[5/4, 10:10 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU BARKAN KU DA SALLAH DA FATAN MUNYI SALLAH LAFIYA *Yadda muka fara Allah yasa mu gama lafiya, kura-kuran da zamuyi a ciki Allah ka yafe mana, har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba Wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 1&2 Kishingid'a tayi kan kujera me mazaunin mutun uku, da ka ganta kaga halaman tana cikin farin ciki, saidai ga dukkan alamu tana dan jin barci, ji tayi an turo 'kofa hade da sallama cikin tattausar murya me dad'in sauraro. Duk da ta ji dadin muryan amma kuma tuni farin cikin dake fuskarta ya kau, ta mi'ke cikin tsorata da ganin sa, murya na rawa ta ce "Sannu da zuwa Ya Umar" Ba tare da ya amsa ba ya kauda kai dan irin yadda yake ji a jikin sa, baisan me yasa ba, a duk lokacin da yayi arba da yarinyar yana jin wani abu na masa yawo a jikinsa harma kwakwalwansa, shi yasa baya son ganin ta kwata-kwata, yanzu ma da yasan ita kad'ai zai Tarar a falon da ba abin da zaisa ya shigo. Kallonta yayi a karo na biyu yaga ta sunkuyar da kai, ya ce "Munafuka sai ka ce wata mutuniyar kirki, ina su Abubakar" Da sauri ta ce "Sun fita" Ya ce "Abba fa" Ta ce "Bai dawo ba" Ya ce "Keda waye a gidan" Ta ce "Ni da Ummice Umma ma ta fita" Ya ce "Yi min magana da Ummin" Da sauri ta tashi tayi ciki cikin ranta kuwa sai tsine masa take, tana shiga ta samu Ummi a tana kishingid'e a gado, ta hau gadon ta ce "Ya Umar yana falo ya ce na miki magana" Ta tashi ta zauna ta ce "Gani nan zuwa" Ba 'bata lokaci Ummi ta fito yayin da ita kuma ta kwanta a gadon. Yana ganin Ummi ya zame daga kan kujeran ya gaisheta cikin ladabi da biyayya sannan ya mi'ka mata wasu takardu ya ce "Gashi Baba ya ce Abawa Abba" Ta amsa sannan ta ce " ya Baban naku da Maman naka" Ya ce "Suna lafiya" Ta ce " To ka gaishe su" Ya ce "Insha Allahu zasu ji" Zai fita kenan sai ga wata yarinyar ta shigo da uniform a jikinta tana goye da Jakarta a baya tana ganin sa ta ce " Ina yini Ya Umar" Bata jira amsawarsa ba ta wuce don irin yunwar da take addabarta. Kai tsaye tayi dakin Ummi tana daga kwance taji shigowan ta tuni ta diro daga kan gadon ta mike ta ce "Khadiyo wa ya dawo da ke" Ta ce " Su Ya Abubakar ne" Ay da gudu ta fito har tana bige Khadiyo, Khadiyo ta ce "Wallahi Aunty bana yin abin da kike yi haba kamar yarinya" Bata jira cewarta ba ta fito ta samu suna tsaye da Umar bata damu ba ta d'ale bayan Usman da yake shi yake kusa da ita, shi kuma ya ce "Ohh BILKISU zaki karya ni" Abubakar ya zuba mata dundu a baya ya ce "Khadiyo bata yin abin da kike sister" Ta sauka a bayan Usman ta fara bubbuga kafa kamar karamar yarinya tana cewa "Ni wallahi tunda ka dake ni to bayanka zan hau" Du'kawa yayi ya ce "To hau abinki ya isa" Tsaki Umar yayi saboda haushinta ya wuce abin sa, duka suka kalle shi sannan suka kada kai suka shiga, sai da ya kaita falo sannan ya sauketa kan kujera ya ce "Kawo mana abinci" Da sauri ta shiga kicin ta dauko musu tare da plate tana gama ajiyewa Khadiyo ta fito da alama ta watsa ruwa ne, ta zauna aka fara cin abincin da ita suna hiransu. ASALINSU Garin Bauchi garine me tarin Albarka, da yawa mutanen garin basa zaman banza, mazansu da matansu suna neman na kansu, saidai kalilan me a ciki wanda basu damu su nema ba, akwai yan kasuwa akwai kuma masu aikin gomnati saidai yan aikin gomnatin sunfi yawa akan yan kasuwan. Malam Hamza yana daya daga cikin yan kasuwan da suke garin Bauchi yana da Yara biyu, Ibrahim shine Babba sai kuma 'kaninsa Jafar Malam Hamza bai bar yaransa haka ba, ya sasu makarantar boko da ta Allo sannan kuma suna bin Mahaifin nasu kasu idan kuma sun dawo suna taya Mahaifiyarsu Hauwa aikin gida. Koda suka yi karatu suka gama Ibrahim ya ce shi kasuwanci zai ci gaba da yi, shiko jafar fannin dabbobi ya karanta, yana da sha'awan zama likitan dabbobi. Alhamdulillah duk kansu burinsu ya cika a nan ne kuma Inna Hauwa ta fara masa maganan aure, Ibrahim yana da wacce yake so mai suna Aisha, Jafar ne ko nena ma baya yi, amma da Mahaifiyar tasu ta bukata sai ya samu wata yarinya Sauda tana kawo 'kwai asibitinsu na dabbobi wato inda yake aiki, Sauda ta fito daga gidan arziki gidan tarbiyya saidai kuma tarbiyan da gidan su suka bata ta watsar dashi, Sauda bada damu da ibada ba, saidai idan taji ankira Sallah idan da mutane a kusa zata yi Sallah a nutse kamar muminan gaske, idan ko ba kowa zatayi zaman ta idan ta wuce ta wuce kenan baza ta yi ta ba, ko kuma Idan tayi alwala a gaban mutane sai ta shige daki tasa hijabi tayi zaman ta. Aisha kuwa ta fito daga gidan tarbiyya kuma tarbiyyan da aka bata bata watsar dashi ba. Malam Hamza yayi bincike sosai sannan ya yadda da auren inda aka daura auren Ibrahim da Aisha sai Jafar da Sauda watansu biyu ko wannen su suka biya wa matansu da su kansu saudiyya a lokacin kuma suna da 'kananan ciki koda suka je sukayi ta rokon Allah ya basu zuri'a ta gari yayin da Sauda kuwa gaba daya kasar ne ma ta ishe ta tana Allah-Allah su koma kasar su, dan ba wani ibadan take ba, Aisha bata lura da hakan ba saboda ita tata ibadan tasa a a gaba. Haka suka dawo gida da tsaraba niki-niki Haka suka ci gaba da rayuwa Jafar ya fara gane Sauda bata damuwa da ibada dan wanda take ma na ganin ido ne don haka ya yi mata nasiha tare da tsoratarwa da fada mata irin azabar da zata shiga ranan gobe 'kiyama, ta tsorata matuka, ya lura harda rashin ilimi ke damunta dan haka yaringa koya mata karatu da yadda zata gudanar da ibadan ta. Alhamdulillah yanzu tana damuwa da ibadan kuma tana yi hakan yasa Jafar yayi farin ciki, cikin haka ne cikin su ya Tsufa Aisha ta fara Haihuwan d'a namiji sai bayan kwana biyu kuma Sauda ta haihu itama namiji, Duk da Malam Hamza baida lafiya amma yayi tarnan ganin jikoki har guda biyu, har gida aka kawo su ya fara daukan Babban wato dan Ibrahim ya masa huduba da suna ABUBAKAR SADIQ sannan dan Jafar ya saka masa UMAR FARUQ. Da yake kan iyayen a hade ne, tare yaran suka girma kamar 'yan biyu ko yaushe kayansu iri daya, saidai ita Sauda bata kaunan hakan a cewar ta kowa ya rike nasa, dan ita kan tunda ta samu Umar ma ta daina haihuwa dan bata son ta tsufa mijinta yace zai auri wata, kullun cikin masa kwalliya take don kada ya kyalla ya gano wata shiko ma ba abin da ya dame shi ba kenan, ganin ta samu abin da take so yasa, taje aka juya mata mahaifa ta ci gaba da abin da take yi. Shekaran Abubakar Biyu Aisha ta kuma samun wani cikin murna gurin dangin ba'a magana, Jafar yaso ace Matar sa ma ta samu dan su haihu tare, saidai yana tunanin kila kafin ta haihu ita ma ta samu. Cikin yana kaiwa haihuwa ta haifi d'anta namiji, wannan karan ma Malam Hamza da kansa ya rad'a masa suna USMAN, A sannan ne kuma Mahaifiyar su take jinyan ajali, tare sukayi ta jinyar ta Usman yana wata shi da ta ce ga garin ku, sunyi bakin cikin rashin mahaifiyarsu saidai ba yadda suna iya tunda ubangijin da ya halicceta ya fisu sonta. Tun lokacin Malam Hamza yaki yayi wani auren yana cike da damuwa ga hawan jini dad'i da ya samu jikin girma. Haka suka ci gaba da rayuwa Aisha tun daga haihuwan Usman bata kuma na sake wani haihuwan ba, ta fara nuna damuwarta saidai mijin ta ya nuna mata illar yin haka. Alhaji Ibrahim ba me ra'ayin zama da mace daya bane dan haka ya samu Aisha da lallashi da kalamai masu kwantar da hankali kan cewa zaiyi aure, taji damuwa a ranta amma da yake ita din bata da tashin hankali yasa tayi murmushi ta ce "Allah ya sanya Alheri Alhaji nidai roko na gare ka ka zama me adalci a tsakanin mu" Murmushi yayi ya ce "Na gode kuma ki taya ni da Addu'a Allah yasa na zamo me yin adalcin " Ta ce "Amin" Tana cikin damuwa sosai dan haka ta dukufa Addu'a ta haka taji zuciyarta tayi wasai sannan ma ta ji tana son wannan aure da mijinta zaiyi. Sauda kuwa tana jin labarin karin auren da Alhaji Ibrahim zaiyi ta shiga damuwa sosai a ganin ta ita ma mijinta zaice zaiyi dan haka ta garzaya taje ta samu Aisha bayan sun gaisa ta ce "Umman Yara naji Wai Alhaji zaiyi aure" Aisha tayi murmushi ta ce "Kiyi hakuri laifina ne da ban fada miki ba, amma naso naje har gida na same ki da maganar " Sauda ta ce "Haba Umman yara za'a miki kishiya amma ko ki nuna damuwa, kinsan wacece kishiya kuwa?" Mrs Aliyu ce🥰 lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/14, 6:59 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 3&4 Aisha kan kallon mamaki tayi ta mata har ta dire sannan ta ce "Amma Maman Yara kin bani mamaki, Dan Alhaji zaiyi aure sai in tada hankalina akan me, nima fa auto ni yayi, A'a ni gaskiya kada ki kara kawo min irin wannan maganan ina farin ciki da auren da zaiyi ay karuwa ce" Shiru Sauda tayi ganin bata samu nasara ba ta ce "Kiyi hakuri insha Allah bazan kara zuwa miki da irin wannan magana ba Allah ya baku zaman lafiya" Aisha ta ce "Amin" Koda bikin yazo da ita akayi komai ita kanta Aishan taji dadi da taga Saudan tana shiga da fita ita ko Sauda karfin hali ne kawai take a tunanin ta Mijinta zaice zaiyi auren shima tunda d'an uwansa tayi. Anyi biki an watse amarya Suwaiba ta tare a dakin ta, zaman lafiya sosai ya wakana a gidan ita take yiwa su Abubakar komai dan ma Umman su tana hanawa takance "Haba kina Amarya kina wahalar da kanki a kan yaran nan" Takance "Ay nima yarana ne kinga ko ay baza ki iya raba ni da su ba" Hakan akayi karshe sai su Abubakar din suka koma gurin ta, idan Umar ma yazo a can yake tarewa tayi ta koya musu karatu. Ba haka Sauda ta so ba, taso Mama Suwaiba ta kasance yar ba'kin hali irin saboda su hadewa Umma, saidai bata samu wannan ba, taso ta hana Umar zuwa gidan saidai kuma Babansa da kansa yake kai shi, ba yadda zata yi dole ta hakura. Shekara biyar kenan da auren Mama Suwaiba amma ko batan wata batayi ba, sunje asibiti lafiyanta kalau Umma ma shiru ba labari, ita kan ma Mama Suwaiba bata damu ba tunda ta samu su Usman. Alhajin ne dai yaso su kara haihuwa tunda shi yana bukatar yara da yawa. Tafiya yake a mota a hanyar dawowan sa daga Kumo ta jihar gombe, dan yin ta'aziyyar wani abokinsa da matarsa ta rasu, yana sauraron karatun Al-qur'ani mai girma ganin yariya yayi da kayan Fulani da kwaryan Nono a kan ta kafin ya Ankara ya bugeta Nonon ya kwaranye a titi ita kuma ta fadi kasa warwas, Alhaji ya duba yaga ba kowa a gurin ya dubeta yarinya ce karama bata wuce shekara sha hudu ba, ya dauke ta, daukanta yayi ya sata a mota ya karasa cikin gombe da ita ya kaita Asibiti, saida ya gama biya kudin komai tukun sannan ya ce su kula da ita bari yaje ya duba 'yan uwanta, yana zuwa gurin yaga wata mace ita ma baffulata ce tana kuka da fasheshen kwaryan a hannunta cikin muryanta na Fulani tana cewa "Sikenan Na rasa 'yarnan yanzu Halin ma an tafi da ita," Gefenta akwai namijin sai ya matsa kusa da na mijin ya ce "Assalamu Alaikum, ka fada mata ta daina damuwa yarta tana nan ba tafiya da ita aka yi ba" Da Sauri ta juyo ta ce "Alhaji ina take" Ya ce "Ta samu hatsari ne an samu kuskure ne na bugeta a mota" Sake fashewa tayi da kuka tana cewa "Sikenan ta mutu Ko Baffa mun rasa Hali ma" Baffa ya daga sandan zai bugawa Alhaji sai kuma ya sauke ya ce "Kayi sa'a naji wa'azi da na karka" Alhaji ya ce "Ay hakuri dai muje in kaika inda take" Duka suka duri motar shi dama Baffa yana shiga mota idan zaije cin kasuwa, ita ce dai bata taba shiga ba shi yasa ta kasance a tsorace. Suna zuwa suka samu ta farfado tana ganin iyayenta ta fara cewa Inna kiyi hakuri bansam mato na zuwa ba gashi Nonon duka ya zube," Baffa ya ce "Ay ko sai ya biyà" Hali ta ce "Ayya Baffa bafa laifin sa bane nice naje ketare titin zan nemi motan gombe ban ji karan motar sa ba" Inna ta ce "Dama laifin ki ne", taje ta fara dukanta Alhaji da ya tsaya yana ganin ikon Allah yaje ya ce " Kiyi hakuri Inna zan biya kudin bari ta samu lafiya" Kawar da kai tayi ta koma gefe, alamun kunya, haka yayi ta lallashin su har ya gama biyan komai ya tafi da niyyar zai dawo washe gari ya sake duba su. Washe gari yana komawa ya samu dakin ba kowa ya sake dubawa basa nan, ya wuce office din likita, saida ya zauna ya ce "Likita ina maras lafiyan nan da na kawo jiya" Likita ya ce "Alhaji wallahi sunƙi zama sun tafi rigar su, nayi nayi da su wai su basu yadda da mu ba, ay an fada musu duk wani likita dan mafiya ne" Alhaji ya ce "To yaya jikin yarinyar to" Ya ce "Alhamdulillah ta samu sauki " Ya ce "To yanzu kasan inda suke kuwa" Likita ya ce "Ban sani ba amma kaje can inda kuka samu hatsarin ka bincika ko zaka same su" Godiya ya masa ya masa sallama ya wuce, yana zuwa dai-dai gurin kuwa ya ci karo da shanu a gefen hanya suna kiwo yana dube-dube can ya hango Baffa a karkashin saniya da kwarya a hannunsa yana tatsan nono, daga nesa ya yayi sallama Baffa ya ɗago yana kallon sa ya taso da kwaryan yana washe baki ya iso gurin ya ce "Hannu Alhaji, kai amma kai mutumin kirki ne tunda har ka iya biyo mu, dama haka mashu mota shuke, Ay ni nayi tunanin duk baku da imani " Alhaji Ibrahim ya ce "Ay ba duka aka taru aka zama daya ba" Baffa ya mika masa ƙwaryan nonon ya ce "Gashi Alhaji shanye du" Alhaji ya amsa ya kurba ya mika masa ya ce "Ya isa haka" Ya ce "A'a Alhaji shanye du, du zaka shanye" Alhaji ya sake kurɓa ya ce "Ay ban iya shan danye bane " Ya ce "To muje can gida dama akwai wanda Hali ta tatsa ka tafi gida da shi" Alhaji Ya ce "Nagode dama nazo in duba jikin Halin ne sannan na bada kudin Nonon da tsautsayi ya fada kansa" Baffa ya ce "Kada ka damu Alhaji ay nikan ma sa riga na samawa Hali Mijin aure" Alhaji ya ce "Masha Alhaji sai a fada mana ranan sai muzo a daura auren dani kaga na kawo iyalaina ma ayi miki da su" Baffa ya ce "Ay kaine mijin Alhaji yanzu za'a daura ku tafi da ita" Tsayawa yayi Ya kasa tafiya, Baffa ya juyo ya ce "yarana sun jima ba suyi aure ba, har mutanen rigagen da muka zauna suna cewa hala tsafi zanyi dasu, to ni kuma ina son zaɓa musu mijin da zai rike su tsakani da Allah ne, nayi niyya a raina koda yara na zasu tsufa ne bazan aura musu mungun miji ba, to Alhamdulillah na aurar da Bilki a wani mutumi me kirki har ta haifi yaro ma kuma tana zuwa gun mu, saura ita Hali, ita ma yanzu na gano mata miji, Alhaji Sadaki kawai zaka kawo a daura, dan baza kabar rigar nan ba saida Matarka Hali. Alhaji ya ce "Mata na biyu kuma ay Hali tayi ƙarama a aurar da ita” Tab to idan da na aurar da ita lokacin auren ay da yanzu tana da yara. Ya ce "Mubar wannan maganan muje in ganta kawai" Suka tafi cikin rigar duk inda suka ratsa yaran rugan suna kallon Alhaji har sukaje ƴar bukkan su Buba Inna tana ganinsa ta shege daki da sauri ta dauko tabarmar kaba ta shimfida masa tana masa sannu da zuwa, Hali ya hango can gefe itako tana ganin sa tazo ta durkusa ta gaishe shi kanta a kasa sannan ta shiga cikin bukka ta dauko masa madara ta mika masa Inna kuma ta kawo masa ruwa, yasha ruwan kadan, sannan ya ce "Inna ya kuka bar asibiti kuma bayan ba'a sallame ku ba" Ta ce "Kaidai bari mudai fa bamu yadda ba asibiti ba gaskiya duk da 'yar nan idan tazo tana nuna mana muna yadda amma ina baza mu taba yadda ba" Alhaji ya budi baki zayi magana kenan yaga mutane sun shigo tare da Baffa cikin su harda limamin da kuma Sarkin Fulanin rigar, Baffa ya ce "Ga nan liman wannan kuma sarki ne yazo da kansa dan haka sadaki kawai zaka bada a daura ka tafi da matar ka." Alhaji ya kasa cewa komai, yayin da Inna da Hali suka yi cikin bukka. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/15, 7:17 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 5&6 Baffa ya dauko babban taburmar kaba ya shimfida suka zazzauna shikan Alhaji Ibrahim yana ta kallon ikon Allah. Liman yayi gyaran Murya ya ce "Alhaji ina Waliyyinka? " Kafin yayi magana Baffa ya ce "Ni zan wakilce shi, Allah gafarta Sarki kuma zai wakilci HALIMA" Alhaji kan yana shiru, sai a lokacin ma yaji sunan ta. Liman ya ce "Ina Sadakin" Shiru Alhaji Ibrahim yayi yana tunanin wannan wani irin mutum ne zai bada ƴarsa a mutumin da bai sani ba, hakan yana nuna masa ƙauna ne ko tsabar yadda ne da yayi da shi, to ma idan ya aure ta ina zai kai ta, me zai cewa iyalen sa game da ita, ya sani Suna da fahimta kuma zasu fahimce shi to amma ay hakan bai dace ba. Jin Muryan Baffa yayi ya ce "Alhaji kawo duk abin da ya sauwaka kawai kada ka damu" Ya ce "Dubu goma ne a jikina Baffa barin je mota in dauko" Ya ce "Dauko su" Ya sa hannu a Aljihu ya ciro ya mika masa Baffa ya cire dubu biyar ya mika masa sauran ya ce "Biyar ma ya isa" Mamaki Alhaji ya kuma yi, yana kallon su suka daura auren sa da Hali kan sadaki dubu biyar anan aka raba goro kowa sai farin ciki yake, shiko yara sa cikin farin ciki yake ko baƙin ciki wannan wani irin aure ne. A hankali aka watse aka barshi a gurin ya rasa inda zaiyi, yana daga zaune yaga Hali ta fito Inna tana rike kullin kayan suna kuka, Baffa ya ce " To Hali kiyiwa Mijinki biyayya Allah ya kara lafiya Allah ya baku zaman lafiya, kuma kiyi wa Abokan zaman ki biyayya kinji" Ya kalli Alhaji yace "Alhaji ga Halima Amanace a gurin ka Allah ya baku zaman lafiya" Sai a lokacin Alhaji ya ce "Baffa a bari tukun zan dawo na dauke ta" Ya ce "A'a Alhaji dauki matarka ku wuce kawai" Alhaji zaiyi magana sai gani yayi Baffa ya dauki kullin kayan ya ce "Muje Alhaji kada dare ya muku" Baida ta cewa haka ya bisu ita kuwa Hali makofta ne suka rakota har bakin mota yayin da Inna ta koma ciki tana kuka ita ma. Baya ta shiga da kullin kayanta sai lokacin ne Alhaji Ibrahim ya ce "To Baffa na gode " Ya ce "Kada ka damu Alhaji Allah ya kiyaye" Ya ja motar ya fara tafiya yana sake sake cikin ransa yayin da ita kuwa take ta kuka marar sauti. Suna Isa gida Yaran su uku lokacin Umar ma yazo suka zo har bakin motar suna masa oyoyo, koda suka ga Hali sai suka fara kallon ta tana kuka. Abubakar ya ce "Abba ka siyo mana Aunty ne" Da yake baiji abin da ya fada ba, shi ya san ya masa maganar ta sigar tambaya ne yasa ya ce masa "eh" Da gudu suka juya suna cewa Mama Suwaiba Abba ya siyo mana Aunty. Kallon su kawai yayi ya kada kai ya dauki faggon kayan nata ya ce "Ki daina kukan nan haka, mu shiga ciki " Yana tafe tana binsa a baya har suka shiga falon ba kowa a falon ya ajiye kayan ya ce "Zauna ko" Ta zauna can gefe guda a takure tana kuka, shi kuma ya shiga ya kira matan gidan suka fito Umma Aisha tana ganinta ta ce "To Alhaji ina ka samo mana bafulatana haka kuma kukan me take" Zama yayi ya ce "Ku bata Abinci da ruwa kafin kuji wacece ita" Usman yayi saurin miko mata Abincin da ya rage ya na cewa "ay anan zata zauna kuma ita zata na min wanka ko" Mama Suwaiba Ta ce "Bana hana ku idan muna magana kuna zama a gurin ba" Tuni suka watse suka koma gun wasan su. Koda aka bata abincin bata wani ci sosai ba ta barshi dan bata ma saba da irin abincin ba, ko da ta saba ma baza ta iya cin ba. Saida ta zauna Alhaji Ibrahim ya fada musu komai game da yariyar sannan ya ce "To Ya kuke ganin ya dace ayi kenan yanzu" Umma Aisha ta ce "Daki za'a gyara mata a sata a ciki ita ma ay a matsayin mu take yanzu" Mama Suwaiba ta ce "Alhaji basai ka boye mana ba idan zakayi aure, ka fito fili ka fada mana kana son yin Aure kuma ka auri karamar yarinya kawai, taya za'ayi daga gaisuwa ubanta be sanka ba ya ce ya aura maka ita gaskiya wannan da sake" Baidai ga yin magana ba Umma ta ce "Haba suwaiba mijin kuma kike karyatawa kuma a gaban sa kai gaskiya ban san ki da haka ba" Ta ce "haba Yaya kina yanzu kin yadda da wannan zancen, idan zakayi auren ka ay bamu hana ka ba, amma bai dace kazo kana fadan irin wannan maganan, ba taya za'ay yarinya kamar wannan siyi wa yarsu haka nikan gaskiya ban yadda ba" Alhaji zaiyi magana sai Umma ta dakatar da shi ta ce "Alhaji kaje ka huta a daki kaga a gajiye kake zamu ji da komai" Ya ce "Amm..." ta dakatar da shi "Kada ka damu kaje kawai zanji da komai" Ya kalli Hali da har lokacin kanta a sunkuye tana hawaye wannan lokacin ba kukan sai hawaye, ya ce "Ki sannan yarinyar tayi shiru haka dan Allah" Yana gama fada ya tashi yayi dakinsa, ita kuwa kama hannun Hali tayi ta ce "Haba Halima kiyi shiru haka kukan nan ya Isa haka kanki zaiyi ciwo kuma gashi ba lafiya gare ki ba, kuje ki dan kwanta ki huta kafin Magrib tayi ko" Ta miƙar da ita sukayi daki sannan ta ce "Idan kina da bukatar wani abu kiyi magana kinji, saida ta kwantar da ita sannan ta wuce dakin Mama Suwaiba ta same su ita da yaran duka a kan gado ta ce "Kuje falo zamuyi magana da Maman ku, " Suka fita da gidunsu ta kalli Mama ta ce "Haba Maman yara me yasa kika yiwa mijinki haka kin sani bazai ji daɗi ba " Ta ce "Haba Yaya yanzu ke kin yadda da wannan maganan tasa, ya za'ayi ace yarinya kamar wannan amma ace iyayen ta sun Mata hakan basa son ta ne ko me" Ta ce "Ni na yadda da shi mijina bai taba min karya, kuma bana tunanin randa zai min karyan, wannan na dauke shi a matsayin jarabawa ce da Allah ya aiko mana da ita daga mu har shi, banda abinki wannan ay yarinya ce mu zamu bata tarbiyyan da ta dace, mu zamu lankwasa ta yadda mike so idan muka bata tarbiyya me kyau mu zamu ci riba idan kuma muka yi mata akasin haka, mu zamuyi kuka nan gaba dan haka ki cire wannan a ranki mu rungumeta hannu bibbiyu. Ta ce "Yaya kenan nasan baya min karya amma wannan karan ban yadda ba" Umma tayi murmushin karfin hali ta gano kishi ne ke damun ta, ita din ma haka to ba yadda ta iya haka ta danne zuciyarta tare da yiwa Allah tasbihi, amma ita ta kasa danne nata, amma haka tayi ta tausan ta har Mama Suwaiba taji kunyar Alhaji da kuma ƙaramar yarinyar haka taje ta bashi hakuri. A dakin Umma Hali ta zauna tun tana kewan Innan ta har ta hakura saboda ta saba da su Abubakar Aunty suke ce mata sai Mama Suwaiba ta ce "Ummi zasuna kiran ta ay ita ma uwa ce" idan zasu shiga kicin tare suke shiga har ta koyi girkin zamani harma da wasu na gargajiyan biyayya sosai take musu tana ganin Mama Suwaiba zata yi abu ta ce "Mama kawo inyi, ko kuma idan Umma ne ta ce kawo inyi Umma, kullun idan yara zasu tafi makaranta ita take musu girki, Hali tayi kyau sosai ta zama yar gayu ita kanta idan ta kalli kanta a madubi tana ba kanta sha'awa ta zama ƴar gida ba inda bata sani ba a gidan kuma duk abin da taso take yi ba me mata magana, lokaci-lokaci takan yi tunani yanzu waɗannan kishiyoyinta ne, ita dai a rigagen da suka zauna idan anyi wa mace kishiya sun ringa bala'i kenan, sai daga baya ta gane ay kishiyoyin ma akwai masu ilimi, to ita da masu ilimin ta hadu. Shekaranta daya da wata hudu a gidan Mama Suwaiba ta ce "Ya kamata mu dubo su Baffa Buba kaga tunda ka daukota bamu kara zuwa ba" Umma ta ce "Gaskiya kika fada kan" Ya ce "To sai ku shirya mana tafiyar kusa mana rana" Umma ta kalli Hali ta ce "Ko dai bakya son zuwa ne Halima" Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta ce "Ina so mana Umma" Duka dariya suka mata Mama Suwaiba ta ce "Zanga randa zaki daina wannan kunyar taki, kuma muna dawowa zaki tare a dakin mijinki dan yanzu kan zaki iya karban miji" Tana jin maganan Miji ta tashi ta ruga da gudu sai dakin Umma, duka dariya sukayi Mama Suwaiba ta ce "Alhaji wannan kunyar taka idan kuka tare sai kasha fama da ita" Ya ce "Shi yasa nima nace ku kyale ta ba yanzu ba, sai ta kara girma " Umma ta ce "Ayko muna dawowa zaku tare, hada mu dau hakki, Hali tana da jikin girma idan ta kara yaya, gwara ka tare da matar ka idan ma kasar zaku bari tare kuje can ku kare" Ya ce "Naga Halama matan nan sun daina so na tunda suna nema su hada ni da bafulatana" Mama Suwaiba ta ce "Son kenan akwai wani so ne da ya wuce wannan" Su suka haɗa tafiyar tare da tsaraba, suka shirya suka tafi riga saidai Labari ya sha bam-bam dan gurin bukkar ba kowa ko bukkar ma babu, Hali tana ganin haka tasa kuka Umma ta ce "Ke me haka kika sani ko sun canza waje ne" Ta ka'da kai cikin kuka ta ce "Wallahi Umma basu kada kai ba sun tashi ne sun tafi sun barni " Alhaji Ibrahim ya ce "Ko sun tashi ay su sarki zasu san inda suka je " Ta sake kada kai ta ce "Ba wanda zai sani baza su fada wa kowa ba kuma ma baza su san lokacin da zasu tashi " Alhaji ya ce "Muje gun sarki", bayan an musu tarba ta musamman Sarki yake basu Mummunan Labari ya ce "Bayan tafiyan ku Mutanen ringan nan suka ringa tsegumi wai Buba ya siyar da Bilki yanzu gashi ya siyar da Hali, na tsawatar amma ina har saida taka idan an ganshi ake gudu wai ya siyar da yaransa ma balle su, abin da ya ishi Buba sai ya kaɗa shanun sa ya dauki matarsa suka bar rigar nan, da daɗewa ita Addan nata Bilki tazo ita ma tasha kukan ta har tana cewa da tasan da auren da baza'a taba yi wa ƴar uwanta irin wannan aure ba. Haka ta koma" Hali ta ce, "To ka kaini gurin ta mana" Ya ce "Garin da take Babban gari ne ko munje baza mu gano inda take ba tunda bamu sani ba" Alhaji ya ce "wani gari ne" Ya ce "Tana cikin birnin Kaduna" Shiru Alhaji Ibrahim yayi yayin da Sautin kukan hali ke tashi Su Umma na lallashin ta. Karshe haka suka dawo gida saidai sun bada Address kan cewa duk lokacin da Addan ta tazo a kawo ta, duk da sunsan baza ta zo ba tunda tasan ba Iyayen ta... _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/15, 7:50 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *Wa shafi naki ne Mrs Basakkwace kiyi yadda kike so da shi in kinga dama ki hana kowa karantawa, Ina son ki Khadijatul kubra* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 7&8 Sunyi niyyar ta tare da Alhajin ganin tana cikin damuwa yasa suka kyale ta kuma suka yi ta kwantar mata da hankali suna bata baki kan cewa ko ta rasa iyayen ta ay tana da su, kuma suna sa ran ko wani lokaci Addan ta Bilki zata zo gare ta. Saida ta kwantar da hankalinta sosai sannan suka gyara mata daki aka saka mata kaya sosai Mama Suwaiba ne tayi ta sata a kan hanya ta yadda zata kula da shimfiɗar mijinta, da farko taki ta ce ita a dakin Umma zata c gaba da zama saida suka nuna mata ɓacin ransu sannan ta amince, ta tare a ɗakinta, sun ce ta huta zasuna aikin gidan amma taki nan ma saida Mama Suwaiba ta mata da gaske sannan ta Amince, da hutun saidai ba satin ta guda taki ta fito tana yin aikin gidan badan sun so ba suka kyale ta, Sassafe idan ta tashi zata fara gyaran gidan sannan ta shiga kicin ta musu kumallo bata barin su suyi wani aikin sudai nasu Miji ya shiga dakin su, Alhaji Ibrahim yana lure da ita yana jin dadin kasancewarsa matarsa bata rage shi da komai ba, ko fushi taga yana yi sai tasan yadda tayi ta kwantar masa da hankali, da farko yana jin kunyar kasancewa tare da ita kasancewanta yarinya karama amma daga baya ya lura yarinyar ba irin wacce za a ji kunya bane, dan su Mama Suwaiba sun nuna mata koda zana jin kunyar kada ta ji kunyar mijinta. Mama Sauda kuwa ganin Hali yariya ce ta fara shiga dan ta zugata saidai kuma bata samu nasara ba dan Umma da Mama Suwaiba sun ɗora ta akan turba me kyau karshe ma ce mata tayi "Kinga Mama Sauda Idan fa baki barni ba zan fada wa Umma da Mama su dau mataki a kanki" Ta ce "Eyeh! Umma da Mama ma kike ce musu, niko me zaisa iyi wannan in kira kishiya ta Umma ko Mama" Hali kuwa Murguɗa mata baki tare da jan wani dogon tsaki tayi ta tashi a gurin. Haka ta hakura bata sake bi ta kansu. Watanta biyar da tarewa Umma ta fahimci Hali ciki gare ta, saboda farin ciki bata iya boyewa ba ta fada wa yan gidan, tana ji kuwa Hali ta shige ɗaki ta kasa fitowa duka dariya suka yi har kowa yayi shiru Alhaji ya kasa rufe bakin ji yake kamar yau za'a fara masa haihuwa, Mama Suwaiba ta ce "To Alhaji rufe bakin mana" Ya ce "Ohhh wai bakin a buɗe yake" Tunda aka bayyana cikin take zaman ɗaki bata fitowa sai idan taga ba kowa a faron zata fito da dogon hijabinta tayi abin da zata yi ta koma, suna lure da ita hakan ma ya basu daman yin aikace-aikacen da ta hana su ne" Idan ko ta fito taci karo da Umma ko Mama Suwaiba da gudunta zata koma ɗakin saidai suyi mata dariya kawai, su Abubakar ne bata jin kinyarsu kuma sukan shiga ɗakin har ta musu tatsuniya. Cikin hakan ne cikin ta ya kai na haihuwa, tana zaune kan Sallaya bayan ta idar da Sallah isha Usman na zaune bakin gadon ta, yana jiran ta masa tatsuniya ta kalle shi ta ce "Usman yau bana jin dadi zan kwanta da wuri kuje kuyi karatu da Mama " Ya ce "Nima anan zan kwana" Ta ce "To Abubakar fa" Ya ce "Ohonsa" Tun tuni take jin maranta na murɗawa yanzu kuma taji tana jin bayan gida ta tashi zata naɗe sallayan sai ta koma ta durƙusa a gurin saboda wani azababben ciwon da koda uwarta ta haife ta bata taba yi ba. Ta durƙusa tana salati, ganin Halin da take ciki ne yasa Usman ya fita da gudu yayi Falo dukan su suna falon ya ce "Ummi bata da lafiya kuzo kuga yadda take" Kafin kowa ya tashi Abubakar yayi gaba da Gudu Umma ne ta jawo shi ta ce "Kada naga ka shiga ɗakin nan" Suna shiga suka samu tana nishi ga zufa da ta hada ga kuma kwaton hijabinta, suka kamata zasu ɗagata tayi wani dogon Nishi sai ga Yarinya ta sulluɓota, tana fitowa ta zandara kuka da kara, da sauri Umma ta tare ta tana faɗin Alhamdulillah, Mama Suwaiba kuwa fita waje ta fada wa Alhaji cewa Hali ta haihu, ya washe baki ya ce "Me aka haifa? " Ta ce ay sai sun fito Suna zazzaune Umma ta fito da Babyn ta miƙawa Alhaji ta ce "Barka Alhaji an samu ƴa mace" Ya amshe ta yana mata Addu'a, Sannan ya miƙawa Mama Suwaiba ita ma ta amsa tana mata Addu'a sannan ta miƙawa su Abubakar sai murna suke, Tuni aka kira yan uwa da abokan arziki ana shaida musu haihuwa Saida aka gasa mata jikinta aka yiwa jaririyar wanka ita ma tayi wanka sannan Alhaji ya dauke su tare da Umma suka yi asibiti, aka duba su, da uwar da ƴar duka lafiya. Sai dai kuma Hali sam taki yarda ta amshi yar wai kunyar ta take ji idan an mika mata ma saidai ta kauda kai ta rufe idonta. Umma tayi tayi amma ko ɗago ido ta kalli ƴar ma taƙi yi, Mama Suwaiba kuwa da tazo bata mata da wasa ba haka ta ɗaga mata riga tasa mata ƴar a cinya ta kama hannun ta ce "Idan baki rike ta kin bata nono ba wallahi baza mu shirya da ke ba, wannan wani irin abu ne " Haka ta rike tana bata saidai kanta na gefe ko kallon ƴar bata yi. Basu ce mata komai ba sudai burin su ya cika da har ta yadda ta batan. Bayan kwana biyu kuwa Alhaji ya ce zai raɗa mata suna to dama Mahaifinsu Malam hamza ne mai raɗawa yaransu sunan saidai shi ya rasu dan haka ya samu Hali ya ce "Wani suna za'a sawa ƴar taki" Ta kwanta ta nutsa kan ta cikin filo a hankali ta ce "A saka mata Sunan Adda Bilki" Dariya yayi ya fito falo ya amshi yar a hannu Umma ya raɗa mata suna BILKISU, Dama ƴar a gurinsu take sai in zata sha nono ne suke kaita sai kuma bsrci, da daddare kuwa sai ta tashi tayi ta kuka amma Hali haka zata juyar da kanta gefe tana jin ta sai wani daga cikin su ya shigo ya dauketa a mata magana ta bata nonon. Anyi taron suna inda yarinya taci suna BILKISU, Saidai yarinyar kwata-kwata bata san daɗin uwa ba, saidai Mama Suwaiba ne ke jigila da ɗawainiyarta, Haka rayuwa ta ci gaba inda Bilkisu tayi girma amma bata san daɗin uwa ba, ko tana kuka saidai yayyenta su lallashe ta ko Umma ko Mama amma da zata kwana tana yi Ummi baza ta ce mata ci kanki ba sadai ta kawar da fuska. ( Nikan na ce ohhh wannan kunyar Fulani na ɗan fari bata yi ba) shekaranta ɗaya aka yayeta Mama Suwaiba ce ta dauke ta ta kwashe kayanta ma daga dakin Hali ta kawo dakinta, a tunanin su zata damu sai suka ga ma hakan da aka yi tafi sake wa. Gata kuwa tana samu gun yayyen ne ga Umma ga Mama har da Alhaji suna ji da ita, amma banda Hali, ita kan Bilkisu ma ko gurin ta bata zuwa, saidai idan su Abubakar sunje suna barin gurin ita ma zata bar gurin. Shekaranta biyu suna zaune suna wasa da su Abubakar ita kuma Ummi tana kicin su kuwa su Umma suna Falo suka ji Sallama Suka fito Sarkin Fulani ne tare da wata Mata da yaron ta sa'an Abubakar sai yarinya mace a bayanta, Mama Suwaiba ne ta shigo da su har falo Matar ta kyalla idon ta a kan Bilkisu sai kallonta take, Mama Suwaiba da taga haka sai ta dauke ta ta sata a baya, Mama Suwaiba ta shiga kicin dan ta kawo musu abin sha taga Hali a ciki ta ce "Ki fito munyi baƙi" Hali ta dauko ruwan yayin da Mama Suwaiba ta tsaya haɗa musu kayan ciye-ciye ta fito da ruwan kenan suna haɗa ido da Matar Hali ta saki abin shan hannunta ta ruga da gudu tana cewa "Addana" suka rungumi juna sai suka saki wani kuka me ban tausayi, Saida sukayi Kukansu sosai ba wanda ya lallashe su sai tausayin da akayi ta ji, Saida suka ci suka sha sannan Sarki ya ce "Halima duk abin da kika ji daga bakin ƴar uwar ki kada ki tada hankalinki ki kwantar da hankalinki haka Allah ya kaddaro muku. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[5/16, 7:38 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ _Gaskiya bana ganin Sharhi kuma ya kamata a na yi ɗin_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 9&10 Kallonsa duka falon suka yi Umma ne ta ce "To baza ka jira Alhajin ku gaisa ba" Ya ce "A'a zan tafi kawai" Yana tafiya Hali ta ce "Adda kinga yadda Allah yayi da mu ko" Ta fara bata labari daga farko har ƙarshe har irin yadda su Umma ke kula da ita, saidai kwata-kwata bata sa labarin Bilkisu a ciki ba, ko faɗa ma ta haihu bata yi ba. Saida tayi shiru shiru Mama Suwaiba ta ce, "Lallai ma Ummin Yara kin iya fada mata komai amma baki fada mata labarin takwaranta ba" Ta ce "Hmm " Umma ta ce "Ay dama na san baza ta faɗa ba, to dai nata faɗa miki maganan haihuwa ba" Umma ta bata labarin komai da yadda akayi ta fama da ita wajen renon yarinyar karshe ta ce "Tunda Maman yara ta dauke ta har yau ko kallo ba ya haɗa su da ita, na rasa wannan wace irin uwa ce, ace ka haifi ɗa a cikin ka amma ka nuna rashin kulawa." Adda ta ce "Ni ya kamata nayi wannan rainon wa yara na, tunda ni nasha wahala, dan na taso koda ina buƙatan taimako idan ban samu ba zan mutu mahaifiyar mu ba za ta taɓa taimaka min ba, Sai Baffa shine gata na shine ya raine ne, Amma Inna ko zan mutu ba ruwan ta dani. Amma kin ganni tunda nayi aure na haifi Aliyu naga yadda ƴan binni suke ji da yaran su nima na ɗauka, Aliyu y more ni sosai dan ban kuma haihuwa sai kwana nan yanzu Maryam watan ta bakwai bazan bari su sha wahala ba, ni tunda na shigo naga yar sai naga Fuskar Hali, don abin da tabar Hali tana ƙarama. Hira suka yi sosai kamar sun san juna Daga baya ne Hali ta ce "Adda me ya faru naji ɗazu sarki yana min wani magana wai inyi haƙuri da abin da zaki faɗa min" Adda Bilki ta ce "Haka ne Hali Saidai muyi haƙuri da iyayen mu, an samu labarin su a wani riga saidai kuma bukkan su ta kama da wuta sun ƙone gaba dayan su " Hali ta dafa kirji ta ce "Inna da Baffan? " Nan fa ta fasa kuka Adda ta rungume ta tana kuka tana bata hakuri sannan taci gaba da fada mata, An kawo wa Sarkin Fulani Shanun na cesa ya ci gaba da mana kiwo" Alhaji da ya dawo yaji wannan Al'amari ya tausaya musu matuƙa kuma ya kwantar musu da hankali. Kwanan Adda da yaran ta huɗu a gidan sannan ta koma Kaduna Alhaji kuma ya mata Alƙawarin zai kai mata Hali. Hakan kuwa aka yi ya kaita din daga baya kuma ita da kanta take zuwa ko ita Addan ta je, ko yaushe Addan nata tana bata baki akan tana kula da ƴarta Bilkisu amma ina ba ma abin da ya dame ta da ita ita ma Bilkisun yanzu bata damu da ita ba. Idan yayyenta suna gida kullun tana tare da su, wataran ma Idan Umar yazo dashi ake, sun shagwabata sosai, ko abu take so sai tasa kuka, idan ance menene sai ta ce "Ita a bata kaza" Haka kuma iyayen basa son suji ko da nishi ne, uwar gayyar ko ko oho. Tunda ta gane Umar zuwa yake yi, yasa da zaran ta ganshi sai tasa kuka idan ance menene, sai tace "Ya Umar ya je gidan su " Abubakar ya kalle shi ya ce ka mata wani abu ko, yakan ce A'a sai ya ce to tafi gidan ku, nan kuma zai fara lallashin ta, ita kuma ta ƙara narkewa, ta jina tana yiwa Umar haka kuma abin da take masa yana bashi haushi dan haka ya sa mata ƙahon zuƙa da zaran ya shigo tana ganin sa kafin ta fara kuka sai ya bubbuge mata baki yace "kuma kika fada sai na ballaki, shegiya zabiya" Hakan yasa ta fara jin tsoron sa haka zai shigo ya bubbugeta idan anzo anga tana kuka idan aka tambayeta sai tayi shiru su kuma su lallashe ta. Shekaranta tara Mama Suwaiba ta kwanta ba lafiya koda aka kaita asibiti aka tabbatar tana ɗauke da juna biyu, murna gurin ba'a magana, saidai cikin nata yazo mata da laulayi ƴan gidan suke taimaka mata da komai Musamman Bilkisu duk da yadda take da ƙananun shekaru amma ba'a barta a baya ba, Makaranta take rabata da Maman nata da ta taso saidai ta zauna ɗaki tare da ita, ko ta ce su fito falo, kullun tana jikin ta da yake Allah yasa ita ɗin me son jiki ce. Har cikin yakai haihuwa tana abu ɗaya ga kumburi da tayi, bata cin gishiri, daban ake mata girkin ta. Lokacin haihuwan kuwa nayi riƙe ta suka yi asibiti saboda jikin nata, kullun Bilkisu na tare da ita wata ran ma bata zuwa makarantar, koda haihuwan tazo tasha wahala dan saida aka saka mata ruwan naƙuda ta haifi ƴarta mace, tubar kallah da ita, saidai kuma ita ta haɗu da tsinka-tsinka Bilkisu kan kuka ta sa Abubakar ya fita da ita, shi ɗin ma ya daure ne saboda ƙanwar tasa, tana kukan Umar ya shigo yana mata wani kallo duk kuka da take ta gimtse ta kwanta cinyar Abubakar ta rufe Fuskar ta da tafin hannun ta. A ciki kuwa tana dawo wa hayyacin ta ta kalli Hali dake rike da ƴar Hali ta ce "Kinga abin da kika haifa" Tasa hannun ta a akan jaririyar ta ce "Allah ya mata Abarka, Allah yasa ta Amfane mu haba ɗaya, " Umma ta ce "Ɗan rungumeta ki bata Nono" Ta kaɗa kai ta ce "Ummin yara zan bar miki Amana, ga Bilkisu Amana ce a gurin ki, ina son daga nan har ƙarshen rayuwarki ki kula min da ita, nasan su Umma da yayyen ta zasu bata kulawa, kece baza ta samu ba, amma ina roƙon ki ki cire kunyar nan ki rungumi ƴarki dan Allah. " Hali dasaurin kuka nan da nan ta fara kuka tana cewa "Ni ki daina wannan magana lafiyarki ake nema yanzu " Ta ce "Bazan bari ba har sai kin min Alƙawari daga yanzu zaki jata a jiki" Ta ce "Eh nayi Alƙawari kema kiyi shiru" Ta ce "Alhamdulillah nagode miki" Ta kauda kai ta yi kallar shahada daga nan kuma tayi ƙatuwar shaƙuwa sannan rai yayi halinsa. Suna zaune suka ga Ummi ta fito tana kuka Umma ma nayi Abubakar ya miƙe ita ma ta miƙe ta ce "Umma Mamana ta mutu ko" Umman ta rungumeta tana kuka tana cewa "Muyi haƙuri Bilkisu " Kuka tasa me tsuma zuciyar me sauraro, Abubakar ya kamata shima yana zuba hawayen yana bubbuga mata baya alamun rarrashi, Baba Jafaru Mahaifin Umar shi ya maida su gida Alhaji da sauran Al'umma kuma suka taho da gawar. Nan aka mata sitira aka kaita gidanta na gaskiya, (Gidana, Gidanki, Gidanka, Allahu Akbar Allah yasa mu shiga a sa'a) Bayan anyi bakwai kowa ya watse yarinya dai aka mata huɗuba da suna Khadija Hali take shayar da ita, kuma shayarwa ba irin wanda akayi wa Bilkisu ba, ta bata kulawa sosai ta mata kyakykyawan shayarwa. Tun bayan rasuwan Bilkisu ta fara ganin abin Mamaki wai Ummi tace take sata a cikin maganar ta har ta ke kiran ta Addana ko ta sata aiki, Amma hakan baisa Bilkisu walwala ba har yanzu tana jin mutuwar Mamanta. Tun tashin Khadija bata samun kulan da akewa Bilkisu a gidan bata shagwaban da Bilkisu take, ta girma ma amma abu kaɗan saita fara kuka, nan kowa yan gidan zasu zo kanta har Khadija ma da Ummi take ce mata Khadiyo shine kowa ya ɗauka ta gane dane idan abin ya tashi da ita ake lallashi. Umar ne ke taka mata burki idan yazo gidan bata sakewa kwata-kwata, shi kuma hakan ya bashi daman yi mata mugunta yadda ransa ke so idan su biyu ne a gurin. _Kan labari_ _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/16, 8:11 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *Wannan page ɗin naki ne Juwairiyya Adam (Aunty Juuuu Ƙamshi) kiyi yadda kike so dashi ƴar uwa* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 11&12 Bayan sun gama Su Bilkisu su ka kwashe kayan suka je suka wanke da suka dawo ne Khadoyo ta ɗauko jakar ta tayi gun Ya Usman ta ce "Muyi karatu, ita kuwa shagwababbiyar jikin cinyar Abubakar taje ta kwanta Khadiyo ta kalle ta ta ce "Wallahi kamar baki girma ba Aunty" Ta ce "Barni nayi ay lokacina ne" Umma ce ta shigo da Sallamarta Bilkisu ta tashi tana cewa "Umma ina kika shiga kika barni ni ɗaya a gidan" Ta ce "eh da yake Ummin naki naki ba mutum ba ce ko" Ta ce "Nidai ban faɗa miki haka ba" Alhaji ne ya shigo fuskarsa da damuwa yana zuwa ya zauna a kan kujera mai zaman mutum ɗaya ya kama kansa Umma tazo ta zauna kusa da shi ta ce "Alhaji lafiya kuwa" Ya dago kai yaga yadda yaransa suke kallon sa yayi Murmushin ƙarfin hali ya ce "Ku taya ni da Addu'a" Umma ta ce "Me ya faru" Ya ce "Akwai wata mace wacce take son aure na, ni kuma ban aminta da tarbiyyan ta ba shine naki ita kuma ta ce ko ta yaya sai na aure ta, na shiga damuwa da jin hakan" Umma tayi murmushi ta ce "Haba Alhaji wannan ne zai dame ka, kaida kake da Allah zamu yi Addu'a in Allah ya yarda ba yadda za'ayi ka aure Allah ya fita " Bilkisu ta ce "Abba ni ka faɗa min wacece inje in same ta" Ya ce "Adda wannan ba hurumin ki bane ke dai ki taya ni da Addu'a kawai" Bayan Sati ɗaya da yin hakan kuwa Alhaji ya tara iyalensa duka saida suka hallara kowa da kowa ya ce "Abin da yasa na tara ku, shine ina son sanar da ku cewa zanyi aure " Shiru kowa yayi Umma ce ta yi karfin halin cewa "To Alhaji wa zaka aura kuma" Ya ce "Ina ga ay kinsan ta, wacce na taba faɗa muku Ummin yara ne bata san zancen ba" Shiru Umma tayi ta kasa cewa komai Bilkisu ce ta ce "Amma fa Abba kai kace baka amince da tarbiyyan ta ba, kuma ka ce mu taya ka Addu'a akan ta, ay muna maka" Usman ya ce "Eh haka ne muna yi, To yanzu me yasa zaka aure ta" Ya ce "Auren wannan mata lada zan samu, kunga tana da ƴa mace, kuma daga ita har yar yawon banza suke, kinga idan na aure ta sai in hana wannan yawon banzan" Umma ta girgiza kai ta ce, " Lalle baka cikin hayyacin ka Alhaji, da bakin ka ka ke cewa tana yawon banza kuma kake son haɗa zuri'a da ita" Hali ta ce "Idan kana neman shawaran mu ne Alhaji to zancen gaskiya kada ka aure ta, dama kamilalleya ce mana" Shiru yayi kamar mai tunani Bilkisu ta ce "Abba ka duba mana, ni dama ka bar maganan wani aure tunda ga su Umma" Ya ce "Adda bana jin daɗi idan ina ganin su su biyu Ina son wanda zata maye min gurbin Suwaiba ba ne" Umma ta ce "Aure bamu hana ka ba amma kuma bamu yadda ka auri wannan matar ba" Ya ce "To na ji, idan na aure ta zan raba muku gida zan ajiye ta a wani gidan daban " Sai lokacin Khadiyo tayi magana ta ce "Gaskiya Abba kabar zancen nan" Ita kan Bilkisu kuka ta saka jin kukan Bilkisu yasa ya mike ya koma ɗakin sa ya rufe, kowa ya zuba masa ido cikin mamaki, Bilkisun ma kukan nata ya tsaya cak tana kallon ƙofar, sun san dai ko yaya Bilkisu ta sa kuka to fa duk abin da yake ya daina zai lallashe ta, yau gashi tana kuka ya kyaleta. Duka gidan sun rasa kansa baya zama a falo a yi hira idan ya shigo gidan to yana ɗakin sa, Idan zai fita kuwa ko Sallama baya yiwa kowa, kowa abin ya dame shi. Abubakar ya fito kenan sai yaga zai fita ya tare shi ya ce "Abba dan Allah kayi hakuri ka daina ƙaurace mana bamu san abin da muka maka ba kake yi mana wannan horon" Bilkisu tana daga ɗaki tana jin Muryar yayan ta ta fito ta kama hannun Alhaji ta ce, "Abba dan Allah ka dawo gare mu kada wata banzar... " Maganan ta yanke sakamakon marin da ya bata har saida tayi taga-taga zata faɗi Abubakar ya tarota, ya nuna ta da yatsa ya ce "Ke har kin isa ki hana ni abin da nayi niyya to bari kiji daga ke har iyayen ki baku isa ba, Kuma nan da Sati biyu za'a ɗaura min aure da Talatuwa, duk cikin ku wanda baya son wannan aure ya bar gidan, gida ay nawa ne ba na wani ba" Yana gama faɗa ya fita abin sa. Abubakar kuwa yaja kanwarsa zuwa ɗakinsu yayita rarrashinta, dama me neman kuka an jefe shi da ɓawon gyaɗa. Tun lokacin ba wanda ya ƙara tunƙaran sa, Sati biyun yana cika kuwa Aka daura aure, sai zuwa musu yayi da goro ya kira Umma da Ummi har daki ya ce "Yau an ɗaura min aure da Talatuwa Mama Ruky na kiraku daki ne na faɗa muku saboda naga yanzu ƴaƴan ku basu da kunya... _Ayi hakuri da ɗan wannan wayar ba caji_ _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[5/18, 8:15 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 13&14 Umma tayi murmushin ƙarfin hali ta ce "Allah ya baku zaman lafiya Alhaji, kuma yaran mu ba suyi maka wani rashin kunya ba, idan kana tunanin haka ma to kayi haƙuri yarinta ne, muma ba munƙi auren bane, yadda matar take ne amma Allah ya bamu zaman lafiya" Ya ce "Amin idan da gaske kike" Ƙara kallon sa sukayi kamar masu nazarin wani abu, shi kuwa ba abin da ya dame shi harkokin gaban sa kawai yake yi. Ba wanda ya kuma masa maganan shi ma baiyi maganar a kowa, baya ma zama dasu yayi wani taɗi da su, Sati biyu da yin hakan ya shigo bayan Isha ya same su duka a falo ya zauna Ummi miƙe ta kawo masa Abinci ko kallon abincin baiyi ba sai cewa yayi "Yau Talatuwa ta tare gidan ta ma zanje in kwana" Umma ta ce "Ina ce anan zata tare" Ya ce "A'a na kama mata haya kunsan ita da ƴarta ne " Ta ce "To ay a gani na ɗakin Marigayiya ya isheta ita kuma Ƴar tata sa haɗu da su Bilkisu " Ya ce "A'a ita ta ce tana son a ware wa ƴarta ɗaki ɗaya ne kinga ay ba gun zama a nan" Umma ta ce "To Alhaji ay shikenan Allah ya baka ikon yin Adalci a tsakanin mu" Ya miƙe yayi hanyar ƙofa Bilkisu zata yi magana Umma tasa ɗan yatsan ta a bakinta alamun tayi shiru. Bayan ya tafi Abubakar ya ce "Umma me ke faruwa ne, kiga fa ko abincin da aka kawo masa ya ƙi ci" Ta ce "Ina tunanin Sauri yake yi, muyi masa uzuri" Bilkisu ta ce "Uzuri Umma, amma fa... " Umma ta ce "Bana son dogon zance" A ƙa'idar musulunci kwana uku yake a ɗakin bazawara amma Alhaji saida ya share sati bai shigo gidan ba, ranan da sati ya cika Ummi ta kalli Umma da take kusa da ita ta ce "Yaya anya Alhaji lafiyansa kuwa, idan Amaryarsa budurwa ce ya kamata ace yau ya dawo gare mu" Umma ta ce "Haka ne, amma mu bashi uzuri" Ta ce "Amma wani uzuri zamu bashi yanzu, ya kamata a ce ko a waya ne ya kira mu" Ta ce "Mu sai mu kira muji ay" Umma ta ɗauki waya ta latsa number sa bugu ɗaya aka ɗauka saidai maimakon taji muryan Alhaji sai taji wata ƙatuwar Murya har saida ta tsorata "Hello waye" Ta ce "Dan Allah ina mai wayar" Aka ce "Wai ke wace irin ƴar tasha ce zaki kira min miji kina kuma kuma tambayar ina yake" Anan Umma ta gane Matarsa ce sai ta ce "Kiyi haƙuri ni uwar gidan sa ce" Taja wani dogon tsaki ta ce "To ya shiga wanka sai ki bari idan ya fito, shashasha kawai" Tana gama fada taji ɗif alamun an kashe wayar. Umma ta bi wayar da Kallo yayin da Ummi kuma take kallon ta dan duk taji abin da suka yi. Ummi ta ce "Yaya... Wannan wacce irin mace Alhaji ya auro? " Ta ce "Allah kaɗai masani" Suna jira suga ko ya kira shiru har suka shiga kowa ya kwanta, washe gari da safe ma shiru, har saida rana sai gashi ya shigo duka suka masa sannu da zuwa suka gaishe shi ya amsa zasu masa magana ya katse su ya ce "Me yasa dan kin kira ni Talatuwa ta ɗauka amma tsabar rashin hankali kika zage ta, me ta miki" Ummi salati ta fara yi tana tafa hannu yayin da Umma kuma take kallonsa cikin mamaki dan ta kasa magana, shiko ya ci gaba "Dama tunda na ƙirƙiro wannan auren na lura bakwa so, kun ziga ƴaƴanku suna min rashin kunya kun ɓata min tarbiyyan ƴaƴa to bari kiji sai kisan yadda zaki yi Talatuwa zata dawo wannan gidan kuma ta zauna wanda bazai iya zaman gidan ba sai ya kama gaban sa" Umma ta ce "Ita Talatuwan ne ta faɗa maka haka to na barta da Allah" Ya ce "Nidai na faɗa da daddare zata zo ta zaɓi ɗakin da take so" Umma ta ce "Allah ya kawo ta " Baice komai ba ya fita, bayan ya fita Ummi ta kalleta ta ce "Yaya... " Saboda ɓacin rai bata ce komai ba. Da daddare kuwa suna zaune a falon su Abubakar suna ta cin Abinci ita ko Bilkisu ba cin abincin suke ba amma ta dame su tsokana ta taɓa wannan ta tsakuli wancan, Khadiyo kuma tana kwance tayi matashi da cinyar Umminta. Ganin wata ƙatuwar mace suka yi ta shigo fuskarta ba alamar fara'a ba Sallama tana zazzaro ido sai wata matashiya a bayanta, ta saka wasu shegun kaya, rigane wanda duk rabin nononta a waje suke sai sket wanda aka tsaga shi har iya cinya, ita ɗin ma fuska a ɗaure, duk kan su sun zuba musu ido. Babbar macen tayi ciki zatayi hanyar kicin Usman ya miƙe ya sha gaban ta ya ce "Baiwar Allah lafiya zaki shigo mana gida kai tsaye kuma kin ganmu kina neman shiga inda ba'a baki izini ba, ko da yake yanzu ma ba'a baki izini ba" Tayi masa wani kallo daga bisani ta kutuntumo ashar ta yaɓa masa sannan ta ce "To Bari uban naka ya shigo dan... " ta ƙara lailawo wata ashar ɗin ta yaɓa masa. Bilkisu ta miƙe zatayi gurin su Umma ta tare ta sannan ta ja hannun Usman ta ce "Matar Abban ku ne shi ya turo ta, ta zaɓi ɗaki" Bilkisu ta ce "To dan ya turo ta sai ta nemi ta ci mana mutunci ita ɗin wacece" Ƴar matashiyar ta nuna Bilkisu da ɗan yatsa ta ce "Keeeee idan kina faɗa wa Mamana magana zan ci abu ta kazan ubanki" Bilkisu ta ce "Ehhhh an saba zaman tasha dole a iya ashar" Zuwa tayi ta kama Bilkisu da kokawa ganin haka Abubakar ya jawota ya kwaɗa mata mari, daga marin sai ta kwanta shame shame, ita kan Talatuwa ta kwala ihu tana cewa "Wayyo Alhaji zasu kashe min ƴata Ruky, " Da sauri Alhaji ya shigo yaga Ruky kwance shame-shame. _Ayi haƙuri da wannan ɗin ma mun samu matsalar wuta ne._ *Kuma dan Allah ku taya mu da Addu'a Allah ya tsayar da yajin aikin da ake a jihar mu ta Kaduna.* _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/19, 8:35 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *_Gaskiya bana samun abin da nake so a gurin ku, wato comment da sharhi ko ba komai nima ina son insan cewa labarin yana shi kuma ana jin daɗin sa_* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 15-16 Ya ce "Wa ya mata hakan ita da waye" Nan da nan Talatuwa ta sa kuka wiwi kamar ƙaramar yarinya cikin kuka ta ce "Daga shigowan mu suka kama yi mana faɗa har wacce yarinyar taka tazo tana dukanta suka haɗu da wannan yayan nata suka yi ta duka" Ya ce "Na fa daɗe ina faɗa muku duk wanda bazai iya zama da su ba ya bar min gida na" Bilkisu ta ce "Abba Wallahi ba haka aka yi ba" Tana rufe baki taji ya buge mata baki, da Sauri Abubakar da Usman suka ce "Ahhh" ta tare suka rike ta Abubakar ya ce "Abba yanzu wannan matar har takai tasa kana dukan Bilkisu" Shi ɗin ma mari yaji ya kwaɗa masa, Umma kan ɗakin ta tayi, ita ma Ummi ta shiga, Khadiyo tabi bayan ta, ya kalli Talatuwa ya ce "Ki zaɓi ɗakin da ya miki ita ma Ruky ta zaɓi nata ɗaki" Ganin Inda Umma ta shiga yasa ta nuna ɗakin Umma ta ce "Shi take so, ita ko Ruky ta nuna ɗakin su Bilkisu" Shiga yayi ɗakin ya sami Umma kwance ya ce "Ki tattara kayan ki ki koma ɗakin Suwaiba Amarya ta ce "Tana son ɗakin" Umma ta miƙe ta fito falo ta kalli Talatuwa ta ce "Idan kina son zaman gidan nan ki shiga can dakin, sannan ƴarki ta haɗu a ɗakin yara ƴan matan amma ba wanda zai fita ya bar miki ɗaki" Shiru tayi tana yiwa Alhaji wani kallo wanda kai idan kaga kallon kasan na umurni ne, shi ɗin ma kuma ya gane hakan yasa ya ce "Aisha yaushe muka fara musanyan yayu da ke" Ta ce "Yau! Bazan taɓa barin ɗakina ba, kuma su Bilkisu ba inda zasu je" Talatuwa ta ce "To Alhaji ni gaskiya ka sake ni, tunda naga alama Iyalenka sunfi ƙarfinka" Abubakar ya ce "Ayko sai dai ya sake kin" Da sauri Alhaji ya tunƙaro shi gadan-gadan da sauri Umma tasha gaban sa haɗi da cewa "Ba zai yuyu ina gani ka sake dukan min ƴaƴa ba " Komawa yayi ya zauna yana huci, ita ko Umma ta kalli Bilkisu ta ce "Kije ki kwanta, " sannan ta kalli su Abubakar ta ce "Kuma ku shige ɗakin ku" Duka suka fita daga falon sukayi ɗakin su ita ma Bilkisu tayi nata ɗakin. Umma ma juyawa tayi zata yi nata ɗaki sai ji tayi ya ce "Kada ki sake ki koma ɗakin nan, na gaya miki gida nawa ne, idan baza ki zauna a wancan ɗakin ba ki bar min gidan" Ta juyo ta ce "Ba inda zanje, kuma ina ɗakina banga wanda ya isa ya fitar dani ba" Talatuwa ta ce "Idan kana son in zauna a gidan nan to sai dai ka sake ta, dan idan ba haka ba ta bar min ɗaki" Bilkisu tana daga ɗaki ta jiyo da sauri ta fito tayi ɗakin Ummi ta same ta kwance saidai ba barci take ba ta ce "Ummi dan Allah ki fito kada Abba ya aikata mummunan kuskure" Ta ce "Menene" Ta faɗa mata duk abin da taji, da sauri Ummi ta mike ta fito ta samu Talatuwa tana girgiza ƙugu Ummi ta ce "Haba baiwar Allah ya zaki zo ki samu mace a ɗakin mijinta amma kice dole ta fita, ay ina ga baki mata adalci ba" Ta ɗago wa Ummi hannu ta ce "Banyi da ke ba, " Ta dubi Alhaji da yayi shiru ya sunkuyar da kai ta ce "Malam ina jiranka fa" Ya ɗago ya kalli Umma sanna ya kalli Talatuwa ya ce "Kinga fa ita ce Uwar gida na bazan iya ba" Ta ce "Shikenan Ruky tashi mu koma cikin tasha" Ya ce " Kada kije ko ina" Ta ce "To ka sake ta" Ya kalli Aisha sannan ya kauda kai gefe ya ce "Aisha kinƙi jin magana ta, To koje na sake ki saki ɗaya" Ihu Bilkisu ta saka ta fita afalon tayi ɗakin yayyen ta tana kuka ta samu suna zaune sun haɗa kai da gwiwa, jin kukan ta yasa suka ɗago suna kallon ta tana cewa "Abba ya saki Umma" Da sauri sukayi Falon suna zuwa suka durƙusa gaban sa, Suka kama gwiwarsa Abubakar ya fara magana "Haba Abba shekara nawa kuna tare da Umma amma wata zata raba ku" Usman ya ce "Abba baka cikin hayyacin ka, meyasa zaka aikata haka yaushe ka haɗu da wannan mata" Shidai kallon su kawai yake, Bilkisu kuwa tana ganin yadda Umma ta fito da Akwatin ta Ummi na kuka tana bata haƙuri akan kada ta tafi, ta kalli Talatuwa ta ce "Kema barin gidan nan zaki yi Wallahi " Umma ta ce "Bilkisu bana son rashin kunya ku koma ɗakin ku, su Usman kuma ku tafi ɗaki, Ummin Yara ga yara ki ci gaba da hakuri da su" Ta hango Khadiyo tana kuka can nesa ta je ta rungumeta ta ta ce "Kiyi shiru " Suna gani Umma ta fita sannan ta ce "Kada su koma kada su biyo ta" Kowa sai kuka yake, banda Talatuwa da ƴarta wanda suke jin kansu kamar a Aljanna, shiko Alhaji yayi shiru an kasa gane halin da yake ciki ma. Sai da suka san Umma tayi nisa Bilkisu ta fara magana cikin kuka tana cewa "Wallahi gidan nan ba zaman Lafiya, Abba ka mayar da gidan ka filin yaƙi, dan baza mu taɓa yiwa wannan matar biyayya ba" Abubakar ya ce "Gidanka yana cikin zaman lafiya ka tarwatsa shi, kana tunanin zamu dauke ta da mutunci ne, saboda ita ka kora mana mahaifiya, to yau itama sai ta bar gidan nan, ta koma can gidan hayan da ka kama mata idan ba haka ba zamu mata lahani. Ummi ta rike hannun Abubakar ta ce "Bansan ka da haka na" Bata ankara ba taga ana kokawa da Bilkisu da Ruky, yayin da Khadiyo ma ta shiga suka kwantar da Ruky ƙasa suna duka, gefe guda kuma Usman yayi kan Talatuwa da sandar moper a hannunsa. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/20, 7:08 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Alhamdulillah mun gode wa Allah da ya kawo mana ƙarshen wannan yajin aikin, muna ƙara godewa waɗanda suka mana Addu'o'i* *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 17&18 Sa sauri Ummi taje ta sha gaban sa ta zaro idon ta ta ce "Usman kana hauka ne me kake da niyyar yi, " Ganin haka yasa Talatuwa taje don ceton ƴarta, tana zuwa ta ɗago Khadiyo da hannu ɗaya ta wugar gefe kafin ta kai ga ɗago Bilkisu kuwa ta tashi ta arce da gudu, tana ɗago ƴarta tayi waje da ita daga bakin ƙofa ta ce "To Malam ay sai ka tashi mu tafi" Miƙewa yayi baiyi magana ba su kuwa suna kallon sa ya fita. Usman yaje ya ɗago Khadiyo ya ce " Sannu ko, baki ji ciwoba, ina yake miki ciwo" Ta girgiza kai kwalla yana zuba mata ta ce "Banji ciwon komai na," Suna tunanin zai dawo shiru bai dawo ba ganin dare nayi yasa Ummi ta ce "Kowa yaje ya kwanta a ɗakin sa" Duk da sunje sun kwanta ɗin ba wanda ya rintsa a cikin su, ko wannen su yana tunanin yaya zai raba wannan mata da mahaifinsu. Da safe kowa ya shirya ya tafi inda zaije mazan duka suka yi gun sana'an su da yake suna hutu, matan kuma makaranta dan Bilkisu zata zana junior waec ne Yayin da Khadiyo tana primary 3. Su Khadiyo suna riga tashi dan haka su aka fara tashi drivern da Abbansu ya ɗauka musu ya fara kai Khadiyo gida kafin nan daga bisani ya biya ya Bilkisu a get ya ajiye ta ta shigo falon kai tsaye ba tare da Sallama ba, ganin Talatuwa tayi kwance a tsakiyar falon sai Ruky tana zaune kan kujera tana danne-dannen waya. Ruky ce ta fara magana ta ce "Malama lafiya zaki shigo mana gida ba Sallama ma" Ta ce "Ay baku cancanci Sallama ba, tana gama faɗa ta wuce ɗakin su " Talatuwa ta ce "Barta Ruky Bari uban ta ya shigo ni da uban ta zanyi, dan uwarta ma ta min kaɗan " Shiga tayi ɗakin nata taga ya canja mata tana juyowa taga Ruky ta shigo ta ce "Malama fita min a ɗakina" Yunwa take ji yasa bata tamka mata ba, tayi ɗakin Ummi nan ma komai ya canja sai ji tayi Talatuwa ta ɗuro mata ashar haɗi da cewa "Fita min a ɗakina" Ummi ce da Khadiyo suka fito Ummi ta kama hannunta suka yi ɗakin da Mama Suwaiba ta zauna ta ce, "Yanzu nan ne ɗakin mu dukan mu, " Bilkisu ta ce "Amma Ummi... " Ta ce "Muyi haƙuri bana son wani magana Adda" Shiru tayi ta cire kayan ta tayi wanka sannan ta shiga kicin ba alaman Abinci ta fito ta dawo ta ce "Ummi yau ba abinci ne a gidan" Ummi ta ce tana kallon Khadiyo "Akwai mana, da kika ci ina kika kai sauran" Ta ce "Ay nima naje na duba ba komai a kulan, shine naje ɗakin su Yaya na haɗa Tea na sha" Ummi ta ce "Shine baki min magana na dafa muku wani ba yaushe tea zai ɗauke ku" Bilkisu ta ce "Barin dafa mana Indomei sai muyi Abincin saboda idan su Yaya sun dawo su samu" Ummi ta ce "Abin zai bani Mamaki fa Abincin fa da yawa, mije kicin ɗin in gani" Suka je kicin ɗin ba komai a kulan dan haka Bilkisu ta dafa musu Indomie ta ajiye a tsakiyan Falo tayi ɗaki dan ta kira Khadiyo su ci tare, suna dawowa tare da Khadiyo suka ga Ruky tasa plate ɗin a gama tana ci. Bilkisu tazo da sauri ta ɗaga plate ɗin ta ce "Me haka kuma" Ruky ta kamo plate ɗin Abincin ya zube a ƙasa, haushin haka yasa Ruky ta mari Bilkisu nan aka fara kokawa, Ruky ba Karfi gare ta ba ita ko Bilkisu tasan dabarun kokawa tunda har yanzu yi suke da yayyanta haka ta kaita ƙasa, Ruky kuwa ganin zata cutu yasa ta gantsarwa Bilkisu cizo a damtsen ta, da sauri Bilkisu ta kama gurin ta ce "Kika cije ni" Tayi kanta Ruky kuwa tayi ɗakin Talatuwa da gudu, Khadiyo ta share gurin Karshe itama Bilkisun zuwa tayi ta haɗa tea a ɗakin su Abubakar saboda duk kayan tea ɗin kicin ɗin babu. Alhaji yana dawo wa gidan Talatuwa ta fara kuka tana faɗan karya da gaskiya karshe ta ce "Bazan zauna ba gidan mu zan tafi" Alhaji ya kwala wa Bilkisu kira ta fito, ya ɗauki wayan USB ya ringa zane ta dashi tana kuka Ummi ta fito ta zanye ta, ta ce "Haka ake yi baza ka tambayi ba'a si ba sai ka hau dukan ta" Finciko Bilkisun yayi ya kuma sake zane ta Ummi ta sake rungumeta ta ce "Ina ji Ina gani baza ka kashe min ƴa ba, saidai ka kashe mu tare" Wannan kalma da Ummi ta faɗa yafi komai adaɗi a zuciyar Bilkisu, ji tayi bata jin zafin dukan kuma, sai ta juyo ta ƙara rungume mahaifiyarta tana jin ƙaunarta a ranta, cikin ranta kuwa tana tambayar kanta, dama Ummin ta tana son ta. Alhaji ne ya fara magana da kakkausar Murya, Ruky yayar kice, ta girme ki nesa ba kusa ba, dan haka daga yau kada na ƙara jin wani raini ya shiga tsakanin ku da ita, sannan kuma duk abin da ta saku kuyi shi cikin hanzari" ya Nuna Talatuwa ya ce "Wannan kuma ni na kawo ta gidan nan, uwarku ce, kada na ƙara jin wani ya ƙira sunan ta, daga yau MAMA AMARYA zakuna ce mata, saura Su Abubakar ɗinma zasu dawo su same ni ina dai dai da su" Bilkisu zata yi magana Ummi ta toshe mata baki da hannunta, Alhaji ya ce "Kyale ta tayi wani magana in karya ta" Khadiyo kan kukan da take yi kaɗan-kaɗan ne ya kufce mata ta durƙushe a gurin ta ringa ihu kamar wanda aka aiko mata da saƙon mutuwa. Su Abubakar Suka shigo suka yi kanta suna tambaya, Alhaji ya ce "To ku tsaya kuji" Suma ya gindaya musu sharuɗan da ya gindaya wa su Bilkisu basu ce komai ba sai ɗaure fuska da suka yi tayi. Ummi kan jansu tayi duka suka yi ɗakin da Mama Suwaiba ta zauna wanda shine ɗakin su a yanzu. Abubakar da ya zauna bakin gado ya girgiza kai ya ce "Gaskiya bazai yuyu ba, haka zamu zauna muna kallo, ana ci mata mutunci" Usman kuwa kallon hannayen Bilkisu yayi ya kama hannunta ɗaya ya ce "Me wannan" Ɗora kanta tayi akan kafaɗan sa ta fashe da wani sabon kukan cikin kuka ta faɗa masa irin dukan da Abban ya mata. Abubakar ya matso suka ringa lallashi. Ummi ce ta ringa lallashin su tana musu nasiha tare da basu haƙuri, sannan ta ce suyi haƙuri su bi Umurnin mahaifinsu. Sun ɗauki nasihan ta, suma tea suka sha, sannan Ummi da su Bilkisu suka shiga kicin suka haɗa abincin me ɗan sauƙi, suka shiga da nasu cikin ɗaki na su kuma suka bar musu a kicin. Haka suka ci gaba da zama a gidan suna haƙuri Ummi kuwa kullun tana cikin basu haƙuri da yin Nasiha, lokaci-lokaci sukan ziyartar Umma ita ma nasiha da da basu haƙuri take. Ummi da Su Bilkisu kullun su suke aikin gidan ita ko gimbiya da ƴarta ba abin da suka ita saidai su ci su koshi su ɓata gurin. Bilkisu tana zaune ɗakin Ummi Ruky ta shigo da under weres dinta ta watso su sai fuskar Ummi bata damu ba ta ce " gashi ki wanke min yanzun nan" Bilkisu ta kwasa tayi ɗakin Mama Amarya (Talatuwa) daidai lokacin Ruky ta shiga ɗakin ta watsawa Mama Amarya a Fuska ta ce "Ay uwa bata fi uwa ba" _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *Sannunku da ƙoƙarin comment* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 19&20 Cafko mata wuya Ruky tayi ta ce "Lalle baki da kunya yarinyar nan, a Maman nawa" Buge hannun ta tayi ya ce "Ohhh Maman ki ne Uwa ko, ni Ummi na ba Uwa bace, duk gadaran ku sai dai kuyi amma Wallahi ƙarya kuke ku wulaƙanta min uwa in kyale daga ke har Maman naki, Maman kin banza" Zata juya ta jiyo Mama Amarya ta fizgo ta ta fara duka har da hawa kan ruwan cikin ta, Ummi ne ta fito da taga haka taje gaban ta ta ce "Kiyi haƙuri dan Allah kinga yarinya ce, zan mata faɗa baza ta ƙara ba" Zaro wa Ummi ido tayi saida hantan cikin Ummi ya kaɗa saboda muni da take dashi, ga kuma jajayen ido yasa a duk lokacin da kuka haɗa ido sai ka tsorata, amma duk da haka Ummi tayi ta maza ta ce "Kiyi haƙurin dai baza ta kuma ba" Ta ce "Ta ma kuma dan Ubanta" Ta ɗaga ta Bilkisu tana numfashi da kyar saida taje bakin ƙofar fita ta ce "ba ubana ba" Ta ruga da gudu sai ɗakin yayyenta ta rufo ƙofa kenan ta hangi mutum kan gado zata hau gadon kenan sai gani Umar tayi da sauri ta sauƙa ta fito da gudu tayi bakin falon tana leƙawa taga ko suna nan, sai ji tayi Alhaji ya ce "Ke kuma fa laɓewan me kike" Sai ji tayi Mama Amarya daga ciki ta ce "Yauwa tunda Allah ya dawo da kai, dakai zanyi a gidan nan tunda ta zage ni" Ita kan Ummi ɗaki ta koma, sannan ta ce wa Khadiyo kada ta fita. Alhaji kuwa shiga yayi ya ce "Me aka yi kuma? " Ta ce "Wai ni Bilkisu zata zaga har tana cewa ba'a san ubana ba" Bilkisu ta shigo ta ce "Wallahi Abba ba... " Ganin ya ɗauki abin duka yasa ta kwasa da gudu ta koma ɗakin ta rufo ƙofa Umar ya daka mata tsawa ya ce "Wai me kike shigowa yi ne" Ta ce "Dan Allah kayi haƙuri Wallahi Abba zai dake ni ne, kuma idan ya kama ni sai yayi kusan kashe ni" Ya finciko ta yayi waje da ita ta ƙara komawa, wannan karon bayi ta shiga ta rufe kanta a ciki yayi yayi ta buɗe taƙi, sai ya ce "To ko zan kira shi in nuna masa inda kike" Kuka ta fara tana cewa "Dan Allah ya Umar kayi haƙuri Wallahi idan ya kamani sai ya kusan kashe ni" Da yaga baza ta buɗe ba sai kawai yafito ya ga Alhaji da bulala a hannun sa ya ce "Abba lafiya " Ya ce "Ina Bilkisu? " Ya ce "Abba me tayi ne" Ya ce "Zagin Talatuwa take yi bata da mutunci yarinyar nan" Ya ce "Tana nan a cikin bayi" Alhaji ya shiga, ita kuwa jin shiru yasa ta buɗe ta je ta zauna a bakin gadon, Alhajin yana shigowa kafin ta ankara har ya kamata ya ringa dukan ta ba, tun tana ihu har ta kasa yi, Umar daga waje ya ringa jiyo kukan ta har ya fara tausaya mata ya shiga ɗakin, ita kuwa tana ganin sa, dama neman me ceto take da sauri tayi bayansa ta cukwikuye shi, shiko ya durƙusa ƙasa yana cewa "Abba dan Allah kayi haƙuri baza ta ƙara ba, ta tuba" Ganin haka yafita daga ɗakin. Ya shiga ciki " Tausayinta ya kama Umar ganin yadda jikinta yayi raɗa-raɗa wasu gurin ma saida jini ya fito abin ka da farar fata ya ce "Me yasa kika zage ta" Cikin sheshsheƙar kuka ta ce "Wallahi ban zage ta ba" Ya ce "To me kika yi" Cikin kuka ta faɗa masa komai, Tausayin ta ya kama shi, ya kama hannunta ya miƙar da ita suka fito suka yi falo ya samu ba kowa ya zauna ya ce "Ki kira min Ummi " Ta shiga tana ɗingisawa ta kira ta ta fito, saida ya gaishe ta ya ce "Ummi A ɗan gasa mata jiki zan siyo mata magani, kuma ki daina bari yana mata wannan duka yayi yawa " Ta ce "Adda bata jin magana Wallahi gashi ta jawa kanta ay" Ya ce "komai tayi bai kamata ayi mata wannan dukan ba" Shiru tayi ta je ta haɗa ruwan zafi shi kuma ya fita, suka je bayi Ummi tana mata Faɗa tana kasa mata jiki da nasiha, daga baya ta ce Tayi wanka. Daidai lokacin da tasa kaya Umar ya dawo ya bata magungunan sannan shima ya mata nasiha da mata faɗa akan tana yin haƙuri ( Nikan nace Ohhh su Umar harda su Nasiha) Mamaki fal cikin ranta, kuma taji daɗi sosai. Koda Su Abubakar suka shigo bata faɗa musu ba, ita dai tasa a ranta zata na yin haƙuri da su baza ta ƙara tamka musu ba duk abin da zasu mata kuwa. *** Umar kuwa yana komawa gida ya Samu Mama Sauda ya faɗa mata komai, dama tasan da sakin Umma amma bata san me yasa aka sake ta ba, yanzu a labarin da Umar ya bata t gano Talatuwa sheɗaniya ce, Hatsabibiya ce na ƙarshe dan haka dole ta haɗa kai da Ita. Saidai ta nuna wa ɗan nata ta tausaya wa Bilkisu sosai, saidai a ranta ta tsani Bilkisu musamman yadda ƴan gidan gaba ɗaya suka ɗora mata so. Sun zama bayi a gidan, su suke aikin komai, Ummi har cikin ɗakin Mama Amarya take shiga ta gyara mata ɗaki sannan ta tambayeta ko akwai abin da take so, girki haka zasuyi su zauna su ci, aikin Mama Amarya shine ta kwana da Alhaji a ɗaki, ita kuma Ruky kullun cin kwalliya tasa ƙananan kaya ta fita gun samarinta, duk Bilkisu ta rame ta zama wata iri, tsakaninta da Alhaji sai harara, gwara ma Khadiyo yakan amsa mata a lokacin da ta masa magana. Mama Sauda kuwa an samu abin da ake so dan ta samu shiga gun Mama Amarya tare suke kulle kullen su. Tunda Ruky ta ga Umar taji a duniyarta ba namijin ta kasance da shi irin Umar amma shi ba ta tata yake ba ma, dan yana kallon irin shigar ta bata burge shi kwata-kwata. Basu da wani aiki a gidan sai Addu'a Allah ya juyo musu da kan Alhajin su, Ko yaushe Ummi tasa goshi a ƙasa saidai kayi ta jin ajiyar zuciya alamun kuka da take yiwa ubangijin ta. Ruky kuwa da taga ta na cusa gun Umar amma yaƙi kula ta sai taje ta yiwa Mamanta magana, ta faɗa mata komai. Mama Amarya ta ɓata rai ta ce "Shine tuntuni baki faɗa min ba, Umar ɗin banza, da tuni kun daidaita, yanzun ma barin kira uwar sa a waya In ji" Ta ɗauki waya ta danna number Mama Sauda bugu biyu ta ɗauka bayan sun gaisa ta ce "Kin san menene kuwa, Kamar ɗana da ƴarki sun daidaita kansu" Mama Sauda ta ce "Ban gane ba" Mama Amarya ta ce "Ina ganin da Umar da Ruky sun daidaita me zai hana mu haɗa su Aure" Mama Sauda tayi jim kaɗan, ko kaɗan baza ta so Umar ya kasance da Ruky ba, Yarinyar da bata da kamun kai, yarinyar da uwarta take jigata tabi Maza har ita ce za'a ce sun daidaita kai baza ta saɓu ba. Jin shirun yasa Mama Amarya ta ce "Ya naji kinyi shiru ko baki aminta bane" Ta ce "Ba haka bane Gani nayi Bansan zancen ba, kuma shi Umar ɗin bai faɗa min ba". Murmushi tayi ta ce "Ay bazai faɗa ba, kinsan su da kunya" Mama Sauda ta ce "Idan nazo za muyi magana" A hankali Hankalin Alhaji ya fara komawa kan iyalen sa dan yanzu yakan kira Bilkisu ya zaunar da ita suna hira, saidai ta kasa sakin jikin ta dashi. Yau ta dawo daga makaranta da ƙafa ta gaji ga rana ga yunwa ta shigo gidan da Sallama ta samu Alhaji yana ganin ta ya ce "Adda na tura a ɗauko ki a makaranta ance ba'a ganki na ina kika shiga" Ta ce "Na taho da ƙafa na ne, saboda Mama Amarya tace da driver din ya daina zuwa, kuma Abba ban san zaka tura ba, da na jira dan nima na gaji da zuwa da dawowa a ƙafa" Mama Amarya tayi karaf ta ce "Ay ina da dalilin da yasa nace hakan, Yarinyar da ba karatun take ba, ta ƙware a zuwa ɗakin samari, kagan ta nan ba ɗakin ɗan iskan da bata sani ba, " Ya ce "Adda dama ba karatun kike ba" Ta ce "Wallahi Abba karatu nake zuwa" ta karashe maganan da fashewa da kuka. Ya ce "Wa ya faɗa miki hakan ke Talatuwa " Ta ce "Da idona nake ganin ta, nima nayi shiru ne kada ace na mata sharri dan ba ƴata ba" Bilkisu ta kuma fashewa da kuka zata yi Magana Ummi ta jawota, ta rungumeta ta ce "Ƴata bata bin maza, nasan halinta nasan wacece ita, dan haka kada ki ƙara jifan ta da mummunan furuci idan ba haka ba... " Ta nuna ta da yatsa sannan ta yarfar da hannunta. Mama Amarya ta ɗaga murya ta ce "Ƙarya na mata kenan" nan tayi kanta a lokacin Zuciyar Ummi ta ƙeƙashe, kanta yayi tsauri, komai zata iya yi wa Mama Amarya Zuciyanta na ingizata ta ɗauki makami dan abin nata ya wuce gona da iri, kafin ta ƙaraso Ummi tayi kicin ta ɗauko Wuƙa ta fito tayi kan Mama Amarya da shi gadan-gadan Alhaji ya riƙe ta yayin da Mama Amarya tayi ɗakinta da gudu, Ummi ta fizge a hannun Alhaji ta bita har ɗakin, zuciyarta na ingiza mata yau sai ta ji mata rauni. Shiga tayi ɗakin ta sameta Allah ya ba Alhaji Sa' a ya sake rike ta ya amshi wuƙar ya ce "Baki da hankali ne me kike niyyar yi" Nan fa Ummi ta fara masifa tana faɗa masa maganganu marassa daɗi, "Tunda ka auro ta ka maida mu bayi a gidan mu muke komai kana kallon ta tana abin da taga dama, to Wallahi idan baza ka yi adalci ba ka ringa ganin masifa da tashin hankali a gidan ka kenan, sai anyi magana kace wanda bazai iya zama da ita ba ya bar maka gidan ka, to baza mu bar gidan ba, kuma mun shirya karban ƴancin mu a gidan nan ni da ƴaƴa na" Ya ce "Bazan ga tashin hankali ba, dama naga alama shi kike nema, tunda har kika ɗauko Wuka zaki kashe min matata saboda haka kije na Sake ki Saki ɗaya. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *Auntu Juuu Ina jin daɗin Comment ɗinki yana sani farin ciki kuma ina godiya* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 21-22 Da gudu Bilkisu ta ƙaraso ta riƙe hannunsa tana cewa Abba dan Allah kada kayi haka ka ce ka janye, Abba dan Allah idan kayi hakan ka tarwatsa farin cikin gidan ka ne Abba" Fizge hannunsa yayi ya shiga ɗaki yana jin ɗaci a zuciyar sa da ya iya sakin Amanar da aka bashi. Yana tafiya Mama Amarya ta fito ta ce "Oya maza a koma daji" Ummi ta juya ta fara haɗa kayanta Bilkisu tana kuka Khadiyo nayi Ummi ta tafi, ana haka ta tuba bata ci komai ba tayi kicin dan ta ɗebo ta fara ci tana kuka ji tayi an ƙwace abincin tana ɗaga kai taga Mama Amarya, bata ce komai ba ta koma ɗaki ta kwanta ta kuma wani sabon kukan, har barci ya kwashe ta, cikin barcin ta taji ana dukanta a cinya ta tashi ganin Mama Amarya tayi ta ce "Ki tashi kije ki ɗora mana Abincin dare. Ta tashi a hankali tana jin jiri taje ta fara shirya Abinci tana gamawa ta ɗibi nasu ita da Khadiyo suka yi ɗaki suna ci su Abubakar suka shigo ɗakin tana ganin su ta saki kuka Abubakar yayi ta lallashin ta, Khadiyo ne take faɗa musu komai, komai a kunnen Mama Amarya ake Lalle akwai sauran aiki a gaban ta tunda yanzu akwai wanda zai lallashi Bilkisu, ta fi so ta kasance bata da kowa, tunda yarinyar bata da kunya kuma ta lura Alhaji yafi son ta duk cikin yayan sa. Tana wannan tunanin Sauda ta shigo gidan, suka shiga Ɗaki Mama Amarya ta ce "Albishirinki" Ta ce "Goro" Ta ce "Yanzu Hali tayi waje " Mama Sauda tayi shewa ta ce " Yanzu kika kasance Hajiyar Alhaji" Mama Amarya ta ce "Ban kasance ba tukunna dan akwai sauran rina a kaba" Mama Sauda ta ce "Menene" Ta ce "Su Abubakar bana son su kasance da ita, nafi son sai Bilkisu ta raina kanta duk da yanzun ma ta raina ina son ta kasance a wulaƙance ne" Mama Sauda ta ce "To ki koma gun boka ya watsa su a duniya mana " Ta ce "Ay ita ma Bilkisun hankalin Alhaji ya Fara komawa kanta, dan ina haɗawa da kissa ne yasa dai yake dan ɗage mata kai amma wata rana kinsan komai zai iya lalacewa" Ta ce "Ay gun boka kawai zamu tafi komai ma yayi Ya ƙara dulmiyar da Alhajin sannan ya watsa kan ƴaƴan suje can su lalace, kinga baƙin cikin zai kashe uwarsu in yaso daga baya Bilkisu ma san yadda zata yi ta bar gidan" Mama Amarya ta girgiza kai, ta ce "Bana son tabar gidan nan saboda yarinyar akwai iya girki, ban taɓa cin girki mai daɗi irin nata ba, ko na uwarta, kinga tunda na kora uwar ay ita din ta zauna ko dan gyaran gida da yin girki, amma duk da hakan ina son Alhaji ya yadda da zance na kan cewa tana bin maza" Ta ce "Eh haka ne kan kin kawo shawara kinga ko ta nan ma ya tsane ta, " Dariyan ƙeta Mama Amarya tayi ta ce " To ya maganan Ruky da Umar ɗin" Nan da nan Annurin fuskan Mama Sauda ya canja, Mama Amarya ta dano ta dan haka ta ce "Sauda muna tare da ke amma baki son ki haɗa zuri'a da mu" Ta ce "Wallahi ba haka bane, kin san saboda bai zo min da maganan ba amma ni idan na koma zan masa maganan, haba ya za'ayi na ƙi Ruky ay Ruky ƴata ce" Mama Amarya kan bata aminta da zancen ba dan haka dan haka cikin ranta ta ce "Zaki gane kuren ki, koma ko kinƙi ko kin so sai Umar ya auri Ruky " Ita ko Mama Sauda tana tunanin irin rashin mutuncin da zata yi wa Umar da har ya yarda yake Soyayya da karuwar yarinya irin Ruky. Mama Amarya ta ce "To tashi muje gun bokan muyi yadda za'ayi" Ta miƙe suka tafi. Cikin kursumin daji suka shiga suna ta tafiya gaba daji baya daji har Mama Sauda ta fara tsorata dan bata taɓa zuwa irin dajin ba, suna zuwa gurin Mama Amarya ta ce "To daga nan zamu fara rawan tsohon mawaƙin nan Michel jockson" Mama Sauda ta zaro Ido sai ga Mama Amarya ta fara, itama ta fara lakwashe lankwashe dan ba iyawa ta yi ba, suna isa bukkan sai gashi ya fito yana yin rawan shima saida yazo gaban su ya zauna, suko suna tayi, ya daka musu tsawa saida Hantar Mama Sauda ya kaɗa ita ko Mama Amarya taci gaba da yi sai da ya ce "Zauna Hajiya ya isa amma kuma daga yau kada ki sake zuwa min da wannan sakaryar dan bata iya rawan ba" Ta ce "Za'a koya mata ay" Ya ce "To me ke tafe da ku, ya kike da Bilkisu nasan zaki ce Hankalin Mijinki ya koma kanta, kuma kina son yayyenta su shiga duniya, kuma kina son Mijinki ya yadda Bilkisu tana bin maza ko mu sata tabi mazan" Mama Sauda kuwa Mamaki fal cikin ta, Mama Amarya ta bashi kuɗi ya ce "Kuje za'ayi komai, kwanan nan Alhaji zai kora ƴaƴan sa, sannan Bilkisu zata fara bin maza, kuma zai tsane ta, nasan akwai abin a ranki kuma Sirri ne zan miki Aiki a kan sa shima" Mama Amarya tasan maganan Ruky da Umar ne dan haka ta ce " To Sheɗanina" Zasu tafi ya ce "Yau baza ki bani ba, kinsan idan baki bani ba aiki bazai yi ba" Ta ce "Ay naga kaine baka yi magana ba" Ya ce "To Mu shiga ciki" Mama Amarya ta shige bukkar shima ya bita, suka rufo ƙofa aka bar Mama Sauda a gurin. Sun daɗe sosai a ciki kafin suka fito Mama Amarya tana gyara zanin ta, Mama Sauda tana ganin ta ta gane sunyi Zina ne. (Wa iyazibillah) Boka ya kalli Mama Sauda ya ce " Idan kina son zuwa nan kije ki koyo rawa sannan, dan da rawa ake zuwa" Da sauri ta ɗaga kai dan a tsorace take. Suka tashi suka fita a gurin suna rawan, yayin da Sauda take ta lankwashe lankwashe. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 23-24 Har suka isa gida Mama Sauda Hankalin ta a tashe tunani kala-kala take a zuciyarta, ita dai tasan duk iskancin ta baza ta taɓa bawa wannan ƙazamin bokan kanta ba, kuma ma ko ba shi ba baza ta iya ba, ita dai barta da iskancin ta da hassada. Har tabar gidan tana mamakin ta, ita ko Mama Amarya ko a jikinta harkokin ta take yi kawai. Sun dawo daga gun Sana'an su, kai tsaye ɗakin da Bilkisu take suka shiga suka ganta kwance tasha aiki ta gaji, yayin da Khadiyo take danna mata ƙafa, Usman shima ya zauna bakin gadon ya sa hannu yana danna mata ya ce "Sannu ko Sister kin sha aiki ko, Allah ya baki lada, nasan mijinki zaiyi farin ciki da ke. Murmushin jin daɗi tayi ta ce " Yayana kenan kuka nasan matan ko zasuyi farin cikin samun ku" Abubakar ya ƙarasa hawa kan gadon ya shafi fuskanta ya ce "Kiyi haƙuri da irin zaman da kike a gidan nan na ƙunci, Allah zai dube mu" Hira suka yi daga bisani suka suka fito ta fito raka su, suka ga Ruky ta fito zata fita, wani mini sket ne a jikinta tasha kwalliya, wanda kwalliyar kwata-kwata bata yi kyau ba, ta gansu sarai amma kuma ta taho ta bangaje Usman, ya yi mata mungun kallon ta kalle shi ta ja tsaki, ya kai mata duka Bilkisu ta riƙe hannun, Ruky ta ce "Barshi ya ja ma kansa bala'i dan ubansa" Fizge hannunsa yayi ya je ya bugeta ta faɗi ƙasa warsar, da sauri Bilkisu ta tura shi waje har ɗakin su sannan ta dawo dan ta san Ruky zata iya musu wani sharrin. Ita kuwa da taga ba kowa sai ta tashi ta bisu ɗakin Bilkisu ma ta bita, tana shiga ta samu sun cire kaya suna ƙoƙarin kwanciya ta kama Usman da kokuwa, shi kuma ya ɗauki charger na fitila ya ringa zuba mata a baya dama gashi jikinta ba ishashen kays ba, sai ihu take Bilkisu tana ƙoƙarin hana shi. Alhaji yana daga ɗakin Mama Amarya ya jiyo ihunta a tunanin sa ma Bilkisu ne, yana fitowa falo Mama Amarya tana biye da shi a baya, cikin ranta tana cewa Allah yasa kwarto ne a ɗakin Bilkisu, yaji a ɗakin su Usman ne ya fito zai shiga yaga Ruky ta fito da gudu tana sosa jikin ta, Mama Amarya ta rungumeta ta na cewa menene, shima Alhaji ya zuba mata ido yana jiran jin amsa, Cikin kuka ta ce "Ba Usman bane ya ce In kawo masa ruwa shine na kai masa, shine suka rufe ƙofa shi da Abubakar suka haɗu suka cire min kaya wai zasu min fyaɗe, shine naƙi yadda, shine suka zane ni, kuma Usman ya min fyaɗen bayan nan Abubakar ma wai zaiyin shine yake ta zane ni wai idan na galabaita sai yayi" Daga ciki suke jinta, daga su har Bilkisu da take tsaye a gurin, kasa magana suka yi. Abba ya kalli Bilkisu ya ce "Adda me gaskiyar maganan faɗa min" Lokacin ta samu daman yin magana muryanta na rawa ta ce "Wallahi Abba ba haka aka yi ba ita ce..." Mama Amarya ta katseta ta hanyar cewa "Yi min shiru munafuka kawai, duk halin ku ɗaya ne, to bari yau zamu bar muku gidan ku sannan sai na kaisu koto lalata min yarinya da Usman yayi" Ya ce "Ba inda zaku je, su zasu bar min gidan dan banga amfanin zama da ƴan iska irinsu ba" Bilkisu ta ce "Haba Abba ƴaƴanka ne fa kafi kowa sanin halin su baza su iya aikata haka ba" Kiran su yayi suka fito, ya ce "Ku tattara ku bar min gidana" Abubakar zaiyi magana ya dakatar dashi da hannu haɗi da cewa kuje can kuje kuyi iskancin ku, amma ba a nan gidan ba" Usman ya ce "Abba kayi haƙuri dan Allah ina zamu je, bamu da gurin da ya wuce nan" Ya daka musu tsawa a tare suka tashi zasu koma ɗaki ya sake daka musu tsawa "Kada wani ya shigar min ɗaki" Usman ya ce "Kalli jikinmu Abba ba kaya zamu sa kayan mu ne" Suka shiga kaya suka saka suka ɗauki jakan kayan su suka fito, zasu wuce Bilkisu taje ta rungume bayan Abubakar tana cewa "Ina zaune ne a gidan nan dan ku nima binku zanyi Wallahi bazan zauna ba" Abubakar ya kalle ta yayin da Usman ya sa hannunsa a fuskarta ya ce "Ba inda zaki ce, kedai ki ci gaba da Addu'a, wata rana sai labari" Ta ce "Dan Allah zan biku duk inda zaku je Yaya bazan iya sake zaman gidan ba" Ji tayi Alhaji ya riƙota ya bata wani gigitaccen mari har sai da taga walƙiya, Abubakar ya kalle shi kanar zaiyi magana sai kuma ya juya yayi hanyar fita, Usman ko sai da yayi magana, ya ce "Ita kuma me tayi? " Sake bata mari yayi a ɗayan gefen, ta faɗi ƙasa sai kuma ta miƙe, ya ce "A gaba na kike cewa kina zaune ne saboda ƴan iska, har kina cewa zaki bisu" Zata yi magana cikin kuka, taji Khadiyo ta riƙe mata hannu ta jata ciki, suma basu ƙara magana ba, suka fita waje. Suna Fita Usman ya ce "Ina zamu je yanzu" Abubakar ya ce " Muje gun Umma mu faɗa mata sannan muyi gun Baba Jafar dan bamu da inda ya wuce gun sa" Gun Umma kuwa suka wuce har tayi barci amma saida aka tashe ta, suka faɗa mata komai tayi Mamaki, sannan ta ce "Gwara da kuka zo nan, kuma ba inda zaku je, Karatu zaku tafi kuma ba'a ƙasar nan ba, domin ina son ku tsayu da ƙafar ku, ku wuce wulaƙanci" Suka jinjina kai duka, Ta ce "Yanzu Ina Bilkisun" Abubakar ta ce "Tana gida saidai tana buƙatar Addu'a Umma so suke su nakasa yarinyar nan" Umma ta ce " Baza su nakasa ta ba, tana tare da Allah " *************** Haka rayuwa taci gaba da tafiya Bilkisu ko yaushe tana fuskantar ƙalubale, tun tana ganin hanya ko zata ga yayyen ta amma babu su, Khadiyo kan tunda taje gidan Kakanninta ta faɗa musu halin da suke ciki, Kakarta ta hana ta dawowa, tunda ta tafi kuma Alhaji bai nemeta ba, Bilkisu kuwa da yake tasan inda take bata damu ba ma. yanzu an hana ta zuwa makaranta ma tun tana Ss 2 aka hana ta daina zuwa. Soyayya kuwa ta shiga tsakanin Umar da Ruky, saidai kuma Umar sam baya yadda ya taɓa jikin ta, ita ko bata so haka ba, ta so ne suyi soyayyar shan minti, suna kasancewa, saidai ya ce baya ra'ayin wannan soyayyar auren ta yake son yi. Mama Sauda tayi-tayi ta raba amma yaƙi karshe ma ya daina shigo mata gidan sai dai ya zauna can part dinsa. Yau tasha aiki ta gaji ta kwanta a Falo tana hutawa sai taji Mama Amarya daga kicin tana waya da Alhaji tana cewa "Ka dawo da wuri zan nuna maka, Ina jin ta tana waya tana cewa ita Kaza zata ci ya kawo mata, ashe kullun idan mun kwanta sai ta shigo da shi su kulle ƙofa, wata rana ma a gidan yake kwana, nidai so nake kagani da idon ka. " Sam bata fahimci akan waye ake maganan ba, dan haka bai shafe ta ba, idon ta ya fara rufewa dan barci yasa ta tashi, taje ta watsa ruwa sannan tasa kayan barci Tana son ta kulle ƙofan taga makullin ƙofar an balla, bata damu ba, ta kwanta, barci ya kwashe ta. Cikin barcinta sai taji an shigo, ta tashi ta zauna, taga mutum a gaban ta yana mata murmushi, ya ce "Babyna ga kazar da kika ce kina so, amma kafin nan ki gyara min ki bani daddadan abin da kika saba bani, dan yau a yunwace nazo" Zata yi magana sai Alhaji ya turo ƙofa Mama Amarya tana bayansa, tana cewa "Munafuka to yau asirinki ya tonu, ƴar iska kawai" Shiko kafin a ankara yabi ta gefen su ya fita da gudu. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 25-26 Mungun Kallo Alhaji yayi mata ya sannan ya kalli ledar da Kwarton ya ajiye ya buɗe Kaza ce a ciki gasassiya gashin inji sai ƙamshi ke tashi, ya kalle ta ita ma cikin ledan take kallo tana ganin sun haɗa ido tayi baya dan ta san komai zai iya faruwa, jin muryan sa tayi yana rawa ya ce "Waye shi" Ɗagowa tayi taga hawaye a idon sa, ta shiga tashin hankali wanda yafi na da, muryan ta na rawa ta ce " Wallahi Abba ban san shi ba, shi... " Mari ya bata shima muyan na rawa ya ce "Adda Kin cuce ni kin cuci kan ki, dama halin ki ɗaya da yayyen ki, nayi nadama da na bari kika shaƙu da kannen ki, da nasan haka zaki kasance da ko uwarki naki aure lokacin da aka cusa min ita, auren uwarki ƙaddara ce a gurina tunda ta haifo min ke, kije na sallama ki a duniya BILKISU na yafe ki a duniya, baza ki zauna kina min iskanci a gidan nan ba, kije can yawon barikin kije kiyi tayi" Bilkisu ta ce "Abba dan Allah kada ka kore ni, kaga ko hanyar rigan su Ummi ban sani ba ina zanje, duk kan mu da daddare ka kore mu, Umma ka koreta da daddare tasan inda zata je, haka ma Ummi ita ma tana da gun zuwa, sannan ka kori ƴan uwana, su maza ne ko a Titi zasu kwana ba abin da zai same su, niko Abba ba inda nasan zan nufa kuma idan nace zan kwana a titi Wallahi akwai ɓata gari suna nan zasu lalatani" Ya ce "Dama kin riga kin lalace dan haka kije can kici gaba da lalacewan" Ta kalli fuskarsa taga yadda hawaye ɗaya na bin ɗaya ta miƙe ta sa hannu ta fara share masa ta ce "Abba ka daina kuka nasan kana baƙin ciki akan abin da kake zargi, kuma Wallahi ba haka bane, Abba Wallahi ban taɓa yin zina, kuma ban taɓa kusantar ta ba ko sau ɗaya, nasan hukuncin yin zina, kuma nasan irin abin da zan fuskan bayan nayi aure, Abba ka yadda da ni, bana son ka kore ni, idan ka kore ni ina zan je, ina zan fuskanta, kuma ma Abba ko na yi abin da kake zargi bai kamata ka kore ni ba, sabo da ni mace ce, Addu'a zaka min, dan Allah Abba ka duba min kada ka kore ni" Tayi shiru hawaye ɗaya na bin ɗa ga majina, haka shima. Ganin maganganun zaiyi tasiri yasa Mama Amarya ta ce "Dama haka karuwai suke akwai iya tsara magana " Wani mungun kallo Bilkisu ta mata ta ce "Kada ki kara sa min baki idan ina magana da mahaifina" Kallonta yayi ya nuna mata hanya ya ce "Fita min a gida" Ta ce "Abba kayi haƙuri dan Allah kada ka... " Ya bata mari ya sa ƙafa ya hankaɗata waje ta fito falo ta bugu da kujera a goshinta sai jini, ta dawo ta kama ƙafarsa tana kuka ta na cewa "Abba goshina ya fashe ka kaini asibiti" Ya sake hankaɗata ta faɗi ta kuma tashi ta ce "Abba ba inda zanje ka taimaka min" Ya kama hannunta yayi da ita waje ya hankaɗata, ta faɗi tana miƙewa ta sake biyo shi tana cewa Abba bansan inda zanje ba, ya tokare tada ƙafa a cikin ta, ta sake ƙoƙarin tashi ta koma saidai kuma ya rufe kofar har ya haɗa mata da babbar yatsarta na hannun daman ta, ta jingina da jikin get ɗin ta ci gaba da kuka jini na zuba daga goshinta, can kamar wanda aka tsikara ta miƙe ta fara tafiya tabar unguwar tana tafiya tana kuka, dare yayi sosai ba mutane a hanya taga ƴan sanda da motar su, tana isowa gurin ɗaya ya ce "Daga ina kike" cikin kuka ta ce "Abbana ne ya kore ni daga gidanmu shine zanje gidan Ƙaninsa" Ɗaya ya ce "Me kika yi" Ta ce "Wai yana zargin ni karuwa ce ina kawo maza gida kuma Wallahi ba haka bane" Ogan su ya fito a mota ya kama goshin ta ya ce "Sannu ko kina zubar da jini da yawa muje cikin mota ki huta sannan muje asibiti" Ta bishi suka shiga cikin motar tare, ya kwantar mata da kujera ya ce ta kwanta, ta kwanta, sai jinshi tayi yana shafa mata wuya da sauri ta miƙe ta kalle shi, sai ji tayi ya ce "Baby tsaya mana ba wanda zai ganmu, muna gamawa zamu je in kaiki asibiti, kuma muje ki kaini in kama Baban ki" Ta girgiza kai tace "Kayi haƙuri dan Allah ni... Ji tayi ya rungumeta ya rike ta yana ƙoƙorin cire mata rigar barcin da ta saka. Ita ko duk ƙarfin ta ya ƙare. _Ayi haƙuri da wannan_ _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 27-28 Ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba wajen kokawa dashi, ankwa ta gani a gefe ta dauka ta buga masa a goshin sa, jin zafin gurin yasa ya sake ta, ita kuma tayi sauri ta buɗe mota ta fita da gudu, gudu take tsulawa duk da gidan da nisa bata iya tsayawa ba saida taje bakin get ɗin gidan Baba Jafaru, jiri ta fara ji amma duk da haka ta buga ƙofa da ƙarfi, tayi ta bugawa. Umar kuwa cikin barcin sa yaji ana buga ƙofar da ƙarfi kuma anƙi a daina, tsaki yayi ya miƙe ya ɗauki wata ƴar ƙaramar wuƙa ya fito yaje jikin get ɗin yayi magana da ya ce "Waye" Ba magana sai nishi da ake, ga duk kan alamu nishin mace ce dan haka ya buɗe ya kalle ta ya ce "Bilkisu su, kece,? me ya faru da ke,? Wa ya ji miki wannan raunin? " Bata iya amsawa ba sai raɓawa tayi ta jikin sa zata wuce, jiri ya kwasheta zata faɗi ya tare ta, daga nan kuma numfashin ya ɗauke, jijjiga ta ya ringa yi amma shiru, ya kalli jikin ta duk jini, ga irin kayan dake jikin ta, kayan barci ne, riga da wando, daga shi ba komai a jikin nata danko bra babu balle ƴar singlet, ɗaukanta yayi kamar jaririya yayi ɗakin sa da ita ya ajiyeta kan gado, ya duba agogo ƙarfe 1:45am ya sake kallon ta, a fili ya ce "To me ya fito da yarinyar nan cikin dare a cikin wannan yanayin, kodai wani ne ya mata fyaɗe" Kasancewan sa likitan dabbobi kuma likitan dabbobi suna iya duba mutane, sannan yana da kayan aiki na mutane yasa ya ɗauko ya fara mata dressing din goshin ta da ta bugu sannan ya mata Allura a hannun ta, ya goge mata jinin dake fuskarta ya ɗaga rigar yana goge wanda ya gangaro cikin ta ya fara kaiwa zuwa kirjinsa yaji yanayin shi na neman sauyawa, dan haka ya bari, ya jawo bargo ya rufe ta, ya zauna a bakin gadon ya ɗauki waya ya kira number Baba Jafar, kasancewa dare ne saida ya kira shi kusan sau uku sannan ya ɗauka ya ce "Lafiya kuwa" Ya ce "Lafiya ba lau ba, Bilkisu ce" Ya ce "Wace Bilkisun kuma me ya same ta" Ya ce "Ban sani ba, gata nan dai a ɗakina cikin mummunan yanayi" Da sauri ya tashi ya buɗe ƙofa yana zuwa ɗakin Umar yaga abuɗe kai tsye ya shiga shima ya zauna a bakin gadon ya kalleta ya ce "Ta zubar da jini da yawa ɗauke ta muje asibiti" Kayansa ya saka sannan ya janye bargon ya ɗauke ta, lokacin Baba ya je ya sanar da Mama Sauda ita ko tana ji ta koma ta kwanta abin ta abin ta, bai bi ta kanta ba yaje ya tada mota Umar ya shiga baya rungume da ita, saidai ba ƙaramin dauriya yayi ba kasancewan yadda gaba ki ɗaya yana yin sa ya sauya, har idonsa ya fara canja kala, Tunawa yayi Ruky irin yadda take masa, tana yawan nuna masa suran jikinta sannan tana yawan mannewa a jikin sa, bata taɓa birge shi ko bashi sha'awa ba, saiga ƴar ƙaramar yarinyar nan tana neman dagula masa lissafi, lallai da Bilkisu ce take masa hakan da ta jima da saka masa tarko. Suna isa aka karɓe ta hannu bibbiyu, jinin ta aka fara gwadawa dan a duba ko yayi ƙasa, sun samu yayi ƙasa sosai amma kuma ba sai an ƙara mata ba, idan tana shan kayan ƙarin jini ma ya wadatar, Allura suka sake mata, sannan suka ce idan ta farfaɗo zasu iya komawa gida da safe dan an riga an gama mata komai tun a gida. Ganin yadda likitan ke kallon ta yasa Umar yaja mayafi ya rife mata jikinta ya watsawa likitan kallo, tuni likitan ya kama hanya ya fita. Baba waje ya fita, shiko Umar ya zauna a kujera a ɗakin daga baya ya kifa kansa a bakin gadon barci ya kwashe shi. *** *** *** Tuni Umma ta haɗa musu komai da taimakon Allah sannan ƴan uwan ta suka haɗa musu komai suka tafi Saudi Arabian Karatu, kuma ta ci Alwashin baza ta taɓa faɗawa kowa a cikin dangin mahaifinsu cewa tasan inda suke ba, bata barsu haka nan ba ta dage da musu Addu'a Allah yasa su samu abin da suka je nema, so take ƴaƴan nata suma su tsayu da ƙafan su, saidai wasu su nemi taimako a gun su badai suje neman taimako wani guri ba, ta gargaɗe su idan suka je, in sun samu sana'a kada su zauna haka suna yin sana'a ɗin ma. *** **** *** Ana kiran Sallah Asuba ta farka ta tashi ta zauna tana dube-dube taga Mutum ya kifa kai a tunaninta Abubakar ne yasa tasa hannu a kansa a hankali ta ce "Yaya Ina kuka yafi kuka barni ina ta shan wahala, dan Allah yaya ku tafi dani inda kuke, yana jinta bai ɗago ba, sai ta kama hannun sa, wani yarrrr yaji a jikinsa yayi saurin janyewa ya ɗago suka haɗa ido da sauri ta ɗan matsa baya ta fara tunowa da abin da ya faru, ta lumshe idon ta wasu hawaye masu zafi suka sauƙo, ya ce "Kukan me kike kuma, me ya fito dake daga gida cikin daren nan" Shiru tayi sai kuka da take yi, yayi ta tambaya amma shiru ba magana, fita yayi ya shigo da Baba shima yayi ta tambaya amma ta shiru, ya ce "To yanzu daga nan muje gidan naku muji ko menene" Lokacin tayi magana ta ce "Dan Allah idan munje ka bashi haƙuri na zauna bana son barin gidan mu" Ya ce "To menene ya fito da ke" Faɗa masa komai tayi bata ɓoye ba, har yadda suka yi da ƴan sanda. Shiru yayi can kuma ya ce "Muje gidan muji" Fita suka yi ta bisu a baya ta rungume hannunta a ƙirji saboda yanayin inda take, Tunda ta faɗi wannan magana Umar sai hararanta yake wannan ya tabbatar mata bai yadda da ita ba kenan. Suna zuwa ta shiga ɗakinta ta cire kayan barcin nata tasa doguwar riga sannan ta fito lokacin kuma taga Alhaji da Baba suna magana tana zuwa ta durƙusa gefe ta ce "Abba kayi haƙuri dan Allah na tuba bazan ƙara ba, kada kace zaka kore ni" Mungun kallo ya watsa mata sannan ya nuna mata hanyar fita, Baba ya ce "Kinga abin da kika ja wa kanki ko, idan aure kike so me yasa baza ki faɗa ba" Ta kalle shi ta ce "Baba kaima ka yadda kenan dan Allah kada kumin mummunan zato" Alhaji ya ce "Kai ka shigo da ita saboda haka ka Fita min da ita idan ba haka ba zan saɓa maka" Ya ce "Haba Yaya ay hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yar, hukuncin da ka mata ma ya isheta ishara, kuma ga duk kan Alamu tayi nadama, kayi haƙuri ka kyale ta" Ya nuna shi da yatsa ya ce "Ku fitar min daga gida, ay kana da gida ka kaita gidan ka mana" Miƙe wa yayi ya tashi ya ce "Muje Bilkisu " Ta bishi a baya Umar ma ya miƙe sai hararanta yake. Suna zuwa gida a falo ta zauna, ya shiga ciki ya kira Sauda suka fito tare ita ma ta zauna a kan kujera Baba ya ce "Bilkisu zata zauna a gidan nan na ɗan wani lokaci kafin ta koma gidan su" Miƙewa tayi ta ce "Wallahi bazai yuyu ba baza ta zauna ba ta koma can gidan su, ay naji abin da ya faru, wato ubanta ya kore ta saboda tana kawo kwartaye gida ni ta zauna min tana kawo min, kuma ma ay Ina da ɗa zata ɓata min tarbiyyan yaro" Shima miƙewa yayi ya ce "Gidan ki ko gidana, dole Bilkisu ta zauna a gidan nan kuma idan naga dama ta dawo kenan. " _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 29-30 Ɗaki ta wuce fuuuuuuu Baba ya kalli Umar ya ce "Gobe kaje ka ɗauko mata kayanta " Baice komai shima ya fita, ya kalli Bilkisu yadda ta takure guri ɗaya tana zubar da hawaye tausayinta ne ya kama shi Ya ce "Kiyi haƙuri kuma kiji tsoron Allah ki tuba gare shi, sannan ki dage da ibada, idan kina buƙatan wani abu ko menene shi ki faɗa min, ko ki faɗa wa yayanki Umar kinji ko" Bata da zaɓi sai dai ta amsa masa, haka kuwa ta ɗaga kai. Ya nuna mata ɗaki ya ce "Wannan ɗakin baƙine ki shiga ciki idan an kawo miki kayan naki ki ajiye a ciki, tashi ki shiga ciki" Tana hawaye ta ce "To Nagode Baba Allah ya... " Ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu da ce wa "Ya isa haka tashi ki je" Ta miƙe ta take ta zauna a ƙasa kusa da katifar ta fara rera kuka, cikin kuka tana cewa "Ya Allah gani gare ka." Sai kalmar take ta maimaitawa, ta jima a zaune a gurin tana kuka da taji ya ishe ta sai yayi shiru tana ajiyar zuciya, turo ƙofa taga anyi ta kalli ƙofa taga Umar ne ya cillo mata akwatin kayan ta ya haɗi mata akan ƙafarta taji zafi dan haka ta kama gurin tana sosawa tana sake kallon sa, kamar zai fita sai kuma ya juyo ya zauna kusa da ita a bakin katifar, ya kama tsolon gashin kanta ya ja, tasa hannu takai yayin da idon ta yayi jajur, ya ce "Da nasan abin da kika aikata kenan lokacin da kika suma da na kaiki daji cikin dare nan" Ta ce "Da zafi fa, dan Allah ka sake ni" Sake ja yayi ya ce "Wawiya mazinaciya, kamarki ƙaramar yarinya kinsan kinsan kawo kwarto ɗakinki dana ay an faɗa akwai karuwan da suke zama gidan iyayen su" Maganan sa ta ishe ta dan haka ta ce "Ni ba karuwa bace amma ka sani, wacce kake neman aure wato Ruky a ita zaka faɗawa haka, dan tun lokacin da su Yayana suka bar gidan ɗakin ya koma jahannaman ta, dan kullun sai ta kawo kwarto, nasan da wannan kuma Mama Amarya ta sani, Ina tausaya maka idan ka auri Ruky domin ka auri cikekkiyar karuwa wanda ta ajiye ɗaki a cikin gidan su," ta nuna masa yatsa manuniya ta ce "Ya kamata kasan wannan, ni ba mazinaciya bace ka adana kalaman ka zasu maka amfani lokacin da kasan waceece mazinaciya" Tunda ta fara magana yake kallon bakinta, kamar zai yadda sai kuma ya ce "Ohhh so kike ki rabani da Ruky ta, to ƙarya kike, Ruky wayayyiya ce, ban taɓa kamata da wani saurayi ba, kefa har ya tsallaka gidan ubanki, ya tsallaka falo ya shige ɗakin ki, amma ki sani idan kika ce zaki haka a nan sai mun karya ki" Sa hannu tayi a kirjinsa ta ture shi ya faɗa kan katifa, saboda zafin da take ji a kanta dan yaƙi ya sake mata gashi, da sauri ya shige bayi ta kulle kanta a ciki. Tashi yayi ya zauna da yaga bata da niyyar fitowa ya miƙe ya fita abin sa. Yana fita ta fito ta kama kanta da yake ta mata ciwo, ta ce "Allah ya isa tsakani da wanda ya min sharri, Allah ka saka min tun a duniya ma" Mama Sauda ce ta shigo ɗakin ta kalleta ta ce "To Tsinanniya ay hutawa zaki yi da kika zo gidan ba dan haka ki fito ki fara aikin gida" Ta tashi ta ta fito tayi kicin duk yayi kaca-kaca kamar ba'a taɓa shara na, kwanuka kuwa duk kudaje nabi, wanke wanken yafi ƙarfin a yi shi a cikin kicin ɗin dan plates dun sunyi yawa ga datti da yawa, ta ringa kwasa tana kaiwa bakin pampo da yake ta baya saida ta gama kwashewa ta gyara kicin din tas, ta goge ko ina, sannan ta dawo kan wanke-wanken ta fara yi, tana cikin yi ne Baba ya shigo ya kalle ta ya ce "Bilkisu baza ki huta ba, kika kama aiki, ko da yake nasan Sauda ce ta saki barin je in sameta" Da Sauri ta ce "Aa fa Baba ba ita bace nice nazo ina yi da kaina, ita kan ma bata sani ba, kaga ay wanke-wanken ba yawa" Ya ce "Da yawa mana, da kinsan kwana nawa aka tara wanke-wanken nan da kin riƙe baki, Sauda ƙazamar mace ce, koda yake tana yarinya ma bata da tsafta balle yanzu," Ita dai Bilkisu shiru tayi dan bata son ma maganan, ganin haka yasa ya shige ciki. Saida tayi komai ta gyara gidan tas sannan ta koma ɗakinta ta sake gyarawa tayi wanka. Tun Sassafe ta tashi ta fara gyare-gyaren gidan saida ta gama tayi wanka ta koma ta kwanta, bata daɗe da kwanciya ba taji an turo ƙofa, Sauda ta ce "Baza kiyi mana abin karyawa bane?" Ta ce "Zanyi dama ina jiran ki tashi ne ki faɗi abin da za'ayi" Ta ƙarazo ta kama kunnenta ta ce "Daga yau, Ina tashi in samu kin gama shiryawan komai idan ba haka ba na lahira sai ya fiki jin daɗi" Cikin ranta ta ce "Na lahira kan akwai masu jin daɗi, amma bama fatan in kasance ta ɗayan ɓagaren. Wucewa tayi kicin ta fara abin karin kumallo cikin ƙanƙanin lokaci ta gama, ruwan tea ta dafa sai Arish da ta soya da kwai sai farfesun naman rago da ta ɗumama, sannan ta kuma girka abinci dan dai kada tayi laifi. Tazo ta jera komai akan dinning sannan ta gyara kicin din sai da ko ina ya koma tas sannan taje ta sake yin wanka ta shirya kanta ta zauna bakin katifar. Bata daɗe ba, Baba ya turo ƙofa ya ce "Kizo mu ci abinci mana" Ta ce " To" hijabi tasa ta fito Ta fito ta same su duka sun zauna tana zuwa ta gaida Baba sannan ta gaida Umar, Mama Sauda kan ta riga ta gaidata dukda amsawantan masifa ce" Baba ya ce "Yau ƴata ce zata zuba mana abinci" Ta tashi ta ɗauki plate ta zuba wa Baba sannan ta ɗauka ta zuba na Mama sauda ta ce "Aa barshi, ta miƙawa Umar, " Baba yayi mata wani kallo ita kuma sai ta kauda kai ta ce "Ina da hannu ay zan zuba da kaina" Baice komai ba, sai ya kalli Bilkisu yaga ta zuba nata kaɗan ya ce "Ayko sai kin zuba da yawa, ji yadda kika sa nawa da na Yayanki ke kuma naki kaɗan" Ya amshi plate din ya sake zuba mata d yawa ya haɗa mata tea ya tura mata kwai da Arish ya ce "Ko kina son bread ne, dan mu idan mun samu wannan bama hadawa da shi saidai wannan yayan naki ne sai yaci, kinga idan zaki ci kuny biyu" Ta ce "Aa Baba nima bana ci" suka fara cin Abinci Mama Sauda ma ta zuba nata tana ci tana harare-harare duk Baba yana lure da ita, duka abincin ya ƙare, Umar ya buɗe kulan Abincin yaga wayam, ya ce "Wai ya ƙare ne" Baba yayi dariya, yace "Bilkisu yau kinsa munyi ɗurin Abincin da bamu taba yi a gidan nan ba" Ya kalli Sauda da take ta ɗurawa ya ce "Ga Mamanki ma sai Ɗurawa take tayi" Miƙewa tayi ta tashi tayi ɗaki, shi kuma Umar ya dauki sauran na Maman yasa a nashi plate din yana ci, Baba ya ce "Allah ya miki Albarka, yanzu ni nasan mijinki zaiyi alfahari da ke, kota ta wajen girki, balle ma ba tanan kaɗai kika tsaya ba, kalli gidan nan yadda ya sauya a zuwanki jiya-jiya nan, kafin mu samu abinci irin haka a gidan nan tun Mamanku tana Amarya, mun gode Allah ya miki Albarka Bilkisu, Allah ya kare ki daga sharri mutum da Aljan" Ta ce "Amin Nagode Baba" Umar ya gama zai tashi da kofin tea a hannunsa Baba ya ce "Zo ka bata tukuici Malam, ka cika ciki ka tashi zaka yi gaba" Ya ce "Ba wani daɗi fa abincin yayi ba, na cinye ne kada ayi asaransa" Baba ya ce "Ƙarya kake, ruwan tea da bread kadai kake sha a gidan nan, ko anyi abinci baka ci saidai ka barshi ya bushe anan, amma yau har ragowan na wani ka cinye, kafi kowa ci, anan, Ni mamakin ma da nayi, da naji tea din yana wani kalan ƙamshi, na kasa barinsa duk da na ƙoshi" Umar kan shiru yayi ya fita abinsa, Baba ya ce "To yau kada kiyi abincin rana da shi" Yayi murmushi ya ce "Ashe ko ita baza ta ci ba" Nasiha Baba ya mata, sannan ya ce "Zan fita koda abin da kike son na siyo miki" Ta ce "Ba komai, Allah ya tsare Allah ya dawo mana da kai lafiya" Ya ce " Amin" Shiga ɗakin Mama Sauda yayi, can ya fito ya fita, Motarsa tana fita Mama Sauda ta fito ta same ta tana haɗa plate zata wanke. Ta ce "Kinzo kin sa mijina ya fara faɗa min magana ko to bari kiji idan ya sake faɗa min magana sai na karya ki Wawiya, kuma kije ki gyara min ɗaki da na mijina" Ta koma, Umar ya shigo rankwashinta ya fara yi sanna ya wuga mata key ya ce "Kije ki gyara min ɗaki yanzun nan, kuma akwai ƙananan kayana a bayi ki wanke min su tas, saura in dawo in samu bakiyi ba, ko inzo in samu kin kawo min kwarto ɗaki" Ɗauka key ɗin tayi ta ajiye a kan table ɗin tayi ɗakin Mama Sauda tana shiga saida gabanta ya faɗi ganin yadda ɗakin yayi kaca-kaca kamar ba ɗakin mace ba, nan ta shiga gyarawa da tazo shara kuwa kamar tana share bola, tana shiga bayi dan ta wanke saida ta toshe hancin ta dan wari, saida ta ɗauki dogon lokaci tana gyarawa sannan ta gama, ta shiga ɗakin Baba, nan ma yayi datti amma baikai na Mama Sauda ba nan kan bata sha wani wahala wajen gyaransa ba, Ɗakin Umar kan gyaran kaɗan ne, kana shiga zaka san me ɗakin yana da tsafta, dan komai nashi a kintse, haka bayin ma, under weres din ne ma ya ɗan tara da yawa, ta wanke su, ta shanya sannan ta rufe ɗakin ta fito da makullin. tana fito wa ta ɗora tuwon semonvita da miyar ɗanyen kuɓewa sai bushashshen kifi da tasa a ciki, gida ya buɗe da kamshi. Bayan ta gama komai tayi wanka bata yi wani kwalliya ba tasa kayanta ta fito ta je, ta kwaso kayan, harda goge su tayi, wai dan yaji daɗi ya yaba mata ya daina ci mata fuska. Tana gamawa ta koma ɗakin ta, ta kwanta, barci ya fara daukanta, bata jima da yin barcin ba, aka kira Sallah la'asar ta tashi taje ta ƙara kintsa Falon da gurin cin abincin, dan tana fashin Sallah, ta zauna, Umar ne ya fara shigowa yana zuwa ya nufi gun abinci da kansa ya zuba ya fara ci, sannan yasha kunun ayan da ta haɗa, ya tashi kenan zai tafi Baba ya shigo tayi masa sannu ya miƙa mata leda yace "Gashi naki ne" Ta masa godiya ta ajiye, ya shiga ɗakin MAMA Sauda can ya fito ya samu Umar Zaune lokacin ya gama ci ya zauna a falo yana kurɓan kunun aya. Ya ce "Nima a zuba min ko" Ta zuba masa ta kawo masa tsakiyan falo ya fara ci yana santi, saida ya gama ya ce "Ki huta da daddare wannan sauran ya ishe mu" Fita yayi ya barta da Umar shi ɗaya ta miƙe taje ta dauki tuwon guda ɗaya ta zuba miya a plate din da Baba ya ci, ta wuce ɗakinta, ta zauna ta fara ci kenan Umar ya shigo ya ce "Bani key" Ta sa hannu ta miƙa masa, saida ya kama hannun ya matse mata sannan amshi key ɗin, ta ce "Allah ya isa na" Ya ce "Barin dawo ki faɗa min awa kike jan Allah ya isa" Tuwon ta taci gaba da ci, a ranta tana cewa "Ka dawo duk abin da zaka min ka min, idan duka ne, na saba sha ba kashe ni zaiyi ba" _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 31-32 Yana shiga yaji ɗakin sa ya bada wani daddaɗan Ƙamshi mai sanyawa zuciya farinciki, ko ina ya shiga ƙamshi har bayin komai ta ajiye shi a ma'adanan sa, kamar dama tasan yanayin ɗakin, yaji daɗi kan kan har zaka iya ganewa a fuskarsa idan ka shiga sai dai idan ya tuna yarinyar da ta masa wannan abin irin halinta sai ya fara haushi, kuma yaji ya tsane ta, ya tsani yarinyar da ta bada kanta a waje, kyamar ta yake yi koda ta matso kusa da shi, saidai ita wannan ba inda zai da ita saboda Babansa, sake jin haushin da kyamarta yaji, ya fara duba ɗakin yana son yaga wani abin kushewa yaje ya kusheta, shi yasan ba abin kushewa, tayi abin da za'a yaba mata, kuma ƙarya take ya yaba ɗin. *** *** *** Mama Amarya kuwa tayi nadama da tasa aka kori Bilkisu gashi yanzu aikin gidan ya caɓe mata, dama Ruky ba taya take ba saidai tayi wanka tasa ƙananan kayanta ta fita abin ta, yanzun kan ma abin nata ya daɗa gaba, dan har ɗaki take shigar da saurayin ta suyi abin da zasuyi su fito, gidan duk a lalace shiko uban gayyar ba abin da ya dame shi, baya neman yaransa, ko Khadiyo baisan inda takeba amma kuma baya ko neman ta, yana musu kallon masu takura masa a rayuwa, yanzu Mama Amarya ce da ƴarta a cikin ransa ko ɗan uwansa baya son yana raɓansa, baida wani dangi da ya wuce Mama Amarya da ɗiya. Ta dawo kenan da ƙananan kaya a jikin ta, sai nishi take saboda yadda kayan ya matse ta. Ta zauna akan kujera ta fito da kuɗin ta tana ƙirgawa Mama Amarya ta matso ta ce "Wannan fa a ina kika samu" Ta ce "Wallahi Wani shegen Alhaji na haɗu da shi mai sakin kuɗi Mama kinga kuɗin da ya bani" Mama Amarya ta ce "Shege yaga kyakykyawan mace, kinga dama muna neman kuɗin da zamu kaiwa boka akan maganan auren ku da Umar, muna son mu jawo hankalin Uwarsa ma, kinga saida yardan ta za'ayi komai ko" Turo baki Ruky tayi ta ce "Haba Mama ba kina da kuɗi ba, ki tambayi mijinki ya baki mana, ni a dan wannan kuɗin nawa za'a sawa ido ni gaskiya A'a bazan yadda ba" Mama Amarya ta wafci kuɗin ta ce "Duk abin da ake ba akan ki ake ba zaki ce a bar miki kuɗin ki" Kai hannu Ruky tayi zata wufta suka fara kokawa har wasu daga cikin kuɗin suka yage, nan fa Ruky ta buga tsalle ta ce "Wallahi sai kin biyani kuɗi na" Mama Amarya "Ruky me zaki da kuɗi haka ne" Nan fa Ruky tayi ta yi masifa wa uwarta karshe dai uwar ta fara rarrashin ta sannan ta ce zata biya ta. *** *** *** Aikin gidan sam baya damun ta, abin dake damun ta bazai wuce tsangwaman Umar da Uwarsa ba, suma idan Baba yana nan basa mata, watan ta kusan biyu a gidan, yanzu tunanin Ummin ta take ko a wani hali take ciki, tana son taje ta duba ta ganta. Baba kuwa ya gane tana cikin damuwa dan haka ya kira ta falo ta zauna a gefen ƙafan sa Ya ce "Bilkisu lafiya na ganki bakya walwala me ya faru ne faɗa min" Ta ce "Ina son in je inga Ummi ne" Ya ce "Shine baza ki faɗa min ba, gobe lahadi ki shirya sai yayanki Umar ya kaiki, ay kinsan inda take ko? " Ta ce "Nasan bazai wuce tana gidan Sarki ba" Ya ce "To shikenan Umar zai kaiki, ya baro ki a can kiyi kwana biyu sai ya ɗauko ki, kuma zaki fara zuwa makaranta ki zana jarabawa, bayan kin zana idan kina da tsayayye sai ki fitar kiyi auren ki, in yaso sai kici gaba da makarantan a ɗakin mijinki" Shiru tayi idanuwanta ya ciko da kwalla, ganin haka yasa ya ce "Faɗi abin dake ranki" Ta ce "Baba kayi haƙuri ni nafi son makarantan abar maganan auren nan, ni bana kula kowa ma" Ya ce " Shikenan dai, goben ki shirya ko, ki rubuta me da me za'a kai mata sai a siyo mata" Ta ce "To Nagode Baba " Washe gari Sassafe ta shirya ta haɗa da tsaraba ta fito, tana tsaye, Baba ma ya fito ganin Umar bai fito ba yasa Baba ya ce "Shiga ciki ki masa magana" Ta shiga saboda gan ɗoki ko Sallama bata yi ba ta faɗa ciki, ganin sa tayi da towel a ƙugunsa yana tsane ruwan jikin sa da ɗan ƙarami, ta juya ta bashi baya ta ce "Baba ya ce "Ka fito mu tafi" Bata san yana matsowa ba sai ji tayi an kamo mata hannayen ta ta baya ya banƙaro ta ya kai fuskarsa daidai kunnen ta ya ce "Ke wace irin daƙiƙiya ce baza ki sallama ba, ko kwartancin naki ne ya motsa" Tana ƙoƙarin ta kwace hannunta amma ta kasa. Ya riƙe hannun nata da hannu ɗaya, ya nuna ta da yatsa ya ce "Saura idan munje kije ki samo kwarto ƙauye" Jin haushin maganan sa yasa ta tofa masa miyau a fuskar sa, ya sake ta ya ce "Ke! " Zata gudu ya kuma kamota ya haɗata da kirjin sa, ta kalle shi cikin ido ta ce "Wannan wani irin iskanci ne, " Ya ce "Saikin lashe ƙazantar da kika zuba min " Kokawa suka fara, gaba ɗaya ta canja masa yanayi a jikin sa dan ji yayi kamar tana masa cakulkuli a jiki, baida wani ƙarfi a jikin sa, hannu tasa a kirjin sa ta tura shi kan gado, da sauri ta fita, shiko gunda tasa hannu ya kama yana jin zuciyar sa tana wani irin bugu wanda bai san ko na menene ba. Ido ya lumshe ya miƙe da kyar ya fara shiryawa. Da ta fito kuwa Baba ya ce "Ina yake" Ta ce "Yana shiryawa" Ba jimawa ya fito, Baba ya saka mata kayanta a mota ta shiga shima ya shiga gurin driver Baba ya musu Allah ya kiyaye, sun fara tafiya zasu fita a get ɗin Ya ce "Bari mu fita a cikin gari, zaki san kin zuba min ƙazantarki a fuskata" Shiru ta masa ita dai burinta ya kaita gun Ummin ta _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/27, 9:21 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 33-34 Hanya suka ɗauka sai dai kirjinta na dukan uku-uku, sun shiga cikin daji saidai ga mamakin ta ko tsayawa ma baiyi ba har suka sauƙa akan titi inda zasu ɗauki hanyar rugan, suna isa ta nuna masa gidan Sarkin Fulani a ƙofar gidan yayi parking, ya ce "Allah yasa ma baza a ganta a gidan ba, kije ki duba " Bata ce komai ba ta fita a motar ta shiga gidan da Sallamartar, ta gaida mutanen gidan bayan sun gama gaisawa ta ce " Inna neman Ummina" Ɗaya daga cikin matar ta ce "Wacece kuma wannan" Ta ce Hali Wata daga ciki ta ce "Kodai kece Balki" Ta ce "Eh nice" Ta ce "Bari a kira miki ita ko" Ta mike ta shiga wani ɗakin saiga Ummi ta fito daga qani ƴar bukka, Bilkisu taje da gudu ta rungumeta sai kuma ta saki kuka mai ban tausayi, cikin kuka tana cewa "Haba Ummi, tun da kika tafi ko ko waiwaye mu kiga halin da muke ciki amma kika ki, kinsan irin ƙalubalen da muka fuskanta ne, Haba Ummi me yasa" Share mata hawaye ummi tayi tayi ta jata zasu yi ɗaki sai kuma ta ce "Tare da Ya Umar fa muke yana waje" Ta ce "Je ki shigo da shi" Ta fita yana ganin fuskar ta duk hawaye yayi Dariya ya ce "Allah ya amshi Addu'a ta" Ta ce "Ta ce ka shigo ciki" Bata masa magana ba ta ɗauki kayanta da tsarabar da Baba ya mata, tayi gaba ya bita a baya saida suka je soron gidan ya tare ta, ya ce kawo akwatin munafuka, salon muje Ummi ki taji haushi na barki da kaya da yawa" Cikin ranta ta ce "Ay ba munafuki irin ka," Ya fizga harda sauran kayan, ita ko kamar zata yi dariya dan Abin ma dariya ya bata, tayi gaba ba tare da komai ba, shi kuma ya rike kayan. Suna shiga Suka samu Ummi ta shimfiɗa musu tabarmar kaba, suka zauna, ta kawo musu ruwa da madara, suka sha, nan akayi ya gaisawa da shi, Ummi taji dadin yadda taga Umar yana kula da Bilkisu, wanda sabanin da da yake hantaranta. Bayan ya ɗan huta, ya ce "Ummi ni zan koma, kwana biyu zata yi, zan dawo in ɗauke ta" Ta ce "To Umar nagode idan kaje ka gaida min kowa da kowa, kayi wa Baban ka godiya " Bayan ya shiga mota kuwa aka kawo masa ƙwan zabi da kuma madaran shanu, bayan kowa ya koma Bilkisu zata shige Umar ya kirata, ta koma da baya taje, yayi mata alama ta buɗe ta shigo, ta buɗe ta shiga ta zauna, ya riƙe mata kunne ya ce "Saura kuma kije ki bawa wani ɗan ƙauye kanki ko kuma idan nazo ɗaukanki nazo na samu baki shirya ba, sai kin yaba wa aya zaƙinta" Saida ta fita sannan ta ce "Ina ruwan ka, idan na nawa wani kaina ɗin ma ay ba kai nabawa ba, kuma jikina ne ba jikinka ba, kuma ay bani nasa kazo ka ɗauken ba idan kaga dama ma kada kazo, ni ina ruwana tunda ina tare da uwata" Buɗe murfin ƙofa yayi zai fito sai kuma ta kwasa da gudu ta shige ciki. Girgiza kai ya shige mota ya tafi abin sa. Tana shiga ta samu Ummi, Ummi ta ce "Ya baku zo min da ƴata ba" Bilkisu ta ce "Hmm Ummi ay labari ne mai tsawo, " Ta ce "Me ya faru da Khadiyon" Nan ta bata labarin komai bayan tafiyanta har komawanta gidan su Umar, saidai abin da ta kasa, ta kasa faɗan irin cikin zalin da Umar yake mata, a ganinta ayt tunda Baba ya riketa har yayi alƙawarin zata koma makaranta bai kamata ta damu da rashin mutuncin ɗansa ba har tana faɗa wa wani. Bayan tayi shiru ne Ummi ta nisa ta ce "Kiyi haƙuri Allah ba azzalumin kowa bane, muna nan muna ta Addu'a, ni yanzu da kike gani na nan ma aure zanyi a wannan ƙauyen " Bilkisu ta ce "Haba Ummi naga Saki ɗaya Abba ya miki ya kamata ki bari ki koma gun Abban mu" Ta ce "To Adda Abban naki, yaushe zai maida ni, nima ina so idan ya maida ni, to amma da wuya ya maida ni sai dai muyi haƙuri kawai, kuma nima bazan so na yi ta zama a wannan gidan ba, tunda kinga ba gidan mu bane, dama ace gidan iyayena ne da zan iya zama, kuma Shima Sarki yana magana akan nayi auren tunda wai yana cewa da saura na" Ta ce "Nidai Ummi banso wannan auren ba, gaskiya " Ta ce "Kada ki damu kedai mu dage da Addu'a kuma idan kin samu lokaci kina zuwa kina duba Umman ku, da Khadiyo" Ta ce "Insha Allahu Ummi" A kwana biyun da tayi tayi samari sosai, Musamman da suka ga ba budurwa kamarta, tunda inda a ƙauyen take da tuni tana da ƴaƴa uku zuwa huɗu, ga ƙawaye da tayi saidai ƙawayen nata duk matan aure ne. Da Sassafe ta shirya dan tasan zai iya yin sammako yazo dan ya samu bata shirya ba ya ci mata mutumci. Bai zo ba sai ƙarfe 6:00pm ita kan ma harta fidda rai zaizo ɗin, wani saurayinta Tsammani me mata biyu, yazo suna zaune akan wani kututturen icen dake ƙofar gidan sarki, ya tsaya da mota a daidai inda suke, mungun kallo ya mata, ita kuma tayi kamar bata ganshi ba, sai kuma ta tuna tare zasu tafi ga dare yayi, zai iya ci mata mutunci a mota. Ta tashi zata shiga Tsammani Ya ce "Haba Balki ina zuwa kuma" Ta ce "Yaya na yazo zamu tafi ne" Ya kalli Umar yaga yadda yake musu mungu kallo, tana shiga Umar ya ce "Me tsakanin ka da ita" Tsammani ya duƙa dan yaji ta ce Yayanta ne Ya ce "Ayi haƙuri Yaya Idan da so samu ne ina son zan turo iyayena a ɗaura min aure da Balki" Tsaki Umar yayi ya koma mota, ya zauna yana jiran ta, ita kuma sai gata ta fito da mutanen gidan kowa da ɗan abin da zai bata, masu zabbi ne, masu kaji ga madaran shanu da ƙwan zabbi, sai kuma Su kayan miya, su kuka da daddawa da sauran su, Umar ya buɗe baya ana sawa Tsammani yazo ta gefenta ya ce "Wannan dai ba Yayan ki bane Balki, naga kamar son ki yake, amma kuma bana son ya ɗauke min ke" Umar kuwa ya gama sa komai kenan ya rufe ya hango su, saidai baisan me suke cewa ba, yazo ya buɗe ƙofa ya ce "Shiga muje" Ta shiga, ya rufe sannan yaje yayi Sallama da Ummi harda mata kyautar kuɗi, ta amsa harda sa masa Albarka, yaja motar suka tafi ƴan ƙauyen suna ta ɗaga musu hannu. Saida suka ɗau hanya ya ce "Me tsakaninki da wannan ƙazamin" Ta kalle shi, bata ce komai ba ya sake magana, "Bakya jine" Ta ce "Saurayina ne kuma bashi ɗaya bane, suna da yawa" Da sauri ya tsaida motar ya kuma kallonta, "kika ce suna da yawa?, maza nawa kika bawa kanki kenan a wannan ƙauyen, kinzo kin nuna musu halinki ko" Idon ta yaciko da ƙwalla ta ce "Wallahi ya Umar Allah zai saka min akan..." Ji tayi ya buge mata baki, ta kama gurin ta ce "Allah ya isa mungu kawai" Ya kalle ta ya ce "Ni kika jawa Allah ya isa, bari muje gida, zaki san da wa kike" Ta ce "Da Umar nake" Ya kalleta ya girgiza kai yaja motar da gudu kamar zasu tashi sama, ita kanta tana tsoro ita dai kawai tayi shiru ne. Suna isa gida duhu ya fara yi, Baba suka gani a tsaye tana fitowa Baba ya ce "Ina kuka tsaya," Kafin tayi magana Umar ya ce "Na biya ta wani guri ne, kafin na je na ɗauko ta" Ya ce "Amma saboda bana son tafiyar dare yasa tunda la'asar na tura ka amma saida kaje wani guri ko" Ya ce "Kayi Haƙuri Baba" Suka kwaso tsaraban suka shiga ciki da shi, Mama Sauda suka Samu a falon ta gaishe ta ko amsawa bata yi ba. Ciki ta wuce tayi sallah sannan ta je dan ta sa kayan da tazo dasu a kicin Kaji da zabin kuma tuni Umar ya fita da su dan a yanka su. Samun kicin din tayi kamar anyi dambe a cikin sa, plate kuwa wanda aka bata sunyi yawa, dan haka ta fara gyara kicin ɗin, sannan falo ta wanke plate din sai da ta gama ta koma ɗaki tayi Sallah, tayi wanka tasa doguwar rigar barci, ta kwanta, ji tayi an buga ƙofa ta tashi ta buɗe taga Umar ne, ayko da tasan shine da baza ta buɗe ba, shima kayan barci ne a jikin sa, da alama kwanciya zaiyi. Kallonsa tayi, yakai hannu zai riƙeta ta koma ciki dan ɗayan hannun wayar wuta ta hango, ya biyo ta yana cewa yau naxo ne in koya miki hankali, haƙuri ta fara bashi amma ya fara zaneta, ta riƙe wayan ta ce "Umar so kake ka kashe ni ko" Ta ce "Da kin mutun ma da zanfi jin daɗi" Ta saki wayar ta koma kan katifa ta kwanta ruf da ciki ta ce "Ka kashe ni ko nima na huta da muguntan" Ya fara zuba mata, a gadon bayan ta, yayin da ita kuma ko motsi bata yi, idon ta kuma ya bushe ko alamar hawaye babu, ganin haka ya sa hannu ya fara zuge mata zip ɗin riga, ta kama hannunsa tare da matsawa jikin bango ta ce "Me haka" Ya ce "Ina tunanin baya shigan ki ne dan haka fatan jikinki zan doka" Ta ce "Sai kayi ta duka, har sai ka kashe ni" Ta koma ta kwanta ganin ta masa nisa yasa ya hau kan katifar ya sa hannusa yana jan zip ɗin ƙasa kenan, Baba ya turo ƙofa tare da cewa "Bilkisu haɗa min lipton mana nayi kewan... " Maganan ne ta katse ganin yadda ya gansu, ya fara faɗin "Innalillahi wa'inna'ilaihir raju'un" Duk kan su suka tashi a tsorace ko wannen su yana muzurai da ido. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[5/27, 9:21 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 33-34 Hanya suka ɗauka sai dai kirjinta na dukan uku-uku, sun shiga cikin daji saidai ga mamakin ta ko tsayawa ma baiyi ba har suka sauƙa akan titi inda zasu ɗauki hanyar rugan, suna isa ta nuna masa gidan Sarkin Fulani a ƙofar gidan yayi parking, ya ce "Allah yasa ma baza a ganta a gidan ba, kije ki duba " Bata ce komai ba ta fita a motar ta shiga gidan da Sallamartar, ta gaida mutanen gidan bayan sun gama gaisawa ta ce " Inna neman Ummina" Ɗaya daga cikin matar ta ce "Wacece kuma wannan" Ta ce Hali Wata daga ciki ta ce "Kodai kece Balki" Ta ce "Eh nice" Ta ce "Bari a kira miki ita ko" Ta mike ta shiga wani ɗakin saiga Ummi ta fito daga qani ƴar bukka, Bilkisu taje da gudu ta rungumeta sai kuma ta saki kuka mai ban tausayi, cikin kuka tana cewa "Haba Ummi, tun da kika tafi ko ko waiwaye mu kiga halin da muke ciki amma kika ki, kinsan irin ƙalubalen da muka fuskanta ne, Haba Ummi me yasa" Share mata hawaye ummi tayi tayi ta jata zasu yi ɗaki sai kuma ta ce "Tare da Ya Umar fa muke yana waje" Ta ce "Je ki shigo da shi" Ta fita yana ganin fuskar ta duk hawaye yayi Dariya ya ce "Allah ya amshi Addu'a ta" Ta ce "Ta ce ka shigo ciki" Bata masa magana ba ta ɗauki kayanta da tsarabar da Baba ya mata, tayi gaba ya bita a baya saida suka je soron gidan ya tare ta, ya ce kawo akwatin munafuka, salon muje Ummi ki taji haushi na barki da kaya da yawa" Cikin ranta ta ce "Ay ba munafuki irin ka," Ya fizga harda sauran kayan, ita ko kamar zata yi dariya dan Abin ma dariya ya bata, tayi gaba ba tare da komai ba, shi kuma ya rike kayan. Suna shiga Suka samu Ummi ta shimfiɗa musu tabarmar kaba, suka zauna, ta kawo musu ruwa da madara, suka sha, nan akayi ya gaisawa da shi, Ummi taji dadin yadda taga Umar yana kula da Bilkisu, wanda sabanin da da yake hantaranta. Bayan ya ɗan huta, ya ce "Ummi ni zan koma, kwana biyu zata yi, zan dawo in ɗauke ta" Ta ce "To Umar nagode idan kaje ka gaida min kowa da kowa, kayi wa Baban ka godiya " Bayan ya shiga mota kuwa aka kawo masa ƙwan zabi da kuma madaran shanu, bayan kowa ya koma Bilkisu zata shige Umar ya kirata, ta koma da baya taje, yayi mata alama ta buɗe ta shigo, ta buɗe ta shiga ta zauna, ya riƙe mata kunne ya ce "Saura kuma kije ki bawa wani ɗan ƙauye kanki ko kuma idan nazo ɗaukanki nazo na samu baki shirya ba, sai kin yaba wa aya zaƙinta" Saida ta fita sannan ta ce "Ina ruwan ka, idan na nawa wani kaina ɗin ma ay ba kai nabawa ba, kuma jikina ne ba jikinka ba, kuma ay bani nasa kazo ka ɗauken ba idan kaga dama ma kada kazo, ni ina ruwana tunda ina tare da uwata" Buɗe murfin ƙofa yayi zai fito sai kuma ta kwasa da gudu ta shige ciki. Girgiza kai ya shige mota ya tafi abin sa. Tana shiga ta samu Ummi, Ummi ta ce "Ya baku zo min da ƴata ba" Bilkisu ta ce "Hmm Ummi ay labari ne mai tsawo, " Ta ce "Me ya faru da Khadiyon" Nan ta bata labarin komai bayan tafiyanta har komawanta gidan su Umar, saidai abin da ta kasa, ta kasa faɗan irin cikin zalin da Umar yake mata, a ganinta ayt tunda Baba ya riketa har yayi alƙawarin zata koma makaranta bai kamata ta damu da rashin mutuncin ɗansa ba har tana faɗa wa wani. Bayan tayi shiru ne Ummi ta nisa ta ce "Kiyi haƙuri Allah ba azzalumin kowa bane, muna nan muna ta Addu'a, ni yanzu da kike gani na nan ma aure zanyi a wannan ƙauyen " Bilkisu ta ce "Haba Ummi naga Saki ɗaya Abba ya miki ya kamata ki bari ki koma gun Abban mu" Ta ce "To Adda Abban naki, yaushe zai maida ni, nima ina so idan ya maida ni, to amma da wuya ya maida ni sai dai muyi haƙuri kawai, kuma nima bazan so na yi ta zama a wannan gidan ba, tunda kinga ba gidan mu bane, dama ace gidan iyayena ne da zan iya zama, kuma Shima Sarki yana magana akan nayi auren tunda wai yana cewa da saura na" Ta ce "Nidai Ummi banso wannan auren ba, gaskiya " Ta ce "Kada ki damu kedai mu dage da Addu'a kuma idan kin samu lokaci kina zuwa kina duba Umman ku, da Khadiyo" Ta ce "Insha Allahu Ummi" A kwana biyun da tayi tayi samari sosai, Musamman da suka ga ba budurwa kamarta, tunda inda a ƙauyen take da tuni tana da ƴaƴa uku zuwa huɗu, ga ƙawaye da tayi saidai ƙawayen nata duk matan aure ne. Da Sassafe ta shirya dan tasan zai iya yin sammako yazo dan ya samu bata shirya ba ya ci mata mutumci. Bai zo ba sai ƙarfe 6:00pm ita kan ma harta fidda rai zaizo ɗin, wani saurayinta Tsammani me mata biyu, yazo suna zaune akan wani kututturen icen dake ƙofar gidan sarki, ya tsaya da mota a daidai inda suke, mungun kallo ya mata, ita kuma tayi kamar bata ganshi ba, sai kuma ta tuna tare zasu tafi ga dare yayi, zai iya ci mata mutunci a mota. Ta tashi zata shiga Tsammani Ya ce "Haba Balki ina zuwa kuma" Ta ce "Yaya na yazo zamu tafi ne" Ya kalli Umar yaga yadda yake musu mungu kallo, tana shiga Umar ya ce "Me tsakanin ka da ita" Tsammani ya duƙa dan yaji ta ce Yayanta ne Ya ce "Ayi haƙuri Yaya Idan da so samu ne ina son zan turo iyayena a ɗaura min aure da Balki" Tsaki Umar yayi ya koma mota, ya zauna yana jiran ta, ita kuma sai gata ta fito da mutanen gidan kowa da ɗan abin da zai bata, masu zabbi ne, masu kaji ga madaran shanu da ƙwan zabbi, sai kuma Su kayan miya, su kuka da daddawa da sauran su, Umar ya buɗe baya ana sawa Tsammani yazo ta gefenta ya ce "Wannan dai ba Yayan ki bane Balki, naga kamar son ki yake, amma kuma bana son ya ɗauke min ke" Umar kuwa ya gama sa komai kenan ya rufe ya hango su, saidai baisan me suke cewa ba, yazo ya buɗe ƙofa ya ce "Shiga muje" Ta shiga, ya rufe sannan yaje yayi Sallama da Ummi harda mata kyautar kuɗi, ta amsa harda sa masa Albarka, yaja motar suka tafi ƴan ƙauyen suna ta ɗaga musu hannu. Saida suka ɗau hanya ya ce "Me tsakaninki da wannan ƙazamin" Ta kalle shi, bata ce komai ba ya sake magana, "Bakya jine" Ta ce "Saurayina ne kuma bashi ɗaya bane, suna da yawa" Da sauri ya tsaida motar ya kuma kallonta, "kika ce suna da yawa?, maza nawa kika bawa kanki kenan a wannan ƙauyen, kinzo kin nuna musu halinki ko" Idon ta yaciko da ƙwalla ta ce "Wallahi ya Umar Allah zai saka min akan..." Ji tayi ya buge mata baki, ta kama gurin ta ce "Allah ya isa mungu kawai" Ya kalle ta ya ce "Ni kika jawa Allah ya isa, bari muje gida, zaki san da wa kike" Ta ce "Da Umar nake" Ya kalleta ya girgiza kai yaja motar da gudu kamar zasu tashi sama, ita kanta tana tsoro ita dai kawai tayi shiru ne. Suna isa gida duhu ya fara yi, Baba suka gani a tsaye tana fitowa Baba ya ce "Ina kuka tsaya," Kafin tayi magana Umar ya ce "Na biya ta wani guri ne, kafin na je na ɗauko ta" Ya ce "Amma saboda bana son tafiyar dare yasa tunda la'asar na tura ka amma saida kaje wani guri ko" Ya ce "Kayi Haƙuri Baba" Suka kwaso tsaraban suka shiga ciki da shi, Mama Sauda suka Samu a falon ta gaishe ta ko amsawa bata yi ba. Ciki ta wuce tayi sallah sannan ta je dan ta sa kayan da tazo dasu a kicin Kaji da zabin kuma tuni Umar ya fita da su dan a yanka su. Samun kicin din tayi kamar anyi dambe a cikin sa, plate kuwa wanda aka bata sunyi yawa, dan haka ta fara gyara kicin ɗin, sannan falo ta wanke plate din sai da ta gama ta koma ɗaki tayi Sallah, tayi wanka tasa doguwar rigar barci, ta kwanta, ji tayi an buga ƙofa ta tashi ta buɗe taga Umar ne, ayko da tasan shine da baza ta buɗe ba, shima kayan barci ne a jikin sa, da alama kwanciya zaiyi. Kallonsa tayi, yakai hannu zai riƙeta ta koma ciki dan ɗayan hannun wayar wuta ta hango, ya biyo ta yana cewa yau naxo ne in koya miki hankali, haƙuri ta fara bashi amma ya fara zaneta, ta riƙe wayan ta ce "Umar so kake ka kashe ni ko" Ta ce "Da kin mutun ma da zanfi jin daɗi" Ta saki wayar ta koma kan katifa ta kwanta ruf da ciki ta ce "Ka kashe ni ko nima na huta da muguntan" Ya fara zuba mata, a gadon bayan ta, yayin da ita kuma ko motsi bata yi, idon ta kuma ya bushe ko alamar hawaye babu, ganin haka ya sa hannu ya fara zuge mata zip ɗin riga, ta kama hannunsa tare da matsawa jikin bango ta ce "Me haka" Ya ce "Ina tunanin baya shigan ki ne dan haka fatan jikinki zan doka" Ta ce "Sai kayi ta duka, har sai ka kashe ni" Ta koma ta kwanta ganin ta masa nisa yasa ya hau kan katifar ya sa hannusa yana jan zip ɗin ƙasa kenan, Baba ya turo ƙofa tare da cewa "Bilkisu haɗa min lipton mana nayi kewan... " Maganan ne ta katse ganin yadda ya gansu, ya fara faɗin "Innalillahi wa'inna'ilaihir raju'un" Duk kan su suka tashi a tsorace ko wannen su yana muzurai da ido. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/28, 7:54 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ _Ƴan group ɗin *IHU BAYAN HARI* Ina jin daɗin sharhin ku, kuma ina Alfahari da ku ɗa bisa ɗari, Allah dai yabar ƙauna❤️❤️❤️❤️❤️_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 35-36 Ya ce "Dama abin da ua tsayar da ku kenan har kukai dare, shine zaku dawo kuci gaba a nan" Bilkisu ta kalle Umar shima ya juyo suka haɗa ido Baba ya kuma daka musu tsawa "Baza ku min magana ba" Murya na rawa Bilkisu Ta ce "Wallahi Baba ba abin da kake zargi bane, Shine fa... " Ya kuma daka mata tsawa "Kefa nace zan miki aure kika ce A'a ke karatu kike so, a haka zaki karatun" Kallon Umar ta sake yi, tana son yayi magana amma yaƙi yin maganan. Baba ya sake cewa "Ku fito nan falo ina jiranku" Ya fita ta sake kallon sa ta zubda ƙwalla ta ce "Dan Allah ka faɗi abin da kamin, ka faɗi gaskiya ya kyale mu, bana son wannan zargin" Sauƙa yayi daga kan gadon ya fita a ɗaki ita ma tabi bayansa suka samu Baba zaune durƙusawa suka yi duka yayin da ita kuma take kallon Umar tana son yayi maganan. Baba ya kalle shi, ya ce "Shashasha me yasa da kake son ta baza ka faɗa na muku aureba, sanin kanka ne zanfi kowa farin ciki idan kace kana son ta" Lokacin yayi magana ya ce "Baba ba abin da kake zargi bane fa, ka tsaya na maka bayani" Ya ce "Na yanke hukuncin nan da sati biyu za'a ɗaura muku aure, nasan kana da kuɗi ka haɗa ka kawo zan ƙara maka wani ka haɗa mata lefe, ni zan biya maka sadaki" Jin muryan Mama Sauda suka yi a bayan su ta ce "Aure da Bilkisu Allah ya sauwaƙe ɗana ya aure wannan abar shi yasa na faɗa maka wannan karuwan zata lalata mana ɗa amma kaƙi ji gashi ta lalata shi... " Bab ya ɗaga mata hannu ya ce "Ya ishe ni haka dan Allah, ita ce me lalata shi ko, shi da yake namiji, a ɗakin ta fa na ganshi, me ya kaishi banda lalata, ita kuma da yake sokuwa ce ta biye masa" Mama Sauda ta ce "To maganan Aure ma ka janye dan yana da wacce yake so" Ya ce "Ya faɗa min ne, ni wannan ido na ya gane min " Ta ce "Ruky yake so, ƴar gidan matar yayan ka" Ya kalli Umar ya ce "Faɗa min da gaske Ruky kake so" Ya ce "Eh Abba kuma ita ma tana da Saurayi a ƙauye sunan sa Tsammani " Ya kalle ta yana neman ƙarin bayani ta ɗaga kai alamun eh Baba ya ce "To ba ruwana da wani Tsammani ko Ruky abin da na yanke kenan, kuma kada na sake ganin ka kayi ƙofar ɗakinta, haka kama kada na sake gani ko ƙofar ɗakinsa kin kalla, idan kunyi auren kuje can ku ƙarata" Bilkisu ta ce "Baba kayi haƙuri" Ya ce "kije ki haɗa min lipton " Ta tashi jiki na ƙwari tayi kicin, shi kuma ya fita shima jikinsa ba kwari. Duk kan su ba wanda yayi barci, itakan kuka ta kwana tana yi, dan tana ganin idan aka musu aure da Umar zai iya kashe ta, dan Umar mungu ne, akan ta auri Umar gwara ta auri Tsammani ta ƙwammace taje a ta uku, kuma ta zauna a ƙauyen. Baba kuwa Samun Alhaji yayi da maganan auren Umar da Bilkisu, sannan ya faɗa masa abin da ya gani da idon sa" Alhaji ya nisa ya ce "Hakan da kayi yayi daidai " Tsangwama gurin Mama Sauda ya ƙaru, kullum tana mata gargaɗin idan ta yadda aka ɗaura auren nan ita da jin daɗin duniya sun har ta mutu. " Yauma tazo ta same ta a kicin tana tsaka da aiki ta ce "To karuwa kin faɗa an fasa auren ko" Shiru tayi Mama Sauda ta kuma matsowa ta ce "Malama kina jina fa" Ta ce "Haba Mama nima bana son Ya Umar Wallahi ina da masoya da yawa, Wallahi da ina da daman hana wa da na hana, ke ya kamata ki hana Mama" Ta ce "To shikenan mu zuba ni da ke, kuma ina mai tabbatar miki Umar na Ruky ne" Shiru tayi saidai zuciyar a cunkushe take da baƙin ciki, tana neman a lallashe ta tunawa tayi da yayyen ta sai kuma ta fashe da kuka cikin kuka tana cewa, shi yasa nace zan biku, gashi ba mai iya lallashi na, yanzu da ina tare da ku da hakan bata faru ba" Saita tayi kuka da kanta ta share hawayen ta, bayan ta gama aikin tayi wanka ta shirya Abba na dawowa ta same shi ta ce "Abba yau ina son naje gidan su Umma na gano ta" Ya ce "To Sai kin dawo idan kinje sai ki faɗa mata zancen auren naku, na aika wa Ummin ki ma, saidai tace baza ta samu zuwa ba saboda ita ma jiya tayi aure" kudi ya ciro ys bata ya ce "Gashi sai ki samu abin hawa ko" Ta amsa ta ce "Nagode " Tana sauƙa a keke napep ta shiga a ƙofar ɗaki taga Umma tana ganinta ko Sallama bata yi ba ta fashe da kuka ta faɗa jikin ta, Umma kuwa ta ce "Ohhh ni Aishatu, me yake so ya faru ne haka" Bubbuga bayanta ta ringa yi tana lallashi, dama abin da taje buƙata kenan dan haka tayi shiru, ganin tayi shirun ta ce "Adda faɗa min me ke faruwa ne" Labari ta bata tun bayan Tafiyan Yayyen ta har zuwanta gidan su Umar da wannan aure da ake so a ɗaura. Umma ta ce "Kiyi haƙuri ayi auren kinji, ita kuma Umminki, ki kyaleta taje tayi ta auren bazaa ƙara aika mata bama, Yanzu yakai ace tayi hankali ay, amma mace kamar ba hankali, ace za'ayi auren ƴarki amma kice ke jiya kika yi aure, ki kyaleta ay kina da mu, kuma zan kira Adda Bilkisu, takwaranki nasan zata zo ay, Idan zaki koma zamu je tare sai na roƙe shi ya bar min ke ana gobe ɗaurin auren sai ki koma, dan baza a barki haka ba ay, za'ay miki gyaran jiki. Kusan Magrib suka sauƙa a gidan suna isa kuwa sukayi sa'a yana nan, bayan sun gaisa ne "Umma ta roƙi alfarmar a bar mata Bilkisu ana gobe ɗaurin auren sai ta dawo da ita" Nan da nan Baba ya amince sannan yayi wa Bilkisu kyautar kuɗi suka koma. Adda Bilkisu kuwa ana faɗa mata maganan auren da auren Ƙanwar ta, Adda ta ce "Nikan ma ban san auren ya mutu ba ma balle nasan da wani aure da zata yi, kyale ta, nima bazan kula ta ba ma, tayi ta zaman ta a can kauyen," Washe gari kuwa ta turo kuɗi ta ce da Umma ayi abin da ya dace na gyara amarya kafin ta zo. Hakan tundaga lokacin aka fara gyara Bilkisu. Su Mama Amarya kuwa suna jin maganan auren hankalin su ya tashi aynun dan haka suka yi gun Boka, boka kuwa ya amshi kuɗin sa dan ya yi musu aiki. Kullun Ruky kuwa tana manne da waya suna waya da Umar, tana masa kukan a fasa wannan aure, shima ya ce "Ba son ransa bane kuma ya faɗa mata koda anyi bazai taɓa haɗa gado da ita ba, saboda ya tsaneta. Da wannan furucin nasa take murna. Ana saura kwana Uku Adda Bilkisu ta iso tare da yaranta Aliyu da Maryam. Aliyun da zaikai sa'an angon ya kalle ta ya ce "Amarya kenan yaushe rabon in ganki, tin kina yarinya, kinga yadda kika girma kuwa wai kece zakiyi aure, amma taki aka sa miki ko" Ta ce "Eh takin da aka saka maka ka girma shi aka saka min, kaima idan kana da zuciya kayi auren mana" Dariya Maryam tayi ta ce "Kamar ko kinsan a gida abin da Mommy da Daddy suke masa magana akai kenan" Bilkisu ta ce "Tuzuru kawai" Ya ce "Dan nazo bikinki kike ce min tuzuru" Adda Bilkisu tasa baki ta ce "Ay gaskiya ne" Ranan juma'a aka ɗaura Auren Umar Jafar Hamza da da kuma Amaryansa Bilkisu Ibrahim Hamza. Koda na gano Baba cikin fararan kayansa yana farin ciki dan yafi kowa murna da wannan haɗin saɓanin ango da Amarya da suke baƙin cikin wannan auren. Adda Bilkisu tasa Takwaran tata a gaba ta ce "Bilkisu ki saurareni da kyau, naji labarin komai tsakanin ki da mijinki, bawai baya sonki ba, to kiyi haƙuri, kuma ko auren soyayyar kikayi haƙurin ne shine ya dace da ke, balle irin auren ki. Kiyi masa biyayya, banda ƙwiya ki kasance me tsabta a gidan ki, kada ki bar gidan ki da ƙazanta ki kula da kayan mijinki, idan kuna kai wanki ne, kada kina haɗawa da ƙananan kayansa, ke zaki na wankewa, kada ki damu da wani cin mutunci da tsangwama a gurin sa, aure ibadane, Allah zai baki lada, yanzu Allah ya ɗaga martabar ki da darajarki saboda aure, kiyi masa biyayya iya iyawanki, maganan girki kuwa, kada ki bar mijinki yana cin abinci a waje, kin kasance ko yaushe kina canja masa abinci da abinsha, ki kula da tsabtar jikinsa da na shimfiɗarsa ki lura da yadda zakina tashinsa daga barci idan idan ya kama dole sai ya tashin. Kiyi haƙuri, ki riƙe Addu'a Kada kiyi sakaci da shi, domin ita Addu'a makamin mumini ne. " _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/28, 9:12 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 37-38 Ita ko Bilkisu kuka take tayi tasan idan aka bar amanarta a gurin Umar tabbas sai yaga bayan ta, ita kan kwanan ta ne ya kusa ƙare wa domin Umar mungu ne. Da kan ta Adda Bilkisu ta kira Umar yazo da kan sa ya same ta bayan ya gaishe ta, ta ce "Kaji tsoron Allah Umar, nasan Bilkisu ba tsabin ka bace baka son ta, an muku auren dole ne, Bilkisu Amana ce a gurinka, duk da baka sonta, yanzu maganan ƙiyayya babu ita tunda ta zama matarka abokiyar rayuwarka, saboda haka ka riƙe Amana kayi haƙuri da abin da ya faru a baya ka fuskanci gaba, yarinya ce mai haƙuri zaka iya tanƙwarata ta inda kake so, Kai zaka bata tarbiyyan da kake so, domin duk tarbiyyan da ka bata tabbas naka zata bi ta watsar da ta gida saboda haka ina roƙon ka kayi haƙuri ka manta da komai ka rungumi matar" Ya ce "To Nagode insha Allahu baza a samu matsala daga ɓangare na ba" Taji daɗi amsar da ya bata sosai, saidai kuma abin da bata sani ba duk abin da ta faɗa masa ya shiga ta kunnen dama ne ya fita ta kunnen hagu, tunanin sa yadda zai hukunta Bilkisu idan ta tare a gidansa a matsayin mata, gidan da ya jima yana gina shi yana mafarkin sun shige shi shida Ruky Uwar ƴaƴansa, sai kuma ace wata mazinaciyar yarinya ce, zata Shiga yarinyar da ya tsana tun tana yarinya yanzu ace ita ce abokiyar rayuwan sa, Ina ay bazai yuyu ba. Da daddare Su Umma da Adda Bilkisu suka kaita, Nasiha suka sake mata suka tafi suka barta tana kuka, ita ba kukan rabuwa da gida take ba, kukan yadda zata zauna da mijin da aka aura mata take, bata san da wani sabon salon muguntar zai shigo ba, hala yau saboda haushin an aura masa ita da wuƙa zai shigo ya yanka ta, ya tona rami ya bunne. Tana cikin haka kuwa taji motsin shigowa a falo gabanta ya faɗi ta sauƙo da kafafunta ƙasa da suke kan gado tana ji ya buɗe ɗayan ɗakin ya shige. Takai kusan minti talatin a haka, ganin bai shigo yasa ta shiga bayi ta watsa ruwa tasa kayan barcin ta ta kwanta barci ya kwashe ta. Shi kuwa yana shigowa ɗakinsa yayi ya watsa ruwa yayi kwanciyar da, dan ma Baba ya matsa masa sai yazo ne amma da ba abinda zai kawo shi wannan gida. Waya ya ɗauko ya kira masoyiyarsa Ruky suka raba dare suna hiransu. Saidai duk da haka bai makara ba, ya tashi yayi alolo ya fito zai nufi masallaci ya kalli ƙofarta, ta murɗa ƙofar ta buɗe ya hangeta a kan gado tana ta shaƙar barcinta hankalinta kwance doguwar rigar barcin ta ɗaga cinyoyin duk a waje sai sheƙi suke, gashi dama sunsha gyara, ya daɗe a gurin yana kallon cinyoyinta ya yin da yakai kirjin ta ya hango rabin kirjin a waje, ji yayi kamar yaje ya cire rigar duka, ji yayi an shiga Sallah da sauri yaje jikin gadon yana cewa "Ke! Ke!! Ke!!!" Da yaga bata motsa ba ya buga mata duka a cinya, da sauri ta tashi tana sosawa ta kalle shi, ya ce "Kin barni ina ta tashin ki, to lokacin Sallah yayi idan kinyi niyya sai ki tashi idan kuma Sallah ɗin ma bakya yi Zina kika sa a gaba to, dan da kin saba d Sallah ma da ba sai an tashe ki ba" Yana gama faɗa ya fita, ta sauƙo daga kan gadon tayi bayi tana hawaye ta shiga bayi tayi alola tazo tayi Sallah, yana dawowa ya leƙa ɗakin ya ganta a kan sallaya alamar ta idar tana Addu'o'i ne, ɗakin sa ya shige yayi kwanciyarsa. Ita kuwa bayan ta gama ta ɗan kwanta, can ta tuna da shawarwarin Mommy (Adda Bilkisu) Ta miƙe tayi kicin komai ansa ba abin da babu dan haka ta fara shirya kumallo, da yake ƙwararriya ce, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama, ta gyara komai, ko ina fes falon ma ta sake gyarawa dukda dama a gyare yake. Ta shiga ɗakinta nan ma ta gyara sannan ta faɗa bayi tayi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa ta fito, ta ɗebi abinci taci. Da ta gama ta wanke abin da ta ɓata ta dawo falo tayi zaman ta, tana kallo. Tana tsaka da kallo ya fito da alama wanka yayi dan ƙananan kayane a jikin sa, ya hangi dinning table a cike yayi gurin ba tare da ya ce komai ba, ita ɗin ma bata ce masa ba. Buɗe-buɗe ya fara yi sannan kuma ya zauna ya fara ci, yana cikin ci ya kalle ta ya ce "kin gyara ko ina a gidan nan amma saboda raini bazaki gyara ɗaki na ba". Tashi tayi ba tare da ta ce "Komai ba ta shige ɗakin ta fara gyarawa cikin ƙanƙanin lokaci ta gama da yake ɗakin ba wani ɓaci yayi ba, ɗayan ɗakin ta shiga nan kan baya buƙatar gyara saboda ba'a kwanta a ciki ba ma. *** *** *** Ruky tayi gun Mama Amarya tana kuka Mama Amarya ta kalle ta ta ce "To menene kuma" Ta ce "Nidai gaskiya ina son ayi auren mu da Umar da wuri dan kada wannan shegiyar yarinyar ta mallake min shi" Mama Amarya ta ce "Ta ina zata mallake shin, basai ya sake mata fuska ba" Ruky ta ce "Kinsan shi wawa ne, zaije ya buɗe ciki yayi ta cin girkin ta, taje ta masa barbaɗe a ciki ya ci ya fara son ta" Mama Amarya ta ce "Zamu je gun bokan ay zan sake masa bayani, kinsan Baban sa ne baya so, idan Boka ya tura masa abin a zuciya shikenan ba yadda suka iya dole ki aure shi kuma ki zama ƴar gaban goshi a lokacin kuma zaki ci uban shegiyar yarinyar kafin ki koreta ta bar gidan domin Umar naki ne ke ɗaya" *** *** *** Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya baya mata magana saidai yazo ya samu abinci ya cika cikin sa, idan yana buƙatar wani abu kuma zai mata magana cikin gatsali, yanzu idan da sabo ta saba da halin sa, baya damun ta, ita dai tunda ba dukanta zaiyi ba da sauki, kusan kullun sai Baba ya kira ta sun gaisa kuma ya tambayeta idan da matsala ta ce babu Ko yaushe idan yana gidan yana maƙake da waya a kunnensa suna soyewa da Ruky yana faɗa mata irin son da yake mata. Ita ko wannan baya damunta sam. Ya rasa inda zaiyi Babansa ya yarda ya auri Rukynsa. Shiko dama Baba baya son ya auro wata yaje yaci mutumcin Bilkisu, to yanzu ya lura hankalin ya kwanta kuma Bilkisun bata da wani matsala, yasa ya amince duk da ya lura Rukyn ba mace mai tarbiyya bace, amma tunda ya masa biyayya a baya shima ko zai faranta masa rai ta hanyar aura masa wacce yake so. Da kansa Baba yaje gidan ya samu ko ina fes, taji daɗi ganin sa ta kawo masa abin sha sannan ta kaishi dinning dan ta bashi abinci, Ya ci sosai, ya ce "Nayi kewan girkin ki ƴata, tunda kika tafi gidan mu ya lalace ba gyara," Ta ce "Allah Sarki Babana, nima nayi kewarka, wata rana idan na tuna ka kamar nayi tsuntsuwa naje na ganka" Falo suka dawo ya kalle ta ya ce "Ya naga baki yi ɗan kiba ba, irin na amare kodai ba matsala ne" Ta ce "Ba wata matsala Baba komai lafiya" Ya ce "To sai kiyi haƙuri da abin da zan faɗa miki Umar zai kawo miki ƙanwa" Dam! Kirjinta ya ce Ta san hakan zai faru kuma kuma ko da suna waya da Umar a gabanta bata jin komai sai gashi yanzu tana jin wani iri a ƙirjinta... _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/29, 7:10 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 39-40 Ba ya kalle ta ya ce "Yaya Bilkisu ko akwai matsala ne" Tayi murmushin ƙarfin hali ta ce ", Ba wata matsals komai lafiya lau" Ya ce "To kiyi haƙuri ko zai sake yin auren ne badan baya son ki ba" Cikin ranta ta ce "Dama can baya sona dama tsinka auren aka yi da yafi" Nasiha ya mata sosai sannan ya tafi. Bai taɓa fada mata maganan auren sa, ita kuma bata tambaye shi ba. Ana saura kwana uku auren kuwa Ruky ta shigo wannan karon da dogon hijabinta har ƙasa, Bilkisu kan da ta ganta sai da ta waro ido, yaushe Ruky ta koma haka. Tana cikin yin wannan tunani ne Ruky ta ce "Kira min Umar Ke" Zama Bilkisu tayi ta ce "Yaje a koya masa Sallama tunda daga shi har ke ba ku iya ba, kinga idan ya koyo sai ya koya miki" Ta ce "Kan buuu ni keke faɗawa haka to bari kiji nan da kwana uku zan kasance a gidan nan daga lokacin kin daina farin ciki har ƙarshen rayuwanki" Bilkisu ta ce "Baki isa ba, ƙarya kike ki hana ni sakewa a gidan mijina" Yana tsaka da barci ya jiyo hayaniya ya fito yana tsaki Yana ganin su ya kalli Bilkisu ya ce "Ke menene haka kuma" Ruky ta matso kamar zata shafi jikinshi ta ce "My dear Dama nazo ne na zaɓi ɗakina ko" Ya ce "Ɗaki ɗaya ya rage a gidan nan, sai ki shiga tunda kinki ki zauna a wancan gidan, ni gani nayi wannan ɗin ya miki kaɗan" Ta ce "Ni nafi so ma ka haɗa mu gaskiya" Ya ce "Ga can ɗakin da ya rage sai ki ɗauke shi, ay ina ga ma ba sai ansa komai ba, saboda akwai komai a ciki sai dai ki shiga ki duba abin da babu sai a siyo a saka" Ta leƙa ɗakin sannan ta sake leƙa ɗakin Bilkisu ta gata kayan alatu a ciki kuma yafi na wancan ɗakin ta dawo ta ce "My dear ni wancan ɗakin nake so, ka mata magana ta koma wannan din" Ya ce "To kinji Matar gida ta ce tana son ɗaki ki koma wancan ɗin kawai, zan kira masu aiki su mayar miki kayanki can ɗakin a dawo mata da nata" Kafin Bilkisu tayi magana Ruky ta ce "No ni kayan ɗakin ma nafi so ay" Ya ce "To shikenan ba sai an canja ba ma" Bilkisu ta ce "Duk cikin ba wanda ya isa ya canja min ɗaki balle kayan ɗaki, baka faɗa mata cewa kayan ɗakin nan ba kai ka siya ba, Mommyn Kaduna ta siya min kuma da sunana ta siya, dan haka ɗaki ina zaune a ɗaki ba wanda ya isa ya fidda ni, idan baza ta zauna a wancan ba ta bari" Ya kalle ta ya ce"Ke... " Ta ɗakatar dashi ta ce "Saidai ka kashe ni ka fitar da gawata a ɗakin ko kuma ka tsinke igiyar auren ay tana hannun ka, amma ka sani kaya nawa ne bak isa ka raba ni da shi ba" Ruky ta ce "Ka bincika yarinyar nan anya bata sha wani abu ba" Ta ce "Abin da kike sha shi nima nasha yau" Tana tsaye tana girgiza yazo ya riƙe kunnenta ya ce "Ke bakya ji ko" Ta ce "Wallahi idan ka takura min zan faɗawa Baba" Hankaɗata yayi ya kalli Ruky ya ce "Baby ki kyale ta ki zauna a can ɗakin kawai keda gidan ma ya kusa ya zama naki ke ɗaya, bari dai ayi auren" Ta ce "Oho idan ma gida ya koma nata to ay Kaya nawa ne, da su zanyi gaba " Zata yi magana Bilkisu ta ce "Rufe baki nifa na zama ciwon ido sai haƙuri " Umar ya ce "Kije gida zanyi maganin ta ay" Ba musu ta fita ya zauna a kujera ya ce "Kije ki haɗa min lipton zan sha" Kicin ta shiga ta haɗa masa ta kawo ta miƙa masa yana amsa tayi ɗakin sa. Alhaji shine wanda ya wakilci Ruky Yayin da Umar kuma wani Abokin Baba ya wakilce shi inda aka ɗaura Auren su. Murna gun Ruky da Mama Amarya ba'a magana haka, ƙawayenta ta gaiyato sukayi partyn su sukayi baɗala da junan su. Lokacin da za'a kai amarya kuwa har ɗoki take yi ayi-ayi a kaita, inda suka tasa a ɗakinta. Daga cikin masu mata nasiha kuwa tsohuwa ɗaya ne ta mata nasihar arziki. A haka kowa ya watse aka bar Amarya a ɗakinta sai Uwar gida da take cikin nata ɗakin. Saida kowa ya tafi Ruky ta fito Falon ba kowa sai ƙamshi dake ta tashi a falon, ɗakin Bilkisu ta shiga ta sameta a kan sallaya ta ce "Ashe kina jinmu kika ki fitowa to ay ba kowa sai ki fito ki haɗa min tea zan sha" Ba ta ce komai ba Ruky kuwa ta na tsaye a kanta, saida Bilkisu ta gama Addu'o'inta sannan ta juyo ta ce "Baki san inda zaki more ni ba sam, da kin haɗa ni da Allah ne da Wallahi ba abin da zai hana ni haɗa miki saboda a halin yanzu ke baƙuwa ce, amma tunda dole zaki sani sai ki sani dolen in gani" Komawa tayi ta ce "Ay wanda zai saki dole zai shigo kuma sai kinyi" Kallon ta kunna tana yi Umar ya shigo da sauri ta mike taje ta rungume shi ta kiss a kumatu shima rungumeta yayi da ɗayan hannun ɗayan kuma leda ne manya guda biyu a hannun sa, ta ce "Ko yau ma zaka hana in taɓa ka ne" Ya ce "A yau kan duk abin da kike so zakiyi saboda ni ɗin naki ne" Sai ta ce "To ka ɗauke ni ka kaini ɗaki irin na ƴan india" Ɗaukan ta yayi ga ga ledodin a hannunsa, bai direta ko ina ba sai ɗaki, raba ta ya fara yi da kayan jikin, ita ma tana raba shi da nashi daga nan suka yi bayi wanka suka yi sannan suka fito, shikan saida yayi alola ya fito ya kalleta ya ce "Ki koma kiyi alola sai muyi Sallah raka'a biyu dan nunawa ubangiji godiyar mu" Turo baki tayi ta ce "Ni gaskiya na gaji bazan iya ba" Ya ce "To shikenan muci abinci mu kwanta" Ɗauko ledan yayi ya buɗe musu a cikin ledan sukayu ta ci, Ruky kan tsakanin ta da Allah take ci Bil hakki da gaskiya, Hollandia din kan ma da bakin abin ta ɗauka ta kwankwaɗa, suna gamawa suka kwanta, ita kan tashi tayi ta cire kayan jikin ta haihuwar uwashi ta ce "Saidai shima ya cire nashi, hakan ya biye mata suka shiga bargo suna wasa da junan su, sai dai shi Umar kwata-kwata baiji sha'awanta ba, suran jikin ta ma bata burge shi ba, yana biye mata ne kawai dan kada taji haushi. Gaba ki ɗaya nonuwanta sun kwanta kamar uwar da ta shayar da yara goma, gwara ma wata uwar saboda tana gyarawa, ba wannan yafi bashi haushi ba, sai lokacin da ya shigeta yajita kamar bakin bokiti, saidai ba yadda ya iya haka ya biya mata buƙatarta, dan ba ita ta biya masa ba. Mikewa yayi zai shiga bayi dan tsarkake jikin sa sai ji tayi ta ruko shi ta ce "Bai ishe ni zo ka ɗan ƙara min mana" Juyo wa yayi yayi mata wani mungun kallo. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/30, 2:39 PM] Mim😘: _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 41-42 Ta sake damƙe shi ta ce "My dear lafiya" Ya fizge hannunsa Ya ce "Ni ɗan akuya ne kamar ki" Ya shige bayi yana da na sanin auren ta, a rayuwansa ya tsani macen da ta bada kanta a waje kyamar su yake ji, sai gashi yau yayi taraiya da ita, yau me zai mata ya huce takaici, wai me yasa shi baida sa'ane duk auren da yayi guda biyu duk wasu mazan sun sun riga shi moran jikin matan sa, tir da halin mata tasu irin wannan halin. Yana fitowa ya samu ta haɗa kai da gwiwa tana kuka yasa kayan sa zai fita ta ce "Nasan abin da yasa kayi fushi dani dan na rasa budurci na ne, hakan da ya faru ba yin kaina bane nima, tsautsayi ne ya faɗa min, shekara biyar kenan da wasu suka sace ni suka min fyaɗe har su uku, dama nayi tunanin wannan rana zata zo min mijina zaiyi baƙin cikin samuna a hakan, kayi haƙuri na ɗauki duk wani hukuncin da zaka min amma kada kayi fushi dani, saboda ni ba mazinaciya ba ce" Tausayin ta yaji yazo ya dafa ta ya ce "To ya isa haka kiyi haƙuri, ina tare dake " Rarrashi yayi tayi yana mai jin tausayin ta ita ko Daɗi fal cikin ranta. Da Sassafe Bilkisu ta kama shirya musu break saida ta gama komai sannan tayi wanka ta fito kenan zata ɗeba ta gansu sun fito Ruky sai kwanciya a jikin sa take, Bilkisu kan ta kawar da kanta gefe guda zata ɗebi abincin Ruky ta ce "Me zaki dashi kuma kije ki girka wani" Bilkisu ta kalleta ta ce "Uban kuturu yayi kaɗan bare na makaho" Ta ɗeba yadda zai isheta ta wuce ta gefensu, Ruky zata yi gunta Umar ya jawota ya ce "Kyaleta so take ta ɓata mana wannan rana" Ta koma suka zauna suka ci abincin su. Umar dai haka ya manta ma ta yaya ya samu Ruky ko yaushe suna tare yana biya mata buƙata dare da rana safe da yamma ta maida shi ɗan bunsuru, saidai kuma sam yaƙi barinta ta wulaƙanta Bilkisu Aduk lokacin da taso yin hakan takan mata wayo tun bata gane wa har ta gane wayo yake mata, gashi ita kuma sai rashin kunya, abin ya fara isan ta, dan haka tana zuwa gida na farko ta faɗawa Mama Amarya, Mama Amarya ta ce "Lalle kuwa ina ganin da son yarinyar nan a ransa, amma kuwa zanje gun boka zai raba su kuwa" Ta kuma ware hannunta ta ce "Ya maganan kuɗi fa yana sakar miki kuɗi ko" Ta ce "Gaskiya baya sakar min komai" Mama Amarya ta ce "Sha kurumin ki saura kuma idan kin fara samu ki manta da ni" Ta ce "Haba Mama yaya zan miki haka ay kema kinsan hakan baza ta faru ba" Hiran su sukayi tayi duk rabin hiran nasu na ta yadda zasu ga bayan Bilkisu ne. Da yamma kuwa tayi gurin watsewarta dan a cewar ta baza ta iya rayuwa da namiji ɗaya ba, ita ko Mama Amarya gun boka tayi. A gun watsewantan kuwa saida tayi lalata da maza uku, mace ɗaya, dan gurin Maɗigo ma ba'a barta a baya ba, kuma ta samu abin da take so wato kuɗi dan sun cika mata jakarta da kuɗi. Sai ƙarfe 9:00pm ta dawo ta samu Umar shi ɗaya a falo ta zauna a cinyarsa ta ce "My dear kai ɗaya ne haka" Ya shafi fuskrta ya ce "Dawa kike son na kasance to ko so kike na kira yarinyar nan" Ta ce "Da kuwa lahira tayi baƙuwa" Dariya yayi ya ce "Nayi kewanki My Ruky kin riga kin sabar min da jikin ki, ina zaune a nan ina ta tunanin ki " Nanko suka faɗa abin da aka saba. Zaman sa da Ruky tasa ibadan sa ta ragu, yana sallah amma ba'a yin ta akan lokaci ita ma yana sallama zai miƙe ba zancen yin tazbihi wa ubanginsa balle kuma Addu'a. Yau ƙarfe 10: 45am ya tashi alola yayi yayi Sallahr asuba da haushin Bilkisu yau ya tashi, kwana biyun nan ta raina shi shida matar sa, dan haka yau zai zane ta, fita yayi ya ga ta haɗa musu break kamar yadda ta saba yau, gidan tsab yake a gyare ko ina saidai inda yake kwanciya ne kuma datti har kuɗin cizo sun fara yawo suna cizon sa. Ɗakinta ya shiga ya ganta kwance tana barci ya buga mata duka a cinya da sauri ta tashi tana sosawa, ya nuna mata hannayen sa da jikin sa yana cewa "Dan ubanki kalli jikin, kalli hannayena yadda kuɗin cizo suka cije ni, sai ki gyara ko ina a gidan nan amma baza ki gyara gun kwanciyar mu ni da Mata na ba" Bilkisu ta ce "Ahhh Lalle ma, ita matar taka bata da hannu ne da baza ta gyara muku ba, kuɗin cizo ku ya shafa ay, ina ruwa na" Ya ce "Kinga ina kyale ki shine zaki nemi ki raina ni" Kwanciya tayi ta jawo bargo ya rufe kanta shi kuma ya janye ya kuma ɗaka mata duka a cinya ta kuma ta ce "Allah ya isa mungu kawai" Bulala ya ɗauka ya ringa zana ta shi tana kuka tana cewa "Allah isana" Saida ya gaji dan kansa ya ƙyaleta, kuka ya ce "Dole taje ta gyara musu ɗaki" Fita tayi tana kuka ta shiga ɗakin da tun da aka tare a cikin sa baiga tsintsiya ba, sai tsami da wari yake, zanin gadon kuwa sai wari yake saboda ƙazanta yayi yawa akan sa, haka tana kuka ta gyara ba laifi yayi kyau ɗakin saidai bangon ɗakin ne da ya ɓaci da jinin kuɗin cizo, inda in an gansu ake kashe su a jiki. Haka take kasancewa da laifi da ba laifi ba kullun a duka, har Ruky ta fara nata ita ma, kai tsaye zata ce tana son mata abu kuma dolen ta ta mata. Idan ba haka ba tasha duka. Ruky kan yanzu ta gaji da Umar dan zabbin maza take so yanzu, kwata-kwata bata son mu'amala da shi, wannan yasa ta ƙirƙiro tafiya, ta ce zata yi tafiya zata yi sati, ya ce "Ina zaki je ne" Ta yi masa wani kallo, ta ce "Dallah Malam matsa kuma sai na faɗa maka inda zanje, to bazan faɗa, nidai abin da nake so da kai kuɗi zaka bani" Ya karyar da kai ya ce "To ba damuwa" Sassafe ya shirya mata kaya ya bata kuɗi da yawa ta tafi ɗakin Bilkisu ta ce "To Bilkisu zanyi tafiya saura kuma ki fito falo kina masa feleƙe da wannan tsinannun suran naki dan na lura shi ɗin ɗan akuya ne zai iya nemanki" Bata ce mata komai ba har ta fita, haka ta tafi ba a son ransa ba. Gidan ya masa wani iri baya jin daɗi dan haka shima da wuri ya fita gurin aikinsa. Ko da aka tashi ya dawo yaci Abinci ya kuma fita Bilkisu kan ma bata san ya shigo ba, haka ya gama ya fita, sai dare ya dawo ya shiga ɗakin sa ya kwanta sai juyi yake yana tunanin yadda zaiyi da munguwar sha'awar da take damunsa. Ga Ruky ta sabar masa da kanta duk da ba wani daɗinta yake ji ba. Tunawa yayi da wata matar, ya miƙe da sauri yayi ɗakin ta ya murɗa ya hangota ta baje a kan gado tana ta barcinta. Ciyarta ya zubawa ido daga bisani yakai hannunsa kan cinyar yayin da ita kuma ta buɗe ido jin an taɓa ta... _Ina masoya Bilkisu ku bata shawara ta yadda da Umar ne ko taƙi shi_ _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [5/31, 9:39 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 43-44 Tashi tayi ta zauna tana kallon sa, gani tayi ya hau gadon ya rungumeta ta matsa can gefe jikin bango, ya kuma matsawa ta fara kuka ta ce "Dan Allah kada ka dake ni kaga ban maka komai ba" Ya ce cikin wata irin murya, "ke dalla ba dukan ki zanyi ba" Gani tayi yana ƙokarin cire mata riga nan fa suka fara kokawa tana son kwatan kanta, duk da bata da ilimin sanin wannan harka yanayinsa ya tabbatar mata da halin da yake ciki kuma tasan me zai mata, hakan yasa tayi saurin barin ɗakin, ya riƙota suna kokawa, da yake ƙarfin su ba ɗaya ba, yasa ya iya rabata da kayan jikinta. Ganin zaici nasara a kanta yasa ta fara kuka tana cewa cikin kuka "Dan Allah kayi haƙuri kada ka min komai " Harara ya mata, ya ce "Kin manta ni waye a gurinki, da baza ki yadda da ni ba, ohhh kin fi son ki yadda da mazan banza a kaina. " Yo wa kanta ya kuma yi ta dunƙule hannu ta masa naushi a idonsa ya kama gurin ya kwanta kan gado taja bargo ta rufe jikinta zata fita, ganin halin da yake ciki yasa ta dawo tana cewa "Dan Allah kayi haƙuri Wallahi ban sani bane" Sake riƙeta yayi ya matse ya ce "Kin bawa wasu ma balle ni, har kina ƙoƙarin ji min ciwo" Kokawa ce ta barke tsakanin su saidai kuma yaci nasa a kan ta, inda take ta kuka da yaƙushi harda su cizo amma Umar ya jure, saboda yadda yaji Bilkisu a cike tam, cikekkiyar budurwa, jikinta kuwa ga ƙamshi ga kuma ni'ima mai sawa mai gida farin ciki, bai taɓa tunanin haka zai samu Bilkisu ba, bai taba sanin ana iya samun irin wannan ni'imar a jikin mace ba, gaskiya ya cuci kansa, kuma ya cuci Bilkisu. Ko da ya samu nutsuwa ya juya yaga yadda take zubar da hawaye, shima ji yayi hawayen na zuba a idonsa ya jawota ya rungumeta yana bubbuga bayanta, kukan ta ne ya tsaya jin yana bubbuga mata baya, alamun yana rarrashinta miƙewa tayi daga jikinsa ta koma gefe tana cewa "Allah ya isa tsakani da kai, bazan taɓa yafe maka ba" Hannunta ya kama ya ce "Haƙiƙa na cancanci duk wani hukuncin da zaki min kuma zan ɗauka, nayi miki mummunan zato kin faɗa min ke ba mazinaciya bace amma naƙi yadda yau na tabbatar da hakan fizge hannunta tayi ta sauƙa zata tafi nan taji baza ta iya tafiya ba ta koma ta kwanta ta kuma fashewa da wani sabon kukan. Bayi ya shiga ya haɗa mata ruwan ɗumin da dettol ya dawo ya sa hannu ya ɗauke ta kamar jaririya, tana wutsil-wutsil da ƙafa haka ya kaita ya tsomata a ciki tana dukansa da zaginsa amma haka ya dannata a ciki, da taji daɗin ruwan sai ta zauna sau uku yana canja mata, sannan ya fita ya barta, ita kuma tayi wankan tsarki a ranta tana ƙara tsine masa. Taba fitowa taga ya canja zanin gado ya shimfiɗa wani sabo, ya ɗauki zanin gadon a hannun sa yana son ya shiga bayida shi yana kallon ta, ita kuma sai hararansa take, ya shiga cikin bayin, ita kuma ta shafa mai tasa wani kayan barcin ta kwanta, gani tayi ya fito da zanin gadon da ya wanke a hannunsa ya fita da shi, yana fita ta rufe ƙofa tasa key ta dawo tayi kwanciyarta. . Shi kuwa yana shanyawa ya dawo ɗakin amma yaji a rufe ya bubbuga shirubata buɗe ba haka ya haƙura ya koma ɗakinsa, yana jin farin ciki yana ziyartarsa . Daga bisani kuma ya ringa murmushi yana zubda kwalla. a haka barci ya kwashe shi. Kiran sallahr farko ta tashi, ta shiga bayi a hankali ta sake yin tsarki da ruwan zafin ta sake jin daɗi, sannan tayi Alola tayi raka'atainil fajr sannan tayi tayin Addu'o'i har aka kira Sallah tayi Sallah asuba. Nan ma tayi ta ƴan Addu'o'inta. Sannan ta kwanta a gurin barci ya kwashe ta. Sai ƙarfe 10:15am ta tashi fitowa tayi falo taji ƙamshin girki na tashi alamun ana girki, shiga tayi kicin ɗin ta ganshi yayi kaca-kaca da kicin ɗin wai yana haɗa kumallo, komawa tayi ya jawota ya rungumeta ya ce "Nasan har yanzu kina fushi da ni ko" Haushi ya bata ta kama hannunsa tana son ta raba shi da jikinta amma ina. Zamowa yayi ƙasa ya durƙusa ya rungume ƙafafunta ya ce "Kiyi haƙuri dan Allah kada ki azabtar dani, ki yafe min nasan na miki mummunan zato a baya na alaƙanta ki da abin da baki aikata ba, Har ga Allah Ina sonki, to abinda yasa nake miki hakan saboda abin da aka ce kinyi ne, wanda a yanzu nasan ƙazafi aka miki, ki taho gare ni, muyi rayuwar ma'aurata" kallon sa take yayin da ta hango hawaye daga cikin idon sa yana zuba da sauri itama ta durƙusa tana share masa hawayen shi kuma ya rungumeta yana bubbuga bayanta yayin da shi kuma yake sake zubar da hawayensa. Tunani kala-kala fal cikin ranta, wai ita ce Umar ke lallashi har yake zubar da hawaye akan ta. Ɗagowa tayi ya riƙeta ya ce "Ina kuma zaki je? " Ta ce "Zanje na haɗa mana kumallo" Ya ce "Na gama mana komai ay, saidai in baza ki iya ci ba" Ta miƙe zata tafi ya ce "Ina zaki je" Ta ce "Wanka zanyi" Ya ce "To je ki kiyi barin ƙarasa" Ba musu ya tafi tana zuwa ta faɗa kan gado daɗi ne taji a ranta wai ita Umar ke tattali, dama can ashe yana son ta, saboda ƙazafin da aka mata ne yasa ya tsane ta, yau dai ya san wacece ita, yasan cewa bata taɓa yin zina ba, inko son da yake mata gaskiya ne to lallai ita ma zata rungumi mijinta. Sai da ta gama tunaninta ta shiga tayi wanka, yau kan sai ta tsinci kanta da tsara kwalliya kamar zata je gasar sarauniyar kyau, Atamfa koriya ta saka ɗinkin riga da sket aka yi, ta ɗaura ɗan kwanlin ta ɗaurin zamani, tayi kyau matuƙa, ta fito tayi kicin ɗin taga yana ta gyarawa, ya juyo ya kalle ta ya isa gurinta ya kama hannunta ya ce "Kinyi kyau sosai" Murmushi tayi ta ce "Ka fini kyau ay" Ya ce "Kalle ni fa yadda nayi datti fa" Ta ce "Kaje kayi wanka zan ƙarasa" Ya ce "Nagode, " Ya shige ɗakinsa ita kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta gama gyara kicin ɗin ta haɗa da falo da kuma ɗakin ta, ta shiga ɗakin sa taga ya shirya da shadda ɗinkin kaftan ya saka hula yana gyara sajen sa a gaban madubi. Ta ce "Zaka fita ne kuma" Ya kalle ta ya ce "Wannan kwalliya duk naki ne, ba inda zanje yau" Gyara ɗakin ta fara yi yayin da ya taya ta, bayan sun gama ne suka je dan su karya, A baki ya ringa bata abincin tana ci saida ta ƙoshi shima ya ci. Yini suka yi suna Soyayya a gidan, Idan lokacin Sallah yayi ita da kanta take cewa yaje masallaci. Ƙarfe biyar ya ce "Ta shirya suje su gaida Baba" Ta shirya tsab suka shiga mota suka yi gidan Baba, a yana parking ta fito ya ce "Ina zaki je, ki jira ni" Ta jira ya rufe motar yazo ya riƙe mata hannu suka shiga falon tare, Baba suka tarar a falo yana ganin su ya washe baki, Mama Sauda ta fito daga kicin tana ganinsu a haka ta ɗaure fuska tana musu wani kallo, Bilkisu na ganin haka tayi ƙoƙarin ƙwace hannunta yayin da shi kuma ya damƙe hannun. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/2, 7:12 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ _*Allah ya jiƙanki Dada Wasila Isah Musa, yau shekara karanki goma kenan da tafiya, Allah yasa kin huta, Allah yasa kina cikin rahman sa, yayi wa ƴaƴanki Albarka, Munyi kewanki Dada Wasila"*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 45-46 Baba ya lura da hakan yasa shima ya mata wani kallo wanda yasa ta koma ba shiri, ya kalle su ya ce "To Kun tsaya min a kai ku zauna mana" Murmushi suka yi duka suka zauna a ƙasa suna, gaishe shi, bayan sun gaisa ne Baba ya kalli Umar ya ce "Ina kuka bar Rukayyan" Umar ya ce "Tayi tafiya ay" Ya ce "Ina taje kuma" Kai tsaye ya ce "Ban san inda taje ba ta ce dai sati guda zata yi" Baba ya kalle shi ya ce "wani irin aure kake haka har matarka tayi tafiya amma baka san inda taje ba" Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi Baba ya ce "Baka cikin hayyacin ka Umar, ya za'ayi ka saki mace tayi abin da take so" Faɗa yayi ta masa sosai sannan ya ce "Idan kun koma gida ka buga mata waya ta dawo ko ta faɗa maka inda take" Ya ce "To Baba" Ya kalli Bilkisu ya ce "Bilkisu yaya kuna zaune lafiya dai ko" Ta ce "Lafiya lau Baba" Ya ce "Baki da wata matsala ko " Ta ce "Ba komai " Ya ce "Masha Allah mun gode Allah, kuje ku gaida Maman naku" Suka tashi a tare suka yi kicin ɗin Suna zuwa Mama Sauda ta harare su duka ta ce "Wannan wani irin karuwanci ne, a gida na zaku na yin haka, wato ki nuna wa mutane ke cikekkiyar Karuwa ce yasa kika wani riƙe masa hannu kai kuma da yake wani hotiho ne ka biye mata, ay dama na faɗa lalata min ɗa zaki yi" Ta fizge hannunta daga nasa zata koma Umar ya tare ta ya ce "Haba Mama nifa bana son kina faɗan haka, Bilkisu fa ƴarki ce ki daina faɗa mata wannan sunan kinsan ba daɗi" Ta ce "Ƙarya ne ko ba da kwarko aka kama ta ba, ohhhh ka ta mantar da kai ko, saboda ta barbaɗe ka kasha kunu ko, kasha a shayi, kaci a abin ci ko, to ko har abada sunan nan bazai canja na" Fashewa tayi da kuka ta koma falo shi kuma ya biyo ta Maman tana kiransa amma ko ya juyo. Baba miƙewa yayi ganin tana kuka ya taro ta, ya kama hannun ta ya zaunar da ita kan kujera ya kalli Umar da yake tahowa ya ce "Menene kuma" Umar ya ce "Ita da Mama ce " Shiga yayi Umar kuma yazo yana bata haƙuri ta sigar lallashi. Yana zuwa ya sami Mama Sauda ya ringa zazzaga mata faɗa amma tayi shiru ko a jikin ta, ya koma gun su ya samu Umar ɗin yana lallashin ta, ya ce "Ɗauki matarka ku tafi gida ka lallasheta" Ya miƙe ita ma ta miƙe suka tafi Baba ma ya raka su har gurin mota yana bata haƙuri. Har gida suka je tana kuka, shiko sai faman lallashi yake daga bisani ya kifata a jikin sa yana bubbuga bayanta, jin an kira Sallah Magrib yasa ta tsaida kukan ta ce "Ka tafi masallaci nima zanyi Sallah " Ya ɗan karyar da wuya ya ce "Amma baza ki rufe min ƙofar ki ba" Ta ce "Eh amma saidai idan kaje kada ka dawo, ka tsaya kaji wa'azi zuwa Isha idan anyi Sallah Isha ka dawo" Ya ce "To amma kada nazo na samu kina wannan kukan kiyi haƙuri ". Ta ce "Komai ya wuce ba damuwa" Ya ce "Ina son ki nuna min ya wuce ɗin ta hanyar tanada min kanki" Murmushi tayi haɗi da shigewa ciki don yin alola. Shima fita yayi zuciyarsa cike da tunanin matarsa. *** *** *** "Gaskiya Abin da kake baya dacewa wannan ay bokanci ne" Ya daka mata tsawa "Ke kin isa ki hana ni abin da nasa a gaba ne, wannan sana'an da kike kallo dashi nake samo muku tuwon da kuka raina, kuma tun kafin kizo gidan nan ake yin ta idan baza ki iya gani ba kiyi gaba" Ummi ta ce "Ni gaskiya nake faɗa maka" Ya ce "Hali ki kiyaye ni da irin wannan maganan banzan naki" Ummi kenan da mijin da ta aura, da bincike dama ta aure shi matansa biyu ita ce ta uku, sai daga baya ta gane halisa, wato Ɗan bori ne, kuma boka, kullun daga safiya zuwa yamma mataye ne suke zuwa masa suna faɗan masa sirrinsu, yana basu magani ta hanya marar kyau, ko a wulaƙanta kishiya ko wani ɗan uwa, mazan ma ba'a barsu a baya Musamman ƙananan ƴan siyasa sai su fake da sunan a musu Addu'a. Wasu suna dacewa wasu kuwa saidai suyi ta ɓata kuɗin su. Duk samun kuɗin da ake yi abinci ɗaya ake ci a gidansa Safe rana dare, wato tuwon masara da miyar kuka, daga su har yaran tuwon ya ishe su suna ci ne kawai da haƙuri, ga gidan ba tarbiyya yara basa ganin girman babban sai iyayen su, suma manyan basu kama girman su ba, haka zaka ji yaro ya kutuntumawa kishiyar uwarsa ashar kuma uwarsa baza ta ce komai ba haka uban ba. Sassa Shida ne a gidan, Sassa na farko shine na asalin mai gidan wanda tun asali shine silar taɓarɓarewan gidan, yaran sa bakwai biyar maza biyu mata, matan sunyi auren su, mazan kuwa kowa yayi aure ya kama sassan sa, Zalimu shine babba shine kuma mijin su Ummi matansa uku, wanda shima bai kama girman sa ba, haka zai cire riga yayi dambe da matan ƙannen sa, saidai yaran gidan suna tsoron sa sosai. Sai na biyun su shine Sallau shi direban mota ne yana ɗaukan fasinja zuwa gari gari, akwaishi da aure-aure yanzu haka dai matans uku. Shima bai kama girman sa ba. Sai na ukun su, shima direban ne ne, shi da daman sa, matan sa biyu, sai kuma na huɗu hadi shiko matan sa ɗaya, sai ɗan autan su da baiyi auren ba, shima da sassansa sai dai akwai shi da lalata yaran mutane, har na gidan bai kyale ba, idan aka akayi magana maman ta ce ay yaran su suka kai kan su. Ummi tayi nadaman auren wannan mutumi ga gida ba tarbiyya haka ƙaramin yaro zaiyi ta zaginta. *** *** *** Rayuwa me daɗi suke a gidan ta saba da shi shima ya saba da ita sosai, idan ya tafi gurin aiki Allah-Allah yake ya dawo ya kasance da Matarsa. Satin Ruky biyu ba ita sukan sun man ta da wata aba wai Ruky sai dai lokaci-lokaci yakan tuna ta yakan ce ko ina ta shiga, saidai ya raya a ransa idan har ta dawo dole su ya raba musu kwana don bazai iya rayuwa ba Bilkisu da take sanyaya masa zuciya ba. *** *** *** Mama Amarya ne ta ɗaga waya ta kira Ruky tana ɗagawa ta kutuntumo mata ashar "Dan abu kazan ubanki kina ina ne" Ta ce "Haba Mama ina tare da sabon kamu ne dai, kinga yadda yake sakar min kuɗi ne," Ta ce "To Boka ya ce asirinmu yana gab da karyewa dan haka kiyi sauri ki dawo kuma, ki dawo da kuɗi sosai dan za'a bawa boka" Ta ce "To shikenan ina nan dawowa kada ki damu Mama Umar nawa ne ni ɗaya. *** *** *** Ya dawo a gajiye saidai yana ganin matar tasa yaji ba wata gajiya, wanka yayi yasa ƙananan kaya T-shirt da dango three quater yazo ya ci abinci bayan ya gama ta haɗa kayan ya bita ya taya ta suka wanke tare da sake gyara gidan, ko ina fes da ƙamshi, yana zaune a tsakiyar falo tazo ta kwanta tayi matashi da cinyarsa ya shafi fuskanta, suna a haka suna hira cikin nushaɗi Ruky ta shigo idon ta ya kai kansu tuni kayan hannun ta suka zube yayin da wayarta ta tarwatse, lokacin suka juyo duka suka ganta... _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/2, 7:45 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ _*Dada Rabi Isah Musa Macen da take haɗa kan ƙannenta, Allah ya ƙara miki zaman lafiya keda mijinki ya albarkaci yaranki*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 47-48 Tsawa ta daka musu "Wannan wani irin iskancine, ke ƙaramar ƴar iska me na faɗa miki" Bilkisu ta miƙe Umar ya tashi ya ce "Me haka zaki zo kina cika mana kunne" Kallon su take sakaka sannan ta shigo jiki a sanyaye ta ce "Amma hakan kafin adalci kalli yadda kuke fa kasan bazan ji daɗi ba" Ya ce "Wannan ɗin ba mata ta bace kike nufi ko me, ina da ikon yin komai da ita saboda mata ta ce dan haka ko ki zauna in raba muku kwana ko kuma ki koma inda kika fito" Shiru tayi ta tashi tayi ɗakinta ta faɗa kan gado ta fasa kuka. Da dare yayi kuwa Bilkisu kwanciyarta tayi don tasan yau gun matarsa zai tafi, ga mamakin ta ta jishi yana buga ƙofa, ta miƙe taje ta buɗe ta ganshi Kafin tayi magana ya wuce ya kwanta a kan gado ta juyo ta ce "Ya Umar ba ga Ruky ta dawo ba, yakamata ka kwana a ɗakin ta ne" Ya kalleta ba tare da ya ɗago ba ya ce "Aa kada ki min haka ki kyale ni a gurin ki, rabuwa ta da ke masifa ce, na saba da ke" Ta girgiza kai ta ce "Haƙuri zaka yi kada Allah ya kama ka da laifi, ka tafi kada fushin Allah ya kama ka, tana da hakki a kanka, idan kaƙi zuwa gurin ta tabbas zamu haɗu da fushin Allah" Tsaki yayi ya kwanta, ita ko taci gaba da masa nasiha karshe dai yaji jikinsa yayi sanyi ya miƙe yayi ɗakin Ruky ita kuma ta rufe ƙofa ta dawo ta kwanta, ji tayi ba daɗi ta saba da mijinta yanzu gashi zaije ya kwana a ɗakin wata, yanzu abin da yake mata haka shima zaiyi wa waccar, kuka ta fara yi wi-wi da taga ba mai iya lallashi ta share hawayen ta ta tashi tayi alola ta ɗauki Al-qur'ani mai girma ta fara karantawa da sautinta mai daɗi. Lalle Al-qur'ani waraka ce domin taji wasai a zuciyar ta kuma da ta kwanta barci ya kwashe ta. Koda yaje gun Ruky kuwa ta kama masifa, yana Yana jinta da yaji masifar ta ishe shi ne ya miƙe ya ce "Wai ke me ya same ki ne, me yasa kika fiya son ki, tunda na auro yarinyar nan ban taɓa bi ta kanta ba, ina ganin irin wulaƙancin da kike mata na sani sarai na kyale ki, yanzu dan na kasance da iya na lokacin ƙalilan shine kika damu kanki, to bari kiji Bilkisu mata ta ce, ba wanda ya isa ya raba mu, kuma zan raba muku kwana, kwana bibbiyu zannayi a ɗakin ko wannen ku idan baza ki zauna ba ga hanya nan" Shiru tayi ta samu gu ta kwanta amma kuma taci Alwashin ɗaukan mataki. *** *** *** Kunna redia akayi aka kure vulum waƙar bori ke tashi a gidan, yayin da Zalimu yake taka rawa haɗi da buga ƙafa, ƴaƴansa ma suka shigo suna yi da buga ƙafa idan kuma akayi tsalle sai a buga ɗuwawu a ƙasa. Ummi kuwa tana ɗaki tana ta cin tuwon haɗi da nadaman auren wannan mutumin, uwar gidan sa Shaga ce ta shigo ta ce "Kai Hali tsabar munafunci sai ki shige ɗaki kina kuka ga mai gidan mu yana raɓashewa baza ki fito mu taya shi ba" Ta ce "Nikan bazan yi wannan shirmen ba" Zalimu naji ya shigo ya ce "Kyaleta so take na sake ta ta koma gidan tsohon mijinta kuma ba yadda za'ayi na sake ta, bafulatanan banza kawai, ay duk Fulani munafukaine" Ta tsakiyan da yake baffulatana ce ita ma ta ce "Ahhhh Zuminu ka daina sa munjaye, kada ka sake zagin mutane idan ba haka ba sai mu bada hamata iska" Ya ce "To Tsaro nake ji, yanzun nan sai na ballaki na kaiki gidan ubanki su ɗaure ki samu sauƙi kuma dole ki dawo" Ta nuna shi da yatsa ta ce "Wallahi ƙarya kake baka isa ba, " ya bata mari nan fa suka fara dambe yara kuwa suna ihu har da su ɗa da shewa, dukan su sunji jiki dan asabe ita ma mace mai ƙarfi, saidai tsirara da ya mata yara suna ta ihu, ganin haka Ummi ta fito tana rabiya ta kama Asabe tana son tura ta ɗaki dan jikin ta ba kaya Ita kuma ta ɗauki farantin silver zata rotsawa Zalimu sai aka yi rashin sa'a ta rotsawa Ummi. Ummi ya kama gurin tayi ɗakin ta Zalimu kuwa ya ce "Maganin ki kenan ba shiga abin da ba ruwan ki ba" *** *** *** Haka Ruky ta haƙura ya raba musu kwana bibbiyu, duk lokacin da yake ɗakin Bilkisu takan sashi ibada da kanta take tashinsa ya wuce masallaci, baya taɓa rasa Sallah asuba yana yinta akan lokaci kuma, amma idan a ɗakin Ruky ne, wankan tsarkin ma sai zai fita yake yi sannan yayi Sallah asuba, girki kan Bilkisu ta yadda zata ringa yi sabo da Ruky bata iya komai ba, shi kansa idan yana ɗakin Bilkisu yafi sake wa, kuma yafi samun farin ciki. Suna kwance kan gado ya kalleta cikin murmushi ya ce "Baby kwana biyu naga kina rama da yawa kuma bakya cikin kuzari kodai wani abu na damun ki ne" Ta girgiza kai ta ce "Ba komai amma nima dai kwana biyu sai ina jin kasala Wallahi wataran da kyar nake gama aikin gidan nan ga tashin zuciya da rashin kuzari, amma ay ba komai bane canjin yanayi ne" Ya sake kallonta da kyau sannan ya kalli kirjinta yayi murmushi ya ce "Eh tabbas canjin yanayi ne, gashi Allah ya nuna min kina ɓoye da ajiyata" Ta ce "Me kenan " Ya ce "Bayan ramar da na gani, kin kuma yin waji ja, kinyi haske musamman kuma kirjinki da ya cicciko wannan ya tabbatar min da kina da ciki" Ta mike ta sauna ta ce "Jishi sai kace wani uwar mata ina kasan wannan kai kuma" Ya ce "kin manta aiki na ne, bayan dabbobi da nake lura da su, ina lura da mutane, sai dai kuma aikina akan dabbobi ne, bama mu ba duk wanda ya ganki zai san kina da ciki idan kuma kina musu tashi muje a miki scaining" Ta ce "Hmm nidai barci nake ji" Murmushi yayi ya kyale ta sukayi barcin su. Cikin ikon Allah kuwa sai gashi cikin ta yana girma, yana kaiwa wata huɗu ta fara jin motsi, ranan yana dawowa ko barin sa yaci abin ci ta kasa yi ta ce "Ya Umar Macijin ciki yana damuna, kaji yadda yake min zillo a ciki" Dariya yayi ya ce "Ɗan nawa ne maciji, " Ta ce "Ni gaskiya muje asibiti haka cikin yake, kasan inda yake min ne, zillo fa yake min" Ya ce "To barin ci abinci" Ta ce "A'a ka Bari sai mun dawo gaskiya" Yayi dariya ya ce "Muje to" Hijabinta ta ɗauko tasa suka tafi, suna zuwa aka mata gwaji aka tabbatar mata tana da ciki wata huɗu ta riƙe cikin ta kalli likitar ta ce "Wai ni ɗane a ciki na" Likitan tayi murmushin ta ce "Ƙwarai kuwa ko kina mamaki ne" Ta ce "Ikon Allah " Shiko Umar bakin nan yaƙi rufuwa ya wangale 32 a waje, aka basu shawarwari suka koma gida, ita kan hannunta na cikin ta sai shafawa take, ita kaɗai tasan irin farin cikin da take ciki. Ruky kuwa tana fahimtar cikin jikin Bilkisu da kuka tayi gun Mama Amarya tana faɗa mata yanzu Umar baya son ta ya raba musu kwana da Bilkisu yanzu kuma har ciki ya mata. Mama Amarya ya ce "Kwantar da hankalin ki kinji zanyi wa boka bayanin komai idan yaso a zubar da cikin kowa ya huta," Ruky ta ce '"Nifa gaskiya ciki nake so nayi nima ko ta yaya, kinga yadda yake ji da ita ne, har fa kicin suke shiga tare" Mama Amarya ta shirya tayi gun boka ta faɗa masa komai ya ce "Cikin nan bazai taɓa zubewa ba sai an haife shi, sai dai a sa ya tsane ta ita da cikin" Mama Amarya ta ce "To shikenan duk ba damuwa zanje na amso kuɗi a gurin ta zan kawo maka" Sai da suka gama shirin su na sharri sannan ta tafi. *** *** *** Tunda aka rotsamata farantin silver bata kuma shiga rabiya ba, idan an fara faɗan ma saidai ta koma ɗaki, tadai Addu'a take Allah ya rabata da wannan gidan. Idan ko ya tashi tsiyar sa, ya ce dan munafunci kuma sai ki zaunaa ɗaki. Ta fito kenan zata shiga bayi sai ta juyo ana dambe a ɗakin Zuminu bata yi niyyar shiga ba sai ganin sai ganin wata mace tayi ta fito tana cewa "Wallahi sai ka biyani kuɗi na, kai ka ce zai sake ta kuma har yanzu shiru Wallahi sai ka biya ni" Ya ce "Bazan biya ba na riga na miki aiki ay" Ummi kuwa tunda ta juya ta kalli inda suke bata ce komai ba, ganin haka kuma yasa ya ringa zaginta wai tana gani ana ci masa mutumci tayi shiru. Shirun ta kuma yi nan kuma ya ringa zazzaga mata masifa. *** *** A hankali cikin ta ya ta girma saidai wani abu da bata gane ba shine, Yanzu Umar ya canja mata ya daina rawan kai akan cikin nata, saidai kuma idan sha'awarsa ya tashi kai tsaye yake zuwa mata, batare da ƴan wasanni ba. Wannan ma sai dare yayi ko ranan girkin ta ne yanzu ya koma gun Ruky idan da ranane da daddare kuka yaje ya kwana a ɗakinta. Ruky tayi tayi ta sa ya daina kwana ɗakin Bilkisu amma yaƙi wannan yasa ta samu Mamanta ta ce "Boka yasa ya saki Bilkisu kawai, wannan karon tare suka tafi gun bokan, saida suka masa bayani Boka ya kalli Ruky yaga tayi kala yasa ya ce "Ta shigo ɗaki zan fara ɗanɗanata a cikin abin da zamuyi zan saka mata magani" Mama Amarya ta ce "Haba kodai ni da muka saba amma ay hakan baiyi tsari ba kayi da ni ga kuma ƴata" Ya ce "Akwai maganin da zan saka mata ne" Mama Amarya ta kalli Ruky ta ce "Ku shiga " Ruky ta ce "Haba Mama ji fa wani ƙazami da shi duk wari yake" Ta ce "Ohon ki sai ki zauna kina ganinta da ciki" Ta tashi ta shege ciki yayin da Mama Amarya take waje tana jira saida Suka ɗau wajen awa a ciki sannan suka fito, duk wanda yaga Ruky yasan taji jiki. Ya fito yana lashe baki ya ce "Kuje ku yau ɗin nan zai saketa tabar gidan amma da sharaɗi kada tabar cikin garin bauchi idan kuwa ta bari komai zai lalace dan haka a kiyaye" Mama Amarya ta ce "Idan ya sake ta ay gidan Sauda zata yi tana nan" Suka tashi suka tafi suna farin ciki.... _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[6/3, 6:54 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ _*Habiba Isah Musa Allah ya sauƙe ki lafiya*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 49-50 A gajiye ta dawo gida lokacin an fara kiran Magrib ita kuma da ƙaton cikinta tana jera musu abinci zata shige ciki ta ce "Ya Umar ana ta kiran Sallah fa" Ya ce "Kin ɗauke ni bani da kunne ne ko me, ay naji" Ita kan gun abincin ta kalla ta ce "Wallahi yunwa nake ji dama ashe na dawo a daidai an gama" Ya ce "Barin zo in taya ki nima tun ɗazu aka cika min ciki da ƙamshi " Ruky ta ce "A baki fa yau zaka bani kaji ko" Ya ce "To duk abin da kiks ce hakan ay za'ayi" Tana jinsu ta shige ɗakin tayi Sallah Magrib sannan tayi ƴan Addu'o'inta ta jira Isha nan ma tayi sid tayi shafa'i da wuturi sannan t fito, ganin sa tayi yayi matashi da cinyar Ruky kamar zata yi magana sai tayi shiru saboda yau a ɗakinta yake, ta wuce dan taci abinci taga babu komai ta kallesu ta ce "Ina sauran Abincin kuma" Umar ya ce "Ruky ta ce in kaiwa Almajirai saboda bata son abinci ya kwana" Ta kalle shi sai kuma ta kalli Ruky ta ce "Amma kuma ay kasan ni ban ci ba, kuma nice yakamata nasa a bawa Almajirai ba kai ita ba, saboda ni na dafa" Ya ce "kina faɗa min kin dafa abinci to na bada sai ki yi bin da zakiyi " Ruky ta miƙe ta ce "Idan kika ƙara magana yanzu zan bubbuge shegen cikin kin nan" Ta ce "Zo ki buge ni tunda baki da hankali " Ta tashi tayi kan Bilkisu da niyyar bugeta sai Bilkisu ta matsa da sauri Ruky ta bugu da dinning nan ta faɗi a gurin warwas, Umar yazo ya ɗaga itako Kicin ta shige ta haɗa tea ta dawo ɗaki tasha sannan ta sa doguwar rigar barcin ta ta kwanta. Cikin barcinta taji ana buga ƙofa da ƙarfi ta miƙe cikin tsoro ta buɗe ta ga Umar ya ce "Baki da hankali kinga yanzu kinji wa Ruky ciwo amma da yake baki da hankali ko ki ce mata sannu" Tsaki tayi zata tura ƙofan ya turo ya shiga Ruky ta biyo bayan sa ta ce "Ka tsaya kana kallon ta baza ka bubbuge ta" Ya ce "Kyaleta tausayin ta nake ji saboda cikin nan". Ta ce "Ina ruwan ka da ciki " Bilkisu ta kalleta ta ce "Ki fita min a ɗaki idan ba so kike in miki duka ba, ku duba fa ƙarfe 12 saura yanzu amma kun hana ni barci ka ja matarka ku fita bana so idan ba haka ba a daren nan zan kira Baba ya min tsakani da ku, tunda baku da... " Maganar ce ta katse sakamakon barin da ya bata daga bisani ya fara dukanta, da taga zai mata illah yasa ta fara ɗaukan kayan kan madubinta tana jifan sa da shi Yayin da Ruky ke gefe tana dariya, ganin bazata daina jifansa ba yasa ya fita ita kuma ta zauna a ƙasa ta kifa kanta a kan gado tana kuka, ba jimawa ya dawo jin muryansa tayi yana cewa "Ki tashi ki bar min gidana na Sake ki saki Uku " Da sauri ta ɗago ta kalleshi taga yana miƙa mata takarda tasa hannu ta amsa ta duba ta gani ta kuma rushewa da kuka, ya jima a tsaye yana kallon ta tana kuka can ya ce "Ki tashi ki fita min a gida na" Ta ɗago ta ce "Dare yayi sai da safe " Ya ce "Safe! Karya kike yanzu zaki bar min gidana, ay bana ubanki bane" Ta ce "Yanzu fa duba a gogo a daren nan zan fita" Ji tayi ya fara zanata ta miƙe ta ɗaki kayan da ta cire ta cire rigar barcin ta sa ta a kan gado ta sa hijabi ta ta kalle shi ta ce "Umar baka cikin hayyacin ka, amma shawaran da zan baka ka kula da ibada' Ta fita ta ga Ruky a falo tana dariya ta ce "Abi wani sarkin" Tana fita tayi ta yafiya, ita kan tsabar takaici ma ko wayanta bata ɗauka ba balle kayanta. Da kyar ta samu Keke napep ta shiga ya kaita gidan Baba tayi buga ƙofa shiru, ta dade tana bugawa sannan Mama Sauda ta fito ta ganta ta ce "Lafiya " Ta ce "Mama Ina Baba, Umar ya koreni daga gida" Mungun kallo ta mata ta ce "To kuma sai kice min wani Baba dalla matsa min zan rufe gida, " tana rufe ƙofa ta ce "gwara da ya kore kin ma ay yanzu nasan na haifi ɗa" Komawa tayi gun me Napep ɗin ta ce "Sun rufe ƙofa" Ya ce "Yanzu ne dare yayi shi yasa ki kira wani a waya mana" Ta ce "ba waya a hannuna ay" Ya ciro waya ya ce "ga waya idan kin san number ki kira" Ta haddace number Baba yasa tasa tayi ta kira shiru bai ɗauka ba, " Me Napep ya ce "Ki masa saƙo kin san yanzu dare ne ba kowa yake son ɗaukan waya da daddare ba musammam baƙuwar number. Ta tura text ta yi typing _"Baba gani a ƙofar gida ina cikin matsala, Baba dan Allah ka taimaka bani da gun zuwa kai kaɗai kake ƙaunata"_ Ta tura suko ɗan jima amma shiru bai fito ba, suka sake kira shiru, ƙarshe ma suka ji wayar a kashe Me Napep din ya ce "Hajiya dan naga ke mace ce kuma ga ciki yasa na tsaya a gurin amma da yanzu ina gida " Ta ce "Kayi haƙuri dan Allah ka kaini gidan mu" Ya ce "Muje" Suka tafi gidan Abba nan ko tana buga ƙofa Abba ya fito ya kalle ta ya ce "Kefa daga ina" Ta ce "Abba dan Allah ka barni na kwana a gidan ka, ko a ɗakin su yaya ne zan kwana da safe zan tafi" Jin muryan Mama Amarya tayi a bayan sa ta ce "To daga ina kuma, kinzo mana da cikin shege kice mana mu buɗe miki gida, Umar ya gane ba cikin sa bane kenan" Ta ce "Wallahi Abba cikinsa ne, ban taɓa yin zina" Mama Amarya ta ce "Ƙarya kike irin mazan da kike kaiwa gidan mijinki ki ne, wannan cikin cikin ɗaya daga cikin kwartayen ki ne" Bilkisu ta fashe da kuka cikin kuka ta ce "Allah ya isa tsakani na da ke, tun a duniya Allah zai saka min, kuma idan kinje lahira zaki gani " Me Napep din yazo ya kalli Alhaji ya ce "Alhaji tun bansan tsakanin ku ba, amma yanzu na sani, kuyi haƙuri ku barta ta kwana zuwa da safe" Mama Amarya ta ce "Kaima ban yadda da kai ba, hala kwarton ta ne ma, ka gama abin da zaka yi da ita ka kawo ta" Juyawa yayi ita ma ta bishi a baya ya kalleta ya ce "Kije ki shege ta gefensa" Ta tafi kai tsaye zata shege ta gefe Abba yasa ƙafa ya tokareta ta faɗi, ta mike ta ce "Abba wai ka manta ni wacece, Bilkisun ka ce fa" Turota waje yayi ya rufe ƙofa. Tashi tayi tayi gun me napep din ta ce cikin kuka "Badan kuɗin ka ba da nace kaje kawai amma yanzu kayi haƙuri ka kaini wani gidan zan haɗa maka kuɗin ka duka" Ya ce "Hajiya ba kuɗi bane damuwata, inda zaki kwana, gashi kina mace, muje can ɗin idan suma sun hana zan kaiki gun Mamana" Ta ce "Nagode Allah ya saka maka da Alheri" Ya ce "Kada ki damu, Hajiya dole mu taimaka wa irin ku" Suna zuwa gidan su Umma kuwa shiga tayi saboda gidan ba ƙofa taje jikin ƙofar ɗakin Umma ta buga kofar sosai daga ciki Umma ta ce cikin muryan barci "waye" Ta ce "Umma Bilkisu ce" Ta ce "Wace Bilkisun kuma" Ta ce "Adda Bilkisun ki ce, ƙanwar su Ya Abubakar " Shiru taji sai kuma taji buɗe kofar, Umma na ganin ta ta ce "Innalillahi wa inna'ilaihir raju'un, daga ina haka" Kuka ta fashe da shi ta ce "Mu shiga ciki" Ta ce "Aa ki bani kudi na kaiwa mai Napep yana waje" Umma ta ɗauko ɗari biyar suka fito tare suka same shi Umma ta miƙa masa ya ce "A'a dama na jira ne naga idan ba'a karɓeta ba, Allah ya kiyaye gaba" Bilkisu ta ce "ka amsa" Ya ce "Hajiya kada ki damu kawai kimin Addu'a " Ya juya kan Napep dinsa ya tafi. Komawa ciki suka yi, Bilkisu tana kuka tana faɗa mata abin da ya faru, Umma kuwa tayi ta lallashinta tana bata baki, har barci ya ɗauke ta, ita ma Umman ta kwanta. Washe gari Sassafe bayan sin karya Umma ta ce "Zaki bar garin nan, gun Adda Bilkisu zaki je a Kaduna ki haihu a can, yanzu ki tashi kije gidan Umar ki ɗauko kayan ki" Ta ce "Ta sani ne" Ta ce "Bata sani ba amma kuma yanzu zan kira ta, yanzu ki tashi kije ki ɗauko kayanki, idan ya hanaki kizo ki faɗa min ina dai dai da su daga su har iyayen nashi da duk wani mai goye masa baya" Kuɗin Abin hawa ta bata sannan ta tafi, gidan a buɗe yake da alama tunda ta fita ba'a rufe ba, falon ma a buɗe ɗakinta tayi tana shiga ta ganshi yashe a ƙasa sai sharan barci yake. Ta ɗauki takarda da biro ta masa rubutu kamar haka _Umar ka cuce ni, bai kamata ka rabu da ni a cikin halin da nake ciki ba, kuma duk da haka bai maka ba saida ka kore ni a gidanka saboda matarka, sai da ka tura min sonka a cikin zuciyata kai kuma kazo ka ƙimu nida gudan jinin ɗanka, da kake faɗan irin son da kake masa. Nasan tuntuni dama baka sona daga baya kazo kace kana sona, ashe ba so bane, duk salon ƙiyayya ne, ka tura min sonka ni kuma ka guje ni, to ni na tafi Kaduna zanje na haihu a acan kuma kamar yadda ka zabi sunan da za'a saka wa ɗanka shi zan saka masa_ Tana gamawa ta ajiye ta fara tattara kaya sai ya farka, ya kalle ta ya ce "Baki tafi ba dama" Ta ce "Kayana zan ɗauka" Ya ce "Ba abin da zaki dauka dan haka ko ki tafi ko in miki duka" Fita tayi ta tare me napep ta koma gun Umma ta faɗa mata komai, Umma ta ce "Munyi waya ta ce Yanzu ki shiga motan haya kije Kaduna, da na faɗa mata kin tafi ɗauko kayanki ta ce da ban tura ki ba, saboda haka yanzu muje tasha in saki a mota" _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/3, 9:20 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ _*Nafisa Isah Musa Allah ya sauƙe ki lafiya*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 51-52 Suna zuwa tasha suka samu mota Umma ta biya kuɗin motar saida taga tashin su sannan ta koma gida. Suna isa a cikin tashan kawo aka sauƙesu ta fito, tana kalle-kalle sai yanzu gashi bata san gidan da zata je ba. Tana kalle-kalle sai taji murya ta bayanta "To Ƴar ƙauye kallon me kike" Tana juyowa taga Aliyu ta ce "Lah Ya Aliyu" Ya ce "Ina kayanki muje gacan mota" Ta ce "Muje kawai bani da kaya" Bude mata gefe yayi yayi ya shiga gurin driver ya ja suka tafi, suna isa gidan yayi parking a gurin Adana motoci saida ya kashe motar sannan ya buɗe ya fito sannan ya buɗe mata ta fito ya rufe yayi gaba ta bishi a baya suka shiga falon Adda Bilkisu ta fito ta rungumeta tana jinta a jikin Adda Bilkisu sai ta saki wani kuka mai ban tausayi. Adda Bilkisu ta yi ta bubbuga bayanta tana cewa ya isa haka duk wanda ya zalince ki Allah zai saka miki, yanzun kan komai ya ƙare ay, ki kyale kowa da halin su, kuma ba Babban mai laifi irin Umminki da ta kyale ki, bana son ki faɗawa kowa kina nan ki kyale su, " Ta gyaɗa kai. Wani ɗakin ta kaita ta haɗa mata ruwan wanka a bayi ta ce "Ki shiga kiyi wanka " Ta shiga tayi wanka tana fitowa taji bata da wata gajiya kuma, Sallah azhar tayi. kaya ta gani akan gado ta ɗauka ta saka mai kawai ta shafa sannan ta zauna bakin gado, ba jimawa sai ga Adda da Abinci harda flask din ruwan zafi, ta fara haɗa mata tea ta ce "Ki fara shan wannan dan hanjinki ya warware ko" Ta amsa tana sha a hankali ita kuma ta fita, bayan ta shanye ta zuba abincin faran shinkafa ne da miyar Alayyahu da naman rago a ciki kaɗan taci taji ta ƙoshi. Adda ta shigo ta tattara kayan ta fita da su. Sannan ta dawo, ta ce "Ki kwanta ki huta ko" Maryam ce ta shigo da gudu ta rungumeta Adda ta faka mata duka a baya ta ce "Baki da hankali ne, bakya ganin yanayin yadda take ne" Maryam ta ce "Momy ni fa ban gani ba" ta juya ga Bilkisu ta ce "Ina shigowa Yaya ya faɗa min Wallahi, ke kice munyi kusa haihuwa, yeeeee" sai kuma ta fara tsalle. Momy ta ce ", To ki kyale ta ta huta mana" Ta shafi cikin ta ce "Babynmu ka huta lafiya kaji" Sannan ta fita da gudu kuma, ita dai Bilkisu murmushin ta take ta yi, Mommy ta ce "Bansan yaushe Maryam zatayi hankali ba, kwanta kinji" Tana kwanciya kuwa barci ya kwashe ta. *** *** **** Zai fita kenan ya duba kan gadon ba wayar sa, ya kalli matar tasa ya ce "Ina wayata kuma, ni da na ajiye a gefena da zan kwanta" Drawer ta buɗe ta miƙa masa ya ce "Ya akayi ta mutu bayan da caji" Bata ce komai ba ta fita ya buɗe wayan yaga Miscall da baƙuwar number da massage ɗaya ya buɗe ya karanta saƙon Bilkisu ya duba da sauri ya fita ɗakin Mama Sauda yayi ya ce "Me yasa kika kashe min waya saboda Bilkisu ta kira ni ko, tana buƙatan taimako kin sani amma kika ƙi taimaka mata a cikin tsohon daren nan ina zata shiga, yau idan wani abu ya samu yarinyar nan daga ke har ɗanki sai na ɗaure ku tunda baku da mutumci" Fita yayi kamar wani zararre ya shiga mota yayi gidan Umar. *** *** *** Umar kuwa yau ya kasa fita kwata kwata yana zaune a ɗakin Bilkisu wani azababben ciwon kai ne ke damunsa, ko Sallah ya gagara yana nan kwance a tsakar ɗakin Bilkisu anan fa barci ya kwashe yayi barcin sosai ƙarfe 11:00am ya farka yaji ba wani ciwon kai kuma saidai kuma ya koma tunani dabam wato Bilkisu, fitowa yayi ya Ruky a falo ya ce "Ke Ina Bilkisu kuwa take" Ta ce "Ba kai ka koreta jiya ba" Shiru yayi yana tunani duk abubuwan da suka faru ya dawo masa a tsakiyar kan sa. Komawa ɗakin yayi yana kalle-kalle kamar taɓabbe wayarta ya gani ya ɗauka, ga kuma akwatin da ta ɗauka ya hana ta rigar barcin da ta cire ya gani ya ɗauka yana dubawa can kuma ya hango takarda ya ɗauka ya karanta, sai kuma ya yar a ƙasa ya fito falo ya samu Ruky ya ce "Faɗa min ina Bilkisu ta je" Ta ce "Ka manta da hannun ka ka rubuta mata saki uku" Tunawa yayi tabbas haka akayi a daren jiya ya rubuta mata saki uku kai ya kama, sai ji suka yi an banko ƙofa Baba ya gani ya miƙe kafin Ya kai ga Magana Baba ya riga shi" Ina Bilkisu? Sai shiru bai iya cewa komai ba, Mari Baba ya bashi ya ce "Me ka mata jiya da daddare ka kore ta" Shiru ba Amsa nanfa Baba Ya ringa dukan sa kamar ya samu ƙaramin yaro, can kuma ya sake shi ya fita, yana fita, Umar ya kalli Ruky wani tsanan ta ne ya kama shi, abubuwan da suka faru suka ringa dawo masa kwakwalwa, ya riƙe mata wuya ya ce "Faɗa min me kika bani naci hankalina ya ɓace kika sa na saki matata" Shiru tayi tana son ta ƙwace nan fa ya ringa dukanta kamar Allah ya aiko shi, ya kamata ya ɗaga sama ya doka ta jikin bango nan fa hannunta ya karye ta fara kuka ya kalleta, ya ce "Kamar yadda kika sa na rabu da ita kema kin rasa ni, dama can bana son ki, ban san yadda aka yi kika samu nasara a kaina ba. Allah ya isa tsakani na da ke, ki dube ki fa, me zanyi da ke, ƙazama irin, kuma bari kiji baza ki sake fita ko ina ba, kina nan a gidan nan wahala kuma yanzu kika fara gani. Ɗakin Bilkisu ya kuma komawa ya zauna yana kuka can ya tuna da Sallah asuba ya miƙe yayi alola sannan ya zo ya rama Sallah da ake bin sa ya kuma zauna yana Addu'a neman gafaran Ubangijinsa. *** *** *** A firgice ya farka daga barcin da yake ya tashi ya zauna ya kama kai ya ce "Adda na kore ta ni da kaina? Me ke shirin faruwa dani, Tunda na kori su Abubakar ina suka je basu dawo ba, kwanciya yayi Abubuwa suna dawo masa haushin kansa ya fara ji, bai kamata ya kore ta ba, dan kawai ya kama ta da wani a ɗaki, kuma a hakan ta dawo masa da ciki wani ya wulaƙanta ta ya kore ta, me ke shirin faruwa da nine, Mama Amarya ce ta shigo ta ce, ", Ni dalla Malam ka tashi ka shirya ka bar min gidan nan tun safe ka wani zauna" Kallon ta yayi ta yi "Ta ja tsaki ta ce "Ka wani zauna a gida ni ka fita min a gida mana" Ya ce "Ina kika tura min ƴaƴana da Matana, Ina Addana, Aisha, Abubakar Usman da Hali da kuma Khadija" Jin muryan ɗan uwansa yayi a falo ya miƙe ya fito falo yana ganin sa ya ce "Allah yasa Bilkisu tana gidan ka" Ya ce "Nima ita nazo nema" Baba ya faɗa masa komai, Shima Alhaji abin da ya sani game da ita ya faɗa, nan fa suka fara jajantawa junan su. Yinin ranan a gidan suka yini daga bayane Baba ya koma gida yana zuwa ya tarar Mama Sauda tana kuka, ko girki ta kasa yi a gidan abinci ma ta kasa cin sa ya tambaya lafiya. Ta ce "Mun cuci Bilkisu " Ya ce "Me kuma ya faru" Nan ta fara faɗa masa Abubuwan dake faruwa har zuwa jiya da ta kore ta. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/4, 7:04 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 53-54 Girgiza kai yayi ya ce "Wannan wani irin Imani me ta muku haba Sauda, to gaskiya bazan iya zama ci gaba da zama da ke ba, dan haka kije na sake ki saki ɗaya" Kuka tasa ta ce "Haba Baban Umar kayi haƙuri dan Allah kada ka min tunda baka min haka ba sai yanzu da girma ya kama ni" Ya ce "Kamar yadda kika koreta, ɗanki ma ya koreta kema ki bar min gidana bana son ganin ki" Ɗaga kai tayi ta kallo ƙofa taga Umar a tsaye yana kuka yaje ya durƙusa gaban Baban yana kuka yana son yayi magana amma ya kasa Baba ya ce "Kada na sake ganin ka a gida na, kaje kaima na Sallama ka a duniya " Lokacin tayi magana haɗe da kuka "Baba ban san lokacin da nayi haka ba Baba ka taimaka min dan Allah " Ya ce "Wai kan na tambaye ka, Bilkisu ba ƴar uwarka bace, ko a gidan wani ta fito baza ka iya riƙeta ta haihu a gidan ka ba, ka koreta a cikin wannan daren kasan ina ta kwana, ga gari da ƴan iska, so kake ta dawo da halinta na baya kenan ta kuma lalacewa" Ya girgiza kai ya ce "Cikin kuka Abba tun da ma can sharri aka mata amma Wallahi Bilkisu ba haka take ba, bata taɓa zina ba, nine nan shaidan ta Allah ne kuma shaidata, Abba nima kaina nayi mamakin da na samu Bilkisu cikekkiyar budurwa wanda banyi zato ba" Baba ya duba maganan sa ba rashin kunya illa tsantsan gaskiya da yake faɗa da kuma yanayin da yake ciki, kan sa ne ya sara ya tashi ya fita a gidan mota ya shiga ya kuma yin gidan ɗan uwan nasa yana shiga da mota, yaga wani mutum a rakuɓe jikin bango yaje gurin ya ce "Malam lafiya " Muryan sa na rawa ya ce "Dan Allah ka haɗa ni da Alhaji " Ya ce "Me zaka masa kuma, kaga yanzu za'a shiga Sallah Magrib ka bari muyi Sallah mu fito" Kuka ya fara yi sannan ya juya, Baba ya bishi da kallo kawai, yayi Alola ya shiga masallacin ƙofar gidan Alhajin yabi Jam'i suka gabatar d Sallan Magrib, bayan sun fito ne shima ya haɗu da Alhajin sai ga wannan Mutumin yana takowa a hankali kamar a tsorace yake yazo ya durƙusa a gabansu ya ce "Alhaji na kasa samun Sukuni, komai ma taɓa yana lalacewa, an bani jari da yawa dan nayi sana'a jarin ya lalace, Nayi Aure matar taƙi zama, to sai na tambayi wani Malami yake cewa akwai abin da nayi wa Allah wanda na fusata shi yasa yake jarabta ta da hakan" Alhaji ya ce "Mu kuma menene namu" Ya ce "Alhaji na cuci ƴarka Bilkisu dani aka haɗa baki aka mata sharri dan ina neman abin duniya, dan Allah Alhaji a min magana da ita ta min hukuncin da ya dace ko ta yafe min" Baba ya ce "Bilkisu bata nan, amma me ka mata" Ya ce "Da daɗewa matar gidan nan, Maman Ruky ta ce nazo na shiga ɗakinta a matsayin Saurayinta wanda muke lalata da ita zata min kyauta me tsoka kuma zata kuɓutar dani na gudu, munyi hakan kuma an samu nasara kuma kwanaki ma naji ance ka kore ta" Alhaji ya ce "Kenan kaine wanda na kama a gadon Bilkisu, ashe bata san da zuwan ka ba, tayi ta min rantsuwa amma naƙi yadda da hannuna kasa na koreta, tashi kaje, Bilkisu dai bata nan, bamu san ma inda taje ba muma nemanta muke, mu baza mu iya yafe maka ba har sai tazo" Tashi yayi yana kuka yana Tafiya Baba ma ya faɗa masa yadda sukayi da Umar Ayko Alhaji ya fara kuka kamar ƙaramin yaro, Baba yana lallashin sa. *** *** *** Yau sai taji ta tashi da kewan dangin ta, Lalle tayi Babban kuskure ta zaɓi aure akan dangin ta, miƙewa tayi tayi ɗakin Zalimu ta sameshi yana cin naman kaza, tuni yawonta ya tsinke, rabonta da ta ci shi tun tana gidan Alhaji, a ƙauye ma zabuwa suke ci, a nan ko sai da suga yana ci, ya kalleta ya ce "Ya dai damo sarkin haƙuri" Ta ce "Dan Allah ina son kamin izini naje na duba ƴata Bilkisu tunda tayi aure banje ba, ina son naje naga ɗakinta" Ya ce "Kinsan dai idan mutum zaiyi tafiya bana bada kuɗin mota, ƴaƴana ma saidai samarin su su basu, uwayen su kuwa ƴaƴansu ƴan mata suke samo musu, amma ke tunda baki da ƴa kuma na farko ne, zan je har tasha na biya miki kuɗin mota, kuma ay naga ke ɗin me haƙuri ce" Ta ce "To Nagode" Ya ce "Kije ki shirya gobe kije zan baki aika ma ki kaiwa Bilkisun dukda ban taɓa ganin ta ba" Ta miƙe tana ƙara godiya, ya yago tsokar kazan ɗan ƙarami kamar wanda zai bawa ƙaramin yaro dake bayan uwarsa ya ce "Hungo gashi sa a bakin ki, naga yayunki ya tsinki" tasa hannu ta karba dan kar tayi laifi amma badan tana so ba, duk da tana kwadayinsa baza ta amsa ba dan bazata iya cin wannan abin ba, ay sai ya maƙale a haƙori. *** *** *** kwananta ɗaya a gidan ta zama ƴar gata, tana ɗan motsi kadan zakaji ance kina son wani abu ne, koda Alhaji Yusuf wato Daddy ya dawo shima yayi farin cikin ganin ta, ta saba da su sosai ga wasa da dariya. Yanzu haka Sassafe aka haɗa mata ruwan wanka tayi wanka wani sabbi kaya tasa saida Maryam taga bata buƙatar komai sannan ta shiga wanka ita ma, tana kishingiɗe a bakin gado ta fito ta fara yin kwalliya ta ce "Muje mu karya to" Suna shirin fita Aliyu ya shigo Maryam ta gaishe shi, ya amsa, ita ma ta gaishe shi ya amsa sannan ya sake kallonta ya ce "Zan fita me kike so a siyo miki" Ta girgiza kai ta ce "Ba komai" Maryam ta ce "To ni in faɗa" Ya ce "Yanzu fa kema zaki tafi Makaranta ita kuma kiga fa halin da take ciki" ya sake kallonta ya ce "Baza ki faɗa ba ko" Ta ce "Ba komai fa, bana buƙatar komai" Ya ce "To idan kika haifo mana yaro da rowa ni da kene" Maryam ta ce "Maida shi zamuyi" Ita dai murmushi take tayi ya ce "To na tafi ni kumin Addu'a " Maryam ta ce "Yaya yau da wuri zaka fita baka karya ba fa" Ya ce "Momy ta haɗa min tea nasha kuma yau ina shari'a da wuri, kuma tana ta jiran ku" Yana faɗa ya fita su kuma suka masa Addu'a haɗi da binsa a baya. Koda suka je gun cin abincin ma ana ci ana barkwanci tun tana noƙewa har ta ware tana ɗan sa baki. *** *** *** Washe gari ta shirya kayanta Zalimu ya ɗauketa a mashin ya sata a mota sanna ya sake bata ɗari biyar a hannun ta. Suna isa Gidan Su Umma tayi bayan sun gaisa ta ce "Zata je gidan Bilkisu, Umma ta nuna mata bata san komai ba, saidai kuma ta faɗa mata su Abubakar suna nan lafiya suna nan dawowa yau, dan sun gama karatunsu. Su ɗinma dan zasu dawo yasa ta faɗa musu. Dan haka suka tashi, kai tsaye gidan su Alhaji suka wuce suna zuwa suka sami Alhaji duk ya rame ya zama abin tausayi, shi kuwa yana ganin su sai yaga kamar sun dawo ne, ko amsa musu gaisuwan baiyi ba ya ce "Kunga yadda Allah yayi da ni ko, Ba Bilkisu ba su Abubakar, Khadiyo ce kawai naji labarin ta, itama ta min Alƙawari zata zo ta ganni yau. Umma ta ce "Su Abubakar suna nan dawowa yau daga Makaranta" Da sauri ya ce "Addan fa" Ta ce "Adda ita muka zo gani muma" Ya ce "Bamusan inda take ba, munyi cikiya mun sa poton ta a gidan tv munyi cikiya amma shiru ba labari" Ummi ta ce "Addan nawa ne, ta ɓata, ba ɓata tayi ba, kai kasan inda ka kaita kuma sai ka nemo min ƴata" Ya ce "Ki saurare ni Hali" Ya faɗa mata komai, ayko sai ta miƙe ta ce "Wallahi bazan yadda ba, sai kun nemo min ƴata, dan baka son ta shine zaka kore ta saboda matarka, " Hango Mama Amarya tayi tana leƙen su ayko ta miƙe taje ta cakumeta tana cewa "Ina ƴata, ina kuka kaimin ita, sai na kulle ki, shima Umar din zan same shi" Umma ne taje ta riƙeta taba bata baki. Yamma kuwa nayi sai ga baƙin Saudiya, sun zama ƴan gayo kamar ba su ba, fatan su ta murje tayi kyau gwanin sha'awa, duk macen da ta gansu sai sun kyasa. Sunyi waya da Umma ta faɗa musu suzo gidan Baban su suna can, Suna zuwa suka ji Mummunan abu, nan fa wata bala'in ta tashi ba zancen hutu Usman ya ce "Muje gun Umar ɗin idan bai fito da Bilkisu ba Wallahi baza mu bar shi ba," Ummi ta ce "Nima Wallahi binku zanyi saina gwada masa abin da baiyi zato ba" Shidai Alhaji kallon su kawai yake ta yi, Har suka bar gidan yayin da Umma kuma tana zaune a falon ta rasa abin da yake mata daɗi. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/4, 3:50 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 55-56 Suna isa gidan Baba suka shiga ciki suna parking ɗin mota shi kuma ya fito daga ɗakinsa na samartaka dan nan ya koma. Yana ganin su gaban sa ya faɗi, zai koma Usman ya ce "Ka tsaya kada ka koma ko ina, ka bamu ƙanwar mu, mu tafi da ita" Shiru yayi yana kallon Ummi yana son ya gaishe da ita saidai ba fuskan hakan ta ce "Ina Addana" Muryansa na rawa ya ce "Ummi kiyi haƙuri nima neman ta nake Wallahi, Abubuwa sun min yawa, Babana yaƙi min magana kuma ya saki Mamana saboda da ɓatan Bilkisu yanzu haka tana gidansu, nima bai san ina wannan gidan ba, da bazai barni in zauna, Kiyi haƙuri Ummi nima ba'a son raina na mata hakan ba" Tausayin sa taji, Shiko Usman yayi kansa, Ummi ta riƙe shi ta ce "Ku kyale shi kawai mu tafi Addu'a zamu ci gaba da mata kawai" Abubakar ya ce "Ummi ki kyale shi, dama can ina lura da shi tun Bilkisu tana ƙarama ya tsane baya son ganin ta, yanzu an aura masa ita yaga sai yadda yayi da ita shi yasa ya wulaƙanta ta, to kaje ka nemo mana ƴar uwar mu idan ba haka ba zan maka ka a kotu" Ya ce "Zan tafi, zan shiga duniya neman ta bazan dawo ba, sai na sameta, na muku Alƙawari zan dawo muku da Bilkisu," Hanyar fita yayi kamar wani marar lafiya ya fita a get ɗin gidan ya fara tafiya da ƙafa. Shiga mota suka yi suka koma gida. *** *** *** Tunda ya mata duka ya kulle gidan bai ƙara bi ta kanta ba, yana buɗe ƙofar ya ganta a kwance tana kuka hannunta ya kumbura. Ya kalleta ya ce "Tun ranan kina cin abinci dai ko" Tace "Eh tea nake haɗawa, " Zai wuce ta ce "Dan Allah hannuna, ka taimaka min" Ya kalle ta ya bude mata baki saida yayi jini ya ce "Dama nasan halin da Bilkisu take ciki ne da zan iya tausayin ki, ban sani yanzu hala ma ta fiki shan wahala" Ɗakin Bilkisu yayi yaga inda ya bar ɗakin haka yake, Takardan ya gani ya kuma karantawa, da sauri ya naɗe ta cikin ransa ya ce "Wato kaduna tayi, to Kaduna a ina, ya tambayi kansa saidai ba amsa. Rigar barcin ta ya ɗauka ya rungume yasa kuka, ya dade yana yin kuka sai kuma ya ɗauki wayarta haɗi da rigar ya fito yayi ɗakin sa da shi, kayansa ya bayan ya gama ya sa rigar barcin nata da wayarta yasa a ciki ya ɗauka yana zuwa Falo ya kalli Ruky ya ce "Ki tafi gun uwarki ta miki jinya idan na dawo kuma zamu ci gaba daga inda muka tsaya" Ta tashi da hannu a kumbure tayi hanyar waje, shi kuma sai da ya kulle ko ina a gidan sannan ya fita, gidan Baba ya wuce ya kwana, washe gari sassafe yayi tasha ya shiga mota sai jihar Kaduna garin gomna. A tashan kawo aka ɗauke shi, to gashi daiba kaduna amma baisan kowa ba kuma bai san inda zashi ba, sannan baisan ta ina Bilkisu take ba, Lalle yana da aiki a gaban sa. *** *** *** Gata kan Bilkisu ta same shi wannan yasa ta koma Bilkisunta na da, tana shagwabanta yadda take so, daɗi da ta samu Maryam ma ƴar shagwaɓan ce, haka suke haɗuwa suyi tayi. Cikinta ya kai haihuwa tare da Momy suke zuwa awo, da yamma kuma Aliyu ya raka ta suyi ta zaga unguwar tasu a ƙafa. kullun shi yake rakata randa Maryam take gida kuma ita ma ta bisu. Yaukan ta dawo kenan suna zaune a ɗakin a ɗakin Maryam suna cin maƙulashen da suka siyo taji maranta ya kullu ta ɗan rintse ido, dama yau tunda Safe take jin ɗan ciwon mara, Maryam ta kalle ta ta ce "Ya dai, kodai abin yazo ne" Ta ce "Haba an gaya miki wasan yara ne haihuwan" Ji tayi ya sake murɗa mata wanda yafi na da ta kama gurin, sai kuma taji wani ciwon wannan karan abin dake bakinta ta fito da shi, saboda azaba, Aliyu da Maryam kuwa tashi sukayi da gudu suna rige-rigen kiran Mommy, ita ma da gudun tazo ta kama Bilkisu ta ce kalli Aliyu ta ce "Maza ɗauko mota muje asibiti haihuwa ne" Kamata tayi suka fara takawa bakin ƙofa Bilkisu ta tsaya ta kasa ɗaga ƙafa ta ce "Mommy bazan iya tafiya ba, Mommy zan mutu, " Mommy ta ce "Kina Addu'a ne kinji, insha Allah zaki haihu lafiya" Jan ta Mommy ta kuma yi sai kuma Bilkisu ta durƙusa a gurin tayi wani nishi babba sai ga baby, da sauri Mommy ta tare sai a hannunta, sai ta kimu yin wani nishin da baikai wancan ba, saiga Mahaifa ta faɗo, Mommy ce tayi ta cewa "Alhamdulillah Allah mun gode maka" Ita ta yanke cibi ta duba ta mace ce, ta sako kai ta ce da Maryam faɗawa yayanku ta haifi mace, da gudu taje ta same shi a cikin mota da yake jiransu ta faɗa murna gurin su ba'a magana. Mommy ce ta gyara Baby da Uwar Baby sannan aka fito da babyn Falo, Aliyu ne ya amsa yana farin ciki sai washe baki yake yi, haka Umar ma, saida Bilkisu ta gama shirya wa sannan ta fito suka tafi asibiti, ko da aka je aka samu jaririya da uwarta duk lafiya sai ƴan gwaje-gwaje da aka musu sannan suka dawo. Daddy ma yana dawowa ya sami Baby ya ɗauka yana ta murna, Aliyu kan cewa yayi "Mun samu ƙarin ƴan shagwaba a gida" Daddy ya ce "Ita ma idan ta tashi taga iyayen ta suna yi yi zata ay" Ita kan Bilkisu tana ɗaki abin ta. Ashe gari da Sassafe Daddy ya shigo har ɗakin mai jegon ya same su duka a ɗakin Maryam ta shirya zata tafi Aliyu Kuma ya kalmashe ƙafa yana cin tuwon me jego Daddy ya kalle shi yace "Kai kuma yau anan kake karyawan " Ya ce "To Mommy ta tare anan wai sai ta sallami me jego ni kuma zan tafi kuma yunwa nake ji" Mommy ta ce "Shine ay nasa mata tuwon bata ci ba ta miƙa masa shi kuma da yake maye ne ay gashi ya cinye" Ita ko Bilkisu kanta na sunkuye so take ta gaishe da Daddy amma yana ta surutu. Daddy ya kalleta ya ce "To kuma ita da safen nan tuwo take ci" Mommy ta ce " To ay shi zai kawo mata ruwan nono, bayan taci tuwon sai tasha tea " Suna ta magana har Maryam da Aliyu suka tafi bayan sun tafin ne ya ce "Mommyn yara kin kira mutanen nan kin faɗa musu maganan haihuwan nan kuwa, kinga sai su faɗi sunan da za'a sawa yarinyar su" Ta ce "Ay ko baza su ji ba ba wanda zaiji haihuwar, maganan suna kuma ga uwarta ta zaɓar mata" Ya ce "Haba ya kamata a faɗa musu dai" Ta ce "Alhaji yarinyar nan ta wulaƙanta a gurin su, sai aka samu ma uwarta bata kula da ita ba, ta barta kara zube, ka kyale su kawai " Ya ce "To shikenan nima zan tafi idan kunyi shawaran sunan da za'a saka mata, da yamma idan Aliyu ya dawo sai ya mata huɗuba. " Daddy yana fita Mommy ta ce "Kun taɓa shawaran sunan da za'a saka mata ne da Baban yarinyar nan" Ta ce "Eh, Dama ya ce idan mace ne sunan mahaifiyarsa za'a sa, idan Namiji ne mahaifinsa" Ta ce "Ya sunan Mahaifiyar tasa" Ta ce "Sauda" Ta ce "Sauda suna mai daraja ne, sunan Matar Annabi Muhammad (SAW) ta biyu kenan. " _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/4, 8:44 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 57-58 Da yamma kuwa kuwa Aliyu naya dawo wa aka masa bayanin komai, ayko ya mata huɗuba da Suna NANA SAUDA. Ranan suna kuwa bikin akayi sosai Aliyu ya yanka mata rago, anci ansha, Sauda da uwarta sun samu kyautuka daga wajen ƙaqayen Mommy da Abokan arziki, Haka Aliyu ma ba'a barshi a baya ba dan ya gayyato abokanan sa sun musu kyauta sosai, Maryam kan kamar ita ce mai jegon sai shiga take tana fitowa Sauda kuwa tasha jagwalgwalo a gurin ƙawayenta har kwalliya saida tasha. Maryam ta ce "MAISUN Za'a na kiran ta saboda da sunan Uwarsa ce bai kamata ana kiran sunan ba" *** *** *** Tunda Ruky ta dawo gidan Alhaji bai kula su ba, an mata ɗauri amma abu yaƙi ko yaushe hannun a kunbure kullun cikin tsinewa Umar take kuma taci Alwashin sai ta rama abin da ya mata idan ya shigo hannunta. Mama Amarya ke jinya. Duk kuɗinsu ya ƙare akan hannun kullun cikin kuka da hannun Ruky take. Shi kuwa Alhaji yanzu tunanin sa shine ya zaiyi ya dawo da Umma yana kunyar yi mata magana, gashi ita kuma takan kira ta gaishe shi lokaci-lokaci kuma takan kwantar masa da hankali, haka yaran nasa ma, sukan kwantar masa da hankali, duk abin da yake so suna bashi da yake ko wannen su yana aikinsa, duk kan lauyoyi ne masu zaman kansu kuma Albashinsu me tsoka ne, tunanin su yanzu inda Bilkisu take abin yana damun su a rayuwa. Sun shigo a tare Cikin falon suka ga Alhaji ya zauna a kujera ya zuba tagumi, Sunyi magana amma shiru Usman yaje ya kama hannunsa yayi firgigit Abubakar ya ce "Tunanin Bilkisu kake ko" Ya ce "Ba Bilkisu kadai ba, harda Umar ko ina ya shiga shima har yau shiru ba'a ganshi ba, ko yana lafiya, duk inda yake nasan shima yana cike da tunaninta duk da shi ya sata a wannan halin amma ay ba a hayyacin sa yake ba, Sai kuma tunanin Umman ku, ina son ta dawo ɗakinta amma kuma na rasa yadda zanyi in sanar da ita" Usman yayi murmushi ya ce "Haba Abba ko mu yara baza muyi wannan ba, Umma fa taka ce, amma kace ta dawo kawai yanzu zaka ga ta dawo" Ya ce "Ina jin kunyar yi mata magana ne ay, irin abin da na mata ay da kunya ace na dawo" Abubakar ya ce "To Abba kada ka damu mu zamuyi maka komai, ay mu bama jin kunyar ta, Umma zata dawo ɗakinta, an bar wannan matsala ko" Ya ɗaga kai, Abubakar ya ci gaba "Maganan Bilkisu da Umar kuma ka daina damun kanka, mudai muyi ci gaba da yi musu Addu'a, sannan kuma Abba ya zaka yi da wannan matar kasan dai baza ka ci gaba da zama da ita ba ko" Ya ce "Talatuwa ta cuce ni ban san irin hukuncin da zan mata ba ay" Abubakar ya ce "Kayi haƙuri Abba ka daina sa wannan a ranka" Yayi murmushi ya ce "To yaushe Aishan nawa zata dawo" Dariya suka yi Abubakar ya ce "Kwanan nan ka zuba ido ka gani" *** *** *** Umar dai an zama ƴan gari a tashan kawo dan kuwa yanzu an sanshi, ya zama ɗan dako, duk wanda zaiyi tafiya yana zuwa tasha harda Umar yana cikin masu ɗauka masa kaya ya kaishi motar garin da zaije, ya cire girman kai, kuma duk aikin da ya samu na ƙarfi zaiyi a biya shi lada, wani abokinsa ya kira shi ya ce "Akwai wani Mai gidana da yake son a masa fiɗa gobe sunan matarsa zai yanka rago, ko ka iya" Ya ce "Allah ya kai mu goben " Ya ce "Amin" Washe gari kuwa suka shirya abokin sa sale ya kaishi gidan, cikin ƙanƙanin lokaci ya gama fiɗan, aka biya shi sanna aka basu nama. Sun shirya zasu tafi kenan Umar ya hango tinkiya zata haihu tana ta kuka, amma haihuwar ta gagara. Zuwa yayi gurin Sale ya ce "Me zaka yi " Baice komai ba yaje ya kama kunkumin tinkiyar da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma yana shafa mata baya a hankali sai kuma gashi ta haihu. Mai gidan yana kallonsa ya matso ya ce "Malam Umar ya akayi haka, duk haihuwan da wannan dabbar zata yi sai ta sha wahala sosai" Umar ya ce "Ay abin da na karanta kenan" Ya ce "Ahhh dama kuwa a zango inda ake siyar da dabbobi ana neman likitan dabbobi ya kamata muje can kana musu magani ana biyan ka" Ya ce "To Alhaji na gode" Ya ce "Gobe sai kazo in kaika ko" Ya ce "To nagode" *** *** *** Tana yin arba'in Aliyu ya nema mata makaranta ta fara zuwa, dama bata yi waec ba yanzu ko sai da tayi sannan, da yake har yanzu akwai ƙwaƙwalwan tana nan tana ja. Maisun kan gun Mommy take barin ta har taje ta dawo. Watan ta biyar tayi girma tayi wayo tana gane kowa musamman Mommy da yake tafi zama a gunta. Barci ke rabasu da Mommy *** *** *** Ba ɓata lokaci aka maida auren Alhaji da Aisha ranan da ta dawo kuwa Mama Amarya taso tayi bala'i amma da taga baxa ta ci riba ba, sai ta kyale taji da jinyar hannun ƴarta. Farin cikin su ya fara dawowa dan Khadiyo ma tana zuwa lokaci-lokaci Sun dawo kenan suka ga ɗakin su a buɗe sunyi mamaki da suka samu a buɗe. Usman yana shiga ya yi karo da mutum ya ce "waye kuma anan" Abubakar ya ƙarasa ya kunna wutar ɗakin haske ya gauraya a ɗakin sa ganin Ruky suka yi daga ita sai towel a jikin ta, ta kama towel ɗin tana neman cirewa da hannu me lafiyan, Abubakar ya ce "Me haka ne me kike nema" Ta ce "Na mallaka muku kaina kyauta kuyi abin da kuke so da ni, Idan ma kwana kuke so nayi ma zanyi koda ku biyu ne zan iya ɗauka" Usman ya kwaɗa mata mari ya jawota ya cillo ta waje ta faɗi a kan hannunta me ciwon tasa kuka ya biyo ta ya ce "Idan muna neman matan banza ke kin isa mu neme ki, du be ki fa yadda kika dawo me zamu samu a jikin ki ƴar iska irin ki" Ta ce "Wallahi sai na maka sharrin da baza ka manta da ni ba" Ta tashi da kyar tana jin zafin hannun tayi ciki tana kuka Alhaji ta gani a falon ta ce "Kaga su Usman sun min fyaɗe" Ya kalli ta ya ce "Sun maki fyaɗe ko kin musu fyaɗe, lalata min yara kike so kiyi ko yaya" Mama Amarya ta fito da kukan ta tana cewa "nikan na gaji da wannan wulaƙancin gwara a Sallame ni nida ƴa ta" Ya ce "To kuje na sake ki, ku bar min gidana, nima ay na huta, kuma ƴaƴana sun huta, maganan Bilkisu kuma ina nan kan bakata, duk lokacin da ta dawo sai kun fuskanci hukunci, dan ina ji a jikina ƴata zata dawo. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/6, 9:05 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 59-60 Shiru suka yi duka Ruky ne tazo da hannun ta ce "Abba dan Allah ka barni na zauna a nan ɗin kaga ni ƴarka ce, kuma ma ni ban maka komai ba" Ya ce "Ƴata a ina, ni ban haife ki ba, ki tashi ki bi uwarki, to ma kin taɓa ce min Abba tunda kike, sai yanzu wai Abba, ki bar min gida ko insa yarana suyi kaca-kaca dake. " Mama Amarya ta turo baki ta ce "Muje Ay in shi ya sake ki Umar bai sake ki ba, sai mu tafi gidan sa, mu zauna kafin ya dawo kuma" Ruky ta ce "Mama ni ba inda zanje gwara ma ki bashi haƙuri muci gaba da zama" Jawo Ruky tayi ta ce a hankali "Ke banza ce, yaushe zan bari in bar gidan nan, ay ni da shi mutu karaba, kizo muje kisa ido ki gani, ba akwai boka ba, kamar yadda Aisha ta bar gidan nan a wancan lokacin yanzu zata barshi, su ma yaran sake barin gidan zasuyi" Basu ankara ba, sai jin muryan Usman sukayi ya ce "gwara ma ku sami wajen zama dan a wannan lokacin ƙarya ne boka yayi nasara a kan mu, idan kuma kunga ba haka ba, GA FILI GA DOKI" Abubakar ya ce "Saura sukuwa" Jan Ruky Mama Amarya tayi feeeeee sai waje. *** *** *** Kwanci Tashi babu wuya a gurin Allah yau Maryam ta zama cikekkiyar lauya, sannan kuma a ranan ne Maisun ta cika shekara biyu Bilkisu da Aliyu ne suka haɗa musu walima sosai anci ansha, saidai Aliyu ya lura da Bilkisu kamar hankalinta baya jikin ta, sauri sauri take taga halama fita take son yi ba da sanin kowa ba, mamaki yaji sosai, Lalle idan haka ne, akwai mai hure mata kunne" Yana gani tayi wa Maisun wayo ta zame, ta gudu, cikin gidan tayi, can sai gata ta fito da basket cike da abinci tayi hanyar waje da shi, da sauri ya bita ya shiga mota ya bita, Makarantansu yaga tayi ana sauƙeta ta shiga ciki gani yayi ta miƙa wa wani ɗalibi amma kuma ya manyanta Abincin ya matsa ya laɓe ta jikin bango inda basa ganin sa, buɗe abincin yayi ya ce "Nagode miki, yanzu sai muje gida ko" Ta ce "Ni bazan bika gidan ka ba gaskiya, shi yasa nace mu haɗu a nan" Ya ce "Lalle na lura bakya sona Bilkisu, tunda baza ki iya kai min ziyara gidana ba" Ta ce "Kai da na gayyacenka walimar ƴar uwata kaje ne, ay tilasta min kayi sai dai na kawo maka abinci, haka na kawo maka a ɓoye ba wanda ya sani, amma kuma yanzu kace in bika gidan ka kuma ba kowa, gaskiya bazai yuyu ba" Murmushi yayi ya ce "To shikenan mu shiga ciki sai ki juye min abincin, akwai kula na a ciki ko " Ba wani tunani ta shige ciki zai bita a baya Aliyu yayi saurin bayyana a gurin daidai lokacin kuma yaga wannan mutumin Aliyu ya ce "Kaine kuma dai" Bilkisu tayi saurin juyowa da taga Aliyu ta zaro ido, Aliyu ya ce "Har yanzu baki da wayo, akwai kuruciya a tare da ke, da har zaki biye wa namiji ya ce ki shiga office ɗinsa amma ki shiga, Ina tunaninki yake, Ya yaudare ki da maganan so yana nema ya lalata ki" Ta ce "Ya lalata ni kuma" Ya daka mata tsawa ya ce "Ɗauki abincin ki shiga mota mu tafi gida" Ta tsaya tana kallonsa hannun ta ya kama ya jata feee yayi da ita cikin mota da ya wugata ya dawo ya ɗauki basket ɗin abinci ya nuna shi da yatsa ya ce "Ƙaryan ka Wallahi, kuma Wallahi na sake ganin ka da wata ƴar uwata sai nayi ƙaranka" Ya dawo ya shiga motar ya ja suka yi gida, suna zuwa Maisun ta taho da gudu tayi gunsa ya ɗaga ta sama suna suna ta dariya. Ita ko gimbiyar shigewa tayi ciki rai a bace, ɗakinsu ta shiga ta kwanta a kan gado ba jimawa sai gashi ya biyo ta ya zauna bakin gadon ya ce "Wai dan na raba ki da ɗan iskan nan kike fushi" Shiru tayi ta kuma juyawa ya ce "Kinsan wanene wannan mutumin kuwa? Shine fa yaso ya yaudari Maryam, aikin sa kenan ya yaudari ƴan mata ya ringa lalata da su, a wancan lokacin badan Allah Ya kawo ni ba da ya lalata " Ta juyo ta ce "To bashi ɗin bane baka sanshi ba" Ya ce "Dole kice haka saboda kina sonsa" Sake juyawa tayi ya kalli Maisun ya ce "Kije gun Mommy kiyi wasa ko" Ta tafi da ɗan gudunta ya ce "Kiyi haƙuri banso ranki ya ɓaci, Amma ina son kisan wanene Jabir. Wata rana na ɗauki wayar Maryam sai naga Chat ɗinsu wai bashi da lafiya ta kai masa abinci ɗakinsa, a da taƙi daga baya sai ta amince saboda nacin da take masa, koda na bincika sai naga a ranan zata kai masa girkin, saida ta gama na bita, ta shiga ta same shi a kwance, saidai kuma tana shiga yaje ya rufe ƙofa da ƙyar na samu na balla ƙofar na shiga naga suna kokawa yana neman keta mata mutunci, ki gwada tambayan Maryam waye Jabir. " Yana gama faɗa ya fita cikin damuwa yana jin ɗaci a cikin zuciyar sa. Da suka kwanta kuwa da Maryam Bilkisu ta kalli Maryam ta ce "Waye Jabir" Maryam ta ce "Badai ɗan iskan nan kike tambaya ta ba, na tsane shi, badan Ya Aliyu ba da tuni bani da wata amfani a duniyar nan" Bilkisu ta ɗauki wayarta ta nuna mata potonsa ta ce "Wannan shine" Ta ce "Shine Wallahi munafuki mai fuska biyu" Bilkisu ta bata labarin komai yadda suka yi da Aliyu, Maryam ta ce "Ki godewa Allah sannan Ya Aliyu, amma ina son infaɗa miki wani sirrin da Ya Aliyu ya ɓoye, sannan ina so kiyi tunani akan maganata, kada ki ɗauketa da wani manufa" Bilkisu ta ɗaga kai, Maryam ta ci gaba "Ya Aliyu yana Sonki, yana son ki zama matarsa, ni kadai nasan wannan, tunda kika haifi Maisun nake fama dashi ya faɗa miki yaƙi, wai yafi so ki gane da kanki, ke kuma kinki ganewa, kiyi tunani mai kyau zaki gane maganata" Tana gama faɗa ta juya dan yin barci. Ita ko Bilkisu ta shiga kogin tunani, tabbas ta fahimci hakan, amma sai tayi tunanin saboda ita ɗin ƴar uwarsa ce, tabbas idan ta samu Aliyu a matsayin miji ta more. Wayanta ta ɗauka ta shiga whatsapp ta ganshi online. Ta tura masa saƙo "Kayi haƙuri" Ba jimawa ta turo mata da amsa "Da kika min me" "Da na kasa fahimtar ka, kuma na fahimci wanene Jabir na rabuda shi har abada" "To kina da wani saurayinne sai ki fito da shi na aurar da ke tunda naga alama auren kike so" "Hmm babu kowa " "To akwai wani wanda yake son auren ki ko zaki iya manage da shi tunda baki da kowa " "Eh to ya ya kawo kansa idan naga yamin shikenan" "Kina son yazo ɗakin ki yanzu" Daɗi ya kamata dan ta fahimci akan ta yake magana amma sai ta tura masa "Ay dare yayi ko zaka bari wan gardi ya shiga maka ɗakin ƙannen ka" "Kedai kawai kice yazo ki gani zaki gan shi" "To yazo amma idan bai min ba kada yaji haushi dan na fatattake shi" "Ki fito falo yanzu zaizo" "Allah ya bashi sa'a" Amin" Tashi tayi tasa hijabi kan Kayan barcinta ta fito ta zauna a falon. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/7, 8:29 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 61-62 Tana zaune taga ya shigo kallo ɗaya ta masa ta kauda kai ya zauna a ɗaya daga cikin kujeran ya ce "Ina Maisun ta ke" Ta ce "Suna barci ita da Maryam" Ya ce "Ke kin zo nan jiran masoyinki ko" Ta ce "To ba kai kace nazo na jira shi ba" Ya ce "To ay gashi yazo shi, ko zai samu karɓuwa" Shiru tayi tana kallonsa ya ce "Kinyi shiru kina kallona ko ban samu karɓuwa bane" Rufe fuskanta da tafukan hannayenta tayi, shiko murmushi yayi ganin ya samu nasara a kanta, saidai yana son ta tabbatar masa da bakinta, dan haka Ya ce "Ban samu karɓuwa ba kenan, ko da yake dama kina ce min tuzuru, ina ga ba yadda za'a yi ki auri Tuzuru iri nah" Da sauri ta ce "Nifa ba haka bane" Ya ce "To yaya ne" Ta ce "Kaga ni bazawara ce, ina tunanin kada Mommy da Daddy suce baza ka auri bazawara ba, kana saurayin da baka taɓa aure ba" Ya ce "Wannan duk ba hujja bace Mommy da Daddy zasu fi kowa farin ciki idan hakan ta faru, sai dai idan kece bakya sona ko kina da wani wanda ya fini" Ta ce "Ni bani da kowa" Ya ce "To baki sona kenan " Ta ce "Nifa ban ce haka ba" Ya ce "To ki faɗa min mana " Ta ce "To kaje zan faɗa maka a a chat" Ya ce "Kinyi Alƙawari " Ta ce "Nayi" Ya ce "Idan kuma banga komaiba, to nasan banyi bane, kuma bazan iya barci ba" Ya ce "Zaka ga saƙona" Tayi ɗaki tana zuwa ta samu wayarta ta mutu, ta kunna taga taƙi kawowa tasa a chaji. Shiko gogan naka da taji ta shiru ya tura mata saƙo "Yanzu nasan matsayina a gurin hala kina da wani ne wanda kike so amma ba damuwa zan zamo me haƙuri akan rashinki" Yana tura mata ya kashe wayarsa, ya kwanta, sam barci ya gagari idon sa, yasan ya samu nasara a kanta amma yana tunanin me ya hanata yi masa saƙon. Wayar tana ɗan yin chaji ta kunna saƙonsa ya shigo tana karantawa, tayi kira shi a waya amma a kashe ta tura saƙo shiru, kwanciya tayi tana ta juyi, ta kasa jurewa, da sauri ta tashi ta ɗauki dogon hijabinta har ƙasa tasa tayi ɗakinsa, daga nesa ta hango wutan ɗakin a kunne alamun baiyi barci ba, tana zuwa jikin ɗakin tayi bugu ɗaya, daga ciki ya ce "Waye" A hankali ta ce "Bilkisu ce, waya ta ce fa ta mutu ba chaji shine nasa chajin, ina buɗewa naga saƙonka Wallahi ba haka bane, ni bani da kowa, kuma dama nayi niyyar in faɗa maka ne fa" Wani daɗi yaji yana murmushi ya tashi ya buɗe ƙofar, ya ce "To shigo ki faɗa min" Ta shigo ya nuna mata kujera alamun ta zauna, ta zauna ya ce "To faɗa min" Ta ce "Ka buɗe wayanka zan faɗa maka" Ya ce "Aa ni anan nake so" Ta ce "To Ina sonka" Murmushin jin daɗi yayi ya ce "Ɗan ƙara faɗa inji" Ta sake faɗa ta miƙe tayi bakin ƙofa ta sake maimaitawa sai kuma ta kwasa da gudu ya biyo ta a bakin ƙofa ya tsaya saida yaga shiganta ciki sannan ya rufe ƙofa ya koma ciki yana ta hamdala wa ubangijinsa. Ita kuwa tana shiga ta ɗauki wayarta saida ta tura masa kalaman Soyayya sannan ta kwanta saidai barci sam yaƙi ziyartar idanun nata (Allah Sarki Mu mata bamu iya faɗawa Soyayya ba, har na tuna lokacin da na faɗa soyayyar Baban Mufeed Wallahi bana barci ko cin abinci, da naje makaranta ma karatuna ya gagara, kullun tunanin sa nake, ni kawai so nake na ganshi) Washe gari kowa ya fito da shirin sa, Maryam dama ba ko ina zata je ba, amma ta shirya su ita da Maisun Mommy ma da Daddy duk sun shirya, shima yazo a shirye suka zauna duka dan karyawa, ya kasa sa komai a bakinsa yana jiran yaga ta fito amma shiru, Mommy ta lura da shi ta ce "Wai kaikan baza ka fita bane" Ya ce "Zan fita" Ta ce "To naga ne kaƙi ka maida hankali kaci abincin ka" Ya ce "Bana jin cin komai ne ma fa yau Barin wuce kawai " Har ya kai bakin ƙofa ya juyo ya ce "Maisun Ina Mommyn ki" Cikin tsamin bakinta ta ce "Tun tuni ana ta tashinta taƙi tashi, sai barci take, sai ta tashi ma ta sake faɗuwa" Ya ce "Muje in ganta ko bata da lafiya ne" Ta wuce ya bita a baya suna shiga ya ganta a kan gado ta baje ta rufe rabin jikinta da bargo, wannan barcin da take ke ya nuna masa alamun bata samu na dare ba, gyara mata bargon yayi ya kalli Maisun ya ce "Idan ta tashi kice ina gaidata," Ta ce "To" Sai ƙarfe 11:35am sannan ta tashi bayi ta faɗa tayi wanka ta fito wanka da towel a jikinta ta ɗauki waya taga kiran Aliyu ratata, da saƙonninsa sai buɗewa take tana karantawa tana murmushi, saida ta gama zata ajiye kenan sai ga kiran sa. Ta ɗaga da Sallamarta a bakin ta, ya amsa sannan ya ce "Da fatan kin tashi lafiya uwar ƴaƴana" Ta ce "Lafiya lau, " Hiransu suka yi sannan ya kashe wayar. Tana cikin shirin ta ne Maryam ta ce "Kina ganin yayanki saboda baki fito kin karya ba shima yaƙi ya karya ya tafi haka " Ta ce "Da gaske bai karya ba" Ta ce "Wallahi bai karya ba, ta faɗa mata yadda yayi. Ya ce "Allah sarki, barin kira shi ya dawo gida ya karya gaskiya. " Kira tayi yana ɗauka ta ce "Dama baka karya ba ka tafi, gaskiya banji daɗi ba, haka zaka na bar min cikinka da yunwa nikan gaskiya ka dawo gida yanzu" Kwata-kwata ta manta da Maryam tana gurin sai zuba shagwaɓan ta take yi shi kuma yana biye mata, Maryam kan kallon ta take ta riƙe haɓa, har sai da ta kashe wayar sannan Bilkisu ta kalli Maryam ta ce "Wai dama baki tafi ba" Ta ce "Taya za'ayi na tafi na tsaya ganin ikon Allah ne" Ta ce "Kin tsaya gulma dai" Soyayya ce mai tsabta suke zubawa, basu sanar da iyayen sun ba su suka gane da kansu, dan Aliyu baya jin kunyar faɗa mata abu a gaban su. Sunyi farin cikin hakan musamman Mommy tanajin daɗi idan tagansu tare, sun yanke hukuncin yi musu Aure ita da Alhaji Yusuf amma kuma ya ce a ji ta bakin su tukun saboda haka, Mommy ta kira su duka dama suna tare suka zo. Alhaji Yusuf ya ce "Na fahimci wani abu game da ku, kamar kuna son junan ku, to na yanke shawara zan haɗa ku aure yaya kuka ce " Aliyu ya ce "Eh Daddy hakan yayi " Ya kalli Bilkisu ya ce "kefa Bilkisu me kika ce" Ta ce "Duk abin da kuka yanke a kan mi daidai ne" Ya ce "A'a ba wannan nake so naji ba, Zaɓin ki nake son ji, kina son sa ne koko kina da wanda kike so" Sake Dukar da kanta tayi ƙasa yayin da Aliyu kuma ya zuba mata ido, ta ce "Bani da kowa sai shi" Ya ce "Masha Allah ku tashi kije, sannan ki faɗawa Mommyn ku abubuwan da kike so a saya miki dan bana son auren ku ya wuce wata biyu. Aliyu ya ce "Mun gode Daddy Allah ya saka da Alheri Allah ya ƙara girma ba arziki" Ita kan bata ce komai na, saidai da zaran ka kalli fuskanta zaka san tana farin ciki sosai. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/8, 7:11 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 63-64 Shirye-Shirye ake tayi ba kama hannun yaro, Bilkisu kuwa tuni Mommy ta fara gyara ta saboda jin da tayi Daddy ya ce bazai wuce wata biyu ba. Haka kuma tasa Aliyu ya Mata lefe na gani na faɗa Alhaji Yusuf ya ce wa Mommy "Kada muyi aiki ba dai-dai ba fa, ya kamata mu sanar da iyayen yarinyar nan kada muyi son kan mu". Ta ce "Ka kyale su kawai ita kanta Bilkisu bata son ma susan tana tare da ni dani, dan haka ka kyale su, nadai faɗa wa Umman su Abubakar ta ce zata zo bikin." Ya ce "To shikenan " *** *** *** Ganin yana sonta kuma yana jin maganan ta yasa ko da yaushe take masa wa'azi akan abin da yake ba kyau, gashi dai bata da wani ilimi, amma ɗan abin da ta sani da shi take amfani wajen jan hankalin sa. Harda jahilci ke damun Zalimu, ɗan abin da take faɗa masa yasa ya fara ɗan ragewa, amma kuma ya ce mata bazai iya bari duka ba, saboda dashi yake samu yake ciyar da ƴaƴansa da matansa, ya kwashi yaransa duka ya sasu a makaranta muhammadiyya da ta zamani dan ya ce baya son yaran sa su tashi da jahilci kamar sa. Idan yana da kuɗi a jikin sa, duk matar da tazo karanta yake ya ce ya daina, amma kuma da zaran yaji baida ko sisi da kansa ke neman matan dan ya musu sihiri su biya shi. Yanin haka yasa Ummi ta same shi, ta ce "Ka ce kanason ka bari sai dai rashin abin da zaka bamu yasa kake yi, to ga wata yarjejeniya, zanje ƙauye, zan kama shanuna guda biyu na saida zan baka kuɗin kaja jari kayi wata sana'ar, saidai baza ka sake yin bokanci ba ka yadda" Ya ce "Na yadda wallahi, kuma zan na ajiye ribar har na biya ki duka kuɗin ki" Girgiza kai tayi ta ce "Idan na baka bana buƙatar ka biya ni kyuta na baka nidai buƙata ta ka daina wannan aikin" Ya ce "Wallahi na daina, kai daga yau ma na daina Wallahi " *** *** Ana saura kwana uku Ɗaurin aure Umma ta sauƙa a Kaduna, Murna gurin Bilkisu ba'a magana Koda suka gaisa da Mommy ta ce "Me kika ce a Alhajinki ya barki kika taho" Ta ce "Ce masa nayi zanje Biki Kaduna amma baisan bikin waye ba, har ya ce idan nazo na nemi gidan ki in faɗa miki ɓatan takwaranki" Ta ce "Ayko zanje na same shi na masa jaje Bilkisu kan ta dawo nan sai sun gama shan wahala tukunna ba wulaƙanta suka yi ba" Umma ta ce "Ayi haƙuri dai Adda a barsu haka ay sun ƙwalu, har yanzu Umar ma tunda ya tafi bai dawo ba, Sauda ko tana ta Bibiyar Jafar akan ya dawo da ita yaƙi" Bilkisu ta ce "Umma ina labarin su Yayana" Ta ce "Sunanan suma sun dawo, yayyenki sun zama lauyoyi duka" Ta ce "Gaskiya Umma ki faɗa musu yanzu yayyen nawa zan yi aure ba wanda ya sani ay ya kamata ko Albarka ne su saka min" Ta ce "Kada ki damu na komai ay, kuma ko yaushe ina kwantar musu da hankali. Ni Umar ma nake tausayawa, ko ina ya shiga, ko yana mace ko yana raye" Bilkisu ta ce "Ohonsa can ta matse masa, ina ruwana da shi ya mutu mana" Dariya suka mata Mommy ta ce "Ay da yana nan shine waliyyinki" Ta ce "Allah ya sauwaƙa ba gwara ince Ya Aliyun ya ɗauke ni mu gudu wani gari muyi auren ba, daga baya ma dawo " Dariya suka mata duka. Rana bata ƙarya saidai uwar ɗiya taji kinya, yau ne aka ɗaura auren Aliyu Yusuf da Bilkisu Ibrahim, kowa cikin Murna yake ɗaurin auren ya tara mutane da yawa. Alhaji Yusuf da kansa yaje zango ya samo Saniya mai kyau dan a yanka ta koda zai tafi ya ce "Su tura masa da mai fiɗa, Umar ne yaje ya feɗe masa saniyar ganin Umar bai masa ha'incin komaiba ya yi saboda Allah yasa yasa Alhaji ya masa biya mai tsoka sannan ya bashi kai da ƙafafuwan Saniyar, sannan ya ce "Yana gayyatarsa ɗaurin auren yaran sa" Ranan ɗaurin auren kuwa Umar da Sale sunzo ko da yaji an kira sunan Bilkisu a gurin gaban sa ke faɗuwa, da kyar ya iya cin Abincin ya kalli Sale ya ce "Sale zo mubar gidan nan kaje" Ya ce "Buje muyi Sallama da Alhajin " Umar ya ce "Jeka kawai ina jiranka " Maisun ce tazo ta gabansu Umar ya ganta yaji yayi zuciyarsa ta buga da ƙarfi har saida ta kama gurin ya kama hannunta ya ce "Yarinyar ina zakije cikin wannan jama'a haka " Cikin tsamin bakinta ta ce " Daddyna nake nema yace yanzu yana zuwa yaƙi zuwa shine na fito neman sa" Yace "To keɗin a wani gida kike" Ta nuna gidan ya ce "To ki koma gida zan turo miki Daddyn naki ko, kije ki zauna kusa da Mommyn ki yana zuwa yanzu" Ta tafi shiko yana kallon ta, ji yayi wani son yarinyar ya shige shi, yanzu yasan idan nashi ɗan yana raye yasa zaikai wannan yarinyar a girma, kai shidai a rayuwansa yana son ƴaƴa mata, Allah yasa shima tasa macen ne, Can kuma ya ce cikin ran sa To idan ma macen ne yanzu ina suke" Hawaye ne yayi ta zuba masa Sale ya ce "Ka tuna Bilkisu ko, mu tafi kawai yanzu kada ka tara mana jama'a aganka babba da kai kana kuka kuma farin ciki ya kawo kowa nan gurin" Aliyu ya ce baya buƙatan wani Program dan haka walima kawai ya haɗa musu ita da ƙawayenta. Da daddare aka zo ɗaukan Amarya ba zanjen yin Kuka ko damuwa zata bar gida, Maryam ta ce "Ko kuka babu" Ta ce "Wani kuka kuma ina so yana sona" Nasiha kan tasha shi gun ƴan uwa da abokan arziki. Maryam da wata ƙawar Bilkisu da suka haɗu a makaranta ta sunan ta Husaina, su suka mata rakiyya. Nasiha aka kuma mata kowa zai tafi ta ce "Maryam da Husaina amma anan zasu kwana" Maryam ta ce "Gidan masoyin naki tafiya zamuyi" Husaina ta ce "Ba ke kika ce, kina so yana so ba, to gaku mun barku ku biyunku" Idonta ya cicciko da ƙwalla ta ce "Dan Allah mu kwana nikan" Maryam ta ce "Nabar Maisun mawa kema kinsan bani ba ke kuka zata sa, ga ba ubanta, dama yau sai neman sa take yi" Tana gani suka tafi ta fara kuka su kuwa Dariya sukayi ta mata Da Maryam taga da gaske ta ke taje ta ce "To a ina zamu kwana" Ta ce "Anan mana" Ta ce "To Ya Aliyun fa" Ta ce "Sai yaje ɗakinsa ma na" Hasaina ta ce "Baki da hankali kenan mu kinga tafiyar mu, ayi auren yau mu kuma mu ɗale masa gado" Tana ji tana kallon suka tafi, ba jimawa ta ji muryansa da abokan ango a falo yana cewa "Wallahi ba wanda zai shigar min ɗakin mata, wannan ay iskanci ne, a leƙa min ɗakin mata" Dariya suka yi ɗaya ya ce "To muje ka raka mu muma" Ya ce "Saidai inje na kulle ƙofar gida" Binsu yayi a baya yaje ya kulle gidan sannan ya dawo kai tsaye ya shiga ɗakinta da ledodi guda biyu a hannun sa, ganinta yayi a tsakiyar gado tana kuka, ya ajiye ledan ya hau gadon ya ce "Wai wannan kukan na amare ibada ne, nifa bana so, kinga kin ɓata min kwalliyar yanzu dole sai kin sake min wani, dan ni ina son kwalliya" Ta ɗago ta ce "Maryam da Husaina ce fa nace su kwana amma suka ƙi" Ya kalle ta, tabbas har yanzu akwai yarinta akan ta dan haka ya ce "To banda abinki gani wani Maryam da Husaina zaki nema" Rarrashinta ya ringa yi saida tayi shiru ya ce "To je kiyi alola mu nuna wa ubangijinmu godiya ko Babyna" Ta mike ta shiga bayi ta ɗauro Alola shima yayi tasa, suka gabayar da Sallah raka'a biyu, sannan ya jima yana musu Addu'a tana amsawa da Ameen saida ya gama ya tambayeta fannin Addinita tana bashi amsa sai yaga ashe da iliminta. Kicin ya shiga ya ɗauko plate ya saka musu kaza kai ya ringa bata a baki tana ci saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya tsiyaya mata lemo tasha, shima kuma yaci nashi sannan yace "Muje mu kwanta ko" Ta ce "Barin watsa ruwa, ta shiga bayi, ta fito ta samu baya nan dan haka tayi shirin ta, tare da yin ɓarin turaruka a jikin ta, dan tasan yau Yayan nata zai yaye mata kunya. Kwanciya tayi lokacin shima ya shigo da kayan barcin sa ya kwanta ya rungumota ya ce "Wannan ƙamshi haka" Murmushi tayi shigo Yayan nata daga nan ya ringa canja salonsa. Asuba ta gari Amarya da Ango... _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/8, 12:58 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 65-66 Washe gari da safe Maryam ce ta kawo musu breakfast ko zama bata yi ba ta koma. Shi da kansa yake bata a baki har sai ta ƙoshi. Cikin kwana biyu Bilkisu ta koma Bilkisun da, dan shagwaɓa ce ta ƙaru a kan na dan kuwa kullun shawaɓan ƙaruwa yake yi, shi kuma ƙara biye mata yake. Satinsu biyu Aka kawo Maisun da kayan ta dan ya ce zai sata a makaranta, Islamiyya ya fara saka ta saida tayi wata biyu kuma ya sata a boko, a lokacin ne kuma Bilkisu ta fahimci tana da shigar ciki, dan taji alamomi kuma bataga Al'adanta ba. Bata yi wata-wata ba ta faɗawa Aliyu ayko murna kamar yasa ruwa a ƙasa yasha. Nan kuma ya kuma ji da ita kamar zai maida ta ciki. A haka taci gaba da karatunta dan tana son ta zama likita ne. *** *** *** Tuni Zalimu ya fara Sana'an gwanjo kasuwanni yake bi kuma Alhamdulillah Allah yasa wa abin Albarka, Yana ganin Mutumcin Ummi sosai, idan ya dawo daga kasuwa a ɓoye yake kawo wa Ummi har ɗaki ba tare da sauran matan sun sani ba, Ummi kuwa a rashin sani takan amsa ta masa godiya, tunda ta fahimci hakan sai taƙi yadda ta ce "Yana kawo musu duka dan duk ɗaya suke a gurin sa, " Maganar tuwo kuwa yanzu babu shi sai lokaci kaɗan-kaɗan idan an ji sha'awan tuwon, duk ƴan gidan sai aka zo ana ganin Mutuncin Ummi sosai, kuma duk abin da ta hana yana hanuwa, duk abin da ta buƙata nan da nan zaka ga ana rige-rigen bata, sirkar tasu ma tana girmama Ummi duk abin da zata yi saidai tayi wa matan gidan amma tana taɓa Ummi tuni ƴaƴanta zasuyi cahhh akanta. Ummi ta zama ƴar gata gidan yanzu tunanin ta ɗaya shine Bilkisu Lalle tayi babban kuskure bata neman Addanta ko rabon ta da ita tun auren Bilkisu lalle yakamata ta nemi ƴar uwarta, maganan Bilkisu kuwa tabar komai a hannun Allah tunda anyi nema har an gaji ko tana raye ko tana mace oho. Amma abin da ta sani yanzu shine dole taje ta duba ƴar uwarta a Kaduna duk da bata san guri ba, zata nemi numberta suna waya. Koda ta tambayi mijin ya ce "To ba damuwa zai binciko mata number a gun Umman su Abubakar dan anan kawai suka san zata samu, da kansa yaje ya amso number yana dawowa tasa a wayarta ta kira Ringin uku tayi Addan nata ta ɗauka da Sallamartar ta bayan sun gaisa Ummi ta ce "Addana" Ta ce "Halima ashe zaki neme ni" Nanfa Ummi ta fara mata kuka a cikin waya, nan fa Addan ta fara rarrashinta kamar suna kusa, abin ka da ƴan uwa tuni Ummi taji zuciyar ta tayi sanyi ta fara bata labarin abinda ke faruwa nan fa Addan nata ta fara faɗa tana cewa yanzu wannan abin ya faru amma Halima ki kasa faɗa min, auren ki ya mutu harda sabon aure, wa kike da shi wanda ya wuce ni" Ummi ta ce "Kiyi haƙuri Adda zan zo in sake naki haƙuri " Ta ce "Yanzu ina labarin Bilkisun" "Har yanzu dai ba labarinta" Daga ƙarshe dai Addan nata tayi ta rarrashinta. Zalimu kan yayi mata shiri kaf harda su tsaraba harsaida Ummi ta ce ya isa haka. Ta shirya kayanta tsab dan gobe ana Sallah asuba zata shiga mota ta tafi, sai jin mummunan Al'amari sukai, Zalimu ne yayi hatsari a hanyar dawowan sa daga kasuwa da suka je cin kasuwa, duk cikin motar shi ɗaya ne yayi rai, saidai shi ɗin ma yana nan ya jigata sosai ya samu karaya a ƙafa, haka hannunsa ma na hagu. Haka aka kawo shi gida, a lokacin aka masa ɗaurin gida. Washe gari Zalimu ya ce "Ki faɗawa ɗaya daga cikin ƙannena su kaiki tasha tunda kinga abin da Allah ya aiko min" Ta girgiza kai ta ce "A'a na fasa zuwa, baka da lafiyan kuma sai na bika, kaima kasa hakan bazai yuyu ba ay" Ya ce "Ba komai kije kawai" Ta ce "Ay bazan iya zuwa ko ina ba gwara na zauna muyi jinyar ka" *** **** Cikin haka ne cikin Bilkisu ya fara girma yakai wata shida kula gun Aliyu ba irin wanda bai bata ganin mai wankin su ya tafi gida yasa Take yi da kanta, shi kuma yaga kamar tana wahala yasa ya fara nema musu mai wanki, da bai samu ba yayi magana wa Daddy, Daddy ya ce "To shikenan zanyi magana da wani yaro Umar sai ya samo muku" Alhaji kuwa ya ɗaga waya ya kira Umar ya ce "Kazo gida ina son ganin ka" Umar ya ce "To an gama Alhaji" Sai yamma Umar ya samu zuwa gidan, a gurin adana motoci Daddy ya same shi, bayan sun gaisa ne ya ce "Akwai ɗana Aliyu yana neman mai wanki shine nace zan maka magana ka idan za'a samu a gurin ka sai ka samo masa" Ya ce "Ay ba komai Alhaji idan wankin ya taru zan na zuwa ina musu" Ya ce "Da yawa fa, ga nashi ga na matarsa da ƴarsu fa" Ya ce "Ba komai Alhaji ay zan iya" Ya ce "To shikenan zan masa magana sai kaje can gidan nasa" Daddy ya ɗaga waya ya kira Aliyu Suna gama magana Daddy ya kalli Umar ya ce "To zaka same shi a gida wai, amma aikin bazaiyi yawa ba ga wanda kake yi a zango" Umar ya ce "Ba damuwa Alhaji " Kwatanta masa gidan yayi tare da bashi number n Aliyun akan idan yaje ya kira shi. Yana zuwa kuwa ya kira shi bayan sun gasa ya ce "Nine wanda Aka ce nazo zan muku wanki" Aliyu ya ce "To gani nan fito wa ma" Aliyu yana zuwa da ya kalle shi ya ce "Amma fa kamar na sanka" Umar yayi murmushi ya ce "Kama ne kawai Alhaji ni ba ɗan garin nan bane ma" Ya ce "To shikenan yanzu zaka fara ne ko sai gobe" Ya ce "Yanzu zan fara goben idan nazo sai na goge muku ko" Umar ya shiga ciki ya ɗauko kayan harda matarsa da na Maisun da sabulu da omo ya bashi. Kayan Aliyu ya fara wankewa sannan ya fara na matar, saidai a duk lokacin da ya ɗaga rigar ta ko wani abu nata, sai yaji wani ƙamshi wanda ada ya saba jinsa wanda yanzu ya ƙaurace ma hancinsa. Tun yana tunanin ina ya san wannan ƙamshin har ya tuna wannan ƙamshin irin na Bilkisu ne, cikin ransa ya ce "Lalle Hajiya ma ma'abociya ƙamshi ce irin Bilkisuna" Yana wanke kayan yana nishaɗi har har ya gama. Da yake ana iska wasu sun bushe ya naɗe su. Yana naɗewa ne aka dawo da Maisun daga Makarantar Islamiyya tana zuwa ta wajen ta ce "Sannu da aiki" Ya ce "Yawwa ƴar lele kece ashe kin tuna ni kuwa" Tayi shiru kamar me tunani ta ce "Na tuna ka, kaine na ganka ranan auren Daddyna" Ya ce "Eh nice ranan baki faɗa min sunan ki ba, ya sunan ki" Ta ce "Maisun Amma a makaranta ana kirana da SAUDAT UMAR" Yace "Da kyau sunan Mama ta ce ke ashe, kuma suna ƴata idan na haihu" _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/10, 5:25 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 67-68 Zata ƙara magana ya ce "Ki shiga ciki kada Mommynki ta ga baki shigo ba ko" Ta ce "To" Ta fara tafiya shiko yana kallon ta har ta shiga ciki, Kaunar yarinyar yaji ta shiga ransa, tunawa yayi da Bilkisu da cikin ta tuni ƙwalla ya fara zubo masa yasa Babbar yatsar s ya ɗan share ya ci gaba da abin da yake. Washe gari kuwa ya dawo ya fara guga duk da an wanke kayan amma ƙamshin Bilkisu yake yana gogewa yana jin wani iri a zuciyar sa, kai gaskiya bazai jure wannan aikin ba, yana tayar masa da hankali da yawa, saida ya goge duka sannan ya kwasa, dan Mai gidan ya ce "Idan ya gama ya kawo masa falo" Falon yayi yayi Sallama Aliyu yazo ya buɗe masa ƙofa ya amshi kayan ya ce "Ka shigo Matar gidan tana son ganin ka don wata rana koda bana nan idan kazo sai ta baka ko" Ya ce "To Yallabai" Har zai juya ya ce "Nawa ne kuɗin da zan baka, ko sai wata zan na baka" Ya ce "Duk yadda ka yanke Alhaji " Ya ce "To nawa zan na baka, gwara dai a ringa biyanka a lokacin da kayi aikin ko" Ya ce "To na gode" Ya shigo ciki, ya zauna a ƙasan kafen, abin mamaki ƙamshin falon ma irin na Bilkisu ne, lumshe idonsa yayi yana jin daɗin ƙamshin. Shiko Aliyu shiga yayin ciki ya ajiye kayan ya kalle ta da take kishingiɗe ya ce "Kisa hijabinki kizo ki ganshi ko" Ta ce "To" Ta ɗauki hijabinta tasa ta biyo bayansa Aliyu ya zauna idon Umar ko yana rintse yaji muryan Aliyu ya ce "Malam Umar ga iyalina zuwa" Ya buɗe idonsa kenan daidai lokacin ita kuma ta iso tsakiyar falon da sauri ya miƙe yana nunata da yatsa, ita kuwa bayan Aliyu tayi da gudu ta cakume shi. Aliyu ya daka masa tsawa "Me haɗinka da Matata" Muryan Umar na rawa ya ce "Bil... Ki... Su" Aliyu ya juyo ya kalli Bilkisu da ta riƙe shi ta baya yaga sai hawaye ke zuba ya kamata ya dawo da Ita gaban sa ya ce "Faɗa min waye shi" Cikin kuka ta ce "Umar ne fa, ka kawo shi gidan mu dan Allah ka kore shi bana son ganin sa na tsane shi, ganinsa yana sa in shiga tashin hankali, ka kore shi, ni kayan da ya wanke ma bana so a fitar da su" Ya ce "Wai kina nufin Umar Mahaifin Maisun" Ta ce "Bana so kana haɗa shi da Maisun, Maisun bata da wani uba da ya wuce kai" Umar kan ƙafafunsa rawa suka fara yana kuka daga bisani kuma ya durƙusa akan gwiwarsa cikin kuka ya ce "Ku saurare ni dan Allah, Bilkisu ki tsaya zan faɗa miki ba yin kaina bane" Aliyu ya zaunar da ita kan kujera yaje ya kama kafaɗan Umar ya ce "Haba kana namiji kana kuka ya isa ka daina kukan haka " Ya ce cikin kuka "Dole nayi kuka na rasa Bilkisu yanzu ta min nisa nidai roƙona gare ta, ta taimaka tazo muje gida domin nayi Alƙawari bazan taɓa komawa gida ba tare da ita" Da sauri Bilkisu ta miƙe ta ce cikin ɗaga murya "Baka da hankali ne, ko ka haukace ne, Ina da auren zan bika, ko da yake dama da alamun hauka a tare da kai" Hannunsa ya haɗa yana sake roƙonta ta ce "Ka tashi ka bar min gidana, Ya Aliyu ka kore shi bana son ganin sa, na tsani ganinsa a rayuwata" Aliyu kan da yaga tana faman haukace masa yasa yaja Umar suka fita waje, saida suka je gun mota ya ce "Umar ya akai haka, me yasa kayi mata haka a wancan lokacin" Ya ce "Wallahi ba yin kaina bane bana cikin hayyacina" Ya ce "Ya aka yi haka to" Umar ya bashi labari tun farkon auren su da Bilkisu har izuwa inda ya koreta haɗi da saki. Aliyu ya ce "Kayi haƙuri dan Allah ka tsaya a nan barin je na lallasheta " Umar ya ce "Yanzu dama Maisun ƴata ce" Ya ce "Eh ƴarka ce " Hawaye ne suka ci gaba da zarya a idonsa, shiko Aliyu ya shiga ciki ya sameta zaune akan kujera tana huci kamar taga Umar ɗin a gabanta, Yazo ya durƙusa a kan gwiwarsa yasa hannu kan cinyarsa ya ce "Haba My Billy ban sanki da haka ba, ki manta da baya ki fuskanci gaba, Umar ɗan uwanki ne, bai kamata ki masa haka ba, duk da ya miki kuskure a baya ay ba yin kan sa bane, baya cikin hayyacin sa, Asiri suka masa. " Ta ce "Asiri, to Ƙarya yake Ay tun tuni dama ya tsane ni, tun ina ƙarama yake tsangwama ta, tare da cin zali na, Shine fa musabbabin da yasa Babansa ya mana aure saboda shi ɗin ɗan Iska ne" Aliyu zai sake magana ta ce "Dakata Malam wai me yasa kake bin bayan sa, dan ba a kai yayi ba" Murmushi yayi ya ce "Ke kina masifar ma bata miki kyau Wallahi ki canja masifa ba taki bace" Haushi ne ya kamata tayi fuuuu ta wuce ɗaki ta jawo ƙofar ta rufe. Kallonta yayi kawai ya fito gun Umar ya buɗe masa mota ya shiga, shima ya shiga gun driver yaja suka yi gidan Daddy. Har Falo Aliyu ya shiga da shi ya samu Mommy tana falo amma Daddy baya nan Mommy tana kallonsa ta miƙe ta ce "Wannan kamar Umar" Aliyu ya ce "Eh shine ashe dai zaki gane shi" Da sauri ta tashi tsaye ta nuna hanyar waje da hannunta ta ce "Fitar min dashi daga gida, me tazo ya min kuma" Aliyu ya ƙarasa ya kama hannun ta ya ce "Haba Mommy ki saurara kiji mana ba yin kansa bane fa" Ta ce "Tun muna saida juna da ka ka fitar min da wannan azzalumin daga gida " Ta daka masa tsawa tare da nuna shi da yatsa "Kai! Fitar min daga gida tunda ba gidan uban ka bane" Da sauri Umar ya fita waje, yana fita ita ma tayi ɗakinta tabar Aliyu a tsaye a gurin. Fitowa yayi ya samu Umar a jikin mota yana kuka yaje ya tsaya gefen sa ya fara kiran Daddy ya faɗa masa komai game da Umar, Daddy ya ce "To Ku jirani gani nan zuwa" Suna tsaye a gurin sai ga Daddy ya shigo da motar sa, yana kallon Umar ya ce "Ashe kai ɗin ma na gida ne, to Bismillah ku shigo ciki" Suka ƙarasa amma Umar ya kasa shiga saida Aliyu ya kama hannunsa suka shiga tare. A ƙasa suka zauna dukan su. Daddy ya shiga ɗakin Mommy Nasiha yayi ta masa da nuna masa Umar ba a hayyacin sa yake ba lokacin da ya aikata wannan kuskuren har ya sauƙo, suka fito tare suka zauna a kan kujera ta ce "To Yanzu dai kaga Bilkisu tana da aure ya kenan za'ayi" Daddy ya ce "Yanzu dai maganan ɓoye-ɓoye ya ƙare gobe da safe zamu shirya duka mu tafi Bauchi har ita Bilkisun " Mommy ta kalle shi ya ce "Eh, idan yaso daga baya ta dawo ɗakin mijinta, amma banga dalilin da yasa zamuna ɓoye yarinya mutane suna cikin damuwa ba" Shiru tayi bata ce komai ba, ya kalli Aliyu ya ce "Ka kaishi ɗakinka ya yi abin da ya dace, gobe mu ɗau hanyar Bauchi" Ya ce "Tukun na ma yaje yayi aski ko, dube shi yadda ya tara gashi " Shidai Umar yana shiru abinsa. Aliyu ne ya kaishi aski sannan ya kawoshi gida yayi wanka, Aliyu ya bashi kayan sa sabbi yasa sannan ya kawo masa abinci. Bayan nan ya koma gida gun Gimbiyar tasa, A faro ya ganta fuskan nan a ɗaure yazo ya zauna gefenta ya kama hannunta ya ce "Kina fushi dani ko, kiyi haƙuri ki sake min fuska dan fushinki masifa ce a gare ni" Kuka ta fasa cikin kuka ta ce "Ba ka nuna min ka fi son Umar akaina ba, kuma Umar ɗin da ya cuce ni" Ya ce "Wa ya faɗa miki, Lalle har yanzu baki san yadda nake ji da ke ba, yanxu dai mubar wannan zancen Daddy ya ce "Gobe zamu je Bauchi dukan mu " Hararansa tayi ta ce "Ni ba inda zanje" Ya ce "Baki son ganin su Ya Abubakar ko" Shiru tayi can kuma ta juyo da jikinta gurinsa ta ce "Ehhhh haka ne, su ya Abubakar suna nan, amma badan su ba ba inda zani " Da yamma kuwa saiga Mommy, Daddy, Maryam da Umar, Bilkisu ta musu tarɓa ta Musamman ta gaida su Amma Umar ko kallon sa bata yi ba. Daddy ya fara magana ya ce "To Bilkisu abin da nake so da ke, kiyi haƙuri ki manta da komai gobe zamuje Bauchi gun iyayen ki" Ta sunkuyar da kai ta ce "To Daddy duk abin da ka ce haka za'a yi" Maisun ce ta fito da yake yau Alhamis ba Islamiyya tana ganin su ta faɗa jikin Daddy tana gaishe shi, Daddy ya nuna mata Umar ya ce "Ga can Daddynki kije ki gaishe shi" Kallon sa ta ringa yi can ta ce "Daddy na kuma, wannan fa me wanki ne, " Ta nuna Aliyu ta ce "Nika ga Daddy na nan" sai kuma ta faɗa jikinsa. Kunya ce ta kama Aliyu sai ya janye ta ya ce "Maisun wannan ma Daddyn ki ne kije ki gaishe shi" Ta je ta hau jikinsa ta ce "Shine tun tuni baka zuwa sai yanzu" Shidai Umar yana Shiru ba Magana. Sai daɗi da yake ji ƴarsa na jikin sa. Washe gari Sassafe suka ɗauki mota ɗaya Aliyu ne ke jan mota, sai Bilkisu a gaba, Daddy da Mommy kuma suna can baya, sai Maryam da Umar riƙe da Maisun sune a bayan su Aliyu, wato tsakiya kenan. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/10, 7:24 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 69-70 Aliyu ya iya gudu a mota, wai dan ma Daddy yana masa magana, wannan yasa suka isa da wuri. Gidan Abba suka yi da Umma ce kawai a gidan sai Khadiyo da tazo dama Umma tasan da zuwan su taji komai, Khadiyon ɗin ne bata sani ba, tana ganin Bilkisu ta je da gudu ta rungumeta sai kuma tasa kuka tana cewa Aunty ina kika shiga ne mukai ta neman ki, kinsan jalin da muka shiga kuwa?" Zama suka yi Umma da Khadiyo suka kawo musu abinci da Abinsha, kafin su gama kuwa Umma ta kira Abba, Baba, Abubakar da Usman. Ita kan Bilkisu sam ta kasa cin Abincin ma tana cewa da Umma ita yayyenta. Ba jimawa suka Baba ya shigo gidan yana ganin Bilkisu yaje ya zauna gefenta ya kama hannunta ya ce "Bilkisu! Kece haka ina kika shiga" Murmushi kawai yake take tayi. Ana ta gaishe shi ko ya kula shidai ta Bilkisun yake kawai sai daga baya ne suka gaisa Umar kuwa ya matso ta jikin ƙafar sa ya ce "Baba Tun tuni ina ta gaishe ka baka amsa min ba" Shiru ya masa baice komai ba Bilkisu kuwa tana lure da haka. Can saiga Abubakar da Usman ayko bata bari sun ƙaraso ba ta tashi da gudu taje ta rungume su Aliyu kan yana ta cewa " Ahhhh" Mommy ta masa ido alamun ya bari a hankali ya ce "Mommy Cikin ta fa take gudu" Ta ce "Wai a kanka aka fara ciki ne" Yayi shiru. Sun daɗe ruƙe da juna suna murna sannan suka saki juna suka fara gaisawa da jama'a Usman ya kalli Maisun ya ce "Wannan ce ƴarmu " Ta ce "eh" Ya ɗauke ta suka fito waje ay bata iya zama ba ta bisu Aliyu ma ya tashi ya bita a baya Ɗakin su Abubakar yaga sun shiga ya bisu zama suka yi shima ya zauna ya ce "Baki ci Abinci ba fa ina kallon ki, dan Allah kizo kici kada ki zauna da yunwa" Ta kalle shi ta ce "Ayya Yayana, ni na ƙoshi ma da naga ƴan uwa na" Usman ya ce "Kodai shine mijin yanzun" Kafin ta amsa Aliyu ya amsa da "Eh yayan mu" Dariya suka yi duka Abubakar ya ce "Harda saurin Amsawa " Aliyu ya ce "To na kawo miki Abincin nan" Ta ce "A'a" Abubakar ya ce "Khadiyo zata kawo mana zamu ci anan ma, Kaima nasan baka ci da yawa ba tunda taƙi ci" Suna haka kuwa Khadiyo ta shigo da Abincin, tare suka ci duka har Aliyun ma. A falo kuwa Baba ne yake maida Maganan yadda akayi da irin cin Amanar da Umar yayi" Alhaji Yusuf ya ce "Ka daina faɗan haka fa ka dubi ɗanka tunda ka shigo nan yake baka haƙuri baza ka haƙura ba" Ya ce "Nifa na riga na Sallama wannan ɗan a duniya dan haka yaje kawai, bani da wani ɗa " Abba ne ya shigo Falon shima gaisuwar akai tayi Umar ya gaida Abba ya Amsa ya ce "Kai dai baka da dattaku Umar sai ka wuce ka tafi baza'a a ganka ba kaƙi dawowa gida ina hankalin naka yake" Ya matso ya ce "Abba kayi haƙuri " Baba ya ce "Yanzu ma komawa inda ya fito zaiyi" Abba ya ce "Ba ya dawo maka da ƴarka ba. To ka kyale shi kuma ya isa haka" Bayan sun gama suka shigo duka Bilkisu ta faɗa jikin Abbanta tana murna ya ce "ni dai ɗaga ni ay dama kin watsar damu kin yaye mu" Ta ce "Ay haƙuri Abbana bazan kuma ba" Magana Aka ci gaba da maidawa aka yafi juna amma sam Baba yaƙi ya saurari Umar. Baba ya ce "Kai me yasa kake da taurin kaine haka" Alhaji Yusuf ya ce "Shine nima na gani ay" Abba ya ce "Ka ganshi tun yana ƙarami akwai kafiya da taurin kai" Ganin Umar yadda yake kuka yasa gaba ki ɗaya zuciyar ta ya tsinke, Namiji kamar wannan amma yayi ta kuka haka, dan haka ta matsa kusa da Baba ta ce "Baba kayi haƙuri ka yafe masa ni na yafe masa, idan saboda ni kaƙi yafewa kayi haƙuri Baba" Baba yayi shiru yana kallon ta Can kuma ya ce "Kin manta abin da ya miki ko" Ta ce "Baba ka manta da komai kaima dan Allah " Ya ce "To shikenan Allah ya yafe mana gaba ki ɗaya" Wani sanyi Umar yaji a ransa ya ce "Nagode Ƙanwata Allah ya sauƙe ki lafiya " Abubakar kan tun da ya shigo yake lure da Maryam da duk da ake magana bata sa baki ba, tayi shiru Maisun na jikinta, Miƙewa yayi ya kira Bilkisu ta taso suna zuwa ya tarar da Usman yana waya suka zauna ya ce "Wacece waccar ƴar budurwan da kuka zo tare" Ta ce "Wai Maryam, Ƙanwar Mijina ce" Ya ja hancin ta ya ce "Baki da kunyar cewa mijinki a gaba na, ko da yake naga mijin ma ba kunya gare shi ba, Ita Maryam ɗin An mata miji ne" Ta ce "A'a amma kasan baza ta rasa masoya ba" Ya ce "To idan so samu ne a sani a ciki" Da sauri Usman ya kashe wayar ya miƙe ya ce "Tab amma ko yau ga abin Al'ajabi" Bilkisu ta ce "Dan ya ce yana sonta " Ya ce "Ay baki san wani abu ba, shifa a rayuwan sa bai taɓa yin budurwa ba, ga ƴan mata sai bibiyansa suke amma duk yaƙi su har ana cewa Aljana ce ta aure shi" Ya ce "Ni kawai banga abin da zaisa ina ɓata lokacina bane kawai, wannan ɗin ma idan ta nuna min tana da wanda take so zan barta" Bilkisu ta ce "Ayko baza'ayi haka ba, idan Maryam ne kamar ka same ta" Ya ce "Yawwa My sister Nagode miki" Usman ya ce "Su sabon shiga fa an faɗa" Abubakar ya ce "Tashi ka gyara mana ɗakin yanzu za'a kira min ita" Ta ce "Kaga kuwa ita ma Barrister ce" Ya kama hannunta ya ce "Dan Allah fa! Kai kashe wayan nan kazo ka gyara mana ɗaki yanzu zata zo" Usman ya miƙe ya ce "Kaga ni fita ma zanyi bazan gyara ɗaki saboda mace ba" Bilkisu ta ce "Yi shirun ka Yaya ni barin gyara " Gyarawa tayi sannan ta shiga ta kira Maryam suka shigo tare, Abubakar kan harda canja kaya yasa kaftan ya saka hula. Maryam kan zama tayi a can gefe Bilkisu kuma ta miƙe zata tafi Maryam zata bita Ta juyo ta ce "Magana za kuyi dai" ita ko Bilkisu ta koma ciki ta samu wai su Mommy zasu koma sun yanke shawaran zasu bar Bilkisu da Maisun su kwana biyu. Bilkisu ta ce "Mommy abar Maryam ma dan Allah" Ta ce "Idan zata zauna sai a barta tunda ay bata da aikin komai" Ita ko Bilkisu tayi hakan ne dan su samu su daidaita kansu da yayan nata. Tuni Maryam da Abubakar suka daidaita kansu. Ita kan ya burge ta, koda ta shigo Mommy ta ce "Maryam zaki zauna idan yayanki yazo sai ku tafi tare ne ko zaki bimu" Ta ce "Zan zauna Mommy " Ta ce "To" Da yake sunyi Sallar Azhar yasa suka shirya tafiya, Mommy ta kira Bilkisu gefe ta ce "Idan Umar ya ce zai karɓi ƴarsa ki bashi kayansa, sai a turo masa kayan ta daga nan' Ta ce "Mommy kuma... " Ta katseta ", Kiyi haƙuri idan yace yana buƙata ki bashi amma idan bai buƙata ba shikenan" Ta ce "To" Aliyu kan baiso barin matar sa ba, amma ba yadda ya iya haka suka tafi. Da yamma kuwa ƙarfe biyar saiga Mama Sauda duk ta rame kamar ba Mama Sauda mai ji da kanta ba. Tans zuwa ta rungume Bilkisu tana cewa "Ki yafe min dan Allah Bilkisu, ganin Umar na kallonsa yasa Bilkisu ta ce "Haba Mama ni ƴarki ce ay kada ki damu komai ya wuce" Umar kuwa matsowa yayi Bilkisu ta ce "Mama Yaya yana magana" Tana ganin sa rungumeshi tayi tasa kuka tana cewa "Ina ka shiga ne, nayi rashin Baban ka gashi kaima nayi rashinka" Rarrashinta ya ringa yi har saida tayi shiru. Bilkisu dai taga gata duk inda ta matsa Bilkisu Shiko Umar yana maƙale da Maisun, Sauda ma da tazo har goya ta sai da tayi, tana mamaki halarci irin na Bilkisu da ta iya sa Sunanta bata yi tunanin irin cutar da suka mata ba. Da daddare kuwa ɗakin su Abubakar suka tafi duka, Bilkisu, Usman Khadiyo da Umar riƙe da ƴarsa Abubakar kan janye maryam yayi suka tafi Ɗakin Umma. Hira sukayi ta sha kamar daga Sama saiga Ruky ta shigo har ɗakin, kowa ya juyo yana kallon ta. _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/10, 6:15 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 71-72 Umar ne ya ɗaure fuska ya ce "Kefa me ya fawo ki" Ta ce "Nazo ne ka mu tafi gida" Ya waro ido "Gidan wa" Ta ce "Naji labarin dama ance ka samo Bilkisu kuma da auren ta, to tunda tayi aurenta ba shikenan sai mu ci gaba da zama ba tunda dama baka sake ni ba" Ya ce "wa ya ce Miki zaki koma gida na, ƙarya kike ay, aurenki kuma sa ke kaina kije na Sake ki, kada na ƙara ganin kina bibiyata, Kinci darajan Ƙanwata Bilkisu amma badan haka ba... " ya yarfar hannunsa. Komawa tayi kamar zata tafi sai kuma ta dawo ta ce "Umar dan Allah kayi haƙuri" Usman ya ce "Wai kai ka kira yarinyar nan ne da baza ta bar nan ba" Umar ya ce "Saina balla ɗayan hannun ya kuma lalacewa tukun na" Usman ya miƙe tuni tabar gurin. Kwanan su biyu Aliyu yazo ya ɗauke su, Umar kan yayi wa Maisun hidima da yawa yayi mata siyayya kuma bai nuna alamun zai amshe ta bama. Saida suka biya suka gaida Zalimu mijin Ummi tukun dan tin da yayi hatsarin nan kasancewan ba asibiti aka kaishi ba, daga baya aka gane dama ya samu matsala a haƙarƙarinsa, kuma gurin yana damunsa sosai. Ummi ji tayi kamar kada ta rabu da ƴar tata amma ya zata yi dole suka rabu da Alƙawarin zasu dawo mata idan ta haihu. Daga nan suka ɗau hanya suka koma Kaduna saidai sunyi dare sosai dan ma Aliyun yana gudu sosai a mota. A gidan Maryam ta kwana saida Washe gari ta koma gida. Cikinta yakai wata takwas lokacin kuwa ansan da Maganan Abubakar da Maryam dan har an sa musu rana nan da wata biyar. Aliyu yana zaune ita kuwa tayi matashi da cinyarsa wayan sa ne yayi ƙara ta ɗauka ta miƙa masa dan bata son ya motsa dan taji daɗin kwanciyar. Ya duba yaga Mommy ce ya ɗaga da Sallama daga can ta ce "Ina Bilkisu ne ana ta kiranta bata ɗaga waya ba" Ya ce "Wayar tana ɗaki ne, ita gata a falo" Ta ce "To saidai haƙuri Mijin Umminku ne Zalimu ya rasu" Ya ce "Innalillahi wa Inna'ilaihir raju'un Allah ya jikansa da rahma" Mommy ta amsa "Amin, Daddynku ya ce Gobe zamuje ya kace kai" Ya ce "Mommy makarantan Maisun fa" Ta ce "Nima nayi tunanin haka to amma zata zauna da Maryam, zamu barta a gida. Ya ce "To Allah ya kaimu goben, amma Maryam nan zata zo ko" Ta ce "Eh" Sukayi Sallama suka kashe wayar ya kalli Bilkisu ya ce "Wai Mijin Ummi ne ya rasu" Ta tashi zaune ta ce "Allah sarki Ummi, Allah ya jiƙan Baba Zalimu" Ya ce "Amin" Washe gari tun Sassafe sukayi shirin su dan sai zasu dawo a ranan ne shi yasa ma ko kaya basu ɗauka ba, Bilkisu kan jikin t ne yayi sanyi duk bata jin ƙarfin jikinta ya kalleta ya ce "Yaya dai,? Ta ce "Ni Wallahi duk bana jin daɗin tafiyar nan Yaya dama a fasa ba yanzu ba" Ya ce "A'a taya za'a fasa kuma, gaisuwa ne idan munyi sai mu dawo" Ta kama hannunsa tasa a daidai zuciyar ta ta ce "Yaya taɓa ƙirjina kaji sai wani bugawa yake Wallahi kamar wani abu zai same ka" Ya ce "Kina min Addu'a ba abin da zai same ni Insha Allahu" Ta ce "Yaya dan Allah kada ka rabu dani duk wuya duk daɗi ka kasance dani" Rungumeta ya yayi ya sa kanta bisa kirjinsa ya ce "Wa ya ce miki zan rabuda ke, mai raba mu da ke sai mutuwa " Daidai lokacin suka ji horn alamun su Daddy sun zo, ya je ɗakin Maisun yaga tana barci ya mata kiss a kumatu sannan suka fito Maryam ta fito ta shiga ciki tana ɗaga musu hannu, Aliyu shine mai jan motar sai Bilkisu a gefen sa sai kuma Daddy da Mommy a bayan su. Nan fa suka ɗau hanya, basu ɓata lokaci ba suka isa saboda gudun da suka sha. Nan fa suka yi mata gaisuwa tare da mutanen gidan Aliyu da Daddy waje suka koma yayin da Mommy da Bilkisu kuma suke ciki tare da Umma dan ita ma tazo da Abba shine ya koma. Suna zaune saiga Mama Sauda ita ma tazo, duk tana rame zanin jikin ta maa koɗe yake. Bilkisu ta ce "Mama Ciwo kika yi ne" Ta ce "Bilkisu kenan ay dama ciwo nayi da yafi, zama rayuwan gidan da nake babu daɗi kwata-kwata ga Baban Umar ya ce gwara yayi aure da ya maida ni" Ta ce "To banda abin Baba ma tinda ba auren zaiyi ba ya maida ki mana" Ta ce "Nikan ma na haƙura idan na samu miji aure zanyi, saidai yanzu mazajen yanzun ne sai a hankali duk wanda zaizo saidai yazo da maganan iskanci" Tausayin taji ta ce "Kada ki damu Mama za kira Babam A waya muyi magana insha Allahu zaki koma" ƙarfe biyu daidai na rana suka ce zasu koma zuwa Isha ay sun isa, Suka yi wa Ummi Sallama sannan Bilkisu ta ce "Zata zo ta zauna mata idan ta haihu tunda anan zata yi takaba " Haka sukayi Sallama wa mutane suka ɗau hanya kuma. Nan fa ya fara gudun nasa Daddy ya ce "Ka daina gudun nan mana, ɗazu ma naso na maka magana kai idan baka yi gudu ba baka jin daɗi" Nan ya rage Daddy kuma ya ci gaba "Tafiyan nan mu muka sa kanmu ba wani ya samu ba dan me to zaka damu kanka sai kayi gudu" Haka sukayi ta tafiya a hankali har sukay dare a hanya, A pambegua suka yi sallah Isha sannan suka ci gaba da tafiya. Ji yayi motar tayi shiru ya juya yaga Mommy da Daddy duk suna barci ita ma Bilkisu tayi barci, ya ɗora hannunsa ɗaya akan cikin yaji yadda babyn yake ta motsi kamar zai faso cikin nata. Murmushi yayi ya kunna ƙira'ar Karatun Al-qur'ani Mai girma cikin suratu Yusuf an yi yana bi a hankali, sautin kaɗan yasa shi yasa basu tashi ba, ya kuma ƙara gudu a motar hannunsa ɗaya nakan cikin Bilkisu yana jin yadda Babyn ke motsi. Bai ankara ba yaga an hasko shi alamun motar ta biyo ta hannun da yake, yaso jan burki dan kaucewa motar gaban sa, ashe bayansa kuma akwai wata motar nan fa motar bayan nasa ta bugi motarsa ya da murɗa sitiyari yayi cikin daji tuni motar tayi daji ta bugi wani ƙaton dutse. Tun lokacin da abin ya fara Mommy, Daddy da Bilkisu suka farka sukayi ta salati, saidai lokacin da Motar ta bugi dutsen Daddy ne ya ci gaba da Addu'a, kafin kace me sauran motacin sun tsaya suka kawo agaji, da kyar Daddy ya samu ya fito sai ya zaga gun Bilkisu ya kamata ya fito da ita, ya kwantar da ita, sauran jama'an kuwa suka fito da Aliyu da Mommy da ko motsi basa yi. Kafin ka ce motar Ambulance tazo nan da nan aka kwashe su Daddy ma ya shiga aka ƙarasa asibiti da su, Tin a cikin motar aka fara da Bilkisu kasancewan ta me ciki, sannan suka fara da Mommy da Aliyu, a cikin Motar Mommy ta farfaɗo, Aliyu da Bilkisu kuwa shiru, emergency aka yi da su duka, Mommy kan taƙi yadda su mata komai burin ta taga Bilkisu da Aliyu sun farka, haka suka gyaleta sai can dare ne Bilkisu ta farka ita ɗin ma tashi tayi tayi tana cewa Ina mijinta. Aka hana ta shiga gurin sa nan fa ta fara kuka Mommy na lallashi. Aliyu yaji jiki da yawa dan ma likitan kwararrune kusan asuba ya farfaɗo. Wani likita ne ya fito ya ce "Alhamdulillah mun samu nasara ya farfaɗo zaku iya ganin sa, sannan ku fito kuma kuna buƙatan a duba ku". Rige-rigen shiga suka yi suna shiga ya miƙo wa Bilkisu hannu yazo ta kama ya kalli Ummi ya ce "Ummi ki kula min da takwaranki dan Allah, bana son ta shiga cikin damuwa bayan babu ni" Bilkisu ta ce "Me haka ka daina min wannan magana dan Allah" Mommy ta ce "Zaka samu lafiya in Allah ya yarda" Ya kauda kansa ya ce "Daddy ka yafe min, Mommy ki yafen min, Bilkisu kema ki yafe min" Daddy ya ce "Mun yafe maka, amma ya isa surutu n" Ya kauda kai yayi kalmar shahada sai kuma rai yayi halin sa. Innalillahi wa Inna'ilaihir raju'un " likitan dake bayansu ya faɗa tare da matsowa ya rufe masa fuska da mayafin dake jikinsa.. 😭😭😭😭😭 So Sad😭😭😭😭😭 _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/11, 4:25 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 73-74 Daddy baya ya juya ya kalli ƙofa ji yayi jikinsa ya ɗau zafi, Mommy kuwa tuni ta fara kuka tana salati. Bilkisu kan shiru tayi sai ji tayi numfashinta na neman ɗaukewa ƙafafuwanta sun kasa ɗaukanta, koda Daddy ya juyo yaga halin da take ciki yazo ya kama kafaɗanta ya girgiza kai a hankali ya ce "Addu'a zakiyi" Bai ankara ba ta faɗi ƙasa ko motsi bata yi. Da sauri Mommy tayi kanta cikin kuka tana cewa kada kumin biyu dan Allah ki tashi. Zuwa akayi aka ɗauketa aka yi da ita wani ɗakin. Shiko Masallaci ya wuce don yaji ana kiran Sallah asuba amma saida yasa aka rufe ɗakin. Bayan ya dawo ne ya leƙa ɗakin da Bilkisu take ya samu Mommy ta idar da Sallah tana Addu'a tana kuka. Ita ma ta farfaɗo tana yin Sallah saidai ko alamar hawaye babu a fuskar ta. Tausayin su yaji ya koma ya ringa kiran ƴan uwa da abokan Arziki yana faɗa musu. Tuni aka zo aka ɗauki gawa likitocin sukayi sukayi akan Mommy da Bilkisu su zauna amma suka ƙi. Gidan Daddy aka wuce da gawar Su Mommy ma can aka wuce da su. Daddy ya tura aje gidan Aliyu a ɗauko Maryam da Maisun. Tana zaune kan sallaya tana tunanin abin da ya hana su dawowa jiya taji ana buga ƙofa ta tashi cikin tsoro saida ta leƙa ta ƴar kafa taga Driver ne ta buɗe ya kalleta ya ce "Alhaji ya ce kuzo na kaiku gida keda Maisun" Ta ce "Sun dawo ne" Ya ce "Eh " Ta ce "To barin shirya Maisun sai a ajiyeta a makaranta " Ya ce "Hajiya kizo kawai mu tafi ki ɗauko ta a haka muje" Ta ce "Lafiya kuwa" Ya ce "Lafiya lau kizo muje Hajiya " Ta koma ciki ta ɗauko Maisun ta fito jikin mota taga yana kuka ta ce"Na tambayeka lafiya kace lafiya me yasa baza ka faɗa min ba, me ya faru da Daddy na" Ya fito ya buɗe motar ta shiga da Maisun a hannun ta ya ja mota suka tafi. Suna zuwa taga ƙofar gidan cike da jama'a wasu suna ta alola. Makara ta hango ana shiga da ita, wannan ya tabbatar mata mutuwa aka mata, ta sauƙe Maisun ta taka da ƙafarta ta fito tana ratsawa cikin mutane sai kunnen ta ya jiyo mata wani yana cewa "Allah sarki Aliyu mutumin kirki ne, Allah ya jiƙan shi" Da gudu ta ƙarasa shiga ciki tana kuka tana zuwa falon ta tarar har an shirya shi an saka shi a cikin Makaran da aka shigo da shi. Faɗawa tayi jikin gawar tana kuka Daddy ya riƙota ya tiƙe hannun Maisun da take bayanta yayi da ita ciki inda su Mommy suke. Tana zuwa ta rungume su tana kuka, saidai Bilkisu kan ba magana, ko kwakkwaran motsi bata yi. Mommy ne ta jamota jikinta ita ma Maryam tana ta gefenta. Ana fita dashi saida maza suka gama wucewa Mommy taja Bilkisu suka je suka masa Sallah Maza suka ɗauke shi suka yi da shi gidan sa na gaskiya. Koda suka dawo Bilkisu kan shiru ko an gaisheta bata amsawa Maryam da Mommy kan ita suka fi tausayawa, sun san su kansu basu ji raɗaɗin da take ji a zuciyar ta. Azhar kuwa ƴan Bauchi suka iso harda Umar da Mama Sauda. Bayan sun gaisa sunci Abinci. Sai Mommy take faɗa musu halin da Bilkisu take ciki gashi ko abinci bata iya haɗiya Abubakar ya miƙe yayi ɗakin maryam da yake anan akace masa take ya buɗe ƙofar ya ganta ta jingina da gado idonta na kallon sama tana jin motsinsa ta ɗago ta kalleshi sai ta kawar da kanta gefe. Ya durƙusa ya kama hannunta ya ce "Kina da ilimi kina da hankali da tunani, ya kamata ace kin bar ma Allah komai kin rungume ƙaddara, mijinki lokacin sa ne yayi, munsani kina son sa shima yana sonki amma ki sani son da kuke yiwa junan ku bashi zai hana Allah ya barshi ba, ki rungumi ƙaddara kina yiwa mijinki Addu'a, dan yanzu abin da yake buƙata kenan a gurin ki, ke baki son ya dinga Alfahari da kene, nasan akwai raɗaɗi amma ba yadda zamuyi haka zamu rungumi ƙaddara mu masa Addu'a" Wasu hawaye ne masu ɗumi suka fito mata yasa hannu ya share mata ya ce "Barin ce Maryam ta haɗa miki tea ko" Ta girgiza kai alamun A'a Zaiyi magana sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi ta ɗora kanta a jikinsa ta ci gaba da rera kukanta cikin kukan kuwa tana cewa "Allah ya jiƙan ka Ya Aliyu, nayi rashin miji na gari Allah yasa halinka na gari ya bika" Hannu yasa a kanta yana jin kukan nata zuciyar sa tana masa wani iri. Saida ta kusan yin awa tana kuka sannan ya fara rarrashinta yana bata haƙuri da kyar ta iya sayawa da kukan nata sannan ta janye jikinta ta koma kan kafet ta kwanta hawaye na ci gaba da zuba mata. Tashi Yayi ya yi magana wa Maryam ta haɗo tea sannan ya kai mata, ya ɗagota yana bata a hankali tana sha, saidai ko rabi bata yi ba ta miƙe ta shiga bayi ta ringa amayo shi saida ta amar da shi tas ta dawo ta sa wani sabon kukan ta ce "Bana son cin komai Yaya ka kyale dan Allah baka san yadda nake ji ba" Ya ajiye kofin tea ɗin yana mata nasiha saidai tana jinsa ne kawai amma bata ɗaukan komai. Haka sukayi ta fama da ita bata cin komai ko taci ma sai ta amayar da shi, sai ran da akayi uku ne abincin ya fara zama a cikinta, ta rame sosai sai ɗan talin cikin da yake da girma, kasancewar ita ɗin mai Addu'a ce kuma ƴan uwanta suna mata yasa ta ɗan fara samun sauƙi a zuciyarta har take ɗan magana idan taji ana yi ko ansata a ciki. Ranan ukun kuwa duka suka tafi dama su Abba tun a ranan suka koma, lokacin ne kuma jama'a suka watse sai masu zuwa gaisuwa. Mommy kuwa ita take yawan kwantar mata da hankali a kullun haka Maryam ma, yanzu kan hankalinta ya kwanta saidai tana tunanin sa kaɗan-kaɗan lokaci-lokaci Abubakar yana kiranta suna gaisawa ya kuma mata nasiha, haka Umminta ma. Rayuwa kenan Yau Aliyu ya cika kwana arba'in an masa Addu'a sosai yau kuma Bilkisu ta tashi da naƙuda. Mommy ce ta kaita asibiti. Tasha wahala sosai amma duk wahalan da take bai hana ta yiwa mijinta Addu'a ba, taba cikin wahala amma bakin ta na motsi tana roƙa masa rahman ubangiji. Awanta 6 tana abu ɗaya sai kusan Magrib ta haifi ɗanta namiji. Suna gyara shi suka miƙo mata ayko tana ganin fuskarsa sai taga fuskar Aliyu a fuskar yaron hawaye ta ringa yi, Mommy ce ta shigo tana hamdala ko da taga tana kuka ta ce "Lafiya " Ta miƙa mata shu ta ce "Mommy kalli fuskansa ki gani" Mommy tana amsan sa ta ce "Wannan ay ba abin da ya bar Aliyu, lokacin da na haife shi inda kika san wannan " Hawaye ta ci gaba da yi, Mommy ta dafa kafadar ta ta ce "Ki ci gaba da masa Addu'a kedai Allah ya baki ladan takabarki" _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/11, 9:04 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 75-76 "Amin" ta ce ta ci gaba da share hawayen ta Basu wani jima a asibitin ba aka sallame su suka dawo gida. Tuni gida ya cika da ƴan barka kowa ya ganshi sai ya ce wannan ay Aliyu ne ya dawo, dan kamannin su ɗaya da uban sa. Kwana uku da haihuwan Umma da yaranta suka zo Mommy ta ce "Yawwa tunda ga iyayensa ma sai kuzo kuyi masa huɗuba, nace Daddyn ku yayi masa ya ce saidai ku kuzo kuyi" Usman ya ce "Wannan Ay Babansa yayo kawai a saka masa sunan Babansa" Umma ta ce "A'a uwarsa da taji wahalan haihuwan ita zata zaɓa masa suna ku sai kuyi masa huɗuba" Bilkisu ta ce "Nima Aliyun nake so a saka masa" Abubakar ne ya masa huɗuba da suna ALIYU bayan ya gama ya miƙa mata ya ce "Allah ya raya Aliyu" Tayi murmushi ta ce "Haidar za'ana kiransa" Ranan Suna kuwa sai ga Umar yazo da Akwatuna biyu ɗaya cike da kayan Haidar ɗayan kuma Kayan uwar haidar sai kuma na Yayar Haidar Wato Maisun da ya saka mata riguna masu tsada guda huɗu. Ana kawo kayan aka buɗe ana sam barka da kayan ita ko Bilkisu ta ɗaure fuska Umma ta kalle ta ta ce "Menene wai". Ta ce "Nikan gaskiya a mayar masa da kayan sa, ay ba'a ce masa tsirara zamu zauna ba" Umma ta ce "Ba inda za'a mayar dole ki amsa tunda ya baki" Ta ce "Na yadda na ƴarsa za'a amsa, amma nawa da na Haidar kan mayar masa zamuyi" Umma ce tayi ta mata wani kallo da ta fahimci kallon da take mata ne ta ce "Umma kinsan waye Umar Wallahi wata rana zai iya mana gori, ni kuma yanzu bazan ɗau wulaƙancinsa gwara a mayar kawai" Umma ta ce "Wai yarinyar nan yaushe kika fara rashin kunya ne" Shiru Bilkisu tayi Umma kuma ta ringa mata faɗa ƙarshe kuma ta ce "Zai shigo nan ganin Haidar saura ki masa wani rashin kunyan kuma". Shiru ta kuma yi bata ce komai. Can kuwa saiga Umar ya shigo Umma ce ta miƙa masa Haidar sannan ta miƙe ta fita, ya tsura wa yaron ido sai kuma ya kalle ta yayi murmushi ya ce "Kamar babansa ne yayi kaki" Bata ce masa komai ba shima shirun yayi yana rungume da yaron can kuma ya fara mutsu-mutsu kamar zaiyi kuka ta matso ta ce "Ni bani ɗana zan bashi Nono" Ya miƙa mata ya ce "To ay nima ɗana ne" Baki ta turo masa ya ce "To kafin ki koreni barin tafi" Ya miƙe zai fita kenan ta ce "Yawwa barin faɗa maka wani abu, ni da ɗana baza mu taɓa zama tsirara ba dan haka daga yau bana son ka sake aiko mana da wani abu naka bama so, kada kaga dan ubansa ya mutu kayi tunanin zamuyi maraici" Dawowa yayi ya zauna ya ce "Banga laifinki ba dan kin faɗi haka saboda na cancanci haka daga gurinki, amma ki sani ko Aliyu yana raye zanyi wannan, balle yanzu da baya raye, kuma ay ina ganin shima Haidar ɗin ma ɗana ne" Ta ce "Ba abin da ya haɗa ka da Haidar, kada ka sake haɗa kanka da shi" Kuka Haidar ya fara yi Umar ya kalle shi ya ce "To ki bashi Nono mana" Harara ta galla masa ta ce "To kuma a gabanka zan bashi Nonon ko Iskancin da kamin da ne shine zaka min yanzu" Tuni ya fita bai sake magana ba. Ita kuma ta fara bashi Nonon. Washe gari Abubakar da Umar suka tafi Usman kan tunda ya haɗu da Husaina ya ce sai Umma zata tafi su tafi tare. Tunda yake da ƴan matan sa bai taɓa samun wacce ta kwanta masa ba irin Husaina, yarinyar akwai nutsuwa da kamun kai wannan yasa tunda yazo garin ya liƙe mata. Saida suka sake kwana biyu da Umma sannan suma suka tafi suka bar mai jego da ɗanta da kuma kyautukan su. Kula sosai Mommy take basu ita kanta Bilkisu har ƴar kiba ta fara yi Haidar kuwa zuwa kwana Arba'in yayi girma da shi ya fara gane uwarsa. Watan Haidar uku aka fara Shirye-Shiryen bikin Abubakar da Maryam yanzu hankalinta ya kwanta sosai har ƙiba tayi ga Haidar ma da yayi girma abinsa sai wayo. Umar ne yanzu ke yawan damunta da waya yana ce mata yaushe zata dawo, ita ko banda wulaƙanci ba abin da take masa, duk da ita ɗin ma tana son ta dawo amma saboda tsana da take masa ta kwammace ta zauna, shi kuma marar zuciya yaƙi ya daina damun ta. Yauma ta gaji da aiki sosai tazo ta kwanta Haidar yayi barci wayanta tayi ƙara ta duba taga number Usman ne murmushi tayi ta ɗaga, sai jin muryan Umar tayi, tsaki tayi ta ce "Wai kai wani irin marar zuciya ne Umar" Ya ce "Ohh yanzu ba ko ɗan yayan ma tunda kika haihu kika canja " Ta ce "Ay baka cancanci na kira ka yaya ba Yaya ada kenan" Ya ce " Nima bana son Yayan gwara ma Umar ɗin ya fi min daɗi dan idan kika kira sai naji kinfi kowa iya kira" Ta ce "Ni barci nake ji ka kyale ni in kwanta, Umar kana damu na da yawa me yasa baka da zuciya ne" Murmushi yayi kamar tana gurin ya ce "Ina da zuciya amma bazan taɓa yin zuciya dake ba ƙanwata, ko kashe ni kika yi na dawo bazan taɓa zuciya da ke ba, duk abin da kika min kin isa kiyi ne ke ɗin ta daban ce a zuciyata, fatana ki amince ki dawo Bauchi ina ganin fuskar ki kullun koda zagina zaki nayi, balle kuma baki taɓa zagina ba" Ta ce "Ayko idan baka kyale ni ba zan iya zaginka" Ya ce "Wallahi ko Al-qur'ani zan iya dafawa baza ki iya zagina ba, wannan ba halin ki bane, kuma koda kin zage ni ba abin da zai canja" Mtswwww tsaki taja yasan zata kashe yasa ya ce "Mu kwana lafiya Gimbiya " Wayan ta jefar gefe tayi Addu'a ta shagawa yaran sannan ta kwanta. Rana bata ƙarya saidai uwar ɗiya taji kunya, Yaudai aka ɗaura auren Abubakar Ibrahim da Maryam Yusuf, Bilkisu kan ta kasance kamar ita ce Amaryar Haidar ma Ummi ce ta riƙe shi, da yake ita ma tazo akan idan za'a kai Amarya sai su tafi can tare, ita ma taci kwalliyarta da yake dama can Yarinya ce yasa yarintar ta ta sake fitowa a fili, idan ka ganta zaka rantse da Allah ba ita ta haifi Bilkisu ba sai dai ace ita ce Uwar Haidar da yake ita take riƙonsa sai kuma akayi sa'a yaron bai ƙita ba, duk da yana ɗan taɓa ƙyiwar. Bayan ɗaurin Auren walima aka yi aka yi wa'azi sosai akan zaman aure da kuma tarbiyyan yara. Washe gari kuwa da Safe aka tafi kai Amarya su Umar su suka kawo motocin Maisun kuwa tana ganinsa ta liƙe masa Bilkisu ta kwashi kayansu da yawa saboda anyi hutun makaranta dan tana sa ran zata daɗe a can kafin ta dawo amma idan taga Umar ya takura mata dawowa zata yi ta kyale shi. Umar kan yana ganin kayan da ya ɗauka yaji daɗi a ransa. Matsawa yayi ta gefen ta ya ce "Zo ga mota ko Gimbiyar " Hararansa tayi tayi motar da Ummi ta shiga dan Haidar na hannunta, Maisun kuma ta zauna gun Uban ta. Suna Isa ana kiran Sallah dan haka kowa ya fara shirin yin Sallah. Bayan anyi Sallah aka fara gaishe-gaishe, Ummi kan da kanta taje gaida Abba koda ya kalle ta, sai ya kalli Umma ya ce "Ina ga fa bayan wannan bikin za'ayi nawa bikin" Ta ce "Biki kuma na me" Ya ce "Aure zanyi mana" Umma ta ɗaure fuska ta ce "Wani aure Alhaji kana nan tsofai-tsofai da kai gashi ka fara tara jikoki" Ya kalli Ummi ya ce "Haba Aisha ina kallon wannan ƴar fulanin in barta, ay kawai ki yadda asha biki" Ummi ta sunkuyar da kai tana murmushi ta ce "Kaji Alhaji sai kace wasu yara wai za'a sha biki"... _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/12, 8:21 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 77-78 Umma ta ce "Ahh idan ay ita ce ko baka ce ba zan aura maka ita ni zan biya Sadakin ma" Shirin zuwa Diner aka fara da yake Bilkisu a ɗakinta na da ta sauƙa tayi kwalliya sosai ta shirya tsaf tayi kyau matuƙa wani tsadadden leshi ta saka sannan ta ɗauki Haidar ta fara bashi nono tuni barci ya ɗauke shi, ɗakin Umma taje ta kwantar dashi a gefen Maisun sai jin Sallamar Umar tayi a ɗakin gaishe su yayi ita kuma ta fita ta koma ɗakinta, ko da ta fito binta yayi har ɗakin ya sameta a zaune a bakin gado shi kuma ya zauna a kujeran dake ɗakin ya ce "Da kika gudu ma na biyo ki" Tsaki taja ta tashi zata fita ya riƙe hannunta ya ce "Ina zaki kuma" Hararan sa tayi ta ce "In da ka aike ni dalla sake ni nikan" Ya kuma damƙe hannun ya ce "Tunda kin shirya muje ga mota can mu tafi Diner ɗin ko" Ta ce "Akwai wanda zai ɗauke ni" Ya ce "Wa kike da shi bayan ni" Ta ce "Masoya da yawa" "Duk a bayana suke Wallahi basu kaini sonki ba" Ta ce "Allah zan maka ihun kwarto, mema ya kawoka cikin ɗakina, sai in maka ihu ince kana son ka cire min kaya" Ya ce "Wannan ba halin ki bane, da zaki hakan ma da ns gode miki kinga sai ayi na wancan karan" Fizge hannunta taje yi suka fara kokawa ta samu hannun sa ta gantsara masa cizo har saida ta cire fatar da sauri ya sake hannun yana yarfar da hannu ta fito waje ya biyo ta ta samu ana ta tafiya motan Usman ta hango tana zuwa taga Husaina a gabab mota ta ce, "Malama yaushe kika zo ban sani ba" Ta ce"Tare aka kawo amarya dani" Ta ce "Shine ban sani ba" Ta kalli Usman t ce "Shi ay ya sani" Ta ce "Saura naku ay" Sai ji tayi daga bayanta ance "Namu dai, ƙarya yake yana ƙanina ya riga mu aure" Juyowa tayi ta ɗaga hannu kamar zata mare sai kuma ta sauƙe hannun ya ce "Ya kika fasa " Juyawa ta kuma yi da niyyar shiga motar sai taga wayam sub tafi ta juya taga ba wata mota sai ta Umar tayi bakin titi yana kiran ta. Tana tsayawa a bakin mota wani ya tsaya ya zuge glass ɗin mota ya ce "Hajiya ina zaki je ne haka" Ba wani tunani ta buɗe motar ta shiga dan dai kada Umar yazo ya same ta , sannan ta faɗa masa inda zata je yaja mota suka tafi Umar kuwa yabi motar sa kallo, ya ɗauko tasa motar yabi bayan su saida ya ƙara gudu sannan ya iso su suka isa gurin tare. Ya kalleta ya ce "Zamu iya shiga duk da ba'a gayyace ni ba" Ta ce "Zaka iya" Ya fito suka shiga tare Umar ma yabi bayan su, duk wani abin da take yi harda gayya take yin sa kuma a wannan lokacin Umar ya shaƙa yaji haushin ta dan harda rawa ta fito tayi da wannan mutumin. Suna rawan ma yana son ya rike hannunta amma ya lura ita taƙi yadda Saida aka tashi kuwa Sun fita Umar yabi bayan su yaje yaja hannunta ya kaita jikin motarsa ya haɗa bayanta da motar ya ce "Bilkisu Ina son a maida auren dan Allah ki daina min wannan hukuncin yamin tsauri da yawa kinji yadda nake ji kuwa cikin zuciya ta da kikai rawa da wannan mutumin, Ada duk abin da kika min bana jin haushi amma yanzu kin samu abin da zaki tarwatsa min zuciya dashi, dan Allah kiyi haƙuri haka ki bani dama na sake auren ki zaki zama ƴar gata " Ta ce "Bana son ka Umar na tsane bazan kuma sake auren ka a karo na na biyu ba, yanzu kai ba dai-dai kake dani ba, dan haka Ruky ita ce dai-dai da kai, amma ni bazan taɓa auren ka ba, don bana son ka" Ji yay daga bayan sa ance to kaj bata sonka bani ita mu tafi. Wannan mutumin ne ya matso gurin, Umar ya ce "Dan ta ce bata sona ba Lalle bane in baka ita tare zamu tafi saboda ƙanwata ce " Ta ce "Ba abin da ya haɗa ni da kai malam kyale ni na tafi gun habibina" Ya ce "Ba inda zaki je tare zamuje gida" Ganin hawaye tayi a idon yana gangarowa ta tausaya masa amma tasa hannu a kirjinsa ta ture shi sukayi gun motar mutumin ya buɗe mata mota ta shiga shima ya shiga, basu tafi ba sai suka kunna wutar motar ya ɗauko ice cream ta amsa tana sha shima ya fara Umar yana hangosu yana jin zuciyar sa tana masa wani iri, koda ta juya taga alaman yana hangosu sai ta kashe wuta, suka ci gaba da sha a hakan can kuma Umar yaga sun tada motar suntafi ya bisu a baya, saidai maimakon suyi hanyar gida sai kuma yaga sun yi wata hanya. Ce mata yayi muje gidana nima tunda na raka ki ko, Ta ce "A'a ni gida zamuje " Nan ko ya ce "Dole ta bishi suka " Ta ce "To zata fita shine fa suka dara kokawa dashi, koda taga motar Umar da gudu sai ta sauƙe glass ɗin tana ɗaga masa hannu shi kuma yana ganin haka ya ƙara wuta a motar ya iso ra gefen ta ya ɗago mata hannu ta ce "Dan Allah ka taimake ni " Ganin haka yasa ɗan iskan ya ɗaga glass ɗin har yana matse mata hannu ya kulle ko ina. Sannan ya ƙara gudu a motar sa, Umar ma gudu ya ƙara a motar ya bisu, wani get suka zo suka tsaya dan a buɗe get ana buɗewa motar ta shige Umar ma ya samu nasaran shiga, motar tana tsayawa Umar ya tsaida tasa ya fito yayi gun motar Bilkisu tana fitowa tayi gun Umar ta ɓoye a bayansa shi kuma yaja hannunta yana son yayi da ita cikin mota, sai gani yayi mutumin ya fito da bindiga a hannunsa ya saita shi ya ce "Ko shiga cikin gidana ko yanzun nan na harbe shi kuma dole ki shiga dan yau sai na ɗanɗani zumarki" Ta fara jan hannun ta da ya rike a hankali Umar ya ce "Shiga zaki yi" Ta ɗaga masa kai Ya ce "Ba inda zaki je" Ta girgiza kai. Ya ce "ki tsaya anan kada ki matsa ko ina" Komawa mota yayi kamar zai tafi ya barta a gurin ya ɗauko wata powder da ake watsawa dabbobi dan su hankalinsu ya ɓace yayi gaban da mota yana zuwa ya watsa masa ya dawo gun Bilkisu ta shige mota suka bar gidan. Suna zuwa gida ya tsaya tana son masa magana amma sam yaƙi bata fuska, zata fita ya ce "Kince bakya sona ko, nagode kuma insha Allahu bazan ƙara miki magana akan son da nake miki ba, nima na haƙura amma ki sani idan zuciya ta ta fashe kece sanadi" Kallonsa take yi ba tare da ta ce komai ba, ya ce "Jeki kawai, kuma idan hukuncin da kike min bai isa ba a shirye nake da na ci gaba da ɗauka" A hankali ta fita a motar saida yaga shigarta gida sannan ya bar ƙofar gidan. Tana shiga ta samu Ummi da Umma suna ta hira, ɗakinta tayi tayi alola sannan tasa kayan barcin ta taje ta ɗauko Haidar ta yi musu Addu'a suka kwanta. A haka dai ƴan biki suka watse Umar kuwa bai sake kiranta koda a waya ba, rashin kiran nata ya dame ta. Gashi bata da daman tambayar kowa, Maisun ce take tambayarta ina Daddynta bata ganin sa kwana biyu, sai ta ce bata san inda yake ba. Sati guda kenan ba Umar ba labarin sa dan haka ta shirya ita da Maisun da Haidar ba wanda ya sani ta tafi gidan Baba tana zuwa Baba ta samu ta gaishe shi ta amsa ta kalli gidan ta ce "Baba yaushe Mama zata dawo ne" Ya ce "Ba rana, bazan dawo da ita ba" Ta ce "Kai Baba kayi haƙuri dan Allah ka dawo da ita mana gidan ba daɗi ba mata Wallahi " Ta ce "Bilkisu da bakin ki kike cewa haka" Ta ce "Eh Baba Mama tayi nadama kuma yanzu zata bi umurnin ka" Ya ce "To shikenan zan duba, munje anyi maganan Ummin ki da Abbanki ba jibi za'a ɗaura auren su" Ta ce "Nikan ban sani ba ma" Maisun ce ta ce "Baba Ina Daddy na ne" Ya ce "Kyale Daddyn ki yana can bashi da lafiya nayi-nayi da shi muje asibiti amma taƙi zuwa sai dirkawa kansa Alluran dabbobi yake" Bilkisu ta ce "To kuma Baba ba'a hana shi ba kada ta masa illa fa" Ya ce "Taurin kai gare shi, kuma baza ta masa illa ba" Ta ce "Barin je na duba shi" Suka tashi suka bar Haidai a hannunsa ta tura ƙofar ta jita a buɗe ta shiga ciki ta ganshi a kwance a kan gado ta je ta zauna a bakin gadon Maisun kuma ta hau gadon kusan kansa ta ce "Daddy meke damunka ne" Ya ce "Ba komai" Bilkisu ta ce "Me yasa kaƙi zuwa asibiti" Ya ce "Taya zanje asibiti bayan kece maganin nawa" _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [6/12, 5:45 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐BILKISU Labari da rubutawa MAIMUNA ISAH MUSA (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- INA DANGINA IZZAR MULKI JININA YAK'I A SOYAYYA AMANATA FAHIMTA FUSKA MAIMUNATU MAHAUKACINA and now BILKISU *Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679* _Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Last Page 79-80 Ta ce "Hmm ni kuma to gani ay" Ya ce "Ba wai ganin ki kawai nake buƙata Idan na ganki ban bakya sona fa, kinfi son wani a kaina" Ta girgiza kai ta ce "Nikan bana son kowa, bani da wani sama da kai, yanzu na gane bani da wanda ya fika" Ya tashi a hankali Ta ce "Kwanta kawai basai ka tashi ba, barin gyara maka ɗakin kalli yadda ɗakin ya dawo" nan fa ta fara gyara masa ɗakin yana kallonta saida ta gama tazo ta haɗa masa ruwan mai zafi a bayi ya shiga ya ya fara wanka ita kuma ta gyara gadon ta cire zanin gadon ta saka masa wani, yana fitowa ta fita taje cikin falon ta haɗa masa tea mai kauri ta kawo masa, duba tayi taga akwai kayan abinci, nan fa ta fara shirin girki, cikin lokaci kaɗan ta gama. A kula ta sa ta kai masa ta zuba masa plate ya amsa ya kalli abinci ya kalleta yayi murmushi ya ce "Nayi missing ɗin abincinki gaskiya " Ta ce "Gashi yanzu ay sai kaci" Ya ce "Tare zamu ci amma" Cokali tasa suka fara ci tare har Maisun ma. Sai yamma tabar gidan ta koma gida da daddare kuwa suka yi waya sosai ita kanta tasan tayi sake da yayi zuciya da kuma waye zai maye mata gurbin Aliyu, tasan duk duniya Umar ne zai maye mata gurbin sa, zai zame mata mijin marainiyya. Bayan kwana biyu aka ɗaura auren Abba da Ummi Baba ma ya maida Mama Sauda ɗakinta tayi nadama sosai yanzu biyayya take masa sau da ƙafa, bayan nan ne kuma aka fara maganan Auren Bilkisu da Umar, sai aka haɗa da Usman da Husaina, Mommy ce tace "Bilkisu tazo kaduna dan ta gyara ta" Umma kuwa tasa ta yaye Haidar da yake yakai shekara ɗaya kuma ya saba da su sosai, ta ce baza ta tafi da su ba daga baya a kai mata su. Tuni Umar ya sama wa Maisun Makaranta taci gaba da zuwa. Kaduna taje Mommy ta mata gyara na musammam ta ƙara komawa yarinya ɗanya shataf. Ana saura kwana biyu ne biki suka zo da Mommy. Ranan tana zuwa kuwa ba ɓata lokaci aka ɗaura auren Bilkisu da Umar, washe gari kuma aka ɗaura auren Usman da Husaina. Anyi shagarin biki sosai inda Amare da angwaye suka tare a ɗakunan su. Ha biki ya watse kowa yana sam barka. Maryam ne dai na aci moriyar bikin da ita don tana da tsohon ciki da ƙyar take tafiya saidai tana zaune ne. Bayan bikin ne da kwana huɗu ta haifi ɗanta namiji, Ranan Suna kuwa yaci sunan Abba ana kiransa da Ajman. BAYAN SHEKARA BAKWAI Yaran Bilkisu Shida Maisun ta farko da take shekara goma sha ɗaya sai Haidar da yake sha takwas sai Ibrahim da ake ce masa Khalil shekaran sa shida Sai Halimatu mai sunan Ummi d ake kiranta Ummita ita shekaranta huɗu sai kuma ƴan biyunta Mata shekaransu biyu Aisha da Suwaiba shekaransu Biyu sai ƙaraminsu da take goyo wato Jafar. Abubakar yaransa huɗu Ibrahim sai Yusuf sai jafar sai ƙaraminsu Aliyu, shikan baida mace ko ɗaya kuma yana son ya samu saidai nan gaba. Usman shima yaransa biyar na farkon Aisha da Halimatu ƴan biyu ne sai kuma Ibrahim sai kuma Maimunatu da Aliyu suma ƴan biyu ne. Sai Khadiyo ita kuma tana da yara biyu yaranta biyu Suwaiba sai kuma Halimatu. Family ne ya haɗu ko yaushe cikin farin ciki suke da ƙaunar juna. Bilkisu ta zama likita Umar ya buɗe mata asibiti inda shi kuma ya buɗe asibitin dabbobi kusa da nata asibitin. Ya tashi kenan da yamma yabar likitocin dabbobi a ciki ya shiga asibitin Bilkisu office ɗinta ya shiga kai tsaye da Jafar a hannunsa tana ganinsa ta ce "Haba Abeey ya zaka ɗauko min shi ban gama ba" Ya ce "Yana ta wahalar da Ummi da yawa shi yasa na taho da shi nasan kema kin gama ko sai muje gida" Wata Nurse ce ta shigo ta gaisheta ta ce "Madam wata ce me HIV tana jiranki tun tuni " Ta ce "Kiyi mata abin da ya dace kinga Mai gidana yazo sai gobe kuma" Ya ce "Kije ki duba ta mana daga nan sai mu tafi ko" Ta ce "To barin shirya daga nan na tafi ko" Ta kalli Nurse ɗin ta ce "Kice mata ta ɗan jirani ina zuwa" Ta fita ita ko ta Amshi Jafar ta fara bashi Nono saida yasha ya ƙoshi sannan ta miƙa masa ta shirya sannan suka fito, gaba tayi tabar Umar a baya tana zuwa gurin taga Ruky da hannu ɗaya, ɗayan hannun an yake shi, kallon mamaki take mata ita ko Ruky ta ce "Bilkisu me kika zo yi asibitin nan, dan Allah kije ki kira min wannan likitan tazo ta duba ni ta bani shawarwari " Nurse ɗin ta ce"Ay ita ce Likitan " Ruky ta fara kuka Bilkisu ta ce "Tsaya yi shiru muje in duba ki" Umar ne ya ƙaraso gurin ya kalle ta ita ma kallon sa tayi ta ce "Umar " Ya sake kallon ta ya ce "Sannunki" Kuka ta kuma fashewa dashi ya juyo ya ce "Kukan me kike yi" Ta ce "Umar bani da kowa ka taimake ni Mamata Tayi mutuwar wulaƙanci a ƙarƙashin gada ba wanda ya iya binneta sai ruwa ne ya tafi da ita, kuma HIV ne ya kashe ta, abin baƙin ciki ma wanda ya saka mata shi ya saka min" Ya ce "To yanzu me kike so in miki" Ta ce "Ka maida aurena da kai" Kallon banza ya mata ya kuma kallon Bilkisu ya ce "Baby bata shirya ki duba ta ba muje gida kawai" Bilkisu ta ce "Ki kalle ki fa toma kina da ciwo muna da lafiya shine zamu aure ki, Allah ya kiyaye baki ma yi nadama ba, idan zaki zo muje in duba ki kizo idan baza ku zo ba kuma ina da Abin yi, mijina yana jira na" Ta taka a hankali tabi bayan Bilkisu suka shiga ta mata ƴan gwaje-gwaje ta fito ta rubuta mata magunguna sannan ta bata shawarwari, suka fito, Ruky ta kalli Umar ta ce "To dan Allah ko Sadakan ɗari biyar ne ka ɗan bani" Bilkisu ta ciro kuɗi dubu biyar ta miƙa masa suka tafi Ruky sai kallon su take tana cije leɓe. Da hannunta ɗaya. Da daddare ko duk yaran suna nan Maisun tana koyawa Ummita Home work Haidar kuma yana koyawa Khalil, gefe kuma ƴan biyu ne suke da damun Bilkisu da Umar Jafar kuma yana ta barcin sa. Can da aka gama Home work ɗin Ummita ta shigo da gudu ta faɗa kan Umar sai Khalil ya biyo ta ta tashi ta tsallaka Jafar tayi jikin bango Umar ya riƙe Khalil ya ce "Me ta maka" Ya ce "Bata jin magana kullun sai tana ce min mai ƙaton kai" Ya ce "Kayi haƙuri, ke kuma idan kina masa rashin kunya zan sa yana zane ki" Bilkisu ta ƙwalawa Maisun kira ta amsa tazo ta ce "Yaran nan sunyi Sallah isha kuwa" Ta ce "Eh" Ta kalle su ta ce "To kunyi wa Abban ku Aliyu Addu'a " Khalil ya ce "Nidai nayi amma Ummita bata yi ba ina kallonta" Nan fa Ummita ta fasa kuka ta ce "Wallahi ina yi kullun har a makaranta kuma in ƙarya ne Allah na kallon mu" Bilkisu ta ce "To kuje ku duka Auntyn ku ta gyara muku shimfiɗa ku kwanta ga ƴan biyu ma kuma ku bisu" Duka suka tafi da gudun su. Umar ya bisu da kallo yana musu Addu'a ya ce " duk cikin Haidar baida rigima" Ta ce "Ba ruwansa amma idan suka masa bai iya duka ba dan Ummita tafi shan wahala saboda tana da tsiwa" Ya ce "Ummita ay ko Maisun bata bari ba " Ta ce "yawwa kaga Maisun tana tausaya mata amma Haidar idan ya kamata da bugu ko" Ya ce "Allah dai ya shirya mana su ya musu Albarka" Ta ce "Amin" ALHAMDULILLAH INA GODIYA GA ALLA MAI KOWA DA KOMAI DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LABARI MAI SUNA *BILKISU* ABIN DA MUKA FAƊA DAIDAI ALLAH YA BAMU LADA WANDA MUKAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MANA. Sai kuma mun haɗu a sabon littafina Mai zuwa insha Allah wato ma suna *A MASARAUTATA* NAGODE🥰🥰 _*Mrs Aliyu ce*_ lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻