[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```(The Abandoned Prince)``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *Note:* _Banyi alƙawarin Posting kullum ba😁, sannan kuma labari na ƙagagge, ne banyi shi dan cin zarafin wani koh wata ba, kowa dai yasan da cewa ɗan Adam ajizi ne, dan haka duk wani kuskure da aka samu cikin labarin nan toh a bisa rashin sani ne, ba zan kar6i cin mutunci koh wasu ƙananun maganganu ba, MHIZZ JIDDHERR batada abokin faɗa, kowa nawa ne, dan haka idan kin zage ni koh a 6oye ne na yafe miki😁_ _Bismillahi_Rahmanin_Rahim_ _*YAA WAHHABU,KAMAR YADDA NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA,KASA NAGA ƘARSHEN SA LAFIYA BA TARE DA AN SAMU WATA MATSALA BA,Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum🤲🏽*_ *001...* *Cairo [Egypt]* ..............."My life my rules, nobody has the audacity to interfere in my life, and nobody has the gut to decide what is good or better for me...this is my life so let me live it the way i want it, Your highness ni ba yaro bane why then duk abinda zanyi sai wani ne zai yanke hukuncin hakan,why ba za'a barni nayi rayuwa ta cike da ƴanci ba kamar yadda akasan kowane cikakken ɗan sarki mai ragamar mulki a ƙasa ba?, am tired, am fed up with all this shit, so let me be, i need freedom...so freed me from all this...Please" ya ƙarashe cikin cize haƙora yana kallon farin dattijon dake kishingiɗe kan kujerar alfarma inda fuskar sa ke fitar da tsantsar 6acin rai. A fusace ya juya ya fara tafiya, daidai isowar sa bakin ƙofa ya tsinkayo muryar dattijon nan. "ZEEYAD!" ya ƙira shi cikin kakkausar murya. Runtse idanu yayi yana dakatawa ba tare da ya juyo ba. Miƙewa dattijon nan yayi daga kan Kujerar sa yayin da fadawan da suka zagaye shi suka shiga gyara masa doguwar alkyabar dake jikin sa. "How dare you hun?, babu wani mahaluƙi da ya ta6a karya koh ƙetare dokar da na gindaya a wannan masarautar, yau kai ɗan da na haifa baka isa ka karya min doka kuma na kyaleka ba, dan kana gudan jini na ba hakan na nufin zakayi dukkanin abinda kaga dama kuma na barka ba, dole ne kabi doka kamar yadda kowane mahaluƙi keyi a masarautar nan, idan kuwa ba haka ba lallai zaka fuskanci hukunci mai tsanani." A fusace ya juyo yana fuskantar Uban nasa yace "I know it,I know you will never change,your mind has already been poisoned, but sooner or later zaka gane cewa what you're doing is totally wrong Father, am your Son your own flesh and blood, but you never gave me a Fathers love..." "ZEEYAD!, Enough of this Nonsense...." "You better keep your mouth shut,save your words it maybe useful for you next time, this is between me and my Father, so you better not interfere in it, understand?" ya faɗa cikin katse ta yana aika mata da mugun kallo. "ZEEYAD!" ya Faɗa yana mai wanke sa da wani irin zazzafan mari. "Ashe bakada kunƴa har haka bansaniba?, a matsayin uwa take a wurin ka." "Ba uwata bace, Mahaifiya ta ta daɗe da mutuwa kowa yasan da hakan,wannan matar ba mahaifiya ta bace, this selfish and disgusting woman here is nothing but a mess to our Family" ya faɗa yana nuna ta da yatsa,inda kuma idanun sa suke daɗa canza launi zuwa jaa. "ZEEYAD!" ya faɗa a zafafe yana sake ɗaukesa da wani marin. Hannun mahaifin nasa ya ruƙo kafin ya shiga dukan kansa dashi yana faɗin "Beat me, beat me as hard as you can, you enjoyed it right, you enjoyed beating your Only lovely son don't you, ka tsane ni koh, then why don't you just kill me Dad?." Sosai ran Mahaifin nasa yayi mugun 6aci,wanda kallo ɗaya zakayi masa ka firgice tsabar zallar kwarjini dama kuma jinin sarautar dake yawo a jijiyoyin jikin sa. Wani marin ya sake ɗauke ɗan nasa dashi kafin yace "Kuje ku ɗauke sa,sannan ku tabbatar da kunyi masa hukunci mai tsanani wanda koh da kuɗi aka basa nangaba ba zai sake sha'awar aikata abinda yayi ba yanzun" ya ƙarashe faɗa yana kauda kansa daga kallon da ɗan nasa keyi masa. Da umarnin Sarki suka ƙaraso wurin tare da kamasa sukayi waje dashi,ba tare da yayi gardama ba yabi su,kasancewar hakan ya rigada ya zame masa jiki. Kallon Juna itada ɗan saurayin dake kusada ita sukayi kafin duk su saki wani irin murmushi mai cikeda zallar ma'anoni iri-iri. Wani irin ɗaki da ya kasance kamar Kurkutu aka jefa sa kafin a garƙame kwaɗo a ƙofar sukayi gaba suka barsa. Bakin ƙofar ya matso yana kama ƙarafunan ƙofar, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci irin tsantsar 6acin ran dayake ciki. Kansa ya ɗaga sama yana kallon yadda hadari ya haɗu wanda ƙiris take ruwa ya sauƙo. Sam bai damu ba,sai ma samun ƴar ƙarfen gadon dake ajiye a ɗakin da yayi ya kwanta fuskar sa na fuskantar sama. Sama da shekaru goma na cikin rayuwar sa yana tafiyar da ita ne cike da ƙunci da wahala tun bayan mutuwar mahaifiyar sa,inda ya kasance bashida kowa face mahaifin nasa wanda yake tunanin zai zame masa gatan sa,sai dai kash! akasin hakan ta kasance wanda tun bayan mutuwar mahaifiyar tasa ya rasa gane kan mahaifin nasa kwata-kwata,balle ma dayake ƙarƙashin kishiyoyin uwa har uku wanda tunda ya taso bai ta6a samun wata kulawa ta musamman daga gare su ba sa6anin ƴaƴan cikin su da suka haifa. ZEEYAD,matashin yaro mai kwazo da kaifin basira,Dukda mulki da ƙarfin iko irinta mahaifin sa hakan bai sanƴa shi fita daga cikin ƙangin rayuwa mai cike da ƙunci da rashin ƴanci ba. A kaf cikin yara Shida da mahaifin sa ya mallaka babu marar gata kamar sa,Makaranta mai tsada,Tsadaddun sutura irinta ƴaƴan manƴan sarakuna,tsantsar ƙauna daga wurin mahaifa,rayuwa mai cike da jindaɗi da ababen more rayuwa iri daban-daban kowane yaro dama kuma ƴaƴan ruƙon gidan sun mallake sa sa6anin shi da koh almajirin cikin gida ya fisa gata. ZEEYAD yaro ne mai ƙoƙari sosai dukda kasancewar yana cikin ɗaya daga cikin makarantu masu sauƙin kuɗi a ƙasar hakan bai sanƴa guiwar sa ta sace ya kasa yin abinda zai fice shi a rayuwa ba. Dukda cewa dukkanin yaran gidan ba a ƙasar suke karatu ba hakan bai sanƴa shi jin baƙin cikin da zai hana sa cigaba ba,burin sa shine ya samu ya jona makarantar gaba tunda ya kammala karatun secondary ɗinsa,ya jona Jami'a kasancewar sa na son zama hamshaƙin ɗan kasuwar da duniya keji dasu. ZEEYAD yaro ne mai tarin baiwa,6oyayyiyar baiwar da babu wani mahaluƙi da yasan sa dashi. Dukda kasancewar sa ɗa namiji babba a wurin mahaifin nasa hakan bai hana sa nuna masa *TSANTSAR ƘIYAYYA* da warayya a tsakanin sauran ƴaƴan nasa ba. Koh dan ya kasance mai rauni ne a cikin su wanda ba komai bane ya dame sa,bai kuma damu da shiga harkar da bata shafe sa ba yasa hakan ke faruwa dashi kokuwa tsantsar son zuciya ce kawai dama kuma makirci irin ta kishiyoyin mahaifiyar sa yasa hakan ke faruwa dashi. Ya taso ne a rayuwa ba tare da yasan mecece soyayya ba sai akasin ta wato tsantsar ƙiyayya. Tun bayan mutuwar mahaifiyar sa bai sake dariyar farin ciki ba,yau shekaru goma kenan,laifi kaɗan ne zaiyiwa mahaifin sa ya sanƴa a hukunta shi,hukunci mai tsanani,wanda koh a cikin bayi sai wanda ya aikata babban laifi akeyiwa hakan. Dayawa daga cikin bayi sun fisa gata,wanda hakan yawancin su ke ɗaukar alhaƙin hakan wurin yi masa dukkanin abinda suka so domin kuwa dasu dashi ɗin babu wani bambamci tsakanin su,kamar yadda suke faɗa. A yau yanada shekaru Ashirin a duniya sai dai koh da da wasa bai baryin addu'a wurin neman taimako daga wurin wanda ya dace kuma maji roƙon bayin sa ba. Da akwai lokacin da ya gindaya wa kansa na zama cikin wannan ƙunci da wahalar da zaran lokacin nan ta cika kuwa,tabbas ba zai saurarawa koma waye ba,kama daga kan Mahaifin nasa dama kowa dake cikin Masarautar nan,amma kafin burin sa ya cika dole ne ya samu damar tseratar da rayuwar sa daga wannan kangin wuyar da yake ciki,ta haka ne kaɗai burin sa dama kuma mafarkin sa zai zamto gaskiya,da zaran kuma hakan ta faruwa toh tabbas kowa zaiji *A JIKIN SA..............* *Share Fisabillah👏🏽* *MHIZZ JIDDHERR........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```(The Abandoned Prince)``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *Note:* _Banyi alƙawarin Posting kullum ba😁, sannan kuma labari na ƙagagge, ne banyi shi dan cin zarafin wani koh wata ba, kowa dai yasan da cewa ɗan Adam ajizi ne, dan haka duk wani kuskure da aka samu cikin labarin nan toh a bisa rashin sani ne, ba zan kar6i cin mutunci koh wasu ƙananun maganganu ba, MHIZZ JIDDHERR batada abokin faɗa, kowa nawa ne, dan haka idan kin zage ni koh a 6oye ne na yafe miki😁_ _Bismillahi_Rahmanin_Rahim_ _*YAA WAHHABU,KAMAR YADDA NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA,KASA NAGA ƘARSHEN SA LAFIYA BA TARE DA AN SAMU WATA MATSALA BA,Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum🤲🏽*_ *002...* ................A firgice ya tashi sakamakon sauƙar ruwan sanƴin da yaji an kwara masa a jiki. "Kai ƙasƙantacce marar galihu, gari ya rigada ya waye gara ka fito ka kama ayyukan da kasan kana yi tun kafin ran sarki ya sake 6aci ya sanƴa ayi maka horor da tafi wannan" cewar bawan dake gadin gidan kurkukun. Wiping fuskar sa yayi da hannun sa yana aikawa wannan bawa wani irin kallo da shi kaɗai yasan ma'anar sa. "Ba zaka tashi bane ka tsare ni da wadannan firgitattun idanun naka yawa na Aljanu, ka sani sa'a ɗaya kaci na matsayin ka ɗan sarki da babu abinda zai sanƴa na hukunta ka da wannan kallon da kakeyi min." Dariya sauran masu gadin suka sanƴa kafin ɗaya daga ciki yace "Toh ai koh ka hukunta shi ba laifi bane, ubansa ma yakeyi masa wannan horor balle kuma kai da kake matsayin mai kula da dukkanin abinda yakeyi, ai daɗin yin maganin sa kenan dan kuwa koh ya kai ƙara babu wani matakin da za'a ɗauka." Dariya suka sake sanƴawa kafin na farkon yace "Ai kawai ina raga masa ne, amma lokaci na zuwa da nima zan aiwatar da nawa hukuncin akansa hahaha." Sunkuyar da kai yayi yana jinsu, kafin kuma daga bisani ya buɗe masa ƙofar ya fito bayan sun gama ci masa mutunci. Ƙafa ya sanƴa masa take yaci tuntu6e ya faɗi, nan take suka sake sanƴa wata dariyar kuma. "Lalatacce kawai, tashi" ya faɗa yana bugun sa da ƙafar sa. Miƙewa yayi ya karkaɗe jikin sa kafin ya nufi tsakiyar Ƙaton gidan yarin inda wata ƙatuwar rijiya take. Ruwa ya fara janƴowa kafin ya kwara a jikin sa yana sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, dan kuwa sosai zuciyar sa ke tafarfasa. ƙara janƴo wani ruwan yayi kafin ya shiga gabatar da alwala, ganin haka yasa wannan arrogant mutumin nan ƙarasowa wurin sa. Ball yayi da gugar kafin ya finciko shi ya tsayar dashi yana faɗin "Naga rashin kunƴar ka ƙara gaba take, aiki ne birjik a gaban ka,amma kazo nan kana wani shashancin kuma daban." Kallon sa yayi da gajiyayyun idanun sa kafin kuma ya furzar da hannun sa daga riƙon da yayi masa yace "Sallah zanyi, ba zan iya ta6uka komai ba ba tare da nayi sallah ba, ba shashanci bane,haske ne babba a cikin rayuwa ta." Sunkuyawa yayi ya ɗauko gugar ya shiga jan wani ruwan,shaƙo wuyar sa yayi ta baya kafin ya kifar da kansa zuwa saitin rijiyar kamar wanda zai jefa shi ciki yace "Kai ƙasƙantacce baka isa ina baka umarni kuma kaƙi bi ba, lallai naga kana wasa da rayuwar ka,babu abinda zai hana ni jefa ka cikin rijiyar nan muddin ka sake yunƙurin yin jayayya dani." "Mai ke faruwa ne anan?" Suka tsinkayo wani murya ya faɗi hakan. Da sauri ya sauƙo da ZEEYAD ɗin yana ture sa gefe kafin ya juyo zuwa ga wanda yayi maganar,inda yayi saurin rissinawa yana faɗin "Yallabai nayi dashi akan yaje ya gabatar da aikin da sarki ya sanƴa sa amma kuma yanayi min gardama." Ƙarasowa wannan mutumin yayi wanda ke sanƴe da kayan fatar damusa kamar yadda sauran dakarun wurin ke dashi duka,sai dai nasa ya ɗan bambamta da nasu. Kallon ZEEYAD dake ta faman huci yayi yace "Ku kyale shi yayi abinda yaga dama, zaku iya komawa bakin aikin ku." "Amma Yallabai..." "Banason jin wata magana" ya faɗa cikin katse shi. Wani irin mugun kallo ya watsawa ZEEYAD kafin yace dashi "Ka kammala duk abinda zakayi kazo ka same ni." Juyawa ZEEYAD ɗin yayi da niyar barin wurin kafin ya tsinkayo muryar mutumin nan na faɗin "Yarima ZEEYAD kada ka kula abinda Mulah yake faɗa maka a kullum..." "Babu ruwanka dani, ka tsaya a matsayin ka na sarkin Dakaru, furucin ka babu abinda zai ƙaramin sai ƙunar zuciya da 6acin rai" yana faɗin haka ya bar shi nan tsaye a wurin. Da kallo sarkin Dakaru ya bishi dashi kafin ya saki murmushi ya juya ya bar wurin. Hanƴar Babbar Masarautar ya nufa, sosai yake a galabaice ga kuma ƴunwa da take nuƙurƙusar sa,a haka ya daure ya ƙarasa bakin ƙofar shiga farfajiyar masarautar. Wucewa yayi niyar yi sai dai yaga masu tsaron wurin sun sanƴa dogin takoban su masu bakin kibiya sun toshe hanƴar shigan. Ɗagowa yayi ya kallesu yace "Mai hakan ke nufi?." "Mai kake buƙatar ji kuwa?, saƙo bai zo mana cewa ka aiwatar da umarnin sarki ba, ba kai babu shiga ciki muddin baka kammala aikin da aka sanƴa ka ba" cewar ɗaya daga cikin dakarun. "Babu inda zanje sannan ba zanyi wani aiki ba muddin ba'a barni na shiga ciki ba, wannan gidan namu ne ba na kowa ba a cikin ku, dan haka bakuda damar hana ni shiga." Dariya sukayi kafin ɗaya yace "Gidan ku ne, amma kuma ai ba'a girmama ka kamar ɗan gidan." "Wannan ba damuwar ku bace, ku buɗamin yanzun nan" ya faɗa a tsawace. Ƙin kulasa sukayi hakan yasa shi bangaje su ya tsallaka ya wuce. "Ka dakata anan Yarima ZEEYAD kokuma na harbe ka" faɗin ɗaya daga cikin su yana saita masa kibiyar kwari da baka. Tsayawa yayi yana lumshe gajiyayyun idanun sa tare da cize haƙora ya juyo yana kallon su, dawowa yayi ya wuce su ba tare da yabi ta kansu ba ya bar wurin. Da Kallo suka bisa kafin ɗaya yace "Haƙiƙa yana bani tausayi." Kallon sa ɗayan yayi yace "Rayuwar sa abar tausayi ce,sai dai fah ka kiyaye yin magana akan tausayin da kake yi masa a koh ina,dan kuwa wannan Masarautar cike take da munafukai" yana faɗin haka ya tsuke bakin sa tare da yin shiru,hakan yasa shima na farkon yin shiru suna kallo ZEEYAD ɗin har ya 6acewa ganin su........... __________________ "ZEEYAD,ZEEYAD ka tsaya mana" ya faɗa yana shan gaban sa. "ZEEYAD maiyasa kake haka?, kazo muje gidan mu kayi wanka kaci abinci mana idan yaso sai ka wuce wurin aikin naka." Kallon ɗan saurayin dake tsaye gaban sa wanda ba zai wuce sa'an sa ba yayi yace "Nagode Sadeeq da wurin sallahr da ka bani,amma ba zan iya zuwa gidan ku ba gudun kada na sanƴa ku cikin matsala." "Wane irin matsala kuma ZEEYAD, ka manta abinda Baba yace ne?, duk ranar da aka kore ka daga gidan ku zaka iya zuwa gidan mu ka huta kayi duk abinda kake so, ZEEYAD ni fah abokin ka ne dan Allah kazo muje mana." "Sadeeq da akwai idon mutane a kaina, muddin na bika gidan ku har na aiwatar da wani abin toh fah ka sani sarki ba zai ta6a kyale Mahaifin ka ba, ka rabu dani Sadeeq banason wani abu ya same ku sabida ni." "Dan Allah ZEEYAD." "Just leave me alone, please!" ya faɗa a tsawace yana yarfar da hannun Sadeeq ɗin daga jikin shi kafin ya wuce a fusace zuwa inda zasa. Saurin mara masa baya Sadeeq yayi yana faɗin "Ba zan jure ganin ka cikin wannan halin ba ZEEYAD muje ni zan tayaka da aikin koma menene." Babu wanda ya kula ɗan uwansa haka suka ƙaraso filin da aka ke6anta kawai dan horar da bayi. "Sabida kai ka kawo taurin kai duniya sai yanzu kake zuwa?" cewar Mulah yana aika masa da kallo mai cike da tsantsar mugunta. "Kai kuma fah daga ina?" ya faɗa yana kallon Sadeeq. "Ni...na...nazo ne taya shi yin aikin." "Iyeh, wato kai har lalacin naka ta kai haka,sai ka kawo mai taimaka maka?." "A'a wallahi ba shi ne ya gayyato ni ba nine na kawo kaina" cewar Sadeeq ɗin. "Kai yimin shiru munafuki kawai" ya faɗa yana ture shi. "Sadeeq" cewar ZEEYAD ɗin yana ɗago sa tsaye. "Duk abinda zakayi kayi shi a kaina Mulah,ba sai ka ta6a wani koh kaji wa wani rauni a kaina ba" ya faɗa yana kallon Mulah ɗin. "Au haba, bari mu gani koh zaka iyayin aikin kai kaɗai kokuma murɗaɗɗen jikin duk na banza ne babu ƙarfin, kai kuma maza ka 6ace daga nan wurin yanzun nan idan ba so kake nayi maka 6alli-6alli a maƙogoro ba" ya faɗa yana ciro wata ƴar ƙaramar wuƙa daga bakin takalmin sa. Juyawa ZEEYAD yayi zuwa ga Sadeeq yace "Sadeeq ka bar nan wurin yanzun nan." Girgiza kai Sadeeq yayi yace "Zan tafi amma ka sani ina nan ina jiran ka a mahaɗar mu, dan Allah kayi a hankali." Kai ya jinjina masa kafin Sadeeq ɗin ya juya ya bar wurin, cakumo rigar sa ta baya Mulah yayi har zuwa cikin inda jibgin ayyukan suke yace "Buɗe idanun ka ka gani da kyau ya kai ƙasƙantaccen Yarima, wadannan ayyukan duk gabaɗaya kai zakayi su, sannan awa uku kawai aka baka, ka sani ka rigada ka cinƴe awa ɗaya a yawace-yawacen banzan da ka gama yi, yanzu awa biyu ya rage maka kayi clearing nan wurin baki ɗaya." Tunda Mulah ya fara magana ZEEYAD ke kallon uban Karar ƙaiƙayin dake jibge a wuri ɗaya, ga kuma manƴa-manƴan ƙayoyin masu kama da kibiya a jikin su, uwa uba kuma da hannun sa zai yaye su baki ɗaya ya kai chan ƙololuwa ya zubar. "Wannan aikin ba na hannu bane, ina shovel da wheelbarrow?." "A gidan uwarka, kaje ka tashi uwarka dake kwance cikin kabari tazo ta baka." Iya ƙololuwa ran ZEEYAD yayi mummunar 6aci wanda bai san sadda yayi kukan kura ya kaiwa Mulah uban naushi a baki ba, take ya zube ƙasa inda kuma baiyi ƙasa a guiwa ba ya haye kansa ya cigaba da basa wasu irin azabbabun naushi a fuska, kai kace ba ƙarfin sa bane yake aikata wannan aika-aikar. "How dare you?, she is my mother, she is a queen, the greatest queen among all, ba zan ta6a kyale duk wanda yace zai zage ta ba, zan iya yafe komai amma ba zan ta6a yafewa wanda yaso cin mutuncin mahaifiya ta ba,babu abinda tayi maka, dukkanin ku kun kasance butulallu ne,babu irin kyautatawar da mahaifiya ta batayi muku ba sadda take raye,why then zaka zage ta bayan mutuwar ta?, ba zan ta6a kyaleka ba yau ɗinnan, sai na kashe ka, sai na kashe ka Mulahhh" yana faɗin hakan ne cikin azababbiyar 6acin rai yayin da hannun sa bai gushe daga kaiwa Mulah duka ba, yayin da ake ta kiciniyar ɗaga sa amma an kasa yin hakan. Babu wanda yayi nasarar ɗaga ZEEYAD daga kan Mulah har sai da ya tabbatar da Mulah baya motsi tukun kafin ya barshi yana sauƙe wata iriyar azababbiyar huci, yayin da fuskar Mulah ba'a cewa komai wurin muni dama chan ba kyan gani ne dashi ba, balle yanzu da yasha uban bugu. Hayaniya ce ta ƙecere a wurin inda kowa ke mamakin yadda akayi kamar ZEEYAD ya kai Mulah ƙasa yake bugu harda sumar dashi. Hannayen sa ya shiga dubawa kafin ya kalli fuskar Mulah ganin abinda ya aikata ne yasa shi saurin sauƙa daga kansa, kafin kuma yayi hanƴar fita daga wurin cikin gudu. Wurin haɗuwar su da Sadeeq yaje inda ya same sa zaune gindin wata ƙatuwar bishiya yana zaman jiran sa. Hango sa da Sadeeq yayi ne yasa shi saurin miƙewa yana taro sa da faɗin "Har ka gama?, i know you can do it abinda yafi aikin nan ma zaka iya" ya faɗa cikin murmushi yana bubbuga kafaɗar shi. "Zeeyaaaddd" sukaji an ƙira da ƙarfi, juyawar da sukayi suka hango tawagar abokan Mulah ne ke tunkaro su, ba tare da ya tsaya yin wata-wata ba yace da Sadeeq "Run" ya faɗa yana fita da gudu ganin haka yasa Sadeeq da bai fahimci komai ba mara masa baya shi ma cikin gudu........... *Share Fisabillah* *MHIZZ JIDDHERR.........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E YA D* ```(The Abandoned Prince)``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *004...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ .............Kujera aka ja masa ya zauna kafin ya shiga ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya. Idanun sa ne suka sauƙa kan ZEEYAD da kansa ke sunkuye take yaji ransa ya 6aci,juyar da kansa yayi tare da buɗe tray ɗin breakfast ɗin dake gaban sa tare da ɗaukar fork da wuƙar da aka ajiye dan cin abincin,kafin yayi bismillah ya fara ci. Ganin haka ya sanƴa kowacce buɗe nata abincin ta shiga ci,sa6anin ZEEYAD da bai buɗe nasa ba kuma har yanzu bai ɗago ba. "ZEEYAD my dear,eat your food" faɗin Sarauniya Naseeba tana kallon sa. Kallon ta Sarauniya Hafeezah tayi ta ƙasan ido kafin kuma ta kalli ZEEYAD ɗin shima a zuciyar ta tace _"What on earth is going on between them, she seems very nice to him, koma dai menene i must find it out very very soon"_ ta ƙarashe tana kallon ZEEYAD. Kai ya jinjina tare da ɗaga murfin da aka rufe tray ɗin dashi,ƙurawa abincin dake kan tray ɗinsa idanu yayi yana jin wani abu na taso masa daga chan ƙasan zuciya. Slice ɗin bread ne kwaya biyu sai kuma wata fale-falen soyayyiyar kwai da bata wuce yayi mata loma ɗaya koh rabi ba, kasa ɗagowa yayi ya kalle su dan kuwa yasan kowa shi yake kallo,dukda baya cin kwai haka nan ya daure ya sanƴa hannun sa tare da ɗaukar bread guda ɗaya ya haɗa da kwai ɗin tare da yin basmala ya kai bakin sa. Kallon sa kawai Sarauniya Hafeezah keyi dan ganin reaction ɗinsa,dan kuwa itace wacce tasa akayi masa serving ɗin wulaƙancin nan. Idanun mai Martaba ne ya faɗa kan tray ɗinsa,magana zaiyi sai dai yaji bakin sa tayi nauyi ya kasa buɗe ta,hakan ya sanƴa sa maida hankalin sa kan abincin da yake ci. _"Mai kuma wannan yaron ke son nunawa,kamata yayi ya tada husuma anan wurin ta yadda zai fusata mai Martaba a yi masa hukunci mai tsanani,sai dai ya fuske yana cin abincin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata damuwa ba,what is he actually up to?"_ cewar Sarauniya Hafeezah tana kallon sa har yanzun. Bai iya cinƴe koh rabin wanda ya ɗauka ɗin ba sakamakon kwai ɗin da ya haɗa ta da ita yaji zuciyar sa na tashi,ga kuma jiri da ya fara ji duka a lokaci ɗaya. Murmushi Sarauniya Hafeezah ta saki a cikin zuciyar ta tace _"Wow"_ Tashi yayi tsaye da kyar sakamakon kansa da yakejin tana juya masa,runtse idanun sa yayi yana sake ware ta tare da jijjiga kansa koh zai dawo saiti. Ya san ba zai ta6a dawowa saiti yanzun ba indai har ba wai ya samu hutu da bacci bane,komawa yayi zaune kan kujerar tare da ɗaukar fork ɗin dake kan tray ɗin abincin sa yana damƙe ta a hannun sa inda yake trying so very hard ganin ya dawo nutsuwar sa,dan kuwa har dishi-dishi yake gani. Miƙewa mai Martaba yayi bayan ya gama cin abincin sa tare da barin dining area ɗin ya haura sama. Tashi Sarauniya Nazeerah tayi ba tare da ta tanka ba itama ta fice zuwa part ɗinta inda ya saura Sarauniya Hafeezah da kuma Naseeba. Murmushi Sarauniya Hafeezah tayi tare da miƙewa itama ta fice ta zuwa nata part ɗin. Kallon sa Sarauniya Naseeba tayi kafin kuma ta hau duba arear wurin dan ganin babu hankalin wanda ke kansu, tasowa tayi ta ƙaraso wurin sa tana shirin kai hannu jikin sa ne yace "Don't you dare...don't you dare touch me" ya faɗa cikin muryar dake nuna alamun yana jin jiki. Murmushi tayi tare da ɗago fuskar sa tana kallo tace "I can see that you are so allergic to Egg, come on zo muje part ɗina nikuma zan kula da kai yadda yakamata, irin kulawar da koh a wurin Mahaifiyar ka baka same sa ba." Hannun ta ya buge yana miƙewa tsaye ya fara tafiya cikin tangaɗi. Fizgo sa tayi ta baya tare da riƙe sa gamm idanun ta na yin jaa tace "Babu inda zaka ZEEYAD, dan kana ganin ina nuna maka kulawa a gaban sauran mutane ba hakan na nufin na baka umarni kuma kaƙi bi bane ba, ya zama dole ne ka biya min buƙata ta idan kuwa ba haka ba sai na tabbatar da na ya6a maka baƙin fentin da har ka mutu ba zaka ta6a zama fari a idanun jama'a ba." "You are such a Monster" ya faɗa yana fuzge hannun sa daga riƙon da tayi masa. Murmushi mai ciwo tayi tace "Ka dube ni da kyau ZEEYAD, har yanzu ni sabuwar jini ce wannan tsohon uban naka babu abinda zai iya yimin,wanda kafin na gansa ma wataran na kan shafe watanni, a haka kake tunanin zan zauna ba tare da namiji ba a matsayi na ta lafiyayyar mace?". Kai ya girgiza kafin kuma ya shiga tafiya inda tabi sa da kallo a zuciyar ta tana faɗin _"You could avoid me as hard as you can, but i will make sure that i get what i have been craving for from you."_ A hanƴar sa ta fita yaci karo da sarkin Dakaru,ganin halin da ZEEYAD ɗin yake ciki ne yasa shi saurin riƙo sa tare da faɗin "Yau ɗinma kwai aka sake baka kaci?, what a cruel world." Dakarun dake jeka ka dawo daga wurin ya sanƴa su kama ZEEYAD ɗin su kai sa ɗakin sa,ba tare da musu ba suka zo suka kama sa dan aiwatar da abinda ya umarce su. Har ɗakin sa suka kaisa suka kwantar kan motsatsiyar katifar sa, kafin su fito suna mai ja masa ƙofar. "She just wants to see me dead" ya faɗa chan ƙasan muryar sa yana sauƙe nannauyar numfashi. Ya sha fama kafin ya samu wani irin wahalallen bacci ya ɗauke shi........ **************** .............A hankali ya shiga buɗe idanun sa da sukayi masa nauyi yana ware su kan 6antararriyar ceiling ɗin ɗakin nasa da idan akayi ruwa mai ƙarfi da iska zata iya faɗowa kafin kuma ya miƙe zaune yana jinsa dama-dama. Tashi yayi ya fito waje tare da ɗaukar wata motsatsiyar bokitin ƙarfe ya nufi wurin tuƙa-tuƙar da aka ware wurin wankin bayi mata ya ɗebi ruwa inda duk ta 6u66ule ruwan na tsiyayewa. Haka nan ya kawo ta zuwa banɗakin da yake wanka,Wankan yayi da kyau kafin ya fito ya koma ɗakin sa. Koɗaɗɗiyar Ghana-Must go ɗinsa da duk ta yayyage kamar wanda aka kwato daga bakin kura ya janƴo kafin ya shiga bincika kayan da zai sanƴa a ciki. wata jallabiya mai hula a baya brown colour wacce itace mai ɗan kyau a cikin kayan nasa ya ciro duk da itama wasu wuraren sun 6ule kwari sun cinƴe amma haka nan ya sanƴa abarsa. Wata ƴar ƙaramar drawer ya buɗe ya ciro wata sarƙa,sai sheƙi take da ɗaukar ido, jujjuya ta yayi a hannun sa tare da buɗe abin dake jikin sarƙar inda hoton wata Kyakkyawar mace ta bayyana fuskar ta ɗauke da murmushi, murmushin shima yayi kafin yace "You are the only treasure i have left." maida abin yayi ya rufe kafin kuma ya sanƴa sarƙar a wuyar sa yana cusa ta cikin rigar sa. Baƙar sumar kansa dake ta taruwa kullum bata samun isasshen aski da gyara ya taje inda ta bazu masa har kan kafaɗa,kafin ya shafa mai da jikin sa ya fito. Hanƴar barin fadar ya kama har ya fice bai tanka wa kowa ba dukda kuwa kallon da bayi da dakaru dayawa ke binsa dashi suna gulmar sa hakan sam bai sanƴa sa yaji haushi ya tanka musu ba, dan kuwa koh kaɗan hakan baya basa haushi face ma gani yake wata daraja ce da Allah ya bashi tunda har ana iya nuna sa idan yana tafiya koh ayi maganar sa a bayan idanun sa. Tafiya mai nisa yayi kafin ya iso gidan su abokin sa Sadeeq, kasancewar gidan ba baƙon sa bane ya sanƴa sa shiga har ciki bakin sa ɗauke da sallama Sadeeq ɗin ya tadda da iyayen sa da ƙannen sa zaune suna cin abinci, hakan ya sanƴa shi saurin komawa. "Abhi...ZEEYAD ne" cewar Sadeeq ɗin da ya miƙe tsaye dan kiran ZEEYAD ɗin, sakamakon kallon da mahaifin sa ke binsa dashi ne yasa shi dakatawa. "Daga yau nayi maka iyaka tsakanin ka da yaron nan, kai ba ɗan kowa bane dan haka ka tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ka na ɗan talaka mai ƙoƙarin neman na kansa tun kafin a kwace wannan matsayin daga gare ni, kana sane da irin kashedin da mahaifin sa Sarki Abbas yayimin akanka da ɗansa, ba zan iya ja da Adalin sarki mai nagarta irinsa ba koh da kuwa ina da ikon yin hakan balle kuma da banida shi, kai kanka kasan Sarki Abbas baya magana sau biyu, dan haka rabuwar ka da yaron sa shine alkhairi a tsakanin mu baki ɗaya sannan kuma shine zaman lafiyar mu." "Amma Abhi indai har sarki Abbas adali ne kamar yadda ka faɗa maiyasa yake muzgunawa ZEEYAD kamar wanda ba ɗan cikin sa ba?, koh da ƴan waje baya yi musu abinda yakeyi masa." "Wannan ba damuwar ka bace Sadeeq, wannan tsakanin su ne, bakasan komai ba dan haka ka bar komai a yadda yake kai dai naka idanu ne, sannan koh da da wasa kada ka kuskura makamancin wannan maganar ta fito daga bakin ka a wani wurin, zaka iya zuwa ka sallame sa ya tafi idan kuma ba zaka iya ba ni zan fita da kaina na faɗa masa." Shiru Sadeeq yayi yana kallon mahaifin nasa kafin kuma daga bisani yayi hanƴar waje dan aiwatar da abinda mahaifin nasa ya umarcesa, tsinkayo muryar sa yayi yana faɗin "Sannan kuma kada ka manta da faɗa masa cewar ya fita daga hanƴar ka, koh da a hanƴa kukayi kici6us dashi ku nuna bakusan juna ba." Juyowa yayi ya kalli mahaifin nasa kafin kuma ya jinjina masa kai ya fice. A bakin dakalin gidan su ya sami ZEEYAD ɗin zaune yana jiran shi. Cikin sanƴi ya ƙaraso wurin sa, ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa tare da yin murmushi yace "Ka gama?." Kai Sadeeq ɗin ya jinjina masa zuciyar sa a cunkushe dan baisan mai zai cewa ZEEYAD ɗin ba. "Alright, shall we?" ya faɗa yana miƙewa tsaye. "ZEEYAD" Sadeeq ɗin ya kiraye shi. Kallon sa ZEEYAD yayi nan yaga damuwa fal fuskar Sadeeq ɗin ba kamar yadda ya saba ganin sa kullum cikin walwala da nishaɗi ba idan suna tare. "ZEEYAD, inason faɗamaka wani abu amma fah ka sani babu yadda na iya ne, Umarnin mahaifi na kawai zan bi, inaso daga yau...." shiru yayi yana kallon ZEEYAD ɗin da ya zuba masa idanu yana kallo dan son jin abinda zai faɗa. "Ba zaka iya faɗa masa bane?" ya tsinkayo muryar Mahaifin nasa ta bayan sa. Ƙarasowa yayi wurin su kafin ya kalli ZEEYAD yace "Kayi haƙuri ɗa na ZEEYAD, amma abinda zan faɗamaka a yanzu ƙila kaji babu daɗi, inason daga yau ka rabu da Sadeeq sannan kuma kada ka sake nunawa ka sanshi a wani wurin koh da kuwa haɗuwa kukayi a hanƴa, ZEEYAD ka tsaya a matsayin ka na ɗa ga shugaban wannan ƙasa, shima Sadeeq zai tsaya a matsayin sa na ɗa ga sarkin manoman wannan gari, ina tsoron faɗamaka cewa alaƙar ka da Sadeeq ɗana daga yau babu ita..." "Alright" ya katse shi cikin rawar murya kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Duk dan nine abinnan yake faruwa, kowa bayason alaƙa ta tsakanin sa da ɗansa, kowa gudu na yakeyi, ba sabon abu bane a wuri na, am already used to it, so why should i feel bad dan Mahaifina ya yanke alaƙa ta da Sadeeq?, koh bakomai yanada wasu abokan ai, dama ni kaɗai akeson muzgunawa kuma kullum suna samun nasarar hakan, i won't put the blame on anyone of you coz i guess i was born to suffer, ƙaddara ta ce hakan dan haka kada ku wani damu kanku, kuma zanyi duk abinda kakeso sabida ai kaima ka ɗauke ni ne tamkar ɗanka...Unlike my Father, so why should i said No to what you ask?, nima ba zan so wani abu ya sami kyakkyawar Family ɗinku ba, koh bakomai kunyi min gata a rayuwa, and now....ba zanyi musu da duk abinda kace ba, zanyi yadda duk kace dani kuma zan rabu da Sadeeq" ya ƙarashe cikin jinjina kai. "ZEEYAD..." "Sadeeq, in dai har ni zanji maganar mahaifin ka, maiyasa kai ba zaka ɗau abinda zai faɗamaka ba, you know what?, na daɗe ina fatan wannan ranar tazo ta, ranar da za'a raba ni da kai, ba dan komai ba sai dan kawai rayuwar ka ta inganta, dan kuwa rayuwa tare dani dai-dai take da rugujewar duk wani farin ciki naka kaima, am Glad Sadeeq, so very Glad" yana faɗin haka ya juya yayi tafiyar sa trying so very hard to control his tears. Da kallo Sadeeq da mahaifin sa suka bi ZEEYAD dashi dukkanin su zuciyoyin su cike da tausayin sa har ya 6acewa ganin su. Dafa kafaɗun Sadeeq yayi yace "Kayi haƙuri Sadeeq, nasan kanajin zafin rabuwa da aminin ka a zuciyar ka." Saurin goge hawayen da suka kawo masa yayi kafin yace "No...inaga hakan shine dai-dai" kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Abhi kace yau zamuje Gona, zamu iya tafiya yanzu?." Kai mahaifin nasa ya jinjina masa kafin kuma ya dafa kafaɗun sa,suka koma cikin gidan............... _Yauwa nace ƴan ZEEYAD fans group kodai kurame na tara ne ni bansaniba🤔, kun iya karanta littafi mai read more biyu zuwa uku amma sharhi ya gagare ku?, toh gaskiya bana kar6an ƴan la6e a cikin group ɗina, almost 300+ participants amma bai wuce mutane biyar bane masu comment, lallai daɗi ne yayi muku yawa toh tsaf yau ɗinnan zanyi aiki a kanku insha Allah😑da ba zan kar6i hakan ba yauwa_ *Share Fisabillah* *MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```(The Abandoned Prince)``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *(MHIZZ JIDDHERR)* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* _Bismillahi_Rahmanin_Rahim_ *003...* ......"ZEEYAD, mai ka aikata ne haka, maiyasa suke bin ka, mai kayi musu?" cewar Sadeeq da har yanzu basu bar gudun ba cikin huci. Tuntu6e yaci ya faɗi a ƙasa, Juyowa ZEEYAD yayi nan yaga ƙafar Sadeeq ɗin na fitar da jini, alamun ciwon da yaji ba kaɗan bane. Kallon tawagar su Mulah da suka kusan isko su yayi kafin kuma yaje da sauri ya kamo Sadeeq ɗin tsaye suka cigaba da gudu. "ZEEYAD, just go ba zamuyi sauri ba, zasu iya taddo mu" faɗin Sadeeq dake ɗingisa ƙafar sa. "You just shut up now, idan ba so kake suyi maka dukan mutuwa ba" faɗin ZEEYAD ɗin. Wani ƙaton ƙarfe suka wullo nan ya same shi a kai, take kuma duk suka zube a wurin,nan kuwa akayi nasarar cafke su. "Kai ɗan iska ƙasƙantacce, har kai ka isa ka aikata wannan mummunar laifin kuma kace zaka gudu?, ba dai a cikin wannan masarautar ba" cewar wani dogari yana ɗago sa tsaye. ZEEYAD kansa ne ke mugun juya masa dan kuwa bibbiyu ma yake ganin su sakamakon abinda suka buga masa a kai, nan aka tusa su gaba daga shi har Sadeeq ɗin zuwa fadar sarki.......... ************ ............Durƙushe suke a gaban mai Martaba da kallo ɗaya zakayi masa ka gano 6acin rai ɗauke akan fuskar sa. Duban sa ya maida kan ZEEYAD da har yanzu baijin kansa dai-dai kafin kuma ya Kalli Sadeeq yace "Ku saki abokin nasa, shi kuma da ya aikata laifin ku tabbatar da kun yi masa hukunci mai tsanani ta hanƴar horar dashi." Kallon sarkin Dakaru yayi yace "Wannan aikin naka ne Najeeb, ka tabbatar ya fuskanci hukunci dai dai da abinda ya aikata." Kai wanda aka kira da Najeeb ya sunkuyar alamun amsa maganar sarkin, kafin kuma ya bada Umarnin fitar da ZEEYAD ɗin. Bayan Fadar ta watse ne ya saura daga mai Martaba sai kuma Uwargidar sa *Sarauniya Nazeerah*. Cike da tsantsar makircin da tayi course akai ta kalle shi tare da faɗin "Allah yaja ran Sarki, amma nace kana ganin wannan hukunci da kakeyi wa ZEEYAD baya yin tsanani kuwa, ka tuna fah ɗanka ne kuma...." "Ya ishe ki haka Nazeerah" ya faɗa cikin ɗaga mata hannu kafin kuma yace "Ina buƙatar ke6ancewa ni kaɗai." Sum-sum ta tashi daga kishingiɗen da take ta fice, nan dakarun ta suka take mata baya zuwa Side ɗinta. Ajiyar zuciya sarki ya sauƙe kafin kuma ya tashi daga kan Throne ɗinsa ya fara yin safa da marwa a cikin fadar. Sosai da sosai har chan cikin ƙololuwar zuciyar sa yake Ƙaunar ZEEYAD wanda ya samo asali ne daga ƙaunar da yakeyi wa Mahaifiyar sa. Lokacin da Mahaifiyar ZEEYAD keda rai babu abinda yafi so da Ƙauna bayan su,sai dai yanzu ganin ZEEYAD ɗin da yake ba ƙaramin baƙan ta masa rai da sanƴa shi fushin da baiyi niyya ba yake. Tsanar da yakeyi wa ZEEYAD ɗin koh maƙiyin sa baya yi masa shi wanda har cikin zuciyar sa ba haka bane ba,sai dai kawai ba zai iya controlling anger ɗinsa bane aduk sadda ya ɗaura idanu akansa. Yayin da ya kasance baya kusa dashi kuma babu abinda yake muraɗi da kwaɗayin gani kamar sa. Ajiyar zuciya ya sauƙe inda kuma wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa akan ƙunci,kai ya jinjina kafin kuma ya bar cikin fadar zuwa ɗakin sa....... ********** .........."Stop being nice to me General, kayi abinda aka umarce ka a kaina, coz that won't change things." Kallon sa sarkin Dakaru yayi kafin ya furzar da iska yace "ZEEYAD, kaci abincin nan tukun, koh da zan hukunta ka ɗin ya zamto da ƙarfin ka." Kallon tray ɗin abincin da akayi serving ɗinsa yayi kamar wani ɗan gidan yari, kafin kuma ya ture yace "Am not eating it, just let me be" ya faɗa cikin rawar murya. Zama sarkin dakaru yayi a gaban shi yace "Look ZEEYAD, being always bored won't make things right, ka rigada ka saba da wannan rayuwar tun kana ɗan shekara goma, dan haka it's now high time da yakamata kayi accepting ƙaddarar ka, babu wani abu da zakayi dan canza ra'ayin mahaifin ka akanka, ba cewa nake ka cire rai da samun sauƙin rayuwa ba, amma yakamata ka kasance cikin farin ciki kullum koh da kuwa kana cikin bad mood ne, ganin ka kullum cikin ƙunci shike baiwa maƙiyan ka damar cigaba da munana maka dan kuwa shi maƙiyi babu abinda yafi tsana kamar ganin farin cikin wanda ya tsana ɗin, shawara ce ZEEYAD kada ka ta6a bari maƙiyan ka su gano weak point naka dan kuwa dashi ne zasu cigaba da muzanta maka kullum, try and change your way of life ZEEYAD and stop being bored always" ya faɗa yana buga kafaɗun sa kafin kuma ya tashi ya fice ba tare da ya jira cewar sa ba. Da kallo ZEEYAD ɗin ya bishi kafin ya maida duban sa kan abincin dake gaban sa, tabbas yana jin ƴunwa sai dai ba zai ci abincin nan ba, dan kuwa ba yarda yayi da sarkin dakarun ba shima. Bayan kamar mintina sha-biyar Sarkin Dakaru ya dawo ɗakin, murmushi yayi ganin koh ta6a abincin baiyi ba, lallai ba ƙaramin jinjinawa taurin rai irin na ZEEYAD yake ba. "So, lokacin hukunta ka yayi ZEEYAD." Ba tare da yace komai ba ya miƙe ,chain aka ɗaura masa a hannaye kafin a tusa ƙeyar sa zuwa waje. Fili ne ƙato aka kawo shi, kafin kuma a kaisa kan wani abu kamar mumbari aka ɗaure masa hannaye a sama. Mutane da dama sun halarci wannan wuri dan ganin wane irin hukunci za'a yiwa Yarima ZEEYAD da yayi faɗa da babban dakare kamar Mulah,a gaban mahaifin sa sarki. Wata Ƙatuwar dorina mai baki uku aka ɗauko,wacce take da tsayi da kauri. Kafin kuma aje ta bayan sa a shiga shauɗa masa ita bisa ga umarnin mahaifin sa. Lafiyayyun bulala ɗaɗɗaya har zuwa Hamsin akayi masa, amma koh gezau baiyi ba balle idanun sa su tara hawaye, zuciyar sa ce kaɗai ke mugun yi masa tafarfasa, dan kuwa yayi alƙawarin ba zai sake yin kuka ba a duk hukuncin da za'a yi masa,dan idan da sabo ya saba. Sunce sa akayi nan ya faɗi a wurin hannayen sa dafe da ƙasa, da idanun sa da sukayi mugun jaa ya ɗago ya kalli mahaifin nasa da shima shi yake kallo. Saurin kauda kai yayi daga kallon da ZEEYAD ɗin keyi masa kafin kuma ya tashi dogaran sa suna mai gyara masa hanƴa tare da yi masa kirare-kirare ya bar wurin............ *TWO DAYS AFTER* Zaune yake yana gasa bayan nasa da yaji shatin bulalar da akayi masa, kasancewar bashida wani mai taimaka masa. Bayan ya gama ne yayi wanka sannan ya shirya cikin ƴar tsofaffiyar kayan sa, kafin ya kama hanƴar zuwa cikin gida, kasancewar ɗakin sa ma a chan bayan gidan yake wurin arean Bayi Mata. A hanƴar sa ta zuwa ne ya haɗu da wata Dattijuwar mata, da kallo ta bisa har ya ɗan wuce kafin tace "Hmm,Yaro kana ganin Rayuwa kai da Masarautar Ubanka." Tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba, ita ɗinma tsayuwa tayi ganin koh zai kula ta, juyowa yayi tare da sake mata murmushin da ya sanƴa ta daskare wa a wurin tana kallon sa har ya 6acewa ganin ta. Cike da mugun sauri ta nufi 6angaren *Sarauniya Hafeezah* dan shaida mata abinda idanuwan ta suka gani. Zubewa tayi a gaban ta tana kwasar gaisuwa. Wani irin Kallo ta watsa mata cike da ƙasƙanci kafin tace "Lafiyar ki kika faɗomin ɗaki haka kamar wacce aka jefo, bayan kinsan yanzu lokacin hutu na ne?" cewar Sarauniya Hafeezah. Cikin 6arin jiki da mugun gulmar dake cinta tace "Allah ya taimake ki Sarauniya ta,mata mafi soyuwa ga sarki *Abbas Ibn Qazeem*, nazo miki ne da wani babban labari yake Sarauniya ta. Murmushi tayi tace "Shiyasa nake Ƙaunar ki Jakadiya Nadiya, domin kuwa a kullum kina kawomin labarin dake sanƴa ni cikin nishaɗi na tsawon kwanaki, ina jinki wane labari kuma kika zo min dashi yau?" ta ƙarashe tana 6antarar Apple ɗin dake hannun ta. "Ai Sarauniya ta yau nazo miki da abun ban mamaki, yau idanu na sun ganemin abinda zai hana ni sukuni ya kuma hanaki kema, a yau dai da wadannan idanuwan nawa naga yaron nan Yarima ZEEYAD yana murmushi." A matuƙar razane ta ɗago tana kallon Jakadiya kafin ta ɗau hannu ta wanke ta da wani irin azababben mari tace "Tashi ki bani wuri matsiyaciyar banza da wofi wacce bata gaji arziki ba, ni zaki zo wa da wannan mummunar labarin da koh a mafarki wani yazo min dashi toh tabbas sai naga bayan sa?, Useless old hag, wannan mummunar labari ce, how dare you ruined my happy mood?." "Allah ya huci zuciyar ki, sarauniya ta, ba dan na ɓata miki rai na Kawo miki labarin nan ba, ina ganin Kamar zaki ɗau mataki akai ne tunda babu abinda kika fi tsana kamar farin cikin shi, Allah ya huci zuciyar ki yake Sarauniya ta" tana faɗin haka taja jikin ta ta baro wurin riƙe da ƙunci. Nazarin maganar Jakadiya ta shiga yi kafin Kuma taja dogon tsaki tare da dakawa bayin nata tsawa take suka watse daga wurin. Tashi tsaye tayi tana fidda wani irin huci mai zafi dake tasowa daga chan ƙasar zuciyar ta dake yi mata ƙuna tace "Baikamata ka kasance cikin farin ciki ba ZEEYAD, yakamata ka ƙare rayuwar ka ne cikin ƙunci,wahala dama kuma baƙin ciki, kamar yadda naga bayan Mahaifiyar ka kaima haka nakeson ganin bayan ka, sai dai taurin rai irin naka yasa har yanzu na kasa aiwatar da ƙudiri na akanka, kasancewa cikin farin ciki sam ba naka bane ZEEYAD ya zama dole nayi gaggawar yiwa wannan lamari tufkar hanci, tun kafin sirrin da nake 6oyewa shekaru da shekaru ya tone" ta faɗa tana tattare doguwar gown ɗin dake jikin ta tayi hanƴar ficewa da sauri.......... ************* ............Tundaga inda take ta hango ZEEYAD ɗin tsaye a bakin ƙofar shiga fada, wanda da alama dakaru ne suka hana sa shiga, hakan ba ƙaramin faranta mata rai yayi ba dan kuwa burin ta shine a kullum ya kasance cikin ƙunci da wahala. Ƙarasowa wurin tayi nan kuwa dakarun nan suka shiga kwasar gaisuwa kafin su buɗa mata, kallon ZEEYAD da koh da wanzuwar ta baisan dashi bane tayi kafin ta gyara tsayuwar ta tana juyowa gareshi tare da harɗe hannaye a ƙirji tace "ZEEYAD my Boy, shin ba zaka durƙusa a gaba na ka roƙe ni na sanƴa wadannan ƙasƙantattun bayin barin ka ka shiga izuwa wurin mahaifin ka ba?, au koh dayake ashe ma fah Mahaifin naka ya tsani ganin ka toh akan mai kuma kake son nuna masa fuskar ka?." Hannu tasa ta ɗago ha6ar sa tace "Wannan kyakkyawar fuskar taka kamata yayi ace duk sadda akayi arba da ita mutum ya kasance cikin farin ciki ba baƙin ciki ba, amma abin mamaki kowa ya tsane ka a wannan nahiyar koh maiyasa hakan oho" ta faɗa tana ƙiƙƙifta idanu cikin makirci. "ZEEYAD, a matsayi na ta mata ta biyu ga mai martaba Sarki, Mahaifiya ga Babban Yarima kuma ɗa mafi soyuwa ga sarki wato *YAZEED* ina mai umartar ka da ka durƙusa a gaba na yanzun nan kayimin gaisuwar safiya koh hakan zai sanƴa naji tausayin ka a matsayin ka na ƙasƙantaccen ɗan da ya rasa Mahaifiyar sa, koh hakan zai faranta min rai na sanƴa a buɗa maka wannan ƙofar ka shiga ba tare da ka fuskanci ƙalubale ba" ta ƙarashe cikin ƙuntume fuska dake nuna tsantsar tsanar sa tana kallon sa. ZEEYAD sam bai damu da maganganun da take faɗa masa ba dan kuwa idan da sabo toh yaci ace ya saba da baƙaƙen maganganu irin na *Sarauniya Hafeezah da Nazeerah* Ganin yaƙi kulata kuma koh kallon gefen ta baiyi bane yasa ta jin wani irin ƙululun abu ya tokare mata maƙoshi, da kyar ta haɗiye ƴawu tsabar baƙin ciki tace "Tsayawa magana da ƙasƙantaccen yaro kamar kai ba ƙaramin zubar min da mutunci da ƙima zaiyi ba, ina ƙoƙarin fitar da kai daga ƙunci amma kuma kai kana sake tsoma kanka a ciki, hakan ma yayi dai-dai dan kuwa zama wuri ɗaya da irin ka babu abinda zai haifarwa mutum sai cuta sabida ƙazantar dake tattare da kai" tana faɗin haka ta wuce fuuu kamar wacce iska ke turawa ta faɗa cikin fadar nan kuwa aka maida ƙofar aka rufe. Juyawa yayi da niyyar komawa inda ya fito nan idanun sa suka faɗa cikin nata tana yi masa wani irin kallo. "Subhanallah" ya faɗa a zuciyar sa yana kauda kai, dan kuwa idan akwai wacce yake mugun tsoron haɗuwa da ita bata wuce *Sarauniya Naseeba* ba, itace matar sarki ta uku sannan kuma tun mutuwar Mahaifiyar sa sarki bai ƙaro wani auren ba. Ƙarasowa tayi wurin kuyangin ta na taka mata baya kafin tace "Ku buɗe masa ya shiga." Juyowa yayi ya kalle ta kafin kuma ya sake kauda kai,dan kuwa kwata-kwata baya ƙaunar haɗa idanu da ita. "ZEEYAD my dear, come on zo mu shiga daga ciki" ta faɗa tana sakin masa wani irin tsadadden murmushin da ita kaɗai tasan ma'anar sa. "No thanks" ya faɗa yana ƙoƙarin wuce ta. Riƙo hannun sa da tayi ne yasa shi faɗin "Alright" cikin rawar murya kafin kuma ya wuce ya shiga, dan kuwa sam baya ƙaunar abinda zai haɗa shi da ita. Da kallo ta bisa tana mai kintsa abubuwa dayawa a cikin zuciyar ta game dashi, kafin ta take masa baya suna shigewa da ita da kuyangun nata.......... *************** ..........Dining ne haɗaɗɗe dogo mai faɗi wanda a ƙalla zai ɗau mutane Talatin. Duk zaune suke inda kowacce idanun ta da hankalin ta na kan ZEEYAD ɗin, sai dai kowacce da nata ƙudirin da yasa take kallon sa. Sarauniya Naseeba ce a saitin sa, shiyasa duk ya kasa samun sukuni, babu damar ya ɗago da kansa zai tsinci tana kallon sa, hakan ba ƙaramin takura sa yake ba tunda ya fahimci manufar ta akansa, yasa yake kiyaye duk wata hanƴa da zai sanƴa sa haɗuwa da ita. Sarauniya Hafeezah da sam bata fahimci zaman ZEEYAD ɗin a cikin su bane tace "What's this pathetic shit of trash doing here?." Kallon ta Sarauniya Naseeba da taji haushin maganar tata tayi tace "Enough of this, ya isheki haka Hafeezah, maiyasa zakiji haushin zaman sa a nan wurin koh kin manta shima ɗa ne ga mai Martaba?." Kallon ta Hafeezah tayi tace "Kada ki nemi ki gayamin maganar banza akan wannan yaron Naseeba, wai ma tukun dakata maiyasa akoda yaushe kike ƙoƙarin karesa a duk sadda wani daga cikin mu ya nemi gaya masa magana, baikamata ki dinga karesa ba sabida that is what he actually deserves." Ido Naseeba ta haɗa da Sarauniya Nazeerah dake jinsu tana sakin murmushin gefen baki wacce da alamu tasan komai, kafin kuma tayi saurin faɗin "Ba wai ina ƙoƙarin karesa bane ba, amma yakamata ki gane cewa ZEEYAD dai-dai yake da kowane ɗa a cikin gidan nan." A zafafe ta miƙe tsaye tana nuna ta da yatsa tace "Kul! Kada ki kuskura ki sake haɗa ƴaƴa na da wannan abin, idan ba haka ba toh tabbas zaki fuskanci fushi na, koh dayake dama juya kamar ki mai ta sani gameda ƴaƴa shiyasa kike haɗa ƴaƴan da na haifa dashi." Fitowar mai Martaba ya sanƴa Sarauniya Naseeba yin shiru ba tare da ta furta abinda tayi niyya ba............. *Share Fisabillah👏🏽* *MHIZZ JIDDHERR.........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *005...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..............Tsaye yake akan ƙatuwar bridge inda ruwa ke ta gudana yana wucewa da gudu ta ƙarƙashin sa, he feels so very empty, ji yake komai na rayuwa ya fitan masa a kai, he wishes ina ma ba'a halicce shi ba, rayuwa tayi masa mugun zafi, babu wanda yake sonsa except family ɗin mahaifiyar sa, sai dai su ma mai Martaba yayi musu iyaka dashi, bashida kowa bashida komai sai Allah. Ajiyar zuciya ya sauƙe yana lumshe idanun sa sakamakon sassanƴar iska mai shiga jiki dake busawa a wurin yana ratsa cikin jikin sa. Idanun sa ya buɗe tare da sauƙe su kan wani Ƙaton jirgin ruwa dake tafiya akan ruwan, idanu ya zubawa jirgin har yayi nisa, kafin kuma ya furzar da iska a bakin sa. Necklace ɗin wuyar sa ya ciro daga cikin rigar sa yana kallo kafin kuma ya ɗan saki murmushin da ta tsaya masa saman le6e yana maida ta. Juyawa yayi ya fara tafiya a hankali dan komawa inda ya fito, ya ɗanyi tafiya mai nisan gaske kafin ya shigo cikin Masarautar tasu. Tsadaddun manƴan Baƙaƙen Motoci ne da aƙalla zasu kai ashirin ya gani jibge an fito dasu sun sha wanki sai ɗaukar idanu suke wanda da alama fita za'a yi dasu. Wani ɗan dakali ya samu daga ɗan nesa da farfajiyar wurin parking space ɗin ya zauna. "Kai mai kakeyi zaune anan?" ya jiyo an faɗi hakan ta bayan sa. Juyawa yayi tare da kallon mutumin da yayi maganar, nan ya sake cewa "Au ashe kaine, ai na ɗauka koh almajiran da suka saba shigowa ne suka shigo dah sai nace musu yau babu sadaka, miye ka wani ƙure ni da idanu koh dama bakayi kama da almajiran bane iye?" ya faɗa kamar wanda zai buge shi. Kauda kai ZEEYAD yayi daga kallon sa, dan kuwa idan yace zai biye masa tsaf zasuyi faɗa anan wurin, bakomai ya sanƴa shi zama anan ba sai jiran fitowar mai Martaba. Ganin ZEEYAD ɗin bai tanka masa bane yasa shi jan ƙatuwar jikin sa yayi gaba yana surutai. "You will all reap what you sow oneday.....i promise" ya faɗa a hankali yana bin mutumin da kallo har ya 6acewa ganin sa. Ya ɗan jima zaune a wurin kafin Mai Martaba ɗin ya fito tare da dakarun sa dama kuma wasu manƴan mutane wanda daga gani suma jinin sarautar ne. Tashi yayi daga zaunen da yake ba tare da wata fargaba ba ya doshi wurin su. Ƙofa aka buɗewa mai Martaba yana shirin shiga ne ya tsinkayo muryar da yafi tsana ya kira shi "Your Highness" ya faɗa. Runtse idanu mai Martaba yayi na wasu ƴan seconds ba tare da ya juyo ya kallesa ba yace "What do you want?." "I need to talk to you." "You can't talk to him right now, he have an important meeting to attend" cewar ɗaya daga cikin mutanen dake tare da mai Martaba ɗin. "It's urgent..." bai ƙarasar ba wannan mutumin ya sake cewa "Get him out of here." Zuwa sukayi zasu kama shi nan mai Martaba yace "Let him talk" nan duk suka ja baya dan cika umarnin mai Martaba ɗin. "What do you want?" Cewar Mai Martaba. "I want some Money to buy new clothes." Duk idanu ƴan wurin suka zuba masa jin abinda ya tambaya, sai a sannan mai Martaba ya juyo ya kallesa sama da ƙasa kafin yace "Yeah, i guess you need new clothes, Abdulhakeem ka basa kuɗi yaje ya saya dukkanin abinda yake buƙata bana kuma son ya dame ni akan maganar wata kuɗi, bana ƙaunar ganin fuskar sa, ka bashi kuɗin da zai ishe sa yayi komai dashi bama sayan kaya kaɗai ba na shekara ɗaya" yana faɗin haka ya shige motar aka rufe. Kallon sa Wanda aka kira da Abdulhakeem yayi yace "How lucky of you!...anyways yanzu fita zamuyi ka jira idan mun dawo sai na baka kuɗin." "No i need the money right now." "What, rashin kunƴa zakayi min, alright then mai zai hana kawai ka zama ƙuda ka shige cikin aljihu na ka ɗau kuɗin ka fito, you scoundrel" bai jira cewar ZEEYAD ɗin ba yayi gaba tare da shigewa ɗaya daga cikin motocin da aka jera ɗin. "Kai ƙasƙantacce ba zaka matsa bane koh dai sai an kwashe maka ƙafafu ka rasa na tafiya" ya jiyo muryar Mulah ta bayan sa. Juyawa yayi ya kallesa fuskar nan duk tasha Bandage da plaster, ƙarasowa gaban sa Mulah yayi yace "I can't believe kai ne kayimin wannan abin, anƴa ma bakada Aljanu kuwa kokuma dai nace fatalwar uwarka ce ta taso ta shige jikin ka ka aikata min hakan." Sosai ran ZEEYAD ya 6aci hannu ya kai da niyar bugun Mulah sai dai yayi nasarar cafke hannun nasa tare da faɗin "Kayi kaɗan yaro bansan dai koh nangaba idan ka ƙara girma ba, wancan ranar ma tsautsayi ce ta faɗa min, hukuncin da mahaifin ka yayi maka koh kaɗan bai faranta min rai ba, a yanzu kuwa inada damar yi maka duk wani abinda naga dama sabida babu mai kar6ar ka" dogon gashin kansa ya damƙo yace "Wannan gashin naka naga kamar tana buƙatar gyara, muje mu na gyara maka shi yanzun nan" ya faɗa yana ture shi da ƙarfi ya faɗi. Nan hankalin mutanen wurin ya fara dawowa kansu, fizgo sa yayi tsaye ta baya tare da tusa sa gaba suka bar arear cikin gidan. Buɗe ƙofar ɗakin yayi tare da tura sa ciki yace "Ba zaka fito ba har sai sauron dake jibge a cikin ɗakin nan sunyi min yaga-yaga da naman jikin ka, koh da jinin jikin ka zasu zuƙe gabaɗaya ba zan damu ba, dan dama bakada wata amfani da mutuwar ka da rayuwar ka duk ɗaya ce" ya faɗa yana garƙame ƙofar da ƙatuwar sakata ta waje. "Oh no!, Mosquitor bites are so dangerous to health" faɗin ZEEYAD ɗin kafin kuma ya ankare yaji mil wani irin zazzafan cizon sauro a gefen kumatun shi, da sauri ya kai hannu tare da marin fuskar sai dai da alamu bai sami sauron ba. Kukan sauro ne suka cika masa kunne kafin ya ankara kuwa tuni sun mamaye shi sun fara cizon sa, cikin ɗagun murya yace "Get me out of here Mulah." "Hahahahahaha, so nake suyi gunduwa-gunduwa da naman jikin ka kafin na fitar da kai, koh an gayamaka ka bugi banza ne?" cewar Mulah tare da ɗaukar bowl ɗin barasa ya kafa akansa, gyatsa mai ƙarfi yayi tare da goge bakin sa yana lumshe idanu. ZEEYAD abu goma ya haɗu yayi masa yawa, tsananin duhun ɗakin, zafi, kukan sauro dama kuma cizon su, irin cizo mai zafin gasken nan. Zubewa yayi wurin tare da fara lalume koh zai sami abinda zai kori sauron dashi sai dai ɗakin babu komai sai ƙasa da yake ta shafawa. Toshe kunnuwan sa yayi kawai tare da ƙanƙame jikin sa,dan kuwa babu yadda ya iya face ya bari su cize sa ɗin. Sai da yayi mintina ashirin a cikin ɗakin nan kafin Mulah ya buɗe shi, dariyar mugunta ya saki yace "Koh bakomai yanzu ka horu, nangaba ba zaka sake gigin kwatanta abinnan akan wani bama balle ni, au ashe fah na manta nace zan aske gashin nan koh?, kai maza kuzo ku riƙemin shi ku kaisa wurin Hakim yayi masa aski da kwalba, kai ba mace ba ka tara wannan uban gashin, kodai ka fara yawo da ƴan iskan gari ne bansaniba?." Tahowa sukayi tare da kama ZEEYAD ɗin da jikin sa baki ɗaya kama daga kan fuskar sa duk yayi jan tabo sakamakon cizon sauron, haka nan suka ja shi kamar kayan wanki suka kaisa wurin wanda Mulah ya umurce su. "Kai Hakim gashi nan Mulah yace mu kawo maka shi ka mule masa kai, askin kwalba zakayi masa kada ka bar gashi koh kaɗan akansa." Dariya wanda aka kira da Hakim yayi yace "Madallah, madallah da wannan rana, na daɗe ina farautar ka sai kuma gashi yau Allah ya kawomin kai har cikin fada ta ba tare da na sha wata wahala ba, ku miƙa saƙon gaisuwa ta ga Mulah sannan kuma kuce dashi ina mai gayyatar sa liyafa yau da daddare a gida na" ya ƙarashe yana tamƙe fuska tare da kallon ZEEYAD. "Masha Allah, maza ka tashi yanzun nan na aske maka wannan gashi da ka tara kamar ɗan bokaye, sai dai babu laifi kuma yayi maka kyau, amma fah hakan ba zai sanƴa naƙi aiwatar da nufi na akanka ba" ya ƙarashe yana washe yellow ɗin haƙoran sa. Miƙewa yayi daga zaunen da yake tare da zuwa wani lungu daga cikin shagon sa ya ɗauko wata ƙatuwar kwalba. Zuwa yayi ya fasa ta yana dariya kafin yace "Wannan zai yi matuƙar taimakawa wurin kammala askin da wuri kuma sakamako ya fito da kyau, koh ya kace hahaha." Da idanu kawai ZEEYAD ke bin sa da kallo dan kuwa babu ta yadda zai yarda ne a sanƴa masa kwalba a kai da sunan aski. Takowa yayi zuwa inda ZEEYAD ke durƙushe tare da kama bakin doguwar gashin nasa da niyar yankewa. Shigar abu mai kaifi a gefen cikin sa ne ya sanƴa sa yar da kwalbar hannun nasa yana faɗi zaune riƙe da gefen cikin sa, idanun sa na sauƙa akan ma'askar dake riƙe a hannun ZEEYAD. Miƙewa yayi tsaye ya tako inda Hakim yake ya tsuguna yace "Aski kakeson kayimin?, you don't have that right, yes i would became so very bad since naga kamar hakan kukeso, you would be my first victim, i promise i will make sure kayi nadamar shiga gona ta, i have suffered alot for the past 20years, dan haka yanzu lokaci yayi da yakamata nima na tsayawa kaina, but before i vanished without a trace i would make sure i killed you first Hakim" ya faɗa in a serious tone yana kallon Hakim da ya haɗa wani irin uban gumi yana zaro idanu waje. Jefar da askar askin yayi kafin ya miƙe tsaye ya fice yana mai kama gashin nasa ya ɗaure ta wuri guda......... ******** ..........Zaune yake bakin famfo yana wanke fuskar sa, jikin sa yabi da kallo wanda duk yayi tabo yana yi masa zafi, kafin kuma ya miƙe tsaye yana gyara hannun rigar sa. Hango Abdulhakeem yayi da wasu dogarai hannun su riƙe da ƙatuwar ghana must go suna ƙarasowa wurin sa. Murmushi Abdulhakeem yayi yace "ZEEYAD my boy kalli wannan kaya ne na kawo maka, ina ta gararin neman ka tunɗazu cikin PALACE ɗinnan sai dai ban sameka ba, banason ka kalle ni a matsayin macuci wanda ya cinƴe kuɗin da mahaifin ka ya bada a baka, hakan yasa na tako zuwa wannan arear da kaina dan kawo maka, sai dai gashi har jikina ya fara ɗaukar ƙaiƙayi i wonder yadda kake rayuwa anan wurin." ya faɗa cikin ɗan dariya yana ƙarewa wurin kallo. ZEEYAD bai kula shi ba sai kallon sa kawai da yakeyi hakan ya sanƴa shi faɗin "Ohh kada kace na cika surutu, gashi nan ka buɗe kaga abin dake ciki" ya faɗa yana nunawa ZEEYAD bagco ɗin. Kallon sa yayi sannan kuma ya duƙa tare da kai hannu ya buɗe ta, kaya ne birjik a ciki sai dai daga ganin su an sanƴa su. Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa nan ya sakar masa murmushi yace "Sunyi kyau koh?." "What Nonsense, already kayan nan an rigada an sanƴa su." Tamƙe fuska yayi yace "Mai kake nufi, kai kasan nawa ne kuɗin kayayyakin nan kuwa, kai koh godewa Allah ba zakayi ba da ya kawo maka wannan ɗin?." "I don't want it, kuɗi mai Martaba yace ka bani ba wadannan tsofaffin kayan da ƴaƴan ka suka sanƴa ba." Dariya yayi yace "Naji daɗi da ka fahimci cewa ragowar kayan da ƴaƴa na masu daraja suka sanƴa ne, yakamata ka amshe su hannu bibbiyu ba wai ka raina ba dan kuwa na tabbata koh nan da shekaru ɗari ne ba zaka iya sanƴa irin su ba." Murmushi ZEEYAD yayi yace "Really?, kana nufin haka zan ƙarashe rayuwa ta?." "Babu tantama kuwa" ya faɗa cikin ɗan dariya. "OK then, we will see to that, but i just need my money now." "No, ba zan baka kuɗin ba sabida.....na cinƴeee" ya faɗa saitin kunnen sa kafin kuma ya fashe da dariya. "Ka cinƴe?" ya faɗa yana kallon sa. "Kwarai kuwa, koh akwai abinda zakayi ne ZEEYAD?." Kai ya girgiza masa yace "Not now though" kafin kuma yayi murmushi haɗi da ɗaga kafaɗu yace "Alright then shikenan tunda ka cinƴe, i will keep managing with the little i have." "Come on ZEEYAD, tayaya zakayi manage da wadannan tsofaffin kayayyakin har zuwa wani shekara kana tunanin kallon mutum ma kaɗai ba zai yaga su ba tun ba'a ta6a su ba, ka ɗauki wadannan kaje kayi ta amfani dasu sabida sun zama tsofaffin yayi baikamata a gansu a jikin yara na jinin sarauta ba, but kaga kai nasan zasuyi matuƙar kar6ar ka suyi maka kyau sabida sam baka ta6a sanƴa irin su ba, don't be shy Okay, ba wanda zaiyi gulmar ka zan tabbatar da na rufe bakin kowa daga yin maganar ka, koh ya kace?" ya faɗa yana dafa kafaɗar ZEEYAD ɗin. Jinjina masa kai yayi kawai yace "Okay, but wait please" ya faɗa yana juyawa zuwa cikin ɗakin sa. Ashana ya ɗauko ya fito dashi ya kalli Abdulhakeem yace "Uncle Abdulhakeem you want me to wear these don't you?." "Ofcourse ZEEYAD" ya faɗa cikin murmushi yana kallon sa. "Sun zama mallaki na yanzu, right?." "Ofcourse, miye kuma kake sake tambaya, nacemaka sun zama naka yan..." bai ƙarasar da maganar ba ganin ZEEYAD ya kyarta ashana tare da jefawa kan kayan, take expression na fuskar sa ta sauya. "What the hell..." ya faɗa. Katse sa ZEEYAD yayi da faɗin "Uncle Abdulhakeem, baikamata kayi fushi ba sabida ba kayan ƴaƴanka na ƙona ba, koh ka manta ne kai kace sun zama mallaki na yanzu, so i guess kamar yadda babu ruwan kowa da rayuwa ta baikamata kaji haushi ba dan na ƙona kayan da yake mallaki na ne, sabida bana buƙatar su." Sosai Abdulhakeem yaji mugun haushi, nuna ZEEYAD yayi da yatsa yace "How dare you, ni zaka watsawa ƙasa a ido?, sai na tabbatar da kayi nadamar abinda ka aikata yanzun nan" yana faɗin haka ya juya fuu da ƙatuwar alkyabar dake jikin sa kamar zai tashi sama. "Lallai yaro ka samu wuri" cewar ɗaya daga cikin dogaren sa kafin suyi saurin mara masa baya. Da kallo ZEEYAD ya bisu har suka 6acewa ganin sa,kafin yaja Bagco ɗin kayan zuwa chan gefe yana ƙara mata wuta........ ***************** ........"What!, bai sanƴa kayan ba?" ta faɗa cikin tashin hankali tana miƙewa tsaye daga kan kujerar ta. "Ya kina magana kamar wacce bataji abinda na faɗa ba, koh so kike na ɗau lasifika nayi ta yawo a gari ina maimaitawa kafin kiji?." Kallon Abdulhakeem tayi tace "Ya isheka haka nan,ka tsaya a matsayin ka na ƙanin ga mai Martaba, kada ka wuce iyakar ka ka nemi gayamin magana" ta faɗa cikin fushi. Kallo ya ƙare mata tsaf sama da ƙasa yace "Mai kike nufi da na tsaya a matsayi na, kina nufin kice min shashasha kika ɗauke ni tsawon lokacin nan bansaniba koh miye?, kece yakamata ki tsaya a matsayin ki Hafeezah sannan kuma ki kiyayi dukkanin wani abu da zai 6ata min rai dan kuwa babu wani baƙin sirri naki da bansaniba." Kallon sa tayi da idanun ta da kamar zasu faɗo daga ramin su kafin kuma ta haɗiyi ƴawu tana daidaita nutsuwar ta tace "Shikenan naji, amma ka sani ba zan ta6a samun kwanciyar hankali ba muddin banga bayan yaron nan ba." "Ki bar komai hannu na Sarauniya Hafeezah, ni nan zanji dashi."................... _Yau insha Allahu akwai shara, dan gaskiya comments ɗinku yana yin kaɗan, wasu sun bani shawarar maida shi na kuɗi dan haka indai banga comments ɗinda ya gamshe ni ba toh hakan zan aiwatar, kokuma na daina yi muku posting ɗinsa kullum, idan kuma littafin ne baiyi muku daɗi ba sai ku faɗamin na daina 6ata lokaci na wurin son faranta muku, tunda ku ba zaku iya faranta min wurin yimin zazzafan comment ba😑, dan Allah ku gyara comment ɗinku fah shine kwarin guiwar mu wlh, Masu turo sticker da Tnx ku bar abin ku dan Allah na yafe😑_ *Share Fisabillah* *MHIZZ JIDDHERR..........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *006...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..........Sosai dare ya ratsa yayin da kowanne ɗan Adam a wannan lokaci kafaɗun sa ke ƙasa yana bacci lokacin ne kuma ZEEYAD ya kasa koh da runtsawa ne sakamakon wani irin azababben zazza6i da ya rufa masa. Sosai jikin sa ke karkarwa ji yake kamar ana yanka naman jikin sa koh ana hura masa wuta haka nan yakejin zafi na taso masa a jiki, yayin da kuma yake ta karkarwar sanƴi. Fitowa yayi waje ya zauna gindin bishiya dan ya sha iska dan kuwa koh da kwan wuta babu a ɗakin sa balle kuma fanka. Zaman sa gindin bishiyar nan babu abinda ya ƙara masa sai sanƴin da yakeji hakan ya sanƴa shi sake komawa ɗakin sa, sosai jikin sa da hannayen sa ke rawa haka nan ya zazzage kayayyakin dake cikin jakar sa baki ɗaya ya ciro tare da lullu6e jikin sa dashi kasancewar bashida bargon lullu6a. Lullu6ar da yayi babu abinda ya rage masa daga jin sanƴi da karkarwar da jikin sa keyi. Sosai ya sha baƙar wahala cikin wannan dare dan kuwa koh runtsawa baiyi ba har wayewar gari bai iya samu ya dawo hayyacin sa ba. Sosai gari ya waye sai dai koh taka ƙafar sa bai iya ya fito waje ba, hayaniyan da yaji a bakin ƙofar ɗakin sa ne yasa shi ɗago da gajiyayyun idanun sa yana kallon bakin ƙofar shigowa. Da mugun bugu aka 6allo ƙofar ɗakin inda yayi saurin kare idanun sa sakamakon hasken rana da ya dallo masa idanu. Bai ankara ba yaji anyi masa wata iriyar muguwar fuzga an miƙar dashi tsaye, inda kuma aka wullo sa waje. Bai ankara ba kuma aka hau bugun sa ta koh ina, sosai sukayi masa lilis kafin ya basu umarnin dakatawa. ZEEYAD dake kwance duk yabi ya galabaita dakyar yake iya motsa ƴar yatsar sa ne ya ɗago dan ganin koh wanene. Durƙushewa ɗan Saurayin yayi wanda ba zai wuce sa'ar sa ba yayi yace "Hello Bro, long time no see." "You.." ya faɗa cikin maida numfashi. Murmushi ɗan Saurayin nan yayi kafin kuma ya damƙo gashin ZEEYAD ɗin yana zaunar dashi tare da kallon saitin idanun sa yace "Kai har ka isa, who the fuck do you think you are da har mahaifina zaiyi maka kyautar kaya na ka ƙona right infront of him?." Shiru ZEEYAD yayi bai iya tanka masa ba inda kuma yake ta fitar da numfashin wahala yana runtse idanun sa cike da azabar da yakeji a jikin sa. "Sooraj let go of him" ta faɗa tana zuwa ta ture shi daga riƙon da yayiwa ZEEYAD ɗin, kafin kuma ta ɗago da ZEEYAD ɗin tana shafa fuskar sa cikin kuka. Daddagewa yayi tare da kwashe ta da wani irin azababben marin da sai da ya sanƴa ta ganin wasu irin taurari masu tsananin haske yace "Dan Ubanki mai ya kawo ki nan?." Riƙe da ƙunci cikin kuka tace "Ai dama nasan zaka zo nan wurin tunda naji abinda Abhi ya faɗa maka akan ZEEYAD nasan sai ka biyo sa kayi masa illa, maiyasa wai ku bakuda imani ne?." Kallo ya ƙare mata sama da ƙasa kafin ya ɗago ta tsaye yace "Ni kike faɗawa haka akan wannan bolan?, how the hell ma aka barki kika fito bayan ɗakin ki a rufe?." "Eh ɗin na faɗamaka ɗin, mugu kawai azzalumi kuma wallahi sai kunyi nadamar abinda kukeyi masa dukkan ku." Wani marin ya sake ɗebe ta dashi wanda ya sanƴa ta zubewa a wurin, nan ya kalli dogaran da yake tafe dasu yace "Ku sake yi masa dukan da yafi wanda kukayi masa yanzu, dukan da zai sanƴa sa guduwa da ƙafafuwan sa da zaran yaga dosowar wani daga cikin Family ɗin mu." Ai kuwa kamar jira suke nan suka ha bugun sa da ƙafafuwan su, ita kuwa yarinƴar nan babu abinda takeyi sai kuka da ihun su sake shi inda yayan nata kuma ya riƙe ta gam yanajin wani irin tululun baƙin ciki ya tokare masa zuci, babu abinda yake fitarwa sai huci. Sai da suka tabbatar da ya daina motsawa kafin su kyale shi, tusa ta gaba yayi yana janta suka bar wurin. Barin su wurin keda wuya bayi matan dake harkokin su a wurin suka zo suka zagaye shi kowa na magana ƙasa-ƙasa suna tofa albarkacin bakin su "Ya mutu fah", "baya motsi", "Uhm nikam kunga tafiya ta", "Allah ya kyauta,lallai akwai hisabi ranar ƙiyama" Shine abinda wasu daga cikin su ke ta faɗa kafin duk su fara watsewa ɗaɗɗaya kowace na kama gaban ta........... *************** ........."Abhi! Abhi!! Abhi!!?" yake ta ƙira da ƙarfi kamar zai kai wa na gaban sa duka hannun sa damƙe da na ƙanwar tasa da har yanzu bata bar kuka ba. Wata kyakyawar mata ce ta fito daga wani lungu wacce da alama ita ɗin Mahaifiyar su ce tana faɗin "Lafiya kake kwalawa mahaifin ka kira haka kamar wanda zaka tashi sama?." Tura ƙanwar tasa yayi tana faɗawa jikin mahaifiyar tasu yace "Wannan shashashar ƴar taki mana da take neman zubar mana da mutunci a idon bayi." "Mai kuma ta aikata wannan karon?." Nan ya kwashe abinda ya faru ya faɗa mata, ai kuwa batayi wata-wata ba ta kwashe ta da mari tare da ture ta daga jikin ta tace "Ni zaki jawowa abin kunƴa da zubar mutunci a idanun matan gidan nan, miye akayi akayi wancan banzan ZEEYAD ɗin da har zaki dinga tada hankali a kansa, kin kuwa san mai kike neman jawo mana?, Mutuniyar banza da wofi wacce batasan mai takeyi ba." "Ummie, ya akayi ma kika barta ta fita waje?, i swear idan na sake kama yarinƴar nan ta kira sunan wancen ƙasƙantaccen koh da da wasa ne nothing would Stop me from killing her." A razane Mahaifiyar ta ɗago tana kallon Sooraj ɗin dan kuwa yadda yayi maganar ya nuna tabbatuwar zai iya aikata hakan dagaske, dan kuwa sam yaron bai san wani abu wai shi imani koh Tausayi ba, tun yana ƙarami yake da wani irin baƙin mugunta koh da yake girma sake ƙaruwa yakeyi, ga kuma baƙin ciki da hassada dan kuwa a cewar sa sune yakamata su zamto masu mulkar ƙasar Cairo ba Sarki Abbas ba, burin sa a kullum shine sarki Abbas ya mutu mulki ya dawo 6angaren su. Kallon Yarinƴar tayi tare da jan hannun ta tayi ciki da ita, zaunar da ita tayi tare da nuna ta da yatsa tace "Jalilah kin dai san yayan ki baisan tausayi ba koh?, sannan kullum ƙara girma yake muguntar sa na daɗa ƙaruwa, ina mai gargaɗin ki da ki fitar da wannan yaron ZEEYAD a zuciyar ki idan ba haka ba ni babu ruwa na da dukkanin abinda zai same ki." Cikin kuka tace "Amma Ummie laifin mai ya aikata haka da sai ayi ta muzguna masa kullum?, kuma ai shine ɗan sarki babba amma aka tauye masa wannan hakkin..." Saurin rufe mata baki tayi tace "Shhh, koh da wasa kada ki kuskura ki bar wannan zancen ya sake fitowa daga bakin ki, idan ba haka ba daga ni har ke mun mutu kenan ranar, ki share hawayen ki yanzu haka nan kinji, sannan ki bar tunanin yaron chan kin dai san halin mahaifin ku" ta faɗa tana goge mata hawaye. "Ki tashi yanzu zan turomiki kuyangun ki suzo suyi miki wanka sannan su kawo miki abinci kici." Kai ta jinjina kawai kafin mahaifiyar tasu ta fice. "Ina fatan dai kin gargaɗi ƴarki?" cewar Abdulhakeem dake zaune kan wata doguwar kujera yayi naƙe-naƙe a kai inda kuma Sooraj ke zaune ta gefen sa sai hura hanci yake. Kai ta jinjina masa cike da girmamawa tayi wucewar ta, da kallo yabi ta kafin yace "Yarinƴar nan sam bata ɗebo halina ba shiyasa take tausayin wancan yaron, amma nan ba da daɗewa ba zanyi maganin ta." Murmushi Sooraj yayi yace "Abhi indai kana dani nikuma nayi alƙawarin yin dukkanin yadda zanyi dan ganin mulkin nan ta dawo hannun mu." Dariya Abdulhakeem ya kwashe dashi cike da alfaharin halin irin na ɗan nasa yace "Shiyasa nake matuƙar ƙaunar ka fiye da kowa."............. ********* .......Haka nan yake yashe anan wurin ba tare da ya sake motsi ba har hadari baƙiƙirin ya haɗu ruwa mai ƙarfi ya sauƙo. A kansa aka ƙare ruwan tass har mutane suka fara fitowa dan cigaba da harkokin gaban su ZEEYAD bai farka ba. Sai dai kuma ganin babu wanda ya damu dashi ya sanƴa kowace jan bakin ta tayi shiru ba tare da sun iya kai ƙarar abinda ya faru ba, dan kuwa sun san babu wani mataki da za'a ɗauka a kai. Yatsar sa ce ta fara motsawa kafin kuma yaja wani irin dogon numfashi yana ware idanun sa da sukayi matuƙar yin jaa sosai. Yunƙurawa yayi ya miƙe zaune kamar kuma wanda aka tsikara ya tashi tsaye cikin tangaɗi ya ƙarasa bakin ɗakin sa da ruwa ya shiga yayi masa gyara, zubewa yayi tsugunne kan guiwowin sa wasu irin zafafan hawaye suka shiga kwaranƴo masa, kafin kuma ya sanƴa wani irin ihu da ƙarfin gaske ya shiga buga kansa da hannayen sa. Sai da yayi mai isarsa kafin ya tsagaita, nan ya wuce cikin ɗakin nasa ya hau dube-dube, hannu ya kai wuyar sa nan yaji sarƙar tana nan, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana sumbatar ta kafin kuma ya fito ya kama bin hanƴar ficewa daga Masarautar kamar ba shine wanda yasha jinƴa cikin dare kuma akayi masa dukan mutuwa ba dan kuwa da ƙarfin sa yake tafiya. Duk inda yabi kuwa da kallo ake binsa ganin yadda yayi jina-jina kamar wanda yayi faɗa da kura, babu inda ya nufa sai gidan su abokin sa Sadeeq, tundaga nesa ya hango sa yana zuwa hakan ya sanƴa shi zuwa ya taro sa da sauri ganin jikin sa. "ZEEYAD, mai ya sameka haka, waye yayi maka wannan aika-aikar?." "Ina Abhi?" kawai ya faɗa yana janƴe jikin sa daga riƙon da Sadeeq ɗin yayi masa. "Abhi yana cikin gida, lafiya, mai ya sameka ne haka ina tambayar ka?." Bai kula Sadeeq ba ya nufi cikin gidan nasu, Abhi dake zaune baisan sadda ya miƙe tsaye ba sakamakon ganin ZEEYAD da kuma halin da yake ciki da yayi. Zuwa ZEEYAD yayi wurin sa yace "Abhi ina buƙatar Takardun gama makaranta ta dake wurin ka." "ZEEYAD...Maiyasame ka haka?." "Babu, ina buƙatar takardu da na baka ajiya ne." Kallon sa kawai Abhi ɗin ya tsaya yi na wasu daƙiƙu kafin kuma ya shiga wani ɗaki ya ɗan daɗe a ciki kafin ya fito ɗauke da wata jaka a hannun sa "Gasu nan" ya faɗa yana miƙawa ZEEYAD ɗin. Amsa yayi ya buɗe ta nan yaga komai ya cika kafin ya rufe ta yana rataya ta a kafaɗar sa. Duk idanu suke binsa dashi kafin yace "Am living, zan bar musu ƙasar su tun kafin suga baya na na rasa damar ɗaukar fansar abinda sukayi min, i will never give up in this life, dole ne nima na zamto mutum mai daraja ba kamar yadda suka ɗauke ni ba..." kafin ya ƙarasa Abhi yayi saurin faɗin "Ina kake tunanin zakaje, wa kake tunanin zai kar6e ka ya mutunta ka a wani yanki chan daban da babu wanda ya san ka?." "I don't care whether za'a mutunta ni a kar6e ni, all i know is that dama chan babu mai ganin daraja ta, ba zai dame ni ba dan wasu daban da bansaniba basu mutunta ni ba sabida bansan hakan ba tun farko sabida, ba'a koyamin ba, please Abhi ina roƙon ka kada ka hana ni yin tafiyar nan sabida shine kaɗai kwanciyar hankali na." Shiru Abhi yayi yana kallon sa kafin kuma ya numfasa yace "ZEEYAD ɗa na, ba zan hana ka yin tafiyar nan ba tunda haka kakeso, sai dai inaso ka sani kada ka ta6a manta cewa kana cikin jarabawar Ubangiji ne, sannan kuma kada ka ta6a tunanin Allah baya sonka shiyasa ya sanƴa ka cikin wannan hali, kada ka manta da cewa Allah yana jarabtar bayin sa da yakeso ne ta hanƴa daban-daban, sannan kuma bakomai zai sanƴa ka cin wannan jarabawa ba face haƙuri, kayi haƙuri ZEEYAD, kayi haƙuri da yadda rayuwa tazo maka, babu tantama watarana zaka ci ribar sa" ya faɗa yana shigewa cikin ɗakin sa kafin kuma ya fito hannun sa ɗauke da kuɗi yace "Ungo wannan kuɗin ka sashi a jikin ka, zaka iya cin abinci dashi a hanƴa." Kai ya girgiza yace "No Abhi, ba zan amshi kuɗin ka ba, sabida i don't need anyone's support to build myself up, ni da kaina zan gina kaina da gumi na bana buƙatar taimakon kowa, kuma ƴunwa ai na saba da ita koh ka manta ne nakan shafe kusan kwanaki uku ba tare da na sanƴa abinci a baki na ba face ruwa?, ƴunwa ba damuwata bace ba dan kuwa na saba da ita." Shiru kawai Abhi yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba. "ZEEYAD, ina goyon bayan ka, na san kai mutum ne mai ƙoƙari da nagarta nasan zakayi dukkanin yadda zakayi dan ganin ka inganta rayuwar ka ba tare da taimakon kowa ba, amma dan Allah ZEEYAD inaso kayi min wani alƙawari." "Tell me" ya faɗa yana kallon Sadeeq ɗin. "Inaso kayimin alƙawarin ba zaka canza amini ba, sannan kuma inaso kayimin alƙawarin komin daren daɗewa zaka dawo ƙasar ka ta haihuwa." "Nayi maka alƙawarin ba zan canza amini ba, tayaya ma zan iya canza ka Sadeeq? idan nayi hakan na zama butulu, kai ne kaɗai baka guje ni ba lokacin da nake buƙatar aboki kuma ɗan uwa a rayuwa ta, ba zan ta6a mantawa da Family ɗinku ba sabida kunyi min gata, a gidan ku nake samu nakecin abinci wataran koh da banso hakan ba sai ka tilasta ni na ci, bakomai zai sanƴa ni dawowa nan ƙasar ba sai dan ku,kune babban dalilin da zai sanƴa na dawo." Rungume juna sukayi shida Sadeeq ɗin na ƴan mintina kafin kuma su rabu kowanne na ƙoƙarin maida hawayen da yazo masa. Abhi ne yace "ZEEYAD ɗa na inaso kayimin wannan alfarmar, mai zai hana ka bar tafiyar nan har sai gari yayi duhu sawun mutane sun fara ɗaukewa, kafin nan kuma ni zan je wurin wani tsohon aboki na wanda ya san inda ake ficewa daga ƙasar nan ta 6oyayyiyar hanƴa, zan sanƴa sa yayi maka jagora har zuwa inda zaka ba tare da an sami wata matsala ba." Shiru ZEEYAD yayi bai ce komai ba alamun yana tunani,nan Sadeeq yace "Abhi yayi gaskiya ZEEYAD, fitar ka a yanzu ba ƙaramin haɗari bane dan kuwa idon kowa a kanka yake sannan da zaran an ganka da jaka dole ne a kai ƙarar an ganka zuwa MASARAUTA, daga nan kuma kaga komai ya kwa6e." Kai ya jinjina alamun ya yarda nan duk suka saki murmushin farin ciki kafin Abhi yace "Sadeeq ka kar6i jakar sa, nikuma zanje wurin Abdulsalam na dawo kafin dare ya rufta" yana faɗin haka yaje ya hau keken sa mai bayan napep yana yi musu sallama ya fice. Amsar jakar sa Sadeeq yayi yace "Ka zauna anan nikuma zan shiga wurin Ummie ta ɗaura maka ruwan zafin da zakayi wanka dashi, sannan na baka kaya na ka sa ka cire wannan na jikin naka, zan kawo maka magani ma sabida naga kamar akwai zazza6i a jikin ka." Kai kawai ya jinjina masa yana zama kan tabarmar kabar dake shimfiɗe a wurin. Ruwan zafi dayawa aka dafa masa wanda zai gasa ciwon jikin sa dashi dama kuma wanda zaiyi wanka dashi. Wanka yayi Sadeeq ya basa kayan sa sabo ya sanƴa, sannan ya amso masa abinci da ruwan sha a wurin Ummie, tare da maganin zazza6i. Sosai ZEEYAD yaji daɗin jikin sa dan kuwa har bacci sai da yayi, sallah ce kawai ke tada shi, har Abhi ya dawo daga wurin abokin nasa. Da misalin ƙarfe sha ɗayan dare bayan sawun mutane ya fara ɗaukewa ne suka fito da Abhi, ZEEYAD da kuma Sadeeq inda hannun Sadeeq ɗin ke riƙe da wata ƴar madaidaiciyar jaka. Tafiya mai nisan gaske sukayi kafin su iso inda zasu ɗin, kai tsaye suka shige gidan inda yake kama da garage. Mutane ne birjik Zazzaune kowanne da jakar kayan sa a gaban sa. Abokin Abhi ne ya taho nan sukayi sallama kafin Abhi ya gabatar masa da ZEEYAD a matsayin wanda zaiyi tafiyar. "Masha Allah naji daɗi da kukazo akan lokaci dan kuwa ƙarfe ɗaya motar mu ke tashi." Murmushi Abhi yayi yace "Nagode sosai abokina Abdulsalam, Allah ya biyaka da alkhairin sa." "Babu komai abokina Mas'ud duk yiwa kaine, nima bansaniba koh watarana zan iya zuwa neman wani taimako daga gareka ba, ai ka taimaki wani kai ma Allah zai taimake ka, gashi chan yaje yabi layin chan kafin mu fara shirin tafiya" ya faɗa yana nuna musu gefen da wasu matasa dama kuma manƴan mutane ke zaune. "Insha Allah" cewar Abhi kafin ya juya ga Sadeeq yace "Sadeeq ka bashi jakar, ZEEYAD wannan jakar abinci ne na leda wanda baya 6aci dama kuma ruwa wanda abokin ka ya tanada maka shi, dukda banida tabbacin zai isheka kafin ku ƙarasa inda zaku amma nasan zai rage maka wani abin, dan Allah kada ka ƙi amsa kaji?." "ZEEYAD, dan Allah ka amsa kyauta ce daga gareni a matsayi na na aminin ka." Kai ya jinjina tare da amsar jakar ya goya a bayan sa yace "Nagode muku, Allah ya bani ikon da zan biya ku da abinda kukayi min na alkhairi a rayuwa" ya faɗa tare da goge hawayen da suka zubo masa. Announcing aka fara kan kowa ya fara shirin shiga mota, nan fah duk suka miƙe kowa ya fara kokuwar shiga maza da mata da kayayyakin su, wasu da iyalan su wasu kuma su kaɗai inda mafi yawa masu kasuwanci sunfi yawa, sai dai tsabar son banza irin tasu ba zasu iya biyan kuɗin jirgi suyi tafiyar su cikin kwanciyar hankali ba sai sun bi ta 6oyayyiyar hanƴa. Abokin Abhi ne ya dawo yace "Aboki na Mas'ud, na tanadar wa ɗanka wurin zama mai kyau inda zai sake dashi da kayan sa, ku biyo ni muje mu." Motoci ne trailers manƴa irin na kwasar shanaye guda huɗu inda kuma saman su yake rufe da tent, ɗaya daga cikin motocin ya kai su inda ZEEYAD ya shiga ya samu wurin zama mai kyau da kayan sa, dukda kuwa babu shimfiɗa sai dai hakan ba damuwar sa bace tunda baya cikin matsi kuma bai saba kwanciya kan abu mai laushi ba. Hannu suka shiga yiwa juna waving dukkanin su kafin a maida tent ɗin a rufe, kafin a ɗauko sandar busassun karan dawa a lafta a kai ta yadda babu wanda zai san da cewa mutane aka ɗebo a ciki. A gaban su Abhi motocin suka tashi kafin su rakasu da ido kowanne na share hawayen da ta zubo masa na tausayi. Dafa kafaɗun Sadeeq yayi cikin kwantar masa da hankali kafin su koma inda suka fito. ZEEYAD kuwa very Umcomfortable yakejin sa, ji yake kamar ya baro wani abu mai muhimmanci wanda baikamata ya baro sa ba a baya, sai dai ya kasa gane koh menene, zuciyar sa a cunkushe take ya kasa samun sukuni. _"Why should i worry myself about him?, he always wants me out of his sight"_ ya faɗa a zuciyar sa bayan ya tuna mahaifin sa mai Martaba. Da kallo yabi ƴan cikin motar wanda sam basuyi kama da ƴan cikin gari ba sunfi kama da wadanda suka fito daga ƙauye yayi sakamakon akwai hasken fitila a ciki, kafin ya sunkuyar tare da kafa kansa kan guiwowin sa yana tunanin wace iriyar rayuwa zaiyi a inda bai san kowa ba, uwa uba kuma sam bai san wace ƙasar suka dosa ba. "Kai yaro kayi hattara dai da jakar ka, dan kuwa akwai masu sata, na faɗamaka hakan ne dan naga kamar wannan ne farkon tafiyar ka." Ɗagowa yayi ya kalli dattijuwar matar kafin yace "Nagode" yana janƴo jakar zuwa jikin sa. Shiru yayi kawai yana maida kansa, yana saurarar yadda motar ke ta jigila akan hanƴa wanda da alama ba kwalta suke bi ba. Tsinkayo muryar wani yaro yayi yace "Abhi wace ƙasa zamuje wannan karon?, kuma naga bamuda yawa a cikin nan maiyasa?." "Ai wannan karon inaso muyi tafiya cikin kwanciyar hankali ne, shiyasa na za6i na biya kuɗi dayawa dan mu samu gurbin zama inda babu mutane dayawa, kaga zamu sake kuma mu wala." Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon su tare da tunanin dama kuɗi mai yawa Abhi ya cire ya bada dan kawai ya sami gurbin zama mai kyau?, muryar yaron yaji yana faɗin "Eh, hakane toh ina zamuje?." "Nigeria zamuje, dan kuwa naji ance ƙasa ce da Allah yayi musu arzikin kayan alatu da more rayuwa kala-kala, uwa uba kuma Kasuwanci da shine suka fi yi kuma muma shi zai kai mu chan, dan kuwa naji ance chan sunada kan kasuwanci sosai komai ka kasa na sayarwa zaka samu kasuwa sannan kuma basu cika raina kuɗi ba komin ƙanƙantar ta, wani abin ba sai na faɗa maka ba idan munje mu zaka gani da idanun ka." Tunda ya fara magana ZEEYAD ya ɗago yana kallon sa, shi dai a iya ilimin da yake dashi kan ƙasashe yasan Nigeria tayi ƙaurin suna wurin kar6ar cin hancin da rashawa, uwa uba kuma insecurity da suke fama dashi ga kuma terrorist da suka sanƴa su gaba, kullum cikin kashe Al'ummar da basu ji ba basu gani ba ake, kenan wannan ƙasar za'a kai sa kenan yanzu?. "Nigeria?" ya maimaita hakan.............. _Littafin ZEEYAD na kuɗi ne, kan Naira ɗari biyar kacal (500), VIP group masu son posting sau biyu a rana kuma duba ɗaya ne (1000), zaki yi payment ɗinki Via 1489237499, Muhammad Hauwa Gana, Access Bank, sannan ki turo da shaidar biyan ki ta wannan number 07061979284, banda VTU please, ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali_ ```Kun tsorata koh?😠, Toh yaceen haka zakuji na faɗa a next page indai baku shararo min zazzafan comment ba😏``` *Kiyi sharing sabida Ƙaunar Allah da Annabi👏🏽* *MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *007...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..............Tafiya mai nisan gaske sukayi dan kuwa sun kai awanni huɗu akan hanƴa kafin su iso inda zasu. Nan duk motocin sukayi Parking kafin a fara bada umarnin fitowa. Duk mutane ne suka fara fitowa,sai da kowa ya fita kafin ZEEYAD ya fito. Ƙaton bakin ruwa ne wanda ke ɗauke da manƴan jiragen ruwa dayawa wasu sun fara tafiya wasu kuwa suna zuzzube a bakin ruwan ba'a fara tafiya ba. Wannan Abokin Abhi ɗinnan ne yayi wa ZEEYAD jagora zuwa wurin wani daban, gefe suka ja suka ɗanyi magana kafin ya haɗa sa da ZEEYAD da ya zamto ɗan kallo a wannan wuri. "Yaro wannan mutumin shine zaiyi maka jagora har zuwa inda zaku, duk wata buƙata taka ka tambaye sa zai yi maka ita bakada wata damuwa kaji?, ni zan koma inda na fito yanzu ka kula Allah Ubangiji ya sauƙe ku lafiya." Kai ZEEYAD ya jinjina tare da furta "Aameen" sannan yabi bayan wannan mutumin nan zuwa cikin wani jirgi. Ciki chan ƙasa suka shiga inda ya kasance kamar gida ne da ɗakuna a cikin sa harda falo da abubuwan da ba'a rasa ba na cikin manƴan jiragen ruwa. Wani ɗaki ya kai ZEEYAD yace "Tafiyar nan zata ɗauke mu tsawon makonni biyu, dan haka anan ne zaka dinga kwana sai dai ba kai kaɗai bane da akwai wasu ƴan kwanan ma, idan kana da abin shimfiɗa ka shimfiɗa shi ta gefen chan ka kwanta sannan kuma kayi takatsantsan da jakar ka, idan kana buƙatar wani abu koh ƙarin bayani zaka iya samu na a waje" yana faɗin haka ya juya ya fice. Da kallo ZEEYAD yabi ɗakin dashi, ɗaki ne shi ba ƙarami ba kuma ba babba ba ɗan madaidaici ne dai, inda kuma akwai tabarmai shimfiɗe wanda da alama akwai masu wurin. Gefe ɗaya ya samu ya zauna yana rungume jakar sa a jiki, kafin kuma ya shiga tunanin iriyar rayuwar da zaije ya tarar achan wani wurin da koh mafarki da tunanin zuwa bai ta6a ba. Maganar wannan mutumin da ta ɗansa ne ya faɗo masa rai, nan ya furta "Business?." Wasu ne suka shigo ɗakin nan ya maida hankalin sa kansu, duk da kallo suka bisa kafin su sami wuri kan wani tabarma su zauna. Ɗaya daga cikin su ne yace "Wai kowa ma ya waye ya gane da barin ƙasar sa yanzu zuwa wata, kai kuwa ɗan Saurayi mai zakaje yi a Nigeria, kuma daga ina kake?." Shiru ZEEYAD yayi bai iya tanka musu ba, nan ɗayan yace "Kai ina ruwan ka ne dashi, ka sani koh rayuwa ce tayi masa zafi ya gudo?." Haka nan suka cigaba da firar su yana jinsu bai tanka musu ba, sai ma ɗaukar jakar sa da yayi ya fice. Wannan mutumin da ya kawo sa ɗakin ya shiga nema kasancewar da akwai mutane dayawa ya sanƴa sa samun sa da kyar. ZEEYAD ne yace "Dan Allah, a'ina ne zan sami ruwa da abin sallah?." Kallon sa mutumin yayi yace "Kana nufin kace bakazo da komai ba?, ai komai na nan wurin na saidawa ne da akwai masu saida duk abinda kakeso har a sauƙa, idanma canjin kuɗaɗen ka kakeso ayi maka zuwa na Nigeria duk akwai wadanda zasuyi maka, kaje ta bayan chan nan ne inda aka ware wurin sallah sannan akwai masu saida ruwa a wurin." Kai ya jinjina yace "Nagode" kafin ya juya yabi hanƴar da mutumin ya nuna masa. Wuri ya samu ya zauna sai a sannan ya buɗe jakar da Sadeeq ya basa, kaya ne kala biyu a ciki, sai su bread da biscuits sai kuma ruwan gora, ruwa ɗaya ya ciro kafin ya maida zip ɗin jakar ya rufe. Wurin da aka ware kamar banɗaki ya gani nan yaje yayo tsarki kafin ya dawo ya ɗaura alwala sannan yayi sallah, Hannun sa ya ɗaga sama tare da kwararo addu'o'i sosai sannan ya miƙe ya ɗau jakar sa ya koma ciki inda ya fito. Matashi yayi da jakar tasa ya kwanta, dan kuwa ba ƙaramin bacci yakeji ba, da tunanen da bai san ranar yankewar su ba bacci ta kwashe shi. ************* ..........Bai farka ba sai da rana tayi lokacin kuwa har jirgin ya tashi yayi nesa da fara tafiya, fita ya sakeyi yayi alwala yayi sallah. Bai komo ciki ba sai ma samun ƙarafunan jirgin da yayi ya riƙe yana kallon ƙatuwar ruwan dama kuma yadda jirgin ke zuba uban gudu a kanta. Ya jima sosai anan har akayi sallahr La'asar yayi, a takaice dai anan wurin ya wuni har dare kafin ya koma cikin ɗaki. Kasancewar ya fara jin ƴunwa ya sashi buɗe jakar sa ya ɗauko biscuit guda ɗaya ya buɗe ta ya fara ci,sannan ya kora da ruwa a kai. He was so very emotional and lonely hakan yasa wasu hawayen da bai san da zuwar su ba shiga sauƙo masa, kansa ya sunkuyar ba tare da ya iya controlling hawayen nasa ba, babu abinda yake tunawa sai mahaifiyar sa dama kuma irin rayuwar da sukayi a baya harda Abhi ɗinsa dake tsananin ƙaunar sa amma daga baya kuma shine wanda yafi tsana wanda har ganin sa baya son yi. "Kai ɗan saurayi" yaji an faɗi hakan. Ɗagowa yayi nan yaji ɗaya yace "Ka dame mu fah da shessheƙa bakaga bacci muke yi bane?." "Kuyi haƙuri" kawai ya faɗa yana maida kansa. Sati ɗaya ya wuce sai dai har yanzu basu iso inda zasu ɗin ba, inda kowa da ka gani a cikin wannan jirgi toh fah rayuwar sa yake cikin kwanciyar hankali sa6anin ZEEYAD da kullum yake cikin ƙunci tare da rashin walwala, ga kuma kayan abincin sa da ya fara ƙarewa inda sau ɗaya kawai yake ci a rana ba zai sake ci ba sai washe gari duk dan gudun kada ta ƙare ya rasa na ci wataran, ga kuma yanayin yadda yaga mutanen cikin jirgin kowa na harkar gaban sa ne, babu wanda yakeyi wa ɗan uwan sa tayin abin ci koh sha, kowa rayuwar sa yake. A haka rayuwa ta cigaba wa ZEEYAD a cikin wannan jirgi, yau lafiya gobe babu lafiya har Allah yasa suka iso ƙasar Nigeria. Mutane ne yaji sun fara shewar "an iso, an iso, kowa ya adana kayan sa sannan ya 6oye kuɗaɗen sa." ZEEYAD da ya zamto ɗan kallo babu abinda ya fahimta, tafiya kaɗan jirgin tayi ta sauƙa a bakin ƙaton tekun ɗin. Mintina goma da tsayuwar ta mutane suka fara kokuwar fitowa sai a sannan yaga adadin cunkoson mutanen dake cikin wannan jirgi. "Kowa ya kula da dukiyar sa" yaji ana faɗa hakan yasa shi damƙe jakar sa a hammata. Sosai ya zama soko a wannan wuri inda kowa sai bangaje shi yake yana ficewar sa. A haka shima ya samu ya kutsa kansa cikin mutanen dukda kuwa irin ture sa da akeyi, a hankali yaji kamar ana jan jakar hannun sa ta baya, mamaki ne ya cika shi nan ya sake damƙe ta a hannu. Ihun wata tsohuwa ya jiyo tana faɗin an kwace mata jakar kuɗin ta, babu wanda ya kula ta sai ma baki da kowa ke turowa yana yin gaba abinsa. Ratsawa yayi cikin mutane zuwa gun wannan tsohuwa ganin mutane sun jefar ta sai tattaka ta akeyi. Hannu ya kai da shirin ɗagota, aikuwa caraff ta kamo hannun nasa tana ihun "Ga shi nan ga 6arawon da ya ɗauke min jakar kuɗi ta, yau Allah ya kama ka, dama kune masu yiwa mutane sata ai, Allah ya kama ka yau" ta ƙarashe cikin kuka. ZEEYAD ba ƙaramin mamaki yaci ba ganin tsohuwar nan na neman ɗaura masa sharri alhalin babu abinda ya aikata. Fuzge hannun sa yayi daga riƙon da tayi masa ɗin, ganin kowa na wucewa cikin sauri bai saurare ta ba yasa shi shima jan baya da ita yana kallon ta, ƙarshe dai nan ya baro ta sai kukan 6atan kuɗin ta take yayi gaba. Fitowa yayi daga cikin jirgin inda wani iska mai daɗi ya huro shi wanda ya sanƴa sa lumshe idanun sa, yayin da kuma tsikar jikin sa ya shiga tashi yana feeling so nervous wanda da kyar ya iya taka ƙafarsa ya fara tafiya yana bin mutanen wannan wuri da kallo kamar ɗan ƙauye. Bakin tekun ɗin haka yake kamar wani kasuwa mutane kala-kala, ga kuma wasu yellow ɗin Vans zuzzube dayawa duk sunji jiki sunji duniya inda kuma suke ta ihun neman passengers ɗinda zasuyi cikin gari dasu. "Central Market, Central Market, Central Market" shine yaji wani baƙin mutumi yana faɗa, inda ya zamto mummuna a idanun ZEEYAD ya tsaya yana ƙarewa wagegen bakin mutumin dake ta nanata" Central market" kallo dan kuwa karon sa na farko kenan da ya kalli baƙar fata sai dai fah dukda haka yaga na wannan mutumin ya bambamta da na saura, hakan yasa kansa ƙullewa ganin dai gasu nan dukkanin su baƙaƙe za'a kira su amma kowane da kallar baƙin sa masu haske ɗaɗɗaya yake gani. Kallon ZEEYAD da ya saki idanu yana kallon sa yayi yace "White Broda how far na, where u wan go?." Kai kawai ZEEYAD ya Jinjina masa dan kuwa idan ba "How far?" ba babu abinda ya gane cikin maganar sa sauran duk baiji ba kasancewar yadda yayi maganar cikin muryar ƴan shaye-shaye. Gaba yayi yana ta kalle-kalle ba tare da ya san inda yake sanƴa ƙafafuwan sa ba, in banda kallon mutane babu abinda yakeyi. Ji yayi an bangaje shi ya faɗi, nan ya juya ya kalli lukutar matar da ɗuwawun ta kamar wadanda aka hura musu iska tana sanƴe cikin Mini skirt ɗinda ya tsaya mata a guiwa sai harɗe ƙafafu take tana tafiya, idanu ya zaro waje wondering koh ita ma mutum ce, dan kuwa bai ta6a ganin ƙatuwa irinta ba. Haka nan ya miƙe tsaye tare da karkaɗe jikin sa yana kallon matar da tayi nisa sai dai bai bar kallon ta ba har yanzun dan kuwa mamaki yadda take iya tafiya ma yakeyi. Haka nan ya cigaba da tafiya duk inda ya samu ya jefa ƙafarsa haka ya fito daga cikin mutane. Nan kuma yaga ƴan acha6a birjik a gefe suma da alamun passengers suke nema. Ji yayi an riƙo jakar sa ta baya nan yaga ana jansa ana faɗin "Where u wan go?, pay 500 naira i will take you everywhere you want in Lagos." yaji mutumin ya faɗa tare da amsar jakarsa yana Ɗaurawa kan mashin ɗin nasa. Mamaki ne ya kama ZEEYAD nan yace "No, actually i don't have any money with me." "Ahh bro u must be joking nah, keep joke aside na, as fine boy as u are, u no get money?" an european boy" ya faɗa yana washe haƙora. "No am not from Europe" ya faɗa cikin sanƴi yana ƙoƙarin amsar jakar sa. "Are u waiting for someone to pick u up?, this one that ur body dey fresh like dis i know u must be from a wealthy Family" ya faɗa cikin washe masa haƙora yana maida masa jakar sa. Shiru kawai ZEEYAD yayi ya amshi abinsa tare da yin gaba, dan kuwa sam baya fahimtar turancin ɗan acha6ar nan. Tafiya ya cigaba da yi nan yaji ana yi masa horn a bayan sa, ɗan acha6ar nan ne dai ya sake biyo sa,nan yace dashi "Are u a lost, where u wan go?, make i take u for free." "For Free?" ZEEYAD ya tambaya yana kallon sa. "Ehen na, oya be fast oo before dis stupid cops arrived." Zuwa ZEEYAD yayi inda dakyar ya iya hawa machine ɗin dan kuwa bai saba ba, Hannun sa ya ɗaura a kafaɗar ɗan acha6ar gudun kada ya su6ule ya faɗi, nan ya tada ta suka hau tafiya. "Broda, where u wan go na?." "You mean, where i want to go?." "Yes." "Actually, i don't know." Slowing down ɗan acha6ar yayi yace "U don't know?." "Yes" ya basa amsa. "Where are you from, which country are you from?." Shiru yayi kafin kuma a hankali yace "Egypt." "Ehnn, no wonder u look so handsome and fresh like fresh tomato" ya faɗa cikin dariya. "So bro where should i take u now?" ɗan acha6ar ya sake faɗa. "Anywhere" ya faɗa. Kara gudun mashin ɗin yayi, tafiya mai nisan gaske sukayi kafin su fara shigowa cikin gari, da kallo ZEEYAD ke bin wuraren da kallo, ganin duk tsofaffin gine-gine sunfi yawa ga kuma saman langa-langar su da duk a kokkoɗe sunyi tsatsa, ga kuma wani uban traffic jam da aka haɗa akan hanƴa. Sosai ɗan acha6ar nan ya cika shi da surutu, har suka iso inda zasuje yayi parking. "Yauwa kaga nan garage ne na kawo ka, ba zaka rasa wurin kwana ba." Rungume jakar sa yayi yace "Thank you so very much." "Don't mind na, it's my pleasure to meet such a handsome guy like u and even have a Conversation with." Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi ba tare da yace dashi komai ba. "Alright bro, good luck i pray we met somewhere again" ya faɗa cikin dariya yana jan Babur ɗinsa yayi gaba. Da kallo ZEEYAD ya bi shi yana mamakin dama akwai mutanen kirki har haka, ya ɗauko shi daga wuri mai nisa sai dai koh biyar bai caje sa ba, inama ya ƙarashe guntun rayuwar sa cikin haɗuwa da ire-iren wannan ɗan acha6ar. Kallo ya ƙarewa tashar motar , kafin kuma ya samu wuri daga gefe ya zauna yana bin mutane da kallo. Kowa na harkar gaban sa, yayin da masu sayar da abinci da toye-toye suma na yin nasu. Hango table ɗin wata inƴamura yayi plate ɗauke a hannun ta tana ɗebo farin shinkafa daga cikin kula sai fitar da tururi yake, ƴawu ya haɗiya lokacin da yaji cikin sa tayi wani irin ƙarar ƴunwa. Rabon sa da ya sanƴa abinci a bakin sa kwana biyu kenan, miƙewa yayi daga inda yake zaune ya nufi wurin wannan mata. Hango sa da tayi ne yasa ta washe haƙora tace "Ah ah Customer, welcome, u too fine oo ehnn,welcome" ta faɗa tana kallon sa. "Hi" yace da ita. "Hi, have a seat na, what do you want to buy?." Murmushi yayi yace "Nothing...i...i am hungry pls help me with...." Ai bai idda ba yaji ta daka masa wani irin tsawar da bai ta6a jinta ba tunda yake a rayuwar sa, hakan yasa shi jan baya da sauri. "Help?, help my foot, help u with what?, abeg my friend get lost from here, are you the one that gave me the profit to start this business, idiot, abeg move ur dirty body away from here don't come and infect my food,broke white guy mtssswww," ta ƙarashe cikin jan doguwar tsaki kamar bakin ta zai faɗi ƙasa sai masifa take ta zubawa cikin yaren da baya fahimta. Da sauri ya bar wurin yana danasanin sa na zuwa gashi a banza tayi disgracing ɗinsa gaban mutane kowa ya gane barar abinci yaje yi abinda bai ta6a ba, sosai yaji ciwon hakan, wuri ya samu ya zauna kawai yana cigaba da aikin kalle-kallen sa.............. ******************* .........."Your Highness, we have searched everywhere but the Prince is nowhere to be found" ya faɗa cike da girmamawa kansa duƙe a ƙasa. Sosai Ran mai Martaba yayi mummunar 6aci jin labarin da ake kawo masa kullum tsawon sati biyu da 6acewar ZEEYAD. "It's been two weeks now, sai dai har yanzu no one knows his whereabout, mun samu bayanan cewa tun lokacin da Sooraj ɗan wurin Abdulhakeem yazo da dakarun sa sukayi wa Yarima ZEEYAD dukan mutuwa tundaga ranar kuma ba'a sake ganin sa ba" ya sake faɗa cikin girmamawa. Tashi tsaye mai Martaba yayi yace "Ku kawomin Abdulhakeem dama kuma Sooraj nan wurin, bama su kaɗai ba da dukkanin wasu dangi ku aika musu da cewa ina buƙatar su a fada yanzun nan, include the QUEEN'S" Ya ƙarashe cikin kakkausar murya idanun sa na yin jaa. Duƙawa yayi cike da girmamawa sannan ya fice dan zuwa aiwatar da umarnin mai Martaba. Mintina ashirin mai kyau fada ta cika Family kowanne zaune da iyalan sa a gefe wanda aƙalla zasu kai su biyar. Da kallo mai Martaba ya bisu dukkanin su kafin kuma yace "Ɗa na Yarima ZEEYAD, yau sati biyu kenan da 6atar sa ba'a gansa ba, sannan rahoto yazo min cewa Sooraj ɗa ga Abdulhakeem shine wanda aka gansu tare ƙarshe ya sanƴa bayi sunyi masa duka, Sooraj" ya kiraye sa da ƙarfi yana aika masa da mugun kallo. A razane Sooraj ya miƙe tsaye cike da girmamawa ya duƙa yace "Yes your Highness." Shiru mai Martaba yayi kafin yace "A'ina ka kai min ɗa na?." Kame-kame ya fara kafin yace "Wallahi ranka shi daɗe, tun lokacin da muka samu sa6ani dashi ban kuma sake sanƴa sa a idanu na ba, sabida na dai san lafiya ƙalau na...na taho na bar sa a wannan wurin" ya ƙarashe yana kallon Mahaifin sa. Mai Martaba ne yace "Kada ka nemi ka raina min hankali mana, Abdulhakeem koh kasan da abinda ɗan ka ya aikatawa Yarima ZEEYAD?." Tashi Abdulhakeem yayi yace "Kwarai kuwa ranka ya daɗe, dan kuwa nayi masa faɗa sosai akan hakan kuma yayi nadama yace ba zai sake ba, har ma nace ya koma yaje ya baiwa Yarima ZEEYAD haƙuri amma kuma sai ya dawomin da labarin cewa bai gansa ba ya bar wurin." "Tayaya zaka yarda da ɗanka bayan kasan muguwar zuciya irin tasa, koh ka sani shine wanda yayi sanadiyyar 6acewar Yarima ZEEYAD sannan kuma ya 6oye maka gaskiya." Cikin ruɗewa Sooraj ya fara faɗin "Abhi wallahi bansan komai kan 6acewar Yarima ZEEYAD ba, nidai nasan kawai nasa dogarai sunyi masa duka ne amma bayan nan kuma babu abinda ya sake shiga tsakani na dashi." "Hafeezah!" cewar mai Martaba a tsawace. Sarauniya Hafeezah da duk hankalin ta yayi gaba jin mai Martaba na kiran ZEEYAD da sunan ɗansa har ma da kiran sa Yarima yasa hankalin ta mugun tashi, a razane kuma ta ɗago tana kallon sa sabida yadda ya kira sunan nata. "Ina ɗana?" ya faɗa yana kallon ta. Cikin in-ina take faɗin "Bansaniba, bansan inda yake ba nayi maka rantsuwa da Allah babu abinda na sani game da 6atar sa." Tsaye ya miƙe yana sarƙe hannaye a baya yace "Na baku nan da kwana ɗaya ku nemo inda ya shige, idan kuma baku aiwatar da hakan ba toh ina mai tabbatar muku da cewa sai kun fuskanci hukunci mai tsananin gaske" yana faɗin haka ya wuce fuuu tare da haurawa sama ya bar su nan zaune kowa da abinda ke gudana cikin zuciyar sa. Murmushi Sarauniya Nazeerah ta saki dan kuwa ita babu abinda yafi burgeta face taga ana rigima,dan kuwa ita bata tsani kowa ba amma burin ta shine kullum ace rigima bata ƙarewa. Sarauniya Hafeezah kuwa idanun ta yayi zuru-zuru,inda kuma take tunanin komawa wurin bokan ta dan kuwa taga kamar asirin ta na shirin tonuwa. Sarauniya Naseeba kuwa ba ƙaramin tashin hankali da baƙin cikin 6acewar ZEEYAD ɗin take ba, dan kuwa bata samu ta aiwatar da burin ta akansa ba, sai dai fah bata cire rai ba komin daren daɗewa sai ta aiwatar da abinda tayi niya akansa. Duka sauran miƙewa sukayi suna ficewa da Family ɗinsu ɗaya bayan ɗaya, kafin Abdulhakeem ma ya tashi suka fice da nasa iyalan. Kallon Sarauniya Hafeezah Nazeerah tayi tace "Uhm, idanu sun raina fata yau Hafeezah, da alamu kamar muguwar ƙullin ki na shirin warware wa koh?." Tsaki taja tana miƙewa tsaye ta fice kamar zata tashi sama. Da kallo ta bita tana murmushi kafin kuma ta dawo da idanun ta kan Naseeba, murmushi ta sakar mata tace "Ke kuma fah, kina kewar masoyin naki ne?, sai ki bada himma wurin gano inda ya shige." Kamar zatayi kuka haka nan ta tashi itama tana ficewa ba tare da ta tanka Nazeerah ba. "Wow! Wow!! Wow!!!, inajin daɗin wannan drama sosai da sosai, dukkanin su sun ɗaurawa kansu babban aiki, basu san da cewa dukkanin abinda suke aikatawa mai Martaba na sane ba kawai kyale su yake yaga iya gudun ruwan su, mahaukatan banza da wofi, yanzu kuma da suka kai sa maƙura bari muga mai zai aiwatar akai dan kuwa da alamun yanzu aka fara wasan, yayin da nikuma zan zama ƴar kallo" ta ƙarashe cikin murmushi mai cike da jindaɗi............. ********** .........."Tsaye yake gaban tafkeken hoton ta yana kallo inda kuma hawaye suka shiga yi masa zarya a kan fuska. "Lateefat, Haƙiƙa naci amanar ki, ban kula da amanar da kika barmin ba, na gaza kula da ɗa kwaya ɗayan da kika bari,na ruguza masa rayuwar sa dama kuma mafarkin sa, bana ta6a tunanin zai iya yafemin, Hafeezah tayi nasarar raba ni dashi, Haƙiƙa ina matuƙar ƙaunar ZEEYAD fiye da kowa, sai dai nazo na wayi gari babu shi babu labarin sa, sai a sannan ne kuma hankali na ya dawo, bayan ɗa mafi soyuwa a gareni yayi nisa dani, bayan sunyi nasarar cusa masa tsana ta a zuciyar sa, bana tunanin zan yafewa ɗaya daga cikin su akan abinda suka aikata."............. *Idan kin karanta kiyi sharing sabida ƙaunar Allah da Manzon sa👏🏽* *MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *008...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..........Haka nan yayi ta zama a wannan wuri shi kaɗai inda kuma yake bin kowanne mahaluƙi da yazo wucewa da idanu. Sosai ya jigata da ƴunwa wannan karon dan kuwa ga abinci nan na saidawa yana gani amma babu damar ci, dan kuwa ya lura ma da cewa mutanen wannan tasha kamar ɗabi'ar su ce masifa da faɗa, dan kuwa a ɗan zaman san nan anyi faɗa a gaban shi ya kai sau shida, ga kuma ƴan shaye-shaye da bushe-bushe nan birjik abin ba'a cewa komai. Tashi yayi da jakar sa a hannu ya fice daga tashar. Tafiya mai nisan gaske yayi kafin ya samu gindin wata ƙatuwar bishiya ya zauna. Jakarsa ya ajiye anan tare da ɗaura kansa akai kan kace miye kuma baccin wahala ta kwashe shi. Sosai ya sha bacci kafin ya farka, dube-dube ya hau yi ganin babu jakar sa babu alamun ta. Tashi yayi tsaye yana duddubawa har bayan bishiyar ya zaga babu an sace. "It was Stolen" ya faɗa kamar zaiyi kuka. Da sauri kuma ya kai Hannu kan wuyar sa nan dai yaji sarƙar tasa na nan, wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furta "Alhamdulillah" yana maida ta cikin rigar sa, kafin kuma ya hau tafiya yana barin wurin........... *THREE WEEKS LATER* ........Rayuwa a haka tayi ta tafiyar wa ZEEYAD cike da wahala da ƙunci. Dakyar yake samun na ci da sha balle kuma na wankan tsaftace jikin shi. Duk inda ya shiga kowa tsangwamar sa da hantarar sa yake, musamman yarbawa da inƴamuran nan masu shegen masifa kamar saci kai. Da kyar da ikon Allah ya samu wani local Restaurant inda wata mata ke saida abinci yana yi mata wanke-wanke inda ita kuma take biyan sa da abinci, a takaice dai ya zama ɗan aiken ta dan kuwa shi ke serving customers abinci ma yana kai musu idan sun zo saya koh ci. Yau ma zaune yake yana wanke plates ɗinda akaci abinci dashi sabida sunyi ƙaranci sai an wanke kafin a samu na sanƴawa wasu abinci. Bayan ya wanke ne ya ɗauka ya kai yana miƙa mata cike da girmamawa. Amsa tayi cike da masifar baya sauri sai ya kora mata customers ta fara zuba abincin kan ta miƙa masa ya kai. Cikin ɗan ɗakin da aka ware na zaman customers ya shiga tare da nufar teburin wanda akace ya kaiwa abincin. Samun mutumin yayi zaune yana waya inda kuma yake ta kyakyata dariya da alamun dai wani abin ake faɗa masa a wayar. Ajiye masa abincin ZEEYAD yayi sannan yaje ya ɗauko masa ruwan pure water guda ɗaya ya ajiye masa yana shirin ficewa ne wannan mutumin ya yafito shi da hannun sa kan ya tsaya. Tsayuwa yayi jiran sa inda shi kuma ya cigaba da wayar sa yana kyakyata dariya ga kuma abinci da ya sanƴa a gaba yana ci. Da kallo kawai ZEEYAD ke binsa ganin ya barsa tsaye shi bai ce masa komai ba, sannan kuma bai barsa ya tafi ba. Har saida ya kusa idda cin abincin kafin uwargijiyar ZEEYAD ta shigo ciki kafin kuma ta hau balbale sa da masifar ya shanƴa ta a waje bai zo ya baiwa sauran customers abinci ba "So kake ka kora min customers su daina zuwa wuri na kalan ma suce ba'a kar6ar su yadda yakamata, ni banma san uwar miye da tsautsayin da ya kai ni ɗaukar ka aiki ba dallah wuce kaje ka wanke min plates mutane na jira" ta ƙarashe tana aika masa da muguwar kallo. Wannan mutumin kuwa da kallo kawai yake bin su bai ce komai ba yana cigaba da wayar sa da cin abincin sa. "But he asked me to wait" ya faɗa. "Zaka wuce ne kokuwa sai raina ya 6aci?." Wucewa yayi yana mamakin wai a hakan ma ranta bai 6aci ba kenan da wannan uban masifar da ta rufe shi. Fitowa tayi kamar zata tashi sama dan masifa ta hau aikace-aikacen ta. Da kallo yabi mutumin da ya fito yana biyan matar kuɗin ta kamar baya so sannan yayi gaba yana jin kamar ya bishi ya rufe shi da duka dan haushi. A haka har dare kafin ta sallame sa da naira ɗari biyu tace "Yau ka 6ata min rai shiyasa ba zan baka ɗari uku ba, ina mai tabbatar maka idan ka sake ka kuma 6ata min rai zan daina ma baka abincin baki ɗaya da tukwuicin aikin" ta faɗa tana wani yayyatsina fuska. Amsa yayi ba tare da ya raina ba yayi godiya yana sanƴawa cikin aljihun sa kafin yayi mata sai da safe ya wuce. Tsinkayo muryar ta yayi tana faɗin "Ka tabbatar fah gobe ka fito dawuri sabida kasan akwai share-share da gyare-gyaren da zakayi koh?." Kai ya jinjina mata yana wucewar sa. Gidan wani wanka ya biya ya biya kuɗi yayi wanka da wasu ƴan buƙatun sa kafin ya wuce inda yake kwana. Rumfar wani mai shayi ne yake zuwa ya kwana inda yake biyan sa naira ɗari kullum kuɗin kwana. A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a garin na Lagos wanda babu laifi ya ɗan tara kuɗaɗen sa, sannan kuma duk wani aiki idan ya samu na ƙarfi Wanda za'a biya sa yin abinsa yake, a haka har ya fara ganewa da yanayin rayuwar Lagos ɗin ya rage shan wahala kamar dah. Cikin kuɗaɗen da ya ɗan tara ne yaje kasuwa ya ɗan sayi kayan sawa da ɗan abubuwan da ba'a rasa ba na amfanin shi. Wata rana yana zaune Shi kaɗai kasance matar da yake mata aiki ta daɗe da korar sa hakan yasa yake shan wahalar samun wani aikin kuɗin. Aljihun sa ya duba ya ciro ƴan kuɗaɗen sa dake ciki tare da ƙirga su, dubu ɗaya ce da ɗari uku da hamsin ta rage masa a hannu. Tunani yake tayi dan kuwa indai bai sami wani aikin ba, babu inda zai dinga samun kuɗin biyar wurin kwana indai wadannan na hannun sa suka ƙare. Miƙewa yayi dan kuwa yau yayi alƙawarin sai ya samu wani aikin yi ɗin. Sosai yayi yawo sai dai babu abinda ya samu, wuri ya samu ya zauna yana hutawa. Wata Mota ce ƙirar Golf tayi parking kusada wani gida da yake zaune, inda wani mutum ya fito daga ciki jikin sa sanƴe da manƴan kaya irin ta Hausawa. Da kallo yabi ZEEYAD kafin ya shige cikin gidan nan. Ya daɗe sosai kafin ya fito nan yaga har yanzu yana nan ya haɗa kai da guiwa, zuwa wurin sa wannan mutumin yayi tare da dafa sa. Da sauri ya ɗago yana kallon sa buɗar baki mutumin yayi yace "Mai kakeyi anan?" cikin muryar turanci. "Babu komai ina hutawa ne sabida gajiya da nayi" ya basa amsa. "Da alamu kai ba ɗan ƙasar nan bane koh, daga wace ƙasar kake?." Shiru ZEEYAD yayi bai basa amsa ba hakan yasa mutumin cewa "Na gane bakason faɗamin, amma koma dai menene da alamun kana buƙatar taimako koh?." Da sauri ZEEYAD ya girgiza masa kai yace "Duk aikin da ka bani zan iya shi kuma nayi maka alƙawarin ba zan 6ata maka rai a aikin ka ba, zanyi maka aiki ne tsakani da Allah." "Kai musulmi ne?" mutumin ya tambaye shi. Kai ya jinjina masa nan yace "Masha Allah, zan baka aiki idan kanaso amma fah ni ba anan nake zaune ba kuma ba anan nake aiki ba, sai dan nakan zuwa kowane ƙarshen sati biyu ina duba iyali na, nan ne gida na sannan kuma ni mutumin Kano ne kuma bahaushe." "Kaima musulmi ne?" cewar ZEEYAD ɗin. "Kwarai kuwa." Murmushi yayi yace "Sai yau na haɗu da musulmi tunda nazo wannan ƙasar, kuma kai ne mutum na farko da ka tausaya min har kake ƙoƙarin bani aiki bayan ban sanka ba, Nagode." Murmushi mutumin yayi yace "Badamuwa, duk yiwa kai ne, yanzu haka Kano zani, shin zaka iya bina yanzu kokuwa zaka jira sai nazo wani hutun kuma?." Da sauri ya jinjina masa kai yace "Zan bika indai har hakan zai sa na sami na kaina." "Insha Allah, kada ka damu taso muje." Nan ya tashi yabi wannan mutumin da baisan koh wanene shi ba suka kama hanƴa....... ********** .....Kamar yadda wannan mutumin ya faɗa sai gasu a garin Kanawan dabo. Da kallo kawai ZEEYAD ke bin koh ina da kallo dan kuwa daga ganin wannan garin yafi garin da ya baro fasali dama kuma daɗin zama. Hotel ne mai kyau da tsada suka nufa inda wannan mutumin ya biya kuɗin ɗakin mutum biyu, sannan yayi ordern abinci. Ɗakin ZEEYAD ya nuna masa kafin ya umarce sa da yin wanka ya huta kafin a kawo masa abinci. Haka kuwa akayi bayan yayi wanka ya sauya kayan sa zuwa wata ne aka kawo masa abinci da abin sha mai rai da lafiya yaci ya sha ya ƙoshi. Mutumin ne ya dawo yace dashi Nasan mun ɗebo gajiya ka kwanta ka huta kafin zuwa gobe da safe dan kuwa akwai baƙon da zamuyi shine zai baka aikin nan. Kai ya jinjina yace "Nagode." Nan mutumin ya fice kafin shi kuma yabi lafiyar gado ya kwanta. Bacci yayi cike da jindaɗi da kwanciyar hankali, cikin dare ya farka yayi Nafilolin sa kafin zuwa washe gari yayi sallahr Asuba. Da safe aka kawo masa breakfast mai rai da lafiya yaci, kafin wannan mutumin ya shigo ya basa wasu kaya sannan yace dashi yayi wanka ya gyara jikin sa baƙon ya kusa zuwa. ZEEYAD da bai kawo komai cikin ransa ba yayi kamar yadda wannan mutumin yace dashi,wanka yayi ya sanƴa kayan nan, shadda ce janfa da tayi matuƙar kar6ar sa yayi kyau dukda kuwa ba iya sanƴa ta yayi ba amma ta kar6e sa matuƙa inda mutumin nan kuwa yayi ta yaba kyawu da haɗuwa irin ta ZEEYAD ɗin kamar wani mace, shi kuwa sam bai kawo komai a ransa ba dan kuwa ya ɗauka wannan mutumin na Allah ne. Bayan wani lokaci wannan mutumin ya shigo da wani Alhaji ya sha manƴan kaya cikin nan nasa kamar tulu sai zuba ƙamshi yake. Ganin ZEEYAD kuwa ya sa shi rikicewa nan yace da wannan ɗinnan cikin muryar hausa da bai fahimci mai suke cewa ba yace "Lallai aikin ka na kyau Lawal, a ina ka samo wannan santalelen hallitar haka, tunda nake ban ta6a ganin kyakkyawa kamar yaron nan ba, lallai kyautar ka ta musamman ce wannan karon da fatan dai kayi masa bayanin komai?." Cike da girmamawa yace "Godiya nake ya Alaj, ai banyi masa bayani ba tukun dan kuwa baya ma jin hausa sannan kuma ba ɗan ƙasar nan bace da alama neman kuɗi ce ta kawo sa nan, wannan ne dalilin da yasa nayi amfani da wannan dama na kawo maka shi kaji daɗin ka, dan kuwa tundaga Lagos na ɗauko shi sannan bashida kowa anan." "Madallah aikin ka na mugun kyau Lawal, bani jakar kuɗin nan." Nan ya miƙa masa Briefcase ɗin hannun sa kafin ya nufi ZEEYAD cikin muryar turanci yace "Yaro ya sunan ka?." "ZEEYAD" ya bashi amsa. Murmushi yayi yace "masha Allah, Allah yayi halitta anan wurin" nan ya buɗe jakar inda rafa-rafa ɗin American dollars suka bayyana. Idanu ZEEYAD ya waro kafin ya kalli mutumin. Dariya mutumin yayi yace "Na san da ganin kuɗin nan ba zai sa kaƙi amincewa da buƙata ta ba, indai ka amince wadannan kuɗaɗen gabaɗaya sun zama naka har ma da ƙari idan kana buƙata, zakayi dukiyar da har ka mutu ba zaka gama cinƴe ta ba." ZEEYAD da zuciyar sa ta fara raya masa ba alkhairi tattare dasu ne yace, "Mai...mai Kake nufi, wadannan kuɗaɗen dollars ne, aikin mai zanyi muku da har zaku biya ni da wannan uban kuɗaɗen?." Dariya yayi yana shafo gashin kan ZEEYAD tare da lashe baki yace "Kai dai kawai ka bada haɗin kai wannan aikin sirri ce, ba kowa ne ya santa ba sai mai sa'a da rabon yin dukiya." Ja da baya yayi ransa na 6aci yace "You are a Gay." Murm mutumin yayi yace "Ya'akayi ka gano dawuri haka, shikenan ma tunda ka fahimce ni, ka bani haɗin kai muyi abin nan ka amshi wadannan ɗumbin kuɗaɗen." "Never" ya faɗa tare da Ɗaurawa da faɗin "Ba abinda ya kawo ni ba kenan neman kuɗi ta hanƴar haram, i will never engage myself into that shit, koh da kuwa zan mutu ne da talauci, zuciya ta ba matacciya bace kuma ba gur6atacciya bace, duk halin da na tsinci kaina jarabawar Ubangiji ce, dan haka ba zan ta6a yarda na faɗi ba akan wadannan kuɗaɗen da basuda albarka kuma suke saurin cinƴewa kamar wuta na ƙona takarda, sai dai ku nemi wani mai kwaɗayin irin halin ku amma ba ZEEYAD ba, kai kuma na ɗauka na haɗu da mutumin kirki ne kamar yadda ka nuna min a farko ashe dai ba haka bane, all of you are a disgrace to our religion, kunyi asara duniya da lahira muddin baku tuba ba" yana faɗin haka ya ɗau ledar kayan sa tare da bangaje su yayi ficewar sa zuciyar sa na mugun ƙuna. Ya rasa dalilin da ya sanƴa yake ta haɗuwa da gur6atattun mutane marasa tsoron Allah a rayuwar sa hakan na nufin ba zai ta6a haɗuwa da na kirki koh ɗaya ba kenan komiye?. Sosai yaga garin na Kano ya sha bambam da inda ya baro, garari ya sha sosai kafin ya samu wani wuri ya fake yana maida ajiyar zuciya. Lalumar aljihun sa yayi koh nan yaji wayam babu kuɗin sa, nan kuma ya tuna fah ashe ba kayan bane a jikin shi. Wani lungu ya samu ya shiga ya canza kayan jikin nasa yana zubar da wanda suka basa "They are so disgusting" ya faɗa yana barin su a wurin, dan kuwa da da hali ma abincin da suka basa amayar da banza zaiyi dan ba zai iya cin haram ba. Hamsin ya ɗauka daga cikin kuɗin wurin sa ya sayi ruwan sha da biscuit yaci kafin kuma ya sake kama hanƴa duk inda yabi kuwa sai dai ayi ta kallon sa. A haka har ya samu ya shigo wani ungwa dukda baisan koh ungwa bace amma dai yaga gidajen mutane dama kuma yara na ta wasan su. Gefe da wani Islamiyya ya samu ya zauna yana ta6a wuyar sa yaji har yanzu sarƙar sa na nan. Anan yakeyin sallahr sa har yamma tayi aka tashi daga wannan islamiyya. Yara ne suke ta fitowa suna wucewa gidajen su, wasu na tsalle-tsalle wasu kuwa da guje-guje haka suke tayi. Ɗago kai yayi ya hango ta ta ƙura masa idanu tana kallo, kamar wacce taga wani sabon halittar da aka jefo daga sama. Maida kansa yayi sakamakon zuciyar sa da yaji tayi wani irin bugu lokacin da ya haɗa idanu da yarinƴar. Sake ɗagowa yayi nan yaga dai shi take kallo har yanzun, 6ata fuska yayi yana kallon cikin manƴan idanun ta da ta kafe sa dashi. _"Is she a witch?"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa. _"I know she must be one, dan naji labarin mayu sunyi yawa a chan garin, Maybe nan ma hakan ne"_ ya sake faɗa. Kauda nasa idanun yayi yana faɗin "Her eyes are so damn wide." "Ke dallah banza wuce mu tafi kin wani kafawa mutane da idanu kamar wata mayya yau kika fara ganin bature ne koh miye" Cewar Yaron yana makar ƙeyarta. Barin kallon sa tayi nan ya kama hannun ta suka wuce, dukda haka saida ta sake waigowa tana kallon ZEEYAD ɗin. _"Yeah, babu tantama she must be a witch, who knows ma if she has an evil eye"_ ya faɗa a zuciyar sa yana kauda kai daga kallon ta. Yarinƴa ce da ba zata wuce shekaru goma ba, ba baƙa bace sannan kuma ba fara bace ita, tana da wani irin kyau mai ɗaukar hankali, kyakkyawa ce sosai, hannun nata na riƙe cikin na yayan nata har suka 6ace wa ZEEYAD da gani bata daina kallon sa ba. Sallama sukayi suka shiga cikin gidan mai ƙaramin ƙofa ne, amma babu laifi gidan da ɗan girman sa, sannan part biyu ne a ciki ɗaya na kallon ɗaya. Mata matashiyar mata ce suka tarar tsakar gidan ta hura wuta a mukubur tana girki, sai dai ita ɗin fara ce sosai kamar yaron. Yaron ne da ba zai wuce 13years ba yace "Umma kinga DEENAH har yanzu bata daina kallon mutane kamar ta samu TV ba koh?." Ɗagowa matar tayi tace "Dama ai mai hali baya fasa halin sa, bari wataran ta samu masu yi mata duka zata dawo hayyacin ta ta daina ne, wuce ki cire uniform ɗin naki kici abinci kizo ki daka min wannan tarugun yanzu." Wucewa tayi sum-sum ba tare da tace komai ba ta buɗe ƙofar net ɗinda akayi sa dan rufe barandar gidan inda kuma nan ne kayan kitchen ɗinsu ke ajiye a gefe guda, ɗayan gefen kuma ɗaku na ne guda biyu a jere. Ɗayan ta shiga inda ya kasance bedroom ne ta hau cire uniform ɗin jikin ta. Canza kayan nata tayi zuwa doguwar riga sannan tasa hula ta fito barandar. Abinci ta ɗeba a plate kafin ta shimfiɗa tabarma ta buɗe ƙaramin fridge ɗin dake tsaye ta ɗau ruwa ɗaya. Abinci taci Sannan ta fito ta kamawa Ummar tata aikin da ta sanƴa ta. "Ki gama kije ki sayomin maggi a shagon Manu, nama manta Maggin ta ƙare. Sai a sannan ta buɗi ɗan ƙaramin bakin ta tace "Toh." Bayan ta gama ne Ummar tata ta bata Naira ɗari tace "Ki Sayomin maggin Ɗangote na hamsin star na Hamsin, kuma dan Allah ki ɗaga ƙafa ki dawo dawuri bance ki tsaya kalle-kalle ba." Zuwa tayi ta sako Hijabin ta kafin ta sanƴa takalmin ta ta fice. Tundaga nesa ta hango sa zaune inda suka gansa ɗazu,nan kuma ta fara aikin kallon nasa ga kuma sam bata sauri a tafiyar tata a hankali take tafiya har tazo ta wuce shi bai sani ba kasancewar kansa na kan guiwowin sa. Sayo aiken tayi ta dawo nanma ta tarar yana nan har yanzun, lailaya ledar maggin hannun ta ta fara tana cigaba da kallon shi harda leƙe koh zata ga fuskar sa. Ɗagowa yayi nan suka haɗa ido, mamaki ne ya cika ZEEYAD ganin kamar itace yarinƴar da ya gani da uniform ɗazu. Kallon kallo suka shiga yi kowanne bai ɗauke idanun sa ba, ita tana yi masa kallon da ta saba yi ne idan taga mutane, shi kuwa kallon mamaki yakeyi mata wondering mai take nema a jikin sa. Gasping tayi lokacin da ledar da take lailaiyawa ɗin ya fashe maggin ta zube a ƙasa. Da kallo ya bita ganin yadda ta saki baki tana kallon maggin. A zuciyar sa yace _"Ba abin ka taimake ta ba yanzu ta lashe maka ƙuruwa, Mayya"_ Hannu tasa ta ɗebi maggin ta sanƴa su cikin Hijabin ta kafin ta kallesa sannan tayi wucewar ta. Sallama tayi ta shigo gidan tare da miƙawa Ummar tata aiken,tsaye kawai tayi tana kallon ta tsabar takaici ace a aiki mutum tunɗazu kamar wanda ba'a yi masa warning ba sai yanzu yake dawowa. "Kin kyauta ai" kawai ta faɗa tana amsar maggin. Zama tayi kan dakalin bakin part ɗin nasu tana kallon Ummar ta dake girki. "Kinci abincin ne?" ta tsinkayo muryar Mahaifiyar tata. Kai ta ɗaga mata kawai kafin kuma tace "Umma akwai wani almajiri a waje, na ɗau sauran abincin na kai masa?." Kallon ta tayi tace "Ki duba idan yayan naki yaci nashi sai ki ɗauka ki kai masa." Da sauri ta miƙe ta shige tare da buɗe tukunƴar abincin, juyawa tayi ga yayanta dake cin nasa abincin kafin kuma ta ɗau kula da murfin sa ta juye sauran a ciki ta ɗau cokali tare da ɗaukar ruwa ɗaya a fridge ta ɗaura akanta ta fito. Mamaki ne ya cika mamar tace "Ke kuma ina zaki da kula?." "Umma ai almajirin yana ta wurin islamiyyar mu ne zan kai masa ya juye sai na dawo da kulan." "Yi sauri toh karki daɗe,kinga dai Magrib ta gabato koh?." Ficewa tayi da sauri dan kar ya tashi ta isa gareshi. Tsaye tayi a kansa tana kallon sa ba tare da tace komai ba. Ɗagowa yayi jin kamar tsayuwar mutum akansa, it's that same girl dai. Bai san sadda ya haɗe rai murtuƙ ba yace "What?." Kular abincin ta miƙa masa ɗauke da ruwa a kai, da kallo yake bin kular hannun nata da kallo nan yace "No thanks" ya faɗa yana kauda kai daga kallon da take masa. Sake tura masa kular tayi, nan ya ɗago ya kalleta yace "I don't trust you, so i won't eat this food, take it away." Sake tura masa kular tayi kamar zata sa masa a baki,a fusace kuma cikin tsawa yace da ita "I said i don't want it." Da mugun tsoro taja baya jin yadda yayi mata maganar ransa na 6aci wanda ya sanƴa ta yar da kular hannun nata abincin ya zube. Da mugun kallo ya bita kafin kuma ya tashi yana ɗaukar ledar sa ya barta nan tsaye kamar zatayi kuka............... *Babu Posting On Week days* *MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *009...* _So i decided nayi posting yau ganin yadda kuke ta tambayar ZEEYAD, So here is he now, enjoy😉_ _Banyi editing ba_ .............Hannu tasa ta ɗau kular ta kafin ta bisa da kallo idanun ta na tara hawaye. Tafiya ta fara nan taji yace "Hey." Tsayawa tayi tana kallon sa daga inda yake zaune nan yace da ita "Am sorry" dan kuwa yaga kamar ranta ya 6aci, shi kuma ba zai so ya zamto sanadiyyar 6acin ran wani ba dukda kuwa taimakon sa tayi niyar yi sai dai yayi alƙawarin ba zai sake yarda da wani ba a rayuwar sa dan kuwa duk gur6atattun mutane yake haɗuwa dasu, ita ɗinma kallon mayya yake yi mata dan kuwa bai yarda da cewa wannan kallon nata na lafiya bane. Juyawa tayi a hankali kawai ta cigaba da tafiyar ta dan kuwa ta fahimci mai yace mata, haƙuri ya bata dan haka sai taji ta daina fushin ta nufi gida. Shigar ta gidan aka shiga kiran sallahr Magrib, dan haka buta ta ɗauka tayi alwala sannan ta shige ciki. Ɗayan ɗakin ta shiga inda ya kasance falo ne masha Allah mai kyau dashi babu laifi sai tada ƙamshin turaren wuta mai daɗi yake. Sallaya ta ɗauka ta tada sallah tana cikin yi Ummar ta tazo itama ta tada nata sallahn kusa da ita. Suna idarwa sukayi addu'o'i kafin Mahaifiyar tata ta kar6i haddar karatun da take ɗaura mata a gida,kuma Alhamdulillah duka ta kawo su daidai. Murmushi mahaifiyar tata tayi dan kuwa Allah ya bata ƴaƴa masu albarka, ilimi dama kuma kaifin basira nan tace "Masha Allah, Allah yayi miki albarka DEENAH ta." "Aameen Ummah na" ta faɗa tana sakin murmushin jindaɗi wanda ya sanƴa dimple ɗin ha6ar ta lotsawa. Basu tashi a wurin ba sai da sukayi sallahr Isha'i, ta sake ɗaura mata wani karatun a lokacin kuma yayan DEENAH ɗin ya dawo shima daga masallaci yazo ya jona su. Nan shima aka kar6i tasa haddar inda ya kawo ta dai-dai, hakan ba ƙaramin faranta ran mahaifiyar su yake ba, dan kuwa Allah ya cika mata burin ta da ya bata ƴaƴa masu albarka, tarbiyya dama kuma nutsuwa. "Allah yayi muku albarka" ta faɗa. Amsawa sukayi da "Aameen" kafin kuma ta haɗa litattafan karatun cikin wani jaka tace "Jafar kai Jakar ɗaki bari na zubo mana abinci koh?." Cikin girmamawa yace "Toh Umma" kafin ya ɗau jakar ya fice zuwa ɗaki ya kai ya ajiye sannan ya dawo falon ya zauna. TV ya kunna ya kai tashar Cartoon Network inda aka sanƴa film ɗin *Tom and Jerry*, nan duk suka gyara zama suna kallo fuskar su na fidda murmushi. Shigowa tayi da ɗan madaidaicin tray mai kyau ta iyo musu serving ɗin jellof rice sai fidda ƙamshi da tururi yakeyi, ajiyewa tayi kafin ta fice ta ɗauko musu ruwa akan plate ta dawo. "Toh ni kun cika min kunne da dariya, maza ku sauƙo kuci abinci." Sauƙowa sukayi suka zauna tare da maida hankalin kan abincin suna ɗaukan cokali tare da yin bismillah suka fara ci. Shiru falon ya ɗauka babu abinda kakeji sai Ƙarar hayaniyan TV ɗinda Tom da Jerry keyi. Faɗo mata yayi a rai lokacin da take shirin kai cokalin abincin bakin ta, _"koh yanzu ya ci abinci?"_ ta faɗa a ranta dan kuwa taga kamar bashida kowa basuda gida. Bayan sun idda cin abincin ne kuma Jafar ya kwashe kwanukan ya fitar baranda ya ajiye a robar kayan wanke-wanke, sannan suka cigaba da kallon su dukkan su inda Ummar su kuma ta fice zuwa ɗaki. Kallon sa tayi tare da matsowa kusada shi tana ta6a sa tace "Yaya." "Miye?" ya faɗa yana kallon ta. "Yaya kaga wannan ɗin nan na ɗazu?." "Waye?." "Wannan mai kama da indiyawan da muka gani ɗazu ɗinnan." "Ni nasan miki shi" ya faɗa yana maida hankalin sa kan TV. "Yaya har kacemin na daina kallon sa." "Eh natuna, menene?." "Ɗazu ma da Umma ya aike ni sayan maggi ai na ganshi a wurin zaune, kuma shine wanda na kaiwa abinci." "Toh sai akayi yaya kuma dan kin kai masa abinci?." "Naga kamar bashida kowa kuma basuda gida." "Ke kam ina ruwan ki dashi, wallahi gara kin shiga taitayin ki dan yanzu ba kowa bane abin yarda kin dai ga yadda ake ta sace yara koh?." Manƴan Idanun ta ta zaro jin abinda ya faɗa,nan ta koma wurin zaman ta tana cigaba da tunani har bacci ya ɗauketa a wurin. 6angaren ZEEYAD kuwa Kan Varender ɗin islamiyyar ya samu ya kwanta, dukda uban sauron dake cizon sa haka nan yayi haƙuri har gari ya waye. Gindin bishiyar nan dai ya sake komawa ya zauna yana ganin fice da shigen ɗaiɗaikun mutane da alama dai aiki zasu. Yana nan zaune har takwas na safe kafin kuma ya fara hango zuwan yara da irin kayan islamiyyar jiya. Sai a sannan kuma ta faɗo masa a rai nan yace "That witch must be on her way." Mintina talatin mai kyau bai ƙara a zaune ba sai gata sun shawo kwana itada yayan ta. Kallon ta yake dan yaga kamar bata gansa ba yau ɗin kafin kuma ya kauda kansa yana yatsine fuska. "Assalamu Alaikum" yaji muryar yaro yayi masa sallama, ɗagowa yayi ya amsa da "wa'alaika Assalam" yana kallon Jafar. Jakarsa ya buɗe ya ciro Wata ƴar ƙaramar lunch box yana miƙa masa yace "My sister asked me to give you this." Da kallo yabi Jafar ɗin dashi kafin kuma ya sanƴa hannu ya amsa yace "Jazakallahu Khair." "Aameen" ya amsa kafin kuma ya ciro ruwan pure water biyu ya ajiye masa sannan ya juya ya tafi. Da kallo ZEEYAD ya bishi kafin kuma ya maida duban sa ga kular yace "Wato dai basuda wata hanƴar da zasu yaudare ni sai wannan, No i won't easily fall into their trap" ya faɗa yana maida abincin gefe. Misalin sha biyu suka fito break inda kuma kowane yaro ya fito da lunch box ɗinsa yana cin abincin sa, yayin da wasu ke ta wasan su. Wucewa tazo yi zata koma gida, nan tagan sa kwance yana bacci yayin da lunch box ɗin ke gefe a ajiye. Lalla6awa tayi taje ta bayan bishiyar tare da ɗaukar ganƴen maina ta zuge Leaves ɗin jiki sannan ta shiga sanƴa masa a kunne tana yi masa tafiyar tsutsa dashi a fuska. Saurin kawo hannun sa yayi yana korarwa dan kuwa ya ɗauka koh wani ƙwaron ne. Dariyar dake son kawo mata ta gimtse tana toshe bakin ta. Sake kai tsinken tayi a karo na biyu tana sosa masa kunne. Hannu ya sake kaiwa da sauri ya buge yana korarwa da hannun sa. Gimtse dariyar ta tayi sai da tayi mai isarta kafin kuma ta sake kai tsinken saitin fuskar sa zuwa hancin sa. Furzar da hanci ya fara yana goge fuskar sa, dariyar ta da ta kusan fitowa fili ta gimtse,kan kuma ta sake kai tsinken a karo na huɗu. Caraff ya cafke hannun nata yana buɗe idanun sa, idanu ta waro kafin ta fara jan hannun nata sai dai ta kasa ƙwata. "Kayi haƙuri dan Allah" yaji ta faɗa cikin zazzaƙar muryar ta Jawo ta yayi ta fito daga bayan bishiyar nan yace "Ke kika san abinda kike faɗa, what are you doing here?" ya faɗa cikin tsare ta. "Bakomai fah...nothing." "Ohh zuwa kikayi ki lashe ni, dama nasan shiryawa kukayi dake da wancan yayan naki dukda dai naga kamar shi salihi ne Unlike you da nake tunanin mayya ce." Sosai idanun ta yayi zuru-zuru, bata ta6a tsokalar wani koh wata ba sai akansa gashi kuma asirin ta ya tonu dan itama batasan maiyasa taji tana son aikata masa hakan ba. "Your eyes are so large and Scary, you Look exactly like a 100years witch, who even knows if you're one, what do you want from me?" ya faɗa yana cika hannun nata. Kallon sa kawai take idanun ta na tara hawaye dan ta fahimci zagin ta yakeyi dukda abubuwa kaɗan kaɗan take tsinta cikin maganar tasa, tasan miye ma'anar witch kenan mayya ya ɗauke ta kenan. "Take this i don't want it, Okay?" ya faɗa yana ɗauko kular Lunch box ɗin ya dire a gaban ta sannan yace "Get out of here." Buɗe kular tayi nan taga bai koh buɗe abincin ba balle ya ta6a, doya ne soyayye da kwai sai yaji a gefe, ɗaya ta ɗauka tare da yin bismillah ta kai bakin ta ta fara ci. "Oh girl, i have escaped millions of traps before, so what made you think that your silly plan would make me fall for your stupid trap?, get out of here, i don't want to see your face." Da watery eyes ɗinta kawai take kallon sa hakan ya sanƴa shi kauda fuskar sa daga kallon ta yana jin kamar ya make ta nan wurin dan haushi da takaici. A haka ta gama cinƴe abincin ta ta tashi tayi hanƴar islamiyyar su zuciyar ta babu daɗi, sabida taga kamar bayason taimakon ta. Da kallo ya bita yana furta "Thank GOD" kafin kuma ya koma yayi kwanciyar sa. Yau ma da yamma bayan an tashe su daga islamiyya yana nan zaune inda yake suka zo wucewa itada Jafar. Ɗauke kansa yayi daga kallon da takeyi masa nan Jafar yace da ita "Ke dallah wai ba zaki daina kallon shi bane?." Ɗauke idon ta tayi tana maidawa kan Jafar ɗin nan kuma yace "Ni bance ki kalle ni ba, cewa nayi ki daina kallon sa" ya faɗa yana kama hannun ta suyi gaba da sauri. Kamar kullum sallama sukayi suka shiga gidan nan suka tarar da Ummah su tsaye da wani mutumi, take kuma fuskar Jafar ya canza yana 6ata rai, kamar jiran su yake nan yace "Yauwa kuma wadannan gantallallun yaran naki suma kisan yadda zakiyi dasu, indai ba zaki biya ni kuɗin haya nan da ƙarshen sati ba toh ki tabbata kinsan inda dare tayi miki" ya ƙarashe cikin kumfar baki. Shiru Mahaifiyar tasu tayi tana sauraron sa kafin kuma tace "Dan Allah Alhaji kayi haƙuri, ka ƙaramin zuwa ƙarshen wata insha Allahu da zaran an biya albashi zan tabbatar da na baka kuɗin ka a cike, ai ba sai ka tona min asiri a gaban yara ba, kuma dan Allah ka daina aibata min ƴaƴa dan kuwa bakasan wahalar da nasha wurin tarbiyantar dasu ba, indai kuɗin ka ne insha Allah nayimaka alƙawarin biyan ka zuwa nan da ƙarshen wata." "Oho dai koma dai menene ki tabbatar da kin tanadi kuɗin nan dubu goma sha biyar cir tun kafin na haɗa ki da hukuma wallahi, haka kurum kaida haƙƙin ka ka riƙe a hana ka" ya faɗa yana buɗe ƙofar ɗayan part ɗin ya shige. Nan tace "Haƙƙin marayu dai, koh ka manta ne?." Nan ya dawo da wuri yace "Mai kika ce?." Bata kula sa ba ta haɗa kan ƴaƴan ta tace "Muje." Nan suka shige part ɗinsu suna rufo ƙofa,kwafa yayi yace "Zamu gamu ne" yana komawa ciki. "Umma wa maiyasa kawu Sale yake yi miki haka ne, koh dama ba Abban mu bane ya gina gidan nan?." "Toh nikam ya na iya ne dashi dan Allah Jafar, ai dama idan mutum yafi ƙarfin ka kawai ka kai kukan ga Allah shi zaiyi maganin azzalumai, idan ni banida yadda zanyi na kwato muku haƙƙin ku da dukiyar ku da ya cinƴe ai akwai Allah kuma yana ganin komai, shine wanda zai kwatar muku sabida babu wanda yafi ƙarfin sa, kuje ku ɗau abincin ku kuci" ta faɗa tana ficewa zuwa ɗaki ta barsu nan falon idanun ta na tara hawaye. Da kallo duk suka bita suna mai jin tausayin Mahaifiyar tasu matuƙa a zuciyar su, dan kuwa ba ƙaramin ƙoƙari takeyi akansu ba na ganin ta inganta rayuwar su, tana iya sadaukar da komai nata akansu burin ta shine rayuwar su ta inganta tayi kyau, bata ta6a barin su sunyi kukan rashin uba ba, itace ta zame musu Uwa sannan kuma Uba, duk wani abu da Uba yakamata yayi itace keyi musu dukda kuwa ɗan uwan mahaifin su na raye sai dai babu abinda yakeyi musu, dukiyar da Mahaifin su ya bari ma yayi nake-nake akai a cewar sa zai kula da rayuwar ƴaƴan da ya bari, wanda hatta gidan da suke ciki na mahaifin su ne ya gina ta sai dai dukda haka wai sai sun biya kuɗin haya, sannan daidai da Naira biyar bai ta6a kashe musu cikin wannan kuɗin ba, komai Mahaifiyar su ce keyi musu kasancewar tana aikin gwamnati kuma albashin ta babu laifi, dashi takeyi musu dukkanin buƙatun su kafin tayi na kanta, shiyasa suma suke burin wataran su girma su sanƴa mahaifiyar su farin ciki fiye da wanda ta basu. Jafar ne yabi ta ɗaki dan kuwa yasan kuka takeyi, DEENAH kuwa kula ta ɗauka ta ɗebi abinci a ciki tayi ficewar ta. Kwance ta same sa idanun sa na kallon sama,motsin da yaji ne yasa shi ɗago da kansa ganin itace yasa shi runtse idanu yanajin kamar ya tashi ya faffale fuskar ta da mari tsabar takaici. Ya rasa mai take nema daga garesa, kowa.gudun sa yakeyi sai dai shi yayin da yake gudun ta shine ita take son shigowa rayuwar sa, sam bayason hakan musamman ma da bai san ta ba, bai san daga ina take ba, gata kuma yarinƴa ƙarama hakan yasa sam bayaso ta dinga kusanto shi koh dan kar tasa mutanen ungwa su fara zargin sa da wani abin suyi masa korar cin mutunci, dan kuwa ba zai so barin arear nan ba coz he feels safe there. Sam baya ƙaunar alaƙar sa da wasu kuma yanzu, yafison yayi rayuwar sa shi kaɗai ba tare da takurar wani koh wata ba, amma wannan yarinƴar na neman takura masa. Ajiye kular tayi kawai ta juya tayi tafiyar ta inda kuma ya bita da kallo yana mamakin abinda ya hana ta tsayawa kallon nasa yau, gashi kuma yaga kamar ranta a 6ace yake fuskar ta a ɗaure. Koh da ta koma gida a bakin ƙofar shiga taci karo da Kawun nasu yana shirin fita, nan yayi wuff yace "Ahaf, an fita yawon gantalin koh?, yarinƴa koh kayan makaranta bata cire ba amma ta ɗau shegun ƙafafuwan nan nata ta fice sabida ba'ayi mata tarbiyya ba, kinje inda aka saba kwakule ki a baki kuɗin koh tunda haka uwarki ta koya miki, zaki daina kallo na ne da wadannan idanun naki kamar na mujiya koh sai na sanƴa hannu na kwakwule su, munafukar banza da wofi, zaki wuce ne koh sai na haɗa wannan kan naki da bango tukun?, tsinanniya." Da sauri ta shige ciki tana haɗawa da ɗan gudu, dan kuwa sam bata ƙaunar abinda zai haɗa ta da kawun nata sabida ba mutumin kirki bane shi, baya ganin mutuncin mahaifiyar ta shiyasa ta tsane sa daga shi har matar sa Rabi'atu sam basu san miye tausayi ba, shiyasa takejin tsanar su a ranta sosai. 6angaren ZEEYAD kuwa abincin ya buɗe ya gani, shinkafa ce da wake da mai da yaji, maida ta yayi ya rufe dan kuwa shi fah ba wai ya iya cin irin abincin nan bane bashida yadda zaiyi ne kawai. Sati ɗaya kenan DEENAH na kawo wa ZEEYAD abinci, sai dai taurin rai da rashin yarda irin nasa ya hana sa ci, ga kuma wulaƙanta ta da yakeyi dukda baya so amma yaga alamun kamar yarinƴar batada zuciya komai yayi mata zata nuna tayi fushi sai dai kuma washe gari zai sake ganin ta da wani kular abincin kuma. Yau kuma Through out bai ganta ba bai ga wulgawar ta koh na yayan ta ba, hakan yasa shi jindaɗi sosai dan kuwa a cewar sa sun gaji dashi ne shiyasa suka haƙura basu samu abinda suke so ba. Shiru shiru kwanaki huɗu sun wuce baya ganin DEENAH sai yayanta da yake ganin gilmawar sa kullum idan zashi islamiyya koh makaranta. Tun yana jin daɗin hakan har kuma yaji zuciyar sa ta daina jindaɗin hakan, yau dai ya yanke shawarar tarar Jafar ɗin dan tambayar sa koh lafiya baya ganin ƙanwar sa. Bayan an tashi ne daga islamiyyar kamar kullum Jafar yazo wucewa nan yace dashi "Hey." Tsayawa Jafar yayi kafin kuma ZEEYAD ɗin ya ƙarasa wurin sa yace "How are you?." "Fine" ya basa amsa a takaice. Kamar kuma ba zaiyi magana ba ya buɗi baki yace "Ina ƙanwar ka, maiyasa bana ganin ta ta daina zuwa islamiyya?." Shiru Jafar yayi kamar zaiyi kuka nan yace "DEENAH?." "What's wrong with her, is she Okay?" ya faɗa cikin ɗan damuwa. Kai ya girgiza masa alamun A'a kafin kuma yace "Nima bansaniba, bansan wane hali ƙanwata take ciki ba, bansaniba koh tana lafiya kokuma sunyi mata wani mugun abun ba." "Mai kake nufi, su waye sukayi mata mugun abu?." Kallon ZEEYAD ɗin yayi kafin kuma yayi gaba ba tare da ya basa amsa ba. Saurin binsa yayi yace "Tell me." "Kawu ne ya ɗauke ta ya kai ta ƙauye, yace ba zata dawo ba har sai Ummar mu ta biya sa kuɗin hayar sa, idan ba haka ba kuma ba zai dawo da ita ba kuma zai aurar da ita ga ɗan sarkin Ƙauyen." Wani irin bugu ZEEYAD yaji zuciyar sa tayi lokacin da Jafar ya idda maganar sa wanda bai san ma da cewa Jafar ɗin ya wuce yayi tafiyar sa ba. He was shocked for a moment jin abinda ya fito daga bakin Jafar ɗin, he can't believe how cruel people can be. Duniyar nan ta cika da azzalumai dayawa,he feel so sorry for little DEENAH, how comes za'a aurar da yarinƴa mai ƙarancin shekaru kamar wannan?, he couldn't believe it. Addu'a yayi Allah yasa mahaifiyar su ta samu kuɗin ta biya sa ya dawo da DEENAH. Samun wuri yayi ya zauna zuciyar sa cunkushe yanajin babu daɗi sosai. Haushin kansa ne yake kama sa idan ya tuna irin wulaƙancin da yakeyi mata idan ta kawo masa abinci, amma haka nan zai rufe ido ya gasa mata magana son ransa duk dan taji haushi amma hakan baya tasiri. Haka nan ya kwana da tunanin DEENAH da halin da take ciki ya tashi dashi. So yake ya sake ganin ta koh da sau ɗaya ne ya bata haƙurin abinda yayi mata, sannan kuma yayi mata alƙawarin ba zai sake yi mata hakan ba. Yarinƴa ce ƙarama amma kuma zuciyar manƴa gareta. "Am so sorry" ya faɗa cikin rauni zuciyar sa nayi masa zafi tare da jin haushin kansa sosai, da yasan hakan zata kasance da ba zai ta6a 6ata mata ba a rayuwa. Wani satin ya sake wucewa amma babu DEENAH babu labarin ta sai Jafar kaɗai da yake ta gani yana wucewa kullum shima fuskar sa babu walwala da alamun dai ba ƙaramin kewa yaji na rashin ƴar uwar tashi kusada shi yayi ba............... **************************** .............It's been two months kenan da 6atan Yarima ZEEYAD, tun mutane na ɗaukar abin wasa har yazo ya wuce tunanin su sabida ganin yadda ran sarki yake ta ƙara 6aci a kullum, yayin da kuma ya sanƴa aka garƙame duk wani bawa koh dogari da ya ta6a ƙuntata wa ZEEYAD a rayuwa, ba zasu fito ba har sai Yarima ZEEYAD ya dawo koh kuma an sami labarin inda yake, koh da kuwa za'a ɗau shekaru masu yawa ne. Hukunci mai tsanani aka haɗa su dashi kama daga kan Mulah, Hakim dama kuma duk wani wanda ya ta6a muzguna masa. Haka ma yake a 6angaren Abdulhakeem da ɗansa Sooraj, hukuncin da sarki yayi musu shine ya kar6e duk wani abu da za'a gani a danganta su da wadanda suka fito daga gidan mulki ya kwace hatta haɗaɗɗen gidan da suke zama suke kuma taƙama dashi ya kwace shi daga garesu inda suka koma rayuwa kamar ta talakawa har sai Yarima ZEEYAD ya bayyana. "That Asshole, yaushe ne zai bayyanar da kansa?, mu fita daga cikin wannan ƙazamar rayuwar, just take a look at me kamar ni the great Sooraj ace ina rayuwa a wannan kangon, abokai na duk sun gama raina ni, wallahi Abhi duk kai kaja mana dah baka kira ni na dawo ba da yanzu ina chan school abuna ina holewa ta, duk girman school ɗinmu dama kuma squad ɗin mu ni ake ganin nafi girma sabida irin 6arin kuɗin da nakeyi, amma kaga inda nake rayuwa yanzu, imagine idan friends ɗina suka gano ya kake tunanin zanji, wane irin kunƴa kake tunanin zanji, it's been two months now amma ji nake kamar nayi shekaru ɗari a cikin nan just take a look at this rusted place please mtssww" ya ƙarashe cikin ƙunar rai kamar zaiyi kuka. Ta6e baki Abdulhakeem yayi yace "Koma dai mai zaka ce ka faɗe sa anan wurin, kada ka kuskura kayi su6utar baki a gaban kowane dogari, idan kuwa ba haka ba kai kanka sai ka raina wayon ka, ka godewa Allah ma ana baka ci da sha amma a hakan kake complaining." "Why ba zanyi complain ba?, dama ai haka zakace sabida duk laifin ka ne, kai ka jawo, har ZEEYAD ɗinne ba zaka iya tattaka sa da kanka ba sai ka kira ni, yanzu fisabillah ka dubi halin da ka jefa ni, duk wani ɗa dake cikin Masarautar nan is out there suna karatun su cikin kwanciyar hankali except me, the great me." "Hafeezah tace min ta koma wurin bokan ta sannan kuma yace mata ZEEYAD na raye, sai dai fah ya kasa gano inda yaron yake dama kuma yaushe ne zai dawo." A fusace ya miƙe tsaye yace "What, the rascal is alive, then toh Uwar miye yakeyi da ba zai dawo ba?, this is bad, i wish nasan inda yake" ya faɗa cike da muguwar takaici. Kallon sa Abdulhakeem yayi kafin yace "Kana tunanin zai dawo ne?, idan ma kana tunanin hakan ne toh kayi gaggawar kauda shi a ranka, tayaya kake tunanin tunda ya samu ya tseratar da rayuwar sa zai kuma dawowa nan, bana tunanin zai dawo koh nan da shekaru ɗari ne..." "Hell no!, bakin ka ya sari ɗanyen kashi Abhi, dole ne ya dawo koh kana tunanin zai yafe zaluncin da akayi masa ne?, ni nasan zai dawo sannan kuma da zaran ya dawo wasan zata fara tsakanin nida shi ne, dan kuwa duk dan shi ne nake cikin wannan halin na rantse sai na sashi yayi nadamar hakan" ya faɗa yana huci kamar wani tsohon maƴunwacin zaki............... _*Am so Bored Today😩, dan Allah ku sanƴa ni farin ciki da zafafan comments ɗinku, kunji?, ba dan ni ba sai dan wanda yayi mu*_ *MHIZZ JIDDHERR............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *010..* ..........Haka rayuwa ta cigaba wa ZEEYAD cikin ƙunci kullum, a yanzu ƴan kuɗaɗen dake jikin sa ma sun kusa ƙarewa kasancewar kuɗin wanka da yake biya kullum Naira Hamsin, ga kuma sayan abinci dasu wanki da yakeyi duka. Ga kuma zuciyar sa dake cike da damuwar rashin ganin DEENAH da baya yi yau sati uku kenan, kullum idan ya tambayi Jafar sai dai yace dashi bata dawo ba, hakan ba ƙaramin sake sanƴa shi cikin rashin sukuni yake ba, so yake kawai ya nemi yafiyar ta akan abunda yayi mata. Yau ma zaune yake kamar Kullum jikin bishiyar da ya saba zama ya haɗa kai da guiwa, yana tunanin yadda zaiyi ya tafiyar da rayuwar sa dan kuwa ba zaiyiwu ya cigaba da zama anan ba kullum ba tare da abin yi ba, dole ne ya fita ya nemo wa kansa mafita zama haka kurum ba nasa bane indai har yana so ya zama very successful a rayuwar sa. Tsayuwar mutum yaji a kansa sai dai sam bai damu da ya ɗago ba, dan kuwa da akwai wani mutum da ya sanƴa shi gaba ƴan kwanakin nan bashida wani aiki sai takura masa. Dire masa kular abincin tayi a gaban sa kafin kuma ta juya da sauri tayi tafiyar ta kasancewar an fara shiga aji. Ganin an ajiye masa kula yasa shi saurin ɗagowa yana kallon bayan ta, wani irin murmushin da bai san da zuwan sa bane ya su6uce masa yana faɗin "She is back." Sosai zuciyar sa ta cika da farin cikin da baisan zai sake jinta nan kusa ba, har ta shige cikin class ɗin bai bar ganin ta ba. Numfashi ya sauƙe kafin kuma ya maida duban sa ga kula ɗin, buɗe ta yayi nan yaga soyayyiyar indomie ce da ƙwai, saurin rufewa yayi lokacin da ƙamshin kwan ya bugo masa hanci har sai da yaji kansa ya ɗan juya masa. Rufewa yayi ya maida gefe ya ajiye yana jin zuciyar sa na tashi. Kifa kansa kawai yayi a guiwar sa yana lumshe idanu, ya daɗe sosai a haka kafin kuma ya tashi ya ɗau kular ya nufi inda ya saba zuwa yin wanka. Ajiyar abincin ya bada sannan ya biya kuɗin wanka ya shiga yayi tare da sauya kayan sa ya fito. Amsar kular yayi, aka lakuta masa man shafawa a hannu ya shafa, sannan kuma ya dawo inda ya saba zama lokacin har an tashe su a break. Tsaye ya ganta a kusada bishiyar tana dube-dube da alamu dai neman sa take. Takowa yayi ya ƙaraso wurin yace "Are you looking for me?" ya faɗa yana samun wuri ya zauna tare da ajiye kular. Idanu ta zuba masa kawai tana kallo ba tare da tace komai ba. Ɗan murmusawa yayi ya ɗau kular yana miƙa mata. Amsa tayi jinsa da nauyi yasa fuskar ta matuƙar sauyawa, zama tayi tare da buɗe kular nan dai taga bai ta6a abincin ba. Ɗagowa tayi da fuskar ta da ta ɗanyi fayau kamar ta ɗan rame inda kuma idanun nata suka ɗan ƙarayin girma tana kallon sa. Kauda idanu yayi daga kallon ta yana wasa da sarƙar sa da ya ciro. Idanu ta maida kan sarƙar tana kallo, tana kallon yadda yake lailaya ta a hannun sa. Ɗagowa yayi nan suka haɗa ido, mamaki ne ya cika shi ganin kamar bata ta6a gajiya da kallon mutane, a yanzu ya gane ba mayya bace but naturally kawai haka Allah yayi ta da yawan kallo. Baki ya buɗe yace "Don't cast an evil eye on my Necklace, this Necklace means the world to me, gara ma ki daina kallon sa" ya faɗa yana maidawa cikin aljihun rigar sa. Barin kallon sa tayi dan yau ɗinma taga kamar zagin ta yayi dan haka kawai ta sauƙe jakar goyon ta ta ciro ɗan ƙaramin fork a ciki, sannan ta shiga cin abincin ta. Kallon yadda take cin abincin yake kamar batason ci, bata iya cinƴewa ba ta rufe sauran ta maida kular cikin jakar makarantar ta. Tana shirin tashi ta tafi ne yace "Hey." Dakatawa tayi kawai tana kallon sa, nan yace "Wai ke bakya magana ne komiye?, anyways give me pencil and a Book." Tsayawa tayi kallon sa dan bata fahimci abinda yake faɗa ba, ganin hakan yasa shi shiga yi mata gwari-gwari cikin gwada mata yace "Pencil and Book." Sai a sannan ta gane abinda yake nufi dan haka kawai jakar ta ta buɗe ta ciro takarda da Pencil ɗin ta miƙa masa. Kallon ta yayi kafin ya kalli ƙasan Pencil ɗin da duk a tattaune da alamu cinƴe sa takeyi _"Poor Pencil, shi ɗinma bata barsa ba tsabar maita, oh ashe ba mayya bace, and she didn't look like one"_ ya faɗa a zuciyar sa kafin kuma ya buɗe tsakiyar Book ɗin ya shiga zana Pencil a jiki wanda da alamu abu yake rubutawa, sai dai ya kan ɗago ya kalleta lokaci zuwa lokaci yana cigaba da rubutun da bata san na mene yakeyi ba, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kuma ya gama abinda yake rubutawan, ya hau kallon cikin takardar. Murmushi yayi sannan kuma ya miƙa mata takardar tata, amsa tayi idanun ta akan fuskar sa da bata gajiya da kallo kullum, kafin kuma ta maida duban ta cikin takardar dan ganin abinda ya rubuta a ciki. Sosai ta waro manƴan idanun ta dake nuna alamun mamaki tana ƙarewa kanta dake manne a jikin takardar kallo. She can't believe her eyes, sak ita take kallo a jikin takardar nan, kamar wacce ke ganin reflection ɗinta a jikin madubi. Tsinkayo muryar sa tayi yana faɗin "Do you like it?." Kallon sa tayi har yanzu fuskar ta bai bar fitar da mamaki ba, kafin kuma ta saki murmushin da ya ƙara mata kyau sosai tana kallon cikin takardar tace "It's me." _"She is beautiful"_ ya faɗa a zuciyar sa ba tare da ya iya ɗauke idanun sa daga kan fuskar ta dake murmushi ba. "This is me" ta sake faɗa cike da jindaɗi tana kallon cikin takardar. "DEENAH" ta jiyo muryar Jafar ta bayan ta. Da sauri cike da jindaɗi tace "Yaya, yaya kazo kaga ni, ni ya zana a cikin takardar nan" ta faɗa tana nufar wurin sa ta shiga nuna masa. Waro idanu shima Jafar yayi cike da ɗumbin mamaki kafin ya kar6i takardar daga hannun DEENAH ya shiga ƙare masa kallo yana kallon fuskar DEENAH ɗin. "Wooww" ya faɗa cikin sakewar baki kafin yace "Waye yayi miki?." Da hannu ta nuna ZEEYAD dake zaune kawai yana kallon su. Zuwa yayi ya zauna kusada ZEEYAD ɗin yace "This is amazing, you're so talented, nima zaka zana min?" ya faɗa yana kallon ZEEYAD ɗin cikin murmushi. Sai a sannan ZEEYAD ya saki fuska yayi murmushi yace "Yeah sure." Da sauri ya buɗe jakarsa ya ciro takardar sa yace "Gashi nima ka zana min irin na DEENAH, nima ka zana ni ina dariya." Zama DEENAH tayi kusada yayan nata tana kar6ar takardar ta a hannun sa tana sake kallo cike da farin ciki. Cikin ƙanƙanin lokaci yayi zanen Jafar da DEENAH da takardar dake hannun su suna kallo suna murmushi. "Done" ya faɗa yana miƙawa Jafar takardar. "Wooww DEENAH ki kalla, mu biyu ya zana" ya faɗa yana nunawa DEENAH takardar. Dariya ta saki nan tace "Kamar hoton mu ya ɗauka yasa a ciki." Da sauri Jafar ya ɗago ya kallesa yace "Zaka iya zana Ummar mu?." Murmushi ZEEYAD yayi yace "Bansan Ummar ku ba, sai dai idan zaka kwatanta min yadda take." Da sauri ya sake miƙa masa takardar yace "Zan faɗamaka yadda take, da DEENAH take kama, sai dai ita fara ce kamar ni, idanun ta basu kai na DEENAH girma ba amma kuma yafi nawa da kaɗan, hancin ta dogo ne mai ɗan tudu da kauri, bakin ta kuma ƙarami ne irin na DEENAH, sai dai kasan ita Babba ce" ya ƙarashe faɗa yana kallon ZEEYAD dake ta zane a jikin Book ɗin. "Is that all?" ya faɗa yana kallon Jafar. Kai Jafar ya jinjina masa, murmushi ZEEYAD yayi yace "No baka ƙarasar da kammanin ta ba." "Mene ya saura da ban faɗa ba?." "Her eyebrows, her eyelashes, her cheeks komai yadda yake a fuskar ta." Nan yace "Eh hakane" kafin kuma ya shiga sake yi masa bayani dalla-dalla yadda Ummar su take. Miƙawa Jafar takardar yayi nan ya kar6a dawuri dukkan su shida DEENAH suna maida duban su ciki. "Umma ce" dukkan su suka haɗa baki wurin faɗa suna dariya. "Ya'akayi kasan haka Umma take?" faɗin DEENAH tana ɗagowa ta kalle shi. "Ke dalla baya jin hausa dai" faɗin Jafar kafin yayi wa ZEEYAD bayanin abinda DEENAH ɗin tace "You are so wonderful, ya akayi kayi haka, Ummar mu ce sak ka zana" cewar Jafar ɗin yana kallon sa. "Kawai na sani ne, ba kai ka faɗamin yadda take ba." "Kenan kana nufin, idan muka faɗa maka yadda komai yake zaka iya zana shi sak?." "Insha Allah" ya faɗa. "Zaka zama abokin na?" cewar Jafar ɗin. Murmushi ZEEYAD yayi jin yadda yayi maganar nan ya girgiza masa kai. Cike da jindaɗi ya rungume DEENAH yace "Yace zai zama aboki na daga yau." Murmushi tayi tana kallon sa, ƙarar bugun bell ɗinda sukaji ne ya sanƴa su tashi da sauri nan Jafar yace "Gashi zan bar maka takarda ta ka zana ni ni kaɗai, kaji?" ya faɗa yana ajiyewa ZEEYAD takardar tasa. DEENAH ma ajiye nata tayi tana murmushi tana kallon sa. "Mungode sosai, Allah yayiwa rayuwar ka albarka" cewar Jafar kafin yaja hannun DEENAH sukayi gaba. Juyowa tayi tana kallon sa hakan yasa shi sakar mata murmushi kafin kuma ta juyar da kanta suna cigaba da tafiya. Takardar DEENAH ya ɗauka ya shiga ƙarewa zanen hoton ta da yayi a jiki kallo kaifin yayi murmushi ya juya zuwa ga next page ya shiga yin wani zanen kuma. Bayan an tashe su da yamma suka biyo ta wurin ZEEYAD fuskar su ɗauke da murmushi suka zauna a gaban sa, nan Jafar yace "Alhamdulillah, Mun tashi ka gama yi mana zanen?." Takardar ya ɗauko ya basa kafin ya shiga buɗe nasa cikin farin ciki "Wooww" ya faɗa yana buga tsalle kafin ya shiga nunawa DEENAH, "Kinga ni ya zana da irin hular larabawa akaina, kiga yadda nayi kyau." Murmushi DEENAH tayi tace "Ina nawa fah?." Nata takardar suka buɗe Jafar, da har farin cikin da yake ciki yayi masa yawa yace "Ki ganki, kyakkyawa dake kiga har flower ya zana miki akanki kamar head-band kina murmushi." Dariya tayi tana kallon cikin takardar tace "Muje gida mu nunawa Umma." Kallon ZEEYAD Jafar yayi yace "Ya Sunan ka?." Idanu DEENAH ta zuba masa jin koh mai zai ce, sai dai kafin ya buɗi baki yayi magana suka jiyo murya ta bayan su. "Kan bantar Uba, mai kukeyi anan bayan kowa ya watse ya tafi gida?, ƴaƴan marar mutunci tsinannu" ya ƙarashe yana ɗaukar ƙatuwar bulala ya nufo su. ZEEYAD ya gane shi, shine mutumin da yasa masa ido ƴan kwanaki biyun nan. Hannun DEENAH Jafar ya ruƙo suna shirin rugawa ne a tsawace yace "Idan kuka kuskura kuka motsa koh da ƴar yatsar ku ne toh wallahi sai na lahira ya fiku jindaɗi a garin nan yau." Duk tsayawa sukayi suna kallon sa had ya ƙaraso gaban su, nan ya shiga nuna su da bulalar yana faɗin "Ku gaku ƴaƴan tsinanniya kuma gantalalliya koh?, ita uwarku ta fice yawon karuwancin da ta saba ku kuma kuna nan wurin baƙon da baku san daga inda ya fito ba yana kwakule ku ya baku wani abin koh?." "Mu ai Ummar mu ba yawon karuwanci take zuwa ba, aiki take zuwa ta samar mana abinda zamu ci kuma ta kula damu..." bai ƙarasar ba yaji wani irin bugu a bakin sa nan kawun nasu yace "Idan ba yawon karuwanci take zuwa ba, ina take samun kuɗin da har take iya ɗaukar ɗawainiyar ku duka, kuma wurin aikin nata ba duk maza ne suka cika ba, Allah ne kaɗai yasan 6arnar dake faruwa achan, kai kuma nan har ƙanwar ka shegiya mai idanun mujiyar nan kake kawo wa wani ƙato yana tatta6a ta koh?" ya faɗa yana shirin fizgo DEENAH da ta 6uya bayan Jafar. "Ka sake ta, ka sake ta idan zaka dake ta ni ka dake ni a maimakon ta" cewar Jafar yana riƙo ta tare da miƙawa kawun nasu hannun shi. "Kai ni zaka yiwa rashin kunƴa koh?, toh bari ka gani" ya faɗa yana ɗaukar bulalar da niyyar zuga mata ne yaji an riƙe bulalar taƙi yin gaba taƙi yin baya. Maido duban sa kan ZEEYAD dake tsaye hannun sa riƙe da bulalar yayi yace "Eh tabbas babu shakka, kaga zan dake ta nayi mata lahani ina zaka samu damar shafa jiki mai laushi, ai dole ka riƙemin bulala." "What is he saying and who is he?" ya faɗa yana kallon Jafar. "Kawun mu ne, yayan Baban mu ne shi." "Yeah, naga alama" ya faɗa yana maida duban sa ga kawu dake sake da baki yana kallon su. "Leave the Kid's alone, and don't you dare try to raise your hands on them again"ya faɗa yana fuzge bulalar hannun kawun. "Bakomai, bakomai zamu gamu ne a gida, ai idan kun samu mai tare muku anan waje, ita uwarku ta gida bata isa ta hana ni dukan ku ba, shaiɗanun banza da wofi" ya faɗa cikin borin kunƴa yana yin gaba. Duk da kallo suka bisa kafin Jafar yayi murmushi yana kallon ZEEYAD yace "You scared him away." "Did i?" ya faɗa cikin ɗan waro idanu. "Yeah, idanun ka suna cike da kwarjini ne, inaga shiyasa ya tsorata ya gudu" ya faɗa yana ɗan dariya. Murmushi ZEEYAD yayi sannan yace "Yakamata ku tafi gida haka nan, sai gobe kuma." Kai ya jinjina masa kafin yace "Toh sai gobe, DEENAH zo mu tafi" ya faɗa yana sanƴa hannun sa kan kafaɗun ta suka wuce. Da Kallo ya bisu, wondering wane irin rayuwa sukeyi a cikin gidan su tare da wannan shaiɗanin mutumin........... ************************** .........."Ke zo nan" ta faɗa dai-dai lokacin da su DEENAH suka shigo cikin gidan. Cikin sanƴin jiki ta ƙarasa wurin ta, nan tace "shiga ciki ki gyara min ɗaki da falo banajin daɗin jiki na." Kallon ta kawai DEENAH ta tsaya yi, hakan yasa ta daka mata uban tsawa tace "Dan Uwarki ba dake nake magana bane, kin wani sanƴa ni a gaba kina kallo haba ku kaɗai yara a cikin gidan nan amma sai kubi kuyi ta sawa mutum ciwon kai kuna sashi ihun da baiyi niyya ba, zaki wuce ne koh sai na ham6are ki?" ta faɗa cike da masifa da hargowa tana aikawa da DEENAH muguwar kallo. Jafar ne yace "Yanzu fah dawowar mu daga islamiyya koh hutawa bamuyi munci abinci ba, kuma kice zaki sata aiki?." "Toh ɗan masu iya yi, ai dah kawai duka ka kawomin nasan dagaske kake jin haushin abinda nakeyi wa ƙanwar taka, marar kunƴar banza da wofi kawai, tsabar baƙin halin ka da rashin kunƴa baka isa a sanƴa ka aiki a gidan nan kayi ba, kuma dan tsabar rashin mutunci yaushe rabon ku da ku ganni a cikin gidan nan amma koh sannu da zuwa baku iya yimin ba koh?, yayi kyau ba laifin ku bane." A fusace ya juya ya buɗe 6angaren su ya shige. Maida duban ta tayi kan DEENAH tace "Wai ba zaki wuce bane banza." "Toh ai Anty kin tare ƙofar shigan" ta faɗa cikin sanƴi kamar zatayi kuka. Tsaki taja tace "Wuce, kuma wallahi kika buge ni na haɗa kanki da bango" ta faɗa tana ɗan matsawa kaɗan. Ƙafa DEENAH tasa tare da ƙoƙarin wucewa a rashin sa'a ta taka mata Hijabi. Fizgo ta tayi waje tare da shimfiɗa mata mari a fuska ta zungure ta har kamar zata faɗi tace "Duk girman idanun nan naki baki gani ba sai da kika taka min Hijabi da wannan takalmin naki da kika ɗebo uban najasa da datti a waje?, toh jeki gama gyara ɗakin ki fito ki wanke min shi dan dashi zanyi sallah akanki kuma ba zan ciro wani sabon Hijabin ba, kuma ki cire takalmin nan yanzu anan wurin, ba zaki shigar min dashi ciki ba." Da sauri ta cire takalmin nata tana shigewa haɗi da matsar kwalla. Koh da ta shiga kaca-kaca falon yake, ga kuma wani uban datti kamar bola kwanukan da akaci abinci dasu wanda da alama sun daɗe a wurin sakamakon abincin da duk ya bubbushe a jiki duk ta tattara su wuri ɗaya ta fito dasu baranda ta ajiye. Tsintsiya ta shiga nema bata gani ba, hakan yasa ta faɗin "Anty ina tsintsiyar sharan?." "Banidashi, jeki ɗauko na uwarki,kiyi amfani dashi" ta faɗa cikin yatsina fuska. Wucewa tazo tayi taje part ɗinsu ta ɗauko tsintsiyar shara da mopper da abubuwan gyaran ɗaki duka ta fito. Da kallo ta bita nan tace "Duk wadannan abubuwan na Ummar ku ce koh arowa tayi?." "Na Ummar mu ce" ta bata amsa. Baki ta ta6e tace "Wuce." Wucewa tayi ta shiga kafin kuma ta hau gyaran cikin falon, kafin ta gama kuwa har an kira Magrib, gashi koh rabin gyaran bata yi ba. Sosai ta fara sauri dan kuwa yau tasan ta shiga uku a hannun Rabi'atu ga kuma ɗaku na uku ne a cikin part ɗin nasu wanda duk sai tabi ta gyara su, gashi tunda ta dawo bataji muryar Ummar su ba, da alama dai bata dawo daga wurin aiki ba yau ɗin dawuri. "Kutumar kan Uban chan" ta faɗa tsaye daga bakin ƙofar falon. "Dan Allah Anty kiyi haƙuri, ƴunwa nakeji shiyasa banyi sauri a aikin ba" ta faɗa kamar zatayi kuka. "Au bakici abinci ba koh?, zakiga bakici abinci ba dan Ubanki" ta faɗa tana bata mari a fuska sannan ta ɗaura da faɗin "Na baki minti goma ki gama tattara min cikin falon nan kiyi mopping ɗinsa mai kyau,kije ki ɗauko turaren uwarki ki sanƴa min." "Toh" kawai ta faɗa tana cigaba da aikin nata da sauri. Zama Rabi'atu tayi akan cushion tana aika mata da mugun kallo. Itace bata gama aikin ba dawuri har sai da bakwai ɗin dare ya gifta kaɗan duk ta haɗa gumi sai kuka take sakamakon gajiya da kuma ƴunwa da takeji. "Maida abubuwan ki ɗauko turaren wutar ki sanƴa min, gobe tunda bakuda makarantar safe kizo ki ƙarasar min da aikin." "Muna da makarantar Boko fah gobe da safe." "An biya muku kuɗin makarantar ne?." Kai kawai ta jinjina mata hakan yasa ta daka mata tsawa tace "Da kai nayi miki magana?." "Eh, an biya mana." "Wuce dalla ki bani wuri." Da sauri ta tattara kayan aikin ta fice daga part ɗin. A komai part ɗin su Rabi'atu yafi nasu DEENAH kyau da tsaruwa dama kuma girma wanda shine ya kasance nasu DEENAH ɗin tun lokacin da Mahaifin su yake raye, amma tunda kawu ya auro amaryar sa Rabi'atu yasa ta a ciki Part ɗin ta daina samun isashhiyar gyara, ga kuma shegen ƙazanta a cikin ta, Rabi'atu irin matan nan ne da basu damu da gyara ba, ga kuma shegen hassada da baƙin ciki dama kuma sa ido a cikin ta, duk irin kayan da ta gani a jikin Ummar su DEENAH sai ta tada jaraba an siya mata irin sa idan kuwa ba haka ba tayi ta tada masifa da jarabawar tsiya kenan a cikin gidan, sosai ta ɗauki Ummar su DEENAH a matsayin kishiyar ta, dan kuwa ba ƙaramin kishi take da cigaban ta ba dukda mijin ta baya raye,amma bata zauna ba kasancewar tayi karatu sosai kuma har kwalin degree ne da ita, gashi kuma a yanzu tana shirin samun aikin Lawyer kasancewar abinda ta karanta kenan sai dai Rabi'atu batasan da hakan ba, da irin baƙin ciki da hassadar da zatayi mata ba kaɗan ba. Fitar ta daga part ɗin ta hango Ummar su a tana girki akan Gas, da sauri ta ƙarasa tace "Ummah dama kin dawo?." Kallon ta tayi tace "Na dawo, sai dai ban daɗe da shigowa ba, kinga yanzu ma na ɗaura girki." "Amma Umma maiyasa baki dawo dawuri ba yau ɗin, kuma baki neme ni ba?." "Aiki ne yayimin yawa a office shiyasa ban samu na kammala dawuri ba, ga kuma na wuce kasuwa yi mana siyayya, ban samu abin hawa dawuri ba, kuma ai na hango takalmin ki a bakin ƙofar Rabi'atu shiyasa ban damu da na neme ki ba, tunda yayanki yace min kina chan kina yi mata aiki, ashe ta dawo?." "Toh Umma sannu da dawowa." "Yauwa ƴar albarka jeki ajiye abubuwan hannun naki kizo kinji." Da "Toh" ta amsa kafin ta shige ciki. Ajiye abubuwan tayi a mazaunin su sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko kaskon wuta da turaren wuta ta fito. "Ina zaki dasu?." "Anty ce tace na kawo mata nasa mata a ɗaki." Shiru Ummar su tayi bata ce komai ba, hakan yasa ta wucewa. Da sallama ta shiga nan ta sameta gaban TV tana kallo koh amsa sallamar ta batayi ba. "Anty gashi nan." "Ina wutar da za'a sanƴa turaren a ciki?." Tsuru-tsuru tayi da idanu kafin tace "Babu wutar." "Kamarya babu wutar?, ba yanzun nan naji muryar Ummar ku ba, bata hura wuta bane?." "Eh, ba na mukubur ta hura ba yau ɗin." "Tohh, a miye ta hura?." "A Gas ne?." Ta6e baki tayi tace "Manƴa, jeki anso min kaskon wutar ta na electric ɗinnan kizo ki samun a shi." "Ai ya 6aci" ta faɗa tana kallon ta. "Ya 6aci, kamarya ya 6aci, wa ya 6ata?." "Tun rannan ne da kika ce na kawo miki, har ya faɗi a hannun ki ne bai sake kawo wuta ba." Ta6e baki tayi tace "Bani turaren." Miƙa mata tayi nan ta buɗe tare da kaiwa hancin ta, sosai yake da ƙamshi maimakon ta yaba sai tace "Ina wannan ɗinnan da nakejin ƙamshin sa har nan idan tasa ɗinnan?." "Shi ɗin ya ƙare kuma bata sayi sabo ba." "Mttssww, jeki kar6o min jafaran ki samin shi a haka nayi maneji" ta faɗa cikin yatsina tana ajiye turaren a gefen ta. Ficewa tayi dan kuwa tasan shikenan kuma turaren ba zai sake dawowa wurin su ba. Jafaran ta ɗauko ta kunna mata a falon harda cikin ɗaku nan part ɗin duka, inda duk datti ya cika su babu gyara tayi ficewar ta. Koh da ta koma ta samu Ummar ta tasa mata ruwan wanka a kettle nan tayi wankar ta shirya cikin riga da wandon baccin ta, tayi sallahn Magrib ɗin da batayi ba, sannan ta zauna akan sallayar tana jiran a ƙira Isha'i tayi. Bayan duk sunyi sallahr Isha ne kuma duk suna zaune a falon nasu suna kallo kasancewar girkin daren bai ƙarasa bane Jafar yace "Umma bari kiga wani abin mamaki" ya faɗa yana zuwa ya ɗauko jakar Islamiyyar sa. Da kallo ta bisa nan DEENAH tace "Yaya, ka tsaya nima bari na ɗauko nawa" ta faɗa tana fita da gudu taje ɗaki ta ɗauko ta dawo fuskar ta ɗauke da murmushi. "Umma kinsan mene?." "Ina zan sani, ku faɗamiki meke saku farin ciki haka nima na tayaku." "Zamu nuna miki amma sai kin rufe idanun ki." "Tohh" ta faɗa cikin ɗan zaro idanu. "Umma ki rufe" cewar DEENAH tana zagayawa ta bayan ta ta rufe mata fuska. Dariya tayi tace "Toh na rufe, ku nuna min." Ciro takardar da ZEEYAD yayi zanen su a jiki yayi ya buɗe page ɗin tsakiya inda Zanen hoton Ummar su yake ya buɗe yace "Umma kada ki buɗe sai na ƙirga uku." Nan ya gyara takardar yana nuna wa a saitin ta kafin ya shiga ƙirga "One, Two, There....Surprise" ya faɗa da ƙarfi lokacin da DEENAH ta buɗe mata idanun nata. Baki ta buɗe kawai cike da ɗumbin mamaki tana ƙarewa hoton kallo, hannu tasa ta amsa tana cigaba da kallo cike da mamakin da take ciki tace "Who drew this, did you?" ta faɗa cike da farin ciki tana kallon sa. "Noo" duk suka haɗa baki wurin faɗa kafin yace "Abokin mu ne yayi." "What really?, he is so very talented, wannan ne hobby ɗinshi, ya sanni ne?" ta tambaya. "Bamu saniba, kawai ya zana ne, bayan munyi masa kwatancen kamannin ki, bari kiga nawa da na DEENAH" ya faɗa tare da buɗe page ɗin baya take hoton sa ya bayyana. "Wowww" ta faɗa. "Umma kiga nawa, har biyu ya zana ni" ta faɗa tana kawowa kamar zata shigar da takardar fuskar Ummar ta. Amsa tayi cikin farin ciki ta shiga ƙarewa DEENAH dake manne a jikin takardar kallo. "Wowww, look at my cute gorgeous daughter" ta faɗa cikin murmushi tana kallon DEENAH. "Umma kinga wanda ya zana mu, mu biyu nida DEENAH." Amsa tayi ta shiga dubawa tace "Masha Allah, abokin ku yaro ne ya zana wannan abin i can't believe my eyes, lallai wannan yaron nada baiwa ta musamman, toh kuma nawa kuka bashi?" ta faɗa cikin murmushi tana kallon su. "Bamu basa koh biyar ba?." Baki ta buɗe tana kallon su kafin tace "Lala baku kyauta ba ƴaƴan nan, mutum yayi muku zanen nan kuma baku basa komai ba, lallai yanada kirki sosai." "Umma ana bada kuɗi ne idan anyi?." "Ehmana, kuɗi sosai ma kuwa, ki ganki fah ke sak ya zana babu bambamci, kuma kice baki basa komai ba." "Kenan Umma kina nufin zai iya yin na kuɗi, idan yayi zanen mutane su basa kuɗi?." "Yeah it's a good ambition ai, just take a Look masu baiwa ta musamman ne zasu iyayin wannan zanen, sannan kuma su iya neman kuɗi dashi, da akwai wadanda aikin su kenan kuma ba ƙaramin kuɗi suke samu ba, musamman ma ace a ƙasashen turai yake, suma girmama irin masu wannan baiwar sosai da sosai and with this he can make alot of billions idan Allah yasa masa albarka a ciki." Kallon juna shida DEENAH sukayi suna waro idanu cike da mamaki kafin kuma su tsinkayo muryar Ummar su na faɗin "Wanene abokin naka, sannan a wane gida yake?." Kallon juna sukayi yayin da fara'ar fuskar su ke ɗaukewa.............. *Dan Allah ku dinga yimin sharing mana saboda Allah👏🏽😩* *MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* _Kada wacce tayimin Kuka a page ɗinnan😩_ *011...* _*Banida lafiya ku sani a addu'oin ku, banyi editing ba*_ ...............Da kallo suke bin juna wondering wane irin amsa yakamata su bawa Mahaifiyar tasu, Jafar ne yace "Umma ai basuda gida, shi kaɗai ne yake rayuwa." "Um!, bangane ba, kamarya shi kaɗai yake rayuwa?." "Umma Balarabe ne fah, ba ɗan nan ƙasar bane, kuma bashida wurin kwana da zama sai gindin ƙatuwar bishiyar dake hanƴar islamiyyar mu." "Balarabe, then toh a'ina ya san ku har kuka zama abokai dashi?." "Shine wanda DEENAH take kaiwa abinci kullum." "Shine yayi wannan zanen?." "Eh Umma kuma fah bayajin hausa ma, sai turanci kaɗai" cewar DEENAH tana kallon ta. Tunani Ummar tasu ta shiga yi kafin ta rufe takardun tace "Ku maida cikin jakan ku, bari na dubo mana girkin" ta faɗa tana tashi ta fice zuwa waje. Da kallo suka bita kafin Jafar ya kalli DEENAH yace "Ya naga fuskar Umma ya canza?." "Koh ka sani zata ce kada mu sake kula shi tunda bamu sanshi ba" ta faɗa kamar zatayi kuka. "Umma tana da kirki ba zata raba mu dashi ba." Takardar ta sake ɗauka tana sake kallon hoton dake jiki fuskar ta na fitar da murmushi........... ****************** ...........Washe gari bayan gari yayi haske tuni sunyi shirin makarantar su kowa ya sanƴa uniform ɗinsa inda Ummar su ma tayi shirin fita aiki. Kallon Umma dake ta sauri tayi tace "Umma baki fah zuba min abincin ba." "Wane abinci kuma DEENAH?" ta faɗa tana kallon ta. "Abincin da zan kaiwa abokin Yaya." "Ina shi yayan naki?." "Yana waje." "Kira shi yazo ya kai masa dawuri, kinga dai zanyi latti koh?." Da sauri ta fice taje ta kira Jafar da har ya fice waje ta dawo. Abincin Umma ta miƙa masa tace ya kaiwa abokin sa ya dawo da wuri su wuce. Amsa yayi cike da farin ciki yace "DEENAH zo muje." "A'a ba zata ba, kai kaje" cewar Ummar tasu hakan yasa farin cikin dake ɗauke kan fuskar DEENAH gushewa. Ficewa yayi nan Ummar tasu ta kalli DEENAH da kanta ke ƙasa alamun tayi fushi kafin kuma tace "Kinason ganin sa kullum?." Da sauri ta ɗago tana kallon Mahaifiyar tata jin abinda ta faɗa. "Kinason ganin sa kullum?" ta sake tambayar ta. Da sauri ta jinjina mata kai alamun eh, nan ta sake cewa "Daɗi kikeji a ranki idan kin ganshi?." Shiru tayi tana kallon fuskar mahaifiyar tata kafin kuma tace "Umma idan yaƙi cin abincin da na kai masa ne nakejin babu daɗi." "Maiyasa baya cin abincin da kike kai masa?." "Nima ban sani ba, amma idan naje har korata yakeyi yace na daina zuwa kusada shi, kullum baya cin abincin da nake kai masa sai dai na baiwa almajirai a hanƴa." "Bashida kowa, bashida wurin kwana kuma bayacin abincin da kika kai masa, strange" ta faɗa cikin ɗan nazarin abin kafin kuma ta numfasa tace "Okay muje." Fitowa sukayi bakin ƙofar gidan suna jiran dawowar Jafar. Suna tsaye suna jiran dawowar Jafar kawu ya fito daga cikin gidan, kallo ya ƙare musu sama da ƙasa kafin yace "Toh za'a fita harkar karuwancin da aka saba kenan?." Ɗauke kai Umma tayi bata kulasa ba sai ma danne-dannen wayar da takeyi fuskar nan nata a murtuƙe. Nan ya sake cewa "Ke, ki koma ba zaki makarantar ba, Rabi'atu bata jin daɗin jikin ta dan haka ki tsaya ki taya ta da ayyukan ta tukun." "A wane dalilin?" cewar Umma dake kallon sa cikin mamaki tunda ya fara magana. "A dalilin matata batada lafiya sannan kuma a matsayi na Na wan Mahaifin ta." "Toh gaskiya kayi haƙuri, yanzu makaranta zata kuma ta riga da ta shirya, idan yaso idan ta dawo sai tayi mata aikin, amma yanzu kam gaskiya makaranta zata." "Ni nace ba zata makarantar ba, Koh so kike dama ita Rabi'atu ɗin ta mutu koh, ke baki taimaka mata ba, ke kuma baki bar ƴar ki ta taimaka mata ba, kinayin haka ne duk dan kinsan batada ƴan uwa anan babu mai zuwa mata kullum taya ta aiki shiyasa kike haka, yanzu idan nayi magana nace ke kike 6ata ƴaƴanki da kanki sai ki hau ni da rashin kunƴa kina cewa ƴaƴan ki masu tarbiyya ne, ina tarbiyyar take bayan kina yi musu da hani da taimakon mutane." Ummar su DEENAH sam batason surutu da hayaniya irin na Kawu gashi kuma akan hanƴa suke kowa na wucewa yana kallon su, ga kuma kawun baya magana a hankali, bai ƙi ya tara mata mutane ba yanzu sannan ya aibanta ta a gaban su tare da yi mata sharri, wannan ba damuwar sa bace, dan kuwa bashida mutunci koh kaɗan, hakan yasa Umma buɗe jakar ta ta ciro makullin part ɗin nasu ta bawa DEENAH tace "Yi haƙuri MADEENAT ƴar albarka, ki haƙura da makarantar yau ɗin ki taya antyn ki aiki,kinga batada lafiya koh?." DEENAH da idanun ta suka tara hawaye ne tasa hannu ta kar6i makullin tace "Toh Umma bakomai zanyi mata aikin ai na kwana ɗaya ne kawai." "Yauwa yarinƴa ta Allah yayi miki albarka" ta faɗa tana shafa kanta. Tsaki kawu yaja sannan yace "Ni za'a nunawa tijaranci da munafurci?, ke kanki kinsan a matsayin ƴaƴa na suke sannan kuma ina da kowane irin iko akan su ke baki isa ki hana ni yin abinda nayi niyya game dasu ba, shima wannan jan ƙosan kwanan nan zan fara maganin ka kaima" ya faɗa yana nuna Jafar dake ƙarasowa wurin nasu yana aikawa da kawu da mugun kallo. "Jeki kinji" ta faɗa tana share maganar Kawu ɗin. "Umma ina kuma zata je?, sati uku fah bata je makaranta ba duk dan sabida Kawu da ya ɗauke ta ya kaita ƙauye ta sha wahala ta dawo dakyar kika samo kuɗin amso ta, shine kuma yanzu zai ce ba zata je makarantar boko ba, shi yake biya mana kuɗin makarantar ne?" ya faɗa cike da muguwar haushin kawun nasu dake cinsa. "Kin gani koh, kina dai ganin irin maganganun da yaron nan ke faɗamin a gaban ki amma kin kasa hana sa, sabida kina jin daɗin yadda yake min magana kamar wanda shine na sama dani, toh koh mahaifin ka da yake raye baya yimin magana gatsai haka balle kai ɗan da ya haifa jiya-jiya, jeka makarantar ka dawo zaka dawo ne ka same ni anan gidan, ɗan iskan banza ɗan iskan wofi." Hannun Jafar kawai Umma taja sukayi gaba ba tare da tabi kan maganar kawu ɗin ba. Da kallo DEENAH ta bisu tana matsar kwalla, dan kuwa tasan ba ƙaramar baƙar wahala zata sha a hannun su ba yau. Tsaki yaja sannan ya juyo ga DEENAH tare da daka mata tsawa yace "Zaki shiga ciki ne kokuwa sai nayi kwallo dake, shegen kanta yawa yawa tayan tifa." Tusa ta gaba yayi har part ɗinsu sannan ya hau ƙwala kiran "Rabiya" A ƙufule ta fito idanun nan duk a kumbure kwantsa ya cika da alama ma tashin ta kenan daga bacci nan tace "Haba dan Allah Mai-gida, wannan wace iriyar wulaƙanci ce?, ina cikin bacci na kayi ta kwala min kira haka sai kace wanda za'a tashi ƙiyama mtssww" ta faɗa tana tufar da ƴawu. Haƙora ya washe yace "Allah ya huci zuciyar ki gimbiya ta, jeki kawai kiyi kwanciyar ki ga nan mai aiki na samo miki, ita zata yi miki dukkanin ayyukan cikin gidan nan, ni yanzu bari na fita naje nayo cefanen kayan miyar da za'a yi, ai kince kaza kike so koh?." Yatsina fuska tayi tace "Eh kaza nakeso, sannan kuma ka haɗomin da gasasshiyar ta da 5Alive, na samu naci sabida ƴunwa nakeji yanzun." Dariya yayi yace "Kada ki damu bari naje ni yanzun nan na dawo, ke kuma ki tabbatar da kin kammala dukkanin ayyukan ki kafin na dawo cikin gidan nan idan ba haka ba yau sai jikin ki yayi tsami a gidan nan, kinji koh bakiji ba?." "Naji" ta faɗa kanta a ƙasa. Maida duban sa yayi ga Rabi'atu yace "Shalele ta bari naje ni yanzun nan na dawo." "Toh" kawai tace koh ladar samun addu'ar dawowa lafiya bai samu ba haka nan ya fice kamar ya tashi sama dan sauri. Kallon DEENAH dake tsaye tayi tace "Ke dan gaki isashhiya jiya ban ce miki akwai aikin da zaki ƙarasar min ba, amma dan munafurci shine kika shirya kika kama hanƴa da niyar ficewa zuwa makaranta?." "Kiyi haƙuri mantawa nayi." Rankwashi ta zuba mata a tsakiyar kai tace "Mantawa kikayi, ni zakiyi wa ƙarya toh dan Ubanki ki wuce kije ki ƙarasar min da aikin jiya." Hannun ta dafe da kanta tayi hanƴar part ɗinsu tana matsar kwalla. "Ina kuma zaki?." "Canzo kaya na zanyi." "Zo nan" ta faɗa. Zuwa DEENAH tayi ta tsaya a gaban ta nan ta miƙa mata hannu tace "Bani makullin." Makullin DEENAH ta bata nan kuma ta sake cewa "Ina abincin makarantar ki?." "Yana cikin jaka na." "Ciro shi" ta faɗa cikin tsuke fuska. Sauƙe jakar makarantar tayi ta ciro lunch box ɗinta a ciki da ledar bredi ta miƙawa Rabi'atu. Amsa tayi tare da buɗe kular nan ƙamshi ya bugo mata hanci harda su lumshe idanu, Farfesun Cow- tail ne sai shining yakeyi mata a idanu nan ta haɗiyi ƴawu tace "Cha6 ana bura uba a cikin gidan nan, wato ku nan har farfesu akeyi muku ku kai makaranta lallai daɗi yayi muku yawa, yanzu da ban tambaya ba haka nan zakije ki ajiye shi tsabar baƙar zuciya da mugunta irin taki bayan kinsan banida lafiya ga kuma ƴunwa dake nuƙurƙusar ƴan hanjin ciki na, lallai ƴar gata" ta faɗa tana tsamo nama ɗaya ta jefa a bakin ta tana tauna harda su lumshe idanu. Suɗe hannu tayi tace "Wuce kije ki fara yi min aikin" ta faɗa tana amsar jakar makarantar ta. Shigewa DEENAH tayi zuwa falon nan ta gansa kaca-kaca kamar ba jiya ta gyara sa ba, tattare ledojin da ta gani anci abu a ciki tayi ta fito ta sasu a dustbin kafin kuma ta kalli part ɗinsu da yake a buɗe da alamu Rabi'atu na ciki nan taje ta dan ɗauko tsintsiya. Inda suke ajiye kayan shara ta nufa ta ɗauko, motsin da taji a ɗakin Ummar ta ne yasa ta zuwa ta leƙa, daidai lokacin kuma Rabi'atu ke ƙulle abu a bakin zanin ta. Jin kamar tsayuwar mutum ne yasa ta juyowa a firgice tana kallon DEENAH dake tsaye tana kallon ta, Wata iriyar azababbiyar ashariya ta dumulmulo tare da sauƙe shi akan DEENAH tace "Dan bahun ubanki mai kikeyi anan, ba cewa nayi kije kiyi min aiki na ba?." "Kayan shara nazo ɗauka fah." "Kayan shara kika zo ɗauka shine zaki sanƴa ni gaba kina kallo da wadannan mayun idanun naki, shegiya mai suffar kafiran aljanu, algunguma kuma wallahi kika kuskura kika buɗi baki kika cewa Ummar ki na ɗau mata abu a ɗaki wallahi sai kin gane kurenki a gidan nan kin dai san hali na koh?, zaki ficemin ne koh sai nazo nayi wurgi dake anan shegiya mai kama da farar mayu." Da sauri DEENAH ta fice ta juya ta bar ɗakin, nan kuma Rabi'atu ta cigaba da binciken ta har dasu sauƙe akwati tana cicciro abubuwan dake ciki, duk wanda taga yayi mata kuwa sai ta ɗauke shi tana faɗin ai itace yakamata ace tana sanƴa irin su. A haka ta gama ɗaukar wadanda sukayi mata kafin ta fito zuwa part ɗinta. Anan ta tadda DEENAH har ta gama gyara mata falon ta koma gyara ɗaki. Ɗakin ta shigo anan ta dire abubuwan da ta ɗebo nan ta shiga gwadawa, kama daga kan su kaya, ɗan kunnaye da sarƙa dasu awarwaro da ma kuma dayawa na ado. Idanun DEENAH ne suka sauƙa kan wani sarƙa da ɗan kunnen GOLD na Ummar ta nan taje ta ɗauke shi tana faɗin "Anty wannan shine kyauta na ƙarshe da Abban mu yayi wa Ummar mu kafin ya rasu baikamata ki ɗauke shi ba." Hannu tasa ta fuzge tare da tsinka mata mari tace "Na ɗauke ɗin munafuka, idan Ummar taki ta dawo kice mata ni Rabi'atu ce ta ɗebe mata kaya, wadannan tsadaddun kayan ni yakamata na dinga sanƴa su ba Ummar ku ba, dalla wuce ki bani wuri koh na ham6are ki yanzun nan." Ficewa tayi daga cikin ɗakin idanun ta na tara hawaye. Sosai ta gyara mata koh ina sai tada ƙamshi yake, bayan ta gama yi mata gyaran ne kuma ta sake loda mata uban wanke-wanke da wankin kayan ta da basu wuci kala huɗu ba ta wanke. Sosai DEENAH ta gaji wanda har tana yin aikin tana kuka, sosai jikin ta keyi mata ciwo. Tana cikin yin wanke-wanken Kawu ya dawo da cefanen da yaje iyowa. Sai a sannan ne Rabi'atu ta ta6uka abu wurin yin aikin gidan nata, sai dai dukda haka bata bar DEENAH da ɗaukomin wancan ɗaukomin wannan ba. A haka ta gama girkin ta sai dai koh ta6i bata baiwa DEENAH ba dukda kuwa uban aiki da gajiyar da tayi, ga kuma ƴunwa da takeji. Part ɗinsu ta koma tayi wanka ta shirya cikin atamfa ɗinkin riga da skirt kafin ta samu wuri ta kwanta. Cikin bacci taji ana shafa ta, kafin taji an fara ɗaga mata skirt ɗin dake jikin ta. A razane ta buɗe idanun ta tana sauƙe su cikin na Kawu dake shirin zare igiyar wandon sa. Ihu tasa nan yayi saurin rufe mata baki yana zare mata jajayen idanun sa yace "Idan kika kuskura kika yi ihu, sai na ɗauke ki na maida ki ƙauye, sannan kuma duk wani aiki na Rabi'atu ke zaki dinga yinsa, kuma makarantar boko da ta islamiyya babu ke babu zuwa har abada." Sosai jikin DEENAH ya kama rawa kuka kuwa harda majina, nan fah kawu ya fara kiciniyar ware mata ƙafafu inda ita kuma take matse wa. Wani uban rankwashi ya zuba mata a tsakiyar kai yace "Ba zakiyi shiru ba sai kin tona min asiri?." "Dan Allah Kawu kayi haƙuri, mai kake son yi min dan Allah kayi haƙuri wallahi banyi maka laifin komai ba, kada ka dake ni." Sosai Kawu ya haɗa uban gumi fuskar nan tasa yawa an naushi fura, idanun sa wuri-wuri yake lashe baki yace "Ba dukan ki zanyi ba, ƙafafun ki kawai zaki buɗe min, wani abu mai daɗi zanyi miki, sannan kuma kada ki faɗa wa kowa kinji" ya faɗa yana ciro naira ashirin a cikin aljihun sa yace "Sannan kuma idan kika yarda nayi miki ,zan baki wannan kuɗin ki sayi minti, ai kinaso koh?." "Dan Allah Kawu ka sake ni, ai Umma tana saya mana mintin da yafi na ishirin ma, dan Allah Kawu kayi haƙuri." "Ke kinga ki barni nayi abinda nazo yi cikin kwanciyar hankali, kinga babu kowa a cikin gidan nan, daga ni sai ke dan kuwa Rabi'atu ma ta fice ungwa, kuma kinga koh sha biyun rana batayi ba balle a taso su yayan ki daga makaranta, babu mai kwatar ki dan koh kinyi ihu ba wanda zai jiyo ki" ya faɗa yana kai hannun sa cikin skirt ɗinsa. A razane tasa ihu tare da gantsara masa cizo a kunne kafin ta fito a guje. A razane ya tashi cike da firgice wa ya ɗau hular sa ya bi bayan ta, sai haɗa uban zufa yake. DEENAH kuwa tuni ta fice a gidan sai falfala gudu take da dagaggen skirt a hanƴa tana ihu da kuka, sai dai kamar haɗin baki babu kowa anan hanƴan kasnacewar ungwa ce da kowa na cikin gidan sa musamman ma da yau ranar aiki dayawa sun fice zuwa wurin aiki da makaranta. Tuntu6e taci ta faɗa kan wani tsohon langa-langa inda ya yanke ta a ƙafar ta sosai take kuma jini ya 6alle ya fara zuba. Hango Kawu da tayi a bayan ta ne yasa ta tashi ta ƙara ƙaimin gudun ta. Tundaga inda yake zaune jugum dashi ya hango ta da gudu tana kuka. Miƙewa tsaye yayi yana taro ta cike da tashin hankali ganin yadda take ta zuba kuka. "Hey, mai ya sameki, mai yasa kike kuka, waye ya dake ki?" ya faɗa cikin jero mata tambayar. Turus Kawu yayi yana kallon su cike da tashin hankali ganin DEENAH na nuna shi da hannu. "That Monster, mai yayi miki?." "Shine yace wai na buɗe masa skirt ɗina" ta faɗa cikin kuka sosai. Jin ta ambaci skirt ne yasa shi maida duban sa kan skirt ɗin, nan yaga jini na biyo mata ƙafa ya 6ata mata skirt ɗin. Sosai zuciyar sa ta hau bugu, gashi bata bar kuka da maimaita "Shine yace wai na buɗe masa skirt ɗina." ZEEYAD da bai fahimci mai take cewa bane yasa shi nufar Kawu tare da cakumo wuyar rigar sa yace "Mai kayi mata?." Cike da hargowa Kawu ya fara ihun "Jama'a a kawo ɗauki zai yiwa yarinƴar mutane faɗe, zumu zumu na kama sa yana shirin ƙetawa ƴata haddi, jama'a a kawo ɗauki" yadda Kawu yake ihu ne kuma yasa mutane suka fara taruwa, da kuma wadanda suke kan hanƴar wucewa duka, kan kace miye kuma wurin ya cika da jama'a gashi har yanzu Kawu bai bar faɗin cewa "ZEEYAD zaiyi wa DEENAH fyaɗe ba." Wani dattijo ne yace "Haba malam Sale ka dawo nutsuwar ka mana haka nan kayi mana bayanin abin dake faruwa." "Ya kake nayi, tayaya za'ayi na dawo cikin nutsuwa ta yana shirin lalata rayuwar marainiyar Allah, bamu san shi ba, bamu san daga wace nahiyar ya faɗo ba, yau rana tsaka na kama sa da wannan mummunar laifi." "Mai kake son faɗa ne haka?." "Gashi nan, wannan balaraben shi na kama yana shirin yiwa yarinƴa ta fyaɗe yau." "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" duka ƴan wurin suka faɗa kafin kuma duk su rirriƙe ZEEYAD da baisan mai ke faruwa ba, bai kuma san abinda suke faɗa ba. "Kai ku tsaya, ku tsaya, bari muji komai daga bakin ita yarinƴar tukun" faɗin dattijon nan kafin su nufi wurin DEENAH dake tsaye har yanzu tana kuka da alama bata cikin hayyacin ta sabida tsorata da tayi, ga kuma cinƴar ta da ta matse guri guda tana cigaba da kuka. Wannan dattijon ne ya nufi wurin ta yace "Ke yarinƴa kinsan wannan?" ya faɗa yana nuna mata ZEEYAD. Abinda take nanatawa ta sake faɗa "Shine yace wai na buɗe masa skirt ɗina." "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" duk ƴan wurin suka hau nanatawa. "Kun gani koh ai na faɗa muku, wannan dama daga ganin sa ba shida aiki sai lalata yaran mutane, na daɗe da fara zargin sa, toh wallahi ba zan yarda ba, dole ne a kirawo hukuma suyi gaba dashi, dole ne a samarwa ƴata ƴancin ta wallahi, dan kuwa ba zaiyiwu ya lalata mata rayuwa bane ba kuma na kyale shi." Kan kace miye kuma har an kirawo ƴan sanda, ZEEYAD da sai yanzu ya fahimci abinda ke faruwa ne yace "Babu abinda nayi mata, mai zai sa nayi mata haka, itace tazo wuri na wannan mutumin na biye da ita" ya faɗa yana nuna Kawu. Ɗaya daga cikin mutanen ne yace "Ƙarya kake yaro, na daɗe da sanin irin ku, yau Allah ya toni asirin ka, kanaso kayi wa yarinƴa fyaɗe sai kuma Allah ya kama ka, dole ne ƴan sanda su zo su tafi da kai wallahi" cewar wannan mutumin cikin muryar turanci, sai a sannan ZEEYAD ya fahimci Kawu sharrin yiwa DEENAH fyaɗe ya ɗaura masa. "What, fyaɗe?, bani bane i would never do such thing, shine yayi mata fyaɗe, and she came running to me for help, you can asked her again bani bane nayi mata fyaɗe." "Karya kake ita ma ai yarinƴar an tambaye ta kuma tace kai ne kayi mata fyaɗen, yanzu dai an ƙira Uwar Yarinƴa da ƴan sanda suna kan hanƴar zuwa dole ne kayi bayani wallahi" nan suka sake ƙanƙame sa yayin da wasu kuwa har sun fara kai masa duka. Kawu kuwa babu abinda yake cewa sai "yauwa ku ƙara masa, shine, shine wallahi sai hukuma sun hukunta ka, macucin banza da wofi" ya faɗa yana yin wurin DEENAH tare da kamo ta, kafin ya sunkuya ta saitin kunnen ta ganin hankalin mutane ya koma ga ZEEYAD ya raɗa mata "Kina jina wallahi kika kuskura kika ce nina nayi miki abinnan sai na kashe Mamar ki da Yayan ki, sannan kuma na maida ki ƙauye ba zaki sake dawowa nan ba ,idan Ummar ki tazo kice mata shine yayi miki hakan idan kika kuskura kika ce nine sai na yanka ki na binne ki, kinji?" ya faɗa yana muskular ta. Kai kawai ta jinjina masa jin abinda ya faɗa, kafin kuma ya cigaba da faɗin "Ku ƙara masa, koh ku kashe sa ma shine daidai." Motar ƴan sanda ne suka iso wurin tare da Ummar su DEENAH, babu abinda take faɗi sai kiran sunan DEENAH cikin kuka, jin abinda aka faɗa mata a waya an yiwa DEENAH fyaɗe. Da sauri ta nufi wurin DEENAH dake tsaye tana ta kuka tare da rungumo ta tace "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, Wane azzalumin ne ya aikata miki haka?, mai kikayi masa da zai nemi 6ata miki rayuwa...?" "Gashi nan, gashi nan shine wanda yayi mata fyaɗe" cewar Kawu yana nuna ze da ya sha bugu a hannun jama'a, inda dakyar ƴan sanda suka kwace shi. Da sauri ta miƙe tana kallon ZEEYAD ɗin zuciyar ta na yi mata zafi kamar zai fito waje, cukumo sa tayi tace "Kai ne, kai ne kayi mata fyaɗe, kai ne kayiwa DEENAH ta fyaɗe, mai tayi maka da zaka saka mata da wannan mugun aikin, maiyasa, har kai wanene da zaka ta6a jikin ƴata kayi mata fyaɗe?" ta ƙarashe tana zuba masa mari a ƙunci tana jijjiga shi. "I...i didn't do it, i swear i didn't do it, bani bane, ba zan ta6a yin hakan ba, ki yarda dani." "Na yarda da kai, bakada hankali ne?, wallahi sai ka fuskanci hukunci mai tsanani sai kayi nadama aikatawa ƴata haka, koh dan saboda kai sai nayi dukkanin yadda zanyi na cika buri na na zama Lawyer, sai na tabbatar da anyi maka hukuncin da ba zaka ta6a fitowa daga gidan yari ba muddin ka tafi." Da kyar ƴan Sanda suka raba riƙon da tayi wa ZEEYAD, nan kuma aka karkata ƙeyar su dukkanin su zuwa police HEADQUATER dan ɗaukar bayanai. Isar su keda wuya dukkanin su aka kai su wani office harda ZEEYAD da aka garƙama wa handcuff a hannu. Kujera aka bawa Ummar su DEENAH da har yanzu bata bar kuka ba, kamar wacce ake sarar naman jikin ta, sosai takejin zuciyar ta kamar ta fito waje. Kawu ma samun wuri yayi ya zauna sai zazzare idanu yakeyi, yawa tsohon munafiki. Nan fah aka fara ɗaukar Statement ɗin kowa daga cikin su. Kawu ne ya fara da faɗin "Na aike ta shago akan ta sayo min ruwan sanƴi sabida matata Rabi'atu bata nan bansan inda ta sanƴa makullin firijin mu ba, ta kai kusan awanni biyu bata dawo ba, hakan yasa ni yanke shawarar bin bayan ta, anan ne kuma na tarar da wannan mai jan kunnen yana aika mata mummuna" ya faɗa cikin fashewa da kukan munafurci. Nan aka dawo kan ZEEYAD aka tambaye sa koh gaskiya ne abinda kawu ya faɗa nan yace "Bani bane, bani bane nayi mata hakan, zaku iya tambayar ta, bani bane." "Sau nawa kakeson a tambaye ta, bayan kuma ita yarinƴar ta shaida cewa kai ne kayi mata hakan." "Ku sake tambayar ta, little DEENAH nine nayi miki hakan?." Shiru kawai tayi tana bin kowa da manƴan idanun ta da suka kumbura da kuka,kafin ya sake faɗin "Tell them, ba ni bane koh?" ya faɗa yana kallon ta. Ɗan sandar nan ne ya tambayi DEENAH yace "Kada kiji tsoro kinji, babu wanda zai iya ta6a ki anan, ki saki jikin ki kinji?." Kai ta jinjina nan yace "Good girl, yanzu faɗa mana wanene yayi miki abinnan?." Shiru tayi tana binsu dukkanin su da idanu, inda Kawu kuwa babu abinda jikin sa da zuciyar sa keyi sai rawa. Maida duban ta tayi kan ZEEYAD tana kallon cikin kwayan idanun sa kamar yadda shima yake kallon nata. Maganar da kawu ya faɗa mata ne ya shiga dawo mata kai _"Idan kika kuskura kika yi ihu, sai na ɗauke ki na maida ki ƙauye, sannan kuma duk wani aiki na Rabi'atu ke zaki dinga yinsa, kuma makarantar boko da ta islamiyya babu ke babu zuwa har abada."_ Kafin kuma ta sake tuna _"Kina jina wallahi kika kuskura kika ce nina nayi miki abinnan sai na kashe Mamar ki da Yayan ki, sannan kuma na maida ki ƙauye ba zaki sake dawowa nan ba ,idan Ummar ki tazo kice mata shine yayi miki hakan idan kika kuskura kika ce nine sai na yanka ki na binne ki, kinji?"_ Hawaye ne suka shiga kwaranƴo mata daga idanu, batason rasa Mahaifiyar ta sannan batason rasa ɗan uwanta mafi soyuwa a gareta, dukkanin su su biyun nan sunada muhimmanci a rayuwar ta. Idan ta ɗaurawa balarabe sharri bata kyauta masa ba, sabida yana da kirki sannan kuma yayi mata zanen hoton ta dama kuma na yayan ta da Ummar ta, idan tayi masa sharri bata kyauta masa ba sannan kuma ba zai ta6a yafe mata ba. Kawu kuwa zai iya aikata abinda ya faɗa akanta muddin bata ce Balarabe bane yayi mata hakan. Sake tsinkayo muryar Police yayi yace "Kada kiji tsoro ki faɗa mana wanene?." Idanun ta a cikin na ZEEYAD dake kallon, kafin kuma ta ɗau hannu a hankali tana pointing ɗinsa tace "Shine." "Kun gani koh, mai na faɗamuku, ai na faɗa muku cewa shine, munafukin banza da wofi" faɗin Kawu. "What, me?" ya faɗa cikin rawar murya. A hankali ya shiga girgiza mata kai yace "No, she is lying, bani bane, she is lying to me i would never do this" ya faɗa idanun sa na yin jaa sosai yana kallon DEENAH cikin 6acin rai. "Tell them, tell them the truth, tell them that i didn't do it, tell them" ya faɗa mata a tsawace yana fitar da zazzafar huci. Hannu Ummar DEENAH ta ɗauka ta wanke fuskar sa da mari tace "How dare you, how dare you raise your voice on my daughter, ba zata yi ƙarya ba, kai ne mana ka aikata mata hakan, idan ba kai bane ba zata ta6a nuna ka ba sabida yarinƴa ta bata ƙarya." "DEENAH stop pointing and tell them the truth." "What truth?" faɗin Police yana tashi tsaye cikin 6acin rai kafin kuma yasa azo a kama ZEEYAD ɗin a tafi dashi. Rirriƙe sa sukeyi sai dai yaƙi tashi tsaye kamar ya kwace haka yake zaburowa yana kallon DEENAH da har yanzu bata sauƙe hannun ta kan pointing ɗinsa ba. Abar wuyar sa ce ta tsinke ta faɗo bai saniba, sabida baya cikin hayyacin sa, burin sa kawai ta buɗi baki tace ba shi bane. Da kallo tabi abin dashi har aka fice daga office ɗin da ZEEYAD yana kiran sunan ta. Duk mara musu baya ƴan cikin office ɗin sukayi kafin kuma ta sunkuya ta ɗauki sarƙar tana kallo. Police ɗinne ya dawo yace mata "zo" nan ta damƙe sarƙar a hannun ta tana binsa. Jikin Ummar ta taje ta raku6e tana cigaba da kuka mai ƙarfi. "Kada ki damu insha Allah sai anyi masa hukunci daidai da abinda ya aikata miki, muje" faɗin Ummar tata itama cikin kuka. Sai a sannan kuma aka kaita asibiti dan yi mata gwaji dama kuma duba lafiyar ta................. *MHIZZ JIDDHERR................✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* _Da yawan ku na cewa wahalar ZEEYAD tayi yawa a sassauta masa, sai dai fah ku sani ba zan canza koh da (A) bane daga cikin labari na, idan zaku karanta a yadda tsarin labarin yazo ku karanta, idan kuma baiyi muku ba na ajiye abina, dama dan ku karanta nakeyi idan kuma kunce bakwa so toh nima kun kawo min sauƙi, sai na ajiye shi kawai, dan haka ku bar ni na tafiyar da abuna yadda na tsara shi please👏🏽, babu abinda zan canza a ciki._ *012...* ...........Koh da sukaje asibiti gwaje-gwaje akayi mata sosai, nan dai aka gano babu wata matsala tattare da ita sannan kuma ba'a yi mata fyaɗe ba, illa ciwon da taji kawai da akayi mata dressing ɗin shi. Sosai zuciyoyin kowa ya cika da mamaki jin ba'a yiwa DEENAH fyaɗe ba, nan kuma aka fara tuhumar ta akan mai ZEEYAD ɗin yayi mata. Cikin kuka tace "Babu abinda yayi min, shine yace wai na ɗaga masa skirt ɗina" ta faɗa tana goge hawayen fuskar ta da hannu ganin Kawu na zare mata ido ta baya. "Yayi attempting yin fyaɗen ne kenan, duk da haka yanada laifi sannan kuma sai hukuma ta hukunta shi da izinin Allah" cewar ɗan Sanda. "Toh ai shikenan, mu godewa Allah da bai kai ga lalata mata rayuwa ba, ke kuma Fatima ki dinga kula, shiyasa nace zan ɗau yarinƴar nan na kai ta chan ƙauye wurin Uwar gida ta Rakiya amma kika ƙi, da achan take yanzu da babu abinda zai sameta" cewar Kawu. Shiru kawai Umma tayi tana mai yin hamdala a ranta ganin ba'a lalatawa ƴar ta rayuwa ba. Sallamar su akayi daga asibitin inda ɗan Sanda yace zasu cigaba da tuhumar ZEEYAD har sai sun gano wasu bayanan game dashi. Gida suka dawo, abinci kawai Umma ta zuba mata ta bata magani ta sha sannan ta kwanta, har yanzun bata bar kuka ba, A haka bacci ya ɗebe ta anan wurin. Bata farka ba sai bayan Azahar, dan haka sallah kawai tayi ta zauna ta sake dasa wani sabon kukan. Zuwa Umma tayi ta zauna kusada ita tace "Menene kuma ƴar albarka, akwai inda keyi miki ciwo ne?." Kai kawai ta girgiza mata tana cigaba da kuka. "Toh maiyasa kike kuka?." "Umma ni babu abinda yayi min ai baiyi min fyaɗen ba tukun kice a fito dashi dan Allah." Shiru Umma tayi tana janƴo ta jikin ta ta share mata hawaye tace "Yi shiru toh haka nan ki daina kuka kar kisa wa kanki ciwon kai, ai koh bai kai ga yi miki wani abin ba ai yanada laifi tunda yana ƙoƙarin aikatawa ne aka kama shi, kinga dai da abinda ya saka miki koh?, da zuciya ɗaya kika ɗauke shi, kinyi masa halacci ba tare da sanin koh wanene shi ba, yanzu da ya kai ga lalata miki rayuwa fah?, dole ne a hukunta shi sabida gaba, yi shiru haka nan kinji?." Jafar dai kawai da idanu yake bin su, amma sam bai yarda da abinda DEENAH ta faɗa ba, haka kuma bai yarda da Kawu ba, ganin yadda yake ta rawar ƙafa tunɗazu yana zuwa ya tambayi lafiyar DEENAH abinda bai ta6a yi ba kenan. Rarrashin ta Umma tayi har saida tayi shiru kafin kuma ta fice zuwa ɗaki. Sauƙowa Jafar yayi zuwa inda take zaune yace da ita "Kiyi haƙuri DEENAH ki daina kuka haka nan kinji, ai kince baiyi miki komai ba koh?." Kai ta jinjina masa, nan yace toh "Idan baiyi miki komai ba, waye ne yayi miki, kuma mai ya kai ki wurin shi?." Shiru tayi bata basa amsa ba tana cigaba da kuka. Dube-dube ya hau yi kafin kuma cikin raɗa yace "Kawu ne koh?." Da sauri ta hau girgiza masa kai tana faɗin "Ba shi bane Allah." "Ƙarya kikeyi DEENAH, Kawu ne yayi miki haka, shine yace ki ɗaurawa balarabe sharri, ke kuma kika ɗaura masa dan kawai ya tsoratar dake da wani magana tasa, ke kuma kika yarda zai iya yin hakan, kika ɗaurawa balarabe sharri, kinsan miye Balarabe yace min ɗazu da safe da na kai masa abinci?." Shiru tayi bata basa amsa ba, nan ya cigaba da faɗin "Cemin yayi kina da kirki, tunda ya shigo Nigeria bai ta6a haɗuwa da mutum ɗaya daya taimake sa dan Allah har yaji tausayin sa ba sai ke, yace na baki haƙuri da ce miki mayya da yayi a baya dama kuma wulaƙancin da yayi tayi miki idan kin kai masa abinci yaƙi ci, sannan kuma yace a shirye yake yayi miki wani zanen muddin zaki cigaba da farin ciki, yace min kece Mace ta farko da ya fara yarda da ita tun bayan mutuwar mahaifiyar sa, sai dai kuma a yau DEENAH kin ruguza yardar da yayi miki, shi mai son ganin ki ne kullum cikin farin ciki sabida kema kinyi iya ƙoƙarin ki na ganin ki sanƴa sa farin ciki, sai dai kuma a yau kece kika ruguza masa wannan farin cikin, ya bani labarin sa kuma shi ɗin abin tausayi ne sosai, sai gashi kuma yau rana tsaka kin sake kwa6e komai kin cusa masa ƙunci ta hanƴar yi masa sharrin yunƙurin yi miki fyaɗe bayan kuma bashida laifi sai ma ƙoƙarin sa na kare ki da yakeson yi, ke butulu ce DEENAH kuma nasan balarabe ba zai ta6a yafe miki ba akan wannan sharri da kikayi masa, sannan kuma ba zai sake yarda da kowa ba, sabida ya ɗauka ke ɗin mutuniyar kirki ce..." Kukan da ta fashe dashi ne yasa shi dakatawa da zancen sa bai idda ba, Umma ce ta fito daga ɗaki jin ta fashe da matsanancin kuka nan ta hau faɗin "Menene kuma, miye yasa ta kuka, Jafar kai ne koh, mai ka faɗamata?." Tashi yayi tsaye yace "Umma ni babu abinda na faɗamata sai gaskiya." "Jafar zan sa6ar maka fah, fice ka bani wuri kai da zaka kwantar mata da hankali kuma shine zaka sake sanƴa ta cikin damuwa, haka na koyar da kai halin yaya na kwarai?." Ficewa Jafar yayi dan kuma sosai yaji haushin DEENAH dan ya gane cewa sharri ne tayi wa Balarabe. Rarrashin ta Umma ta fara sai dai kamar sake zuga ta take, da kyar dai ta samu ta ɗan sarara da kukan bayan tayi mata alƙawarin zata sa a fito dashi.......... ******************** ........Yau sati biyu da faruwar wannan lamari, kuma har yanzu DEENAH bata bar kuka ba ga wata iriyar rama da tayi, sosai takejin wani abu a zuciyar ta da ta kasa gane koh menene shi, wanda yake yawan sata rashin sukuni, kullum jin zuciyar ta take a cunkushe, bata da wata walwala. Tun Umma na lallashin ta kullum har ta gaji ta daina kula ta, ga Jafar ma yanzu ya daina sakar mata fuska yana kula ta kamar dah, Islamiyya ma ya daina zuwa tare da ita komai shi kaɗai ɗinsa yakeyi ya daina kula DEENAH muddin ba ta faɗi gaskiyar Kawu ne ya sanƴa ta aikata hakan ba. Ita kuwa DEENAH sosai ta ɗau maganar Kawu da gaske dan kuwa babu ranar da zasu haɗu bai sake yi mata warning ɗin da yafi na dah firgitar wa ba, dan har wuƙa yana cire mata yace dashi zai kashe Umma da Jafar, wannan ne dalilin da yasa har yanzu ta kasa faɗar gaskiya sannan kuma take jin zuciyar ta a cunkushe. 6angaren ZEEYAD kuwa watanni shida aka yanke masa zama gidan yari, dukda an gano baya harƙallah da kowa kuma shi kaɗai ke rayuwa bai sanƴa an sake sa ba, sabida kawai laifin da aka ɗaura masa na yunƙurin aikata fyaɗe. Sosai yakejin tsanar DEENAH a zuciyar sa, ta ruguza masa komai na rayuwa, sanadiyyar ta zai 6ata watanni shida a kurkuku, sanadiyyar ta yayi losing diamond Necklace ɗinsa that is worth billion of dollars, the last gift da Mahaifiyar sa tayi masa, dashi ne yake tuna Mahaifiyar ta and now yayi losing ɗin wannan Necklace ɗin yayi losing farin cikin sa har abada, ji yake ya tsani komai ya tsani kowa, sai dai tsanar da yayi wa DEENAH ya wuce gaban misali, da farko ya ɗauka ita ɗin mayya ce sai dai kuma a yanzu ya gano sharrin ta ya wuce gaban na maita, ita ɗin annoba ce sannan kuma shaiɗaniya kamar yadda ya ɗauke ta. Koh wane bugun zuciyar sa na bugawa ne da tsanar DEENAH, a yanzu ji yake babu babbar maƙiyar sa a duniya da ya wuce ita, koh da tsabar da yayiwa family ɗinsa bai kai wanda yake yiwa DEENAH ba. Ta shigo rayuwar sa ta ƙarfi da yaji dan kawai ta ruguza masa ita, yanzu dole yayi wasting rabin shekara anan cikin ƙunci da baƙin ciki, bashida komi, bashida kowa, asarar wata shida a cikin rayuwar sa ta kama shi wanda yakamata ace da shi ne zai fara gina kanshi, tunda har Jafar yace dashi zai iya making kuɗi a drawing ɗin da yayi musu............. ****************** ........"Nikam dan girman Allah ba zaki daina kukan nan bane, wallahi zan naɗa miki na jaki sai ki dinga yin kukan kawai da dalili, haba tsawon wata ɗaya ace mutum bashida aiki kullum sai kuka, ai koh mutuwar ubanki bakiyi kuka haka nan ba. toh wallahi ki fita daga ido na na rufe na gayamiki" Faɗin Umma cikin tsananin 6acin rai tare da jin haushin DEENAH. Ta6e baki Rabi'atu dake zaune tayi tana habaice-habaicen ta "Ya mutum ba zaiyi kuka ba, an maida sa fanko, dama gado aka ci, sabida an saba da yawa-yawacen bin maza tun iyaye da kakanni, Allah sarki." Sosai Umma taji zafin maganar Rabi'atu sai dai bata kula ta ba kasancewar bata iya rigima ba kwata-kwata, haka ma tasan ita ce ta kwashe mata abubuwa a ɗaki sai dai koh a fuska bata nuna hakan ba. Jafar ne ya dawo daga aiken da Umma tayi masa ya miƙa mata yayi ciki abin shi ba tare da ya kalli inda DEENAH take ba. Tashi tayi tabi bayan shi tana kuka ta kira sunan shi. "Yaya." "Nace ki daina yi min magana muddin baki shirya faɗar gaskiya ba." "Yaya dan Allah kayi haƙuri." "Ni kika yi wa laifi ne da zaki bani haƙuri, ai ba ni kika wa laifi ba Balarabe kika yiwa laifi." (Kasancewar basu san sunan ZEEYAD ba yasa suke kiran shi da Balarabe). "Yaya wallahi zan faɗa, zan faɗi dukkanin abinda ya faru amma ina tsoron kada Kawu ya kashe ka kai da Umma." Da sauri ya sauƙo zuwa inda take ya riƙo hannun ta, cikin kwantar da murya yace "DEENAH Kawu ne yasa kiyi hakan koh?." Da sauri ta jinjina masa kai, hakan yasa shi fara kiran Ummar su. "Menene dan Allah, banason damuwa fah." Fita yayi yaje ya sameta yana kamo hannun ta yace "Umma kizo kiji." Ajiye tray ɗin hannun ta tayi tana bin bayan shi zuwa falon nasu. Baki Rabi'atu ta ta6e tana faɗin "Mtssww wai su gasu masu soyayyar uwa da ɗa." Zama tayi kan kujera nan yace "Umma ai dama na faɗa miki Balarabe ba shida laifi kuma ba zai ta6a aikata abinda ake zargin sa dashi ba." "Akan wannan maganar ka kira ni, idan ba shida laifi maiyasa tun farko ta buɗi baki tace shine, kaga fah Jafar ka fita idona na rufe." "Umma gata nan ki tambaye ta da kanki, ita ta faɗa min." Kallon DEENAH dake matsar kwalla tayi tace "Zo nan." Zuwa tayi kusada Umma kafin Umma tace "Faɗamin gaskiya tsakanin ki da Allah, kinga dai Allah yana ganin ki kuma yana hukunta masu ƙarya koh?." Kai ta jinjina mata, nan ta cigaba da faɗin "Kuma kinga Allah bayason masu ƙarya koh?." Nan ma jinjina mata kai tayi sannan tace "Kuma duk wanda ya zalunci wani koh da kuwa wanda aka zalunta ɗin ya kasance mai aikata sa6o ne, indai ya kai kukan sa ga Allah yana bi masa haƙƙin sa koh bajima koh ba daɗe koh?." "Kai ta jinjina nan Umma tace "Toh ki faɗamin tsakanin ki da Allah, wane ne yayi miki haka indai ba balarabe bane?." Cikin kuka tace "Wallahi Umma zan faɗa miki banaso Allah ya kama ni da laifi." "Toh faɗamin ina jin ki." "Umma wallahi Kawu ne..." "Kawu?" ta faɗa cikin katse ta. Kai ta jinjina mata kafin ta kwashe dukkanin abinda ya faru ta faɗawa Umma tare da ɗaura da faɗin "Umma wallahi Balarabe bai ta6a yi min komai ba, da naje wurin sa ina kuka ne shine Kawu ya ɗaura masa sharri sannan yace min zai kashe ki keda Yaya indai har ban ce balarabe bane, Umma dan Allah kije ki ciro shi kuma ki bashi haƙuri wallahi ba zan sake ba, ga kuma Kawu zai kashe ku." Umma tsabar baƙin ciki da taƙaici batasan sadda ta hau jibgar DEENAH da duka ba. "Dan Ubanki kawun mala'ika ne, da har zakiji tsoron abinda ya faɗamiki ki ɗaurawa bawan Allah sharri baiji ba bai gani ba, haka na koya miki ɗaurawa mutane sharri,koh haka aka koya miki a makaranta?, wawuyar banza da wofi marar wayo" ta faɗa tana tunkuɗa ta daga jikin ta ta faɗi. Kuka Umma ta fashe dashi, dan kuwa DEENAH ta gama zubar da ita, yanzu da wane ido zata kalli Balarabe ta bashi haƙurin abinda ya faru,yaro yana zaman zaman shi DEENAH ta ja masa masifa da bala'i, ashe yana da gaskiya da yayi ta cewa ba shi bane, ashe ƴar ta ce mai ƙaryar. A fusace ta tashi ta fice tana kwala kiran Kawu "Sale!, Sale!!." Miƙewa tsaye Rabi'atu tayi cike da tsiwa tace "Toh yana bacci, lafiya kike kwala..." Bata ƙarasa ba taji wani irin mari a fuskar ta,kafin Umma ta tunkuɗa ta gefe ta shige, muciyar da ta gani a bakin ƙofa ta ɗauka tare da shigewa cikin ɗakin. Naƙe-naƙe ta sami Kawu sai baza bacci yana munshari bakin nan a wage. Bata yi wata-wata ba ta zuba masa muciyar a baki take ya rufe ta yana tashi a zabure, kafin yayi wani abin kuma tuni Umma ta hau moɗa masa muciya tana faɗin "Wallahi kayi asara.mafi muni a rayuwar ka, insha Allah sai kayi nadamar abinda kayi kafin ka mutu, sai ka sha wahalar rayuwa ka rasa mai taimakon ka kafin ka mutu, abin naka bai tsaya a iya cin dukiyar marayu da muzguna musu ba, har ya kai ga kayi yunƙurin yiwa ƴar cikin ka fyaɗe, fyaɗe fah wallahi kaji kunƴa kuma insha Allahu sai kaga sakayya akan ƴaƴan ka ba kaima ka haifa ba?, kamar yadda kake lalata rayuwar ƴaƴan mutane kaima sai an samu mai lalata naka ƴaƴan, mazinacin banza da wofi, ƙaramin mutum asararre kawai" har suka fito waje bata daina bugun sa ba, Kawu kuwa sai ihu yake zubawa a taimake sa Fatima zata kashe shi, sai zagaye cikin gidan suke kasancewar Jafar ya rufe ƙofar fita da makulli babu damar Kawu ya fita sannan babu wanda zai kawo masa taimako. Sosai Jafar ke farin cikin yadda yau Ummar su ke jibgan Kawu dariya kuwa yayi ta harda riƙe ciki ganin yadda Kawu ke ihu yana bawa Ummar su haƙuri kamar ƙaramin yaro. Rabi'atu kuwa miƙit tayi idanun ta zuru-zuru tana ganin yadda Umma ke jibgan mijin ta Sale. Sai da Umma tayi wa Kawu lilis kafin ta kyale sa nan ta cewa "Jafar ɗauko min mayafi na kuzo muj." Da sauri ya shige ɗaki farin ciki kamar yayi yaya ya ɗauko mata mayafin ta nan ta yafa ta rufe side ɗin ta ta kaɗa kan Ƴaƴan ta suka fice. Mutane dayawa ne a bakin ƙofar gidan babu wanda ta kula ta ratsa ta cikin su suka wuce. Abin hawa suka tara inda ya kai su har Police HEADQUATER, luckily wannan wanda ya kar6i case ɗin shine a duty yau dan haka iso akayi musu zuwa ofishin sa. "Dan Allah yallabai yaron da ka kama nakeso ka sake sa, bashida laifin komai bai aikata komai ba, dan Allah a sake sa haka nan." Gyara zama yayi ya kalle ta yace "Bangane a sake sa ba, case ɗinnan ya riga da yayi nisa kuma har an yanke masa hukunci, mai kuma kuke buƙatar proving anan?." Jawo DEENAH tayi tace "Ƴata ce ta amsa cewa yayi laifi toh ba gaskiya ta faɗa ba, ba kowa bane mai laifin face Kawun su." Kallon DEENAH yayi yace "Kinason kice min wanda aka kama da laifi ,he is not the one at fault kenan?." "Kwarai kuwa abinda nake nufi Kenan." "Amma maiyasa, sai yanzu ne zaku zo da wannan maganar?." "Gata nan ita da kanta, kayi mata dukkanin tambayar da zakayi mata, ita kuma zata faɗa maka gaskiyar abinda ya faru." Kallon DEENAH yayi yace mata "Zo." Zuwa tayi nan yace da ita "Ki saki jikin ki, ki faɗamin abinda ya faru a wannan ranar." Goge hawayen fuskar ta tayi kafin ta shiga koro masa bayanan dukkanin abinda ya faru. Sosai ɗan sanda yayi mamaki, nan yace "Babu shakka that Man sounds guilty." "Dan Allah ina shi yaron yake yanzu?, a sako shi dole ne mu nemi yafiyar sa." "Sergeant" ya kwala masa kira. Shigowa wanda aka kira da sergeant yayi tare da sara masa cikin girmamawa nan yace "Kuje ku taho da wannan Balaraben nan." "Yes sir" ya faɗa cikin sarawa yana ficewa. Sosai zuciyar DEENAH ke tsinkewa haka kurum ta rasa dalilin maiyasa. Zuwa akayi aka taho da ZEEYAD, sosai yayi baƙi ya rame, nan duk suka maida duban sa zuwa garesa. Sosai fuskar sa ta sake ɗaurewa lokacin da ya haɗa idanu da DEENAH. Umma ce ta durƙusa har ƙasa ta shiga baiwa ZEEYAD haƙurin sharrin da akayi masa. Koh kaɗan bai ga laifin Umma ba sabida ai ita ɗin Uwa ce, kuma duk Uwar da taji an yiwa ƴar ta fyaɗe dole ne ta fice cikin hayyacin ta idanun ta su rufe musamman idan ya kasance ta tarbiyan tar da ƴaƴan ta. "Stop begging me please, banga laifin ki ba, i just want you to know that ni bani bane nayi wa ƴarki fyaɗe." "Na san da hakan, wannan ne dalilin da yasa nazo da kaina dan na baka haƙuri, dan Allah kayi haƙuri haƙiƙa an zalunce ka dukda nasan ba lallai bane ka iya yafe mana, Kawun ta shi ke da laifi" ta faɗa cikin harɗe hannayen ta. Sunkuyar da kai ZEEYAD yayi dan baya son tsayuwar sa a nan he can't stand this DEENAH girl, sosai yakejin ta fita a kansa, sam bayason ta baya son ganin ta. "It's alright" kawai ya faɗa kansa a ƙasa. "Nagode, Nagode Allah yayi maka albarka, ban ta6a zaton zaka yafe mu cikin ƙanƙanin lokaci ba." "Take him away" cewar Ogan nan aka fita dashi, kafin ta juyo zuwa gareshi tace "Dan Allah ku sake shi, ba shi bane mai laifin, mai laifin na chan gida mun baro shi, shi zaku kama ba wannan bawan Allahn ba." "Zamu sake shi tunda har aka gano yanzu bashida wani laifi, sai dai ba zamuyi hakan ba har sai mun sami saƙo daga kotu an wanke shi daga laifin da ya aikata." Kai ta jinjina tace "Wannan zai zo da sauƙi tunda har an gano wanda yayi laifin, buri na shine ku kama sa sannan kuma ku hukunta shi." "Insha Allah, muje." Nan duk suka miƙe kafin su ɗau motar Police guda ɗaya da polisawa guda biyu suka fice, basu tsaya a koh ina ba sai bakin ƙofar gidan su. Ratsa ɗan ɗaiɗaikun mutanen da suka rage sukayi suka shiga cikin gidan, nan fah suka tadda Kawu kan tabarma Rabi'atu nayi masa fifita. Ganin ƴan Sanda yasa hankalin sa matuƙar tashi ba tare da wata wata ba aka garƙame sa aka tafi dashi, ba tare da damuwa da ciwon dake jikin sa ba. Bayan wata ɗaya akayi zaman Kotu, inda dakyar Kawu ya amsa laifin shi, bayan an kuma kama sa da laifin tauye haƙƙin Marayu dama kuma case ɗin laifin fyaɗe daga ƙauye. Haƙƙin marayu aka kwatar musu, wanda kuɗi ne dayawa a hakan ma ba kaɗan Kawu ya cinƴe ba, sannan kuma aka wanke ZEEYAD daga laifin da ake tuhumar sa na aikata fyaɗe. Koh kaɗan baiji farin cikin hakan ba, dan kuwa baya tunanin zai iya yafewa DEENAH, ta sa shi yayi spending watanni biyu a gidan yari, Uwa Uba ya rasa abu mafi muhimmanci a gareshi duk domin ita. Sosai Umma ta cika da farin cikin wanke ZEEYAD da akayi, ga kuma farin cikin dukiyar marayu da aka kwato musu abin su, Kawu kuma yayi gidan yari har ƙarshen rayuwar shi. Gida suka wuco harda ZEEYAD ba dan yaso ba, dan kuwa sosai yake so yayi musu nisa, bama su kaɗai ba da kowa ma yakeson yin nisa. A bakin ƙofar gidan suka tsaya sabida ZEEYAD yaƙi ya shiga yace shi tafiyar sa zaiyi. "Dan Allah kar muyi haka dakai mana, kayi min halacci wurin yafe mana laifin da mukayi maka...." "Na yafe muku, sai dai banda ita" ya faɗa yana kallon DEENAH da ita ma ke kallon sa. Sosai zuciyar Umma ya buga jin abinda yace "mai....mai kake nufi?." "Ta ruguza min rayuwa, i spend two months in jail all because of her, tasan ba ni na aikata laifin ba amma tayi shiru bata ce komai ba, and just because of her nayi losing abu mafi muhimmanci da soyuwa a wuri na, how do you expect me to forgive her then?." Shiru Umma tayi bata iya cewa komai ba, dan kuwa ta hango tsantsar 6acin rai dama kuma gaskiyar abinda yake faɗa a idanun sa na cewa ba zai yafewa DEENAH ba. "She is just a little girl..." "No she is not, she knows exactly what she is doing, am sorry to say this to you as a mother, but nothing would make me forgive her for ruining my whole life, am living and don't try to Stop me please, coz i need to move on with my life, ta koya min hankali sannan ta koyamin kada na sake yarda da kowa komin irin kirkin da suke nunawa maka kuwa, i just hate and despised her." Sosai Umma taji zafi dama kuma rashin jindaɗin maganganun sa akan DEENAH nan tace "Alright then, i won't stop you from leaving but let me make one thing clear to you, my daughter has a clean heart and she is pious, dan ta aikata kuskure ba shi ke nufin ba zaka yafe mata ba, koh da baka yafe mata ba Allah ba zai kama ta da laifi ba dan kuwa ita ɗin tana cikin ƙaddarar ka ne, nayi niyyar taimakon ka ne amma sai dai ba zan iya jurar irin kalmomin da kake jifar ƴata dashi ba, you should get going then, i won't stop you." Da kallo ya bisu dukkanin su kafin kuma ya juya ya fara tafiya. "Umma ina zai je?" faɗin DEENAH. "Bar shi ya tafi shi ya za6i hakan." Da gudu ta mara masa baya tana riƙo rigar sa ta baya tace "Ina zaka je?." Runtse idanu yayi kafin kuma ya cire hannun ta daga riƙon da tayi masa. Sake ruƙo shi tayi tace "Dan Allah kayi haƙuri." "Stay away from me, you're nothing but a problem to me, i just hate seeing your face for good" ya faɗa yana tunkuɗe ta ta faɗi ya cigaba da tafiyar sa ba tare da ya waiwaye ta ba jin Kukan da take. Da sauri ta koma wurin Ummar ta tace "Umma dan Allah kice ya tsaya, Umma ki basa haƙuri kada ya tafi, dan Allah Umma." "Shi ya za6i ya tafi DEENAH, ba zan iya hana sa ba, kiyi haƙuri." "Nidai dan Allah Umma kice kada ya tafi, shikenan ba zan sake ganin sa har na kai masa abinci ba kenan, Umma kice ya tsaya" ta faɗa tana kallon ZEEYAD ɗin da yayi nisa. Riƙo ta Umma tayi ta shigar cikin gidan kafin Jafar da jikin sa yayi mugun sanƴi shima yana kallon ZEEYAD ɗin ya shige cikin gidan. Bayan sati biyu Umma ta nemi transfer ɗin aikin ta zuwa Sokoto kasancewar chan zasu koma da zama yanzu, sabida anan Babbar Yayar su take aure, shiyasa ta za6i ta koma chan ɗin da zama kusada ƴar uwarta. Shirye-shiryen tafiya kawai suke inda DEENAH kuwa sam batason tafiyar, kullum sai taje inda ZEEYAD yake zama bata ganin sa, kenan hakan na nufin yayi mata nisa. Buɗe tafin hannun ta tayi tana kallon sarƙar da batasan koh na mecece ba, iya tsawon kwanakin nan babu wanda yasan tana tare da sarƙar nan. "DEENAH?" ta jiyo an kira sunan ta, saurin 6oye sarƙar tayi tana amsa kiran da Umma tayi mata ta fito. "Zo kici abinci mu wuce haka nan." "Umma na ƙoshi" tana faɗin haka tayi wucewar ta ɗaki tana ciro sarƙar da ta 6oye ɗin tasa a jikin ta. Da kallo kawai Umma ta bita dan kuwa har yanzu bata bar tunanin ZEEYAD ba, inbanda ma yarinta irin ta DEENAH. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gama shiryawa, kafin su fito bayan Jafar ya kira musu adaidaita sahu har zuwa ƙofar gida. Kayayyakin su suka sanƴa kafin duk su shiga, inda daga baya kuma za'a zo a kwashe manƴan kayan ɗakin. A tashar mota ya sauƙe su suna zuwa kuwa motar Sokoto ta cika ba tare da 6ata lokaci ba kuma motar ta tashi suka kama hanƴa.........TOH SU DEENAH SAI DAI MUCE ALLAH YA KIYAYE. *10 YEARS AFTER.............* ********************* *TOH, Ance idan ansan farkon rikici ba'a san Ƙarshen ta ba, bayan shekaru goma shin yaya kuma rayuwar wadannan mutane zata kasance dai Oho, waya sani koh zasu sake haɗuwa ko kuma dai shikenan rabuwar kenan har abada?, toh dai Allah ne masanin wannan mu haɗu a page na gaba dan ganin yadda rayuwar kowanne daga cikin su ke tafiya* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *013...* *10 YEARS LATER* ...............Tafiya take cikin sauri tana haɗa wa da ɗan gudu ta shige cikin ƙatuwar mall ɗin. Wani abu ta danna, nan take Ƙofar mall ɗin ya buɗu ta shiga. Da kallo ta fara bin mall ɗin tana hange-hangen ta inda zata nemo sa yayin da hannun ta ke ɗauke da roses flower a cikin ledar sa. Juye-juye ta fara tana kuma bin saman stairs ɗin dake cike da dandazon mutane da kallo. Ƙaton mall ne sosai domin kuwa har lifter mai stairs akwai a cikin mall ɗinnan, tsayawa faɗin haɗuwa da tsaruwar mall ɗinnan 6ata lokaci ne, sai wanda ya gani kawai. Ja ta fara yi da baya tana shirin juyawa ne taji ta bugu da mutum take tayi baya-baya ta faɗi yayin da flowers ɗin hannun ta suka tarwatse. Baki ta saki tare da runtse idanu flowers ɗin na zubo wa kanta. "Sorry" taji an faɗa cikin wata iriyar daddaɗar husky voice kafin kuma ya miƙo mata hannu da niyyar taimaka mata ta tashi. Da kallo tabi farin hannun nasa ba tare da ta miƙa masa nata hannun ba. Yunƙurawa tayi ta tashi tsaye kafin ta fara tattara flowers ɗinta da suka zube ba tare da tabi ta kanshi. Kallo ɗaya ya sake yi mata yana damƙe hannun sa kafin kuma ya juya ya fara tafiya. Ɗan ta6e baki tayi tana cigaba da kwashe flowers ɗinta ta miƙe tsaye. Waige-waige ta fara bata gansa ba hakan yasa ta komawa wurin Reception ta sami wuri ta zauna. "Hey" taji an faɗa ana ɗago mata hannu, wani kyakkyawan saurayi ne fari tass dashi. Murmushi tayi tana miƙewa daga zaunen da takeyi ta nufe shi tare da rungume shi, murmushin shima yayi yana ɗago ta tare da ɗan jan kumatun ta yace "Sorry, i kept you waiting." Turo baki tayi cikin sigar shagwa6a kafin ta saki fuska tace "Happy birthday" tana miƙa masa flower ɗin hannun ta. "Oh thank you" ya faɗa cikin murmushi sosai yana amsa, nan yace "Kin biyo ni nan just to give me this?." Kai ta jinjina masa tace "Yeah, yakamata muje mu sha ice-cream tunda yanzu kam nazo, sabida kullum sai dai kace aiki yana yi maka yawa, dakyar ma mutum zai sami ganin ka wataran balle kuma muyi spending time tare." Kallon flowers ɗin yayi yace "Thanks for the flowers, muje mu sha ice-cream" ya faɗa yana ɗaura hannaye a kafaɗun ta kamar wata ƙawar sa suka fito. Fitowa sukayi daga wurin kafin kuma su nufi wani building ɗin kuma daban, ice-cream suka saya kafin su fito kowannen su na sha suna tafe suna hira cike da Nishaɗi. Baki take shirin kai ice-cream ɗin nan ta sake ji tayi banging mutum ice-cream nata ya karye ya faɗi ƙasa. Da Kallo tabi bayan sa ganin bai koh tsaya bata haƙuri ba, sai ma waya da yakeyi tare da ɗago mata yatsu biyu alamun sorry kuma bai juyo ba. Juyawa tayi ta kalli saurayin nan dake gefen ta tana 6ata fuska nan ya ɗaga mata kafaɗa yace "Muje mu sake yankan wani." Murmushi tayi kafin kuma suje ya sake saya mata wani, cike da farin ciki suka gama sha, sannan sunyi spending time da juna sosai kafin kuma ta tafi.............. ************************* .........Wasu baƙaƙen Mercedes BMW ne wanda aƙalla zasu kai ashirin biye da juna, suna sharara uban gudu akan kwaltar kai kace na gidan uwar su ne koh su kaɗai ne motoci akan hanƴar. Kai tsaye wata ƙatuwar gini wanda da alamu company ne da aka rubuta A&A ENTERPRISES, suka shiga inda kowanne ya samu gurbin parking. Da sauri aka buɗo motar aka fito bodyguards ne guda biyu cikin baƙaƙen suits fuskar nan tasu murtuƙe babu alamun fara'a, ga wani uban black shade da suka manna wa idanun su suka nufi ɗaya daga cikin motocin tare da buɗe ta. Almost 2mins wanda aka buɗewa motar ya ɗauka kafin kuma ya zuro farar ƙafar sa da tasha black shoe companyn GUCCI sai sheƙi takeyi yana sanƴe cikin black suit shima kamar bodyguards ɗinsa, fuskar nan murtuƙe babu alamun fara'a, jacket ɗin kan rigar sa ya gyara yayi gaba, nan duk suka mara masa baya yayin da biyu ke gaba dashi ta gefe da gefe, kowannen su na tafiya kamar zai tashi sama tsabar sauri kasancewar abinda suka ga Uban gidan nasu nayi kenan. Kyakkyawa ne sosai, dogo mai murɗaɗɗen jiki wanda daga gani kasan baya rabuwa da Exercise kullum, dukda fuskar sa babu fara'a hakan bai 6oye irin tsantsar kyawun da Allah yayi masa ba. Buɗe masa glass door ɗin akayi nan suka kutsa kai ciki kafin kuma kai tsaye su nufi wurin lifter inda biyu ne kawai biye dashi sauran kuma suka tsattsaya kowanne na patrol da bindigar sa a hannu. Kai tsaye hawa na goma sha biyu kamar yadda suka danna numbern jikin lifter ɗin ya kai su. Suna isa kuwa ya buɗe suka fito, inda kai tsaye kuma suka nufi ƙofar dake chan ƙarshen haɗaɗɗen corridor ɗin wanda tsaya faɗar tsaruwa da haɗuwar sa 6ata lokaci ne, buɗe masa ƙofa akayi nan ya shige inda kuma ƙatuwar hall ɗin mai ɗauke da wani dogon table da kuma seats ɗin da aƙalla zasu kai talatin kowanne da mutane akai, shigowar sa yasa hall ɗin ɗaukar tsit kafin kuma ya tako zuwa ga babban seat ɗin da yafi kowanne kyau da girma a cikin su inda kuma shine yake a center suna bin sa da kallo har ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin bodyguards ɗinsa su tsaya ta kansa ɗaya a gefen hagu ɗaya a na dama. "You're late ZEEDAN" Cewar ɗaya daga cikin mutanen dake zaune akan table ɗin. Kallon sa wanda aka kira da ZEEDAN yayi kafin kuma ya gyara zaman sa yana fuskantar su kafin kuma ya hau ticking ɗin yatsun sa akan table ɗin, cikin zazzaƙar husky muryar sa yace "Am born to be a king, No one orders me and no one dares to command me except GOD, i can arrive at anytime i wanttt" ya faɗa cikin jan kalmar ƙarshen. Shiru mutumin yayi kafin kuma wani ya kar6i maganar da cewa "Let's get back to business then, as we all know My company is falling apart, i mean we are going bankrupt wannan ne dalilin da yasa nake neman taimakon ku kan ku taimaka kuyi investing a Company na domin farfaɗo dashi daga faɗawa halaka." "Am not investing, but i can buy the company idan kaso" cewar wani daga cikin su. "Yes, i don't think i can invest too, but if you're ready to sell the company out, zan iya saya" cewar wata daga cikin su. Nan duk kowa ya fara kawo nasa ƙorafin akan ba zaiyi investing ba sai dai ya saya. "Alright, alright am ready to sell it out, nawa zaku saya?." Wata ce ta fara cewa "100million." "150million" cewar wani. "180million." "200million." "210million." Haka kowa yayi ta faɗar kuɗin da zai saya wani yana ƙara yawan kuɗin akai duk dan su samu ya sayar musu da company ɗin. "210million shikenan kuma babu mai ƙarawa akai?" cewar mai son sayar da company ɗin. "1billion" suka jiyo ya faɗi hakan cikin calm voice ɗin sa, nan duk suka maida duban su gare shi, nan ɗaya yayi wuff yace "3billion." Nan kuma kowa ya sake gyara zaman shi dan ganin ƙarshen karawa tsakanin wadannan biyu da basa son raini musamman wurin harkar business inda za'a sai da wani abu kowannen su burin sa shine ace ya fitar da kuɗi dayawa, shiyasa da yawa ke son gayyatar su su biyu aduk sadda suka tashi saida wata babbar kadara tasu. "5billion" ya faɗa. Nan wannan ɗin kuma ya sake cewa "10billion." Murmushin gefen baki ZEEDAN yayi dan kuwa ya riga da ya gama gano gayen nan, nan yace "100billion" yana matse fuska. "200billion" wannan ɗinnan ya sake faɗa. "400billion" ZEEDAN ɗin ya sake faɗa. Shiru wannan ɗin yayi dan kuwa ba zai iya ƙara wani abu a saman 400billion ɗinnan ba. "Da akwai wanda zai iya ƙara wani abu a kai?" cewar mai son saida companyn. Shiru meeting hall ɗin ya ɗauka hakan yasa shi juyawa ga ZEEDAN tare da yin murmushin farin ciki dan kuwa yasan ba ƙaramar riba yaci ba yace "Sold." Murmushin gefen baki yayi yana kallon ɗayan nan, kafin kuma ya miƙa hannu wa bodyguards ɗinsa, nan suka ciro cheque da biro suna miƙa masa. "The Documents?" ya faɗa yana kallon wanda ya saida masa company ɗin. Da sauri ya ciro wasu takardu yana turawa gaban ZEEDAN. Ɗauka yayi ya fara bi yana karantawa kafin kuma ya kalle sa yace "Many has regret selling their company off to me, i hope you won't fall a victim?." Shiru mutumin yayi yana kallon sauran ƴan hole ɗin kafin kuma yace "What do you mean?." "I mean dayawa sunyi nadamar sayar min da Company ɗinsu, ina fatan ba zaka zamto ɗaya daga cikin su ba, do you know why?, that is because zan iya farfaɗo da company ɗinda yayi shekaru goma a mace in just 3months, ina fatan ba zakayi fushi ba idan kaga yadda Companyn ka zai dawo nan da watanni uku?." "Hahaha..mai kake faɗa ne haka ZEEDAN?, just sign the papers." Murmushi yayi ya sanƴa hannu yayi signing, inda shima mutumin yayi signing kafin ya rubuta masa cheque ɗinsa ya basa. Bodyguards ɗinsa ya miƙawa Documents ɗin nan suka amsa kafin ya miƙe tare da ɗaga musu hannu yana barin cikin hall ɗin............ ******************** ............Tsaye take a jikin window ɗin ɗakin ta tana kallon waje fuskar nan nata babu wata walwala tattare da ita. Buɗo ƙofar ɗakin akayi akace "MADEENAH?." Da sauri ta juya ga Umma kafin kuma cikin sanƴi tace "Na'am." "Fito" ta faɗa tana komawa, nan ta fice itama tana binta zuwa falon ƙasa. "Tunda kince ba zaki bar tunanin wanda baki ma san duniyar da yake ba zan tura ki gidan Mami kije kiyi mata sati biyu ki dawo koh nima na huta da wannan halin ƙuncin naki da kullum kike ciki babu walwala." Ɗan 6ata fuska tayi tace "Umma gajiya kikayi dani?." "Tayaya kuma zan gaji dake?, na dai gaji da halin ki ne." "Umma amma ai rashin yaya a kusa ne yasa bana walwala." "Ba wanin nan, mutumin dake kwana a gidan nan ya tashi a gidan nan ne ɗin kike cewa dan bakya ganin sa ne, maza tashi ki tafi kinga sai kira na take tunɗazu koh kin taho." Miƙewa kawai tayi ta haura ɗakin ta, kafin kuma ta haɗa kayan ta cikin ɗan madaidaicin akwati wanda ya kasance duk baƙaƙe ne kuma dogin riga Arabian wears da dai English wears masu kyau da musulmi zai iya sanƴawa ya fita, sannan tayi rolling kanta da gyalen kayan jikin ta, lip balm kawai ta shafa a pink lips ɗinta, sosai tayi kyau nan taja akwatin ta ta sauƙo. Umma ta tarar a falo nan tace "Umma na shirya ke zaki kai ni koh?, dan kinsan yaya baya nan." "Kin ganni nan yadda na zauna anan da wadannan takardun a gaba na, toh babu inda zan motsa har sai na kammala abinda nakeyi, dama wa ya hana ki koyan motar?." "Haba Umma ta, ni sam banason wannan aikin naki kullum cikin stress." "Sai kizo ki sa ni ajiye shi ai, zaki tashi ki tafi ne kokuwa?." Murmushi tayi tana miƙewa tsaye ta ja Akwatin ta tana faɗin "Toh Umma sai na dawo." "A dawo lafiya ki gaida min dasu." "Insha Allah" ta faɗa tana ficewa daga cikin falon......... ************* ......."Ughhh, am extremely tired and fed up with this fucking life, when ZEEYAD, when zaka bayyana ne?" ya faɗa kamar zaiyi hauka yana zagaye cikin gidan nasu tare da yin wurgi da duk wani abu da ya gani a hanƴar sa. "Sooraj ana neman ka a waje?" cewar wani dogare yana idda shigowa cikin gidan nasu. "You son of a bitch!" ya faɗa yana shaƙo wannan dogarin ya hau jibgar sa. Ihu da ƙururuwar neman taimako wannan dogari ya fara dan kuwa ba ƙaramar shaƙa Sooraj da ya murɗe ya zama ƙato yayi masa ba. "How dare you, har yaushe aka haife ka, yaushe ka girma da zaka dinga yi min magana garangatsai haka babu respect, sai na tabbatar na gyara muku zama dukkanin ku ɗaya bayan ɗaya, move your fucking legs out of here" ya faɗa yana yin ball dashi, kafin kuma ya biyo bayan sa ya fito a fusace dan ganin wane banzan ne ke neman sa. Sadeeq ya gani tsaye cikin shigar sa ta alfarma, nan yace "This Asshole, naji labarin ance ya zama likita, yana ɗan talakawa but look at me, nida na riga sa fara makarantar wai yau shine ya zama wani, koh mai yazo yi a wuri na?" ya faɗa yana ƙarasawa gaban Sadeeq ɗin ya tsaya. Nan yace "Kai ne kake nema na, mai ya kawo ka toh, bayan kai ba aboki na bane." Murmushi Sadeeq da ya zama Handsome guy kamar ka ɗauke shi ka gudu yayi yace "No, bakomai nazo ne kawai na tunatar maka da cewa a yau ZEEYAD ya cika shekaru goma da 6ata, sannan kuma har yanzu ba'a san inda yake ba koh labarin sa babu, sannan kuma na tunatar maka da cewa kaima ka kusa yin shekaru goma a wannan wuri, nazo ne na tunatar maka in case idan ka manta kokuma kanason throwing party shine nazo na tunatar maka idan ka tashi shirya liyafar kada ka manta da gayyata ta a matsayi na na aminini ga ZEEYAD." Sosai Sooraj ke huci kamar ya haɗiyi bishiya yace, dan kuwa dama Sadeeq yazo ya ɗura masa baƙin ciki ne kuma yayi nasara. "Kai har waye kai, kai har ka isa kazo nan gaba na ka faɗamin maganar banza?" ya faɗa kamar ya buge Sadeeq ɗin yana kukan kura. "Ni ba kowa bane, sai dai inaso ka sani a yanzu ni na fika nesa ba kusa ba, then just imagine a wane matsayi ZEEYAD yake yanzu indai har ni na kai wannan matsayin." "Noooooooooo" ya faɗa cikin ihu kafin yace "Ƙarya kake ɗan matsiyata, ZEEYAD ba zai ta6a zama wani ba bai isa ya kai wannan matsayin ba, dan kuwa na tabbata har yanzu takalmin ƙafa ta ta fisa daraja, idan ya isa ya dawo nan indai har ya zama wani abu, maganar banza ma kake faɗi dan kuwa ZEEYAD ya daɗe da mutuwa." Murmushi Sadeeq yayi dan dama abinda yakeso kenan, ya ɗurawa Sooraj baƙin ciki kuma yayi nasara, nan yace "Kana ganin ba zai dawo bane?, kada ka damu tunda har ka iya haƙurin shekaru goma kana jiran dawowar sa ai kamar yau ne zakaga ya dawo, what's the haste for?, anyways ni nan bari naje na duba jikin mai Martaba, dama nazo na duba ka ne kawai naga ya kake, and yes kada ka manta ZEEYAD ya cika shekaru goma yau incase kanason haɗa liyafa" yana faɗin haka yayi murmushi ya wuce. Sosai Sooraj ke huci idanun sa sunyi matuƙar yin jaa, fuskar nan a cunkushe yana fitar da wata iriyar huci yace "Koh da abinda wannan wawan ya faɗa ya tabbata dagaske ne, toh na rantse ZEEYAD ni ne ajalin ka."................. _*MUJE ZUWA......YANZU WASAN ZAI FARA😅*_ *Ba kwa comment koh?😩, Allah zanyi fushi ba zan sake typing ba sai bayan 2weeks😒* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* _Masha Allah Readers sun roƙeni alfarmar na dinga yi musu post sau biyu a rana😃, insha Allah zan ƙoƙarta sai dai banyi muku alƙawarin zaku dinga samun pages biyu kullum a rana ba, haƙiƙa kun matuƙar nuna min Ƙauna a wannan littafi na ZEEYAD dan haka nima dole na faranta muku, Allah Ubangiji ya bar Ƙauna tsakanin mu, yayi wa rayuwar albarka🥰❤️ , Ku dinga suburbuɗo min zafafan comments nikuma na cigaba da suburbuɗo muku post ɗin 2pages kullum Non-stoppable💃🏽🤘🏼😂_ *014...* ..............Da sallama ɗauke a bakin ta ta ƙarasa shigowa babban falon gidan, sai dai babu kowa a ciki. Wuri ta samu ta zauna tana ajiye akwatin ta a gefen ta. Ji tayi an rufe mata ido ta baya, murmushi ta saki tana kai hannu ta ta6a na wanda ya rufe mata fuskar. "Wanene" ta faɗa cikin sweet calm voice ɗin ta. Shiru akayi ba'a bata amsa ba nan ta sake cewa "Please wanene?." "Yeeehhhh, nice bata gane ni ba" faɗin budurwar da ba zata wuci sa'ar MADEENAH ba tana buga tsalle, kafin tazo ta rungumo ta tace "You're welcome sis, yau dai gaki nan a gidan mu yin hutu, amma mu kullum sai dai muje ke bakya zuwa." Murmushi tayi tace "Ina zuwa mana, ba gani nazo ba yanzu." "Ba wani nan, ai nasan ba yin kanki bane, Anty ce ta tilasta ki." "Shikenan toh tunda baki yarda ba" ta faɗa to cut the conversation short, dan kuwa sam batason surutu da yawan magana, ga kuma ƴan matan gidan nan ɗin ba dai surutun tsiya ba, shiyasa sam batason zuwa, tafison rayuwa ita kaɗai kawai tayi ta tunanin sa. "Ku jita wai ita a dole batason surutu." "Ina Mami fah?." "Mami ta fita ungwa, zo muje na kai miki akwatin naki ciki" ta faɗa tana miƙewa tsaye ta kamo hannun MADEENAH. Babu musu ta tashi ta bita zuwa ɗakin nasu. Kayan akwatin ta ta jere mata a cikin ƙaton wardrobe ɗin ɗakin kafin ta ɗaura akwatin a sama. Wata budurwa ce ta fito daga Bathroom da alamu wanka tayi ta fito, ganin MADEENAH yasa ta daka tsalle cike da farin ciki tana rungume ta tace "Yau wa nake gani a gidan mu, kodai mafarki nakeyi ne" ta faɗa tana murza idanun ta. "Wace kuwa idan ba DEENAH ba" cewar ɗayan. "Amma tare suka zo da Anty koh?." "Ita kaɗai, bakiga harda akwatin ta ba." "Dan Allah kice kwana zamuyi?." "2weeks Umma tace nayi muku na komo" ta faɗa tana kallon su cikin murmushi. "Kai sis 2weeks, sai kace nan ɗin ba gida ba?." "Ke bakisan MADEENAH da baƙin hali ba kenan, sam batason shiga mutane, kullum tafison ke6ewa ita kaɗai, tayi ta rubuta emotional waƙoƙin ta n da ta saba, ni dan Allah ɗan rera min ɗaya ma naji daga ciki" ta faɗa tana zama kusada ita. Murmushi tayi tace "Ni ki rabu dani dan Allah, ba zanyi ba" ta faɗa tana sunce rolling ɗin kanta. Shafa dogon gashin kanta ɗayar tayi tace "Kekam DEENAH yaushe ne zaki fara kitso a rayuwar ki?." "Ke ki rabu da ita taga gashin baya zubewa ne shiyasa take iskanci, ni da nawa ya fara ƙwaiƙwayewa ta ƙeya ai tuni na nemi gidan kitso." Haka nan suka cigaba da hirar su DEENAH bata tanka musu ba, sai ma ficewa kawai da tayi ta bar musu ɗakin................. ******************** ...............Zaune yake cikin ash color ɗin sport wears wanda suka bayyanar da fararen murɗaɗɗun muscles ɗinsa, wanda da alama bai daɗe da idda motsa jiki ba, fuskar nan tasa manne da baƙar shade, inda hannun sa ke riƙe da mug ɗin coffee kafafun sa kan table ɗin gaban sa yana sipping a hankali. Yatsun hannun sa na hagu ya fara tausawa a hankali suna bada ƙara kan kuma ya duba rolex watch ɗin dake manne a wrist ɗinsa yana duba time. 9:00am yake da meeting and yanzu bakwai ta ɗan wuce, hakan yasa shi ajiye mug ɗin hannun sa yana tashi tsaye tare da zura hannayen sa cikin aljihun wandon sa yana tafiya cike da muguwar ƙasaita. Fresh korayen shukoki ne zagaye da wurin kala daban-daban inda sukayi mugun ƙawata wurin sosai. Tsaya faɗin haɗuwa dama kuma tsaruwa irin na wannan gida 6ata lokaci ne, dan kuwa haka take mansion guda wanda daga gani ba ƙaramin kuɗi aka zuba mata ba. Cikin katafaren falon ya shigo kafin kuma ya nufi left handside ɗinsa ya haura stairs. A bakin ƙofar wani ɗaki ya ja ya tsaya kafin kuma ya tura ta ya shiga, ɗakin akwai duhu sai dai ba sosai ba tunda ana iya ganin abubuwan dake ciki. Wasu abubuwa ne kamar standing boards haka suke a tsaye kowanne rufe da farar kyalle, wanda aƙalla zasu kai ashirin koh sama da hakan. Tsayawa yayi yana bin kowanne da kallo kafin kuma idanun sa su faɗa kan ɗaya dake ta hannun damar sa. A hankali ya taka zuwa wurin kafin kuma ya sanƴa hannu ya yaye farin kyallen dake rufe dashi, take kuma kyakkyawar hoton ta ya bayyana fuskar ta ɗauke da murmushi. Sai dai shi wannan ba zaka ta6a ce masa zane bane sabida yadda fuskar ta ta fito sosai, kamar ita aka ɗauko aka manna jikin board ɗin. Yatsar sa ya kai yana shafar dimple ɗin ha6ar ta trying to get rid of all the old memories da suka riga da suka wuce. "Atleast yakamata yau ka faɗamin wacece yarinƴar nan dama kuma matsayin ta a wurin ka" ya jiyo an faɗi hakan ta bayan sa. Sosai fuskar sa ya sake tamƙe ta jin muryar ta, nan ya juyo gareta yace "What are you doing here?." Kyakkyawar budurwa ce fara wanda daga gani kasan hutu da Naira sun zauna mata. Murmushi tayi tana ƙarasowa wurin sa tace "Ni ɗin, har sai na nemi izinin shigowa cikin gidan ka kenan?, we are in a relationship so zan iya shigowa cikin gidan nan duk sadda naga dama." Juyawa yayi tare da ɗaukar farar kyallen yana shirin rufe hoton ne ta sake faɗin "Yakamata yau ka faɗamin wacece yarinƴar nan, sannan kuma maiyasa kake son zana ta a duk sadda kake zaune?." "That is non of your business." "Really, but why dama baikamata ace nasan komai game da kai bane?." "Bakisan komai game dani ba Surayya, so just ki tsaya a matsayin ki." "What do you mean, a matsayi na ta budurwar ka dama baikamata nasan komai bane?." Shiru yayi ya rufe hoton ya fice daga ɗakin ya bar ta nan tsaye. Mara masa baya tayi zuwa cikin tafkeken falon tare da kiran sunan sa "ZEEDAN?." Tsayawa yayi nan ta ƙaraso gaban sa tace "Maiyasa kakeyi min haka ne duk sadda nayimaka maganar yarinƴar nan sai ka 6ata rai ka kama fushi dani?." "Sabida babu ruwanki da sanin koh wacece ita, she mean nothing to me, Infact i hate her, so Stop disturbing your Peace and asking to know who she is, hakan ba zai amfane ki da komai ba." "You hate her, but why?, she is such a cutie" ta faɗa cikin ɗan murmushi. "That's non of your business" ya faɗa yana ra6a ta ya wuce. Saurin shan gaban sa tayi, nan yace "What again?." "Please yau ɗaya dai kam kazo mu fita shaƙatawa, it's been long da ka ɗauke ni muka fita, why are you behaving as if baka sona yanzu?" ta faɗa kamar wacce zatayi kuka. "Don't say that, you know i love you and dan bamu fita tare ba that doesn't mean kiyi irin tunanin nan." "Alright then, ka faɗamin yaushe ne zamu fita tare?." Shiru yayi kafin kuma yace "On Sunday Evening." "Wow that would surely be a great outing" ta faɗa tana rungume shi, da sauri ya janƴe ta daga jikin shi kafin ya wuce ya haura sama. Da kallo ta bishi kafin tayi blowing masa kiss tana murmushi........... ********** ...........Zaune yake a katafariyar offishin nasa yana rubuce-rubuce a jikin wasu papers. Turo ƙofar akayi kawai aka shigo kafin ya sami wuri ya zauna fuskar sa ɗauke da murmushi yana kallon ZEEDAN. "Good Morning Sir" ya faɗa. "Morning Mansoor, ka tashi lafiya?." "Alhamdulillah Sir." Sai a sannan ya ɗago ya kalle shi yace "Naji labarin ance zakayi aure, Congratulations." Cike da farin ciki ya amsa da "Thank you sir, ai yanzu ma Invitation Card ɗina na kawo maka, nan da 2weeks ne auren, shine nakeso dan Allah kayi attending sir" ya faɗa cike da girmamawa yana miƙa masa Card ɗin. Amsa yayi ya shiga karantawa nan ya ɗago yace "You're my MANAGER, so ba sai ka roƙe ni zuwa auren ka ba, i will surely attend it, although last week na dawo daga Sokoto, but don't mind Okay?." "Nagode sosai sir, Allah ya ƙara buɗi." "Aameen" ya amsa. "And sir idan ba zaka damu ba ranar ɗaurin auren akwai Dinner party da dare, i hope ba zaka ƙi amsa gayyatar zuwa ba." Murmushi yayi kafin yace "Kaima kasan ban cika attending Party ba, but i will surely attend tunda ka buƙaci hakan." "Thank you so much sir, Nagode sosai da amsa gayyata." "You're welcome, Saura one month mu fara ɗaukar sabbin workers, hope you're working on that?." "Yes sir, ai mun rigada mun kusa kammala komai ma." "Alright, idan ka fita ka turomin Secretary." "Yes sir, thank you sir" ya faɗa yana ficewa daga office ɗin. Ba'a jima ba Secretary ya shigo tare da gaida shi cike da girmamawa, nan ya buƙaci a kawo masa breakfast kafin ya amsa da toh yana ficewa. 10mins mai kyau bai ɗauka ba ya dawo hannun sa ɗauke da ɗan madaidaicin tray da breakfast akai. Wuraren couch ɗin da aka ware a gefe kamar falo a cikin office ɗin ya nufa ya ajiye akan Table kafin ya fice. Kammala abubuwan da yake yi yayi kafin ya taso yazo ya zauna tare da haɗa Black tea ya sha, sannan ya buɗe plate ɗin abincin tare da yin basmala ya hau ci. Tunanin ta ne ya faɗo masa kwakwalwa lokacin da take kawo masa lunch box ɗinta a matsayin breakfast ɗinsa yaƙi ci, kafin kuma yayi saurin kauda wannan tunanin yana tuno da sharrin da tayi masa. Rufe plate ɗin yayi ya koma kan chair ɗinsa tare da danna wani abu kamar Alarm. Ba'a jima ba Secretary ya shigo nan ya umurce sa da ya kwashe breakfast ɗin, ba tare da musu ba yaje ya ɗau tray ɗin ya fice yana mamakin mai ya 6atawa Uban gidan nasa rai da sassafen nan ganin 6acin rai ɗauke a fuskar sa............ *************** ..........."2Weeks to bikin Ruqayyah kuma har yanzu bamuyi anko ba Wayyo ni Khadija" ta faɗa kamar wacce zata yi kuka. "Kema Anty Khadija in banda abinki fisabillah ga Abba nan kije mana ki kar6a a wurin sa kin zo kina ta tada hankalin ki kawai." "Hmm ba zaki gane bane Amirah, kin manta last 2Weeks akayi bikin wata ƙawar mu kuma na kar6i kuɗin fitar biki almost 70k, yanzu kuma ki sake cewa na koma na kar6o wani kuɗin a wurin sa dan kawai banida tausayi?." "Toh ai yana dashi dah kamar bashida shi ne zakiyi shakkar zuwa ki tambaye sa, amma dama dan su waye yake neman kuɗin ba dan mu bane, sabida kar muga wani abin a wani wuri muji muna so kuma ace ya kasa yi mana shi, balle kuma shi da bakin sa yace duk wacce take da buƙata ta faɗa masa zai biya mata indai bai fi ƙarfin sa ba, toh miye a ciki dan kinje kin tambaye sa kuɗin anko?." "Toh please kije min dan Allah kice ankon ƙawarki ne ki samo min kuɗin,kinji ƴar ƙanwata?." "Cha6 Allah ba zani ba, ba kece kike da buƙata ba dan haka kije ki wallahi." "Haba Masoyiya ta..." "Nikam wallahi ba zakiyi min daɗi baki ba, dan babu inda zani." Sai a sannan ta ɗago ta kallesu daga karatun da takeyi, sabida sun cika ta da surutu. Tashi tayi kawai ta fice daga ɗakin inda suka bita da kallo kafin Khadija tace "Nikam ina mamakin halin DEENAH." "Nima dai haka, koh meke damunta, na tambayi Yaya Jafar yace wai haka nature ɗinta yake." "But she looks disturbed from the inside." "Maybe she was heartbroken." "Heartbroken?, no it can't be that, ban fah ta6a ganin ta da Saurayi ba, maybe gaskiya Jafar ya faɗa haka take Naturally." "Kinsan maiyasa na faɗi haka, coz i caught her crying last night na tambaye ta tace min babu komai and she left, bakya tunanin maybe saurayi ne ya yaudare ta." "Really?, but wane asararre ne zaiyi dumping DEENAH?, she is beautiful and gorgeous , and so calm also ta haɗu ne ta koh ina, she is classy and total definition of a wife material, she doesn't deserved it." "And she is kind also, ita dai matsalar ta shine she is always moody and sannan batason yawan shiga mutane da surutu, she feels safe and comfortable when she is alone, i guess." "Inaso muje bikin Ruqayyah da ita, kina tunanin zata yarda ta bi ni muje?." "Cha6, bikin friends nata ma yaushe taje, bale kuma azo ga na wata Ruƙayyah, but maybe you should try asking her koh zata yarda." "Idan ma bata yarda ba, zan sa Mami koh Anty suyi forcing nata." "Why zakiyi forcing nata?, inaga dai idan tace ba zata je ba, you shouldn't have to force her." "Allah ya kaimu kawai, bari dai naje wurin Abba haka nan, ace bikin best friend ɗinka bakayi komai ba ai da matuƙar kunƴa ban isa ba" ta faɗa tare da ɗaukar Hijab ɗinta ta fice daga ɗakin.......... ****************** .........Kwance take tayi matashi cinƴar wata mata mai kama da Umma sak sai dai Umma ta fita farin fata. DEENAH ce tace "Mami maiyasa har yanzu zuciya ta ta kasa samun sukuni tun ranar da abin nan ya faru?, ina tsoron kada na mutu ba tare da na nemi yafiyar sa ba, Mami yace ba zai ta6a yafemin ba kuma ya tsane ni, shekara goma fah kenan amma har yau ban sake ganin sa ba, what if yayi nisa dani ba zan sake ganin sa ba har abada" ta faɗa tana tashi zaune hawaye na biyo mata fuska. Cike da tausayin ta Mami ta shiga share mata hawayen tace "MADEENAH a lokacin da abin nan ya faru kina ƴar ƙaramar ki ne, baikamata ace har yanzu abin nan na damunki kin kasa mantawa dashi ba, you have to let go of all your sorrows and move on with your life, you have to live happy koh da na rana ɗaya ne, stop disturbing your Peace kina ɗaurawa kanki damuwar da bakisan ranar yankewar ta ba, am definitely sure shi ya ma mance da abinda ya faru kuma ya manta dake, but i can't believe ke har yanzu abin nan na ranki." "Mami ya manta ni fah kika ce?." "MADEENAH, zai iya yiwuwa mana, shekaru goma fah ba wasa bane, abubuwa dayawa su kan iya faruwa cikin shekaru goma wanda Allah ne kaɗai yasan dasu, but inaso ki sa a ranki cewar koh ba daɗe koh ba jima indai har Allah yace kina da rabon sake ganin sa toh tabbas zaki ganshi, sai dai fah zakiyi haƙuri ne kawai da wannan jarabawa, gashi kuma koh sunan sa fah baki sani ba, amma kin sa shi a ranki har yau kin kasa cire shi, you've to move on MADEENAH." "Mami i can't, i can't move on happily indai har ban sake ganin sa ba, how do you expect me to be happy bayan akwai haƙƙin wani a kaina, indai har bai yafemin ba then i would never be happy har ƙarshen rayuwa ta." Share mata hawaye Mami tayi tana rungumo ta jikin ta tana rarrashi............... *MHIZZ JIDDHERR............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *015...* ............Khadija ce zaune a gaban mirror sai tsarawa kanta kwalliya take, kasancewar ta make-up artist, sosai tayi kyau kasancewar dama kyakkyawar ce ita. Kallon DEENAH da ta fito daga wanka tayi tace "Sai yanzu kike fitowa daga wankan?, zaki sani latti wallahi." Zama DEENAH tayi kafin tace "Anty Khadija ni nace miki ba zanje ba kije abin ki dan Allah." "Haba rabin zuciya ta, ya zakiyi min haka fisabilillah?, ni shigar da kikayi wanka ma i thought koh zakije ne, na tsaya zaman jirar ki." Shiru DEENAH tayi bata kula ta ba sai ma lotion ɗin da ta ɗauka gaban mirror ta shiga shafawa, nan Khadija ta sake faɗin "Naji yau ba zakije kamu ba, amma ai gobe zamuje ɗaurin auren koh?." Kallon ta tayi kafin tace "Dan Allah Anty Khadija ki bar ni" ta faɗa kamar zatayi kuka. Shiru Khadija tayi ta cigaba da ɗaurawa kanta ɗan kwali, nan ya zauna tayi kyau sosai sannan tace "Wallahi Aliyu ba zai kalli kwalliyar nan a banza ba tunda ba shi ya bani kuɗin sayen kaya da kayan kwalliya ba har sai ya biya." Murmushi DEENAH tayi kawai, kafin ta nufi wardrobe ta ɗauko kayan sawar ta ta rufe. Tashi Anty Khadija tayi tare da ɗaukar gyalen ta ta yafa da jakar ta tace "Toh ni na tafi, sai na dawo." "A dawo lafiya" DEENAH ta faɗa. Sanƴa kayan ta tayi wanda yayi mata kyau sosai kasancewar straight gown ne English wear yasa shi ɗan kama jikin ta inda ya fito mata da shape ɗin hips ɗinta wanda yayi daidai da yanayin jikin ta, dan kuwa batada ƙiba kuma ba siririya bace har chan. Wani drawer ta buɗe ta ciro English novel, kafin ta haura kan bed ta zauna tare da buɗe sa. Sarƙar ta gani a cikin Book ɗin sai sheƙi yakeyi. Ɗauka tayi tana ƙare masa kallo, kafin ta buɗe abin dake jikin sarƙar hoton kyakkyawar matar ya bayyana. _"She must be his Mom, i have ruined his entire Happiness, nayi masa sharri sannan kuma na raba sa da abu mafi muhimmanci a gareshi, i know he would never forgive me for hurting him, he trusted me but i fucked off"_ ta faɗa a zuciyar ta tana manna sarƙar a ƙirjin ta. "Hey, what's that?" cewar Amirah tana hawowa kan bed ɗin kusada DEENAH. Hawaye fuskar ta ta lakuto tace "You're crying again, what on earth is wrong with you?" ta faɗa cike da damuwa. DEENAH goge hawayen da batasan sun zubo mata ba tayi kafin tace "I..i bansan sadda hawayen suka zubomin ba, am not crying." "Uhm i can see that, please sis tell me, meke damunki you always looked disturbed." Rufe takardar tayi tace "Nothing, am fine." "What is that Necklace?" ta faɗa tana kallon sarƙar dake hannun DEENAH. "It's nothing" ta faɗa tana damƙewa a hannun ta kafin ta tashi ta nufi wardrobe ta buɗe tare da ɗaukar wata ƴar ƙaramar jaka ta sanƴa shi a ciki. "You're hiding something from me." "Amirah babu abinda nake 6oye miki, i have nothing to hide OK, so just let me be please" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Kitchen tayi ta sha Kuka sosai kamar ranta zai fita kafin kuma ta fito ta koma ɗakin. Akwatin ta ta sauƙar ta fara shirin haɗa kayayyakin ta a ciki. "Wait, what are you doing?." "Am leaving, dama ai sati biyu Umma tace nayi na dawo." "What, are you kidding me?, you can't go anywhere, wallahi zan kira miki Mami." Tsayawa tayi da haɗa kayayyakin nata kafin kuma ta fashe da kuka tana zama bakin bed ɗin. Sosai hankalin Amirah ya tashi nan ta nufe ta tare da tambayar ta abinda ya same ta. Ganin taƙi kulata ne yasa ta fita taje ta kirawo Mami. Rarrashin duniyar nan Mami tayi wa DEENAH amma kamar sake zugata take ta cigaba da kukan. "Mami i hate myself, dan Allah Mami ku nemo min shi duk inda ya shiga, mutuwa zanyi idan ban sake ganin sa na bashi haƙuri ba, dan Allah Mami ku taimaka min kada na mutu Allah ya hukunta ni" ta faɗa cikin shesheƙa kamar zata shiɗe. Haƙuri kawai Mami ke bata cike da tausayin ta. "Mami rayuwa ta baya yimin daɗi, banajin daɗin rayuwa a haka Mami, dan Allah ku bar ni naje na nemo shi idan ku ba zakuje ba, am so bored Mami komai ya daina yimin daɗi, na gaji da zama cikin damuwa da ƙunci kullum, nayi dukkanin ƙoƙari na ganin na kasance cikin farin ciki koh da na awa ɗaya ne amma na kasa, dan Allah Mami ki faɗamin maiyasa hakan ya faru dani?" ta faɗa tana kamo hannun Mami ɗin. Rarrashin ta Mami tayi sosai tare da yi mata wa'azi kafin ta samu DEENAH tayi shiru. Amirah kuwa duk hankalin ta ya tashi kuma kanta ya ɗaure dan batasan abinda ke faruwa ba. A haka ta raya wunin wannan ranar cikin ƙunci da rashin walwala kamar kullum............ *********************** ...........Agogon hannun sa yake dubawa time to time yana kaɗa ƙafafu. Ba'a jima ba ta shigo ɗauke da wata ƴar ƙaramar akwati tana jan shi. Ƙarasowa tayi tana murmushi sakamakon kallon da yake binta dashi nan tace "Am so sorry babe, i kept you waiting bayan nasan tafiya zakayi" ta faɗa tana zama cikin ɗaya daga cikin cushions ɗin falon. "Are you travelling somewhere?" ya tambaya cike da mamaki yana kallon akwatin nata. Kallon akwatin tayi tace "Oh Yeah, ba tare zamu ba?, i can keep you accompany all day long sabida kaɗaici." "Are you kidding me?." "What do you mean?" ta faɗa cikin ɗan dariya. "Do you think this is funny?, am not going anywhere with you." "Oh come on calm down, ba bin ka zanyi ba, nima biki zani Sokoto shiyasa na biyo ta wurin ka muje tare since kai ma nan zaka." "No ba zaki bini ba, i don't hang around with indecent girls like you" ya faɗa cikin ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kana tsuke fuska. "What, what do you mean, are you trying to insult me?." "Look Surayya, sai dai ki bi wani ku tafi amma ba ni ba, a hakan kike tunanin zan aure ki?, you're not decent at all, just take a look at yourself and the way you dress...." "Enough of this ZEEDAN" ta faɗa a ƙufule tana miƙewa tsaye kafin kuma ta ɗaura da faɗin "Ai ba sai ka ci min mutunci ba, ai dama na daɗe da gano sam ba so na kake ba..." "Then kuma sabida kwakwalwar kifi ne dake kika kasa rabuwa dani tuntuni bayan kin daɗe da sanin hakan?, don't you dare raise your voice at me, i respect you sabida ke macece, i guess lokaci yayi da zakije kiyi aure ki daina 6atawa kanki lokaci a kaina, ni dake sam bamu dace ba, hali na da naki sun sha bambam infact koh kaɗan bakida tsarin irin macen da nake burin rayuwa da ita, your life is totally disgusting." "What, you can't do this to me ." "And why shouldn't i?, kece kika kawo kanki da kanki gareni ba ni na shigo dake cikin rayuwa ta ba, you proposed to me and i couldn't deny or disappoint you infront of your friends, da farko i thought you would be good for me but then i realized that i made a great mistake for allowing you into my life." "Kana nufin ka daina sona kenan?" ta faɗa kamar zatayi kuka tana matsowa kusada shi. "I never loved you, banta6a sonki ba sannan kuma ba zan ta6a son naki ba" ya ƙarashe cikin ɗaure fuska yana kallon ta. "And you keep Playing me all this while?." "That is because ke kika takura min, koh kin manta ne kece kika ce kina sona ba ni ba?." "Amma maiyasa kaƙi sanar dani hakan tuntuni sai yanzu, idan halaye na ne baka so, i promise to change for good just please don't leave me i beg you." "Yanzu na faɗa miki, it's not late though we've been together for 5months and banga amfanin ki cikin rayuwa ta ba, i only keep valuable things in my life not people like you." Kuka ta fashe dashi, nan ya fice ya bar ta nan tsaye, sai da tayi mai isar ta kafin ta tsagaita tace "Why is he ignoring me all of a sudden, kodai yayi wata sabuwar budurwar ne?, he can't do this to me." "Ma'am yallabai yace idan kin gama ki fice zamu rufe ƙofar" cewar wani bodyguard ta bayan ta fuskar nan tasa a murtuƙe. Jan akwatin ta tayi cike da haushi ta fice tana faɗin "Sai muga ta yadda zai fitar dani daga rayuwar tasa ai.".......... *********************** ...........Yau Saturday sannan kuma yau ne ɗaurin auren ƙawar Anty Khadija, sai shirye-shirye suke ita da ƙawayen ta da suka zo dan tayi musu kwalliya. Ɗaya ce tace "Please Khadija ki gwangwaje ni a party ɗinnan nafi kowa kyau, i can't believe wai that Famous rich and Handsome artist will be there." "Ke kam dai Aisha kinji kunƴa da shegen son samari wallahi mtssww" cewar ɗaya daga cikin ƙawayen. Ɗaya ce tace "Ke kinga laifin ta ne, kika san wani ikon Allah idan ya ganta yace yana so, ai koh nima wallahi gwangwaje ni za'a yi shiyasa ma musamman naje aka sake yimin wani ɗinkin kece raini ɗin." "Toh gaskiya dai kunji jiki wallahi, wannan guy ɗin ma mai zaiyi daku?, wallahi koh kaɗan ku ba ajin sa bane kuna tafiya kamar iska ya ɗebe ku ɗin, musamman ma da naji shegen girman kan tsiya garesa." "Wallahi dai kema kya faɗa musu, naji ance balarabe ne fah koh?" cewar Anty Khadija. "Aa nikuma kamar ji nayi ance ɗan Nigeria ne, sai dai koh half-cast ne shi." "Kai anƴa?, toh dai ba zanyi musu ba tunda ba ganin sa mukayi zahiri ba, but the guy is damn hot and Handsome wallahi, i can't wait to set my eyes on him, messages ɗina sun fi dubu a dm ɗinsa na Instagram but he isn't replying koh buɗewa baya yi" cewar ta farkon cike da damuwa. Dariya duk sauran suka kwashe dashi nan ɗaya tace "Wallahi Aisha kinji jiki, yoh angayamiki ma shine tukun, yanzu idan kika bibiya kawai Boys ɗinsa ne masu using da account ɗin ba shi ba, amma kenan tsabar aiki bai ishe ki ba kullum bakya gajiya da commenting akan posts ɗinsa kamar wata mayya." "Wallahi kuwa shi ina ma yaga time ɗin tsayawa su posting da chatting, ke nan kinzo kina ta hauka, Allah ya shirye ki" cewar Anty Khadija cikin dariya. "Allah sarki matar sa kam ta more wallahi" cewar Aisha. "Kiyi ta addu'a maybe ke ki zama." Shigowar MADEENAH yasa su duk maida duban su gareta kowacce cikin sakin fuska. Ɗan murmusawa tayi tana kallon su kafin tace "Ina wunin ku?." Duk amsa mata sukayi da "Lafiya ƙalau." Kallon Anty Khadija tayi tace "Dan Allah anty Khadija kinga headphone ɗina?." Shiru tayi bata kula ta ba sai ma cigaba da zana kwalliyar ta da take. "Anty Khadija magana fah nake, kodai fushi kike dani ne?." "Ɗaga min kanki" cewar Anty Khadija tana faɗawa wacce take yiwa kwalliyar. "Anty Khadija dan nace ba zan biki bane kike fushi dani?." "Kai Khadija ba dake ake magana bane wai?" cewar ɗaya daga cikin ƙawayen nata. Suma ƙin kula su tayi ta cigaba da harkar gaban ta, DEENAH kuwa ficewa tayi hawaye na kawo mata na rashin jindaɗin manna mata da Khadija tayi. "Nikam, dakyar nake iya ɗauke idanu na akan yarinƴar nan" cewar ɗaya daga cikin su. "Aikuwa dai wallahi nima, ta haɗu ta koh ina dama nice" cewar Aisha. Duka ɗaya ta zuba mata tace "Cha6 idan kece da wannan kyawun ai mun boni a cikin garin Sokoto wallahi." Dariya sukayi kafin ɗaya tace "Wallahi babu saurayin da ba zai santa ba,bama cikin garin Sokoto kaɗai ba kaf Nigeria." Haka nan sukayi ta hirar su har aka gama yi wa kowace kwalliya masha Allah dukkan su sunyi kyau sosai sun sha anko abin su gwanin ban sha'awa. Duk fitowa sukayi zuwa falon gidan anan suka tadda su Mami, Amirah da ma kuma MADEENAH. Duk sake gaida Mami sukayi kafin Khadija tace da ita "Mami sai na dawo." "Zo nan" cewar Mami ɗin. Zuwa tayi ta zauna kusada ita tace "Gani Mami." "Mai MADEENAH tayi miki tana yi miki magana kin share ta?." Kallon DEENAH tayi kafin tace "Babu abinda tayimin Mami." "Ƙarya kike, babu abinda tayi miki kuma tana yi miki magana kina share ta, hakan ya kyautu kenan Khadija, mutum yazo muku hutu amma kina nuna mata halin nan, ƴar uwarki ce fah miye amfanin hakan toh?, bana fah son irin abin nan na faɗamiki." "Mami dan fah kawai MADEENAH tace ba zata bita dinner ɗin ƙawar su bane yasa take ta nuna mata halin koh inkula" cewar Amirah. "Toh dinner ɗin na ƙanwar uwarta ne da zakice sai kin tilasta ta ta tafi?" cewar Mami cike da mamaki. "Mami ni fah kawai gani nayi yawan zaman ta cikin ƙunci yayi yawa shiyasa na kawo idea ɗin tafiya da ita koh zata rage shiga damuwa, amma tunda tace bata so ai shikenan" cewar anty Khadija. "Toh ana dole ne, kema sai na hana ki tafiyar yanzu iskanci kawai" cikin faɗa Mami ta faɗi hakan. "Mami zanje" cewar MADEENAH. Kallon ta Mami tayi tace "Aa MADEENAH, babu inda zaki tunda bakya so." "Allah Mami zanje, gaskiya Anty Khadija ta faɗa idan naje ni ɗin maybe na samu sassaucin abinda ke damu na." "Kin tabbata?." Kai ta jinjina mata nan Anty Khadija tace "Yauwa kaji ƴar albarka, zo muje na shirya ki" ta faɗa tana kamo hannun DEENAH kafin tace da ƙawayen ta "Kuzo ku zauna ku jira ni, yanzu zamu fito mu tafi." Ɗaki suka koma, kasancewar tayi wanka kawai kayan ta ta ciro set ɗin komai baƙi hatta takalmin da zata sanƴa. "Ke kam bakida wani kaya ne sai baƙi?" cewar Anty Khadija. Murmushi kawai tayi kafin Anty Khadija tace "Toh zo ki zauna na gyara miki face ɗin naki tunda bakya son kwalliya." Babu musu taje ta zauna, taje mata gashin kanta tayi ta kama mata shi sannan ta sanƴa mata jel a kai tare da fidda mata style mai kyau ta gaban, simple make-up kawai tayi mata ta gyara mata face ɗin, amma kyawun da tayi ba'a magana sai wanda ya gani. Bayan ta gama mata ne ta shirya cikin kayan ta, kallon ta Anty Khadija tayi tace "Nikam wannan dressing ɗin naki bansan ma da wane suna zan kira shi ba, gashi dai ke ba ƴar Turkey ba kuma ba ƴar Korean ba Kuma ba balarabiyar dubai ba, amma kuma kinason yin shiga irin tasu." Kallon kanta tayi a mirror tayi murmushi dan kuwa ita kanta ta san ba ƙaramin kyau tayi ba, nan tace "Inajin daɗi idan nayi dressing irin wannan sannan kuma inason baƙin color shiyasa dukkanin kayayyaki na suke baƙi." "Uhmm no wonder, wannan kyanta ace kin zama Fashion blogger." Kallon Anty Khadija tayi tace "Muje dare yana yi." "Wallahi fah ƙarfe takwas fah za'a fara dukda nasan sai anyi african time an kai tara kafin a fara event ɗin amma kuje da wuri kam yafi mutunci." Fitowa sukayi nan duk idanu ya dawo kansu, Mami ce tace "Kai masha Allah, ƴata tayi kyau" ta faɗa cikin murmushi. Amirah kuwa baki kawai ta saki tana kallon DEENAH haka ma ƙawayen Anty Khadija sai binta da ido suke suna kallo. "Toh Mami mu zamu wuce sai mun dawo." "Adawo lafiya, Allah ya tsare dan Allah Khadija kada kuje ku zauna kinga dai dare ne koh?." "Insha Allah Mami" ta faɗa suna ficewa. "Yanzu fah duk wankan nan da muka ci Taxi zamu hau koh?" cewar Aisha. "Taxi zaku hau dai amma banda mu" ta faɗa tana nufar wata danƙareriyar mota chan gaba da gidan su. "Kutt, kar dai Aliyu ne zai kai ki?." "Toh miye amfanin shi, yana da mota kuma naje ungwa a Taxi ƙarya ne wallahi, kunga gara fah kunje kun nemi abin hawan ku, kuma ba rasa samari kukayi ba, ni da DEENAH ce kaɗai zamuje a motar sa, wallahi babu ƙatuwar da zata bini a cikin ku, kuna da kuɗi ba wai bakuda shi bane." Sun san sarai Khadija batada mutunci indai ta wurin Aliyu saurayin ta ne, sun san koh mutuwa zasuyi ba zata bar su su bisu ba, Aisha ce tace "Dallah kuzo mu tafi wa zata yiwa wulaƙanci, dukkanin mu nan babu mai saurayi matsiyaci kema kin sani, kuma ai tun farko baki ce mana Saurayin ki ne zai zo ɗaukar ki ba, dah tuni munyi tafiyar mu wallahi." "Kwaji dashi" ta faɗa tana riƙo hannun DEENAH suyi gaba. Da kallo duk suka bisu nan ɗaya tace "Wallahi Khadija ƙarshe ce wurin iya rashin mutunci, sai muje mu tari Taxi ɗin ai ya muka iya?." "Mtssww Allah ta ƙular dani, ni matsala ta ma yarinƴar nan da ta ɗauko tsaf zata kashe mana kasuwa a wannan wurin." Dariya sukayi ɗaya tace "Kyaji dashi, idan kinga dama ki biyo mu, idan kin ga dama kuma kyayi ta tsayuwa anan" ta faɗa sunayin gaba. Taxi suka tara suka faɗa masa inda zasu kafin su shiga yaja ya bar wurin, dan tuni su Anty Khadija sun tafi................ ************************ ..............Ƙaton hotel ne da ya amsa sunan sa wurin haɗuwa da tsaruwa, haske gauraye ta koh ina. Babu abinda kakeji sai karar sauƙar motoci da tashin su, ga kuma ƴan mata da samari kowanne cikin shigar sa ta alfarma, da alamu dai party ɗin ba na biki ɗaya bane. Duk fitowa sukayi daga cikin motar bayan yayi parking, sallama sukayi kafin ya wuce. Dafa DEENAH da duk takejin ta a takure tayi tace "Ki saki jikin ki, bari na jira zuwan su Aisha sai mu shiga." Kai kawai ta jinjina mata but sam haka kurum take jinta so remorsed, bata da wata walwala ga kuma sanƴi da wani irin karkarwa da zuciyar ta takeyi, har cikin tafin ƙafar ta takejin sanƴin. "Are you Okay?" cewar Anty Khadija tana kallon ta. "Am fine" ta bata amsa. "Naga kamar kina karkarwa ne." "No, am fine." Ƙarasowar ƙawayen Anty Khadija ne yasa su nufar cikin ƙaton hotel ɗin. Motoci ne a ciki birjik kowanne na ƙece raini, nan Aisha tace "Um bari mu natsu koh Allah zai sa muyi kamu" ta faɗa tana gyara nutsuwar tafiyar ta. "Toh wannan kuma wanene haka?, naga bodyguards koh ta ina" cewar ɗaya daga cikin su. "Maybe wani babban ne, kema kinsan auren nan na manƴan mutane ne, amma kuma kina wata tambayar daban dan kinga securities." "Kuma fah." Juyawa Anty Khadija tayi ga DEENAH dake chan baya tana tafiya kamar wacce kejin tsoro "kuyi gaba ina zuwa" ta faɗa tana komawa wurin DEENAH. "DEENAH put yourself together, kinji?." "Anty Khadija zuciya ta rawa takeyi,tsikar jiki na tashi yake, bansan meke damuna ba." "Duk sabida baki saba shiga cikin jama'a bane yasa kike jin hakan, but da zaran mun shiga ciki zaki dawo normal, Okay?." Kai ta jinjina mata kafin ta kama hannun ta suyi ciki. Hawa huɗu ne wajen, dan haka hall ɗin da za'ayi nasu Event ɗin shine a hawa na huɗun. Stairs suka hau ya kai su har bakin ƙofar hall ɗin. Ƙaton hall ne sosai wanda aƙalla zai ɗauki mutane ɗari-biyar koh sama da haka, sai dai iya mutanen dake ciki ba zasu haura ɗari zuwa ɗari da hamsin ba. Sosai hall ɗin ya ƙawatu da kwalliya wanda da ka gani kasan bikin na masu hannu da shuni ne. Ja tayi ta tsaya tana girgiza kai, kallon ta tayi tace "Menene?." "Ba zan iya shiga ba, akwai mutane dayawa." "Ina mutanen suke, come on DEENAH karki ba dani mana, a hakan ma fah kaɗan aka gayyata sabida party ɗin ya bada ma'ana, baki ma ga kowa na harkar gaban shi ba, babu wanda hankalin sa ke kanki, yanzu muje chan na bada ticket ɗin gayyatar mu sai mu shiga koh?." Shiga sukayi ta bada ticket ɗin gayyata kafin a bar su su shiga, riƙo hannun DEENAH tayi suka shige main hall ɗin bikin. Wani irin shock ne taji ya ɗebe ta wanda sauran kaɗan ta faɗi Anty Khadija ta taro ta "DEENAH" ta faɗa. Wani haɗaɗɗen table ne daga chan gefe wanda aka ƙawata shi yafi kowane table haɗuwa ta kai ta ta zaunar tace "Ki zauna anan ina zuwa kada ki tashi fah, kuma kada ki kula kowa." Kai ta jinjina mata kafin Anty Khadija ta juya ta tafi. Gyara zaman ta tayi tana bin mutanen cikin hall ɗin da kallo, inda kowa sanƴe da anko ya kai kala biyar ƴan matan nan kansu sai rawa yake. ***************** .........."So you made me wear this kaftan just for your wedding?" ya faɗa yana kallon cikin madubi yana gyara zaman hular kansa. "Yes sir, baka ga yadda kayi kyau ba, Allah yasa dai kar amarya ta tace ta fasa daga ganin ka" cewar Mansoor yana dariya. Murmushi ZEEDAN yayi yace "Alright ango, muje kada amaryar taka ta fara gajiya da jiran ka." Fitowa sukayi kamar yadda Mansoor ke sanƴe da farar shadda haka shima ZEEDAN ke sanƴe dashi yasha binjima kai ka rantse shine angon sabida yadda kayan ta zauna tayi masa kyau ba'a magana sai wanda ya gani kawai. Hall ɗin suka nufa direct, suna cikin tafiya ne yaji an kira sunan sa "ZEEDAN?." Ja yayi ya tsaya kafin yace da Mansoor yayi gaba yana zuwa. Surayya ce ya gani itama cikin shigar atamfa ɗinkin fitted gown sosai tayi kyau, ƙarasowa wurin sa tayi tana murmushi tace "Dama kaima wannan auren zakayi attending?, Oh my GOD i just couldn't take my eyes off of you, shigar nan tayi maka kyau sosai Oh my GOD" ta faɗa kamar ta ɗauke sa ta haɗiye. "OK" kawai ya faɗa ya juya ya fara tafiya. Saurin mara masa tayi suka jera dashi suna tafiya, duk inda suka gitta kuwa idanu ne ke binsu both maza da matan kowa sai yaba shi yake, yayin da zuciyar wasu mazan ya cika da kishin ganin ZEEDAN sosai. Surayya kuwa ji take kanta na yin ƙato sabida kowa ganin budurwar ZEEDAN yakeyi mata. "Sir this way" faɗin wani bodyguard yana yi masa iso da shigowa cikin hall ɗin. Kafarsa da ya sanƴa ya shigo cikin hall ɗin shine ya faɗaɗa bugun zuciyar ta, damƙe jakar hannun ta tayi da ƙarfi tana jin kamar ta 6ace ta ganta a gida. "Excuse me ma'am" taji an faɗa. A ɗan tsorace ta ɗago tana kallon sa nan yace "Wannan seat ɗin is not for regular guests, it's made for someone special, please change your seat." Tsayawa tayi kallon sa dan kuwa idan tace zata tashi toh babu makawa zata iya zubewa anan wurin. "Ma'am" ya sake faɗa yana yi mata alama da hannu akan ta tashi. Kai ta jinjina masa tana niyyar tashi ne kuma akace "Let her be." Juyawa yayi ga ZEEDAN yace "but sir..." Bai ƙarasar ba ya ɗaga masa hannu hakan yasa shi yin shiru kafin yaja masa kujera cike da girmamawa ya zauna. Tunda taji muryar sa ne kuma bugun zuciyar ta ya ƙaru sosai, runtse idanu tayi kanta a ƙasa dan kuwa bata iya ɗagowa ta kallesa ba. Ƙamshin turaren sa kuwa duk yabi ya addabe ta, sosai taji kamar ta ta6a jin irin wannan ƙamshin a wani wuri sai dai ta mance koh a ina ne. Kallon ta yayi dan kuwa gefen fuskar ta kawai yake iya gani sakamakon ta juya daga saitin sa kuma idanun ta a ƙasa. _"Toh ita wannan kuma daga ina, why is she behaving so strange"_ ya faɗa a zuciyar sa. Kan kace miye kuma an cika gaban su da abubuwan ci da sha dayawa dama kuma kalolin abinci ba'a magana. Surayya dake ta jin kanta na ƙato ne ta jawo kujerar ta kusa dashi tace "Babe." "Stop calling me that" ya faɗa ƙasa-ƙasa ta yadda babu wanda zai ji. "Come on look around kowa da boyfriend nashi anan, let's stick together and be like them please." Share ta yayi dan kuwa ya gama ganewa batada kunƴa ne. Ji tayi an ta6a ta, nan ta ɗago daga tana sauƙe idanun ta kan Anty Khadija. Ajiyar zuciya ta sauƙe tace "Anty Khadija ina kika je tunɗazu?." "Ke kinsan waye a kusada ke kuwa?" ta faɗa ƙasa-ƙasa. "Dan Allah mu bar nan wurin, bana jin daɗin zama anan." "Cha6 ai ni ingayamiki ma zama nazo yi babu inda zani" kasancewar seat huɗu ne yasa ta faɗin "Excuse me can i?" ta faɗa tana nuna seat ɗin. Bodyguard ɗaya ne yace da ita "No." Kallon sa ZEEDAN yayi hakan yasa shi yin shiru ya cigaba da patrol ɗinsa. Murmushi tayi ta zauna tare da furta "Thank you." Rolling idanu Surayya tayi ganin kowace mace idanun ta na akan ZEEDAN hakan na ƙona mata rai matuƙa. Kama hannun DEENAH tayi tace "ki saki jikin ki mana." "Sir you have an important call" cewar wani bodyguard yana miƙa masa wayar. Ba tare da ya ɗago ba yace "Who is that?." "Your Mom." "Mom?" ya faɗa yana amsar wayar kafin ya kara a kunnen sa. Ganin surutu da kiɗa yayi yawa a wurin ne yasa shi tashi ya bar wurin ya fice daga cikin hall ɗin. Da kallo kawai tabi bayan shi tana ɗan jin bugun zuciyar ta na raguwa. Sai a sannan ta ɗago tana gyara zama tace "Anty Khadija mu bar nan wurin." "Cha6 ke bakiga idanun su Aisha ba kamar zai fita, shegiya da zata samu wuri anan da da gudu zata zo ta zauna." Kallon Surayya Khadija tayi tace "Hello." Ɗan ɗagowa tayi ta kalle ta tace "Hi." "Is he your boyfriend?." Murmushi ta saki tace "Yeah, sannan ma we are about to get married soon." "Wow, Congratulations." "Thanks" ta faɗa cikin murmushi tana cigaba da danne-dannen wayar ta. Cikin ƙasa da murya tace "Kinsan wani ana ce masa *ZEEDAN AL-ABBAS*, The most Famous and richest artist in the world to shine wannan, just look at how Handsome he is, koh sau ɗaya ki ɗago ki kalli face nasa am.definitely sure sai dukkanin damuwar ki ya yaye." "Stop it Anty Khadija." Tashi Surayya tayi da juice a hannun ta tana danne-dannen waya tazo wucewa ne cup ɗin hannun ta ya su6uce ya faɗa kan DEENAH inda gabaɗaya ya zube mata a kaya. "Oh GOD!" ta faɗa tana ajiye wayar da sauri kafin tace "Sorry ban lura bane." "It's Okay" ta faɗa tana tashi tsaye. "Muje akwai toilet ta lungun chan ki shiga ki wanke jikin ki" cewar Anty Khadija tana kamo hannun ta. Ajiye jakar ta tayi kafin su bar cikin hall ɗin. Wayar Anty Khadija ne ya hau ringing nan tace "Ga chan hanƴar toilet ɗin a cikin corridor ɗinnan kije, bari na amsa kiran nan." Wucewa tayi kawai da sauri tana tsane jikin ta. Boooomm taji ta bugu da mutum inda wayar dake hannun sa ta faɗi ƙasa. Da sauri ta sunkuya ta ɗago masa wayar tana faɗin "Sor.." Maganar ta ce ta carke lokacin da idanun ta suka sauƙa cikin nashi. Amsar wayar yayi yace "It's alright" ya faɗa yana wucewa. Daskare wa tayi anan wurin ba tare da ta iya motsa koh da ƴar yatsar ta bace................ *Yawan Comment, yawan typing* *MHIZZ JIDDHERR............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *016...* ...............Manƴan idanun ta da ta waro tun sadda ta haɗa idanu dashi ne ta kasa ƙiftawa har yanzu, sannan kuma ta kasa motsa koh da ƴar yatsar ta ne, haka nan ta tsaya in shock kamar wacce tayi sumar tsaye. Tabbas shine, ta gane shi kallo ɗaya tayi masa ta gane kamannin sa, like a flash haka fuskar sa da kamannin sa suka faɗo mata cikin kwakwalwa. "DEENAH!, DEENAH!!" cewar Anty Khadija tana girgiza ta. A firgice ta ɗago tana kallon ta. "Meke damun ki, bakije kin wanke bane?." Dube-dube DEENAH ta fara ganin ya bar wurin bata gansa bane yasa ta nufar hanƴar cikin hall ɗin da gudu. "DEENAH Stop" cewar Anty Khadija tana mara mata baya. Tsaye DEENAH da takejin zuciyar ta kamar zata faso waje tayi a tsakiyar hall ɗin tana dube-dube, duk wanda ta gani da farin kaya kuwa sai taje ta duba fuskar sa taga koh shine. Haka nan tayi ta yawo a cikin hall ɗin tana lelleƙa fuskar mutane cike da kiɗima, yayin da mamaki ke cike a fuskar kowa ganin yadda ta gigice ta daburce kamar wata zautacciya, nan duk kallo ya dawo kanta kuma. Anty Khadija ce ta kamo ta tace "DEENAH miye hakan kike yi, bakiga kowa na kallon ki bane?." "I saw him, i just saw him now" ta faɗa tana cigaba da bin mazan wurin tana leƙa fuskokin su. Haka nan tayi ta zagaye hall ɗin baki ɗaya but bata ga ZEEYAD ba, batasan inda ya shiga ba. Ficewa tayi daga cikin hall ɗin da gudun ta inda kowa ya bi ta da kallo Anty Khadija na mara mata baya. Tsaye tayi ta sama stairs ɗin tana jejjefa idanun ta koh Allah zai sa ta ganshi a cikin mutanen nan. Bata gan shi ba hakan yasa ta sauƙa zuwa hawa na uku tana duba shi bata gansa ba har ta fice zuwa waje. Nan ma dube-dube ta fara tana waige-waigen neman sa, kamar a mafarki ta gansa yana shirin shiga motar sa da aka buɗe masa waya kare a kunnen sa. Bata tsaya yin wata-wata ba kuma ta nufe shi cikin gudu tana kuka tare da ihun "Stop" kamar wata zautacciya. Kafin ta isa motocin suka bar cikin hotel ɗin, DEENAH zubewa tayi tare da rushewa da kuka mai tsuma zuciya, sai a lokacin Anty Khadija tayi nasarar fitowa daga ciki ta same ta tana kuka kamar zata shiɗe. "DEENAH, DEENAH mai ya sameki?." DEENAH bata iya kula ta ba sai ma kuka da take tayi tana faɗin "I saw him." "DEENAH, waye ne, waye kika gani?." "He is the one, i saw him." Ƙarasowa ƙawayen Anty Khadija sukayi wurin suna tambayar abinda ya faru. "Khadija mai ya sameta?." "Nima bansani ba, abinda nake tambayar ta kenan bata bani amsa ba" ta faɗa ita ɗin ma kamar zatayi kuka tana rungumo DEENAH jikin ta. "Kinga mutane sun fara taruwa, mu tada ta mu bar nan wurin" cewar ɗaya daga cikin su. Duk kama ta sukayi da niyyar tayar da ita tsaye sai dai taƙi ta bari. "Leave me alone" ta faɗa cikin kuka. "DEENAH, ki tashi haka nan, gida kikeson tafiya koh?" faɗin Anty Khadija. "He is gone, i have lost him again." "Waye kike magana wai akai?." Da sauri ta ɗago ta kalli Anty Khadija tace "Anty Khadija, kinsan shi koh, wannan ɗinnan da kikayi min maganar sa, kinsan inda yake koh?." "Waye, wa kenan?." "Balarabe" ta faɗa. "Balarabe, wane balarabe kuma DEENAH?." "Na ganshi, na ganshi kafin na ƙaraso wurin sa kuma motocin sa sunja sun tafi, Wayyo Allah na, na shiga uku" ta faɗa cikin shesheƙa. "DEENAH ni ban gane wanda kike magana a kai ba, waye ne shi kwatanta min shi." "W..wani...wani ne balarabe ne, ya sanƴa farin kaya, na ganshi da zanje wanke jiki na kafin na dawo kuma ya tafi, ya tafi Anty Khadija shikenan kuma na sake rasa shi, dan Allah ku nemo min shi." "Toh wai kodai ZEEDAN take nufi?" cewar Aisha. "ZEEDAN kuma, a'ina zata san shi." "Toh naga shi kaɗai ne Balarabe anan da ya sanƴa farar shadda." "Tabbas shine" cewar Anty Khadija. "Kina da tabbacin shine?." "Na ga lokacin da ya fito daga corridor ɗin da DEENAH ta shiga, koh da naje na tadda ta kamar bata cikin hankalin ta seems like ta san shi kenan." "How sure are you?." "Ina Aisha, shiga mana page ɗinsa a instagram muga koh shi take nufi" cewar Anty Khadija. Aisha wayar ta ta ciro tare da kunna data ta shiga instagram ɗinta. Ƴan danne-danne tayi kafin ta miƙowa Anty Khadija wayar. Nuna mata tayi tace "shine wannan?." Da sauri ta amshi wayar ta shiga kallon hotunan nasa idanun ta na manƴa. "Shi..sh..shine, shine Anty Khadija wallahi na gane shi, ba zan ta6a manta fuskar sa ba, dan Allah ku kai ni wurin shi" ta faɗa tana kallon Anty Khadija. Kar6ar wayar Anty Khadija tayi tana maidawa Aisha abin ta nan tace "Babbar magana." "We should locate him" cewar Aisha. "And how do you think that is possible?, the guy is Famous he can't easily be found or seen, dan mungan shi a auren nan doesn't mean zamu iya kuma ganin sa cikin sauƙi" faɗin Anty Khadija. "Anty Khadija ya sanni, dan Allah ku kai ni wurin sa." "Kinga DEENAH tashi mu tafi gida." "Dan Allah..." "Tashi mu tafi, idan munje gida zamu nemo mafitar inda zamu samo sa cikin sauƙi" ta faɗa tana ɗaga ta tsaye. Ficewa sukayi zuwa bakin titi, nan Anty Khadija tace "Dan Allah wata ta ɗaukomin jaka na a table ɗinda ZEEDAN ya zauna na mance shi." Biyu daga cikin su ne suka koma suka ɗauko mata jakar kafin su tari Taxi suka shige, inda su kuma ƙawayen suka koma wurin party........... ************************ ............"Toh da kuka ganshi ɗin kuma mai ya hana ku tsaida shi?" faɗin Mami. "Mami ita ce ta ganshi, kafin kuma ta isa gareshi ya riga da ya fice, infact a table ɗaya muka zauna dashi." Ɗagowa tayi ta kalli Anty Khadija, nan ta girgiza masa kai "Kwarai kuwa shine wanda nake faɗamiki ki ɗago ki kallesa amma kika ƙi sakin jikin ki, ashe ma shi ɗin is someone very important to you." "Mami dan Allah ku nemo min shi idan ban basa haƙuri ba ba zan ta6a samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba, dan Allah ku nemo min shi tunda yana cikin garin nan." "Haba mana MADEENAH ki kwantar da hankalin ki haka nan, insha Allah za'a nemo sa da izinin Allah indai yana cikin garin nan, na kira yayanki Jafar yana hanƴar sa ta zuwa, insha Allah damuwar ki ta kusa zuwa ƙarshe, kiyi haƙuri." Sautin kukan ta ne kawai ya cika falon inda su kuma ke ta rarrashin ta cikin son kwantar mata da hankali, sai dai koh kaɗan taƙi saurarawa. Bayan kamar 20mins Jafar ya shigo falon bakin sa ɗauke da sallama. Da gudu taje tana faɗawa jikin sa tana sake ƙara volume ɗin kukan ta. Bayan ta ya hau bubbugawa cikin rarrashi amma kamar sake zuga ta yake. Ɗagowa tayi cikin kuka tace "Yaya na gan shi wallahi na gan shi yaya." "Wanene?" ya tambaya. "Balarabe, wallahi na ga balarabe yaya." Idanu ya zaro cike da mamaki yace "Balarabe kuma DEENAH?." Saurin jinjina masa kai tayi tana cigaba da kuka. "Jafar ƙaraso mana" cewar Mami. Hannun DEENAH ya janƴo suna samun wuri su zauna. Gaida Mami yayi cike da girmamawa kafin tace "Sannu Jafar, sai yanzu kake ƙarasowa?." "Wallahi Mami ina chan wurin aiki ne." "Toh masha Allah hakan yayi kyau sosai, ka dai ji abinda ƙanwar taka ke faɗa koh?." "Abin da mamaki, tayaya kuma zaki ga balarabe?." "Wallahi shi na gani yaya, gashi nan ka tambayi Anty Khadija ma ai har hoton sa ta nuna min." "Wai dagaske?" ya faɗa yana kallon Anty Khadija. "Haka dai tace wai shine, but kai ka san shi ai koh?." Saurin jinjina mata kai yayi nan tace "Toh bari na dubo hoton sa ka gani." Latsa wayar ta ta shiga yi, nan ta nemo hoton sa tana miƙawa Jafar wayar tace "Shi ne?." Amsar wayar Jafar yayi ya shiga kallon hoton, sosai ya kalla kafin kuma ya ɗago ya kalli DEENAH yace "DEENAH wannan ne kike cewa shine balarabe?." Kar6ar wayar yayi tana kallo nan tayi saurin jinjina masa kai tace "Eh yaya shi ne, ba ga shi nan kana gani ba." "Come on DEENAH, wannan sam ba balarabe bane koh kama ma basuyi ba." Sake duba hoton tayi tana girgiza kai tace "Yaya ka sake dubawa da kyau wallahi shi ne." Amsar wayar yayi yana miƙawa Anty Khadija yace "Inaga she is just eager to see him shiyasa take ɗauka kamar shi ne, but sincerely speaking wannan ba shi bane." Kallon Jafar kawai ta tsaya yi tana mamakin kalaman sa na cewa ba balarabe bane ta gani. "Yaya" ta faɗa. "DEENAH yakamata ace kin dawo cikin nutsuwar ki haka nan, this is not balarabe koh kama basuyi ba, how kike tunanin a homeless person like him can be so rich and Famous like this in just shekaru goma." "Shekaru goma is not a just yaya, maiyasa wai dukkanin ku kuka kasa fahimta ta ne, i told you wannan balarabe ne na gani amma dukkanin ku kuna ɗaukar lamari na wasa, bakusan abinda nakeji a cikin zuciya ta ba, sai dai kawai kuyi ta bani haƙuri, i know i saw him but you doesn't seem to believe me har kana cemin ba shi bane bayan kasan shi, he is your friend back then." "DEENAH listen to me..." "No i won't listen, dukkanin ku babu wanda ya damu da damuwata dama kuma halin da nake ciki kullum, tunda babu wanda zai nemo min shi a cikin ku, then ni zan nemo shi da kaina" ta faɗa tana barin cikin falo ɗin ta fice waje. "DEENAH" duk suka kira ta suna tashi su mara mata baya. Riƙo ta Jafar yayi yace "DEENAH ki kwantar da hankalin ki, ina dai kince wannan balarabe ne koh?." Saurin girgiza masa kai tayi tace "Amma ai kaƙi yarda dani cewa shi ne." "DEENAH look, zan kai ki wurin balarabe but sai kinyi min alƙawarin zaki daina sanƴa damuwa a cikin ranki, nikuma nayi miki alƙawarin zan kai ki wurin sa zuwa next week." "What, kasan inda balarabe yake?." Shiru yayi yana kallon ta kafin kuma yace "Yeah na sani." "What, kasan inda yake?." "Yeah." "Kuma baka ta6a damuwa da ka faɗamin ba" ta faɗa cike da mamaki tana kallon sa. "Look DEENAH i will Explain everything to you, but you need to calm down, Okay?." "I should calm down, you want me to calm down after all the pain i had went through for ten years, kasan inda balarabe yake tsawon lokacin nan amma baka damu da cewa ka sanar dani ba bayan kasan irin wahalar da nake sha a kullum, maiyasa zakayi min haka, i thought kai yaya na ne mai sona kuma mai son ganin farin ciki na, ashe ba haka bane ka san abinda zai sanƴa ni farin ciki kasan inda yake but you're keeping me away from him all this long, maiyasa haka yaya" ta faɗa cikin kuka tana ture shi daga jikin ta. "DEENAH..." "Don't come near me and leave me alone" ta faɗa tana komawa cikin gidan da gudu cikin kuka. "Jafar, kasan inda yake?" cewar Mami tana kallon shi. Kai ya jinjina yace "Eh Mami." "What, Jafar but why, maiyasa ka 6oye sanin inda yake bayan kasan halin da DEENAH take ciki." "Sabida hakan shine alkhairi a gareta Mami." "Bangane ba mai kake nufi?." "Jafar kana nufin kace ZEEDAN shi ne balarabe?" cewar Anty Hafsat. "Yeah" ya faɗa kafin kuma yace "I need to go now, zan dawo gobe please take care of DEENAH" yana faɗin haka ya juya tare da zuwa ya shige cikin motar sa ya ja ta ya fice bayan mai gadi ya buɗe masa.............. ************************* .............Sosai take kuka kamar zata shiɗe idanuwan ta baki ɗaya sun kumbura sabida kukan da ta dinga yi cikin dare bata samu isasshen bacci ba. Ji takeyi Jafar ya cuce ta kuma bayason farin cikin ta tunda har yasan inda balarabe yake tsawon lokacin nan amma bai ta6a faɗa mata ba. "DEENAH ki fito yayan ki yazo wurin ki." Ƙin kula ta tayi sai ma cigaba da tayi da kukan ta tana jin haushin Jafar sosai a zuciyar ta. "DEENAH..." "Ni banason ganin shi" ta faɗa tana rufe pillow akanta ta kwanta. Bayan mintina biyar taji yana kiran sunan ta "DEENAH." "Ka rabu dani" ta faɗa cikin kuka. "DEENAH am sorry i know ban kyauta miki ba, and it hurts me so bad to see you in pain na rashin ganin balarabe, but i can't endure to see you in more pain bayan kin ganshi." Ɗagowa tayi tace "He is my cure, ganin sa ba zai sanƴa ni cikin wani baƙin cikin ba, i can't believe kasan inda yake all this while amma kayi shiru baka faɗa wa kowa ba." "DEENAH ba haka bane, ina guje miki abinda zai faru ne duk sadda kika haɗu da balarabe." "Babu abinda zai faru, kawai haƙuri nakeson basa bakomai ba, da zaran kuma ya yafemin zan sami kwanciyar hankali, kai ba yayan kwarai bane tunda har kana iya jurar ganin ƙanwar ka cikin tashin hankali." Sosai bayajin daɗin kalaman dake fitowa daga bakin DEENAH na kiran sa yayan da bai dace ba, bakomai yake nema wa DEENAH ba sai kwanciyar hankali, shi kaɗai yasan abinda zai biyo bayan haɗuwar ta da balarabe. "Alright, kije ki shirya zan kai ki wurin balarabe, but kada kice ban gargaɗe ki ba, haɗuwar ki da balarabe babu abinda zai haifar miki sai ƙarin damuwa wannan shine abinda nake guje miki, amma tunda kince ganin sa shine kwanciyar hankali dama kuma farin cikin ki, then i will make sure na kai ki kin gan shi kafin ya bar cikin Sokoto gobe, and that Mall da nake aiki a matsayin MANAGER Mall ɗin ZEEYAD ne, sannan kuma that Man da kikayi banging dashi har sau biyu ZEEDAN ne, ZEEDAN and ZEEYAD duk mutum ɗaya ne, you go and get ready i will be waiting for you outside" yana faɗin haka ya fice daga ɗakin DEENAH ɗimauce wa tayi tsabar farin cikin dake fizgar ta, da sauri ta miƙe taje tayi wanka ta fito. Kafin ta shirya so very quickly wanda da wanka da shirin bai ɗauke ta good 20mins ba ta fito. Bata kula kowa a falon ba ta fice da sauri zuwa waje. Anan taga Jafar a cikin mota nan ta shige kawai tace "Yaya make it fast please,i wanted to see him." Tada motar kawai Jafar yayi ya jata suka bar cikin gidan. Tafiya mai nisa sukayi kafin su iso ga wani haɗaɗɗen hotel mai kyau da tsada. A inda motoci ke parking yayi kafin tayi saurin fitowa tana riga shi. Tausayin ta kawai Jafar keji dan kuwa shi kaɗai yasan abinda ke ran ZEEYAD game da DEENAH. Bayan sa tabi kamar zata tashi sama dan daɗi, sai dai gefe guda kuma ji take zuciyar ta kamar zata faso waje dan gudu. Lifter suka shiga ya kai su har flat ɗin da ɗakin ZEEYAD yake. Bakin ƙofar wani ɗaki yaja ya tsaya ya kalleta yace "Yana cikin ɗakin nan ki shiga, i will be waiting for you outside" yana faɗin haka ya juya ya tafi ba tare da ya bata damar furta abin dake bakin ta ba. Da kallo ta bishi har ya shige cikin lifter kafin kuma ta maido da duban ta kan ƙofar zuciyar ta na matuƙar rawa sosai. Tsoro ne da fargaba suka darsar mata a zuciya lokaci guda, kafin kuma cikin rawar hannu ta murɗa handle ɗin ƙofar a hankali bugun zuciyar ta na ƙaruwa. A hankali ta shigo idanun ta a ƙasa kamar munafuka, kafin ta fara bin cikin hadaɗɗen falon da kallo cikin ƙasa da idanu. A hankali ta shiga ɗago da kanta tana ƙarewa falon kallo. Babu kowa a ciki hakan yasa ta takowa ciki tana rufe ƙofar ta ƙaraso tsakiyar falon. Kan kujera ta samu ta zauna tana wuwwula idanun ta dan ganin ta inda zai fito. Shiru ta ɗauki almost twenty mins a zaune sai dai bataji alamun kowa ba, har ta fara tunanin koh baya ciki ne. A garin kalle-kallen ta ne idanun ta suka faɗa kan wata farar A4paper dake ajiye akan center table ɗin falon inda aka ɗaura remote da Pencil akan sa. Hannu ta kai zata ɗauka nan taji alamun motsin mutum hakan yasa ta saurin daidaita nutsuwar ta tana gyara zama kanta a ƙasa tayi zuru-zuru da ita, kamar kace kyatt ta fece. Ta bayan ta yake tsaye yana ƙare mata kallo, fuskar nan tasa a matuƙar ɗaure. Takowa yayi a hankali yana dafa kujera da take kai ta baya. "MADEENAH" ya faɗa a hankali cikin daddaɗar husky voice ɗin sa................. _Nasan da yawan ku nada tambayoyi, toh kada ku damu insha Allah a hankali zan warware muku zare da abawa🤘🏼🤩_ *Yawan Comment yawan typing, kiyi sharing fisabilillah idan kin karanta👏🏽* *Kada ku manta Babu Posting ranar weekend😂🤘🏼* *MHIZZ JIDDHERR............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *017...* ............DEENAH kawai daskare wa tayi zaune zuciyar ta na mugun racing kamar zata faso ƙirjin ta ta fito. Idanun ta da ta waro kasa ƙifta su tayi sumar tsaye kawai tayi a zauna jikin ta yayi mata nauyi sosai bata iya koda motsa ƴar yatsar ta bane. Ƙaramar stool ya ɗauka sannan ya zagayo ya ajiye a gaban ta ya zauna. Idanun ta ta sanƴa cikin nashi tana jin wani irin abu na taso mata a chan ƙasar zuciya. Kallon ta shima ZEEYAD yake ba tare da dukkanin su sun iya ɗauke idanuwan su daga cikin na juna ba. Sosai wani irin farin ciki da annashuwa ke taso mata ganin yau ta haɗu da wanda take burin sake sanƴawa a idanun ta tsawon shekaru, ji tayi dukkanin wani ƙunci da baƙin cikin ta ya fara yayewa. Almost 10mins suna kallon juna babu wanda ya iya janƴe nasa idanun, sai shine ya fara kauda kansa inda DEENAH kuwa kamar wacce aka ɗauko sabuwar halitta aka jefa mata a gaban ta. Yatsun sa ya kaɗa mata a fuska nan tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa. Cikin rawar murya tace "You..you..." "What are you doing here?" shine tambayar da ya jefa mata ba tare da ya bari ta ƙarasar da abinda take shirin faɗa ba. Shiru tayi tana kallon sa kafin daga bisa ni kuma ta buɗi baki tace "I can't believe i can see you again in my life." Kallon ta yayi yace "DEENAH?." Kallon sa take jin yadda ya kira sunan nata, nan yace "It's been a long time." Sunkuyar da kanta tayi ganin irin kallon da yake yi mata, nan ta sake tsinkayo muryar sa yana faɗin "Did you missed me that bad?." Ɗagowa tayi ta kallesa tace "Ina...inaso ne na baka haƙuri, am sorry for causing you alot of pain back then." Murmushin da ya tsaya masa kan le6e yayi yace "And how do you expect me to forgive you?." "You're the worst person i have ever met" ya sake faɗa cikin ɗaurewar fuska. DEENAH tuni idanun ta sun taru da hawaye "Maiyasa ba zaka yafe min ba?." "Sabida baki cancanci na yafe miki ba." "You can't do this to me." "And shouldn't i, kin manta lokacin da kikayi pointing finger ɗinki on me claiming cewa ni ne nayi miki fyaɗe?" ya faɗa cikin ƙunar rai fuskar sa na canzawa zuwa 6acin rai. "But it wasn't my fault" ta faɗa cikin kuka. "It wasn't your fault, kina nufin kicemin that rascal Uncle of yours shine yayi forcing naki or what?." Magana zata yi nan yace "Tell me, tell me nawa ya baki dan kiyi min sharri?." "Please just hear me out." "Ohh na gane, tell me one thing, shin ya saba danne ki ne kullum da yaga asirin sa zai tonu ya baki kuɗi dan ki ɗaura min sharri or what, hun?." "Mai kake faɗa ne haka?, ni babu wanda ya ta6a yi min fyaɗe, not even my Uncle." "You're lying, you've to be ashamed of yourself for showing your Ugly face to me after what you've done." Kuka ta fashe dashi nan yace "So now tell me iya adadin mazan da kikayi tarayya dasu after your Uncle." Ɗago da manƴan idanun ta tayi tana kallon sa, miƙewa tayi tsaye tana jin yadda zuciyar ta ke matuƙar ƙuna da abinda ya faɗa mata. "Zargi na kake da yin karuwan ci?" ta faɗa tana kallon sa. Ɗan ta6e baki yayi shima yana tashi tsaye yace "Ba zargi bane, ya kike tunanin dama rayuwar yarinƴar da Uncle ɗinta ya lalata tun tana ƙarama zai kasance bayan ta girma?." "Stop it" ta faɗa cikin kuka. Ɗan murmusawa yayi yace "It hurts right?, abin akwai ciwo idan an ɗaurawa mutum laifin yin fasiƙanci doesn't it?." Juyawa tayi da niyyar tafiya dan kuwa ba zata iya jurar irin maganganun da yake faɗa mata. Tsinkayo muryar sa tayi yana faɗin "Tell me iya adadin kuɗin da kike chajar customers ɗinki a dare ɗaya, nikuma zan biya ki dukkanin kuɗin ki bar bada kanki haka nan." Juyowa tayi tana kallon sa fuskar nan nata sha6e-sha6e da hawaye. "You want to walk away bayan baki roƙe ni yafiya ba." "But you said you won't forgive me." Idanu ya ɗan waro yace "Really, did i?, i thought you will keep begging me, holding my feet and asking for forgiveness." Ƙarasowa gaban sa tayi tace "Am sorry please forgive me for hurting and ruining your life." "Not like that, you need to hold my feet and beg" ya faɗa yana kallon cikin idanun ta. Shiru tayi tana kallon cikin idanun sa kafin tace "Okay then, If that would make you to forgive me then, i would do it" ta faɗa tana shirin durƙusawa ta kai hannuwan ta ƙafafuwan sa. Saurin riƙo ta yayi ransa a 6ace ya miƙar da ita yana kallon ta. "Have you lost your mind?" ya faɗa yana kallon ta. "Idan nayi hakan zaka yafe min, won't you?." "Na ɗauka ba zakiyi hakan ba, Maybe you should give me a hug instead" ya faɗa yana jawo ta jikin sa ya rungume ta. DEENAH numfashin ta ne ya kusa ɗaukewa jin ta a cikin jikin shi, sosai ta tsorata tayi sumar tsaye almost one minute suka ɗauka a hakan, muryar sa ta tsinkayo yana faɗin "So zargi na akan ki ya tabbata gaskiya, you really enjoyed hugging men don't you?." Saurin kwacewa tayi tana ja da baya hawaye na bin fuskar ta. "Don't pretend to be innocent, that's exactly what you're." "What am i?." Shiru yayi yana kallon ta kafin yace "What you are, you're asking me what you're?, idan na kira ki da wannan sunan then you will be shattered." "Are you trying to call me a Prostitute?." Idanu ya waro yace "I didn't said that, kece kika faɗi hakan da bakin ki." "That is exactly what you mean, isn't it?." Kafaɗu ya ɗaga yace "Duk yadda kika ɗauka." "Alright then, thank you, that won't hurt me sabida nasan kanaso ka rama abinda nayimaka ne wurin cusa min baƙin ciki shiyasa ka faɗamin haka, toh ka sani hakan ba zai dame ni ba sabida nasan ba hakan nake, but you..... it's been ten years now but har yanzu abin na damun ka." "What do you mean?" ya faɗa yana sake tamƙe fuska. "What i mean is duk abinda zuciyar ka ta baka shi nake nufi." "You called me a Prostitute kai kuma duk abinda zuciyar ka ta baka then haka kake" ta sake faɗa. "Dan haka tsakani na da kai kuma yanzu babu wata yafiya da zan nema, sabida ka rama abinda nayi maka, a yanzu ma ba zaka sake gani na ba bale kuma na sake yi maka wani laifin da zai sanƴa ka riƙe ni a zuciya, duk zafi da ciwon da kake ji a zuciyar ka bai kai kwatankwacin wanda naji a shekaru goman nan ba, kullum buri na bai wuce Allah ya sake nuna min kai na baka haƙuri ba i have suffered and went through alot all because of what i have done to you as a little girl forced by her Uncle, amma baka ga hakan ba ka riƙe ni a zuciyar ka all these years da gaba, i am so mad na ganin na haɗu da kai, and now here you're i thought zaka ce ka yafemin but sai ma wani ƙarin baƙin cikin da ka cusa min akan na dah, gaskiyar yaya Jafar ganin ka babu abinda zai ƙaramin sai damuwa, you want to hurt me so bad kuma kayi nasarar hakan, and you're happy with that aren't you?" ta ƙarashe tana goge hawayen fuskar ta. Tunda ta fara magana ZEEYAD ke kallon cikin idanun ta, babu abinda yake gani sai tsantsar ciwo da zafin da zuciyar ta keyi, ofcourse so yake ya cusa mata baƙin ciki and yayi nasarar hakan, kuma koh kaɗan bai damu ba coz ganin yake that is what she deserve. "Are you done?" ya faɗa yana kallon ta. Shiru tayi tana kallon sa bata ce komai ba, nan yace "Get out, coz am sick of seeing your face." Yanzu koh kaɗan maganar da tayi bai ta6a masa zuciya ba kenan sai ma korar ta da yakeyi ta fita ya gaji da ganin fuskar ta, shine tunanin da tayi a ranta. Tsayawa kallon sa tayi nan kuma yace "Kina tunanin sharrin da kikayi min kaɗai ne yasa nake fushi dake?, No, sabida ke nayi losing the most Precious thing a gare ni, My diamond Necklace that is worth billion of dollars with my Mom's photograph in it, that diamond Necklace can change my life in just 5mins, but i choose not to sell it sabida dashi ne nake tuna Ummie na, and all just because of your selfishness i lost it, i lost my entire Happiness just sabida ke, that's the last gift that my Mom gave me on her dying bed, banida komai kuma banida kowa except wannan sarƙar and now i lost everything, my life would never be completed without that Necklace, but you..." ya faɗa yana nuna ta da yatsa 6acin rai ɗauke fal akan fuskar sa yace "You take everything away from me, you took my Mom away from me, sabida duk sadda nake tare da sarƙar nan i feel like am with my Mom, get out of here, idan ina ganin fuskar ki then sake tsanar ki nake" ya faɗa yana juya mata baya. Sosai jikin ta yayi bala'in sanƴi da jin abinda ya faɗa _Kenan wannan Necklace ɗin dake wurin ta diamond ne, amma toh a'ina ya sami diamond Necklace bayan a chan baya rayuwa yake kamar almajiri kuma marar gata, Who is he?_ Shine abinda ta faɗa a zuciyar ta. "Get out" ta sake tsinkayo muryar sa cikin tsawa har tana tsorata. "I.." bai bari ta ƙarasar ba ya juyo tare da kamo hannun ta ya fitar da ita waje yana rufe mata ƙofa a fuska. Tsaye tayi tare da dafa ƙofar tana kuka sosai, sai da tayi mai isar ta kafin taja ƙafafun ta da takeji sunyi mata nauyi ta bar wurin........... ****************** ...........Jafar da ya kai almost two hours yana jiran fitowar ta ne ya hango ta tafe tana kuka. Da sauri ya fice daga cikin motar yana zuwa ya taro ta. "DEENAH?" ya faɗa. Kuka kawai takeyi sosai, riƙo ta yayi ya shigar da ita motar kafin ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar cikin hotel ɗin. Tafiya suke amma babu abinda takeyi sai kuka "I warned you, didn't i?" ya faɗa. "Yaya ka maida ni gida wurin Umma" ta faɗa cikin kuka. Ba tare da ya musa mata ba suka kama hanƴar gidan su, horn ya danna a bakin gate ɗin gidan nan mai gadi yazo ya Wangale masa ƙofar ya kutsa kai ciki. Inda ake parking ya nufa yayi parking motar "Umma bata gida" ya faɗa. Bata kula sa ba ta fito tayi cikin gidan da gudu. Ɗakin ta ta nufa ta sanƴa masa key kafin ta faɗa kan gado tana sakin kuka sosai. Knocking Jafar keyi mata akan ta buɗe ƙofar sai dai taƙi, sai ma sake cusa kanta da take a ƙarƙashin pillow, haka nan ya gaji ya rabu da ita ya fice daga gidan ma baki ɗaya............ ****************** ........."DEENAH has went through alot and still, you aren't ready to forgive her?." Ajiye Pencil ɗin hannun sa yayi ya ɗago ya kalli Jafar yace "Maiyasa ka kawo ta gare ni?." "Sabida tanason ganin ka, nikuma na gaji da ganin ta cikin damuwa kullum, Although na faɗamata meeting you won't do her any good, but dukda haka ta yarda, she just wants to meet you and apologise for her misdeeds." Shiru yayi ya ɗau Pencil ɗin ya cigaba da zane-zanen shi. "Kace baka shirya yafe mata ba, and here you're now kana zanen ta, i just don't understand what kind of person you're" cewar Jafar yana mamakin ZEEYAD ɗin. Murmushin da shi kaɗai yasan ma'anar sa yayi kafin yace "Already na daɗe da yafe mata, i just want to hurt her sabida Necklace ɗina da tayi sanadiyyar 6atar wa." "But maiyasa baka faɗa mata hakan ba?, na baro ta a gida yanzu crying her heart out, she is in deep pain." Shiru ZEEDAN yayi bai ce komai ba, Jafar ganin yayi shiru ne yasa shi faɗin "DEENAH is a good girl...." "I know that, i know she was forced by your Uncle da yayi mata barazanar kashe ka da Mom naku." "Yeah ni na faɗamaka haka, but you doesn't seem to believe me." "Jafar, maybe we should talk about something else" ya faɗa yana ɗagowa ya kalli Jafar. "Yes Sir" ya faɗa. Murmushi yayi kafin yace "Am leaving tomorrow, ka bani bayanai akan yadda business ɗin nan ke tafiya"ya faɗa yana ajiye Pencil ɗin hannun shi............... ********************** .............Rungume take a jikin Umma tana kuka inda ita kuma ke ta lallashin ta. "Umma yaƙi ya yafemin kuma yace wai ya tsane ni, baya ma koh son ganin fuska ta" ta faɗa cikin kuka. "Kiyi shiru haka nan MADEENAH, ni na kasa gane bayanai koh ɗaya da kikayi min bari mu jira zuwan Jafar idan yaso sai ya sanar dani komai dan kuwa ni kai na ya gama ƙullewa." "Umma zafi nakeji a cikin zuciya ta, baya sona kuma bayason gani na." "Ke kam kiyi shiru haka nan mana, za fah ki ɗaurawa kanki wani ciwon fah, kiyi shiru nace miki." Sassauta kukan nata tayi tana sauƙe ajiyar zuciya........... ********************* ...............Umma ce tace "Jafar ni fah kaina ya ƙulle, dagaske ne kaga wannan yaron nan balarabe har ka kai DEENAH wurin sa?." "Kwarai Umma dagaske ne" faɗin Jafar dake danne-danne cikin system ɗinsa. "Dan Allah ni ajiye abin nan haka nan ka saurare ni haba." Rufe system ɗin yayi yace "Ina jin ki Umma." "Bani labarin abinda ka sani game da balarabe." Shiru yayi yana kallon Umma kafin yace "Umma mai kikeson sani game dashi?." "Komai da komai ma" ta faɗa. "Toh ai Umma bakomai bane na sani akan shi." "Naji faɗamin iya abinda ka sani akan sa." "Iya abinda na sani shine shi ɗin Boss ɗina ne, sannan kuma shine mai Mall ɗin da nake aiki a matsayin MANAGER." "Wasa kake koh?." Dariya yayi yace "Umma zancen gaskiya nake faɗamiki, idan ba zaki manta ba Last year da naje ni Kano Interview ɗin aiki a wani Company ɗin sarrafa shinkafa, i was asked to met with the CEO of the Company, and to my surprise Balarabe shi ne mai wannan Company ɗin, Shine ma wanda ya gane ni coz ni ban gane shi ba sabida yadda ya canza, da sunana kawai ya gane ni, na tambaye shi taya akayi ya gane waye ni and then ya bani labarin rayuwar da mukayi dashi a baya, sai kuma anan ne na gane fuskar sa ta faɗo min na gane tabbas Balarabe ne, kuma abinda na sani shine Asalin sunan sa *ZEEYAD AL-ABBAS* Kamar yadda na gani ajiye a Tag ɗin offishin sa, sannan shi ɗin Cikakken Balaraben Egypt ne gaba da baya." Baki Umma ta buɗe tana kallon Jafar nan tace "Sai kuma miye?, ya akayi yayi kuɗi haka har ya mallaki Companies dayawa irin wannan?." "Wannan kuma bansaniba, all i know is he is an artist sannan yana yiwa ƙasashen turawa dayawa aiki, sannan kuma ba ƙaramin kuɗi suke biyan sa ba, i guess zai kai shekaru shida zuwa bakwai yana aiki dasu." "Allahu Akbar, Masha Allah, lallai babu abinda Allah baya iyayi, Allah mai canza tsarin rayuwar mutum cikin sakon ɗaya, bamu san tarihin rayuwar sa ba, amma idan aka bibiya tabbas ya cancanci wannan sabuwar rayuwar tasa." "And yes Umma i heard him talking about wani Necklace that he lost it because of DEENAH, the Necklace is so Precious to him coz it contains his Mom's picture, yace tun yana ƙarami yake tare da Sarƙar but yini ɗaya ya rasa ta sabida abinda DEENAH tayi masa, wannan ne dalilin da yasa har yanzu yakejin haushin DEENAH, but already yace ya daɗe da yafe mata." "Sarƙa?" ta faɗa. "Yes Mom." "Wane irin sarƙa?." "Is like yace it's a diamond Necklace." Idanu ta waro tace "Diamond?." "Yeah." La6e take tana jin dukkanin abinda suke faɗa, komawa tayi cikin ɗaki tana zama bakin bed. "Idan na basa Necklace ɗinsa that means zai dai jin haushi na kenan?" ta tambayi kanta. Miƙewa tayi ta shirya ta fito. "Ina zaki?" cewar Umma. "Umma gidan Mami zanje." "Da wannan daren, mai zakiyi?." "Kaya na zan ɗauko." "Wuce ki koma, kya bari gobe kije ki ɗauko." Tsaye tayi kawai tana kallon su. "Wuce ki koma babu inda zaki da wannan daren." Wucewa tayi ta koma ciki hawaye na kawo mata, indai har bata samu ta kai masa sarƙar zuwa gobe ba da zai koma ba, kenan ba zata sake sanƴa shi a idanu nan kusa ba, har ma ya daina jin haushin ta ba. Tuno da irin maganganun da ya faɗa mata tayi, nan taji zuciyar ta tayi baƙa, but ita ba zata riƙe sa a zuciya ba, dole ne ta danne zuciyar ta ta maida komai ba komai ba............. *********************** ...........Washe gari bayan ta gama ayyukan safen ta Umma ma ta fice zuwa wurin aiki, shiryawa tayi da sauri taje ta gidan Mami. Amirah da Anty Khadija kawai ta tarar a cikin gidan, dan haka ɗaki kawai ta wuce ta sauƙe ƙaramar akwatin ta. Kayayyakin ta ta jera a cikin akwatin nata, kafin ta shiga neman ƙaramar jakar ta da ta sanƴa sarƙar a ciki. "DEENAH mai ya faru, mai kike nema, maiyasa jiya baki dawo gida ba?" cewar Anty Khadija cikin jero mata tambayoyi. "Abuna...jaka ta nake nema wani baƙin purse baku ganshi ba?." "Wane Purse?" cewar Anty Khadija. Kallon Amirah tayi tace "Amirah wannan purse ɗin da kika ga na sanƴa sarƙar nan a ciki, ina kika ga na ajiye shi?." Tunani Amirah ta tsaya yi kafin tace "A cikin wardrobe naga kin saka ai koh?." "Ban ganshi ba" ta faɗa tana cigaba da bincika wa. Nan suka shiga taya ta dubawa kawun ta jiyo Anty Khadija na faɗin "Shi ne wannan?" tana ciro shi daga lungu. Da sauri tazo ta kar6a hannu na rawa ta buɗe shi ta ciro sarƙar. Murmushi tayi tace "Shi ne" ta faɗa kuma tana barin ɗakin cikin gudu. Duk da Kallo suka bita cike da mamaki. Koh da ta fita adaidaita ta tara ya kaita har cikin hotel ɗin da yake. Bata yi wata wata ba ta isa ga flour ɗin da yake. Kafin ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin ta shiga Knocking. Handle ɗin ta murɗa ta ji shi a rufe, nan ta cigaba da knocking kamar zata 6alla ƙofar tana faɗin "Gashi nan na kawo maka sarƙar." "Hajiya lafiya dai?" cewar wani Ma'aikacin hotel ɗin. "Yauwa...dan Allah mai ɗakin nan, yana ina?." "Ohh ai ya kai awa ɗaya da barin cikin hotel ɗinnan" ya faɗa yana kallon ta. "Ya tafi?" ta faɗa a hankali kamar zata yi kuka. Wucewa kawai yayi yayi tafiyar sa ya bar ta nan tsaye................ *_Zan dinga posting ranar Asabar amma banda Lahadi_* *Idan kin karanta kiyi sharing saboda Allah*👏🏽 *MHIZZ JIDDHERR................✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *018...* _Kuyi haƙuri yau na gantalar daku👏🏽😰_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *_Banyi Editing ba_* ................Barin ta hotel ɗin babu inda ta nufa sai wurin aikin Jafar, koh da taje dakyar aka bar ta ta shiga dan kuwa ba waya ce da ita ba balle tace zata kira shi. Kuka ta sanƴa mishi tana faɗin "Yaya ya tafi naje ni ban ganshi ba." Zaunar da ita yayi yace "Wa kenan?." "Balarabe, naje ni inda ya sauƙa ban ganshi ba." "Balarabe yana nan, he is in the Gym." Miƙewa tsaye tayi tace "Really, he is here?, Dan Allah Yaya ka nuna min ta inda yake, inaso nayi magana dashi ne please." "DEENAH, why are you behaving like this, ki bar shisshige masa haka nan please" ya faɗa yana samun wuri ya zauna. Kwa6e fuska tayi tana zuwa kusada shi tace "Dan Allah yaya, ka kai ni wurin sa abin sa kawai nakeso na basa ba wani abu ba." "Abun sa, what's that?." "Sarƙar sa, sarƙar sa na wuri na all this while." "What, how comes, sarƙar sa na wurin ki?." Kai ta jinjina masa tace "Eh." "But how...how comes ya akayi sarƙar yazo wurin ki?." "Ranar nan ne, da mukaje Umma taje yin bailing nasa, a ranar ne sarƙar ya faɗo daga wuyar sa, and i silently took it ba tare da sanin kowa and i kept hiding it har izuwa yau." Sarƙar ta ciro ta nuna masa tace "Here." Idanu Jafar ya waro yana kar6ar sarƙar yace "This..diamond Necklace ɗin ne wannan?." Kai ta jinjina masa tace "Dan Allah yaya ka kai ni wurin sa." "Sure" ya faɗa yana miƙewa tsaye tare da damƙa mata Sarƙar yace "muje." Da sauri tayi gaba tana ficewa daga office ɗin, waje suka tare da nufar motar sa suka shiga. Sun ɗanyi tafiyar da bai wuci 3mins a mota ba suka iso gym ɗin. Da sauri ta buɗe ta fito tana nufar hanƴar cikin Gym ɗin, nan yace da ita "Ba nan ba, that way" ya faɗa yana nuna mata wani hanƴa ta chan ƙarshen building ɗin. Biyo sa tayi suka nufi wurin har zuwa hawa na uku. Sosai floor ɗin ya sha tsaruwa da haɗuwa, ɗaki na uku ya nufa tare da danna wasu codes ƙofar ta buɗe da kanta suka kutsa kai ciki. Zaune ta ganta da wani ɗingilelen riga sai kuma matsetsen mini-skirt a jikin ta tana daddana waya. Sosai ƙaton ɗakin ya ƙawatu da abubuwan motsa jiki kala daban-daban. (Nidai ba sanin sunan su nayi ba balle na lissafo muku su🥴). Daga chan ƙarshen ɗakin yake zaune cikin gym wears ɗinsa baƙaƙe har takalmin ƙafar sa, yana motsa hannun sa da wata nannauyar ƙarfe. Ganin ta yasa shi ajiye ƙarfen nan yana sake tsuke fuska a zuciyar sa yace _Am just sick of seeing her everyday_ tare da kauda kai kamar bai gansu ba. Samun kujera tayi ta zauna akai tana kallon Surayya da kallo ɗaya kawai tayi musu tare da kauda kanta zuwa ga wayar ta. "Excuse me ma'am, please ina sir yake?" faɗin Jafar ɗin yana tambayar Surayya dan kuwa bai ga ZEEYAD ɗin ba. Kamar ba zata amsa masa ba tace "Yana chan ciki." "Come on" ya faɗa yana kallon DEENAH, nan ta tashi tare da mara masa baya. "Who is she?" DEENAH ta faɗa cikin hankali. "Shushh" kawai ya faɗa suna ƙarasawa chan ciki. Zaune suka same sa inda Jafar yace "Sir." Ɗagowa yayi ya kalli Jafar nan ya tashi tsaye yana ajiye abinda yake motsa hannun nasa yace "I told you kada ka sake kawomin ita nan." "Sir tanason yin magana ne da kai." Wucewa kawai yayi yana ɗaukar ƙaramar toilet ya shiga goge fuskar sa. Nan duk suka mara masa baya. Ruwa Surayya ta miƙa masa nan ya amsa tare da furta "thank you" yana samun wuri ya zauna. "Sir maybe i should get going" juyawa yayi ga DEENAH yace "Idan kin gama kizo ki same ni" ya faɗa yana shirin wucewa. Riƙo sa tayi tace "Ka tsaya na bashi sai ka tafi" ta faɗa a hankali. "DEENAH baki ga na bar mutane dayawa suna jira na ba?, idan kuma so kike muje mu dawo bayan na sallame su shikenan." Sakin sa tayi tace "Okay." Murmushi yayi ya wuce yana ficewa. Tsaye tayi a kansu kamar wacce aka dasa tana bin su da kallo ta ƙasan ido. Sosai take mamakin ganin sa tare da christian, bayan ya gama ci mata mutuncin tana bin maza amma yau ga shi tare da karuwa a wuri ɗaya. Muryar Surayya ta tsinkayo tana faɗin "Babe, jibi birthday ɗina, what kind of gift are you buying me?." Ɗan ɗagowa tayi ta kalli Surayya ɗin kafin kuma ta sake sunkuyar da kai. Ɗan satar kallon DEENAH yayi yace "What do you want?." Cike da zumuɗi Surayya tace "Really, kana nufin duk abinda nakeso?." "Yeah" ya faɗa. "Alright, tunda kace haka so nake ka turo gidan mu a sanƴa mana ranar aure" ta faɗa cikin murmushi. Kallon ta yayi shima yayi murmushin yace "Done." "Oh really?, Oh my GOD thank you, I love you" ta faɗa cike da jindaɗi tana tasowa daga inda take zaune ta rungume shi. DEENAH ji tayi wani irin abu ya tokare mata zuci nan tace "I want to talk to you." Murmushin gefen baki ZEEDAN yayi yace "Talk." "Not here" ta faɗa kamar zatayi kuka. "Not here, a'ina kenan?." "Maybe somewhere else." "What do you want from me, i told you that i despised seeing your face, didn't i?." Shiru tayi tana kallon sa da Surayya da har yanzu bata bar jikin sa ba tace "Fine then, am leaving" ta faɗa tare da juyawa da niyyar barin ɗakin. Da sauri ya ture Surayya dake jikin sa yana aika mata da wani irin mugun kallo kafin ya maida duban sa gun DEENAH dake kiciniyar buɗe ƙofar amma ta kasa. "Kin manta ne sai kin sanƴa code kafin ƙofar ta buɗe?." Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba zuciyar ta nayi mata zafi. "Come let's talk then" ya faɗa yana juyawa yayi inda ya fito. Juyowa tayi tare da mara masa baya tana satar kallon Surayya dake bin su da kallo. Tsayawa yayi tare da zuba hannaye cikin aljihu yace "Tell me." Ɗago da watery eyes ɗin ta tayi ta zuba masa, taune le6e yayi tare da kawar da kai gefe. Goge hawayen nata tayi tace "Inaso na baka wani abu mai muhimmanci but you aren't ready to listen to me." Ta ƙasan idanu ya kalle ta nan yace "Something important?" he then chukles and said "You have nothing important to give me, wait" ya faɗa yana kallon ta kafin ya ɗaura da faɗin "Something important kina nufin kin jawo ni nan ne dan ki danne ni kiyimin abinda kika saba?, i see nothing important left in you..." "Stop this, stop it, i have had enough of this, maiyasa kake danganta ni da irin mummunar abin nan ne?." "Because that's what you're." "Kana yi min abubuwan nan ne duka dan kawai kanajin haushin 6atar sarƙar ka da nayi sanadiyya right?" ta faɗa cikin sanƴin murya. Magana zaiyi nan ta ciro sarƙar tana nuna masa. Da sauri ya kai hannu zai ɗauka tayi saurin damƙe shi a hannun ta tana kawar dashi. "My..m..my...that's my Necklace" ya faɗa cikin rarrabewar harshe idanun sa akan hannun nata yana ƙoƙarin kar6a. Sake damƙewa tayi a cikin hannun ta tace "Sabida shi ne ka tsane ni kuma baka son gani na isn't it?, ka faɗamin baƙaƙen maganganun da sukayi matuƙar ƙona min zuci duk dan abinda ya faru shekaru goma da suka wuce." "Give it" ya faɗa. "Zan baka sabida mallakin ka ne, but you've to admit your mistake for insulting me first, and you've to apologise." Wani irin kallo ya zuba mata jin abinda ta faɗa, wato ya bata haƙuri. "Apologise now" ta faɗa tana kallon sa. Iska ya furzar yana sake kallon ta from down to top. "Kana targeting yadda za'ayi ka kwace ne, toh ba zaka iya hakan ba, sabida ba zan bari ba nima har sai ka bani haƙuri." Resting bed ɗin dake wurin ya samu ya kwanta yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tare da lumshe idanun sa. Mamaki ne ya kama DEENAH nan tace "Do you think am joking, ba zan baka ba har sai ka..." "Toh ki bushe tsaye anan mana" ya faɗa kafin ya sake lumshe idanun sa. "What!?" ta faɗa. "Alright then, am leaving" ta faɗa tana juyawa ta bar wurin tare da nufar ƙofar direct da niyyar buɗewa ta fita. Ji tayi wani irin kunƴa ya zubo mata, dan kuwa batasan pin ɗin buɗe ƙofar ba. Satar kallon Surayya dake bin ta da kallo tayi kafin kuma ta sake jan ƙafafu ta koma inda yake tare da yin tsaye akan sa. Fuskar sa ta ƙurawa idanu tana kallo babu koh kyaftawa tana jin wani abu na taso mata daga ƙasan zuciya tare da bin surar jikin sa da kallo. Saurin kauda idanun ta tayi nan ta tsinkayo muryar sa yana faɗin "Da alamu zaki iya yi min fyaɗe da wannan kallon da kike yimin ɗin" ya faɗa yana tashi zaune. "Give me the Necklace" ya faɗa yana kallon ta daga zaunen da yake. "Apologise first" ta faɗa. Kai ya jinjina yana miƙewa tsaye kamar mai shirin make ta hakan yasa ta jan baya da sauri. "What?" ya faɗa yana kallon ta. Tsuke fuska tayi tace "Ka buɗemin ƙofa." Murmushi yayi jin yadda tayi maganar nan yace "Na buɗe miki ƙofa while kuma kina riƙe da farin ciki na, do you think kwakwalwa ta irin naki ne?." Matsowa yayi kusa da ita yace "give me the Necklace." 6oye hannun sarƙar tayi a bayan ta tana sake tsuke fuska. "Give it" ya sake faɗa. Sake matsowa yayi daf da wanda har yana jin sauƙar numfashin ta akan fuskar sa yace "Give me the Necklace or else i will kiss you." Da sauri ta ɗago ta kallesa, nan take kuma hawaye ya taru a idanun ta, kwafa tayi tare da ciro hannun daga bayan ta ta buɗe masa. Tsaya kallon Necklace ɗin nasa yayi yana murmushi kafin ya sanƴa hannu ya ɗauka tare da sumbatar sa. "Finally, you're now back to me, 6arawo kuma yaji jiki" ya faɗa yana damƙe sarƙar a hannun sa. Magana zatayi nan yace "Don't you dare say anything, so kike ki musa kice ba sata kikayi ba right?, i know abinda kike shirin faɗa kenan, can you remember ten years back lokacin da kike kallon sarƙar since from that day na fara zargin yayi miki kyau kuma kike son satar sa, but you know what a kullum bana gajiya da sallahn dare akan Allah ya bayyanar min da 6arawon sarƙa ta, then boom finally ashe kece." "I didn't steal it." "Ohh really, kuka zakiyi?, koh dayake dama marasa gaskiya idan aka carke su a lungu sun iya ƙirƙiro kuka dan aji tausayin su, but that won't work on me." Wucewa zatayi nan yayi saurin dafa bangon yana tare ta yace "Where do you think you're going?, am not done with you yet." "Mai kuma kake so?." Shiru yayi yana kallon ta yadda hawaye suka taru a idanun ta, kafin kuma cikin calm voice nasa yace "Thank you." Da sauri ta ɗago da idanun ta tana kallon sa, nan ya sake faɗin "You returned my Happiness to me, so ya zama dole na gode miki, and i can't believe yadda kika iya ajiyan shi har tsawon wannan lokacin, you're unbelievable and amazing." Batasan sadda murmushi ya su6uce mata ba, nan ta share hawayen ta zuciyar ta fal da farin ciki. "I guess i should gift you something." Ɗago da idanun ta kawai tayi tana kallon sa nan yace "Tell me, tell me dukkanin abinda kikeso and i promise to give it to you no matter how expensive it is, koh da kuwa ba anan ƙasan yake ba i promise to get it for you komin nisan inda yake" ya ƙarashe yana kallon cikin idanun ta. Sunkuyar da kai tayi tana murmushi ba tare da ta iya cewa komai ba. "Hey look, don't be shy Okay, just tell me dukkanin abinda kikeso, please" ya faɗa pleadingly. "Kayi alƙawarin dukkanin abinda nakeso zakayi min shi." "Yeah i promise." "I...i...i..." "Come on tell me" ya sake faɗa. "I...i want..." "You want what, get away from her" ta faɗa tana janƴe ZEEDAN ɗin, tare da ɗaukar hannu tana shirin kwaɗawa DEENAH mari taji cak hannun nata a sama. ZEEDAN tabi da kallo tace "You're mine, you have to understand that, who the hell is she?" ta faɗa kamar zata shaƙo DEENAH da tayi tsuru-tsuru da idanu. Sakin hannun nata yayi yace "Are you trying to raise your hand on her, infront of me?" ya faɗa cikin 6acin rai. Kallon DEENAH tayi tace "Ke, who the hell do you think you're?, why are you so closed to him, he is my Man, no one else can have him, understand?" ta faɗa tana nuna DEENAH da tayi tsuru-tsuru da idanu tsoro fal a cikin idanun ta da yatsa. "Do you wanna know who she is?" ya faɗa calmly cike da kwanciyar hankali yana samun wuri ya zauna. Murmushi yayi yana kallon DEENAH yace "She is that little cutie." "Look ZEEDAN, ya kake behaving as if nothing big is wrong here?." Kallo ya ƙare mata tsaf yace "Babu wani babban lamari dake faruwa anan, if you want something big to happen then just try raising your hand on her." "ZEEDAN you're mine..." "Am not yours, and i will never be yours Surayya" ya faɗa cike da mugun jin haushin ta. Zuwa tayi ta zauna kusa da shi tana kamo fuskar sa tace "Look ZEEDAN, ka ƙaremin kallo da kyau babu abinda yarinƴar nan zata nunamin, she is not that beautiful, na fita komai why don't you just concentrate on me?." Tashi tsaye yayi ya ƙarasa gaban DEENAH da duk hawaye ya gama wanke mata fuska yace "Who told you that?, only i can see how beautiful she is, her wide captivating innocent eyes and how her cute her face is, only i can see that, i don't care whether kin fita kyau or ta fiki all i know is that babu wacce nakeso a cikin ku, so why all the misunderstanding, she is not my girlfriend i told you to stop stressing yourself like this, you're just wasting your time on me" ya ƙarashe yana juyowa ga Surayya ɗin. "Lies, you're lying to me" cewar Surayya. "Alright then, continue wasting your time pursuing me" ya faɗa yana yin gaba. Da sauri ta mara masa baya. DEENAH kuwa ta rasa mai takeji a zuciyar ta, ta rasa daɗi zata ji koh haushi. Zubewa tayi zaune anan wurin tana sakin silent kuka. Sai da ta ɗanyi mai isar ta kafin ta goge hawayen ta ta miƙe ta bar wurin. Tsaye ta gansu shi da Surayya da ta ƙanƙame sa ta baya tana kuka fuskar nan tasa a matuƙar murtuƙe. Wucewa tayi zuwa bakin ƙofa ta tsaya ba tare da tasan abinda zatayi ba, dan kuwa batasan code ɗin buɗewa ba. Juyowa tayi ta kallesa nan taga shima ita yake kallo, saurin kauda face nata tayi tana sake jin zuciyar ta na zafi, haushin sa da na yarinƴar da taji ya ƙira da Surayya wacce sam batayi kama da musulmai ba duk ya gama cika mata zuci. So kawai take ta tafi ta daina kallon su koh zata ji sassauci a ranta. _Ashe haka Balarabe yake bashi da kunƴa koh kaɗan, i thought he is a good guy_ ta faɗa a zuciyar ta tana sake juyowa ta kalle su. Saurin sake kawar da kanta tayi tanajin wani irin abu da batasan koh miye bane na taso mata daga chan ƙasar zuciya. "Dan Allah don't do this to me i beg you" ta jiyo muryar Surayya. "It's alright Stop crying" ya faɗa cikin rarrashin ta yana share mata hawaye, yau cike yake da farin ciki but this Surayya na neman 6ata masa mood. DEENAH ganin yana share mata hawaye ba ƙaramin sake ƙulewa tayi ba, but ta dake dan ganin gudun ruwan su da ƙarshen iskancin su. Bata ankara ba taji yana ƙoƙarin sanƴa pin ɗin buɗe ƙofar. Buɗuwa ƙofar tayi, ɗagowa tayi ta kallesa nan yace "You should get going." Sosai taji zafi, nan kawai tasa kai ta fice da gudu trying so hard ganin ta riƙe kukan dake son zuwan mata. Da kallo ya bita, haka kuma kurum yakejin rashin daɗin hakan a ransa, ta6e baki yayi tare da wurgawa Surayya mugun kallo yana wani jin tsanar ta da haushin ta na ƙaruwa masa a zuci. Ficewa yayi shima tare da mara mata baya................ *Yawan Comment, yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *019...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ...............Da sauri yabi bayan DEENAH da har ta fice zuwa flour ɗin ƙasa. Tsayawa yayi ta sama tare da kiran sunan ta "MADEENAH?" ya faɗa. Cak DEENAH taja ta tsaya tana jin zuciyar ta nayi mata zafi sosai, nan tayi saurin goge hawayen fuskar ta. Sauƙowa yayi ya tako zuwa inda take tsaye yana kallon ta, kafin a hankali ya sake cewa "MADEENAH." Kallon sa tayi suka haɗa ido nan tayi saurin kawar da nata idanun. "Am Sorry" ya faɗa cikin sanƴi. Kallon sa tayi tace "Sorry...for what?." "I said alot of bad things about you, and i know you..." "It's alright, If you think am bad that won't hurt me, my family knows who i really are and they have trust and believe in me, dah suna suka faɗamin abubuwan da ka faɗamin then i would be sad forever, but kai a matsayin ka na wanda bansaniba bansan komai akan sa ba, haka kuma baisan komai a kaina ba maiyasa zanyi fushi dan ka kiraye ni da sunayen banza?." Shiru yayi yana kallon ta cikim cize baki. "Ohh kana tunanin ina takurawa rayuwar ka koh?, all this while abu biyu ne kawai ya sanƴa ni faɗawa halin neman ka, kuma kake tunanin kamar ina shisshige maka ne, na farko dan na nemi yafiyar ka, na biyu kuma dan na baka sarƙar ka dake tare dani nothing else, look MADEENAH ba kamar cheap ladies ɗinnan da kake hanging around dasu kullum bane, i have my own way of living, kana tunanin dah ba dan dalilai biyun nan ba zaka sake gani na ne kuma anan?" Kai ta girgiza sannan ta cigaba da cewa "Koh da inuwa ta ba zaka gani ba, and now Alhamdulillah finally babu komai tsakanin mu kuma, a yanzu zanyi bacci cike da kwanciyar hankali sannan zanyi farin ciki, dariya dama kuma walwala kamar kowa" ta ƙarashe cikin murmushi tana kallon sa. Sosai ya sha jinin jikin shi, hannaye kawai ya zuba a aljihu yana kallon ta. Juyawa tayi ta cigaba da tafiya kafin kuma ta tsaya ta juyo tace "And yes, kada ka wani sanƴa damuwa a ranka saboda ni, coz a yanzu na dawo maka da farin cikin ka, yakamata ka saki fuska kayi dariya cike da farin ciki, koh da murmushi ma kayi sabida koh bakomai zai ɗan ƙara maka lafiyar zuciya" tana faɗin haka ta sanƴa kai ta fice. Da kallo ZEEDAN da ya rasa ta cewa ya bita yanajin jikin sa yayi sanƴi, shikenan kuma yanzu ya rasa ta yadda zai kuma sanƴa DEENAH a idanun sa, all this abin nan da yakeyi mata dan kawai ya ringa sanƴa ta a idanun sa ne, tun ranar da ya ɗaura idanun sa akanta idanun ta sukayi captivating nasa yakejin wani abu game da ita, but he can't just tell what it is, but now yayi realizing DEENAH is part of farin cikin sa ne, and now she is getting away of his hand. Haka nan ya gama tsayuwar sa anan wurin ya juya ya koma ciki.............. ********************** ..........Office ɗin Jafar ta nufa baya ciki hakan yasa ta zaman jirar sa. Bayan kamar Mintina goma ya shigo, ɗagowa tayi ta kallesa fuskar ta na fitar da murmushi. "Hey, you looks happy" ya faɗa yana samun wuri ya zauna. Murmushi tayi tace "Yaya na basa Necklace ɗinsa and he was so very happy." "Uhm i can see that, shiyasa kema kika kasance cikin farin ciki?." "No, am just happy ne kawai dan na rabu da nauyi." Murmushi yayi yace "Am so happy for you, atleast kullum zaki kasance cikin farin ciki yanzu." Murmushi tayi tare da jinjina kai tace "Yauwa yaya ni zan koma gida yanzu, idan ka tashi dawowa ka tahomin da abin daɗi sannan ka saya min waya." Idanu ya zaro cike da mamaki yace "Phone?." Kai ta jinjina tana murmushi. "So finally, kinyi deciding ki fara riƙe waya?." Kai ta jinjina cikin murmushi. Murmushi shima yayi yace "Alright, i would make sure na sayo miki brand new Phone na yayi." "Thank you so much blood" ta faɗa cike da jindaɗi. "Never mind dear." "Muje ka saya min Ice-cream sai na tafi gida." "Toh sarkin shan ice-cream, muje mu." Miƙewa tayi daga zaunen da take, hannu ya sanƴa a kafaɗun ta kamar wasu abokai suka fice......... *********************** ...........Zaune take kan bed ɗinta da takarda da biro a hannu. Nazarin abinda zatayi ta fara, kafin kuma cikin zazzaƙar muryar ta ta shiga rero waƙa tana rubutawa. _I used to think that_ _I would never fall in love_ _And then you showed me_ _That you could be everything I want_ _I gave my heart away_ _They put it on a shelf_ _And took it down only to break it into pieces_ _And then you came around_ _Picked me up off the floor_ _You put me back together_ _I couldn't believe it_ _Let me get this straight_ _You don't want to date_ _You just wanna be someone I can always turn to_ _Right until the end_ _Can you say that again?_ _I'm sorry, I just wanna make sure that I heard you_ _I waited for you my whole life_ _You don't know what you mean to me_ _If you asked me to be your wife_ _I would turn around and say_ _You mean to tell me that_ _I could have you whenever I want_ _I could tell you that I love you when you love me too_ _No more waiting, forever our love_ _But I would wait all over again_ _If it means I get you_ _I never been more sure of the unknown_ _Just wanna show you how far my love goes_ _You mean to tell me that you feel the same?_ _Then, baby, I'm here to stay ehh_ _I can't believe that I found the one_ _Yeah, my search is done now_ _When you said to me_ _Will you be my wife for the rest of my life?_ _For better or worse_ _Baby, no, these ain't just words to me_ _So take me to your home_ _We'll be forever and ever_ _Every woman deserves a king_ _You mean the world to me,_ _yeah_ _We could be everything_ _Together just us_ _I waited for you my whole life_ _You don't know what you mean to me_ _If you ask me to be your wife_ _I would turn around and say_ _You mean to tell me that_ _I could have you whenever I want_ _I could tell you that I love you when you love me too_ _No more waiting, forever our love_ _But I would wait all over again_ _If it means I get you_ _I've never been more sure of the unknown_ _Just wanna show you how far my love goes_ _You mean to tell me that you feel the same?_ _Then, baby, I'm here to stay ehn_ _Anywhere in the world_ _I would go with you_ _(I would go with you, babe)_ _We could be anywhere in the world_ _As long as I'm with you_ _(As long as I'm with you, babe)_ _And I can't wait_ _No, I can't wait for you, babe (no, I can't wait)_ _I can't wait for your love (to be with you, baby)_ _For the rest of my days, yeah (for the rest of, rest of my days)......._ Knocking ɗin da taji a bakin ƙofar ɗakin ta ne ya sanƴa ta dakatawa tana maida duban ta kan ƙofar. Ajiye takarda da Biron tayi tana miƙewa daga kan gadon ta sauƙo. Zuwa tayi ta buɗe ƙofar nan taga Umma tsaye. Murmushi tayi tace "Umma, yaushe kika dawo?." "Ina zaki san yaushe na dawo, ace mutum kullum yana cikin ɗaki maƙale yawa sabuwar amarya, fito kizo kije cikin gari ki iyo mana siyayya gobe zamuyi baƙi" ta faɗa tana komawa. Bin ta DEENAH tayi tace "Baƙi kuma ummi, su waye zasu zo?." "Ke ni kinga banason surutu, ɗauko biro da takarda kizo kiyi list kada ki manta." "Toh" kawai ta faɗa tana komawa cikin ɗaki. Paper ta tsinka tare da ɗaukar biro ta fito. Zama tayi kusada Umma tace "Umma mai da mai za'a saya?." "Kiyi figuring abinda yakamata ayi musu kawai sai ki iyo siyayyar." Tunani ta shiga yi kafin tace "shikenan toh, ki kawo kuɗin." ATM Umma ta ciro ta miƙa mata tace "Ki sayo da Stock fish bamu dashi a gida kizo kiyi mana faten doya muci da rana." "Toh Umma, bara naje na shirya" ta faɗa tana tashi ta shige ciki........... ******************** ............Tsaye take a kitchen tana girki ƙamshi sai tashi yake, Umma ce ta leƙo tace "Ohh ni Faɗimatu, har yanzu abincin nan baiyi ba sai ƴunwa ta gama kwaƙule min ciki?." "Umma saura kaɗan yanzun nan zaiyi." "Toh ai shikenan, dan Allah dai kiyi sauri." "Toh Umma" ta faɗa tana jujjuya abincin nata. Bayan ta kammala ne ta zuba a cikin warmer mai kyau ta kai musu shi falo. Komawa tayi ta ɗauko plate da spoon, kafin ta wuce fridge ta ɗauko musu ruwa da drinks. Serving tayi a plate ta ajiyewa Umma nata kafin itama ta ɗeba akan plate ta fara ci. "Umma" ta faɗa. Ɗagowa Umma tayi ta kalle ta nan tace "Umma, ki canza min makaranta." Kallon ta Umma take kafin tace "Maiyasa?." "Ni makarantar baya burgeni, ki nema min transfer zuwa wani." "Toh shikuma first semester ɗin da kikayi fah?." "Umma nidai kawai banason makarantar ne, nafison kawai ki maida ni University banason Nursing ɗinnan" ta faɗa cikin tsuke fuska alamun dgsk bata so ɗin. "Toh shikenan ai, bari yayan ki ya dawo." Cike da jindaɗi tace "Yauwa Umma ta, shiyasa nake Ƙaunar ki."........... ********************* *TWO WEEKS AFTER* ............Wayar ta dake ajiye kan Dressing mirror ɗinta ne ya hau ruri. Da sauri ta shigo cikin ɗakin nata tana ɗagawa taga sunan dake yawo a jiki take fuskar ta ta sauya zuwa 6acin rai. Har ta tsinke bata ɗaga, nan ta sanƴa wayar a silent dan kuwa tasan indai bata ɗaga ba, ba zai ta6a gajiya da kiran ta ba, musamman ma da yake bashida zuciya koh kaɗan, itakuwa sam batason hayaniya. Ficewa tayi daga ɗakin tana 6ata fuska taje ta cigaba da gyare-gyaren da takeyi a falo. Tana cikin gyarar ne Jafar ya fito daga ɗakin sa yace "DEENAH?." Ɗagowa tayi ta kallesa nan yace "Maiyasa ana kiran ki bakya picking call?." "Babu" kawai ta faɗa tana cigaba da aikin ta. "Look DEENAH maiyasa kikeyin haka, atleast yakamata ki basa dama ku fahimci juna right?." "Yaya ni nace banaso, ni banason sa ya daina kira na" ta faɗa kamar zatayi kuka. "DEENAH, what's wrong with you, idan bakyason shi then waye kike so?, yakamata ki fahimce shi kinsan fah babu kyau wulaƙanci koh?." Shiru kawai tayi ta tsaya tana kallon shi. "DEENAH bansanki da haka ba, dan Allah ki saurare shi kinji?." "Sabida kawai ka haɗa ni da Allah zanyi" ta faɗa tana komawa cikin ɗakin ta. Wayar tata ta ɗauka nan taga almost ten missed calls, bata kai ga ajiye wayar ba wani kiran ya sake shigowa. Picking tayi tare da karawa a kunnen ta, ajiyar zuciya taji ya sauƙe tare da yi mata sallama. "Wa'alaika salam" ta amsa a takaice. "Ina ƙofar gidan ku" kawai yace tare da katse kiran. Da wani irin mugun harara tabi wayar kamar ta fashe da kuka haka takeji. Dogon Hijabin ta kawai ta zura tana ficewa daga cikin ɗakin. Cikin gidan kawai ta fito taje wurin mai gadi gaisawa sukayi kafin tace "Tijjani dan Allah ka leƙa waje zakaga wani kace dashi ya shigo." "Toh ranki ya daɗe" ya faɗa yana ficewa zuwa waje. Ba'a jima ba ya dawo tare da wanda yaje ɗaukowa ɗin. Kallo ɗaya tayi masa kawai ta kauda idonta kafin ta fara tafiya. Murmushi yayi ya mara mata baya. A tsakar gidan ta fito da plastic chairs ta ajiye da table, kafin ta koma cikin gidan. Abubuwan ciye da sha ta jero masa akan tray ta fito fuskar nan tata a matukar tsuke. Akan table ɗin ta ajiye, kafin taja ɗayan kujeran ta zauna. Kallon ta guy ɗin yayi murmushi ɗauke akan fuskar sa, kyakkyawa ne babu laifi sannan kuma yana da ɗan haske ya haɗe cikin brown ɗin shadda sai zuba ƙamshi yake. "Ina yini Hajiya?" ya faɗa yana kallon ta. Tsaki taja a ranta jin ya kira ta da Hajiya "Lafiya" kawai ta amsa tana sake kauda kai tare da tsuke fuska. "DEENAH, mai nayi miki ne haka kika tsane ni?." "Ni ban tsaneka ba" ta faɗa. Murmushi yayi yace "Amma gashi nan bakya son gani na, kuma idan na kira ki bakya son ɗagawa, haka ma idan nayi miki magana ta whatsapp bakya replying, i don't know why." Shiru tayi kafin tace "Banida lokaci ne." Murmushi yayi yace "Please DEENAH na roƙeki da Allah ki bani dama na gwada miki sirrin dake cikin zuciya ta, i fell inlove with you at first sight, tun ranar nan da na ganki naji na kasa samun nutsuwa a raina, dan Allah ki bani dama nikuma nayi miki alƙawarin ba zakiyi regretting damƙa min zuciyar ki ba." Shiru tayi bata basa amsa ba, dan kuwa koh muryar sa haushi take bata bale kuma tace zata kula sa. "Please DEENAH, ni mai ƙaunar ki ne tsakani da Allah, ki bani dama nikuma nayimiki alƙawarin shayar dake farin ciki, DEENAH kaso mai sonka yafi kaso mai ƙin ka." Shiru tayi kafin kuma tace "Naji, bakomai na baka dama, ka shayar dani farin ciki kamar yadda ka faɗa ɗin." Murmushi ya sake cike da farin ciki ya hau yi mata godiya. "Kada ka godemin tukun, ka bari har sai na fara sonka kamar yadda kake sona kafin ka godemin sannan kuma kayi farin ciki." Kai ya jinjina yace "Insha Allah wannan ma ba zata gagara ba, insha Allah zaki soni kamar yadda nakeson ki, sai dai fah idan kin tashi sona ɗin kada kiyimin wanda zai zarce wanda nakeyi miki, idan ba haka ba kuma babu ruwan Abdul." Ji tayi wani irin haushi ya turnuƙe ta "Allah ma ya kiyaye, sai anjima" ta faɗa tana tashi ta koma ciki. Da kallo yabi ta tare da yin murmushin farin ciki kafin kuma shima ya miƙe ya tafi.............. *Kun ganshi kaɗan koh?, zan cigaba anjima* *Yawan Commew, yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *020...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..............Zaune yake idanun sa akan fakeken plasma TV ɗin dake manne jikin bangon office ɗin nasa, kallo kawai yake sai dai sam tunanin sa da hankalin sa na wani wurin daban. Sosai fuskar sa take matuƙar ɗaure yawa wanda yaci guna. Ƙofar office ɗin ce ta buɗe wani ya shigo hannayen sa riƙe da wasu documents. "Good afternoon sir" ya faɗa. Hannu kawai ya ɗaga masa alamun amsawa ba tare da ya juyo ya kallesa ba. Rissinawa yayi yace "Sir, ga nan files ɗin nan komai ya kammala, sa hannun ka ne kaɗai ya rage" ya faɗa cikin tura masa files ɗin. "Alright" kawai ya faɗa ba tare da ya ɗago ɗin ba. Rissinawa ya sake yi tare da ficewa daga cikin office ɗin. Idanun sa ya maida ya lumshe yana ɗan jujjuyawa akan kujerar da yake gefe da gefe. Karar buɗewar ƙofar da ya sake ji ne ya sanƴa sa buɗe idanun sa, inda fitinannen turaren ta ya dako masa hanci. Sanƴe take cikin jan riga da black trouser wanda sukayi matuƙar amsar jikin ta tare da bayyanar da duk wata sura ta jikin ta, fuskar ta manne da ƙatuwar baƙar shade bakin nan nata ya sha red lipstick sai yalƙi yake, kyakkyawa ce sosai. "Hello honey" ta faɗa. Bai ɗago ya kalle ta ba sai ma yi da yayi kamar baisan da wanzuwar ta ba a wurin, dan kuwa a yanzu yaji yayi mugun tsanar ta, sai dai har yanzu taƙi rabuwa dashi yana ɗaga mata ƙafa ne kawai domin mahaifin ta. Kujera taja ta zauna tana kallon sa tace "Honey?." Juyo da kujerar yayi ya zamto yana fuskantar ta. Kallon da yakeyi mata ne ya sanƴa ta shan jinin jikin ta, sai dai da yake gogaggiya ce ita ta dake tana sake gyara zamar ta ba tare da ta sake kallon sa ba, dan kuwa a duk sadda yakeyi mata wannan kallon bata ta6a iya haɗa idanu dashi komin iskancin ta, dan kuwa da zarar ta haɗa idanu dashi zataji ba zata iya yi masa komai ba, shiyasa duk wani abu da zata yi masa sai dai ta kalli fuskar sa ba dai cikin idanun sa ba. Wani abu ya danna, cikin abinda bai wuci minti.ɗaya ba ƙofar ta buɗe Secretary ya shigo. "Yes sir" ya faɗa cike da girmamawa. "Get her out of my sight" kawai ya faɗa yana komawa ya jinginu da kujerar da yake kai tare da lumshe idanun sa. Magana Secretary zaiyi mata nan ta wani daka masa tsawa tare da wurga masa harara tace "Notin kanka ya kunce ne, yace ka fitar dani daga nan kuma dayake bakada kunƴa sai kuma kace zaka buɗi baki kacemin na fita, let's see uban wanda ya isa ya fitar dani daga office ɗinnan mtssswww" ta karashe cikin jan doguwar tsaki. Shan jinin jikin sa Secretary yayi, dan kuwa mugun tsoron ta yakeji yasan koh kaɗan batada mutunci ba ƙaramin aikin ta bane yanzun nan ta tsitsinka masa mari tayi disgracing ɗinsa. Duk abinda sukeyi ɗinnan ZEEDAN bai buɗe idanun sa ba. "ZEEDAN, kai ne yakamata ka fitar dani ba wannan ƙasƙantaccen ba" ta faɗa tana wurgawa Secretary muguwar harara. Buɗe idanu ZEEDAN yayi lokacin da yaji ta ambaci ƙasƙantacce. Tashi ZEEDAN yayi daga kan kujerar da yake tare da zuwa ya ɗauki coat ɗinsa akan hanger ɗin dake ajiye a office ɗin nasa ya sanƴa akan kayan sa tare da ficewa daga office ɗin. Tashi tayi haɗi da wurgawa Secretary harara kafin taja doguwar tsuka ta fice tare da mara masa baya. Tafiya take but koh ina na jikin ta na shaking, inda kuma kowa sai bin ta yake da kallo yana haɗiye ƴawu. Lifter yake shirin shiga nan tayi saurin kiran sunan sa da ƙarfi "ZEEDAN?." Cikin sauri ta ƙarasa wurin sa ta tsaya ta bayan sa tace "It's been a year kenan rabo na da Nigeria, but tunda na tafi outside dan gabatar da final exams ɗina koh ƙira na baka ta6a yi ba, a hakan kenan kake tunanin riƙe amanar da aka damƙa maka?." Juyowa yayi gare ta yace "Babu wanda ya bar min amanar ki, stop deceiving yourself" ya faɗa cike da 6acin rai idanun sa na yin ja. Hannu ta harɗe a ƙirji tace "Bakada ikon yi min tsawa ZEEDAN, yakamata ka girmama ni a matsayi na ta ƴa ga mai gidan ka." Cize baki yayi yana kaɗa kai cike da muguwar taƙaici yayin da 6acin rai ke sake tsattsafo masa akan fuska dama kuma zuciya. "Kada kuma ka manta da cewa we're getting ENGAGED next week, ZEEDAN koh kaƙi koh kaso ni Khairat sai nayi rayuwa da kai, kasan kuma maiyasa nace hakan?, sabida mahaifi na, ina da tabbacin ba zaka iya ja dashi ba sabida irin halarcin da yayi maka a rayuwa ya ciro ka daga tsumma ya maida ka cikakken mutum har ka zama abinda ka zama yau, ɗaya daga cikin manƴan Artist ɗin da akeji dasu a duniyar zane, ZEEDAN my love, ka daina 6atawa kanka lokaci sabida na tsani ganin wannan kyakkyawar fuskar taka cikin fushi dukda kuwa yana yi maka kyau sai dai ba ƙaramin tsorata ni yakeyi ba" ta faɗa tana kai hannu da niyyar shafo gefen fuskar sa. Riƙe hannun nata yayi, sam dukan mace ba zai bada wani ma'ana koh armashi ba, idan ba haka ba babu abinda zai hana sa lakaɗawa Khairat duka a yanzun, sosai yaji daɗin nisan da tayi masa, but a yanzu da ta dawo dole ne ta zame masa ƙarfen ƙafa ta kuma hana sa sukuni, duk inda yaje tana biye dashi, duk macen da ta ra6e sa kuwa koh da ma'aikaciya ce babu abinda zai hana ta sanƴa guards ɗinta yi mata dukan cin mutunci, daɗi ɗaya zaiji na dawowar ta wato tayi maganin Surayya ma dake maƙale dashi kullum yawa chewing gum batason rabuwa dashi, but bayan wannan kuma babu wani abin so koh sha'awa tattare da Khairat, duk wani irin hatsabibanci Khairat ta san shi, da ta ga ZEEDAN tare da wata gara ace an zuba mata tafasasshen mai a jikinta sabida yadda zuciyar ta ke matuƙar ruruwa wuta na cin shi, yana ɗaga mata ƙafa ne kawai dan sabida mahaifin ta da ya kasance mutumin kirki dama kuma mahaifiyar ta Unlike Khairat da take rayuwa kamar ta ƴaƴan turawa, shiyasa ta wani 6angaren sam bai damu da takura masa da Surayya take yi ba, dan kuwa yasan da zarar Khairat ta dawo ita da ƙafafun ta zata gudu. Sakin hannun nata yayi, cikin kakkausar murya yace "I warned you, didn't i?." Harɗe hannaye tayi s ƙirji tace "Sorry honey, but komin daren daɗewa you will be mine, from that day kuma babu wanda zai hana ni ta6a ka, not even you" ta faɗa cikin wani irin shu'umin murmushi dake nuna ita ɗin gogaggiyar ƴar iska ce. Juyawa yayi a fusace tare da danna lifter ɗin ya buɗu kafin ya shige yana danna number ɗin flour ɗin da zashi. Ganin yadda ya fito a matuƙar fusace 6acin rai ƙiri-ƙiri akan fuskar sa ya sanƴa guards ɗinsa saurin iyowa kansa. Makullin mota kawai ya kar6a a hannun ɗaya daga cikin su kafin ya buɗe motar ya shiga tare da yi mata key ya tada ta ya bar cikin ƙatuwar company ɗin kamar zai tashi sama............... *********************** .............Tsaye yake a gaban faskekiyar hoton ta dake manne a jikin wall ɗin ɗakin sa yana kallo. Haɗuwa da tsaruwa irin na ɗakin kaɗai ya isa ya sanƴa ka ɗilalar ƴawu, abin sai wanda ya gani. Sosai yaji komai ya fita a kansa bayan rabuwa da ita dama kuma sanƴa ta a idanu da baya yi, tun abin baya damun sa har yazo ya fara basa tsoro, baya ta6a samun sukuni a zuciyar sa muddin bai sanƴa idanun sa kan kyakkyawar hoton ta bane ba, ya ɗauka farin cikin sa zai gama cika ne a lokacin da yake tare da sarƙar sa, but a yanzu ya gane farin cikin sa ba zai ta6a cikewa ba muddin bata kusa dashi ne, and now rayuwar sa zata sake rugujewa ne kwata-kwata ya koma kamar marayan da bashida uwa kuma bashida uba sabida dawowar Khairat. Hannun sa ya buga a jikin bangon yana fitar da wata iriyar zazzafar huci, sosai zuciyar sa ke mugun tafarfasa, he just wants to see DEENAH, ganin ta a hoto ba zai sanƴaƴa masa zuciya ba, he wants to see her in person koh zai samu sassauci a cikin zuciyar sa, ganin ta na sati biyu da baiyi ba kasancewar dawowa da yayi is like yayi shekaru goma ne bai ganta ba, he feels so empty without her, but dukda haka he can't tell actually abinda yakeji game da ita ba................. ************************* ..............Sanƴe take cikin farar uniform ɗinta wanda yayi matuƙar kar6ar ta. Jujjuyawa takeyi a gaban mirror tana ganin yadda shape ɗin jikin ta ya fito a cikin kayan. Umma ta shiga kwalawa kira cikin muryar kuka. Da sauri Umma tazo ta same ta "lafiya, meke faruwa?." Cikin kuka tace "Umma ki gani fah, kiga abinda uniform ɗinnan yayi min duk ya kwanta min a jiki ya fito min da shape ɗin jiki na, ni banaso gaskiya nikam ki canza min makaranta." Baki kawai Umma ta saki tana kallon ta nan tace "Haba Auta, idan ya kwanta miki a jiki ba kina da wani ba, ki sanƴa sa mana." "Umma suma duk haka suke yi min, nidai gaskiya banason su." "Shikenan yanzu dai ki bari idan kinje kin dawo sai kije ki ɗinka wani." "Aa Umma, nidai gaskiya ba zan iya fita dashi ba." "Toh shikenan ai sai ki zauna a gidan tunda dama naga hakan kikeso" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Kallon jikin ta ta sake, kafin kuma ta ɗau farar safar ta ta sanƴa tare da farar half-cover shoe ɗinta. Baƙar ƴar ƙaramar jaka ta goyo ta ɗauka tare da saƙala shi a kafaɗar ta, kafin kuma ta nufi ƙaton closet ɗin ta ta ciro baƙar After-dress ta ɗaura akan uniform ɗin nata. Sosai ta sake gyaggyarawa kafin ta fice daga cikin ɗakin. "Au kajimin Ja'irar yarinƴa, ke dama kinsan da wannan dabarar kuma kikayi ta tada hankalin ki?" cewar Umma tana kallon ta. Ƙarasowa tayi ta zauna tace "Umma ba fah a bari ana ɗaura wani kayan akai, nidai dan Allah kawai ki canza min school, wanda zan iya sanƴa duk wani irin kayan da nakeso." "Amma Auta ai idan akace za'a canza miki makaranta yanzu sai kin sake zana wata jarabawar Waec da Neco ɗin, ga kuma Jamb duka." "Eh nidai Umma na yarda." "Toh ya na iya tunda ke zakiyiwa kanki karatun, naji toh." Cike da farin ciki ta rungume Umma tare da bata peck a kumatu tace "Ina matuƙar Ƙaunar ki Umma ta." Murmushi Umma tayi tace "Naga dai ranar da zakiyi aure mu rabu yadda zakiyi." Rau-rau tayi da idanu kafin ta sake rungume Umma tace "Nidai kam Allah babu wanda zai raba ni dake Umma ta." "Ke kinga ni sake ni hakanan ki kama hanƴa ki tafi, koh so kike kiyi latti, sarkin kuka kawai" cewar Umma ganin tana shirin yi mata kuka. Dubu biyu ta ciro a purse ɗinta ta bata tace "Gashi nan kiyi kuɗin mota da na break." "A'a Umma akwai kuɗi a wuri na Yaya ya bani, ki riƙe abin ki." "Toh shikenan Allah yayi masa albarka." "Aameen, nikuma fah?" ta faɗa cikin shagwa6a. "Kema Allah yayi miki albarka, Allah ya albarkaci rayuwar ku dukkanin ku, ya nuna min ranar auren ku har naga jikoki na." "Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum, Umma na, toh Umma ni na tafi." "Allah ya kiyaye ya tsare hanƴa, Allah ya bada sa'ar karatu." "Aameen Umma na" ta faɗa tana ficewa, da kallo Umma ta bi ta tana share hawayen idanun ta............. ************************** ............Koh da taje school ɗin sai da ta shiga class ta zauna kafin ta cire rigar sama ɗin da ta ɗaura tana ajiye shi kusada ita. 2hours lectures sukayi kafin su fito break. Masallaci ta nufa tayi sallar azahar kafin ta idar ta fito. Cafeteria ta nufa ta sayo Burger da drink sai ruwan gora kawai ta iyo gindin wani bishiya inda babu kowa ta samu bench ta zauna. A hankali ta shiga ci kamar bataso har ta kammala, kasnacewar hutun 1hour kaɗai suke dashi yasa ta yin sauri ta kammala ta koma class. Sosai suka sha lectures ɗin 2hours, inda sai da La'asar kafin lecturer ɗin ya fita. Sallama kawai ta yiwa ƴan class ɗin nasu kasancewar ba wani shiga harkar su take ba, dan kuwa tafijin daɗin rayuwa ita kaɗai babu ƙawaye. Kasancewar sunyi da Jafar zai zo ya ɗauke ta ne yasa ta yin masallaci tayi sallar La'asar, bayan ta idar ne kuma ta shiga zaman jirar sa. Wayar ta ta ciro daga cikin jaka ta hau buga game. Tana cikin yi ne kuma kira ya shigo wayar ta, kasancewar sabuwar lamba ce kuma shiyasa bata ɗaga ba dan kuwa bata cika ɗaukar kiran sabbin numbers ba. Sau biyu kawai aka kira aka haƙura, nan kuma kiran Abdul ya shigo wayar ta. Har kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta ɗaga, dan kuwa tasan ba ƙaramin cika ta da surutu zaiyi ba. Sallama yayi mata ta amsa ba yabo babu fallasa, kafin su shiga gaisawa. Nan dai suka hau yin hira duk da kuwa rabin da kwatar hirar shi yakeyi, ita dai nata bai wuce eh koh a'a ba. Sun ɗau almost 15mins suna waya kafin yayi mata sallama ya katse kiran. Time ta duba taga biyar saura dan haka ta latso lambar wayar Jafar tare da buga masa kira. Ringing biyu ya ɗaga tare da ce mata "Am on my way" yana ajiye wayar. Turo baki tayi dan kuwa ba ƙaramin gajiya tayi ba, a haka har ya ƙaraso yace da ita yazo. Ficewa tayi taje ta same sa a inda yayi parking motar kafin ta shiga yaja sukayi gida............ ************************* .............Kwance take cikin shirin baccin ta, Abdul ya kira ta. Sun ɗan daɗe suna waya kafin suyi sallama. Numbern da yayi ta kiran ta bayan lokacin da suke waya da Abdul ta gani kafin kuma ta share tana gyara kwanciyar ta. A haka har bacci ya ɗauke ta............ ************* .............Washe gari 12pm suka gama lectures ɗinsu na ranar duka, dan haka kai tsaye gida kawai ta dawo. Wanka ta sake sannan ta shirya cikin kaya marasa nauyi, sai da tayi sallah kafin ta ɗebi abinci ta fara ci. Wayar ta da ta ɗau ringing ta kalla, kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta ɗaga tana kaiwa kunnen ta. Shiru taji anyi hakan ya sanƴa ta furta "Assalamu Alaikum." Nan ma shiru akayi babu amsa. "Hello" ta sake cewa. Katse kiran tayi tana ɗan jan ƙaramin tsaki kafin ta cigaba da cin abincin ta............ ***************** ............6angaren ZEEDAN kuwa ba ƙaramin rashin walwala yake ciki sakamakon rashin ɗaukar kiran sa da DEENAH bata yi ba. Haka nan ya haƙura har zuwa dare ya sake buga mata sai dai jinta tana waya a wannan lokacin ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, musamman da ya kai kusan 10mins yana bugawa but sai dai yaji ance tana waya, haka kurum yaji hankalin sa ya kasa kwanciya da wayar da takeyi ɗin. Zaune yake a office ɗinsa, kallo ɗaya zakayi masa kaga damuwa akan fuskar sa. Wayar sa ya ɗauka tare da sake dialing numbern ta, dukda yasa ran ba zata ɗaga ba kuwa. Sai dai bisa ga mamakin sa yaga an ɗaga kiran tare da kuma yin sallama, he can't help it but yayi shiru yana saurarar zazzaƙar muryar ta. Bai ta6a zaton zata amsa kiran nasa nan kusa ba, jin ta yanke kuwa duk yaji wani farin cikin da yake ciki ta yanke. Sauƙe wayar yayi a kunnen sa yana damƙe hannayen sa tare da runtse idanu. Jin muryar ta babu abinda ya ƙara masa sai kewar ta, ji yake idan bai sanƴa ta cikin idanun sa ba, ba zai iyayin bacci ba yau. Wayarsa ya ɗauka tare da yin wasu ƴan danne-danne kafin ya ajiye ta........... ********************** *THE NEXT DAY* ..........Zaune take ita da Abdul da ta ɗan fara sakin jikin ta dashi, dan kuwa ta lura shi ɗin mutumin kirki ne sosai, hakan ya sanƴa ta fara sakin jiki dashi. Hira kawai suke ba yabo ba fallasa take amsa masa, idan yayi abin dariya tayi murmushi, amsar ta a gare shi bai wuci eh koh aa ba, sai kuma murmushi. Ƙarar horn ɗin motar da sukaji ne ya sanƴa su maida duban su gun gate ɗin, musamman ma DEENAH da ta san wannan ba horn ɗin motar Jafar bane, Umma kuma bata fita koh ina yau da tata motar ba _"Who could it be?"_ shine abinda ta faɗa a ranta tana maida hankalin ta kan Abdul dake yi mata magana. Buɗe ƙofar akayi take wata zazzafar mota ta kunno kai cikin gidan, kafin ya nufi parking space ɗin gidan yana parking motar. Hango su yayi ta cikin tinted glass ɗin motar tashi, wani irin abu yaji ya tsaya masa a zuciya. Hannu yasa ya buɗe murfin motar ya fito tare da tunkaro su kamar zai tashi sama. DEENAH ba ƙaramin mamakin ganin balarabe tayi a gidan su ba. _"What is he doing here?"_ shine abinda ta faɗa a ranta tana zazzare ido. Saurin daidaita nutsuwar ta tayi tana sake ƙirƙirar murmushin ta mai ƙara mata kyau akan fuskar ta tana kallon Abdul. Fuskewa ZEEDAN yayi yana controlling mugun kishin dake taso masa a zuci ya ƙarasa wurin su murmushi akan fuskar sa. Dafa table ɗin dake tsakanin su yayi tare da furta "Hi." Ɗagowa Abdul yayi ya kallesa kafin shima yace "Hi" yana miƙa masa hannu alamun su gaisa. Cike da mugun basarwa ZEEDAN ya juyar da kansa zuwa ga DEENAH yace "Is your Mom around?." Kai ta jinjina masa tana kauda idon ta daga kallon sa. "Zaki iya yi min jagora zuwa wurin ta?" ya sake faɗa. "Sure" kawai ta faɗa, kafin ta miƙe daga kan kujerar da take. Kallon Abdul tayi tare da sakar masa murmushi tace "Yi haƙuri dear, bara nayi masa iso zuwa wurin Umma." Murmushi shima Abdul da yaji haushin basar dashi da ZEEDAN yayi ya maida mata kafin yace "Bakomai." Wucewa tayi kawai nan ya mara mata baya, zuciyar sa na matuƙar yin suya sosai. _"Dear! Dear!! Dear!!!"_ yake ta maimaitawa a zuciyar sa. Falon nasu suka shigo wanda ke ta tada ƙamshi na musamman kafin tace dashi "Ka zauna, bari na kira Umma" ta faɗa tana shigewa wani lungu. Ɗakin Umma taje ta sanar da ita da cewa tayi baƙo, nan ta sako Hijabin ta suka fito tare. ZEEDAN ganin Umma ba ƙaramin kunƴa ce yaji ta kama sa ba, sunkuyar da kai yayi kawai, yayin da Umma kuma ke ta bin sa da kallon mamaki. "Wa nake gani kamar Balarabe?" faɗin Umma dake shirin zama kan kujera. Wucewa DEENAH tayi kitchen ta haɗo masa abin ci da sha akan tray ta fito. Zaune ta gansa kusada ƙafar Umma, dan haka zuwa tayi ta ajiye masa a gaban sa kafin tace "Umma ni na wuce Abdul yana ta jira na babu daɗi na bar sa." "Aikuwa dai kam yakamata ace kinje kada ki barsa yayi ta jira." Ficewa tayi inda ya bita da kallo ta ƙasan idanu. _"Is she going back to that frog?"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa yana jin kamar ya tashi ya mara mata baya. Sosai zuciyar sa ke mugun yi masa zafi................ *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *021...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ............Sun ɗan daɗe da Umma kafin ya tashi ya fito. Hango su yayi har yanzu suna nan, ganin yadda Abdul ke zuba murmushi ne ya sanƴa ZEEDAN jin kamar yaje ya shaƙo wuyar sa ya murɗe tsabar haushi da takaici. _"He seems so very happy with her, ita kuma da yake sokuwa ce tana biye masa"_ Ya faɗi hakan a zuciyar sa yana jin kamar ya tunkare su ya tarwatsa wannan wurin nan, but ba zaiyi hakan ba koh dan ajin da yake dashi kada ya zube. Hannaye ya zuba cikin aljihu kafin ya fara tafiya a hankali kamar wanda bayaso kan shi a sama ya wani haɗe fuska da rai kai kace guna yaci. Ganin ya kusa kawowa wurin su ne yasa shi yin slowing tafiyar sa yana kallon su ta gefen ido ta yadda ba zasu gane hakan ba. Zuwa yayi ya wuce su, sai dai ganin yayi gaba DEENAH bata kula sa ba ba ƙaramin sake 6ata masa rai hakan yayi ba. Tsayawa yayi yana jin zuciyar sa na mugun tafarfasa, musamman dan ita ya taso tundaga inda yake dan ya samu sukuni a zuciyar sa, but instead of hakan sai ma wani ƙarin baƙin cikin da ya sake kwasa akan na dah. Ganin ta da wani daban is like ana sossoka masa wuƙa ne a cikin zuciyar sa. He can't help it but yayi tafiyar sa, hakan ne kaɗai zai sanƴa sa jin nutsuwa a ransa, dan kuwa ba zai iya ganin ta da wani tana sakar masa tsadaddar murmushin ta ba, wanda shi yakamata ace yana ganin hakan kullum ba wani daban. Juyowa yayi yana kallon su _I wonder what he looks like, there is nothing interesting about this guy, why take 6ata lokacin ta akan shi?"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa kafin kuma ya furzar da huci ya wuce ya shige motar sa. Tada ta yayi tare da danna horn da ƙarfi still idanun sa akansu, but DEENAH yi tayi kamar ma batasan da akwai mota a cikin gidan ya dame su da ƙara ba. Steering ɗin ya nausa yace "Why isn't she responding?." Buɗe gate ɗin da mai gadin yayi ne yasa shi jan motar a zafafe ya fice daga cikin gidan. Motar Abdul da ya gani ne ya sanƴa shi slowing yana ƙare mata kallo. Yatsine fuska yayi yace "The Guy is a little bit rich, tunda yana iya hawa motar miliyan 12" ya ƙarashe yana tsuke fuskar sa kafin ya sake jan motar a tsiyace yana harba ta kan kwalta................. *********************** .................Cikin sauri take shiri kasancewar tayi latti yau, yasa duk ta kasa samun kwakkwarar sukuni. Ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta cikin makarantar. Da sauri ta fito kasancewar Umma ta fita wurin aiki haka ma Jafar ya sanƴa ta rufo ƙofar da key tana baiwa mai gadi ajiya kafin ta fice. Tsaye tayi a bakin kwaltar tana jiran adaidaita, inda da kyar ta samu wani ya ɗauke ta. Zuwa yayi ya sauƙe ta a school kafin ta biya sa tana saurin shigewa cikin makarantar kasancewar bai shiga da ita ciki ba. Zuwa tayi ta tarar har an shiga musu an fara lectures ga kuma ƴan latti nan a waje da alama lecturer ɗin baya kar6ar masu latti. Ba tare da ta 6ata lokacin ta ba ta nufi inda ta saba zama babu kowa ta zauna. Earphone ta ciro a cikin jakar ta tana sanƴawa akan kunnen ta, kafin ta ciro Book ɗinta ta shiga bitar karatun da sukayi a baya. Ji tayi sam karatun baya shiga kwakwalwar ta dan haka ajiye takardar tayi tana folding hannayen ta a ƙirji. Shiru tayi tana kalle-kalle kafin kuma ta shiga rero waƙa cikin zazzaƙar muryar ta _I have been reading books of Old_ _The Legends and the Myths_ _Achilles and his gold_ _Hercules and his gifts_ _Spider-Man's Control_ _And Batman with his fists_ _And clearly i don't see myself upon that list_ _But she said, “where do you wanna go?”_ _How much you wanna risk?_ _Am not looking for somebody with some superhuman gifts,_ _Some superhero,_ _Some Fairy tale bliss_ _Just something i can turn to somebody i can kiss_ _I want something just like this_ _Tu-ru-ru, Tu-ru-ru_ "Woo bravo!" aka faɗa saitin kunnen ta. Da sauri ta ɗago tana cire headphone ɗin kanta tare da binsa da kallo. Zama yayi kusada ita, nan tayi saurin matsawa gefe. Kallon ta yayi kafin kuma ya ɗan ta6e baki shima yana kauda kansa daga kallon ta yace "You're late today, why?." Shiru tayi pretending tana duba takardar hannun ta. Kallon ta yayi jin taƙi kulasa, hannu yasa ya kar6i takardar hannun nata ya shiga dubawa. Ta6e baki yayi yace "Uhm this topic, sai yanzu kukeyin sa?, i have done it in my secondary school, but ku how comes sai yanzu kuke yin sa, strange" ya faɗa yana still idanun sa a cikin takardar. Bata kula sa ba sai ma wayar ta da ta ciro ta hau daddanawa, ba tare da tabi ta kanshi ba. Kallon ta yayi ta gefen ido bai ce komai ba sai ma maida duban sa da yayi cikin takardar yana kallo. _"She is trying to show me attitude"_ ya faɗa a ransa yana kallon ta ta gefen ido. Rufe takardar yayi kawai ya zauna tare da crossing legs ɗinsa yana neman ta hanƴar da zai jata da hira. "Ahm..oh yeah tell me, ke mawaƙiya ce?, you have a sweet voice." Bata ɗago ta kallesa ba sai kai kawai da ta girgiza masa alamun "a'a." _"She should atleast fake a smile on her face koh da bata so, i can't believe ta zage tana yiwa wancan tiny thing ɗin murmushi but taƙi sakar min fuska"_ ya faɗa a ransa yana kallon ta. Ɗagowa tayi ta kallesa nan yayi saurin sakar mata murmushi, kafin kuma ta sake sadda kai ƙasa tana cigaba da danne-dannen ta. _"Oh GOD, did she just ignore my beautiful smile?"_ Takardar ta ta ɗauka ta shiga buɗewa tana bi a hankali. Buɗe jakar ta tayi ta ciro farar glass tare da sanƴawa a idanun ta tana cigaba da duba takardar hannun nata. Duk abin nan da take bata ɗago ta kallesa ba, sai shi da ya zama kamar soko yana ta bin ta da kallo. A haka suke zaune babu wanda yace da wani uffan a cikin su har lokacin second period lecture ɗinta yayi. Tattare komai tayi ta sanƴa a jaka kafin ta miƙe tana rataye jakar a kafaɗa. Kafar uniform ɗinta da ta ɗanyi ƙura ta sunkuya to goge shi da handky ɗinta kafin ta jefa shi cikin jaka ta fara tafiya. Sai da ta ɗanyi nisa kaɗan kafin ya ɗauke idanun sa da ya zuba akan coca-cola shape ɗinta yana mai mara mata baya. Har cikin class ɗin ya biyo ta ta sami wuri ta zauna shima ya zauna, nan kuma hankalin ƴan class ɗin baki ɗaya ya dawo kansu. Babu abinda kakeji sai maganar mutane ƙasa-ƙasa, da kaji kasan kowa tofa albarkacin bakin sa yake. Shi kuwa koh kaɗan bai damu da kallon da ƴan mata da samarin class ɗin ke binsa dashi ba, sai ma sake tsuke fuska da yakeyi yana basarwa. Ita kuwa DEENAH ba ƙaramin mamakin sa bane ya kama ta, ganin sai bin ta yake yawa jela koh bodyguard ɗin ta. A hakan Lecturer ɗinsu ya shigo nan duk suka maida duban su tare da tattare dukkan nutsuwar su zuwa kansa. Haka ma DEENAH hankalin ta ta maida kan lecturer ɗin bata sake kallon ZEEDAN dake zaune gefen ta ba. Lecturer hango Farin mutum mai suffar larabawa da yayi ba ƙaramin mamaki ne ya kama sa ba. Takowa yayi zuwa kansu tare da tsayawa yana ƙare musu kallo ta ƙasan glass ɗin sa, babban mutum ne. ZEEDAN kuwa wani irin basarwa yayi yana sake tsuke fuska tare da cin guna. Buɗe baki lecturer yayi zaiyi magana nan DEENAH tayi saurin cewa "Am so sorry sir he is just my guard, baya ta6a samun sukuni indai ba ya aiwatar da abinda Mahaifi na ya sanƴa shi bane na lura dani kullum ba, he is just doing his job." "Bodyguard kuma har cikin class?" cewar lecturer ɗin yana kallon ta. "Kayi haƙuri sir, nasan an karya doka but nayi dashi to let me be, but he just don't wants to listen, zanyi ƙoƙarin naga na shawo kansa yanzu ya fita, am sorry." Kai lecturer ya jinjina nan ta kalli ZEEDAN tace "Abyad, dan Allah ka tafi ni ba yarinƴa bace yanzu, zan iya kula da kaina and nasan kaima ba zaka rasa wasu abubuwan yi ba, just excuse us please" ta faɗa tana kallon shi. Tunda DEENAH ta kira sa da bodyguard ɗinta ya kafe ƙaramin bakin ta dake motsi da idanun sa, he was lost a duniyar tunanin kallon ta, babu kuma abinda ya sake rikita masa lissafi sai sunan da ta kiraye sa dashi. _Abyad_ ya maimata hakan a zuciyar sa. "Yeah sure, i would be waiting for you outside" ya faɗa bayan ya miƙe tsaye tare da gyara zaman coat ɗin jikin shi. Ficewa yayi daga class ɗin inda idanu dayawa suka bisa da kallo, especially ladies ɗin class ɗin. Kan kace miye kuma class ɗin ya ɗau hayaniya, maganar lecturer ne ya sanƴa kowa saita nutsuwar sa. Ajiyar zuciya DEENAH ta sauƙe tana maida duban ta kan board. 12pm suka fito dan haka Masallaci kawai ta nufa ta tare achan, sai da tayi sallar azahar kafin ta fito ta nufi Cafeteria dan sayan abinci. Doughnut guda biyu ta saya sai ruwa da Malt kafin ta dawo inda ta saba zama ta zauna. Bata iya cinƴe doughnut ɗin duka biyu ba dan haka maida sauran tayi cikin jakar ta kafin ta tashi ta koma class. Suna cikin lectures ne taji marar ta ta fara murɗa mata sosai, kafin kuma tayi wani yunƙuri ta fara jin alamun damshi ta ƙasan ta, da alamu dai jinin ya riga ciwon marar zuwa. _"Oh no, what's happening to me?"_ ta faɗa tana matse cinƴoƴin ta tana gyara zama. Shal ta manta da cewa yau ne zata ga baƙon watan ta, sosai marar tata ta shiga murɗa mata gashi sam idan yazo baya yi mata da wasa, ba ƙaramin azaba take ci ba. Sosai ta shiga tashin hankali dan kuwa already tasan farin kayan jikin ta ya 6aci, gashi kuma bata zo da after-dress ɗin da take ɗaurawa akai ba, tasan yau tata ta ƙare a cikin school ɗinnan. Da kallo kawai take bin ƴan class ɗin da kallo tana runtse idanun ta. Kifa kanta tayi akan bench ɗin da take, tana maida numfashin wahala. A haka har aka gama musu lectures DEENAH bata cikin hayyacin ta, tsoro da rashin mafita ne suka haɗu mata da ciwon mara mai tsanani. Da kallo ta fara bin ƴan class ɗin da suka fara fita babu wanda yabi ta kanta. Riƙo rigar wata tayi ta baya tana kallon ta. Juyowa yarinƴar tayi tana kallon fuskar DEENAH da ya gama zama do very pale kamar marar lafiya. Sunkuyo da kai yarinƴar tayi DEENAH tayi mata magana. Idanu yarinƴar ta zaro tana kallon DEENAH kafin ta kira sauran ƙawayen ta ta faɗa musu abin dake faruwa. "Wayyo Allah, mu kuwa ba a hostel muke ba, gashi bamuda wani rigar karewa da sai mu bata" cewar ɗaya daga cikin su. "Ƴan cikin hostel ɗinma duk sun tafi fah, dah sai mu bisu mu kar6a mata abin karewa" faɗin ɗaya. "A'a tsaya, ta zauna, ke Rahila ki zauna tare da ita, mu kuma zamuje Hostel mu taho mata da wani sabon kayan ta canza." Hakan kuwa akayi wacce aka kira da Rahila ce ta zauna tare da DEENAH kafin kuma sauran biyun su fice daga cikin class ɗin........ ******************* .........Tsaye yake yaga fitowar ta daga cikin class ɗin, sai dai har ƴan ciki duka suka fito bai ba fitowar DEENAH ba. _"Why isn't she out yet?"_ ya faɗa a ransa yana kallon ƙofar class ɗin. Tsayuwar 10mins ya ƙara sai dai har yanzu bai ga ta fito ba, hakan yasa shi yanke shawarar duba cikin class ɗin. A hankali ya fara takowa gaban class ɗin yana kaɗa key ɗin motar hannun sa. Hango ƴan mata biyu yayi a ciki ɗaya a zaune ɗaya kuma kanta kwance akan desk. Ƙarasowa bakin class ɗin yayi tare da yin knocking ɗin door ɗin. Ɗayar ce ta ɗago ta kallesa kafin tayi saurin kallon DEENAH tace "Ga nan Bodyguard ɗin ki ya biyo sawun ki." Da sauri DEENAH ta ɗago da kanta suna haɗa ido. "MADEENAH?" ya furta a hankali yana ƙarasowa cikin class ɗin. Ɗagowa tayi tana gyara zaman ta tare da sunkuyar da kanta ƙasa. "Hey, i have been waiting for you since, what are you still doing here?." Goge gumin fuskar ta tayi tace "Nothing." "Alright, shall we?." Kallon yarinƴar kusa da ita tayi tana maida kanta kan benchin tare da runtse idanu. "MADEENAH, is she Okay?." "No, bata jin daɗi ne, but i think you should get going, zata samo ka a gida." "What?" ya faɗa yana durƙusawa kusada ita. "What's wrong with her?" ya faɗa. Ɗagowa tayi tace "Am fine, ka tafi kawai, i would be alright." "Have you lost your mind, bakida lafiya and you expect me to leave you here alone." "Am not alone, bakaga akwai friends ɗina bane, they would be back soon" ta faɗa tana runtse idanu tare da riƙe ciki lokacin da ya sake murɗa mata. "MADEENAH?" ya faɗa cikin tashin hankali. Ƙawayen yarinƴar ne suka dawo da jaka a hannun su, nan duk suka tsaya kallon ZEEDAN suna ƙarasowa. "Gashi mun kawo mata kaya ta canza" cewar ɗaya. Ɗagowa DEENAH tayi ta kallesu kafin kuma ta kalli ZEEDAN tace "Ka fita waje please, zan fito yanzu." Kallon ta yake kafin yace "No, am not going anywhere, ki faɗamin meke damunki." "Just get out please" ta faɗa cikin ƙosawa. Cikin idanun ta yake kallo nan kuma tayi saurin kauda idon ta. "Are you on your period?" ta jiyo ya faɗi hakan. Da sauri duk ƙawayen suka kallesa kafin su kalli juna suna ware idanu, DEENAH kuwa wani irin kunƴa ne taji yayi mata rumfa, she can't believe maiyasa Balaraben nan bashi da kunƴa koh kaɗan. Rasa ya zata yi tayi kai kawai ta juya masa idanun ta a runtse. Miƙewa yayi daga durƙushen da yakeyi yace "I understand, get up i will take you home." Bata juyo ta iya kallon sa ba, sai ma kunƴar shi da takejin yake sake lullu6e ta. "MADEENAH?" ya furta yana kai bakin shi saitin kunnen ta. "I can't stand up, ba zan iya tashi nayi tafiya ba, ƙafa na ya riƙe, so just go please i don't need your help, just let me be, please" ta faɗi hakan ba tare da ta juyo ta kallesa ba. Baki ya cize kawai kafin kuma yaja ƙafafun sa ya bar cikin class ɗin. Ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallon ƴan matan "Thank you so much" ta faɗa. Zuwa sukayi tare da taimaka mata ta tashi tsaye, sosai bayan ta yayi staining dan haka taimaka mata sukayi ta canza kayan jikin ta tare da bata sabon Pant da Pad ta saka. Taimakawa sukayi tare da gyara inda ta zauna ɗin, kafin su sanƴa wanda ta cire a ƙaton baƙin leda suka ƙulle. Ta ɗan ji ta comfortable yanzu, dukda kuwa a matuƙar takure take, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a cikin ɗakin ta. Ɗingisawa tayi ta zauna tana jin kanta na sara mata, ciwon ciki da na ƙafa duka sun haɗe mata wuri ɗaya. "Sannu" sukayi ta jera mata kamar su ari baki. Da kyar dai suka taimaka mata ta tashi tare da riƙo ta sukayo waje. Hango su yayi daga inda yake tsaye duk ya rasa sukuni, nan ya iyo kansu yana kiran sunan ta. A galabaice ta ɗago ta kallesa tace "mai kakeyi har yanzu baka tafi ba, dan Allah ka tafi nace koh?." Kallon ta yake, sosai yakejin kamar ciwon a jikin sa yake, ganin yau kaɗai har ta ɗan faɗa ba ƙaramin tausayi ta bashi ba. Kallon ƙawayen yayi yace "I will take care of her, you should get going." "How can you take care of me, how?, dan Allah ka tafi haka nan mana" ta faɗa cikin ɗan ɗagun murya dan kuwa ya fara bata haushi. "MADEENAH...." "Suna na ya fita a bakin ka haka nan, stay away from me please, Okay?." "Let's go" ta faɗawa ƙawayen nata. "Motar zamu kai ki?." Kai ta girgiza musu alamun a'a. Wucewa sukayi inda ya bisu da kallo yana jin ba daɗin yadda tayi masa maganar a zuciyar sa. Komawa yayi ya jinginu da motar sa tare da folding arms ɗinsa yana kallon su. Adaidaita suka tara tare da sanƴa ta a ciki, suna ƙara yi mata sannu kafin yaja suka fara tafiya. Motar sa ya shiga tare da mara musu baya. Sun ɗanyi tafiya mai nisa, kafin kuma ya ƙara gudun motar tasa yana shan gaban su. Burki mai Napep ɗin yaja da ƙarfi ya tsaya yana fitowa daga cikin napep ɗin, dan ganin wane marar hankalin ne wannan. Fitowa ZEEDAN yayi daga cikin motar sa ya tunkaro su, kai tsaye wurin DEENAH dake ta aikin kallon sa cike da mamaki yayi yace "Come out." Kawar da kai tayi alamun ba zata fito ba ɗin ba. "MADEENAH?" ya kira sunan ta. "Nace maka ka rabu dani haka nan, ba zan iya takawa ba, ka barni mana nik..." Bata iya ƙarasar da maganar ba sakamakon jinta da tayi cak akan hannun sa. "Idan ba zaki iya takawa ba, then nikuma miye amfani na a matsayi na na guard ɗinki?" ya faɗa yana kallon cikin idanun ta da ta waro su cike da mamaki ta saki baki tana kallon sa. "Pu..pu..put me down" ta faɗa cikin rawar baki tana niyyar sauƙa. Sake ƙanƙame ta yayi yace "I won't put you down, ba'a ja da abinda na faɗa, when i said i want to take you home then i mean it and nothing can change that, so now stay still" ya faɗa cikin harɗe fuska yana kallon ta. Motar ya nufa ya sanƴa ta a ciki yana kwantar mata da seat ɗin. Dubu ɗaya ya ciro ya baiwa mai Napep ɗin da ya saki baki kawai yana kallon su kafin ya wuce ya shige cikin motar. Lumshe idanu tayi sosai take jin matuƙar haushin shi, how dare him da zai dinga ta6a ta yadda yaso, koh ya ɗauka ita ɗin irin Karuwar sa Surayya ce? Ta faɗi hakan a zuciyar ta idanun ta a lumshe. Ƙamshin turaren sa da ya mannu mata a kaya ne ya cika mata hanci, hakan yasa take sake 6ata rai cike da jin haushin sa. Sun ɗanyi tafiya kafin taji motar ta tsaya, daga nan kuma ya buɗe ta ya fita. Idanu ta buɗe tare da bin sa da kallo kafin taja ɗan ƙaramin tsaki tana hararar sa. Sosai ya jido mata fruits kala-kala a cikin leda ya dawo motar kafin ya jata suka cigaba da tafiya. Shiru motar ta ɗauka kafin kuma wayar sa ta hau ringing. Dubawa yayi yaga sunan Mom ke yawo a jikin screen ɗin. Amsawa yayi yana sanƴa wa a hands-free tare da tattara dukkanin nutsuwar sa zuwa kan tuƙin da yake. "Assalamu Alaikum" ya faɗa. "Wa'alaika Assalam, ɗan albarka ina ka shiga ne kwana biyu ban ganka ba?." "Am sorry Mom, tafiya ce ta taso min urgently shiyasa ban faɗa miki ba, kuma i thought koh zan iya dawowa a ranar." "Toh ai shikenan, Khairat ta dawo kun haɗu kuwa tunda ta dawo?." Shiru yayi yana tare da haɗiye wani abu mai ɗaci yace "Yes Mom." "Masha Allah, nima goben nan zanyi tafiya zuwa London dan samo muku engagement ring mai kyau da tsada, domin ƴaƴan nawa na musamman ne" ta faɗi hakan cikin dariya. Shiru yayi yana cize baki zuciyar sa na mugun ƙuna, yace "Hakan yayi kyau Mom, maybe we should talk later ina driving ne yanzu." "Alright, idan ka sauƙa ka kira ni, we have alot to discuss, kaji?." "Yeah" ya faɗa. Katse ƙiran yayi yana cigaba da kallon gaban sa. Har suka iso gidan babu wanda ya yiwa wani magana a cikin su. Parking motar yayi a parking space, kafin ya ɗaga seat ɗin da take ɗin, fuskar nan tata a matuƙar tsuke. Fitowa yayi ya zagayo tare da buɗe mata ƙofar yana miƙa mata hannu. Da kallo tabi hannun nasa zuciyar ta na daɗa yin zafi sosai, kafin ta yunƙura ta tashi da kyar tana dafa murfin motar. "Careful" ya faɗa cikin muryar sa da tayi rauni. "Zan wuce" kawai ta faɗa, hakan yasa shi matsa mata. Ledar kayan ta da jakar ta ta ɗauka, kafin dai ta daure ta fara takawa a hankali. Abubuwan da ya saya mata ya ciro tare da bin bayan ta dashi. A falo ta sami Umma zaune da waya a hannun ta. Jin sallamar DEENAH yasa ta ɗagowa tace "Yanzun nan nake shirin ƙirar ki, naga kin daɗe." Zuwa tayi ta faɗa jikin Umma tana sakin kuka sosai. "Subhanallah, lafiyan ki, daga dawowa kuma sai kuka auta, mai akayi miki?." "Umma ciki na ne ke ciwo, period ɗina ne yazo min a makaranta ya 6ata min kaya sai da wasu ƴan ajin mu ne suka kawomin wani kayan nasa." "Toh alhamdulillah, gaskiya sun kyauta Allah yayi musu albarka, toh kuma miye abin kukan toh?, gashi nan ma har jikin ki yayi zafi" cewar Umma tana tatta6a wuyan ta. Shesheƙa kawai DEENAH keyi kafin Umma ta taimaka mata ta tashi ta kaita ɗakin ta. Ruwan zafi ta haɗa mata na yin wanka tace "Ki shiga kiyi wankan, ki fito kici abinci ki sha magani sannan ki kwanta koh?." Kai ta jinjina mata kafin Umma ta fice, ita kuma ta tashi tare da yin shirin wankan, har yanzun bata bar kukan ba. Sosai taji daɗin wankan da tayi shiryawa tayi ta fito falo wurin Umma. "Yauwa ƴar albarka, zo ki zauna na kawo miki abincin" cewar Umma tana zaunar da ita kafin kuma ta tashi tayi cikin kitchen. Dawowa tayi da plate ɗin abincin a hannun ta, kafin ta ɗauko ruwa marar sanƴi ta shiga bata abincin a baki. "Toh su kuma wadannan hawayen na menene haka da suka kasa tsayuwa?." Goge hawayen tayi tana cigaba da amsar abincin da Umma ke bata. Ta ɗan ci sosai kafin ta 6alli magani ta bata ta sha tace "Tijjani ya kawo min ledar fruits wai inji wani a waje yace a baki, yana kitchen idan kin tashi sha, yanzu dai kije ki kwanta koh kyaji sauƙin ciwon." Kai kawai ta jinjina mata tana tashi ta koma ɗaki. Bed ɗinta ta hau tana jawo bargo ta rufawa kanta tare da jinjina tsantsar yaudara dama kuma kwashe-kwashe irin ta Balarabe. Babu maganar dake tayi mata yawo a kwakwalwa sai _"Masha Allah, nima goben nan zanyi tafiya zuwa London dan samo muku engagement ring mai kyau da tsada, domin ƴaƴan nawa na musamman ne"_ Rufa bargon tayi har kanta tana fashewa da kuka.............. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *022...* بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم _"Surely with every hardship there is ease" (Q94:5)._ ```May Almighty ALLAH (SWT) justify your efforts, purify your faith, beautify your character, satisfy your needs and make things easy for you and your entire family now and always, Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum. Juma'at Mubarakah``` _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..............6angaren ZEEDAN kuwa mai gadi kawai ya baiwa saƙon nata ya wuce ba tare da ya bita ɗin ba............ ********************* ..............Masauƙin sa ya nufa yayi wanka sannan yayi shirin zuwa masallaci, sai da yayi sallar Isha'i anan kafin ya dawo. Bayan ya dawo ne already yayi ordern abinci aka kawo masa yaci sannan kuma ya ɗauko Laptop ɗinsa ya kama aiki. Sosai yayi abubuwan da yakamata yayi a ciki kafin kuma ya rufe ta. Wayar sa ya ɗauka nan dai yaga missed call kaca-kaca, nan ya fara bin masu amfanin yana kiran su. "Assalamu Alaikum Dad" ya faɗa bayan yayi dialing number ɗinda ya gani a ƙarshen yi masa missed call. "Wa'alaikumusalam, ZEEYAD, dafatan kana lafiya?." "Alhamdulillah Dad." "Naji Mom naku tace kayi tafiya koh, yaushe ne zaka dawo?." Shiru yayi yana tunani kafin yace "Dad da zaran na gama abinda ya kawo ni, but idan akwai wani abinda kakeson nayi maka ne zan dawo koh gobe ma." "A'a kada ka damu, ka bari idan har ka gama abinda ya kai ka, duk ranar da ka dawo sai mu tattauna game da maganar ka dama kuma Khairat." "Yeah sure" ya faɗa. "Madallah, sai anjima koh, take care." "Thank you sir" ya faɗa yana ajiye wayar. Komawa da baya yayi ya jinginu da kujerar da yake kai yana dafe goshi. Sosai yake tunanin haɗin auren sa da na Khairat da iyayen ta ke son yi musu, Khairat sam batada irin qualities ɗin da ake buƙata a wurin mace ta gari, batasan darajar kanta ba balle kuma na wasu, ta ɗauki rayuwar yahudawa ba a bakin komai ba, dan kuwa a cewar ta hakan shine wayewa. Sosai ya shiga cikin damuwa, sam ba zai iya rayuwa da mace kamar Khairat ba, dole ne yayi dukkanin yadda zaiyi na ganin ya dakatar da wannan haɗin nasu, amma tayaya, tayaya zai fara hakan iyayen ta sunyi masa halacci, kenan buɗar baki zaiyi yace musu bayason ƴar su komiye? Wannan shine tunanin dake ta yi masa yawa a zuciya da kwakwalwa sannan kuma ya hana sa samun sukuni. Wayar ya sake ɗaukawa ya shiga kiran lambar ta, jin sa a kashe yasa duk yaji babu daɗi a zuciyar sa, hakan na nufin yau ba zaiyi bacci mai daɗi ba kenan............... *********************** ...........Da misalin ƙarfe goma na safe aka kawo masa abinda yayi ordering. Amsa yayi ya dawo cikin Apartment ɗinshi kafin ya zauna tare da ciro wata ƴar madaidaiciyar kwali. Buɗe ta yayi take wani abin hannu mai kyau na mata golden colour ya bayyana sai sheƙi da yalƙi yake yi. Murmushi yayi tare da ciro ta yana ƙare mata kallo. "I just do hope she accept this gift" ya faɗa kafin kuma ya maida ta cikin kwalin ta ya rufe. Wrapping ɗinta yayi a cikin ledar gift mai kyau mai zanen love a jiki kafin kuma ya miƙe yayi shirin wanka. Bayan ya fito ne ya shirya cikin ash colour ɗin suit mai kyau, gashin kansa da ya sha gyara mai kyau sai sheƙi yake yi, sosai yayi kyau kamar kullum. Tsayawa yayi a gaban mirror yana ƙarewa kansa kallo inda yaga baiyi ba sai ya gyara duk dan kawai ya burge ta ta kasa ɗauke idanun ta a kansa. Atlast murmushi yayi yana gyara tsayuwar zaman coat ɗinsa kafin kuma ya ɗau makullin motar sa da Gift ɗin ya fice sai ƙamshi yake tayi. School ɗinsu ya nufa yana zaman jiran ta har aka fito first period bai ganta ba, haka kuma koh ɗuriyar ta bai gani ba, bayan ya leƙa class ɗin nasu. Bai tsaya tambayar kowa ba ya nufi gidan su. A bakin gate ɗin gidan ya danna horn, take mai gadi ya leƙo da kansa dan ganin koh wanene. Fitowa yayi tare da zuwa kusa da window ɗin motar, sauƙe glass yayi nan yaga ZEEDAN ne. Haƙora ya washe yace "Kai mai gida ashe dai kai ne, barka da zuwa bari na buɗe maka gate ɗin." Kai ZEEDAN ya jinjina masa dan kuwa har yanzu ba wai Hausar ya iya sosai ba balle ya biye masa. Buɗe gate ɗin keda wuya ya kutsa kan motar tasa cikin gidan. "Ohh this Mother-fucker is here again" ya faɗa cikin cize haƙora yana kallon motar Abdul dake fake a parking space ɗin gidan. Parking tasa motar yayi ya fito zuciyar sa kamar zata tarwatso waje tsabar haushi. Inda ya gansu zaune ya nufa tare da janƴo kujera ɗaya ya zauna fuskar nan tasa a matuƙar ɗaure. DEENAH kallon sa tayi kafin kuma ta kauda idanun ta tana mamakin mai yake nema da ita haka, bayan duk ƴan matan da yake dashi. Kallon sa Abdul yayi cike da mamaki kafin yace "Excuse me, Malam lafiya?." Kallo ɗaya ZEEDAN yayi masa ya ɗauke kai tare da sauƙe idanun sa kan DEENAH yace "I want to have a word with you." Ba tare da ta ɗago ba tace "Maybe later, amma yanzu ina tare da baƙo ne." Ta gefen ido ya kalli Abdul kafin a zuciyar sa yace _"Har wannan abin yana da wani value a wurin ta?."_ Kafin kuma yace "Yanzu nakeson muyi maganar." Ɗagowa tayi ta kallesa kafin tace "No not now..." "I want it now" ya faɗa a ƙufule yana katse ta. "Sweetheart, waye shi, why is he talking to you like this?" cewar Abdul yana kallon DEENAH. "Ka rabu dashi dear, aiki ne bai ishe shi ba." Dunƙule hannu ZEEDAN yayi yana jin yadda zuciyar sa ke tafarfasa "MADEENAH?" ya faɗa. Kallon sa tayi nan yace "I want to talk to you." "Nikuma nace ba zanyi magana da kai ba, just let me be please, maiyasa kake shisshigewa rayuwa ta haka ne?" ta faɗa cike da jin haushi tana kallon sa. Sosai yaji zafin yadda tayi masa magana a gaban wannan ga6on kalan kawai ya raina shi take so. "Wanene shi, kuma miye tsakanin ki dashi?." "I don't even know, kawai ya bi ya takura min ne, babu komai tsakani na dashi." Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon ta, kafin kuma yace "Let's talk, for GOD's Sake please." Shiru tayi ba tare da ta ɗago ta kallesa ba, dan kuwa ta gane so yake yayi Playing da feelings ɗinta kamar yadda yayi wa ƴan matan sa, daga baya kuma yayi dumping nata yaje yayi auren shi, dukda batasan koh Surayya kaɗai bace budurwar sa but ta tausaya mata dan kuwa sai da ya gama lalata mata rayuwa tukun yake shirin yin aure yanzu, shiyasa koh kaɗan ba zata sakar masa fuskar yi mata wasa da hankali ba. "MADEENAH?." "Just let me be please, just stay away from me, ka bar bibiya ta haka nan, babu komai tsakani na da kai why then kake neman takurawa rayuwa ta ne, bana binka bashin komai haka kaima, toh mai kuma kake sake nema daga gare ni, i thought tunda na sauƙe nauyin dake kaina mun rabu kenan, but you kept pursuing me, mai kake nema ne daga gareni haka?" ta faɗa bayan ta miƙe tsaye tana kallon shi. Tsaye ya tashi shima yanajin zafin yadda take yi masa magana sosai a ranshi but haka nan ya daure, abinda yasa ransa ke 6aci bai wuci ganin Abdul ɗinnan da ya kafe su da ido yana kallo bane, shi kuma ba zai ta6a yarda bane ta yarfa sa a gaban shi. Shiru yayi kawai yana kallon ta ba tare da ya iya cewa komai ba. Abdul ne ya miƙe tsaye tare da dafa kafaɗun ZEEYAD yace "Look bro bansan koh menene alaƙar dake tsakanin ku ba, but the best thing you can do shine ka rabu da ita, since hakan take da buƙata, you can't just keep pursuing a girl that doesn't like you, i can clearly see that you've feelings for her, but am sorry to say you're late..." "No am not late, but maybe you're" ya faɗa yana cire hannun Abdul daga dafa shi da yayi, kafin yace "Do you really thinks she liked you, No she is just pretending to be inlove with you, but the one who she truly loves is....Me" ya faɗa yana juyawa ya kalli DEENAH da idanun ta ke ƙasa ta harɗe hannayen ta a ƙirji. Ɗagowa tayi tana kallon sa cike da mamakin abinda ya faɗa. "W..wha..what are you saying?" ta faɗa still idanun ta akansa. Murmushi yayi tare da sarƙe hannaye cikin aljihu yana ƙarasowa gaban ta yace "Isn't that true, you like me don't you?." Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "No..i don't like you, and babu abinda zai sa na so mutum kamar ka, koh da kuwa kai ne kaɗai namijin da ya saura a duniyar." "Lies." "Am not lying, gaskiya nake faɗamaka, baka kai matsayin da zanyi maka ƙarya ba, idan ma kana tunanin inason ka ne yasa kullum kake bibiya ta then you're wrong, coz am inlove with someone else, and you know what?, yana da halaye masu kyau, sannan kuma ya tara dukkanin qualities ɗin da ake nema a wurin miji na gari, Unlike you da bakasan koh ɗaya daga cikin abubuwan nan ba, wanda bakada aiki sai kula matan banza sannan kuma kayi dukkanin abinda kaso dasu, kana tunanin ni irin matan nan ne da har zaka dinga bibiya ta dan kawai ka samu damar shawo kaina ka kuma yaudare ni da kalaman ka, ka cika mummunar manufar ka a kaina?" kai ta girgiza tana kallon sa kafin ta cigaba da faɗin "Ba zaka ta6a samun hakan ba, idan kana tunanin kuɗin ka dama kuma kyawun ka zasu ruɗe ni then you're mistaken, dan ni ba su ne a gaba na ba, samun miji na gari wanda yasan darajar mace yake kuma girmama ta tare da sauƙe dukkanin haƙoƙin da ya rataya a kansa irin sa nake biɗa kuma Alhamdulillah na riga da na samu, ba irin ka mai tara matan banza kana lalata musu rayuwa ba, ni Abdul shi ne za6i na kuma shi nakeso, kuma shi zan aura ba kai ba, ban ta6a sonka ba kuma ba zan ta6a son naka ba, idan ma kana tunanin inada interest akanka ne gara kayi gaggawar farkawa domin kuwa mafarki kakeyi, ni ba zan ta6a zama taka ba, keep that at the back of your mind, i will never be yours, never....ever" ta ƙarashe hawaye na gangaro mata idanun ta cikin nasa. Sosai da Sosai maganganun ta sukayi mugun tasiri wa zuciyar sa dama kuma gangar jikin sa, da kyar ya iya motsa ƴar yatsar sa tare da wiping ɗin fuskar sa, sosai jikin sa yayi matuƙar sanƴi da maganganun da ta faɗa masa, he can't believe ganin sa da Surayya ne yasa ta ɗauke shi mutumin banza kuma take yi masa kallon hakan. He can't believe DEENAH zata iya buɗar baki ta iya faɗa masa magana haka, sosai yaji dukkanin wani ƙuzarin dake tattare dashi ya gudu, he was stunned sosai kalaman ta sukayi matuƙar shigar sa, he was heartbroken for loving the wrong person cikin shekaru goma na rayuwar sa, he loves DEENAH but yau guda tayi turning ɗinshi down, tayi refusing nasa tun kafin ya bayyana mata abinda yakeji game da ita, sosai da sosai yakejin zafin hakan a ransa. "Get out of my house, sannan kuma kada ka sake dawowa, yakamata ka fita daga cikin rayuwar mu dukkanin mu haka nan, dan kuwa hakan ba zai sa ka same ni ba" ya jiyo ta faɗi hakan. Kai ya girgiza cike da dauriyar abinda yakeji a ransa yace _"You won't easily get me out of your life, and maganar bibiyar ki kuma yanzu na fara shi koh da kuwa hakan na nufin zan rasa dukkanin wani abinda na mallaka ne"_ kafin kuma yayi murmushi a fili yace "Oh come on girl, ban furta cewa inason ki ba tukun why then kika ɗau abin da zafi haka, koh kin ta6a ji a bakin wani cewa ni ZEEYAD inason ki ne?, well then forget, dama abinda ya kawo ni wurin ki shine, nazo nayi wa Mom naki sallama ne akan i will be going back tomorrow and just to check on how you're doing, nothing else, so relax please" ya faɗa yana kallon ta. Juyawa yayi ga Abdul da ya zama ɗan kallo yace "And you, i just hope dukkanin abinda ta faɗa akan ka turns out to be the truth, coz you doesn't seem innocent." Ganin Abdul ɗin ya haɗe fuska ne yasa shi yin murmushi yace "Relax Mehn, just don't try to break her heart, idan kuwa kayi hakan then i will make sure you regret it, Okay?" ya ƙarashe yana bubbuga kafaɗar Abdul ɗin. Murmushi Abdul ɗin yayi yace "I won't break her heart, she deserves a pure relationship, idanma kana tunanin hakan zai faru then..." Cike da basarwa ZEEYAD ya juya ga DEENAH yana ignoring maganar Abdul dan kuwa ba ƙaramin haushi yake bashi ba, koh kaɗan gayen baiyi masa ba, but ya rasa miye DEENAH ta gani tattare dashi har take ikirarin shi takeso, kafin yace "Is your Mom home?." Kai ta girgiza masa alamun a'a. Nan yace "Okay then tell me, ya jikin ki?." "Am Okay" ta faɗa cikin sanƴi tana kauda kai. Kai ya jinjina yace "Good, alright then i will take my leave, ki gaida Mom naki idan ta dawo." Kallon sa tayi kafin kuma ya wuce trying so hard ganin yayi controlling abinda yakeji a cikin zuciyar sa. Ƙarasawa wurin motar sa yayi ya buɗe ta ya shiga mai gadi na buɗe masa gate ya bar cikin gidan da mugun gudu kamar zai tashi sama, bai koh kula mai gadi dake ta faman ɗaga masa hannu yana washe haƙora ba. Sosai DEENAH taji jikin ta yayi sanƴi, a haka ta sallami Abdul ɗinma ya tafi dan kuwa bata tunanin zata iya cigaba da hirar dashi............. *********************** .............Juye-juye kawai takeyin akan gado ta rasa meke yi mata daɗi. Sosai takejin ba daɗi tare da jin haushin kanta kan maganar da tayi masa ɗazu. Haka ma 6angaren ZEEYAD he was heartbroken, bai iya runtsawa cikin dare ba, sabida jin DEENAH ba shi takeso ba sai wani daban. The Next day ya bar garin Sokoto zuwa Kano.............. ******************* ******************* ................"ZEEDAN wait" ta faɗa tana shan gaban sa. Niyyar wucewa yake ta riƙo hannun sa tace "Ka faɗamin maganar da kukayi da Daddy." Tsayawa yayi yana janƴe hannun ta cikin nasa, shiru yayi kafin kuma daga bisani yace "I can't refuse your Dad, coz i respect him, sannan inajin sa ne kamar mahaifina, ba zan iya ja da abinda ya faɗa ba, yayi min abinda koh Uban da ya haife ni ya gaza yi min shi, why do you think cewa zan iya buɗar baki na nace masa banason auren ki Khairat?." Murmushi mai nuna tsantsar farin cikin da take ciki tayi tace "Wowww, so that means we are really getting ENGAGED within the next four days, what a good news." Ra6a ta yayi ya wuce kafin kuma tayi saurin mara masa baya tana rungumo hannun sa tace "Don't you think we should go out for a romantic date since we are getting ENGAGED soon" ta faɗa tana kallon sa. "No am not going." "Well you have to, koh da kuwa bakaso hakan ba, zan koma ciki yanzu sannan na sanar da Daddy cewa tunda muke da kai baka ta6a nuna min kulawa ta musamman ba, idan ya tunkare ka da hakan kai kuma ba zaka iya yi masa ƙarya ba, dole ne ka faɗa masa abinda ke faruwa, daga nan kuma kaga dole ne dukkanin wani ƙimar ka da yake gani ya zube sabida ka kasa kula da ƴa ɗaya tal da ya haifa, bayan kuma irin halaccin da yayi maka ya fito da kai daga cikin ƙangin wuya" Shiru ZEEDAN yayi yana jinjina makirci irin na Khairat. Bai kula ta ba yayi gaba inda kuma ta mara masa baya, motar ya buɗe ya shiga ita ma ta shige, zuciyar ta cike da tsantsar farin ciki sabida zata mallaki irin mijin da ta daɗe kuma take mafarki tare da burin aura. ZEEDAN ya haɗu ne koh ta ina, babu abinda yafi ɗauke mata hankali game dashi face sexy body ɗinsa, infact komai game dashi abin sha'awa ne dama kuma burgewa, shiyasa take mutuwar ƙaunar sa take kuma mutuwar kishin sa tare da kuma toshe duk wata hanƴa da zata bi dan haɗuwar sa da wata macen, koh da ta koma US karatu hankalin ta na kan ZEEDAN yayin da kuma zuciyar ta ke cike da mugun kishin sa, dan kuwa tasan yana chan ƴan mata kowacce na kawo tata harin, ita kanta tasan idan ta mallaki ZEEDAN toh tabbas ta gama cirar tuta ne a cikin ƙawayen ta dama kuma abokan ta, dole ne su bata award ɗin mallakar wannan santalelen saurayin. Duk tana tunanin nan ne cikin murmushi sabida burin ta na daf da cikewa. Idanun ta ne suka faɗa kan wani ɗan ƙaramin gift da akayi wrapping ɗinsa. Hannu ta kai ta ɗaukaka tana jujjuya shi tana kallo kafin kuma ta yaga ledar gift ɗin ta ciro kwalin tare da buɗe shi. Idanu ta waro tare da furta "Wowww" tana ciro abin hannun dake ciki tana kallo. Duk abinda take ZEEDAN bai kula ta ba dan kuwa idan yana yi mata magana ji yake haushi da takaicin kansa na kama sa. "Is this for me?" ta faɗa tana kallon sa. Ajiyar abin ta ya bata ba tare da ya koh kalle ta ba idanun sa na kan tuƙin da yakeyi. Murmushi tayi tace "Am definitely sure nawa ne, ka saya ne dan kayimin gifting ɗinshi a Engagement ɗinmu, am sure nawa ne coz it's diamond and the design is so beautiful kai ne ka zana shi akayi maka irin sa?." Da ƙarfi ya danna parking ɗin motar zuciyar sa na tafarfasa, hannu yasa ya warce bracelet ɗin a hannun ta yana maida shi cikin kwalin sa tare da ajiyewa a gaban sa. Da kallo ta bisa cike da jin haushin abinda yayi mata tace "How dare you?." Shiru yayi kafin yace "Get out of my Car." Murmushi tayi tace "Your car?, kokuma motar da Daddy na yayi maka hanƴar samun kuɗin sayar ta?." Juyowa yayi ya kalle ta kafin ya saki murmushin kan le6e yace "Your Dad?, Yes Dad ɗinki ne yayi min hanƴar samun aiki but don't forget cewa da gumi na nayi aiki na samu kuɗin da koh Dad ɗin naki bai mallaki irin su ba, you know what?, ina ɗaga miki ƙafa ne saboda Dad naki da kuma Mom naki da suka kasance mutanen kirki, banaso nayi abinda zai 6ata musu rai, but tunda kince ba zaki gyara halayen ki ba then there is no way da zan dinga haɗa inuwa ɗaya dake, and this diamond bracelet here, not even your family can afford it, so there is no way da zan bar ki ki sanƴa shi coz it's not made for you, it's for someone so very special and dear to me, so now get the hell out of my car" ya faɗa yana kallon ta cikin tsukewar fuska. Sosai ta sha jinin jikin ta da yadda yayi mata magana kuma yake kallon ta, sai dai tayi ƙarfin hali tace "Someone so dear and special to you, who the hell is she?" ta faɗa cikin rawar murya alamun ranta yayi mugun 6aci zuciyar ta na tafarfasa. Scoffing yayi tare da maida duban sa kan box ɗin yace "Knowing who she is won't do you any good, out of my car....now" ya faɗa yana juyowa ya kalle ta. "Am not going out, babu inda zanje har sai ka faɗamin wacece ita, you can't love someone idan ba ni ba, no one deserves to be loved by you except me Okay?, am not going out until you tell me who she is" ta faɗa idanun ta na kawo hawaye. Cize baki yayi kafin ya buɗe motar ya fita yana zagayowa inda take ya buɗe yace "Get your fucking body out of my car." Maƙe kafaɗa tayi tana harɗe hannaye a ƙirji tace "Babu inda zanje, taya zaka sauƙe ni a local area ɗinnan, and baka ga irin shigar dake jiki na bane, babu inda zanje ni." Sai a sannan yama san irin shigar dake jikin ta, doguwar riga ce mai hannun vest irin ta turawa wanda koh guiwa bai kai mata ba duk fararen cinƴoƴin ta a waje, kanta kuma head-band kawai tasa tare da kama gashin ta da ɗan ƙaramin ribbon. Kauda idanun sa yayi yana sake jin yadda zuciyar sa ke tafarfasa, tabbas idan ya bar ta a haka bai kyautawa iyayen ta ba, sometimes kana yiwa mutum abu ne sabida irin halaye masu kyau da na kusa dashi kuma wadanda kakejin kunƴar su suka tara, idan ba haka ba wasu mutanen halin su ma kaɗai ya isa idan suna daf da faɗawa wuta basu sani ba,ka kauda idon ka a zumar cewa kai ɗinma bakasan da wutar ba. Zagayawa yayi ya koma cikin motar tare da fizgar ta a tsiyace kai kace zai ɗauke kan kwaltar ne................. _*Idan kuka jini shiru ku dinga yi min uzuri, duk ranar da baku ga posting da safe ba, toh kuyi haƙuri zuwa dare zaku gani, duk ranar da baku gani da dare ba toh kuyi haƙuri zuwa wayewar gari, yin typing da posting ba shi kaɗai ne aiki na a matsayi na ta ƴa mace kuma budurwa wacce ke gaban iyayen ta ba, dole ne da akwai abubuwan da sai anayi wa mutum uzuri, masu cewa har kun gaji da jira kun cire rai, ku daina faɗar haka please, banajin daɗi wlh👏🏽🥹*_ *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *023...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _Ina Masoyan Amjad da Mhizz jidderh?, zamu fara sabon novel, wanda ba'a ta6a kawo muku irin shi ba, namu salon na daban ne, ya ƙunshi tausayi, ƙin biyayyah ga iyaye da Sauran su, kude ku kasance damu a wannan tafiya da zamuyi cikin littafin *BANI DA ZAB’I*, salon na daban ne, inaso ku nuna mana soyayya fiye da yadda kuka nuna mana a cikin ZEEYAD dama kuma TAREEQ👏🏽🥰_ *Wannan Page ɗin maimakon na jiya ne da banyi posting ba😆* A matuƙar fusace yayi parking motar ya fito ba tare da yabi ta kanta ba ya nufi ƙatuwar ƙofar da zai sada shi cikin office nasa. Murmushi Khairat ta saki tare da buɗo ƙofar ta fito kafin ta mara masa baya cikin takun ta ɗai-ɗai hannayen ta sarƙe a ƙirjin ta. Lifter ya shige kafin ya sada shi da flour ɗin office ɗinsa. Ba tare da yabi ta kan masu yi masa gaisuwa ba ya buɗe ta ya shige ƙofar ta rufu. Ja yayi ya tsaya yana ƙare mata kallo ransa na matuƙar sake 6aci. Zagayowa yayi tare da zama kan seat ɗin sa yana lumshe idanu. "Babe?" ta kira shi. Jin yayi mata shiru yasa ta cigaba da faɗin "Babe, yaushe rabon da ka ganni yanzu, amma koh nema na bakayi ba afterall ina chan hospital banida lafiya sai jiya aka sallame ni, but you didn't even bother to know my whereabout, ka kyauta da hakan kenan?" ta faɗa tana kallon sa. Buɗe idanun sa yayi yana kallon ta cike da haushi yace "Bakida lafiya ai ba mutuwa kikayi ba, sannan maiyasa zan neme ki ai tun da chan ma kece kike nema na, i thought kin.saduda kuma kin rabu dani ne but i can see har yanzu kina kan bakar ki." "Babe please maiyasa kakeyi min haka ne, maiyasa ba zaka soni ba koh da bai kai wanda nakeyi maka ba, dan Allah kaji tausayi na mana...." Sauƙar marin da taji a ƙuncin ta ne yasa ta saurin dafe kumatu tana, hannayen ta riƙe da ƙunci tana ɗagowa ta kalli Khairat dake ta huci kamar zata haɗiƴe ta. Tashi Surayya tayi tsaye hannayen ta har yanzu dafe da ƙunci tana kallon Khairat cike da mamaki. Hannu Khairat ta ɗaga da niyyar kai mata wani marin tayi saurin riƙe hannun nata. Daddagewa tayi itama tare da baiwa Khairat wani irin zazzafar mari a fuska. "How dare you?" cewar Khairat cike da mamaki tana kallon Surayya. "Kokuma how dare you ba, who gave you the gut da zaki faɗo from nowhere ki mare ni har ma kike ƴunƙurin ƙarawa, dayake nikuma sakarya ce kike tunanin na barki ki mari banza kenan komiye, who the hell do you think you're?." Sosai ran Khairat ya 6aci, nan kuma tace "He is my Man, so you better stay away from him indai kinason kanki da lafiya." Riƙe kunkumi Surayya tayi tana kallon Khairat from head to toe tace "Hun, your Man or my Man?." Kallon ZEEDAN da ya miƙe tsaye yana shirin ficewa Khairat tayi kafin tayi saurin shan gaban sa tana faɗin "Ina kake tunanin zakaje, ya zama dole ne ka tsaya ka warware ƙullin da ka haɗa sannan kuma kayi min bayanin wacece wannan karyar dama kuma matsayin ta a wurin ka, idan kuma ba haka ba sai na tabbatar da nayi mata mugun illa anan wurin." "Alright go ahead then, tunda ke Mahaukaciya ce" ya faɗa yana ra6a ta ya wuce. Da sauri ta riƙo kwalar rigar sa ta baya tana shan gaban sa tace "Na faɗamaka babu inda zakaje ka, ya zama dole ne ka faɗamin koh wacece ita" ta faɗa cike da 6acin rai idanun ta na yin jaa sabida irin muguwar kishin dake cinta. Kallon Surayya yayi yace "Try to defend yourself from her, dukkanin ku bakuda wani value a gare ni, so why would i waste my time wurin ganin haukan ku, after all i have alot of important things to do" ya faɗa yana maido duban sa kan Khairat. "ZEEDAN, wacece wannan ɗin wai, maiyasa take abu kamar mahaukata?." "Kece mahaukaciya, jaka kuma akuya mai maƙalewa mazan mutane, toh bara kiji na gayamiki ZEEDAN nawa ne gara kinyi gaggawar zuwa kin samu wani saurayin, amma aure tsakani na dashi tamkar an ɗaura ne." Kallon ta kawai Surayya take kafin kuma tayi murmushi tace "Au ashe ma dai kice layi ɗaya muke dukkanin mu ɗin akuyoyi ne tunda kema binsa kike tsirara, GOD forbid ZEEDAN ya auri mahaukaciya irin ki, ai baikamata kice ni ina binsa ba tunda kema ba wai an ɗaura auren naki dashi bane, bale ma kuma ba auran naki zaiyi ba." Zuwa tayi zata riƙo Surayya nan tayi saurin ja da baya tace "GOD forbid bad things, wai kina nufin faɗa zakiyi dani, ashe ma bakida aji koh kaɗan gaki nan dai kamar wayayyiya amma kwakwalwar babu saiti, naji ZEEDAN baya sona amma koh bakomai yafi sona akanki koh dan hauka da rashin kamun kai dake tattare dake, jaka kawai" ta ƙarashe haɗi da jan dogon tsaki tare da fuzgar jakar ta ta bar cikin office ɗin, dan kuwa ZEEYAD tuni ya daɗe da ficewa ya bar su. Daskarewa khairat tayi tsaye anan hawayen baƙin ciki na kawo mata, ta lura idan ba tsaye tayi akan wannan banzar Surayya ɗin ba, ba zata rabu da ZEEDAN cikin sauƙi da kwanciyar hankali ba. A matuƙar fusace ta fice daga office ɗin itama zuciyar ta na matuƙar ƙuna sosai. Koh da ta fita farfajiyar Company ɗin, bata hango motar ZEEDAN a parking space ba, hakan na nufin tafiya yayi ya barta kenan. *********************** Zaune suke dukkanin su a ƙatuwar falon gidan da ya ƙawatu da kayan alatu da more rayuwa iri-iri, tsaya musalta girman falon da kyawun sa 6ata lokaci ne. Khairat ce rungume jikin wata kyakkyawar mata sai kuka take kamar ranta zai fita, inda kuma matar ke ta rarrashin ta. ZEEDAN kuwa a ƙasa yake zaune kusa da wani babban mutum falon ta ɗau shiru babu abinda kakeji sai sautin kukan Khairat. Numfasawa mutumin yayi tare da gyaran murya yace "ZEEYAD ɗana, kaji dai bayanin da Khairat tayi, shin dagaske ne kana kula wata daban a waje?." Shiru ZEEDAN yayi kafin kuma ya saita nutsuw sa yace "Hakane, amma maganar gaskiya shi ne yarinƴar itace take bibiya ta, babu soyayyar ta koh kaɗan a cikin zuciya ta, nayi dukkanin iya ƙoƙari na na ganin ta rabu dani sai dai taƙi yin hakan." Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe kafin yace "ZEEYAD nasan ba zakayi min ƙarya ba, amma inaso ka faɗamin tsakani da Allah, akwai soyayyar Khairat a zuciyar ka koh babu?." Shiru ZEEDAN yayi yaji tambayar tayi masa mugun nauyi da tsauri, tayaya zai fara buɗar baki a gaban su yace bayason ƴar su?, bayan su kuma sun nuna masa so da ƙauna tamkar su suka haife shi, idan yace yanason Khairat then ya cuci kansa, idan kuma yace bayason ta baisan wane irin kallo zasuyi masa ba. "Kayi shiru ZEEYAD, ka faɗi ra'ayin ka, babu wanda zai tilasta maka, koh dai akwai wacce kakeso ne daban, ka faɗamin nikuma nayimaka alƙawarin nemo maka auran ta." _"MADEENAH, but bataso na, she loves someone else, ba zai iya raba ta da abinda takeso ba muddin hakan ne zai sanƴa ta farin ciki, she seems so happy with that guy, she would never be happy with me, sai ma burin ta kaɗai da mafarkin ta da zan ruguza"_ ya faɗi hakan a ransa kafin kuma cikin dauriya yace "No." Haɗa ido Momy da Daddy sukayi tare da yin murmushin jindaɗi, nan Daddy yace "Masha Allah, kana nufin a shirye kake da ka auri Khairat, sannan kuma kanason ta?." Kai ya jinjina kawai ba tare da ya iya cewa komai ba. Murmushi sukayi kafin duk su furta "Alhamdulillah." Momy ce tace "Toh ai sai ki share hawayen naki hakanan koh tunda kinji abinda ya faɗa, ki bar sanƴawa kanki damuwa hakanan" ta faɗa tana sharewa Khairat ma dake murmushi hawaye. "Masha Allah, kasan nan da kwana uku ne Ranar sa ranar auren ku, zamu tattauna batun da kawunan ta dama kuma mahaifiyar ta dan ganin yaushe yakamata a sanƴa ranar auren." Kai ya jinjina kafin yace "I need to go, inada aiki a office." "Bakomai, zaka iya tafiya." Miƙewa yayi idanun sa sunyi matuƙar yin duhu yanajin kansa na sara masa ya fice daga cikin falon. Motar sa ya shiga yana kifa kai akan steering zuciyar sa nayi masa zafi sosai. Tunanin family ɗinsa ya shiga, tayaya yana da family kuma wasu suzo su ɗaura masa aure da ƴar su?, yana tunanin yanzu lokaci yayi da zai koma garesu, bayason ɗaura wata damuwa koh nauyi akansa, dan kuwa har yanzu zuciyar sa bata bar ƙuna tare da kwaɗayin ɗaukar fansar abinda sukayi masa ba, a duk sadda ya tuna dasu yanajin wutar tsanar su na sake ruruwa masa ne a zuciya, especially mahaifin sa da ya kasance Sarki ya kuma kasa kula dashi, baya tunanin zai yafewa kowanne daga cikin su, dukkanin su sai sun ɗanɗani guɗar su ne, yayi alƙawarin ba zai bar kowa ba, sannan kuma zaiyi mulkin da ba'a ta6a yin irin sa a ƙasar ba, bayason tunowa dasu shiyasa ya toshe dukkanin wata hanƴa da zai sanƴa sa yin kasuwanci da ƴan ƙasar kokuma yaji wani labari da ta shafi ƙasar, hakan yasa bayason kallon News dan gudun ma kada ya kalli wani abu game da ƙasar da zai sanƴa sa cikin damuwa ya hana shi sukuni, balle kuma ya tuna masa da cewa shi ɗin ɗan Sarki ne. Hannun sa ya nausa akan steering ɗin idanun sa na matuƙar yin jaa sosai, fuskar sa ta canza launi zuwa jaa, sosai baƙin ciki da 6acin rai suka sake samun gurbin zama a cikin zuciyar sa. Wacce yake tunanin zata zame masa waraka kuma wani daban takeso, wani chan daban da baikamata ace shi zata so ba, amma ta bar zuciyar ta ta rinjaye ta ta fara sonsa. A haka yaja motar tasa ya bar cikin gidan zuwa gidan sa. ******************** Tsaye yayi a gaban ƙatuwar hoton ta da ya zana yanajin baƙin ciki sosai ganin ba shine zai mallaki DEENAH ba. Zuciyar sa DEENAH takeso ba Khairat ba, sai dai sun kasa gane hakan, tayaya suke tunanin zai iya buɗar bakin sa yace musu wata daban yakeso ba ƴar su ba, bayan irin halarcin da sukayi masa a rayuwa?. Sauƙe jajayen idanun sa yayi cikin nata yana kallo, maganganun da ta faɗa masa ne suka shiga dawo masa cikin kwakwalwa. _"Am not lying, gaskiya nake faɗamaka, baka kai matsayin da zanyi maka ƙarya ba, idan ma kana tunanin inason ka ne yasa kullum kake bibiya ta then you're wrong, coz am inlove with someone else, and you know what?, yana da halaye masu kyau, sannan kuma ya tara dukkanin qualities ɗin da ake nema a wurin miji na gari, Unlike you da bakasan koh ɗaya daga cikin abubuwan nan ba, wanda bakada aiki sai kula matan banza sannan kuma kayi dukkanin abinda kaso dasu, kana tunanin ni irin matan nan ne da har zaka dinga bibiya ta dan kawai ka samu damar shawo kaina ka kuma yaudare ni da kalaman ka, ka cika mummunar manufar ka a kaina?"_ Zubewa yayi akan couch yana runtse idanun sa "Please don't do this to me" ya faɗa cikin rawar murya. Wayarsa dake kan center table ce ta ɗau ringing ɗin da ya tsinkar masa da zuciya tare da faɗar masa da gaba. Kallon wayar ya tsaya yi har ta tsinke bai iya ɗagawa ba. Sosai yaji gaban sa na wani irin mummunar faɗuwa har wani kiran ya sake shigowa. Hannu ya kai ya ɗau kiran yana kafawa a kunne. Muryar Jafar yaji cikin kuka, hakan yasa shi miƙewa tsaye yace "Tell me." Bansan mai Jafar ya faɗa masa ba, wanda ya sanƴa shi sakin wayar tasa a ƙasa glass ɗinta na tarwatse wa ba. Sosai idanun sa sukayi jaa, kafin kuma jikin sa ya shiga rawa tsabar irin shock ɗin da ya shige sa. Sosai ya girgiza da abinda kunnuwan sa suka jiye masa. Da sauri ya maida duban sa kan ƙatuwar hoton DEENAH yana kallo, kafin kuma yayi hanƴar fita cikin tashin hankali ya fice daga cikin falon da gudu. ************************* Tun da ZEEYAD ya tafi DEENAH ta kasa samun kwakwarar sukuni a zuciyar ta. Sosai take tunanin sa haɗi da mafarkin sa a kullum. Hankalin ta bai tashi ba sai da Jafar yace mata ZEEYAD is getting ENGAGED nan da 3days. Sosai take rufe kanta a ɗaki ta sha kuka, ita kanta tasan ƙarya ne tace batason ZEEDAN. Sosai soyayyar sa ke nuƙurƙusar mata da zuciya tana neman illatar da ita. She can't believe mutumin da taso tun tana ƙarama turns out to be wata daban yake so ba ita ba. Zuciyar ta koh kaɗan batason Abdul sai ZEEYAD, gashi rana guda yana neman su6uce mata. Ganin da takeyi masa ne kaɗai yake sata jin nutsuwa a ranta, amma kuma batasan maiyasa take tsintar kanta da gayamasa maganganu marasa daɗi ba, sosai takejin zafi da haushin kanta a duk sadda ta faɗa masa magana marar daɗi. Bakomai bane ya jawo hakan sai ganin sa da Surayya da tayi, shi ya 6ata komai, but koh da ace shi ɗin ya kasance mutumin banza kamar yadda take hasashe bata ta6a tunanin zuciyar ta zata daina son sa. Tsaye take a gaban mirror tana ganin yadda ta faɗa sosai. Jakar makarantar ta ta ɗauka, tana jin kamar ta fasa zuwa makarantar dan kuwa wani iri takejin ta yau ɗin, ga kuma zuciyar ta da bai bar tsinkewa ba wanda takejin hakan tun cikin dare. Falo ta fito ta samu Umma zaune tana breakfast. "Umma na tafi" ta faɗa. Kallon ta Umma tayi tace "Ba zakiyi breakfast ɗin ba?." "Na ƙoshi Umma, bana jin ƴunwa." "Kin sha maganin ciwon kan kuwa?." "Na sha Umma, ni zanyi latti bari na tafi." "Toh shikenan,a dawo lafiya, Allah ya tsare hanƴa, ki tabbatar fah kinci abinci a makaranta." "Insha Allah Umma" ta faɗa tana ficewa. Adaidaita ta tara ya kaita makaranta ya sauƙe. Lectures sukayi but duk hankalin ta baya kai har lecturer ɗin ya fice. Ƙawayen ta da ta ɗan saba dasu cikin kwana biyun nan ne suka fita tare, sai da suka je sukayi sallah sai dai banda ita kafin su fito suje cafteria su sayi abinci. Gida kawai takeson komawa sakamakon jin ta da take very nervous, tsikar jikin ta na tashi, tanajin wani irin strange feeling tattare da ita. Bata bisu sun koma class ba ta kama hanƴar gida. A hankali take tafiya har ta fice daga cikin school ɗin. Idanun ta ne suka hango mata mai saida agwaluma ta chan tsallaken titi sai feshe ta yake da ruwa a cikin gora, gasu fresh dasu. Murmushi tayi tare da jiran motocin dake kan kwaltar su ragu. DEENAH nada tsoron tsallake kwalta musamman ma wannan dayake high way, shiyasa duk tsoro ya kama ta takejin kamar ta fasa sayan agwalumar. Hango sa da tayi yana shirin jan kuskus ɗin sa ya bar wurin ne yasa ta sanƴa ƙafar ta kan kwaltar tana shirin tsallakawa da gudu. Horn ɗin wani mota da batasan da zuwar sa bane ya gigitar da ita, kamar kuma wacce aka ɗaurewa ƙafafu haka ta kasa motsa ƙafar ta ta tsaya tana kallon ƙatuwar motar. Within a blink of an eye kafin kuma tace zata sake motsa ƙafar ta motar nan har ta iso ta tare kwashe ta yayi sama da ita. Burki motar taja da ƙarfin tsiya kafin kuma ya sake jin ƙarar sauƙar abu a gaban glass ɗin motar tasa, inda jini ya wanke masa shi. Take kuma ta sake gangarowa ta faɗo ƙasa. Babu abinda kakeji sai muryar mutane na nanata kalmar "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un." A matuƙar firgice mai tuƙin motar ya fito hannayen sa akai shima yana nanata "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un." Kan kace miye kuma mutane sun taru akanta, babu abinda kake ji sai salallami da hayaniya. Ɗaukar ta akayi fuskar ta da aka rufe da farar Hijabin ta yayi matuƙar 6aci da jini, haka ma kayan jikin ta. Mota aka samu aka sanƴa ta sannan kuma akayi asibiti da ita, inda wasu suka wuce nearest police station dake wurin dan sanar da faruwar lamarin. Koh da aka kaita asibiti kasancewar akwai ƴan sanda tare dasu yasa akayi saurin admitting ɗinta. ICU shine abinda aka rubuta a samar ɗakin da aka shigar da ita. Jakar makarantar ta aka bincika koh za'a samo wani clue ɗin inda take da zama. Wayar ta suka ciro nan dai suka ga babu security, kai tsaye kuma Contacts suka shiga. *BLOOD🩸💦❤️* shine abinda suka ga anyi saving numbern da akayi last kira dashi, kafin kuma su danna dialing numbern. Bugu biyu Jafar ya ɗaga tare da yin sallama yace "Sis?." "Assalamu Alaikum" cewar police. "Wa'alaikumusalam" Jafar ya amsa muryar sa na nuna alamun ɗan mamaki. "Kai ɗan uwan mai wannan wayar ne?." "Eh ɗan uwanta ne, maiyafaru ta jefar da wayar ne?." "A'a ba jefar da wayar tayi ba, ta samu hatsari ne a hanƴar ta ta zuwa makaranta, she was knocked down by a truck." "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, DEENAH, wane hali take ciki yanzu, tana ina yanzu?" ya faɗa cikin tashin hankali. "Zaka iya zuwa nan general hospital..." Tun bai idda ba Jafar ya katse kiran, kafin kuma cike da tashin hankali ya baro office dan zuwa asibitin. A hanƴa ya kira Umma akan ta same shi a asibiti sai dai bai faɗa mata abin dake faruwa ba, hakan yasa ita ma hankalin ta yayi mummunar tashi ta baro wurin aikin ta. ******************* Safa da marwa kawai sukeyi a gaban ƙofar ICU ɗin, Umma inbanda kuka babu abinda takeyi, shi kansa Jafar kawai daurewa yakeyi amma ya kasa rarrashin Ummar tasu. Gashi tunda suka zo kusan awanni uku kenan ba'a bar su sun shiga ba, likitocin ma basu bari sunyi musu magana ba. Waya ya ɗauka ya kira ZEEDAN tare da shaida masa abin dake faruwa ba tare da ya iya controlling kukan da yazo masa ba. ****************** Su Umma na zaune jugum har dare sallah ne kaɗai ke tada su, kamar daga sama suka ga ZEEYAD ya faɗo. Da sauri Jafar ya nufe shi nan ya riƙo Jafar yace "How is she, tana ina yanzu?." Ƙofar ICU ɗin kawai yayi masa nuni, ba tare da kuma ya jira cewar sa ba ya nufi ƙofar ya buɗe ta tare da shigewa ciki. Duk da kallo su Umma da Jafar suka bisa Umma na tashi tsaye. Turus yaja ya tsaya ƙafafuwan sa na neman gaza ɗaukar sa. DEENAH ce kwance bata numfashi kanta ya sha ɗauri da farin Bandage an sanƴa mata irin abinda ake sawa patience ɗinda suka samu karaya a wuyar su, ga kuma abin shaƙar numfashi dake manne a hancin ta, injinan dake zagaye da ita suna taimaka mata wurin inganta lafiyar ta kuwa ba'a magana. "Ma..MADEENAH?" ya kira sunan ta a hankali. Takawa ya fara zuwa wurin ta likitocin sukayi saurin riƙe shi. Cike da 6acin rai yace "Let go of me" yana fuzgewa. Cakumo wuyar ɗaya daga cikin su yayi yace "Don't...don't let her die..." "Koma miye matsayin ka a wurin ta yakamata ka fita yanzu bamu gama aikin da mukeyi akanta ba tukun, we can't save her life muddin bamu samu nutsuwar yin hakan ba" cewar ɗaya daga cikin su. Cika wanda ya cakume ɗin yayi yace "Yes...go on save her please, don't let her die, idan ta mutu nima mutuwa zanyi, please don't let her die" ya faɗa.pleadingly yana haɗa hannayen sa wuri ɗaya. "Zamu yi iya ƙoƙarin mu na ganin mun ceto rayuwar ta, but please ka fita waje tukun." Tsayawa yayi yana kallon DEENAH idanun sa na kawo ruwa, kafin kuma yayi saurin kauda kansa yana jinjina musu kai ya fice a hankali cikin mutuwar jiki. Ganin yadda ya fito ne yasa su Umma tunkarar sa cike da tashin hankali. "How is she, ka ganta, miye likitocin suka faɗa?" cewar Jafar yana kallon sa. Kallon Umma da ta sha kuka ta godewa Allah ZEEDAN yayi, nan duk tausayin ta ya kama shi nan yace "She would be fine." "We have waited for so long now, but har yanzu basu bari mun ganta ba almost 8hrs now." Shiru ZEEDAN yayi yana sunkuyar da kai kafin kuma ya wuce ba tare da ya sake tanka musu ba, dan kuwa shi kaɗai yasan irin abinda yakeji a cikin zuciyar sa. ******************* Around 2am na dare har yanzu babu wanda ya rintsa a cikin su. Kallo ɗaya zakayi musu kaga irin tashin hankalin da suke ciki. Buɗe ƙofar ICU ɗin akayi, kafin wata nurse ta fito cikin gudu, nan duk suka bita da kallo tsoro da fargaba na ƙara ƙaruwa musu a zuciya. Ba'a jima ba ta dawo da wani abu a hannun ta tana shigewa ciki. Bin bayan ta duk sukayi suka shige dan ganin abin dake faruwa. Abin da nurse ɗin ta kawo ne aka shiga manna mata shi a ƙirji yana ɗago ta da ƙarfi da alamu dai numfashin ta da yayi ƙasa sosai ake son dawo dashi. Kusan sau biyar akayi mata hakan, suna kaiwa na shida kuma shiru kakeji abin bai ɗago ta ba. Sake manna mata shi sukayi nanma shiru kakeji. Kallon juna doctors ɗin sukayi kafin ɗaya ya girgiza kai. Numfashi duk suka sauƙe da ƙarfi, kafin kuma su shiga cire mata life saving machines ɗin da suka sanƴa mata ɗin. "What's going on?" cewar Jafar yana kallon su. Duk juyowa sukayi suna kallon su kafin ɗaya yace "Am sorry, she is..." "Oh really, you are trying to tell us that she is gone, isn't it?" faɗin ZEEYAD yana kallon sa. Takowa yayi bakin bed ɗin tare da jan kujera ya zauna yace "Look at her, just look at her face, tayi maka kama da wanda ya mutu?." Murmushi yayi kafin yace "I know she is not dead, she is alive you need to check her again" ya faɗa a tsawace yana miƙewa tsaye. Umma kam tuni ta sume anan wurin nan nurses biyu sukayi kanta. Jafar kuwa sumar tsaye yayi yana kallon fuskar ƙanwar tasa. ZEEDAN kan DEENAH ya nufa ya shiga marin fuskar ta a hankali yana faɗin "Hey wake up, wake up, everyone is here for you, your family are here, all of us are here, you can't just die easily like this, MADEENAH wake up, i know baki mutu ba, just wake up please" ya faɗa yana cigaba da bubbuga fuskar tata. Dafa shi doctor ɗaya yayi yace "Ba abin mamaki bane idan ta mutu, koh ka manta da cewa dama dukkanin mai rai mamaci ne?." A fusace ya juyo cikin tsawa yace "Ban manta ba, but MADEENAH ba zata mutu yanzu ba, she is supposed to be my wife, i know she is not dead you're jusr making this up, MADEENAH wake up please" ya faɗa cikin hawaye yana rungumo ta jikin shi. "Please you can't do this to me babe, you can't leave me so soon, i know you're not dead." Shiru yaji baiji motsin komai a jikin sa ba, but dukda haka ya kasa yarda da cewa DEENAH ta mutu. Sakin ta yayi yana ɗan janƴe jikin sa, nan yaga ta koma ta faɗa kan bed ɗin jikin ta a sake. Durƙushewa yayi a wurin yana kamo hannun ta ya damƙe cikin nashi yace "Please MADEENAH kar kiyi min haka, ke kaɗai ce farin ciki na da ta rage, ke kaɗai ce kike sani farin ciki, i know you don't like me, kuma bakya sona, but please kar ki mutu nikuma nayi miki alƙawarin ba zan sake shigowa rayuwar ki na takura miki ba, i promise you this, just wake up please." "She is not waking up" cewar Jafar. Kallon sa ZEEDAN yake, nan ya sake cewa "She is dead for sure." "No she is not, i know she is not dead." Ƙarasowa Jafar yayi wurin yana kamo hannun DEENAH ya sanƴa cikin nasa, cikin kuka yace "Bata motsi, bata numfashi, look nima ba zan yarda da cewa ta mutu ɗin ba, amma tun da muka rasa Abban mu kuma har yau bai dawo ba, then na yarda da cewa na rasa ƙanwata ma, yes it really hurts to believe this but we can't change the fact, DEENAH..." ba tare da ya ƙarasar ba ya tashi ya fice daga cikin ɗakin da sauri sakamakon kukan da yazo masa. ZEEDAN yana gani suka ƙarasa cire mata abubuwan da aka sa mata kafin su rufa mata farar kyalle a fuskar ta. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *024...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ZEEYAD na durƙushe a wannan wurin helplessly yana kallon DEENAH dake rufe da farin kyallin. Rayuwar su ta baya ne ya shiga dawo masa kwakwalwa, how kind she is, the way she used to stare at him with her captivating wide eyes, and a lot of things, kawo izuwa ga ranar da ya fara ganin ta bayan haɗuwar su da shekaru goma. "Noooo" ya faɗa da ƙarfi crying his heart out. "Am sorry, am so sorry, don't leave me please i beg you DEENAH" ya faɗa yana kifa kansa kan bed ɗin hannun ta cikin nasa. ***************** Ɗagowa yake a hankali da idanun sa dama kuma fuskar sa da yayi mugun jaa yana mai addu'ar Allah yasa dukkanin wannan mummunar abin a mafarki ya gansa. Hannun ta dake cikin nasa ya kalla kafin kuma ya shiga bin ta da kallo har yanzu tana rufe da farar kyalle. Baki ya cize yana runtse idanu, miƙewa yayi zaune tare da yaye farar kyallen yana kallon fuskar ta. No!, he can't believe DEENAH is gone, he can't believe kyakkyawar fuskar nan is gone. "May be she just fall asleep" ya faɗa trying to get rid of his sorrows. "MADEENAH?, MADEENAH??" ya faɗa yana ɗan bubbuga kumatun ta. "Look MADEENAH, bansan ki da irin wannan wasan ba, your family is all worried about you, those stupid doctors da basusan aikin su ba are saying that you are dead, but i know that you are still alive, i guess basu gwada ki dai-dai bane, you just wait here, dole ne na kira su suzo su sake gwada ki, just wait here please, i will be right back" ya faɗa kamar wani mai sumbatu yana miƙewa ya fice daga ɗakin. Jafar ya gani zaune ya haɗa kai da guiwa, ba tare da ya kula sa ba ya wuce. Wani doctor ya gani yana wucewa nan yayi saurin kiran sa yana faɗin "Hey you wait right there." Ƙarasawa yayi gaban doctor ɗin kafin yace "Come with me, i want to show you something" ya faɗa yana riƙo hannun doctor ɗin zuwa ɗakin da take. Kanta suka tsaya nan yace "Look those silly doctors said that she is dead, i want you to check her again, coz i know she must still be alive, come on." Kallon sa Doctor ɗin yake cike da mamaki kafin yace "What are you saying?, she is already dead, mun riga munyi confirming hakan tun jiya, she is just a corpse...." "No she is not a corpse, my DEENAH is not a corpse, MADEENAH sunan ta ba gawa ba, get it?" ya faɗa cike da 6acin rai yana kallon sa. "Look why don't you get some rest?, you look so stressed, inaga shiyasa har yanzu you refused to accept the fact that she is dead, it's already 4am da zaran anyi sallar Asuba zamuyi discharging naku." "Let's see who you discharge then" ya faɗa yana juyawa ga DEENAH. Hannu yasa ya ɗago ta yana kallon fuskar ta yace "Inaji a jikina baki mutu ba, and i will make sure that i prove them all wrong na cewar kin mutu" ya faɗa yana ɗagowa ya kalli doctor ɗin. Ficewa yayi daga ɗakin Doctor ɗin ya bisa da kallo cike da mamakin sa na dagewa cewa DEENAH bata mutu ba. Jafar ne ya ɗago ya kalli ZEEYAD da ya fito da DEENAH riƙe a hannun sa, nan ya tashi cike da mamaki yace "Where are you taking her?." Bai kula Jafar ba yayi gaba, hakan yasa Jafar saurin mara masa baya. Ficewa sukayi zuwa farfajiyar asibitin kafin ya nufi parking space inda ya ajiye motar sa, Jafar ne ya buɗe masa bayan ya sanƴa DEENAH. Kafin duk su zagaya su shige cikin motar. "Where...where are we going?." "Somewhere, that i can prove them all long" ya faɗa yana jan motar a tsiyace ya bar cikin asibitin. Kai tsaye wani Babban private hospital mai kyau da tsada ya nufa. Zuwan su kuwa aka kar6i DEENAH duk da kuwa basu ga alamun rai tattare da ita ba. "She will be fine, i know she will" ya faɗa yana kallon Jafar. Sallar Asuba aka fara kira dan haka dukkan su masallaci sukayi. Basu dawo ba sai da gari ya ɗan waye. ZEEDAN ne yace "I know bata mutu ba, kafin mu isa yanzu she must be awake." Jafar dai kawai jinsa yakev dan kuwa yaga alamun kamar ZEEYAD ɗin kwakwalwar sa ta ɗan ta6u ne, but shi ya san DEENAH ta mutu, amma shi sam babu alamun zai yarda da hakan nan kusa. "Wait...don't tell me cewa kaima ka yarda cewa ta mutu?" ya faɗa yana kallon Jafar da yayi shiru yana saurarar sa. Shiru Jafar yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba, dan kuwa abinda yakeji a cikin zuciyar shi ba zai musaltu ba, dan kuwa DEENAH tamkar farin cikin sa haka take, ita ɗin ta kasance abar alfaharin sa ce, tabbas yayi rashin ƴar uwa, yarintar su kaɗai abar burgewa ce wanda idan ya tuna sai yaji wani irin kewar da yakejin har a abada ba zai daina ta ba, su kaɗai kawai iyayen su suka haifa, Mahaifin su tun DEENAH nada shekaru biyar ya rasu, inda ya saura daga shi sai Ummar su da DEENAH, su uku kaɗai, sun taso cikin so da ƙauna dama kuma kulawar juna, sai dai yau guda wannan ƙaunar ta yanke Saura shi da Umma kaɗai cikin family ɗinsu, bai san yaya rayuwar su zata kasance da rashin DEENAH ba, rayuwar su ba zata ta6a tafiya cikin farin ciki kamar ta dah ba, maiyasa DEENAH bata mutu tun a ƙaramar ta ba sai yanzu da ta zama budurwa wacce kowa ke so dama kuma ƙulla alaƙa da ita?. Kuka Jafar yasa yana rufe fuskar sa da tafukan hannun sa, sosai zuciyar sa ke yi masa zafi, ganin gari ya waye kuma ya kusa rabuwa da ƴar uwar sa, rabuwa ta har abada, ba zai sake ganin ta ba, shi kaɗai yasan irin abinda yakeji a zuciyar sa, he can't believe it shima, sai dai babu yadda ya iya da lamarin Ubangiji, tunda dama duk Allah ne ya hallice mu sannan kuma wataran dole ne mu koma gareshi, koh ba jima koh ba daɗe, dan kuwa babu wanda zai dauwama a duniyar. Sosai ya baiwa ZEEYAD tausayi inda shima har ya fara sanƴawa ransa cewa dagaske MADEENAH ɗin sa ta mutu ba, kafin kuma yayi saurin kawar da tunanin daga ransa yana girgiza kai. A inda suke tsaye wata Nurse ta fito ta same su tare da sanar dasu cewar doctor na neman ganin su. Mara mata baya sukayi zuwa office ɗin doctor ɗin, zuciyar su cike da zulumin abinda zai fito daga bakin sa. Duk wuri suka samu suka zauna kowanne zuciyar sa cike da fargaba dama kuma tsoro musamman ZEEYAD da ya kasa zaune properly. Kallon su likitan yayi yace "Menene matsayin ku a gare ta?." Kallon juna sukayi kafin Jafar yace "Mu ɗin yayun ta ne." Kallon ZEEYAD yayi alamun mamaki kafin kuma ya share yace "Well am sorry to said this, but...." "Don't tell me please, please Doctor don't tell me that she is dead" cewar ZEEYAD kamar wanda zaiyi kuka. Shiru doctor yayi yana kallon sa kafin kuma yace "Well am sorry..." "Ta mutu right?, alright then zamu tafi da ita tun jiya da dare aka tabbatar mana da hakan a asibitin da muka fara zuwa, and gashi nan anan ma hakanne, I told you sir DEENAH is dead." Sosai ZEEYAD ke jin wani irin abu mai ɗaci a maƙoshin shi, har yanzu bai yarda ba, babu ta yadda za'ayi ace DEENAH ɗinsa ta mutu ne, No it can't be. Gyaran murya Doctor yayi yace "Well maybe ku tsaya ku saurari abinda zan faɗa tukun." Duk maida duban su sukayi kansa dan jin abinda zai faɗa. Nan yace "Your Sister is Half death, i mean she has fallen into a deep sleep which is, She is in a Coma, bata mutu ba, she is still alive." Tunda ya fara magana duk suka saki baki da ido suna kallon sa, Jafar ne cikin rawar murya yace "Kana nufin, DEENAH bata mutu ba?." Kai likitan ya jinjina masa kafin yace "Yes, but tana buƙatar aiki da gaggawa, da akwai internal injuries tattare da ita so ya zama dole ne muyi mata aiki in less than an hour..." "Just tell me, nawa ne kuɗin aikin i will pay any amount indai zata samu lafiya, i know she is not dead,i know it, just tell me how much you need for the surgery" faɗin ZEEYAD da ya rasa farin ciki zaiyi koh baƙin cikin faɗawar ta Coma. "Yeah sure she will definitely be fine muddin mukayi aikin, the amount is 3million." "Just start preparing for the surgery and make sure that she is fine, i will bring the money as soon as i can, now." "Yes sure, but don't forget the money is for her Internal surgery, not for the Coma." "What do you mean?." "I mean, ba lallai ne ta tashi daga Coma ɗin ba koh da kuwa munyi mata aikin, sabida da akwai raunikan da taji su zamuyi aiki a kai,but for the Coma sai dai kuyi ta yi mata addu'a Allah yasa ta farfaɗo nan kusa kawai." "What?." "Yes." "But like how many days zata ɗauka a hakan?" cewar Jafar yana kallon likitan. "It depends, i can't decide it gaskiya, but zaiyiwu maybe a week or couple of WEEKS, a month, a year or even decades." "What, a DECADE!?" ya faɗa cikin zaro idanu yana kallon likitan. ZEEYAD ne yace "I will go get the money just make sure that she is alright please." "Sure" cewar Doctor. Miƙewa ZEEYAD yayi ya fice daga cikin office ɗin ba tare da yabi ta kan su Jafar da doctor ɗin ba kuma. Motar sa ya nufa ya buɗe ta ya shiga, Cheque ya ciro tare da rubuta amount ɗin kuɗin yayi signing sannan ya fito ya koma ciki. Amsa likitan yayi ganin harda ƙarin 2million akai dukda kuwa basa kar6ar cheque. Wani takarda ya basu Jafar ya sanƴa hannu akai kafin kuma a shiga tiyatar. Kallon Jafar ZEEYAD yayi yace "She would be fine." Rungume sa Jafar yayi hawaye na kawo masa yace "Ban yarda da kai ba tun farko da kacemin DEENAH bata mutu ba, but yanzu i can clearly see that you're saying the truth, how did you know cewa bata mutu ba?" ya faɗa yana ɗagowa. Murmushin kan le6e ZEEYAD yayi kafin kuma ya sanƴa hannu ga dafe saitin zuciyar sa. Kallon sa Jafar yayi na ƴan seconds kafin yayi murmushi yace "Kanason DEENAH, don't you?." Ɗagowa yayi ya kalli Jafar kafin ya saki murmushi mai ciwo yace "But she doesn't like me, she hate me." Shiru Jafar yayi bai iya cewa komai ba. Kallon sa ZEEYAD yayi yace "Your Mom, you should go to her, and tell the good story of DEENAH being alive." Kai Jafar ya jinjina yace "Yeah sure, zanje na faɗamata yanzun nan, i know she must be so worried musamman idan ta farka bata ganmu ba." Kai ZEEYAD ya jinjina kafin yace "See you." Tafiya Jafar yayi ya bar ZEEYAD, wuri ya samu ya zauna minutes after minutes yana ɗagowa ya kalli ƙofar ɗakin tiyatar. ************************* *2 DAYS AFTER* Sosai suka yi matuƙar damuwar rashin ganin ZEEYAD yau tsawon kwana biyu kenan. Sun buga kiran wayar tasa tun tana shiga ba'a ɗauka har yazo ya zamto switched off. Khairat kuwa kuka har tayi shi ta gaji dan kuwa ta sadaukar ZEEYAD guduwa yayi dan kawai kada ya aure ta. "Daddy i told you bayasona, Daddy ka duba afterall wahalar da kasha akan shi ka maida shi mutum,m yau ya butulce maka, bayan yau ne ranar Engagement namu, amma ya gudu, he left ba tare da ya sanar da kowa inda yaje ba" ta ƙarashe cikin kuka. Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe kafin yace "ZEEYAD ba zai ta6a guduwa ba, wani abin ne dai ya faru dashi, nasa anje chan gidan shi an bincika min but they found his cell-phone scattered on the floor, sannan guards ɗinsa sun ce ya fita ne cike da tashin hankali sannan tundaga nan kuma basu sake sanin inda yaje ba, sannan kuma har yau da muke maganar nan bai dawo ba, something must be very wrong Khairat." "Haba Alhaji, ba'a yiwa ɗan yau shaida fah, ni dama sai da aka gargaɗe ni akan yaron nan wataran zai iya butulce mana, gashi nan ai yau daga cewa zaka haɗa shi aure da ƴar ka ya gudu, amma kai nan sam bakaga laifin sa ba, sai ma cewa da kakeyi wani abin ne ya faru dashi bayan an zagaye kaf garin nan ba'a ganshi ba, hatta abokan kasuwancin sa basu san inda yake ba, gaskiya dai wannan yaron ya bani mamaki ban ta6a zaton abinda zai saka mana dashi ba kenan" ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata. "A'a Hajiya, baikamata muyi saurin yanke hukunci ba, ZEEYAD must be somewhere in this country, tayaya zai gudu bayan rabin business nasa a wannan ƙasar yake running ɗinta?, mu sake bashi lokaci su kuma baƙin da aka gayyata zan fita na basu haƙuri akan cewa an ɗaga saka ranar" yana faɗin haka ya fice daga cikin ɗakin. Da kallo suka bishi kafin Khairat ta sanƴa kuka, nan kuma Momy ta shiga rarrashin ta. "Kada ki damu kinji, kisa a ranki indai ZEEYAD mijin ki ne toh fah babu abinda zai hanaki mallakar sa da izinin Allah, maganar mahaifin ki na kan gaskiya, maybe wani abin ne ya faru da ZEEYAD, ki kwantar da hankalin ki." "How Momy how, tayaya zan kwantar da hankali na, kinsan irin burirrikan da naci ne akan wannan engagement ɗin, wane irin kallo kike tunanin friends ɗina zasuyi min, maiyasa komai kuke goyon bayan sa ne, amma nikuma duk abinda nayi banyi dai-dai ba, hakan na nufin kun fi sonsa a kan ƴar da kuka haifa komiye?." "Haba Khairat ya zakice haka, muna sonki mana, ki daina irin wannan maganar please." "Zan daina ne ranar da kuka aura min shi ya zama mijina mallaki na ni kaɗai" tana faɗin haka ta tattari wedding gown ɗin ta irin ta turawa sak da ta sanƴa tayi waje. ************************ Zaune yake kusada ita, tana kwance helplessly kamar gawa, hancin ta manne da oxygen dama kuma wasu life saving machines ɗin da aka jona mata. It hurts ZEEYAD sosai fiye da yadda yaji lokacin da akace dashi ta mutu ganin ta cikin wannan hali, bata motsi, bata jin wadanda ke kusa da ita, haka take kwance kawai ba tare da ta san meke wakana around ita ba. Hannu yasa cikin aljihun sa ya ciro wata ƴar ƙaramar box ɗin zobe. Ciro zoben yayi yana jujjuya ta a hannun shi, kafin kuma ya kalli fuskar ta tare da kamo hannun ta yace "Am supposed to get ENGAGED to someone else today, but ƙaddarar mu ta yanke yiwuwar hakan, MADEENAH you're my source of happiness, i can't be happy with someone else idan ba ke ba, So i guess we should get ENGAGED instead" ya ƙarashe yana kallon fuskar ta. Yatsar ta ya kama tare da sanƴa mata zoben, nan ya zauna cif yayi mata kyau sosai. Murmushi yayi yanajin zuciyar sa na yin zafi ganin yadda take kwance motionless bata motsi. Allah ne kaɗai yasan yaushe ne zata farka, abinda yafi tsorata shi shine maganar da Doctor ɗin ya faɗa musu na cewar da akwai posibilities ɗin zata iya samun stroke or maybe memory loss. "No, that won't happen insha Allah" ya faɗa cikin girgiza kai yana sarƙe yatsun su wuri ɗaya. Jafar ne ya shigo cikin ɗakin tare da ajiye ledar take-away ɗin abincin da ya iyo musu, kafin yaja kujera ya zauna shi ma yana kallon DEENAH. "Yau ne Engagement naka and you haven't called them ka faɗa musu abin dake faruwa ba, wane irin tunani kake ganin zasuyi akan ka?." Shiru yayi yana saurarar Jafar kafin kuma yace "That doesn't matter, all what matters here is naga MADEENAH taji sauƙi, i want to see her talk and smile again, i want her to yell at me it cheers me up akan ganin ta kwance haka. Knocking akayi a ƙofar shigowa, nan Jafar ya tashi yaje ya buɗe. Amirah ce dama kuma Anty Khadija, hanƴa ya basu suka shigo kafin su sami bakin bed ɗin su zauna. "Ya jikin nata yanzu?" cewar Anty Khadija. Jafar ne yace "Alhamdulillah." "Allah ya tashi kafaɗun ta" suka faɗa. "Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum." Sun ɗan zauna kaɗan kafin tace "Bari muje wurin su Anty itama mu duba jikin ta." Kai kawai Jafar ya jinjina mata kafin kuma su fice. ********************* Umma ce zaune cikin tagumi ta sanƴa DEENAH a gaba tana kallo, kallo ɗaya zakayi mata ka san ita ɗinma ba isasshen lafiyar gare ta ba. Yau 5days kenan, amma haka nan take kwance kamar gawa koh wata mai bacci bata motsa ba. Jafar ne yace "Umma ki kwantar da hankalin ki, insha Allah zata samu sauƙi, Umma yakamata ki dinga shan magungunan ki, da wanne kukeson naji ne, dukkanin ku bakuda lafiya and ke kuma kin ƙi kisha maganin ki kin sanƴa damuwa a ranki" ya ƙarashe kamar wanda zaiyi kuka. Ɗagowa Umma tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya tace "kawomin maganin na sha." "A'a Umma, mu koma ɗakin da akayi admitting ɗinki kici abinci sannan ki sha maganin naki ki samu hutu, idan yaso sai kizo ki duba ta anjima." Babu musu Umma ta miƙe kafin ya taimaka ya riƙe ta suka fice daga ɗakin. Da kallon tausayi ya bisu kafin kuma ya maido duban sa kanta. Zuwa yayi ya zauna dan kuwa koh kaɗan bayason yin nisa da ita. Fuskarta ya ƙurawa idanu yana kallo tare da kiran sunan ta "MADEENAH?" kamar wani mai son tada ta daga bacci. Idanun sa ya ɗan waro yana sake kallon fuskarta da kyau ganin kamar ta motsa idanun ta. Matso da fuskar sa yayi yana cigaba da kallon ta tare da sake kiran sunan ta. Idanun ta ta fara motsawa alamun tanason buɗe su, murmushin farin ciki ne ya fara forming akan fuskar ZEEYAD nan ya tsaya kallon ta yadda take ƙoƙarin buɗe idanun nata a hankali har ta gama buɗe su tana ware su cikin nasa da ya kafe ta dasu. Murmushin farin ciki ya sake yace "MA...MADEENAH, you're awake, Alhamdulillah" ya faɗa cike da farin cikin yana faɗawa Sujudu Shukur, kafin ya sake tasowa yace "Wait..i will call the doctor i will be right back" ya faɗa yana ficewa daga ɗakin cikin gudu. Da idanun ta da su kaɗai take iya motsawa ta bisa. Ba'a jima ba ya dawo tare da Doctor ɗin yace "Look ta buɗe idanun ta, she is awake" ya faɗa cike da tsananin farin ciki. Duba ta Doctor ɗin ya shiga yi, sai dai ya tabbatar komai is normal kafin ya ɗago yana kallon ZEEYAD. Maida duban sa ZEEYAD yayi kanta yana kallon idanun ta da ta kafe su wuri ɗaya bata motsa ƙifta su bale ta motsa su. Farin cikin da yake ciki ne ya fara gushewa nan yace "Why..why is she not moving her eyes, i just saw her blinking kafin na fita kiran ka, why then yanzu..." "Her health is improving, thank GOD ta fito daga Coma, but i told you that there is posibility ɗin zata iya samun stroke or brain loss, and now that is exactly what is happening to her." "W...w..what?" ya faɗa cikin rarrabewar harshe. "Yes, amma ka kwantar da hankalin ka sannan ku cigaba da addu'a zata ji sauƙi very soon insha Allah" yana faɗin haka ya fice tare da barin ZEEYAD da sakakken idanu yana bin DEENAH da kallo. Juyawa yayi ya fice daga ɗakin trying so hard ganin yayi controlling kukan dake cin zuciyar sa. "Sir?" Jafar ya kira shi. Saurin tsarewa yayi cikin dauriya ya juyo yace "Jafar, ka bawa Ummar taku maganin ta?." Kai ya jinjina masa nan yace "Mu koma ciki." Duk ciki suka koma Jafar ne yaga idanun DEENAH a buɗe, da sauri ya ƙarasa farin ciki na cin shi yace "DEENAH?, look she is awake, DEENAH ta tashi." Kallon sa kawai ZEEYAD keyi cike da tausayin sa. Jafar ne ya lura da bata motsa idanun ta nan yace "But...maiyasa bata motsa idanun ta, i guess she is fully awake, right?" ya faɗa yana juyowa ya kalli ZEEYAD. "No" ya faɗa a taƙaice. Ɗagowa Jafar yayi kawai cikin sanƴi ya samu wuri ya zauna yana dafe kansa da hannayen sa. ******************* *A WEEK LATER* Sosai Umma taji sauƙi dan haka hutu ta ɗauka a wurin aikin ta har sai DEENAH ta gama warkewa, wanda kullum take cikin addu'ar hakan. ZEEYAD kuwa kullum yana kan DEENAH daga safe har zuwa dare da zai koma masauƙin sa, kasancewar yanzu Umma ce ke kula da ita. Umma tayi da ZEEYAD akan ya maida hankali kan business ɗinsa amma yaƙi dan kuwa indai ba gani yayi DEENAH ta warke gabaɗaya ba, ba zai iya ta6uka komai ba, haka take tayi masa kullum har ta gaji ta kyale shi. Zaune suke dukkanin su inda Umma da Mami ke hira ƙasa-ƙasa. DEENAH kuwa pillow aka jingina mata aka ɗan zaunar da ita akan bed ɗin. Inda kuma ZEEYAD da Jafar ke zaune kan Couch kowa da abinda ya dame sa, Jafar maganar business ɗinsu yakeyi masa discussing sai dai koh kaɗan shi hankalin sa baya kai, idanun sa na kan DEENAH yana kallon ta kamar kullum baya gajiya, hakan yasa Jafar jan bakin sa yayi shiru. Banko ƙofar ɗakin akayi aka shigo hakan yasa su saurin ɗagowa dan ganin koh wanene. Tsaye tayi tana ta faman huci kamar wata zakanƴa, fuskar nan tata manne da ƙatuwar shade kamar kullum ta sha make-up. Miƙewa yayi tsaye yana kallon ta, kafin kuma idanun sa su sauƙa kan Momy da Dady dake shigowa. Sosai ZEEYAD yaji wani irin kunƴa ta kama shi hakan yasa shi sadda kai ƙasa, yana lumshe idanu. "Toh macuci, butulu wanda baisan alkhairi ba, Allah ya toni asirin ka, ashe dama nan wurin kazo ka maƙale a wurin wata banza nan, miskiniya..." Tsawar da Daddy ya daka mata ne yasa ta yin shiru da bakin ta tana kumbure-kumbure tare da hararan ƴan cikin ɗakin. Kallon DEENAH dake kan bed Momy da Daddy sukayi, kafin kuma Daddy ya haɗa hannayen sa alamun neman yafiya yace "Dan Allah ina baku haƙuri akan halayyar ƴata Khairat." Duk shiru sukayi suna kallon su kafin Momy tace "Dan Allah muna baku haƙuri, kuyi haƙuri kwata-kwata Khairat batada hankali, kuyi haƙuri dan Allah, mun faɗo muku ɗaki haka babu koh sallama." "Bakomai" inji Mami cikin ɗan murmushi. Murmushi suma sukayi kafin kuma su shiga gaisuwa tare da kuma bada haƙuri akan halin Khairat, idanun su akan DEENAH cike da tausayin halin da take ciki. Daddy ne ya kalli ZEEYAD yace "ZEEYAD, ka kwantar da hankalin ka, ni dama nasan dole da akwai wani abin dake faruwa, dan kuwa haka kurum ba zaka 6ace mana mu kasa samun inda kake ba, amma tunda ka kira ka shaida min komai naga yakamata ace mun taho dan ganin abin dake faruwa." Sunkuyar da kai ZEEYAD yayi yanajin zuciyar shi na mugun ƙuna da sunan Miskiniya da Khairat ta kira MADEENAN sa dashi. "ZEEYAD, kayi haƙuri haƙika nayi maka mummunar fahimta akan halayen ka, kayi haƙuri kaji?" cewar Momy. Sai a sannan ya ɗago yace "Bakomai Mom, ni ne yakamata na baku haƙurin watsa muku ƙasa da nayi a ido, sannan kuma na baku kunƴa a gaban baƙin da kuka gayyato bayan kuma kunyi ta tsanmanin zan dawo a ranar but i didn't show up, am sorry." "Bakomai ZEEYAD, kada ka damu kaji?." Idanu kawai su Umma ke bin su dashi dan kuwa basusan meke faruwa ba. "Daddy tunda yanzu an ganshi, kuyi Engaging ɗin mu gudun kada a sake samun wata matsalar." "Khairat ai koma dai menene kya jira mu fita daga nan wurin tukun koh?" cewar Momy cike da mugun takaicin hali irin na Khairat ɗin. Baki ta turo tana harɗe hannaye a ƙirji, tare da cika tana batsewa. "Koh da an fita daga nan ɗin ZEEYAD ba zai auri Khairat ba" cewar Daddy. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *025...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*BANYI EDITING BA*_ """"""""""""""Shiru ɗakin ya ɗauka inda kuma kowa ya zubawa Daddy idanu yana kallo. Ficewa Daddy yayi daga cikin ɗakin inda duk suka bisa da kallo musamman ma Khairat da bata yarda da abinda kunnuwan ta suka jiye mata ba, yayin da ZEEYAD ma da ya cika da mamaki yayi saurin mara masa baya. "W..w...what the hell is he saying?" faɗin Khairat cike da ɗumbin mamaki. Wuri Momy ta samu ta zauna not minding Khairat dake tsaye. "Momy kinajin abinda Daddy yake faɗa, he must be kidding right?." Ajiyar ta Momy ta bata bata kula ta ba, dan kuwa itama ta fara gajiya da hali dama kuma ɗabi'u irin na Khairat ɗin. "Momy am talking to you" ta faɗa da ɗan ƙarfi tana kallon Mom ɗin. "Maybe you should lower your voice" cewar Jafar yana kallon ta. Wani irin mugun harara ta wulla masa haɗi da jan dogon tsaki kafin cikin tsiwa tace "A wane dalilin zan sassauta murya ta?, zanyi magana ne yadda raina ke so a duk inda naga dama, who do you think you're ma da zaka buɗi baki kace min nayi lowering voice ɗina, a wane dalilin?." "A dalilin marasa lafiyar dake kwance anan, koh kin manta a asibiti kike ne?." Maida duban ta tayi kan DEENAH da ta kafe wuri ɗaya da ido bata motsi nan tace "Ohh wai wannan miskiniya mai shanyayyen jikin?, mttssww, who even cares about her, akanta dai ba zan fasa yin magana da ƙarfi yadda naso ba." Hannu Jafar ya ɗaga da niyyar bata mari Umma tayi saurin dakatar dashi da faɗin "A'a Jafar, kyale ta." "Umma baki..." "Ka kyale ta nace." Sauƙe hannayen sa yayi zuciyar sa na mugun ƙuna yana kallon Khairat ɗin dake bin sa da kallon Up&down. "Wai kana nufin dah ɗin hannu zaka ɗauka ka mare ni dan bakada hankali, ƙarya nayi ne ba miskiniyar bace?, i just do hope that ba akanta ZEEDAN ke wulaƙanta ni ba" ta ƙarashe tana kallon cikin idanun DEENAH dake saitin ta. Momy ce ta tashi tare da fizgo hannun Khairat sukayi waje. Duk da kallo su Umma suka bisu, zuciyar su cike da ɗumbin mamaki akan Khairat ɗin. "Wannan wace iriyar yarinƴa ce haka, anƴa kuwa kwakwalwar ta ɗaya?" faɗin Mami. Shiru kawai Umma tayi tana kallon DEENAH idanun ta na kawo ruwa. "Su waye su ɗin, maiyasa suke son ƙarawa ƴata damuwa?" ta faɗa tana tashi tayi wurin DEENAH tana rungumo ta jikin ta. "Umma am definitely sure yarinƴar nan bata da hankali, ki daina wani damuwa akan abinda tayi, bakya tunanin idan DEENAH taji kina kuka hakan ne zai sanƴa ta cikin damuwa?" cewar Jafar. "Kai kuwa Jafar tayaya zata ji mutumin da babu abinda ke motsi a jikin shi" cewar Mami cike da mamaki. "Mami tanajin dukkanin abin dake faruwa, sai dai kawai ba zata iya reacting bane sakamakon motsin da bata iya yi, amma dukkanin abinda akeyi tana ji." Kallon ta kawai Mami keyi cike da tausayin ta, ace ƙaramar yarinƴa kamar DEENAH da cutar stroke "Allah ya baki lafiya, ya tashi kafaɗun ki" ta faɗa. Da Amin Jafar ya amsa kafin yace "Umma nikam na tambaye ki mana, tunda deen ta samu hatsari Abdul yazo duba ta kuwa?." Kai kawai Umma ta girgiza masa alamun a'a kafin kuma tace "DEENAH tace min yayi tafiya kafin ta samu hatsarin nan, maybe har yanzu bai dawo ba dan kuwa nasan babu abinda zai hana shi zuwa." Yatsina fuska Jafar yayi dan kuwa shi dama Abdul ɗinnan ba wani burge shi yake ba duba da yadda yabi yayi ta takurar sa har ya samu ya shawo masa kan DEENAH, ba dan yaso hakan ba sai dan kawai shi ɗin ya kasance ɗa ne ga Ƙawar Umma. "Amma Umma mahaifiyar sa fah?, ai ita yaci ace ta sani koh tunda ƙawar ki ce." "Hajiya Dija ai bata ma ƙasar ita, amma na sanar mata bansan koh ta faɗawa Abdul ɗin koh bata faɗa masa ba." Shiru kawai Jafar yayi ba tare da ya sake cewa komai ba. ********************* "Dad maiyasa kace ka..." "ZEEYAD sabida idan nayi hakan toh haƙika na cuce ka, sabida na daɗe da gano cewa zuciyar ka ba Khairat takeso ba sai dai dan kawai kada ka sa6awa umarnin mu yasa ka amince da hakan, bayan nan kuma ɗabi'u da halayyar Khairat sam basu dace da mutum kamar ka ba, haƙiƙa idan na aura maka Khairat na cuci rayuwar ka ne, duk da kuwa bansan komai akanka ba, amma nayi tunanin idan na baka auren Khairat ban kyauta maka ba, dah ace kanason Khairat dah ka bar dukkanin abinda kasan kakeyi kazo anyi muku Engagement, sai dai kuma ka kasance wurin wacce zuciyar ka ke so wato wannan yarinƴar, na san ba ƙaramin so kakeyi mata ba tunda har ka iya kasancewa da ita tsawon wadannan kwanaki, ZEEYAD ba zanyi maka dole koh tilasta maka cewa sai ka auri Khairat ba bayan da akwai wacce kakeso, ni nan zan tsaya maka indai kanason yarinƴar chan da aure nikuma zan nema maka auren ta, sannan kuma na tabbatar da cewa ba'a sami wata matsala game da gano koh ainihin wanene kai ba, ni nan zan zame maka uba." Sosai ZEEYAD yaji farin ciki a ransa game da maganganun da Daddy yayi, tsugunnawa yayi ya hau korawa Daddy godiya "Nagode, Nagode maka Daddy da Allah yasa ka fahimce ni, kayi haƙuri da ƙin amintar da zuciya ta tayi wa ƴar ka, tun ban kai haka ba na fara son MADEENAH, she is my first love, ita ɗin ta daban ce a cikin mata, tana da kirki kuma tana da hankali, she was 10 and i was 20 back then, zuciya ta ta fara sonta ne tun lokacin da na ɗaura idanu na akanta, sai dai ban gane hakan ba har sai bayan rabuwar mu da shekaru goma, ta kyautata min sannan kuma bata kyamace ni ba a lokacin da nake yawo tamkar almajiri, bata guje ni ba a lokacin da kowa yake gudu na sannan kuma yake nisan ta kansa da kaina a lokacin ne kuma ita take sake kusanto ni, ta yi min abinda koh Family na basuyi min ba a rayuwa, why then ba zan sota fiye da haka ba ma, she is a girl with a golden heart, I Love Her Dad." Dafa kafaɗun sa Daddy yayi yana miƙar dashi tsaye yace "Alright ZEEYAD, just consider auren ka da ita kamar ya ɗauru ne, i will make sure it happens." "Thank you so much Dad, kayimin abinda koh wanda ya haife ni baiyi min ba." "Stop saying that ZEEYAD, koh ka manta tun kana ƙarami iyayen ka suka mutu ne?, haka Allah ya tsara taka rayuwar ba tare da zakaci moriyar mahaifin ka ba." Shiru ZEEYAD yayi yana kallon Daddy kafin kuma yace "Actually Dad, na daɗe inason na faɗamaka gaskiya, am sorry but nayimaka ƙaryar koh ni wanene." "What, what are you saying ZEEYAD." "I know ranka zai 6aci sabida nayimaka ƙarya tun farko that i have been fooling you all this while, the truth is that...." shiru yayi bai iya ƙarasawa ba yana kallon Daddy ɗin. "Come on tell me, menene baka faɗamin ba game da rayuwar ka?." "Actually Dad, my Father is alive, sannan kuma ina da family, ban rasa family na a hatsari kamar yadda na faɗamaka a farko ba, sabida gudun kada kace na koma garesu." "What, you have a Family?." Kai ya jinjina masa nan yace "Come on let's sit and discuss this" ya faɗa yana samun wuri ya zauna. Zama ZEEYAD ma yayi kafin Daddy yace "Tell me everything about your life ZEEYAD." Shiru ZEEYAD yayi na ƴan mintina kansa a ƙasa yace "The truth is that, i wasn't a begger but...but an Abandoned Prince" ya faɗa kansa a ƙasa zuciyar sa na zafi. Shiru Daddy yayi yana duban sa cike da mamaki, dan kuwa sam bai fahimci inda zancen ZEEYAD ɗin ya dosa ba "An Abandoned Prince?, bangane ba, can you explain further?." Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa kafin yace "I mean am a Prince, but my Dad abandoned me when i was 10." "Kana nufin kace min kai ɗan Sarki ne?" cewar Daddy cike da mamaki yana kallon sa. Kai ZEEYAD ya jinjina masa, nan Daddy ya sake cewa "But..how could you be a Prince i mean bakayi kama da ɗan sarki ba." "That is because i was Abandoned after my Mom's death, my own Father Abandoned me, he treated me like an outsider." "ZEEYAD tell me more about yourself." Shiru ZEEYAD yayi na ƴan mintina dan kuwa sam bayason tuno irin rayuwar wahalar da yayi a baya, bayason tuno da kowa daga cikin family ɗinsa hakan na matuƙar ƙona masa zuciya tare da ƙara tsanar su a cikin zuciyar sa, babu abinda zai sanƴa shi komawa ƙasar sa a yanzu face saboda Family ɗinsa dake chan wato Family ɗin abokin sa Sadeeq, dan kuwa Family ɗinsa maƙiyan sa ya ɗauke su ba ƴan uwa ba, sai dai dukda haka ba yanzu yakeson komawa ba tukun har sai yayi gagarumar shirin da koh kallon banza mutum bai isa yayi masa a bayan sa ba, so yake yayi proving ɗinsu wrong kan cewar ba zai ta6a samun cigaba a rayuwar sa ba, sai dai yanzu baya cikin nutsuwar da zai tinkare su har sai MADEENAHn sa ta samu lafiya ta hakan ne kaɗai zai sami kwanciyar hankalin aiwatar da abinda yayi niyya. Ɗago da jajayen idanun sa yayi kafin kuma ya miƙe tsaye tare da zuba hannayen sa cikin aljihu, juyawa Daddy baya yayi kafin kuma yace "20 Years Ago, A Heir was born to the King of Egypt(Cairo), bayan jiran da yayi shekaru goma Allah bai basa haihuwa ba, One fateful day, my Mom got pregnant to me, and after nine good months....i was Born." *20 YEARS BACK* """""""""Cike da matuƙar girmamawa suka zube gaban mai Martaba "Your Highness, an turo mana cewar mu faɗa maka cewa naƙuda ya kama Sarauniya LATEEFAT dama kuma Sarauniya Hafeezah, zaka iya zuwa dan ganin wacce zata riga haifa maka magaji a cikin su kamar yadda al'adar wannan MASARAUTA ta tanadar." Cike da kiɗima mai Martaba ya fice daga ƙatuwar faffaɗar Fadar tasa izuwa babban asibitin Masarautar dan shaida wa idanun sa wacce zata riga haihuwa tsakanin matan nasa biyu wato Hafeezah dama kuma Lateefat. Isar sa asibitin bai zarce koh ina ba sai ɗakin haihuwar, inda mata biyu ke kwance koh wacce akan gado daban, inda kuma wasu dattijai mata uku ke kan kowacce daga cikin su dan kar6ar haihuwar ta. Duban sa ya maida gun ta gefen dama wacce da alamu tafi ɗayar shan wahala sosai sakamakon irin nishin da take. Da sauri ya tako wurin ta yana kama hannayen ta cikin muryar tausayi ya furta "Lateefat?." "Your Highness...mu...tuwa zanyi" ta faɗa cike da azabar da take ciki inda kuma gumi duk ya gama wanke mata fuska da jiki. "Ki bar faɗin haka Lateefat ba zaki mutu ba, zaki haifa mana ɗan mu sannan kuma mu rayu cikin aminci da ƙaunar juna, ba zaki mutu ba" ya faɗa yana sumbatar ta a goshi. "Your Highness, muna buƙatar ruwan maganin gargajiyar nan dan baiwa Sarauniya Hafeezah dan kuwa da alamu har yanzu haihuwar tata da ɗan saura, gashi kuma ba ƙaramin wahala take sha ba, wannan ruwan maganin shi zai rage mata zafin naƙuda." "Wanne irin maganin gargajiya kuma, Ina ruwan addu'ar da Liman ya aiko?" cewar mai Martaba da ya ruɗe ganin halin da Lateefat ke ciki. "Allah ya huci zuciyar ka ranka ya daɗe, amma wannan ruwan Sarauniya Hafeezah ta zubar dashi bayan munyi-munyi akan ta sha amma taƙi." Cike da zafin zuciya mai Martaba yace "Ku kyale ta, ku cigaba da kula da ita har lokacin haihuwar tata tayi" ya faɗa yana juyawa ga Sarauniya Lateefat. Bayan doguwar naƙuda dama kuma gwagwarmaya da Sarauniya Lateefat ta sha ne, ta haiho santalelen ɗanta kyakkyawa sosai son kowa ƙin wanda ya rasa, wata iriyar doguwar ajiyar zuciya taja tare da furta "Alhamdulillah." Murna a wurin mai Martaba ba'a cewa komai, dan haka saurin goge yaron akayi bayan an yanke masa cibi akayi wrapping ɗinsa da towel sannan aka miƙa shi ga mai Martaba dake ta miƙo hannu tunɗazu dan kar6ar ɗan nasa. Kallon fuskar yaron da yake kama dashi yakeyi ba tare da murmushi ta gushe daga kan fuskar sa ba. Sumbatar yaron yayi tare da rungume sa yanajin soyayya dama kuma ƙaunar yaron na baibaye duk wani 6argo dama kuma cikin jini haɗi da jijiyoyin jikin shi. Bakin sa ya kai kunnen yaron tare da yi masa huɗuba da sunan *ZEEYAD* yana sake rungume sa a jikin shi. Ɗan tallafowa yayi yace "Lateefat, ba na faɗamiki ba, zaki haihu lafiya sannan kuma mu rayu da ɗan mu cikin ƙaunar juna." Murmushi tayi tana miƙa masa hannu alamun ya bata yaron. Yaron ya bata kafin ta rungume sa tanajin soyayyar sa sosai a cikin zuciyar ta, Allah ya amsa addu'ar su yau bayan shekaru goma da sukayi basu samu haihuwa ba, babu abinda zasu ce sai dai su ƙara miƙa godiya marar iyaka ga Ubangijin sammai da ƙassai. Yaron aka amsa kafin mai Martaba ya fice dan zuwa ya sa a sanar da haihuwar mata mafi soyuwa a gareshi cikin matan nasa. Fitar sa bai wuci da mintina goma ba Sarauniya Hafeezah ta sambaɗo nata kyakkyawan yaron shima. Inda kuma zuciyar ta ke cike da ɗumbin baƙin cikin riga ta haihuwa da Lateefat tayi. A haka aka sallami kowacce bayan sun huta. **************** Duk wani lungu da saƙon wannan MASARAUTA cike take da dumbin jama'a kowane na kai da komowa, kallo ɗaya zakayi musu kaga irin tsantsar farin cikin da suke ciki, sakamakon sadakar kayan abinci haɗi da na sawa da ake tayi musu. Yayin da kuma kiɗan Drums ke ta tashi ta koh ina, fadar ta cika da ɗumbin jama'a dan taya sarki murnar samun ƴaƴa maza a lokaci guda. Zaune suke kusa da sarki Inda shi kuma yake tsakiya kan doguwar throne ɗinsa fuskar cike fal da farin ciki. Gefen sa Queen's ɗinne kowacce da nata jaririn a hannu, hankalin su na kan wasannin da ake gabatar wa dan taya su murna. Sai dai kallo ɗaya zaka yi wa Sarauniya Hafeezah ka gano tsantsar baƙin ciki akan fuskar ta, babu abin dake ƙara mata hakan sai ganin Sarauniya Lateefat dake farin ciki tana murmushi. _"Kiyi murmushin ki yadda kika so, muddin ina raye wannan murmushin ya kusa zama baƙin ciki a gare ki, i will make sure that i ruin your happy life"_ ta faɗa a zuciyar ta cike da mugun nufi. Sarauniya Nazeerah kuwa da ta kasance Uwar gida kuma bata samu haihuwa ba, koh a fuska bata nuna alamun baƙin ciki da haihuwar kishiyoyin nata ba, sabida ta san da akwai wata babbar gwarama da ta kusa afkuwa tsakanin wadannan kishiyoyi biyu da suka haifu rana ɗaya, nata dai bai wuci kallo ba, dan kuwa bata ga abinda zai sa tayi baƙin ciki dasu ba, dan koh bakomai ita ya fara sani kafin su, sannan kuma babu abinda ta nema ta rasa a cikin gidan, kama daga kan dukiya, abinci sutura da sauran su, haka kuma baya ƙunsa mata baƙin ciki koh yi mata gori akan rashin haihuwa, dan haka bata ga wani abin tada hankali ba, ita dai nata bai wuci taji daɗin husuma ba. A gaban ɗumbin mutane aka naɗa Sarauniya Lateefat a matsayin *QUEEN MOTHER* kasancewar ta uwa ga babban yarima kuma ɗan da zai gaji sarki. Sarki da kansa ya ɗaura mata Diamond Crown a kanta tare da yi mata Tsadaddun kyaututtuka, haka ma kuma ƴan uwa da abokan arziki kowa yaba ta yake da ɗan da ta haifa tare da yi mata kyaututtuka masu kyau da tsada. Ganin anfi koɗa Sarauniya Lateefat akanta hakan ya sake hura mata wutar tsanar ta dama kuma tsanar jaririn da ta haifa ɗin a cikin zuciyar ta. Haka aka gama taro mutane suka watse daga fada. Kallon ta Sarauniya Lateefat tayi daga inda take zaune tana tashi ta ƙarasa wurin ta ganin ta kafe wuri ɗaya da ido ne yasa ta ta6a ta. Ɗagowa Sarauniya Hafeezah tayi tana kallon ta, murmushi Sarauniya Lateefat tayi tace "Sannu ƴar uwa datafan mun samu kanmu ƙalau, ki bani YAZEED na ɗauke sa" ta faɗa tana kai hannu zata kar6i yaron. Riƙe ɗan ta tayi gam cike zafin harshe tace "Kada ki nemi ki raina min hankali mana Lateefah, tunɗazun sai yanzu kikaga damar zuwa ɗaukar sa?, tayaya ma zan baki ɗana ki riƙe bayan an tabbatar min da cewar iyayen ki dama kuma kakannin ki riƙaƙƙun mayu ne, ɗana YAZEED yafi ƙarfin duk wani asiri da tsubbu irin naku dake da iyayen ki, na tabbatar da cewa kune wadanda suka jinkirta haihuwa ta har kika riga ni, bayan kuma na riga ki samun ciki." Sosai Lateefat taji zafin kalaman ta, sai dai kasancewar ita ɗin mai haƙuri ce ta dake tare da yin murmushi tace "Mai kike faɗa ne haka ƴar uwa, ai YAZEED dama kuma ZEEYAD dukkanin su ɗaya suke a wuri na..." "Ba ɗaya suke ba, kada ki kuskura ki sake haɗa ɗana da wannan ɗan naki, kowa yaje yayi rayuwar sa sannan ya raini ɗan sa, koh da a bayan idona ne na haramta miki ɗaukar ɗana koh zuwa kusada shi, idan kuma baki kiyaye ba wani abin ya faru dashi toh tabbas kece zan baiwa laifi" tana faɗin haka ta miƙe a fusace ta bar cikin fadar inda kuma Sarauniya Lateefat ta bita da kallo. *10 YEARS LATER* """"""""" "ZEEYAD!, ZEEYAD!!, ka tsaya mana haka nan ina kiran ka" ta faɗa tana biyo shi cikin fadar da gudu. Zuwa yayi ya faɗa jikin mai Martaba yana dariya tare da 6oyewa a bayan shi. "Abhi kaga Ummie ba" ya faɗa yana sake 6uya a bayan nasa yayin da ita kuma ke ƙoƙarin kamo shi. Dariya Abhi yayi yace "Lateefat?". Ɗagowa tayi ta kallesa kafin yace "Mai yaro na yayi miki haka kike bin shi, mai kikeson yi masa?." "Bayajin magana, nace dashi ya tashi yaje wurin kakar sa tana ta tambayar sa kwana biyu ga kuma kewar sa da tayi amma yace shi ba zaije ba yawo zai fita." "Toh ki bar shi mana, abinda yakeson yi ɗin kenan, kada ki dinga tilasta shi akan abinda baya so, koh kin manta shi ɗin babban mutum ne?." "Ba wani nan dama ai kai bakason a faɗi laifin sa koh kaɗan, duk abinda yayi sai kace wani shi babban mutum ne, a haka zai mulki mutane idan ba'a horar dashi tun daga ƙarami ba" ta faɗa tana samun wuri ta zauna. Daura shi ma Martaba yayi akan cinƴar sa ya shiga yi masa wasa cike da ƙaunar da yakeyi masa. "Abhi, yaushe ne nima zan girma na zama sarki kamar kai?" cewar ZEEYAD. Murmushi duk sukayi kafin kuma yace "Kafin ka zama sarki sai ka baiwa shekaru 28 da takwas baya, na tabbata zakayi adalci tare da yin mulki cikin gaskiya fiye da yadda nakeyi a yanzu." Murmushin sa mai ƙara masa kyau yayi yace "Toh Abhi idan na girma ɗin ni zan zama sarki sannan kuma na zama shugaban ku kai da Ummie kenan?." Dariya sukayi kafin kuma yace "Aa mu iyayen ka ne ba zaka ta6a zama shugaban mu ba." Haka sukayi ta hirar su cike da so da ƙaunar juna. ***************** Tsaye yake cikin faffaɗar ƙayatacciyar filin wasar tasu ta ta sha ababen wasan yara kala daban-daban, hannun sa ɗauke da ball yana buga ta yace "YAZEED, kazo muyi wasa." Juyowa kyakkyawan yaron da ya kira da YAZEED yayi kafin kuma ya taso daga kan lilon da yake kai cikin murmushi yana ƙarasowa wurin ZEEYAD yace "Ɗan uwa na inason yin wasa da kai, amma Ummie na kullum sai tace wai na daina yin wasa da kai idan ba haka ba, Ummien ka zata cinƴeni" ya faɗa alamun bayajin daɗin hakan. ZEEYAD ji yayi ransa ya 6aci dan kuwa kullum Sarauniya Hafeezah batada magana sai ta aibanta Ummien shi, jefar da ball ɗin hannun sa yayi tare da juyawa zai bar cikin filin wasan nasu. Cikin gudu YAZEED ya mara masa baya yace "ZEEYAD ka tsaya, maiyasa kayi fushi, ka fasa yin wasan dani ne?." Tsayawa yayi ya juyo cikin huci yace "Ba zan sake yin wasa da kai ba, sabida kullum Ummien ka sai tayi ta faɗin magana marasa kyau akan Ummie na, indai har kanaso na cigaba da wasa da kai sai Ummien ka ta gyara halayen ta da kalaman ta tukun" yana faɗin haka ya fice. Da kallo YAZEED ya bisa yanajin zuciyar sa babu daɗi, ƙafa ya ɗaga zai bi bayan shi nan yaji anyi saurin dafa kafaɗar sa ta baya. Juyowa yayi yana sauƙe idanun sa kan Ummien sa nan yace "Ummie ba nace ki daina faɗin munanan kalamai akan *QUEEN MOTHER* ba, gashi yanzu kinsa ZEEYAD yayi fushi dani har yace ma ba zai sake wasa dani ba." Cike da muguwar zuciya irin tata tace "Ka kwantar da hankalin ka ɗana, rashin yin wasa dashi shine alkhairi a gareka, idan ba haka ba tabbas Ummien sa sai..." "Ƙarya kike Ummie, Ummien ZEEYAD mutuniyar kirki ce, kece kike 6ata mata suna a wurin mutane, amma ni kullum idan naje wurin ta ƙara sona takeyi, tana yi min abinda koh ke bakya yi min, kuma tana bani dukkanin abinda nakeso, kuma batayi min tsawa da faɗa koh ta dake ni kamar yadda kikeyi min ba, ni ba ke bace Ummie na daga yau, Ummien ZEEYAD ita ce Ummie ta" yana faɗin haka ya bar wurin da gudu yana bin hanƴar da ZEEYAD yabi. Sosai zuciyar ta ke mugun tafarfasa akan kalaman ɗan nata "No this can't be, i can't let her take my only son away from me, ta kar6e komai daga gare ni, tanayin nasara akan komai idan tasa gaba, so i guess lokaci yayi yanzu da zaki bar duniyar Lateefat, dan kuwa ganin mutuwa ta ya fiye min ganin ki a cikin gidan nan, i will make sure you die a painful death" ta faɗa cikin fidda zazzafar huci tana barin wurin. ******************** *3 MONTHS LATER* """"""Kwance take akan Gadon asibitin wanda da alamu bata ma san su waye ke kanta ba. Mai Martaba ne zaune ZEEYAD akan ƙafafun sa, dama kuma wasu dattijai wadanda ba zasu wuce iyayen Lateefat ba, kowannen su fuskar sa ɗauke da damuwa. "Abhi, yaushe Ummie na zata tashi?." "Soon insha Allah, ka bar damuwa kaji?." "Abhi naji ance duk wanda hantar sa da ƙodar sa ta lalace basa sake yin rayuwa mai nisa zasu mutu, hakane?." Shiru Abhi yayi kafin kuma yace "Aa ZEEYAD, ba haka bane, waye ya faɗa maka hakan?." "A makaranta ne Malamin mu ya faɗi hakan." "Aa wasa yakeyi muku amma babu wani mutuwa da akeyi kuma ana samun sauƙi." Shiru yayi kawai tare da ƙure Ummien tasa da idanun da suka tara hawaye yana kallo. *Yawan Comment, Yawan Typing* _*Zan iya cewa sai mun haɗu bayan sallah daga nan?😉*_ *MHIZZ JIDDHERR............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *Ina yiwa ɗaukacin Al'ummar musulmai, sannan kuma masu bibiyar littafin ZEEYAD barka da sallah, Allah Ubangiji ya maimaita mana na shekaru aru-aru masu zuwa cikin rai da ƙoshin lafiya, dafatan dai baku manta da barka da sallah ta ba, dan kuwa har yanzu ban gama nawa sallahn ba😌, zan ajiye account number na, dafatan dai ba zaku sace min guiwa ba wurin ƙin turomin nawa goron sallahr, Yauwa sannan kuma ZEEYAD yace na sanar da masoyan sa cewa kowacce ta ajiye nata account number ɗin nan da kafin a gama bada labarin sa kowacce zata ji alert ɗin miliyan ɗaya cikin account ɗin ta, yayi hakan ne dan soyayyar da kuke nuna masa da DEENAHr sa, wadanda suke jin haushin DEENAH kuma irin su Lateefat da Fatima bet masu ƙaton kai yace na sanar daku cewa babu ku, babu miliyan ɗaɗɗayan da zai raba, dan kuwa ni kaina miliyan ɗari ya bani kuji, shiyasa kuka jini shiru, ina chan ina tawa budirin cikin walwala da arziƙi😂🤘🏼* *026...* *_Ayi haƙuri idan anga kura-kurai a ciki, banyi editing ba_*🥲 *TWO WEEKS AFTER* """"""""Yau tsawon watanni uku da sati biyu kenan Sarauniya Lateefat na kwance bata da lafiya. Sosai little ZEEYAD yayi kewar rashin jin mahaifiyar tasa a kusa dashi. Yau ma zaune yake kusa da mahaifiyar tasa yana kallon ta. Murmushi ta sakar masa tana miƙo masa hannu yazo gareta. Tashi yayi daga inda yake zaune yaje kusa da ita, kafin kuma ta rungumo sa jikin ta, tana jin wani irin ƙaunar sa har cikin jinin jikin ta. Sosai takejin a ranta mutuwa zata yi ba zata kuma ƙara wasu tsawon kwanaki ba zata koma ga mahaliccin ta, zata bar mutanen da tafi so da ƙauna a duniya, Iyayen ta, mijin ta dama kuma ɗa ƙwalli ɗaya da ta haifa wanda shi ne farin cikin ta a kullum, batasan ya rayuwar ZEEYAD zata kasance na rashin ta ba, sosai take tausayin ɗan nata, sai dai kuma idan ta tuna da irin ƙaunar da mahaifin sa keyi masa sai taji zuciyar ta tayi sanƴi dan kuwa ta san zai kula da ZEEYAD ɗinta sosai. "Ka bar kuka haka nan yaro na, maza fah basa kuka musamman ma kai da kake jarumi, wanda zai mulki mutane nan gaba, Jarumai basa kuka" ta faɗa cikin muryar ta dake fita da kyar tana shafa kwantacciyar sumar kansa. "Ummie wai dagaske ne mutuwa zakiyi ki bar ni?" ya faɗa yana ɗagowa ya kalle ta. Murmushi ta ƙaƙaro tayi tace "A'a wannan ba gaskiya bane, wanene ya faɗa maka hakan?, ba zan mutu ba har sai naga ka girma ka zama sarki." Maida kansa yayi ya kwanta a jikin ta tare da rungume ta yace "Ummie ni banaso ki mutu koh na girma ɗin." Kansa kawai take shafawa kafin ta maida duban ta ga wata dattijuwar mata dake tsaye akan su tana kallon su tace "Ummie na, kin tahomin da ajiyar nan kuwa?." Kai kawai matar ta girgiza kafin kuma ta sanƴa hannu cikin jakar dake rataye a kafaɗar ta ta ciro wata sarƙa tana miƙa mata. Amsa tayi tana kallo kafin ta kalli ZEEYAD tace "Ba yanzu nayi niyyar baka wannan sarƙar ba, na fiso sai ranar da za'a naɗa ka sarki na baka kyautar ta, sai dai kuma hakan ba zai ta6a yiwuwa ba dan kuwa bana tunanin zan kai wannan lokacin, zan baka ita ne sabida idan na tafi ka ringa tunawa dani, ka ɗauka cewa kullum ina tare da kai ɗana, idan na tafi kada kayi kukan rashi na kokuma kaji kewa ta, ba zan ta6a jin daɗin hakan ba, nasan mahaifin ka zai kula da kai yadda yakamata sannan kuma ba zai bar ka kayi kukan rashi na ba, kawo wuyar ka na sanƴa maka sarƙar" ta faɗa tana ɗaga sarƙar ta sanƴa masa a wuya. A daidai lokacin kuma mai Martaba ya shigo dama kuma sauran Sarauniyoyin. ZEEYAD ne yayi wurin sa da sauri yana kamo hannun sa yace "Abhi, ba kunce min Ummie na ba zata mutu ba, maiyasa toh take magana kamar wacce zata yi nisa damu?." Shafa kansa mai Martaba yayi kawai ba tare da ya iya ce masa komai ba. Wani irin tari ne sukaji ya sarƙe Sarauniya Lateefat, dan haka duk kanta sukayi a ruɗe suna kiran sunan ta, kafin kuma wasu su fita kiran likita. Da kallo ZEEYAD ke bin su, kafin kuma ya tsinkayo muryar mai Martaba na cewa "Hafeezah kuyi waje da Yarima ZEEYAD." A firgice Hafeezah da ta faɗa duniyar tunanin ta cike da jindaɗin plan ɗinta yayi working ta ɗago kafin kuma ta kama hannun ZEEYAD da niyyar suyi waje. Tirjewa ya fara yana kiran Ummien sa, hakan ne yasa kuma cike da mugun haushi da mugun ta ta fizgo sa tayi waje dashi tana tsinka masa mari. Idanu ta zaro ganin ga dogarai nan birjik sai dai baƙar zuciyar ta ta rufe mata ido bata gansu ba, yanzu ganin da sukayi ta tsinkawa ZEEYAD mari tasan tabbas sai sun sanarwa da mai Martaba, daga nan kuma kashin ta ya bushe. Cike da muguwar makirci irin nata ta fashe da kukan ƙarya tana faɗin "Ohh ni Hafeezah yau da wanne zanji ne, da mutuwar Lateefat koh da taurin kai irin naka?, naji zafin mutuwar Lateefat sosai hakan yasa idanu na suka rufe na mari wannan kyakkyawar fuskar taka, ka gafarce ni ya kai Babban Yarima" ta ƙarashe cikin haɗa hannayen tana kuka. ZEEYAD sosai ransa ya 6aci dan kuwa yasan Hafeezah bata wani damu da Ummien sa ba, yasan duk makirci ne irin nata. Mai Martaba suka hango ya fito idanun sa sunyi jaa sosai, ba tare da yabi ta kan kowa ba yayi wucewar sa hakan yasa dogaran sa mara masa baya da sauri. Wani irin farin ciki da annashuwa ne suka cika wa Hafeezah rai, ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha dan daɗi, ta riga da ta gama da Lateefat, saura kuma ɗan da ta haifa, dan kuwa taci alwashin indai da ranta ba zata ta6a barin ZEEYAD ya zamto Sarki ba, tayi alƙawarin sai taga bayan shi kamar yadda taga ta Uwar sa. Harara ta zabga masa kafin kuma ta wuce fuu kamar zata tashi sama. ZEEYAD ne ya koma ɗakin, nan ya tarar da duk kuka sukeyi ga Ummien sa kuma kwance da farar kyalle an rufa mata shi. Raku6ewa yayi a jikin ƙofar hawayen baƙin ciki na zubo masa. Tuno da cewar Jarumai basa kuka yasa shi saurin goge hawayen fuskar sa, tare da yin dukkanin ƙoƙarin sa na ganin baiyi kukan ba. Hannayen sa ya kai kan sarƙar wuyar tasa yana shafa ta. ********************* Yau sati ɗaya kenan da mutuwar Sarauniya Lateefat, duk inda ka zaga a cikin MASARAUTA zaka fahimci kowa jikin sa yayi sanƴi da wannan mutuwa. Mai Martaba kuwa ya daina kula kowa sai ZEEYAD, ya daina fitowa fada kullum yana cikin ɗakin sa gaban hoton marigayiyar matar sa. Hakan kuwa ba ƙaramin ƙonawa Sarauniya Hafeezah rai yake ba, hakan ya sanƴa ta tashi tsaye na ganin ta raba tsakanin uba da ɗansa, dan kuwa tabi duk wata hanƴa na ganin an kashe mata ZEEYAD amma hakan yaci tura. Ɗago da jajayen idanun sa yayi yana kallon Daddy yace "1 year after my Mom's death, i started facing some kind of hatred from my family, they despised me, they don't want me close to them, basa son nayi wasa da ƴaƴan su, sun raba ni da ƴan uwa na, sun raba ni da YAZEED, shine kaɗai wanda yake nuna min ƙauna a cikin ƴan uwa na, but later on, his Mom took him far away from me, sun canzawa duk wani yaro dake gidan makaranta except me, and since from that day da suka raba YAZEED dani, i never set my eyes on him again, koh da hutu ba'a barin sa yazo duk dan kada mu ga juna dashi, but duk wannan ba damuwa ta bace, babbar damuwa ta shine yadda mutumin da yafi kowa ƙaunata yazo ya canza zuwa wanda yafi kowa tsana ta a wannan gidan, shi ya sanƴa aka cire ni a makaranta mai tsada aka maida ni ta ƴaƴan talakawa, ya sanƴa an kwace dukkanin wani abu da zai sa a danganta ni da ɗan sarki dashi, sannan kuma yasa aka ɗauke ni daga cikin gida aka maida ni yin rayuwa cikin arear bayi mata, cikin wani ɗaki da koh da dabbobin da ake kiwon su a cikin gidan sun fi ni walwala da jindaɗi, hatta bayin dake cikin Masarautar babu wanda yake da irin ƙasƙantacciyar ɗaki da rayuwar nan sai ni, sun kwace komai daga gareni, but dukda haka nayi ƙoƙarin kula da sarƙar da Ummie ta bani na ganin banyi missing nashi ba, na fara rayuwa kamar ta almajirai ne a cikin gidan uba na tun inada shekaru goma sha ɗaya, no one cares about me sannan kuma babu wanda ya ta6a yunƙurin kawomin ɗauki, after family ɗin mahaifiya ta sunji labarin halin da nake ciki sun yanke shawarar ɗauka na su tafi dani, but that selfish and disgusting Man ya hana su yin hakan sannan kuma ya yanke duk wata alaƙar dake tsakani na dasu, he took everything away from me, ya nesan ta ni da dukkanin wani abin da zai sanƴa ni jin farin ciki a rayuwa, hakan yasa nayi deciding barin masa ƙasar, am sure yana chan yana rayuwar sa happily da mutanen da yafi so, he wants me out of his sight, and i decided to stay out of his life for good, ba zan iya cigaba da baka labari ba sabida hakan bakomai yake ƙaramin ba sai tsanar sa, i just hate him like hell" ya faɗa cikin zafin zuciya fuskar sa na yin jawur jijiyoyin nan duk sun bayyano raɗo-raɗo a jikin shi wanda da alamu dai ba ƙaramin tsanar mahaifin nasa yayi ba. Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe cike da tausayin ZEEYAD, dan kuwa shi tunda yake bai ta6a jin wai Sarkin da yaƙi jinin sa ba, he can't believe irin rayuwar da ya tarar da ZEEYAD a ciki ya zamto ɗan sarki ne hakan, Sarkin ma ba na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya ba, na chan ƙasar Cairo, dukda dai yana zargin da akwai sa hannu a cikin wannan lamari sai dai ZEEYAD ɗin baisan da hakan ba, duba da yadda tun yana ƙarami mahaifin nasa ya taso dashi cikin wannan halin. "ZEEYAD haƙiƙa ka bani tausayi, but tell me one thing yaushe ne ka yanke zaka koma ƙasar ka u haihuwa?." Shiru yayi kafin kuma yace "Ba yanzu ba tukun, ba zan iya tafiya na bar MADEENAH cikin halin nan ba." "Amma ZEEYAD baka ganin lokaci yayi da yakamata ace ka koma, kasan fah da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, yakamata ace ka koma yanzu ka san wane irin hali mahaifin ka ke ciki dama kuma abokin ka da family ɗinsa." "Who even cares about that Man, i don't care if he dies, abu ɗaya ne zai maida ni Egypt shi ne Family ɗin Sadeeq, and koh da zan koma wurin su ba mulki ne zai kai ni ba, i just wants to show them how far i have made it in life." "ZEEYAD yaci ace yanzu zuciyar ka tayi sanƴi game da tsanar mahaifin ka da kayi..." "No, zuciya ta ba zata ta6a yin sanƴi ba until na ɗau fansar abinda yayi min." "ZEEYAD..." "Am sorry to said this father but babu abinda zaka faɗa da zaiyi conviencing ɗina koh ya sanƴaƴa min zuciya akan wancan mutumin" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Miƙewa tsaye shima Daddy ɗin yayi yana takowa wurin ZEEYAD ya dafa kafaɗar shi yace "ZEEYAD nasan ba zan iya hana ka aiwatar da abinda kakeso ba muddin hakan ne zai sanƴaƴa maka zuciya, but kada ka manta cewa Uba komin laifin da zai aikata a rayuwa ba zaka iya canza shi daga matsayin mahaifin ka ba, koh da kuwa shi ya kawo ta'addanci da mugunta duniya babu yadda za'a yi ka iya canza shi daga matsayin Uban da ya haife ka, koh da kuwa ya kasance shi ɗin Mahaukaci ne he still remains your father, koh bakomai kai ya soka lokacin da mahaifiyar ka ke raye, dan haka kayi tunani tare da binciken abinda ya sanƴa shi canza hallayyar sa akanka na komawa mutumin da yafi kowa tsanar ka, Think about it ZEEYAD" yana faɗin haka ya fice daga cikin falon ya bar ZEEYAD tsaye. Da kallo ZEEYAD ya bishi dan kuwa koh kaɗan maganar da Daddy yayi bata ta6a sa ba, ficewa yayi shima dan kuwa har ya fara kewar DEENAH. ****************** Asibitin ya dawo Umma da Jafar ne kaɗai ɗakin. Gaida Umma yayi ta amsa ba yabo ba fallasa kafin ya sami wuri kusa da Jafar ya zauna. Kallon sa Jafar yayi cikin ƙasa da murya yace "Har ka dawo?." Kai ya jinjina masa, nan ya sake cewa "Am sorry to say, amma dai ba wannan mahaukaciyar yarinƴar zaka aura ba koh?." Kallon DEENAH ZEEYAD yayi kafin yace "Are you trying to call your own sister Mad?." "No, thats not what i mean, that rude girl da tazo nan da mutumin da kuka fita tare." "Ohh" ya faɗa cikin yatsina fuska. "Ita ce?." "Yeah" ya faɗa kai tsaye. "Na taya ka murna da mahaifin nata yace ya fasa auren ka da ita, sabida the girl doesn't seem normal to me." Murmushin kan le6e yayi kawai ba tare da yace komai ba. Muryar Umma suka tsinkayo tana faɗin "Jafar ni zan wuce gida ɗauro girkin dare, ka kula da ƙanwar taka koh?." "Toh Umma bakomai, sai kin dawo." Jakar ta ta ɗauka kawai ta fice daga ɗakin cikin sanƴin jiki. Tashi Jafar yayi ya koma kusada da DEENAH ya zauna yana kallon ta. "DEENAH, why don't you just try very hard ganin kin motsa koh da idanun ki ne, though nasan kullum kina iya ƙoƙarin ki na ganin kinyi hakan amma yaci tura, but you have to try very harder DEENAH, am just sick of seeing you in this condition" ya faɗa yana kamo hannun ta. Kallon su kawai ZEEYAD keyi, but shima ganin DEENAH a hakan ba ƙaramin takurawa zuciyar sa yake ba, ita ba statue ba then atleast yakamata ace ta motsa koh da idanun ta ne. Kallon cikin idanun ta dake saitin sa yayi yanajin zuciyar sa na yi masa zafi sosai. Kauda idanun sa yayi daga kallon ta kafin kuma ya tashi ya fice daga ɗakin. Three Months kenan DEENAH bata warke ba har yanzun, sai ma abinda ya ƙara gaba akan ciwon nata. Zaune yake a office ɗin Doctor ɗin dake yi masa bayani akan rashin lafiyar DEENAH. "The best solution is a fitar da ita waje kamar yadda na faɗa maka, coz her condition is getting more worse day after day, inda kuma zan tura ku yanzu sun fi mu kayayyakin aiki, and suna da expert doctors da suka kware ta wannan fannin sosai." Kai ya jinjina masa kafin yace "Tell me, where is that place?." "Cairo(Egypt), da akwai wani kwararren likita da zan haɗa ka dashi, am definitely sure indai kukaje chan then cikin ikon Allah zata samu lafiya." Tunda ya ambaci Cairo zuciyar ZEEYAD ya hau bugu, No way babu ta yadda zai ɗauki DEENAH ya kaita Cairo ne, a wannan ƙasar yayi losing farin cikin sa, ba zai kuma iyayin risking rayuwar abar ƙaunar sa a chan ba, zai iya kaita kowane ƙasa ne a duniyar nan but banda that fucking Egypt country. "Ya kayi shiru?" ya tsinkayo muryar likitan. Ɗagowa yayi ya kalli Doctor yace "Maybe you should prescribe another Country, but not Egypt." "A chan ne kaɗai na san Likita kwararre ta fannin rashin lafiyar ta, da akwai kwararrun likitoci a wannan ƙasar that can take a very good care of her har ta samu lafiya i promise you." "Alright" kawai ya faɗa kafin ya baiwa likitan hannu su gaisa yana tashi tsaye. "Mr ZEEYAD, don't forget that guarantee ɗin kwana biyar ne kawai muke dashi akanta, she need to be admitted soon." Kai kawai ya jinjina masa yana ficewa daga cikin office ɗin. Ɗakin ya koma nan ya sami DEENAH kaɗai ce a cikin ɗakin, tana nan as usual kamar yadda take, sai dai wannan karon ba akan bed take ba, tana zaune ne akan wheel-chair Ƙarasawa yayi yaja kujera ya zauna yana kallon ta cike da tausayin ta. Murmushi ya ɗanyi kafin yace "Maybe we should go out on a date today" ya faɗa yana kallon ta. Tashi yayi yaja wheel-chair ɗin ya karkata kansa zuwa hanƴar waje. Chan cikin garden ɗin asibitin ya kaita inda babu kowa, baka jin kukan komai sai na tsuntsaye suna shawagi, ga kuma wani irin sanƴin iska mai cike da ni'ima dake kaɗawa. Zagayowa yayi gaban ta yana kneeling akan guiwowin sa, idanun sa cikin nata. Ɗan murmusawa yayi yace "I know you can feel me around you and even heard me, but i don't know why you still can't react to it, MADEENAH babu abinda nake buri da kuma fata a duniyar nan face samun lafiyar ki, you really mean the world to me ganin ki a cikin halin nan makes me very sad, i just need the real you back, i don't care if you shout or disgrace me infront of your boyfriend, all i want is for you to be back to your normal health, i can't afford to lose someone so important to me again, na riga da na rasa Ummie na, so please ki tausaya min and never leave me, ke kaɗai ce farin ciki na yanzu idan na rasak ki then my life would be useless forever DEENAH" ya ƙarashe cikin rawar murya zuciyar sa cike da tsoro dama kuma fargabar kada ya rasa DEENAH. Goge ɗan hawayen da ya zubo masa ta gefen ido yayi yana jin zuciyar sa nayi masa wata iriyar rawa. Baisan sadda DEENAH zata warware daga rashin lafiyar ta ba, dukda baya cire tsanmanin samun lafiyar tata komin daren daɗewa, yasan Allah zai amsa masa addu'ar sa da yakeyi kullum cikin dare akan DEENAH, sai dai zaiyi haƙuri ya cigaba har zuwa ranar da Allah zai amshi addu'ar sa ta samu lafiya ba tare da ya nuna wata gajiyawa ba. On the other hand kuma dole ne ya yarda da maganar likita na kai DEENAH Egypt ƙarƙashin kulawar kwararrun likitoci, zaiyi hakan ne kawai dan samun lafiyar ta, but sam ba yanzu ne ya shiryawa zuwa Egypt ba. Wayar sa ce ta ɗau ƙara, dan haka ciro ta yayi daga aljihu, nan yaga dai ita ɗin ce, sam bata gajiyawa da kiran shi, tunda mahaifin ta yace babu labarin auren su ta kama wata iriyar hauka akan shi, ya rasa gane Khairat wace iriyar yarinƴa ce nacacciya marar aji da kamun kai, sam bayason yana yi mata wulaƙanci shiyasa ma idan ta kira baya takurawa kansa wurin amsa kiran tata. Maida wayar yayi aljihu yana sanƴa ta a silent, kafin kuma ya kalli DEENAH, murmushi ya ɗan sakar mata yana miƙewa daga kneeling ɗin da yayi. "I know yanzu kin sha iska right, so i guess we should go back for now" ya faɗa yana kama kan wheel-chair ɗin ya juya ta suka fara tafiya. Ciki ya koma da ita, anan ya tadda Jafar tsaye, ganin su yasa shi nufar shi yana faɗin "Yanzun nan dawowa ta, shan iska kuka fita?." Kai ya jinjina masa suna shigewa cikin ɗakin. "Likita yace min za'a fitar da DEENAH waje hakane?." Shiru yayi yana zama kafin kuma yace "Yeah." "Bana tunanin Umma zata yarda." "What, why?." "Idan ma zata yarda sai dai idan da ita za'a tafi, ba zata ta6a yarda tayi nesa da DEENAH ba, Likewise me too" ya ƙarashe cikin ƙasa da murya. Murmushi ZEEYAD yayi yace "Kace kawai zakayi kewar DEENAH, but Mom naku babu abinda tafi buri a yanzu face samun lafiyar MADEENAH why then zata ƙi a fitar da ita waje?." Murmushi Jafar yayi yace "Kayi gaskiya, i would miss DEENAH, ina ma dani za'a yi tafiyar." "Seriously, idan ka tafi kuma waye zai cigaba da kula min da business ɗina?." "But Sir, baka tunanin lokaci yayi da zaka fara maida hankalin ka ga business ɗinka?, i mean kana samun Customers akan harkar zanen ka from ƙasashe daban-daban, but duk sabida ka damu da DEENAH ta samu lafiya you turned everything down, bakason yiwa kowa aiki yanzu, bana tunanin wannan as good." "Who even cares about wani zane yanzu, ba zan ta6a yi musu aiki mai kyau ba a wannan halin so i decided to quit it for some time." "For some time, how sure are you cewa DEENAH zata samu sauƙi nan ba da jimawa ba, you can't gave up on your career like that, kana nufin koda shekaru goma DEENAH zata ɗauka a haka then, kaima a hakan zaka cigaba da zama?." "Look Jafar ba zaka gane ba, koh bakomai inada dukiyar da zanyi rayuwar nan da shekaru talatin da shi, so just stop disturbing me akan na koma bakin aiki na, idan companies ɗina ne inada masu running min su a ƙasashe daban-daban..." "Amma ai gaskiya Jafar ke faɗa maka." Duk ɗagowa sukayi suna kallon Umma dake shigowa. "ZEEYAD, abinda Jafar ya faɗamaka gaskiya ne, yakamata ace yanzu ka kwantar da hankalin ka sannan ka koma bakin aikin ka, baka tunanin Career ɗinka zata iya faɗuwa warwas sabida aikin da ka daina yi wurin ƙin amsar tayi daga manƴan customers ɗinka, rashin lafiyar DEENAH baikamata ya sanƴa ka giving up akan aikin ka ba, tun kafin ka sake haɗuwa da DEENAH ka gina kanka har ka kawo matsayin nan, kai mutum ne da yakamata ya zamto mai wuyar samuwar gani, amma sabida DEENAH ka za6i kayi living simple life tare da kuma hulɗa da kowanne irin mutane, lokaci yayi yanzu da yakamata ka ajiye batun DEENAH a gefe haka nan, kasancewar ka kullum kusada ita ba shi ke nuna alamun mahaliccin ta zai iya kar6ar abar sa kokuma ya bata lafiya ba, lokaci yayi yanzu da yakamata ka ajiye sabgar DEENAH a gefe ka cigaba da ƙoƙarin gina kanka, ni zan ɗauki DEENAH na kaita chan Egypt ɗin kamar yadda likita ya faɗa, sannan ba zan amince ka biyo mu ba, yakamata kayi nesa da DEENAH haka nan, ba zan so ta zamto sanadiyyar rugujewar arzikin ba, Nagode da irin kulawar da ka nuna mata tsawon wannan lokaci, yakamata ace ka tafi yanzu haka nan." "What, are you trying to separate me with DEENAH?" ya faɗa yana kallon Umma. "Ba ƙoƙarin raba ka nakeyi da ita ba, ina ƙoƙari ne na ganin bata zamto dalilin rugujewar arzikin ka dama kuma career ɗinka ba." "You can't do this to me?." "Jafar kaje ka fara yi mana dukkanin wasu shirye-shirye, gobe zamu bar ƙasar." "Amma Umma..." "Banason naji kace komai, kai dai kayi abinda na sanƴa ka, muma ba rasa arzikin kula da DEENAH mukayi ba." Kallon ZEEYAD da duk jikin sa ya gama mutuwa ya gama sanƴi yayi yace "Sir kayi haƙuri but gaskiya Umma ta faɗa." "Your Mom doesn't like me, tanason sake raba ni da DEENAH for the second time ne." "Sir baka fahimce ta bane..." "Ofcourse na fahimce ta, i can clearly see that tun farko bata ƙaunaci alaƙa ta daku ba, and tayimin proving hakan yau, but ba zan iya rabuwa da DEENAH ba, and nothing can Stop me from going with her" ya faɗa cikin 6acin rai. "Jafar da kai nake magana har yanzu kana tsaye ɗin" cewar Umma da ranta ya soma 6aci. Ficewa Jafar zaiyi ZEEYAD yayi saurin riƙo shi yace "I will take care of everything." Shiru Jafar yayi kafin yace "Amma ai Umma tace a'a..." "Let me take care of everything." "ZEEYAD, taimakon da kayi mana a baya ma ya isa haka nan, sannan kuma mungode, amma yanzu lokaci yayi da zaka zame hannayen ka daga rashin lafiyar DEENAH, a matsayi na ta mahaifiyar ta zan ɗauki nauyin komai, ba sai ka kuma spending wani abu a cikin dukiyar ka akanta ba, ka bari duk sadda ta zamto mallakin ka ba zan hana ka kashe mata koh da dukiyar da ka mallaka duka bane, amma banda yanzu ni zan kula da ƴata, dan haka ka zame hannun ka daga ciki haka nan, Jafar wuce kaje." Jafar ɗan kallo ya zama a tsakanin su, baisan dalilin Umma na son nesanta DEENAH da ZEEYAD ba, amma koh bakomai Umma nada gaskiya, baikamata ace ZEEYAD ya yasar da komai ya tattara dukkanin hankalin sa da nutsuwar sa kan DEENAH ba. "Jafar?" Umma ta sake faɗa. Saurin ficewa Jafar yayi daga ɗakin dan zuwa aiwatar da abinda Umma ta sanƴa shi. Sosai ran ZEEYAD ya 6aci zuciyar sa nayi masa mugun zafi, tun ba yau ba ya lura sam Ummar su DEENAH bata ƙaunar sa, gashi yanzu tana yin dukkanin ƙoƙarin ta na ganin ta raba sa da DEENAH, sai dai sam ba zai bar hakan ta faru ba. Ficewa yayi daga ɗakin kamar zai tashi sama. ***************** A Airport Jafar ya sauƙe su kafin kuma su shige cikin reception kafin tashin jirgi yayi. Sosai Jafar kejin kewar ƙanwar tasa tun basu tafi ba, duk tafiya zasuyi su bar shi shi kaɗai, ya san komai ya daina yi masa daɗi kenan. "Umma dan Allah ku dawo immediately after DEENAH ta samu sauƙi, nima zan dinga kawo muku ziyara a duk sadda na ɗan samu hutun aiki." Sosai Umma taji tausayin sa, dan kuwa ita ma ba ƙaramin kewar ɗan nata zatayi ba, haka kuma tasan ba ƙaramin kewa zasu bar sa a ciki ba. "Kada ka damu Babban Yaya kaji, insha Allah ba zamu daɗe ba zata sami sauƙi mu dawo." Kai kawai ya iya jinjinawa yana kallon DEENAH dake kan Wheel-chair. "Ai Jafaru kam ba ƙaramin kewa zaiji ba, yanzu dai kawai sai ka dawo wurin mu da zama" cewar Mami. Murmushi yayi kawai ba tare da yace komai ba. Suna nan tsaye aka fara announcing tashin jirgin dan haka duk rakiya sukayi musu zuwa filin jirgin. Sosai sukayi sallama da juna, inda Jafar ya rungume DEENAH kamar kada ya sake ta ya ɗago yana share hawayen shi. Rungume Umma yayi sosai yana jin shi so empty kafin kuma yayi musu addu'a sosai suka kama hanƴa. Tsaye suke a bakin ƙofar shiga jirgin, inda ana ƙoƙarin shigar da DEENAH ne kuma sukaji an riƙe wheelchair ɗin nata. Da mamaki Umma ta ɗago ta kallesa fuskar nan tasa a matuƙar murtuƙe ya sha baƙar shade. "What's this?" cewar Umma. Cire glass ɗin idon sa yayi kafin kuma yace "Am sorry, ba zuwa nayi na hana ku tafiya ba, nazo ne muyi sallama." Kai kawai Umma ta jinjina. Kafin kuma ya sake cewa "Ba zan iya ja da abinda kika yanke ba, but am sorry to say this; i can't stay away from DEENAH, am going with her." "Don't try to underestimate me ZEEYAD, idan ba haka ba zan iya raba ka da DEENAH kwata-kwata ka fice daga cikin rayuwar ta." "You can't do that." "Zan iya yin fiye da hakan ma, muddin hakan zai kawo wa ƴata zaman lafiya, raba ka da ita ba abu ne mai wuya a gareni ba, sannan kada ka manta na yiwa ƴaƴa na tarbiyyar da basa iya ja da magana ta, ka fara shige min hanci dayawa, ban saba hulɗa da wadanda ke ja da maganar manƴan su ba, a hakan kake tunanin zaka so DEENAH kuma na baka auren ta?." Ɗagowa yayi ya kalle ta yace "Am sorry, i didn't mean to hurt you, it's just that na damu da DEENAH ne hakan yasa bana iya barin wurin ta for more than an hour, but please kada ki raba ni da DEENAH." "Zamu tafi yanzu, jirgi ya kusa tashi." Riƙo hannun DEENAH yayi a cikin nashi yana kallon ta. "And what kind of Nonsense is that, let go of her hand now." Sakin hannu DEENAH yayi nan Umma tace "Sannan koh da ziyara banason ka kawo wurin DEENAH, ka tsaya ka maida hankalin ka kan abinda yayi dalilin ka na zuwa ƙasar nan." Kai kawai ya iya jinjinawa yanajin zuciyar sa na zafi sosai, kafin kuma ya juya ya bar su nan. Zuwa yayi ya wuce su Jafar da suka saki baki suna kallon su tunɗazu ba tare da ya tankawa wani daga cikin su ba. Sai da suka ga tashin jirgin su Umma kafin su baro Airport ɗin. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR................✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *027...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT,* *HELIOPOLIS EGYPT* _____________Ƙarfe takwas ɗin dare su Umma suka sauƙa a ƙasar Egypt, dan haka already akwai masu jiran su wadanda su zasu kai su masauƙin su kasancewar Jafar ya gama yi musu komai ta yadda ba zasu wani sha wahala ba idan sunje. Hotel ne mai kyau da tsada aka kai su kafin ayi musu iso har zuwa masauƙin su. Umma dai kallon garin take dan kuwa yanayin ƙasar da garin kaɗai zai tabbatar maka da akwai kwanciyar hankali da daɗin zama. Kasancewar akwai komai na buƙata a Apartment ɗin hotel ɗin yasa abinci kaɗai aka kawo musu da abin sha. Ɗan zazzagaye ɗakin Umma tayi Falo ne da ɗakuna guda biyu sai kitchen dama kuma Toilet a kowane ɗaki. Sosai taji tsarin hotel ɗin yayi mata dan haka toilet ta kai DEENAH tare da yi mata wanka suka fito. Canza mata kaya tayi zuwa masu ɗan nauyi kasancewar garin akwai ɗan sanƴi-sanƴi, kafin ita ma ta shiga ta watsawa jikin ta ruwa ta fito. Sallolin ta ta rama kan kuma taci abinci tare da ɗaukar waya ta kira Jafar da sabon layin ta na chan. Bugu biyu taji Jafar ya ɗaga daga ɗayan gefen tare da yin sallama. "Wa'alaika Salam, ɗan albarka." "Umma na, kun bar ni cikin kewa." "Toh ya muka iya, haka Allah ya ƙaddara." "Hakane Umma, dafatan kun sauƙa lafiya, Ya DEENAH fah?." "Lafiya ƙalau alhamdulillah, yanzu ma zamu kwanta duk da dai ba wata gajiya na kwaso ba, kasan gobe da safe zamu wuce asibiti." "Hakane Umma, yakamata kam ki huta, ya kikaji yanayin ƙasar?." "Toh dai gashi nan dai, babu laifi zaiyi daɗin zama daga gani." "Masha Allah, hakan yayi kyau, gobe da safe wanda zai kai ku asibitin ku haɗu da likitan zai zo shi insha Allah." "Toh shikenan ai bakomai, Allah ya kaimu, ya wurin su Mami fah?." "Lafiyan su ƙalau ban daɗe da barin wurin su ba ina gida yanzu." "Toh masha Allah, zan kira su gobe, yanzu dai bari na kwanta." "Toh Umma, sai da safe." "Allah ya tashe mu lafiya." "Aameen" ya amsa kafin ta datse kiran. Keken da DEENAH ke kai ta tura zuwa ɗaya daga cikin ɗaku nan, kafin ta kwantar da ita akan bed, addu'a tayi mata tare da rufa mata bargo. Wutar ɗakin ta kashe kafin ita ma ta sami wuri ta kwanta. ********************* _________Da misalin takwas na safe wanda zai kaisu asibitin ya iso. Dan haka shirya DEENAH tayi tare da ɗaukar dukkanin wasu abubuwan buƙata suka kama hanƴar asibitin. ********************* *AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL* *CAIRO, EGYPT* Babban asibitin gwamanti ne wanda ya amsa sunan sa wurin kyawu da haɗuwa, haɗi da ƙwararrun likitoci dama kuma ingantattun kayan aiki. Kai tsaye amsar DEENAH wasu Nurses sukayi daga hannun Umma aka tura ta zuwa wani ɗaki da ba zan iya fasalta koh wane irin ɗaki bane. Ba'a bar Umma ta shiga ba sai ma iso da akayi mata zuwa wani ɗakin daban, wanda dai da alamu nan ne wurin zaman jiran patients. Umma kam da kallo take bin koh ina, hankalin ta duk ya koma kan inda aka kai DEENAH. Batayi awanni biyu masu kyau da zama ba wadannan nurses ɗin suka dawo. Ganin su ya sanƴa Umma tashi daga zaunen da take tana tambayar su lafiyar DEENAH. Cikin turanci suka ce da ita "Kece Mahaifiyar MADEENAH ABDULSALAM?." Kai Umma ta jinjina tace "Eh, Nice." "Alright, Likita na buƙatar ganawa dake, biyo ni muje." Ficewa sukayi daga ɗakin zuwa ofishin likitan. Kansa a ƙasa yana wasu ƴan rubuce-rubuce suka shigo da sallama a bakin su. Cikin harshen larabci Nurse ɗin tace dashi "Sir, ga nan mahaifiyar patient ɗin da aka kawo ɗazun." Ɗagowa yayi ya kalli nurse ɗin tare da jinjina mata kai yana ajiye biron hannun sa. "Bismillah, zaki iya zama" ta faɗa tana nunawa Umma kujera. Zama Umma tayi kafin nurse ɗin ta ɗauki wasu files akan table ɗin Likitan ta fice. Kallon Umma yayi yace "Good Afternoon Ma'am." "Afternoon doctor, how is work?." "Alhamdulillah" ya amsa. "Kasa a kirawo ni." "Kwarai kuwa, kune wadanda Doctor Sagir ya turo daga chan Nigeria, right?." Kai ta jinjina masa nan yace "Well, lucky you da kuka zo akan lokaci, but dukda haka bakuyi escaping risk ɗin faɗawar ta memory loss ba." "What..ban fahimce ka ba likita, Memory loss kamarya?." "Actually Ma'am, am sorry to utter this out but ƴarki tayi losing memory ɗinta." "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, mai kake faɗa min haka, amma ai basu ta6a sanar damu labarin nan a chan Nigeria ba sai kai kuma zaka zo ka faɗamin hakan yanzu." "Sorry Ma'am, dalilin da ya sanƴa suka turo ku nan kenan, but don't worry insha Allah, just keep praying ta samu lafiyar fitowa daga stroke, da zaran hakan ya faru kuma abu mai sauƙi ne tayi recovering memory ɗinta, zamu cigaba da bata kulawa ta musamman insha Allah ƴar ki zata samu lafiya." Goge hawayen da suka zubo mata Umma tayi tace "Toh shikenan, bakomai Allah ya bata lafiya, amma sam banji daɗin wannan labarin naka ba, kana nufin kenan fah ƴar da na haifa da ciki na nunawa zatayi bata sanni ba." "Kiyi haƙuri Ma'am, wuyar ta shine dama tayi recovering daga stroke, amma zata iya recovering memory ɗinta wurin nuna mata iriyar rayuwar da tayi a baya da makamancin su." "Toh ya na iya, mai zanyi idan ba haƙurin ba dama?, Allah ya baki lafiya Auta, haƙika nayi kewar ki sosai yarinƴar kirki, ƴar albarka, zan iya ganin ta yanzu?." "Yeah sure" ya faɗa yana miƙewa daga zaunen da yake. "This way" ya faɗa yana nunawa Umma hanƴa suka fice daga ofishin. Sun ɗanyi tafiya kafin su iso wani ward, shiru kamar babu kowa haka arear wurin yake, a cikin jerin ɗakunan wurin mai lamba ta 25 ya buɗe suka shiga, da alamu dai ɗakunan VIP rooms ne. Ɗaki ne babba mai ɗan girma, Bed guda biyu ne a ciki na marar lafiya dama kuma na mai jinƴa, sai wasu ƴan madaidaitan couches guda biyu daga gefe, Fridge sai kuma wata ƴar madaidaiciyar closet daga gefe, sai kuma bathroom da Valcony. DEENAH ce kwance kan bed ɗin an jona mata wasu na'urori, sai dai wannan karon idanun ta a rufe suke kamar mai bacci. Da sauri Umma ta ƙarasa wurin ta tana faɗin "Likita, ta motsa ne?." Kai ya jinjina mata alamun "Eh." "Toh amma maiyasa baku kira ni ba, ya zakuyi min haka?." "Ai koh da mun kira ki ɗin ba zata san kina wurin ba, alama ne na ta ɗan fara recovering kaɗan-kaɗan." Shafa kan DEENAH dake kwance kamar mai bacci tayi tace "Allah ya tashi kafaɗun ki ƴar albarka." "Ni zan wuce, da akwai Nurses biyu da zan turo, sune zasu cigaba da kula da ita yadda yakamata har ta samu sauƙi." "Toh shikenan Doctor, Thank you so much." "You're welcome, Allah ya bata lafiya." "Aameen" ta amsa kafin kuma ya fice daga ɗakin. Waya ta ciro a cikin jakar ta, missed call ɗin Jafar ta gani dana su Mami dan haka Jafar ta fara kira. Sai da suka gaisa kafin ta koro masa bayanin yadda sukayi da likita, sai dai bata faɗa masa cewar DEENAH tayi losing memory ɗinta ba, sosai Jafar yaji farin cikin jin DEENAH ta fara samun ɗan sauƙi, bayan sun gama waya da Jafar ne kuma ta kira su Mami suka gaggaisa dasu Anty Khadija duka. ********************** *THE PALACE* _________Kasancewar ya saba zuwa kullum duba jikin mai Martaba yasa ba tare da wani bincike ba ake barin sa ya shiga. Kai tsaye har uwar ɗakar mai Martaba ya nufa. Zaune yake akan kujera cikin shigar sa ta alfarma, kamar kullum ya sanƴa hoton matar sa a gaba yana kallo, yayin da kuma hawayen nadama basu ta6a ƙaura daga idanun sa ba. Ganin kamar baisan da shigowar Sadeeq ɗin bane yasa shi yin gyaran murya. Dawowa yayi daga duniyar tunanin da ya faɗa, kafin a hankali ya juyo da kujerar da yake kai yana fuskantar Sadeeq, sosai ya manƴan ta sai dai dukda haka kamannin ZEEYAD basu 6ace akan fuskar sa ba, kamar kullum fuskar sa a murtuƙe take babu fara'a akanta koh kaɗan. Gaida shi Sadeeq yayi ba tare da ya amsa ba ya ɗaga masa hannu kawai. "Ayi haƙuri ranka ya daɗe, yau ban ƙaraso da wuri ba, a gafarce ni nayi sabbin patients ne daga wasu ƙasan." Kai ya jinjina cikin muryar sa da tayi rauni alamun marar lafiya yace "Bakomai." Murmushi Sadeeq yayi yace "Your Highness dafatan dai ka sha maganin naka?." Kai ya jinjina masa kafin ya ɗaura da faɗin "YAZEED yazo ya bani maganin, sai da ya tabbatar da nasha kafin ya tafi." "Masha Allah, hakan yayi kyau sosai." Gwaje-gwaje ya sake yiwa mai Martaba kafin yace "Your Highness, har yanzu kaƙi ka daina barin tunanin nan, kullum BP ɗinka na ƙara sauƙa ne." "Kwanaki na na ƙara ja kuma har yanzu Yarima ZEEYAD yaƙi ya dawo gare ni, tayaya kake tunanin hankali na zai kwanta bayan ban san inda ɗa mafi soyuwa a gare ni yake ba, bansan koh yana a raye koh a mace ba, tayaya hankali na zai kwanta bayan iriyar rayuwar da na taso dashi akai wanda ya sanƴa shi guduwa da ƙafafuwan sa, tayaya hankali na zai kwanta bayan ban san koh ya yafe min koh bai yafe min ba, banason na mutu wani ya gaji gadon masarautar nan idan ba Yarima ZEEYAD ba." Sosai mai Martaba ke baiwa Sadeeq tausayi, a kullum bashi da tunani wanda ya wuce na ZEEYAD, a kullum kalaman sa basu wuce kada ya mutu ba tare da ya sake sanƴa ZEEYAD a idanun sa ba, shi kansa yasan lokaci yayi da za'a ce ZEEYAD ya dawo yanzun, amma baisan maiyasa yaƙi dawowa ba, shi kansa ya gama fidda ran cewa koh ZEEYAD na raye har yanzun, dan kuwa shekaru goma kenan tun ranar da suka rabu bai sake jin ɗoriyar sa ba, he just hope and prayed that ZEEYAD na raye sannan kuma zai dawo ga family ɗinsa soon. "Your Highness, insha Allah ni nasan Yarima ZEEYAD na raye inaga dai koh akwai lokacin da ya gindayawa kansa na dawowa ne, amma ni inajin a jiki na cewar yana raye sannan zai dawo nan ba da daɗewa ba." "Allah yasa hakan." "Aameen, ka kwantar da hankalin ka." Kai kawai ya jinjina yana juyar da kujerar sa zuwa kan hoton ya cigaba da kallo. Kai kawai Sadeeq ya girgiza kafin ya ɗau jakar kayan aikin sa ya fice. ******************* __________Yau Watan su Umma biyu da ƴan kwanaki a asibitin sai dai har yanzun DEENAH bata farko ba. Umma tun tana yarda da maganar likita har tazo ta daina yarda kuma, sabida kullum maganar sa bai wuce DEENAH ta kusa samun lafiya ba, amma shiru kakeji, duk da kuwa iriyar kulawar da suke bata sosai. 6angaren ZEEYAD kuwa yana dukkanin iya kan ƙoƙarin sa na ganin ya maida hankalin sa kan career ɗin sa sai dai hakan yaci tura, har sai da Daddy ya zaunar dashi yayi masa faɗa sosai tukun kafin ya ajiye batun DEENAH a gefe duk hakan kuwa kullum tana ransa, gashi bayason karya dokar da Umma ta gindaya masa na cewar bata buƙatar ganin sa a chan wurin su. Yau ma zaune yake a ofishin shi yana zanen wani irin gida da za'a iya cewa hotel ne, ƙofar ce ta buɗu aka shigo. Secretary ɗinsa ne dan haka cike da girmamawa yace "Sir, Madam tazo neman ka, gata chan sai hayaniya take da guards ɗin da kasa sabida sun hana ta shigowa." Ɗan ƙaramin tsaki yaja sabida takaicin hali irin na Khairat, duk maitar Surayya bata kamo koh da hannun Khairat bane balle ƙafar ta. "Sir, mai za'a ce musu, a bar ta ta shigo?" ya faɗa jin ZEEYAD ɗin yayi shiru. Wani irin mugun kallo ya watsa masa kafin kuma yace "Kace dasu muddin naji koh da muryar ta ne then a bakin aikin su." Amsawa yayi cike da girmamawa kafin ya fice daga ofishin dan zuwa aiwatar da abinda ya sanƴa su. "Mayyar yarinƴa kawai" ya faɗa a hankali yana cigaba da zanen sa. Yatsina fuska yayi yana jin sa so very boring tun bayan tafiyar su DEENAH, gashi ba magana take ba balle yayi waya da ita, a wurin Jafar kaɗai yake samun labarin ta yaji hankalin sa ya ɗan kwanta. *************** Zaune Umma take akan DEENAH dake kwance ta tafka uban tagumi, sosai ta lula duniyar tunanin halin da DEENAH ke ciki. Nurses masu kula da ita ne suka shigo kamar kullum dan duba yana yin lafiyar ta. Dube-dube suka fara irin tasu na likitoci yayin da ɗaya ke yin recording a cikin takardar hannun ta. "Wait...did she just moved her fingers?" cewar mai ɗaukar record ɗin tana kallon DEENAH. "What, really?" cewar ɗayar duk suna maida duban su gun ta. Idanu Umma ta zuba musu tana kallo dan kuwa sun ma tare mata DEENAH gashi sam bata fahimci abinda suke cewa ba kasancewar hankalin ta yayi nisa. DEENAH dake kwance sama-sama takejin maganar su nayi mata yawo cikin kwakwalwa, inda takejin kuma kamar a mafarki take. A hankali ta shiga motsa nannauyar idanun ta da suka gama jeme wa yayi duhu sosai sabida irin daɗewar da sukayi a rufe tana ƙoƙarin motsa yatsun hannun ta. Sama-sama haka takejin maganar su har izuwa lokacin da ta gama ware idanun ta akan su sai dai sakamakon duhun da idanun nata sukayi yasa take ganin su dishi-dishi. "She is awake, call the doctor" haka Umma ta faɗa cikin ruɗewa tana tura su gefe kan kuma ta shiga kiran sunan "DEENAH." Da gudu nurses ɗin suka fice dan zuwa kiran likita, basu daɗe ba suka dawo tare dashi dan haka wuri Umma ta bashi kafin kuma ya shiga aiwatar da aikin sa cikin kwarewa Nurses ɗin na taya shi. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah Nagode maka, Allah kasa tashin ta kenan daga wannan rashin lafiya, haƙiƙa kai maji roƙon bayin ka ne ya Wahhabu, wanda bai bika ba kuma bai yarda da cewa kaine sarki mai rayawa da kuma kashewa ba kuwa yayi asara duniya da lahira, yaa Zul-arshil majid ka tashi kafaɗun baiwar ka ka bata lafiya mai ɗorewa, Allah Nagode, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" haka Umma ke ta faɗi cikin kukan murna, tare da sa ran DEENAH ta tashi daga rashin lafiyar kenan. Sun ɗan ɗauki lokaci akanta kafin su samu komai ya daidaita. Ɗagowa yayi yana sharce gumi tare da kallon Umma yace "Muje Office." Da sauri ta mara masa baya tana waigawa ta kalli DEENAH da idanun ta ke a rufe nurses ɗin na cigaba da rubuce-rubucen su. Wuri ta samu ta zauna tana addu'ar samun jin kyakkyawar labari daga bakin likita. "Likita ka faɗamin meke faruwa, ƴata ta tashi ne koh yaya?." Murmushi yayi yace "Sunana Sadeeq." "Toh ni ba wannan ba, yanzu ka faɗamin halin da ƴata ke ciki na roƙe ka." "Ki kwantar da hankalin ki Ma'am, sannan ki godewa Allah, Alhamdulillah bayan dogon jinƴa ƴar ki ta samu sauƙi daga stroke ɗin da ta faɗa, sannan ta fita daga risk ɗin samun wani cuta makamancin hakan, this is a real miracle ko dayake babu yadda Allah baya yi sannan kuma ba'a mamaki da ikon Allah." Zubewa Umma tayi a ƙasa tare da yin Sujudu-Shukur tana miƙawa Allah godiyar ta. Ɗagowa tayi tare da fashewa da kuka sosai wanda ita kanta batasan koh na menene ba. Sadeeq ne yayi ta rarrashin ta har ya samu ta ɗan tsagaita kafin kuma yace "Amma..." Kallon da tayi masa ne yasa shi kasa idda maganar. "Amma mai?." "But, ba zata iya taka ƙafafun ta ba yanzun, dole ne sai an koya mata yin tafiya, and for that to happen har mu samu tayi recovering memory ɗinta then zaku sake spending like 2-3months under our care." "Bakomai wallahi, ai tunda ta warke daga babban ciwon nan na san sauran duk zaizo da sauƙi, zan iya jiran fiye da hakan ma indai ƴata zata samu cikakken lafiya ta dawo kamar bata ta6a ciwon nan ba wannan ba damuwa ta bace, Allah ya bata lafiya kawai." Murmushi yayi yace "Insha Allah, zata samu sauƙi very soon, yanzu munyi mata allurar bacci da zaran ta farko kuma bamason ayi stressing ɗinta dole ne mu bari kwakwalwar ta huta tukun kafin ki tunkare ta da wata maganar." "Amma har zuwa yaushe zan jira hakan?." "Zuwa gobe insha Allah." Shiru Umma tayi alamun yayi mata nisa kafin kuma tace "Toh bakomai, Allah ya kaimu goben da rai da lafiya." "Aameen" ya amsa. Ɗakin Umma ta dawo kafin ta zauna gefen gadon tana kallon fuskar DEENAH da ya zamo so very pale sosai tausayin ta na cika. "I can't believe zaki tashi amma ba zaki san koh ni wacece ba, ba zaki san wacece Ummar ki da kika saba ra6ar jikin ta kullum ba, am so very sad da jin wannan labarin sai dai na san komai mai wuce wa ne, sannan zaki zo ki warke baki ɗaya ki dawo asalin ke." Miƙewa tayi tare da tattare kayayyakin ta cikin ɗan madaidaicin jaka, kafin ta fito. Nurses ɗin ta nema dan haka ce musu tayi zata je ta dawo. Hotel ɗin Umma ta koma sannan tayi musu wanki sai da ta jira suka bushe ta kwashe su, tare da dafo Black tea a cikin flask ta sake kwaso wasu kayayyakin sannan ta komo asibitin. Koh da ta dawo tararwa tayi an canzawa DEENAH ɗaki, dan haka iso sukayi mata zuwa cikin ɗakin. Ɗaki ne mai kyau shima na mutum ɗaya sai dai bai kai na farkon kyau ba. Jere komai tayi mai kyau kafin ta samu wuri ta zauna. Wayar ta ta ciro tare da danna kiran Jafar. "Assalamu Alaikum Umma na." "Wa'alaika Assalam, kana lafiya?." "Lafiya ƙalau Umma dafatan kema haka?." "Alhamdulillah ɗan albarka." "Ya jikin DEENAH fah?." "Jiki Alhamdulillah lafiyar ta na ƙara improving kullum sai dai mu godewa Allah, yanzu ma an canza mana ɗaki." "Umma kenan ta fara samun sauƙi?." "Sosai ma kuwa." Cike da murna yace "Alhamdulillah, Yaushe zaku dawo kenan, Umma muyi video call na ganta." "A'a kai kuwa ba sai ta gama warkewa tass zamu dawo ba, koh zamu zo muyi abinda za'a sake maido ta asibitin ne, kaga ni wannan video call ɗin naku ba gane kansa nake ba, ban iya shi ba." "Haba Umma kinyi karatu fah, ba abu ne mai wahala ba, toh ki nemi ɗaya daga cikin masu aiki a asibitin su nuna miki." "Toh shikenan kada ka damu insha Allah zanyi hakan." "Yauwa Umma na yanzu fah." "Toh inbanda abin ka Jafar ai basa kusa yanzu sai sun zo tukun." "Toh shikenan Umma nima yanzu ina wani aiki ne a office, idan na idda zan kira ki." "Toh shikenan, Allah ya taimaka yayi maka albarka." "Aameen Umma na." Yanke kiran tayi tana jin hankalin ta na kwanciya. *THE NEXT DAY* A hankali take buɗe idanun ta har ta idda buɗa su duka tarr akan ceiling ɗin ɗakin asibitin da take ciki. Idanun ta ta shiga wulla wa tana bin ɗakin da kallo kafin kuma a hankali cikin mutuwar jiki ta shiga ɗagowa zaune. Hajijiyar da ta ɗebe ta ne yasa ta komawa da sauri tana runtse idanu jin kanta na juyawa kamar gudun fanka. Resting tayi kaɗan kafin kuma ta sake yunƙurin ɗagowa zaune, dakyar dai ta samu ta zauna idanun ta na juyawa. Lafewa tayi a jikin frame ɗin gadon idanun ta runtse tana maida numfashi. Ɗakin ta shiga ƙarewa kallo wondering koh a ina take. Abubuwan da ta gani maƙale da hannun ta na hagu ta sanƴa hannun ta na dama tare da fuzge su tana yunƙurin sauƙa daga kan bed ɗin. Kafafun ta da sukayi bala'in nauyi ta kasa koh da ɗaga su ne ya dakatar da ita daga yunƙurin sauƙar da take niyyar yi. Yunƙurin motsa su take sai dai ta kasa hakan, hannu ta kai ta yaye rufar bargon nata tana kallon ƙafafuwan nata. Shiru tayi tare da ƙure su da ido tana mamakin abinda ya hana su motsawa bayan koh ina a jikin ta na motsi. Hannu ta kai ta fara shafar ƙafar tata idanun ta akan su. Ƙarar buɗewar ƙofar da taji ne yasa ta maida hankalin ta wurin tana kallon matar dake shigowa. Umma ganin DEENAH zaune har ta ɗago suka haɗa ido ne yasa ta sakin ledar hannun ta tare da zaro idanun ta tana ƙarasowa wurin ta da sauri. Fuskar DEENAH ta kamo da hannayen ta bibbiyu cikin kuka take faɗin "DEENAH?, my beautiful daughter, Alhamdulillah, Allah Nagode maka" ta faɗa tana rungume DEENAH da ta saki baki da ido kawai tana kallon ta. Sosai Umma ke kuka nan ta ɗago tana kallon DEENAH ɗin, tana jin kamar ta maida ta ciki tsabar ƙauna da farin cikin dake bibiyar ta. DEENAH ganin wani abu da batasan menene shi ba na fitowa daga cikin idanun matar yasa ta kai hannun ta a hankali ta lakuto hawayen Umma tana kallo. Da kallo kawai Umma ke bin ta tana share hawayen fuskar ta. Shigowar Sadeeq ya sanƴa su maida duban su gunshi. Da kallo DEENAH ke binshi har ya ƙaraso wurin su, murmushi yayi yace "Finally, she is awake." Kai kawai Umma ta iya jinjina wa tana cigaba da goge hawayen dake yi mata zirya a fuska. Hannu ya kai da niyyar duba idanun ta, nan tayi saurin matsawa kusa da Umma tana shigewa jikin ta tare da lafewa. Murmushi Sadeeq yayi yace "Seems like ta manta komai da komai." Ƙoƙarin ɗago ta Umma keyi amma taƙi ɗagowar hakan yasa ta cewa "Ta manta komai da komai, hakan na nufin ta mance komai game da rayuwar da tayi, yin magana, yin dukkanin wasu ayyuka da jikin ta, duka ta manta su sai an koya mata komai kenan kamar ƙaramar yarinƴar dake kan tashi?." Kai ya jinjina yace "Exactly." Ajiyar zuciya Umma ta sauƙe tare da kallon DEENAH tace "Allah sarki ƴata, ya muka iya haka taki ƙaddarar tazo miki, dole ne mu rungume shi." "Hakane" cewar Sadeeq, kafin ya ɗaura da faɗin "Zan aiko magunguna anjima dama kuma jerin irin abincin da yakamata take ci insha Allah, muddin kuka kiyaye dokoki then komai zai zamto kamar ba'a yi ba." "Insha Allah likita, Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi." "Aameen, bakomai" ya faɗa kafin kuma ya fice. Maido duban ta gun DEENAH dake ta bin bakin su da kallo tayi kafin tayi mata murmushi tace "A hankali zaki gane komai insha Allah." ****************** *A WEEK AFTER* Tun bayan farfaɗowar ta Umma ke fita da ita zuwa shan iska, tare da taimaka mata itada da Nurses guda biyu wurin koya mata tafiya. Yau ma Nurses biyun ne suka fita tare da ita, taimaka mata sukayi ta miƙe daga kan keken nata kafin su damƙa mata sandar koyan tafiyar tata a hannu ɗaya tace "Kin kalli chan" ta faɗa tana yi mata pointing wurin "Toh zuwa nan zaki taka kije, kamar yadda mukayi miki jiya." Kallon ta tayi alamun bata fahimci mai take cewa ba. Ɗaya ce tace "Bata san mai kike cewa ba, gwada mata zakiyi kina faɗa." "Oh exactly" ta faɗa kafin ta ɗauko wani sanda tana gwada mata shi yadda zatayi. Murmushi tayi kamar yadda taga sunyi kafin kuma a hankali ta shiga taka ƙafar ɗaɗɗaya tana yin yadda ɗayar keyi har sukaje suka dawo bata faɗi ba. Tafi suka kama yi suna jinjina mata "Wooww you did it." Murmushi tayi kawai kasancewar shi ne maganar ta yanzu. "Alright, one more try" faɗin ɗayar tana kar6ar sandar a hannun ɗayar kafin su shiga yi har sukaje suka dawo. Tafawa suka shiga yi nan ma hakan yasa ita ma ta shiga yin tafin. "Alright, alright ya isa, yanzu ita kaɗai ce zata gwada, right?." "Yeah." Sandar suka miƙa mata akan taje ta ita kaɗai. Kai ta jinjina musu kafin kuma tabi hanƴar da kallo nan dai taga yayi mata tsayi. Juyowa tayi ta kalle su hakan yasa sukayi mata alamun da taje. A hankali ta shiga takawa har dai dakyar ta isa wurin, murmushi tayi ganin suma suna yi suna haɗawa da tafi kafin kuma tayi shirin juyowa. Step ɗaya tayi taji ta bugu da mutum take tayi tangal-tangal ta faɗi sandar tata na yin gefe. Saurin juyowa yayi yana sauƙe wayar daga kunnen sa kafin kuma cikin sweet voice ɗinsa yace "Sorry" yana miƙo mata hannu. Da kallo tabi hannun nasa dashi, kafin kuma wani irin abu yayi mata flashing a cikin kwakwalwar ta hakan yasa ta saurin runtse idanu tana dafe kai. Da sauri nurses ɗin suka ƙaraso suna ɗaga ta tsaye, hannayen ta dafe da kai. Buɗe idanun ta tayi tana jin kamar abu makamancin wannan ya ta6a faruwa da ita. "Is she Okay?" suka tsinkayo muryar sa. Duk maida duban su sukayi kansa, kafin kuma cikin girmamawa suce dashi "Yes sir" suna washe baki. Ɗagowa tayi tana sauƙe idanun ta kan kyakkyawar fuskar sa. Murmushi yayi mata kafin ya ɗauko sandar ta da ya faɗi yana miƙa mata. Ƙin amsa tayi sabida bata san shi ba kuma bata saba dashi ba. "Ai yallabai ba zata amsa ba, sabida bata sanka ba." "Oh is that so?" ya faɗa. Ɗaya daga cikin nurses ɗin ya miƙawa sandar kafin kuma yace "Alright bye, take care" ya faɗa yana juyawa ya bar su nan tsaye. Miƙa mata sandar tayi kafin ɗaya tace "Bakya ganin kamar ƙara kyau yake kullum?." Murmushi ɗayar tayi tace "I just love his smile." Dariya sukayi kafin su kama DEENAH suyi ciki da ita. *Yawan Comment, Yawan Posting* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *029...* *THE HEARTBREAK💔* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _________Cikin rufewar idanu da ƙunar zuciya ya koma cikin motar sa zuciyar sa na beating so fast kamar zata faso ƙirjin sa ta fito. He can't believe abinda idanun sa suka gane masa, that killer smile da ta baiwa wannan mutumin har kuma ya ta6a ta shi yafi komai ƙona masa rai. Wani irin abu mai ɗacin gaske ya haɗiya yana furzar da huci hannayen sa kan steering ɗin motar tasa. Tunani yake ya sake komawa ne kokuwa dai ya bar su kawai ya taho. Kai ya girgiza tare da cire Mask ɗin fuskar sa ya furta "No" a hankali yana runtse idanu. Murfin motar ya buɗe ya fito kafin kuma ya sake tunkarar hanƴar cikin asibitin zuciyar sa nayi masa lilo. Jah yayi ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin kafin kuma ya sauƙe wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya yana kai hannu tare da knocking ƙofar. Umma dake baiwa DEENAH abinci a baki ɗagowa tayi tana maida duban ta gun ƙofar. Niyar tashi take nan wannan saurayin yayi saurin cewa "No please, i will get the door" ya faɗa yana tashi daga zaunen da yake tare da zuwa ya buɗe ƙofar. Wannan saurayin ɗazun nan ne ya sake gani dan haka sake tamƙe fuskar sa da ta fara yin jaa saboda 6acin rai yayi tamau yawa wanda yaci guna tare da kauda idanun sa daga kallon da saurayin keyi masa. "Are you looking for someone?" cewar wannan saurayin. Magana ZEEYAD ya kasa sabida 6acin ran dake cin sa dan kuwa har yanzu hoton sa na riƙe da DEENAH yaƙi 6ace masa a idanu har yanzun, sai dai baya tunanin yana da lokacin da zai tsaya kula sa yanzun. Kallon sa yayi kafin kuma kamar wanda bayason yin maganar yace "DEENAH." "DEENAH?" saurayin ya maimaita. Kallon sa ZEEYAD yayi ganin yana neman raina masa hankali da kuma 6ata masa lokaci ne yasa shi ra6a wa ya wuce ciki. Da kallon mamaki saurayin ya bisa kafin kuma a hankali ya furta "He seems so arrogant" ganin kamar shi ɗin baƙo ne a gare su yasa shi bar musu ɗakin yana ficewa. Tsaye yayi yana kallon yadda Umma ke bata abincin tana amsa, zuciyar sa na wani irin forming farin ciki ganin ta dawo hayyacin ta har tana iya zama taci abinci, abinda ya daɗe yana jira kenan. Cikin calm voice ɗinsa yace "MADEENAH?." Tsayawa tayi baki buɗe ba tare da ta kai ga kar6ar abincin da Umma ke bata ɗin ba. Duk juyowa sukayi daga ita har Umma suna kallon shi. Kallon juna suka shiga yi da ita ba tare da kowannen su ya iya janƴe idanun sa daga cikin na ɗan uwan sa ba. Yadda take kallon sa da manƴan idanun ta kaɗai ya sanƴa sa jin wani irin mugun kewar ta wanda baisan har haka yayi missing ɗin nata ba. Umma ganin duk sun mace a kallon juna ya sata faɗin "I have had enough of this." Saurin juyowa DEENAH tayi tana kallon ta hakan ya sanƴa ZEEYAD ma ɗauke duban sa yana dawo dashi kan Umma. Kafin ya kai ga cewa komai Umma ta riga shi da faɗin "What do you think you are doing here?." Shiru yayi kafin kuma daga bisani yace "Am sorry, i.." "Sorry for yourself" ta faɗa cikin katse shi, kafin kuma tace "So ka kasa idda bin dokar da na sanƴa maka shine ka ɗauko ƙafa ka biyo ta har nan?." "Am sorry, but na kasa daurewa ne." "Ka kasa daurewa, what do you mean by ka kasa daurewa?, kana nufin ban isa na sanƴa doka kuma kabi bane komiye?." Saurin girgiza mata kai yayi yace "Ba haka bane, it's just that..." "It's just what?" ta faɗa cikin katse shi. Shiru ZEEYAD yayi ba tare da ya sake ce mata komai ba yana sadda kansa ƙasa. "Indai har ba zaka iya bin ƴar dokar nan da na gindaya maka ba, why then kake tunanin zan iya baka amanar ƴata kuma ka riƙe da kyau?." Ɗagowa yayi yana kallon ta jin abinda ta faɗa, zaiyi magana tayi saurin katse shi da faɗin "Babu abinda zaka faɗa min, DEENAH kazo gani koh ba haka ba, sabida ita ka watsar da komai naka a chan ka taho nan saboda rashin haƙuri irin taka koh ba haka ba, alright then gata nan ai a gaban ka ka ganta, tunda har ka ɗauko ƙafar ka kazo nan dukkanin wasu sauye-sauye da zaka gani daga gare ta blame yourself for that, tunda har ba zaka iya haƙurin dawowar ta gida ba" ta ƙarashe cikin 6acin rai kafin kuma ta fice daga cikin ɗakin kamar zata tashi sama. Maida duban sa yayi kan DEENAH da ta zama ƴar kallo tunɗazu a tsakanin su. Sosai yake mamakin yadda tayi kamar wacce bata san shi koh wannan ne karon farko da ta fara ganin sa, dan kuwa bata wani nuna alamun hakan ba. Da sauri ya ƙarasa wurin ta yana kiran sunan ta, ja yayi ya tsaya ganin tayi baya da sauri tana kya6e baki kamar zatayi kuka. Mamaki ne fal ya cika zuciyar ZEEYAD yana mai bin ta da kallo. Pillow ta ɗauka tare da rungume wa a ƙirjin ta tana kallon shi. "What..what are you doing?" ya faɗa cike da mamaki yana ƙara step ɗaya kuwa tasa ƙara tare da cusa kanta cikin pillow ɗin. Dakatawa ZEEYAD yayi yanajin zuciyar sa na running so very fast wanda ke sanƴa sa feeling uncomfortable. "Actually she had a memory loss" yaji an faɗi hakan daga bayan shi, kafin kuma ya sake jin "Besides, who are you?." Zuciyar sa ce tayi wani irin mugun harbawa jin an ambaci memory loss, inda kuma wani irin jiri da zazzafar ciwon kai suka darsu masa lokaci guda hakan ya sanƴa sa saurin dafe ƙarfen gadon yana runtse idanun shi. Ɗagowa yayi yana kallon DEENAH da har yanzu bata ciro kanta daga pillow ɗin ba zuciyar sa na karyewa. Da sauri ya ƙarasa wurin ta tare da janƴe pillow ɗin yana ɗago da fuskarta yayi cupping a hannun sa. Cikin rawar harshe yace "You..you...you doesn't remember anything?." DEENAH da ta zaro manƴan idanun ta cike da tsoron wanda bata sani ba yayi mata hakan ne, yasa ta sakin ƙara cike da firgici tana ƙoƙarin kwace fuskar ta. "Stop" ya faɗa a hankali yana ƙoƙarin saita nutsuwar sa. ZEEYAD sam bai yarda DEENAH tayi losing memory ɗin ta ba, dan kuwa ganin yake kamar shi ɗin ne kawai bataso ba wani abin ba hakan yasa ta faking cewar tayi losing memory ɗinta. "Stop it" ya sake faɗa. "I said Stop it" ya faɗa a tsawace yana tsare ta da jajayen idanun sa. Cak ta tsaya tana kallon shi. Wani abu mai ɗaci ya haɗiya yace "why...how could you loss your memory, i know you're faking it right?, just tell me that baki manta koh ni wanene ba, please" ya faɗa idanun sa cikin nata. Shiru tayi tana kallon sa ba tare da tace komai ba. "Please" ya sake faɗa cikin raunanniyar muryar sa. "Please DEENAH" ya sake faɗa. "Just tell me that baki manta dani ba, idan kika ce kin manta ni then bakiyi min adalci koh kaɗan ba." Yatsun hannayen ta ya kamo tare da kallon zoben da ya sanƴa mata lokacin da take kwance a asibiti yace "See this, i gifted you this, remember?" ya faɗa yana kallon ta. Zoben ta ƙurawa idanu tana kallo wanda bata ta6a lura dashi a hannun nata ba sai yanzun. A tsorace kuma ta hau kokuwar cire shi daga yatsar hannun ta. Riƙe hannun nata yayi yace "What are you doing, wannan ma baki tuna shi ba, oh yeah ba zaki tuna shi ba, then what about my face?" ya faɗa yana nuna mata fuskar sa. "She can't remember anything" yaji an sake faɗa ta bayan shi. Ba tare da ya juya ya kalli wanda yayi maganar ba yace "And i would make her remember it." "You can't do that." "Of course i can" ya faɗa cike da fusata yanajin zuciyar sa na zafi. "I am an expert Doctor and when i said ba zata tuna komai yanzu ba, then so be it." Share mai maganar yayi yana tattaro hankalin sa da nutsuwar sa kan DEENAH yace "Look MADEENAH, i know atleast yanzu kin tuno wani abin da kika sani, you can't do this to me, please talk to me please." Shiru tayi kawai tana kallon sa dan kuwa babu abinda ta tuna game dashi, infact a takure ma take sabida tsoron sa takeji sakamakon tsawar da ya daka mata, hakan yasa duk ta kasa sake jikin ta. "MADEENAH?" ya faɗa. "What is going on here?" ya jiyo muryar Umma. Cike da 6acin rai Umma ta ƙaraso wurin, ganin yadda ya damƙe hannun DEENAH cikin nashi ba ƙaramin 6aci ranta yayi ba. Hannun DEENAH ta kama tana fuzgewa daga cikin nasa cikin 6acin rai tace "How dare you, ka fara wuce gona da iri." Shiru yayi bai ce komai ba dan kuwa baya tunanin zai iya sake tankawa Umma idan tana magana. DEENAH saurin 6oyewa tayi a bayan Umma. Kallon sa Umma tayi tace "I warned you didn't i?, dah ace zaman ka kayi achan da baka zo ka tadda 6acin rai da damuwa ba, abinda nake gudu kenan hakan yasa ban sanar da Jafar halin da take ciki ba, had he know nasan babu abinda zai hana shi zuwa nan, duk ƙaunar da kakeyi mata kana tunanin yafi wanda ɗan uwanta keyi mata ne?, amma shi yabi doka ta ya zauna inda na umarce shi, but look at you sai da kayi dukkanin yadda kayi ka kasa controlling zuciyar ka ka biyo ta nan, kana tunanin zuwa tarar da farin ciki sai dai ya tadda akasin hakan, tunda yanzu ka samu abinda kake nema zaka iya tafiya, duk ranar da muka dawo zaka iya zuwa ka duba ta." "Please don't send me away, i care so much about your daughter." "Kana nufin mu bamu isa mu bata isasshiyar kulawa bane komiye, dukkanin halin da DEENAH ke ciki baka kai ni jin zafin hakan ba, so now stay beyond your limits, DEENAH bata buƙatar ka yanzu a rayuwar ta dan kuwa wahalar da kanka kawai zakayi, i guess kaima ba zaka rasa family ɗin da zaka kula dasu ba, so from now on...nayi maka tsakani da DEENAH babu kai babu ita, i want you to stay out of her life for good, kaje ka nemi wacce kuka fito daga ƙabila ɗaya tare, dan kuwa a matsayi ta ta Hausa-Fulani bana tunanin zan iya baka auren ƴata" ta ƙarashe in a serious tone. ZEEYAD jin maganganun Umma yake kamar ana watsa masa ruwan zafi a jiki, kai ya fara girgizawa yana faɗin "No...no i can't do it, i can't leave without DEENAH..." "Of course zaka iya rayuwa babu DEENAH tunda ba tare aka haifo ku ba, sannan kuma ka iyayin rayuwa tun kafin ka haɗu da ita." Kai ya girgiza yace "That was a different thing, but DEENAH...i just couldn't imagine my life without her." "Bana buƙatar ja in ja da kai, i have said my mind and i won't take back my words." "I have suffered enough in my life, but please kada ki sake nesanta ni da DEENAH i beg you Aunt" ya faɗa yana zubewa kan guiwowin sa. Ɗauke kai Umma tayi kafin tace "Bana magana sau biyu, sannan ba ƙoƙarin nesanta ka da DEENAH nake ba, ina nufin ka rabu da ita ne har abada." "Please Aunt, i can't live without DEENAH, i promise zan koma inda na fito indai har ba zaki raba ni da ita ba." "You don't have to do that, as i told you earlier i would repeat myself again, as from now on babu kai babu DEENAH, don't let me repeat myself for the third time, stay away from my daughter, Forever." Shiru ZEEYAD yayi yanajin dukkanin wani sungun farin cikin sa na gushewa, zuciyar sa yakejin kamar zata fito waje da maganganun Umma, wani irin abu yaji ya tokare masa maƙoshi zuciyar sa na mugun suya sosai, baisan dalilin da ya sanƴa Umma bata ƙaunar sa ba, baisan laifin da ya aikata mata ba, DEENAH itace farin cikin sa amma gashi yau guda tana neman yanke alaƙar dake tsakanin su, yanason DEENAH da dukkanin zuciyar shi, da dukkanin jinin jikin shi, yana jinta tamkar numfashin sa ne, bai ta6a kyashin ta ba, soyayya yakeyi mata na gaskiya, ba tare da duban cewa ya fita wani abin ba, babu abinda yayi lacking a rayuwa except farin ciki sai dai a duk sadda wani abin farin cikin ke neman kusanto shi, a lokacin ne kuma za'ayi dukkanin yadda za'ayi na ganin an raba shi dashi, baisan yaushe ne zai sake samun farin cikin da zaiyi lasting kwana ɗaya a cikin ta ba, kullum zuciyar sa a cunkushe take, kullum zuciyar sa cikin kewa da begen ta yake, da ita yake kwana kuma ya tashi, and now Umma na ƙoƙarin raba sa da ita, and ita kuma ba zata iya hana hakan ba sabida matsalar mantuwa da ta samu, runtse jajayen idanun sa yayi yanajin yadda zuciyar sa ke racing da ƙarfi. "Doctor, why don't you just led him away from here, koh haka zaku zuba ido kuna ganin abin dake faruwa, my sick daughter need to rest domin samun lafiyar ta" cewar Umma. Maido duban sa kan ZEEYAD dake durƙushe tunɗazu bai juyo yaga fuskar sa ba, but haka kurum yakejin wani irin strange feeling akansa, idan ma shi ɗin ɗan uwa ne a garesu ai baiyi kama dasu ba koh kaɗan, sannan baya tunanin ɗan asalin cikin Nigeria akwai mai irin farin nan, daga ganin sa kaga balarabe koh ba indiye, kallon bayan sa kawai Sadeeq keyi dukda baisan asalin kan zancen nasu ba sai dai ya tausayawa bawan Allahn sosai, sabida rabo da masoyi sam babu daɗi. Umma ganin Sadeeq ɗin yaƙi kula ta sai ma tsayuwa da yayi yana kallon ZEEYAD ya sanƴa ta fizgo hannun DEENAH da niyyar su fice waje. Saurin riƙe DEENAH ZEEYAD yayi ransa na mugun 6aci. Tsayawa Umma tayi tare da juyowa ganin DEENAH taƙi biyo ta ta tsaya. Ganin ZEEYAD riƙe da hannun ta ba ƙaramin 6ata mata rai yayi ba. "You can try as hard as you can to separate me with DEENAH, but that won't work" ya faɗa yana tashi tsaye tare da juyowa. Kallon sa kawai Umma keyi cikin 6acin rai. Wayar dake hannun Sadeeq ne ya su6uce ya faɗi sakamakon arba da idanun sa sukayi akan fuskar ZEEYAD. "Let go of her...now" cewar Umma. Bai motsa ba haka kuma bai saki hannun DEENAH ba, dan kuwa ya ƙudurta a ransa cewar muddin ya saki hannun DEENAH ba tare da Umma ta tausaya masa ba then...ya barta kenan har abada kamar yadda mahaifiyar ta ta buƙata. "So you won't let go um, alright" ta faɗa tana sakin hannun DEENAH kafin tace "Let's see idan ita DEENAH ɗin choose to be with you or prefer to walk away" ta faɗa tana kallon sa. Cize bakin sa yayi trying so hard to control his emotions. Juyowa DEENAH tayi tana kallon shi, kafin kuma tayi saurin juyawa ga Umma tana miƙa mata hannu. Kallon su kawai Umma keyi ba tare da ta baiwa DEENAH hannu ba. Sadeeq da sauran nurses ɗinma ƴan kallo suka zama a wurin. Juyowa DEENAH tayi kafin ta sanƴa ɗayan hannun ta tare da fara kiciniyar cire hannun ta cikin nasa. Riƙon da yayi mata ne ya sanƴa ta kasa kwacewa. Sosai tayi trying wurin ganin ta kwace hannun ta sai dai ta kasa hakan ya sanƴa ta fara yi masa kuka. Runtse idanun sa yayi zuciyar sa na matuƙar zafi sosai yanajin zafin kukan ta sosai a cikin zuciyar sa. Fara sassauta riƙon da yayi mata yayi hakan ya sanƴa ta saurin fuzge hannun ta sai dai kafin ta kai ga cirewa baki ɗaya yayi saurin riƙo ƴar yatsar ta dake sanƴe da ring ɗin da ya bata. Wani kukan ta sake sanƴawa hakan yasa shi saurin sassauta riƙon inda tayi saurin fuzge yatsar ta ring ɗin na ficewa cikin hannun sa. Kallon ring ɗin ya tsaya yi kafin ya damƙe shi cikin tafin hannun shi yana ɗagowa ya kalli DEENAH da ta rungume Umma tana kuka. "So now DEENAH da kanta ta guje ka, are you still going to force yourself into her life again, kokuwa ka haƙura?." Duban sa ya maida kan hannun sa dake damƙe da zoben yace "No, i would do as you said, i won't force myself into your daughters life again..am...am living her for good not just because she doesn't like me, but because you forced me to, and i will make sure ban sake shigowa rayuwar ƴar ki ba, i will make sure i stay far away from you guys, i will make sure i became exactly who you wants me to be, Thank you for all you've done to me and i really appreciate it, banyi fushi dake just because kin raba ni da DEENAH ba, but nayi fushi ne da kaina for spending years loving someone that can never be mine, you're a mother and am sure you make the right decision for your daughter, which she will never regret, and yes duk sadda DEENAH ta dawo hayyacin ta don't tell her that kece wacce kika raba mu but i chose to leave her on my own, sabida banason rusa farin cikin happy family like you, just tell her that nine nace ba zan rayu da ita ba, idan kikayi hakan then i know that she would hate me forever sannan kuma ta cire ni daga zuciyar ta dukda kuwa bana tunanin idan ina ciki tuntuni, daga nan kuma zatayi ƙoƙarin ganin ta mance dani kamar yadda nima zanyi yanzun, am sorry idan na ta6a 6ata miki...am living" ya ƙarashe yana maida duban sa kan DEENAH da har yanzun bata ɗago ba, kauda idanun sa yayi daga kanta kafin kuma ya ɗaga ƙafa dakyar ya fice yana buge Sadeeq da ya saki baki da hanci yana kallon shi, ba tare da ya koh kalli fuskokin wadanda ke tsaye cikin ɗakin ba. Da kallo Umma da itama jikin ta ya gama yin sanƴi tayi sai dai ta dake tana shafa kan DEENAH dake rungume da ita. Cikin gudu Sadeeq ya fice dan mara masa baya sai dai koh alamun sa bai gani ba, kamar wanda iska ya ɗauke. "Yanzun nan ya fita, where could he be?" ya faɗa cikin gigicewa yana yin hanƴar waje da gudu tare da bangaje dukkanin wanda ke gaban sa ya wuce. Har farfajiyar asibitin Sadeeq ya fice sai dai baiga ZEEYAD ba baiga alamun sa ba. "Ohh no" ya faɗa kamar wanda zaiyi kuka yana riƙe kai cikin mugun takaicin wautar da yayi har ya bari ya fice daga ɗakin. Office ɗinsa ya dawo tare da ɗaukar makullin motar sa yaja ta tare da barin asibitin. Dai-dai lokacin ZEEYAD dake tafiya yanajin kamar ruhin sa ta bar jikin sa ya fito, kai tsaye motar sa ya nufa tare da buɗe ta ya shiga. Kansa ya ɗaura kan steering ɗin motar yanajin wani irin zazza6i mai zafi na neman rufe shi, sosai idanun sa sukayi jaa kansa na mugun sara masa. Da kyar ya samu yaja motar ya bar cikin asibitin. *Yawan Commen, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *028...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ___________Yau ma Ficewa sukayi dan kai DEENAH motsa ƙafafuwan ta a inda suka saba. After so many attempts da tayi da kanta, ta samu tafiyar tata ta ɗan daidai ta sai dai tana yin kaɗan zata zauna alamun ta gaji. "Wowww seems like tafiyar ki ya fara miƙewa, i can't believe it" cewar ɗaya daga cikin nurses ɗin. Murmushi kawai DEENAH tayi Kasancewar shine abinda taga suna yi. "So now mai kuma ya rage?" cewar ɗaya. "Ummm, i think gudu." "Gudu kuma?." "Yep." "No ba zata iya ba, ƙafar tata bata yi wani kwarin da zata iya yin gudu ba." "Alright then, sai mu koma ciki." Riƙo DEENAH sukayi suka koma ciki. Zaune suka sami Umma na waya, dan haka zaunar da DEENAH sukayi kafin su tsaya jiran Umma ta gama wayar. DEENAH idanu kawai ta zubawa Umma tana kallo har ta idda wayar ta ajiye. Murmushi Umma tayi, kafin ta kalle su tace "Har kun gama?." "Yes Ma'am, sai gobe kuma." "Masha Allah, Nagode muku sosai, Allah ya biya ku." "Kada ki damu Ma'am, ai aikin mu ne." "Mu zamu wuce yanzu, sai gobe kuma." "Alright thank you so much." Murmushi sukayi kafin su juya da niyyar tafiya. Tashi ita ma DEENAH tayi tana mara musu baya. "A'a DEENAH?" cewar Umma. Miƙewa Umma tayi daga inda take zaune tare da zuwa ta kamo DEENAH tace "Zo nan ki zauna, sai gobe kuma zasu dawo." Hannun ta shiga kwacewa tana kya6e baki alamun zata yi kuka. Ɗaya daga cikin nurses ɗin ce tace "DEENAH je ki zauna kinji, gobe zamu dawo mu sake fita." "Come on" cewar Umma tana riƙo ta. Ƙara tasa tana kwace hannun ta tare da maƙe kafaɗa, kafin kuma tayi bayan su tana 6oyewa. Murmushi Umma ta ƙaƙalo kafin tace "Meke damun ta?." "Ma'am ki kwantar da hankalin ki, damu ta saba yini kullum shiyasa batason mu tafi mu bar ta." "DEENAH dear, zo nan gare ni kinji?" cewar Umma tana kai hannu ta kamo ta. Sake 6oyewa tayi tana ƙanƙame su. "Ma'am sai kinyi haƙuri, kinsan yanzu kwakwalwar ta ta koma tamkar irin ta yara ne, a hankali zata saba dake." Sosai Umma taji babu daɗi a ranta wai yau DEENAH ce ke gudun ta sabida bata santa ba. Wuri kawai ta samu ta zauna kafin tace "Shikenan kuje toh." Ficewa sukayi still tana maƙale dasu. Office ɗin su suka koma da ita kafin kowacce tayi wurin table ɗin ta. DEENAH kuwa wurin kawai take bi da kallo, duk abinda ta gani kuwa sai ta ɗaga shi tana kallo tare da son tuno koh menene shi, idan ta kasa kuma sai ta ajiye shi ta kama wani. Wata nurse ce ta shigo ɗakin tare da ƙiran sauran Emergency call, ba tare da 6ata lokaci ba dukkan su suka dunguma suka fice daga office ɗin cikin sauri. Da kallo DEENAH da ta kya6e baki kamar zatayi kuka ta bi su, kafin ita ma ta fice daga ɗakin a hankali cikin tafiyar ta da bata gama warkewa ba. Ficewar ta kuwa bata ga alamun su ba dan haka wani hanƴar da take tunanin nan suka bi tayi. Tafiya take har ta sauƙo ƙasa tayi hanƴar waje amma bata gan su ba, dan haka wani hanƴar ta sake kamawa ta fara bi har ya kaita zuwa wani wurin da babu mutane sosai. Waige-waige ta fara yi kafin kuma ta samu irin kujerun ƙarfe masu kyau da akeyi ɗinnan ana ajiye su a wajen asibiti ta zauna idanun ta na kawo hawaye. Ɗilowa hawayen yayi dan haka ta kai hannu ta shafo shi tana kallo dan kuwa batasan menene shi ba, taga dai kamar irin abin nan ne da take gani a idanun matar nan wasu lokutan, ga kuma taga sai zubowa suke ta kasa controlling ɗin su, ga kuma wani irin yanayi da takejin ta wanda batasan koh na menene shi ba. Kwanciya tayi akan kujerar tana cigaba da rera kukan ta a hankali. Ta kai almost 10mins a haka kafin ta jiyo muryar a saman ta "Are you Okay?." Tsaida kukan nata tayi tana buɗe idanun ta. Jin tayi shiru bata ɗago ba ya sa shi sake faɗin "Do you maybe need some help?." Shiru ta sake yi tana wuwwula idanu kafin kuma ta shiga ɗago da kanta a hankali tana sauƙe idanun ta cikin nasa. Saurin maida kanta tayi tana runtse idanun ta. Mamaki ne ya kama shi a ransa yace _"Is she normal?"_ yana mai tsugunnawa. "Hey" ya sake faɗa. A hankali ta miƙe zaune tana wuwwula idanun ta kanta a ƙasa. "Are you Okay, why are you sitting here alone crying?." Shiru tayi bata basa amsa ba sai ma idanu da ta kafa masa tana kallon idanun sa kasancewar fuskar sa ɗauke da facemask. Waving hannayen sa yayi akan fuskar ta inda tabi hannun nasa da kallo, tana sake maido idanun ta kansa. "What's your name?" ya faɗa. Shiru tayi nan ma just staring at him. _"Toh kodai kurma ce?"_ ya faɗi hakan a ransa kafin kuma yace "Are you lost?." Nanma shiru tayi tana kallon sa, kafin kuma ya miƙe daga tsugunen da yake yana faɗin "Well, am living then tunda ba zakiyi magana ba" ya faɗa yana juyawa da niyyar tafiya. Riƙo rigar sa tayi ta baya hakan ya sanƴa shi tsayawa tare da juyowa yana kallon ta. A hankali yace "Seems like ta shirya magana" kafin kuma yayi magana yadda zata ji yace "So now tell, what are you doing here all alone?." Ta inda ta 6ullo tayi masa pointing da yatsar ta hakan ya sanƴa sa maida duban sa wurin. "What, bangane ba" ya faɗa yana kallon ta. Sake nuna masa wurin tayi har sau uku kafin kuma yace "Okay, okay" yana duba agogon dake saƙale a wrist ɗinsa kafin kuma yace "Alright, i guess daga nan wurin kika fito koh, get up then." Kallon ta ya tsaya yi ganin ta zuba masa idanu tana kallo hakan yasa shi sake faɗin "Get up lady." Ganin yayi mata alamu da hannu ya sanƴa ta yunƙurawa ta miƙe dakyar, kafin kuma yayi gaba yana faɗin "I wonder ta yadda kamar ki zata iya 6ata a cikin asibitin nan, i have alot to cover but kina neman 6ata min lokaci." Duk shi kaɗai ke maganar shi not knowing DEENAH na chan tsaye inda ya baro ta. "Why are you so quiet lady, kodai ke kur...." bai iya idda maganar ba sakamakon juyowa da yayi ya ganta chan tsaye inda ya baro ta ta zuba masa watery eyes ɗinta. "Seems like she is looking for my trouble" ya faɗi hakan yana komowa inda take. "Are you sure you're Okay?" ya faɗi hakan yana kallon ta. Ƙafar ta t tayi mata nauyi ta taka da kyar cikin ɗingishi kafin ta tsaya. Kallon ƙafar tata yayi yace "Ohh, you can't walk properly" kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Aren't you thesame girl i saw the other day?." Shiru tayi tana kallon sa hakan yasa shi faɗin "Alright, come on" ya faɗa yana miƙa mata hannun shi. Ganin ya gane cewar ba zata iya tafiya ita kaɗai bane yasa ta basa hannun ta, kafin ya riƙo ta su fara tafiya. Ciki suka koma kafin kuma ya fara tambayar duk wanda suka haɗu dashi koh sun santa. A haka har suka haɗu da wata nurse tace "Ohh yeah sure, kamar na santa she is from Room 106 chan upstairs." "Thank you" ya faɗa kafin yaja hannun DEENAH da ta zama ƴar kallo kawai sukayi. Taimaka mata tayi ta haura stairs ɗin kafin kuma ya shiga bin lambobin ɗakunan yana duba number ɗin da Nurse ɗin ta faɗa masa. "Got it" ya faɗa lokacin da ya hango room ɗin. Ƙarasawa sukayi bakin ƙofar kafin kuma ya hau knocking a ƙofar. Ba'a jima ba aka buɗe ƙofar, DEENAH ganin Umma yasa ta ƙarasawa da sauri tana faɗawa jikin ta ta ƙanƙame ta. "Menene, meke faruwa?" faɗin Umma tana shafa kanta. "Hello ma'am." "Hi" ta amsa tana kallon sa. "Is she your daughter?." "Yeah, she is." "Oh i see, actually i saw her outside crying..." "What crying, mai ya same ta?" ta faɗa cikin katse shi tana ɗago DEENAH. "Well actually, ina tunanin ta 6ata ne batasan hanƴar dawowa ba, so i decided nayi tambaya koh akwai wanda ya santa and i met one nurse on our way ita ce ta sanar dani cewar a ɗakin nan take." "Oh Thank you so much, Allah yayi maka albarka." "It's alright, take care" ya faɗa cike da girmamawa kafin kuma ya wuce ya tafi. Rufo ƙofar Umma tayi tana janƴo hannun DEENAH ciki ta zaunar da ita tace "Ina su wadanda kuka fita tare dasu ɗin sukayi?." Shiru tayi bata bata amsa ba, hakan ya sanƴa Umma ma yin shirun tana komawa da gefe ta zauna tare da rabka tagumi. *************************** _________"Why are you like this Ummie, maiyasa a komai sai kin nuna son kai ne?, wane irin gata ne mai Martaba baya bani, but kullum kina cikin complain akan abu ɗaya wato ZEEYAD, you told me that ZEEYAD ya mutu da daɗewa, why then kuma kullum maganar ki bata wuce wa akan sa, i thought kin tsane sa ne kasancewar shi aka fara haifa and shine zai zamto sarki, why then yanzu da ya mutu ba zaki saurara da maganar sa haka nan ba?" ya ƙarashe cike da takaicin halin mahaifiyar tasa. Cike da fusata ta fizgo shi yana fuskantar ta tace "You fool, ce maka nayi guduwa yayi da ƙafafuwan sa maybe yana mace koh a raye, muddin ina da yaƙinin ya mutu mai zai kai ni tada hankali na kullum akan sa, shekaru goma kenan da 6acewar sa, sai dai har yanzu na rasa dalilin da ya sanƴa hankali na ya kasa kwanciya akansa, dukda cewa boka na ya daɗe da sanar min da cewar ZEEYAD ya mutu sai dai har yanzu zuciya ta ta kasa yarda da hakan." "Well then i have had enough of all this nonsense Ummie, maiyasa ke kullum zuciyar ki babu abinda ke cikin ta sai sharri, ZEEYAD bai tauye miki komai ba a cikin gidan nan but sai da kika bi dukkanin wata hanƴa da zaki bi na ganin kin raba shi da farin cikin shi, how then kike tunanin zaki kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kullum bayan munanan abubuwan da kika aikata?, ina baƙin ciki sosai na ganin duk sabida ni kike wannan haukan dan ganin kawai na zamto shugaba a wannan yankin, tayaya dama kike tunanin zaki zauna cikin kwanciyar hankali bayan kin sanƴa wani ruhi cikin baƙar wahala...?" Marin da ta tsinka masa ne yasa shi saurin haɗiye maganar sa bai iya ƙarasar wa ba "How dare you hun, how dare you a matsayi na ta mahaifiyar ka kake faɗa wa wannan maganar?." "Well am even ashamed to call you my own mother, i wish i can change you" ya faɗa cikin ƙunar rai. Sosai take mugun takaicin halin YAZEED, sam bataso halin sa ya kasance a haka ba, dah ace ana canza hallayyar mutum, dah babu abinda zai hana canza sa da Sooraj, taso ace YAZEED ne ke da muguwar zuciya irin ta Sooraj, sai dai kash akayi rashin sa'a yafi mai martabar ma kyawun zuciya. "And babu tantama kece sanadiyyar 6acewar ZEEYAD, and i know that kinsan inda yake kuma kinsan cewa yana raye, tell me Ummie ina ɗan uwa na yake?." "You're talking nonsense, i told you ZEEYAD ya daɗe da 6ata, am definitely sure zuwa yanzu dabbobin jeji sun daɗe da yin kaca-kaca dashi." A tsawace yace "You're lying Mother, just tell me the truth, kinsan inda ZEEYAD yake don't you, indai har bakisan inda yake ba kuma baya raye, maiyasa kullum maganar ki akansa take farawa ta kuma ƙarewa indai har ba tsoron dawowar sa kike ba?." "Don't you dare try to challenge me." "Am not challeging you, i know that kinsan inda yake, you're just hiding the truth, aren't you?." "Ka haukace ne komiye YAZEED?, i told you bansan inda ZEEYAD yake ba sannan bansan komai akan 6atar sa ba, why don't you trust me?." "Trust, you want me to trust you, why should i trust someone like you?." "Am your Mother." "You are not my Mom, kin haife ni ne kawai but baki yi min tarbiyyar da zai sanƴa na kira ki Uwa ta ba, i just wish that *QUEEN MOTHER* tana raye har yanzu, itace uwata ba ke ba" ya faɗa cikin mummunar 6acin rai. Kallon ta yayi yanajin zuciyar sa na mugun ƙuna kafin kuma ya fice daga wurin kamar zai tashi sama. Da kallo ta bishi tanajin mugun taƙaicin hali irin na YAZEED, she wonders ma anƴa ba'a canza mata shi ba kuwa, sam ba haka taso hallayyar sa su kasance ba. ****************** *TWO WEEKS AFTER* _________"Umma ni fah gaskiya nayi kewar ku sosai am coming over kawai naga DEENAH." "Kai dai Jafar in banda abin ka kwata-kwata yaushe ne ya rage mu dawo ma, da zaran ƙanwar taka ta gama samun sauƙi zamu tattaro mu dawo mai kuma zamu tsaya jira?." "Amma Umma..." "Kaga ni banason wani dogon surutu dan Allah, tunda nace ba zaka zo ba ina nufin kada kazo ɗin." "Shikenan toh Umma tunda kin faɗi haka, ina DEENAH fah?." "Sun fita chan wurin motsa ƙafa basu dawo ba." "Umma kince bata magana koh?." "Kwarai hakane Jafar." "Toh dan Allah Umma inaso na kasance mutum na farko da zai fara jin muryar ta idan ta fara magana." "Insha Allah ɗan albarka." "Ni zan ajiye waya Umma, anjima zan kira." "Toh shikenan sai anjima, Allah yayi maka albarka." Da "Ameen" ya amsa kafin ta yanke kiran. ****************** _________"Are you sure that your Mom isn't hiding something? Cewar ZEEYAD da ya gama daburcewa da rashin ganin DEENAH. Kallon sa Jafar yayi yace "Am suspecting so, amma koma dai menene it wouldn't be something serious." Shiru yayi yana karkaɗa ƙafa dan kuwa bayajin zai iya ƙara koh da kwana ɗaya ne ba tare da ya sanƴa DEENAH cikin idanun sa ba. "Am sorry but i guess i can't continue living so empty like this, i need to see her." "Mai kake shirin yi?." "Am going there." "What?." "Yes" ya faɗa yana miƙewa tsaye. "But ka manta da sharaɗin da Umma ta gindaya maka ne?." Shiru yayi kafin kuma yace "Ban manta ba, but my mind would never be at ease without knowing halin da take ciki." "No you can't do this, babu abinda hakan zai janƴo sai fushin Umma akan ka." "Look am sorry but i can't do this anymore" ya faɗa kafin kuma ya fice daga office ɗin. Baki sake Jafar ya bisa da kallo "He is madly inlove with DEENAH" ya faɗa kafin kuma shima ya tashi yana bin bayan sa. ******************* _______Safa da marwa kawai yake yi a cikin ɗakin nasa, so boring haka yakejin komai, he can't find Happiness anywhere, jin sa yake so very empty all he wants and craves for shine ya sanƴa DEENAH a idanuwan sa, hakan yasa shi yanke shawarar zuwa Egypt a gobe sabida he can't wait any longer. Sai dai his biggest fear shine sam bai shirya tunkarar wannan ƙasar da rabon sa da ita ten years ba, ji yake kamar ya fasa tafiyar sakamakon zuciyar sa da ta kasa samun sukuni a duk sadda ya tuno da cewa ƙasar sa ta haihuwa zashi, but idan ya tuno da cewa farin cikin sa na chan duk sai yaji babu abinda yake buƙata kamar ganin sa a ƙasar. Kan couch ya zauna tare da janƴo Laptop ɗin sa yayi wasu ƴan danne-danne kafin kuma ya rufe ta ya ajiye. Wasar sa dake kan center table ya ɗauka tare da yin typing message ya tura ya ajiye ta. Runtse idanun sa yayi sakamakon jin sa da yake very remorsed. Huci ya fesar tare da wiping face ɗin sa kafin a hankali ya furta "Yaa Rabb I need you." *THE NEXT DAY* _______Ƙafar sa da ya sanƴa cikin ƙasar ne ya sanƴa dukkanin wata tsika ta jikin sa tashi. For the first time after 10yrs, he is now temporary back to his Birth country. Wata iriyar iska mai haɗi da sanƴi ce yaji ta huro shi, hakan ya sanƴa shi shaƙar iska haɗi da furzar da ita yana lumshe idanu. Baƙar shade ɗinsa ya ciro ya maka a face ɗinsa tare da gyara zaman coat ɗin jikin sa yana sake tamƙe fuska kai kace wani babban maƙiyin sa ya hango tafe. Wasu mutane ne suka tunkaro su cike da girmamawa kowanne cikin shigar baƙar suit fuskar su manne da baƙar shade. Iso sukayi masa izuwa wasu tsala-tsalan motoci masu masifar ɗaukar hankali tare da buɗe masa ya shiga suka rufe. Duk shigewa cikin motar sukayi kafin kuma su jata tare da barin cikin airport ɗin. Wata katafariyar hotel mai matuƙar tsada da kyau aka kai sa tare da yi masa iso zuwa ciki cike da girmamawa kai kace zasu kife ƙasa ne, kafin kuma ayi masa iso har izuwa masauƙin sa. Sai da yayi wanka ya huta sosai kasancewar dare ne ya sanƴa shi fitowa Balcony ɗin apartment ɗin nasa yana dafa ƙarafunan. Sosai yake ƙarewa yanayin city ɗin kallo daga inda yake tsaye, tabbas ba ƙaramar cigaba aka samu a ƙasar nan ba, daga ganin yanayin wannan city ɗin kasan suna samun nasarori sosai. Ɗan ta6e baki yayi kafin yace "So haka mutumin nan yake aiki?." Kafin kuma ya yatsine fuska yana cize baki. Iska ya shaƙa ya fesar kafin kuma ya koma cikin ɗaki. Sosai ya sake yin danne-dannen sa cikin Laptop kafin kuma ya nemi lafiyar gado, zuciyar sa cike fal da tunani dama kuma murnar zai ga farin cikin sa gobe. *********************** __________Da sassafe ya shirya, inda ya haɗe cikin baƙar shadda mai ɗinkin armless, wanda yayi matuƙar amsar jar fatar sa tare da yi masa bala'in kyau, fuskar sa dama kuma baƙar sumar kansa da ta sha gyara sai sheƙi suke, kasancewar Jafar ya turo masa address ɗin asibitin yasa ba tare da 6ata lokaci ba ya fice daga ɗakin sai tada ƙamshi yake. Sabuwar motar da ya saya wanda already an riga da an kawo masa ita ya shiga tare da yi mata key ya bar cikin hotel ɗin. Tracing location ɗin da Jafar ya tura masa yayi wanda ya kai sa har cikin asibitin, kafin ya nemi parking space yayi parking. Jinsa yake wani iri sosai, Face-Mask ɗinsa ya sanƴa tare da ɗaukar glass ɗin sa ya maka a fuska, kafin ya sanƴa hannu ya buɗe murfin motar ya fito yana sake shan ƙamshi. Tsayawa yayi tare da ƙarewa farfajiyar asibitin kallo kafin kuma cikin tafiyar sa mai haɗi da muguwar ƙasaita ya nufi ciki fuskar nan tasa tamau. Wani Nurse ya tsaida kafin kuma cikin muryar larabci ya tambaye sa ward ɗin da akayi admitting ɗin DEENAH. Kwatance yayi masa kafin kuma yayi masa godiya tare da bin hanƴar da ya nuna masa. Tafiyar 10mins ce ta ɗauke sa zuwa wurin dan haka kutsa kai yayi kawai ciki yana wani cika haɗi da batsewa ganin kowa na bin sa da kallo. _"Toh wannan idan na cire mask ɗina suma zakuyi kenan?"_ ya faɗi hakan a ransa kafin kuma ya ɗan ja ƴar ƙaramar tsaki. "Fifth flour, Room 106" ya faɗa a hankali yana bin matattakalar benin. Isowar sa flour ɗin yaja ya tsaya kafin kuma a hankali ya shiga takawa yana bin numbern kowane room da kallo. Ja yayi ya tsaya, Room 105 ya gani a rubuce a ta hannun damar sa, zazzafar iska ya fesar yace "That is the room on my left hand side" ya faɗa yana juyawa ya kalli saitin room ɗin. So, yau Finally zai sake sanƴa MADEENAHn sa a idanun sa. Murmushin da bai san da zuwan ta ba yayi kafin ya tunkari ƙofar yana kai hannu da niyyar murɗa handle ɗin. "Careful" yaji an faɗa ana tunkaro inda yake tsaye. Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke idanun sa, kafin kuma yayi saurin sake maida duban sa kansu idanun sa na sauƙa a kanta. He became speechless for some moments, ganin ta tare da wani hannayen sa riƙe a kafaɗun ta da alamu dai taimaka mata yake wurin tafiya. Kauda kai yayi tare da runtse idanun sa, sabida he can't believe abubuwan da idanun sa ke gane masa, No wannan ba MADEENAHn sa bace, ba zata ta6a bari wani ya ta6a jikin ta ba, koh da kuwa da sunan taimaka mata yake sonyi ɗin. Bai san da ƙarasowar su ba sai ji yayi ana yi masa magana "Excuse us please" yaji wannan saurayin ya faɗa. Juyowa yayi yana sauƙe idanun sa cikin na saurayin, wanda dukkanin su wata iriyar shock ta ziyarce su lokaci guda, ZEEYAD ne yayi saurin ɗauke idanun sa yana sauƙe su cikin manƴan idanun ta da ta kafe sa dashi tana kallo. Saurin basu hanƴa yayi kafin wannan Saurayin ya sake ta tare da buɗe mata ƙofar. Kallon sa tayi tare da sakar masa murmushin da ya kusa tarwatsa zuciyar ZEEYAD kafin kuma ta shige ciki. Kallon ZEEYAD saurayin yayi yace "Nan kakeson shiga?." ZEEYAD da zuciyar sa ke mugun yi masa zafi idanun sa sun fara canza launi ba tare da ya kula shi ba ya bar nan wurin yana tafiya kamar zai tashi sama yanajin wani irin abu mai ɗaci a maƙoshin sa. *Yawan Comment, Yawan Typing* *_ZEEYAD FANS GROUP, kunga kwana biyu na lafa koh😌?, dan bana removing yasa kuka koma turomin stickers daga nan kuma kuyi miƙit wai ku ga masu wayo, Toh tsaf nake sane daku harda masu karantawa suyi shiru duk kun kusa jin ku a waje insha Allah_* *MHIZZ JIDDHERR................✍🏽* [8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *030...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*BANYI EDITING BA*_ _____________"Abhi am serious i saw him, he was standing right infront of me, i just don't know how i lose sight of him, Abhi ka yarda dani naga ZEEYAD with my own eyes." Kallon Sadeeq Abhi yayi kafin yace "Ya kake tunanin zan yarda cewa ZEEYAD ka gani?, indai har shi ne wanda ka gani mai zai hana sa zuwa garemu bayan dawowar sa daga inda yaje?." "Abhi believe me, ka yarda dani i really do saw him, fuskar sa ba zata ta6a 6acemin ba, he is ZEEYAD." Shiru Abhi yayi yana jeka ka dawo a cikin falon yana jin maganar Sadeeq ɗin kamar almara, koh shi kan shi Abhi ya cire ran idan ZEEYAD na raye har yanzun ganin har izuwa wannan lokacin bai bayyana ba. "Abhi ka yarda dani." Shiru yayi tare da kallon Sadeeq yace "Na yarda da kai, amma indai har shine wanda ka gani dagaske, maiyasa kayi gangancin barin sa ya tafi bayan kuma a wuri ɗaya kuke ba tare da kayi masa magana ba?." "Abhi wannan shine kuskuren da nayi wanda har yanzu nakejin haushin kaina akan hakan, but duk inda ZEEYAD yake nayi alƙawarin nemo shi, sabida lokaci yayi da yakamata ya dawo ga mahaifar sa yanzu." ************************* __________Zubewa yayi akan lallausar couch ɗin dake falon yana maida numfashi. Idanu ya runtse yana komawa da baya ya kwanta inda maganganun Umma suka shiga yi masa yawo a kwakwalwa. "No!" ya furta da ƙarfi yana watsar da dukkanin abubuwan dake kan center table ɗin gaban shi. Sosai yake fidda huci mai zafi kamar ransa zai fito "Why, how could you do this to me, i love her with all my heart and soul, how could you" ya faɗa da ƙarfi yana buga hannun sa jikin table ɗin inda glass ɗin ta tsage tare da tarwatsewa. Bai damu da hannun sa da ya yanke yana tsiyayar da jini ba, dan kuwa zafi da raɗaɗin da yakeji a cikin zuciyar sa ya zarce tunanin mai tunani, shi kaɗai yasan mai yakeji, shi kaɗai yasan iriyar wahalar da yake sha, ransa a mugun 6ace yake, ji yake komai ya sunce masa zuciyar sa a mugun cunkushe take duk sabida raba sa da abar ƙaunar sa da akayi, bai ta6a sanin menene so ba sai akan DEENAH, idan aka cire irin soyayyar iyaye toh itace first love ɗinshi, akanta ya fara son wata ɗiya mace, ya sha haɗuwa da mata iri-iri sai dai duk cikin su babu wacce ya kula, ya tanada wa DEENAH kanshi tsawon shekaru, bai ta6a kawo cewa zai iya rasa ta ba, gashi yau mutuwa bata raba su ba amma mahaifiyar ta ta raba su, mahaifiyar ta tayi breaking heart ɗinsa tasa shi cikin halin ƙunci da wahalar da bai ta6a shan ta ba, ji yake wahalar da yasha a baya bai kai wanda yake sha yanzu akan DEENAH ba, sabida ya kwallafa rai sosai akanta shiyasa yakejin zafin rashin ta fiye da komai da za'a iya kwatantawa, bai ta6a furta mata cewa yana sonta ba ganin kamar hankalin ta ba'a kansa yake ba, but yana sonta so dearly fiye da komai na rayuwar sa a yanzu, ba zai ji ciwon rasa dukiyar sa ba kamar yadda yakejin ciwon rasa DEENAH a yanzu, gani yake tarin dukiyar da ya tara bayida wani amfani dan kuwa sun kasa samar masa farin ciki, bai rasa komai na rayuwa ba sai dai ya rasa abar da zata kawo masa farin ciki. Sosai idanun sa dama dukkanin jikin sa sukayi jaa tsabar 6acin rai, abin ka da jar fata. Miƙewa yayi da kyar yana layi ya wuce cikin bedroom tare da faɗawa kan bed ɗin idanun sa na rufuwa. ************************ _______A hankali ya shiga buɗe nannauyar idanun sa da suke matuƙar zugi yawa wanda aka zuba masa barkono a ciki kafin kuma ya sake maida su ya rufe yanajin haushin farkawar sa daga baccin, baiƙi ya dawwama cikin barci ba har abada muddin hakan zai mantar dashi damuwar da yake ciki. Ya ɗau almost ten mins a haka kafin kuma ya buɗe idanun sa yana mai miƙewa zaune. Kansa dake yi masa mummunar ciwo kamar zata tsage ya riƙe yanajin duniyar na yi masa juyi. Da kyar ya samu ya lallafa ya faɗa bathroom. Wanka yayi ya tare da ɗaura alwala ya fito. Shiryawa yayi cikin farar jallabiya sannan ya tada sallah. Bayan ya idda tare da yin adhkar ne ya miƙe tare da komawa falon. Inda Telephone ke ajiye ya nufa tare da danna yin kira ya dawo cikin falon. Ba'a ɗau lokaci ba ma'aikatan cikin hotel ɗin suka shigo ɗaya ɗauke da tray ɗin abinci a hannun sa, ɗaya kuma ɗauke da kayan shara. Amsar order sa yayi tare da komawa ɗaki. Zama yayi akan sofa ɗin ɗakin tare da buɗe tray ɗin abincin. Abincin ya zubawa idanu yana kallo, abinci ne na ƴan ƙasar su wanda bansan sunan sa ba. Rabon sa da yaci irin abincin nan tun Ummin sa na da rai, it was his favorite meal, ganin abincin ya sanƴa shi tunawa da ita, itace take zaunar dashi ta bashi abincin a baki koh da kuwa baiso hakan ba zata tilasta masa yaci, sai dai kuma gashi yau shi zai ciyar da kansa. Hannu ya kai ya ɗau spoon kafin ya kai cikin bowl ɗin dake ɗauke da wata miya wacce bansan ta mecece ba tare da ɗebo ta ya kai baki yana yin bismillah. Ji yayi abincin salam babu taste a bakin shi dan haka cokali ɗaya kawai yaƙara yana maida ta ya rufe. Juice ya tsiyaya a cikin cup ya sha kaɗan tare da barin sauran kafin kuma ya ɗau tray ɗin abincin yana fitarwa falo. Ma'aikatan hotel ɗin ya kira suka zo suka fita da tray ɗin. Zaune yake shiru idanun sa da sukayi masa nauyi a lumshe ya rasa meke yi masa daɗi. Haka ya kai almost 15mins yana nazari, kafin kuma a zabure ya buɗe idanun sa yana miƙewa tsaye. "Grandma?" ya furta, kafin kuma ya zuri makullin motar sa yana yin hanƴar ficewa da sauri. ******************** ________A gaban wani tsohon gida yayi parking motar sa yana mai fitowa daga ciki. Kallo tsaf ya ƙarewa gidan, wanda ya kasance babba ne sosai, tabbas gidan ne dan kuwa bai ta6a zatan zai iya gane hanƴar ta ba. Ya kai 5mins yana kallon gidan da yake tunanin babu kowa ganin ta garƙame da ƙatuwar kwaɗo wacce har kamar ta fara yin tsatsa ma. Wucewar wasu samari guda biyu ya gani dan haka saurin tarar su yayi, bayan sun gaisa ne kuma cikin harshen larabci yake tambayar su inda mutanen wannan gidan suka je. Ɗaya daga cike ne yace "Mutanen gidan nan ai sun daɗe da tashi." "Koh zaku iya faɗamin inda suka koma?." "Ehto naji dai kamar ance mai Martaba Sarki Abbas ne yazo ya ɗauke su tare da maida su chan cikin fada." Zuciyar ZEEYAD ne yayi wani irin mugun faɗuwa jin an ambaci sarki Abbas, inda kuma tsoron abinda ya sanƴa shi maida kakannin sa MASARAUTA ya darsu masa. "But...zaku iya faɗamin tun yaushe ne barin su nan?." "Ehto, zai iya kaiwa shekaru takwas zuwa bakwai haka." Idanu ya zaro da jin abinda suka faɗa, kenan hakan na nufin 6atar sa ya sanƴa mai Martaba maida kakannin sa cikin MASARAUTA, toh mai zaiyi musu, mai yake nema dasu, he just hope ba wani abin cutarwar yayi musu ba. Ganin yayi shiru yana tunani ya sanƴa samarin yin tafiyar su. "That wretched Man" ya faɗa angrily kafin kuma ya koma cikin motar sa ya jata a fusace yana barin wurin. Sosai ransa ya 6aci he wonder mai Sarki ke nema dashi da har zai biyo iyayen mahaifiyar sa ya maida su custody ɗinsa dan kawai ya 6ace ba'a gansa ba. But a yanzu yana ganin it's high time da yakamata ya koma cikin MASARAUTAR sannan kuma yayi maganin duk wani tantiri da ɗan iskan dake jin kansa cewa shi ɗan iskan gaske ne, he would make sure ya koyawa kowanne daga cikin su hankali ta haka ne kaɗai zaiji ransa ya ɗan kwanta da irin abubuwan da sukayi masa, ya za6i ya ajiye batun wata DEENAH a gefe muddin yanason yayi achieving goals nasa, dan sunci galaba akansa wancan karon ba hakan ke nufi zai sake basu wani damar bane yanzu har ma su samu nasarar ta6a kakannin sa, ba wai dan ya manta dasu bane ya sanƴa shi baije wurin su tun farko ba, sai dai yayi hakan ne dan yin nesa da azzaluman da suka cika PALACE ɗin nasu, and now lokaci yayi da zai nunawa kowannen su wurin zaman sa. Da wannan tunanin ya ƙarasa Babban hotel ɗin. Bathroom ya shige ya sake iyo wani wankan ya fito. Gaban mirror yazo ya zauna tare da gyara baƙar sumar kansa sai tada ƙamshi da sheƙi take. Zuwa yayi ya buɗe closet ɗin ɗakin ya fito da wata kwali mai ɗan faɗi. Ajiye ta yayi akan gado sannan yayi unwrapping nata yana buɗe ta. Take wata baƙar suit dama kuma complete abubuwan da za'a yi dressing ɗin dashi ya bayyana. Ciro ta yayi yana ƙare mata kallo, shi kanshi yasan ba ƙaramar kuɗi ya 6arar akanta ba, dan haka ba tare da 6acin lokaci ba ya shirya cikin ta. Komai baƙi ne kama daga kan kayan jikin sa zuwa kan tsadaddar takalmin sa, except fatar jikin sa dama kuma rigar ciki da yakasance fari. Gaban mirror ɗin yazo yana gyara zaman coat ɗin jikin sa, shi kansa yasan bai ta6a yin kyau kamar wannan rana ba dukda kuwa fuskar sa tamau take babu fara'a koh kaɗan. Feshe jikin sa yayi da turarukan maza masu kyau da matuƙar tsada sai tada masifaffen ƙamshi mai kwantar da rai yake, sannan ya ɗauka baƙar shade tare da mannawa a fuskar sa. Sosai yayi looking hot a wannan shiga, dan kuwa dama shi ɗin ba baya bane wurin iya ɗaukar wanka ga kuma iriyar kyakkyawar haliitar sa da ta dace da shigar sa, everything is perfect about him, except one thing wato *FARIN CIKI* Card, waya dama kuma makullin motar sa ya ɗauka yana ficewa daga ɗakin. Motar sa ya shiga tare da janta ya bar cikin hotel ɗin. Tafiya mai nisa yayi kafin ya iso wani kamfanin saida motoci na ɗaukar hankali da ƙece raini. Parking motar sa yayi yana fitowa. Wani mutumi ne ya tunkaro shi ba tare da 6ata lokaci ba sukayi musabaha kafin ZEEYAD yace "I come to claim what i ordered." "This way Sir" ya faɗa yana nuna masa hanƴa nan suka jera har zuwa cikin wani ƙaton ɗaki da za'a iya kiran sa da garage, wanda ke ƙawace da manƴa-manƴan zafafan motoci na masu manƴan ragamar mulki. Leading ɗinsa yayi zuwa wurin wata tsadaddiyar baƙar *Bugatti la voiture noire* sai sheƙi da ɗaukar hankali take. "Here it is sir" cewar mutumin cikin girmamawa. Kallon motar ZEEYAD keyi kafin kuma yace "Alright, here is my card, ka ɗau haƙƙin ka and return the card to me." Amsa mutumin yayi tare da furta "Sure, Sir." Yaran sa mutumin ya ƙira kafin su fito da motar waje tare da sake kwaskware ta da yin sauraran abubuwan da yakamata. Takardun motar dama kuma key ɗinta mutumin ya bashi haɗi da card ɗinsa. Amsa yayi tare da yin godiya, sannan ya buɗe motar, cikin motar kaɗai abar kallo ce. Addu'ar yayi tare da shigewa yana rufo ta, kafin kuma ya tada ta yana ficewa da gudu daga cikin Company ɗin. Tafiya yake yana duba location ɗin wayar tasa har ya iso Ungwar da PALACE ɗinsu yake. Tabbas ya gane nan wurin daga nan zai iya kai kansa har cikin PALACE ɗin. Sosai yaga arear ta canza masa an sake gyara ta sosai kai kace duka ungwar ce cikin PALACE ɗin tsabar haɗuwa da tsaruwar ta. Ɗan sassauta gudun motar tasa yayi lokacin da ya shigo layin da ƙatuwar PALACE ɗin tasu take. Gabaɗaya layin cike take da jami'an tsaro koh ta ina sai patrol suke, inda girman PALACE ɗin ya fara daga farkon layin har izuwa ƙarshen ta ne, tsayawa faɗin haɗuwa dama kuma tsaruwar ta 6ata lokaci ne. Kallo ya ƙare musu tundaga nesa, lallai ba ƙaramin wulaƙanci aka ƙaro ba a wannan MASARAUTA. Kallon tafkekiyar gate ɗin MASARAUTAR wacce ke facing inda yake yayi, kafin kuma ya ɗau Mask ɗinsa tare da sanƴawa, yana mai ɗaura seat belt ɗinsa tare da tightning ɗinsa sosai. "Let's see if you can try and stop me" ya faɗa lokacin da yake ƙure dukkanin iya speed ɗin motar ya nufi hanƴar ƙofar. Jami'an duk watsewa sukayi ganin yadda motar ta iyo kansu da bala'in gudu kamar zata tashi sama. Ɗan murmusawa yayi yana maida duban sa kan hanƴa tare da furta "Rascals." At high speed yazo tare da buge gate ɗin PALACE ɗin yana shigewa ciki. Ƙarar da hakan ya bayar ne ya janƴo hankalin mutane da dama dake ta kai kawo a cikin MASARAUTAR izuwa inda abin ya faru. Da kyar ya samu yayi controlling ɗin motar yana zuwa ya buge wani Statue dake cikin tsakiyar PALACE ɗin kafin motar ta tsaya. Babu abinda kake gani sai tashin hayaƙin da ya cika wurin sakamakon irin tuƙin da yayi wa motar dama kuma abinda ya buga. Kan kace miye dogarai sun taru a wurin inda kowa ya saita kwari da bakar sa izuwa saitin motar dan ganin wane mai son ƙare rayuwar sa a gidan yarin ne yayi aika-aikar nan. Haka ma jami'an tsaro dukkanin su suka zo suka zagaye motar riƙe da bindigogin su suna jiran fitowar wanda ke cikin motar. Ta cikin tinted glass ɗinsa yake kallon su, hakan yasa shi sakin murmushi mai ɗan sauti ganin duk yadda sukayi ready ɗin harbi suna jiran fitowar sa. "Silly guards" ya faɗa hannayen sa kan steering ɗin motar yana ticking. Babban daga cikin jami'an aka ɗaukowa micro-phone nan ya fara magana ta yadda na cikin motar zai ji da kyau "Koma wanene kai, kayi gaggawar miƙa wuya ba tare da ka wahalar da hukuma ba, sabida mummunar laifin da ka aikata, ka miƙa wuya yanzun nan" ya faɗi hakan har sau uku sai dai wanda ke cikin bai fito ba. Kallon ɗaya daga cikin yaran sa yayi kafin yayi masa alama da kai akan yaje ya duba motar. Ƙara saita bindigar sa yayi yana tunkarar motar. Hannu ya kai tare da buɗe motar inda bai kai ga ganin wanda ke ciki ba, sai jinsa yayi a yashe a gefe sakamakon wani irin blow da aka bashi da ƙafa, hakan kuma ya sake sanƴa sauran saurin maida duban su kan motar baki sake suna sake saita bindigar su da kibiyar su. Farar ƙafar sa da tasha baƙar tsaddadar takalmi ya fara zurowa, kafin ya dafa murfin motar da hannun sa da tasha tsadaddiyar diamond ring sai walƙi take kafin kuma ya idda fitowa fuskar nan tasa tayi wani irin murtuƙewar da bai ta6a yi mata ba. Tun daga ƙasa suka fara kallon sa har izuwa kan ɗaurarriyar kyakkyawar fuskar sa. Maida murfin motar yayi ya rufe ta kafin ya zaga zuwa gaban motar yana kallon inda ya bige da ta lotsa kafin ya maida duban sa kan statue ɗin da ta faɗi ƙasa ta 6antare gida biyu. Motar tasa ya shiga shafawa tare da furta "Oh my poor *Bugatti la voiture noire*." "Hey" yaji an daka masa tsawa hakan yasa shi saurin runtse idanu yana ayyana irin hukuncin da zaiyiwa koma wane mai ru6a66en bakin ne wannan. "Who the hell are you, and where did you come from?" yaji an sake jefo masa tambaya. Sosai yaji tambayar ta 6ata masa rai, babu makawa idan ya kama mai maganar nan ya fara gurza bakin sa a ƙasa sai yayi nadama. Juyowa yayi garesu yana zura hannaye cikin aljihu, kafin kuma ya lankwasar da wuya gefe yace "Wane mai dolphin mouth ɗinne yayi maganar nan a cikin ku?." Duk kallon juna sukayi suna mamakin iriyar tantiran ci da isa irin na gayen nan, wanda zagaye yake da bindigogi da kibiyu ta koh ina amma har yana da bakin da zai iya zagin wani a cikin su. "Sir seems like wannan fah baisan a inda yake ba" cewar ɗaya daga cikin dogaran. "Surrender yourself, now" cewar babban nasu. Maida duban sa ZEEYAD yayi kansa yace "Ohh i see, kaine kake magana, i got you." "Soldiers, get ready to shoot indai har ba zaiyi surrending kanshi ba." Ta6e baki ZEEYAD yayi yana mai gyara zaman glass ɗin idon sa. Duk sake shirin harbi sukayi suna kallon ZEEYAD dake tunkaro su. "Stay right there or else i will shoot." "Really, what are you waiting for then?" ya faɗa still yana tunkaro su ba tare da ya tsaya ba. "What the hell is going on here?" ta faɗa cikin tsawa. Dakatawa ZEEYAD yayi lokacin da yaji amon muryar ta cikin kunnen sa. Duk buɗa mata sukayi, tsaye take cikin doguwar rigar ta dake jan ƙasa bayin ta na take mata baya. Idanun ta ne suka sauƙa akan murɗaɗɗen saurayin dake tsaye a gaban ta inda zuciyar tayi wani irin faɗuwa tana kallon sa. "My queen, he caused some damages to the PALACE while driving recklessly, sannan babu wanda ya san shi koh ya san daga inda yake, ya aikata mummunar laifi ya zama dole a hukunta shi koh shi waye." Zuciyar ta ce ke ta up and down still idanun ta a kansa. Takowa ZEEYAD da zuciyar sa ta gama munana sabida ganin ta da yayi zuwa gaban ta, kafin kuma ya saki wani irin killer smile yace "QUEEN NASEEBA." Dum-dum haka taji zuciyar ta ta bada wata iriyar mummunan sauti tana zaro manƴan idanun ta. Cikin tsukewar face yace "It's been Long." Cikin rawar harshe da mummunar faɗuwar gaban da take ciki tace "Z...Z...ZEE...ZEEYAD?." Slight murmushin da ya saki ne yasa ta gasgata abinda tunanin ta ya bata, sai kuma a lokacin ne kammanin sa suka dawo mata cikin kwakwalwa. "ZEEYAD?" Ta sake faɗa idanun ta kamar zasu faɗo daga ramin su. Da sauri ta kai hannu zata shafi fuskar sa sai dai wani mugun kallon da ya watsa mata da ganin yanayin fuskar sa ne yasa ta saurin tsaida hannun nata tana sauƙewa ƙasa. Duk da kallo dogarai dama securities ke bin juna dashi, sakamakon basu fahimci abin dake faruwa ba. "ZEEYAD" ta sake faɗa yayin da wani irin farin ciki dama kuma tsoro suka darsu mata duk lokaci guda. Sake tsuke face yayi ganin yadda take ta bin sa da kallo kamar zata haɗiye shi. "Surprise, surprise Naseeba" ya faɗa cikin calm voice ɗinsa wanda ya sake gigita Sarauniya Naseeba.. Saurin juyawa tayi ga dogaran tace "Put your guns down now, he..he is the lost prince" ta faɗa. Mamaki ne ya cika mutanen wurin baki ɗaya, inda kuma baki sake suke bin ZEEYAD da kallo. "Put your weapons down...now" ta sake faɗa da ƙarfi, hakan ya sanƴa su fara sauƙe makaman su, kafin ta juyo ga ZEEYAD cikin murmushi tace "My Sweet Boy..." tana kai hannu zata shafi fuskar sa. Saurin riƙe hannun ta yayi cikin kakkausar murya yace "Not anymore Naseeba" ya faɗa tare da sakin hannun nata yana ra6a ta ya wuce. Sosai ranta yayi mugun 6aci sakamakon dizga ta da yayi gaban ɗumbin bayin ta, juyawa tayi tana kallon bayan sa, kafin ta bisu da kallo ta ƙasan ido cike da masifa kuma tace "Get back to your work now." Nan duk suka shiga watsewa kowa na kama hanƴar sa, inda dayawa ke tattauna akan Yarima ZEEYAD da ya 6ata shekaru goma da suka wuce ace ya dawo. Cikin takun ƙasaita irin tasa ya ƙaraso babbar ƙofar shiga cikin fada wanda shima ba ƙaramin ƙawata aka sake yi ba. Tundaga nesa dogaran suka sanƴa dogin takoban su tare da toshe hanƴar. Ta6e baki ZEEYAD yayi dan kuwa yaga kamar har yanzu wasu dokokin na cikin MASARAUTAR are still intact. Ja yayi ya tsaya yana kallon su yadda suka wani ƙame wuri ɗaya basa kwakkwaran motsi duk a cikin sunan gadin fadar sarki. Kallo ya ƙare musu tsaf tabbas ƙarfafa ne sai dai koh kaɗan basu bashi tsoro ba. Kan ya buɗi baki yayi magana wani dogari yayi saurin ƙarasowa wurin yana yin wurin masu tsaron tare da raɗa wa ɗaya daga cikin su abu a kunne. Zaro idanu yayi yana kallon ZEEYAD dake tsaye yana kallon su. Ƙarasawa yayi wurin ɗayan nasa ya faɗa masa abinda aka faɗa masa a kunne nan duk suka sake maido duban su kanshi suna kallon sa. Kauda kai yayi yana yatsine fuska kafin kuma a buɗe masa doguwar ƙofar cikin girmamawa kuma suka ce "We apologise for our misdeeds the great prince." Kallon su yayi tsaf kafin kuma ya ɗaga ƙafarsa tare da takawa zuwa bakin ƙofar ba tare da ya shige ba, yana mai bin katafariyar fadar da girman ta kaɗai ya isa a gina ɗakuna huɗu a ciki banda tsaruwar ta da ba'a iya cewa komai. Doguwar ajiyar zuciya yaja idan ya tuna cewa zai ga mahaifin sa, sai dai wannan karon ba zai lamunci duk wani rashin mutunci koh rashin daraja daga gareshi ba. Idda shigewa yayi kafin su maida ƙofar su rufe, shiru fadar take babu kowa a cikin ta. Takawa yayi ya ƙarasa zuwa tsakiyar falon, kafin kuma cikin ɗagun murya ya fara kiran sunan "Grandma!." ************************ Zaune yake kamar kullum gaban hoton ta yana kallo. Tun safiyar yau yakejin wata iriyar faɗuwar gaba wacce ba zai iya kwatanta yadda yakejin ta ba. Kamar daga sama ya jiyo muryar da ya sanƴa shi ware idanun sa daga lumshe su da suke, inda kuma ya darsar masa da wata iriyar faɗuwar gaba, amon grandma da ya jiyo ne ya sanƴa sa miƙewa tsaye yana maida duban sa zuwa bakin ƙofa. ZEEYAD bai damu da mutanen da suka fiffto suna kallon sa ba, sakamakon duk sabbin fuska ne a wurin sa, babu abinda yake kira sai "Grandma." "Grandma, where are you?." Duk da kallo suke binsa, suna mamakin daga inda ya fito. Miƙewa yayi daga kan kujerar da yake haɗi da ɗaukar kyakkyawar sandar dake taimaka masa wurin tafiya ya fito. Tundaga saman stairs yake hango bayan shi, har ya sauƙo izuwa farfajiyar falon staring at him. Sarauniya Nazeerah da Hafeezah ma fitowar su kenan suna kallon ikon Allah, inda duk suke Allah-Allah suka wanene wannan ɗin. Juyowa yayi yana kiran "Grand..." maganar sa ce ta ƙaƙare sakamakon idanun sa da suka sauƙa cikin na mai Martaba. Ji yayi gaban sa yayi wani irin mummunar faɗuwa, kafin kuma ya haɗe rai tamau kamar wanda yaci guna yana ƙarasowa gaban sa kamar wanda bai san shi ba yace "Tell me...ina ka kaimin Grandma?." Baki mai Martaba ya saki yana kallon haɗaɗɗen saurayin dake gaban shi inda kuma idanun sa suka shiga taro hawaye. Sarauniya Naseeba ce ta shigo cikin fadar sai hure-hure take kamar zata fashe. Sadeeq da yazo sanar wa da mai Martaba cewar yaga ZEEYAD ne shima ya shigo cikim fadar ya tadda abin dake faruwa. "Tell me, where is my Grandma" ya sake faɗa a karo na biyu yana kallon mai Martaba ɗin. "A..are..are you my son?" cewar mai Martaba yana nuna shi da yatsa. Kallon tsaf ZEEYAD yayi masa kafin kuma cikin ƙunar rai yace "Your son, who is that, your son is dead isn't he?." Baki da hanci duka Sarauniya Hafeezah ta saki, she was stunned to death sakamakon abinda idanuwan ta ke gane mata, she can't believe her eyes, she can't believe it sai dai idan a mafarki take, but this can never be true, saurin murza idanuwan ta tayi tana girgiza kai tare da sake buɗe idanuwan ta. "Hmmm, ba mafarki kike ba Hafeezah, dagaske shi ɗin ne dai ya dawo" ta jiyo muryar Sarauniya Nazeerah dake enjoying drama ta gefen ta. Zuciyar ta ce tayi wani irin mummunar bugawa tanajin kanta na juya mata sosai, kamar ta zarce haka takeji. "Tell me, where did you take my grandma to?." Mai Martaba da hawaye suka gama wanke masa fuska ne ya kai hannu da niyyar rungume ɗan nasa sai dai kafin ya kai ga haka ZEEYAD yayi saurin sanƴa hannaye kan ƙirjin sa yana tare shi ba tare da ya bari ya aikata hakan ba. "Who do you think you're old Man?" ya faɗa yana yi masa wani irin kallo. Murmushi Sarauniya Nazeerah ta saki tana kallon Hafeezah dake ta sharce gumi ta gefen idanu kafin ta maida duban ta kan su mai Martaba da ZEEYAD tana cigaba da kallon drama. "ZEEYAD, my Son" cewar mai Martaba yana ƙoƙarin kamo fuskar sa. Ja da baya yayi yana kaucewa riƙon nasa yace "Can somebody please tell me where my Grandma is?." Idanun sa ne suka sauƙa kan Sarauniya Hafeezah da idanun ta ke ƙasa tanajin kamar ba'a duniyar take ba. Ɗauke idanun sa yayi yana sauƙe su kan Sadeeq da ya saki baki yana kallon sa. Gaban sa ya ƙarasa yace "Sadeeq, i know you're a good friend, tell me where is my grandma, kodai this wicked Man here ya riga da ya kashe ta?." Kallon sa Sadeeq yayi jin abinda yake faɗa zaiyi magana ne sukaji ance. "Am alive and healthy Son." Saurin maida duban sa yayi inda maganar ta fito. Wata ƴar tsohuwar mata ce ya gani tsaye cikin shigar ta ta alfarma. Murmushi ne ya su6uce masa nan yaje da sauri yana rungume ta tare da furta "Grandma?." Kansa ta fara shafa hawaye na kawo mata. Sosai ZEEYAD ya rungume ta sakamakon jin zuciyar sa da yayi ta fara yin sanƴi dan ganin uwar mahaifiyar sa. "Grandma, i miss you, i missed you so much" ya faɗa. Kuka kawai Grandma keyi, dan kuwa ba ƙaramin kewar jikan nata tayi ba, rabon ta dashi tun yana ɗan shekara goma, dan haka dole ne tayi kuka sosai irin wanda bata ta6a yi ba. Ɗagowa yayi yana cupping fuskar ta tare da faɗin Grandma are you Okay, tell me how you've been doing?." Kuka kawai take bata iya buɗar baki ta bashi amsa ba hakan ya sanƴa shi sake rungume ta yanajin kamar Ummien sa ya runguma. Mai Martaba kuwa ji yayi kamar an zare duk wata ƙuzarin dake jikin sa, sosai yaji babu daɗin yadda ZEEYAD yayi masa, sai dai koh kaɗan bai ga laifin sa ba, dan kuwa koh da shine a matsayin ZEEYAD abinda zaiyi ɗin kenan koh fiye da hakan ma. *Yawan Comment, Yawan Posting* *MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽* [7/22, 12:41 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *031...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *_NOT EDITED_* __________Rungume yake jar yanzu da Grandma ɗinsa bayason rabuwa da ita, sabida he feels safe and calm a jikin ta, ji yake tamkar da Ummien sa yake rungume, a rayuwa ya ɗauka bayida wani sungun farin ciki but a yanzu yasan Grandma ɗinsa ita ce zata basa farin ciki fiye da kowa a rayuwa. Cikin kuka Grandma ta ɗago shi tare da yin cupping fuskar sa tace "Oh my lovely boy, ina ka shiga ne haka, ina kaje tsawon shekarun nan, maiyasa kayi nesa damu ka barmu cikin wahala da ƙuncin rashin ka, where have you been all this long?" ta faɗa tana sake rungume shi. Ta gefen ido ya kalli mai Martaba dake tsaye da sandar sa yana kallon su kan yace "It's alright Grandma, am here now, no harm would come to you i promise" ya faɗa in a calm voice cikin son kwantar mata da hankali. Ɗago dashi tayi tana ƙare masa kallo zuciyar ta fal cike da farin ciki tace "You've grown so strong and Handsome Young Man, look at your muscles and beautiful face" ta faɗa murmushin farin ciki na forming akan fuskar ta. Murmushi yayi shima yayi kafin ta kama fuskar sa tana manna masa kiss a goshi tare da sake rungume sa cikin farin ciki. Sosai ZEEYAD yake cikin farin cikin ganin Grandma ɗinsa, he wish farin cikin ba zai sake gushe masa ba har abada. Ɗagota yayi yace "Let's go Grandma" ya faɗa yana riƙo hannun ta. Kallon sa tayi kafin tace "Let's go to where?." "Am taking you away with me, you will no longer stay in this Mansion again, you will no longer stay in this Man's custody again, let's leave and go far away from here Grandma." "But..." "Please Grandma, i know ba daɗin zama kikeji anan ba, tell me something Grandma, menene wannan mutumin yayi miki da har kike zama a gidan sa after all he did to me?." "Stop it Boy" ta faɗa. "Grandma please let's go." "No we aren't going anywhere" ta faɗa tana kallon sa. Da mamaki ZEEYAD ke kallon ta kafin kuma yace "Grandma?." "Yes, babu inda zamu, you should be proud na ganin ka cikin family ɗinka, we've have waited so long dan jiran dawowar ka, a yau Allah ya dawo mana da kai and you want to leave, i won't allow you to go anywhere Boy." "Grandma what are you saying?, listen Grandma sabida naji labarin kina cikin gidan nan ne yasa ni zuwa tafiya dake, let's go away from this people muje muyi rayuwar mu daban, they aren't worth yin rayuwa tare damu." "What are you saying Boy?, why should we leave, this is your home, this is your destination, ka dawo yanzu sannan zuciyar masoyan ka cike take da murnar dawowar ka, munyi doguwar jirar zuwan wannan rana kuma gashi alhamdulillah Allah ya kawo ta, bayan tafiyar ka zuciyar kowa cike take da alhini musamman ma mahaifin ka..." Bata ƙarasar ba ya katse ta da faɗin "Oh come on Grandma, what are you saying now, koh kin manta ne banida wani masoyi a duniyar nan face ku da kuke dangin Ummie na, all this people here are nothing but monsters, and this Man here" ya faɗa yana nuna mai Martaba. "Wannan mutumin ne kike cewa yana baƙin ciki da 6ata na?, this Man here never wished anything but my disappearance, koh kin manta ne Grandma how he used to treat me, how he cut all the ties between me and you ya kuma nesanta ku dani, this Man here is nothing but a Monster..." "ZEEYAD..." ta faɗa jin abubuwan da yake faɗa. Kai ya girgiza mata yace "Don't stop me Grandma, allow me to say what is in my mind, everyone around this PALACE knows exactly how this Man treated me like his own freaking enemy, he never shows me love, he never shows me care, all he wished for is for me to go far and stay away from him forever, shine kuma kike cewa yana farin ciki da dawowa ta, Grandma babu wanda ke farin ciki da dawowa ta anan except ke da Sadeeq, i would never forget and forgive how this people hated me and make my life a living hell, not even this old Man here" ya faɗa yana aikawa da mai Martaba dake tsaye jugum yawa an shuka shi a wurin mugun kallo. "ZEEYAD my boy, don't misunderstand your father..." "He is not my father, no father treated his son the way he did, My Mom and Dad are all dead Grandma, stop calling this man here my father." "Boy ya isheka haka nan, kana neman wuce gona da iri fah." "No Grandma bai ishe ni ba, Grandma kinsan menene why don't we just go away from here ganin fuskar wannan mutumin babu abinda yake ƙaramin sai tsanar sa." Murmushin gefen baki Sarauniya Nazeerah dake bala'in enjoying wannan drama tayi kafin a ranta tace _"Oh God, Thank you so much for keeping me alive to witness this good and exiting day in my life, how sweet"_ ta ƙarashe cikin murmushi tana sake kallon Sarauniya Hafeezah ta gefen ido. _"Ohh Hafeezah Darling, jibi yadda take tsattsafo da gumi sai kace wacce taga mutuwar ta, you never see anything dramar bata fara ba until this ZEEYAD here ya zamto Sarki, daga nan ne kuma zaki yabawa aya zaƙin ta hhhh."_ ta faɗa tana maida hankalin ta dan cigaba da kallon drama. "Grandma please i beg you mu bar nan wurin, come on" ya faɗa yana kamo hannun ta da niyyar su tafi. "No" ta faɗa cikin tsare gida kafin ta daura da faɗin "Am not going anywhere haka kaima, ka dawo kenan Prince, ba zaka fita koh da nan da ƙofar fada bane, this is your home and kingdom" ta faɗa tana riƙo hannun sa kafin kuma tace "Come on" tana jan sa su fara tafiya. "What, Grandma what are you doing?." "Am doing the right thing" ta faɗa dai-dai lokacin da suka iso gun Doguwar Throne ɗin dake cikin fadar kafin ta saki hannun sa tace "See this Throne here, shekaru goma kenan ba'a hau kansa ba, and you know why?, duk sabida dalilin 6atar ka." Cize baki yayi yana kauda kai gefe. "Tun bayan 6acewar ka your father here has live nothing but a grief and lonely life, he cried all day, all night praying and crying his heart out just kawai dan ka bayyana ya sake sanƴa ka a idanun sa, i know that rayuwar ka cike take da jarabawa iri-iri sannan an zalunce ka but sometimes we have to let go of our past in order to move on a happy life, you've suffered ten years of your life a ƙarƙashin mahaifin, bayan ka tafi kuma shima yayi suffering ten years na rashin ka, mahaifin ka yafi kowa sonka fiye da yadda kake tsanmani, ya ajiye dukkanin wata ragamar mulkin sa sabida rashin ka, yayi fama da rashin lafiyar da har yanzu bai gama farfaɗowa ba duk saboda rashin ka, koh dan wannan ma yakamata ace ka sassauta zafin da kakeji a zuciyar ka game dashi ka rungumi mahaifin ka wanda yayi tsawon jira yana biɗar ranar da zai sake sanƴa ka a jikin sa ya rungume, ZEEYAD my boy mahaifin ka bai ta6a tsanar ka ba..." "Grandma please" ya faɗa cikin katse ta kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Did he bribe you or something, maiyasa kike goyon bayan sa..." "Ba goyon bayan sa nake ba, am just telling you the truth." Kai ya girgiza kafin kuma ya kalli mai Martaba yace "Listen here old Man, why don't you just tell my Grandma yadda ka tsane ni kuma kake fatar 6acewa ta a kullum, and now tazo tana faɗamin abinda kunne ba zai iya ɗauka ba, why don't you tell her the truth?." "I never hated you Son" ya faɗa cikin raunanniyar muryar shi. "Oh stop it now, who even cares either you hated me or not, that doesn't matter to me coz i love myself sannan ina da masu sona, just tell my Grandma irin abubuwan da kayimin a cikin gidan nan." "Am so sorry Son, please forgive me." "A big sorry for yourself Oldy" ya faɗa cikin aika masa da wani irin kallo. "My boy..." "Grandma please" ya faɗa yana kallon Grandma dake ƙoƙarin hana shi magana. Shiru Grandma tayi sai dai sam batajin daɗin yadda yake yiwa mahaifin nasa magana dukda bata ga laifin sa ba sai dai ai yakamata atleast yayi showing some respect, dan kuwa ta lura dukkanin wani abinda zata faɗa dan gamsar da jikin nata akan mahaifin sa ba zai ta6a yarda ba, sai dai sam ba zata ta6a barin sa ya bar cikin gidan nan ba, yin hakan tamkar makiyan sa sunyi nasara akansa ne, sannan hakan babu abinda zai haifar sai rigima da tashin hankali. Kallon sa ZEEYAD ya maida kan Sarauniya Nazeerah dake ta sambaɗa murmushi tunɗazu, haɗa ido dashi da tayi ne yasa ta saurin gimtse fuskar ta tana kauda idanun ta. Kallon Sarauniya Hafeezah da kanta ke sunkuye har yanzu a ƙasa bata ɗago ba yayi kafin ya kauda kansa yana ayyana iriyar fansar da zai ɗauka akanta a cikin zuciyar shi. Maido duban sa yayi kan mai Martaba dake tsaye yawa an jiƙa tsumma a randa yayi kafin kuma ya saki slight murmushi yana kaɗa kai. Tabbas wannan MASARAUTAR tasu cike take da mugaye, munafukai, annamimai dama kuma tarin maƙiyan juna, so babu abinda ba zasu iya yi ba dan ganin buƙatar su ta biya. _"Wow wow, seems like dukkanin ku nan kuna enjoying drama ɗin dake faruwa anan isn't it, zuciyoyin dayawan ku cike take da farin cikin ganin yadda ɗa ya tsare uban sa da maganganu, so let me show you my own kind of trick, ance idan baka iya kama 6arawo ba shi zai kama ka, i would make sure nayi confusing ɗinku to death, i will stay in this PALACE and rule it the way i want it, but first i have to make things right between me and this old man here, am doing it because of my Grandma not because i wanted to"_ ya faɗa a cikin zuciyar sa yana bin kowanne mahaluƙi dake cikin fadar da kallo ta ƙasan ido ganin yadda duk sukayi shiru suna sauraran abinda ke faruwa ba tare da koh ɗaya daga cikin su ya tofa albarkacin bakin shi ba, hakan na nufin sunji daɗin hakan kenan, sai dai kuma shi ba zai ta6a yin abinda zai sanƴa su jindaɗi ba face wanda zai ƙona musu rai. "My Boy, please forgive your father, ka baiwa maƙiyan ka kunƴa" cewar Grandma. Kallon ta yakeyi kafin kuma ya kalli mai Martaba, har cikin zuciyar sa ya tsani mahaifin nasa sai dai babu yadda ya iya ne, zaiyi hakan ne dan kawai farin cikin Grandma ɗinshi dama kuma cikar burin abinda yayi niyya, tattaro dukkanin dauriyar sa yayi tare da ƙarasawa gaban mai Martaba ya tsaya yana kallon sa eye to eye. Tabbas babu abinda yake hangowa cikin idanun mahaifin nasa sai tsantsar nadama da tarin jin kunƴa, sai dai hakan sam ba zai gamsar dashi har ya iya yafe masa abinda yayi masa a rayuwa ba. Hannu ya kai tare da share hawayen mahaifin nasa kafin yace "Cry no more Father." Kallon sa mai Martaba keyi cike da mamaki zaiyi magana ZEEYAD yayi saurin rungume shi. Sosai mamaki ya cika mai Martaba dan haka sake sandar sa yayi yana mai rungume ɗan nasa shima, kafin kuma ya saki kukan da ta fito masa tundaga chan ƙasar zuciya yana faɗin "Am sorry Son, am so Sorry, ka yafe ni ɗana." Jin kukan mahaifin nasa ne yasa shi sake rungume shi ƙam, yanajin kukan har cikin zuciyar sa, dan kuwa daga jin kukan kasan ba wai fake bane koh wani abu dole ne ya ta6a zuciyar mai sauraron ta musamman ma shi da yake kusa da mahaifin nasa yana jiyo bugun zuciyar shi. "It's alright Abhi" ya faɗa. Sarauniya Nazeerah sam bataji daɗin ganin hakan cikin idanun ta ba _"What Nonsense, he ruined everything"_ ta faɗa a zuciyar ta cike da jin haushi. Sarauniya Hafeezah kuwa ji tayi kamar zuciyar ta zata fito waje dan bugu dan haka ficewa tayi daga fadar fuuuu yawa wacce iska zai ɗauke tana tafiya tana harɗe ƙafafu dan kuwa idan ta cigaba da tsayuwa anan zuciyar ta zata iya fashewa. Daga cikin mutanen dake tsaye a fadar kuwa kowa fara ta6e baki yayi dan kuwa basu so dramar nan ta tsaya anan haka ba. Sadeeq da Grandma kuwa wani irin murmushin farin ciki suke tayi kamar haƙoran su zasu zubo. Ɗagowa yayi tare da mannawa ZEEYAD kiss a goshi yana sake komawa ya rungume shi. Tsuke fuska ZEEYAD yayi kafin kuma a hankali ta yadda babu wanda zaiji abinda yace yace "Listen Old Man, do not get too excited yet, am not doing this for my own wish, am doing it for my Grandma, just keep in mind that i ZEEYAD hated you to the core" kafin kuma ya ɗago yana sakar masa murmushi. Murmushin shima mai Martaba ya ƙaƙalo ya saki. Sandar sa da ya yasar ya kalla, kafin yayi wani yunƙuri kuma ZEEYAD ya ɗauko masa ita tare da damƙa masa a hannu, kafin kuma yace "You need to rest Abhi, come on i will take you to your room" ya faɗa yana rungumo kafaɗar mai Martaba ɗin. Kallon Grandma yayi yace "Grandma i will take him to his room." Kai kawai ta jinjina masa tana murmushi. _"Why is Grandma so excited to see me back together with this Man?"_ ya faɗa a zuciyar sa. Har ɗaki ya kai mai Martaba tare da zaunar dashi kan bed ɗinsa. Ɗakin ya shiga ƙarewa kallo kafin kuma ya ta6e baki yace yana niyyar juyawa. "Listen son" yaji mai Martaba ya faɗa. Tsayawa yayi akan shi yana kallon sa. "I want to discuss something important with you." "No time for that Old Man, i have alot to cover." Shiru mai Martaba yayi kafin kuma yace "OK, zan jira zuwa lokacin da bakada wani abin a gaban ka." Tsayawa ZEEYAD yayi kallon sa kafin kuma yayi saurin yatsina face yana juyawa. Idanun sa ne suka sauƙa kan hoton Ummien sa dake manne a bango hakan ne ya sanƴa shi ja ya tsaya yana kallo. Ya ɗauki almost 10mins yana kallon hoton nata yayin da zuciyar sa ke bala'in yi masa zafi kafin kuma ya fice a fusace daga cikin ɗakin. Da kallo mai Martaba ya bishi yana mai jin tausayin sa tare da yin nadamar dukkanin abinda ya aikata masa a baya. Sauƙowa yayi izuwa lokacin kowa ya watse except Sadeeq da Grandma da suka rage. Sauƙowar sa yasa Sadeeq saurin ƙarasawa wurin sa tare da faɗin "Hey" yana murmushi. Murmushi ZEEYAD ma yayi kafin kuma su rungume juna cike da murna da kewar da sukayi. Sun ɗan jima kafin su ɗago kowanne da murmushi kan fuskar sa. Sadeeq ne yace "I thought ka daɗe da mutuwa." Ɗan bugun sa ZEEYAD yayi a kafaɗu kafin yace "Why don't you think of something good." Murmushi yayi yace "I thought ba zaka ta6a dawowa ba." "Why not, i have a family, remember?." Kai ya jinjina kafin kuma ZEEYAD yace "Tell me how is Abhi?." "He is good, should we go and see him?." Shiru ya ɗan yi kafin kuma yace "Yeah sure." Kallon Grandma yayi kafin yace "Grandma, i will be right back." Rungume sa tayi tace "Take care, Allah yayi maka albarka." Amsawa yayi da "Aameen" kafin kuma ya ɗaura hannayen sa kan kafaɗun Sadeeq suna ficewa daga fadar. Fitowa sukayi tare da jerowa tafe. "So tell me, how you made it." "It's a long story" ya faɗa cikin murmushi. "Really, but tell me what were you doing at the Hospital?." "Hospital?" ya faɗa a ɗan mamakin ce, DEENAH ce ta faɗo masa a rai take kuma mood ɗinsa ya fara sauyawa. "Yeah i saw you, i mean kana da wani alaƙa ne tsakanin ka da matar nan da ƴar ta?." Shiru yayi kafin kuma yace "No." "Really, but why were you begging her akan kada ta raba ka da yarinƴar." "Wait, how did you know all this?" ya faɗa tare da tsayawa da tafiyar yana kallon Sadeeq. "I was standing right there, i mean am the Doctor that you talked to." Ƙanƙance idanu yayi tare da faɗin "Really, you mean you became a doctor?." "Yeah" cewar Sadeeq cikin murmushi. "Wow, that is wonderful, Congratulations Bro" ya faɗa yana bashi runguma. "Thank you, and you tell me wane irin aiki kakeyi?." Kallon sa yayi kafin yace "Aikin sayar da mutane nake." "What?" ya faɗa cikin zaro idanu waje. "Yep" cewar ZEEYAD suna cigaba da tafiya. "What, you kidding me bro?." "No, why should i, na ta6a 6oye maka wani abu ne?." "Serious bro?" ya faɗa tare da tsayawa yana ƙare masa kallo. Murmushi ZEEYAD yayi yace "Just kidding you." Murmushi shima yayi kafin su cigaba da tafiya, duk inda sukayi kuwa da kallo ake bin ZEEYAD da ya zame sabon halitta a gare su. "But ZEEYAD honestly speaking mai Martaba yayi nadamar abinda ya faru da kai a kullum bashida magana wacce ta wuce taka, i was Surprised da yadda ya canza bayan tafiyar ka, do you know what he did?, yasa an garƙame dukkanin wadanda suka ta6a muzguna maka tare da yi musu horo mai tsanani har na tsawon shekaru uku, hatta Abdulhakeem da ya kasance ɗan uwansa sai da ya kore sa daga fada sannan ya kwace duk wata dukiya da kadara tasa dake hannun sa, sabida yana sane da abinda Sooraj yayi maka amma yayi shiru, babu wanda ya tsira a cikin mutanen da suka muzguna maka har sai da sarki ya sanƴa su ɗanɗana guɗar su, sai dai fah akwai aiki a gaban ka." Kallon sa ZEEYAD dake saurarar sa tunɗazu yayi kafin ya jinjina masa kai yace "Yeah, Sooraj a kullum bayida wani buri wanda ya wuce ka dawo ya ɗauki fansar abinda akayi masa ta dalilin ka, sabida ya gaji da zama cikin talauci wanda yake ganin hakan ya faru ne duk ta dalilin 6acewar ka hakan yasa akayi musu wannan hukunci." "Sooraj my foot" ya faɗa cikin tsukewar fuska ba tare da ya ɗauki maganar Sadeeq ɗin serious ba. A haka suka ƙarasa gidan su Sadeeq,inda Abhi ba ƙaramin murna yayi da dawowar ZEEYAD ba, inda shima ya sake jaddada masa da irin halin da mai Martaba ya shiga bayan tafiyar sa, sai dai dukkanin abin nan da suke faɗa koh kaɗan babu wanda ya ta6a zuciyar ZEEYAD. *********************** *1 MONTH AFTER* ________Sati uku kenan da dawowar Yarima ZEEYAD fada, duk da ba wani kula mai Martaba yake sosai ba sai dai hakan bai damu mai Martaba ba sabida yana samu yana ganin shi hakan ke sanƴa hankalin sa kwanciya. ZEEYAD kullum a part ɗin Grandma ɗinsa yake wuni, sosai take nuna masa wata iriyar kulawa ta musamman wanda bai ta6a samun irin ta ba tunda yake. Shiyasa a kullum baya rabuwa da maƙale mata sabida wurin ta kaɗai yake samun farin ciki da kwanciyar hankali, duk da kuwa babu abinda ya nema ya rasa a nashi part ɗin. Sosai kuma ya maida hankalin sa karankatakaf kan business ɗinta, wanda shi kanshi yasan ba ƙaramin profit ya samu a ƴan kwanakin nan da ya maida hankalin sa ba. YAZEED ma ya kan zuwa part ɗin Grandma time to time dan kawai su zauna yayi hira da ɗan uwan nasa. YAZEED da ZEEYAD tamkar ƴan biyu haka suke dan kuwa koh da ganin su kayi sun jera suna tafiya ba zaka iya banbance wanne ne ZEEYAD koh YAZEED ba muddin ba wai ka kalli fuskar su bane ba. Sosai MASARAUTAR ta koma ainihin ita sakamakon dawowar ZEEYAD, kasancewar mai Martaba baya rabuwa da fitowa cikin fada kullum suna tattaunawa akan matsalolin yau da kullum yasa komai ke tafiya smoothly a cikin MASARAUTAR. ZEEYAD baya kula kowa haka kuma baya shiga harkar kowa, daga shi sai Grandma ɗinsa da YAZEED ne kaɗai suke zama suyi hira. Sarauniya Hafeezah kullum neman hanƴar raba ZEEYAD da YAZEED take sai dai hakan yaci tura, hakan ne kuma ya sanƴa ta canza wani sabon boka dan a cewar ta wancan babu abinda ya iya. Sarauniya Naseeba kuwa kullum zuciyar ta soyayyar ZEEYAD ce ke ƙaruwa mata a ciki, ji take zata iya rasa rayuwar ta muddin bata mallake shi ta gusar da ƙishin ruwan da takeji akan sa ba, dan kuwa gayen yayi mugun haɗuwa. Sarauniya Nazeerah kuwa ita dama ƴar a bi Yarima asha kiɗa ce, babban burin ta bai wuce kullum taga ana hayaniya da cece kuce ba, wannan shi ne tata damuwar. Abdulhakeem da iyalan sa kuwa tuni sarki ya maido dasu cikin fada bayan Abdulhakeem yayi rantsuwar ba zai sake aikata abinda yayi ba. Mugunta dama kuma baƙin halin Sooraj bai ragu ba sai ma abinda yayi gaba, sabida kullum burin sa shine rigima ta shiga tsakanin sa da ZEEYAD, ya tsani ZEEYAD fiye da komai, musamman yadda yaga how wealthy and successful he become, hakan na mugun ƙona masa rai bama shi kaɗai ba hatta Sarauniya Hafeezah dama kuma sauran dangi. *(Duk zasu bayyano nan gaba)* Grandma kullum cikin farin cikin ganin ɗan jikan nata take, batason yin nesa dashi koh kaɗan. 6angaren su Jafar kuwa ba ƙaramin baƙin cikin raba ZEEYAD da DEENAH da Umma tayi yaji ba. Yasan DEENAH ba zata ta6a samun masoyin gaske kamar ZEEYAD ba, he loves her wholeheartedly sai dai Umma ta watsa masa ƙasa a idanu, and now yasan ZEEYAD yayi wa DEENAH nisan gaske dan kuwa koh shi yanzu ba sosai suke magana a waya ba, sosai yakejin baƙin ciki da haushin abinda Umma ta aikata. Yau ma kamar kullum, zaune suke a ƙatuwar falon Grandma, gaban su kuwa kayan fruits ne kala daban-daban jibge akan tray suna sha. Kallon su Grandma tayi tace "Kuna ji na ku gama ku tashi dawuri haka nan, mai Martaba na jiran ku a fada kun dai san yau zaiyi manƴan baƙi sannan yakamata ace dukkanin ku biyu kuna wurin." Yatsina face ZEEYAD yayi yana tsuke fuska yace "Am not going YAZEED yaje shi." Kallon sa YAZEED yayi shima yace "Am also not going, duk wadannan baƙin ba zuwan Allah da annabi suke ba, they just wants to find a suitor for their daughters." "Toh miye a ciki ai wannan abin farin ciki ne ma..." "Grandma, menene abin farin ciki anan ɗin?, haka kurum aje ayi ta tallata mu yawa wadanda sukayi kwantai, nidai nafi ƙarfin a haɗa ni aure da wata wallahi" cewar YAZEED. Murmushi ZEEYAD yayi kafin yace "You're right bro, kafi ƙarfin a tallata ka, i mean look at you what if aka haɗa ka da wacce batayi maka ba fah." "Toh uban zigi, idan ka gama sai ka tashi kuje koh." "Grandma please..." "Ba wani zancen please, ya zama dole ne ku tafi idan ba haka ba kuma ku haɗu da 6acin raina yanzun nan." "Alright, alright zamuje." "Da yafi muku kam." Nan dai suka cigaba da hirar su inda sai da Grandma ta sake yin dagaske kafin su tashi su wuce fada. *********************** _______Yau ma kamar kullum da sassafe ya fice jogging da motsa jiki. Sosai ya haɗe cikin gym wears ɗin nasa wadanda suka yi matuƙar amsar sa haɗi da bayyanar da murɗaɗɗiyar jikin sa da muscles ɗinsa kasancewar kullum baya rabuwa da yin Exercise ɗin da zasu ƙara masa ƙarfi da ƙarfin jiki. Kwance yake akan ƴar ƙaramar carpet ɗin sa da ya saba fita da ita yayi matashi da hannayen sa inda yayi crossing legs nasa idanun sa a lumshe. "Hey bro" ya faɗa yana zama gefen shi. Buɗe idanun sa yayi yana kallon YAZEED kafin kuma ya tashi zaune yana kallon sa. "What?" cewar YAZEED. "Nothing kawai ina mamaki ne wai kaine ka fito motsa jiki yau." Ɗan dariya yayi kafin yace "Who told you cewa da ɗin bana yi it's just that ba kullum nakeyi kamar kai ba." Ɗan murmusawa yayi kawai ba tare da yace komai ba. Kallon sa YAZEED yayi yace "You know what?." "No" ya faɗa. "Am Inlove." Juyowa yayi ya kallesa kafin kuma ya ɗanyi murmushi mai sauti yace "You what?." "You heard me right, don't you?." Ɗan ta6e baki yayi yace "Love is just a waste of time" ya faɗa cikin karyewar zuciya. Dariya YAZEED yayi yace "Waste of time, you really take love as a time waste, well actually ni ba haka na ɗauke shi ba, besides tell me ka ta6a yin soyayya ne da kake cewa haka?." Ɗan murmusawa yayi tare da yin shiru bai ce komai ba. "Well actually i guess love is a beautiful thing, don't you think so?." Shiru ZEEYAD yayi kafin kuma yace "Well i don't know, i have never been inlove." "Really?, lallai ka bar daɗi." "Kana nufin kai ka ta6a soyayya ne?." Dariya yayi yace "Yeah, with wata yarinƴa a chan cyprus, but i dumped her." "What, you did?" cewar ZEEYAD cikin mamaki yana kallon sa. "Yeah actually, the girl is non-muslim and you know a MASARAUTA ba zasu ta6a yarda da auren non muslim ba, thats why i dumped her don't get me wrong, i didn't broke her heart." "Kana nufin kace bataji ciwon rabuwa da kai ba?." "She understands me bro." Kallon sa yayi kafin kuma ya ɗan murmusa yana yin shiru. "So, zaka raka ni hira anjima?." "No, am not going." "Oh come on please." "I said no" ya faɗa yana tashi tsaye. "Alright then, i won't force you, where are u heading to now?." "Grandma." "OK see you then." Kai ya jinjina masa kafin ya tattari carpet ɗinsa yayi gaba............... *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [7/29, 8:08 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *032...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ Alhamdulillah, Allah yayi mun dawo, Nagode sosai *ZEEYAD FANS CLUB* haƙiƙa da bazar ku nake taka rawa, Nagode Sosai masu kira, masu message dukkanin ku ina godiya har ma da ƴan likimo duka, da addu'ar da kukayi tayi min kuna sake nuna kulawar ku akan ƙanina, Alhamdulillah ya samu lafiya kuma mun dawo gida zamu cigaba daga inda muka tsaya, Haƙiƙa ina matuƙar Ƙaunar ku fisabilillah❤️🥰 *_NOT EDITED_* _________Tafe yake riƙe da ƴar ƙaramar rug ɗinsa a hannu, tun daga nesa ya hango Sooraj tafe hakan yasa shi sake tamƙe fuskar sa sosai kasancewar bayason raini koh wani abin da zai shiga tsakanin sa da Sooraj ɗin. Sooraj ma tundaga nesa ya hango ZEEYAD tafe dan haka murmushin gefen baki ya sake yana shafa gemun fuskar sa. Zuwa sukayi zasu wuce juna kafin kuma Sooraj yayi saurin sanƴa hannu yana dafe ƙirjin ZEEYAD cikin tsayar dashi. Da kallo ZEEYAD yabi hannun sa dashi izuwa kan fuskar sa, koh kaɗan baiyi mamaki ba sabida kaɗan daga cikin halin Sooraj kenan, tun yana ƙaramin sa he is a bully bale kuma da ya taso da halin babu mai iya kwa6ar sa. "Seems like you're avoiding me, loser" cewar Sooraj ɗin cike da muguwar baƙin hali irin nasa. Cize baki ZEEYAD yayi tare da karkaɗa kai ba tare da yace dashi komai ba. "You got something to say?" ya sake faɗa. "Why don't you just mind your own fucking business with me Sooraj?." Cikin hura hanci Sooraj yace "Mind my business hahaha, ai yanzu na fara shiga gonar ka ƙasƙan..." Kallon da ZEEYAD ya ɗago yana yi masa ne ya sanƴa shi haɗiye saurar maganar kafin kuma cikin borin kunƴa yace "Miye kake yimin irin kallon nan, koh kana tunanin zanji tsoron ka ne iyeh?." Cikin clicking tongue ZEEYAD ya yatsine fuska yana kan yace "Idan kaji tsoro na ma wannan damuwar ka, just know one thing for sure that ba wannan old ZEEYAD ɗin da ka sani bane a gaban ka yanzu, just don't try to mess up with me, uhm?" ya faɗa yana kallon Sooraj ɗin da kamar ya tashi sama sabida haushi. "Har kai wanene da zaka ce zaka tsare ni da maganganu...?." "Oh come on, i told you not to try to messed up with me didn't i?." "Mai zaka iya yi?" ya faɗa cikin aika masa da mugun kallo. Kallon sa ZEEYAD keyi kafin kuma cikin ɗagun murya yace "Guards!." Duk fitowa sukayi daga spot ɗin da kowanne ke tsaye suna iyowa wurin da ZEEYAD da Sooraj ke tsaya, cikin girmamawa da duƙar da kai suka ce "Yes the great Prince." Ba tare da ya kalle su ba yace "Lock him up in the dark room for 3hours." "Yes Prince" suka amsa cikin girmamawa suna iyowa kan Sooraj da niyyar kama shi, tsawar da ya daka musu ne ya sanƴa su dakatawa duk suna kallon sa kafin ya kalli ZEEYAD cikin hura hanci da huci yace "Ni zaka wulaƙanta, how dare you?." Ɗan ta6e baki ZEEYAD yayi yace "I warned you, didn't i?." "I will make sure kayi nadamar abinnan da kayi" ya faɗa yana nuna ZEEYAD ɗin da yatsa. "Take him away" ya faɗa. Duk iyowa kansa sukayi tare da kama shi sukayi gaba dashi kamar yadda ZEEYAD yace musu. Muguwar kallo mai cike da ma'anoni iri-iri kawai yake aikawa ZEEYAD yanajin zuciyar sa kamar ta tarwatse tsabar ƙunar da takeyi masa. Barin wurin ZEEYAD yana kimtsa iriyar rayuwar da zai bi kowanne daga cikin fadar tasu dashi, ba zai ta6a samun salama ba har sai yaga kowannen su ya ɗanɗana ƙuɗar sa fiye da yadda sukayi masa, one after the other zaiyi maganin su. Da wannan tunanin ya isa ga part ɗinshi da tafi na kowane ɗa a cikin masarautar girma da haɗuwa. Da kallo yabi bayi matan dake ta aikace suna kai komo dashi, kafin kuma cikin 6acin rai yace "I want to be alone." Sum-sum kowacce ta fice da kayan aikacen ta yana sake tsuke fuska ya haura sama, sam baiga dalilin da zai sanƴa ana barin masa bayi mata sukayi masa aiki ba, hatta ruwan wanka da kanshi wankan ma wai masu yi masa daban aka ware tsabar ance musu shi ɗin shege ne, sai da ya yiwa abin tufkar hanci kafin su daina shigo masa ɗaki, iyakan su cikin falo da sauran ɗakunan dake cikin part ɗin ba dai su taka zuwa ɗakin kwanan shi ba. Ɗakin motsa jikin sa ya nufa wanda ke ƙawace da ababen Exercise kala daban-daban na bada ƙarfi. Ƴar ƙaramar rug ɗin hannun sa ya ajiye kan couch, kafin ya nufi ɗaya daga cikin *DECLINE BENCH PRESS* ɗin dake jere cikin instrument ɗin motsa jikin ya kwanta, kafin kuma ya ɗaga ƙarfen ya fara aiki da ita cikin kwarewa. Ya kai almost 30mins yana yi inda Knocking ɗin da yaji a bakin ƙofa ya sanƴa shi saurarawa. Knocking aka sake yi a karo na biyu hakan ya sanƴa shi faɗin "The door is opened" ya faɗa yana cigaba da aikin shi. Rufe bakin sa keda wuya aka turo ƙofar aka shigo cikin sallama. Sadeeq ne da wata kyakkyawar budurwa a bayan shi hannun ta riƙe da tray sai sambaɗa murmushi take. Wuri Sadeeq ya samu ya zauna kafin ita kuma ta ajiye tray ɗin akan table tana maida duban ta gun ZEEYAD, murmushi take dan kuwa ba ƙaramin burge ta yake idan ta ganshi ya fito fili yin jogging ba. "Hey" cewar Sadeeq yana duba agogon hannun sa. Dakatawa ZEEYAD yayi yana ajiye ƙarfen kafin kuma ya ɗago zaune, ganin ta ne ya sanƴa shi saurin gimtse fuskar sa yana kallon Sadeeq. Kafaɗu Sadeeq ya ɗaga masa alamun oho kafin kuma ya tashi yana janƴo ƴar ƙaramar towel ya shiga goge jikin sa yana ƙarasowa ya zauna kusa da Sadeeq ba tare da ya kula ta ba. Murmushin yaƙe ta saki ganin yadda yayi kamar bai ganta ba tace "Ina kwana Akhi?." Kamar ba zai amsa ba kuma yace "Am good." Murmushi tayi kafin tace "Kayi haƙuri ban shigo da izinin ka ba, dama breakfast na kawo maka, i made your favorite" ta faɗa tana buɗe tray ɗin ta ciro wani bowl tare da buɗe murfin shi tana miƙa masa. Da kallo yabi bowl ɗin dashi kafin kuma ya sanƴa hannu ya amsa yace "Thank you." Murmushi tayi cike da jindaɗin gode mata da yayi tana kallon sa. Da gefen ido ya kalli Sadeeq dake kusa dashi yana tsuke fuska. "Na jira ka gama ci sai na tafi da kwanukan ne?" ta faɗa. Shiru yayi kafin kuma yace "No, thanks." Tsaye tayi sam bataji daɗi ba kafin kuma tace "Okay, zan dawo anjima na ɗauka." Kai kawai ya jinjina mata kafin kuma ta fice zuciyar ta fal farin ciki. Duk da kallo suka bita ficewar ta ya sanƴa shi saurin dire bowl ɗin yana juyowa ya kalli Sadeeq. Surrender Sadeeq yayi da hannu yace "She saw me coming here sannan ta san guards ba zasu bar ta ta shigo ba hakan ya sanƴa ta roƙo na kan na jira ta mu shigo tare." "Well then i guess kaima hana ka shigowa zanyi" ya faɗa yana miƙewa tsaye. "Oh let's pretend baka faɗi hakan ba." "You know bama good time da Abhi da Akhi ɗinta, and you let her into my place." "But the girl is decent, bata ɗauko hali irin na family ɗinta ba, maybe you should get married to her sabida seems like she loves you." Wani irin mugun kallo ZEEYAD ke binsa dashi kafin yace "Get out." Murmushi Sadeeq yayi yace "Am going to work yanzu, nazo ne na sanar maka da cewa that girl da Mom nata yau zanyi discharge nasu seems like kamar ka san su koh?." ZEEYAD ji yayi zuciyar sa tayi wani irin bugawa, idanu ya runtse kafin kuma ya samu wuri ya zauna. Kallon sa kawai Sadeeq keyi ganin yadda mood ɗinsa ya canza nan take. "Are you alright?" ya faɗa. Kallon Sadeeq yayi kafin kuma yace "maiyasa zakayi min maganar su?." "Does that annoy you?" ya faɗa yana kallon sa. Shiru yayi masa sai wuri ɗaya kawai da ya kafe da idanu yana kallo. "Am sorry then" cewar Sadeeq. Ɗagowa yayi ya kallesa kafin ba tare da yace masa komai ba. Shiru shima Sadeeq yayi yana kallon ZEEYAD ɗin, kafin kuma daga bisani ya numfasa yace "I think i should be going, inada aiki dayawa" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Da kallo ZEEYAD ya bishi har ya kai bakin ƙofa kafin kuma yace "Ta samu lafiya?." Juyowa Sadeeq yayi yana kallon sa, kafin kuma yace "No, da ɗan saura but ta tuna wasu abubuwan kuma ta fara magana, idan ta cigaba da shan magunguna kuma ta koma inda ta fito zata iya tuna komai da komai." Kai kawai ZEEYAD ya jinjina yace "Okay." "Are you coming or something?" cewar Sadeeq. Kai ya girgiza masa alamun A'a. "Okay then, see you" ya faɗa yana buɗe ƙofar ya fice. Idanu ya runtse yana komawa ya jingina da kujerar da yake kai. Idan suka tafi does that mean ya rasa ta gabaɗaya kenan?, yayi alƙawarin ba zai sake zuwa kusa da ita ba, sannan yayi alƙawarin ya rabu da ita kenan har abada, dan haka ya zama dole ne ya yaƙi zuciyar sa na ganin ya yaƙice ta, sannan kuma ya rabu da tunanin ta, sunyi rayuwa a baya yakamata ya sanƴa ta cikin past life ɗinsa ya zamto ba zata ta6a dawowa ba, kamar rayuwar ƙuncin da yayi a baya, he needs to forget her ba ma ita kaɗai ba dukkanin family ɗinta, he knows that hakan ba abu mai sauƙi bane a gareshi but he needs to try so very harder na ganin hakan ya faru. Da wannan tunanin ya tashi ya bar ɗakin gym ɗin izuwa cikin ɗakin kwanan shi. Wanka yayi ya shirya cikin shigar sa ta alfarma kafin kuma ya fice zuwa part ɗin Grandma dan kuwa nan ne kaɗai zai iya samun sassaucin abinda yakeji a cikin zuciyar sa. *********************** ___________Kwance yake yayi matashi da cinƴar grandma, idanun sa a lumshe yanajin duk wata damuwar sa na gushewa sakamakon tausar da take yi masa cikin gashin kansa. Grandma ba ƙaramin ƙauna take yiwa jikan nata ba, duk wani abu da zai sanƴa shi farin ciki shi take yi masa, dan kuwa shi kaɗai take gani taji zuciyar ta tayi sanƴi musamman da ya kasance sauran ƴaƴan ta sunyi nesa da ita. Wata baiwa ce ta ƙaraso inda suke zauna cikin girmamawa tace "Ranki ya daɗe an kammala breakfast ɗin." Kallon ta Grandma tayi kafin kuma tace "Maiyasa kuka 6ata lokaci dayawa wurin kammala wa, je ki tahowa da Yarima nashi, nasan yana jin ƴunwa." Amsawa tayi cike da girmamawa kafin kuma ta bar wurin zuwa aikata abinda aka sata. Ba'a jima ba ta dawo ɗauke da tray ɗin abin karin kumallon ta ajiye. Ganin tayi tsaye ne ya sanƴa Grandma cewa "Zaki iya tafiya." "Nagode ranki ya daɗe" ta faɗa tana juyawa ta tafi. Kallon ZEEYAD Grandma tayi tace "Boy ka tashi kaci abinci kaji." Tsuke fuska ZEEYAD yayi dan kuwa wani irin bacci mai daɗi ne ya fara fizgar sa nan yace "Grandma bacci nakeji, kuma ba zanci abincin da suka girka ba." "Toh girkin wa kakeson ci ɗan nan?." ''Naki" ya faɗa. Murmushi tayi tace "Toh ai shikenan an gama bari na tashi naje na girka maka yanzun nan." "No Grandma, sai na tashi a bacci tukun, coz am very sleepy." "A'a fah bakajin ƴunwa ne?." "No" ya faɗa alamun mai jin bacci. Hakan yasa ta yin shiru tana cigaba shafa sumar kanshi. ******************* __________"Umma?" ta faɗa tana kallon Umma dake tattare kaya cikin ƴar ƙaramar jaka. Ɗagowa Umma tayi tana kallon ta kafin ta bar jakar tazo kusa da DEENAH cikin kulawa tace "Menene?." Shiru tayi kamar mai son tuna abu kafin kuma tace "Ina zamu je?." Murmushi Umma tayi kafin kuma tace "Gida zamu koma Auta." "Gida?, ina ne gidan?." "Zamu je mu goben nan kinji?." Kai kawai ta jinjina kafin kuma Umma ta koma ta cigaba da haɗa kayan. Sadeeq ne ya shigo ɗakin da takardar sallamar bayan sun gaisa da Umma ne ya bata yace "Alhamdulillah, finally za'a koma gida, make sure anyi abiding da rule ɗin da na gindaya, insha Allah zata samu full recovery, sannan kuma zaku dinga zuwa check-up after every 3months, dan ganin lafiyar kwakwalwa ta har izuwa lokacin da zata samu lafiya gabaɗaya." "Insha Allah Doctor, mungode sosai da sosai, zamu kiyaye duk wata doka da izinin Allah." Murmushi yayi kafin ya sake yin wasu rubutu a jikin files ɗinta sannna ya fice. Ɗaukar file ɗin Umma tayi ta sanƴa a jaka kan kuma ta cigaba da haɗa kayayyakin ta. Bayan ta kammala ne Nurses ɗin dake kula da DEENAH suka shigo ɗakin dan haka taimaka mata sukayi suka fidda mata kayan waje. "Tashi muje koh?" cewar Umma. Shiru DEENAH tayi tana kallon ta nan Umma tace "Ba fah zai zo ba dan haka tashi muje mu, kinji?." Kya6e baki tayi idanun ta na cikowa da hawaye, hannun ta Umma ta kama suka fice daga cikin ɗakin. Cikin farfajiyar asibitin suka tsaya jiran Taxi, inda DEENAH duk hankalin ta yayi gaba so take kawai ta sake ganin shi koh zata ji daɗi a ranta, sai dai yau ɗin kamar bai shigo asibitin ba. Umma ce tace dasu "Ku jira ni anan bara naje shagon chan na dawo." Da "Toh" suka amsa mata kafin kuma ta wuce. Ɗaya daga cikin nurses ɗin ce tace "DEENAH, yau fah Doctor YAZEED bai shigo office ba koh kin manta ne yau Thursday baya shigowa?." Murmushi ɗayar tayi tace "Seems like tayi kewar shi ne?." "Yeah he is nice, ai kinga dole taji kewar shi." Cikin kwantar da murya ɗayar tace "Kina tunanin yana sonta ne, kokuma dai kawai a matsayin ƙawar wasar sa ya ɗauke ta?." "What no, ba sonta yake ba imagine kamar sa kuma ɗan sarki yaso ta, he is just kind to her kamar yadda yake yiwa kowa." "But, yadda yake sakin jiki da ita suyi hira idan mun fito motsa ƙafa bakya tunanin akwai wata a ƙasa, duba da yadda yake kallon ta?." "No, he is just being nice kawai." Hango Umma tafe ya sanƴa ɗayar saurin yin shiru. Murmushi tayi tace "Thank you girls, gaskiya kunyi matuƙar ƙoƙari sosai akan DEENAH Allah yayi muku albarka." Murmushi sukayi ɗaya tace "Ai bakomai aikin mu ne, sai dai zamuji kewar DEENAH sosai." Ɗayar ce tace "Dama ki bamu lambar wayar ki kullum mu dinga gaisawa da DEENAH." Murmushi Umma tayi kafin tace "Of course zan baku idan kuna so." Saurin ciro wayar ta ɗayar tayi tana miƙawa Umma tace "Muna so." Amsa Umma tayi ta sanƴa musu lambar ta na Nigeria kafin ta miƙa musu wayar. Godiya sukayi mata kafin su tara musu Taxi, duk rungume DEENAH sukayi kafin su buɗe mata motar ta shige. Hannu sukayi ta ɗaga musu har motar ta 6ace daga ganin su. ********************** __________Washe gari Ƙarfe bakwai ɗin dare jirgin su Umma ya sauƙa. Zuciyar Jafar cike take da ɗumbin farin ciki, sabida yau zai ga ƙanwar sa, tun kafin ayi magrib ya tafi jiran su inda achan yayi sallar ma. Ganin sauƙar jirgin su kuwa kamar an sauƙo masa da farin cikin sa ne. Hango Umma yayi riƙe da hannun DEENAH suna sauƙowa daga kan matattakalar benin jirgin, idanu ya zuba musu har suka idda sauƙowa suna ƙarasowa, da sauri ya nufe su yana cewa "Umma?." Wani irin ƙayataccen murmushi Umma ta sakar masa tana buɗa masa hannu. Da sauri ya rungume ta yanajin wani irin tsantsar farin ciki na dabaibaye shi. Kallon DEENAH da ta kafe shi da ido tana kallo yayi da alamu dai bata gane shi ba. Ɗagowa yayi yana sakar mata murmushi ganin sai kallon sa take yi. "Umma nayi kewar ki." "Ai baka kaini kewa ba, babban yaya" ta faɗa cikin murmushi tana shafa kanshi. Murmushin shima yayi yace "DEENAH?." Murmushi ta sakar masa tana kallon shi. Riƙo ta Umma tayi kafin kuma tace "Muje gida koh?." Kai Jafar ya jinjina kafin ya ɗebi luggages ɗin su ya kai mota. Nan duk suka shige kafin ya tada motar ya bar wurin. ****************** _______Horn ya danna a bakin ƙofar gidan nan take mai gadi ya wangale gate ɗin sai ɗaga hannu yake yana washe haƙora cike da farin ciki shima. A parking space yaje yayi parking motar, tun kafin su buɗe motar suka ga an buɗe, cike da farin ciki Anty Khadija da Amirah suka rungume Umma suna yi mata oyoyo. Saurin buɗe inda DEENAH take sukayi tana fitowa kafin itama su rungume ta cike da farin cikin ganin ta da sukayi suna ɗagowa. "DEENAH?" duk suka faɗa suna kallon ta. Murmushi kawai DEENAH tayi musu tana bin su da kallo. Mami ma ƙarasowa wurin tayi tana yi musu lale da zuwa. Duk ciki suka nufa kowanne ka ganshi fuskar nan farin ciki fal a cikin sa. DEENAH kuwa da kallo take ta bin gidan tana ganin kamar ta san shi. Bayan sunyi wanka sun huta ne kuma aka gabatar musu da abinci da na sha kala daban-daban, dan kuwa su tun jiya Mami ta turo su Anty Khadija yi musu gyaran gida da sauran abubuwa. Sosai Umma taji daɗi sai godiya da sanƴa albarka take yi musu, duk haɗuwa sukayi suka fara cin abincin. Jafar idanun sa na kan DEENAH ganin yadda take ta bin gidan da kallo kamar yau ta fara ganin sa. A haka suka wuni cikin raha da farin ciki har sai da dare yayi tukun kafin su koma gida. Umma ɗaki ta kai DEENAH ta taimaka mata tayi shirin bacci kafin itama ta fice zuwa nata ɗakin. Kwance take idanun ta na akan p.o.p ceiling ɗin ɗakin, zuciyar ta fal tunani, ga kuma rashin sukuni da ta kasa yi tunɗazu, haka tayi ta juye-juye har bacci ya ɗauke ta. ***************** ______Washe gari kuwa makwa6ta ne sukayi ta shigowa gaisuwa dama kuma ƴan wurin aikin su Umma, kowa yana zuwa duba mai jiki, sosai Umma taji daɗin hakan. Jafar kuwa wurin aiki ya fice after so many attempt da yayi na kiran ZEEYAD dan sanar dashi su DEENAH sun dawo amma wayar tasa bata shiga haka nan ya haƙura ya tafi office ɗin zuciyar sa babu daɗi. 6angaren DEENAH kuwa ɗaki ta dawo dan kuwa ji tayi ba zata iya zama cikin mutanen ba, dan kuwa a takure takejin ta a cikin nasu. Zama tayi a bakin bed ta shiga ƙarewa ɗakin kallo na kusan 10mins kafin kuma ta kwanta tanajin kewar Ƙawayen ta nurses dama kuma abokin ta Doctor. *TWO WEEKS AFTER* ________A ƴan kwanakin nan sosai take gane dukkanin abinda ta gani tare da tuna koh menene shi. Yau ma tsaye take tana bincika closet ɗinta taci karo da school uniform nata. Tsayawa tayi tana kallon farin kayan kafin kuma ta saki murmushi a hankali tace "School?." Kafin kuma dukkanin wani abu da tasan tayi a makarantar ya shiga dawo mata cikin kwakwalwa. "Bodyguard?" ta furta daidai lokacin da ta tuna inda take faɗawa wannan malamin nan nasu cewar shi ɗin bodyguard ɗinta ne. "Who is he?" ta faɗa sakamakon kasa tuno fuskar sa da tayi. Maida uniform ɗin tayi kafin kuma ta samu bakin bed ta zauna tana rabka tagumi. "DEENAH?" taji an faɗa. Juyowa tayi tana kallon Umma kafin kuma tayi saurin miƙewa tace "Umma waye...waye bodyguard?." "Bodyguard kuma?" cewar Umma cikin mamaki tana kallon ta. Kai ta jinjina mata tana kallon Umma ɗin. "Waye kuma bodyguard?" cewar Umma ɗin. Shiru DEENAH tayi tana tunanin kafin tace "Ban..banga fuskar shi ba." "Toh fito kizo kici abinci ki sha maganin ki." Kai ta jinjinawa Umma tace "Toh." Ficewa Umma tayi kafin ita ma ta tashi tabi bayan ta. ******************** _________A ƴan kwanakin nan ji yayi ya mance da wata DEENAH koh family ɗinta, sabida Grandma ɗinsa ta zame masa komai haka kuma bata ta6a barin sa cikin ƙunci da 6acin rai. Zaune yake a wani ƙayataccen wuri wanda kai tsaye za'a iya kiran sa wurin hutu, babu abinda kakeji sai kukan tsuntsaye da shawagin su, gaban sa kuwa system ɗinsa ce sai kuma mug ɗin coffee a hannun sa yana sipping a hankali fuskar sa manne da baƙar shade. YAZEED ne ya ƙaraso wurin ya zauna fuskar nan tasa a cunkushe babu walwala. Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon sa, ganin kamar da damuwa a ransa yasa shi faɗin "Meke damunka?." Kallon ZEEYAD yayi yace "Bakomai." "Are you sure, ina faɗamaka damuwa ta fah, remember?." "Yaushe ka ta6a faɗamin, you never tell me anything about your life." Murmushi ZEEYAD yayi yace "Actually baka ta6a tambaya ba." Kallon sa yayi kafin yace "Okay, that girl da nake faɗamaka." "What girl, the one you're inlove with?." "Yeah ita." "What's wrong with her, did she betrayed you or something?." "No tayaya zata fara yaudara ta bayan ba soyayya muke ba?." "What happened then?." Shiru yayi yana tsuke fuska kafin yace "I lost her, i mean ta tafi ba tare da na san inda take da zama ba." "Kamar ya?" cewar ZEEYAD yana gyara zaman shi. "The girl is a patient and..." "And you fell inlove with her?" cewar ZEEYAD cikin katse shi. Kallon ZEEYAD yayi kafin yace "Actually yes, and an riga anyi discharge nasu almost 3weeks kenan, am so bothered you know, i don't even know where to find her." "You fell inlove with your patient?." "Yeah, menene a ciki, she is not my patient though, kawai ina ganin ta ne and i fell inlove with her at first sight." Murmushi mai sauti ZEEYAD yayi dan kuwa shi abin ma dariya ta bashi ganin yadda YAZEED ɗin keyi. "What's funny bro?, actually this isn't funny you know, i really love her am so disturbed da rashin ganin ta." Tattare dukan nutsuwar sa ZEEYAD yayi ganin dai YAZEED ɗin is serious. "Why don't you just find her then?." "Where, daga ina zan fara, i don't know anything about her." "Ba kasan Doctor ɗin da ya kar6e ta ba?." Shiru yayi kafin kuma cike da jindaɗi yace "Yo, Exactly guy, why didn't i think of that?" kafin kuma ya tashi yana buga kafaɗun ZEEYAD yace "See you in a while" ya bar wurin da sauri ba tare da ya sake bi ta kan ZEEYAD ɗin ba. Da kallo ZEEYAD ya bishi kafin kuma ya saki murmushi yana maida duban sa kan aikin da yakeyi. **************** _________"Umma!, Umma!!" ta ƙira da ƙarfi a karo na biyu. Da sauri Umma dake zaune a falo ta itada Jafar ta shigo cikin ɗakin DEENAH ɗin. Tsaye ta same ta ta kafe wuri ɗaya da idanu tana kallo yayin da hawaye suka wanke mata fuska. "Lafiya, menene?" cewar Umma tana ƙarasawa wurin ta tare da riƙo ta. Saurin kwace hannun ta tayi daga cikin na Umma kafin tace "Umma ina yake?." Cikin rashin fahimta Umma ta kalle ta tace "Bangane ba, wa kenan?." "Kin fi kowa sanin wanda nake tambaya." "Meke damunki ne DEENAH?, talk softly mana." "You want me to talk softly then tell me where he is" ta faɗa tana kallon Umma ɗin. "DEENAH lafiyan ki kuwa, wa kike magana ne a kansa." "Balarabe mana" ta faɗa idanun ta na cigaba da tsiyayar da hawaye. Umma ji tayi gaban ta ya faɗi da jin abinda DEENAH ta faɗa. "Balarabe, he is nothing a cikin rayuwar ki." "Of course he is..." "Then tell me amfanin da yake dashi cikin rayuwar ki?, he left you Okay." "No he didn't left me, kece kika tursasa masa ya bar ni, i remember everything, how could you do this to me?" ta faɗa tana kallon Umma ɗin. "Alhamdulillah da kika tuna komai, inaga mu bar maganar yaron nan yanzu, we should all be happy by now come on" ta faɗa tana riƙo hannun DEENAH. Sake fuzge hannun ta tayi tace "Well then ai baki za6i ayi murnar ba yau, coz i would never be at peace from now on, kin raba ni dashi, i remember lokacin da kika kore shi a asibitin nan, i remember everything, ban ta6a tunanin zaki aikata hakan ba, how could you be so selfish, dan bakya son shi ba hakan ke nufin zaki kore shi daga cikin rayuwa ta ba, because i need him." "You need him, ni kike wa magana cikin tsawa because of a random guy?." Shiru DEENAH tayi bata ce komai ba, tanajin zuciyar ta na matuƙar suya kamar ta fito waje. "You listen to me carefully, of course nice wacce na tilasta masa ficewa daga rayuwar ki, sabida banason alaƙar ki dashi, already zuwa yanzu nasan yayi moving on da life nasa you should also try and do so, and besides maiyasa bakya son rabuwa dashi tunda ba wai soyayya kuke ba, kodai kina son shi ne?." Ɗagowa tayi tana kallon Umma ba tare da ta iya cewa komai ba. "Answer me, son sa kike komiye?." Maida duban ta tayi gun Jafar dake tsaye bakin ƙofa yana kallon su ba tare da ta bawa Umma amsa ba. "Well i guess ba sonsa kike ba koh?, then ina buƙatar ki cire shi daga cikin rayuwar ki, koh da da wasa bana buƙatar jin sunan sa daga bakin ki, sabida ya riga da yayi miki nisa and am definitely sure idan shi mai zuciya ne ba zai ta6a dawowa ba, sabida na riga da na yanke alaƙar dake tsakanin ku, dan haka ki kwantar da hankalin ki sabida hakan ba zai sanƴa shi sake dawowa cikin rayuwar ki ba, haka ma hawayen da zaki zubar so i need you to give it a rest, no more tunanin da babu gaira babu dalili, yin hakan tamkar tsokano fushi na ne" tana gama faɗin haka ta fice daga cikin ɗakin ba tare da ta tankawa Jafar dake tsaye yana kallon su ba. Duk da kallo suka bita kafin ya idda shigowa cikin ɗakin, rungume shi tayi tana sakin kuka sosai inda shi kuma ya hau rarrashin ta. "Maiyasa Umma zatayi haka, maiyasa batason alaƙar mu dashi, maiyasa ba zata dubi halin da na shiga dama kuma wahalar da yayi akaina ba, Yaya yana sona koh ba haka ba?" ta faɗa tana ɗagowa ta kalle shi. Kai ya jinjina mata alamun eh kafin yace "He was ready to sacrifice anything da ya mallaka akanki, actually balarabe yana matuƙar ƙaunar ki, he never rest tsawon watannin da kika ɗauka a asibiti, he just can't imagine life without you, yana sonki DEENAH hakan ya sanƴa shi karya dokar da Umma ta gindaya na kada wanda ya biyo ta a cikin mu har sai kin samu lafiya,but shi ya gaza yin hakan sabida kawai yanason ganin ki and ready to face and endure duk wani abu da Umma zata faɗa masa, but it turned out to be that Umma da kanta ta kore shi, not wondering irin halin da zaki shiga bayan hakan, ita dai burin ta shine taga ya bar cikin rayuwar mu ba tare da ma ta lura da cewar a ƙarƙashin sa nake aiki ba, and abin baƙin cikin shine ya saida company ɗinsa na nan Sokoto, that means kenan ba zai kuma dawowa ba DEENAH, i think he is out of our lives forever DEENAH." Kuka sosai DEENAH ta fashe dashi tana komawa kan bed ta zauna "Maiyasa Umma zatayi haka, shikenan yayi laifi dan ya soni kenan, ina laifin wanda yaso naka?, maiyasa zata yimin haka?." "Well DEENAH maybe she has a reason behind it..." "Wane irin dalili ne hakan, koma menene dalilin ta baikamata tayi masa hakan ba, he doesn't deserved that, she humiliated him after all the love and care he had shown me, ba zan manta lokacin da ya durƙushe kan guiwowin ba sa pleading her akan kada ta raba shi da DEENAH but she turned a deaf ear ta wulaƙanta shi, sam bai cancanci hakan ba, menene laifin sa?." Shiru Jafar yayi yana mai jin tausayin ƙanwar tasa ganin yadda take ta kuka, baisan wane irin kuka zata yi ba bayan ta gano cewar ba zata kuma haɗuwa da shi ba maybe yace har abada, he is very sad da abinda Umma tayi gashi kwata-kwata yanzu he can't get through ZEEYAD, hakan na nufin yayi nesa dasu sannan ba zai sake dawowa Nigeria ba, da wannan tunanin ya bar cikin ɗakin tare da ficewa daga gidan ma baki ɗaya. DEENAH kuwa wuni tayi a ɗaki ranar koh abinci bata fito taci ba, sosai takejin haushi da zafin abinda Umma tayi, dah Umma tasan irin son da take yiwa ZEEYAD dah bata fara yi masa hakan ba, tasan yanzu ita da farin ciki kuma wataƙil sai a lahira, sabida Umma zata sake jefa ta halin da yafi na baya da tayi, sosai take kuma jin haushin kanta na kasa tuna ZEEYAD da tayi a wannan lokacin, after irin wahalar da ya sha a kanta, what if dagaske ta rasa shi har abada kenan, toh tabbas itama zasu rasa ta ne. ************************ __________Tsaye take ta a gaban wani ƙaton tekun, wurin shiru yake bakajin ƙarar komai sai na iskar dake kaɗawa dama kuma ruwan tekun ɗin dake kai komo yawa zai haɗiyo mutum, tana sanƴe da farar gown ɗin da ya kai mata har ƙasa kanta ɗaure da farar ɗankwali, ta juya baya. A hankali yake takowa wurin ta staring at her back. Juyowa tayi suna haɗa idanu kafin kuma ta sakar masa wani irin murmushi tana cigaba da kallon sa. "DEENAH?" ya furta. Hannu ta miƙa masa alamun yazo gare ta, babu musu yayi saurin ƙarasawa yana shirin kama hannun nata. Wata budurwa ce wacce baiga fuskar ta ba tayi saurin shigewa tsakiyar su, kafin ta juya ga DEENAH tana tunkuɗa ta cikin ƙaton tekun ɗin. "DEENAH!" ya furta da ƙarfi, a daidai lokacin ne kuma ya farka daga mafarkin da yake yi ɗin. Dafe kansa yayi da hannayen sa yana jin yadda zuciyar sa ke mugun gudu, idan da wannan sau huɗu kenan yana yin thesame mafarki da DEENAH, wanda ya rasa gane mai hakan ke nufi, addu'a yayi sosai yana mai ɗago da kansa. Idanun sa ne suka sauƙa kan wata Baƙar kuliya mai wani irin manƴan Hazel eyes staring at him in the dark. Koh kaɗan bai wani ji koh da ɗar bane a cikin zuciyar shi sai ma idanun kuliyar da yake kallo shima. "So it's you again, it's been long since i saw you" ya faɗa. Wani irin kuka mai ban tsoro kuliyar tayi kafin kuma tayi saurin sauƙa daga kan gadon tana ficewa da gudu ta window ɗin ɗakin. Da kallo yabi inda tabi kafin kuma ya miƙe tare da zuwa ya tsaya ta window ɗin. "I know you're evil, but whatsoever you may be i would make sure i get you one day." *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [7/31, 12:45 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *033...* *A NEW LIFE* ____________Kwance take kan bed ɗinta da duƙunƙune kanta cikin pillow. Buɗe ƙofar ɗakin Umma tayi ta shigo, ganin har yanzu DEENAH ɗin na yadda ta barta yasa ta fara magana cikin takaici da baƙin cikin halin da ta 6ullo dashi ƴan kwanakin nan "MADEENAH watau dai ba zaki bar wannan kukan na dalilin banza da wofin da kika tsirowa kanki ba koh, shikenan ke kullum bakida aiki sai rufe kanki a ɗaki kiyi ta kuka, ai yaci ace koh ciki ɗaya aka haifo ki da yaron nan kin manta dashi yanzu, toh ki sani ba zan kuma lamintar hakan daga gareki ba, zaki tashi ne tukun ki wuce kizo kici abinci koh sai ranki yayi mugun 6aci yanzun?." DEENAH da ta ƙara volume ɗin kukan ta, ɗagowa tayi tana wurgi da pillow ɗin kafin kuma ta tashi tana faɗawa cikin bathroom ta rufo ƙofar da ƙarfi. Da kallo Umma ta bi ta kafin kuma ta ƙarasa bakin ƙofar bathroom ɗin tace "Idan kin gama kukan naki marar dalili ki fito yanzun nan ina jiran ki, idan kuma kika kuskura kika sa raina ya 6aci baki fito dawuri ba ni dake ne a gidan nan" tana faɗin haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin. Kuka mai ƙarfi DEENAH dake cikin banɗaki ta sanƴa, sai da tayi mai isarta kafin ta wanke fuskar ta da duk ya kumbura tsabar kuka ta fito. Cikin falon ta fito ta zauna ba tare da ta tankawa Umma dake binta da kallon takaici ba. "Zaki zo ki ɗau abincin kici ne kokuwa?." Tashi tayi daga inda take zaune ta sauƙo inda Umma take tare da ɗaukar plate ɗin abincin tana niyar barin wurin. "Ina zaki?, dawo nan ki zauna kici." Dawowa tayi ta zauna tana ƙoƙarin haɗiye kukan dake son ku6uce mata tare da buɗe plate ɗin ta hau cin abincin. Tusawa kawai takeyi ba wai dan tanajin daɗin sa ba, yayin da hawaye ke gangaro mata kan ƙunci. Bai fi cokali huɗu tayi ba taji amai na ƙoƙarin zuwan mata, dan haka ajiye cokalin tayi tana kya6e fuska inda dakyar ta iya haɗiye na cikin bakin ta. "Ba dai ki cemin har kin ƙoshi ba." "Umma dan Allah kiyi haƙuri wallahi bana jin cin abincin" ta faɗa cikin kuka. "Aa ba dai a gidan nan ba kam, banga dalilin da zai sa kice bakya jin ƴunwa ba bayan lafiyar ki ƙalau, maza ki buɗe baki kici abincin nan yanzu." Hannu ta kai ta ɗau cokalin tana sake ɗebo abincin ta kai bakin ta. Bata kai ga haɗiye wa ba, taji amai na zuwa mata ba tare da wani 6ata lokaci ba kuwa ta shiga kwararo shi anan yawa ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago duka. A ruɗe Umma ta iyo kanta tana kama ta, tare da jero mata sannu yawa zata ari baki, kafin kuma ta kama ta suyi cikin ɗaki, bathroom ta kaita ta wanke mata bakin ta kafin kuma ta fito dan barin ta tayi wanka. DEENAH idanu ta ƙurawa cikin mirror ɗin banɗakin tana kallo da idanun ta da sukayi luhu-luhu tsabar kuka wanda gani ɗaya zakayi mata kasan ba isasshiyar lafiya gare ta ba. Wanka tayi ta fito kafin ta shirya cikin wasu irin Baggy ɗin riga da wando tana komawa kan bed ta kwanta tare da rufo bargo har izuwa kanta. Sosai ta shiga halin tunani da ƙuncin rashin sa, a dah tasha ƙaryata kanta cewar bata sonshi but a yanzu ta gane gaskiya, tanason ZEEYAD sannan kuma tun ba yau ba ta kamu da son nasa, and now Umma tazo ta ruguza komai, tana neman kai rayuwar ta ga halaka, a yanzu babu abinda takeji a cikin zuciyar ta sai zafi da ƙunci, sosai zuciyar ta keyi mata raɗaɗi, musamman idan Umma tayi maganar ta mance dashi dan kuwa ya riga da yayi mata nisa, ita kanta tasan indai ZEEYAD ya cika mai zuciya toh kuwa koh da waiwayar ta ba zai sake ba. Duƙunƙunewa tayi tana cigaba da rera kukan nata da ya zame mata jiki a hankali. ********************* _________Da dare ganin jikin DEENAH ya rikice ya sanƴa Umma kiran likita yazo ya duba ta har gida, inda akayi mata ƙarin ruwa dama kuma allurai. Zaune Umma take kusa da ita tana jin yadda take ta rera kukan nata da yaƙi ci yaƙi cinƴewa tunɗazun. Jafar ne ya kalli Umma yace "Umma inason magana dake?." Kallon sa Umma tayi tace "Inajin ka." "Maybe in private" ya faɗa. Ajiyar zuciya Umma ta sauƙe kafin ta tashi tana ficewa daga ɗakin inda Jafar ma ya mara mata baya. Kallon ta yayi yace "Umma nasan ni ban isa na ja dake kokuma naga rashin kyautatawar ki akan dukkanin wani hukunci da zaki yanke a matsayin ki ta uwa a gareni ba, sannan kiyi haƙuri ki gafarce ni da maganar da zan faɗa miki yanzu, maganar gaskiya Umma shine sam baki kyautawa ZEEYAD ba haka ma DEENAH, duk da bansan dalilin ki na ganin kin raba alaƙar mu dashi ba amma inason nasan menene dalilin da yasa bakya ƙaunar sa kokuma ya ra6e mu har ma wata alaƙa ta dauru tsakanin sa da DEENAH?." Kallon sa Umma keyi kafin tace "Ba wai ƙaunar sa bane bana yi, sai dai kamar yadda ka faɗa sam banason wata alaƙa ta ƙullu tsakanin sa da DEENAH." "Amma Umma maiyasa, Umma he loves DEENAH so very much, sam baiyi deserving abinda kikayi masa ba, Umma ke kanki kinsan yadda yake matuƙar nuna kulawar sa akan DEENAH wanda koh wannan so called saurayin nata Abdul bai nuna mata koh da kwatan hakan bane, Umma ZEEYAD bai guji DEENAH ba bayan rashin lafiyar da ta faɗa a baya, that means he has a good heart sannan a shirye yake da yayi accepting ɗinta duk yadda take, bai ta6a nuna gajiyawar sa na nuna kulawar sa a gareta ba, he was always worried about her na rashin samun lafiyar ta, Umma ZEEYAD has a good heart sannan tsakanin sa da Allah yakeson DEENAH ke kanki kinsan da hakan but maiyasa zaki saka masa da breaking heart nasa wurin raba shi da DEENAH, after all what he did." "So kana son na ɗauki auren ƴata na baiwa total stranger wanda bansan menene tushen sa da asalin sa ba, bance bashida kirki ba, ofcourse he is kind hearted sai dai barin sa cikin rayuwar mu shine yafi alkhairi a gareshi dan kuwa koh da yana nan ɗin, babu abinda zai sanƴa na ɗau auren DEENAH na basa, bayan ban ta6a sanin kowa nasa ba, hasali ma ba sanin ingantaccen inda ya fito koh wanene shi mukayi ba, bansan ta wace hanƴa ya samu ɗumbin arzikin da yake juyawa ba, bayan daga gani bashida kowa koh wata alaƙa da wannan ƙasar, how comes yaron da na sani yake yawo tamkar almajiri a dah chan turns to be yayi wannan uban kuɗin alhalin bayida wani gata koh mai tsaya masa a ƙasar, and you expect me na ɗau auren DEENAH na basa, daga nan kuma na shiga bakin duniya cewar arziki da kuɗi sun rufemin ido na ɗau ƴata na aura wa wanda bansan asalin sa da tushen sa ba, he had done enough for us, tayaya kake tunanin zan barsa ya cigaba da yiwa DEENAH hidima bayan nasan ba bashi auren ta zanyi ba, yaje shi Allah zai haɗa kowa da rabon sa." Baki kawai Jafar ya saki yana kallon Umma har ta idda zancen ta nan yace "But...but Umma Allah ya kan sauya rayuwar mutum cikin abinda bai fi daƙiƙa ɗaya ba, dama duk sabida bakisan asalin sa da tushen sa dama kuma yadda akayi yayi arziki bane ya sanƴa ki yanke wannan hukuncin?." "Kwarai kuwa, koh kai kasan asalin sa da tushen nasa ne, kana aiki ne kawai a ƙarƙashin sa sannan a iya zaman ka dashi ya ta6a buɗar baki ya baka cikakken labarin koh shi wanene?." Shiru yayi yana nazari kafin kuma ya girgiza kai alamun Aa, sannan yace "Ya dai ta6a cemin shi ɗan ƙasar Egypt ne." "Egypt?" Umma ta faɗa tana kallon sa. Kai Jafar ya jinjina nan tace "Who knows if faɗamaka hakan kawai yayi, but koh kaɗan baiyi kama da Balaraben Egypt ba, he must be from Asian countries, koh ma dai menene i have already made up my mind, and i won't go back on my words." "Amma Umma, think about DEENAH..." Hannun ta ɗaga masa tace "DEENAH will be fine, am sure kawai tausayin sa dama kuma kyautatawar da yayi mata lokacin da batada lafiya ke damun ta, idan ta ɗanyi kwana biyu yanzu ita ma mantawa zatayi dashi." "Umma yakamata ace kin fahimci DEENAH, she is inlove with him." "No she is not, she is still a child, ƙuruciya ce kawai ke damunta, dah zaka yi bincike mai zurfi yanzu zaka gane ba wata soyayya da takeyi masa, just let me deal with her issue." "Umma you misunderstood DEENAH's feeling, she is actually inlove with him, if not then maiyasa tun bayan dawowar ta hayyacin ta bata kuma sake samun nutsuwa ba, batada wani magana kullum da ya wuce nasa, sannan batada wani aikin yi sai kuka and you called it tausayin sa take, of course akwai tausayin nasa haka kuma akwai soyayyar sa tattare da DEENAH, think about it Umma kina neman jefa rayuwar DEENAH ga halaka ne tun ba'a je koh ina ba ta fara zazza6i imagine kuma mai zai faru nan gaba." "Enough of this Jafar, babu abinda zai faru, am sure DEENAH will be fine, kayi mata addu'ar samun lafiya kawai." "Umma ai it's a must nayi mata addu'a, but Umma kinyi kuskuren raba DEENAH da ZEEYAD coz am sure ba zata kuma samun mai sonta kamar sa ba." "Have you lost your mind koh menene Jafar?, addu'a zakayi mata Allah ya musanƴa mata shi da wanda yafi alkhairi ba wai ka dinga irin maganganun nan ba, it doesn't make sense, and mind you banason sake jin maganar wani ZEEYAD or something similar to that a cikin gidan nan, kayi ƙoƙarin ganin kayi calming ƙanwar ka na ganin ta mance dashi sannan kuma she have to move on,DEENAH ba zata rasa masoyin gaske ba da izinin Allah, banason ka kuma sake yimin wannan maganar, kaji?." Kai kawai ya jinjina yace "Am sorry, ki gafarce ni idan na 6ata miki rai." "It's alright, muje mun barta ita kaɗai a ɗaki." Juyawa sukayi tare da komawa cikin ɗakin. Kallon DEENAH da har yanzu bata bar kukan nata ba yayi cike da tausayin ta kafin yace "DEENAH, it's okay haka nan kinji, stop crying kada ki jawa kanki wani ciwon." "Umma...Umma bata sona yanzu." Kallon juna Jafar da Umma sukayi kafin yace "No DEENAH ki bar faɗin haka, kema kinfi kowa shaida yadda Umma ke ƙaunar mu, take kuma iya ƙoƙarin ta na ganin ta faranta mana da dukkanin wani abu da ta mallaka, Umma ba zata ta6a aikata wani abu da zai zamto cutarwa a gareki ba." "Mai kake nufi, kana nufin Abyad shi ɗin cutar dani zaiyi ne, maiyasa Umma ta kasa ganewa ne, yanada kirki sosai maiyasa zatayi masa abinda ta aikata, bai cancanci hakan ba." "No DEENAH ki bar faɗin haka, bance ZEEYAD cutarwa ne shi ɗin a gareki ba, but am definitely sure indai har keda shi a destined to be together then babu abinda ya isa ya hana yiwuwar hakan,.just kawai ki kwantar da hankalin ki kici gaba da addu'a kinji?." Kai ta jinjina masa cikin kuka tana lumshe idanu ba tare da ta kalli Umma dake zaune gefen ta ba. ************************* __________Tsaye yake gaban mai Martaba dake zaune kan Throne ɗinsa kafin yace "You asked of me." Murmushi mai Martaba yayi masa yace "Yeah of course, inaso ne mu tattauna da kai." Yatsine fuskar sa yayi kafin kuma ya dubi manƴan mutanen dake wurin kowanne idanun sa akan su, sannan kuma ya saki fuska yace "Yeah tell me" ya faɗa yana zama a gaban mai Martaba ɗin. Sosai mai Martaba yaji daɗi nan ya kalli ɗaya daga cikin mutanen dake zaune kan kujera yace "Sarkin yaƙi, i guess lokaci yayi da yakamata a fara koyawa Yarima amfani da takobi." Wani irin kallo ZEEYAD ya ɗago yana yiwa mahaifin nasa, wani wai amfani da takobi sai kace wanda zai fita yaƙi. Murmushi sarkin yaƙi yayi yana miƙewa tsaye cike da girmamawa yace "Your wish is my command your Highness, gaskiya ne lokaci yayi da yakamata ace Babban Yarima ya koyi amfani da Takobi koh dan kare kai daga farmakin maƙiya, musamman da ya kasance yana da ƙira da sura irin ta gwarzayen jarumai" ya ƙarashe yana kallon ZEEYAD cikin murmushi. Kai sarki ya jinjina cike da farin cikin abinda sarkin yaƙi yace "Nan yace kayi gaskiya, aje a fara shirye-shirye zuwa gobe ku fara, Yarima wannan ne dalilin da ya sanƴa ni kiran ka nan dafatan zaka so hakan, sannan zakayi biyayya ga abinda na buƙata." Miƙewa tsaye ZEEYAD yayi ya kalli sarki yace "Listen Old Man....i mean your Highness i don't want to do this faɗa da makami baya cikin tsarin rayuwa ta." "Ai kuwa dai yakamata ace ka sanƴa ta a matsayin ka na wanda ya fito daga gidan Sarauta irin wannan" cewar ɗaya daga cikin mutanen wurin wanda shima daga gani babban muƙami yake dashi a fada. "Wait, i don't understand i guess kakannin mu ne sukayi faɗa da makami a dah, but yanzu duniyar ta cigaba and akwai zaman lafiya, what do i need a sword for?." "No Son, al'ada ce ta wannan MASARAUTA tamu duk wani yaro a gidan nan toh lallai ya zama dole ne a fara koya masa faɗa da makami tun daga ƙaramin sa, sauran yaran sun daɗe da fara koya kaida YAZEED ne yanzu wadanda za'a fara koyawa wannan karon, am sure you can do it." Shiru yayi yana kallon mai Martaba ɗin _"Mai wannan mutumin ke nufi ne, ba dai yaƙi zai tura ni ba, i mean koh wuƙa ban iya riƙewa ba talkless of a whole sword, so yake a dawo masa da kaina cikin buhu kenan wataran idan an fita yaƙin"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa idanun sa akan mai Martaba ɗin. "Mai kace Yarima?." "I..i mean zanyi magana da Grandma tukun, idan ta amince nayi then i will do it." Murmushi mai Martaba yayi dan kuwa yasan Grandma ɗin tasa batada wani matsala sai ma guiwa da zata sake ƙarfafa masa. "Alright Son, na baka damar kaje kayi shawara da ita ɗin" cewar Mai Martaba. Kai ZEEYAD ya jinjina kafin yace "Zan iya tafiya?." Kai mai Martaba ya jinjina, dan haka ba tare da ya jira yi komai ba ya juya ya fara tafiya. Idanun sa ne suka sauƙa kan Abdulhakeem dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon sa, kauda kai ZEEYAD yayi kawai ya cigaba da tafiya yana barin cikin fadar. Da kallo Abdulhakeem ya bisa yace _"Oh Poor ZEEYAD, babban Yarima da kansa ace baisan yadda ake sarrafa takobi ba, what a waste"_ ya faɗi hakan a zuciyar shi. ******************** ________Fitowar sa da ta gani daga cikin fadar ne ya sanƴa ta saurin mara masa baya, ba tare da yasan tana biye dashi ɗin ba. Har part ɗin Grandma sukaje tana biye dashi, everything about him burge ta yake, ina ma yace yana sonta yace zai aure ta,da kuwa she will be the most happiest girl on the planet. Murmushi tayi kafin kuma ta kira sunan sa "Akhi" daidai lokacin da zasu shige cikin falon Grandma ɗin. Tsayawa yayi yana mai tsuke fuska ba tare da ya juyo ya kalle ta ba. Ƙarasowa tayi wurin sa tana kallon sa. Juyowa yayi yana sauƙe idanun sa kan kyakkyawar fuskar ta dake fidda murmushi, tabbas kyakkyawa ce sosai, haka ma halayen ta, but hakan ba zai ruɗe shi ya faɗa tarkon sonta ba. Kauda idon sa yayi daga kanta yana kai hannu yayi knocking ƙofar falon. Ba'a jima ba wata baiwa ta buɗe dan haka gaida sa tayi ba tare da ya tanka mata ba ya shige ciki yana tambayar ta inda Grandma ɗinsa take. "Tana chan ɗakin ta tana karatu" ta basa amsa. Kai kawai ya jinjina kafin ya nufi hanƴar stairs. Tsuke baki tayi ganin bai kula ta ba, kafin kuma ta samu wuri ta zauna. A bakin ƙofar ɗakin Grandma yayi knocking tare da kiran sunan ta. "Shigo mana Boy" yaji ta faɗa. Wani irin farin ciki ne ya lullu6e masa zuci dan haka tura ƙofar yayi ya shiga bakin sa ɗauke da sallama. Zaune ya ganta kan couch hannun ta riƙe da littafin addini tana karantawa. Zuwa yayi ya zauna kan sofa yana ɗaura kansa kan ƙafafun ta yace "I miss you Grandma." "Kai ɗan nan kaji tsoron Allah, ba da safen nan ka bar nan wurin ba?." Murmushi yayi yace "Am serious Grandma, Old Man ne ya kira ni." "Kul nace ka daina kiran sa hakan koh?." "Am sorry ina nufin mai Martaba." "Uhum, i hope kunyi spending good time da juna?." "No there is nothing good a abinda ya sanƴa sa kira na, he wants me to learn yadda ake faɗa da takobi." "Masha Allah, abinda na daɗe inason nayi maka magana akai kenan." Ɗagowa yayi yana kallon ta yace "Seriously?." Kai ta jinjina masa tace "Kwarai kuwa." "You mean kinason na koyi yadda ake faɗa da takobi?." "Sosai ma kuwa, ai shine zai nuna kai ɗin cikakken jarumi ne." Murmushi yayi yace "All right, zan koya since kema kina so." Murmushi tayi tana shafa sumar kansa tace "Muje mu na dafa maka favorite ɗinka yau, nasan bakayi breakfast ba." "Seriously Grandma, i will love to have it." "Kwarai kuwa, tashi muje" ta faɗa tana ɗaga kansa, kafin su tashi su fice daga ɗakin. Sauƙowar su ya sanƴa Jalilah dake zaune.saurin miƙewa tsaye tana kallon su cikin murmushi dan kuwa, soyayyar dake tsakanin sa da Grandma ɗinsa ba ƙaramin burge ta yake ba. Da sauri ta ƙarasa wurin su tana faɗin "Grandma, ina kwana?." Cikin murmushi Grandma ta amsa mata da "Kin tashi lafiya ƴar albarka, ya kike?." "Lafiya ƙalau Grandma, ya ƙarfin jikin ki?." "Alhamdulillah" ta faɗa tana samun wuri ta zauna. ZEEYAD ma zama yayi kafin yace "Grandma, kin zauna baki kawomin breakfast ɗin ba." "Mai kake ci na baka na zuba?, gashi chan a dining Jalilah taimaka ki ɗauko masa." Da "Toh" ta amsa tana zuwa ta ɗauko kulolin abincin tare da jerewa a gaban shi. "Toh maza sauƙa kaci" cewar Grandma. "Grandma, bakiyi serving ɗina ba fah" ya faɗa cikin ɗaga gira ɗaya sama. "I will serve you" cewar Jalilah tana kallon sa cikin murmushi. "Grandma please" ya faɗa yana ignoring maganar Jalilah ɗin. Sosai taji babu daɗi a zuciyar ta, but sam bataji wani haushi sosai ba, dan kuwa bata tunanin akwai abinda zaiyi da zai bata haushi sai ma ya burge ta. "Jalilah dear,zo ki sanƴa masa abincin kinji?." Cike da jindaɗi ta jinjina kai tana zuwa ta zauna tare da ɗaukar plate ta shiga serving ɗinshi. Sosai ya sake tsuke fuska, dan kuwa baiga dalilin da zai sa ace yarinƴar nan ce zatayi serving ɗinsa abinci ba, he wonders ma idan turo ta akayi tayi poisoning abincin sa dan yaci ya mutu "That won't work on me" ya faɗa yana kallon ta. Ɗagowa tayi suna haɗa ido tace "What?." Tunawa yayi ashe ba'a zuci yayi maganar ba nan yayi saurin yatsine fuska yana kauda kai ba tare da ya bata amsa ba. Miƙa masa plate ɗin abincin tayi tace "Here." Da kallo yabi abincin kan Plate ɗin kafin kuma yace "Ajiye." Ajiyewa tayi tana komawa gefe ta zauna tana cigaba da kallon shi. Spoon ya ɗauka yana kallon abincin, yayin da kuma yake kallon ta ta ƙasan ido _"She looks innocent, she can't poisoned someone's food"_ ya faɗi hakan yana ƙoƙarin kai abincin bakin sa sai dai yana tsoro. _"Yeah, i know what to do, i will asked her to join me, then nan ne zan tabbatar ta sanƴa guba cikin abincin kokuwa."_ Gyaran murya yayi yace "Hey." Duk kallon sa sukayi itada Grandma nan yace "Would you mind joining me?" ya faɗa yana kallon ta. Murmushi tayi irin abin ya bata mamaki sosai ɗinnan nan tace "Of course i would love to, amma kaci tukun actually bana jin ƴunwa." _"That's it"_ ya faɗa yana yi mata wani irin kallo. Saurin sunkuyar da kai tayi tana murmushi, she can't believe yau ZEEYAD ne ya gayyace ta cin abinci tare dashi, what a great day for her. "But i insist" ya faɗa cikin 6ata rai. Kallon sa tayi kafin ta kalli Grandma, nan Grandma tace "Come on Jalilah kizo mana kuci." Murmushi tayi cike da jin kunƴa kafin kuma ta tashi daga inda take tana zuwa ta zauna gaban abincin tare da ɗaukar cokali ɗaya. Kallon ZEEYAD dake kallon ta tayi kafin kuma tayi saurin sunkuyar da kai tana kai cokalin ta ɗebi abincin tare da kaiwa bakin ta. Murmushin ta mai ƙara mata kyau tayi tace "Uhm, abincin yayi daɗi sosai." _"What?"_ ya faɗa a zuciyar sa yana kallon ta lokacin da ta kai cokali na biyu. _"She is actually eating"_ ya sake faɗa. "Boy kaci abincin mana" cewar Grandma. "Yeah kokuma na cinƴe ba" cewar Jalilah cikin murmushi. Da kyar ya kai cokali ya ɗebi kaɗan tare da yin bismillah yana kaiwa bakin sa. Idanu ya lumshe lokacin da yaji wani irin daɗi ya ziyarce shi. Har dai ya kai cokali na uku yaga babu abinda ya same shi sai a sannan kuma ya saki jiki a zuciyar sa yana faɗin _"Sorry girl, i really thought you poisoned the food"_ ya faɗa yana kallon bakin ta yadda take cin abincin idanun ta kan ƙaton TV ɗin dake aiki cikin falon. Wata baiwa ce ta shigo inda suke, cikin girmamawa tace "Ranki ya daɗe, ana magana da Shugaba ta Jalilah a waje." Duk juyowa sukayi suna kallon ta kafin Grandma tace "Wa ke neman ta?." "Ɗan uwanta ne Sooraj" ta bata amsa. Jalilah zaro manƴan idanun ta yayi, inda kuma gaban ta yayi wani irin mummunar faɗuwa jin Sooraj na neman ta, kenan yasan tazo nan wurin kenan?, shine tunanin da takeyi a zuciyar ta. "Je kice gata nan zuwa" cewar Grandma. Kallon Jalilah tayi tace "Tashi kije." Sosai tsoro ya bayyana kan fuskar ta, shi kuwa ZEEYAD ta6e baki yayi dan kuwa koh bakomai zata daina biye-biyen shi yanzu. Da kyar ta iya miƙewa ta fice tana harɗe ƙafafu. A chan bakin mashigar part ɗin ta hango shi tsaye yana ta kai komo, hakan kuwa ba ƙaramin sake faɗar mata da zuciya yayi ba. A hankali cikin rawar jiki ta ƙarasa wurin sa idanun ta na cikowa da hawaye. Ganin ta da yayi ya sanƴa shi saurin iyowa kanta yana damƙo yalwataccen gashin kanta da ya sha gyara da style yayi gaba da ita. Ƙara tasa sabida iriyar damƙar da yayi wa gashin nata kamar zai raba shi da fatan kanta. "Dan Allah Akhi kayi haƙuri" ta faɗa cikin kuka. Bai kula ta ba saima sake damƙe gashin nata da yakeyi cike da baƙar mugunta har suka isa part ɗin da yake nasu ne. Ture ta yayi tana yin gaba ta faɗi kafin kuma ya hau kiran sunan "Ummie" kamar zai tada gidan. Da sauri ta fito cikin ɗan gudu dan kuwa wannan kira na Sooraj sam tasan babu alkhairi a cikin ta. Jalilah da ta gani zube a ƙasa tana kuka ne ya sa ta tabbatar da hasashen ta, nan ta ƙarasa da sauri tana ɗago ta. Kallon ta Sooraj yayi yace "I warned you several times cewar ki kula da wannan akuyar ƴar taki da batada aiki kullum sai yawon zuwa gidan maƙiya amma kin ƙi ji, bansan uban mai ake bata a chan ba da kullum take hanƴar zuwa sabida rashin zuciya irin tata, babban abin taƙaicin ma shine gaba ne tsakani na da ZEEYAD amma kuma kullum biye take dashi yawa wata jela, so take ta zubar min da mutunci da ƙima a idon maƙiyi ne kalan ya raina ni yace ƙanwa ta kullum tana maƙale dashi da nufin tana sonshi, toh wallahi ina mai gargaɗin ku daga ke har ita, muddin na kuma sake kama ta a arear su then babu abinda zai hana ni aika ta lahira wallahi" ya ƙarashe cikin ƙunar rai yana wani irin huci kamar zai tashi sama. Tunda ya fara magana Ummien nasa ke kallon sa Jalilah kuwa babu abinda take sai kuka, tana ji tana gani Sooraj na shirin raba ta da ZEEYAD. "Ummie maiyasa nima ba za'a barni nayi rayuwa ta yadda naso ba?, koh banida ƴancin da zuciya ta zata so wani ne, i don't care whether shi maƙiyin ka oh masoyin ka ne, wannan tsakanin ka dashi ne,just leave me nayi rayuwa ta yadda naso..." walƙiyar da ta gani a idanun ta haɗi da wani irin zafi ne ya sanƴa ta saurin dafe kumatun ta sakamakon wata iriyar zazzafar marin da ya ɗauke ta dashi. Huci yake kamar wani tsohon zaki yace "How dare you, ni zakiyiwa magana haka?, fine then dah nayi niyyar barin ki ba tare da na ta6a lafiyar jikin ki ba, amma yanzu dole ne ki ɗanɗana ƙuɗar ki" ya faɗa yana jan doguwar dorinar dake hannun sa. Idanu Ummien su ta waro nan tayi saurin shigewa tsakanin su tace "Ka haukace ne da zaka daki ƙanwar ka da irin bulalar nan?." "Eh na haukace, tabbas zan nuna miki na haukace" ya faɗa yana ture ta gefe kafin ya ɗaga dorinar sama yana mai shauɗa mata shi a jiki. Ihu tasa cike da azabar da ta ziyarce ta, sai da ya tabbata yayi mata liliss iya son ranshi kafin ya kyale ta yana wurgar da dorinar gefe tare da ficewa daga gidan. Da sauri Ummien tasu ta iyo kanta itama hawaye ya gama wanke mata fuska tana ɗago Jalilah da ta gama ficewa a hayyacin ta, jikin ta kuwa duk shatin bulalar ce. ******************** _________"So kana ji na, i have gathered all information ɗin da nake nema akan yarinƴar i even got her Mom's number daga wurin wasu nurses" cewar YAZEED yana kallon ZEEYAD. "Wow awesome, so tell me where she lives." "No, not yet coz sai na tabbatar da na samu shiga tukun kafin nayi yunƙurin bayyana ta wa family." Murmushi ZEEYAD yayi yace "That's wise of you bro, can't wait for that day." Murmushin farin ciki shima YAZEED ya saki yana mai jin daɗin burin sa na daf da cika, he just wish Allah yasa DEENAH tayi accepting nasa, and shi kuma yayi alƙawarin samar mata farin ciki mai ɗorewa. *********************** _________Zaune suke shi da Grandma suna hirar su cike da ƙaunar juna kamar yadda suka saba. Grandma ce tace "Nikam kaga fah yau kwana uku kenan rabon Jalilah da nan gidan tunda ɗan uwanta ya aiko a kira ta, baka tunanin yayi mata wani abin ne?." Ta6e baki ZEEYAD yayi in i don't care tone ɗinnan yace "Who knows." "Au haka ma zakace, nida nake cewa kaje ka dubo mana ita." Juyowa yayi yana kallo Grandma da jin abinda ta faɗa "What?" ya faɗa yana kallon ta. Murmushi tayi tace "Wasa nake maka, but Allah yasa dai tana lafiya." Shiru yayi bai ce komai ba sai ma hankali da ya maida kan wayar sa. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [8/2, 10:11 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *034...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*NOT EDITED*_ *_A NEW LIFE 2_* *TWO WEEKS AFTER* __________Zaune yake as usual da sassafe inda yake fitowa jogging, yana mai motsa jikin sa. "You need a massage?" yaji an faɗi hakan ta kansa. Dakatawa yayi da abinda yakeyi, kafin kuma ya ɗago yana sauƙe idanun sa cikin nata da take binsa da kallo kamar ta ɗauke shi ta haɗiye. Sanƴe take cikin baƙar doguwar jallabiya kanta sanƴe da Niƙab ɗinta da ta ɗaga shi. Kauda idon sa yayi daga kanta ba tare da ya bata amsa ba yana mai cigaba da abinda yakeyi. Murmushin gefen baki ta saki kafin ta sami wuri ta zauna tana mai bin kyakkyawar surar jikin sa da kallo. Ganin bai kula ta ba yayi kamar baisan da mutum a wurin bane yasa ta faɗin "Listen ZEEYAD shin ka manta da ina zaune ne anan wurin?." Sosai zuciyar ZEEYAD ke mugun tafasa, ya lura muddin bai takawa Sarauniya Naseeba burki, toh tabbas ba zata ta6a barin sa ya huta ba. Dakatawa yayi da abinda yakeyi yana mai nannaɗe ƴar ƙaramar rug ɗinsa. Saurin miƙewa tayi tsaye tana kallon sa, kafin tace "Are you leaving?." Bai kalle ta ba, haka kuma bai kula ta ba, sai ma gaba da yayi ya fara tafiya. Idanu ta zuba masa ganin yana niyyar ficewa daga wurin ne ya sanƴa ta saurin mara masa baya cikin gudu tana shan gaban sa. Da kallo ya bita ba tare da yace mata komai ba. Kyakkyawar fuskar sa ta ƙure da kallo kafin tace "Listen sexy, na taso all the way daga part ɗina cikin sauya shiga ta dan kawai nazo na ganka, and now you're living ba tare da ma ka yimin kyakkyawar kallo ba?, listen ZEEYAD just tell me everything da kake so daga gareni and i promise zanyi maka shi koh kuma na baka shi, but kaji tausayi na please and give me a chance na ganin na sanƴa ka farin ciki for the rest of your life, i promise you ba zaka yi danasanin yin tarayya dani ba, i mean just look at me am just 40 har yanzu da ƙuruciya ta, am sure we will be perfect for each other, please babe" ta faɗa da niyyar kai hannu ta shafi faffaɗar ƙirjin sa wanda ke ɗaya daga cikin abubuwan da ke sake ɗauke mata hankali game dashi. "Don't you dare" ya faɗa cikin kakkausar murya yana mai aika mata da wani irin kallon da ta kasa gane koh na menene. Dakatawa tayi tana kallon fuskar kan fuskar sa, sosai yayi mata kwarjinin da bata ta6a gani tattare da wani mahaluƙi ba, hannun ta na rawa ta sauƙe, idanun ta na kawo kwalla. Rataye rug ɗin yayi kan kafaɗar sa kafin ya sanƴa hannaye cikin aljihu yana kallon ta cikin murɗaɗɗiyar fuskar sa yace "Listen Naseeba, karen hauka ya cije ki ne komiye?, you really want me ZEEYAD to get intimate with you, koh kin manta ke ɗin mata ce a wurin mai Martaba, you know what, zanyi ƙoƙarin ganin na rufa miki asiri for the last time, don't you dare try this shit with me again, if not then i swear you will regret messing around with me for the rest of your life, ni ZEEYAD nafi ƙarfin ki, koh kin manta ne am not that Abandoned Boy da yayi ta yawo cikin ƴunwa da rashin muhalli mai kyau bane?, look koh da mata sun ƙare a duniya babu abinda zanyi da tsohuwar kilaki kamar ki, bakida wani sungun mutunci a wuri na, koh da wanann mummunar fuskar taki kika sake nuna min then..." Shiru yayi yana kallon ta kafin ya ɗaura da faɗin "I will make sure kin bar cikin gidan nan, bana tunanin rayuwar zawarci akwai daɗi haka kuma bana tunanin idan kin fita daga nan zaki kuma sake samun wani wurin da yafi wanann koh ya kai shi ma, just pretend cewa baki ta6a nema na ZEEYAD da wani abu ba and enjoy arzikin da kike samu cikin gidan nan" ya ƙarashe cikin wurga mata kallon da ya sanƴa cikin ta ɗurar ruwa kafin kuma yayi gaba yana barin ta nan tsaye yawa an shuka dusa koh motsi ta kasa. Jujjuya idanun ta dake cike taf da kwalla tayi, kafin tace "You can try as hard as you can na ganin ka nesan ta dani, but ba zanyi ƙasa a guiwa ba har sai na cika buri na akanka, i must taste how good you're at bed Darling" ta faɗa tana juyawa tabi inda ya fice da kallo. "This is my promise" ta sake faɗa in a serious tone kafin ta ɗaura da faɗin "I will make sure i make you mine, sannan na ɗanɗani zumar ka kafin kowace ƴa mace ta ɗanɗana, hakan nayi sassauci kenan dan kuwa koh na barka kayi auren ba zan ta6a bari kaji daɗin mu'amala da wawuyar da zata zamto matar ka ba, i swear koh sama da ƙasa zasu haɗe ba zanyi ƙasa a guiwa ba Darling ZEEYAD, you just wait and see yadda ake yin ta" ta ƙarashe cikin sakin wani irin shu'umin murmushi kafin ta maida Niƙab ɗin fuskar ta ta rufe tana ficewa daga arear wurin. ******************* __________"Boy meke damunka ne?, you look so moody koh breakfast ka kasa ci" cewar Grandma tana mai shafa lallausar gashin kanshi. Idanun sa a lumshe ya sake tsuke fuska yace "Am fine Grandma, dama inaso ne muyi wata magana dake." "Ka tabbata kana lafiya?." "Yeah Grandma, am all okay." "Toh shikenan, faɗamin maganar." Shiru yayi kafin yace "Am Travelling out of country jibi." "Tafiya kuma, zuwa ina Boy?" ta faɗa cikin sanƴin murya. Idanun sa ya ware akanta jin yadda tayi maganar, kafin kuma ya tashi zaune yace "Come on Grandma, miye kuma na fushi?." "Hmm toh ba dole nayi fushi ba, kayimin maganar da koh a mafarki banson jinta." "Grandma idan naje ba daɗewa zanyi ba, 2months kawai zanyi na dawo." "2 miye?" ta faɗa tana kallon sa cikin waro idanu. "Yes Grandma, inason zuwa dukkanin ƙasashen da nake da ƙadarorin business ɗina ne dan ganin yadda take tafiya." "Hmmm, dama dai kawai haƙura kayi Boy, dan kuwa bana tunanin koh nan da ƙofar shiga MASARAUTA zan sake barin ka ka fita." Murmushi yayi yace "Grandma please, kada kice a'a, Career ɗina ne fah idan ban maida hankali nayi abinda ya dace ba then i will be ruined Grandma." Tsuke baki kawai Grandma tayi tana kauda kai, dan kuwa koh da wasa bata tunanin zata sake barin ZEEYAD yayi nesa da ita. "Okay Grandma, then zamu tafi tare tunda bakyason na tafi na barki." Juyowa tayi ta kallesa tace "A'a ni bance kaje dani ba, tafiyar ce nace ba zakayi ta ba, dan haka ka bar yimin maganar haka, banson jin ta." Riƙo hannun ta yayi cikin nashi yace "Grandma i know kina tsoron kada ki sake rasa ni, but i promise you hakan ba zai faru ba, ki tuna fah kece nake gani nake ji na cikin farin ciki, kinsan idan nayi kwana biyu ban ganki ba da gudu zan dawo, Grandma na dawo nan kenan har abada ba zan sake yin nesa dake ba, muddin ba wai wani abin business ɗina bane ya taso da dole sai naje ni, nan gida na ne banida inda ya fishi musamman da ya kasance kina cikin ta babu ta yadda zan iya yin nesa dashi ba tare da na dawo na ganki ba, you're the source of my happiness Grandma, dah ba dan ke ba then da zuciya ta ta daɗe da bugawa, i thought wata chan daban zata iya bani farin ciki but ke kin nuna min cewa ba zan ta6a samun farin ciki mai ɗorewa ba kamar yadda zan samu a wurin family ɗina, Grandma kece Family ɗina and kullum ina farin cikin kasancewa tare dake, ba zanso yin nisa dake ba indai har ba wai ya zama dole bane" ya ƙarashe yana kallon idon ta dake fidda hawaye. Hannu ya kai ya share mata hawayen yana rungume ta yace "Grandma please, menene kuma abin kuka?, indai har bakyason nayi tafiyar then i promise zan fasa indai har hakan ba zai sake sanƴawa naga hawayen ki ba." Ɗago dashi tayi tana cupping fuskar sa tace "A'a boy, kamar yadda ka faɗa wannan aikin career ɗinka ce, kuma dashi ne Allah yasa kazo har wannan matsayin, ba zanso kayi watsi dashi ba, sabida Allah ne ya kawo ka level ɗin, ba zan hana ka abinda zai kawo maka cigaba ba, kaje ka kaji nasan zaka dawo kamar yadda kayi alƙawari idan kuma baka dawo ba sai dai kazo ka tadda gawa ta" ta faɗa cikin fashewa da matsanancin kuka. Rungume ta yayi ya shiga rarrashin ta tare da kwantar mata da hankali "Grandma zan dawo ki bar faɗin haka, babu inda zan sake zuwa i promise." Sai da tayi kukar mai isarta kafin ta ɗago, kunnen sa ta kama tare da murɗewa tace "Kuma sai da tafiyar ta kama sauran kwana ɗaya tukun zaka faɗamin tsabar lalaci koh?." "Ouch!" ya faɗa yana yamutsa fuska alamun yanajin zafi kafin yace "Grandma it hurts please." Sakin sa tayi tana kama fuskar sa tare da sumbatar sa a goshi tace "Come on" ta faɗa tana rungumo shi jikin ta cike da farin ciki. Murmushin farin ciki ZEEYAD yayi dan kuwa he feels very safe aduk sadda Grandma ta rungume shi, ya kanji duk wata damuwar sa ta ƙaure. ********************* __________Da dare misalin 2:11 na dare, zaune yake kan ƙatuwar dardumar dake ɗakin sa, da alama dai Nafila ya idar yana mai yin tasbih. Motsin ƙarar buɗewar ƙofar da yaji a hankali ne ya sanƴa shi ware idanun sa dake a lumshe yana ɗago da kansa. Tattakin tafiyar mutum ya fara jiyowa ta bayan sa a hankali. Shiru yayi bai juya ba haka kuma bai motsa ba. Ji yayi an dafa shi hakan ya sanƴa sa saurin runtse idanun sa, yayin da bakin sa ke motsi da alama dai addu'a yakeyi. Kafin kuma daga bisani yaji babu hannun an ɗauke, haka kuma babu alamun mutum akan nasa. Shiru yayi still idanun sa a runtse ba tare da ya buɗe ba, kafin kuma ya shiga buɗe su a hankali yana sauƙe su kan wannan baƙar ƙatuwar kuliyar nan. Kallon kallo suke tsakanin su, idanun kuliyar kaɗai ya isa ya tsoratar da wanda yayi tozali dashi, bale shi kuma da yake hango tsantsar ƙiyayya a cikin idanun kuliyar. Murmushi ya saki yana kallon kuliyar kafin kuma a hankali ya furta "Hafeezah Mom?." Ɗan ja da baya kuliyar yayi still idanun sa a cikin na ZEEYAD, kafin kuma ya hau yin wani irin gurnani mai ban tsoro yana iyo wani irin super zuwa kanshi. Caraff ya cafke wuyar kuliyar a hannun shi yana shaƙewa da dukkanin ƙarfin shi, fuskar sa na nuna alamun tsantsar 6acin rai, kafin kuma cikin soft voice yace "Let's put an end to this today Hafeezah, you can try as hard as you can na ganin kin kashe ni but that won't work, your stupid spell won't work on me, ina taya ɗan uwa na YAZEED baƙin cikin samun kamar ki a matsayin mahaifiya, kinyi dukkanin ƙoƙarin ki dan ganin kin kawo ƙarshen rayuwa ta, i know all your moves, plans and steps against me, and now gaki nan a hannu na, but i won't kill you, kinci darajar YAZEED ne kawai, if not for him then nothing would stop me from putting an end to your life" yana faɗin haka ya saki kuliyar, kafin kuma ta fice a ɗari ta window tana zabga uban kuka. Da kallo yabi ta har ta fice, zuciyar sa na mugun yi masa zafi da ƙuna, dukkanin wasu masu neman sa da sharri yana iya gane su tare da lura dasu a dukkanin wani yanayi na 6atar da kansu da sukayi, yanajin dukkanin wani kusanci da maƙiyin sa yayi dashi a jikin shi, wannan ma na ɗaya daga cikin baiwar da Allah yayi masa. Haka nan ya zauna a wurin staring at the dark ba tare da ya motsa ba, sabida iriyar baƙin cikin da yake ciki. A yanzu ya gano Sarauniya Hafeezah, sauran kuma ya gano ta cikin mafarkin sa da yake gani kullum. ****************** _________"So you mean tafiya zakayi gobe, and you didn't even bothered to tell me?" cewar Sadeeq yana kallon sa cikin ɗagun gira. "Yanzu ai iska nake faɗawa right?." "But you should have told me as your best friend, koh da yake ma yanzu you no longer take me as someone very dear to you, you only care about your Grandma, bayan kace muma Family ɗinka ne" ya faɗa cikin rashin jindaɗi. Kallon sa kawai ZEEYAD keyi, nan kuma yace "Hey don't think like that, Grandma ce bata bari na na fita zuwa koh ina, da zaran taji nayi spending awa ɗaya bata ganni ba, zata fara nema na a waya, and yanzu ba gashi a gidan ku nake, so cheer up please." "Yes a gidan mu kake, but ai sai da tafiya ta kama ka tukun zaka zo sanar dani." "Wannan ma na nuna i care about you, if not mai zai kawo ni nan dan sanar da kai zanyi tafiya?." "Whatever, ehem YAZEED yazo ya same ni akan yana neman information..." Maganar mahaifiyar Sadeeq ne ya katse masa abinda yake shirin faɗa. Murmushi ZEEYAD yayi yana amsar plate ɗin dake hannun ta wanda ke ɗauke da wasu mulmulallun abubuwa kamar shadaka tare da faɗin "Nagode Ummie." Kallon ta Sadeeq yayi yace "Ummie ina nawa fah?." "Kai ba kaci naka ba?, ka bari shi yaci tukun tunda anyi kwana biyu ba'a haɗu ba, gobe ma zan sake haɗa wani zaka samu kaci" tana faɗin haka ta bar wurin inda yabi ta da kallo baki sake. Kallon ZEEYAD dake cin abin yana lumshe idanu yayi kafin yace "So ina yi maka magana." "Yeah inajin ka." "YAZEED came to me and..." Ƙarar ringing ɗin wayar ZEEYAD ne ya katse shi, hakan ya sanƴa sa yin shiru kafin ZEEYAD ya ɗau kiran yana faɗin "Grandma?". "Ina gidan su Sadeeq, but yanzu zan dawo i promise." Katse kiran yayi bayan sun gama kafin ya ajiye plate ɗin yana tashi tsaye. "Ba dai tafiya zakayi ba?" cewar Sadeeq. "Grandma na nema na." "Alright, muje" ya faɗa shima yana tashi tsaye. "Wait, hope your aren't annoyed?" ya faɗa yana kallon Sadeeq ɗin. "No, muje nima kasan nayi kwana biyu banje arean naku ba." Mahaifiyar Sadeeq suka yiwa sallama kafin su fice daga gidan. Koh da suka iso MASARAUTA, part ɗin Grandma suka nufa, anan falon ta suka tadda ta zaune ita da Jalilah wanda da alamu dai rarrashin ta take. "Grandma?" ya faɗa yana samun wurin zama idanun sa kan Jalilah dake ta faman 6oye fuskar ta. Gaida Grandma Sadeeq yayi ta amsa kafin shima ya sami wuri ya zauna. "Har ka dawo?" cewar Grandma ɗin. "Yeah Grandma, ba kece kika ce na dawo ba?." "Nikuma kai Boy, daga tambayar ka inda kaje?." "I know it, ba Grandma bace tace ka dawo sabida dah kace mata gidan mu kaje ba zata ce komai ba." Yatsina fuska ZEEYAD yayi yana kauda kansa zuwa ga Jalilah da har yanzu bata ɗago ba. "Kai kyale abokin nan naka, ba ƙaramin wulaƙanci ya ƙaro ba kana ganin sa ɗinnan" cewar Grandma. Dariya Sadeeq yayi yace "Hakanne dai-dai ai Grandma." Murmushi tayi kafin tace "Jalilah tashi mana kuma kin 6oye fuskar." Ɗago da kai Jalilah tayi tana kallon Grandma, a hankali tace "Grandma zai kalli tabon dake zagaye da ido na, idan yaga na zama mummuna fah?" ta faɗa kamar zatayi kuka. Murmushi Grandma tayi tace "Tabon ki bai ƙara miki wani muni ba sai kyau, ai kuma a hankali zai 6ace insha Allah ya dawo normal." Shiru kawai tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannayen ta. ZEEYAD kallon ta kawai yake ganin sai 6oye fuska take taƙi ɗagowa, ta6e baki yayi a zuciyar sa yace _"What's good about her face da har take wani 6oyewa"_ kafin kuma ya kauda kansa daga kallon ta yana mai maida hankali cikin wayar hannun sa. Ɗago da manƴan idanun ta tayi tana kallon sa, ganin hankalin sa na kan wayar sa ne yasa ta miƙewa tsaye tace "Grandma, ni zan wuce." "Yakamata kam, kafin yayan ki ya fara neman ki." Kai ta jinjina kafin kuma ta fara tafiya cikin ɗingisa ƙafar ta. Har ta kai bakin ƙofa ta tsinkayo muryar sa. "Hey" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Dakatawa tayi tana runtse idanu kafin kuma ta sanƴa hannu ɗaya ta rufe idonta na hagu dashi. "Maiyasa kike ɗingisa ƙafar ki?" ta jiyo ya faɗi hakan ta bayan ta. "I...i actually, ciwo ne naji a ƙafar" ta faɗi hakan cikin rawar murya ba tare da ta juyo ba. "Ciwo?, let me see" ya faɗa yana ƙarasawa wurin ta. "Ya fah yi sauƙi, kawai dai har yanzu ban iya taka ƙafar bane mai kyau" ta faɗa tana juyowa ta kallesa. "What's there around your eye?" ya faɗa cikin tsuke face yana kallon ta. Saurin rufe shi tayi da hannu tace "Yeah i know it disgusts you, but am sorry" ta faɗa tana juyawa ta buɗe ƙofar tana niyyar ficewa. "Wait" ya faɗa. Tsayawa tayi tare da juyowa tana kallon sa, nan yace "Take your hands off, who did this to you?." Shiru tayi idanun ta na tara hawaye. "Ohh i see Sooraj" ya faɗa kafin kuma yace "Mai kikayi masa?." Ɗago da idanun ta tayi tana kallon sa kafin cikin kuka tace "Wai...wai sabida yace na daina zuwa wurin ku, dan kawai kai da shi bakwa shiri, shiyasa yayi min wannan dukar a cewar sa wai kaɗan ma na gani idan na sake kuma aikata abu makamcin haka, ka...kashe ni zaiyi" ta ƙarashe cikin sakin kuka sosai. Sosai ran ZEEYAD yayi mugun 6aci da jin abinda ta faɗa, sosai yaji tausayin ta, ya rasa maiyasa masu kyawawan halin cikin su suka kasance ƴaƴa ga azzaluman MASARAUTAR, yasan Sooraj bashida hankali koh kaɗan, but bai ta6a kawowa a ranshi zaiyiwa mace haka ba, macen ma kuma ƙanwar sa, lallai dukkanin abinda akace masa Sooraj ya aikata ba zaiyi musu ba, komin munin abin kuwa. "It's Okay, Stop crying" ya faɗa cikin son lallashin ta. Tsagaitawa tayi da kukan nata, nan ya ciro farar handky a aljihun sa yana miƙa mata yace "Wipe your tears." Amsa tayi kafin kuma ta shiga goge fuskar ta da idon ta dashi. Juyawa yayi ya kalli Grandma da Sadeeq dake kallon su, gira ɗaya ya ɗaga cikin mamaki ganin ta tana murmushi. _"Seems like she is so happy dan na kula yarinƴar nan, stop thinking something else Grandma, it's just that tausayin ta nakeji."_ Juyowa yayi ga Jalilah yace "You should get going." Kai ta jinjina masa kafin kuma ta buɗe ƙofar tana ficewa. Da kallo ya bi ƙofar dashi kafin ya sauƙe ajiyar zuciya yana juyowa ya dawo ciki. Har ya zauna suna kallon sa, cikin mamaki ya ɗago yana kallon su yace "What, maiyasa kuke yimin wannan kallon?." "Are you worried about her?" cewar Grandma. "Of course i am, i mean it's just that ta ban tausayi ne." "Pity leads to love you see" cewar Grandma tana kallon sa cikin murmushi. Wani irin tsuke fuska yayi yace "Stop it Grandma, ba sonta nake ba." "Really, then ka faɗamin wacece kakeso, i know ba zaka rasa budurwa ba." Miƙewa yayi tsaye yace "Yes, i was once in love but yanzu am free, i mean babu wata yarinƴa kuma a zuciya ta i promise" ya faɗa in a serious tone yana 6ata rai. "Really?, you were once im love kuma baka ta6a faɗamin ba?, zo nan kazo ka bani labarin ta." "Grandma i don't want to talk about this please" yana faɗin haka ya fice daga cikin falon. Baki sake suka bisa da kallo kafin Grandma tace "This is serious." Koh da ya fita Garden ɗin part ɗin Grandma kawai ya nufa ya tare a chan. Koh kaɗan he doesn't want to talk about lamarin sa da DEENAH, ya fara mancewa da ita, duk da kuwa tana maƙale cikin zuciyar sa, but ya daɗe da yin erasing duk wani memory nata da yake ɗauke dashi a kwakwalwar sa, baya tunanin yana jin sonta har yanzu, sabida already ya sami komai a wurin Grandma, baya buƙatar wata Girlfriend, koh da kuwa zaiyi soyayya toh ba nan kusa ba, sai ya bari zuciyar sa ta gama hutawa kafin. Hango Jalilah yayi zaune ta chan cikin garden ɗin ƙasar bishiyar cashew, mamaki ne ya kama shi na abinda takeyi a wurin ita kaɗai zaune. Kamar ba zai tashi ba, sai kuma wani abu yace dashi yaje ya duba. Miƙewa yayi daga kan Chair ɗin da yake ya tunkari wurin ta ta yadda ba zata san da akwai mutum a bayan ta ba. Tsaye yayi a kanta yana ganin rubutun da takeyi a ƙasan wurin ita kaɗai. Sai da ya gama karancewa tsaf kafin kuma yace "What are you doing?." A ɗan razane ta juyo tana kallon sa kafin tayi saurin share abinda ta rubuta ɗin da hannun, tana miƙewa tsaye. Ta6e baki yayi a zuciyar sa yace _"Daga baya kenan."_ Cikin in ina tace "I...i ina ɗan zane ne." Kallon ta ya tsaya yi from head to toe kafin kuma ya juya ya barta nan tsaye tare da komawa inda ya taso ya zauna. Mara masa baya tayi inda yake binta da kallo ganin yadda take tafiya cikin ɗingishi har ta ƙaraso wurin sa. Tsaye tayi a kansa ba tare da ta iya cewa komai ba. "Sit" taji ya faɗi hakan. Murmushin farin ciki tayi tana mai zama kusa dashi. Shiru ne ya biyo bayan zaman nasu like kamar 10mins tace "Ka...ka kalli abinda na rubuta a chan?." Juyowa yayi yana kallon ta kafin kuma ya girgiza mata kai alamun a'a. Murmushi tayi tana mai jindaɗin ganin ta zaune kusa da ZEEYAD, ba ƙaramin farin ciki da hakan takeyi ba. "Zan wuce tun kafin Sooraj ya fara nema na." Kallon ta yayi yace "Are you scared of him?." Shiru tayi tana sunkuyar da kai kafin tace "If he founds out cewar nazo gidan ku then he will be mad at me, and bayajin maganar kowa a gidan kowa tsoron sa yake." Murmushin gefen baki ZEEYAD yayi kafin kuma ya tsare yana kallon wani wurin. Miƙewa tsaye tayi tace "Bye." Kai kawai ya jinjina mata ba tare da ya kalle ta ba, nan ta wuce tayi tafiyar ta. Tafiyar take cikin ɗingishi ta fito daga cikin part ɗin Grandma ta nufi hanƴar gidan su. Tsaye tayi tana waro manƴan idanun ta, ganin Sooraj tafe kamar zai tashi sama tsabar bala'in dake cinsa. Wani irin mugun tsoron da fargaba ne suka darsar mata, nan ta hau juye-juyen neman wurin 6uya. Kafin ta ɗaga ƙafa ya dako mata tsawar da ya sanƴa ƴan hanjin cikin ta hautsinewa, tun kafin ya ƙaraso wurin ta fashe da kuka dan kuwa tasan yau tata ta ƙare, ta gama numfashi kenan a duniyar. Yana isowa ya ɗau hannu tare da wanke ta da marin da ya sanƴa ta zubewa nan wurin idanun ta na juyi. Damƙo gashin kanta yayi yana miƙar da ita tsaye cikin muguwar 6acin ran da yake ciki ya hau faɗin "i will make sure na ƙona wadannan ƙafafuwan naki da basu iya zama wuri ɗaya ba once and for all, how many times kike son naja miki kunne akan zuwa gidan nan, but dayake ke mai kunnen ƙashi ce kika bijirewa dokar da na sanƴa miki, wannan karon zan sanƴa dokar da tafi kowacce tsanani, daga yau you will be living in the storage room tare da 6erayen dake ciki, babu ke babu kallon hasken rana ever again, kina wahalar da kanki akan wani ZEEYAD da baisan da kina yi ba, yaron da ya ƙaro uban wulaƙanci baya ganin kan kowa da gashi shi zaki bi ki maƙalewa, ke chewing gum ce or what?." Cikin kuka tace "Dan Allah Akhi kayi haƙuri, ba zan sake ba." "Ba zaki sake ba?, haka kullum kike faɗa no more excuses this time, this will be the last time da zaki sake aikata hakan, i promise you" ya faɗa yana tunkuɗa ta gaba ta faɗi. Kuyangun da suka tsattsaya suna kallon su yabi da kallo, kafin ya daka musu tsawa yace "What are you all staring at, get out of here before i pluck the hell out of your eyes out" ya faɗa cikin hargowa kamar jijiyoyin wuyan sa zasu tsinke. Duk watsewa sukayi cikin sauri dan kuwa sun san halin Sooraj da muguwar mugunta yanzun nan sai ya sauƙe fushin sa akan su, ƙanwar sa ma bai bari ba bale su banzaye. Maido duban sa yayi gun Jalilah yace "Zaki tashi daga nan ne koh sai na tattaka ki?." Cikin kuka tace "Ba zan iya ba, ƙafa ta ta riƙe." "Alright, ki za6i ɗaya koh ki tashi mu tafi kokuma nayi dragging ɗinki a ƙasa har zuwa gida, i don't fucking care kema kin sani." Kallon sa kawai take dan kuwa tana tunanin ya sake targaɗa mata ƙafar ne, sam ba zata iya tashi ta taka ba. "Get up now" ya faɗa cikin tsawa. "I can't" ta basa amsa. Zuwa yayi ya fizgi hannun ta ya fara janta a ƙasa yawa wanda ya sami buhun wani abu mai nauyi da ba zai iya ɗauka ba. Duk abinda suke ZEEYAD na tsaye daga ta part ɗin Grandma yana kallon su, sosai zuciyar sa ke muguwar tafarfasa ganin yadda Sooraj ke jan Jalilah a ƙasa kamar ba mutum ba. Runtse idanu yayi ya juya ya fara tafiya dan kuwa koh kaɗan bayason shiga sabgar da bata shafe sa ba, but tsayawa zaiyi yaga kamar Sooraj na wulaƙanta mace haka kuma ya bar sa ba tare da ya tanka ba. Tsayawa yayi da tafiyar da yakeyi ɗin ya juyo yayi hanƴar fita daga part ɗin. Daga inda yake tsaye ya kwala kiran "Sooraj?." Tsayawa Sooraj dake jan Jalilah a ƙasa yayi yana sakin wani shu'umin murmushi yace "Finally, ka shiga hurumin da ba naka ba." Kafin kuma ya tamƙe fuska yana juyowa yana kallon ZEEYAD dake tsaye hannayen sa zube cikin aljihu. Sakin hannun Jalilah yayi yana tunkuɗa ta gefe, kafin kuma ya fara takowa inda ZEEYAD ke tsaye zuciyar sa cike taf da ƙiyayya yana kallon sa. "You don't have the gut to shout out my name like that you know" cewar Sooraj ɗin yana kallon sa. Kauda ido ZEEYAD yayi daga kallon sa kafin ya ra6a sa ya wuce yayi gaba. Sosai Sooraj yaji haushin rashin tanka masa da baiyi ba, yanajin zuciyar sa kamar ta wantsalo waje tsabar ƙuna. ZEEYAD ƙarasawa yayi gun Jalilah dake zaune tana kuka, durƙusawa yana bin ta da kallo yanajin zuciyar sa na zafi. "Get up" ya faɗa yana kallon ta. Kallon ƙafar ta da yayi mata nauyi tayi kafin kuma ta fara yunƙurin tashi. Ƙafar tata yabi da kallo kafin kuma yace "ba zaki iya tashi ba?." Kai ta jinjina masa alamun Eh, miƙewa yayi tsaye kafin kuma ya kira wasu kuyangun da suka zo wucewa. "Take her home" ya faɗa yana kallon Jalilah ɗin. Amsawa sukayi cike da girmamawa kafin su taimaka mata ta tashi, kallon sa tayi tace "I won't go home Sooraj kashe ni zaiyi." "Don't worry, i will take care of him." "Wow, har kai kanada gut ɗin shiga hurumin da bata shafe ka ba?, this is between me and my sister, why not ba zaka ja girman ka and stayed out of it ba?." Kallon su ZEEYAD yayi yace "Kuje." "Don't you dare take a step" faɗin Sooraj yana mai aika musu da mugun kallo. "Listen abandoned prince, this is between me and my sister, so why don't you stayed out of it, babu wanda ya gayyace ka nan, i mean maiyasa zaka shiga hurumin da bai shafe ka ba?." Chuckling ZEEYAD yayi kafin kuma yace "Yeah babu wanda ya gayyace ni, but don't you think time yayi yanzu da yakamata ka shiga taitayin ka, sabida kana wuce gona da iri abinda kakeyi koh ɗan da ya fito daga cikin sarki baya yinsa, so who the hell do you think you're, lokaci yayi Sooraj, lokacin da yakamata ka girbi dukkanin abinda ka shuka." Kallon sa Sooraj yayi yace "Mai kake nufi da hakan?." Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa tare da yin murmushi kafin yace "Lokacin da yakamata ace an taka maka burki daga duk wani shashanci da isa da kakeji dashi." Dariya Sooraj ya fashe dashi kafin ya tsagaita yana gimtse fuska yace "Waye, wa ya isa ya dakatar dani koh da tsohon ka mai Mar..." "Don't you dare?" cewar ZEEYAD cikin tsukewar fuska yana kallon sa, kafin yace "Are you trying to insult my father infront of me, and kana tunanin zan barka kayi hakan koh, No" ya faɗa cikin tsare gida kafin ya ɗaura da faɗin "Don't let that be the biggest mistake da zaka aikata a rayuwa, insulting my father infront of me is like tsokano dukkanin wani 6acin raina ne, do watch your tongue." Mamaki ne ya cika Sooraj wai yau har ZEEYAD ne ke kare mahaifin sa. "So Sooraj i guess it's time da yakamata a kai ka gidan gyaran hali, Guards" ya faɗa cikin ɗan ɗagun murya. "Mai kake shirin aikatawa wannan karon?" faɗin Sooraj. "The right thing" ya bashi amsa kafin yace "Take him, and make sure kun koya masa yadda ake girmama mace komin ƙanƙantar ta." Muguwar riƙo sukayi wa Sooraj sakamakon son kwacewa da yakeson yi, yana ƙoƙarin kawowa ZEEYAD ɗin hari. "You won't get away with this easily ZEEYAD, i will make sure kayi nadama, i swear wannan alƙawari na ne, baka isa kaci bulus a kaina ba, you will regret this, i will make sure na ɗau fansa na akan koh waye naka ne, gaba tsakani na da kai yanzu ya soma ZEEYAD" yana faɗin hakan ne har aka fice dashi daga arear kamar zai kwace. Kallon Jalilah da itama ke kallon sa tunɗazu yayi. Rungume sa tayi tace "Thank you so much Akhi" hawayen idanun ta na samun damar zubowa. Murmushi ZEEYAD yayi yana shafa doguwar gashin kanta yace "It's alright." "Yo, are these love birds or something?" cewar YAZEED dake ƙarasowa wurin fuskar sa ɗauke da murmushi. Ɗagowa tayi tana share hawayen fuskar ta, kallon kuyangun yayi yace "Take her home." Kama ta sukayi kafin suyi gaba. Juyawa YAZEED yayi yana kallon Jalilah yace "What's wrong with her, she looks like kamar wacce aka kwato daga bakin kura." Murmushi ZEEYAD yayi kawai yana kallon YAZEED ɗin, kallon sa yayi yace "Oh sorry, are you guys in love?." Tsuke fuska ZEEYAD yayi kawai yana juyawa ya fara tafiya. Saurin mara masa baya YAZEED yayi yana ɗaura hannaye kan kafaɗun sa yace "I have something to gist you." "Really?" cewar ZEEYAD. "Of course bro, muje ciki, Grandma ma yakamata taji labarin nan." Murmushi kawai ZEEYAD yayi suna ƙarasa shigewa part ɗin Grandma. *Jiya ina typing ina gyangyaɗi kamar kaina zai faɗi ya tsinke😂🤌🏽, nace ba dole bane nasan zakuyi min uzuri koh, dan kuwa ba'a wasa da bacci wlh🫡* *MHIZZ JIDDHERR...................✍🏽* [8/3, 11:42 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *035...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _________Tsaye take a kitchen tana chopping tomato kan board inda duk hankalin ta yayi nisa bata ma san da abinda ke wakana around ita ba. Ɗaga wuƙar da take amfani dashi tayi tana kallon sa. Babu abinda kwakwalwar ta ke ayyana mata face huɗuba da yakeyi mata na cewar ta ɗau wuƙar ta cakawa kanta, maybe taji sassaucin halin da take ciki kullum. Sosai brain nata keyi mata whisper ɗin aikatawa kanta mummunar abu a duk sadda ta ɗau wani abu da zai iya harming lafiyar mutum. Wuƙar ta kai saitin kan jijiyar hannun ta, inda kuma cikin kanta takejin ana yi mata umarnin ta aikatawa kanta hakan. Sake saita wuƙar tayi tana ƙoƙarin yanka kan nata kamar yadda kwakwalwar ta ke ayyana mata. "Meow" taji kukan kuliya, hakan ya sanƴa ta sakin wuƙar a razane. Duba ta ƙasar ƙafarta tayi tana ɗauko kyakkyawar magen tata a hannun ta. Ajiye ta tayi kusa da ita kafin ta ɗau wuƙar ta cigaba da aikin ta. Komai yinsa take cike da rashin sukunin da take ciki har ta gama girkin tayi serving akan plate ta ɗaura kan tray ta fito dashi falon. A gaban Umma da Jafar ta dire tray ɗin kafin taje ta ɗauko musu abin sha a fridge ta dire musu a gaban su. "Ina naki abincin?" cewar Umma tana kallon ta. "Na ƙoshi" kawai ta faɗa kafin ta wuce ciki ta barsu nan ba tare da ta jira cewar wani daga cikin su ba. Koh da ta shigo ɗakin nata key tasa masa kafin ta haye kan bed tana janƴo bargo ta rufe kanta. Wayar ta ta ɗauka tare da sanƴa ear-piece tana lumshe idanun ta. Yau tsawon sati biyu kenan da samun lafiyar ta, sai dai tunda taji sauƙi ta bidiro da wani hali inda zata rufe kanta a ɗaki ta rufe kanta da bargo komin zafin da akeyi, ta tsani shiga cikin mutane fiye da dah, indai har ba wai school taje ba, shima idan taje har ta dawo ba zata yi magana ba, haka kuma ba zata kula kowa ba, koh da a gida ma ba magana take da kowa ba indai har ba ta kama bane, sosai ta zama so silent, koh kaɗan batason hayaniya, burin ta a kullum bai wuce ta ganta ita kaɗai ba wanda kullum tunanin ta baya wuce ta kasance ita kaɗai a duniyar ba tare da kowa ba, she feels so very empty ji take a yanzu batada wani amfani, haka kuma takejin kowa ya daina sonta hatta Umma da Jafar, ganin kowa take a matsayin masu son kai, she just wished inama kowa yayi disappearing a duniyar nan koh hakan zai kawo mata farin ciki, but a yanzu zuciyar ta a matuƙar cunkushe take haka ma kwakwalwar ta, babu abinda zata gani wanda zai sanƴa ta dariya koh jin farin ciki, jinta kanta take a cikin duhu koh ina nata bayida haske, bata da wata walwala koh annashuwa, she is always bored, kukan da takeyi ɗinma yanzu ya daina zuwan mata, sosai takejin jiki a wannan hali da ta tsinci kanta a ciki wanda har rama ya sanƴa ta. Ta gama yadda da cewa ta rasa ZEEYAD, rashi na har abada, but tasan ita kuma tata rayuwar ta lalace kenan har abada. Juyi kawai take akan bed ɗin ta rasa inda zata sanƴa ruhin ta taji daɗi, ji take ta tsani komai da kowa kamar yadda take ganin kamar kowa ya tsane ta, tana cikin matuƙar ƙuncin da koh da mutum batason taga yana dariya hakan na matuƙar sake ƙona mata zuciya da sake jefa ta cikin halin loneliness. Fiddo da kanta tayi daga cikin bargon tana fuzge earpiece ɗin kunnen ta ta sauƙo daga kan bed ɗin. Bakin window ɗin ɗakin ta taje ta tsaya tana mai yaye labulen window ɗin, tsaye tayi tana ganin waje wanda batasan iya adadin lokacin da ta ɗauka a hakan ba, kafin kuma ta sake dawowa ta zauna kan bed ɗin tana mai zame hulal kanta inda dogon gashin kanta da ba'a kame yake ba ya zubo mata har kan kafaɗa. Jelar gashin ta kama ta shiga lailayewa a hannun ta, kafin kuma ta sake zubewa kan bed ɗin tana mai kwanciya flat idanun ta kan P.O.P ceiling ɗin ɗakin nata. Ganin hakan baiyi mata bane ya sanƴa ta miƙewa zaune, kafin kuma ta tashi tsaye ta shiga zagaye ɗakin, tana mai ra6ar bangon ɗakin. Dawowa tayi ta zauna tana mai facing ɗin mirror, sosai take ganin fuskar ta da ta zama so very pale, idanun nan sun ƙara girma, kallo ɗaya zakayi wa idanun ta ka gane ba ƙaramin jinƴa ta sha ba. Gashin nata ta kama tana mai kallon sa kafin kuma ta miƙe tsaye daga inda take zaune tana zuwa ta janƴo drawer ɗin jikin mirror ɗin ta hau bincika shi tare da ciro scissors a ciki ba tare da ta kuma gyara abubuwan da ta watso daga cikin drawer ɗin ba. Komawa tayi ta zauna tana kallon cikin mirror ɗin kafin ta tattaro gashin kan nata tana kama jelar, inda ta saiti iya inda yayi mata tare da sanƴa scissors ɗin ta yanke shi. Da kallo tabi gashin dake cikin hannun nata, kafin kuma ta watsar dashi tana jefar da almakashin tare da komawa ta kwanta tana rungume kanta. Hakan ma baiyi mata ba, dan kuwa a matuƙar takure take jin kanta. Zubewa tayi a ƙasan ɗakin zaune tare da ɗaukar gashin kanta da ta yanke ɗin ta shiga zare shi ɗaɗɗaya tana jefarwa. Knocking ɗin da ake tayi a bakin ƙofar ɗakin nata bai sanƴa ta ɗago ba, haka kuma batada niyar tashi taje ta buɗe, sai ma yi da tayi kamar bataji ba. "DEENAH?" taji Umma ta kira ta. Shiru tayi bata amsa mata ba saima cigaba da abinda takeyi da tayi. Sosai taji Umma ta dame ta da knocking da kiran sunan ta, yayin da kuma ranta ke sake jagulewa, a fusace ta miƙe taje ta buɗe ƙofar kamar zata haɗiyi zuciya. Magana Umma zatayi sai kuma ta kasa sakamakon ganin gashin DEENAH da tayi a yanke bai wuce iya tsayin wuyan ta bane ya rage. "What...what is this?" cewar Umma tana kallon ta. Kallon ta kawai DEENAH keyi cikin 6acin rai dan kuwa ganin Umma babu abinda yake ƙara mata kullum sai 6acin rai. "Miye hakan kikayi MADEENAH?" cewar Umma tana kamo bakin gashin. Ra6a ta Umma tayi ta shigo cikin ɗakin, inda ta hau binsa da kallo ganin duk ta birkita kayan cikin closet nata ta zubo dasu, ga kuma gashin kanta da ta yanke nata yawo tsakar ɗakin. "What the hell is this DEENAH, meke damunki ne haka?" cewar Umma tana fizgo ta. "She is Depressed" cewar Jafar dake tsaye daga bakin ƙofa. "What...mai kake nufi?" cewar Umma tana ƙarewa DEENAH kallo. "Your daughter is depressed, and i hope you know that depression leads to death" ya faɗi hakan ne cikin muryar dake nuna shima haƙuri kawai yake da halin Umma ɗin. Kallon DEENAH kawai Umma keyi ba tare da tace komai ba. "Depression!, she is too young to suffer from depression, i mean she is not lonely." "Ofcourse she is, you really think that zamu iya bata dukkanin farin cikin da take buƙata ne, you took someone very important away from her, and you expect her ta wanƴe lafiya ba tare da ta faɗa cikin wani hali ba, you're the cause of everything dake faruwa da DEENAH Umma, maybe idan ta mutu nan ne zaki fahimci kuskuren da kika tafka" ya faɗin hakan cikin muguwar 6acin rai kafin kuma ya fice daga ɗakin. Fizge hannun ta DEENAH tayi daga riƙon da Umma tayi mata tana barin mata cikin ɗakin. "DEENAH!, DEENAH?" ta faɗa tana mara mata baya. Riƙo ta tayi tana shirin ficewa daga falo tace "Ina zaki?." Kallon ta kawai DEENAH keyi ba tare da tace komai ba. "Talk to me mana" ta faɗa tana kallon ta. Shiru tayi mata haka ma bata daina kallon ta ba. Rungumo ta Umma tayi jikin ta ta hau bubbuga bayan ta. "Am so sorry Sweetheart, ki yafemin kinji?, i did all this for your own good, but kunƙi ku gane hakan keda ɗan uwanki." Kwace jikin ta DEENAH tayi tana komawa cikin ɗakin ta ta sake sanƴa masa key. Kunnen ƙashi tayi tare da ignoring dukkanin kiran da Umma keyi mata har ta gaji ta daina. ************************** __________"So Grandma as i was telling you, the girl isn't actually my patience and ba ƴar nan ƙasar bace, she is sick aka kawo ta nan treatment, ina yawan ganin ta da wasu nurses suna fitar da ita zuwa motsa ƙafa, and i fell inlove with her, and now i don't know yadda zan sake haɗuwa da ita so i have to wait har sai sun dawo check-up, it's been a month kenan da ƴan sati kenan tun bayan komawar su i have to wait for another month da ƴan sati akai kafin na sake sanƴa ta cikin idanu na, my biggest fear is that kada tace batasona while nikuma nake kwana da ita kullum na tashi da ita, actually Grandma i never thought zan iya son wata yarinƴa kwatankwacin yadda nakejin sonta a raina, the girl is amazing, beautiful and above all she is decent, calm and has an innocent cute face, shine abinda ya birgeni tattare da ita Grandma, i really love her Granny" ya faɗa yana lafewa jikin kujerar da yake kai yana mai lumshe idanun sa. Murmushi kawai Grandma take tunda ya fara bata labarin DEENAH, she is happy for him dan kuwa tamkar yadda ta ɗauki ZEEYAD haka ta ɗauki YAZEED, sai dai halin mahaifiyar YAZEED kaɗai ya isa ya sanƴa ka 6oye irin ƙauna da kulawar da kake yi masa, dan kuwa yanzu sai ta fassara mutum tace ana ƙoƙarin kashe mata ɗa ne koh wani abin, hakan yasa Grandma take ɗan rage wasu abubuwan daga cikin ƙaunar da takeyi masa. Grandma ce tace "Zanso kuwa naga wannan yarinƴar, dan tunda har ka iya faɗawa tsananin tarkon sonta haka i know ta tara dukkanin qualities ɗin da ake buƙata wurin mace ta gari, ya sunan ta dama kuma ƙasar da take, dan kuwa kasan babu abinda nake da buri a kullum da ya wuce naga ranar auren ku da kai da Boy" ta ƙarashe fuskar ta ɗauke da murmushi tana kallon YAZEED. Ɗagowa YAZEED yayi yana murmushi yace "Her name is DEENAH and ita ɗin ƴar Nigeria ce." "Masha Allah, nasha jin labarin matan Nigeria, tabbas ba za'a nuna musu komai wurin iya zaman aure da kulawa da miji ba, uwa uba akwai girmama baƙi da nuna musu tsantsar ƙauna, zanso naga wannan jikar tawa yadda naga kake ta rawar ƙafa akanta ɗinnan." Murmushi YAZEED yayi cike da farim ciki kafin yace "Don't you worry Grandma, soon zan kawo ta ki ganta." Murmushi Grandma tayi tace "Masha Allah, Allah ya kaimu lokacin." Da "Aameen" ya amsa yana murmushi. "Grandma?" cewar ZEEYAD dake tsaye kan stairs yana kallon ta cikin shagwa6e fuska. "Au har ka tashi daga baccin?, toh ƙaraso mana" cewar Grandma tana kallon sa. Sauƙowa ZEEYAD yayi yana zuwa ya rungume ta yace "Grandma, na fara missing naki." "Ai duk kewar da zakayi ba zai kai wanda zanyi maka ba Habibi." Ƙara rungume ta yayi yace "Grandma, why not ba zamuje tare dake ba?." "A'a nikam ka ganni nan banga dalilin da zai sanƴa ni barin ƙasa ta ta haihuwa zuwa wata ba, ka ma bar yimin maganar tafiya tare dani, banga dalili ba." "Where are you going?" cewar YAZEED. Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa yace "Am going to found the love of my life." Ɗan zaro idanu YAZEED yayi yana tasowa yazo kusa da ZEEYAD ɗin yace "Really?, tell me more about her." "What about her?." "I mean, everything about her, i want to know the lucky girl." Murmushi ZEEYAD yayi kafin yace "Well you need to work alot before samun ganin ta." "What, this is serious." "Yeah it is" ya faɗa cikin murmushi. Grandma ce tace "Nima fah na kasa kunne naji koh wacece wannan" ta faɗa tana kallon ZEEYAD. Kallon ta ZEEYAD yayi tare da ɗan yin murmushi kafin yace "Duk kunason ganin ta then work hard." "Work hard?" duk suka faɗa wurin haɗa baki. "Yep" ya faɗa. "Who is she da har sai munyi working hard zamu iya ganin ta?." Murmushi yayi yana kallon su yace "What do you think she is other than Money?." Duka Grandma ta kai masa yana kaucewa, inda YAZEED kuma yayi dariya tare da faɗin "But seriously am so eager to know the lucky girl." "Wa kake tunanin will be the lucky girl other than Jalilah?" cewar Grandma. Murmushi YAZEED yayi yace "Really?, the girl is cool yeah." Duk kallon su yayi kafin yace "Grandma, stop it who told you cewa inason Jalilah?." "Kenan dagaske ne kanason nata kenan, tunda babu wanda ya faɗamin ni na fahimci hakan da kaina." Kallon ta ya tsaya yi kafin kuma ya 6ata fuska yana kauda kai. "I know it ai, kaga yayi shiru koh, he loves her" cewar Grandma. "No Grandma i don't." "Toh ai sai kuma kayi koma dai menene ai gaskiya zatayi halin ta, mudai namu ido, koh ya kace YAZEED?." "Ofcourse Granny, but do you really think dagaske yana son nata, i mean banga hakan tattare dashi ba." "Kai ka kyale ja'iri mana, he is just trying to hide his feelings, bai san na gano komai ba." Jinsu kawai ZEEYAD keyi bai tanka musu, dan kuwa shi baiga dalilin da zai sanƴa shi son Jalilah ba. "Ya bani labarin komai daga cikin rayuwar sa amma ya 6oyemin labarin soyayyar sa sabida bayason na sani" cewar Grandma. "Maybe then, the girl broked his heart" cewar YAZEED. "Kai no way, i pretty know babu yarinƴar da zata yaudari Boy, wannan santalelen Saurayi ai duk wacce ta barshi ya ku6uce mata ta tafka babbar asara" cewar Grandma cikin koɗa jikan nata. "Exactly Grandma, then maybe da akwai abinda shi ya barwa kansa sani." "Koma dai menene ai in tayi tsami zamuji." Tashi ZEEYAD yayi ya bar musu cikin falon, inda duk suka bisa da kallon mamaki, ganin yadda mood ɗinsa ya canza fiye da kullum. Part ɗinsa ya koma yana zuwa ya zauna bakin bed tare da kafe wuri ɗaya da ido yana mai damƙe hannun sa ɗaya, sosai yanayin fuskar sa ya canza zuwa 6acin rai dan kuwa ba zai ta6a manta yadda Umma taci masa mutunci akan dan yaso ƴarta ba, bai so DEENAH bane sabida wani abu nata, haka kuma bai ƙi ta sabida wani naƙasu da ta samu lokacin da take kwance babu lafiya ba, hasalima ya sha haɗuwa da mata iri-iri a rayuwar sa sai dai haɗuwar sa da DEENAH na ɗaya daga cikin tarihin rayuwar sa ne hakan yasa ba zai ta6a manta ta ba, but aduk sadda yayi nisa da cire ta daga cikin kwakwalwar sa sai Grandma koh YAZEED sun ɗauko masa maganar da zai sanƴa shi tunawa da ita, ba ƙaramin fama yasha ba wurin cire soyayyar DEENAH a ransa shi kaɗai yasan halin da ya shiga, koh shi a yanzu yanajin daɗin rayuwar sa without her but baisan maiyasa aduk sadda aka tuno masa da ita yakan ji ƙunci da 6acin rai tattare dashi ba, yasan tayi masa nisa yanzu haka shima yayi mata nisa tunda har ya yanke dukkanin wata alaƙar sa da family ɗinta sabida gudun sake tunato ta, he wants to live a new life ba tare da DEENAH ba, but da wata daban?... Dakatawa yayi da tunanin da yakeyi, tabbas he wants to live a new life tunda gashi nan cikin new world ɗin da babu DEENAH or any of her family, but koh da yace zaiyi sabuwar rayuwa ya mance da ta baya, baya tunanin zaiji soyayyar wata mace daban kamar DEENAH. Tashi tsaye yayi tare da zuba hannaye cikin aljihu ya hau yin safa da marwa cikin ɗakin nasa, yana mai tunanin yadda yakamata ya tafiyar da rayuwar sa. Knocking ɗin da yaji a bakin ƙofar sa ne ya sashi dakatawa da tunanin da yakeyi, kafin ya taka zuwa bakin ƙofar yana buɗewa tare da leƙa kansa. Wata kuyanga ya gani tsaye kanta a ƙasa kafin cikin girmamawa ta fara faɗin "Afuwan babban Yarima, nasan ka haramta mana zuwa koh da kusa da bakin ƙofar ɗakin ka ne." Kallon tsaf ya ƙare mata kamar ba zaiyi magana ba, kafin kuma yace "Uhum?." "Dama Jalilah ce tace nayi mata iso zuwa gunka, nace mata hakan ba zaiyiwu ba..." Lumshe idanu ZEEYAD yayi ya sake buɗewa cike da ƙosawa yace "Let her in" yana faɗin haka ya koma ciki ba tare da ya jirayi cewar ta ba. "What does she want again, i thought she fractured her leg" ya faɗi hakan yana mai zama bakin bed ɗinsa. Bayan kamar mintina biyar ya sake jiyo ƙarar knocking, lumshe idanu yayi cike da ƙosawa kafin kuma ya tashi yaje ya buɗe. Idanu ya ɗan waro ganin ta tsaye tana yi masa murmushi. Kallo ya bita dashi tundaga ƙasa, tana sanƴe ne cikin light-blue ɗin gown, fuskar ta ɗauke da light make-up ɗin da yayi matuƙar amsar cute face nata, inda kuma dogon gashin kanta da babu koh da ɗankwali kamar kullum yasha style da gyara mai kyau wanda ya sake taimaka wa wurin fito da tsantsar kyawun ta. Da kyar ya iya ɗauke idanu akanta yana wani irin murtuƙe fuska ganin yana neman bada kansa a gaban ta. Barin bakin ƙofar yayi yana komawa cikin ɗakin ya zauna kan couch. Da ɗingishin ta ta idda shigowa cikin ɗakin tana maida ƙofar ta rufe. Ɗagowa yayi yana kallon ta ba tare da yace mata komai ba. Ganin kallon da yakeyi mata ne yasa ta faɗin "I...am sorry i know baka tsanmaci zuwa na ba, but ƙafar tawa ta ɗanji sauƙi ina iya taka ta, shine nace bari nazo na sake yi maka godiya, Nagode sosai Akhi." Kallon tsaf ya ƙare mata kafin kuma ya miƙe tsaye yace "Thank you for what?" ya faɗa yana kallon ta. Sunkuyar da kai tayi ganin yadda yake kallon ta, tana wasa da yatsun hannun ta tace "Dah ba dan kai ba then Allah ne kaɗai yasan abinda Sooraj zaiyi min yau, sabida nasan babu abinda zai hana shi aikata abinda ya faɗa koh fiye da hakan ma." Tausayi ta basa nan yace "You don't have to worry Okay?, i promise Sooraj ba zai sake yi miki wani mummunan abu ba kuma, uhm?." Kai ta jinjina cikin murmushi kanta a ƙasa. "I should be going now" ta faɗa. Kallon ta yayi kafin kuma ya jinjina mata kai. "Naji Grandma tace zakayi tafiya gobe, would you mind idan na haɗa maka chips-cracker, i know you will love it, zaka iya ajiyewa kana ci kullum ba zai 6aci ba." Ɗan waro idanu yayi yace "Really?." Kai ta jinjina masa nan yace "Ofcourse i will love it." Ɗagowa tana yi masa murmushi kafin tace "Alright, zan haɗo maka shi zuwa anjima koh gobe." Kai ya jinjina mata kawai kafin tace "Ni zan wuce." "Bye" kawai yace kafin kuma ta fice daga cikin ɗakin yana binta da kallo. Idanu ya lumshe yana komawa ya zauna kan couch ɗin yana cize baki. Ɗan ƙaramin tsaki yaja dan kuwa yaga ta fara shigewa gonar sa dayawa, dole ne ya taka mata burki tun kafin ta zaci shima sonta yake yasa yake barin take ra6ar sa, alhalin shi kawai tausayin ta yakeji haka kurum. ************************ ___________Da dare bayan ya gama hirar sa da Grandma ya koma part nasa, idda shirya kayayyakin sa yayi kafin kuma yabi lafiyar gado. ************************ __________Washe gari ƙarfe takwas na safe ya gama shirin sa, dan haka part ɗin Grandma kawai ya wuce dan yi mata sallama. Sosai Grandma tasha kuka ganin fah dagaske tafiyar zaiyi ya sanƴa ta cewa ta canza ra'ayin ta kan cewar babu inda zaije shi. Sai da ya rarrashe ta sosai tukun kafin ta kwantar da hankalin ta. Da kanta ta raka sa part ɗin mai Martaba dan yi masa sallama, a cikin fada ya same shi zaune akan Throne nasa kamar kullum da manƴan mutane suma Zazzaune. Hango Grandma da ZEEYAD ne yasa shi miƙewa tsaye daga kan Throne ɗinsa yana tako ƴar matattakalar da akayiwa wurin ya sauƙo. Gaisuwar mutunci sukayi da Grandma kafin ya maida duban sa kan ZEEYAD dake kallon sa yana yi masa murmushi. Ɗan murmusawa shima ZEEYAD yayi yana kuma harɗe fuska lokaci guda. "Boy yazo yayi maka sallamar tafiyar tasa ta yau ne." Da mamaki mai Martaba ke kallon su kafin yace "Tafiya?." "Kwarai kuwa, bai sanar da kai bane?" cewar Grandma. Kallon sa sarki yayi kafin yace "Tabbas ya sanar dani." Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon sa, kafin Grandma tace "Ai yau ce tafiyar tasa, watanni biyu kawai zaiyi ya dawo, nasan kaima ba ƙaramin tashin hankali ka shiga da ya sanar da kai hakan ba, amma ya muka iya tunda harkar kasuwancin sa ce zata kaishi." Sosai yanayin fuskar mai Martaba ya canza da jin abinda Grandma ke faɗi cewar ZEEYAD zaiyi tafiya har ma yayi watanni biyu, alhalin bai sanar dashi hakan ba, murmushi mai Martaba ya ƙaƙalo yace "Hakane" kallon ZEEYAD yayi yace "Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, inaso ka manta da dukkanin abinda ya faru a baya ka ɗauka nan ɗin gidan ka ne sannan bakada inda ya fishi, ka dawo lafiya ɗana" cewar mai Martaba yana ɗaura hannaye kan kafaɗun ZEEYAD ɗin. Karo na farko kenan da yaji mahaifin nasa ya bashi tausayi dan haka murmushi kawai yayi tare da jinjina kai kafin kuma ya rungume shi. Sosai mai Martaba ya cika da farin ciki dan kuwa bai tsanmaci zuwan wannan runguma ba, bubbuga bayan ZEEYAD yayi yana murmushi kafin yace "Allah yayi maka albarka." Ɗagowa ZEEYAD yayi yace "I promise you zan dawo." Duk murmushi sukayi kafin kuma ya kama hannun Grandma yace "Grandma, jirgi na ƙarfe goma zai ɗaga, i should be going." Kai ta jinjina masa tana rungume kafin ta ɗago tana bashi kiss a forehead tace "Muje." Kallon mahaifin nasa ya sake yi, ɗan murmusa masa yayi kafin kuma ya kama hannun Grandma su fice daga fadar. Da kallo mai Martaba ya bisu har suka fice, kafin ya sanƴa hannu ya goge ƴar siririyar hawayen da ta zubo masa, yana juyawa ya koma kan Throne ɗinsa. ************************ __________YAZEED, Sadeeq, Grandma dama kuma ZEEYAD ɗinne tsaye a gaban wasu danƙara-danƙaran motoci na azo a gani da alama duk rakiya zasuyi masa. "What are we waiting for, ba cewa kayi 10 jirgin ka zai tashi ba?" cewar Sadeeq. Kallon agogon hannun sa ZEEYAD yayi yace "She must be on her way." "Who?" duk suka haɗa baki wurin faɗa. Hango ta da yayi tana zuwa ne yasa shi faɗin "There she is." Duk maida duban su sukayi gun Jalilah dake zuwa tana ɗan sauri hannun ta riƙe da silver lunch box tana ƙarasowa wurin. "Ku gafarce ni, nayi latti." "Oh come on, muje kada mu sashi ya rasa jirgin" cewar Grandma. Duk buɗe ƙofar akayi musu suka shige, ZEEYAD da bai shiga bane ya juyo yana kallon Jalilah dake tsaye tana kallon sa yace "Aren't you going?." Kai ta girgiza masa kafin kuma ta miƙa masa box ɗin tace "Here, abinda nayi maka alƙawari ne, i just hope zakaji daɗin shi." Kallon ta yake kafin kuma ya sanƴa hannu ya amsa yace "I appreciate it." Ɗan murmusawa kawai tayi tana controlling hawayen dake son kawo mata. "Are you going to cry?" ya faɗa yana kallon ta. Saurin girgiza masa kai tayi tana sunkuyar da kai ƙasa. "Mai zai hana a ƙarasa tattauna dukkanin abinda ake son faɗa a waya?" cewar Grandma cikin ɗagun murya. Duk dariya su Sadeeq sukayi. Kallon ta Jalilah ZEEYAD yayi yace "Bye." Ɗagowa tayi tana kallon sa da Idanun ta da suka cika taf da kwalla, shigewa motar yayi inda aka maida murfin aka rufe. Sai da motar taga ficewar motar daga arear wurin kafin ta juya cikin sanƴin jiki ta koma. ********************** _________"What do you mean na ƙara trying?, that boy almost got me killed a wannan ranar, i wonder maiyasa na kasa samun nasarar ganin bayan sa har yanzu, abinda yafi bani mamaki yake kuma ɗaure min bai wuce yadda akayi ya fahimci nice wannan magen ba." Dariya bokan nata ya sanƴa kafin ya tsagaita yace "I warned you didn't i?, muddin kika takurawa kanki na cewar sai kinga bayan Yarima ZEEYAD toh tabbas zaki iya aikata babban kuskuren da zai kai ki ga kashe Yarima YAZEED maimakon shi, amma kece kika tilasta nikuma banida wata hanƴar da ta wuce wannan da na faɗa miki, muddin kika samu kika cize sa toh tabbas gubar dake jikin haƙorin kuliyar zata yaɗu zuwa chan cikin zuciyar sa ne, a haka zaiyi ta fama har lokacin sa yayi, amma kin kasa hakan, kaɗan daga cikin alamun ba zaki ta6a yin nasara akansa ba kenan." Sosai zuciyar Sarauniya Hafeezah ya cika da mugun 6acin rai nan tace "Tabbas sai nayi nasara akansa tamkar yadda nayi akan Uwar sa, ni Hafeezah banta6a cin burin aiwatar da abu kuma abin yazo ya gagare ni ba, tabbas sai na baka kunƴa wurin aiwatar da ƙudiri na tare da cimma buri na akan ZEEYAD, wannan alƙawari ne na ɗauka" ta faɗi hakan in a serious tone tana zaro idanu cike da muguwar ƙiyayya. Dariya boka ya fashe dashi yace "Kada kice ban gargaɗe ki ba yake Sarauniya ta." Mugun kallo ta wurga masa kafin tace "Ka iya bakin ka, kai kanka kasan gaban wacce kake, bana ɗaukar rainin hankali da zancen banza." Shiru bokan yayi yana mai zazzare idanun shi. "Ka jira ka gani, zaka ga yadda akeyin ta." *********************** _______"Ya bar ƙasar yau?, how on earth then zan samu damar cika burina akansa, who knows yaushe zai dawo koma ba zai sake dawowa ba." Murmushi gayen yayi yace "Aunt miye na wani damuwa dan ZEEYAD ya bar ƙasar?, i mean ba gani ba, miye ba zan iya yi miki ba wanda shi zaiyi miki?." Wani irin mugun kallo ta watsa masa tace "Kai ka kalli kanka da kyau ragon banza yi ɗaya sai kace ka gaji, har miye abin sha'awa a jikin ka da, manage Kawai nakeyi da kai sabida babu yadda na iya ne, but ZEEYAD kai kanka kasan dole he must be different from all men, surar jikin sa kaɗai ya isa ya zautar da mace bale kuma aje ga how good he tastes in bed." Kishi fal cike a zuciyar saurayin yace "Naji yana da kyawun fuska da na jiki, but how sure are you cewar zai iya biyawa mace buƙata bayan ba ta6a gwada shi kikayi ba." Kallon sa tayi tace "Lafiyayyen namiji kallo ɗaya nakeyi masa na gane cewa shi ɗin lafiyayye ne, ka bar cika ni da surutun banza kayi tunanin yadda zamu samo mafita." 6ata fuska saurayin yayi kafin yace "Wai tukun kinma san wani abu kuwa?." "Menene?." "Yarinƴar nan Jalilah na fahimci son ZEEYAD take, sabida inda jiya sau biyu kenan ina ganin shigar ta part ɗinshi, and i saw him rungume da ita jiya seems like sun fara soyayyar ma dan kuwa yau da zai tafi har gifting ɗin abu tayi masa cikin lunch box." Tunda ya fara magana Sarauniya Naseeba ke zaro manƴan idanun ta kamar zasu faɗo ƙasa "Kai wane irin mahaukaci ne daƙiƙi, maiyasa baka sanar dani wannan batun ba sai yau?." Ɗaga kafaɗa yayi yace "Well ai gashi yanzu na faɗamiki, hope zaki bani tukwuici da wannan labari da na kawo miki?" ya faɗi hakan yana lashe baki. Wani irin azababbiyar mari ta ɗauke shi dashi tace "A wannan mummunar labarin kake son na baka tukwuici, kayiwa kanka ka tashi ka fice ka bani wuri yanzun nan tun kafin raina ya idda 6aci, tashi yayi cike da muguwar fusata yana niyyar ficewa tace "Suhail?." Dakatawa yayi ya juyo yana kallon ta kafin tace "Inason ka tabbatar min da gaskiyar zance Jalilah son ZEEYAD take kokuwa, idanma zai yiwuwu ka bibiyi YAZEED koh abokin sa Sadeeq kayi dukkanin yadda zakayi na samomin report ɗin cewa shi ZEEYAD ɗin na sonta kokuwa, idan kayimin hakan toh tabbas kanada tukwuici mai girma." Murmushi yayi kafin ya jinjina kai yana ficewa. "Oh Jalilah darling, mai kuma kike ƙoƙarin sanƴa kanki ciki yanzu, kika shiga gona ta then mai kike tunanin zai faru dake, why don't you just wait a matsayin that decent yarinƴar da na sani, ba zanso illatar da innocent ƙaramar yarinƴa kamar ki ba" ta faɗi hakan cikin harɗewar fuska. *Yawan Comment, Yawan Typing*(kunga bansa hakan a post ɗin jiya ba shiyasa duk kuka karanta kukayi shiru bai wuci mutane biyar bane sukayi comment, ku kunji daɗi nikuma kun barni da takaici koh?, toh ku daiyi hattara😌) *MHIZZ JIDDHER...................✍🏽* [8/5, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *036...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *LONDON, UNITED KINGDOM, (UK).* ___________ZEEYAD ne zaune a wani irin ƙayataccen office shi kaɗai babu abinda kakeji sai ƙarar sketching ɗin da yake da Pencil akan paper ɗin dake gaban sa. Knocking ƙofar shigowa akayi inda ya bada izinin shigowa, wasu mutane ne biyu suka shigo mace da namiji, kallo ɗaya zakayi musu ka fahimci suɗin turawa ne. Macen ajiye tray ɗin lunch ɗin da ta shigo dashi tayi daga chan gefe inda aka ware tare da ƙayata shi kamar falo, kafin kuma ta fice. Wuri Namijin ya samu ya zauna, sai da ZEEYAD ya gama abinda zaiyi cikin zanen kafin ya tattaro wadanda ya zana baki ɗaya ya haɗa kansu cikin wata ƴar madaidaiciya folder yana ɗagowa ya kalli ɗan matashin saurayin dake gaban sa. Hannu ya miƙawa ZEEYAD suka gaisa kafin ZEEYAD yace "Here, aikin su ya kammala, kamar yadda sukayi alƙawarin sai an kammala aikin zasu bada sauran 50% ɗin kuɗin then am waiting" ya ƙarashe yana tura folder ɗin gaban Saurayin. Saurayin mai suna Ben ne yace "Yes sir, but ba'a yi musu painting ɗin da suka buƙata ba." "What kuna nufin kuce bakuyi musu bane komiye?." "No sir bamuyi ba." "But why, na faɗamuku cewa kuyi musu didn't i?." "Yeah, but sir sunce aikin ka suke so ba na wani ba, hakan yasa nayi deciding idan kazo kawai kayi musu." "Mai dame suke so a zana musu?." "Abubuwa goma ne kawai sabida akwai wani tsohon babban Museum da suke son sake ƙawata shi, and sunce suna son aikin ne cikin satin nan." "This week?, but kasan dai ba zanyi sati ɗaya a ƙasar nan ba, but i will try na ganin na kammala musu in 2days da zan ƙara anan, su kuma sauran kuji dasu." "Yes, Boss." ya faɗa. "Anything else?" cewar ZEEYAD. "Yeah Sir, da akwai wani Babban Engineer daga ƙasar Canada, yaga ayyukan ka and he was very impressed sunyi matuƙar tafiya dashi, shima yana buƙatar haɗuwa da kai dan tattauna wasu abubuwa, sannan yace da akwai contracts dayawa da yakeson baka, nayi masa alƙawarin idan kazo zan sanar masa shikuma zai taso tundaga chan yazo ya sameka." Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ZEEYAD ya sauƙe yana lumshe idanu, numfasawa yayi yace "Fine then, but don't forget idan ya wuce jibi then ba zai samu gani na ba, anything else?." "No, sir shikenan we will take care of the rest." "Good" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Tsaye shima MANAGER ɗinsa Ben ya tashi, kafin ZEEYAD yayi gaba yana mara masa baya suka fice daga office ɗin ba tare da yabi ta kan abincin da aka kawo masa ba. Bayan ya bar Company ɗin Guest House ɗinsa ya dawo, sai da ya sake yin wanka sannan yayi taking Nap, bayan ya farka ne kuma ya nemi abinda zai ci. Hot chocolate coffee ya haɗa cikin ƴar madaidaiciyar mug kafin ya fito falo ya zauna ya hau sipping kaɗan-kaɗan. Tunowa yayi da Chips-Cracker ɗin da Jalilah ta bashi, dan haka tashi yayi ya koma cikin ɗaki ya ɗauko ya dawo falon ya zauna. Hawa biyu ne silver lunch box ɗin dan haka buɗe hawa na farko yayi inda yaci karo da farar paper a ciki. Ɗan frowning face yayi cikin mamaki yana ɗauko farar paper ɗin a ciki ya hau jujjuya ta a hannun sa. Buɗe ta yayi inda akayi rubutun ta larabci, kafin ya shiga karantawa. Sai da ya kai ƙarshe kafin ya ɗanyi chuckling beneath his breath yana ajiye paper ɗin, kafin ya ɗau box ɗin ya buɗe ɗayan hawan, nan ne yaci karo da chips ɗin wanda akayi masa yankan chops. Hannu yasa ya ɗauko ɗaya tare da jujjuya shi yana kallo kafin kuma a hankali ya kai bakin sa yana mai yin basmala. Ƙurus-ƙurus haka ƙarar taunar da yayi mata ya bada "it's cracking indeed" ya faɗa yana sake ɗauko ɗaya ya kai bakin sa. Mug ɗin Coffee ɗinsa ya ɗauka tare da kaiwa baki yayi sipping. System ɗinsa da ya jona a chaji ya tashi ya ciro kafin ya hau danne-dannen sa yana cin chips ɗinsa yana haɗawa da sipping coffee. Idanun sa kan system ɗin ya kai hannu cikin box ɗin a karo na ba adadi, nan yaji ta wayam. Sake kai hannun yayi yana yawo da ita cikin kwanon kafin ya ɗago yana maida duban sa kai cike da mamaki yace "Did i really ate it all alone?" ya tambayi kansa. Sam baiji daɗin cinƴe chips ɗin da yayi a zama ɗaya ba, dan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi masa ba, haka nan yayi ta kora zallar coffee ɗinsa yana 6ata fuska. Bayan ya kammala dukkanin aikin da zaiyi cikin System ɗin tasa ne kuma ya ɗau wayar sa ya shiga kiran Grandma. Kamar jira take tana ɗauka tace "Assalamu Alaikum Habiby." Murmushi ZEEYAD yayi yace "Wa'alaikumusalam Grandma, ya kika san cewa nine?." "Ya ba zan san cewa kai bane, bayan sunan ƙasar da kaje ya fito jikin lambar taka." Ɗan murmusawa yayi yace "I miss you so much Grandma." "Nima gani nan ka barni da kewar ka, shima YAZEED ɗin dake ɗan tayani hirar yayi tafiyar sa yin uzurin gaban sa, ni kaɗai yaushe zaka dawo ne?." Murmushi yayi yace "Grandma, koh kwana ɗaya banyi ba amma har kin fara tambayar yaushe zan dawo?." "Toh ai ka barni ne da kewar ka Habibi." Murmushi kawai yayi yana mai son tambayar Jalilah sai dai yasan yana kama sunan ta yanzu Grandma ba zata barsa da tsokana ba. "Ka kira mai Martaba kuwa Boy?" ya tsinkayo muryar Grandma. Idanu ya ɗan lumshe ya buɗe kafin yace "No Grandma?." "Maiyasa?" ta faɗa. "Actually Grandma, i was busy all this while and have to cover abubuwan da banyi scheduled ɗinsu cikin ayyukan da zanyi yau ba, i was very tired and need to rest a bit so i take a Nap, daga nan kuma i had my lunch sannan nayi ƴan wasu ayyuka a system ɗina, so i decided to call you first kafin wani abin ya sake shige min gaba, banma wani samu hutun da zan tsaya kiran mutane ba." "Um um Boy, mahaifin naka ne mutane?, yanzu ka kira ni kaji lafiya ta am totally fine sai dai kawai kewar ka, you should call your father now sabida nasan shima yana chan yana ta tunanin ka, i know he must be so worried about you." "Alright Grandma" ya faɗa a hankali. "Good Boy, toh yanzu sai yaushe kenan?." "Maybe later, maybe tomorrow Morning" ya faɗa. "Toh shikenan, sai na sake jinka koh?." "Yes Grandma take care." Yanke kiran tayi, ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya shiga lalu6o lambar mai Martaba ɗin cikin wayar sa. Ta6e baki yayi ganin bashida contact nasa kafin kuma ya nemo landline ɗin cikin fadar dan kira koh zai same shi. ******************** Duk zaune suke suna yin Dinner kasancewar dare ne a wurin su. Ƙarar Telephone ɗin da ya kauraɗe ilahirin Babban falon ne ya sanƴa su maida duban su gun da Telephone ɗin ke ajiye. Ɗaya daga cikin guards ɗin cikin falon ne ya ƙaraso yana ɗaukar ƙiran tare da karawa a kunnen sa. "Hello" ya faɗa. Kallon inda mai Martaba ke zaune yayi kafin kuma yace "Yes, Who are you?." 6angaren ZEEYAD jin yace masa wanene shi ba ƙaramin haushi yaji ba, dakewa yayi yace chan ƙasan maƙoshi yace "ZEEYAD." Rissinar da kai dogaran yayi kamar wanda yake gaban ZEEYAD ɗin yace "Afuwan Prince, hold on zan kai masa wayar yanzu" ya faɗa yana ɗaukar Telephone ɗin yayi wurin mai Martaba dashi yayin da duk ƴan dining ɗin suka biyo shi da kallo su Naseeba da Hafeezah kamar idanun su zai faɗo ƙasa. Rissinar da kai yayi cike da girmamawa yace "Your Highness Prince ZEEYAD wants to talk to you." Hannu na rawa mai Martaba ya kar6i Telephone ɗin yana karawa a kunnen sa tare da yin sallama. Ajiyar zuciya ZEEYAD ya sauƙe daga ɗayan 6angaren yana amsa sallamar mai Martaba. "How are you Son?." "Am good and you?." "Alhamdulillah" cewar mai Martaba cike da farin ciki sannan yace "Ina fatan ka sauƙa lafiya?." "Lafiya, Alhamdulillah" ya amsa. "Masha Allah." Shiru ZEEYAD yayi kafin yace "Are you Okay i mean ya ƙarfin jikin ka?." Farin ciki ne ya cika mai Martaba nan yace "Alhamdulillah." "And kasha maganin ka?." Kai ya jinjina kamar yana gaban sa yace "Yanzu mukeyin dinner, da zaran munyi kuma zan sha maganin." "Okay, Good" cewar ZEEYAD. YAZEED ne ya taso daga inda yake yana amsar wayar a kunnen mai Martaba yace "Sorry Abhi" kafin yace "Hey bro." Murmushi ZEEYAD yayi jin muryar YAZEED yace "Hey dude, what's up?." "Yane, ka sauƙa lafiya?." "Yeah Alhamdulillah, how is Grandma kaje wurin ta right?." "Yeah, ban daɗe da barin wurin ta ba, but zan koma when i finished having my supper." "Alright good, take care of her please, and...and make sure mai Martaba yasha maganin shi." Juyawa YAZEED yayi yana kallon mai Martaba dake kallon sa yace "Yeah insha Allah, i will" ya faɗa cikin murmushi. Sallama ZEEYAD yayi masa kafin ya katse kiran. Juyowa YAZEED yayi nan duk yaga suna binsa da kallo, wani irin haɗe fuska yayi musamman yadda yaga Ummien sa ke wurga masa mugun kallo, ɗaga gira ɗaya yayi yace "What, why are you all staring?" ya faɗa yana miƙawa guard Telephone ɗin hannun nasa. Duk kauda kai sukayi suna maida duban su kan abincin da suke ci. Kujerar sa yaja ya zauna yana mugun haɗe rai ganin har yanzu mahaifiyar tasa bata daina kallon sa ba. Miƙewa tayi tace "YAZEED?." Ɗagowa yayi yana kallon ta, nan tace "I need to talk to you" tana faɗin haka ta bar wurin a fusace. Da wani irin kallo ya bita kafin ya tashi yana mai mara mata baya. Sarauniya Nazeerah murmushi ta saki, yayin da gefe guda kuma takejin haushin missing ɗin drama da zatayi. Part ɗinta ya bita tana mai rufo ƙofar ɗakin, kallon sa tayi tsaf kafin tace "How many times do you want me to warn to stay away from that boy..." "Oh hold it please, dama abinda ya sanƴa ki kira na nan kenan, i thought it was something important da kikeson discussing" ya faɗa yana niyyar barin ɗakin. "Wait right there" ta faɗa cikin kakkausar muryar dake nuna alamun ranta ya 6aci sosai. Tsayawa YAZEED yayi ba tare da ya juyo ya kalleta ba. Ƙarasowa gaban sa tayi, kafin ta nuna shi da yatsa cikin fushi tace "You just listen to me Okay?, i want you to separate all ties with that boy, you think cewar yana ƙaunar ka kamar yadda kake ƙaunar sa ne, he is supposed to be your enemy, someone da zakayi kishi dashi sakamakon abubuwan da ya mallaka, after all dukiyar da ya tara kuma shi ne wannan zai zamto heir ɗin family ɗinnan, amma duk da haka kullum kana maƙale dashi sabida rashin zuciya irin taka sannan kuma bakasan abinda kakeyi ba, he is more successful than you, you're supposed to be envy of him, baikamata ku dinga haɗa inuwa ɗaya dashi ba, koh bakaga yadda Sooraj yakeyi bane maiyasa ba zakayi koyi dashi ba..." "You just shut up and reserve your words please" ya faɗa cikin 6acin rai yana wurga mata mugun kallo kafin ya ɗaura da faɗin "Kada ki sake kwatanta ni da that fool called Sooraj, i wonder ke wace iriyar mahaifiya ce mai yiwa ɗanta mummunar huɗuba, koh dayake duk a banza kikeyi sabida ba zan ta6a ɗaukar koh ɗaya daga cikin abubuwan da kike faɗamin ba, think about it koh da nake ɗan ƙanƙani ban biyewa gurguwar shawarar ki ba, sai yanzu kike tunanin zanyi obeying ɗinki after nasan ciwon kaina na kuma gane abinda yake dai-dai dama kuma wanda yake ba dai-dai ba?, idan halayen Sooraj na birgeki why not then kawai ki zamar dashi ɗan ki nikuma kiyi watsi dani, listen mother indai dani kikeson amfani wurin cimma mummunar manufar ki then you made the wrong choice, who even cares about wani mulki, as far as inada hanƴar samun kuɗi na wanda zan iya kula da family ɗina ba tare da sun nemi wani abu sun rasa ba then am good with it, but maganar wani mulki ki ajiye shi a gefe, sabida bani da ra'ayin sa, Okay?" ya ƙarashe yana mai watsa mata mugun kallo cike da haushi dama kuma baƙin cikin kasancewar ta mahaifiyar sa. Murmushi mai ciwo tayi tace "Hmm, Wow YAZEED ni kake faɗawa magana son ranka kamar wanda ba nice na sha wahalar haihuwar ka ba, na sha wahalar goyon cikin ka tsawon watanni tara sannan na shayar da kai for good 2years, amma wai yau nice nake sanƴa ka abu kana ƙi har ma kake gayamin magana iya son ranka?, Wow YAZEED lallai wuyar ka ta kai yanka, ni Hafeezah mahaifiyar ka zaka kalla ido cikin ido sannan ka gayamin baƙar magana yadda kaso dan kawai ina neman maka abunda zai fice ka a rayuwa." "No, no, no wait please" ya faɗa cikin ɗaga mata hannu kafin yace "upon all abinda kika lissafo banji inda kika ce kin zaunar dani kin koyamin tarbiyya ta hanƴa madaidaiciya ba, you're not a good Mom Ummie, har abada ba zan ta6a regretting kasancewar ki mahaifiya ta ba muddin baki canza halin ki ba, although nasan Allah ne ya ƙaddara cewar zan zamto ɗanki but...but sam ban ta6a ƙaunar ki ba, ZEEYAD's Mom itace Mahaifiya ta not you." A matuƙar fusace cikin tsawa tace "Enough of this YAZEED, Queen Mother, Queen Mother, Queen Mother, Queen Mother my foot, bakada wani magana kullum da ya wuce ace itace uwarka, koh ka daina yimin maganar matacciyar nan kokuma ranka yayi mugun 6aci a cikin gidan nan, babu wanda ya ta6a ja da magana ta, kai ɗan da na haifa baka isa ka bijire min kuma na kyale ka hakanan ba, ya zama dole ne kabi umarni na YAZEED sannan ka rabu da ɗan wancan matacciyar tunda ba ciki ɗaya aka haife ka dashi, haka kuma kada na kuskura na sakejin labarin ka taka ƙafa zuwa wurin mahaifiyar matacciyar matar nan, that old hag nasan duk itace ke hure maka kunne kana sake bijirewa umarni ne, i have had enough of you da halayen ka YAZEED, whether you like it or not dole ne ka rabu dasu muddin ba so kake na ɗau mummunar mataki akanka ba, kai wane irin wawa ne marar wayon yaro?, ana nema maka arziki kana ta tsiya, kasancewar ka a successful Doctor\Surgeon ba shine zai sanƴa ni haƙura da ƙudiri na ba, why don't you understand YAZEED kasancewar ka Sarki is all i have dreamt of, so i would never allow you to ruin my plans, na daɗe da ɗaukar wannan alwashin a zuciya ta YAZEED, ya zama dole kayimin biyayya sannan kayi dukkanin abinda na sanƴa ka or else" ta ƙarashe cikin fiddo idanun ta da sukayi jaa sabida 6acin rai tana nuna sa da yatsa tace "Or else you will regret it" ta ƙarashe in a serious tone ɗin dake nuna zata iya aikata komai. Light scoff YAZEED yayi yana tsuke fuska yace "You know what Ummie?, do your worst then" yana faɗin haka ya fice a fusace ya bar mata ɗakin nata. Da mugun kallo ta bisa tanajin zuciyar ta nayi mata mugun tafarfasa yawa zai wantsalo waje tace "Kada ka kuskura ka kaini bango YAZEED, zan iya yi maka abinda baka ta6a tsanmani ba, but ya na iya i really need you to fulfill my dreams, thats the only reason kepting me away from doing something bad to you Son, but sooner or later haƙuri na zai iya ƙarewa daga nan kuma zan iya aikata koma menene, koh da kai baka cika min buri na ba then ni zan cika wa kaina da kaina" ta ƙarashe cike da muguwar ƙulin dake take ƙullawa cikin ranta ƙirjin ta na yin up and down tsabar fushin da take ciki. ********************** _______B'angaren ZEEYAD kuwa tunda ya gama waya dasu ya kira Sadeeq suka gaisa. Sallar La'asar yayi kafin ya sake ficewa, shine bai dawo ba har saida akayi isha yayi kafin ya dawo ya kwanta. Washe gari ƙarfe takwas ya gama shirin fita, sai da yayi waya da Grandma tukun kafin ya fice zuwa Company ɗinshi. Bayan yayi clearing dukkanin wasu abubuwan da zaiyi ne kuma ya wuce gym, kasancewar kwana biyu bai motsa jiki ba yasa duk yake jinsa wani iri. Anan ya shafe rabin day ɗinsa kafin ya wuce gida ya huta. Washe gari ma hakan ce ta kasance bayan yaje ya gama komai da komai nasa ya wuce gym sannan ya dawo gida, kasancewar gobe zai wuce wata ƙasar, daga nan kuwa ya wuco Nigeria dan kuwa so yake yaje ya gaida iyayen Khairat, dan kuwa mahaifin ta ba ƙaramin halacci yayi masa a rayuwa ba. ******************** _________Zaune suke da YAZEED da Grandma suna hira, inda duk ta lura YAZEED ɗin kamar da akwai abin dake damunsa. "Ya dai Habibi meke damunka ne, kamar da akwai abin dake damunka dan kuwa ban saba ganin ka cikin halin ƙunci haka ba." Ajiyar zuciya YAZEED ya sauƙe, zuciyar sa na mugun ƙuna yace "Grandma, are you sure cewar Ummie na ce ta haife ni?." "Mai kake faɗa ne haka YAZEED, mahaifiyar ka ce fah dukkanin wani abu da zatayi maka baikamata ka ɗauke shi da tsanani ba dole ne kayi haƙuri ka dinga kauda kai muddin kanason gamawa da duniya lafiya." "But Grandma matar nan batason na gama da duniya lafiya haka ma itama batason gamawa da duniya lafiya, batada wani buri a kullum da ya wuce ta dinga aikata munanan abubuwa take kuma son ɗaura ni akan hakan, Grandma that woman is nothing but a big mess to my life, ta sanƴa ni a gaba all she wanted shine na rabu da ɗan uwana haka ma kema na bar zuwa wurin ki, bansan menene abinda ZEEYAD ya tauye mata ba da tabi ta ɗau karar tsana ta ɗaura masa, i doubt idan ba uwa ɗaya bace ta haifeni da ZEEYAD kawai an ɗauke ni ne an baiwa matar nan just dan kawai bata samu haihuwa, but ba ita ce ta haife ni ba, ban ta6a ganin uwar da take neman buɗewa ɗanta hanƴar faɗawa halaka ba sai wannan matar, she is totally disgusting Grandma, idan nace miki ban tsane ta ba then nayi miki ƙarya" ya ƙarashe maganar kamar zai haɗiyi zuciya dan baƙin ciki, sosai fuskar sa ke nuna alamar tsantsar 6acin rai. Sosai ya baiwa Grandma tausayi, cikin kwantar da murya tace "Kayi haƙuri YAZEED kaji?, addu'a zaka cigaba da yiwa mahaifiyar ka Allah ya shirye ta yasa ta gane dai-dai, but kasan kowace Uwa na ganin abinda ta yankewa ɗanta shine dai-dai a wurin ta, Uwa nada son kai a duk sadda take nemar wa ɗanta wani abu wanda take tunanin zai amfane shi, kada kaga laifin ta na tabbata dah zaka zaunar da ita kayi mata nasiha a matsayin ka na ɗan da ta haifa zata saurare ka sannan ta rage yin wasu abubuwan, take heart dear and ka cigaba da addu'a kaji?" ta faɗa tana shafa sumar kanshi. Kai ya jinjina mata kawai idanun sa na yin jaa, rungumo sa tayi tana cigaba da kwantar masa da hankali tare da basa baki. ************************ ________Sati biyu ZEEYAD yayi a ƙasar Poland kafin ya wuco Nigeria. Ji yayi dukkanin tsigar jikin sa na tashi da isowar sa garin Kano. Kai tsaye motocin da aka tanada wanda zasu ɗauke sa zuwa masauƙin sa ya nufa kafin a buɗe masa ya shiga suka ja tare da barin airport ɗin. Kai tsaye Guest House ɗinsa aka kaisa, wanka yayi ya shirya cikin kaya marar sa nauyi kafin ya sauƙo ƙasa. Ƙarewa gidan kallo yake, tabbas sosai yayi missing gidan, duba da nan ne wurin zaman sa kullum. Ordern abincin da yayi aka kawo masa, sai da yaci tukun kafin ya shiga zagay gidan. Wani corridor yabi cikin jerin ɗakunan dake cikin farfajiyar falon kafin ya buɗe ɗakin farko ya shiga wanda ya kasance ɗakin zanen sa ne. Kallo yake ƙarewa fararen board ɗin zanen nasa dake rufe da fararen kyalle duk sunyi ƙura kafin ya taka ƙafarsa yana idda shigewa ciki duka. Sauƙe idanun sa yayi kan board ɗin da yasan zanen ta ne a jikin su kasancewar ya ware su daban a gefe guda kafin ya taka ƙafarsa zuwa wurin. Hannu yasa ya yaye farar kyallen board ɗin farkon inda zanen fuskar ta lokacin da take yarinƴa ya bayyana. Kallon zanen yakeyi, kafin kuma ya shiga yaye sauran kyallen jikin sauran boards ɗin inda duka zanen kyakkyawar fuskar ta suka bayyana akai, da ɗaɗɗaya yake bin kowane board da kallo yanajin wani abu na taso masa daga chan ƙasan zuciyar sa, yayin da kuma ta wani fannin zuciyar sa cike take fal da 6acin ran da mahaifiyar ta ta ƙunsa masa da irin cin mutuncin da yayi mata dan kawai ya haukace a son ƴar ta. Idanun sa ya lumshe yanajin yadda zuciyar sa ke zafi sosai. Ficewa yayi daga ɗakin ba'a daɗe ba kuma ya dawo da galan ɗin kero dama kuma Ashana a hannun sa. Ciro hotunan zanen yayi ya haɗe kansu wuri ɗaya, kafin kuma ya shiga tsiyaya musu kerosene ɗin. Ta rigada ta zama tarihi cikin rayuwar shi, dan haka baya tunanin ajiye wani abu game da ita as a good idea, Kyarta ashanar yayi ya shiga kallon flame ɗin wutar har sai da ta kusa mutuwa kafin kuma ya jefa ta kan photunan drawing ɗin, nan duk suka kama da wuta. Sam baiji daɗin ƙona su ba, but bashida wani option da ya wuce yayi hakan. Ɗakin ya baro kafin ya fito harabar cikin gidan nasa, securities yayi wa maganar suje su kula da wutar idan ta gama cinƴe hotunan su kashe sannan su tsaftace ɗakin, kafin ya dawo ciki suna mara masa baya inda ya haura sama su kuma suka nufi ɗakin zanen dan zuwa aiwatar da abinda ya sanƴa su. Satin ZEEYAD biyu ya gama abinda ya kawo sa, inda ya sayar da duk wata ƙadara tasa da yasan yana da ita a Nigeria. Tsaye yake gaban mirror yana gyara dressing ɗin blue ɗin suit ɗin dake jikin shi, wanda ba ƙaramin kyau da sake fiddo hasken fatar sa yayi ba. Makullin motar sa ya ɗauka tare da ficewa daga cikin ɗakin yana sauƙowa ƙasa tare da ficewa zuwa harabar gidan. Inda motar sa ke ajiye ya nufa ya buɗe ta ya shiga, kasancewar an buɗe masa gate ya sanƴa shi jan motar tare da barin harabar gidan zuwa gidan su Khairat. ******************* ________Kasancewar securities ɗin gidan sun waye shi ya sanƴa su buɗe masa tafkekiyar gate ɗin gidan yana kutsa kai ciki. Parking ɗinta yayi a parking space, kafin ya buɗe ta ya fito yana maƙala baƙar shade ɗinsa. Bai wuci 5mins a tsaye ba ya hango Khairat ɗin da iyayen ta sun nufo shi. Khairat ganin ZEEYAD ba ƙaramin sake losing control ɗin kanta tayi ba, wani irin ƙara tasa tana iyowa kanshi da gudu da niyyar rungume shi. Cire baƙar shade ɗin fuskar sa da yayi haɗi da wulla mata wani irin mugun kallon da ya kusa kifar da ita a wurin ne ya sanƴa ta saurin jan burki tana jan reverse haɗi da shan dukkanin jinin jikin ta. Kauda kansa yayi daga gareta yana wani irin tamƙe fuska yawa wanda aka aiko masa da tragic labari. Khairat jiran iyayen ta tayi suka ƙaraso kafin ta mara musu baya. Cike da sakin fuska da farin cikin ganin sa da sukayi suka tar6e sa. ZEEYAD ɗan sakin fuskar sa yayi kafin ya shiga gaida su cike da girmamawa kamar yadda ya saba. Sosai sukaji daɗin yadda yayi musu, ganin bai nuna musu wani girman kai koh makamancin hakan ba, inda sukayi masa iso zuwa cikin gidan. Babu musu ya mara musu baya ba tare da ya koh dubi gefen Khairat dake ta aika masa kallo kamar ta ɗauke shi ta haɗiye ba, ganin yadda yaƙara kyau haɗi da sakeyin wani irin fresh, ga kuma tarin kwarjini da haibar dake tattare dashi yasa ta kasa yin magana sai kallo kawai da take ta binsa dashi har suka isa ƙayataccen falon cikin gidan. Zama yayi cikin ɗaya daga cikin lallausan cushions ɗin falon, yana sake tamƙe fuskar sa. "Welcome Son, ashe da baka manta mu ba?" cewar Momyn Khairat cikin farin cikin ganin sa da tayi. Ɗan Murmusawa kawai yayi nan Dady yace "Nima i thought koh dagaske ya mance damu ɗin, sai kuma yau gashi ya kawo mana surprise visit." Murmushi ZEEYAD yayi yace "Ba zan ta6a mantawa daku ba, no matter how rich and famous i become, ku ɗin tamkar iyaye ne a wuri na." Murmushi duk sukayi kafin Daddy yace "Masha Allah, ya ka baro mutanen dama kuma mahaifin naka?." "Alhamdulillah Sir" ya faɗa. "Masha Allah, ke baki iya gaisuwa bane?" cewar Daddy yana kallon Khairat dake ta bin ZEEYAD da eyes yawa zata haɗiye shi. A ɗan razane ta ɗago tana sosa wuya tace "Welcome." Bai kalleta ba haka kuma bai amsa mata ba sai ma yi da yayi kamar bai jita ba, sosai zuciyar ta ta sosu da hakan sai dai maimakon ya bata haushi taji ya burgeta sosai, dan kuwa komai yayi mata a yanzu ya kai yayi ɗinne, ɗan babban sarki kamar sa kamata yayi yaja aji fiye da yadda yakeyi ma a yanzun. Inviting ɗinsa sukayi zuwa dining sai dai fur ZEEYAD yaƙi amincewa a cewar sa zai wuce ne sabida akwai wuraren da zaije. Basu tilasta masa ba tunda ra'ayin sa ne hakan, sai dai Khairat koh kaɗan bataji daɗi ba ganin zai tafi. Har bakin motar sa suka rako sa, sosai ya lura da Khairat a matse take da son yi masa magana, sai dai koh kaɗan bai bata fuskar hakan ba, bale ma ta nemi kawo masa raini koh wani abin. Ita kanta Khairat ta san ZEEYAD ba ajin ta bane dama chan ma karfin hali kawai takeyi na yi masa gori kala-kala dan kawai mahaifin ta ya taimake shi a wani fanni na rayuwar sa, amma tunda taji labarin asalin koh wanene shi taji tayi mugun raina kanta, musamman yanzu da ta sauƙe idanun ta a kansa ta ƙara gasgata lamarin cewar ZEEYAD yayi mata nisa kuma ba zai ta6a zama nata ba. Sallama yayi da Momy da Daddy, kafin yaja murfin motar sa ya rufe yana tada ta. Sosai idanun Khairat suka cika taf da kwalla zuciyar ta nayi mata mugun zafi, wai yau ita ZEEYAD ke ignoring kamar baisan da wanzuwar ta a duniyar ba. Tana gani yaja motar sa ya bar cikin gidan, inda ta fashe da wani irin matsanancin kuka tana yin ciki da gudu. ********************** ___________Jafar ne tsaye bakin ƙofa yana ta rarrashin DEENAH da tun wayewar garin yau bata fito ba, gashi har ana neman ƙarfe biyun rana yanzu. "DEENAH dan Allah ki buɗe ƙofar nan haka, why are you doing this?." "DEENAH?" ya sake faɗa ba tare da nuna wani gajiyawa ba. "DEENAH please i beg you ki buɗe ƙofar nan, i have been standing here for almost 30mins yanzu amma kinƙi buɗe ƙofa, are you sure you're alright?." "DEENAH?" ya faɗa yana knocking door ɗin. "Please Lil sis, open the door, i just wanna see how you're doing and i promise ba zan takura miki ba dan Allah DEENAH." Tunda yazo bakin ƙofar ɗakin yake ta bugu tare da kiran sunan ta, amma koh kaɗan baiji motsin ta ba, hankalin sa ne ya fara tashi koh wani abin ya same ta ne, sake knocking ƙofar yayi da ɗan ƙarfi yana kiran sunan ta "DEENAH?." Shiru ya sake ji hakan yasa shi barin bakin ƙofar zuwa ɗakin Umma. Zaune ya same ta da Qur'an a hannu tana karantawa, cikin mugun fushin da yake ciki yace "Umma anƴa kin damu da ƴarki kuwa?." Tsagaitawa tayi da karatun bayan ta kai ƙarshen aya kafin ta rufe tana ɗagowa ta kalle shi. Kallon ta yakeyi shima kafin yace "You doesn't seem to care at all, DEENAH locked herself up tun jiya da dare har yanzu bata buɗe ƙofar ba i have been knocking on her door for almost 30mins now, amma koh motsin ta banji ba, amma ke banga wani damuwar rashin fitowar ta tun safe da batayi ba tattare dake, kuma koh takawa bakiyi kinje kin duba kinji koh tana lafiya ba, Umma what has come all over you ne wai?, you've changed alot ba kamar dah ba" ya faɗi hakan ne cikin fushin da yake ciki. Miƙewa Umma tayi daga zaunen da take tana zuwa ta ajiye ƙur'anin wurin ajiyar sa, kafin ta cire Hijabin jikin ta tana hanging ɗinsa tace "Zaka iya ficemin daga ɗaki idan ka gama yimin faɗa na Uba na." Mamaki ne ya cika Jafar ganin Umma koh nuna damuwa akan hakan batayi ba. "Koh dai bakaji mai nace bane na maimaita?." "Umma what's wrong with you?, DEENAH tana chan..." Bai ƙarasar ba ta katse shi cikin faɗa da cewa "Ya kake so nayi mata Jafar, mai kakeso nayi, wane irin ƙoƙari ne banyi ba na ganin DEENAH ta bar wannan halin nata na ƙunshe kai a ɗaki?, wane irin ƙoƙari ne banyi ba na ganin na jawo ta jiki na tare da bata dukkanin kulawar da take buƙata kaima kayi ƙoƙarin hakan amma mai ya ragu cikin halayyar ta?, babu, sai ma abin da yayi gaba, ya toh takeson ayi mata tunda ta kasa haƙuri ta rungumi jarabawar da Allah ya ɗaura mata, a hakan takeson samun sauƙi kullum itace cikin tunani da kuka, akanta aka fara rashin masoyi komiye, dah mutuwa kuma shi ZEEYAD ɗin yayi ya zatayi da ranta kenan, bata ga damar samawa kanta sauƙi ba Jafar, bata shirya rungumar ƙaddarar ta ba, kai kanka ka sani nayi dukkanin iya ƙoƙari na amma tayi ƙeƙe da kunne bataji, jiya a gaban ka ta gama yimin rashin kunƴa ta kuma ce na fita harkar ta, har cewa tayi ta tsane ni, ni Jafar upon all mutanen dake duniya sai ta rasa wa zata tsana sai ni, menene banyi muku ba a rayuwa?, wane irin farin ciki ne ban baku ba, ban ta6a bari kunyi kukan rashin mahaifi ba, baku ta6a neman abu a guna kun rasa ba koh na hana ku ba, koh da kuwa ace dukkanin kuɗin da ya rage min kenan indai kuka kawo buƙatar ku inayi muku Jafar, yau dan kawai DEENAH tayi rashin masoyi sanadiyya ta na zama maƙiyar ta, ta ɗau karar tsana ta ɗaura min har take ikirarin bana sonta, yanzu da abinda yakamata ta saka min kenan, ai gani nake inada iko wurin za6awa DEENAH mijin aure, yau dan na hana ta abu ɗaya a rayuwar ta sai na zame mata gagarumar mai laifi a wurin ta, har kaima kake goya mata baya kuke ganin rashin kyautatawa ta, dukkan ku da abinda zaku sakamin dashi kenan Jafar?, Bakomai" ta ƙarashe maganar cikin share hawayen fuskar ta tana samun bakin gado ta zauna, zuciyar ta nayi mata mugun zafin da ita kaɗai ta san abinda takeji. Sosai jikin Jafar yayi sanƴi da maganganun Umma, sai yanzu yake gano rashin kyautatawar su a gareta, Umma mahaifiyar su ce, sannan babu farin cikin da bata basu a rayuwa ba, haka kuma she has the right ɗin yanke decision koh wani choice cikin rayuwar su, tabbas indai har kanason gamawa da duniya lafiya toh fah ya zama dole kabi maganar Mahaifiya, koh da kuwa ace bata wani bada gudunmawa sosai wurin gina rayuwar ka ba, but Umma babu abinda batayi musu ba, bata ta6a bari sunyi kukan rashin mahaifi ba kamar yadda ta faɗa, ta kan sadaukar da dukkanin wani farin ciki nata wurin ganin nasu farin cikin koh da kuwa it will cost her dukkanin abinda ta mallaka a wannan lokacin, ta tsaya wurin gina rayuwar su tare da basu tarbiyya mai kyau, tayi rayuwar ta ne wurin gina su tare da tafiyar dasu kan hanƴa madaidaiciya, tayi sacrifing alot akan su, and now dan tayi sanadiyyar barin ZEEYAD cikin rayuwar su suka ɗau laifi suka ɗaura mata, ba tare da sunyi nazarin cewa maybe Allah bai ƙaddara cewa zasuyi rayuwa ta har abada dashi ba, ba tare da sunyi nazarin mutane dayawa su kan zo su bar cikin rayuwar ka ba, wasu ma mutuwa sukeyi, wasu kuma zakuyi zaman mutunci dasu kamar ba za'a ta6a rabuwa ba sai dai kuma ka wayi gari babu su sunyi maka nisa wataƙil kuma shikenan ba zaku sake haɗuwa ba kuma sai a lahira, wataƙil hakan ce ta kasance tsakanin su da ZEEYAD ma maybe su sake ganin sa wataran maybe kuma ba zasu sake haɗuwa a duniya ba, Umma tayi sanadiyyar barin sa cikin rayuwar su ne, amma idan kayi dogon nazari dama chan haka Allah ya tsara rayuwar tasu zata zo ta kasance, basuda wani abin da ya wuce kawai suyi haƙuri, kowa na yin laifi kasancewar ɗan adam ajizi ne, amma su idanun su ya rufe sun ɗaurawa mahaifiyar su laifin abinda ba ita ta tsara ba kacokan akanta, ba tare da sunyi tunanin Allah ne ya tsara cewa rayuwar su zata kasance hakan ba, sannan kuma abinda yakamata suyi shine haƙuri musamman ma DEENAH da takejin itace tafi kowa rashi. Kallon Umma dake ta kuka yayi bayan dogon nazarin da yayi, nan kuma duk yaji tausayin ta ya kama shi yanajin babu daɗin dukkanin abinda sukayi mata a ransa, kunƴa ce ta lullu6e shi wai yau sune suka sanƴa mahaifiyar su mai son ganin farin cikin su a kullum kuka. Zuwa yayi ya rungume ta yana patting nata a baya ba tare da ya iya furta komai ba. DEENAH dake tsaye bakin ƙofar ɗakin tun bayan barin ƙofar ɗakin ta da Jafar yayi ta buɗe ta fito tana sauraren su saurin komawa ɗakin ta tayi tana rufo ƙofar tare da zuwa bakin bed ta zauna tana fashewa da wani irin matsanancin kuka. Kuka take sosai harda shessheƙa kamar zata shiɗe zuciyar ta nayi mata zafi sosai. Wato kenan ta rasa ZEEYAD har abada kenan?, dan kuwa taga har yanzu Umma na kan bakar ta bata ga alamun zata sauƙo nan kusa ba, ita kuma maybe ta mutu zuwa lokacin da zata sauƙo ɗin. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽* [8/7, 1:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *037...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*Masha Allah ZEEYAD FANS CLUB, Gaskiya Comments naku ba ƙaramin burgeni tare da sanƴa ni farin ciki yake ba, haƙiƙa kuna matuƙar ƙoƙari wurin faranta min, babu abinda zance daku sai Allah Ubangiji ya bar Kauna, ya faranta muku kamar yadda kuke faranta min, yayi wa rayuwar ku data iyayen ku, ƴaƴan ku dama kuma mazajen ku da ƴan uwanku albarka🤲🏽🥰, Nagode sosai da iriyar ƙaunar da kuke nunamin , Allah Ubangiji ya bar zumunci*_ *LONG PAGE🤸🏽‍♀️* _________Jafar ne zaune yake ta rarrashin Umma da har yanzu bata sauƙo ba, sakamakon zuciyar ta dake mugun zafi da halin DEENAH. "Menene banyi wa DEENAH ba a rayuwa, mai ta nema ta rasa daga gareni, wai akan ɗa namiji DEENAH ke furta min kalmar tsana har take ikirarin kada nazo kusa da ita bata buƙatar gani na, take gani na a matsayin mai son zuciya." "Umma dan Allah kiyi haƙuri haka nan, DEENAH tana cikin mawuyacin hali and am definitely sure ita kanta tayi nadamar abubuwan da ta faɗa miki, Umma she is depressed am sure batasan tayi wasu abubuwan ba, dan Allah ki bar kukan nan haka hakan zai iya jawo fushin Ubangiji akan mu, ace mun sanƴa mahaifiyar mu zubda hawaye, please i beg you ki bar kukan nan haka" ya faɗa cikin rarrashin ta. Hawayen ta ta shiga gogewa yana taya ta kafin tace "Insha Allah, Allah ba zaiyi fushi daku ba banyi kukan nan dan jawo muku fushin Ubangiji ba, sai dai ina yinsa ne kawai dan tausayin DEENAH bakomai ba." Ajiyar zuciya Jafar ya sauƙe kafin yace "Umma nasan abunda DEENAH tace miki ne ya ƙona miki zuciya haka, dan Allah Umma kiyi haƙuri ki yafe mata, nima kuma ina neman gafararki, sannan ki cigaba da yiwa DEENAH addu'a har Allah yasa ta dawo dai-dai, na tabbata ita kanta ba zataji daɗin abinda tayi miki ba." "Bakomai Jafar, komai ya wuce, insha Allah zan cigaba da yi mata addu'a sannan kaima inason kayi hakan, Allah yayi muku albarka duka." "Aameen Umma, insha Allah zanyi yadda kika ce, kuma Umma yakamata ita ma kanta DEENAH ɗin ta tashi tsaye da addu'a, sannan ta yawaita karatun Alƙur'ani sabida rage shiga ƙunci, am sure idan ta riƙe wadannan abubuwan Allah zai kawo mata ɗauki tare da gusar mata da dukkanin wani damuwa da ƙuncin ta." "Ai sai dai kai kayi mata magana, koh bakaji abinda tace min bane?." "Umma ba zaki biye mata ba, am sure a yanzu babu abinda tafi buƙata kamar ke, it's just that kawai halin ƙunci da baƙin cikin da take ciki ne zai sa ba zata bar ki ki ra6e ta ba, Umma baikamata ki biye mata akan wannan furucin da tayi ba, DEENAH tafi buƙatar ki fiye da kowa a yanzu i know kinyi dukkanin ƙoƙarin ki, but indai har kika cigaba da janta a jiki am sure zata warware ta kuma manta komai." Shiru Umma tayi kafin tace "Toh shikenan Jafar zanyi hakan." "Yauwa Umma, zanje na sake confronting ɗinta naga koh zata buɗe ɗakin." Bata ce komai ba ya tashi ya fice zuwa ɗakin DEENAH, ganin ƙofar a buɗe ya sanƴa shi turawa yana leƙa kansa. Zaune ya ganta tsakiyar bed ɗin tayi crossing ƙafar ta tana zane da hannun ta jikin bedsheet ɗin. Sallamar da taji yayi ne yasa ta ɗago kanta tana kallon sa. Idda shigowa ɗakin yayi yana maida ƙofar ya rufe, DEENAH maida kanta ƙasa tayi tana cigaba da abinda takeyi. "DEENAH?" ya kira ta calmly. Bata ɗago ba haka ma bata amsa masa ba, zama yayi bakin bed ɗin yana facing nata, bai ce da ita komai ba sai kallon ta kawai da yakeyi, kafin kuma daga bisani yace "Do you mind us going on an outing?." Tsayawa tayi kafin kuma ta ɗago kanta tana kallon shi, kai ya jinjina mata yace "Maybe zaki ɗan ji sassaucin abinda kikeji." Maida kanta tayi tace "No." "Why?" ya tambaye ta. Shiru tayi kamar ba zata amsa ba kafin kuma tace "I don't feel like going out." Shiru Jafar yayi kafin yace "What of idan mukaje Cinema anjima?." "No" ta amsa. "Ice-cream?." Kai ta jinjina masa tace "No." "Burger?." Ɗagowa tayi tana kallon sa, kallon ta yayi yace "You want Burger right?, i will get it for you." "I...i don't want anything" ta faɗa tana sadda kai ƙasa. Kallon ta yake kafin yace "Look DEENAH, lets talk serious Okay, why are you doing this to yourself?." "You need to move on DEENAH, ZEEYAD ba zai dawo ba, he is gone forever kenan DEENAH, ki bar yawan sanƴa kanki cikin ƙunci da tunanin sa haka, i know yanzu shima yayi moving on da rayuwar sa..." "No" ta katse shi kafin ta ɗaura da faɗin "Kai kacemin yana sona sosai and he is ready to sacrifice everything for my sake, and you expect him yayi moving on da rayuwar sa so soon haka bayan abinda Umma tayi masa, i know that he still loves me sannan zai iya dawowa gareni ko wane lokaci ne" ta ƙarashe wani irin siririn hawaye na biyo mata fuska. "Look DEENAH Stop blaming Umma for all this, she is not at fault..." "She is not at fault then laifin wanene kenan, she is responsible for everything thats happening to me." "Stop it DEENAH" ya faɗa a tsawace, kallon idon ta yayi yace "Let me tell you maganar gaskiya, ZEEYAD ba zai ta6a dawowa ba sannan ba zai ta6a neman ki ba, haka ma ba zai ta6a dawowa ƙasar nan ba, stop deceiving yourself, ke kina nan believing cewa yana tunanin ki kamar yadda kika addabi kanki da nashi kullum ba tare da kin san meke faruwa chan tattare dashi ba, who even knows koh ya riga da ya manta ki, ke kina nan kina baiwa kanki wahala, people change DEENAH, and sometimes for the worse, you need to understand this." Sosai zuciyar DEENAH ke zafi da maganganun Jafar, pillow ta janƴo tana wurga masa in a rude manner tace "You're lying, i know bai manta dani ba, and he still loves me sannan zai dawo anytime for me, he still loves me, Okay?." Ran Jafar ne yayi mugun 6aci, sai dai ya dake tare da girgiza kai yace "You have changed alot DEENAH, ba haka kike dah ba, you need to get back to your old self tun kafin lokaci ya ƙure ki rasa rayuwar ki a banza, while shi kuma ya samu wacce yake so yayi auren sa, ke kuma ki tsaya tunanin sa ya kashe ki tunda shi kaɗai ke sonki mu baki ɗauke mu matsayin masoya ba, i can't believe how rude you've been to our Mom jiya na cewar kin tsane ta sannan bakyason ta kusa dake, kinsan how badly kika yi hurting nata kuwa?, instead of kiyi nadamar hakan kinzo nan kina tunanin abinda ba zai fice ki ba, look DEENAH daga yau nida Umma kowa ya fita harkar ki kije kiyi dukkanin abinda kike ganin shine dai-dai da rayuwar ki, babu wanda zai sake interfering a rayuwar ki bale ki faɗa masa babu daɗi, just do what you think is right for you" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Tashi tsaye tayi itama a fusace tace "Yes i would do what i think is right for me" tana faɗin haka ta nufi wurin closet ɗinta tare da buɗe shi ta ciro akwatin kayan ta, kafin ta buɗe sauran 6angare biyun ta shiga fiddo da kayayyakin ta tana wulla su kan bed. Da kallon mamaki Jafar ke binta dashi har ta gama fiddo kayayyakin, kafin ta ɗago akwatin zuwa kan bed ta buɗe shi ta fara zuba kayayyakin nata a ciki. "What...what are you doing DEENAH?." Bata kula sa ba sai ma cigaba da jera kayayyakin nata da tayi a ciki. "Am sorry DEENAH, i didn't mean to..." katse shi tayi da faɗin "Am doing what i think is right for me, koh ba kai bane ka bani go ahead ɗin yin hakan?." "Yes nace kiyi dukkanin abinda kika ga dama but bance kiyi packing kayayyakin ki ba, where do you think you're going?." "Zan tafi inda za'a nuna min so da ƙauna tare da kulawa ne" ta ƙarashe tana zipping akwatin bayan ta gama jera kayayyakin tare da sauƙo dashi ƙasa tana jan shi. Da sauri Jafar yaje yana tare bakin ƙofar yana kallon ta yace "What has come all over you DEENAH?." "Mai kuke so nayi muku a cikin gidan, no one values my feelings, babu wanda ya nuna kulawar sa akan abinda nakeji, bakuda abin cemin kullum da ya wuce na manta shi sannan nayi haƙuri, but kun ƙi ku gane cewa it's so hard for me, nikaɗai nasan mai nakeji ba zaku ta6a fahimta ba." "Let her go Jafar?" ya tsinkayo muryar Umma a bayan shi. Juyowa yayi yana kallon Umma yace "Let her go..., to where exactly?." "To where ever i want" cewar DEENAH ɗin. Juyowa yayi yana kallon ta kafin yace "No, you aren't going anywhere, not even nan da ƙofar falo." "Alright then, try and stop me" ta faɗa tana shirin wucewa ta space ɗin da ya bari. Saurin sanƴa hannun sa yayi yace "I told you babu inda zakije DEENAH." Kallon sa tayi tace "Ka barni na wuce." "Please DEENAH" ya faɗa. "Kai kace nayi dukkanin abinda naga dama." "Yeah, i said that but bance ki haɗa kayan ki ki tafi ba." "Move out of the way" ta faɗa tana kallon sa cikin fushin da ya fara taso mata. Kai ya girgiza yace "Maybe over my dead body." A tsawace cikin sarƙewar numfashi ta sake cewa "Stay out of the way, now." Idanu kawai ya zuba mata ba tare da ya ɗauke hannun nasa kuma ya motsa ba. "Stay out" ta faɗa cikin azababbiyar fushin da tazo mata tana ɗauke fuskar sa da mari tana huci inda kuma numfashin ta ya shiga sarƙewa. Umma kwalalo idanu tayi tana rufe baki da hannayen ta biyu lokacin da DEENAH ta mari Jafar. Jafar ɗago da fuskar sa da tayi jaa yayi yana kallon DEENAH da itama shi take kallo. Fashewa tayi da kukar nadamar da tazo mata tana zubewa kan guiwowin ta. Sosai take dizgar kukan kamar ranta zai fita, inda duk suka tsaya kallon ta babu wanda ya iya tanka mata. Shiɗewa ta farayi da kukan inda kuma numfashin ta ya shiga seizing kukan nata na yayyankewa, duk sake maida duban su kanta sukayi kafin suyi wani yunƙurin kuma tayi collapsing a wurin, Jafar ne yayi saurin taro ta yana kiran sunan ta "DEENAH?." Umma da sauri itama ta shigo ɗakin tana riƙo ta tare da kiran sunan ta "DEENAH?." Kallon Jafar da shima duk hankali tashe tayi tace "Ya dai...meke faruwa ne Jafar, Mai ya same ta?." Kallon Umma Jafar yayi kafin ya miƙe tsaye yace "Umma bari na ɗauko key ɗin mota mu kaita asibiti" yana faɗin haka ya fice da sauri. Jijjiga ta Umma ta shiga yi cike da tashin hankali tana kiran sunan ta. Dawowa Jafar yayi riƙe da key ɗin mota a hannun sa yace "Let's go Umma." Cicci6ar ta yayi tare da yin waje da ita, Umma ɗaki ta wuce ta ɗauko mayafin ta cike da tashin hankalin da take ciki ta mara masa baya. ************************ ________Likitoci ne suka duƙufa kan DEENAH da numfashin ta yayi low sosai suna iya bakin ƙoƙarin su wurin ganin sun ceto rayuwar ta. Umma dake ta kai kamo babu abinda take sai kukan halin da DEENAH ke ciki, tana tsoron kada ta rasa ƴar tata a wannan karon. Jafar rarrashin ta kawai yake shima cikin dauriya, kallo ɗaya zakayi masa shima kaga tashin hankali ɗauke kan fuskar sa. Da kyar da siɗin goshi likitoci suka samu numfashin ta ya ɗan daidaita, dan haka Oxygen suka sanƴa mata da wasu na'urorin su kafin su fice. Tare ɗaya su Umma sukayi bayan fitowar su yayin da sauran suka wuce uzurin gaban su. Cike da muguwar 6acin rai Likitan ke kallon su kafin yace "Muje Office" yana faɗin haka yayi gaba inda suka mara masa baya. Cire coat ɗinsa likitan yayi yana lanƙaya ta jikin hanger, kafin yaja kujerar sa ya zauna yana nunawa su Umma kujerar dake facing ɗinsa alamun su zauna. Zama sukayi idanun su akan sa inda duk sun ƙagu suji abinda zai ce. Wani file ya ɗauko ya ɗanyi rubuce-rubucen sa a jiki kafin ya ɗago yana kallon su yana mai harɗe yatsun sa yace "We did everything that we can na ganin mun ceto rayuwar ta and alhamdulillah munyi nasarar hakan, but inaso ku faɗamin abu ɗaya for how long ƴar ku ke fama da ciwon da ta tashi dashi and tun bayan samun sauƙin ta kun koma an sake duba lafiyar kwakwalwar ta kokuwa?." "I guess ta kai kusan 5months a kwance babu lafiya, sannan maganar check-up wata uku likitan ya bamu mu dawo yanzu haka sati ɗaya ne ya rage mu sake komawa" cewar Umma. Ajiyar zuciya doctor ɗin ya sauƙe kafin yace "Well kamar yadda kuka sani tun farko kwakwalwar ƴar ku ba ƙaramin buguwa yayi a accident ɗin da ta samu ba, baya ga haka tayi fama da cutar stroke in the other hand kuma memory loss, i mean tabbas abin yayi mata yawa but nayi mamakin ganin yadda rayuwar ƴar ku ke shirya faɗawa halaka a karo na biyu fiye da wanda tayi fama dashi dah amma baku wani ɗau abin serious ba kuka barta." "Mai...mai kake nufi likita?." Gyara zama likitan yayi yace "Tun bayan farfaɗowar ta da kuma dawowa hayyacin ta da tayi, baku ga wasu physical changes tattare da ita ba, be it wurin ɗabi'u, tafiya koh magana ba?." Shiru Umma tayi tana kallon Jafar dake kallon likitan kafin tace "Tabbas mun gani..." "Why then baku yi mata abinda takeso ba?, koh kun manta cewa brain nata bai gama warkewa completely ya dawo normal ba, kuka zo kuka ƙara mata stress ɗin da kwakwalwar ta ba zata iya ɗauka ba har ya kai ga jawo mata matsalar depression, wanda ba ƙaramin illa yake dashi ba haka ma kuma ba saurin warkewa ne dashi ba komin maganin da za'a baka kasha except indai ba na kusa da ita bane suka jawo ta jikin su tare da bata dukkanin kulawa dama kuma abinda zai sanƴa ta farin ciki, sannan su tabbatar tana shan magungunan ta kan lokaci haɗi da cin lafiyayyen abincin da zaiyi boosting brain nata, kunsan ƴarku bata gama fita daga haɗarin ciwon da tayi a baya ba, instead of ku jata jikin ku ku nuna mata tsantsar kulawa tare da bata dukkanin abinda zata buƙata taji daɗi, but No bakuyi hakan ba sai ma sake jefa rayuwar ta da kukayi at risk" ya ƙarashe cikin faɗa kamar zai ham6are su. Tunda ya fara magana Umma ke ta hawayen da ta kasa controlling ɗinsu, shiru office ɗin ya ɗauka kafin kuma likitan ya sake cewa "Well i guess banida wani abu da zan iya yi muku yanzu wanda ya wuce nace muku ku maida ta wurin likitan da kuka gani farko tun kafin rayuwar ta ta gama faɗawa cikin illa ta koma gidan jiya or fiye da hakan ma." "Yes Doctor, zuwa yaushe kake ganin yakamata ace an maida ta ɗin?." "Today, tomorrow, Next Tomorrow, but indai ya wuce sati koh kuka ɗau wani dogon time then the risk is yours to take." "Alright, Thank you" ya faɗa kafin ya kalli Umma yace "Umma muje." Kamata yayi ta tashi tsaye kafin su fice a office ɗin yana rarrashin ta. Ɗakin da aka kwantar da DEENAH suka shiga, inda suka ganta kwance unconcious an laƙa mata abin shaƙar numfashi, ga kuma drip da aka jona mata da sauran abubuwa. Kuka Umma ta fashe dashi tana faɗin "Kaico na!, ki yafe ni DEENAH nasan duk nice dalilin faɗawar ki wannan hali, kinyi gaskiya da kika ce bamusan abinda kike ji ba, ya Allah ka yafe ni." Patting ɗinta Jafar keyi a baya yana faɗin "It's alright Umma, ki bar faɗin haka, dukkanin wani abu dake faruwa nada dalilin faruwar sa, stop blaming yourself for all this please, kin ta6a ganin inda uwa ke ƙoƙarin kai ƴar ta halaka ne, bale kuma ke da kullum kike fatan rayuwa mai inganci wa DEENAH?, dan Allah ki bar sawa kanki damuwa and DEENAH insha Allah zata tashi in good health har tafi dah ma, just keep praying." Kai ta jinjina tana share hawayen fuskar ta kafin yace "Zanje na fara shirye-shiryen komawar ku Egypt, DEENAH will be fine insha Allah, yakamata ace zuwa jibi dai kuna chan." Kai kawai ta iya jinjina masa, kafin yaja mata kujera ta zauna shi kuma yana ficewa. ************************ __________B'angaren ZEEYAD yau 3days da barin sa Nigeria zuwa wata ƙasar, ayyukan sa yake gudanar wa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Yayin da kullum kuma suna cikin waya da Grandma ɗinsa 24\7, inda sauran masa 1month ya ƙarashe abubuwan da suka kaisa ya dawo. Yau ma zaune yake cikin wani ƙayataccen madaidaicin falo mai ɗan karen kyau, ƙafar sa ɗaya kan ɗaya yana mai daddana wayar sa. After some seconds ya kai wayar kunnen sa, murmushi ya saki bayan an ɗau kiran yace "Grandma?." "Habiby, ya kake?." "Am food Grandma, and you?." "Alhamdulillah, Alhamdulillah Habiby sai kewar ka kawai, ka duba fah yau watan ka ɗaya baka nan, kada kaso kaga yadda duk na rame." Murmushi mai ɗan sauti yayi yace "Grandma kenan, kada ki damu maybe na gama abubuwan da suka kaini zuwa next two weeks, so bana tunanin zan cike sauran wata ɗayan." "Toh alhamdulillah, naji daɗi sosai Boy, Allah yasa dai hakan ta yiwu." "Insha Allah Grandma" ya faɗa cikin murmushi. "Toh ga Jalilah nan na son magana da kai, tace tunda ka tafi baku gaisa ba." "Yeah" ya ɗan faɗa. "Assalamu Alaikum" yaji ta faɗa. "Wa'alaiki Assalam" ya amsa mata. "Ina wuni Akhi?." "Lafiya, am good, and you?." "Lafiya ƙalau alhamdulillah, ya ayyuka?." "Alhamdulillah" ya amsa a takaice. "Masha Allah, Allah ya taimaka, dama gaisuwa ce." "Aameen, Thank you" ya faɗa kafin yace "Grandma?." Muryar Grandma yaji a wayar tana faɗin "Masha Allah Boy, Allah ya taimaka yayi maka Albarka." "Aameen Yaa Rabb Grandma." "Toh sai anjima koh?." "Yeah" ya faɗa kafin kuma ta katse kiran. Murmushi ne yayi forming kan fuskar sa yana komawa da ya jingina da kujerar da yake kai yana lumshe idanu. ********************** *EGYPT* ________Yau kwanan su Umma ɗaya a asibitin sai dai tunda aka shiga da DEENAH ba'a bari ta ganta ba har yanzun, sosai ta nesa da tunanin da ta lula. Dafa ta akayi nan ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula ta ɗago tana kallon nurses ɗinnan tsaye akanta. Murmushi suka sakar mata suna zama gefen ta. Wacce ta dafa ta mai suna Marwa ce tace "You look so disturbed Aunt, ki kwantar da hankalin ki DEENAH will be alright, ashe kun dawo ma sai yanzu da muka fito muke ganin ki." Ɗayar mai suna Azeemah ce tace "Please Aunt, kada ki wani sawa ranki damuwa, DEENAH zata samu lafiya ta tashi kamar bata ta6a yi ba." Kai kawai Umma ta jinjina musu, nan suka cigaba da rarrashin ta tare da kwantar mata da hankali. ****************** _______Sai Ƙarfe goman dare aka barta taga DEENAH. Kwance take kan bed tayi nisa cikin tunani, shigowar Umma ne ya sanƴa ta maida duban ta gun ƙofa tana kallon ta. Kallon ta Umma tayi tana ƙarasowa ta zauna gefen ta. "DEENAH?" ta faɗa tana shafo fuskar ta. Da idanu kawai DEENAH ke binta ba tare da tace mata komai ba. Hannun ta Umma ta kama tana cigaba da kallon ta, DEENAH zame hannayen ta tayi daga cikin na Umma tana kauda kanta zuwa ɗayan 6angaren. "DEENAH, akwai abinda kike buƙata ne nasa a kawo miki?." Kai kawai ta girgiza mata alamun A'a ba tare da ta juyo ta kalle ta ba. "Kin tabbata bakyajin ƴunwa, tun fah shekaran jiya baki sanƴa komai a cikin ki ba, sai ruwan nan da ake ƙara miki." "Bana jin ƴunwa" ta faɗa. Ajiyar zuciya Umma ta sauƙe kawai ba tare da tace komai ba ta buga tagumi tana kallon wuri guda. Ba'a jima ba aka buɗo ƙofar aka shigo, nan duk suka maida duban su kan YAZEED dake tsaye. Sallama yayi yana ƙarasowa ciki, inda duk suka bisa da idanu Umma na amsa sallamar tasa. Zuwa yayi ya gaida Umma cikin girmamawa yana tambayar mai jiki. "Alhamdulillah, she is much better now" ta faɗa. Ɗan murmusawa yayi yana kallon DEENAH da ita ma shi take kallo. "Hi DEENAH" ya faɗa. "Hi" kawai ta basa amsa. "How are you feeling now, how is your health?." "Alhamdulillah" ta bashi amsa. "Masha Allah" kawai ya faɗa. Sadeeq ne ya shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakin sa, amsa masa sukayi yana ƙarasowa ciki. Buga kafaɗun YAZEED yayi yana yi masa murmushi, murmushin shima YAZEED yayi yana kauda kai zuwa kan DEENAH. "Well done Aunt" cewar Sadeeq. "Thank you Doctor" ta faɗa. "Sadeeq" ya faɗa. Ɗan murmusawa kawai tayi kafin ya kalli DEENAH da ta kasa ɗauke idanun ta kan YAZEED, gyaran murya Sadeeq yayi yace "Hello patient, ya jikin ki?." Kallon sa tayi tace "Alhamdulillah." "Good, akwai wani abin da kikeji ne kuma?." Kai ta girgiza masa alamun a'a, kafin tace "I just want to be alone." Duk kallon ta sukayi kafin yace "Alone?, ofcourse you need some rest, and in the other hand you need something to cheer you up." Kallon sa take kafin yace "Maybe a kunna miki TV ɗinnan a sanƴa miki Cartoon ɗin Tom&Jerry, i know it would surely cheer you up." Ɗan murmusawa tayi a zuciyar ta, Tom&Jerry sai kace wata yarinƴa ƙarama, Ofcourse shine best cartoon ɗinta lokacin da take ƙarama but yanzu bata tunanin tana ma da lokacin kallo. "A kunna?." "Ofcourse ka kunna what are you still waiting for, she needs something to cheer her up, right DEENAH?" cewar YAZEED yana kallon ta. Kallon fuskar sa da yanayin maganar sa kawai take, sosai yaso yayi mata shige da ZEEYAD sai dai idan ta tuna fuskar ZEEYAD ɗin sai taga basu wani shige, ɗauke duban ta tayi daga kansa tana lumshe idanun ta. Umma ta san sarai ita ce DEENAH bata so kusa da ita shiyasa ta faɗin tana son kasancewa ita kaɗai. Miƙewa tayi daga zaunen da take tare da kallon Sadeeq tace "Tana son Cartoon ɗin Tom&Jerry, ka kunna mata shi am sure it will cheer her up kamar yadda ka faɗa, i will be outside so that tayi enjoying kallon ta" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin. Har ta fice DEENAH bata buɗe idanun ta ba, muryar YAZEED taji yana faɗin "Alright DEENAH, ni zan wuce ina da patient ɗin da zan duba, take care Okay?." Kai kawai ta jinjina masa tana kallon sa, murmushi yayi tare da ɗan baiwa Sadeeq blow ta baya yana ficewa daga ɗakin. Sadeeq kamar yadda ya faɗa jona mata kallon yayi tare da kaiwa tashar da akeyin Cartoon ɗin, juyowa yayi yana kallon ta yace "Alright DEENAH, Enjoy" ya faɗa cikin murmushi yana ficewa. Da kallo ta bisa kafin kuma ta maido duban ta kan TV ɗin da takejin ƙarar fashe-fashen da Tom da Jerry ɗinsa keyi tana kallo. Ta kai kusan 20mins tana kallo, sai dai babu wani murmushi koh dariya da yayi forming kan fuskar ta, sosai ita kanta tayi mamakin hakan ba kamar dah da idan tana kallo tayi ta kyakyata dariya yawa mahaukaciya sabuwar kamu ba, har sai Umma tayi mata magana kafin ta rage, tuno da irin yadda takeyi a wancan lokacin idan tana kallon ne ya sanƴa ta sakin light smile wannan moments ɗin na Playing cikin memories ɗinta. Lumshe idanu tayi tana cigaba da sakin murmushin. ******* "I told you right, just look at yadda take smiling" cewar Sadeeq da idanun sa ke kan System suna kallon DEENAH wanda da alama seta camera sukayi a ɗakin. Murmushin farin ciki Umma ta saki, kallon ta YAZEED yayi yace "Don't worry Aunt, she will be fine insha Allah." Kai Umma ta jinjina tana share hawayen farin cikin da suka zubo mata. "Oh wait... what makes her sad again?" cewar Sadeeq yana kallon cikin system ɗin ganin ta bar yin murmushin fuskar ta ta koma kamar dah. Umma ji tayi farin cikin da take ciki ya fara gushewa. DEENAH dake kwance so bored ka ƙarar katun ɗin da ya cika mata kunne, idanu ta lumshe tare da sanƴa hannu ta toshe kunnuwan ta kafin kuma in a calm voice cikin zazzaƙar muryar ta ta fara rero waƙa _Here's to the ones that we got_ _Cheers to the wish you were here,but you're not_ _Cause the Drinks bring back all the memories_ _Of Everything we've been through_ _Toast to the ones here today_ _Toast to the ones that we lost on the way 'cause the drink bring back all the memories, and the memories bring back, memories bring back you_ _There is a time that i remember_ _When i did not know no pain_ _When i believe in forever_ _And now everything would stay the same_ _Now my heart feel like December_ _When somebody say your name_ _'Cause i can't reach out to call you, but i know i will one day, yeah_ _Everybody hurts sometimes_ _Everybody hurts someday, Ayy-Ayy _But everything gon' be alright, go and raise a glass and say, Ayy_ _Here's to the ones that we got_ _Cheers to the wish you were here but you're not_ _'Cause the drink bring back all the memories_ _Of Everything we've been through_ _Toast to the ones here today_ _Toast to the ones that we lost on the way 'cause the drink bring back all the memories, and the memories bring back, memories bring back you_ _Doo-Doo, Doo-Doo-Doo-Doo_ _Doo-Doo, _Doo-Doo-Doo_ _Memories bring back memories bring back you..._ Buɗe idanun ta tayi shiru lokacin da aka buɗo ƙofar ɗakin aka shigo. Maida duban ta tayi kan Sadeeq da YAZEED dake tsaye suna kallon ta. "Aren't you enjoying the show?" cewar Sadeeq. Cire hannayen ta tayi daga kunnuwan ta tana maida duban ta kan TV ɗin, kafin kuma ta kalle shi ta jinjina masa kai. "Oh strange" ya faɗa yana idda shigowa ɗakin tare da zuwa ya kashe kallon. Kallon YAZEED dake tsaye bakin ƙofa ya harɗe hannaye a ƙirji tayi, murmushi ya sakar mata kafin kuma tayi saurin kauda kanta tana maida idanun ta lumshe. Ƙarasowa inda YAZEED ke tsaye Sadeeq yayi kafin cikin harshen larabci yace dashi "Why are you staring at her like this?, go on maybe ta saki jiki da kai kuyi hira." Kallon sa YAZEED yayi kafin yace "Tana yi like bata sanni ba, she will be like, _"hey, who are you?"_, _"Do you know me?."_, _"Have we shared any relationship before."_ Irin tambayoyin da zata jero min kenan, and what answer should i gave her, tell her that we met lokacin da bata dawo hayyacin ta ba or what?." Dariya Sadeeq yayi yana jawo sa suyi waje tare da rufo ƙofar. Buɗe idanun ta tayi tana bin ƙofar da kallo. *********************** ________Duk inda ka zaga lungu da saƙon part ɗin Grandma toh kuyangu mata ne ke ta kai komo kowacce na busy da aikin da aka sanƴa ta. Sosai akayi decorating part ɗin da flowers masu ɗan karen kyau da ɗaukar hankali, ga kuma wutar lantarki da ta haska koh ina na part ɗin, sai kuma wani irin fitinannen ƙamshi mai sanƴaƴa ruhi ɗan Adam dake tashi ta kowane lungu da saƙo. Magana Grandma dake sauƙowa kan beni keyi cikin ɗan faɗa take cewa "Wai mai kukeyi ne har yanzu baku idda gyaran nan ba?, Prince na kan hanƴa zai iya isowa kowane lokaci yanzu, amma ku nan kunzo kuna aiki simi-simi yawa wadanda basuda jini a jiki, ku kuma da kuka zuba min ido kuna kallo yawa wacce suka ga sabuwar halitta fah, zaku wuce ne koh sai ranku ya 6aci yanzun, iyayen tsegumi kawai." Da ɗan gudu Jalilah tazo tana kamo hannun Grandma tare da ɗanyin juyi da ita tace "Grandma?, irin wannan kyau ɗin da kikayi yau ba dole kowa ya tsaya kallon ki ba" ta faɗa cikin ɗan dariya. "Ohh ni yarinƴar nan ai sai ki sanƴa ni jin hajijiya da wannan juyi, yoh toh ba dole nayi kyau ba abin ka da kyakkyawa" ta faɗa cikin murmushi. Murmushi itama Jalilah tayi kafin Grandma tace "Toh maza kema jeki ki shirya dawuri kafin ya iso kada ya raina ki tunda kin kammala girkin." "Toh Grandma" ta faɗa cike da farin ciki tana hawa kan matattakalar benin cikin gudu. Murmushi Grandma da tasha kyau cikin shigar ta ta alfarma tayi tana cigaba da masifar ayi sauri a gyara komai yayi steady prince ya kusa ƙarasowa. 6angaren Jalilah kuwa tunda ta haura sama ta shige cikin ɗaya daga cikin ɗakunan dake jere a corridor ɗin. Sosai ɗakin yake da bala'in kyau da ɗaukar hankali. Cikin farin ciki ta nufi haɗaɗɗen closet tare da ciro wasu gown dresses kala huɗu masu matuƙar kyau da ɗaukar ido. Zuwa tayi ta tsaya gaban mirror ta shiga gwaggwada su a jikin ta ba tare da ta sanƴa su ba ganin koh wanne ne zaiyi mata kyau. Ta kai minti goma a tsaya ta kasa za6ar ɗaya a ciki, knocking taji a bakin ƙofar ɗakin dan haka ba tare da nuna wani tsanani ba ta bada izinin shigowa. Buɗe ƙofar akayi aka shigo inda wata mata da ba zata wuci shekaru arba'in da biyar ba ta shigo bayan ta wasu kuyangun ƴan mata biyu biye da ita. Kallon su Jalilah tayi tana ƙanƙance cikin mamaki kafin tace "Hanifa Humairah, mai kuka zo yi anan, and wacece wannan?" ta faɗa tana kallon matar. Dariya matar wacce tunda suka shigo take ta bin ɗakin da kallo tace "Come on Jalilah, kina nufin baki gane ni bane, babu wanda bai sanni ba cikin MASARAUTAR nan, kodai baki ta6a jin labarin Kiki bane, ai nice nan Kiki" ta ƙarashe cikin dariya. Ɗan murmusawa Jalilah tayi tace "Kiki!, wane irin suna ne haka?, yi haƙuri amma bangane ki ba." Juyawa kiki tayi ta kalli ƴan mata biyun dake tsaye a bayan ta tace "Ku kuyi mata bayani mana." Kallon ta ɗaya daga cikin su tayi tace "Ranki ya daɗe, ita ɗin mahaifiyar Rumaisa ce, tazo ne dan maye gurbin aikin da Rumaisa keyi miki kafin ta samu lafiya ta dawo bakin aiki." Tunda ta fara magana Kiki ke jinjina kai tana washe haƙora. Murmushi Jalilah tayi tana zuwa ta kamo hannayen ta tace "Ke mahaifiyar Rumaisa ce?, gaskiya ƴarki nada matuƙar kirki da iya aiki mai kyau, tana da juriya da ƙoƙari sosai wurin yi min dukkanin abinda nake buƙata, itace kuyanga mafi soyuwa a gareni, sai dai ba zan bari kiyi aiki a gurbin ta ba, kinga kin haife ni baikamata ace kinyi min wasu abubuwan ba, Hanifa da Humairah sun maye gurbin aikin da Rumaisa keyi kada ki wani ji damu kinji?." 6ata rai Kiki tayi alamun bataji daɗin hakan ba kafin kuma tace "Haba ranki ya daɗe, Rumaisa da kanta ta turo ni nan dan kulawa dake, duk wani aiki da kika ga tana yi miki duk a wuri na ta gaje shi ni na koya mata komai, naji ance yau Yarima ZEEYAD zai dawo kina ganin baikamata ace kinyi shiri mai matuƙar kyau wanda zai siye zuciyar sa bane?." Blushing Jalilah tayi kafin tace "Hakane..." "Toh kada ki wani ji damuwa ni nan zan kula dake sannan nayi miki shiri mai kyau wanda zai sanƴa shi kasa ɗauke idanu akanki" cewar kiki cikin katse ta. Murmushi tayi tace "Toh Nagode sosai." Kallon kayayyakin dake ajiye Kan bed tayi kafin tace "A cikin wadannan zaki sanƴa?." Kai Jalilah ta jinjina mata kafin tace "Eh amma tunɗazu na kasa za6ar guda ɗaya da yayi min kyau" ta faɗa cikin ɗan frowning face tana turo baki. "Kada ki damu ranki ya daɗe, nazo miki da wani kaya mai kyau da tsada nasan zaki soshi sosai sannan zaiyi miki kyau ba kaɗan ba, ku bani jakar nan" ta faɗa tana amsar jakar dake hannun ɗayar. Buɗe shi tayi kafin ta ciro wani kyakkyawan gown dress ash colour jikin sa wasu duwatsu ne masu kyau da kyalli, ya dai haɗu sosai. Amsa Jalilah tayi tana furta "Wow yayi kyau sosai, amma a ina kika same shi haka dan kuwa daga gani yana da tsada sosai." Rarraba idanu Kiki ta fara kafin idea yayi saurin faɗo mata kasancewar ta mace mai wayo da kaifin basira nan tayi murmushi tace "Ai a kasuwa na kar6o miki ita ki gani koh zatayi miki kyau, kinga sai ki bani kuɗin na kai musu, yanzu ki gwada shi ki gani idan yayi miki sai ki saya idan kuma baiyi miki ba sai ki za6i wanda kika ga yafi Kwanciya miki a cikin wadannan." "Bashi?, amma dai ba da sunana kika kar6i bashin ba koh?." "Aa koh kaɗan tayaya ma zasu fara yarda cewar zaki kar6i bashi, na riga da na biya musu kuɗin, yanzu kinga idan kika bani sai na riƙe abu na." Mamaki ne ya kama Jalilah tayaya kamar ita zata samu kuɗin sayen kayan nan, kauda tunanin hakan tayi a ranta kafin tayi murmushi tace "Toh shikenan hakan yayi kyau, lokaci na ƙurewa yakamata mu gaggauta koh?." "Kwarai kuwa ranki ya daɗe, ku shiga ku haɗa mata ruwan wankan, nikuma zanji da sauran." Kamar yadda ta faɗa sukayi, ruwan wanka suka haɗawa Jalilah, nan ta shiga tayi ba tare da ta bari an taya ta ba. Bayan ta fito ne kuma suka hau shirya ta, inda ƴan matan sukayi mata light make up wanda ya kar6i fuskar ta yayi mata kyau sosai haɗi da yi mata gyaran gashi mai ɗaukar hankali. Taya ta sukayi ta shirya cikin haɗaɗɗen gown ɗin, wanda yayi mata bala'in kyau kamar ka ɗauke ta ka gudu. "Wowww" gaskiya ranki ya daɗe kinyi kyau sosai. Murmushi Jalilah tayi dan kuwa ba ƙarya sukayi ba, ita kanta tasan ba ƙaramin kyau tayi ba. Ƙarar jiniya da sauƙar motocin da suka fara jiyowa ne ya tabbatar musu da cewa prince ya dawo daga tafiyar da yayi. Duk kallon ta suke kafin Kiki tace "Ina tabbatar miki da sai ya kasa ɗauke idanun sa akanki yau ranki ya daɗe." Blushing tayi cike da farin ciki tana ficewa daga ɗakin. Da wani irin mugun kallo Kiki ta bita kafin ta kalli ƴan matan tace "Kuna jina, duk wacce tayi kuskuren fidda abinda muke shiryawa ba sai nace komai ba, ta san yadda makomar ta zata kasance." Duk kansu a ƙasa ba tare da sun iya ɗagowa sun kalleta ba. "Lale lale, Marhaba bika ya Habiby" cewar Grandma tana buɗa masa hannayen ta. Rungume ta yayi cike da farin cikin ganin ta yana murmushi yace "I miss you Grandma." Ɗagoshi tayi tana bashi peck a kumatu tace "Ai baka kaini jin kewa ba Habiby, maza ƙaraso ciki" ta faɗa tana riƙo hannun sa zuwa cikin katafariyar falon ta zaunar dashi. Da kallo yake bin yadda aka gyara part ɗin da irin decorating ɗin da akayi masa, nan yace "Grandma, wake yin birthday ne yau, i can see duk kun hau wanka like masu shirin zuwa wani taro." Kallon sa Grandma tayi tace "Ba dole mu gyara gida mu tsaftace shi kuma mu hau wanka ba, yau Boy ɗina guda ya dawo, ai duk sabida kai akayi wannan abin." Murmushi yayi yace "Me?" yana tashi tsaye ya kamo hannun ta. "Kwarai kuwa Habiby, koh dai baiyi maka bane?." Murmushi yayi yace "Yayi kyau sosai amma bai kai Grandma ɗita ba" ya faɗa yana ɗan jan kumatun ta. Buge hannun sa tayi tace "Ni sa'ar wasar ka ce da zaka ja min kumatu koh?." Riƙe kunnen sa ɗaya yayi yace "Sorry." Murmushi tayi kafin tace "Jalilah, ina Yarinƴar nan ta shiga ne tunɗazu?, ke zo" ta faɗa tana yafito wata kuyanga da hannun ta. Ƙarasowa tayi tace "Gani ranki ya daɗe." "Jeki sama ki kirawo min Jalilah yanzun nan, kuma bance ki tsaya kalle-kalle da shige-shigen da ba'a saki ba, dan kunyi masters akan wannan, jeki." "Grandma?" cewar ZEEYAD ɗin cikin murmushi. "Barni ai ni nasan halin su ne shiyasa na faɗi hakan." Jalilah dake la6e a sama tana kallon su ta kasa sauƙowa sabida kunƴa ne ta runtse idanun ta da ƙarfi tana sake ware su, "Yaa Rabb" ta furta tana fitowa daga inda ta la6e ɗin ta hau sauƙowa a hankali. "Grandma mai..." maganar tasa ce ta ƙaƙare sakamakon idanun sa da sukayi arba da Jalilah dake sauƙowa kanta sunkuye sabida kunƴa. Baki sake Grandma ke kallon sa kafin tace "Inajin ka, mai kake kallo ne..." itama kasa idda maganar tata tayi bayan ta juya dan ganin abinda yake kallo. "Tabarakallah masha Allah, Masha Allah" kawai Grandma ke furtawa tana kallon Jalilah. Idda sauƙowa tayi tana ƙarasowa wurin su, hannun ta Grandma ta kamo tace "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan kyakkywar halittar." Kunƴa ce ta kama Jalilah dan haka blushing kawai take tayi ba tare da ta iya ɗagowa ta kalli idanun su ba, musamman ZEEYAD da yayi losting a kallon ta. Tsaye suke la6e daga saman benin suna kallon su kafin Kiki tace "Nan da Awa ɗaya maganin zai fara aiki a jikin ta, ku sani indai wannan aikin yayi kyau ba ƙaramar kyauta da karramawa zamu samu daga wurin Uwargijiya ta Sarauniya Naseeba ba." Kiss Grandma ta manna mata a goshi tana kamo ta ta zaunar da ita. "Lallai ba ƙaramin kyau kikayi ba ƴar nan, wannan duk wankan tar6ar Boy ne haka?." Murmushi kawai Jalilah tayi ba tare da tace komai ba. ZEEYAD ɗauke idanun sa yayi akanta yace "Grandma, i will be right back" yana faɗin haka ya sanƴa kai ya fice ba tare da ya jira cewar Grandma ba Da kallo duk suka bisa kafin Grandma tace "Barshi kinga yana basarwa ba ƙaramin kyasawa yayi ba." Murmushi mai sauti Jalilah tayi tana sadda kai ƙasa. *********************** ______ZEEYAD bai dawo ba sai da yayi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya wanda ba ƙaramin kar6ar sa sukayi ba. A dining ya hango Grandma da Jalilah tsaye suna jere plates. Zama zaiyi nan Grandma tace "Maza ƙaraso nan wurin." Tashi yayi inda taja masa kujera ya zauna. Ba'a daɗe ba YAZEED da Sadeeq suka shigo inda suma sukayi joining nasu a dining ɗin. Jalilah ce ta shiga serving ɗin kowa, kafin ita ma ta sami wuri ta zauna. A nutse kowannen su ya shiga cin abincin gaban shi, inda ZEEYAD dake ta iya ƙoƙarin sa na ganin kada ya sake kallon ta ya ɗago tare da yi mata slight kallo yana kauda kai. "What's wrong, ai yaci ace yanzu, poison ɗin ya fara reacting a jikin ta" cewar Kiki da har yanzu suke la6e ta sama suna kallon su. "Mu ɗan bada kamar minti goma haka" cewar ɗaya daga ciki. Gyara tsayuwa sukayi duk suna zuba idanun ganin abinda zai faru da Jalilah. "Jalilah dear, yi haƙuri kije kitchen ki ɗauko min Inibi cikin fridge, wannan abinci yayi yaji dayawa." "Toh Grandma" ta faɗa tana tashi tayi kitchen ɗin inda ZEEYAD yabi bayan ta da kallo. Haɗa ido Sadeeq da YAZEED sukayi kafin Sadeeq yace "Looks like someone is inlove." Kallon Sadeeq wanda kamar ba shi yayi maganar ba ZEEYAD yayi kafin yace "Grandma, kinajin shi koh?." "Boy kenan, toh ai ni na daɗe da fahimtar hakan idan baka sani ba." Tsuke fuska yayi yana kai cup ɗin juice baki yayi sipping. "Oh Grandma, i forgot ban faɗamiki ba, remember the girl i told you about?." Kallon YAZEED dake magana tayi tace "Yeah, nace dai ka samu shiga?." Ɗan sosa kai yayi yace "Tukun nan dai, actually the girl is sick again." "Subhanallah, meke damunta, har yanzu jikin nata ne bai dai-dai ta ba." "Yeah Grandma." "Allah Ubangiji ya bata lafiya mai ɗorewa." "Aameen Granny will you mind idan mukaje gobe kika duba ta?." "Masha Allah, zanso hakan" ta faɗa cikin murmushi tana kallon sa. Ɗan ta6e baki ZEEYAD yayi yana tsakurar abincin gaban shi a hankali. Ihun Jalilah da suka jiyo ne yasa su duk sake kasa kunnuwa dan jin koh gaske ne. _"Grandma?"_ suka jiyo da ƙarfi cikin kuka. Duk miƙewa tsaye sukayi muryar ta da suka sake jiyowa a karo na uku ne ya sanƴa su dugunzuma zuwa hanƴar kitchen ɗin. ZEEYAD dake gaba ne ya fara shigowa, inda ya same ta durƙushe rungume da jikin ta tana susa. "Jalilah?" ya faɗa yana cupping fuskar ta. Ƙara ta saki tace "Jiki na, my body is burning" ta faɗa tana sosa hannun ta da takejin kamar ana zuba mata ruwan zafi a jiki dama kuma dukkanin jikin ta. Duk kwalalo idanu sukayi waje ganin yadda lokaci guda jikin ta yayi wani irin manƴan jajayen tabo a duk inda ta sosa, abarka da jar fata. "What...what is this?" cewar ZEEYAD dake riƙe da ita cikin rawar murya. "Grandma help me, my body is burning bansan meke faruwa ba, the pain is unbearable" ta faɗa cikin kuka, tana ƙoƙarin unzipping rigar, ZEEYAD yayi saurin riƙe hannun nata yace "Ki bar sosawa haka nan, you guys should do something." Ɗage doguwar gown ɗin tayi cike da muguwar azabar da takeji a ƙafafun ta da cinƴoyin ta, saurin maida gown ɗin ZEEYAD yayi yana rufe mata cinƴoƴin ta dake waje free ana kallo, kafin ya juyo ga Sadeeq da YAZEED da suka tsaya kamar poster suna kallon su, a tsawace yace "What are you all staring at?, do something." "Sai dai muje hospital" cewar YAZEED. Cicci6ar Jalilah dake cikin azaba bata ma san abinda take yi ba yayi, nan duk suka mara masa baya, Grandma hankalin ta a mugun tashe. *Yawan Comment, Yawan Posting* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [8/8, 11:47 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *038...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _________Umma ce zaune kusa da DEENAH da taƙi ta kalle ta tun wayewar garin yau, haka ma taƙi ta amshi wani abu daga gare ta. "DEENAH, kici wani abu mana, kodai ba zaki ci abin hannu na bane?." Juyowa tayi ta kalli Umma jin abinda ta faɗa, tashi tayi zaune daga kwancen da take kafin ta amshi plate ɗin soyayyen chips da kwai ɗin dake hannun Umma ta fara ci. Shayi mai zafi Umma ta tsiyaya mata cikin mug tana miƙa mata. Amsa tayi tana sipping a hankali, bata wani sha sosai ba ta ajiye. "Kin ƙoshi ne?" cewar Umma. Kai kawai ta jinjina mata tana komawa ta kwanta. "Bara naje na sayo wadannan magungunan na dawo yanzu, you will be fine koh?" cewar Umma tana kallon ta. Kai kawai ta jinjina mata kafin ta tashi ta fice. Da kallon DEENAH ta bita kafin kuma ta miƙe tana sauƙowa daga kan bed ɗin tana sanƴa takalmi. Zuwa tayi tana yaye labulen window ɗin ɗakin tana kallon waje. Sosai tayi nisa a tunani, inda batasan da shigowar Sadeeq ba sai muryar sa da taji yana yi mata magana. Juyowa tayi tana kallon shi kafin kuma ta bar bakin window ɗin tana komawa bakin bed ta zauna. Murmushi yayi mata yace "Good Morning?." "Morning" ta maida masa martani. "So zan iya yin aiki na?" ya faɗa. Kai ta jinjina masa nan yace "Alright, let's start from duba level na blood pressure ɗinki." Kai ta jinjina masa tana gyara zama, nan ya shiga aiwatar da aikin shi cikin kwarewa. "Where is your Mom?" ya tambaye ta. Shiru tayi kamar ba zatayi magana ba kafin kuma tace "Tace zata je ta dawo." "Okay" kawai ya faɗa, nan ya gama aikin sa ya fice. Shiru tayi zaune ita kaɗai, ganin zaman ba zaiyi mata bane ya sanƴa ta miƙewa ta fice daga cikin ɗakin. Fitar ta keda wuya ta hango YAZEED da Grandma tafe. Daga inda YAZEED da ya hango DEENAH ta fito yace "Yo Grandma, there she is" ya faɗa yana ɗaura hannayen sa kan kafaɗun Grandma yana murmushi. Murmushi Grandma tayi suna ƙarasowa gun DEENAH da ta tsaya kallon su har suka ƙaraso. Murmushi Grandma tayi cikin muryar larabci ta kalli YAZEED tace "Tabarakallah Masha Allah, lallai Allah yayi halitta anan, i just hope yadda take kyakkyawa ɗinnan haka halayen ta suke kyawawa" cewar Grandma ɗin tana maida duban ta kan DEENAH dake kallon su da gajiyayyun idanun ta. Riƙo hannun ta Grandma tayi cikin murmushi tace "Ƴar nan ya kike, ya kuma ƙarfin jikin naki?." Ɗan murmusawa DEENAH tayi tace "Alhamdulillah" tana kallon Grandma ɗin. YAZEED ne yace "Grandma ɗita ce ita ɗin, she came to see you." Kai DEENAH ta jinjina kafin Grandma tace "Ina Mahaifiyar tata fah, sannan ina zataje ita da batada lafiya?." Kallon DEENAH YAZEED yayi yace "Ina Ummien ki?." "Ta...ta fita sayo magani, yanzu zata dawo." "Toh ke kuma ina zakije haka, keda bakida lafiya?" cewar Grandma tana kallon ta. Ɗan murmusawa kawai tayi ba tare da tace komai ba. "Daga gani kinsha dogon jinƴa, muje daga ciki kada mu tsaya anan" cewar Grandma ɗin tana kamo hannun ta zuwa cikin ɗakin. Zaunar da ita tayi kan bed itama tana samun wuri ta zauna, kafin tace "Ai YAZEED yana yawan bani labarin ki, babu ranar da zata zo ta wuce ba tare da yayi min zancen ki ba, ashe dai duk ba a banza bane, kyakkywar haliita iriyar ki ai dole ta sace zuciyar maza dayawa bama YAZEED ba, menene kake yimin ido ɗin koh ba gaskiya na faɗa ba" cewar Grandma dake kallon YAZEED dake tayi mata alamu da hannu da ido kan tayi shiru. DEENAH da bata wani fahimci inda zancen ta ya dosa bane tace "Ban..bangane ba." "Listen DEENAH, Actually Grandma ta ɗauka ke ɗin masoyiya ta ce" ya faɗa yana sosa kai. "Kamar ya na ɗauka, kai da bakin ka fah kacemin kullum da tunanin ta kake kwana kuma kake tashi, toh mecece ita ɗin idan ba masoyiyar ka ba?." YAZEED ji yayi kamar ya nutse anan wurin jin yadda Grandma ke ta sakin zance barkatai haka, duk sai yayi nadamar kawo ta duba DEENAH ɗin. Fara'ar dake kan fuskar DEENAH ne ya ɗauke diff kamar an ɗauke wutar nepa. "Grandma we should get going idan Ummien ta ta dawo anjima sai mu dawo koh?." "Kinga ƴar nan, muma nan marar lafiya ce damu, yarinƴar da ɗan uwansa zata aura ce babu lafiya, mu nan zamu wuce idan mahaifiyar ki ta dawo ki gaida ta sannan kice zamu dawo zuwa anjima." Haka kawai DEENAH taji gaban ta yayi mummunan faɗuwa, murmushin gefen baki kawai tayi tana kallon Grandma ɗin. YAZEED kuwa sakin baki yayi yana kallon Grandma jin abinda take cewa "Grandma?" ya faɗa. Miƙewa tayi daga zaunen da take tana faɗin "Toh ƴar albarka mu mun wuce koh, Allah ya tashi kafaɗun ki ya baki lafiya mai ɗorewa, muje" ta faɗa tana kallon YAZEED. Kallon DEENAH YAZEED yayi yace "Bye DEENAH." Kai kawai ta jinjina suna ficewa daga ɗakin. "Grandma what do you think you're doing?" cewar YAZEED bayan fitar su. "Kamar ya?, bangane ba dama mai kace min?." "Grandma ce miki fah nayi inason ta but har yanzun batasan da hakan ba, but..." "Toh ai dai-dai kenan, miye kuma wani abin damuwa, kai bakasan sauƙi ma na kawo maka ba?, yanzu tunda tasan abinda kake ji game da ita indai itama ta kyasa da kai tuni za'a wuce wurin, da kai da Boy fah ku ɗin na musamman ne duk wacce tayo dacen auren ku ai ta more." Kallon Grandma kawai yake ba tare da yace komai ba har ta idda zancen ta, nan yace "But Grandma naji kince Jalilah yarinƴar da ZEEYAD zai aura shi yace miki yana sonta?." "Kai kaji ka da wani magana, ai koh bai ce yanason ta ba ni naga hakan tattare dashi, kai bakaga duk yadda yabi ya nuna damuwar sa akanta ba yanzu, koh wurin ta ya kasa bari." Numfashi YAZEED ya sauƙe cike da gajiyawa da halin Grandma ɗin nan yace "Alright Grandma, muje" ya faɗa yana nuna mata hanƴa. Gaba tayi yana binta a baya inda take ta sake jaddada masa yadda ta hango soyayyar Jalilah a idanun ZEEYAD, shi dai bai tanka mata ba har suka isa ɗakin da akayi admitting ɗinta. Zaune suka samu ZEEYAD yana danne-danne a wayar sa, kan bed kuma Jalilah ce kwance jikin ta shafe da wani farin abu da alamu dai magani ne, inda kuma akayi mata ƙarin ruwa. "Ha'a mai nake gani haka, kai da zaka ɗebe ta da hira ne kuma ka sanƴa wayar ka a gaba kana daddanawa, toh miye amfanin zaman ka anan ɗin dama?." Ɗagowa yayi ya kalli Grandma, bai ce da ita komai ba sai ma sake sadda kansa da yayi yana cigaba da abinda yakeyi. "Toh ai shikenan, tunda banza tayi magana ba." Ɗagowa yayi yana kallon ta, kafin kuma ya kashe wayar yana tashi yayi inda take zaune yace "Sorry Grandma, ina ɗan wani aiki ne shiyasa." "Toh koma dai menene dai kaji dashi, YAZEED ka sake kiran Marwa a waya mana kodai ba zata zo ta duba ya ƴar tata take bane?." "She is not coming?" cewar Jalilah. Kallon ta duk sukayi kafin Grandma tace "Toh maiyasa, a wane dalilin?." "Sabida Abhi ba zai bar ta ba, a cewar sa yanzu babu ruwan sa dani tunda nice nayi sanadiyyar rufe Sooraj da akayi, bana tunanin zai bar ta tazo." Duk kallon juna suka shiga yi, kafin YAZEED yace "Zan iya kiran mai Martaba na sanar dashi, maybe yayi masa magana ya bar ta tazo." "A'a kyale su kawai tunda zuwa anjima ma zamu koma gidan" cewar Grandma. Kallon YAZEED ZEEYAD yayi yace "Ya jikin budurwar taka?." Ɗan hararar sa YAZEED yayi yace "Ba kaƙi zuwa ka duba ta ba, she is pretty fine....maybe" ya faɗa. "Maybe?" cewar ZEEYAD ɗin. "Yeah, you know she has a brain tumor or is it problem ne, so she have to fight for full recovery, and i can sense something huge na damunta deep down." "Really, and ka tambaye ta koh menene shi?." Shiru yayi yana kallon ZEEYAD kafin ya girgiza masa kai alamun a'a sannan yace "The girl is kinda cool, she is an introvert batason magana da kowa or maybe tayi sharing feeling ɗinta wa wasu, and i guess tun dah chan ma haka yanayin rayuwar ta yake." Shiru kawai ZEEYAD yayi bai iya cewa komai ba, kafin yaji muryar YAZEED ɗin na sake faɗin "Anjima da kai zamuje mu duba ta, coz Grandma tayi mention ɗinka a wurin ta and yanzu idan bakaje ba, ba zata ji daɗi ba, right Grandma?." "Ofcourse right, ai dolen sa ma yaje tunda bama wani nisa ne ke tsakanin nan da ɗakin nasu ba." "Nima zanje, i want to see her too" cewar Jalilah da tayi shiru tunɗazu. "Keda baki da lafiya, idan kika je musu haka ai sai yarinƴar ta ɗauka koh mutuwa ce tazo mata yadda kika sha farar abu a jiki haka" cewar Grandma. Duk dariya sukayi harda Jalilah dake kwance babu lafiya ɗin, except ZEEYAD da yakejin zuciyar sa ta kasa yin resting tun jiya da ya tako ƙafar sa cikin asibitin, musamman yanzu da ya tsinci wasu bayanai game da abinda YAZEED ya faɗa masa akan yarinƴar da yakeso ɗin. ************************ __________Kallon Umma dake zaune tayi tace "Umma?." Ɗagowa Umma tayi ta kalle ta kafin tace "Inaso zan fita waje...shan iska." "But DEENAH..." "Yanzu ma hana ni zakiyi right?, i know ba zaki barni ba, sabida kin daina yimin duk wani abu da nakeso yanzu." "A'a DEENAH ba hana ki zanyi ba, ki bari ki jira ƙawayen naki kinga idan sunzo sai su kai ki koh?." "No i don't want them, nikaɗai nakeson fita ba da kowa ba." Shiru Umma tayi bata ce komai ba tana kallon DEENAH ɗin fuskar ta fal damuwa. "Are you worried koh wani abu zai same ni right?, i will be fine and i will take care of myself." Kai Umma ta jinjina mata nan tace "just kada ki daɗe please kinga dare ya kusa da zaran kinji an fara shirin kiran sallah ki dawo, sannan ki faɗamin inda zakije ɗin." "Wurin da muka saba fita motsa ƙafa zani, wurin yafi daɗin zama da sha'ani." "Alright, be careful, Okay?." Bata ce da ita komai ba ta sauƙo daga kan bed ɗin tana maƙala mickey sleepers ɗinta a ƙafa kafin ta bar ɗakin inda Umma ta bita da kallo. A hankali take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki. Sadeeq taga ya fito daga wani ɗaki, murmushi yayi da ganin ta da yayi nan yace "Patient, what are you doing out here?." "I...inason fita shan iska ne." "Wow how great, see you later then" ya faɗa yana ƙoƙarin wucewa. "Listen?" ta faɗa. Tsayawa yayi yana kallon ta yace "Yes?." "Ɗazu YAZEED and his Grandma came to check on how i was doing, sun ce suna da patient anan suma, zaka iya nuna min ɗakin da suke?." "Oh yeah sure, Cousin sis ɗinsu ce ba lafiya, anjima kaɗan ma za'a yi discharge nasu, idan kika bi straight haka zaki ga hanƴar da yayi left and right, take the left hand side, ɗaki na 78 anan suke, sorry ba zan iya raka ki ba i have alot to cover" ya ƙarashe cikin murmushi. "It's Okay, Thank you" ta faɗa. "You're welcome" ya faɗa yana wucewa. Kamar yadda yayi mata kwatance hakan tabi nan kuwa ta tsinci kanta bakin ɗakin. Ƙarasawa tayi kafin ta shiga knocking door ɗin, zuciyar ta na harbawa. "Wa'alaikumusalam, ƙofar dai a buɗe take" cewar Grandma. Hannu tasa tare da murɗa handle ɗin ƙofar tana tura ƙofar ta shige bakin ta ɗauke da sallama. Ɗagowa Grandma tayi tana sauƙe idanun ta kan DEENAH da ta shigo tana ra6ewa jikin ƙofar kamar mai tsoro. "DEENAH?" cewar Grandma tana kallon ta Murmushin kan le6e DEENAH tayi tana kallon Grandma ɗin. "Come on ƙaraso mana" cewar Grandma tana kallon ta cikin murmushi. Ƙarasawa tayi tana zama kusada Grandma ɗin. "Ya kike, and how is your health?." "Alhamdulillah" ta faɗa. "Masha Allah, Ummien taki bata dawo ba har yanzu?." "Ta dawo, niɗin na fito shan iska ne, shine nace bari nazo na duba marar lafiya" ta faɗa kanta a ƙasa. Murmushi Grandma tayi cike da farin ciki tace "Masha Allah how kind of you, ai sun fita tare da Boy wai suje ya saya mata kayan maƙulashe, kinsan abin ka da masoya yanzun nan zasu dawo." Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba. Kallon ta Grandma tayi kafin tace "DEENAH dear, tell me mai kikeji game da jika na YAZEED?." Ɗagowa DEENAH tayi tana kallon ta, kafin kuma tayi saurin sadda kai ƙasa zuciyar ta na racing. "Ki kwantar da hankalin ki, i know kunƴa ta kikeji, but daga gani kema nasan kin kyasa da ɗan kyakkyawan jikan nawa" faɗin Grandma cikin murmushi. Ita dai DEENAH kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa ta kalli Grandma balle ta maida hankalin ta kan abinda take faɗa, zuciyar ta babu abinda takeyi sai bugu kamar zata fito waje ganin Grandma na neman jawo mata ruwa. Buɗo ƙofar akayi aka shigo inda Grandma ta maida duban ta gun mai shigowar. Jalilah ce tafe tana murmushi tazo ta rungume Grandma ɗin tana cewa "Grandma." Murmushi Grandma tayi tana ɗago ta nan tace "Wannan leda menene haka a ciki?" cewar Grandma cikin riƙe ha6a tana kallon Jalilah. Jalilah kallon ledar hannun ta tayi kafin cikin murmushi tace "Duka fah Akhi ne ya sayamin, shi yace na ɗau duk abinda nakeso." "Iyeee, kice kawai soyayyar ku kuka shawo, toh shi ɗin ina ya tsaya kuma?." Zama tayi tace "Yana waje yana amsa kira" ta faɗa idanun ta akan DEENAH dake zaune kamar wacce aka dasa ba tare da ta ɗago ba. "Toh masha Allah" cewar Grandma kafin tayi murmushi tace "DEENAH dear, wannan ita ce Jalilah marar lafiyar tamu amma yanzu alhamdulillah taji sauƙi anjima ma muna sa ran za'a bamu sallama, yakamata kusan juna tun yanzu dan kuɗin zaku zo ku zamto matar ya da ƙani ne, haka nake sa rai insha Allah" ta faɗa tana kallon su duka. Murmushi Jalilah tayi tana kallon DEENAH da ta ɗago tana kallon ta kafin tace "Hi, ya kike ya jikin ki?." "Hi, Alhamdulillah, ya naki jikin?." "Alhamdulillah, naji sauƙi sosai but ke i don't think kin gama warkewa completely maiyasa kika fito?." Ɗan murmusawa kawai DEENAH tayi tana sadda kai ƙasa, Grandma ce tace "Iska ta fito sha, shine tace bari ta shigo taga ya jikin ki, kinga batada lafiya ma amma ta iya takowa ta duba ki." "Wow Thank you so much, gaskiya kina da kirki sosai." Jinsu kawai DEENAH keyi inda duk taji ta takuru, ɗagowa tayi ta kallesu tace "Grandma, i think ni zan wuce kada mahaifiya ta ta fara nema na." "Haba ƴar nan, tafiya tun yanzu?, ki bari mana Boy ya shigo ku gaisa, kinji tace yana waya da zaran kun gaisa sai ki tafi koh?." Kai kawai DEENAH ta jinjina tana jinta a matuƙar takure ga kuma wani irin feeling da ta kasa gane koh na menene, musamman yadda zuciyar ta ke harbawa yana tsinkewa tanajin duk tsikar jikin ta na tashi haɗi da wani irin sanƴi da taji yana ratsa dukkanin wani 6argo na jikin ta. Sadda kai tayi ƙasa tana runtse ido da ƙarfi koh zata rage jin abinda takeji. Shigowar sa ɗakin yayi daidai da wani irin bugawar zuciyar ta da taji, wanda yafi kowanne ga kuma wani irin gudu da yake yana beating so fast, runtse idanun ta tayi tana sauƙe ajiyar zuciya sama-sama. Da shigowar sa Grandma ta kallesa tace "Yauwa gara dai da ka shigo dawuri, ƴar nan nata son tafiya tunɗazu na hana ta nace ta bari kazo ku gaisa kafin ta wuce." Har Grandma ta idda maganar tata bai kalli inda DEENAH ke zaune ba. Jalilah ce tace "Yeah, i guess girlfriend ɗin YAZEED ce, she is so damn beautiful, right Grandma?." "Ahaf ai zai ganewa idanun sa yanzu." Maida duban sa kan DEENAH da kanta ke sadde da ƙasa yayi bayan sunce dashi girlfriend ɗin YAZEED ce. A hankali ya buɗi baki yace "Hi." Da sauri ta ware idanun ta da suka kasance a runtse jin muryar sa da ta ratsa dodon kunnuwan ta tana mai ɗago da manƴan idanun ta tana sauƙe su cikin nashi. Zuciyar ZEEYAD ce tayi wani irin harbawa lokacin da idanun sa sukayi masa arba da fuskar ta. DEENAH sake waro idanun ta tayi tana binsa da kallo inda ta shiga tashi a hankali daga zaunen da take still idanun ta cikin nasa. Murmushi Grandma da bata wani fahimci komai ba tayi tana miƙewa tsaye kafin tace "DEENAH dear wannan shine Boy ɗina ZEEYAD shi ɗin yaya ne a gun YAZEED kokuma kawai ace dasu ƴan biyu ne tunda tazarar mintina goma ce kawai tsakanin su, sannan dukkanin su jikoki na ne." Dukkanin su babu wani wanda ya maida hankali kan maganar da Grandma keyi, sosai sukayi losting a kallon juna, inda kowane ya kasa ɗauke idanun shi kan ɗan uwan shi. "DEE...DEENAH?" cewar ZEEYAD a hankali cikin rarrabewar harshe yana binta da kallo. DEENAH batasan wane irin feeling takeji game da ganin sa ba, ta rasa daɗi takeji koh baƙin ciki, ji tayi zuciyar ta na murnar ganin sa ta wani 6angaren, ta wani gefen kuma akasin hakan ne, lumshe idanun ta tayi hawayen da suka taru mata suna samun damar sauƙowa kafin ta sake ware su akan sa tana cigaba da kallon shi. Grandma da Jalilah kawai ƴan kallo suka koma suna bin kowanne da ido tunda sukaji ZEEYAD ya ambaci sunan DEENAH. ZEEYAD kauda idanun sa yayi daga kallon DEENAH, yana kallon Grandma da ta saki baki tana kallon su. "Boy...ka santa ne?." Shiru yayi ya ɗan kalli DEENAH da har yanzu bata bar kallon sa ba, cikin tattaro dukkanin nutsuwar sa yace "I...no...i don't know her" ya faɗa kamar wanda aka matse masa baki. "Toh ya akayi kasan sunan ta?." Ba tare da ya kalli DEENAH ɗin ba yace "I know she is DEENAH, right?, YAZEED's girlfriend." Murmushi Grandma ta saki kafin tace "Haka ne, ita ce DEENAH." Murmushi Jalilah tayi tace "She came to check on me, even though she is also sick." Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi yace, kafin yace "That's so kind of her." "Yeah dole ka faɗi haka ai tunda tazo duba rabin ranka koh?" cewar Grandma. Tsuke fuska ZEEYAD yayi kawai yana sadda kansa ƙasa hannayen sa zube cikin aljihu. Murmushi Grandma tayi kafin tace "Dama ni nace ta jira kazo idan kun gaisa sai ta tafi." "Uhm" kawai ya faɗa cikin jinjina kai. DEENAH ji tayi zuciyar ta na breaking into tiny pieces da jin abinda ZEEYAD ya faɗa, she feel completely shattered and useless daga yadda yake avoiding kallon ta and pretend like everything is all okay with him, har yake iya forming murmushi kan fuskar sa a gaban ta, how he told his Grandma cewar bai santa ba and how he called her budurwar YAZEED make her feel so stupid. How she spend half of her life dashi maƙale a zuciyar ta and how take ganin babu wani wanda ya saura mai ƙaunar ta except him, and how take ta tunanin cewar shima yana chan yana tunanin ta kamar yadda takeyi, and how take tunanin baiyi moving on ba sabida irin ƙaunar da yakeyi mata make her feel like a fool. "DEENAH de..." Grandma bata ƙarasar da abinda take shirin faɗi ba DEENAH ta wuce a fusace fuuu tana bangaje ZEEYAD dake tsaye yawa an kafa shi ta fice daga cikin ɗakin. Duk da kallo suka bita kafin Grandma tace "What's wrong with her?." "Seems like wani abin na damunta ne" cewar Jalilah. "We should check on her" faɗin Grandma tana mara mata baya inda Jalilah ma ta bita. Shiru ZEEYAD yayi yana shafa inda ta bangaje shi ɗin kafin a hankali ya furta "Am sorry DEENAH." DEENAH da fitar ta gudu ta kama bata tsaya koh ina ba sai ɗakin da akayi admitting nata, tana zuwa ta tura ƙofar ta shiga tare da rufowa tana sakin wani irin marayan kuka mai tsuma zuciya. Ɗagowa Umma tayi a razane tana kallon ta, ganin ta faɗo ɗakin tare da sakin kuka ba ƙaramin ɗaga hankalin Umma yayi ba. "DEENAH?" ta faɗa tana tashi daga inda take zaune tayi kan DEENAH. Da gudu DEENAH tazo tana faɗawa jikin ta tare da rungume ta ƙam tana cigaba da kuka kamar wacce za'a zarewa rai. Rungume ta Umma ma tayi tana ɗan bubbuga bayan ta a hankali, jin yadda DEENAH ke kuka yasa itama taji hawayen sun zo mata. "Am so sorry Umma na dan Allah ki yafemin, for getting you all wrong akan dukkanin abinda kuka cemin." Bayan ta Umma ta cigaba da bubbugawa a hankali ba tare da ta iya cewa komai ba sai hawaye kawai da Itama keyi. Ɗagowa DEENAH tayi tana cupping fuskar Umma ɗin a hannun ta tace "Dan Allah Umma kiyi haƙuri ki yafemin da dukkanin abubuwan da nayi miki, nayi miki alƙawarin ba zan sake ba, sannan zanyi duk wani abu da kika sanƴa ni ba tare da nayi miki gardama ba, kice kin yafemin dan Allah" ta faɗa cikin kuka. Share mata hawaye Umma tayi tace "Bakiyi min komai ba DEENAH, nice nayi miki laifin raba ki da..." Yatsa ta sanƴa tana rufe bakin Umma kafin ta girgiza mata kai tana sake rungume ta tace "Baki raba ni da kowa ba, as long as ina tare dake da yaya Jafar then i will be happy forever, am so sorry for everything, am sorry da nuna muku cewar baku isa ba, and am sorry for proving you all wrong akan duk wani abinda kuka so fahimtar dani, am sorry for everything Umma na." "It's alright dear, ki bar kukan nan haka kinji?, komai zai daidaita insha Allah." Kai kawai ta jinjina tana lumshe idanun ta dake cike taf da kwalla. Ɗagowa tayi tana kama hannun Umma tace "Umma am all fine now, mu tafi mu bar nan wurin, sannan kada mu sake dawowa i feel so useless here." "DEENAH, meke damunki ne, mai ya faru?." Girgiza kai tayi tace "It's nothing, just mu bar nan wurin naji sauƙin komai i promise." "No DEENAH you doesn't seem alright, ki faɗamin meke damunki, lafiya ƙalau kika fita daga nan, tell me meke damun ki?." Cikin kuka tace "Kwarai lafiya ƙalau na fita daga nan, amma da naji maganar ki na cewar kada na fita da babu abinda zan gani koh shaida wanda zai zamto sanadiyyar tashin hankali na na har abada, but daga yanzu nayi miki alƙawarin zama ƴar ki wacce kika sani a dah, ba zan sake bijirewa umarnin ki ba." Kallon ta kawai Umma keyi har ta idda maganar tata. "Naji dukkanin abinda kika faɗa amma baki sanar dani abinda ya sanƴa ki cikin tashin hankali haka ba, tell me DEENAH meke damunki?." Shiru kawai tayi tana kallon Umma idanun ta na tsiyayar da hawaye ba tare da ta iya buɗar baki tace mata komai ba. "Tell me DEENAH, talk to me" Umma ɗin ta sake faɗa tana kallon ta. Idanun ta dake yaji ta lumshe kafin a hankali tace "Na...i..." Ƙarar buɗewar ƙofar da akayi aka shigo ne ya sanƴa ta kasa idda maganar ta. "DEENAH dear" cewar Grandma tana ƙarasowa wurin ta Jalilah na biye da ita. Da kallo Umma kawai Umma ke binsu dan kuwa batasan su ba. Grandma ce tace "Afuwan, daga gani kece mahaifiyar DEENAH koh?." Kai kawai Umma ta jinjina tana kallon Grandma. "Masha Allah ni ɗin kakar YAZEED ce ina kyautata zaton kin sanshi." Murmushi Umma tayi tace "Kwarai." "Masha Allah, bansan mai ya sami DEENAH ba, muna tsaye and she suddenly left, shiyasa muka biyo ta dan jin abinda ke damun ta." Kallon DEENAH Umma tayi kafin tace "DEENAH ki faɗa mana meke damun ki?." Goge hawayen fuskar ta tayi ta juyo tana kallon Grandma tace "Am completely fine, kawai nazo ne dama nace miki mahaifiya ta zata neme ni shiyasa na dawo." Kallon ta Grandma keyi kafin tace "Kin tabbata gaskiya kike faɗamin DEENAH, ba wani abin bane?." Kai kawai DEENAH ta jinjina mata tana kallon Jalilah dake tsaye bayan Grandma, kafin tayi sauran kauda idon ta. Dama tasan tunda ya sami kamar wannan babu ta yadda zai sake bin ta kanta ne, and seems like wadannan ɗin dagaske family ɗinsa ne, sai kuma yanzu take hango kamannin jinin ZEEYAD a fuskar YAZEED, ashe dai they are related ne. "DEENAH, are you sure babu abinda ke damun ki?." Kai ta jinjina mata kawai. Nan Grandma tace "Toh shikenan dai dukda dai ban yarda ba akwai abinda kike 6oyemin, amma tunda kince babu komai shikenan." "Thank you" cewar Umma. Murmushi Grandma tayi tace "Babu komai, your daughter is so sweet and lovely, kallo ɗaya nayi mata naji ta kwanta min a rai, just do hope that zaki yarda ki aurawa YAZEED ita." Kallon DEENAH Umma tayi kafin ta ƙirƙiro murmushi kawai ba tare da tace komai ba itama. "Mu zamu wuce koh, zuwa anjima muma za'a sallame mu, wannan ita ce Jalilah sannan itama matsayin jika ta take, ƴa ce ga ƙanin mahaifin YAZEED." "Masha Allah" faɗin Umma cikin murmushi. Murmushi Jalilah tayi itama, kafin ta kalli DEENAH tace "Bye DEENAH, Allah ya baki lafiya." Kallon ta kawai DEENAH keyi ba tare da ta bata amsa ba. Sallama Grandma ma tayi musu kafin su fice daga ɗakin. Da kallo DEENAH ta bisu kafin taje tana zama bakin bed. Da kallo Umma tabi ta kafin tazo tana dafa ta. Rungumo Umma ɗin ta sakeyi tana runtse idanun ta trying so hard na ganin tayi controlling feeling ɗinta dama kuma hawayen ta. Kanta kawai Umma ke shafawa cikin kwantar mata da hankali. *********************** ________ZEEYAD tun bayan ficewar su shima ya fice, babu inda ya nufa sai gida. Sosai yake ta jeka ka dawo cikin tsakiyar ɗakin nasa, zuciyar sa fal nadamar abinda ya aikatawa DEENAH. Yasan yayi hurting ɗinta so deeply, how could he do such a thing bayan yaga yanayin ta, seems like har yanzu bata gama samun sauƙi ba duba da yadda ya ganta da uniform ɗin patients a jikin ta, and in the other hand DEENAH itace yarinƴar da YAZEED ɗan uwan sa keyi masa maganar ta kullum, wanda ba ƙaramin so yakeyi mata ba. He thought DEENAH ta riga da ta zama past nasa ne, sai dai kuma ganin ta a yanzu babu abinda ya tayar masa, sai tsohon feeling ɗin da yakeji tattare da ita. Zubewa yayi bakin bed ɗinsa yana sanƴa hannayen sa duka biyu cikin gashin kansa, sosai yakejin nadama haɗi da tausayin ta cikin zuciyar sa. He knows koh kaɗan batayi deserving abinda yayi mata ba coz she is completely innocent, he thought koh zuciyar sa ta fara tafiya ga Jalilah ne but ganin DEENAH a yanzu ya tabbatar masa da cewa itace abinda zuciyar sa ke so da bege a kullum, kasancewar Grandma ɗinsa kusa dashi ne yasa shi jin like ya mallaki komai da komai na farin ciki, but now ya gane that da akwai abinda ya rasa tattare dashi wanda kullum yakejin sa incomplete, and now tozali da yayi da abar nan yau ya tabbatar masa da cewar he still needs her and loves her dearly, he may be sad da abinda mahaifiyar ta tayi masa but hakan ba zai ta6a goge soyayyar ƴar ta daga zuciyar sa ba, and yau ya tabbatar da hakan. Sosai idanun sa sukayi jazir yanajin sunayi masa wani irin zugi but ya kasa yin kukan koh yaji sassaucin abinda yakeji cikin zuciyar sa, babu abinda yafi tada masa hankali wanda ya wuce son DEENAH da YAZEED ɗan uwan sa keyi. Ya san YAZEED ba zai ta6a jindaɗi ba idan ya gano cewar yanason DEENAH, shi kuma ba zai ta6a bari wani abu ya sami relationship nashi da ɗan uwan sa ba, so the best abinda yakamata yayi shine yayi pretending like baisan DEENAH ba, yasan ba ƙaramin hurting feeling nata yayi da hakan ba, but babu yadda ya iya, wannan shine kaɗai abinda zaiyi na ganin komai na tafiya smoothly tsakanin sa da ɗan uwan sa wanda shine yayi sacrificing love nasa wa YAZEED ɗin, yasan it will be hard for him but this is the only way na ganin ya sanƴa ɗan uwansa farin ciki, and zaiyi hakan ne sabida bashida 100% sure cewar DEENAH na son sa. "Am sorry DEENAH" ya faɗa cikin raunanniyar muryar sa. ******************* _______Tun abinda ya faru jiya DEENAH ta sake zama so pale, batada aiki sai bin Umma da idanu duk inda tayi. Burin ta bai wuci ta ganta a gida ba, sannan ta baiwa Jafar haƙuri su dawo kamar dah. Tayi alƙawarin mance komai game dashi sannan ba zata sake tunanin sa ba, tayi alƙawarin moving on da rayuwar ta, kamar yadda shima yayi hakan. Sosai take nadamar 6ata lokacin ta wurin tsayawa tunanin sa a kullum. Sai yanzu ta yarda da wannan karin magana ta hausawa wai *Namiji ba ɗan goyo bane* akan shi ta kusa hallaka kanta, sannan take ganin babu mai sonta da ƙaunar ta hatta mahaifiyar ta da ɗan uwanta, ta ɗau gaba dasu duk sabida namiji. Gashi yau yayi mata abinda ba zata ta6a mantawa dashi ba, yayi moving on da rayuwar sa har soyayya yake da wata yayin da ita kuma ya watsar da ita kwandon shara. Tun jiya da abin ya faru take tsanmanin ganin sa yazo ya bata haƙuri tare da shaida mata yayi nadamar abinda ya aikata, koh hakan zai sanƴa ta sauƙowa amma bata ganshi ba, hakan na nufin yayi giving up akanta kenan completely. *Yawan Comment, Yawan Typing* _*Muje Zuwa Lovelies, Yanzu fah za'a soma wasar😎*_ *MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽* [8/12, 6:17 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *039...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *_NOT EDITED_* ___________Cikin ƴan kwanakin nan babu ranar da Grandma bata zuwa asibiti duba jikin DEENAH, indai bata zo da safe ba zata zo da rana, idan kuwa bata zo da rama ba kuwa zaka ganta da dare, a haka har Umma ta saki jiki da ita suka ɗan saba, dan kuwa taga Grandma ɗin sam bata da wani matsala. Haka ma YAZEED shima baya rabuwa da zuwa duba DEENAH, tun Umma batajin daɗin hakan har tazo hankalin ta ya fara kwanciya dasu dan kuwa ta lura su ɗin mutanen kirki ne sosai. Yau ma Grandma ce zaune ta tasa DEENAH a gaba da zance wanda a kullum baya wuce maganar YAZEED da takeyi mata, yadda yake da kyawawan halayya dama kuma kusancin dake tsakanin sa da ɗan uwan sa ZEEYAD, DEENAH tun tana jin takaicin hakan har kuma tazo ta saba sai dai kawai tayi ta yiwa Grandma ɗin murmushin yaƙe, but deep down cikin zuciyar ta batason tana yi mata maganar YAZEED ɗin koh kaɗan. "Ai ƴar nan nake faɗamiki indai kika amince kika auri jika na YAZEED yadda yake sonki ɗinnan, na tabbatar miki babu wani abin farin ciki da zaki nema ki rasa, ai ni a kullum banida wani buri da ya wuce Allah ya nuna ranar auren su dashi da ɗan uwan shi, na tabbata yadda duk kuke kyawawa ɗinnan ba ƴaƴan da zaku haifo sai anyi sanitizing hannu kafin ya ta6a su dan kyau" ta ƙarashe cikin dariya. Murmushi kawai Umma dake jin su take tunɗazu, nan Grandma ta sake cewa "Koh ya kika ce Ummien DEENAH, bakya tunanin YAZEED da DEENAH ba ƙaramin dacewa zasuyi ba?." Murmushi kawai Umma tayi tace "Allah shine masanin gaibu, Allah ya haifar da abinda shine alkhairi." "Aameen Yaa Allah, insha Allah DEENAH sai kin zamto ɗaya daga cikin family ɗin mu" cewar Grandma cikin murmushi. Tashi tsaye DEENAH dake zaune tayi, kallon ta Grandma tayi tace "Ina zaki kuma?." Ɗan murmusawa tayi tace "It's hot in here, inason fita waje ne." "Toh kodai na dame ki da surutu ne ƴar nan?." Saurin nodding kai DEENAH tayi tace "No, koh kaɗan." "Toh ai shikenan kije ki dawo, naga ma dare na tayi bara na kira Boy yazo ya maida ni gida." DEENAH bata jira ƙarashin maganar ta ba ta fice da sauri, kai tsaye Office ɗin Sadeeq ta nufa dan kuwa tayi mugun gajiya da zaman asibiti, daurewa kawai takeyi. Da isar ta door step ɗin office ɗin nasa ta fara knocking, nan take ya bata izinin shigowa. Murɗa handle ɗin ƙofar tayi ta shiga, turus taja ta tsaya zuciyar ta na bugawa ganin sa zaune. Saurin juyawa tayi zata fice dan kuwa hankalin sa ba'a kanta yake ba, nan taji Sadeeq yayi saurin cewa "Patient?." Dakatawa tayi tana runtse idanun ta, ba tare da ta juyo ba taji yana faɗin "Where are you going, kodai ba nan kike son zuwa ba?." Sauƙe hannun ta tayi daga jikin handle ɗin ƙofar tana jiyowa kanta a sunkuye ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna. ZEEYAD wani irin tsuke face yayi tare da kauda kai kamar wanda bai ganta ba, sai dai tsaf yake ƙare mata kallo ta gefen ido. Murmushi Sadeeq yayi yana kallon ta yace "Do you came to see me?." Kai ta jinjina masa, nan yace "Alright, ina jinki." Tattaro dukkanin nutsuwar ta tayi tana mai son kawar da existence ɗinsa a wurin tace "I...inaso ne dan Allah ka sallame mu mu koma gida." Waro idanu Sadeeq yayi yana kallon ta kafin yace "Sallama kuma, but why?, i mean har yanzu da sauran ki baki gama warkewa ba." "Yes i know but it's just that na gaji ne da zaman nan ɗin, i want to go home, staying here irritates me alot." Shiru Sadeeq yayi yana kallon ta har ta idda maganar tata, numfashi yaja yace "Am sorry DEENAH but ba zan iya sallamar ki yanzu ba har sai kin warke completely, komawar ki gida yanzu babu abinda zai ƙara sai worsening ɗin ciwon ki, don't you want to recover fast?, idan kikayi haƙuri then zakiga kamar bakiyi ciwon ba." Shiru tayi kawai tana juya manƴan idanun ta da suka fara tara ruwa. "Am sorry Okay?" cewar Sadeeq ɗin. Kai ta jinjina masa kafin kuma ta miƙe a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta fara tafiya. "Listen" ta tsinkayo muryar sa lokacin da ta ɗaura hannun ta kan handle ɗin ƙofar da niyyar buɗewa ta fice. Tsaye tayi tare da rolling idanun ta tana jin zuciyar ta nayi mata mugun zafi. ZEEYAD da kamar ba shine yayi maganar ba hararar Sadeeq dake ta kallon sa yayi kafin kuma ya miƙe daga zaunen da yake yana ƙarasawa gun DEENAH dake tsaye. Shiru yayi na wasu ƴan seconds kafin yace "I just want to ask how you're doing." Ji tayi wani irin abu ya tsaya mata a maƙoshi yayin da haushin sa ke sake turnuƙe mata zuciya. Bata juyo ta kallesa ba haka ma bata kulasa ba, saurin riƙe handle ɗin ƙofar da take shirin murɗawa yayi idanun sa akanta. Bin hannun sa dake kan nata tayi kafin ta janƴe nata hannun zuciyar ta nayi mata bala'in zafi. "Can we talk please?" ta jiyo muryar sa. Ɗago da idanun ta tayi tana kallon sa, sam bata tunanin zata iya buɗar baki tayi masa magana, juyawa tayi gun Sadeeq da ya zama ɗan kallo tace "Why don't you tell your friend here cewa ya bani hanƴa na fice." "Ohw" cewar Sadeeq yana bin kowannen su da idanu kafin kuma yace "Why don't you give him some seconds out of your time, he said please, if you want then i can leave you two to talk" ya faɗa tare da miƙewa tsaye ya tattari abubuwan da zai buƙata yana zuwa ya tsaya a gaban su, duk kallon su yayi kafin yace "I need a space to pass please." Sauƙe hannayen sa ZEEYAD yayi daga jikin handle ɗin kafin Sadeeq yayi saurin buɗewa ya fice yana ɗaga masa gira, DEENAH yunƙurin bin bayan Sadeeq tayi sai dai kafin tayi hakan har yayi saurin rufo ƙofar. Tsaye ZEEYAD yayi jikin ƙofar yana binta da kallo. "What sort of nonsense is this?" ta faɗa tana kallon sa. Tsuke fuska yayi tare da zuba hannayen sa cikin aljihu ya shiga takowa daf da ita. Da kallon mamaki DEENAH ke bin sa tana sake waro manƴan idanun ta tana ja da baya. Table ɗin da ya tare ta ne ya sanƴa ta dakatawa tana bin sa da kallo har ya ƙaraso daf da ita. Rumfa yayi mata da hannayen sa yana sanƴa ta a tsakiya nan tayi saurin runtse idanun ta da ƙarfi tana kawar da face ɗinta yayin da zuciyar ta ta shiga beating so fast. Kyakkywar fuskar ta yake bi da kallo kafin kuma ya kai bakin sa saitin kunnen ta ya kira sunan ta "MADEENAH?." Sake damƙe idanu DEENAH tayi lokacin da taji sauƙar numfashin sa haɗi da sautin muryar sa cikin kunnuwan ta. A hankali ta shiga buɗe idanun ta tana sauƙe su cikin nasa da ya kafe ta dashi kamar zai cinƴe ta. Hannun ta ta kai kan faffaɗar ƙirjin sa tana ɗan tura sa baya sakamakon miƙewa da takeson yi. "Please...let me go" ta faɗi hakan a hankali cikin kauda idanun ta daga cikin nashi. "But we need to talk" ya faɗin hakan cikin cool sexy voice ɗinsa. Sake runtse idanun ta tayi jin wani irin abu na tsirgar mata tundaga yatsar ƙafar ta. "Please..." ta sake faɗa hannayen ta kan ƙirjin sa. Murmushi gefen baki ya saki yana sake tamƙe face ɗinsa ganin yadda duk tabi ta rikice. Ɗagowa yayi daga rufa mata ɗin da yayi, hakan ya sanƴa ta sauƙe wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya tana gyara tsayuwar ta. Da sauri ta wuce dan ficewa yayi saurin riƙo hannun ta yana dawo da ita. "What do you want?" ta faɗa cikin rawar murya tana kallon sa. ZEEYAD da yakejin kamar ya ɗauke ta daga duniyar nan zuwa wata chan daban suje suyi rayuwar su su kaɗai ne cikin calm voice ɗinsa kamar mai raɗa yace "I miss you." Kallon ƙaramin bakin sa daya furta hakan ta tsaya yi, kafin ta ƙare masa kallo tsaf tana kauda kanta tace "Lies." ZEEYAD da shima ke kallon ta ne yace "Trust me DEENAH..." "Trust you?" ta faɗa tana kallon sa kafin ta ɗaura da faɗin "Aren't you even ashamed of yourself na tsayawa a gaba na yanzun, you missed me after all i know shine kana avoiding ɗina, you don't want me near you anymore don't you." "Listen DEENAH i..." "No i won't listen, Okay?, ka nuna a gaban Grandma ɗinka cewa baka sanni ba just to impress your girlfriend and make her happy don't you?, you chose to hurt me deeply just to make your girlfriend happy sabida ita ce mai zuciya ni bani da zuciyar jin zafi, right?, and kayi nasarar hakan, i was indeed deeply hurt but...but am fine now bana buƙatar ganin ka, sabida baka neme ni ba, and now that ka ganni anan you even have the gut to stop me, telling me that you want to talk to me?." Tunda ta fara magana yake bin ta da idanu, babu abinda yake hangowa cikin idanun ta sai tsantsar ciwo, ya san bai kyauta mata ba, but he didn't mean to hurt her koh kaɗan. Sauƙe idanun sa yayi ƙasa yana lumshe su, kafin ya sake ɗago su yana kallon ta. "Wait... are you jealous?." "You think we're joking here or something, you doesn't seem to care about my feelings." "Feelings, do you have any feelings for me?" ya tambaya cikin tsare ta da idanun sa. Kauda kai tayi kawai nan yace "Oh gashi nan a fuskar ki ƙiri-ƙiri, you've feelings for me, that is why you're hurt da abinda nayi miki, right?." "Zaka iya faɗamin abinda ya sanƴa ka tsaida ni anan." Shafo gemun fuskar sa yayi dan kuwa shi kansa bai san wani kwakkwaran dalilin da ya sanƴa shi tsaida ta ba, bayan ya yanke a zuciyar sa cewar zai yanke duk wani hanƴa da zai sada shi da ita, but tun ba'a je koh ina ba hakan na neman gagarar sa, he just missed her so much sannan bai ƙi su kasance tare kullum ba, and now zaiyi taking babban risk ɗin bar wa ɗan uwan sa ita, anƴa kuwa zai iya hakan? Ganin yayi shiru bai amsa ta bane ya sanƴa ta faɗin "Baka da wata hujjar tsayar dani da kayi, right?, fine then niɗin ba wai inason jin komai daga gareka bane" ta faɗa tare da wucewa. "Listen, it's about YAZEED." Dakatawa tayi jin ya ambaci YAZEED, juyowa tayi tana kallon sa har ya tako gaban ta ya tsaya kafin ya ɗaura da faɗin "Yes YAZEED is my twin brother so i value duk wani abu da yake so and i will make sure ya sami wannan abin cikin salama ba tare da yasha wahalar komai ba" dakatawa yayi yana kallon ta ganin yadda ta kafe sa da idanu tana kallo. Cikin ƙarfin hali ya cigaba da faɗin "YAZEED loves you wholeheartedly, and kamar yadda Grandma ta faɗa miki a kullum bashida wani magana da ya wuce naki, i know you got alot of questions da kikeson yimin, but we should keep that aside now and talk about something...something that will benefit you and him in the future, thats what i hope insha Allah, i want you to accept YAZEED's proposal and be his future wife please" ya ƙarashe cikin muryar dake nuna alamun daurewa kawai yayi ya faɗi hakan. Sosai mamaki ya cika DEENAH, nan ya sake faɗin. "Let's forget about the feelings we got for each other, i guess kunfi dacewa da YAZEED and am pretty sure you would never regret knotting ties with him, he is a Man with a good and caring heart." DEENAH da baƙin ciki da takaici ya gama rufe ta ruf kasa cewa komai tayi, wato ma cewa yake su ajiye son da suke yiwa juna a gefe ta auri ɗan uwan sa, just dan kawai ya sami wacce ta fita. "Okay" kawai ta iya faɗa takaici na turnuƙe ta. Kallon ta yake yace "Okay, what?." "I will do as you say, ba kanason naso ɗan Uwanka kuma na aure sa bane, i will do so, maybe zai bani farin ciki ma fiye da yadda ka faɗa, i will accept his love request, get engaged to him and then married him, kamar yadda ka buƙata, but before i do that inason sanin komai game da kai tukun, bama ni kaɗai ba inason ka faɗi komai ne a gaban family ɗina da naka, if you do so then zan auri ɗan uwanka kamar yadda ka buƙata." Wani irin abinda ya tokare masa maƙoshi ya haɗiya, shi sam request ɗin da ta nema daga gareshi bai dame shi ba, but cewar ta na ta amince da auren YAZEED ba ƙaramin cilla ruhin sa cikin ɗimuwa tayi ba, wanda daga fuskar sa zaka gano hakan, bai ta6a tsanmanin zata amince da request ɗinsa ba, sai gashi kuma ta yarda zata yi rayuwa da ɗan uwan sa a maimakon shi, he can't believe it tun hakan ma bata fara faruwa ba, he couldn't describe wane irin yanayi yakeji game da hakan, tabbas yanason samarwa ɗan uwansa farin ciki but seems like hakan da zaiyi zai haifar masa da nasa baƙin cikin ne na har abada. Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin yace "Alright, na yarda." Ɗan murmusawa tayi dan kuwa ita kaɗai tasan irin abinda take ƙunsawa cikin zuciyar ta, nan tace "So now tell me, yaushe za'ayi hakan and inaso kayi conviencing doctor ɗinnan da ya bani takardar sallama coz am totally fine now, dan kuwa tun kafin na fara rayuwa da ɗan uwanka nake hango irin farin cikin da zan kasance a ciki, kaga kuwa i.have nothing to worry about kokuma naji cewa that am not loved or something a duk inda na shiga, sabida kuka na yakusa ƙarewa." Kirƙiro murmushi yayi tare da jinjina kai kawai ba tare da ya iya cewa komai ba. Juyawa tayi ta isa ga bakin ƙofar kafin ta juyo ta kallesa kamar wanda aka zarewa ƙuzari a jiki haka nan ya tsaya, murmushi tayi kafin tace "Zaka iya sanarwa YAZEED cewar zai iya fara fitowa hira daga gobe, coz kasan dole ne mu fahimci juna dashi before abubuwa suyi nisa, right?."na Kallon ta kawai yakeyi kafin daga bisa ni kuma yace "Yeah." Juyawa tayi ta fice daga office ɗin tare da barin sa nan tsaye. Zubewa yayi kan kujera yana lumshe idanun sa. "What have i done?" ya furta hakan Inda duk zuciyar sa ta kasa samun kyakkywar sukuni. Tashi yayi tare da ficewa daga cikin office ɗin. ************************* __________DEENAH ɗakin ta dawo nan ta tadda har yanzu Grandma tana nan sai hira take ta zubawa Umma. Samun wuri tayi ta zauna tana kallon su. "Har kin dawo kenan?" cewar Grandma tana kallon ta. Murmushi DEENAH tayi tare da jinjina mata kai. "Toh masha Allah, bari dai na kira Boy yazo ya maida ni gida haka nan, sai gobe kuma idan Allah ya kaimu na dawo" ta faɗa tare da ciro ƴar wayar Cellular ta daga jikin handbag ɗin ta ta hau danne-danne. Knocking ɗin da sukaji bakin ƙofa ne ya sanƴa Umma bada izinin shigowa. Buɗo ƙofar yayi bakin sa ɗauke da sallama ya shigo yana sauƙe idanun sa cikin na DEENAH dake kallon sa, nan tayi saurin kauda kai tana 6ata fuska. Kallon Umma da ta saki baki da hanci duka tana kallon sa yayi tare da ɗan murmusawa. "Toh ai gashi nan ma Boy ɗin, yanzu nake shirin kiran ka kazo ka maida ni gida haka nan" cewar Grandma tana sauƙe wayar a kunnen ta. Kallon Umma ZEEYAD yayi cike da girmamawa ba tare da kuma ya nuna wani abu ba yace "Good day Aunt." Tashi tsaye Grandma tayi tana kallon Umma da har yanzu mamaki ƙarara kan fuskar ta ta kasa cewa komai tace "Wannan shine Boy ɗin nawa da kukaji na dame ku da maganar sa kullum, shine jika mafi soyuwa a gareni, ɗan albarka ba" ta ƙarashe cikin murmushi tana kallon ZEEYAD. Umma miƙewa tsaye tayi fuskar ta ƙarara mamaki tace "How is this possible?" tana kallon ZEEYAD ɗin kafin ta kalli DEENAH da tayi kamar bata gansa ba tace "DEENAH?." Ɗagowa DEENAH tayi tana kallon Umma ɗin, kafin ta shiga nuna ZEEYAD ɗin da yatsa tace "Is he not..." "Ofcourse Umma shine" cewar DEENAH ɗin ba tare da ta nuna wani damuwa ba. Kallon su kawai Grandma keyi kafin ta saki murmushi tace "ZEEYAD kenan, ai jika na ne, kinsan shi ne koh kin ta6a ganin sa a wani wurin, koh da yake ai ba abin mamaki bane, dan kuwa akwai shi da fita ƙasashe daban-daban, tunda koh sati uku mai kyau bai cika da dawowa daga ƙasar taku ba." "Well Aunt i know you may find this STRANGE but she is actually my Grandmom" ya faɗa yana kallon Umma ɗin. "But...but how comes, i mean you were homeless back then, sannan bakada wani family, how then is she your Grandma?" cewar Umma ɗin cikin mamakin da har yanzu bata gama fita daga cikin sa ba. "Umma he would tell us everything soon, probably idan mun bar ƙasar nan tukun." "Do you know about this?" ta faɗa tana kallon DEENAH. Kai kawai DEENAH ta jinjina mata kafin tace "listen Umma i know kina da tambayoyi dayawa da zakiyi masa, but he promised to tell us everything soon." "Meke faruwa ne, mai suke cewa ne?" faɗin Grandma ɗin tana kallon su. Murmushi ZEEYAD ya ɗanyi kafin yace "The Mom is Surprised to see me." "Ka san su ne?." "Probably yes" ya faɗa. Murmushi Grandma tayi kafin tace "Masha Allah, a'ina ka san su?." "It's a long story Grandma, but i will tell you everything soon, coz da akwai abubuwan da ban faɗa miki ba." Kallon sa Grandma keyi kafin tace "Kana nufin kacemin kayi rayuwa dasu lokacin da kaje chan Nigeria ɗin kenan?." Kai ya jinjina mata alamun Eh, nan tace "Amma kuma shine kacemin bakasan DEENAH ba?." Shiru ya ɗanyi kafin yace "Grandma, we should discuss this idan mun isa gida please." Shiru tayi tana kallon DEENAH da Umma dake magana. Gyaran murya Grandma tayi tace "Toh mu zamu wuce, sai gobe kuma." Juyowa Umma tayi tana kallon su, babu yabo babu fallasa tace "Alright, Nagode sosai da kulawar ki." Murmushi Grandma tayi tace "Ai bakomai, you've such a sweet daughter ne shiyasa." "Muje mu ɗan nan, dan kuwa na fara jin bacci" cewar Grandma tana kallon ZEEYAD da idanun sa ke kan DEENAH. Kai ya jinjina kafin ya kalli Umma yace "Good night Aunt." Kai kawai Umma ta iya jinjinawa tana bin su da kallo har suka fice. Juyowa tayi tana kallon DEENAH kafin tace "DEENAH, tell me ya akayi hakan ya faru, maiyasa banga wata damuwa koh farin cikin ganin sa tattare dake ba?." Kallon Umma tayi kafin tayi murmushi tace "Umma kece baki haɗu dashi ba, amma ni tun satin chan da ya gabata na gansa, tabbas yaya Jafar yayi gaskiya, people change, and sometimes for the worse, i thought koh he still needs me kamar yadda na daɗe ina begen ganin sa, but sam a wurin sa ba hakan bane, he had really moved on Umma and he even have a girlfriend." "What?" faɗin Umma cike da mamaki kafin DEENAH tace "You remember the girl da tazo ranan da Grandma?." Kai Umma ta jinjina nan tace "She is his girlfriend Umma, he totally disposed me like i never exist, tabbas naji baƙin cikin hakan but...not anymore Umma." "DEENAH kina nufin kin haƙura dashi kenan, remember sabida shi kike cikin halin nan." "A'a Umma, yanzu na fita daga cikin halin nan tunda har na san matsayi na a wurin sa, his Brother likes me doesn't he, then i will date his brother..." "What, ɗan uwan sa fah, no i can't let you do that DEENAH, that won't make any sense." "Ofcourse it would, tunda har shi ya iya soyayya da wata then menene a ciki dan ni naso ɗan uwansa, am doing this ne kawai so that i will make him regret what he did." Kallon ta kawai Umma keyi, nan ta juyo tana kallon ta tace "Kada ki wani ji damuwa Umma, ni DEENAH have moved on since ranar da na gano matsayi na a wurin sa, daga yanzu kuma babu wani abinda zai sake samuna, haka ma kuma ba zan sanƴa damuwar abinda ba zanci ribar sa a cikin zuciya ta ba, zan kar6i soyayyar ɗan uwansa ne so that i will show him what he really missed." ******************** *TWO DAYS AFTER* ____________"Bro what are you saying ne, it's time da yakamata ace kun haɗu kun gaisa, why are you avoiding ɗin duk wani request da na kawo maka na meeting ɗinta, remember she accepts my love and they are living zuwa country ɗinsu jibi, yakamata ace zuwa yanzu kun san juna da ita, right?." Kallon YAZEED dake ta damunsa da batun yaje yaga DEENAH su gaisa tun ba yau ba yayi, kafin ya sauƙe kafarsa dake ɗaure kan ɗaya yana gyara zama yace "They are living next tomorrow?." Zama YAZEED ɗin yayi yana fuskantar sa kafin yace "Yeah, wannan ne dalilin da ya sanƴa nake damunka tun ba yau ba akan you should meet her ku gaisa, remember baka ta6a zuwa duba jikin ta ba." Murmushin ƙarfin hali ZEEYAD yayi kafin kuma yace "Alright, i will do so, muje mu yau da dare." Wani irin farin ciki ne ya turnuƙe zuciyar YAZEED nan yace "Yo, koh kaifa?, and you know what?." Kai ZEEYAD ya jinjina masa idanun sa kan system ɗin gaban sa. Gyara zama YAZEED yayi yace "Why don't we take them out on a date tomorrow night, i mean that would make sense, right?." Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon sa, kafin yace "On a date?." "Yeah, i mean idan ma hakan ba zaiyiwu ba we should invite her to our house sannan mu gabatar da ita gun mai Martaba, i mean na gabatar da ita gun mai Martaba as yarinƴar da nakeso, kai kuma ka gabatar da Jalilah as taka yarinƴar, kaga gara su san da cewa muna da wadanda muke so ba wai su haɗa mu da wasu ƴaƴan sarakuna chan ba kamar wadanda suka rasa mashinshina." Murmushin maganar tasa ZEEYAD yayi kafin yace "Do you think that would work out?." "Yeah, kana kokonta ne?." Kai ya girgiza kafin yace "I mean ka tabbata Ummien ka bata yi maka mata ba?." Wani irin tsuke fuska YAZEED yayi kafin yace "No, only i have the right ɗin chosing matar da nakeson rayuwa da ita ba wata ba, whether she likes DEENAH or not that won't stop me from marrying her, sai dai idan Allah ne baiyi cewar zata zamto matata ba." Kallon sa ZEEYAD keyi har ya idda maganar tasa kafin kuma yace "Alright then, ka faɗawa Grandma?." "Grandma bata da matsala, she would support this 100% dearly." "And ita yarinƴar taka, do you think zata yarda tazo nan?." Shiru YAZEED ya ɗanyi kafin yace "Zan faɗawa Grandma ta shawo mana kansu daga ita har Ummien ta, i know zasu zo." Shiru kawai ZEEYAD yayi yana jinjina kai kafin kuma daga bisani yace "So yanzu mu bari sai goben kawai idan sun zo, right?." "No, you should be ready by anjima zamuje mu." Murmushi ZEEYAD yayi kafin yace "Alright, see you then, i need some rest i guess" ya faɗa yana tashi tsaye tare da tattara abubuwan sa. Miƙewa YAZEED ma yayi suka jera inda kowannen su ya wuce nasa part ɗin, kan anjima zasu sake haɗuwa suje gun DEENAH. ZEEYAD part ɗinsa ya dawo inda ya ajiye system ɗinsa da sauran abubuwa ya wuce bedroom. Zama yayi kan bed yana riƙe kansa da hannaye duka biyu, it's so hard for him yaga DEENAH tare da wani, ji yake kamar zuciyar sa zatayi bombing ta faso waje, and now ya jawowa kansa abinda ba zai iya kaiwa ƙarshe ba, baya tunanin zai iya jurar ganin DEENAH da YAZEED a matsayin masoya, shiyasa yake dukkanin ƙoƙarin sa na ganin ya toshe hanƴar faruwar hakan, and gobe kuma yake shirin inviting ɗinta zuwa ganin family ya kuma gabatar da ita matsayin yarinƴar da yakeso, baya tunanin zuciyar sa zata iya jurar ganin hakan. Kwanciya yayi fuskar sa na kallon sama, sosai ya rasa sukuni ya kuma rasa abinda keyi masa daɗi, bai ta6a tunanin haka hukuncin da ya yanke zata zo tayi turning tana bibiyar sa tare da azabtar masa da zuciya ba. Idanun sa ya lumshe yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa tana beating really fast, huci mai zafi ya furzar yana miƙewa zaune, kafin kuma ya tashi ya hau zagaye ɗakin zuciyar sa a matuƙar cunkushe. ********************* _______Da dare kamar yadda suka shirya hakan ce ta faru, kaya iri ɗaya suka sanƴa shi da YAZEED, kafin su ɗau wata zazzafar mota daga cikin na Masarautar su nufi asibitin. DEENAH dake ta faman shirye-shirye sosai ta haɗe cikin riga da skirt ɗinkin atamfa, wanda yayi mata ɗass a jiki, batayi kwalliya ba koh kaɗan face lip-gloss ɗin Umma da ta shafa a bakin ta sai kuma kwalli, sai dai irin kyawun da tayi ba'a magana sai wanda ya gani kawai. Ita dai Umma da kallo kawai take bin ta, dan kuwa itama rabon da taga DEENAH cikin wannan shiga mai kyau haka ta manta tun kafin ta kwanta rashin lafiya, kuma da yake ita ɗin gwana ce wurin son ƙananun kaya shiyasa duk ranar da ta sanƴa atamfa take yi mata bala'in kyau. Ɗagowa DEENAH da sai zuba ƙamshi take tayi tace "Umma wallahi kinyi dabara da kika ɗauko min wannan kayan atamfar kamar kinsa kuwa zan buƙace ta." Murmushi kawai Umma tayi tana kallon ta kafin tace "Yanzu shi wannan wankan duk na YAZEED ɗin ne koh na ZEEYAD?." Tsayawa tayi tana kallon Umma kafin kuma ta ɗaga kafaɗa alamun bata sani ba. Kai kawai Umma ta girgiza tare da faɗin "Allah ya kyauta." Murmushi DEENAH tayi tana jujjuyawa tace "Umma nayi kyau sosai, koh na canza?." Kallon ta Umma keyi tace "Kinyi kyau sosai amma matsalar ai babu mayafi bamu taho dashi ba, idan kuma zaki sanƴa Hijabin ne gashi chan ki ɗauka ki saka." Shiru tayi tana kallon Umma kafin tace "Umma idan na sanƴa Hijabin tayaya zai ga wankan nawa yaji kishi da haushi?." "Shi wa?" cewar Umma. Ɗan turo baki tayi kafin tace "Ni koma waye a cikin su." Murmushi kawai Umma tayi ba tare da ta sake cewa komai ba. Zuwa DEENAH tayi ta zauna bakin bed ɗin tana jiran isowar su, dan kuwa tunda YAZEED yace mata tare suke da ZEEYAD ya sanƴa ta ɗaukar alwashin ƙunsa masa baƙin ciki tare da sanƴa sa nadamar sadaukar da ita da yayi mawa wani. After kamar 20mins suna zaune da Umma ta suka jiyo knocking a ƙofar. Kallon juna sukayi ita da Umma kafin kuma ta miƙe a hankali cikin takun ta mai ɗaukar hankali ta isa ga bakin ƙofar. Juyowa tayi tana kallon Umma sakamakon zuciyar ta da taji tana bugu, ɗauke kai Umma tayi kafin kuma ta murɗa handle ɗin ƙofar tana buɗewa. Idanun ta ne suka sauƙa kan YAZEED dake tsaye saitin ƙofar, wani irin tsadaddan murmushi ta sakar masa tana basa hanƴa. Kallon ZEEYAD dake controlling kansa yayi tare da faɗin "Come on dude." Bin bayan sa ZEEYAD yayi suka shigo cikin ɗakin bakin su ɗauke da sallama. Da kallo DEENAH tabi bayan su ganin duk sun wani sanƴa kaya iri ɗaya babu ta yadda za'ayi ka gane wanene wannan a cikin su indai har ba sun juyo bane. Murmushi Umma ta sakar musu suna samun kan couch su zauna kafin su shiga gaisawa da ita. Tashi tayi ta basu wuri tana ficewa daga cikin ɗakin. Ƙarasowa DEENAH tayi tana zama facing ɗinsu fuskar ta ɗauke da murmushi ta shiga gaida su. YAZEED da yakejin sa a sararin samaniya tsabar farin ciki ne yace "Hi DEENAH, you look..." shiru yayi ya kasa iddawa sabida sam baisan da wace iriyar kalma zai misalta kyawun da tayi ba. Murmushi DEENAH tayi tana sunkuyar da kai kafin ta tsinkayo muryar sa yana faɗin "What kind of dress is this, is it your traditional attire?." Kai ta jinjina masa tace "Yeah , do you like it?." "Yeah, it's pretty Wow, i mean you look so gorgeous in it, right bro?" ya faɗa yana ɗan bugun ZEEYAD da ya kasa ɗagowa ya kalli DEENAH ɗin tunda suka shigo da kafaɗun sa. Ɗago da idanu yayi yana sauƙe su kan DEENAH dake zaune fuskar ta ɗauke da murmushi tana kallon YAZEED. Sosai ya shagala da kallon ta, sabida wani irin kyawu da yaga tayi masa, har sai da YAZEED ya sake ta6a sa kafin ya dawo hayyacin sa yana wani irin mugun haɗe rai yawa wanda yaci guna. Murmushi YAZEED yayi yace "Look he couldn't get his eyes off you, i told you kinyi kyau sosai, he is my brother ZEEYAD meet him." Kallon sa DEENAH tayi tare da faɗin "Hi, nice meeting you ZEEYAD." Wani irin mugun haushi ne ya mamaye masa zuci yana mimmicking yadda tayi maganar a zuciyar sa, wato kar dai har ta fara jin daɗin soyayya da YAZEED ta fara zuba sa kwandon shara?, shine tunanin da yakeyi a ransa. Maida kansa kawai yayi yana haɗe rai, sosai wani irin bala'in kishi ke taso masa, bai ta6a ganin tayi kyau kamar na yau ba, she is just perfect a komai, baikamata ace tayi disposing body structure ɗinta a wani haka ba. _"So waye wanin anan yanzu, nine or YAZEED?"_ ya faɗi hakan a ransa fuskar nan tasa a matuƙar ɗaure. Shiru yayi yanajin yadda suke hira tsakanin su, kamar ba wannan DEENAH ɗin da ya sani ba, ɗago da idon sa yayi yana kallon ta ganin yadda take yiwa YAZEED ɗin magana cike da shagwa6a shi kuma yana biye mata. Ji yayi ba zai iya jurar ganin su hakan a tare ba, miƙewa yayi daga zaunen da yake yace "Idan ka gama ina Mota" yana faɗin haka yayi gaba ba tare da ya jira yi cewar YAZEED ɗin ba. Da kallon gefen ido ta bisa, tasan koh bakomai ta ƙunsa masa kishi da baƙin ciki ne ya sanƴa shi tashi ya fice, but bai ma ga komai ba tukun tunda hakan yaso. Kusan almost 20mins ya ɗauka a mota yana jiran fitowar YAZEED amma yaji shiru, inda tsaki kuwa yaja ta yafi sau miliyan a zaman nasa. Hango su da yayi tafe ne ya sashi kafa mata idanun sa daga cikin motar yana bin duk wani motsi da surar jikinta da kallo. Wani irin zazzafar huci ya fesar ganin ta haɗa komai da ake buƙata wurin cikakkiyar ƴa mace tattare da ita, babu abinda yafi ɗauke masa hankali a jikin ta kamar waist ɗin ta. Tsaki yaja a karo na barkatai ganin yadda suke wani taku kamar ba zasu taka ƙasar ba, ga kuma wani irin nonnoƙe kai da takeyi da alamu dai shagwa6a take zuba masa. Har suka ƙaraso wurin idanun sa akan DEENAH, buɗe wurin mai zaman banza YAZEED yayi ya shiga tare da rufo murfin motar yana sauƙe glass ɗin. Wani irin haushi ne ya turnuƙe ZEEYAD nan yace "Aren't you guys done?." "1 minute please" ya faɗa yana masa nuni da hannu ba tare da ya juyo ya kalli ZEEYAD ɗin ba. Sako kanta tayi ta cikin window ɗin motar tace "Bye take care of yourself." "Sure" faɗin YAZEED ɗin cikin murmushi kafin tayi masa waving tana sakar masa murmushi tare da barin jikin motar. Maida glass ɗin motar yayi ya rufe, kafin ya kalli ZEEYAD da saura ƙiris ya fashe tare da sosa kai yace "Sorry bro i kept you waiting." ZEEYAD bai kula shi ba haka ma bai tanka masa ba yaja motar a mugun tsiyace suka bar cikin asibitin. Murmushi DEENAH ta sakar tare da bin motar da kallo tace "Let this serve as a lesson to you Abyad, this is just the BEGINNING." *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..................✍🏽* [8/12, 1:27 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *040...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ________Liyafa ce mai rai da lafiya ake shiryawa cikin MASARAUTAR a yau, kasancewar the princes zasu gabatar da wacce suke so yau a gaban fada. Da kaga fuskar mai Martaba washe take da iriyar tsantsar farin cikin da yake ciki, kasancewar girma dama kuma ƙimar sa zai daɗa ƙaruwa a idanun ɗumbin jama'a, tunda har ya iya ajiye gwarzayen samari biyu da zai aurar. Grandma kuwa tsabar farin ciki ma rasa inda zata sanƴa kanta tayi, sosai ta kasa zaune ta kasa tashi, sai kai komo take duk dan ganin komai yayi steady yadda ake buƙata. 6angaren JALILAH cike take da wata iriyar tsantsar farin ciki, she can't believe mafarkin ta na zama matar ZEEYAD zai zamto gaskiya, dan kuwa koh da da wasa bata ta6a zaton zai sota har ma yace zai aure ta ba. Zaune take gaban mirror tana cancaɗawa kanta ado, dan kuwa bata tunanin zata sake yarda da wata baiwa ta sake shirya ta, dukda kuwa ido rufe take neman su Kiki da take zargin su suka aikata abincan. Sosai tasha ado cikin Maroon ɗin gown mai matuƙar kyau da tsada. Tashi tayi tsaye tana jujjuyawa cikin shigar tata dan kuwa ba ƙaramar kyau tayi ba. Tana cikin haka ne ta hango mahaifin ta tsaye ta cikin mirror, hakan ya sanƴa ta saurin dakatawa da abinda takeyi tana juyawa ta kalle shi tare da shan dukkanin jinin jikin ta sakamakon irin kallon da yake aika mata. Takowa yayi ya shigo cikin ɗakin hannayen sa ɗaure a bayan sa, yana ƙare mata kallo from head to toe, kafin ya fara magana cikin tsare gida "Seems like kina cikin farin ciki sabida burin ki ya kusa cika koh?, amma ga chan ɗan uwanki kulle kamar ƙasƙantaccen bawa ke nan koh a kwalar rigar ki, sai ma farin ciki da kike da hakan, i have never seen a worst sister like you wacce ta sanƴa a hukunta ɗan uwanta, kuma dan bakida kunƴa sai ki rasa wanda zaki so kaf duniyar nan sai yaron da ya kasance maƙiyi ga ɗan uwanki, yaron da bashida isasshiyar tarbiyya yake ganin kowa a tsakiyar kansa, yaron da baya mutunta iyayen ki tare da girmama su shi kikeson aura har kuma kike farin ciki da hakan, uhm?" ya ƙarashe yana kallon ta. Ita dai JALILAH kanta sunkuye a ƙasa ta kasa ɗagowa ta kalli mahaifin nata. "Fine then, kije kiyi dukkanin abinda kika ga dai-dai ne a gareki, sannan dukkanin abin da ya biyo baya kiyi kuka da kanki, kar ki kuskura kice zaki kawo mana damuwar ki cikin gidan nan, kada kice ban gargaɗe ki ba." Takawa yayi zuwa bakin ƙofa ya tsaya kafin ya juyo yace "And inason ki sanarwa shi wanda zaki aura ɗin da ya sanƴa a sako min ɗana, idan kuma ba haka ba...kinsan dai nine uba a gurin ki sannan da izini na da kuma amincewa ta za'a ɗaura miki aure koh?" yana faɗin haka ya fice daga ɗakin ba tare da ya kula mahaifiyar JALILAH dake tsaye bakin ƙofa ba. Da kallo tabi mijin nata kafin ta shigo cikin ɗakin tana kallon ƴar tata tace "Grandma ta aiko a taho dake, suna chan suna jiran ki." Ɗago da idanun ta da sukayi sha6e-sha6e da hawaye tayi tana kallon mahaifiyar tata da itama bata wani damu da ita ba, kasancewar tsoron mahaifin ta da take bala'in yi. "Ba...ba zakije bane?." Shiru mahaifiyar tata tayi tana mai tausayin JALILAH ɗin tare da girgiza mata kai tace "Mahaifin ki bai yarje min naje ba." "Yanzu kina nufin haka za'a yi liyafar ke bakya wurin?, dan Allah kizo Ummie" ta faɗa cikin hawaye tana riƙo hannun mahaifiyar tata. "Kada ki damu ai koh banje ba mahaifin ki zai kasance a wurin." Shiru kawai JALILAH tayi tana share hawayen fuskar ta, bata sake tankawa mahaifiyar tata ba ta tattari dogon gown ɗinta tayi gaba. ******* "Have you lost your mind ne YAZEED, ace yau zaka gabatar da wacce kakeso a gaban fada, amma kuma ace banida masaniya akan hakan, sai dai naji a bakin mutane, dah ba dan Jakadiya Salima ta kawomin wannan labarin ba kenan kana nufin har aure zakayi ba zan sani ba." Ta6e baki YAZEED da fuskar sa ke tsuke tunda mahaifiyar tasa tayi kiran sa yayi kafin kuma yace "Well i guess babu wani abin tada hankali anan tunda yanzu kin sani, i was about to call you dan sanar miki sai kuma kika aika a kirawo ni." "You was about to call me, kana nufin ban isa ka tako da ƙafar ka ka sanar dani ba, sai dai ka kira ni ta waya, what has come over you YAZEED har kanada ikon za6ar wacce kakeson ka aura ba tare da ni mahaifiyar ka nasan da hakan ba, sannan gaka nan koh a jikin ka sai ma farin ciki da kake ciki." "Ummie please, bakiji excuse ɗin da na baki bane, atleast ai sai kiyimin uzuri koh, introduction ɗinnan sai nan da awa ɗaya za'a fara shi, why not ki jira har sai bayan an gama ban faɗa miki ba sannan kice zaki ɗau mataki, hun for God-sake?." Kallon sa kawai Sarauniya Hafeezah keyi ganin yadda yakeyi mata kamar wanda shine ya haife ta, hakan ba ƙaramin 6ata mata rai yake ba, yadda YAZEED ke disobeying ɗinta a komai, haka ma kuma baya including ɗinta cikin komai na rayuwar sa. "Fine then, ka faɗamin ƴar gidan wacce sarki koh mai mulkin zaka aura, nasan ba zaka bani kunƴa ba ta wannan fannin." Wani irin kallo ya bita dashi kafin yace "What do you mean?." "Ina nufin da akwai ƴaƴan manƴan masu mulki dayawa a wannan ƙasar, dama wajen ta, nasan tabbas ba zaka auro min wacce iyayen ta ba sanannu bane a duniyar kokuma ƙasar tasu." Scoffing yayi yana kallon mahaifiyar tasa cike da mamaki yace "Na auro miki as how?." Rolling idanun ta tayi kafin tace "Koma dai menene ka fahimci abinda nake nufi, ba zan kar6i surukar da ba ƴar gidan kowa bace ba, ɗan sarki kamar ka kamata yayi ace ka auro ƴar gidan sanannu kuma masu ragamar mulki wadanda suke faɗa a ji a ƙasa." Murmushin takaici ya saki yace "Kinfi son na kawo miki ƴar masu mulki kuma masu faɗa aji a ƙasa, Wow." Murmushi tayi tace "Kwarai kuwa ɗan albarka, faɗamin ƴar gidan wacece ita?." "Listen Ummie, wacce nakeso kuma nake da burin aure ba ƴar nan ƙasar bace, sannan kuma ba ƴar masu mulki koh dukiya bace, suna da rufin asiri sosai, look koh da a cikin bayin gidan nan na sami wacce nakeson aura why do you care, ke zaki zauna da ita koh ni?, i guess i have the right to chose whoever i want to marry..." Dakatar da shi tayi ta hanƴar ɗaga masa hannu tace "Enough, mai kake shirin faɗamin ne haka, yarinƴar ba ƴar ƙasar nan bace, sannan kuma ba ƴar gidan kowa ba, kasan abinda kake faɗa kuwa YAZEED?, ƴar talakawa kakeson ɗauko min a matsayin suruka, a whole me da girma na da daraja ta ka ɗaukomin wata kucaka chan daga wata ƙasar wacce ba ƴar gidan uban kowa ba kace zaka kawomin ita a matsayin suruka, are you insane?." "Ummie what's wrong with you, maiyasa kike yimin haka ne, duk wani abu da zanyi shikenan ba zan burge ki ba, a komai kinfi son ki ɗaura ni kan abinda ba shine ra'ayi na ba, am a grown up now Ummie and i have the freedom da zan yankewa kaina hukuncin duk wani abu a cikin rayuwa ta, i love DEENAH sannan babu wani mahaluƙi da ya isa ya hana ni auren ta, so just rest your mind ki zuba ido, idan kina ganin ba zaki iya jurar kallo ba then ba sai kinje wurin ba" yana faɗin haka ya fice a fusace ya bar ɗakin nata. Da mugun kallo ta bisa tanajin zuciyar ta nayi mata zafi, tabbas YAZEED na neman kaita bango, babu ta yadda za'ayi ta bari ya auri wata ƴar matsiyata ne bayan ga yaran manƴan mutane nan kyawawa kaca-kaca. ****** Kwance yake shi kaɗai cikin ɗakin nasa idanun sa a lumshe kamar mai bacci, sai dai a zahiri ba baccin yake ba. Sosai ya luma duniyar tunanin DEENAH, wanda tun jiya da dare da ya ganta, dama kuma yadda sukeyi da YAZEED ya kasa samun kyakkywar bacci bale sukuni tattare dashi, he was very disturbed ganin kamar ya 6allowa kansa ruwa, and yau DEENAH zata shigo MASARAUTAR su a matsayin matar da ɗan uwan sa zai aura while shi kuma an barsa da JALILAH, yeah chosing JALILAH a matsayin matar aure is not a big deal, tunda the girl is cool and decent, but dukkanin zuciyar sa ta karkata ne zuwa ga DEENAH, he just couldn't believe iriyar wautar da yayi. Knocking ɗin da yaji a bakin ƙofar ɗakin nasa ne ya katse masa tunanin sa, dan haka miƙewa yayi yaje ya buɗe nan yaga YAZEED tsaye cikin shigar sa ta alfarma, sosai yasha kyau kamar mai zuwa gasar kyau ta maza. Murmushi ZEEYAD ya saki na ganin ɗan uwan nasa, shigowa YAZEED yayi ɗakin yana bin ZEEYAD da koh alamun shiryawa bai fara ba. "What is this bro, baka shirya ba, abin nan is less than 30mins yanzu a fara." Zama ZEEYAD yayi akan couch ɗin dake ajiye a ɗakin yace "Yeah i know, yanzu zan shirya." "And munyi waya da DEENAH tacemin sun shirya so na aika driver su ɗauko su, you should get ready too, and you know what?." Girgiza kai ZEEYAD yayi nan YAZEED yace "I saw your JALILAH, she looks so takeaway." Murmushi ZEEYAD yayi kawai ba tare da yace komai ba. "You should get ready please." "Yeah" ya faɗa yana miƙewa tsaye. "Ni zanje na dawo" cewar YAZEED yana ficewa daga ɗakin. Da kallo ZEEYAD ya bisa kafin shima yayi shirin wanka. ****** "Toh dai gashi yau ZEEYAD ɗinki ke shirin gabatar da JALILAH a matsayin wacce zai aura, bakya tunanin mu ɗau wani mataki ne?." Wani irin mugun kallo ta watsawa Kiki kafin tace "Rufemin baki chan sakarya kawai, na baki aiki kiyi wancan karon banga kyakkyawar result ba sai yanzu zaki wani dameni da batun mai za'ayi, koh da zan bada aiki ba zan sake baki ba sabida shirme kawai zakije kiyimin." Sunkuyar da kai Kiki tayi tare da faɗin "Afuwan ranki shi daɗe, yanzu kina nufin kice kin samu mai yi miki wani aikin ne kokuwa?." "Koh ma dai menene, kedai naki ido" ta faɗa cikin murmushin mugunta. ****************** Sosai aka ƙawata cikin fadar tayi kyau, duk wani lungu da saƙo da zakabi gauraye take da hasken kwan fitila haka ma mutane ke ta kai komo kowa na harkar abinda aka sanƴa shi. Tundaga layin mashigar MASARAUTAR dake gauraye da hasken kwan fitila DEENAH da Umma suka saki baki suna kallon Aljannar duniyar dake gaban su, ganin irin ƙatuwar faffaɗar MASARUTAR dake gaban su ya sanƴa ta kallon driver mai jan nasu tace "Bawan Allah, anƴa ka tabbata nan aka ce ka kawo mu kuwa?" dan kuwa ita duk ta tsorata haka ma DEENAH dake ta wuwwula manƴan idanun ta dan kuwa sun fara zargin idan ba sayar dasu driver ɗin ke son yi ba. "Nan ne ranki shi daɗe, babbar MASARAUTAR CAIRO kenan, koh ba kune wadanda Yarima YAZEED ya sanƴa na ɗauko ba?." Kallon juna Umma da DEENAH sukayi a mamakin ce jin abinda ya faɗa "Yarima YAZEED kuma, kodai Doctor YAZEED?." Dariya driver yayi yace "Ai duk shi ɗin ne, shi ɗin ɗan sarki ne haka ma ɗan uwansa ZEEYAD da ya dawo bayan shekaru goma da 6atar sa" ya faɗa daidai lokacin da aka ɗaga buɗe musu ƙofar MASARAUTAR suna shigewa. Baki, hanci duk Umma da DEENAH suka saki jin abin kamar almara, kenan hakan na nufin su ɗin ƴaƴan sarki ne komiye?, shine tambayar da kowannen su ke buƙatar sanin amsa. Haka nan aka isa har gaban fada dasu yayi parking ya juyo ya kallesu yace "Mun iso ranki ya daɗe, wannan ita ce ƙofar shiga fada, sannan anan za'ayi taron." Umma da ta sha adon ta cikin Lace ɗinkin bubu ne ta kalli DEENAH da duk jikin ta ya gama sanƴi tace "Amshi wayar ki kira sa kice mun iso" ta faɗa tana miƙa mata wayar. Amsar wayar DEENAH tayi tare da ƴan danna kiran lambar YAZEED ɗin, har ya tsinke bai ɗaga ba tana shirin sake ƙira taga nasa kiran na shigowa. Ɗagawa tayi tare da sanar dashi cewar sun iso. Driver ta miƙawa wayar kamar yadda ya faɗa, bayan sunyi waya da driver ɗinne kuma ya maida mata wayar ta kafin yaja motar su bar wurin. "Toh, ina kuma zamu yanzun?" cewar Umma. Yace na kaiku chan 6angaren "Hajiya Babba, wato Grandma." Sauƙe ajiyar zuciya Umma tayi tana jin hankalin ta na ɗan kwanciya. Sauƙe su yayi a gaban wani babban part, suna zuwa suka hango YAZEED ɗin da Grandma tsaye suna jiran isowar su. Da sauri Grandma ta ƙaraso tana buɗe 6angaren da Umma take tana yi musu maraba da zuwa. Runguma ta baiwa Umma cikin jindaɗin ganin ta, kafin tayi saurin ƙarasawa wurin DEENAH da ta haɗe cikin baby pink ɗin gown ɗin da ta tilastawa Umma saya mata shi tana rungumo ta haɗi da manna mata kiss a ƙunci tana yi mata barka da zuwa. Murmushi DEENAH ta saki tana maida duban ta kan YAZEED dake kallon ta yana murmushi. "Hi" tace masa. Maida mata martanin murmushin yayi yace "I can't take my eyes off you." Murmushi DEENAH ta saki tana sunkuyar da kai ƙasa, Grandma ce tace "Toh ya isa haka nan, muje daga ciki ayi komai a gama dawuri." Duk jerawa sukayi suka shiga ciki duk wayewar Umma da DEENAH wannan MASARAUTA bata ishe su da kallo ba. JALILAH ce tazo cikin ɗan gudu gown ɗinta dake ɗan jan ƙasa a hannun ta. "Welcome Aunt" ta faɗa cikin murmushi tana kallon Umma. Murmushi Umma ta maida mata tace "Thank you dear." Kallon DEENAH tayi tare da sakin baki kafin tace "Wow" tana ƙarasawa wurin ta ta riƙo ta. "You look good" cewar DEENAH tana kallon ta cikin murmushin yaƙe dan kuwa itace ta kwace mata Abyad ɗinta. "Thank you, sai dai ban kai ki ba" cewar Jalilah ɗin. Murmushi DEENAH tayi a zuciyar ta tana faɗin _"Uhm tunda har ya iya ganin ki kika ɗauke masa hankali wa yafi haɗuwa cikin mu kenan?"_ "I like this your head tie, ya akeyin sa?" cewar JALILAH tana kallon ɗaurin dake kan DEENAH. Baƙin dogon gashin ta da ya sha gyara ya sauƙa mata har gadon bayan ta kanta babu ɗankwali DEENAH tabi da kallo a zuciyar ta tana mamakin yadda basu cika son rufe gashin nasu ba, nan tace "Kina so ne kema, sai nayi miki." "Yeah, ofcourse amma dai ba yau ba tukun" ta faɗa cikin ɗan dariya. Murmushi DEENAH tayi kawai zuciyar ta fal mamaki ba tare da tace komai ba. Kallon su Grandma tayi tare da yin murmushi tace "Tabarakallah Masha Allah ƴaƴan nan ba ƙaramin kyau kukayi ba a tare, ina roƙon Allah yasa zumuncin ku tayi kyau fiye da yadda kukayi kyau a yanzun. Ita dai DEENAH Grandma ba ƙaramin mamaki take bata ba da wannan surutun da ba'a tambaye ta, wai ita nan har ta gama yankewa ita YAZEED zata aura JALILAH kuma ZEEYAD. "Kuje ku sami wurin zama kafin mazajen naku su ƙaraso koh" cewar Grandma. _"Mazaje?"_ faɗin DEENAH cikin ranta tana mai samun wuri ta zauna. Ba'a jima ba YAZEED da yaje kiran ZEEYAD suka shigo dukkanin su cikin shiga iri ɗaya ta alfarma. DEENAH idanu ta zuba musu har suka ƙaraso wurin dan kuwa ba ƙaramin burge ta sukayi ba, ganin sun kusa haɗa idanu dashi ne yasa ta saurin kauda kanta zuwa wani wurin pretending bata ganshi ba. Haka ma 6angaren Umma da mamaki ya jiƙa ta ya shanƴe ke binsu da kallo har ZEEYAD ɗin ya gaida ta cikin girmamawa ta amsa masa. Kallon kowannen su da ya sha kyau ba'a magana Grandma tayi kafin tace "Masha Allah, yanzu tunda kowannen ku ya halarta anan yanzu duk sai mu lula zuwa chan fadar mai Martaba, nasan yana chan yana jiran isowar surukan nasa. DEENAH ji tayi gaban ta ya faɗi, anƴa kuwa abin nan da take shirin aikatawa ba kuskure bane, anƴa kuwa ba zata yi wasa da feeling ɗin YAZEED ba?, idan shi ZEEYAD ya yarda yayi sacrificing soyayyar sa then ita kuwa bata tunanin batayi kuskuren amincewa da soyayyar YAZEED ba tunda ba wai tana sonsa bane, idan ta bari wani abu na aure ya ƙullu tsakanin su yanzu then kanta ta cuta kokuma dai ZEEYAD ɗinne ya cuce su baki ɗaya?, da wannan tunanin a ranta take kallon JALILAH da ZEEYAD dake zaune kusa da juna shi kansa a sunkuye yayin da ita kuma take yi masa magana cikin murmushi. Kauda kanta tayi tana danne abinda ke taso mata cikin zuciya. "Maza duk ku tashi muje, ga nan motocin sun iso duk ku tashi muje" cewar Grandma tana yi musu magana. Duk tashi sukayi inda Grandma da Umma suka jera. YAZEED ne ya ƙaraso wurin DEENAH yace "Lets go princess." Kallon sa tayi tare da maida masa martanin murmushin kafin ta kalli 6angaren su ZEEYAD dake jiran JALILAH wacce ke gyara ɗaurin igiyar takalmin ta, ganin tana neman 6ata musu lokaci ne ya sanƴa shi durƙusawa ya shiga gyara mata, DEENAH batasan sadda tayi rolling manƴan idanun ta tana wani irin frowning fuska ba. Kallon ta YAZEED yayi yace "On your lead" ya faɗa yana nuna mata hanƴa. Murmushi tayi kafin tayi gaba sabida karma zuciyar ta yayi bursting da baƙin ciki yana mara mata baya. Da kallon gefen ido ZEEYAD dake gyarawa JALILAH takalmi ya bita, dan kuwa shima yau yayi alƙawarin ƙunsa mata kishi da gangan tamkar yadda tayi masa jiya. Bayan ya gyara mata ne ta tashi tsaye kafin suma su bar cikin part ɗin Grandma. Duk motoci suka shiga cikin abinda bai fi mintina biyu ba suka iso fadar mai Martaba ɗin. Duk buɗe musu ƙofa akayi suka fito. ZEEYAD da zagayowa yayi ta 6angaren JALILAH tare da buɗe mata ƙofar yana miƙa mata hannun sa. JALILAH da zuciyar ta ke cike taf da farin ciki nata hannun ta basa kafin ya taimaka mata ta fito, hannun ta ɗaya riƙe da gown ɗinta da ta ɗan tattare shi, kallon ta yayi yace "Ina maids naki?." "I don't need them today, i can manage things on my own." Kai ya jinjina hannun ta cikin nasa yayi leading ɗinsu zuwa ciki, kasancewar su DEENAH har sun shige. Shigar su keda wuya aka maida ƙofar fadar aka rufe. Sosai aka ƙawata faffaɗar fadar da kwalliya da kujera masu kyau da ɗaukar hankali, Umma da DEENAH kam mamakin da suke ciki har yanzu bai gama ficewa daga zucin su ba. Hango sa tafe riƙe da hannun JALILAH ba ƙaramin ƙona mata rai ba _"Seems like he enjoyed touching girls da ba muharamman sa ba"_ ta faɗi hakan cikin ranta tare da kauda kansa daga garesu. Sosai mutane suka hallara cikin fadar, inda kowa sai bin DEENAH da Umma yake da kallo, hakan ya sanƴa jikin su yin sanƴi ganin su tsakiyar wasu ƙabilu. Umma ce ta ƙaraso inda DEENAH da YAZEED ke tsaye tana kamo ta ta yadda babu wanda zai ji mai take cemata tace "DEENAH, ban fah gane komai ba, i mean such a big Mansion kamar wannan..." "Umma am also nervous, just look at yadda kowa ke kallo na, maybe idan aka tashi taron nan su fayyace mana komai, ki koma wurin Grandma." "Don't be nervous dear, Okay?, ni bari naje" ta faɗa tana komawa wurin Grandma kafin ta shiga introducing ɗinta ga ƴan uwa da abokan arziki. Kallon DEENAH YAZEED yayi yace "Are you...alright?." Murmushi tayi tare da jinjina masa kai tace "Yeah, yeah am fine." "Come on, thats my Mom over there, you should meet her" ya faɗa yana nuna mata saitin inda Sarauniya Hafeezah da wasu matan ke tsaye suna gaisawa. Kallon sa tayi nan yace "No ki saki jikin ki, Okay?." Kai ta jinjina masa kafin tabi bayan sa zuwa gun mahaifiyar tasa. Haka kawai DEENAH taji tsoron matar ya darsar mata a zuciya, ga kuma fargabar tunkarar ta da take. Suna isa ya kira sunan ta "Ummie?" fuskar sa a ɗaure dan kar ma ta sami damar kawo masa wasa. Kallon sa Sarauniya Hafeezah da hankalin ta ke kan aminan ta tayi tare da sakar masa murmushi tana kamo sa tace "My boy, ka gaisa da Aminai na suma iyayen ka ne, wannan shine YAZEED ɗana ne" ta faɗa cikin murmushi tana introducing ɗinsa garesu. Duk kallon sa mata ukun sukayi suna faɗin "Masha Allah." Ɗaya ce tace "Lallai kin iya haihuwa Hafeezah, wannan santalelen saurayi haka?." Murmushi tayi jin yadda suke ta yabon YAZEED ɗin. "Wannan kyakkywar yarinƴar dake tare dashi fah, kodai itace amaryar tasa?" cewar ɗaya daga cikin su wacce daga gani ita ce mai sauƙin kai. Juyowa Sarauniya Hafeezah tayi tana sauƙe duban ta kan DEENAH da sai yanzu ma ta lura da existing ɗinta a wurin, kallon ta ƙare mata daga sama har zuwa ƙasa yayin da murmushin fuskar ta ke gushewa. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽* [8/13, 5:26 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *041...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*NOT EDITED*_ _________Sosai DEENAH tasha jinin jikin ta da ganin expression ɗin fuskar mahaifiyar YAZEED, hakan ya sanƴa ta sunkuyar da kanta zuciyar ta na bugu. Sosai Sarauniya Hafeezah ta gimtse fuska tana bin DEENAH da wani irin wulaƙantaccen kallo kai kace ba mutum bane a gaban ta. "What is this?" ta faɗa tana kallon YAZEED. Kallon DEENAH YAZEED yayi kafin ya kalli mahaifiyar sa yace "DEENAH?, meet my Mom please." Da kyar DEENAH ta iya ɗagowa tare da buɗar baki tace "Good day Aunt." "What is good about this day young lady?" ta faɗa cikin gimtsewar fuska tana kallon DEENAH. Cikin kwantar da murya YAZEED yace "Ummie what are you doing?, she is..." "Don't tell me wannan ce abar da kake son kawomin a matsayin suruka YAZEED." Cize baki YAZEED yayi ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu yace "Ummie please don't try to create a scene here, please i beg you don't said anything stupid da zaiyi annoying DEENAH anan wurin" ya faɗa pleadingly cikin kwantar da murya. Murmushi tayi kafin tace "Hm, mai na faɗamaka tun farko YAZEED?, ban cemaka kada ka ɗauko min ƴar talakawa a matsayin suruka ba, so duk wani abu da ya faru anan kai ka jawa kanka." DEENAH da batasan abinda suke cewa ba, amma dai tasan akanta ne suke magana dan kuwa sam bataga alamun jindaɗin ganin ta a fuskar mahaifiyar YAZEED ba, sosai jikin ta yayi bala'in sanƴi da hakan. "Listen Young lady, ina iyayen ki suke?" ta faɗa tana kallon DEENAH. Ɗagowa DEENAH da idanun ta suka fara tara kwalla tayi tare da faɗin "My...my Mom is here" ta faɗa tana ciccila idanun ta a inda zata hango Umma. "So you're here with your Mom, hoping cewa za'a yi accepting ɗinku zuwa cikin family ɗinnan, who the hell ma ya barku kuka shigo cikin MASARAUTAR nan har ma cikin wannan fadar?, talakawa irin ku aren't worth that." Riƙo Ummien nasa yayi yace "Ummie let's talk this out please." Kwace hannun ta tayi daga riƙon da yayi mata cikin fushi take kallon DEENAH "Listen Young lady, kije ki nemi mahaifiyar ki ku bar cikin MASARAUTAR nan da gaggawa tun kafin na wulaƙanta ku anan wurin." Juyawa YAZEED da idanun sa suka canza launi sabida 6acin rai yayi ga DEENAH tare da faɗin "Listen DEENAH please kada ki ɗau wani abu da mahaifiya ta zata faɗamiki da zafi, am really really sorry okay?" ya faɗin hakan kamar zaiyi kuka tsabar taƙaici. Kai kawai DEENAH ke jinjina masa tana ƙoƙarin controlling hawayen ta. Ɗaya daga cikin ƙawayen Sarauniya Hafeezah ne cikin sigar ziga tace "Your Son is Handsome and wealthy, mai zaiyi da yarinƴar nan, just look at her she isn't not just his type." Hakan ba ƙaramin sake tunzura Sarauniya Hafeezah yayi ba, a tsawace tace "Get this piece of trash out of my sight now YAZEED." Nan duk fah hankalin kowa ya dawo kansu, kowa ya tsaya kallon su. DEENAH wani irin gumi ne ya shiga ƙeto mata kanta a ƙasa, jikin ta inbanda rawa babu abinda yakeyi, a rayuwa babu abinda ta tsana kuma take tsoron faɗawa ciki kamar tozarci da humiliation. A tsawace YAZEED da ransa yayi mugun 6aci yace "Stop this Ummie, what's wrong with you, maiyasa kike yimin haka ne, mai kike nema ne haka da kullum burin ki bai wuce ki 6ata min rai ba?." "Your Mom is right YAZEED, i mean wannan yarinƴar sam ba tsarin ka bace, kalli fah kayan jikin ta, such a cheap dress..." "Enough, wannan tsakani na ne da mahaifiya ta, babu wanda ya nemi magantuwar ki a ciki." "YAZEED stop it, she is like a Mom to..." "No she is not, why not ba zata riƙe girman ta ba, must she interfere?." Babu abinda kakeji sai maganar mutane ƙasa-ƙasa. Kallon DEENAH tayi kafin kuma yadda kowa zai ji ta fara magana "My son here sai ya rasa wacce zai so sai wannan abar, i mean just look at her, a middle class girl like her itace zan yarda ɗana ya aura?, and ina kika samo wannan kaya mai arha haka wanda koh bayin da suke yimin aikace-aikace basu sanƴa kaya irin wadannan na ƙazaman talakawa." Nan fah wurin ya kacame da dariyar masu hali irin na Sarauniya Hafeezah, suma suna tofa albarkacin bakin su. Wata ce tace "YAZEED needs a good looking princess, not a poor brat like her." "And naji ance tana tare ne da mahaifiyar ta, where is your Mom girl?, she needs to stand for you." DEENAH tuni ta fashe da kuka tana jin kamar ta nutse a wurin tsabar kunƴar da suka ya6a mata, YAZEED kawai tsayawa yayi yama rasa abinda zaiyi, idan ransa yayi dubu toh ya 6aci. Sarauniya Nazeerah dake tsaye gefe tana kallon abin dake faruwa a ranta taji babu daɗin abinda akeyiwa DEENAH, sai dai sam ba zata yi interfering ba sabida bata shiga abinda bai shafe ta ba. Sarauniya Naseeba dake tsaye a gefe ta6e baki kawai tayi dan kuwa ba tasu take ba, idanu kawai take ta cillawa koh zata hango inda ZEEYAD da JALILAH suke ta samu ta aiwatar da ƙudirin dake ranta. YAZEED da baisan mai zaiyi wanda ya wuce roƙon mahaifiyar tasa bane yace "Ummie please, stop all this baikamata ba, you're making her cry." "Let her cry all her tears out, who even cares, kwaɗayin su da son abin duniya da kuma bin ƴaƴan masu kuɗi ya jawo mata, banason jin komai daga bakin ka YAZEED, the more ka ɗaga min murya nikuma the more zan cigaba da tozarta ta, the best thing da zakayi shine ka ɗauke ta ka fitar da ita daga nan wurin, muddin bakason ganin hawayen ta." "DEENAH am sorry please, kiyi haƙuri and let's go from here." "No, you won't go anywhere with her, i want her to leave by herself." Bai kula mahaifiyar tasa ba sai ma hanƴa da ya nunawa DEENAH yace "Kiyi haƙuri DEENAH, muje please am so sorry on my mom's behalf..." "Stop begging her on my behalf YAZEED, ka ta6a ganin inda na baiwa wani haƙuri bale kuma wannan kucakar da ka ɗebo min?." "Let's go DEENAH." "Don't you dare take a step or else nothing would stop me from cursing you." Cakk yaja ya tsaya da jin abinda mahaifiyar tasa ta faɗa yana runtse idanun sa. Kallon sa DEENAH tayi tace "You don't have to worry about me...i...zanje na nemi Umma ta kawai mu tafi." "Am sorry DEENAH." "Hafeezah, abinda kikeyi sam bai dace ba, bai zama dole kai zaka yankewa ƴaƴan ka wasu abubuwan game da rayuwar su ba, suma suna da ikon za6ar abinda suka ga ya fiye musu, but ki rage tsanantawa ɗanki haka, abinda kikayi yanzu sam bai dace ba ya kike tunanin yarinƴar nan zataji a zuciyar ta?" faɗin ƙawar ta ta farkon. Wani irin wulaƙantaccen kallo Sarauniya Hafeezah ta wurga mata kafin tace "Ke fah shiyasa bana buƙatar sako ki cikin wasu abubuwan Zakiyya, sabida sam bakisan ina ne ma yakeyi miki ciwo ba bale har kisan abinda yake dai-dai da wanda ba dai dai ba, wannan Ƙazamar yarinƴar kike tunanin zan bar ɗana ya aura?, why not ki bata ɗanki tunda kema mai arzikin ce." Kallon DEENAH matar tayi tace "Banga wani aibu tattare da yarinƴar nan ba Hafeezah, kuma ai da ɗana zai ganta yace yana so kuma ya kawomin ita matsayin suruka babu abinda zai hanani amincewa da hakan." Rolling idanu Hafeezah tayi cike da takaicin halin ƙawar tata, kallon DEENAH dake tsaye har yanzu tayi tace "What is she still doing here, get her out of my sight, and you YAZEED kaji abin da nacemaka idan ka kuskura kayi wani yunƙuri wurin kareta then babu abinda zai hanani buɗar baki na kwashe maka albarka, get out of here lady" ta ƙarashe a tsawace tana aikawa DEENAH da ta kasa motsa koh da ƴar yatsar ta ce mugun kallo. DEENAH fashewa tayi da kuka sosai, tana danasanin amincewa da tayi na zuwa wannan gidan da basu san darajar mutane ba, gashi bata ga Umma koh ZEEYAD a kusa ba, kenan babu mai tsaya mata sai shi YAZEED ɗin, kuma shima mahaifiyar tasa na neman tsine masa muddin yayi yunƙurin sake tankawa. YAZEED can't stand the humiliation da akeyiwa DEENAH dan haka barin wurin yayi zuwa ɗakin mai Martaba yaji dalilin da ya hana shi fitowa har yanzun, da kallo DEENAH ta bisa tausayin kanta na kama ta, ta san shikenan tata ta ƙare tunda har ya bar ta tsakiyar wadannan awakin. Murmushin jindaɗin barin sa wurin Sarauniya Hafeezah tayi, dan kuwa daga yau ta sami kalmar faɗa aduk sadda yayi yunƙurin yi mata gardama akan abinda ta sanƴa shi. Wata ƴar budurwa ce ta ƙaraso kusa da DEENAH tana ta6a material ɗin kayan jikin ta, kafin ta kalle ta tace "Irin kayan nan ai koh karen da nake kiwon sa bana sanƴa masa kaya masu arha haka nan." Duk dariya shaiɗanun wurin suka sanƴa. "Aunt Hafeezah, kada kiyi gaggawar fitar da ita daga fadar nan tukun har sai mun tozarta ta iya son ranmu wanda nan gaba koh motar masu arziƙi ba zata iya ɗaga ido ta kalla ba." Murmushi Sarauniya Hafeezah tayi kafin tace "Na baku damar hakan, ku koya mata hankali yadda yakamata." Hannu yarinƴar ta kai da niyyar fuzge ɗaurin kan DEENAH sai dai ta kasa hakan sakamakon muryar sa da taji. "What's going on here?" ya faɗa yana bin kowannen su da kallo. DEENAH buɗe idanun ta da ta runtse tayi sakamakon jin muryar sa da tayi a bayan ta dan haka da sauri ta juya tana kallon sa da fuskar ta da ya 6aci da hawaye sha6e-sha6e. "DEENAH?" ya kira sunan ta yana ɗan waro idanun sa cike da mamakin ganin hawaye kan fuskar ta. DEENAH sai yanzu ta ɗanji relief dan haka da gudun ta taje tana faɗawa jikin sa tana ƙanƙame shi tare da sakin wani sabon kukan fiye da na dah. Hankalin sa tashe ya ɗago da fuskar ta yana tambayar ta abinda ya same ta. "Tell me DEENAH, mai ya sameki, did something happened to you? tell me wa ya saki kuka?" ya faɗa cikin 6acin rai idanun sa na canza launi. Kuka kawai DEENAH keyi ba tare da ta iya bashi amsar tambayoyin sa, maida kanta yayi ya rungume a ƙirjin shi tare da lumshe idanun sa yanajin kukan nata na ratsa duk wani 6argo na jikin sa. Sosai kowa na wurin ya cika da mamakin ganin su a hakan, inda kuma murmuring ɗin mutane ya fara tashi ƙasa-ƙasa. Sarauniya Hafeezah, Nazeerah, dama kuma Naseeba duk sakin baki sukayi suna kallon su, hatta mutanen dake zagaye dasu baki ɗaya, haka ma JALILAH da Sadeeq dake tsaye a bayan su. Bai sake ta ba har sai da yaji ta tsagaita da kukan nata tukun ya ɗago ta tare da cupping fuskar ta yana kallon ta. "DEENAH, tell me wa ya sanƴa ki kuka, and where is YAZEED, who the hell have the gut to make you shed tears like this?." Cikin muryar sabon kukan dake zuwa mata tace "Kada kaga laifin sa, ma...mahaifiyar sa ce tace zata tsine masa muddin yayi yunƙurin tankawa." Ɗago da jajayen idanun sa dake nuna tsantsar 6acin rai yayi yana sauƙe su kan Sarauniya Hafeezah dake tsaye tana kallon su. "Mai tayi miki?" ya faɗa yana kallon DEENAH ɗin. Kuka kawai take ta kasa basa amsa, koh ba'a ce masa komai ba yasan tayi humiliating ɗinta ne gaban mutane. Kauda idanun ta tayi daga kallon da yakeyi mata, janƴe DEENAH yayi daga jikin sa yana ƙarasowa gaban ta tare da nuna ta da yatsa yace "You..." shiru yayi yana sauƙe hannun sa tunawa da yayi ita ɗin mahaifiyar YAZEED ce, komin munin halin da zata nuna, dole ya ɗaga mata ƙafa albarkacin ɗan uwan shi. Juyawa yayi a fusace ba tare da yabi ta kan kowa ba yana riƙo hannun DEENAH ɗin ya jata suka fice daga cikin fadar. Wata iriyar 6oyayyiyar ajiyar zuciya Sarauniya Hafeezah ta sauƙe tana bin inda suka bi da kallo. "What the hell nake gani cikin idanu na haka?" cewar Kiki tana kallon Sarauniya Naseeba da mamaki ya gama shanƴe ta ta kasa koh da ƙifta idanun ta ne daga bin inda suka bi da kallo. "Ban fah gane ba, he became so mad and angry da ganin hawaye kan fuskar yarinƴar nan, meke faruwa ne?" faɗin Kiki ɗin cikin nazari. Barin fadar Sarauniya Naseeba tayi inda Kiki ɗin tayi saurin mara mata baya. JALILAH ji tayi jikin ta yayi sanƴi, zuciyar ta fal cike da tunanin abinda ya faru anan. Sadeeq kuwa jan jikin sa shima yayi ya bar cikin fadar, he can't believe wauta irin na ZEEYAD da DEENAH, yanzu dole zuƙatan mutane dayawa ya cika da zargi kala-kala. ***************** ______"It's alright DEENAH, stop crying please" ya faɗa idanun sa kan fuskar ta da ta kasa barin kukan har yanzu. "Just...just ka kaini wurin Umma ta, where is she?." "I guess tana tare da Grandma a part ɗinta." "Take me to her, i don't wanna stay here any longer" ta faɗa cikin goge hawayen fuskar tata. Kallon ta kawai ZEEYAD yake cike da tausaya mata, yasan halin Sarauniya Hafeezah zatayi fiye da abinda tayi wa DEENAH a yanzun, but ta wani 6angaren kuma zuciyar sa cike take da haushin YAZEED da ya bari mahaifiyar sa ta ciwa DEENAH mutunci a gaban ɗumbin jama'a. Cupping fuskar ta yayi yana share mata hawayen yace "Stop crying DEENAH." Cire hannun nasa tayi daga riƙon fuskar ta da yayi tana faɗin "Ka kaini wurin Umma ta." "Listen am sorry for not been around lokacin da ake ci miki zarafin nan." Kallon sa tayi tace "Koh kana nan ɗinma what can you do, is she not your Mom?, you can't do anything." Kallon ta yake yadda take maganar cikin kuka tana share hawayen ta. Ɗan murmusawa yayi kafin yace "No she isn't my Mom." Tsagaitawa tayi da goge hawayen nata tana kallon sa. "She is YAZEED's Mom and my Stepmom" ya sake faɗa. "Where...where is your Mom then?." Shiru yayi yana kallon ta kafin ya ɗan kauda fuskar sa yana cize lips nasa. "Tell me" ta sake faɗa tana kallon sa. "I only have my Grandma and... Dad maybe." Ji tayi jikin ta yayi bala'in sanƴi, cikin calm voice tace "Am so sorry for your lost..." "Don't be sorry please, nobody is meant to stay in this world permanently, just pray for her." Kai ta jinjina masa tace "Allah yasa tana makoma mai kyau." Kai ya jinjina mata kawai cikin murmushi. "We should go to your Mom" ya faɗa yana buɗe murfin motar da suke ciki. Saurin riƙo hannun sa tayi, hakan ya sanƴa shi tsayawa kallon ta, maido ƙofar yayi ya rufe. Kai ta girgiza masa tace "Tell me more about you, i need to know who you really are, and how you end up being a homeless person back then, and how you turned to be so rich and Famous like this." Murmushi yayi yana riƙo hannayen ta yace "I will tell you everything, but not now." "Har sai yaushe then?, we are living tomorrow Morning and you don't want to tell me anything about what you are." Kallon ta yake cikin murmushi, nan yace "Why do you want to know everything about me?." "Never mind" kawai ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe murfin motar yace "Listen..." Juyowa tayi tana kallon sa nan yace "I will tell you what you wanna hear." "Tell me" ta faɗa tana kallon sa. Kallon cikin idanun ta yayi kafin ya buɗi baki cikin calm muryar sa yace "I love you DEENAH." Ji tayi zuciyar ta ta wani irin bada sauti da jin abinda ya furta, kallon sa kawai take idanun ta na tara hawaye. A fusace ta buɗe motar ta fice ta fara tafiya cikin sauri tana goge hawayen fuskar ta. Buɗe motar yayi shima ya fito da sauri yana mara mata baya tare da kiran sunan ta "MADEENAH?" sai dai taƙi tsayawa sai ma tafiyar tata da take haɗawa da ɗan gudu. "What, why is he after her, mai kuma sukeyi a cikin motar tunɗazu?" cewar Kiki tana kallon Sarauniya Naseeba da kanta ya gama ƙullewa. Mugun kallo ta watsawa Kiki kafin tace "Dallah ki rufemin wannan ru6a66en bakin naki, da wanne kikeson naji, i thought koh JALILAH yakeso but...but sai naga kuma kamar he is into this girl wacece itama tukun, kuma daga ina take?." "Are you sure sonta yake, itace fah yarinƴar da ɗan uwansa ke son gabatarwa matsayin wacce yakeso, does that mean..." shiru tayi tana waro idanu cikin murmushin munafurci. "Ki lalla6a ki bisu, ki ganemin mai ke tsakanin su." "Angama ranki ya daɗe" ta faɗa tare da ɗan jawo mayafin kanta yana rufe mata fuska ta fice daga inda suka la6e ɗin. ****************** _________"You have to believe me Okay?, kowa shaida ne, yarinƴar da kakeso is having an affair da wannan yaron da kake ƙira ɗan uwanka, he is cheating on you tare da wacce kakeso." A fusace ya miƙe tsaye yana nuna mata hanƴa yace "Get out, just move yourself of my sight please, you think zan yarda da dukkanin abinda kika faɗa ne, babu wani abu da zaki sake faɗamin na yarda dashi, waye baisan koh ke wacece a wannan PALACE ɗin ba?, bakida wani aiki sai haɗa husuma da tada ta, just move out please i don't even want to see you face" ya faɗa cikin tsananin fushi yana juya mata baya. Murmushi Sarauniya Hafeezah ta saki kafin tace "I don't care koh ka yarda koh kada ka yarda wannan damuwar kace, aure ne dai da kai da wannan yarinƴar babu shi dan haka kayi gaggawar cire ta daga cikin ranka, dan kuwa muddin ina raye ba zata ta6a zama matar ka ba." YAZEED ji yayi kamar ya saki kuka dan jin muryar ta kamar ana gasa masa zuciyar sa yakeji, ya tsane ta gabaɗaya, babu yadda ya iya ne kawai, shiyasa yake ɗaga mata ƙafa a matsayin ta na mahaifiyar sa. "Mai zai hana ka nemi inda yake yanzun ka tabbatar da abinda nake faɗamaka da idanun ka, sabida ɗaukar ta yayi suka fice daga fadar kamar yadda baiji kunƴar rungumar ta a gaban mutane ba." Runtse idanu YAZEED yayi yanajin kamar ya shaƙo mahaifiyar tasa koh zaiji sauƙin abinda yakeji cikin zuciyar sa. "Alright, naji just get out please" ya faɗa ba tare da ya juyo ya kalleta ba. "Zan fita, sai dai ina mai sake tabbatar maka da cire yarinƴar nan a zuciyar ka would be the best for you" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin nasa. Zuwa yayi ya sanƴa key a ɗakin yana komawa da bakin bed ya zauna tare da dafe kanshi. Shi ya san munafurci irin na mahaifiyar sa, zata iyayin komai dan ganin ta raba shi da DEENAH tunda har ta nuna bata ƙaunar ta, yasan tunda ZEEYAD yazo ya tafi da DEENAH zai kula da ita sannan ya kwantar mata da hankali, munafurci ne kawai irin na mahaifiyar sa sabida kawai tana son haɗa shi da ɗan uwansa. Tashi yayi ya fice daga ɗakin zuwa neman ZEEYAD ɗin. ****************** _______Duk inda Sadeeq zai zaga neman abokin nasa ya zaga sai dai bai ga koh da mai kama dashi bane, ya kira sa a wayar ma baya ɗagawa. Shi dai burin sa bai wuce kada ZEEYAD ya kwafsa ya kasa danne kishin da yake wa DEENAH a gaban mutane ba, har a gane da akwai wani abu a tsakanin su. Part ɗin Grandma ya wuce anan ya tadda ta da Umma da wasu matan suna hirar su basu ma san abin dake faruwa ba. Ganin sa ya sanƴa Grandma cewa "Mai Martaban ya fito ne?." Kallon su yayi duka kafin ya girgiza kai yace "A'a, bayajin daɗi dan haka ba zai sami damar fitowa ba." "Subhanallah, meke damunsa haka?." "Jinin sa ne ya hau but he is fine now, sabida ya koma bacci ma." "Toh masha Allah, su Boy ɗin kuma fah?." Shiru yayi kafin kuma yace "Suna chan duka, dama nazo sanar daku ne cewa ba zai samu damar fitowa ba." "Toh ai shikenan, gara da ka sanar damu kam, wai mu nan duk shantaƙewa mukayi muna jiran fitowar sa kafin mu koma chan ɗin." "Bari naje na same su ni" ya faɗa yana ficewa ba tare da ya jirayi cewar su ba. Da kallo Umma dake jin wani iri ta bisa kafin kuma ta kawar da dukkanin wasu negative thoughts suna cigaba da hira da Grandma dake ta zuba musu surutu. ********************* _________Tadda ita yayi zaune ta kafe wuri ɗaya da idanu dan haka ƙarasawa yayi yana durƙushewa a gaban ta. Ɗagowa tayi da idanun ta tana kallon sa kamar yadda shima yake kallon ta, nan tace "You're Playing with my emotions, you love me and yet ka haɗa ni da ɗan uwan ka, kasan ba zaka iya jurar gani na tare dashi ba then maiyasa tun farko ka kawo shawarar amincewa da soyayyar sa, yin hakan tamkar cutar da zuciyar sa ne, sabida shima yana sona, ya kake tunanin zaiji a zuciyar sa bayan ya gano cewa ba shine a zuciya ta ba kuma na amince masa, i can't do this anymore, you've to tell everyone the truth or else am living you forever" ta faɗa tana haɗa kanta da guiwa ta cigaba da shessheƙar kukan ta. Kallon ta kawai ZEEYAD yake dakyar ya buɗi baki yace "DEENAH please, stop crying, it hurts to see you sad." A fusace ta ɗago tana kallon sa tace "I won't stop crying, why do you even care?, you're nothing but a pain to my life, i wish ban ta6a haɗuwa da kai, am suffering, can't you see that?, i have waited for you all my life only to see you with another girl kana claiming cewa ita zaka aura, and now kazo ka sake sani gaba cewa kana sona, kai wane irin mayaudari ne?, maiyasa ba zaka so mutum ɗaya ba, kai koh kunƴar ƙarya ma bakayi zaka zo ka wani cemin kana sona, you're a liar, and i hate liars, shigowar ka rayuwa ta bai ƙare ni da komai ba sai ƙunci da baƙin ciki a kullum, stop pretending cewa kana sona, i know baka sona kuma baka ta6a sona ba, indai kana sona da gaske ba zaka ta6a aikata abinda kayi ba, you think ni banida zuciya ne da zaka dinga yimin wasa da hankali?, just stop staring at me and get lost from my sight" ta ƙarashe cikin kauda kanta daga kallon sa. Shiru yayi yana kallon ta sabida yasan yayi kuskure, sannan baisan ta yadda zai fara bata haƙuri ba, dan kuwa baya tunanin zata fuskance shi ma. Sunkuyar da kansa yayi yace "I have never loved any girl bayan ke." Bata kallesa ba haka kuma bata tanka masa ba. "I never thought zaki zamto wata 6ari na jiki na, you're my first love DEENAH, after all abubuwan da suka sha faruwa a baya ban ta6a manta ki ba daidai da minti ɗaya, i may pretend like am okay, but deep down am suffering from rashin ki a kusa dani DEENAH, and JALILAH i like her because tana da zuciya mai kyau and a kullum Grandma bata da wani zance da ya wuce na ganin ta haɗa ni aure da ita, my Grandma means alot to me so ba zan iya musu akan duk wani abu da ta yanke a gareni ba, i never thought kece yarinƴar da YAZEED yake magana akai kullum, and bayan na gano hakan i thought the best kyautar da zanyi wa ɗan uwa na shine sadaukar da soyayyar da nakeyi miki a gareshi, but i later found out irin kuskuren da na tafka, you're my Happiness DEENAH, you mean everything to me, i just couldn't imagine life without you, you showed me love a lokacin da kowa bayason na ra6e shi, bakiji kyankyami na ba a lokacin da nake yawo a titi, you've a good heart wanda a kullum burin ki bai wuce kiga naci na ƙoshi ban kwana da ƴunwa ba duk kinyi hakan ne ba tare da sanin cikakken koh wanene ni ba, baki damu da zan iya cutar dake koh akasin haka ba, DEENAH... I thought bayan rabuwar mu ta farko dake ba zan sake tunanin ki ba, but things turned out to be the Opposite, you're always on my mind wanda hakan ke sanƴa ni zana hoton ki a duk lokacin da nake zaune bana komai, kuka na yazo ƙarshe ne after 8yrs da rabuwar mu bayan na haɗu da yayan ki Jafar, trust me DEENAH baki ta6a barin zuciya ta ba koh da na minti ɗaya ne...I love you DEENAH, and i promise to always" ya ƙarashe cikin ɗago da jajayen idanun sa yana sauƙe su cikin nata da ta kafe shi dashi tana kallo tunda ya fara magana. Kallon juna suke for about 1min, DEENAH batasan sadda wani irin light murmushi yayi forming kan fuskar ta ba "You... Really do?" ta faɗa still tana kallon nasa. "Forever" ya faɗa. Hannu tasa ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta, yes yayi gaskiya tabbas kalmar *Inason ki* shi ta daɗe tana biɗa tare da tsumayin ji daga gareshi, ta rasa wace iriyar farin ciki yakamata tayi, jin komai takeyi tamkar a mafarki ba gaske bane ya furta mata kalmar so da bakin shi, sai dai kuma kafin ta kai ga farin ciki, ya zatayi da innocent bawan Allah YAZEED wanda shima ke sonta tamkar ran shi? Zai sake kula ta kuwa, tunda har mahaifiyar sa ta ɗau alwashin tsine masa muddin yayi hakan, kokuma zata tsaya ne taji daga gareshi kafin ta sakarwa Abyad ɗinta? Wadannan sune tunanin da suka yi mata ƙawanƴa cikin kwakwalwa, nan kuma tayi saurin kau dasu tana buɗe fuskar ta. Mamaki ne ya cika ta ganin baya nan, waige-waige ta hau yi koh zata ganshi sai dai babu shi babu alamun sa. A hankali ta furta "Am i dreaming?." "No" taji an faɗa saitin kunnen ta. Saurin juyowa tayi a ɗan firgice tana kallon sa tace "You scared me." Murmushi yayi ganin yadda ta shagwa6e fuska, wata ƴar doguwar flower mai kyau ya ciro yana nuna mata. Amsa tayi cikin murmushi tana kallon flower ɗin. "You like it?" ya faɗa yana kallon ta. Kai ta jinjina masa cikin murmushi tace "I love it." Jerawa sukayi tare suka fara tafiya yayin da take jujjuya flower ɗin a hannun ta. Part ɗin Grandma suka nufa anan suka tadda kowa tsaye, nan duk kallo ya koma kansu. "Glad you're here, where have you been, tunɗazu ake neman DEENAH zasu tafi" cewar Sadeeq. DEENAH kallon YAZEED dake tsaye yana kallon ta tayi, kafin tayi saurin sadda kanta ƙasa tanajin babu daɗi sosai a cikin zuciyar ta. "Inaga mu zamu tafi, tunda gasu nan sun dawo" cewar Umma cikin murmushi tana kallon Grandma. "Sure dear, ku jira i have something to gift DEENAH" kallon JALILAH dake tsaye tana bin ZEEYAD da DEENAH da kallo tayi kafin tace "JALILAH dear, kije ɗaki na ki ɗauko wannan abin nan, am sorry DEENAH jikin mai Martaba ɗin yau babu daɗi, da kaina zan je har chan Nigeriar taku na taho dake idan an tashi yin baiko." Murmushin yaƙe kawai DEENAH ta iya yi jikin ta na yin sanƴi. Ba'a daɗe ba JALILAH ta dawo da wani ƙaton kwali anyi wrapping ɗinsa. Murmushi Grandma tayi tace "Ki baiwa DEENAH, nata ne, kyauta ce daga gareni ki amsa kinji koh?." Murmushi DEENAH tayi tana amsar kwalin daga hannun JALILAH tace "Jazakillahu Khair Grandma." "Kada ki wani ji damuwa ƴar nan, yakamata ku wuce haka nan dare nayi, gashi kuma kunce da safe jirgin naku zai tashi, muje haka nan." Nan duk suka fice daga part ɗin Grandma ɗin. Kallon driver ɗin da zai ja motar ZEEYAD yayi yace "I will drive the car." Babu musu ya miƙa masa key ɗin. YAZEED so yake yayi wa DEENAH magana sai dai yana tsoron bakin mahaifiyar sa, dan haka kallon Umma yayi yace "Thank you so much for your time Aunt, we really appreciate it." Murmushi Umma tayi tace "Mune da godiya" tana shigewa motar da aka buɗe mata ɗin. "Nima zanje" cewar JALILAH. Kallon ta ZEEYAD yayi yace "Maybe you don't have to." "A'a ka barta mana taje, ai kaga ka sami abokiyar hira idan ka tashi dawowa koh?." Murmushin yaƙe kawai yayi yace "Alright." Buɗe gidan gaban tayi ta shiga, dan haka DEENAH zaga wa tayi ta ɗayan 6angaren tana zama kusa da Umma. Sosai suka sake yiwa juna sallama, kafin yaja motar ya bar gidan. ************** __________A cikin ƙatuwar hotel ɗin da suka sauƙa yayi parking motar inda duk suka buɗe suka fice. Booth ɗin motar ya buɗe DEENAH ta ɗauki tsarabar da Grandma tayi mata, kafin ya maida ya rufe fuskar nan tata a matuƙar tsuke. "Why are you sad?, i don't like seeing you like this." Banza tayi dashi ta nufi wurin Umma ta tsaya. Zuwa yayi cikin murmushi yace "Thank you so much Aunt." Umma da jikin ta yayi sanƴi sosai ne tace "Listen...am sorry for..." bai bari ta ƙarasar ba yace "Come on Aunt... don't said anything please." Shiru tayi tana kallon sa, murmushi yayi yana kallon DEENAH yace "Bye." Ji tayi duk batason tafiyar tasa, dan kuwa batasan yaushe ne zasu sake haɗuwa ba, gimtsa fuska tayi idanun ta na tara hawaye, ganin ya shige motar shi da JALILAH. Sosai takejin wani irin kishi na taso mata, har yaja motar ya bar wurin. "Muje" faɗin Umma tana yin gaba, nan ta mara mata baya suka koma apartment ɗinsu. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽* [8/15, 9:45 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *042...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *LOVE IN THE AIR🎈❤‍🔥🤸🏽‍♀️* __________A gajiya ta tashi sabida isasshen baccin da bata samu ba jiya da dare. Addu'ar tashi daga bacci ta karanto kafin ta rarrafa ta sauƙa daga kan bed ɗin tana zuwa ta kunna wutar ɗakin. Bathroom ta faɗa ta iyo alwala ta fito, sallahr Asuba tayi, bayan ta idar ne tayi Adhkar ɗinta tare da ɗaurawa da karatun ƙur'ani. Miƙewa tayi bayan ta idda kafin ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta fice. Ɗakin Umma taje ganin ta zaune kan sallaya ya sanƴa ta komawa idan ta idar ta dawo. Ɗakin Jafar ta leƙa nan dai taga shima bai dawo daga masallaci ba. Falo ta dawo tare da yaye curtains ɗin falon duka ta cire su, kasancewar gidan bai sami isasshen gyara ba kwana2 da sukayi basa nan, hakan ya sanƴa ta yanke shawarar yin sanitation. Bayan ta cire labulayen ne duka kuma ta nufi toilet ɗin falon dasu, tare da sanƴa su cikin washing machine, fitowa tayi ta hau nannaɗe carpet ɗin falon, ganin yayi nauyi sosai ba zata iya bane ya sanƴa ta bari kawai ta nufi kitchen. Ƙofar da ya fita ta cikin gida ta buɗe a kitchen ɗin nasu kafin ta hau fidda kayayyakin ciki, har ta gama. Sai da ta fara gyara store ɗin ta maida komai steady abubuwan da ba'a buƙata ta fiddo su kafin ta hau gyaran kitchen ɗin, wanke fridge ɗin kitchen ɗin tayi ya fita ƙal, kafin ta goge sauran abubuwan da ba za'a iya fiddawa ba, sannan ta wanke ƙasan kitchen ɗin tass ta fice. Ruwa ta tara a famfo kafin ta hau wanke dukkanin utensils da items ɗin da ta fiddo, tana cikin wankewa ne Umma ta leƙo ta kitchen ɗin tana kallon ta. Shagwa6e fuska tayi tace "Allah sarki Umma na kitchen ɗin fah bai gama bushewa ba." Murmushi Umma tayi tana kallon ta tace "Yau kuma da aiki aka tashi, toh sannu Allah yayi miki albarka." Cike da jindaɗi tace "Aameen Umma na, Umma kije dan Allah kafin nan kitchen ɗin ya bushe." "Allah ya huci zuciyar ki, kinga tafiya ta ma" ta faɗa tana barin cikin kitchen ɗin. Aikin ta ta cigaba dayi, har sai kusan ƙarfe taran safe kafin ta kammala. Izuwa lokacin sosai ƴunwa ya gama nuƙurƙusar ta, dan haka falon ta dawo ta samu har an fidda carpet da kujerun. Ɗakin Jafar ta sake leƙawa taga baya nan, nan kuma taga babu carpet ɗin ɗakin sa, kafin kuma taje ɗakin Umma, nan ta same ta zaune. Shigowa tayi tana zama kusada Umma ɗin tace "Umma ina kwana?." "Kin tashi lafiya, ya gajiyan ki?." "Alhamdulillah" ta amsa kafin tace "Wa ya fidda kujeru da carpets ɗin?." "Yayan ki ne ya kai wurin wankewa bai dawo ba tukun." "Allah yasa dai bai manta da nawa ba." "A'a duka ya kai." "Yauwa, Umma zan gyara ɗakin naki." Kallon ta Umma tayi tace "Baki gaji bane, kya bari dai anjima ki ƙarasa koh?." "A'a Umma indai nace zan bari yanzu anjima ba zan iya ba gara kawai na haɗa nayi su kai ɗaya yanzu na huta." "Toh shikenan, bari yayan naki ya dawo tukun muyi breakfast." Da "Toh" kawai ta amsa tana kwanciya, runtse idanu tayi jin bayan ta ya wani riƙe yaushe rabon ta da tayi irin aikin nan ta manta tun kafin ta faɗa rashin lafiya. Da sauri kuma ta miƙe tana zuwa ta janƴo kwalin da Grandma ta bata ta buɗe dan ganin menene a ciki. Blue ɗin doguwar rigar gown ce mai kyau iriyar wacce taga JALILAH na sawa da takalmi mai kyau sai kuma bangles a ciki. "Wow, Umma kinga" ta faɗa tana ƙarasowa kusa da Umma. Kallon kayan Umma ma take tace "Masha Allah sunyi matuƙar kyau sosai." Murmushi tayi tace "Aikuwa dai sosai." Ƙarar motar da taji ne ya tabbatar mata da Jafar ɗin ya dawo dan haka tashi tayi ta fice cikin gudu, dan kuwa ba wai sun samu sun gaisa mai kyau jiya bayan dawowar su bane ba kuma ƙaramin kewar sa taji ba. Cikin farfajiyar gidan nasu ta fita tana nufar inda yayi parking motar. Buɗe motar yayi fuskar sa washe da murmushi. "Oyoyo yayana" ta faɗa tana rungume shi. Farin ciki ne cike fal a zuciyar Jafar ganin ƙanwar tasa ta dawo ainihin ita babu kuma wata damuwa tattare da ita. "I miss you lil sis" ya faɗa cikin murmushi yana patting bayan ta. Ɗagowa tayi cikin murmushi tana kallon sa tace "Yaya mai ka samu ne haka sai wani kyau kake ƙarawa kana sake yin fresh" ta faɗa tana shafa fuskar sa cikin murmushi. Ɗan sosa kai yayi kafin yace "You wanna know, it's a secret but ke kaɗai zan faɗawa and kada ki sanar da Umma, Promise?." Kallon sa take cikin murmushi kafin kuma tace "Promise" tana tafa hannayen ta da nashi. Kumatun ta yaja tare da ɗaura hannayen sa kan kafaɗun ta suka fara tafiya, wayar sa ya ciro ya ɗanyi danne-danne kafin ya miƙa mata. Amsa tayi fuskar ta ɗauke da murmushi yace "Is she beautiful, do you like her?." Shiru tayi tana kallon hoton tana sake zooming ɗinsa kafin tace "Uhmm....kamata yayi ace ka nemo matar da tafi ƙanwar ka kyau." Tsayawa yayi yana kallon ta kafin kuma ya kar6e wayar sa yana faɗin "You mean kin fita kyau?." Kai ta jinjina masa kafin tace "She is just fair in complexion, but look at her nose" ta faɗa tana ta6a hancin ta. Sake ƙure hoton yayi da idanu kafin kuma yace "Lies there is no way zaki fita kyau, ." Nan fah suka hau musu tsakanin su kamar wasu yara, inda yake cewa budurwar sa ta fi DEENAH kyau, ita kuma take cewa tafi budurwar tasa kyau. "Ok, ok, ok, naji let's bait, indai har dagaske girlfriend naka ta fini kyau zan haɗa cake mai kyau ka kai mata, and indai it turns out that na fita kyau zaka saimin sabuwar waya, agree?." "Yeah, bait" ya faɗa yana tafa hannun ta da ta miƙa masa. Nan tace "Yauwa muje wurin Tijjani mai gadi ya tantance mana." Nan fah duk suka ɗeba sukayi wurin sa suna cigaba da musun su. Tijjani mai gadi dake ta washe haƙora yana kallon su tun daga nesa ne yace "Hajiya DEENAH, lafiya ta samu, Allah Ubangiji yaqara miki lafiya mai ɗaurewa." "Aameen Tijjani, yauwa Tijjani musu zaka raba mana dan Allah kar6i hoton nan ka gani, Yaya ka bashi wayar" ta faɗa tana kallon Jafar dake ta faman hura hanci. Miƙawa Tijjani wayar Jafar yayi kafin tace "Wannan budurwar Yaya ce, dan Allah musu zaka raba mana wai cewa yayi ta fini kyau haka ne?." Kallon cikin wayar yake yana kallon DEENAH haƙora washe yace "Toh kai yallabai Jafar ai Madam ɗin taka jar fata kawai zata nuna wa Hajiya DEENAH amma ba dai kyau ba kam." Ihu DEENAH tasa haɗi da yin tsalle tana faɗin "Mai na faɗamaka Yaya" ta faɗi hakan cikin dariya tana riƙo shi. Sosai Jafar ya cika yayi fam sai hura hanci yake yace "Ba wani nan kinyi bribing ɗinsa ne, haɗa baki kawai kukayi." Dariya duk sukayi kafin yace "Toh yallabai Jafar inbanda abin ka tayaya zamu haɗa baki ita da ma bata ƙasar." "Koma dai menene, ban waya ta" ya faɗa yana kar6ar wayar sa. "Mungode Tijjani" cewar DEENAH tana marawa Jafar baya tana cigaba da yi masa dariyar shaƙiyan ci. Ja sukayi suka tsaya a falon nan ya juyo ya kalle ta yace "Da nayi niyyar taya ki aikin but yanzu na fasa." Dariya tayi tace "Nidai ba wannan ba, yaushe zaka kawomin waya ta?." Ɗan ta6e baki yayi yace "Wani waya?." Tsaya kallon sa tayi kafin tace "You promised to buy me a new Phone, koh ka manta bait ɗin da mukayi ne?." "Ohh, ai banyi alƙawari ba, i just said _"Bait"_ ba wani abu ba kuma." 6ata rai tayi ta tsaya tana kallon sa, murmushi yayi yace "Don't worry, i promised to buy it for you on your 20th birthday." Murmushi tayi tace "Really?." "Yeah" ya faɗa. "Toh amma fah saura 2weeks kenan jira zanyi har lokacin?." "Yeah, indai kinason na saya miki mai kyau ba." "Alright then, amma zaka dinga bani naka ina amfani dashi koh?." Ɗan waro idanu yayi kafin yace "Amfanin mai?, ina wanda ke hannun ki?." "What are you saying?, na dawo na tarar ya ɗauke gabaɗaya baya kawowa." "Alright ba case." Murmushi tayi cike da jindaɗi kafin tace "Toh yanzu ka tayani mu gyara gidan, gashi ma ƴunwa nakeji" ta faɗa cikin yamutsa fuska tana shafa cikin ta. "Ohh, kinga kinsa har na manta akwai food-stuffs na kawo suna booth, muje mu kwaso" ya faɗa yana ficewa kafin tabi bayan shi. Kwaso kayan abincin da ya sayo sukayi suna shigar wa ciki har suka kammala, Umma ce ta shiga kitchen dafa musu breakfast inda kuma ita da Jafar suka ƙarasar da gyaran gidan baki ɗaya. Bayan sun gama ne suka yi breakfast, Jafar shiryawa yayi ya fice ita kuma ɗaki ta koma, wanka tayi ta shirya cikin armless doguwar riga marar nauyi kafin ta tada sallahr Azahar tayi, bayan ta idar ne kuma ta haura kan bed, dan kuwa ba ƙaramin gajiya tayi ba. Idanun ta ta lumshe kafin kuma murmushi yayi forming kan fuskar ta, babu abinda take tunawa sai moment nasu na shekaran-jiya dashi, sai dai har yanzu ta rasa dalilin da ya sanƴa bai kira ta ba. Mirginawa tayi tana gyara kwanciyar ta, kafin bacci mai daɗi yazo ya kwashe ta. ************************** ________Kallon sa Sadeeq yake kafin kuma yayi gyaran murya yace "Ya zakayi da JALILAH kuma?." Buɗe idanun sa dake lumshe yayi yana zuba su kan Sadeeq ɗin kafin ya gyara zama yace "Na baka ita." Da wani irin kallo Sadeeq ya bisa yace "An gaya maka cewa nayi kwantai ne komiye?, you know tun farko kai ka kwafsa abin nan why hiding your feelings you should have told her cewar kana da wacce kake so, it isn't a big deal maybe ta fahimce ka sannan ta haƙura tunda tana da sauƙin kai, but yanzu babu ta yadda za'a yi ka fara confronting ɗinta akan wannan zancen ne sabida she thinks koh kaima you have feelings for her, ta kwallafa rai a kanka sosai and telling her cewa kanada wacce kakeso won't make a sense to her, it may broke her heart." Shiru ZEEYAD yayi yana sauraren Sadeeq ɗin har ya kai aya a zancen nasa, "What about YAZEED then?." "Bakaji abinda Ummien sa ta faɗa masa bane, it's like ta haramta masa dukkanin wata alaƙa da DEENAH, so i don't think zai sake confronting ɗinta kuma." "But he loves her and he may think that koh nayi masa kwace ne." "No, he would never think that way, bale ma ba kwacen kayi masa ba." Shiru yayi ya rasa ta cewa nan Sadeeq ya sake faɗin "Ka bar damun kanka haka nan, idan kana tunanin zaka iya hurting JALILAH why not kawai ka haɗa su biyun ka aura?." "What?" ya faɗa yana kallon sa. Kafaɗu ya ɗaga masa yace "Yeah kaga babu wacce zata ce ka yaudare ta a cikin su." "Two wives, at same time?, listen i don't have that niyyar yin mata biyu" ya faɗa cikin 6ata rai. "Alright then choose between the two of them, DEENAH or... JALILAH" Cewar Sadeeq ɗin cikin murmushi. "You think this is funny?, zanje wurin Grandma, i will tell her everything idan yaso then ta warware ƙulin da ta haɗa." "You mean bakason JALILAH?, poor her i feel so bad for her." Tashi tsaye ZEEYAD yayi yana faɗin "Am going home now, idan Abhi ya dawo ka gaida shi." Tashi shima Sadeeq yayi yace "Insha Allah." Jerawa sukayi suka fito tare, inda yayi wa Ummien Sadeeq sallama kafin ya wuce. ************* A hanƴar zuwa part ɗin Grandma yaci karo da YAZEED dake fitowa daga nan. Murmushi yayi masa inda YAZEED ɗin ya kallesa yace "I have been looking for you" ya faɗa fuskar sa babu yabo babu fallasa. "Are you Okay?" cewar ZEEYAD yana kallon sa. Shiru ya ɗanyi damuwa fal akan fuskar sa yace "It's about DEENAH... I want you to call her and apologised to her on my behalf please, am worried tun ranar da abin ya faru, i know kai kaɗai ne zaka iya conviencing ɗinta ka kwantar mata da hankali." Kallon sa kawai ZEEYAD yake cike da tausayawa yace masa "No i guess kai yakamata ka bata haƙuri da kanka, you should call her on phone, i guess kana da numbern Ummien ta, right?." "Yeah ina dashi, but... I can't do that Ummie duk ta 6ata komai, she doesn't like DEENAH for the first time and ka santa i know ba zata ta6a son nata ba koh ya kuwa nayi da ita, so i don't think i can go any further with our relationship... I guess am living her for good." ZEEYAD was shocked for a moment jin kalaman da suka fito daga bakin YAZEED, he knows that YAZEED is deeply inlove with DEENAH but baisan dalilin da ya sanƴa shi saurin haƙura da ita haka nan ba, he think ba zaiyi minding kalaman mahaifiyar sa ba zai cigaba da kula DEENAH sai dai kuma ba hakan bace ta kasance, he feels so bad wa ɗan uwan nasa sam baiyi dacen mahaifiya ba. Muryar YAZEED ne ya katse masa tunani da faɗin "You know koh da na tilastawa kaina auren DEENAH then ba zata ta6a jindaɗin rayuwa dani ba, coz seems like she loves someone else, there is someone else in her mind, and above all kuma halin Ummie kaɗai ya isa ya dawwamar da ita cikin ƙunci na har abada, so what's the point of marrying her indai ba zan ta6a bata farin ciki ba?" ya ƙarashe yana kallon ZEEYAD. Cikin sanƴi ZEEYAD yace "Am sorry, it's really painful indeed." "No everything will be alright insha Allah, i guess Allah baya ɗaurawa bawan sa abinda ba zai iya ba right?, so i will be patient na ganin na sami kalar matar da takeso na aura." Rungume ɗan uwan nasa yayi yanajin babu daɗi sosai a ransa. Patting bayan sa YAZEED ya shiga yi suna ɗagowa nan yace dashi "So are you calling her for me?." "Yeah" ya bashi amsa. Murmushi yayi yace "Thank you" yana sake rungume shi. Ɗagowa duk sukayi suna murmushi nan YAZEED yace "Muje so that na baka numbern ka kira" jerawa sukayi suka shige part ɗin Grandma ɗin. A falo suka yaɗa Zango kafin YAZEED ya kira masa numbern Umma ɗin yana sawa a wayar sa. Wayar ya miƙawa YAZEED bayan yayi dialing number ɗin. ******* ______DEENAH da ta kar6i wayar Umma tana game ne taga kirar sabuwar layi ta shigo wayar, gashi kuma ba na ƴan Nigeria bane. Murmushi tayi dan kuwa koh ba'a faɗa mata ba, ta san shine, sai da taga ya kusa yankewa tukun ta ɗaga tana mai yin sallama. Kallon ZEEYAD YAZEED yayi jin ba Umma bace ta ɗau wayar, dan haka saurin miƙa masa wayar yayi a hankali yake faɗin "I guess it's DEENAH." Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi yana kai wayar kunnen sa tare da furta "DEENAH?." Murmushi DEENAH tayi tace "I know it must be you, so are you missing me already?." Cize baki yayi kafin kuma yace "Actually YAZEED is here with me, he asked me to call you." Expression na fuskar ta ne ya canza nan tace "Ohh." "He wants to apologise to you about what happened the other day, he is very sorry DEENAH, please forgive him and his Mom too." Cikin sanƴi tace "It's alright, actually komai ya wuce, kace masa kada ya wani samu damuwa, and ya kwantar da hankalin sa, ni nama manta ma da anyi hakan." Murmushi ZEEYAD yayi nan yace "Thank you, he really appreciate that." "He is welcome" ta faɗa. Kallon YAZEED yayi tare da yi masa alamun komai ya wuce, murmushi yayi yanajin daɗin hakan a ransa. "So Bye DEENAH." "Bye" ta faɗa a hankali tana datse kiran, turo baki tayi tana 6ata fuska ganin ba kiran shi bane na musamman. "So how do i tell her that our relationship is over?." "Maybe you should text her." "This is her Mom's phone, what if she saw it instead of her?." "Maybe then you should go visit her." "Really?, what if kai kaje maimakon ni fah, you know it i can't talk to her right?." "You really want me to go?." "Yeah, i know kasan abinda zaka faɗa dan ganin bataji haushin hakan ba." Murmushin gefen baki kawai ZEEYAD yayi ba tare da yace komai ba. "Yakamata kaje a cikin week ɗinnan please." "This week?, i mean why not mu bari sai next upper week?." "Alright then, duk yadda kace." "So you want me to find a new girl for you?" ya faɗa cikin murmushi yana kallon YAZEED. "No, let her find one for me, what if wacce na kawo ma tace batayi mata ba fah?." "What if wacce ta kawo maka kuma batayi maka ba fah?." "Then i will manage her, na rungumi haƙuri har mu rabu lafiya." "Wow" cewar ZEEYAD ɗin cikin jinjina hali irin na ɗan uwan nasa. ******************* _________Zaune take tsakiyar bed ɗinta tana gyara faratan hannun ta. Sallamar Jafar taji bakin ƙofar dan haka izinin shigowa ta bashi. Bai ce da ita ba kawai ya miƙa mata wayar sa cikin murmushi yana ficewa. Da kallon mamaki ta bisa tana juyo fuskar wayar. Ƙanƙance idanu tayi tana ƙara ƙure screen ɗin da kallo ganin kamar shi take gani cikin wayar. "Why are you looking so ugly Babe?" taji ya faɗi hakan. Saurin matsar da wayar tayi daga kusada fuskar ta tana wani irin tsuke fuska jin ya kira ta da mummuna. Ɗan murguɗa masa baki tayi tace "A mummunar ne kuma a maƙale min ba." "Yauwa you look better now" ya faɗa. "Wait a minute" ta faɗa tana ajiye wayar kafin ta sauƙa daga kan bed ɗin ta sako doguwar Hijabin ta ta dawo ta zauna tana saita wayar da kyau. "Uhm, kin ɗanyi kyau yanzu." Murmushi tayi tana tallafe kumatun ta tace "When are you coming to see me, and tun ranar chan baka kira kaji ya nake ba sai yanzu?" ta ƙarashe cikin shagwa6e fuskar ta. "Come on tell me, i will come duk ranar da kikeson gani na." "Seriously, koh da yanzu nakeson ganin ka zaka zo?." "Only if idan Aljani ne ni kenan" ya faɗa. Ɗan dariya tayi kawai ba tare da tace komai ba. "Babe?" ya kira ta. Kallon sa tayi kamar wacce ke gaban sa a zahiri nan yace "I miss you." Murmushi tayi tana rufe fuskar ta tace "You really do?." "Yes Babe." "If you really do then, kazo cikin kwanakin nan, let's spend more time together." "You really want that?." "Uhum" ta faɗa cikin jinjina masa kai nan yace "Alright then, your wish is my command." Murmushi tayi kawai tace "I Know ba zuwa ma zakayi ba." Murmushin shima yayi yace "Don't worry, i will surprise you." "Alright then, dare yayi nikuma bacci nakeji." Ɗan 6ata fuska yayi dan kuwa sam bai gaji da kallon ta ba yace "So soon?." "Yeah, inada school gobe, Bye" ta faɗa tana yi masa waving da hannu kafin tayi saurin yanke kiran. Ita ɗinma sam ba wai ta gaji da kallon sa bane, but dole sai tana ja masa class yadda zai cika da kewar ta sosai har ya taso daga inda yake zuwa ganin ta, ba wai tayi ta sakar masa sosai haka ba. 6angaren ZEEYAD kuwa ji yayi duk wata farin cikin sa ta yanke, dan haka rufe Laptop ɗin tasa yayi yana wani irin tsuke fuska kai kace wani gagarumin laifi akayi masa. *FIVE DAYS LATER* _____Zaune take ita da su Anty Khadija kasancewar suma kwana biyu da ya wuce suka dawo daga tafiyar da sukayi, hakan ya sanƴa ta kawo musu ziyara. "Wai ke dan Allah dagaske kike ni fah ban yarda ba" cewar Amirah tana kallon DEENAH dake basu labarin Abyad ɗinta. Tsaki Anty Khadija taja tace "Ke nikam dallah ki rabu da wannan ki cigaba da bamu labari, yanzu dai kina nufin kice wata sabuwar soyayyar ce ta ƙullu tsakanin ku, kai gaskiya am very happy for you, after all the struggles da kikayi fama dashi a rayuwa kukan ya kusa zuwa ƙarshe yanzu." Murmushi kawai DEENAH tayi tana sauraren ta, Amirah ce tace "Yanzu fah kenan balarabe zaki aura, kinji daɗi kice zaki sha tarairaya da soyayya." "Aikuwa dai larabawa ba ƙaramin iya soyayya da tarairayar matan su suke ba, dukda dai bansan ya salon nasu soyayyar yake ba" faɗin Anty Khadija. Ƙarar wayar Anty Khadija ne ya katsewa Amirah maganar da take shirin yi. Ɗagawa Anty Khadija tayi tare da karawa a kunne tana amsa sallamar mai maganar. "DEENAH?, gata nan" ta faɗa tana miƙawa DEENAH wayar. Amsa DEENAH tayi tana karawa a kunne ganin Yayan ta ne "Ki fita ƙofar gida kinyi baƙo" shine abinda yace mata, waro idanu tayi tace "Wane ƙofar gidan, ina gidan Mamy fah." "Yeah i know, nan ɗin he is waiting for you" daga haka ya katse kiran ba tare da yaji ta cewar ta ba. Da kallo tabi wayar kafin ta kalli Amirah tace "Amirah dan Allah leƙa min ƙofar gida kiga waye ne?." "Baƙo kikayi ne?" cewar Amirah ɗin tana ɗaukar Hijabin ta. Kafaɗa ta ɗaga tace "Haka Yaya Jafar yace min, dubo min kiga waye ne please." Ba tare da Amirah ta amsa ba ta fice dan dubo mata koh wanene. Maidawa Anty Khadija wayar ta tayi nan tace "Ke yaushe zaki yi sabon wayar ne nikam?." "Yaya Jafar cewa yayi wai sai ranar birthday ɗina, zuwa next week kenan." "Kice akwai shagali, Allah ya kaimu." Haka suke ɗan ta6a hira har Amirah ta dawo tana cire Hijabin ta tace "Cha6 kinsan waye kuwa?." Kallon ta duk sukayi tare da haɗa baki wurin furta "waye?." "Wannan tsohon saurayin nan naki Abdul koh miye sunan shi." "Kan uba mai yazo yi, baki tsigewa ɗan iska rigar rashin mutunci ba" cewar Anty Khadija cike da bala'i. "Ni ina zan iya dashi, gara ke zaki iya ci masa mutunci tunda kinyi masters anan." Tsaki Anty Khadija taja tace "Dallah share shi, bar shi yayi ta tsayuwa idan ya gaji dai zai ja a kori kurar motar sa ya tafi, iskanci kawai shi koh kunƴan tako ƙafar sa baiyi ba, kai gaskiya dai namiji bashida kunƴa, toh da yazo yanzun yace mata uban mai?." Ganin bala'in Anty Khadija na neman yi yawa yasa Amirah saurin katse ta da faɗin "Toh Anty bala'i, ni wasa nake banma ga waye a cikin motar ba yadda tasha baƙar tinted yawa na munafukai, kije wani mai zazzafar mota ke jiran ki a waje." "Ke fah wallahi ƴar iska ce Amirah, haka kurum kisa na ɗau alhakin bawan Allah yanzu." "Masifar ki da rashin haƙurin ki ya jawo miki." "Toh keda akace ki dubo koh waye kuma kin dawo ba tare da sanin koh wanene cikin motar ba." "Ni Aishatu, rufamin asiri wa ya sani ma koh mai guntule kan mutane ne a ciki naje ya arce min da ƴar kan nawa da nake ta fama dashi, ku kuna nan shantaƙe baku san meke faruwa ba." "Mtssww ke dai wallahi banza ce, ni bara naje na dubo" cewar Anty Khadija tana ɗaukar mayafin ta ta fice daga ɗakin. "Maybe wani sabon kamu kikayi" cewar Amirah tana zama kusada DEENAH. Murmushi kawai DEENAH dake jinsu tayi tana tunanin koh wanene yazo neman ta. Kusan 5mins Anty Khadija tayi a waje kafin ta faɗo cikin ɗakin yawa wacce aka cillo ta tana nufar wurin closet ɗin Amirah. "Malama ya dai, ya da buɗemin closet mai kike nema?" cewar Amirah da ta tashi riƙe da kunkumi tana kallon Khadija. Cike da zumuɗi Anty Khadija tace "Aron kayan ki zaki bamu, DEENAH taso babban baƙo kikayi kiji." Da mamaki DEENAH ke bin ta kafin tace "Babban baƙo?" cikin mamaki. "Kwarai kuwa" ta faɗa tare da ciro set ɗin atamfa ɗinkin doguwar fitted riga mai kyau. "Wai waye yazo neman ta?" cewar Amirah. "DEENAH ki taso mana" cewar Anty Khadija tana kallon ta. Tashi DEENAH tayi tana ƙarasawa wurin ta, tace "Menene ya sami kayan jiki na da ba zan iya zuwa gun baƙon dashi ba?." Murmushi Anty Khadija tayi tace "Sabida baƙon yafi ƙarfin special a gunki, dole kiyi shigar da zata tafiyar masa da hankali, kar6i wannan yanzu kisa." Kar6ar kayan tayi tana jujjuya shi a hannun ta tace "Kayan Amirah ne fah, yayimin kaɗan kema kin sani, ki bari naje da na jiki na." "Aa cha6 rashin wayewa kenan, ke idan bakiyi masa shigar da zata zuzuta shi ba, idan yaga wata a waje da iriyar shigar ya kikeson yaji a ransa kenan, gara ke kinyi tunda ma shi zai zama mijin ki." "Ni fah bangane ba" cewar DEENAH cikin mamakin kalaman Anty Khadija. "Bari zaki gane idan kinje kinga koh wanene, sa kayan." Doguwar rigar jikin ta ta shiga ragewa, sannan ta sanƴa wanda Anty Khadija ta bata. Sosai kayan ya kamata ta kunkumi inda kuma ya zauna tare da yi mata ɗas a jiki yayi mata kyau sosai. Ɗaurin ɗankwali mai kyau Anty Khadija tayi mata tare da ɗan gyara mata fuskar ta, duk da batayi kwalliya sai dai kyawun da tayi ba'a magana sai wanda ya gani. Gyale mai ɗan girma wanda ya shiga da kayan nata ta yafa mata tace "Perfect, kinyi kyau sosai." Ita dai DEENAH 6ata rai tayi tana sake rufe jikin ta da gyalen dan kuwa sam batajin ta comfortable cikin kayan. Turare mai wani irin sassanƴar ƙamshi ta ɗauko ta fesa mata sama-sama tana faɗin "Kar muje ki zuzuta bawan Allah dayawa." Kallon ta Amirah tayi daga sama har ƙasa tace "Cha6 wallahi ki canza shigar nan, lallai wannan baƙon zai sha kallo komai fah free hmm." "Dallah rabu da munafuka, idan kina neman babbar ƴar ƙauye bagidajiya kika sami Amirah kin gama." Takalmi irin kayan mai ɗan tsayi ta ɗauko ta bata ta sanƴa tare da gyara mata zaman dressing ɗin nata nan tace "Masha Allah,you're free to go yanzu." Tsaye tayi tana kallon Anty Khadija ɗin. "Kije mana." "Ina wai?." "Yana falon baƙi na kai shi chan." Da kallo kawai take bin Anty Khadija nan tace "muje na rakaki" ta faɗa tana tura ta su fice daga ɗakin. Har bakin ƙofar falon baƙin ta kaita nan tace "Ki shiga tunɗazu fah yake jira." "Ki shiga mana kuma kin tsaya kallo na" cewar Anty Khadija ɗin ganin yadda DEENAH ke kallon ta. Gyara zaman mayafin tayi a jikin ta tana tura ƙofar ta shige, juyowa tayi tana kallon Anty Khadija nan tayi mata alama da hannu akan taje. Rufo ƙofar tayi tana jin yadda ƙamshin turaren sa ke bugo hancin ta. Hannaye biyu tasa tare da ɗan yaye curtain ɗin tana leƙa idanun ta dan ganin koh wanene. A bayan sa idanun ta suka sauƙa, waro idanu tayi tana maida labulen ta rufe da sauri ta furta "Abyad?." Tsaye tayi like na minti ɗaya kafin ta sake buɗe labulen tana cigaba da kallon sa. Sosai take mamakin ganin sa, wato dai dagaske ne da yace zaiyi mata bazata ya kawo mata ziyarar. Murmushi tayi tana sake gyara zaman gyalen jikin ta tare da yaye labulen ta ƙaraso cikin falon bakin ta ɗauke da sallama a hankali. Zuwa tayi tana tsayawa ta bayan kujerar da yake zaune ganin kamar baisan ta shigo ba. Ta kai kamar 20seconds tsaye akansa kafin kuma ta shiga zagayowa a hankali tana zama kan hannun kujerar. Ƙamshin turaren da ya jiyo ne ya sanƴa shi shiga buɗe idanun sa dake lumshe a hankali yana sauƙe su kanta. He couldn't take his eyes off of her ganin yadda tayi masa bala'in kyau fiye da koh yaushe. Juyowa tayi tana kallon sa ganin ya kafe ta da idanu ya kasa ce mata komai. Janƴo gyalen ta tayi tana sake rufe jikin ta fuskar ta babu yabo babu fallasa tace "You are welcome." Sai a sannan ya ɗan murmusa yace "Seems like you aren't happy to see me." Kallon sa take kafin kuma tace "Ofcourse i am, but why zaka zo baka sanar dani ba, i hate surprises." "Uhm really?" ya faɗa yana kallon ta. Shiru tayi tana kauda kai daga kallon sa. Ji yayi babu daɗi ganin yadda tayi kamar bata wani damu da ganin sa ba bale ta nuna ɗaukin hakan, tashi yayi daga zaunen da yake yace "Maybe i should take my leave then." Kallon sa tayi tace "Why?." "Coz bakiyi murna da gani na ba" ya faɗa cikin rashin jindaɗi. Yadda yayi maganar ne ya sanƴa ta jin babu daɗi tausayin sa na kama ta, nan ta tashi tsaye tana ƙarasowa daf dashi tace "So how do you want me ta welcome you then?." Kafaɗu ya ɗaga still fuskar sa a 6ace. Murmushi tayi tare da rungumar sa firmly cikin sauƙe numfashi tare da lumshe idanu tace "Am so very happy to see you Abyad darling." Murmushin da baiyi niyya ba yayi, shima yana rufa mata hannayen sa cikin ƙasa da murya yace "I miss you so much baby." Murmushi tayi tare da ɗagowa tana kallon sa tace "Alright then kiss me." Murmushi yayi tare da ɗan ɗago ha6ar ta da niyyar kai bakin sa kan nata ya sumbace ta. Saurin ture kansa tayi tace cike da mamakin sa tace "Are you being for real?, am just kidding you, dama ai inason gwadaka ne and now look you really want to do it." Sumar kansa ya shafo kafin yace "But you asked me to do it." "But ai da wasa nake maka, dama inason ganin gudun ruwar ka ne, kai koh kunƴa ma bakaji ba, you do really want to kiss me, i can't believe you" ta faɗa tana cire hannayen sa daga jikin ta. "Well i thought maybe we could have a little romance here" ya faɗa cikin kashe mata ido ɗaya. "Lallai ma balarabe" ta faɗa. "What?" ya faɗa yana kallon ta. "Kana nufin kacemin bakajin hausa ne komiye?." "Well, i don't understand what you're saying." Baki sake take kallon sa kafin tace "You mean duk zaman ka a Nigeria bakaji hausa ba?." "No" ya faɗa. Kai kawai ta jinjina kafin kuma tace "Alright, have a seat kasha ruwa da lemo." Riƙo ta da yayi ne ya sanƴa ta tsayawa kallon sa. Kallon ta yake yace "Did you came all the way from your house dressed like this?." "Like wha...?" sai a sannan ta kula da gyalen ta dake riƙe a hannun sa. Idanu ta ɗan waro tace "Kut" tana kai hannu da niyyar amsar gyalen. Ɗaga hannun gyalen yayi sama yana cigaba da kallon ta cikin murmushi. "What...what are you doing?, give it back." "No" kafin kuma in a whisper yace "I like seeing you like this." Sosai tayi ƙoƙarin kwatar gyalen sai dai ta kasa sakamakon tsayin ta bai kai ta iya amsa ba. Gajiya tayi tare da juya masa baya tana ƙanƙame jikin ta. Sai da ya ƙarewa ƙugun ta kallo tsaf iya son ransa kafin ya ware mayafin yana rufa mata, hannayen sa kan shoulders ɗinta yace "You're 100% perfect Baby." Jin tsinin hancin sa kan wuyar ta ne ya sanƴa ta saurin juyowa tana kallon sa cikin rawar murya tace "Listen...i...i... ka maida duk wani abu da na faɗa anan as shashanci sabida banida hankali, kasan kwakwalwa ta ta samu matsala koh?, toh duk bansan nayi ba, kaima ka bar dukkanin wani abu dake cikin zuciyar ka ba yanzu ba tukun" ta faɗa tana gyara rufar gyalen har kai kamar wata tsohuwa. Murmushi kawai yakeyi ganin yadda take maganar cikin kikkifta idanu kamar marar gaskiya, nan yace "Well then, i can't wait for that day though." Zama tayi kawai ba tare da ta kula sa ba tana turo baki. Zuwa yayi ya zauna kusa da ita yace "Baby?." Shiru tayi bata kula sa ba kanta a ƙasa. "Fushi kikayi dani, am so sorry idan nayi wani laifin, i promise not to annoy you again." Bata ɗago ba haka ma bata kula sa ba "Babe?" ya sake faɗa yana leƙa fuskar ta. Juya masa baya tayi tana tsuke fuska. Sauƙowa yayi daga zaunen da yake yaba kneeling a gaban ta ya sake kiran "Baby?." Ɗan ɗago da idanu tayi tana kallon sa, kafin kuma ta sake maida kan nata. Murmushi ya ɗanyi kafin yace "Okay, i have something for you, a gift." Ɗan ɗagowa tayi tana kallon fuskar sa kafin ya jinjina mata kai yace "Yeah, wait a sec" ya faɗa yana sanƴa hannu cikin aljihun sa ya fiddo da wata ƴar ƙaramar akwatin zobe. Ita dai kawai da idanu take binsa har ya ciro diamond ring ɗin yana nuna mata yace "Remember this?." Kallon ring ɗin take tana son tunato shi kafin kuma tayi recalling lokacin da yaje ya sameta a hospital har ya cire ring ɗin daga jikin yatsar ta. Kai ta jinjina masa tana kallon sa, murmushi yayi yace "Can i?" ya faɗa yana buɗa mata hannun sa. Da kallo tabi hannun nasa kafin kuma ta shiga ɗago nata a hankali tana ɗaurawa kan nashi. Murmushi yayi staring at her cute fingers kafin ya shiga sanƴa mata zoben a ring finger ɗinta, nan kuwa ya zauna tare da yiwa hannun nata bala'in kya In a calm voice nasa cikin murza yatsun hannun ta yace "Babe, earth may stop rotating, birds may stop flying, candles may stop melting, fishes may stop swimming, heart may stop breathing, but I will never stop LOVING you... some people say happiness is life, others say it’s freedom and some say it’s money, but happiness for me is just having the opportunity to know you, I Love You So Much DEENAH!" ya ƙarashe cikin bata light peck akan fingers ɗin nata. Ɗago da idanun sa yayi yana kallon idanun ta da ta kafe sa dashi, a hankali ta shiga janƴe hannun ta daga cikin nashi cikin sanƴi tace "Thank you." Murmushi yayi yana kallon ta for about a minute, kafin kuma yace "I have something for you." Ɗagowa tayi tana kallon sa tace "Again?." Kai ya jinjina mata kafin ya sanƴa hannun sa cikin aljihun sa yana ciro wani folded white sheet ya miƙa mata. Da kallo take bin paper ɗin ba tare da ta amsa ba. "Kar6i mana" ya faɗa yana kallon ta. Hannu tasa ta amsa kafin ta shiga buɗewa a hankali tana bin dogon rubutun dake ciki da idanu. "What...what's this?" ta faɗa tana kallon sa. "It's from YAZEED" ya faɗa a hankali. Maida duban ta tayi cikin paper ɗin ta shiga karanta saƙon dake ciki. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/17, 10:26 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *043...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*NOT EDITED*_ _________ _"Dear DEENAH,_" _"I know this is hard, but i just wanted to say sorry again for all that happened the other day, my Mom is kind of harsh and selfish, When you do not get along with your partner’s family, you might be dating only your partner, but you must also get along with his family. That is the best way the relationship can work. If you don’t, it is best to move on, i don't know how to say this, but i think rabuwar mu shine mafi alkhairi a garemu baki ɗaya, though banida tabbacin whether you will be hurt or not akan hakan, but tunda soyayyar mu ba wani nisa tayi ba i know zaki iya danne zuciyar ki kiyi haƙuri kamar yadda nake kan yi a yanzu, there is no way da zan iya baki farin ciki since Ummie na ta nuna bata ƙaunar ki, i know it hurts to disappoint or make jest of someone in public, but i'm really sorry DEENAH, it was all because of me hakan ya faru, and am also sorry on my Mom's behalf too, please forgive me as i ask you poilitely to end things here, we will still be friends for each other, and also... I really do want to ask you a favor, ke mutuniyar kirki ce and you're very decent so ba zan so ace kinyi skipping family ɗin mu ba, you and my brother will really make a beautiful couple, so i thought maybe shi zai iya maye gurbi na cikin zuciyar ki, am sure he will be a good partner and ba zakiyi nadamar kasancewar sa soulmate naki ba, i just do hope that zaki duba magana ta and accept him warmly._ _Yours sincerely_ *_YAZEED AL-ABBAS._* Ɗagowa tayi bayan ta gama karancewa duka tana kallon ZEEYAD dake kallon ta tunda ta kafa idanu a jikin paper. "Have you read this?" ta faɗa cikin ɗaga masa paper ɗin. Ɗan murmusawa yayi yace "No, but i guess kin karanta buƙatar da yake nema dake cikin letter ɗin, right?." Nannaɗe paper ɗin tayi fuskar ta babu yabo babu fallasa tace "But i feel so bad for him, i mean ba abu mai sauƙi bane a raba ka da wanda kake so." "Yeah, i feel bad for him also." "He really wants me and and you to get together." Murmushi yayi yace "Yeah, haka yacemin, and i accept it without hesitating." "You're unbelievalble, koh irin ɗan jan ajin nan ma bakayi ba?." "What... Idan naja aji then ajin zata tsinke and maybe then i will lose you for someone else." "Okay then, what about..." shiru tayi tana ɗagowa ta kallesa. "What about what?" ya faɗa yana kallon ta. "Your girlfriend." "JALILAH?" Ya faɗa yana kallon ta. Ɗan kallon sa tayi kafin a hankali tace "Yes, do you love her?." Murmushi yayi yana tashi ya zauna kusa da ita yace "Maybe a little bit." Da sauri ta juyo tana kallon sa nan tace "You really do?, i thought koh ni kaɗai kakeso kuma zaka aura, you mean itama auren ta zakayi kenan?" ta faɗa idanun ta na cikowa da hawaye. Gimtse dariyar dake son zuwa masa yayi hango tsantsar kishi da yayi cikin idanun ta. "You think this is funny?, i mean how could you, ni ka fara so right, why then zaka fara son wata just because ɗan misunderstanding ɗin da aka samu a baya?." "Well Grandma suggest her for me." "Seriously, why don't you tell her cewa kana da wacce kakeso?, i thought you will be only mine." Shiru yayi yana kallon cikin idanun ta. Tashi tayi kawai ba tare da ta sake tanka masa ba tayi hanƴar fita daga falon ta fice. Ta ɗau like 20mins kafin ta sake dawowa hannun ta ɗauke da ɗan madaidaicin tray. Ajiyewa tayi a ƙasa kusa da ƙafarsa kafin ta ɗauko lemu da ruwan da Anty Khadija ta ajiye masa tana faɗin "Ka sauƙo." Babu musu ya sauƙo tare da nannaɗe ƙafafun sa yana kallon ta. Buɗe tray ɗin tayi inda plates biyu ke jere akai ɗaya na cakes ɗaya kuma cookies ne aciki. Cup ta ɗauka ta tsiyaya masa lemun 5alive ɗin tana miƙa masa, amsa yayi still idanun sa a kanta. "Ni ka daina kallo na haka kayi harkar gaban ka." Ɗan murmusawa yayi yana kai hannu ya ɗauko cup-cake ɗaya "Ohh so soft" ya faɗa yana latsa cake ɗin. Itadai bata ce dashi komai ba har ya kai cake ɗin bakin sa. Tauna ɗaya yayi mata ya gimtse fuska yana saurin ɗagowa ya kalleta da idanun sa da suka fara canza launi. "What, menene?" ta faɗa staring at him. Runtse idanu yayi yana jin yadda kansa ta fara juyawa. "Are you Okay?" ta sake faɗa tana kallon sa. Idanun sa a runtse ya kasa buɗewa haka ma ya kasa taune sauran na bakin shi. "Meke damunka ne wai?" ta faɗa cikin ɗan fara tsorata da yanayin shi. Da hannu ya nuna mata cake ɗin ba tare da ya buɗe idanun sa ba "baiyi daɗi bane?" ta faɗa cikin kallon sa. Da kyar ya iya girgiza mata kai "Yayi sugar dayawa?" ta sake tambayar sa, nanma kai ya girgiza mata, shiru tayi tana kame-kame cikin zuciyar ta dan kuwa ta rasa nayi, da sauri tace "Amai kakeji?" saurin jinjina mata kai yayi. "Alright, come on let me help you" ta faɗa cikin tashi tsaye tana zuwa ta riƙo shi tsaye, dakyar ya iya miƙewa hannayen sa kan kafaɗun ta ta kai shi toilet ɗin cikin falon "Alright, spit it out" ta faɗa cikin patting bayan shi gently, sunkuyar da kansa yayi yana tofar da na cikin bakin nasa, ruwa ta tara tana sanƴa masa ya kurkure bakin sa kafin ta wanke masa fuskar shi tana ɗago shi "Are you Okay now?" ta faɗa tana kallon sa Kai ya jinjina mata still idanun sa a lumshe, taimaka masa tayi suka fito daga banɗakin tare da taimaka masa ya zauna gently, da gyalen jikin ta ta hau goge masa fuska, tana ɗan tatta6a goshin sa da ya ɗanyi zafi. Sosai zuciyar ta ta cika da tsoro dama kuma mamakin abinda ya same sa daga sanƴa cake a baki. Cikin ɗan galabaita yace "I...i...need a nap." "You can sleep here" ta faɗa cikin damuwa tana kallon sa. Da kyar ya iya buɗe idanun sa da suka ɗanyi jaa yana kallon ta, a hankali yace "Help me get to my car." "Zaka iya kwanciya anan" ta faɗa, "No" ya bata amsa a hankali. Tashi tayi tana riƙo hannun sa ya tashi, kafin su fara tafiya, ganin yana tangaɗi kamar mai jin hajijiya ne ya sanƴa ta saurin riƙe sa sosai suka fice daga falon ta ɗayar ƙofar. Har motar sa dake waje ta kai sa ta buɗe seat ɗin baya tana taimaka masa ya shiga, kafin ta rufe tana komawa ta ɗayan gefen ta shige, kallon sa take with pity dan kuwa batasan menene ya haddasa masa losing control ɗin kansa suddenly haka nan ba, ganin kamar akwai zafi ne ya sanƴa ta kunna ac ɗin cikin motar tana riƙo hannun sa cikin nata. Yadda take yi masa ɗinne ya sanƴa bacci ɗaukar sa nan take. Kyakkyawar fuskarsa ta ƙurawa ido tana kallo, ɗan murmusawa tayi kafin ta rungumo hannayen sa tana ɗaura kanta a kafaɗun sa. Ta san tabbas ƙaddara ce ta haɗa su idan ba haka ba babu ta yadda za'ayi ta haɗu da kamar sa, he is one in a million, ya tara komai, kama daga kyau, nasaba, arziki, addini, kwarjini da dai sauran su, sai dai with dukkanin abubuwan nan da ya tara hakan bai sanƴa shi looking so down akanta tare da ƙin ta ba, he loves her wholeheartedly and ready to sacrifice duk wani abu duk dan ya mallake ta, at first she thought koh ta rasa shi kenan har abada but a yanzu ta fahimci cewa ita ɗin ƙaddarar sa ce tunda ƙaddarar ce ta haɗa su, dah ba dan ƙaddara ba there is no way da zata haɗa koh da inuwa ɗaya ne dashi. Ɗagowa tayi tana sake kallon fuskar sa kafin kuma ta sake maida kanta tana lumshe idanu. ******************** _______"Yes, and what about this?" ya faɗa yana kallon ta. Cikin rawar murya take kallon sa da idanun ta da suka tara hawaye tace "It...it was a picture of them together." "A'ina kika samo shi?." "Kawomin akayi." "Who?" ya faɗa yana kallon ta. "I don't know, kawai dai an bawa maids ne su kawomin suma sunce basu ga fuskar wacce ta kawo musu ba." Sake duba hotunan hannun nasa yake kafin ya sami wuri ya zauna yana faɗin "I don't think wannan is something to worry about JALILAH." "You don't think, she is your girlfriend isn't she, and he..." shiru tayi ta kasa iddawa. "And he is what, look JALILAH i guess is time da yakamata ki fahimci cewa ZEEYAD has no taste akanki, yana kula ki ne kawai for his Grandma's sake." "What?, ya zaka ce haka, he loves me" ta faɗa idanun ta na tara kwalla. Kallon ta yayi yace "No he doesn't." "Ofcourse he do, and DEENAH is she not your girlfriend?." "No she was my girlfriend." "Mai kake nufi da she was?." "Listen JALILAH, I know you may find this strange, but maganar gaskiya is that ZEEYAD and DEENAH have known each other for a very long time now, ita ce first love nashi." "What do you mean, that can't be possible." "Nothing is Impossible JALILAH." "But how did you know that, ya akayi kasan hakan?." Shiru yayi yana sake kallon photon hannun sa yace "Ranar da aka ɗau hoton nan, i accidently bumped into them and over-heard their conversation, they know each other for a very long time, bansan menene sanadiyyar rabuwar su ba, i can't believe ZEEYAD yayi ƙoƙarin sadaukar da farin cikin sa just because of me, i can't believe how stupid he was na ganin yayi sacrificing love nasa just to see me happy, DEENAH belongs to him and he chose ya barmin ita and decided ya 6oye komai daga gareni, but i can't endure ganin hakan ta faru, that is why na yanke decision ɗin haƙura da DEENAH not just because akan kalaman Ummie na but because of my brothers happiness." Sosai jikin JALILAH yayi sanƴi tanajin zuciyar ta na karyewa, cikin rawar murya tace "I can't believe you did this to me, i love him and you decided to re-unite him with his Ex." "She isn't his Ex JALILAH, they are inlove, he loves her so very much more than anything you can imagine JALILAH, how then kike tunanin na shiga tsakanin su tare da datse farin cikin su after inada mafita, wanda bai wuci na basu space suyi rayuwar su yadda yakamata ba, they love each other JALILAH and they are happy together, so there is nothing i can do da ya wuce na sake uniting ɗinsu." Kuka JALILAH ta fashe dashi inda ya ɗago yana kallon ta, ajiyar zuciya ya sauƙe nan yace "You have to take heart JALILAH, i know it's not easy ace kanason mutum kuma shi ba hakan bane a ransa." "But he is all my hope, a wurin sa da Grandma kaɗai ne nake samun farin ciki, i just can't do without him." "Well then dole ki koyawa kanki cewar bakomai ne kake so kuma ka same shi, sometimes wasu abubuwan ba alkhairi bane a gare mu, so dole sai munyi haƙuri mun rungumi yadda Allah ya tsara mana rayuwa no matter how worst it is." Cikin gudu ta fice daga falon tana cigaba da rera kuka, da kallo ya bita kafin kuma ya ɗan ta6e baki. Part ɗin Grandma ta nufa tana cigaba da kuka, Grandma dake zaune tana duba wasu sabbin kaya da aka kawo mata ta saya ɗagowa tayi da sauri tana kallon JALILAH dake kuka. "Subhanallah, Allah kasa dai kukan alkhairi kike, zo nan mai ya sameki?." Ɗagowa tayi da idanun ta da sukayi sha6e-sha6e da hawaye tace "Akhi ne..." "Wane Akhi ɗin, ba sai Sooraj ba koh?" cewar Grandma cikin waro idanu. Kai ta girgiza tana cigaba da kuka. Kallon mutanen da suka kawo mata kayan tayi tace "Ku ɗan sallame mu." Cike da girmamawa suka tashi tare da ficewa daga falon. Kallon ta Grandma take tana cikin share mata hawaye tace "Faɗamin ina jinki, meke damunki?." "Akhi, dama ba sona yake ba?." "Ban fahimce ki ba, Boy kike nufi kowa?." Kai ta jinjina tana kallon Grandma. Murmushi Grandma tayi tace "Ka jiki dai da wani magana, yana sonki mana, maiyasa kike wannan tunanin, wa zai ƙi kyakkyawar ƴa kamar ki." "Bu... but YAZEED ne yace min ba sona yake ba, yana da wacce yake so." "Ki jiki kuma du, indai akan wannan maganar ne ki share hawayen ki ki daina kuka, insha Allah Boy mijin ki ne, kuma na tabbata yana sonki har cikin zuciyar sa, ki bar damun kanki kinji?." Kai kawai ta ɗagawa Grandma ba wai dan hankalin ta ya kwanta ɗin ba. Rungumo ta Grandma tayi tana cigaba da kwantar mata da hankali. ******************* "Seems like you've lost your stupid mind YAZEED, a matsayi na ta mahaifiyar ka nake umartar ka da kaje kaga yarinƴar nan, ƴa ce ga tsohuwar aminiya ta,am sure you will like the girl sabida tafi wancan abar da ka kawo a farko komai, amma kazo kana cemin ba zakaje ba, how dare you?." "Please Ummie i guess kin nuna batayi miki ba kuma nace na haƙura da ita koh, toh dan Allah na roƙe ki kada ki sake maganar ta ya isa haka nan." "Whatever, miye ma zan ƙaru dashi idan nayi maganar asararriyar?, you just do what i asked of you muddin ba so kake ka fuskanci fushi na ba." Cike da ƙosawa yace "Fine, fine then i will do whatever you asked of me, ba so kike ki haɗa ni aure da ƴar aminiyar ki ba, then bakida case da wannan, you can do whatever you think is right, but mind you... duk wani abu da ya biyo bayan hakan don't blame me for it." Murmushi tayi kafin tace "That sounds good, ka shirya gobe kaje kaga yarinƴar na riga da na sanar da mahaifiyar ta and they are ready to welcome you anytime, just don't messed things off idan kaje ka, behave like a real good boy mai bin umarnin mahaifiyar sa, and yes... ka tabbata kaje musu da kayan alatu dan sake tabbatar da cewa ba gidan ƙananun mutane zasu bada ɗiyar su ba, koh dayake ka bar komai a hannu na i will take care of that, kai dai ka zamto a shirye kake zuwa gobe, clear?." Shiru yayi zuciyar sa na ƙuna kamar ba zai amsa ba kuma ya buɗi baki dakyar yace "Yeah." Murmushi tayi tace "Good" juyawa tayi ta fara tafiya, sai da ta kawo bakin ƙofar fita ta tsaya ba tare da ta juyo ba tace "Ƙannen ka zasu dawo sati mai zuwa, so be ready to welcome them" tana faɗin haka ta fice. _(Idan baku manta ba a first page munyi mention ƴaƴa shida mai Martaba ke dashi, soon sauran zasu bayyana)_ Huci ya fesar yana naushin table ɗin gaban sa yace "Fuck your friend and her damn family." ******************** ________Idanun sa da suka ɗanyi masa nauyi ya shiga warewa a hankali, numfashi ya sauƙe yana bin hannun ta dake sarƙe da nashi da kallo. Motsa hannun sa yayi yana squizing ɗin hannun ta, hakan ya sanƴa ta fara buɗe ido a hankali, kafin kuma ta ɗago da sauri tana sauƙe idanun ta cikin nasa. "You're... alright?" ta tambaya cikin tatta6a goshin sa. "Yeah am fine actually, am fine" ya faɗa. Lumshe idanun ta tayi tana sake ware su tace "You scared me... i have never seen you like this." "Not as much as you scared me lokacin da baki da lafiya." Kallon sa take kafin kuma ta ɗan saki murmushi tace "But tell me, what happened to you, da akwai wani abu a cikin cake ɗinne da baiyi maka ba?." "Who made the cake?" ya tambaye ta. Shiru tayi na ƴan seconds kafin kuma tace "Actually siyowa mukayi a wani gida daga ƙasan street ɗinnan, it's just that naga babu daɗi ne na barka babu abin da zaka ta6a, so Anty Khadija tayi mana ordern shi daga gidan su ƙawar tata." "What, you went out dressed like this?" ya faɗa cikin haɗe fuska yana kallon ta. Kallon kanta tayi kafin kuma ta kallesa tace "No i can't go out dressed like this." Lumshe idanun sa yayi kafin yace "Actually nayi perceiving kwai a ciki ne, thats why kika rasa gane kaina, i don't like egg." "Oh God, you're allergic to egg na tuna hakan, you once told me cewa baka cin kwai." "Not allergic though tunda baya fito min da sign a jiki." "I guess duk ɗaya ne, coz yana cutar da kai, but the egg is disolved how comes kuma ka iya ganewa akwai kwai a ciki?." "I can smell it no matter how tiny kika sanƴa shi cikin girki, it's smell makes me go a little wild crazy." "Am so sorry" ta faɗa kamar zatayi kuka. "For what?." "For being so stupid na manta da cewar baka cin kwai, it's because of me that you're in this state." "Oh come on baby, why the cry?" ya faɗa hugging her lightly." "Am sorry" ta sake faɗa. "It's alright babe you did nothing wrong" ya faɗa giving her a light peck a forehead. Ɗagowa tayi tana kallon sa, nan ya shiga goge mata hawayen fuskar tata, kumatun ta duka biyu ya kama yaja tare da faɗin "Cry cry baby." Murmushi tayi tana 6oye kanta kan faffaɗar kirjin shi. "Thank you so much baby, for taking a good care of me" ya faɗa calmly cikin murmushi. Shiru tayi ta lafe kawai tana sauraron bugun zuciyar sa haɗi da shaƙar daddaɗar ƙamshin dake tasowa a jikin sa, bata ƙi ace sun dawwama a haka ba, dan kuwa har wani irin bacci mai daɗi taji yana zuwan mata. Jin tayi shiru kuma taƙi ɗagowa ne ya sanƴa shi faɗin "Babe, bacci?." DEENAH buɗe lumsassun idanun ta tayi tana ɗagowa tare da zuba masa idanun ta da sukayi kama da na mai jin bacci. "Bacci kikeji?." Kai ta jinjina masa kawai, nan yace "Alright, you should go back inside, i will be back anjima." Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "Are you sure ka warware, can you drive?." "Yeah, am fine yanzu" duba agogon hannun sa dake nuna 12:23 pm yayi kafin kuma ya kalleta yace "I will be back at night." "Alright" kawai ta faɗa tana murza idanun ta. Buɗe murfin motar duk sukayi suna fitowa, inda ya shige gidan gaba, waving tayi masa da hannu tare da yi masa addu'ar Allah ya tsare, kafin ta juya ta shige cikin gida. Sai da yaga shigar ta gidan kafin ya tada motar sa ya bar wurin. _*Ayi haƙuri da wannan, zazza6i ke son kama ni, kuyi addu'ar Allah ya kawar dashi daga kaina zuwa kan LATEEFAT dan kuwa sati ɗaya kenan bata comment tsabar samun wuri irin nata🙄🤧*_ *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [8/19, 10:37 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *044...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _*NOT EDITED*_ __________Motoci ne kusan huɗu a jere suka shigo cikin MASARAUTAR kowanne na samun gurbin parking. Bai wuci da ƴan sakonni da tsayuwar su ba driver ɗin dake jan motar da ta kasan ce ta biyu a jerin huɗun ya fito da hanzarin sa yana zuwa ya buɗe murfin motar kamar zai kife ƙasa tsabar hanzari da yadda jikin sa ke rawa. Tunkuɗe driver ɗin yayi da ƙafar sa yana mai fitowa daga cikin motar, kyakkyawan saurayi ne sosai wanda ba zai wuci 25yrs ba ya fito fuskar nan tasa a wani irin mugun tsuke, yana sanƴe cikin shigar ƙananun kaya irin ta ƴan gayun zama ni wanda sukayi matuƙar kar6ar sa tare da amsar fatar jikin sa, hannu ya sanƴa tare da cire baƙar shade ɗin idon sa yana mai sake bin farfajiyar MASARAUTAR da kallo, chan ƙasan maƙoshi ya "Wow" yana barin jikin ƙofar kafin driver ɗin ya maida ta ya rufe. "OMG!, this place is so fucking hot" cewar wata ƴar matashiyar budurwa dake ƙarasowa kusa dashi cikin rangwaɗa tana fifita da hannun tana wani irin yatsine fuska, sosai na ƙare mata kallo, tundaga kan curly dyed gashin kanta har izuwa kan doguwar takalmin da take sanƴe dashi, kyakkyawa ce sosai ba laifi, inda itama ke sanƴe cikin shigar ƙananun kaya, doguwar riga irin ta turawa wacce bata wuce mata guiwa ba, ƴar matashiyar budurwa ce da ba zata gaza shekaru ashirin ba. Kallon ta saurayin yayi kafin yace "Seems like mutanen nan basu wani damu da dawowar mu ba, nobody even cares da zuwa tar6ar mu." Yatsine fuska tayi kafin tace "Damn them, let's find our way inside." Kallo yake ƙarewa farfajiyar inda suke tsaye yana kallon yadda bayi maza da mata kowanne ke fice da shige. Daga nesa macen ta hango mahaifiyar su tafe kuyangun ta na take mata baya, nan tace dashi "Seems like she is happy da ganin dawowar mu." "She looks a bit kind of Old." Ɗan dariya tayi tana ƙarasawa wurin mahaifiyar tata. "What kind of beautiful Mom i have got" ta faɗa cike da jindaɗi tana rungume mahaifiyar tata. Sosai Sarauniya Hafeezah tayi murnar da dawowan ƴaƴan nata, ɗago ta tayi tare da sumbatar ta a ƙunci tana sake rungume ta tace "Welcome home my beautiful princess." Sun ɗan daɗe rungume da juna kafin su ɗago, nan Sarauniya Hafeezah tace "Rahila ku raka Rahinah izuwa masauƙin ta sannan ku samar mata da dukkanin wani abu da ta buƙata." Duƙar da kai wacce aka kira da Rahila tayi tana faɗin "Angama ranki ya daɗe" ta faɗa tana riƙo Farha da niyyar janta su tafi. Wani irin wawan mari ta ɗauke baiwar dashi in a rude manner tace "Yuck!, what the hell do you think you're doing, touching me with your fucking dirty hands?." Rolling idanu kawai Sarauniya Hafeezah tayi kafin tace "Calm down princess, she will be careful next time." Sosai ran Rahinah ɗin ya 6aci tana wiping inda baiwar ta ta6a ta kafin tace "I don't care, baki faɗa musu dukkanin rules ɗina bane, she must be punished for her misdeeds, i mean how could she touch me with this ugly, dirty and disgusting hands of her?." "Apologised to her now" faɗin Sarauniya Hafeezah cikin tsawa. Baiwar da ta sha rikitaccen mari duk ta rikice ne tayi saurin rissinawa tana faɗin "Ki gafarce ni ranki ya daɗe gimbiya, a bisa rashin sani na aikata miki hakan." Kallon ta Sarauniya Hafeezah tayi tace "Listen princess, kiyi mata haƙuri kinji?." Kamar ba zata yi magana ba tace "Dan kawai kince hakan ne, am tired of standing here a nunamin masauƙi na mana, are they going to keep staring at me like this?." "Show her to her room, and make sure kunyi avoiding duk wani abu da zai sanƴa ta 6acin rai." "Insha Allah ranki ya daɗe" suka amsa cikin girmamawa. Biyu ne suka shiga gaba biyu kuma suna take mata baya inda suka sanƴa ta a tsakiya "ughh they stink" ta faɗa cikin doɗe hancin ta tana korewa da hannayen ta suka wuce. Sarauniya Hafeezah maida duban ta tayi gun saurayin dake tsaye ya wani 6ata fuska haɗi da naɗo baki wanda daga gani ƙiris yake ya fashe tace "Ayaan my boy" ta faɗa tana ƙarasowa kusa dashi tana rungumar sa. "I guess am not your favorite anymore how could you ignore me kamar baki ganni ba kinje kina kula wata Rahinah chan daban?" ya faɗa cikin ɗagowa yana aika mata da wani irin kallo ƙasa-ƙasa. "Am sorry Sweetheart, kasan bama haka da kai koh, come on na sanƴa an girka maka favorite ɗinka am sure you will enjoy it." Sai a sannan ya ɗan saki fuska yace "Really?." "Kai dai kazo muje" ta faɗa tana riƙo sa suyi gaba. Da kallo yabi wata baiwa da tazo wuce su tana gaida su cikin girmamawa yana wani irin cize baki. "Control yourself Ayaan, wadannan matan are like your servants dan haka ka ɗauke idanun ka daga kansu." "Sorry Ummie" ya faɗa suna cigaba da tafiya a haka har suka iso part nata. Da wasu bayi ta haɗa shi inda shima akayi masa iso zuwa nashi part ɗin. **************** _______Sosai taci kwalliya cikin baƙar doguwar gown ɗin ta, kasancewa shine Favorite color nata. Sosai ta dami Anty Khadija dake yi mata ɗaurin head-tie akan tayi sauri. "Anty Khadija yana ta jira fah, fisabilillah." "Lallai ma DEENAH da ake kwalliya baki ce nayi sauri ba sai yanzu, toh wallahi ki zauna ki natsu kinsan dai banason abu da gaggawa, yanzu idan ban natsu na fidda ki mai kyau ba ai sai kije yace bakiyi kyau ba koh ma yaƙi yaba kwalliyar taki." Ɗan turo baki tayi tana kallon fuskar ta cikin mirror ɗin. Ameerah ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Miye nake ganin kamar duk kun shirya?." Kallon ta Anty Khadija tayi tace "Toh da ɗin mai kikeso muyi idan ba shirin ba?." "Malamai ban fah gane ba, wai kuna nufin kuce har tafiya zakuyi yanzu?." "Tsaya anan." Jafar ne ya leƙo cikin ɗakin shima cikin shigar sa mai kyau yana faɗin "He is here." Kallon sa Amirah tayi baki sake tace "Bangane he is here ba, wallahi ba zaiyiwu ba, tayaya zakuyi ku tafi ku bar ni bayan nasa rai" ta faɗa idanun ta na tara hawaye. "Toh kuma laifin waye, ina zuwa kikayi kika kafa TV a gaba kina kallo yawa baƙauyiyar da ta fito daga karkara, kuma da nayi ta kiran ki kizo ɗin ba manna min kikayi ba, kyaji dashi ai dan mu kam ba jiran ki zamuyi ba" cewar Anty Khadija. Cikin kuka Amirah tace "Wallahi in ta yiwu na zama albasa, wallahi baku isa ba" ta faɗa tana ficewa tayi ɗakin Umma. Kallon su Jafar yayi yace "Ya zakuyi mata haka?." "Kyale ta nasan koh taje inbanda ƙauyanci babu abinda zata nuna, gara tayi zaman ta da akan ta kunƴatar damu." "Anty Khadija, make it quick please." "Ke ni dallah mai nakeyi ne yanzun, sai kisa na fasa na bar miki abin ki haka." "Yi haƙuri" ta faɗa cikin sanƴi tare da tsuƙe bakin ta tayi shiru. Ficewa Jafar yayi yana faɗin "We're waiting." Ba'a daɗe ba Amirah ta dawo da Umma a bayan ta tana matsar kwalla lokacin har an gama ɗaurawa DEENAH ɗankwalin. Daga bakin ƙofar Umma ta tsaya tana kallon su tace "Amirah tace kunje ba zaku tafi da ita ba, maiyasa?." Anty Khadija ce tace "Anty tunɗazu fah nake ce mata tazo ta shirya amma taƙi kula ni taje ta ƙura TV a gaba wai ita nan tana kallon favorite series ɗinta." "Wallahi ba haka bane, ni babu wacce ta kira ni a cikin su, kawai dai basa son zuwa ne dani kuma sai naje" ta faɗa cikin kuka. "Toh ya isa haka nan jeki shirya da wuri, ku kuma ku jira ta." "Amma Umma Abyad fah yana ta jira" cewar DEENAH ɗin cikin 6ata fuska. "Kuyi mata haƙuri yanzun nan zata shirya ku tafi, abu na lokaci ɗaya kam menene dalilin ku na ware ta, wuce kije ki shirya." Daɗi ne ya cika Amirah dan haka saurin wucewa tayi zuwa bathroom tana dariya ƙasa-ƙasa ganin yadda Anty Khadija da DEENAH suka 6ata fuska. Ficewa Umma tayi daga ɗakin cikin ɗagun murya yadda Amirah ɗin zataji Anty Khadija tace "Kuma wallahi minti biyu ki idda wankan nan ki fito, minti uku ki shirya kinga dai 5mins kenan koh, idan kika wuce haka kuma kya same mu a chan." Sanin halin Anty Khadija ya sanƴa Amirah saurin fitowa daga wankan tana tsuke baki. Da sauri ta ɗau kayan ta mai kyau ita ma tasa kafin ta shiga shirin nata cikin sauri ganin yadda duk suke bin ta da harara yawa idanun su zai fito. "Inbanda ma ƴar wahala iriyar ki kowa nan da kika gani da saurayin sa zashi ke koh da uwar wa zaki oho" cewar Anty Khadija tana aika mata da harara. "Hmm Anty Khadija kenan nima fah saurayin nan ba rasa shi nayi ba..." "Dallah ki rufewa mutane baki kiyi sauri, da wani ƙazamin saurayin naki a wurin hammata duk gumi idan yazo yawa wanda yayi gudun tsere kafin ya ƙaraso, ke har kina iya zama dashi a hakan ba tare da kinji komai ba mtssww." "Oho dai, koma dai menene ba za dai ace banida saurayin ba." "Da wannan abin ai gara babu, ke DEENAH kin ganshi kuwa, ni wallahi ina tantama ma idan ba irin samari ƴan ghetto masu yiwa ƴan mata ƙarƴar nan bane, who even knows koh baban bola mai ajakuta ne, dan kamar na ta6a ganin mai kama dashi yara na bin sa da gwangwan a baya." "Nasan fah duk dan naji haushi nace na fasa bin ku kike faɗamin haka, kuma wallahi ahir ɗinki kin dai san bana fushi da wuri." "Toh dama mutum marar zuciya ina shi ina fushi komin ɗacin a da za'a faɗa masa, kina ganin wannan Amirah ɗin koh kaɗan batada zuciya wallahi, ka gama faɗa mata magana iya son ranka amma koh a jikin ta, dallah kiyi sauri da wani rigar ki yawa wacce zata wasan ƴan bori koh kyau." Ita dai Amirah bata kula ta ba, haka Anty Khadija tayi ta gaggasa mata magana duk dan taji haushi amma ita koh a jikin ta sai ma waƙar ta da take tana dariya. A haka Jafar ya sake dawo ya same su nan yace "It's already 8:30 fah." Miƙewa DEENAH tayi tana gyara zaman rigar jikin ta tace "Muje Yaya, ku same mu a waje." Miƙewa Anty Khadija ma tayi tace "Toh su Amirah sai a iske mu a waje koh." Tsaye Amirah tayi da kwalliyar da take tace "Dan Allah Yaya Jafar ka jira ni, wallahi na kusa kammalawa dan Allah." Kallon ta yayi yace "Amirah, kafin mu wuce yanzu zan biya na ɗau Ruqayyah da siblings nata, and kafin mu ƙarasa dare zai iya yi, kin dai san kuma bama son dare yayi sosai mu dawo koh?." "Shikenan bakomai kuje" ta faɗa cikin sanƴi tana barin bakin mirror ɗin. "Alright, 5mins ya isheki ki gama shiryawa?" ya faɗa. Kai ta jinjina masa tace "Eh wallahi yanzu zan idda na fito." "Alright, make it fast." "Kashh wallahi na ɗauka kinyi zuciya ne, ashe dai duk burga ce" faɗin Anty Khadija. Hararar ta Amirah tayi tana komawa ta cigaba da kwalliyar ta. DEENAH marawa Jafar baya sukayi zuwa ɗakin Umma dan yi mata sallama. "Jafar kada fah ku daɗe" cewar Umma. "Insha Allah Umma." Kallon Umma DEENAH tayi tace "Umma gift ɗina fah?." "Ai dai kya je ki dawo tukun koh?." Murmushi tayi tace "Toh shikenan" tana marawa Jafar baya. Ficewa sukayi daga gidan, motar sa da ta hango ne yasa ta kallon Jafar tace "Tare dashi zamuje?." "Yeah ke dasu Amirah ni zan wuce ɗauko Antyn ki da siblings nata." "Cha6 wannan yarinƴar ce Anty na, na fah girme ta." "Well she is your Aunt then tunda yayan ki na sonta." "No case then" ta faɗa tana yin gaba. Da kallo ya bita yana murmushi kafin shima ya wuce motar sa. Knocking tayi jikin glasses ɗin window ɗin dake a zuge, ɗan buɗe murfin motar yayi kafin ta ƙarasa buɗewa tana kallon sa. Sosai ya haɗe cikin shigar shadda baƙa mai ɗinkin armless wacce tayi matuƙar amsar farar fatar sa sai zuba ƙamshi yake. Tsayawa tayi kallon sa ba tare da ta shiga cikin motar ba. "Come in" kawai ya faɗa staring at her. Shigewa tayi tana rufo ƙofar kanta a ƙasa tace "Sorry, i kept you waiting." "It's alright babe, shall we?." Kallon sa tayi kafin tace "Su Anty Khadija basu fito ba, yi haƙuri dan Allah ka sake jira." "Okay" kawai ya faɗa idanun sa kan steering. "Are you Okay?" ta faɗa tana kallon sa. Kallon ta shima yayi yace "Mai kika gani?." "You look somehow different, kodai kayi fushi ne mun 6ata maka lokaci?." "Not at all, by the way you look so gorgeous" ya faɗa cikin murmushi yana kallon ta. "Thank you, kaima kayi kyau, thats because you wore my favorite color." Murmushi yayi yace "And you always look beautiful koh da baki sanƴa favorite color ɗinki or wore make-up ba." Kallon sa tayi cikin murmushi tace "You mean banyi kyau da make-up ba?." Kallon ta yake yace "Of course kinyi kyau, but not as beautiful as your natural look." Murmushi tayi kawai tana kauda kai tace "Gasu nan sun fito." "Alright" ya faɗa yana tada motar. Baya su Anty Khadija suka buɗe suka shiga tare da gaida shi ya amsa musu cikin sakin fuska. Kallon DEENAH yayi yace "Shall we Ma'am?." Kai ta jinjina masa cikin murmushi kafin yaja motar sukayi gaba. Amirah dake ta rarraba idanu ne tace "Uhm kaga soyayya wai motar ma da zai ja sai ya tambaya ta, lallai DEENAH kin more." Gwa6e bakin ta Anty Khadija tayi tana aika mata da harara. Murmushi ZEEYAD yayi tare da kallon DEENAH yace "What's is she saying?." "Don't mind her, ta ɗan zauce ne." Murmushi yayi yana maida hankalin sa kan tuƙin da yake. Satar kallon Anty Khadija Amirah tayi kafin tace "DEENAH kice yasa mana ɗan kiɗa mana, mota shiru haka biya." "Wai ke miye haka ne?" faɗin Anty Khadija ƙasa-ƙasa kamar ta make ta, kafin kuma tayi kwafa tana kauda kanta. Ta6e baki Amirah tayi haɗi da yin shiru sai rarraba idanu take har suka isa inda zasu. Babban Event center ne mai kyau da tsaruwa, koh ina gauraye yake da hasken wutar lantarki kasancewar dare ne. Wuri ya samu yayi parking motar, nan duk suka buɗe suka fito. Amirah ce tace "Uhm lallai rabon da nazo wuri irin wannan ai tun auren Anty Salma." Tsaki Anty Khadija taja dan kuwa ba ƙaramin haushi Amirah ɗin ta bata ba. "Shall we?" ya faɗa nan duk suka juyo suna kallon sa, nuni yayi musu da hanƴar da zasu bi kafin ya shige gaba suna take masa baya. Amirah ce tazo kusa da DEENAH tace "Ke DEENAH anƴa ba asirce wannan bawan Allahn kikayi ba kuwa?, wallahi ya haɗu Kafci." Harara DEENAH ta zuba mata dan kuwa itama ba ƙaramin haushi Amirah ɗin ta bata ba, ta 6ata musu lokaci gata bakin ta baya iya yin shiru indai taga abu. "Allah ya huci zuciyar ki, ni da ba dan nazo bama wallahi da sai na koma tunda naga sai wani gani-gani kuke yimin dake da Anty masifatu ɗin chan." DEENAH dai bata kula ta ba har suka iso entrance ɗin hall ɗin da aka kama musu ɗin, yadda aka ƙawata wurin ba ƙaramin kyau yayi ba, style akayi wa wurin da balloons baƙaƙe ga kuma dim lights da suka sake ƙawata cikin wurin abin sai wanda ya gani. Wow duk sukayi exclaiming bale ma Amirah da ta saki baki tana sake bin wurin da kallo. Juyowa yayi ya kalli DEENAH yace "You have a seat, i will be back in a moment." Kai ta jinjina masa tare da zama cikin kujerun da aka zuba a wurin tana sake bin ɗan daidaikun mutanen dake jeka ka dawo a wurin da kallo. Fitar sa keda wuya Anty Khadija ta hau Amirah da faɗa "Ke wace iriyar banza ce Amirah, ke shikenan kwata-kwata ba zaki ta6a hankali ba, miye amfanin abinda kikayi yanzu ke koh kunƴa bakiji ba, shikenan ke baki baya iya yin shiru a komai, ai dama abinda yasa nace ba zaki bimu ba kenan sabida kwata-kwata bakida hankali ne amma sai ake ganin kamar banason ki ra6e mu ne, ke shikenan ba zaki ta6a wayewa ba kenan a rayuwa, kina komai kamar baƙauyiya, haba yaci ace kin gyara yanzun babu abinda kika nema kika rasa a gidan ku amma duk inda kikaje sai kin nuna ƙauyanci har inda mutanen ba zasu nuna miki komai bama, toh wallahi koh ki gyara koh mu yi ta samun matsala dake, wannan ai daƙiƙanci ne." Shiru Amirah tayi kamar ba ita ce mai bakin surutu ɗazun nan ba. Wuri Anty Khadija ta samu ta zauna ranta fal a 6ace. Basu fi 5mins da zama sai ga Jafar ne tafe da wata kyakkyawar yarinƴa da ba zata wuci 17-18yrs ba, bayan su kuma wasu yara ne da ba zasu wuci 10yrs ba mace da namiji, da alama dai ƴan biyu ne yaran sabida yadda suke ɗan kama da juna. Murmushi DEENAH da ta hango su tayi tana miƙewa ta nufe su zuciyar ta fal farin ciki tace "Yaya itace?." "Yeah" ya amsa mata cikin murmushi. "Wow tafi kyau a zahiri akan a cikin hoto" ta faɗa tana kallon yarinƴar. Murmushi itama yarinƴar tayi tace "Ina wuni?." Kallon Jafar DEENAH tayi kafin ta amsa mata gaisuwar cikin ɗan dariya, kafin kuma ta riƙo hannun ta tana nuna mata seat ta zauna da ita da ƙannen nata. Kallon su Anty Khadija yarinƴar tayi ta gaida su cike da girmamawa suka amsa mata. Kallon DEENAH Jafar yayi yace "Where is he?." "Ahm, yace min zai dawo yanzu." Kai ya jinjina yace "Okay, you wait here i will be right back, Okay?." "Okay" ta amsa masa kafin shima ya bar wurin. Jafar bai daɗe da barin wurin ba ZEEYAD ya dawo, duk zuba masa ido sukayi suna kallo har ya wuce wurin DEENAH ɗin, ɗan duƙawa yayi yana yi mata magana a kunne kafin ya ɗago yana kallon fuskar ta. Kai ta jinjina masa tana miƙewa tsaye, kallon Anty Khadija tayi tace "Dan Allah Anty Khadija zamuje mu dawo yanzu, ki kular min da baƙin nawa." "Okay toh, bakomai" ta faɗa. Kallon sa tayi tace "Muje." Mara mata baya yayi suka wuce, yayin da duk suka bisu da kallo, Amirah magana ne fal a bakin ta sai dai ganin kada Anty Khadija ta sake dizga ta a gaban budurwar Jafar ne ya sanƴa ta tsuke bakin ta tayi shiru. Waje suka fito nan ya kalle ta yace "Actually, i have nothing to said." "What?" ta faɗa tana kallon sa. Shafo lallausar sumar kansa yayi cikin murmushi yace "I just wanna spend some time with you alone." "You're unbelievable" ta faɗa. "Am i?." "Without a doubt." "Alright, muje chan na saya miki sweet-cotton" ya faɗa yana nuna mata wurin wani mai saida sweet-cotton a farfajiyar wurin. "It's my birthday, we should be celebrating, dare yana yi fah." "Yeah we will celebrate, but atleast we should have a little date here." Folding hannaye tayi tana kallon sa ba tare da tace komai ba. "Shall we?" ya faɗa yana kallon ta. "Yeah, but muyi sauri kar mu 6ata musu lokaci." "Alright" ya faɗa yana miƙa mata hannun sa, da kallo tabi hannun nasa kafin kuma ta miƙa masa nata hannun yana riƙewa cikin nasa suka fara tafiya. Isowa wurin sukayi nan ya kalleta yace "Tsinke nawa kike so?." "Kasan ni ba wani shan sa nake sosai ba, koh da muna yara ma idan baban-bola yazo ni ban cika amsar sweet-cotton ba, tsinke ɗaya ya ishe ni." "Really?, ba shida auki fah" ya faɗa yana kallon ta. "Yeah ni ba dayawa nakeso ba." "Alright" ya faɗa yana ciro wallet ɗinsa, wayar sa da tayi ƙarar shigowar message ya ciro yana miƙa mata wallet ɗin yace "Pay him" yana yin gaba. "Nawa ne kuɗin?" ta tambayi mai saida abin. "Ɗari biyar ne Hajiya" ya amsa mata. Baki sake take kallon sa tana sake maida duban ta kan tsinken sweet-cotton ɗin. Shiru tayi kawai tana ciro 1k ta miƙa masa tace "Toh ka kawo biyu." Tsinke biyu ya ɗauko yana miƙa mata ta amsa kafin tace "Nagode" tana juyawa ta tayi inda yake tsaye. Wallet ɗinsa ta miƙa masa ya amsa tana bashi tsinke ɗaya. "No bana shan zaƙi" ya faɗa. "What, why?." "I just don't like ire-iren abubuwan nan, it's for kids like you." Kallon sa take kafin tace "Kids, you mean am a kid?." "Yeah, i can't believe sai yau kike cika 20yrs." "Kids are children's below 10, and am 20." "Well then that doesn't make any difference, believe it or not you're still a Kid." "No am not." "What are you then, a teenager?." Something similar to that" ta basa amsa. Murmushi yayi kawai ba tare da ya sake cewa komai ba har suka iso inda suka bar su Anty Khadija zaune. "Where are they?" ta faɗa tana ƙarewa wurin kallo ganin babu su. "Maybe in there" ya faɗa yana nuna mata wata ƙofa. "Anan za'ayi taron?" ta tambaya tana kallon sa. Kai ya jinjina mata yana yin gaba nan ta mara masa baya. Buɗe ƙofar yayi ya shiga kafin ita ma ta mara masa baya. Cak taja ta tsaya ganin wani irin duhu mamaye cikin ɗakin gabaɗaya. Idanu ta fara rarrabawa tare da yin lalume tana yin gaba "Abyad?" ta ƙira sunan nasa a hankali. "Where are you, why is it so dark in here?." "Abyad?" ta sake faɗa cikin ɗan tsoron da ya fara darsar mata tana cigaba da laluma hannayen ta. "Ab..." bata kai ga ƙarasar maganar tata ba taji an saki ihun _Happy Birthday to you_ dai-dai lokacin da wutar wurin ya kawo wasu flowers suka shiga zubo mata akai. Sosai ta tsorata da yadda sukayi mata ɗin dan haka hannaye tasa ta rufe fuskar ta ta fara kuka a hankali, inda kuma wurin ya cika da sautin flute ɗin happy birthday. Fuskar kowa washe yake da murmushi, Jafar ne ya fara tafa hannayen sa yana yi mata waƙar _Happy birthday to you_ _Happy birthday to you_ _Happy birthday dear DEENAH_ _Happy birthday to youuuuu_ Zuwa tayi da ɗan gudu tana rungume shi cike da farin cikin da take ciki. _How old are you now?_ cewar Anty Khadija cikin ɗan waƙa. _She is 20yrs old now_ Amirah ta amsa. Duk ɗan dariya ƴan wurin sukayi suna kallon Jafar da DEENAH ɗin. Ɗagota yayi yana share mata hawayen yace "Why the cry?." "Actually you guys scared me" ta faɗa cikin ɗan dariya. Kallon ZEEYAD da yayi folding hannaye a gefe tayi tana ƙarasawa wurin sa tace "Thank you." Cike da ɗan mamaki yace "For what?." Wurin ta ƙarewa kallo wanda daga gani ba ƙaramin naira aka zuba masa ba tace "This is all your doing, isn't it?." Murmushi yayi yace "Actually, you deserve anything, more than this." Murmushi tayi tana sadda kai ƙasa. "It's getting late, muyi abinda ya kawo mu mu tafi, let's cut the cake" faɗin Jafar. Duk nufar inda ƙaton kyakkyawan cake ɗin yake sukayi, Jafar ne ya kallesu yace "Am eager naji cake ɗinnan cikin baki na." Murmushi duk sukayi kafin tace "Muje." Murmushi yayi ya mara mata baya, tsakiya duk suka sanƴa ta. Anty Khadija ce ta ɗau ƴar ƙaramar knife ɗin yanka cake ɗin tana miƙawa DEENAH. Amsa tayi cikin murmushi tana saita shi kan inda zata yanka, waƙar happy birthday ɗin suka cigaba da yi mata har ta yanka cake ɗin suna cigaba da tafa mata. Slice ta ɗauko tana sanƴawa Jafar a baki inda shima ya gutsuro da niyyar bata sai dai ya fuzge yana sanƴawa girlfriend ɗinsa tare da barin DEENAH da sakakken baki, juyowa yayi tare da ɗaga mata gira yace "Wife first." Turo baki tayi tana juyawa ta kalli ZEEYAD dake gefen ta. Murmushi yayi yace "Don't mind him" ya faɗa yana ɗaukar knife ɗin ya yanka ɗan madaidaicin slice, kallon ta yayi yace "Haa." Buɗe baki tayi nan ya sanƴa mata cake ɗin, yana goge cream ɗin da ya ɗan 6ata mata gefen baki da tissue, duk tafi suka sanƴa, DEENAH kuwa sosai zuciyar ta ke cike da tsantsar farin ciki marar misaltuwa. Wani yanka ta sake iyowa tana baiwa Anty Khadija a baki, kafin duk ƴan wurin ta bisu ta basu suma. Amirah ce tace "Toh shi ba zaki bashi bane?." Kallon ZEEYAD tayi duk sai taji babu daɗi, kafin a hankali tace "Baya ci." "Ohh" duk suka faɗa. Murmushi tayi tana samun wuri ta zauna tare da rufe idanu tace "Alright, am waiting for my presents." "Happiest birthday DEENAH, Allah ya ƙarawa rayuwar ki albarka" cewar budurwar Jafar tana miƙa mata wani box da akayi wrapping nashi. Buɗe idanu DEENAH tayi tana amsar gift ɗin cikin murmushi tace "Thank you so much Sweetheart." Anty Khadija ce ta ƙaraso ita ma tana miƙa mata nata gift ɗin tace "Happy birthday babyn Abyad, Allah yayi wa rayuwar ki albarka ya cika miki dukkanin burikan ki na alkhairi." "Aameen Yaa Rabb Bestest, thank you so very much" ta faɗa tana ajiye shi a gefe. Jafar ne ya ƙaraso shima da ƴar tashi madaidaiciyar gift ɗin yace "Barka da murnar zagayowar ranar haihuwar ki lil sis, i love you so much." Amsa tayi tare da faɗin "Wow, thank you Blood, i love you more" ta faɗa tana ajiye nashi shima. Kallon Amirah da ƙannen Ruqayyah girlfriend ɗin Jafar da sukayi tsaye suna bin kowa da ido tayi tace "Am waiting guys." Dariya ƴan biyun sukayi suna 6oye fuskokin su, Amirah dake ta rarraba idanu ne ta sanƴa hannu cikin Jakar ta tare da ciro wani ɗan ƙaramin kwali da akayi wrapping nasa tana zuwa ta miƙawa DEENAH. Amsa DEENAH tayi tana jujjuya ɗan ƙaramin kwalin a hannu kafin tace "Miye a ciki?." Ɗan ta6e baki Amirah tayi tace "Kibiya ce da mataji, dan Allah ki dinga kitsa kanki" tana faɗin haka tayi gefe abin ta. Duk dariya ƴan wurin suka sanƴa, kwafa DEENAH tayi tana ajiye box ɗin a gefe. Ƴan biyun ne suka ƙaraso gaban ta nan suka ce "Bamu da abinda zamu baki, sai wannan" suka faɗa kowanne na kai mata kiss a kumatu. "Aww" ta faɗa cike da jindaɗi tana rungume su tace "Thank you so much cuties." "Allah ya ƙarawa rayuwar ki albarka" suka faɗa. "Aameen Yaa Rabb" ta amsa musu cikin murmushi. Kallon ZEEYAD tayi cikin murmushi nan ya ƙaraso da bunch of flowers ɗin dake hannun sa tare da durƙushewa a gaban ta yace "Happy Birthday Wifey, i love you." Hannu tasa ta amshi fulawar cike da farin ciki tana kaiwa saitin hancin ta ta shinshina kafin tace "Thank you so much Abyad Darling." Murmushi yayi yace "This isn't gift ɗin da zanyi miki." "Really, where is it then?" ta faɗa tana kallon sa. Miƙewa tsaye yayi kafin yace da ita "Up." Tashi tayi nan ya ciro farar kyalle yana zagayawa ta bayan ta yayi blindfold ɗinta. Murmushi tayi tana ta6a kyallen tace "Why did you blindfolded me?." "You will see" ya faɗa yana riƙo hannun ta su fara tafiya. Duk mara musu baya su Jafar sukayi suma dan ganewa idanun su abinda zai bata. Waje suka fito still hannun sa jaye da ita inda yake controlling duk wani step nata dan ganin bata sami matsala wurin tafiyar tata ba. A haka har suka ƙarasa wani gu, nan yaja ya tsaya, duk waro idanu sukayi ganin abin dake gaban su. "Inalillahi" cewar Amirah cikin waro idanu, nan Anty Khadija tayi saurin gwa6e mata baki. Jafar ma baki ya sake cike da mamaki yana bin ZEEYAD ɗin da kallo. "Mun iso?" faɗin DEENAH ɗin dan kuwa ta ƙosa ya buɗe mata idanun dan ganin kyautar abinda zaiyi mata. "Yes babe" ya amsa mata cikin murmushi. "Alright, menene mu ganshi" ta faɗa tana miƙa masa hannun ta. Zuwa yayi ta bayan ta tare da sunce mata ɗaurin da yayi mata ɗin yana zagayowa ta gefen ta ya tsaya. Murmushi tayi idanun ta da takejin sunyi mata duhu a runtse tace "Na buɗe?." "Yeah." "Okayyy" ta faɗa tana buɗe idanun nata a hankali har ta gama ware su tarr. Side hug ya ɗan bata yace "Here is your gift baby." She was stunned for some moments as she stared at the car speechlessly inda kuma murmushin kan fuskar ta ya shiga gushewa. "W...wha...what is this?" ta faɗa still idanun ta kan baƙar *Toyota venza 2010* dake gaban ta. "It's your birthday gift" ya faɗa shima idanun sa kan motar. Shiru DEENAH tayi idanun ta na tara hawaye tace "This... this... why will you gift me such an expensive car?, i mean how much did you bought it?." "Yes please... this car is worth #7million, it's to expensive for DEENAH, kuma as a birthday gift" cewar Jafar yana kallon sa. Murmushi ZEEYAD yayi yace "No it's not expensive as far as she likes it." Lumshe idanu tayi hawayen fuskar ta na samun damar sauƙowa, she can't believe her eyes, wai yau ita aka yiwa kyautar mota as birthday gift, and yayi hakan ne just to make her happy. "You don't have to do this" ta faɗa cikin kuka. Kallon ta yayi yace "Why are you crying, you should be happy, idan ma baiyi miki bane then i will change it na saya miki wani wanda kike so" ya ƙarashe cikin share mata hawayen fuskar tata. Kallon sa take tace "I...bansan ta yadda zan fara gode maka ba." Murmushi yayi yace "You like it?." "I love it" ta faɗa cikin murmushi. "Well then you don't have to thank me, farin cikin ki is worth everything." Cike da murna ta rungume shi tana faɗin "Thank you so much." Murmushi yayi yana ɗan bubbuga bayan ta, nan ta ɗago tana kallon sa tace "I don't know what to repay you back." Cike da ɗan mamaki yace "Ofcourse you do." "Really, how?." Murmushi yayi yace "By marrying me." Rufe fuskar ta tayi tana murmushi. "So will you Marry me?." Shiru tayi tana kallon sa cikin murmushi kafin kuma tace "Maybe" tana gimtse fuska. "Congratulations lil sis" faɗin Jafar cikin murmushi. Zuwa tayi shima tana rungumar shi tace "Thank you." Duk congratulations sauran sukayi mata ta amsa musu cike da murna. "So i think we should get going dare nayi." "Yeah sure" cewar ZEEYAD. Key ɗin motar ya ciro yana miƙa wa Jafar yace "It will be safe a hannun ka, muje na baka documents ɗin." "Yes, Sire" ya faɗa suna jerawa tare. ********************** *3 DAYS AFTER* ________"Am not happy you're living" ta faɗa cikin turo baki gaba. Murmushi yayi yana kallon ta yace "Am not happy as well, but you know Grandma, she missed me and i missed her too." Murmushi tayi tace "Hakane, so now tell me, yaushe zaka sake dawowa?." "To do what exactly?" ya tambaye ta. "To see me" ta faɗa tana kallon sa. "No, i won't only come back just to see you, but to take you away with me." Murmushi tayi tace "And when is that?." "Maybe in the next two weeks." "2 weeks, but how can you Marry me in the next two weeks?." "Well you just wait and see." "Uhm, alright we will see then." Murmushi yayi yana buɗe motar sa ya shige. Sauƙe glasses ɗin motar tasa yayi yana kallon ta yace "I can't wait to have you as my wife baby." Hannu ta kai ta ɗan mari fuskar sa tace "Let's see then, ka rama Marin ka ranar auren, bye" tana faɗin haka ta juya ta koma cikin gida. Da kallo ya bita murmushi ɗauke akan fuskar sa yace "Sure zan rama" kafin ya tada motar tare da janta ya bar wurin. *GUDU, GUDU, SAURI, SAURI🚴🏽‍♀️🚴🏽‍♀️🚴🏽‍♀️* ______"Grandma i have never loved JALILAH, please don't force me to marry her." "But the girl loves you boy, why ba zaka tausaya mata ka haɗa da ita ɗin ka aura ba?." "Two wives at same time?, no i can't do that Grandma" ya faɗa yana samun wuri ya zauna. "Boy..." "Grandma, i feel bad for her, i know it's not easy wanda kakeso turns out to be akwai wata a ransa, but what can i do to help?, tayi haƙuri kawai." Zama Grandma tayi kusa dashi tana dafa kafaɗun sa tace "Ofcourse you can help boy, kai fah Namiji ne, zaka iya auren mata har huɗu, what is the big deal idan ka haɗa JALILAH da ita DEENAH ɗin ka aura, i know ba zaka sami wata matsala daga garesu ba, tunda they are all decent, think about the poor girl boy, ta kwallafa rai sosai akanka, baikamata ka watsa mata ƙasa a ido ba." "But Grandma..." "Listen Boy, ba zan tursasa maka auren JALILAH ba, but zan baka time kayi nazari akai ka gani, kaji?." Shiru yayi bai amsa mata ba, dan kuwa baya tunanin wannan karon ƙorafin Grandma ɗin zata kar6u a wurin sa, he only loves DEENAH, muddin ya kuskura ya amince da auren JALILAH then ba zata ta6a samun kanshi ba. "Kaje ka gun mahaifin naka, he must be waiting kaga tunɗazu ya aiko." Tashi yayi kawai yana ficewa. Ƙofar fadar aka buɗe masa ya shigo, kai tsaye wurin zaman mai Martaba ya nufa ganin bai fito bane, ya sanƴa shi nufar hanƴar Babban falon fadar dan zuwa ɗakin sa. Ganin su zaune akan dining suna karin kumallo ne ya sanƴa shi juyawa da niyyar komawa. "ZEEYAD?" cewar mai Martaba ɗin, hakan ya sanƴa shi ja ya tsaya. "Ka ƙaraso nan mana." Kallo ya ƙarewa ƴan rainin hankalin kan dining ɗin kafin kuma cikin tsukewar fuska ya ƙarasa wurin ba tare da yabi ta kan kowannen su da kallo ba. "Yes your Highness" ya faɗa bayan ya ƙarasa wurin. Cikin kulawa mai Martaba ya kallesa yace "It's been decades da muka zauna tare da niyyar cin abinci, come on please have a seat and have breakfast with me." "No, am full naci abinci a wurin Grandma." "You only consider your Grandma as your family isn't it?, it's alright banga laifin ka ba" faɗin mai Martaba ɗin cikin rashin jindaɗin maganar ZEEYAD ɗin. Tsayawa kallon sa ZEEYAD yayi kafin kuma yaja kujera ya zauna yana faɗin "Actually, you're also my family, you're my father, it's just that things were not as it was before." "Yeah and it's all my fault." "No please, stop blaming yourself for everything, let by-gone be by-gone" ya faɗa cikin dafa hannun mahaifin nasa. Murmushi kawai mai Martaba yayi yana kallon ɗan nasa. "I will dine with you someday" cewar ZEEYAD yana kallon sa. Kallon sauran yaran dake zaune a dining ɗin mai Martaba yayi yace "Seems like duk kuna buƙatar a dawo da old rules na cikin MASARAUTAR nan, and this is exactly abinda zai faru ɗin kenan, ZEEYAD here is your eldest brother and you must show him respect where ever you see him." Ɗagowa Ayaan yayi yace "But he should respect our mothers too, before he gain some respect from us." "Ayaan" cewar mai Martaba ɗin a tsawace. Tsaye Ayaan ya miƙe yana faɗin "Your Favorite boy here will never gain any respect from me, he should respect my Mom before na girmama shi." "Guards" cewar mai Martaba ɗin. Karasowa guards sukayi kafin yace dasu "Take him away." A fusace Sarauniya Hafeezah ta tashi tace "Hold it right there" kafin kuma ta juyo gun mai Martaba tana faɗin "You can't get your son arrested sabida ya faɗi abin dake ransa." "He should know how to respect his elders a duk inda ya gansu..." "There is nothing to be respected here, everyone knows yadda ka tsani yaron nan..." "That is because you cast a spell on me Hafeezah" faɗin mai Martaba cikin 6acin rai yana miƙewa tsaye kafin ya ɗaura da faɗin "Ina raga miki ne dalilin ƴaƴan dake tsakanin mu, and most especially because of my lovely innocent Son YAZEED, he would never be happy aduk sadda yaji na rabu da mahaifiyar sa, i know all your doings and how you made me hate my Son here duk sabida son zuciya irin naki, kada ki kuskura ki kai ni maƙura or else abin ba zai ta6a yi miki kyau ba" ya faɗa yana nuna ta da sandar hannun sa. Sosai idanun Sarauniya Hafeezah suka raina fata dan haka shiru tayi ba tare da ta iya cewa komai ba. Murmushin gefen baki Nazeerah ta saki tana tsakurar abincin gaban ta a hankali dan ma kar ta cinƴe drama bai ƙare ba kallo ya bar ta. Miƙewa ZEEYAD yayi kafin yace "Calm down Abhi, why don't you get some rest." Cike da 6acin ran da yake ciki yace "No, inaso a kira min manƴan ministoci na, i have an urgent meeting with them, it's time we put an end to things here, and it's time da yakamata a sauya salon mulkin wannan ƙasa zuwa wata tsarin daban, my son is back and now lokaci yayi da yakamata mulkin wannan ƙasa ta dawo hannun sa, ba sai na jira har rai yayi halin sa ba, and you Hafeezah get ready to sow what you reap, take the arrogant boy away and make sure kun hukunta shi ya gane kuskuren sa" yana faɗin haka ya baza alkyabar jikin sa yayi gaba tare da barin kowa da buɗaɗɗen ido da sakakken baki, musamman Sarauniya Hafeezah da takejin maganganun nasa tamkar a mafarki, ga kuma wani irin hajijiya da taji na neman ɗibar ta, wanda bata ma bi ta kan Ayaan dake ta faman kiran sunan ta ba yana son kwacewa daga hannun guards ɗin ba. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR....................✍🏽* [8/21, 9:58 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *045...* ________Duk jigum sukayi suna sake bin inda mai Martaba yabi da kallo, ZEEYAD da yaji maganar tayi masa banbarakwai saurin marawa mai Martaba baya yayi zuwa ɗakin sa. Zaune ya iske shi kan bed ya ƙure hoton Masoyiyar sa da idanu yana kallon. Shigowar ZEEYAD ne ya sanƴa shi ɗago da idanu yana kallon sa, kawar da kai yayi daga kallon ZEEYAD ɗin zuciyar sa babu daɗi. "Abhi?" ZEEYAD ya kira shi yana ƙarasawa kusa da ƙafar mahaifin nasa ya zauna. Kallon sa mai Martaba yakeyi kafin kuma ZEEYAD ɗin ya buɗi baki yace "Abhi sometimes we need to let go of our past domin ganin present dama kuma future ɗinmu yayi kyau, dukkanin wani abinda ya faru tsakani na da kai a baya let's forget it mu ɗau hakan a matsayin ƙaddara, you're my father and someone i will always be proud of, i realized that dukkanin wani abu da ka aikata a baya wasn't on your own doing, i know you will never treated me so different after Mom's demise muddin ba tilasta ka akayi ba, so stop thinking negative tare da tunanin cewa koh ban yafe maka bane, na yafe maka long ago am now your son wanda zaka iya juya shi and treated him like kowane ɗa a cikin gidan nan, wanda zaka ce masa bari ya bari, sannan kuma ka umurce shi, shi kuma zaiyi maka biyayya, Abhi let's change things between us mu gina sabuwar alaƙa, show me a fathers love that i have long been craving for, and nikuma zan mutunta ka tare da baka dukkanin girman ka a matsayin ka na mahaifi na" ya ƙarashe yana riƙo hannun mahaifin nasa cikin nashi ya damƙe. Sosai jikin mai Martaba yayi sanƴi yayin da kuma zuciyar sa ke cike da tsantsar farin ciki jin kalaman ɗan nasa inda hawayen farin ciki, tausayi dama kuma nadamar abubuwan da ya aikatawa ɗan nasa suka shiga gangaro masa. Rungume sa ZEEYAD yayi cikin patting bayan sa yace "It's alright Abhi, let's build a new world together." Ɗagosa mai Martaba yayi suna miƙewa tsaye cike da tsantsar ƙaunar da yake yiwa ɗan nasa yace "GOD bless you Son, haƙiƙa cike nake da kunƴa a yanzu, after all what i did to you, you decided to forgive me so soon, you will surely make a great King Son" ya faɗa yana sake rungume ɗan nasa cikin tsantsar farin cikin da yake ciki. Ɗagowa sukayi suna kallon juna nan ZEEYAD ya duƙar da kai yace "But..." shiru yayi bai iya iddawa ba. "Talk Son, faɗi dukkanin abin dake ranka." "Am not ready to be a King." Murmushi mai Martaba yayi yace "You don't have to be ready in order to be a King, ka sanƴawa ranka cewar dukkanin wani abu da zai shige maka gaba zaka iya dealing ɗinsa komin nauyin sa, sannan kuma ka kasance mai yawan addu'a addini da neman jagorar Ubangiji a duk wani abu da zaka sanƴa a gaba, ka kuma kasance mutum mai nutsuwa da sanin yakamata, ka kuma kasance mai adali da gaskiya, indai ka riƙe wadannan abubuwan then you're good to go Son, and am sure ka tara dukkanin wadannan abubuwan da na lissafa, kai matashi ne na tabbata zakayi shugaban ci mai kyau sannan kuma Al'umma zata soka, it's time that i step down, kada ka manta da cewa that i will always be there to guide you har zuwa ran da rai zaiyi halin sa and your Grandma is also here to support you, i know fargabar ba bai wuce ta ina zaka fara ba, do not worry Son we are here for you" ya ƙarashe cikin patting shoulders ɗin ZEEYAD ɗin. Shiru ZEEYAD yayi kafin yace "But i don't have any passion for ruling, i mean duk wani abu da yakamata ace Sarki ya tara ni banida wannan, ban iya faɗa da takobi ba, ban iya riding doki ba, and i...i don't even have a wife" ya ƙarashe cikin sunkuyar da kai. Murmushi mai Martaba yayi yace "Duk wannan abu mai sauƙi ne, zaka iya koyon takobi da tuƙa doki a ƙalilan lokaci, and besides ka tara dukkanin qualities da ake buƙata dan gane da Sarki, and a wife, da akwai yaran Abokai na Sarakuna ba zaka rasa wacce tayi maka a..." "No" ya katse mahaifin nasa kafin yace "Ina da wacce nakeso." "Masha Allah, tell me who she is, and ƴar ina ce?" ya faɗa yana kallon ɗan nasa. Cikin duƙar da kai ZEEYAD yace "I know ban ta6a sanar da kai wani abu dangane da rayuwar da nayi bayan na bar MASARAUTA ba, but the girl and her Family have done alot for me, itace mace ta Farko da ta fara nuna min ƙauna da kulawa bayan Ummie na so tanada matuƙar muhimmanci a zuciya ta and i respect her for that, and above all i love her..." "Just tell me where she is, nikuma nayi maka alƙawarin nemo maka auren ta cikin lokaci ƙalilan muddin hakan zai sanƴa ka farin ciki, labarin rayuwar da kayi bayan barin ka nan kuwa i know komin daren daɗewa zaka zo ka same ni sannan ka sanar dani dan kuwa ba zan tilasta maka abinda bakayi niyya ba, tell me Son, a ina ita wannan yarinƴar take?." "She is a Nigerian, and am afraid kada kace dole sai ƴar ƙasa ta zan aura." "Is she a Muslim?." Kai ya jinjina masa yace "Yeah she is, a pious one." Murmushi mai Martaba yayi yace "Then you've nothing to worry of Son, ba dai kanason ta ba, then you will Marry her, i will make a formal annoucement zanje dani da ƙalilan daga cikin ministoci na dan zuwa neman maka auren yarinƴar." Wani irin tsantsar farin ciki ne ya mamaye zuciyar ZEEYAD ɗin, rungume mahaifin nasa yayi yace "Thank you so much Abhi, you're the best." Ɗan dariyar manƴan ta mai Martaba yayi yana ɗan buga bayan ɗan nasa. Ɗagowa ZEEYAD yayi yace "Zanje na sanar wa Grandma" ya faɗa yana shirin ficewa mai Martaba ya kira sunan shi, dakatawa yayi yana kallom sa nan yace "Don't forget, daga gobe zaka fara koyon dukkanin wasu abubuwa da bakada masaniya a kai, so be ready." Kai ZEEYAD ya jinjina masa cikin murmushi yace "Yes Abhi" yana ficewa daga ɗakin. Murmushi mai Martaba yayi yana komawa ya zauna. *********************** __________Cike fadar take da manƴa-manƴan mutane wadanda kai tsaye za'a iya kiran su da na hannun damar mai Martaba wato su ne wadanda yake zantawa kafin ya yanke shawarar komai. Kowannen su sanƴe yake cikin shigar sa ta alfarma inda kowanne ke haƙimce kan kujerar sa wanda akalla zasu kai su ashirin da biyar. Shiru fadar ta ɗauka kafin wani dattijo daga cikin su ya miƙe tsaye, hannun sa riƙe da wani kundin littafi da alama dai irin litattafan nan ne na dah. Cikin gyarar murya ya fara magana kamar haka "Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'alah Wabarakatuhu" tsagaitawa yayi yayin da suke amsa sallamar sa kafin kuma ya cigaba da faɗin "Kamar yadda kuka sani, ni sunana Abdulbasid Ibn Omar shugaba kuma wakilin gidan tarihi na wannan MASARAUTA, kamar yadda mai Martaba sarki ABBAS ya umarta a yau za'a canza dukkanin wani ƙa'idoji da aka sani a dangane da wannan MASARAUTA sakamakon sabon mamulki da zata samu wato babban ɗa gun Sarki Abbas wanda aka fi sani da Yarima ZEEYAD, a yau zamu zanta daku mutanen amana kuma na hannun daman sarki dangane da wannan batu, sai dai kafin na kai ga lissafo dukkanin wasu sharuɗa dama kuma sabbin dokoki na wannan MASARAUTA ina so naji daga gareku idan akwai mai wata ingantacciyar shawara kan wannan batu, idan kuwa babu kai tsaye sai mu tafi ga abunda ya tara mu anan" ya faɗa yana mai bin mutanen cikin fadar da kallo. Ganin babu wanda yake da ta cewa ne a cikin su ya sanƴa shi cigaba da faɗin "Masha Allah, toh kamar yadda dai kuka sani wannan daddaɗiyar MASARAUTAR tamu wanda aƙalla zata kai shekaru ɗari biyu da tamanin da kafuwa sannan kuma Sarakuna daban-daban suka mulke ta har izuwa kan Sarkin mu na wannan zamani wato Sarki Abbas muna fata tare da addu'ar wannan MASARAUTA zata cigaba tafiya tare da ginuwa kan gaskiya da adalci kamar yadda ya samo asali daga Kakannin mu da suka mulke ta suka shuɗe, dayawa daga cikin ƙa'idojin wannan MASARAUTA ta dah sun shuɗe sakamakon yanayin da zamani yazo mana dashi, sai dai a yau kamar yadda mai Martaba kuma Adalin shugaban mu sarki Abbas ya umarta, tsarin wannan MASARAUTA zata canza ne izuwa ta Kakan sa Marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM" dakatawa yayi sakamakon murmuring ɗin mutane dake tashi ƙasa-ƙasa. Da ɗan ƙarfi yayi gyaran murya kafin kuma yayi shiru yana kallon su duka, kallon mai Martaba dake kishingiɗe kan Throne ɗinsa yayi kai ya jinjina masa alamar ya cigaba, nan ya cigaba da faɗin "Dayawa daga cikin mu muna ƴan ƙanana Marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM yayi mulkin sa, nasan kuma da akwai abubuwan da wasu daga cikin mu zasu iya tunatowa lokacin da yayi mulki..." Cikin ɗaya daga cikin ministocin ne ya katse shi da faɗin "Kowa yasan lokacin da Marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM yayi mulki, mulkin da yayi cike take da ɗumbin tsanani da takura, tabbas iyayen mu sun bamu labarin lokacin da yayi mulki, dawo da irin tsarin mulkin sa a yanzu tamkar takurawa rayuwar Al'umma ne duba da yadda duniyar ta canza a yanzu dama kuma yanayin rayuwar da ake a yanzu sam bashida wani kamanceceniya da ta dah, mutanen mu na yanzu sun kasance masu rauni ne, bakomai ne zasu iya ɗauka da jura ba muddin aka dawo da iriyar mulkin Marigayi Sarki ZAYYAD." "Tabbas kayi gaskiya Hisham, ba abu ne mai sauƙi ga Al'ummar mu ba, dukda munsan cewa ba'a yi Adalin sarki kamar sa ba, sai dai fah mu sani ya Al'ummar mu zasu ji da wannan sabuwar salon mulkin da basu ta6a fuskantar ta ba?." "A hankali zasu saba dashi, you've made the right decision Abhi, mulki irin na Marigayi Sarki ZAYYAD shine ya kamaci mutanen mu na yanzu, be it hakan zai zamto takura a garesu koh jindaɗi that doesn't count, muddin mutum ya yarda da kansa mai gaskiya ne sannan yana aikata alkhairi then baikamata hankalin sa ya tashi dan yaji an ambaci mulki irin ta Marigayi ba, there is no need aji shawarar wani daga cikin ku, the decision is been concluded, i will rule like my great-grandfather and no one dares to stop it from happening" ya ƙarashe cikin dafa teburin dake gaban sa. Duk speechless suka tsaya kallon ZEEYAD ɗin wanda shigowar sa kenan yaji suna maganar. "Am totally against this, there is no way da zamu yarda da wannan juyin mulkin and besides, ZEEYAD is too Young to rule us, i guess a al'adar wannan masarautar sai yaro ya kai shekaru talatin da biyar kafin a miƙa masa ragamar mulki, why then za'a canza tsarin komai haka kurum ba tare da dalilin komai ba?" cewar wani daga cikin ministocin cikin miƙewa tsaye. "Abdulrashid yayi gaskiya, there is certain age da idan mutum ya kai ake basa ragamar mulki, haka kuma bamu yarda da dawo da tsarin mulkin Marigayi ba, a kullum cigaba ake nema ba ci baya ba, dawo da tsarin mulki irin na Marigayi tamkar faɗuwar wannan MASARAUTAR ne, yakamata ka sake nazari kan wannan batu Mai Martaba." Ɗaga sandar sa mai Martaba yayi alamun yana son kowa yayi shiru kafin kuma ya fara magana cikin kakkausar murya "Ban kira ku nan bane dan neman shawarar ku goyon bayan ku, ku kanku kunsan bana jaye dukkanin wani abu da na yanke, ZEEYAD here shine wanda zai zamto shugaba a gareku, be it you like it or not, duk wani wanda yaga hakan baiyi masa ba zai iya zame kansa daga cikin membobin wannan fadar, i have made up my mind and so be it." Shiru fadar ta ɗauka kafin ɗaya daga cikin ministocin ya tashi tsaye yana faɗin "There is no way ƙaramin yaro zai dinga umurtar mu, so am stepping down muddin wannan yaron ne zai zamto wanda zai mulke mu." "Then so be it, anyone else willing to step down?" faɗin ZEEYAD yana bin kowannen su da kallo. Biyu daga ciki ne suka tashi tsaye, murmushin gefen baki ya saki kafin yace "Well then this kingdom will do it's great without you, who else?." Duk miris sauran sukayi basu tashi ba, dan kuwa sunsan wannan MASARAUTAR ita kaɗai ce hope ɗinsu, muddin sukayi kuskuren barin wata muƙami da suke dashi a cikin ta toh tabbas sun gama ne. Jan sandar su sukayi duka sukayi hanƴar ficewa, ɗaya ne ya tsaya daga cikin su yana kallon ZEEYAD kafin yace "I just hope ka iya mulkar wannan ƙasar da kyau young Boy, sabida babu abinda nake hangowa sai faɗuwar ta warwas" yana faɗin haka ya wuce yana baza alkyabar jikin sa tamkar zai tashi sama. Kallon sauran dake zaune Wakilin gidan Tarihi yayi kafin yace "Shin akwai mai magana?." "Ka lissafo musu dokokin" cewar mai Martaba. Cike da girmamawa ya duƙa kafin yayi gyaran murya yace "Sorry for the inconveniences, kamar yadda mai Martaba sarki ya umarta ga sabbin dokokin wannan MASARAUTA kamar haka." "Doka ta Farko zamu ɗauko ta ne daga kan matsalar tsaro, matsalar rashin tsaro kowa ya sani babu ita a lokacin mulkin marigayi, a yanzu mutane dayawa, talakawa, matafiya, makiyaya, manoma, matsinta, ƴan kasuwa da dai sauran su na ƙorafi akan fama da rashin tsaro da suke a wuraren biyan buƙatar su da samar wa kansu da iyalan su abinci, dan haka matsalar rashin tsaro a wancan lokacin babu ita sakamakon zuba jami'an tsaro ƙarfafa wadanda akayi musu horo mai kyau a kowanne lungu da saƙo na, tare da ajiye na'urorin da zasuyi alarming ɗin mutane aduk inda wani mummunan abu ke gab da afkuwa, wanda a wancan lokacin ana amfani ne da ƙararrawa mai ƙarfin ƙara wacce zatayi alarming dukkanin wasu sojoji dake kusa da wannan wuri dan kai taimakon gaggawa, wanda kuwa aka kama shi da aikata laifi wurin kwatar haƙƙin mutane, wanda kai tsaye za'a iya kira da sata, hukuncin sa shine za'a yanke masa hannuwa duka biyu tare da yi masa horo mai tsanani, wannan hukunci yayi tasiri sosai a wancan lokacin domin kuwa an samu raguwar rashin matsalar tsaro sosai da sosai dan kuwa cikin kaso dari bai wuci kaso goma bane wanda suma sun fi aikata hakan ne ta hanƴar amfani da asiri koh wani abu makamancin shi, wanda shima hukuncin amfani da tsafi a wancan lokacin shine kisa, duk wanda aka kama yayi amfani da tsafi koh asiri wurin cutar da wani Marigayi ya bada umarnin a yanke masa hukunci ta hanƴar rataye sa har lahira, domin hakan ya zamto izina ga ƴan baya masu aikata shirka a doron ƙasa." Idanu kawai ZEEYAD ya zuba masa yana kallo kafin ya cigaba da faɗin "Doka ta biyu kuwa itace Tsaftace muhalli, ya halarta ga duk wani ɗan ƙasa be it cikin MASARAUTA yake koh wajen ta, be it cikin garin CAIRO yake koh wajen ta, duk wani wanda aka kama koh da ƙofar gidan sa ce da datti toh tabbas za'a hukunta shi ta hanƴar yi masa bulala zafafa kwaya hamsin kacal, idan ya kuma ƙarawa aka kama sa a karo na biyu za'a yi masa bulala sittin har izuwa ranar da zai gyara ya daina muddin kuma bai daina ba toh kuwa kullum goma zata dinga ƙaruwa kan wannan hamsin ɗinnan, tsafta na daga cikin koyarwar Manzon Allah haka kuma cikon imani ce, Marigayi bai lamunce wa rashin tsafta ba a ƙasar sa komin ƙanƙantar ta." Doka ta Uku itace, Girmama juna musamman ma mata, sau tari rahoto na zuwan wa marigayi akan Maza dake harassing mata, koh ci musu mutunci da zarafi a idanun Jama'a kokuwa dai wani abu makamancin haka, duk wanda aka kama da wannan laifin hukuncin sa shine zaman gidan kaso na watanni shida tare aikin horo mai wahala dan gane kuren sa tare da fahimtar cewa mata na da matuƙar daraja dan haka girmama su ya zame dole ga jama'a, Doka ta huɗu itace Fyaɗe, kowa ya san fyaɗe mummunar laifi ce a musulunci, dan haka duk wani wanda aka kama sa da laifin fyaɗe hukuncin sa shine za'a yanke masa mazaƙuta ta hanƴar dandaƙa, koh da kuwa ya kasance ɗan cikin gidan Masarautar kanta ne, dan kuwa Marigayi baya nuna bambanci tsakanin bayin sa da mutanen cikin gidan sa, Doka ta biyar itace ya zama wajibi ne a baiwa kowane mahaluƙi damar aiwatar da abinda yaso muddin ba wai ta sa6awa koyarwar addinin musulunci bane, kowane mahaluƙi koh da kuwa bawa koh baiwa ce suna da freedom na kansu, tunda suma mutane ne ba wai injina ba, ya zama dole idan lokacin hutu yayi a bar su su hutu sannan a daina tsanan ta musu aiki musamman ma bayi mata, Doka ta shida ita ce kamar yadda na faɗa, duk wani wanda aka kama da aikin asiri koh tsafi toh lallai hukuncin sa shine kisa ta hanƴar rataya..." Magana zai sake ZEEYAD yayi saurin katse shi da faɗin "It's Okay, zan kar6i kundin naje na karanta dukkanin wata doka da kaina." Duƙar da kai yayi cike da girmama kafin ya kalli mai Martaba yace "Your Highness, kaɗan daga cikin dokokin kenan, Yarima yace zai idda karanta sauran da kansa." "Tunda yace haka, hakan za'ayi zaka iya basa kundin dama kuma dukkanin wasu litattafai masu muhimmanci." Cike da girmama ya amsa yace "Insha Allah, ranka ya daɗe" ya faɗa yana samun wuri ya zauna. Gyaran murya sarki yayi kafin yace "Dafatan dukkanin ku kunji wadannan dokoki sannan kunyi na'am dashi?." "Insha Allah Ranka ya daɗe" duk suka amsa. "Masha Allah" ya faɗa a hankali kafin ya kalli inda ZEEYAD ke tsaye yace "A Man needs a Woman to support him in other to achieve something great in life, dan haka dani da kai Liman, Waziri dama kuma likitan gargajiya, ku shirya zuwa jibi zamu je neman wa Yarima ZEEYAD aure a wata ƙasar daban, dan haka ku tabbatar kun shirya duk wani abu da za'a buƙata wurin zuwa neman aure, za'a gudanar da komai ne tamkar yadda ake zuwa tambayar aure a wannan ƙasa." "Masha Allah" shine abinda ya karaɗe ilahirin fadar. ZEEYAD bai san sadda ya saki wani irin ƙayataccen murmushi ba yana duƙar da kai. Tsinkayo muryar mai Martaba yayi yana faɗin "Ku barmu haka nan, inason zantawa da dukkanin Family na, kowa da kowa da muka haɗa alaƙa ta jini dasu ina buƙatar su anan hatta ƴaƴa da jikokin su kada a bar kowa." Duk miƙewa sukayi tsaye suna gyara zaman alkyabar jikin su, cike da girmama wa sukayi masa sallama suna mai ficewa daga fadar. Miƙewa tsaye mai Martaba yayi yana sauƙowa daga kan kujerar sa, ƙarasa wurin sa ZEEYAD yayi yana riƙo sa, kallon ɗan nasa yayi yace "I can see how happy you're Son, da alama kanason yarinƴar sosai, how lucky she is da samun kamar ka." Murmushi yayi kafin yace "Am so proud of you" yana rungume mahaifin nasa. Ɗan bubbuga bayan sa mai Martaba yayi kafin ya ɗago sa yace "Bari na wuce ɗaki na ɗan kwanta." "But... kace kana neman kowane family member." "Yeah, ban manta ba, kafin su iso ni zanyi baccin na tashi." "Alright, muje na raka ka" ya faɗa cikin hannayen sa kan kafaɗun mahaifin nasa. *TALLAH* Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻 _*infection*_ Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI* _07084653262_ *************************** *CIGABA...* ________Zaune suke kowa jugum, daga mai naɗaɗɗen baki, sai mai dogon baki, kowannen su zaune yake gefe ɗaya da iyalan sa haka kuma kowanne a cikin su da ka ganshi zaka hango iriyar tsantsar rawar kan dake tattare dasu musamman ma ga samarin dake wannan wurin. Abdulhakeem na hango da family ɗinsa, kallo ɗaya zakayi wa Sooraj ka hango iriyar 6acin ran da yake ciki wanda dai da alama ba'a daɗe da fitowa dashi daga kullen da akayi masa ba, babu abinda yake sai wani irin cika yana batsewa wannan daga gani ƙiris yake a ta6a sa ya fashe. JALILAH kuwa zaune take kusa da mahaifiyar ta, haka kurum takejin gaban ta na faɗuwa na tara su anan da mai Martaba yayi. Ayaan da Rahinah suma duk zaune suke kusa da mahaifiyar su, kallo daya zakayi wa Ayaan ɗin shima ka gane a wuya yake. Sarauniya Nazeerah ita ma wasu ƴan mata kyawawa biyu ne kusa da ita, wanda dai da alamu ƴaƴan ta ne, daga gefe kuma Yara Uku ne maza biyu sai mace ɗaya wanda dai da alamu Jikokin Sarauniya Nazeerah ne. Naseeba kuwa zaune tayi ita kaɗai yayin da kowane motsin ZEEYAD idanun ta na akan sa tamkar ta ɗauke sa ta cinƴe. Grandma na hango a gefe haƙimce akan kujera ita ma. Sai kuma wasu wadanda bansan dasu koh su wanene ba wanda dai da alamu suma Family ne. Mai Martaba dake zaune gefe da gefen sa YAZEED da ZEEYAD ne yayi gyaran murya tare da karanto addu'o'i kafin ya ɗaura da faɗin "Na san zakuyi mamakin tara ku anan da nayi duka, we're all family here, idan akace Family ana nufin an zama ɗaya babu wani bambanci koh warayya, sannan ansan Family da haɗin kai dama kuma kasancewa da juna a dukkanin wasu al'amura, ba sai na tsaya dogon surutu ba zan wuce kai tsaye ne ga abinda ya sanƴa ni tara ku duka anan wurin, Yarima ZEEYAD ɗana ne haka kuma gudan jini na ne shi, kamar yadda na zanta da dukkanin ministoci na yau suka shaida ina son kuma ku shaida cewa daga yau Ni Sarki Abbas Ibn Hakim na naɗa Yarima ZEEYAD a matsayin magaji na sannan kuma future King na wannan MASARAUTA..." Abdulhakeem ji yayi kamar ya wantsilo daga kan kujerar da yake da jin abinda mai Martaba ya furta wanda baisan sadda ma ya buɗe idanun sa dake runtse ya saki baki yana Kallon mai Martaba ɗin ba. Sarauniya Hafeezah ji tayi kanta yayi wani irin gudun fanka wanda ya sanƴa ta ganin mutanen wurin bibbiyu na wasu ƴan lokuta zuciyar ta na mugun bugu da tafarfasa kamar zai wantsalo waje. Kallon ZEEYAD YAZEED yayi tare da sakar masa murmushi yana yi masa alamun Kudos da yatsar sa, murmushi shima ZEEYAD ɗin ya maida masa yanajin ƙaunar ɗan uwan nasa sosai cikin zuciyar sa. Grandma ji tayi wani irin farin ciki ya lullu6e ta, jin Boy ɗinta ya kusa zama sarki, hawayen farin ciki ta share, sai dai gefe guda na zuciyar ta na matuƙar tsoron kasancewar sa sarki ɗin wanda batasan dalilin hakan ba. JALILAH da mahaifiyar tama murmushi suka saki sa6anin Sooraj dama kuma sauran mutanen dake cikin falon gaba ɗaya. "A King?" cewar Abdulhakeem yana kallon mai Martaba ɗin. Ba tare da mai Martaba ya amsa shi ba ya cigaba da faɗin "Sannan zai gudanar da mulkin sa ne ƙarƙashin dokokin tsohon Sarki wato Kakana marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM." Abdulhakeem bai san sadda ya miƙe tsaye daga zaunen da yake ba, yana bin mai Martaba da kallo, a hankali ya furta "Sarki Zayyad?." "Abdulhakeem, ka sami wuri ka zauna ban gama ba tukun." "This is totally against the law of this Kingdom your Highness, ba zaiyiwu ZEEYAD ya mulke mu ba har sai ya kai shekaru talatin da biyar da haihuwa" cewar ɗaya daga cikin family members ɗin. Ba tare da mai Martaba ya kallesa ba yace "Bakomai ne sai anbi tsarin doka ba, wasu lokutan wasu abubuwan kama wa yake ba tare da ka shirya musu ba, so am stepping down and ZEEYAD will be the King." "This can't be possible, indai har sauƙa ɗin kakeson yi why not ba zaka bani matsayin sarkin ba, tunda har ni ƙani ne a gareka sabida ɗan ka bai kai shekarun zama sarki ba tukun" faɗin Abdulhakeem cikin 6acin ran da ta fara zuwan masa. "I said sit, Abdulhakeem" cewar mai Martaba. Zama yayi zuciyar sa tamkar ana balbala masa ruwan zafi cikin ta. "ZEEYAD will be the King immediately bayan an ɗaura masa aure da wacce yakeso." JALILAH ji tayi zuciyar ta ta tsinke, kallon inda ZEEYAD ke zaune tayi taga ma hankalin sa ba'a kanta yake ba. Kallon ta mahaifiyar ta tayi tare da yin murmishi a hankali tace "Don't panic dear am sure kece zaki zamto Sarauniyar wannan MASARAUTA tunda har yana sonki. Murmushin yaƙe kawai JALILAH tayi ba tare da ta iya cewa komi ba. "And kaima YAZEED na san ba zaka rasa wacce kakeso ba, ka faɗi koma wacece idan yaso sai a haɗa bikin ka da na ɗan uwan naka ayi." Satar kallon mahaifiyar sa YAZEED yayi wacce gabaɗaya hankalin ta baya jikin ta, zai buɗi baki yayi magana Grandma tayi caraff tace "Ofcourse, yana da wacce yakeso ba kowa bace illa JALILAH" Ta ƙarashe cikin murmushin yaƙe. Duk kallon ta sukayi daga ZEEYAD, YAZEED har JALILAH ɗin cike da mamaki. Murmushi mai Martaba yayi yace "Masha Allah, hakan yayi matuƙar kyau, nan zuwa makonni biyu masu zuwa za'a ɗaura auren nasu duka, ku kuma ku hau dukkanin wasu shirye-shiryen da ya dace domin tar6ar surukan naku." Murmushin farin ciki Grandma tayi ba tare da ta kula kallon da su ZEEYAD ke bin ta dashi har yanzun ba. "Wannan shine dalilin da ya sanƴa ni tara ku anan duka, zaku iya tafiya domin kuwa ina buƙatar hutu." *********************** "Grandma what have you done?, YAZEED bai ce miki yanason JALILAH ba." Murmushi Grandma tayi tace "Ina matuƙar ƙaunar yarinƴar nan JALILAH, wacce mahaifiyar sa ke son haɗa sa da ita sam ba ƴar gidan mutunci bace ba, kaga kuwa koh da ace ya aure su su biyu ɗin na tabbata ba zai wofantar da JALILAH ba koh dan kyawawan halayyar ta ma." Sosai ZEEYAD ya cika da mamakin ta, tsuke bakin sa yayi kawai tare da yin shiru nan tace "Ka kuwa sanar da Ummien DEENAH zasuyi baƙi jibi?." Kai ya girgiza mata alamun a'a, nan tace "Toh mai kake jira ne, maza ka ɗau waya ka sanar dasu, koh da yike ma ka bar wannan a hannu na ni yakamata na sanar dasu wannan kyakkyawar labarin" ta ƙarashe cikin murmushi kafin ta fara dube-dube tana faɗin "Ina kuma wayar tawa tayi ne?." Ficewa kawai ZEEYAD yayi ba tare da ya sake bin ta kanta ba, sosai yakejin babu daɗi wa JALILAH but ya ya iya, muddin ya yarda ya aure ta then ba zai wani bata isasshen kulawa kamar yadda zai baiwa DEENAH ba, da wannan tunanin ya ƙarasa part ɗinsa. ******************* "Ummie can you imagine, ZEEYAD a matsayin sarki, isn't that odd?." Shiru Sarauniya Hafeezah wacce tun maganar sarki ta kasa furta komai kamar wacce aka ɗauke mata ji da maganar ta tayi tana sauraron Ayaan ɗin. "Ummie you've to do something akan hakan, why ina magana tunɗazu kuma kinyi min shiru i hate that, and i thought kince Akhi ƴar wurin aminiyar ki zai aura why kuma that Old hag zata kawo maganar wata aba wai Jalilah like tana da wani iko akan sa, after all she is nothing a cikin MASARAUTAR nan, i wonder why take raye har yanzu" ya ƙarashe a hankali yana yatsine fuska. "Ummie?" ya sake faɗa. "What kake tunanin zata ce, she have nothing to say" cewar YAZEED da shigowar sa kenan. Sarauniya Hafeezah kamar jiran shigowar sa take, dan haka kansa tayi a matuƙar haukace tana ɗebe sa da wani irin kyawawan maruka jere kafin ta cakumo kwalar sa cikin azababbiyar 6acin ran da take ciki ta fara faɗin......... _Ayiriri casss shagali, ZEEYAD fans kuzo mu cashe😂😂💃🏽💃🏽💃🏽, Yanzu dai kafin nace komai wacece zata je cikin gari ta yanko mana Ankon aure?, dan kuwa ba za'a yi babu mu ba, abu namu maganin a kwa6e mu💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽_ *YAWAN COMMENT, YAWAN POSTING* *MHIZZ JIDDHERR................✍🏽* [8/23, 10:40 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *Jinjina ta ban girma gareku my best Commenters😍* *Sadysglam🌹* *Mrs Nuruddeen🌷* *Mrs Kabeer🌺* *Ice♥️😂* *Lateefat😍❤️* *Fatima Bet🥰❤️* *Ummu Muhseenah🥰* *Queen Hafsy❣️* *Haseenerh💞* *Mom Misrah😍* *Ammy❤‍🩹* *Nana Ruqayyah💕* *Deejarmerh*💝 *Rafi'at Darajat*💖 *Mum Intisar*💗 *KHADIJA*😍😍 *Asiya Abdulkhadir*🤎 *Meenorrhh❣️* *Mrs H💛* *Beebarh♥️* *Khadija Usman💚* _Dama dai wadanda banyi mention ɗinsu ba, haƙiƙa ƙaunar ku ta daban ce a cikin zuciya ta, naga comments naku duka kuma alhamdulillah sun nishaɗantar dani sosai, Allah ya dawwamar daku cikin farin ciki na har abada Habibties🤲🏽🥰_ *046...* _*NOT EDITED*_ ________"You are so happy aren't you, you're happy that my plans are backfired aren't you, you're happy for that boy isn't it?, you chose to hurt your mother and make some random boy happy, i wonder if you're even my son, koh kaɗan baka gaji arziki daga gareni ba, i may say that i regret giving birth to you, menene amfanin haifar yaron da ba zai iya sanƴa ka farin ciki ba, ka haɗemin kai da wadancan banzan mutanen da koh kaɗan basu da daraja, all because of you burin da naci alwashin cikawa shekaru da shekaru ya ruguje, giving birth to you is the worst thing da na ta6a fuskanta da nasan haka zaka bani kunƴa ka kuma watsa min ƙasa a ido da babu abinda zai hanani toshe hancin ka ka mutu kawai a jariri, and let me make one thing clear to you, babu kai babu auren JALILAH muddin ina raye koh da kuwa wancan munafukin mahaifin naka ya tilasta ka toh babu abinda zai hana ka haɗa dukkanin su biyu ka aura, and i swear YAZEED... you will regret watsa min ƙasa a ido da kayi" ta ƙarashe cikin tunkuɗa shi baya tana wani irin huci mai cike da 6acin rai da haɗi da tafarfasar da zuciyar ta keyi. Sosai YAZEED yaji tamkar ya mutu a wannan wurin, sam baiga amfanin rayuwar sa da wannan matar a matsayin mahaifiyar sa ba, babu komai a zuciyar ta sai sharri, zuciyar sa zafi takeyi masa fiye da tunanin mutum, sam babu sukuni tattare da zuciyar sa, kullum cikin fargabar hali irin na mahaifiyar sa yake, baisan yaushe ne zata canza halayen ta ba, ance mata sunfi yawa a wuta tabbas baya cire ran mahaifiyar sa na ɗaya daga ciki, he hate her completely sabida munanan halayen ta. Juyawa yayi zai fice daga ɗakin tayi saurin dakatar dashi da faɗin "Hold it right there, kaje ka sami mahaifin ka ka sanar dashi da akwai wacce kakeso ba ƴar wurin Abdulhakeem ba, ƙinyin hakan babu abinda zai ja maka sai tsinuwa ta and that girl JALILAH i will make sure i ruin her life forever muddin ka kuskura ka sake aka ɗaura maka aure da ita, and that Old Hag nayi alƙawarin koya mata hankali soon, who is she da har take tunanin yanke wani hukunci cikin rayuwar ka, kayi abinda na umurce ka, ƙin yin hakan dai-dai yake da 6acin ran kowa a wannan MASARAUTAR, get out of my sight." Ficewa yayi ba tare da ya tanka mata ba. ********************* _______"I thought cemin kikayi the king to be zaki aura, yaushe kuma kika koma kan ɗan uwan sa?" cewar Abdulhakeem yana kallon JALILAH dake durƙushe a gaban sa tana kuka. "Abhi bansan ya akayi hakan ba, ni babu komai tsakani na da YAZEED" ta faɗa cikin kuka. Dariya Abdulhakeem yayi yana kallon Sooraj dake zaune cikin kujerun alfarmar da ya ƙawata falon nasu. "Abhi daga ita har YAZEED ɗin babu wanda yakeson juna, dan haka hukuncin ta shine ka yarda a aura mata shi let her suffer tamkar yadda tasa wancan ZEEYAD ɗin ya sanƴa a rufe ni for almost 2months a jail, sakarya kawai" cewar Sooraj cikin hargowa kamar ya ɗauke ta da ball. "Well hakan za'a yi, tunda chan ba son auren nata da wannan marar mutuncin yaron nake ba, but yanzu kin shigo hannu dan kuwa Hafeezah kaɗai ta isheki magani a wannan gidan, da akwai ƴaƴan Sarakuna dayawa da suka nuna interest akanki amma haka kika rufe ido kika ƙi amince musu yayin da nikuma kika watsa min ƙasa a idanu, kika kuma zubar min da mutunci kika ƙeƙashe dake da mahaifiyar ki akan sai ZEEYAD kike so, gashi nan ai wanda kika tsaya jira tsawon shekaru ɗin ya watsa miki ƙasa a ido zai auri wata ba ke ba, na tabbata Kakar sa na ƙaunar ki yasa ta haɗa ki da YAZEED da kuwa haka zaki gama tsofewa a cikin gidan babu aure, kinyi wasting shekaru biyar cikin rayuwar ki waiting for wanda ba zai ta6a sonki ba, na tabbata cikin shekarun da haƙuri kikayi kikayi auren ki da yanzu muna da jikoki, ga kuma arziki da zamu ci mu more, but kin watsa min ƙasa a idanu tare da maida ni ƙaramin mutum a idanun mutanen da suke ganin girma na, koh dan wannan abinda kika aikata min ma ba zai sanƴa na bar ki ki cika burin ki ba, marar mutuncin banza da wofi." Ita dai JALILAH sosai take kuka da jin abinda mahaifin nata ke faɗa mata, bata ta6a tsanmanin ZEEYAD zai watsa mata ƙasa a ido ya auri wata bayan ita ba, sam bata ƙi ta zamo matar sa ta biyu ba muddin zai aure ta ya kuma nuna mata ƴar kulawar da yake ɗan nuna mata a baya. Tashi tayi da gudu tana ficewa daga gidan nasu dan kuwa zaman ta anan babu abinda zai ƙara mata sai damuwa da baƙin ciki sabida duk babu mai nuna damuwa koh kulawar sa a gareta bale su kwantar mata da hankali. Mugun kallo Abdulhakeem ya watsawa Matar sa dake tsaye zuciya babu daɗi tana kallon su nan yace "What are you staring at, faɗa zakiyi min koh duka na zakiyi sabida na ta6a ƴarki?." Bata tanka masa ba ta juya fusace ta koma ɗakin ta. *********************** ______"Wace iriyar maganar banza ne wannan, i have already annouced batun auren ka da ƴar wurin Abdulhakeem, dan haka babu abinda zai sanƴa ni janƴewa, kai kanka kasan bana magana biyu, batun auren ka da ita kuma babu janƴewa, ita kuma yarinƴar da kacemin kana son nata za6i ya rage gareka either ka haɗa su su biyu kokuma ka kyale ta, but aure da kai da Jalilah babu fashi." Tunda mai Martaba ya fara magana kan YAZEED ke duƙe a ƙasa, sam mahaifiyar sa ta hana rayuwar sa sukuni, ta wargaza masa tunani da farin ciki, abinda ta damu dashi shine kawai ta ganta cikin farin ciki, bata damu da feelings ɗin wasu ba, gashi yanzu tana neman jefa rayuwar sa cikin sarƙaƙiya, bashi da wani za6i da ya wuce ya amincewa auren ƴar wurin aminiyar ta koh dan kada Jalilah ta shiga ƙunci da ƙiyayyar da zata ke nuna mata. "Abhi... na amince zan aure su su duka biyu, and i promise to do my best wurin kwatanta adalci a tsakanin su." Shiru mai Martaba yayi yana kallon YAZEED ɗin da har yanzu bai ɗago ba, cikin kwantar da murya yace "Tell me Son, Hafeezah ce ta tilasta maka auren yarinƴar koh ba haka ba, kai kuma ƴar wurin Abdulhakeem kakeso ita kuma Hafeezah bata ƙaunar ta da kai, hakan ya sanƴa ta tilasta maka wurin auren ƴar aminiyar ta." A hankali YAZEED ya jinjina masa kai. "Tell me, mai tace zatayi maka muddin baka auri ƴar wurin aminiyar tata ba?." Shiru YAZEED yayi ya kasa basa amsa, ajiyar zuciya mai Martaba ya sauƙe yana mai mamakin hali irin na Hafeezah, koh ba'a ce dashi komai ba yasan ta tilastawa ɗan nata tare da ɗaukan masa alwashin wani abu muddin baiyi abinda tace ba. A hankali ya furta "Alright, you will Marry them all, ka cika alƙawarin ka na ganin cewa ka kwatanta adalci a tsakanin nasu, yin hakan zai sanƴa Allah ya taimake ka ya kuma kawo maka sassauci a rayuwa, kayi ƙoƙarin ganin ka rabu da mahaifiyar ka lafiya wurin yin abunda ta umurce ka muddin ba wai ya sa6awa doka da addini bane." Kai ya jinjina cikin raunanniyar muryar sa yace "Insha Allah Abhi." "Kaje ka kira wo ɗan uwanka, da akwai abubuwan da nakeson tattaunawa daku yanzu." Miƙewa YAZEED yayi daga zaunen da yake cikin girmamawa ya amsa mai Martaba kafin ya fice daga fadar. ************************** *WASHE GARI* _______Zaune DEENAH take jugum, tunda taji labarin dangin ZEEYAD na hanƴar zuwa tambayar hand in marriage ɗinta take jin abin kamar almara, she can't believe, dah ace shi ya faɗa musu ba Grandma ba dah ba zata ta6a yarda ba, mamaki take why yake cikin eager ɗin mallakar ta da wuri haka. Shigowar Jafar ɗakin ya sanƴa ta ɗagowa tana kallon sa har ya ƙaraso kusa da ita ya zauna. Murmushi yayi mata kafin yace "I thought zan zo na same ki cikin farin ciki, coz mafarkin ki ya kusa zama gaskiya, atlast ZEEYAD is gonna be your Husband, no more cries, no more being depressed, no more over-thinking, sai kice Alhamdulillah." Rungume sa tayi hawaye na biyo mata ƙunci, sosai takejin ta fara kewar su tun yanzun, sam batason yin nesa da family ɗinta, yanzu kuma fah tafiya zatayi kenan zuwa gidan zaman ta na kanta wanda ita ma zata tara nata future Family ɗin, sosai takejin wani irin kewa na dabaibaye mata zuciya. Ɗan dariya Jafar yayi yace "Toh tun ma basu ƙaraso anyi maganar ba kike kuka, ranar da zasu tafi dake kuma fah ya zakiyi?." "Ba sai na fasa bin su ba" ta faɗa cikin muryar shagwa6a. "Well ai kuma bamu isa mu hana su tafiya dake ba, coz kin riga kin zamto ɗaya daga cikin family ɗinsu." "Nidai ku kaɗai ne Family ɗina" ta faɗa cikin ɗagowa tana share hawayen ta. Dariya yayi kafin yace "Yeah koh kin tafi ɗin we will still be family forever." Murmushi tayi tace "Koh wane sati sai nazo na ganku na tafi." Idanu ya waro kafin yace "Ai koh gari ɗaya muke ba zaki dinga zuwa bayan sati ba bale kuma chan Egypt." Baki ta turo tana ƙunƙunai ƙasa-ƙasa. Wayar sa ya ciro cikin aljihun sa kafin ya shiga ta whatsapp nasa ya binciko wani number ya shiga, hotunan kayan ɗaki da falo aka turo masa masu kyawun gaske da tsada, miƙa mata wayar yayi yace "Ki za6i wanda yayi miki anan." Amsar wayar tayi ta shiga duddubawa, ɗagowa tayi ta kallesa tace "Wadannan kayan ɗakin sai kace wata ƴar gwamna, basuyi tsada ba kuwa?." "Kinga kuɗin su ne da kike cewa sunyi tsada?" ya faɗa yana kallon ta. "Amma ai daga gani zasuyi tsada fah Yaya." "Babu ruwan ki da wannan just chose wanda yayi captivating mind naki." Sosai ta shiga kallo kafin kuma ta ɗago tana kallon sa tace "Gaskiya ni ba zan iya za6ar mai kyau ba, ka za6a min da kanka" ta faɗa tana miƙa masa wayar. Murmushi yayi ya amsa kafin yace "Alright duk wanda kikaje kika gani koh da baiyi miki ba kada ki ba kowa laifi." "Ai nasan zaka za6a min mai kyau sosai." "Alright, anjima su Mami zasu zo a fara shirin tar6an baƙin, sai kema ki shirya kafin nan" ya faɗa yana miƙewa tsaye. "Insha Allah" ta bashi amsa. Ficewa yayi daga ɗakin kafin ta kwanta flat kan bed ɗin fuskar ta na fuskantar sama. Sosai takejin ta wani iri duk jikin ta yayi sanƴi. Ƙarar shigowar text message ne ya sanƴa ta jawo wayar tata tare da buɗe text ɗin nasa tana karantawa. Murmushi ta saki tana ajiye wayar, kafin ta tashi ta fice daga ɗakin. ************************** ________Sosai Grandma ke shirye-shirye kai kace ranar bikin ne ya gabato. Kayayyakin da ta haɗawa DEENAH da JALILAH kama daga na sanƴawa, takalma, ƴan kunne dasu awarwaro wadanda duk suka kasance na Gold ne masu matuƙar tsada, da dai dukkanin wasu abubuwan da ake buƙata idan za'a kai tambaya kamar yadda yake a al'adar MASARAUTAR tasu. Shi dai ZEEYAD da idanu kawai yake bin ta dukkanin wani abu da zatayi dan kuwa ta haɗa kayan ta ta ƙeƙashe tace da ita za'a je tambayar auren DEENAH, tun mai Martaba bai yarda ba har yazo ya yarje duba da yadda ta takura. Sosai ta gama kintsawa tare da sanƴawa aka fidda dukkanin wadanda yake na DEENAH ne kasancewar mota na jiran ta zasu wuce airport. "Toh mukam mun wuce Nigeria tambayo auren matar da Boy zai aura, dan haka ku tabbatar kun kula min da gida kada naga wata dameji koh abinda ba shi ne ba, idan kuwa ba haka ba rai zai 6aci dan kuwa ba wani babban aiki bane a wuri na na fatattaki mutum yaje chan yaƙare tunda ba zai yimin abinda raina ke so ba" ta ƙarashe cikin kallon Bayin dake yin hidima a side ɗin nata kasancewar tara su da tayi a layi. Duk amsa mata sukayi da ba za'a sami wata matsala ba, kafin tayi hanƴar ficewa. Saurin mara mata baya ZEEYAD yayi yana faɗin "Grandma." Dakatawa tayi tare da juyowa tana kallon sa tace "A'a kaga kada ka dameni da wasu ƙananun maganganu nasan abinda zaka faɗa bai wuce kace a aura maka DEENAH a taho maka da ita ba, kada ka damu indai hakan kakeso kamar anyi an gama ne, ka sanni da nacin tsiya koh mutum baiyi niyyar abu ba sai na takura shi yayi, sai dai idan banyi niyya ba." Murmushi yayi yace "Grandma ni ba wannan maganar nakeson yi miki ba, she refused to answer my call since day before yesterday, please idan kinje talk to her ta ɗau kira na." "Yoh toh dama tayaya zata ɗau kiran ka, kana neman rabo ta da dangin ta, nikam kaga tafiya ta ma ƙarasa sauran maganar a waya, kasan zamuyi ne mu dawo zuwa gobe sabida zuwa tambayo na ɗan uwanka." Bai tanka mata ba ya mara mata baya har zuwa motar ya buɗe mata ta shiga, sallama suka sakeyi kafin driver yaja motar su wuce. ************************* _______Sosai gidan ya bazu da ƙamshin girki wanda ya gauraye da ƙamshin turaren wutan da ya gauraye ilahirin gidan baki ɗaya. Sosai duk sukayi busy wurin shirin kar6ar baƙin, Umma kam ta kasa zaune ta kasa tsaye, tama rasa inda zata sanƴa kanta wai yau ita ce zata aurar da ƴar ta izuwa wata MASARAUTA, MASARAUTA ba ɗaya daga cikin Nigeria ba, sosai zuciyar ta ke cike da farin cikin da ba zata iya kwatantawa ba, bama ita kaɗai dukkanin su mutanen cikin gidan. Sosai suka kammala komai da shirin su tun kafin su ƙarasowar baƙin. Mijin Mami kuma mahaifin su Anty Khadija shine wanda zai tsayawa DEENAH a matsayin Uba, dan haka shima tunɗazun ya iso da abokan sa na amana na kusa dashi, suna jiran isowar baƙin. DEENAH kuwa sosai tasha dark blue ɗin Laffaya mai tsada, batayi wani kwalliya sosai ba, amma kyawun da tayi ba'a cewa komai. Sosai takejin zuciyar ta ta kasa samun sukuni, wai yau ita za'a zo tambayar auren ta daga wata ƙasar, she can't believe it. Su Anty Khadija ne ke ta kwantar mata da hankali. ************************ _______Tundaga kwaltar mashigar ungwar tsala-tsalan baƙaƙen motocin wanda aƙalla zasu kai ashirin da biyar koh fiye da haka ne suke ta kunno kai cikin layin gidan su DEENAH ɗin, inda motar Jafar ce a gaba wanda dai da alamu shine keyi musu jagora. Mutane ne suka tsaya kallon motocin suna mamakin wane mai ragamar mulkin ne wannan haka, basu tashi shiga mamaki ba sai da suka ga an wangale gate ɗin gidan su Jafar wasu daga cikin motocin sun kutsa kai ciki, ga kuma securities kaca-kaca everywhere kamar wanda ruwan su akayi kowanne riƙe da bindiga a hannun sa sun sha baƙaƙen shades. Anty Khadija da Amirah dake leƙe ta ɗakin DEENAH ne suka buga wani irin tsalle cike da murna suna tafawa. "Ke wallahi harda sarki da gwamanan garin nan, kutt DEENAH ba ƙaramin goshi kikayi ba, inalillahi" faɗin Amirah cike da tsantsar murnar da take ciki. "Ke dallah ki sassauta muryar ki kalan kisa su jimu, mu shiga uku yadda suke tare da sojoji ɗinnan" faɗin anty Khadija tana sake leƙa kanta. "Sun shigo, sun shigo, ku tashi mu fita" ta faɗa tana ɗaukar gyalen ta. Amirah dake leƙe har yanzu ne tace "Ke ni wallahi nama kasa ganin fuskar baban ZEEYAD ɗin wadannan masu bindigogin sun tare shi, hegu masu ƙatiƙatin kai." DEENAH dai shiru tayi tana kallon su jikin ta na sake yin sanƴi sosai, hannun ta ma dakyar take iya ɗaga shi. Muryar Grandma taji a falon su hakan ya sanƴa ta waro idanu tana faɗin "Har da Grandma aka zo." Su Anty Khadija basu tsaya bata amsa ba, sukayi hanƴar waje da gudu har suna tunkuɗe juna wurin fita. Dariya suka bawa DEENAH dan haka murmusawa tayi dan kuwa yadda takejin ta ɗinnan bata tunanin zata iya buɗar haƙora tayi dariya. "Masha Allah, Masha Allah, Ina jikar tawa take ne dukkanin ku na ganku amma ita da yakamata na fara ɗaura idanu akanta ban ganta ba." "Tana cikin ɗakin, kizo na kai ki" cewar Amirah cike da zumuɗin ganin Balarabiyar tsohuwa a gaban ta sai kallon Grandma ɗin take tayi. Grandma da sauri ta mara mata baya tana faɗin "Mai kuma kike jira ƴar nan, maza muje ki kaini." Tun kafin su ƙaraso Amirah ta fara doka kiran DEENAH, DEENAH jin muryar Grandma ya sanƴa ta saurin jan Laffayan jikin ta yana rufe mata fuska. Shigowar su ɗakin Grandma da fuskarta fal farin ciki ta ƙaraso kan DEENAH tana faɗin "Masha Allah dake ƴar nan, tun kafin naga fuskar ki na san ba bala'in kyau kikayi ba, ta faɗa tana zama kusa da ita tare da rungumo ta. Lafewa DEENAH tayi jikin Grandma ɗin tanajin wani irin sanƴi a cikin zuciyar ta. "Toh dai ni fah ba Boy bace bale ayimin rowar fuska, buɗe kyakkyawar fuskar taki na gani mana ƴar nan." Ɗagowa DEENAH tayi daga jikin ta tana sake jan mayafin nata. "Toh ai shikenan, inaga dai so take na buɗe da kaina na gani" cewar Grandma tana tashi tsaye tare da sanƴa hannu ta yaye rufin kan DEENAH ɗin, cupping fuskar ta tayi cike da farin ciki tare da bata kiss a goshi da ƙunci tace "Masha Allah, what a beautiful angel you're, haƙiƙa Boy ɗina ba ƙaramin za6e ya iya ba, Allah yayi wa rayuwar ki albarka ƴar nan." Murmushi DEENAH tayi tana sadda ƙasa cike da kunƴar Grandma ɗin. Kallon su Umma Grandma tayi tace "Kuyi haƙuri ku ɗan barmu da jikar tawa, akwai abubuwan da nakeso mu ɗan tattauna da ita ne." Cikin sakin fuska Mami tace "Ai bakomai, ku wuce muje" ta faɗa tana riƙo Amirah da tunɗazu ta kasa rufe bakin ta suka fice dukkan su. ************************ _________Gaf da Magrib suka gama abinda ya kawo su, inda mai Martaba ya nemi ganin surukar tasa, kan DEENAH a ƙasa Umma na riƙe da ita suka shigo cikin falon baƙin dake cike daf da manƴan mutanen cikin garin Sokoto ɗin, ciki kuwa har da Sarki da Gwamnan wannan garin. A gaban sa DEENAH ta durƙushe tare da gaida sa cike da girmamawa, murmushi mai Martaba yayi yana kallon ta, a hankali ya furta "masha Allah, she will surely make a great and beautiful Queen" ya ƙarashe cikin dariyar manƴan ta sauran mutanen na taya shi. Murmushin Farin ciki Umma ta saki tana sadda kai ƙasa Kyauta mai tsokan gaske mai Martaba yayi mata, after all abubuwan da suka taho dashi, bama shi kaɗai ba hatta mutanen da suka zo tare dashi sai da sukayi wa DEENAH kyauta, a cewar su tunda marainiya ce ita baikamata iyayen ta su kashe kuɗi wurin yi mata duk wani kayan ɗaki da abubuwan da za'a kashe a auren ba. _(Nikuwa dai nace sabida dai kunga mai Martaba ne yasa kuke son nuna gwanin ta, idan yana da wasu ƴaƴan kuyi shisshigin haɗa su da naku sabida kunga random girl kamar DEENAH zata yi aure gidan sarautar wata ƙasar ina ga kuma ƴaƴan ku😁, koh dayake Ayaan yana nan🥲)_ Umma harda hawayen farin ciki tayi, godiya kuwa tayi musu shi yafi cikin maliya, ta rasa inda zata tsunduma ranta tsabar farin ciki, bata ta6a tunanin zata yi witnessing irin wannan rana a rayuwar ta ba, sai yau gashi haihuwar DEENAH is big a blessing ba wa ita kaɗai bama ga dukkanin family ɗinsu. DEENAH ma kukan take a hankali, albarka duk suka sanƴa mata kafin su fara shirin tafiya. Duk tare suka bar gidan da mijin Mamy, Grandma kuwa cewa tayi anan zata kwana tunda sai gobe ne tafiyar tasu, idan yaso sai a biyo a ɗauke ta kawai su wuce. Rungume DEENAH Umma tayi cike da farin ciki, hawaye kawai take tana sake sanƴa mata albarka a cikin zuciyar ta. Duk wucewa sukayi tare da yin sallahr Magrib da ake ta kiraye-kiraye, sune basu samu zama ba har sai bayan anyi Isha'i. Sosai suka ji daɗin zama da Grandma inda ta baje sai labari take basu da wanda aka tambaye ta da wanda ba'a tambaye ta, su Amirah kam dama abin nema ya samu ne, ita ke ta biyewa Grandma ɗin, sauran kuwa nasu dariya ne kawai. ********************* ______Washe gari da sassafe driver yazo ɗaukar Grandma, sai masifa take wai ai yazo da wuri, sai da ta tabbatar ta gama kintsawar ta tsaf kafin su kama, hanƴa bayan sunyi sallama dasu Umma sosai kamar ba zasu rabu ba. Grandma bata daɗe da tafiya ba Alhaji Lawal mijin Mami ya iso gidan, domin tattauna batun da sukayi jiya da mai Martaba ɗin. Dan haka dashi da Umma da Mami ne suka wuce falon baƙi dan tattauna komai achan ɗin. "Alhaji sati biyu fah kace, ai yayi wuri yaushe za'a samu isasshen lokacin komai bayan kasan auren al'adar mu ta Hausa Fulani, da akwai wasu shirye-shiryen da yakamata ayi wa amaryar kafin wannan lokacin, yaushe zamu gama komai cikin sati biyu" faɗin Mami bayan mijin nata ya gama yi musu bayanin yadda sukayi da mai Martaba. "Toh ya muka iya Hajiya, kin dai ga ba ƙananun mutane bane ba, babu ta yadda za'ayi na iya yi musu jayayya da wannan alfarmar da suke nema, dan hakan ne ya sanƴa shi Sarkin tasowa tundaga ƙasar da yake yazo shi nan, toh ya kike tunanin kuma zance masa A'a, baya ga haka kuma ai ana barin halak dan kunƴa irin ɗawainiyar da suka iyo wanda hatta ni kaina naci moriyar hakan ai kaɗai ya isa mu amince da batun su, yanzu dai ku gama duk wani abu da zakuyi cikin sati biyun nan, nasan idan kuka haɗa ƴan dabarun ku na mata komai zai daidaita." Ajiyar zuciya ta sauƙe tace "Toh shikenan, Allah ya nuna mana ranar da cikin rai da ƙoshin lafiya da alkhairi." "Shine kawai addu'ar da yakamata muyi dama, yanzu kije ku sanar wa da ita yarinƴa tasan abinda ake ciki, nasan suma ba zasu rasa shirye-shiryen su na kyalkyali banzan ƴan matan zamani ba." Dariya duk sukayi kafin Umma da duk jikin ta yayi sanƴi tace "Aikuwa dai kam." "Masha Allah, ni bari na wuce wurin aiki dama nazo ne na sanar daku yadda mukayi dasu, idan da akwai wasu abubuwan da kuke da buƙata sai ayi gaggawar sanar dani." "Insha Allah" duk suka amsa suna miƙewa tsaye, inda shi ya fice su kuma suka dawo cikin ƙaramin falo. Tunda aka sanar da DEENAH auren nasu sati biyu aka sanƴa ta sake shiga damuwa, babu abinda take sai sharce hawaye a 6oye dan kuwa wani irin kewar mahafiyar ta da ɗan uwanta ne suka lullu6e mata zuci, she can't believe zata koma cikin wasu family ɗin ta barsu, sam batason kan family ɗinsu ya wargazu, su biyu kaɗai Umma ta mallaka Jafar namiji ne ba zama yake a gida ba musamman ma da ya kasance yana da aikin yi, zai sauran saura Umma kaɗai babu mai ɗebe mata kewa koh taya ta hira idan ta dawo daga wurin aikin ta ita ma, sosai gidan zaiyi mata babu daɗi ita kaɗai, ta san abinda Umma keji a yanzu yafi wanda takeji a cikin zuciyar ta, bata ƙi ta dawwama tare da Ummar tata har abada ba, sam ba zata iya jurar ganin ta cikin halin kewa ba, tasan sosai hakan zaiyi affecting ɗinta, dah kamar tana da wasu ƙannen ne ma da sauƙi, but duk tausayin Umma ya cika mata zuciya, rayuwar Family ɗinsu zai zamto babu daɗi ba kamar ta dah ba, shima Jafar yanayin aure shikenan kafin Umma ta sanƴa sa a ido tasan zai ɗan dinga jan lokaci dukda tasan yayan nata ba zai ta6a wofantar da mahaifiyar su ba, but tanajin babu daɗi sosai da sosai cikin zuciyar ta, babu abinda take sai kallon Umma da ta lura jikin ta a matuƙar sanƴaye yake, dariya da murmushin da take kawai ta yaƙe ce, but da akwai damuwa cikin zuciyar ta. Tashi tayi ta bar musu falon ba tare da tabi ta kan kayan alatun da suke dubawa ba, wanda mai Martaba da Grandma suka kawo mata. Ɗakin ta ta koma ta sha kuka sosai kamar babu gobe, sai da tayi mai isarta kafin ta janƴo wayar ta. Missed calls ɗinsa ta gani dan haka dialing number ɗin tayi, ringing biyu yayi ya katse kiran tare da kiran ta. Ɗagawa tayi tana kaiwa kunne tare da yin sallama. "Habibty" ya faɗa cikin sanƴin muryar sa. "I want to discuss something important with you please" ta faɗa cikin muryar sabon kukan dake zuwan mata. "Babe are you Okay, what's wrong with you, wa ya ta6a ki?" ya faɗa cikin ɗan ruɗewa da jin kamar kuka take. Kai take girgiza masa kamar wanda yake gaban ta tace "Dan Allah kada ka raba ni da Umma ta da Yaya Jafar" ta faɗa cikin shessheƙa. "Babe ba zan raba ki dasu ba, what made you think of that?." "Banason yin nesa dasu, tun yanzu nakejin kewar su, banason nayi nesa dasu." Huci ya fesar yace "Babe..." "Please i beg you kada kacemin a'a." "Listen please Baby, ki kwantar da hankalin ki and stop crying ba zan ta6a raba ki dasu ba, they are your family." "But you're taking me far away from them." Cikin kwantar da murya da rarrashi yace "Baby, ki kwantar da hankalin if that is the case then zaki dinga zuwa gida ganin su, are you Okay with that." Kai ta jinjina masa kafin tace "Kullum koh?." Ɗan waro idanu yayi yana sosa goshi kafin a hankali yace "Yeah, koh da after every 1hour kikeso, please stop crying, Okay?." "Yes" ta faɗa tana goge hawayen ta. Murmushi yayi yace "Thats my baby." Murmushi tayi tana sadda kai ƙasa. A haka suka cigaba da hira cike da soyayya da ƙaunar junan su. *********************** *RANAR ƊAURIN AURE* *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽* [8/25, 11:33 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *047...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *Wannan shafin kacokan naku ne ZEEYAD FANS CLUB😍🤗, bama ku kaɗai ba dama duk sauran mabiyan littafin ZEEYAD, alkhairin Allah ya isar muku aduk inda kuke, haƙiƙa addu'a da sharhin da kukeyi min a kullum shine sanadiyyar ƙarin ƙarfin guiwa ta, Allah ya biya muku dukkanin buƙatun ku na alkhairi🤲🏽🥹❤️* _________Dandazon Mutane ne cike maƙil a babban Masallacin gidan sarkin Sokoto, duk inda ka waiga manƴa-manƴan motoci kawai kake gani kai kace auren ƴar gidan gwamna koh sarkin ake ɗaurawa sabida irin manƴan mutanen da suka halarci ɗaurin auren. Ana idar da sallahr Jumma'ah, aka nemi awallin kowane ɗaya daga cikin su, inda Dadyn Khairat ya kasance awwalin ZEEYAD, Abban su Amirah kuma na DEENAH. Cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗaura auren *ZEEYAD IBN ABBAS* da kuma amaryar sa *MADEENAH ABDULSALAM* akan sadaki dubu Hamsin kacal kamar yadda Abban su Khadija ya buƙata sabida aure da sadaki kaɗan yafi albarka. Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ZEEYAD dake sanƴe cikin shigar fararen kaya irin tasu ta larabawa ya ɗaura brown alkyabba mai matuƙar kyau da tsada akan sa, yanajin wani irin farin ciki da annashuwa na ratsa kowacce saƙo na jinin jikin sa, yana mai nana ta kalmar Alhamdulillah tare da sake miƙa dubbun godiyar sa ga Allah na cika masa burin sa da yayi a cikin zuciyar sa. Dafa kafaɗun shi Sadeeq dake kusa dashi yayi shima cike da tsantsar murna a hankali yace "Finally, Congratulations bro." Murmushi ZEEYAD ya saki tare da jinjina masa kai dan kuwa baya tunanin zai iya buɗar baki magana sabida irin farin cikin da yake ciki. Albarka manƴan wurin suka sanƴa masa da amaryar tasa tare da sanƴawa rayuwar auren su albarka, mai Martaba kam dama bai zo dan kuwa zai tsaya ne a wurin ɗaurin auren YAZEED dan nuna masa ƙauna da kulawa shima. Mutane ne suka fara fitowa bayan an ɗaura auren, Jafar ne ya ƙaraso gun ZEEYAD tare da rungume sa a hankali yake faɗin "I know you're a good Man with a kind heart, and i know ba zakayi abinda bai dace ba, i trust you completely banida wani tantama akanka, i know DEENAH tayi dacen miji, please take a very good care of my sister fiye da yadda ka nuna mata a dah, don't let her shed tears da sunan kewar mu, ita ɗin amana ce a gareka and i do hope ka riƙe amanar ta da kyau" ya faɗa yana ɗagowa cikin sanƴin jiki dan kuwa sosai yakejin zaiyi kewar ƴar ƙanwar tasa, she means alot to him and gashi yau zatayi nesa dashi zuwa wani wurin, wanda bai kuma sanin taƙaitaccen ranar sake haɗuwar su ba, ji yake tamkar su koma rayuwar su ta dah lokacin da suke ƙanana, baisan yadda zai iya misalta yadda yakejin kewarta cikin zuciyar sa ba. Murmushi ZEEYAD yayi cikin sanƴi da tausayin Jafar ɗin ya dafa kafaɗun sa yace "I promise to take good care of her fiye da yadda zan baiwa kaina kulawa, trust me." "I trust you" ya faɗa kafin ya ɗaura da faɗin "We should get going, don't you wanna see your Bride?." "Ofcourse he does, he is very eager ma kuwa" faɗin Sadeeq cikin ɗan dariya. Duk jerawa sukayi suka fito kamar wasu ƙuda haka securities da fadawa suka mara musu baya har izuwa motocin su, kafin su jera duka zuwa gidan su amarya. ************************* _________Sosai ta haɗe cikin tsadaddiyar doguwar farar wedding gown da yake ja mata har ƙasa, kyawu irin wanda DEENAH tayi a wannan rana ba zai kwatantu ba, duk da kuwa fuskar ta a matuƙar tsuke take babu walwala kamar yadda zakaga wasu amaren amma hakan bai hana irin kyawun da tayi fitowa ba. Sosai take sake kallon family picture ɗin nasu tana sake jin kewar mahaifiyar ta da ɗan uwanta na ratsa ta. Buɗo ƙofar ɗakin akayi aka shigo, tsaye Amirah da tayi matuƙar haɗuwa cikin shigar leshi tayi tana kallon ta kafin kuma ta buɗi baki tace "DEENAH sun ƙaraso fah wai kizo kije ki gaida manƴan baƙin." Shiru DEENAH tayi mata bata tanka mata ba, ganin taƙi kula ta ne ya sanƴa ta ficewa. Ba'a ɗau lokaci ba Mami ta leƙo a karo na ba adadi wannan karon cike da masifa take faɗin "Wai ba zaki tashi daga wannan gun bane nikam, akanki aka fara aure ne komiye, kowa fah da kika ganshi da aure haka yayi passing level ɗinnan ya wuce ba dan yaso ya bar gidan iyayen sa ba, zaki tashi ki fito ne dai kokuwa sai ranki ya 6aci, ayi tayi miki magana ɗaya tunɗazu sai kace yarinƴa ƙarama, kin bar mutane nata faman jiran ki sai kace wasu sa'annin ki, maza tashi ki wuco mu tafi." Miƙewa tsaye DEENAH da ta turo ƙaramin bakin ta tayi idanun ta cike taf da kwalla ƙiris ya rage ta fashe ta tattari gown ɗinta a hannu tana bin bayan Mami ɗin da riga da tayi gaba. Ɗakin Umma ta fara kaita inda ƴan office ɗin Umma ɗin suke ta gaida su, sai yaba ta suke kamar su ari baki, kafin kuma Mami ɗin ta ɗauko wani farin mayafi tana rufa mata akai tare da riƙo hannun ta sukayi falon baƙi. Su Daddyn Khairat ne da Abban su Khadija dama kuma uku daga cikin manƴan ministocin fada, sai kuma mataimakin gwamna dama kuma ƙarin wasu manƴan mutane uku. Durƙushewa DEENAH tayi a gaban su tana sake jan mayafin jikin ta, kafin ta buɗi baki dakyar ta gaida su. Duk cike da fara'a suka amsa mata gaisuwar fuskar su washe. Addu'a sukayi mata da fatan alkhairi dama kuma samun rayuwa mai inganci cikin rayuwar ta, kafin su ɗaura mata da nasiha dai-dai iya gwargwadon abinda zasu iya faɗa mata sannan sukayi mata kyaututtuka. Hawaye kawai DEENAH keyi bata ma iya yi musu godiya ba Mami ta ɗaga ta suka fice. Falon su ta kawo ta nanma ta gaida baƙin da sukayi suma sai yaba ta suke kafin ta maida ta ɗakin Jafar inda ta ɗauko ta tana faɗin "Ki zauna anan, idan kina buƙatar wani abin ki kira ni a waya, ina dai akwai waya a hannun ki koh?." Kai ta jinjina mata alamun eh tana nuna mata inda wayar take ajiye. "Yauwa toh, kuma dan Allah banda kuka, kukan nan ya isa haka, mu zamu je mu cigaba da shirye-shiryen tafiyar taku, dan naji labarin shi mijin naki ma sun iso suna waje." Zuciyar DEENAH ne ya tsinke nan tace "Shirye-shiryen tafiya ina?." "Bangane shirye-shiryen tafiya ina ba, dah so kike mu saki a gaba muna ta kallo komiye, tafiya mana da mijin ki." Shiru tayi ta kasa cewa komai nan Mami taja ƙafafuwan ta ta fice, DEENAH sam batayi zaton yau ne zata bar gidan su ba. Kamar wacce aka tsikara haka ta sake fashewa da wani kukan harda shessheƙa. Hoton nasu ta ɗauko tana cigaba da kallo duk hawaye ya 6ata fuskar hoton. A haka Jafar ya shigo ɗakin nasa ya sameta zaune sai kuka take, tsayawa yayi kallon ta for about some minutes kafin ya taka ƙafar sa cikin sanƴin jiki ya ƙaraso. "DEENAH?" ya kirayi sunan ta a hankali. Tsagaitawa tayi da kukan da takeyi ɗin tana juyowa ta zuba masa idanun ta da fuskar ta da yayi cha6a-cha6a da hawaye. Ji yayi jikin sa ya ƙarayin sanƴi sosai fiye da dah, a hankali ya buɗi yace "It's time." A hankali ta shiga miƙewa tsaye tana kallon shi kafin ya ƙare cewa "Everyone is waiting." Da gudu tazo ta shige jikin shi tana ƙanƙame sa tare da sake fashewa da wani kukan. Jafar ji yayi shima kukan na zuwan masa dan haka saurin runtse idanun sa yayi yana bata tight hug shima. Sun ɗan jima a haka DEENAH bata bar kukan ba, a haka Mami ta shigo ta same su. Ji tayi duk tausayin su ya kama ta, ƙarasowa wurin su tayi tare da faɗin ''Ai ya isa haka nan koh, sai kace wanda za'ayi rabuwa ta har abada." Ɗago DEENAH yayi ba tare da ya kuma kallon ta ba ya fice daga ɗakin da sauri. Riƙo ta Mami tayi ta shiga share mata hawayen "Haba kekuwa DEENAH haƙuri fah zakiyi wannan kuka dai ai yakamata ace kin dakatar dashi haka nan, ace tun shekaran jiya bakida aiki sai abu ɗaya kuka, kiga duk kinbi ma kin 6ata kwalliyar fuskar taki da wannan kukan, ya isa haka nan kinji insha Allah muma zamu ke kawo miki ziyara kar ki damu kinji?." Kai kawai ta iya jinjinawa tana sassauta kukan nata, a haka suka ƙarasa ɗakin Umma. A bakin bed aka zaunar da DEENAH, kallon Umma da ta sunkuyar da kai Mami tayi tace "Toh ga ƴar taki nan, sai kizo kiyi mata nasiha irin ta uwa dan gashi chan suna ta jira za'a tafi, ga Alhaji ma tunɗazu yake ta damu da ƙira ayi a fito. Umma da duk jikin ta yayi sanƴi kasa kallon DEENAH tayi dan kuwa ji take kamar ta fashe da kuka, sam bata zaci DEENAH zata bar gidan nan zuwa gidan auren ta soon haka ba. Da kyar ta iya miƙewa daga inda take tazo kusa da DEENAH ta zauna tare da rungumo ta tace "Allah yayi miki albarka, Allah ya sanƴa albarka cikin rayuwar auren ki, Allah ya albarkaci zuri'ar da zaku tara nan gaba, ki ɗauke ta kuje kawai Yaya ni banida ta cewa, Allah Ubangiji ya tsare ku ya sauƙe ku lafiya ya kare ku daga dukkanin sharrin masu sharri." Zama Mami ma tayi suka sanƴa DEENAH dake rungume da Umma sai kuka take a tsakiya kafin ta kira yi sunan DEENAH har sau uku. Tsagaitawa DEENAH tayi da kukan nata tana sauraran yadda Mami ke ta zuba mata nasiha mai rastsa jiki ƙawayen Umma na taya ta, sosai suke sake ƙara mata kewar Umma har takejin kamar ba zata iya barin su ba. Amirah ce ta shigo ɗakin tace "Wai ma inji Abba ayi sauri ya isa haka nan." Kallon ta Mami tayi tace "Ina Khadija fah?." "Tana ɗaki tare da ƙawayen ta." Kuje a sake gyara mata kwalliyar nan tukun kafin a tafi ɗin." Ƙanƙame Umma DEENAH tayi tana kuka sosai take faɗin "Umma na dan Allah kar ki bar ni." Rungume ta Umma tayi sosai ita ma tana sharar hawayen kewar ƴar tata. "Ki ɗauke ta kuje Yaya" ta faɗa cikin muryar kukan dake zuwan mata. Kama DEENAH da ta riƙe Umma ƙamƙam Mami tayi tana faɗin "Umma na dan Allah kar ki bari su tafi dani, banason rabuwa dake, dan Allah Mami ki sake ni." A haka aka fitar da ita zuwa ɗakin su, Anty Khadija dake zaune da ƙawayen ta suna cin abinci ne ta miƙe tsaye tana faɗin "Lafiya?" ganin yadda DEENAH ke ta kuka ɗin. "Tafiya zasuyi mana ke kinzo nan sai ɗirkawa cikin ki abinci kike" cewar Amirah. "Yau kuma?" ta faɗa cikin waro idanu. "Dan Allah banson surutu, maza gyara mata kwalliyar nan gayi chan suna ta jira tunɗazu" cewar Mami tana zaunar da DEENAH. Kallon DEENAH dake ta zabga kuka tayi kafin kuma ta wuce toilet ta wanko hannun ta ta fito. Kit ɗin kayan kwalliyar ta ta ɗauko ta hau gyarawa DEENAH kwalliyar tata. Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala, kallon Mami tayi tace "Mami taci abinci kuwa?." "Kamarya taci abinci baku bata abinci bane?." Amirah ce tayi caraff take "An bata taƙi ci, da kaina na kai mata ɗakin Yaya Jafar amma tace ba zata ci ba." "Shikenan ai, maza tashi muje" cewar Mami tana ɗago ta tare da kama ta suka fice daga ɗakin. ZEEYAD dake zaune a motar ƙafar sa ɗaya a waje idanun sa kafe a hanƴar fitowa daga falon nasu tunda aka ce musu yanzu za'a fito su tafi, miƙewa yayi ya fice daga cikin motar lokacin da idanun sa suka sauƙa akan DEENAH da ake fitowa da ita, zuciyar sa cike da tsantsar farin ciki ya ƙarasa inda suke, sake DEENAH su Mami sukayi inda shi kuma ya rungumo ta so tightly yana rufa mata alkyabar jikin sa haɗi da lumshe idanun sa yana sauƙe wata iriyar 6oyayyiyar ajiyar zuciya. Fuskar kowa washe da murmushi yake kallon su. DEENAH wata iriyar ajiyar zuciya ta sauƙe lokacin da taji ta manne cikin faffaɗar ƙirjin sa, inda ƙamshin sa na musamman taji na dausar mata da wata iriyar nutsuwa cikin zuciyar ta. Kiss ya manna mata a forehead yana sake shigar da ita jikin shi. "Alright, i think you guys should get going by now" faɗin Abban su Amirah da suke tsaye suna kallon su. Ɗago da DEENAH yayi ya shiga share mata hawayen kan fuskar ta, kafin kuma ya riƙo hannun ta suna juyawa su fara tafiya, dakatawa yayi tare da juyowa ya kalli su Mami dake tsaye sun zuba musu idanu, ɗan duƙar da kai yayi tare da furta "Thank you so much Aunt." Murmushi Mami ta saki kafin ya juya su cigaba da tafiya. Da kansa ya buɗe mata murfin motar tana shigewa tare da tattare mata jelar gown ɗin nata ya rufe, kafin ya zaga zuwa ɗayan 6angaren ya buɗe ya shige. Shigar sa keda wuya suma duk sauran fadawa da ma kuma securities ɗin da suka taho daga Egypt dama sauran mutane duk suka bubbuɗe motocin su suka shige, already dama gate a wangale take dan haka a hankali suka fara kutsa kai suna ficewa daga cikin gidan. DEENAH juyawa tayi tare da dafa seats ɗin da take tana kallon ƴan uwanta dake ta waving da hannayen su dama kuma gidan nasu baki ɗaya. Ta lura bata sake ganin Jafar ba har suka fice daga gidan a hankali ta furta "Yaya?" idanun ta na sake tara wasu sabbin hawayen. Ganin haka ya sanƴa ZEEYAD riƙo hannayen ta da suka sha baƙin lalle da jaa irin na amaren zamani a hankali ya furta "You will see him again oneday." Jaye hannayen ta tayi daga cikin nashi tana kauda fuskar ta idanun ta kan glasses ɗin motar. Matsowa kusa da ita yayi giving her a warm hug yace "It's alright, am here" ya faɗa tare da bata light peck a gefen ido. Kwantar da kanta tayi kan faffaɗar ƙirjin sa tana lumshe idanun ta. A haka suka ƙaraso Airport, kasancewar Private Jet nasu na kansu ne wanda already yana jiran su ya sanƴa babu wani 6ata lokaci motocin suka ƙarasa kusa da jirgin. Da kansa ya buɗe ƙofar ya fito yana saurin dakatar dogarin da yazo da niyyar buɗe ƙofar ya buɗe da kansa tare da riƙo hannayen ta ta fito. A haka suka ƙarasa matattakalar benin yana tattare mata gown ɗin har suka shige. Inda aka ware wurin zaman VIPs suka nufa ya taimaka mata ta zauna, kafin shima ya zauna kusa da ita yana kamo hannun ta ya sarƙe da nashi tare da ƙurawa ƙunshin hannun ta da yayi bala'in tafiya da imanin sa idanu yana kallo. Kanta ta ɗaura kan kafaɗun sa tana lumshe idanun ta, sun ɗau almost 10mins kafin jirgin ya fara ƙoƙarin ɗagawa, ƙanƙame sa tayi dukda kuwa seat-belt ɗin da ta sanƴa har sai da jirgin ya ɗaga sama tafiyar sa ta saitu kafin ta sassauta riƙon da tayi masa ɗin. Ɗan ɗago kanta tayi tana kallon fuskar sa taga shima ita yake kallo, murmushi ya sakar mata kafin ta sake maida kanta. Suna nan zaune masu aikin cikin jirgin suka kawo musu abinci tare da jera musu a gaban su. Ɗan motsa ƙafaɗar sa yayi nan ta ɗago tana kallon sa, da ido yayi mata nuni da abincin, nan ta maida hankalin ta kan abincin kafin kuma ta ɗan yatsine fuska tace "Na ƙoshi." Ɗan janƴo table ɗin abincin yayi tare da buɗe plate ɗin chips ya ɗau fork ya cakalo chips ɗin a jiki yace "I promised your Family to take good care of you, and i know you're hungry right now, so haaa" ya faɗa yana kaiwa saitin bakin ta. Kallon sa take kafin ta buɗi baki a hankali yana sanƴa mata a baki, wasu siraran hawaye ne suka biyo mata ƙunci nan ya shiga girgiza mata kai yana faɗin "Please, i don't want to see those tears again, everything will be alright, i promise" ya faɗa cikin riƙe ha6ar ta yana kallon fuskar ta. Sauƙe idanu tayi ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye kukan nata, a haka ya cigaba da bata abincin tana kar6a har sai da taci kusan rabi tukun kafin tace masa ta ƙoshi, juice ya tsiyaya mata a kofi tare da bata ta sha, kafin ya ɗau tissue sheet ya goge mata bakin dashi tare da sakar mata da murmushi. Ji tayi hankalin ta ya ɗan kwanta da abincin nan da taci, ganin yana ta kallon ta ne ya sanƴa ta kauda idanun ta tana tsuke fuska. Murmushi yayi kafin yace "I don't know ranar da zan gaji da kallon face naki, your gorgeous face is like a charm that captivate my eyes" ya ƙarashe yana leƙa fuskar ta da take ta kawar masa tun ɗazun. Murmushi ya saki kafin yace "I know you're tired so come on, rest here" ya faɗa yana buɗa mata hannayen sa. Kallon sa tayi kafin kuma ta sake kawar da kai tana 6ata face, ya lura she is moody but nan da ƴan kwanaki zata warware ne. Jinginuwa tayi a jikin seat ɗinta tana lumshe idanu, ta ɗan jima a haka kafin bacci ya ɗauke ta. Ganin kamar tayi bacci ne ya sanƴa shi matsawa daf da ita yana gyara mata kwanciya kan faffaɗar ƙirjin sa tare da bata peck a goshi. ************************ __________Hancin ta da taji ana ɗan lakuta mata shi ne ya sanƴa ta fara buɗe idanun ta a hankali tana ware su kan kyakkyawar fuskar sa da yayi tagumi da hannayen sa yana kallon ta daga ɗaya seat ɗin dake facing wanda take. Idda ware idanun nata tayi tana gyara zaman ta tare da ƙarewa cikin jirgin kallo ganin kamar ya tsaya. Kallon sa tayi tace "Mun zo?." Kai ya jinjina mata ba tare da ya ɗauke idanun sa daga kanta ba. "Ƙarfe nawa?" ta tambaye sa. Wayar sa ya ciro tare da dubawa kafin yace "It's 8pm." Ɗan waro idanu tayi kafin kuma ta shagwa6e fuska tana faɗin "Ni na gaji, wannan kayan yana takura min." Miƙewa yayi tsaye daga zaunen da yake yana takowa gaban ta tare da miƙa mata hannu. Nata hannun ta sanƴa cikin nasa kafin ya taimaka mata ta tashi suka fice daga wurin. A hankali suke takowa daga kan matattakalar benin tanajin wani irin iska mai sanƴi na hura ta, wasu baƙaƙen zafafan motoci ta hango tsattsaye da alama dai jiran fitowar su suke. Buɗe ƙofar motar yayi mata tana shigewa ciki kafin ya zaga ta ɗayan side ɗin shima ya shige. Nan aka ja duka motocin tare da barin cikin airport ɗin. ********************** _________Tsaye Grandma take cikin tsadaddiyar shirin ta na alfarma, sosai tasha kyau kamar babu gobe, jin Boy ɗinta da DEENAH na hanƴar tahowa MASARAUTA duk sai takejin ta cikin wani irin tsantsar farin cikin da ba zata iya musalta shi ba. Sosai aka gyara MASARAUTAR inda tayi kyau sosai fiye da dah, koh ina ka wulga mutane ne ke ta sabgogin gaban su kamar ba dare ba. Cikin minti talatin suka ƙaraso cikin MASARAUTA inda ɗumbin jama'a suka taru dan shaida amaryar Yarima ZEEYAD ɗin. Part ɗin Grandma aka wuce dasu kamar yadda ya buƙata, sauƙar su keda wuya Grandma ta fito da wasu kuyangu a bayan ta hannayen su riƙe da wasu abubuwan da bansan koh menene ba. Cike da farin ciki ZEEYAD ya fito daga motar yana zuwa ya rungume Grandma cike da tsantsar farin cikin da yake ciki. "Masha Allah, masha Allah kyakkyawan yaro na ya zama babban mutum, ni yanzu matsamin tukun naga ƴar kyakkyawar jikar tawa, ƴar amana" ta faɗa tana jaye shi daga gaban ta kafin ta nufi motar da sauri tana buɗe 6angaren inda DEENAH take. Wani ƙayataccen murmushi Grandma ta saki tana riƙo hannun DEENAH ta fito daga cikin motar, rungumar ta tayi tightly kafin ta ɗaga ta manna mata kiss a duka ƙuncin ta dama kuma goshin ta tana cupping fuskar ta a hannu tace "Barakillah feek." Ɗan murmusawa DEENAH tayi tana sadda kanta ƙasa, juyowa Grandma tayi tana kallon kuyangun tace ku matso nan. Takowa sukayi inda take tsaye kafin ta kar6i wani farin mayafi mai kyau tana rufawa DEENAH akai ya rufe mata har fuska kafin ta juya ga ɗayar ta amshi wani abu kamar burner tare da kunna shi wani irin hayaƙi mai daɗin ƙamshi sosai ya fara fitowa daga 6uli-6uli abin, turarawa DEENAH tayi tana faɗin "Allah ya raba ki da sharrin dukkanin wani mugun abu walau mutum ne koh aljan, wannan turaren da kike gani haɗe yake da maganin mayu dama kuma na asiri, komin sharrin mutum akanki sai dai ya koma kansu, kaima zo nan na turara maka shi" ta ƙarashe tana kallon ZEEYAD dake tsaye gefen ta. Murmushi yayi yace "Grandma zaki sanƴa mata mura da wannan hayaƙin naki, you know banason wani abu ya same ta koh?" ya faɗa yana ƙarasawa kusa da DEENAH yana rungume kafaɗun ta. "Kaji min ja'irin yaro, ni zaka nunawa salawaitun gantalewa, toh kaima da kake ƙarami kullum sai na turara maka ita, koh yanzu duk wani turare da ake sanƴa maka a 6angaren ka haɗe yake da wannan maganin, ni yanzu dai ka barmin ƴa mu shiga ciki haka nan nasan ba ƙaramin gajiya ta kwaso ba" ta faɗa tana maidawa ɗayar kuyangar burner ɗin hannun ta kafin ta kamo hannun DEENAH su shiga ciki da ita. Daga inda suke tsaye suke leƙe Kiki tace "Ranki ya daɗe ni fah banga fuskar matar tasa ba." "Zo muje kawai, koma dai wacece gobe da safe ma ganta a fada" tana faɗin haka ta janƴo mayafin kanta yana rufe mata fuska ta bar wurin nan Kiki tayi saurin mara mata baya. ************************* _________Washe gari da sassafe Grandma ta shigo ɗakin da DEENAH take, zaune ta same ta ta kafe wuri ɗaua da ido, shigowar su ne ya sanƴa ta saurin dawowa hankalin ta tana miƙewa tsaye tare da ƙarasawa gun Grandma ɗin tana gaida ta. "Allah yayi miki albarka ƴar nan, dafatan dai kin kwana lafiya?." "Lafiya ƙalau" ta amsa tana sadda kai ƙasa. "Masha Allah naji daɗin jin hakan, kai ku kuma zaku ajiye karin kumallon ne kokuma zaku tsaya kallon ta ne, kokuwa dai baku ta6a ganin kyakkyawa bane a rayuwar ku, magulmatan banza saura kuma akai gaba." Da sauri suka rissina suna gaida DEENAH kafin su nufi kan wani table dake tsakiyar ɗakin suna ajiye tray ɗin hannun su. Kamo ta Grandma tayi tana zaunar da ita bakin bed kafin tace "Ni na girka miki abincin nan da kaina, sabida kinsan halin mutanen cikin MASARAUTAR nan duk munafukai da annamimai aka tara sai mutum yana takatsantsan, amma ke kam kar ki wani damu da izinin Allah turaren da nayi miki jiya koh maƙiyi sai yaji tsoron haɗa idanu dake, yanzu kici abincin nan ki shirya sabida yau za'a je fada duk kuje ku gaida Sarki" ta faɗa tana ɗauko plate ɗin abincin. Wani irin abinci ne kamar fankasau sai dai shi ɗin nama ne birjik a tsakiyar sa, tauna ɗaya DEENAH tayi masa taji yayi mata daɗi sosai. Murmushi Grandma tayi tace "Yayi miki daɗi sosai koh, ai nasan zaki so shi shiyasa nayi miki shi, kada ki damu a hankali zan koya miki irin girkunan mu na nan, sannan a hankali zaki koyi cin wasu." Ita dai DEENAH kawai murmushi take tana saurarar ta. Bayan ta gama breakfast ɗinne Grandma da kanta ta haɗa mata ruwan wanka gudun wai kar a sanƴa wani abin cutarwa a cikin ruwan, bayan DEENAH ta fito daga wankan ne kuma ta tadda wani dogon gown ɗin kuma mai kyau akan bed, ta komai nasa, kallon ta Grandma tayi tace "Masha Allah, wannan shine kayan da zaki saka bari na bar ki ki shirya cikin kwanciyar hankali, ni zan fita yanzun nan zan dawo kafin ki kammala. Kai DEENAH ta jinjina mata cikin murmushi tana binta da kallo ta fice daga ɗakin tare da rufo mata ƙofar. Maida duban ta tayi kan kayan kafin ta sake maida duban ta kan mirror ɗin dake shaƙe da kayan kwalliya kama daga kan lotions ɗin shafawa da dai sauran su, ɗakin ta kuma ƙarewa kallo tana sake jinjina girma dama kuma haɗuwar sa ganin irin dukiyar da aka sheƙa mata a ciki. A hankali taja kujera tana zama gaban dressing mirror ɗin kafin ta ɗau lotion mai kyau daga ciki ta shiga shafawa a jikin ta, dukda kuwa batasan koh zai kar6e ta ba dan kuwa sam ba irin company ɗin da take amfani dasu bane a wurin. Gashin kanta da ya sha ƙananun kitso ta sake feffesawa spray mai daɗin ƙamshi tare da sanƴa gashi walƙi, kwalli kawai tasa tare da shafa glowing lip-gloss a bakin ta. Miƙewa tayi ta shirya cikin inner-wears ɗinta da suka kasance irin kayan ne kafin kuma ta ɗau doguwar rigar tana jujjuya ta a hannu tana sake yaba irin kyawun sa. Tana cikin haka ne taji an buɗo ƙofar an shigo, saurin juyawa tayi tana sauƙe idanun sa cikin nashi, da sauri ta ɗaga rigar tana kare kanta dashi. Murmushi yayi yana kallon ta kafin yace "I promise i didn't saw anything." 6ata fuska tayi tace "What are you doing here?." "I...i..." shiru yayi yana kallon ta. "Get out and let me get dressed." Tsaye yayi yana sake dafe bakin ƙofar yace "No." Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "Please." "I can get you dressed" ya faɗa cikin ɗaga mata gira. "No, get out please." Sake gyara tsayuwar sa yayi kafin yace "I really wanna see you get dressed, go on." "This isn't right" ta faɗa. "What is not right here, seeing my wife get dressed infront of me?, strange." A hankali ta shiga ja da baya, tana targetting ƙofar bathroom ɗin bayan ta, a hankali shima ya shiga takowa hannayen sa sarƙe cikin aljihu yana ƙare mata kallo. "S...s..s..stop right there, don't you dare come closer" ta faɗa cikin rawar harshe. "I really can't imagine this, my own wife forbidding me from watching her get dressed." "Please Abyad, ka tsaya a inda kake, baikamata ka kalle ni haka ba." Ganin tana yi kamar wacce zatayi kuka ne ya sanƴa shi dakatawa yace "Fine then, five minutes ki gama shiryawa or else zan dawo idan na dawo kuma ba zan fita ba." Saurin jinjina masa kai tayi nan ya saki murmushi yana juyawa ya fice daga ɗakin tare da rufo mata ƙofa. Ajiyar zuciya ta sauƙe a hankali tace "He is unbelievable" kafin ta shiga sanƴa kayan. Sosai ya zauna mata ɗarass a jiki kamar wanda an gwada ta kafin a haɗa shi. Mayafin sa da ɗankwalin sa ta gani nan ta ɗau ɗankwalin ta shiga ɗaurawa akanta. "Ba haka ake ɗaura shi ba" ta sake jiyo muryar sa yana buɗo ɗakin ya shigo. Mamaki ne ya cika ta nan ta saki baki tana kallon sa, murmushi yayi yana ƙarasowa tare da amsar ɗankwalin a hannun ta. Ganin yadda take yi masa kallon tuhuma ne ya sanƴa shi faɗin "I promise ban leƙe ki ba." "Really?, ban fah tambaye ka ba tukun, that means la6ewa kayi kana kallo na kenan koh?." "Ahm well, maybe" ya faɗa. Tsuke fuska tayi kawai tana cigaba da kallon sa. Nan ya sake faɗin "By the way you have an attractive body shape." Sake tsuke fuska tayi mamakin sa fal cikin zuciyar ta, ashe haka yake bayida kunƴa take faɗa a zuciyar ta. Murmushi yayi ganin yadda take kallon nasa, ɗankwali ya shiga ɗaura mata irin yadda ake yi. Kafin ya ɗauko mayafin ya shiga yi mata rolling ɗinsa irin yadda sukeyi. Dube-dube ya fara nan tace "What are you looking for?." "Pins" ya bata amsa. Hannu tayi masa pointing gaban mirror still fuskar ta a tsuke shi dariya ma ta bashi daukar pin ɗin yayi ya shiga tying mata. Sosai tayi kyau kayan ya kar6e ta kamar wata Balarabiyar. Grandma ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Ƴar nan kiyi haƙu..." kasa idda maganar tayi kafin kuma tace "Kai mai kakeyi anan?." "Ohh me?" ya faɗa yana nuna kansa. "A'a wancan" ta faɗa tana pointing reflection ɗinsa na jikin mirror. Murmushin da batayi niyya bane ya su6uce mata, kallon ta Grandma tayi kafin tace "Masha Allah kiyi kyau sosai, wa ya ɗaura miki wannan gyalen lallai yayi kyau sosai." Murmushi tayi tana kallon ZEEYAD da shima murmushin yake. Takalmin mai ɗan tsayi Grandma ta ɗauko mata tare da bata ta sanƴa, kallon ZEEYAD tayi tace "Zaka wuce kaje ka shirya ne koh yaya." Murmushi yayi idanun sa kan DEENAH ya bar ɗakin. Taimaka mata da sauran shirin Grandma tayi, nan ta fito tayi kyau sosai. ************************ ________Zaune suke a fadar inda ya tara manƴan baƙi dama kuma Family baki ɗaya. YAZEED na hango zaune cikin kyakkyawar shigar sa da tayi masa matuƙar kyau, gefe da gefen sa kuma matan nasa ne, sosai fuskar sa ke a matuƙar ɗaure babu walwala koh kaɗan. Ita ma Jalilah sam fuskar ta babu wata wadatacciyar walwala, sam bata yarda ta kalli inda DEENAH da ZEEYAD ke zaune ba, dan kuwa tunda har aka ɗaura auren ta da YAZEED ta cire sa daga ranta. Ɗayan gefen kuwa wata ƴar budurwa ce itama ba laifi da ɗan kyawun ta sai dai koh kaɗan bata kamo ƙafar Jalilah ba. Fitowar sarki ya sanƴa kowanne daga cikin su nutsuwa inda take surutun da akeyi yayi ƙasa. Zama mai Martaba yayi yana kallon ƴaƴan nasa cike da ƙaunar su, kafin kuma yayi gyaran murya ya fara faɗin "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, this is indeed a happy day for me, ganin yara mafi soyuwa a gareni sun mallaki nasu iyalan, babu abinda zan iya cewa sai Allah yayi muku albarka ya kuma sanƴa albarka cikin rayuwar auren ku." Duk da Aameen wasu daga ciki suka amsa, murmushi yayi yana kallon ZEEYAD da DEENAH kafin ya maida duban sa kan YAZEED da matan nasa, duk sai yaji zuciyar sa babu daɗi ganin babu wata annashuwa akan fuskar YAZEED ɗin. Kowane ango na kasancewa cikin farin ciki ne a ranar auren sa ba amma sai gashi YAZEED baya farin ciki da hakan which is all because of son rai irin na mahaifiyar sa. Gyaran murya yayi kafin ya kalli ɗaya daga cikin ministoci tare da kiran sunan sa yace "Ka gabatar musu da kyaututtukan wa amaren nasu." Duƙar da kai yayi cike da girmamawa kafin kuma cikin ɗagun murya ya fara faɗin "Mai Martaba adalin sarkin mu yana maraba da surukan sa hakan ya sanƴa shi yiwa kowacce daga cikin matan ƴaƴan nasa kyauta mai tsoka, amaryar Yarima ZEEYAD wanda yake shi ne babba daga kanta za'a fara, mai Martaba ya mallaka mata biyar daga cikin manƴan raƙumar sa haɗi da kujerar Hajji ta wannan shekara." Ɗago da idanu DEENAH tayi tana sake damƙe hannayen ta dake cikin na ZEEYAD, she can't believe her ears. "Yayin da kuma amaren Yarima YAZEED kowacce daga cikin su itama tana da kyautar raƙuma biyar haɗi da kujerar Hajji, baya ga haka kuma Sarki yayi wa Uwargidan Yarima YAZEED kyauta ta musamman wato kyautar santaleliyar mota ta miliyan goma sha takwas, yayin da amaryar sa kuma akayi mata kyautar babban fili dake a wajen MASARAUTA." Wani irin gimtse fuska yarinƴar tayi da jin kyautar da akayi mata, above all abubuwan kyalli-kyallin duniyar nan sai a rasa kyautar abinda za'a yi mata sai na fili? "Wannan shine dalilin tara ku anan da akayi kowa yaga sabbin amaren sannan kowa ya shaida kyautar da sarki yayi musu dan haka zaku iya watsewa." Wani ne ya gaya masa magana a kunne nan yayi saurin dakatar da mutanen dake shirin tafiya da faɗin "Ku ɗan jinkirta kaɗan da akwai manƴan baƙi dake son yiwa amaren kyautar ban girma." Kallon ZEEYAD DEENAH dake jin ta kamar a ƙaya tayi, duk a takure take gani take ita kaɗai ce bare a cikin su sabida babu ƴan uwanta koh ɗaya a wannan wurin, a hankali tace "Abyad?." Kallon ta yayi yace "are you Okay?." "Zamu iya tafiya?." Damƙe hannun ta yayi cikin nasa yace "Don't panic please am here." Shiru tayi kawai bata sake cewa komai ba. Baƙin dake wurin ne suka fara zuwa suna presenting gifts ɗinsu a gaban amaren, sosai DEENAH da Jalilah suka kwashi gifts masu yawa inda dukkanin su murmushin yaƙe kawai sukeyi. Sarauniya Nazeerah ce itama ta taho da kuyangun ta a baya suna riƙe da abubuwan da zatayi wa amaren kyauta dashi. Gun DEENAH ta fara nufa, ɗago da ha6ar DEENAH tayi tana kallon ta tace "You're such a cutie Darling." Ɗan murmusawa kawai DEENAH tayi tana sadda kai ƙasa, kar6ar kwalin hannun ɗaya daga cikin su tayi tana ajiyewa DEENAH a gaban ta tace "This is for you dear, for the first time i saw you that day na tabbatar da wadannan awarwaro zasuyi miki kyau, accept them from me please" ta ƙarashe cikin murmushi tana kallon ta. Kai DEENAH ta jinjina mata nan ta buɗe kwalin inda wani set ɗin hand Bangles na gold masu bala'in kyau da tsada suka bayyana. Waro idanu amarya YAZEED tayi ganin irin babban kyautar da Sarauniya Nazeerah ke baiwa DEENAH, she just hope ace nata ma kamar hakanne koh fiye dashi ma. Hannun DEENAH ta kama ta sanƴa mata awarwaron inda suka zauna mata ɗas sukayi mata kyau sosai a hannu, murmushi tayi tace "Masha Allah, Allah yayi wa rayuwar ki albarka." "Nagode sosai" cewar DEENAH. Kallon ZEEYAD da fuskar sa ke a matuƙar tsuke Nazeerah tayi bata ce dashi komai ba ta miƙe ta nufi wurin Jalilah, Itanma Bangles ɗin GOLD mai kyau da tsada tayi mata, sai dai design ɗin nata ya banbanta da na DEENAH. Kafin kuma ta nufi gun amaryar YAZEED nan tace mata "Tun farkon gani da nayi miki ba zan 6oye miki ba jini na bai ɗauke ki ba, so accept this little gift from me please, don't be offended" ta faɗa tana miƙa mata kwalin sarƙa da ƴan kunne. Amsa tayi kafin a hankali tace "Are they GOLD?." Murmushi Nazeerah tayi kafin tace "Kwarai kuwa gwal ce, kin ta6a ganin inda matar sarki tayi kyautar da ba gwal ba, sai dai Let me be honest with you naki bai kai nasu kyau da tsada ba" tana faɗin haka ta miƙe ta bar ta nan zaune. Sosai zuciyar yarinƴar ya shiga burning ganin duk kowa yafi nunawa Jalilah ƙauna akan ta most especially DEENAH wanda ta rasa abinda suka gani a jikin ta da suke ta rububin ta haka, kallon tulin kyaututtukan dake gaban DEENAH tayi tanajin zuciyar ta na ɗaci, kafin ta maida duban ta kan fuskar DEENAH ɗin. Mistakenly DEENAH ta ɗago tana sauƙe idanun ta cikin na yarinƴar taji gaban ta yayi wani irin mummunar faɗuwa. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR..................✍🏽* [8/28, 7:58 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *048...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _________Saurin sadda kai DEENAH tayi tana runtse idanun ta zuciyar ta na dukan tara-tara. Motsa hannun sa ZEEYAD yayi nan ta ɗan ɗago ta kallesa, alamun yayi mata da meke damun ta inda tayi saurin girgiza masa komai kan bakomai tana maida kanta ƙasa. Kauda kanta amaryar YAZEED tayi tana wani irin tsuke fuska haɗi da hura hanci. Kallon inda ZEEYAD da DEENAH ke zaune Sarauniya Hafeezah tayi kafin ta miƙe daga kan kujerar ta, Rahina ce tayi saurin faɗin "Ummie ina zaki?." Hafeezah bata kula ta ba tazo tsakiyar wurin ta tsaya inda kowa ya tsaya yana kallon ta nan, idanun ta kan DEENAH take faɗin "Your Highness how on earth zaka yarjewa ɗanka auren wannan yarinƴar, she was his brothers Ex, am definitely sure da wani mummunar ƙudirin ta shigo cikin MASARAUTAR nan, tayi soyayya da YAZEED ganin burin ta ba zai cika akansa bane kuma tayi dukkanin yadda zatayi ta koma soyayya da ɗanka, ba wai ina faɗin haka bane sabida na damu da ZEEYAD but sabida ina da ƴaƴa cikin wannan MASARAUTAR and GOD knows abinda zata aikata muddin ta zamto Sarauniyar ga wannan fadar..." "Hafeezah!" mai Martaba ya katse ta a tsawace. Juyawa tayi tana kallon sa kafin kuma yace "Mai kike faɗa ne haka?, you should know your limits." "Yakamata ka fahimci cewa ina ƙoƙarin kare ƴaƴan ka ne daga tuggun wannan yarinƴar, ni na tabbata ba haka kurum ta bar ɗanka ba, babu ta yadda za'ayi ZEEYAD yaso kamar ta, na tabbata asirce shi tayi dan ta samu damar biyan dukkanin buƙatun ta..." "Enough of this, i can't take this anymore" faɗin ZEEYAD da ransa ya soma 6aci sosai. "Hold it there Young boy, ba da kai nake ba so don't you dare try to interrupt me, am doing this for my children's Peace, ba zan ta6a bari wannan abar da ka ɗauko a matsayin mata ta nemi lalata mana MASARAUTA akanka ba, ƴar talakawa irin ta, she is not even from a royal family so then how on earth zaka amince da auren sa da yarinƴar da ba ma ƴar ƙasar sa bane, itace zaku ɗauko a matsayin wacce zata zamto future Queen na wannan MASARAUTAR, i can't believe you guys, yakamata ka sake tunanin ranka ya daɗe this girl here doesn't deserve to be the Queen of this kingdom." "Ya isheki haka Hafeezah." "Let me talk your Highness, let me said my mind, kodai kai ɗinma ta asirce ka ne, kada ka bari son da kake yiwa ɗanka ya rufe maka ido ka kasa ganin gaskiya, nasan ni ba wacce zaka yarda da ita bane sabida baka ɗauke ni da muhimmanci ba, but atleast yakamata kayi nazarin kalamai na, yarinƴar nan sam ba haka nan ta bar wannan yaron ba, she has something bad in her mind trust me." "Enough of this Hafeezah, i won't let you said something bad about DEENAH again" faɗin Grandma itama cikin 6acin rai. "Am not saying anything bad about your in-law face gaskiyar abinda na sani kuma na gani, this girl here is using a spell against all of you shiyasa ba zaku ta6a ganin laifin ta ba, kuma kuke ƙoƙarin kare ta, sannan duk mun sani amfani da sihiri mummunan laifi ce a dokar MASARAUTA..." Sosai ZEEYAD yake neman tanka mata sai dai ganin YAZEED ya sanƴa shi jin ba zai iya tozarta mahaifiyar sa a gaban sa ba, komin ƙin ta da yake yi dole ne yaji babu daɗi game da abinda zai iya yi mata a yanzun. "Hafeezah stop accusing an innocent girl, she just arrived to the PALACE yesterday, how on earth kuma kike zargin ta da aikata wannan mummunar laifin?." "Ba zargin ta nake ba, bata kai matsayin da zan zarge ta kokuma na ɗaura mata sharri ba." "Then wacce shaida kike dashi kan batun da kike faɗin ta aikata?." Shiru tayi wani irin farin ciki na lullu6e mata zuci na ganin plan ɗinta is about to be achieved, nan tace "Ofcourse ina da shaidu bama shaida ba." Duk tsaya kallon ta sukayi cike da mamaki kafin ta juyo ga DEENAH da hawaye ya gama wanke mata fuska tace "What happened young lady, kina tsoron tonuwar asirin ki ne?, muddin kinsan kina da gaskiya baikamata kike zubda kwalla haka nan ba, ai duk wani mai gaskiya bayajin tsoron tonuwar abinda bai aikata ba." Janƴo DEENAH ZEEYAD yayi jikin sa yana wullawa Hafeezah mugun kallo, murmushin gefen baki Hafeezah ta saki kafin ta tsinkayo muryar mai Martaba na faɗin "Hafeezah, kinsan da cewa duk wanda aka kama da aikata aikin asiri dumu-dumu hukuncin sa ba mai sauƙi bane, inason ki gabatar min da shaidun da kike dashi yanzun nan anan." Kallon mai Martaba ZEEYAD yayi cike da mamaki kafin yace "Your Highness what are you saying?, matata ba zata ta6a aikata abinda ake zargin ta dashi ba, she is innocent and i trust her." "Yardar da ka bata ne ya sanƴa ta samun damar aikata dukkanin wani abu da taga dama a gareka." "We can't prove how innocent your wife is until an bincika an gano hakan kamar yadda doka ta tanada." "What are you saying, wannan tozarci ne babu wanda ya isa yazo min kusa da mata da sunan bincika wani abu a jikin ta." "Ba a jikin ta abin yake ba, but a ɗakin da aka sauƙe ta" cewar Hafeezah. "I know you don't like me, but dukkanin wani abu da zaki aikata ya tsaya akaina, do not include my wife please" cewar ZEEYAD yana kallon Hafeezah dake kallon sa. "Hafeezah kiji tsoron Allah, yaushe ne har kikaje ɗakin da aka sauƙe DEENAH kika gano tana aikata wani mummunan abin da sunan asiri?" faɗin Grandma. Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Ba nice naje koh na gano hakan ba, bayin dake aiki a 6angaren ki ne suka gano hakan." Wani irin mugun kallo Grandma ta watsa mata kafin tace "Kada ki nemi ki kawo mana rainin wayo anan Hafeezah, DEENAH ba zata ta6a aikata abinda kike zargin ta dashi ba..." "Seriously, i can't believe har kin yarda da ita haka tun kafin ki zauna da ita ki san abinda zata iya aikatawa dama kuma wanda ba zata aikata ba, the girl is controlling you guys, by casting a spell on you." "Enough, ina shaidun da kika ce kina dasu, ina buƙatar ganin su yanzun nan anan wurin." "Kwarai kuwa nasan da cewa za'a neme su hakan yasa na umurce su da su kasance kusa" kafin kuma ta hau waige-waige tare da faɗin "Kuna ina?." Wasu mata ne guda uku suka fito daga cikin crowd ɗin kansu rissine a ƙasa suka zube gaban sarki. "Gasu nan, sune shaidun da nake dasu, sannan sune suka kawomin labarin." Kallon su Grandma tayi kafin tace "Layuza, Rakiba, mai kukeyi anan?..." "Sun zo bada shaida ne akan abinda idanun su suka gane musu" cewar Hafeezah cikin katse Grandma tana kallon ta. Mai Martaba ne yace "Hafeezah, muddin dukkanin abinda kika faɗa ya zamto ba gaskiya bane, toh ki sani hukuncin ki sai ya cuna wanda akewa wadanda aka kama da aikin asiri, idan kuwa ya zamto abinda kika faɗa gaskiya ne toh tabbas za'a hukunta mai laifi dai-dai da abinda dokar MASARAUTA ta tanadar." "You can't do this, and i won't let you do this, why will you even believe what she said?..." "Son am sorry but kai kanka kasan sabuwar dokar MASARAUTAR and you approved it yourself, jin zance da ya shafi asiri koh da an san mutum ba zai iya aikata abinda ake zargin sa dashi ba ya zama dole a bincika a gano gaskiyar lamari, ni kaina ban yarda da maganar Hafeezah ba sai dai wajibi ne a gareni a matsayin adalin shugaba nayi duba akan abinda ta faɗa, zuwa gareku, kune kuka zo wa da Hafeezah da zancen kunga amaryar Yarima ZEEYAD na aikata wani abu da yayi kamanceceniya da asiri?" ya faɗa yana maida akalar tambayar sa kan bayi matan dake zube a gaban sa. "Kwarai kuwa ranka ya daɗe, ni nan baiwa ce a sashin Sarauniya Hafeezah, su kuma wadannan ƙawaye na ne sannan suna aiki ne a sashin Hajiya babba sune suka zo min da wannan labarin, nikuma banyi ƙasa a guiwa ba naje na sanar da Sarauniya, shine ta yanke shawarar yiwa abin tufkar hanci tun da wuri." "Hakane?." Kai suka jinjina masa kafin ɗaya tace "Haka ne ranka ya daɗe, da idanun mu muka ganta jiya." "They are lying, how dare them accuse my wife of doing such a terrible thing..." "Enough Son, ka bar su su ƙarasar da abin da suke faɗi." "I can't believe you also, kana biye musu that means ka yarda da sharrin da suka ɗaura mata kenan" ya faɗa cike da 6acin rai yana kallon mahaifin nasa. Shiru mai Martaba yayi yana maida duban sa kan bayin kafin yace "Proceed." Shiru sukayi na ƴan seconds kafin ɗaya tace "A daren da aka kawo ta wato daren jiya kenan, bayan mun zo wucewa ta ƙofar ɗakin da aka sauƙe ta ne muka ji kamar alamun wasu sumbatu cikin yaren da bamu san koh menene ba, koh da muka ji hakan, sai muka yanke shawarar leƙawa ta taga dan ganin abin dake faruwa cikin ɗakin..." shiru tayi ta kasa iddawa. Ɗayar ce ta ɗaura da faɗin "Koh da muka leƙa ba ƙaramin tashin hankali muka shiga ba da abinda idanuwan mu suka gane mana, durƙushe muka ganta idanun ta a rufe yayin da bakin ta ke ambatar abinda bamu da masaniya akan koh menene, ba'a jima ba wani jan haske ya fito daga cikin tafin hannun ta, nan mukaji tana kiran sunan Yarima Z..." "Hold it right there lady, jiya da misalin ƙarfe nawa ne kika faruwar abin" faɗin Grandma cikin katse ta. Shiru duk sukayi kafin tayi saurin faɗin "Da misalin ƙarfe sha ɗayan dare ne." Dariya Grandma tayi tace "Silly souls, ai jiya har ƙarfe ɗayan dare muna tare da DEENAH, babu abinda muka kwana munayi tare da ita wanda ya wuce sallah da roƙon Allah akan sharrin makiya, mahassada dama kuma annamimai irin ku, ranka ya daɗe mai Martaba ina da shaidar da zai tabbatar maka da cewa ina tare da ƴar jika ta jiya har misalin ƙarfe ɗayan dare, idan ma shaida kake so ga nan manƴan hadimai na kusa dani ka tambaye su." Kallon matan dake bayan Grandma mai Martaba yayi yace "Menene gaskiyar wannan lamari?." Ɗaya daga ciki ce tace "Kwarai kuwa ranka ya daɗe jiya ai a ɗakin Hajiya Babba ma ta kwana sabida gudun kada ta kasance ita kaɗai wani mummunan abin ya same ta, tunda ba wai masoya shi mijin nata ke dashi cikin fadar nan ba." Kallon su yayi yace "Mai zakuce akan wannan batu, Hajiya babba ta shaida cewa tana tare da amaryar Yarima haka ma hadiman ta, ku kuma mai zaku iya cewa game da wacce kuka gani ƙarfe sha ɗayan?." Shiru duk sukayi suna wuwwula idanu cike da rashin gaskiya, kafin ɗaya tayi caraff tace "Nayi maka rantsuwa ranka ya daɗe mun ganta, har ma abinda ta sanƴa ƙarƙashin gado dan asirce wani daga cikin ku." "They are lying i...i...i didn't do anything" faɗin DEENAH cikin kuka ganin yadda suke ta ya6a mata sharri. "Naji dukkanin bayanan ku, muje a duba ƙarƙashin gado inda kuka ce ta sanƴa abin, muddin aka samu wani abu toh tabbas hukunci zai hau kan matar Yarima, muddin kuwa na gano sharri kukayi mata toh tabbas sai kun fuskanci hukunci mai tsanani tare da nadamar hakan." "Mun amince ranka ya daɗe" suka haɗa baki wurin faɗa. Murmushi Hafeezah tayi tana juyawa ta kalli DEENAH tace "Wannan karon haƙar ki ba zata cimma ruwa ba Young lady, let's go and find out what she is hiding under that bed." Hawaye kawai DEENAH keyi haɗi da nadamar kasancewar ta cikin wannan family masu nuna wa junan su tsantsar ƙiyayya, riƙo ZEEYAD tayi ƙam a hankali take faɗin "They are lying babu abinda na aikata muku, please believe me." Rungumo ta yayi kawai dan kuwa baya tunanin zai iya magana jin yadda wani abu mai ɗaci ya tokare masa maƙoshi. "Alright then Hafeezah tunda kin ƙeƙashe cewar DEENAH ta aikata asiri then muje a duba cikin ɗakin nata, muddin aka samu wani abu toh ina goyon bayan hukunta ta bisa ga karya dokar MASARAUTA da tayi, muddin kuwa ba'a sami Wani abu kamar yadda suka faɗa ba then ya zama dole DEENAH itace wacce zata za6i irin hukuncin da za'ayi musu bisa ga sharri da suka ɗaura mata." Kallon juna sukayi kafin suce "Mun amince, ayi mana dukkanin hukuncin da aka tanadar muddin ya kasance sharri mukayi mata." Kallon Grandma ZEEYAD yayi nan ta jinjina masa kai akan ya kwantar da hankalin sa. YAZEED tashi yayi ya bar musu fadar dan kuwa abin na mahaifiyar sa ya fara yin yawa, da kallon tausayi ZEEYAD ya bisa kafin kuma ya tsinkayo muryar mai Martaba na bada umarnin aje a duba ɗakin da aka sauƙe DEENAH ɗin. Kallon su Hafeezah tayi tace "Am trying to save my children daga faɗawa halaka ta sanadiyyar wannan abar da ka auro, dan haka let's wait and see koh ita ɗin mai gaskiya ce kamar yadda kai da kakar ka ke faɗi." Jan hannun DEENAH yayi da niyyar barin fadar ya tsinkayo muryar mai Martaba. "You know that you're not allowed to leave here until an aiwatar da dukkanin bincike." Juyowa yayi a fusace yace "This is humiliating and i can't stand someone accusing my wife of doing something bad, kamar yadda i won't allowed anyone to touch her da sunan kama ta da aiwatar da wani laifi." "Boy lower your voice, sannan ka jira sakamakon abinda zasu taho dashi bayan sunje sun bincika ɗin." "Grandma you're supporting them, kema kin yarda DEENAH zata aikata abinda suke zargin ta dashi, we all know this selfish woman here only cares about her happiness and she would stop at nothing har sai taga farin cikin wasu ya ruguje, i can't believe all of you here da yarda da zancen ta dama kuma na wadannan bayin da ta saya against DEENAH." "Listen Boy, daga ni har mahaifin ka babu wanda ya yarda da abinda Hafeezah ta faɗa but in order to prove her wrong ya zama dole a gudanar da bincike kamar yadda doka ta tanadar." "But Grandma i did nothing, why will she accuse me of using a spell against you?" cewar DEENAH da zuciyar ta ke mugun burning. Share mata hawaye tayi kafin tace "Listen DEENAH, i know baki aikata abinda ake zargin ki dashi ba, this doesn't make sense at all, i mean jiya shigowar ki cikin gidan nan, koh da kuwa da sharri kika shigo ba zaki fara aiwatar da ƙudirin ki tun wuri haka nan ba, i know you're innocent and gaskiya zatayi halin ta yau ɗinnan." Ita dai DEENAH kanta sadde a ƙasa tana cigaba da shessheƙa. Mai Martaba ne ya sanƴa aka kira masa guards wadanda aikin su ne bincike aduk sadda aka kama wani da laifin aikata wani abin, kafin ya umurce su da suje su dubo masa ɗakin. Kallon DEENAH amaryar YAZEED tayi tanajin wani irin farin ciki a ranta, dan kuwa ba ƙaramin burge ta Hafeezah tayi ba. JALILAH kuwa jikin ta ne yayi matuƙar sanƴi duk sai tausayin DEENAH ɗin ya kama ta. Naseeba dake tsaye da munafukar jakadiyar ta Kiki ce tace "I wonder mai ya gani jikin yarinƴar nan da har zata ɗauke masa hankali ya auro ta a matsayin mata." Murmushin gefen baki Kiki tayi tace "Ranki ya daɗe ai kishi ma kaɗai ba zai hana ki ganin abinda ya gani jikin yarinƴar nan ba, but zan iya yin rantsuwa duk matan dake cikin nan babu wacce zata nuna mata kyau sai dai hasken fata, uwa uba gata da diri mai kyau dan dama naji ƴan chan ƙasar tasu ba dai iya kula da namiji ba tare da basa dukkanin wasu haƙƙin auren sa ba, kinga kuwa Yarima abubuwa dayawa ya gani game da yarinƴar nan wanda shi kaɗai ya barwa kansa sani, ni duk sai naji ta burge ni ma..." Mugun kallon da Naseeba ta watsa mata ne ya sanƴa ta saurin sadda kai ƙasa tana jan mayafin kanta tare da faɗin "Afuwan ranki ya daɗe, ni banyi dan na 6ata miki rai ba, kawai dai na faɗi ra'ayi na ne tunda ba wai nasan koh kin tsane ta koh baki tsane ta bane ba." "Wannan wace iriyar maganar banza kike?, ke kanki kinsani duk wacce ta ra6i ZEEYAD a shirye nake da dealing da kowace sakarya ce ita, it's a pity da ya kasance ba ni kaɗai ce maƙiyar ta ba, but that won't Stop me daga aiwatar da abinda na ƙudurta a raina, ya zama dole nayi gaggawar aiwatar da wani abin tun kafin ya kusance ta, ta nan ne kaɗai zan iya samu burin dake cikin raina ya cika, ki koma wurin kakar ki ki kar6o min dukkanin wasu abubuwan da zan buƙata wurin aiwatar da aiki na kafin dare yayi a kaita ɗakin sa, dan kuwa i won't stop at nothing har sai haƙa ta ta cimma ruwa jeki yanzun nan." "An gama ranki ya daɗe" ta faɗa cikin sadda kai tana wucewa da sauri dan zuwa aiwatar da abinda Uwargijiyar tata ta sanƴa ta. Ajiyar zuciya Sarauniya Nazeerah ta sauƙe tana ƙarasowa inda Hafeezah ke tsaye cikin raɗa yadda babu wanda zai ji mai take cewa bale ta san da ita take magana tace "Listen Hafeezah, don't you dare try to do something silly to this innocent girl here, bata tauye miki komai ba, da mijin ta kaɗai kike ƙiyayyar ki, everyone knows bana shiga abinda bai shafe ni ba, but, you just be careful ki rage wannan ƙiyayyar taki da bata da ranar yankewa coz da dukkanin alamu wannan yarinƴar ce zata zamto sanadiyyar tonuwar asirin ki, the girl da kika raina tabbas will be your downfall Hafeezah" tana faɗin haka ta ɗan ja da baya tana kallon reaction ɗin Hafeezah wacce daga gani ranta ya kai maƙura wurin 6aci. Suna nan tsaye wadannan Guards ɗin suka dawo kai tsaye gaban mai Martaba suka zube kansu duƙe. Kallon su mai Martaba yayi yace "Inajin ku." Babban su ne ya fara faɗin "Duk wani wanda yayi wa sarki ƙarya toh kuwa babu shakka ya aikata babban laifi sannan hukuncin hakan zai hau kansa kamar yadda dokar MASARAUTA ta tanada, musamman ma ace ga wanda akayi wa ƙazafin ya kasance ɗan cikin MASARAUTA ne, mun je mun duba koh ina na cikin ɗakin sannan..." "Wannan wace iriyar maganar banza kake faɗi, ka tafi kai tsaye ga abinda aka tura ka nema mana, miye kuma na wani jan zance, ka faɗa kowa yaga gaskiyar ainihin wannan annobar da ya ɗauko..." Maganar ta ce ta katse sakamakon jin abinda ya faɗa, manƴan idanun ta ta waro tamkar zasu zubo daga cikin socket ɗinsu. "Maganar banza kake faɗi, na yarda da baiwa ta sannan nasan ba za..." "Hafeezah" mai Martaba ya katse ta a tsawace kafin ya ɗaura da faɗin "Tabbas kin raina mana hankali sannan kin maida ni ƙaramin mutum a idanun jama'a musamman a gaban innocent girl da kika ɗaurawa sharrin aikata abinda batayi ba." "M...mai..mai kake faɗa ne haka ranka ya daɗe?, tayaya zanyi mata sharri ba fah ni na ganta da idanu na ba, ga nan wadanda suka kawomin labarin abinda ya faru, dama ba shaidu uku ake nema ba kafin aje ga aiwatar da wani abin, su suka shaida min da..." "Ke wace iriyar sakarya ce da zaki ɗau maganar bayi ki yarda dashi har ma ki kai ga tozarta yarinƴa a gaban jama'a?, hukunci zai hau kan kowannen ku daga ke har su bayin naki." Idanu ta waro cike da tashin hankali tana kallon sa tace "Hu..hukunci, toh akan mai?, akan nayi ƙoƙarin ceto ku daga faɗawa halaka sabida an zo min da zancen kuma har mutane uku na tabbatar da hakan daga garesu, shine kake cewa hukunci ya hau kaina ai a doka ma banida laifi, sabida ba ƙarya nayi na cewar na ganta da idanu na tana aikata sihiri ba, koh da akwai wadanda za'a hukunta bai wuci wadannan bayin bane, ba kai kaɗai aka raina wa wayo anan ba hatta ni nan sun maida ni ƙaramar mutum sabida yadda na dage akan gaskiya suke faɗi, sai gashi kuma ba haka bane." "Dan girman Allah ranka ya daɗe kayi haƙuri kayi mana rai, mu mun tabbatar da abinda idanuwan mu suka gani ne, sai dai koh idan basu duba bane da kyau." Grandma ce tace "Kai ku dakata haka nan, ai daman nasan sai an kai ga haka wannan ne dalilin da ya sanƴa ni tanadar shaida sabida nasan tsinannen makirci irin taku, yanzu sai ku haɗa ƙarya tuburan duk sabida ku sanƴa wani cikin gagarumar matsala toh ahir ɗinku dan kuwa tundaga sama har ƙasa na tofe ƴata da turaren da addu'ar masu mugun hali ire-iren ku, ku ba'a tauye muku komai ba amma ku kunfi kowa tsanar mutum, Allah yayi wa Boy ɗina albarka da saya min ƴar wayar zamanin nan da yayi ai koh bakomai yau tayi rana, dama jira nake naga iya gudun ruwan ku, daga shigowar yarinƴa jiya har kun fara kai mata hari, ku abin ma yayi muku yawa, ga talauci ga kuma hassada da ta mamaye maku zuci tayi muku naƙe-naƙe, ai daman jira nake naga iya gudun ruwan ku, tunda kuka ɗaurawa DEENAH sharrin abinda bata aikata ba toh kuwa kun buɗo wa kanku ƙofar wahalar da bata da ranar yankewa har ku mutu shegu masu kama da ƴaƴan 6era." Shiru duk fadar tayi kowa ya tsaya kallon Grandma da ta ciro wayar ta cikin aljihun rigar ta tana latsawa, inda ta haɗa da faɗin "Ni za'a nunawa tantiran ci na daɗe da gano akwai munafukai a 6angare na, sai gashi yau asirin biyu ya tonu da izinin Allah na sauran da nake targetting zai tonu dan kuwa ba'a jini na bane zama da munafukai, duk inda munafuki yake kusa dani toh tabbas sai naji a jiki na, miƙawa mai Martaba wannan wayar yaga abin dake ciki da idanun sa" ta faɗa tana miƙa wayar wa ɗaya daga cikin guards ɗin da suka je binciken. Mai Martaba aka baiwa wayar inda ya kafe ta da idanu yana ganin lokacin da suke sanƴa abin a ƙarƙashin gado suna ɗan waige-waige kamar yadda suka ce DEENAH tayi, kafin su sanƴa ɗaya cikin ƙasan rug ɗin dake shimfiɗe a ɗakin, sai da suka gama kafin su sake waigawa suna ficewa daga ɗakin da sauri, nan Grandma kuwa ta shigo tana cire abubuwan da suka sanƴa ɗin mai kamar wasu manƴan layoyi. Sosai ran mai Martaba ya 6aci da ganin video ɗin, dan haka maidawa Grandma wayar ta akayi, ba tare da ya kalli ministocin sa ba yace "Menene hukuncin wanda yayi wa wani ƙazafin asiri alhalin shine mai aikata hakan ya ɗaurawa wani?." Shiru fadar ta ɗauka kafin ɗaya daga cikin ministocin yace "Bisa ga dokar marigayi hukuncin sa shine, horo mai tsanani na watanni biyu kafin kuma azo a rataye shi sabida shima ya aikata asirin ne koh da kuwa sanƴa shi akayi ba yin kansa bane." "Dan girman Allah ranka ya daɗe kayimin rai, wallahi nayi nadamar aikata hakan, kayi min rai" cewar ɗaya daga cikin su cikin ihu da ƙururuwa . "Kuje dasu sannan ku yanke musu hukunci dai-dai da abinda suka aikata." Sosai Sarauniya Hafeezah taji haushin rashin cikawar plan ɗinta, tsoron ta ɗaya kada su buɗi baki suce itace wacce ta sanƴa su, duk da kuwa ba ƙaramin warning da barazana tayi musu ba. "Wait" cewar ZEEYAD. Tsayawa guards ɗin sukayi daga fitar da matan waje nan yace "They can't leave without apologising to my wife." "Haka ne they should apologise for there misdeeds" cewar mai Martaba. Tunkuɗa su guards ɗin sukayi suna zubewa gaban ƙafafun DEENAH dake rungume a jikin ZEEYAD, cikin riƙo ƙafafuwan ta suke cewa ta yafe musu ta kuma sa a janƴe hukuncin da aka yanke musu ba zasu sake ba. Ɗauke kanta tayi daga kansu tana shigarwa jikin ZEEYAD tare da janƴe ƙafafun ta. "The future Queen batada niyyar yafe musu." "Then they should be executed, let this serve as a lesson to those having the intention ɗin aikata abinda sukayi" cewar mai Martaba. Ɗago su guards ɗin sukayi tare da fitar dasu daga fadar suna ihun ayi musu rai. Tsaye mai Martaba ya tashi tare da ƙarewa ƴan fadar kallo yace "Let this serve as a sound warning to you all, duk wani wanda ya aikata abinda wadannan mutanen sukayi toh babu shakka irin hukuncin da za'a yi masa kenan, Hafeezah" ya kira cikin Kakkausar murya. Tsorata tayi da yadda ya kira sunan nata nan ya cigaba da faɗin "You must be punished for believing your maids against an innocent girl, hukuncin ki shine zaki fita daga fada ki koma zama cikin bayi na tsawon sati biyu, the next time da na sake kama ki da irin wannan laifin i won't spare you, and i want you to apologise for your mistake." Shiru Hafeezah tayi tana kallon mai Martaba har ya kai zancen sa, there is no way da zata baiwa DEENAH haƙuri ba zai ma yiwu bane ba. "Yes i made a mistake but that doesn't mean i should bow infront of this little girl da sunan neman yafiya." "But you hurt her, so you must Apologise." "It's Okay, we're fine, we don't need her apology" cewar ZEEYAD kafin ya ɗaura da faɗin "Just tell her to be careful, and mind her own business with my wife, coz i won't take a single shit from her next time" yana faɗin haka yaja hannun DEENAH sukayi gaba. Da kallon tuhuma Grandma tabi Hafeezah da tayi tsuru-tsuru da idanu kafin itama ta mara musu baya tana faɗin "Just be careful next time Hafeezah." Da mugun kallo Hafeezah tabi ta zuciyar ta fal cike da baƙin ciki. ****************** _______"Kiyi haƙuri DEENAH, i know you're hurt da abinda Hafeezah tayi miki but tunda har gaskiya tayi halin ta ki godewa Allah sannan kiyi haƙuri ki daina kuka" cewar Grandma cikin rarrashin ta. Ita dai DEENAH sai kuka take bata ƙi ta ganta a gidan su yanzun ba, duk taji zaman nan ɗin baiyi mata ba, koh 24hrs bata cika a gidan ba amma gashi har an fara kawo mata hari kamar dama jiran ta ake. "Grandma she needs to rest so am taking her to my part" cewar ZEEYAD. Harara Grandma ta wulla masa tana faɗin "Mai kake nufi da zaka kai ta part ɗinka, leave her here ka kaita ɗaki na ta huta." "Ahm...actually she would like it more a part ɗina, she is even scared da zama a part naki yanzun." "Shikenan ai sai ka ɗauke ta ku tafi, sannan ka tabbatar da ka dawo da ita cin abincin rana, kuma ban ce kayi mata wani abin ba." Kallon ta yayi kafin kuma ya riƙo hannun DEENAH da har yanzu bata bar kuka ba suka fice. Zaunar da ita yayi bakin bed yana tsungunnawa a gaban ta tare da ƙura mata idanu yana kallo, he can see how deeply she is in pain. Tashi yayi tare da zuwa ya buɗe wani kyakkyawan ƙofa cikin ɗakin yana kutsa kai ciki, bai wani jima sosai ba ya fito hannun sa ɗauke da wata baƙar Abaya yana ƙarasowa kusa da ita yace "Get up let's get your dress changed." Tsagaitawa tayi da kukan tana ɗago da idanun ta ta kalle shi. Gira ya ɗaga mata yace "Bakya jin nauyin sa ne?, we should change it right?." Sauƙe idanun ta tayi tana share hawaye kafin ta miƙe tsaye tace "I will change it myself." Placing hannu yayi around her waist yana jawo ta jikin sa yace "I can see how tired you're, so let me help" ya faɗa yana kai hannu ya fara unzipping ɗin zip ɗin bayan rigar tata. Saurin kwacewa tayi tana ja da baya tare da faɗin "What are you doing?" zuciyar ta na racing, kafin kuma ta ɗau kayan tayi saurin shigewa inda taga ya shiga ya ɗauko kayan tana rufowa. Murmushi yayi haɗi da ɗan cize lips yana zama bakin bed ɗin. Da kallo taƙe ƙarewa inda ta shiga ɗin ganin kayayyakin sawa a jere kowanne da wurin zaman sa kai kace wani shopping mall ne na kayan sawa, ajiyar zuciya ta sauƙe tana sake jinjina kai a karo na ba adadi. Muryar sa ta jiyo yana faɗin "Am coming in." Waro idanu tayi, kafin da sauri tace "No" ta faɗa cikin ɗagun murya, kafin kuma ta ƙarasa bakin door ɗin wurin tare da sanƴa masa lock tana sauƙe ajiyar zuciya. Sanƴa kyakkyawar abayar tayi tare da naɗa gyalen sa, ƙarewa kanta kallo tayi cikin mirror ɗin wurin kafin kuma ta buɗe ƙofar tana fitowa, tsaye ta gansa bakin ƙofar nan tace "You're peeping on me again?." "No, what are you saying?, you should be glad the door isn't transparent." Rolling idanu tayi tana ƙarasawa bakin mirror ɗin ɗakin. Kujera taja ta zauna, tana gyara fuskar ta, kafin ta ɗau turare masu ƙamshi ta ɗan feffesa sama-sama a jikin ta. Harar sa tayi ta cikin mirror ɗin ganin yadda yayi tsaye akanta yana kallon ta. Knocking akayi a bakin ƙofar ɗakin, tsuke fuska yayi kafin kuma ya ƙarasa ga bakin ƙofar yana buɗewa ya leƙo da kansa. Wata baiwa ya gani tsaye hannun ta riƙe da tray, nan tace "Afuwan ranka ya daɗe, Hajiya babba ce ta aikowa Gimbiya da wannan." Kallo ya ƙare mata tsaf kafin ya sanƴa hannu ya kar6i tray ɗin yana shigowa ciki. Kallon DEENAH dake kwance kan bed yayi kafin ya dire tray ɗin yana ƙarasawa ya zauna kusa da ita yace "Grandma ta aiko miki da abu." Buɗe idanun ta dake a lumshe tayi tana kallon sa. "But wait, let me call her first and confirm whether itace ta aiko ɗin." Maida idanu DEENAH tayi ta lumshe, inda shi kuma ya kira Grandma dan tabbatar da koh itace ta aiko da abin. Ajiyar zuciya ya sauƙe yace "Tace itace, so stand up and eat." "Bana jin ƴunwa." "Are you kidding me?." "But naci abinci kafin muje fada so har yanzu ciki na a cike yake." Zuwa yayi ya zauna kusa da ita kafin kuma ya ɗan ja mata bargon yana rufa mata shi da kyau yace "Sleep then." Ɗan murmusawa tayi tana maida idanun ta ta rufe. Murmushi yayi yana kallon ta, a hankali ya sumbaci lips ɗinta kafin kuma ya tashi ya bar ɗakin. *Yawan Comment, Yawan Typing* 07061979284 *MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽* [8/30, 12:14 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *049...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _________Razana tayi cikin baccin da take tana ware idanun ta. Addu'a tayi cikin zuciyar ta kafin kuma ta miƙe zaune tana sauƙar da ƙafafun ta daga kan bed ɗin. Shiru ta zauna tana jinta so lonely, kewar gida na nuƙurƙusar zuciyar ta. A hankali ta miƙe tayi ƙofar da take tunanin toilet ne ta tura tana shiga, kamar yadda tayi hasashen kuwa Toilet ne, baki DEENAH ta saki tana ƙarewa cikin ƙaton bathroom ɗin da yake kamar ɗaki kallo, komai is neat and tidy kamar mutum yayi bacci a ciki, abubuwan zamanin da aka ƙawata bathroom ɗin dashi kuwa su kansu abun kallo ne, ficewa tayi daga bathroom ɗin ta wuce ɗakin closet inda anan taga akwatinan ta da sauran abubuwan ta. Abubuwan da ta san zatayi amfani dasu ta hau cirowa kafin ta fito ɗakin ta jere wadanda tasan zata ke amfani dasu a ɗakin, na toilet ma haka ta kai ta jere su. Ficewa tayi daga ɗakin zuwa falo tana sake ƙarewa ƙaton falon kallo, wani ƙofa da ta gani ta tura nan dai taga wani ɗakin ne shima komai steady a cikin sa, haka ma na kusa dashi duk. Wani ƙofa ne ta gani kusa da ta Balcony ɗin cikin falon, tura shi tayi nan dai taga ɗakin Gym ne, rufo shi tayi kafin ta sake bin wani lungu da ta gani, ɗakuna biyu ta gani a jere ɗaya na kallon ɗaya, tura na left handside ɗinta tayi nan taga wani irin ƙaton kitchen haɗaɗɗe hakan ya sanƴa ta sakin baki tana bin kitchen ɗin da kallo, shigewa tayi nanma wani ƙofa ne ta gani ta tura shi food storage ne shima babba komai na kayan abinci kowanne jere a mazaunin sa. Fitowa tayi daga kitchen ɗin ta tura ƙofar dake facing ɗinsa, wannan ɗin wayam yake ɗaki guda babu komai a ciki sai dai sosai yake so neat dashi, rufo ƙofar tayi ta fito falo kafin ta kama hanƴar sauƙa daga stairs, irin abinda yake a sama shine anan ƙasa ɗin, sannan kowanne da furnitures a ciki. Sama ta dawo ta koma cikin ɗaki agogon dake manne jikin bango taga har sha biyu ya ɗan wuce, dan haka toilet kayan da ta sanƴa ta shiga ragewa, kafin ta wuce toilet ɗin. Turarukan wanka masu daddaɗar ƙamshin da aka haɗa mata a gida ta zuba cikin ruwan wankan nata. Sosai tayi wanka ta tsaftace jikin ta tare da ɗaura alwala ta fito. Kayan ta ɗinkin leshi fitted gown ta sanƴa, dogon Hijab ta sanƴa ganin har an fara kiraye-kirayen sallah, dan haka tada sallah tayi bayan ta iddar ne tayi addu'oin ta kafin kuma ta naɗe sallayar tana maida shi wurin zaman sa. Gaban mirror tazo ta zauna fuskar ta da yake fresh dashi ta ɗan gyara tare da sanƴa kwalli sai lip balm sannan ta ɗaura ɗankwalin kayan. Sosai tayi kyau cikin shigar tata da ya zauna mata a jiki ɗarass, gyalen kayan ta ɗauko tana ɗan yafa shi kan kafaɗun ta kafin kuma ta tashi ta ficewa zuwa falo. Turaren wuta mai dausar da nutsuwa da sanƴin cikin zuciyar mutum ta sake turare part ɗin dashi duk da kuwa a gyare yake hakan bai hana ta sake tsaftace shi ba. Remote ɗin AC ta ɗauko tare da rage gudun sa kafin kuma ta miƙe kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman couchs ɗin dake zube a falon. Shiru tayi tare da ƙure wuri guda da ido, so boring haka takejin ta gashi wayar tata kam ta manto shi a chan bale ta ɗanyi game, ga kuma tsoron gidan MASARAUTAR nan tasu ZEEYAD da yaƙi barin zuciyar ta har yanzun, idanu ta lumshe, sosai takejin kewar ƴan gidan su. Ta kai kusan 10mins idanun ta a lumshe, motsa idanun ta fara a hankali jin kamar tsayuwar abu akanta. Sosai zuciyar ta ta hau racing dan kuwa koh kaɗan batajin motsin shigowar mutum ba balle tace koh ZEEYAD ne ya shigo, jin feeling ɗin mutum na dab da ita ne ya sanƴa ta saurin ware manƴan idanun ta tana miƙewa zaune. Waige-waige ta hau yi nan dai taga babu kowa, sosai zuciyar ta ta cika da tsantsar tsoro, a hankali ta koma ta tana ɗosana mazaunan ta kan couch ɗin. Ji tayi an buɗo ƙofar ɗakin ɗaya daga cikin ɗakunan falon, a firgice tayi saurin maida duban ta gun bugun zuciyar ta na tsananta. ZEEYAD taga ya fito daga cikin ɗakin wayar sa kare a kunne, hango DEENAH da yayi ne ya sanƴa shi sauƙe wayar yana ganin yadda tayi tsuru-tsuru da idanu kamar kace kyat ta arta a guje. Ƙarasowa inda take zaune yayi yana kaɗa yatsun sa kan fuskar ta ganin yadda ta kafe sa da idanu tana kallo. Zama yayi facing ɗinta yana faɗin "You're awake?." Ita dai kallon sa take cikin tsoro kafin tace "Yaushe ka shigo?." Kallon ta yayi kafin yace "Na shigo ina?, i didn't go anywhere." Sake kallon ƙofar ɗakin da ya fito tayi kafin tace "But na duba dukkanin ɗakunan cikin gidan nan and koh kaɗan banji motsin ka a cikin gidan ba." Murmushi yayi yace "What are you saying?, babu inda naje by the way why is it nake ganin kamar a tsorace kike." Saita nutsuwar ta tayi kafin tace "No, kawai ina mamaki ne." Ɗan murmusawa yayi kafin yace "Alright, kinci abincin da Grandma ta aiko miki?." Kai ta girgiza masa alamun a'a, nan yace "Why, you should eat it koh da ɗan kaɗan ne." "No, ba tace ka kaini muci abincin rana a chan ba, muje ka kaini yanzu." Idanu ya ƙure ta dashi kafin kuma ya miƙe yayi cikin ɗaki, bai jima ba ya fito ɗauke da tray ɗin abincin a hannun sa nan yace "Ba sai munje mu ba, you can eat this" ya faɗa cikin tsukewar fuska. Hannu ta kai ta buɗe tray ɗin taga wani irin abinci ne ma da bata ta6a ganin irin sa ba, maidawa tayi ta rufe tana ɗagowa ta kallesa kafin tace "I... bansan yadda ake cin irin abincin nan ba." Wani irin kallo yayi mata kafin kuma ya sanƴa hannu ya ɗau spoon yana ɗebo abincin a ciki, kallon ta ya sake kafin yace da ita "Haa." Ita dai shiru tayi tana kallon sa kafin a hankali ta girgiza masa kai tana faɗin "Bana ma jin ƴunwan fah." "Look DEENAH, this food can't go to waste, you've to eat it coz Grandma ba zata ji daɗi ba." "Don't force me please" ta faɗa kamar wacce zatayi kuka. "Am not forcing you DEENAH, you've to eat it, and besides yana ƙara lafiya da ƙuzarin jiki." "Really?." "Really" ya faɗa. Ɗan murmusawa tayi kafin tace "I will eat it sabida Grandma, ba dan kai ba." "Whatever, all that matters is for you to eat it" ya faɗa cikin kallon ta. Spoon ɗin hannun sa ta amsa kafin ta kai ta ɗebo abin tana kallon sa, murmushin gefen baki ya saki kafin ta kai abin baki tana ɗan runtse idanu. Idanu ya zuba mata yana kallo har ta haɗiye abincin, spoon ɗin ta ajiye dan kuwa koh kaɗan baiyi mata daɗi ba. Ganin irin kallon da yake binta dashi ne ya sanƴa ta faɗin "Why are you staring at me like that?." "Coz i can't really believe how fool you're and easy to fall into a trap our future queen" ya faɗa cikin murmushi suffar sa na komawa na Sarauniya Naseeba. A wani irin mugun razane DEENAH ta waro manƴan idanun ta cike da kiɗima take bin Naseeba da ta miƙe tsaye da kallo. Murmushi Naseeba ta saki kafin tace "Oh my Darling future Queen, i can't believe wane irin tsautsayi ne ya ɗebo ki zuwa wannan MASARAUTAR a matsayin matar ZEEYAD, the boy that i have been craving to taste how good and sexy he is in bed will finally be in my custody today" murmushi ta ƙara saki tana gimtse fuska cikin wullawa DEENAH mugun kallo take cigaba da faɗin "ZEEYAD is mine, and only i can get intimate with him, i will make sure that i keep you far away from him wanda koh ƙamshin sa ba zaki sake ji ba balle muryar sa, you've made a very big mistake na kawo kanki cikin wannan fadar, this food that you just ate now, it's poisoned" ta faɗa cikin murmushi still idanun ta akan DEENAH da ta kasa motsi daga inda take bale tayi moving eyes ɗinta daga kan Naseeba. "But... luckily for you ba irin poison ɗin da zai kashe ki bane, it's that kind of poison that will knock you down to sleep forever." Tsugunnawa tayi daf da DEENAH da jikin ta ya gama yin lagwai bata iya motsa koh da ƴar yatsar ta tana shafo gefen fuskar ta haɗi da hura mata iska a hankali take faɗin "Sleep, sleep tight beauty, am sure zakiji daɗin sabuwar duniyar da zaki tsinci kanki ciki yanzun." A hankali DEENAH take lumshe idanun ta da take ganin dishi-dishi sakamakon maganin da ya fara tasiri cikin jinin ta. "Sleep so that i can take your position, sleep so that i can have ZEEYAD for all myself, sleep so that i will be the next Queen of this Kingdom." Ture DEENAH da jikin ta ya gama sakewa tayi tana faɗi kwance kafin idanun ta da suke tsiyayar da wasu irin siraran hawaye su gama rufewa ruff. Da kallo Naseeba ke bin ta, kafin ta miƙe tsaye tana kyakyata dariyar mugunta, sai da ta shafe almost 1min tana yi kafin ta tsagaita tana gimtse fuska "Finally, i told you ZEEYAD didn't i?, nothing will ever stop me from having you as mine, am sending your dear wife inda ba zaka ta6a ganin ta ba, you will live with me a matsayin ita, and we will live a life full of love and care" ta faɗa cikin yin hajijiya tana dariya. Tsagaitawa tayi kafin ta kuma takowa inda DEENAH ke kwance, hannu ta sanƴa a jikin ta tare da karanto wasu irin makaran tsafi take kuma komai nata ya koma irin na DEENAH, kai kace DEENAH ɗin aka raba biyu. Murmushi tayi tare da miƙewa tsaye tana kallon DEENAH ɗin kafin kuma ta shiga karanto wasu irin makaran tsafi cike da yaren da ba zaka san koh na menene ba, take wata tsohuwa gijib ta bayyana, kallon Naseeba tayi tare da faɗin "Burin ki ya cika, and now the girl is mine, kin cika alƙawari bani ita akan lokaci kamar yadda kika faɗa" ta faɗa cikin jinjina kai tana kallon DEENAH. Murmushi Naseeba tayi kafin tace "Take her, take her far awayyy from here, take her to inda babu wani mahaluƙi da zai iya gano ta, yadda zanji daɗin rayuwa da wanda na ɗau shekaru ina begen sa." Dariya tsohuwar tayi tace "Ofcourse tunda kikayi min abinda nakeso dole nayi abinda kema kika ce, zan ɗauke ta na kaita inda babu wani ɗan adam da ya ta6a taka ƙafafun sa zuwa wurin, ita ɗin sadaukar wa ce garemu dan haka zan ɗauke ta nayi nisa da ita inda duk neman da za'a yi mata cikin duniyar ba za'a gano inda take ba, sai dai kema ki kiyaye sharuɗan da na gindaya miki indai kikayi hakan toh tabbas komai zai tafi dai-dai yadda kowannen mu yaso." Alamu tayi mata da hannu tana faɗin "Take her tun kafin ya dawo cikin gidan nan." Murmushi tsohuwar tayi tare da jinjina kai tana kallon DEENAH, wasu surutan ta tayi tana nuna DEENAH da sandar hannun ta take kuma dukkanin su suka 6ace ya saura sabuwar DEENAH wato Naseeba. Wata iriyar ajiyar zuciya ta sauƙe cike da relief zuciyar ta fal farin cikin burin ta ya cika. Zubewa tayi kan couch ɗin ɗakin tana sake bin jikin ta da ya zama DEENAH sak da kallo, murmushi tayi tare da faɗin "I can't believe this." Miƙewa tayi ta koma cikin ɗaki, tare da tsayawa a gaban mirror tana ƙarewa kanta kallo, sake gyara ɗaurin kanta tayi kafin ta sake yiwa fuskar ta kwalliya ɗan kaɗan inda ta fito tare da yin kyau sosai da sosai. "Uhm what a great day for me" ta faɗa cikin murmushi tana faɗawa kan bed ɗin ɗakin. ********************* __________ZEEYAD bai tashi dawowa part ɗin nasa ba sai da akayi sallahr la'asar kai tsaye ya wuce cikin part ɗin nasa. Haurawa sama yayi tare da tura ƙofar falon bakin sa ɗauke da sallama. Lumshe idanu yayi sakamakon ƙamshin turaren da ya bugo sa, idda shigewa yayi yana rufo ƙofar falon. Ganin baiji motsin DEENAH bane ya sanƴa shi nufar ɗaki, sai dai wayam yaga bata nan. Shiru ya zauna dan koh a tunanin sa tana toilet ne, sai dai jin shiru ya sanƴa shi miƙewa yana yin bakin toilet ɗin tare da kwankwasawa a hankali yace "DEENAH?." Jin shiru ya sanƴa shi sake faɗin "Are you in there?." Tura ƙofar toilet ɗin yayi ya shige inda ya duba kowane lungu da saƙon ciki yaga bata nan, fitowa yayi wondering koh ina ta shige. Muryar ta yaji daga cikin ɗakin closet tana faɗin "Abyad kazo ka taimaka min na anan." "Ohh" ya faɗa a hankali yana ƙarasawa bakin ƙofar kafin yaja ya tsaya yana faɗin "Should i come in?." "Yes come in" ta faɗa. Tura ƙofar yayi ya shiga inda ya ganta tsaye ɗaure da towel ɗin da kaɗan ya wuce mazaunan ta. Juyowa tayi tana kallon sa cikin murmushi, murmushin shima ya saki cike da mamakin ta ba tare da ya iya ɗauke idanun sa daga kanta ba. Ƙarasowa tayi inda yake tsaye hannun ta ɗauke da doguwar rigar kanti take faɗin "Zip ɗin ya cize, will you please help me ka gyara min shi." "Sure" ya faɗa yana amsar rigar daga hannun ta, nan yace "By the way, when did you loose your hair" ya faɗa yana kallon gashin kanta dake a tsafe. Hannu ta kai ta ta6a gashin tare da faɗin "My hair?, ɗazun nan ne bayan ka fita." Gyara mata Zip ɗin rigar da ya cize yayi yana miƙa mata, amsa tayi cikin murmushi tana kallon sa haɗi da furta "Thank you." Folding hannu yayi a ƙirji yana kallon ta, nan kuwa ta fara shirin warware towel ɗin jikin ta ba tare da ta kore sa ba, ɗan waro idanu yayi kafin yace "Are you being real?." "What?" ta faɗa. Murmushi yayi tare da jawo ta jikin sa yace "I thought zaki kore ni ne." Murmusawa tayi kafin tace "No why zan kore ka, you're my Husband aren't you, and dukkanin wani abu dangane dani is all yours" ta faɗa cikin shafo lallausar gashin gefen fuskar sa. Haɗe hancin su yayi guri ɗaya yace "I thought you will wait har sai Grandma ta kawomin ke da kanta, but i can see you're so eager to get this done." Murmushi tayi tana sake shigewa jikin sa tace "Let's do it now" ta faɗa cikin riko gaban rigar sa. Shi dai ZEEYAD sosai ya cika da mamakin DEENAH ɗin ganin canzawar ta lokaci guda haka, riƙe hannun ta yayi daga 6alla buttons ɗin rigar sa da take kafin ya kalleta yace "This will be more interesting at night" ya faɗa yana maida su ya rufe, kafin ya ɗan ja hancin ta yace "I will see you tonight, i know Grandma zata iya aikowa any moment from yanzu azo a tafi dake, and nima inason zuwa ganin YAZEED, so make sure you're well prepared tonight" ya faɗa cikin bata peck a gefen kumatu kafin kuma ya fice daga cikin ɗakin ma gabaɗaya. Da wani irin kallon mugun haushi ta bishi, nan kuma tace "Anyways then, i will wait for you tonight Darling, koh da nan da zuwa gobe kace i will wait, muddin i can have you then banida wata matsala" ta faɗa tana sanƴa kayan jikin ta tare da fitowa cikin ɗakin. ********************* __________Grandma da kanta ta kawowa ZEEYAD amaryar sa har kan bed ɗinsa. Sosai ta sanƴawa DEENAH albarka kafin kuma tace "Ni zan barki haka nan, duk wani abinda yayi miki wanda bakiji daɗin sa ba ki kawomin ƙarar shi nikuma zanyi maganin sa kinji koh?." Kai ta jinjina wa Grandma ɗin kafin kuma tace "Ni na barki cikin farin ciki ƴar nan, Allah ya dauwamar da farin ciki cikin rayuwar auren ku" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin tana rufo ƙofa. Fitar ta keda wuya fake DEENAH ta buɗe fuskar ta dake cikin mayafi tana bin ƙofar da kallo tare da sakin wani irin shu'umin murmushi. Maida duban ta tayi ga agogon dake manne a ɗakin taga ƙarfe goma saura. Miƙewa tayi daga kan bed ɗin tana sauƙa ƙasa kafin ta nufi closet room, bata jima ba ta fito cikin wasu irin tsinannun night wears wanda marabar su da babu kucil ne. Feshe jiki tayi da turaruka masu daɗin ƙamshi kafin ta koma kan bed tana jawo bargo ta rufe a jikin ta tare da faking baccin ƙarya. Like after 20mins aka buɗo ƙofar ɗakin, sosai ya haɗe cikin shigar sa ta manƴan kaya sai zuba ƙamshi na musamman yake. Jinginuwa yayi da bakin ƙofar yana kallon ta cike da mamaki ganin kamar har tayi bacci. A hankali ya shiga takowa bakin bed ɗin yana durƙushewa kan guiwowin sa tare da ƙure kyakkyawar fuskar ta da kallo. Sai da ya gama kallon ta tsaf kafin ya miƙe yana shigewa ɗakin closet, bai wani jima ba ya fito cikin ƙananun kaya da 3quater wando tare da yin hanƴar toilet, alwala ya ɗauro ya fito kafin ya tako inda take, a hankali ya shiga buga pillow ɗin da kanta yake kai. Lamo tayi kamar bata ji ba, har sai da yayi ya gaji ya daina. Zuwa yayi ya kashe wutar ɗakin inda ya rage saura hasken side lamps, suma rage hasken su yayi. Hawowa kan bed ɗin yayi yana cuddling ɗinta ta baya tare da manna mata sumbata a neck. Kame jikin ta tayi wani irin farin ciki na nuƙurƙusar zuciyar ta finally yau burin ta zai cika. Kwanciya ta gyara tana juyowa facing ɗinsa still idanun ta a lumshe kamar mai baccin gaske. Hannu ta kai kan faffaɗar ƙirjin sa tana rubbing gently, riƙe hannun nata yayi sabida haka kawai yakejin duk wani ta6a sa da tayi ya kanji wani iri a zuciyar sa. A hankali cikin muryar bacci ta kira sunan sa "Abyad." Kallon fuskar ta yayi tare da amsa mata da "Um." Shiru tayi kamar wata iriyar mai magagin baccin nan tana sake shigewa jikin sa. Rungume ta shi ɗinma yayi yana mai manna mata kiss a goshi tare da rufa musu bargo. ********************* _________A razane ya tashi daga mafarkin da yayi ɗin, yana dafe kansa da hannuwa bibbiyu, same mafarkin da yake yi kwanaki akan ana tura DEENAH cikin ruwa ya sake yi wannan karon ma. Addu'a ya karanto sosai cikin zuciyar sa kafin kuma ya ankara da rigar jikin sa dake a tu6e. Kallon DEENAH dake shar6ar baccin ta cikin kwanciyar hankali yayi wondering koh itace wacce ta cire masa rigar. Miƙewa yayi daga kan bed ɗin yana faɗawa toilet, fuskar sa ya wanke kafin kuma ya ɗauro alwala ya fito. Darduma ya shimfiɗa kan chinese carpet ɗin dake ɗakin kafin ya tada sallah. Sosai yayi sallahr haɗi da karanto addu'oin neman tsari da sauran su, bai idda ba har sai da yaji ana kiraye-kirayen sallahr Asuba. Miƙewa yayi ya koma toilet ɗin tare da sake ɗauro wani alwalan yana zuwa inda DEENAH ke kwance tare da buga pillow ɗin da take kai. A hankali ta ware idanun ta akansa, alamu yayi mata da anyi sallah kafin kuma ya juya ya fice daga ɗakin zuwa masallaci. Da kallo tabi sa kafin kuma ta wani turo baki tana komawa ta kwanta ta cigaba da baccin ta. ZEEYAD bai dawo ba har sai ƙarfe bakwai bayan rana ta fito, dawowa ɗakin yayi yadda ya barta haka nan ya same ta still tana bacci. Zuwa yayi ya sake tada ta akan ta tashi tayi sallah, zaune ta miƙe tana wage baki ba tare da ta koh rufe sa ba, gashin kanta duk ya wani barbaje yawa sabuwar mahaukaciya. Da mamaki fal ransa ya fice daga ɗakin. Miƙewa tayi tare da faɗawa Toilet, wanka tayi ta fito kawai kafin ta shirya cikin English wears ɗin doguwar riga iya cinƴa mai hannun vest. Bata damu da ta gyara kan gadon ba ta fito zuwa falon ƙasa, bayin dake ta gyare-gyare t umurci ɗaya da ta kawo mata breakfast yanzun nan kafin kuma ta koma sama. Buɗe sauran ɗakunan tayi taga baya ciki hakan ya sanƴa ta nufar gym room ɗinsa anan ta tadda sa yana motsa jiki. Murmushi tayi tana ƙarasawa gun sa tare da faɗin "Good Morning." Dakatawa yayi da abinda yakeyi tambayar da ya wullo mata shine "Have you prayed?." "Yeah of course, sorry kana ta tashi na ban farka dawuri ba, na gaji ne sosai shiyasa." Shiru yayi bai tanka mata ba, sabida sam bai zaci haka halayen ta suke ba, rashin yin sallah akan lokacin sa. Ganin kamar ransa a ɗan 6ace ne ya sanƴa ta ƙarasawa inda yake tana rungumo sa ta baya. Sosai yakejin wani iri idan ta ta6a shi, dan haka zame hannayen ta yayi daga jikin sa yace "I need a Morning coffee to warm me up, can you prepared it right away?." "What, a coffee?" ta faɗa tana kallon sa. "But i'm the future Queen, how do you expect me to make some coffee for you after all akwai masu aiki dayawa cikin MASARAUTAR nan, am sure they can make a nice one." "Don't worry then, i will make it da kaina." "No you don't have to do that, sabida na sanƴa a haɗo mana breakfast." Da mamaki yake kallon ta kafin kuma ya fice daga ɗakin zuwa ɗayan ɗakin. Tarar da bed ɗin yayi scattered kamar yadda ya barsa, juyowa yayi ya kalleta kafin yace "Are you that tired that gado ma ba zaki iya gyarawa ba?." Rolling idanu tayi kafin tace "I guess we should talk about dalilin da ya sanƴa baka bani haƙƙi na jiya da dare ba, bayan munyi da kai cewa we will have alot of fun." "I need you to answer my question first, why isn't this room tidy DEENAH?." Shiru tayi tana kallon sa kafin kuma tace "Sabida ban saba ba, sannan kuma dukkanin abinda nakeso yi min shi akeyi." Mamaki ne ya cika ZEEYAD ganin yadda take maida magana garangatsai haka, shiru yayi mata yana shigewa closet room, nan ma wasu kayayyakin ya tadda a wawwatse an ciro su ba'a maida su gurbin zaman su ba, koh shi nan wasu bayi basu ta6a tsaftace masa ɗaki ba bale kuma DEENAH. Sosai ya kai maƙura a 6acin rai sabida ya tsani ƙazanta kwata-kwata a rayuwa. Tarar sa tayi da faɗin "Don't be mad please, the maids are here zasu tsaftace komai." Kallon ta yayi yace "Bana buƙatar wasu bayi cikin ɗaki na, don't you ever make the mistake of asking them in" yana faɗin haka ya fice a fusace. Da kallon mamaki ta bisa, she thought yana mugun son DEENAH and ba zai ta6a yin fushi da ita dawuri haka ba, sai dai koh kaɗan hasashen ta bai zamto gaskiya ba, tun jiya ya kasa ta6a ta, duk kuwa iya ƙoƙarin ta na ganin ta kusance shi cikin dare sai dai bai bari hakan ta faru ba, ta rasa mecece matsalan kodai dama bayason DEENAH ɗin ne?, shine tambayar da tayi wa kanta. Cike da mugun haushi ta hau gyara ɗakin duk bata ma wani iya ba ta dai kwa6a shi ne kawai. *BAYAN SATI BIYU* _________Sosai suke samun rashin jituwa tsakanin su, Grandma har mamaki abin yake bata, ZEEYAD kuwa koh kaɗan baisan haka halin DEENAH yake ba, though yayi mamakin canzawar ta but baisan abinda ya faru ta canza all of a sudden ba. Mai Martaba ne ya gayyace su fada yin Dinner tare dashi da dukkan su family ɗin, zaune ZEEYAD yake DEENAH kusa dashi inda dining ɗin ya ɗau shiru sosai. Hafeezah ce tace "You should contact Naseeba ta dawo daga tafiyar da tayi haka nan, naga dai bata saba daɗewa idan taje gaida iyayen ta ba, tsananin ta tayi kwana uku but yau har sati biyu kenan." Tari DEENAH ta saki nan ta kai hannu da sauri tana ɗaukar glass ɗin ruwan gaban ta, hannu na rawa ta kafa akai ta fara sha. Koh gefen da take ZEEYAD bai kalla ba, Hafeezah ce ta kallesa ganin halin koh in kula ɗin da ya nunawa DEENAH, ta6e baki tayi tana kauda kanta daga garesu. Amaryar YAZEED ce tace "DEENAH, what's wrong shin kun samu wani matsala ne da mai gidan ki, i thought zai nuna damuwar sa ne ganin rabin zuciyar sa na tari." JALILAH ƙarasowa tayi tana jan kujera ta zauna da alamu dai fitowar ta kenan, kallon ta Hafeezah tayi kafin tace "What took you so long?." Kanta a ƙasa take faɗin "Am sorry Ummie, na tsaya gyara ne." "Gyaran mai, ba akwai maids ba?." "Actually, nafison nayi gyaran ɗaki na da kaina ne." Ɗago da idanu ZEEYAD yayi tare da ɗan satar kallon ta kafin ya maida kansa ya sadda zuciyar sa na burning tare da wasi-wasin kodai he chose the wrong person ne ya yada right person ɗin. Satar kallon sa fake DEENAH tayi ta gefen ido yayin da ta ɗau alwashin sai ta cika burin ta yau akan sa. Shiru kowa yayi hankalin su kan abincin da suke ci, YAZEED ne ya kwaru inda ya fara tari, saurin miƙa masa ruwa JALILAH dake kusa dashi tayi tana ɗan patting bayan shi haɗi da jero masa sannu, harara amaryar ta wulla mata ta gefen ido tana wani irin tsuke fuska. Tashi YAZEED yayi ya bar dining ɗin yana cigaba da tarin sama-sama. Kallon amaryar Hafeezah tayi tace "Sairah kibi mijin naki mana ki bashi kulawa mai kyau." Yatsine fuska tayi kafin tace "Ba kwana na bane yau." Kallon JALILAH tayi tace "So kike sai nayi miki magana kafin ki tashi ki bishi?." Da sauri ta miƙe haɗi da faɗin "Am sorry" tana mara masa baya. Harara Hafeezah ta gallawa Sairah dan kuwa ta lura koh kaɗan bata ɗaukar hannu. Miƙewa ZEEYAD ma yayi yana yiwa mai Martaba da bai tankawa kowa cikin su ba sai da safe, kafin ya kalli fake DEENAH yace "Let's go." Tashi tayi kasancewar ta gama cin abincin tana mara masa baya. Da mugun kallo Hafeezah ta bisu dan kuwa yanzu tunda ta dawo cikin fada dole ne ta ɗaura daga inda ta tsaya. ************************* _________Rungumo sa tayi ta baya hannayen ta kan faffaɗar ƙirjin ta. Shiru ZEEYAD yayi bai tanka mata ba, zuciyar sa sosai take cike da doubts akanta. "DEENAH?" ya kira ta. "It's been two weeks rabon ki da kiyi waya da ƴan gidan ku, i have been waiting naji kinyi maganar su but you didn't." Sake sa tayi cikin kame-kame take faɗin "That isn't something to worry about, gobe zan kira su but we should go to bed now." Juyowa yayi yana kallon ta nan ya sake faɗin "I need an answer to my question, kodai har kin fara enjoying dukiya kin wofantar da Family ɗinki ne?." "What are you saying, koh kaɗan ba haka bane?." "Then tell me your reason, listen DEENAH i have a lot of doubts about you, i really doubt if you are my DEENAH, the DEENAH that i know doesn't act this way, but koma dai menene i will find out." "What are you saying, nice mana nice DEENAH, i can see that kai ne ka canza completely, ka daina nuna min wata kulawa, kullum kana cikin tsangwama ta..." "Thats because you're not my DEENAH, DEENAH ta doesn't behave the way you do, i know her and i can feel her presence a duk inda nake, but being with you for these days banajin wannan feeling ɗin a jiki na, being with her made me feel like hugging her for the rest of my life na dawwama a jikin ta, but for you i never get that feeling, i feel so empty since the day Grandma ta kawo ki ɗakin nan, i never feel the presence of my DEENAH beside me, zuciya ta is full of doubts akanki, i feel like my DEENAH is somewhere far away from me waiting for my rescue, and dukkanin wani hali da kike yi koh kaɗan ba halayen DEENAH ɗin da na sani bane, you've changed alot" ya faɗa idanun sa da fuskar sa na yin jaa sabida 6acin rai. Ita dai kallon sa take zuciyar ta na mugun bugu ganin kamar asirin ta na daf da tonuwa. Kallon ta yayi kafin yace "Whats the name of that your younger brother again?." Shiru tayi tana wuwwula idanu cike da rashin gaskiya. "Tell me" ya sake faɗa. Cikin rawar murya tace "Why are you asking his name, i thought kasan kowa daga cikin dangi na, why then kake sake tambaya ta sunan ƙani na" ta faɗa da niyyar juyawa yayi saurin cafko hannayen ta fuskar sa na fitar da wani irin tsantsar 6acin rai ya sake faɗin "Tell me the name of your younger brother." Fuzge hannun ta tayi tace "Fine then, why don't you just called them and asked them what the name of my younger brother is, wannan rainin hankali ne kake nunamin." Sake ruƙo hannun ta yayi yana kallon cikin idanun ta, saurin kauda kai tayi tana ƙoƙarin kwace hannayen ta. "Look into my eyes DEENAH." "Mai zan tsinta idan na duba cikin idanun naka, listen am tired of having a quarrel with you always, idanma ka daina sona ne why don't you just tell me." "But i never loved you, i only love my DEENAH" ya faɗa yana kallon ta. "This isn't fair, why kake tunanin ni ba DEENAH bace, you think dama yadda halaye na suke kafin muyi aure haka zamu dawwama ba zai canzu ba." Riƙo kafaɗun ta yayi cike da mugun 6acin rai yake faɗin "You're not my wife, i have been a fool for falling into your traps this time, all you've craved for your whole life is to have me in bed with you, baki san ta wacce hanƴa zaki bi ki cika burin ki ba, sai ta wannan by posessing my wife and had yourself turned into her, wannan ne kaɗai hanƴar da kike dashi na ganin kin cika burin ki akaina, i now get to know who you really are, Naseeba" ya ƙarashe cikin kakkausar murya fuskar sa da idanun sa na canza launi. A matuƙar kiɗime ta waro manƴan idanun ta tana kallon fuskar sa. Cikin mugun 6acin rai har maganar tasa na seizing yace "Where is my wife?." "Answer me" ya faɗa a tsawace yana jijjiga ta. Sosai ta tsorata da yanayin shi ganin jikin sa har rawa yake saboda 6acin rai. Cikin rawar murya tace "I...i...i'm your wi..." "Lies" ya faɗa a tsawace yana ture ta. Naseeba ganin asirin ta ya tonu ya gano ta ne ya sanƴa ta waigowa cikin ainihin kamannin ta tana kallon sa da idanun ta da sukayi jazir. Da kallo ZEEYAD ke binta cike da muguwar 6acin ran da baisan yana da ita ba. "Yes, i'm not your wife, but inaso ka sani ba zaka sake ganin ta ba har abada." Zuwa yayi yana cakumo gashin kanta kamar zai raba shi da fatar kanta yace "Tell me, where is my wife, where is DEENAH, what have you done to her?." Dariya ta saki cike da mugunta dukda kuwa irin riƙon da yayi mata nan tace "She is dead long ago." Ture ta yayi da ƙarfi dan kuwa baisan ta inda ma zai fara hora ta ba, mai ma zai daka a jikin mace yaji daɗi ya san kuma ya huce haushin shi, babu. Zubewa yayi akan guiwowin sa, zuciyar sa na mugun rawa haka ma gangar jikin sa, hannu ya sanƴa yana cakume gashin kansa da ƙarfi, he can't believe how foolish he is da har Naseeba ta kasance dashi for good 2weeks har ma suke haɗa shimfiɗa tare ba tare da ya fahimci cewa ba DEENAH bace ba, sosai da sosai yakejin haushin kansa, sosai yakejin rashin gazawar sa na kasa riƙe amanar da aka bashi, DEENAH koh 24hrs bata cika a gidan shi ba ya rasa ta, sakamakon mugun irin dake zagaye dashi, sa'ar sa ɗaya shine bai ta6a kusantar da sunan mu'amalar aure ba duk da kuwa jarabar da tayi ta masa, ba zai iya kwatanta iriyar tashin hankalin da yake ciki ba a yanzu, komai ya sunce masa baisan ta ina zai fara ba, baisan ta ina zai nemo mafita ba, yasan duk inda DEENAH take a yanzu tana cikin mawuyacin hali, ba zai ta6a yafewa kansa ba, sabida dalilin sa ne duk wani abu ke faruwa da DEENAH. Tsaye Naseeba da takejin zuciyar ta kamar ta fallatso tayi tana kallon sa tace "You want to see your wife, then you must give me abinda nayi longing nake nema daga gareka, only then zan faɗamaka inda matar ka take. Ɗago da rikitattun jajayen idanun sa yayi yana kallon ta nan yace "I will find my wife wherever she is, babu abinda zaki samu daga gareni." Dariya ta fashe dashi kafin tace "Seriously?, let's see then how and where you find the love of your life, tabbas tana nan a raye sai dai kafin ka samo ta daga inda take you must pay a higher price, sannan she is deep beneath inda babu wani mahaluƙin da zai iya gano ta komin neman sa, da ita da matacciya duk ɗaya suke a yanzu, da zaran na bada permission ɗin kashe ta toh tabbas babu makawa hakan ne zai faru, so the best abinda zakayi yanzu dan ceto rayuwar matar ka is to give me what i need from you." _Toh nikam dai takaici ba zai kashe ni ba, na dakata haka nan idan na huce ma cigaba, haka kuma idan naga comment dayawa zan cigaba, dan kuwa kaɗan ya rage ban haɗiyi zuciya ba a page ɗinnan, kuma ku dinga yi Kuna yayyafawa zuciyar ku ruwan sanƴi, dan kuwa ni fanta ta mai sanƴi na sayo ina yi ina kur6a abina😕_ *MHIZZ JIDDHERR....................✍🏽* [9/1, 10:30 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *050...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ___________"Think about it ZEEYAD, wane irin hali lovely DEENAH ɗinka take ciki a yanzun, sannan kuma a'ina take a halin yanzu wanda zaka iya nemo ta cikin ƙanƙanin lokaci, kaga duka amsoshin nan ni kaɗai ne na san su, and in other to get them... you must do as i say" ta faɗa idanun sa akanta. ZEEYAD jin maganganun ta yake tamkar ana watsa masa tafasasshen ruwan zafi cikin tsokar zuciyar sa, idanu ya runtse yana tunanin ta yadda zai bi mata dan fito masa da DEENAH. A hankali ya shiga miƙewa daga tsugunen da yake yana kallon ta yace "I want DEENAH back, sannan zaki nuna min ita ne muddin nayi abinda kike buƙata dani right?." Murmushi tayi tace "For sure." Jinjina kai yayi yana ƙarasawa bakin ƙofa a hankali tare da turawa ya rufe yana sanƴa key. Da kallo nasee ta bisa tana sakin murmushin gefen baki cike da farin ciki. Juyowa ZEEYAD yayi hannayen sa cikin aljihu yace "Am ready to do anything muddin zaki dawomin da DEENAH." Murmushi tayi tace "Wow, i can see that kayi matuƙar damuwa da ita tunda har kana shirin yaudarar ta a yanzu..." A tsawace yace da ita "I will do as you said Naseeba, just bring DEENAH back to me." "Fine then, let's do it" ta faɗa tana nuna masa kan bed. Da kallo yabi kan bed ɗin kafin kuma yace "But you've to promise me one thing Naseeba." Juyowa tayi tana kallon sa kafin ta saki murmushi tace "Our secret is safe with me, no one will know about this sai mu biyu kawai, ba shi ne alƙawarin da kakeson nayi ba?" ta faɗa tana ƙarasowa gaban sa. "Thats not what i want." Harɗe hannaye tayi a ƙirji tace "Fine then, tell me mai kake so." "Inaso ki faɗamin inda DEENAH take." Kallon sa take kafin kuma ta saki dariya tana sake kallon sa tare da nuna kanta tace "You want me to tell you where your wife is, do you think am insane or something, listen ZEEYAD i can't easily be fooled by your by your easy tricks, do you think you can outsmart me, no am not that fool like your wife." Key ɗin ɗakin ya ciro yana miƙa mata yace "You've the keys and tell me where DEENAH is, and i promise to make your day fabulous." Hannu ta kai zata amshi key ɗin nan yayi saurin damƙewa a hannun sa yana faɗin "First tell me where my wife is." Murmushi tayi tana kallon sa kafin kuma tace "Ba zan faɗa maka exactly inda take ba, but i will give you a clue, let's see if you're smart enough to find her whereabout." Shiru yayi yana kallon ta kafin yace "Fine then." "Give me the keys first" ta faɗa cikin miƙa masa hannu tana kallon sa. Shiru yayi yana kallon ta nan tace "Well, i can't trust you then." "You have the keys, you tell me where she is, deal?." Shiru tayi kafin kuma tace "Deal." Sakar mata keys ɗin yayi a hannu nan yace "Now tell me." Ɗagowa tayi daga kallon keys ɗin cikin hannun nata cikin murmushi tace "Well, your wife is still alive kamar yadda na faɗa maka, but she is half death, idan nace maka half death ina nufin gaf take da mutuwa muddin ta ƙara kwana ɗaya cikin inda take..." Katse ta yayi da faɗin "just tell me where she is." "I didn't promise to tell you where she is, but to give you a clue." Shiru yayi yana kallon ta kafin yace "Fine then." Hannaye ta harɗe a kirji Kafin ta fara faɗin "Matar ka tana inda babu wani normal mahaluƙi da ya ta6a taka ƙafarsa zuwa wurin, masu zuwa wurin sai masu manƴan tsafi, aljanu koh bokaye, sannan kuma wurin ya kasance wuri ne mai haɗarin gaske wanda ke ƙunshe da tarko iri daban-daban, a wannan wurin matar ka take garƙame cikin wani abu deep beneath ƙasan wani abu wanda taku ɗaya zakayi masa ka nutse cikin sa, thats all" ta faɗa cikin ware hannayen ta. "This is nonsense, give me a clear clue, atleast ki faɗamin sunan wannan wurin." Murmushi tayi tace "I only promise you na baka clue ɗin yadda wurin yake shine kawai." Shiru yayi yana nazari cikin kwakwalwar sa ya tsinkayo muryar ta "So now it's time da kaima zaka cika min nawa burin" ta faɗa tana karkaɗa masa makullin hannun ta a fuska. Takawa yayi zuwa ɗakin closet ya canzo kayan sa ya fito, zaune ya ganta kan bed ɗin ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tan karkaɗawa bai kalleta ba yayi hanƴar bathroom yana shigewa ya rufo ta. Zuwa yayi ya ɗan kunna pump ɗin bathtub ɗin cikin toilet ɗin ruwa yana ɗan zuba. Takawa yayi izuwa bakin tamfatsetsen mirror ɗin dake manne jikin wall ɗin bathroom ɗin daga gefe, kafin ya buɗe drawer ɗinta ya ciro tissue sheet, ya ajiye hannu ya sanƴa cikin aljihun wandon jikin sa tare da ciro syringe ɗin allura da wani maganin ruwa cikin ƴar ƙaramar kwalba, syringe ɗin allurar ya sanƴa ya zuƙo maganin duka a ciki, kafin ya ɗau tissue ya goge hannun sa dashi yana rufe syringe ɗin ya sanƴa cikin aljihun sa. Takawa yayi zuwa wurin ruwan dake zuba tare da wanke kansa zuwa fuskar sa da hannayen sa tare da rufe famfon, ƴar ƙaramar towel yaja kafin ya buɗe banɗakin ya fito yana goge fuskar sa. Zaune ya ganta bakin bed ta canza shigar jikin ta zuwa ta kayan bacci, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa yana ƙarasawa bakin mirror ɗin ɗakin. Turare mai ƙamshi ya feshe jikin sa dashi, tashi Naseeba tayi tare da ƙarasowa tana rungume sa ta baya a hankali tace "Why are you keeping me waiting Handsome." Runtse idanu ZEEYAD yayi cike da mugun takaici zuciyar sa tamkar zata tarwatse yakeji, he can't believe this wai matar mahaifin sa ke neman yin tarayya dashi, this is totally disgusting. Jaye jikin sa yayi yana barin bakin mirror ɗin, bin bayan sa tayi nan yace da ita "You're wasting my time Hafeezah, i need to get my wife back." Murmushi tayi tana ƙarasowa gaban sa tace "Kai ne ke 6atawa kanka lokaci, sabida ni already a shirye nake." Fuskar sa tayi cupping cikin hannayen ta tana kallon sa, baki ta kai da niyyar sumbatar sa nan taji tsinin shigar abu siririn abu a gefen wuyan ta. Da sauri ta kai hannu wurin tana dafewa tare da zaro manƴan idanun ta cikin azaba, tangaɗi tayi da baya tana faɗawa kan bed ɗin zaune. Ɗago da idanu tayi tana kallon sa tace "What have you done?." "What i think is right" ya faɗa. Murmushi tayi tace "Kana tunanin zaka tsira ne daga hannu na, i have the keys, and your wife is in my custody, there is no way you can get away with this, kafin ma ka isa inda zakaje zan bada umarnin a kashe ta har zuwa lahira ba zaka kuma sake ganin ta ba har..." maganar ta ce ta katse sakamakon wani irin knocking da jiri yayi mata a kai. "Well, maybe sai dai idan a cikin mafarki zaki bada umarnin hakan" yana rufe baki ta faɗi kwance kan bed ɗin. Takawa yayi zuwa inda yaga ta 6oye makullin lokacin da ya shiga canzo kayan shi, ɗaukar key ɗin ɗakin yayi kafin yaje ya buɗe ta ya fice yana sake rufo ɗakin. ************************ _________"Grandma?" ya kira da ƙarfi lokacin da ya iso part ɗinta. Tsaye Grandma ta miƙe tana taro sa ganin yadda ya faɗo mata kamar wani zautacce. Riƙo sa tayi tana faɗin "Boy lafiya dai koh?, ya na ganka haka a firgice, nace dai lafiya?." "Grandma... tell me ina ne cikin ƙasar nan inda babu wani normal mutum ya ta6a taka ƙafar sa yaje, sai dai koh Aljani kokuma babban matsafi, ina ne wurin Grandma, nasan ba zaki rasa masaniya akai ba." Shiru Grandma tayi tana kallon sa kafin tace "Boy kana lafiya kuwa maiyasa kake tambaya ta wurin, wani abin ne ya faru?." Kai yake girgiza mata yace "Grandma please, its so urgent just tell me idan kin sani please Grandma" ya faɗa cikin riƙo ta. Kai ta girgiza masa tace "Ban ta6a jin wuri makamancin hakan ba Boy, ka sanar dani meke faruwa mana." Kai ya girgiza cike da tashin hankali, ba zai iya sanarwa da Grandma ba dan kuwa bayason hankalin ta ya tashi, dukda kuwa yasan she can be of help." Sakin ta yayi kawai yana barin falon nata cikin gudu, da sauri ta mara masa baya tana kiran sunan sa. Part ɗin Nazeerah ya nufa dukda kuwa yasan babu wata jituwa tsakanin su, but ganin yadda take nunawa fake DEENAH kulawa cikin ƴan kwanakin nan yasan maybe she can be of help. Bangaje kuyangun ta kawai yake yana ratsawa ciki har ya iso cikin fankacecen falon nata, karon farko kenan da ya taka ƙafar sa zuwa cikin part ɗinta. Nazeerah dake kishingiɗe gaban ta ɗauke da fruit miƙewa tayi tsaye cike da mamaki ganin ZEEYAD ya faɗo mata kamar wanda ake korar sa. Ƙarasowa gaban ta yayi yana riƙo kafaɗun ta yace "Please, please Big Mom, can you help me?." Mamaki ne ya cika Nazeerah tana kallon ZEEYAD ɗin ganin yadda ya firgice nan tace dashi "What's wrong with you?." Kamar wanda zaiyi kuka yace "DEENAH..." Zaro idanu tayi tace "What's wrong with her, kada kacemin Hafeezah taci galaba akanta." Kai yake girgiza mata nan yace da ita "Ba Hafeezah bace wannan karon, i know that ban ta6a zuwa wurin ki neman wani abu ba but can you please tell me..." "ZEEYAD?" cewar Grandma cikin katse shi tana ƙarasowa ta fizgo shi tace "Mai kake yi anan, mai ya kawo ka nan wurin, i thought duk wani abu da ya shafe ka kana iya faɗamin sannan na kan baka shawara mai kyau, but this time ka tsallake ni kazo nan wurin Nazeerah mai kake tunanin zata iya yi maka wanda ni ba zan yi maka ba" ta faɗa cikin 6acin rai. "Grandma please..." "Banason jin wani abu, wuce muje" ta faɗa tana nuna masa hanƴa. "Grandma DEENAH, i can't find her" ya faɗa cike da tashin hankali yana kallon Grandma ɗin. Kallon sa Grandma take kafin tace "Mai kake faɗa ne haka Boy, ya zakace min baka ga DEENAH ba, ba ɗazun nan da safe kuka zo gaida ni ba." "Grandma, that wasn't DEENAH." "Ban...bangane ba, mai kake nufi da ba DEENAH bace." Riƙo Grandma yayi yana jan hannun ta yace "Come with me." "Don't you need my help anymore?" cewar Nazeerah. Dakatawa yayi yana juyowa ya kalleta, duk wani gulma na PALACE ɗinnan ta sani so maybe ta san wani abu akan Naseeba dama kuma abubuwan da take aikatawa, nan yace "You should come too" yana faɗin haka yaja hannun Grandma sukayi gaba. Da kallo Nazeerah ta bi su kafin kuma ta mara musu baya koh da bata samar da wani alfanuwa a wurin ba ta samarwa idanun ta da kunnuwan ta abinci. Part ɗinsa ya kawo su tare da buɗe ƙofar ɗakin da ya rufe Naseeba suna shigewa ciki. Kwance suka ganta duk suna ƙarasowa wurin ta inda duk suka zaro idanu cike da tashin hankali duk suka furta "Naseeba!." Juyowa Grandma tayi tana kallon ZEEYAD nan tace "Mai ya kawo nasee cikin ɗakin ku, sannan kuma ina DEENAH?." Shiru yayi kafin ya ƙaraso yana kallon Grandma yake nuna Naseeba dake kwance yace "This witch here have been fooling us all a matsayin itace DEENAH, she have DEENAH in captivity and took her shape duk dan ta biyawa kanta buƙatar da ta daɗe tana nema a wuri na, DEENAH have been away for 2weeks Grandma yayin da wannan matar ke pretending a matsayin ita, i have been living with her wanda duk a tunani na she is my DEENAH." Hankali tashe Grandma ke maimaita kalmar "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un." "Kana nufin kace ka kusanci Naseeba a matsayin matar ka DEENAH?" ta faɗa cike da tashin hankali tana kallon sa. Kai ya girgiza mata yace "No Grandma, but tayi duk wani ƙoƙarin ta na ganin hakan ya faru, but ban bata haɗin kai ba, sabida naji sam hankali na bai kwanta da ita ba duba da wasu irin halaye da ta tsiro dasu, i have been blaming innocent DEENAH akan halayen wannan witch ɗin." "Where is DEENAH then, ina ta kai ƴar mutane?." "I don't know, i don't know where to start Grandma, i don't know where to find her, she gave me a clue ɗin inda zan same ta and kince bakisan wurin ba, what do i do now Grandma?." Shiru Grandma tayi babu abina take sai salallami tana jero tsarkakan sunayen Allah. "Where did she said DEENAH take?" cewar Nazeerah tana kallon sa. Ba tare da ya kalleta ba yace "Tace wani wuri ne da babu wani mahaluƙi da ya ta6a taka ƙafarsa yaje wurin except idan ba matsafi koh Aljani bane." Shiru Nazeerah tayi tana nazari idanun ta kan Naseeba. Shiru duk ɗakin ya ɗauka babu abinda kakeji sai muryar Grandma dake ta jawa Naseeba tsinuwa cikin muryar kuka tana haɗa wa da addu'a da kiran sunan Allah. Nazeerah ce tayi caraff tace "I don't know the place but seems like Naseeba na neman yi maka wasa da hankali ne, ba abin mamaki bane idan DEENAH na cikin gidan nan." Sai a sannan ya ɗago yana kallon ta, kai ta jinjina masa kafin tace "Tun kana yaro Naseeba ke bibiyar ka take kuma son cimma manufar ta akanka, hakan ya sanƴa ba zata yi ƙasa a guiwa ba har sai taga burin ta ya cika, da akwai wata Maid ɗinta Kiki tare suke shirya duk wani makirci da ƙulli, na tabbata idan aka nemo Kiki zata faɗi inda DEENAH take dan kuwa ba zata rasa masaniya ba." "Where is this Kiki?" ya faɗa yana kallon ta. Shiru tayi kafin tace "Bana ma tunanin idan idan ƴar garin nan ce, koh tantama bana yi ta koma chan garin su idan Naseeba ta cika burin ta sai ta dawo a zumar cewa duk tafiya sukayi kamar yadda Naseeba ta sanar." Kai ya jinjina kafin kuma yayi saurin ficewa daga ɗakin inda duk suka bisa da kallo. Grandma dake cikin tsananin tashin hankali kallon Nazeerah tayi tace "Tunda nake ban ta6a yarda dake ba, wa ya sani ma koh bakin ku ɗaya da wannan iftila'in dake kwance, duk kun bi kun takurawa rayuwar yaro kun hana shi sukuni, duk abubuwan da kukayi masa a baya bai isheku ba, ku shikenan ba zaku sarara ba har sai kunga bayan shi, yayi auren ma kun soma bibiyar matar sa, yarinƴa ashe koh kwana ɗaya batayi cikin gidan nan ba wannan tsinanniyar ta kar6e gurbin ta, insha Allah Naseeba ƙaryar ki ta ƙare yau, azzaluma insha Allah wannan ƙatoton kan naki sai an guntule shi yau sai naga ta tsiya, tsinanniya kawai mai bakin iyaye" ta ƙarashe tana sharce hawaye. Ɗan ta6e baki Nazeerah tayi kafin tace "Ni ba wannan ba tukun Hajiya, mu kama Naseeba mu ɗaure ta dan kar ma ta samu damar tserewa idan ta farka, ke kanki kinsan bana shiga sabgar da ba tawa ba, ZEEYAD ne ya gayyato ni da kansa idan ba haka ba ai koh murya ta ba zakiji ba har a gama case ɗinnan." Cikin kuka tace "Eh kuma kinyi gaskiya" tana goge hawayen idanun ta. *************** ________Cikin abinda bai fi awanni biyu ba aka nemo Kiki da ta gudu ƙauyen su kamar yadda sukayi da Naseeba. Durƙushe take gaban mai Martaba fadar cike da mutane kamar kullum, da kaga idanun ta kaga sun raina fata sai jujjuya su take yawa warwaro a langa, tsabar munafurci da yayi mata ƙatutu cikin zuciya. "Gata kamar yadda akace itace Jakadiyar Sarauniya Naseeba, sannan da sanin ta take aiwatar da duk wasu hukunce-hukuncen ta" cewar ɗaya daga cikin ministocin. Tsaye ɗaya ya tashi bisa ga Umarnin mai Martaba nan ya hau tambayar Kiki "Menene ainihin sunan ki, sannan daga wace ƙabilar kike, sannan kuma menene gaskiyar abinda Yarima YAZEED yake faɗa har ya sanƴa aka kamo ki daga chan garin da kika gudu..." "Wait, wait, sake tambayar ta kake do you think i can lie to you or something?" kafin kuma cikin tsawa ya ɗaura da faɗin "My wife is in their captivity and you're here asking her koh abinda na faɗa akansu is true, just ask her where my wife is or else i will take action in my own." "Calm down Prince, komai cikin ruwan sanƴi akeyin..." "What kind of ruwan sanƴi, irin wadannan mutanen ba'a binsu ta lallama, what about my wife then, do you have any idea yadda rayuwar ta ya kasance tare dasu tsawon makonni biyun da tayi a wurin su, and you expect me to calm down, calm down on what, my wife being captured or what?" ya faɗa cikin tada jijiyoyin wuya yana iyowa kan minista ɗin. Maganar mai Martaba ce ta dakatar dashi, sai hura hanci yake cike da tsantsar 6acin rai yana fidda huci mai tsananin zafi, juyawa yayi ga mai Martaba ɗinma ya hau faɗin "Are you trying to stop me or what your Highness?, why would he tell me to calm down, does he have any idea ɗin halin da nake ciki...? Shiru yayi ya kasa iddawa sakamakon wani tululun baƙin cikin da yazo masa maƙoshi. Tasowa mai Martaba yayi daga inda yake zaune yana takowa inda ZEEYAD ke tsaye ya hau buga kafaɗun sa yace "We should take everything easy Son, insha Allah matar ka zata bayyana." "If anything happens to her then... then i don't know ya tawa rayuwar zata kasance nima." "Don't say that, i promise you zata dawo cikin gidan nan yau." Juyawa yayi ga ministan nan yace "The Prince don't want her to be confronted like this, ku kai ta ku garƙame sannan a haɗa mata da horo mai tsanani har sai ta faɗi gaskiya akan dukkanin abinda suke shukawa da ita da Naseeba, sannan ta faɗi inda matar Yarima take, take her." Cikin ƙururuwa tace "Kuyimin rai, wallahi zan faɗi komai dan kuwa nasan koh da nayi shiru azaba zan sha sannan kuma nazo na faɗi gaskiyar da banason faɗa ɗin, wallahi nasan inda take kuma shirye nake da na faɗi gaskiyar komai." Kai sarki ya Jinjina yana komawa wurin zaman sa, nan ministan yace "We are all ears." "Wallahi amaryar Yarima tana nan da ranta, sannan tana chan ƙarƙashin kulawar kaka ta ne." "Kulawa kokuma azabtarwa?" ya sake tambayar ta. "Azabtarwa nakeson faɗa, ayimin rai." "Wacece kakar taki sannan a ina take da zama?." "A chan wani ƙauye ne wanda tafiyar awanni sha biyu ne tsakanin sa da wannan MASARAUTA, sannan Kaka ta ta kasance tsohuwar matsafiya ce wacce ba'a ta6a yin irinta duk ƙauyen ba, haka ma batada ɗigon imani koh kaɗan muddin an biya ta makuɗan kuɗaɗe, sai dai wannan karon bata kar6i kuɗi ba sakamakon cewar jinin amaryar Yarima ZEEYAD yayi mata dan kuwa irin sa ta daɗe tana nema dan cikar wani burin ta, maganar da nakeyi maka yanzu ma a yau ɗinnan take niyyar sadaukar da ita ga ƴan ruwa sakamakon wani matsayi da zasu bata." Cike da tashin hankali duk suke kallon Kiki, Sarauniya Hafeezah kuwa wani irin farin ciki ne ya mamaye mata zuciya, koh bakomai Naseeba ta kawo mata sauƙi yanzu saura ita da ZEEYAD ne, dan kuwa babu shakka kafin mu su isa ga kar6o DEENAH an riga da an sadaukar da ruhin ta ga aljanun ruwan, sai dai suje su sami gawar ta. A matuƙar ruɗe sarki ya tashi tsaye cikin tsawa yace "Find her." Duk fadawan dake cikin fadar ficewa sukayi cike da girmamawa cikin bin umarnin sarkin suka je suka fara shirye-shiryen kaiwa Ƙauyen farmaki, inda aka tafi da Kiki dan yin jagora. ZEEYAD kuwa tsaye yayi kamar wanda aka ɗauke masa dukkanin wasu ƙuzarin jikin sa. Dafa shi YAZEED yayi yace "We will find her." Runtse jajayen idanun sa da suke yi masa yaji sosai yayi yanajin sa kamar ma ba a duniyar yake ba. He can't believe wai DEENAHr sa za'a yi wa sacrificing soul nata wa ƴan ruwa, this is odd. Juyawa kawai yayi ya fara tafiya kafin YAZEED ma yayi saurin mara masa baya. Komawa mai Martaba yayi ya zauna yana sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, kallon ministocin sa yayi yace "Naseeba, Jakadiyar ta dama kuma duk wasu masu sanƴa hannu cikin wannan lamari duk a yau za'a yanke musu hukuncin da aka tanadawa masu laifi irin nasu." Amsawa sukayi cike da girmamawa kowanne zuciyar sa cike da al'ajabin wannan lamari. ********************* ________Ƴar ƙofar karar da aka buɗo ne ya sami damar baiwa haske gurbin shiga cikin ɗakin. A hankali take motsa nannauyar idanun ta da hasken ranar ya dallo mata shi da bakin ta da ya bushe ƙaƙarau kamar wacce ta ɗau tsawon kwanaki bata sha ruwa ba. Kutsa kai akayi aka shigo cikin ɗan ƙararramin ɗakin wanda kai tsaye za'a iya kiran sa da kurkuku tsabar matsi da ƙanƙantar sa, ga kuma tarin wasu tsoffin abubuwa da aka rufe su cikin buhu da alamu dai sun daɗe duba da yadda spiders suka zagaye shi da gine-ginen su. Turo mata tray ɗin silver akayi wanda ke ɗauke da busasshiyar slice bread guda ɗaya kafin tsohuwar ta fara magana cikin muryar da ba fahimtar komai take ba "Ina mai gargaɗin ki da kici wannan abincin dan kuwa shine zai kasance abinci na ƙarshe da zakici a duniya, ƙin cin sa dai-dai yake da rasa ranki nan da ƙanƙanin lokaci, nikuma ba zanso hakan ya faru ba kafin ki mutu dole naje na sadaukar da ruhin ki koh dan samun cikar buri na." DEENAH dai saurarar ta take ba dan tana gane wani abin da take cewa bane, gashi kuma a mugun galabaice take, sau ɗaya take bata busasshiyar bread a rana ɗaya matsayin abinci ruwa kuwa, idan ta bata cikin wani ɗan madaidaicin kofi a rana ɗaya shikenan, shima dai tana bata ne dan kar ta mutu kafin lokacin da zata bayar da ita yayi. DEENAH dai kawai da idanu take bin ta, har ta fice daga cikin ɗakin tana rufo ɗakin take ya gauraye da wani irin duhu kai kace dare ne yayi. Jan ɗuwawu tayi daga inda take zaune zuwa inda taga ta ajiye tray ɗin kasancewar hannayen ta da ƙafafuwan ta da akayi musu ɗaurin goro. Da kyar ta miƙa hannu ta lalumo busasshiyar bread ɗin wanda shima ya fara huhhuna ta kai bakin ta inda kuwa wasu irin siraran zafafan hawaye suka shiga yi mata zarya kan kumatu, a haka ta lunƙuma bredin a baki dan kuwa idan bata ci ba wani abincin take kawo mata daban wanda bata tunanin mutane ma suna cin sa, sannan ta sanƴa ta dole sai ta cinƴe shi. Sosai zuciyar ta ke cike da baƙin ciki da ƙunci, babu wanda ya san da ita anan wurin sai Allah, Abyad ɗinta bai san tana nan wurin ba da ya daɗe da zuwa neman ta, yana zama da Naseeba ne a matsayin ita, babu ta yadda zaiyiwu ya gane cewa ba ita bace ba, shikenan ita kuma tata rayuwar tazo ƙarshe kenan dan kuwa she have no idea mai tsohuwar nan take shirin aikata mata, maybe dama chan Allah bai tsara zasuyi rayuwa tare dashi ba, maybe dama haka Allah ya tsara ƙaddarar rayuwar ta zata mutu ne ba tare da kowa nata ya san cewa ta mutu ba, ta san shikenan ƙarshen ta yazo kenan tunda har tsawon kwanakin nan babu labarin da taji na ana neman ta koh asirin Naseeba ya tonu, wani irin matsanancin kuka ta sanƴa da ƙarfi tana yi harda shessheƙa, sosai koh ina na jikin ta keyi mata zugi da raɗaɗi, musamman hannayen ta da ƙafafun ta da tunda ta tsinci kanta anan ba'a ta6a sunce mata su ba, except idan zata banɗaki ne, ba'a barin ta taje koh ina, kullum tana cikin wannan ɗaki mai matsanancin wari da duhu, ga kuma tarin kwari da cinnaku kamar ruwan su akeyi, bata ta6a runtsawa na awa ɗaya ƙwakkwara cinnaka bai gallaza mata cizo ba, ga kuma azababbiyar ƴunwa da ishi da kullum take cikin sa, ga ruwa tana gani amma a bata ta sha ya zama aiki. ************************** _________Naseeba ce ta fara buɗa idanun ta a hankali tana ware su kan Grandma da Nazeerah da suka sanƴa ta a gaba, tuna abinda ya faru tsakanin ta da ZEEYAD ne ya sanƴa ta saurin waro idanun ta tana sake bin su da kallo. Duk tsare ta sukayi da idanu duk suna bin ta da kallo, jijjiga kujerar da take ɗaure akai ta fara tana ihu cikin bakin ta dake a toshe sealing tape. Grandma dake bin ta da mugun kallo ne ta taso inda take, cike da mugun ta ta ɗaye gum ɗin bakin nata take ta saki wani ƙara cike da azaba, kafin kuma ta hau faɗin "Let me go or else i will make you all regret it." Mari Grandma ta ɗauke fuskar ta dashi tace "Mu daɗe bamuyi nadama ba Naseeba." Sosai zuciyar Naseeba ke burning, juyo da fuska tayi tana kallon Grandma kafin cike da fusata tace "How dare you Old hag." Wani marin Grandma ta sake ɗauke ta dashi wanda yafi na farkon. Magana zata sake ta sak ɗebe ta da wasu tagwayen marin kafin ta ɗaura da faɗin "You said a word, you get a Slap." Huci kawai Naseeba ke fitarwa zuciyar ta na wani irin tafarfasa. "How dare you Naseeba, ke bakiji kunƴa ba, da girman ki kike neman ɗan mijin ki da Alfasha, how could you do such a thing, well koma dai menene ya faru yanzu ke kika jawa kanki, sabida mai Martaba dama kowa ya gano ki asirin ki ya tonu Naseeba, da zaran an ɗauko DEENAH yanzu babu 6ata lokaci zaki baƙunci lahira" cewar Grandma cikin tsananin fushi. Baki ta buɗe tare da faɗin "You think you can find her so easily am pretty sure kafin aje gareta ta riga da ta mutu." Wani azabbaben mari Grandma ta ɗauke fuskar ta dashi a karo na huɗu tana faɗin "Shut up and don't say a word..." "What will you do old hag, are you going to kill me, fine then go ahead koh bakomai buri na na kusantar jikan ki ya cika." Mari Grandma ta sake kai mata tana faɗin "We know everything, Boy ba zai ta6a yarje miki ba, koh da mata sun ƙare a duniya bana tunanin zai tsaya ya kalle ki sabida babu wani abin burgewa da ɗaukar hankali tattare dake." "Oh come!, how do you expect ke6ewar mace da namiji wuri ɗaya kuma ki tabbatar da cewa mai afkuwa bata afku tsakanin su ba, i know ba zai faɗa muku gaskiya ba, but he did get intimate with me" ta ƙarashe cikin shu'umin murmushi. Gum ɗin bakin ta Grandma ta maida tana faɗin "Non of your tricks can work on me Naseeba, you just wait and see how i teach you a lesson" ta faɗa tana dube-dube cikin ɗakin kafin kuma tayi saurin ficewa. Kallon ta Nazeerah tayi tare da sakin murmushi tace "What a shame Naseeba, i told you didn't i?, i told you to stay away from the Boy but kince bakiji ba, so dama baki tanadi zuwan wannan ranar bane kike ta shuka tsiya, you think asirin ki ba zai ta6a tonuwa bane komiye?, kinga shiyasa ban ɗau damuwar komai na ɗaurawa kaina ba, Allah ya bani ƴaƴa mata na aurar dasu da mutuncin su da komai banga abinda zai sanƴa ni tada hankali na kan wani abu da nasan ba zan ta6a mulkar sa ba, koh da bakiji tsoron Allah ba ai kyaji tsoron zuwan ranar tonon asirin ki, who even cares da wani abin duniya, kinga wannan bakin nawa sam baya magana muddin ba'a gayyato sa bane ba, yaushe nake da lokacin 6atawa ina shirme, kinga gulma ta a ciki na take ƙarewa bata fita koh ina, na baiwa kunnuwa na da idanu na abinci ya isheni nishaɗin gidan duniya, but kinga yadda rayuwar ki ta kasance, kada kiso kiga yadda ran mai Martaba ya 6aci, na tabbata ba zai ɗaga miki ƙafa ba, dan kuwa har Jakadiyar ki Kiki aka kama yanzu haka an kaɗa ƙeyar ta izuwa ƙauyen da kakar tata take, nasan yanzu haka ma sunyi nisa da tafiyar." Murmuring Naseeba ta fara tana jijjiga kujerar da take kai, ba'a jima ba Grandma ta shigo hannun ta riƙe da hockey stick, kallon Naseeba tayi tace "Ba zan bar ki ki tafi haka banza ba ba tare da nima na huce takaici na akanki ba, you must suffer today" ta faɗa kafin ta shiga zabga mata sandar hannun nata. Sosai Naseeba ke jin azaba sai dai babu bakin magana kasancewa bakin a toshe ga hannaye duk a ɗaure babu damar kwacewa. Sosai Grandma ta bubbuge ta iya son ranta har sai da ta gaji ta bari tana zama bakin bed kafin ta shiga sauƙe ajiyar zuciya akai-akai. Sosai Naseeba takejin idan ta kwace babu abinda zai hana ta aika Grandma lahira. "So now nayi miki nawa hukuncin, yanzu sai ki jira kuma na mai Martaba, kema dai kinsan hukuncin ki ba sai an faɗa miki ba, ke abin naki ma yayi yawa ga laifin aiki da asiri ga kuma laifin neman ɗan mijin ki, na tabbata binne ki kawai za'ayi a rami a bar ƙatoton kanki a waje a kuma tara yara suyi ta wulli har sai sun gaji kafin kuma a ɗauko takobi a yanke ɗan iska." Suna haka Guards suka faɗo cikin ɗakin, kallon Naseeba dake a ɗaure ta waro idanun ta kamar zasu faɗo waje sukayi kafin su kalli Grandma suce "Mai Martaba ya umarce mu da mu kai Sarauniya Naseeba izuwa fadar sa, sannan kuma yana buƙatar ganin ku anan wurin." Miƙewa Grandma tayi tace "Masha Allah, ai dama abinda nake ta jira kenan, yau dai duhun ki ya cika Naseeba, sai dai kuma uwarki ta haifo wata idan tana haihuwar kenan, Allah sarki sai kuma aje a haɗu da hukuncin da ba'a ta6a ganin irin sa a duniya ba wato hukuncin Allah, ai tunda kika nuna bakiji tsoron sa da kunƴar sa ba toh wallahi sai kin kunƴata duniya da lahira, ku ɗauke ta kuje gamu nan biye daku." Ƙarasawa sukayi tare da sunce ta daga jikin kujerar da take ɗaure kafin su riƙe ta su fitar. Kallon Nazeerah Grandma tayi tace "Toh ke kam dai ba zance kina burge ni ba, dan kuwa kema bansan koh kina da wata sharrin a ƙasa ba, amma dai mungode da ba da ke ba ai da ba zamu san da wata Keke koh ya sunan nata yake ne ma, muje mu dan kuwa nasan ba zaki so kallon abinda zai faru a fada ya bar ki ba." Murmushi Nazeerah tayi tana marawa Grandma baya suka fice. ****************** _______Time to time yake duba agogon dake maƙale jikin tsintsiyar hannun sa, sosai yake cike da damuwa sam baya ganin gudun motar tasu duk da kuwa irin gudun da YAZEED keyi mata. Ɗan kallon sa YAZEED yayi yace "Don't panic please, am sure zamuyi arriving before time ɗin yayi." "We've almost 4hrs kafin mu ƙarasa and it's 4pm now, GOD knows what will happen to DEENAH idan bamu ƙarasa dawuri ba" ya faɗa cike da damuwa. Wayar YAZEED dake silent ne ta sake kawo wuta a karo na ba adadi, tsaki yaja ganin dai mahaifiyar sa ce ke kira, daga baya ma katse kiran yayi yana switching ɗin wayar off. ZEEYAD dai bai kula shi ba dan kuwa tashin hankalin da yake ciki kaɗai ya ishe sa. *************************** _________Daf da Magrib suka ƙarasa wannan ƙauyen da bai wuci wani 6angare cikin MASARAUTAR su ba. Da kaga mutanen ƙauyen ma kansu kasan yin asiri gadon ta sukayi. Duk firfitowa sukayi inda kowa ya fara shigewa gidan sa yana rufowa ganin guards ɗin MASARAUTA koh ta ina. Kiki ce tayi musu jagora har izuwa gidan kakar tata, koh da zuwan su basu same ta ba, sai wata mata suka samu inda take shaida musu cewa Kiki ta ɗau DEENAH sun fice. "Find her, ku dubo kowane lungu da saƙo har sai kun gano inda take don't let her escape" cewar YAZEED cikin ɗagun murya. Nan fah duk suka dunguma izuwa neman wannan tsohuwar, kallon Kiki ZEEYAD yayi yace "You know where we will find her don't you?, tell me dan nasan ba zaki rasa masaniya kan inda take kai ran mutane ta sadaukar ba." "Wallahi ranka ya daɗe bansan komai ba, nayi maka alƙawari wallahi bansan komai ba." "Damn" ya faɗa a hankali. YAZEED ne yace "We must find her, ina ne babban kogi koh ruwa a wannan ƙauyen, maybe idan muka bi nan zamu same su." Wannan matar ce tace "Yallabai." Duk kallon ta sukayi nan tace "Zan faɗa muku inda ta kaita amma nima kuyimin alƙawarin zaku cece ni daga hannun ta, dan kuwa so take ta hallaka cikin dake jiki na, sannan Kiki ƙarya takeyi muku babu abinda bata sani game da kakar tata ba." Duk irin idon da Kiki keyi mata bai hana ta magana ba, kallon Kiki ZEEYAD yayi a tsawace yace "You lied to me." Batasan sadda ta zube ƙasa tsabar ruɗewa ba tana riƙo kafafun sa, janƴe ƙafar sa yayi yana wani irin ball da ita cike da tsantsar 6acin ran da yake ciki kafin ya kalli matar yace "Take us there." Kai ta jinjina kafin ta shige gaba suna mara mata baya, inda wasu daga cikin guards ɗin suka garƙame Kiki. Tafiya mai nisan gaske sukayi, babu abinda suke ratsawa sai jeji a hanƴar tafiyar su ne take faɗa musu cewa "Kiki tana amfani ne da tsafi wurin kawar da hankalin mutum sannan ta asirce shi yadda zaiyi dukkanin wani abu da ta umarce sa, zata sadaukar da ran wanda taso ga aljanun ruwa sabida samun ɗaukaka a duniyar matsafa ya zamto babu matsafi koh matsafiyar da ta kaita ƙarfi, koh yanzu sai munyi a hankali, dan kuwa muddin tasan da zuwar mu babu abinda zai hana ta ganin bayan mu, da akwai wani sanda a hannun ta dashi ne dukkanin wani ƙarfin tsafin ta yake ciki, muddin muka sami damar ɗaukar sandar nan toh babu abinda kuma zata iya, koh da ta karanto makaran tsafi, dan kuwa muddin sandar ya shiga hannun wani toh tsafin ta ya karye kenan, shiyasa a kullum sandar ke tare da ita, koh da da wasa bata rabuwa dashi." Shi dai ZEEYAD jinta kawai yake but dukkanin hankalin sa na kan DEENAH ganin har yanzu basu isa bane ya sanƴa shi faɗin "How far is the place?." "Mun kusa ƙarasawa sai dai ni zan ɗan dakata daga gaba kaɗan ku ku ƙarasa, koh dan lafiyar abin dake cikin ciki na." Kai YAZEED ya jinjina mata, har sai da ta kai su wurin wani dutse kafin tace dasu" ku bi wannan hanƴar sai dai ku sani dole sai kun haɗa da addu'a, sabida akwai hatsari sosai muddin mutum ya wuce wannan dutsen shiyasa ni zan barku daga nan." YAZEED ne yace "But aren't you afraid to go back alone?." Kai ta girgiza masa cikin murmushi tace "Koh kaɗan bana tsoro indai har ba wai na wuce dutsen gaban nan bane, nan ne abin tsoron yake, ni zan koma ku ku wuce tun kafin Kiki ta gama aiwatar da ƙudirin ta, ni kaina kun cece ni, dan kuwa nice target ɗinta ta gaba dukda kuwa matsayi na na matar jikan ta sai dai tayi alwashin sadaukar da abin dake ciki na, nayi dukkanin yadda zanyi dan tseratar da raina amma abin yaci tura, kuje ku kada na 6ata muku lokaci." "Mungode" YAZEED ya faɗa yana saurin marawa ZEEYAD da ya riga da yayi gaba baya. Sosai dajin ke cike da duhuwa babu abinda kake ji sai ƙarar kukan mujiya da ma kuma wasu mugayen tsuntsayen. Wayar sa YAZEED ya kunna yana haska musu ganin yadda duhu ya mamaye wurin. Dukkanin su babu abinda sukeyi sai karanto addu'o'in neman tsari daga sharri, a haka har suka ƙaraso wani fili sai a sannan suka samu ganin sararin samaniya da tayi haske da ita sakamakon hasken farin watar da ya gauraye ilahirin wurin baki ɗaya, daga gaban sa chan kuwa wani ƙaton tekun ne inda suka hango wannan tsohuwar nan hannayen ta riƙe da na DEENAH cikin tsakiyar ruwan. "DEENAH..." cewar ZEEYAD bai ƙarasa ba YAZEED yayi saurin toshe masa baki yana riƙo shi. A hankali yake faɗin "This is our only chance, kada muyi wasa dashi, remember what that lady told us, that stick" ya faɗa yana nuna sandar ta dake ajiye a gefe. Kallon sandar ZEEYAD yayi nan YAZEED ya cigaba da faɗin "Damar mu shine mu samu mu ɗauke sandar kafin mu tunkare ta." "But DEENAH..." "We will deal with her later, let's find a way to get her distracted first." "But how?" ya faɗa. "Like this" cewar YAZEED yana tura shi kafin shi kuma yayi saurin la6ewa. Da sauri ta juyo tana kallon ZEEYAD da idanun ta da suka canza, tana sakin hannun DEENAH tare da fitowa daga cikin ruwan tana faɗin "Waye kai, mai kakeyi anan?." Surrending ZEEYAD yayi da hannu idanun sa kan DEENAH da tayi tsaye cikin ruwan kamar wata gunki, a hankali ya fara waina tsohuwar yana faɗin "I...i...i was just passing by and i thought i should say hello." "Ka raina min hankali ne yaro, kana neman wasa da rayuwar ka ne, do you want to die young?." Ɗan murmusawa yayi yace "What are you saying?, i mean it's just that aikin naki ne ya burge ni, and i thought that you're making alot of money with that, so i decided to confront you..." "Shut up" ta faɗa a tsawace tana nuna shi da sandar ta. Shiru yayi still hannayen sa a sama, a hankali ya fara juyawa har ya zama na ita ta zamto tana fuskantar DEENAH, nan shi kuwa YAZEED ya fito daga ma6oyar sa ya shiga takowa cikin sanɗa. "Please... Please i really want to work with you, i wanted to be your help boy, just don't kill me." "Don't say another word Young boy, tell me who you are." Kallon YAZEED dake tsaye a bayan ta yayi kafin yace "Well, maybe you should get to know who he is first." Juyawa tayi dan ganin waye a bayan nata, juyowar tata ke da wuya YAZEED ya gwara mata kanshi, nan fah ta tafi tangal-tangal, Inda ZEEYAD kuma yayi nasarar kwace sandar hannun ta, kafin ta sake wani yunƙuri tuni YAZEED ya sake ham6arar ta da bayan hannun sa take ta faɗi ƙasa warwas, dama gata ba aukin komai ba. Duk shewa suka sanƴa suna tafa hannayen su haɗi da rungume juna, juyawa ZEEYAD yayi ga DEENAH da har ruwan ya fara tafiya da ita, cike da tashin hankali ya shiga gudu cikin dukkanin ƙarfin sa yana faɗawa cikin ruwan. Nutsawa yayi ciki yadda zaiyi saurin tadda ta kasancewar ya iya ruwa ya sanƴa cikin ƙanƙanin lokaci ya lalumo ta a cikin ruwar yana ɗagota. "DEENAH" ya furta da ƙarfi yana ɗan marin fuskar ta. Rungume ta yayi sosai a jikin shi kamar wanda za'a kwace masa ita, yayin da yakejin wani irin ƙauna da sonta na ƙara yi masa dirar mikiya tare da ratsa dukkanin wani jijiyoyi da 6argo na zuciya da jinin jikin sa. Ɗago da fuskar ta yayi yana kallon ta kafin kuma ya haɗe bakin su wuri guda yana sumbata. "Let's get going Bro" ya tsinkayo muryar YAZEED. Sakin lips nata yayi kafin kuma ya ɗauke ta a hannu suka fito daga cikin ruwan. Ƙarasowa inda YAZEED ke tsaye yayi yana kallon sa, murmushi YAZEED ya sakar masa tare da furta "Alhamdulillah." Murmushi ZEEYAD ya sakar masa tare da faɗin "Let's go home, let's go" ya faɗa yana kallon fuskar DEENAH. "Is she breathing?" cewar YAZEED yana kallon sa. Fuskar ta yake bi da kallo kafin yace "I know she is alive, she isn't dead." "Then we should get going, it's getting late." Gaba yayi kafin YAZEED ya kalli tsohuwar da har yanzu ke yasha sakamakon bugun da tasha yace "What about her?." "Leave her there, but come along with the stick" ya faɗa ba tare da ya juyo ba. Kallon ta YAZEED yayi kafin kuma ya riƙo ƙafafun ta yana janta zuwa bakin ruwan tare da faɗin "Why don't you sacrifice yourself instead" yana faɗin haka ya marawa ZEEYAD da har yayi nisa baya cikin gudu. ********************* _________Duk tsaye sukayi akan DEENAH da har yanzun bata farka ba, hannun ta kuwa ruwa ne aka jona mata. Kallon ZEEYAD da ya kasa koh da barin wurin ta Grandma tayi tare da dafa shi tace "Boy kaima yakamata ace ka sami hutu, tun jiya da kuka dawo baka wani sami baccin kirki ba." "Grandma please, i don't want to leave her, ba zan sake yin nesa da ita ba, what if something bad happens to her again?." Sauƙe ajiyar zuciya tayi tace "But am here, koh da baccin awa ɗaya ka samu kayi..." "No Grandma" ya faɗa kai tsaye. Shiru Grandma tayi ta kyale sa kawai dan kuwa tunda yace a'a ɗin toh yana nufin a'a ɗin ne. Kissing hannayen DEENAH dake cikin nashi yayi yana murzawa kafin ya fara faɗin "Am sorry DEENAH, i caused you all this." "Stop it Boy" cewar Grandma. "I will never stop feeling guilty until na ganta ta buɗe idanun ta sannan ta kira sunana ta cemin she is Okay." "Insha Allah hakan zai faru, you know how hard it has been for her, dole she needs more rest zuwa anjima zata iya farkawa." Kai kawai ya jinjina mata ba tare da yace komai ba. Ƙarfe sha ɗayan safe ya wuce DEENAH ta farka, ware idanun ta da sukayi mata nauyi tayi tana sake bin ɗakin da kallo. Da sauri ta miƙe dan kuwa ta zaci koh mafarki take, murza idanun ta tayi nan dai tags ba mafarkin take ba, bin riga da wando na baccin jikin ta tayi kafin kuma ta maida idanun ta gun inda take jiyo motsi. Fitowa yayi daga ɗakin closet ɗin yana sauƙe idanun sa cikin nata da ta kafe sa dashi. Da sauri ya ƙaraso wurin ta yana kiran sunan ta. Ja da baya tayi dan kuwa bata yarda koh shi ɗin bane ba. "DEENAH" ya kira sunan ta. "Don't come close to me" ta faɗa cikin tsoro tana sake ja da baya. "Babe it's me, not Naseeba." Shiru tayi tana kallon sa kafin a hankali tace "Abyad?." Kai ya jinjina mata, rarrafowa tayi da sauri tana shigewa jikin sa tare da sakin kuka. Rungume ta yayi tightly yana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyar sa. Sosai ta sha kuka kafin ta ɗago da idanun ta tana kallon sa, hawayen da ya 6ata mata fuska ya share mata, kafin yayi kissing lips nata yace "I miss you." "You've been living with your step Mom all this while not me, she is evil, they are all evil" ta faɗa cikin kuka kafin kuma ta ɗago hannayen ta dake ɗaure da Bandage sakamakon ciwon da taji sakamakon igiyar da aka ɗaure ta dashi da yayi tighting ɗinta sosai, nan ta cigaba da faɗin "The old woman, where is she?." "She is dead" ya faɗa yana kallon ta cikin kulawa. Sake manna kanta tayi a ƙirjin sa kafin tace "What about your step Mom then?." "She is still alive, ke ake jira ki farka a yanke musu hukunci a gaban ki." Ɗagowa tayi tana kallon sa, nan ya jinjina mata kai, cikin kuka tace "I don't want to... i don't want to go anywhere, am afraid your PALACE is full of wicked souls, babu wanda yake sona sai kai da Grandma, babu inda zan sake fita." Cupping fuskar ta yayi yace "Calm down please, kina jin tsoro?." Kai ta jinjina masa da sauri nan yace "Shiyasa suke samun damar cutar dake coz you're afraid of them and what they can do, just show them cewa ke babu wanda kike tsoro sai Allah and dashi kika dogara, idan kinyi hakan then babu wanda zai sake raina miki hankali wurin kawo miki farmaki sabida kin riga da kinyi musu nisa." Shiru tayi kawai tana kallon sa, murmushi ya sakar mata yana sake kissing lips ɗinta. Lamo tayi a jikin sa tana rungume sa so tightly kamar wanda zai gudu ya barta. ********************** _______Da yamma mutane ne birjik a wani ƙaton fili da alama dai duk sunzo baiwa idanun su abinci ne bisa ga irin hukuncin da za'a yiwa Naseeba da Jakadiyar ta Kiki. Hannayen su duk a ɗaure yake aka fito dasu daga cikin kurkukun da aka garƙame su guards na biye dasu aka shigo dasu filin kan dakalin da za'a yanke musu hukunci ɗin. Kallo ɗaya zakayi musu ka hango tsantsar tashin hankali da fargabar da suke ciki. Miƙewa sarki yayi hakan ya sanƴa ilahirin wurin baki ɗaya ɗaukar tsit. Cikin mic ya fara magana da cewa "Ance 99days for the thief, one day for the owner, as you can all see here the person i called my wife is about to be executed together with her maid, sakamakon mummunar laifin da suka aikata wacce ta sa6awa dokar Allah dama kuma ta MASARAUTA, wannan doka bata duban girman mutum koh level ɗinsa, muddin hukunci ya hau kanka toh tabbas dole ne ka fuskance shi koh kai waye, ta haka ne kaɗai zamu rage yawaitar aikata miyagun laifuka a doron ƙasa, Naseeba here has crossed the line dukda kuwa cewa ta san hukuncin duba da ita ɗin matata ce doesn't mean za'a yi mata sassauci ya zama dole ne a yanke mata hukunci kamar kowa, kowa ya san laifin da ta aikata dan haka she will be executed." Shewa ne ya karaɗe wurin rabi da kwatan mutanen wurin duk suna bada goyon baya akan hukuncin yayin da wasu kuma ke ta Allah wadai da wannan sabuwar hukunci. Bisa ga umarnin sarki aka kama Naseeba da Kiki aka ɗaura su kan wasu dogin abubuwa yayin da aka rataye kawunan su jikin igiya kafin a rufe musu fuska da baƙar abu kamar hula. Sosai Kiki ke kuka babu abinda take sai tsinewa Naseeba, haka ma 6angaren Naseeba wata iriyar tarin kunƴa da nadama ce ta rufe ta. DEENAH ji tayi ba zata iya jurar ganin hukuncin da za'ayi musu ɗin ba, gani take yayi tsauri tunda ba wai kashe mutum sukayi ba. Kallon ZEEYAD tayi tare da faɗin "Abyad stop them." "What, why?." "Stop them please" ta faɗa kamar wacce zatayi kuka. "What are you saying DEENAH, they tried to get you killed." "But am alive, just stop them please" ta faɗa hawaye na kawowa idanun ta. Rungume ta yayi yace "Ba dole sai kin kallesu ba then" ya faɗa yana kare idanun ta daga kallon wurin. Ita dai dukda haka bata yarda ba, dan kuwa bata tunanin zata iya bacci muddin akayi kisar nan a gaban ta. Ɗagowa tayi ya sake maida ta, gently yake rubbing bayan ta tare da faɗin "Relax." _"Pull_" shine abinda ta jiyo an faɗa da ƙarfi, kafin ta ankara kuwa tuni su Naseeba suka hau shure-shuren ƙafa har rai yayi halin sa, ƙara DEENAH ta saki tana sake ƙanƙame ZEEYAD ɗin. Patting bayan ta yake a hankali yana sake rungume kanta a ƙirjin shi. Wurin ne ya ɗau hayaniya bayan an kashe Naseeba da Kiki. Kuka JALILAH dake kusa da YAZEED ta sanƴa inda ya juyo cike da mamaki yana kallon ta wondering koh menene ya sanƴa ta kuka kuma ita. Ta6e baki Sairah tayi kafin tace "This is so interesting to watch, why is she crying?." YAZEED bai kula ta ba, but hankalin sa na kan JALILAH ɗin dake ta sharar hawaye, tashi tayi ta bar wurin tana cigaba da goge hawayen ta. Da kallon gefen ido ya bita yana karkaɗa ƙafafun sa dake yi masa zogi tare da umartar sa da akan ya bita, ɗan jim yayi kafin shima ya miƙe ya bar wurin. Da kallo Sairah ta bisa kafin ta miƙe itama tana mara masa baya. ********************* ________Kwance take tayi lamo kan faffaɗar ƙirjin sa, har yanzun tunanin su Naseeba yaƙi barin mata kwakwalwa, da ta rufe idanun ta su kawai take gani. Sake rungume ZEEYAD tayi tana 6oye kanta a ƙirjin shi, dan kuwa she feels so safe idan tayi hakan. Gently yake patting bayan ta, lumshe idanu tayi tana sake cusa kanta cikin chest ɗinsa. Ɗan murmusawa yayi kafin kuma yayi mata rumfa da hannayen sa yana kallon ta. Buɗe idanun ta tayi kafin a hankali tace "What are you trying to do?." "What i have been long waiting for" ya faɗa calmly yana goga hancin sa kan nata. "I... i... i don't understand" ta faɗa cikin rawar harshe. In a whisper yace da ita "It's just for an hour, i promise." "What... bangane..." maganar tata ce ta carke sakamakon haɗe bakin su da yayi wuri guda. _Toh ni dai har ga Allah naso tsayawa jiye muku gulma dama kuma kawo muku rahoton abinda zai wakana tsakanin su cikin wannan dare, sai dai iriyar muguwar kallon da oga ZEEYAD ya watso min ne ya sanƴa ni saurin fice musu daga ɗakin har biro ta na faɗi ƙasa, yanzu dai sai washe gari idan Allah ya kaimu na koma na ɗauko abina sannan na cigaba da suburbuɗo muku rahoto, yauwa_ *Yawan Comment, Yawan Posting* 07061979284 *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [9/4, 9:20 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *051...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _________Buɗe idanun ta da sukayi mata nauyi sosai ta fara, koh ina na jikin ta ciwo yakeyi mata, abubuwan da ya aikata mata cikin dare ne suka shiga yi mata playing a kwakwalwa,lumshe idanu tayi wasu irin hawaye masu zafi na tsiyayo mata. Da kyar ta iya yunƙurawa ta miƙe zaune tanajin yadda ƙasan ta keyi mata zugi sosai duk da kuwa irin ruwan zafin da ya taimaka ta shiga a jiyan cikin dare. Yaye bargon dake rufe da ita tayi tana sauƙo da ƙafafun ta ƙasa, da kyar ta iya yunƙurawa ta miƙe ta nufi bathroom. Wanka tayi sosai ta sake gasa jikin ta, sai a sannan ta ɗan ji dama-dama sakamakon ruwan zafin da ta sake shiga. Fitowa tayi ɗaure da wata ƴar guntun towel tare da zuwa ta zauna bakin mirror. Hand-dryer ta ɗauka ta shiga busar da jiƙaƙƙen gashin kanta da ta wanko, sai da ta tabbata ya bushe tass kafin ta gyara shi tana parking ɗinsa a baya sai sheƙi da ƙamshi na musamman yake tayarwa. Lotions masu kyau da ƙamshi ta shiga mulke jikin ta dashi, tana cikin hakanne ZEEYAD ya buɗo ƙofar ɗakin ya shigo bakin sa ɗauke da sallamar wanda iya le6en bakin sa ne kawai sukayi motsi. Sadda kai ƙasa DEENAH tayi cike da jin kunƴa har ya ƙaraso yana dafa kujerar da take kai. Ba tare da ta ɗago ɗin ba ta kai hannu ta ɗau deodorant ta shiga shafawa a jikin ta. Ganin yayi shiru har wannan lokacin ne ya sanƴa ta ɗan ɗago da kanta tana kallon cikin mirror ɗin nan suka haɗa ido kafin kuma ta sake saurin maida kanta tana ɗan turo baki. Hanci ya kai yana shinshinar daddaɗar ƙamshin gashin kanta, kafin kuma ya sumbace ta a wuya tare da yi mata raɗa a kunne yace "Good Morning Baby." Cikin rawar murya take faɗin "Please ɗan miƙa min Hijabin chan." Kallon ta yayi ta cikin mirror ɗin kafin yace "What Hijab?." "Gashi chan." "Ni ban gani ba" ya bata amsa. Ɗan ɗagowa tayi ta kallesa kafin tace "Baka fah duba ba, idan ka juya bayan ka zaka ganshi." Cikin kallon ta yake faɗin "Maybe sai dai idan zaki tashi ki nuna min inda yake sai na ɗauko." Ɗan turo baki tayi cikin shagwa6e fuska tace "Please Abyaaad." Yadda tayi maganar cikin langwa6ar da kai ne yayi bala'in tafiya da imanin sa, hakan ya sanƴa shi sakin baki yana kallon ta. Sadda kanta tayi tana wasa da ƴan yatsun hannayen ta. Murmushi ZEEYAD yayi kafin ya bar wurin zuwa closet room ɗinsu, ganin ya tafi ne ya sanƴa ta saurin miƙewa tana zuwa inda Hijab ɗinta yake ta sanƴa shi kafin ta sake dawowa gaban mirror ɗin ta cigaba da kwalliyar ta. Shi kuwa fito mata yayi da kayan da zata sanƴa a hannun sa, murmushi kawai yayi ganin sai wani 6o66oye jikin ta take, shi kuwa babu abinda bai ƙarewa kallo ba a daren jiya. Ajiye mata kayan yayi kan bed kafin yace "Idan kin shirya YAZEED is waiting for you downstairs kizo a canza miki sabon bandage." Kai ta jinjina masa kawai, tana ganin ya fita ta miƙe tsaye ta taka zuwa bakin bed ta ɗau kayan da ya fito mata dashi ɗin. Ba tare da ta cire Hijabin ba ta shiga shiryawa dan kuwa bata yarda koh yana la6e yana leƙen ta ba. Cire Hijabin tayi tana nannaɗe shi, nan kuwa ta jiyo muryar shi a bayan ta yana faɗin "Seriously?." Juyowa tayi nan ta ganshi ya haɗe girar sama da ta ƙasa yayi folding hannaye a ƙirji yana kallon ta. Dama ta sani yana nan la6e yana leƙen ta, murmushi tayi kawai tana zuwa ta rataye Hijabin inda shi kuma ya ƙaraso cikin ɗakin yana riƙo waist ɗinta ta baya tare da saƙala kansa ta wuyan ta, cikin cool voice ɗinsa yace "Are you sure ban ji miki ciwo ba?." Shiru DEENAH tayi tana rarraba idanu nan tace "What?." Sake holding ɗinta yayi tightly bakin sa saitin kunnen ta yace "Well last night was full of..., i really don't know how to describe it, but you are so very very special babe." Kunƴa ne ya kama DEENAH idanu ta runtse tana jin yadda palms ɗinsa ke yawo a cikin ta, hannun ta ta kai kan nasa tana riƙewa kafin ta shiga zame jikin ta. Sake riƙo ta yayi yace "Am sorry i made you cry yesterday, i mean na ƙara miki ciwo akan wanda kikeji..." Katse shi tayi da faɗin "It's alright, am fine" dan kuwa ta lura ma kamar bayida isasshiyar kunƴa kwata-kwata. Murmushi ZEEYAD yayi yana juyo da ita tana fuskantar sa, kallon cikin idanun ta yayi kafin ya saki murmushi yace "Idan kin warke gabaɗaya, we're going on a honeymoon daga nan kuma zamu wuce Nigeria ki gaida ƴan gida" ya ƙarashe cikin ɗan jan ha6ar ta. DEENAH bata san sadda ta saki wani irin murmushin farin ciki ba, nan tace "Really?" cike da farin ciki da zumuɗin da ya darsar mata lokaci guda. Kai ya jinjina mata cikin murmushi, rungume shi tayi ƙam cike da farin ciki tace "Wow am so happy" kafin kuma ta ɗago tana duban sa tace "Yaushe zamuje." "Idan kin warke gabaɗaya" ya faɗa. "Nidai gaskiya na warke yanzu" ta faɗa cikin muryar shagwa6a. Ɗan waro idanu yayi kafin yayi murmushi yace "Sabida kinji nace zan kai ki kiga ƴan gida, i can't take you there like this coz babu tantama idan na kai ki a haka then ba zasu bar ki ki dawo ba" ya faɗa cikin rashin jindaɗin abubuwan da ya faru da ita ɗin kafin ya ɗaura da faɗin "And it's all my fault, the blame is all on me, tun ba'a je koh ina ba na kasa baki kyakkyawar kulawa and i hate myself for that." Saurin cupping fuskar sa tayi tana kallon sa tace "What are you saying Abyad, ka bar faɗin haka komai da kaga ya faru damu then a rubuce yake haka Allah ya ƙaddara rayuwar auren mu zata kasance, ba laifin kowa bane but jarabawar mu ce haka, i know we've gone through alot in life but that doesn't mean zamu baiwa kanmu koh wasu laifi akan dukkanin abinda suka faru, those that did wrong to us Allah ne ya ƙaddara hakan a garesu but sun kasa controlling ƙiyayyar su a garemu tare da rungumar yadda Allah ya ƙaddara musu rayuwar su shiyasa ƙarshen su batayi kyau ba, i know you and i know how much you love me koh da da wasa ne ba zaka ta6a attempting yin wasa da rayuwa ta ba, na shaidi hakan tun ba yau ba, i just can't imagine what my life will turn without you Abyad, so stop blaming yourself i know kana dukkanin ƙoƙarin ka na ganin ka kula dani but 6ata garin dake biye da rayuwar ka suna neman hana yiwuwar hakan, ba kai kaɗai ne yakamata ace ka kula dani ba, nima lokaci yayi da zan kula da kaina dama kai kanka, we will now both look after each other and make sure that no harm ever visit our ways again, just promise me that you will always be there for me though nasan kullum you always stood for me a duk lokacin da wani yaso cin zarafi na, nima i guess lokaci yayi da yakamata na kula da kaina and make sure ban kar6i duk wani cin mutunci koh zarafi daga wurin wani koh wata ba, na daina nuna tsoron su a fili, domin kuwa maƙiyi na samun hanƴar cutar da kai ne a duk lokacin da yaga wani gazawa tattare da kai musamman idan ya hango tsoron sa a cikin idanun ka then ya dinga farautar ka kenan har sai ya cimma burin sa, banason ka sake baiwa kanka laifi akan dukkanin wani abu da maƙiya zasu yi mana nan gaba ba fatan hakan nake ba, and i know insha Allah ba zasu sake samun damar ƙuntata mana koh cin galaba akanmu ba" ta ƙarashe tana shafa gefen fuskar sa. Kallon ta kawai yake har ta kai aya a zancen nata, murmusawa yana rungume ta tsam a jikin shi yace "Insha Allah, we're ready to fight our enemies, and ke kanki yanzu kin ƙarfafa min guiwa fiye da tsanmanin ki, i love you so much DEENAH, you really mean the world to me" ya ƙarashe cikin raunanniyar murya yana rubbing bayan ta. Murmushi DEENAH tayi, ji take wani irin farin ciki na fizgar ta, though ta san bai wuci alƙawarin zuwa Naija da yayi mata ba. Ɗagowa yayi yana cupping fuskarta, murmushi tayi ganin yadda yake kallon ta, kissing lips nata ya shiga yi har sai da yayi mai isar sa kafin ya ɗago yana sake bata peck a goshi. Gyalen kayan jikin ta ya ɗauko daga kan bed ɗin yana yafa mata a kafaɗu kafin ya riƙo hannun ta su fito. Tun daga kan stairs ɗin take hango JALILAH da YAZEED dake zaune babu mai yiwa juna magana a cikin su, duk sai taji babu daɗin hakan sam baikamata ba atleast JALILAH ta cancanci kulawa daga gun YAZEED koh dan kyawawan halayen ta ma. Taimaka mata yayi ta sauƙo daga stairs ɗin kafin ya zaunar da ita daga cikin couchs ɗin dake zube a kyakkyawan falon. Murmushi JALILAH tayi mata tana tasowa ta zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗun ta tace "How are you doing DEENAH, ya lafiyar jikin ki?." Maida mata martanin murmushin DEENAH tayi tace "Alhamdulillah." "Good Morning DEENAH, how is your health?" cewar YAZEED dake facing ɗinta. Amsa masa tayi da da sauƙi kafin kuma ya ɗau first aid box ɗin gaban sa yana ƙarasowa inda take zaune. Bandage ɗin ƙafar ta ya shiga warware mata kafin ya sake yi mata dressing wurin yana ɗaura mata sabo, inda haka yayi wa hannun ma. Kallon ZEEYAD dake tsaye akansu yayi kafin yace "Ka 6ata min lokaci bayan you know Hospital zani." Idanu ZEEYAD ya ɗan waro yace "Actually ba nine na 6ata maka lokaci ba, it was DEENAH" ya faɗa yana nuna DEENAH dake zaune. Waro idanu itama tayi tace "No it wasn't me" ta faɗa tana hararar ZEEYAD ɗin. "Ofcourse i know it wasn't you, coz nasan ba zaki 6atamin lokaci ba." Murmushi tayi tana ɗan yiwa ZEEYAD dake tsaye gwalo. YAZEED ne yace "Alright, i will take my leave, see you later." Rakiya ZEEYAD yayi masa kafin su fice DEENAH tayi saurin faɗin "Baka yiwa matar ka sallama ba." Duk juyowa sukayi inda Jalilah kuma ta sadda kanta ƙasa, ɗan murmusawa YAZEED yayi yana kallon ZEEYAD da ya zuba masa ido shima yana jiran abinda zai ce. Hararar ZEEYAD yayi in a whisper yace "How do i said it?." Murmushi ZEEYAD yayi shima cikin raɗa ya shiga faɗin "You walk gently to her, bind your kneels down, lean her hands gently and look straight into her eyes then you say Bye Wifey am gonna miss you so badly." Kunkumi kawai ya riƙe yana kallon ZEEYAD ɗin, kallon sa ZEEYAD yayi nan yace "Come on do it." "You think this is a joke, i just want to do it yadda ba zataji wani iri ba." "Then you must do as i told you, it's the only way da ba zataji wani iri ba." "Are you guys planning something?" ya faɗa yana kallon DEENAH da ta tsare su da ido tana kallo. Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi yace "Go on with it bro" ya faɗa yana nuna masa hanƴa. Kai kawai YAZEED yayi nodding yana takawa zuwa inda JALILAH ke zaune, ɗan duƙawa yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma ya ɗanyi gyaran murya yace "Am leaving for work, da akwai abinda kike buƙata na taho miki dashi?." Kai kawai ta girgiza masa alamun a'a tace "No nothing." "Are you sure?" ya sake faɗa yana kallon ta. Kai ta jinjina masa nan yace "Alright, bye then." Ɗan murmusawa tayi kawai tana jinjina kai, kallon DEENAH dake kallon su yayi kafin ya ɗan saki murmushi yana sauƙe 6oyayyiyar ajiyar zuciya, juyawa yayi yana takawa zuwa wurin da ZEEYAD ke tsaye yana ɗan 6oye dariyar dake son zuwa masa. "Best friends never make fun of each other talkless of best brothers" cewar YAZEED yana ficewa daga falon nan ZEEYAD ma yayi saurin mara masa baya. Kallon DEENAH JALILAH tayi kafin tayi murmushi tace "Zan iya taya ki zama?." Kai DEENAH ta jinjina mata tace "Sure." Murmushi JALILAH tayi dan kuwa koh ta koma part ɗin YAZEED ba daɗin zama takeji ba koh dan rigima da tsokanar da Sairah ke damun ta dashi ma. Ba'a jima ba ZEEYAD ya dawo, kallo ɗaya yayi musu yana haurawa sama coz atleast yakamata ya ɗan basu space koh sa samu suyi hira sosai koh dan su saba da juna ma sannan DEENAH ma ta rage wasu daga cikin damuwar ta. *THREE WEEKS LATER* _______Sosai DEENAH ta warke taji sauƙin jikin ta, a yanzu har ta saba da zaman part ɗin nasu ita kaɗai, kasancewar ZEEYAD ya saya mata waya kullum tana cikin waya da ƴan gida hakan na rage maka kusan kaso 70 cikin damuwar da take ciki, ga kuma wata iriyar kulawa ta musamman da take samu daga 6angaren ZEEYAD da Grandma ɗinsa hatta mai Martaba ɗin ba'a barsa a baya ba wurin nuna mata ƙauna da kulawa. Hakan ba ƙaramin baƙanta ran Sairah yake ba, ganin duk cikin surukan sa yafi ɗaukin DEENAH haka ma sauran mutane kowa ji da ita yake ita ɗin da ba komai ba. Tsaye take gaban mirror tana rolling gyalen peach abayar dake jikin ta, dan kuwa so take ta kaiwa JALILAH da bata gajiya da zuwa duba ta ziyara ita ma yau. Sosai tayi kyau cikin shigar tata, wayar ta kawai ta ɗauka tare da fitowa tana sanƴawa ɗakin nasu key kafin ta shiga sauƙowa ƙasa. Bayin dake ta aikace-aikace ne tace dasu "Ku bar aikin haka nan, zan fita idan na dawo zan ƙarasar da kaina." Cike da girmamawa suka tattari kayan aikin nasu suka fice. Bin bayan su tayi tana rufo ƙofar falon, wasu bayi mata ne da aƙalla zasu kai biyar suka doso ta dawuri ganin kamar fita takeson yi. Saurin ce musu tayi "Kuje ku huta bana buƙatar rakiya ba nisa zanyi ba." Kasancewar part ɗinsu na kallon juna ya sanƴa kawai kwalta ta tsallaka tana shigewa ciki babu wanda yayi yunƙurin tsaida ta saima gaisuwa da tayi ta kwasa har ta isa ga falon ƙasa wanda yadda komai na part ɗinsu haka ma wannan ɗin yake. Zama tayi cikin ɗaya daga couchs ɗin falon, wata kuyanga ce ta ƙaraso inda take tare da faɗin "Sannu da zuwa ranki ya daɗe gimbiya, da wa kikeson ayi miki sallama?." "Da uwargidan" ta bata amsa a takaice. Duƙar da kai tayi cikin girmamawa kafin ta shige wani lungu cikin falon. Ba'a wani jima ba sai gata baiwar ta dawo tace "Tace na iyo miki iso zuwa ciki." Miƙewa DEENAH tayi tana mara mata baya, JALILAH ta gani a kitchen da alama dai abincin rana take ƙoƙarin haɗawa. Murmushi ta sakarwa DEENAH dake shigowa inda ta maida mata martani. Kujera DEENAH taja daga cikin kujerun dining ɗin kitchen ɗin tana zama, kafin kuma wasu bayin su shiga serving ɗinta. Wanko hannu JALILAH tayi kafin tazo taja kujera kusa da DEENAH tana zama tare da faɗin "Kece yau a gidan mu?." Murmushi DEENAH tayi kafin tace "I thought yakamata nima yau na shigo, koh bakomai zan huta da gori." "Gaskiya kam kin wanke kanki" ta faɗa cikin ɗan dariya kafin ta ɗaura da faɗin "Kin zo a daidai, favorite ɗin mijin ki nake ƙoƙarin haɗawa, mai zai hana ki koya ki dinga yi masa?." Murmushi DEENAH tayi kafin tace "I will love to." Miƙewa tsaye JALILAH tayi tace "Come and have a look then." Miƙewa ita ma DEENAH tayi tana mara mata baya zuwa inda tukunƴar girkin take, sosai ta maida hankali gun abinda JALILAH ke koya mata ɗin har suka kammala. Serving musu tayi bayan sun kammala girkin, suna cikin ci Sairah ta faɗo kitchen ɗin. Tsaye tayi tare da riƙe kunkumi tana aika musu da wani irin mugun kallo. Murmushi JALILAH tayi tace "Sairah?, ki ƙaraso mana ki zauna." Kallo ta ƙare mata sama da ƙasa kafin ta buɗi baki tace "Mai kike taƙama dashi ne?, i was waiting for my lunch tunɗazu only to find out kin ajiye wannan abar kuna cin abinci tare, ina nawa kason toh, kema dai kinsan ba girki na iya ba bale kice zan girka da kaina naci, idan ma kina tunanin akwai bayin da zasu girka su bani naci ne then miye amfanin ki, you know how to cook well that means kece zaki dinga yi mana girki muna ci baki ɗayan mu, wane irin salon rainin wayo kuma kika 6ullo dashi na hana ni abincin rana, a gidan miji na, i can't believe you JALILAH." Shiru JALILAH tayi mata kamar wata mai tsoron ta, kallon ta DEENAH take ganin koh zata tanka mata amma batayi hakan ba, kenan ya tabbata tsoron ta takeji dagasken. "You know what, dole ne Ummie taji wannan maganar." "No please" cewar JALILAH ɗin tana miƙewa tsaye ta ƙaraso wurin ta tare da dafa kafaɗun ta tace "Ba sai maganar yaje gun Ummie ba, am sorry i thought we're sisters and..." Yarfar da hannun JALILAH tayi tace "Sisters with who?, listen JALILAH ni fah kawai ina zama dake kuma ina ɗan kula ki coz i have no other choice, but that doesn't mean zaki dinga yimin dukkanin abinda ranki keso dan kawai an baki matsayin uwar gida ba shi ke nufin zaki yimin abinda ranki yaso bane..." "But ban hana ki abinci ba, abincin ki a ajiye yake, why don't you try to make some peace koh da na kwana ɗaya ne a tsakanin mu, you always have a way of insulting me koh da abu bai kai ya kawo ba, sannan bakida aiki a kullum sai ɗaura min sharri a gun Ummie, babu abin dake a raina wanda ya wuce muyi zaman lafiya tsakani na dake but you always have a way of mocking and criticizing me a duk abinda nayi, and yarda da Ummie keyi dake a kullum shi ke ƙarfafa miki guiwar cigaba da halayen ki, why don't you understand cewa ni banason rigima atleast you should try to make some peace with me tunda har kika gane ni rigima ba abinda na kware a kai bane." "Hmm, Peace?" ta faɗa tana kallon ta kafin ta ɗaura da faɗin "I never learnt what that was, bansan shi ba bale nayi zaman shi dake, ke kishiya ta ce which means am sharing a Husband with you, how do you expect me to make Peace with you then?, ban ɗau kishiya a matsayin abokiyar zaman lafiya ba, sai dai kuma kash you're so fucking calm sam banso halayen ki a haka ba..." "Ba zan ta6a yin rigima dake ba, ina faɗamiki ne sabida kin fara kai ni bango, kiyi ƙoƙarin gyara halayyar ki towards me please." Murmushin gefen baki ta saki kafin tace "Ai baki ma fara ganin komai ba tunda har dani kike kishi kaɗan kenan kika gani daga cikin abubuwan da zan iya aikatawa, sannan zan so ace na tunzura ki na kai ki bango ɗin sabida rigima cikin jinin jiki na take, bansan wani abu wai shi lumana koh makamancin sa ba, maganar da kikayi min yanzu ki tabbatar shine sanadiyyar buɗewar ƙofar duk wasu fitintinun da zasu cigaba da wakana tsakanin mu nan gaba, you just wait and see muddin ina cikin gidan nan then keda farin ciki kunyi hannun riga kenan, this is my promise to you" tana faɗin haka ta fice a fusace daga kitchen. Wasu irin zafafan hawaye ne suka sauƙowa JALILAH a ƙunci tana bin inda Sairah tabi da kallo. Juyowa tayi ga DEENAH da ta zuba musu ido tunɗazu tana kallo, murmushi ta ɗan saki kafin tazo taja kujera ta zauna. Koh kaɗan DEENAH batayi mata magana akan rigimar tasu ba, sai ma wani shafin hirar ta daban da ta buɗe har sai da taga Jalilah ɗin ta saki jikin ta sosai kafin ta tashi ta tafi. ********************** _________Zaune yake gaban sa ɗauke da system ɗinsa yana dannawa, DEENAH dake kwance tayi matashi da laps ɗinsa ne ta kira sunan sa a hankali "Abyad?." Rufe Laptop ɗin yayi kafin ta tashi zaune tana kallon sa, cikin kulawa yake kallon ta kafin yace "Seems like akwai magana a bakin ki, tell me." "Abyad it's about JALILAH." "What about her?" ya faɗa yana kallon ta. Shiru tayi kafin tace "Baka fahimci tana cikin damuwa ba?." Ɗan murmusawa yayi kafin yace "Well ni kullum ke nake gani ba wata ba, how then zan san irin halin da take ciki." Abinda ya faru tsakanin JALILAH da Sairah ta kwashe ta faɗa masa kafin ta ɗaura da faɗin "You should talk to you YAZEED he is their Husband and i know ba zai rasa hanƴar tackling ɗin issue ɗin ba, atleast JALILAH deserves to be loved, cemin fah tayi mahaifin ta da yayan ta koh taje gidan su sunyi ta ya6a mata baƙar magana suna sanƴa ta baƙin ciki in the other hand kuma YAZEED'S Mom tana yarda da dukkanin abinda Sairah ta faɗa mata akan JALILAH ita kuma ba zata so ji daga bakin ta ba sai ta hau ta da faɗa tana gaya mata baƙi, and YAZEED in the other hand sam shima baya nuna mata wani damuwa iyaka cin su gaisuwa ne kawai tsakanin su, talk to him please i know yana jin maganar ka sannan zai ɗau shawarar ka, kaji." Huci ya fesar kan ya numfasa yace "Alright, i will talk to him tunda hakan kikeso, you happy?." Kai ta jinjina masa nan ya rungumo ta jikin sa yana patting bayan ta a hankali yace "Your wish is always my command Queen." Murmushi DEENAH tayi kafin kuma yace "Jibi zamu tafi Honeymoon ɗinmu, i know zaki so yin nesa da nan for sometime." Cike da farin ciki ta rungume shi tightly tana murmushi tace "Allah ya kaimu." Agogon dake manne jikin wall ɗin falon ya duba kafin kuma yace "It's getting late, mu kwanta haka nan." Ɗagowa tayi tana tashi tsaye, shima ɗaukar system ɗinsa yayi tayi gaba yana biye da ita. Canza kayan ta tayi izuwa silky doguwar rigar bacci, kafin ta nufi bathroom ta ɗauro alwala ta fito tare da nufar Bed ta kwanta bayan ta tofe jikin ta da addu'a. Shima ZEEYAD canza kayan sa yayi izuwa brown Jallabiya ya ɗauro alwala kafin ya kashe musu hasken ɗakin, ƙarasowa yayi ya rage musu hasken side lamps ɗin kafin ya haye kan bed ɗin yana janƴo ta jikin sa. Hannun ta ɗaura kan nasa dake manne a cikin ta a haka har bacci ya ɗauke ta. Cikin bacci yaji kamar ana hura masa iska mai tsananin zafi koh wanda ake kwarawa dukkanin jikin sa ruwan zafi. Tun yana iya daurewa har ya kasa ya shiga buɗe idanun sa da sukayi tsananin kaɗawa yayin da zuciyar sa keyi masa zafi da wani irin raɗaɗi haɗi da bugu tamkar zai faso ƙirjin sa ya fito. Buɗe idanun sa ke da wuya yaga shigewar wani irin baƙin hayaƙi cikin jikin sa. Runtse idanu yayi sakamakon wani irin zafi da zugi dake ta ƙara sukar zuciyar sa haɗi da fatar jikin sa. Ƙame jikin sa da ya fara rawar sanƴi yayi yana jin kamar wanda ake yayyanka tsokokin jikin sa a haka har ya faɗi ƙasa dafe da saitin zuciyar sa, daga nan kuma duhu mai tsananin gaske ya mamaye masa idanu. Alarm ɗin ƙarfe ukun da ta saita a wayar ta ne ya shiga ringing, idanu ta buɗe tana janƴo wayar daga kan bedside drawer tare da kashe alarm ɗin, zaune ta miƙe ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci kafin ta kunna bedside lamp tana maida duban ta gefen da yake kwanciya, wayam ta gani dan haka maida duban ta tayi ga inda suke sallah nan ma dai bata gansa zaune ba. Miƙewa tayi ta sauƙo daga kan bed ɗin ta shiga takawa zuwa bakin ƙofa, jin ƙofar tayi a rufe alamun dai ba'a fita daga ɗakin ba. Wutar ɗakin ta kunna take ɗakin ya gaurayu da haske, bathroom da nufa tare da buɗewa ta shige sai dai tayi dube-duben ta bata ga kowa a ciki ba, tsoro ne ya fara kama ta, toh ina yayi?, shine tambayar da ta yiwa kanta. Takowa tayi da niyyar zuwa ta duba closet room taji tayi tuntu6e da abu take ta faɗi ƙasa dan sam bata lura dashi ba, ƙara ta ɗan saki sakamakon goshin ta da ya ɗan bugu kafin tayi saurin maida duban ta kan abinda tayi tuntu6e dashi ɗin. ZEEYAD ta gani kwance, ba tare da ta kawo komai ranta ba ta rarrafa zuwa inda yake hannayen ta ta ɗaura kan ƙirjin sa ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa akan ya tashi suyi sallar Nafila. Gani tayi koh motsawa baiyi ba "Abyad?" ta sake kira a hankali. "Abyad ka tashi mana" ta faɗa tana sake jijjiga shi. Ji tayi kodai wasa yakeyi mata ne tashi tayi ta ɗauko ruwan gora kafin ta shiga yayyafa masa, nanma gani tayi koh gezau baiyi ba. Dropping ruwar gorar tayi yana faɗi ƙasa kafin ta durƙusa da sauri tana manna kanta da ƙirjin sa tare da saurarar bugun zuciyar sa. A razane ta ɗago zuciyar ta na dukan tara-tara, sake maida kanta tayi dan koh tana tunanin bataji bane mai kyau, nan ɗinma dai thesame thing ta sake ji. Ɗagowa tayi da sauri idanun ta na tara hawaye ta shiga lalumar jikin sa, hannun sa ta ɗaga tana saurarar pulse ɗinsa, sakin hannun tayi da sauri tana ja da baya kafin kuma ta shiga girgiza kanta cikin kukan dake zuwan mata ta shiga faɗin "No... no... this... this can't be... you can't be dea.." bata ƙarasar ba ta sake rarrafawa da sauri tana komawa wurin nasa tare da ɗago da kansa tana rungume shi a ƙirjin ta, fuskar sa ta shiga kallo kafin tace "I know you're kidding me, i know you're not dead, maybe... maybe you're sick... yes i know you must be sick that is why you're unconcious" ta faɗa cikin tatta6a fuskar sa zuwa wuyar sa da yake sanƴi babu alamun zazza6i. Kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri tana zuwa ta lalumo wayar sa kafin kuma cikin rawar hannu ta shiga neman numbern Grandma. Kafa wayar tayi a kunnen ta lokacin da ya shiga ringing, har ya katse bata ɗaga ba, dan haka ta sake dialing sai a karo na uku kafin ta ɗaga kiran, ba tare da DEENAH ta jira cewar ta ba ta shiga faɗin "Grandma... Grandma kizo dan Allah Abyad ba shida lafiya... dan Allah kizo da wuri" tana faɗin haka ta katse wayar da sauri tana komawa wurin sa tare da tallafo kansa tana sake kiran sunan sa "Abyad dan Allah ka tashi, kada kayimin haka you can't be dead now, baikamata ka tafi ka bar ni ba i will be doomed without you Abyad dan Allah ka buɗe idanun ka and talk to me i beg you Abyad please" ta ƙarashe cikin kuka sosai tana shafa fuskar sa. Bai fi da 5mins ba Grandma ta ƙaraso kafin ta shiga kwankwasa ƙofar tana kiran sunan "DEENAH." Da sauri DEENAH dake rungume da ZEEYAD ta tashi tana ƙarasawa bakin ƙofar ta buɗe, tare da riƙo Grandma cikin kuka take faɗin "Thank GOD you're here, ina ta tashin shi tunɗazu baya motsi bansan mai ya faru dashi ba." Hankali tashe Grandma ta ƙarasa inda yake kwance da sauri tana kallon sa a hankali kuma ta shiga kiran sunan sa "Boy" tana shafo fuskar sa. Cikin kuka DEENAH tace "He isn't waking up tunɗazu nake tashin sa amma baya motsi, am scared kada wani abin ne ya same shi." "He will be fine insha Allah, i know he will be fine, ɗaukomin waya na kira YAZEED." Da sauri ta miƙe tana zuwa ta ɗau wayar sa tare da miƙawa Grandma, amsa tayi kafin ta lalumo wayar YAZEED ta shiga buga masa. Firgigit Sairah da wayar ke riƙe a hannun ta tayi lokacin da ya ɗau vibration, ganin mai kiran ne ya tabbatar mata da cewa aikin su ya tafi according to plan, ta san DEENAH ce mai kiran, murmushin gefen baki ta saki har kiran ya katse bata ɗaga ba. Wani kiran taga ya sake shigowa shima har ya tsinke bata ɗaga ba, kira na uku taga ya sake shigowa dan haka tayi rejecting call ɗin, har sau uku ana sake kira tana rejecting kafin ta rubuta text message da faɗin _"Stop disturbing Bro"_ murmushi tayi kafin kuma ta danna send button take text ɗin ya tafi. Goge duk wani call log da text ɗin tayi yadda dai ba za'a gane ta ɗau wayar ba, kafin kuma ta shiga settings tayi disabling ɗin fingerprint ɗinta da ta sanƴa, wayar ta ta ɗauko kafin ta yiwa Sarauniya Hafeezah text da _We did it, everything went according to planned"_ tare da danna send button ya tafi. Lalla6awa tayi izuwa ɗakin YAZEED dake bacci kamar ma wanda baisan inda kansa yake ba, ta ajiye masa wayar sa tare da ficewa cikin sauri. Wurin Hafeezah kuwa murmushi ta saki bayan tayi receiving text ɗin Sairah "So now let's see how you become the king, muddin ina raye only YAZEED can be the King no one else, you were my biggest problem but now that i have get ridden of you i feel like the world is my hands" ta ƙarashe cikin dariya ranta fari sol sabida ta gama da ZEEYAD sai dai wanin sa kuma ba shi ba, tunda taji nan da jibi za'a naɗa shi Sarki kamar yadda Abdulhakeem ya sanar da ita hakan ya sanƴa batayi ƙasa a guiwa ba ta aiwatar da shirin ta bayan ta sami wani babban boka da ya kware wurin aikin sa. Dariya tayi kafin tace "Let's see who you Surprised then your Highness, idan bakayi surprising ɗinsa wurin naɗa sa sarki ba, ni nan nayi surprising ɗinka da gawan ɗanka gobe da safe, so prepared to cry the tears of true remorse your Highness, your dearest son is no more, let's see who you give your throne to then" ta faɗa cikin gimtsewar fuska. 6angaren Grandma kuwa mamaki ne ya cika su ganin abinda YAZEED yayi musu. DEENAH ce tace "Grandma, ki kira Sadeeq i know he will be here soon." Kallon ta Grandma tayi kafin tace "Kafin Sadeeq ya iso nan yanzu gari zai iya wayewa, sabida tsakanin gidan su da nan akwai nisa sosai." "But what do we do Grandma, we've to save him kafin wani abin ya same shi" ta faɗa cikin kuka. Kallon ZEEYAD da baya motsi Grandma tayi, sosai jikin ta yayi bala'in sanƴi dan kuwa bata tunanin inda akwai rai tattare dashi, ta san maƙiya sunyi nasara akan shi. Sunkuyar da kai tayi wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubo mata, a hankali itama ta fara sakin shessheƙar kuka ganin angama mata da ɗan jikan nata wanda shi kaɗai ne yanzu gatan ta a duniya. Cikin rawar murya DEENAH dake kallon ta tace "Grandma, maiyasa kike Kuka, bai fah mutu ba, bashida lafiya ne kawai." Shiru Grandma tayi mata tana cigaba da kukan ta. "Grandma?" ta sake faɗa wasu hawayen na sake biyo ƙuncin ta. Kallon ZEEYAD ɗin take, tayaya ma za'a ce ya mutu, yes ta san Allah ne mai rayawa da kashewa a duk sadda yaso but tayaya za'ayi ace Abyad ɗinta ya mutu?, ta san bai mutu ba wani abin kawai maƙiyan sa sukayi masa. "Grandma, dan Allah mu kai shi asibiti a duba shi koh wani abin ne ya same shi da baya motsi" ta faɗa cikin kuka tana kallon Grandma. Goge hawaye Grandma tayi kafin kuma tace "Bari naje waje na kira wadannan masu gadin suzo mu kaisa asibiti" ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Kallon ZEEYAD tayi tace "Insha Allah you will be fine, no harm can come to you." ******************** ________Sosai DEENAH ke kuka a gaban gawan ZEEYAD da akayi masa shiru makwancin sa ne kaɗai ya rage a kaisa. Sosai fadar da ɗau shiru kukan ta kaɗai akeji, YAZEED ne ya faɗo cikin fadar tamkar wanda ake korar sa, turus yaja ya tsaya yana kallon ɗan uwansa dake sanƴe cikin sutura irin ta matattu. Idon kowa a wannan wurin yayi jaa sosai alamun dai sun sha kuka Except Hafeezah da Sairah da nasu kukan ya kasance na munafurci ne, Grandma kuwa sobbing kawai takeyi yayin da mai Martaba shima ya kasa barin kan gawar ɗan nasa, da ka gansa kasan yana cikin shock da ɗimuwa koh kukan ma ya kasa yi. Ɗaya daga cikin ministocin ne ya ƙaraso wurin a hankali yace "Yakamata a kai Yarima ZEEYAD makwancin sa haka nan, tunda har anyi sallahr azahar ɗin." A tsawace DEENAH tace "No... babu wanda zai ta6a shi i know bai mutu ba, ku ɗan dakata zuwa anjima kaɗan ni nasan zai farka amma yanzu kam bai mutu ba" ta faɗa cikin rungume shi. Shiru kawai mutumin yayi yana ɗan ja da baya cikin sanƴin jiki. Cire audugar dake hancin sa DEENAH tayi tana jefarwa tare da faɗin "Idan ma yana raye tayaya zamu sani da wannan abin a hancin sa, i know he isn't dead doguwar suma kawai yayi..." Grandma ce ta katse ta da faɗin "What are you doing DEENAH?, likitoci sun tabbatar mana da cewa Boy baya..." "They are liars, babu abinda suka iya, ni mijina bai mutu ba, mu ɗan jira zuwa anjima kaɗan zakuga ya tashi." Shiru Grandma tayi mata tausayin ta na kama ta, ita kanta jurewa kawai takeyi, amma dai abin da duba. Cikin dashewar murya sarki yace "Azo a kaishi." Ɗagowa DEENAH tayi tana kallon sa kafin ta shiga nodding kanta tana kare shi daga mutanen dake zuwa da niyyar su ɗauke shi ɗin. "No... no... no please, kada ku tafi dashi bai mutu ba, dan Allah ku kyale ni wallahi bai mutu ba, babu ta yadda za'ayi ace ya mutu, let go of me" ta faɗa tana kwacewa daga hannun wadanda suka riƙe ta ɗin tabi bayan su da gudu. Da sauri YAZEED ya taro ta, fuzge hannun ta tayi daga riƙon da yayi mata cikin 6acin rai kuma take faɗin "Let go of my hand, you're happy now aren't you?, i know kafi kowa murna da mutuwar sa though nasan bai mutu ɗin ba, duk soyayyar nan da kake nuna masa ba na tsakani da Allah bane, ashe kana ɗaya daga cikin maƙiyan sa masu son ganin bayan sa..." "DEENAH..." Grandma ta katse ta. Ba tare da DEENAH tayi shiru ba ta cigaba da faɗin "Don't stop me Grandma, you saw it ai, kema kinsan abinda ya aikata, dah ace yayi responding a wannan lokacin then maybe Allah ya taimake mu mu iya ceto rayuwar sa, but what did he do, ya nuna cewa bai damu da ɗan uwansa ba, sannan dukkanin wata soyayya da yaye yi masa was all fake." "Stop it now" cewar Hafeezah cikin tsawa tana ƙarasowa inda suke kafin ta ɗaura da faɗin "How dare you accused YAZEED of your husband's death, wa ya baki gut ɗin yi masa magana in such a manner?, ki kiyaye harshen ki or else..." Ba tare da tsoron komai ba tace "Or else what, what will you do, nima kashe ni zakuyi, well then why don't your just go ahead sabida na tabbata nice next target ɗinku, but i will make sure that kun girbi dukkanin wani abinda kuka shuka, ran Abyad ɗina ba zai ta6a tafiya a banza ba, you must all paid a heavy price for his death this is my promise to you, i will make sure you all regret it." A tsawace Hafeezah tace "Take this mad girl out of my sight, akan mijin ki aka fara mutuwa ne kokuwa?, mijin ki ya mutu ne ba tare da an gano abinda yayi silar mutuwar sa ba, hakan na nufin lokacin sa ne yayi, no one is to be blamed for his death." "You're all to be blamed, you monsters, you will all regret this i promise." "Watch your tongue DEENAH, ashe haka kike bakida tarbiyya, Ummie need to be respected..." Katse Sairah tayi da faɗin "This woman here means nothing to me da har zanyi respecting ɗinta, she is nothing but a devil..." "DEENAH" Grandma ta kira ta tana zuwa taja hannun ta su fara tafiya. Dukda haka bakin DEENAH bai rufu ba take faɗin "I know you're all behind this, and i will make sure you all regret it." "She is totally out of her mind, how dare her" cewar Hafeezah. YAZEED da jikin sa yayi matuƙar sanƴi kallon tuhuma yayi wa mahaifiyar tasa, bai ce dasu komai ba yaja ƙafar sa ya fice daga fadar, zuciyar sa na matuƙar zafi sosai koh kaɗan maganganun DEENAH basuyi masa zafi ba dukda baisan akan mai take basa laifin mutuwar ZEEYAD ba. Yana fita yaji an fizgo shi zuwa wani lungu. Kallon Hafeezah Nazeerah tayi tace "How cruel Hafeezah" tana faɗin haka itama ta bar cikin fadar ƴaƴan ta suka mara mata baya ya saura Hafeezah, JALILAH, Sairah da kuma Rahinah. Mugun kallo Hafeezah ta watsawa JALILAH da fuskar ta yake sha6e-sha6e da hawaye kafin ta daka mata tsawa da faɗin "Ke kuma mai kikeyi tsaye anan, zaki iya ficewa ki bisu banason shashancin banza." Da sauri tayi hanƴar ficewa daga fadar. Ajiyar zuciya Sairah ta sauƙe kafin tace "Wow so finally, nice nan zan zamto matar sarki, i can't wait to see that day." Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Hakane, but first we will have to get rid of this so called JALILAH sabida ke kaɗai nake buƙata ki kasance mata ga YAZEED." Murmushi tayi kawai tana ta saƙe-saƙen abinda zatayi cikin ranta. ********************** ________DEENAH ce rungume da Grandma, a yanzu kam kukan zuci kawai take, sosai yanayin ta ya canza, bata iya koh da kwakkwarar motsi ne daga inda take zaune, sosai takejin ta so empty, she can't believe wai ZEEYAD ɗinta ya mutu, sai dai kuma dama Ubangiji maɗaukakin Sarki da kansa yace dukkanin mai rai mamaci ne, zai ɗauki ran wanda yaso a lokacin da babu wanda yayi tsanmani haka kuma ya raya wanda yaso a lokacin da kowa ya cire rai da samun lafiyar sa, ya kan ɗauki ran bawa ba tare da yayi koh da ciwon kai bane, wannan shi ake kira kana naka Allah na nashi, sai dai ita har yanzu tanaji a jikin ta ZEEYAD bai mutu ba, sai dai kuma dole ne tayi haƙuri tunda har zuwa wannan lokacin ba'a zo mata da labarin bai mutu ba, hakan na nufin dagaske ya mutu ɗin kenan, ba zata kuma sake ganin sa ba har duniya ta naɗe, runtse idanu tayi sakamakon wani kukan da yazo mata, gimtsewa tayi kasancewar Grandma ta hana ta yin kukan. Sosai takejin zazza6i da wani irin hajijiya dukda a zaunen take, ji tayi zuciyar ta na tashi tanajin amai na zuwa mata. Miƙewa tayi da sauri tana faɗawa toilet ɗin ɗakin Grandma ɗin ta shiga kwaro aman wanda duk ruwa ne ma kasancewar babu abinda ta sanƴa a cikin ta tun safe. Riƙo ta Grandma da ta biyo ta cikin tashin hankali tayi ta shiga jero mata sannu. Wanke bakin ta tayi kafin ta riƙo ta su dawo cikin ɗakin. Ji tayi ba zata iya zama ba dan haka kwanciya tayi tanajin yadda jikin ta ke rufuwa da zafin zazza6i. Sosai Grand ɗin ta sake shiga wani tashin hankalin kuma, babu abinda take jerowa DEENAH sai sannu cike da damuwa. ******************** _______"What are you saying?." "I mean he isn't dead, i saw him moving his eyes at the hospital, it was indeed a miracle coz gwaji na farko da nayi masa ya tabbatar min da cewa ya mutu, but by the time da na lura da cewa ya motsa idanun sa na sake running wani test ɗin only to find out that he is still alive." "You know this kuma ka bari aka kaisa makwancin sa?." "Yes i know it, but i decided to keep it a secret hakan ya sanƴa ni yi masa allurar da zai sanƴa shi unconcious for 8hrs, so ba zama zamuyi yanzu ba we've to find a way na ganin mun tono sa before he gets suffocated, i thought that yaga wani abu before incident ɗinnan hakan ya sanƴa ni keeping this as a secret har sai munji daga garesa." "Then what ate we waiting for?, we should get him back now." "The problem is that masu gadin maƙabartar,ya zamuyi dasu?." "Leave that to me, kai kuma kaje ka fara shirye-shiryen komai tukun." "Yes" ya faɗa kafin duk su fice. ********************** *TWO DAYS LATER* ________Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zubowa Grandma a ƙunci sakamakon result ɗin DEENAH da ya fito. Kallon DEENAH dake kwance kan bed hannun ta ɗaure da drip tayi tana sake maida duban ta cikin papern hannun ta. Kallon ta Umma dake zaune gefen ta tayi tace "Lafiya dai koh, meke damun DEENAH?." Miƙa mata result ɗin tayi nan ta amsa itama ta shiga karantawa. Jikin ta ne yayi sanƴi sosai itama tana tausayin DEENAH ɗin dama kuma tausayin yadda rayuwar ɗan dake cikin ta zai kasance babu mahaifi. "DEENAH nada juna biyu na tsawon sati biyu" cewar Grandma cikin muryar kuka. *YAWAN COMMENT, YAWAN TYPING* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [9/5, 9:01 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *052...* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ _________Bayan kwana uku aka sallami DEENAH daga asibiti suka koma gida. Sosai take samun kulawa daga both gurin Grandma dama kuma Umma, suna dukkanin ƙoƙarin su na ganin sun kasance kusa da ita a kullum tare da bata kyakkyawar kulawa duba da ƙaramin cikin dake jikin ta. DEENAH kuwa tunda ta gano tana da ciki ta rage yawan damuwa da ƙunci tare da wallafawa Allah komai koh dan lafiyar abin dake cikin ta, dan kuwa dashi ne kaɗai zata dinga tuna ZEEYAD ba zata so wani abu ya sami cikin nata ba shiyasa a kullum take takatsantsan ɗin ganin ta kula mai kyau. Babu wanda aka sanarwa da DEENAH nada ciki sai mai Martaba kaɗai da ya sani sai kuma Sadeeq dasu Grandma koh dan gudun kada maƙiya su kawo mata farmaki su sanƴa cikin nata a gaba. Bayan ta gama takaba lokacin cikin nata har ya ɗan fara bayyana Umma ta nemi ta koma da ita, sai dai fur Grandma ta katse ta tsare babu inda za'a je mata da DEENAH, ita kaɗai take gani taji sanƴi a ranta ga kuma cikin ZEEYAD dake jikin ta dan haka babu inda DEENAH zata je tana nan tare da ita. Ganin yadda Grandma tayi ta kuka ne ya sanƴa Umma haƙura ta bar DEENAH tunda taga ita kanta DEENAH ɗin batason tafiyar, hakan ya sanƴa ta haƙura tare da yarjejeniyar idan cikin DEENAH ya kai watanni bakwai zata zo ta ɗauke ta idan yaso sai ta haihu achan. Ba dan Grandma taso ba ta yarda da hakan koh dan maƙiyan da yaron zai samu ma. DEENAH ce zaune a ɗaki rungume da hoton ZEEYAD a ƙirjin ta tana kallo, yayin da hawaye suka wanke fuskar hoton. Grandma ce ta zame hoton daga rungumar da tayi tana buɗe wani drawer ta sanƴa shi kafin ta zauna gefen DEENAH ɗin tana faɗin "DEENAH, yakamata ace kinyi haƙuri haka nan sannan kuma ki san da cewa kukan ki ba zai ta6a dawo da mijin ki ba, kefa kikayi min alƙawarin kin daina sanƴa damuwa a ranki, koh dai so kike hakan yayi affecting abin dake cikin ki ne?." Saurin girgiza mata kai DEENAH tayi wasu hawayen na sake biyo mata ƙunci. "Toh muddin bakyason hakan ya faru then yakamata ace kin bar sanƴawa ranki damuwa haka nan, kinji koh?." Jinjina kai DEENAH tayi tana share hawayen fuskar ta, murmushi Grandma tayi tace "Koh kefa, toh kiyimin murmushi mana na gani." Murmushin da ya tsaya mata iya le6e ta ƙaƙaro tayi, nan Grandma tace "Masha Allah, bari na kawo miki abinci kici kisha maganin ki sannan ki koma bacci ki huta, kinji?." "Toh" kawai ta bata amsa, nan Grandma ta miƙe ta fice daga ɗakin, da kallo DEENAH ta bita kafin ta ɗan miƙe akan bed ɗin tana shafo cikin nata. ********************** _________Tsaye sukayi akansa yayin da kuma wani Malami ya sanƴa shi gaba da alama dai magani yakeyi masa. YAZEED ne ya kalli Sadeeq yace "Are you sure wannan malamin ya san aikin sa, it's been a month kenan da yake ta fama but har yanzu babu wani labari, kullum excuses daban-daban yake kawo mana." Shiru Sadeeq yayi kafin kuma yace "Na fara tantama, but mu sake bashi nan zuwa gobe mu gani, indai bai samo wani kwakkwaran solution ba then sai mu canza wani malamin." "But a'ina zamu samo shi?, you know bamason kowa ya san da cewa yana raye hakan ya sanƴa mu ɗauko sa nan wurin." Shiru Sadeeq yayi kafin kuma yace "I guess zan sanarwa da Abhi ɗina, na tabbata zai samo mana solution." "No, what if kuma ya sanarwa mai Martaba fah?." "Am sure ba zai faɗa masa ba, zan sanar dashi da dukkanin abinda muka tsara." Jinjina kai kawai YAZEED yayi dai-dai lokacin da mai maganin ya ɗago ya dube su yace "Ku ɗan sake bani lokaci, aljanin dake cikin jikin sa ba ƙaramin takadiri bane, na tabbatar idan muka cigaba da dagewa da yi masa magani zai farfaɗo da izinin Ubangiji." Jinjina masa kai kawai sukayi kafin ya tattari kayan aikin sa ya fice daga ɗakin. Sadeeq ne yace "You're right, canza shi zamuyi, kai ka zauna nikuma zan fita na sallame shi daga nan na wuce gida na sanarwa da Abhi abin dake faruwa." "Alright" kawai ya faɗa yana samun wuri ya zauna kafin Sadeeq kuma ya fice. ************************ _________Mahaifin Sadeeq ne tsaye akan ZEEYAD ɗin yana kallon sa cike da tsantsar tausayin sa, juyowa yayi ga su Sadeeq yace "Kuna tare dashi cikin wannan larurar tsawon lokacin nan amma baku ta6a gigin sanar dani ba, wannan ba ƙaramin ganganci bane, dan kuwa banga alamun ana yi masa magani ba anan wurin." Shiru duk sukayi, nan ya numfasa yace "Wannan lamari ya wuce tunanin mu duka, da akwai wani babban malami da na sani sai dai yana zaune ne a wani ƙauye chan, ya kware wurin dealing da ire-iren wadannan abubuwa, ku shirya zuwa gobe a ɗauke sa a kai shi." "Insha Allah" duk suka amsa. Washe gari da sassafe YAZEED yaje ya sanarwa mai Martaba kan cewa zaiyi tafiya sannan zai iya jimawa bai dawo ba. Ɗagowa mai Martaba yayi ya kallesa wanda kallo ɗaya zakayi kasan bayida wata isasshiyar lafiya yace "Ina kake tunanin zakaje ka YAZEED?, kai kaɗai ne ɗan da nake gani a yanzu naji zuciya ta tayi sanƴi, ba zan so kayi nisa dani ba sabida kai ne wanda zai zamto magaji na sabida kai kaɗai ne wanda zai riƙe wannan kujerar mulkin cikin imani." Numfasawa YAZEED yayi tace "Your Highness zan iya dawowa muddin aikin da naje yi ya kammala akan lokaci, taro ne na likitoci zamuyi, da zaran mun gama kuma zan dawo insha Allah." Ba dan mai Martaba yaso ba ya yarje masa tare da yi masa fatan alkhairi, kai tsaye part ɗinsa ya koma ya ɗau dukkanin wasu abubuwan buƙatun sa ya fito, tarar da JALILAH dake jera breakfast a dining yayi a falon. Da sauri ta ƙaraso wurin sa tare da faɗin "Zaka fita kuma bakayi breakfast ba" kallon suitcase ɗin dake riƙe a hannun sa tayi cikin sanƴi tace "Tafiya zakayi ne?." Kai ya jinjina mata, sosai yake son koyawa zuciyar sa sabawa da ita sannan ya kasance yana kyautata mata a kullum, sabida sam batada naƙasu cikin halayen ta, murmushi yayi kafin yace "Yeah, zan ɗanyi tafiya ne na ɗan kwana biyu, anjima za'a kawo miki ƙarin food stuffs, and na bar miki kuɗi cikin bedside drawer ɗinki in case zaki buƙata kiyi wasu uzurin ki dashi." Gaba yayi kafin ya sake dawowa yana kallon idanun ta da ya ɗan tara hawaye nan yace "I will miss you" kafin kuma ya bata light hug yana ɗagowa tare da bata peck a goshi sannan yaja suitcase ɗinsa yayi gaba. Da kallo ta bisa har ga Allah taji daɗin yadda yayi mata, koh bakomai taji damuwar ta ya ɗan ragu hakan ya sake bata hope akan cewar komin badaɗe zai zo ya fara nuna mata kulawa, murmushi tayi kafin kuma ta nufi dining tana jan kujera ta zauna. **************** Wani ƙauye ne suka iso wanda tsakanin sa da MASARAUTAR su akwai nisan kilomitoti kai tsaye gidan wannan malamin nan suka tambaya, kasancewar shi ɗin ba 6oyayye bane a ƙauye yasa akayi musu iso har izuwa ƙofar gidan sa. Tsaye suka same sa a bakin ƙofar gidan sa da wasu samari biyu, Abhi ɗin Sadeeq ne ya fito daga motar kai tsaye wurin malamin ya nufa nan suka shiga gaisawa cikin mutunci da alama dai su ɗin tsoffin abokai ne. Umarni ya baiwa wadannan samarin da su ɗau ZEEYAD su shiga dashi daga ciki, gidan nasa babba ne sosai kai tsaye wani ɗaki aka kai ZEEYAD tare da shimfiɗe sa kan gado. Iso malamin yayi musu izuwa cikin ɗakin da yake babba ne sosai nan suma suka sami wuri suka zauna kan shimfiɗaɗɗiyar carpet ɗin ɗakin. Gaisawa duk suka sakeyi kafin Abhi ya sake yi masa bayanin abin dake tafe dasu. Kai malamin ya jinjina yace "Tabbas kunyi dabarar kawo sa nan wurin sabida nan ne dai-dai da irin shaiɗanin aljanin dake jikin sa, sai dai ina tsoron zai iya ɗaukan tsawon lokaci anan kafin ya warke." Duk kallon juna sukayi kafin Abhi yace dashi "Allah ya gafarta malam, baka fah duba shi ba tukun." "Bai zamto lallai sai na duba shi ba, sabida kallo ɗaya nayi masa na fahimci iriyar lalurar dake tattare dashi, koma wanene yayi masa wannan aika-aikar lallai ba ƙaramin maƙiyi bane a gareshi, baƙaƙen shaiɗanun Aljani ne a jikin sa, garawa dasu ba ƙaramin aiki bane, dan haka dole ne sai kun bada tsawon lokaci har izuwa samun lafiyar sa baki ɗaya, sannan idan kun koma gida ku cigaba da yi masa addu'o'i dama kuma sadaka a kullum hakan ne kaɗai zamu iya samun nasara kan wannan Aljani." "Insha Allah" Abhi ya amsa. YAZEED ne yace "Kenan tafiya zamuyi mu barsa anan?." "Kwarai kuwa?" cewar Abhi. "Toh amma har tsawon wane lokaci zai ɗauka kafin ya warke?" cewar Sadeeq. Malamin ne ya numfasa yace "Ya danganta da iya lokacin da Allah ya tsara masa na samun lafiyar sa, wasu kan ɗau shekaru da dama kafin su warke mafi ƙarancin lokacin da ake ɗauka kafin a warke shine shekara ɗaya zuwa biyu, da akwai wadanda ke ɗaukar tsawon shekaru goma ya danganta da irin ciwon da aljanin zai sanƴa musu kafin ya bar jikin su." Duk cikin tashin hankali suke kallon sa, murmushi malamin yayi da alama dai ba yau ya saba dealing da harkar aljanu ba kafin yace "Ku kwantar da hankalin ku, addu'a da yawaitar sadaka itace kaɗai abinda zaku dage da yi masa a yanzu." Abhi ne ya sami ƙarfin guiwar basa amsa da "Insha Allah." Ɗaya daga cikin yaran sa ya kira nan yace dasu yayi wa su Abhi ɗin rakiya zuwa ɗakin da zasu kwana. Kamar yadda ya umarce sa ɗin ɗakin da zasu kwana ya kai su, kafin kuma a kawo musu abinci da sha, bayan duk sun huta ne kuma kowannen su ya samu wuri ya kwanta bayan sun yanke shawarar tashi sallar dare dan neman wa ZEEYAD ɗin addu'ar samun lafiya. ************************* _________Kallon JALILAH Hafeezah keyi kafin tace "YAZEED yace miki zaiyi tafiya amma baki damu da ki sanar dani mahaifiyar sa ba, maiyasa?." Kanta a ƙasa take faɗin "Kiyi haƙuri bansan da cewa bai sanar miki bane ba shiyasa ban faɗa miki ba." Wanke fuskar ta tayi da mari kafin ta ɗaura da faɗin "Na tabbata kinyi masa wani abin ne ya sanƴa shi fara nuna miki kulawa, koh kin manta da cewa keda kwanciyar hankali kunyi hannun riga tunda har kika auri ɗana." Cikin kuka take faɗin "Wallahi banyi masa komai ba, tadda ni kawai yayi a falo lokacin da zai tafi shine yake sanar dani." Mugun kallo ta watsa mata nan tace "Ba wannan ba ma tukun, tun bayan mutuwar ZEEYAD ban sanƴa matar sa a idanu na ba, naji labarin cewa dake da ita akwai jituwa tsakanin ku, hakan yasa nake son yi miki wasu tambayoyi akanta tare da baki wani aiki." Ɗago da idanu tayi tana kallon Hafeezah da ta tsare ta da idanu "aikin da nakeson kiyimin kuma bana buƙatar a sami wata matsala koh da ƴar ƙanƙanuwa ce, sannan banason kiyimin ƙarya akan tambayar da zanyi miki, yin hakan daidai yake da barin ki fadar nan kokuma wani naƙasu tattare da rayuwar ki." Saurin sadda kai ƙasa JALILAH tayi hawaye na biyo ƙuncin ta kafin ta tsinkayo muryar Hafeezah tana faɗin "Inason ki faɗamin dalilin rashin fitowar ta fada koh gaida mai Martaba dukda cewa ta gama takabar ta." Shiru JALILAH tayi zuciyar ta na dukan tara-tara. "Ke nake saurara sannan kada ki kuskura kiyi gigin yimin ƙarya." Cikin rawar murya tace "Babu komai, bata fitowa ne kawai sabida batada lafiya." Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Zan baki dama ta ƙarshe muddin kika kuskura kikayi min ƙarya sai kinyi nadamar kasancewar ki cikin MASARAUTAR nan." Shiru tayi kafin cikin kuka tace "Gaskiya nake faɗamiki, har yanzu tunanin mutuwar sa bai bar jikin ta ba, hakan ne ya haddasa mata rashin lafiya sannan bata kuma son fita koh ina." "Inaji a jiki na ƙarya kike yimin." Saurin ɗagowa tayi tana girgiza mata kai tace "Ki yarda dani Allah yana gani ba ƙarya nakeyi miki ba." "Sairah ki kama ta ki shiga ciki da ita kiyi mata duk wani irin hukuncin da kikeso har sai ta buɗi baki ta faɗi gaskiyar abinda ta sane game da wancan yarinƴar da kullum ake 6oye ta ba'a barin fitowar ta." Yatsine fuska tayi kafin tace "Miye na baiwa kaina wahala ke daga ganin idanun ta kinsan ƙarya takeyi da akwai abinda take 6oyewa kyanta shine mu tilasta mata ta faɗi gaskiyar abinda ta sani kokuma jikin ta ya gayamata." Rahinah ce tace "Mai kuwa kuke tunanin zai sanƴa a dinga 6oye ta, cikin ɗaya ne koh biyu it's either dagaske batada lafiyar ne kokuma ciki gareta shiyasa ake 6oye ta ba'a son fitowar ta." Duk shiru sukayi tare da zubawa JALILAH da kanta ke sadde a ƙasa ta runtse idanun ta ido. Fizgo hannun ta Hafeezah tayi tana aika mata da wani irin mugun kallo tace "Ciki ne da ita koh ba haka ba?." Da sauri ta shiga girgiza mata kai ba tare da ta iya buɗar bakin ta ba. "Answer me" ta faɗa cikin daka mata tsawa. "Ba zatayi magana ba, we should force her ta hanƴar koya mata hankali." Jawo hannun ta Hafeezah tayi zuwa cikin wani ɗaki tana rufe ta a ciki tace "A cikin nan zaki dawwama koh da mutuwa zakiyi ba zaki fito ba, muddin ba wai kin shirya faɗar gaskiya bane ba." Kallon ta Sairah tayi kafin tace "Har yaushe ne zamu jira ta faɗi gaskiyar?, samu zamuyi wata daga cikin bayin dake aiki a 6angaren su nemo mana bayanin abin dake faruwa." "Bana tunanin koh su ana barin su su ganta, sabida na ta6a tunkarar wasu daga cikin su suma sunce rabon da su sanƴa ta a ido ya kai watanni uku." "Toh ya zamuyi kenan?" cewar Rahinah. "Wannan banzar JALILAR zamu matsawa ta faɗa mana gaskiya nasan tana 6oye mana ne, amma muddin ya zamto dagaske DEENAH tana da ciki..." "Ba zamu bar abin cikin nata da rai ba" cewar Hafeezah cikin ƙarar da maganar Sairah ɗin. Buɗe ƙofar da JALILAH take ta fiddo ta kafin ta sanƴa ta zama kan kujera, kallon ta tayi tsaf tace "Cikin lallama nake sake tambayar ki JALILAH ki faɗamin abubuwan da kika sani game da DEENAH, menene dalilin da ya sanƴa bata fitowa, muddin kuma kika kuskura kika sake yimin ƙarya wannan karon toh lallai zakiyi nadama, ke nake sauraro." Cikin kuka JALILAH tace "Ummie maganar gaskiya nake faɗamiki, ban...bansan komai ba..." Marin da Sairah ta ɗauke ta dashi ne ya sanƴa ta dafe ƙuncin ta cikin azaba kafin tace da ita "Farko kince rashin lafiya take, yanzu kuma kince bakisan komai ba, hakan ne ya sake tabbatar min da cewa ƙarya kikeyi sannan ke munafuka ce, koh ki faɗi gaskiya kokuma jikin ki ya gayamiki." Kuka kawai take hannayen ta dafe da ƙunci, tasan muddin ta faɗa musu gaskiya they won't stop at nothing har sai sunga bayan DEENAH da abin dake cikin ta, muddin kuma ta buɗi baki ta faɗi gaskiya then taci amanar DEENAH kenan, ita kuma ba zata ta6a barin hakan ya faru ba. Barin wurin Sairah tayi bata daɗe ba ta dawo riƙe da ƴar ƙaramar wuƙa tazo gaban JALILAH ta tsaya tare da nuna ta da wuƙar tace "Ki faɗi gaskiya koh kuma uwarki ta haifi wata." Hafeezah ce tace "Koh ta faɗi gaskiya kokuma ki yanke mata maƙoshi idan yaso sai ta mutu kawai." Rahinah ce tace "Ba haka zakuyi mata ba, sai wuƙar zakuyi a idanun ta muddin ta sake yin ƙarya ki da6a mata shi cikin ido, idan taƙi faɗar gaskiya ki sake soke ɗayan idon dashi, da kanta zata faɗi gaskiya." Da shawarar Rahinah tayi amfani dan haka cakumo gashin kan JALILAH tayi tana lankwasar mata da wuya haɗi da saita wuƙar a idanun ta tace "Kin dai san dama tun chan ba sonki nake ba koh, ke kishiya ta ce kuma ni ban ɗau kishiya matsayin abokiyar zaman lafiya ba, zan iya yin komai idan nace komai ina nufin harda kisa muddin jini na bai ɗauki mutum ba, dan haka indai har bakya buƙatar rasa idanun ki inaso ki faɗamin gaskiya menene ke wakana da DEENAH a cikin wannan gidan da kullum take a killace?." Shiru JALILAH tayi tana cigaba da kuka "Talk kokuma ki rasa idanun ki." Kai ta shiga girgizawa tana faɗin "Gaskiya na faɗamuku." Haushi ne ya kama Sairah dan haka da6a mata wuƙar take shirin yi a ido Rahinah tayi saurin tsaida ta. "Dakata tukun, cire mata ido azabar ƙanƙanin lokaci ne, ni na san mai zanyi mata ku bani minti biyar naje na dawo yanzu" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin. "For the last time JALILAH ki faɗi gaskiya kokuma ki shiga uku." Shiru tayi da ka ganta kasan tana cikin gagarumin tashin hankali, Rahinah ce ta dawo ɗakin hannun ta riƙe da ƙaton kaskon wutar gaushi. Murmushi tayi tare da kallon su tace "Da wannan zaku horar da ita da ba zatasan lokacin da zata buɗi baki tayi magana ba" ta faɗa tana dire kaskon. Murmushi Sairah tayi tace "Tabbas kinyi dabara" tana ƙarasowa ta ɗau kaskon kafin tace ku kama min ita ku ɗaure." Cike da mugunta suka ɗaure JALILAH jikin chair yadda ba zata iya motsi ba tare da liƙe mata baki. Ƙarasowa gaban ta Sairah tayi haɗi da sakin murmushin mugunta kafin ta ajiye gaushin wutar a ƙasan ƙafar JALILAH yadda raɗaɗin zai dinga dukan tafin ƙafarta kafin su koma gefe su tsaya suna kallon ta. Sosai tururin wutar ke ƙona tafin ƙafarta, babu abinda takeyi sai gumi da take haɗawa ga kuma hawaye dake tayi mata parate a kumatu, sam babu damar ihu. Sai da suka ga ta fita hayyacin ta sosai tukun kafin Sairah ta janƴe wutar inda Rahinah kuma ta kwara mata ruwa a fuska tare da ɗaye abin bakin ta cike da mugunta. Wani irin azababbiyar ajiyar zuciya JALILAH ta saki kanta dake lilo Sairah ta riƙo kafin tace "Faɗamin yanzu." Shiru tayi mata tana cigaba da sauƙe ajiyar zuciya sosai dukkanin ilahirin jikin ta keyi mata zugi da raɗaɗi musamman tafin ƙafar ta. Wanka mata mari Sairah tayi a tsawace tace "Kina mugun 6ata min rai, tell me now." Rahinah ce ta ɗauki gaushin wutar tare da tsunbula ƙafar JALILAH a ciki kafin Sairah tayi saurin sanƴa hannu tana toshe mata baki daga ihun da takeyi ɗin "Faɗamin yanzu." Tsabar azaba batasan sadda ta shiga jinjina kanta ba. "Ciki ne da ita?." Nanma jjinjina mata kai tayi kafin kuma tayi murmushi tana ɗauke hannun ta daga rufe mata baki da tayi inda Rahinah kuma ta cire mata ƙafar daga kan gaushin. Sunce ta sukayi kafin Sairah ta tura ta tana faɗin "Amfanin ki ya ƙare." Murmushi Hafeezah tayi tace "Am so proud of you girls" ta faɗa tana basu kyakkyawar runguma. Kiran kuyangun ta tayi kafin tace dasu "Show her the way out." Kallon JALILAH dake kwance a galabaice sukayi kafin su nufe ta tare da ɗaga ta suka fice da ita. Wheel-chair suka nema suka ɗaura ta akai kafin su shiga tura ta dan maida ta part ɗinta, sosai take a matuƙar galabaice har dishi-dishi take gani. Hango Yayan ta Sooraj dake tafe kamar zai tashi sama tayi kullum shi kam a ƙufule yake da cikin tsananin fushi ta san muddin ya ganta a haka babu abinda zai nuna mata sai ma yayi mata Allah ya shi ƙara yayi wucewar sa, saurin sadda kanta tayi har sun wuce shi kafin kuma yayi saurin dakatar dasu. Tsayawa sukayi daga tura ta ɗin, tana jan rigar ta ya rufe mata ƙafafun ta, ƙarasowa wurin yayi yana kallon ta ganin kanta a sadde ya sanƴa shi faɗin "Mai kikeyi akan wannan keken guragun?." Cikin rawar harshe tace dashi babu komai. Kallo ya ƙare mata kafin ya kalli kuyangun da suma kansu sadde a ƙasa kafin ya sake maido duban sa kan JALILAH yace "Ƙarya kike yi." Shiru tayi bata ce dashi komai ba, zagayowa yayi ya tsaya a gaban ta yana sake ƙare mata kallo, ƙafarta da yaga tana ta kiciniya dashi ta cikin rigar ta ya duba ba tare da yace da ita komai ba ya sunkuyo yana ɗaga rigar tata, a matuƙar hasale ya ɗago yana duban ta tuni kuma ya fara sakin huci yana ɗago ƙafar ta tare da ƙure tafin da ido ganin yadda ya kwakkwaile, cikin hucin 6acin rai yace "Wane ɗan kasadan ne yayi miki wannan aika-aikar?." Shiru tayi tana fashewa da kuka, tsawa ya daka mata cike da 6acin rai yace "Shut the fuck up and tell me who did this to you." Cikin kuka take faɗin "Sairah, Rahinah da Ummie ne..." "Uban mai kikayi musu?" ya faɗa a tsawace. Kai ta girgiza masa alamun babu komai. Sosai ransa ya 6aci babu abinda yake sai huci, miƙewa tsaye yayi yace "Ku kaita gida" kafin kuma ya wuce fuu kamar wanda iska zai tashi sama dashi. Bai tsaya koh ina ba sai faɗowa da yayi cikin falon Hafeezah ya hau kwala kiran sunan ta "Hafeezaaahhh" kamar zai tashi ginin gidan yana bangaje duk wani abu da ya shige masa gaba. Duk fitowa sukayi sakamakon yadda ya kira sunan nata, bai tsaya koh ina ba sai gaban ta yana nuna ta da yatsa yace "How dare you?." "Kai mahaukacin ina ne...?." Bata ƙarasar ba ya daka mata tsawa da faɗin "Shut up, so you're this merciless?, i will make sure na koya miki hankali dake da wadannan fitsararrun ƴaƴan naki for torturing my sister" ya ƙarashe kamar zai kifo kansu. "Wannan mahaukacin kuma daga ina?" cewar Sairah tana kallon Sooraj ɗin. Marin da ya kifa mata a ƙunci ne ya sanƴa ta saurin dafe wurin har kanta na wani irin juyawa. Dorina ya gani rataye jikin wall baiyi ƙasa a guiwa ba ya shiga zuga mata a jiki "I will show you that ba hauka kaɗai ne dani ba, duka psychiatry ne a kaina." Ihu kawai Sairah keyi kamar zata shiɗe, finciko Rahinah dake shirin guduwa yayi yana wani irin kwallo da ita kafin ita ma ya hau zuga mata dorinar ba ji ba gani, babu abinda duk sukeyi sai ihu suna kiran sunan Ummie ta taimake su, sosai Sooraj yayi musu jina jina ya haɗa musu majina da jini kafin ya shiga nuna su da yatsa yana faɗin "Dan mun aurarwa ƴar mu wa ɗanku ba hakan ke nufin mun sallamar da ita wa duniya kokuma batada gata bane ba, koh kun manta wanene Sooraj da abinda zai iya yi?, daga yau duk wani wanda ya ƙara yi mata koh da banzan kallo ne i will make sure i pluck the hell out of the bitch eyes out." Sosai Sarauniya Hafeezah ta tsorata dashi har ya gama dukan su bata iya tankawa koh ta hana ba dan kada ma ya haɗa da ita dan kuwa sai yau ta sake tabbatarwa da bashida hankali koh kaɗan. "And you" ya faɗa yana juyowa ga Hafeeza har sai da ta tsorata yadda ya zaburo mata ɗin yace da ita "Daga yau kulawar ƙanwata ya koma Ƙarƙashin ki, zanje na maido da ita yanzu na baki kwana biyu ki dawo mata da ƙafar ta mai kyau yadda yake, idan kuma ba haka ba sai na tabbatar da na haɗa ki da wadannan abubuwan da kike kira ƴaƴa na ƙona ku duka, idan yaso sai nima a kashe ni dan ban damu da rayuwar ba yanzu, tunda ZEEYAD ya mutu na fahimci cewa duniyar nan bakomai bane, sannan har yanzu ina baƙin ciki da rashin neman yafiyar sa da banyi ba, dan haka duk wani wanda yaso shiga gona ta kokuma ya kuskura ya sake ta6a min lafiyar ƙanwa sai na tabbatar da yayi nadamar hakan, kinji koh bakiji ba?" ya faɗa a tsawace yana kallon ta da rikitattun idanun sa. Da sauri ta shiga jinjina masa kai tana faɗin "Naji." Kallon Rahinah da Sairah dake zube a ƙasa jina-jina yayi kafin yace "Kaɗan daga cikin abinda zan iya aikatawa kenan, ku sake ta6a min ƙanwa na gani zan dawo da ita yanzun nan ku tabbatar kun rissina har ƙasa kun bata haƙuri sannan babu wanda zai kula da ita da lafiyar ta sai ku, kunji koh bakuji ba?." Kai suka shiga gyaɗa masa, a tsawace cikin baiwa kowannen one-one lashes yace "Bakuda baki ne?." "Munji wallahi munji" suka faɗa cike da tashin hankali. Wiping fuskar sa yayi yace "Good, Good" kallon abubuwan da ya bibbirkita yayi kafin yace "Ku tashi ku tsaftace nan wurin yanzun nan, ku tabbatar da cewa babu datti koh kaɗan, sabida ƙanwata ba zata dawo cikin gidan nan ta tadda datti ba sabida ba ma'abociyar ƙazanta bace irin ku." Tun kafin ya gama rufe baki suka yunƙura dakyar cikin ɗingishi da alama dai ba mugun rauni yaji musu ba, suka shiga aiwatar da abinda ya sanƴa su, wuri ya samu ya zauna kafin ya kalli Hafeezah dake tsaye yace "Har dake." Da sauri ita ma taje jiki na rawa ta shiga taya su. Sawa yayi aka kawo masa lemo mai sanƴi ya naɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana korawa yana kallon su. Sau uku sunayi yana ce dasu baiyi ba su sake gogewa su gyara, sosai da sosai suka jigata Rahinah da Sairah sai kuka suke ganin girman falon amma koh tausaya musu baiyi ba gashi kuma dama ba sabawa sukayi ba, sosai sukejin kamar bayan su zai 6alle ya faɗi. Sai da yaga gidan ya fita tass kafin ya miƙe yace "Ku tabbatar kun gyara mata ɗakin da zata sauƙa idan tazo, muddin kuma naga koh da tsakuren datti ne kuyi kuka da kanku" yana faɗin haka ya fice a fusace. ********************** _______Sosai hankalin DEENAH da na Grandma ya tashi ganin abinda su Hafeezah sukayi wa JALILAH. DEENAH ce cikin kuka tace "Grandma they won't stop at nothing har sai sunga bayan babyn jiki na, sai dai ba zan ta6a bari hakan ya faru ba kafin su ga bayan mu ni sai na kawo ƙarshen su." "DEENAH tayaya, just take a look akan abinda suka yiwa JALILAH think of abinda zasu yi miki ke da suke farauta, cikin ki watar sa biyar ne kawai da ƴan kai, am sure ba zasu sarara ba har sai sunga bayan shi." Dafe cikin tayi lokacin da taji motsin sa, cikin kuka ta runtse idanun ta tana samun kujera ta zauna, kafin ta shiga girgiza kai tana faɗin "Sunga bayan mahaifin shi nikuma ba zan bari suga bayan shi ba, mai suke nema ne damu, ba dama mahaifin sa suke so ba kuma sun raba mu dashi, why kuma yanzu suke sake harin mu nida ɗana" ta faɗa cikin kuka tana rungume cikin nata. Cike da tausayin ta Grandma ta zauna a gefen ta tana faɗin "DEENAH har abada kada ki gaji da neman addu'ar tsari daga wurin Ubangiji, ni inaji a jiki na ba zasu ta6a yin nasara akanku ba komin asiri da tsafin su Allah ba zai ta6a basu galaba akanku ba, ya kama ta ki zamto mai dauriya, jajiratacciya dama kuma jaruma koh dan saboda ɗan dake cikin ki ma, muddin kina son ɗaukar fansar ran mahaifin sa then yakamata ki rage rauni dama kuma yawan shiga wannan ƙuncin ki nuna musu cewa ke bakya tsoro sannan babu abinda zasu iya yi miki keda ɗan cikin ki." "Grandma is right DEENAH, lokaci yayi da yakamata kema ki nuna musu cewa a shirye kike da ki kare kanki da ɗanki, ki kuma nuna musu cewa Allah yana tare daku and no harm can come to you, zamu goya miki baya akan dukkanin wani hukunci da zaki yanke" cewar JALILAH da har anyi mata dressing ɗin ƙafar tata. Grandma ce tace "Kwarai kuwa DEENAH, idan suna taƙama su su uku ne zasu iya ja damu ai mu mun fisu yawa, kinga da ɗan cikin ki mu huɗu kenan, mu nuna musu cewa muma fah ƴan iskan kanmu ne sannan ba zamu sake kar6ar wani rashin mutunci koh nuna tsoron su a fili dama kuma zuciya ba, na tabbata ɗan cikin ki shima yana goyon bayan mu a wannan harkar dan nasan shima ba zai so ayi babu shi ba wurin ɗaukar fansar ran mahaifin sa." Dariyar da batasan da zuwan sa ba tayi jin abinda Grandma ke faɗi, murmushi Grandma tayi ganin DEENAH ɗin tayi dariya nan tace "Ehmana ai gaskiya ne duk zamuyi maganin su ɗaya bayan ɗaya da izinin Allah." Murmushi sukayi dukan su kafin kuma su rungume juna. *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR............✍🏽* [9/6, 10:49 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *QUARTER FINAL* *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *053...* _Ku tanadi Hanky tukun kafin ku fara karatun😭_ ________"Ni fah wannan mahaukacin Sooraj ɗin bai daki banza ba wallahi, sai na rama duk wani rauni da yayi min akan ƙanwar tasa na nuna masa cewa nima fah da tawa gatar, dan aure ya kawo ni wannan MASARAUTAR ba shi ke nufin koh banida gata bane sannan wani banza chan ya ta6a min lafiyar jiki kuma ya wanƴe lafiya, sai na tabbatar na ɗau fansa ta akan ƙanwar tasa idan yaso koh kashe ni zaiyi sai dai ya kashe ni" ta ƙarashe cike da fusatar da take ciki. Rahinah ce tace "Ke ki raba kanki da Sooraj wallahi bayida hankali koh kaɗan ni kunga tattara inawa-inawa zanyi na koma London da zaran na ɗan ƙara jin sauƙi ban isa ya kashe ni a banza ba tare da na gama more rayuwa ta ba." Shiru Hafeezah dake ta kai komo cikin ɗakin tayi tana saurarar su. Katse su tayi da faɗin "We must get rid of DEENAH's baby." Wani irin kallo Sairah tayi mata kafin tace "Just look at our condition, koh nuna alamun kin damu bakiyi ba, kedai kawai akan burin ki hankalin ki ya karkata baki damu da kiyi mana jajen abinda ta6a66en nan yayi mana ba, and kinzo kina maganar wata banzar DEENAH chan daban." Kallon ta Hafeezah tayi kafin tace "Kuma dan Sooraj yayi muku lahani sai hakan ya dakatar dani daga aiwatar da niyya ta komiye kike nufi, this is for your own good ke gaki nan koh cikin bakiyi ba and YAZEED ne zai zamto sarki nan ba da jimawa ba, muddin muka bari DEENAH ta haihu then komin daren daɗewa sai abinda ta haifa ya gaji mulki muddin ya kasance namiji ne." Shiru tayi tana tunani sai yanzu take ganin wautar ta tun farko da ta kada seducing YAZEED, nan ta miƙe tsaye tana kallon Hafeezah tare da faɗin "What do we do then?." Murmushi Hafeezah tayi tare da faɗin "We kill the unborn child." "But how, tayaya JALILAH is our only hope and mahaukacin yayan ta won't let us rest muddin muka sake yunƙurin yi mata wani abin." Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Wayo zamuyi mata da daɗin baki mu janƴo ta cikin mu." "That won't be easy, zuciyar ta gauraye take da imani, ba zata ta6a yarda damu ba har ta iya bamu haɗin kai, and besides kishiya ce a gareni there is no way zan haɗa inuwa ɗaya da ita a matsayin team, we all want her dead sabida ya kasance ni kaɗai na rage matar YAZEED why kuma zamu jawo ta cikin mu?." "Kina tunanin koh nima kaina ina ƙaunar ta da YAZEED ne, ke kaɗai ce matar YAZEED sannan kece zaki zamto Sarauniya ga wannan ƙasa ba da wata ba, da zaran ta gama yi mana amfani sai kuma muga bayan ta." Murmushi Sairah tayi kafin tace "Yanzu kikayi magana, ta ina yakamata mu fara yanzu?." *********************** __________DEENAH ce tsaye bakin mirror ta ƙurawa cikin nata ido, hannu ta kai ta shafi cikin tanajin yadda yake yi mata motsi a ciki. Murmushi tayi kafin tace "You're my only happiness now and i will do everything it takes dan ganin kazo duniyar nan da ranka, i can give my life dan ganin kai ka rayu, no enemy da ya isa yayi galaba akanka, this is my promise to you little ZEEYAD." Rolling ɗin gyalen hannun ta tayi akanta tana gyara dressing ɗin jikin ta kafin kuma ta fice daga ɗakin. Tundaga sauƙowar ta kuyangu matan suke binta da ido har tsayawa sukayi suna kallon ta, DEENAH tamƙe fuska tayi tamkar bata ta6a yin dariya ba ganin yadda har wasun su sun fara ƙus-ƙus ƙasa-ƙasa. Har ta fice daga part ɗin Grandma basu daina binta da kallo ba, tana fita kai tsaye hanƴar fadar mai Martaba ta nufa sam bata damu da kallon da kowa ke bin ta dashi ba duk inda ta ratsa, a haka har ta iso ƙofar fadar. "What a beautiful being" ta tsinkayo murya daga bayan ta hakan ya sanƴa ta dakatawa ba tare da ta juyo ba. Ayaan dake binta da tsinannen kallo ƙarasowa wurin yayi kafin ya shiga zagaye ta yana binta da kallo, dakatawa yayi a gaban ta kafin yayi murmushi yace "You look more beautiful fiye da yadda ake kwatancen ki." Bata kallesa ba haka ma kuma bata kulasa ba. Baki ya lashe yana sake matsowa kusa da ita kafin yace "Sai dai koh kaɗan baki dace da ciki a jikin ki ba, i mean ZEEYAD is already dead why keeping abinda ya bari har yanzu cikin mahaifar ki, you deserve a better life like this carrying a dead persons heir in your womb..." Kallon da tayi masa ne ya sanƴa shi haɗiye sauran maganar, sosai maganar da yayi yayi mata zafi har wani irin huci ta shiga fitarwa cike da 6acin rai. Hannaye ya ɗaga sama tare da faɗin "Oops those that hurt you?" kafin kuma ya sauƙe hannun cikin murmushin ƙeta yace "Seriously DEENAH you're much younger than your age and more beautiful than your expectation ZEEYAD is dead... why don't you give me a chance?" ya faɗa cikin ɗaga mata gira ɗaya. Hannu ta ɗaga tare da wanke fuskar sa da mari, dafe ƙunci yayi yana juyowa ya kalleta cikin tsananin 6acin rai idanun sa na canza launi. "How dare you?" ya faɗa yana ture ta da ƙarfi. Tangal-tangal ta tafi zata faɗi kafin tayi saurin riƙe wani ƙarfe dake bayan ta yanw tsaida ta, wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe tana riƙe cikin ta kafin kuma ta sauƙe numfashi ganin tana runtse idanun ta. Ƙarasowa yayi inda take tare da fizgo ta tana kallon sa, murmushi yayi kafin yace "You think ana ta6a lafiyar jiki na kuma a wanƴe lafiya ne?" ya faɗa yana shafa kafaɗun ta cikin salon iskanci. Su dai guards ɗin koh motsawa basuyi ba bale su tanka abin dake faruwa haka suka ƙame a wurin tamkar gumaka. Ganin yadda yake shafa mata jiki ne ya sanƴa ta tattarar dukkanin karfin ta tana tura shi. Baya yayi yana ja ya tsaya, dariya ya saki yana sake binta da wani irin kallo. Saurin nufar ƙofar fadar tayi nan taga ya sake ɗaura mata hannu a kafaɗa wurin tsaida ta. Idanun ta ne suka sauƙa kan wani ɗan guntun takobin dake maƙale gefen wandon ɗaya daga cikin guards ɗin, ai kuwa batayi wata-wata ba tayi saurin kai hannu tana zaro kafin ta juyo a fusace tana fille masa hannu da wannan takobin har jini na 6ata mata fuska. Wani irin ƙara Ayaan ya saki cike da mugun firgita yana ja da baya tare da faɗi ƙasa ganin damtsen hannun sa guntule a ƙasa ga kuma yadda jini ke ta bulala tamkar an buɗe shower. Ihu kawai yakeyi sai a sannan ne guards ɗin suka iyo kansa, kan kace miye kuma har mutane sun fara taruwa kowa na zuwa ganewa idanun sa abin dake faruwa ganin yadda Ayaan ɗin ke ta ihu har yanzu tamkar zai zauce. "Arrest her" ɗaya daga cikin guards ɗin ya faɗa da ƙarfi yana nuna DEENAH dake tsaye tana ta faman sakin huci tamkar ranta zai fito. Kanta wasu guards ɗin sukayi suna sanƴa mata handcuff a hannu, sam koh kaɗan bataji wani tsoro koh fargaba cikin ranta ba sai ma ji take da tayi dai-dai, sannan duk wani wanda yayi yunƙurin shiga gonar ta a shirye take da ta fuskanci wannan mutumin, yanke hannun Ayaan da tayi a yanzu ji tayi wani irin jarumta tazo mata, da mugun kallo take binsa har suka wuce shi kafin ta saki wani irin murmushin gefen baki. Kaita akayi aka rufe cikin cell sam bata damu ba dan kuwa tasan komin daren daɗewa dai sai ta fita dan ba zata dauwama cikin nan ba. Wuri ta samu ta zauna tanajin zuciyar sa fes koh bakomai ta ɗau fansar ta6a mata jiki da yayi. ******************** ________Sosai Hafeezah ke wani irin mugun kuka a gaban ɗan nata ganin hannun sa a yanke, musamman da taji wacce ta aikata masa hakan ba ƙaramin fusata tayi ba, ji take zata iya kashe DEENAH muddin ta haɗa idanu da ita, sai ta ɗau fansar cire mata hannun yaro da tayi sai dai uwarta ta haifo wata amma ba dai ita ba. Ganin mai Martaba baiyi magana bane ya sanƴa ta nufar sa a mugun fusace tana faɗin "Kaga abinda matar wancan mataccen ɗan naka tayi wa ɗana amma har yanzu ka kasa cewa komai, banji ka bada umarnin aje a yanke mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata ba, ta cire min hannun yaro amma kayi shiru tamkar wanda ba ɗanka bane shi ɗin, maiyasa ba zaka ɗau mataki akanta ba?." A tsawace mai Martaba yace da ita "DEENAH have done the right thing, your son here tries to humiliate her ba tare da yayi tunanin ita ɗin matar wansa bane ba, koh a dokar ƙasa laifi ɗaya ta aikata shine na ɗaukar mataki da hannun ta..." Cikin kuka ta katse shi da faɗin "Ni zaka dubi idanu na kacemin ta aikata dai-dai, kasan ciwon da nakeji cikin zuciya ta na ganin yaro na babu hannu ɗaya?, ta maida min yaro miskini cikin ƙanƙanin lokaci dan haka nima ba zanyi ƙasa a guiwa wurin ɗaukar fansa wa yaro na ba, muddin kai ba zaka ɗauki mataki ba ni nan zan ɗauka" ta faɗa a haukace tana nufar hanƴar ficewa, kwala mata kira mai Martaba keyi sai dai inaa koh ta juyo ta kallesa balle yasa ran zata amsa har ma ta tsaya. Bata tsaya koh ina ba sai part ɗin Grandma saurin miƙewa tsaye duk sukayi ganin yadda Hafeezah ta faɗo cikin falon nasu hannun ta ɗauke da takobi tamkar zata tashi sama. Kai tsaye kan DEENAH ta iyo cike da fusata ba tare da tunanin komai ba idanun ta sunyi matuƙar rufewa da tsanar DEENAH ta ɗaga takobin, DEENAH saurin runtse idanun ta tayi tana jiran shigar takobin cikin cikin ta sai dai taji shiru, ihun JALILAH da taji ne ya sanƴa ta saurin ware idanun ta tana sauƙe su a bayan sa. Duk mutanen cikin wurin idanu suka zaro cike da mugun tashin hankali ganin wanda wuƙar ya soka. Da sauri Hafeezah ta saki takobin tana ja da baya a mugun razane tare da sakin wani irin ƙara tana ware idanun ta kan wanda takobin ke jikin shi. Ɗago da idanun sa da sukayi matuƙar kaɗawa YAZEED yayi daga kan takobin yana kallon mahaifiyar tasa, zuciyar sa cike da tsantsar baƙin ciki, baƙin cikin da ba zai ta6a gushewa daga ransa ba har izuwa ranar da za'a busa ƙaho. A hankali ya furta "Um... mie..." yana zubewa kan guiwowin sa wasu irin hawaye na biyowa ƙuncin sa. DEENAH ji tayi zuciyar ta na breaking into tiny-tiny pieces sakamakon ganin YAZEED da tayi cikin sa soke da takobin da mahaifiyar sa tayi niyyar kashe ta dashi. Bata koh iya motsa koh da ƴar yatsar ta bane wasu irin zafafan hawaye na biyo mata ƙunci. Grandma kuwa zubewa tayi kan kujera itama tamkar wacce aka zarewa ruhin ta daga jikin ta. Cikin maganar sa da bata fitowa mai kyau yake kallon mahaifiyar tasa yace "Are... you... happy now?." Kai kawai Hafeezah ke girgizawa cike da tashin hankali hawaye na biyo mata ƙunci. Babu wanda ya iya tunkarar YAZEED sakamakon wani irin shock da ya ziyarci kowannen su, cikin kuka ya sake faɗin "Are you happy now... Ummie?" yana zubewa kwance a wurin inda kuma jini ya shiga wanke wurin. Da gudu Hafeezah ta iyo kanshi mai Martaba ya daka mata wani irin tsawa "Don't you dare go near my Son Hafeezah." Amma inaa bata saurare sa ba tayi kan YAZEED ɗin sai gurzar kuka take tamkar ranta zai fita. "Oh no!, no... my lovely son YAZEED, i killed you, i killed my own Son, na shiga uku na lalace na kashe YAZEED ɗana..." "Sieze her" cewar mai Martaba ɗin ai basuyi wata-wata ba guards ɗin suka iyo kanta suna ɗagota, hannun YAZEED ɗin ta riƙo gam babu abinda take sai kuka shikenan ta kashe ɗanta da kanta a garin son zuciya da baƙar zuciya irin tata. Dakyar suka iya kwace YAZEED daga hannun ta, da gudu JALILAH ta iyo kansa bata ma damu da ciwon ƙafarta ba dan kuwa tama daina jinsa baki ɗaya ne a jikin ta tana ɗagoshi, sosai take kuka tana girgiza masa kai. Murmushi yayi mata kafin yace "Don't... cry." Kai kawai take girgiza masa tana kuka. "Please...please i beg you kada ka mutu ka barni, ba zaka mutu yanzu ba baikamata ace ka mutu ba, no... no please, please" ta faɗa da ƙarfi cikin kuka tana ɗan bubbuga fuskar sa ganin idanun sa na neman rufewa. Riƙo hannayen ta yayi yana kallon fuskar ta kafin yace "Am sorry..." "No...ba zaka mutu ba, ba zaiyiwu kaima mu rasa ka ba, dan Allah kada ka mutu na roƙeka, dan Allah..." Shafa fuskar ta yayi yana share mata hawayen dake biyo mata fuskar, "Please forgive me..." ya faɗa cikin rarrabewar harshe. Kallon DEENAH dake tsaye akansu tana hawaye yayi kafin yace "Z...EE...ZEE..." bai ƙarasar da zancen nasa ba jami'an dake aiki da emergency Ambulance suka zo suka ɗauke shi. Cakumo ɗaya sarki yayi yace "Save him... Save my son please shi kaɗai ne ya rage min..." Kwacewa mutumin yayi daga riƙon da yayi masa kafin yayi saurin marawa ƴan uwan sa baya. Tari mai ƙarfin gaske ne ya sarƙe mai Martaba ɗin, take shima cikin gaggawa aka ɗauke sa suka fice. Sosai JALILAH ke kuka tamkar zata shiɗe tana kallon hannun ta da yake kaca-kaca da jinin YAZEED haka ma kayan jikin ta. Tashin hankalin da DEENAH da Grandma ke a ciki baya misaltuwa, dukkanin su kuka suke an rasa mai rarrashin wani, jikin DEENAH har rawa yake, tasan itace tayi sanadiyyar mutuwar YAZEED da ace bata tankawa Ayaan ba dah Hafeezah bata haukace tazo da niyyar kashe ta abin ya faɗa kan YAZEED ba. Zubewa tayi akan kujerar dake bayan ta tana shessheƙa mai cin rai, sosai take cikin shock ɗin ganin mutuwar YAZEED a gaban ta, shikenan JALILAH ta zama ƙaramar bazawar kamar ita though ita tana da magajin da zata dinga tuna mijin ta dashi but JALILAH fah yanzu ne ma sabo ya soma shiga tsakanin ta da YAZEED gashi kuma ya tafi ya bar ta, this is very shocking, sam bata tsanmaci zuwan wannan incident ba, sosai zuciyar ta ke rawa, sosai take baiwa kanta laifin afkuwar wannan lamari, tasan YAZEED ba zai rayu ba shikenan shima ya tafi tamkar yadda ZEEYAD ya yafi tsawon watanni biyar kenan bata ga ya dawo ba, haka shima YAZEED ɗin zai tafi ba zai dawo ba har abada dan kuwa bata tunanin zai rayu, sosai takejin tausayin mai Martaba ma ace ya rasa ƴaƴan sa matasa wadanda zasuyi gadon mulkin sa, bashida wani magaji na kirki kuma da har za'a iya bashi mulkin ƙasar ya riƙe, gashi shima dama bai gama farfaɗowa daga shock ɗin da ya shiga na mutuwar ZEEYAD ba ga kuma na YAZEED "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" take ta nanatawa a ranta. ************************ _________Sosai likitoci suka rufu akan YAZEED suna iya bakin ƙoƙarin su na ganin sun ceto rayuwar shi. Mai Martaba gabaki ɗaya ya rikice ya zangwame lokaci guda, hankalin sa a matuƙar tashe yake, Abhi ɗin Sadeeq ne ke ta ganin ya kwantar masa da hankali amma kamar sake ƙara masa damuwa yake, ya kasa zaune ya kasa tsaye, damuwa da fargaba sunyi masa ƙatutu a cikin zuciya bai ma damu da tasa lafiyar ba, burin sa shine YAZEED ya samu lafiya nan ne kaɗai hankalin sa zai kwanta. Fitowar wani likita daga ɗakin tiyatar ne ya sanƴa mai Martaba iyo masa wani irin riƙo yana faɗin "How is he, how is my Son?." "Calm down your Highness, muna iya bakin ƙoƙarin mu ne na ganin mun ceto shi, zai fi kyau ka sarara haka muyi aikin mu cikin kwanciyar hankali" yana faɗin haka yayi gaba da sauri. A takaice dai sun ɗau awanni da dama akan YAZEED kafin su fito daga ɗakin tiyatar kusan likitoci shida ciki harda Sadeeq. Duban idanun Sadeeq Abhi yayi kafin ya kalli mai Martaba da shima shi yake kallo. "How is YAZEED?, sannan zuwa yaushe zai samu lafiya mu tafi dashi gida?." Kallon Abhi ɗinsa Sadeeq yayi cikin sanƴi yace "I'm sorry..." Kallon da mai Martaba yayi masa ne ya sanƴa sa kasa idda maganar tasa. "Yes, tell me." "YAZEED have only 30% chance of survival munyi nasarar cire takobin daga cikin sa wanda yayi nasarar huda small intestine ɗinsa, so munyi masa dukkanin wani ƙoƙarin ma na likitoci but..." "Kana nufin kacemin kana tantama zai rayu koh ba zai rayu ba kenan?" cewar mai Martaba ɗin. Kai Sadeeq ya jinjina masa, nan mai Martaba ya sake faɗin "Zancen banza ne wannan likita, ran YAZEED ba a hannun ka yake ba, you have no gut to tell me ba zai rayu ba, ni nasan insha Allah ɗana zai rayu na rasa na farko ba zan iya jurar rasa wannan ba, our kingdom needs someone very trusthworthy da zai mulke ta, YAZEED is the only person da nake sa ran zai cika min buri na, this kingdom will fall apart muddin YAZEED ya mutu..." hawayen da suka zubo masa ne ya sanƴa maganar tasa ƙaƙarewa. Ido Abhi yayi wa Sadeeq akan ya wuce yaje kafin kuma shi ya shiga baiwa mai Martaba ɗin baki. Sadeeq Office ɗinsa ya koma, kifa kansa yayi akan table ɗin ofishin nasa, wasu hawaye masu zafi na wanko masa fuska, he can't believe iriyar ƙaddarar wannan MASARAUTAR yana tsoron rasa YAZEED tabbas idan YAZEED ya mutu then komai lalacewa zaiyi, and ZEEYAD kuma har yanzu babu wani labarin cigaba a fannin lafiyar shi. Yasan rai ba a hannun sa yake ba but zaiyi dukkanin ƙoƙarin sa tare da addu'ar ganin YAZEED ya rayu haka ma ZEEYAD, su ɗin abokai ne amana a gareshi dan haka it's a must for him ya dage da yi musu addu'a dukkanin su, kowa nasu tausayi suke basa DEENAH, JALILAH Grandma dama kuma Mai Martaba, ɗago da jajayen idanun sa yayi kafin kuma ya tashi ya fice daga office ɗin. ************************* *6 MONTHS LATER* _________Hafeezah na hango cikin Katuwar cell hannayen ta dama kuma duka ƙafafun ta ɗaure da chain, sosai tayi kaca-kaca tayi jina-jina da ita, sosai ta koma wata iriyar shiru-shiru tamkar ba Hafeezah marar imanin nan ba. Sosai takejin baƙin cikin kashe YAZEED da tayi, sai dai ta dangana laifin ne akan DEENAH wanda har yanzu bata cire ran kashe ta ba da ita da abinda ta haifa ɗin bayan ta fito daga kurkuku, dukda batasan dalilin da ya sanƴa ba'a yanke mata hukunci har yanzu ba but batada wata damuwa tunda akwai Sairah da Rahinah su zasu ƙarasar mata da sauran aikin da batayi ba. "Chill out DEENAH, soon dake da abin da kika haifa ɗin zaku baƙunci lahira, i don't care yadda makoma ta zata kasance all i want and need is your death, i won't stop at nothing until a avenge my Son's death dama kuma Ayaan da kikayi sanadiyyar naƙasar masa da halitta, i hate you DEENAH yadda ban ta6a tsanar wani mahaluƙi a duniya ba, ba zan ta6a samun Peace of mind ba har sai naga gawar ki da ta ɗan da kika haifa da idanu na, i have spent six months cikin wannan kurkukun duk saboda ke, i swear... i swear DEENAH dole ne ki mutu only then i can be happy" ta ƙarashe idanun ta na kaɗawa suyi jazir. ********************** ________Zaune DEENAH take akan dukda ba sallar takeyi ba sai dai bakin ta ɗauke yake da tasbih dama kuma kiran sunan Allah tare da nemawa YAZEED dake kwance har yanzu lafiya, yayin da 6angare guda kuma take yiwa mijin ta addu'ar da kullum bata gajiya dayi masa. Ƙananan kukan da Jaririn dake kan gado yayi ne ya sanƴa ta miƙewa tana zuwa kan gadon tare da ɗaukar sa, a hankali ta shiga jijjiga shi tana faɗin "It's Okay Baby, Momy is here banyi nisa da kai ba" ta faɗa tana rungume shi a ƙirjin ta. Lumshe idanu tayi hawaye na sauƙo mata tace "You left us a lokacin da babu wanda ya ta6a tsanmani, a lokacin Allah ya ɗau ranka, but gashi Allah ya dawomin da photocopy ɗinka, wanda dashi ne zan dinga tuna ka sannan dashi ne nakejin present ɗinka a kusa dani, you may not be here with us but we were always with you and we will forever be Abyad" ta ƙarashe tana zama kan bed ɗin kafin ta kwantar da yaron da alamu dai ya koma bacci, yaye fuskar sa da tayi daga cikin towel ɗinne ya sanƴa wayar hannu na kusan su6ucewa da ganin kyakkyawar halittar yaron mai kama da mahaifin sa sak tamkar an tsaga kara. Murmushi DEENAH tayi tana sake kallon fuskar yaron, kishingiɗa tayi kusa dashi tana a haka har Asuba tayi. Kiran farko ta farka tana sauƙe idanun ta kan fuskar kyakkyawan Baby boy ɗin nata. Murmushi tayi tana miƙewa tare da gyara masa kwanciya kafin ta tashi ta nufi bathroom, Alwala tayi ta fito kafin ta tada sallah, bayan ta idar ne kuma tayi azhkar da Tasbih ɗinta, ta daɗe akan sallayar tana addu'a kafin kuma tayi karatun Al'ƙurani mai girma, bayan ta idda ne ta miƙe tare da nannaɗe sallayar tana maida shi gurbin zaman sa. Yaron da taga idanun sa a buɗe ne ya sanƴa ta yin murmushi kafin ta ɗauke sa tana yin ɗakin Grandma dashi. Akan sallaya ta tadda ta dan haka shimfiɗe shi tayi akan gadon Grandma kafin ita kuma ta fice. Wanka ta iyo tayi shirin ta mai kyau tamkar kullum kafin ta dawo ɗakin Grandma nan ta tadda har ta yiwa jaririn wanka, gaida Grandma tayi kafin DEENAH ta kar6i yaron tana dawowa ɗaki dashi. Tana cikin shirya shi JALILAH ta shigo ɗakin fuskar ta ɗauke da murmushi take faɗin "Mai raino tazo." Murmushi DEENAH tayi tana miƙa sa wa JALILAH bayan ta shirya shi. Kallon sa JALILAH take kafin tace "Har gobe ba zan daina cewa fuskar mahaifin sa nake gani tattare dashi ba." Murmushin yaƙe kawai DEENAH ta iya yi, ita kaɗai tasan abinda takeji cikin zuciyar ta, abin akwai ciwo ciwon da babu wani mahaluƙi da ya isa ya kwatanta ya yake koh da kuwa ya ta6a shiga irin halin sai dai kawai yayi ta 6oye damuwar dake cikin zuciyar sa da murmushi, but tabon da hakan ke yiwa zuciyar mutum ba ƙarami bane. Ganin yadda yanayin ta ya canza ne ya sanƴa JALILAH miƙewa tsaye tana faɗin "Toh mu mun wuce." Kai kawai ta iya jinjina mata kafin kuma ta miƙe akan bed ta shiga kukan da batasan ranar dainawar ta ba. *********************** *3 DAYS LATER* ________Zaune Sadeeq yake a ofishin shi kira ya shigo wayar sa, gaban sa ne ya faɗi ganin malamin nan ne mai kira. Ɗagawa yayi tare da yin sallama cikin sanƴi. Shiru yayi yana saurarar abinda mutumin ke cewa, hankali tashe ya miƙe tsaye yana faɗin "What do you mean...?." "He is under your care, and kayi alƙawarin bashi dukkanin kulawa how comes kuma zakace baka ganshi ba yanzu." "This is Nonsense, kai kacemin bai sami lafiya ba har yanzu, ya kuma zakace min ba sace sa akayi ba." "Hold up, i will be right there yanzun nan, duk inda yake ka tabbatar kun nemo shi before i arrived" yana faɗin haka ya ajiye wayar tare da ficewa cikin kiɗima. Sai da ya leƙa ya duba lafiyar YAZEED tukun kafin ya fice ba tare da ya sanarwa kowa ba. ******************* ______Daga cikin closet room ɗinsu take jin kishi-kishin ɗin yaron yana surutan su irin na jarirai inda ita kuma take amsa masa, kayan su take haɗawa kasancewar gobe da sassafe zasu koma Nigeria dan kuwa taga sam wannan zaman MASARAUTAR ba zata ta6a yiwuwa a garesu ba, muddin tana son ɗanta ya rayu ya zama dole ta tafi tayi nesa dasu dan kuwa kusan sau huɗu ana kawowa jaririn ta hari tana kamawa, hakan ya sanƴa ta zuwa part ɗinsa da ta mance yaushe rabon ta da ta shiga tana harhaɗa abubuwan ta. A hankali yake tafiya har ya idda shigowa cikin ɗakin, turus yaja ya tsaya yana bin ɗakin da kallo kafin kuma ya shiga lalla6awa a hankali yana nufar jaririn da ya hango akan tsakiyar bed ɗin ɗakin. Tsaye yaja yana ƙarewa kyakkyawar yaron kallon wanda ba zai wuci watanni biyu da haihuwa ba, wutsil-wutsil yaron keyi da ƙafarsa yana cigaba da surutun sa irin ta jariran. Gyara rufar bargon jikin sa kamar kuma mai tsoro ya kai hannu tare da ɗaukar jaririn yana kallon sa. Shiru yaron yayi tare da ƙure fuskar wanda ya ɗauke shi ɗin da idanu yana kallo. Sosai suke kallon juna shi da jaririn, cikin wasa yaron ya kai hannu ya shiga jan doguwar gemun fuskar sa da tayi buzu-buzu da ita. Murmushin kan le6e ya saki ganin yadda ɗan jaririn keyi masa wasa. Rungume shi yayi a ƙirjin shi yana lumshe idanun sa. Dai-dai lokacin DEENAH da taji shirun ɗan nata yayi yawa ta fito dan ganin meke faruwa, turus tayi taja tana kallon bayan mutumin da jikin sa ke rufe da bargo har zuwa kansa. Batayi wata-wata ba ta hau dube-duben abin duka ganin 6arawo ya shigo yana neman satar mata ɗanta. Idanun ta ne suka faɗa kan flower-vase dake ajiye a dan haka da sauri ta kai hannu tana ɗauko shi kafin ta shiga takawa a hankali zuwa bayan mutumin, a hankali tace "Stay away from my child." Saurin buɗe idanun sa dake a lumshe yayi yayin da zuciyar sa ta shiga running very faster. Ganin bai juyo ba kuma bai motsa bane ya sanƴa ta sanƴa hannu tana yaye rufin da yayiwa kansa, idanun ta kan doguwar gashin kansa da ya sauƙo har baya tace "Surrender yourself... now." Ganin har yanzun bai motsa bane ya sake sanƴa ta faɗin "Please ka ajiye min ɗana, i will give you everything you want, just don't hurt my child please" ta faɗa dan so take ya ajiye mata ɗanta kafin ita kuma tayi maganin shi. Ganin ya motsa yana shirin juyowa ne ya sanƴa ta saurin ja da baya tana bada gap tsakanin su idanun ta akansa. A hankali ya shiga juyowa still yaron rungume dashi yana sauƙe idanun sa cikin nata, kallon ta yake kafin kuma in a calm voice ɗinsa ya kira sunan ta "MADEENAH." *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽* [9/8, 5:11 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *SEMI__FINAL* *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *054...* _________A razane taja da baya tana yada vase ɗin hannun ta take ya tarwatse a ƙasa. Manƴan idanun ta da ta waro tamkar zasu faɗi ƙasa ne ta kafa masa tana kallo cike da ɗimuwa da tashin hankali. She can't believe her eyes, she can't believe mutumin da ya mutu kusan shekara ɗaya kenan shine tsaye a gaban ta, no inaa tayaya za'ayi hakan?, bayan kowa ya tabbatae da mutuwar sa har ma aka kai shi aka binne a idon ɗumbin jama'a, shine za'ace tsaye a gaban ta, toh kodai fatalwar sa ce? Tasan tabbas ba shi bane ba, jikin ta ne ya kama rawa haka ma bakin ta da takeson buɗewa tayi magana sai dai ta kasa, a hankali kuma cike da tashin hankali ta shiga lalumar jikin bangon ɗakin still idanun ta akansa wanda shi ɗinma bai bar kallon nata ba har ta kai bakin ƙofar fita. "DEENAH?" ya sake kiran ta. Sake firgicewa DEENAH tayi jikin ta inbanda kyarma ba binda yakeyi, babban damuwar ta shine little ZEEYAD dake riƙe a hannun sa. "DEENAH?" ya sake kiran ta yana taka ƙafarsa. Ihun da ta saki ne ya sanƴa shi dakatawa daga tunkarar ta "Stay away from me, ka ajiye min ɗana ka tafi na roƙeka dan girman Allah kada ka cutar min da ɗana" ta faɗa cikin kuka dama kuma tsoron da ya cika mata ruhi. Sake rungume yaron yayi a jikin sa yana mamakin abinda ya sanƴa DEENAH ke gudun sa, kodai bata gane sa bane ba, shine tambayar da yake wa kansa. Sake takawa yayi zai tunkare ta ta sake sanƴa masa wani ihun tana ja da baya, bai tsaya ba ya cigaba da tunkarar tata, cikin kiɗima ta fice daga ɗakin cikin gudu, ZEEYAD baiyi ƙasa a guiwa ba ya mara mata baya shima. Dai-dai tazo sauƙa daga stairs wani irin sul6i ya kwashe ta bata kai ga faɗuwa ba ya taddo ta yana riƙo hannun tare da fizgo ta tana faɗawa jikin sa. Ƙara ta saki tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta ganin fatalwa ya riƙo ta. Kamar wacce kuma wani abin ya gitta mata a kwakwalwa ta tsagaita da kukan nata cak na kusan seconds kafin kuma ta shiga buɗe fuskar ta da ta rufe da tafukan hannayen ta tana ware su akan shi. Da hannu ta shiga tatta6a ƙirjin sa ganin tana iya ta6a sa ne ya sanƴa ta ɗago da kanta da sauri tana kallon sa. "DEENAH?" ya sake kiran ta cikin calm voice ɗinsa. Shiru tayi tana kallon sa da idanun ta dake tsiyayar da hawaye, kallon juna duk suke na kusan 2mins kafin cikin rawar murya tace "A... Ab... Abyad?." "Baby" ya kira ta. Kanta ta shiga girgizawa cikin kuka tana riƙo fuskarsa dake cike da gashi ta sake kiran sa "Abyad." Kuka ta fashe dashi tana rungume sa take faɗin "I know it, i know it... nasan baka mutu ba ban ta6a yarda cewa ka mutu ba, wayyo Allah na nagode maka." Da hannun sa ɗaya shima ya rungume ta ɗayan hannun nasa rungume da little ZEEYAD. Sosai DEENAH ke kuka kamar zata shiɗe, bai iya hana ta ba sabida yasan mai takeji da shima zai sami damar kukan da babu abinda zai hana shi yin kukan, lumshe gajiyayyun idanun sa yayi yanajin wani irin kewa haɗi da so da ƙaunar ta na huda dukkanin wani sassa na jikin sa. Sun daɗe a haka zuciyar su cike da kewar juna, ƙishi-ƙishin ɗin kukan little ZEEYAD ne ya fargar dasu, ɗagowa tayi tana kallon sa kafin ta dubi yaron hannun sa inda shima ya ɗago yaron yana kallon sa. Murmushi DEENAH tayi tana amsar sa shi dai ZEEYAD da kallo kawai yake binta dan kuwa ya rasa ɗan waye wannan ɗin. Kallon idanun sa dake cike taf da alamun tambaya DEENAH tayi, kamo hannun sa tayi suka koma cikin ɗakin dan kuwa ta lura da akwai tarin stress da gajiyawa tattare dashi. Rufe ƙofar tayi tana kwantar da little ZEEYAD kan bed kafin ta tunkaro ZEEYAD dake tsaye tana kallon sa. Ganin tana sake shirin wani kukan ne ya sanƴa shi janƴo ta jikin sa yana bata tight hug mai kyau, sai dai har izuwa wannan lokacin babu koh burbuɗin murmushi akan fuskar sa, runtse jajayen idanun sa dake yi masa yaji yayi kamar wanda zai maida ta cikin sa ya huta da kewar ta dama kuma ƙaunar ta dake sake ninkuwa kullum cikin zuciyar sa, shi kaɗai yasan halin da ya shiga a wannan kwanciya ciwon da yayi na kusan shekara ɗaya. DEENAH jin abinda take duka tamkar a mafarki, ta rasa da wasu irin kalamai zata kwatanta yadda takeji cikin zuciyar ta, she can't believe it, ta rasa ya akayi hakan ya kasance a raye bayan kowa ya shaida mutuwar sa, jana'izar sa dama kuma binnewar sa, ya kuma za'ayi ya dawo, sai anan ne kuma tunanin abinda YAZEED ke son faɗa mata lokacin da mahaifiyar sa tayi masa aika-aika ya shiga dawo mata kwanƴa, da alama sunan ZEEYAD yakeson kama mata a lokacin sai dai aka katse sa, kenan ya san wani abu ne dangane da hakan komiye?. Ɗagowa tayi tana kallon sa, ɗan ɗagyal tayi tana manna masa long kiss a goshi kafin tace "I miss you" hawaye na biyo mata ƙunci. Shi dai kawai da kallo yake bin ta yanajin wani irin ɗaci a zuciyar sa da maƙoshin sa, bakomai ke sanƴa shi jin hakan ba sai tsanar Hafeezah dama kuma wadanda take aiki tare dasu. Cire masa bargon jikin sa tayi tana ajiyewa a gefe, kafin ta shiga rage masa kayan jikin sa, Bathroom ta nufa ta haɗa masa ruwan wanka mai zafi yadda zaiji daɗin wankan. Fitowa tayi da towel riƙe a hannun ta kafin ta nufe sa tana miƙa masa, amsa yayi daga hannun ta yana bin ta da kallo duk inda tayi, ji yake tamkar ya fashe da kuka sabida irin baƙin cikin da yake ciki, he can't believe kusan 1year baya tare da Family ɗinsa all because of Hafeezah da son zuciyar ta, sadda kai ƙasa yayi yana cize la6an sa sosai da sosai zuciyar sa ke wani irin bombing shi kaɗai yasan abinda yakeji dama kuma Iriyar abinda zaiyi mata. Muryar DEENAH da ya tsinkayo tana yi masa magana tunɗazu ne ya sanƴa shi ɗago da kansa a hankali kafin ya tashi ya nufi bakin bathroom ɗin inda take tsaye. Saurin tura shi ciki tayi lokacin da tajiyo muryar JALILAH a bakin ƙofa tana rufo shi cikin bathroom ɗin. Juyowa tayi ga JALILAH da ta shigo tana sakin mata murmushin yaƙe. Murmushi JALILAH tayi mata kafin tace "Grandma tace na dubo ki na taya ki haɗa kayan taga kin daɗe ne." Murmushi DEENAH tayi kafin tace "A'a ki barshi nima zan ƙarasar, amma ga Abyad nan ki tafi dashi nima yanzun nan zan fito" ta faɗa tana ɗaukar little ZEEYAD. Amsar sa JALILAH tayi cikin murmushi tace "Are you sure you don't need a hand?." Kai ta girgiza mata tace "Yeah, yanzun nan zan ƙarasar nazo ni." Juyawa tayi zata tafi idanun ta suka faɗa kan tsohon bargo da kayan da ZEEYAD ya dawo dasu a ajiye, kallon DEENAH tayi nan tayi mata murmushi tace "Inaga tsoffin kayan Abyad ne." Murmushi JALILAH tayi kawai tana ficewa daga ɗakin. Da sauri DEENAH ta sanƴa masa key kafin ta koma bathroom ɗin, tsaye ta ganshi dafe da sink ɗin ƙaton mirror ɗin bathroom ɗin ƙugun sa ɗaure da towel. Motsin shigowar ta ne ya sanƴa shi ɗagowa yana kallon ta, murmushi ta sakar masa kafin kuma tayi inda su cream da sabulan wanka ke jere tana lodo su ta zuba gaban mirror ɗin. Stool taja masa ya zauna kafin ta buɗe drawer ta ɗauko scissors, clipper da dai dangin kayan aski da gyara suma tana zuba su gaban mirror ɗin. Kallon sa take kamar yadda yake kallon ta, ba tare da tace dashi komai ba ta tattari dogon gashin kansa tare da sanƴa scissors ta shiga yanke shi, she can't believe cikin shekara ɗaya ya tara uban gashin da ya zarce nata. Shaving cream ta mulka masa a fuska, sai da ta gama yi masa gyaran gashin kan nasa ya koma kamar na dah kafin kuma ta shiga gyara masa na fuskar sa, take kuma asalin kyawun sa da kamannin sa suka shiga bayyano wa. Murmushi tayi tana jinta so very emotional kamar tayi kuka takeji haka kuma wani 6angare na zuciyar ta ke cike da farin cikin da ta kasa bambamce wane iri ne. Almost hour ɗaya da rabi suka ɗauka kafin ta maida shi ainihin ZEEYAD ɗinsa, sai tada wani irin ƙamshi na musamman yake, sosai yaji wani irin iska na ratsa dukkanin ƙofofin gashin jikin sa, sai a yanzu yaji dama-dama haka kuma yaji kusan 50% na 6acin ransa ya gushe ganin yadda matar sa ta zage ta gyara shi ya dawo ainihin shi cikin ƙanƙanin lokaci. Kallon sa take ganin yadda yayi kyau sosai, sai dai idanun sa da suka faɗa dama kuma ɗan ramewa da yayi sakamakon tsawon lokaci da ya ɗauka a kwance. Sai dai ta rasa dalilin da yasa har yanzu babu fara'a kan fuskar sa dukda kuwa taga ya saki fuskar ba kamar ɗazun ba. "You should get some rest" ta faɗa tana kallon sa. "Only with you" ya bata amsa yana kallon ta. Riƙo hannun ta yayi tare da sumbata, runtse idanun sa yayi yana sauƙe wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya, sosai abubuwa dayawa ke ci masa rai, sau tari an so aga bayan sa sai dai Allah na kareshi baya nasu nasara, but wannan karon a matuƙar fusace yake fiye da tunanin mai tunani, ji yake zai iya aikata komai idan yace komai yana nufin komai dan ganin bayan masu son ganin bayan sa, wannan karon karankatakaf zai maida hankalin sa ne ga fansar da zai ɗauka, ba zai ji kunƴar idon kowa ba koh da kuwa na ɗan uwan sa YAZEED ne, an kai sa maƙura wanda yakejin ba zai iya saurarawa koh tausayawa ba, all he needs and craves for shine yaga bayan Hafeezah muddin bai ga bayan ta da na ire-iren ta ba toh tabbas hankalin sa ba zai ta6a kwanciya ba, ba zai ta6a samun nutsuwa cikin zuciyar sa ba. Cikin tsananin fushin da yake yayi magana wanda har muryar sa bata iya 6oye hakan ba yace "The Baby..." Kallon sa DEENAH tayi kafin tace "He is... our Baby." Ɗago da jajayen idanun sa yayi yana zuba su cikin nata "Our Baby?" ya faɗa 6acin ransa na gushewa. Kai ta jinjina masa tana sadda kai ƙasa. Ɗago da ha6ar ta yayi yana kallon ta kafin kuma yace "Kin raini cikin babyn mu all on your own?" ya faɗa kamar wanda zaiyi kuka ransa na daɗa 6aci kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Am sorry i wasn't there with you." "But it's not your fault" ta faɗa tana kallon sa da idanun ta dake tara hawaye. Cize baki yayi tare da jinjina kai, sosai yake baƙin ciki baƙin cikin yadda Hafeezah tayi nasarar nesanta shi da family ɗinsa, DEENAHr sa dama kuma baƙin cikin rashin kasancewar sa lokacin da ta sami ciki ta raine shi ita kaɗai har ta haife shi, kenan dah ace Hafeezah tayi nasarar kashe sa then DEENAH will remain a single Mom har izuwa tsawon lokacin da zata sake samun wani wanda zai maye gurbin sa sannan ɗansa zai taso ba tare da soyayyar uba koh ganin mahaifin sa ba, ji yayi ransa ya sake 6aci fiye da dah, wuri ya samu ya zauna bakin bed ɗin, shi kaɗai yasan abinda yakeji cikin zuciyar sa, bayida wani buri da ya wuce na ganin bayan Hafeezah. Dunƙule hannayen sa yayi yana runtse idanun sa da suka canza launi. Zama DEENAH tayi akan sofa tana yin matashi da laps ɗinsa kafin ta shiga faɗin "Ranar da suka cemin ka mutu Allah ne kaɗai yasan irin halin da na tsinci kaina, i was shattered and alone, ban ta6a yarda da cewa ka mutu ba amma babu wanda ya saurare ni they all believed cewa ka mutu sannan ba zaka ta6a dawowa ba, it was the next day after your false death aka gano ina da cikin 2weeks, nayi kukan da ban ta6a yin irin sa ba a wannan ranar sabida ni kaɗai ce zan raini yaron mu sannan zai taso a maraya babu uba, but luckily for me Grandma was always there for me na ganin ta kwantar min da hankali tare da bani baki, a haka na raini ciki na cikin kariyar Ubangiji sabida irin hare-haren da akayi ta kawo masa, a haka na raine shi har izuwa ranar da na haife shi sai sannan ne na yarda da cewa ka tafi dagaske sannan ba zaka ta6a dawowa garemu ba, nayi kewar ka fiye da tunanin mai tunani, babu ranar da bana zubar da hawaye tare da yi maka addu'a, Hafeezah tayi dukkanin iya bakin ƙoƙarin ta na ganin taga baya na da abin dake ciki na sai dai hakan ya gagara hakan ya sanƴa ta ɗaukar ƙarar tsana ta ɗaura min..." shiru tayi sakamakon kukan da yaci ƙarfin ta nan ta shiga rera shi. Zamewa yayi ya sauƙo kafin ya rungume ta a jikin sa tare da lumshe idanun sa, wani irin abu mai ɗaci ya haɗiya yana cigaba da patting bayan ta. "Am here now, insha Allah komai yazo ƙarshe, no harm will come to you or our Baby, i promise you this" ya ƙarashe yana buɗe jajayen idanun shi. Cikin kuka DEENAH tace "Hafeezah is in jail right now, she... she tried to kill me but..." shiru tayi ta kasa iddawa sakamakon kukan da yazo mata. "Tell me" ya faɗa yana cigaba da shafa bayan ta. Labarin dukkanin abubuwan da ya faru ta basa ba tare da ta rage komai ba. Iska mai ƙarfi yaja tare da furzar wa tamkar wanda yaci abu mai yaji sosai, sosai idanun sa suka sake kaɗawa tsabar 6acin ran da yake ciki jikin sa har rawa ya shiga yi yayin da jijiyoyin jikin sa suka mimmiƙe ruɗu-ruɗu kamar ka zaro su daga jikin nasa. Dukda baiyi magana ba ita kanta DEENAH ta tsorata da yanayin sa, miƙewa yayi itama tana miƙewa da sauri, safa da marwa ya kama yi cikin ɗakin hakan ya sanƴa DEENAH riƙo shi tana faɗin "Kabi komai a hankali Abyad." Furzar da hannun ta yayi daga riƙon da tayi masa ɗin har tana kamar zata faɗi. "Abyad" ta kira shi, hanƴar ficewa yayi daga ɗakin a fusace tana mara masa baya ta riƙo ƙofar tana faɗin "Ina zakaje, you can't go out like this." "Get out of my way..." ya faɗa cikin huci. "Ina kake tunanin zakaje, atleast you should get some rest first?." "Rest, you want me to get some rest DEENAH?." Shiru tayi kawai tana kallon sa. "Out, out of my way" ya sake faɗa yana tsare ta da jajayen idanun sa. "Abyad ka..." "Out of my way?" ya katse ta cikin tsawa. Sosai ta tsorata har batasan sadda ta basa hanƴa ba, buɗe ƙofar yayi ya fice a fusace kafin tayi saurin mara masa baya. Sosai yake tafiya tamkar zai tashi sama, kallo ɗaya zakayi masa ka gano tsantsar 6acin ran dake cikin zuciyar sa. DEENAH haɗa tafiyar tata take da ɗan gudu dan kuwa ta kasa taddo shi, duk inda suka ratsa kuwa sai dai ayi ta basu hanƴa wasu na ihun fatalwa yayin da wasu kuwa na kare kawai suke arta wa ƙafar su. A haka suka ƙarasa cikin fadar sam bai jira an buɗe masa ƙofar shiga ba ya bangaje ta ya shige, sosai idanun sa suka rufe baya tunanin zai kyale duk wani rashin ɗa'a da akayiwa matar sa, duk sai kowa ya girbi abinda ya shuka ɗaya bayan ɗaya. Duka ƴan fadar miƙewa sukayi cike da mugun kiɗima suke bin ZEEYAD da kallo tayaya mutumin da suka binne sa suka rufe masa fuska da ƙasa zai faɗo musu cikin fada tamkar wanda aka koro shi. Kai tsaye kan Ayaan dake zaune daga gefe yayi kamar yasan zai same shi anan ɗin kuwa, baiyi wata-wata ba ya cakumo kwalar rigar sa kafin kuma ya shiga basa kyawawan mari ba tare da yama damu da rashin hannu ɗaya da bayida shi ba, sosai yake laftawa Ayaan marin da yake sanƴasa wuntsilawa har yake ji da ganin sa suke ɗaukewa na wucin gadi kafin ya farfaɗo kuwa ya sake jin sauƙar wata marin, ɗaga sa ZEEYAD yayi yana basa wasu irin kyawawan blow a fuska yana haɗa shi da bango, ihu kawai Ayaan keyi gashi babu wani wanda yayi kuskuren takowa inda yake bale yasa ran za'a cece shi daga hannun mai bugun nashi dan kuwa koh fuskar sa bai samu ya gani ba, sosai yayiwa Ayaan jina-jina har kamannin sa sai da suka sauya ya koma mummuna dashi fuskar nan tasa tayi luhu-luhu yawa kwa6a66en flour ɗinda yaji yeast, sosai ZEEYAD ya haɗa masa jini da majina a fuska, haƙoran sa da suka zube kuwa sun kai huɗu tsabar bugun da yasha, dukda irin wannan bugun ZEEYAD bai ji ya sami nutsuwa a ransa ba, inda ake rataye takobi ya nufa yana zaro guda ɗaya tare da nufar kan Ayaan ɗin da ya kasa motsa koh da ƴar yatsar sa ne, ɗaga takobin yayi yana shirin sara masa DEENAH tazo da gudu tana riƙe hannun sa ta baya, cikin kuka take faɗin "Control yourself Abyad, zaka kashe shi fah." Sai a sannan ya dawo hayyacin sa yana sauƙe takobin, rungume sa tayi ganin yadda jikin sa ke rawa cike da 6acin rai tana kuka. Yasar da takobin yayi shima yana rufa mata hannayen sa, a hankali yake faɗin "Are you satisfied now?." Kai kawai take jinjina masa tana cigaba da shessheƙa, kiss ya manna mata a kai cike da ƙaunar ta yana shafa kan nata. Sun jima a hakan sosai basu ma lura da mutanen dake tare a wurin kowa na kallon su cike da mamaki ba. "Boy?" Grandma ta kira sa. Buɗe jajayen idanun sa yayi lokacin da yaji sauƙar muryar Granny ɗinsa cikin kunnuwan sa. Zame jikin sa yayi daga na DEENAH yana juyowa ya kalleta, sosai ta sake waro idanun ta tana dafe ƙirji cike da kiɗima dan kuwa da aka kai mata gulmar da ya gama maye gari sam bata yarda ba, sai yanzu da idanuwan ta suka sauƙa akansa. DEENAH ce tayi saurin faɗin "Ba na faɗamuku ba, nacemuku Abyad bai mutu ba amma babu wanda ya yarda dani, and here he is now, kowa ya ganewa idanun sa sannan kuma nasan zaku daina ɗaukata matsayin zautacciya yanzu." "Grandma" ya faɗa yana iyowa kanta. A ɗan tsorace taja da baya still idanun ta akansa. Kamar wanda zaiyi kuka ya miƙa mata hannayen sa, sai da ta tsaya tana sake ƙare masa kallo kafin kuma ta shiga takowa gareshi, hannayen nasa ta fara ta6awa cikin tsoro. Waro idanu tayi ganin dai dagaske ba fatalwa ta ta6a ba, ɗago da idanun ta tayi tana kallon sa ta sake kiran sa "Boy." "Grandma" ya faɗa yana rungume ta. Kuka Grandma ta fashe dashi tana faɗin "Allah mai iko kenan" sake ɗagosa tayi tana tatta6a jikin sa kafin ta sake rungume shi tana faɗin "Ba Fatalwa bane ba, Boy ɗina ne Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah abin godiya, tabbas duk wanda bai yarda da akwai Allah ba ya ta6e duniya da lahira, ikon Allah ya wuce gaban tunanin ɗan Adam, babu abinda Allah baya iyayi, lallai Allah ba azzalumin bayin sa bane, duk kuwa wanda yace zaija da ikon Allah ya shiga uku." "How is this possible" cewar wani daga cikin mutanen da suke wurin. "The prince is dead, we all witnessed him being buried, how comes kuma za'a ce shine wannan, bayan koh lokacin dah bamu ta6a jin inda akayi mutuwa kuma aka dawo ba." "Yeah ofcourse he isn't dead" cewar Sadeeq dake tsaye a wurin tunɗazu. Duk juyowa sukayi suna kallon sa, ɗaya ne yace "How sure are you about this?." "Sabida mune wadanda muka tono shi bayan an binne shi, bayan na gano cewa bai mutu ba he is alive." Grandma ce ta ƙaraso gun Sadeeq tana kallon sa kafin kuma ta ɗau hannu tana wanke fuskar sa da mari tace "You know this since but you decide to keep the truth away from us, bayan kafi kowa sanin halin da DEENAH ta shiga bama ita kaɗai ba da mai Martaba ma kanshi, amma koh da wasa baka ta6a furta mana wani abu akan sa ba." Sadda kai ƙasa YAZEED yayi yace "Am sorry Grandma..." "Don't be sorry, am just mad at you sabida 6oye mana hakan da kayi amma yanzu na gano amfanin hakan ma sannan kayi abinda ya dace, come on give me a warm hug ɗan albarka." Murmushi Sadeeq ɗin yayi yana rungume Grandma ɗin, Albarka ta sanƴa masa kafin ta ɗago tana kallon sa tace "Ya jikin YAZEED, har yanzu mai Martaba na chan wurin nasa ne?." Kai ya jinjina mata kafin yace "Shima his health is improving." Murmushi tayi cike da farin cikin jin hakan kafin ta kalli ZEEYAD dake riƙe da DEENAH tace "Yakamata a sanarwa da mahaifin ka wannan kyakkyawar labarin sabida ya samu hankalin sa ya kwanta, tunda YAZEED ya faɗa rashin lafiya da sakamakon mummunar abinda Hafeezah ta aikata ya kasa samun sukuni sabida gani yake zai rasa shi shima kamar yadda ya rasa ka, dama ance bayan wuya sai daɗi Allah ne kaɗai yasan dalilin shi na jarabtar wannan ahali ta wannan hanƴa gashi nan kuma mun fara ganin sakamako mai kyau. Shiyasa akace dukkanin wani tsanani da zaka tsinci kanka a ciki kada ka kuskura ka cire rai daga samun rahamar Ubangiji haka kuma kada ka gajiyawa da yawan addu'a, Allah na jarabtar bayin sa ne ta hanƴoƴi da dama sannan ba wai dan baya ƙaunar mu bane yake jarabtar mu hasalima yafi jarabtar bayin sa da yafi so, dan haka mu sake godewa Allah da wannan jarabawar da yayi mana domin kuwa gashi nan mun fara cin moriyar ta dukda kuwa ance wata hisabin sai a lahira, Allah ne kaɗai zaiyi mana maganin azzaluman cikin mu." Kallon wata kuyanga tayi tace "Ke Marwa, kije ku ɗaura girki mai rai da lafiya wanda zai ishi kowa dake cikin MASARAUTAR nan ayi sadaka, abinci zaku dafa irin ta ƴan gayu sannan a fitar a rabawa mabarata da almajirai sannan akai masallatai kowa da kowa ya samu." Cike da girmamawa wacce tayi wa maganar ta amsa. "Kai kuma Najeeb kaje ka bada sanarwa wata sati a ranar ita yau akwai gagarumar Walima da za'a gabatar a cikin MASARAUTA sannan ana gayyatar kowa da kowa ya hallara, za'ayi walimar da ba'a ta6a yin irin sa ba a wannan MASARAUTA." Cike da jindaɗi da girmamawa shima ya amsa yana ficewa, mutane ne suka fara yiwa ZEEYAD jaje dama kuma murna kafin kuma kowa ya shiga watsewa. Kallon Sadeeq ZEEYAD yayi yanajin ƙaunar aminin nasa sosai cikin zuciyar sa, ya wuce matsayin amini sai dai ɗan uwansa, murmushi Sadeeq ya sakar masa yana ƙarasowa gaban sa, rungume juna sukayi cike da farin ciki. "Grandma ce tace, ya isa haka nan maza kuzo mu garzaya muje asibitin mai kuma muke jira?" ta faɗa cike da farin ciki da zumuɗin da take ciki. Idanun ta ne suka sauƙa kan Ayaan dake ta maida numfashin wahala da kyar nan tace "Waye wannan ɗin?" lura da tayi da hannun sa ne ya sanƴa ta faɗin "Ayaan, hatsari yayi ne haka komiye?." Ganin babu wanda ya bata amsa ne ya sanƴa ta faɗin "Toh ai shikenan, kai kuzo ku ɗauke sa ku kai shi wata asibiti dan mu sauri muke da mun taimaka masa, nama yi maka hakan ne sabida tausayi da ka ɗan bani." Tana faɗin haka ta kaɗa kawunan su sukayi gaba. Riƙo hannun ZEEYAD DEENAH tayi cikin nata, murmushi ya sakar mata itama tana maida masa martani. ********************* ________"Da kinsan abin dake faruwa cikin MASARAUTA da kin bar maganar cewa kin gama da ZEEYAD saura DEENAH da ɗanta." "Mai kike nufi?." Dariya Sairah tayi tana faɗin "ZEEYAD bai mutu ba yana nan da ransa..." Katse ta tayi da faɗin "Maganar banza maganar wofi..." "Kina nufin kice ƙarya nakeyi miki ne kokuwa?, ZEEYAD na nan da ransa bai mutu ba..." "Maganar banza kike faɗi, Boka ya tabbatar min da cewa ya mutu sabida aljanin da ya tura masa Ƙaƙƙarfa ne dan kuwa da zaran ya shige jikin mutum koh shurawa baya sakeyi, sannan da idanun mu aka fitar da gawan sa akaje aka binne sa." Murmushi tayi tace "Toh bara kiji ZEEYAD bai mutu ba, aikin bokan ki baiyi tasiri akansa ba, koh da aka binne shi wannan likitan abokin nasa dashi da YAZEED ne sukaje suka tono sa sabida sun san yana raye sannan suka 6oye sa a inda babu wanda ya sani tsawon wannan lokacin har izuwa yanzu da ya warke yake neman fansa ido rufe, inama jiye miki tsoron idan Ayaan bai mutu ba zuwa yanzu." Zaburowa tayi tana waro manƴan idanun ta, gumi ne ke ƙeto mata yawa wacce ake yayyafa mata ruwa, cikin tashin hankali tace "Ayaan ɗana, mai yayi masa, a'ina Ayaan ɗin yake yanzu?." Ta6e baki tayi tace "Rai a hannun Allah aka kaishi asibiti, waya sani ma koh ya mutu a hanƴa." "Kada ki nemi ya6a min maganar banza mana, ina Rahinah fah?." "Hmm, Rahinah ai tuni ta zame hannun ta dan kuwa kinsan matsoraciya ce, nice keta ƙoƙarin ganin naga bayan DEENAH da abinda ta haifa amma hakan yaci tura, yanzu kuma da ZEEYAD ya dawo na tabbata kashin ki ya bushe sabida ni koh sake ganin fuskata ba zakiyi ba daga yau, dama nazo ne na sanar miki da abin dake faruwa kuma dama cin arziki ya kawoni kuma na tara iya rabo na, ina fah godiya da bani access akan dukkanin wasu dukiyoyin ki, ni yanzu kinga tafiya zanyi koh bakomai kwalliya ta biya kuɗin sabulu." Kamar zata 6alla ƙofar cell ɗin take faɗin "Mai kikayi min da dukiya Sairah?." Murmushi tayi cike da mugunta kafin tace "Ai yanzu duk wasu dukiyar ki na hannu na, kama daga kan gwalagwalan ki, azurfa, zinare, diamond kuɗaɗe da dai sauran su dan haka ni nayi gaba ba sai na tsaya ganin irin hukuncin da za'a yi miki ba, kinga koh dukan da Sooraj yayi mana ya isa hukunci a gareni, dan haka ni yanzu tafiya zanyi banida wani sauran lokaci, a mutu lafiya Hafeezah" tana faɗin haka ta juya tana yi mata waving da yatsu. Cike da tashin hankali Hafeezah ke jijjiga ƙofar kurkukun tana kiran sunan Sairah amma koh amsa ta bata yi ba. Sosai ta shiga tsananin tashin hankalin da bata ta6a tsintsar kanta a ciki ba, ji take kamar ta 6ace har abada kada ta sake dawowa MASARAUTAR. *********************** ______Koh da isar su asibiti kai tsaye ɗakin da mai Martaba yake suka nufa, Grandma ce ta fara shiga sai DEENAH sai kuma Sadeeq dake biye dasu. Fargawa mai Martaba yayi dasu, murmushi ya saki ganin DEENAH nan yace "A'ina kuma aka baro min yaron nawa?." Murmushi DEENAH tayi tana sadda kai ƙasa tace "Yana gida tare da JALILAH." Kai ya jinjina kafin ya gaida Grandma cikin Girmamawa, amsa masa tayi tana sake yi masa ya jiki. Duba shi Sadeeq yayi kafin yace "Insha Allah damuwar ka tazo ƙarshe." Kallon sa mai Martaba yayi yace "Insha Allah, ai na faɗamaka da izinin Allah YAZEED zai rayu." Murmushi Sadeeq yayi yace "Am sure abin da zaka gani yanzu sai ya zama silar warkewar ka." Shi dai mai Martaba murmushi yayi kawai. Zama Sadeeq yayi kafin yace "Da akwai abubuwa dayawa da suka faru wanda bakada masaniya akai, daga ni sai Abhi ɗina sai kuma Sadeeq ne muka san da wannan abu sai Ubangijin da baya koh da gyangyaɗi ne bale bacci." "Mai kake son faɗamin?" cewar mai Martaba. Gyara zama Sadeeq yayi kafin ya shiga koro masa bayanin dukkanin abinda ya faru. Sosai mai Martaba ya cika da mamaki, bai gama mamakin nasa ba ZEEYAD ya shigo ɗakin. Miƙewa yayi daga zaunen da yake ya shiga nuna shi da yatsa, murmushi ZEEYAD yayi tare da kiran sa "Abhi." "He is real" cewar Sadeeq. Kallon Grandma da DEENAH yayi kafin ya sake maida duban sa kan ZEEYAD ɗin. Rungume sa ZEEYAD yayi sosai yanajin ƙaunar mahaifin nasa na ratsa cikin dukkanin zuciyar sa. Sosai mai Martaba yayi mamaki dama kuma farin cikin dawowar ɗan nasa. Ɗago shi yayi yana kallon shi yace "I can't believe this" yana sake rungume shi tsam. Sun jima rungume da juna kafin su ɗago, sharewa mahaifin nasa hawaye yayi tare da faɗin "Cry no more Abhi." Grandma ce tace "Yakamata dai yanzu ace munje mun sami YAZEED ma shima mu duba ya jikin shi." Duk dugunzuma sukayi izuwa ɗakin da YAZEED ke kwance. Na'urori jojjone a jikin shi, ZEEYAD ne ya ƙarasa bakin bed ɗin yana kallon ɗan uwan nasa cike da tausayin sa yana riƙo hannun sa, yaso yayi sacrificing rayuwar sa na ganin ya ceci DEENAH da abin dake cikin ta, baisan iya adadin ƙaunar da yake yiwa ɗan uwan nasa ba. Sosai yake tausayin sa na iriyar mahaifiyar da Allah ya jarabce shi dashi, baisan ya ƙarshen Hafeezah zai kasance ba. Hannun YAZEED dake cikin nasa ne ya fara motsi nan yayi saurin maida duban sa yana sauƙe idanun sa cikin na YAZEED ɗin da ya ɗan buɗe yana kallon sa. ZEEYAD baisan sadda ya saki murmushi ba yana kiran sunan YAZEED ɗin "He is awake" ya faɗa nan duk suma suka ƙaraso bakin bed ɗin suna kallon sa. "You're alive?" cewar YAZEED yana kallon ZEEYAD ɗin. Murmushi kawai ZEEYAD yayi yana sake damƙe hannun sa cikin nashi. Da ido ya bisu farin ciki na cika zuciyar sa na ganin family ɗinsa akansa, murmushin da yakeyi ne ya ɗan gushe yace "Where is my wife?." Murmushi DEENAH tayi tace "At home nursing our Baby" ta faɗa tana dafa kafaɗun ZEEYAD. Kallo YAZEED ya ƙare mata kafin yace "Yaushe kika haihu, i mean jiya-jiyan nan na ganki da ciki, how then..." Sadeeq ne yace "Banza, you've spent almost 6months a kwance anan." Ɗago da kai yayi yana ɗan waro idanu yace "6 months?." "And our baby is almost 2months now." Kallon ZEEYAD yayi yace "Yaushe ka dawo?." "Just a while ago" ya bashi amsa. Maida kanshi yayi yace "Nayi shiru." Duk dariya sukayi, nan Sadeeq ya sake duba lafiyar jikin sa, sun yini sosai a asibitin suna ɗebe wa YAZEED ɗin kewa. *********************** *BAYAN KWANA UKU* _______Sosai farin ciki kwanciyar hankali ya wanzu cikin wannan ahali a ƴan kwanaki ukun nan, sake ɗaura auren DEENAH da ZEEYAD akayi dan kuwa ana zaton wancan na farkon ya warware sakamakon nesa da yayi da ita na tsawon lokaci har ma tayi masa takaba *(Allahu A'alamu)*. Kwance tayi kan faffaɗar ƙirjin sa, sosai suka luma cikin duniyar masoyan da sukayi kewar junan su na tsawon lokaci. Kukan little YAZEED ne ya katse musu abinda sukeyi, nan ZEEYAD ya tsuke fuskar sa tamkar zaiyi kuka. Dariyar ta DEENAH ta danne tana miƙewa zaune ta ɗauki yaron ta shiga jijjiga shi. Kallon ZEEYAD tayi kafin tace "Maybe bayason ka dinga zuwa kusa dani ne shiyasa yake kuka." Cikin marairaicewa yace "Ki kai shi gun Grandma ya kwana achan please." Waro idanu DEENAH tayi kafin tace "Wannan ɗan mitsitsilin abun zan kai gun Grandma ya kwana?, he is just 2months." Sosa ƙeya yayi yana kallon ta, nan tace "Alright then, idan yayi bacci yanzu sai ka ɗauke sa ka kai sa." "Why me?." "Daga nan sai ka yiwa Grandma bayanin abinda yasa ka kaishi ya kwana a gun ta." Murmushi yayi yana miƙewa zaune yana ganin yadda DEENAH ke yiwa yaron wasa, peck ta bashi a lips tana goga hancin ta da nashi. "Why will you kiss him?" cewar ZEEYAD yana kallon ta. Kallon sa tayi ganin yadda ya haɗe girar sama da ta ƙasa, ɗan dariya tayi tace "Are you jealous of your own Son?, i didn't even kissed him it was just a peck." Shiru yayi yana hura hanci, rolling idanu tayi kafin ta miƙe ta koma closet room, da kallo ZEEYAD ya bita yana murmushi dan kuwa kullum haka take idan zata shayar da yaron sai ta tashi a wurin ita a dole kunƴar shi takeji. Fitowa tayi lokacin har yaron yayi bacci, shimfiɗe shi tayi cikin gadon sa kafin ta kalli ZEEYAD tace "Abyad kayi masa addu'a please" ta faɗa tana nufar bathroom. Da kallo ya bita kafin ya nufi gun bed ɗin yaron yana kallon shi, murmushi yayi ganin how cute he is, addu'a ya tofe shi dashi yana ɗan rufa masa bargon jarirai. Fitowa DEENAH tayi kafin ta canzo kayan ta zuwa na bacci, gaban mirror ta nufa ta shafe jikin ta da turaren jiki masu daɗin ƙamshi kafin ta dawo kan bed ɗin ta kwanta. Kallon ZEEYAD dake kallon ta tayi tare da lumshe idanu tana faɗin "ka kashe mana wutar Abyad." Tashi yayi yaje ya kashe wutar ya dawo yana jawo ta jikin sa. Shiru duk sukayi kafin kuma ya kira ta "Baby?." Amsa masa tayi nan yace "Let's do it again." "Do what?" ta faɗa cikin ɗan waro idanu. "Please baby" ya faɗa cikin marairaice murya. Turo baki DEENAH tayi kafin tace "Abyad is just 2months what if ka sake yimin wani cikin fah?." Murmushi yayi jin yadda tayi maganar, nan yace "No i won't." "Nidai wallahi kawai so kake kayimin wayo" ta faɗa kamar zatayi kuka. "Baby please." "Ai bakasan zafin haihuwar bane shiyasa kake faɗan haka." "But that isn't a big deal." "Haihuwar?." Hancin sa ya manna kan gashin ta yace "Yeah." Shiru tayi masa tana turo baki gaba. "Baby please" ya sake faɗa kamar wanda zaiyi kuka. Juyowa tayi tana fuskantar sa har numfashin su na gauruwa tace "But be easy on me please." Murmushi yayi cike da farin ciki yace "I will Babe." Labari ne ya shiga canzawa tsakanin su, nan naja yam legs ɗina na baro musu ɗakin bayan na yiwa little ZEEYAD good night tare da gargaɗin sa kada ya farka daga baccin da yake ɗin. ******************** ______Zaune duk suke a dining ɗin mai Martaba suna breakfast wanda DEENAH da JALILAH ne suka girka shi na musamman harda YAZEED ɗin da yaƙi zaman asibitin a cewar sa yafison ya gansa cikin family ɗinsa, hatta Nazeerah ba'a barta a baya ba. Fuskar kowa ka gani a cikin su ɗauke yake da farin cikin da baki ba zai iya misalta shi ba. Duk motsin da DEENAH tayi idanun ZEEYAD na yawo akanta, tamkar ya ɗauke ta ya cinƴe koh irin abin da yakeji game da ita zai ragu haka yakeji. Serving abincin suka gama yiwa kowa kafin duk su sami wuri su zauna. Riƙo hannun ta ZEEYAD yayi cikin nashi nan tayi saurin janƴewa tana ƙirƙiro murmushin yaƙe. Sake kai hannu yayi yana riƙo ta gam, ɗan satar kallon sa tayi taga ma hankalin sa baya kanta, ita tsoron ta a gaban mai Martaba suke ga kuma Grandma da sauran mutane idan wani ya gansu fah. Take ƴan yatsun ƙafar sa tayi da ƙarfi, nan ya cika ta yana faɗin "Ouch." Duk kallon sa sukayi nan ya ƙirƙiro murmushin yaƙe yace "Abincin ne da zafi." Kujerar sa yaja daf kusa da DEENAH, yana sanƴa hannayen sa round her waist. Cire hannun nasa tayi tana buge hannun. Ganin yadda suke ta mutsu-mutsu ne ya sanƴa Grandma cewar "DEENAH, i need more sausages please." Da sauri DEENAH ta miƙe tace "Yeah sure, bari na ƙaro miki" ta faɗa tana yin hanƴar kitchen ɗin. Kallon abincin gaban sa da bai fara ci ba yayi yace "Ahm... i guess i need more salad on this" ya faɗa yana ɗaukar plate ɗin ya mara mata baya da sauri dan kar ma wani daga cikin su ya tsaida shi. Da kallo Grandma ta bisa kafin ta girgiza kanta. Tsaye ya ganta a kitchen ɗin wanda bata ma san da shigowar sa ba, tiptoeing ya fara kamar wani 6arawo dan kar ma tasan ya biyo ta. DEENAH ƙamshin turaren sa da taji ne ya tabbatar mata da cewar ya biyo ta ne, kafin tayi wani yunƙuri kuwa sai ji tayi ya rungumo ta ta baya yana saƙala kansa ta wuyar ta. Serving spoon ɗin hannun ta ya kar6a ya ajiye kafin ya juyo da ita yana kallon ta, sunkuyar da kansa yayi kafin ya shiga bata wani irin cool kiss a lips. Dukan bayan sa DEENAH ta shiga yi tana son kwacewa amma yaƙi sake ta, tsoron ta kada wani yazo ya same su a haka tasan ita zai tarawa abin kunƴa shi kuma koh a kwalar rigar sa. Gajiya tayi da dukan bayan nasa ganin yaƙi ɗagowa, sai da ya gama sanƴaƴa mata jiki kafin ya ɗago yana kallon ta, gira ɗaya ya ɗaga mata yana yi mata murmushi. Tsuke baki tayi tana barin wurin ta shiga haɗa Sausage ɗin da Grandma tace ta kawo mata akan plate. Bin ta yayi yana sake riƙo ta, "Abyad please, what if aka ga mun daɗe fah?." Ɗan ta6e baki yayi yace "Sai nace musu i was just romancing you." Kai ta girgiza tana zuba sausage ɗin akan plate, sake riƙo ta yayi yana bata wani kiss ɗin, da kyar ta iya kwacewa cikin sanƴin jiki tana ture shi gefe. Saita nutsuwar ta tayi kafin ta ɗau plate ɗin tayi saurin ficewa. Da kallo yabi ta yana cize lips ɗinsa, huci ya fesar kafin ya ɗau plate ɗin abincin sa yana mara mata baya, sam bai ƙi su dauwama har abada a wannan yanayin ba. Fuska ba walwala yazo ya zauna, kallon sa Grandma tayi kafin tace "And where is the salad?." Kame-kame ya fara yana kallon abincin gaban nasa, nan Grandma tace "Ba ga Salad ɗin a gaban ka kuma kaje kitchen neman sa." Haɗa ido yayi da YAZEED dake yi masa kallon tuhuma nan ya saki murmushi yana buɗe silver bowl ɗin salad ɗin, dukda kuwa akwai akan abin nasa haka nan ya sake loda wani, DEENAH kuwa dariya take ƙasa-ƙasa ganin yadda yake loda salad ɗin. "Ya isa haka nan mana kodai kai kaɗai ne zaka cinƴe duka?" cewar Grandma. "Ohh" ya faɗa yana rage ta a ciki kafin ya maida bowl ɗin ya rufe. Tusa abincin kawai yake amma ba wai dan yanajin ƴunwar sosai bane ba. Hayaniya da ifface-ifface suka fara jiyowa daga bakin ƙofa nan duk suka saurara kan kace miye kuma ta bangajo ƙofar ta shigo. Duk miƙewa tsaye sukayi, cike da mugun 6acin rai sarki yace "Wane mai ganganci da aikin sa ne ya bar wannan matar ta shigo min cikin fada?." Da gudu guards ɗin suka ƙaraso suna rissinawa, ɗaya ne yace "Ka gafarce mu ranka ya daɗe, ba a son ranmu ta shigo ba." Kallon Hafeezah dake tsaye ta saki baki da hanci tana kallon ZEEYAD da YAZEED yayi kafin cikin 6acin rai yace "Mai ya kawo ki nan, get her out of my sight." Kai ta shiga girgizawa idanun ta akan ZEEYAD take faɗin "No... no... how could this be, how could you be alive... i killed you... na kashe ka baikamata ace kana raye ba bayan na tabbatar da cewa ka mutu, you can't be alive" ta faɗa cike da tashin hankali tana kallon sa idanun ta kamar zasu zubo. Duk ja kowa yayi yana kallon ta jin abinda take faɗi, kallon inda YAZEED ke tsaye da sandar dake taimaka masa wurin tafiya tayi kafin ta nufi wurin sa da sauri tana kamo fuskar sa "Oh my lovely Boy, ka gafarce ni dan Allah, ka gafarci mahaifiyar ka am glad you're still alive, thank GOD." Idanun YAZEED ne ke fidda tsantsar 6acin rai wanda kana gani kasan daga ƙasan zuciyar sa take fitowa tunda yaji abinda mahaifiyar tasa ta ambata. Kamar wacce aka tsikara kuma ta shiga waige-waige tana faɗin "Ayaan, ina Ayaan ɗina?." Bata ankara ba taji an fizgo ta tare da ɗauke ta da wani irin azababben marin da ya sanƴa ganin ta ɗaukewa na wucin gadi. Dafe ƙunci tayi tana kallon mai Martaba dake tsaye ransa tayi mummunar 6acin rai, cikin kakkausar murya yake faɗin "So you're the one Hafeezah?, kece kike bibiyar rayuwar yaron nan..." Bai ƙarasar ba ta katse shi da faɗin "Eh nice, nice nake bibiyar rayuwar sa and i won't stop at nothing har sai naga bayan shi kamar yadda naga bayan mahaifiyar sa daga shi har matar sa da abinda ta haifa..." shiru tayi tana waro idanun ta da sukayi jaa ganin yadda ta saki layi a zancen nata tsabar baƙin zuciya irin tata. "What?..." cewar Grandma da wani irin shock ya ziyarce ta lokaci guda bama ita kaɗai ba kowa na wannan wurin sai da ya tsinci kansa cikin wata iriyar shock da kiɗimewa wanda basu ta6a tsintar kansu ciki ba musamman ma YAZEED da yaji tamkar an raɗa masa wani irin makeken dutse akai, ZEEYAD kuwa jin sa da hankalin sa ne suka bar jikin sa na wucin gadi musamman yadda yake ganin ɗakin na mugun juya masa wani irin abu na dukan tsakar kansa, a takaice dai halin da ya tsinci kansa ciki ba zai misaltu ba. Mai Martaba ma hakan take a wurin sa koh da ƴar yatsar sa ya kasa motsawa bale ya buɗi bakin sa yace zaiyi magana, sosai yakejin kansa dama kuma harshen sa sunyi masa mugun nauyi, nauyin da ya rasa yadda zai fara kwatanta wa. A haukace ta iyo kan ZEEYAD da yayi tsaye tamkar gunki tana cakumo kwalar rigar sa take faɗin "Ka zame min ciwon ido tun kafin kazo duniya, dukkanin wani abu dake faruwa yanzu ba laifin kowa bane face na mahaifin ku wanda ya ɗauki so da ƙaunar duniya ya ɗaurawa LATEEFAT haka ma ya ɗau soyayyar sa ya ɗaura maka tun kafin kazo duniya, a kullum bashida magana da ya wuce na QUEEN MOTHER, duk wani ƙiyayya da ƙuncin rayuwar da ka tsinci kanka a ciki ya faru ne duka sanadiyyar mahaifin ka da ya fifita mata ɗaya cikin duka matan sa, wannan ne dalilin da ya sanƴa ni jin tsanar mahaifiyar ka har nake harin rayuwar ta ta mutu kowa ma ya huta, sai dai na sake wayar gari da wani mummunar labarin da ya sake hura min wutar tsanan ta dama kuma kai lokacin da naji tana ɗauke da cikin ka, nayi dukkanin iya ƙoƙari na na ganin baka zo duniyar ba dukda nima lokacin ina ɗauke da cikin amma hakan yaci tura, Yes nice nan na kashe mahaifiyar ka ta hanƴar sanƴa boka na ya ɗaura mata ciwon da koh da anyi magani ba zata warke ba sannan ba wanda zai zargi asiri ne akayi mata, yayin da kai kuma nayi dukkanin shige da ficen da zanyi na ganin na ɗaurawa mahaifin ka dama kuma dukkanin kowa dake wannan gidan tsanar ka sabida nayi-nayi ka mutu ka ƙi mutuwa hakan ya sanƴa ni ɗaukar alwashin sai na wulaƙantar da kai ka zamto koh da bayin gidan ku sun fika gata sannan nayi nasarar hakan, tafiyar ka ya sanƴa asirin da nayi karyewa har mahaifin ka ya shiga neman ka ruwa a jalo, raina ya sake 6aci ne bayan dawowar ka cikin MASARAUTA dama kuma yadda ka zamto mai kuɗin da ban ta6a tsanmani ba, nayi shige da fice dayawa akanka amma duk a banza, ina yi maka tsanar da ban ta6a yiwa wani mahaluƙi a wannan duniyar ba sannan har na mutu ba zan bar yi maka wannan ƙiyayyar ba, ya zama dole ne ka mutu daga kai har iyalan ka, dole ku mutu koh da kunƙi" ta faɗa tana jijjiga shi kamar wata zautacciya. Tunda ta fara magana ZEEYAD bai iya koh da motsa ƴar yatsar sa bane ba balle tasa ran zai tanka, sosai shock ɗin da ya shige sa yayi tasiri a jikin sa, sosai idanun sa suka kaɗa sukayi jazir yayin da zuciyar sa yakejin tana wani irin bleeding. Kukan Grandma ne ya cika wurin fizgo Hafeezah tayi kafin ta shiga bata mari "Allah ya isa tsakani na dake Hafeezah ashe kece kika kashe min ƴata, mai tayi miki mai ta tsare miki, son zuciya da hassada ya sanƴa kika kashe ta kuma kike farautar ɗan da ta haifa dama matar sa da ɗansa suma ki kashe toh insha Allah kin gama yawo a duniyar nan, ya zama dole ne ki girbi abinda kika daɗe kina shukawa, miye ribar ki yanzu, ribar mai kikaci a aikata sharri cikin rayuwar ki Hafeezah,gashi nan ke da kanki kinzo kina tonawa kanki asiri, ai dama Allah ba zai ta6a barin ki ba, mutuwa ta tabbata akanki Hafeezah, a rayuwa sharri kaɗai kika maida abinci da shan ki dama kuma suturar ki, kaicon ka YAZEED bawan Allah bakayi dacen uwa ba kaga abinda uwar ka ta janƴowa kanta, Allah ne kaɗai yasan dalilin sa na jarabtar ka da uwa kamar Hafeezah yaron kirki ɗan albarka" ta ƙarashe tana goge hawayen fuskar ta da bakin mayafin jikin ta. YAZEED komawa yayi ya zauna tare da sadda kansa dake barazanar tarwatse wa, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga yi masa zarya jin kayan kunƴar da mahaifiyar sa ta aikata, sosai yake ƙarajin tsanar ta na ninkuwa cikin zuciyar sa, da wane irin ido zai dubi ɗan uwan sa, shi kaɗai yasan mai yakeji cikin zuciyar shi, ji yake tamkar zuciyar sa zata tarwatse, wani irin ciwon kai mai tsanani ne yaji ya kama shi gashi dama yanzu yake farfaɗowa daga rashin lafiyar da yake. Saurin riƙo sa JALILAH tayi tanajin wani irin tausayin sa na ratsa dukkanin zuciyar ta, tabbas Allah ya jarabce shi, Allah ne kaɗai yasan irin halin da yake ciki sannan mai yakeji a yanzu. Runtse idanun sa dake yi masa zugi ZEEYAD yayi, maganganun Hafeezah jinsu yake tamkar ana feshe zuciyar sa da tafasasshen ruwan zafi. Mai Martaba zubewa yayi kan kujerar da yake dan kuwa idan ya cigaba da tsayuwa toh tabbas zai iya zubewa anan koh a ɗauki gawar sa ma. Guards ɗin dake tsaye ne suka zo suka tafi da Hafeezah, dukda iriyar ihun sai ta kashe ZEEYAD da iyalan sa da take tana neman kwacewa basu sake ta ba. Fadar ce ta ɗau shiru sai shessheƙar Grandma kawai akeji, DEENAH rasa nayi tayi tama rasa wurin wa zata fara zuwa tayi comforting, tsaye ita ɗinma tayi hawaye sun gama wanke mata fuska. Da kyar ZEEYAD ya iya motsa ƙafar sa yaa fara tafiya dan barin cikin fadar. Kallon sauran tayi kafin tayi saurin mara masa baya. Ja tayi ta tsaya bakin ƙofar ɗakin su durƙushe ta ganshi kan guiwowin sa bayan sa take kallo kafin ta shiga takawa a hankali dukda kuwa tsoron tunkarar tasa take. Zagayowa tayi gaban sa tana ta6a shi tare da kiran shi a hankali "Abyad?." Ɗago da jajayen idanun sa da suka ƙanƙance yayi yana zuba mata su kamar jira yake ta shigo ya rungume ta sosai yana runtse idanun sa, sosai takejin yadda zuciyar sa ke gudu da sauri-sauri kamar zata 6allo ƙirjin sa ta fito, sake ƙanƙame shi tayi a jikin ta wani irin tausayin sa na ratsa zuciyar ta, a hankali take hura masa iskan bakin ta a kunne tana patting bayan sa gently dan ganin ya sauƙo daga fushin da yake ciki. Hawayen da yayi shekaru da shekaru yana jiran fitowar su ne suka shiga yi masa zarya a fuska yana sake ƙanƙame DEENAH, sosai jikin sa ke rawa zuciyar sa na sake yi masa zafi, sun jima a haka ƙanƙame da juna har izuwa lokacin da taji gudun zuciyar tasa ta sassauta. Lumshe idanu tayi tana cigaba da rubbing bayan sa gently, ɗago da fuskar sa da tayi jaa sosai tayi tana kallon sa, haɗe bakin su tayi tana basa cool kiss kafin ta ɗago tana sake rungume shi a jikin ta, a hankali ta shiga faɗin "It's alright" tana ɗan bubbuga bayan shi. ***************************** *THE NEXT DAY........* *Yawan Comment, Yawan Typing* *MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽* [9/10, 2:30 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *FINALE🤸🏽‍♀️* *(FINAL)* *Z E E Y A D* ```[The Abandoned Prince]``` *NA* *JIDDAH BINT MUHAMMAD* *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *055* _______Kai da komowa mai Martaba keyi cikin ɗakin sa, kansa a matuƙar ƙulle yake, ya rasa ta ina zai fara 6ullowa wannan lamari na Hafeezah, babu wanda yafi tausayawa kamar YAZEED ɗan albarka, tayaya zai fara yankewa mahaifiyar da hukuncin kisa a gaban sa, sai dai kuma wani 6angaren na zuciyar sa na umartar sa da ya shashashantar da lamarin YAZEED ya yanke mata hukunci a bisa dokar Allah (SWT), ya sauƙe mata dokar MASARAUTA koh dan albarkacin YAZEED ma, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana maida duban sa kan hoton QUEEN MOTHER, ya jima yana kallon hoton nata kafin kuma ya sauƙe numfashi tare da ɗaukar sandar tafiyar sa a hankali cikin takun ƙasaita ya bar cikin ɗakin nashi. A fadar sa ya yaɗa zango inda ministocin sa ke zaune suna jiran fitowar sa, tattaunawa sukayi sosai kafin kuma duk su miƙe su nufi filin da aka ware dan yankewa masu laifi hukunci. Sosai mutane suka hallara tsofi da manƴa dama kuma ƙananun dan shaidawa idanun su irin hukuncin da za'a yankewa matar sarki Hafeezah. Inda aka ware na zaman mai Martaba ya nufa ya zauna sai dai ya gama wulla idanun sa bai hango ZEEYAD da YAZEED ba anan wurin. Bafaden dake tsaye a kansa yayi wa magana kan ya dubo masa su, cike da girmamawa ya amsa masa kafin ya bar wurin kafin wani yayi saurin replacing wurin tsayuwar sa yana ƙamewa. *************** _______Zaune YAZEED ɗin yake yayi jugum dashi, kwakwalwar sa cunkushe take da tunanika kala-kala, he can't believe wai uwar da ta haife sa za'a yankewa hukuncin kisa a gaban ɗumbin mutanen gari, sosai yakejin wani iri a ransa, baya tunanin zai iya fita zuwa wurin taron nan, dan kuwa ba zai iya shaida irin hukuncin da za'a yi mata ba, sosai zuciyar sa ke rawa tana karyewa, shi kaɗai ya san abinda yakeji. Knocking yaji daga bakin ƙofar ɗakin nasa ba tare da ya bada izinin shigowa ba JALILAH ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo, tsaye tayi tana kallon sa cike da tausayawa, ɗagowa yayi ya kalleta kafin kuma ya kauda kansa ƙasa. Idda shigowa tayi tana zama kusa dashi tare da dafa kafaɗun sa tace "Inaso ka sani cewa, Allah ya ɗaura maka wannan ƙaddarar ne ba dan bayason ka koh baya ƙaunar ka ba, koh wane bawa mai imani Allah na jarabtar sa ta fanni daban-daban dan ganin ƙarfin imanin sa, haƙiƙa kai mai imani ne hakan yasa ka iya tsallake duk wani tuggu da mahaifiyar tayi ƙoƙarin cusa maka a baya haka kuma Allah na son ka da rahama hakan ya sanƴa shaiɗan baiyi galaba akanka ka biye mata ba dukda cewa ita ɗin mahaifiya ce mai iya umarta ayi ba tare da musawa ba, Allah na sonka da rahama YAZEED kada ka ta6a manta wannan, dah ace bayason ka na tabbata da kai za'a yankewa wannan hukunci ba iya mahaifiyar ka kaɗai ba, ka godewa Allah da ya sanƴa ka zamtowa mai tsarkakakkiyar zuciya, irin ƙaddarar mahaifiyar ka kenan babu wanda ya isa ya gujewa hakan koh ya canza shi, kayi haƙuri, kayi haƙuri YAZEED ka rungumi jarabawa, ba zaka ta6a iya canza ran sarki ba akan hukuncin da zai aiwatar, koh ka manta faɗin Allah ne na cewa duk wanda ya kashe shima a kashe shi, da akwai mutane da dama da suka shuɗe da tasu jarabawar tafi taka tsarkakiya da wahala amma sunyi haƙuri sun jure gashi komai ya zamto labari su kansu sun zamto labari, inaso ka sani cewa ZEEYAD ma bayida mahaifiya amma yana da mata, Kaka, mahaifi dama kuma ɗa, kaima kuma hakan take a wurin ka, kana da mahaifi, Grandma ta ɗauke ka tamkar ZEEYAD ne, kanada mata sannan kada ka cire ran zaka samu ɗa wataran kaima, mai yafi samun wadannan abubuwa farin ciki a rayuwa?, har yanzu kana da family ZEEYAD, Grandma, Mai Martaba, DEENAH, Rahinah, little ZEEYAD, Ayaan dama kuma ni, na tabbata wadannan sun isa su samar maka da farin cikin da kakeso na har abada, kayi haƙuri haka nan, ka sani rayuwar da ZEEYAD yayi fama da ita a baya ta wuce ƙuncin da kake ciki a yanzu, yanzu kuma da ya gano mahaifiyar ka ce tayi sanadiyyar mutuwar tasa mahaifiyar ya kuma ganka cikin halin ƙunci sabida za'a yankewa mahaifiyar ka hukunci mai kake tunanin zaiji cikin ransa cewar bakason a ɗaukar wa mahaifiyar sa haƙƙin ranta komiye?." Ɗago da jajayen idanun sa yayi yana sanƴawa cikin nata da take kallon sa, murmushin kan le6e ta saki tana riƙo hannun sa cikin nata kafin ta cigaba da faɗin "Nasan ba zaka so yaji wani abu game da hakan ba, ka ɗauki QUEEN MOTHER tamkar mahaifiyar ka ne, dan haka ka ɗauka cewa mahaifiyar ka ta daɗe da mutuwa kaima tamkar ZEEYAD, sannan ka sanƴa a ranka cewar fansar ranta za'a ɗauka yanzu tamkar yadda Ubangiji ya halatta, kada ka kuskura ka bari ɗan uwanka ya gano kanajin ƙunci game da wannan lamari, nasan it will be hard for you, sabida har yanzu jinin ta ne ke yawo a jikin ka amma daurewa zakayi, daurewa zakayi YAZEED ka maida komai ba komai ba, ka toshe idanuwan ka da kunnuwan ka ka cire damuwar hakan tattare da kai idan kayi hakan then with time zakaji komai ya zamto tarihi cikin rayuwar ka lokacin da ka buɗi ido ka ganka zagaye da family ɗinka masu sonka kuma kullum suke ƙoƙarin ganin sun sanƴa ka farin ciki, bin hukuncin Allah shi kaɗai zai haifar da zaman lafiya cikin zuri'a dama kuma ƙasa baki ɗaya, ƙuncin da zakaji na lokaci ƙanƙani ne nayi maka alƙawarin hakan da zaran kaga kowa cike da farin ciki da walwala ba zaka san sadda kaima zaka warware al'amura su cigaba da tafiya dai-dai tare da kai ba, i know it's hard YAZEED but na ƙanƙanin lokaci ne bi-iznillah" ta ƙarashe tana kallon sa kamar yadda yake kallon nata. Sosai yaji kalaman ta sunyi matuƙar tasiri tare da sanƴaƴa masa zuciyar sa, ya ɗauka ba zai ta6a samun sanƴi cikin zuciyar sa nan kusa ba, sai dai kuma cikin ƙanƙanin lokaci kalaman JALILAH suka sanƴaƴa masa zuciya tare da bashi hope ɗin tabbas watarana komai zai zamto tarihi tamkar ba'ayi ba haka kuma farin ciki marar yankewa zata darsu cikin wannan family nasu, gusar da gur6atattun mutane kamar mahaifiyar sa daga cikin ahali dama kuma ƙasa baki ɗaya shi kaɗai ne hanƴar wanzar da farin ciki marar yankewa, shima damƙe hannun ta yayi cikin nashi yana jinjina mata kai yayin da murmushi ke wanzuwa kan fuskar sa. Maida masa martanin murmushin JALILAH tayi tanajin daɗi sosai a ranta na yadda ta kwantar masa da hankali, sun daɗe suna kallon juna kafin kuma yayi saurin kauda kansa yana miƙewa tsaye. Tsaye itama ta miƙe kafin tace "Nasan abu mai wuya ne kaje wurin taron nan, zaka iya kwanciya ka huta koh zaka sami ƙarfin jikin ka." Kai kawai ya iya jinjina mata, murmushi tayi ta nufi hanƴar ficewa. "JALILAH" ya kira sunan ta, tsayawa tayi tare da juyowa tana kallon sa "Thank you" yace da ita, murmushi tayi masa kawai kafin ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice. ******************** _______Cikin mutane tayi ta ratsawa cike da tashin hankali har ta iso inda mahaifin nata ke zaune da gudu tazo zata isa garesa wani dogari yayi saurin tare mata hanƴa da takobin hannun sa. A tsawace tace dashi "Get out of my sight you stinking being" ta ƙarashe cikin wulla masa mugun kallo da idanun ta da sukayi jazir alamun tasha kuka ta gaji ne. Hankalin sarki ne ya dawo kansu, fuskar sa ya sake ɗinkewa ganin Rahinah ce tsaye tana yiwa dogarin rashin kunƴa. Cikin tsukewar fuska wannan dogarin yace da ita "Mai Martaba baya buƙatar ganin kowa yanzu har sai bayan an aiwatar da abinda ya tara jama'a anan wurin." Hannu ta ɗauke ta wanke fuskar sa da mari kafin ta nuna sa da yatsa tace "How dare you, uba na ne shi dan haka babu wanda ya isa ya hane ni daga zuwa ganin sa a duk lokacin da naso, ƙasƙantaccen bawa kamar ka bai isa ya taremin hanƴa da sunan tsare ni daga zuwa wani wuri ba musamman ma wurin mahaifi na, so get your ugly face out of my sight now." Sosai dogarin yaji zafi cikin zuciyar sa, sa'ar ta ɗaya ita ɗin ƴa ce ga sarki dah kuwa babu abinda sai hana shi tattaka ƴar banza ƙaramar yarinƴa da ita. Hanƴa ya buɗa mata nan tayi saurin wucewa tana aika masa da mugun kallo, kafin ta isa ga mahaifin nata tana zubewa a gaban shi tare da riƙo ƙafafun sa. Cikin kuka take faɗin "Abhi dan Allah, dan Allah ka kyale Ummie kada ka yanke mata wannan tsattsauran hukuncin, ka tuna fah mahaifiyar mu ce tayaya zaka yanke mata hukunci gaban mu?, Abhi gashi Ayaan ma yana chan asibiti kwance rai a hannun Allah, hannun sa sai ƙara ciwo yake infection ya shiga likitoci sun ce zasu sake yanke masa hannun, dan Allah Abhi kayi haƙuri kada kayi mana haka, ina zamu sanƴa ranmu idan ka ɗauke mana Ummie, ita kaɗai ce gatan mu kuma ita kaɗai ce mai son mu, dan Allah kayi haƙuri ka janƴe maganar hukuncin nan" ta ƙarashe cikin fashewa da wani irin matsanancin kuka. Sosai jikin mai Martaba yayi sanƴi, yana tausayin yaran nasa sai dai hakan ba zai hane shi daga aiwatar da abinda ya zamto wajibi a gareshi ba, dukkanin wani baƙin hali daga gun mahaifiyar su suka ɗauko shi, shiyasa kaf cikin ƴaƴan sa yafi ƙaunar ZEEYAD da YAZEED sai kuma ƴaƴan Nazeerah wadanda kowacce ya aurar da ita tun suna 18yrs kuma alhamdulillah suna nan zaune gidan mazajen su lafiya ba tare da sun ta6a kawo masa rahoton wata matsala ba dan kuwa yasan halin mahaifiyar su suka biyo wacce bata shiga sabgar da bata shafe ta ba take kuma ɗauke ido akan dukkanin wani abu da ta gani muddin ba wai ka tambaye ta bane ba, sa6anin Ayaan da Rahinah da koh kaɗan basu ɗauko hali mai kyau ba sai karatun da uwar su Hafeezah ta koyar dasu, yanajin tausayin wannan rayuwar tasu sai dai ya zama dole ya yankewa Hafeezah hukunci koh suma sa samu su gyara halayen su dan kada hakan ya faru a kansu nangaba. "Take her away" kawai ya iya faɗa, sake riƙo ƙafar sa tayi tana kuka tare da kiran sunan sa amma yayi mata biris har aka fitar da ita daga wannan wurin. Taro ne ya sake cika mutane sai halarta suke, ganin ƴaƴan nasa basuda niyyar fitowa ya sanƴa shi bada umarnin a fito da Hafeezah dan yanke mata hukunci. Ba'a jima ba aka kawo ta hannayen ta ɗaure da chain, kallo ɗaya zakayi mata ka hango tsantsar tashin hankali da firgici akan fuskarta, ganin yawan mutanen da suka hallara ne ya sake darsar mata da tsoro tare da gasgata mata cewar dagaske fah yau tata zata ƙare a duniyar. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga yi mata zarya akan kumatu, wani irin nadama, tsoro dama kuma fargaba na sake darsar mata cikin zuciya, sosai take nadamar abubuwan da ta aikata wanda daga ƙarshe bata ci kyakkyawar ribar komai daga cikin sharrin da ta aikata ribar ta kuwa shine hukuncin kisa a gaban ɗumbin jama'ar gari idon kowa na kallo, sosai ta shiga yin kuka tana ta shiga uku ta lalace a yafe mata ba zata ƙara ba. Biris guards ɗin dake biye da ita sukayi har suka rakata zuwa inda zata hau a rataye ta ɗin. Zubewa tayi a wannan wurin tana cigaba da kukan da ba zata amfanar da ita komai ba, babu abinda take tunani sai iriyar rayuwar da tayi a baya kamar ba zata mutu ba, tayi ta cutar da bayin Allahn da basuji ba basu gani ba dukda sunan ita mai mulki ce, ta kashe innocent baiwar Allah LATEEFAT duk dan son zuciyar, ta kuma wulaƙantar da rayuwar ZEEYAD sabida bata tsoron Allah bata tuna ranar ƙin dillanci, bata tuna cewar zata mutu fah wataran, gashi mai mulkin da babu irin sa a yau ya nuna mata iyakar ta, ya nuna mata cewa babu wani sarki koh mai mulki sai shi, ya nuna mata cewar duniyar a hannun sa yake, ya nuna mata cewa baya gyangyaɗi bale bacci, ya nuna mata cewa shi mai ji ne jin da babu wani mahaluƙi da ya isa ya kwatanta ya yake, ya nuna mata cewa kowane ɗan adam nada iyakar sa a rayuwa sannan ya nuna mata cewa lokaci kowane ɗan Adam ke jira, lokacin da ya tanadar masa na ranar girbar abinda ya shuka walau alkhairi ne koh sharri. Sosai take kuka kamar ranta zai fita, koh kaɗan babu wanda yaji tausayin ta a wannan wurin sai ma shewa da mutane ke tayi kan cewar _A kashe ta_, sosai wannan kalma da suke ambata ke sake firgitar da ruhin Hafeezah, ji take kamar ta nutse a wurin saboda kunƴa, sosai zuciyar ta ke mugun bada sauti mai cike da tsoro da firgici ganin dai tsakanin ta da mutuwa bai wuci taku ɗaya ba, mutuwa na jiran ta a gefe, babu damar tuba koh neman yafiyar Ubangiji, sabida bakin alƙalami ya riga ya bushe, sauƙin ta ɗaya a kashe ta kamar yadda ta kashe ta haka ne kaɗai zata ji sassauci cikin kabarin ta, though ta riga da yanke wa kanta cewar makomar ta ba mai kyau bace, sannan wannan hukunci da za'a yi mata yanzu ba hukunci bane hukunci sai taje cikin kabarin ta inda zata tadda babu kowa sai ita sai kuma halayen ta be it masu kyau ne koh munana. Murya taji an bada umarnin a aiwatar da hukunci, nan fah ta sake ruɗewa har dasu sakin fitsari mai zafi da zawo a wando tsabar tsoron mutuwa da tsoron abinda zata tarar a rayuwar da zatayi har abada babu mutuwa nangaba, bata ankare ba taji a ɗaure mata hannaye ta baya an rufa mata baƙar hula akan fuska tare da saƙala mata igiya a wuya. Kalmar shahada malamin dake kusa da ita ke bata amma inaaa Hafeezah koh jinsa bata yi tsabar fargaba da tsoron da ya rufe ta ga kuma harshen ta da yayi mugun nauyi, babu abinda take sai ihu kamar zata shiɗe tana kiran sunan mai Martaba da ƴaƴan ta musamman YAZEED akan ya taimake ta gasu nan zasu kashe ta, haka wannan malamin ya kyale ta yaja gefe, matse mata igiyar akayi a wuya, tare da ɗaura ta kan wani dogon abu, hankalin kowa da kowa ne ya dawo filin ya ɗau tsit babu abinda kakeji sai ihu da shewar Hafeezah, bata ankare ba kuwa aka ja igiyar dake rataye da wuyar ta sama kafin a tunkuɗe abinda ƙafafun ta ke kai, take filin ya ɗauki sautin *ALLAHU AKBAR* babu ƙaƙƙautawa, shure-shure Hafeezah tayi tayi tana ciccila ƙafafu a haka har ta gama ƙafafun suka saki haka ma jikin ta da alamu dai rai yayi halin sa. Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya sarki ya saki yana sadda kai ƙasa, wasu 6oyayyun hawaye ne suka zubo masa jikin sa yayi bala'in sanƴi, da kyar ya iya miƙewa ya tashi ya bar wurin a sanƴaƴe fadawan sa na mara masa baya. B'angaren YAZEED kuwa jin ƙuwa da tashin sautin *Allahu Akbar* ya tabbatar masa da cewa an yankewa mahaifiyar sa hukunci. Zamewa yayi ya zauna daga tsayen da yake wasu irin hawaye masu zafi na tsiyayo masa, riƙe kansa dake barazanar 6allewa yayi da hannu bibbiyu yana tsoron irin makomar da mahaifiyar sa zata tarar, a haka ya wuni cikin ɗakin ba tare da ya fita koh da jana'izarta bane ba. *BAYAN SATI ƊAYA* ________Har izuwa wannan lokaci basu gama fita daga cikin shock ba dukda kuwa Hafeezah mai laifi ce a wurin su amma hakan bai hana jikin su gabaɗaya yin sanƴi ba da rashin ganin ta cikin su ba. Sosai YAZEED ke ƙoƙarin yakice abinda ya faru da ita daga cikin zuciyar sa, koh kaɗan baya son tunano ta sai dai kuma a kullum baya gajiya da yi mata addu'a da kuma nema mata sassauci wurin Ubangiji. ZEEYAD ma hakan take a wurin sa, gabaɗaya ya rasa meke yi masa daɗi, zuciyar sa cike take da jimamin mutuwar Hafeezah ga kuma tausayin ɗan uwansa da ya cika masa zuciya, though a kullum DEENAH na iya ƙoƙarin ta na ganin ta kwantar masa da hankali, sai dai hankalin nasa yaƙi kwanciya dan kuwa tun bayan yankewa Hafeezah hukunci bai sake sanƴa YAZEED ɗin a idanu ba, he just do hope yana cikin ƙoshin lafiya ga kuma dama bai gama warkewa har chan ba. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin watanni biyu kowa ya mance da wata Hafeezah inda suka tsiro da sabuwar rayuwa mai cike da so da ƙaunar juna abin gwanin ban sha'awa. Rahinah yafiyar JALILAH da kowa ta nema cikin fadar akan gur6atattun halayen ta a garesu, nan kuwa duk kowa ya kar6e ta tare da nuna mata babu komai. Ayaan kuwa sake yanke hannun sa likitoci sukayi inda akayi masa aiki aka sanƴa masa ta roba, shima yayi nadamar halayen sa sannan ya nemi yafiyar kowa da kowa musamman ma DEENAH da ZEEYAD. Cikin wannan shekarar duk suka jesu aikin Umarah dan sake roƙon zaman lafiya mai ɗorewa da farin ciki a wannan ahalin nasu. Sosai suke gudanar da zaman lafiya mai cike da ƙauna a wannan family ɗin. DEENAH da ZEEYAD kuwa Nigeria suka zo tare da kawowa su Umma ziyara, sosai da sosai Umma, Jafar, Mami, Anty Khadija wacce itama auren ta ya kusa dama kuma Amirah da mahaifin su sukaji daɗin wannan ziyara ganin yadda DEENAH ta zama wata fresh da ita gwanin ban sha'awa ga kuma little ZEEYAD mai kama da mahaifin sa wanda a halin yanzu yake da shekara ɗaya da ƴan watanni. Sati biyu sukayi wa su Umma suka koma Egypt, inda kuma anan ne suka cigaba da gudanar da rayuwar farin ciki. Cikin wata shekarar da ta zagayo mai Martaba ya sauƙa ya baiwa ZEEYAD mulki dan kuwa a cewar sa ya gaji da mulkin haka shima yana buƙatar hutu, ai kuwa an samu adalin sarki mai kwazo wanda kuma yafi mahaifin sa iya aiki da tafiyar da mulki, sosai jama'a ke jin daɗin mulkin sa, cikin shekaru biyu ya dawo da wannan ƙasa abar kwatance a ƙasashen duniya baki ɗaya. Su DEENAH kuwa an sake murjewa an zama manƴan mata kuma Sarauniya, farin ciki gun wannan ahali ba'a cewa komai. A yanzu su YAZEED ma na da ɗansu mai shekara ɗaya, Grandma kuwa ta sake tsufa amma har yanzu da sauran ƙarfin ta, sosai takejin farin cikin kasancewa cikin ahalin ta. *5 YEARS LATER* _____Abubuwa da dama sun faru cikin wannan shekaru, ciki kuwa harda mutuwar Grandma da mai Martaba, sosai sukayi baƙin ciki da mutuwar wadannan mutane biyu mafi soyuwa a garesu daga ƙarshe dai sun wallafa Allah komai inda suka cigaba da yi musu adduar samun rahamar Ubangiji a kullum. Yau ma kamar kowacce ƙarshen wata su kan haɗa family re-union dan ganawa da dangi dama kuma abokan arziki. Wurin hutu ne ƙato cikin MASARAUTA wanda daga gani kai kasan special ne wurin ba kowa ne ake bari yake ma ra6ar arear wurin ba, sosai tsari dama kuma gine-ginen cikin MASARAUTAR suka canza da alama dai ba ƙaramin cigaba ake samu kullum ba, ga kuma yadda Bodyguards ke zagaye da wurin kowanne hannun sa riƙe da bindiga. Kyau da tsaruwar wurin hutun ba zai faɗu a baki ba, daga nesa daga ciki kuwa na hango su zazzaune kan manƴa-manƴan darduma masu kyau na alfarma, duba na na maida gun wasu dattijai dake zaune suma nasu wurin daban, kallo na ƙare musu tsaf Abdulhakeem, Abhi, mahaifiyar Sadeeq, mahaifiyar Jalilah dama kuma Sarauniya Nazeerah ne zaune gaban su kuwa abubuwan more rayuwa ne kala-kala suna ci suna ɗan ta6a hira cike da nishaɗi. Maida duba na nayi kan dardumar dake tsakiya wanda ya kasance wasu irin kyawawan yara ne akai wanda aƙalla zasu kai su goma koh ɗan ƙasa da haka gwanin ban sha'awa kamar dai ka sace su ka arce, kundai san yaran larabawa da shegen shiga rai😝, sannan manƴan cikin su ba zasu wuci 13yrs ba, suma wasan su suke duk fuskokin su ɗauke da walwala except yaro ɗaya wanda duk ciki shine kyakkyawan cikin su fuskar nan tasa a matuƙar ɗinke yaja gefe ɗaya ya zauna yana gungunai tare da aikawa da sauran yaran kallo cike da haushin su. Daga ɗayan gefen kuwa su ZEEYAD, DEENAH, YAZEED, JALILAH, Sadeeq wanda Rahinah ce matar sa yanzu, Ayaan, Sooraj da wata budurwa a gefen sa wacce da alama dai matar sa ce, sai kuma ƴaƴan Nazeerah mata Layla, Raudat dama kuma mazajen su, sune duk zazzaune da ka gansu kasan kwanciyar hankali da jindaɗi ta zauna musu kowannen su fuskar su ɗauke da fara'a suna hira suna cin abubuwan dake jibge kaca-kaca a gaban su. Ɗaya daga cikin yaran wanda ba zai wuci shekaru huɗu bane yayi masa gwalo hannun sa riƙe da wata kyakkyawar yarinƴa da ba zata wuci watanni bakwai da rabi ba sai lagwaigwaya ta yake wai shi a hakan riƙon ta yayi da kyau. A fusace yaron farkon wanda ba zai wuci 7yrs ba ya iyo kansa kafin ya shiga jan yarinƴar a hannun sa, ihu ɗayan ya fara yana faɗin ya sake masa ƙanwar sa ai batason sa ne yasa bataje wurin sa ba. Shi kuwa ɗayan in banda huci babu abinda yakeyi daga ƙarshe dai yayi nasarar kwace yarinƴar daga hannun sa yana rungume ta a jikin shi, Kuka ɗayan ya fashe dashi ganin yafi ƙarfin sa ya kwace masa ƙanwar sa. Hankalin mutanen wurin ne ya dawo gun su, DEENAH da suma tasu wurin zaman daban miƙewa tayi a fusace tare da faɗin "Abyad." Juyowa yaron yayi yana kallon ta bar yanzu yana nan rungume da yarinƴar sai huci yake da alama dai zuciya ne dashi. Ƙarasawa wurin mai kukan tayi tana tayar dashi tsaye kafin ta shiga share masa hawaye tana bashi haƙuri. "Ummie ai shine ya kwace Ummu-kulsum a wuri na" cewar yaron yana nuna inda Abyad ke tsaye. "Shushh, kayi shiru haka kaji?, zanyi maganin sa itama yanzu zan kwace ta sai hankalin ka ya kwanta koh?." Kai ya jinjina mata yanajin daɗi a zuciyar sa. Ƙarasawa tayi gun Abyad kafin ta sanƴa hannu tana amsar Kulsum a hannun shi, da yatsa ta nuna sa kafin tace "I warned you several times akan yawan zuciyar ka amma baka ji, daga yau ba zaka sake ta6a kulsum ba, kana sonta amma kuma kullum kana cikin faɗa da yayan ta tayaya itama zata ji daɗi ta soka idan taga kullum kana cikin faɗa da yayan ta, eh?." Shiru yayi yana kallon ta kafin ya buɗi baki kamar wanda bayason maganar yace "But he is hurting her bai iya riƙe ta ba." "Just do as i asked you to." "Ba zan ƙara faɗa dashi ba indai Kulsum zata soni akan hakan." Murmushi tayi tana basa peck a kumatun sa tace "Good Boy maza kaje ka rungumi Zaid ku shirya yanzun nan." Kamar yadda ta umarce sa ya ƙarasa gaban Zaid yace "Am so sorry Zaid, ka yafemin kaji?." Kai Zaid ya jinjina masa kafin kuma su rungumi juna cike da farin ciki. Murmushi duk mutanen wurin sukayi, juyawa tayi tana komawa wurin zaman ta, Kulsum hango Ummien ta ya sanƴa ta fara yayyarfa mata hannu alamun ta ɗauke ta, murmushi JALILAH tayi tana amsar ta daga wurin DEENAH. Cikin raɗa ZEEYAD yace da DEENAH "I wonder why your Son yake da zuciya haka." Murguɗa masa baki tayi tace "Kaji ka da wani magana, halin ka ya ɗauko, which means a gunka ya ɗauko komai ma." Murmushi yayi yace "Do you think the Boy is in love?." Wani irin kallo tayi masa kafin tace "Mai kake faɗa ne haka?, mai ma ya sani he is just fond of Kulsum shine kawai." Ɗinke bakin sa yayi tare da yin shiru dan kuwa ba ƙaramin halin ta bane yanzu ta balbale sa da masifa tunda ta samu sabon ciki abu kaɗan ke bata haushi. Kukan wani yaron suka sake jiyowa nan duk suka juya suna kallon sa Abyad ne da wani daga cikin yaran da zai wuci sa'an sa ba kowanne riƙe da kafaɗar juna kamar wasu raguna zasuyi karo suna faɗa, dafe goshi DEENAH tayi, ZEEYAD ne ya daka masa tsawa take ya saki yaron ya tsaya kamar wani Boss yana aika masa da mugun kallo. "Mai ya haɗa ku ku kuma?" cewar Nazeerah tana kallon su. Ɗaya daga cikin yaran wacce ba zata wuci 9yrs bane tace "Wai dan Latif yace idan mun girma shi zai auri Kulsum shine kawai Abyad yaji haushi ya wanke sa da mari, shine fah suka hau yin faɗa, suka takawa Imran ƙafar sa" ta ƙarashe da yin kwafa tana sunkuyawa gun yaron dake kuka ya riƙe ƙafar tasa. Duk baki suka saki suna kallon yaran cike da mamaki, yafito Abyad DEENAH tayi da hannu, nan ya tako zuwa inda take, kallon sa tayi tace "On your kneels." Ba tare da yayi musu ba yayi kneeling ɗin yana ɗaga hannayen sa sama fuskar nan tasa a matuƙar tsuke. Kunnen sa ta kama taja tace "Maiyasa bakajin magana?." Runtse idanu yayi kafin yace "Shine yace wai Kulsum..." Cikin faɗa ta katse shi da faɗin "Shikenan kuma kada kowa ya ra6i Kulsum sai kai, let this be the last warning da zanyi maka, muddin ka sake yin faɗa da wani then babu abinda zai hana ni maida ka gun Grandma a Nigeria sannan ba zaka sake dawowa ba, ba zaka sake gani na koh Abhi ba bale kuma Kulsum, kaji?" ta faɗa tana murɗa kunnen nasa. Kai ya jinjina mata kawai yana runtse idanu cike da zafi. "Zauna anan, ba zaka koma cikin su ba har sai an tashi." Zama yayi inda take nuna masa ɗin yana naɗe ƙafa tare da sadda kai ƙasa. Kallon DEENAH ZEEYAD yayi tare da sakar mata da murmushi, ɗan makar ƙeyar sa tayi tace "Stop staring." Dariya ƴan wurin sukayi baki ɗaya kowa ya cigaba da harkar gaban sa. Rarrafowa Kulsum tayi gun Abyad tana hawa jikin sa, ta gefen ido ya saci kallon iyayen nasa kafin ya ɗan riƙo ta yana bowing kansa dai-dai kunnen ta ya raɗa mata "I love you Kulsum, and oneday... you will be my future wife" ya ƙarashe a hankali. Dariyar da ya bayyanar da cute dimples ɗin ta ta saki kamar wacce taji abinda ya faɗa nan shima ya saki murmushin yana kallon ta. Ɗagowa yayi nan yaga duk kallon sa suke sadda kansa yayi ƙasa yana murmushi. ZEEYAD ne ya ɗago glass ɗin champaigne ɗin hannun sa yace "Cheers y'all." Duk ɗaga nasu sukayi tare da faɗin "Cheers" kafin kowa ya kafa nasa a baki. ALHAMDULILLAH, LAIFIN DAƊI ƘAREWA. Yake 6oyayyiyar makaranciyar ZEEYAD, koh da ba zakiyi min comment a last page ɗinnan ba toh ina mai roƙon ki da girman Allah kiyi min addu'ar dacewa duniya da lahira koh da kuwa cikin zuciyar ki, sannan kuma ki faɗamin darasi ɗaya da kika ɗauka cikin wannan littafi musamman ku masu yimin comment da nuna min ƙauna a kullum *WANE DARASI KIKA ƊAUKA CIKIN LITTAFIN ZEEYAD??* *Alhamdulillahillazi bini'imatih tatimmus salihat, ina miƙa dumbin godiya ta ga Allah(SWT), da ya bani aron lokaci har izuwa yau da nake kammala littafin ZEEYAD, ina mai roƙon Allah da ya bani ikon nishaɗantar daku tare da wa'azantar daku ya kuma bani wani aron lokacin na gabatar muku da wasu litattafaina na nangaba, ina roƙon Allah da ya yafemin a duk inda nayi kuskure cikin wannan littafi ya kuma bani ladar saƙon da na isar muku cikin sa🤲🏽🥰* *GODIYA TA MUSAMMAN* Godiya ta musamman gareku *ZEEYAD FANS CLUB*, haƙiƙa kaunar ku daban take cikin zuciya ta, inayi muku so fisabilillah, alkhairin Allah ya isar muku aduk inda kuke a faɗin duniya. *JINJINA TA BAN GIRMA* Gareku my best Commenters, haƙiƙa comments naku is something else wollah, ina matuƙar jindaɗi da nishaɗi aduk sadda nake karanta comments naku Lateefat Fatima Bet Ice Mrs Nuruddeen Sadysglam Queen Hafsy Mom Misrah Mom Fauxullah Mrs Kabeer Ummu Muhseenah Beebarh Halimatu Umar Mmn suhailat Nucieey Maesart Ummu Khaleel Maman shurem Maryearma Aysha s.b.a Maman Ameer Nana Ruqayyah Ammy Zainab Jaja Ummu Mahbub Haseenerh Maman Arpha Asiya Abdulkadir Umma Ammar Maryam Abdulmajalil Kai gaskiya kuna da yawa dama dai wadanda ban lissafo ba kuyi haƙuri, duk kuna raina kuma ina ƙaunar ku sosai da sosai, Allah Ubangiji ya bar Kauna tsakanin mu🤲🏽🥰 *JINJINA GAREKU ƳAN UWANA MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION, ina ƙaunar ku fisabillah, Allah Ubangiji ya bar mu tare yaqara mana basirar rubuta litattafai masu tsabta.* Yanzu kuma sai wani Lokacin idan Allah ya kaimu inda zanzo muku da sabon littafi na mai ɗauke da sabon salo watau *ABHI* ku daga jin sunan shi ba sai nace daku komai ba, kudai kawai ku shirya alƙalamin comment naku nikuma zan shirya alƙalamin yi muku typing, zai zo muku very soonn insha Allah.............. *MHIZZ JIDDHERR🖊️*