[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna siyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/Tiktoc:TikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *CI- MA- ZAUNE* *NA* *MAMAN AFRAH* Daga marubuciyar: Malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu,Jalli joga, ƙara,in nna delu, bilal da sauransu. *09025576222* 🅿️1️⃣ A hankali Dada ta fito daga cikin ɗakin nata tana ƙoƙarin kulle ɗakin da kwaɗo, sai wani taɓe baki take, dakatawa ta yi da rufe ƙofar tana bin bayan kishiyarta Ladiyo da kallo haɓa ta riƙe a zuciyarta ta ce. 'Allah mayar da ƙoƙo masaki tun kike tafiya irin ta guragu kina wani botsaro mazaunai, yo Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, na rasa mai Malam ya gani a jikin matar nan ya auro ta, abu babu kyan gani babu fasali ko mamora babu a jikinta ba gaba babu baya kamar sawun tayar keke, ni dai an cuceni a rasa da wa za a mini kishiya sai wannan mai haƙora kamar kacar keke' Ta kai ƙarshen maganar a zuciyarta tana jin kamar ta yi kuka. Fitowar Malam daga turakarsa shi ya ankarar da Dada ta mayar da hankali wurin rufe ƙofa. 'To ayawu sai ina kuma?" Ya ce yana aika mata harara, karkata kai gefe ta yi cike da kissa ganin Ladiyo ta dawo daga bayin ta ce "Allah sarki Malam gidan auta zan je mana, yarinya ta yi aure a gidan naira amma ba a leƙota ba, yau kimanin wata guda ban je ba shi ya sa na ce bari na je na ganta ta ganni ka san uwa da ɗa bare kuma ita auta jaja manya auta tafi na fari" Dada ta faɗa cikin sanyin murna tana wani karkata kai gefe. Shi kuma Malam sanin wacece Dada sai bai ji ko wani tausayin sanyaya murya da ta yi ba don ya san saboda kissa da kisisina take domin kishiyoyinta amma da zarar sun ware wuri guda shi da ita za ta sauke masa kwandon masifa. "Yanzu da tsakar ranar nan za ki je gidan mutane? Bakya gani sirikin ki ne" "Yo kana ma kenan wai dambe da kishiya, siriki ai ɗa ne, kuma idan mutum zai je ganin yadda ɗansa yake zaune a gidan aure ai sai ya yi bazata wato ya je lokacin da ba a tsammatar zuwan baƙo" Ta ce tana sakin murmushin yake, tare da aikawa Ladiyo harara ganin tana ƙunshe dariya, bata san ita kuwa Malam tun da ya mata kishiyoyi biyu ragas to ya taro aradu da ka don bai isa yake katse mata hanzari ba "Ni dai a tawa shawarar ki bari sai da dare ki je ku gaisa ku dawo" "A haba Malam sai ka ce munafurci da daddare mai zan adar to? Ai zuwan dare ba zan adar da baccin makaho ba, tun da dai shawara ce ba umarni ba ni ka ga tafiya ta don da zafi-zafi ake dukan ƙarfe!" Ta ce tana juyawa ta shiga datse ƙofar, shi kuma ya juya ya shige turakarsa ba tare da ya sake cewa komai ba. "Ai ka haifi mace ka aurar da ita gidan daɗi gidan daloli inda za ta huta kaima ka huta, wani naka ma idan ya raɓe ta ya huta shi ne, amma ka aurar da mace inda sai dai ta kawo maka klin da sabulun wanki ai ci bayan ya yi yawa" Cewar Dada tana aikawa Ladiyo wani kallo irin na kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake. Haushi ne ya turnuƙe Ladiyo saboda ta san Dada magana ta faɗa mata, cikin ƙufula ita ma ta buɗe baki da zummar ramawa tun da ta san auren jari ne Dadar ta yi wa ƴar tata Amina tun da ba a ce Malam ba tun da shi ma ido ne nasa, kuma auren jarin ma sai aka duba wanda ya haifi Aminar aka bashi aure saboda son hutu da kuma son abin duniya. "Yarinya an cuce ta an haɗa ta da tsoho, tabbas kwa an cuce ta wa zai mata kalaman soyayya" Ladiyo ta ce cikin waƙa, har Dada ta juya za ta mayar mata da martani sai kawai ta tuna abin da ta faɗa mata na farko ma ya isa ta tuna take jin takaici tun da ta san Ladiyon ma auren mai kuɗin ta so ƴarta Halima ta yi sai dai bata samu attajirin ba, gashi kuma tana so ta je gidan Aminar don ta ci mai daɗi saboda haka ne ma ya sa bata ci komai ba tun safe domin kar cikinta ya cika, gudun hakan ya sa ta juya riƙe da mukullin ɗakin nata da kuma ledar viva marar komai. Tana shirin ficewa sai ga Mero ɗaya kishiyar tata ta fito daga ɗaki tana aikawa Dada wani kallo, juyawa Dada ta yi ta mata kallo ɗaya ta ce "Ni in na raina kasuwa ko sautu ba na bayarwa, aikin ɓur in ji tusa" Tana gama faɗa ta fice don ta san Mero ta shaƙa gashi idan aka faɗa maka magana baka mayar da martani ba ta fi yi maka ciwo duk da wasu suna ganin cewar shiru ma amsa ce amma ga mai hankali. A ƙofar gida suka yi kiciɓis da jikokinta ƴan biyu ƴaƴan Hafsa babbar ƴarta wacce ta rasu a wajen haihuwar su ya bar mata su wato Hassana (Hassu) Da Husaina (Usai) Yara ne masifaffu masu jan magana basa ganin kan uwar kowa da gashi duk wanda ya takalo su da faɗa ya san sauran babba ne ko yaro duk girmanka ka shigo gonar su to za su biya maka karatun rashin mutunci kusufa -kusufa shi ya sa ma mutane suke cewa halin Kakar su ne sak suka ɗakko, saɓanin ita Amina ƙanwar mahaifiyar ƴan biyun dama su biyu Dada ta haifa da Hafsa da Amina. Amina babu ruwanta ga sauƙin hali don ko Alhaji Sabo ma biyayya ta yi wa mahaifiyarta wato Saude wacce suke kira da Dada amma ba wai don tana son sa ba. "Hajiya Dadansy sai ina kuma da tsakar ranar nan?" Suka haɗa baki wajen faɗa. "Ku dai ku bari ƴaƴan nan gidan Amina zan je in gano daular da take ciki" "To ai dama don kin ƙi mu je da tuni mun gano miki ita" Hassu ta ce tana ƴar dariya. "Yanzu ma ni kaɗai zan je kun ga ledar viva na ɗakko duk wani naman kaji da lemon kwalba a ciki zan zubo muku kason ku, ku ci ku yi nak mu ajiye sauran muke tsakura muna ɗumama wa muna mayar da mugun yawu" "Gwara dai mu je tare"ɓ zuwa da kai ya fi sako" Usai ta ce tana ɗan ɓata rai. "Ke daɗi na da ke saurin fishi bana so mu je tare ku musu tijara amma idan na je yau ku sai ku je jibi in ya so muke fashin kwana ɗai-ɗai to ai dama tun da ya aure ta mu duka zai ke ɗaukan ɗawainiya" Ta ce tana tuntsurewa da dariya don ta san su da abincin gidan Malam sun yi hannun riga tun da Allah ya musu gyaɗar dogo ƴarta ta raɓi gidan arziƙi. Su ma dariyar suka yi ta basu mukullin ɗakin ta juya ta tafi tana ta sauri tana tafiya yawu yana taruwa a bakinta tsabar yadda ta saka a ranta za ta yi wankin ciki da na baki ga cikin ta sai ƙugin yunwa yake. Tana tafiya tana murmushi tana godewa Allah da saka wa Alhaji Sabo albarka da ya auri ɗiyarta da ta rage mata yanzu sai jikokin nan guda biyu, tun kuɗin da Alhaji sabon ya bata ƴan ɗari bibbiyu sabbi ranar ɗaurin aure su ne take cancantawa tana kashewa amma yau da safe ta kashe kuɗin ƙurmus don ta san yau idan ta je da kanta ba saƙo ba to tabbas zai bata kuɗin da ya fi wancan tun da ya bata wancan lokacin ma bare kuma yanzu da ta zama sirikarsa ka'in da na'in. Duk da tana mamakin rashin zuwansa gaishe da ita tun da aka yi auren wanda a baya ya saba kullum yana zirya amma sai ta danganta hakan da wataƙila aiki ne ya masa yawa, saboda ita ko tunawa ta yi cewar Alhaji Sabo ya zama sirikinta wani daɗi take ji. Tun daga ƙofar gidan take jin daɗi a ranta ganin ƙerarran gidan da za ta shiga, wanda take ganin gidan auren ɗiyarta ne ta cikinta, daga can ƙasan bishiya ta hangi Alhaji Sabo zaune a kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sai wasu zazzaune a kan tabarma. In dai ba idanunta ne suka mata gizo ko ƙarya ba sai ta ga kamar Alhajin ya haɗe rai da suka haɗa ido duk da tana washe mssa baki ita ala dole sirikarsa amma sai ta ga kamar ma bai santa ba amma sai ta danganta hakan da ko don yana cikin mutane ne ko kuma dai bai shaida ba duk da ta san hakan zai yi wuya. Da saƙa da warwara ta wuce su, ta san wata shekarar ma bata cire ran zuwa makkah sauke farali wataƙila ma a haɗa har su Hassu da Usai, da wannan tunanin ta yi wa gidan kutse. Tun daga farko take rafka sallama, amma ta ji gidan shiru, tana cikin yin sallamar sai ga Amina ta fito daga bayin riƙe da buta ta shiga amsa mata sallamar. Mamaki ne ya rufe Dada ganin yadda ta ga Aminar a rame ta yi wani baƙi tana tafiya salalo-salalo baki sake take ƙare mata kallo har ta kasa haɗa laɓɓan bakinta a yadda ta ga Aminar sai ta ga tamkar wanda rabon ta da ita kamar an shekara ba wata guda ba. "Sannu da zuwa Dada" Ta ce don katse shiru saboda ta ga Dada ta mutu da mamaki, ko ita ta san ta sauya nesa ba kusa ba amma ya ta iya shi faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi. Bin bayanta kawai Dada ta yi ba tare da ta amsa sannun ba, falon suka shiga ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ta yi ƙuru ta siyawa Aminar guda biyu duk cikin kuɗin da suka tatsa a wajen Alhajin. Duk da ran Dadar a ɓace amma ganin filas a ajiye an jera su, filas ɗin da duk cikin wanda aka siyawa Aminar sun fi kyau da tsada don a fitar da ita kunya saboda kishiyoyi duk da gidanta da ban. Sai ta ɗan ji salama tun da yanzu dai ta san sai dai jinya Aminar ta yi dama ko a mafarki ba za ta yi gigin yin tunanin rashin abinci bane. "Wai Amina amma cutar amai da gudawa kike tun da kika zo ko?" Ta jefa mata tambayar tana haɗiye yawun da ya taru a bakinta saboda daga ta kalli filas ɗin nan da aka jera su sai ta ji yawunta ya tsinke kwaɗayinta yana linkuwa. "Amai da gudawa kuma Dada?" "Yo cutar mai kike, duk kin fita hayyacinki kin yi baƙi kin rame sai ka ce wacce tukunbu (Tinubu) Ya yi sallama a gidanki" "Wallahi Dada lafiyata ƙalaw ko ciwon kai ban yi ba" "Haba Amina ya da haka an ce da kuturu a gama lafiya, kin gan ki kuwa hajaran majaran shiga motar alƙali? Babu nutsuwa irin ta amare, ke da kika yi aure a gidan naira maimakon ki sakata ki wala amma kin zo kina ƙeƙashewa son ƴan hana ruwa gudu su mana dariya?" Shiru ta yi bata yi magana ba ta sunkuyar da kai hawaye yana cika idanunta amma bata bari Dadar ta gani ba. Wurin kwanukan ta wuce ta janyo su guda uku ta kawo gaban Dada ta fita ta ɗakko cokali da faranti. 'Amin da shegen sanabe da shiga shari ba shanu kike yanzu wanda zai ci naman kaza yana karya ƙashi ina ruwansa da cokali bayan ga yatsunsa' Ta ce a zuciyarta tana sakkowa ƙasa ta zauna zaman dirshan ta naɗe ƙafafu. "Kin ga ma ledar viva da na taho da ita a zubawa marayun Allah su Hassu su mayar da yawu amma ki bari idan na ci na yi nak sai ki juye sauran ki ɗakko wanda kika ajiye a tukunya ki juye mana, kya ɗora wani da dare tun da ku naman kaji kullum ne mu kuwa daga sati sai wata albarkacin auren ki a nan ma ke mayar da mugun yawu" Ta ce tana murmusawa. Gaba ɗaya jikin Amina ya yi sanyi amma Dada bata lura ba. Sai da ta buɗe ledar ta ajiye a gefe maganin mantuwa don kar ta fara ci daɗi ya ratsa ta manta da ledar ƴan biyu ta koma ta shiga uku a wajem su duk da ta san ba za a rasa wani naman da shinkafa kaza a gidan ba tun da dai ba a rasa nono a ruga. Mayafinta ta cire ta ajiye tana gyara hannun riga ta buɗe babban fiɗas ɗin wanda a nan ne take saka ran ganin kajin, buɗewarta ke da wuya har sai da ta zabura tamkar ta ga abin tsoro. Salati ta shiga rafkawa tana kallon Amina. "Amina mai zan gani? Biski (Burabusko tuwon gero da ake ɓarza geron) Awannan lafiyayyan kwanon da rana tsaka? " Ta ce bata jira amsar Aminar ba ta buɗe ɗaya kwanon faten wake ne ko kayan miya bai ishe shi ba tana buɗe ɗayan ta ga wata miyar kuka ta yi kauri kirtif da ita kore sharrr ko alamar maiƙon mai babu bare a saka ran daɗi. Da ƙafa Dada ta hankaɗa filas ɗin miyar aikuwa kwacar ya kife miyar ta zube, ta shiga surfa bala'i "Uban me ƙasƙantaccen abincin nan yake a gidan nan wannan wane irin ɗaukan magana ne Amina da rana tsaka ki tuƙa tuwon biski da miyar kuka kalli ko da na zubar da miyar ma ko ƙashi babu sai waken miya " Dada ta faɗa ranta yana ƙuna. "Dada cimar gidan ce fa a haka kuma ba iya ni kaɗai nake yi ba har gidan matansa kwano uku ne nake tuƙawa da dare kuma sai a yi tuwon dawa wallahi tun da na zo ban ci nama ba in banda irin kifin nan ƙanana masu kamar fara kana ci suna maka ɗaci su ne kazar amarcina" Wani salati Dada ta ɗauka tamkar an yi mutuwa ko wani gagarumin abu ta shiga tafa hannuwa. "Amina kike tuƙa tuwon kwano shida a rana? Na rana uku na dare uku yo ba dole ki yi baƙi ki rame ba dama haka auren mai kuɗin yake? Ni ina can ina baza hanci ina ɗagawa kishiyoyi kai ƴata ta yi aure a gidan naira, ko yanzu sai da ta jefarwa su Ladiyo baƙar magama na fito amma in tarar da ke babu yadda kike ke ma kina buƙatar taimako" Ta faɗa tana tashi daga ƙasan ta koma kan kujera ta zauna jin cikinta yana ƙaran yunwa don yanzu yawun nata da yake taruwa baƙinciki ya sa ya kafe tun da babu wani abu na kwaɗayi. "Ai Dada ki daina cewa ma na yi auren mai kuɗin don cimar gidan nan sai wanda ya gani... "Wai to wannan rusheshiyar tumbin cikin nasa da ya ajiye yana tafiya tirtsi-tirtsi kamar mai cikin wata tara dama ba tsabar cin daɗi bane?" Ta katse mata maganar. "Wannan tuwon dai shi yake ci" "Na ga annabi in na yi hali na gari ni Saude, wane tsautsayi zagin mahaifin ne y kai mu ya baro da wannan sabga lallai an biki a gidanmu wai in gani a ƙasa in ji kare, wannan ai wutar ƙaiƙayi muka kunnowa kanmu garin son banza, lallai Sabo bashi da amana ni da nake ganin girma cikinsa tsabar cin mai maiƙo ne ashe da basir ne ya kumbura masa teɓa, ja'iri mai kai tun na haihuwa ashe shi ya sa da ya ganni ya kawar da kai gefe ya mere baki tamkar ya ga kashi to wallahi mu zuba mu gani ni da shi ɗan halak ka fasa zai shigo ya same... Ƙaran sawun takalminsa ne ya katsewa Dada maganar da take, a take ta shiga huce tamkar kububuwa tana jiran ya shigo ya durƙusa ya gaisheta ta ƙi amsawa ta ƙare masa cin fuska tas. "Amina" Ya ƙwalawa Aminar kira yana hura hanci. Amsawa ta yi ta fito jiki yana rawa Dada kuwa da kallo ta bita tana jijjiga kai don yau sai ta nunawa Sabo ya taɓo gidan rina. MAMAN AFRAH 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *CI MA ZAUNE* *NA* *MAMAN AFRAH* *Daga marubuciyar* *Malamin bogi, Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, Jalli joga, Ƙara,in inna delu, Beelal da sauran su* *09025576222* 🅿️2️⃣ "Ki wanke mini farar shaddar nan ki goge mini" Ya ce yana haɗe rai zai juya ya koma waje, da to Aminar ta amsa duk abin da ake Dada tana kallon su ta gefen labule. "Sabo! Sabo!! Sabo!!!" Dada ta shiga ƙwala masa kiran sunansa muraran yau babu Alhajin ma, ganin ya shigo gidan tamkar bai san tana nan ba, bare ya je ya gaishe ta. Sai da ya ɗan yi jim sai kuma ya amsa a shelaƙe. "Iyee" Ya ce a daƙile maimakon ma ya ce na'am ran Dada har zafi yake ba don tsoron habaicin kishiyoyi ba da a yanzu zai sakar mata ƴarta. A bakin ƙofa ya tsaya bayan ya buɗe labulen ua tsaya getsetse a kan Dada da take zaune a kan kujera yana riƙe da ƙugu. Wani takaici ne ya dirar mata tana jin tamkar ta hau cikin nasa da duka ko ta rage damuwa. "Ya aka yi ne" "Au Allah gaskiya ne Sabo ni za ka nunawa salalan tsiya? Ni za ka sincewa zani a kasuwa na ɗauki ƴar budurwa gagal a leda na baka amma ko wata ba a rufa ba gaisuwa ma ban isa ka gaishe ni ba?" "Yo ai mun gama bajat ni da ke kuɗi dai kika aura mata kuma na sha baku shi kafin na aure ta kun gama cin rabonku yanzu kuma sai yadda hali ya yi sai abin da kuka gani" Ya ce yana saka hannu a aljihu ya ɗauki naira ashirin ya ajiyewa Dada a kusa da ita wai ta sayi goro ya juya ya fita Amina tana jin daɗi da bai ga miyar da Dada ta zubar ba bare ya mata faɗa. Lallaɓowa Amina ta yi ta zauna ta doka uban tagumi. "Oh ni Saude in da ranka ka sha kallo, ashe mutumin nan lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi ita bata ci ba ta haɗe ko ina da hayaƙi, yanzu lalacewar son kuɗin nawa har ya kai a ɗauki murtala (20) A ce na sayi goro wato ga wacce talauci ya gama baibayewa, ni Saude ina zan kai wannan bala'in wannan abin kunya da mai ya yi kama har nake kasa fitowa daga ɗaki, ni ban san ba ma ko dai su Ladiyo suna da labarin halin da kike ciki nake musu kallon biri suna mini kallon ayaba" Ta ce tana doka wani uban tagumi ga yunwa tana ƙwaƙular ƴaƴan hanjinta. "Ki yi haƙuri Dada wannan ce ƙaddara ta" "Ah ah zan yi duk yadda zan yi ko mai gari sai na kai masa ƙara ya raba wannan auren" Da wannan ta baro gidan riƙe da ledar vivan da ta saka zanin Amina da ko wanki bashi da shi don ta yi basaja kar a ce bata kawo komai ba, a yi gulmarta ko a yaɓa mata magana kasancewar zama da kishiyoyi komai kake yi a ido yake. A inda ta wuce su Sabo yanzu ma suna zaune ko kallo basu ishe ta ba yunwar cikinta ma ta ishe ta, lokacin ana sallar la'asar ta shiga gida ita da ta ce sai dare sai ga shi rana ma ko sanyi bata yi ba ta dawo bare a yi zancen dare. Rai ta haɗe ta shigo tana muzurai. "Ga Dada ga Dada yau akwai wankin baki auren mai kuɗi akwai riba" Hassu da Usai suka haɗa baki lokacin da suka fito daga ɗaki suna murnar dawowar Dada. Dada jin furucin su sai ta shiga dariyar yaƙe sai dai ta kada mayar da martani don yanzu gani take kamar Ladiyo da Mero sun san abin da yake faruwa. Ƙafa Usai ta saka ta yi ball da kwanon teba da aka musu da miyar ɗanyar kuɓewa dama tun da aka zuba musu ta yi balla da shi wai ba za su ci ba su yau sai abincin gidan Alhaji Sabo, ganin dawowar Dada shi ne ta ƙara ball da shi. Zaunawa Dada ta yi jugum da ita, su kuma har rige-rigen buɗe ledar suke sai dai ganin zani marar wanki ya karya musu lago suka hau bin Dada da kallon tuhuma sai lokacin ma suka lura da damuwar da take ciki. "Dada Antyn ce bata da lafiya?" Hassu ta tambaya ita ma Usai kallon Dadar take don jin amsar tambayar. "Yo ina fa yaran nan tana lafiya sai dai bata cikin jin daɗin da muka tsammata" Ta ce tana kwashe komai ta faɗa musu cikin raɗa don kar a musu laɓe a ji abin da suke cewa. "Dama haka yake matsiyaci ne" Suka haɗa baki wajen faɗa. "Hmmm! Wai ni Sabo zai kalla ya ba naira ashirin sai ka ce almajira, tabbas ba wahalalle sai kwaɗayayye, tun da an ci moriyar ganga sai ayada korenta. "Ki ƙyale shi Dada za mu nuna masa kurensa" Bata ce musu komai ba don ta san za su iya. "Yunwa ce take addabata wallahi kamar in ci babu" Dada ta ce tana kallon su. "Aikuwa Usai ta cewa Ladiyo ba za ki ci teba ba kar ma a yi rabo da ke, mu ma namu da aka bamu gashi can a ƙofar ɗaki da muka yi ƙwallo da shi" "Na shiga uku ni Saude shikenan ni da ku mun yi haihuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance" Ta ce tun da kowa yunwa yake ji kuma ga shi sun yi sagegeduwa ba wan ba ƙanin karatun ɗan koli, wato basu ci na gidan Aminar na gashi na gidan ma ya gagare su kuma babu damar a tambayi Ladiyo abincin Dadar ta ce bata kasa da ita ba ko ma ta musu gori. Haka suka zauna sai dare da aka gama tuwo kowa ya zuba yana muzurai don ma kar a yada musu magana. *DARE* Wajen ƙarfe goma sha ɗaya na dare lokacin dawu ya fara ɗaukewa, Hassu da Usai ne suka zo wurin ƙatuwar kwatar kwalbati inda suka san nan ne wurin wucewar Alhaji Sabo idan ya dawo daga majalissar gabas inda yake zuwa kullum hira da dare. Gadar da aka yi a kwalbatin guda ɗaya ta katako wacce sai ta nan Alhajin zai bi, gatari suka saka suka daddatsa ta yadda ba za a gane ba, sai da suka gama suka gyaggyara katakon yadda ba a a gane ba. Kan bishiya da take kusa da wurin suka haye suna jiran dawowarsa. Ba ɗau lokaci ba kuwa sai ga shi ya taho da tulelan cikinsa yana tafiya cikin yana rinjayarsa, riƙe yake da wani kafcecen rake yana tafiya yana gaftara abinsa, kwalbatin cike yake da ruwa taf. Sun kallonsa kowacce ta saka hannu ta rufe bakinta don ma kar a samu matsala dariya ta ƙwace musu, yana zuwa hankali kwance yana cikin giyar rake ya hau gadar da yana takawa gaba ɗaya ya rufta ciki, da yake dama sun gama ragargaza gadar kuma ga nauyinsa sai ya zama yana takawa ta rabe gida biyu shi kuma sai gashi yana iyo a tsakiyar tafkeken kwalbatin, wutsil-wutsil yake yana neman ɗauki amma babu kowa a wajen ga shi don ƙarfin hali zungureran raken sa yana riƙe a hannunsa. Su Hassu suna ganin duk abin da yake faruwa da a ce ya ɗaga kai saman bishiya zai iya hango su amma ta ceton ransa yake domin ya faɗa a bazata ga shi kwalbatin da mugun zurfi da faɗi sai wasu shegun ƙurunƙusan duwatsu a ciki wanda tun lokacin da Alhajin faɗa bayansa ya bugu da jikin wani abu da bai san mene ne ba. Mage da suka taho da ita Usai ta ɗaukota tare da saita Alhaji Sabo da yake iyo yana facal-facaltun yadda zai fito ta jefa masa ai kuwa ta sauka a saitin wuyansa, maƙalƙale masa wuyan ta yi tana ta faman karta faratan ta a wuyan ga wani kuka da take yi wanda yake zuwar wa Alhajin a kamar sautin kukan kare wannan magen ita ta saka Alhaji ya fara tsorata da lamarin ganin ya kasa fita daga kwalbatin da bai kai ya kawo ba kuma ga wata mage da bai san daga inda take ba ta mayar da wuyansa tamkar jikin bishiya. Wannan dalilin ya sanya ya fara tunanin magen ko dai ƴar ruwa ce a gefe guda kuma yana tunanin ko dai igiyar ruwa ce ta ja shi tun da ga shi ma yana jin bayansa tamkar an sara ƙashin bayan, tun da tun bayan da ya bugu da bayan ya kasa kataɓus. Yunƙurawa ya yi a karo na ba adadi yana ƙoƙarin fitowa amma abin ya ci tura! Magen kuwa tamkar wanda aka haɗa ta da abokin dambe haka take kokawa da Alhaji, ƙeyarsa ta baro ta dawo daga gaba ta maƙalƙale wuyansa ga farcenta da ta maƙaleshi da shi ji yake tamkar an caccake shi da allura duk faratan sun nutse a cikin ƙosasshiyar tsokar wuyan nasa. Tamkar wanda aka faɗa wa magen ta sako bakinta ta kama gemun Alhaji da yake reto kamar jelar ɗan akuya wanda yake jiƙe da ruwa sharkaf ruwan sai ɗisa yake tana damƙa da haƙoranta masu tsini don sai da ta haɗo har fatar jikin haɓar ta gatsa sai ta riƙe gemun a bakin tamkar za ta cisge shi daga haɓar. "Wayyo Allahna! Ya furta a galabaice yana sakin ɗan ƙara. Ana cikin haka Hassu ta yi wani tsalle ta diro daga saman bishiyar , faɗowarta ke da wuya sai Usai ma ta biyo bayanta sai a lokacin na ƙare musu kallo ta cikin haken farin wata, sanye suke da baƙaƙen dogayen riguna kan su babu ɗankwali sun barbaza gashin kan su sai kuma suka samu ƙahon kan saniya suka saka shi a gefe da gefen kansu wato wajen kunnuwan su, suka yi dibara suka ɗaure da siraran tsimma sai ƙahon ya zauna daram tamkar dama a haka suke amma kana ganin su za su baka tsoro don basu da maraba da aljannu. Alhaji Sabo wanda a kan idanunsa Hassu ta faɗo ƙasa kuma maimakon ta zo a tsaye sai ta zo a tsigunne, shi dai da yake yana cikin tashin hankali ne bai san daga saman bishiya ta diro ba duk a tunaninsa ta saman iska ta diro. Bai gama mamakin kasancewar hakan ba sai Usai ma ta diro a take ya ki duk damuwar faɗawa ruwa da yake ciki da kuma azabtar da gemun haɓarsa da mage take yi sun zama nafila yanzu ne yake ganin tashin hankali na farilla saboda ganin idanunsa a kan ƙahon su ya sauke idanun. Ƙuuuuuiiiit Wata tusa da ta kuɓuce masa ta samu damar fitowa da yake yana cikin ruwan shi kaɗai ya ji sautin fitowarta amma hakan shi ba damuwarsa bane ko da a ce kashi ne zai ƙwace masa a kan tashin hankalin da yake ciki tun da babu alamar wani mau taimakonsa zai zo abin ka da ƙauye kowa ya shige gidan baka jin komai sai kukan karnuka. Yana ji yana gani su Hassu suka fara tashi tsaye daga tsugunnon da suka yi, cikin wata tafiya mai kama da ta mutanen ɓoye suka fara doso wurin da yake. Boootttttt, ya saki wata ƙatuwar tusar a cikin ruwan yana ciccira idanu yana fatan kafin su zo ya arce don a zuciyarsa ya fara tunanin cikin ɗayan biyu ko dai sheɗanun aljannu saboda ya ji an ce sheɗan yana da ƙaho, kuma aljannu ma suna da ƙaho, bai manta ba a majalissar su wata rana ana hira ya ji an ce dujal ma yana da ƙaho. Mala'iku ma an ce suna da ƙaho shi dai kokwanto yake don bashi da wani ilimin addini da na zamani bare ya jahilci zallah yanzu bai san takamaimai waɗanne ne suka zo ba. Alhaji dama mugun matsoraci ne, yana ganin sun ƙaraso wajensa kallo ɗaya ya yi wa fuskarsu wacce take shafe da baƙin gawayi duk shirin nan sun yi shi ne a gidan wata tsohuwa makauniya da yake kusa da wajen da yake ita ba bani take yi ba sai suka yi shirin su a zauren gidan gudun kat su shirya a gida asirin su ya tonu. "Wayyo ni Sabo ɗan gidan Rakiya yau kuma da wannan muka fara kuturu ya ga mai ƙyasbi, tabbas abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa" Ya ce a zuciyarsa yana jin tamkar ya ɓace ya tabbatar idan dai mala'ikun mutuwa ne to tabbas zai mutu ya tarar da abin da ya shuka na zakunci da yake yi qa al'umma hatta da iyalansa bai bari ba tauye haƙƙoƙin su da yake amma ya saka bokansa ya rufe musu baki basu isa su faɗi aibun sa ba. Hassu ce ta zo ta gabansa da yake daga gaba ya fi kusa da bakin kwata tana kuma tsoro ta je ta baya ita ma ta wuntsila cikin kwatar a yi haihuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance. Hannu ta miƙa saitin kafaɗarsa ta dafa shi har lokacin magen nan tana riƙe da jelar gemunsa a bakinta shi zuwa lokacin ma ya daina jin zafin ja masa gemun da take yi domin kuwa yanzu ya ƙara tabbatar da gaba da gabanta aljani ya taka wuta! Usai ma bata yi ƙasa a gwiwa ba ta tsugunna a gefen ƴar uwarta ta kai nata hannun ta dafa ɗaya kafaɗar tasa. Duk da a cikin ruwa yake kuma fuskarsa a jiƙe da ruwan amma kuma hakan bai hana su ganin yadda gumi yake tsirnano masa dama bahaushe ya ce marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake. Tun da hannayen su ya sauka a kafaɗar sa jikinsa ya shiga karkarwa kamar wanda zazzafan zazzaɓi ya rufe, yanzu kam ya tabbatar da mala'ikun mutuwa ne. 'Tabbas rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya yau ranar tafiyata lahira ta zo ba tare da na shirya ko ta yi tsammanin zuwanta a kwana kusa ba' Maganar da ya yi a cikin zuciyarsa ta fito fili cikin karkarwar baki. Ta wutsiyar ido Hassu da Usai suka kalli juna yanzu kam tarkon su ya kama tsuntsu!. Da ƙarfin su suka danna kafaɗar tasa sai da ya shige ruwan gaba ɗaya kansa suka bashi minti biyu sannan suka saka shi ya ɗago daga ciki, sai da suka masa haka sau uku dama su buƙatar maje hajji sallah wato su azabtar da shi kamar yadda yake azabtar da ita saboda suna tsoron su masa kashedi ya yi wani tunanin da ban. "Sabooooo" Hassu ta faɗa cikin wata muryar tsoratarwa. Hannu ya kai ta cikin ruwan ya shafo cikinsa wanda yake tamkar mai cikin ƴan uku yana jin da a ce babu rusheshen cikin nan da tuni ya fito daga ruwan ya gudu tun kafin ma su zo. "Saboooo mutuwarka tana tafe ko da wane lokaci sannan kuma kana cikin haɗarin bibiyarka da aljannu za suke yi don sanin mai za kake aikatawa har zuwa ranar cikin wa'adinka" Usai ta dawo da shi daga tunanin da yake kai ya shiga gyaɗawa tamkar wani ƙadangare, yana ganin allura ta tono garma tun da har rayuwarsa za ya zama da bibiyar aljannu dama an ce na shiga ban ɗauka ba bata fitar da ɓarawo. Sai da suka gama bashi wuju-wuju sun tabbatar da cewanya karɓi hukunci sannan suka ce minti biyu suka bashi ya fita daga kwalbatin in ba haka ba mutuwa za ta riske shi. Facal-facal yake a ruwan tamkar agwagwa tana wanka a kwata yana ta neman hanyar fitowa don tun da suka ɗauke hannun su daga kafaɗarsa yake jin ko makka suka bashi umarnin zuwa a ƙafa babu abin da zai hana shi zuwa saboda zaman hannunsu a kafaɗarsa ko yi masa magana da kuma nutson da suka masa a ruwa ba ƙaramin halin tsoro bane. Taimakon da Allah ya masa yana ɗaga ƙafarsa ya sauke a kan wani dutse mai ɗan tudu wanda shi ne ya taimaka masa ya yunƙuro, hannu biyu ya ɗoro a saman ya ɗare sai kuwa ya wuntsila sai ga shi a reran cikin nan kamar an ɗora ƙwarya mirginawa biyu ya yi sai ga shi a zaune amma ya rasa mai ya samu bayansa ya kasa tashi amma yana tunanin hakan ba ya rasa nasaba da buguwar da ya yi lokacin da ya faɗa kwalbatin. Ganin tashin ba zai samu ba sai kawai ya shiga jan mazaunai yana nufar hanyar da za ta sada shi da gidansa da yake ranar ma a bakin Amina yake don haka can ya nufa yana tafiya hawaye suna masa sintiri kamar an kunna lalataccen famfo. Su Usai suna kallonsa yadda yake jan mazaunan ma cikin sassarfa ga wannan ciki nasa kaya guda shi kaɗai zai baka dariya saboda su ko tausayinsa ma basu ji ba tun da shi ma ba ya tausayin kowa. Sai da suka daina hango shi sannan suka cire ƙahon a kwalbatin ma suka jefa suka cire dogayen rigunan suka saka a leda dama a kan wani kayan suka ɗora, kuma sun cire ne saboda tsaro ba don tsoro ba don sun san za su iya haɗuwa da wani a hanya ko dai su a gida a gano su don sun san tabbas gobe Alhaji zai iya bada labari kuma wanda ya gan su za a iya hango jirgin su kuma hukunci zai biyo baya. *Alhaji Sabo* Tun da ya kama hanyar nan ko waiwaye ba ya yi ba ma ya fatan abin da zai sa ya waiwayo ya ƙara arba da masu baƙaƙen kayan nan da har sula sallame shi bai gama gane wane rukunin jinsi bane, shin mala'iku ne ko kuma aljannu. Yadda yake gurzar mazaunansa a tantagayyar hanya ce ga ƙurunƙusan duwatsu, yana dab da shiga ƙofa ya ji magen nan da take maƙale shi kwata-kwata ma ya manta da ita don tun da ya ga masu baƙaƙen kaya wanda ya yi wa laƙabi da mutuwa kusa sai ya manta ma da wanzuwarta dama an ce gaba da gabanta aljani ya taka wuta!. A ƙufule ya kai hannu ya warto ta har lokacin tana riƙe da gemun a bakinta, wani irin matse cikinta ya yi aikuwa ta saki gemun tana sakin kuka ta ce miyau, sai da ya wujijjigata yadda ya san ya rama abin da ta masa ya yi wurgi da ita ta kuwa ruga da gudu, shi kuma ya ƙara ƙaimi wajen gudun jan mazaunansa, ya shige gida sai lokacin ya tuna takalminsa da rakensa mai zaƙi da ya baro a kwalbati. "Ana ta kai wa yake ta kaya" Ya furta a wahalce yana kusa kai cikin gidan ko ta kan rufe ƙofar bai bi ba bare ya rufe. MAMAN AFRAH 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *CI-MA-ZAUNE* *NA* *MAMAN AFRAH* *Daga marubuciyar* *Malamin bogi, Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, Ƴan adaidaita sahu, jalli joga, Ƙara'in inna delu, Beelal da sauran su* *09025576222* 🅿️3️⃣ Tun kafin ya shigo cikin gidan yake rafkawa Amina kira, Amina tana banɗaki ta jiyo muryarsa yana ƙwala mata wani irin kira mai kamar ba lafiya ba. Fitowa ta yi ta nufi hanyar turakarsa a ɗarare don ya hana ta zuwar masa ɗaki, ta kusa ƙarasawa ta ji ya ƙara ƙwala mata wani kiran sai lokacin ta gane daga ɗakinta kiran yake fitowa da sauri ta nufi ɗakin tana fatan ba wani gagarumin laifin ta yi ba. Tana shiga ɗakin ta yi same shi zaune yaraf a tsakar ɗaki ya miƙe ƙafafu wannan tumbi nasa ya yi yaraf a kan cinyoyinsa. Makaki ne ya rufe ta ganin yadda yake wurjanjan ga shi a jiƙe jagaf kuma ko alamar nutsuwa babu a tare da shi sai wani raba idanu yake tamkar an kama kwarto a ɗakin sabuwar amarya. "Amina maza rufe ƙofar ɗakin nan" Ya faɗa har lokacin babu nutsuwa a tare da shi. Ita ma abin ya ɗaure mata kai har ta manta yaushe rabon da ya mata magana cikin taushin murya, da sauri ta rufe ƙofar tana mamakin abin da ya sanya shi a halin da yake ciki. "Amina ɗauke ni ki ɗora ni a kan gado" Ya ce bayan ta rufe ɗakin ƙare masa kallo ta shiga yi tana tunanin ta inda za ta fara. "Wallahi ba zan iya ɗaga ka ba" Ta furta a tsorace amma abin mamaki bai mata jaraba ba, haka suka kwana a zaune bacci sai gyangyaɗi saboda ya ce ba zai yarda ya kwanta ba dalilin da ya sa ma ya zo ɗakin nata tun da an ce yanzu tare zai ke sabgogi aljannu suna tare da shi, shi ya sa ya ƙi dosar turakarsa, a nan ɗin ma an gudu ba a tsira bane saboda daga bacci ya fara ɗaukansa masu baƙaƙen kaya da ƙaho biyu yake gani wannan dalilin ne ya sa baccin nasa ya kasance rabi da rabi. A ƙarshe ma sai yake zazzabura yana surutai hakan ya sa Amina ta fara tunanin ko jifa aka masa don abin da yake yi ya nuna kamar ba ya cikin hayyacinsa komai ya yi a firgice yake yi. Da asuba da ta masa maganar ya je ɗakinsa ya canja kayan duk da dai sun sha amma kuma har lokacin da damshin lema amma sai ya ƙi don ko da daren ma da ta tambaye shi mai ya jiƙa masa kayan sai ya ce wai ruwan sama aka yi ita kuwa ganin ba damuna bace sai ta ƙyale shi. Bayan ta idar da sallah tana lazimi sai ta ji wani ɗoyi ya cika ɗakin kafin ta gama addu'a sai take jin sautin darrr, bayan ta shafa addu'ar da mamaki ta juyo tana son gano ta inda ɗoyi ya baibaye ɗakin. "Daina ba kan ki wahala Amina ni ne nake sakin iska tamkar keken da tayarsa ta caku da ƙusa, ni ba bodari ba amma tusar nan nayi-nayi na na danne ta na matse abata amma abin ya ci tura! Ki yi dabara ki kai ni banɗaki mana" Ya ce yana kallonta. Gaba ɗata yadda ya haɗe ɗakin da wari tamkar mushe ya mutu a ɗakin, ji take warin har maƙoshin ta tamkar ta yi amai. A lan rusheshen cikinsa ta yi wa idanunta masauki wanda yake tatul. "Wallahi ba zan iya ɗaukan ka ba" Ta ce cikin sanyin murya tana so ta ce mai ya sa ya ƙi tashi amma tana tsoron ya mata jaraba. Kashin da bai yi ba sai sakin tusa a kai-a kai haka ta daure ta zauna da shi har gari ya waye sannan yana mata faɗa ya ce ta je gidansa ta kira uwar gidan da mai ɗakin tsakar tun da su suka san darakarsa ba za su ƙi taimaka masa ya tashi ba. Tun da matan nasa suka zo suka ce ba za su iya ɗaga shi ba a nan yake ce musu faɗuwa ya yi sai mai baro aka kira zai kai shi gidan mai gyara don mai gyran tsoho ne kuma ba ya zuwa ya gyara ko waye sai dai a je gidansa. Ga shi ya ce kar a taɓa masa mota saboda tsabar son abin duniya. *HASSU DA USAI* Da lallaɓe suka koma gida suka rufe ƙofar suka shige ɗakin Dada, ita ma Dada tana jiran dawowar su don haka ko da suka labarta mata abin da ya faru har da rawa ta taka. "Shegen mutumi da ciki kamar motar lodin shanu, shi don haɗama duk yadda tukumbu(Tinubu) ya shashshafa mutane duk suka ƙare kamar hatsin guzuri kowa ka gani a rame a ƙanjame amma shi jikinsa kaf babu ƙashi sai tsoka luƙum-luƙum ga cikin nan nasa ina ga ma ko kayan cikinsa linki biyu ne to na ga dai da alama girman cikin nasa ya yi yawa" Ta ce tana taɓe baki. Haka suka ringa labarin Alhaji suna shan dariya tare da gwadawa Dada acting ɗin da ya sha yi, a haka har bacci ya yi awon gaba da su. Da safe Hassu ta fita sayan ƙosai ta zo da labarin wai Alhaji sabo ya karye a kwankwaso. Wannan labari ya yi musu daɗi musamman Dada saboda ta ce ta samu kangarar raba aurensa da Amina. Bayan sun karya ta saɓi mayafi sai gidan Amina, a nan ta samu matan nasa sun yi faɗa uwar gidan ta kai ƙaran amaryar wajen Mai Gari da yake gidan Mai garin babu nisa da gidan Aljahi Sabo. Dada ko gidan Amina bata shiga ba sai kawai aka ɗunguma zuwa wajen Mai gari don tana ganin faɗuwa ce ta zo daidai da zama ita ma tana da magana da Mai garin. "Wallahi Mai gari ita ce bata da gaskiya ni na fara ɗaukan wando da ƴar cikin shi ne ita kuma ta ɗauki babbar rigar a kan na ce sai ta bani shi ne muka kaure rigima" Cewar matar Alhaji Sabo mai ɗakin tsakiyar. "Ke mai ya haɗa ku" Mai gari ya jefawa uwar gidan tambaya. "Kawai don ta ga shaddar tana da kyau kuma tana da tsada ai tun da ni ce uwar gida sai ta bar mini tun da ta samu kusan kala ashirin" Uwar gidan ta ce tana damƙe bakkon (Ghana most go) Da take kusa da ita wanda a kan ta kayan sakawar Alhajin ne da suke ɗauka tun da basho da lafiya shi ne kowacce ta kwashi rabonta. "To shi Alhaji Sabon da yak rashin lafiya ba mutuwa ya yi ba, amma kuke raba kayansa bayan yana can yana shan azaba a wajen gyara amma ba za a tausaya masa ba sai faɗa har gaban Mai gari" Mai gari ya ce yana kallonsa. "Yo ai da shi da gawa babu maraba, auren sa ne na gama" Uwar gidan ta ce. "Ko ni ba zan zauna da shi ba "Mai ɗakin tsakiya ta ce "Ko ni Amina ta gama zama da gurgun mage, yarinya samtaleliya ba za ta ƙare a zaman jinyar wannan mutumi da ba san ranar warkewarsa ba, haka kawai take cicciɓarsa tana kai wa bayi a je allon bayanta ko ƙirjinta ya lotse in shiga uku, bayan ita kaɗai ta rage mini sai marayun ƴan biyun can Allah na tuba idan Amina ta zauna tana taimaka masa yana tashi tsaf kafaɗunta za su bar gangar jikinta, wato hannayenta ya baro jikin daga kafaɗar haka kawai a tashi zaune tsaye wai sarki ya ji naɗin sarautar dogarinsa" Ta ce har ca share guntun hawaye. "Haba ku kuwa larura fa tana kan kowa, ku ma yanzu Allah zai iya jarrab... "Bakin ka ya sari gatarin aikin gona kar ka mini baki ni dai don baki ba ɗan uwa bane... Hango Alhaji Sabo an turo shi a cikin baro yana ciki yamutse a zaune kamar kayan wankin da aka daɗe ba a wanke ba, shi ba a zaune ba shi ba a kwance ba ya ringisa gaba kamar dai wanda ya sunkuya, hakan ne ya katse maganar da Dada take yi sai kowa hankalinsa ya koma gare su. "Bawan Allah gashi nan ma yau ko motar ma ƙin shiga ya yi ya gwammace a kai shi a baro(kura) Mai gari ya ce yana kallon sa. "Haba ai yanzu zama a gidan Sabo ya zama larura auren namiji da ƴaƴa ko kaɗan duk wanda ya zauna to ya tabbatar wahala ce" Dada ta ce tana taɓe baki. "Sannu Dada ke ma kin zo dubiyar, ashe kun ji tsautsayin da ya rufta da ni" Alhaji ya faɗa yana sakin wani ɗan nishi tamkar wanda ya daɗe yana jinya a gadon asibiti. "Waye zai zo dubiyar taka? Ni? Taɓ ala suturi buƙwi in ji kishiyar mai doro rabani da tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe, ai babu mai rabon shan duka sai mai waiwaye idan yana tafiya ni nan zuwa na yi ka sakar mini ƴata tun da ba tare muka yi naƙudarta da kai ba" "Haba Dada a lokacin da mutum yake cikin buƙatuwar mai tallafa masa ai ba a yi zacen saki ba duk da dai ba ita kaɗai bace matar tawa amma kowa yana da amfani sai suke baki-baki kowa ranar bakinta sai ta tallafe ni karaya ce a kwankwaso zan iya warkewa... Tun da ya fara maganar Dada take aika masa saƙon harara, har ta ji ba za ta jure saurarensa ba ta katse shi da faɗin "Ƴata ba wahalalliya bace da a ce kai tsohon arziƙi ne sai ta zauna amma dai ba za ta zauna yanzu da mai karyayyan kwankwaso ba, haka kawai da yarintar ta kuma da kake maganar matanka gasu nan ai sai mu gani in tusa tana hura wuta tun da gasu nan har sun fara rabon gadon kayan sawarka har suna faɗa a kan riga" Cewar Dada tana aika masa kallon iska tana yawo da mai kayan kara. Sakin baki ya yai yana bin matan nasa da kallon mamaki jin furucin Dada ganin ƙamshin gaskiya ya sa wasu zafafan hawaye suɓuce masa suka shiga zarya, yana ganin ga ƙosho ga kwanan yunwa domib alamu sun nuna babu wata mace da za ta zauna a dashi. "Ni Sabo na ga ta kaina daga karayar kwankwaso shikenan sai a fara guduna tamkar wanda nake cin mutane?" Ya faɗa yana rushewa da kuka, uwar gidan nasa da mai ɗakin tsakiyar ne suka damki wuyan rigarsa suna jijjiga jiki a kan sai ya sawwaqe musu ga kuma Dada tsaye a gefe guda ita ma tana jiran takardar ƴarta bayan ita Aminar bata san wainar da ake toyawa ba. Dakyar da suɗin goshi Mai gari ya ba wa matan nasa hakuri suka fasa neman sakin bayan ya faɗakar da su cewa babu kyau neman saki, haka suka hakura Dada kuwa ta saka auduga ta toshe kunnuwanta dan daga karshe ma sai ta je ta sako Aminar a gaba tana kuka amma haka Dada ta saka aka saki Amina. Malam sai na mujiya ya zuba musu don a ranar sai da aka kwaso kayan Amina kaf aka kawo gida aka zuba a wani tsohon ɗaki sa ake saka tarkace. BAYAN AMINA TA GAMA IDDA Tafe Dada take ita da ƴan biyun ta suna tafiya suna hira daga gidan kawarta da take can karshen gari suke. Wata haɗaɗɗiyar mota ce ta zo gifta su wacce sai sheki take da kallo suka bi motar Dada a zuciyarta tana raya ina ma Amina ta samu miji mai mota kamar wannan da kakarsu ta yanke saka. Har motar ta gifta su sai ta dawo da baya, a saitin su ta tsaya aka zuge gilashin. "Ɗan Ibra?" Dada Hassu da Usai suka haɗa baki wajen faɗa. Wani murmushi ya sakar musu ya kwama wani uban gilas a fuska. "Dada ku shigo in rage muku hanya na karasa da ku gida ... "Ɗan Ibra daga tafiya birni sai in ganka a galleliyar mota to in dai ba yankan kai kake ba ta yaya za ka samu mota ya wannan?" Dada ta ce tana ɗan ja da baya kamar yadda su Hassu suka ja. "Dada direbanci nake a birnin gidan su yallaɓai Sagiru to yanzu cewa ya yi bai taɓa zuwa kauye ba shi ne na kawo shi ya gani" Ya faɗa yana kallon na gefen mai zaman banza wanda sai lokacin su Dada suka lura da shi, sai wani gyara zama yake yana yatsina. "Allahu akbar kabiran, Allah sarki Ɗan Ibra ka yafe ni har na ɗauki alhakinka ka san duniya ta ki daɗi ashe da yallaɓai kuke tafiya" Ta ce tana washe baki idanunta kurrr a kan wanda aka kira da yallaɓai Sagiru. "Ba komai Dada" Cewar Ɗan Ibra. Dada kuwa gaishe da yallaɓan ta yi tana wani bashi girma kamar ta ari baki, inda Hassu da Usai ko kallo bai ishe su ba. Kai kawai ya gyaɗa bai yi magana ba kamar wani mai ciwon hakori. "Ku shiga mu tafi" Ɗan Ibra da ya fito ya buɗe musu kofar ya ce yana rike da murfin, sai da suka shiga ya rufe ya shiga ya tada motar suka tafi Dada sai jan shi da hira take tana tambayarsa bayan saduwa tana kallon Sagiru tana rayawa a ranta dama ya zama sirikinta ko Allah ya musu gyaɗar dogo su samu hanyar zuwa birni. A daidai kofar gidan suka tsaya da motar su Dada da Ɗan Ibra ya buɗewa suka fito Dadar tana ta faman zabgar godiya tamkar ta ari baki. Har Ɗan Ibra zai ja mota Dada ta ce "Ɗan Ibra ko ruwa baku sha ba da kun shiga kun sha ruwa" "Haba Dada ai sai dai ni in sha hakan ma don ana cewa kowa ya bar gida, gida ya bar shi amma yallaɓai sai ruwa gora yake sha ɗan kamfani" Gyaɗa kai kawai Dada ta shiga yi kamar kadangaruwa jin wani babban al'amari wai ruwa ma sai na kamfani hakan ya kara tabbatar mata da wuya wai gurguwa da auren nesa wato burinta ya kai ga cika saboda yanzu komai ya zama akwai ya babu kakar wajen uba. Su Hassu tuni sun shige gida tana shirin juyawa ita ma sai ga Amina za ta shiga gida. "Ɗan Ibra" Dada ta shiga kwalla masa kira don tuni ya fara jan motar ta fara tafiya. Birki ya ja kafin ya dawo da baya Dada har ta karasa a gefe guda tana kiran Amina. "Dama cewa na yi ga Amina ku gaisa" Ta ce tana kamo hannun Aminar ta kawo ta windown motar saitin da Sagiru yake. Gaishe da su Amina ta yi cikin girmamawa tana jin babu daɗi a zuciyarta yadda Dadar ta kawo ta sai ka ce wanda suka ajiyeta wai ta gaishe su. "Ai Amina da budurwa marabar su kaɗan ne wallahi, yo sakin wawa ce wawan ma mai runtumemen ciki silgar didi in ji ƴan birni (Sugar daddy )" Dada ta ce tana kallon Sagiru. "Haba Dada kin manta abokina ya nemi Amina amma da yake ba rabonsa bace bai aure ta ba ai ba zan iya neman budurwar da abokina ya nema ba dama ya ce mini aurenta ya mutu" Ɗan Ibra ya ce yana kallon Dada. 'Ka ji wani sakarci jiran jirgi a tashar mota haba Ɗan Ibra kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi va, ana maganar inda za a samu mai maiko amma kana maganar ka, kaima da gaka nan jiya iyau baka gaba baka baya kullum kana kwan gaba kwan baya sharar mai son jiki, kowa ya ganka ya ga wanda tikumbu ya shafa taɓ lallai da sauran aiki wai tukumbu ya ga talaka da tumbi' Dada ta ce a zuciyarta a fili kuma ta ce. "Dama mai gidan naka" Sagiru da yake wani ɗauke kai kamar ya ga kashi ya mata wani kallo da ya sa ta fara inda-inda. "Taɓ lallai Dada da ake miki kirari da Dada idon cin naira ashe dai haka ne daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki ba tare da an saka nama ba?' Ya ce w zuciyarsa a fili kuma ya buɗe baki zai yi magana Sagiru ya katse shi da cewa "Mu tafi" Umarninsa ya bi suka bar Dada tsaye da sakakken baki don Amina tuni ta shige gida. MAMANA AFRAH 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ac_t *CI-MA-ZAUNE* *NA* *MAMAN AFRAH* Daga marubuciyar *MALAMIN BOGI* *ƘAZAMIN MIJI* *BONONO* *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* *ƳAN ADAIDAITA SAHU* *ƘARA'IN INNA DELU* *JALLI JOGA BEELAL* *ƳAR ZAMAN WANKA* Da sauran su *09025576222* 🅿️4️⃣ Dada abin duniya ya haɗe mata goma da ashirin gabaɗaya ta ɗora rai a kan Sagirun da Ɗan Ibra yake direbanci a gidan su bare kuma mutumin da yake zaune a birni ai duk ranar da Amina ta aure shi kakarsu ta yanke saka. Sau uku tana fita dab da magriba ko Allah zai nuna mata motar su Ɗan Ibra don ta gwammace ko sadaka ne ta ba Sagirun Aminar saboda kawai ta aure ɗan birni kuma ɗan masu kuɗi. A cikin gari ta ji labarin tafiyar su Sagirun tun daga ranar Dada ta daina baccin dare kwana take tana sallah tana addu'ar Allah ya dawo da Sagiru ya auri Amina. Kwatsam bayan sati guda sai ga Sagiru da Ɗan Ibra a wata motar da ban har kofar gidan Dada. Bayan an musu iso Dada ta sa suka shio har ɗaki bakin nan nata kuwa ya ki rufuwa ganin Sagiru har tsakar ɗakinta ya sha galleliyar shadda tana sheki ga wata katuwar leda da aka ciko mata da kayan marmari. Jin fata da addu'ar ta sun karɓu wato Sagiru ya zo da maganar auren Amina lamarin da ya saka Dada sakin wata uwar guɗa da ta karaɗe gidan, wanda hakan ya kara janyo hankulan kishiyoyinta, sai bayan ta yi guɗar kunya ta kama ta ta shiga sunkuyar da kai. Amina kuwa tamkar an tsoma ɓera a ruwan zafi haka ta koma jikinta sanyi kalau don ita yanzu auren ma kansa ba ya gabanta bare wani auren masu kuɗi tana dai ganin yadda ta koma a gidan Alhaji Sabo. Dakyar Dada ta tilasta mata musu rakiya zuwa zaure kasancewar ma Malam ba ya gida bai ma san wainar da ake toyawa ba. Bayan sun fita Dada ta ɗakko lemon fata huɗu ayaba huɗu ta fito tsakiyar gidan ta shiga yin guɗa sai da ta yi kwarara sau uku sannan ta sauke idanunta a kan fuskokin kishiyoyinta wanda suka fito daga ɗakunan su suna ganin ikon Allah kunnuwan su cike da son sanin dalilin guɗar tata. "Allah sarki duniya gidan kashe ahu, tabbas duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta yi zafi ba to tasa ko ɗumi ba za ta yi ba. Sannan daren tuwo ba yana nufi za a kwana da yunwa ba" Dada ta ce tana sakin wata dariyar. "Wai Saude a kan mai za ki zo kike yadawa mutane magana da habaice-habaice? Kina guɗa kamar wanda ake saka amarya a lalle" Ladiyo da ta cika ta yi faful saboda bakin ciki ta faɗa saboda ta san dai zancen gizo ba ya wuce na koki kuma dai ruwa ba ya tsami banza tun da har ta ji Dada Saude tana wannan murna ta da walakin goro a miya. . "Kema dai kya faɗa don abin ba na wasa bane wai ɓera ya gutsurewa amarya hanci tana bacci" Mero ta faɗa tana kama haɓa. "Kai duniya rawar ƴanmata na gaba ya koma baya, ai gani ya kori ji" Dada ta ce yana mikaws kowacce lemo biyu ayaba biyu. "Aunty Amina ce ta samu miji ɗan birni mai mota shi ne ya ka... Kafin Hassu ta kai karshen maganar da take yi cikin tsiwa lemo da ayabar da Dada ta ba Ladiyo ya suɓuce ya zube saboda jin ba a rabu da bukar ba an haifi habu suna murna auren Aminar da Alhaji Sabo ya mutu sun samu abin faɗa da yada magana a tsakar gida har suna musu wakar kwaɗayi mabuɗin wahala, kan kwaɗayi kuda ya wahala ashe dai taki suke karawa shuka. Baki sake suke kallon Dada da take sakin murmushin kun dai gani ai. "In ka ga tsohuwa tana rawa a kasuwa tabbas ta daɗe tana yi" Dada ta ce tana juyawa ta koma ɗaki ta bar su da sakakken baki. "Lemo da ayabar taki sun faɗa, ungo ki yanka a je a tsotsa a bakin salati a saka albarka"Usai da ta ɗauki lemo da ayabar ta mikawa Ladiyo ta faɗa cike da shekiyanci saboda ta san ji suke kamar su haɗiye zuciya su mutu. Karɓa Ladiyon ta yi tana jin tamkar ta rusa ihu, ganin Usai ta shege ɗakin ya sanya Ladiyo ta nufi nata ɗakin bugujun-bugujum ko ta kan Mero bata bi ba, ita ma Mero nata ɗakin ta nufa zuciyarta yana suya don su ma zuwa yanzu nasu ƴaƴan sun fara kawo musu korafin zamantakewar da suke da mazajansu duk da dai ba yabo ba fallasa domin zaman aure dama ɗan hakuri ne amma dai lamari ne mai girma a ce Amina za ta yi aure a birni to tabbas sun san da sauran rina a kaba don sai sun kaɗe har ganyen su a wajan Dada saboda ba gori ba har goriba sai sun fuskanta. Amina kuwa tun da ta fita zauren baya ce musu komai ba sai wasa da take yi da yatsunta kasancewarta dama nutsatstsiya kuma mai kawaici, Sagiru kuwa gabaɗaya baki ya ki rufuwa sai kallonta yake tana washe bakinsa ganin kyakkyawar mace wacce yake da burin ya aura kwana kusa duk da bai ajiye ba bai kuma ba kowa ajiya ba amma ko ta halin kaka ya yi alkawarin ba zai bari wannan garaɓasar ta wuce shi ba. Ɗan Ibra ne yake hirar yana neman amincewarta tun da dai bazawara ce ba wani dogon lokaci za a ɗauka ba, ita kuma ganin ko tana so ko bata so tun da Dada tana so to ta san babu gudu babu ja da baya dama shi Malam ba a ma zancen shi saboda shi ma sai yadda Dada ta yi da shi ko da ya mata magana bai isa ba. Bayan sun gama jawaban su a kan nan da sati biyu suke so a gama komai za su aiko magabata sai kuma a kawo kayan lefe a ɗaura aure don ya ce lefe zai yi mata irin na budurwa. Da za su tafi ya ɗaukko rafar ƴan goma -goma ya bata dakyar ta karɓa shi ma don ta san matsawar ta ki karɓa sai ta gwammace kiɗa da karatu a wajan Dada. "Kai gaskiya na tsinci dami a kale" Sagiru ya ce yana kyalkyalewa da dariya lokacin da suka kama hanya domin komawa birnin Gumel suna tafiya a mota. "Ka yi dai a hankali wallahi wannan uwar tata masifaffiya ce don duk ranar da ta gano fakiri ne kai to kuwa ka kaɗe har ganyenka" ."Yo ai ba za ta gano ba domin lokacin da za ta gano tuni na kurewa tayar motarta gudu, don ba tsimi babu dubara tun da ni ne dai zan saki yarinya to kuwa ba zn sake ta ba, don sai in nuna mata ni ma ɗan zamani ne yadda take tsohuwar zamani dama ai wayon a ci ne ya sa aka kori kare daga bakin ɗinya" Ya kara faɗa yana waya dariyar. "Ai ni sai kashina ma ya fi naka bushewa saboda ni na kai ka garin... "Ka bar wannan maganar mu ji da badakalar da take gabanmu, ta samo aron kayan lefe da gidan haya da kuma iyayen aro" "Ka bar komai a hannuna yanzu dai bari mu karasa ka je ka cirewa wannan masifaffan mutumin wannan shaddar ka kara goge masa kar ya zo karɓa gobe ya yi kuli-kulin rakiya da kai" "Wallahi kuwa ni ma tunanin da nake yi kenan, wannan hular ma da na aro nake so in je in mayar ka san shi ma ya ce mini in ta kai bayan magriba sai na kara masa ɗari huɗu, ni kuma wancan sabbin kuɗin da na bayar ma raina ciwo yake ko gajiyar wankin da na yi aka bani ban huce gajiyar ba amma na ɗauki kuɗin sukutum na bata" "Dalla malam rufewa mutane baki, rafar ƴan goma-goman kake yi wa ido to ai sai ka sauka ka koma ka karɓo kayanka ka ga in tsohuwar nan bata tsige ka daga mai aurenta ba, ni kuma fa da na saka mana mai a mota wannan man mai tsada, ga haɗarin da na saka kaina na ɗaukan motocin Alhaji don baya kasar wallahi ka kula a yi auren nan kafin su Alhaji su dawo Nigeri'a don in suka dawo baka da mota mai kyan da za ka cigaba da karya da ita a kauyan amma in aka gama komai ka ai ko sun dawo ta famjama-fanjam" "Haka ne wallahi kai dai da Allah ya taimake ka, ya manta da mukullin motar a wajanka da ka kai su filin jirgi ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba" Suna ta tattaunawa har suka shigo garin Gumel ɗin. Washe gari Malam Saminu da yake islamiyar su Amina dama tun kan ta yi aure yake sonta amma tun da Dada ta kyalla ido ta hana shi sakat saboda bashi da masu gidan rana har ya gaji ya hakura ba don ya so ba. Yanzu kuma tun da aurenta ya mutu ganin ta gama idda yake dibdibtu, yau ma da la'asar sakaliya ya shirya tsaf domin zuwa wajan Amina sanye yake da yadi yalo wanda ko aiki babu a jiki yadin ko inda guga ta bi bai biyo ta wajan ba sai dai babu cukurkuɗewa. Rike yake da karamar bakar leda da ya sako yalo da goba da mangwaro wanda ya siyo a kasuwar da yaje ci jiya sai kifi naɗe a takarda shi ma a ledar yake. A zauren gidan ya tsaya daga gefe bayan ya aika yaro ya masa iso, yaron yana sanar da sakon Dada ta yi karaf ta ce ya ce masa tana zuwa, yaron yana fita Dada ta ɗauki mayafi ta nufi zauren don ita Aminar ma tana ɗaki bata san wainar da ake toyawa ba. Lokacin da ta iso zauren Malam Saminu hankalinsa yana a ledar da ya zo da ita ya buɗe yana lekawa sai murmushi yake ganin zai farantawa abar kaunarsa Amina musamman da ya ji an ce tana zuwa wato Dada bata hana ta zuwa ba hakan ya sa a ransa ya fara jin cewa sannu -sannu ba za ta hana zuwa ba sai dai a daɗe ba a je ba wato ko ba daɗe ko ba jima zai auri Amina domin in da rai tabbas da rabo. Tsaye ta yi a gabansa tana kallonsa shekeke kamar wanda ta ga kashi, sai lokacin ma ya san da wanzuwarta a wajen hakan ya sa gabansa bugawa da karfi don ya san in ba tijara ba babu abin da zai kawo ta. Cikin rawar jiki ya tsugunna yana mika gaisuwar da a maimakon ya ce ina wuni kasancewar da yammaci ne sai ambaton ina kwana yake yana karawa kamar dai wanda aka ce ina kwanan sau ɗaya bata gamsar ba duk da babu ko ɗaya da Dadar ta amsa kuma bata da niyyar amsawa sai kallon da wa kuka zo take masa. "Kai hamago! An ce maka yau tun da garin Allah ya waye babu wanda ya gaishe ni ne da ka hamgame baki kake mini gaisuwa babu kakkautawa kamar dai wanda na roke ka?" "Allah huci zuciyarki Dada" Ya ce cikin sanyin murya yana mikewa daga tsugunnon da ya yi. "To da mai zai samu zuciyata da za ta yi zafi, ni nan da kake gani ɓacin raina sai dai a kan naira wato kuɗi saboda kuɗi su ne ake cewa suna son maso wani wato ina son su su kuma suna son wasu. Wa ya gayyaceka gidan nan sau nawa na faɗa maka Amina ba sa'arka bace in banda sakarci jiran jirgi a tashar mota ta yaya za ka ɗakko wasu koɗaɗɗun kafafunka tsiri-tsiri kamar itace ka zo gidan nan, dube ka don Allah mai na sama ya ci bare ya ba na kasa kai nan wai wanka ne ka ɗauka na zuwa wajan zawara a ganinka ka kure adaka shi ne ka ɗauki wani yadi tsarrr da shi ruwan ɗorawa sai ka ce gaskami wai nan hira ka zo babu wani kamshin turare sai uban karnin kifi da ka cikawa mutame zaure da shi kalli takalmin kafarka kamar wanda aka bar maka gado duk ya suɗe ya katale, to wallahi tun muna shaida juna ka ja guntun mutuncinka ka koma inda ka fito in ba haka ba zan saɓar maka gwara ka koma ka samu ustaziya a cikin ɗaliban islamiyae taka ku rufawa kan ku asiri ku yi auren ustazai amma Amina dai ta fi karfin samun ka don matar manya ce, shi ya sa ma yanzu nake tura ta makarantar toka (Makarantar allo) Saboda kar ma take zuwa makarantarka ka sace mata zuciya" Tun da ta fara faɗar maganganu na cin fuska da wulakanci Malam Saminu ya sunkuyar da kai yana jin ciwon abin da take masa tabbas ba don albasa bata yi halin ruwa ba da babu dalilin da zai sa yake son Amina sai dai kasancewar tana da nutsuwa shi ya sa ma amma dama yadda Dada take bata ganin kan tsohuwar kowa da gashi da ba zai zo wajenta bama. "Za ka wuce da wani kalar yadinka yana ɗaukan ido wal-wal-wal ko kuwa sai na koma ciki na ɗakko katon faskaren icce na gurɗa maka kafa?" Ta ce tana aika masa harara. Sumi-sumi ya juya rike da ledarsa ya fita zuciyarsa tana masa zafi ita kuma ta koma cikin gidan tana faman kumfar baki, sai da ta je ta gargaɗi Aminar ma sannan hankalinta ya kwanta. Da daddare Dada tana zaune a turakar Malam tana shan rake tana ɗora ɓawon a murfin kwano sai da ta gutsiri raken ta tauna tana wani gyaɗa kai sannan ta ce "Malam nawa na kaina" ."Faɗi bukatarki". "Kamar yaya?" "To ai na san ruwa ba ya tsami banza" "Yanzu kenan ba zan faɗa maka abu ba sai ina bukatar wani abu?". "Kamar haka hasashe ma ya nuna mini" "Haba kai kuwa mai ya yi zafi hakan shi ba wuta ba" "To yanzu ya kike so na yi Saude kin uzzura sai da yarinyar nan Amina ta auri Alhaji Sabo haka na yarda ba da son raina ba amma kuma auren bai je ko ina ba kika yi uwa kika yi makarɓiya kika kashe mata auren ta dawo ta zauna kin mayar da ita karamar bazawara, kuma yau ɗin nan zan shigo na ga malamin islamiyar su ya fito daga zauren gidan nan fuskarsa alamar damuwa ta bayyana karara har kusan bangaje ni ya yi saboda bai ma lura da ni ba, ki ban tambaya ba na san hakan ba ya rasa nasaba da ke" "To ya kake so a yi ne haka kawai sai in bar ƴata ta yi auren talauci, kuma da kake maganar kashe aure kana nufin in barta ta zauna a gidan mai karyayyan kwankwaso to ba zai iyu ba kuma shi wancan mai yadi ruwan ɗorawar ai bai dace ya auri Amina ba mutumin da sai in kirga maka layan sawarsa kaf ina ga basu fi kala biyar ba daga wani yadi kore sharrrr sai wannan mai kalar ɗorawar sai wani jaaa da wani mai dishi-dishi... "Ya isa don Allah ni ban saka ki lissafa masa kayan sawa ba, shin yadika za ta aura?" "Ko bata auri yadika ba na san dai sai yana ɗinkawa zai ɗinka mata ko barw ni ma sirikarsa in samu yake bani tirmin zani ka ga kuwa ai bamu ga ta zama ba wai an saci ɗan ɓarawo don shi kansa bai mora ba bare a samu mamora don wallahi kana kallonsa ka san Tukumbu (Tinubu) Ya bi ta gabansa ya wuce ma'ana tsananin talauci ya masa katutu wato Tukumbiyya (Tinubiyya" Ta mamaye shi 0902557622 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *CI-MA ZAUNE* *NA* *MAMAN AFRAH* Daga marubuciyar *Malamin bogi* *Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, Jalli joga, Beelal, Ƴar zaman* *wanka, Ungozoma da sauran su.* *09025576222* 🅿️5️⃣ Kallonta kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba. "Yo ni da a ce ma na kashe mata aure, ka san an ce rabo shi yake kashe rabo wato yanzu ba ga shi ta yi babban kamu ba kamun ma a birni ni wallahi wannan gutsiri tsomar na guda shi ya sa yaron nan Sagiru ɗan birni abokin Ɗan Inba da ya zo haka ya kawo abin arziki bakko guda amma saboda kar na faɗa maka ka dinga kawo kauli da ba'adi shi ya sa na yi gum da bakina" "To da kika yi gum ɗin ma ai na ji komai a gari'. "A gari ko dai a gida ka ce dai waɗannan munafukan matan naka sun labarta maka, to duk mai bakin ciki sai dai ya mutu don na fahimci so suke ka hana a yi to kuwa na gani nan bari farar tumfafiya iya gani iya kalewa, dama ai duk wanda yake da kishiyoyi sai ya ga hassada ko da ba masa kiri-kiri ba to za a masa a bayan idanunsa" Ta ce tana gutsirar rakenta hankali kwance. "Duk tsiya kuma tun da ni ne ubanta dole sai da izinina ba' "Kuma dai ai ka san budurwa ake yi wa dole zawara kuwa gashin kanta take ci don haka Amina sai ta zaɓa ta darje" Ta ce tana mikewa tsaye . "Allah bamu alheri bari na je na irga ƴan matsabban kuɗaɗena na kwanta bacci ka san an ce mai kuɗi bai kwana da haushin kowa ba, saboda haka ma idan mutum yana lissafa kuɗi ba ruwansa da damuwa to sun yi hannun riga ɓacin rai" Ta ce tana saka kai ta fice ko abin da ta tara ɓawon raken bata ɗauke ba. Tun da Sagiru suka koma Gumel bai samu kara zuwa ba, sai dai yana bugowa wani mai cajin wayar garin su Amina ya ce ya kai mata su yi magana, don ya ce ya yi tafiya ba ya kasar ma domin ko da ya ce a ba Dada wayar ma sai da ya kara jaddada mata sun tafi kasar waje shi da iyayansa su siyo kayan lefe wannan maganar ce ta kara saka kan Dada da na su Hassu da Usai fashewa suna jin ba ya su domin Amina za ta yi auren kece raini basu san cewa Sagiru yana can ya dukufa ba dare ba rana yana wanki da guga domin ya tara kuɗin da zai ari iyayan karya su je nemo masa auren Amina da kuɗin da zai yi kowace hidima saboda iyayansa sun mutu a wani kauye yake a hannun kawunsa wanda gagararsa ta sanya kawun ya kai shi Gumel makarantar allo a can ɗin ma ya gagari malamin maganar da ake yi yanzu ya bar makarantar ma gabaɗaya tun da daɗewa. Sagiru tsawon sati guda yana aikin wahalar wanki sai da ya tara kuɗi yadda yake so sannan ya je ya ɗauki hayar mutane maza uku mata biyu wanda suka je cikin shigar alfarmar kayan sa shi ma arowa aka yi, su kan mazan hayarsu aka yi don aikin su kenan su je nemowa mutane aure a biya su. Sun je maganar auren inda Malam ya amince ba don komai ba don Dada ko bincike ta hana a yi tana ganin idan aka yi bincike tamkar za a binciko abin da zai hana auren wanda bata fatan hakan shi ya sa ta yadda da maganar kazantar da ba a gani ba tsafta ce. Daga Malam ya yi maganar bincike sai ta ce ai a gidan da Ɗan Ibra yake aiki yake kuma aure taya shi ake yi. An yanke maganar aure sati guda saboda kayan lefe suka taho set guda na akwati ga kaya tsala-tsalan leshina da atamfofi tsabar murna Dada sai da ta zuba ruwa a kasa ta sha saboda kayan lefen da ta gani na gani na faɗa. Sai ana saura kwana uku ɗaurin aure sannan Sagiru da Ɗan Ibra wannan karon har da wani abokin su suka je, Amina duk da ba wani karewa Sagiru kallo take yi ba amma a ranar ta ga ya sauya sosai ya yi baki ya rame ko Dada ta lura da hakan amma a ranta sai ta raya ko rashin lafiya ya yi basu san cewa tsabar wanki da gugar tara kuɗin hayar kayayyakin da za a fita kunyarsu bane. Ranar ɗaurin aure motoci biyu su Sagiru sula ciko da mazan da suka je neman auren sauran kuwa wasu abokan su ne aka ɗaura aure, aka yi hidima amm sai ango ya ce sai washe gari za a ɗauki amarya har ma Ɗan Ibra yana jaddadawa Dada cewa ba wani gayya za a yi ba kuma ana zuwa za a dawo da wanda suka je kai amarya. Dada dai duk da bata san dalili ba amma ta yi mamakin wannan magana sai dai saboda gudun ƴan tsurku sai ta ja bakinta ta tsukw don ya ce musu ma iyayensa suna kasar waje amma wani satin za su dawo wanda suka zo nema masa auren kannen babansa ne. Washe gari gida ya kacame da murna ana ta shirye-shiryen tafiya kai amarya, don mutanen da suka taru sun fi karfin mota biyar ma kowa yana son zuwa birni kai amarya Hassu da Usai an caɓa gayu Dada kuwa ji take ba don ita uwar amarya bace da babu abin da zai hana ta tafiya. Mero da Ladiyo Usai Hassu sai wasu mata guda uku su kaɗai ne za su je kai amaryar, su Ladiyo ma Dada ta zaɓe su ne don su je su ga abin da zai hana su baccin saboda bakinciki. La'asar sakaliya suka iso da motocin guda biyu wanda babu ango sai abokin ango Ɗan Ibra da wani wanda yake tuka wata motar haka aka yi tururuwa a kofar gidan har aka shishshiga motar da amarya da take sanye da jar atamfa an lulluɓe ta da mayafi. Abin da ya so ba ruɗawa Dada ciki shi ne yadda Ɗan Ibra ya jata gefe yake mata batun tafiya da kayan lefen da babu abin da suka taɓa a ciki sai su Hassu da suka ɗauki kayan kwalliya, amma abin da ya sa ta ji ɗan daɗi jin wai angon ne ya ce a tahowa amarya da kayan saboda a gobe zai kwashe ya kai a ɗinko mata domin take shiga ta alfarma kar danginsa su rainata kuma zai kai ta ta sake zaɓo wasu. Wannan maganat ce ta sanya Dada jin salama tana ganin idan har za a ke kai Amina tana zaɓo kaya a shgo to kuwa ta san ita ma akwai nata rabon. Don haka bata ɗauki komai ba ta basu suka loda a boot ɗin mota suka tafi mutane suna ɗaga musu hannu suna ganin Aminar ta yi babbar sa'ar auren ɗan masu kuɗin wasu , zawarawan ma da ƴanmata suna jin ina ma su ne. A kofar wani tangameman gida motocin suka tsaya, Ladiyo da Mero tsabar bakin ciki kamar su haɗiyi zuciya su mutu. Don Ladiyo da yake bakinta a buɗe yake babu abin da yake kwaranyowa daba bakin sai yawu saboda haɗuwar gidan sai da wata da take kusa da ita ta ankarar da ita zubar yawun sannan ta ga har gaban hijabin nata ya jike cike da wayincewa ta shiga rufe bakin tana lulluɓe wajen da yawun ya jika. Get ɗin aka buɗe a nan ne kallo ya koma cikin gidan ƴan cikin mota sai kus-kus ake yi ganin gidan kamar gidan sarki ko wani gwabna, dama basu ɗakko kayan jere ba saboda an ce ba sai ta je da komai ba. Unguwar ma da alama ta manyan mutane ce shiru babu hayaniya ana gama shiga cikin gidan kowa allah-allah yake ya fito ya kashe kwarkwatar idanunsa. Mero tana tafiya bata ma san ta samu wuri ta tsaya ba tana kallon haɗuwar gidan ga wasu shukokin fuɗawa duk sai ta kasa cigaba da tafiya tana jin ina ma ƴarta ce ta samu wannan ɗanɗasheshen gida. Ladiyo tintiɓen da ta yi ne da wani dutsi ya ankarar da ita katoɓarar da ta yi na raja'a a kan kallon benen da take yi. ."Mero wallahi har da gidan sama" Ladiyo ta ce tana nunawa Mero. .."Gidan sama ko gidan bene ai wallahi mun kaɗe har ganyenmu don kaju da gori dai a wajen Saude sai dai mu tashe kummuwanmu"Ta ce tana taɓe baki. Gyaɗa kai kawai Meron ta yi don ta ma kasa magana. Ɗan Ibra kuwa katafaren falon Hajiya mai ɗakinsa gidan da yake direbanci nan ya nuna musu a matsayin falon amarya suka shiga cike da murna. Basu san cewa Ɗan Ibra ne ya yi dibarar buɗe ɗakin ta karfin tsiya tun da yana ganin basa kasar kuma sun rasa gida mai kyau inda za su yi karyar da shi. Har bedroom suka shiga da ita aka zaunarta a bakin gado, kowa cewa yake aljannar duniya. Wasu ko zama basu yi ba aka fara cewa su fito a mayar da su lokacin ana kiran sallar magriba amma aka hana su yin sallah wai masu motar sauri suke nan kuwa Ɗan Ibra da gangan ya ce haka saboda yana tsoro mutanen unguwar wani ya ankara da abin da ake yi ya faɗawa iyayen gidan nasa, dama saboda ban ruwan shukoki da kuma zubawa kifayen da ake kiwo a gidan abinci aka bashi mukullin gidan dama kuma akwai mai gadi. Sun tafi sai amarya kaɗai a bakin gado ta buɗe mayafin tana karewa ɗakin kallo sai sannan ta gane ashe dai haɗuwar gidan ta kai haɗuwa shi ya sa ta ji Hassu da Usai suna ta cewa yau har sai sun rasa mai za su cewa Dada saboda bada labarin tsaruwa da haɗuwar gidan ɓata baki ne sai Dada ta zo da kanta domin gani ya kori ji. 'Oh ni Aminono wannan wane irin miji na aura mai bala'in kuɗi haka, wannan ai sai a ɗauka yankan kai yake' Ta ce a zuciyarta tana mamakin hatta gadon ma abin kallo ne. Kasancewarta mai yawan ibada bata wasa da sallah bata bari lokacin sallah ya wuce da gangan, hakan ya sa ta tashi don yin alwalar sallar magriba, duk da tana tsoron yin kauyanci, ganin kofar da Hassu ta buɗe wanda ta ji suna ta kyalkyala dariya ita da Usai wai banɗakin ƴan gayu har da famfo a ciki. Wannan ya sa ta ɗan tura bayin tana kare masa kallo ga fitilun wutar lantarki ko ina haske ral kamar safiya. Alwalar ta yi da ruwan famfom ta fito tana waiwayen inda za ta ga sallaya ganin jakar kayanta a ajiye tare da akwatinan lefen ta je ta zige jakar za ta duba ko Dada ta saka mata sallaya don ko haɗa kayan ma Dadar ce ta yi wai na za ta kwashi tsummokara ba kafin ta fara dubawa ta hangi sallaya guda biyu a gefen karamar loka kusa da gado jakar ta zige ta je ta ɗakko sallayar sai kamshi yake fita daga jikin sallayar, bayan ta shimfiɗa ta gabatar da sallar magriba ta sake tashi ta kabbara nafila tana cikin sallah ta ga shigowar mutum kamar ma babu nutsuwa a tare da shi, kiii ya fara jidar akwaitinan yana fita da su, lokacin da ya dawo ya ɗauko sauran ta idar da sallar nan ta ga Sagiru ne bai ko kalleta ba ya ɗauka ya fita abin da ya fi bata mamaki ma yadda yake a firgice kuma sanye da wasu kaya ba irin wanda ya saba zuwa garinsu da su a jikinsa ba wato wannan kayan yadi me mai saukin kuɗi kamar ma ya ji jiki. Mamaki kwalli a kunne tana cikin wannan tunanin ya dawo, bata san cewa tun kayan ɗaurin auren da ya aro ganin kuɗaɗen hannunsa sun kare shi ya sa bai kara aro wasu kaya ba. Ga shi kwana biyu ma ba a kawo wanki da guga ba bare har ya samu na sakawa aro. "Ki taso mu tafi" Shi ne abin da ya ce yana rike da jakar kayanta da mamaki take kallonsa tana ta wasi-wasi a zuciyarta a kan ko dai dama ba gidan da za a kawota bane suka yi ɓatan hanya amma da ta tuna har da Ɗan Ibra aka je ɗakkota sai abin ya kara ɗaure mata kai tun da dai ta san duk tsiya Ɗan Ibra ba zai kasa sanin gidan ba. Bata ce masa komai ba ganin ko fuska bai bata ba, hakan ta bi bayansa suka fito sai lokacin ta kuma ganin gidan ashe ba karamin girma gare shi ba. "Ka ga ango da amaryarsa" Mai gadin ya ce cikin zolaya. "Bari ina zuwa ka ce wa Ɗan Ibra idan sun dawo mun tafi zan dawo amma" "To ango kamar ka faɗa a kunnensa" Cewar mai gadin yana dariya. "Amarsu ta ango" Furucin mai gadin ya dawo da ni daga tunanim inda za mu je wanda na ji yana cewa ma wai zai dawo wato ni ba da ni za a dawo bama a can za a barni ko mai yake nufi oho. "Ina wuni" Na iya furtawa cikin sanyin jiki. "Lafiya amarya ta ango an iso lafiya ko" Ya furta yana ƴar dariya ni kam ban samu zarafin bashi amsa ba, gabaɗaya alhinin fitarmu da kuma inda za mu je ya tsaye mini a rai kafin in gama tantancewa sai jin hannun Sagiru na yi a cikin nawa ba shiri ya shiga jana kiiii muka fita fitowarmu daga get ɗin ya yi daidai da wata adaidaita sahu da na hanga za ta sha kwanwa wanda hasken kwayayan da suka haske unguwar tarrr ya mini nuni da akwatinan aurena wanda Sagiru ya fito da su. Na zama kamar wani mutuntume na kasa gane mamaki zan yi ko al'ajabi ko kuwa wasi-wasi a kan wannan ɗanyan lamari marar alkibla. "Hau mu tafi" Na tsinkayi muryrsa ina ɗagowa na sauke idanuna a kan wani tsohom machine, baki sake nake kallon machine ɗin amma sai na yi kokarin kawar da mamakin da nake na ɗaga kafa na hau bayansa domin ya saka jakar kayan a gaba haka ya tada machine ɗin da yake wani kara "Ko dai gida zai mayar da ni ya fasa aure? Ko kuwa karayar arziki?" Na shiga jefawa kaina tambayoyi da bani da mai bani amsar su. Yadda ya tada machine ɗin duk sai da hayaki ya buɗaɗe su. Hanyar da mai napep ya bi da ban shi gabas ya yi mu kuwa yamma muka bi, tun da muka fara tafiya bai tanka ba ni ma hakan. A daidai wani gidan kasa ya tsaya zato na sako zai karɓa sai na ji ya ce na sakko babu musu na sauka. Ganin ya faka machine ɗin ya ɗauki jakar ya ce in taho bayansa na bi ina ganin yadda ginin gaban gidan ya rufto kamar ma ya kusa zubowa. Ni dai ban ce komai ba ko gidan mu da yake kauye bai yi wannan tsufan ba. Muna shiga gidan na ga ɗakuna reras, da yake gidan yana da girma kuma da yake yanayin sanyi ne kowa yana ɗaki sai dai ina jiyo tashin maganganu, ɗakin da yake karshe da suke ɓangaren farko guda uku ya shiga na karshe ni ma shigar na yi don zatona zai yi sallama da neman iso amma abin ya ci tura saboda ɗakin kawai ya shiga kamar ma dai ya samu kufai. Ciki da falo ne na kasa falon ko arzikin tabarma babu duk ɗakin ya ɓurɓurje. "Wannan shi ne inda na kama mana haya a nan za mu zauna can inda aka kai ki gidan uban gidan Ɗan Ibra ne bari zan je na dawo" Ya ce lokacin da yake shimfiɗa mini wani tsohon buhu kato. Laɓɓana ma na kasa haɗawa bare na samu kwarfin gwiwar bashi amsa ba komai ne ya cika kwanyata ba sai hango yadda Dada za ta yi a lokacin da ta samu wannan labari. MAMAN AFRAH 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 MASOYANA INA MUKU FATAN ALKAIRI DON ALLAH KU SHIGA WANANN LINK ƊIN KU MINI LIKE (👍) WANDA YA MIN ALLAH KA BIYA MASA BUƘATARSA KA YAYE MASA DAMUWARSA👏 👇👇👇👇👇👇 https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1 : CI -MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH. 🅿️6️⃣ *DADA SAUDE* Tun daga lokacin da su Hassu suka zo suka bawa Dada labarin kyau da tsaruwar gidan da aka kai Amina gabaɗaya ta ji kanta ya mata girma ta ji a yadda take ji tana iya fito na fito ko da da shugaban kasa ne, saboda kuɗin da sirikinta yake da shi musamman yadda ƴan rura wuta wato wasu daga cikin wanda aka kai amaryar da su suke kara kambaba hauhawar girman kan nata. "Allah kai damo da harawa ɗiyan nan dama rabo ne ya kashe auren Amina da Sabo gashi yarinya ta yi goshi a bazawara ma ta samu miji a birni son kowa kin wanda bai samu ba a birnin ma ɗan masu hannu da shuni ai ni wallahi Amina ta yi goshi yarinyar nan farin jini gare ta" "Ai Dada da a ce kin ga yadda Ladiyo da Mero suka saki baki suna kallon gida aljannar duniya da abin sai ya baki dariya" Usai ta ce tana dariya. "Ni yadda suke kallon ɗakin da gadon ne ma ya bani dariyar, Mero cewa take Ladiyo kina ganin abin da nake gani kayayyaki kamar a kasashen turawa" Hassu ta ce tana kyalkyalar dariya su duka dariyar suke yi kafin daga bisani Dada ta ce "Ai mu yanzu gidanmu ya zama biyu birni da kauye, idan aka shafi kwanaki sai ku je can ku huta ɗan abin kasafin da kuka samo sai ta harhaɗo muku ku kawo mini " "Wallahi Dada ai kakarmu ta yanke saka" Suka haɗa baki wajen faɗa. Tun daga wannan rana Dada ta kasa zaune ta kasa tsaye don bata da burin da ya wuce ta je ta ganewa idanunta gidan Amina gori habaice-habaice shi take yi wa su Ladiyo su kuwa ganin irin daular da ƴarta take ciki su suka ja bakinsu suka yi shiru domin sun san faɗan da ya fi karfinka wasa kake mayar da shi tun da dai sun san irin ɗimbin daular da ƴartata take ciki. Wat ranar asabar ta kasa hakuri domin bata da burin da ya wuce ta je ta kwana biyu a gidan Amina tun da dai Allah ya horewa mijinta tana so taje ta ɗan kwana biyu a gidan Aminar ko ta ɗan lasa zumar arzikin da suke ciki a bakinta. Saboda ɗorawa rai ma watarana sai ta yi ta jin lamin duk abin da ta ci saboda ta ɗorawa kanta son cin abu mai daɗi idan ta je birni. Shagon mai caji ta nufa wanda a wayarsa Sagiru yake kiran Amina kafin a yi auren suna waya. "Dada Saude ko dai caji kika kawo" Ya tambaya cike da zolaya. "Yaro man kaza ko don an ce ta yaro kyau take bata karko, ka jira kwanaki kalilan zan yi waya ƴar dangwale ma kuwa(Torch secreen) Yanzu ma dai zuwa na yi ka kira mini mijin Aminar in ji lafiyarta ka san idan aka ce ɗanka yana gidan daula" "Allah dai ya ja da kwananki Dada yo kaf kauyan nan akwai wanda zai ce bai san cewa Amina gidan daula ta yi aure ba ai tuni zance ya gama karaɗe ko ina labarin da ake kenan" "Yawwa ko da na ji" Ta ce ranta fari kal jin wai kaf gari an san Amina a gidan mai kuɗi ta yi aure. Wajen sau uku yana kiran wayar tana shiga amma ba a ɗauka. . "Wayar tana ta shiga ba a ɗauka ba" "Ka san gidan ƴan gayu yanzu haka bacci suke yi mu da muke kauye ai mu ne aka bari da tashin sassafe kuma talaka ai ko don fita neman abin sanyawa a bakin salati ya fito da safe wanda yake da kuɗi kuwa ai ya huta sai ya sha baccinsa ya tashi lokacin da ya ga dama" Ta ce tana murmusawa jin tsabar hutu ne ya sa ko waya sai a yi ta kira ba a ɗaga ba. Daga can ɗaya ɓangaren kuwa a lokacin da ake kiran wayar Sagiru rakani kashi wacce tsufa ya samu wajen zama a jikinta tana ta tsitsi kamar kukan gyare amma shi gogan yana kwance a kan buhu a ɗakin yana sharɓar baccin asara saboda dama tun da ya yi aure ɗan wankin da yake ya ce ya daina aikin wahala tun da ya yi aure matarsa take sana'ar cikin gida suna cin abinci. Amina da take zaune a gefe ta yi tagumi saboda lokacin karfe goma ta ɗan gota tana shirin mika hannu ta tashe shi ta sanat masa ana kiransa a waya sai ta ga ya tashi ya ɗauki wayar. "Eh nine ina ji wa ke magane" Ta ɗaya ɓangaren Dada har da ɗan rusunawa ta shiga gaishe da shi tamkar gana ganinta. "Lafiya kalau muke" "Allah sarki ai tun ɗazu ake kira kiran yana shiga amma ba a ɗauka ba" Dada ta ce cikin ɗan sanyaya murya don ita ya gama mata komai tun da yana mai mugun kuɗi ya yarda ya auri ƴarta ƴar kauye ƴar kauyan ma bazawara. "Wa yake magana wai?" "Allah sarki ɗan albarka sirikarka ce Dada Saude dama na ce a kira mini kai mu gaisa in ji lafiyarku to na san baka shaida murya ta bane na san abin ne da yawa wai mutuws ta shiga kasuwa" "Au to ashe Dada ce ga Aminar to" Gaisawa suka yi da Aminar Dada ta shiga rattabo mata wasu jawabai wanda da to kawai ta bi ta amma abin na Dada ya zarce hankali da tunani bata ma san halin da take ciki ba. "Amina ana nan ana cin mai kyau a sha mai kyau a kwanta a mai kyau" Dada wacce duk tunaninta Amina take yi wa magana bata san cewa Sagiru ya karɓi wayar ya kara a kunne, sai da ya gama jin bayanan sanna ya shiga faɗin "Ai Dada yanzu ma karyawa muke yi da naman kaji da wainar kwai ga kuma shayi mai kauri da ya asha madara" Ya ce yana haɗe rai kar Aminar ta ce ya yi karya. Wani yawu Dada ta haɗiye muduk jin kayan daɗin da ta zayyama mata sai da ta ji tamkar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gidan Aminar. "Allah maka albarka ɗan nan yadda ka auri Amina ka kaita gidan daula Allah sa ta zama silar cigaban arzikin ka" Ta faɗa tana washe baki kamar yana ganinta. "Amin Dada" Ya ce yana yanke kiran" "Kai Allah ya mana gyaɗar dogo ban taɓa sa ran wani daga tsatsona zai rakaɓi daula haka ba" Ta ce mika masa wayar ta masa godiya ta juya ta tafi. Watan azumin ramadan ya karato wanda hakan ya sanya Dada da jikokinta cikin farinciki, saboda shirin ko ta kwana na tafiya birnin Gumel yin azumi a gidan Amina. "Haba wai kam ke Saude wace irin mace ce da baki da kamun kai ta yaya kuma a wane garin gaɓa-gaɓan kika taɓa ji sirika ta je gidan siriki ta zauna tsawon wata guda kuma ba ma ita kaɗai ba har da waɗannan jikokin yaran da gasu nan sun zama ƴanmata sun isa a kai su ɗakin miji" Malam da Dada ta ishe shi tambayar ya barta tafiya birni gidan Amina su yi azumi ita da su Hassu ya faɗa yana hayayyako mata. "Malam daga neman izini sai cibi ya zama kari? Kar ka manta ni fa izini na neman ba kuɗin mota ba kuma kai mene ne naka a tafiyata gidan siriki ni a nawa ganin idan ka faɗaɗa tunaninka ai za ka ga nauyi na rage maka nauyin ciyarwa da ɗawainiya tsawon wata guda nake so na yi azumina a can mu murmure abin mu... "Wai Saude mai ya sa ke duk inda jin nauyi yake baki bi hanyar yanzu gidan sirikin ne za ko je har ki zauna tsawon wata guda? Kuma ni na ce miki na gaji da ɗaukan ɗawainiyarki ne da za ki ce an rage mini haba sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa kamar dai baki da mafaɗi... "Kar dai ka ce mini mahaukaciya don ba yarda zan yi ba kuma wallahi tafiya kamar na yi na gama babu mai hana ni domin ana gobe azumi za ku yada zango a can a tashi azumi da mu washe gari ehe" Ta ce tana tafa hannu a cinya. "Wallahi ba zan barki ki tafi ba son ki je ki kashewa yarinya aure" "To tun da haka ka ce mu zuba mu gani ɗan halak ka fasa kuma ko yaran nan da kake batun zan tafi da su Allah na tuba nawa suke yaran da ko shekaru sha biyar basu rufawa baya ba kawai girman jiki ne yo ni ko tahowa na tashi yi ai sai in bar su a can su mata zaman ɗaki in Allah ya sa suka samu miji a can ba shikenan ba ai ni tun da na ji daɗin aurar da ƴa a birni gidan naira to fa ba gudu ba ja da baya " Saura kwana biyu a tashi da azumi Saude da su Usai sai shiri suke, gabaɗaya sun wanke kayayyakin wankin su, saboda Dada ta ce ko azumin ya kare sai sun warware sun maida ramar azumi sannan za su dawo duk da tana ikirarin cewa ba lallai bane ma in suna cin mai kyau su yi ramar azumi. Gabaɗaya cikin kauyan sun gama yaɗawa cewa a birni za su yi azumi hatta Dada gidan mutuwa ko suna ko biki idan ta je sai ta ɓinta cewa ita bana azumi a birni za ta yi sirikinta ya ce ta je can ta huta. Bare su Hassu duk sun gama faɗawa kawaye suna firiritar tafiya can. Malam yana zaune a kofar gida inda yake saka tabarma ya huta, suna ɗan tattaunawa da abokinsa sakon kiran mai gari ya riske shi duk da ya yi mamakin kiran bagatatan amma sai ya dangana hakan sa cewa ko mutuwa ma da tashin kiyama bagatatan za su zo wa mutane ba tare da sun shirya ko sun tsammaci zuwansu a wannan lokacin ba. Shi da abokin nasa suka rankaya domin jin ba'asin kiran, tun daga nesa ya hango Dada zaune a gaba mai gari ga su Hassu ma duk suna zaune a gefenta sun saka ta a tsakiya ga mutane nan a zazzaune a wurin. Cike da mamakin ban al'ajabi ya karasa wajen yana tunanin dalilin kasantuwar su Dada a wajen don shi tuni ma ya manta da wani tafiyarta birni a tunaninsa ta janye kudurin nata ganin bai amince ba. "Malam na ji daɗi da ka amsa kiranmu a kan lokaci dama iyalinka ce ta ga na isa a matsayina na shugaba kuma jagora da na isa da kowa a garin nan, a kan waya da kuma aiken sa sirikinta yake mata ta je can birnin ta huta ta yi azumi amma kasa ka tsare ka hanata tafiya" Mai gari ya ce yana kallonsa. Bakin magana Malam ɗin ya rasa sai bin Dada da su Hassu da suke share hawaye. "Da kai fa ake magana" Mai gari ya ce yana kallonsa. "Allah ja da ran mai gari ni a matsayina na mijinta na bata umarni a kan kar ta tafi amma bayana haka ni ban san wani aike da kuma waya da shi sirikin nata yake yi ba". "Ai yanzu ka ji, domin bakina da nata ta faɗa mini ga ta nan zaune ai kana gani. "Jiya ma sai da ya mini waya a kan cewa ko dai ban ɗauke shi a matsayin ɗa ba da zan ki zuwa in yi azumi bayan shi ko kaura na yi gidansa zai rikeni ko har abada ne domin uwa ya ɗauke ni" Ta faɗa tana sakin kukan kissa. "To yanzu tun da ka ji da kunnuwanka ka barta ta je ta azumin" "To ba komai na amince tun da abin har ya kai ba za mu kashe magana a gida ba sai ta kawo mi fada gaban jama'a ana mana shari'a" Ya ce cike da takaici don ganin kowa ya yi tsit shi ake kallo ana ɗan jijjiga kai kuma ya san duk mazan da suke wajen dole su ba matansu labari. Ganin ya amince mai gari ya sallame shi, bayan sun tafi Dada ta shiga yi wa mai gari godiya har da bashi ɗari biyar wai ya ci goro ya karɓa yana washe baki. Haka suka baro wajen cike da murna don gobe suke so su tafi ya yi daidai da azumi saura kwana ɗaya. Tun da suka baro fada suke jin ana musu a dawo lafiya da alama labari ya gama baza kauyan. Don ko da suka dawo gidan ma su Ladiyo suke musu wani kallo ana ɗan kuskus na bakin cikin ganin za su tafi birni suke cin kayan daɗi. Ko da daddare da Dada ta je ɗakin Malam ko fuska bai bata ba bare su yi magana mugun haushinta yake ji yadda ta je ta kai shi gaban hukuma a kan gaskiyar da ya faɗa mata. "Malam ka san dai shiga abin hawa yana da haɗari shi ya sa ake yi wa mutane fatan sauka lafiya amma kai na zo har ɗakin ka kana wofantar da ni sai ka ce wanda na kashe ma mutum" "To dama ni na ce miki bana miki fatan sauka lafiya ne ki je umma ta gaishe da ashshe kuma indai tusa tana huta wuta ai ga wurin nan" Ya ce yana juya mata baya. ."Tun da haka ka ce ai babu komai rana dai bata karya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya gobe ya wannan muna can ana ta yi wa ciki hidima" Ta ce tana sakin murmushi tare da ficewa ta bar masa ɗakin. "Ni wallahi na matsu gobe ta yi mu je mu ci kayan daɗi" Hassu ta ce tana murmusawa. "Ni kuma kawai so nake in ga na kara shiga wannan katuwar kofar(Get) Wanda ko mota sai a buɗe mata ta shige ciki" Usai ta ce ita ma cike da murna. "Yara kenan manyan gobe ku ɗin ma kenan da kuka taɓa zuwa bare ni da sai labari nake ji ai sai na fiku ɗoki" Dada ta ce tana hango yadda za ta ga tsararran gida da Aminarta a ciki ta murmure. "Wai Dada dama har aike mijin Anty Aminar yake a kan mu je har yana miki waya" Hassu ta ce tana tsare Dada da ido, Usai ma tsare ta da idanun ta yi domin tana son jin amsar. "Yo in fa ni dai ce na faɗi hakan don wancan kakan naku ya barni kuma shi ma Mai garin ai da ban ce haka ba ba lallai ne ya karɓar mini fansa ba dama bukatar maje hajji sallah, shi kuma wannan yaro Sagiru idan ya ga mun je ai babu yadda zai yi da mu tun da dangin matarsa ne to dama ya gara ta kan yi da dutse ai sai kallo" "Wallahi kuwa Dada Allah dai ya kaimu lafiya don ni cikina zan buɗe in yi ta lodar abinci" Hassu ta ce tana dariya. "Ni kuma naman kaza idan na kafa kahon zuka sai dai a ga kasusuwan" Usai ma ta ce tana tata dariyar. "Ni fa ina ga ko bacci ba zan iya ba sai dai in ɓarawo, ji nake tamkar am mini albishir ɗin samun aljanna saboda daɗi" Tun da asuba suka tashi Hassu da Usai suka balbala wuta bayan sun yi sallah suka ɗora ruwan zafin wanka, garin na gama yin haske suka yi wanka Dada ma ta yi suka shirya tsaf su Usai an sha uban jambaki kan ta kile ga wata ɗamara da ka ci a kugu. Karfe tara suka fito tsakar gidan lokacin Malam tuni ya fita sai Ladiyo da Mero sun kafa kujeru a tsakar gidan sun kasa sun tsare sun son ganin kwakwaf. Hassu ce ta datse ɗakin Dada an sha atamfa har da jambaki su Usai suka shafa mata a leɓe, Usai ta ɗauki bakkon kayan ta ɗora a kanta ita kuma Hassu jakar wasu kayan a hannunta. "To mutanen gida mun fito mu za mu tafi, birni ta yi kira shi ya sa bahaushe ya ce ɗa mai rana ko kana gudu haifi ka yada, yau dai za mu ci gajiyar haihuwa saduwar alheri mu da ku ga kafafunmu a gidan nan watakila ma sai watan babbar sallah wato bayan sallar layya ah to ai sai an yanka mini katon tirkakken rago mai kamar saniya in sha Allahu zan taho muku da kakide(Kitse) Kwa ke cin tuwo" Ta ce tana musu dariyar irin ta in fitsari banza ne kaza ma ta yi mana. Kafin a samu mai bata amsa sai ga Malam ya shigo da sallama, Ladiyo ce ta amsa ko kallon kurar da ya ɗakko su Dada bai yi ba. "To Malam za mu tafi in da rai za mu gana wata rana" Dada da ta bishi ɗaki ta ce tana daga tsaye don ta san zaman ma aiki zai zame mata. "Sauka lafiya ya ce yana ɗaukan rediyonsa ya kunna. Baki ya taɓe ta juya ta fito suka fita tana jin su Ladiyo suna kuskus ta san gulmarta suke yi. Gaba ta yi rike da igiyar akuyarta don ta ce ba za a ci daɗin birni babu ita ba dole ita ma akuyar ta murmure. KAMAR YADDA NA SAKA LINK NA YOUTUBE CHANNEL A SAMAN PAGE ƊIN NAN DAN GIRMAN ALLAH KU SHIGA KU DANNA MIN LIKE 👍 NA SAN NA FI ƘARFIN NEMAN ALFARMA A WAJENKU LIKE ƊIN DA ZA KU MIN ZAI BANI DAMAR LASHE GASA GA LINK👇 https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 Ku shiga wannn youtube channel ɗin ku danna min like 👍 gasa ce kuma da like za a fitar da sakamako 👇👇👇👇👇 https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1 : CI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️7️⃣ Wurin motar da za ta tashi suka je wacce take a tsakiyar dandalin garin, tun da suka fito suke sallama da mutane ana ta musu fatan alkairi kowa yana ta cewa ƴarta ta auri mutumin arziki har yana aikowa ta je can ta huta harkar arziki ta yi ana ta mata sambarka wasu har tana cikin mota ma sai da suka je suka mata sallama har tana rasa wa za ta amsawa yadda suke dafifi wajen zuwa. "Mutane kenan kowa yana so ya raɓe ka idan kana da arziki in kuwa talaka ne kai babu mai raɓar inda kake sai dai gani daga nesa wani ma in ya ce warin talauci kake, idan ma baka da kuɗin ko magana baka iya ba yo wa ma zai saurare ka" Cewar Dada lokacin har mota ta tashi sun ɗau hanya akuyarta a boot aka saka mata ita. "Ai dama yanzu rayuwa sai kana da shi idan baka da shi kare ma ya fika" Wata mata da take kusa da Dada ta ari zancen ta yafa, da yake so Hassu a boot aka saka su. Haka dai suke hira da labaran duniya har suka isa birnin Gumel a tasha direba ua faka suka sauka bayan Dada ta biya kuɗin mota. "Ya sunan unguwar ma?" Dada ta tambayi su Usai sunan unguwar da gidan Aminar take. "Mayanka sunanta" Usai ta ce tana gyara rikon jakar hannunta. Napep suka tare suka shiga Dada tana rike da akuyarta ya ɗauki hanyar unguwar da suka faɗa masa kowa sai washe baki yake yi. ."Ke daina kan ki akuya sai kin san arziki ya shigo dangi , ah to ai daga yau kin daina cin dusa da ciyawa abincin mutane za kike ci mai rai da lafiya", Cewar Dada jin akuya tana kuka. "Wallahi kuwa ai shi ya sa aka ce da arziki a garin wasu gwara a garinku" Su Usai suka ce suna dariya. "Za dai ku gane gidan ko, kar fa mu je muke bulayi" "To Dada da tun a can baki tambayi za mu gane gidan ba sai yanzu" Hassu ta ce tana kyakkyalewa da dariyar shekiyanci. "Haba bayin Allah dama baku san gidan da za ku je ba shi ne kuka taho da ni son mu je muke bulayi man nan mai shegiyar wahala ya kare mini a banza" Mai napep da yake tuki ya ce cikin kakkausar murya dama saurayi ne ɗan bana bakwai. "Kai yaro bar ganin mun zo daga kauye ka zata bamu san mai birnin take ciki ba to da in baka ɓata mai ba mene ne amfanin zubawa ni nan na sam duniya ciki da bayanta ka bar mini kallon kitse a maimakon rogo" Dada ta faɗa cikij hargagi ɗan napep bai kara magana ba ya ja bakinsa ya yi shiru dama faɗan da ya fi karfinka wasa kake mayar da shi. "Ni zan gane gidan ma babu wani bulayi"Usai ta faɗa. "Yo yarinya mene ne na ɓata bakin ki, ai na san dai gida kamar gidan Alhaji Sagiru ba zai yi wuyar gani ba saboda duk inda gida ya bambanta da saura to fa da wuya ka kasa sanin wandaya san shi" A bakin get ɗin ya sauke su Dada ta bashi kuɗinsa ya tafi Hassu da Usai har rige-rigen zuwa buga get ake yi kowa baki a washe kamar gonar auduga" "Ku buga a sannu mana watakila ta shiga banɗaki ne mu jira" Dada ta ce tana waige-waigen karewa unguwar kallo take yi. "Wallahi na kasa gaskata cewa ba mafarki ba nake a zahiri ne Aminata ce a wannan rantsatssan gidan kai Alhamdulullahi Allah kadiran na ga annabi in na yi hali na gari yanzu wannan gidan aljannar duniya ake mini bakinciki ba zan zo in ci arziki in barshi a nan" Mai gadi da yake banɗaki jin ana bugun kamar me ya yi sautin gamawa ya fito da yake Hassu da Usai ne masu bugawar. Yan zuwa ya buɗe yana bin su da kallon mamakin ganinsu don shi iya tsawon rayuwarsa a gidan bai taɓa ganin baki irin wannan ba har da akuya saboda haka sai ya yi tunanin neman abinci suka zo. Hassu da Usai tamkar su bangajeshi ganin ya yi kememe a jikin kofar ko hanyar wucewa bai yi ba. "Bayin Allah ba sai kun damu da bugawa ba shi "Ni Saude na ga annabi in na yi hali na gari" "Hajiyar tana sama sai dai kwa sake sawowa t... "Allah ɗan Allah baku mu samu, ka san da wa kake magana kuwa? To ka tausasa kalamanka in ba haka ba za ka yi da ma sani za ka yi sanadiyyar suɓucewar aikin gadin naka"Baki sake yake kallonta ga wannan jikokin nata kowacce ta yi ɗamara da tamkar wanda za su je gasar dambe. "Baiwar Allah abin ba na zafi bane cewa na yi tana sama... 'Saman uban wa ? in ce dai saman bene take ba to ni nan na baka izini ka hau ka ce uwarta mahaifiya ce ta zo fa kanta ba sako ba" Ta ce tana zazzare ido, mamaki ya kama mai gadin don ya san mahaifiyar matar amma ya ji ita tana ikirarin ita ce mahaifiyarta. "Allah baki hakuri" Ya ce cikin sanyin murya. "Da in banda iskanci mutum uwarsa ta zo amma sai ta zauna zaman jiran iso" A daidai wannan lokacin Alhajin ya fito daga ciki sai ya ce direban ya zo za au fita tafiyar gaggawa da sauri mai gadin ya zo. "Dada hango mutumin zai shiga mota bayan an wangale get ɗin, ganin Alhajin ya sa ta bankamo cikin gidan ita da jikokinta. "Baiwar Allah lafiya?" "Dama amaryar da aka kawo nan gidan ne muka zo ganin gida... "La baiwar Allah ai ba nan bane ganin Alhajin" ya juya yana waya mai gadin ya yi saurin faɗa jikinsa ya hau tsuma yana karkarwa don muddin aka ce ga abin da ya faru wato an kawo musu amarya gida da basa nan shikenan da kashin ya bushe. 'Ai gidan gaba da mu ne ma" Ya ce yana tsoron kar wani ya ji maganarsa ga tunanin Ɗan Ibra kar ya zo a daidai wannan lokacin a samu matsala. Baki galala Dada take bin su Hassu da kallo jin katoɓarar da suka yi ita dama ganin gidan ya tsorata ta faɗa ne kawai bata yi ba dama da a ce wannan gidan ne na Amina to da hatta su Ladiyo sai sun zama kamar bayinta da ɗaga kan da za take yi sai ya shallake tunanin mutane. Alhajin bai bi ta kan su Dada ba bayan an buɗe masa motar ya shiga direba yana shirin jan motar ya saka hannu a aljihu ya ɗakko kuɗin da a su kai dubu goma ya jefowa mai gadin yana masa nuni da ya ba su Dada don shi a nasa tunanin naiman taimako suke, yana gama jefowa motar ta tashi suka fice. Mai gadin ne ya ɗakko kuɗaɗen nan ƴan ɗari biyar -biyar sababbi ya nufo Dada yana yi yana waiwayan bayansa kar Hajiya ko wani daga cikin ƴan aikin su ji su kai mata rahoto, saboda ya san tabbas tsakin kuka a masaki ba zai rasa magani ba muddin wannan magana ta fita sunansa korarre tun da da haɗin bakinsa aka yi komai. "Amma ku dai an yi shashashu wallahi ya za ku kawo mu gidan da ba gidan Amina ba? Ni dama na aan a rina wai an saci zanin mahaukaciya ta yaya gari birni kamar Gumel a ce kun iya gane gida sai ka ce a wani karamin kauye to wallahi da sake yadda muka kwaso kayan nan himili guda yaushe za muke yawo da su?" Dada ta faɗa cike da takaici tana kallon yadda yaran suke kara karewa gidan kallo don tabbas sun san basu yi ɓatan kai ba nan ne gidan amma kuma abin mamaki kwalli a kunne gashi dai abu yana neman ya sauya salo wai gemu a kafaɗa. "Wallahi Dada nan gidan muka kawo Aunty Amin... Kafin Usai ta kai karshen maganar mai gadin ya karaso da kuɗin a hannu yana wani warwara su don su kuɗin ya ɗauke musu hankali su yi shiru da maganar gudun tonuwar asirin su har ya samu ya musu maganar da za su fahimta ba tare da wani ya ji ko ya gani ba. Kyarrr idanun Dada a kan sabbin kuɗin da suke filfil a mike ita kuwa mai idanun cin naira. "Ga wannan kuɗin in ji Alhaji ya ce a baku" Ya faɗa yana mika wa Dada duka kuɗin duk son kuɗinsa sai da ya danne ganin asirinsu zu tonu ya rasa ɗan aikin da yake takama da shi. "Yo mu da ba bara muke ba kuma ba neman taimako ba" Dada ta ce lokacin da ta damke duka kuɗin a tafin hannunta. "Anya ma zan yarda in koma kauye, yo ni ba don Allah ya mini gyaɗar dogo ba Amina mai kuɗi ta aura ai da na ga wurin zuwa don wallahi sai in kauro Gumel ɗin da zama in lankwashe kafa in karkace baki in ke ta annabi Allahzi wahidin, kawai daga ganinmu ko ratrabo masa matsaloli bamu yi ba ya cake kuɗaɗe sabbi dal ƴan ɗari biyar biyar ya bamu?' Dada ta jefawa kanta tambayar tana kara damke kuɗin gudun akasin lissafi. "Bawan Allah mai ka ce? Mu fa gidan ɗiyata muke nema to da yake ni ban san gidan ba wannan yaran ne masu kai tun na haihuwa aka zo da su amma suka kawo mu nan ashe dai gidan kama ya musu da na Aminar" ."Ikon Allah" Ya ce yana ɗan wayancewa so yake ya samu bakin zaren yadda zai faɗa musu". "Sunan mijin nata Alhaji Sagiru ita kuma Hajiya Amina"Cewar Dada tana ɗan kafe motoci guda biyu da idanu wanda suke a fake a harabar gidan wanda indai ba gizo idanun nata suke mata ba, kamar motocin da Sagiru da Ɗan Ibra suke zuwa garinsu in ma ba ta yi mantuwa ba ɗayar ita ce wacce ta fara ganin su a ciki ransr da suka zo garin har suka rage musu hanya sai dai tuno ba su kaɗai aka kerawa motar ba sai ta kawar da tunanin. "Taɓɗi! Wai Alhaji Sagiru mutumin da ko hanyar filin jirgi bana jin ya taɓa sani shi ne har aka lakaba masa Alhaji, hatta ita ma matar dalilin kasancewarta matar Alhaji ita ma ta zama Hajiya tabbas yau akwai cakwakiya musamman yadda kuka lodo kayan nan kuka taho alamu sun nuna ba tafiya ,a ku yi a kwana kusa ba bana jin ko abincin da za ku ci yau akwai shi a gidan Sagiru, don tun da ya yi auren nv ya daina wanki da guga ya zama CI-MA-ZAUNE babu aikin sile barr na sisi sai dai ya zauna a can majalissar ya tashi ya koma wancan' Mai gadin ya ce a zuciyarsa yana gyara murya domin yin bayani a gefe ɗaya kuma yana danne dariyarsa don har ya hango diramar da za a kwasa da tsohuwar nan idan ta je ta ga mazaunin ƴarta. "Ayya Allah sarki wai dama gidan Alhaji Sagiru kuke nema wanda ya auro matarsa Hajia Amina daga Bausuwa?" "Yauwa shi fa ai dama na san yaran nan shirme suka mini ba nan ne gidan ba, Allah sarki ashe dai ka san shi yo ai dama mai kuɗin ɗan masu naira kamarsa zai yi wuya a kasa sanin sunansa Allahu akbar! Duniya labari ashe dai Amina ma an fara sanin zamanta a birni wannan ne amfanin auren mai hannu da shuni kaima sai sunanka ya shahara" Dada ta ce tana washe baki. "Yo dama ai sai dai ba a ambaci sunansa ba, kuma yaran nan da gaskiyarsu, ai nan aka kawo amaryar tasa to basu jima ba a gidan ya bawa wannan Alhajin sadakar gidan ya koma wanda ya fi wannan" Mai gadin ya ce don ganin ya kara rura wutar son samun Dada. Kurrr take kallon gidan jin wai sadakarwa mijin ƴarta ya yi kenan yana da dukiyar da zai iya sadakar gida kamar wannan ya ba Alhajin da ya ɗakko wannn uban kuɗin ya bata sadaka tabbas ta kusa kaurowa Gumel da zama dole ya nemi kyankyatsetsan gida daga cikin gidajansa ya bata ta zauna a matsayinta na sirikarsa ta barowa su Ladiyo can su karata su da Malam ɗin don ita hatta tsohuwar igiyar aurenta da take reto ta kusa cirewa sai ta tsinke ta don ba zai iyu ba ta cigaba da zama inuwa ɗaya da igiyar auren Malam ba dama tun da ya mata kishiyoyi take jin haushinsa. "Allah kara buɗi" Ta ce tana kallon kayan da suke ɗakko na sawa tana ji a ranta da a ce ta san har haka mijin Amina ya shahara da kayan nan ba za su taho da su ba, yanzun ma tana tantamar ko dai su watsar da su a bola don abin kunya ne tana sirikar Alhaji Sagiru tana saka wannan kayan. 'Dan na san haka yake da ɗimbin dukiya da ranar da na kai Malam kara wajen mai gari da sai na sa an saka shi ya since mini igiyoyin da suka kullini ni da shi" Ta ce a zuciyarta. A fili kuma sai ta ce " Yanzu wa zai kai mu gidan ko kana da lambar wayarsa ka kira shi ka ce sirukarsa ce Saude ya aiko mota a ɗauke mu muna gidan da ya bada sadaka" Ta ce tana kallon mai gadin da ta rasa dalili rashin nutsuwarsa sai waige-waige yake na marar gaskiya. Sai da ya yi da gaske ya danne dariyarsa jin har ta hau ta zauna a kan maganar sadakar gida. "Wane mutum in ji mutuwa bani da lambarsa sai dai na saka ku a adaidaita sahu(Shin kin karanta littafina ƳAN ADAIDAITA SAHU? Idan baki karanta ba ki nema ki karanta ki ji yadda cakwakiyar jika da kakarsa a hayar adaidaita sahu ki mini magana ta no ta 09013181851) " "To muna godiya ɗan nan ai ba don a ce kana aiki a nan gidan ba da saboda karamcin da ka mana na sama maka aiki a wajen sirikin nawa" Ta ce lokacin da ta jua su Hassu suka bi bayanta su ma baki ya ki rufuwa. "Ba komai wallahi" Ya ce a fili lokacin da ya biyo bayansu ya janyo get ɗin don ya kwatantawa mai adaidaitar gidan da zai kai su. A zuciyarsa kuma sai ya ce. 'Hmmm shi kansa sirikin naki da za ki sama aikin so yake tun da dai CI-MA ZAUNE ne. Mai napep ɗin ya taro musu ya faɗa masa sunan unguwar da gidan da zai kai su. "Na san gidan ma ai wannan gidan ba ɓoyayye bane" Cewar mai napep ɗin. "Yo dama gidan hamshakin mai dukiya irin wannan ina zai ɓuya ai in ka je ana cewa ba a san gida ba to gidan ya ku bayi ne wato gidan malam shehu wato talaka nan ne za ka ga babu wanda ya sani daga ƴan uwa sai dangi amma gidan masu hannu da shuni ko babu haɗi sai ka ji an ce an sani saboda shahara" Cewar Dada lokacin da take shigewa cikin adaidaita sahun rike da ƴar akuyarta dama su Hassu tuni sun shiga sun zauna suka linga jakununan kayan a baya. "Yawwa ka kai su za ta baka kuɗin" Cewar mai gadin nan don ba ya so mai adaidaita sahun ya ce wani abu game da maganar da Dada ta yi saboda ya ga ya saki baki cike da mamakin furucinta shi kuma mai gadi ya fi so har sai ta je ta ganewa idanunra domin bahaushe ya ce gani ya kori ji. "Ungo ɗan nan ka sha ruwa ka ji mu ai yanzu kuɗi ba matsalar mu bace" Cewar Dada tana lissafo dubu ɗaya daga cikin sabbin kuɗin nan ta mikawa mai gadin shi kuma cike da murna ya mika hannu ya karɓa ya juya ya shige gidan ya rufo get ɗin Dada tana ta jero masa godiya kamar ta ari baki shi kuma mai gadin a zuciyarsa yana cewa 'Da kin san inda za ki je da ba za ki yarda ko naira ɗari ki bani ba bare har dubu guda' Mai napep dai ja ya yi suka tafi ga ya kure kiɗa a napep ɗin ji kake dumm-dummm-dumm m su Hassu sai kaɗa kai ake Dada kuwa sai rausayi kai take daga gefen hagu zuwa na dama tana jin duniya ta mata daɗi tabbas yau ta yarda da maganar kyankyaso da yake cewa garin daɗi yana nesa lokacin da ya leka masai. Suna tafiya mai gadi ya ji horn a kofar gidan da sauri ya taso ya buɗe ya ga Ɗan Ibra ne bayan ya shigo ya faka mai gadi ya ja shi gefe ya shiga labarta masa zuwan su Dada. "Wallahi Allah me ya maka gyaɗar dogo yanzun nan suka bar nan " Ya ce yana kwashe duk yadda suka yi ya faɗa masa. "Taɓ lallai Allah tarfawa garina nono yau za a sha artabu kenan don wannan matar idon cin naira ne da ita ta ki jinin talauci amma kuma sai Allah ya yi ta talakar, tabbas iska tana yawo da mai kayan kara lallai yau Sagiru zai gamu da gamonsa duk da shi ma ba kanwar lasa bane" "Aikuwa na ga take-takenta sai dai Allah daidaita".. "To amin za a ce don har na hango yadda bakinta zai kasance a buɗe wayam idan ta je ta ga inda ƴarta take zaune" Ɗan Ibra ya ce yana tuntsurewa da dariya "Ai na faɗa maka Allah ya sa Hajiya ta aike ka da a ce yau kai ne za ku fita da Alhaji da tsuhuwar nan ta ganka ka kaɗe har ganyanka tun da a gaban Alhajin za ta shiga rattabo maka tambayoyi" "Allah ne ya rufa mini asiri" Ya ce yana juyawa da sauri ya tafi ya isarwa da Hajiya sakon aiken da ta masa Masoyana masu bibiyar rubutuna ina buƙatar ku danna min like a wannn link ɗin na shiga gasa ne da littafin da like 👍 za a fitar da sakamako wanda ya min ina gdy ss https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1 Ga link ɗin [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls* 👇👇👇👇👇 https://youtu.be/Qne4qxr3CGw?si=scht05CDUP-pKVpB *CI-MA-ZAUNE* *NA* *MAMAN AFRAH* *Daga marubuciyar Malamin bogi, Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, Jalli joga, Beelal, Ungozoma da sauran su* *09025576222* 🅿️8️⃣ *DADA* Tun da suka shawo kwanar da za ta sada su da gidan ta fara yi wa idanunta masauki a wani tamfatsetsan gidan wanda take kyautata zaton a nan za a sauke su. Sai dai hasashen ta bai zama gaskiya ba don suna zuwa ko kallon gidan nai napep ɗin bai yi ba ya wuce. . "Yaro ka ce ka san gidan Alhaji Sagirun ko?" Dada da ta ɗaga murya tana tambayar mai napep ɗin ta faɗa cike da mamakin ganin ya wuce gidan da tale zato nan zai kai su. "Wane Alhaji Sagiru kuma? " "Kamar ya wane Alhaji Sagiru kuma to gidanku za ka kai mu? Ko kana ganin bamu yi kama da wanda za su je gidan ba gani kake bamu da dangantaka ko? To ni nan ni ce mahaifiyar Hajiya Amina matarsa ka ga kuwa ai mu ne kirjin shiga gida" Ta ce tana hayayyako masa don ta ga abin nasa kamar raini ne yake son nuna wa bayan an faɗa masa inda zai kai su ya ce ya san wurin gidan ba ɓoyayye bane amma kuma yanzu yana raina mata hankali yana rainawa kansa ajawali. "Ke kika san su ma ni ina na san su, abu ɗaya na sani dai ya ce mini tsamiyar osi zan kai ku gidan yawa shi ne na ce na san gidan saboda gidan ba ɓoyayye bane" "Au to dama shi Alhaji Sagirun har wani mutane ya tara suka cika masa gida ko dai ƴan aiki ne har ake wa gidan lakabi da gidan yawa? Son hayaniya take hana Amina hutawa to da sake uban miji zai auri matar ɗansa" Ta ce tana ji a ranta duk sai ta sa an sallame su sai dai a bar kaɗan don ba zai iyu ita da ta baro kauye don ta zo ta huta kuma sai ta zo ake hayaniya ana hana su rawar gaban hantsi. Shi dai mai napep bai sake cewa komai ba dama karan ya ɗan rage yana gama baya amsa kuwa ya kara kure karan kiɗan. "Dada ki rabu da shi kawai ina jin babu ce take damunsa" Usai ta ce tana kallon Dada. "Yauwa ƴar nan ashe kin gano shi ina jin fa yadda ya ganmu yamutsai ɗin nan zatonsa almajirce za mu je gidan" Ta ce tana ɗakko dubu ɗaya cikin sabbin kuɗin ta mika masa. "Ga dubu nan ka rike canjin tun da ɗari takwas ka ce" Ta faɗa tana mika masa hannu ya miko ya karɓa yana ta godiya "Ahaf ai kin ji zancen yanzu ba gashi ya ware ya karɓe kuɗi ba, ya saki fuska ai na faɗa muku kuɗi masu gidan rana mutum da kuɗi abokin tafiyar kowa" Sun ɗan kara tafiya kenan sai kuwa mai napep ɗin ya tsaya a kofar wani kwaraɓaɓɓan gidan kasa, su Dada basu kawo komai ba don duk zaton su ko wani abu zai karɓa. Shi ma ganin basu da niyyar fita sai ya ce "Ko tare za mu koma?" "Ina ɗin?" Dada ta tambaya cike da mamaki. "To ai na ga kun ki fita ko dai kuɗinku kuke lalewa wanda kika kara mini wato ɗari biyu?". "Kai bana son iya shege kuɗin me zan lale a zama a cikin adaidaita sahu ni in banda larura ma auren namiji da ƴaƴa ai ba zan shiga adaidaita sahu ba sai dai a kai ni duk inda zan je a mota" "Yanzu dai ga shi adaidaitar ya miki ranar da motar bata miki b... "Kai yaro kar ka mini rashin kunya in za ka kai mu inda za mu je to idan kuma ba za ka je ba mu nemi wani ya kaimu don kuɗi ba matsalar mu bace yadda nake surikar mai sadaka da makeken gida ai sai dai tayar mota ta yi kuka" "Wai ina kike so na kai ku ne? Na kawo ku har kofar gida amma sai maganar a kai ku kike haba don Allah kuna ɓata mini lokaci ni da na fito nem... "Ban gane ba to ko dai saɓo kake son yi ai ko ni da nake kauye gidan da nake zaune ya fi wannan sau goma idan baka san gidan ba ai sai ka mini bayani amma ba borin kunya ba kana neman ka naɗe tabarmar kunya da hauka" Ta katse shi cikin ɓacin rai. "Ni kam na ɗebo ruwan dafa kaina ni dai wannan gida aka kwatanto mini in kawo ku". "To tun da uwarka ta haifeka ka taɓa jin mai suna Alhaji ya shiga irin wannan gidan, ai sai dai talaka talakan ma fukara'u" "Ni ku fita mini a adaidaita" Ya ce cikin kufula don ya ga sun ki fita wato ba niyya ango ya kwana da wando. "Kai ku fito daga kwaraɓaɓɓan gwangwanin nan, ina dalili za a ke gaya mana magana a kan adaidaita ai ba girma na bane ku fito mu tare wata kila da tambaya ma je gidan Alhaji Sagiru tun da matambayi ba ya ɓata" Dada ta ce daidai lokacin da ta fito rike da igiyar akuyarta akuyar sai faman meee take, haka suka shiga fito da himilin kayansu su Hassu ma suna ta masa fitsara da tsaurin idanu. Yana shirim jan adaidaita sahun sai ga Sagiru ya fito daga cikin gidan yana sakin wata doguwar hamma. Da mamaki su Dada suke bi sa da kallo don ya musu kama da wani wanda suka sani. Sanye yake da wani yafi ruwan omo(Blue) Yadin ya ci gidansu duk ya yi gashi har da inda ya ɓarke daga kafaɗa. Shi dai Sagiru bai gansu ba da yake yunwa ce take addabarsa. "Lah Dada wallahi mijin anty Amina ne" Hasuu ta ce da ɗan karfi wanda ya sanya Sagiru maido da hankalinsa kanta. A daidai nan ne mai adaidaita sahun ya tafi a ransa yana raya yauma tublar sara,il. Baki sake Dada take kallonsa don ta tabbatar ba wai kama yake da Sagirun da suke nema ba anya ba kama bace suke yi da wancan? To idan ma kama suke yi ai gwara mu sani. Sagiru kuwa har sai da ya zaro idanu ganin Dada da jikokinta yana jin kunyar kayan da yake jikinsa. Wani yamushashshan yadi ne ya gama jin wuyar duniya amma a haka yake lallaɓa shi ga kuma uwa uba kayan ma kamar ko wanki basu da shi in ma suna da wankin to wannan ba karin farko bane da alama an saka maimaici ne wannan. Dada wani irin bugawa zuciyarta take lokaci guda yawun bakinta ya kafe a take wata iska ta busar da laɓɓanta da suke da ɗan damshi so take ta yi magana amma ta kasa harshenta da laɓɓan bakin sun gagara bata haɗin kai ta furta komai dakyar ta yi yaki da hannunta ta ɗaga yatsanta manuniya ta nuna Sagiru a lokaci guda fargaba da wani abu wanda take ganin yana kama da da na sani suka ziyarci kwanya da zuciyarta. Tuno da irin tijarar da ta yi wa mijinta a bainan nasi a kan sai ya barta ta taho har ma da ƴan gari da take ta famkamar gidan siriki ita da ta ɗakko wata guda har da ɗoriya za ta yi azumin ramadan kai a takaice ma dai sai an ganta yanzu kuwa ai karya da ciwo ta ce za ta koma gida tabbas ko daga bacci ta tashi wannan wanda take gani a gabanta ba wai kama yake da Alhaji Sagiru mijin ƴarta ba tabbas ko tantama bata yi shi ne domin kuwa shi ma yana ganinsu duk ya sha jinin jikinsa dama masu iya magana sun ce marar gaskiya ko a cikin ruwa yake sai ya yi gumi. "Sa,Sa,Sa" Dada take ta ambaton Sa a nufinta so take ta furta Sagiru wannan karon da alama ta janye sunan Alhajin daga jikin sunan nasa wanda saboda sa rai har ma take lakabawa ƴarta Hajiya. "Sagiru" Ta samu nasarar warto kalmar sunan daga bakinta. "Dada babu Alhajin yau" Hassu ta tambayeta cike da shekiyanci duk da ita ma ta girgiza da lamarin amma tana so ta ga yadda diramar za ta kaya. "Na yi kutubol da sunan Alhajin Sagiru zan ce kema shegiyar yarinya mai bakin kamar an ɗaga shantu sama" Ta faɗa a fusace tana jin kamar ta kama Sagiru da Hassu ya yi ta duka ko ta huce daga takaicin da take jin zuciyarta a ciki. "Ta bi sunan Alhajin da gudu ba takalmi" Usai ta ce tana danne dariyarta saboda yadda Dada gabaɗaya ta shiga tashin hankali abin tamkar ka zauna kake kallon fuskarta kana sha dariya. "Sannunku da zuwa Dada" Sagiru ya yi karfin halin furtawa a kokarinsa na ganin ya naɗe tabarmar kunya da hauka. Wannan furucin ne ya tabbatarwa da Dada zarginta ya zama gaskiya tabbas Sagiru ne ba mai kama da shi bane kuma ba gizo yake mata ba. A maimakon ta amsa sai ta ɗaga kai tana karewa gidan kallo gidan da ya dace ya amsa sunan mutuwa kusa yadda ya kusa ruftawa ka san dab yake da ya rushe musamman in lokacin damuna ya zo, da a ce bata ga kayan jikinsa ba da sai ta ce ko taimako ya kawowa mutanen gidan amma ganin suturar jikinta ya tabbatar mata da cewa daga gidan yake. 'Kika sani ko yana cikin masu kuɗin da basa sin a san suna yin alkairi ko ɓadda kama ya yi ya kawowa mutanen gidan sadaka' Wani sashi na zuciyarta ya kai mata wannan tunanin. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har ta ji ɗan dama-dama a ranta wannan tunanin tana fatan ya zama gaskiya hakan ya sa ta ɗan tattaro karfin da ya rage a sauran jikinta wanda bai salwanta ba sanadin tashin hankalin da take ciki ta ce "Ina Aminar kuwa?" "Tana ciki" Ya ce yana nuni da cikin gidan duk ya wani haɗa uban gumi saboda kunya. 'Watakila tare suka zo kawo taimakon ita ta tsaya bata fito ba' Zuciyarta ta sake raya mata hakan. "Yanzu za ta fito itama?" "A'a tana kulla daddawa da kukar kaɗi ne" Ya ce cikin sanyin jiki. "Shikenan ta faru ta kare an yi wa mai damu ɗaya sata, wato dai a gidan nan suke da zama na shiga uku ni Saude yanzu Aminar ce take kulla kalwa da kukar kaɗi na siyarwa ne ko na mene ne?' Ta jefawa zuciyarta tambaya. "Shikenan Anty ta koma mai kalwa da kuka" Hassu da Usai suka haɗa baki wajen faɗa. Tsabar takaici Dada bata kara furta komai ba, domin tana buɗe bakinta watakila kukan takaici ne zai fito don haka ta tafi fuuu kamar za ta tashi sama ta nufi kofar shiga gidan gadan -gadan Sagiru da yake tsaye a kofar gidan da sauri ya matsa ya bata hanya ganin za ta bangaje shi. Da kallo ya bita idanunsa a kan ƴar kosasshiyar akuyarta wacce koshin nata ta nuna tamkar tana da juna biyu. Hassu da Usai ma baya suka take mata suna aikawa Sagirun sakon harara. "Salama alaikum" Dada ta buɗe baki take rafka sallama, wata tsohuwa da take wajen jigon dabobi tana basu abinci ta ɗago ta yi wa Dada kallo ɗaya ta kauda kai gefe tana cigaba da abin da take yi ba tare da ta kalli ko iskar da ta ɗakko Dadar ba bare har ta amsa sallamar ta. "Wai ba kowa a gidan ne ake sallama babu mai amsawa" Hassu ta ce cikin muryar irin ta gagararru mai kuma shige da muryar ƴan daba. "Wa kuka ajiye don yake amsa muku sallama idan kuma kun matso sai an amsa sai ku biya kuɗin amsawar'' Matar nan ta ce cikin halin ko in kula. "Ikon Allah na kwance ya faɗi yanzu don tijara dambe sa kishiya sallamar ma sai an biya za a amsa? Ni in ba larura ba ma mai zai kawo ni na sako kafa a wannan gidan mai kamar makabarta ai da ganin gidan nan ya ci sunan tafi da farin likkafaninka saboda ko yaushe zai iya rushewa ya danne mutum" Dada da ranta yake dama a kololuwar ɓaci ta ce Ko kallon su matar bata yi ba ga gidan da girma sai wasu kashin nakuna kashi-kashi tamkar an yi kashin dankali a kasuwa, hakan ne ya sanya ma suka kasa gane inda za a samu Amina to ga shi sai artabu ake wajen amsa sallama bare a tambayi inda take. "To Dada amsar sallamar dole ne rabu da ita kawai" Usai ta ce cikin tsiwa. ."Kaka zan yi" Wani katon saurayi da ya fito da wani katon foo na kashi kato yana tsotsar babban ɗan yatsan sa. "Allah sarki kashin ne to maza je ka banɗakin ka hau foo ɗin in ka gama sai in je in zubar" Tsohuwar nan ta faɗa cikin karya harshe da lallaɓawa. "Ni dai ke za ki je ki ɗora ni" Ya ce cikin ɓaci "Yi hakuri ka ji ɗan kirki maza jeka zan siyo maka alewa" Da sauri ya wuce ya shige bayin inda ya bar su Dada da sakakken baki mamaki al'ajabi ya gama baibaye su ita kuma tsohuwar ta ɗauki wata katuwar silba daga gaban wata tinkiya ta juya ta nufi wani ɗaki daga can ɓangaren da wannan saurayin ya fito ta shige ɗaki. Suna shirin juyawa domin tambayar Sagiru inda Aminar take sai ga wani matashi yana busa sigari yana rike da kare wanda ya saka masa wata sarka a wuya daga ya cire tabar sai ya saki fito tamkar an hura usur. "Baby sannunku da zuwa gidan yawa" Ya ce yana yi wa Dada wani kallo tare da busa mata hayakin taba a fuska. Da baki sake suke binsa da kallo don ba maganar babyn ma ba da su Hassu yake ba da Dada take wai ita ce baby. Shi ma wani ɗaki ya shige daga can ɓangaren da suke jere daga inda suke wato na biyun karshe. Shigowar Sagirun ne ya dakatar da su daga saka da warwarar da suke wato sakar jaki. "Ga can ɗakin Aminar" Ya ce a wani yatsine lokacin kamar ma bashi ne ya ji kunya a waje ba hankalinsa kwance wannan lokacin har wani fisga yake yi. Yana gama faɗar hakan ya musu nuni da ɗakin ya sanya hannu a aljihun wandonsa yya juya yana wani bobbokara tamkar wani mai doro su duka ukun sai sa suka bi bayansa sa kallo har ya fice daga gidan. 'Na ga annabi in na yi hali na gari ni Saude wane irin miji na aurawa Amina kuma' Ta ce a zuciyarta tana jan igiyar akuyar tata suka nufi ɗakin da ya musu nuni da cewa nan ne ɗakin Aminar lokacin ma ana ta kiran sallar azahar. Hassu da Usai ne suka yi karfin halin yin sallama a kofar ɗakin amma ita Dada kasake ta yi tana bin ɓurjajjan kofar ɗakin da kallo. Amina da ta yi nisa cikin tunani tana rike da ledar da take kulla kukar miya babu zato ba tsammani sallamar su Hassi ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lulu har bata san lokacin da ta yi jifa da ledar hannunta ba ta taso fa nufo su. Da gudu suka yo wajen suka rungumeta Dada kuwa kallon abin take kamar almara yadda Amina ta yi wani mugun baki ta rame tamkar ta shekara tana jinya.Wata kwallar tausayin Aminar ce ta cika mata idanu tana ji a ranta ta ma rasa ma'aunin da za ta ajiye tunanin abin da yake faruwa fatan ta ɗaya Allah sa mafarki take don idan gaskiya ne to tabbas ta kaɗe har ganyenta. Sagaggun kafafunta ta ɗaga itama ta shiga ɗakin jiki sanyi kalau tana shiga ta yi wa idanunta masauki a kan kuka da kalwar da Aminar take kullawa. Wani irin kankance idanu ta yi saboda yadda take jin zuciyarta tana mata zafi. "Anty kin ganki kuwa" Hassu da Usai suka faɗa suna tattaɓa jikinta. Bata iya ce musu komai ba sai ta kawar da zancen da cewa "Ku kwashe kayan ku ajiye a can" Ta ce tana musu nuni da kusurwar ɗakin. Dada kuwa har lokacin tana rike da igiyar akuyarta wacce take ta meeee. "Dada sannunku da zuwa ku zauna ga wuri, wannan akuyar fa ya aka yi kuka taho da ita?" Ta ce tana nunawa Dada buhun da yake shimfiɗe a tsakar ɗakin. Ita Dada tamkar an yi wa bakinta dabaibayi haka take ji ta kasa cewa ko da kanzil dakyar ta yi yaki da bakinta ta ce "Amina wai mai nake gani haka kamar almara? Wa na aura miki ne amma na san ko karayar arziki ne ya same shi bai ci a ce kun samu kan ku a cikin wannan bakin talaucin ba" Shiru Aminar ta yi hawaye yana gangaro mata ita ba talaucin ne damuwarta ba ma yadda Sagirun yake CI-MA-ZAUNE babu sana'ar sisi bare kwabo, sai zaman yunwa kawai sai dai ya ɗora rai a ƴar sana'ar da take yi ta siyar da kuka da kalwa ko yanzu ma a cikin kuɗin ne ta bashi ɗari da hamsin wai zai siyo musu rogo wata rana ma sai dai su zauna sa yunwa idan bata da kuɗin ya gwammace ya kwanta yana baccin asara. "Ba magana ba nake miki Amina" Dada ta zafice ta cikin takaici. "Dada CI-MA-ZAUNE ne kika aura mini bashi da sana'ar komai almajirci ya zo nan garin bashi da kowa ma a nan, gidan wannan ma gidan haya ne tun a ranar da ka kawo ni ya fita da kayan lefen ya ɗakko ni ya dawo da ni wannan gidan" Ta shiga basu labarin komai salati Dada ta shiga rafkawa tana yi tana maimaitawa daga ta kai karshen salatin sai ta sake kamo wani. "Na shiga uku ni Saude yanzu fakiri ne dama na aura miki na je na addabi jama'ar kauye da kuri da tinkaho ina ɗagawa kishiyoyi kai ni ga mai ƴa tana auran mai kuɗi har da kai Malam wajen mai gari kara a kan ya barni in taho mu yi azumi a gidan hutu har da akuyata na taho ita ma ta murmure ashe dai gabaɗaya namijin hotiho ne ina zan kai wannan abin maganar ni Saude " Ta kai karshen maganar tana zaunawa daɓas a kasa tare da sakin igiyar akuyar hannunta da take ta faman meeee sai Usai ce ta rike igiyar Dada kuwa wani uban tagumi ta buga tamkar an aiko mata gagarumar mutuwa. *Masoyana ina neman arziƙin ku shiga youtube ku danna min like👍 a kan labarin MALAMIN BOGI gasa ce na shiga da littafin kuma da like za a tantance ina gdy ss* *Ko kuma ku shiga link ɗin can na saman page na youtube direct zai kai ku sai ku min like* MAMAN AFRAH 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls* 👇👇👇👇👇 https://youtu.be/eEW4fiSAxOg?si=koWZsBTo1F3rQZb8 *CI-MA-ZAUNE* *NA* *MAMAN AFRAH* *Marubuciyar* *Malamim bogi* , *Ƙazamin miji, Bonono* , *Ruɓaɓɓiyar igiya, Ƴan adaidaita sahu, Jalli joga, Ƙara,in inna delu, Beela, Ƴar zaman wanka da sauran su* *09025576222* 🅿️9️⃣ Gabaɗaya sun shiga jimamin abin da ya faru don ita Dada ko magana ma bata yi saboda takaci tana ganin duk laifinta ne da ta aurawa Amina wannan mijin amma dama cikin rashin sani ne da ta san haka yake da ta gwammace Aminar ta yi ta zama da Alhaji Sabo duk da yana da larura dai amma ba a rasa abinci ba duk kaskancin abincin kuwa yanzu ta yarda da ake cewa kwaɗayi mabuɗin wahala kwaɗayi kuda ya wahala tun da gashi basu da tsuntsu basu da tarko. Babban ɓacin ranta ma yadda ta kwaso su Hassu har da akuya suka taho gashi yanzu sun gama yaɗawa cewa su tafi birni a can za su yi azumi duka kai cewa ma suke sai an gansu idan kuwa suka koma lallai har sai an saka su a waka kai sai fita ma ta gagare su a kauyan domin gori dai har da goriba sai an musu. Dada ban da yunwa da take addabarta babu abin da suke ji Amina ce ta kama akuyar ta je ta ɗaure ta a wajen da ake ɗaure dabbobin gidan sai da ma suka mata jigo don gudun gutsiri tsoma. Sagiru dai tun da ya fita bai dawo gidan ba tun suna sa ran zai dawo ya kawo ɗan abin saukar baki kai ko da ma rogon da ya tafi siya ne amma shiru tamkar malam ya ci shirwa sai Dada ce ta cire kuɗi aka siyo musu alala sannan suka samu suka farfaɗo ƴaƴan hanjin su daga doguwar suman da suka yi. Har magriba Sagiru bai dawo ba duk da Dada shirya masa tijara tana so ya zo ta juye masa kwandon masifa da jaraba duk da Amina ma ta faɗa mata shi ba ba kanwar lasa bane ba mutunci ne ya ishe shi ba, ita ta yadda za ta samu ta ga Ɗan Ibra ma shi ne abin da ya fi damunta don duk sai sun raina kan su a kan yaudarar da suka mata duk da har lokacin ta kasa ganin laifinta a kan son abin duniya da son ganin ƴarta ta auri mai hannu da shuni. "Dada ni gaskiya yunwa nake ji" Usai ta ce kamar ta saki kuka dama alalar da suka ci ba wani koshi suka yi ba. "Ke dalla rufewa mutane baki ni nan da kika gani cikina tun daɗewa yake kiran ciroma kawai dai dan ba yadda zan yi ne, haka kawai ni ba da cin shinkafa da kaza ba abinci kowane iri ma ya gagareni ai wallahi na yi dana sanin auran Sagiru da Amina ta yi don wulakanci ina sirikarsa ya ganni ya wofantar da zuwana saboda takamar yana auran ɗiyata auran ma na cin amana da yaudara da karya shi ne bai isa ma ya gaishe ni bare in sa ran zai mini sannu da zuwa ya sheka yawon gararamba ya barmu da ciki fal yunwa" Ta ce har vakinta yana kumfa tsabar faɗan da take yi. "Dada dama fa shi ko da yana nan ba ya kawo abinci na faɗa miki CI-MA-ZAUNE ne" Amina ta ce cikin takaici duk da ba laifinta bane laifin Dadar ne da ta aura mata shi a shegen san samun nata amma kuma tana jin tausayinta ga shi ita ma naira saba'in ne kuɗinta. "Kar ki kara ɗunguma ɓacin raina Amina, kar fa ki manta gobe za a tashi da azumi to don Allah wanda ya wuni da yunwa ina zai tashi da yin azumi ni wallahi ba don na yi tijara a kauye ba da gwara na koma can duk tsiya dai ina da tsayayyan abincin ci amma kwaɗayi ya sa na zo inda abincin ma ba zan samu" Ta ce kamar ta kai wa Amina duka. "Haba Dada ba ita ta kai zomon na fa rataya aka bata ya za kike neman ɗaura mata laifi bayan ke kika matsa mata ta aure shi ai maganin... Kafin Hassu ta kai karshen maganar Dada haushi ya sa ta kai wa bakinta bugu. Ɗif ta yi kamar an yi ruwa an tsafe. Suna nan zaune har aka fara kiran sallar isha'i babu Sagiru babu dalilinsa Dada ta kara ɗaukan dubu ɗaya da ɗari biyar su Hassu suka fita suka siyo awara ta ɗari biyar biredi na dubu ɗaya haka Dada ta raba har ƴar akuyarta. ."Haba Dada wai ya za a yi kike raba mana abinci da akuya don Allah mu bamu koshi ba ita bata koshi ba dabba ai ciyawa ya kamata a bata ta ci ba abincin mutane ba. ",Ki kiyaye ni Usai idan ba a bata abincin mutanen ba ina na ga dusa ko ciyawa ko so kike in barta da yunwa ta je ta mutu in yi asara, ni da na taho da ita ta murmure amma kina gani wuni ɗaya dk cikinta ya faɗa" "Ke ma kan ki kin faɗa bare ita" Hassu ta ce tana danne dariyarta ganin idanun Dada duk sun yi zuru-zuru sun faɗa ga wannan uban ɗaurin ɗankwali duk ya zame fatar bakin nan duk a bushe tana ganinta ko sallar isha'i a zaune ta yi saboda yunwa wai jiri take ji ta ringa jin kamar za ta faɗi. "Bari dai ɗiyar nan ai bansan inda Sagiru zai kai tulin alhakina da ya ɗauka yau ba" Ta ce tana jan ɗankwalinta ta gyara ɗaurin ta rufe kunnuwan ruf sai fuskar ta yi tamkar ta biri. "Dada ko akwai zannuwa a cikin kayan naku in shimfiɗa muku" Cewar Amina tana gyara hannun rigarta da kafaɗar take zamewa. "Ai sai ki duba ki gani ni wallahi kaɗan ma na jefar da su Allah ne kawai ya takaita mini asarw a zatona idan na zo kaya za a ɗinka mini masu yawa" Ta ce cikin takaici. "Wai to Dada ya za a yi kwana ɗaki ɗaya da siriki, zaman mu fa kamar ba zai iyu ba da a ce kwanciyar zafi ce ma sai mu kwanta a waje" Hassu ta ce. "Ke ni ina ruwana da wani siriki ba ciki da falo bane sa kwanta da matarsa a can ciki mu sai mu kwanta a nan ɗin in ba larura bam auren namiji da ƴaƴa ta yaya ma zan kwana a ɗakin nan bare har na kwana ɗaki ɗaya da siriki ni da na taho a niyyata a ware mana ɓangare guda mu yi yadda muke so da ɗakuna masu luntsuma -luntsuman gadaje da katifu ashe dai ɗakin da zan kwana ko albarkacin ledar tsakar ɗaki ban samu a ciki ba f... "Gafaranmu dai" Sagiru ya shigo ɗakin yana haɗa hanya kaɗan ya rage ya faɗa kan Dada wacce ta yi saurin yin gefe guda gudun tsautsayi da ba ya wuce rana. Baki buɗe Dada take kallonsa ganin a buge ma yake, har ya gota ta ya sake yin ribas tsautsayi ya sa ya take mata yatsan hannu har suka bada sautin kasss. Da sauri ta janye. "Sorry Dadancy ban gani ba don Allah yaushe kika zo kin mana ba zata" Ya ce cikin muryar wanda ya sha ya bugu. Salati Dada take jerowa tana sakewa. . ."Amin bayan CI-MA ZAINE ne hallaw ɗan ganye mashayi kika aura ?" "Yo ai yanzu shaye ,,,-shaye ya zama wayewa ke ma kan ki Dada na ɗakko... Ya shiga faɗa cikin maye "Inda ranka ka sha kallo ni ina nan ina jiran ka dawo ka same ni ashe dai a buge za ka dawo kwakwalwa a hargitse" Cewar Dada ita kuma Amina ɗaki ta ja Sagirun ta dawo tana share hawaye. Dada ta buga uban tagumi abin duniya ya haɗe mata goma da ashirin. "Ni Saude yau kaza mai tone-tone yau dai ta tono wukar yankanta, yanzu haka yaran nan Sagiru da Ɗan Ibra suka ci amata banda rigar bakin talauci da ya masa kakagida har da zuke-zuken iska yake" Ta ce tana jin tamkar ta rusa kuka don takaici. 'Dada yanzu ɗaki ɗaya za mu kwanta' Usai ta ce "Ke ban sani ba idan kin guji wannan kin fita wajen tsakiyar gidan kina dai gani wani duk karti runtumeman kato ya isa a saka shi a lalle wato ya isa aure amma don tijara wai zai hau fooo ya yi kashi, ga kuma wani mai ruwan inyamurai da ya zo wai don tijara da ɗora hau gado wai ni zai kira da baby ' Ta ce tana rushewa da kuka ita abin ya fi ɗaga mata hankali shi ne yadda za ta kwanta da yunwa ga azumi gobe ga shi ko kyakkyawan koshi gabaɗaya an dagula mata lissafi . Ko ta kan Amina da su Hassu bata bi ba ta tashi fuuu kamar tana tafiya a saman iska ta shige bedroom ɗin tana shiga wani uban wari ya daki hancinta amma ba ta warin take yi ba ita dai ta saukewa Sagiru kwandon bala'i ko ta ji dama-dama. Ita dai Amina tsoron masifar Dada ya sa bata samun karfin gwiwar mata magana ba kar ta sauke a kanta. Bare kuma Hassu da Usai da duk yunwa ta rage musu kuzari. "Sagiru???" Dada ta shiga kwaɗa masa uban kira kamar za ta kai masa duka. Sagiru da yake kwance shame -shame a tsakiyar ɗakin da ko arzikin shimfiɗa bai samu ba. "Yeeeeesssss" Ya amsa dakyar saboda buguwa. "Yassso, na ce yasso uban waye ya ce ka tafi ka bar mini ƴa babu abinci sai dare za ka dawo bayan ka tafi da kuɗin rogo amma babu kai babu rogo yanzu ka shigowa mutane gida hannu yana dukan cinya ka mana same-same? Dama kai matsiyaci ne ashe baka da ko sisi kuka yaudari mutane ka sa na ɗauki zankaɗeɗiyar ƴar na baka amma ka mayar mini da ita mai sayar da daddawa da kukar kaɗi" Ta kai karshen maganar tama wani huci kamar kubuwa ga ta rike kugu kamar mai shirin yin dambe. "A sha ruwa ba laifi bane" Sagirun ya ce yana gyara kwanciyarsa daga kwanciyar gefe ya yi reran cikin maye ya mika hannu ya kai jikin maɗaurin wandonsa ya fisgi karamin wanda idan an ka yake sincewa. A sukwane Dada ya juya har tana yin tuntuɓe a bakin kofar ɗakin tama saurin riko zaninta da ya kwance ta ɗaura hankali tashe ta fito daga ɗakin ba shiri. Su Amina da suke zaune sai ganin Dada suka yi bidik ta fito kamar an jefo ta ga shi ta yi shiru da jarabar da suka ji ta fara yi wa Sagirun. Babu wanda ta tankawa sai ganinta suka yi ta koma mazauninta da ta tashi ta zauna daɓas tana muzurai tare da sakin wata ajiyar zuciya. "Ni Saude na ga ta kaina ashe ɗan duniya na aurawa Amina, yanzu a gabana shegen yaron nan yake jan maɗaurin wando yanzu ba don Allah ya sa na fito ba da shikenan tsirara zai yi" Ta ce a zuciyarta tana jin da na sani ya fi cikin kwando na son zuciyar da ta tafka ta aurawa Amina tantirin mashayi. Haka kowa ya kwanta jiki babu kwari, ko da lokacin sahur ma ya yi babu abin da suka ci sai ruwa kowa ya sha. "Ni dai ba azumin da zan yi gobe haka kawai na wuni da yunwa babu abincin kirki dama da yunwar na kwanta kuma in sha ruwa in ɗore azumi taɓ" Usai ta ce tana zuɓura baki. ."To kar ki yi mana duk wanda ba zai yi azumu bama wunin yunwa zai yi saboda babu wani abincin da mutum zai ci su ma masu abincin sayarwa basa yi da azumi in ma suna yi to sai dai idan satowa za ki don ni da ko biyar ba zan bayar ba. Ah to in ji ma da kuɗin da zan ke sayan abin buɗa baki tun da shi wannan saunan mijin na Amina ba kawowa zai yi ba don na ga ba niyya wai ango ya kwana da wando shi ma dai kuma gani ya kwalfi ruwa ya sha, tun da muka kawo kanmu haka za mu jure ukuba mu rungumi kaddara don ni dai a kan in koma kauye a saka ni a waka da goro da habaici da zunɗe gwara na zauna duk tsananin wuya har sai azumin nan ya kare" Dada ta ce cikin takaici. "Yo ke ma Dada ai da kin masa wankin babban bargo da ko ina ne zai ke zuwa yana samowa amma sai da kika shiga ɗakin jiya sai gaki kin fito ba tare da kin gama masa tass ba yana baki hakuri" Hassu ta ce tana wani haɗe rai tun da basu san dalilin da ya fito da ita lokaci guda ba. 'Ta yaro kyau take bata karko, yaro man kaza ni dai in ba tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe ba mai zai saka na kara kaɗaicewa da fitsararran yaron can Sagiru ba, ai sai dai in mutu da yunwa a kan in bishi cikin ɗaki mutumin da kunya ta yi gabas ya yi yamma' Ta ce a zuciyarta a fili kuma sai ta ce. "Uhmmm in ji mai ciwon hakori kuma mahakurci mawadaci" Ta ce tana tsuke bakinta ta cigaba da lazimi kafin a shiga sallah ta gabatar da sallar. Da safe suna zaune zugum-zugum don kowa tun lokacin har sun fara jin azumin kasancewar kuma yau rana a buɗe take. Sagiru ne ya fito daga cikin kuryar ɗakin ya zo zai wuce ba tare da ya kalli Dada ba ya ce "Barkanmu da safiya, an zo lafiya ya aka baro su, ashe kun zo yin ramadan to Allah baku ku bamu" Ya ce yana mikawa kofar ɗakin ya fara kokarin saka silifas ɗinsa da ya ji jiki tsabar takaici Dada bata ko kalli inda yake ba. 'Asararre CI-MA-ZAUNEN banza wai don mutuwar zuciya Allah bamu mu basu, wato ba ma Allah bashi mu samu ba himm ai wallahi da sake ɗaurin aure da fatalwar bazawara' Dada ta ce a zuciyarta tana jan mayafinta ta rufe fuska. Amina kuwa kai ta sunkuyar ganin Dada ta samu daidai da ita. "Wallahi har gwara auren gidan Alhaji Sabo sau miliyan a kan auren wannan sha ka tafin, duk tsiya dai a gidan Alhaji Sabo akwai tuwon burabusko da miyar kuka amma a nan ko ina kayau " Dada ta ce fuskarta a rufe har lokacin shi kuwa Sagiru ya fice abinsa. "Dada Allah ba don ba don ba da mun lakaɗawa Sagirun nan dukan kawo wuka da ya saitu tuni zai dawo hayyacinsa kinsan dai mu dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka mu ba a taɓo mu bama masifa muke bare kuma da dalili da tuni mun tunatar da shi dangin wa ya aura" Usai ta ce cikin cije leɓe don ta ga abin na Sagiru ya fara wuce gona da iri. "Wallahi dai ni ma haka na gani ai da ko yaya rainin wayon ya yi sauki amma ya yaudari mutane sannan kuma ya zo yana yi wa mutane rainin wayo" Hassu ma ta ce cikin ɓacin rai. Shiru Dada ta yi don ita gabaɗaya ma tsoro Sagirun yake bata tantirancinsa ya yi yawa ai a kalla ko laushi ne ya yi ya ji kunyar abin da ya aikata amma ko a kwalar rigarsa uzurinsa yake hankali kwance. "Ku ne za ku masa dukan?" Amina ta ce cikin tamke fuska. "A'a ni uwaki ce zan masa shegiya figaggiya kar dai ki ce mini Amina kamuwa kika yi da son wannan mai idanun a tsaitsaye?" Shiru Aminar ta yi bata ce komai ba. Da yamma Dada ta fito yin alwalar la'asar sai bin bango take kamar kadangaruwa, tsabar yadda take jin juwa tana kewayata don ji ma take kamar iska ma za ta iya ɗagata *A je dai youtube a min like👍 a MALAMIN BOGI plsss kun ji mutanena😍🤝 ku min in ci gasar nan* 🥺 MAMAN AFRAH *09025576222* [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls* 👇👇👇👇👇 https://youtu.be/coj7sT4KTro?si=GbgZ6t-pReZv1Quf *Marubuciyar* *Ƙazamin miji, Malamin bogi, Bonono,* *Ruɓaɓɓiyar igiya, ƙara,in inna delu, Jalli joga, Beelal, Ƴar zaman wanka, ƴan adaidaita sahu sauran su* *09025576222* CI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣0️⃣ Dakyar ta kama ruwa a bayin ma ta yi alwala ta kama bango ta mike tsaye dakyar, idanun suna mata hazo-hazo . "Yau ba za ki fita daga nan ba sai kin goya ni" Ta tsinkayi muryar sakaran yaron nan wanda ta ji Amina tana bata labari jiya wai aljannu dubu uku ne a kansa shi ya sa ma kwakwalwarsa ta taɓu dama kuma haka aka haifeshi babu cikakkiyar lafiya. Gabanta ne ya yi mugun bugawa da karfi ga shi da ta waiwayo ma sai juwa take rufe mata ido bata hangarsa. "Ni dai ki goya ni ko a yi bikin aljannu dubu a cikin bayin nan" Kulululuu Cikin Dada ya bada wani sauti na tsurewa da na yunwar da har zuwa yanzu ma babu abin da za su yi buɗa baki da shi don shi Sagiru ma tun da ya fita ko keyarsa basu gani ba bare har su saka ran zai kawo wani abu. " Bikin aljannu dubu? A waran ramadanan? Dama ana samun aljannu har su yi biki da ramadan ko dan akwai musulmai ai' Dada ta ce a zuciyarta tana ba kanta amsa. A gefe guda tana ta kokarin yin addu'a a zuciyarta sai dai ruɗanin da take ciki na kasancewarsu ita da Sani ɗan Inna da kuma jirin yunwa da azumin da take ya sa idan ta buɗe idanun duhu take gani yana gilmawa, ga bayin da ɗan tsawonsa haka yake zototo kamar shantu. Dada jin takun tafiyarsa a cikin bayin da yake ko takalmi baya sakawa jin sa a daf da ita sai ta fara bin bango tana shafawa tamkar ta samu ka'aba. "Aljannu ko saka mana kiɗa mu sha rawa" Ya ce yana mika hannu ya rafko Dada, sai a lokacin Dada ta samu nasarar buɗuwar idanunta ta sauke a kan Sani Ɗan Inna da yake sanye cikin rigunan mata kusan guda biyar ya ɗora wata kan wata da alama ma na Innarsa ce rigunan sai hula ta maza wata wacce tsabar dauɗa ta rinar da ita daga fara zuwa ruwan kasa, sai wandonsa wani jabgegen tiri kwata wanda kafar wandon ta yi a saka kafar mutane uku. Hannunsa rike da wata sharɓeɓiyar sabuwar wukar adda sai sheki take da alama ma sabuce. Wani yawu Dada ta haɗiye mukut har tana rike numfashinta na wasu sakanni kafin ta sakin numfashin da wata doguwar ajiyar zuciya. A take ta ji ta daina jin jirin da take ji duk karfinta da take jin wuyar azumi ta tafi da shi sai ji ta yi duk ya gushe. Ta wutsiyar ido ta kara kallon addar sai kuwa ta shammace shi ta yi can karshen bayin ta je ta raɓe daga jikin bango kusa da shaddar da take mata kallon ta kusa ruftawa. "Ki zo ga baki na sun cika suna jiran zuwanmu amaryarta ya kike gudun angonki" Ya ce yana ɗaga addar nan yake wulwulata take wani walwal ga bakin nan nasa sai zubar da yawu yake. So take ta buɗe baki ta yi magana amma ta kasa ga shi tana so ta yi ihu don a kawo mata ɗauki amma tana tsoron ya fille mata kai da addar don ta ji Amina ta ce idan aljannunsa suka zo ƴan gidan ma kowa ta kansa yake har kakar tasa kuwa. Matsowa ya yi Dada ta sauke idanunta a kan fuskarsa da akalla za ta yi wata baya ga ruwa ba sai wani tashin wari yake, matsowa ya yi yana kallon saman banɗakin yana surutai abin da ya kara ɗagawa Dada hanlali kenan yanzu ne take tabbatar da cewa aljannu dubun ne a bayin kamar yadda ya faɗa, a haka ya karaso dab da Dada yana nuna mata addar nan da take ganin kamar kai ai fille mata da ita, nuna ta da addar da yake take yanke wata tusa marar sauti ta kwace mata hakan ya tabbatar mata da alwalar da ta yi karye. "Taho amarya ki bar guduna kar aljannu su ɗauki mini ke" Ya ce yana wani girgiza jiki Dada sai gangaroear hawayen da bata san da zamansu a kwarmin idanunta ba ta yi. Tana ji ta gani ya zo ya mika hannu ya kamo hannunta babu musu ta bi umarnin da zuciyarta take bata na kin bijire masa kar ta yi wasa da numfashinta ya aikata barzahu da addar nan. Bata tantance ba sai ji ta yi ya fisgeta kaɗan su wuntsila daga ita har shi ɗin. Sai da ya kawo ta gabansa tana danne kukan da yake neman kwace mata gudun yin laifi. Ga yunwa ga fargaba yana kawo ta gabansa baya san lokacin da ta durkusa ta ce . "Ina wuni Babana y... "Ni ba babanki bane" "Tun da an gama bikin ka bar ni in tafi sallah zan yi" "Ai biki a gaba za a fara mana ni da ke ne amarya da ango ni ba babanki bane tashi kar ki ɓata kayanki masu kyau" Ya furta cikin wata murya mai kamar tsawa ya mata kana kallonsa ka san yau a cikin hauka yake tuburan. Babu shiri Dada ta mike tsaye a zuciyarta tana ja wa Sagiru Allah ya isa don shi ya ja mata kowace masifa da take ciki da a ce yana gidan kerarre ai da tuni suna can suna jiran a yi magriba su yi asuwaki da naman kaza. Tana mikewa ya juya a hankali ya tafi bakin kofar bayin ya tsaya dama ba wata kofar kirki bace a jiki shi ya sa ma ya shigo Dadar tana ciki. Bake-Bake ya yi a bakin kofar ya bata baya sai kuma ya tattale kafafunsa, ganin hakan Dada ta fara shirin arcewa don bata son wani tsautsayi ya ritsa da ita, tun da in ba tsautsayi ba ta yaya za a ce kana keɓance da mutum da ba cikakken hankali gare shi ba kuma yana ɗauke da makami. Wata dibara ce ta faɗo mata don ita har ga Allah bata shirya mutuwa yanzu ba duk da dama mutuwa ba shirya mata ake ba zuwa kawai take yi bagatatan. Auna tsakanin kafafunsa take wanda ya tattale, take auna kofar don so take ya shammacesa ta bi ta tsakiyar kafafun ta tsira in ya so in ta fita ta yi ta kanta don ta san yanzu ko ihu ta yi babu mai ceton ta. Ganin hankalinsa yana ga surutai mararsa kai da kafa ya sa ta lallaɓa ta shige kofar kafafun nasa, sai da kanta da kafadarta suka fita ta farw hango tsakar gidan kamar an yi shara babu kowa wannan ya kara tabbatar mata da akwai gagarumar matsala matsawar bata kuɓuta ba. Sani kuwa jin an shiga tsakanin kafafunsa sai nasa sauran hankalinsa ya bashi ya matse kafafun, Dada tana ji aka matse saitin cikinta wanda yake kiran ciromawa ba ma ciroma ba. Tana cikin haka sai ji ta yi ya zauna a bayan nata. "Kai jama'a yanzu katon gardin nan ne a bayana bayan ina da igiyoyin aure a kaina kai ai in aka ce maka babu hankali to sai ta Allah" Ta ce a zuciyarta tana dukufa wajen addu'a a zuciyarta Allah ya sa ya ɗaga ɓata baya don tana ganin idan aka jima bayanta zai haɗe da cikinta ko dai ta sume don wahala. Kamar an tsikare shi ya tashi daga bayanta ita ma sai gata a tsaye tana rarraba idanu. Bata ankara ba sai ta ga ɗakko hular kansa ya saka mata. "Kar ki cire" "To" Ta ce tana kara gyaɗa kai. Riga ɗaya ya cire ta atamfa ya ɗora mata a kafaɗa, ya kara ciro wata ya ɗora mata a kanta wato a kan hular kamar dai mayafi haka ya mata. Babu yadda ta iya tana gani ya ɗauki addar ya kama hannunta suka fito daga bayin yadda aka damke hannu Dada kaɗai ya isa ya nuna maka ba mai hankali bane ya yi rikon. Sai da suka zo tsakiyar gidan ya ɗaga addar nan ya karta a kasa, lokacin kowa ya lura da abin da yake faruwa don haka wanda suke cikin ɗaki suka banko suka saka sakata kakar Sani wato Inna da ta je baiwa dabbobi ruwa kamar an ce ta juyo lokacin ya yi daidai da karta addar da ya yi ai tana ganinsa da tsohuwar da suka zo jiya da rana wato bakin Amina amarya mai daddawa kamar yadda suke mata lakabi ai bata san lokacin da ta mika hannu ba a maimakon ta ɗauki daron robarta wanda bata so a barshi su fasa mata. Karamin ɗan tinkiyar da aka haifa ta sunguma cikin rashin sani ta arce ɗaki a guje shi ma ɗan tinkiyan sai ya shiga mutsu-mutsu yana son kwacewa amma Inna ta ce da wa Allah ya haɗa ta in ba da shi ba ta kankame shi a gefen hamatarta sai gudu ta shige ɗaki ta banko tana mayar da numfashi don ta san yau yadda kan nasa ya motsa har ta ɗau adda to sai mai sauran kwana don ta san in ya yi wa Dada da arziki yi wa namanta filla-filla ba gutsin-gutsin ba. Tunkiyar da Kakar Sanin ta ɗauke mata ɗiyarta ita ma ta hangame baki tana kuka ganin an tafi mata da ɗa sai fisga take tana son sincewa daga jigon da aka ɗaure ta. Ɗaya ɗakin dama na wasu yarbawa ne amma musulmai me mata da miji ne da ɗan su guda ɗaya. Tun da mai mijin ya leko zai fito ya hangi Sani da adda yana kartawa a tsakiyar gidan a guje ya koma ɗakin matar tashi da take kan sallaya tana lazimi bacci ya ɗauketa take gyangyaɗi a zaune bata zata ba bata tsammata ba sai ji ta yi an yi ciki da ita wato shi mijin tsabar bai gaji sa duniya bama dama ko zancen mutuwa ba ya kaunar a yi bare kuma yau ya ga mutuwa kusa don haka bai ma kula da matar ba ya yi tuntuɓe da ita ya rafku da kasa bai bari ya ji ciwon faɗuwar bama ya mike da rarrfe ya shiga can cikin ɗakin yana shiga ya banke kofar ya haura kan yamushashshiyar katifarsa ya yi runda ciki yana mayar da numfashi. Matar da ta ga hakan sai ta doka tsaki ta zata tsoron nasa ne da yake da shi baki ta taɓe ta tashi ta naɗe sallayar za ta fito ya ɗora musu ɗan abin dw za su ci, fitowa ta yi gadan gadan ta nufi inda murhun nasu karan karta addar a karo na babu adadi shi ya sa ta ɗago don ganewa idonta aikuwa ta sauke a kan Ɗan Inna yana rike da hannun wata mata da kana ganin kayan da aka libga mata a jiki ka san shirin mahaukaci ne siyam-siyam ta juya a kan sawunta gabanta yama faɗuwa don hatta takalminta a can wajen murhun ta baro su, ta bankamu ɗakin ta rufo kofar don ta tabbata matsawar ta je wajen mijinta ya buɗe mata bedroom to hakika ɓatawa kanta lokaci saboda tsoron bala'i ne da shi. Zama ta yi tana mayar da numfashi. A can kuwa ɗan daban nan wanda ɗakunan suke jere da na Amina. "Gafara dai masu gida" Ya shigo yana wani tafiya yana kanbo shi ala dole niga don karfi yake ji tamkar ma azumin ba ya bashi wahala. Yana tafiya yana wani ciccije wa bai tashi yin arba da oga Sani ba sai da ya zo tsakiyar gidan wato yana dab da shiga ɗakinsa amma bai je kofar ba. Karan karta addar ne ya ankarar da shi wannan karon ya sakalo hannunsa a kugun Dada wacce ta takure waje ɗaya ko motsin kirki bata yi wai ita amarya amaryar ma ta mahaukaci. "Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir ramanir rahim" Ya ce a zuciyarsa ganin mahaulacin gidansu ya yi kamu. 'Wa kake nema?" Ya jefa masa tambayar. . "Wallahi ni ba gandai bane ina azumi' Baffalo niga ya ce a ruɗe don shi bai san bama a kan me ake tambayar shi dai abu guda ya sani yana so ya bada amsa daidai gudun kar kwaɓarsa ta yi ruwa ya shiga amsawa ne don mugun tsoron Sani yake yi kamar mai bare ynzu ga shi da makami kuma ya san duk wanda ya duka ya daki banza don ba wanda zai yi shari'a sam da mahaukaci domin kowa ya san kansa ba nashi bane. A duke Baffalo ya shiga yin baya-baya ɗamamman cikinsa da yake kamar zai haɗe da baya ya shiga karta masa, so yake Allah ya taimake shi kar Sani ya dakatar da shi yana dab da zai shige ya ji ya ce "Za ka taka almutsutsai" Da sauri ya iyo cikin gidan a tsorace don duk duniya babu abin da yake tsoro irin aljani musamman da ake musu kirari da su suke ganinmu bamu muke ganin su ba. Ya san kuwa Sani yana da aljannu manya ma kuwa don idan aka zo masa rukiyya yana jin yadda ake artabu da su. Tsayawa ya yi yana zare ido yana jiran umarni don ba ya so ya shige ɗaki a ce suna ciki. "Wayyo Dada" Usai da Hassu suka haɗa baki wajen faɗa. Amina kuwa sai sharɓar kuka take yi ganin mahaifiyarta tana tare da mahaukaci ga kuma adda a hannunsa ta san matsawar ta masa musu to komai yana iya faruwa. Masoyana a shiga youtube a yi searching littafina malamin bogi a danna mini like masu tambayar basu gane ba idan kun shiga wajen hannun nan kawai za ku taɓa shiknn👍 ina gdy sosai maman afrah🥰 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *Don Allah da son annabi S.A.W ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls* 👇👇👇👇👇 https://youtu.be/_zBSgYkvrzY?si=yglDNBJ5uwIMjHGT CI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣1️⃣ "Kake yi wa amaryata kiɗan indiya tana rawa" Sani ya ce yana buga masa wani tsohon kwanon silbar da yake gabansa. Da sauri Baffalo ya tsugunna ya ɗauki silbar tare da ɗaukan wani tsohon ludai da icce karami ya shiga kiɗan jikinsa yana tsuma. "Maza kike mini rawar indiya amaryata" Kai kawai Dada ta shiga gyaɗawa don zuwa yanzu babu karfin gwiwar furta komai musamman da ta lura ashe tamkar dodo haka ƴan gidan suke tsoron Sani saboda haukarsa. Sosai Dada ta shiga yin rawa tana juyi irin ta indiyawan kamar yadda ya bukata domin ta san yadda indiyawa suke rawa saboda ta sha gani a wayar mutane kuma akwai wani mai shago a kauyansu da bashi da aiki sai kunna wakar indiya tana ganin yadda yara suke dandazo daga gefen shagon suna ta kwatanta rawar wakar da ya kunna. Tsabar tashin hankalin da take ciki na rayuwa ko mutuwa ya sa ko wahalar azumin bata ji, har wani karkaɗa kugun da indiyawan suke take kwatantawa gudun matsala sai kuma ta yi gefe da gefe hatta hannuwa da suke ɗan kare fuskarsu idan suna rawa sai da Dada ta kwatanta tun da ta san gyara ba zai taɓa yin kamar kashi ba. Duk da kasancewar kiɗan ko hanya bai haɗa sa na indiya ba domin baka jin komai sai kwalkwalkwal da Baffalo ya dage yana yi. "Kai ana wani abu a wajen nan wai rawar indiya gaskiya kin cuci indiyawa" Bayerabiyar nan ta faɗa cikin hausar ta da bata fita duka, don duk abin da ake tana gani ta wata karamar tular jikin kofar ɗakin. "Gaskiya ɗan Inna kana shuka tsiya ai sabga da mahaukaci ma sai dole in ba haka ba ka samu sa'ar kakarka ka ce wai ita ce amaryarka in ban da babu hankali" Cewar Kakar Sani da komai yake wakana a kan idanunta. Matsawa Sani ya yi ya kama Dada suke ta gewaya wa shi ala dole rawa suke shi da amaryarsa sai da ya gaji da kansa ya saka ta. "Me kike a nan wajen bar nan" Ya ce cikin tsawa da sauri Dada ta nufi kofar ɗakin Amina har tana haɗawa da gudu don gabaɗaya ma ta manta da batun banɗaki bare ta tuna alwalar sallar la'asar ta je yi a bayin. Sai da ta buga sannan Amina ta yi karfin halin buɗe mata duk da kuwa a kan idanunsu aka yi komai amma tsoron kar ya biyo Dadar ɗakin ya sa suka ɗan dakata sai da ta zo ta buga. "Wash Allah nah" Dada da ta yi zaman dirshan a tsakiyar ɗakin ta ce tana mayar da numfashi da yake duk rigunan da ya yaɓa mata sun faɗi a garin rawar indiya hula ce kaɗai a kanta ita ma cisgewa ta yi ta jefar. "Allah ya isa tsakanina da Sagiru yaron nan ya ɗauki alhakina da ya sa na baro kauye na taho domin zaton Amina a gidan naira take, yanzu babu damar komawa kauye a saka ni a wakar na yi karya ga shi a tara ko wuri ɗauka ba sai yau za a kai azumi ɗaya" Ta ce tana rushewa da kuka domin gabaɗaya ta tsorata da lamarin mahaukacin bare kuma a ce ana zaune gida ɗaya da mahaukaci wannan kam ya zama tsautsayi zagin mahaifi. "Dada baki ji yadda kirjina yake bugawa ba in na ga yana wasa addar nan a kasa ba" Usai ta ce cikin tausayin kakarta. "Ni wallahi baki ji yadda nake shiga tashin hankali ba" "Ku ɗin ma kenan da baku bane a hannunsa ni ai gabaɗaya ma na saddakar cewa kai zai fille mini domin kuwa babu tabbas a al'amarin wanda bashi da cikakken hankali. "Wallahi Dada kwanaki da ya damki wuyan kakar tasa sosai ta ringa makyarkyata mun ɗauka ma ta mutu Allah ne ua sa da kwananta a gaba shi ya sa ita ma bata yadda ta tsaya gabansa in haukar ta motsa don wani lokacin sai ki ga kamar mai lafiya" Amina ta ce cikin tausayawa mahaifiyarta. "Ai da ni da ita ba maraba tun da ni ma ɗan uwan hakan ne tun da har gwara ita hannu ne ni kuwa adda ce kin ga kuwa ai babu gwara amma ni shegen yaron nan Sagiru ne duk ya jaza mini da a ce na san talauci ya masa katutu da ba zan tarki zuwa bama to rashin sani ya fi dare duhu" Ta ce tana buga uban tagumi da ta tuna ko abin da za su kai bakinsu babu idan an sha ruwa. Bayan ya yi jifa da addar hannunsa ya juya ya shige ɗakin kakarsa wanda suka raba ɗakin shi a bedroom ita a falo, yana shiga ta shiga makyarkyatar tsoronsa sai da ta ga ya fashe da dariya ya zauna sannan ta ki hankalinta ya kwanta dakyar ita ma don bashi da iyaye sun mutu kuma babansa shi kaɗai ne ta haifa a duniya shi ya sa take zaune da shi amma in ba haka ba babu abin da zai haɗa ta zama ɗaki ɗaya da mai taɓin hankali. Kowa ganin Sanin ya shige ɗakin kakarsa sai aka fara lallaɓowa ana fitowa don samun abin da za a kai baki idan an sha ruwa. Baffalo kuwa tun da Sani ya yi wurgi da addar nan yana ganin ya shige ɗaki ya yi wurgi da ludai da iccen da yake kiɗa don ko bayan an dakatar da Dada an sallameta bai daina kiɗan ba tun da ba a ce ya bari ba gudun kar ya yi laifi sai ya cigaba da kiɗan, don haka a sukwane ya yi hanyar waye ba tare da ta shiga ɗakinsa ya ɗauki kuɗin da ya zo ɗauka ba wanda zai je siyan kankana da lemo. "Hassu ke da Usai ku tashi ku siyo mana abin da za mu yi buɗa baki kun ga an kusa yin magriba " Cewar Dada. "Dada a wannan makotan namu na dama matar tana siyar da dankalin hausa kima tana siyar da man gyaɗa ko shi za su siyo a soya" Amina ta ce cikin sanyin murya don tana ganin ita ya kamata ta tanadar musu abin buɗa bakin sai dai bata da halin yin hakan. "Ku sayo dankalin na ɗari biyar man na ɗari uku" Ta ce tana mika musu ɗari takwas. Karɓa suka yi suka tafi. "Ai ba don wancan mutumin arzikin ya bani kuɗin nan ba ban san yadda zan yi ba wallahi ga shi dai su nake gurgura" Cewar Dada tana kwantawa a kan buhun nan da yake shimfiɗe a falon shiru Amina ta yi saboda ta kasa cewa komai ma duk da dai Dadar ce silar faruwar komai amma kuma kaddarar ce a haka. Da ɗan damar dankalin haka su Hassu suka fere suka soya, sai kuma wani garin kunu da wata yarinya ta kawo talla Dadar ta saya da tsamiya suka dama kunun suka saka hasfatin don Dada ta ce wallahi ba za ta sayi suga ba. Har suka sha ruwa babu labarin CI-MA-ZAUNE. Da yake dankalin rabawa aka yi kowa ya ɗauki nasa Dada a biyu ta raba ta ce sai da asuba za ta ci sauran. "Assalamu alaikum ya mutanen ɗakin nan" Sagiru ya shigo da sallama cike da shekoyanci fuskarsa sanye da wani gilashi, banu wanda ya amsa sai Amina don haka sai da ya nemi wuri ya zauna ya ce "Babarmu Dada sannu da shan ruwa Allah karɓi ibada" Ya ce yawunsa yana tsinkewa jin wani kamshi hakan ya sa yake fatan a san masa abin daɗin da ake ci shi sai yake jin in ma ba karya hancinsa ya masa ba sai yake jin kamar kamshin doya da kwai. Dada kuwa wani abu ne ya tokare mata a makoshi jin yana ambatar ita ce Babarsa abin takaicin ma tun safe baya nan yanzu ma alamu da dama sun nuna akwai wata a kasa. Jin bata amsa ba kuma babu wanda ya kula shi hatta Amina ya ga sai wani abu take ci a ƴar roba sai karan taunar kowa yake ji amma shi bakinsa wayam. "Wai anya Amina kina son shiga aljanna kuwa? Yanzu a ce an kai azumi amma mijinki ya dawo ki bar shi haka nan" Ya ce don ya ankarar da ita ta sallame shi. 'Ikon Allah na zaune ya faɗi wato su dai maza har kullum mata suke kaiwa wuta da bakinsu kasancewar an ce aljannar matan tana karkashin mazajan, shi ya sa su mazan suke tunkaho basa ganin abin da suke yi wa matan in ban da laifi ma tudu ne ka danne naka ka hangi na wani ya za a yi tana matsayin matarsa ba ya bata abinci, yau ma tun safe da ya fita ko gishiri bai bar mata ba sai yanzu bayan magriba ya dawo kuma amma shi ba ya tunanin nata hakkin sai nasa to mai ka bar mini da zan kawo maka' Ta ce a zuciyarta a fili kuma sai ta ce "Ka yi hakuri" Ta ce tana tashi ta ɗakko masa ruwa a wani jug da ta siya ta zo gabansa ta ajiye masa ta koma mazauninta ta zauna. Kuri ya mata da idanu yana jiran ya ga an miko masa wani abun amma ɗif babu niyya ango ya kwana da wando. ."Dada Amina har kashina ta haɗa ta cinye?" "Kashin uban me wai ka dameni, ka ba wani shege ne ajiyar wani abu da za a yi kashi da kai ka fita idona in rufe ka bar mu muji da ɗawainiyar kanmu da muke ɗauka" Ta ce cikin hargagi don dama a kufule take da shi. "Maida wukar Dada kamar wanda dama kike jira? To shikenan ai tun da ku kaɗai za ku ci wanda ya ci shi kaɗai kuma shi kaɗai zai mutu" Ya ce yana mikewa ya kama hanyar bedroom ɗin. "Ashe ma biki aka yi a gidan nan da la'asar ɗazu Baffalo yake bani labari a majalissa" Ya ce lokacin da zai shige bedroom ɗin yana kunshe dariyarsa don Baffalo ya faɗa masa komai ko ɗazu ma da suka je masallaci shan ruwa ya karasa masa a hanyar zuwa masallacin. Wani uban tsaki Dada ta ja don ta lura cin fuska yake son yi mata. Amina tana jin takaicin abin da yake sai dai tsoronsa take, su kuma su Hassu sai sun yi yinkurin yin abu sai Dada ta dakatar da su. *DARE* Ko da ya dawo daga yawonsa a buge ya dawo don haka sai ya shige ɗakin ya samu wuri ya zauna da yake lokacin da ya shigo ma sai da ya so yi wa Dada tijara amma sai ta watsa yinsa duk da a bigen yake amma Amina ta ko haushin bakaken maganganun da ya yi saboda haka yana shigewa ɗakin Amina ta bi bayansa a fusace. "Sagiru ya isheka haka ba a wasa dan iyaye kuma uwa ko mahaukaciya ce sunanta uwa" Ta ce tana kama tsantsa banza ya mata sai da ya bari ta kai aya tana huci ya tashi tsaye ya ɗaga hannu hagu da dama ya faffalla mata mari. Wani uban kara Amina ta saka wanda da karan marukan da ta sha da kuma karan da ta kwalla Dada bata san wanda ya ɗugunzuma zuciyarta ba tana jin zunzurutun bakinciki da takaici cikin takun da bai wuce huɗu ba ta ganta a bedroom ɗin ta ma manta da cewa mata da miji ne kuma siriki ne tafin hannunta har kaikayi yake mata a kan marin da takanas ta je don ta ramawa Amina ta nuna wa Sagiru cewa Aminar tana da gata ba kamar yadda yake ganin bata da galihu bane. Tana shiga ta gan su a tsaye carko-carko Aminar rike da kumatu shi kuma yana rike da kugu sai huce yake kamar wanda ya yi tsaren gudu, Dada har za ta ɗaga hannu ta dalla masa nasa marukan kamar an ce ta kalli kwayar idanunsa ta cikin hasken fitila wani irin jaaa ta ga idanun nasa sun yi tamkar jini ya taru wannan ya tabbatar mata da ba karamin buguwa ya yi ba wato a maye yake hannunta ta damke tana ba kanta hakuri a zuciyarta. Cikin karfin hali ta daddage ta ce "Zo mu tafi Amina Allah zai saka miki" Ta ce tana kama hannun Aminar suka fito daga ɗakin don tana tsoron ta mare shi ya mata tijara dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, tun da idan ba a buge yake bama fitsararre ne bare kuma ya bugu. Ki yi kwanciyarki kin ji ai Allah yana madakata zai yi maganin duk wani azzalumi " Dada ta ce "Haba don Allah Dada na ɗauka ma rama mata za ki yi" Usai ta faɗa . "Ni wallahi duk a zatona idan kika shiga sai dai muke jin karan mari falfalfal' Hassu ta ce 'Haba ɗiyan nan yo karen hauka ne ya cijeni ko kuwa hauka nake wannan yaro mai ido a tsakiyar ka kamar duniya haka kawai ya je ga mangareni a banza in shiga uku shi da ba a hayyacinsa yake ba' Dada ta faɗa. Shiru suka yi babu wanda ya sake magana sai karan sheshshekar kukan Aminar da suke ji. 'Da mai ya kai ki musu da miji ai ko kana mutunci ba ka zakewa amma kya tsaya faɗi in faɗa da miji' Cewar Dada don ganin ta kawar da maganar. "Ke kuwa Dada tun da aka zo garin nan kamar an dakusar da zuciyarki yanzu sa,insar ce da miji babu kyau bayan ... "Ke ni kar ki dame ni kin fi so take masa musu yana jigbarta a aikin banza ko ni da girmana sai in ke shiga faɗan ma,aurata" Ta ce cikin waskewa don ganin ta dakatar da maganar. Bayan kowa ya yi bacci Dada da ta ajiye sauran kununta a kofi fa kuma sauran dankalinta a yar roba ta ce idan ta tashi da shi za ta yi sahur. Sagiru da cikin dare ya falka daga baccin lokacin mayen ya sake shi sai wata yunwa da yake ji falon ya nufo da rarrafe ta hasken farin watan da ya shigo ɗakin ta window ga Dada wacce take jikin bango dan kafin hali sai ya karasa ganin kofi da ɗan kwano, dibara ce ta faɗo masa ya lallaɓa ya kai bakinsa jikin yatsun kafarta hakori ya saka ya shiga ɗan gwigwiyar yatsun da hakori Dada cikin bacci ta ji ana gwagwiyar kafarta hannu ta kai cikin bacci ta doke kafar ta cigaba da bacci sai da ya mata karo uku sannan ya tabbatar baccin take kofin kunun ya ɗauka ya kurɓe duka yana jin yadda zakin ya ji kakau har yana lashe baki. A hankali ya ɗauki robar dankalin, ya kwashe duka ya zuba a aljijunsa ya juya yana lallaɓawa don kar wani ya ji shi. Har ya shige bedrioom ɗin babu wanda ya ko da motsawa ne a haka ya samu wuri ya kwanta yana mika hannu cikin aljihun yana ɗakko dankalin ya jefawa a baki. *Masoya domin ƙaunar Allah da manzon sa S.A.W ku yi searching littafina MALAMIN BOGI a youtube ku danna min like 👍masu min magana suna cewa basu gane mai za a yi ba, kawai daga kun shiga wajen hoton hannun nan za ki taɓa, a taimakawa mar,atus saliha gasa ce aka sanya mana ta marubuta. Sannn ina ɗora Link ɗin a saman page a duba a ɗauka Luv you Fisabilillah😍🥰* 🤝 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 👇 https://youtu.be/34d9aLUO7k4?si=4Zjm3y9K90Kja14G *Assalamu alaikum! Don Allah a taimaka mini da LIKE a wannan Link ɗin gasar rubutu aka saka mana a youtube. Link ɗin nan a sama👆 Na gode sosai* *Daga marubuciyar* *Ƙazamin miji,* *Malamin bogi, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, Ƴar zaman wanka, ƴan adaidaita sahu, Jalli joga, Ƙara,in inna delu, Beelal da sauransu 09025576222* CI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣2️⃣ Budurwa ce ƴar kimanin shekara ashirin take sakkowa daga matakalar benen sanye take da riga da farare mai pink ɗin plower a gaban rigar kanta babu ɗankwali ta yi parkin na gashin kanta da ribon hannunta rike da waya tana tahowa kamar bata son taka kasa. Fara ce amma kana ganin farin ka san na mai ne don gabaɗaya tabon kuraje ya fito jefi-jefi a fuskar. Tana gama sakkowa daga step ɗin ta karasa kan ɗaya daga cikin kujerun tangamemen falon da suka kawata shi. Baka jin karan komai a falon sai karan TV da take ta aikinta gabaɗaya kana ganin fuskar budurwar ka san tana cikin ɓacin rai lokaci-lokaci tana saka wayar a kunne sai kuma ya cire ta saki wani guntun tsaki da alama wani take son samu a wayar kuma bata same shi ba. Cilli ta yi da wayar a kan kujerar ta saka tafin duka hannunta ta rufe fuskarta tana jin raunin zuciyarta na karuwa a gefe ɗaya son da take masa tana jin yadda wutar son nasa take ruruwa tana kara yaɗo a dukkan sassan jikinta cikin jini da tsoka tabbas ko da ba a faɗa mata ba ta san ba za ta iya rayuwa a duniya ba matsawar bata tare da SURAJ ba domin shi ne farincikinta kuma shi ne walwalarta matsawar aka samu saɓanin hakan wato bata same shi a matsayin abokin rayuwa tana ganin daga ranar numfashinta zai tsaya za ta yi bankwana da duniyar ma baki ɗaya idan kuwa har mutuwa bata ɗauke ta ba to za ta rayu cikin matsanancin hali da kunci wanda har sai ranar da numfashinta ya bar gangar jikinta don ta tabbatar da son SURAJ za ta mutu!. "Haba zuciyata ta yaya kike kaunar wanda ba ya kaunarki? Kin san a duk lokacin da aka samu saɓanin zuciyoyi ɗaya tana so ɗaya bata so to dole sai wacce take son ta fuskanci matsaloli da kalubale kai ko da a ce ɗayar nata son ya fi yawa to sai ta yi hakuri ta jure daga wacce nata son ya zama kaɗan" Ta ce a zuciyarta tana tunani wanda take kaunar ma bata gabansa dama ya faɗa mata shi ba ya son ta abin da ta kasa ganewa ta rasa wane irin murɗaɗɗan mutum ne Suraj da duk abin da ya saka a gaba shi yake yi babu ruwansa da kowa. "Baby Iky" Ta tsinkayi muryar mahaifiyarta, duk kokarinta na son ganin ta danne kwallar da ta taru a idanunta amma kuma sai da ta ganganro da sauri ta sanya hannun nata da ta kare fuskar da shi ta share hawaye, Mummy tata kuwa da sanyin jiki ta karaso ta zauna a kusa da ita ta dafa kafaɗarta tana jin babu daɗi a zuciyarta ganin ɗiyarta tilo a cikin damuwa. "SURAJ" Mummy ta ambata don ta san duk duniya ƴarta bata da damuwar da ya wuce SURAJ ɗin babu abin da ta nema ta rasa sai shi, shi kaɗai ne matsala da damuwarta ko da hawayenta sum zuba to ta dalilinsa ne. "Shi ne Mummy tun jiya nake kiran wayarsa amma ya ki ɗauka kuma tana shiga wani lokacin ma sai dai ya katse mini" Ta ce tana kifa fuskarta a kan cinyar Mummyn ta rushe da kuka. "Ni na rasa yaron nan mai yake takama da shi, duk son nan da kike masa amma a banza to ya yake so ki masa ko so yake ki ciro zuciyarki ji danka masa ya gani sannan ya yarda da son da kike masa" Mummy ta ce cikin faɗa. "Zan iya komai ma a kansa zan iya ɗayo fatar jikina na shimfiɗa masa ya taka ya wuce zan iya bashi komai Mummy amma ba yarda ne bai yi ina son sa ba shi kawai so na ne ba ya yi" Ta ce cikin muryar kuka. "Na gaji da wulakancin nan da yake miki kuma ki rubuta ki ajiye sai SURAJ ya so ki kamar ya mutu don duk hanyar sa zan bi sai na bi ko zan yi yawo tsirara kan bin malamai da bokaye sai kin mallake shi, ba wai ke ce za ki shimfiɗa masa fatar jikin ki don so ba shi da kan shi ne zai so ki kamar ya mutu sai ya zo yana durkusa miki yana neman soyayyarki a lokacin ne za ki mayar masa da hannun agogo baya don sai ya ɗanɗana kuɗarsa". "Ina son ki Mummy in kika mini haka kin min komai a rayuwa, ni kuma duk ranar da na samu damar nan sai ya gwammace kiɗa da karatu don sai ya zama tamkar bawa a fadar saraki sai na wulakanta shi na kaskantar da shi" Ta ce cikin cin alwashi don tana ganin babu wani abu da yake sosa ranta sama da SURAJ kuma ba wai wulakanta ta yake yi ba kawai yana nuna halin ko in kula a kanta wannan ne abin da yake ci mata tuwo a kwarya saboda tana ganin ta fi karfin ko wane irin cin kashi a duniya. "Yawwa my Baby ai dama maganin kowane shege karen maguzawa kuma in baki musgunawa namiji ba ai ba ni na haife ki ba, ai namiji zuma ne sai da wuta!" "Shi dai ramin kura kurarre ne kuma sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba" Murya Alhaji da ta karaɗe musu kunnuwa ta cika falon. "Daddy barka da safiya" Ikram (Iky) Ta ce cikin wayancewa. "Barka" Ya ce kawai yana nufar dining domin karyawa saboda shi dai a duniya ya san bai yi sa'ar mata ba wacce za ta ba ƴarsa tarbiya ingantacciya kullum tufka yake tana masa warwara duk ɗorim da ya yi wa Ikram to sai Mumynta ta sauke mata haddar ta nuna mata nata karatun da bashi da madogatara ko hanyar ɓullewa. Wata matashiyar budurwa ce ta shigo falon bakinya da sallama tana rike da tire mai ɗauke da filas guda biyu da wasi plates a gefe ta zo ta jera a kan dining ɗin dama ta kawo komai waɗannan ne suka rage. Tana gama ajiyewa ta koma da tiren, Ikram da Mummy ne suka nufi dining ɗin suka zauna Mummy sai wani taɓe baki take tana aikawa Daddy harara. Da kansa ya zuba abin da yake bukata Ikram ce ma ta ɗauki kofi ta haɗa masa tea don ita Mummy dama ya san bata da lokacin masa aiki. "Allah miki albarka" Ya ce yana ɗaukan cibi (Fork) Ya yi Bismillah ya kai dankali da kwan wanda aka yi wa sorce bakinsa. "Amin Daddy" Ikram ta ce tana kurɓat tea. "Mu ma da ba a saka mana albarkar ba tuni namu iyayen sun saka mana" Cewar Mummy tana haɗa custard. Bai kula ta ba don tuni ya bai wa bango ajiyarta, har ya kammala ya ɗauki jakar tafiya office ya fita direba ya ja motar suka tafi. "Baby zan tafi office fa " Mummy ta ce tana rike da hand bag tata. "To Mummy ni ma yanzu zan fita scul... Bata kai karshen maganar ba tsohuwar da take kwashe kwanukan da suka kammala cin abinci ce kofin glass ya kufce daga hannunta ya faɗi ya fashe sai ruwan ya fatsu a fuskar Ikram a harzuke ta tashi daga danna wayar da take ta ajiye wayar a kan kujera ta ɗaga hannu hagu da dama ta kai wa tsohuwar kyawawan maruka guda biyu. . "Da kyau Baby Iky kin min daidai su talakawa basu san darajar kaya ba gani suke masu kuɗi kamar a bola suke tsintar kuɗin da muke siyan kayan, kuma ki sani a cikin albashinki zan cire kuɗin kofin da kika fasa" Ta ce hankali kwance tana juyawa ta fice abinta. "Minti biyu na baki ki zo ki sharewa mutane wajen nan sakarai kawai" Ikram ta ce tana haurawa sama. Tsohuwar da take dafe da kuncinta tsabar zafin marin da ya ziyarci fuskarta da ta fara yamushewa saboda girma a kalla ta haifi Mummyn ma amma rashin tausayi da rashin sanin darajar ɗan adam ya sa suke wulakanta duk wani wanda yake karkarshin su saboda Allah ya basu dama. A hankali ta fita daga falon jikinta yana sanyi kalau ga kuma karkarwa da jikinta yake na zafin marin da yarinyar da ta yi jika da ita ta mata su amma kuma mahaifiyar yarinyar ma tana nuna mata cewar daidai ta yi saboda babu tarbiya da sanin ya kamata. "Allah na gode maka kai ka san dalilin da ya sa baka bani haihuwa ba da a ce na haihu da ƴaƴana ba za su bari a ci zarafina ba, da a ce na huihu ƴaƴana ba za su bari na taho nema ba su za su nemo mini amma kasancewar bani da ƴaƴa kuma mijina ya mutu saboda nake samun abinci nake aikin nan Allah ka bani hakuri da juriya a kan neman halal" Ta ce lokacin da take wanke kwanukan a kicin don tana cikin share kofin da ya fashe lkram ɗin ta fito sanye da wani karamin mayafi da ta yi rolling ta fito tamkar ba ƴar musulmi ba ta fice, tana jiyo karan fitar motarta daga gidan. *SURAJ* Fitowarsa daga wanka kenan bayan ya saka fararen kaya doguwar tazarce da hula ya feshe jikinsa sa turaruka masu kamshi, sallaya ya shimfiɗa ya gabatar da sallar walaha tare da yin addu'a ya shafa ya ɗakko carbinsa na dannawa white colour ya sakala a ɗan yatsan sa, sumar kansa da take a kwance ya kara fesa mata turaren gashi mai sanyin kamshi ya saka brush kumb ya kara kwantar da ita sai ya ɗora hula jakar office ɗinsa ya ɗauka har zai fita ya tsaya kara kallon gadonsa da yake a ɗame da zanin gado mai kyau wanda jiya Hajiya ta bashi ya shimfiɗa to da ya tashi da safe sai ya kara gyara gadon yana kara yaba kyau da ingancin yadin da kuma ɗinkin da aka yi wa zanin gadon tamkar ba a Nigeri,a aka ɗinka ba. A al'darsa bai yarda kowa ya shigar masa ɗaki ba shi ya sa yake gyara komai nasa amma bai yarda ƴan aikin gidan sub gyara masa ba saboda yana da tsantsani ba ya so ma su gyara masa. Ɗauke da jakarsa da take sakale a kafaɗarsa ya fito daga ɓangarensa sai kamshin turarensa da yake tashi. Babban falon ya shiga bakinsa da sallama sai da aka amsa sannan ya shiga, har sun zazauna a dining ɗin suna taɓa hira da alama shi kawai ake jira. Kan kujera ya karasa ya ajiye jakar sannan ya karasa dining ɗin kafin ya zauna ya durkusa ya gaishe da Abbansa, sannan ya gaishe da Umminsa. "Yaya ina kwana" "Lafiya lau my Ruma, ya saukin jikin ki" Ya ce yana zaunawa. "Da sauki Yaya gobe zan fara zuwa scul tun da na ware" Yarinyar ƴar shekara goma ta ce tana dariya. "Yawwa haka ake so Allah kara lafiya". ."Amin yaya" Ka'idar su idan suka yi Bismillah suka fara cin abinci ba sa magana har sai an kammala. "Ummi wannan wane turaren wuta ne aka kunna a falon nan mai wani irin daɗin kamshi?" Ya tambaya yana wani lumshi idanu tare da kara baza hanci yana shakr kamshin turaren wutar da ta saka a bunner. "Yanzun nan Abbanka ma ya gama tambaya ita ma Ruma ta tambaya sai na ce su bari sai ka zo in muku bayanin tare don na san kaima kana zuwa sai ka tambaya" Cewar Ummi tana dariya. "To muna sauraren ki kar ki makarar da mu wajen aiki" Abba ya ce tana dariyar shi ma saboda rayuwa ce suke cikin farinciki. "Waɗannan kayayyakin gabaɗaya wajen MAMAN AFRAH na yi oder, kowa na sauya masa bedsheet jiya to wajanta na siya, zannuwan gado ne masu matukar inganci da kwari basa koɗewa basa gashi, ni ma wajen aminiyata na gani na tambaya ta bani no ta. Tana sayar sa zannuwan gado masu bargo, da masu labulaye, da masu filo huɗu da mai filo biyu, tana siyar da turarukan wuta da turare na jiki da na kaya da humra freshner, tama sayar da set na kayan gyaran gashi mai cire dandruf ya sa gashi baki da sheki ga abin wankin banɗaki da na mopping da turaran wanka, atamfifi lesuna dogayen riguna shaddodi har da ɗinkakkun kayan yara masu kyau da inganci abin jin daɗin har sari take bayarwa duk yawan da mutum yake so tana aika masa ko a ina yake" "Kai irin wannan lissafi Hajiyata kamar wanda kike mata talla sai yabawa kike" Abba ya ce yana dariya. "Ba yabawa bane Abban yara kayanta ne wallahi babu ha'inci ba cin amana komai ka saya sai ka yaba". "Au ni Ummi ki bani lambar wayarta tun da gobe za a tashi da azumi wajen ta zan saya kayan rabon salla da zan yi" SURAJ ya ce yana fito da wayarsa daga aljihu". "Aikuwa ni ma wajen ta zan saya" Abba ya ce yana tashi tsaye don tafiya wajen aiki. "Ummi bani lambar". "Ni na tafi sai na dawo idan na dawo za mu zauna sai mu ji yadda za a yi ki mana oder" Cewar Abba. "A dawo lafiya Allah tsare" Suka haɗa baki wajen faɗa". "090? Ka rubuta?" "Eh Ummi". "09013181851 za ka iya kiranta kuma za ka iya mata magana don da lambar take wtsapp sai ta baka samfura ka gani ka zaɓa" "Ashe ma har tana tura samfura".. . "Eh mana kawai dai bata son wanda ba siya zai yi ba ya mata magana" ."Bari na karanto ki duba mini ko daidai na saka 09013181851". "Yawwa daidai ce" "Sai na dawo" Ya ce yana ɗaukan jakarsa. ."A dawo lafiya Allah bada sa'a". Cewar Ummi. "A dawo lafiya yaya".. "Amin ya rabbi" Ya amsa musu yana fita. Alhaji Matawalle da Hajiya Zaituna da ƴaƴan su biyu SURAJ da Ruma suna zaune a Garin Gumel a unguwar wazirawa. Juyi Dada ta yi idanunta a rufe tana sakin wata hamma, idanun ta buɗe jin karan kiran sallah da sauri ta tashi zaune tana kankame robar dankali tare da kunun ta mayar gefe guda ta ajiye ba tare da ta buɗe su ba tsaye ta mike tana kunna fitilar ta fita ruwa ta ɗauka a buta ta nufi bayin tana jin faɗuwar gaba gudun kar abin da ya faru da ita jiya da la'asar ya sake faruwa da ita na Sani da ya bita. Da sauri ta kama ruwa ta fito da sauri ta yi alwala ta nufi ɗaki jin koea na gidan ya tashi ta koma ɗaki "Ke Amina, Hassu, Usai ku tashi mana ko ruwa kwa sha tun da ku kun cinye dankali da kunun naku ai ni kam bana iya ɗoren nan ba shi ya sa na ajiye kayana, ku yi sauri kar a kira sallar ku makara" Ta ce tana zaunawa ta mike kafa ta janyo ƴar robar dankali da kuma kunun nata duk kauɗin nan da take yi Sagiru yana jin ta. "La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Dada ta ɗauki salati da mugun karfi duk ta karaɗe ɗakin tana tafa hannuwa karan salallamin da take yi ne ya tashi duk kan ƴan wanda suka yi tunanin ma ko wani gagarumin abu ne ya faru. "Dada mai ya faru?" Amina ta tambaye ta a firgice ko wartsakewa daga baccin bata yi ba. Masoyan rubutuna a shiga youtube a mini like a kan littafin malamin bogi ina gdy ss [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls*👇 https://youtu.be/y_DlU3d7lzs?si=LPgsMFnnVlyjZMsW lCI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣3️⃣ "Ya ɗin nan mai ya faru Amina wane ɗan gwafar uban ne ya shanye mini kunu da dankalin da na ajiye zan yi sahur?" Ta ce tana dangwarar da robar can gefe robar ta suka gangara suna gwaruwa da juna. "Dankali da kunu kuma Dada?" Hassu da Usai suka faɗa cikin mamaki ita ma dai Aminar mamakin take don ta san daga ita har su Usai babu wanda zai ɗauka mata amma abin mamakin da tambayar waye zai shigo ɗakin har ya je ya ɗauki dankalin da kunun a gaban Dada?. Fitowar Sagiru daga ɗaki yana sakin ƴar gyaran murya da yin hamma lokacin da ya zo tsakiyar falon. "Ke Amina mene ne dalilin da za ku fara yi wa mutane hayaniya da asubar farin nan duk kun hana ni bacci bayan idan na tashi ba wani abun sahur za ku bani ba ai sai ku barni in koshi da baccin " Ya ce cikin ɗan faɗa-faɗa mai kama da na mai burin kunya zai naɗe tabarmar kunya da hauka. Cije baki Dada ta yi tana jin mugun haushin Sagiru ga haushin marin da ya yi wa Amina jiya ga shi kuma yanzu yana musu wata magana ta rainin hankali wanda ta ma kasa gane dalilin yin hakan sai take ganin kamar ma mantawa da ita yake yi in yana abu kamar yana mantawa sirikarsa ce ita. "Wai ni kai Sagiru mantawa kake akwai uwar Amina a ɗakin, sai ka ce wasu mararsa galihu a ce mu da bakinmu da Allah ya tsaga mana ba za mu yi magana ba" "Ni fa ba haka na ce ba kawai dai gani na yi ba wani abu bane da za a dinga ka ce na ce" "Saboda ba abincin uwaka bane ko? An zambaɗa mini zabgegiyar sata an sace mini kunu da dankalin sahur amma ni da ƴata da jikokina mu jajantawa juna ba". "Yanzu Dada dama a kan dankali sa kunu ne ake wannan hayaniyar.?" "An yi, na ce an yi tun da dai ba wani ne zai kawo mini ba ai a gidan nan da satar kunu da zinare duk ɗaya ne" Dada ta ce cikin hargowa don gabaɗaya ya kawo ta wuya ji take kamar ta danne wuyan shege ta yi da jibga har sai ya daina numfashi don yanzu zarginta ya bata cewa shi ne kaɗai zai iya sace mata abin sahur ɗin tun da jiya ya ce a bashi na buɗa baki an hana shi, shi ne ya sace na sahur ɗin don ta san su Hassu da Usai ba za su ɗauka ba bare kuma Amina. . "Kowa ya fito kafin mu bu ɗaki-ɗaki nu fito da mutane" Suka tsinkayi muryar Sani yana faɗa a tsakar gida, wani irin kartawa cikin Dada ya yi Hassu da Usai suka fara makyarkyata. "Wayyo mun shiga miliyan" Sagiru ya ce a tsorace yana yin hanyar ɗakin da ya fito a maimakon ya yi waje. Dif-dif-dif suka ji karan gudu daga kowane ɓangare da alama mutanen gidan ne suka fara fitowa daga ɗakunan don su amsa kiran Oga Sani. "A fito a yi sahur" Suka kara ji ya faɗa. "Yo ai shikenan ta kwana gidan sauki kun ji mun samu abincin sahur" Dada ta ce tana tsitstsilla idanu. "Dada tun da kika ji wannan kiran ba na lafiya bane watakila ma aljannun jikinsa ne suke buɗe masa idanu yake ganinsu suna sahur "Yo kuma dai in kin ji kira ai samu ne" Hassu ta ce "A kiran mahaukaci ai sai dai a ce in an ji kira wahala ce" Amina ta ce cikin sanyij murya. Daga can ɗakin Baffalo suka fara jim ya yi gyaram murya da karfi ya fara rafka kiran sallah, da yake ɗakinsa yana jere da na Amina. "Duk wanda bai fito ba yanzu aljannu za su bi ɗaki -ɗaki su goyo shi su fito d... Ruuuu aka fara ƴar tsere Sagiru ne ya fito daga ɗaki a guje rigar a wuyansa ya sakala kan bai saka hannayen ba ya ji wannan maganar ta Sani, hakan ya sa ya taho ba tare da ya tsaya saka hannuwan rigar ba, don ba zai juri ganin aljannu sun goyo shi a bayansu ba, domin daga lokacin da suka goyo shi to watakila kwanansa ya kare. Dada da take zaune kafafu a mike jin furucin a take ta shiga dafa kasan da hannu biyu ta mike tana saurin taro zaninta da yake neman kuncewa gudun kar ta yi tsirara a gaban siriki ta rike zanin da sauri ba tare da ta ɗaura ba ta nufi hanyar fita jin ana zancen aljannu za su goyo wanda bai zo ba. A kofar ɗakin har kusan karo suka yi da Sagiru da zai fita shi riga makale a wuya ita zani rike a hannu. Amina ce ta mara musu baya Hassu ganin Usai a gabanta ita ce a karshen baya ta riko rigar Usai kiiiii suka fito wajen tamkar yara masu wasan motar kara. Baffalo kuwa dama jin Sani yana kiran a zo sahur jikinsa ya bashi wata ukubar ce saboda ya san ruwa ba ya tashi banza dama gama sahur ɗinsa kenan ya ji wannan kiran hakan ya sa ya shiga rafka kiran salla da karfi wanda ya cika gidan a tashi dibarar don a ce sallah yake amma jin ana batun aljannu za su goyo wanda bai zo ba hakan ya sanya shi ya yayumo sallayarsa da wani dogon carbinsa ya fito gajeran wando ne ma a jikinsa. Kowa ya fito an hallara a tsakar gidan da ya samu wadatuwar hasken farin wata. "Ku je ku ci abinci jama'a" Sani ya ce yana bushewa da wata dariyar su ta mahaukata, gabaɗaya sai aka fara kallon-kallo ganin abin da yake kira da suna abinci. Foo ɗin da yake kashi ne shake da kashin sa a ciki ya ajiye a tsakiyar gidan wai shi ne yake cewa abincin da za a yi sahur. "Ni dai Sagiru ka cuce ni da ka sa na rabo kauyanmu ina can cikin rufin asirina ka sa na kwaso yara na taho don son in murmure amma ga shi sai gashin kuma nake sha, kuma babu damar na koma kauye a dame ni da gori watakila ma shan ruwa ya gagare ni" Cewar Dada a zuciyarta ganin wai kashi za su ci yau kuma. "Duk wanda bai ci ba aljannu ne za su masa ɗura... Kafin ya gama faɗa su duka suka fara rige-rigen zuwa gaban foo ɗin suna jin takaici. "Wannan gidan haya ko gidan jaraba haka kawai an zo an haɗa mahaukaci da masu hankali a gida ɗaya saboda son kuɗi a bai wa mai hankali haya a ba mahaukaci ... Muryar Kakar Sani ta katsewa Baffalo tunani "Ka yi hakuri ɗan Inna ba a cin kashi" "Kowa sai ya ci kashi har da ke ma" Ya ce yana nuna ta da yatsa tare da bushewa da dariya. Su duka a gaban foo ɗin suka yi kawanya wani wari duk ya cika wurin. Gabaɗaya babu wanda ba ya hawaye yarbawan nan ma su duka kuka suke marar sauti amma kaf an rasa wanda zai fara cin kashi. "Ai dama tsohuwar nan mai gararambar tsiya ka sa ta cinye na san duk tsiya idan ta cinye kashin nan dole ta kama gabanta ta koma inda ta fito dan jaraba ko gama wankar amarcin ban yi ba sun zo su tare mini a ɗaki" Sagiru ya ce yana aika mata da wata muguwar harara a fakaice. "Kashi ne sarki kowa zai ke zagaya shi yana rawa yana masa waka" Sani ya ce yana tsalle. Tun kan ya rufe bakinsa an hau layi an yi kawanya an fara rawa Dada ce a gaba sai Sagiru sai Baffalo sai sauran suka take musu baya, ana ta wake kashi ana rawa kwata-kwata Dada ta manta da wani siriki Sagiru haka shi ma ya manta da ita. Har sai da gari ya yi haske sannan suka watse zuwa yin alwala suka yi sallar shi kwa gogan Sani bacci ne ya yi awon gaba da shi a zaune. Sallah kowa ya yi azumin kuwa waɗanda basu yi sahur ba ɗore suka yi bare su Dada dama da basu da abin sahur ɗin. Duk da haka dai zuciyarta bata daina bata cewa Sagiru ne ya sace mata abin sahur ba. Yau abin mamaki Sagiru tun da yamma ta dawo rike sa wata bakar leda da babu wanda ya san mene ne a ciki, da farko ma Dada ta ɗauka kayan buɗa baki ne ya kawo amma ganin bai ba Amina ba kuma ya shige ɗaki Dada har da ce mata ta yi saurin zuwa yau ya yi abin kirki dama yau garin tuwo ne Dadar ta bada aka siyo ake tuwo da miyar busasshiyar kuɓewa, sai dusa da aka aunowa akuyar kwano ɗaya, aka tsakura mata sauran tana ɗaki a ajiye ta fi rabin kwano tun da bata kwata aka bata ba. "Ya na ganki kin dawo hannunki yana dukan cinya?" Dada ta tambaye ta rai a ɓace sai muzurai take. "Kayan sakawarsa ne a ciki ba abin ci bane" Ta ce cikin sanyin jiki don ganin ran Dadar ɓaci. Har aka kusa shan ruwa amma Sagiru bai it fito ba daga ɗakin ba. "Dada ina ga fa don a yi kashin abinci da shi ya dawo gida" Usai ta ce cikin raɗa . "Ai bar ɓata bakin ki yarinya don faɗa ma ɓata baki ne don kuwa ya yi tsarara kamar shayi ko a daginsa ba zan bashi ba" Ta ce cikin faɗa. Ana fara kiran magriba Amina ta ɗauki ruwa ta kai masa amma abin mamakin sai ta same shi a tsaye yans ta kewaya ɗakin da alama dai ko wani abu ne yake damunsa. Tana shigowa ya yi saurin zaunawa yana damke bakar ledar da ya shigo da ita sosai rashin gaskiya muraran ya bayyana a tare da shi. ."Amin mai ya sa bakya sallama wai haba sai ku shigo ɗaki babu neman izini " Ya ce yana muzurai. "Na yi sallama sai dai ko kai ne dai baka ji ba" "Kar ma ki ajiye mini bakin ruwa don ba sha zan yi ba ku bakwa bawa mutum abinci sai wani ruwa a ce ka kai azumi guda amma a haɗa ka da ruwa salon cikin ka ya kulle" Ya ce yana kauda kai gefe. Wani kululun bakin ciki ne ya tsaye mata jin furucinsa wato ita yake so take ciyar da shi bayan ɗawainiyar hakkinta a kansa take ko kuma abincin da mahaifiyarta take tsakura mata yake so ta bashi ita ta hakura. Juyawa ta yi da ruwan za ta fice. "Ai sai ki zo ki ajiye" Ba tare da ta ce masa komai ba ta zo ta ajiye ta juya ta fita tana fitowa falon ta ga su Dada suna shigowa ita ma wuri ta samu ta zauna. Suna cin tuwon ya fito daga ɗakin rike da bakar ledar Dada ce ta bi ledar da kallon tana jan dogon tsaki a zuciyarta. 'Aikin ɓur in ji tusa, wallahi an ji kunya ga doki har doki amma kofato na sakaina" ' Tsakar gidan tsitt kamar an yi shara kowa yana ɗaki amma ɗakin Baffalo a kulle yake. Kana ganin Sagiru za ka ga rashin gaskiya ya bayyana a tare da shi kuru-kuru saboda sai kalle -kalle yake a tsakar gidan yana son kara tabbatarwa da babu kowa domin yana son aiwatar da kudurinsa. Sai da ya tabbatar komai yana tafiya yadda ya dace sumi-sumi ya shige wurin jigon dabobin da yake an sanya langa- langa an zagaya wurin. Sai da ya shige ya karasa wajen jigon akuyar Dada ya buɗe ledar tashi ya fito da zani ya ɗaura a kan kayan jikinsa ya kunce akuyar ya damke mata bakin ya saka wani danko ya ɗauro bakin ya kai wajen wuyanta ya ɗaure tam-tam ya ɗauke ta ta saɓa ta a bayansa ya ɗauko ɗaya zanin a cikin ledar ya goye ta tsaf tamkar ɗan mutum ya ɗauko hijabi a cikin ledar ya saka ya ɗauki ledar wacce a ciki saura dusar da Dada ta siyawa akuya ita ma a falo suka ajiye ya ɗauka. Saɗaf-saɗaf ya fito daga jigon ya fara nufar kofar gidan sai kawai ya hangi Dada ta fito daga ɗaki ta tsaya ta kafe shi da idanu da alama so take ta gane waye watakila bai mata kama da mutanen gidan ba. "Ina wuni an sha ruwa lafiya" Sagiru da ya makale murya ya mayar ta mata ya ce yana kallon Dada. "Lafiya kalau, ruwa kam an sha Alhamdulillah" Ta ce tana kallonsa a yadda yake gani sai yake gani tamkar dai hankalinta bai kwanta ba shi kuwa ba zai bari ta masa sakiyar da ba ruwa ba haka kawai ya gama bajat ɗinsa na zai taɓa bari ta rusa masa ba. Digdifdif ya kuya ya yi hanyar kofar gida yana zuwa zaure da yake akwai duhu, sai ya laɓe a wani ɗan lungu don ya san da ganin matar nan za ta yi bin kwakkwafi saboda ya ga bata yarda da shi ba sai kallon rashin sani take masa. Sagiru kuwa kamar wanda ya yi duba domin kuwa Dada bata yarda da matar ba tun da ta ga hijabi ranta bai kiyasta mata komai ba, amma dai ta san da walakin goro a miya. Saɗaf-saɗaf ta bi bayan wacce ta fita domin so take ta gane mai matar ta shigo yi gidan da har take sanɗa ko dai wani abu ta ɗauka a gidan. Sagiru kuwa dama ya gama tama ta saboda ya ji karan tahowarta.. "Ba ke mai bin kwakkwafi ba daga yau za ki daina amma bari kafin sannan in bambance miki aya da tsakuwa in nuna miki a sirikin zamani" Ya ce yana saita inda za ta bi ya bari sai da ta dab da wurin tana cewa "Ai sai na san wacece don daga ganinta babu l A alamun rashin gaskiya ne a tare da ita suka bayyana murara... Kafar da Sagiru ya sanya mata ta yi tuntuɓe ita ce ta hana ta karasa maganar tata. Jirif kake jin karan faɗuwarta, tana faɗuwa ya yi sauri yin wufff ya fice ya barta a duhun zauren. "Amina, Hassu, Usai ku zo ku kawo mini ɗauka jama'a" Dada ta ce cikin jin zafin faɗuwar gashi kuma tana kyautata zaton babu wanda ya ji maganarta don haka dakyar ta samu hawa kan gwiwoyinta ta rarrafa ta koma cikin gidan don kar a je a latse mata kai ta shiga uku saboda bata lura da ya fice ba. "Dada lafiya?" Su Amina da suka iyo kanta suke tambayarta ganin ta shigo ɗakin da rarrafe bayan da kafafunta ta fita. Sun ma fi zaton ko Sani ne ya mata wani abu, babu wanda ya cewa kala kawai ta karasa ta zauna tana mayar da numfashi inda su Hassu suka ɗan leka tsakar gidan amma abin mamaki babu kowa sai Baffalo suka gani da shigowarsa kenan yana buɗe ɗaki. "Dada lafiya kuwa mai ya faru" Amina da hankalinta ya tashi ta tambaya a kiɗime don ta tsorata da lamarin. ."Anty kuma fa babu kowa a tsakar gidan sai Baffalo da shigowarsa gidan ma kenan" Usai ta faɗa tana kallon Dada. "Kayya! Ku daina ɓata bakin ku, wata mata ce ta mini wannan aikin ni dai da na fita na hangi wata mata da hijabi har ta gaishe ni ta mini sannu da shan ruwa to ni dai ban yarda da ita ba hakan ya sa na bi bayanta in ga wacece ashe almurarar yarinyar nan tana laɓe a zauren sai da ta bari na shiga ra saka mini wata shegiyar kafarta mai kama da katako na faɗi" Cewar Dada tana matsa kwabrinta. Usai da Hassu danne dariyar da take cin su suka yi jin wai kwakkwafi ta bi. ."Dada ya za a yi gidan hayar har ki ce sai kin san waye ya shigo waye ya fita waye kuma zai a ciki ba ba kuma saboda gidan haya gidan ka zo na zo ne tun da ba mu kaɗai bane" "To uwata Amina wannan kenan na ce miki ban san gidan haya bane?'Ta hayayyako ta *Kar a gaji da ni a mini like a link ɗin youtube ɗin can na saman page gasar marubuta ce aka saka like ɗin ne za a tantance da shi 👍ko bakya yin youtube za ki iya taɓa link ɗin ki yi, ya Allah wanda ya yi mini domin ka ka yaye masa damuwar sa ka sanyaya ransa da frnck mai ɗorewa amin.* 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls* 👇👇👇👇👇 https://youtu.be/LF5ghcuWK8E?si=r18ACby14OehC-P_ h: CI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣4️⃣ *SAGIRU* Yana fita daga gidan sauri ya fara duk da ya san da wuya Dada har ta tashi ta biyo bayansa, ko da a ce za ta tashi sai dai ta nemi taimako a ɗaga ta kafin a zo a kawo mata ɗauki har a bi bayan wanda ya kayar da ita ya san lokacin ya tsira. Wajen abokinsa ya nufa wanda da shi suka yi shawarar yadda zai sato musu akuyar don hatta zannuwan da hijabin ma shi ya nemo. "Shegen sama wai kura ta hangi biri a saman bishiya wato dai komai ya tafi kamar yadda muka tsara" Abokin Sagiru da yake zaune a benci yana jiran zuwan Sagirun ya faɗa. "Ka bari Baabaa ai wannan matar mai shegen sa idon jaraba sai da ta yi kokwanto a kaina" Sagiru ya ce yana zaunawa a kan bancin goye da akuyar da take ta mutsu-mutsu da alama tana son yin kuka jin bakon al"amarin da ya same ta ga shi an goyata kamar ɗan mutum ga kuma an ɗaure mata baki. "Caɓ ka ce ka tsallake rijiya da baya kuma ya aka yi ka kuɓuta?" . ."Kai dai bari ai laɓewa na yi a zauren tana zuwa na mata arangama da kafata ji kake tikkk ta sha kasa na sulale na tafi abuna" ."Kafin daidai maganinta ma kenan wa ya ce mata ana bin bayan ɓarawo in ba tsautsayin takaba auren shaɗaɗɗe ba". "Waye ɓarawon?" "Kamar ya to kana da wani sunan da ya wuce wannan ne yanzu ma da sata ka yi" "Ya isheka yanzu dai ya za a yi?" ."Daga nan sai inda muka saba zuwa in mun yi ɗauki ɗam baka ajiye ba(Sata) Dama na faɗa masa za mu zo in an dace ka ga kuwa yanzu muna zuwa ciniki za a yi in kuma ka fi so a yanka ta to in je gida in samo wuka mu yi watanda da namanta ka ga kai sai ka si gidanka a dafa maka tun da kana da aure ni kuma sai in samu wajen masu tsire in sayar musu ko su mayar mini da shi tsiren" "Amma kai dau dukan iska ne baka da hankali to in dai kai ba sha tara bane ta yaya ni da na ɗauko akuya kuma in kai naman gida ai dole ma a ɗora mini zargi" ."To mu je a ci kasuwarta" Tafiya wajen wani wanda yake siyan kayan sata a wajensu suka yi, dama duka abin da suka samo a wjensa suke siyarwa. "Kun iso kenan amma ya na ganku sinkin fakitin?" Ya ce yana kallonsu. .."Ita ce fa a baya aka goya saboda gudun ɓacin rana duk da dai ana cewa akwai ranar tonuwar asiri ga mai mumafurci?" "Sagiru wai sama kai ne da hijabi ni fa na ɗauka mace ce " Ya ce yana bushewa da dariya. ."Ah ka manta mata-maza ne" "Mu yi abin da ya kawo mu" Abokin Sagirun ya ce. "Gata ai sai ka mata kuɗi" ! Na sanka da siyan abu babu daraja to a kan akuyar nan dai ba za mu lamunta ba" Sagiru ya ce yana ɗaga hijabin ya juyo masa baya wai ya gani . "Taɓ a ina ka taɓa ganin an yi cinikin biri a sama? Ai ja sakkota kawai in kare mata kallo sai in mata kuɗi" Goyon kuwa ya since zanin amma kuma abin mamaki da al'ajabi akuya ta ki sakkowa. "Ke tun da ba bayan tsohuwarki bane sai kin sakko har da wani makalkalewa" Ya ce yana fisgota amma ko gezau bata yi ba bare ya sa ran za ta sauka. Tun abin suna ɗauka wasa har ta kai sun yi tarayya suna kokarim sauke akuya amma gaba ɗaya kamar a jikin Sagiru aka halicce ta. "Baabaa anya kuwa wannan akuya ce ka ɗakko?" Cewar abokin Sagiru da mamaki. "Ubanka ne to a bayana in ba akuya ba". "To ni dai akuya ce na ɗakko. "Ko dai wannan mahaukacin na gidan ne aljnnunsa suka mayar da shi akuya ka goyo shi... Abokin Sagiru bai karasa ba maganar kirjin Sagiru ya yi wata irin mugun bugawa da karfi, da sauri ya saka hannunsa yana kara fisgo akuyar don so yake ya ɓanɓato ta ba ya ma fatan maganar ta zama gaskiya. Amma sai ya ji tamkar mayen karfe haka akuyar ta lake a jikinsa don yanzu ta buɗe kafafun nata ta kara kankame bayan Sagiru kamar a bayan aka halicce ta. ."Baabaa wallahi ba dabba bace da alama a bayanka ka ga yadda take kara kankameka kuwa... Tun kafin abokin nasa ya kai aya hawaye ga riga karasa maganar fitowa tuni da na sani da kuma mugun fargaba masu tsanani sun cika zuciyar Sagiru musamman da ya ga abokinsa da wanda yake siyan kayan sata idan sun samo sun fara ja da baya alamu sun nuna suna son nesanta kanau daga gare shi saboda su tsorata. Wani abin tashin hankalin ma yadda Sagiru ya ji akuyar ta kafa bakinta a kashin hannunsa wanda yake a baya tana gwagwiya idanu ya zaro. ."Baabaa kur'ani nono take nema ka ga yadda take kafa maka baki kuwa?" Cewar abokin Sagiru yana zare ido kamar wanda ya yi wa sarki karya. Kafin ya yi wani yunkuri sai gani ya yi da abokinsa da mai siyan kayan sun dare ɗaya ya kama hanyar gabas ɗaya ya yi yamma bai gama tabbatar da yana cikin tashin hankali tsamo-tsamo ba sai sa ya ji akuya ta buɗe baki cikin ɗaga murya tana cewa" Ku bil adama ku tsaya mu mana" Kafin akuyar ta gama maganat fitsarin da Sagiru ya saki daga tsaye ya gama wanke kafafunsa su kuma jiyo muryar akuya tana magana da wata murya kamar ta tsahuwa tukuf sai kowanne ya kara cikawa wandonsa iska ko waiwaiye basa yi bare Sagirun ya sa ran za su tsaya shi ga shi kuma wajen ko alamar mutane babu da yake dama wajen sayan kayan satar a inda babu idanun jama'ar saboda tsaro ba don tsoro ba. Kuka yake tun karfinsa hawaye yana zuba fitsari ma yana zuba ya ma rasa dalilin da ya sa fitsarin ya ki daina zuba sai dai ya alakanta hakan da cewa ruɗun sa yake ciki ne ya ma kasa dakatar sa shi tun da ya san dai shi ma bai san ya aka yi yake zubowar ba. "Mu ma mu bisu mana" Ya ji akuyar ta sake cewa bayan ta ɗauke bakinta daga jikinsa da yake da ta yi maganar ɗazu sai ta maida bakin ta cigaba da gwagwiya don shi yanzu ya san ma ta yaga masa rigar da yake yana jin alamar hakoranta a jikin fatarsa. Bare wannan maganar ta kara tsorata shi don tun da yake bai taɓa jin inda aka ce akuya ta yi magana ba ko da a labarai kuwa kai shi ko a labaran nan da ake cewa inda ranka ka sha kallo bai taɓa ji ba sai yau ga shi ya faru a kansa. Ba komai yake kara hauhawar tashin hankalinsa ba sai ganin shi kaɗai babu kowa bare ma yanzu ya san va akuya bace tun da da kunnuwansa ya ji ta ce musu bil adama. "Mu tafi mana" Ta sake faɗa bata san shi firgice take saka shi ba idan ta yi magana so yake ya yi dabarar yadda zai ɓanɓareta daga jikinsa ma amma gabaɗaya kansa ya kulle ya ma rasa tunanin da zai tabbas ya yi da na sanin sato akuyar nan ga shi nan shi bai ci nanin- nanin ba nanin tana neman cinsa da ya san haka ne da a hannu ya kamo ta, da yanzu ya sake ta ya zura da gudun yanzu kuwa ko da ya gudun suna manne kamar tif da taya. "Kawai ka fita a guje da kanta za ta gaji ta sake ka, ka huta da alakakai" Wani ɓangare daga cikin zuciyarsa ya kissama masa wannan shawarar da yake gani tamkar gurguwar shawara ce amma dai zai jaraba. Sai da ya saita hanyar da zai yi kawai sai ya shiga yin girgiza da karfi don ganin akuyar ta fita amma ina abin ya ci tura! Zanin jikinsa ya tattare wanda ya ɗaura a saman wandonsa don yin basaja da zai saci akuyar, yana gama tatrarewa ya zuba a guje saboda yana ganin hakan ba karamin mafita bace don kar ta ga babu idanun mutane kar ma ya je ta cinye shi da wannan gwagwiyar saboda sannu-sannu ba ta hana zuwa don a haka sai ta cinye shi ko ma in ta ga babu kowa ta gudu da shi tono yadda Sani ɗan Inna yake cewa zai sa aljannu su tafi da mutum hakan ba karamin tashin hankali ya kara saka shi ba yana jin zunzurutun damuwa. Cike da alhinin halin da ya saka kansa a sanadin son zuciya yake falfala gudu, jin hijabin wuyansa yana shake shi ya cikwikuyo shi ya yi jifa da shi yana kara wutar gudun sai kafafunsa yake hanga tsilli-tsilli don takalminsa ma tuni ya cire shi ya baro shi a can. Yana cikim gudu zanin ya taɗe shi, rigif ya zube a cikin caɓalin wata makwaranyar wani gida kasa tashi ya yi yana tuno rashin imanin da ya yi wa tsohuwa ɗazu wato sirikarsa ya saka kafa da gangan ya kwalfe ta yanzu shi ma ga faɗuwar ta zo kansa tabbas ya ji faɗuwar musamman ma yadda kirjinsa ya bugu da kuma yadda ruwan kwatar ya fallatsu a fuskarsa har bakinsa. Ammin duk faɗuwar nan da ya yi bai ji alamar akuyar za ta sauka ba sai ma kara kaimi da take wajen gurgurar bayan nasa. Dibara ce ta faɗo masa ya saka hunnunsa ya cire zanin jikinsa yana daga kwance rubda ciki don a rubda cikin ta faɗi. Kwantawa ya yi reran ya zamana yana kwance a kan akuyar ita tana kasa ya shiga murtsuka bayan nasa a kan akuyar ransa fari kal har wani murmushin jin daɗi yake da ketar ya samu hanyar da zai rama fargabar da ya shiga a dalilinta, ai yana jin ta fara kukan su na akuyoyi meeee ya ji a ransa ukubar da yake bata tana tasiri. ."Sai na kashe ki murus har lahira" Ya furta a fili bai gama tantancewa ba ya ji ta daddage karfinta ta yanka masa wani uban cizo. A kiɗime ya mike zaune daga kwance da yake, babu zato ta sake sakar masa wano cizo wanda ya yi kiyasi tun da ya zo duniya bai taɓa jin cizon wannan mai masifar zafi da raɗaɗi irin wannan ba. Da mugun sauri sa tsananin gigicewa ya mike tsaye har santsin wajen yana neman ya kayar da shi amma a haka ya tashi ya yanka a guje. Shi kansa bai san ya karaso inda da jama'a ba sai da ya ga duk inda ya gifta yana jin ana cewa. "Jama' a a kauce ga mahaukaci nan" Shi dai ya ga mutane suna ta gudu to sa yake shi ma a matse yake da ya fita daga ukubar da yake ciki ba wacce yake ganin gwara mahaukaci sau dubu a kan damuwar da yake ciki. Shi bai ma san da shi ake magana da aka ganshi da akuya a goye a baya daga shi har akuyar kamar sun yi wanka da taɓo ga shi ko takalmi babu a kafarsa kuma ga akuyar tana ta cewa meeee. Majalissar su da suke zama ya nufa don ya san tabbas zai samun CI-MA-ZAUNE ƴan uwansa. A guje ya shawo kwanar bai ma lura ba kowa a wajen ba sai da ya zo dab da wurin wani uban birki ya ja yana sakin wani marayan kukan tausauyin kansa. "Ka koma gida Amina za ta san yadda za ta raba ka da ita" Kai ya shiga girgizawa don ba ya so ya je gidan saboda shi ma ya san ko giyar wake ya sha ba zai maido dadar kuɗin ba. Kara kwasa ya yi a guje akuyar kamar jira take ta kara kukanta shi dai da ya bi layin ma yanzu ana ta cewa ga mahaukaci nan ya dawo shi da. Wani layi ya bi yana ta surfa gudu duk inda ya bi sai ya ga mutane suna darewa kowa sai ya kama gabansa bai yi burki a ko ina ba sai a gidan su abokinsa da yake ɗakin abokin nasa a zaure yake don haka yana zuwa ya bankama cikin ɗakin. Abokinsa kuwa da tun gudowarsa gida ya taho yana ta hailala da salatin annabi S.A.W akan wannan al'ajabi da ya faru tun da da kunnuwansa ya ji maganar akuya kuma ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Da yake dama tun da ya dawo a tsorace yake ko cikin gida bai shiga ba ya zauna a ɗakin yana rarraba idanu. Jin bankamowar da aka yi a guje ya tashi ya nufi banɗaki ya rufe don shi bai ma taɓa kawowar ba wai Sagiru ne abu ɗaya kawai ya sani shi ne a cikin tsoro, fargaba da kuma ruɗani. Yana shirin shigewa Sagiru ya yi taku ɗaya biyu sai kuwa ya kamo rigarsa ta baya. Jin an damki rigarsa ta baya sai ya fara kuka marar a sauti kiii Sagiru ya juyo da shi suka fuskanci juna, a take ya fara karkarwa kamar masassara ganin Sagiru muraran goye da akuyae don yanzu babu zanin da aka goya shi ɗin ma ba ya jikin goyon kawai kankamar da aka yi wa jikin ne ta masa. "Baabaa don Allah ka mini rai wallahi tsoron su nake ni yanzu har kai ɗin ma tsoro kake ba ni" "Wallahi baka isa ba ai kai ka ce in sato mana akuyar mu ci kasuwarmu kuma yanzu za ka gujeni?" Kuka kawai abokin nasa yake hawaye shaɓe-shaɓe shi a dole ma gani yake Sagirun ma duk caɓali ne a jikinsa da na akuyar hakan ya sa yake tsoronsa har hannu biyu ya haɗe yana rokonsa. Su duka kuka suke wiiwii babu mai lallashin wani ga akuya a gefe guda ita ma tana meeeee wanda kukan nata yake kara tsorata su. "Ku wa mutane shiru" Suka ji ta faɗa. Ɗiffff suka yi tamkar ruwa ya ci su. Babar abokin ce ra taho saboda tana jiyo tashin kuka kuma ba na yara ba. ",Kai lafiyarku daga shan ruwan mutane za ki zo ku dame su?" Su ka ji muryarta tana kafe bayan Sagiru da idanu ganin akuya a bayansa. Haba Sagiru yana juyowa bai ma san lokacin da ya saki rigar abokin nashi ba ya juya ya je gabanta ya durkuwa yana kuka shaɓe-shaɓe da ta rasa ma dalilin kukan "Kai bana son shashanci ni da na ce ku wa mutane shiru amma sai ka kara kaimi wajen kukan. "Ki mini rai ki tofawa akuyar nan ko kulhuwallahu kafa uku ce ta sauka daga bayana" Sagiru ya ce cikin gunjin kuka Masoya daga yanzu har december ana iya mini LIKE na gasa a youtube na littafina MALAMIN BOGI domin taimaka mini in ci wannan gasa ta marubuta MAMAN AFRAH 09025576222 [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇 *Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana* CI-MA- ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣5️⃣ "Akuyar waye?" Ta ce cike da masifa dama masifaffiya ce. Wani yawu ya haɗiye mukut jin furucinta ya san yana faɗa mata satowa aka yi satar ma a gida a gidan ma ta sirikarsa to babu shakka sai an ka ruwa rana. "A gidansa ya ɗakko ta ta sirikarsa ce shi ne ya makale ta ki barin bayan nasa kuma wallahi har magana ta yi" Ya ji muryar abokin nasa ya jika masa aiki tun da ya feɗe biri har wutsiya. "Ka ce dai sato ta aka yi ba wai ɗakkowa ba, to ba kulhuwallahu kafa uku ba ko tabbatyada ba zan karanta ba, dama ai duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa" Ta ce tana juyawa za ta fita daga ɗakin Sagiru ya kamo kafarta yana kuka yana rokonta. "Yawwa kin birgeni" Ta ji akuyar ta yi magana, kwuiiitt ta saki wata tusar marar kara ta tsoro a zuciyarta tana raya ashe da gaske suke da suka ce tana magana tabbas wannan ba akuya bace akwai lauje cikin naɗi tsoro ta ji ya kama ta don haka ta shiga kiciniyar kwace rikon kafarta da Sagiru ya mata. "Ka sakar mini kafa tun da ku bakwa jin magana yanzu da auranka amma don zubarwa iyali kunya kake sata? Yanzu ga shi a garin dogon hannun naku kun ɗakko abin da ya fi karfinku ka ga kuwa ko kuka ya kama ba ni ba" Ta ce tana aika musu sakon harara. "Ni don Allah ki cire mini ita na miki alkawarin na daina" "Yo ka cigaba da yi ma mana tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ya kan duka" Ta ce. Dakyar ta samu nasarar fincike kafar tata tana huci saboda ba karamib artabu suka sha ita da Sagiru ba kafin ya sakar mata kafar. Kafa ya mike kawai yake sharɓar kukan takaici ganin babu tsumi babu dubara, akuya kuwa in ta gurguri jikinsa sai ta saka ta yi kuka. Hannu biyu ya ɗora a kan yana jinjina wannan masifa da ya kefa kansa a ciki. Ganin hakan sai ya taso ya baro ɗakin abokin ya nufi cikin gidan, da kuka ya shiga tamkar wani karamin yaro har ya zo ya zauna a kasa kusa da mamar abokin nasa ya zauna hannu bibiyu ya haɗe yana rokonta a kan ta taimaka ta yi wa akuyar rukiyya tun da ba dabba bace ya samu ta ɓanɓaru daga jikinsa. "Yau na ga abin da ya fi karfina in ji bazawarar da ta rasa miji, lokacin da kuka shirya abin ku ma san ma an y? Sai yanzu ne za taso da wasu siraran kafafuwanka ka ce na yi wa akuya rukiyya to ban iya ba" Ta ce tana masifa tana shan lemon fata da kankana. Kuka ya zauna yana mata wiwi har ta gaji da magiyar ta sakala mayafinta ta ce ya tashi ta raka shi gidan malamin da take rukiyya. "Na gode sosai Allah ya saka da alheri 'Ka bari dai ka ga yadda halin zai yi a toh don wannam badakalar ba ta wasa bace" A baya ya bita yana jin damuwarssa ta ragu. Suna zuwa ɗakin zauren ta kalla kamar yadda ta yi zato hka ce ta faru domin kuwa kwance yake ya libgawa kansa bargo baka jin karan komai sai salatin annabi. Ganin ya rufa har kansa sai ta lallaɓa ta shiga ɗakin ta haɗa hannu biyu da damke kafaɗarsa. A take komai ya kwance masa maganar da yake faman yi ta salatin annabi S.A.W ta kwace ya ma rasa ina zai sa kansa wata irin jijjiga jikinsa yake tsabar tsoro sai makyarkyata yake yana neman yadda zai yi ya buɗe fuskarsa sai dai yana tsoron mai zai gani don a nasa tunanin akuyar nan ce ta bayan abokinsa Sagiru ta zo ta makale masa shi ma musamman da ya san tare suka haɗa baki aka sato akuyar sai ya yi zaton tasa ukubar za a gana masa. "Sama dai iccen maraya sama dai iccen kosai, ba don rashin uba ba, da ban shuka ka ba" Ya ci ya fisgo wata waka da ya san tun suna yara ana musu ita a cikin wata tatsuniya. Don yanzu shi a yadda yake a ruɗan nan ba ya jin ma bakinsa da kwakwalwarsa za su bambance masa tsakanin waka da karatu saboda bashi da nutsuwa ko miskala zarratin. Babar tasa kuwa jin abin da yake faɗa ya so bata dariya kai hatta Sagiru da yake cikin halin kakanikayi sai da dariya marar sauti ta kwace masa yake ganin yanzu an dafa sa ma yana shiriftu saboda tsoro to ina da shi akuyar ta makalewa kuma yana ji take magana watakila ya suma. Dama ta gaji da shaye-shyen nan da yake kullum tana masa faɗa amma ba ya ji ga shi daga shaye-shaye ya afka sata kuma daidai gwargwado tana masa nasiha amma kuma mu'amala da abokan banza ba ya sa mutum ya sauya halin don haka yanzu ta kudurta a ranta za ta tsoratar da shi watakila ya rage abin da yake ko da bai daina duka ba. Ganin ya zube yaraf ya kwanta wanda da a zaune yake sai ta kai hannunta ɗaya wajen kafaɗarsa ta kai ɗayan saitin kafafunsa ta fara kokarin kamar za ta masa ɗaukan jarirai. Jin ana kokarin ɗaga shi gabaɗaya sai ya ya saddakar tashi ta kare don sai ya fara tunanin kenan lamarin Sagiru da da dama -dama wai kibiya a ido tun da shi Sagirun basu ɗauke shi ba kawai akuya aka lika masa taki fita shi kuma ga shi zunzurutun tashin hankali ya mamaye shi tun da suna kokarin ɗaga shi kuma ya sam suna ɗaukan nasa daga na kuma sai inda hali ya yi watakila ma su tafi da shi duniyar su ta aljannu shi ma ya kwatse da su ya zama aljani. Ai wannan tunanin sai ya sa jikinsa ya fara tsuma ya ji ba zai iya zama a duniyar da ba ta bil adama ba wato ta aljannu a take ya fara kokarin kwace kansa amma kash! Abin ya fassakara domin ita Babar tasa sai ta kara kaimi wajen kankame saitin wuyansa da kuma kafafunsa. "Maza ya jibu alaika, mene ne ya wajaba a gareka, an ta'amalahu, ka aikata shi, kablal salati kafin ka yi sallah" Wannan karatun tun na islamiya da suke zuwa kafin su gagara su daina zuwa islamiyar ma baki ɗaya shi ne ya samu nasarar cafkowa daga bakinsa da yake kokarin gagararsa furta komai saboda karkarwar da yake har hakoransa suna gwaruwa da juna saboda yadda suke haɗuwa kamar wanda zazzafan zazzaɓi ya rufe a lokacin muku-mukun sanyi. Sagiru tsabar dariya har sai da ya zube a kasa don bai taɓa tunanin tsoron da abokin nasa yake da shi ba ya kai haka ba, shi tsabar diramar da yake gani ana tafkawa tsakanin uwa da ɗanta har ya manta da nasa tashin hankalin da yake ciki wanda yake goye da akuya tana makale tana gwagwiyar bayansa. Kara ɗaga kafafun ta yi sama alamar dai ba za ta saurara daga abin da take ba. Da mugun karfi ya buɗe murya ya ce "Jama'a ku kawo mini ɗauki, mutanen ɓoye sun kawo mini farmaki, don Allah ku zo za su tafi da ni duniyarsu, wayyo uwata wayyo ubana wayyo ni Allah na shiga uku yau na yi angamo" Ya ce yana sakin wani wahalallan marayan kuka da ya karaɗe ɗakin da yake ɗakin ma a zaure yake ihu da karaɗin da yake har kofar gida. Gudun kar hankulan mutane masu wucewa ya iyo cikin gidan nasu don ya dage da iface-iface na neman taimakon jama'a su kawo masa ɗauki sai ta saki wuyan nasa ta kama uban jikin ta shiga jijjiga shi a take ya saddakar da cewa shi tashi ta kare don jijjigar da take masa sai ya yi zaton kashe shi ne aljannun suke son yi hakan ya sa ya saki iface-iface da kiran jama'a su kawo ɗauki yaje yaki da bakinsa a kan ya samu ya karanto kalmar shahada ko ya dace ya cika da imani. "Innal mu'uminuna, wal mu'uminati, wal muslimuna, wal musilimati" Wannan kawai yake maimaitawa don ya kasa karanto kalmar shahadar. "La'a'abidu mata'abiduun" Ya sake warto wata ayar a cikin kuliya ayyuhal kafirun yana kyautata zaton in har yana karanto duk abin da ya zo bakinsa matsawar dai ba ihu bane to da sannu zai samu karanto kalmar shahadar tun da sannu -sannu bata hana zuea sai dai a daɗe ba a zo ba. "Wattini wazzaituun, walɗurisinin, wa hazal baladul amiin" "Wayyo Allah na" Ya furta da karfi jin har yanzu kame-kamen ayoyi yake bai kai ga samo nasarar kalmar shahada ba gabaɗaya ruɗu ya hana shi ga shi kuma ya ji sai jijjiga shi ake yi shi kuma yanzu ya daina kiciniyar buɗe bargon daga fuskarsa don ba ya ma kaunar ya yi angamo da fuskar aljani. Wata iriyar jijjiga ta masa da karfi a take ya ji ya yi nasarar warto kalmar shahada da karfi kamar wanda aka fisgo maganar ya ce "Ashshadu an la'ilaha ilallahu, wa ashshahadu anna muhammadur rasulullahi.... Ya dakata yana sakun wani marayan kuka mai kamar jiniyar sarki ta wuce "La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Ya faɗa wannan karon har da sakin tusa da fitsari na wahala da tsananin tsoro. Da karfi ta fisgi bargon ta yace masa shi duka ya haɗa uban gumi idanunsa a rufe. Shi kuma jin an buɗe shi sai ya kara rufe idanunsa gagam don a nashi zaton ya ɗauka so suke sai sun gama tsorata shi da kamannin su kafin su kashe shi, shi kuma ya san yana ganin halittar su to tabbas zai karasa mutuwa kafin su kashe shi saboda ya san dai ganin siffar aljani dai babu sauki wai ciwon arne Ganin bai buɗe idon ba sai ta ɗaga hannu ta falla masa mari da zafin marin ya sa ya buɗe idanun a gigice ba tare da ya san ya buɗe ba ganin ta tsaye ya sa ya wani taso tsaye da shakarkaɓin wandonsa ya rirrike ta yana fashewa da kuka ya ce "Wayyo Baba she dai za ki zo ki cece ni dama an ce mutuwa tana tsoron idon mahaifi ashe dai aljannu ma suna tsoron idon mahai... "Ɗan kwal uba wuce ku kama hanya mu tafi gidan malam Kailu ai thn da baku da hankali baku san annabi ya faku ba to kuwa dama ai kun ringa ganin abin da ya fi wannan ma ai duk wanda ya ja ruwa shi ruwa ya kan duka" Ta cw cikin hargowa tare da ture shi daga jikinta don bata so ma ya gane ita ce ta masa duk abubuwan da ya ji ta fi so a tafi a hakan har su je gidan malamin yana ruɗe hakan zai sa watakila in za Allah ya nufe shi ya yi taubatun nasuha wato tuba na ha abada ya daina sata da shaye-shayen. Sagiru da sai yanzu da Babar abokin nasa ta fara faɗa ya dawo daga duniyar dariyar ketar da yake ta faman sha, hakan ya sa ya mike tsaye yana tsayawa dakyau don gabaɗaya dariyar ma ta ki sakin sa sai yanzu yake kara tabbatar da yanayin tsoro mai haɗe da tsurewa ba karamin abin dariya bane idan ana gani ga shi, har ya sa ya manta da nasa tashin hankalin. "To, to, to, to, to" Yake ta faman maimaitawa don shi yanzu gabaɗaya ma a ruɗen yake ba wai ya gama dawowa daidai bane, sai wani kallon ɗakin nasa yake yana jin wai wannan ɗakin ne aljannu suka shigo har suka yi ta jijjiga jikinsa, da wannan tunanin ya fito daga ɗakin Babar tasa tana biyo bayansa bai damu ma da wandonsa da yake jike sharkaf ba don shi yanzu a halin da ya shiga ya samu damar kuɓutowa gani yake ko tsirara aka ce ya fita zai fita saboda yadda ya tsallake rijiya da baya. Yana fitowa kallo ɗaya ya yi wa Sagiru ya ɗauke kai tare da yin gaba ba tare da ya masa magana ba, na farko haushinsa yake ji saboda yana ganin duk wannan halin da ya shiga da sa hannun Sagirun tun da shi ya ɗakko akuya mai aljannu na biyu kuma yanzu da ya fito ya masa kallo ɗaya ya lura akwai alamar dariya shimfiɗe a fuskarsa, wannan ya tabbatar masa da cewa shi yake yi wa dariyar keta, ga shi ma shi yanzu daɗin daɗawa mugun tsoron Sagirun yake ji yanzu saboda akuyar da take makale a bayansa don har ita bai ɗaukewa zargin da ita aka jijjiga shi ba. Abokin Sagirun ne a gaba sai Sagirun sai kuma Babar ita ce a karshe tana fitowa ta banko gidan. "Ka yi ta kan ka, don daga gidan Malam Kailu babu inda zan kara raka ka matukar ba a dace a haka ba don daga can ma sai dai ka wuce gidanka ku je can a dage da fatiha da salatin annabi da rokon Allah har zuwa ranar da Allah zai sa ta yarda ta ɓamɓaru daga jikin ka, tun da kai har kana da bakin dariya baka duba bala'in da kake ciki a ce akuya da ranta makale da jikin ka har tana magana amma har kake da bakin dariya bayan ga bayanka nan duk ta kwarzane ta gwigwiyar da take amma ko don bahaushe ya ce bakin dariya shi ne na kuka" Ta ce tana wuce shi ta wuce ɗan nata ya zamana ita a gaba sai ɗan nata sai kuma Sagirun da jikinsa ya yj sanyi yana ji tashin hankalin kalamanta da ta faɗa a ganinsa kenan ma ba tabbas idan an je gidan malamin babu tabbas za a raba shi da akuyar. "Na shiga uku na! " Ya furta a zuciyarsa gabansa yana tsananta faɗuwa. Shi kuma abokin nasa sai kaimi ya kara wajen sauri yana so ya wuce Babar tasa don yanzu mugun tsoron akuyar bayan Sagiru yake don gani yake kamar za ta iya yin tsuntsuwa ta koma nasa bayan. "Ahmadu ka tsaya shi ku tafi tare mana da abokin naka, ka wuce shi ni kuma ina so ake sauri sa ni ko bayanka zan dawo ko na Baba tun da na ga duk kun wuce mu" Suka tsinkayi ajuyar nan tana faɗa. Kukuiiiit wata bahaguwar tusa ta kwacewa Ahmadu don shi ko Sagiru bai fiya kiransa da sunansa ba sun fi kiran junansu da Baabaa amma kuma ita ga shi ta kira shi da sunan nasa kenan dai sha'anin aljannu sai su. Ɓeeetɓaɓetttt Baba ma ta saki tata iskar tusar guda biyu a jere jin an ce ita ma za a dawo nata bayan taimakon da Allah ya mata ma tusar iyakar kumnuwanta karan ya ziyarta bai kai kunnuwan su Sagiru ba don ko da ya kai ma ba lallai tashin hankalin da suke ciki ya bari su gane daga inda karan yake ba. Fuusssssssss Sagiru ma ya saki karan tashi tusar saboda tsoro cikin su yake sace iskar tusa don gabaɗaya sun tsure. "A'a ranki ya daɗe gaot" (Akuya) Shi sai ma ya ji ya manta sunanta da hausa shi ya sa ya faɗa da turanci. "Na... tsaya... shi ...mu tafi... tare" Ya ce cikin ciccira maganar saboda tsoro da ya ji ya kara baibaye shi na ambaton sunansa da kuma na cewa za ta dawo bayansa. . 'Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahiiiiiiiim" Baba ta ce a zuciyarta ganin ta jefa kanta a wani halin tana ganin in har ita akuya mai magana ta makalewa to ba ma lallai ta samu karfin halin taka ko da kafarta ba saboda tsoro. A fili kuma sai ta ce "Ai ba sai an kai ga haka bama ai dama ni taimakon su ne zan yi amma in kika ce in koma gida sai in juya yanzu- yanzu sai su tafi su kaɗai" Baba ta ce don ganin ta tsame kanta daga cikin wannan bala'i don bata taɓa zaton abin zai kai har haka ba da bata shiga ba yanzu ne take jin ba lallai bane ma akuyar ta yarda ta fita tun da gashi har tana ikirarin komawa bayan wani. "Don Allah Baba kar ki mana haka" Ahmadu ya ce yana danne kukansa don ya fara tunanin in aka bar su su biyu to tabbas in bata zauna a bayan Sagiru ba tabbas bayansa za ta koma in kuma da Babar ne watakila tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe ya sa akuyar ta koma bayan Babar tasa. "Ku taimaka mini" Cewar Sagiru da yake ɗaga kafarsa dakyar sanadin sanyin tsoron da jikinsa ya yi. "Nooooooo ke ki shiga gaba, su sai su jeru mu tafi tare ke ai sai ki mana jagora" A kuyar ta faɗa da wata siriryar muryar matashiyar mace a maimakon muryar da take magana da ita kamar ta tsohuwa. ."An gama, an gama, an gama" Su duka ukun suke haɗa baki wajen faɗa don yanzu kuma abin ya shallake tunanin su. Baba tana gaba amma ba wanu tazara ta basu sosai ba da yake kuma layin gidan Malam Kailun a can karshen sama layi yake kuma shi ne gida na karshe don wajen ma babu gidaje sosai kasancewar sabuwar unguwa ce wannan ya sa ma yanzu duk babu mutane a hanyar da suke bi. Ahmadu na dawowa kusan Sagiru a ɗarare babu zato ba tsammani ya ji kofaton kafar akuyar nan a jikinsa wato ta sakalo bayansa ta rungumashi a jikin Sagiru ta haɗe su a wuri ɗaya sun zama tamkar tif da taya ya kasance tana bayansu su duka da yake kafafunta huɗu biyu na kasa ta makalawa kowannen su ɗaya biyu na sama sai ta sakala ɗaya a wuyan kowanne ta zamana a tsakiya kanta yana a tsakanin kawunan su kamar an ce Baba ta waiwayo sai kuwa ta yi arba da wannan badakalar. *MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇 *Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana* [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 CI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣6️⃣ SANARWA *Assalamu alaikum CI MA ZAUNE 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp ki fara min magana PC na miki bayani. Wanda 500 zai saka ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana* Wani yawu Baba ta haɗiye mukut tana jin wani tsoro yana baibayeta, tabbas yau suna ganin harkalla. Sauri-sauri ta fara don ta matsu su karasa gidan Malam Kailu in ya so su ta bar su a can ta yi tafiyarta dama ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa yake duka. Sagiru kuwa da abokinsa ba sai an faɗi yanayin da suke ciki ba duk da Sagirun ya ji daɗin yanzu dai ba shi kaɗai ne a makale a bayansa ba yanzu kam sun zama su biyu amma duk da haka fargabarsa ta karu don yanzu ya tabbatar akuyar nan ba da wasa yake ba shi ba don kar ya musu baki bama da sai ya ce ba lallai ta yarda ta ɓanɓaru daga jikinsu ba amma dai bahaushe ya ce wai sai an gwada a kan san na kwarai. Ahmadu kuwa faɗa ma ɓata baki ne don Allah kaɗai ya san halin da yake ciki ji yake ina ma ya buɗe idanunsa ya ga mafarki yake ba da gaske bane. "Baba saurin naki ya yi yawa fa" Baba da ta ɗan dage da sauri-sauri gudu-gudu ta tsinkayi muryar akuyar nan ta sake magana sai dai wannan karon da muryar yara ta yi maganar. Baba kuwa bata san lokacin da ta ja wani uban burki ba, tamkar wata mota ko machine, bata tsaya a nan ba bayan ta ja birkin sai ta shiga yin da baya da baya don gudun yin laifi don duk abin da zai sa a ce akuyar nan ta yi kawanya da ita da su Sagiru to ba kaunarsa take ba, sai da ta ga ta kusa zuwa inda suke sannan ta fara wata tafiya mai kamar sanɗa tamkar wanda take tsoron wani ya ji takun tafiyar ta Ahmadu kuwa bakinsa ne ya shiga kaiwa da komowa yana ta addu'ar da ko da za a saka masa wuka a makoshi bai san mai yake karantawa ba ya dai san yana motsa baki ne kuma motsa bakin da yake na neman tsaru ne daga ukubar wannan akuyar saboda shi idan ya ji ta yi magama da muryar mutane ba karamin ruɗani yake shiga ba musamman da ya kasance tana yin muryoyi idan ta yi ta tsofaffi sai ta yi ta ƴan mata yanzu kuma ga shi ta yi muryar yara. Sagiru kuwa shi zuwa yanzu ma bai san a halin da nasa bakin yake ba abu guda ya sani shi ne yana nin yadda bakin nasa yake ta kaiwa da komowa yana jin yadda yake motsawa. Haka dai ake tafiyar marar daɗi babu daɗaɗawa har suka kusa isa gidan Malam ɗin kowa yana tafiya a sannu-sannu gudun yin gagarumin laifi. A lokacin ne suka ji wani. Dururumdummmm wannan karan ne ya sanya Baba ta sheka a mugun guje ba tare da ta shirya ba, gudu kawai take zabgawa abin ka dama da wanda yake cikin tsoro, ba iya Baba kaɗai ba hatta Sagiru da abokinsa sun razana musamman ma su da sula ji karan a dab da su wanda karan ya fi musu kama da na bindiga don su ma sun so zabgawa da gudun amma sai suka ji an kara manna su a waje ɗaya don su hatta kunnuwan su sai dai suka yi dummm saboda karan. Baba babu zato babu tsammani sai ji ta yi ana mayar da ita baya, kafin ta yi yunkuri sai ganinta ta yi a wajen su Sagiru. Da aka kara sakin wani karan sai kawai aka kasa tsere daga Baba har su Sagiru suna cikin gudun ne suka ji tamkar an rike musu kafafun don babu wanda ya samun karfin gwiwar ko da ɗaga kafa ɗaya ne. "Haba ku kuwa sai an muku abu kuke ganin ba a kyauta muku ba ko? Haka kawai saboda na saki tusa sai kuke tsorata a kan mai daga tahowar mu nan a hanya kowanne a cikin ku sai da ya saki tusa son ransa wa na hana ko wa na toshewa kofar fitowar tusa? Sai ni don na yi za kuke fita da gudu to tusar ƴan shayi ce(Kaciya) Kowa ya san dai ƴan kaciya da sakin tusa to ni ma ɗan shayi ne Baba ko ƴan shayi basa tusa?" Akuyar nan ta faɗa da muryar wani katon gardi. "Su...su...su...na...yi" Baba ta ce a ciccire saboda gabaɗaya ta razana yanzu duk uban karan nan da suka ji tamkar an saki booom amma a ce wai karan tusa ne wannan tusar ma ta ƴan shayi wannan karan ma bai yi kama da ta yara ba. "Sagiru da Ahmadu ku lokacin da aka muku shayi(Kaciya) Bakwa tusa?" Muryar gardi mai kamar ka zura da gudu ta tambaya. "Wallahi muna yi" Suka haɗa baki wajen faɗa tamkar za su fashe da kuka. "Yawwa ko da na ji to daga yanzu kar kowa ya kara tsorata da karan tusa ta" Ta ce su sai yanzu ma suka ji warin tusar duk ya buɗaɗe hanyar da suke. A haka suka tafi kowa a firgice har suka je kofar gidan Malam wani abu bai sake faruwa ba. "Ku jira in yi iso" Baba ta ce tana kallon Sagiru da Ahmadu ga kuma kan akuya a tsakanin kawunansu. Babu wanda ya samu zarafin bata amsa, cikin gidan ta shiga tun daga zauren gidan ta ci karo da cincirindon mata a zazzaune da alama a layi suke kowa tana jiran layinta ya zo da yake lokacin ma an yi sallar isha'i tun daɗewa, haka ita ma ta bi sahu ta zaune ta kifa uban tagumi haka suka ringa shiga suna fitowa da ɗan kullin magani sai da matar da ta fito ta karshe wacce daga ita sai Babar ta ɗan taɓa Babar ta ce "Baiwar Allah layinki fa ya zo amma na ga kamar ma baki sani ba" "Wallahi kuwa ban sani bama" "Allah sarki wannan daga gani kina cikin ukubar kishiya, irin kishiyoyin nan masu hana wali" Cewar matar tana yin gaba.Baba kuwa bata tanka mata ba don da ta san dalilin da ya saka ta a halin da take ciki da bata kwatanta da kishiya ba don ai kishiya ita bil adama ce amma karo da aljani ba daɗi take raya hakan a zuciyarta ta je bakin kofar ta rafka sallama amsa mata aka yi ta bankaɗa labulan ta shiga mutum ne wanda a kalla zai kai shekaru sittin yana sanye da shadda ruwan omo (Blue) Sai wani uban rawanin da aka riɓa hiramin biyu sai kuma wani jan hirami da yake shimfiɗe a kafaɗarsa, ga wani faranti mai kasa da kuma kwarya ita ma kasarce a ciki. Bayan sun gaisa ko ma a ce bayan ya gaishe ta tun da ita gabaɗaya ma firgice ya sa ta manta ana wani abu wai gaisawa a duniya tun da take bata taɓa shiga tashin hankali mai tsoratarwa muraran ba irin na yau a ce akuya tana magana irin ta mutane kuma da kalolin muryoyi. "Wallahi malam wannan ce matsalar... "Ai da baki ɓata bakin ki ba wajen bani bayani don muna da labarin zuwanku da kuma abin da zai kawo ku an faɗa mana shi dalla-dalla, ai karyar aljani wallahi karyarsa dubu, karyarsa ta sha karya don buhun ubansa ni malam kare kukan ka na ci dubu sai ceto ko kukar bulukiya ce sai mun yi maganinta bare wata karamar alhakin aljana da take zama akuya, na bari ne dama ki faɗa da bakin ki kin san ƴan magana sun ce waka a bakin mai ita ta fi daɗin ji" Malam Kailu da ya yanko wata uwar karya ya faɗa yana kallonta don babu wani labarim zuwanta da kuma abin da zai kawo su da ya sani kawai dai ya faɗa ne don a kara yarda da maluntarsa to in ma ba mai aiki da aljannu ba ya za a yi ya san labarin in ba aljannun ne za su faɗa masa ba. "Allah sarki malam ai dama shi ya sa muka zo nan ni ma sau ɗaya na taɓa rako wata kawata nan ta karɓi maganin mallakar miji kuma da ka bata ta turara masa ta mallake shi don yanzu ko wurin zama sai ta nuna masa yake zama" Ta ce cikin jin ɗan karfin gwiwar sun samu warakar damuwarsu ita dai ta san ta rako kawarta wajensa to amma a ciki basu san maganin wane malami bane ya yi maganin tun da wuri biyu suka je ita. "Allahu akbar a mu nan kare kukan ka sunanmu shi ya sa wasu har sunana na Malam Kailu ya ɓata a wajensu sai dai ki ji ana kiran Malam mai kare kukan ka" Ya ce yana ƴar dariya. "Bari na turo maka su" Ta ce don a nata shirin daga ta turo su za ta san na yi don guduwa za ta yi in an cire musu sa taho tun da dama ba ita ta aike su ba. "Tare za ku zo nan ɗin ai babu wata damuwa kinsan aljani shege ne za su iya binki gida gwara ki tsaya rukiya zan yi in fitar da ita" Ya ce mata, ɗan jim ta yi amma dai jin ya ce za a iya bin ya gida sai ta ji ma zuwa gidan ya fita daga ranta kuma ma ta tsorata da zuwa gidan gwara ta tsaya a gama ɗin kamar yadda ya ce mata shi kare kukanka sunan shi kenan kuwa ai kikan su ya kare. Tana shirin tashi ta fito ta ji wani uban kara daram-dam-dammmm bata yi aune ba sai ganinta ta yi ita da Malam kare kukan ka sun nufi kofar shiga cikin gida da yake kofar guda biyu ce a ɗakin nasa akwai ɗaya ta zaure wanda bakinsa suke shigowa akwai kuma ɗaya wacce in ka bi za ta kai ka cikin gida. Malam shi kansa abin ya razana shi har ya manta da maluntakar tashi don haka dama ya ɗaga kwarya zai yi zane a cikin kasar da take cikin kwaryar ai yana jin karan nan sai ma ya manta da Baba da take zaune a gaban malam mai kare kukan ka, sai gasu sun tashi a guje suna tseren fita daga kofar har malam ɗin yana bangaje Baba, a haka suka shiga tsakar gidan Malam, matar malam ma da take gurin murhu tana za ta kaɗa miya jin karan da kuma ganin malam da kansa ya sheko da mugun gudu babbar rigarsa tana cin saɓularsa tana taɗe shi yana neman faɗuwa da wata mata tana binsa ita ma da gudun, ita ma a sukwane cikin rashin sanin makamar abin yi ta kinkimi zazzafar tukunyar miyar mai ɗaukr da ludan da za ta kaɗa miyar ta take wa su malam baya da suka nufi turakarsa shi da matar da bata san ma wace ce ba. Bata da burin da ya wuce ta isa ɗakin kar su banko kofar su tashe ta tsaye don a yadda ta ji karan tashin boom ɗin nan ta san ba mutane kaɗan ba zai sa su yi bankwana da duniya ba, kuma ta san watakila ƴan bindigar da suka saka boom ɗin su bi gida-gida hakan ya sa ta gwammaci ta kasance tare da mutane a kan ta je ɗakinta ita kaɗai. Shi ma malam ɗin dama can ɗakin zauren wajen karɓar bakinsa ne. Har an bankamo kofa an kusa rufewa cikin zafin nama ta bangaza kofar ta shige tana ɗauke da tukunyar miyar da ita kanta bata san dalilin ɗakkota ba ga wani uban zafo don bata da nutsuwar kama tukunyar da tsumma. A can ma kofar gidan malam lokacin da akuyar nan ta jijjiga mazaunanta tare da kaɗa jelarta sai ta ɗan karkata gefe shi ne ta saki tusar da ita ce ummul aba'isin gudun famfalakin da su malam da da matarsa da Baba suka yi. A ɓangaren su Sagirun ma hakan ce ta faru don gabaɗaya sun manta cewa akuya ce take tusa kuma sun manta ta ce musu tusar ƴan shayi ce take yi, don haka lokacin da karan ya ziyarci kunnuwan su sai suka ɗauka karan tashin boom ɗin ne don haka babu wata-wata suka yanki cikin gidan malam ɗin da yake basu ma lura da kofar ɗakin zauren ta malam ba wacce yake ganin baki ko kuma don suna cikin halin tsoro ne basa cikin nutsuwar su oho, suna shigowa zimbet suka nufi kofar da za ta sada su da tsakar gidan, duk da kasancewar kofar an karo ta an ɗan rufe ta haka suka bankama ciki a guje. A ɗakin malam ma kuwa zaune yake a tsakiyar ɗakinsa wannan babbar riga ta baje a kasa naɗin hiramin kansa da hular sun kalli arewa maso gabas sai mayar da numfashi yake. Baba kuwa lungun kujera ta shige da yake akwai kujeru biyu a ɗakin, ita kuma matar malam tana shigoea ta diri tukunyar a tsakiyar ɗakin malam ɗin daga can gefen inda yake zaune ta koma can wajen tulin kayan wankinsa ta kwasa ta yaɓa a kanta a nata tunanin ko da ƴan bindigar sun zo ba za su ganta ba. Jin karan banko kofar gidan ya saka cikin malam murɗawa babu ɓata lokaci ya saki wata sassanyar tusa marar kara mai bala'in wari saboda tsurewar da ya yi, a ɓangaren Baba ma kuwa jin karan ba karamin saka ta cikin ruɗu ya yi ba, don ita a halin da take ciki yanzu ta ma manta da wasu su Sagiru da ta bari a bakin kofa bare har ta tuna cewar akuyar da suke tafe da ita tana tusa mai kamar karan booom. Matar malam kuwa jin karan banko kofar sai ta kara cusa kanta cikin kayan wankin malam ɗin da ban da wani uban warin dauɗa babu komai a ciki. A tsakar gida kuwa lokacin da su Sagiru suka shigo sai suka fara rarraba idon inda za su ga maɓoya duk abin da suke akuya tana kallonsu kuma tana sane da su so take kawai ta ga gudun ruwansu. Har lokacin suna manne da juna kamar yadda akuya ta haɗa su da kafafunta suka zama tif da taya da juna. Basu yi wa idanunsu masauki a ko ina ba sai a kofar turakar malam da take a rufe don matar malam tana shiga malam ya banke sai dai ya sha'afa bai saka sakata ba. Suna zuwa suka daki jikin kofar da kafafunsu, malam da yake zaune a tsakiyar ɗakin yana lazimi da baki hannunsa da yake kai komo ya ma manta da sharɓeɓan carbinsa mai ƴaƴa dubu da yake rataye a wuyan nasa, jin karan banko kofar ya tashi da sauri yana son ya samu maɓoya saurin tashin da ya yi a firgice sai ya yi tuntuɓe da kwarya da take ajiye a ɗakin yana yin tuntuɓen ya koma babu shiri tamkar an jefa shi ya yi zaman ƴan bori a kan sabuwar kwaryar ji kake fushhhhh kwarya ta daddare. Shi malam ba damuwarsa bace faɗuwar burinsa kawai ya tserewa karan booom da kuma alburushin bindiga. Su kuma ganin sun yi bugu ɗaya kofar bata buɗu ba sai suka sake bugawa, sai kuwa ta buɗe, malam jin karan gwaruwar buɗewar kofar sai ya tabbatar kwanan su ya kare tun da ga ƴan bindiga a garinsu a kuma unguwarsu a gidansa, a gidan nasa ma a ɗakinsa. Da sauri ya buɗe tukunyar nan mai zazzafan ruwan miya ya cinbula kansa a ciki, zafin ruwan da ya ziyarci fuskarsa da zafin yajin da ya shaka a hancinsa shi ya sanya ya ɗago kan babu shiri yana sakin atishawa a kai- a kai, duk da haka bai daddara ba ya ɗaga tukunyar ya kelayar da ruwan miyar a tsakar ɗakin ya ɗaya tukunyar ya kifa a kansa da yake tana da girma sai ta rufe masa har fuskarsa jin karan shigowar mutane sa kuma yadda suka rufe kofar ga sanya ya fara ja da baya. "Taimako jama'a taimako" Ya yi furucin a wahalce don dakyar yake iya jan numfashi a cikin tukunyar. "Allah ka mana rahma ka haɗamu da mala,ikun rahma" Ya ce a fili don ya san tun da ƴan bindiga suka shigo ɗakin da yake kwanansa ya kare, ganin ruɗun da suka tsinci mutumin nam yana ciki sai suka gane ashe dai kowa ya ji abin da suka ji. Akuya kuwa duk abin da ake tana kallon su. '"Ku taimaka ku bamu mafaka"Sagiru da abokinsa suka haɗa baki wajen faɗa. Gaban malam ne ya faɗi a take kwanyarsa ta shiga laluɓe yana tunanin ya za a yi ƴan bindigar suke neman wajen ɓuya. Matar malam ma da take kwance dukunkune a cikin kayan wanki tana shakar warin dauɗa ita ma mamaki da al'ajbi ne ya kamata saɓanin Baba da jin muryrsu raɗau sai tashi tsaye tana faɗin. MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇 *Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana* [8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *CI -MA-ZAUNE* NA MAMAN AFRAH PAGE 1️⃣7️⃣ MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇 *Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana* CI-MA-ZAUNE NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣7️⃣ "Sagiru" Baba ta furta don ita gabaɗaya ma ruɗanin da suka shiga ya sa ta manta cewa tare suka zo kuma sai yanzu ne kwanyarta ta shiga tuno mata karan tusar akuyar ne musamman da suka yi ido huɗu da akuyar sai ta ga akuyar tana harararta har da murguɗa baki wanda hakan ya sa ta kauda kanta da sauri. "Baba karan boom" Ahmadu ya ce yana tsilla idanu. "Karan fitar iskar ƴar shayi ce(Ƴar kaciya) " Baba ta ce kamar za ta yi kuka don abin takaici yake bata wai akuya da shayi. Malam kuwa jin suna surutu ya yi saurin cisge tukunyar kansa don ya ganewa idanunsa wace irin tusar ƴan shayi ce don yanzu ya ji cewa ba abin da yake zato bfe wato ƴan bindiga tun da ga shi su ma a firgicen suke. Ita ma matar malam da sauri ta fito daga cikin kayan wankin da warinsu suka cika mata hanci. Kallon -kallo aka shiga yi kowa malam yake kallo yadda ya yi wani wurjanjan da shi gabadaya a firgice yake tamkar an jijjiga ɓera a buta. "Malam waɗannan ne bakin da muka zo da su" Baba ta ce don kawo karshen wannan daru da ake. "Ka ji wani shashanci jiran jirgi a tashar mota yanzu duk ɗakin karɓar bakin da yake zaure bai isheku ba sai kun shigo mini har cikin gida garsama-garsaman samari da ku har cikin turakata" Ya ce cikin wayincewa don gabaɗata bai so ya kunyata ba amma kuma ta faru ta kare wai an yi wa mai dami ɗaya sata, tun da mai afkuwa ta afku ai dai a kiyayi gaba. "Ka yi hakuri malam" Baba da su Sagiru suka haɗa baki wajen faɗa saboda basa kaunar dalilin da zai sa ya ki raba su da wannan jarababbiyar akuyar. "To na ji ku je ɗakin zauren ku jira ni kuma a yi a hankali in an je ɗakin kar a zauna a kan tabarmar aljannu wacce suke zaune don zama a tabarmar da aljani yake zaune daidai yake da mazaunan mutum su manne su ki fita har gaba da abada" Ya ce yana muzurai don so yake ya maido da ɗan guntun mutuncin nashi da ya zube saboda a nashi ganin yadda yake malami bai kamata a ce yana gudub famfalaki ba. Sumi-sumi suka juya suka fita daga ɗakin gabansu yana dakan lugude domin jin sabon salo wai kiran salla da usur wato kashedin da aka musu na kar su zauna a tabarmar aljannu. Ɗakin suka nufa kowa yana togewa musamman Baba da ita rakiya ta iyo amma abu yana neman wuce makaɗi da rawa wato cibi yana neman ya zama kari. Haka dai ta zauna amma Sagiru da Ahmadu da suka je za su zauna sai suka ji an ce "Za ku zauna a kan kofato" Da sauri suka tashi daga kokarin zaman da suke yi, suka matsa can gefe ita ma Baba jin furucin da akuya ta yi sai ta fara jan mazaunai ta matsa daga wurin. "Ka taka kan ɗan kundalo" Akuyar ta sake faɗa a karo na biyu wannan ya sa suka ja da baya har sai da suka koma bakin kofa suka tsaya a tsaye tun da zaman ya zama larura auren namiji da ƴaƴa. Baba kuwa tun da ta zauna ta shiga lazimi saboda ta lura abin ba na kare bane sai lokacin da Allah ya yanke musu. A can turakar malam kailu kuwa bayan fitar su Ahmadu sai ya shiga yin muzurai matarsa kuwa take masa dariya ganin gabaɗaya rawanin kan nasa ya jike sa ruwan miyar da ya tsoma kansa a ciki ga kuma warwarewa da ya yi ga shi kuma shi malam sai wai ɓata rai yake yana muzurai shi ala dole ba ya so a kawo masa raini, tsaye ya tashi da jagaggaɓar rigarsa da duk ta naɗe ruwan miyar da ya zubar a kasa. "Wai malam da kake cewa kar zauna a kan tabarmar aljannu idan kuma aljannun suka je ɗakin naka suka shimfiɗa tabar... "A bakin ki mugun fatanki ya sari bango" Ya ce yana aika mata sakon harara. "Ana tsoronka ɗan mayya ya ce daga ni har uwata" ,Cewar matar malam tana danne dariyar ta saboda ita kanta ta san cewa mijin nata muna malam ne amma babu wata malunta yana yana cewa yana aiki da aljannu ne kawai amma duk ba gaskiya bane hasali ma mugun matsoraci ne. Tukunyarta ta ɗauka ta fita shi kuma ya sauya kaya da rawani ya yafo hirami ya riko carbinsa ya fito yana baza babbar riga ya nufi ɗakin zauren. Da sallama ya shiga Baba da duk jikinta ya yi sanyi ta amsa masa yana wani bokara da wani bada faɗi ya samu wuri ya zauna. 'Hmmm! Allah fitar da A'i daga rogo' Cewar Baba tana kallon yadda rawanin kansa ya zauna daram. "Mun ci dubu sai ceto maganin biri karen maguzawa iya gani iya kalewa" Malam ya ce yana duba duka kusurwowoyin ɗakin. "Malam su ne fa za a yi wa aikin" Baba ta ce jin yana tofe ta da yawu. Bai tanka mata ba ya cigaba da tofe tofensa gabas da yamma kudu da arewa. Sai da ya kammala ya ce. "Almutsutsai ne kewaye da ɗakin shi ya sa kuma kin ga aikin naku babba ne don haka sai an shiry" Kai kawai Baba ta shiga gyaɗa masa don ita gabaɗaya a tsorace take tamkar ta zura da gudu. "Kai ku karaso nan ku saki jikin ku ku kaddara babu akuya a bayanku rukiyya zan yi da kanta za ta san na yi don karo sa mu babu daɗi" Ya ce yana janyo wani kwano mai ruwa a ciki. Sai da ya kawo ruwan gabansa sannan ya kalleta ya ce "Ladan abin sadaka bama faɗa amma dai kuma a kan abin da za ku bayar za ku ɗoro mini katon turkekken rago kosasshe da bunsurun ɗan akuya" Ya ce cikin halin ko in kula. Gaban Baba ne ya faɗi don ita ɗari biyu ce a leɓen zaninta take so idan ya gama ta bashi sadaka amma yanzu jin gagarumin abin da ya zana wai kuma ba shi kaɗai bane ma abin sadakar shi a matsayij abin da za a ɗora masa a kan abin da za a bayar ne. Ina ta ga wani katon rago da bunsurun ɗan akuya. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Sagiru da Ahmadu jin furucin malam bayana dama babun da suke ciki ce ta ishe su suka je suka sato akuya to yanzu ina za su samo rago da ɗan akuya. "In ba zai samu ba kar ma in wahalar da kaina don wannan akuyar sai an sha fama za ta ɓanɓaru daga jikin su in ba za su samu ba a bar su da kayansu amma ku sani sai ranar da ransu ya bar gangar jikinsu za ta fita" Ya katse musu zancen zucin da suke shi ma kuma fa bai zaci abin ya kai yadda yake ba duk a tunaninsa dai kawai akuya ce take da gardama shi ne yake son damfarar waɗannan abubuwan. "A yi wallahi za mu nemo duk inda suke" Ahmadu ya yi saurin faɗa. ."Ko da na ji ku dawo daga nan" Ya ce yana nuna musu gefensa ita dai akuya tana lakuɓe a bayansu. Hannu ya saka a ruwan ya kamfato ya watsa musu har akuyar, baki ta buɗe cikin wani karaji ta ce meeeee. "Ai yau sai kin gwammace kiɗa da karatu za ki san kin zo hannun malam kailu kare kukan ka" Ya ce yana kara ɗakko ruwan ya watsa mata. Akuya bata yi bori da sanyin jiki ba ta saki tusa mai bala'in karan da malam ya ɗaga kwaryar kasar da yake zane a ciki ya sheke a kansa, da ta sake sakin wata a guje ya yi taku biyu ya tsallake Baba da ta dukunkune kanta ta toshe kunnuwanta shi kuwa bai yi masauki a ko ina ba sai a saman buhun hatsin da yake ɗakin, yana ɗare buhun ya mika hannu yana kokarin neman inda zai kama ya fake a jikin saman silin ɗin ɗakin. Bai yi aune ba sai ganinsa ya yi suuuu yana bin jikin bango tamkar wani kadangare shi dai a saninsa ya shi yake tahowa ba amma sai ya ji tamkar janyo shi ake yi sai da aka kawo shi har kasa sannan ya daina jin ana ja masa kafa a zahiri dai babu kowa ma a kusa da shi amma a baɗini yana jin yadda aka yi ta jan kafarsa. Raba idanu ya shiga yi cikinsa yana karta masa. "Jama'a kuna jin yadda ake tada boom a garin nan namu na Gumel tabbas yau ƴan bindiga sun kawo ziyara. Baba da yake akuya ta bata baya sai ta shiga yi wa malam nuni da akuya tana alamanta masa cewa daga gare ta ne karan saboda shi ɗazu a turakarsa da ake cewa karan iskar ƴar shayi ce ai ba wai ya gama fahimtar manufarsu bane shi ya sa ma yanzu ya kasa yaki da zuciyarsa wajen danne tsoron danya dirar masa ta sanadiyyar karan da ya kareɗe kunnuwansa "Ina miki maganar booom kin nuna mini wannan karamar alhakin da na kusa yin mganinta ki bari karan nan ya lafa sai na gama mata aiki ga wani wari ma da nake ji yana baibaye mini hanci tamkar an ajiye mushe a ɗakin" Ya ce yana kallon su Sagiru da gabaɗaya ido ya raina fata. Dakyar ya samu dawowa daidai ya koma kan buzunsa ya zauna tare da gyara babbar rigarsa da ya gama yakune ta wajen gudun famfalakin karan sai kuma ya daidai naɗin rawanin ya janyo kwaryarsa da ya shekar da kasar ya ajiye a gefe ya janyo farantin mai kasa ya ce "Innama amruhu iza arada shai'an an yakula lahu kun fayakun" Ya ce yana tofawa a satin fuskar akuyar. Idan har ba gizo idanunsa suke masa ba idan kuma ba wai kwayar idanunsa ce bata gani daidai sai ya ga akuyar murmushi take masa har da hararar kasan ido. Dimmmmm kirjinsa ya buga da karfi ya razana don ya san tabbas akuyar nan va wai akuya ce aljannu suka shige ta ba, ba don ma kar ya faɗi ba daidai ba sai ya ce aljana ce sak babu sirki. Amma saboda karfin hali da kuma kar ya nuna gazawarsa a aikin sai ya yi kamar bai gani ba saboda ba ya so su Baba su fahimci zunzurutun tsoron da yake ciki tun da ya gama faɗa cewa karyar aljani ya gagare shi, ya fi so kamar yadda yake kare kukan ka to yana so idan sun yi gaba su adar saboda ba ya so sunan nan nasa ya sauya don matsawar aka samu akasin lissafi to zai ɓata rawarsa da tsalle ne domin kuwa wanda suke cincirindon zuwa wajensa karɓar magani za su masa tawaye bayan kuma sana'ar maluntakar nan da ita ya dogara. Duk da daji yake zuwa ya samo sassaken bishiyoyi na magani matarsa ta daka a ɗaɗɗaura yana ba wa masu zuwa wajensa abin da ya sa kuma suke ganin maganin yana yi saboda dama duk abin da ka yarda zai maka magani to zai maka ne to matsawar kuwa aka ji ya razana ya kasa cire aljanar akuyar nan ya san sai sunansa ya dushashe. Daurewa ya yi, ya jure ya yi ta maza ya kara kallon fuskar akuyar nan, kawai sai ya ga ta kashe masa ido ɗaya da ya kara kallo ma sai ya ga fuskar ta sauya zuwa ta mutum kyakkyawar darar mace sai kuma ta rikiɗe ta zama ta akuya duk abin nan da ake yi su Baba basu san wainar da ake toyawa ba musamman su Sagiru da suka runtse idanu suna jiran tsammani. Malam Kailu kai ya sunkuyar yana jan lahaula wala kuwwata, ji yake kamar ya tashi ya zura a guje don ya san da a ce ita ma Baba ta ga abin da ya gani watakila da tuni ta daɗe a hanyar gida su dama su Ahmadu ba a maganarsu tun da su tif da taya suke da akuyar babu damar gudu duk inda za su je to kuwa suna tare. Kan da ya sunkuyar sai kawai yake ganin fuskar farar matar nan a dab da fuskarsa. 'Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir rahim, wailul likulli humazatin lumaza, wattini wazzaitun, tabbat yada abi lahabin wattabbu' Malam waɗannan ayoyin ne ya samo a kwakwalwarsa duk ayar da ya janyo ba ya iya ta gabanta ji yake ya manta cigaban sai dai ya kara kamo wata. "Malam ya ka dakata?" Ya ji Baba ta jefo masa wannan tambayar ɗagowa ya yi ya kalleta gani ta yi ya haɗa gumi sharkaf zufar sai kwaranya take a fuskaraa da wuyansa idan ma ba idanunsa sun nuna mata ba daidai ba da sai ta ce kamar hawaye ta gani yana fita daga idanun don idanun ma sun yi jajur kamar mai kuka a ɓoye. Dariyar yake ya sakarwa Baba wacce ta fi kuka ciwo yana ji a ransa yau ya ɗakko aikin da ya fi karfinsa domin kuwa dala ba gammo ce, shi ba ya son mutanen ɓoye tsoronsu yake duk abin da yake faɗa dama cika baki ne. Don akwai lokacin da suka buɗe musu ido shi da matarsa suke ganinsu muraran ranar kwana suka yi basu runtsa ba. Duk da ba wai aljannun suna tsayawa bane kawai dai suna fitowa su ga wulginsu ko kuma suke ji maganganu a ɗakin da kuruftun taɓa kayayaki bare kuma yau da ya yi arba da akuya tana murmushi da kashe ido, ya san yau kam abin ba sauki ciwon arne. "Malam" Baba ta kira shi ganin gabaɗaya ba ya cikin nutsuwarsa kuma ya ki magana. "Uhmmm" Ya amsa mata uhmm don yana buɗe bakinsa watakila kuka ya kwace masa a yi abin kunya. "Na ce aikin nan kuwa zai iyu?" 'Su fa suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba da a ce kin yi arba da abin na gani yanzu a tattare da akuyar nan watakila da yanzu kin yi gudun kilomitoci ni ma don babu yadda zan yi ne' Ya ce a zuciyarsa a fili kuma sai ya ɗaga ido ua kalli akuyar a fakaice ya ga har lokacin tana kallonsa kurrr da idanu a wannan karon kuma sai ya ga ta masa wani kallo kamar na soyayya sai kuma ya ga ta turo masa baki wato ta cure bakinta wajen ɗaya ta masa alamar kiss. "Alif lamra, ha karami minjaye" Ya shiga faɗa cikin ruɗu a fili ba tare da ya sani ba. "Alif lam ra, ha karami minjaye" Ya ga bakin akuyar ya buɗe ya faɗa har cikin kunnensa amma da alama shi kaɗai ya ji ta maimaita abin da ya ce don da alama su Baba basu ji ba. "Malama kai da za ka yi rukiyya ka raba su da wannan abu amma duk ka sauya na kasa gane a cikin aikin kake ko a gaba za ka yi aikin? Kuma yanzu sai ka ce alif lam ra, ha karami minjaye don Allah ya kake so a yi daren azumi ne fa an daɗe da yin isha'i da sallar tarawihi ana jimawa kafafun jama'a za su ɗauki.... Kwuuuuuiiiiiuttttt Baba ta ji Malam ya saki wata tusa mai kara kamar an danne kan kwaɗo da alama tusar ya yi yaki da ita ne wato ya zauneta don kar ta bayyana amma ta fito tun da a fitar karan kana jin yadda aka danne karan. Malam kuwa Baba bata san lokacin da take masa magana kan ajuyar nan ya ga ya zama kai biyu sai kuma daga tsakiya ya ga kan wannan farar matar wannan ne ya tsorata shi ya ji tusa za ta kuɓuce masa don kar su Baba su ji su yi zaton wani abu sai ya danne amma kuma bashi da karfin rike tusar ya hana ta fita wannan dalilin ne ya sa suka ji karan kamar an danne kan kwaɗo musamman da ya lura shi kaɗai ne yake ganin waɗannan abubuwan. Saura page ɗaya mu gama free pages, ko dai ki biya 500 ko ki yi like MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇 *Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana* [8/25, 9:31 AM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *IMZEED VENTURE* Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo! Tuntuɓemu 07077532253 Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1 *CI-MA-ZAUNE* NA MAMAN AFRAH PAGE 1️⃣8️⃣ MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇 *Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana* CI-MA-ZAUNE. NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣8️⃣ 'Baki san duniyar da nake ba muraran nake ganin akuyar tana caccanjawa' Ya ce a ransa amma a fili ya danne tsoronsa ya ce "Yanzu dai nake kan aikin kin san aikin ne babban aiki duk ni a wajena ba wani babba bane" Ya ce tamkar ya yi kuka. Baba kai ta shiga gyaɗa masa su Ahmadu kuma suna jiran zaman jiran tsamani, akuya kuwa jin abin da malam ya ce wato aikin a wajensa ba wani babban aiki bane kawai sai ta mika kanta ya zaman wuyanta ya kara tsawo ta kai bakinta kusa da na malam. "Subhanallahi wa bihamdihi subhanallahil azim" Shi ne abin da malam ya shiga ambta a zuciyarsa ganin bakin akuya yana dab da nashi wato akuya tana shirin doɓara bakinta a kan nasa da alama dai sumbata ce za ta masa. Idanu ya runtse yana jin faɗuwar gabansa tana tsananta don a nasa tunani watakila bakinta yana sauka a nata za su iya ɓacewa tare. Ganin hakan da akuyar ta yi sai ta yi wani tashi tamkar mai tafiya a saman iska bata yi masauki a ko ina ba sai a kan bayan malam ta sakalo kafafunta na gaba a wuyansa. Sagiru da Ahmadu wani irin bugu gabansu ya yi lokacin da suka ji alamar ta bar jikinsu basu ankara ba lokacin sai da suka fara laluma bayansu suka tabbatar bata nana wani daɗi ya rufe su a nasu tunanin malam ne ya raba su da ita musamman da suka ji ya ce ba wani babban aiki bane a wajensa sai dai kuma me? Ashe dara ake yi sai kuma dare ya yi wato dai suna ɗagowa suka yi wa idanunsu masauki a kan akuyar makale da jikin malam. Buɗe bakin da akuyar ta yi ta yi wani kuka shi ya sanya Ahmadu da Sagiru darewa a sukwane cikin gudun ceton rai suka garzaya wajen Baba. Baba wacce kukan akuyar ya sa ta yi zaman ƴan bori ba tare da ta shirya ba, kafafun ta duka biyu a mike da yake ma a jikin bango ta zauna. Don haka su Sagiru suna zuwa kowa ya yi wa kansa masauki a kan cinyarta guda ɗaya, amma kuma Baba bata ma san a kan cinyarta suke ba. Malam jin saukar abu a gadon bayansa sai ya kwalalo idanu, wanda yake son ta tabbar ta hanyar kallon su Sagiru don dama tun da ya ga bakinta yana dab da nasa sai ya rufe nasa idanun yake jiran tsammani. Ganin babu bakin akuyar a kusa da bakinsa kuma babu akuyar a bayan su Ahmadu sai gabansa ya harba da karfi a sannan ya lura da kawanya da aka yi wa wuyansa da wani abu mai kamar icce cikin karfin hali ya kai hannunsa bayansa don ya tabbatar a kan jelar akuyar ya ɗora hannunsa wacce ta cika da gashi luɓuɓu. Wani tari ne ya kwace masa don sai ya ji ya manta ma yadda ake kuka mai sauti ko tarin ma tsintar kansa ya yi da yi. 'Yau na janyo jafa'i ni Kailu aka ce ana ɗaure aljannu da azumi to ko dai musulmin ba a ɗaure su?" Ya jefawa kansa tambayar. "Malam Kailu mai kare kukan ka" Ya ji ta raɗa masa a kunne jin haka sai hawaye suka shiga sirnano masa, domin gabaɗaya ya fashimci kashin sa ya bushe. Ganin abin yana neman fin karfinsa sai ya shiga kokarin rarrafawa saboda ya saka a ransa cewa babu yadda za a yi su Baba su zo su goga masa kashin kaji. Dakyar ya iya jan gwiwarsa ya nufi wajan su Babar a ransa yana jinjina kokarin su Sagiru da suka iya jurewa ko dom idan ma basu jure ba ya za su yi tun da basu da mafita. Baba da take son su samu su suɓuce su gudu tun da har Allah ya taimake su akuyar ta bar jikin su Ahmad amma sai ta hango Malam ɗin ya nufo su da rarrafe. Kokarin mikewa tsaye ta shiga yi amma sai ta ji kafafun nata kamar an ɗaɗɗaure baya san cea su Sagiru ne suka yada zango a kan su ba. "Ku taimaka wa malam Kailu jama'a musulmi ɗan uwan musulmi ne" Cewar malam lokacin da ya taho wajen su yana ta maimaita musulmi ɗan uwan musulmi ne tamkar wanda ya samu karatun fatiha. Kowa da kallo ya bishi ganin shi gabaɗaya ya rakwakwkwaɓe tamkar wani karamin yaro. "Malam kai da muka kawo wurinka ai sai ka yi addu'ar ta fita amma mu ina za.mu iya wannan sha'ani sa za mu iya da bamu kawo wurinka b... "Ni dai an cuce ni an zaluncr ni haka kawai ina zaman-zamana an watsa mini hatsi kaji suna bina" Malam ya katse Baba cikin gunjin kuka don yana ganin su ne ummul aba'isin komai. "Ka yi addu'ar mana" ."Ina ma zan iya addu'ar gabaɗaya an dagula mini lissafi duk ayoyin da na gaddace a kan nan nawa amma yanzu in biya ɗaya ma abin ya faskara duk sun gudu sun bar ni" Su Baba ganin ya zo dab da su sai suka cure a waje ɗaya tamkar kuli-kuli(Karago). "Wallahi ni ma cikin ku zan kwatsima ba zan zauna ni kadai ba gwara a yi wake da shinkafa" Ya ce yana kara saurin rarrafensa. "Kar ka kuskura ka karasa wajen su" Ya ji muryar akuyar raɗau a kunnensa. Kittt ya ja wani uban birki ga koshi ga kwanan yunwa. "Ki taimaka ki sauka daha bayana" Ya ce da kuka shaɓe-shaɓe. "Ka yarda da sharaɗi?" "Ni ba ma sai kin faɗa mini sharaɗin ba in dai za ki sauka daga jikina... Tun bai kar karshen maganar ba ya ga akuyar ta sauka ta tsaya a tsakiyar ɗakin sai aka shiga kallom kallo tsakanin malam da akuya da su Baba. Dama shi ya yi hakan saboda ya ribace ta, ta sauka yanzu kuma shammatar ta yake so ya yi ya fice da gudu daga ɗakin ya je turakarsa ya rufe don gabaɗaya ma ya manta cewa ko ta bango za ya iya shiga ta masa hukunci daidai da laifinsa. Kowa da mamaki yake kallon akuya ganin ta zauna ɗam a kan mazaunanta, malam da yake fakonta kuwa ba ta ita yake ba so yake ya garzaya zuwa kofa ba ma ta mamakin zaman da ta yi yake ba tun da ta yi magana shi bai ga wani abu da za ta kasa yi ba baya ta juya musu hakan ya sa malam cikin sanɗar rarrafansa ya durfafi kofa su ma su Baba ganin haka suka shiga akamantawa juna yana fita za su fice. Ai malam yana dab da fita bai yi aune ba sai ji ya yi an damko wuyansa aka ɗaga shi sama cidik, idanu ya shiga zarewa sai dai bai ga wanda ya ɗauke shi ba har yanzu kawai dai an ɗaga shi ɗin ne kuma yana reto sannan akuya dai tana yadda take wato ta juya bayansa. Kana kallon fuskar malam za ka ga a firgice yake don yanzu tsoronsa ya ruɓanya jin an ɗaga shi amma ko alama bai ga wanda ya ɗaga shin ba. Su Baba sai suka yi ɗiff suna ganin ikon Allah saboda yanzu an cire musu sha'awar fita don ganin an ɗaga malam yana reto a saman iska, ba a ɗau wani lokaci ba sai ga malam zaune a cinyar akuya ta rungume shi a kan cinyarta ko dai kafafu ne ma oho. Malam kawai zare ido yake saboda ya nemi addu'a ma ya rasa shi yakin da yake ma da numfashinsa wajen shaka kaɗai ya ishe shi bare kuma akuyar nan da ba ya kaunar ganinta. "Na daina tarkar fita a mini afuwa ina bada hakuri cikin kwando" Ya ce yana haɗa hannu alamar roko. Kafadunta na gaba ta saka ta dokewa malam hannun inda ya ji wajen kofaton ya buge shi da sauri ya janye hannayen gabansa yana bugawa. Akuyar nan mamanta ɗaya ta kamo(Breast) Malam yana jiran ya ga mai za ta yi da shi sai kuwa ta nufi bakinsa da shi, har wani kara rungume shi ta yi irin yadda ake yi wa yara in za a shayar da su. Malam bakinsa ya shiga dantsewa da mugun karfi don shi ba zai taɓa yarda aljanar akuya ta shayar da shi ba ya je ma ya zuki maman ya haɗiye ya ɓace ɓata ya koma jinsin aljannu. Bata masa magana ba bata kuma fara nufar bakin nasa da maman ba. 'Na shiga uku ni Kailu bayan gyatumata da ta shayar da ni wata goma sha takwas yanzu a ce in sha nonon akuya, nonon akuyar ma ba kindirmo ba a jikinta kuma akuyar ma aljana jama'a ku kawo ɗauki Malam Kailu mai kare kukan ka zai fita daga jinsin bil adama ya koma jinsin aljannu taimako jama'a wayyo ni aradu maluntar ma na daina kowa ya je ya ji da jinyar da take damunsa tun da abin ya zama haka daga taimako sai a ɗora mini JALLI JOGA( Shin kin karanta littafina JALLI JOGA kin ji yadda matan makaho suke kishi bayan kuma aminai ne tun na yarinta badakalar bata tsaya a nan ba yadda uwar gida da jikarta suka sunkuma sabuwar amarya a kasan gado suka cinye kazar amarcin turka-turkar sai kin karanta dariya kuwa sai cikin ki ya faɗa miki tuntuɓe ni a 09013181851). "Malam ya ce a zuciyarsa yana jin da na sani wacce ta kasance keya ce! Akuya dai bata saurare shi ba ta sake cafo gabaɗaya maman nata(Breast) Wanda yake dogo jalailai da shi ta sake tunkarar malam, tuni malam hawayen tausayin kansa ya gama wanke masa fuska sai jujjuya kai yake alamar a'a amma kuma ya ga akuyar bata fahimtar karatun kurman da yake biya mata ta hanya jijjiga kai. "Haba ɗan lele ka sha maman Babarka mana" Ta ce tana dungura masa maman a baki, sosai ya ji wani warin dabobi ya bugi hancisa har amai yana yunkuro shi amma ya dantse bakin saboda ba ya kaunar bakinsa ya buɗu ko da miskala zarratin bare a samu akasin lissafi. "Baba mai kosai kasa ta daɗe da rufe idanunta(Ta mutu) Wallahi na sha nono har ya mini karo ki mini afuwa in ina son nonon na sayi kindirmo a wajen fulani a dama mini fura" Ya ce yana kare bakinsa da hannunsa don ma kar a samu akasi yana magana ta saka masa a bakin. "To in gani kake ka girmi shan nonon ne ai sai in mayar da kai ɗan kundalo(Wada) Yanzun nan zan mayar da kai wada ka kankance ka zama jariri sai ka sha ko?" Ta ce "Wallahi an yaye ni, an daɗe da yaye ni, har na girma don Allah kar ki mayar da ni ɗan kundalon wada" Baba, Sagiru da Ahmadu wanda suka faki idanun akuya da malam suka sulale da rarrafe suka bar ɗakin ba tare da an lura ba. Haka suka samu suka kuɓuto suka fita wajen da rarrafe don ma kar a ankara a dawo da su, domin gabaɗaya sun tsorata da lamarin ganin abin da yake wakana sun san layi yana dab da zuwa kansu ma'ana ana gamawa da malam watakila a shiga shayar da su ɗaya bayan ɗaya. Sai ga shi dai cikin ikon Allah sun kuɓuto ba tare da asirinsu ya tonu ba. A can cikin ɗaki kuwa akuya bata san su Sagiru sun fice ba sai da ta ɗago ta ga wayam don haka sai ta mayar da hankali kan malam tana jira ta gama da shi tukunna. Bata yi kasa a gwiwa ba tana dafa kan malam da yake rawanin ma ya faɗi har hular tana dafa kansa ta yi mismis da baki sai ga malam yana kankancewa sai da ya koma kamar yaro ɗan shekara biyu sannan ta ɗauke kofaton hannun nata daga saman kan nasa. Malam yana ji yana gani ya koma ɗan karamin yaro kukan takaici kawai yake a zuciyarsa wanda ya fi na fili ciwo. A haka ya ga ta tattaro duka maman nata guda biyu ta nufi bakinsa da shi. "Gwara in ruɓanya maka biyu ko ya fi kosarka" Ta ce "Wallahi ɗaya ma albarka bare biyu ni a koshe nake ma" Ya ce gabansa yana matsanancin bugawa jin maganar da ya yi ma ta koma muryar kananan yara a take ya shiga tunanin idan yanzu aljanar akuyar nan ta ɓace haka zai rayu ɗan karami kuma da muryar kananan yara. Ita dai bata kula shi ba har yanzu tana kokarin shayar da shi da mamanta biyu kuma har lokacin yana kwance a kanta alamar runguma da ake yi wa yara in za a shayar da su. Malam ganin haka sai ya yi yaki da zuciyarsa ya shiga karanta abin da ya zo bakinsa saboda ya lura addu'a ce kawai za ta kuɓutar da shi da yake yanzu ma ya ɗan kalli wajen da su Baba suke rakuɓe sai ya ga kamar an yi ruwa an ɗauke wato babu su babu dalilinsu babu wata alama da za ta nuna wanzuwwarsu ma a wajen ganin haka sai ya fahimci ya shiga casa'in da tara domin kuwa a nasa ganin ya yi nutsu a cikin rijiya mai gaba dubu da zai yi wuya ya fito. Fatiha ce ya samu nasarar cafkowa yake karantawa a fili duk da yana jin yadda muryarsa take tamkar ta kananan yara, don har wani dabalbalewa take irin ta yara masu koyan magana ko wanda bakin nasu bai gama buɗewa sosai ba, amma a haka yake karantawa har ya samu nasarar kai karshen fatihar duk da yana jin yadda akuyar take wasu maganganu amma kuma bai saurara ba sai ma ya kamo falaki da nasi ya shiga yi babu saurarawa. Wani kara ya ji akuyar tana yi kamar wata haniniyar doki sai kuma ya ga ta ɗaga shi da hannunta daya ta yi jifa da shi can ya je ya doku da bango ya faɗa kan wasu kwanuka da suke ajiye a ɗakin da ba amfani ake da su ba, kafin ya ga ta tashi ta shiga zaga ɗakin tana kukan su na akuyoyi meeee kafin cikin minti biyu ta bi kofar da mutane suke shigowa ɗakin ta zaure fittt ta fice yana iya jiyo kukanta. Ɗif ya yi kamar an yi ruwa an ɗauke yana tunanin ko su Sagiru sun tsira ko kuwa za ta cin musu da wannan tunanin ya shiga kokarin tashi yana karewa jikinsa kallon yadda ya dawo kamar yaro ɗan shekara biyu sai gemunsa da yake reto jalai-jalai. Da adungure ya gangaro daga saman kwanukan, ya mike tsaye yana shirin tattara babbar rigarsa ya zuba a guje amma abin mamaki sai kawai ya ga babu babbar riga babu dalilinta asali ma ba kayansa bane a jikinsa riga ce tafe da wando(Over roll, cike da mamaki ya kai hannu kan mazaunansa sai jin pampers ya yi ga fida makale a jikin aljihun rigar da alama ma nonon akuyar ne a ciki saboda wani abu ne fari kamar madara. ."Kai jama'a inda ranka ka sha kallo ni malam kailu mai kare kukan ka ni ne sanya da rigar yara tafe da wando har da nafkin(Pampers) Ga bulunboti(Fida) kai wallahi na ga rayuwa yau dai tabbas wannan aljanar akuyar a cikin musulman aljannun ma da ba a ɗaure ba saboda falalar ramadan ita takidara ce' Ya ce a zuciyarsa yana share hawayen tausayin kansa yana tunanin ko dai zaluntar mutane da yake yi ne Allah ya jarabce shi yau don sai ya ji a ransa ma bai yarda da su Baba ba ya fara zargin su duka ma aljannun ne suka yi ɓadda kama, ga shi yana tunanin yadda za su kare da matsoraciyar matarsa ba lallai ma ta tsaya ya mata bayanin shi ne mijinta ba aljana ce ta mayar da shi haka, watakila ma idan ta faɗa mata aljana ce shikenan ma ta kara tsorata. Da wannan tunanin ya surfafa tsakar gidan a guje. Kwararaf ya yi tuntuɓe da wata tsohuwar fashashshiyar roba a tsakar gidan sai da ya yi dungurawa uku sannan ya je a zaune. Karan faɗuwarsa ne ya ankarar da matarsa wacce take zaune a kujera a wajen murhu tana kara kaɗa miyar da ya zubar, tana waiwayowa idanunta suka sauka a kan karamin yaro zaune da riga tafe da wando (Over roll) Kafarsa ƴar ɗul a mike kan nan nasa a salsale ya sha kwal kwabo hasken farin wata ya haske kan ral amma kuma abin da ya kara wutar tsoro da bugun zuciyarta ganin zangareran gemo yana jalaitu. Da karfi gabanta ya buga saboda a cikin mintin da bai wuce ɗaya ba ta gama kare masa kallo har sakon ya kai kwakwalwarta cewa aljani ne ba mutum ba don a wannan daren ba yadda za a yi a ga yaro karami da bai fi shekara biyu ba shi kaɗai ba tare da uwarsa ba, domin ita ko karan tafiya bata ji ba karan faɗowar kawai ta ji abu ɗaya da ya fara zuwa a ranta shi ne ko daga sama ya faɗo. Kokarin raba mazaunanta da kujerar da take zaune ta shiga yi amma cikin ikon Allah abin ya gagara sai lokacin take tunanin ashe ma ka ga abin tsoro ka samu damar guduwa arziki ne. Don gabaɗaya kamar an mata dabaibayi, duka jikinta sai karkarwa yake robar kukar miyar da take kaɗawa da ludan tuni suka yi ɓatan dabo a hannunta kowanne ya kama gabansa. "Ni ne malam" Ta ji yaron ya furta mata bata ankara ba sai gani ta yi ya dafa kasa ya mike tsaye gemun nasa har kirjinsa ga wata fida tana reto a aljihunsa bata gama gane tana cikin tashin hankali ba sai da ta ga ya nufo ta yana ɗaga mata hannu. *Tirka tirka, badaƙala, cakwakiya, shin malam zai dawo daga ƙaramin yaron da akuya ta mayar da shi kuwa? Mai zai fari da matar malam da ta ga mijin ta a siffar yara yana magana da muryar yara, shin za ta karɓe shi ko gudunsa za ta yi. Ya batun su Baba da su sagiru shin za su tsira kuwa kun dai san aljanar akuyar nan tana iya zuwa cikin sakanni ma ta cim musu, shin mai zai faru? Ya rayuwar su *Dada za ta kasance shin za ta koma ƙauyen ko kuwa xa ta gwammaci zama a wannan yunwar, akwai wasu ɓangarori da bamu nutsa ba a cikin labarin na sabbin taurari ko dai kar ku bari a yi tafiyar babu ko da 500 ko LIKE za ku sha karatu* * *A nan na kawo ƙarshen feee pages mai son cigaba zai biya 500 ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222 opay. Ko kuma a min magana a karɓi link a mini like na saka mutum a paid grp ya karanta.*