma tayi tana amsa sallamar, k'arasawa tayi ta karbi briefcase d'in hannunshi, cikin yanga tayi mishi barka da dawowa. d'akinta ta wuce taje ta ajiye briefcase d'in, ta hada masa ruwan wanka, ta d'auko masa jallabiyya da gajeren wando ta ajiye masa akan gado ta fito daga dakin. A kusa da humaira ta same shi kome suke tattaunawa oho musu da alama dai rarrashinta yakeyi. Aranta tace kudai kuka sani jarababbu kawai🀣🀣🀣🀣, kuma insha Allahu duk sihirin da tayi maka seya karye in dai kana shan zob'on nan. Cikin murmushi ta kalle shi tace na hada maka ruman manka. dubanta yayi shima murmushin dauke akan fuskar sa ya amsa mata, sannan ya tashi ya shiga d'akin. Mugun kallo humaira ta jefa mata tace "tsabar iya karuwanci ne harda had'a masa wani ruwan wanka?" murmushi salma tayi tace aiba lefi bane tunda wa mijina nayi, kuma kowa yasan ban taba yawan bin maza ba, bare a kirani da sunan karuwa tayi wucewarta d'aki. bin bayanta da kallo humaira tayi dan tasan magana ta fada mata, wato ita ce tayi yawan karuwancin lalle wannan shine in kasan nafad'a bakasan na mayarwa ba. Atare suka fito yayi wankan shi se kamshi yake zubawa, ita kuma tana dauke da abinci akan tray, se da ta bari sun k'araso cikin falon sannan ta kalleshi tace " Akan dining zaka ci ko na ajiye akan carpet? A k'ule humaira ta ce kin taba ganin munci abinci akan carpet?? murmushi salma tayi kafin tace aunty wai ai naga ya dawo daga aikine ya gaji bansani ba ko zai iya hawa kan dining d'in. ki ajiye akan carpet d'in, inaga zaifi. ya fada yana zama akan kujera, ajiyewa salma tayi sannan ta zuba musu. Abincin suke ci ba wanda yake magana a cikin su, sosai yaci abincin dan ya manta rabon dayaci tuwo, dan shine best food d'insa amma humaira bata taba sawa anyi masa ba. Humaira ma taci taliyar sosai amma bata sha zob'on ba, exotic ta dauko a cikin fridge din falon. Bayan sun gama salma ta tattara kayan takai kitchen, ta sake wanka tasa kayan bacci tayi kwanciyarta. Ganin salma bata dawo bane yasa A.A yima humaira se da safe, ya ce mata bacci yakeji dan ya gaji da yawa, be jira jin abinda zata ce ba yayi shigewar sa part din salma, ya barta a zaune ta rasa ma abinda ya dace tayi.πŸ™‰ Yana shiga dakin ya cire jallabiyar ya saka kayan bacci, kwanciya yayi ya jawota jikinsa yayi musu addu'a. yauma haka suka tashi cikin dare sukayi sallah,da karatun alqurani. da asuba bayan sunyi sallah, ganin da salma tayi fuskar sa a sake yasa ta dauko hisnul muslim ta mik'a masa tace ya karanta azkar d'in. beyi musu ba ya karb'a ya fara karantawa. bayan ya gama ya dubeta yace " please idan akwai saura tuwon nan kiyi min dumamensa" Amsawa tayi sannan ta gaishe shi, ta tashi ta had'a masa ruwan wanka. A gurguje ta hada breakfast tayi wanka ta shirya. Bayan da suka gama karyawa ta d'auki briefcase d'in, har bakin mota ta raka shi. Basket d'in jiya ya ciro mata, tayi masa fatan alkhairi, har ya tayar da motan ya lek'o yace "kina da waya kuwa?" Kallon shi takeyi cike da mamakin canjawar shi. kafin ta girgiza kai, bece komai ba yaja motar sa ya fita bayan me gadi ya bud'e masa get. Da rana tayi jallop din cous-cous wanda yasha kayan lambu da hanta, tayi had'in coslow, ta had'a zob'onta kamar yanda tayi jiya, tunani takeyi yau wazata samu yakai masa? sega jamila me aikinta ta shigo "aunty ga drivern gidan hajia yazo" fitowa tayi bayan sun gaisa yake ce mata " hajia ce ta aikoni akan zan dinga zuwa ina kaiwa Alh. karami abinci, saboda jiya dana koma take tambayata ya akayi na dad'e shine nayi mata bayani" Godiya salma tayi ta d'auko abincin ta kawo masa,ta mika masa bak'in leda wanda ta saka turmin atamfa da shadda se turaruka masu tsada, tace ya kaima hajia. Duk da tasan suna da kudin da zasu siya wanda yafi wannan amma ihsani yana da dad'i. Aikuma hajia halimat taji dadin kyautar dan har Abdul takira take fad'a masa, sosai yayi farin ciki k'imarta ya sake daduwa a idanunsa (mata mu kula yin kyauta ma 'yan uwan miji yana dada miki kima a idanun mijinki, koda su d'in basa kaunar ki to karki ce baza kiyi musu komai ba kiyi musu gwargwadon iyawan ki ALLAh yasa mu dace) Da daddare da A.A zai dawo ya siyo ma salma waya ki'ran iphone 7. sosai salma tayi farin ciki,tayi masa godia sannan tace ya bata numbern hajia tana son zasu dinga gaisawa, yaji dad'i kuwa ganin yanda take nuna tana son iyayen sa. Atak'aice haka suka cinye kwana 7 ba abinda ya tab'a shiga tsakanin su na auratayya, sannan kullum se sun tashi cikin dare sunyi nafila da karatun alqur'ani da safe ta bashi littafi yayi azkar ga kuma zob'o da take hada masa da ganyen magarya da ayoyin shifa dan karya sihiri. Acikin kwana 7 dinnan kusan duk wani sihiri dake jikinsa ya karye, har tunani yakeyi ta yanda ya auri humaira. Yanzu kullum seyaje ya gaishe da iyayensa ga wata irin shak'uwa da ta shiga tsakanin su, sosai yake jinta aransa. Iyayensa sunyi farin cikin ganin yaron su ya dawo gare su lallai sun yarda salma ALKHAIRI ce a gare su. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 25 A gidan su salma washegarin da akayi yini 'yan uwa suka shirya domin suje ganin dakin amarya saboda aranar kowa zai watse. Har zasu tafi mallam amadi ya shigo yake tambayar su ina zasu je? suka fada masa, masifa yahau yi yace ba wacce zataje kalan suje su bata musu gida, haka kowa ya tattara ya kama gabansd. Wata rana suna zaune a majalisan su na dattawa, wani daga cikinsu yake bada labari "wato wani mutumi ne ya aurawa 'yarsa wani mekudi, wai shi a zaton sa idan 'yar ta auri Alhajin shima za'a bashi dukiya ne, ashe be sani ba Alhajin d'an yankan kai ne, tunda ya auri yarinyar aka kaita gidansa har yau har gobe ba'a sake ganin suba" ansha zuwa gidan da aka kai yarinyar se a tarar da bakowa agidan. kuma daman beyi bincike ba ya aura mata mutumin, besan kowa yana shi ba, kudi kawai ya zuba mishi. Tunda mallam Amadi yaji wannan labarin hankalinsa ya tashi, ya shiga damuwa sosai, fatansa kawai Allah yasa kar wani abu ya samu salma, duk da yasan mijinta baida wani mugun hali amma yasan kishiyarta muguwar mace ce. Da sallama ya shigo gidan inna saude tana zaune akan taburma tana ninke kayanta data wanke,ta amsa masa sallamar tare dayi masa sannu da dawowa. A kusa da ita ya zauna ya kalleta yace nikam saude kinajin labarin halin da salma take ciki kuma? kallon shi inna saude tayi cikin jin haushin tambayar tace " mallam ai kai zan tambaya, tunda 'yarka ce, kuma kaika aurar da ita, nida ko gidanta bansani ba zaka zo kana tambaya na? shiru yayi cikin nadamar abinda ya aikata, kasa daurewa yayi ya jefo mata wata tambayar "ina ce su hadiza sunje sunga gidan? me zasuje suyi mallam? ko ka manta bakayi mata komai bane? duk da yaron yace baya bukatar akaita da komai amma ai ya kamata ko gara kayi mata. data maka magana kace ko cokali baza ka saya ba. inda kasaya ne to da wanda suka kai se susan gidan. kuma ai kasan ba gidanta aka fara kaita ba gidansu mijin aka kaita se washegari ta wuce gidanta.kuma a washegarin 'yan uwa aka shirya za'aje kace baza'aje ba ko ka manta? dan haka nina riga na fidda tunanin salma a raina tunda ta riga ta shiga wannan gidan. tana gama magana ta tattara kayanta ta shige d'aki ta barshi a wajen cikin tsananin mamaki, dan be tab'a tunanin zata iya kallon idon shi ta fad'a masa wad'annan maganganun ba, lallai me hakuri be iya fushi. tashi yayi ya bita cikin dakin ya nemi waje ya zauna sannan ya fara magana "saude kiyi hakuri nasan ban kyauta muku ba, amma ki dubi girman Allah ki fada min halin da salma take ciki" hawayen da take b'oyewa ne suka zubo ta kalleshi tace "mallam kenan se yanzu ne ka damu da halin da salma take ciki? tunda salma ta girma ta mallaki hankalin kanta kake tsangwanar ta, duk da ita kadai muka haifa hakan besa ka kyautata mata ba a matsayinka na mahaifinta, duk da haka bata fasa yi maka biyayya ba. A karshe ka aura mata mijin da matar sa tafi k'arfinsa duk dan saboda abin duniya. se yanzu da lokaci ya kure zaka zo kace a fada maka halin da take ciki to nima bansan halin datake ba, se kaje ka samu uban mijin ka tambaye shi. Girgiza kai yayi yace tabbas nasan ni me lefine amma wallahi saude ki yarda nayi nadama dan Allah ki yafe min insha Allahu zan canja daga yanda kika sanni. Mallam ni ai baki min komai ba saboda haka kama dena neman yafiyata, ta fad'a tana barin d'akin, dan idan taci gaba da zama tana iya yi mishi abinda bai tab'a zato ba. 。。。。。 Humaira tana zaune ta zuba tagumi ta rasa abinda yake yi mata dadi, tanaji tana gani komai ya kwab'e mata, gashi lina cta gari tayi tafiya bare susan yanda zasu b'ullowa al'amarin. Amma tunda gobe zata karbi girki zatasan yanda zatayi ta zubama yarinyar nan maganin taci ta mutu kowa ma ya huta. Washe gari da safe bayan sunyi wanka sun shirya A.A yace yau baza'a bani breakfast bane? kayi hakuri yau ba girki na bane aunty humaira ce zatayi maka breakfast. b'ata fuska yayi yace ashe yau kina son natafi office da yunwa kenan?? ita da take bacci yaushe lokacin tashinta yayi bare har ta bani breakfast? ki tashi kawai ki nema min abinda zanci dan lokaci na k'urema ya fada yana kallon agogon dake daure a hannun shi. mik'ewa tayi ta shiga kitchen ta hada mishi tea ta soya mishi kwai ta dauro akan taray. akan centre table d'in dake tsakiyar falonta ta daura mishi. Bayan ya kammala ta raka shi zuwa bakin k'ofar falon ta mik'a mishi briefcase din, kallonta yayi yace yau kuma anan zaki barni? yaufa ba girki na bane, dukda bata tashi ba amma ya kamata na kiyaye wani abin saboda gudun shiga hak'k'i dan ko mani akayima haka bazanji dad'i ba. sannan ya ba lallai ne akawo maka abinci ba saboda bani ce da girki ba. karb'an briefcase d'in kawai yayi ya juya ya tafi, tana mishi a dawo lapia beko kulata ba. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳 [1:37PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳 ZAB'IN MAHAIFINA 🌳🌳🌳🌳🌳 Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan) 🌐HAJOW πŸ“πŸŒ πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐 Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM AYSHA BICHIKI Page 26 Yana zuwa office ya kira mahaifiyar sa akan ta aiko masa da abinci da rana, " ina matan naka suke da zan aiko maka abinci daga nan?" ta tambaya "Momy yau fa girkin humaira ne" "Ita 'yar mulkin naka bazata iya aikowa da abincin ba kenan ko?" to momy yaushe ta tashi ma bare tayi wani girki ita da take tashi 11:00am ko breakfast batayi ba alokacin bare ayi maganan na rana. "Allah ya kyauta" tace sannan ta kashe wayarta. karfe d'aya ta aiko driver ya kawo masa abincin. Da rana humaira tasa blessing tayi jallop din shinka fa da wake da nama, ta aikawa salma dashi. Zuciya d'aya salma ta karb'a, har zata faraci sega me aikinta ta shigo. Tsugunawa tayi a gnfenta tace "sannu aunty" Kallonta salma tayi ta amsa, sannan tace lapia dai jamila??ko kina bukatar wani abu ne? sunkuyar dakai jamila tayi kafin tace "aunty daman akwai maganar da nake son zan fada miki amma dan Allah kar kice a bakina kikajiπŸ™πŸ™" "Ina sauraronki" salma ta fad'a. dan Allah Aunty kar kici abincin nan, yanzu blessing take fada min wai tazo shiga falon taga hajia tana zuba wani abu a cikin abincin. kuma tace ta tabajintana waya akan zata zuba miki magani abinci kici ki mutu. "Nagode!jamila" amma dan ALLAh banason naji maganar nan a bakin kowa." "to aunty" jamila ta amsa tashi salma tayi ta dauko bakin leda ta juye abincin aciki ta mika mata "gashi kije ki saka a cikin shara amma ki boye kar wani ya gani" karba jamila tayi ta saka a cikin hijabinta ta fita. Ajiyar zuciya salma ta sauke, tanayi ma Allah godia daya kubutar da ita daga fadawa kaidin humaira. karfe 8:00pm abdul ya shigo gidan, be tarar dasu a falon ba kamar yanda suka saba zama. part din salma ya fara shiga, a kwance ya sameta tana chatting, tun randa ya bata wayar tayi dawlooding whatsapp da facebook. ba wasu mutane bane a contact dinta daga numbern surukanta sena kannen shi sannan nashi. wani group ta shiga a whatsap . "UMMU AFFAN NOVELS" wanda hafsat kanwar shi tayi adding dinta a ciki. gaskiya ana turo littafai masu dadi da ma'ana. yanzu ma wani littafi take karanta KAINUWA (dashen Allah) na ayusha littafin yayi mata dadi sosai. sallama yayi ya shigo falon, ajiye wayar tayi ta mike ka karbi jakar hannu shi, tana mishi barka da dawowa. waje ya nema ya zauna,yana cewa "wash!gaskia na gaji da yawa, hada min ruwan wanka nayi, Ko gajiyan zai ragu. kusa dashi ta zauna kamar zata shige jikinsa tace "wannan ai aikin aunty humaira ne yau" jawota yayi jikinsa yana shakar daddad'an kamshinta, se da ya gaji dan kansa sannan ya saketa ya dauki briefcase dinsa ya fita ya nufi part din humaira. kuyi hakuri da wannan wallahi se da nayi ya goge. 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳