[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* ➰➰ *1 to 2* *Gombe State* Garin gombe garine na fulani mai tarin albarka duk da kasancewarta garin Fulani, hakan bai hanata tara ƙabilu dabam dabam ba, kama daga tangale, kanuri, bolawa, wajawa, terawa, Daɗawa, Dadiyawa, da sauran su, haka ta tara ƙauyuka na fulani a cikin wannan jihar ta Gombe akwai local government wanda ake kira da *DUKKU* acikin wannan local government ɗin na dukku akwai wani ƙauye na fulani Usul ko hausa basa ji sosai, wanda ake kira da *TULDEN FULANI* Tulde ƙauye ne mai tarin albarka, kama daga kiwon dabbobi noma harma da ƴaƴan itatuwa, a cikin wannan ƙauyen suna zaune ne cike da farin ciki, da ƙaunar junansu kasancewar Fulani mutane ne masu haɗin kai, mutum biyu ne kawai matsalarsu wanda kullum suke jawo musu fitina wato *INNO* da jikarta *JUMMO* INNO ta kasance gagararriyar tsohuwa wacce kullum bata da aikin daya wuce hura sigari da gabzar goro rashin mutunci kuwa wajen INNO ya ta'azzara bata da tsoro bare shakka, INNO bata da mutunci ko kaɗan tamkar ba bafulatana ba, kowa shakkar ta yake cikin ƙauyen, wannan ɗabia ta INNO jikarta JUMMO ta biyo wasu daga ciki, sai dai koda wasa Jummo bata taɓa shawa'ar sigari ba, ita dai barta da rashin kunya gami da masifa bata tsoron kowa, mahaifiyarta Sikayel da kakanta Baffa suna mungun takaicin halin INNO da Jummo, domin kuwa toka ce ta haifi wuta, Sikayel macece mai sanyin hali da tarbiyya tana bawa Jummo duk wata tarbiyya daya dace, sai dai INNO sam bata bari ta ɗauka hakan yasa Sikayel dagewa da addu'ar Allah ya shirya mata Jummo, Jummo tafi dukkan ƴan matan ƙauyen kyau da diri duk inda ake neman cikakkiyar mace, Jummo ta tsaya a nan matsalarta ɗaya rashin tsafta, domin kuwa Jummo cikakkiyar ƙazama ce, wannan kenan. Zaune take gaban INNO ta tanƙwashe ƙafafuwan ta, tare da saka hanu ta tallafi fuskarta tana kallon INNO dake famar hura sigari tana gugar goro kasancewar ta bata da haƙori, dole sai da guga, taɓe bakinta Jummo tayi cike da rashin mutunci tace wa INNO. " Cap!!! Wallahi INNO kin shiga Uku, yanzu haka zaman da nake a gabanki hango masauƙin ki nake a cikin wutar jahannama!!! Yanzu ke INNO idan banda rashin tsoron Allah, Baffa ya tara almajirai a waje yana koya musu ƙur'ani, ke kuma kina nan zaune anan kina bitar sigari, Allah ka kashe INNO gobe ta shiga Uku a hanun walakiri!!!!'' Jummo tayi Maganar tana sheƙewa da dariya, INNO kuwa jikinta na ɓari ta bar gugan goron tare da ajiye tabar ta fuskanci Jummo, kanne ƙananan idanunta tayi, alamun rashin mutunci tace. " Ubanki Jauro da uwarki Sikayel, masauƙin su kika hango!!! To dan kutumar ubanki, da kike kira min mutuwa, ni nan da kike gani bazan mutu yanzu ba, sai na gama ganin taku sai naga ta uwarki naga ta ubanki sannan naga taki, kuma duk da haka ina nan daram, shegiya mai kai kamar ƙoƙiya, kin faɗawa ubanki Jauro!!!' INNO tayi Maganar tana saka hanu ta ɗauki goronta ta cigaba da guga, Sikayel dake gefe tana surfa hatsin dawa ne ta girgiza kanta kasancewar tana sauraron dukkan hirar su, wai damma a haka ƴar ɗakinta JUMMO ne tayi Maganar, da wani ne yayi wannan maganar ba Jummo ba, mai shiga tsakanin su da INNO sai Allah, Jummo dariya tasa har tana sunkuyawa tace. " INNO kice gadin duniya zakiyi kenan, to idan kowa ya mutu ya barki ke kinyi ta karshe waye zai miki sallah bare a rufeki a ramin ki?'' Ɗago kanta INNO tayi take ranta ya ɓaci ta haɗa fuska tamkar zata danna kuka, a duniya ta tsani a kira mata mutuwa, musamman a kira mata kabari sai taji tamkar ta zura da gudu, hantar cikin ta ya kaɗa, ranta na ɓace tace. " Jummo kiyi hkr ki daina kira min mutuwa, banason sunan kabarin nan, Allah ni na yadda nayi ta ƙarshe a duniya, babu ruwana da wani mai min sallah, idan na mutu ai shikenan ni ina ruwana yama fimin dama bana son zaman wannan kabarin, kina gani rami ɗan karami za'a tona a saka mutum a cikin sa, a rufe ko ina tsabar mugun ta ko hujin da zakasha iska baza'a bari ba shikenan an raba ka da kowa iskar ma baza'a bari ka shaƙeta ba." Dariya ce taso kwacewa Sikayel, sai ta danne dariyar gudun masifar INNO, ta cigaba da surfen ta, tana sauraron su, Jummo kuwa murmushi tayi tare da miƙewa tsaye, ta zari sandarta, gyara rigarta na fulani dake jikinta tayi, ta sunkuyo kan INNO daidai kunnenta ta raɗa mata. " Ko zaki hallaka sai kin mutu an saki cikin wannan kabarin da bakya so, muddun baki daina shan wannan sigarin ba, da wani magulallen bakin ki, da babu haƙori." Tana gama maganar ta zura da gudu tana dariya tace. " Sikayel mi dilli sai mi warti (na tafi sai na dawo)" Sikayel da kallo tabi Jummo tace. " Garta jam (a dawo lafiya)" Jummo bata ma ji Sikayel ba tuni ta fice, da gudu. Ai kuwa INNO bala'i ta hau da mita. " Sai naga uban da zai binne Ni, shegiya mai mungun fata, da ɗan iskan bakinki kamar murfin shadda, ina nan zaki dawo ki sameni." Baffa dake zaune cikin tarin almajiransa ne ya kwalawa Jummo kira. " Jummo!!!" Cak ta tsaya tare da tura baki, tana ƙunƙuni, tasan bazai wuce zancen hadda Baffa zai mata ba, ita tun jiya da ta ajiye allonta bata kuma ɗauka ba, muryar Baffa taji yana cewa. " Waro mana Jummo" Ta kowa tayi gabansa tare da tsugunnawa cikin bagwariyar Hausar ta da bata nuna ba tace. " Sannu da karatu Baffa." Murmushi yayi yana kallon yanda ta haɗa rai, yasan wannan fushin da tayi duk dan karya mata zancen hadda ne, girgiza kansa yayi tare da cewa. " Meyasa baki tafiya a nutse ne, Jummo kullum kina razane tamkar baki da hankali, ki dinga tafiya cikin nutsuwa wannan shine ɗabiar mace, kul na kuma ganinki kin fito da gudu." Kanta ta ɗaga alamun to tare da ƙoƙarin miƙewa zata tafi Baffa ya dakatar da ita da cewa. " Meya hanaki zuwa ki biye karantun ki, yau tun safe." Ƙara haɗa ranta JUMMO tayi dama ta sani dole sai ya mata wannan tambayar, cuna baki gaba tayi sannan tace. " Dama jiya dana koma zanyi karatu harna ɗauko allon, INNO ta aikeni shagon manu na saya mata karar sigari, dana dawo kuma dare yayi shine kawai na kwanta amma gobe zanzo na biya." Girgiza kansa Baffa yayi cike da ƙyamar halin INNO yace. " Tafi abinki Jummo!!" Tashi tayi cikin sauri tabar wajen jugum Baffa yayi yana nazarin mummunan ɗabiar matar tasa, ya rasa ya zaiyi da ita dukkan ta inda ya ɓullo mata dashi, sai tabi ta toshe, wannan wacce irin munguwar rayuwa INNO ke fama dashi, numfashi yace ( " Allah ka shirya INNO" ) ya cigaba da biyawa almajiransa karatu. " Ni Jummo Jummo jummala!!! Jummo me nake bukata faɗi muji jummala🎸🎸 ni dai taliyar turawa nake bukata jummala, wai shin ina zana samu jummo ce, taliyar turawa akwa.............'' Katse waƙar tayi ganin Gaɗɗo tsaye a gabanta sai haki take da alamu gudu tasha, cikin tashin hankali take cewa Jummo. " JUMMO rumfar Ja'e Sumaye!!! Yako zai kasheta!! Zai kasheta ki taimaka min Jummo!" Gyara tsayuwarta Jummo tayi tana dariya domin kuwa yau ta samu, murmushi ta saki take yalon hakwaranta suka bayyana tacewa gaɗɗo. " Ta faɗi ƙasa gasassa dama kuwa aradu goma nake nema, biyani Naira goma naje na sayi faɗan'' Tayi Maganar tana riƙe kunkumi harda jijjiga tare da miƙawa Gaɗɗo hanu alamun ta bata, gaɗɗo babu musu ta danƙawa Jummo murtala ɗaya kuɗin da innar ta, ta aiketa sayo dunƙule, karɓa Jummo tayi ta ɗaure a bakin zaninta tare da tattare zaninta, ta kwasa a guje ta doshi shagon Ja'e, Gaɗɗo ma rufa mata baya tayi basu tsaya ko ina ba sai rumfar Ja'e, tsakiyar Sumaye da Yako Jummo ta tsaya tare da riƙe kunkumi ta haɗa fuska tamau, sunkuyawa ƙasa tayi ta ciko tafin hannayenta da ƙasa ta miƙawa Yako. " Na sayi faɗan ganaa masifa gana bala'i zaɓi wanne zamuyi a ciki" Dariya Yako yasa dama kuwa ya juma yana jiran wannan ranar, ranar da zaici uban Jummo domin kuwa mungun haushin ta yake tun sanda ta yiwa ƙanƙara Jaɓɓo duka, na bala'in ya buge, ai kuwa Jummo bata jira mai zaice ba, tayi wani irin zillewa ta sunkuya ƙasa kafin Yako ya ankara ta kwashi ƙafafuwan sa, ji kake tim!!! Yako ya faɗi ƙasa, kafin ya yunkura ta doka masa sandar ta a ƙafafuwan sa, wani irin ƙarar azaba Yako ya danna, kansa Jummo ta ɗale tare da shaƙo wuyansa, Sumaye ta kalla tace mata. " Ɗebo ƙasa ki cikawa shege a baki." Ai kuwa sumaye ba musu ta ɗebo ƙasar Jummo ta matse bakin Yako suka ɗura masa sai famar muƙurƙusu yake ya gagara kwacewa jinsa duk yayi tsami, ada gani yake duka ɗaya zai yiwa Jummo sai ruwa amma yanzu ya fahimci tabbas yarinyar aljana ce, Ja'e daya fito daga bayi ne, ya karaso wajen da sauri yasa hanu yana janye Jummo daga jikin Yako, da ƙyar ya ɓanɓareta, yana haki Yako kuwa idanunsa yayi jajur sai famar furzar da ƙasan bakinsa yake, da ƙyar ya tashi ya zauna Ja'e ne yace. " Haba Jummo, meyasa zaki masa haka Yako fa ba sa'an ki bane sa'an yayanki Sauru ne, ki shige ki tafi a nan ke sam baki jin magana kowa faɗin fitinarki yake cikin rugar nan." " Karma ta tafi dan ubanta!!" muryarsa ta doki dodon kunnen ta wani irin lumshe idanunta tayi tare da saka hannunta ta dafe ƙirjinta *Mai oda* yaushe yazo cikin garin nan? Ta jefawa kanta tambayar, juyowa tayi ta taho da gudu zata rungumesa tana. " Oyoyo my oda ta!! Oyoyo yaya *GARKUWA* kifiyar sonka ta soke ni aradun Allah ina sonka." Saurin kaucewa Garkuwa yayi gudun karta taɓa sa da wannan dattin, ransa ya haɗa fuskarsa a ɗaure dama can shi ba ma'abocin dariya bane a hankali tamkar baya son magana ya nuna ta da yatsa. " Ke kam wacce irin jaka ce, dabba ce ke, wawiya jakar ƙauye, mahaukaciya, idan kika kuskura koda wasa hanunki ya taɓa koda gefen rigata ne, wallahi sai na kwantar dake mtsss!!! Nonsense mtsss!" Yayi Maganar yana buɗe motarsa fara sol mai kyawun gaske ya shige, idanu Jummo tabi sa dashi a duniya tana mungun son Garkuwa soyayya ta zahiri, motar ta nufa da gudu tana cewa. " Wallahi ina sonka my oda ta, my hanta ta, kai kayan ciki nane ma kai, kuma wallahi sai ka soni, zaka aureni ya garkuwa." Girgiza kansa garkuwa yayi tare da figar motar da ƙarfi ya buleta da ƙura, tsayawa Jummo tayi shuru sai kuma ta kwasa da gudu tamkar mahaukaciya tabi bayan motar, tama manta da su Sumaye a wajen, Gaɗɗo ganin Jummo tabar wajen ya sata kama hanun Sumaye suma suka gudu, gudun kar Yako ya tashi su shiga Uku. Yako kuwa idan banda huci babu abinda yake, ji yake cikin ransa wallahi bazai bar Jummo ba, ƙara zai kaita wajen Lamiɗo, bazai yadda da cin mutunci ba. Ja'e kuwa babu abinda yake sai yiwa Yako sannu domin dai yaji jiki. Tsakanin ta da Allah Jummo take gudu tana bin motar, ƙofar gidan kakansa garkuwa yayi parking, a hankali ya fito daga motar kina ganinsa kinga cikakken bafulatani kasancewar sa fari sol siriri kyakkyawa, sai dai mutum ne mai izza da iko gami da jin kai, tamkar aljana ya ganta tsaye a gabansa. " Allahumma ajirni fil musibati, Allah ya haɗa ni da mayya, wai meyasa kika addabeni kika damu rayuwata ne, dole ne sai kin shiga sabgata yau naga mayya ayi mutum shi bashi zuciya tamkar kare." Bakinta ta tura tana murguɗa bakin tace. " Ni dai sonka nake ka Aure ni." Zaro idonsa garkuwa yayi yana nuna kansa da yatsa yace. " Ni kike so na aureki, lallai ya tabbata ke mahaukaciya ce, Allah ya tsari gatari noma kauce ki bani waje mahaukaciya ƙazama" Ƙara turo bakinta tayi tace. " Ni dai ba mahaukaciya bace!!! Ehem sai dai idan kaine mahaukaciyan ko Mamma Amma dai bani ba, kuma wallahi Allah sai ka aureni. Zaro idonsa yayi ya furta. " Ni da Mamma mune mahaukatan?''' " Eh kune ba niba" Wani irin mahaukacin mari Garkuwa ya ɗauke ta dashi yana nuna ta da yatsa yace. " Na tsaneki tamkar na kasheki haka nake ji, na tsaneki na tsaneki, kinga daga yau idan na shigo wannan ƙauyen kika kuma tareni sai naci ubanki!!!" Yayi Maganar da ƙarfi yana hankaɗata da hanunsa ta faɗi ƙasa, shigewa cikin gidan kakan nasa yayi yana tsuka, ita kuwa Jummo kuka ta saki mai cin rai, tashi tayi da gudu ta nufi gidan su tana danna ihu tamkar wacce za'a kashe. Da sallama ya shiga cikin gidan, Kakarsa Mamma na zaune tana ƙoƙarin dafa dambu ya shigo, kanta ta ɗaga tana murmushi tace. " Ameen wa'alaiku mussalam, Garko kaine tafe da rana tsaka, lale maraba sannu da zuwa." Ranshi na ɓace ya amsa mata da yauwa sannu, yana jawo kujera ƴar tsugunno kallon sa Mamma tayi ransa a yana haɗe cike da tsokana tace. " To uban ƴan bakin rai, me kuma aka maka kake yamutsa fuska kamar kwanannen lawashi, ni tsiya ta da kai baƙin hali." Harara garkuwa ya daka wa Mamma yace. " Anyi baƙin halin, ba yamutsatsiyar lawashi ba Allah yasa yamutsatsiyar Albasa, nifa Mamma Daddy na shiga haƙƙina da yake turoni wannan ƙauyen, ayi ƙauye duk sheɗanu, Allah na kusa daina zuwa wannan ƙauyen idan baki shiga tsakanina da wannan shegiyar aljanar yarinyar ba, joma take jumma." Dariya Mamma tayi, tare da cewa. " To uban ƴan baƙar magana, ubanka ma sheɗanin ne kenan tunda shima nan aka haifesa, wai meye laifin Jummo ne kam da bazaka sota ba, kyakkyawar yarinya, ni dai banga laifin ta ba" Mamma tayi Maganar tana ɗauko sigari ta saka a bakinta, ashana ta ɗauka zata kunna, Garkuwa ya ƙwace ashanar yana haɗe rai cike da ɓacin rai yace.............. Wannan labarin yana ɗauke da abubuwan al'ajabi iri iri labari ne mai ɗauke da tsantsar tausayi, bariki ga kuma ban dariya, ku dai ku biyoni sannu a hankali domin jin inda zaren labarin zai kai mu. *Na faɗa muku wannan book ɗin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi 150 kacal masu TRANSFER to account number na 0006064512 Rashida Usman jaiz bank ga masu turo kati kuma MTN card zasu turo na 200 ta wannan numbern 08147537180 banda VTU* Vote Share and comments 08147537180 Alƙalamin Rasheedat Usman. UMMU NASMAH✍🏻 [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *😆😆😆😆😆 Sai TAMBAYATA akeyi menene ma'anar sunan BOOK ɗin nan wasu suce da wani yare ne wasu kuma suce sunan ya musu tsauri sun kasa faɗa akwai wacce tace min sunan kamar da indian ci😆😆 to bari na faɗa muku ma'anar book ɗin, da farko dai da harshen fullanci na bada sunan BOOK ɗin GELLE ƁINGEL da Hausa yana nufin (GARIN SU YARINYAR) ga dai shi na fassara muku, sai ku barni nasha iska* *WAƊANDA SUKA BIYA KUƊIN SU ZASU GA NAYI ADDING ƊINSU A PAYMENT GROUP BAZAN IYA BINKU ƊAYA BAYAN ƊAYA NA GAYA MUKU BA, ZAKU GANKU CIKIN PAYMENT GROUP* ➰➰ *5 to 6* 7:25pm A hankali take sauƙowa daga step ɗin cikin taƙama da iko, fuskarta sam babu annuri cike da gadara ta sauƙo daining table ta nufa tare da zama ta jawo ɗaya daga cikin plast ɗin dake jere a daining ɗin da alamu dener zasu yi, bata juma da zama ba, Aunty Zarah ta sauƙo itama ta zauna, can sai ga Sadiya ƙanwar Aunty Zarah, shi kuwa gogan, shine yayi ƙarshen zuwa, Momy plast ɗin ta buɗe, yamutsa fuska tayi tana kallon abincin dake cikin plast ɗin, Indomie ce tasha kayan haɗi, Momy cike da iko ta turawa Aunty Zarah plast ɗin tare da cewa. " Meye wannan kika dafa, Indomie kike nufin zamuci da daren nan, baki da hankali ne Zarah, kullum sai na gargaɗeki akan dafa mana taliya da daddare, amma kunnen ki baya ji, yanzu kina nufin daddyn ku shima wannan abun zaici idan ya dawo Saboda baki da hankali, mtsss!!! Ki tashi kije ki ɗaura tuwo da miya yanzun nan, tunda ke kince bakya jin magana" Momy ta ƙarisa Maganar tana tashi daga daining ɗin alamun bazata ci Indomie ba, Aunty Zarah kamar zatayi kuka ta kalli agogon hannunta, 7:30 pm, yaushe zatayi tuwo har tayi miya, cikin raurau da murya tace. " Momy tuwo kuma yanzu, bakwai da rabi fa, har yaushe zanyi tuwo nayi miya, dan Allah kiyi hkr Momy insha Allah zan kiyaye gaba bazan........" Hanu Momy ta ɗaga mata tare da cewa. " Bana son dogon turanci umarni na baki idan kuma baza kiyi ba fine." Tana gama faɗin haka ta haura sama numfashi Garkuwa ya sauƙe tare da bin Momy da kallo harta haura, kallon sa ya mayar kan Aunty Zarah tare da cewa. " Matar yaya, laifin kine, tunda kinsan bata son taliya ita a rayuwar ta, da sai ki kiyaye, idan ke kina son taliyar sai kiyi sannan ita kuma ki mata abinda take so, kiyi hkr kije ki ɗaura tuwon, Sadiya kije ki tayata kuyi bibbiyu." Aunty Zarah tamkar zatayi kuka ta miƙe ita dai tana mungun takura a cikin gidan nan, uwar mijinta ta sata a gaba bata da kataɓus sai faɗa da iko, duk aikin gidan an jirge mata shi a kanta ita kaɗai ta hana a kawo mai aiki, bata da ikon ta dafa abinda take so a gidan mijinta sai abinda Momy ke so wannan wacce irin rayuwa ce, kitchen ɗin ta nufa ba tare da ta cewa Garkuwa komai ba, Sadiya tashi tayi zata bita Garkuwa ya saka hanunsa ya kamo hanun Sadiya tsayawa tayi ta zuba masa idanu cike da ƙauna tamkar zata haɗiye sa, murmushin yaudara ya sakar mata a hankali tamkar mai raɗa yace mata. " 12:00pm ina jiranki kisan duk yanda zakiyi ki zo ki sameni zan barmiki ƙofa a buɗe, kinsan dai 2days nayi missing ɗinki." Cike da shagwaɓa Sadiya tace. " Babu wani missing ɗina da kayi da kayi missing ɗina, da kazo inda nake, amma tunda nabar gidan nan baka nemi inda nake ba, ko a waya ne idan ba na maka plashing ba bazaka kirani ba, a hakanne zakace kayi missing ɗina." Murmushi ya saki yana murza tafin hannunta, tare da cewa. " Oh my sweet girl, kin dai san ina sonki koh, rashin isasshen time yasa ban cika kiranki ba, amma kullum kina maƙale a ƙirjina, yanzu dai kije ki taya Aunty Zarah aikin sai na ganki." Ya ƙarisa Maganar yana sake mata hannunta tare da kanne mata ido, murmushi Sadiya tayi tare da cewa. " Okay baka da damuwa sweetie na insha zaka ganni." Tayi Maganar tana shigewa cikin kitchen murmushi Garkuwa yayi tare da buɗe plast ɗin ya ɗebi Indomie ɗin a plet tare da tsiyayan fresh milk, a hankali yake cikin abincin cike da nutsuwa, harya gama, bedroom ɗin Momy ya shiga tana zaune bakin bed dinta tana duba littafin Azzakar ya zauna a gefenta. " Garko ya kabar su Mamman.?" " Duk lafiya na barsu, Momy wai meyasa Mamma bazata iya rabuwa da shan sigari bane, wallahi Momy bana jin daɗin ɗabiar Mamma ko kaɗan." Numfashi Momy taja tare da ajiye littafin a gefe ta maida hankalinta ga garkuwa a hankali ta fara cewa. " Garko Mamma mawiyacin abune ta daina shan sigari, da zata daina da tuni ta daina tun sanda Malam kakan ku yake raye malamin islamiyya ne,. Babba duk wani nasiha da wa'azi daya kamata a yiwa Mamma domin ta rabu da sigari yayi amma taƙi ɗauka harya mutu cikin wa'azi yake mata, bayan mutuwarsa mahaifinku ya ɗaura daga inda Malam ya tsaya amma Mamma taƙi ji, akwai aminiyarta INNO itace take ƙara kangarar da ita, domin kuwa INNO gagararriyar tsohuwa ce mai taurin kan masifa, duk wani wa'azi da zaka yiwa Mamma sai INNO ta koresa, domin kuwa dalilin INNO Mamma taƙi dawowa cikin gari, muddun ba INNO bace ta daina shan sigari ba, Mamma bazata daina shan sigari ba." " Hmmm!!! Lallai kuwa naga alama domin kuwa ko yau dana bata kuɗi cewa tayi sai ta tsakurawa INNO wani abu a ciki tasha sigari, yama kamata fa mu tambayoyi malamai game da bawa Mamma kuɗi kinga dai sigari take sha dashi, kar muje ta dinga ɗiban zunubi da kuɗin mu tana yaɓa mana, amma dai wannan INNOn Allah ya kasheta mu huta." Murmushi Momy tayi tare da cewa. " A'a karka kuma kira mata mutuwa ka mata fatan Allah ya shiryesu duka, ya kamata kaje kayi wannan tambayar domin kuwa nima yana cimin tuwo a ƙwarya." " Shikenan Momy insha Allah zanje, kunyi waya da Khalil kuwa." " Eh ya kiran da safe yace ya nemi layinka baya tafiya." " Network ɗin Tulde gaskiya ba kyau ba lallai bane ya sameni, amma zan kirasa anjuma." Da to Momy ta amsa kafin Garkuwa ya tashi ya fice daga bedroom ɗin yayi nasa. Aunty Zarah cikin awa biyu ta gama girkin 9:00pm dai-dai, dake Sadiya ta tayata da miya, a daining ɗin suka jera sannan Zarah taje ta sanar da Momy ta gama da to Momy ta amsa sannan Aunty Zarah ta shige nata bedroom ɗin tsabar takaici da haushi da take ji yasa bazata iya cin abincin ba, haka ta kwanta da yunwa. Da misalin tara da rabi dai-dai Daddy ya shigo cikin gidan a gajiye sannu da zuwa Momy ta masa sannan ta kai masa ruwan wanka sai da yayi wanka sannan ya sauƙo falo, a tsakiyar falo aka shimfida masa darduma kasancewar baya cin abinci a daining, abinci Momy ta ɗauka ta kawo darduman ta ajiye, malmalar tuwo biyu ta saka masa da miyar ɗanyar kuɓewa, kasancewar Daddy mutum mai son tuwo ko dan ya tashi a ƙauye ne, cike da nutsuwa Daddy yake cin abincin Momy na gefen sa harya gama ruwa yasha sannan ya wanke hanunsa, idanunsa ya dago ya kalli Momy tare da cewa. " Zainab Garko ya dawo kuwa." " Eh ya dawo tun ɗazu yana bedroom ɗinsa." " Jeki kira min shi.?" Da to Momy ta amsa tare da tashi ta haura tare suka dawo da Garkuwa kusa da Daddy ya zauna tare da cewa. " Sannu da dawowa Daddy" "Yauwa sannu Garko ya ka samu Mamman tana lafiya dai ko.?" " Tana lafiya Daddy sai dai hali ne har yanzu bata fasa ba, ya kamata ka dawo da Mamma gidan nan idan akayi dace sai ta daina shan wannan sigarin." Girgiza kansa Daddy yayi tare da cewa. " Mamma bazata yadda ta dawo ba, ni na sani ka rabu da ita kawai mu cigaba ba da mata addu'a idan da rabon zata gyara ko a ina take zata gyara, gobe da safe ka tuna min zan aikeka kasuwa bakin Cross zakaje min shagon Alhaji yawale akwai saƙon da zaka amso min." " To shikenan Daddy Allah ya kaimu." Da ameen Daddy ya amsa yana miƙewa tsaye yace. " Bari naje na kwanta na gaji sosai." Kansa Garkuwa ya ɗaga sannan Daddy da Momy suka haura. Ko da misalin 12 na dare Sadiya bata tsallake umarnin Garkuwa ba, sanda ta tabbatar ƙafa ta ɗauke babu kowa ta faɗa bedroom ɗinsa, itace bata fito ba sai wajen 2 na dare, bedroom ɗin da take sauƙa idan tazo ta faɗa, tare da shigewa tolet, wankan tsarki tayi, sannan ta dawo bed dinta ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka mai cin rai, a hankali cikin shashsheƙar kukan take cewa. " Meyasa na kasance mai saɓon Allah meyasa bana iya kaucewa umarninsa, na kasan cikin mutanen da Ubangiji yake fushi dasu, ina ji ina gani na maida kaina karuwa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Meyasa na kamu da matsananciyar soyayyar Garkuwa, duk halin dana shiga sonka shine ya jamin, meyasa meyasa dole sai kayi zina dani, innalillahi!!!" Ta ƙarisa Maganar tana kuma sakin kuka, sosai take kukan idanunta suka bushe, har sai da aka yi sallar asuba sannan ta samu bacci ya dauketa, ko da gari ya waye da jikinta a sanyaye ta fito falon, Daddy ta fara gaishewa cike da sakin fuska ya amsa yana ce mata. " Halima kinzo mana hutu kenan, ya gidan naku, kika baro su.?" " Duk suna lafiya Daddy, suna gaishe ku" Momy ce tace. " Sadiya meya sameki idanunki suka kumbura, kuka kikayi ne." Ras zuciyarta ya buga, ɗan murmushi tayi tace. " Ciwo idanun suka kwana suna min shiyasa suka kumbura" Ta ƙarisa Maganar tana kallon gefe da gefe ko Garkuwa yana wajen wayam babu shi a wajen, numfashi ta sauƙe tare da zama aka cigaba da breakfast da ita, itama Aunty Zarah yau bata zauna anyi da ita ba da alamu fushin jiya ne bata huce ba. Bayan sun gama breakfast ɗin ne Sadiya ta haura bedroom ɗin Aunty Zarah tana zaune tayi shiru kusa da ita Sadiya ta zauna tare da cewa. " Good morning Aunty" '' morning Sadiya, Sadiya, jiya ƙarfe biyu na dare nagan ki bakin bedroom dinki zaki shiga, ina kika fita kikaje" Zuciyar Sadiya ne ya tsinke cike da tsoro muryar ta na rawa tace. " Ina kuma naje Aunty, daga ina kika ga na fito."? Tsurawa Sadiya ido Aunty Zarah tayi tare da cewa. " Banga inda kika fito ba, amma dai na ganki sanda kike ƙoƙarin shiga bedroom dinki, ina kikaje." Numfashi Sadiya ta sauƙe cikin zuciyarta tana godewa Allah da Aunty Zarah bata ga fitowar ta da bedroom ɗin Garkuwa ba, cike da waskewa tace. " Kitchen naje na dan ɗibi abinci naci yunwa ce ta tashe ni." " Okay,am dan Allah Sadiya kije ki gyara min falo da bedroom ɗin Momy kafin tazo ta fara min mita." Dariya Sadiya tayi tana miƙewa tace. " Kai Aunty Momyn ce mai mitar." " Eh mana!! Ayi mata kullum cikin takura mutum ita jikinta bazai taɓu ba, sai jikin wani, Allah dai ya dawo da khalil lafiya, dole ne fitar dani daga wannan gidan na gaji wallahi." Dariya kawai Sadiya tayi tare da ficewa taje ta hau aikin da Aunty Zarah ta sakata. *TULDEN FULANI* "INNO da Mamma zaune a cikin gidan Mamma gefen su Jummo ce, dukkan su hanunsu riƙe da sigari sai busawa suke, tagumi Jummo tayi tana kallon su, yanda suke busa sigari suna tauna goro, kamar ba Fulani ba, Jummo kasa shuru tayi tace musu. " Ikon Allah, duk wanda Allah ya shiryar shine shiryayye, umhm!!! Wasu dai wallahi su jira mutuwar su, muddun suka yadda suka mutu a haka babu abinda zai hana Allah babbaka mutum, ku zauna kuna haƙar sigari kuna tauna goro tamkar ƴan bariki, ya Allah kasa INNO da Mamma su................." Saurin yunƙura Mamma tayi tana bige bakin Jummo tace. " Kiinci kutumar ubanki, kaji min shegiyar yarinya dan ubanki sai kizo ki fara kona mu, Kafin Allah ya kona mu, shegiya mai bakin tsiya baki iya gani kiyi shuru, a hakan zan baki jikan nawa ki aura shegiya mai kai kamar ƙoƙiya." INNO ce tayi carap ta karɓa. " Barni da ita shegiya mai shegen baki, ke dai Jummo kin shiga Uku da bakinki bazai gani yayi shuru ba, to shan sigari yanzu muka ɗaura ɗamara sai muga shegen da ya isa ya hanamu a CIKIN garin nan, ko a ɗakin uwarki muke Shane, kaji min jaraba da nacin tsiya kekam Jummo da mayya ce wallahi sai kin cinye mutum ko kashin shi bazaki bari ba." Turo baki gaba Jummo tayi cike da jin haushi tayi tsalle ta dire tace. " Sai kuta zagina kuta zagina saboda kawai na faɗa muku gaskiya, kuma wallahi ko zaku kasheni bazan fasa faɗa ba, idan yaso ku tsire Ni, kuji Mamman nan dai har wani cewa kike (a haka zan baki jikan nawa ki shegiya mai kai kamar ƙoƙiya) tayi Maganar tana kwaikwayon Mamman ta ɗaura da cewa, da wani magulallen bakin ki, a wajen da ba hakwaran kirki, yo nida ke ɗin waye mai kai kamar koƙiyar, ai gara kaina ma da naki, ke naki kuma ai sai dai ace kamar ƙwallon goruba, ko kina so bakya so, ko zaki mutu karshen baƙin ciki sai na auri yaya garkuwa, ke kuma INNO na juyo kanki, mai ƙunnen ƙashi, idan aka barni dake ɗin me kika iya dani, dan Allah idan kuna so randa kuka mutu ma, a kunna muku sigarin a asa muku a bakinku ku je kabarin ku dashi ni ina ruwana waye Allah zai babbaka walakiri ya jibgi banza, ni ina nan duniya ina gaɗa da nanaye mun rage iri.........................." *Karku manta da wannan littafin na kuɗi ne ku HANZARTA ku biya domin kuwa kuɗin babu tsada* *Ga masu TRANSFER to account number na zasu turo 150 kacal ta wannan account ɗin 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank* *Ga masu turo katin waya kuma zasu turo mtn card na 200 saboda idan an sai dashi yana rage farashi ta wannan numbern 08147537180* *Da zaran kin tura sai ki yi screen short ki turo shaidar biya ta wannan numbern 08147537180* Vote Like Share and comments *Alƙalamin Rasheedat Usman* *Ummu Nasmah✍🏻* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata ƙawar sirri ƙawar amana *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. https://chat.whatsapp.com/E72lrz6syKr4CNvD9usiuA *Ga waɗanda suka min magana kan cewa wancan group ɗin ya cika sunyi joining yaƙi to ga wani amma fa ki sani iya Free page kawai zaki samu a ciki idan kina da ra'ayi biya kudinki kawai ki wuce wajen* *Dan Allah kar namiji ya shiga mata ne zallah, dan Allah karku shiga wannan gidan* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* Free page. ➰➰ *3 to 4* " Haba Mamma wai yaushe zaki gane Annabi ya faku ne wannan ba mutuncin ki bane wallahi shan sigari, da mutuncin ki, wallahi wannan da'a cikin gari ne da sai kin jawo mana abun gori, ya kamata kinsan kin girma, kusan 86 kike da shekaru yanzu amma ace har yanzu baki daina saɓon Allah ba, haba ya kamata ki daina shan wannan sigarin haka ki duba kiga yanda bakinki yayi baƙi tafin hannunki taɓin ƙafarki kaf ya rine ya koma baƙi saboda shan sigari shiyasa Khalil baya zuwa wajenki saboda ya tsani yazo ya ganki a wannan halin, wallahi idan kika mutu a haka wuta zaki shiga gara tun w......." Dakatar da Garkuwa Mamma tayi itama tana sauya fuska tace. " Dalla rufe min baki dan ubanka, shan sigari ne saɓon Allah, to ai mutuncin nawa ya juma da zubewa idan shan sigari shine rashin mutunci tunda tun kafin na haifi ubanka nake sha banga kuma shegen da zai hanani shanta ba, idan na shiga wutar ina ruwanka kabarin mu ɗaya ne da kai da zaka damu, dan ubansa shi kalilun Allah yasa kar yazo har abada ina ruwana dashi, ni mantawa ma nake dashi jikana ne a duniya, dan haka ka kiyaye i ko ubanka Buba bai isa ya hanani shan sigari ba, ni da sigari mutu ka raba takalmin kaza, dalla!!! Bani ashanata ai ba ubanka bane ya sai min ita, gacar wanda zakaje ka yiwa faɗa wacce bata da mutunci bata ƙaunar dangin mijinta bata ƙaunar wani ya raɓesa yaji sanyi Uwar ka, Zainabu nake faɗa ita zaka je ka yiwa wannan wa'azin ba niba da na gama da iyayen mijina lafiya." Ta ƙarisa Maganar tana wafce ashanar ta daga hanunsa ta kunna sigarin tana zuƙa, tare da wulla masa harara, sosai garkuwa yaji zafin maganganun Mamma akan mahaifiyarsa ya rasa menene tsakanin ta da Momy, basa shiri, haɗiye ɓacin ransa yayi tare da miƙewa tsaye yana kwalawa A'illo kira, A'illo dake cikin bukkar Mamma taji kiran Yaya Garkuwa ai kuwa da gudu ta fito tana. " Oyoyo Bandirawo!! Yaushe kazo ɗazu nake cewa, Ya Jalo yaushe zaka zo yace min bai sani ba sannu da zuwa." Murmushi Garkuwa yayi tare da cewa. " Yanzu shigowata Ai ina Jalon yake zai shigowa da Mamma kaya a cikin mota ni zan koma ne yanzu." Ɗan murmushi tayi, harga Allah bataji daɗin tafiyar da Garkuwa zaiyi ba da wuri haka, kallon sa yana kwantar mata da hankali, duk da tasan ya garkuwa yafi ƙarfin ta, amma zuciyarta na mungun ƙaunarsa, cewa tayi. " Ya Jalo yanzu ya fice kasuwa, amma dai banji daɗin tafiyar da zakayi ba, yanzu fa kazo meyasa bazaka kwana ba." Mamma ce tayi carap tace. " Saboda naci ubansa na faɗa masa gaskiya, shi kuma ga ɗan masu ido da kwalli wanda ba'a masa faɗa idan kaga dama ka dawo tsuntsu sai ka bar garin da wuri, kai ga isasshe malakakke baza'a faɗi lefin uwarka ba, to ka buɗe waɗannan fala falan kunnuwan naka masu kama da ƙosai kaji, Uwarka bata kirki bata da mutunci ubanka kuma ya zama hotiho, idan kaje ka faɗawa gagararriyar Uwar taka cewa nice na faɗa har kana wani haɗa min rai dama ya fuskar taka take kullum a haɗe tamkar hadari, kaga fice min daga gida ka koma inda ka fito." Dariya ce ta ƙwacewa Garkuwa har haƙwaransa suka bayyana dimple ɗinsa ya loɓa yace. " Dan Allah dubeki ko kunya bakya ji, kinsa surikar ki a gaba tamkar zaki kasheta itako bata ma san kinayi ba, waima ke da kinyi zaton wannan ɓaɓatun da kike shi zaisa na tafi, to bashi bane dama can banzo da niyar kwana ba, a yau zan juya, kuma wallahi bazan fasa faɗa miki shan sigari haramun bane kuma zai kaiki ga wuta idan baki daina ba aljanna sai dai kiga muna shiga, kin wani tsareni da mitsimitsin idanunki tamkar ƙwarƙwata wai ke ga masifaffiyar tsohuwa, ki gyara ko ki shiga Uku." Ya ƙarisa Maganar yana zaro dubu talatin a cikin aljihunsa ya ajiye mata yana cewa. " Da alamu talauci ke saki faɗa yau ga wannan na taimaka miki badan halinki ba, kuma idan kika sha sigari da kuɗina ban yafe ba." A'illo dariya tasa ganin dramar Mamma da Ya Garkuwa dama sun saba da wannan faɗan duk sanda yazo sai sun rikito suke dawowa dai-dai Mamma haɗe girar sama data ƙasa tayi tana ƙarewa kuɗin kallon wulaƙanci tace. " Ka faɗawa ubanka Buba, domin kuwa har idanuna sunso sufi na ubanka girma , ubanka Buba shine mai ido kamar ƙwarƙwata kuma dan uwarka zainabu, da wannan kuɗin naka zan sayi sigari harsu ƙare, kai har aminiyata INNO sai na tsakura mata wannan kuɗin itama ta zuƙi koda kwali goma ne da kuɗin idan ma zunubin ne kaima sai ka samu naka tunda ka bamu gudumowa." " Hmmm!!! Wannan tsohuwa INNO wannan INNOn ina mungun jin haushin ta, duk harda ita a cikin wanda suke daɗa kaiki ga hallaka, Allah dai ya shirya ku, amma dai mun haɗu da jarabawa tunda Allah ya haɗamu daku." Fesar da hayaƙin sigarin Mamma tayi tace. " Oho dai munfi ƙarfin ku, waima ya maganar Auren naka da Jummo, dan dai wallahi sai ka Aure ta." Tsuka garkuwa yaja yare da haɗe rai yace. " Har kina wallahi Saboda kece ubana, to idan kin isa kimin Auren dole, amma Allah ya isa tsakanina dake Mamma wannan jakar yarinyar kike dangantani da ita dan kawai ina wajenki mtsss." yayi tsuka yana kallon A'illo yace. "A'i muje ki shigo da wasu kayan idan naga yara a waje sai su tayaki ko." Yayi Maganar yana ficewa ba tare da ya yiwa Mamma sallama ba, ya tsani koda sunan yarinyar a kira masa, ba ƙaunar ta ko kaɗan, A'illo bayan sa tabi tana murmushi, Mamma kuwa mita ta hau tana cewa. " Kaji ɗan ƙwal Uba to dan ubanka idan ban haifeka ba, ai na haifi ubanka koma wallahi tunda kace sai na nuna maka na isa, baka da wata mata sai Jummo kaji min yaro dai mai baƙin halin tsiya, kai kullum cikin hali mtsss!!!" Ta ƙarisa mitar tana fesar da hayaƙin sigarin, shi kuwa Garkuwa fitarsa ya samu yara a waje ya basa 5k suka shigo wa da Mamma kayan abinci, dubu goma ya bawa A'illo sannan yaja motar sa ya tafi ba tare daya haɗu da Jummo ba. " Wayyo Allah na shiga Uku!!!! Wayyo na shiga Uku na lalace, wayyo Allah na!!!" Jummo ce ta shigo gidan su da wannan ihun ta zauna a ƙasa sai rafkar kukan take, Sikayel da gudu ta fito tare da ƴar Jummo Boɗɗo a tsorace, INNO kuwa tana can banɗaki tana gudawa tunda Jummo ta mata zance mutuwa da rayuwar kabari take sintirin jawo, da sauri INNO ta fito daga bayin ko butar bata ɗauka ba, tana cewa. " Wani shege tsinannan ne ya saki kuka, wani shegen ne?" Tayi Maganar tana karisowa wajen Sikayel jikinta na ɓari take cewa. " Menene ya sameki Jummo, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Kiyi magana mana Jummo keda waye."? Ƙin yin magana tayi sai da taga INNO ta iso wajen ta fara cewa. " Bazai aureni ba INNO yace baya sona, jikan Mamma na binni, wallahi shi nake so ɗan gaye ne, kuma kyakkyawa, ni dai na shiga Uku mutuwa zanyi INNO zan mutu idan bazai aureni ba." Wani ƙuwƙuw cikin INNO ya yi jin Jummo na kiran zata mutu, cikin rawar jiki tace. " Ke dalla ki daina kirawo wannan mutuwar bazaki mutu ba, ehe, badai Garko bane to kwantar da hankalin ki, kamar kin aure shi, ai dai jikin Aminiya Mamma ne, karki damu zamu kitsa mu haɗa, karkaɗe jikin ki ki tashi kije ki sayo min sigari." Wage yalon hakwaranta Jummo tayi tace. " Da gaske zai Aure ni INNO ni dai wallahi shi nake so." " Kwarai kuwa zai aureki." Dariya Jummo tasa cike da murna ta miƙe tsaye tana cewa. " Bani kuɗin sigarin na sayo miki, Allah ya barni dake INNO ta, ki daɗe kiyi ƙargo kiyi shekaru irin na dabino." Sikayel cike da takaici da haushi tace. " Amma Jummo baki da mutunci baki da kirki wallahi, yanzu tsabar ɗaukar alhaki akan wannan shirmen zaki shigo da ihu tamkar an kasheki ki tsinka mana zuciya, kekam wacce irin mutum ne Jummo wawiya marar lissafi." INNO ce ta hau kan Sikayel da faɗa tana cewa. " Kul kul ɗinki!!! Kiyayeni wallahi, karki kuskura ki ɓata mata rai ina ruwanki wani gulman ne yace ki fito, tayi ihun ai dai akan rayuwarta take ihun yau naji tsiya a daki mutum ace za'a hanasa kuka to baki isa ba wallahi baki isa kisa min jika a gaba ba." Shuru Sikayel tayi idanunta suka ciko da hawaye tana mungun jin zafin Rayuwar da INNO take ɗaura Jummo akai, domin kuwa ita macece gidan wani zata idan har ta tafi a haka tabbas akwai matsala, juyawa tayi cike da ɗacin rai suka koma bukkar su, Jummo kuwa cuno baki tayi, INNO kuɗi ta ciro naira hamsin ta danƙawa Jummo tace. " Rabu dasu jeki sayo min sigari ƴar kwali yanzu ki dawo muje gidan Mamman." Ai kuwa da gudu Jummo ta fita sayowa INNO sigari. *GOMBE LOCAL GOVT* *NEW G R A* wani makeken get Garkuwa ke dannawa Hom hom!!! Gaban gidan kansa abin kallo ne bare kuma idan an shiga ciki mai gadi ne ya wangale get ɗin danna hancin motar Garkuwa yayi cikin gidan wohoho kuzo kuga kyawu cikin gidan, kana kallon gidan zaka tabbatar da gidan attajirin mai kuɗi ne, parking space yayi parking a hankali ya fito daga cikin motar, ya nufi part ɗin mahaifiyar tasa, babban falo ne mai cike da kayan alatu wanda aka ƙawata sa da adon Black and White, sosai falon yayi kyau babu kowa cikin folon shuru, kansa ya ɗaga ya zubawa babban elagement ɗin dake manna a falon kallo, wani dattijo ne fari kyakkyawa gefen sa wata dattijiwar mace ce caculate color ita ba fara ba ita ba baƙa ba, sai a hanun damanta hoton wani kyakkyawan saurayi da kakin soja a jikinsa fari sol gefen Wannan dattijon kuma garkuwa ne, sai wata ƙaramar yarinya Black beauty a tsakiyarsu, a ƙasan hoton anyi rubutu da manyan harufa *ALHAJI ABUBAKAR BUBA TULDE FAMILY* murmushi Garkuwa yayi yana ƙarewa ahalin nasa, muryar Zarah yaji tana cewa. " Bandirawo!! Yaushe ka tafi harka dawo"? Murmushi Garkuwa yayi tare da komawa ɗaya daga cikin kujerun falon ya zauna yana cewa. " Daman ai a yau zan dawo matar Babban yaya, ina Momy naji gidan shuru."? " Momy tana bedroom ɗin ta da alamu ma wanka ta shiga, mutumiyar ka tazo Sadiya tun ɗazu take tambayar ka." Murmushi Garkuwa ya saki cikin zuciyarsa ya furta, (Yau akwai holewa kenan, hmmm ita a nata tunanin zan aureta ne, daga ranar dana gama da jikinta daga ranar zan shafe babin rayuwarki.) A zahiri kuma sai ya haɗe fuska gudun kar Aunty Zarah ta fahimci akwai wani abu a tsakanin su, domin kuwa a hankali yake takunsa yamutsa fuskarsa yayi tare da cewa. " Ayya ta tafi kenan." " No bata tafi ba, kasan sunyi hutu, anan zatayi nata hutun, nina roki mama tabar min ita muyi hutu a nan." Da okey garkuwa ya amsa ya tashi ya haura bedroom ɗinsa, ita kuwa Aunty Zarah ko a zuciyarta bata kawo Garkuwa yana lalata da ƙanwarta ba, ɗauka kawai take shakuwace na zaman tare a tsakanin su................. Wannan kenan muje zuwa mahaukaci ya hau kura yanzu aka fara labarin. *Karku manta da wannan littafin na kuɗi ne* *Wanda zaiyi TRANSFER to account number na 150 zai bada 0006064512 Rashida Usman jaiz bank.* *Ga masu turo katin waya kuma zasu turo da 200 ta wannan numbern 08147537180* *Sannan ku turo da shaidar biya ta wannan numbern 08147537180* *Ga ƴan Niger kuma naji ƙorafin ku, karku damu kuma baza'a barku a baya ba, kumin magana ta wannan numbern 08147537180 zan faɗa muku yanda zaku biya kuɗin ku* *Masoya naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin hanu biyu, dayawa daga cikin ku sun fara biyan kuɗin su, naji daɗi sosai Allah yabar ƙauna* Vote Share and comments. *Alƙalamin Rasheedat Usman* *Ummu Nasmah✍🏻* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *Free page* ➰➰ *7 to 8* Sake baki da hanci su INNO sukayi suna duban Jummo, takalmi Mamma ta ɗauka ta jefa mata tare da cewa. " Eh lallai wuyanki ya isa yanka Jummo kin isa, to tashi ki bar bukkar nan kafin ki dake mu, tunda kin balaga ƙirjinki ya cika, kin fara zubda jini, dole ai ki zagemu." "Zagi kuma Mamma, ni wallahi ban zageku ba, Amma kuyi haƙuri idan ranku ya ɓaci, haba dai Mamma ta, haba INNO ta, kune fa gata na, taya zan zageku, bakin nawa ne babu sakata duk sanda gaskiya tazo sai na faɗa, amma dai na tuba bazan sake ba, kinga Mamma ki rufa min asiri ki taimakeni ki taimaki rayuwata, ki zamo jagorata na auri Oda ta, ya Garkuwa na, idan na auri ya Garkuwa, Mamma katan katan zan dinga saya miki sigari, kuma babu shege ɗan iskan da zai raina min ke, kamar ƙwai haka zan dinga lallaɓa ki, ke kuma INNO duk shekara saina kaiki Makka, har Mamma ma sai ta koma duk da ta taɓa zuwa, dariya Jummo tasa tana kallon INNO tace, Cap wayaga INNO a Makka." Ai kuwa take Mamma ta sauƙa tana wage baki tana dariya tace. " Allahu Akbar ƴar albarka, kinji yarinyar kirki INNO, Oh kinji fa ƴar kirki, Makka zata dinga kaimu duk shekara, kuma fa wallahi akwai kuɗin da za'a kaimu Makka duk shekara a gidan Buba kuma kuɗin bazasu girgiza ba bare su san an ɗebe su, wannan tsinanniyar matar tasa zainabu ke hanasa min alkairi" sai kuma ta fashe da kuka tana mutstsuka idanunta ta cigaba da cewa " Sai gashi ƴar albarkatun jikata tana son ta auri jikina Garkuwa saboda kawai ta share min hawaye na, ko dan wannan niyyar taki ta alkairi, Jummo sai na tabbatar kin auri Garko kafin na mutu, ai dai da arziki a garin wasu gara a garin ku, a garin kuma a ɗakin ku, nayi miki alƙawari Jummo ko bayan raina sai Garko ya aureki ƴar albarka." INNO ma fashewa tayi da kuka tana cewa Mamma. " Ke dai bari Mamma nine da kuka ba ke ba, Allah sarki ƴar albarka, kaf cikin haulata babu wanda ya taɓa maganar zai kaini Makka sai Jummo ƴar albarka, Allah sarki yarinyar kirki, Allah dai ya nuna min wannan Auren, shiyasa nake sonki kaf cikin haulata, idan kin ɓatawa Mutum rai kinsan yanda zaki faranta masa Allah karka kasheni da wuri." Dariya ce ta ƙwacewa Jummo ganin daga ambaton zata kaisu Makka har sun manta tsiyar da ta shuka musu ita kuwa INNO Uwar rashin so mutuwa, harda roƙon karta mutu da wuri, cikin ranta take cewa (Ko Gombe bazaku bari ba, bare Makka, ina ma zaku ƙara ganina ina Aure ya Garkuwa na, yasin ban sanku ba, ni wannan rugar ma ba sake zuwanta zanyi ba) a fili kuma dariya tayi tana kuma tsarasu tace. " To kuma idan ban kaiku Makka ba, waye zan kai, kune fa gatana Mamma nifa da zaki dage ayi wannan Auren nan da sati ɗaya, da nai miki alƙawarin sai na kori Wannan zainabun da ta dameki daga gidan duka har abada bazata dawo ba, kuma dai kinsan zan iya" Zaro idanunta INNO tayi ta cewa Jummo. " Ke Jummo kanki ɗaya kuwa, surikar taki kike cewa zaki kora, eh lallai baki da hankali." Mamma ce tace. " Wannan ma shine hankali yarinya za tayi abun arziki kike ƙoƙarin dakatar da, ita, Jummo daga yau na ɗaura ɗamarar aura miki Garkuwa muddun zaki yayanki yaƙin tumɓuke Zainabu." Tsalle Jummo tasa tare da furta. " Za kuwa aga tsiya yasin na rantse da Allah muddun kika aura min ya garkuwa sai na fidda miki da Zainabun." Ta ƙarisa Maganar tana ficewa da gudu cike da farin ciki, INNO ce ta kalli Mamma tace. " Kinsan me kike cewa kuwa, kina nunawa yarinya hanyar tsiya ta kori matar da ta, shekara talatin a gidan mijinta, to wai ma ina ruwanki da matar nan ne, tana gidan ta, kina gidan ku, garin ku ma ba ɗaya ba, amma kinbi kin ɗaga hankalinki a kanta." Murmushi Mamma tayi tana kallon INNO tace. " Haba kema kinsan abinda Zainabu ta tare min, kuma kin san alƙawari na ɗauka kafin na mutu sai murƙushe Auren Zainabu da ɗana Buba, kuma na samu wannan damar yanzu da nayi shekara talatin ban samu ba, zanyi amfani da soyayyar da Jummo take yiwa Garko na kawo ƙarshen Zainabu kuma nasan Jummo zata iya, kin sani INNO mugayen laifukan da Zainabu da danginta suka min, dole na ɗauki fansa ta hanyar raba Zainabu da farin cikin ta, kin san a rayuwar mace babu abinda za'a mata taji haushi ta shiga cikin damuwa da tashin hankali, irin a raba ta da gidan Auren ta, da yaranta wannan yafi komai ciwo, INNO harta yaranta sai nasa sun tsaneta, ki saka ido kiyi kallo kawai." Numfashi INNO ta sauƙe tare da cewa. " Mamma meyasa ke baki da yafiya ne, meyasa bazaki manta abinda ya faru shekara talatin baya ba, nasan ba a kyauta miki ba, kuma an tozarta ki, an nuna miki iko da fin ƙarfi amma dan Allah Mamma ki manta kiyi hkr tunda har anyi shekaru ya wuce haka." " Hmmm!!! Sai dai idan kene zaki nuna min iko akan jikarki, ki hanata tayani ɗaukar fansa, amma idan ba haka ba, baki da ikon hanani ɗaukar fansa." " Ko ɗaya bazan nuna miki iko akan Jummo ba, yanda take jika a wajena haka take a wajen ki." " To ki samin ido kawai." Numfashi INNO ta sauƙe tare da ɗauko wani zancen daban suka ɗaura a kai. Almajirai ne cike ƙofar gidan, kowane riƙe da Allo suna ta karatu, Baffa dake zaune a gefe ne ya miƙe ya shiga cikin gidan, Sikayel na zaune tana tankaɗen garin dawa, Baffa ya shigo, zama yayi gefen Sikayel tare da cewa. " Ina Jummo!!! Yau satin ta ɗaya bata zo ta biye karantun ta ba, ido na zuba mata amma naga alamar bata jin zuru yau idan na riƙe Jummo sai ranta ya ɓaci na fara gajiya da munanan halinta......." Baffa bai rufe bakinsa ba, almajiransa ya shigo da sallama sunkuyawa yayi tare da cewa. " Malam Yanzu Lamiɗo yayi aika, wai kaxo fada yanzu yana neman ka." Cike da mamaki Baffa yace. " Lamiɗo Kuma to Allah yasa lafiya, Sikayel bari naje kiran lamiɗo." Da a dawo lafiya Sikayel ta amsa Baffa ya fice darect fadar lamiɗo ya nufa. A gefe ya zauna yana gaishe da lamiɗo cike da girmamawa gefen sa ya kalla Yako da innar sa ne zaune sai dogari, lamiɗo gyaran murya yaya tare da cewa Baffa. " Malam Yaya kaji na aika ayi kiranka ko.?" Ɗaga kansa Baffa yayi alamun eh, lamiɗo ɗaurawa yayi da cewa. " To ganan Yako shine ya kawo min ƙarar jikarka Jummo" yanda Yako ya faɗawa lamiɗo haka ya mayarwa Baffa yanda akayi, shuru Baffa yayi babu musu duk abinda akace Jummo tayi zata aikata duban yako Baffa yayi tare da cewa. " Dan Allah Yako kuyi haƙuri na sani Jummo zata aikata fiye da abinda ka faɗa ina mai baka hkr insha Allah kuma zan mata faɗa bazata kuma ba, Inna kiyi hkr kiyi hkr." Darajar Baffa yasa innar Yako jin jikinta yayi sanyi, cike da girmama Baffa innar Yako tasa Yako ya yafe maganar lamiɗo sosai ya yiwa Baffa ƙorafi akan Jummo, shi dai Baffa hkr kawai yake bayarwa cike da ɓacin rai Baffa ya koma gida, cikin dace kuwa ya samu jummo ta dawo ai kuwa cike da faɗa Baffa ya ke yiwa Jummo magana. " Wato Jummo baki da hankali ko, ke kam sai yaushe zaki nutsu ki zamo cikakkiyar Mutum kullum kina nan tamkar marar hankali, wallahi ki nutsu ki fahimci rayuwa, idan bakiyi hankali da duniya ba, wallahi wata rana sai kinyi kuka da idanunki domin muddun akace baka da nutsuwa da tunani wata rana sai kinyi danasanin halayyar ki, yanzu ki faɗa min kwanan ki nawa rabonki da kizo ki biya karatun ki, yau sati guda, saboda rashin hankali da nutsuwa, kiyi hankali da rayuwa, karatun Alkur'ani shine gatan bawa, wawiya kawai dubeki kin girma har yanzu baki san kin girma ba, kin haɗa hankalinki da tuwo kin cinye, idan banda ke wawiya ce waye yake faɗa da namiji, mema zai haɗaki da Yako, to wallahi daga yau karna kuma jin kinyi faɗa da wani namiji idan kuma naji wallahi sai na bata miki rai shashs." Tunda Baffa yake wannan faɗar Jummo ta cuno baki sai ƙunƙuni take sanda Baffa yayi shuru sannan Jummo ta hau. " Haba dai Baffa shikenan dan lamiɗo ya kiraka ya gaya maka ƙarya da gaskiya sai ka yarda, ni dai wallahi wannan lamiɗon na tsanesa munafiki ne ga............" Bige bakin ta Baffa yayi bata ƙarisa Maganar ba yace. " Shi lamiɗon ne munafiki, kinga rashin hankalin naki ko, Allah ya shirye ki Jummo Allah ya kimtsa miki bakinki, shige ki bani waje." Juyawa tayi tana cuna baki ta shige bukkar INNO. *ABUJA CITY* Da sauri yake haɗa takaddun sa daga cikin office ɗin kasancewar time ɗin tashin sa yayi, gashi kuma gobe yake son ɗaukar hutu, na wata ɗaya yaje ganin gida sanye yake da kakin soja fuskarsa zagaye da saje farine tas dogo mai ɗan kauri, wayar sa dake gefe ce tayi ringin, a hankali ya maida kallon sa ga wayar *My Zarah* ya gani rubuce jikin screen ɗin wayar murmushi yayi tare da zama yana ɗaga wayar. " Hasken Khalil, ina shirin tashi daga office kina kira, ya akayi." Zarah dake kwance ruf da ciki taci kukanta ta ƙoshine ya sata ƙara sakin kuka ta kasa masa magana. Shuru khalil yayi yana sauraron kukan ta, cike da tashin hankali yace. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Oh Zarah wai yaushe zaki kirani ba tare da naji sautin kukan ki ba, kullum ke kina cikin ɗaga min hankali, burin ki kawai ki sani cikin damuwa haba Zarah." Zarah share hawayen ta tayi tare da cewa. " Haba Ya khalil meyasa bazaka tambaye ni damuwata ba, sai kawai ka hauni da mita bay........" " Dan Allah rufe min baki tambayar me zan miki bayan baki da wani ƙorafi da mita sai akan mahaifiyata, to na fara gajiya daga yau idan kinsan zaki kirani saboda ki kawo min ƙarar mahaifiyata ne, karki kuma kira na, idan kinga bazaki iya haƙuri da Momy ba, ki tafi gidan ku, domin kuwa bazan jure ƙorafi akan Momy ba." Yana faɗar hakan ya katse wayar sa, yana tsuka, yana mungun jin takaicin Zarah akan mahaifiyarsa, bata da wani aiki sai ƙorafin Momy, tashi yayi ya ƙarisa haɗa takaddun ya fice daga office ɗin *MAJOR IBRAHIM KHALIL BUBA* kenan cikakken Jami'in Soja......... Zarah tana jin ya katse kiran ta saki kuka mai cin Zuciya, " shikenan sai a dakeka a hanaka kuka, mahaifiyarsa ta min shi kuma ya kasa rarrashi na, rana zafi inuwa ƙuna, Momy tana cuta na a cikin gidan nan, amma bani da gatan da za'a bi kadu na, Allah kaine gatana Allah ka kawo wanda zai bimin haƙƙina.............." *Akwai waɗanda suka min ƙorafi dan Allah nabar littafin akan 100 saboda yanayin yau, to naji ƙorafin ku na barshi akan 100 ɗin* *Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira 100 kacal ga masu TRANSFER ta account number na 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank* *Idan kuma katin waya zaku turo mtn card ne na 100 ta wannan numbern 08147537180* *Da zarar kin tura kuɗin sai kiyi screen short ki turo shaidar biya ta wannan numbern 08147537180 kuyi hanzarin biya domin kuwa araha yafi bashi, ina jiran masoyana su nuna min soyayya ta haƙiƙi nasan nafi ƙarfin 100 a wajenku, ina jiran masoyana na haƙiƙa.* Vote Share and comments *Alƙalamin Rasheedat Usman* *Ummu Nasmah*✍🏻 [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *FREE PAGE* ➰➰ *11 to 12* *Ƙauyen Tulde* Tunda Mamma tayi sallar asuba ta sammaka gidan INNO, a bukkar INNO ta sameta tana tasbihi, zama Mamma tayi sai da INNO ta ajiye carbin tace. " Lafiya Mamma kika doko wannan uban sammako haka." Taɓe baki Mamma tayi tare da cewa. " Hmmm!!! Ke dai INNO bari, zuwa nayi na sami mijinki Mlm yauta akan maganar da mukayi na tafiya da Jummo birni, jibi nake son mu tafi idan Allah yasa ya yadda." Murmushi INNO tayi tana gyara zaman ta tace. " Har shakka kike, aini bana tantama zai baki ita tunda yasan gaban Buba zata zauna, sannan daɗi da ƙari idan kika ce masa za'a sata a makarantar Boko, kinsan yana son Jummo tayi ilimin BOKO mai tsawo, da wannan zamu ruɗesa ya baki Jummo, amma fa Mamma ki cika alƙawari idan kunje kisa Buba ya saka Jummo makarantar Boko." Dariya Mamma tayi tace. " Haba INNO har kina tantama a kaina ai dole Jummo ta shiga makaranta." Tayi Maganar tana leƙo tsakar gidan ko zata ga Baffa, ta ɗan juma suna taɗi da INNO kafin Baffa ya shigo gidan, INNO da kanta ta masa magana, ya shigo ya sami Mamma a gefen gadon karamnon INNO ya zauna tare da cewa Mamma. " Inbali jam Mamma" Mamma itama cikin harshen fullanci ta amsa masa. " Sai jam, Mlm Yauta wajenka nazo da wata buƙatar, ina son zan koma can birni wajen ɗana Buba, shine nayi tunanin mai zai hana ka bani Jummo na haɗata da ƴar marigayi Sayoji A'illo mu koma can Birnin tare idan munje burina shine nayiwa Buba magana ya saka min su a makarantar Boko, suma su sami cikakkiyar ilimin BOKO, amma me kace." Shuru Baffa yayi yana nazarin maganganun Mamma tabbas yana son Jummo tayi karatun Boko dana addini, sai dai yana tsoron haɗa Jummo da Mamma sanin rashin kyawun halin Mamma, sai dai yana da tabbacin kuma idan har Buba yana nan bazai bar Jummo ta lalace ba, tabbas wannan ce kawai damar da yake da ita wanda Jummo zata samu cikakkiyar ilimin BOKO, numfashi ya sauƙe tare da cewa. " Mamma zan baki Jummo amma da sharafi idan har kin amince." Murmushi Mamma tayi tace. " Faɗi sharaɗinka insha Allah ni kuma zan ɗauka." Baffa duban Mamma yayi tare da cewa. " Muddun Jummo zata zauna dake, dole ne ki saka mata ido, kina hanata aikata wani aiki mummuna, idan kinga zata kauce hanya ki jawota ki nuna mata daidai, kuma dole ne tayi karatun addini bayan na boko, idan kin yarda da wannan sharaɗin na amince ki ɗauki Jummo ku tafi, Allah yasa inda zatayi hankali zataje." Cike da farin ciki Mamma tace. " To ai alhamdulillah!!! Duk waɗannan abinda ka lissafo, koda baka faɗa ba haƙƙine a kaina na sauƙesa karka damu na amince da sharuɗan ka." INNO ce tace. " To alhamdulillah!!! Hakan yayi, Allah yasa haka yafi alkairi, yaushe ne zaku tafi." INNO ta yiwa Mamma tambayar tamkar bata sani ba. " Jibi Lahadi zamu koma insha Allah.'' Baffa cewa yayi. " masha Allah Allah ya nuna mana zan sanar da uwar yarinyar." Yayi Maganar yana tashi ya fice, itama Mamma bata wani juma ba ta koma gidan ta, koda Baffa ya sanar da Sikayel, ranta baiso tafiyar ba, sai dai batayi jayayya ba jin Baffa ya amince da tafiyar, fatan alheri kawai tayi, farin ciki da murna kuwa wajen Jummo ba'a magana sanda INNO ta sanar da ita tafiyar murna kawai take zataje taga Garkuwanta, da gudu ta bar gidan, duk inda ta ga mutane sai ta faɗa musu zataje birni gidan su mijinta, haka ta wuni cike da farin ciki. A kwana a tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau ta kama ranar Lahadi ranar da Jummo da Mamma zasu koma Birni tuni Mamma ta shirya, Tasiu mai taxi ta kira dake yasan har gidan Buba, ta ɗaukesa shata zai kaita har a gida, Jummo dangwalin kayanta ta ɗauka tare da kallon INNO sai kuma idanunta suka ciko da hawaye, shikenan yau zata rabu da INNO, itama dai INNO ranta duk babu daɗi, hanun Jummo ta kama tare da cewa. " Jummo yau zaki tafi ki barni ban sani ba ko zamu sake haɗuwa, sai dai zan sanar dake abu ɗaya a cikin rayuwa, karki taɓa wasa da addinin ki Sallah azumi yawan ambaton Allah, duk da kallon marar mutunci da ake min bana wasa da addini na, kema kin sani, ki riƙe Mamma tamkar ni, Allah ya miki albarka ya kareki daga sharrin shaidan da mutane." Ta ƙarisa Maganar tana share hawayen ta, Sikayel dake gefe ne cikin sanyin murya tace. " Jummo dan Allah idan kinje karki dinga musu rashin jin da kike anan ki riƙe mutuncin ki, babu ruwanki da rashin ki bi Rayuwa a hankali karki yadda ki zalunci kowa, idan kika kiyaye wannan zaki zauna da kowa lafiya Jummo haka duniya zata miki daɗi, idan kuma kika cuci wani babu shakka kema sai an cuceki Allah ya sa zuwan ki can sanadiyyar ɗaukakarki ne Allah ya miki albarka." Ameen Jummo tace tana kuka duk da son zuwa birni da take sai da taji bata son rabuwa dasu INNO babu wanda zata yiwa SALLAMA dama ba kawa bace da ita a cikin garin, koda ta samu Baffa ma a waje shima sosai ya mata nasiha da faɗa, INNO da kanta ta raka Jummo har gidan Mamma, a camma sabon shafin kukan suke, ita da Mamma, SOSAI suka sha kukan su suka godewa Allah, INNO na kallon Jummo da Mamma da A'illo suka shiga motar Tasiu, suna ɗaga mata hanu har suka ɓace, tun da suka kama hanyar cikin Gombe A'illo bata ko kalli inda Jummo take ba, haka ita Jummo kasancewar basa ko ga maciji akan Garkuwa. *GOMBE STATE* Wani irin Hom hom!!!! Ake dannawa get ɗin, da sauri baba mai gadi ya wangale get ɗin, jerin motoci ne sun kai 15 gabaki ɗaya sojoji ne a cikin su, sai wata baƙa wacce tasha tintak baka iya hango wanda ke ciki, yana ganin motocin ya tabbatar KHALIL ne ya shigo cikin garin, danna hancin motar sukayi, cikin compaunt ɗin gidan a parking space sukayi parking cikin sauri suka fito daga cikin motocin nasu, kowannen su hanunsa riƙe da bindiga, baƙar mota mai tintak ɗin suka zagaye ɗaya daga cikin su ne ya buɗe motar a hankali KHALIL ya fito daga cikin motar yana ɗaga musu hanu alamun su sauƙe bindigoginsu, cike da nutsuwa ya basu umarnin cewa kowa ya koma gida ya huta, Bala da Joseph ne kawai zasu tsaya, sannan ya shige part ɗin su, Momy dake zaune cikin falon ne taji sallamar KHALIL da sauri ta tashi cike da farin ciki, kasancewar tana mungun son khalil, cike da farin ciki shima ya rungume Momy yana cewa. " Welcome Momy nayi missing ɗinki." Murmushi Momy tayi tana ɗan buga bayan sa tace. " Welcome my love, sauƙar yaushe baka sanar damu zaka dawo yau ba, nasan Garko daya taro ka." Murmushi yayi yana zama cikin kujerun falo tare da zuba ido yaga ta inda Zarah zata fito sai dai babu alamun ta, (ko dai ta koma gidan nasu ne, da nace idan bazata iya ba ta koma) zuciyarsa ne ta tsinke, duban Momy yayi yace. " Momy ina Zarah ban ganta ba." Taɓe bakinta Momy tayi tace. " Tana can bedroom ɗinta tana baccin asara, yanzu na gama cin ubanta akan aiki ayi yarinya mai shegen son jikin tsiya, ke ba haihuwa ba kice bazaki aikatu ba, sai dai a baki kici ki kwanta, haba me za'ayi da macen da bata haihuwa." Runtse idanunsa Khalil yayi yana jin zafin maganganun Momy sai dai babu yanda ya iya kasancewarta uwa a garesa, shuru yayi baice komai ba, sai ma miƙewa yayi yace. " Bari na shiga Momy." " A fito lafiya" Momy tace tana jingina kanta jikin kujera. KHALIL kuwa haurawa yayi bedroom ɗin Zarah, tana ya hangota ruf da ciki sai shashsheƙar kuka take, ƙarasawa yayi jikin bedroom ɗin ya zauna a gefen ta, tare da saka hanu ya birkito ta jikinsa idanu ya ƙura mata cike da tausayinta domin kuwa yasan matsalarta duk akan mahaifiyarsa ne, numfashi ya sauƙe tare da saka hanu ya share mata hawayenta,a nutse yace. " My dear, kin san fa na hanaki wannan kwanciyar na ruf da ciki, Saboda haramun ne a musulunci babu kyau ki daina, wannan kukan naki shima bana so yana ɗaga min hankali, kuma zai iya sa miki ciwon kai, nasan matsalarki bata wuce tsakanin ki da Momy ne,zuwa yanzu yaci ace kin saba da damuwar Momy, ki daina saka damuwarta a ranki, ki share hawayen ki, dan Allah ki cigaba da haƙuri insha Allah komai zai wuce, ana son ɗan Adam ya kasance mutum mai yawan haƙuri, da apuwa, my dear ina miki wannan tunatarwa ne domin karki sha'afa ki kasa ɗaukar ƙaddarar ki, nine na kawoki gidan nan, kuma ban taɓa ƙuntata miki ba,. Kiyi hkr da abubuwan da Ammi take miki, bani da ƴancin dakatar da ita ko bata umarni, domin kuwa mahaifiyata ne, itace mai iko dani, dole na mata biyayya muddun ina son na gama da duniya lafiya, dan Allah Zarah ki tayani neman aljannata daga mahaifiyata ki daina nuna min damuwarta akan fuskarki bana jin daɗin hakan, kar wata rana ki tunzurani nayi abunda zai zamowa rayuwata matsala dan Allah my dear." Tashi Zarah tayi daga jikin sa tana jan majina cikin muryar kuka tace. " Ban taɓa manta waɗannan tunatarwar taka ba, saboda abune da ko yaushe kake tuna min, koda karatu ne yaci ace na haddace, bazan taɓa zama silar da zaka samu matsala da mahaifiyar ka ba, sai dai ya kamata ka dinga min adalci, ta hanyar nunawa Momy hanyar gaskiya Ubangiji da kansa yace ku faɗawa iyayenku gaskiya idan kunga sun kauce hanya, amma kai ko da sai ɗaya ne baka taɓa nunawa Momy rashin kyautawar abubuwan da take min ba, Ya Khalil na far............." Hanu KHALIL ya ɗaga mata fuskarsa a haɗe yace. " Ya isa haka my dear, nafi ƙaunar mahaifiyata fiye da komai a rayuwata ta duniya zan iya rabuwa da duk wanda zai nemi zamo mata matsala, ko ya nemi faɗa mata Magana, ciki kuwa har dake, Momy uwata ce wacce tayi ɗawainiya da rayuwata tun ina cikinta taci kashina da fitsarina, ta jure duk wata wahalata bata taɓa gajiyawa ba, dan haka bazan taɓa zama a gabanta na nuna mata bacin raina akan abinda take miki ba saboda kawai kina matata, hakan ba yana nufin kinfi uwata bane, daga Yau karki kuma cewa na nunawa Momy rashin facewar abinda take miki, ki cigaba da haƙuri insha Allah komai zai zamo tarihi." Wani irin baƙin ciki ne ya tokarewa Zarah wuya, wannan rashin ganin laifin Mahaifiyarsa da KHALIL baya yi yafi komai ƙona mata rai, kanta ta mayar ta kwanta, cike da damuwa, tsabar takaici ko ruwan wanka kasa tashi tayi ta haɗa masa, wannan wani irin baƙin ciki ne, mijinta yana da gidan sa, ta hanasa zama a ciki ta ajiyesa a gabanta saboda kawai ta ƙuntata mata, shima KHALIL ganin halin da take ciki baice mata komai ba da kansa yayi komansa ya gama, kasancewar zafin da ake ya sashi saka best da gajeren wando falo ya fito wajen Momy................ 😆😆😆😆 Naso na jira isowar Mamma CIKIN wannan gidan, da zai tara cakwakiya, nasan akwai Magana😆😆 bari dai muyi haƙuri sai gobe😛 🥰🥰 Ina fa ƙaunar ku masoyana sai sayan BOOK ɗin nan kuke, gaskiya ina mungun sonku irin sosai ɗin nan. *Naira 100 kacal zaku turo ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank, ko mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan ku turo shaidar biya* *Araha tafi bashi kuyi maza kuyi registration kafin na rufe 100 ce babu yawa🥰.* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *ASSALAMUALAIKUM ALAIKUM MASOYANA BARKA DA DARE, JAMA'A SAI MAGANA SUKE MIN AKAN COMPLETE ƊIN BOOK DIN HATSABIBIYA SAUDE HAR GA ALLAH BAN KAMMALA BOOK ƊIN BA SAURA KAƊAN WANDA NAKE SAKA RAN INSHA ALLAH ZUWA BAYAN SALLAH ZAKU SAMU COMPLETE ƊIN LITTAFIN, A YANZU GASKIYA BABU COMPLETE ƊIN SA, SANNAN INA KIRA GA MASOYANA DA SUYI GAGGAWAR ZUWA SU BIYA KUƊIN WANNAN LITTAFIN NA GELLE ƁINGEL AKAN FARASHI MAI SAUƘI 100 KACAL* *FREE PAGE* ➰➰ *9 to 10* Tana cikin wannan halin damuwar Momy ta faɗo cikin bedroom ɗin nata cike da faɗa. " Oh wai Zarah kwanciya kikayi tuntuni, aikin gidan waye zai miki shi, wai meyasa kika cika son jikine, ki tashi maza kije kiyi aikin dake gabanki." Cike da ƙunar rai Zarah ta ɗago kanta ta kalli Momy, numfashi mai zafi ta sauƙe tare da cewa. " Aiki kuma Momy, ai nayi duk wasu ayyukan daya kamata nayi, nayi girki nayi shara da mopping, din falo, to kuma Momy me zanyi bayan shi." Momy taɓe bakinta tayi sannan tace. " Sanin kinyi ne yasa na kira ladi mai wanke wanken gidan nace karta zo, sai ki tashi kije kiyi wanke wanken, idan kin gama gacan wanki na, kije ki ɗauka ki wanke min su, kuma ban yarda ki saka Sadiya ba, kece zaki min waɗannan ayyukan, ayi yarinya da shegen son jikin tsiya, baki haihu ba, sannan kice bazaki aikatu ba, a'a dole kiji wahalar aiki tunda bakiji ta haihuwa ba." Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo daga idanun Zarah, tana mungun jin zafin gorin haihuwa da Momy ke mata, har ga Allah ita ta fara gajiya da wannan rayuwar Auren ta fara ji a ranta gara ta kashe Auren ta zauna bazawara zaifi mata kwanciyar hankali ina amfanin auren da babu jin daɗi a cikin sa, uwar miji ta ƙuntata maka, shima miji ya kasa baka farin ciki, yana ganin tamkar baka son mahaifiyarsa ne, muryar Momy ne ya doki kunnen ta. " Ko bazaki tashi kiyi aikin bane kike min hawayen munafurci, karya nayi a cikin maganata, ko kin taɓa yin koda ɓari ne, amsar itace a'a, dan haka dole ki bautu muddun kina son zama a cikin gidan nan, gara ki daina kuka zaifi muku, duk wani take taken munafukar ƙanwarki tana son Garko, to ki sani wallahi ko sama da ƙasa zasu haɗe bazan taɓa bari ɗana ya kuma Auren zuri'ar kuba, tunda da alamu baku da yawan ahali ku biyu fa rak iyayenku suka haifa suma su Uku uwarsu ta haifeshi, kinga kuwa ai ya tabbata baku da yawan ahali, ke bari kiji wallahi khalil ma sai ya ƙara Aure domin ya haihu shima yaga jininsa magajin sa a duniya, ki kuma tashi kije kiyi aikin dana saki." Tana gama faɗin haka ta juya ta fice, kuka mai cin rai Zarah ta saki, harda majina cikin kukan take cewa. " Allah kana kallon halin da nake ciki, ya Allah kai kace mu rokeka zaka amsa mana, ya Allah ka bani haihuwa, idan kuma bani da rabon haihuwa a cikin gidan nan ya Allah ka kawo ƙarshen wannan Auren nawa na huta, ya Allah karka bari baƙin cikin Momy ya samin ciwo, Allah ka dubeni da idon rahama da albarkacin karatun Alkur'ani da nake." Tayi addu'ar tana tashi, ta fito, kitchen ta shiga ta tattara wanke wanken tanayi tana kuka harta gama, ta kuma nufi bedroom ɗin Momy ta ɗauko wanki nata shima taje ta wanke tas ta shanya su, sosai ta gaji jikinta duk yayi tsami, koda ta dawo bedroom ɗin ta, Sadiya ta kira, kafin Sadiya tazo Zarah ta kira aminiyarta Khadijah akan tazo ta sameta, tana nan kwance Sadiya ta shigo a gefen bed ɗin nata ta zauna tare da cewa. " Gani Aunty." Tashi Zarah tayi ta zauna tare da tsare Sadiya da ido, cike da tuhuma tace. " Sadiya zan tambayeki ne dan Allah ki faɗa min tsakanin ki da Allah, wai da gaske kina son Garkuwa, karki boye min komai ni ƴar uwarki ce baki da wanda ya fini.?" Shuru Zarah tayi zuciyarta na bugawa ta sunkuyar da kanta tare da dagawa Zarah kai alamun eh. Shuru itama Zarah tayi sosai hankalinta ya tashi lallai akwai Babban ƙalubale a gabanta dole ne, tayi yaƙin raba Sadiya da Garkuwa koda hakan zai kawo ƙarshen aurenta itama bataji daɗin zaman gidan ba, bare ta bari yiwa ƙanwarta sha'awar ta shigo amma bazan yi gaggawar rabasu ba, zanbi komai a hankali insha Allah a ruwan sanyi zan rabaku numfashi ta sauke tace mata. " Sadiya da zan baki shawara ki ɗauka da nace ki rabu Garkuwa ki nemi wanin mijin Auren." Da sauri cikin kiɗima Sadiya ta ɗago ta kalli Zarah, ras zuciyarta ta buga. "na rabu Garkuwa no ina bazan iya ba, Garkuwa tamkar numfashi nane rasa shi yana nufin rasa rayuwata ne, amma Aunty meyasa kikace na rabu dashi.?" " Nasan a yanzu bazaki fahimce ni ba Saboda zuciyarki tana cikin gigi bazan ce miki komai ba yanzu kije sai na sake neman ki, abinda nake so dake yanzu ki shirya ki koma gida gobe." " Aunty na kom........" Dakatar da ita Zarah tayi tare da cewa. " Karki cemin komai Sadiya, dan Allah na roƙeki ki koma gida gobe, dan Sadiya karki sanar dasu Mama cewa nice nace ki dawo dan Allah kimin wannan alfarmar." Cike da ɗaurewar kai Sadiya take kallon Zarah ta rasa Gane inda maganganun ta suka dosa sai har ranta bataji daɗin korarta da Aunty Zarah tayi a cikin gidan ba ( ko dai ta fahimci suna lalata da Yaya Garkuwa ne, idan ba haka ba meyasa zata koreni, Allah kasa ba hakan ta fahimta ba) duk cikin zuciyarta Sadiya take wannan maganar, tare da miƙewa cikin zafin zuciya ta fita daga bedroom ɗin, tana fita Zarah ta saki kuka tana toshe bakinta, tana cikin wannan halin Khadija ta shigo da sauri ta ƙarisa tana riƙe kafarɗarta. " Subahanallah!!! Zarah lafiya meya faru.?" Zarah tana kuka ta kwantar da kanta a jikin Khadija, cikin muryar kuka tace. " Kinsan matsalata Khadija, Momy zata kasheni, ina tsoron kar wata rana a wayi gari babu ni na mutu." Numfashi Khadijah ta saki tabbas Zarah tana cikin jarabawar uwar miji, maimakon Khadijah ta zagi Momy sai cewa tayi. " Ita Rayuwa tamkar ƙwallon ƙafa take kullum cikin gara bawa take bata taɓa barin bawa ya huta, kana tsallake wannan jarabawar zaka faɗa wata, ki cigaba da haƙuri Zarah ke taki ƙaddarar kenan dan Allah karki dinga sanar da iyayenki abinda Momy ke miki, wata rana zaki iya manta abinda ya faru tsakanin ku, amma su iyaye bazasu taɓa mantawa kullum zasu ke ganinsu dashi." Numfashi zarah ta saki tare da kai dubanta ga Khadijah fuskarta cike da alamun damuwa tace. " Khadijah tunda akayi aurena da Khalil zaman haƙuri kawai nake a cikin gidan nan, kullum bani da burin daya wuce na farantawa Momy Amma sam bata gani na rasa meyasa Momy ta tsaneni, bani na hana kaina haihuwa ba Khadijah amma meyasa take ganin laifina, shima kansa Khalil baya ganin laifin Mahaifiyarsa sai nawa, kullum nayi magana sai dai ace nayi haƙuri ana tusa min baƙin ciki, sai yaushe komai zai wuce, ko sai na mutu ne, Khadijah bazan ɓoye miki ba, wallahi na fara gajiya da wannan rayuwar gidan na gaji da wannan Auren na gaji da hkr." " Zarah ba'a gajiya da hkr, mijinki yana sonki da ƙaunarki dan Allah kar damuwa mahaifiyarsa tasa kibar gidan sa, dama ba kowani ɗan adam bane yake so a dinga yawan kawo ƙarar mahaifiyarsa, kullum ina hanaki kaiwa mijinki ƙorafin mahaifiyarsa domin kuwa maza basa so, hkr da juriya shi zaki riƙe insha Allah zakiga komai ya zamo tarihi babu abinda yazo zama a duniya sai ikon Allah komai yana da farko da ƙarshe ki daure kici wannan jarabawar zarah." Cike da tsantsar damuwa zarah tace. " Khadijah kullum abinda kike faɗa min kenan kalma daya kiyi hkr Khadijah sai yaushe wannan haƙurin zai ƙare ne, haka zan cigaba da rayuwa cikin baƙin ciki da ƙunci.?" Murmushi Khadijah tayi tare da cewa. " Haƙuri baya taɓa ƙarewa na faɗa kuma na maimaita miki, Asali ma sai dai ya kaiki ga cimma nasara, Zarah dole nace kiyi hkr domin kuwa shine abinda duk wani masoyinki na gaskiya zai faɗa miki, Aure ya gaji ƙalubale duk daɗin da mace take ji a gidan Auren ta dole sai kin samu ta da wani matsala koda kaɗan ne." " Shikenan Khadijah zan cigaba da haƙuri har Allah ya kawo min karshen matsalata, bari naje na kawo miki abinci." Khadijah murmushi tayi tace. " A'a barshi wallahi a koshe nske bani da yunwa yanzu haka gidan kaka tabawa zani na dubo jikinta shine fa dana ga kiranki nace fana fara biyo nan ɗin." Zarah ce tace. " Dama kullum kika zo gidana baki cin abinci, ki gaishe da kaka tabawan." " Khadijah tana miƙewa tsaye tare da ɗaukar jakarta tace. " Zataji nikam bara na tafi." Zarah tare suka fito da Khadijah daga bedroom ɗinta a falo suka taradda Momy zauna tana kallo Khadijah har kasa ta sunkuya tace. " Sannu da hutawa Momy Barka da Rana." Harara Momy ta watsawa Khadijah tare da taɓe bakinta tace. " Iyayen munafurci kuma yaushe aka shigo, har kun gama kulla tsiyar ne, baki da aiki sai gulma da munafurci, wallahi ɗana Khalil yafi karfin ku, tun yana yaro nake tsumasa da bauri yafi karfin kaidinki da bokan ku, shige a gabana." Khadijah bata ce komai ba ta miƙe tsaye, Zarah ranta cike da baƙin ciki ta juya zatabi Bayan Khadijah Momy ta dakatar da ita tare da cewa. " Ina zaki fita ki bita baƙar munafuka, duk makircin da kuka ƙulla a ɗakin bai isheku ba, har sai kun fita waje kun ɗaura, to koma ɗakinki bazaki bita ba." Zarah zatayi magana Khadijah ta dakatar da ita. " Karkice komai ki koma zamuyi waya." Juyawa Zarah tayi cike da baƙin ciki, ita kuma Khadijah ta fice tana yiwa Zarah addu'ar samun sauƙi, Momy kuwa tsuka taja. Ita kuwa Sadiya cike da ɓacin rai tabar gidan Zarah babu wanda yasan ta tafi a cewarta Aunty Zarah ta wulaƙanta ta, ta koreta a gidan ta, tana mata baƙin ciki karta auri garkuwa ta huta. Koda Garkuwa ya dawo da daddare sai da ya nemi Sadiya saboda buƙatar kansa, Aunty Zarah ganin bata gidan yasata fahimtar fushi tayi ta tafi, murmushi Zarah tayi tare da cewa Garkuwa. " Sadiya ai tun ɗazu ta tafi, Mama ta kirata zasuyi tafiya." Cike da rashin jin daɗi Garkuwa yace. " Kuma Aunty shine zata tafi kota nemeni bari na kira wayarta" Yayi Maganar yana ciro wayar sa, numbern Sadiya ya kira yaji switch off, Aunty Zarah ya kalla yace. " Switch off." " Wayar nata, maybe ko chaji." " Zai iya yiwuwa" Garko ya faɗa tare da tashi ya haura harya taka step ya juyo ya cewa Aunty Zarah. " Am na manta ɗazu khalil ya ce ya kiraki baki ɗaga ba, so yace a faɗa miki gobe bazai samu dawowa ba sai next week." " Allah ya kaimu Zarah tace tana shigewa kitchen." ✨✨✨✨✨✨ Rayuwa tana gudu yayin da abubuwa ke sauyawa mai daɗi da marar daɗi, Rayuwar Zarah dai a cikin gidan babu wani sauyi wajen Momy, yayin da daga can ƙauye Mamma take ƙoƙarin dawowa cikin birni gidan ɗan ta tare da Jummo domin kawo ƙarshen Momy, Momy da Daddy har Garko basu da labarin dawowar Mamma ita kaɗai tasan zata dawo, bata kuma so su sani sai dai su ganta......................... Tirƙashi lallai akwai lauje cikin naɗi shin wani irin rayuwa za'ayi a wannan gidan idan Mamma ta dawo, shin Mamma zata ci galba akan Momy kuwa, Garko zai yadda da Auren Jummo kuwa, shin Zarah zata samu farin ciki, ya Rayuwar Sadiya zata kasance tsakanin ta da garko, amsar tana sanƙame cikin wannan labarin indan kun biyoni da Naira 100 kacal, ba'ama fara komai ba yanzu za'a fara, ku dai masoyana ku biyoni mu jone. *100 zaki biya ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan kuyi screen short ku turo shaidar biya, karku sake ayi babu ku.* Masoyana ina alfahari daku, sai na ganku. *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *FREE PAGE* ➰➰ *13 to 14* Tafiyar awa ɗaya ce ta kawo su Mamma har ƙofar gidan Alhaji Buba Tasiu mai taxi parking yayi a gefen gidan yana duban Mamma yace. " Allah ya kawo mu, munzo ganan gidan ɗanki Alhaji Buba, sai ki shiga ki karɓon kuɗina." Mamma zaro idanunta tayi tana leƙo kanta daga tagar motar, tana ƙarewa gidan kallo. " Kan bala'i wai da gaske wannan tangamemen gidan duk na Buban Mamma ne, kaga wani makeken ƙyaure na gwal yiwa bakin shige, cap!!! Aa dole Buba ya dawo shirgegen ƙato, ina can ina zaune a shegen gidan zana shiko yana nan cikin wannan aljannar, lallai Zainabu ta shanye Buba." Jummo itama gidan take kallo tana jin wani irin farin ciki, ita fa burinta kawai taga Garkuwanta shine damuwarta, A'illo kuwa uffan bata ce ba saboda tasha zuwa gidan itama Mamman ƙin dawowa tayi tun farko tace sai ƙauye, hanun Jummo Mamma ta kamo suka fito daga cikin motar A'illo bayan su ta biyo, a bakin get ɗin suka tsaya Mamma ta kalli Jummo tace. " To ni yanzu Jummo ta yaya nasan zan iya buɗe wannan ƙatuwar ƙyaure, ki duba fa yanda yake kame tamkar baida mabuɗa." " Mamma ni ina zan sani, gashi ba guntuwar katanga ba, bare mu haura, kawai mu ta bugawa harsu buɗe." Ai kuwa Jummo bata rufe bakinta ba, Mamma ta hau doka ƙofar tamkar zata ɓalle ta, Joseph da keneth sai Baba idi mai gadi cike da tsoro suka miƙe jin mungun bugun da ake yiwa ƙofar, keneth da Joseph bindiga suka ɗaga sama, keneth shine ya buɗe get ɗin tare da saita bindigar sa, dai-dai ƙirjin Mamma bindigar ta tsaya, ai kuwa Mamma bata ankara ba, sai gani bindiga tayi, wani irin ƙara tasa, sai ga fitsari sha ya zubo daga jikin Mamma take ta wanke zaninta da fitsari jikinta ya soma rawa, ta kasa magana sai zufa dake keto mata, Jummo kuwa idanu ta ƙura masa cike da rashin tsoro ko a jikinta, sai kuma ta kwashe da dariya ganin yanda Mamma ta sake fitsari ga famar rawa da take yi, cikin tsawa Joseph yace. " Kai wanene zaka dinga duka ƙofa haka, kai wawane Mama, ko aikeka akayi.?" Joseph yayi Maganar cikin bagwariyar Hausar sa da bata nuna ba, Baba Idi ne mai gadi yace. " A'a Joseph ai ba sai ka tambaya ba, ya wuce irin mabaratan nan ne, masu zuwa bara wajen Alhaji." Tsawa keneth ya dakawa su Mamma. " Ku bar kofar gidan nan ko na ɗauke kanku da bindiga, duk na kasheku YANZU." Ai Mamma bata jira ya rufe bakinsa ba, ta zura da gudu ta koma bakin motar Tasiu, Jummo kuwa batayi motsi ba, tace. " Bafa bara muke ba malam, ya zaka kalle mu kace mana mabarata, wannan tsohuwar da kake gani Uwar masu gidan ne, itace maman Alhaji Buba, baka san Buban Mamma ake ce masa ba a ƙauye, ku bamu hanya mu............." Wani wawan mari keneth ya ɗauke Jummo dashi, tare da hankaɗata ya rufe get ɗin, dafe fuskarta Jummo tayi cike da ɓacin rai tunda take a rayuwarta babu wanda ya taɓa marinta da girman ta, sai wannan mai fuskar fir'aunan, juyawa tayi ta dawo wajen Mamma da har yanzu take cikin firgici sai ɓari take, Jummo duban Mamma tayi tace. " Kin iya kunna sigari ki zarewa mutum ido kuna kunna masa ashar, amma sai tsoron bala'i, ki duba fa yanda kika jiƙe da fitsari Mamma abun kunya, shiga mota mu koma kauye kawai wannan ba gidan shiga bane gidan bala'i ne." Ita dai Mamma yau bata da baki, ko amsa bata mayarwa Jummo ba, ta faɗa motar duk abinda akeyi, Idi drever yaga koma ba musu ya shiga motar, Jummo tana ƙoƙarin shiga idanunta ya kyallo mata motar Garkuwa yana tahowa, tsalle tasa tana dariya tace. " Yeee!!!! Mamma ganan Yaya Garkuwa a mota fito ki tsare mana shi aradu." Ai kuwa but Mamma ta fito, Garkuwa dreving ɗinsa yake, abunsa yana sauraron waƙar auta mg boy, ko kaɗan bai kula da Mamma ba, sai gani yayi ansha gaban motarsa, da sauri garkuwa ya taka burki gudun karya taka ta, zaro idonsa yayi yana kallon Mamma cike da mamakin waya kawo ta, "Lallai wannan tsohuwar akwai rigimar tsiya" buɗe motar yayi ya fito, ras idanunsa suka sauƙa akan Jummo, zuciyarsa ne ta tsinke ras, " dama da wannan aljanar yarinyar tazo, yau kuma mun shiga Uku ai" yayi Maganar a ransa yana haɗe fuskarsa, da gudu Jummo ta ƙariso gaban sa tana. " Oyoyo yaya GARKUWA na, wayyo daɗi, wallahi sai yanzu naji sanyi dana ganka yaya GARKUWA na." Tsuka garkuwa yaja yana nuna ta da yatsa yace. " Ke mahaukaciya, karki kuskura ki ƙara danganta sunana dake, wawiya." Yayi Maganar yana duban Mamma da har yanzu bata cikin hankalinta yace. " Ke kuma meye haka sai kace wadda aka tsamota a kaskon suya, duk kinbi kin fice hayyacinki, anya kuwa lafiyar ki."? Jummo baki ta murguɗa masa, Gabansa Mamma tazo tare da kamo hanunsa tace. " Kaga Garko bana son bala'i yanzu wanda na gani yanzu ma ta isheni, ni dai yanzu biya idi kuɗin sa, sai ka ketarar damu siradin gidan ubanka, tunda kunsa ƙattai masu fuskar fir'auna su dinga ciwa duk wanda zai rabeku mutunci." Cike da rashin fahimtar zancen ta, Garkuwa yaje, motar Idi ya basa dubu goma, tare da tambayar A'illo meke faruwa da Mamma, fayyyace masa A'illo tayi, sosai Garkuwa yake dariya, tare da barin motar sa a wajen ya jawo hanun Mamma yace. " Muje masifaffiyar ƙarya." Tafiyar sukayi har bakin get ɗin Mamma na maƙale jikin Garkuwa, get ɗin a kwankwasa a hankali, jumawa kaɗan keneth ya wangale kofar ganin Jummo yasa zai fara masifa sai kuma yayi shuru sakamakon ganin Garkuwa, gefe ya matsa suka shiga, kafin ya rufe, Garkuwa cike da tahuma yace. " Wani ɗan iskan ne cikin ku ya nunawa wannan tsohuwar bindiga?" Shuru sukayi, tsawa Garkuwa ya Kuma musu. " Magana nake kun min shuru!!" Joseph ne ya nuna keneth da yatsa, numfashi Garkuwa ya sauƙe tare da cewa. " Kasan wacece kuwa wannan daka nunawa bindiga, kasheta zakayi ne, Maman Daddy ne fa, uwar da ta haifesa." Zaro ido dukkan su sukayi cike da tsoro, Garkuwa cije bakinsa yayi tare da cewa. " To kuwa kun jawowa kanku bala'i ku kwana da sanin cewa yanda kuka shuka mata tijara, wallahi Mamma sai ta jaza muku bala'i dan bata barin bashi." Yayi Maganar yana jan hanun Mamma suka shige part ƊINSU, Baba Idi mai gadi kuwa, cikin sa sai ƙugi yake cike da tsoro domin kuwa da wannan aikin kawai ya dogara idan aka koresa ya zaiyi da iyalansa, gara su keneth su gwamnati suke yiwa aiki koda za'a ɗau mataki sai dai a musu horo ba dai kora ba, da wannan damuwar Baba Idi ya zauna. Suna shigowa bakin falon Mamma ta kwace hannunta tare da cewa. " Dallah cikani!!! Dan ubanka, ke zainabu!!! Ke Zainabu!!! Zainabu!!!" Momy da Khalil dake zaune suna hirar yaushe gamo ne ya sata saurin juyowa jin ana ƙwala mata kira tamkar za'a tashi sama, shima Khalil dubansa yakai wajen " Mamma!!" Ya furta yana miƙewa tsaye, Momy kuwa kusan suman tsaye tayi ganin Mamma a cikin gidan ta, shikenan ta shiga Uku, Mamma a cikin gidan ta!!! Dakyar cikin nauyin baki Momy ta amsa. " Na'am Mamma kece tafe, lale marhaban sannu da hanya, kin kwaso rana, Bismillah Mamma ki ƙariso ki zauna." Kallon sheƙeƙe Mamma ta yiwa Momy cikin masifa take kwaikwayon maganar Momy tace. " sannu da zuwa Mamma kin kwaso rana, Bismillah ki ƙariso ki zauna!!! Riƙe sannun ki makira bana so, ina ruwanki da hanyar dana kwaso a kanki na taho da zaki min ƙirafi,. Koko ni makahuwa ce da bazan ga wajen zama ba sai kin gwada min, gidan kine kona ubanki ina dai gidan ɗana ne, ai dole na zauna ba tare da iso ba." Shuru Momy tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa bata tankawa Mamma koda kalma ɗaya bace, Garko kuwa taɓe bakinsa yayi alamun kunfi kusa, shi kuwa khalil tamkar hadari haka ya haɗa fuskarsa a rayuwarsa ya tsani a ƙuntatawa Momy cike da masifa idanunsa sunyi jajur yace. " Haba Mamma!!! Haba meye haka wannan ai cin mutumci ne, taya zaki samu mata tana zaune ki hauta ba tare da ta miki wani laifi ba, gaskiya wannan bai dac........" Hanu Momy ta ɗaga masa tare da cewa " Karna kuma jin muryarkae, baka da hankali ne, Mamman sa'ar kace, ina ruwanka da kai take" kallon Mamma tayi tace " kiyi hkr Mamma Allah ya huci zuciyarki." " Ai da baki dakatar dashi ba, da kin barsa sai yazo ya dokeni, ya gani idan zai share dan ubansa, tambaɗaɗɗe marar mutunci, yo ni ina ma lissafi dakai a cikin jinina ne, kalilu, shege mai baƙar zuciya tunda ka shiga wannan tsinannan aikin ko zama cikakken Bayahude, to dan ubanka na dawo gidan nan da zama, sai ka shiryawa dukana wata rana tunda kace kai marar mutunci ne" tsagaitawa Mamma tayi da maganar sai kuma tasa kuka tana cewa " yanzu tsabar ba'a daukeni da mutunci ba, nan aka ajiye wasu ƙattin arna masu fuskar fir'auna, suka hanani shigowa gidan ɗana, wai harda bindiga aka ɗaura min saboda ba'a so nazo gara a haɗa baki dasu su kasheni, wai tsabar rainin wayo wai wannan ƙeƙashashen mai gadin ƙyauren naku ya kalleni ya kira ni mabaraciya, wallahi yau ɗin nan sai ya bar gidan nan Allah ya kawo Buba, zan nuna masa nice mai iko da gidan ba Buban ba." Cike da takaici da haushi Khalil yake kallon Mamma gashi ba halin ya mata magana Momy ta hausa da faɗa, Garko kuwa dariya yasa tare da haurawa sama yana kiran " Mamma matsala" waje ta samu ta zauna tare da saka hanu a lalitar ta, ta ɗauko sigari da ashana, zata kunna, Khalil ya zaro ido tare da saurin ƙarisawa gabanta yana. " Subahanallah!! Haba Mamma sigari kuma a cikin gidan nan, bazai yiwu ba, baki isa ba wallahi.!!!!" " To fa ubana!!! Bazai yiwu ba kace, to danne ni ka ƙwace, kai ko ubanka fa bai Isa hanani shanta ba, bare kai, waima dakata, kalilu bala'i kake nema dani ne, sai famar shige min hanci kake, to wallahi zan facoka, ka fice daga idanuna na rufe yau naga tsiya, meye haɗin ka kaska da garahumi, nace na cireka cikin zuriata to meye ruwanka dani." Tsuka Khalil yaja tare da saka hanunsa ya murɗe hanun Mamma ba tare da yayi magana ba, sigarin ya ƙwace da ƙarfi yana miƙewa tsaye yace. " Na danne ki na ƙwace!!! Mamma sai kiyi abinda zakiyi, wallahi muddun zaki zauna a cikin gidan nan, to wallahi bazaki sha sigari ba, kuma na isa na dakatar dake, a ƙauyen ne zaki sha sigari ki zauna lafiya amma ba'a cikin gidan nan ba, ni ki daina zaro min idanu, ba tsoro zai bani ba!!!" Yayi Maganar yana zarowa Mamma itama ido tare da ciro bindiga yace. " Kuma kina magana zan ɗauke kanki da wannan bindigar kiyi kuma ki gani." Tsawa ya dakawa A'illo da Jummo yace " ku kuma bazaku nemi waje ku zauna bane kuka tsaya akan mutane kamar mashi." Tura bakinta Jummo tayi tare da zama kusa da Mamma tace. " Kiyi hkr Mamma Allah zai saka miki, wannan ai zalunci ne, wai kema Mamma dama kinsan wannan gidan na azzalumai ne shine kika taho dani, to wallahi ni bazan yadda da zalunci ba, kuma bazan yadda a zalunce ki ba, babu wani ƙato ko ƙatuwar da zai bani tsoro, har wani ciro bindiga ake, to wa yake tsoron mutuwa mtss............................" 😆😆😆😆😆 *GIDAN CAKWAKIYA KENAN, WACCE IRIN RAYUWA ZA'AYI NE A WANNAN GIDAN, KU BIYO NI DA GUDU DOMIN JIN INDA WANNAN CAKWAKIYA ZATA TSAYA* *NAIRA 100 KACAL ZAKU TURO TA WANNAN ACCOUNT NUMBERN 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK, KO HOTON MTN CARD NA 100 TA WANNAN NUMBERN 08147537180 SANNAN KIYI SCREEN SHORT KI TURO SHAIDAR BIYA* *PLEASE DAN ALLAH MASU VTU KU DAINA, BANDA VTU BANA SO, PLEASE KU DAINA* 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ *KUYI SAURI KU BIYA FREE PAGE YA KUSA ƘAREWA, ARAHA TAFI BASHI 100 NE KAWAI BABU YAWA INA ALFAHARI DAKU MASOYANA* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *FREE PAGE* ➰➰ *15 to 16* Zaro idonsa Khalil yayi yana ƙarewa Jummo kallo, nuna ta da yatsa yayi yana zaro mata ido ciki tsawa yace. " Keeee!!!! Dan ubanki waye ƙaton ko ƙatuwar, dawa kike, kai!!! Momy kina jin abinda wannan ajabon yarinyar take faɗa mai kama da Aljana." Yayi Maganar yana ɗauke Jummo da mari, saurin dafe kuncinta tayi ganin wasu taurari masu bala'in haske sun shige ta gabanta, bai sauƙe hanunsa ba, itama Jummo ta ɗaukesa da mari, daga Mamma Momy har su A'illo a razane suka miƙe suna kallon Jummo, duk da Jummo ba yau ta saba dakuwa da maza ba amma wannan marin da tayiwa Khalil sanda ya razana kowa a cikin falon cike da tsantsar mamaki , khalil yake kallon ta, ji yayi tamkar ya ɗauketa da bindigar da take hanunsa, sai kuma yaji hanunsa ya masa nauyi, idan harma yace zai daki wannan yarinyar mai zai samu a jikinta ai sai dai ya ɓallata, amma tabbas wannan babu hankali a jikinta, haka kuma ya tausaya wa rayuwarta domin kuwa duk mace mai ɗabi'ar Jummo abun tausayi ce, tabbas akwai ƙauyanci da jahilci yana yawo a jikinta shi kuwa jahili babu abinda bazai iya aikatawa ba lallai wannan yarinyar tana buƙatar tarbiyya shikaɗai yake zancen zucin yayin da ya juya cikin ɓacin rai, Momy kan Jummo ta hau da masifa tamkar zata daketa cike kuma da ƙyamar ta, Mamma ta dakatar da ita. " Kul kul!!! Kika saka hanu jikinta Zainabu, shi wanda ta mara ɗin ganin mutunci manya yake ai gara itama marinsa kawai tayi, shifa yanzu yaso kasheni Allah ya tsererar dani, waini dama Zainabu haka ake rayuwa a cikin gidan ki babu tarbiyya da kwaɓa eh lallai dole na samu zama a cikin gidan nan duk na gyara muku zama." Momy cike da takaici tana hararar Jummo ta haura sama Zarah ta kwaɗawa kira, da sauri Zarah ta fito tana amsawa a bakin kofa ta samu Momy tsaye tace. " Gani Momy." " Kije ƙasa ki kaiwa Mamma ruwa da abinci, tana can tana mita ni bazan iya zan shiga ɗaki na kwanta." Da to Zarah ta amsa Momy ta shige bedroom ɗinta, Zarah bakinta ta taɓe tana cewa. " Har kin fara jin haushi kenan, hmmm!! Abinda kike min kema shi ake miki, ba gara Mamma bama DUK tsiyar da zata shuka miki, bazata azabtar da mutum da bauta ba, mtss ai naji daɗin zuwan Mamma gidan nan." Ta ƙarisa Maganar tana sauƙa ƙasa, fuskarta cike da murmushi, jikin Mamma ta faɗa tana dariya tare da cewa. " Oyoyo Mamman mu, oh tsohuwar nan, sai yau kika ga damar kawo mana ziyara munyi kewarki har mun gaji." Itama dariya tayi tana riƙo hanun Zarah tace. " Ke dai zara'u bari, gajiya nayi da zaman ƙauyen nace bari na dawo binni na ɗan sha jar miyya, yauwa ƴar albarka zara'u ba ƴar soyayyiyar kaza ne, a kawo mana mu ɗan goge bakin tunda wannan shegen mijin naki mai baƙin ran tsiya ya ƙwace sigarin." Dariya Zarah tasa tare da cewa. " Kai Mamma gidan son da daɗi, ai kuwa ba'a taɓa rasa nono a ruga, bari naje na kawo kaza kici harta isheki." Wangale baki Mamma tayi tace. " Ke dai sannu ƴar albarka, ai duk rugar da aka rasa nono bata amsa sunan ta ruga ba." Dariya Zarah tayi ta cewa A'illo. " A'a harda Hajiya A'illo ne, lallai zuri'a ta haɗu, wannan fa waye ce Mamma ban Santa ba." Ta nuna Jummo, murmushi Mamma tayi tace. " Au wannan Jummo kenan, jummon INNO da Mamma, tare muka zo jikar aminiyata ne, INNO, tare zamu zauna na aurar da abina a gidan nan." Murmushi Zarah tayi bata fahimci Maganar Mamma na ta aurar da Jummo a gidan ba, ta matsa kusa da Jummo tare da cewa. " Sannu da zuwa Jummo, kin min kyau." Dariya Jummo tayi haka kawai taji Zarah ta shiga ranta, tana dariyar tace " Nima kin min kyau, zaki koya min irin gayunki, ina son nima nake irin wannan kwalliyar taki.?" Dariya Zarah tayi tace. " Ai daga yau kin dawo ƙawata, zan koya miki, bari ma kiga naje na kawo muku abinci idan kunci sai na rakaki kiyi wanka na miki kwalliyar." Dariya Jummo tasa tace. " To meye sunanki?" " Sunana Zarah amma ki kirani da AUNTY, tashi muje kitchen ɗin ki tayani kawo abincin." Da to Jummo ta amsa tare da tashi suka shiga kitchen ɗin tare, murmushi Mamma tayi tare da jin Zarah ta ƙara kwanciya a ranta, cikin minti goma Zarah da Jummo suka fito da abinci tare da kazar da Mamma ke so, sosai suka gyara zama suka kwashi abincin, sai Jummo bata wani ci sosai ba, kasancewar ta wanda bata da yawan cin abinci bare kwaɗayi, bayan sun gama ne Zarah ta kama hanun Jummo suka haura bedroom ɗin da Sadiya ke sauƙa idan tazo, fallen zani Zarah ta bawa Jummo tace ta cire kayanta ta ɗaura babu musu kuwa Jummo ta cire tolet suka shiga, gashin kan Jummo dake naɗe timili guda, Zarah ta sunce take gashin ya zubo bayan, gashi ne mai tsayin gaske baƙiƙƙirin sai datti dake danƙare a cikin sa, shanfo ta ɗauka ta fara wankewa Jummo gashin sosai ta wanke gashin ya fita tas, sannan ta matsa mata makilin a sabon brush ta bata tace ta wanke bakin, tana tsaye take gwada mata yanda zata wanke, tsabar yalon da hakwaran Jummo sukayi sai da yayi jini wajen wankewa, alhamdulillah kuma haƙorin ya fara fita ba laifi, sannan ne fa Zarah ta fita tabar Jummo tayi wanka, bedroom ɗin ta ta koma da niyyar ɗaukowa Jummo kaya a cikin nata ta saka, a zaune ta samu khalil ya haɗa tagumi yayi shiru, kusa dashi ta zauna cike da nutsuwa tace. " Ya khalil, meya sameka haka kayi tagumi cike da tunanin, madadin wannan tagumin ai gara ka dinga ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Sai Allah ya sanyaya maka zuciyarka, ya yaye maka damuwarka, tunda kaga dai ba kyau tagumi waima tukunna meya faru haka wannan tagumi Bana son ganinka cikin tunani mijina Please tell me."? ( Haka ake son mace ta kasance mai yawan nuna damuwarta ga mijinta idan ta ganshi cikin wani hali, tambayesa damuwarsa cikin hikima da iya zance, ina tabbatar miki, zai sanar dake matsalarsa.) Numfashi Khalil ya sauƙe tare da kwantar da kansa a kafaɗar Zarah. " My dear!! Tarin matsala zasu ƙaru a cikin gidan nan sakamakon zuwan Mamma ina gudun faruwar abubuwa da yawa nan gaba, bata ƙaunar Momy na tabbatar zaman Mamma cikin gidan nan matsalace ga Momy ko nace tashin hankalin ta, Mamma fitinanniyar tsohuwa ce wacce sam bata da fahimta, bansan taya zan fara fitar da Mamma daga cikin gidan nan ba, ta koma ƙauye, gashi tazo da wata tantiriyar yarinya marar kunya, kinsan yarinyar nan har marina tayi, amma na mata uzuri da alamu akwai jahilci a jikinta, domin baƙauyen mutum zai iya aikata ko wani irin aikin rashin hankali, shiyasa idan kika cewa balaraben mutum ɗan ƙauye, to kin gama masa zagin duniya tana buƙatar mai bata tarbiyya yarinyar." " Hmmm!!! Ya khalil wace irin matsala kuma a tunanina babu wata matsala da Mamma tazo gidan ɗanta, ita dai Momy dole itace zatayi haƙuri da Mamma, Maganar ka maida Mamma ƙauye bai taso ba, Daddy ma ba yadda zaiyi ba, Ya khalil ka ɗauki komai da sauƙi sai yazo maka da sauƙi, yayin da kuma ka ɗauki abu da zafi, to da zafin zai tafi maka, ko yaushe kaine kake bani baki kana nuna min nayi haƙuri da Momy, to meyasa ita Momyn bazaka nuna mata tayi haƙuri da Mamma ba, haba ya khalil karka zamo mutum mai son kai mana, kaso mahaifiyarka fiye da mahaifiyar wani, wannan sam ba adalci bane, kayi tunani akan haka, ya khalil Maganar marin da Jummo ta maka kuma, dan Allah kayi hkr, bazance yarinta ke damunta ba, amma zance maka jahilci ke damunta kamar yadda ka faɗa, to ya khalil meyasa bazaka taimaka mata ba, wajen ganin ka inganta rayuwar ta, domin da alamu Jummo tana da basira idan Allah ya taimaka sai ta amfani al'umma da yawa, ka tallafa mata nima kuma ina da niyyar bata gudumowa." " My dear, na sani nan gidan ɗan Mamma ne, ban miki musu akan haka ba, amma nina san abinda ke baki sani ba, wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba, ba zuwan Allah da Annabi Mamma tayi ba, tazo ne kawai domin ta tadawa da Momy hankali akan wata hujjar ta marar ma'ana wanda dalilin rashin jituwar Momy da Mamma yasa bana shiri da Mamma, ko shaƙuwa ta tsakanin kaka da jika babu tsakanina da Mamma saboda bana taɓa bari Mamma ta ciwa Momy mutunci muddun ina kusa, bazan juri ganin Momy cikin tashin hankali ba, dole ne Mamma ta koma ƙauye, da kike Maganar na taimakawa wannan yarinyar, ta wacce hanyar kike tunanin zan taimaka mata, ni da nake neman yadda zanyi su koma inda suka fito." Numfashi mai nauyi Zarah ta sauƙe tare da ɗaura hanunta a cinyar khalil tace. " Kayi hkr insha Allah babu wata matsala da zata faru a cikin gidan nan, idan ma kuma akwai ta, to na ɗauki alƙawarin dakatar da ita, ina tabbatar maka babu abinda zai faru, idan kuma har abinda kake gudu ya faru, to ka ɗaura laifin komai a kaina, zan dakatar da gabar dake tsakanin Momy da Mamma, na sanya soyayya da shaƙuwa tsakanin su, na ɗauki wannan alƙawarin, Maganar Jummo kuwa, ma yita wata rana, amma dai yanzu kamin alfarma ka yafewa Jummo marin da ta maka, sannan kuma ka saki ranki naga farin ciki da annashuwa a gareka, domin farin cikin ka ya fimin komai daɗi a duniya." Ta ƙarisa Maganar tana murmushi tare da ɗan jawo gemun khalil alamun rarrashi, murmushi Khalil yayi tare da kwanciya yana jawo Zarah ta faɗo jikinsa rungumota yayi yana dariya tare da cewa. " Tabbas samun mace ta gari irinki a wannan zamanin yana matuƙar wahala, a duk sanda na shiga damuwa kinsan yanda zaki sanya ni farin ciki, ke ta dabance a cikin mata." Itama Zarah dariya tayi tare da haɗe bakin ta da nasa, a hankali ta lalumo harshen sa wani irin tsotsa take masa mai fitar da tunani, lumshe idanunsa khalil yayi yana jin wani munguwar feeling yana tsarga masa daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, a hankali ya saka hanunsa ya tallafo kanta tare da aika mata nasa salon, tuni Zarah ta manta da Jummo na jiranta, ta Lula duniyar ma'aurata. Jummo tafi awa ɗaya tana jiran Aunty Zarah shuru babu alamunta, tun tana zaune a ƙasan tayels ɗin sanyin ac na kaɗata, har bacci ya fara kwasarta tun tana gyangyaɗi harta silale ta kwanta, bacci ne mai nauyi ya dauketa sakamakon ac dake kaɗata dama kuwa Jummo gwanar son sanyi ne. Mamma kuwa tana hakince cikin falon zaune tace bazata bar wajen ba har sai Daddy ya dawo ta kurawa tv idanu, tana kallon wasan kwaikwayo na Arewa24 Daɗin kowa, sai dariya take ita ɗaya tana Magana. Garko dake zaune bakin bed ɗinsa yana buga game a wayarsa ne yaji wayar tayi ringin " *SADIYA* " haka ya gani rubuce, numfashi yaja yana yamutsa fuska ya ɗaga kiran tare da yin shuru daga can Sadiya ta fara magana cike da muryar kuka. " Ya Garkuwa, wai kana nufin kace baka ga text ɗina bane, kayi shuru baka kiran ba, baka kuma min refly ba, ya kamata kazo mu san mafita." " Idan naga text ɗin ki To ya kike so na miki, so kike naje na rufeta da duka ne, taya kike tunanin zansan dalilin da yasa take son raba tsakanin mu, kinga Sadiya nifa wannan ba damuwa ta bace, dan haka ya rage tsakanin ki da ƴar uwarki." " Ya Garkuwa!!! Ba damuwar ka ba kace, ƙoƙarin raba mu fa ake amma kake kiran bai dameka ba, ko ka manta da soyayyar dake tsakanin mune, ko kuma dama yaudarata kake jikina kawai kake so, me kake nufi..................?" *Ki biya Nairar ki 100 kacal ƴar uwa, sannan ki cigaba da karanta wannan labarin cike da nutsuwa, biya ta wannan hanyar* *0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan ku turo shaidar biya, karku manta Naira 100 ne kacal Araha tafi bashi🥰* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *FREE PAGE* ➰➰ *19 to 20* " Khalil har kana da zarrar ɗaurawa mahaifiyata bindiga a cikin gida na, Oh kai gaka jami'in soja bari ka taka kowa to kayi ƙarya wallahi zan iya rabuwa da kai akan Mamma, baka isa ka ci mata mutunci ba, muddun kana neman albarkata a rayuwarka dole kabi Mamma, wai ma na tambayeka wannan gidan naka ne ko nawa."? Khalil kansa na ƙasa cike da ɓacin rai, dama ya sani zuwan Mamma cikin gidan nan babu alkairi tazo ne kawai ta tarwatsa musu farin cikin gida, girgizawa Daddy kai yayi alamun a'a. " Okay shine kuma bari ka takurawa Uwata, to ta fika iko da gidan nan kai ko nima ta fini iko da wannan gidan bare kuma kai, wallahi khalil ka shiga hankalinka idan ba haka ba, zaka barmin gidana, kaje ka sunkuya ka bata haƙuri shasha, shima mai gadin zai haɗu dani ne, wannan ai rashin hankali ne, Kai Garko haura ka kira min uwarku naji idan tane ta ɗaure muku gindi ku ci mutuncin mahaifiyata." Shi dai Garkuwa bai ce komai ba kasancewar sa mutum da bai shiga cikin hayaniya, aiken Daddy ya haura, shi kuwa khalil tamkar zai danna ihu tsabar takaici da haushin Mamma, bai cewa Daddy komai ba yaje gabanta ya tsugunna tare da cewa. " Kiyi haƙuri Mamma Allah ya huci zuciyarki." Taɓe baki Mamma tayi tare da kaiwa khalil ranƙwashi a kai tace. " A yanzu dai na haƙura amma wallahi a kiyaye gaba a daina shiga gona ta idan ba haka ba, wallahi na fika iskanci, kai ga ɗan iska har wani zare min idanu kake kana nuna min bindiga, to wallahi duk wanda yaci tuwo dani miya yasha." Cije bakinsa khalil yayi cike da jin haushin ta, ya miƙe tsaye ya bar gidan gaba ɗaya, Momy tare suka sauƙo da khalil ya nemi waje gefe ya zauna yana cigaba da danna wayarsa, Momy gefe da Daddy ta zauna tace. " Sannu da dawowa Alhaji." " Bana buƙatar sannun ki ki riƙe kayanki, yanzu ke Zainab kece zaki wulaƙanta min mahaifiyata, ki watsar da ita a falo ki shige kiyi tafiyar ki, saboda baki san daraja da girman uwa ba, idan ke baki tashi a gaban mahaifiyarki ba, shiyasa baki san girman ta ba, to ni na tashi a gaban tawa kuma nasan daraja da kimarta, muddun za ki cigaba da nuna rashin kulawa akan Mamma zamu samu babbar matsala dake, ba fuska zaki haɗa ba ko mutuwa zakiyi Mamma ta dawo cikin gidan nan kenan da zama idan hakan bai miki ba, kina iya tafiya, amma dai ki sani bazan yadda da cin mutuncin mahaifiyata ba." Momy shuru tayi tana sauraron Daddy, harya gama cikin sanyin murya tace. " Cin mutunci kuma Alhaji ta yaya zanci mutuncin Mamma, nima fa.........." Dakatar da Momy Daddy yayi ta hanyar ɗaga mata hanu yace. " Excuse me Malama, ƙarya Mamman zata miki, baki da bakin kare kanki a wajena, ki tashi ki tafi ki bamu waje." Bata kuma cewa komai ba Momy ta miƙe tare da furta. " Allah ya baku haƙuri." Tayi Maganar tana barin wajen, Daddy Sosai ya dinga bawa Mamma haƙuri har ya samu ta sauƙo da kansa ya nuna mata bedroom ɗin da zata zauna, a ƙasan, sannan ya haura nasa bedroom ɗin domin ya watsa ruwa, A'illo ma haurawa tayi bedroom dinsu ita da Zarah ya rage daga Jummo sai Garkuwa a falon da hankalinsa ke kan wayarsa, Jummo tashi tayi daga inda take zaune ta dawo kusa da Garko ta zauna, muryar ta yaji ta daki kunnen sa. " Ya Garkuwa na, shine bazaka ce nayi kyau ba, kai fa na yiwa kwalliyar nan." Shuru ya mata tamkar bai jita ba, ƙara ce masa tayi. " Ya Garkuwa ka kalleni fa wallahi nayi kyau." Cike da tsawa Garkuwa ya ɗago kansa yana daka mata tsawa cikin sauti mai amo sanda Jummo ta razana. " Ke dalla!!! Mahaukaciya jaka!!! Ni ina ruwana da kwalliyar ki, kin bi kin cika min kunne da zancen banza zancen hauka ke a hakan gani kike kinyi kyau, da kinsan yanda wannan kwalliyar ta mayar dake kamar jaka da baki zo kince min kinyi kyau ba, dubeki dalla wata mummuna dake ko tsari baki dashi tashi a gabana kona hanɓareki!!!" Jikin Jummo sanyi yayi tayi shuru tana duban jikinta wai batayi kyau ba, wai kuma jaka, hawaye ne ya zubo mata, ta tashi da gudu ta haura sama tana kuka, runtse idanunsa Garkuwa yayi harga Allah idan yace batayi kyau ba, ya faɗa ne kawai saboda son ranshi, domin kuwa sosai ta masa kyau, sanin rashin mutuncin Jummo da rainin ta yasa yace mata batayi kyau ba, domin shi mutum ne wanda baya son raini, haka kawai yaji zuciyarsa bataji daɗin abunda ya mata ba, ji yayi zaman falon ma ya isheshi tashi yayi ya fice compaunt ɗin gidan. Bedroom ɗin Aunty Zarah ta faɗa tana kuka, Aunty Zarah zaro idanunta tayi tare da cewa. " Subahanallah Jummo lafiya." Cikin kuka tace. "Aunty wai banyi kyau ba, wai kamar jaka na koma, wai mummuna ce ni?" Murmushi Aunty Zarah tayi tana girgiza kanta tace. " Ikon Allah waye yace miki haka.?" " Aunty Ya Garkuwa ne.?" " Garkuwa kuma!! Hmmm ya faɗa miki son ranshi ne kawai amma shima yasan kinyi kyau, wama ya isa ya kiraki mummuna, ai a cikin kyawawan ma ke ta daban ce, rabu dashi zolayarki yake dan kawai ya saki kuka." Sai yanzu Jummo tayi dariya tace. " Allah Aunty zolayata yake, da har naji haushi." " Ki daina jin haushi haka shi yake ya fiye tsokana." Dariya kawai Jummo tayi tace. " Aunty bari na tayaki aikin." Tare suka ci-gaba da gyaran bedroom ɗin da Jummo, kafin suka koma kitchen. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Bayan sati biyu* Sosai zaman gidan yake yiwa Jummo daɗi domin kuwa Aunty Zarah ta zamo mata tamkar ƙawa komai tana mata, haka komai tare suke yi, har ya zamanto Jummo ta fara iya girki da kanta, wannan yalon hakwaran nata duk ya goge, kwalliya kuwa sosai take yinsa Aunty Zarah da kanta ta saya mata sutura, yayin da zaman su da A'illo suke zaman doya da manja babu mai shiga sabgar wani, Mamma ma Sosai take jin daɗin zaman gidan Aunty Zarah na kula da ita yanda ya dace tamkar ƴar da ta haifa a cikin ta, Momy kuwa tana takure da zaman Mamma domin kuwa bata isa tayi koda motsi bane sai Mamma ta saka mata ido kullum cikin mita take yiwa Momy, hakanne yasa ta fara neman hanyar da zata kori Mamma daga cikin gidan cikin sauƙi ta tafi da kanta ba tare da Daddy ya zargeta ba, ta kira ƙawarta Asabe suka shawara, yayin da suka shirya zuwa wajen boka domin ya kora musu Mamma daga cikin gidan koda Momy zata samu sauƙi a cikin gidan, Zarah sosai taji daɗin zuwan su Mamma domin kuwa a cikin kashi ɗari na wahalar da Momy take bata babu kashi hamsin duk Mamma ta tare mata shi, shi kuwa khalil baima shiga sabgar Mamma iyakarsa da ita ya gaishe ta, da safe sai kuma idan yaga dama ya zauna da ita suyi hira sa'i da lokaci amma duk abinda zatayi ido yake zuba mata, haka take shiga cikin bedroom ɗin ta tasha tabarta ta ƙoshi babu wanda ya isa ya hanata, ganin da khalil yayi Mamma na son Jummo Sosai kuma tana jin maganarta, hakan ya sashi ya ƙudiri niyyar jawo Jummo jikinsa yayi amfani da ita wajen haramtawa Mamma shan sigari. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ " Wallahi wallahi na rantse da Allah Zee wallahi billahil'azim nice ƙalubalen Garkuwa a Wannan Duniyar wallahi muddun ina numfashi bazan taɓa barin wata mace ta kusance sa ba, sai yayi danasanin ɓatamin rayuwata, yau na dawo daga Egypt kuma a yau zan fara bibiyar rayuwarsa, da wannan yaron daya batawa suna yasa muka samesa ta hanyar banza, dashi zanyi amfani wajen ganin ƙarshen Garkuwa Zee koda komai na zai ƙare nayi yawo tsirara na rasa farcen susa muddun zanga bayan Garkuwa wallahi sai nabi Wannan Hanyar, a yanzu gani yake farmaƙin daya saka aka kawo mana duka mun mutu nida iyayena, na tsani Garkuwa duk sanda na tuno shine yayi sanadiyar mutuwar iyayena sai naji tamkar naje na kashe nasa ahalin Bayan ya rabani da mutunci na ya min ciki hakan bai isheshi ba sanda ya kawo ƙarshen iyayena Abbana Ummina Brother Saleem Aunty ummu lil Saleem duk ya saka an kashe su, da badan mahaifinki ba, da nima yanzu babu labarina, ni da abinda yake cikina wannan gidan yaron ne baya son na Haifa, kuma gashi yazo duniya dashi zan tozarta GARKUWA." Numfashi Zee taja tana kallon *SAFREENA* da ke rungume da wani ƙaramin Yaro yana bacci hankalinsa kwance, tausayinta ya kama Zee TABBAS SAFREENA taga ƙalubalen Rayuwa, Soyayya ta zamo mata mungun dafi ta ajiye mata munguwar tarihi, da ana tariyo Rayuwar baya da yanzu SAFREENA cikakkiyar mai gata da iko ne lallai ne Maganar Hausawa *mutum mungun icce ne* 🤔🤔 Wacece SAFREENA menene alaƙar ta da Garkuwa waye mahaifinta duk zaku samu wannan cikakkiyar amsar sanƙame cikin wannan littafin mai matuƙar sarƙaƙiya da cakwakiyar soyayyah ku dai ku biyoni ta hanyar. *Ki biya kuɗin ki Naira 100 ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko hoton Mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sai kiyi screen short ki turo shaidar biya* *ki biya tun yanzu kafin LITTAFIN ya koma 300 domin kuwa ya kusa komawa* *Kuyi haƙuri yau na muku typing kaɗan hakan ya faru ne sakamakon uzuri da yayi min yawa sorry* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *AFWAN AFWAN!!! AFWAN FAN'S JIYA BAN SAMU DAMAR TYPING BA GASHI KUMA BAN BAKU UZURI NA BA, INA NEMAN AFUWAR KU MUSSAMAN ƳAN PAID GROUP AMMA TABBAS UZURI NE MAI ƘARFI YA RIƘENI A JIYA* *FREE PAGE* ➰➰ *21 to 22* Nisawa Zee tayi tana gyara zamanta tare da saka hanu ta ɗauki Abdul ta dawo dashi jikinta, duban SAFREENA tayi ta fara magana cike da nutsuwa. " SAFREENA karki sake wani kuskuren na biyu, domin zai iya jawo miki tashin hankali da yafi na baya, sanin kanki ne ba imani bane da Garkuwa zai iya aikata komai akanki domin ganin ya kawo ƙarshen ki a wannan duniyar saboda ya fahimci baki da wani burin da ya wuce ki tozarta shi, ki daina kafa hujja da Abdul zai iya kasheki ya ɗauki wannan yaron ya fitar dashi daga Nigeria ya kaisa can wata ƙasar yayi Rayuwa ba tare da kowa yasan jinin sa bane, gudun kar asirinsa ya toni a gane shi fasiƙi ne, ubansa sanannan ɗan kasuwa ne kin sani babu wanda bai san Alhaji Buba Garko ba, kinga kuwa dole ya nemi duk hanyar da zai tseratar da mutuncin ubansa, kasheki a wajen Garkuwa ba komai bane, SAFREENA ina tausayinki yasa nake faɗa miki iya gaskiya ta, kina da tarin a hali sai dai ba su da amfani a gareki SABODA basu ƙaunar mahaifinki bare kuma ke, Daddy shi kaɗai ne gatanki a duniya kuma yanzu babu shi, ki riƙe maraicinki SAFREENA karki sake shiga safgar Garkuwa, a baya soyayya ta jefaki cikin mungun yanayi harta yi sanadiyar rasa farin cikin ki, a yanzu kuma na hango ƙiyayya tana shirin ƙara jefaki cikin masifa, dan Allah SAFREENA karki sake hasashena ya zamo gaskiya, ki barsa da Allah ki rungumi ɗanki ki basa tarbiyyar da ta dace, ki manta da Garkuwa a rayuwarki karki sake koda wasa yaga Abdul domin zai rabaki dashi." Hawayene suka zubo daga ƙwayar idanun SAFREENA cikin sanyin jiki da rawar murya tace. " Na sani Zee bani da gata yanzu na rasa gata na ta sanadiyyar Garkuwa Da son zuciyata, dalilin da yasa nake jin bazan taɓa samun sukuni ba, idan banga Garkuwa a ƙasƙance a wulaƙance ba, na rantse miki da Allah bazan bar Garkuwa yaji daɗi a rayuwarsa ba, sai na toshe duk wata hanyar da farin ciki zaizo masa, sai na ɗanɗana masa baƙin ciki fiye da wanda ya sani a cikin sa, dan haka ki adana kalamanki domin bazasu shiga kunnuwa na ba, saboda suna toshe babu abinda yake yawo a cikin su sai sautin ƙara da ihun iyayena, ina jin sautin su acikin kunnuwa na, suna ihu wuta na cinsu, Abba da ummi sun mutu ne da sunana a bakin su, sai ni kuma na kasa ɗaukar fansar su, muddun ban ɗauka musu fansa ba, rayuwata bazata taɓa samun nutsuwa ba, Zee na San a baya soyayya ce ta jefani mungun halin da nake ciki yanzu dalilin da yasa naji na tsani soyayya da duk wani mai yinta, na tsani maza bana son ganin su, wallahi Zee da wannan hanun nawa zan kashe Garkuwa nayi wannan alƙawarin kuma sai na cikasa koda nima zan mutu, menene a rayuwata ban yiwa GARKUWA ba, numfashi nane kawai ban basa ba, amma ki duba kiga a ƙarshe abinda ya saka min dashi, ko wannan yaron idan na kallesa na tuno jinin Garkuwa ne sai naji na tsanesa, ji nake tamkar na shaƙesa masa wuya ya mutu, bazan ɓoye miki ba Zee bana son ganin fuskar Abdul saboda babu inda yabar Garkuwa, Baba ne yafi ƙarfina wallahi da bazan shayar da shi ba." " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Me kike faɗa ne haka SAFREENA shin ƙiyayyar Garkuwa tasa kin haukace ne, sai abubuwa kike ta famar yi irin na mahaukatan da aka saka a turu, shi wannan yaron meye laifin sa, sanda zakuyi zina ku samu cikin sa ya sani ne, shima baiƙi ya fito ta hanyar halak ba, SAFREENA karki haɗawa kanki zunubi biyu akan Abdul, ga zunubin kawosa duniya ta hanyar zina ga kuma zunubin azabtar dashi, baisan komai ba tsakanin ku, dan Allah karki hukuntasa da laifin da ba nasa ba, tunda kince bazaki haƙura kibar Garkuwa ba, shikenan amma shi dai Abdul dan Allah karki cutar dashi ki jashi a jikinki a yanzu bashi da wani gata idan ba ke ba." " Ni ba gatansa bane ki daina kirana a matsayin gatansa, Abdul bashi da laifi kike cewa, karki manta da cewa ƙaddarar haihuwar sa ta hanyar da bata dace ba, shiya jawo min duk wani tashin hankali da nake ciki,. Sannan kice bashi da laifi, HMMM!!!! Idan kika ambato min kalmar zina sai inji tamkar zagina kike, kinsani ni na mazinaciya bace ƙaddara ce ta faɗa min da duhun Soyayya, kin sani rashin kuɗi yake sa ayi zina, ni kuma ban rasa komai ba a rayuwata sanin kanki ubana ya ninka uban Garkuwa goma a kuɗi ki dinga saka lamarina cikin kaddara." Tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice tana kuka, hawayen daya ɗan taru a idanun Zee ta goge tana goya Abdul a bayanta ta hau jijjiga sa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ " Asabe yanzu kina nufin goben dole sai da sassafe zamu tafi kin sani fa Alhaji bazai barni nayi fitan sammako ba." " Haba dai Hajiya Zainab, ya kamata ki nemo duk wata hanyar da zai barki ki fice domin kuwa uban layi ake samu wajen bokan nan, idan ba sammako mukayi ba, ƙarshen ta musha wahalar banza ne bamu samu ganinsa ba, kiyi ƙoƙari kisan ƙaryar da zaki masa mu tafi 5:30am." Shuru Momy tayi kafin tace. " Shikenan zan gwada Allah yasa ya barni, wallahi haushin tsohuwar nan nake ji, ta tsaneni tun ina budurwa har kawo yanzu girma ya fara kamani amma bata barni na huta ba, ni a wannan karon so nake a raba tsakanin su da Alhaji Buba kowa yaji ya tsani ɗan uwansa, uwar ta tsani ɗan shima ɗan ya tsani Uwar, su rabu kawai na huta." " Wannan fa ƙaramin aiki ne a wajen wannan bokan dan haka karki damu duk abinda kike so zai iya miki muddun zaki sake masa kuɗi." " Kinsan kuɗi ni ba matsala ta bace, muddun za'a rabani da Mamma wallahi zan kashe ko nawa ne." " Shikenan ni bari na koma duk yanda kikayi naji kota waya ce." Da to Momy ta amsa tare da tashi ta rako Asabe har compaunt ɗin gidan sannan ta dawo, cike da masifa take kwalawa Zarah kira, Zarah dake zaune ita da Jummo a bedroom ɗin Mamma ne ta jiyo muryar Momy na kiranta wani irin tsinkewa zuciyarta tayi, da sauri ta miƙe tana amsa kiran ta fito da sauri, da kallo Jummo tabi Zarah yanda taga ta gigice, Mamma kuwa dama baccin ta take sha, a falo ta sami Momyn tsaye, ta risina tace. " Gani Momy." " Uban kikeyi a cikin bedroom ɗin Mamma, uban waye zai miki ayyukan cikin gidan nan, naga alamar yanzu kin fara koyon munafurci ko, kega annamimiya uwar iya kissa, Saboda a soki ko, tunda mutanen nan suka dawo cikin gidan nan naga kin nane musu sai shiga jikin su kike, to bari kiji bazan kamu ci munafurci ba, daga yau babu ke babu sake zama a ɗakin Mamma iyakarki da ita ki shiga ki gaisheta ki fito, munafukar Banza, ki shige gacan wanki na sun taru kije ki wanke min, sannan yau tuwo zakiyi mana miyar ganye a cikin gidan nan shasha." Sunkuyar da kanta ƙasa Zarah tayi duk masifar da Momy take babu wanda Zarah ta mayar mata harta bar wajen, numfashi Zarah ta sauƙe tare da nufar bayan momyn ta ɗauko wankin nata zuwa yanzu wahalar da take sha a gidan na aiki yabi jikinta sai dai cin mutunci da zagin da Momy ke mata shi kaɗai ne yake ci mata zuciyarta, a bayan gidan tayi wankin tas ta shanya su, bisa mamakin kafin ta gama wankin ta fito ta samu, Jummo ta gyara mata falon tas har wanke wanke sai da ta mata, dubanta ta kai da gas dake kunne, wajen ta nufa tare da dafa kafaɗar Jummo, targen semonvita ta samu jummo nayi, numfashi ta sauƙe tare da cewa. " Jummo duk ke kikayi wannan aikin wa yace miki tuwo zanyi yau." Murmushi Jummo tayi tana zuba semon ɗin cikin tukunyar tace. " Aunty ina jin duk masifar da Momy take miki, hmmm!!! Aunty Momy bata da kirki wallahi dani take yiwa zagin da ta miki Allah saina rama, naga alamun Momy ta tsaneki, Aunty me kika mata kin taɓa mata wani laifi ne." Numfashi zarah ta sauƙe tare da cewa. " Jummo ban mata laifin komai ba, aikine na makara, kuma kinga dole tamin faɗa a matsayin ta na uwata, kinga mubar zancen nan, tunda kin kusa gama tuwon ni bari na tsinke ganyen." Shuru Jummo tayi bata kuma cewa komai ba, har suka gama aikin Jummo ganin ta gama nata yasa ta fito falo Garkuwa ta gani zaune ya maida hankalin sa ga tv yana kallon BBC news, zama a kujera Jummo tayi tare da cewa. " Ya Garkuwa, kai kullum kana gida, baka zuwa aikine sai zaman banza." Zaro idonsa Garkuwa yayi yana juyo da kansa ya kalleta wani irin bugawa zuciyarsa tayi, take yawunsa ya tsinke, ganin Jummo cikin ƙananan kaya riga da wando wanda ta ɗan kama mata jiki, ga dukiyar fulaninta sun cika rigar tam, shi kansa wandon ya ɗan kamata, gashi tayi fresh tayi kyau, ( wai dama haka take da kyau, hmmm!!! Lallai wannan akwai kayan daɗi a jikinta, Allah ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yayi ɓarna) leɓensa ya cije tare da fasa yin masifar da yayi niyyar mata kau da kansa yayi tamkar baiji ta ba, Aunty Zarah dake tsaye bakin kitchen tana jin maganar da Jummo ta faɗawa Garkuwa ya sata yin dariya tace. " Waya faɗa miki Garkuwa baya aiki, yana aiki a babban Companyn *A,A ASAD INTERNATIONAL AIRPORT* matuƙin jirgin sama ne, hutu ya ɗauka shiyasa kike ganinsa kullum a gida." Taɓe bakinta Jummo tayi tare da miƙewa tsaye tace. " Ummm!!!! Aunty wai fa sonsa Nak..................." " Assalamualaikum." Sallamar Sadiya cikin gidan shiya hana Jummo ƙarisa Maganar da tayi niyya, da kallon waye wannan Jummo tabi Sadiya, Sadiya ranta a matuƙar haɗe tana jefawa Garkuwa wani irin kallo mai wuyar fassarawa Garkuwa ɗago kansa yayi ya zubawa Sadiya ido tare da kau da kansa gefe, sai kuma ya saki murmushin gefen baki, wanda shi kaɗai yasan me yake nufi miƙewa yayi ya shige bedroom ɗin Mamma, numfashi ta sauke Sadiya tare da ƙarisowa ta zauna tana kallon Aunty Zarah. " Sadiya lafiyar ki kuwa kika shigo ranki a haɗe, meya sameki."? " Umhmmm!!! Ba komai Aunty yanayin nature ne, amm Aunty ina ya khalil ashe ya dawo.?" " Eh ya dawo ya fita, sai anjuma zai dawo, zamu kwana ne ko zaki koma gida yau." Kanta ta ɗaga ta kalli Jummo tare da cewa. " Na dawo bani da Ranar tafiya akwati na yana wajen mai gadi yanzu zai shigo min dashi, wacece wannan Aunty."? " Jummo ƴar uwar su................" Dakatar da Aunty Zarah tayi ta furta. " Jummo Jummo Jummo!!! (A zuciyarta tace Oh ko dai itace wacce Garkuwa yake bani labarin ta wacce take sonsa a ƙauyensu, to amma ya akayi har ta waye haka, bura'uba heee lallai banga ta zama ba, domin kuwa wannan nayi wasa wallahi sai ƙwace Garko daga hanuna.) Numfashi ta sauƙe tace. *Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira 100 kacal zaki biya kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko hoton mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan ku turo shaidar biya.* *Ku HANZARTA ku biya Free page yazo ƙarshe Naira ɗari ce ba yawa da zarar Free page ya kare BOOK ɗin ya tashi daga Naira 100 ya koma 300 ku HANZARTA maza kar wannan damar ta shige ku.* *Sorry for typing error banyi editing ba.* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🏺 *GELLE ƁINGEL* 🧺 *(Garinsu yarinyar)* *Na marubuciyar* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Akan ƴar Uwata Indo A Birni So Bai San Jini Ba Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu Doctor Hassan Ƙauyemu And Now *GELLE ƁINGEL* Sadaukarwa ga ƙawata Zarah Abdul Momyn Ahlan. *Dan Allah ina roƙon namiji karya shiga group ɗin nan dan Allah* *Wannan littafin na kuɗine idan kin san ba saya zakiyi ba kema dan Allah karki shiga, haka idan kinsan baza kiyi comments ba nan ma karki shiga Naira 100 ne kaɗai kuɗin littafin ban tsawalla ba in dai kina da niyyar saya, iya Free page kawai zaki samu a cikin gidan nan* https://chat.whatsapp.com/LTWeFGmoKqTDbMbsU37088 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *FREE PAGE* ➰➰ *17 to 18* " Dakata dan Allah Sadiya!!! Wannan maganar taki ta fara toshe min kunne ta fara wuce gona da iri, dama akwai alkawarin Aure tsakanina dake ne yanzu koko nace miki zanyi Aure nan kusa, da zaki sawa zuciyarki nutsuwa ki kwantar da hankalinki idan Aure kike buƙata ki nemi wanda yake da niyyar yi kiyi Auren ki zai fiki alkairi, domin kuwa babu Aure a gabana ke ni aure nan da shekara biyar ma albarka, amma idan har na taɓa miki alƙawarin Aure sai ki tuna min, dan haka kiyi hkr kawai Sadiya Allah ya haɗa kowa da rabonsa." Tamkar sauƙar aradu Sadiya taji Maganar tasa wani gumin azaba ne ya keto mata, take taji ɗakin na juya mata dafe kanta dake sara mata tayi, cikin nauyin baki tace. " Please Ya Garkuwa ka daina min irin wannan wasan bana so yana tsinka min zuciyata, dan Allah ka daina." " Wasa kuma Sadiya na taɓa irin wannan wasan dake, ba wasa nake miki ba Sadiya, wallahi babu Maganar soyayya yanzu tsakanina dake Saboda baki dace da ki zamo Uwar ƴaƴana ba Sadiya idan har namiji kike buƙata, ai naga ina ɗauke miki sha'awar ki idan kuɗi kike buƙata ina baki, meye a cikin Auren ina dai shine to wannene bana miki, idan har zaki iya mu'amala dani a haka babu zancen Aure ƙofata a buɗe take, Aure kam nida shi ba yanzu ba." Runtse idanunta Sadiya tayi hawaye ne mai zafin gaske ya siraro daga idanunta, tabbas namiji ba ɗan goyo da zani ba ne, ta bawa Garkuwa rayuwarta harda mutuncin ta, amma yaci amanar ta koda a cikin mafarki bata taɓa tunanin garkuwa zai juya mata baya ba, ashe burinsa kenan akanta ya ta lalata da ita ƙarshe ya gujeta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Tabbas soyayyar Ya Garkuwa ta zamo min masifa" hawayen ta goge tare da cewa. " Dan Allah ya Garkuwa ka rufa min asiri karka juyawa soyayyata baya, kai kaɗai zuciyata take so, bata da wani farin ciki idan ba naka ba ya Garkuwa, wallahi ina sonka, rasa ka gareni tamkar barazana ce ga rayuwata, karka yaudareni ya Garkuwa dan Allah ka Aure ni Wallahi kai kaɗai nake so meye aibuna da bazaka soni ba?." Shuru Garkuwa yayi yana sauraron ta, sanda ta gama maganar ta cikin sannan Garkuwa ya sauƙe numfashi tare da cewa. " Duk wani Maganar da zan miki ki fahimta, Sadiya nayi amma naga alamar kina da taurin kan tsiya, bazaki fahimta ba, dan haka ina mai gargaɗinki Sadiya karki kuma kiran wayata, idan kuma zaki kira wayata to ki tabbatar cewa kin amince ne mu cigaba da alaƙar mu kamar da, amma karki kuma min Maganar Aure this is the last warning." Yana ƙarisa Maganar ya kashe wayar gabaki ɗaya, yana jan tsuka tare da jin haushin Zarah me take nufi da ƙoƙarin rabasa da Sadiya yasan bata san alaƙar saduwa dake tsakanin sa da Sadiya ba, to meye dalilin ta, na cewa Sadiya ta rabu dashi, harga Allah shi da zuciya ɗaya yake zaune da ita, sai gashi tana cin dunduniyar sa, tsuka yaja tare da ɗaga kafaɗarsa yana Kwanciya ya furta. " Wannan damuwarki ne, dama can ni ba Auren ƴar uwarki zanyi ba, asali ma itace ta liƙemin tamkar cungam domin kuwa babu ta yadda zan yarda na auri mazinaciya,. Uwa ta gari ya dace na samawa yarana ba mace Irin Sadiya ba." Numfashi ya sauƙe tare da lumshe idanunsa yana kallon slim. Ita kuwa Aunty Zarah tuni ta manta da Jummo dake jiranta ta Lula rayuwar Auren ta, bacci ne mai nauyin gaske ya ɗauketa a ƙirjin Khalil, itace bata farka ba sai da taji ana kiran sallar magaruba a hankali ta buɗe idanunta akan fuskar khalil dake baccin sa hankali kwance. " Bismillahil lazi ahayana ba'ada ma amatana wa ilaihinnushur!!! Subahanallah subahanallah subahanallah!!!! Wala hamdulillah Wala hamdulillah Wala hamdulillah!!! Wala ilaha'illallah wallahu akbar." Wannan shine ya zamewa Aunty Zarah ɗabia a rayuwarta duk sanda ta farka daga bacci sai ta yi wannan addu'ar da ake so ko wanni musulmi ya jimance sa yayin tashi daga bacci, a hankali ta saka yatsanta a kunnen Khalil na sosa masa, domin ya farka, cike kuwa da nutsuwa ya buɗe idon yana kallon ta lumshe su yayi ya kuma sake buɗewa murmushi ya sakar mata tare da furta. " Oh My dear wani irin bacci haka mukayi ba tsarki a jikin mu, kamar sallah ma naji ana kira ko.?" " Sallah ake kira ya kamata ka tashi ka HANZARTA kayi wanka Kafin a shiga Masallaci." Miƙewa tayi daga jikin sa tana jawo bargon ta ƙara rufe jikinta hanunta ta saka ta jawo towel dake jikin gadon ta miƙawa Khalil karɓa yayi ya miƙe tare da ɗorawa a ƙugunsa ya shige tolet, ita kuwa Zarah jingina tayi jikin gadon tana lumshe idanunta, Jummo ce ta faɗo mata a rai, saurin ware idanunta tayi tare da furta. " Subahanallah!!! Oh My god, tana can sai zaman jirana take." Sauƙowa tayi daga bed ɗin tare da jawo zani ta ɗaura a ƙirjinta, ta buɗe wadrop ɗin ta ta ɗaukowa Jummo baƙar doguwar riga mai ratsin golden a jiki, hijab ta saka ta fita da sauri bedroom ta shiga, a yashe ta samu jummo a ƙasan tayels sai bacci take murmushi Aunty Zarah tayi tare da furta. " Allah Sarki ta gaji da jirana har bacci ya ɗauketa" sunkuyawa Aunty Zarah tayi a hankali ta dinga tashin Jummo harta buɗe idanunta. " Haba Jummo ganan gado me zai kwantar dake a ƙasan tayels wannan sanyin ai sai ya cutar dake, karki kuma Kwanciya a wajen baki ga A'illo tazo ta ajiye kayanta a gadon ba, nan shine ɗakin ku keda ita akwai ƙanwata da take zuwa ita ma a nan take sauƙa, Kiyi na barki kina ta jirana ko, Ya khalil ya sani aiki, yanzu kin san me za'ayi jekiyi alwala tunda kinji ana kiran sallah idan kinyi alwalar sai na miki kwalliyar sai kiyi sallar ki hankalinki kwance." Ta ƙarisa Maganar tana zama bakin bed ɗin, Jummo da to ta amsa tana shigewa tolet ɗin, alwala ta ɗauro sannan ta fito, Aunty Zarah ta tsara mata kwalliya sosai Jummo tayi kyau bana wasa ba, doguwar rigar ta zauna a jikinta kasancewar Jummo ba dai dukiyar fulani ba, dariya Zarah tayi tare da cewa. " Wow hajiya Jummo kinga kuwa yanda kikayi kyau anya kuwa bazan yiwa mijina kamu ba, kalli madubi kiga." Madubin Jummo ta kalla tana dariya tace. " Aradu nayi kyau Aunty, to Aunty zaki dinga min kwalliyar kullum." Dariya Aunty Zarah tayi tare jan kumatun Jummo tace. " Me zai hana, miki kai insha Allah ma tunda kina son kwalliya zan kaiki shagon makeup ki koya yanda zaki dinga yi da kanki ba sai na miki ba, yanzu dai je kiyi Sallah an shiga Masallaci, nima bari naje nayi sai na fito na shiga kitchen ko" Da to Jummo ta amsa tana dariya ta ɗauki darduma ta hau Sallah, ita kuma Aunty Zarah ta fice nata bedroom ɗin. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Can kuwa masallaci khalil tare sukayi Sallah da Daddy kasancewar ya dawo ana kiran sallah parking kawai yayi ya shiga Masallaci, bayan an idar da Sallah ne khalil ya yiwa Daddy sannu da dawowa, fuskar Daddy cike da murmushi ya amsa yana kallon Garko dake tsaye ya zuba hanu a aljihunsa, murmushi Daddy yayi yace. " Kai Garko ina sakon dana aikeka wajen Alhaji Isma'il?" " Daddy naje ban samesa ba, still na dawo kasuwa wajenka Sadiq yace min ka fita." " Okay mu ƙarisa cikin gidan." Tare suka shiga cikin gidan da Daddy, da sallama suka shiga falon, muryar Mamma itace ta fara amsawa Daddy, sallama, shi kuwa khalil idanunsa ne suka sauƙa akan Jummo da tayi bala'in kyau tamkar ba wannan ƴar ƙauyen da suka zo da Mamma ba, wani bugawa zuciyarsa tayi, yayi saurin dafe ƙirjinsa tare da runtse idanunsa, shikam Garko baima lura da Jummo sam hankalinsa baizo wajen ba, waya ma yake da abokinsa Hashim, daddy waro ido yayi cike da farin cikin ganin Mamma ya ƙariso gabanta ya zauna a ƙasa gefen kujerar da take zaune. " Mamma kece yau a gidan nan, sannu da zuwa, sannu da hanya, wa ya kawo ki Mamma." Fashewa Mamma tayi da kuka tare da kaikaicewa ta fara masifa tana kuka. " Buba ɗazu Tasiu ya kawoni nace ya dawo dani gidan ka na ƙarisa rayuwata anan nida jikokina, amma tsabar walaƙanci tun daga bakin ma shigar gidan ka ake wulaƙantani ana cemin wai ni mabaraciya ne nazo bara wajenka, Buba har bindiga suka samin zasu kasheni, dana tsallake wannan siraɗin wannan ɗan albarka Garko ya shigo dani, sai na kuma samun wata masifar a cikin gidan nan, ina shigowa wannan shegiyar matar taka tana ganina sai ta haɗa fuska tamkar hadari ranta ya ɓaci tamkar taga masifa, na taƙaice maka da ita da wannan ja'irin ɗan naka mai baƙin hali suka zageni tas, ko abinci Zainabu bata bani ba, shi kuwa kalilu bindiga ya ɗaura min yace na kuskura na faɗa maka sai ya kasheni, tunda nazo matarka da ta haura sama ta barni a yashe a nan har yanzu bata fito ba, bare na samu darajar ta bani ruwa sai wannan ƴar kirkin zara'u itace ta ciyar dani ta shayar dani gata kuma tazo muna hira, dan haka yanzun nan ba sai anjuma ba, Buba tashi ka maidani ƙauye tunda ana neman rayuwata a nan, bazan zauna ba." Ta ƙarisa Maganar fuskarta shakaf da hawaye harda shashsheƙar kuka, khalil zaro idonsa yayi yana mamakin Mamma yanda ta ƙarawa yanda akayi gishiri, Garkuwa ma zaro idonsa yayi yana sauraron Mamma, duk da yasan halin Mamma zatayi sharrin da yafi wannan ma, idanun suka haɗa da Jummo, wani ras yaji zuciyarsa ta tsinke, "wannan kamar Jummo" ya furta cike da mamaki tare da taɓe baki ya kawar da kansa gefe, Daddy wani irin ɓacin rai yaji idanunsa sukayi jajur, " taya za a ci mutuncin mahaifiyarsa a cikin gidan sa, ina Wallahi bazai yiwu ba, dole yau sai ran kowa ya ɓaci a cikin gidan nan idan ana son zaman lafiya dole ne abi umarnin mahaifiyar sa............." *Biya Naira 100 ki ƴar uwa ki cigaba da karatu cikin nutsuwa, ki gaggauta biya domin kuwa akwai kwanakin dana ɗebawa wannan BOOK ƊIN da zarar kwanakin ya cika LITTAFIN zai tashi daga 100 ya koma 300 gara ki biya da wuri kafin wannan damar ta wuce ki biya ta wannan hanyar👇🏻* *0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko hoton mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sannan kiyi screen short ki turo shaidar biya* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *FREE PAGE* ➰➰ *23 to 24* " Oh na gane Aunty, bari na shige bedroom na watsa ruwa." Da to Aunty Zarah ta amsa Sadiya ta shige tana hararar Jummo, Jummo kuwa da kallo ta bita tare da sauƙe numfashi itama ta shige bedroom ɗin Mamma, yana zaune kusa da Mamma sai zance suke suna dariya, itama Jummo Zama tayi tare da tura bakinta tace. " Ni fa Mamma na fara gajiya wallahi, shi wannan Ya Garkuwan sai ta shareni yana kau da kansa gefe, baya ma son ganina, ni dai Mamma kice kawai ya soni tunda gani gashi yanzu a gabanki." Dariya ce taso ƙwacewa Garkuwa, sai ya haɗa fuskarsa tamau, Mamma kuwa gyara zama tayi tare da cewa. " Allah dai ya miki albarka, ai gara da kika tuno min da zancen Soyayyar nan taku, kai Garko kalleni da idanun da Allah ya baka sosai dan ubanka." " To fa " Garkuwa ya furta yana zubawa Mamma Ido yace. " To Uwata Mamma na kalleki faɗi kafin ta kasheki." " Ai kuwa sai dai ta kashe uwarka ba dai ni ba, kaga Garko ka sota dan ubanka, kuma dole zaka aureta." Murmushi Garkuwa yayi tare da nuna Jummo da yatsa yace. " Wannan mahaukaciyar zan SO harna aureta, (Allah siddimo asiri Mamma) me zanyi da wannan jakar, hmmm!!! Naga alamar kina son shiga min hanci da ƙudunduno fa Mamma, to ki dakata haka dan dai wallahi nafi ƙarfin wannan jakar ƙauyen." Wani irin zogi da raɗaɗin maganar sa Jummo taji, ta rasa meyasa Garkuwa yake kiranta da waɗannan mugayen sunayen jaka mahaukaciya, miƙewa tsaye tayi tare da cewa. " Ya Garkuwa na rasa meyasa kake kirana da wannan mugayen sunayen, amma ka sani koda na fito daga ƙauye ba baƙin ƙauye na fito ba, da ɗan wayewarsa, kuma ban shigo Birni da jahilci ba, bare ka kirani jaka, kowa yasan kakana cikakken malamin addini ne, haka kuma yayi ƙoƙarin bani ilimin addini alhamdulillah bokon ma nayi primary, kaga kuwa nafi ƙarfin ka kirani jaka, wannan kalmar tana min ciwo a duk sanda ka ambata min ita, Garkuwa indai nice wallahi daga yau na yafe Soyayyar ka har abada, ba kuma zan ƙara ambata maka ita ba, amma ka sani idan ba'a kiraka mahaukaci ba, ni baza'a kirani mahaukaciya ba." A fusace Garkuwa ya miƙe zai shararawa Jummo mari Mamma ta daka masa tsawa. " Karka fara dan ubanka wallahi kana saka hanu a jikinta, sai kayi nadama, wawa marar hankali to ka sani Wallahi baka da wata mata bayan Jummo ka ajiye a ranka, ko na mutu sai na barwa ubanka wannan was....... .." " Aa Mamma ki daina wannan maganar ki barshi yaje ya rayu da wanda yake so yaje ya auri ya Birni, karki shiga haƙƙin sa, ina sauraron Baffa sa'i da lokaci yana cewa, Annabi Muhammad (saw) yana cewa ya haramta Auren dole, me zaisa shi a masa, ki barsa Allah ya haɗa kowa da rabonsa" Tana gama faɗin haka ta juya ta bar bedroom ɗin da gudu, nasu bedroom ɗin ta nufa ta faɗa saman bed kuka mai sauti ta saki, tana jin zuciyarta na mata nauyi tana mungun son Garkuwa sai dai shi sam babu ita a ransa, bata san menene aibunta ba, ko dan saboda ita ƴar ƙauye ce, Sadiya dake zaune gefe ne ta taɓe bakinta, tare da wirgawa Jummo mungun kallo Sosai Jummo tasha kukanta ta godewa Allah har sai da idanunta suka kumbura amma abun baƙin ciki soyayyar Garkuwa dai-dai da gutsure bai ragu a zuciyarta ba, miƙewa tayi ta shiga tollet ta wanke fuskarta, alwala ta ɗauro tazo ta hau Sallah. Karfe tara na dare khalil ya shigo cikin gidan duk suna zaune a falo har Daddy da Momy sai Garkuwa ne kawai baya nan, a kusa da Daddy khalil ya zauna tare da cewa. " Sannuku da hutawa, Sadiya yaushe a gari." " Ɗazun nan na shigo, jiya ai Doctor Naseer yake cemin ka dawo kana gari." " Eh na kwana biyu ma da dawowa, amm Daddy ɗazu naje gombe high school, wajen Mlm Nuhu nayi Magana dashi ina son na yiwa Jummo registration ta cigaba da zuwa school ɗin, amma na tambayi Mamma tace min tayi primary school, so yanzu yace nan da 3month zasuyi jsce so yace tayi jsce ɗin kawai idan yaso sai ta joining daga ss1 so yayi min bill ɗin kuɗin na biyasa 50k sannan ya min magana da wata malamar su Esther zata fara zuwa gobe tana yiwa Jummo da A'illo extra lesson, ita kuma A'illo gobe zamuje a mata registration na Junior secondry school sai ta fara zuwa. Murmushi Daddy yayi cike da jin daɗi tabbas yaji daɗin abinda Khalil ya masa, itama Mamma sosai taji daɗi saboda burin Baffa kenan yaga Jummo tayi karatun Boko mai zurfi, ni sawa Daddy yayi kafin yace. " Alhamdulillah!!! Allah ya maka albarka Khalil Allah ya biya maka buƙatun duniya da lahira kaima Allah ya baka mai rama maka, Allah ya azurtaka da mai rama maka, Allah ya tsare maka gabanka da bayanka, tabbas yau ka faranta min rai." Dariya Mamma tayi itama cike da farin ciki tace. " Khalilu ada ina maka kallon marar hankali, ashe dai kai mutumin kirki ne, yau kayi abinda banyi tunanin zaka yisa ba, Allah ya maka albarka." Da ameen khalil ya amsa cike da farin cikin albarkan da iyayensa suka saka masa Momy kuwa haɗa fuska tayi tamau sosai ranta ya ɓaci da abinda khalil yayi ba tare da shawarar ta ba, sai dai ba tace komai ba, Jummo kuwa tsabar jin daɗi tamkar taje ta rungume khalil take ji, Aunty Zarah ma Sosai taji daɗi abunda take ta son bawa khalil shawara kenan sai gashi ya aiwatar da kansa tabbas mijinta mutumin kirki ne, cike da farin ciki suka kasance har kowa ya watse ya kwanta. Momy kuwa sanda tasan yanda ta yiwa Daddy ƙarya ya barta zatayi sammako su fita da Asabe, a daren ta kira Asabe ta shaida mata cewa an barta. Zarah cike da farin ciki ta rungume khalil tana dariya tace. " Naji daɗin abinda kayi min sosai naji daɗi, daka saka Jummo a makaranta da alamu tana da basira zata iya zama wani abu a duniya wanda al'umma zasu amfana da ita, naji daɗi sosai." Dariya khalil yayi yana daɗa rungumota jikinsa a kunnenta ya raɗa mata. " Kaina na yiwa ba keba My dear, nayiwa Jummo wannan zumuncin ne saboda dalilai guda uku, dan haka ki daina gode min babu godiya tsakanin mu." Murmushi Zarah tayi tana sakesa ta zuba masa ido tare da jefa masa tambaya. " Ya khalil saboda dalili Uku kuma, wani irin daliline wannan.?" " Hmmm!!! Zan sanar dake idan lokaci yayi, kije ki kaimin ruwan wanka." Ɗaga kanta tayi alamun to tare da juyawa ta shiga tollet ta haɗa masa ruwan wanka, kwanciya yayi yana sakin murmushi tare da lumshe idanunsa, tabbas yana jin wani abu dangane da Jummo a zuciyarsa sai dai bai san menene fassarar abinda yake ji ba. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Washe gari da safe* Sassafe Momy suka fita da Asabe ba tare da kowa yasan fitar ta ba, ko sanda Daddy ya tashi ta fita, shima breakfast kawai yayi ya fice. " Saurin me kike haka SAFREENA ina zakije ki.?" Juyowa SAFREENA tayi tare da kallon Zee tace. " Zanje *ASAD INTERNATIONAL AIRPORT* ne" " *ASAD INTERNATIONAL AIRPORT* kuma me zakije kiyi?" " Bai kamata ki tambayeni abinda zanyi acan ba, tunda kin sani, amma tunda kina buƙatar na maimaita miki, zanje na haɗu da wannan azzalumin ne Garkuwa." " Karkije ko kinje ba samun sa zakiyi ba, meyasa akwai fansa cike cikin zuciyarki, amma baki da mission akan fansar ki, jiya naje Asad airport nayi bincike akan Garkuwa, a binciken dana samu, baya aiki yanzu ya tafi hutun tsawon wata biyu, amma dai ya kusa cinye hutun saura sati biyu ya dawo kan aikinsa, amma a yanzu zaki iya samunsa a I'j'j hotel zaije can yau da misalin ƙarfe huɗu na yamma, shida ƙanwar matar yayansa mai suna Sadiya wacce a yanzu haka itace take cikin tarkon sa, da ita yake hole rayuwarsa, ina da tabbacin itama zai iya rabuwa da ita da zarar ya gama samun abinda yake so daga jikinta, a nawa tunanin karki nuna masa kanki yanzu kiyi amfani da wannan damar wajen razana Garkuwa ta hanyar bibiyar duk wasu gurɓatattun ayyukan sa wanda bayaso duniya ta sani a yanzu haka maganar da nake miki na bawa ma'aikacin hotel ɗin 30k ya ajiye mana camera a cikin bedroom ɗin wacce zata ɗauki duk abinda zasu aikata a hotel ɗin da zarar sun gama zaije ya ɗauki Camera mu kuma sai muje mu karɓa sauran aikin shima zan sanar dake idan camerar tazo hanun mu." Da fe kanta SAFREENA tayi tare da zama a daya daga cikin kujerun dake falon tare da furta. " Har abada shi ba zai daina saka mata a matsala shegen kwarjini ne dashi da wuya mace take iya tsallake tarkon sa, bashi da burin daya shige lalata Rayuwar mata ya saka su a cikin matsala, shiyasa nake son kawo ƙarshen sa, Garkuwa bashi da imani innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Zee sai yaushe Garkuwa zai daina lalata Rayuwar mace ya dauki mace tamkar rigar sawar sa, ya saka a lokacin da yaga dama ya kuma cire sanda yake so, idan banga Garkuwa a wulaƙance ba, bazan taɓa yafewa kaina ba wallahi." " Safreena za kiga ƙarshen Garkuwa Da yardar Allah zamu haɗa ƙarfi da ƙarfe ni da ke wajen ganin bayansa, zan tayaki wannan yaƙin safreena sai dai abinda nake so dake dole ne ki bawa Abdul kulawa Saboda shi bashi da laifi baisan komai game da matsalar ku ba, safreena karki kuskura haƙƙin Abdul ya fara bibiyar ki, ki farka daga ƙiyayyar da kike nuna masa." " Ba ƙiyayya nake nuna masa ba babu Uwar da zata haifi ɗa ya tsaga jikinta ya fito ace bata sonsa wallahi ƙarya ne, zafi da suka tare da raɗaɗi nake ji a ƙirjina a duk sanda na ɗaga idanuna na kalli Abdul naga kamansa da Garkuwa, ko na tuno ƙaddarar samunsa ta jefani a cikin halin da nake ciki yanzu sai idanuna su rufe naji ƙiyayyar mahaifinsa ya dira a kansa amma wallahi ina son ɗana." Numfashi Zee ta saki tare da jingina jikin kujerar tana cewa. " Ki cire hijabin naki, babu inda zaki fita yau, a duk sanda kikaji zafin Abdul a zuciyarki to ki anbaci innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allah zai sanyaya miki, ina mai baki tabbacin cewa daga gobe zaki fara razana Garkuwa, zaki saka masa ruɗani da tsoro cikin zuciyarsa wallahi a gobe tsoro da fargaba zasu kasance abin tunaninsa, safreena Garkuwa bazai ga fuskar ki shida kansa zai fara nemo ki dan haka hankalinki ya kwanta ina da tabbacin zakiga karshen sa na miki wannan alƙawarin..................." *Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi Naira 100 kacal babu yawa ki biya ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko kuma ki turo hoton Mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sai ki turo shaidar biya* *Ki hanzarta ki biya Free page saura 3 page ya ƙare idan kuma ya ƙare book ɗin ya koma 300 dan haka hanzarta ki biya ƴar uwa* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *Ina YINKU over masoyana, tabbas kun nuna min ƙauna a wannan book ɗin, kun nuna min kuna tare dani ko da kuɗi ko ba kuɗi 🥰🥰🥰🥰🥰 Love You masoyana muah😘😘😘😘😘😘* Mu kafta🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️ *FREE PAGE* ➰➰ *25 to 26* " Da zanfi kowa farin ciki, idan naji labarin zuciyar Garkuwa ta fara shiga cikin ruɗani, Zee babu abinda zance miki sai godiya, Allah ya bar zumunci domin kuwa kina nuna min ƙauna yanda ya dace na gode sosai." " Ba sai kin min godiya ba, ki dai tashi kije ki bawa Abdul nono nasan ya farka yanzu haka." Miƙewa Safreena tayi fuskarta a haɗe ta shige bedroom ɗin ta, ya tashi kuwa sai mitsilmitsil yake da ƙafarsa, zama tayi a gefe tare da ɗagosa ta saka sa kan cinyarta, nonon ta ta ciro tare da saka masa a bakinsa, saurin capka yayi ya fara tsotso, zuba masa idanu safreena tayi idanunta na cikowa da ƙwalla, tsoro da fargabarta ranar da yaron nan zai girma ya tuhumeta waye mahaifinsa, a wannan ranar bata san wacce irin amsa zata basa ba, hanunta ta saka tare da goge hawayen daya cika mata idanunta, sanda ya sake nonon dan kansa sannan ta ajiyesa ta shiga tollet haɗa masa ruwan wanka. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Tun ɗazu yake zaune cikin motar yana jiran fitowar ta, yayin da yayi parking a bayan gidan nasu, yafi 30 minute a zaune cikin motar sannan ya hango Sadiya tana nufo motar murmushi ya saki mai sauti tare da sakin murmushi, gaban motar ta buɗe ta shiga, idanu suka haɗa ya sakar mata murmushi, motar yaja suka harba titi, murmushi Garkuwa ya saki tare da cewa. " Nayi zaton kinyi zuciya ne dani ba zaki ƙara kulani ba sai kuma naga saɓanin haka, kin ajiye zancen auren a gefe kenan." Kawar da kanta gefe Sadiya tayi ba tare da ta kallesa ba tace. " Ai ka sani bazan taɓa iya rayuwa ba tare da kai ba, ina sonka sosai Garkuwa dalilin da ya saka rabuwa da kai zai bani wahala, a yanzu ma so nake ji shin zaka iya aurena a duk lokacin da ka tashi yin Auren idan har zaka aureni to ni kuma na amince zanyi zaman jiran ka.?" Shuru Garkuwa yayi yana jan motar kafin zuwa can yace. " Bana alƙawari Sadiya Saboda alƙawari yana da matuƙar hatsari, sai dai maybe zan iya auren ki, amma fa ban miki alƙawarin Aure ba." Yayi Maganar yana saka hanunsa ya kamo nata yana Murza cikin tafin hannunta, shuru Sadiya tayi tare da cewa. " Amma meyasa kafi son mu cigaba da lalacewa a waje bayan kana da halin da zaka aureni a gaskiya daga Yau mukayi wannan ni bazan sake ba, kawai gara mu haƙura sai munyi Aure." Bakinsa ya taɓe irin ko ohon nan, bai bata amsa ba har suka isa hotel ɗin. Ita kuwa Momy ƙarfe huɗu na yamma ta dawo cikin gidan fuskarta cike da fara'a hijabin ta kawai ta cire tare da duban Mamma da Aunty Zarah dake zaune tace. " Mamma sannu da hutawa." " Sannu uwar iya gantali tambaɗaɗɗiya, yo Idan banda tambaɗaɗɗe waye zai bar gidan sa tun kafin kowa ya tashi daga bacci, ke de bi duniya a sannu wallahi idan ba haka ba sai ta miki atishawar tsaki, wani wai sannu da hutawa Mamma, to ina ruwana da sannunki, ni kina gabana ne ma shasha kin girma har abada baza kiyi hankali ba." Momy bata ce komai ba sai ma cewa tayi. " Kiyi haƙuri Mamma, Zarah kin ɗaura girki ne.?" Aunty Zarah cewa tayi. " A'a yanzu dai nake so na tashi na ɗaura." " Okay to ki barshi yau ni zanyi girkin." Zaro idanunta Zarah tayi cike da mamaki Momy kuma zatayi girki da kanta, to meyasa anya kuwa muryar Jummo da sukaji daga bayansu ne ya sasu juyawa suna kallonta. " Girki kuma ke da kanki Momy, meyasa bazaki bari mu muyi ba, haba dai ai kekam yanzu kinfi ƙarfin shiga madafi Momy, kije kawai ki huta zamuyi nida Aunty Zarah.?" Murmushin yaƙe Momy tayi tare da miƙewa tsaye zatayi magana Mamma ta rigata. " Yo ina kuwa zata zauna ta huta tunda taje bokanta ya bata wanda zata barbaɗa a girki, ke zainabu karfa ki mayar dani shasha, idanuna a buɗe suke tar duk abinda zakiyi ina sane sarai sai dai na zuba miki idanu, dama zaki saduda ki sawa kanki nutsuwa dama yafi miki domin Ni ɗin nan da kike gani Kainuwa ce dashen Allah, murucin kan dutse ban fito ba sai dana shirya na rantse da Allah da zaki shekara kina min asiri babu abinda zai sameni domin kuwa a tsume nake, karki manta daga inda na fito dan haka ki kiyayeni." A matuƙar gigice Momy take kallon Mamma zaro idanunta Zarah da Jummo sukayi, cike da matuƙar ƙara razana da lamarin Mamma tace. " Asiri kuma Momy, ni kuma mai zai haɗani da miki asiri, haba Mamma........" Ɗaga mata hanu Momy tayi alamun ya isa tare da tashi tabar wajen ranta a matuƙar ɓace. Murmushi Jummo tayi tare da matsowa gaban Momy tace. " Kiyi haƙuri Momy tabbas wajen boka kikaje, nine na sanar da Mamma saboda jiya naje zan shiga bedroom ɗinki Aunty Zarah ta aikeni na ɗauko mata kayan wankin ki, har zan tura door ɗin bedroom ɗinki sai naji muryar ki, kuna zance ƙasa ƙasa da wata mata, sai na tsaya na saurari dukkan hirar ku, wanda kike da burin cutar da Mamma, ni kuma bazan iya jurar abinda zai cutar da ita ba, shiyasa na bayyana mata ƙudurin ki akanta kiyi hkr ba laɓe na miki ba, naje aiken Aunty Zarah ne na jiki dan Allah Momy ki sauya hali ki daina ƙoƙarin cutar da Mamma, Momy Mamma tasha bani labarin yanda kuka wulaƙanta ta, lokacin Auren ki da Daddy har yanzu wannan abun yana cin zuciyar Mamma meyasa baza kiyi ƙoƙarin kyautatawa Mamma ba, domin kawo masalaha a tsakanin ku, ki goge laifin ki daga zuciyarta na tabbata Mamma zata manta da komai ku zauna lafiya." Wani irin sanyi jikin Momy yayi, take gumi ya keto mata kunya duk ya lulluɓeta juyawa tayi ta kalli Jummo tare da zama baki kujera ta kalleta cike da tsana ta nunata da yatsa. " Wato laɓe kike min, hmmm!!! Yau naji wata ƙaddara yarinya ke gida bana ubanki ba, bana dangin ubanki ba, bana dangin uwarki ba, babu dangi tsakanin mu dake amma ki shigo cikin gidan mu ki nemi hanamu sakat, to bari kiji muddun baki fita a harkata ba, na rantse da Allah sai na kawo ƙarshen ki a cikin gidan nan, shegiya mai kama da buzuwa, to bari kiji baki isa ki wargaza min shirina ba, YANDA na ɗauki alwashin ganin bayan Mamma a cikin gidan nan, wallahi sai na gani, dole sai kun barmin gidana ko koma can ƙauye kuje kuta fama da dawa da baƙar kuka mtss." Momy tayi maganar tana juyawa tayi taku ɗaya taji muryar Jummo. "Muddun ina numfashi bazan taɓa bari ƙudurinki ya cika akan Mamma ba, na rantse da Allah yanda Mamma ta shigo gidan babu wanda ya isa ya fidda ita a gidan ɗanta, tazo kenan, Momy ki dawo cikin hankalinki ki fahimci cewa kina kan kuskure ne, da Mamma munguwa ce mai bin doka irinki wallahi da ta juma da ganin bayanki koda bataxo birni ba, domin kuwa ƙauyenmu mun fiku matsafa, amma ita zuciyarta a tsarkake take bata iya mugunta ba, faɗan kawai ta iya dan haka ki kwana da sanin zan tseratar da Mamma daga duk wani sharrin ki, Sai dai ke ki fita kibar Mamma a cikin gidan nan wannan alƙawari na ɗauka." Kunkumin ta Momy ta riƙe tana huci yayin da Aunty Zarah ta daskare tana kallon Jummo, bata taɓa zaton JUMMO tana da baki haka ba, Momy ɗauke Jummo tayi da mari tana nuna ta da yatsa tace. " Ni kike kira munguwar, ehh lallai ɗan zaki ya girma, gaskiyar hausawa da suka ce idan ɗan ƙauye ya shigo Birni ya waye sai yafi ɗan Birnin iya shege, to bari kiji ni ba kanwar lasa bace, nafi ƙarfin ki, kuma ki sani nice ƙalubalenki." Tana faɗin haka ta haura da sauri tana huci, Jummo dafe kuncinta tayi tare da kallon Aunty Zarah, zatayi Magana Aunty Zarah ta ɗaga mata hanu tare da cewa. " Karki cemin komai, na fahimci komai, tabbas Momy bata kyauta ba, amma bai dace ki mata rashin kunya ba, komai tsiya dai Momy ta haifeki, na fahimci kinzo gidan nan ne domin ku fitar da Momy daga gidan ta, wannan kuskure ne, kuma bazan taɓa bari hakan ta faru ba, Farko ɗaukar mutumiyar kirki nake miki ashe ba haka kike ba, ashe munguwa ce mai fuska biyu kin bani mamaki Jummo." A matuƙar firgice Jummo take kallon Aunty Zarah da ta mata munguwar fahimta cikin sauri Jummo tace. " Baki fahimce ni ba Aunty Zarah, meye laifina dan Momy tayi kuskure zan gyara mata.?" " Karya kike Jummo babu gyara a cikin lamarin ki, sai tsantsar munafurci idan ba munafurci ba, meyasa zaki sanar da Mamma Momy taje wajen boka, haka ake gyara, idan gyara zakiyi, kamata yayi ki nunawa Momy kinsan abinda take, ki nuna mata ta gyara cikin masalaha, ba wai ki kwashi magana gulma da munafurci ki kaiwa Mamma ba, wannan haɗa faɗa ne da ƙara rura wutar ƙiyayya a tsakanin su." " Aunty Zarah wallahi ba nuf................" " Karki cemin komai na riga na gama fahimtar waye ke, rogo nake yiwa kallon kitse........................." *Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi Naira 100 kacal zaki biya ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko ki turo hoton Mtn card na 100 ta wannan numbern 08147537180 sannan ki turo shaidar biya.* *Kuyi haƙuri dan Allah yau kun sami readmore kadan abubuwa suka min yawa, amma dai hausawa sunce da babu gara ba daɗi, kuyi manage* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *FREE PAGE* ➰➰ *27 to 28* " Hmmm!!! A iya sanina gyara bai taɓa zama munafurci ba, na sanar da Mamma gaskiya ne domin tasan yanda zata kare kanta daga sharrin Momy, wai ma na tambayeki Aunty Zarah, wani daɗi Momy ta miki da har zaki shiga gabanta ki kareta, ki tsaya a gaban karya domin karya gwiwwar mai gaskiya yin hakan kuskure ne, kuma wallahi Aunty Zarah bazan taɓa sauyawa daga ƙudiri na ba, muddun ina tare da Mamma bazan taɓa bari burin Momy ya cika a kanta ba." " Ai dama bazaki bari ba, Saboda kina da mungun niyyar raba uwa da ƴaƴanta miji kuma da mata, to niyyar bazai taɓa cika akan Momy ba, muddun nima ina cikin gidan nan, domin kuwa baki fini iya wayo ba, daga ƙauye kika fito ni kuma a cikin birnin kika shigo kika sameni dan haka dole na fiki waye wa, zan kare Momy kota halin yaya mugun nufinki bazaiyi tasiri a kanta ba." Murmushi mai sauti Jummo tayi tare da matsowa gaban Zarah tace. " Ina ta baki mutuncin ki amma naga alamar bakya son mutuncin da nake baki, kin min hallaci bazan so ɓata miki ba, shiyasa bana son kisan waye Jummo, ki tambayi A'illo labari na a ƙauye ba'a taɓa Nasara a kaina duk abinda na saka a gabana sai na cimma nasara, amm Aunty Zarah tabbas daga ƙauye na fito, amma zan nuna miki wayon ɗan ƙauye yafi na ɗan Birni mu buga wasan ƙarshen wasan shi zai bayyana mai Nasara, fatan Nasara Aunty na." Tayi Maganar tana murmushi tare da barin wajen ta nufi bedroom ɗinsu, Aunty Zarah dafe kanta tayi ta nemi waje ta zauna cike da tsantsar damuwa, bata taɓa zaton wayon Jummo ya kai haka ba, (duk da babu shiri tsakanina da Momy komai tsiya ai ta zamo uwata tunda ina Auren ɗanta ya zamo dole na kareta daga sharrin Mamma da Jummo, domin barin Momy cikin gidan nan yana nufin rugujewar farin cikin mijinta ita kuwa bazata jure ganin mijinta cikin damuwa ba, farin cikin sa shi take buƙata, zatayi wannan yaƙin ne domin farin cikin mijinta) numfashi ta sauƙe mai nauyi tare da miƙewa ta shige kitchen, itama Jummo bakin gado ta zauna tana ji a cikin ranta bata kyautawa Aunty Zarah ba da ta mayar mata Magana ko yayane Aunty Zarah ta nuna mata ƙauna da duk wata wayewa, "amma ya zamo dole ta kare mutuncin Mamma a da Soyayyar Garkuwa ne ya kawota gidan nan, sai dai a yanzu komai ya juye ta fuskanci matsalar Mamma da ciwo a raba uwa da ɗanta sai gashi Momy ta raba Mamma da ɗanta na tsawon shekaru, ta daɗe Mamma CIKIN ciwon rashin ɗanta a kusa da ita, sai yanzu ta samu damar zama kusa dashi ace za'a koreta sam bazan bari hakan ta faru ba, zan ajiye Soyayyar Garkuwa a gefe domin kare Mamma ta zauna da farin cikin ta Buba, ya zamo dole na zamo ƙalubalen Momy koda hakan yana nufin ƴaƴanta zasu tsaneni na rasa Soyayyar Garkuwa, na yadda na kare Mamma." Bakinta ta cije tare da Kwanciya ta runtse idanunta, A'illo da kallo ta bita tare da saka hanunta cikin na Jummo tace. " Mamma itace ta goyeni tun ƙaramar yarinya ta bani tarbiyya ta mantar dani maraicin iyayena komai tana min babu mugunta, ada ina jin zafin ki, sai kuma gashi a yanzu ina jin ƙaunar ki, kin san meyasa Saboda kin ɗauko hanyar dawowa Mamma na da farin cikin ta, sanda muke ƙauye a ko wani dare sai Mamma tayi kuka tana cewa, Buba ya gujeni baya zuwa wajena ɗansa kawai ki ziyartana sai dai ya min aike nakan fi shekara banga Buba, nafi buƙatar ganin Buba a kusa dani fiye da kuɗi da kayan abinci da yake aiko min A'illo matar Buba ta rabani dashi dama sunyi wannan alwashin ita da iyayenta cewa da zarar Buba ya tafi da Zainabu Birni bazan kuma ganinsa, kinga kuma maganar su ta tabbata tunda buba ya tafi binni bai kuma zuwa wajena ba sai aike kawai da yake min, sai yaushe zan zauna inuwa ɗaya da Buba sai yaushe A'illo" numfashi A'illo ta sauƙe tare da duban Jummo ta cigaba da cewa " Sai gashi ta sanadiyyar ki domin nemo miki Soyayyar ki Mamma tace mu taho Birni neman gidan Buban ta, ƙaddarar ki itace ta dawo da Mamma cikin gidan ɗanta, dan Allah Jummo karki bari Mamma ta koma ƙauye na tabbata idan Mamma ta koma ƙauye baƙin ciki ne zai kashe ta, shikenan ni kuma na rasa gatana na rasa me kula dani." Miƙewa Jummo tayi ta zauna tare da ƙara danƙe hanun A'illo ta fara magana cike da rawar murya. " Yanda ƙaddarata ta dawo da Mamma gidan ɗanta insha Allah haka ƙaddarata zata zaunar da Mamma gidan ɗanta har abada, insha Allah burika na zasu cika ina ji a jikina komai daren daɗewa zan mallaki yaya GARKUWA, sai dai nasan akwai tarin matsaloli a gabana, bani ƙarfi sai na Ubangiji ƙarfin hali kawai nake a wannan yaƙin, addu'a zaki tayani A'illo Allah ya bani Nasara a kansu, Allah yasa kar su suyi Nasara a kanmu, zanyi Magana da yaya khalil maybe shi zai fahimce ni." Kanta A'illo ta girgiza tare da cewa. "A'a Jummo karkiyi Magana da Yaya khalil domin kuwa baya son laifin Momy shi duk abinda tayi akan dai-dai take, gara ma yaya Garko shi mutum mai fidda gaskiya a duk sanda tazo koda akansa ko akan Momy ko Daddy baya tsoron ya faɗawa mutum gaskiya, gara shi kiyi Magana dashi akan yaya khalil." " A'illo ni kuma bazan yi magana da Garkuwa ba, saboda a halin yanzu yana ɗaukata ne a matsayin jahila mahaukaciya wacce bata san abinda take yiba, a haka yake ɗaukata, dan haka bana buƙatar Magana dashi, shima KHALIL ɗin na barsa." " Shikenan to Allah ya mana jagora." Da ameen Jummo ta amsa tana maida kanta ta kwanta. Momy kuwa tunda ta shiga bedroom ɗinta ƙirjinta ke suwa wani irin tsana da haushin Jummo take ji, tunda take a rayuwarta bata taɓa jin tsanar mutum bilhaƙƙi da gaske ba sai Jummo, wani irin mataki ya kamata ta ɗauka akan wannan agolar Yarinyar, ita wannan yarinyar take neman ta tonawa asiri, numfashi Momy ta sauƙe tare da furta. " Hmmm!!! Lallai akwai Babban ƙalubale a gabana dole sai na fara kawo karshen Yarinyar a cikin gidan nan kafin na juyo kan Mamma wannan wani irin masifa ce, kai kaji yarinya da ƙwaƙkwafin tsiya wato ma turo ta Mamma take tamin laɓe, ai kuwa zanci ubanta zan nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, zan nuna mata na haife ta, bata isa nuna min wayo ba." Zama tayi ta dafe kanta ta furta. " Wannan wacce irin masifa ce take tunkaro Ni, dubu hamsin na bawa wannan malamin yamin wannan aikin sannan kuma ace nayi asaran kuɗina, ina Wallahi bazai yiwu ba!!! Dole ne sai Mamma taci wannan maganin" shuru tayi tana tunanin sai can zuciyarta ta ayyana mata mai zai hana tayi amfani da Zarah wajen kalallameta ta samu ta sakawa Mamma wannan maganin "taya zan fara" zuciyarta ce tace mata " ta hanyar nunawa Zarah kulawa da nuna mata cewa Mamma tana neman rayuwarta tun ba yau ba tabbas kika je mata cikin kuka dole zuciyarta zai karaya taji tausayinki ta baki haɗin kai, idan har kika samu nasarar jawo Zarah jikinki tabbas aikinki zaiyi kyau." Murmushi Momy ta saki tare da miƙewa tsaye tana cewa " tabbas haka zanyi" ta ƙarisa Maganar tana shigewa cikin tollet. Jikinsa ta mirgino tana sakin murmushi tare da riƙo yatsar hanunsa ta saka a bakinta, lumshe idanunsa yayi yana jin wata nutsuwa na sauƙa masa a hankali ya furta. " Sadiya kina da ni'ima tamkar Sweet haka kike zaƙinki yayi yawa, hmmm!!!" Murmushi Sadiya tayi ta cire yatsar daga bakinta tace. " Duk daɗi na ban kai kaba kai na musamman ne, shiyasa nake fatar na kasance mata a gareka, dan Allah ka aureni yaya Garkuwa, wallahi da kai kaɗai zan iya rayuwa kaine zabin zuciyata." Gashin kanta ya shafa tare da cewa. " Sadiya tun yaushe nake ce miki ki daina min zancen Aure, ban miki alƙawari ba Sadiya, amma shi Aure mukaddari ne, Allah shi kaɗai yasan matata, dan haka ki dage da addu'a idan Allah yasa kece fine." Shuru Sadiya tayi tana duba agogo 6:30pm duban sa tayi tare da miƙewa daga jikinsa ta ma nufar tollet wankan tsarki tayi tare da fitowa ɗaure da towel kayanta ta mayar tana furta masa cewa. " Lokacin komawa na gida yayi, ni zanje na hau adaidaita." Da to ya amsa yana miƙewa shima, ya ciro 70k ya miƙa mata, hanu tasa ta karɓa tare da ɗaukar bag ɗin ta ta fice tana ce masa sai ya dawo, tollet ɗin shima ya shiga yayi wankan tsarkin tare da ɗauro alwala kayansa shima ya mayar tare da kwasar wayoyinsa da key ɗin motar sa, ko kaɗan bai lura da camera dake maƙale jikin window dake saitin su ba, ya fice, yana fita ma'aikacin ya shiga ya ɗauki camera tare da seving ɗin videon, ya fito yana sakin murmushi, Zee ya kira tare da faɗa mata aiki ya kammala zata iya shigowa ta karɓa, sannan ya katse wayar. Wajen bakwai dai-dai Sadiya ta shigo gidan, babu kowa cikin falon zata haura sama taji muryar Aunty Zarah tana cewa. " Sai yanzu kika ga damar dawowa, amma ba ce miki nayi 5 zaki dawo ba shine kika je kika kai har 7." Juyowa Sadiya tayi tana murmushi tace. " Oh Aunty na faɗa miki gidan su zarina naje, kasuwa na rakata shiyasa mukayi dare." " Kyaji dashi dai" Aunty Zarah ta furta tana shigewa kitchen, murmushi Sadiya tayi ta shige bedroom ɗinsu Jummo ta samu zaune tana lazimi, baƙin ta Sadiya ta taɓe tare da furta. " Wai dama su ƴan ƙauye har sun iya karatun Sallah ne."? Murmushi Jummo tayi domin kuwa taji sarai abinda Sadiya ta faɗa kuma tasan da ita take, ta rasa meyasa Sadiya take jin zafin ta alhakin babu wani saɓanin daya shiga tsakaninsu, ko meyasa take mata haka, ita dai Jummo bata tanka mata ba. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ " Lallai Rayuwarki tana daf da ƙarewa muddun wannan azzalumin shine wanda zaki iya rayuwa dashi." Safreena tayi Maganar idanunta na kan videon da Sadiya da Garkuwa suke tsirara haihuwar uwarsu tana lalata, murmushi safreena tayi tare da ɗago Abdul dake calla kuka ta rungume sa tare da cewa Zee. " Zee Wannan Yarinyar bata da hankali fa, kina ji darect yake sanar da ita bazai aureta ba, amma dake ƙaramar ƙwaƙwalwa ke gareta ta kasa fahimta, da ace Garkuwa ya furta min shigen kalaman gaskiya da yake nunawa wannan Yarinyar wallahi da ban sakankance dashi ba, yanzu meye abun yi." Murmushi Zee tayi tare da amsar camerar ta cire memory ɗin, wata waya Android dake gefe ta ɗauka ta saka memory ɗin, tare da cewa. " Ita wannan yarinya duk inda ta fito jaka ce marar basira dan haka rabu da ita kawai muyi abinda ke gaban mu, kinga wannan wayar na saka mata sabon layin da akayi registration ɗinsa ba hoto, address kuma ba nan garin na saka ba, Bauchi na saka, sannan sunan da nayi amfani dashi wajen registration ɗin shine *D N G* dashi zamuyi amfani wajen tsorata Garkuwa, yanzu zamu tura masa wannan video ɗin ta WhatsApp ɗinsa." Murmushi safreena tayi tare da furta *D N G S* meaning *DANGEROUS* murmushi ta saki tare da karɓar wayar ta tura masa saƙon tana sakin murmushi. Yana tafiya ta kashe datar tare da duban Zee tace. " *Wasan ya fara daga yanzu* .........................." *Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira 100 kacal ki daure ki biya sai ki cigaba da karatu cikin nutsuwa Free page daga 30 ya ƙare zaki cigaba da samun wannan littafin ne idan kin biya ɗarin ki.* *Ki biya ta wannan hanyar 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko mtn card wannan numbern 08147537180 sannan kiyi screenshot ki turo shaidar biya 100 ce kaɗai babu yawa.* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺 *GELLE ƁINGEL* 🏺🏺🏺🏺 *Story* *Rasheedat Usman* *(Ummu Nasmah)* *Littattafan marubuciya* Sauyin Rayuwa Nasmah Ko Nasirah Sara Da Sassaqa Indo A Birni So Bai San Jini Ba Akan ƴar uwata. Hatsabibiya Saude Ruɗanin Zuciya Biyu. Doctor Hassan. Ƙauyenmu. And now *GELLE ƁINGEL* *SADAUKARWA* Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah. *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *LAST FREE PAGE WANDA YA BIYA KUƊIN SA NE KAWAI ZAI CIGABA DA GANIN WANNAN BOOK ƊIN, IDAN KINA RA'AYI ƳAR UWA MAZA HANZARTA KIZO KI BIYA KUƊIN KI NAIRA 100 NE KACAL BABU YAWA BATA FI ƘARFINKI BA, DOMIN KEMA A DAMA DAKE CIKIN WANNAN CAKWAKIYA MAI RIKITARWA 08147537180* *Masu tambayar daga Farko idan kinji kina ra'ayin book ɗin biya ɗarin ki kawai sai ki samu daga farkon🥰🥰* *LAST FREE PAGE* ➰➰ *29 to 30* Murmushi Zee ta saki tana faɗawa saman kujera tace. " Ƙawata aiki ya fara daga yau, na kuma san wasan zai fara armashi ne da zarar Garkuwa yaci karo da wannan saƙon ke dai kwantar da hankalin ki ki naɗe ƙafafunki ki bawa Garkuwa nan da awa ɗaya, zai fara cin karo da ruɗani." Murmushi mai sauti Safreena tayi tare da cewa. " Zee ai a yau kam na fara jin nutsuwa amma fa hankalina bazai taɓa kwanciya ba har sai naga Garkuwa a ƙasƙance." " Hmmm!!! Saurin me kike Safreena, ai Garkuwa kam ya shiga tarkon mu, a yanzu mune zamu ke juya rayuwarsa muna wasa da ita ta yanda ƙwaƙwalwar sa zata gaza jurewa wannan wasan." " Hmmm!!! Na yadda dake ƙawata kuma nasan duk abinda kika faɗa tabbas zaki iya, muje muyi dener dan yunwa nake ji sosai." Dariya Zee tayi tare da cewa. " Da kuma duk bakiji yunwar ba, sai yanzu sorry na manta ban sanar dake ba, Baba da Mama suna hanya gobe zasu shigo Nigeria." Tsalle Safreena tasa tana dariya tace. " Alhamdulillah wallahi naji daɗi dama na tsani zaman mu mu biyun nan, Allah ya kawo mana su lafiya." Da ameen Zee ta amsa suna tashi suka nufi daining table. Khalil shigowar sa cikin gidan babu kowa cikin falo, bedroom ɗin Mamma ya shiga tana zaune ta kunna sigari sai zuƙa take idanunta sunyi jajur dasu gefen ta Jummo ce da A'illo, saurin toshe hancinsa khalil yayi a rayuwar sa ya tsani warin sigari, ransa ne ya ɓaci cike da jin haushin Mamma yaƙi kulata Jummo ya kalla tare da cewa. " Jummo zo falo ki sameni." Tsaki Mamma tayi tare da cewa. " Idan ma ka kulani ka raina Uwar da ta haifeka shege mai baƙin halin tsiya." Khalil bai kulata ba ya fice abinsa Da to Jummo ta amsa ƙirjinta na bugawa domin kuwa tayi zaton Momy ko Aunty Zarah ne suka sanar dashi abinda ya faru, tashi tayi tabi bayan sa a zaune ta gansa, itama zama tayi tare da cewa. " Sannu da dawowa yaya khalil." " Yauwa sannu Jummo" waya ya ciro daga cikin wata ƙaramar leda ya ɓareta da kansa infinix hot9 plus mai shegen kyau ya miƙa mata tare da cewa. " Ki riƙe wannan naki ne, ni na sai miki, zata ɗebe miki kewa, sannan gobe ne malamar da zata fara koya miki lesson zata fara zuwa takwas na dare, wayar ki sakata a chaji idan ta cika ki min magana zan koya miki yanda zakiyi Amfani da ita, sannan akwai alfarmar da nake nema wajenki nasan kuma zaki iya." Cike da murna Jummo ta amshi wayar tana dariya tace. " Yaya khalil Allah wannan wayata ne da gaske ni ka sayawa." Dariya khalil yayi tare da ɗaga mata kai alamun eh naki ne. Dariya tayi tace. " Kai amma na gode sosai yaya khalil, ya khalil faɗa min alfarmar da kake so na maka ni kuma insha Allah zan maka shi." Murmushi khalil yayi tare da gyara zaman sa ya fuskanci Jummo yace. " Jummo So nake ki taimakeni ki taimaki kanki ki taimaki Daddy, ki dakatar da Hajjo daga shan sigari, Jummo kin san illar shan sigari kuwa." Girgiza kanta Jummo tayi alamun a'a, khalil cewa yayi. " Sigari tana haifar da hujewar huhu ta lalata kayan ciki, a ƙarshe Mutum ya mutu a wulaƙance, ƙarin illar sigari, da zarar mutum ya mutu, duk sigarin da yasha sai ya fita daga jikinsa haka zai lalata masa likkafani, Jummo idan muka bar Mamma ta cigaba da shan sigari dole ne zai illata rayuwarta ga shi ta tsufa shekarunta sunja, zai yi saurin illatata, Jummo idan har da gaske kina ƙaunar Mamma mu haɗa ƙarfi ni da ke mu cirewa Mamma ƙaunar sigari a zuciyarta." Shuru Jummo tayi jikinta yayi sanyi, ba Mamma take tunani ba INNO take tunani da bata da wanda zai hanata lallai lafiyar INNO tana cikin hatsari, numfashi ta sauƙe tare da duban khalil tace. " Yaya khalil ba sai mun haɗa ƙarfi ba, ni kaɗai zan iya hana Mamma shan sigari insha Allah amma bazai yiwu ta daina lokaci guda ba dole sai a hankali." " Ba damuwa Jummo, Allah ya bamu Nasara, Jummo dan Allah ki dage kiyi ƙoƙari ki maida hankalin ki ga karatu, karki bani kunya dan Allah, nima monday zan koma Abuja wajen aikina." " Insha Allah Ya khalil bazan baka kunya ba, zanyi ƙoƙari sosai, Ya khalil dama a Abuja kake aiki to aikin me kake a can." " Ni jami'in soja ne, Jummo." Zaro idanunta Jummo tayi tace. " Cap hmmm!!! Soja mugaye ne fa yaya khalil" Dariya Khalil yayi tare da cewa. " Oh mu ɗin mugaye ne, to yanzu kinga nima na miki kama da mungu." " A'a kaikam kana da kir.............." " Khalil!!! Khalil!!! Kai Khalil!!!" Muryar Momy dake tsaye sama ne ya doki kunnen su, tana kiran sunan Khalil a fusace. Ɗago kansa khalil yayi ya kalli Momy tare da amsawa tsawa Momy ta daka masa tare da cewa. " Zancen uban me ka zauna kana yi da wannan tambaɗaɗiyar marar albarka!!!! Har dariya kake da ita?" Cike da mamaki khalil yake kallon Momy tambaɗaɗɗiya kuma, wai meyasa duk macen da yake so Momy bata sonta. " Tambaɗaɗɗiya kuma Momy ban gane ba."? Cike da masifa Momy tace. " Eh tambaɗaɗɗiya zaka gane idan na sauƙo na ci ubanka, ina ruwanka da ita meye haɗinka da ita da har zaka zauna da ita, to kul ka sake koda kallon tane ban yarda ba wallahi.!!" Garkuwa daya fito daga bedroom ɗinsa ne ya zo gaban Momy ya tsaya tare da harɗe hanunsa a ƙirjinsa yana sauraron abinda Khalil zaice. " Momy wai me kike faɗa hakane me jummon ta miki kike mata wannan munanan zagin." Jummo bakin ta taɓe tare da miƙewa tsaye ta ɗaga idanunta suka haɗa ido da Garkuwa, murmushi ya sakar mata tare da ɗaga mata gira ɗaya yana kanne mata ido, wani irin zubawa tsikar jikin Jummo yayi tare tare da jin sonsa ya taso mata murmushi ta saki tare da shigewa daga wajen tayi bedroom ɗin Mamma, murmushi Garkuwa yayi cikin ransa yana zayyano zumar da Jummo zatayi, duban Momy yayi tare da ƙara maida kallonsa ga khalil yace. " Ɗan uwa dan Allah rabu da zancen Momy, da alama dai yau Daddy ya kunnata ne shiyasa zata huce akan budurwar ka." Yayi Maganar yana dariya tare da kallon Momy, tsinkewa zuciyar Momy tayi tare da furta. " Budurwa kuma!!! Kai budurwar fa kace kana nufin Khalil ke son Jummo.?" Shima khalil murmushi yayi tare da kaɗa kansa, shi kuwa Garkuwa ya faɗi maganar ce kawai cikin wasa amma madadin ya cewa Momy wasa yake sai ma ce mata yayi. " Eh mana budurwar sa, ba kece kike so ya ƙara Aure ba, gashi dai ya samu budurwar ƴar cas da ita ƴar rugar su Daddy da Momy." Yayi Maganar yana dariya cike da masifa Momy zata fara zagin khalil kamar walƙiya taga baya wajen harya tashi, gira Garkuwa ya dagawa Momy yana shigewa nasa bedroom ɗin. Cike da masifa Momy take hargowa tana khalil ɗin zaizo ne ya sameta. Shi kuwa Garkuwa datar sa ya kunna yana dariyar Momy kasancewar sa mutum mai barkwanciya, facebook ya shiga ya gama abubuwan da zaiyi har zai kashe datar sai kuma ya shiga WhatsApp saƙonnin mutane ya fara dubawa wani yayi dariya wani kuma yayi tsaki MUSSAMAN na abokan aikinsa, saƙo na karshe daya saura wata baƙuwar Number ya gani wanda bai santa ba, shiga cikin saƙon yayi, video yaga an turo a hankali ya danna video ɗin, ya hau Reading ɗin buɗewa, harya buɗe, danna videan yayi, shigar su bedroom ɗin hotel ɗin ya fara gani shi da Sadiya zaro idonsa yayi yana cigaba da kallon, a matuƙar razane ya miƙe tsaye gumi na keto masa wani irin tashin hankali ne ya ziyarce sa, shine fa tsirara da Sadiya suna zina. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Hmmm!!! Na shiga Uku waye wannan waye ne yamin wannan ɗaukar!!!?" Hanunsa na rawa yake kallon wayar tare da runtse idanunsa yana jin zuciyarsa na tsinkewa, idanunsa ya kai kan profile ɗin ta, online ya gani alamun wanda ya turo saƙon yana online, da sauri hanunsa na rawa ya rubuta saƙo ya tura. " Please waye kai?" Safreena dake riƙe da wayar ce ta dubi Zee tana dariya ta tura masa. " Meye damuwarka da sanin ko ni waye.?" Runtse idanunsa Garkuwa yayi tare da tura mata. " Damuwata itace wannan video da ka turo min, dan Allah waye kai meye ribarka idan ka tozarta Ni, kuɗi kake buƙata to faɗi farashin ko nawa ne zan kawo maka ka goge ɗaukar." Kallon Zee safreena tayi tare da ce mata. " Kinga matsiyaci yayi zaton da namiji yake chat, shi fa zaton sa kuɗi nake buƙata daga garesa." Hanu Zee tasa ta amshi wayar daga hannun Safreena ta Rubutawa GARKUWA sako kamar haka. " Kai!!! Matsiyaci wanda bai san darajar Mace ba, kai kam idan ba Allah ne ya rufa asiri ba, zaka iya zina ma da uwarka, to bari kaji na faɗa maka, nafi ƙarfin amsar ƙazantattun kuɗi daga hanun ka, ka sani cewa wannan video sai na ya ɗasa a ko wacce kusurwa ta social media WhatsApp Facebook Twitter Instagram Snapchat etc da dai sauransu, sai na tona maka asiri duniya tasan ƙazantarka, sai na raguza farin cikin ka dan ubanka Buba, sai na saka ƙuda ma bazai bi FAMILYN ku ba shasha marar BASIRA." Wani irin gumi ne ya ketowa GARKUWA hankalinsa yayi mungun tashi cikin tsawa ya mata voice. " Wanene kai!!! Me kake nema dani!!!!!!!!!!!!!." Murmushi Zee tayi ta kuma tura masa. " Karka kuma min tsawa, ka fara lissafin kwanakin tozartar ka domin kuwa ta kusa, a ko wani numfashi da sakanni da zakayi a yanzu zakayi ne cikin tsinkewar zuciya da nadama, nine Ajalinka *IBRAHIM BUBA GARKO* Inkiyar ka GARKUWA Garko, ka sani farin sani na maka, hakan yasa bazan sha wahala ba wajen ganin ƙarshen ka." Tana gama faɗin haka ta kashe datar. Shuru Garkuwa yayi yana tunanin waye zai mishi wannan tozarcin lallai idan wannan videon ya fita shikenan ya gama yawo,( meye abinyi, anya kuwa ba Sadiya bace tayi wannan ɗaukar saboda na amince na aureta, tabbas Sadiya ce zata raina min hankali)......................." *To fa yau ake yinta wanda ta ɗauki videon daban wanda yake zargi dabam tabbas akwai tarin matsaloli da ƙalubale a cikin wannan gida shin waima wacece SAFREENA wacce irin cuta Garkuwa ya mata, shin Momy zatayi Nasara akan su Mamma gefe guda kuma ga ya khalil yana nuna alamun Soyayyar Jummo ita kuwa Garkuwa ne a ranta shi kuwa Garkuwa mungun nufin ya lalatawa Jummo rayuwa ne a ransa to waye zaiyi Nasara tsakanin su, shin Momy zata samu nasarar haɗin kan AUNTY Zarah, duka wannan amsar tana sanƙame cikin wannan littafin zaki sami wannan amsoshin da jarar kin biya Nairar ki 100 kacal domin kuwa Free Page ya ƙare bazaki kuma ganin wannan littafin ba sai kin sanƙamomin kuɗinki* *Ki biya Naira 100 ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko kuma ki turo hoton Mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan ki turo shaidar biya* *Ƴan payment group ina mungun alfahari daku ina jin daɗin comments ɗinku sosai Allah ya saka da alheri ya bar ƙauna UMMU NASMAH na sonku muah😘* *UMMU NASMAH CE*[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *wannan littafin na kuɗi ne bisa amana, idan kin san baki saya ba karki karanta min novel kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana, idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba.* *Payment group Only* ➰➰ *31 to 32* A matuƙar fusace Garkuwa ya fito daga bedroom ɗinsa idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, bedroom ɗin su Jummo ya faɗa tare da ƙwalawa Sadiya kira. " Sadiya!!! Sadiya!!! Sadiya!!!" Sadiya dake zaune tana famar chat da wayarta ne ta dago idanunta cike da tsoro ta mike tsaye tare da furta. " Lafiya Ya Garkuwa kake min wannan kiran." Cike da zafin rai gami da duhun kai yace. " Munafuka annamimiya kin san komai, harma tambayata kike lafiya, lafiyar uwarki, hanunta ya jawo tare da buɗe tafin hannunta ya ajiye mata wayarsa yace buɗe ki gani munafurcin da kika ƙulla min, wato nace bazan aureki ba, shine bari ki ɓullo min ta bayan gida saboda na aureki dole ko to kinyi ƙarya ki razana ni Wallahi Sadiya!!!". Shuru Sadiya tayi cike da mamaki take kallon Garkuwa harya idda Maganar (me kuma na masa ) Jummo dake zaune da kallon mamaki duk take binsu sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa Sadiya ke mata kallon banza a gidan taɓe bakinta tayi tare da kawar da kanta gefe, Garkuwa kuwa tsabar tashin hankali yasa idanunsa sun rufe kwatakwata bai lura da Jummo dake zaune a wajen ba, a hankali Sadiya ta saka hanu zata danna video ɗin sai kuma ta juya ta kalli Jummo, inda Sadiya tabi kallo Garkuwa ya juya yana kallo, saurin zaro idanunsa yayi (dama tana wajen). " Keeee!!!! Jummo tashi ki fita kibar bedroom ɗin nan muna magana." Taɓe bakinta Jummo tayi tare da miƙewa tsaye ta kalli Garkuwa tace. " Yo ni kuwa ina ruwana da zancen ku, waima kuwa anya kana da gaskiya dan dai ina hango tsantsar rashin gaskiya a tare da kai, amma koma menene idan tayi tsami ma ji, Oh su Oh Oh anyi asara anabin namiji ya Aure ni dole Allah ya sauwaƙa namiji ya zagi uwata na bisa koda shine autan MAZA, wanda dai bashi da zuciya yayi asara.!!" Tayi Maganar tana hararar Sadiya, Garkuwa haushi ne ya kamasa ya miƙa hanu da niyar jawo Jummo ya fasa mata baki, ta ruga da gudu tana cewa. " Yi hakuri malam bafa ni na kar zomon ba rataya aka bani.'' Bakinsa ya cije Garkuwa idanunsa sun dawo tamkar gauta ya jawo gashin Sadiya da ƙarfi sanda ta ɗan danna ƙara cike da tsantsar ɓacin rai yace. " Ki danna playing ki ƙara ganin abinda kika ɗauka, wato ni zaki tozarta Sadiya ni zaki ɗauka tsirara haihuwar uwata." Sadiya cike da azaba gami da rashin fahimta ta danna video ɗin, saurin toshe bakinta tayi tana zaro idanunta cike da tsoro zuciyarta ta tsinke hankalinta ya tashi. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! What waye ya ɗauki wannan videon, na shiga Uku idan aka ga wannan video kashina ya bushe, Ya Garkuwa waye ya turo maka."? Ɗauketa da mari Garkuwa yayi tare da furta. " Karki raina min hankali mana, ni zaki yiwa pretending ki nuna baki san komai ba, uban waye zai ɗauka idan ba ke ba, na ce uban waye zai ɗauka idan ba ke ba!!! Ni da waye mukaje hotel ɗin duk duniya bani da maƙiyin da zaimin wannan aikin, wannan aikin kine!!!!" Ya ƙarisa Maganar yana ƙara ɗauketa da mahaukacin mari, dafe kuncinta Sadiya tayi idanunta na zubar da hawaye cike da tashin hankali tace. " Ta yaya!!!! Ta yaya!!! Ta yaya kake tunanin zan ɗauki kaina tsirara duk rashin hankali na, na rantse da Allah daya busa min numfashi wallahi bani bace na ɗauki wannan video na rantse da Allah bani bane ka yarda dani yaya GARKUWA bani bace." Shuru Garkuwa yayi yana zubawa Sadiya idanu tsantsar gaskiya yake hangowa a ƙwayar idanunta, jikinsa ne yayi sanyi zuciyarsa ta ƙara tsinkewa, silalewa ƙasa yayi ya zauna daɓas a ƙasan tayels yana dafe kansa. " Na shiga Uku to wanene wannan wanene yake ƙoƙarin tozarta Ni, Waye shi Sadiya, me yake nema a gareni yaushe yayi wannan ɗaukar ban sani ba innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Tabbas ina cikin masifa." Shuru Sadiya tayi tare da zama itama ta dafe kanta tace. " Muna cikin masifa zakace ba kana cikin masifa ba, wannan video yana fita shikenan na shiga Uku na gama yawo, to ka kira layin wayar mana." Runtse idanunsa Garkuwa yayi tare da saka hanu ya ɗauki wayar, numbern ya kwafa daga WhatsApp tare danna kira switch Off yaji wayar. " Tana kashe" ya furta, shuru Sadiya tayi tare da cewa. " Abinda za'ayi yanzu shine mu jira zuwa Safiya mu gani ko za'a buɗe wayar." Tashi Garkuwa yayi ya tashi ba tare da yayi magana ba ya fice daga bedroom ɗin, nasa ya koma tare da shiga cikin WhatsApp ya tura mata saƙo kamar haka. " Ko waye kai dan Allah ina roƙon ka da karka watsa video ɗin nan a duniya ka faɗa min nawa kake buƙata zan bawa." Ya tura saƙon tare da Kwanciya ruf da ciki yana tunani, haka Garkuwa ya kwana cikin tashin hankali ko baccin kirki baiyi ba saboda tashin hankali. Washe gari da safe Jummo ta shiga kitchen da niyyar ɗaurawa Aunty Zarah breakfast, harta ɗaura towa ta saka ruwa, Zarah ta shigo, Jummo cike da murmushi tace. " Ina kwana Aunty Zarah." Da LAFIYA Aunty Zarah ta amsa tana haɗa fuska tare da cewa. " Kije kawai zanyi aikina ni kaɗai." Shuru Jummo tayi tana kallon Aunty Zarah girgiza kanta tayi tace. " Haba Aunty ban sanki da fushi ba, a tunanina duk inda gaskiya yake zaki bi bayansa, kin sani Momy ce bata da gaskiya a cikin wannan lamarin amma kike ƙin bin bayan gaskiya saboda kina tsoron Momy, Aunty Zarah tsoron Allah ya kamata kiji ba tsoron Momy ba." Shuru Aunty Zarah tayi tana kawar da kanta gefe tace. " Na sani Momy bata da gaskiya, amma ke yanda kika ɗauko naki salon gaskiyar ne baiyi ba yazo da rashin kunya da neman tarwatsa farin cikin gidan nan.?" " Hmmm!!! Aunty Zarah kenan meye ribata idan na tarwatsa muku farin ciki? Amma Aunty Zarah na tambaye ki, baki son a rusawa Momy farin cikin ta ko a rabata da ƴaƴanta? To meyasa ita kuma Momy take son ta raba Mamma da ɗanta bakiyi yunƙurin hanata ba, Saboda ita Mamma bata da gata ko bata buƙatar farin ciki ko, Momy kawai itace mai gata meyasa Aunty Zarah."? Shuru Aunty Zarah tayi jikinta yayi sanyi tabbas duk maganganun Jummo ta fita gaskiya, shuru tayi bata amsawa Jummo ba, murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Na sani zakiji kunyar amsa min wannan tambayar domin kuwa amsar bazata wuce son Zuciya ba, da neman gindin zama a wajen Momy, Aunty Zarah kema fa Momyn nan bakiji daɗin ta ba, da kike bin bayanta ke kanki bata ƙi ace yau ta koreki kinbar gidan nan ba, komai cikin ƙiyayya take miki shi a cikin gidan nan baki da ƴancin kanki a gidan mijinki sai abinda Momy taga dama kullum cikin zaginki take da aibata ki, amma yau ita kike bi kike ƙoƙarin ture gaskiya, ki sani duk hanyar da zaki bi idan ba ta gaskiya bane bazaki taɓa ganin dai-dai ba, kiyi tunani akan maganata ba rashin kunya ko gori na miki ba, na tuna miki abubuwan da kika manta ne." Jummo tana gama faɗin haka ta juya ta fice daga kitchen ɗin, Aunty Zarah sosai jikinta yayi sanyi jinginuwa tayi jikin bango tana tunani akan maganganun Jummo, tabbas gaskiya ta faɗa mata numfashi ta sauƙe tare da cigaba da aikinta. Ita kuwa Jummo bedroom ɗin Mamma ta nufa ta sameta zaune sai busa sigari take, haɗa fuska Jummo tayi tana tuno maganganun yaya khalil, zama tayi tare da cewa. " Mamma dan girman Allah ki yiwa Allah ki rage shan wannan sigarin, ki daina shanta kamar ruwa, ki dinga sha sau ɗaya a rana, babu kyau fa Mamma kuma kin sani, sannan tana lalatawa mutum kayan cikin sa." Kallonta Mamma tayi tare da cewa. " Eyyye!!!! Sannu malama Jummo yaushe kuma kika fara karatu, to bazan daina ba, bari kiji da sigari tana haifar da matsala da tuni ta kasheni tunda tun kafin a haifi ubanki nake sha, ba fa zan daina shanta ba, babu uban da ya isa ya hanani, ya lalata min kayan cikin mana ina ruwanki." " Mamma da ruwana mana idan kika shiga cikin wani hali ai nima na shiga Uku." Hararar Jummo Mamma tayi tare da cewa. " To ki zubar da ruwan naki kinga shikenan mun rabu, ni fa kin isheni." " Mamma dan girman iyayenki ki ajiye sigarin nan haka." Kashe sigarin Mamma tayi tare da cewa. " To mayya na ajiye karki cinye ni dan Allah." Murmushi Jummo tayi tace. " Yanda namanki yake da ɗaci Mamma ai bazan iya cinye ki ba." A hankali yake sauƙowa daga step ɗin jikinsa a mungun sanyaye tamkar wanda aka yiwa mungun duka, daining ya nufa ya zauna tare da cewa Momy da Daddy dake zaune. " Good morning." Daddy ne ya amsa da " Morning My son, lafiya na ganka cikin sanyin jiki haka." Momy tace. " Ai kuwa nima tambayar da zan masa kenan." Murmushin yaƙe Garkuwa yayi tare da cewa. " Bana jin daɗi ne Daddy kaina ke ciwo." " Subahanallah!!! Kasha magani."? Cewar Daddy. Kansa Garkuwa ya ɗaga alamun eh, ya khalil ne ya sauƙo shima ya zauna yana gaishe da su Daddy hanu ya miƙawa GARKUWA yana cewa. " Bro wai yaushe zaka koma kan aikinka ne, naga yau satina biyu da dawowa cikin gidan nan har zan koma jibi banga kana da niyar komawa ba." Numfashi Garkuwa ya saki tare da cewa. " Bros sai next week zan koma, amm Bros yaushe ne kam zaka dawo min da wannan kuftar da ka tafi da ita." Murmushi khalil yayi tare da cewa. " Oh Bro kai dai baka mantuwa insha Allah zan dawo maka dashi next time idan zan dawo hutu, wai ina Zarah tazo ta haɗa mana abincin nan mana so fa nake na fita da wuri." Bai rufe bakinsa ba sai ga Zarah seving ɗin kowa tayi sannan ta saka nataa, har sun fara cin abincin sannan Jummo da Mamma suka zo, Jummo Daddy ta gaishe CIKIN ladabi amsawa yayi fuskarsa a sake yana cewa. " Jummon INNO, INNO dai tayi kewarki sosai gaskiya nayi mamaki ma da ta iya bawa Mamma kyautarki." Dariya Mamma tayi tare da cewa. " Yo kaji min buba da wani zancen, ai kasan INNO babu abinda bazata iya mallaka min ba, ko ka manta tsakanin mune." Dariya Daddy yayi tare da girgiza kansa yace. " Ina kuwa zan manta Mamma, Mamma ya dai yanayin gidan da fatan dai kina jin daɗin zaman gidan."? Murmushi Mamma tayi tace. " Babu komai Buba gida alhamdulillah ina jin daɗi ba laifi amma dai a fita a hanci na idan ba haka ba zan yiwa matarka tsiya." Khalil ne ya ɗago kansa ya kalli Mamma numfashi ya sauƙe tare da kawar da kansa shi kuwa Garkuwa baima kula sha'aninsu ba, damuwarsa ne kawai a gabansa, Momy cike da baƙin ciki ta kalli Mamma ta rasa me yasa Mamma ta dami rayuwarta, kanta ta mayar ta cigaba da cin abincin ta, murmushi Jummo tayi tare da cewa Momy. " Ina kwana Momy?" Wani irin mungun kallo Momy ta wurga mata tare da cin abincin ta bata amsawa Jummo gaisuwar ba, Daddy cewa Mamma yayi. " Kiyi hakuri Mamma insha Allah za'a gyara." Khalil shine ya fara tashi daga daining ɗin yana cewa Jummo. " Jummo bari idan na dawo sai na gwada miki yanda zakiyi Amfani da wayar ko." Da to Jummo ta amsa tare da adawo lafiya, shima Daddy a dawo lafiya ya masa sannan ya fita, Zarah tabi bayan sa, Garkuwa yana zaune ya kasa cin abincin yaji ƙarar shigowar text ɗago wayar yayi tare da buɗe saƙon. *_ALBISHIR MALAM GARKUWA A YANZU HAKA INA NAN TSAYE ƘOFAR SHAGON UBANKA ALHAJI BUBA GARKO DA WANNAN VIDEO SHINE MUTUM NA FARKO DAYA DACE YA FARA GANI_* Wani irin zabura Garkuwa yayi gumi na keto masa ya furta. " *Whatttt* ................" Wannan littafin na kuɗi ne karki karanta min littafi ba tare da kin biya ba 08147537180 *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba 08147537180*. *Payment group Only* ➰➰ *33 to 34* Ɗaga idanun su Daddy sukayi suna kallon sa cike da tsoro, Momy ne ta furta. " What kuma!!! Meya faru waye ya mutu."? Cike da gigita Garkuwa ya sharce gumin sa, zuciyarsa na cinkewa cike da matsanancin tsoro, muryar sa na rawa yace. " Ba... Ba... Ba... Bakomai Ibrahim ne ya kirani wai Asiya bata da lafiya suna medical center tana cikin mungun yanayi." Ya ƙarisa Maganar yana runtse idanunsa zuciyarsa na harbawa, numfashi Daddy ya saki tare da furta. " Subahanallah!!! Lallai Asiya tana cikin jarabawa Ubangiji Allah ya bata lafiya, ni bara na fita kasuwa." Saurin dakatar da Daddy Garkuwa yayi yana cewa. " A'a Daddy am karka fita ya kamata yau ka zauna da Mamma kuyi hira tunda Mamma ta dawo gidan baku sami zama kun gana kunyi hira sosai ba, ya kamata yau ka zauna, idan yaso ni zan fita kasuwar." Kallon sa Daddy yayi cike da mamaki yace. " What!!!! Na zauna a gida kace, yaushe ka fara son fita kasuwa Garkuwa kai da ka tsani kasuwa yau kuma kake cemin na zauna kaika fita, no bazan zauna ba fita zanyi saboda ko da na barka ka je kasuwa bazaka min abinda nake so ba, so na riga na ware ranar da zan samu zama da Mamma ranar Friday, ka bari kawai zan fita." Dafe goshin sa Garkuwa yayi cike da tsantsar tashin hankali, idan har ya sake Daddy ya fita kasuwa yau ya shiga Uku kashin sa zai bushe asirinsa ya tonu, " ina bazai yiwu na bar Daddy yaje kasuwa ba" saurin kallon Mamma yayi yace. " Am Mamma ki yiwa Daddy magana mana ya kamata yau ku samu zama da Daddy kuyi hira yaji matsalarki, sannan ki faɗa masa damuwarsa, ni zanje ni kasuwar na zauna Allah Daddy duk abinda zakayi nima zanyi shi normal please Daddy." Momy zirawa GARKUWA idanu tayi cike da zargin sa, yanda ya dage sai famar magiya yake taɓe bakinta tayi, Daddy ne yace. " Garko anya lafiyar ka kuwa, waima kana da gaskiya kuwa, ka dage lallai karna fita, to me zai faru idan na fitan, kai bana son iskanci da zancen banza babu abinda zai hanani fita." Idanunsa Garkuwa ya rufe tare da cije leɓensa, wani irin takaici yake ji, ina ma zaiga wannan mai ƙoƙarin saka rayuwarsa cikin tagayyara wallahi da babu abinda zai hana ya kashesa, Mamma ne ta ce " Buba dan kawai yace ka zauna muyi hira shine kake masa wannan masifar har kake kiran maganar sa da zancen banza, zancen nawa ne na banza Yaro yana son kayi abin arziki ka samu lada kana kaucewa, shifa wannan yaron yafi dukkan yaran ka nutsuwa da hankali har uwar tasu, ita waccar Ashfarta take kowa da suna ka kaita can wata uwa duniya karatu inda babu mai kwaɓa sai yarinya ta lalace kuzo kuna danasani, to Buba nace yau babu inda zaka fita, ka zauna ina da magana da kai, kai Garko kaje kasuwan shi BUBA nace yau kan bazai fita ba." Numfashi mai nauyi Garkuwa ya saki yana dafe ƙirjinsa tare da furta (Alhamdulillah!!) A cikin zuciyarsa, murmushi ya saki tare da cewa Mamma. " Ke kin fahimce ni Mamma, ina son Daddy shima ya huta, ni gabaki ɗaya wannan satin ma zan ke fita kasuwar tunda ina hutu ba aiki nake ba, sai naje masa kasuwar dukka wannan satin." Murmushi Mamma tayi tace. " Allah dai ya maka albarka, muje Ina da magana da kai BUBA." Tashi Daddy yayi yana rankwashin kan Garkuwa yace. " Zaka dawo ka sameni ne ja'iri" Dariya Garkuwa ya yiwa Daddy, suka wuce shida Mamma itama Jummo tashi tayi tabar wajen, Momy ne ta kama kunnen Garkuwa ta murɗe tare da cewa. " Wannan dagewa da marairaicewa da kayi ba banza bane akwai dai lauje cikin naɗi." Dariya Garkuwa yayi tare da cewa. " Babu wani lauje cikin naɗi, dan kawai ɗa yace ubansa ta huta shikenan sai ya zamo da biyu, Momy akwaki da fassara." Murmushi Momy tayi tace. " Hmmm!!! Kuma halinka ne ban sani ba Garkuwa, sai ka tashi ka tafi ai tunda ka yi Nasara." Dariya Garkuwa yayi yana miƙewa tsaye tare da ɗaukar wayarsa ya fice yana dariya da adawo lafiya Momy ta masa sannan ya fita itama Momy nata bedroom ɗin ta shige tare da ƙwalawa Zarah kira Zarah da tun ɗazu ta shige bedroom ɗin ta ne ta amsa tare da fitowa ta shiga cikin bedroom ɗin Momy tana zaune bakin bed dinta ta sameta a ƙasa Zarah ta zauna tare da cewa. " Momy gani." Murmushi Momy tayi tare da gyara zamanta tana kwantar da murya tace. " Zarah so nake mu haɗa kai dake, domin kuwa a yanzu a cikin gidan nan na fahimci bani da kowa sai ke, sai yanzu nake danasanin abubuwan da na miki marassa daɗi, ban gane hakan ba sai yanzu da Mamma tamin nasan ina ƙuntata miki, ki yafemin Zarah." Murmushi Zarah tayi kanta na ƙasa tare da jin wani farin ciki ya sauƙa mata, taji daɗi sosai da Momy ta fahimci abubuwan da take mata basu da kyau, numfashi Zarah ta sauƙe tare da cewa. " Momy dama ban taɓa ƙullatanki a raina ba, dan haka na yafe miki Momy naji daɗi sosai da kika gane gaskiya." Murmushi Momy tayi tace. " Ba komai Zarah, zanyi Magana insha Allah a cikin satin nan za'a kawo ƴar aiki, mai wanke wanke da shara da kuma gyaran ɗaki girki kawai zaki dinga yi a cikin gidan nan, kinga ai aikin ya ragu miki." Sosai Zarah tayi farin ciki da wannan aikin da aka rage mata tana dariya ta yiwa Momy godiya, ba komai Momy tace tare da ce mata zata iya tafiya cike da farin ciki Zarah ta koma bedroom ɗin ta dama Momy ce kawai matsalar ta a gidan gashi kuma yanzu Allah ya kawo mata karshen matsalar ta. Momy bayan fitar Zarah murmushi ta saki tare da furta. " Da wannan zan fara yaudarar ki Zarah har sai kin amince dani kin shiga jikina Kafin na bullo miki da ƙudiri na wanda dole sao kin tayani yaƙi babu makawa." Ta ƙarisa Maganar tana sakin murmushi mai sauti. Shi kuwa Garkuwa cike da tashin hankali yake dreving, ya rasa ta ina zai fara solving ɗin matsalarsa, domin kuwa yaga alamun wannan video ɗin yana ƙoƙarin zamo masa barazana ga rayuwar sa, da wannan tunanin ya ƙarisa kasuwar, a ƙofar tafkeken makay ɗin mahaifin nasa ya yi parking tare da ɗaga kansa ya kalli serying boad ɗin wanda akayi rubutu da manyan baƙi, *ALH BUBA GARKO SUPER MARKET* numfashi ya sauƙe yana raba idanun ta ina zai za'a ɓullo kawowa Daddy saƙon video ɗin sai dai shuru harya shiga ciki baiga saƙon komai ba. Shuru shuru har dare yayi suka rufe shago babu saƙo babu alamar saƙon, harya dawo gida kuma alhamdulillah duk aikin da ya dace Daddy yayisu a shop ɗin Garkuwa yayi su, gida ya dawo a gajiye. Garkuwa yana kwance misalin goma da rabi na daren sai yaji shigowar saƙo saurin dubawa yayi. *_KAYI MAMAKIN KO, DA SAƘON BAI SHIGA HANUN UBANKA BA, TO KARKAYI TUNANIN KA TSALLAKE WANNAN TARKON DOMIN KUWA TARKON GABA BAZAKA SAN INDA ZAMU ƊANASA BA, INA SANE NA FASA BAWA UBANKA WANNAN VIDEO ƊIN SABODA NASAN HANKALINKA ZAI TASHI KAYI DUK YANDA ZAKAYI KA DAKATAR SHI DAGA FITOWA KASUWA, KUMA NASAN KO RANTSEWA NAYI BAZANYI KAFFARA BA, YAU BAKA BAR UBANKA YA FITA KASUWA BA, TO BA DABARAR KA BACE TASA VIDEO ƊIN BAI SHIGA HANUN SA BA, RA'AYINA NE KAWAI YASA NA FASA DA NASO VIDEO ƊIN NAN SAI YA SHIGO HAR CIKIN GIDAN KU A YAU SAI DAI BANSO HAKAN BA, KA KIYAYE TARKON GABA DOMIN KUWA ZUWAN SA BAZAI MAKA DAƊI BA_* text ɗin Garkuwa yabi da kallo yana tunanin wani mataki zai ɗauka, domin gano wanda ke masa wannan barazanar " *ABDUL JAY* " GARKUWA ya furta " shine kawai zai iya gano min ko wanene" ɗan cije bakinsa yayi tare da ajiye wayar ya miƙe ya shige tolet. Gyara zamanta Safreena tayi ta kalli Zee tace. " Na tabbata yanzu Garkuwa zaiyi yunƙuri gano wanda ke masa barazana yana da bala'in wayo zai iya gano mu, wani mataki kika dauka domin kaucewa gano mu a wajen Garkuwa." Murmushi Zee ta saki tare da cewa. " Ban shiryawa wannan mission ɗin ba, sai da na toshe dukkan wani Hanyar da Garkuwa zai gano kina raye, dalilin kuwa bana son ya gano mu yanzu har sai mun jijjiga sa ya wahala ya galaibata kafin mu bayyana masa kanmu muda kanmu, karki damu Garkuwa bazai taɓa gane mu ba duk wayonsa." " Hmmm!!! Shikenan Zee, na yiwa Garkuwa wani mungun shiri wanda zai girgizasa fiye da wannan girgizar da yayi, yanzu abinda zamuyi muyi amfani da layin wayarsa wajen gani dukkan wani motsinsa, mu dinga bibiyar duk wani kiran da zaiyi daga nan zamu gano duk wani binciken da zaiyi akan mu, mu kuma sai mu lalata masa dukkan wani shirinsa akanmu." Murmushi Zee ta saki tare da cewa. " Kin yiwa Abdul wanka ne Yakamata fa muje mu taro su Baba sun kusa sauƙa." Murmushi Safreena tayi tare da cewa. " Eh na shirya sa tun ɗazu amm dan Allah Zee karki sanar dasu Baba da Mama fansar da zan ɗauka idan Baba yaji zai hanani, tunda kinga cewa yayi na manta da Garkuwa a rayuwata, ni kuma bazan iya hakan ba dan Allah muyi komai cikin sirri ba tare da sanin su Baba ba." Numfashi Zee ta saki tare da cewa. " Karki damu Safreena bazan taɓa bari Baba susan abinda muke ba, na sani muddun Baba ya sani zai mana faɗa sannan ya hana mu, ni kuma bazan iya ganin Garkuwa yana farin ciki ba, bayan ke ya kassara miki rayuwa insha Allah har mu gama ɗaukar fansar mu Baba bazai sani ba." " Zee tabbas ke Aminiya ce ta gari ina jin daɗin zama dake Saboda kina ƙaunar dukkan farin ciki na, kina ɗaukar damuwata tamkar damuwarki, iyayenki sun rungumeni sun ɗaukeni ƴarsu bani da banbanci dake a wajen su sun mantar dani rashin iyayena, a wannan lokacin samun Irin Ahalinki yana wahala, na godewa Allah daya suturtani da samun wasu iyayen nagari bayan na rasa nawa." Murmushi Zee tayi ta dafa kafaɗar Safreena tace. " Babu godiya tsakanina dake Safreena, mun zamo Jini ɗaya yanzu ahali guda zan iya komai domin cikar muradinki..........." *INA NEMAN AFUWAR KU YAU NA MUKU READMORE KADAN WALLAHI YAU BANJIN DAƊI NE KUYI HKR* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba 08147537180*. *Na gode ƙwarai da gaske tabbas bani da bakin muku godiya ƴan uwana na cikin wannan group ɗin, ina mungun jin daɗin comments dinku kuna ƙara min ƙwarin gwiwwa Sosai ina yin ku OVER 🥰🥰* *Payment group Only* ➰➰ *37 to 38* Numfashi Shagari ya saki tare da gyara zamansa yace. " To amma Ya zakayi da Sadiya kasan dai Auren ka take so da gaske, ta fa mace a Soyayyar ka, taya zaka iya furta mata ka samu matar Aure." Bakinsa Garkuwa ya taɓe yana gyara zamansa ya dubi Shagari tare da cewa. " Wallahi bazan Auri Sadiya ba, na kuma faɗa mata ban ɓoye mata ba, bata da wata hujjar da zata ce na yaudareta." " To amma Garkuwa meyasa bazaka auri Sadiya ba meye aibunta, meye hujjar da ka dogara dashi cewa baka yaudare ta ba, meye hujjar ka." Murmushi Sosai Garkuwa yayi tare da cewa. "Hujjata itace Sadiya Daƙiƙiya ce marar lissafi, Sannan bata da kamun kai ko kaɗan wawiya ce mai saurin amincewa da abu mummuna ko mai kyau, bata da ilimin addini bare na boko, famko ce kuma ballagazar Mace, kaga kuwa rayuwa da Sadiya a matsayin Mata babban kuskure ne, dan haka bazanyi wannan kuskuren ba, nifa Shagari har ga Allah ban taɓa jin cewa ina son Sadiya da Aure ba." " Amma fa Garkuwa kana sane da abinda kake kuskure ne, kana lalatawa ya'yan mutane rayuwarsu, ba tare da duban gabanka ba, baka tsoron abinda kayi kaima a maka, ayiwa ƴarka ko ƴar uwarka, Garkuwa ina tsoron abinda zaije ya juyo maka fa, saboda kayi ɓarna da yawa." " Hmmm!!! Tabbas nayi kuskure sosai a rayuwata duk ban gane haka ba, sai sanda aka turo min da videon tsiraici na, har yanzu hankalina a tashe yake duk da na kwana biyu banji wani barazana daga waɗanda suka ɗauki video ɗin ba, hankalina ya kasa kwanciya, a dalilin wannan video ɗin, na fara gane kuskurena nasan duk sanda wannan video ɗin ya fita mutunci na kam babu shi ya ƙare kunya da baƙin ciki sune zasu zamo abokan mu'amala ta ina danasanin shiga hotel ɗin nan da nayi Shagari, amma kuma sai na godewa Allah da yasa sanadin wannan video naji na fara jin tsoron kunyar duniya, to kaga fa mutanen duniya ma na fara jin kunyarsu, ina kuma ga Ubangiji na, dalilin da yasa a cikin wata Uku naji na tsani zina ina kuma nadamar yinta." Numfashi Shagari ya sauƙe tare da cewa. " Fitar wannan video kam babban tozarta ne a gareka, amma nayi mamaki matuƙa, ya akayi wannan ɗaukar video da farko na zargi Sadiya, amma ka nuna min ba ita bace, gaskiya abun da mamaki, kaina ya kulle, kuma wanda yayi ɗaukar bai bar shaida ko guda ɗaya ba da za'a ganesa, hakan yasa nake mamakin yanda akayi wannan ɗaukar, ya kamata ka dawo hankalinka Garkuwa ka iya takunka ka guji mu'amala da mata domin sharrin su yana da yawa." " Hakane Shagari tun ranar da wannan video yazo wayata na daina bacci mai daɗi kullum na kwanta cikin fargaba nake dame zan tashi, daga Ranar na yanke ƙauna ga matan bariki, shiyasa na yankewa kaina hukuncin gara kawai nayi Aure, insha Allah na shiryawa gyara kuskurena, kuma ku tayani da addu'a." " Yanzu dai Sadiya ce ƙalubalen ka, da ita zaka fuskanci matsala idan taji labarin ka fidda matar Aure, ina ji a jikina zakuyi rigima." Murmushi Garkuwa yayi tare da duban Shagari yace. " Bana ɗaukar Sadiya a matsayin matsalata domin kuwa bani da contract ɗin Aure da ita." " Okay shikenan Allah yasa, kaga manager yace jirginka 4:30 zai tashi sai ka kintsa nima bari naje gida na watsa ruwa, Allah ya tsare." Da ameen Garkuwa ya amsa kafin Shagari ya fita. Ko da Jummo ta dawo cikin gidan Mamma harta dawo tana zaune ta tisa Momy a gaba sai famar mita take. " Ni dai Zainabu kin zamo min ƙaddara a rayuwata idan Banda ƙaddara taya zaki dameni ni da gidan ɗana, wannan ai baƙar mugunta ne, ki sanya a dafa taliyar nan ni dai kin san ba ƙaunarta nake ba, dan haka ya zamo dole ki shiga kitchen da kanki ki dafa min tuwo shi nake buƙatar ci kuma miyar kuka." Taɓe bakinta Momy tayi tana duban Mamma ta miƙe tsaye tare da cewa. " Kiyi haƙuri Mamma, babu garin tuwo a gidan nan ki ci abinda kika samu kawai." Zaro ido Meenat tayi tana kallon Momy cike da mamaki, Uwar mijinta take yiwa wannan tsiwar lallai akwai matsala, Mamma zabura tayi zata tsinke Momy da mari Jummo tayi saurin shiga tsakiyarsu marin ya sauƙa a fuskarta, take shatin yatsun Mamma ya fito ɓaro ɓaro a fuskar Jummo, girgizawa Mamma kai tayi tare da cewa. " A'a Mamma bai dace ki mareta ba, kiyi hkr ni zan shiga na tuƙa miki tuwon kiyi haƙuri dan Allah kibar Maganar." Mamma nuna Jummo tayi da yatsa tare da cewa. " Baki da hankali ne zaki tare mata mari ina ruwanki ki duba yanda na sharara miki mari a karin banza ke bada laifin komai ba, hmmm!!! Ke dai Zainabu wallahi Allah ya wadara................" Saurin dakatar da Mamma Jummo tayi... " A'a Mamma dan Allah karki ƙarisa kiyi shuru dan Allah kibar Maganar dan Allah na roƙeki." Kaɗa kanta Mamma tayi tare da juyawa ta shige bedroom ɗinta ranta a matuƙar ɓace, numfashi Jummo ta sauƙe dubanta ta kai ga Momy ranta a ɓace ta cewa Momy. " abinda baka so a yi maka karka yiwa wani, bakya son a rainaki amma ke kina rena na gaba dake, dan Allah Momy ki saduda ki sauya halinki ki zauna da Uwar mijinki lafiya, gidan duniya ne fa Momy idan kikayi haƙuri dole mutuwa zata raba tunda duk tsiya babu mai tabbata, haba Momy wani daɗi duniya ta miki ko ɗazu da kika saka aka turare mata ƙofar bedroom da hayaƙin bokayenki, bai isheki ba, har sai kin ƙara da saka mata damuwa hmmm!!!" Tayi Maganar cike da ɓacin rai, Momy mari ta ɗauke Jummo dashi tare da cewa. " Idan ana magana da masu gida dangi ɗaya bai kamata ke a matsayin ki na bare ki saka baki ba, karki manta alfarma kike ci a cikin gidan nan bamu da wata alaƙa dake dan haka ki shiga hankalinki ki daina wuce gona da iri, babu ruwanki a cikin harkar daba taki ba, shasha mai kama da buzaye." Jummo fuskarta ta riƙe tana jin zafin marin har cikin ƙwaƙwalwar ta, runtse idanunta tayi zatayi magana Meenat tayi saurin toshe mata baki, jan hanunta tayi suka haura sama, da mungun kallo Momy ta bita tana furta " shasha mai shiga shirgin da bai shafeta ba" A'illo dake tsaye tana ganin dukkan abinda ke faruwa ne ta goge hawayen daya zubo mata a idanunta, a bakin bed Jummo ta zauna tana sakin kuka mai cin ran gaske wanda tunda take a rayuwarta bata taɓa kuka irin haka ba, meenat zama tayi tare da dafa kafaɗar Jummo tace. " Ba kuka ya dace kiyi ba, haƙuri shine abinda ya dace dake Jummo kamar yadda kike ƙoƙarin gyara zamantakewar wannan gidan dan Allah karki sare ki jajurce a duk sanda ka ɗauko hanyar gaskiya kaƙe ƙoƙarin yinta dole sai ka haɗu da tarin matsaloli da ƙalubale meyasa Annabawa suka sha wahala? Saboda sunbi hanyar gaskiya ne suna nuni da a bita, dan Allah ki daina kuka, kuka na rago ne jarumi ba'a taɓa ganin hawaye a fuskarta." Hanu Jummo tasa ta goge hawayen ta, cikin muryar kuka tace. " Meenat na fara cire tsammani daga lamuran gidan nan da alamu Momy bazata sauya ba, bazata ragawa Mamma ba, ina tausayin Mamma bana son wani abu ya sameta, nayi ƙoƙarin nusar da Momy amma ta kasa ganewa, ki duba kiga yanda ta sauya Aunty Zarah daga mutumiyar kirki zuwa na banza, wannan abu ya ƙona min raina, hmmm!!! Shikenan meenat na daina kuka, muje ki tayani na yiwa Mamma tuwo." Tashi Meenat tayi suka shiga kitchen tare. Mamma tunda ta shiga cikin bedroom ɗin ta, take busa sigari idanunta sunyi jajur tunda take ranta bai taɓa ɓaci irin na yau ba, sosai take busa sigarin, Jummo cikin awa biyu suka gama tuwon har bedroom ɗin suka kawo mata turus Jummo ta tsaya tana toshe hancinta, tana bin kararen sigarin da Mamma tashi guda shida a jefe ga kuma ɗaya a hanunta tana zuƙa girgiza kanta Jummo tayi tare da nufo cikin bedroom ɗin ta ajiye plast ɗin tuwon, gaban Mamma tazo ta tsugunna tare da cewa. " Meye haka Mamma me kikeyi haka, Mamma bakya son lafiyarki ne, wai meyasa bazaki daina shan sigari bane!!!! Me kikeji a jikinsa!!! So kike ki kashe kanki ne!!!! Meyasa kuke sani cikin damuwa ne!!!! Dan Allah kubar ƙwaƙwalwata ta huta na roƙeki Mamma na haɗaki da Allah ki rabu da sigari dan girman Allah kimin wannan alfamar wannan dan Allah Mamma!!!!" Ta ƙarisa Maganar tana sakin kuka mai sauti harda shashsheƙa yasar da sigarin Mamma tayi tana binta da kallo tunda Jummo ta data take tafiya bata taɓa ganin kukan Jummo ba sai yau lallai duk abinda ya koro ɓera daga rami ya faɗa kasko yafi wutar zafi, yasar da sigarin Mamma tayi tare da jawo Jummo jikinta muryarta a matukar sanyaye tace. " Ban taɓa ganin kinyi kuka ba tun kina ƙarama sai yau, dama haka kike jin zafi duk sanda nasha sigari, da nasan haka ne da na daina tuntuni, Jummo a kaina kike yaƙi a cikin gidan nan kowa ya tsaneki saboda ki nema min farin ciki a cikin gidan ɗana, to meyasa ni kuma zan kasa miki alfarma, in dai nine daga yau na miki alƙawari na daina shan sigari bazan kuma ba har abada na daina, ki share hawayenki zan zubar da dukkan sigarin dake cikin bedroom ɗin nan idan har hakan zaisa kiyi farin ciki." Share hawayenta Jummo tayi tana murmushi tace. " Muddun zaki daina shan sigari Ni kuma insha Allah zan daina kuka bani da burin daya wuce naga kin daina shan sigari kin zama cikakkiyar mutum wannan shine burina." Shafa kanta Mamma tayi tana murmushi tace. " Insha na daina Jummo, Allah ya miki albarka kina matuƙar kula da rayuwata." Murmushi ta saki tare da cewa. " To ganan tuwon na miki sai kici Meenat muje" Tashi Meenat tayi tana dariya tace. " Mamma da Jummo sai Allah." Jummo MEENAT ta raka har bakin get ta tafi sannan ta dawo. Da daddare Jummo tana zaune tana assignment taji motsin mutum a kanta idanunta ta ɗaga ta kallesa ya zuba hannayensa a aljihu fuskarsa cike da murmushi ya zauna bakin kujerar ya furta. " Kin assignment ne?" " Eh ya khalil, yau ka dawo gida da wuri, ya aikin"? " Aiki ba daɗi Jummo, saboda kullum cikin matsala da tunani aikin mu yake, bamu rabuwa da case sai dai kawai muce alhamdulillah!! Kinyi kyau fa naga sai haske kike ƙarawa meye sirrin?" Murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Kai Ya khalil babu wani kyau dana ƙara kawai idanunka ne suka gane maka haka, amm ya khalil, ya Garkuwa bai dawo ba har yanzu Kuma naga yana rigaka dawowa.?" " Oh Bro bazai dawo gida ba yau yana Ingila yau jirginsa nan yayi, maybe sai gobe ya dawo, aikin su ya gaji haka ba ko yaushe suke kwana a Nigeria ba." Numfashi Jummo ta sauƙe tare da ajiye biron hanunta tana duban Ya khalil tace. " Shi kuma haka nasa aikin yake, to Allah ya dawo daahi lafiya, amm ya khalil akwai Maganar da nake ta son muyi da kai Allah yasa zaka fahimce ni." " Ina jinki Jummo, insha Allah zan fahimce ki." " Ya khalil wai meyasa bakwa kula da Rayuwar Mamma a nan gidan ne, bakwa tarairayar ta bare ku san matsalarta da abinda take so da wanda bata so bakwa zama kuyi hira da ita, ko kun manta hira cikin iyali yakan ƙarawa dangi son juna ya kuma ɗebe musu kewa, shi kansa Daddy ba wani kula yake da ita ba yafi bawa kasuwarsa MAHIMMANCI yau wata Biyar da dawowan mu cikin birni Daddy bai zauna da Mamma yaji damuwarta ba, sunyi hira irin na ɗa da uwa, ko da na minti goma ne, baiyi ba, kunyi watsi da ita tamkar ba kakar ku ba, ita kanta Momy bata ƙaunar Mamma bare ta kula da ita wannan wacce irin rayuwa kuke a gidan nan babu shaƙuwa da ƙauna tunda nazo gidan nan ban taɓa ganin kun taru kun zauna kuna hira ba a matsayin ku na family ɗaya, kowa ya ware kansa rayuwarku kawai kuke yi, to meye amfanin dawowar Mamma daga Birni idan bazaku kula da ita ba, da alamu Mamma tafi samun farin ciki a ƙauye, meyasa haka.?" Saurin kallon Jummo Ya khalil yayi sai kuma jikinsa yayi tabbas su a cikin gidan su kowa rayuwarsa yake babu ruwan wani da damuwar ɗan uwansa, ( tabbas Jummo tana da hangen nesa da zurfin tunani a ɗan zaman da tayi a gidan nan harta fahimci halin da suke ciki) hanunta Zarah ta naɗe tana ƙare musu kallo idanunta ta kanne ranta a matuƙar ɓace ta juya bedroom ɗin ta, nisawa ya khalil yayi tare da duban Jummo yace. " Kinyi tambaya mai kyau Jummo kina da tunani da hangen nesa tabbas duk abinda kika faɗa gaskiya ne, a yanzu bani da bakin da zan kare kaina, sai akan Mamma ya danganta da rashin shaƙuwar dake tsakanin mu da Ita wanda Momy itace ta jawo wannan rashin shaƙuwar, bata da alaƙa mai kyau tsakanin ta da Mamma, ASALi ma bamu san muna da kaka ta wajen uba ba, sai da muka girma, Daddy yake faɗa mana har yakan kai Garko garin ku, amma ni sam Momy bata bari aje dani na rasa dalilin hakan, tun ina jin haushi ana kai Garko ni ba'a zuwa dani, harna daina jin haushi nima na daina damuwa, sai sau ɗaya Munje kaltungo da Garko sai yace mubi, ban masa musu ba mukaje, shine kawai zance miki naje CILO naga Mamma daga nan ban kuma zuwa ba, wannan shine rashin shaƙuwar mu da Mamma, a ko yaushe Momy na yawan ce mana...................." Muryar Momy da ta doki kunnensa itace ta hanasa ƙarisa Maganar da yayi niyya, saurin ɗagowa sukayi suna kallonta. " Uban me kake yi anan Khalil tazo ta tisaka a gaba tamkar zata haɗiyeka, mayya to kurwar ƴaƴana kur tafi ƙarfin ki, kai kuma tashi ka shige bedroom ɗinka sususu ta saka gaba sai kashe maka murya take za'a cuceka, to ki fice min a harkar ƴaƴa." Ya khalil cike da ɓacin rai yace. " Momy amm..............." " Rufe min baki ce maka nayi ka tashi ka tafi bedroom ɗinka, ko bazaka tashi bane."? Tashi Ya khalil yayi yana duban Momy cike da haushin ta katse musu hirarsu ya shige, kanta Jummo ta mayar ga assignment ɗinta tana nemawa Momy shirya, ita kuwa Momy shigewa kitchen tayi. Ya khalil koda ya shiga bedroom ɗinsa Zarah ce tsaye tasha gabansa cike da masifa tace. " Dakata Malam!!! Fice min daga room ka koma inda ka fito." Baki sake ya khalil yake duban Zarah, tare da furta. " Whatttt!!! Me kike faɗi hakane, banson wasa yanzu matsa ki bani waje." " Malam ni ba wasa nake maka ba, Nace ka fita kabar min room ka koma inda ka fito!!!" Murmushi Ya khalil yayi yana cewa. " Saboda sanda aka Auro ki, kinzo da room daga gidan ku ko, dallah matsa min na shige da alamu notukan kanki ya fara sincewa.!!!" Rai Zarah ta haɗa tana riƙe kunkumi tace. " Idan kaga dama ka kirani mahaukaciya ma, amma Wallahi yau bazaka kwana a cikin room ɗin nan ba, sai dai ka koma wajen waccar matsiyaciyar Jummo da kaje ka zauna a gabanta kana sakin murmushi sai kaje ku kwana gado daya da ita amma ba dai wannan room ɗin ba.........." *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *41 to 42* Miƙewa tsaye tayi cike da tashin hankali ta fito daga class ɗin, staff room ta nufa tare da sanar da malamin su, cewa bata jin daɗi zata koma gida, cikin gaggawa ta fito daga makarantar ta tsaya bakin titi tana jiran adaidaita, ta ɗan juma kafin ta samu adaidaitan Allah Allah take ta iso gida domin kuwa har yanzu zuciyarta bata daina tsinkewa ba. Momy kuwa cikin gaggawa tazo ta goge maganin daga ƙofar room ɗin Mamma, tamkar ba'a zubar da komai ba, da sauri ta koma room ɗin ta tana dariya ta rufe. Tana buɗe door ɗin ta ci karo da Mamma zube a ƙasa idanunta sun kafe, cikin tashin hankali Jummo ta kurma ihu, da gudu ta sunkuya tare tallafo Mamma tana " Mamma!!! Mamma!!! Mamma dai!!!! Meyasa meki!!! Ki tashi Mamma!!! " Hanunta Jummo ta ɗaga taga yayi lakwaf ya faɗi ƙasa, zaro idanunta tayi tana zubar da hawaye, kanta ta ɗaura a ƙirjin Mamma nan ma taji shuru ba numfashi, da karfi Jummo tace. " Momy!!! Momy!!! Mun shiga Uku!!! Momy kizo Momy!!! Mamma ta mutu?!! Na shiga Uku." Tayi Maganar tana sakin kuka mai sauti tare da zama daɓas a wajen Aunty Zarah ce ta fito da gudu tana cewa. " Subahanallah!!! Lafiya meke faruwa." " Aunty Mamma ta mutu Aunty Zarah, na shiga Uku" Cike da kiɗima Aunty Zarah ta dago hanun Mamma sakewa hanun yayi ya faɗi ƙasa, shuru Aunty Zarah tayi tana, ɗaga wayarta ta kira Khalil itama a gigice, sosai hankalin Khalil ya tashi, cikin sauri ya bar dukkan abinda yake ya taho gida, Momy duk abinda ake tana ji, bata fito ba, sai Sadiya da ta fito itama ta tsaya gaban Mamma, Jummo Sosai take kuka, idanunta ne suka sauka akan bakin Mamma dake zubar da wani irin kumfa fari sol, ƙafafuwan Mamma ta kalla da yake jiƙe da wani farin ruwa tamkar Madara, hanunta ta kai tare da shafo ruwan ta shinshina wani irin wari ne ya doki hancinta, saurin matsar da hanun tayi daga hancinta tamkar zatayi amai, shuru tayi cike da nazarin menene Mamma ta taka haka, anya kuwa ba kashe Mamma akayi ba, hawaye ne suka zubo mata, AUNTY Zarah ce tace. " Sadiya ki haura sama, ki cewa Momy ta fito Mamma ta mutu." Da to Sadiya ta amsa tare da haurawa ta dinga bugawa Momy door, cikin munafurci Momy ta fito tamkar wacce ta tashi daga bacci, tace. " Menene haka kike doka min ƙofa tamkar zaki ɓallata, mtss kina da damuwa fa Sadiya bacci nake amma sanda kika tashe ni." " Momy Mamma ce fa ta rasu, shine Aunty Zarah tace nazo na ta da ki." " Mamma kuma!!! Tana ina Mamman!!! " Tana falo" Sauƙowa Momy tayi Sadiya ta biyo bayan ta, Gaban Mamma ta sunkuya tana ƙare mata kallo hanu tasa a ƙirjin Mamma taji shuru ba numfashi, ɗan zaro idanunta Momy tayi cikin zuciyarta ta ayyana ( karfa matar nan, ta mutu) numfashi taa sauƙe tare da ɗago kanta ta kalli Zarah tace. " Shiga room ɗina ki ɗauko min wayata zan kira daddyn ku." Da sauri Zarah ta tashi ta haura, khalil ne ya shigo da mungun sauri gaban Mamma ya sunkuya shima tare da saka hanu a hancinta, numfashi ya jiyo tanayi kaɗan kaɗan. " Bata mutu ba" ya furta yana ɗaga caɗak ya fita da ita cikin hanzari bayansa Jummo tabi da gudu, Joseph khalil ya ƙwalawa kira tare da cewa ya shiga mota, buɗe masa motar Joseph yayi suka shiga shida Jummo, sannan shima Joseph ya shiga yaja motar da gudu suka bar gidan, asibitin *AA ARMAN HOSPITAL* suka nufa, da sauri Norse suka taho da gadon tura MARASSA lafiya, aka ɗaura Mamma emargency room aka nufa da ita, tsayawa Jummo sukayi bakin emargency ɗin Khalil ya goya hanunsa a bayansa sai kaiwa da komowa yake, Jummo idanunta na hawaye tace. " Ya khalil!!! Anya kuwa Mamma zata tashi jikina ya bani na ɗebe tsammani daga rayuwar Mamma ya khalil......." Hanu KHALIL yasa ya toshewa Jummo baki yana girgiza mata kai yace. " Ki daina mungun baki babu abinda zai samu Mamma zata tashi, ki mata addu'a kawai shi take buƙata a wajen mu." Shuru Jummo tayi tare da zama a kujerun dake jere wajen, zuwa jumawa kaɗan Momy da Aunty Zarah suka zo, Momy ne tace. " Ya dai Khalil ta farfaɗo kuwa.?" " A'a Momy doctor bai fito ba tukunna bamu san halin da rake ciki ba." Zama Momy tayi ba tare da tace komai ba, Shuru shuru ba'a fito da Mamma ba tun ana awa ɗaya har yanzu wajen awanta shida a ciki babu wani labarin halin da Mamma take ciki sosai hankalina l Jummo yake tashe, Daddy kam shigowarsa yafi kowa shiga cikin tashin hankali, yayi mamaki matuƙa da akace wai kawai ganin Mamma akayi ta faɗi bayan lafiya lau ya fita ya barta, Doctor ne ya fito fuskarsa shakaf da gumi,. " Ku sameni a office" ya furta yana shigewa, Daddy da ya khalil ne suka bi bayan sa, koda suka shiga cikin office din wajen zama doctor ya nuna musu bayan sun zauna ne doctor yayi gyaran murya tare da cewa. " Waye ɗanta cikin ku"? " Ni ne" daddy ya furta. " Okay am gaskiya munyi duk wani gwaje gwaje daya kamata mu mata bamu ga komai ba komai lafiya normal yake nuna mana, mun kasa gane meke damunta tana nan dai har yanzu a yanda take babu wani sanji." Kansa Khalil ya dafe cikin tashin hankali, duban doctor yayi tare da cewa. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati!!!! Doctor ba abinda yake damunta kuma, to meye mafita kenan doctor.!!" " Anan bamu da wata mafita gaskiya, da zan faɗa muku gaskiya ku ɗauka, to dana baku shawara cewa kuje kuyi maganin gida, matsalarta bata asibiti bace idan kuma kun ki to ko wani asibiti zakuje sai dai kawai suci kuɗin ku kawai a banza saboda babu wani ciwon da ya danganci maganin asibiti." Shuru Daddy yayi kasancewar ya yarda da asibitin sosai ya sashi yadda da shawarar doctor, fitowa sukayi tare da sakawa aka turo Mamma CIKIN mota aka sakata, suka koma gida koda Jummo taji cewa maganin Mamma ba'a asibiti yake ba hankalinta ta tashi ƙwarai, bedroom ɗin ta aka maida ta, a ranar ana cikin wannan jimamin, Garkuwa ya dawo sosai shima hankalinsa ya tashi itako Momy ko a jikinta, a Ranar Jummo ce ta kwana akan Mamma bata samu ta runtsa ba domin kuwa babu wani sauyi daga Mamma ko motsi batayi sai numfashi kawai dake fita da ƙyar, A'illo har tafi Jummo shiga tashin hankali, washe gari da safe babu wanda ya iya breakfast cikin Jummo da A'illo har Daddy, bayan an gama breakfast ne Jummo ta dubi Daddy tare da cewa. " Daddy ina so ya Garkuwa zai kaini CILO" Garkuwa da Khalil har Daddy idanu suka zubawa Jummo Daddy ne yace. " Jummo me zakije kiyi a cilo.?" " Daddy zanje wajen Baffana da INNO ne, INNO tasan maganin gargajiya sosai daga na sammu harna mungun baki, dana aljanu, duk wani ciwon da ba'a gane kansa ba, ita INNO tana iya maganinsa da izinin Allah, shi kuwa Baffa yana taimakawa da addu'o'i kasancewar sa babban malamin addini, zanje musu da Maganar ko Allah zaisa mu dace." Murmushi Daddy yayi tare da cewa. " Haka fa akayi INNO na bada magani aini na manta kwatakwata, tayiwa wasu ma bare aminiyarta Mamma, GARKO ka shirya maza kuje CILO ku taho da INNO." Saurin ɗago kanta Momy tayi a gigice ta kalli Jummo cike da tsanarta, tabbas tasan waye INNO kamar yunwar cikinta Momy tana mungun tsoron INNO domin kuwa bata raga mata, INNO macece wacce take da. Mungun kwarjini gata da masifa, numfashi Momy tayi cikin tashin hankali, a hankali ta furta. " Amma!!! Alhaji sai nake ganin ba sai mun nemo INNO ba, tana zaune cikin iyalanta mu ɗaga mata hankali ni a nawa tunanin me zai hana bazamu nemi wani mai maganin anan ba, akwai wani mai bada magani aikinsa yana da kyau kawai mu nemo sa ba sai mun ɗauko INNO." Shuru Jummo tayi cike da zargin Momy domin kuwa tana ji a jikinta Momy ce sanadin ciwon Mamma Daddy ne yace. " Babu abinda INNO bazata iya yiwa Mamma ba, dan haka INNO zamu kira bama buƙatar shawara, Jummo bari Garko ya shirya ku tafi ko." " To Daddy" GARKUWA miƙewa yayi tare da cewa "bari naje na shirya sai mu tafi." Zuciyar Momy babu abinda yake idan ba tsinkewa ba, dole ta nemi mafita kafin INNO tazo garin nan, to meya kamata tayi? ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ " Zee ni fa na saka a sincewa Garkuwa tayar motar sa, bana ƙaunar ganin sa a duniya, Zee na fara gajiya da bibiyar layin sa, da alamu lokaci na nake ɓatawa a banza dan haka gara kawai shima ya mutu yabi bayan su Ummi." Cike da MAMAKI Zee take kallon SAFREENA, tare da cewa. " Ba kida hankali ashe Safreena, kisan kai zakiyi, Safreena kisan kai zakiyi, meyasa bazaki ɗauki mataki cikin lumana ba, sai kinyi kisan kai ki ɗauki duk zunubin sa ki ɗaura a kanki tabbas baki da hankali......." " Kwarai kuwa bata da hankali ko kaɗan." Da sauri suka juyo suna kallon inda Maganar ta fito, Aunty Batul ce tsaye ƙanwar Mama da suka taho tare da Mama, zaro idanu sukayi cike da tsoro, zama a gefen bedroom ɗin Aunty Batul tayi tare da cewa. " Safreena kina ƙoƙarin kashe uban ɗanki ko meyasa Saboda kawai ya miki cikin shege kin haihu." Girgiza kanta SAFREENA tayi idanunta na zubar da hawaye tace. " A'a ba Saboda kashe min iyaye da ya saka akayi, shiyasa nima zan kashesa." " Ba Garkuwa bane ya saka aka kashe iyayen ki." Kallon Aunty Batul tayi tace. "Whatttt!!!" "Ƙwarai kuwa kawunki Ibrahim yasa aka kashe su, saboda ya mallaki dukiyar mahaifinki, Kuma buƙatar sa ta biya tunda ya mallaki rabin dukiyar mahaifinki, bari na baki labarin abinda ya faru kuma ina da shaidar da mahaifiyarki Ummi ta bani, shi dai Garkuwa kunyi takun saƙa dashi akan dole sai kin zubar da cikin jikinki, kika ƙi, dalilin haka ya miki barazana sai ya kasheki da iyayenki muddun baki zubar da cikin ba, sai Kuma Maganar sa, ta zo da mutuwar iyayenki shine ya taka sawun ɓarawo, shiyasa akace baki shike yanka wuya, furta mungun kalma kan saka mutum cikin hatsari, amma a zahiri ba Garkuwa bane yayi kisan, akwai wata Rana ranar talata dana shiga gidan ku. 🤔🤔 *Tuna Baya* "Assalamu alaikum" Ummi dake zaune ta haɗa tagumi ne ta amsa da ameen "wa'alaiku mussalam Batula kece yau a ƙasar tamu" " Nice Ummi, tun jiya ai na shigo." Ɗan dariya Ummi tayi tace. " Masha Allah sannu da zuwa, dama kuwa Batula ina neman ki." " To Ummi Allah dai yasa ba laifi nayi ba, Ummi nama ga jikinki duk a sanyaye tamkar wacce kike cikin damuwa.?" " Hmmm!!! Ke dai Batula bari, ina cikin tashin hankali, Batula ashe dama dukiya idan tayi yawa tana jawo tashin hankali da rashin kwanciyar hankali, Batula a zamanin da muke ciki yanzu kar kace zakayi ƙoƙarin zama shahararren mai kuɗi, kayi ƙoƙarin zama mai rufin asiri, idan kuma har Allah ya azurtaka da kuɗi masu yawa to ka boye sirrinka, saboda kuɗi masifa ce." " Subahanallah Ummi meyasa kika faɗi haka." " Bani wayarki Batula zan baki wata Amana saboda na amince da ke dan Allah Batula karki ci amanata.?" Wayar Batula ta miƙa mata tana cewa. " Insha Allah Ummi bazan taɓa cin amanarki ba, zan riƙe sirrinki." " Batula ga wani record na tura miki a cikin wayarki wannan recording ɗin su Kawu Ibrahim da Alhaji Ahmed na ji suna tattauna wannan maganar, sun shirya zasu kashemu akan su mallaki dukiyar Alhaji, nayi ƙoƙarin dakatar dasu amma sun min barazana muddun na faɗawa wani cewa zasu kashemu to Wallahi sun saka an ɗauki, Hajiyata da Yaya Safwan ina tona musu asiri zasu saka a harbe su Hajiyata, sai dai abun baƙin cikin ban san yaushe zasu kashemu ba, na gwammaci ni da Alhaji da Yarana mu mutu dana rasa rayuwar mahaifiyata da ɗan uwana, wannan recording ɗin basu san nayi ba, saboda basu ma san akwai waya a jikina ba, duk sanda aka nemi bincike akan mutuwar mu, ki bada shi a matsayin shaida, dan Allah na roƙeki karki sanar da kowa wannan maganar saboda Rayuwar mahaifiyata dan Allah Batula." Ta ƙarisa Maganar hawaye masu zafi na sauƙa a fuskarta, sosai batula taji tausayin Ummi tare da mata alƙawarin ɓoye wannan sirrin. ******************* Kallon SAFREENA Aunty Batul tayi ta cigaba da cewa. " Kinji abinda ya faru, Safreena bayan nabar gidan ku, da daddare misalin 1:00pm ina tsaye a saman benen mu da idanuna naga Alhaji Ibrahim ya watsa fetur cikin gidan ku tare da cinna wuta a lokacin nine nayi ihun gobara amma sai dai kash sanadin kayan wuta dake cikin gidan ku kafin a kawo muku ɗauki tuni wutar ta mamaye gidan, banyi tunanin kema zaki fita da rai ba sai kuma Allah ya kuɓutar dake kika fito, Safreena wallahi ba Garkuwa bane ya kashe miki iyaye, nine kaɗai nasan haka hatta Baba Bai sani ba, kin ɗauki laifi kin ɗaurawa Garkuwa, gashi yanzu kinsa an sunce masa tayar motar sa ya zakiyi da haƙkinsa idan ya mutu ta sanadinki?." Tunda Aunty BATUL take Wannan Maganar Safreena take kuka mai cin rai tare da jin wani irin tsanar kawo Ibrahim miƙewa tayi zunbur tana kiran mai gadin gidan su GARKUWA da ta saka ya sunce masa tayun mota, switch Off taji wayarsa a kashe zaro idanunta tayi cike da tashin hankali ya zata dakatar dashi, gyalenta ta zara cikin sauri ta fito, gidan su Garkuwa zata ta faɗa masa ta sa an sunce tayar motar sa karya hau. Shi kuwa cikin shirin sa ya fito tare da yiwa Momy da Daddy SALLAMA ya cewa Jummo. " Mu tafi ko................" 🙊🙊 Tirƙa tirƙa cap ko ya zata kasance Safreena zata iso gidan su Garkuwa kuwa kafin ya tafi? Nima ban sani ba mu haɗu next page🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba*. *Payment group Only* ➰➰ *35 to 36* Bayan Wata Uku Abubuwa da yawa sun faru, a tsakanin waɗannan watannin, inda Jummo tayi jsce ɗin ta cikin Nasara har khalil ya jona mata Senior secondary school, ta fara zuwa mai mata extra lesson ma yana zuwa sosai Jummo ta mai da hankali ga karatun ta, tana ƙoƙari fiye da tsammani, a yayin da ƴar tsama kuma ta cigaba da wanzuwa tsakanin Momy da Jummo, Jummo tayi wata ƙawa mai suna Amina, Amina macece mai tsantsar kamun kai da riƙe ajinta, ƴar gidan Captain Ahmad Surah, aminta ce sosai tsakanin su, inda Zarah kuwa tuni Momy ta ci galba a kanta sun haɗe kansu ya zamanto yanzu Aunty Zarah ko inda Jummo take bata kallo gaba take da ita sosai, a yayin da Jummo itama ta fice harkar Aunty Zarah domin kuwa ta fuskanci inda ta saka gaba, sai dai har yanzu Soyayyar Garkuwa tana nan maƙale a zuciyar Jummo, shima ya khalil ya nemi TRANSFER ya dawo Gombe gaba ɗaya da aiki sosai yake bawa Jummo kula yanda ya dace, haka yake yawan mata kyauta kuɗi ne kayan kwalliya da sauransu yanzu haka Jummo ta waye sosai idanunta sun buɗe, shi kuwa Garkuwa, ya koma kan aikinsa kwatakwata baya samun lokacin kansa shine fita ƙasashen waje kasancewar sa matuƙin jirgin sama, har yanzu SAFREENA bata ƙyale rayuwarsa ba, kullum cikin bibiyar dukkan lamarin sa take, duk wani wayar da zaiyi sai jita hakanne yasa take samun dukkanin wasu sirrikan sa, Sadiya kuwa bata fasa watsewa da Garkuwa ba kullum tana maƙale masa tamkar cungam, inda shi kuma yake garata yanda yake so, Mamma a yanzu shan sigari dinta a cikin kashi ɗari babu hamsin ta rage amma fa kullum cikin yiwa Momy masifa da takura take, wannan kenan. ✨✨✨✨✨✨✨✨ Da sauri take sauƙowa daga step ɗin, tasha baƙar doguwar riga mai ratsin fararen stone ƙafarta sanye da farin takalmi yayin da ta yane fuskarta da farin gyale ɗan ƙarami sosai tayi bala'in kyau ta kuma ƙara gogewa, har zata wuce sai ta jiyo tamkar ana ambaton sunan Mamma dakatawa tayi daga tafiyar a hankali ta leƙa kanta, Aunty Zarah ce tsaye bakin bedroom ɗin Mamma hanunta riƙe da kasko tana ambaton sunan Mamma tare da wani irin surkulle murmushi Jummo tayi, ta sauƙo a hankali ta tako har bayan Aunty Zarah hanunta ta saka ta dafa kafaɗar Aunty Zarah a matukur razane Aunty Zarah ta juyo tana raba idanu zatayi magana Jummo tasa hanu a bakinta tace. " Shishsh!!!! Karki ɗaga min murya bare Mamma ta jiyoki kashinki ya bushe, 0h ni Jummo, mtss!!! Wai Zarah meyasa ke baki da zuciya ne kam meyasa kika rikiɗe daga mutumiyar kirki kika dawo ta banza, hmm!!! Yanzun shi wannan tsafi banzan naku har kuna tunanin zai kama Mamma ne, hmmm shirmen banza cigaba dayi karki fasa mu gani ko zai kama Mamman, hmmm!!! Wai mutumin daya nuna maka ƙiyayya a bayane yanzu zai dawo yace yana sonka kuma harka yadda ka haɗa kai daahi Soyayyar ƙarya kin kasa ganewa duk mutumin da yace baya sonka da safe da rana tsaka yazo yace yana sonka to wallahi Soyayyar ƙarya ce duk yanda za'ayi akwai wata buƙatar sa wanda yake son ya cika ne da taimakon ka,mai hankali ne kawai yake gane haka, amma shi daƙiƙi bazai taɓa ganewa ba." " Jummo ni kike faɗaw................." " Shishsh!!!! Karki min ihu bana buƙatar jin amonki, ina abun yi yanzu amma dai ki sanarwa wacce ta aiko ki cewa munfi ƙarfin ta, mu nan cikin gidan nan babu yanda aka iya damu sai gani sai hange, amm kima faɗa mata na kusa nayi WUF da ɗan ta na mallakesa ya zamo nawa ni kaɗai ya manta da yana da uwa ma, sai dai a cikin ƴaƴan nata har yanzu ban gama yanke shawarar waye zan ɗauke ba, ban sani ba ko Garkuwa ne ko mijinki, har yanzu tunani nake akan haka, kice mata ƴar zaki ta girma." Tana gama faɗin haka tare da dagawa Zarah gira sannan Jummo ta fice, Aunty Zarah cike da ƙyarmar jiki tabi Jummo da kallo, ita yanzu Yarinyar ta fara bata tsoro, tabbas ɗan ƙauye yafi ɗan Birni iya shege, a madadin Aunty Zarah ta juya tabar wajen, sai ma cigaba tayi da kiraye kirayenta, a nufinta idan Mamma ta fito ta tsallake ƙofar bedroom ɗin shikenan sun gama da ita abinda Zarah kuma bata sani ba shine Mamma bata gidan ma gabaki ɗaya tun safe Jummo ta kaita makwabtan su, a cewarta akwai wata tsohuwa mai dai-dai shekarun Mamma mutumiyar kirki mai yawan ibada, ta haɗa su ƙawance, shine yau ta kaita gidan. Murmushi Jummo ta saki bayan ta fito, tana hango wauta da tsantsar rashin wayon Aunty Zarah, ta fito da falon dai-dai Garkuwa zai shigo, da wani irin mungun kallo ya bita tare da haɗiye yawun jaraba, wow!!! Ya furta, hanyar ya tare tare da cewa. " A'isha!!!" Saurin ɗago kanta tayi jin an kirata da ainihin sunan ta na yanka, sosai muryar ta doki kunnenta, dubansa tayi a hankali tamkar bata son Magana ta amsa da "na'am". Murmushi yayi yana ƙaremata kallo yace. " Ina zakije haka kike sauri." Ita dai Jummo cike da mamakin yau kuma ita Ya Garkuwa yake yiwa Magana ta amsa da. " Super market zamuje, Meenat na jirana a waje shiyasa nake sauri." Kansa ya kaɗa yana siɗe leɓe ya ce. " Okay, amm idan kin dawo ki shiga bedroom ɗina ki gyara min, ina sauri zan fita zan ajiye miki key ɗin a saman window na" Ya ƙarisa Maganar yana zaro rafar dubu hamsin ya miƙa mata ya cigaba da cewa. " Yau kinyi kyau sosai ga wannan ki sayo kayan kwalliyar da zasu ƙara miki kyau, ina fatan dai har yanzu kina son Garkuwan ki, domin a yanzu a shirye garkuwa yake da karɓar Aishan sa a matsayin Mata, zaki Aure ni Jummo." Kamar sauƙar aradu Jummo taji maganganun sa, murmushi ta saki kanta na ƙasa zuciyarta cike da farin ciki, ganin tana murmushi yasa Garkuwa zare wayarta daga hanunta " infinix hot9 plus, Wannan wayar ai ta miki ƙarama, dole na sauya miki waya" yayi Maganar yana saka numbern sa plashing ɗin wayarsa yayi sannan ya danƙa mata wayar a dawo lafiya yace mata ya shige yana murmushi, murmushi Jummo tayi tare da bin bayan sa da kallo cike da matsananciyar soyayyar sa harya ɓacewa ganinta murmushi tayi tare da ficewa motar meenat ta hango ƙofar gidan nasu, buɗe motar tayi ta shiga tana dariya. " Ja mota muje Malama." Motar meenat taja tana duban Jummo, sun ɗan yi nisa da tafiya meenat ta juyo tana kallon Jummo tace. " Hajiyata, wai ya naga sai famar murmushi kike tamkar wacce kikayi tsintuwar saurayi meye sirrin.?" Dariya Jummo tasa har dimple ɗinta yana lotsawa tace. " Shegiya Uwar ƙwaƙwaf ke dai akwai ki da hasasho muradin mutum, babbar tsintuwar saurayi nayi, Meenat yau dai Ya Garkuwa na ya furta min yana sona zai Aure ni." " Wow!!!! Congratulations ƙawata, kai Masha Allah, dama ai na faɗa miki mai haƙuri yana tare da Nasara dole ne dama ya Garkuwa ya soki, domin kuwa samun dirarriyar mace tamkarki abune mai wahalar gaske, ƙawata kema fa dole sai kin ja masa aji kafin ki amince, shima yaji yanda kikaji, amma dai bari mu koma gida na ƙarisa miki sauran karatun." Dariya Jummo tasa tare da cewa. " Haba dai ƙawata!!! Dama haka kawai zan amince masa dole nima sai na rama,ke nifa sai ma tukunna na jarabasa kafin na amsa masa, yanzu wani makay zamuje.?" " Kina burgeni ƙawata domin kuwa kin iya takunki, mtss ina ga Alhusain zamuje." Meenat tayi Maganar tana ƙara gudun motar. A Alhusain SUPER MARKET sukayi parking tare da fitowa suka nufi cikin SUPER MARKET ɗin, da ɓangaren takalmi suka fara kafin suka nufi fannin turaruka, Jummo tana cikin tafiya taji an bigi kafaɗarta wayar ta da jakarta ya faɗi ƙasa, cike da ɓacin ran wani makahon ne zai bige mutum Jummo ta ɗago kanta, idanu biyu suka haɗa da Safreena wani irin bugawa da ƙarfi zuciyoyinsu yayi a tare, Safreena ne tayi saurin cewa. " Kiyi haƙuri dan, wallahi ban lura dake bane yaro ke min kuka duk ya gigitani sorry." Shuru Jummo tayi sai cewa tayi. " Babu komai ƴar uwa" Abdul dake kafaɗar Safreena yana ta ihu ta kalla tare da sunkuyawa ta ɗauki jakarta da wayarta hanunta ta saka ta amshi Abdul daga hannun Safreena tare da cewa. " Meya sameshi yake wannan kukan haka gashi kyakkyawa ɗanki ne?" Ɗan murmushi Safreena tayi tace. " Ehh ɗana ne, rikici kawai yake ji dashi." " Ayya yi shuru kaji beautiful boy, ko dai Momy ne ta mintsineka, nasan dai baza kayi kuka haka kawai ba, rabu da Momy zamu rama." Dariya Safreena tayi haka kawai taji Jummo ta burgeta, yanda take rarrashin Abdul Jummo tambayarta tayi. " Ƴar Uwa menene sunan sa?" " Abdul!!! Ni kuma Safreena, kefa.!!!" " Ni sunana Jummo." Murmushi safreena tayi tare da cewa. " Nice name kin burgeni sosai baki da girman kai, zamu iya ƙulla abota." " Ƙwarai kuwa Ƴar Uwa kin burgeni sosai nima." Dariya dukkan su sukayi sannan sukayi exchange ɗin Number, Zee ce ta iso wajen tare da cewa Safreena muje, karɓar Abdul tayi sukayi sallama da Jummo suka tafi. Suma su Jummo basu wani juma ba a cikin SUPER MARKET ɗin suka fito. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Runtse idanunsa yayi yana hango ta cikin idanun nasa, murmushi ya saki tare da furta. " Ashe haka take da kyau tabbas na kusa asara samun mace irinta a yanzu zaiyi matukar wahala, idan har na sameta a matsayin Mata tabbas na dace." Buɗe idanunsa yayi yana murmushi tare da juyawa daga kujerar yana lilo da ƙafarsa, Shagari ne ya turo door ɗin office ɗin ya shigo da sallama, amsawa Garkuwa yayi yana cewa. " Yaushe jirgin ka ya sauƙa." Zama Shagari yayi tare da cewa. " Tun ɗazu, meya samu naga sai murmushi kake." Dariya Garkuwa yayi tare da cewa. " Hmmm!!! Abokina yau naga matar AURENA." Zaro idonsa Shagari yayi cike da matuƙar mamaki yace. " Whatttt!!! Matar Aure yau kai da bakinka kake kiran ka samu matar Aure, waye wannan haka wacce ta cire tuta." Murmushi Garkuwa yayi tare da cewa. " Ina tunanin a yanzu lokaci yayi da ya kamata na watsar da Rayuwar bariki, nayi Aure, hmmm Jummo itace macen daya kamata na samawa ƴaƴana a matsayin Uwa saboda tana da kamun kai, macece da babu ruwanta da maza, bata taɓa zina ba, ita ya dace na aura.!!" Numfashi Shagari ya saki tare da cewa. " Allah Sarki Safreena ita naso ace ka aura a matsayin matar ka ta Aure domin kuwa ta soka tsakanin ta da Allah, ka lalata mata rayuwarta ba tare da saninta ba, kaine ka saka mata ƙwayar gusar da hankali sannan ka lalata mata rayuwa daga baya Soyayyar ka tasa ta amince da kai, naji baƙin cikin mutuwar Safreena na." Kansa Garkuwa ya dafe idanunsa sukayi jajur ɗagowa yayi ya kalli Shagari tare da cewa. " Na fika jin baƙin cikin mutuwar Safreena, wallahi Shagari koda na lalata rayuwar Safreena ina sonta saboda nasan ba mutuwar banza bace naso auren ta, sai dai mutuwa tamin yankan ƙauna, na rasa meya ƙona gidan su Safreena da ahalinta gaba ɗaya, hmmm!!! Duk sanda na tuno Safreena sai naji raina ya baci hankalina ya tashi, ta mutu da cikana a jikinta duk da naso ta zubar da ciki tace min bazata ƙara saɓawa ubanginta a karo na biyu ba, Allah Sarki kamar tasan mutuwa zatayi Allah ya jiƙanki Safreena ya yafe miki kuskurenki.................." *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba*. *Payment group Only* ➰➰ *39 to 40* "What!!! Matsiya!!! Matsiya fa kika ce mata Zarah!!! Anya kina da hankali kuwa yau a jikinki? Jummo ce fa, nake tare da ita ba wata ba, waima dakata duk meye na tada jijiyoyin wuya haka, meya ɗaga miki hankali dan kawai kin ganni da Jummo kin dai san ba yau na fara zama da Jummo a cikin falon mu ba, ko baƙuwa ce jummon? to me zai dameki, Please karki kuma ce mata matsiya, idan kuwa kika Kuma wallahi sai na ɓata miki rai." "Na tada jijiyoyin wuya!!! Nace na tada jijiyoyin wuyan!! Ƙarya nayi ba matsiyaciyar bace, Khalil nace mata matsiya ko zaka ɗauka mata fansa ne? Ehh Lallai da gaske Jummo ta gama da kai Khalil, wai wannan wace irin ƙaddararriyar yarinya ce, to wallahi muddun baka fita a harkar ta ba, ka daina kulata ba, wallahi yanzu zamu saka ƙafar wando daya da kai, masifa da bala'i shine zaike wanzuwa a tsakanin mu, ni zaka munafurta kake Soyayya da wannan abar Wallahi bazai yiwu ba, kuma Wallahi bazaka kwana a cikin ROOM ɗin nan ba, ko ance maka bata sanar dani kana sonta bane itace da bakinta ta faɗa min!!!" " Hmmm!!! Sai yanzu na fahimci inda haukar taki ta dosa, Oh ke wai yanzu wannan haukar da jahilcin da kikeyi duk akan kishi ne, Oh ke taki kalar kishin kenan na hauka, Zarah idan zan ƙara auren zaki hanani ne, nace zaki hanani ne, baki isa ba, ni ba irin waɗannan sususun mazajen bane, shasha, zan fita daga bedroom ɗin nan ne na kwana a falo ba dan saboda shakka ko tsoron ki ba, zan fita ne saboda rantsuwar da kikayi." Ya ƙarisa Maganar yana ficewa daga room ɗin tsuka Zarah taja tana riƙe kunkumi, sosai hankalinta ya tashi, amma duk yanda za'ayi bazata taɓa yadda mijinta ya Auri Jummo ba, tsuka taja tana rufe room ɗin ta koma ta kwanta. Ita kuwa Jummo ta kai kusan sha ɗaya na dare tana assignment ɗin kafin ta shige bedroom ɗin ta harta yi shirin bacci cikin riga da wando, tare da Kwanciya gefe A'illo, Sadiya tana can dungun bed ɗin sai famar yamutsa fuska takeyi, tana chat, Jummo wayarta ta ajiye tare da duban A'illo tace. " Me kikeyi haka har yanzu bakiyi bacci ba?" " Ba komai Aunty idanuna ne kawai suka bushe, hankalina yana tashe da lamarin gidan nan sai nakeji a jikina tamkar wani mummunan al'amari zai faru da Mamma, Jummo ni fa nayi wani tunani mai zai hana mu haƙura da zaman wannan gidan mu koma ƙauye hakan zaifi mana kwanciyar hankali." Murmushi Jummo tayi tare da kallon Sadiya da tayi shuru alamun maganganun su take saurara, numfashi ta sauƙe tare da juya harshe da fullanci tace. " Ki kwantar da hankalin ki A'illo babu wani abu mummuna da zai faru da Mamma ke dai ki cigaba da mana addu'a insha Allah zamu samu mafita, kiyi baccin ki kinga gobe akwai school." " Shikenan Allah ya mana mafita mai kyau" da ameen Jummo ta amsa tana jiyo ringin wayarta baƙuwar Number ta gani hanu tasa ta ɗaga kiran. " Amincin Allah ya tabbata a gareki, har yanzu bakiyi bacci ba?" Jin Muryar Ya Garkuwa yasa Jummo sakin murmushi ta furta. " Ya Garkuwa, kaine.? Saurin ɗago kanta Sadiya tayi jin Jummo ta ambaci sunan Garkuwa, tana dubanta cike da mungun mamaki sai kuma taji wani kishi ya taso mata shuru tayi tana jiran taji me Sadiya zatace. " Ni ne kinga baƙuwar Number ko? Na kasa bacci ne sai tunaninki nake, A'ishah sonki ya min mungun kamu, anya kuwa kina sona kamar yadda nake sonki.?" Murmushi Jummo ta saki tare da cewa. " Ya Garkuwa kaima ka sani Soyayyar ka bata yanzu bace a cikin zuciyata, Ya Garkuwa ina sonka fiye da yadd............" Wafce wayar Sadiya tayi tare da furta. " Kina sonsan ubanki, to dan ubanki ruwa ba sa'an kwando bane, Garkuwa yafi ƙarfinki kisha ruwa dai-dai cikin ki Wallahi" wayar ta kara a kunnen ta tare da cigaba da cewa " Kai kuma na dawo kanka!!!! Ni zaka munafurta, wai meyasa jarabar mata ya maka yawa ne, kai ko wace mace kana so, to baka isa ba wallahi dani kaɗai zakayi rayuwa, ka jawa wannan jakar ƙauyen kunne ta fita a harkar ka, idan ba haka ba wallahi sai na illata rayuwarta." Murmushi Garkuwa yayi tare da juyi a bed ɗin da yake cike da kasalalliyar muryar sa yace. " Sorry Sadiya, daina mini tsawar haka ko, ki bawa mai wayar wayarta bani da lokacin ɓatawa dake a yanzu muryar matata kawai nake buƙatar ji." Wani munduƙun baƙin ciki Sadiya taji ranta ya baci tace. " Ya Garkuwa ni kake cewa baka da lokacin ɓatawa a kaina, nine fa Sadiya.?" " Keee!!! Sadiyan fa ai na ganeki, kinga duk haukar da zakiyi ki jira har na dawo sai min, amma dai yanzu bata wayarta." Runtse idanunta Sadiya tayi, tana jin baƙin ciki, Jummo murmushi ta saki tare da wafce wayarta daga hanun Sadiya tace. " Yi hkr farin ciki na, wannan marar lissafin ta ɓata min rai, zamuyi waya da safe, kai dai ka kwantar da hankalin ka ka samu nutsuwa, ina dai-dai da haukar ta." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Nasan wacece ke, na kuma san zaki iya da ita, kiyi bacci mai daɗi, I love You." Kashe kiran Jummo tayi tana murmushi ta dubi Sadiya tare da cewa. " Daɗina da jaki duk yanda akayi dashi sai yaci kara, karki ƙara kuskuren waftar wayata daga hanuna bare kuma ki kuma zagin ubana yanzu zan miki afuwa saboda wannan shine karon farko, idan kuma kika kuma Wallahi saina banbance miki tsakanin aya da tsakuwa mtsss." Tsabar mamaki da tashin hankali kasa Magana Sadiya tayi a hankali ta sidaɗe ta zauna a ƙasa hankalinta a matuƙar tashe. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Safreena zaune ne tana sauraron dukkan maganganun da Garkuwa yayi dasu Jummo ne, ta saki murmushi tare da duban Zee tace. " Kinga dan tsiya, ya samu wata ita kuma wannan jakar zai jefar da ita, lallai Garkuwa ya cika cikakken taure, ya haɗa ƴan mata biyu a gida ɗaya, hmmm yanzu me zamuyi." " Hmmm!!! Da alamar ita wacce yake kira da Aishan ba son yaudara yake mata ba, yanayin maganganun sa ya nuna aurenta yake son yayi, da ita ya kamata muyi Amfani wajen ruguza farin cikin sa, bari mu bincika lambarta mu fara da aika mata saƙo" Shuru Safreena tayi, tana duban wayarta tare da cewa. " A'ishah to waye ce A'ishah, hmmm?!! Zee binciko numbern ta." Da to Zee ta amsa tana ta ƙoƙarin neman numbern, ta layin Garkuwa, tana isowa dai-dai numbern taga ansa Private number. " Kash!!! Numbern bazata ɗauku ba private number ya ɓoye numbern, Safreena da alamu wannan Yarinyar tana da mahimmanci a wajen Garkuwa ya zama dole mu nemo ta!" Cike da takaici Safreena ta dafe kanta tana jin haushin rashin samun numbern da batayi ba, wayarta ne yayi ringin ta dubi wayar *Jummo* ta gani rubuce, hanu ta saka tare da ɗaga wayar ta na cewa. " Assalamu alaikum" "Ameen wa'alaiku mussalam Barka da dare mom Abdul" " Barka Jummo, ɗazu nake niyar kiranki sai kuma wasu abubuwa suka riƙeni, ya kike kun koma lafiya.?" " Lafiya alhamdulillah ina my boy Abdul.?" " Abdul gashi nan yayi bacci, yasu Mama." "Duk suna lafiya, ki shafa min kan Abdul sai da safe." " Insha Allah na gode." Ta ƙarisa Maganar tana katse kiran. " Jummo ce wacce muka haɗu da safe a super market, yanzu ya zamuyi mu sami yarinyar." " Gaskiya yanzu dai bana ce ga yadda zamu sameta ba, amma mu cigaba da bibiyar layin wayarsa insha Allah zamu sameta." Mama ce ta shigo cikin bedroom ɗin nasu jin alamun kamar Magana. " Safreena me kuke har yanzu bakuyi bacci ba, sha ɗaya da rabi fa!!! Me kuke yi." Dibirbircewa Sukayi, Zee tayi saurin cewa. " Babu abinda muke fa Mama bacci ne kawai baizo ba, shiyasa muke fira." " Fira da laptop a gabanku, kun san fa bana son firan daren nan har sha ɗaya da rabi, ku kashe laptop ku kwanta karna kuma jin muryar ku, ke kuma Safreena ki gyarawa Abdul kwanciyarsa." " To Mama" Fita Mama tayi Safreena ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa. " Alhamdulillah!!! Mama bataji zancen mu ba." Murmushi Zee tayi ta kashe laptop din, gyarawa Abdul kwanciya Safreena tayi suka kashe wutar ɗakin tare da Kwanciya. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Washe gari da safe bayan anyi breakfast ne khalil ya dubi Mamma dake zaune ranta a haɗe yace. " Hajiya Mamma Wannan irin haɗa fuska haka tamkar zaki tada bom, ɗan saki fuskar mana sai kifi kyau." Lumshe idanunta Jummo tayi tare da sakin murmushi da alamu Ya khalil ya farga da zantukanta na jiya, Mamma dubansa tayi har yanzu ranta a haɗe tace. " Taya zan saki raina ana ƙuntata min ana kona min rai a cikin gidan nan." Daddy ne yace. " Ana ƙona miki rai kuma Mamma, meya faru.?" " Ina ruwanka da abinda ya faru ka damu dani ne, da har zaka tambaye ni abinda ya faru, to ban sani ba, sai ka bari idan na mutu sai ka tambayi gawata meya faru?" Cike da tashin hankali Daddy yace. " Subahanallah!!!! Na damu dake mana Mamma dan Allah ki sanar dani me yake faruwa."? Momy zuciyarta ne ta tsinke tare da kallon Mamma taji me zatace, jikinta har bari yake domin kuwa idan har Daddy yaji abinda ta yiwa Mamma jiya kashinta ya bushe, tashi Mamma tayi tabar wajen bata kulasa ba, numfashi mai nauyi Momy ta sauke tana godewa Allah miƙewa Daddy yayi zai bi Mamma Jummo ta dubi yanda Momy ta kuma ruɗewa murmushi ta saki tare da dakatar da Daddy. " Aa karka je ranta na ɓace bazata saurari kowa ba, nine na ɓata mata bisa kuskure kuma na bata haƙuri nace bazan kuma ba insha Allah.!!!" Cike da masifa Daddy ya hauro kan Jummo tamkar zai daketa. " Baki da hankali ne zaki dinga ɓatawa tsohuwa kamar Mamma rai, irin su ai rarrashin su ake ba wai a samusu damuwa, amma saboda baki da hankali sai kije ki daga mata hankali to kul karki kuma idan kuma kika kuma Wallahi ranki sai ya ɓaci." " Kayi hkr Daddy insha Allah bazan kuma ba, nayi laifi!!!" " Ki dai kiyaye" Daddy ya furta tare da ɗaukar jakarsa ta aiki ya fice, Momy baki sake take kallon Jummo duk takun saƙar da suke da ita, sai taga tana tare mata duk wata masifa da ta tunkarota " to meye hakan yake nufi"? Kallon ta ta mayar ga khalil tare da tashi tabar wajar, Aunty Zarah tsuka taja tare da miƙewa tsaye ta furta. "Makircin banza neman gindin zama" tayi Maganar itama tana barin wajen, Sadiya dama tun safe ta kasa fitowa kukan ta tasha a boye sosai take cikin damuwa da tashin hankali, ya khalil duban Jummo yayi yace. " Ba ke bace kika ɓatawa Mamma rai, meyasa kika karesu.?" Murmushi Jummo tayi tace. " Meyasa kace bani bace bayan kuma nice na aikata, babu wanda na kare gaskiya na faɗa Ni ce na bata mata rai.?" " Ƙarya kike Jummo ba ke bace kika ɓatawa Mamma rai ki faɗa min gaskiya waye ne muddun kuna son na kawo gyara cikin gidan nan tell me?" " Ya khalil meyasa kake so ka tursasa min dole sai nayi ƙarya da gaske nake maka nine na ɓata mata rai." " Jummo............" " Dan Allah ya Garkuwa karka tursasani nayi ƙarya dan Allah kabar wannan maganar hanyar gyara tana da yawa mu nemi wata, wannan dai ya riga ya shige." Dole yasa Khalil yin shuru ba tare da ya kuma cewa komai ba, duban A'illo Jummo tayi tace. " Ɗauko mana bag ɗin mu, mu shige school." Tashi A'illo tayi bata juma ba kuwa sai gata ta fito da bag ɗin, karɓa Jummo tayi tare da cewa Ya khalil. " Mun shige school sai mun dawo." Dubu biyu khalil ya basu tare da adawo lafiya sannan su Jummo suka fice da kallo khalil ya bita cike da sha'awar rayuwarta sam bata ɗauki duniya da zafi ba simple take rayuwa, numfashi ya sauƙe tare da haurawa bedroom ɗinsa, Zarah na tsaye jikin wadrop tana gyara kayanta, ya khalil ya shigo, ko inda Zarah take bai kalla ba, ya ɗauki towel zai shige tollet yaji muryar ta. " Ban haɗa ruwan wankan ba, yanzu zan haɗa maka, ka ɗan jira." Hanu KHALIL ya ɗaga mata tare da cewa. " Bana buƙata ina da hanu zan haɗa kayana." Yayi Maganar yana shigewa tollet ɗin zaro idanunta Zarah tayi tana kallon Khalil a zaton ta, zai bata haƙuri ya rarraaheta akan abinda ya faru jiya, shine ma zai ɗau fushi da ita, kanta ta girgiza tare da cigaba da abinda take. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ " Ina jinki Asabe kika ce ya zanyi da maganin.?" " Kin gani Hajiya Zainab ki tabbatar kinje kin zuba maganin nan a ƙofar bedroom ɗin ta, kuma ki tabbata ba wanda ya ganki wallahi Hajiya Zainab kinji na rantse miki muddun ta tsallake wannan maganin wallahi sai faɗi jinyar da baza'a taɓa sanin maganin sa ba, har ta mutu a haka kuma babu mai zarginki." " Masha Allah, insha Allah babu saƙo da kaina zanyi wannan aikin shegiyar Yarinyar ta tafi makaranta, saura Khalil ne kawai a gidan yanzu zai fita yana fita zanje na aiwatar na gode Asabe sai munyi waya." Ta katse wayar tana dariya, tare da juya ƙaramar kwalbar dake hanunta mai cike da wani farin ruwa tamkar Madara. "Hmmm!!! Mamma kenan na rantse da Allah kafin kiga bayana ni sai naga bayanki bazan taɓa zuba idanu ina gani wani yayi mulki a gidana ba, dole ni kaɗai zan bada umarni a gidan nan, daga yau Mamma kin daina takawa da ƙafofinki mu zuba mu gani ni da ke shege ka fasa." Ajiye kwalbar tayi tare da sheƙewa da dariya, khalil ne ya shigo cikin shirin fita office, kusa da Momy ya zauna tare da cewa. " Zan fita Momy hope baki buƙatar komai ko.?" " Dubu arba'in nake buƙata, zan kaiwa Hajiya mairo zatayi bikin ƴarta, kuma ya kamata na bata wani abu, Khalil wai ya zancen dana maka ne, na ka ƙara Aure bazan fa zuba idanu na kalleka zaune da wannan juyar ita kaɗai ba, bata haihuwa sai ajiye ƙaton kashi ka bata taci tasha mai kyau ta ajiye kashi bazai yiwu ba, dole zaka ƙara Aure ko kaima zakaga jininka nima naga jikana, dan haka gara ka fara neman mata kafin raina ya ɓaci na nemo maka da kaina.?" " Haba Momy meyasa kike wannan maganar, koda zan ƙara Aure bazan ƙara Aure da niyar haihuwa ba, domin kuwa ita haihuwa ta Allah ce shike bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, badan baya sonsa ba, sai dan girman ikonsa, Momy kika sani ko nine bana haihuwar Momy............" " Kai dalla dakata haka da wannan zancen banzan kaikam kana haihuwa domin kuwa jinki jinin zuri'a ne, tashi ka tafi karka kuma min Maganar banza, kuma Aure dole ka ƙara Allah ya tsare." Da ameen Khalil ya amsa yana fita, sanda Momy ta tabbatar Khalil ya juma da tafiya sannan ta ɗauko wannan kwalbar a hankali ta fito tana dube dube cikin dalon shuru ba kowa har Zarah tana room ɗinta, murmushi Momy ta saki tare da zuwa cikin gaggawa ta zuba wannan ruwan kwalbar a ƙofar room ɗin Mamma da sauri tabar wajen tana murmushin ƙeta. Mamma kuwa hankalinta kwance tayi wanka tare da ɗaukar mayafinta, zata gidan Hajja Atine, ƙawar da Jummo ta sama mata nan ƙasa da layinsu, bakin room ta nufo tare da sako ƙafarta ta taka wannan ruwan, ta fito falon Momy dake laɓe tana hango dukkan abinda ke faruwa ne ya sata sakin murmushin nasara, Mamma tazo DAI-DAI fita daga falon taji jiri ya fara ɗaukarta, falon ya fara juya mata komai bibbiyu take kallonsa, yankan jiki tayi ta faɗi ƙasa a sume. Jummo dake cikin class ne taji zuciyarta ta tsinke da ƙarfi ƙirjinta ya fara harbawa, tamkar ana buga ganga, saurin dafe ƙirjinta tayi tare da runtse idanunta................" *INA GODIYA SOSAI DA SHARHIN KU PAID GROUP NAJI DAƊI SOSAI A CIGABA DA SUBURBUƊO MIN COMMENTS🥰🥰🥰🥰🥰* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:22 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *43 to 44* Tashi Jummo tayi tare da shigewa bedroom ɗin Mamma A'illo ta samu zaune gefen Mamma ta haɗa tagumi, numfashi Jummo ta sauƙe tare da kamo hanun A'illo tace mata. " A'illo zanje Cilo yau zan taho da INNO, domin ta duba Mamma, insha Allah zamu samu maganin matsalarta, sai dai yanzu abinda nake so da ke, karki kuskura kibar Mamma ita kaɗai koda wasa Saboda ina zargin mutum biyu a cikin gidan nan, Aunty Zarah da Momy su nake suspecting, dan haka ki kula dasu karsu cutar da ita a karo na biyu kina ji ko" Kanta A'illo ta kaɗa tare da cewa. " Shikenan Jummo insha Allah zan kula, Allah ya tsare hanya, kiyiwa INNO bayani sosai dan Allah ta taimakeni tazo ta duba Mamma." " Karki damu A'illo kinsan INNO babu abinda bazata iya yiwa Mamma ba, ni na tafi." " Allah ya tsare a dawo lafiya." Da ameen Jummo ta amsa tana kallon Mamma harta fice, tare suka jera da Garkuwa har cikin mota yaja tare da dannawa Baba mai gadi hom, da sauri ya buɗe get din suka fice daga cikin gidan, suna shan kwanan gidan Safreena na sauƙa a adaidaita, hanunta ta ɗaura a kanta ganin motar Garkuwa ta gifta ta shige da gudu tabi bayan motar tana kwalawa Garkuwa kira sai dai ina shi sam baima jita ba bare ya juya dreving ɗinsa kawai yake, ganin ya ɓacewa ganinta ya sata zama a wajen cike da tashin hankali da fargaba ta shiga Uku idan Garkuwa ya mutu, hawaye ne masu ɗumi suka zubo daga idanunta, sharewa tayi tare da ciro wayarta daga jaka ta kira numbern sa kusan 10 miss call bai ɗaga ba wanda shi wayar tasa ma tana silent bai lura da kiran ba. " Na shiga Uku!!! Yau kuma zanyi kisan kai da wani ido zan kalli Ubangiji na idan ya mutu?" Cike da sanyin jiki ta miƙe adaidaita ta tare tace ya kaita Federal locost ranta sam babu daɗi ta ɗebi hanyar gidan su. Shikuwa Garkuwa dubansa ya kai ga Jummo tare da sakin murmushi ya furta. " Ina cikin farin ciki yau daya kasance zanyi tafiya mai nisa tare da ke, da na kusa yiwa kaina asara na ƙin amincewa da Soyayyar ki, sai daga baya na fahimci cewa kece alkairi na ina sonki Jummo." Numfashi Jummo ta saki fuskarta sam babu farin ciki tace. " Ya Garkuwa, ni kuwa yau bana cikin farin ciki Saboda wacce tayi sanadiyar haɗa kaddarar mu, tana kwance rai a hanun Allah, a halin da Mamma take ciki yanzu na tsakanin rayuwa da mutuwa babu wani farin ciki da zai ziyarce ni, har sai naga motsinta, ina sonka ya Garkuwa." "Hmmm!!! Naji tausayin Mamma ƙwarai, ba'a mamaki da ikon Allah, amma ace mutum yana zaune lafiya lokaci ɗaya ya gamu da ƙaddara, ba komai insha Allah Mamma zata samu lafiya ." " Allahu yasha Ya Garkuwa" Sunyi nisa da tafiya sosai suna zance gwanin burgewa domin kuwa a ɗan wannan awannin Jummo da Garkuwa har ɗan sabo ya shiga tsakaninsu, sun shige Bojuɗe local gvt da kwani, suna cikin Gaɗam birkin motar Garkuwa ya cinke burkin ya ƙwace daga hannun sa, zaro idanun sukayi kusan haɗin baki suka furta. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!!" Garkuwa ne cike da gigita ya dubi Jummo tare da cewa. " Burki ya tsinke Jummo me yake faruwa? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati!!!!" Wani irin mungun gudu motar take yayin da tayar motar ke ƙoƙarin ficewa, duk yanda Garkuwa yaso ya dakatar da motar abu yaci tura, ga tsakiyar titi motaci sai famar gudu suke a Jummo sosai take cikin tashin hankali ta rufe idanunta gam sai innalillahi take furtawa a cikin zuciyarsa, da kanta motar ta yanki kwana ta faɗa wani jeji mai yawan bishiyoyi, bugar bishiyoyin motar take yayin da take gwara kansu jikin glass ɗin motar, tayar gabane ya fice motar tayi sama tare da dawowa ƙasa ta faɗi, ƙofar da Jummo take ne ta buɗu tamkar an wullota ta faɗo waje, kanta ya doku da katon dutsen kwankere wani irin ƙara mai shiga zuciyar mai sauraro Jummo ta danna sai kuma numfashinta ya ɗauke take, shi kuwa Garkuwa ƙirjinsa ne ya doku da jikin sitiyarin motar wani irin numfashi ya saki sai kuma numfashin nasa ya fara sarkewa yana jawo numfashi da ƙyar zuciyarsa sai bugawa take tamkar ganga far!!! Far!!! Far!!! Far!! Haka zuciyarsa ke bugawa, sai kuma ya fara aman jini guda guda, kirjinsa ya danne da hanunsa dake masa azaba tamkar zai ɓalla zuciyarsa zata faso waje, idanunsa sun rune tamkar garwashin wuta, amma tsabar ƙarfin hali irin na Garkuwa baya jin kansa, Jummo kawai yake ji, ƙofar gefensa ya saka hanu da ƙyar ya tura taƙi buduwa, zakuɗawa yayi a hankali yana cije bakinsa cike da azaba ya samu ya fito, layi yake tamkar zai faɗi, wajen sai juya masa yake bakinsa na zubar da jini gumi duk ya lulluɓesa amma a haka yake ta waige waigen ina zaiga Jummo, hangota yayi kwance jini sai zuba yake daga kanta tamkar an kunna fanfo idanunta sun kafe, a hankali ya fara jan ƙafarsa yana ƙoƙarin zuwa inda take sai dai ina taku ɗaya yayi ya yanki jiki ya faɗi a sume. Mutane ne suketa ƙoƙarin shigowa jejin da gudu, take suka ruhu a kansa, kowa yana tausaya musu, ɗaya daga cikin waɗannan mutanen ne ya je ya kirawo police, cikin gaggawa aka kira amblance, akayi dasu Sj gaɗam hospital. Ita kuwa Safreena tun da ta koma gida take tirƙar kuka cike da nadamar abinda tayi, bata san wani hali yake ciki yanzu ba, hanu ta ɗaga tare da fara jero addu'o'i. " Ya Allah ni baiwarka ce mai yawan sadaka, mai yawan ibada, ya Allah nasan naimaka laifi ta hanyar haɗa shinfiɗa da wanda ba muharramina ba, ya Allah na tuba ka yafeni, ya Allah na saka Rayuwar wani a cikin haɗari, cikin raahin sani da kuskure na, ya Allah ka kare wannan bawan naka, ya Allah kasa karya samu rauni Saboda kuskurena, ya Allah ka amshi addu'a ta." Tayi addu'ar tana runtse idanunta, Aunty Batul ne ta dafa ta tare da sunkuyawa a gabanta tace. " Lallai kinyi kuskure bisa rashin sani, sannan tabbas Baba yaji wannan ɗanyen aikin da kikayi ransa zai ɓaci hankalinsa kuma zai tashi, sannan sai ya miki faɗa tamkar zai dakeki, dan haka kiyi shuru da wannan maganar muyi addu'ar Allah ya karesu, kawai, kai duniya ba AMANA tun ɗazu naketa tunani, wai ace da mutumin da ka sashi cikin inuwarka za'a Cutar da rayuwarka, mtsss!!! Nayi mungun jin haushin mai gadin gidan su Garkuwa, kana cin albarkacin ubansa sannan ka nemi kashe masa ɗa, Allah ka haɗa mu da mutanen ƙwarai." Da ameen Zee ta amsa itama tana jin haushin Safreena domin kuwa da ta sanar da ita bazata barta ta aikata wannan mungun kuskuren ba Allah ya kyauta. Tana nan zaune Safreena tayi shiru taji ringin ɗin wayarta dubawa tayi, layin da sukayi connecting da layin Garkuwa ne, wanda take jin duk wani kiran da zaiyi da wanda za'a kirasa, saurin ɗaukar wayar tayi Bros taga ake kira sai da layin ya kusa tsinkewa aka daga daga inda take zaune take jin maganar tasu. " Assalamu alaikum." Da ameen wa'alaiku mussalam ya Khalil dake zaune a office din sa ya amsa yana cewa "Bro har kun isa kenan?" " Bashi bane" Yaji muryar wani ya doki kunnen sa, cike da mamaki Ya khalil yace. " Ba shi bane waye kai ɗin." " Police ne mai wannan wayar sunyi haɗari, a cikin ƙaramar wayarsa muka samu wannan numbern muka kira, kuzo Sj Gaɗam suna asibitin." " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! A wani hali suke ciki suna raye ne ko sun mutu, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! " A halin yanzu bazamu ce ga halin da suke ciki ba gaskiya saboda accident ɗin nasu babu kyau, mun dai shigar dasu asibitin basa motsi, kuzo dan tabbatar da rayuwarsu." Yana gama faɗar haka ya ajiye kiran dafe kansa Ya khalil yayi cike da tashin hankali yana jin wani irin jira zuciyarsa na tsinkewa da sauri ya tashi tare da kwasar wayoyinsa bai kira kowa ya sanar dashi ba, har Daddy saboda gudun sasu cikin damuwa, da motar sojoji biyu Ya khalil ya kama hanyar gaɗam, cike da tashin hankali. Kallon su Aunty Batul tayi ta rintse idanunta hawaye na gudu bisa kuncin ta, wannan shine danasani na Biyu da tayi a rayuwarta. " Aunty Batul na kashesu, nayi kisan kai Aunty Batul, ina zan kai haƙƙin rai, na shiga Uku.!!!" " Baki shiga Uku ba Safreena, baki shiga Uku ba, insha Allah bazasu mutu ba, zasu rayu, sai dai kuskuren kin ɗauki alhakin muddun basu yafe miki ba, sai Allah ya tsaidaku ranar gobe kiyama, hmmm!!! Allah ya ɗaga kafaɗunsu, gacan Abdul yana kuka kije ki rarrashesa." Miƙewa Safreena tayi ta ɗauko Abdul wani irin ihu yaron ya kurma yana ƙoƙarin zillewa daga jikinta, sai kuma ajiyar zuciya yaron keyi, zaro idanunta Safreena tayi tana kallon yaron yanda yake ihu tamkar da wuta a hanunta ta ɗaukesa, Zee ce ta saka hanu ta karɓesa shuru yayi tare da kwantar da kansa jikin Zee, hanu Safreena tasa ta ƙara ɗaukar sa ya kuma cilla kuka, Zee na kuma karbarsa yayi shuru. " Meke damun yaron nan ne, dana karbesa sai kuka tamkar wacce nake jona masa wuta." Bakinta Zee ta taɓe tare da cewa. " Da yiyuwa akwai Soyayya ne tsakanin ɗa da Ubansa, wataƙil yana jimamin ubansa ne, da kuma haushin kina neman ganin bayan jininsa ko iya wannan ya kamata ki fahimci kin aikata zunubi, komai tare muke kina neman shawarata kafin ki zartar da hukunci, da kika tashi aikata zunibinki kuma sai kika ware kanki ki aikata a ɓoye, sai ki girbi abinda kika shuka ke ɗaya. " Haba Zee ya..........." Zee bata tsaya ta ji abinda Safreena zata faɗa ba ta fice ranta a matukar hasale, Aunty Batul ce tace. " Ranta ne ya ɓaci amma zata huce, Zee bazata iya fushi da ke ba, nima bara naje na watsa ruwa." Tayi Maganar itama tana ficewa, kwanciya Safreena tayi tare da yin shuru cike da nadama. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Ƙarfe ɗaya dai-dai Ya khalil ya shiga asibitin, su Daniel suna biye dashi a baya duk wanda ya gansa yasan cikakken soja ne ya iso duk da uniform bane a jikinsa, darect office ɗin doctor ya nufa tare da nocking, UMARNIN ya shiga aka basa sannan ya shigo zama yayi tare da miƙawa doctor hanu Sukayi musabaha. " Doctor nine ɗan uwan waɗanda aka kawo ɗazu da misalin 11 am sunyi hatsarin mota mace da namiji." Gyaɗa kansa DOCTOR yayi tare da cewa. " Tun ɗazu ake jiran isowar ku baku iso ba, har muka fito daga emargency meyasa."? " Doctor muna cikin Gombe ne tsakanin mu da Gaɗam akwai tazara, yanzu ya ake ciki a wani hali suke."? Shuru doctor yayi yana fargar abinda zai sanar da Khalil sai da yayi shuru kafin yace. " I am sorry to say da abinda zan faɗa maka, shi dai namijin mun masa treatment yanzu haka yana ɗakin hutu, a bisa buguwar da yayi a kirjinsa yasa zuciyarsa ta taɓu ma'ana ya kamu da ciwon zuciya sai dai da yiwuwar zai warke idan har aka bi ƙa'idar mu, saboda ciwon zuciya yana warkewa idan baiyi ƙarfi a jikin mutum ba, bugun zuciya ne baya warkewa shine har ya kashe mutum, amma ku godewa Allah ba bugun zuciya bane, amma dai har yanzu bai farfaɗo ba mun masa allurar bacci." Dafe kansa Ya khalil yayi cike da tashin hankali yace. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati wa'akfilni kairan minha!!!! Hmmm!!! Doctor ita kuma macen fa tana wani hali." " Gaskiya nata yafi muni, saboda ta bugu sosai a kanta har yanzu bata farfaɗo ba, kuma bama saka ran zata farfaɗo nan kusa doguwar suma ta tafi da yiwuwar zata kai kwana uku kafin ta farfaɗo, sai dai inda matsalar take ƙwaƙwalwar ta ta juya saboda ta bugu sosai muna tsamanin ma, tayi missing ɗin memory ta ma'ana muna tsamanin zata manta komai na rayuwarta idan ta farfaɗo, idan kuma Allah ya taimaka ta farfaɗo normal, AMMA dai munfi tsammanin tayi missing ɗin memory ɗinta." Wani irin zabura Ya khalil yayi cike da tsantsar tashin hankali ya furta. " Whatttt DOCTOR!!! Tayi missing ɗin memory ɗinta kake nufi....................?" *08147537180* *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:22 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *45 to 46* " Cool down!!! Cool down!!! Bafa nace maka ta kamu da cutar mantuwa bane ce maka nayi muna tsammanin zata iya kasancewa, ba wai ya kasance bane, dan sai mu dage da addu'a Allah yasa ta dawo normal." Zama khalil yayi yana huci har yanzu zuciyarsa a tsinke take dafe kansa yayi tare da cewa doctor. " Doctor yanzu ya ake ciki, da zancen maganin su, duk yanda za'ayi su sami lafiya doctor ayi, idan Maganar kuɗi, bana jin wannan ko nawa ne zan iya kashewa domin su sami lafiya." " Ba damuwa insha Allah zasu sami lafiya karka damu, am yanzu haka akwai list ɗin abinda aka kashe na test da abubuwan da aka musu kasan dai nan private hospital ne, zan baka rasit kaje ka biya." " Okay ba damuwa DOCTOR za'a biya." Sun juma suna tattaunawa game da yanda za'a biyowa lamarin nasu kafin doctor ya bawa ya khalil rasit yaje ya biya komai da aka kashe musu, sannan ne ya shiga dakin da aka kwantar da khalil yana kwance yana bacci yayinda hancinsa ke manne da wata ƙaramar igiyar tiyo wacce take taimakawa wajen numfashi kasancewar numfashin na basa wahala, a gefen sa Khalil ya zauna tare da zuba tagumi shuru yayi ransa a jagule da rashin lafiyar ɗan uwansa ya juma sosai a wajen kafin ya bar room ɗin wanda ke gefen na Garkuwa ya shiga Jummo ce kwance tamkar gawa, numfashi ko kaɗan batayi, sosai yaji tausayin ta fiye da tausayin Garkuwa, duk da Norse na kula dasu amma yana da kyau a samu jinin su a kusa, yanzu idan yace Momy ko Zarah ɗaya yazo ya zaunawa Jummo babu wanda zai yadda cikin su, saboda shi kansa ya fuskanci ƙiyayyar da Momy ke yiwa Jummo, numfashi ya sauƙe mafita ce ta faɗo masa (mai zai hana tunda yana kusa da dukku bazai ƙarisa ya taho da INNO da mahaifiyar Jummo ba, idan yaso ita INNO ta ji da maganin Mamma ita kuma Sikayel ta zauna tare da ƴarta da wannan tunanin yabar asibitin, ya ɗebi hanyar dukku tafiya ce ta minti arba'in ta kaisa cikin dukku har kauyen CILO, tunda Ya khalil ya shiga cikin CILO yake neman gidan su Jummo saboda bai san garin ba ba zuwa yake ba, dakyar ya samu wani yaro ya kaisa har ƙofar gidan su Jummo wajen Baffa dake zaune cikin almajiransa, ya khalil parking a gefe tare da tahowa ya yiwa Baffa sallama, amsawa Baffa yayi yana masa barka tare da nuna masa gefen tabirmar sa yace ya zauna zama Ya khalil yayi tare da gaishe da Baffa cike da mutunci da karramawa Baffa ya amsa sosai Ya khalil ya yaba karancin Baffa, bayan sun gaisa ne ya khalil ya gabatarwa Baffa kansa tare da masa bayanin abinda ke faruwa da Mamma har Jummo, Sosai hankalin Baffa ya tashi, duban ya khalil yayi tare da cewa. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Ikon Allah, ba yadda baya ikonsa, Jummo sunyi haɗari, itama Mamma ba lafiya, ba komai jarabawa ce, babu wanda yafi ƙarfinta, insha Allah zasu sami lafiya, bari muje na kaika wajen INNO daga nan zan ɗan shiga cikin jeji akwai abubuwan da zan tsinko zan bada magani ka tafi musu dashi ka ɗan jirani kaɗan." Da to khalil ya amsa sannan suka shiga cikin gidan, INNO suka samu zaune a barandarta sai famar tiƙar goro take gefen ta kuwa kararen sigari ne wanda tasha zube a ƙasa, a gefe ya zauna yana kallon sigari cikin zuciyarsa ya furta, (Sai hali yazo daya ake abota da Mamman da INNOn duk kwaryar ƙasa ce da ta sama) a kujera ƴar tsugunno ya zauna, Mamma da kallon rashin sani ta bisa tare da cewa Baffa. " Kai kuma Baffa akwai da yayiɓo kara da kiyashi shi kuma wannan koɗaɗɗen mutumin ina ka ɗebosa, bari wata rana ka je ka yayo kidnanas." Zaro idonsa Ya khalil yayi yana kallon rashin mutuncin INNO, kaji tsohuwa da bakar Magana, wato shine ma kara da kiyashin muryar Baffa yaji yana ce mata. " Jikanki, ɗan gidan Buban Mamma, wajenki yazo, kai kalilu sai kuyi magana ko, ni bara naje na dawo." Kaɗa kansa khalil yayi alamun to sannan Baffa ya fita INNO dariya tayi tare da cewa. " Ayyo ai sai da kafaɗa na gano katon kan Buban, ɗan nema falafalan kunnen kuwa kamar kosai, ko da yake na uwarka ne, itama haka nan kunnen ta, kai Oh Zainabu ai hatsabibiya ce, wai na tambayeka, har yanzu uwarka zainabu tana nan da tsiyar ta ko ta daina, dan dai ƴaƴan hayin gada badai tsinantaka ba, kuma ko kaf unguwar gidan su Zainabu sunfi tsiya, shegu ga talauci kamar zai kashe su,sai tsiya, bari kaji kakanka mahaifin Zainabu wallahi cikakken matsafi ne, tsabar tsafi fa Irin nasa, sanda yayi mutuwar walaƙanci, wallahi hauka yayi tuburan sanda aka dauresa da sarƙa, kai karshe fa kafin ya mutu sanda ya makancce ya kurmance, sunmun bukumun kenan kurame makafi, hai inke faɗa maka.............." " INNO ya isa.............." Ya khalil ya furta yana runtse idanunsa tare da cije leɓensa, sosai yaji ƙunar maganganun INNO, da ganin idanunta zaka fahimci gaskiyar ta take faɗi irin matan nan marassa tsoro da faɗar magana ba bu shakkar ido, cikin zuciyarsa ya furta (haka dangin Momy suke da mummunan tarihi?) Muryar INNO yaji tace. " Umm to shikenan nayi shuru tunda gaskiyar ne baka son na faɗa, sai famar zuba ma nake kamar kanya ban tambayeka aminiyata Mamma da jikata Jummo, oh shegiya Jummo tana can binni ta samu duniya ta manta da INNOn ta, ni kuma kullum sai nayi mafarkinta, kasan me, ko jiya sai da nayi mafarkinta wai tana kuka tana nazo na taimaketa." Shuru ya khalil yayi ya zuba mata idanu yanda take Magana ko gajiya batayi ba tare daya ce komai ba " ita ko gajiya da surutu batayi" ya furta a cikin zuciyarsa yana kallon ta. " Wai mayene kai ka tsura min idanu tamkar zaka haɗiye Ni, to kur kurwa ta tafi ƙarfinka da wasu ƙanƙanan idanunka." Dariya Maganar ta bawa khalil lallai wannan tsohuwa akwa comedy yo ko shi mayene mai zai tsinta a jikinta." " Kinga INNO, nifa ba zuwa nayi ki isheni da faɗi ban tambayeki ba, zuwa nayi na sanar dake zan ɗaukeki mu tafi Birni keda Mahaifiyar Jummo." " To ubanmu zoka ɗaukeni ka jani mu tafi, yo ni ko naman ɗawisu ake dafawa a binni ai bani zuwa, anan dai ƙauyen dai zan ƙarisa rayuwata. " Bafa zuwa zakiyi ki zauna ba INNO, Mamma bata da lafiya, tana buƙatar taimakon ki, INNO Mamma tana matuƙar buƙatar ki taimaka mata dan Allah karki ƙi." A matuƙar razane INNO ta dubi Ya khalil tare da cewa. " Mamma bata da lafiya subahanallah!! Meyake damunta." Duk abinda yake faruwa sai da Ya khalil ya sanar da INNO har accident ɗin su Jummo a hanyarsu ta zuwa, jiƙewa INNO tayi sharƙaf da gumi, shuru tayi tare da rufe idanunta, sai kuma ta miƙewa tsaye cike da tsawa da faɗa take cewa. " Babu inda Sikayel zataje, bazamu watse mubar gida mu duka ba kowa ba, ni da ya zamo dole naje zanje ni, gidan naku babu mata ne waɗanda zasu kula da Jummo har sai Uwarta taje to bazata ba, ku barta ta mutu, wallahi wallahi khalilu idan na tabbatar da zargina asiri aka yiwa Mamma na rantse da Allah duk wanda ya mata sai ya gwammace kiɗa da karatu kuma nasan ba wata bace zatayi wa Mamma asiri sai Uwarka Zainabu saboda nasan halinta tamkar yunwar cikina." Tayi Maganar idanunta sunyi jajur tare da shigewa bukkar ta, kayanta na magani ta tattara da abubuwan da take buƙata sannan ta ɗauki mayafinta, wajen Sikayel taje ta mata bayanin abinda ke faruwa sosai Sikayel hankalinta ya tashi game da damuwar Jummo. La'asar lis Baffa ya gama haɗa duk maganin da ake buƙata ya bawa khalil a hanunsa yace a dinga shafawa Jummo a kanta, a kuma dinga ɗiga mata a kunnen ta, insha Allah zata farfaɗo lafiya, wannan kuma ku dinga shafawa Mamma a jikinta kuna bata tana sha Insha Allah zasu sami lafiya." Sosai Ya khalil yaji daɗin abinda Baffa ya masa suka kamo hanyar Gombe da INNO. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ A matuƙar gajiye suka shigo cikin gidan, tare yana riƙe da boron INNO, bata yadda ta shiga cikin falon ba sai da ta ciro wani abu cikin boron nata, ta samu wajen dake da ƙasa ta sunkuya tare da tona rami ta binne wani abu tamkar mulmule, sannan ta miƙe ta cewa Khalil muje, cikin falon suka shiga da sallama, Momy dake zaune ne ta miƙe a razane tana kallon INNO cike da tsoro, mungun kallo INNO ta jefa mata tana kallon kwayar idanunta, sunkuyar da kanta Momy tayi cike da tsoron INNO. " Kalilu ina Mamman take?" . shuru Ya khalil yayi yana kallon Momy da ta sunkuyar da kanta cike da tsoro da alamu abinda INNO ta faɗa akan gidansu gaskiya ne, idan kuwa hakane tir da zuriar Momy, shigewa gaba yayi INNO ta bisa a baya har bedroom ɗin Mamma, da sauri INNO ta matso kusa Mamma tana riƙe hanunta, tafin hannunta ta buɗe tare da ƙarewa tafin hannunta kallo duban A'illo dake zaune tayi tace. " Tunda ta kwanta, akwai wanda ya shigo ya dubata." Hawaye ne ya gangaro daga idanun A'illo cikin rawar murya ta ce. " Babu wanda ya shigo yace ya jikinta tunda ta kwanta sai yaya khalil kawai da Daddy da suke shigowa, da kuma yaya Garko, amma Momy da Aunty Zarah babu wanda yazo yace ya jikin Mamma." Murmushi INNO tayi tare da cewa, "sammu aka mata, kuma insha Allah zan cire mata daga jikinta, na mai dashi jikin wanda ya aikata, karki damu A'illo, ki kwantar da hankalin ki, ki cigaba da addu'a nima zanyi iya ƙoƙarina, ki shirya yanzu zaku tafi da kalilu ya sauƙeki wajen Jummo kije ki kula da ita ga wannan maganin da Baffa ya bayar ki dinga shafa mata a kanta duk bayan awa biyar tare da ɗiga mata a kunnen ta, insha Allah babu abinda zata manta, zata farka cikin hankalinta." " INNO wajen Jummo kuma jummon bata da lafiya ne, mai ya sameta." Tayi Maganar a gigice, INNO cike da kwanciyar hankali tace. " Ki kwantar da hankalin ki A'illo, sunyi haɗari ne a hanyar zuwan su cilo amma alhamdulillah da sauƙi, ki dai kije kiyi abinda na umarceki." Da to A'illo ta amsa tare da ficewa daga bedroom ɗin tayi nasu, Sadiya ta samu tana ƙoƙarin haɗa kayanta sai kuka take tamkar wacce zaa zare mata rai, A'illo bata kula Sadiya ba ta shige tolet. Momy tashin hankali iya tashin hankali ta shigesa ganin INNO a cikin gidan, domin kuwa tasan kashin ta ya bushe "wani irin rashin tunani ne ma ya sani na aikata wannan aikin meyasa ban kasheta ba kawai na huta gashi yanzu na jawowa kaina masifa da hanuna, kona kira Asabe ne ko zan saamu mafita, mtsss to me zata iya min INNO tana cikin gidan nan, mtsss bari dai na kirata muji." Tayi Maganar tana kiran wayar Asabe ringin ɗaya Asabe ta ɗaga cike da tashin hankali, Momy take sanar da Asabe abinda yake taruwa, sun juma suna kitse kitsen yadda zasu sami mafita kafin suka yanke shawarar Asabe zata koma wajen boka domin nema musu mafita." Ta ɗan juma da gama wayar Ya khalil ya shigo tare da zama gefen Momy kansa ya ɗaura a kafaɗar Momy sai kuma idanunsa suka ciko da hawaye cikin sanyin murya yace. " Momy ina son sanar dake wani al'amari sai dai ban san ta ya zan iya faɗa miki ba, dama zakiyi hkr ki rungumi ƙaddara kiyi addu'a, Momy da na sanar dake sai dai ina tsoron sanar dake saboda ban san ya zaki ɗauki maganar ba." Cike da tsinkewar zuciya Momy ta ƙara jawo khalil jikinta tana shafa kansa tare da cewa. " Karka damu da yadda zan dauki Maganar ka sanar dani kawai insha Allah zan ɗauki hkr da koma meye." Hawayen da ya khalil ke ƙoƙarin boyewa ne suka zubo masa, numfashi ya sauƙe tare da cewa. " Momy ɗazu da safe, Garko da Jummo sunyi accident a hanyarsu ta zuwa Cilo" A wani irin gigice Momy ta miƙe tsaye tare da yin baya zata faɗi, Ya khalil yayi saurin taro ta yana cewa. " Subahanallah!!! Momy shiyasa nake ta tsoron sanar dake saboda bansan wani hali zaki shiga ba." Cike da tashin hankali Momy tace. " Yanzu Garko yana ina yana wani hali, ina dai ba mutuwa yayi ba innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Na shiga Uku ɗana." " Oh Momy Garko fa bai mutu ba da ransa, kawai ya samu rauni ne, amma fa da sauƙi sosai harma ya samu bacci, ki kwantar da hankalin ki." Ya khalil ya boyewa Momy cewa Garkuwa ya kamu da ciwon zuciya gudun tashin hankalin ta, wani numfashi Momy ta sauƙe tare da furta. " Alhamdulillah!!! Yanzu yana wani asibiti bara na ɗauki mayafi na ka kaini." " Momy a can gaɗam fa sukayi haɗarin, yanzu kuma dare yayi babu halin muje ki bari sai da safe." " Na bari sai da safe kuma haka za'a barsa babu mau kula daahi a'a bazai yiwu ba, ni zanje na kula da ɗana bazan barsa cikin kaɗai ci ba." " Oh Momy wa yace miki babu mai kula dashi private hospital ne special, akwai nurse masu kula da marar lafiya yanda ya dace dan haka ki kwantar da hankalin ki ɗan lelenki yana nan cikin kulawa." " Shikenan zanyi hkr iya na yau kawai, amma dai gobe dole na je na kula da yarona." Murmushi Ya khalil yayi yana kallon Momy cike da mamakinta hankalinta duk ya tashi akan ɗanta, amma ita Jummo ko ta tambayi wani hali take ciki. " Momy!!!" Ya kira sunanta a kasalance, ɗaga idanu Momy TAYI ta kallesa tare da amsa. " Na'am khalil menene?" " Momy nikam Garko kam shi kaɗai ne ya tafi Cilo.?" Momy ko a jikinta ta amsa da cewa. " Shi da wannan annabor Yarinyar ce, wataƙila ma itace ta sashi yayi wannan accident ɗin, tsinanniy............" " A'a!!! A'a Momy!!! Karki ƙarisa ta juyo kanki, annoba fa kikace Momy, ta ya ta zamo annoba." " Khalil annoba ce tunda Yarinyar suka shigo cikin gidan nan komai na gidan nan ya lalace, babu walwala, bamu da nishaɗi komai ya kacame mana ta watsa mana da farin cikin mu." Murmushi Ya khalil yayi yana kallon Momy yace. " Farin ciki!!! Ina farin cikin yake!!! Dama can babu wani farin ciki, a gidan nan!!! Gidan da iyalansa basu san su haɗu su zauna suyi hira koda na lokaci kaɗan ba, bamu taɓa zama na minti talatin domin jin damuwar ɗan uwan mu ba, hatta mahaifin mu bai damu daya jawo mu a jikinsa ba, kullum da safe zaiyi gaggawar fita kasuwa, da ya dawo kuma zaice a dauko masa system ɗinsa zaiyi lissafi anan lokacin sa yake ƙarewa, kullum rayuwar a cikin haka take, kowa sha'anin gabansa yake babu ruwan wani da wanii babu wanda zai damu da ɗan uwansa, to ki faɗa min ina zumuncin yake, babu Momy!!!babu shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin iyalan mu, misali Momy, Sajida ƙanwar muce Uwa ɗaya uba ɗaya, Daddy ya kaita karatu can Egypt, yau shekarar ta Biyar Daddy dake baku taɓa kai mata ziyara ba, bakwa tunanin wani hali take ciki, nima da Garko sau biyu kawai muka ziyarce ta, bamu san ya take rayuwarta acan taba da wa take mu'amala bamu sani ba, sai kuɗaɗe kawai da muke tura mata, haka shine zumuncin, Babu abinda ya lalace a cikin gidan wanda Jummo ta lalata, dama can gidan mu babu nishaɗi mune muka lalata gidan mu da kanmu!! Ki daina zargin Jummo bata da laifi sai ma ƙoƙarin da take wajen ganin gidan mu yayi kyau." Girgiza kanta Momy tayi idanunta sunyi jajur, nufo Ya khalil tayi ta ɗaukesa da mari tare da nunasa da yatsa. " Ya isheka haka khalil, rayuwarmu muke dai-dai a cikin gidan nan babu wani kuskure, kar zuciyarka tayi gaggawar aminta da zantukan wannan hatsabibiyar Yarinyar, ƙarya take maka ko wani gida rayuwa suke dai dai da tamu, neman watsa mu take, ka kasa ganewa, wai ma na tambayeka shin sonta ka fara da har kake ɗaukar zancen ta.?" " So!!! So!!! So!!! Hmmm, ai kun duƙursar min dashi sanadin kuskuren ahalina, dalilin da yasa zuciyata ke ƙuna a duk sanda na tuna hakan." " Kuskure!!! Wani kuskure muka maka wanda har zai duƙusar da kai...................." 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Nima zanso sanin wannan kuskuren na dai yi nan. 08147537180 *UMMU NASMAH CE* [4/15, 9:22 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *47 to 48* " Hmmm!!! Yaushe naji daɗin Soyayyar wacce nake tare da ita ma, babu soyayya tsakanin ki da Zarah kullum cikin hantarar ta kike da kyara hakan yasa matsaloli suka dinga gudana tsakanin mu kullum nakan danneta aduk sanda kika ɓata mata na bata laifi duk da laifinki ne, saboda karta raina min ke, nafi son ko yaushe a dinga daraja minke, Amma ina Momy kin kasa fahimta bare ki gyara, Momy a karo na biyu naji Soyayyar Jummo bazan ɓoye miki ba sai dai kash sanadin rashin shaƙuwar dake tsakanina da ɗan uwana yasa na kasa gane muna son Abu ni dashi, saboda bamu san damywar juna ba, da na sani Wallahi Momy bazan sake sonta ya shiga zuciyata ba, sai daga baya na fahimci Soyayyar dake tsakanin su, na kuma gane duka suna son junansu ta hanyar jinsu da kunnena suna hirar, tun daga ranar na ɗauki alƙawarin cire Soyayyar ta a zuciyata abun baƙin ciki shine har yau na kasa, mtsss!!! Hmmm!!! Sai dai fa Momy dole ne zan haƙura na barwa ɗan uwana saboda ya fini buƙatar ta, wannan shine kuskuren ki keda Daddy kun ɗauki rayuwar boko, babu ruwanku da ƴaƴan ku, kowa yaje yayi abinda yake so, kun kasa saka shaƙuwa a zukatan mu, hmmm!!! Jummo haske ta kawo gidan mu, kuma na yabawa ƙoƙarin ta, ina kuma bayanta zan bata gudumowa ta kowacce hanya." " Zan kuma tsine maka!!! Muddun ka cigaba da bin wannan Yarinyar kana ɗaukar huɗubar ta, wallahi zan tsine maka, idan yaso kaje ka lalace a duniya." A matuƙar razane ya khalil ya ɗago idanunsa yana duban Momy cike da mungun mamaki, kansa ya girgiza tare da cewa. " Momy zaki tsine min kike cewa, ke da kanki kike furta wannan kalmar?!! Hmmm!! Meyasa kika fiye son kanki ne Momy fiye da kowa bakya son gaskiya, na juma da fahimtar haka tun kafin su Jummo suzo gidan nan, na fahimci hakan ne tsakanin ki da Zarah yadda kike wulaƙanta ta, bata da ƴanci a gidan mijinta, kawar da kaina kawai nake a matsayin ki na mahaifiyata, bana son ɓata miki rai, ina son na gama da duniya lafiya, kuma dole sai na miki biyayya haka zata kasance, Momy!!! A wannan karon bazan bi bayan ki ba, bayan gaskiya zanbi." Yana gama faɗin haka ya fice da sauri yana huci, dafe ƙirjinta dake buga mata Momy tayi tana riƙe bakinta ( Cap innalillahi, tana shirin rusa min farin cikin gidanae, Allah ka kashe Yarinyar nan na huta addababbiya nacacciya) Momy ta furta tana jingina jikin bango, shuru tayi cike da tashin hankali ta tsani Mamma da Jummo saboda tunda suka shigo cikin gidan komai nata yake neman lalacewa . Ya khalil kuwa sosai yaji ransa ya ɓaci game da halayyar mahaifiyarsa, ya rasa Momy wata irin mutum ce mai son kanta, tun kafin Jummo suzo cikin gidan ya juma da fahimtar haka, sai dai bai gane suna zaman rashin shaƙuwa ba sai zuwan Jummo, numfashi ya sauƙe tare da tura ƙofar bedroom ɗinsa ya shige, zama yiyi tare da zama gefen bed ɗinsa, Zarah tana kwance ɗagowa tayi tare da cewa. " My dear! Lafiya kuwa.?" Bakinsa ya cije tare da ciro wayarsa, yana dannawa Daddy kira ringin ɗaya Daddy ya ɗaga cike da damuwa Ya khalil ya sanar da Daddy abinda ke faruwa sosai hankalin Daddy ya tashi, sai dai Ya khalil ya kwantar masa da hankali sosai har sai da Daddy yaji damuwar tasa tayi sauƙi sannan khalil ya katse kiran, duban Zarah yayi yace. " Wannan shine damuwar" Tare da tashi ya shigewa tolet, Aunty Zarah Sosai ta tausayawa halin da su Jummo suka tsinci kansu duk a yanzu ba wai wani shiri bane tsakanin su, sai dai har cikin zuciyarta ta tausayawa Jummo musamman ace mutum ya manta komai na rayuwarsa ai abun babu daɗi. Mamma kuwa har yanzu tana nan yanda take babu wani canji a lamarin ciwon ta, yayin da INNO ta duƙufa wajen mata magani a wunin Ranar bata gajiya ba, sai dai duk binciken INNO ta kasa gano ainihin abunda ya faru da Mamma. Koda A'illo taje taga Jummo ko motsi batayi sosai hankalinta ya tashi, ƙarfe sha ɗaya na dare Garkuwa ya buɗe idanunsa a hankali yana ɗan jin jiri kaɗan, haka yaji ƙirjinsa ya masa nauyi nurse din dake wajensa ne ta fita da gudu kiran DOCTOR a hankali abubuwan da suka faru suka fara dawo masa, Jummo zuciyarsa ta furta tare da yunƙura zai tashi dai-dai doctor sun shigo, da sauri likitan yazo ya riƙesa tare da maidashi ya kwanta, oxygen ɗin dake maƙale a hancinsa ya cire masa, yatsansa ya saka a daidai hancin nasa sai yaji numfashin nasa yana tafiya dai-dai alhamdulillah doctor ya furta, tare da miƙewa daga kansa yace. " Sannu ya kake jin jikin, me yake maka ciwo yanzu?" Lumshe idanunsa ya Garkuwa yayi yana dafe ƙirjinsa, cije leɓensa yayi a hankali ya furta. " Ƙirjina ke min nauyi, kaina shima yana min ciwo, amma doctor bashi yafi damuna yanzu ba, Jummo ina Jummo take, ina son sanin halin da take ciki.?" Numfashi doctor ya sauƙe tare da sunkuyar da kansa baya son faɗawa Garkuwa halin da take ciki, nurse lura da halin da doctor ya shiga ne ya sata cewa. " Itama jikinta alhamdulillah ta dawo normal harma ta samu bacci." " Ina son ku kaini na ganta." Ya furta maganar yana ƙoƙarin zai miƙe, saurin riƙesa DOCTOR yayi tare da cewa. " Bata cikin wannan asibitin tana can ƙasa damu anan ake kula da ita, a yanzu bazai yiwu mu barka ka fita ba, kayi hkr har zuwa mu sallameka, itama tun jiya take cewa a kawota wajen ka, dan Allah duk kuyi haƙuri har a sallameku." Doctor ya yiwa Garkuwa ƙarya duk dan saboda hankalinsa ya kwanta, an kuma yi Sa'a jin cewa itama tana son zuwa wajensa yasa Garkuwa hankalinsa ya kwanta yayi tunanin tana lafiya, da wannan Garkuwa ya haƙura." ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Bayan kwana uku* Yau tun safe Ya khalil yake asibitin shida Daddy, suna nan tsaye akan Jummo tun safe suke tsammanin farfaɗowarta amma shuru har shida na yamma, sosai likitan ya tsorata domin kuwa yana tabbacin cewa muddun ta wuce yau bata farfaɗo ba, ya tabbata zata farka da cutar mantuwa, shi kansa Ya khalil ƙirjinsa dukan uku Uku yake, idanunsa na runtse baya ƙaunar wannan mummunan lamari ya faru da Jummo zuwa wannan lokaci kowa ya fidda rai ga farfaɗowarta, Daddy ne ya dubi DOCTOR tare da cewa. " Doctor me hakan yake nufi, kunce kwana uku zata farfaɗo gashi kuma lokaci yayi har yana neman ƙurewa amma shuru babu wani alamar zata farfaɗo." Shuru doctor yayi cikin jagulewar rai yace " Mu ɗan ƙara jira mu gani idan Allah yasa ta buɗe idanunta zamu mata tambaya Uku idan ta amsa dai-dai to ƙwaƙwalwar ta ta dawo dai-dai idan kuma bata amsa ba to sai dai muyi hkr ta kamu da cutar mantuwa, sai..........." Bai ƙarisa Maganar ba nurse fa'iza tace. "Lah!!! Doctor duba kaga yatsanta yana motsi." Da sauri dukkansu suka maida kallonsu kanta, doctor cikin hanzari yace a rufe dukkan ƙofa da window dake room ɗin tare da sawa aka kashe wuta ita kuwa Jummo a hankali numfashin ta ya fara harbawa sai kuma ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta, tana hango hotunan accident ɗin da sukayi, a hankali harta buɗe idanunta hawaye na gangarowa daga idanunta duhu sosai take ganin room ɗin sai sautin numfashin mutane da take jiyowa kusan 15 minute da farfaɗowarta sannan DOCTOR ya kunna wutar room ɗin gaba ɗaya kallonta sukayi, itama da kallon take binsu ba tare da tayi magana ba, doctor ne ya sunkuya a gabanta tare da kiran sunan ta. " Jummo!!" Shuru tayi tamkar bada ita yake ba, waro idanunsa yayi wannan fa shine tambaya ta farko da zai nuna tana hayyacinta, sau Uku ya kira sunanta bata amsa ba, yawu mai ɗaci ya haɗiye tare da nuna mata uniform ɗin jikinsa dake fari fat yace. " Wannan baƙi ne ko fari.?" Nan ma Jummo kau da kanta gefe tayi, jawo hannun Ya khalil yayi gabanta yace. " Kinsan wannan."? Sai yanzu ta ɗago kanta ta kalli Ya khalil a hankali tamkar mai koyon Magana tace. " Yaya khalil!!! Ya Garkuwa ya mutu ko?" Gabaki ɗayan su alhamdulillah suka furta, cikin dariya Ya khalil ya zauna gefenta tare da kamo hanunta ya girgiza mata kai. " Bai mutu ba, yanzu ma zai shigo ki gansa, ya kike jin jikin naki."? Kanta ta riƙe tace. " Kaina yana min nauyi kamar dutse ya khalil sai dai nauyin da yake min bai dameni ba, kamar yadda zanso ganin Ya Garkuwa, Ya khalil dan Allah ka kaini wajen sa." Doctor ɗago kai yayi ya kalleta cike da mamaki kusan maganarta ɗaya da wanda GARKUWA ya masa sanda ya farfaɗo, da alamu dai akwai wani abu tsakanin su, Ya Garkuwa kam murmushi yayi tare da miƙewa tsaye ya fita, room ɗin Garkuwa yayi tare da samunsa ya kifa kansa yayi shuru idanunsa sun cika da kwalla, kusa dashi Ya khalil ya zauna tare da dafa kafaɗarsa. " Lafiya ɗan uwana, kake ƙoƙarin kuka, karfa ka manta cewa, baka da lafiya, kwanciyar hankali kake buƙata ba damuwa ba, just tell me pls what happening." Karo na farko da Ya khalil ya fara tambayar ɗan uwansa damuwarsa, runtse idanunsa Ya Garkuwa yayi tare da jin wani sanyi, da Ya khalil ya tambaye sa maike damunsa, maimakon da da idan ya gansa a wannan halin sai dai yace, (Kai kuma a wannan ƙarnin mai zai maka zafi harka zauna sawa kanka damuwa a banza, just share koma meyene ka cigaba da rayuwarka) shima hanu yasa ya dafa kafaɗar Ya khalil, duk da a yanzu bazai iya sanar daahi damuwarsa ba, saboda akwai kunya yace Sadiya ta kira ta ci mutuncin sa, bare kuma ya faɗi abinda ke faruwa tsakanin su, juya Maganar yayi kan Jummo tare da cewa. " Na gaji ne ina buƙatar ganinta sunƙi bani dama zuciyata kuma ƙuna take min, ganinta kawai zaisa naji sauƙi." Murmushi Ya khalil yayi yana dukan kafaɗarsa yace. " To mister romio tashi muje ka ganta, kaikam ma yau za'a sallameka mu koma gida, ita dai Jummo nata sallamar sunce ba yau ba." Ɗan murmushi Ya Garkuwa yayi tare da miƙewa suka jera tare da Ya khalil, suna fitowa ya khalil ya doshi room ɗin dake kusa dana Ya Garkuwa, tsayawa Garkuwa yayi tare da cewa. " Bros, me kuma zamuyi a wannan room ɗin." " Wajen Mrs Love ɗin naka zamuje a nan take ba'a waje ba." " Okay!!! Wayo kuka min kenan, kun maidani yaro, kaikam Bros bashi kaci kuma zan rama." " Sai dai ka rame" cewar ya khalil yana shigewa room ɗin bayansa Garkuwa yabi, a zaune ta hangota tayi shuru, da sauri ya nufota, shi kuwa Ya khalil ya tare gabansa yana dariya, hanun Ya Garkuwa ya kama dana Jummo ya haɗa waje guda yana runtse idanunsa, har cikin zuciyarsa yaji zafi, sai dai duk da zafin da zuciyarsa ke masa hakan bai hana annuri bayyana a saman fuskarsa ba, cewa yayi. " Ka kula da ita saboda kayi dace idan har ka samu aurenta duk rintsi duk wuya karka sake ko da wasa ka rabu da ita nasan akwai danja da ƙalubalen da zai fuskanto soyayyar ku, ka daure ka tsallake wannan siraɗin" Daddy Ya khalil ya kalla tare da cigaba da cewa. " Daddy ga Jummo da Garko suna son junansu, sai dai ina da tabbacin zasu fuskanci matsala a cikin Soyayyar su, dan Allah Daddy ka zamo musu katangar da zata ƙetarar dasu siraɗin dake gabansu, idan ka samu a matsayin suruka, Daddy zakayi alfahari da ita." Ya ƙarisa Maganar idanunsa yayi jajur tamkar garwashin wuta, Ya Garkuwa da kallo yabi Ya khalil bakinsa cike da tambayoyin ina khalil yasan akwai Soyayya tsakanin sa da Jummo, sannan menene ƙalubalen da yake tunkarar su cike da nauyin baki yace. " Ƙalubale kuma Bros, wani irin ƙa............" Hanu Ya khalil ya ɗaga masa tare da cewa. " Daga kai har Daddy dan Allah karku min tambaya game da wannan ƙalubalen, lokaci shi zai baku amsar ku." Daddy shuru yayi ba tare da yace komai ba, ya kalli doctor tare da cewa. " Zaku iya bamu sallamar Garko, ita kuma sai ku taimaka ku bani takaddar transfer daga wannan asibitin zuwa medical center, saboda nan ɗin ya mana nisa sosai please help you Doctor." Shuru doctor yayi yana tunani kafin daga baya yace. " Okay ba damuwa ku biyoni office." Da to Daddy ya amsa suka bi bayan doctor har Garko, Jummo jingina kanta tayi jikin gadon tare da yin shuru ta rufe idanunta, Mamma take hangowa "ko wani hali take" ta furta a fili. Can kuwa DOCTOR ya basu sallama yayin da ya bawa Daddy takadda ya kai medical center, su kula da Jummo, haka kuwa sukayi daga sj gaɗam ɗin suka wuto medical, tare da yin duk wani cuku cuku daya dace aka basu room, Ya khalil ne ya bawa Jummo wayarta, wanda cikin ikon Allah babu abinda ya samu wayar, karɓa tayi suka barta da A'illo sannan suka koma gida, koda suka koma Momy da sauri ta rungume Garko tana dariya tace. " Alhamdulillah!!! Allah mun gode maka, sannu Garko sannu." Murmushi Garkuwa yayi yana ƙanƙame Momy cike da so da ƙauna, Ya khalil ne yace. " Momy baki tambayi jikin Jummo ba." Harara Momy ta watsa masa gudun bakin Daddy yasa ta cewa. " Ya jikin nata."? Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa. " Da sauƙi" yana shigewa room ɗin Mamma, tana nan kwance yanda take jikin babu wani sauƙi, sai Zarah dake zaune gefen INNO yayin da INNO ke haɗa wani ruwan magani, kallon khalil tayi tace. " Kalilu ya jikin Jummo ta farfaɗo kuwa."? " Ehh ta farfaɗo kuma Alhamdulillah ta dawo cikin hankalinta, INNO ya labarin jikin Mamma har yanzu babu wani sauyi."? Shuru INNO ta yi cikin sanyin jiki, domin kuwa ita kanta rashin lafiyar Mamma ya fara bata tsoro. " Kalilu gashi nan dai babu wani sauƙi, kullum jiya i yau, hmmm!!! Amma tabbas sihiri ne, sai dai na rasa gane ta ina zan fara karyasa, ni ba duba nake ba bare na duba taya abin ya faru addu'a kawai ya kamata mu dage dashi amma ciwon nata baya jin magani." Shima ya khalil cikin sanyin jiki ya zauna tare da furta. " Allah ya bata lafiya, sun juma sosai suna hira da INNO, a yanzu Aunty Zarah ta ɗan sauƙo daga gabar da take dashi. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Akwana a tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau har satin Jummo Uku a asibiti ana kula da ita saboda suna tsoro matsalar ƙwaƙwalwa shiyasa suka riƙeta, sai yau suka bata sallama sosai Jummo tayi sauƙi tamkar bata samu matsala ba, haka suka dawo gida, baƙin cikin dawowar Jummo tamkar zai kashe Momy, ko sannu da jiki bata cewa Jummo ba, Aunty Zarah kuwa ta mata sannu tamkar babu abinda ya haɗa su. Haka Rayuwa ta cigaba da garawa a cikin wannan gidan yayin da Mamma jiki kam babu sauƙi, Jummo kuwa da Momy ƴar tsama a tsakanin su sai ma ƙaruwa da yayi. Ya Garkuwa dake zaune a cikin room ɗinsa ne yaji wayarsa ta ɗauki kuka, ganin Sadiya ke kira ya sashi ƙin ɗaukar wayar kusan 10 miss call ta masa bai ɗaga ba, shigowar text yaji wayar ya ɗauka tare da duba saƙon yaga abinda ta rubuta. *_Shi dai butulu duk inda yake wallahi yayi asara, Garkuwa ka cuceni ka lalata min rayuwata kai kawar min da mutunci na, sannan ka gujeni, na baka duk wata Soyayyar gaskiya amma ka cutar dani ta hanyar amfani da Soyayyar da nake maka, bazan ce zan tona maka asiri ba, domin kaina zan tonawa, sai dai ka sani na barka da Allah insha Allah a cikin ƴaƴan da zaka haifa sai Allah ya saka min, daga yau bazan kuma shiga rayuwarka ba, kaje kai da Allah, Allah Ya isa tsakanina da kai mungu azzalumi._* Runtse idanunsa ya Garkuwa yayi da ƙarfi yana jin ƙunar maganganun ta, bude idanun nasa yayi take har sunyi jajur, text ɗin ya goge cike da sanyin jiki, cikin zuciyarsa yana neman afuwar Ubangiji. Sadiya kuwa bayan ta tura text ɗin ne ta fashe da kuka tare da Kwanciya ruf da ciki, duk da tasan tarayyar ta da ya Garkuwa kuskure ne, amma bata taɓa tunanin akwai ranar danasani ba a rayuwarta, ba mamaki wannan shine hukuncin zunubin da ta aikata, shin yanzu waye zata Aura ya ganni da mutunci, me zan cewa mijin da zai Aure ni, idan ya tambaye ni ina na kai budurcina mai zance mishi, tabbas na aikata kuskuren da bazai taɓa goguwa a idanun mijin da zan aura ba, Allah ya isa tsakanina da kai Garkuwa ka cutar da rayuwata. Ta ƙarisa zancen zucin tana share hawayen dake gangaro mata tare da alƙawarin mantawa da Garkuwa a cikin rayuwarta. Safreena sosai taji daɗin labarin da Zee ta kawo mata na cewa Garkuwa ya dawo hayyacinsa harma an sallamesa a asibiti ya dawo gida, hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba, a yanzu ƙiyayyarr da take yiwa Garkuwa yayi sauƙi sosai a cikin zuciyarta, a yanzu bata da burin daya wuce taga bayan Kawu Ibrahim, burinta ta ɗaukawa iyayenta fansa wannan shine kawai a ranta. Yau tun safe Mamma take wani irin tari tun sanda INNO ta bata wani ruwan magani take wannan tarin, wani irin yalon kumfa ke fitowa daga bakinta, Jummo ke saka tisue ta goge wannan kumfa, INNO ta sani sarai tasirin gubar asirin da aka sawa Mamma ke fita daga jikinta, amma INNO tayi shuru taƙi faɗawa kowa gudun kar wanda yayi asirin yaje ya lalata mata shiri, su duk a zaton su jikin Mamma tsanani ya ƙara Jummo harda kuka, a yayin da a zahiri Mamma sauƙi takee samu Momy kuwa sosai take murna jikin Mamma ya ƙara tsanani. ******************* Zaune Jummo take a falo tayi shuru cike da tunani, kusa da ita Ya Garkuwa ya zauna ba tare da ta lura da zamansa ba, taɓata yayi a hankali ta juyo tana kallon sa sai kuma ta ɗan saki murmushi. " Ya Garkuwa yaushe kazo nan"? Taɓe bakinsa yayi tare da cewa. " Sanda kike duniyar tunani, meke damunki haka kikayi nisa cikin tunani."? " Ya Garkuwa kasan ai tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, matsalar Mamma ke ɗaga min hankali tana sani cikin damuwa, ciwo kullum ba sauƙi sai ma gaba da ciwon ya ƙara ga INNO ma tazo amma har yanzu jiya i yau, yanzu haka zamu zubawa Mamma idanu a wannan halin." Numfashi Ya Garkuwa ta saki yana dafe fuskarsa yace. " Bazai yiwu a barta haka ba, idan INNO ta kasa ya zamo dole a nemo wani mai bada maganin, ki kwantar da hankalin ki, insha Allah duk inda ake nemo lafiya zamu nemowa Mamma bana son ganinki cikin damuwa." " To shikenan Ya Garkuwa Allah yasa ya bata lafiya, ya Garkuwa ina labarin budurwar kane.?" Cike da tsantsar mamaki yace. Budurwata kuma, waye kuma budurwata bayan ke, kinga nifa gobe zan sanar da Daddy kawai aje Cilo a nemo min Aure ki, ayi kawai mu wuce wajen, na matsu na kasance da ke waje ɗaya Inuwa ɗaya kin san kuwa irin tsantsar Soyayyar da nake miki, ji nake tamkar na mai daki cikina tsabar so ina sonki Jummo." Dariya Jummo tayi har haƙwaranta na bayyana cikin zolaya tace. " A'a malam, aje Cilo da izinin waye, waya faɗa maka ina sonka, kaga fara sanar dani labarin Soyayyar ka da Sadiya kafin ka fara zancen Aure na, da alamu dai kun ɗan soye." Dariya mai sauti ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Ehh mun soye harma mun kusa ƙonewa kwatsam ki shigo rayuwata kika ɓata tsakanin mu." Wani irin bugawa zuciyar Jummo yayi take taji kishin Sadiya har kamar haushinta taji, tsumewa tayi tare da cewa. " Oh nine ma na shiga tsakaninku ko, kuna son junanku na rabaku to meyasa yanzu bazan fita a rayuwar taka ba, idan yaso kuje ku babbake ma ba soyewa ba." Tayi Maganar tana tura baki, hango kishi ƙarara yayi a idanun Jummo, dariya yayi sosai har dimple nasa yana loɓawa yace. " Malama kece fa kika tambayeni ni kuma na faɗa miki gaskiya, to meye kuma na haɗa fuska, bayan kece mai tambayar, bari ma da kiji wato ni da Sadiya ko munsha.................." Yatsanta Jummo tasa ta toshe kunnenta tare da cewa. " Ni ya isheni haka bana son ji, dan Allah kayi shuru karka ƙarisa na roƙeka." Dariya Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Ashe dama haka kike sona sosai, duk wannan kishin wani kike mawa, alhamdulillah!!! Kwantar da hankalin ki farin ciki na, Sadiya dai mun ɗanyi Soyayya amma ba mai tsawo ba, asali ma babu zancen Aure tsakanina da ita, itace take ɗaukar Soyayyar da mukayi a matsayin zan aureta amma babu alƙawarin Aure tsakanina da ita, a yanzu haka albishir ɗin da nake son na miki, shine babu wata alaƙa tsakanina da Sadiya, mun raba Gari kowa ya kama gabansa." Murmushi Jummo ta saki tare da juyowa ta fuskanci Ya Garkuwa tace. " Dole nayi kishi a kanka karka manta da tun kafin nasan meye Soyayya zuciyata take ƙaunar ka, har zuwa yanzu da nasan darajar so, matsuguninka bai sauya a zuciyata ba, sai ma wajen zama ka ƙara samu a gareni, Ya Garkuwa daga yau sunanka ya sauya daga Ya Garkuwa zuwa Heartbeat wato bugun zuciya ta, kaine murmushi na kuma haske na, ban san Soyayyar wani namiji ba, bayan taka, ina sonka zan kuma kasance da kai a ko wani hali ka tsinci kanka a rayuwa bazan taɓa juya maka baya ba, zan tayaka mu rungumi dukkan wata ƙaddarar da tazo maka mai kyau ko marar kyau wannan alƙawari na ɗauka mutuwa ce kawai zata rabani da kai." Tunda ta fara Maganar Ya Garkuwa ya lumshe idanunsa cike da jin daɗin zantukanta, ya sani itace kawai ke masa Soyayyar gaskiya har abada bazai samu mai sonsa da gaskiya irinta ba, sunanta ya furta a hankali. " Jummo!!" Ɗago idanunta tayi tare da amsawa tana murmushi kansa Ya Garkuwa ya kawar gefe tare da cewa. " Karki ɗauki alƙawarin kasancewa dani ta ko wani hali domin kuwa ina tare da aibun da zaki iya tsanata kiji bazaki iya zama dani ba bare kuma Rayuwa ta har abada, a kullum ina son na sanar dake wannan aibun nawa kuma ina tsoron yanda zaki ɗauki zancen wata ƙila ma ki tsaneni ko ki gujeni, ni mai tarin zunubai ne Jummo, duk da tawa ƙaddarar ce tazo da haka, amma a yanzu na tuba nayi tuba ta haƙiƙa shin Jummo zaki iya kasancewa dani idan kikaji mungun halina, ina tsoron kiji ki rabu dani, rabuwa dake a wannan lokacin zai iya zamowa ƙarshen numfashi na.?" Shuru Jummo tayi tana kallon ya Garkuwa cike da mamaki, mungun hali tarin zunubai da yake ambaton yana dashi, cike da ƙwarin gwiwwa tace. " Ka faɗa koma menene ni zan tayaka mu rungumi ƙaddarar, tunda har kace ka tuba, shima kansa Allah ai gafurun rahim ne, bare kuma ni wata banza Jummo, ka faɗa min komai ba tare da tsoro ba, ni kuwa zan karɓi ko mai munin halinka a matsayin ƙaddarar rayuwata." Ya Garkuwa sunkuyar da kansa ƙasa yayi ba tare daya kalli Jummo ba ya fara cewa......." *UMMU NASMAH CE* ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ [4/19, 9:51 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *49 to 50* " Rayuwata ta kasance ne cikin mungun saɓon Ubangiji wanda Allah ke fushi da mai aikata sa, na kasance mutum mai jarabar tsiya wanda sam bana iya riƙe buƙatata, ni mutum ne ma'abocin jarabar mace, akwai wata yarinya mai suna Safreena!! School ɗin mu ɗaya da ita munyi karatu da ita a Oxford University dake ƙasar Amurika, ita set ɗin ƙasan mune, a lokacin da idanuna suka sauƙa akanta naji zuciyata ta aminta da ita naji ina sonta, sai dai ita macece mai kamun da sanin darajar kanta, Asali ma ko ƙawa bata dashi a cikin school ɗin, bare kuma aboki namiji, a sanda naga Safreena na kuma ji ina sonta na fara tunanin ta yaya zan ƙulla alaƙa da ita wanda har zan samu ta saurareni, na kai sati Uku ina nazarin yanda zan fara tunkarar ta, kwatsam wata ranar monday, aka basu assignment Wanda Wannan assignment ɗin shine zai zamo S'A test ɗinsu assignment ne mai matukar wahalar gaske akan biological sciences wanda shi kansa lecturer ɗin daya basu wannan assignment idan aka ajiye sa ba lallai ya iya amsa dukkan waɗannan Quation ɗin ba, hankalin su ya tashi suka haɗa group domin ganin sun amsa wannan Quation amma suka gagara sun karaɗe dukkan school ɗin suna neman amsar amma basu samu ba, hmmm!!" Shuru yayi tare da kallon Jummo ya cigaba da cewa. " kinsan meya faru a wannan lokacin?" Girgiza kanta Jummo tayi alamun a'a cike da sanyin jiki da kuma jin kishin wacce ake bata labari a kanta, cigaba da Magana ya Garkuwa yayi. " Abokina Shetima Ladan ne yazo yake sanar dani zancen assignment ɗin da aka bawa ƴan Cause ɗinsu kuma sun gagara samu, a wannan lokacin wani tunani ya faɗo min, me zai hana naje na ƙarɓo Quation ɗin da zumar zan amsa musu, duk da nasan bazan iya ba tunda ba Cause ɗina bane, amma na ɗauki wannan kasadar da wannan tunanin naje na tunkari Safreena, da farko da naje bata saurareni ba, sanda na nawa ƙawarta Zee bayanin abinda ya kawo ni sannan Zee ta sata saurarana dole, na karɓo assignment ɗin, tare da alƙawarin da safe zan kawo musu, room ɗin na koma na dafe kaina ina tunanin taya zan amsa abinda bani da ilimi a kansa, nakai 11 na dare ina nazari, kafin daga baya tunanin Bro khalil Cause ɗin da yayi kenan ya kuma zo first class, numfashi na sauƙe tare da kiran wayarsa nake sanar dashi halin da nake ciki sosai ya min dariya kafin daga bisani yace na turo masa Quation ɗin ta WhatsApp, haka kuwa akayi na tura masa cikin ikon Allah a 1 hours Bro khalil ya amsa dukkan tambayoyin ya aiko min dasu, cike da farin ciki washe gari na kai mata sosai taji daɗin abinda na musu, da wannan alaƙa Mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Safreena, ya zamanto dukkan wani assignment idan aka bata bata gane ba, sai ta kawo min ni kuwa na bawa Bro khalil ya amsa mata, da haka muka shaƙu har Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu, sosai muka shaƙu da juna yayin da idan ɗaya baiga ɗaya ba hankalinsa baya kwanciya, muna tsaka da tsaftacacciyar Soyayya, na kammala karatuna, mukayi graduation, Sosai hankalina ya tashi ina tunanin ta yaya zan iya rabuwa da ita, itama hakanne a wajen ta harma ta zarta ni shiga cikin tashin hankali, ranar Sunday itace ranar walimar kammala karatun mu, a kuma ranar wani mummunan al'amari ya faru tsakanin mu da Safreena hmmm!!! Wannan baƙar rana ce a gareni wanda bazan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata, Jummo Safreena tamin alƙawarin zuwa walimar kammala karatun mu, a wani holl da muka kama, a ranar dukkan abinda ya faru, nafi Safreena amma itace ta janyo hakan, Safreena ta shigo wannan holl ɗin da wani irin shiga wanda sam bai dace da shigar ɗan musulmi ba, ni kaina ban taɓa zaton Safreena zatayi irin wannan shigar ba, saboda kamun kanta, sai kuma aka samu akasi tayi wannan shigar wanda ita ba wai tayisa da nufin komai bane, rigace fara tas wacce ta kama jikinta sosai da wando jeans Wanda shima yayi mungun kamata tamkar zai fasa jikinta, komai na surar jikinta ya bayyana, gashi kuma ta saka ƙaramin gyale wanda ko ƙirjinta bai rufe ba, tunda na saka idanuna akanta a wannan daren, hankalina ya tashi sha'awa ta ta motsa na gagara control ɗin kaina, duk da haka nayi ƙoƙarin korar sheɗan daga zuciyata, amma banci nasarar korar sa ba, sai ma tunzurani daya yi, Jummo na taƙaice miki a wannan daren sanda nasan yanda nayi na sawa Safreena maganin kawar da hankali a ruwa tasha, na jata zuwa wani room, a wannan daren na lalatawa Safreena budurcinta........." Wani razana Jummo tayi ta miƙe tsaye tare da dakatar da Ya Garkuwa ta hanyar furta. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! What!!! Y..y...y...y... ya garrrrrkuwa!!! Kai ɗin ne kayi wannan mungun aikin.!!!"? Jummo ta furta maganar cike da in'ina daƙyar Maganar ke fita tana nuna Ya Garkuwa Da yatsa. Share hawayen daya wanke masa fuska Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Kin firgita ko, baki taɓa tunanin zaki sameni da wannan mugun tabon ba, ko shiyasa na ce dole zaki tsan.........." " Shittttttt!!!! Karka ƙarisa, ka cigaba da bani labarin kawai." Tayi Maganar itama tana share hawayen ta. Hankalina bai dawo jikina ba sai bayan na gama haye mata daga nan ne na fara jin takaicin abinda ya faru, ko da Safreena ta farfaɗo sosai hankalinta ya tashi ta shiga cikin damuwa da tashin hankali ta dinga kuka tamkar ranta zai fita, a wannan lokacin bani da bakin mata Magana saboda kunyarta, cike da haushina da tsanata Safreena ta miƙe taje tolet ta gyara jikinta ta mayar da kayan jikinta, tana ɗan ɗingishi ta bar holl ɗin gaba ɗaya, a ranar koni ba'a tashi walimar dani ba, hankalina ya tashi na shiga cikin damuwa sosai, na kasa hkr har sai da na sanar da abokina Shetima abinda yake faruwa shima sosai ransa ya ɓaci, yamin masifa tamkar zai dakeni, abun mamaki duk da abinda ya faru tsakanina da Safreena banji sonta ya ragu a cikin zuciyata ba, sai ma ƙaruwa da yayi, munje nida Shetima domin bawa Safreena hkr, amma taƙi ta haƙura ko sauraronmu batayi ba, sai ma Allah ya isa da take jamin, na shiga cikin ɗimuwa da ganin tsanata a idanun SAFREENA, haka dole muka barta ba dan naso ba, tun daga wannan Ranar Safreena ta fita daga rayuwata ta daina kulani, ni kuwa na shiga cikin damuwa, ga kuma zan koma gida, har ƴar wata rama nayi, haka na dinga yiwa Safreena naci ina bata hkr, komawa gidan ma na hkr dashi, ko da ban koma gida ba nasan babu mai tambayata meyasa ban dawo ba, saboda kowa rayuwarsa yake a gidan mu babu ruwan kowa da ɗan uwansa, muddun zamu shekara muna waya da gida bazasu tambaya meyasa na gama karatu ban dawo ba, hakanne ya bani damar zama har sai na samu Safreena ta haƙura, nayi iya yina Safreena taƙi saurarata, kuma ina da tabbacin Zee ke sake nisantani da ita ita a nata tunanin na ɓatawa aminiyarta rayuwa, an kai wajen Wata shida Safreena bata saurarata ko kallo na bata yi, ni kuwa Soyayyar ta tamin kamun da bazan iya hkrn rasata ba, daga nan ciwon ƙirji da tari ya fara sanɗata sakamakon damuwa da nake ciki, tun ina jin ciwon kaɗan har sai da ya yasar dani, ƙarshe har sai da na kwanta a asibiti, nasha rashin lafiya na ciwon ƙirji tamkar zan mutu, kafin Safreena ta dawo gareni, ganin ina ƙoƙarin rasa rayuwata saboda ita, daga nan ta kuma yarda dani a karo na biyu zuciyarta ta aminta son gaskiya nake mata" Kallon Jummo yayi ya cigaba da cewa. " Nayi mamaki da DOCTORn daya kula dani Asibitin Sj gaɗam bai gane ciwon zuciyar dake jikina tsohon ciwo bane, domin kuwa na samu wannan ciwon zuciyar ne ta sanadin Safreena, sakamakon rasata da na kusa yi, ban sanar da kowa damuwata ko soyayyata a gidan mu ba, hatta ciwon da nayi babu wanda ya sani a gidan mu, na ɗauru akan maganin zuciya shekara biyu da suka wuce ba tare da kowa yasan ina da wannan ciwon ba, sai Shetima kawai shima na roƙesa da karya sanar da kowa, harta ita kanta Safreena bata san ina da ciwon zuciya ba, haka Soyayyar mu ta koma tamkar da da Safreena, sosai muke bawa juna kulawa, duk wata hirar mu muna yinta ne akan Maganar Aure, Jummo kuskure na na biyu shine ya shiga tsakani na da Safreena har mukayi rabuwa ta har abada. Jummo kallon Ya Garkuwa tayi tare da cewa. " Bayan wannan kuskuren da ka mata mai muni har kuma akwai wani kuskuren bayan shi.?" " Eh akwai Jummo, Tun daga randa Safreena ta gama zaucewa a soyyayyata daga ranar ta fara amsar umarnina, nakan yawan jin sha'awar Safreena, yayin da bana iya riƙe sha'awata, akwai ranar da Safreena ta zo room ɗina ta sameni ciwon mara tamkar zai kasheni, tun da Safreena ta shigo hankalina ya tashi ciwon marata ta ƙara tsanani, babu abinda nake buƙata fa ce jikin Safreena, a wannan daren na shiga cikin wani irin tashin hankali, a yayin da na jawo Safreena ina roƙonta ta amince min karna mutu tare da mata alƙawarin cewa Soyayyar ta bazata taɓa gushewa a zuciyata ba, na mata alƙawarin cewa zan aureta ta ko wani hali, Soyayyar da Safreena take min ya sata jin tausayin halin da nake ciki, a wannan daren Safreena ta ƙara bani kanta a karo na biyu tun daga wannan Ranar Safreena ta yadda dani na maidata tamkar matar da na biya sadakinta, na kai kusan shekara guda a ƙasar Amurika bayan kammala karatu na, a lokacin ita kuma Safreena sauranta shekara ta kammala nata karatun, ni kuwa na dawo gida Nigeria, sanda zan tafi sosai hankalin Safreena ya tashi tayi kuka sosai, a haka muka rabu kowa zuciyarsa babu daɗi, koda na komo Nigeria kullum muna maƙale ni da Safreena a waya, Soyayyar ta ko kaɗan bata ragu a zuciyata ba sosai nake sonta Soyayya ta gaskiya, kuma har a wannan lokacin ina jin a zuciyata Safreena ce matar da zan aura." Bayan Safreena ta gama karatun ta, ta dawo gida Nigeria a lokacin ni kuma na fara aiki, sai muka cigaba da Rayuwa kamar yadda muke a America, gidan su Safreena kowa ya sanni yasan Soyayyar dake tsakanin mu, haka gidan mu ma, a wannan lokacin an san da maganar mu da Safreena, kwatsam rana ɗaya ciki ya ɓullo a jikin Safreena, sosai hankalinta ta tashi, ko da take sanar dani ban mata musu ba, domin kuwa ina da tabbacin cewa cikina ne, saboda na yarda da tarbiyyar Safreena bata mu'amala da ko wanni namiji sai ni, sai dai na buƙaci Safreena da muje a zubar da cikin, amma Safreena taƙi tace bazata sake aikata wani zunubin ba, bayan na zina ga kuma na kisan kai, duk yanda naso yiwa Safreena dabara a zubar da cikin nan taƙi, mun kusa sati biyu muna bugawa da ita sam taƙi amincewa hakan yasa harna hasala na mata barazana wai ko zataji tsoro ta yadda muje a zubar da cikin, nace mata, idan har bata yadda an zubar da wannan cikin ba, to ta cireni cikin rayuwarta, babu ni babu ita ban sanki ba, sannan karki alaƙanta wannan cikin dani, muddun kuwa kika alaƙanta wannan cikin dani sai naga bayanki da na iyayenki zan ɓatar daku a duniya a daina jin labarin ku, da wannan kalaman na yiwa Safreena barazana wai ko zan samu ta amince a zubar da cikin amma Safreena taƙi, tace ta amince mu rabun amma cikin jikinta sai ta haifesa da wannan muka rabu kuma shine rabuwa ta ta ƙarshe da ita, da kwana biyu sai naji labarin cewa gidan su Safreena yayi gobara dukka mutanen gidan sun mutu babu wanda ya rayu a cikin su sosai hankalina ya tashi nayi baƙin cikin mutuwar Safreena nayi kuka kamar zan mutu, hankalina yayi mungun tashi nayi kewar Safreena." " Jummo wannan shine mungun kuskuren dana aikata amma har yau da nake baki wannan labarin dai-dai da kwayar zarra Soyayyar Safreena tana raina ina sonta tamkar yadda nake sonki, babu bambancin Soyayyar da nake miki da wacce nake yiwa Safreena, Soyayya ɗaya nake muku." Cike da sanyin jiki Jummo ta zauna tare da cewa. " Allah Sarki har naji tausayin ta, ta koma ga mahallicinta da cikin da bana sunnah ba, Allah ya ji ƙanta ya gafarta mata, naji tausayin ta matuƙa, to amma ita kuma Sadiya fa." Kallon Jummo yayi tare da runtse idanunsa yace. " Itama mun taɓa bariki da ita amma babu zancen Aure a tsakanin mu, itace kawai ke sona amma ni banyi mata alƙawarin Aure ba, a yanzu haka mun rabu da Sadiya, na kuma yi sahihiyar tuba insha Allah bazan kuma zina ba, na tuba wa mahallicina." Numfashi Jummo ta sauƙe tare da cewa. " Na fahimci komai, zan kuma kasance da kai har abada, sai dai dole idan kana son zamanmu yayi nisa mu kasance har abada dole ne kayi tsaftacacciyar tuba, Wanda babu gurbata a cikin sa, idan har ka kasance a haka zamu zauna har abada ni da kai, idan kuma kayi tuban muzuru, dole ne zamu rabu, kuma dole muje muyi test kafin ka fito da Maganar Aure tsakanin mu." " Na yadda da duk sharuɗanki kuma zaki sameni mai cika alƙawari." Yana gama faɗin haka ya tashi yabar wajen, da kallo Jummo ta bisa harya shige bedroom ɗinsa, sannan itama ta tashi. A wannan daren sosai Jummo ta ninƙaya tunanin Rayuwar Ya Garkuwa wanda ko da a mafarki bata taɓa zaton haka yake ba, sai dai tana jin a zuciyarta Garkuwa ya sauya, Kuma insha Allah tana jin a ranta zata kawo haske a rayuwar Ya Garkuwa, da wannan tunanin bacci ya ɗebeta. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Bayan Wata Shida* Zuwa yanzu Soyayyace mai ƙarfi ta shiga tsakanin Jummo da Ya Garkuwa, kullum suna maƙale a waya idan kuwa yana gida to suna tare a yayin da Momy ta hango shaƙuwar Jummo da Garkuwa sai hankalinta ya tashi ƙwarai, domin kuwa ta fara zargin Soyayyace a tsakanin su da wannan tashin hankalin ta kira ya Garkuwa. " Ka faɗa min meye tsakanin ka da Wannan Yarinyar Jummo, naga sai famar shishshige mata kake kana maƙale mata, meye tsakanin ku." Cike da nutsuwa Ya Garkuwa ya dago ya kalli Momy kafin yace. " Nayi zaton ko da ban faɗa miki ba, zaki fuskanci abinda yake tsakanin mu, Momy ina son Jummo ita nake so na Aura, ina son ki sanar da Daddy ya fara jin maganar daga bakin............." " Kai mahaukaci shasha wanda bai san abinda yake ba, yanzu idan banda kai shashane marar lissafi, me zai haɗaka da wannan yarinyar me zakayi da ita wawiya jakar ƙauye, wanda bata san darajar manya ba, to bari kaji muddun ni ce uwarka dana kawoka duniya nayi nakudarka na haifeka, bazaka Auri Jummo ba daga yau karna kuma ganinka zaune tare da ita babu kai babu ita na rabaku." A razane Ya Garkuwa ya ɗago kansa yana kallon Momy tare da cewa. " But Momy............." "Dakata karka cemin komai, na yanke hukunci nace maka na rabaku ka fita ka barmin room shasha marar lissafi." " Wai Momy meye haka!!! Mekike faɗane haka!!!! Wani irin hukunci ne wannan meye Jummo ta miki da har zaki yi ƙoƙarin rabani da ita!!! Why Momy?!!! Why!!!?." " Eyye!!! Garko nine kake ɗagawa murya saboda Mace!!! Ko ka manta ni wacece a wajenka!!!! Idan ka manta bara na tuna maka, nine uwar da na ɗauki cikinka wata tara na haifeka na raineka ba tare da ka bani ko sisi ba, dan haka dole kabi umarnina ba dole sai da dalili ba, nace maka bana son wannan Yarinyar ta zamo matarka, ko zaka ja da umarnina ne, ka gani idan rayuwarka zatayi albarka, fice min daga room Wawa."!!! Cije bakinsa ya Garkuwa yayi zuciyarsa na masa ƙuna, a fusace ya juya ya fice da sauri ko gabansa baya gani sosai, step ɗin yake takawa cike da ɓacin rai wani irin bangaja ya yiwa Ya khalil wanda shi baima san yayi ba, cike da mamaki Ya khalil ya kallesa sai kuma ya kira sunansa. " Bro Bro!!!" Sarai Ya Garkuwa yaji kiran ya khalil sai dai ɓacin rai bazai barsa ya iya amsawa ba sai ma tafiyarsa da yake yi, da sauri ya khalil ya biyo bayansa tare da tare gabansa yana cewa. " Kurma ne kai ina maka gana baka amsawa, wai meya faru ne na ganka haka cikin tashin hankali.?" Runtse idanunsa Ya Garkuwa yayi a rayuwar sa ya tsani idan yana cikin damuwa a taresa da tambaya, ba tare da ya kula Ya khalil ba, ya kauce zai shige Ya khalil ya kuma taresa tare da cewa. " Wai Bros ba Magana nake maka bane kake shareni, Please dan Allah tell me, meke damunka."? " Bro please ka kyaleni da damuwata a halin da nake ciki yanzu bazan iya ce maka komai ba, ina cikin damuwa ina cikin damuwa!!! Ji nake tamkar zuciyata zata fashe!!! Na fara tsanar gidan nan!! Domin kuwa na fahimci Rayuwar cikin babu tausayi da jin ƙai babu wanda ya damu da ɗan uwansa kowa son kansa ya masa yawa MUSSAMAN MOMY a yau ji nake tamkar ba uwata bace." Shuru Ya khalil yayi tare da kama hanun Ya Garkuwa ya jasa suka fita garden suka yi tare da zama Ya khalil ya fuskanci Ya Garkuwa cike da nutsuwa gami da taushin murya yace. " Tabbas kowa kansa ya sani a cikin gidan nan ban maka musu ba, Bros amma zancen ka na ƙarshe ya bani tsoro, kar zuwa ya tunzuraka ka shiga wuta ta hanyar ɓatanci ga mahaifiyarka meye Momy ta maka wanda har kake jin ba itace uwar da ta haifeka ba.?" " Ni banyi ɓatanci wa Momy ba, sai illa na faɗi gaskiya na fara jin kamar ba uwata bace ita, saboda babu ruwanta da farin cikin mu, kanta kawai ta sani.?" " Baka amsa min tambayata ba Garko, cewa nayi meye Momy ta maka." " Ya khalil Momy tana ƙoƙarin rabani da Jummo!!! Bansan me Jummo tayiwa Momy ba ta tsaneta da yawa, why Momy zatace na rabu da Jummo, why Bro why!!! Farin ciki nane Momy bata so.?" Shuru Ya khalil yayi, daman yasan dole wannan Ranar tana zuwa, mahaifiyar mu bata son gaskiya tafi son Kanta fiye da kowa a rayuwarta, HMMM!!! Numfashi Ya khalil yayi tare da kama hanun Ya khalil ya fara magana cike da nutsuwa. " Garko dama nasan wannan Ranar zata zo ta, dalilin kenan da yasa na cewa Daddy ya zamo katanga kuma kariya tsakanin Auren ka da Jummo, saboda nasan dole Momy zata zamo matsalarku, ba wani abu Jummo ta yiwa Momy ba, illa kawai suna takun saƙa game da gaskiya, Jummo na ƙoƙarin kawo sauyi da shaƙuwa cikin gidan mu, a yayin da Momy take ganin hakan a matsayin za'a ƙwace mata iyalanta, gani take tamkar wani salo ne da Mamma ta ɗaura Jummo akai domin su kawo ƙarshen zamanta a wannan gidan, amma a zahiri abun ba haka yake ba, ita Jummo babu fansa ko cutar da Momy a cikin ranta, tsakaninta da Allah take ƙoƙarin inganta rayuwar gidan mu, hmmm!!! Garko ka bi komai a hankali karka fara sanar da Daddy Wannan Maganar auren, har sai ka daidaita da Momy, karkayi fushi da ita domin kuwa karka manta da ita uwace gareka wanda Ubangiji yace daga shi sai ita, dan haka ka bita sannu a hankali harka samu ta amince domin neman albarka, nima zan tayaka wannan gwagwarmayar, karka damu ka sawa zuciyarka ruwan sanyi insha Allah Momy zata amince kaji ɗan uwana, gobe idan Allah ya kaimu zanje ƙasar Tailan graduation ɗin Lil Sister Zizah, zamu dawo tare, menene gift ɗinka, koda yake ma tace tayi fushi da kai baka damu da ita ko kiranta bakayi." Numfashi Ya Garkuwa yayi yana dafe kansa har yanzu zuciyarsa a cunkushe take da baƙin ciki, miƙewa tsaye yayi a zuciye tare da cewa. " Sau Uku kawai zan roƙeta ta amince da wannan Auren, idan kuma Momy taƙi to wallahi zanje na samu Daddy ya nemo min Auren Jummo, babu ruwana da damuwar Momy domin kuwa itama bata damu da tawa damuwar ba, ko wani hali zan shiga, koda bata min albarka a AURENA ba, Allah zaiyiwa AURENA albarka tunda dai ban cuci Momy ba, bani da haƙƙinta bare Allah ya kamani, ita kuma Zizah dan ubanta babu gift ɗin da zan bata itama wata baƙar munafukar ce zata dawo mai ƙara rura wutar fitina." Yana gama faɗin haka ya juya yabar wajen ransa a haɗe, Ya khalil bakinsa ya ɗan cije tare da furta. " Garko baahi da haƙuri, Momy kuwa zaiyi wuya ta yarda da auren Garko da Jummo, yayin da nake hango wutar fitina da zai ruru a cikin wannan gidan ga kuma Uwar hura wuta Zizah na dawowa, hmmm!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati wa'akfilni kairan minha!!!! Ya Allah ka kawo mana komai cikin sauƙi Allah kasa kar wannan Auren ya jawo fitina a cikin gidan nan, Allah kasa Momy ta yadda da wannan Auren." Ya yi addu'ar yana miƙewa cike da sanyin jiki ya bar wajen...................... *UMMU NASMAH CE* [4/25, 10:12 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *51 to 52* Koda Ya Garkuwa ya shiga room ɗinsa shuru yayi zuciyarsa cike da tunani, ya rasa meyasa Momy ta fiye son Kanta fiye da kowa hmmm!!! Numfashi ya saki tare da Kwanciya ruf da ciki yayi shuru cike da tunani. Ita kuwa Jummo bedroom ɗin Mamma ta shiga tare da zama gefen INNO duban INNO tayi tare da cewa. " INNO yau watan Mamma shida a kwance har yanzu jikin babu daɗi, INNO meya kamata muyi bai kamata mu zuba ido muta kallon Mamma a cikin wannan yanayin ba." Murmushi INNO tayi tare da dafa kafaɗar Jummo tana kallon Mamma tace. " Jummo Mamma ta samu lafiya, nine nace ta kwanta karta nuna cewa ta samu lafiya domin kuwa duk wanda ya mata wannan sihirin ya gane cewa ta samu lafiya to akwai matsala domin kuwa zai sake sabon shiri ne akanta, yanzu haka shirye shiryen maida sihirin nake kan wanda ya aikata mata shi, shima ya ɗanɗani zafin da taji." Girgiza kanta Jummo tayi tare da cewa. " A'a INNO a'a karkiyi haka karki maida mugunta da mugunta INNO, kibar kowaye ya mata da Allah, Allah zai masa hukunci daidai da abinda ya aikata, babu kyau mai da sharri da sharri, ka mata yayi wanda ya maka sharri ka saka masa da alkhairi, hakan shine cikar imanin mumini." Tashi Mamma tayi ta zauna tare da cewa. " Wai Jummo bara na tambayeki wai yaushe imani ya samu wajen zama a zuciyarki ne, shin da wani sharaɗi nazo dake gidan nan, ba munyi dake cewa zamu haɗa ƙarfi mu kori Zainabu daga wannan gidan, ko so kike ni ban koreta ba ita ta koreni ban cutar da ita ba ita ta cutar dani ki bani amsa.?" Numfashi Jummo ta sauƙe tare da miƙewa tsaye taje ta rufe door ɗin tare da sanya key ta dawo ta zauna tace. " Ban manta ba Mamma da wannan sharaɗin nazo gidan nan, amma har ga Allah ban shigo da niyar na kori Momy a gidan ta ba, na biyoki ne saboda Ya Garkuwa, soyayyata yasa na amince na biyoki, saboda ta hakane kawai zan samu kusanci da Ya Garkuwa, Mamma INNO meye ribarmu idan muka raba mata da mijinta Uwa da ƴaƴanta, meye ribarmu, idan har muka aikata wannan zunubin wallahi Allah bazai barmu ba, meyasa ba zamuyi tunanin kawo sauyi cikin gidan nan ba, meyasa bazamu yi ƙoƙarin sanja Momy daga mutumiyar banza zuwa ta kirki ba, ku gafarceni Mamma bazan iya saka hanu cikin wannan zunubin ba, amma idan kun shiryawa gyara Momy da gidan nan akan gaskiya to ashirye nake da na saka hanuna ciki, sannan INNO ina ƙara faɗa miki karki kuskura ki cutar da wani a cikin gidan nan, dan Allah na roƙeki, Mamma babu amfanin Allah ya baki lafiya ki kwantar da kanki cikin ciwon, hakan yana nuna butulci kika yiwa Ubangijin ki, ina faɗa muku wannan maganar ne kawai domin itace dai-dai ba don rashin kunya ba." INNO da Mamma shuru sukayi jikinsu yayi sanyi tabbas Maganar Jummo ta shiga zuciyarsu, Mamma ce tayi ƙarfin halin cewa. " Kina nufin kenan yaudarata kikayi Jummo, kika amince da ƙudirina saboda kawai Soyayyar ki, idan mu munyi kuskure kema anan kinyi kuskuren cin amanata domin kuwa bai kamata ki yadda da sharaɗi na ba, tunda kinsan ba zaki iya cikawa ba, shin ke dai-dai kikayi, wannan son kaine kikayi." Ya khalil dake tsaye jikin window ɗin Mamma ta falo yana jin dukkan hirarsu wanda su basu ma san yana tsaye ba, ya girgiza kansa yana jira yaji wani amsa Jummo zata bawa Mamma. " Aa Mamma ba YAUDARA bace, bani da burin yaudarar wani ma bare kuma ke, Sai dai na amince da nayi kuskuren amsa miki abinda bazanyi ba, na yadda nayi kuskure, banyi daidai ba, amma kema ya kamata ki gane abinda kika buƙata ba daidai bane, kiyi haƙuri ki gafarceni a bisa wannan laifin dana miki ni dai bazan iya cutar da kowa ba, dana cuci wani gara shi ya cuceni." Kafaɗar Jummo Mamma ta dafa tare da cewa. " Kinyi gaskiya Jummo!! Tabbas ke mutumiyar kirki ce, na fahimce ki, kuma nima na janye, insha Allah zanyi ƙoƙarin jawo Zainabu jikina domin nuna mata dai-dai, ki cigaba da bin wannan hanyar insha Allah bazaki taɓe ba Jummo." Itama INNO murmushi tayi tare da cewa. " Kyan ɗa ya gaji iyayensa, na godewa Allah da yasa baki ɗauko ni ba Jummo, kika ɗauko kakanki Baffa da iyayenki, domin kuwa kullum akan hanyar daidai suke, nima kuma zanbi sahunsu, sai dai fa bana taɓa iya sarrafa zuciyata a duk sanda aka tunzurani, wannan ɗabiar tawa bazata sanju ba." Dariya Jummo tayi cike da farin ciki tace. " Ai nasan halin masifar ki INNO mawuyacin abune ki daina, hakanma ya min muddun zaki daina shan taba, sai nafi kowa farin ciki" kallon Mamma tayi tace " Sai ki tashi ki nunawa kowa kin samu lafiya, domin hankalin kowa ya kwanta mussaman Ya khalil ya damu sosai da halin da kike ciki, zaiyi farin ciki idan yaji labarin kin samu lafiya." Murmushi Ya khalil yayi cike da jinjinawa Jummo idanunsa suka ciko da hawaye tabbas yayi asaran rashin samun Jummo a matsayin Mata, sai dai yana farin ciki ta wani ɓangaren da Jummo bata tsallake tabar gidan su ba, shigewa yayi yana murmushi." Washe gari da safe, bayan sunyi breakfast ya khalil ya fito cikin shirinsa na tafiya Tailan graduation ɗin Zizah, Momy Daddy Aunty Zarah duk sun bada gift ɗinsu a kaiwa Zizah amma banda Ya Garkuwa, cike da ƙauna ya khalil ya tafi, tare suka fita da Ya Garkuwa, Momy sai da ta tabbatar da kowa ya tafi nasa Wajen itama A'illo ta tafi school, Jummo kuwa tana cikin bedroom ɗinsu tana kwance, Momy ta shigo fuskarta a haɗe ta rufe ROOM ɗin da key tare da nufo Jummo. Jummo dake zaune tana waya da ƙawarta meenat sam bataji shigowar Momy ba sai ji tayi tana cewa. " Keeee!!! Kashe wayar nan." Cike da razana Jummo ta ɗago kanta ta kalli Momy jin magana ba tare da taji shigowar mutum ba, numfashi ta sauƙe tare da katse kiran tace. " Momy kece, harna tsorata, lafiya kuwa Momy.?" " Ba lafiya ba, domin kuwa lafiya bazata kawo ni gareki ba, wai kuwa kinsan yadda na tsaneki a rayuwata, wallahi ko fuskar ki bana son gani, muryar kawai idan na jiyota sai naji raina yayi mungun ɓaci!!! Kamar yadda na tsaneki haka bazan taɓa yadda ki zamo sirikata ba, na tsaneki dan haka ki rabu min da ɗana ki fita daga rayuwarsa, kin dai san Ɗana yafi ƙarfinki domin kuwa ko wacce ƙwarya da Abokiyar burminta, dan haka dole ne ƙwarya tabi ƙwarya, idan kuwa ta hau akushi to fashewa zatayi dan ubanta, bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane, idan kikace zakija dani tofa zan lalata rayuwarki, mafi aala a gareki shine ki fice daga Rayuwar ɗana." Runtse idanunta Jummo tayi tana jin zancen Momy tamkar tana sheƙa mata tafasasshen ruwan zafi a zuciyarta, a hali ta kalli Momy tare da cewa. " Naji Momy, sai dai bansan taya zan iya fahimtar dake cewa, bazan taɓa iya rabuwa da ɗanki ba, koda kuwa kullum zaki dinga yankan naman jikina ne, ƙarshen azaba, Soyayyata ta gaskiya ce shiyasa ko yaushe take ƙara ƙarfi a cikin zuciyata, ki gafarceni Momy Garkuwa rayuwata ne rabuwa dashi tamkar mutuwace, na sani Garkuwa yafi ƙarfin ajina, amma ki sani shi Soyayya babu ruwan sa da aji ko asali, tsintar ta kawai ake a cikin zuciya, kamar dai yanda muka tsinci Soyayyar junan mu nida Garkuwa, dan haka Momy karkiyi ƙoƙarin shiga lamarin Ubangiji ki barsa yayi ikonsa." Wani wawan mari Momy ta dauke Jummo dashi, har sai da taga walƙiya nunata da yatsa Momy tayi cike da faɗa tace. "A wannan karon Soyayyar zata duba Asali da kuma aji, domin kuwa muddun ina numfashi idan har nice uwar da ta haifi Garko to wallahi bazai haɗa jini da INNO ba, zuri'ar masifa zuri'ar tsiya zuri'a da basu gaji arziki ba, kullum cikin talauci da tsiya kuke babu ficaccen wanda za'a kira mai arziki a zuri'ar ku, sai jaraba da masifar tsiya da kuka iya, a hakan zan haɗa usuli daku, to wallahi dole zaki rabu da Garko kota halin tsiya ne dani kike zancen." MOMY tana gama faɗin haka ta juya zata tafi ta tsinci muryar Jummo na cewa. " Naji maganganun ki, zan iya jurewa duka da zagi a wajenki amma bazan iya zurewa cin mutuncin iyayena ba, Garkuwa ɗanki ne kece kika haifesa, kije ki basa umarni a matsayinki na Uwa ya rabu dani, idan har ya fita a harkata nima zan rabu dashi, kije ki gwada wannan jarabawar mu gani ko hakan zai yiwu." Murmushi Momy tayi tare da kaɗa kanta tace. " Hmmm!!! Zan kuma nuna miki nice na haifi Garko." Tayi Maganar tana ficewa, Jummo jikinta sanyi yayi take tsoro ya kamata karfa Momy tayi nasarar rabata da zuciyarta. " Na shiga Uku wani hali zan shiga idan Momy ta rabani da Ya Garkuwa, ina ga mutuwa zanyi, Ya Allah ka taimaki soyayyata Allah ka shiga lamarina ya Allah kasa kar Momy tayi nasara a kan mu." Tayi addu'ar tana zuba tagumi zuciyarta duk a dagule. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ " Wai Safreena ina zakije ne haka kike sauri."? " Oh Zee tun jiya fa na faɗa miki cewa, zanje interview na aikin da nake nema ko kin manta ne, ganan Abdul ki kula dashi, Allah dai yasa na samu nasarar aikin." " To ameen insha Allah ma zaki samu, ammm Safreena nikam ina labarin ƙawarki ne da kuka haɗu a makay jummai ne sunanta ko me? Na dai manta sunan amma dai da alamu tana da kirki" Murmushi safreena tayi tana dafe goshinta tace. " Ohsh!!!! Wallahi kinma tuna min da ita, kinsan mantawa nake da ita, ta kirani yafi sau a ƙirga, amma ni ban taɓa kiranta ba ko sau ɗaya maybe tayi fushi ne itama ta rabu dani, bara na kirata yanzu." " Gaskiya ya kamata ki kirata, ka so mai sonka komai tsiya ya dai fi maƙiyin ka, saboda mai ƙaunarka bazai taɓa cutar da kai ba shi kuwa maƙiyi ko yaushe hanyar da zaka mutu yake nema." " Hakane bara na kirata." Safreena tayi Maganar tana kiran wayar Jummo, Jummo dake zaune ta zuba tagumi cike da tashin hankali tana fargabar maganganun Momy domin kuwa tasan halin Momy zata iya aikata komai game da son zuciyarta, ciki harda kalmar da ta furta na zata lalata mata Rayuwa sai dai tayi imani da Allah kuma tasan babu abinda Momy ta isa ta mata sai abinda Ubangiji ya ƙaddara zai faru da ita a rayuwa domin kuwa babu bawan da zai iya gujewa ƙaddararsa muddun aka rubuta masa to tabbas ne sai ya haɗu da wannan ƙaddarar kafin mutuwar sa, ringin ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi kallon ta, ta kai ga wayar Maman Abdul abinda ta gani a rubuce murmushi Jummo tayi tare da ɗaga kiran tana sallama. Daga can Safreena ta amsa sallamar tana murmushi tace. " Ƙawata kwana biyu shuru kin manta dani Allah dai yasa ba laifi na miki ba."? Murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Ni kuwa laifin me zaki min Mmn Abdul, kawai dai naga kamar bakya buƙatata cikin rayuwarki ne shiyasa na ƙyaleki badan kin min laifi ba." " Bana buƙatar ki cikin rayuwata kuma, meyasa kikace haka?" " Mmn Abdul kenan!!! Ai alamun hakan sune suka nuna baki damu dani ba, domin kuwa baki taɓa kirana ko da sau ɗaya bane, ko yaushe Ni ne kawai nake kiranki, sannan nazo nayi kwana da kwanaki bana kiranki, amma baki damu da meyasa bana kiranki ba, bakiyi tunanin anya lafiya kuwa bana kiranki ba, shiyasa kawai na daina kiranki amma kullum ina tunawa dake a cikin raina." Numfashi Safreena ta sauƙe cike da jin kunyar abinda ta yiwa Jummo tace. " Ko kaɗan ba haka bane, domin kuwa ina buƙatar ki a rayuwata tun haɗuwata dake nake jin alkairi ne, ji nake tamkar akwai wani abu nawa mai mahimmanci a rayuwata a jikinki, tabbas nayi maki laifi domin kuwa ban kyauta ba, ya kamata ace koda ba kullum ba na dinga kiranki sai dai Allah bai nufi hakan ba, kimin afuwa insha Allah zan gyara laifuka na." " Ba komai ya wuce, ina ɗana Abdul?" " Abdul yana bacci bai farka ba, ya kk ya gida dasu Mama."? " Ayya Abdul sarkin bacci shi dai a rayuwarsa yana son bacci, kowa yana lafiya, Ya Baban Abdul yake."? Wani ras zuciyar Safreena tayi, jin tambayar Jummo, Allah sarki ita tayi zaton ni matar aurece bata san ban taɓa Aure ba, batasan na samu Abdul ne ta hanyar banza hanyar da bata dace ba, numfashi Safreena ta sauƙe tare da cewa. " Ammm!!! Yi hakuri Jummo bara nazo zan sake kiranki ana kirana sai anjuma ki gaishe da Mama" " Na gode" Katse kiran Safreena tayi tare da sakin numfashi zuciyarta a jagule, dama ta sani komai jumawa dole ne za'a binciki Asalin Abdul, wanda take kunyar sanar da hanyar da aka samesa shin me zata faɗawa duniya game da yacce ta samu Abdul, guntun hawaye ne ya zubo daga idanunta tare da saka hanu ta share cikin zuciyarta tana furta ( A rayuwata nayi kuskuren da bazan taɓa daina danasani ba a rayuwata tabbas Zina abin kunya ce da bazata taɓa bibiyar wanda ya aikata ba har tsufansa, kai harma da bayan rayuwarsa dole ne wata rana sai an yiwa zuri'ar ka gori) kanta ta saka ta fice ba tare da tacewa Zee komai ba, itama Zee bata tankata ba domin raji dukkan hirarsu." ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Jin an dafata yasa Jummo juyowa, Aunty Zarah ne tsaye a bayanta ɗan murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Aunty kece.?" " Ni ce Jummo, me kikeyi a gindin taga lafiya kuwa naga kamar ma kina cikin damuwa.?" Ɗan murmushi Jummo tayi tare da juyowa ta fuskanci Aunty Zarah ta ce. " Babu komai kawai ina hango giftawar ababen hawa ne, meyake faruwa ne kika shigo room ɗin mu."? " Babu komai kawai nazo na baki hkr ne bisa rashin fahimtar ki da nayi a baya, na so na jefa kaina cikin hallaka sanadin Momy sai na rantse miki da Allah babu hanuna cikin rashin lafiyar Mamma." Murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Menene kuma na rantsuwa, ai tunda kin gane gaskiya komai ya wuce Aunty dama ni ban riƙeki a zuciyata ba, Mamma kuwa alhamdulillah tunda ta samu lafiya." " Zuciyarki mai kyau ce Jummo, a fuska gaki kamar zakiyi faɗa amma a zahiri sam ba haka kike ba na gode da fahimta ya kamata idan har kin yafe min ki biyoni zuwa kitchen mu cigaba da girki tare kamar yadda muka saba ƙanwata." Murmushi Jummo tayi tare da kama hanun Aunty Zarah tace. " Faɗan ma ina dashi muddun aka kaini bango, muje Aunty komai ya wuce." Dariya Aunty Zarah tayi tare suka jera har kitchen, Momy kuwa tunda ta shiga bedroom ɗin ta take tunanin ta wacce hanyar ce zata raba tsakanin Jummo da ɗan ta, tana cikin wannan tunanin Ya Garkuwa ya shigo fuskarsa a ɗaure, gefe da ita ya zauna dubansa Momy tayi tare da cewa. " Baka da hankali ne zaka shigo min room babu sallama, ka taho sai famar haɗa fuska kake tamkar zaka dakeni akan wannan shegiyar Yarinyar." " Tabbas hankalin nawa ya fara tafiya saura kaɗan yabar jikina na zamo tantirin mahaukacin zaki wanda idanunsa zasu kulle ya bi duk wata hanyar da yasan zai samu abinda yake farauta, domin kuwa kece Uwar da take shirin haukata ɗanta da kanta take neman kaisa ƙasa ba tare daya shirya ba, ko wacce Uwa burinta farin cikin ɗanta, amma ni tawa uwar baƙin ciki na shine abinda take muradin ta gani buri take ta ganni cikin ciwo, ki faɗa min wani zunubin na aikata miki da kike min wannan azabar a matsayinki ta Uwar da ta haifeni ba yadikko ba, wani laifi na miki, shin biyayya ne bana miki ko kuma kyautatawa ce bana miki, menene na rageki dashi na haƙƙinki wanda yake kaina da kike ƙoƙarin ganin baƙin ciki na, ki faɗa min Momy menene aibun Jummo da kika tsaneta, karuwace ko shegiya ce, ko kuma Tarbiyya ne bata dashi, tana da rashin kunya ne, ko ta taɓa zaginki ne, shin tana da mugun ciwon da zai dakatar da Aure a tsakanin mune, shin iyayenta mutanen banza ne, ko ilimi ne bata dashi, ki faɗa min wanne ta rasa!!!"? Yayi Maganar a harzuƙe tamkar mahaukaci, yana kallon Momy, cike da tsoro Momy ta bisa duk da tasan halin Garkuwa mutum ne shi mai zuciyar gaske wanda baya taɓa ɓoye fushin sa, a duk sanda ransa ke ɓace sosai to fa fusace yanayinsa yake kasancewa duk da sanin halin sa baisa Momy ta saurara masa ba, sai ma hawansa da tayi da masifa. " Ai yanzu ma a haukace kake Garko, sai kaje kabi hanyar da kake gani idan zaka sameta, yau nine kake yiwa Magana cikin faɗa Garko, muryarka harta yi sama da tawa saboda Mace, hakan yana nuna min kenan da zarar ka sameta zakayi watsi dani ka maida hankalinka gareta, kuma bazan bari hakan ta faru ba, badai sai ka aureta ba Kafin ka juya min baya to sai naga ta yadda za'ayi wannan Auren, ina kyautatawa anan Garko ka shigo kaina kana min ihu a matsayinka na ɗana, ina tarbiyya wajen ka tunda na baka umarni kaƙi bi, shin ashe Garkuwa bani da darajar da zan hanaka abu ka rabu dashi komai girman son da kake yiwa abun, shin ko wuta na haɗa nace ka faɗa ashe bazaka min wannan karar ba, karka manta da cewa nice UWAR dana ɗauki cikin ka tsawon wata tare cike da laulayi, da wahala na haifeka ban huta ba, nine wankan ka rainon ka, goyonka , wanke kashin ka da fitsarin ka, kamin amai a jiki da kashi fitsari duk na wanke ban taɓa gajiyawa da ɗawainiya da kai ba har girmanka, amma yau duk ka mance da wannan kazo ina faɗa kana mayar min akan mace, har tambayoyi kake min akanta saboda ka ƙureni, to bazan baka amsa ba Garko ka shaƙe ni koka dakeni Idan naji wahala sai na amsa maka." " A'a Momy ba ihu nake miki ba, zuciyata ne ta kasa ɗaukar hukuncin da kika yanke, Momy bazan taɓa fifita Mace ba sama dake, domin kuwa kinmin ɗawainiyar da bazan taɓa iya saka miki ba, dai-dai da second ɗaya, Momy da ace kin rabani da Jummo gara ace wutar kika bani umarnin na faɗa domin kuwa sai tafi min sanyi fiye da tsanani da azabar da zuciyata zata shiga idan na rasa Jummo ƙarshe ma na iya mutuwa, Momy kin sani a yanzu zuciyata ba cikakkiya bace domin kuwa a cikin ciwo take abu kaɗan kan iya Tarwatsa min ita, ki rufa min asiri Momy ki taimakeni kimin rai a matsayinki na mahaifiyata ki barni da zaɓi na dan Allah Momy badan ni ba, domin samun salamar rayuwata, Momy ki daina ambaton na dakeki, Allah karya nuna min ranar da zan saka hanu a jikinki, da ganin wannan Ranar Gara ace na rasa hanuna ko na mutu." Tsuka Momy taja tana harararsa tare da nuna masa ƙofa. " Fice min daga room karka kuma tunkarata da zancen wannan shashar Yarinyar idan kuma ka sake to zan ja maka Allah ya isa ko kuma ka biyani nono na da ka sha domin kuwa baka cancanci na kiraka da sunan ɗa ba, fice min a gabana." A razane Garkuwa ya ɗago yana kallon Momy cike da matuƙar tashin hankali marar misaltawa, goshinsa duk ya feso da zufa yace. " Momy.............." " Shittttttt!!!! Fice min bana buƙatar kuma jin muryar ka yanzu get out of my room, get out!!!!" *UMMU NASMAH CE* [4/29, 9:44 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *53 to 54* Ficewa Ya Garkuwa yayi zuciyarsa na tafasa izuwa yanzu ya fara zargin tabbas akwai wani mummunan al'amari daya faru tsakanin Momy da Jummo tabbas akwai abinda Jummo ta yiwa Momy na rashin kyautawa, ƙiyayyar tayi yawa dole akwai wani abu domin kuwa bazata tsaneta haka kawai ba, tunda ya fito yake ƙwalawa Jummo kira tamkar zararre, bedroom ɗinsu ya buɗe bata ciki ƙasa ya sauƙo still dai kiran yake mata, jin motsi cikin kitchen ya sashi faɗawa ciki yana kiran. " Jummo!! Jummo!!! Jummo!!!" Jummo da Aunty Zarah dake famar aiki ne suka juyo tare a tsorace Aunty Zarah ce tace. " Garko lafiya kake mata wannan kiran haka, ni wallahi harka razana ni."? Ya Garkuwa da idanunsa suka kaɗa sukayi jajur ne ya fisgo hanun Jummo tare da jawota zai fita da ita daga kitchen ɗin, Aunty Zarah ta tare gabansa tare da cewa. " Wai meye hakane Garko, ina maka Magana kayi banza dani zaka jata ka fita da ita, meyake faruwa ka sanar dani mana."? Idanunsa Ya ɗago da suka gama rinewa har jijiyoyin kansa suna tashi yace. " Ba abinda ya shafeki bane, dan haka babu buƙatar dole sai kinji, kauce min a hanya na shige." Wangale baki Aunty Zarah tayi tare da cewa. " Amma ai Garko ya kam.............." " Ya Isa dan Allah Aunty Zarah, karki matsamin akan abinda bazan faɗa miki ba." Numfashi Aunty Zarah ta sauƙe tare da kaucewa suka shigo, tamkar wawiya haka yake jan Jummo tana binsa, dariya Aunty Zarah ta sheƙe DASHI tare da furta. " Maganin shegen biri karen maguzawa, ita nan tunani take gaskiya na gane harna tuba, bata san tsabar iya taku bane, gaskiya kika faɗa min Momy dole zata amince dani idan na biyo mata a haka, muje zuwa Jummo insha Allah sai mun ga bayanki, burin Momy shine zai cika a cikin gidan nan." Ƙara sheƙewa tayi da dariya tare da juyawa ta cigaba da aikinta. Shi kuwa Ya Garkuwa har garden yayi da Jummo tare da sakar mata hanu yana huci,. Sai yanzu Jummo ta iya buɗe baki da ƙyar tace. " Wai meye kake haka, kazo ka jawoni ina aiki, ka kawo ni nan kana huci tamkar mayunwacin zaki." Cike da tsawa ya Garkuwa yace. " Ai har gara mayunwacin zaki fiye dani, domin kuwa shi zaki idan ya fita farauta zai samu abinda yake so, ni fa koda na fita farautar ba samu zanyi ba domin kuwa duk hanyar da zanbi bi take tana tarewa, kaina ya fara kullewa tunani yamin yawa kuna neman haukata min ƙwaƙwalwa, wai bakwa tausayi na ne, kun san ba cikakkiyar lafiya bane dani why why!!!"? Jummo cike da rashin fahimtar maganganun Ya Garkuwa tace. " Me kake faɗa ne wai haka ban gane ba, kamin magana yanda zan gane kasan ni ba bahaushiya bace, ka min yanda zan gane.?" " Jummo ki faɗa min gaskiya karki ɓoye min komai, meye tsakanin ki da Momy shin kin taɓa mata rashin kunya ne, ko akwai wani saɓani tsakanin ku, ƙiyayyar da take nuna miki tayi yawa, haka kawai bazata miki wannan tsanar ba dole akwai wani abu."? Sai yanzu Jummo ta fahimci inda Ya Garkuwa ya dosa gefe ta samu ta zauna tare da ɗaga kai taa kalli Ya Garkuwa ta fara Magana cikin raunin muryar. " Ko ɗaya Farin ciki na babu abinda ya taɓa shiga tsakanina da Momy, ban taɓa yiwa wani ma rashin kunya ba, bare kuma ita, ni kaina idan na zauna nakan yawaita tunanin me na yiwa Momy ta tsaneni haka, amma nafi zaton zuciyarta ce kawai bata ƙaunata ko kuma na fito da ƙauye ne, ko kuma saboda iyayena basu dashi ne, shiyasa bata ƙaunar ɗanta dani, amma shawarar da zan baka, shine kabi umarnin mahaifiyarka wataƙi babu alkairi ne tsakanin mu shiyasa taƙi Auren abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai taɓa hangowa ba, uwace ita biyayya a gareta ya zama dole muddun kana neman albarka, Allah da kansa sai da ya ambaci Uwa sau Uku kafin ya ambaci Uba, sanda Ubangiji yace ku bini, sai kuma yace daga ni sai Uwa, hakan yana nuna mana girman mahaifiya, a duniya babu wanda yafi Uwa son ɗanta saboda tafi uba sanin zafin sa, Ya Garkuwa ina sonka ina kallon ka a matsayin hasken rayuwata, rayuwa babu kai a gareni tamkar mutuwa tace sai ita ƙaddara tana zuwa ne ba tare da tambaya ba ko shawari wata ƙil babu rabon Aure ne a tsakan.............." Saurin saka hanu Ya Garkuwa yayi ya toshewa Jummo baki yana girgiza mata kai tare da cewa. " Karki ce haka babu abinda zai rabamu sai dai mutuwa ina ji a jikina kece Uwar ƴaƴana, insha Allah sai munyi Aure Jummo, nasan ta inda zan fitowa Momy, tashi kije ki kwantar da hankalin ki karki ɗaga min hankalinki komai zaizo mana cikin sauƙi." Tashi Jummo tayi tare da kallon Ya Garkuwa tace. " Ya Garkuwa, bana son Momy tayi fushi dakai ta dalilina, a kaf faɗin duniya baka da wacce ta fita, kabi komai a sannu karka yadda ka ɓata mata rai idan harta turje ka bi umarnin ta hakan shine cikar ɗa na gari." Tana gama faɗin haka ta bar wajen da sauri tana kuka, Ya Garkuwa kansa ya dafe komai ya kulle masa a yanzu bashi da mafitar daya wuce ya je ya sami Daddy shine kaɗai zai dakatar da Momy daga wannan mungun ƙudirin nata, numfashi ya sauƙe tare fitowa daga garden ɗin, parking space ya nufa tare da shiga cikin motarsa yaja, darect *I D D BARAU NIG LTD* ya nufa kusan tare suka shigo da Safreena da take cikin keke napep, a tsakiyar Companyn aka sauƙeta, ta biyasa tare da nufar cikin Companyn, tayi nisa da tafiya shi kuma Ya Garkuwa ya fito, shima ya doshi ciki, Safreena a kujerun dake zagaye a harabar ta zauna wajen da ake kiran masu interview tana jira, yayin da Ya Garkuwa ya shigo kansa tsaye, Ya saka kai sai yaji wayarsa tayi ringin ɗaga wayar yayi ya kara a kunnen sa yana amsa kiran yayin da ya tsaya gefenta sam bai kula da ita ba, hankalinsa ya tafi ga wayar da yake, Safreena jin ƙamshin turarensa ya tabbatar mata da Garkuwa ne domin kuwa hancinta bazai taɓa manta ƙamshinsa ba, a hankali ta ɗago idanunta ta zuba masa, wani irin bugawa zuciyarta keyi tana jin zuciyarta ta tokare, har yanzu tana jin Soyayyar sa, sai dai ina ya manta da ita a rayuwar sa shi ɗaukar matacciya ma yake mata, numfashi ta sauƙe tare da dafe ƙirjinta sam bata gajiya da kallonsa kanta ta sunkuyar ƙasa sai kuma hawaye ya zubo mata, duk wannan abinda take Ya Garkuwa bai lura da ita ba, katse kiran yayi dai-dai wani farin bafulatanin mutum yazo fuskarsa ɗauke da annuri ya miƙawa GARKUWA hanu yana cewa. " Ehh lallai yau ka cika alƙawari, muje office ɗina." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Anya kuwa bazamuje mota muyi magana ba, sauri nake, ina da uzuri zanje office." " Kai Abokina wani sauri kuma dan Allah muje office muyi magana, Shetima ma yana office ɗin." " Kaji Shetima ɗan iska, wato dai gulma ce ta kawosa, muje to." Yayi Maganar tare da juyowa saitin da Safreena ke zaune, wanda ta sunkuyar da kanta tare da rufe fuskarta da gyalenta yadda babu mai ganeta, Ganin yatsun ƙafar Safreena yasa zuciyar Garkuwa tsinkewa ya zubawa yatsun idanu ji yake tamkar yasan mai wannan yatsun, gangar jikinta yabi da kallo fuskarta rufe hakan yasa bai gane ta ba, numfashi ya sauƙe tare da taɓe bakinsa yabi bayan Kabir Safreena dake kallonsa ta cikin gyalenta ne ta sauƙe numfashi tare da buɗe fuskarta tana bin bayan sa da kallo, harya shige office din. " Abdul kamarka daidai take da ta mahaifinka, Naso ace ƙaddarar samunka ta hanyar aure yasa muka sameka, da tabbas ka samu gatan uba, sai dai ƙaddara tazo maka a murɗe mun sameka ta hanyar Haram, baka da wani gatan uba sai nawa, ina tausayin ka Abdul dolene na ɓata rayuwata wajen baka cikakkiyar gata." Goge hawayen tayi tare da jingina jikin kujerar, tafi awa ɗaya kafin aka kira sunanta ta shige Office din interview, har wannan lokacin Ya Garkuwa bai fito ba, kuma dama haka taso, bata so ya fito ya sameta. " Kabir kaji halin da nake ciki, na rasa meyasa Momy take son rabani da Jummo menene ya kamata nayi dan wallahi ƙwaƙwalwata ta toshe na ma rasa wani irin tunani zanyi."? Shuru Kabir yayi domin kuwa maganar ta ɗaure masa kai, Shetima ne yace. " Kabir a rayuwata ban taɓa tunanin cewa Garkuwa zai so wata mace ba sama da Safreena, da ace kasan Soyayyar su da kasha mamaki, na so ace sunyi Aure sai dai Allah yayi ikonsa Safreena ba mai tsawon rayuwa bace, tana da hankali gami da nutsuwa ga sanin mutumcin ɗan Adam, hakan ma nayi farin ciki daka samu madadinta Garko, domin Jummo ma kyakkyawa ce kuma tana da kyan hali sai dai fa bazata taɓa kaimin Safreena ba, domin Safreena ta MUSSAMAN ce ta maka hallaci a Rayuwa Garko." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Wai kai Shetima kishin gawa kake wanda tabar wannan duniyar ba kuma zata taɓa dawowa ba, ka manta da Safreena ka fuskanci Jummo a cikin rayuwata domin kuwa itace take numfashi kuma itace zan Aura a yanzu bata da bambanci da Safreena a zuciyata, nauyin Soyayya ɗaya nake musu babu son Wanda yafi na wani a zuciyata har gobe ina kewar Safreena, Kabir baka san Safreena bani shawarar abinda ya kawo ni kawai kabar zancen Safreena." Murmushi Kabir yayi tare da cewa. " Ashe dai ka taɓa Soyayyar gaskiya, nayi zaton yanzu ka fara true ashe akwai wacce ta shuɗe, ni fa zancen Momyn nan ya kulle min kai to meyasa ta tsaneta haka, nifa Garko ina tunanin dole akwai wata matsala koda ba tsakaninta da Jummo ba, ko tsakanin ta da iyayen Jummo, yanzu abinda yafi kaje ka samu Daddy karka kuma tayarwa Momy Maganar sai muga shi kuma Daddy ya zai ɗauki Maganar." " Okay hakan za'ayi, na ɗanyi let, bara naje sai munyi waya, muje Shetima." Duk tare suka tashi Kabir ya rakasu har harabar Companyn, sannan ya koma, darect Office ɗin da ake interview ya shiga, ya samu ana yiwa Safreena tambayoyi, zama yayi gefen darecter yana sauraron su yanayin yanda take magana da British American yasa Kabir tsura mata idanu tabbas kyakkyawar gaske ce, " WOW!! She is beautiful Baby" murmushi ya sake tare da saka mata idanu babu ƙiftawa haka kawai yaji ta faɗa zuciyarsa, Soyayyar ta yake ji lokaci ɗaya tamkar shigar iska, har aka gama mata interview ɗin tare da cewa taje za'a nemeta daga baya, tashi Safreena tayi ta fita cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa ta samu aikin, ko da Safreena ta fita bayanta Kabir ya biyo ta fito harabar Companyn ya tare ta tare da cewa. " Ji mana ƴan mata" Sarai Safreena ta jisa ta share tamkar bada ita yake ba ta cigaba da tafiyar ta, tazo daidai get ɗin ya tare gabanta yace. " Baiwar Allah dake fa nake." Tsayawa Safreena tayi tare da cewa. " Ina sauraronka." Murmushi Kabir ya saki tare da cewa. " Sunana Kabir kefa.?" Shuru Safreena tayi tana tuno yanda ta gansa tare da Garkuwa, da alamu kuma akwa alaƙa mai ƙarfi tsakanin su, ƙarya ta masa da cewa. " Kabir nice name, my name is Safrah" Ta ɓoye sunan nata gudun karya fahimci wani abu, murmushi Kabir yayi yana tsura mata idanu cike da so yace. " Like beautiful face like beautiful name, Safrah nice name, hmmm!!! Safrah ni ne manager na wannan Companyn, ina so muyi exchanging ɗin Number, zan kiraki zamuyi Magana." Murmushi Safreena tayi tana jin a zuciyarta wannan ce damar daya kamata tayi amfani dashi wajen samun wannan aikin, Manager ba wasa ba dole zata samu aikin ta dalilinsa, murmushi ta saki tare karɓar wayarsa ta saka masa, shima nasa ya bata sannan suka rabu Safreena ta tafi. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Bayan kwana biyu Cike da farin ciki Daddy yake duban Mamma dake tsaye tana murmushi. " Mamma alhamdulillah!!! Bani da burin daya shige samun lafiyarki, Alhamdulillah!!! Mun gode sosai INNO kinyi namijin ƙoƙari babu abinda zamu ce miki sai godiya" Murmushi Jummo tayi cike da farin ciki tana ganin yadda Daddy da Garkuwa suke cike da farin ciki, Momy ce kawai fuskarta take ɗaure, kanta Jummo ta kawar gefe tare da ɗaga wayarta dake ringin. " Hello Meenat okay to gani fitowa ina room ɗin Mamma ne." Tayi Maganar tare da katse kiran tana fita da kallo Garkuwa ya bita yana sakin murmushi a rayuwarsa yana mungun son Yarinyar. A falo Jummo ta taradda Meenat murmushi tayi tare da kamo hanun meenat suka haura sama bedroom ɗin ta zama sukayi bakin bed meenat ce tace. " Hmmm!!! Wai Jummo meke damunki ne 2days bakya zuwa school, naga alamar kamar Soyayya tana son ta rabaki da karatu to ki dawo hankalinki ki gane cewa karatun da kike yana da matuƙar mahimmanci a rayuwarki." " Kai Meenat daɗina dake saurin fushi da rashin sauraran uzurin mutum, akan Soyayyane zan daina zuwa school, kin dai san naji jinya, dalilin da yasa Ya khalil ya karɓa min hutu harna tsawon wata Biyar a ƙa'ida Monday zan koma school gashi kun kusa zana neco, amma ai ban isa nabar school ba akan so domin kuwa ilimi shine ginshiƙin al'umma." " Na sani Jummo amma ai ya kamata ace tunda kin sami lafiya ki koma school ba sai lokacin da aka karɓa miki hutu ya cika ba, ni yanzu ba wannan bama, wai ya Garkuwa ya ƙare da Momy ne ta amince da Auren naku kuwa.?" " Hmmm!!! Ina kuwa ta amince, ni fa na rasa mena tsarewa Momy bansan wacce irin ƙiyayya take min ba, a zuciyata babu mungun nufi ga Momy kullum neman hanyar da zata rabauta nake amma a hakan nice maƙiyyarta!!! Mtss ina cikin tashin hankali domin kuwa muddun Momy tayi nasarar rabani da Ya Garkuwa zan shiga mungun yanayi, ina sonsa fiye da komai a rayuwata, tun bansan meye so ba nake ɗauniya da sonsa a raina harna girma na san me ake kira Soyayya tun baya sona yana gwada min ƙiyayya ban taɓa jin Soyayyar sa ta ragu a raina ba, sau ma ƙara yawa da take ya zageni ya hantareni babu irin ƙiyayyar da bai nuna min ba a lokacin da nake ƙauye amma ban taɓa jin na tsanesa ba dai-dai da second ɗaya KULLUM ji nake bazan iya numfashi ba muddun babu shi, yanzu kuma Allah ya dubi halin da zan shiga idan na rasashi ya kawo min shi cikin rayuwata ya amince da soyayyata yanzu kuma ace zan rasashi, wani irin hali kike tunanin zan shiga, wallahi kullum da tunani da tsinkewar zuciya nake kwana ina tunanin makomata nida Garkuwa haɗuwa ko rabuwa bansan da wanne zan wayi gari ba, ina tashin hankali Meenat." Cike da tausayin Jummo Meenat ta dafa kafaɗar Jummo tace. " Ki daina tunani ko damuwa Allah shine maiyi yana ganin komai, kuma bazai bari ki wulaƙanta ba, baki cucesu ba, Allah bazai barsu su cuceki ba, ki dage da addu'a insha Allah komai zaizo miki da sauƙi kuma cikin Nasara." " Allah yasa, Ya school ɗin ina buƙatar LESSON ɗinki fa, dan nasan nayi missing ɗin LESSON da yawa." " Wannan ai kinsan ba matsala bace LESSON, fatan dai kin biya kuɗin neco ɗinki dan sun kusa gama karɓar kuɗin.?" " Ya khalil ya biya harma sun bashi slip, Meenat ko kin san har yanzu akwai Soyayyar wata a cikin zuciyar Ya Garkuwa, duk da a halin yanzu gawa ce ta mutu, amma ina jin kishi ta a RAINA." Ɗan zaro idanunta Meenat tayi tare da cewa. " Whatttt!!! Soyayyar wata kuma ƙawata, shi Garkuwan ne ya sanar dake hakan." Murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Ehhh shine ya sanar dani Meenat, amma a yanzu bata raye Yarinyar ta mutu, sai dai yana yawan ambaton ta, tare da yabonta cike da Soyayya, a duk sanda naji yana yabonta sai naji ba daɗi tamkar tana raye bana son yana min hirarta sai dai bansan ta yaya zan dakatar dashi da hakan ba." " Haba ƙawata akan me zakiyi kishi da matacciya, wacce bata raye tabar duniyar ba kuma zata dawo ba, dan Allah ki manta da wannan kishin domin kuwa bashi da amfani shi da babu duk ɗaya ne, ki fuskanci matsalar Momy kawai ta isheki, itama Allah ya fidda ke lafiya, sannan ki maida hankalinki da kulawar ki ga abin sonki ki tarairayesa ki lallaɓasa tamkar kwai ba sai na faɗa miki kwalliya ba domin nasan ke gwana ce, hakan shi zaisa ya manta da wata Mace ya maida hankalinsa gareki ki zamo kece kaɗai Abokiyar tunaninsa a zuciyarki, mantawa zaiyi da ko wacce ke kaɗai zaike kallo." Murmushi Jummo tayi tare da kwantar da kanta jikin Meenat tana dariya tace. " Shiyasa nake daɗa kaunarki ƙawata domin kuwa akwai ki da kawo mafita mai kyau." Murmushi itama meenat tayi sun juma suna hira kafin Jummo ta rakata ta koma gida. *************** Ƙarfe 4 dai-dai jirgin su Ya khalil ya sauƙa a babban airport ɗin dake cikin jihar Abuja, cike da farin ciki take fitowa daga cikin jirgin hanunta riƙe dana Ya khalil, sai murmushi take rabonta da Nigeria 6 yrs numfashi ta sauƙe mai daɗi tare da duban Ya khalil tace. " Wow Bros!!! I am very happy today I missing Nigeria" Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa. " Nigeria ma ai tayi missing ɗin ki Zezah, kin san waye zaizo ya ɗauke mu kuwa?" Kafadarta Zezah ta ɗaga tare da taɓe bakinta tace. " Bazai wuce ɗan uwan da bai damu da ƴar uwarsa bane Garko." Dariya Ya khalil yayi tare da cewa. " Lallai kin manta waye Garkuwa a tunaninki shine zaizo ya ɗauke ki, Lallai kinyi kuskure, ba shi bane Samuel ne zaizo." " Samuel Kuma Bros!!! Wai wata irin kalar ƙiyayya Ya Garko yake minne da bazaizo ya tare mu ba, mtsss!!! No problem bashi ya ci." Murmushi Ya khalil yayi ba tare da yace KOMAI ba har suka hango Samuel motar suka shiga ya dawo dasu, tun a harabar gidan Zizah ta ruga da gudu tana kiran. " Momy Momy!!! Daddy Daddy!!! Momy I am coming!!! I missing you so much Momy!!!" INNO da Mamma dake zaune a falon ne suka miƙe tsaye ganin mutum ya faɗo yana kiran Momy Daddy ba tare da sallama ba, INNO ce ta tare ta tare da cewa. " Ke mahaukaciyar ina ne ke baki da hankali ne, ko baki san gidan musulmai kika shigo bane, ba sallama zaki faɗo mana falo kina wani Momy Daddy, ba Daddy ba Allah yasa Dada ne yau naga shashanci daga ina kika fito marar hankali." Sake baki Zizah tayi tana kallon su cike da haushi da kuma tunanin su kuma wadannan tsofin su waye daga ina aka yayosu da zasu dinga faɗa mata Magana ita da gidan ubanta, bata gama tunanin ba taji muryar Mamma ds ta ƙarewa shirt da jeans ɗin dake jikinta kallo tana cewa. " Kema dai INNO da wata tambayar kike, ai daga ganin wannan kinsan arniya ce, duba fa kiga wasu tsinannun kayan dake jikinta na marassa mutuncin arnan nan, wannan ai Esther ce." Garkuwa dake tsaye a sama yana sauraron su ne ya shiƙe da dariya yana tafawa tare da furta. " Exactly Mamma, kaman kuwa kin sani Esther ce, domin kuwa dai babu ɗan musulmi mai kunya da zaiyi wannan shigar, welcome ƙaramar fitsararriyar Momy." Ɗaga idanunta Zizah tayi tana kallon Ya Garkuwa cike da jin haushin maganganun su, nunasa tayi da yatsa cike da jin haushi tace. " Dama a duniya kai kuma kana da makiyayar da ta wuce ni ne, yo haushin me zanji danka min haka, mtsss." Taja tsuka tare da kallon su Mamma tace " Ku kuma waɗannan tsofi, su waye ku da har zaku shigo gidan ubana kuna faɗa min Magana, ji beki fuska duk ta tattare ta yamutse babu kyan gani shine zaki dinga buɗe bakinki duk jan goro kina faɗa min magana shima dai Daddy da kwashe kwashe ko ina ya kwaso ku oho amma dai da ganinku kunfi kama da Barorin jeji" Tana gama Maganar ta haura sama da gudu, INNO zaro idanunta tayi tana duban Zizah yarinya ƙarama da iya baƙar Magana, murmushi Ya Garkuwa yayi domin kuwa yama yi mamakin da bata zagesu ba, shima ya khalil dake tsaye a gefe ne yasa dariya tare da shigowa yana cewa. " Wai Mamma jikar taki kika manta Aziza ce fa." "Aziza kuma yanzu Azizar ce wannan mai shiga irin ta ƴaƴan arna, ka fa duba kayan dake jikinta, hmmm!!! Ko da yake babu abinda ma bazata aikata ba, tunda an ɗauke ta an Kaita ƙasar arna karatu duk laifin ubanku ne ai." Ɗan murmushi Ya khalil yayi tare da shigewa yana cewa. " Babu ruwana Mamma kinfi kusa keda Daddy." Zizah bedroom ɗin Momy ta faɗa tana kiranta Momy dake zaune ne ta miƙe cike da farin ciki suka rungume juna cikin farin ciki Momy tace. " Wow My Daughter welcome, yaushe kika shigo banji kiba."? Zizah tana dariya ta laɓe a jikin Momy tare da cewa. " Tun sauƙata a mota nake ƙwala miki kira Momy baki amsa min ba, naji daɗin ganinki Momy, ina Daddy ina kewarsa Momy."? Murmushi Momy tayi tace. " Daddyn ku yana kasuwa sai dare zai dawo, yanzu kije bedroom ɗinki kiyi wanka kiji sanyi, sai ki fito akwai muhimin abu dana tanadar miki." Murmushi Zizah tayi tare da cewa. " Shikenan Momy na, bara naje yanzu kuwa zan fito." Tayi Maganar tana fita cike da fara'a, Momy ma murmushi tayi tabi bayan ƴarta ta da kallo cike da ƙauna ita kenan ƴarta mace a duniya,. Zizah bedroom ɗinta ta nufa kanta tsaye, turus ta tsaya hango mutum kwance sai famar chat take, cike da mamaki da kuma faɗa cikin tsawa ta cewa Jummo. " You!!! Who is this!!!"? Jummo da taji Magana cikin tsawa ba zato ta miƙe zaune tana bin Zizah da kallo tare da nuna kanta da yatsa tace. " Me!!!!?" " Ehhh ke, waye ke da zaki shigo min room har ki kwanta min a bed sai kace gadon uwarki, wannan ai raini ne, mtsss!!! Wai su waye ne aka samu a cikin gidan nan can naga wasu koɗaɗɗun tsofi, nan kuma na shigo naga wata koɗaɗɗiyar yarinya, dalla sauƙa min akan bed malama."? Jummo baki ta saki cike da tsantsar ɓacin rai tana kallon Zizah domin kuwa maganar ta tayi mungun ɓatawa Jummo rai, harta kasa maida mata amsa still dai muryar Zizah ta kuma ji cikin tsawa ta na ce mata. " Cewa nayi ki sauƙa min akan gado, da hausa fa na miki Magana kin tsaya kin zuba min ido tamkar wata mayya.................." *Ummu Nasmah ce* [5/4, 11:31 AM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *56 to 57* GARKUWA daya naɗe hanu yana kallon Zizah yanda take zagin Jummo tamkar uwarta dama ya sani muddun Zizah ta samu jummo cikin ROOM ɗin zata mata rashin kunya domin kuwa ita a rayuwarta ta tsani wani ya raɓeta a hankali ya tako ba tare da Jummo ko Zizah sun gansa ba sauƙar marin da Zizah taji ya sata saurin ɗago kanta a gigice tana kallon ya Garkuwa tare da dafe fuskarta a fusace tace. " Mena maka zaka gaureni da mari, mena ma."? Ta jefa masa tambayar tana sakin kuka, Jummo miƙewa tsaye tayi tare da cewa. " Subahanallah!!! Haba Ya Garkuwa meta maka haka zaka mareta wannan ba dai-dai bane."? Ransa ɓace ya Garkuwa yace. " Tamin tunda ta miki, ki daina bin bayan wannan fitsararriyar Yarinyar domin kuwa ba mutunci gareta ba, bata ganin mutuncin manya ni nafi sanin waye Zizah, kuma wallahi Zizah ki buɗe kunnenki da kyau kiji, kin sanni sarai kin san halina to Wallahi ki shiga hankalinki ki nutsu domin kuwa yanzu ina cikin gidan nan, idan kika ce zaki ɗaga mana hankali na rantse da Allah saina mai dake jaka a cikin gidan nan a ƙarshe na karyaki na wurgarki, shasha marar lissafi, Wannan da kike gani zaginta tamkar ni aka zaga a kanta sai na iya nakasa ki, wannan ɗakin anan take zaune ba kuma zata fita ba saboda ke, idan bazaki iya zama da ita ba kina iya neman wani room ɗin, ki shiga hankalinki kin dai sanni." Yaƙarisa Maganar yana ficewa daga Zizah har Jummo binsa da kallo sukayi sosai kan Zizah ya kulle, ita wannan ɗin wacece da Ya Garkuwa zai mata barazana a kanta, muryar Jummo taji tana cewa. " Kiyi hkr ƴar Uwa abinda Ya Garkuwa yayi bai kyauta miki ba, karki sa a rank............." " Dallah dakata min Malama!!! Karki kuma kirana da ƴar uwarki domin kuwa bani da ƴar uwa, sai ɗan Uwa, ta ina na haɗa jini dake, har akanki zai mareni dake ya tsaneni, kuma wallahi sai kin bar wannan room ɗin tunda ba gidan ubanki bane stupid girl.?" Tayi Maganar tare da shigewa tolet, Jummo shuru tayi cike da jin zafin maganganun Zizah tabbas idan ba a gidan ubanka kake ba, zaka fuskanci wulaƙanci halinta sak da na Momy babu inda ta barta wannan wani irin gida ne mai cike da tarin matsaloli, idan kayi ƙoƙarin kawar da wannan sai kuma wani yazo hmmm!!! Ya Allah ka kawo wa wannan gida sauyi, tayi Maganar tana ficewa tayi room ɗin Mamma. Ko da Zizah ta fito bayan ta kimtsa bedroom ɗin Momy tayi cike da farin ciki, a zaune ta taradda da Momy itama ta zauna tana dubanta Momy kallon Zizah tayi tare da rungumota jikinta tana murmushi tace. " Welcome Zizah nayi missing ɗinki da yawa, dafatan komai dai-dai karatu dai yayi kyau ko.?" Murmushi Zizah tayi tare da cewa. " Momy karatu yayi kyau domin kuwa nice nazo second class a department ɗinmu na samu kyautuka masu yawa Momy saura kuma na samu aiki." Dariya Momy tayi tare da furta. " Masha Allah abubuwa sunyi kyau Allah ya yiwa karatun albarka, insha Allah jibi zan haɗa taron tayaki murnar kammala karatun ki, yanzu tashi muje kici abinci ko, Zarah ta haɗa miki abincin da kika fi so." Miƙewa Zizah tayi tana cewa. " Oh Momy ina Aunty Zarah take ban ganta ba."? " Zarah taje gidan su barkan Zaliha matar wanta ta haihu." Da okay Zizah tace tare da fita suka nufi daining. Shi kuwa Ya Garkuwa yau tunda Daddy ya dawo ya maƙale a room ɗinsa kasancewar yana buƙatar magana dashi haka kuwa akayi bayan Daddy ya ci abinci Momy ta kauce sannan Ya Garkuwa ya dubi Daddy cike da nutsuwa yace. " Daddy nazo ne ina son nayi Magana da kai." Gyara zamansa Daddy yayi tare da duban Garkuwa yace. " Ina jinka Garko Bismillah kayi maganarka ina da isasshen lokaci." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Daddy dama maganar itace, amm amm amm dama Daddy akan batun AURENA nane Daddy na samu matar Aure shine nake son ka shige min gaba kaje ka min tambayar auren ko zuwa jibi ne." Murmushi Daddy yayi tare da cewa. " Oh Garko yanzu wannan maganar zaka min shine kake inda inda, wannan ai abun farin ciki ne, naji daɗin wannan maganar taka Garko, a ina ka samu matar waye mahaifinta.?" " Amm Daddy ba wata bace fa, Jummo ce jikar INNO ita na fitar a matsayin matar da zan aure." Cike da farin ciki Daddy yayi murmushi tare da cewa. " Masha Allah, abu yayi kyau shikenan zamuyi tuwo na maina wannan ai duk gida ne Garko babu bare tsakanin ka da Jummo dukkanku ƴaƴana ne, karka damu zanje har ƙauyen next week na samu Baffa muyi magana, insha Allah nan kusa za'a saka lokacin Auren Allah ya maka albarka." Cike da farin ciki Garkuwa yake duban Daddy alhamdulillah Daddy ya amince Momy ce matsalar kuma. " Daddy sai kuma akwai matsala fa." " Matsala kuma Garko wacce irin matsala.?" " Daddy Momy bata son Wannan auren tama ce muddun na matsa akan dole sai na Auri Jummo zata ɗaga min nono Daddy shiyasa hankalina yake tashe bansan meyasa Momy bata son Jummo ba, ka taimake ni Daddy kayi Magana da ita ko zata hkr ta janye." Cike ɓacin rai Daddy ya ɗago idanunsa ya kalli Garkuwa tare da cewa. " Serious ita Hajiya Zainab ɗin ce bata son Auren." " Ehhh da gaske Momy bata so." Numfashi Daddy ya saki tare da cewa. " Garko karka damu wannan Auren za'ayisa babu makawa ko tana so ko bata so ka barni da ita dole zata amince tashi kaje abinka." Tashi Ya Garkuwa yayi yana murmushi ya fita, yayin da Daddy yake cike da mamakin meyasa Hajiya Zainab zata ƙi wannan Auren, amma koma dai menene yasa a ransa gobe zai kira meeting ɗin gaggawa. Washe gari da safe bayan kowa yayi breakfast Daddy yayi gyaran murya tare da duban Aunty Zarah yace. " zara'u maza shiga room ɗin Mamma kice suzo muna falo za'a tattauna magana mai mahimmanci." Da to Aunty Zarah ta amsa shi kuma Daddy ya miƙe zuwa cikin falon, ya khalil da Ya Garkuwa suka rufa masa baya Momy duban Zizah tayi tace. " Muje" Ta ƙarisa Maganar tana miƙewa tayi wajen nasu Jummo kallon A'illo tayi ba tare da ta miƙe ba tace. " Kije mana A'illo bakya jin Daddy yace kuje ku samesa a falo.?" " Naje ko muje, ya kina Magana kuma kina cire kanki acikin Maganar.?" Murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Dole zan cire kaina a ciki domin kuwa wannan meeting ne na FAMILY bayan kuma ni barece a tsakanin ku, Kinga kuwa bani da hurumin shiga cikin ku, ki tashi kije.'' " Ya kamata ki daina kiran kanki bare domin kuwa kin bawa wannan gidan gudumowar da jininta ya kasa bata kin fi ƙarfin bare." Murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Naji amma dai ki tashi ki tafi." Kaɗa kanta Jummo tayi tare da miƙewa tsaye tayi cikin falon, Mamma tare suka shigo da INNO suka zauna cike da girmamawa Daddy ya gaishe su haka itama Momy ta gaishe su cike da ƙuncin Zuciya, duban kowa dake wajen Daddy yayi babu Jummo. " Zara'u ina Jummo take ban ganta anan ba, jeki kirawo min ita."? Da to Aunty Zarah ta amsa tare da tashi taje ta kira Jummo kusan tare suka shigo Jummo ta nemi gefe da INNO ta zauna, nisawa Daddy yayi tare da cewa Mamma. " Mamma na tara kowa ne anan wajen domin na sanar daku wani kyakkyawan albishir wanda yamin daɗi Kuma abin ya burgeni." Murmushi Mamma tayi tare da furta. " Masha Allah, Garba ai abun alheri shi ake so a dinga ji, muna sauraronka." " Mamma jiya bayan na dawo daga kasuwa Garko yazo ya sameni da Maganar cewa ya fidda matar Aure kuma Jummo itace ya fitar, har yake neman alfarmar cewa na je na masa tambaya, shine nace bara na fara sanar daku kafin na isa ga Baffa." Ai kuwa kafin Daddy ya rufe bakinsa Momy tayi carap tace. " Wani Garkon ba dai ɗana ba, domin kuwa bazai Auri Jummo ba, na riga na yanke hukunci mun juma da gama wannan maganar kuma shima gashi gabanka ka tambaye sa, ya hkr." Da kallo kowa na Wajen ya bita har INNO Daddy kuwa dariya yayi tare da gyara zamansa yace. " Naji maganarki Zainab, to amma bara naji hujjar ki kuma na haramta Aure tsakanin su, idan tana da makama sai a duba lamarin sanar dani meyasa bakya son Auren.?" Shuru Momy tayi tare da jefawa Garkuwa mungun kallo kafin tace. " Saboda bana ƙaunar haɗa jini da gidan Arɗo Bazan haɗa jini da Jikar gidan ba, kaima ka sani, a matsayina na Uwar da ta haifi Garko, nace bana son Wannan Auren, bazai Auri wannan fitsararriyar Yarinyar ba, dan haka dole a haƙura da wannan Auren." Murmushi INNO tayi Daddy zaiyi Magana ta ɗaga masa hanu tana cewa. " Ɗan dakata tukunna Garba na tambayeta" Daddy shuru yayi yana duban Momy dake famar huci tamkar kububuwan maciji INNO ce tace. " Lallai Zainabu har yanzu dai kina nan da rashin kunyarki baki fasa ba, yanzu ke idan kina da kunya har kin isa kice bakya son haɗa zuri'a da Arɗo saboda ya ƙarshen ubanki shiyasa kike tsoron itama Jummo jinin sa ta kawo ƙarshen rashin mutuncin ki a cikin gidan nan, kin sani Zainabu Wallahi kaf zuri'ar mu bamu da abun kunya kuma babu Boka ɗan tsibbu a danginmu, malam addini muka tara wanda suka iya karatun Alkur'ani suka san fassarar sa, da littatafan addini, dan haka ki iya bakinki akan zuriata idan ba tonon asiri kike bukatar muyi ba." Daddy ne ya ɗaura da cewa. " Rabu da ita INNO wannan soki burutsu ne kawai take babu wani hujja da take dashi wanda zaisa a fasa wannan Auren Garko ɗana ne, nine Ubansa wanda na ɗauki ɗawainiyar rayuwarsa, dan haka wajibi ne wannan auren babu abinda zai hana ayisa sai tsantsar ikon Allah nine nake da iko dashi ba ke ba dan haka ki fita a idanuna Hajiya Zainab." Miƙewa tsaye Momy tayi a fusace cikin ɗaga murya tace " Ka daina kiran ɗanka kai ɗaya kasa minjaye cikin sautin ka, kace ɗanmu domin kuwa nice na goyi cikin sa, na shayar dashi daga fatar jikina, naci kashinsa da fitsarin sa, na juri duk wata ɗawainiyarsa karka manta kafin Allah ya ambaci Uba sai da ya ambaci Uwa sau uku, ya kuma ce daga shi sai ita kaga kuwa ai ba ƙaramar daraja muke da ita ba, dan haka nace Garko bazai Auri Jummo ba kuma dole ya hkr muddun yana neman albarka ta, idan ba haka ba na ɗaga masa nono." Mamma murmushi tayi tare da tashi ta miƙe cikin gwarin hausarta tace. " *TARIHI YA MAIMAITA KANSA* gaskiyar masu iya magana ne da sukace duk abinda ka aikata mai kyau ko marar kyau ka jira juyowarsa domin kuwa babu makawa sai ya dawo maka, gashi ke yanzu ya dawo miki zaki ɗanɗani wani irin ɗaci naji duk da ni na fiki hujja, ashe dama Uwa tana da wannan darajar da kika lissafo baki taɓa nunawa mijinki shi yabi tasa Uwar ba, ashe Uwa tana da iko da ɗanta, kika nuna cewa Uwa bata da mahimmanci a baya" kallon Ya Garkuwa Mamma tayi cike da ɓacin rai idanunta na ƙoƙarin kawo ruwa tace " Garko a sanda ubankuu zai Auri Mahaifiyar ku haka na nuna tawa ƙiyayyar, duk da ni tawa ƙiyayyar mai hujja ce, da shike gidan uban uwarku ƴan tsubb............." Saurin katseta Jummo tayi tare da cewa. " Ya isa haka Mamma dan Allah kar kuyi tone-tone saboda ni, kibar Maganar karki ƙarisa ta riga da ta shige karki tayar da tsohuwar magana idan nine zan hkr da Ya Garkuwa saboda a zauna lafiya, ko da kuwa Soyayyar sa zata kashe ni, zanyi jahadi domin ganin zaman lafiya a cikin gidan nan, dan Allah Mamma kubar maganar nan haka." Cike da tsantsar ɓacin rai Daddy ya miƙe tsaye tare da cewa. " A'a Jummo, ki rabu da ita karki ɗaga hankalinki ga Maganar Hajiya Zainab, Mamma gaskiya ta faɗa kamar yadda Zainab bata son Auren ki da ɗanta haka itama Mamma, jajurcewa da haƙiƙancewa na mahaifina dana kakanki Baffa da mahaifiyar Mamma shine yasa Auren mu da Zainab ya ɗauru, amma ki duba ki gani yanzu wai itace take cewa ɗanta bazai Auri zaɓinsa ba, Kuma ba mutumiyar banza ya ɗauko ba, gaskiya Zainab baki da kirki ko kaɗan lallai kinyiwa Baffa mummunan sakamako, to ki sani na gama yanke hukunci aure tsakanin Jummo da Garko za'ayisa kuma a gobe zanje na nema masa Auren ba kuma zamuja lokaci ba za'ayi Auren kina iya ɗaga masa nonon sai mu gani ko zai lalace." Cike da huci Momy ta kalli Daddy cikin tsawa gami da tashin hankali ta cewa Daddy. " Wai ya kake ƙoƙarin nuna min gadara ne akan Garko nima ina da iko dashi, wallahi muddun akayi wannan Auren ba tare da izinina ba, wannan auren bazai taɓa albarka ba, ba kuma zasu taɓa samun farin ciki ba, za Kuma kuga abu marar daɗi da zai faru a cikin wannan Auren muddun aka yisa, na muku wannan bakin kaje da umarnin ubanka Garko ka gani idan Rayuwar zata maka kyau babu albarka ta, tunda ni ban isa da kaiba bani da mutunci da daraja a idanunka, har zaka kaini Wajen UBANKA kaje duniya ce, kuma insha Allah bazaka taɓa samun farin ciki a wannan Auren ba." Tana gama faɗin haka ta juya cike da ɓacin rai Ya Garkuwa cikin matsanancin tashin hankali yabi Momy da kallo tabbas maganganun ta sun munana garesa, anya kuwa zaiyi wannan Auren, Maganar mahaifiya tabbas bata da hijabi ga Ubangiji, INNO da kallo itama tabi Momy harta haura nisawa INNO tayi tare da cewa. " Wai Zainab ce take cewa jininta bazai Auri Jummo ba, mu bamuce bazamu haɗa zuri'a da ita ba, wai itace take cewa haka, ɗiyar matsafi ƴan tsibbu wacce ta fito daga gidan da yayi tambari wajen Rashin Ɗa'a, hmmm!!!! Lallai Mutum mungun icce, ki duba Mamma abunda ta aika ya juyo mata amma ta kasa fahimtar hakan" duban Daddy tayi tare da cewa. " Kaga abinda kuskuren ku ya jawo kun aikata abinda ba dai-dai ba ga rayuwar mahaifiyarka, ka zaɓi mace sama da Uwar da ta haifeka, yau gashi kana gani a gabanka tana nuna maka cewa kai uwarka ba uwa bace, yanzu kuma ta nuna cewa ita fa uwace mai ƴanci akan ɗanta, tana da ikon basa umarni yabi, yayinda kai kuma a baya ta nuna maka cewa mahaifiyarka bata da daraja bata da iko da kai, GARBA yanda a wancan lokacin bakaji Maganar Mamma ba, to ka sani yanzu ma Garko bazai ji Maganar zainabu ba, wannan Auren za'ayisa nice kakar Jummo kuma nace na bawa Garko ita duniya da lahira, ka shirya kaje ku tattauna da Baffa" tayi Maganar tana kallon Garkuwa tare da cigaba da cewa. " Karka damu Garko babu abinda bakinta zai muku yanda akayi aurenta babu yardar Uwar mijinta Kuma suka zauna lafiya cikin farin ciki, haka kaima zaka zauna da taka matar Lafiya, ka ƙyaleta, tana cikin fushi zata sauƙa wata rana ta rungumi auren ku dole." Shuru Daddy yayi tabbas dukkan maganganun INNO gaskiya ne, yayi watsi da mahaifiyarsa saboda soyayya, hatta ziyara ya daina kai masa, hmmm ashe dukka mata tunaninsu ɗaya ne akan ɗansu meyasa ya aikata wannan kuskuren dole yana buƙatar neman gafarar Mamma, sai yanzu ya fahimci cewa bai samawa ƴaƴansa Uwa ta gari ba, domin kuwa shi kansa wani lokacin yana lura da yadda ake rayuwar da bata da ce ba a gidan sa, a wannan karon zai nunawa Momy matsayinta zai kuma hukunta ta, akan wannan shirmen, zai tsaya da ƙafafuwan sa wajen tabbatar da wannan Auren, domin farin cikin Mamma, nisawa yayi tare da cewa. " Tabbas nayi kuskure nayi kuskure gareki Mamma a yau idanuna sun buɗe na fahimci hakan, dan Allah kiyi haƙuri Mamma ki yafe min insha Allah zan gyara tsakanina dake kuma zan tsaya da ƙafafuna domin tabbatar da Auren Garko, kuyi haƙuri." Daddy yayi Maganar cikin sanyin jiki, shi dai Ya khalil ya gagara magana domin kuwa kalaman Momy sunyi mungun tsorata sa, bai taɓa tunanin cewa akwai Uwar da zatayi munanan kalamai akan ɗanta harta nema masa tashin hankali, Lallai ne Rayuwar Momy akwai gyara ita ko wacce suruka bata so, wannan wani irin ɗabia ce, duk da yaji zafin maganganun INNO da tayiwa Momy sai dai yasan koma me aka faɗa mata itace ta jawo, miƙewa tsaye yayi cikin sanyin jiki ba tare da yace komai ba ya juya zai bar wajen muryar Daddy yaji yana ce masa. " Tunda aka fara wannan maganar baka ce komai, ka shirya gobe da safe zamuyi sammakon zuwa TULDEN FULANI." Juyowa Ya khalil yayi tare da cewa. " Allah ya kaimu Daddy" Yayi Maganar a taƙaice tare da ficewa ya nufi garden, Shima ya Garkuwa tashi yayi yabi bayan sa, Daddy shima kasuwa ya tafi, Aunty Zarah cike da farin ciki ita da Zizah suka miƙe suka nufi bedroom ɗin Momy ita Aunty Zarah farin cikin ta shine, Momy ta shiga ƙunci domin kuwa Allah ya saka mata abinda ta mata, Momy tunda ta shiga room ɗinta ta kasa zama sai kaiwa da komowa take, ta goya hanunta a baya, sosai take cikin tashin hankali, Zizah ne da ta shigo ta doki mirror da ƙarfi cikin fusata tace. " Why Momy!!! Why!!! Daddy zai ƙasƙantar dake a gaban waɗannan koɗaɗɗun tsofin, ba laifin kowa bane laifin Garko ne Domin kuwa shine baiji maganarki ba, waima meya gani jikin wannan jakar yarinyar, anya kuwa Momy ba asiri suka masa ba, na kasa gane meyake damun Rayuwar Ya Garko, shi a rayuwarsa abinda yaga dama shine yake yi, Ki barta ta shigo gidan Momy, Wallahi sai mun mayar mata dashi kurkuku." Aunty Zarah ce ta taɓe bakinta tare da cewa. " Tayani gani dai Zizah nima banga meya gani a jikinta ba, amma da shike kinsan a ruga suka fito, asiri zasu masa." Girgiza kanta Momy tayi tare da cewa. " Bazasu masa asiri ba, domin kuwa babu boka a gidan su gidan malamai ne, kissa ce kawai da iya munafurci yasa ta mallake min ɗa, ku barni da ita sai tayi danasanin shiga rayuwata, ku fita ku bani waje." Ta ƙarisa Maganar tana zama tare da dafe kanta fita sukayi. Ya khalil zama yayi tare da yin shuru ya rasa me yake masa daɗi maganganun Momy kawai suke masa yawo a kansa. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!" Ya furta tare da sakin numfashi kafaɗarsa Ya Garkuwa ya dafa tare da cewa. " Ni kaina hankalina a tashe yake Momy tamin baki ta faɗa min mugayen maganganu, Momy tamin baki ina tsoro kar bakinta ya kamani, ya zanyi Bro meye mafita." Ɗago idanunsa ya khalil ya yi ya dubesa tare da cewa. " Babu yanda zakayi domin kuwa Daddy ya yanke hukunci, kuma ka sani Magana ɗaya yake yi, Baka da haƙƙin Momy insha Allah bakin ta bazai kamaka ba, kai dai ka cigaba da mata biyayya tamkar yadda kake karka fasa insha Allah komai zai shige Momy zata sauƙo zata gane gaskiya." Shuru Ya Garkuwa yayi cikin tashin hankali, zama yayi shima yayi shuru dukkan su babu wanda ya kuma cewa ɗan uwansa wani abu. Ita kuwa Jummo tafi kowa shiga cikin tashin hankali, bata taɓa tsammanin ƙiyayyar da Momy take mata yakai haka ba wannan wacce irin masifa ce, sai dai tasa a ranta zata dake da addu'a da sadaka insha Allah Allah zai karesu. Yau Daddy da Abokinsa Alhaji Ahmed Sai Ya khalil suka nufi TULDEN FULANI, da niyar Tambayowa Garkuwa Auren Jummo. MOMY sosai ranta yayi mungun ɓaci ganin da gaske fa wannan Auren zai tabbata, sai dai ta ɗauki alƙawarin bazata taɓa bari wannan Auren ya kasance ba. *UMMU NASMAH CE* [5/8, 10:29 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *58 to 59* "Wai ke Safreena me zakiyi da wannan aikin ne, just 30k ne fa kawai suke bawa ƙaramin ma'aikaci a wata, kuma ke kina da master's me zai hana bazaki je AA ƊAN DARMA ki nemi aiki ba, wannan ma'aikatar suna bada Salary mai tsoka, a babu suna bawa ƙaramin ma'aikaci 65k amma sai ki tsaya ki nemi aiki a wannan ƙaramin Companyn me 30k zata miki a wata."? Ɗan murmushi Safreena tayi tare da cewa. " AA ƊAN DARMA ba Companyn daya kamata nayi aiki a cikin sa bane Zee kema kin sani ko karima kanta da ta samu aiki a wajen ki duba kiga yanda take complain akansu basu da uzuri sannan basu ganin darajar ma'aikacin su, to me zakaje kayi a inda baza'a ga darajar ka ba, Su kuwa I D D BARAU NIG LTD company ne da suka san darajar ma'aikaci sukan bawa kowa mutuncin sa, ba kuma sa taɓa wulaƙanta ma'aikaci koda kuwa mai shara ne, ina son inda za'a mutuntani Zee, gara a bani kuɗi kaɗan aga mutuncina, ba wai a bani kuɗi mai yawa ba ana ɗaukata ƙasƙantacciya, Zee wannan 30k ɗin da zasu bani ta isheni nayi buƙatuna da kuma na Abdul saboda na rufa masa asiri yasa na nemi wannan aikin kuma kuɗin zasu isheni buƙatuna dana ɗana, bani burin ƙarya a cikin rayuwata ki gane haka mutunci yafi kuɗi." Numfashi Zee ta saki tare da cewa. " Hakane na fahimta, ɗazu kin fara bani labari, Baba ya shigo kikayi shuru, kikace kun haɗu da Garkuwa a wannan Companyn, ya ganki kuma." Kanta Safreena ta kaɗa tare da sakin murmushi tace. " A'a ban bari ya ganni ba, saboda bana son mu sake haɗa idanu dashi, a zuciyarsa na mutu, hakan nake so ya tabbata na mutu a cikin rayuwarsa, bazan taɓa yadda Garkuwa yasan ina raye ba, nasani har gobe ina zuciyarsa, fahimtar ina raye zai tono abubuwa masu yawa ciki harda barazana ga ɗana Abdul, dan haka na kashe Garkuwa a zuciyata bazan taɓa yadda mu haɗu ba." " Safreena karkiyi haka dama ce yanzu a gareki na Garkuwa yasan kina raye, domin kuwa hakan shine zai fitar dake daga zargin ɗanki ma'ana dai ina nufin Garkuwa ya kamata ki aura domin rufin asirin ɗanki, ya kamata kiyi tunani akan maganata." Murmushi safreena tayi tare da miƙewa tsaye tace. " Bana buƙatar tunani akan wannan maganar taki babu ni babu Garkuwa har abada bazamu taɓa haɗuwa dashi ba ki ajiye wannan a ranki Aure tsakanina dashi abinda bazai taɓa yiwa bane." " Amma Safreena ya kamata ki duba maganata kiyi tunani akan rayuwar ɗanki da kuma hanyar da kuka sameshi hakan zaisa ki fahimci gaskiya nake nuna miki." " Zee bani da tunani akan Abdul muddun Baba yana raye na tabbata zai zamo gatansa bazai bari yayi kuka ba a rayuwarsa." Dafe kanta Zee tayi ganin duk yadda taso Safreena ta fahimce ta abun yaci tura, har ga Allah ita tsakaninta da Allah take faɗawa Safreena gaskiya, duk gatan da Baba zai bawa Abdul koda kuwa kullum goyasa zai dinga yi, Wallahi wata rana sai tambayi waye ubansa da Safreena zata gane Garkuwa ya kamata ta aura tun Abdul yana yaro bai san komai ba ya taso a hanunsa hakan zai kauda hankalinsa ga tunanin shiba ɗan sunnah bane amma ta kasa fahimta, hmmm. Zee taja numfashi tare da miƙewa tsaye tana cewa. " Kinsan dai bazaki tabbata a rayuwarki babu Aure ba Safreena muddun kuwa Baba yana numfashi, idan mijin yazo me zaki ce masa kina da ɗan da kika haifa ba tare da aure ba, ko zaki ɓoye masa, ki sani koda kin ɓoye masa Baba bazai ɓoye ba domin kuwa anayin Aure ne bisa turbar gaskiya mai ɗaurewa dole ne a sanar dashi abinda ke faruwa domin samun ingantaccen aure mai ɗaurewa, a yayin da shima Abdul zai bincike ki waye mahaifinsa, domin kuwa akwai wannan ranar zata zota muddun baki ɗauki shawarata ba, kiyi tunanin wacce irin amsa zaki bayar a lokacin da aka miki wannan tambayar."? Tana gama faɗin haka Zee ta fice daga ROOM tabar Safreena tsaye bakinta buɗe cikin nazari duban Abdul dake wasa tayi kyakkyawan yaro son kowa ƙin wanda ya rasa sai dai ƙaddara ta yiwa rayuwarsa mungun tabo shuru tayi tana nazarin maganganun Zee numfashi ta sauƙe ita kaɗai tasan hukuncin da ta yankewa kanta miƙewa tayi itama ta fita tare da ɗaukar Abdul sukayi ROOM ɗin Mama. Ƙarfe biyu dai-dai na rana suka shiga cikin Tulde robon Daddy da garin tabbas ya juma da kallo yake bin garin abubuwa da yawa sun sauya kasancewar ya juma sosai rabonsa da wajen Ya khalil shine ya musu jagora har gidan su Jummo, a ƙofar gida suka samu Baffa yana cikin almajiransa, har abada Baffa bazai taɓa manta fuskar Garba ba, murmushi Baffa yayi tare da musu sannu tabirmar karamno aka kawo musu suka zauna Baffa da kansa ya shiga ya kawo musu ruwa bayan sunsha ne sukayi musabaha cike da mutunta juna, Baffa ne yayi murmushi tare da cewa. " Garba kaine tafe garin namu, lallai anyi shekaru rabon da mu ganka, har mun fidda tsammanin zakazo, sannu ya Mamman take da INNO, da kuma iyalan naka, wannan kamar kalilu, ya jikin Mamman da ita Jummo."? Ɗan murmushi Daddy yayi tare da cewa. " Gaskiya na juma to ya muka iya abubuwa ne suka riƙemu bamu da isasshen lokaci, kuma kasan komai sai Allah ya nufa, Mamma jiki yayi sauƙi har Jummo, Ina Jauro yana nan kuwa da Garbati abokin faɗa, Baffa amma Jummo ƴar Garbati ne ko."? Murmushi Baffa yayi tare da furta. " Hakane komai sai Allah ya nufa amma idan aka saka niyya sai kuma Allah ya dafa, A'a ba ƴar Garbati bane ƴar Jauro ne, Garbati yana nan hayen tsallake shida matar sa da yaransa shi nasa yaran ai duka maza ne su Shida." " Allah Sarki, Masha Allah, to Baffa so muke zamu koma gida da wuri, Kuma munzo wajenka ne da magana mai mahimmanci." " Ayya to ina sauraronku." Nisawa ALHAJI Ahmad yayi tare da sanar da Baffa abinda ke tafe dasu Daddy ya ɗaura da cewa. " Allah yasa zaka bamu Auren Jummo, domin kuwa abun alfahari ne da farin ciki haɗa zuri'a daku idan akayi duba da tarbiyya da ilimin addini da kuke dashi." Nisawa Baffa yayi yana hango tarbiyyar gidan su Momy da shi kansa Daddyn da yake shakku akan tasa tarbiyyar domin kuwa yayi watsi da mahaifiyarsa ya bi mace bai kuma wauwaice ta ba sai Itace ta nemesa Wannan ma babbar illace da zata hana a basu Aure a duba ta mahangar hankali, domin ana Auren mutum ma saboda nasabarsa, nasabar gidan su Momy ta tsubbu ce da suka maidashi SANA'AR da zasu ci su sha da ita, suka ɗauke ta ɗabiar jini da suke gada daga wajen iyayensu duk wanda yake zaune cikin ƙauyen Tulde yasan wannan asirin nasu, wanda suke gina kansu da haram, ga kuma fitsara da rashin kunya da suka ɗauke ta ɗabia, da hukuncin sa zai yanke tabbas bazai basu Aure ba, sai dai Idan ya hango Mamma baiwar Allah sai yaji bai cancanta ya bata kunya ba ta guje jininta saboda kuskuren ɗanta, numfashi ya sauƙe tare da cewa. " Duk da ina da iko akan Jummo amma mahaifinta shine yake da haƙƙin ya bada Auren ƴarsa, da zaku min hkr ku ɗan dakata kaɗan sai na aika ayi kiransa a jeji muji ta bakinsa, amma bazan ɓoye maka ba Garba kaida matarka baku da hali na ƙwarai da za'a ɗauki yarinya a baku, saboda baku kyautawa rayuwarku ba, ka yi watsi da mahaifiyarka wanda a duniya baka da wanda zaka kyautatawa bayan ita ka samu albarka, domin kuwa uwa itace jigon rayuwar ɗa zata iya sadaukar da komai nata na rayuwa domin inganta rayuwar ɗanta ciki kuwa harda bada rayuwarta, a yayin da ko wani ɗa na ƙwarai yake kusantowa kusa da mahaifiyarsa domin samun albarka, kai kuma lokacin kake nisanta kanka da ita taya albarka da zaman lafiya zasu zamo mafakarka bayan ka juyawa wacce zaka samu albarka a wajenta ba, a yanzu kana da damar da zaka gyara kuskuren ka domin kuwa Mamma tana kusa da kai, kana da sauran lokaci har yanzu, ita kuma matarka kowa yasan asalin gidan su a wannan ƙauyen namu ba Mutane na kirki duk da ban sani ba ko ita zainabun Allah ya shiryeta ta gyara halinta." Gabaki ɗayan su shuru sukayi cike da sanyin jiki suna sauraron Baffa yayin da jikin Daddy YAFI na kowa sanyi, idanunsa ne suka cika da hawaye tabbas ya sani gaskiya Baffa yake faɗa, hanu yasa ya share guntun hawayen yana ɗago kansa ya kalli Baffa tare da cewa. " Koda baka bamu Auren Jummo ba, bazanji haushin ka ba Baffa, domin kuwa duk wanda ya sanni yasan abinda ka sani a kaina dole zai gujeni da haɗa zuri'a, na sani ban kyautatawa Mamma ba, tabbas nayi kuskure, amma a yanzu na gane kuskurena tun kafin na taho nan harma na nemi yafiyar Mamma kuma ta yafe min, na sani Allah ya na sona da shirya shiyasa yabar min Mamma har yanzu a raye domin na gyara laifuka na gareta, kuma a shirye nake ga hakan, zamu jiraka aje a kiran jauron." Murmushi mai sauti Baffa yayi tare da furta. " Masha Allah!!! Haka ake so Idan Mutum yayi laifi ya fahimci yayi kuma ya gyara, Allah ya muku albarka." Baffa yayi Maganar yana yana ƙwalawa Junguɗo kira almajirinsa, tare da basa umarnin yaje ya kirawo masa Jauro su taho dashi tare yanzu, da to Junguɗo Ya amsa tare da tafiya aiken Baffa, Ya khalil sosai hankalinsa ya tashi jin yanda babu mai faɗin alkairin iyayensa a cikin rugar musamman momy, numfashi ya sauƙe yana maida kansa ƙasa, basu wani juma ba kuwa Jauro suka taho tare da Junguɗo, cikin mutunci suka gaisa dasu Daddy, Baffa da kansa ya gabatarwa Jauro abinda Garba ke tafe dashi bayan doguwar tattaunawa a ƙarshe dai Jauro ya bawa Daddy Auren Jummo, harma suka saka rana cewa Auren bazai wuce nan da sati Uku ba, Alh Ahmad da kansa ya bawa Baffa sadakin Jummo Naira dubu hamsin 50k tare da sanar dasu cewa insha Allah a cikin satin da za'a shiga zasu aiko da kayan lefe, cikin mutunci da girmamawa suka rabu yayin da kafin Daddy yabar ƙauyen sai da ya bi ya zaga ƴan uwa, kowa sosai yayi mamakin ganin Daddy sai dai ya masu alkairi marar misaltawa har fadar lamiɗo sai da yaje, sannan suka bar ƙauyen, a cikin lokaci kaɗan labarin Auren Jummo da ɗan gidan Garban Mamma ya zagaye ƙauyen kowa yana mata son barka wasu kuwa suna cece kucen mai zaisa Baffa ya yarda ya haɗa iri da gidan su Zainabu, to dama dai shi Aure ya gaji haka duk sanda ya taso sai kaji ƙorafin kowa da mai faɗan alkairi da kuma mai faɗin sharri koma dai me sai dai muce Allah ya sanya alkairi. A can kuwa Birni hankalin Momy yafi na kowa tashi jin da gaske Auren ya tabbata, gashi a yanzu bata da ikon yiwa Jummo asiri saboda tsoron INNO, Zizah kuwa sosai tasa Jummo a gaba da cakala da neman fitina, sai dai ina Jummo bata kulata mahaukaciya take maida ta har tayi ta gama Aunty Zarah kuwa murnar Auren taji domin kuwa hankalin Momy zai bar gareta zata daina takura mata ta maida hankalinta ga Jummo, shi kuwa Ya Garkuwa yayi farin ciki sosai sai dai hankalinsa yana tashi a duk sanda ya tuno cewa Momy bata son Wannan Auren sai dai babu yanda ya iya dole zaici gaba da hkr harta huce, ko Kayan Auren da Daddy yayi umarnin a haɗa Momy kin sauraran zancen tayi sai Aunty Zarah Daddy ya bawa kuɗi ta haɗa babu laifi ta saka mata kaya masa kyau zannuwa guda arba'in ta saka banda dogayen riguna da sleeping dress, kayan makeup turaruka masu tsada duk ta saka, akwati shida ta saya, koda ta kawo kayan Momy dai taƙi koda zuwa ta kallesu domin kuwa ji take tamkar makara suka kawo mata na kaita kabari, haka taƙi ta sanar da ƙawayenta da abokan mutunci zuwa makwafta suzo suga kayan, itama Aunty Zarah gudun fitina yasa bata faɗawa kowa ba, ko gidan su domin kuwa tasan muddun ta kira wani yazo yaga Kayan ta shiga Uku Wajen Momy, Wajen Mamma ta kai kayan sosai suka sawa kayan albarka hatta Jummo sai da aka kirata ta gani tare da ƙawarta Meenat shima Daddy ya shigo yaga kayan kuma ƙwarai ya yabawa siyayyar AUNTY Zarah, koda Daddy yaga kayan bai saurari Momy ba ya sanar da Hajiya Rabi matar abokinsa suzo su kai kayan ita da Zarah haka kuwa akayi washe gari da safe suka kama hanyar Tulde suka kai kayan cikin daraja da mutuntawa, wannan kenan. Yau ta kama ranar asabar babu makaranta Jummo na zaune a harabar gidan cikin fararen kujerun roba tayi shuru, Garkuwa daya shigo da motar sa ne yayi parking ya nufo ta tare da zama a ɗaya daga cikin kujerun yana kallon ta harya zauna bata san ya zauna ba tana tunani, hanunsa ya tafa a fuskarta, da hanzari ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula tana sakin ajiyar zuciya ganin Ya Garkuwa a gabanta, idanu ya zuba mata cike da tuhuma yace. " Zaƙin Zuciyata, tunanin me kike haka.?" Numfashi Jummo ta saki tare da maida hankalin ta ga Ya Garkuwa zuciyarta sam babu daɗi tace. " Ina tunanin rayuwa ne My HeartBeat, Duniyar tana bani tsoro idan na dubi abubuwan da suke cikinta, hmmm!!! Momy bata sona bansan mena mata ba ta tsaneni haka, naso ace Momy ta ɗaukeni tamkar yar da ta haifa a cikin ta, ni kuma na mata biyayya kamar yadda zaka mata, sai dai ina hakan sam bai yiwu ba, taƙi ta sawa Auren mu albarka, meyasa Momy bazata amince da Auren mu ba muyi rayuwa cikin farin ciki, gashi jibi zamu koma Tulde da INNO tace lallai acan zaayi bikin." Shima numfashi Ya Garkuwa ya sauƙe tare da cewa. " Bani da amsar tambayar ki nima Jummo bansan wani dalili yasa Momy ƙinki ba, sai dai na san insha Allah komai yayi farko zaiyi ƙarshe, da yardar Allah ina ji a jikina wata rana Momy zata sauƙo ta soki tamkar yadda take sona ki daina ɗaga hankalinki akan wannan ke dai ki dage da addu'a Allah ya nuna mana ƙarshen wannan masifar, ga can Invitation card an buga, adress ɗin da aka saka can TULDEN ne tunda Baffa yace anan za'a ɗaura Auren, insha Allah gobe da safe zamuje ki buɗe account zan saka miki kuɗaɗen da zaki buƙata, ina ga yau saura 7 days ko, sai dai fa ni babu wani bidia da zanyi su dener su wani party ni duk bazanyi ba, walima kawai za'ayi kin gane." Kanta Jummo ta ɗaga alamun eh, sun ɗan juma suna hira har akayi kiran sallah sannan suka tashi a wajen. Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a juma baaje ba, yau ta kama ranar Alhamis kuma itace ranar da Jummo zata koma Tulde, can harma sun fara hidimar bikin su tun kafin zuwan su Jummo, a yayin da cikin gidan su Ya Garkuwa kuwa babu wani bikin da aka fara domin kuwa babu wanda Momy ta bari yasan ana Aure a cikin gidan, INNO Mamma Jummo sai MeenatSune zasu kama hanyar Tulde, sam Jummo ta manta bata sanar da Safreena Auren nata ba sakamakon abubuwa da suka mata yawa ga kuma Auren sam babu armashi sakamakon rashin sakewar Momy, INNO da kanta ta bawa Jummo umarnin taje tayi sallama da Momy babu musu Jummo ta amsa tare da nufar room ɗin Momy, a rufe yake ta ciki, nocking tayi tare da tsayuwa tana jiran a buɗe ƙofar tafi minti goma tana tsaye kafin Zizah tazo ta buɗe ƙofar turus ta tsaya tana duban Jummo cike da mamakin me kuma ya kawo ta, wani irin kallon banza Zizah ta watsa mata tare da sakin tsaki tace. " Mtsss!!! Ashema shara ce ke nocking ai ni nayi zaton mutane masu amfani ne suka zo, ashe Kuma jikar mayu ce mtss, marar zuciya." Tayi Maganar tana taɓe bakinta tare da cigaba da zubawa Jummo mungun kallo, wani irin zafin maganganun Zizah Jummo tayi, sai dai a wannan lokacin tana buƙatar ta sarrafa zuciyarta saboda Ya Garkuwa, numfashi ta sauke tare da kauda kanta gefe tace. " Naji na gode, Momy nake nema ba keba Zizah kina iya bani waje na shige." Murmushi Zizah ta saki tare da furta. " Heeee!!!! Na!wa!wo! Oh kaji wata banzar Magana a wajen wannan Yarinyar, to sai naga dama kiga Momyn, ko bokanki ne ya baki wani ƙullin ki sawa Momy, to kinyi ƙarya domin kuwa Momy tafi ƙarfin tuggunki kinji ballagaza.!" Runtse idanunta Jummo tayi ranta na mungun ɓace tace. " Ya isheki haka cin zarafin Zizah, da alamu kin rantse sai nayi faɗa dake, naso ace sanda nake jummon ƙauye ce na tabbata da sai nayi maganinki yanda gaba koda sunana aka kira sai kin tsorota, sai dai kinyi matuƙar Sa'a Jummo ta dawo ta ƙwarai ta barwa karnuka irinku faɗa,da zaki kwana dubu kina nemana da faɗa bazan taɓa biye miki muyi ba domin da alama ke jahilar karatun addini ne, dan Allah a koma makaranta ko za'a samu a zamo na ƙwarai, ni kuwa inama ni ina faɗa da karen Tailan karnukan hauka, ki matsa na shige ko ƙarfina yasa na shige." Wani irin munduƙun baƙin ciki Zizah taji, Momy dake tsaye ta harɗe hanunta ne a ƙirji tana sauraron duk maganganun su sosai Momy taji zafin abinda Jummo ta yiwa Zizah a matuƙar hasale Momy ta nufar ƙofar idanunta na rufewa tsabar baƙin ciki, wallahi yau babu abinda zai hana bata yiwa Jummo shegen dukan da babu mai gane fuskarta. *UMMU NASMAH CE* [5/19, 12:33 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *60 to 61* Tas!!! Tas!!! Tas!!! Momy ta ɗauke Jummo da mari har Uku tana nuna mata hanya. " Get out!!! I say get out!!!!" Tayi Maganar cikin tsawa mai firgitarwa, cike da tsoro Jummo ta matsa baya tana riƙe fuskarta da tayi ja, shatin yatsun Momy ya bayyana a fuskar, runtse idanunta Jummo tayi tare da juyawa cike da ƙuncin Zuciya, tsuka Momy taja tare da cewa Zizah. " Meyasa bazaki mata shegen duka ba, ki kwantar min da shegiya a sume, sai ki tsaya kina cacar baki da ita, na tsani wannan Yarinyar ta rusa min duk wani shirina harta tsarin tarbiyya ta cewa take ba dai-dai bane, bana son koda kallon fuskarta ne, abun baƙin ciki wacce na tsana a rayuwata wai itace take shirin zama surukata, tirrr tirrr!! Zan kalli wannan ƙaddara a matsayin baƙar ƙaddara " Numfashi Zizah ta sauƙe tana zama bakin gadon Momy tare da taɓe bakinta tace. " Momy ina ni ina saka hanu jikin wannan ƴar ƙauyen wacce taci tuwo ta ƙoshi ƙarfinmu ma ai bazai zo ɗaya ba, wallahi Momy baki kaini tsanarta ba, tunda ta mallake min room na fara jin tsanarta tazo kuma ta saki a gaba, hmmm!!! MOMY babu faɗan hanu tsakanina da ita amma wallahi Momy ko anyi wannan auren nine zan kashe wannan Auren bazan taɓa bari auren nan yayi lasting ba, da makirci da kirsa wallahi sai na kashe mata aure, naci wannan alwashin kuma sai na cika da, ki kwantar da hankalinki Momy zanyi maganinta dani take zancen." Murmushi Momy tayi tare da cewa. " Idan har kika min haka tabbas zan tabbatar da cewa ke photocopy ɗina ce, zan kuma yi farin ciki, na baki wuƙa da nama Zizah kiyi duk abinda kikaga ya dace." " Ai kuwa Momy zaki tabbatar da ni ɗin harma na zartaki, na fita waje na zauna da mata da maza iri iri dole nafi Jummo wayewa da sanin duniya da wannan zanyi amfani wajen tozarta ta." Murmushi sukayi tare da tafawa, sun juma suna ƙulle ƙulle, ita kuwa Jummo cikin matuƙar sanyin jiki ta koma bedroom ɗin Mamma, a gefen Meenat ta zauna INNO ce ta dubeta tare da cewa. " Lafiya kuwa Jummo kika shigo cikin sanyin jiki, bata saurareki ba ko.?" Ɗan murmushi Jummo tayi cike da ɓoye damuwarta domin kuwa ba ko wani abun ɓacin rai ake sanar da iyaye ba, cewa tayi. " Sanyin jiki kuma INNO, a'a ai kuwa munyi sallama da ita, harma tace a gaishe da Sikayel." Zaro idanunta Mamma da A'illo sukayi tare da cewa. " Ita Zainabun ce tace ki gaishe da Sikayel, ƙarya kike Jummo Zainabu a halin da take ciki yanzu bazata taɓa sauraronki ba, bare kuma har tace ki gaishe da uwarki, duba fuskarki kiga shatin hanu ne fa kuma zan iya rantsewa da cewa Zainabu ce ta mareki." Kau da kanta gefe Jummo tayi tare da miƙewa tsaye tace. " Bara naje na jawo kayana kafin ku ƙarasa haɗa naku." Tana faɗin haka taja hanun meenat suka bar room ɗin, Mamma duban INNO tayi tare da cewa. " Jummo ta sauya sosai, tayi sanyi tamkar ba ita ba, a yanzu sai ka ɗagawa Jummo hanu harma ka saka mata yatsa a baki bazata kulaka ba, tabbas Soyayya tana sauya mutum, tunda gashi Soyayyar Garkuwa yasa Jummo fuskantar rayuwa da sanin haƙuri, na yadda da cewa komai yana iya sauyawa, amma sam bana jin daɗin ƙiyayyar da Zainabu ke gwadawa Jummo, idan ni tana jin zafina ita Jummo menene laifin ta, ina tausayin Jummo domin na tabbata zata sha wahala a wajen Zainabu, tabbas tayi dacen miji na gari amma batayi dacen surka ta gari ba." Ɗan murmushi INNO tayi tare da cewa. " Hakane Mamma, ni kaina nasan Jummo ta sauya, kuma naji daɗin hakan sosai, ki daina damuwa da Zainabu domin kuwa Jummo tana tare da Allah sannan akwai tsari a jikinta wanda asiri bazai taɓa kamata ba, ko kambum baka, insha Allah Jummo zatayi rayuwar farin ciki." Da Allah yasa Mamma ta amsa tare da miƙewa tana cigaba da haɗa kayanta duk zancen da ake A'illo na jinsu ita kanta tana tausayawa Jummo domin kuwa zama da Momy akwai wahala duk da bata da tabbacin inda Jummo zata zauna. Ita kuwa Jummo sun fito falo sukayi kiciɓus da ya khalil murmushi ya saki cike da tsokana tamkar ba suruki ba yace. " A'a kaga amarya wacce bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida, haba tun fitowata nake jiyo ƙamshi ashe amarya ke tafe, Jummon INNO ba, sai haske fa kike duk cikin shirin Auren ne, yanzu Zarah ke sanar dani cewa YANZUN nan zaku tafi, shine kuma bazaki nemeni muyi sallama ba.?" Dariya Jummo tayi tare da cewa. " Ya khalil baka rabuwa da tsokana wallahi, ni na isa na tafi ba tare dana zoba munyi SALLAMA, to yanzu tunda gashi mun haɗu kawai muyi sallamar anan Yayana." Dariya shima Ya khalil yayi yana cewa meenat. "Kinji ƙawarki da wayo zata kare kanta, to naƙi wayon bani hkr tukunna sai muyi sallamar anan." Ɗan murmushi meenat tayi tace. " Nan ma kana da gaskiya Ya khalil, amma dai amana afuwa mun tuba bazamu sake ba." Dariya ya khalil yayi tare da cewa. " Na haƙura saboda ke" yayi Maganar tare da duban Jummo yace. '' ƙanwata tabbas kinyi dacen miji na gari mai addini da sanin darajar mutum, Garko mutum ne mai riƙe amanar dake kansa na tabbata zai riƙeki bisa gaskiya, ki riƙe hkr Jummo ki kuma riƙe sirrin mijinki, ki masa biyayya domin aljannarki yana ƙasan ƙafarsa, Jummo kiyi hkr da halin Momy ki mata biyayya karki riƙeta a zuciya kiyi ƙoƙarin mantawa da ƙiyayyar da take miki, ki nemo Soyayyar ta, na tabbata wata rana zata soki za kuyi wasa harda dariya da ita, Jummo shi fa aure dole yana buƙatar haƙuri domin kuwa wahalar dake cikin sa yafi daɗin sa yawa, zama ne na har abada, dole wata rana za'a saɓa, harshe da haƙori suma suna saɓawa bare kuma mu ƴan adam, a duk sanda saɓani ya shiga tsakaninki da mijinki, karki ɗauki fushi daure ki rarrashi zuciyarki, ki amshi laifin, basa hkr ina tabbatar miki shi da kansa sai yaji kunya, sannan darajar ki a idanunsa bazai taɓa zubewa ba, karki kuskura ki dinga yawan kawo ƙarar mijinki ko na ƴan uwansa domin yawan kai ƙara kan saka a tsani Mutum, ki kula da wadannan Jummo, Sannan munyi waya da baffanki na sanar dashi kar a miki komai na kayan ɗaki, na ɗauki ɗawainiyar ni na miki komai na Kayan ɗaki zuwa kayan kitchen, ina fatan ya sanar dake cewa zamu zauna ne a Oji Quarters anan ya kama haya kafin ya kammala nasa ginin, ina tayaki murna Jummo Allah ya sawa Auren ki albarka." Ya ƙarisa Maganar yana miƙa mata wani ƙaramin anbulat hanu tasa ta karɓa idanunta na ciko da hawayen farin ciki kaf cikin gidan babu mai gwada mata Soyayyar da Ya khalil yake mata a ƴan uwan Ya Garkuwa, yana mata komai tsakaninsa da Allah babu mugunta, sosai taji daɗin nasihar daya mata ga kuma kayan ɗaki daya mata cewa tayi. " Bansan da wani irin baki zan maka godiya Ya khalil, kamin komai a rayuwata, kainee ka kaini makarantar Boko, ka dage sosai Wajen ganin na dawo mutum, gashi yau kamin kayan ɗaki, Ya khalil kamin nasihar da Baba ya kamata yamin, ni kuwa ds wani irin baki zan maka godiya, Uba kake a wajena Ya khalil, kaima Allah ya baka mai rama maka, Allah baka ƴaranka kaima ka gansu a duniya na gode ƙwarai." Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa. " Kul kika sake min godiya abinda zan yiwa Zizah shina miki, babu godiya tsakanin yaya da ƙanwarsa." Murmushi Jummo tayi suka shige room ɗinsu da meenat, koda suka buɗe ambulat ɗin, rafar kuɗi ne ƴan dubu dubu har Naira dubu ɗari da wata ƙaramar takadda, takaddar ta buɗe tare da karanta abinda ke rubuce a jiki. *_Wannan ƙaramar kyauta ce wacce zaki bawa mamana, ƙanwata ki bawa mama su zasu mata Amfani domin kuwa ko wacce Uwa tana buƙatar kuɗi yayin bikin tilon ƴarta MUSSAMAN Auren fari, Allah ya kaiku lafiya sai munzo ɗaure ki da igiyar Aure Uku ƴar ƙaramar ƙanwata._* Dariya Jummo tayi tare da cewa Meenat. " Kinga ko Meenat haka yake nuna min kulawa tamkar ƙanwarsa Zizah, Momy da Zizah ne kawai basa sona, Meenat shiyasa fa nake jure cin mutuncin Momy, duk abinda take min nake haƙuri ina kauda kaina gefe saboda ƴaƴanta guda biyu Ya khalil da Ya Garkuwa, suna matuƙar bani kulawa shiyasa nake kauda kaina daga Momy." Meenat dafata tayi tana murmushi tace. " Tabbas yana da kirki Sosai, ina bayanki ƙawata ki cigaba da yiwa Momy biyayya kina hkr da ita ko dan saboda su Ya Garkuwa insha Allah komai zai wuce." Da Allah yasa Jummo ta amsa tare da ajiye kuɗin cikin jakarta ta jawo suka fito, Jummo duk yanda taso ta hadu da Ya Garkuwa Kafin su tafi hakan bai yiwu ba, saboda tafiya da ta kamasa ya samu kiran gaggawa daga airport ɗinsu zasu kai fasinjar gaggawa zuwa Egypt, hatta numbern sa basa tafiya, haka Jummo suka tafi Tulde ba tare da ta haɗu dashi ba, Momy kuwa barinsu gidan sai ya zamo mata tamkar aljanna gidan ya mata daɗi, sai dai idan ta tuno da dalilin tafiyar tasu sai taji ranta kuma ya ɓaci sai dai ta saka a ranta dole sai Jummo ta rabu da ɗanta koda anyi Auren. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *TULDE* Su Mamma sun isa lafiya, kowa yana maraba dasu, abun mamaki koda aka sauƙi Mamma a ƙofar gidanta babu wannan dangar karan duk an rushe, sabon ginin bulok aka tayar mata na Zamani mai kyau cike da mamaki Mamma take duban wajen, INNO ma da mamaki suke kallon uban ginin da ake tamɓasawa, Drever ne yayi murmushi tare da cewa. " Kunyi mamaki ko? ai Alhaji ne ya saka ayi wannan ginin, bayan anzo neman auren Jummo da yaga gidan shine ya bada kongilar a tada miki da gini dama yace bazai faɗa miki ba har sai kinzo kin gani da kanki.'' Murmushi Jummo tayi cike da farin ciki ko banza tasan Mamma zatayi farin ciki wannan ma samun nasara ce hankalin ɗanta ya dawo gareta, INNO ce tace. " Ikon Allah!!! Alhamdulillah Masha Allah!!! Gaskiya Garba ya kyauta, Allah ya masa albarka." Da ameen Mamma ta amsa cike da matsanancin farin ciki, a zuciyarta tana ayyana cewa bazata koma gidan Garba ba, zatayi zamanta a gidanta muryar INNO taji tana cewa. " To Mamma kin dai ga gidan ki babu wajen zama, dan haka sai mu wuce gidan mu, ki zauna acan kafin a ƙarasa ginin naki, Garba yayi ƙoƙari sosai Allah ya masa albarka ya ƙara arziki." Murmushi Mamma tayi tare da cewa. " Ni kaina naji daɗin wannan gini da Garba ya tayar min, sai naji a zuciyata ɗana ya dawo gareni, bazan taɓa mantawa da Jummo ba a rayuwata domin kuwa komai ya sauya ne ta dalilinta samun Jummo alkairi ne a rayuwata, muje can gidan naki." Gabaki ɗayan su murmushi sukayi cike da farin ciki suka ƙarasa, sosai su Sikayel sukayi maraba da isowarsu komai na murna yayin da gidan ke cike da ƴan uwa ana hidimar biki, Jummo kuwa abun kallo ta dawo musu domin kuwa ta sauya tayi kyau tayi fari fiye da wanda take dashi ga wani kyau da ta ƙara ƙawayenta su Abu tuni sunyi Aure har sun haihu ɗaya, meenat kuwa taji daɗin zuwan ta Cilo domin kuwa taji daɗin yanayin ƙauyen, cike da farin ciki suka kwana biki kuma sai shirya masa ake, Sikayel da kanta ita da ƙanwarta Inna Mero suke haɗa Jummo da kayan mata na gargajiya, cikin kwana Uku da zuwan su Jummo ana gobe ɗaurin Aure, Jummo harta ƙara sauyawa fatarta tayi kyau har sheƙii take sai dai Jummo hankalinta yana tashe da rashin kiranta da Ya Garkuwa baiyi ba tunda tazo gashi idan ta gwada layinsa baya tafi, zama tayi jikin ceɗiyar dake tsakar gidan nasu tayi shuru, meenat ce ta zauna a gefen ta tare da dubanta tace. " Jummo na fuskanci jiya da yau kamar kina Cikin matsala meke damunki."? Numfashi Jummo ta sauƙe tare da ɗago kanta ta kalli meenat cike da sanyin murya tace. " Ya Garkuwa nake tunani, Meenat tunda na taho garin nan bai kirani ba, ban kuma ga saƙonsa ba, hankalina ya tashi anya kuwa Ya Garkuwa yana lafiya, nasan bazai kwana har Uku a Egypt ba tunda yasan yana da hidimar bikin sa, na kuma san indan yana halin lafiya dole zai nemeni, meenat ya Garkuwa baya lafiya.?" Murmushi meenat tayi tare da cewa. " Mrs love manyan gari, yanzu duk wannan tada hankalin da kikayi saboda wannan dalilin ne, wa ya ce miki Garkuwa baya halin lafiya, ki sani fa tafiya yayi kuma idan ta kama yayi sati ne dole haka zaiyi babu yanda ya iya saboda akan aikinsa yake, ki daina kawo mummunan tunani cikin ranki dan Allah, Garkuwa babu abinda ya samesa, ki kira Ya khalil muji." Shuru Jummo tayi ba tare da ta cewa meenat komai ba ta jawo wayarta numbern Ya khalil ta dannawa kira. Ya khalil dake zaune gefen ya Garkuwa ne ya dubesa tare da cewa. " Kai ɗan iskan ango, ga amaryar ka na kira fa." Dariya dukkan su suka saka, Ya Garkuwa ne yace. " Hmmm!!! Ɗaga kaji me zatace." Ɗagawa Ya khalil yayi ya danna handsfree, tare da sallama bayan ta amsa ne cike da zolaya yace. " Amaryar mu bakya laifi, to ya shirye shiryen biki."? Jummo haɗa rai tayi tamkar yana kallon ta muryar ta kamar Zatayi kuka tace. " Ya khalil, yanzu fisabilillahi abinda kikayi kun kyauta kenan, na tafi har nayi kwana biyu babu wanda ya nemeni, Ya Garkuwa kuma idan na nemi layinsa baya tafiya, Ya khalil anya kuwa Ya Garkuwa yana halin lafiya dan Allah kaje airport ɗinsu ka dubo mana, ko lafiya hankalina yana tashe, nasan bazai yadda yayi kwana uku Egypt ba tunda yasan yana da uzuri." Dariya ce taso ƙwacewa Garkuwa jin yanda take Magana cikin rawar murya da alamu dai ta kusa danna kuka, kafin Ya khalil yayi magana ya Garkuwa ya ƙwace wayar yana cewa. " Ranki shi daɗe gimbiya sarautar Mata farar mace alkebbar mata, fariin cikin Garkuwa, kuma hasken rayuwarsa." Wani irin wawan ajiyar zuciya Jummo ta sauƙe jin muryar Garkuwa ya doki kunnen ta, idanunta ta lumshe sanyi na ratsa zuciyarta kusan minti biyu tayi shuru har sai da ta kuma jin muryar sa yace. " My love!!! Fushi kike dani ne kikaƙi Magana, sorry pls kimin Magana kinji haskena."? Ɗan baki ta tura gami da cewa. " Dama kana gari shine kaƙi nemana ko, duk ka ɗaga min hankali ina ta tunanin ko wani abu ne ya sameka." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Sorry my love nayi laifi naƙi kiranki ne ina sane saboda naga yawan damuwa dani da kikayi, kuma na gani domin naji hankalinki a tashe hakan ya daɗa nuna min ƙarfin Soyayyar da kike min, kiyi haƙuri kinji farin ciki na, gobe insha Allah tara na safe muna garin ku, ina Hajiya INNO da Mamma."? Murmushi Jummo tayi tare da lumshe idanunta tace. " Baka yadda da soyayyata bane yasa ka gwada ni, ina tsammanin baka san cewa zan iya rasa rayuwata ba a kanka, ya Garkuwa kaifa numfashi nane taya rayuwa zata kasance babu numfashi, kasan mutuwa ce zata biyo baya, dan Allah ka daina min irin wannan gwajin kar wata rana ka tafi da numfashi na, ina sonka fiye da komai a rayuwata, ka yadda da soyayyata." Cike da jin daɗi marar misaltuwa Ya Garkuwa ya ce. " Insha Allah bazan kuma ba farin ciki na, Jummo ina sonki fiye da komai nawa, na gwadaki ne badan ban yarda da soyayyar kiba na gwada ki ne saboda na kuma ganin nauyin ta, kuma a yanzu na fahimta, ina sonki Jummo Rayuwa zata min daɗi idan kina kusa dani, rashinki kusa dani kuwa Rayuwar wahala zata mini, dan Allah ki kasance dani har ƙarshen numfashi na, komai wuya kuma komai rintsi, karki juya min baya ki kasance mai mini uzuri a rayuwata dake hakan zai bani ƙwarin gwiwwa wajen riƙeki ina sonki Jummo." Murmushi mai haɗe da dariya Jummo tayi tare da cewa. " Babu abinda zai rabamu da kai komai muninsa muddun ba saɓon Ubangiji kake ba, zanyi hkrn zama da kai ina sonka uzuri ya Zamo min dole a gareka" Ya khalil ne ya ƙwace wayar tare da cewa. " To marar sa kunya masu zance a gaban suruki ba'kunya." Dariya Jummo tayi tare da cewa. " Kai Ya khalil kai ɗinne suruki, ni kam ba ɗauke ka haka ba yaya na ɗauke ka, shi kuma Ya Garkuwa Aboki ya ɗauke ka ko a kwai laifi idan ƙanwa tayi waya da masoyinta kusa da yayanta kamar dai yadda babu laifi Aboki yayi waya a gaban abokinsa." Ta ƙarisa zancen tana dariya tare da kashe wayar tana duban meenat tace. " Ya Garkuwa yana lafiya kinji wai gwadani yayi yaga ko zan nemesa." Meenat dariya tayi tare da cewa. " A to ba na faɗa miki ba, naji ai duk abinda kukayi, ni ki tashi muje wajen Sikayel kinsan tun ɗazu take neman ki." Miƙewa Jummo tayi tana tura baki tace. " Ni wallahi na fara gajiya da wannan ɗan iskan maganin matan da ake famar ɗura min, akwai wani ma mai shegen bauri." Ɗan dariya meenat tayi tare da cewa. " Ai kuwa dole kisha, domin dai gata ake miki." Jummo tana mita suka tafi wajen Sikayel ɗin. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Washe gari ta kama ranar ɗaurin Auren Jummo da Garkuwa, gidan sosai yake cike da mutane domin kuwa ƙauyen suna da al'ada Sosai, har wasan dandali sai da sukayi, Zugar su Ya Garkuwa kuwa basu iso ba sai ƙarfe goma na safe mota uku suka zo duka maza sai Aunty Zuwaira da Aunty Zarah sune kawai mata, suma anzo dasu ne saboda ana ɗaura Auren zasu tafi tare da Jummo, abokanan Ya Garkuwa sunzo da yawa haka Daddy ma da nasa abokan a gidan mai gari aka musu masauƙi cike da girmamawa, koda ƴan gidan su Momy sukaji labari sai da sukaje gidan su Jummo gulma, a lokacin da sukaje Ya Garkuwa bai samu yaga Jummo ba domin kuwa al'adar ƙauyen ne da zarar ranar ɗaurin Aure ne to fa ango bazai ga amarya ba har sai an Kaita ɗakinsa, dole tasa ya Garkuwa ya hkr badan yaso ba, a masallacin juma'a dake unguwar aka ɗaura Auren nasu akan sadaki dubu hamsin, aka shafa fatiha kowa ya tashi sai fatar Allah ya basu zaman lafiya. "Inna sogiji ce ta shigo gidan da guɗa tana cewa. " Ayyiriri!!!! Ayyiriri!!! Ayyiriri!!! Aure ya ɗauru!!" Wannan guɗar itace ta tabbatar wa da kowa dake gidan cewa har an ɗaura Auren, meenat dariya tasa cike da farin ciki tana taya ƙawar tata Murna ita da A'illo tace.......... *UMMU NASMAH CE*[5/22, 11:15 AM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *62 to 63* " Alhamdulillah!!! Masha Allah!!! Ƙawata kiyi sujjada ki godewa Allah domin kuwa ya cika miki burinki, mafarkinki ya tabbata, koni yau ina cikin farin ciki domin kuwa burin ƙawata ya cika Jummo Allah ya baki zaman lafiya a gidan mijinki ya kore fitina tsakaninku zaman lafiya jin daɗi ya tabbata gareku har ƙarshen rayuwarku, ina miki fatan alheri da murnar shiga sabuwar Rayuwa." Murmushi Jummo tayi idanunta ya ciko da hawayen farin ciki, idanunta ta sauƙar ƙasa tare da kama hanun A'illo ta fara magana cike da nutsuwa. " Duk inda zan shiga tare dake zan shiga A'illo, bazan bari ki zauna a ƙauye da Mamma ba, dole zaki koma cikin gari mu CIGABA da karatun mu, insha Allah kema haske zai shigo rayuwarki na sani A'illo kinso ya Garkuwa kin danne sonsa ne kawai saboda ni kika manta dashi a rayuwarki na yabawa ƙoƙarin ki, Kuma insha Allah bazaki taɓe ba, tabbas jajurcewa da haƙiƙancewa gami da zuciya ɗaya yakan kawo gagarumar nasara a rayuwa, waɗannan jajurcewan sune suka kawo ni matakin nasarar cikar burina, alhamdulillah!!! Allah abin godiya!!! Allah na gode maka daka mallaka min Ya Garkuwa a matsayin inuwata, Allah ka dawwamar dani a gidan mijina ka kore shaiɗan tare da saɓani gare mu." Da ameen Meenat da A'illo suka amsa cike da farin ciki, can kuwa su Ya khalil bayan an gama ɗaurin Auren ne suka shigo cikin gidan, yayin da ƴan mata ke famar nuna Ya Garkuwa suna ga nan angon shi kuwa sosai yayi kyau a cikin farar shaddar sa wacce tasha aikin blue ɗin zare hular kansa ma kawai abun kallo ne, Shetima da Khabeer har jabeer shi kansa ya khalil da abokansa uku, duk tare suka shigo, har bukkar Sikayel suka shiga tare da gaishe ta, cike da ladabi, daga nan bukkar INNO sukayi inda sukayi tunanin anan zasu ga su Jummo sai dai wayam babu ita babu alamunta kusa da Mamma Ya Garkuwa ya zauna duk da bukkar cike take da mutane hakan bai hanasa raɗawa Mamma magana a kunne ba. "Mamma ina Jummo take, ina buƙatar ganinta, dan Allah taimaka min." Dariya Mamma tasa tana murɗe kunnen sa da ƙarfi inda hankalin mutane ya dawo garesu tace. " Kunga ja'iri marar kunya, wai matar yake son gani sai kace ba gidansa za'a kaita ba, yau naga yaran zamani, mufa zamanin mu bama ganin miji har sai an kaimu kafin musan wanda muka Aure, to nan ƙauyen bama haka daga kai har waɗannan ƴan koran naka babu mai ganinta har sai an kai ta ɗakinka sai wani tsilli tsilli kake min da idanu yiwa ɓarawo." Ya khalil ne yayi carap yace. " A'a dakata tsohuwa kar kuma ki zagemu mana ga duka ga kuma tsinka jaka mutum da matarsa a hanasa ganinta sannan kuma a haɗa da baƙar Magana, to ki tsaya iyaka haka tsohuwa, har wani lissafi kike mana da zamaninku, to mu ina ruwanmu da zamaninku naku dabam namu dabam, mu mun shige wannan ƙauyancin rayuwa muke cikin wayewa da fahimtar juna." Mamma filo ta ɗauko tare da jefawa Ya khalil tana cewa. " Allah ya wadaran Wannan wayewar taku ta rashin kunya, to dan ubanka ko kaima yau sai na hanaka ganin wannan kodaɗɗiyar" Tayi Maganar tana nuna Aunty Zarah da hanu, dariya Ya khalil yasa tare da cewa. " Wannan ne kuma baki isa ba, sai dai juyi gadara da ta rugar wacce zata raga muku amma badai ta gari ba domin kuwa idanunta a buɗe yake tar, idan kuwa kin musa yanzu zaki ganta a jikina musa kiga ikon Allah." Yayi Maganar yana kashewa Mamma Ido ɗaya, mit bakin Mamma yayi shuru domin kuwa tasan Khalil zai aikata abinda ya faɗa tunda ba kunya garesa ba rayuwarsa yake simple, harara ta jefa masa tare da cewa Garkuwa. " Kai Garko, yaushe ne zaku tafi saboda zan kaiku Wajen kakan Yarinyar kuyi sallama." "Mamma ai bazamu juma ba ƙarfe huɗu Daddy yace zamu juya shima yana shigowa da zarar ya shigo aka gaisa zamu wuce, mu bara mu fita." Yayi Maganar yana miƙewa suma su Ya khalil miƙewa sukayi. Da to Mamma ta amsa kafin suka fice Ya khalil na tsokanar Mamma bata kulasa ba, ko da suka fito tsakar gidan sanda ya ɗan dudduba ko Meenat ya samu ya gani bai ganta ba, ga ya kira wayoyinsu a kashe duk baya tafiya haka dole ya fita ba dan ransa yaso ba. Ƙarfe Uku da rabi Daddy ya shigo cikin gidan, sosai suka gaisa da mutane kafin ya koma Wajen Baffa ba'a juma ba kuwa sai ga khalil da Garkuwa sunzo suka zauna Baffa sawa yayi a sanar da Mamma da Sikayel har INNO su fito da Jummo, haka kuwa akayi suka taho a gefe suka zauna, Baffa ne ya dubi Jummo tare da gyaran murya ya fara magana cike da nutsuwa. " Alhamdulillah!!! Jummo yau dai nauyi ya ɗauru a kanki, domin kuwa kin samu wata daraja wanda a baya baki dashi darajar kuwa itace Aure, duk ƙanƙantar Mutum idan yana da Aure dole za'a mutuntashi, domin kuwa yafi babba wanda ya girmesa daraja idan har shi babban bashi da Aure, Jummo ina son ki saurareni da kunnen basira domin kuwa zan zayyano miki haƙƙin daya rataya a wuyanki Wanda kuma wajibine gareki ki bisu, Jummo, Ga nan mijinki a yanzu shine aljannarki sai kin bisa sannan zaki shiga aljanna, a yanzu ya fimu iko dake dan haka ya zamo dole a gareki ki masa biyayya ki bisa sau da ƙafa duk abinda yace kiyi, ki masa karkiyi musu muddun ba saɓon Ubangiji bane, haƙƙine a kanki ki basa kulawa, ki kuma kula da shimfidar sa, domin itace sunnar Aure, tsafta Jummo karkiyi wasa dashi domin ita tsafta cikon addini ne sannan tana sawa miji ya ƙara son matarsa, ladabi biyayya wajibine a gareki ki yiwa mijinki, ki kula da abincinsa domin kuwa ko wani namiji yana son ace matarsa ta ƙware a wajen girki hakan na faranta ran miji sai Uwa uba haƙuri dole ki kasance mace mai hkr domin kuwa Aure yana tafe ne tare da ƙalubale dole ne duk yanda ake zaman lafiya wata rana a saɓa, ɗacin dake cikin aure yafi zaƙinsa yawa dan haka dole sai kinsa hkr, Banda yawan kai ƙara na dangin mijinki ko na wani hakan na sawa miji ya tsani matarsa, sannan Jummo iyayen mijinki ki kula dasu ki musu biyayya tamkar yadda zaki yima mu iyayenki domin kuwa yanzu baki da iyayen da suka wuce ki, ki kula da haƙƙin maƙwaftaka da kuma mu'amala da mutane mu'amalar ki ya kasance mai kyauce, babu ruwanki da gulma ko gutsiri tsomen ƙawaye karki yadda wata ƙawa ta kaiki ta baro ki ta hanyar miki mummunan huɗuba, ki kula Allah ya baki zaman lafiya keda mijinki ya albarkaci Auren ku ya baku zuri'a ta gari wannan shine nasiha ta gareki." Shuru Jummo tayi kanta na ƙasa idanunta na zubar da hawaye a hankali cikin rawar murya tace. " Naji Baffa kuma insha Allah zanyi amfani da dukkan nasihar ka gareni na gode sosai da tarbiyyar da kuka bani har zuwa aurena ina alfahari daku Baffa." Murmushi Baffa yayi yana kallon INNO da Jauro da kuma Garbati yace. " Gareku idan da akwai mai mata nasiha a cikin ku ni na gama nawa." INNO ce tayi gyaran murya tare da cewa. " Duk abinda zamu faɗa ka wakilce mu ka faɗesa, mu babu abinda zamu ce sai fatan Allah ya albarkaci Auren." Suma su Sikayel abinda INNO tace suka ce, Baffa ne ya dubi Garkuwa tare da cewa. " Na dawo gareka Garkuwa, haƙƙine a gareka ka kula da Rayuwar Jummo da kuma dukkan wasu buƙatunta, ka sani idan ka cuceta ko kaci amanarta Allah bazai barka ba, Jummo amana ce a wajenka a Yanzu bata makusanci ko abokin da ya wuce ka, dan Allah ka kula da amanar ta, idan ta maka ba dai-dai ba ka sanar da ita kuskuren ta, ko ka tsawatar mata, idan bata gyara, ganan mahaifinka a yanzu shine mahaifinta ka sanar dashi na tabbatar da zai tsawatar mata Allah ya muku albarka." Da ameen Ya Garkuwa ya amsa tare da cewa. " Insha Allah Baffa bazan baka kunya ba, zan riƙe Jummo bisa gaskiya da amana farin ciki shine zai wanzu a rayuwarta na gode sosai Baffa da kyauta da kuka bani." Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa. " Baffa bani da bakin da zan maka godiya domin kuwa kunmin abubuwan alheri da yawa a rayuwata kun kula min da mahaifiyata gashi kuma kun ƙara bamu kyautar yarinya na gode sosai ina kuma tabbatar maka da cewa ƴarka bazata taɓa kuka ko baƙin ciki ba, zan zamo mata gata kuma kariya a gareta muddun ina numfashi babu wanda zan bari ya cutar da ita ciki harda mijinta, mun gode mu zamu wuce." Cike da farin ciki Baffa da su Kawu Garbati sukaji daɗin Maganar Daddy, Mamma da INNO ciki suka koma da Jummo sannan suka shiryata bukkar Sikayel mahaifiyarta ta shiga sukayi SALLAMA Sikayel ta juma tana yiwa Jummo nasiha kafin ta fito, Yaya Marka da Goggo Adda sai kuma ƙawar Jummo ta da wato Sadiya, sune suka raka Jummo, Jummo sosai tayi kuka na rabuwa da Mamma da INNO, kowa na kewar kowa, mota guda aka bawa su yaya Marka da amarya, ƙarfe huɗu da rabi suka bar cikin Tulde suka nufo cikin Gombe, sanda suka iso cikin garin motocin rabuwa sukayi biyu tasu Daddy tayi gabar yayin da tasu Jummo tayi yamma, hakan shine ya tabbatarwa da meenat cewa Jummo gidanta za'a shige da ita ba gidan momy ba, sosai abun ya ɗaurewa meenat kai, a mahanga ta hankali kamata yayi akai Jummo wajen Momy ta mata faɗa tare da saka musu albarka sai kuma baayi hakan ba, lallai akwai zargi cikin naɗi tabbas akwai abinda yake faruwa, numfashi Meenat ta sauƙe tare da kallon window ɗin motar, ana kiran la'asar suna shiga cikin babban estate ɗin wanda ya tara manyan gidaje, wani haɗaɗɗen part suka shiga tare da yin parking kowa ya fito, Ya Garkuwa Aunty Zarah ya miƙawa kay ɗin gidan tare da cewa. " Gashi Aunty Zarah ki buɗe ku shiga, za kiga bedroom mai kallon kudu shine na Jummo bari muje muyi sallah mu dawo." Hanu meenat tasa ta karɓa tare da yin gaba ta buɗe ƙofae dukkan su shiga sukayi su kuma suka shige masallaci,koda suka shiga cikin falon sosai yayi kyau ya ƙawatu da adon pink da fari haka kujerun ta suma pink ne da fari labule ma haka komai yayi kyau musamman kitchen yanda yasha jere, Aunty Zarah Sosai abin ya bata mamaki kasancewar iyayen Jummo ƙauyawa ne,ta ina zasu iya saya mata wannan kayan a zuciyarta ta ayyana ko Daddy ne ya saya mata, domin kuwa bata san Ya khalil ne ya saya mata ba bai faɗa mata ba, bedroom ɗin Jummo suka shiga tare da yada zango wasu kuma suka zauna a falo, Jummo tollet ta shiga ta ɗauro alwala tare da tayar da sallar magaruba, duk har sukayi sallah su ya Garkuwa basu dawo ba, kusan sallar isha'i aka shigo da kulolin abincr wanda akayi a gidan daddyn meenal abokin Daddy bayan sunyi Sallah ne sukaci abincin wanda ita dai Jummo gagara ci tayi da ƙyar ta taɓa kaɗan nan ma sanda Inna Marka tA sata a gaba tukunna taci, su Aunty Zarah Takwas da rabi suka bar gidan ita da matar abokin Daddy, sai ya rage daga meenat sai su Inna Marka, sai wajen tara na dare Ya Garkuwa da Shetima suka shigo, Inna Marka suka samu a falon sannu suka mata tare da ajiye mata leda mai ɗauke da gasassun kaji da nono mai sanyi, suka gaisheta sannan suka shige bedroom ɗin Jummo suna zaune da meenat, ya zauna a gefen gadon yana cewa. " Amaryata tun ɗazu nake son ganinki kamar kuɗi amma an hanani, ɗago min fuskar na gani farin ciki na." Ɗan murmushi Jummo tayi tare da ɗago kanta suka haɗa ido lumshe idanunsa ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Tsarki ya tabbata ga ubangin da ya hallice wannan kyakkwawar halittar, kinyi kyau sosai, na kwana biyu ban jiki ba, sai naji kamar shekara nayi ba ganki ba, Mamma ɗazu haramta min ganinki tayi, da fatan komai ya tafi dai-dai ko." Murmushi Jummo tayi tare da ɗaga masa kai alamun eh dubanta ta kai ga Meenat da kwatakwata hankalinsu baya kansu zancen su kawai suke, tace. " Dear nayi kewar ka, sosai fa ba kaɗan ba, kaga yanda ka ƙara kyau kuwa, sai ka dawo tamkar balaraben Saudiyya." Dariya Ya Garkuwa yayi yana ɗan taɓe bakinsa yace. " No ban kaiki kyau ba, saboda kyawun ki ya dusashe nawa, kyanki fa na musamman ne, amma na shigo ne na duba ki hankalina ya kwanta, kar Inna Marka taji haushina bari muje sai da safe. " To shikenan, ka tabbatar kaci abinci kafin ka kwanta bana son ka kwana da yunwa." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Ko banci abinci ba, iya kallonki kawai da nayi ya ƙosar dani, kiyi bacci mai daɗi." Duban Shetima yayi yace. " Kai zancen ya isa haka tashi mu tafi kasa ƴar mutane gaba da zance." Dariya Shetima yayi tare da cewa. " Wa yace maka zuba kawai nake, soyayyata nake gyarawa Malam tunda kai taka ta gama gyaruwa ɗinyarka ta nuna a hanunka." Dariya Jummo da Ya Garkuwa sukayi Ya Garkuwa cike da tsokana ya cewa meenat. " To fa, ashe cinikin harya faɗa bamu sani ba Meenat to Allah ya sanya alkairi." Yayi Maganar yana dariya tare da ficewa, shima Shetima bayansa yabi, Jummo dariya tayi tace. " Hmmm!!! Da alama dai Shetima ne zai kasa samarinki.?" " Kai Jummo shegen gulma, gaskiya yamin ina jin zan iya rayuwa dashi." " Hakamma yayi Shetima bashi da matsala." Sun juma suna tattaunawa akan Shetima kafin suka kwanta. Washe gari da safe still dai daga gidan abokin Daddy aka kawo musu breakfast, Ya Garkuwa bai shigo ba sai kiranta kawai yayi, sai la'asar lis ya zoshi kasancewar zai mai dasu Inna Marka gida, koda Inna Marka zata tafi sosai Jummo tayi kuka sai dai babu yanda ta iya dole tasa ta haƙura, Ya Garkuwa koda suka ɗauki su Inna Marka shida Shetima gidan Momy suka wuce dasu, a falo ya ajiye su tare da haurawa bedroom ɗinta, gefenta ya zauna, kauda kanta Momy tayi ganin Garkuwa ya shigo domin kuwa sosai take jin zafinsa, cike da sanyi jiki ya kira sunanta, ƙin amsawa Momy tayi kusan sau Uku ya kirata kafin ta ɗago idanunta tana jefa masa mungun kallo cikin tsawa tace. " Kiran uban me kake min me zaka bani, me ruwanka dani me zai kawoka wajena, ni yanzu ba uwarka bace domin kuwa baka ɗaukeni matsayin Uwa ba!!! Tashi ka fice min daga room karna kuma ganinka gabana!!!" Kansa ya sunkuyar ƙasa ransa a mungun ɓace hankalinsa na matuƙar tashe yace. " Kiyi hkr Momy bani da wata Uwar da ta fiki a duniya, Momy komai ya faru ne bisa ƙaddara babu ta yadda kowa zai kaucewa tasa ƙaddarar ni son Jummo shine tawa ƙaddarar, Kiyi dan Allah ki fita ku gaisa da Inna Marka ƙanwar.........." Tsawa Momy ta daka masa. " Ƙanwar Uwarka Sikayel ba!!! Haka zakace, na san Marka kaje ka ce mata bazan fito ba, ta riƙe gaisuwarta bana buƙata na baku nan da minti goma kubar min ROOM ɗina ko kuma wallahi na fito na durun uwarku daga kai har Markan cin mutunci zan mata na shan gishiri, fita kabar min room ɗan iska wanda baisan darajar uwarsa ba." Runtse idanunsa ya Garkuwa yayi idanunsa na cikowa da hawaye ya ce. " Momy dan Allah kiyi hkr ki taimakeni ki kankaro min mutuncina ki fita ku gaisa dan Allah Momy ki........." " Ko zaka mutu kana min magiya, WALLAHI bazanje ba, ni sanda nake baka umarni na ke roƙonka ka haƙura da wannan Auren ka min biyayya ne, sai ni zan maka, ka tashi ka fita ko na maka baki kabi duniya ka lalace." Miƙewa Ya Garkuwa yayi cikin sanyin jiki, ya fito Ya khalil ya gani tsaye duk abinda suke yana jinsu kafaɗar Garkuwa ya dafa tare da girgiza masa kai alamun kar ya bari hawayen su zuba, tare suka sauƙa ƙasa Ya khalil ne ya yiwa su Inna Marka ƙaryar cewa ai Momy ta je asibiti ganin likita tare da basu haƙuri,. Su Inna Marka basu kawo komai a ransu ba, suka tashi tare cewa a gaishe ta ace sunzo su danƙa mata amanar Jummo basu sameta ba, Ya khalil dubu hamsin ya basu, shima ya Garkuwa ya basa 100k drever ne ya ɗauke su suka kama hanyar Tulde, shi kuwa Ya Garkuwa cike da baƙin ciki ya fashe da kuka tare da kwantar da kansa jikin Ya khalil....... *UMMU NASMAH CE* [5/23, 9:34 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *64 to 65* Shuru ya khalil yayi cike da tausayin Garko, ya rasa wace irin zuciya ce da Momy da bata yafiya, numfashi ya sauƙe tare da cewa. " Dole fa sai kayi haƙuri Garko, kasan halin Momy dole sai ka mata uzuri uwace babu yanda ka iya da ita hkr dai shine zakayi ka kuma dage da addu'a insha Allah komai zai shige, matsalar dana hango kenan yasa na roƙi Daddy cewa kar a kawo Jummo gidan nan a shige kawai da ita gidan su gudun kar Momy ta jawo mana abun kunya, da ka shawarce ni ma, da bazan barka ka kawo su Inna marka gidan nan ba, hmmm!!! Kayi hkr muna nan muna addu'ar Allah ya shiryi Momy ta gane annabi ya faku." Guntun hawayen dake fuskarsa ya Garkuwa ya goge tare da cewa. " Na sani Bro kai ma kuma ka sani ina hkr da Momy amma a yanzu na fara tunzura wani irin ƙiyayyane haka abun yana min ɗaci a zuciyata yanda Momy take gwada min ƙiyayya ni da matata, ka duba kaga abincin da za'a kai min gidana a bawa baƙi, Momy cewa tayi idan an kai daga gidan Ubana Allah ya isa bata yafe ba, sai gidan abokin Daddy ne aka kai, wannan wacce irin masifa ce." " Hmmm!!! Da alamu bazaka iya yin haƙurin da nayi ba, saboda kafin Momy ta nuna muku ƙiyayya matata ta nunawa, ina ga sai a cikin kwana biyun nan ne Zarah take samun sassauci daga wajen Momy har naga suna hira, meye ya kawo wannan nasarar da Momy take sauraran Zarah yanzu haƙuri da juriya, kai ma ita zakayi ka cinye jarabawarka, ni yanzu Maganar da nake maka, na samu transfer ɗin aiki zuwa Abuja, ranar monday zamu tafi ni da Zarah, za'a barwa Momy gidan ita kaɗai kamar yadda take so sai hankalinta ya kwanta domin abinda na fuskanta zama da wani ne bata so, Mamma dai ba dawowa zatayi ba kaga daga ita sai Zizah sai suyi abinda suka ga dama. " hmmm!!! Shikenan Bro Allah ya bani ikon cinye jarabawa ta, am Anya kuwa Momy zata yarda ka tafi Aunty Zarah gani nayi itace ta hanaka sauya gida bana tunanin zata yarda." Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa. " Ta ma yarda ai an gama, domin kuwa munyi Magana da ita tace ba damuwa muje." " Okay Allah ya kaimu." . Yayi Maganar yana sauƙe numfashi, sun juma suna hira har akayi sallar magaruba, bayan sun idar ma zama sukayi sanda akayi isha'i kafin suka rabu Shetima da Khabeer suka zo suka ɗauki Ya Garkuwa zasu masa rakiyar ɗaki sanda ya tsaya a hanya suka sayi gasasshiyar kaza da fresh milk sannan suka tafi Shetima na famar tsiya yake masa. "Kee!!! Wai mijin naki bazai dawo bane kam, ni fa na fara gajiya 9:30 har yanzu ango bai shigo ɗakin Amaryar sa ba, bana son dare yamin banje gida ba, kinsan na cewa Abba yau zan dawo bana son yamin faɗa, yawwa wai nikam anya kuwa kin sanar da ƙawarki bikinki Safreena maman Abdul." Da sauri Jummo ta ɗago kanta tare da dafe goshinta ta ɗauki salati " Ya Allah!!! Kai wallahi bani da kirki ko jiya ma naga miss Call ɗinta wallahi ban sanar da ita ba, kwana nan bani da sukuni shiyasa na manta da ita itama kuma bawai kirana take ba sai afi sati biyu bata kira ba sai randa taga dama zata kira amma dai koma menene dai ya kamata na sanar da ita bikina, insha Allah gobe da safe zan kirata yanzu dare Ya fara." " Gaskiya ya kamata ki faɗa mata, tana sonki kuma da alamu ita irin matan nan ne wanda basu damu da shiga Rayuwar mutane sosai ba, kuma kina kallon idanunta zaki fahimci tana tare da wani ɓoyayyen lamari amma........" Sallamar su Ya Garkuwa itace ta kana meenat ƙarisa Maganar da tayi niyya, amsawa tayi suka ƙaraso a bakin gado ya zauna su Shetima na tsaye cike da tsokana Meenat tace. " Au ashe dai zakazo ai nayi zaton sai gobe ne zaka shigo, tunda Gashi dai dare harya tsula." Dariya khabeer yasa tare da ɗaurawa da cewa. " Shi wannan uban zumuɗin ne zai iya bari sai gobe, ai kuwa ya dinga sambatu kafin gari ya waye domin ba haƙuri garesa ba." Dariya Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Kuyi sauri ku gama Maganar ku tafi, ko kuma na koreku na rufe gidana." Zaro idanunta Meenat tayi tare da cewa. " Eyyye!!! To ku tashi mu rufawa kanmu asiri mu tafi kafin ya koremu, ni dai ga AMANAR ƙawata na baka dan Allah a riƙe Amana Allah ya baku zaman lafiya." Da ameen Dukkan su suka amsa ita dai Jummo kanta na ƙasa, suma su Shetima Sosai suka yiwa Garkuwa nasiha irin na abokai kafin ya rakasu suka tafi, ya bawa mai gadi UMARNIN ya rufe gidan ya juya zuwa ciki. Kusa da ita ya zauna tare da saka hanunsa ya kamo hanunta, da ɗayan hanun ya ɗaga hijabin da ta ruhu dashi, yana murmushi yace. " Alhamdulillah godiya ta tabbata ga ubangin daya bani ke a matsayin mata, ina farin cikin Kasancewa dake waje ɗaya Jummo Allah ya bani ikon riƙe amanarki, ina cikin farin ciki yau." Murmushi Jummo tayi itama ba tare da tace komai ba haka kawai yanzu kuma take jin kunyar Ya Garkuwa, murmushi yayi ganin bata da niyyar Magana yace. " Dear yau kuma kunyata kikeji hmmm!!! To tashi muje muyi alwala muyi Sallah mu godewa Ubangijin mu." Da to Jummo ta amsa tana miƙewa tsaye, ta nufi tollet yana nan zaune tayi alwala ta fito, shima shiga yayi yayi tasa alwalar sukayi nafila raka'a biyu, bayan sun idar ne ya kama goshinta yayi mata addu'o'i sosai, Ya Garkuwa sosai ya yiwa Jummo tambayoyi game da addinin ta, yasha mamakin yanda ta amsa masa dukkan tambayarsa, tashi yayi tare da ɗauko ledar daya shigo da ita da kansa yaje kitchen ya ɗauko plet ya juye kazar duban Jummo yayi yace Bismillah. " Girgiza masa kai tayi a hankali tace. " Na ƙoshi." Murmushi yayi yace. " Ina ai baki isa ba dole sai kinci kazar nan dan nasan babu abinda kikaci." Yayi Maganar tare da haɗe fuska, duk gardamar Jummo sanda ya Garkuwa yasa taci kaɗan bayan sun gama da kansa ya fitar da plet ɗin sauran kajin kuma ya saka a frich dawowa yayi ya buɗe wadrop ɗinta ya ciro mata sleeping dress wata ƴar ƙarama, ya ajiye mata tare da cewa. " Ki shiga tollet kiyi wanka, ki saka wannan kayan bari naje ROOM ɗina." Bai jira yaji mai zata ce ba ya fice, Jummo rigar ta ɗaga tare da taɓe bakinta a zuciyarta tana furta wannan rigar kuma kamar ta arna zansa, tashi tayi ta ɗauki kayan ta shige tollet, wanka tayi ta saka kayan tare da saka katuwar hijabin ta, ta fito mirror taje ta feshe jikinta da turare tare da humra lungu da saƙo na jikinta kwanciya tayi ta duƙunƙunu bata juma ba bacci ya ɗauketa. Ya Garkuwa bai shigo room ɗin ba sai sha ɗaya da rabi, tana kwance tana bacci cike da nutsuwa, murmushi yayi tare da saka hanu a hankali ya cire mata hijabin lumshe idanunsa yayi yana ƙarewa yanda sleeping dress ɗin ya mata kyau, kamar dan jikinta aka yisa, suffar jikinta duk a waje fuskarta ya shafa tare kai mata kiss a lips ɗinta, murmushi yayi ya shafi fuskar tata, hanu ya saka ya jawota jikinsa tare da mannata da jikinta hanunsa na yawo a bayanta, Jummo kamar cikin mafarki take jin ana wasa da jikinta wani irin miƙar daɗi take cikin barci, hanu yasa ya buɗe botin ɗin rigar ya cire mata shi, breast ɗin ta ya zubawa idanun a hankali ya kai bakinsa, jin abin na neman wuce gona da iri domin kuwa ji take kamar ana tsotson breast ɗin ta, a hankali ta buɗe idanunta ɗan zaro idanunta tayi tare da ƙoƙarin turesa zata miƙe ya zuba mata nauyinsa a jikinta yana girgiza mata kai idanunsa sunyi jajur sha'awarsa ta bijiro dama Garkuwa ya lafiyar kura, cikin sarƙaƙƙiyar muryar sa ya ce mata. " Karki min haka Jummo karki haramta min abinda ubangiji ya halatta min, idan banji daɗi a jikinki ba, a ina kike son naje naji, kina son nayi zina ne bayan ina dake wacce Ubangiji ya halitta min, karki zamo irin matan da Allah ke fushi dashi saboda toyewa mijinta haƙƙin shimfidar sa." Sosai jikin Jummo yayi sanyi, tare da sakar masa jikinta, ganin haka yasa nima ficewa domin bazan tsaya ganin abinda yafi ƙarfin idanuna ba. Kiran sallar farko shine ya tashi Ya Garkuwa daga nannauyan baccin da yake mai cike da nishaɗi, Jummo dake kwance saman ƙirjinsa ya duba wanda take baccin wahala fuskarta kwance da bushashshan hawaye na azabar da taci daren jiya, cike da so da ƙauna ya manna mata kiss a fuskarta tare da furta. " Na sameki yanda nayi tsammani harma kin zarce haka tabbas ina alfahari dake a matsayin mata kin kawo mutuncin ki, wanda yake matuƙar wahala a wajen ƴan a wannan zamanin na godewa Ubangiji da bai jarafceni ba saboda zunubin dana aikata" ya ƙarisa Maganar a hankali yana zameta daga jikinsa ya saka kanta saman filo tare da jawo mata blanket, tashi yayi ya shige tollet wankan tsarki yayi tare da yin wanka yayi alwala, ya fito ya hau sallar nafila yana godewa Ubangijinsa da arzikin matar da ya masa sanda aka kusa shiga sallar asuba sannan ya miƙe yaje ya haɗawa Jummo ruwan zafi kitchen yaje ya ɗebo kishiri kaɗan a hanunsa ya zuba cikin ruwan tare da fitowa yazo ya ɗaga Jummo caɗak dake bacci ba tare daya tashe ta, domin kuwa yasan zata masa gardama, cikin ruwan ya ajiye ta, a firgice ta buɗe idanunta tana runtse idanunta tare da cije baki, zata miƙee ya dannata cikin ruwan yana riƙe da kafaɗarta, Jummo kuwa sosai take jin azaba a ƙasanta gashi ya danneta ba halin tashi, idanunta ta runtse tun tana jin azabar har ta fara jin ruwan ya fara mata daɗi jin ta sake jikinta yasa Garkuwa fahimtar ta daina jin zafi sakinta yayi tare da raɗa mata a kunnenta. " Sorry Dear" Ya miƙe ya rataye mata towel tare da ficewa daga tollet ɗin, zanin gadon ya yaye tare da ficewa dashi, ya dawo ya shimfida wani, harya gama ya fita Sallah Jummo bata fito ba, ko kafin ya dawo Jummo ta fito ta saka kayanta har tayi Sallah ta koma bacci, shi kuwa bai shigo gidan ba har sai da gari ya fara haske, tana kwance tana bacci, murmushi yayi shima ya kwanta tare da jawota jikinsa, bacci ne mai nauyi shima ya ɗaukesa, sune basu farka ba har sai wajen 11:10am nan ma ya Garkuwa ne ya farka falo ya fito turus ya tsaya ganin Zizah tsaye ta na zaune cikin kujara. " Zizah yaushe kika shigo gidan nan?" Ya jefa mata tambaya cike da mungun mamaki yana duban falon yanda akayi mopping aka gyara ko ina har turaren wuta aka kunna kuma shi dai bai ɗauki ƴar aiki ba, Zizah murmushi tayi tare da cewa. " Tun goma na shigo naji shuru shine nace ina ga bacci kuke harma na gyara falon baku tashi ba, abinci na kawo muku." " Abinci Kuma keɗin waye yace ki kawo mana abincin.?" Ya jefa mata tambayar cike da tsarguwa, ɗan murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Kai Ya Garko sai tambaya kake min tamkar wata ɓarauniya, ni babu wanda yace na kawo, nine na ce Aunty Zarah ta zuba na kawo muku, ina Aunty Jummon bata farka bane, bara naje na duba ta." Ta ƙarisa Maganar tana miƙewa tsaye zata shige ROOM ɗin Ya Garkuwa yayi saurin shan gabanta tare da cewa. " Ke baki da hankali ne, uban me zaki shiga kiyi a ciki, bacci take ki ɗauki gyalenki ki koma gida, na gode." Zaro idanunta Zizah tayi cike da jin haushi tace. " Ya Garko korata kake a gidan ka, dan nazo wajenka, Allah ya baka hkr, amma dai zan shiga mu gaisa sai na tafi." Ta yi Maganar tana ƙoƙarin shigewa tsawa Garkuwa ya daka mata tare da cewa. " Ba fa na son iskanci, karki kuskura ki shiga ki tashe ta tana bacci ki shige ki koma gida bana buƙatar ki a gidana." Bakinta Zizah ta cije cike da takaici sanin halin Garkuwa ya sata ɗaukar gyalenta tace. " Allah ya huci zuciyarka ban san me na maka ba kake korata, ka gaishe da Aunty Jummon ni na tafi." Tayi Maganar tana ficewa cike da haushi tsuka Ya Garkuwa yaja tare da sawa ƙofar key ya Kitchen ya shiga da kansa ya dafa musu lipton tare da soya ƙwai ya ajiye a daining ya shige ROOM ɗinsa, ko da Zizah ta fita cike da takaicin rashin Nasara ta kira Momy ringin ɗaya ta ɗaga tare da cewa. " Zizah anyi Nasara, kin ajiye layar kuwa a ROOM ɗin nata.?" Cike da haushi Zizah tace. " Momy yau dai anyi rashin Sa'a, domin kuwa Ya Garkuwa ya hanani shiga, ina hango rashin yarda dani a fuskarsa, amma karki damu Momy idan ba'ayi Nasara yau ba akwai gaba, alwashi naci miki sai nayi sanadin wannan Auren kuma zan cika Alwashi na, yanzu zanbi gidan Su Halilah, shiyasa na kiraki." Momy tamkar zata kurma ihu tace. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Kai Garkuwa akwai ɗan durun'uwa nacacce wannan yaron kamar bani na haifesa ba, ba damuwa nasan zaki iya Zizah sai kin dawo." Tayi Maganar tana katse kiran Zizah shigewa tayi cikin zuciyarta tana ayyana bazata koma gidan Ya Garkuwa ba sai nan da sati biyu. Ita kuwa Jummo ko da ta farka wanka tayi tayi brush tare da shiryawa cikin wata koriyar atamfa jikinta yasha turare batayi wani kwalliya ba powder ta shafa a fuskarta sai lipstick, ta fito falon tana ɗan ɗingishi a zaune ta samu Ya Garkuwa kusa dashi ta zauna tare da cewa. " Ina kwana." Tayi Maganar cike da kunya, dubanta Ya Garkuwa yayi cike da so da ƙauna ya jawota jikinsa yace. " Wai ke kunyata kike jine, ah to kuma Kunyar me zakiyi wani dare ne jemage bai gani ba, a sai dai daren mutuwarsa, da alamu dai kunyar ce ban gama fitar da ita ba, tashi muje na cire sauran kunyar." Kafaɗarsa Jummo ta ɗan daka tare da cewa. " Ni wa yace maka kunyarka nake ji, yunwa nake ji." Murmushi yayi tare da kwaikwayon muryarta. " Yunwa nake ji" dukkan su dariya sukayi yace. " Ga can lipton na dafa na soya ƙwai, muje muyi breakfast, amm Momy ta Aiko Zizah da abinci amma bazamu ci ba gaskiya gara muyi amfani da wanda na dafa." Kallonsa Jummo tayi tare da cewa. " Ba zamu ciba kuma, to meyasa, Momy ne fa ta aiko sannan kace bazamu ci ba, gaskiya ni na Momy zanci." Girgiza mata kai yayi tare da cewa. " Ba fa zakici abincin nan na faɗa miki, kiyi amfani da wanda yayi da hanuna bana son musu." " Ha'a My Love ba musu nake ba, baka yarda da Momyn bane.?" " Eh ban yarda da ita ba, aii uwata ce ko, na kuma fiki sonta tunda nace karki ci, to ki haƙura." Numfashi Jummo ta sauƙe tare da kallon sa tace. " Na yadda da ita, kuma zanci, Momy bazata cutar damu ba, dan Allah ka daina zargin mahaifiyarka." *UMMU NASMAH CE* [5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *66 to 67* " Hmmm!!! Okay Bismillah ga can abincin tunda ina hanaki kina cewa zakiyi, Momy dai uwata ce kuma baki fini sonta ba, na kuma fiki sanin waye Momy, amma tunda kince zaki ci Bismillah." Ɗan tura bakinta Jummo tayi tare da shigewa tayi gaba abinda daining ta zauna tare da jawo basket ɗin da Zizah ta kawo, Chief ɗin dankali ne da kuma soyayyen ƙwai sai ɗaya plast ɗin mai ɗauke da farfesun kayan ciki, murmushi Jummo tayi kasancewarta tana son farfesun kayan ciki. " Ya Garkuwa kamar Momy tasan ina son farfesu, zanci abinci na koshi." Tayi Maganar cike da farin ciki zuciyarta ɗaya, girgiza kansa Ya Garkuwa yayi tare da zama yana jawo plast ɗin ruwan zafin sa, abincin da ya haɗa da hanunsa ya ci bai ci na Zizah ba, ita kuwa Jummo cike da farin ciki ta dinga kwasar farfesun ta, tea ɗin da Ya Garkuwa ya haɗa ta jawo tana kanne masa idanu alamun tsokana ganin ransa ya ɓaci, ta hau shan tea ɗin kauda kansa gefe Ya Garkuwa yayi tare da haɗa wani yasha yana gamawa ya tashi ya dawo falo ya cigaba da kallon tashar alzajira. Jummo murmushi tayi, tare da jawo wayarta numbern Safreena ta kira ringin ɗaya Safreena ta ɗaga tare da cewa. " Dukkan mu bamu da kirki, amma dai nace kiyi haƙuri karki min ƙorafi." Dariya Jummo tayi tare da cewa. " Maman Abdul, bazama ki bari nayi Sallamar ba kenan, to dai a wannan lokaci nine na miki laifi domin kuwa nayi Aure ban sanar dake ba dan Allah kiyi haƙuri wallahi abubuwa ne suka min yawa kuma gashi ba'a nan akayi bikin ba, a ƙauyenmu akayi." Shuru Safreena tayi cike da jin haushi sai kuma tace. " Amma gaskiya baki kyauta ba, nasan da ni ce duk rashin kirki na wallahi bazanƙi sanar dake AURENA ba koda kuwa ba'a ƙasar nan za'ayi ba, baki kyauta min ba." Ɗan murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Na sani Wallahi ban kyauta ba, amma dan Allah kiyi haƙuri." " Shikenan ba damuwa ya wuce amarya, yanzu kuna ina kenan."? " Mun dawo cikin Gombe tun ranar da aka ɗaura Auren, ina nan cikin shango Estate." " Ayya masha Allah, to Allah ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya insha Allah nima zanzo amma sai na dawo daga Egypt saboda gobe nake son zan tafi akwai abinda zai kaini insha Allah ina dawowa zanzo, ya kamata ki buɗe WhatsApp saboda a ringa zumunci tunda kiran wayar yana bamu wahala amma insha Allah kafin ma na dawo zanyiwa Zee Magana zasuzo ita da Abdul suga gidan naki." " To shikenan insha Allah zan buɗe na gode sosai ki gaishe da yarona Abdul da ƙawarki Zee." " Insha Allah zasuji na gode ki gaida angon." " Zaiji na gode." Jummo ta ƙarisa Maganar tana katse kiran, tashi tayi ta tattara plat ɗin da sukaci abincin ta kai kitchen sanda ta wanke sannan ta dawo falon yana nan zaune inda ta barsa, har yanzu da alamun ransa a ɓace yake." Zama Jummo tayi tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa a hankali ta furta. " Kayi hkr dan Allah, wallahi bansan ranka zai ɓaci haka ba, da bazanci ba, amma ni a tunanina Momy Uwa take garemu bazata bamu abinda zai kashemu ba, duk ƙiyayyar da Momy take min, nasan kai tana sonka, bazata saka Wani abu a cikin abincin nan ba saboda tasan zaka ci bazata so ka cutu ba, da wannan hujjar naci abincin amma wallahi da nasan ranka zai ɓaci haka bazanci ba." Hanu Yasa ya rungumota jikinsa tare da cewa. " Hmmm!!! Na sani Momy uwace garemu, amma a yanda na fahimci Momy a halin yanzu babu abinda bazata iya aikatawa ba, akan ƙiyayyar da take miki, nasan halin Momy zata iya cutar dake ta ko wacce irin hanya koda kuwa nima zan cutu, shiyasa na hanaki ci amma bana fushi dake dan Allah ki dinga kaffa kaffa da Momy tana da hatsari a rayuwarki." " Bana ɗaukar Momy a matsayin hatsari ga rayuwata amma insha Allah zan kiyaye, akwai ƙawata Maman Abdul munyi waya da ita tace tana gaisheka." " Ƙawarki dama kina da wata ƙawa ce bayan Meenat.?" " Ehh akwai Maman Abdul mun haɗu da itane a super market sai dai bata taɓa zuwa gidan mu ba, waya dai kawai muke amma fa tana da kirki Sosai." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Yayi kyau ina amsawa bara na fita na samu Sadiq yazo ya duba mana gas ɗin nan." Da adawo lafiya Jummo ta masa ya fita ita kuma tayi bedroom ɗinta ta kwanta. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Safreena yanzu ya kukayi da Khabeer ɗin kin sanar dashi tafiyar taki, sannan ya yadda zai nemo miki izini daga Companyn nasu." " Zee ai kinsan zai tambaya min ko Saboda Soyayyar da yake min, kuma kinga Companyn sune, munyi waya ɗazu yace ya tambaya kuma sun bani izini sai dai za'a dakatar da albashi na har sai na dawo aiki ." " Kuma kin amince da hakan.?" " To Zee ya zanyi idan ban amince ba, kin sani Case ɗin dake gabana idan banga ƙarshen kawu Ibrahim ba, hankalina bazai taɓa kwanciya ba, dole zanje Egypt domin lalata masa duk wani farin cikinsa zan bar Abdul a hanunki jirgin 11 zamubi da Baba ki kula da ABDUL sannan dan Allah kije gidan Jummo zataji daɗi." " Hakane Allah ya kaiku lafiya, nama ga Mama ma ta yiwa Abdul wanka." " Ehh nima bara na shiga wankan." Tayi Maganar tana shigewa tollet. Washegari da safe misalin sha ɗaya jirgin su Safreena ya tashi zuwa Egypt, Zee kuwa ta riƙe Abdul, abun mamaki juyowar da Zee tayi zata shiga mota a airport ɗin sukayi kiciɓus da Ya Garkuwa, shigowarsa kenan airport ɗin yazo amsar saƙo a wajen Shetima, da kallo yabi Zee cike da mamaki rabonsa da ita tun sanda ta kirasa take sanar dashi Safreena ta rasu, ita kuwa Zee saurin kawar da fuskar Abdul tayi gefe gudun kar Ya Garkuwa ya gansa tare da buɗe mota ta sashi cikin sauri tana ƙoƙarin shiga Garkuwa ya taho da sauri yana cewa. " Zee dama kina duniyar nan, na nemeki sosai ban ganki ba, amma meyasa daga ganina za kiyi saurin tafiya." Da sauri Zee ta rufe motar tare da cewa. " Ina nan bana ƙasar nan ne, sati ɗaya kenan da dawowata yanzu ma Baba na rako zai tafi Egypt, ya kk." Ɗan murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Ina lafiya Zee da alamu dai har yanzu kina jin haushina, hmmm Zee ina kewar Safreena ina kuma takaicin abinda na mata a rayuwata, sai dai babu yanda muka iya ƙaddara ta riga fata, ita Safreena rayuwarta ta ƙare babu yanda muka iya Allah ya mata rahama." " Hmmm!!! Bana jin haushinka domin kuwa komai ya riga ya shige, ameen ya Allah, Allah yasa muma idan tamu tazo mu cika da kyau da imani, ina sauri Momy na jirana." Ta ƙarisa Maganar tana buɗe motar da sauri ta shiga Ya Garkuwa na Magana ta basa number bata sauraresa ba taja motar ta da ƙarfi tabar wajen, girgiza kansa ya Garkuwa yayi tare da shigewa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Rayuwa tana gudu yayin da abubuwa suke cigaba da tafiya, Rayuwar Jummo a gidan mijinta alhamdulillah!!! Komai na tafiya mata cikin farin ciki sai dai har zuwa yanzu Momy da Zizah basu daina ƙoƙarin kawowa Jummo hari ba, domin kuwa sun rantse sai sun kashe mata Aure, ya wata huɗu kenan da Auren Jummo, sai Allah yana kareta daga duk wani hari da Momy take kawo mata, zaman lafiya da ƙaunar juna kuwa sosai yake wakana tsakaninta da mijinta, a cikin waɗannan watannin Jummo ta fara laulayin ciki, koda sukaje asibiti aka tabbatar da ciki gareta sosai Garkuwa yayi farin ciki kamar bazai mutu ba tsabar daɗi, Ya khalil dake cikin garin Abuja sai da Ya Garkuwa ya sanar masa sosai ya taya ɗan uwansa murna, da kansa ya sanar da Momy wayyo baƙin ciki Wajen Momy ba'a Magana, A'illo dake zaune gidan sai da ta fahimci baƙin cikin da Momy take da samun cikin Jummo, sai dai a yanzu tayi rantsuwa da Allah cewa kota halin yaya sai Jummo tabar gidan. Ita kuwa Safreena tana can tana bincike akan Kawu Ibrahim game da kisan da ya yiwa mahaifinta da kuma dukiyarsu daya cinye sai dai har zuwa wannan watannin tayi rantsuwa da Allah cewa bazata dawo Nigeria ba har sai tayi Nasara akansa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Yau Jummo ta zaune ita kaɗai a falo kasancewar yanzu laulayin nata da sauƙi taji ƙarar wayarta hanu tasa ta ɗaga kiran ganin baƙuwar number, daga can Zee ta amsa tare da cewa. " Sunana Zee ƙawar Safreena." " Ayya sannu Zee fatan kina lafiya ina Abdul."? " Lafiya Alhamdulillah, ABDUL gashi nan amm yanzu ma shirin zuwa gidan ki muke shine nace bara na sanar dake idan mun shigo shango Estate ɗin sai mu kiraki." Cike da murna Jummo ce. " Kai naji daɗi sosai wallahi Allah ya kawo ku lafiya." Da ameen Zee ta amsa tana katse kiran, Ya Garkuwa ne ya fito daga ROOM ɗinsa daidai sanda Jummo ke ƙoƙarin tashi cike da zumuɗi tana dariya zata kitchen ta haɗawa Su Zee abinci, zama yayi yana kallon ta tare da cewa. " My Dear murnar me kike haka ne ko dai Baby nane yau take saki farin ciki."? Murmushi Jummo tayi tare da kallon cikin ta dake wata biyu da sati biyu, dariya tayi ta koma ta zauna tare da kamo hanun Ya Garkuwa ta ɗaura a cikinta tace. " My love, ina matuƙar ƙaunar ɗan da ke cikina, ina son na haifesa lafiya, ka tayani da addu'a Allah yasa na haihu lafiya." Murmushi Ya Garkuwa yayi ya sunkuya ya yiwa cikin kiss yace. " Na fiki ƙaunarsa Insha Allah zaki haihu cikin ƙoshin lafiya, yanzu faɗa min me ya saki farin ciki."? " Ai ina baka labarin ƙawata Maman Abdul, to yau ƙawarta zata kawo min ziyara, ita bata nan tayi tafiya, da Abdul da ƙawarta sune zasu zo suga gidana, shine zanje na musu girki." " Umm ƙawar Maman Abdul, to jeki musu Allah ya kawo su lafiya." Ameen Jummo tace tare da shigewa kitchen tana murmushi tabar Ya Garkuwa a zaune a falon, kitchen ta shiga ta hau aiki Ya Garkuwa ya juma a zaune a wajen kafin ya tashi ya fita, Jummo ta gama komai na gidanta da kusan minti talatin kafin Zee ta kirata ta sanar da ita tana cikin Estate ɗin, da kanta Jummo ta fito ta ɗauko su Zee tare da amsar Abdul, suka yo part ɗinta. " Sannunku da zuwa, Abdul mamanka ta gudu ta barka ko.?" Dariya Zee tayi tare da cewa. " Ta kusa dawowa ai insha Allah, masha Allah gidanki yayi kyau sosai." " Na gode bara na kawo muku ruwa." Jummo abinci da ruwan ta kawo musu har tsakar falon, tayi seving ɗinsu da kanta a cinyarta ta ɗaura Abdul ta hau fasa dankali tana basa, cike da farin ciki da kuma sabo Jummo ta sake da Zee kamar sun shekara, Abdul zamewa yayi daga jikin Jummo yayi bakin kofa yana wasa, Jummo ne ta dubi Zee tare da cewa. " Zee Maman Abdul ta juma sosai a ƙasar waje aiki take a canne.?" Zee ta buɗe baki kenan da niyyar bawa Jummo amsa aka turo ƙofar Turus ta tsaya tana bin ya Garkuwa Da kallo, cike da firgici ta furta. " Garkuwa!!!" Jin ta ambaci Garkuwa yasa Jummo kallon wajen, shi kuwa yana tsaye cike da tsoro yana kallon yaro mai kama dashi sak babu ta inda ya barsa, ko kaɗan bai kula da Zee ba a falon, murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Oh Mijina ne shi, sannu da dawowa My Love." Garkuwa dagowa yayi ya kalleta sai idanunsa suka sauƙa akan Zee dake gefen sa. " Zee!!! Zee!!!" Ya furta yana kuma kallon Abdul, numfashi ya sauƙe tare da sunkuyawa gaban yaron yana kallon sa sosai, da sauri Zee tazo ta sunkuya zata ɗauki Abdul, Garkuwa yayi saurin saka hanu ya ɗaukesa yana kallon ta tare sakin murmushi yace. " Ina kuma zaki ɗaukesa ki kaisa bayan kuma kin kawo sa gidan ubansa."? Zaro idanunta Jummo tayi, Zee kuwa wani irin tsinkewa zuciyarta tayi cikin tashin hankali tace. " Me kake nufi Garkuwa, ka bani ɗana na tafi, bana son tashin hankali." Murmushi mai sauti ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Kinfi kowa sanin abinda nake nufi, ni kuwa meye tsakanina dake da har zanyi tashin hankali dake, kince na baki ɗanki ki tafi, ina kika samu ɗa Bayan baki haihu ba.?" " A layi na samesa, sai ka bani kayana na tafi." "Hmmm!!! Ko makaho ne yaga Abdul zaice ɗana ne, Ina Safreena take."? Runtse idanunta Zee tayi tare da cewa. " Kana haukane GARKUWA!!! Ya kake tambayata matar da ta juma da mutuwa, kaga ka bani ɗana na tafi." Jummo cike da mamaki gami da tashin hankali tace. " Wai meke faruwa ne kam, kun san junane, ɗanka fa kake kiran Abdul anya kana lafiya." Dariya Garkuwa yayi tare da cewa. " Kema mahaukacin zaki kirani kenan, ita ta sani Abdul jinina ne." " Ƙarya yake ni bansan komai ba Abdul jinina ɗana ne, ta ina zai zamo ɗanka." Jummo runtse idanunta tayi cike da kullewar kai gami da tashin hankali tace. " Wai ya kuke neman juya min ƙwaƙwalwa ne, shi yace ɗansa ke kince ɗanki bayan Kuma Abdul ba ɗanki bane!!!! Kai kuma ya Garkuwa masifa kake neman jawo mana daga ganin yaron Mutane kace naka!!! Iya sanina da hankalinka kabar falon nan yanzu, amma gashi ka shiga tamkar wanda ya taɓu." Kallon Zee yayi tare da furta. " Wasan naki ya ƙare, ki faɗa min ina Safreena!!! Ki faɗa min ina buƙatar ta a rayuwata.!!!!!!!!!!!!!!!! *UMMU NASMAH CE* [5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *70 to 71* Key ɗin ta saka jikin kubar sai dai me ƙin shiga yayi kasancewar na nasa bane, cike da haushi Jummo ta yasar da key ɗin da ƙarfi ta doki ƙofar tana cewa. " Kazo ka buɗeni nabar gidan nan tunda ba gidan ubana bane, na rantse da Allah yau sai nabar gidan nan na tsaneka Garkuwa, na tsaneka!!!!! Zan kasheka idan baka ƙyaleni na tafi ba." Tamkar mahaukaciya Jummo ke doka ƙafar tana surutai sai dai shuru kukeji babu kowa, dole tasa ta neman Waje ta zauna domin kuwa tayi laushi tare da sake wani marayan kuka mai ban tausayi. A ƙofar gidan su Shetima yayi parking tare da kiransa bai juma ba ya fito, tare da buɗe motar ya shiga ya zauna da kallo yabi Abdul kafin ya dubi Garkuwa yace. " Abokina waye wannan kuma ina ka samosa.?" Numfashi Garkuwa ya saki ya amsa masa da cewa. " Abinda ya kawo ni kenan, Shetima wannan yaron da wa ya maka kama."? Shetima sosai ya ƙarewa Abdul kallo tare da cewa. " Kamar yana ɗibin fuskarka,. Akwai kuma wani fuskar da yake min kama da ita na kuma rasa gane mai fuskar, meke faruwa.?" " Abubuwa da yawa sun faru yau domin kuwa wannan yaron da kake gani, ɗan Safreena ne, ɗana kuma Cikin da na mata shine wannan yaron." Tsuka Shetima yaja cike da ɗaukar Garkuwa ya haukace yace. " Wannan wani irin banzan magana ne,. Wacce Safreenan, bayan ta mutu, mtss anya kuwa hankalinka ɗaya da alamu dai baka cikin hankalinka." " Hmm!!!! Gaskiya fa nake faɗa maka Safreena bata mutu ba, ka saurareni da kyau kaji abunda zan faɗa maka." " Hmmm!!! Shiriritar banza ina jinka gama tatsuniyar sai muje asibiti a dubaka da alamu dai ƙwaƙwalwarka ta fara samun matsala." " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, haba dan Allah wai meyasa kake min haka ne Shetima ya zanzo maka da damuwata cikin tashin hankali, sannan ka dinga ƙoƙarin mayar dani mahaukaci, why Idan bazaka saurareni ba sai nayi tafiyata." Numfashi Shetima ya saki tare da cewa. " Maganar taka ce tayi kama da almara, amma ina jinka faɗi muji."? Cike da tashin hankali Ya Garkuwa ya sanar da Shetima dukkan abinda ke faruwa, cike da ɗimuwa gami da matsanancin mamaki cike da tsoro yace. " Whattt!!! Whattttttt!!! Serious abinda kake faɗa min gaskiya ne, idan kuwa hakane tabbas akwai babban tashin hankali, Huuuuu!!! Hmmm!!! Me zaka cewa Daddy da Momy da kuma khalil akan wannan yaron, bama wannan ba, yanzu ita Jummo tana ina, mu fara zuwa wajenta kafin muyi tunani akan lamarin Safreena." Ya Garkuwa baice komai ba, ya ja motar suka koma cikin gidan sa, a yanda yabar Jummo a haka ya sameta sai dukan ƙofar take, tana surutai, shuru Shetima yayi yana sauraronta tare da matsowa jikin ƙofar ya kira sunanta. " Jummo!!! Ki saurareni." Shuru tayi jin muryar Shetima sai kuma da ƙarfi tace. " Shetima ka buɗeni zan mutu zuciyata tana tsinkewa a bedroom ɗin nan, ku buɗeni ko na kashe kaina, bana son GARKUWA na tsanesa, ku buɗe ni zan shiga duniya ne, na lalace kowa ma ya huta." Zaro idanunsa Shetima yayi cike da tsoron kalamanta Ya Garkuwa kuwa yafi kowa tsorata, duban Garkuwa yayi yace. " Garkuwa anya kuwa Jummo bata haukace ba, bata maganganu irin na masu hankali, ba kishin Safreena take ba, dole akwai wani abu da yake faruwa da ita, bama buƙatar magana da Jummo yanzu ko budeta, abinda zai faru, ka kira Baffa kakanta ya haɗaka da INNO, ka sanar da ita abinda ke faruwa tazo da gaggawa, maza kira wayar." Ya ƙarisa Maganar yana karɓar Abdul dake famar kuka yana neman abinci a hanun garkuwa ya hau jijjigasa, Ya Garkuwa numbern Baffa ya kira, bayan Baffa ya ɗaga ne suka gaisa ya buƙaci a bawa INNO wayar babu jumawa kuwa aka haɗasa da INNO bayan sun gaisa, Garkuwa ke sanar da INNO abinda ke faruwa, numfashi INNO ta saki tare da cewa. " Karku buɗeta ku jirani zan hau mota yanzu ina tahowa." Da to Ya Garkuwa ya amsa suna jin masifar Jummo, duban Shetima yayi tare da cewa. " Ina cikin tashin hankali, yanzu abinda nake so ya za'ayi na warware matsalar Safreena." Shetima kansa ya dafe tare da cewa. " Shima ka kira Bro khalil ka sanar dashi abinda duk ya faru tsakanin ku da Safreena, na tabbata ransa zai baci amma tabbas zai kawo mana mafita." " Kai ina tsoron sanar da Bro Wannan Maganar ina tsoro domin bansan ya zai ɗauki Maganar ba." "Sanar dashi shine kaɗai mafitar da kake dashi, kaga kawai ka kirasa ba tare da tunanin mai zaice ba burin mu kawai shine mu sami mafita, sannan kana buƙatar haɗuwa da Safreena." " Okay shikenan bara na kirasa." Yayi Maganar yana dannawa ya khalil kira ringin ɗaya Ya khalil dake zaune cikin Office ɗinsa ya ɗaga tare da cewa. " Ya akayi Bros." Ɗan shuru ya Garkuwa yayi kafin yace. " Bro ya aikin." "Aiki alhamdulillah, amma ba daɗi, ya naji muryar ka da sanyi kamar dai kana cikin damuwa, meke damunka domin dai tabbas kana cikin matsala a yanda na fahimta."? " Bro, GASKIYA akwai matsala kuma bansan ta inda zan fara sanar da kai ba, ina tsoron yanda zaka ɗauki Maganar, ban kuma san kallon da zaka min ba idan ka sani." Ɗan murmushi Ya khalil yayi tare da cewa. " Baka da wanda zaka sanarwa matsalarka sama dani domin kuwa nine ɗan uwanka na jini wanda zai iya rufa maka asiri, idan baka sanar dani ba wa zaka sanar, kaga faɗa min meke faruwa karkaji tsoro.?" Ya Garkuwa kallon Shetima yayi jikinsa a sanyaye, ɗaga masa kai Shetima yayi alamun ya faɗa, cike da in'ina ya fara sanar da Ya khalil labarin sa da Safreena da cikin da ya mata har zuwa abinda ke faruwa yanzu da kuma halin da Jummo ke ciki, ai kuwa wani irin ɓaci ran ya khalil yayi bai taɓa jin haushin ɗan uwan nasa irin na yauba, Sosai ransa ya ɓaci kansa ya kulle, halin da Jummo ke ciki ne ma yafi ɗaga masa hankali a matuƙar fusace yace. " Dole kace kana tsoron sanar dani wannan mungun aikin daka aikata a rayuwarka mai cike da abun kunya, tir!!! Ba dole Jummo ta shiga wani hali ba, taji abinda yafi karfin zuciyarta, na rantse da Allah wani abu ya samu Rayuwar Jummo, ni da hanuna zan jefaka a prison, domin kuwa bazan yarda ka cutar da Rayuwarta ba na zuba ido yarinya mai hkr da burin kawo gyara a rayuwar mutane, shine zakayi burin ka kasheta, wannan wani irin abun kunya ka jawo mana, ɗan layi fa, ya Momy zata ɗauki wannan lamarin so kake ka kasheta, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Ka bani kunya Garko ban taɓa zaton za'a sameka da irin waɗannan mugayen halayyar ba, me kake so nace yanzu naje na samu su Daddy da Maganar ko, nasan shine yasa ka kirani, to ka sani bazani ba, sanda kaje ka tafka abun kunyarka ka yiwa ƴar mutane ciki, ban sani ba, dan haka yanzu kuma sai kaje da kanka ka tari iyayen naka da Maganar idan yaso idan ZUCIYARSU ta buga ka kashesu shikenan sai burinka ya cika." Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa cike da tashin hankali Ya Garkuwa ya dubi Shetima yace. " Kaji ko, abinda nake gudu kenan yanzu ya zanyi shima ransa ya ɓaci, ta ya zan tunkari Momy da wannan maganar ko Daddy." Shetima ne yace. " Kaima kaine ka ɓata shirin meyasa zaka amshi yaron daga hanun Zee, tunda ka gansa ka kuma fahimci ɗanka ne, sai kabarta da yaron, hakan shi zaifi bamu damar bin komai a hankali, saɓanin karɓesa da kayi gashi sai famar kuka yake babu yadda zamuyi dashi,da ace........." Ringin ɗin wayar Ya Garkuwa ne ya hana Shetima ƙarisa Maganar da yayi niyya baƙuwar number a HANKALI ya ɗaga muryar daga can yaji muryar ta cikin tsiwa da faɗa. " Wannan tsakanina da kaine babu ruwan ɗana, dan haka kayi gaggawar mayar min da Abdul hanun Zee, ba ɗanka bane kuma bazai taɓa zama ɗanka ba, wato bibiyata kake shiyasa ka haɗa baki da matarka saboda ka tozarta Ni, ka nunawa duniya ina da ɗan shege, asirina a rufe yake babu wanda yasan ina da ɗan shege kowa ɗauka yake bayan tafiyata American nayi Aure ne shiyasa na dawo da yaro, dan Allah karka tozarta ni, ka ɓata min sunana dana ɗana ina buƙatar farin cikin ɗana, dan Allah ka bari ka fita a rayuwata, na sauya ƙaddarata daga mantawa da ko wani namiji, na shiryawa rayuwa dani da ɗana, dan Allah bana son rigima ka mayar min da yarona ka kuma manta dani a rayuwarka." Ta ƙarisa Maganar tana sakin numfashi, shuru Garkuwa yayi kafin yace. " Har abada bazan taɓa fita daga cikin Rayuwarki ba, bazaki taɓa mutuwa a zuciyata ba, na yarda zan baki ɗanki amma bisa sharaɗi da kuma alƙawari, idan har kin amince zan baki ɗanki amma wallahi kinji na rantse da Allah idan baki yadda da wannan yarjejeniyar ba, bazan baki Abdul ba, koda kuwa zaki kaini kotu duniya tasan halin da nake ciki bazan baki shiba.." " A karo na biyu kana kuma neman zaluntata, duk halin dana shiga a rayuwata kaine sanadi, ka faɗi sharaɗinka ina jinka." Numfashi ya saki tare da cewa. " Ki sanar dani me kikaje yi a Egypt.?" " Ɗaukar fansa, nabi kawu IBRAHIM na ɗaukawa iyayena fansar ransu." " Amma dai kinsan Egypt ba Nigeria bace sannan Ibrahim ya fiki wayo zai iya cutar da rayuwarki kafin ke ki cutar da nasa, ya kamata ki dawo Nigeria." " Na fika sanin Egypt ba Nigeria bace tunda ba mahaukaciya bace ni, matuƙin jirgin Egypt, babu kuma ruwanka da hatsarin da zan shiga wannan ba damuwarka bane. Da okay ya amsa tare da cewa "sharaɗina shine, zan baki Abdul muddun kika min alƙawarin haɗuwa dake, saboda ina da buƙatar tattaunawa dake." Shuru Safreena tayi na ɗan wani lokaci tana tunani, ɗanta kawai take ji domin tasan zuwa yanzu yaci kuka ya ƙoshi, yana buƙatar Zee ce masa tayi. " Zamu haɗu ka mayar da Abdul." " Hmmm!!! Ba haka nake son ki amsa min alƙawarin ba, so nake kice ni Safreena na ɗauki alƙawari tsakanina da ubangijina zan haɗu da Garkuwa." Runtse idanunta Safreena tayi cike da jin haushin garkuwa shida.......... *Kuyi manage yau ina busy kuyi haƙuri dan Allah.* *Ummu Nasmah ce* [5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *72 to 73* "Naji Na ɗauki alƙawari tsakanina da ubangijina zan haɗu da kai, dan Allah ka je ka bawa Zee Abdul please dan Allah." " Okay ki turo min numbern wayarta zan bawa Shetima ya kai mata shi yanzu." Numfashi mai nauyi Safreena ta sauƙe tana godewa Allah, tare da amsawa da to ta katse kiran, bata juma da kashe kiran ba ta turo masa numbern haka kuwa akayi ya bawa Shetima ya kaiwa Zee Abdul, shi kuma ya zauna gadin Jummo cike da tashin hankali. INNO bata iso ba sai daf da kiran sallar magaruba, Shetima ne yaje ya ɗauko ta, koda INNO ta shigo sosai hankalinta ya tashi jin yadda Jummo ke bige bige tamkar ta haukace. " Garkuwa buɗe ƙofar." Babu musu ya buɗe ai kuwa Jummo tamkar jira take ta fito da sauri sai kuma ta haɗa idanu da INNO, tamkar bata san INNO ba zata wuce INNO ta capko hanunta da ƙarfi ta fisge zata fita da gudu Garkuwa yayi sarin tareta, INNO mari ta ɗauke Jummo dashi tare cewa. " Baki sanni bane Jummo.?" Ta mata tambayar tana kallon ƙwayar idanunta, kanta ta ɗaga alamun ehh, murmushi INNO saki tare da cewa. " Yanzu ina kike son zakije na rakaki." Cikin rawar murya tace. " Nima ban sani ba" " Zaki bini gidan mu.?" Nan ma kanta ta daga alamun ehh, hanunta INNO ta kama tare da cewa. " Ɗauko mota ka kaimu gidan ku." Zaro idanunsa Shetima da Ya Garkuwa sukayi tare da cewa. " Gidan mu kuma INNO, INNO bana son Jummo ta zauna a gidan mu." Murmushi INNO ta saki tare da cewa. " Jummo dole a gidan ku zata zauna, karka min musu kazo ka kaimu kawai." Kansa ya kaɗa cike da sanyin jiki, ya je ya dauko motar suka fita ya jasu. Momy da Zezah suna zaune a falon sukaji Sallamar su, da sauri Momy ta kallesu zuciyarta na mungun tsinkewa, INNO murmushi ta saki tare da ƙarasawa cikin falon ta zauna gefen Momy tana cewa. " Barka da hutawa Zainabu, kawai sai kikaga baƙi na bazata, kallon Ya Garkuwa tayi tare da ce masa, Garkuwa aje a share ɗakin Mamma anan zamu zauna." Da to ya amsa yana fita tare da turo Asma'u tazo ta share, massalaci suka wuce INNO kuma taja Jummo bedroom ɗin da Mamma ta zauna, ta sata tayi Sallah, sannan ta fito har yanzu Momy da Zezah suna nan inda ta barsu kina ganin idanunsu zaki hango tsoro, zama INNO tayi tana murmushi tace. " Ohh Zainabu bokan ki ya iya aiki tunda harya iya karya tsarin dake jikin Jummo, nawa kika biyasa." A matuƙar razane Momy tace. " INNO me kike cewa haka, ban gane ba, meya samu jummon." Dariya INNO tayi tare da girgiza tace. " A binda dai kikaji shi nake nufi, kinyi Nasara akan Jummo domin kuwa nasan kin mata sihiri kuma ya kamata, sai dai inaga kin manta da cewa, tana da INNO tana kuma da Baffa, ƴar malamai ce gaba da baya, karkiyi tunanin kinci Nasara, umm ummm!!! Ko rabin Nasara baki samu ba, ki zuba kiyi kallon yanda sharrinki zai dawo kanki." Tayi Maganar tana barin wajen ba tare da ta tsaya taji me Momy zata ce ba, a razane Momy ta miƙe tsaye tana kallon Zezah tace. " Zezah na shiga Uku, lallai akwai matsala domin kuwa nasan INNO sarai Zata iya juyo da sihirin nan kaina kafin hakan ta faru gara mu karya sihirin, kije maza kafin Garkuwa ya koma gidan ki samu ki ɗauko layoyin nan mu ƙonasu." " Haba Momy yaya kawai dan tazo tana miki barazana shikenan sai ki tsorata, babu fa abinda zata miki wallahi, ki barta kawai cikin rashin hankalin idan ya gaji da ganinta a haka ai dole zai saketa." " Zezah bana son rashin hankali domin kuwa naga alama baki da ita, baki san waye INNO ba, duk abinda ta faɗa zata aikata, dan haka ba shawarinki nake nema ba umarni nake baki, tashi kije." Tura bakinta Zezah tayi tare da miƙewa ta haura ta dauki mayafinta ta fice, numfashi Momy ta sauƙe tare da haurawa ta kira Sarah, ringin ɗaya sara ta ɗaga cike da tashin hankali take sanar da sara abinda ke faruwa. " Hajiya Zainab tun farko fa sai da na hanaki, domin kuwa da alamu wannan Yarinyar ƙaddarar ɗanki ne, kawai ki ƙyalesu, sai kika ki kika biyewa shawarar Zezah da ta Hajiya Saude, gashi yanzu sun jefa ki rami sun barki, mtsss" " Banyi tunanin zan juye haka ba, da bazan fara ba, Sarah kece kawai kike bani shawara idan nabi nake samun hanyar bullewa, yanzu meye abunyi, na saka Zizah tayi maza taje ta ɗauko asirin, da cewa nayi zan ƙonesa ke me kike gani." Numfashi Sarah ta saki tare da cewa. Yauwa Gara da kika turata ta ɗauko, ni kuwa wannan INNOn wacce irin shegiyar tsohuwa ce gagararriya, mtsss, yanzu abinda zai faru idan Zizah ta kawo miki, ki tabbatar a tollet kika ƙonesa,, idan kika kuskura kika ƙonesa a waje to asirin kanki zai dawo, makarinsa shine ki ƙonesa a tollet, karki kuskura ki ƙara ƙoƙarin kai Yarinyar wajen boka domin kuwa babu Nasara a kanta, zanzo zan baki shawarar yadda zaki zauna da matsiyaciya." " Shikenan ƙawata na gode sosai, shiyasa nake ƙaunarki domin kuwa akwai da ɓulalliyar hanya, sai kinzo." Tayi Maganar tana katse kiran zama tayi tana dafe kanta, cike da tashin hankali da tsanar Jummo, ta juma sosai har Zizah tazo ta kawo mata asirin, kamar yadda Sarah ta faɗa mata haka tayi ta ƙona a tollet, ranta a matuƙar ɓace. Daren ranar haka Momy tayisa cike da baƙin ciki tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Washegari da sassafe Jummo ta farka a firgice, cikin tsoro tana dube dube ba dai a ROOM ɗin ta take ba, to meya kawota nan tuno da abinda ya faru ya sata dafe kanta tabbas ta tuno zuwan Zee da abinda ya faru tsakanin su da Ya Garkuwa, tasan ta shiga tollet ta kuma ji Sallamar wata kamar Muryar Zizah ta fito ta zauna bakin gadonta daga nan bata kuma sanin meke faruwa da ita ba sai yanzu, kanta dake ɗan sara mata ta riƙe INNO dake bacci ta kalla cike da mamaki tace. " INNO kuma, meya kawo INNO cikin Gombe?" Tashi tayi ta shige tollet wanka tayi tare da brush tayi alwala,. Sallah ta gabatar, ta juma tana addu'a, yayin da kishin Safreena na tokare mata ƙirji, harta Ya Garkuwa shima zafinsa take ji, sai dai zata danne zuciyarta bazata yadda kishi yasa ta bijirewa mijinta ba Za tayi iya kokarinta wajen ganin ta rage kishin duk da tasan dole zataji ciwo a ranta, Tabbas ya faɗa mata komai na rayuwarsa bai ɓoye mata ba, zata zauna da mijinta za Kuma ta tayasa neman mafita a cikin lamuransa. Numfashi ta saki, muryar Daddy taji yayi sallama amsawa tayi kafin Daddy ya shigo a kujerar dake cikin room din ya zauna cike da girmamawa Jummo ta gaishe da Daddy ya jiki ya mata, ta amsa da cewa da sauƙi, INNO ne ta buɗe idanunta ta dubi Daddy tare da tashi ta zauna tana cewa. " Sannu Garba, jiya kawai sai kaji labarin munzo, lamarin ciwon ne lokaci ɗaya kamar hauka ya firgita mu, amma alhamdulillah ta dawo hayyacinta tun daren jiya, ka yiwa Mamma gini na zamani mai kyau, Allah ya maka albarka!!! Allah yasa ka gama da duniya lafiya." Da ameen Daddy ya amsa yana cewa. " Ni kaina da Garko yake sanar dani ciwon nata hankalina ya tashi, to mun godewa Allah da ta samu sauƙi cikin hanzari, dama jiki da jini dole za'a cutu, amma dai bazata koma gidanta ba sai jikinta yayi kwari Kinga ga ƙaramin ciki, dole tana buƙatar hutu ta zauna tukunna har muga yanayin jikin nata kafin ta koma ɗakinta, ni bara na shige kasuwa." Adawo lafiya INNO ta masa kafin Daddy ya fita, INNO duban Jummo tayi tare da cewa. " Yaya kike jin jikin naki." " Bana jin komai sai kaina kawai dake min ciwo." " Shima kan zai daina a hankali, ki dai dage da yawan azkar karkiyi wasa dashi Allah ya tsare gaba." Ameen Jummo tace, Asma'u ne ta shigo ta kawo musu breakfast, Ya Garkuwa bai zo ba sai wajen 11am sosai yaji daɗin yanda yaga jikin Jummo INNO waje ta basu, Ya Garkuwa duban Jummo yayi tare da cewa. " Harna tsorata da lamari ki jiya, nayi zaton Maganar Safreena ne ya sa kika hasala." " My love meyasa zan hasala bayan ka faɗa min gaskiya tun kafin ka aureni karka manta nine fa na amince zan zauna dakai a duk yanda kake meyasa yanzu zan sauya, ko kaɗan bana fatan na juya maka baya, yanzu wani irin hukunci ka yanke akan Abdul." " Babu abinda na yanke har yanzu, zuciyata cike take da tsoron tunkarar Daddy da Maganar bansan ya zai ɗauki lamarin ba, ko Bro khalil dana kirasa, baya ya juya min cikin hasala da ɓacin rai to ya kike gani kuma idan Daddy ne, ni dai ina cikin tashin hankali." " Bana son kana ambatar tashin hankali, kuskure dai ka riga ka yisa babu mai iya gogewa, hkr kuma ya zamo dole, ni na yanke hukunci zan tunkari da Daddy da Maganar ta sigar neman alfarma daya yayi hkr ya karɓi wannan al'amari a matsayin ƙaddara, insha Allah komai zaizo da sauƙi, sannan kaima kana son Safreena har yanzu, ka aureta domin shine cikar rufin asirin ku daga kai har ita, sai ta riƙe ɗanta ina faɗa maka wannan maganar ne da zuciyata ɗaya, ya kamata kaje Egypt ka sameta ku sasanta kafin tafi insha Allah munsha kan matsalar gida, ka kwantar da hankalin ka, komai zaiyi sauƙi, nasan kishi da Safreena bazai cutar dani ba dan nasan wacece ita, nasan halinta mutumce ta gari bata da matsala bazata daga min hankalina ba." Cike da mamaki yake kallon Jummo, cikin sanyin zuciya, domin kuwa ko a mafarki baiyi zaton zata masa wannan alfarmar ba, Tabbas yayi dace da mace ta gari, idan har ƙafa ake ɗagawa mace ta shiga aljanna to shi ya ɗaga tashi Jummo ta shige, numfashi ya sauƙe tare da jawota jikinsa ya rungume ta yana sakin numfashi. " Ban taɓa tunanin zaki ɗauki wannan maganar da sauƙi haka ba, kamar yadda kika faɗa nima hukuncin dana yanke kenan na Auri Safreena domin Rayuwar Abdul, daga ni har Safreena muna son juna ƙaddara ce ta faɗawa rayuwar mu, bazan taɓa fifita Safreena sama dake ba, har abada kece a samanta WALLAHI Jummo Soyayyar da nake miki a yanzu ta ɗara ta Safreena, da badan Abdul ba, zan hkr da Safreena a rayuwata na riƙeki ke kaɗai domin kin isheni rayuwa, matar rufin asiri ce ke, Allah ya miki albarka Jummo, ina sonki fiye da kaina." " Nima ina sonka mijina farin cikin ka shine nawa, dole na ƙwato maka farin cikin ka insha Allah Daddy zai ɗauki wannan zancen tamkar ruwan sanyi, Momy ne dai ban sani ba, ya khalil fushin sa na kanƙanin lokaci ne zai sauƙo bazai iya fushi da kai ba, ransa ne ya ɓaci amma zai huce..............." *UMMU NASMAH CE* [5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *68 to 69* Wani irin jiri ne ya kwashi Jummo jin maganganun Ya Garkuwa take tamkar a mafarki, sai kuma kalaman Garkuwa suka faɗo masa tuno fa tabbas ya sanar da ita Labarin Safreena. "Safreena!! Safreena!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!" Kalmar da Jummo ke nanatawa kenan, kardai ace itace Safreena da Ya Garkuwa ya bata labari amma ai ita yace ta mutu ya za'ayi wanda ya mutu ya dawo, meke shirin faruwa dani.? Tayi zancen zucin tana neman Waje ta zauna daɓas jin jiri na ƙoƙarin kwasarta, tare da zuba musu idanu tana dafe da zuciyarta dake famar bugawa, ita babu abinda yafi ɗaga mata hankali sama da kalmar ɗanda yace nasa ne idanunta ta runtse cikin ƙunar rai, ita kuwa Zee juyawa Ya Garkuwa baya tayi, cikin tsawa mai firgitarwa tace. " Ehhh Safreena bata mutu ba!!!! Bata mutu ba tana nan raye!!! Kuma ta maka zararra domin kuwa babu kai a cikin rayuwarta ta daɗe da kasheka a rayuwarta, dan Allah kamar yadda ta manta da kai kaima ka manta da ita ka yiwa girman Allah ka bani Abdul na tafi, bamu san Jummo matar ka bace ko kana da alaƙa da ita da ba zamuyi kuskuren haɗa zumunci da ita ba, ka bani Abdul dan Allah, wannan yaro ne baisan komai ba." Shuru Garkuwa yayi tare da neman waje ya zauna yana nan riƙe da Abdul a hanunsa, rungumo yaron yayi a jikinsa cike da Soyayya irin ta ɗa da Uba, wani irin soyayyar Safreena ce ke bijiro masa, tabbas yana sonta tsawon rayuwarsa, numfashi ya sauƙe tare da ɗago idanunsa ya kalli Zee cewa yayi. " Shiyasa na kasa mantawa da Safreena a rayuwata, na kasance da sonta tsawon shekaru dai-dai da kwana ɗaya ban taɓa jin koda ɗigon santa ya ragu a zuciyata ba, KULLUM cikin zancenta nake, ashe inuwarta yana yawo a duniya, meyasa kuka min ƙaryar Safreena ta rasu bayan ni masoyine gareta ba maƙiyi ba, meyasa kuka ɓoye min ɗana jinina saboda meyasa shin Safreena bata sona ne, hmmm!!! Lallai zunubai nane Sukayi yawa shiyasa Safreena guduna, ki sanar dani Zee ina Safreena take.?" Shuru Zee tayi cike da sanyin jiki, idanunta na ziraro da hawaye cikin rawar murya ta fara magana. "Saboda munanan kalamanka akan Safreena, Idan bazaka manta ba kasha alwashin cewa sai kaga bayan Safreena muddun bata zubar da cikin jikinta ba, a wannan lokacin hankalin Safreena yayi mungun tashi har ta shigo gidan mu a tsorace take cemin ga abinda ka faɗa mata amma ita hankalinta ya tashi ta hango gaskiya zaka iya aikata ikirarin ka a idanunka, a wannan lokacin ni ne na kwantar mata da hankali na tabbatar mata da cewa bazaka aikata abinda ka faɗa ba, na nuna mata cewa barazana kawai kake mata saboda ta zubar da cikin jikinta, hmmm!!! Da ƙyar na samu hankalinta ya kwanta, a wannan daren ƙin kwana tayi a gidan su saboda tsoro, ta kwana a gidan mu, a cikin wannan daren gobara ya tashi a gidan su wanda duk agajin da aka kawo sanda wutar nan ta cinye komai, na gidan da kowa dake cikin gidan itama Safreena ta tsirane kawai Saboda a gidan mu ta kwana, tun daga ranar da wuta taci gidan su da iyayenta, zargin kaina kasa wutar ya ɗarsu a zuciyar Safreena, iƙrarin daka mata suka fara yawo a zuciyarta, akwai wani Isma'il mai gadin gidan Alhaji badamasi, ya tabbatar da cewa yaga wani matashin saurayi da wasu Uku sun jefa ƙulli da jarga cikin gidan su Safreena, basu juma da juyawa ba wutar ta tashi, tun daga ranar da ni da Safreena da iyayena muka yarda cewa kaine ka saka wuta cikin gidan su domin kashe Safreena karta tona maka asiri, sai tsanarka ya ɗarsu a zuciyarta taji a duniya bata da maƙiyin da ya wuceka, wutar fansar iyayenta ne kawai yake yawo a zuciyarta, mahaifina cike da tsoro ya sa aka yiwa Safreena visa tare da nunawa duniya cewa Safreena ta mutu, ya turata American wajen Momy Atine ta zauna gudun karka kuma cutar da rayuwarta, Safreena bata dawo wannan ƙasar ba sai da ta haifi Abdul har yayi wata Uku sannan ta dawo Nigeria da niyyar ɗaukar fansa tayi niyyar ta kasheka ta ko wani hali, ni da ita muka fara ƙoƙarin saka maka tsoro cikin ranka ta hanyar zuwa hotel muka haɗa baki da ma'aikacin hotel muka ɗauki video ɗinka tsirara kai da Sadiya, muka turo maka domin mu ɗaga maka hankali, mun maka abubuwa da yawa na firgitarwa, a ƙarshe muka haɗa baki da mai gadin gidan ku muka basa kuɗaɗe ya since maka tayar mota saboda kayi hatsari ka mutu, haka kuma akayi a wannan ranar tabbas kayi hatsari kai da wacce zaka Aura, a Kuma wannan Ranar Momy Atine ta sanar damu cewa ba kai bane ka kashe iyayenta, saboda Mahaifiyar Safreena ta sanar da ita cewa ƙanin mahaifin Safreena yana shirin kashesu sai dai bata san yaushe bane, tabbas Safreena tayi danasanin zarginka tayi ƙoƙarin zuwa gidanku ta dakatar dakai daga tafiya da wannan motar amma ina kun tafi, tun daga nan ta daina zarginka ta fita daga rayuwarka, Safreena bata cikin rayuwarka yanzu na tabbatar da bata sonka bata son tunawa da kai, rayuwarta ɗanta shine kawai a ranta, ta ina zata inganta rayuwar sa shine burinta, dan Allah karka lalata mata mafarkinta akan ɗanta ka bani Abdul na tafi." Tunda Zee ta fara Maganar idanun Ya Garkuwa yayi jajur ji yake tamkar wuƙa take daɓa masa, cike da ɓacin rai ya furta. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Hmmm!!! Kusan shekara ɗaya da rabi ina cikin zargi koda a cikin baccina ban taɓa mafarkin na kashe koda ƙuda bane bare kuma ɗan adam tabbas baki shike yanka wuya na shiga ban ɗauka ba kuma bata fidda ɓarawo, ban taɓa tunanin Safreena zatayi tunanin zanyi kisan kai ba, domin kuwa tasan waye ni, sai dai na godewa Ubangiji daya tseratar dani daga sharrin da kuka wurga min ya kuma wanke Ni, sai dai abinda nake son na sani ina Safreena take." " Tana Egypt" Yaji an amsa masa daga bayansa cikin rawar murya mai alamun kuka, da sauri ya juya yana kallon Jummo numfashi ya saki tare da miƙewa yaje gabanta ya sunkuya. " Ban ɓoye miki komai game da rayuwata ba, na sanar da ke dukkan zunuban dana aikata da kanki kika yarda zaki zauna kiyi rayuwa dani a yadda nake, na sanar dake wacece SAFREENA da cikin dake jikinta a gareni ban munafurce kiba, sai dai a yanda nake kallon ƙwayar idanunki ina hango tsana da haushi na a cikin su, Jummo.........." Hanu ta ɗaga masa tare da girgiza kanta ta tashi da sauri tabar wajen, numfashi ya sauƙe Yana maida hankalin sa ga Zee yace. " Meya kai Safreena Egypt ki faɗa min, bazan iya baki Abdul ba har sai nayi magana da Safreena ki sanar da ita cewa idan tana son amsar ɗanta ta nemeni." Yayi Maganar yana shigewa bedroom ɗinsa riƙe da Abdul runtse idanunta Zee tayi cike da ɓacin rai ta juya itama tabar gidan. Sosai hankalin Jummo ya tashi, tabbas bai ɓoye mata komai ga me da Safreena ba, sai dai zuciyarta yana mata zafi ace tana zaune da ɗan shege mijinta na da ɗan layi wannan wacce irin masifa ce, numfashi ta sauƙe tare da ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Ta juma zaune cikin wannan tashin hankalin kafin ta yunƙura cikin sanyin jiki tayi tollet. Zizah da SALLAMA ta shigo cikin gidan shuru babu kowa, bedroom ɗin Jummo ta nufa kanta tsaye da SALLAMA nan ma shuru taji, tsakiyar ROOM ɗin ta tsaya tana ba kowa ne, gyaran muryar Jummo da taji a tollet yasa ta fahimtar Jummo tana tollet, murmushin mugunta ta saki cikin sauri ta buɗe jakarta laya biyu da wata ƙaramar kwalba mai cike da wani ruwa, tayi gaggawar ɗaga katifar Jummo ta ajiye layar, murmushi ta kuma sakewa tare da sunkuyawa ta ajiye kwalbar tare da ɗayar layar a ƙarƙashin gadon Jummo, cikin sauri ta fice daga ROOM ɗin ganin har yanzu babu kowa cikin falon ya sata ficewa maa daga gidan gabaki ɗaya cike da farin ciki. Shi kuwa Ya Garkuwa yana nan riƙe da Abdul cike da tunani iri iri a zuciyarsa, taya zai fara sanar da iyayensa wannan mungun abu daya aikata ta ina zai fara gabatar musu da Abdul a matsayin ɗansa, lallai ya tafka kuskure a rayuwarsa ya Daddy da Momy zasuji wannan maganar shin zasu karɓi Abdul da zuciya ɗaya, numfashi ya sauƙe cike da tsoro sai harga zuciyarsa yana jin Abdul a ransa yana ƙaunarsa tamkar yadda zai ƙaunaci ɗan sunnah, ya yadda zai jure zagi da cin mutunci akan Abdul, lallai ya zamo dole Safreena ta dawo rayuwarsa, yana buƙatar domin samun farin ciki mai ɗaurewa, yana so a yanzu suyi rayuwa a ƙarƙashin inuwar Aure ɗaya rayuwa kuma mai tsafta, tabbas yana da tabbacin Jummo bazata gujesa ba, zata karɓi kaddarar sa da hanu yana da tabbacin haka, miƙewa yayi tare da Abdul suka nufi ROOM ɗin Jummo. Ita kuwa Jummo ko da ta fito daga room ɗin ta duba mai sallama ta hau yi, wayam ROOM ɗin ba kowa, bakinta ta taɓe tana jin wataƙil kunnen ta ne basuji dai-dai ba, bakin bed ɗin ta ta zauna, tana runtse idanunta, zamanta keda wuya kanta yayi wani irin mungun sarawa, saurin dafe kan tayi tana runtse idanunta, zuciyarta ta kuma tsinkewa da ƙarfi take wani haushi da takaici gami da tsanar gidan ya dira a zuciyarta miƙewa da sauri ta fito falo tare da nufar ƙofa zata fice daga gidan a fusace kiciɓus sukayi da Ya Garkuwa, cike da mamakin ganinta a fusace yace. " Ke Jummo lafiya kika fito a fusace haka."? Wani mungun kallo Jummo ta jefa masa tare da cewa. "Gidan mu zan tafi ka sakeni bazan kuma zama a gidanka na tsaneka na tsani gidan ka, ka bani takarda ta." Wani irin tsinkewa zuciyar Ya Garkuwa tayi cike da tashin hankali yace. " Jummo kina da hankali kuwa kin san abinda kike faɗa kuwa, nine fa ya garkuwanki kike kiran na sakeki, haba Jummo karki juya min baya akan matsalar Safreena bani da laifi na sanar da komai kafin Auren mu, ban rufe miki KOMAI ba, meyasa zaki karya alƙawarin da kika min dan Allah Jummo ki tausaya min karki barni bazan iya Rayuwa babu ke ba."? " nima bazan iya rayuwa kaga ka matsa min na tafi idan yaso sai ka biyoni da takarda ta daga baya." Tayi Maganar tana ƙoƙarin turesa ta shige ganin kamar Jummo bata cikin hankalinta ya sashi saurin turata ROOM ɗin ta tare da jawowa da sauri ya saka key a kofar Abdul ya ɗauka tare da ficewa daga gidan da sauri ya shiga mota rasa ina zaije yayi tsabar ya gigice, sosai hankalinsa yake tashe, Momy ya kamata yaje ya samu da Maganar sai dai bazai yiwu naje wajen Momy ba, tabbas ina cikin tashin hankali, Shetima ne ya faɗo masa a ransa, wayarsa yayi saurin ɗauka ya kira numbern Shetima, bayan ya ɗaga ne cike da tashin hankali Ya Garkuwa yace. " Shetima kana ina?" " Lafiya Garkuwa meke faruwa naji muryarka cikin tashin hankali." " Bana cikin kwanciyar hankali, ina cikin tashin hankali Shetima kana ina ina buƙatar ganinka yanzu pls." Numfashi Shetima ya saki tare da cewa. " Ina gidan mu, kazo ka sameni." Katse wayar Ya Garkuwa yayi tare da jan motar cikin tashin hankali mai gadi ya buɗe masa ya fice. Ita kuwa Jummo sai buga ƙofar take cike da tashin hankali da ɓacin rai ga kanta dake mungun sara mata ji take idan ba ta bar gidan ba, bazata taɓa samun nutsuwa ba, tamkar mahaukaciya haka take dukar ƙofar, a birkice ta juya ta fara neman key a cikin ROOM ɗin ta buɗe kanta, komai na ROOM ɗin bincikarsa take tana watsarwa, idanunta ne suka sauƙa akan wani key dake cikin bedside drower da sauri ta kai hanu ta ɗauki key ɗin ta nufo ƙofar.......... *UMMU NASMAH CE* [5/31, 12:40 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *76 to 77* Ƙarfe Uku dai-dai agogon Nigeria jirgin ya Garkuwa ya sauƙa a Birnin Egypt sanda fasinjan duk suka sauƙa ya yi settling ɗin jirgin kasancewar a ranar zai juyo, bayan ya samu hutu yaci abinci sannan ne ya kira numbern Safreena kusan ringin shida bata ɗaga wayar ba, dole tasa ya dakata da kiran, kafin zuwa can ya kuma kira, ai kuwa cikin Sa'a ta ɗaga wayar, numfashi ya sauƙe tare da sakin murmushi yace. " Ina kika bar wayar ina ta kiranki shuru baki ɗaga ba, ina Egypt so nake mu haɗu da gaggawa domin jirgina zai tashi nan da awa Uku." Shuru Safreena tayi zuciyarta sam bata ƙaunar haɗuwa da Garkuwa sai dai ta masa alƙawari kuma tasan girman alƙawari, cikin daƙilalliyar murya ta masa kwatancen inda take babu ɓata lokaci kuwa ya hau taxi a inda ta masa kwatancen ya tsaya tare da kiranta babu jumawa kuwa ta fito jikinta sanye da Kayan sanyi ta yane kanta da jan mayafi, sosai shigar ta mata kyau gefe dashi ta tsaya ba tare da ta kallesa ba tace. " Ina jinka nima sauri nake ina da aiki." Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa. " Ko gaisuwar bazan samu ba, okay hakanma na gode, yanzu dai kafin mu shiga cikin maganar mu kai tsaye, ya labarin abinda ya kawoki ƙasar nan, kina samun Nasara kuwa akan Ibrahim ɗin." Safreena cikin ƙunar rai tace. " Har yanzu babu wata Nasara dana hango game da shirina akan kawu IBRAHIM, na ma kasa samun damar ganinsa, da alamu yayi ƙarfi sosai anan, hakanne ma yasa na yanke shawarar jibi zan dawo Nigeria na sake shiri kafin na komo." Hanunsa ya Garkuwa ya zuba a aljihun sa tare da cewa. " Dama ni na sani cutar da Ibrahim a wannan ƙasar zaiyi wahala, domin kuwa ganin sa ma zaki shekara baki gansa ba saboda done ne shi anan yayi ƙarfi yana kuma tare da manyan ƙasar nan, ni anawa shawaran naji labarin zaizo hutun ƙarshen shekara Nigeria, a Nigeria kuma na Tabbata zaki samu ganinsa cikin sauƙi mai zai hana bazaki hakura ba ki jira dawowarsa Nigeria, sai kiyi Amfani da wannan damar wajen cikar muradinki." Kanta Safreena ta ɗaga cike da gamsuwa da Maganar Ya Garkuwa tace. " Wannan shawarar tamin, ina ga nima hakan zaisa na samu sauƙin aikin, na gode da shawara, tell me meke tafe da kai." Numfashi Ya Garkuwa ya saki tare da cewa. " Harna fidda rai da samunki a rayuwata KULLUM ina miki addu'ar mamaci fatana dai Allah ya kai haske cikin kabarinki, dake KULLUM nake kwana nake tashi duk da ina ɗaukarki a matsayin matacciya, tunda na rabu dake ban kuma samun macen da zata maye mini gurbinki ba, sai Jummo, itace kaɗai nake kallo a matsayin ki, Safreena bazan ɓoye miki ba, ina son Jummo matuƙar so jigo ce ita a rayuwata, sai dai duk soyayyar da nake yiwa Jummo bata saka na manta dake a rayuwata ba, duk ke maƙiyi kika ɗaukeni ta fuskar zarginki, Safreena mahaifina ya amince na karɓi Abdul a matsayin ɗana, ya kuma umurceni dana aureki Saboda Rayuwar Abdul, kuma nima hakan take a zuciyata, ina sonki har gobe farin cikin rayuwata zai cika ya tumbatsa idan kika kasance dani, Safreena ina son muyi Aure." Tunda ya soma Maganar Safreena take binsa da kallon mahaukaci, kafin ta dubesa ido cikin ido tace. " Bazan aureka ba kuma bazan baka Abdul ba, ka sani rayuwata da ta ɗana zata inganta ko babu kowa a tare dani, ka sani babu Aure a gabana yanzu, kuma koda ina da niyyar Auren ma wallahi bazan aureka ba, zaifi maka sauƙi ka fita a rayuwata dani da ɗana, kaje ka riƙe matarka ta isheka rayuwa, sai kuma ka godewa Allah da bai jarrabeka da fitinanniyar mace ba, na zunuban daka aikata, matarka macece ta gari mai kima da mutunci mai Alkunya gami da kawaici samun irinta a yanzu yana matuƙar wahala koni nan ban Kaita ba, kawai kaje ka riƙe matarka ni ka rabu dani, ko sauraranka da nayi yanzu saboda alƙawarin dana ɗaukar maka ne, da ko inuwata bazan yarda mu haɗa ba, na barka lafiya." Tayi Maganar tana barin wajen cikin sauri domin kuwa har cikin zuciyarta take jin bazata iya auren Garkuwa ba, shuru yayi cikin damuwa yana kallon ta, har sai da ta ɓace masa, idanunsa ya runtse yana jin insha Allah sai ya shawo kan Safreena ta amince dashi, juyawa ya bar wajen, ya koma airport ɗin, ƙarfe takwas na dare agogon Nigeria jirgin nasa ya tashi zuwa Nigeria. Jummo ce zaune gaban Momy tana goge mata ƙafafunta tare da ɗan matsa mata, Momy sai bin Jummo take da kallo ba tare da tayi Magana ba, cikin zuciyarta ta fara jin son Jummo bata taɓa tsammanin wacce ta tsana a rayuwarta ba, zata jinyace ta, harta wanke mata kashi da fitsari, abinda ko ɗan uwanka ba kowa bane zai maka wannan aikin, Lallai duk yanda kaga Mutum karka rainasa a rayuwa domin kuwa baka san wacce irin rana zai maka ba a rayuwa zai yiwu shine wanda zai taimakeka a lokacin da kake neman mai taimako, lallai ta tafka kuskure na ƙin Jummo a rayuwarta, gashi ƴarta da ta haifa bata tsaya ta kula da rayuwarta ba harkokin gabanta kawai ta saka a gabanta amma ita Jummo gata da ciki ma amma haka take ɗawainiya da ita, numfashi ta sauƙe tare ɗago hanunta mai amfani da ƙyar ta ɗaura akan Jummo, Jummo ɗago kanta tayi ta kalli Momy, murmushi Momy ta mata, a hankali ta furta. " Na gode Allah ya miki albarka" Murmushi Jummo tayi cike da farin ciki tunda Momy ta kwanta jinya yaune kawai tayi Magana, Ya khalil ne ya shigo da Sallama, a gefen Momy ya zauna cikin sanyin jiki yace. " Momy dan Allah kiyi hkr ki yafewa Garko ki cire damuwa a ranki Garko kuskure yayi ya kuma tuba, nasan bazai kuma ba Momy, Momy ubangiji ma fa muna masa laifi ya yafe mana, bare kuma mu ƴan adam, kiyi hkr Momy dan Allah lafiyarki muke nema yanzu." Jummo ce ta ɗaura da cewa. " Momy duk da nasan ba ƙaunata kike ba, amma zan nemi alfarma a gareki, ki yafe masa ke uwace fushinki garesa zai iya jawo masa wata masifar a rayuwa, Momy ya Garkuwa ya sanar dani dukkan abinda ya faru da rayuwarsa tun kafin ya Aure ni, harta wannan cikin da ya yiwa Safreena ya sanar dani cikin nadama kuma ya tuba tun tuni, wallahi Momy Ya Garkuwa mutumin kirki ne yanzu ƙaddara ce ta faɗa masa ki yafe masa dan Allah." Momy hawayene ya zubo mata daga idanunta cikin ƙasa da murya irin na majinyaci tace. " A irin tarin zunubai na, ai dole ubangiji ya jarrabeni, ni ba mutumiyar kirki bace, shiyasa rayuwa ta juya min baya, ku duba kuga yadda Allah ya mayar min da halitta ta lokaci ɗaya wai nice komai sai anmin, haka Rayuwa take muddun ba alkairi kake ƙullawa ba, to ka jira ranar tozartar ka, domin kuwa Allah bazai taɓa ƙyaleka ba, nayi sihiri iri iri a rayuwata, na raba tsakanin Uwa da ɗanta, Mamma tana cike da tsanata a zuciyarta, bana da kirki, to meyasa ma zanji haushin Garko saboda ya aikata wannan mungun aikin, me yiwuwa nubina ne ya biyo ta kansa, na yafe masa duniya da lahira, kema Jummo ki yafe min." Cike da farin ciki Ya khalil da Jummo suke murmushi, wannan shine burin Jummo a rayuwarta, Momy ta gane gaskiya karta mutu cikin saɓon Ubangiji, cike da farin ciki Jummo ta sanar da Ya Garkuwa cewa Momy fa ta yafe masa sosai shima yayi farin ciki a ranar ya zo wajen Momy cikin farin ciki. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Rayuwa tana tafiya yayin da jikin Momy zaace alhamdulillah sai dai har yanzu ɓarin jikinta babu wani canji bakinta kam ya dawo dai-dai sai ɓarin jikinta har yanzu babu wani canji a yayin da cikin Jummo ke da wata bakwai ganin tayi nauyi yasa Ya khalil neman TRANSFER ya dawo Gombe shida Zarah, Jummo kuma ta koma gidanta Aunty Zarah ta cigaba da kula da Momy. Suna zaune a falo suna hira Jummo ta dubi Ya Garkuwa tace. " My love, gaskiya nifa idan na haihu Tulde zan koma wanka." Zaro idanunsa yayi tare da tsuke fuska yace. " Ban miki alƙawari ba, anan zakiyi wanka, karma ki saka a ranki." Jummo zatayi Magana sukaji Bbc news na sanar da cewa jirgin daya taso daga Egypt zuwa Nigeria yayi hatsari ya faɗi, a yayin da jirgin ya ƙone ƙurmus, Ya Garkuwa a matuƙar razane ya miƙe tsaye wani irin gumi na keto masa hankalinsa yayi mungun tashi, Jummo miƙewa tayi tare da dafa kafaɗar sa tace. " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Safreena fa tana cikin jirgin nan innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!!!" *UMMU NASMAH CE* [6/2, 4:40 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *78 to 79* "Ta mutu kenan Ya Garkuwa.?" "Jummo Safreena tana cikin jirgin nan domin kuwa Zee ta tabbatar min cewa Safreena ta taso yau, kenan tana cikin jirgin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati wa'akfilni kairan minha!!!! Bara nayi gaggawar zuwa airport ɗin mu, nasan suna can sashin bincike zan kuma nemi Zee naji ya ake ciki" "Dan Allah idan kaje duk abinda ake ciki ka sanar dani dan hankalina bazai kwanta ba har sai naji halin da Safreena take ciki." "Karki damu insha Allah zamuji alkairi." Ya mata Maganar cikin sigar rarrashi domin kuwa ya tabbatar da cewa muddun Safreena tana cikin wannan jirgin sunanta gawa, saboda jirgi baya taɓa faɗuwa ƙasa wani ya rayu duk wanda suke ciki sai sun mutu, kanta Jummo ta ɗaga masa alamun to jikinta sai famar rawa yake. Cike da tashin hankali shima yaje airport ɗin nasu sashen bincike ya nufa kusan dukkan ma'aikatan suna cikin wajen, a kusa da Shetima ya tsaya tare da cewa "a wani ƙasa jirgin ya faɗi.?" " Afghanistan anan jirgin ya faɗi kuma an tabbatar da cewa mutum 40 a ciki duka sun mutu harda Samuel drevern jirgin shima ya mutu." Idanunsa ya Garkuwa ya runtse tare da zaro wayarsa ya kira numbern Zee ringin ɗaya kuwa ta ɗaga tana sakin kuka mai sauti, idanunsa ya kuma runtsewa kukan Zee ya tabbatar masa da cewa Safreena tana cikin jirgin kuma ta mutu, cikin raunin murya yace. " Safreena tana ciki ko? Safreena ta mutu innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati!!! Kiyi haƙuri Zee mutuwa rigar kowace kowa dole sai ya saka wannan rigar babu wanda mutuwa zata bari, Ubangijin daya ɗauki Safreena ya fimu sonta, ita da ta tafi batayi sauri ba, mu kuma da muke raye ba muyi jinkiri ba, komai daren daɗewa sai munje mu tadda ta." Ya ƙarisa Maganar hawaye na gudu a saman fuskarsa, Lallai yayi babban rashi, ya tsarawa rayuwa da farin ciki biyu Jummo da Safreena, hmmm sai dai ina Allah ya ƙaddara Safreena ba matarsa bane, katse kiran yayi yana durƙushewa a wajen ya saki kuka mai sauti Shetima ne ya sunkuya tare da dafa kafaɗarsa ya hau masa nasiha da bada baki, kafin ya samu yayi shuru, cikin sanyin jiki yabar airport ɗin bai doshi gidan sa ba, gidan su yayi a falo ya samu Momy zaune kan kenan da aka bata Daddy shima na zaune cikin kujera, kusa da Daddy ya zauna tare da sakin kuka yana cewa. " Daddy Safreena ta mutu, hatsarin jirgin nan ya ritsa da ita Ta mutu Daddy Abdul ya rasa mahaifiya." Ga baki daya falon salati ya ɗauka Daddy ne yace. " Subahanallah!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahu Akbar, oh rai baƙon duniya, Allah ya jiƙanta da rahama dama haka rayuwa ta gada, mutu tana sarƙe da kowa wanda kwanansa ya ƙare sai tafiya, Allah yasa idan tamu tazo mu cika da kyau da imani ita kuma Allah yasa ta huta, dama kuma jiya Zarah da Khalil sunzo sun roƙeni alfarmar cewa ka basu kyautar Abdul su riƙesa matsayin ɗansu na cikin su tunda su Allah bai azurtasu da haihuwa ba, Kuma na yanke shawarar cewa na basa, gobe in Allah ya kaimu zamuje mu yiwa Alh giɗaɗon ta'aziyya idan yaso in an kwana biyu sai naje da kaina na sameshi da zancen Abdul ɗin." Kansa ya Garkuwa ya kaɗa tare da runtse idanunsa yana jin zafin mutuwar Safreena a zuciyarsa, ita kanta Momy ko da bata san Safreena ba, sai da taji mutuwar, ya juma sosai a gidan kafin ya shige gidan su Safreena suna zaune suma zugun zugun masu kuka nayi sosai ya tausayawa Zee yanda duk ta fita a hayyacinta tana maƙale da Abdul, Alh giɗaɗo ya gaisar tare da masa ta'aziyya ya juma a gidan har akayi sallar magaruba sannan ya koma gidan sa, ko da ya sanar da Jummo sosai hankalinta ya tashi, daƙyar cikin sigar rarrashi ya samu hankalin Jummo ya kwanta. Washegari kuwa, aka iso da gawarwakin su Safreena Nigeria Birnin tarayya wato Abuja Alh giɗaɗo shida abokinsa Alh Kabeer, sai Ya Garkuwa sukaje babu wanda ya iya gane gawar ɗan uwansa domin kuwa duk sun babbake, haka dole aka haɗasu aka musu a can, aka binnesu, sunsha kuka sosai tare da baƙin cikin rashin gane gawar Safreena wannan yafi ci musu rai Ranar da suka cika kwana uku da rasuwa Ya khalil da Daddy sukaje suka musu ta'aziyya, a nan ne Daddy yake sanar da Alh giɗaɗo zancen ɗaukar Abdul, haka babu musu ya amince musu, sanin cewa a duniya Abdul bashi da gatan daya wuce su dangin mahaifinsa, Zee Sosai taci kukan rashin Safreena da karɓe Abdul da akayi sai dai babu yanda ta iya dole ya zamo tayi hakuri Jummo ma taje ta yiwa Zee ta'aziyya tare da jajanta mata mutuwar Safreena, Jummo bata so aka raba Abdul da Zee ba. Ko da Daddy suka dawo da Abdul gidan, Zarah sosai taji daɗi tare da amsarta zuciyarta tana sanar da ita itama yanzu ta samu yaro, Momy sanda taga Abdul sosai ya shiga ranta, babu ƙyama ta rungumesa, haka rayuwa ta tafi cikin jin daɗi a cikin wata ɗaya Abdul yayi mungun shaƙuwaa da Aunty Zarah da Ya khalil da kuma Momy, Zizah ne dai baya yadda da ita kasancewar bata cika masa wasa ko ɗaukarsa ba. Misalin ƙarfe Uku na dare wani irin mungun ciwon ciki ya turniƙe Jummo Ga baya da mararta tamkar zai tsage, wani irin azaba takeji wanda tunda uwarta ta haifeta bata taɓa jin wannan azabar ba, ji take tamkar rayuwarta ne yazo ƙarshe, bakinta ta cije goshin ta ya tsattsafo da gumin azaba, Ya Garkuwa dake baccinsa hankali kwance ta riƙesa tana ambaton. " La'iha'illahu Muhammadur Rasulullah!!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!" Sai kuma ta saki kuka jin kamar motsin mutum jikinsa ya saahi buɗe idanunsa a hankali, idanunsa ya zuba a kanta sai kuma ya miƙe a firgice yana rikota tare da cewa. " Subahanallah!!! Jummo kaddai haihuwar ce?" Ina itakam Jummo bata da bakin Magana saboda munguwar azabar da take ji, ga haihuwar tazo mata da ciwon baya, wanda yafi wahalar wa, ai kuwa babu shiri ya Garkuwa ya miƙe jallabiyarsa ya saka da sauri ya ɗauki key ɗin motar sa ya fito mai gadi ya samu tare da ce masa ya buɗe masa get, sannan ya koma ciki, Jummo ya kamo suka fito suka shiga mota, cikin gaggawa yake tuƙin Asibitin Doctor Sirajo suka je, cikin gaggawa aka shiga da Jummo ɗakin haihuwa tare da cewa Ya Garkuwa ya koma ya kawo musu kayan haihuwa da fallen zani, komawa cikin tashin hankali ya ɗauko ya kawo, tunda Jummo ta shiga cikin room ɗin hankalin Ya Garkuwa bai kwanta ba, har kiran sallar asuba ta farko Jummo bata haihu ba, sanda aka fito Sallah sannan ya kira Aunty Zarah yake sanar da ita yana asibiti Jummo zata haihu, Aunty Zarah tana idar da Sallah itama tazo ta, shuru shuru Jummo bata haihu ba sai da gari ya waye 7:30am Allah ya sauƙeta lafiya ta samu santalelen ɗanta fari tas kyakkyawa, koda aka sanar dasu ya Garkuwa haihuwar sosai sukayi farin ciki, Ya Garkuwa ne yace. " Doctor ina mahaifiyar Yaron, tana lafiya dai ko DOCTOR."? Murmushi doctor ya saki tare da cewa. " Tana lafiya bata da wata matsala, taɗan samu ƙari kaɗan mun mata ɗinki, so tana ɗakin hutu ma da jaririn zaku iya shiga ku gansu." Ai kuwa cikin farin ciki suka shiga room ɗin tana kwance tana bacci Babyn kuma an lulluɓesa da towel, Ya Garkuwa cike da farin ciki ya ɗago yaron numfashi ya sauƙe tare da mannasa a ƙirjinsa, kunnen sa ya kama ya masa kiran Sallah, tare da saka hanunsa a cikin aljihun sa, dabino ya tauna tare da sawa yaron a bakinsa, ya ɗiga masa zam zam, Aunty Zarah sai tsiya take masa, ganin suna cikin ƙoshin lafiya ya sashi komawa gida yayi wanka ya samu nutsuwa sannan yayi gidan Momy yake sanar da ita Jummo ta haihu murna Momy tayi tare da musu addu'a domin bata da ƙafar zuwa asibitin, cewa tayi yaje kitchen akwai ruwan zafi a plast da kayan shayi ya kai musu asibiti tare da ce masa idan an basu sallama su taho da Jummo nan Gidanta, cikin farin ciki ya amsa da to zuwa yayi ya ɗauka ya koma asibitin, ya samu jummo harta farka tana bawa jaririn nono, gefenta Ya zauna cikin murmushi yace. " Oh yarinya ta girma." Murmushi Jummo tayi tare da ɗago idanunta ta kalli Ya Garkuwa, cirewa Yaron nono tayi ta miƙa masa ya saka hanu ya karɓe sa, tace. " Ka kira su INNO ne ka faɗa musu haihuwar."? " Ban kirasu ba, na dai gwada numbern Baffa bata tafiya amma zuwa anjuma maybe ya tafi ko matsalar network ne." Aunty Zarah ce tace. " Ai kuwa ya kamata su sani likitan ma yace tunda bata da wata matsala za'a iya Sallamar mu zuwa anjuma." " Okay Momy tace gida zaku koma idan an sallame ta." Da to Aunty Zarah ta amsa, da yamma lis kuma aka sallamesu suka koma gidan Momy, Abdul sai murna yake yaga jariri, Daddy ma ya shigo ya duba jikan nasa, ko da Ya Garkuwa ya sanar da Baffa haihuwar Jummo, Sikayel da kanta tazo ta zauna mata. Kwanan Jummo Uku da haihuwa yayin da jaririnta yayi kyau kamar yayi sati biyu, a ranar ne kuma aka kawo kuɗin Auren Zizah, wani ɗan Kano ne zai aureta wanda suka haɗu a facebook. Meenat tun ranta suka sami saɓani da Momy bata kuma zuwa gidan ba, sai yau ta kira Jummo a waya kamar bazata ɗaga ba, sai kuma ta ɗaga muryar Jummo a daƙile ta amsa sallamar meenat, meenat daga can cikin sanyin murya tace. " Ƙawata har yanzu fushi kike dani ne? Allah sarki Jummo kema kin sani abinda Momy tamin ba dai-dai bane, amma duk da haka ni ina mai baki hkr Allah ya huci zuciyarki, dan Allah kiyi hkr." Cikin mutuwar jiki domin duk wanda ya maka laifi yace maka kayi hkr to Tabbas ya gama kashe maka jiki, numfashi ta sauƙe tare da cewa. " Ba komai ya wuce amma dan Allah gaba karki kuma min irin haka, ana barin halak kodan kunya har yau Ya Garkuwa bai san abinda kika yiwa Momy ba, Kuma bana son ya sani Saboda yana ganin mutuncin ki." " Hakane Jummo na gode sosai, kin sauƙa lafiya."? " Lafiya Alhamdulillah!!! Amma dan Allah Meenat karki zoki gidan nan kin san ina gidan Momy kuma bazataji daɗi ba idan ta ganki gashi bata da lafiya ki bari sai na koma gidana sai kizo." Da babu komai meenat ta amsa sun juma sosai suna hira kafin suka katse cikin farin ciki. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Ranar suna Ya raɗawa yaron sunan Baffa Wato Ahmad, sosai sunan yayi goshi, su INNO da Mamma duk sunzo yaro kuwa sosai ya samu kaya, babansa ma akwati Uku ya cika tam, dana yaron dana Uwar Momy ma tayi nata akwati biyu, shi kuwa Ya khalil, akwatin sa ɗaya yayi Aunty Zarah ma tayi nata turmin atamfa Uku da kayan Baby huɗu harda pampas, anyi taro lafiya an watse lafiya, da Ahmad ɗinsa suke kiransa Ya Garkuwa yace bai amince su sanja masa suna ba, a kirasa da sunan sa. Haka rayuwa ta dinga gudu cikin farin ciki a yanzu Jummo bata da matsala da Momy tana sonta sosai sai dai har yanzu Momy gefen jikinta babu wani canji yana nan a yanda yake, ranar Jummo ta cika kwana arba'in washegari ranar Sikayel ta koma dama su INNO tun ranar da akayi suna washegari suka koma. Itama Jummo washegari ta koma nata gidan ta, a wannan lokacin kuma aka saka ranar bikin Zizah. *UMMU NASMAH CE* [6/3, 12:02 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY* ➰➰ *80 to 81* Jingine yake jikin motar ya harɗe hanunsa, yana ƙarewa gidan kallo yanda mutane ke cike ƙofar gidan suna neman hanyar da zasu gansa , numfashi ya sauƙe tare da leƙa kansa cikin motar alamu yayi musu da idanu akan suzo suje, babu musu suka nufi ƙofar gidan, ɗan sandan dake gadi a ƙofar gidan Ya zaro kuɗi kimanin dubu hamsin ya miƙamasa yana neman abarsu su shiga gidan, aikuwa ganin wannan kuɗin yasa ɗan sandan barinsu a kunnensa ya raɗa masa cewa. " Officer Mai gidan ya samu isowa ne." Kansa ya ɗaga masa alamun a'a " yana hanya dai tukunna jirgin su ya taso waɗannan mutane da kake gani ƴan jiransa suyi roƙo, amma ku kuwa me zakuyi a cikin gidan nan."? Murmushi ya kuma sakewa tare da cewa. " Akwai abinda muke nema, idan har zaka mana jagora zuwa lungu da saƙo dake cikin gidan nan to na maka alƙawarin Naira dubu ɗari bakwai da hamsin, cash." Zaro idanunsa ɗan sandan yayi tare da furta. " 7050 thausand serious.?" " Yes serious" " Baku da matsala muje kawai" Yayi Maganar yana shigewa gaba suka rufa masa baya, tun daga babban falon daya ƙawatu da kayan more rayuwa suka fara bincike har zuwa room ɗinsa basu samu komai ba daga cikin abinda suke nema, duk iya bincike da zasuyi a gidan sunyi amma ina babu komai dole tasa suka haƙura suka fito sunzo dai-dai fita daga falon kamar wanda aka ce mata kalli nan, ta hango kamar ƙofar ROOM ta bayan drower, ai kuwa da sauri tayi wajen tana cewa. " Kunga wata ƙofa, a bayan school drower." Ai kuwa juyowa sukayi tare da rufo mata baya ƙofarce kuwa, drower suka ture gefe cike da mamaki, wani irin ƙura ne a ɗakin har bakan Gizo yayi saka sosai, wayarsa ya zaro tare da kunna haskenta suka hau bincike, dubanta ta kai ga hoton dake manne jikin bangon, hanu tasa ta karkaɗe sai kuwa ga fuskokin ƴan gidan su ya fito ras duk an musu lamun Counsil, hanunta Zee tasa ta shafa a fuskar Safreena sai kuma hawaye ya jiraro mata, Ya Garkuwa dake tsaye a bayanta ne yace. " Ba lokacin kuka bane yanzu, gaggawa zakiyi mu samu mu kammala abinda ya kawo mu kafin mutumin nan ya shigo." Share hawayen tayi tare da saka hanu ta cire hoton wanda Shetima ke famar ɗaukar su video tun daga get ɗin gidan gar suka shigo, sosai sukayi bincike cikin ROOM ɗin wata waya Ya Garkuwa ya tsinta a ciki, tana kashe a ƙulle a leda da alamun ɓoyeta akayi kunna ta yayi, babu inda hanunsa ya shiga sai fannin video, ai kuwa sosai yaga abinda ya ɗaga masa hankali domin kuwa video ne wani daga cikin gidan su Safreena wanda ya kasance shine mamallakin wayar ya ɗauka, taƙaddama ce mai yawan gaske a daren da aka jefa wutar har zuwa sanda wutar ta fara kamawa, inda kawu IBRAHIM yake tabbar da cewa ya saka musu wuta kuma dole ne yau sai sun mutu gabaki ɗayansu, murmushi Ya Garkuwa ya saki tare da duban ɗan sandan ya ciro kuɗinsa cash ya basa ya kuma ce. " Ayi gaggawan maida komai yanda yake kafin mai gidan ya ƙaraso ku kuma kuzo muje." Yayi Maganar suna ficewa da sauri koda suka shiga cikin motar yaja suka kama hanya muryar Zee yaji tana cewa. Station muka nufa ko ya kamata mu shigar da ƙara, yana karasowa ayi Arresting ɗinsa, tunda muna da shaida a hanun mu." "Hmmm baza muyi karar sa Zee." " Baza muyi karar sa ba, to meye amfanin binciken da mukayi tare da hujjar da muka samu na tabbacin shine ya kashe iyayen Safreena.?" " Zee har yanzu baki gama sanin halin ƙasar mu, ba karki manta Ibrahim yana tare da manyan ƙasa, Shari'a dashi ba zai yiwu ba, muna ɗaukar wannan hujjar muna kaiwa ƴan sanda, zasu ɓatar da hujjar su kuma wankesa shikenan yasha, Zee na gama yanke yanda zamu kwantawa Safreena haƙƙinta, gobe zan fara ɗaga masa hankali ta hanyar bawa ƴan jarida wannan hujjar su yaɗawa duniya ɗan siyasa ne dole hankalin manyan ƙasa zai tashi da kansu zasu saka a kamasa Domin wanke siyasar su gashi lokacin zaɓe ne yanzu karki damu ban fara wannan aikin ba sai da nayi tunani mai zurfi ta inda zamu ɓulle." Dukkan su dariya suka saka cike da yadda da shawarar sa. Haka kuwa akayi ya danƙawa Aminci News wannan shaidar tare da aikawa har BBC rediyo, a cikin kwana Uku yayi wannan aikin su kuwa suka dinga bazasa har wasu ƴan jaridun suna ɗauka, tashin hankali iya tashin hankali Ibrahim ya shigesa inda gwamnati tasa aka kamasa, tare da kaisa gidan kaso na sati biyu, kafin a ka fito dashi nan ma aka shiga Shari'a a zama na farko aka yanke hukunci bisa ga duba da hujja mai karfi da ke hanu dukkan dukiyar sa dana mahaifin Safreena sai da kotu ta ƙwace ta danƙawa Baba tare da yanke masa hukuncin rai da rai a gidan kaso. Sai yanzu zuciyar Zee ta samu sukuni da taga an kwatowa Safreena ƴancinta, Baba wannan dukiya ƙin riƙeta yayi yaje ya samu Daddy Ya khalil da Ya Garkuwa ya danƙawa Ya Garkuwa dukiyar Safreena tare da cewa. " Bazan riƙe wannan dukiyar ba saboda Safreena tana baya wannan dukiya duka nata ne ita kuma yanzu bata raye wannan dukiya mallakin ɗanta Abdul ne kai kuma kaine mahaifinsa gashi ka riƙe masa har ya girma ku basa abunsa, babu wanda yasan Abdul ba ɗan sunnah bane, dan Allah karki bari ya sani karku yadda yasan dangin mahaifiyarsa saninsu zaisa yace zai nemo su, inda hakan zaisa ya gane waye shi, dan Allah ku riƙe Abdul da kyau." Numfashi Daddy ya sauƙe tare da cewa. " Babu abinda zai faru da rayuwar Abdul na maka wannan alƙawarin, sannan dukiyar Abdul zata samu kulawa mun gode sosai." Haka suka watse cikin farin ciki, bayan Baba ya tafi ne, Ya Garkuwa ya danƙawa Ya khalil duk takaddaun dukiyar Abdul ya basa tare da cewa shi bazai riƙe ba, Ya khalil shine Uba yanzu a wajen Abdul shine ya dace ya riƙe dukiyar, sosai Daddy yaji daɗin karar da Garko ya yiwa ɗan uwansa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Yau watan Jummo Biyar da haihuwa yayin da Ahmad yayi ɓul ɓul dashi gwanin sha'awa kamar su ɗaya da ABDUL, har yana zama abunsa gashi da dariya yaron. " Sati ɗaya kacal na baki, kuma a ranar zanzo na ɗaukeki." Murmushi Jummo tayi tare da cewa. " Sati ɗaya fa Ya Garkuwa, haba dai dan tun da nayi Aure fa banje gida ba shine kuma naje nayi sati ɗaya dal, ni dai ka ƙara min." Ɗan murmushi yayi tare da rungumota jikinsa ya raɗa mata a kunnenta. " Na sani nima naso kiyi koda sati biyu ne, bazai yiwu bane saboda na biya mana hajji dole zaku dawo bita, ke da INNO da Mamma na biya mana tare ma zaku dawo." Dariya Jummo tasa cike da farin ciki ta kanƙame Ya Garkuwa kiss ta manna masa a fuskarsa tare da cewa. " Wow My Love I love you so much!!! Da gaske ka biya mana hajji, wayyo daɗi ƙasar da nake burin zuwanta a rayuwata, mun gode sosai Allah yabar zumunci Allah ya ƙara arziki." Murmushi Ya Garkuwa ya saki tare da cewa. " Babu abinda bazan miki ba a rayuwata, domin kin min hallaci a lokacin da ya kamata ki gujeni a lokacin kika ƙara aniyar zama dani nine ya kamata na gode miki." Murmushi Jummo tayi sun ɗan juma suna zance cike daso da ƙauna irin na mata da miji. Haka kuwa akayi washe gari ya Garkuwa Da kansa ya kai Jummo har Tulde, ya dawo, sosai Jummo tasha mamakin yanda taga gidan su ya koma ginin block da block mai shegen kyau na zamani ga ruwan bohol da aka tona bata sha mamaki bama sai da ta shiga cikin gidan, domin kuwa ya ƙawatu sosai bedroom ɗin INNO tayels da tayels ne ga wasu uban kujeru da aka zuba mata,haka ɗakin Baffa dana Sikayel ma, koda INNO take sanar da Jummo cewa Garkuwa ne ya musu ginin sosai taji daɗin hallacin daya mata ga kuma hajji daya biya musu, lallai dayi dace da miji na gari, koda taje gidan Mamma haka yake an gyara sa sosai, Mamma Sosai taji daɗin ganin Jummo tayi kyau tayi jajur abinta ita da yaronta, Jummo a wajen Mamma take jin wai ashe rana ɗaya za'a haɗa Auren A'illo da Zizah inda Ashe ALH Auwal ne zai aureta malamin Makarantar su, sosai Jummo taji daɗin hakan. Satin Jummo ɗaya suka tattaro suka dawo tare da su Mamma, inda a kuwa satin akayi auren Zizah da A'illo duk abinda Daddy ya yiwa Zizah haka ya yiwa A'illo sosai Mamma taji daɗin hakan, Mamma da Momy tamkar basu taɓa faɗa ba, kowa ya yafewa kowa sosai Mamma ta tausayawa halin da Momy take ciki na mutuwar ɓarin jiki. Allah sarki abun tausayi ɗan Adam yaji tsoron duniya, koda aka kai Zizah kano sosai suka sha mamaki ashe mijin ƙarya ya musu dashi mai kuɗi ne, bashi da komai asalinsa ma clener ne a wani ƙaramin asibiti dake jihar Kano a gidan haya ya ajiye ta irin gidan nan mai ɗakuna jere ban ɗaki ɗaya kitchen ɗaya, Zizah sosai hankalinta yayi mungun tashi, fir tace bazata zauna a gidan ba, sai da aka kira Daddy ya mata ba daɗi dole yasa Zizah ta hkr ta zauna cikin takaici da ɓacin rai ga ɗaki ɗaya, kujarar ta guda biyu ne kawai suka shiga, sauran kaya duk juyowa dashi akayi. Bayan wata ɗaya da auren su Zizah Jummo suka wuce aikin hajji, a wajen Aunty Zarah tabar Ahmad ta masa yayen dole, suka tafi sauƙe farali.. ✨✨✨✨✨✨✨✨ Bayan shekaru Bakwai Zaune take ita da Ahmad tana masa assignment da gudu Afnan ta shigo tana. " Ammi Ammi!!! Kinga Shahid ya ɗauka min teddy na ko." Murmushi Jummo tayi tare da miƙewa tana cewa Ahmad. " Ka ƙarisa assignment Ahmad bara naje na samu Shahid." Kama hanun Afnan tayi tare da cewa. " Zo muje na baki wata mamana ki rabu da Shahid." Dariya Afnan tasa suka shiga room ɗin yaran, kayan wasa ne da yawa a ciki, kama kunnen Shahid Jummo tayi tare da cewa. " Ina dai kai baka jin Magana ko Shahed, to zan bata wata ka kuma ɗauke mata sai na yanke maka hanu." Bakinsa Shahid ya tura, yaƙi kula Jummo, kasancewar sa miskilan gaske, wata Jummo ta ɗauka ta bawa Afnan ta fita tana murmushi tare da addu'ar Allah ya shiryi Shahid. Bedroom ɗin Ya Garkuwa ta shiga yana zaune da system a gabansa, murmushi ta sa tare da rungumosa ta baya tace. " Ina can yaranka na ƙoƙarin saka min ciwon kai kai kuma kanan zaune hankali kwance." Dariya yasa tare da jawo ta ta dawo ta gabansa murmushi ya saka ya ture system ɗin gefe tare da cewa. " Farin ciki na, kina nan ai bani da matsala da yara, ina sonki matata." Murmushi Jummo tayi tare da kai masa kiss a hanunsa tace. " Ina sonka rayuwata, kallonka na yaye min baƙin ciki, kaine jigona a rayuwa." " Kin zamo hasken gidana Jummo, har abada bazan taɓa daina ganin hasken ki ba." Dariya Jummo tasa tare da ƙanƙamesa cikin farin ciki domin kuwa Rayuwa ta mata daɗi. Tamat bilhamdulillah. Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin, abinda na faɗa dai-dai Allah ya bani ladansa abunda kuma na kuskure Allah ya yafe min. Ina roƙon gareku ƴan PAYMENT GROUP, da idan akwai abinda na muku a zaman mu ku yafe min domin rayuwa ta gaji haka zaka zauna da mutum ka ɓata masa baka sani ba. Sai ku biyoni a cikin sabon NOVEL ɗina mai taken AMINAINA KO ITA? Bissallam *UMMU NASMAH CE*