[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: Zaman 'ya 'ya na Na Mmn Annur Bismillahir rahmanirrahim Page (1) True life story Gajeran labari Wannan labarin gaske ne don haka banyi dan cin fuska ga kowa ba ,Abun da yayi dai-dai da rayuwar ka/ki to sanin gaibu sai Allah ba da kowa nake ba yanayin labarin ne yazo da haka .don Haka a kiyaye a cire zato ,domin manxon Allah (s.a.w) ya yi hani da yin zato ,domin shi zato shine mafi karyar zance. Sumayya shine cikyakken suna na ,ni daya Allah ya mallakawa iyaye na saboda haka suka dauki soyayyar duniya suka dora mun duk da wannan son da suke nuna mun bai hana su tsawatar mun ba yayin da nayi ba dai-dai ba ,Alhamdulillahi Nayi karatu na dai-dai gwargwado Bangaren islam ma haka nayi saukar Alqur'ani nayi littattafai da dama,Nidin nakasance ma'abociyar kunya da kamun kai domin bana iya daga idona in kalli maxa ko a hanya wanda ba haka yake a gun wasu matan ba. Tafiya nake yi cikin nutsuwa sai ji nayi ansha gaba na tare da mun sallama ,da kyar na iya daga kaina na amsa sallamar ina mai kokarin kauce wa wanda ya tare ni din ,don Allah ki tsaya tambayar ki zanyi yace dani tsayawa nayi ba tare da na dago na kalleshi ba .malama don Allah meye sunan ki idan bb damuwa? Lfy nace dashi me zakayi da suna na ne kake tambaya ta? Shiru ne ya biyo baya hakan da naji shine na dago kaina don ganin me ya haddasa shirun nashi ne karaff muka hada ido jinayi bazan iya cigaba da kallon nasa ba na sunkuyar da kaina ,sake mai²tawa yayi hadi da sake hada ni da girman Allah ,sumayya suna na nace dashi .masha Allah nice name Allah ya miki Albarka a hankali nace Ameen . Yawwa nace ba a wani unguwa kike ? A kurna nake layin masallacin juma"a na kurna Asabe ok :yace sai kuma yace dan Allah idan bb damuwa zanzo gobe insha Allah inaso xan miki tambayoyi ne idan bb matsala saboda babu dadi ka tsayar da yarinya a titi wannan ba mutunci bane Kwatancen gidan mu nayi masa na tafi saboda yamma tayi mun sosai a hanya .Saboda mu a gidan mu bama kaiwa magariba a waje sai dai idan da babban dalili. Layin gidan mu na shigo ina sauri duba d magariba ta fara kawo kai ina tsoron ayimun fada ,bana son bacin ran iyaye na. Cikin gidan na shiga da sallama, amsawa umma ta tayi tace sannun ki d dawowa da yawwa na amsa mata na karasa na xauna a kusa da ita nace umma sannu da aiki yau fa ana zafi a garin nan dariya umma tayi tace sumayya zafi ai lokacin sa ne Allah dai ya fitar mu lfy nace mata Amin. Bayan kwana biyu ya kama ranar juma'a kenan ina tilawar Alqur'ani muka ji sallama amsawa mukayi nace wanene? Sai wani yaro yace wai wanine a kofar gida yace ana kiran sumayya gaba nane ya fadi domin ni na manta da mun hadu da wani wlh .umma ce ta kalleni tace sumayya waye kika baiwa damar zuwa gunki ba tare da sanin mahaifin ki ba? Ai fa nan idona ya raina fata nace wlh umma wani ne ya tare ni a hanya na dawo daga hotoro gidan hajiya mamy to shine ina sauri kar magariba tayi mun a hanya shine fa na sanar da shi kwatancen gidan nan banyi tunanin zaizo ba kwata² . Shiru tayi can kuma tace inje inji me ya kawo shi.jikina a sanyaye na tashi na sanya hijabina na fito daga dakin kallona naga umma tayi sai kuma naji tace kije mana ana jiranki tom nace na fita kofar gida na same shi a zaune akan wani dutsi sallama nayi mishi nace dashi ya shigo zauren gidan namu baiyi musu ba ya shigo na gaishe dashi ya amsa mun sai wani murmushi yake yi . "Sumayya nazo gurin ki ne badan komai ba sai dan in tambaye ki wani abu idan Allah yasa zan dace to, sumayya na ganki ne naji ina sonki ina kaunar ki idan babu wanda ya riga ni to ina da burin in aure ki" ai tunda ya fara bayani gaba na yake faduwa har ya Kai aya a bayanin nashi. Da farko dai gaskiya sai kaje ka sanar da mahaifina idan ya amince to shikenan bb matsala,jin jina kai yayi yace gaskiya kin burge ni sosai domin an shayar dake tarbiyya marar algus nagode da wannan bayanin naki kuma insha Allah Zan neme shi inji Allah yasa dai ya amince mun ,ahankali nace amin lokacin da zai samu Abba na a gida na fada mishi mukayi sallama na shigo cikin gida na yiwa umma bayani tace to Allah ya zaba abunda yafi alkhairi Amin nace a zuciya ta. Washe gari asabar bawan Allahn nan da ban san sunan shi ba yaje ya samu Abba na da batun ya ganni yana so ya aure ni idan ya amince kuma yana neman izinin shi akan zaizo gurina mu dai dai ta,Abba na yayi na'am da shi domin ya yaba da nutsuwar shi sannan kuma yana masa kallon mutuman kirki. Lallai yau farar rana take a gunshi domin farin cikin sa bai boye shiba yayi ta yiwa Abba godiya da ftn alkhairi. Amir gidan su ya nufa yaje ya sanarwa da mahaifiyar shi komai itama murna da farin ciki tayi gami da yiwa dan nata ftn alkhairi .sosai Amir yaji dadin Addu'ar nan ta mahaifiyar shi , Washe gari Amir yazo guna da labarin cewa mu dai daita kanmu idan har na aminta dashi to tabbas mahaifina zai bashi aure na.nidai da yake ba wani sabawa nayi da tsayuwa ko doguwar magana da maza ba gaskiya a takure nk jina shiko sai surutu yake mun ina dan basarwa Da zai tqfi ne yace dani wai daga zuwan farko har kin fara laifi,gabana ne ya fadi nace wani irin laifi kuma,murmushi yayi yace ko ki tambayi suna na ko toko bakya yi da ni ne? Yi hakuri nace dashi ina so in tambaya to kunya ne ta hanani in tambaye ka plss kayi hkr waiiiii ai fa Amir ya samu television zuba mun ido yayi yana kallona rufe fuska ta nayi yamun dariya yace kyau kike karayi idan kina magana gashi muryan ki dadin sauraro gareta. Hmmmm nima murmushin nayi nace banda zolaya fa ,babu wani zolaya .sallama mukai da juna na shiga cikin gida shima ya tafi nasu gidan. Soyayya ta kullu tsakani na da Amir domin har manya sunyi magana an tsaida lokacin auren mu inda mahaifina yace yana son bikin akai shi bayan damuna lkcn amfanin gona yazo gida,ba suyi wani ja'inja ba aka amince da bulatar ta mahaifina. Akwai wani bawan Allah da ya nuna yana sona a anguwar mu sunan shi nasir ,nasir mutumin kirki ne bashi da abokin fada mutum ne mai rikon Addini lkcn da yazo gidan mu ya bayyana wa Mahaifina bukatar sa ta neman aure na anan Abba na yake sanar dashi yayi hakuri wllh wani ya riga shi Amma yana masa ftn alkhairi Allah ya bashi wadda tafi ni alkhairi.Amin ya amsa wa Abba sukai sallama cikin mutunci ya tafi. Bayan Abba ya shigo cikin gida ne yake sanar da umma ni kuma ina daki wllh alkcn naji ina jin tausayin shi domin idan kana so baka samu ba bashi da dadi amma kaso a soka yana da dadi.ftn alkhairi na mishi araina ina mai tausaya mishi .wuni nayi a ranar ina tunanin nasir da kyawawan halayen shi sai kuma bugun zuciya ta da yake hau hawa yayin da tunanin nasir ya bijiro min [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA. NA mmn Annur Page (2) True life story Gajeran labari Hakika ina jin soyayyar nasir a kasan raina wanda nasan abun da zuciya ta take neman yi ba abun da zai iyu bane duba da zuwan magabatan Amir duk da ba sanin dukkan halayen na Amir nayi ba ,shiko nasir nasan wasu daga halayen shi mutum ne mai rikon Addini da sanin ya kamata daya ke anguwar mu daya dashi likita ne sannan idan ya samu lkc yakan je islamiyyar anguwar mu ya koyar da maza bayan sallar magariba .A gaskiya duk matar da Allah ya mallakawa nasir tayi dacen samun miji mi hakuri da kawaici . Kwanci tashi babu wuya agun Allah ina kokarin boye Soyayyar nasir a raina duba da yadda Amir ya ke kula dani da bani kulawa ta musamman,Na dage da yin Addu'a akan Allah ya cire mun soyayyar wanda bai san ina yi bama ,hakika Amir shima gwani ne wajan iya soyayya da nuna kulawa domin har waya ya siyo ya bani da kyar na kar6a shima sai da naga ranshi ya 6aci tukun na na kar6a. Bayan na nuna wa umma ne sai tace na ajiye ta sai Abba ya dawo Sai ta nuna masa idan ya amince to sai in rike ta idan kuma bai amince ba to sai dai a mayar masa Bayan Abba ya dawo daga masallaci ne umma ta kawo mishi Abinci da ruwa suna zaune yana cin abincin umma tana mishi fifita suna fira kasancewar babu nepa a garin sun dauke. Anan umma take sanar dashi zancen wayar da Amir ya kawo mun,dan jimm yayi kafin ya nisa yace shin kina ganin rike wayar babu matsala ? Duba da yadda xamanin nan waya ta rugurguza wa matasa tarbiyya duk da mijin da zai aure tane amma bana so ace sumayya taga wasu abubuwan da bai dace ba. Bayan ya kai aya a jawabin nashi ne umma tace to Abban sumayya sai nake ganin in za'a amince mata wajan rike wayar to ina ga sai a ja mata kunne duk da nayi yakinin sumayya ba zata karkace wa tarbiyyar da muka dora ta akai ba kaga wani lkcn shima yaron nan Amir ba sai yana yawan zuwa gun nata ba idan da wayar a hannun ta sake gaisawa ta wayar. Can dai Abba ya jin jina kalamin bakin umma yace to shikenan Allah yasanya alkhairi ,amma fa da sharadin kar inga irin wannan abubuwan da basu dace ba ,umma tace in sha Allahu hakan bazai faru ba .yace shikenan tarike . Har na kwanta naji shigowar umma daki suna na naji ta kira ko tunsnin ta ina bacci ne amsawa nayi gami da tashi zaune miko mun wayar tayi tace gashi Abban ki yace ki rike wayar amma kar yaga abun da bai dace a cikin ta ba amsa nayi nace mata nagode kunna wayar nayi naga har da sim card aciki checking balance nayi naga da kudi a cikin sim din har number shi ya sanya a ciki yayi saving da noor . Aiko kamar jira yake in kunna kiranshi ya shigo dagawa nayi da sallama a baki na a kasan makoshin sa naji amsa sallamar har da ajiyar zuciya gaishe shi nayi ya amsa da kwaikwayon murya ta ,wata siririyar dariya na saki nace zolaya ta kake yi ko? Yace a a ni wane in zolayi sarauniya cikin kwaikwayon muryar tawa Hmmm nace gami da yin shiru shima a nashi bangaren shirun yayi ,katse shirun nayi nace dashi saida safe.dakatar dani yayi yace karki kashe fira nake so muyi shiru nayi can dai nace to ina jinka murmushi yayi yace to kimun firar mana , Haka nace kaine zsks fara mun to shikenan ni bszsn gaji d miki fira ba kece dai xaki gaji ,nima haka nsce bazan gaji ba ,nan fa ya dage yake bsni labari tun ina nonnokewa har dai na saki jiki na biya shi muke fira ai bamu san lkc ya ja da yawa ba sai da yace bari in barki kiyi bacci karki makara tashi da asuba.sallama mukayi yace sai na fada mishi kalmomin da zasu sanya shi bacci da wuri kunya ce wllh ta lullube ni nace I love u. Haka yace bsya son jin tsohuwar kalmar nan so yake in fada mishi abun da ba lallai an taba fadawa wani saurayin ba ,dakyar nace masa good 9ht wish u nice sleep nd sweet dreams ajiyar zuciya yy yace ya gode sai da safe amsa wa nayi na kashe wayar . Wasa-_wasa haduwar mu da Amir har mun dau tsawon wata uku tun ina jin kunyar yin magana da Amir a waya har naxo na daina don in bai kira ni da wuri ba da safe kenan to ni nakan kira shi inji lfyr shi .Alhamdulillah mun fuskanci juna dashi sosai mun shaku don a ganina bazan iya rayuwa babu Amir ba ,ya zama ni na zama shi ya zama jinin jikina [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA. Na mmn Annur . Page(3). True life story Gajeran labari Ban garen nasir idan mun hadu mukan gaisa dashi Amma ba wai muna sakarwa juna fuska bane akwai kanwar shi a anguwar mu lkc xuwa lkc taka zo gdn mu da yake kawata ce tun yarinta to fa daga ji ance yayan ta yana sona shikenan ta sarkafi zuwa gidn mu Idan taxo bata da zance sai na yayan ta nasir tun bana kula ta har nazo na biye mata sai mu kwashe mintoci muna firar shi amma fa ba wai ina jinsa a raina bane bana so ace na wulakanta mata yayan ta saboda babu dadi koba maganar soyayya to nasir dan anguwar mune sannan mu gdn muna mutunta mutane. Lokacin bikin mu yana matsowa nida Amir anan Abba yayi wa umma xancen kayan daki da na hidimomin aure ,kudi ya ware masu yawa umma da kanwar ta aunty masa'uda sune suka je suka dubo kayan dakin da kujeru har da freezer doguwa sai ban garen kayan kicin ba wani tarkace aka yiba amma fa kayan kana gani kasan na masu aji ne dan wllh kaya ne masu kyau masu tsada . Tarkace dai na siyayyar aure anyi shi kamar ba gobe . Kar Ku manata ban sanar da Ku cewa Amir ba wani dukiya ne dashi ba yana da rufin Asiri ne dai dai gwargwado malamin makaranta ne sannan yana sana'ar sai da kayan drinks ne atakaice dai shago ne karami yasa karamin fridge sai lemuka da pure water da snacks a shagon Alhamdulillah babu laifi domin ana samun ciniki sai dai bawani can ba. Biki ya rage saura wata daya mutanen gdn su Amir suka kawo kayan lefe Akwati ne guda biyar da kit guda daya.babu laifi yayi kokari gaskiya kayan ciki babu kananu aikwa an rufe bakin masu tsegumi domin akwai wani lkc wata taxo tace wa umma yaron nan fa ba iya rike sumayya xai yi ba domin ba wani sana'a babba gareshi ba mlamin makaranta ne.anan umma tayi dariya tace to banda abinki ai babu wanda ake haifa da kudi kowa aduniya Allah ya ke bashi ni banga abun magana akai ba ta iyu lkcn yin kudin nashi ne bai yiba ni indai mutum yn da tsoron Allah da addini to sauran ya samu a hankali .anan dai matar ta tafi gwiwa babu kwari Amir ya bamu kudin anko da na 'Yan mata Babu laifi 32k ce nidai da nasan bashi dashi to ban wani damu ba saboda Abba yace abun d Amir din ya bada in bai isa ba to in sanar da umma in yaso Abban shi zai bada . kawaye na kwa sun sha surutu akwai wata daga cikin su mai suna Aslamiyya haka tace mun sumy wllh da in auri talaka gara in auri mai kudi ko da kullum breek fast din shi shine fella mun mari mitss taja tsaki auren talaka ai bs riba sai dai faduwa tunda ranar da babu sai dai ace shirya kuje Ku gida gaishe dasu umma kinga ai bai fito yace miki babu ba da siyasa ya kora ki gdnku cin da'amiy, Dariya wasu daga cikin mu suka yi suna cewa zancen ki haqqun Aslamiyya suka kara kaurewa da shewa . Shirun da nayi nida karima musa ne yasa wasun su sukayi shiru ,raina ne ya 6aci sosai da zantukan banxan su Aslamiyya ,nace dasu waye a cikin ku aka haifa da dukiya ? Ina ga ai kowa a duniya Allah ya bashi KO? To ku iya bakin ku ni bazan lamunci cin mutunci wa mijina ba .sannan in maganar talauci kike ai Amir ba talaka bane,ke bari kiji akwai talakan da yafi mai arzikin kwanciyar hankali nawa ne masu kudin suna nan da kudin amma basa jin dadin shi jinya duk ta cinye kudin har kike har gagin gara mai kudin da zai ke marin ki duk safiyar Allah to wllh ki sake hali. Ba wani hali da zan canja Sumy ,ni fa akan kudi to sai abinda ya turewa buzu nadi kudi ai sune rayuwa mutum yy abunda yaga dama dasu . Yau Alhamis yau ne kamun Amarya ,kar kuga irin kyan da amarya tayi ai fa mutane suka fara fadin masha Allah tabarakallah gaskiya amarya tayi kyau shigar laffaya ce sukai ita da kawayen ta,ita kalar tata blue black sauran kawaye kuma Onion colour gaskiya abun ya kawata duk masu kallo ni kaina abun ya burge ni dan sai da na kudurta a raina idan za'a yi bikin Aisha mamu zan bata shawarar suyi irin wannan shigar domin shigar ta dace d shigar al'adar bare bari sannan kuma shiga ce wadda baza ta nuna tsiraici ba . Duba da yanxu 'yan matan wannan zamani gani suke sun cinye idan suka bayyana tsiraicin su,ita fa shiga ta mutunci mutun ta kai ne da nunawa duniya cewa ke daga gidan mutunci kika fito sannan iyayen ki jajir tattu ne wajan kula da tarbiyya. Wllh banga waye wa ba ga matar da za take bayyana tsiraici a idon duniya ba .idan har waye wa ne to hakika Akuya tafi kowa waye war kai domin ita bindin ta ma sama ya dage al'aurar ta a bayyane. Wllh duk matar da ta waye tasan kanta to ta suturta kanta sai ta samu salama a cikin rayuwar ta .Allah yasa mudace. Ango yazo shida tawagar sa shima babu laifi tabarakallah yayi kyau shima shadda ya sanya kalar laffayar Sumayya blue black yayi kyau da yake kalar fatar shi fari ne sosai sai shigar tasu ta dace da juna. Anyi photuna Amarya da Ango sannan da abokan ango da kawayen Amarya,bayan wani lkc kawayen Amarya suka fita daga baya suka shigo kowacce da kaskon turaren wuta mai kamshi wanda Amina mamu take yi turare ne mai kamshi da kama daki .nan da nan guri yadauki kamshi mai dadi kawar Amarya karima da wasu kawayen ne suka fara raba kayan kamu irin su turaren wuta wanda Amina mamu ta hada da kanta da lalle mai kyau sannan da key holders gaskiya abun ya kawatar domin a tsanake ake gudanar da komai. Bayan angama kamu ne aka maida amarya d kawayenta gida sai kuma gobe in shaa Allah . Washe gari Juma'a bikin farko inda kawaye suka hada wa sumayya shagali sunce dinner za'a yi sun kama gun da zasu gabatar shima sun sha hidima domin amare ankon farin lace suka yi ita kuma amarya tasa jan lace gaskiya fadar irin kyawun da suka yi ma bata baki ne domin akan kan ka in ka hasko abun to zaka kiyasta kyan ne a idon zuciyar ka .sun rarraba cake da samosa da spring roll,sun sha picture Kala kala kamar ba gobe dare ya fara yi inda kowa aka maida shi gdn shi taro kuma sai na gobe in Allah ya so. Yau take Asabar inda za' a daura Auren sumayya Abba Hadi da Mubarak Ali hashim (Amir) . Da misalin karfe 11 na safe aka gudanar da daurin auren akan sadaki Naira dubu dari biyu lakadan ba Ajalan ba .aifa nan maroka suka fara kakatin nasu suna kada ganga suna tayi da bakin su. Bakin Ango yaki rufuwa Sai gaggaisawa ake da jama'a ana masa Allah ya sanya Alkhairi yana ta godiya sai fama yake da babbar riga Bangaren sumy Amarya ana daurawa gaban ta ya shiga dukan tara tara tana cewa shikenan itama ta shiga sahun matan aure Allah kasa inyi biyayya kamar yadda aka umarci mace ta yiwa mijin ta biyayya .Gudar da aka yi ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi Allah ya sanya alkhairi ake mata tare da ftn samun zaman lfy da zuri'a dayyiba. Da yamma sun sha kyau sosai sun yi kwalliya kowa kaga ni ji da kansa yake yi a cikin kwalliyar su to bb laifi domin sunyi kyan d ake tunani koma fiye da tunanin mai karatu. Taro ya watse domin shirye shiryen Kai Amarya ake yi inda aka sanya ta taje ta sake wanka mai shafa lalle ta shafa mata wani kaya naga kanwar umman ta ta dauko mata shadda ce da akayi wa dinki na kece raini doguwar riga ce akai mata aka sa mata hijabi aka feshe ta da turare masu kamshin dadi hannun ta aka kamo aka Kai ta dakin Abba don yin nasiha kamar yadda yake a dabi'ar mu ta mallam bahaushe nasiha suka mata ta ratsa jijiyoyi da jiki sannan aka farfada mata dubarun xama da miji da dangin miji .sosai sumayya take kuka saboda ko bulaguro bata taba yiba dan haka rabuwa da iyayen ta sai ta zame mata tamkar an rabata dasu ne har abada.Allah yayi miki albarka ubangiji Allah yasa gidan kine Allah yabaku zuri'a dayyiba ,ku tashi kuje dakyar aka janye ta daga jikin umman ta suka kaita cikin mota suma suka shiga aka kaita gidan ta. Da kafar dama ta shiga bakin ta dauke da bismillah sannan sai da ta karanta Ayatul kursiyyu da Addu'ar shiga gida sannan ta shiga cikin gidan dakin ma da za a shiga da ita saida ta yi bismillah tashigar da kafar dama sannan ta shiga .Abakin gado aka ajiye ta sannan sauran 'yan uwa suka dan gyaggyara mata wasu abubuwan a gdn sannan suka mata sallama suka tafi kuka ta saki tace ita dai kanwar ummar ta ta zauna su kwana 😳 gdn ku nace sumayya ja'ira dan iyayen ki kin taba ganin an kwanar wa Amarya a gd ? Sai kace al'adar mutanen yobe a a baza a fara a kan muba muma da haka muka girma .kawar ta karima kadai aka bari itama idan an rako ango sai su maidata gida . [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA Na mmn Annur Page (4) TALLA INA KUKE MA'A BOTA KWALLIYA DA SAN CANCAREWA DA SHIGA TA KAMALA SHIGAR DA IN KIKA JE WURI BABU MAI MIKI KALLON DAWA MUKA ZO, HAJIYA TA KIZO KI GWANGWAJE KANKI DA YARA DA MAI GIDA DA KAYAN MU DOMIN MU DIN MUNYI FICE WAJAN KAWO MUKU KAYA MASU KYAU MASU QUALITY WANDA IN KIKA SIYA BAZA KIYI DANA SANI BA. MUNA DA LACES, SHADDA, ATAMFOFI MAYAFAI, SARKOKI, TAKALMA NA MAXA DA MATA, ZANNUWAN GADO, LABULAYE, TARE DA TURAREN WUTA NA GARWASHI, MUNA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI. GA MAI BUKATA YA TUNTUBI WANNAN NUMBER 09069615587 dan Allah idan baki shirya siyan kayan muba to babu bukatar kira ko chatting don 6atawa juna lkc. Ngd. Bayan an rako ango Abokan shi sun musu nasiha sosai dan gane da kowa ya yi kokarin sauke nauyin da Allah ya dora musu.daga haka su kayi sallama suna yiwa ango tsiya,karima suka yiwa magana suka tafi inda Amarya ta fara sheshshekar kuka hakuri ta bata tace da ita gobe in shaa Allah da wuri zata zo haka dai suka rabu suna masu kewar junan su . Asuba ta gari Sumyn Amir. Garin Allah na wayewa sumy ta fito ta shiga kicin tana duddubawa wai ita za ta girka musu break fast,fitowa yayi yace tayi hakuri ta zo su tafi daki zuwa anjima za'a aiko daga gidan su to tace masa suka koma daki don bacci take ji .ko minti biyar ba a yiba bacci yayi awon gaba da su basu tashi farkawa ba sai wajan 10 am. A gurguje suka yi wanka suka shirya kana ganin su kaga amarya da ango sosai sumy tayi kyau wani sky blue lace ta sanya tare da tsara daurin dankwali na zamani zama sukai suna fira gwanin ban sha'awa yana tambayar ta irin abubuwan da take so da wanda bata so zayyano masa tayi shima ta tambaye shi abun da yake so da wanda baya so shima sanar da ita yayi .basu wani dade suna firar tasu ba akayi nockin kofar gdn su tashi yayi ya je dan ya bude tambaya yayi yace waye? Nice yaji muryar kanwar shi ,bude gidan yayi tashigo hannun ta dauke da kula ta abinci ,karbar daya yayi itama ta karaso da dayar a hannun ta Shiga dakin suka yi sumayya ta karasa ta karbi na hannun mijin nata ta ajiye a kasa itama ta'iba ta ajiye na hannun ta xama tayi suka gaisa da yayan nata sannan ta ce aunty sumayya ina kwana ? Itama amsawa tayi cikin sakin fuska da walwala sannan ta tambaye ta mutanen gidan su ,lfy Alhmdllh tace da ita .shiru suka yi daga bisani sumayya ta tashi taje kicin da kulolin ta bude su wow tace ganin abunda take so wato funkaso da miyar taushe wadda tasha nama da kayan kamshi zuba musu taushen tayi a cikin kwanon kass sannan ta zuba funkason a food flask ta kawo musu Kwantaina roba ta dauko tare da ruwa a cikin ta don dauraye hannu bayan sunci abicin ne sun gama sai Amir yace ta'iba ta tashi su tafi yana so yaje ya gaisa da baki aikwa nan sumy tace wllh tsoro take ji gida ita daya kawai yaje yabar ta'iban su zauna ta dauke mata kewa ,to yace mata .sukayi sallama ya tafi gidan su .. Sumayya tashi tayi ta dauko wayar ta ta nemo gun photuna ta baiwa ta'iba tana ganin pic din bikin su Kallo ta kunna gami da mikewa a kan doguwar kujera ta dan kwanta tana tunanin gidan su Allah sarki su umma ta nayi kewar ku sosai . A kwan a tashi babu wuya a gun Allah sumayya ta samu ciki sai dai yana wahalar da ita sosai ga yawan amai gashi bata son miya a abunci ko za tayi girki to sai ta toshe hancin ta da dankwali take samun damar yanka albasa ta yi miya .sai kwadayin tuwo dumame kai ko brush tayi sai ta wuni tana amai sai dai a nemo mata aswakin darbejiya to fa aranan zata wuni lfy , Cikin sumayya ya shiga wata na uku sai aka kara samun wani fi'ilin laulayi domin dan cikin ta zarnin fitsari yake so dadin shi take ji har wani ajiyar zuciya take yi yayin data shaki zarnin nan Kai jama'a wllh iyaye mata suna cikin yanayi kawo kan laulayi rainon ciki da tsufan shi zuwa haihuwar shi ,ranar da kake so ka rabu da cikin wato ranar da zaka haihu tofa shima anan gixo ke sakar domin ranar akwai fargaba da tashin hankali,wata tayi nakuda mai tsayi wata kuma gajerar nakuda tofa ba nakudar ba fasowar kan dan jaririn Kai tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki ubangiji kasa mu gama haihuwa lfy ka rabamu da samun tangar da a cikin ta .wllh baka taba sanin muhimmancin iyaye sai ka haifi naka musamman mace ,kaiii ni dai kam haihuwa tana bani tsoro ybangiji yasa mudace Amin. Gida yau take son zuwa idan ta wuni a can daga nan sai ta wuce gidan iya bbr Amir itama ta gaishe da ita, Bayan taje gida ne murna ta kaure tsakanin iyayen biyu da tilon diyar tasu sai farin ciki suke dan ganin ta cikin kwanciyar hankali suna nan nan da ita mutuniyar uwar shagwaba nan fa ta narke musu sai shagwaba take yi san ranta. Bayan sallahr la'asar ne tace musu gdn su Amir zata wuce daga can zasu wuce gida Sallama ta musu dakyar ta tafi tana mai jin rashin dadin rabuwa d iyayen nata Napep ta tare ta mai kwatancen gidan bayan ta sauka ne ta dauko jakarta da kullin kayan daddawa da kubewa d kuka sai man shanu sannan ta baiwa mai napep kudin shi. KOfar gidan ta karasa gami da yin sallama ,amsawa akayi ai ta'iba tana ganin itace ta raho da gudu ta rungumeta hajiya iya tana mai hararar ta tare da fadin saikin kayar da ita irin wannan gudu haka ai saiki jimata ciwo ,sumayya ce tayi murmushi tace wa hajiya laa hajiya bb komi ai ta'iba tawa ce munyi missing din juna ne shiyasa nima sai dokin inxo in ganku nake .dariya hajiya iya tayi ,taji dadin furucin surukar ta ta don hkn ya nuna macen arziki ce . Sannu ta mata tace ta karaso ta zauna ,zama tayi suka gaisa take tambayarta mutanen gidan su lafiya tace mata sannan ta mika mata sakon umma ,godiya tayi mata tace kai naji dadin wannan kyauta da tabani kai Allah yasaka da alkhairi nagode sosai. Fira suke dayake hajiya iya bb ruwanta mace ce mai san mutane shikenan sai zaman nasu yy dadi domin sumayya bata da kiwar aiki sarai dagewa tayi ta yiwa hajiya iya ayyuka .sai sanya mata albarka takeyi da yi mata fatan sauka lfy. Bayan sumaiyya ta koma gida ne sai ta tarar da Amir ya riga ta dawowa har ya musu shimfida,sannu yayi mata ya hada mata ruwan wanka don ta karfi a jikin ta. Godiya ta mishi kana ta je tayi wanka.kwanciya take son yi amma abu ya gagara marar ta ciwo bayan ta ciwo ta rasa ina ne ma gun da yake ciwon sai salati take gami da fadar lahaula wala quwwata illa billah.Amir hankalin sa ya tashi ganin halin da sumayya take ciki ai nan da nan ya shiga makotan su ya kira hajiya deluwa don taga ni shin haihuwa ce ko kuma wani abun ne na daban, Hjy deluwa tsohuwar ungozoma ce tasan kan aikin ta na goxanci ,tana ganin halin da sumayya take ciki ta tabbatar da haihuwa ce asibiti tace su tafi saboda gudun matsala gashi kuma haihuwar fari ce ,na'am yayi da shawarar ta hjy deluwa ,makocin sa ubale mai adaidaita ya samu yace ya taimaka masa iyalin sa bb lfy yana so ya kaisu asibiti,da to ya amsa ta koma gida ya dauko key suka rankaya asibiti tun sumayya na gane wasu abubuwan har ya xamana bata gane kowa duk ta galabai ta.sannu yake mata bayan an sauke su ne nurses suka taho da gadon daukan marar lfy aka shiga da ita labour room aifa ciwo nan ya dawo gadan gadan ba a dau awa biyu ba sumaiyya ta haihu Allah ya azurta tasu da kyautar yara biyu 'yan maza kaii masha Allah yara da uwar su gwanin sha'awa domin sai da aka gyaresu sannan aka yiwa su Amir albishir. Murna kamar suyi me hjy deluwa kam ciki ta shige ta xauna kusa da sumayya tana mata sannu sannan ta dauki yaran ta yi musu addu'o'i ,dakin hutu aka ce wa Amir ya shiga a miko masa yaran hamdala ya shiga jerawa Allah madaukakin sarki da wannan kyauta da ya musu ba tare da yayi shawara da kowa ba . Bayan an miko yaran ne Amir ya kura musu ido yana jin kaunar yaran nashi a cikin jinin jikinsa godiya yayi ta jerawa rabbi sarki ga gara misali,Addu'a yayi musu kana yayi ta daukan su a photo sosai ya shagala a gun yaran nashi. Ba'a dau lokaci ba aka basu sallama suka dawo gida,Amir da kanshi ya hura wuta ya hadawa sumayya ruwan wanka na jego hajiya deluwa ta taimaka mata suka shiga toilet ta mata wanka na musamman tare da gasa ta sosai ita kanta sumayya taji dadin wankan duk wani ciwo na jikin ta yayi kaura ya tafi sai dai abun da ba'a rasa ba. Kan kace me dangi sun zo ganin twins don a dangin su Amir ba'a taba haihuwar 'yan biyu ba kai koda 6arin su ba a ta6a yiba.kowa sai San barka yake yi ana ta yiwa sumayya barka da arziki Allah ya raya yasa masu taimakon musulunci da musulmai ne Allah ya bada lfyr shayarwa Amin. Siyayya ta musamman Amir yayi wa mai jego da yaran sa,domin kayan barka ne aka musu shi na musamman ita kanta mai jego akwati seti daya yayi mata sai twins suma kowa da akwatin shi kayan su iri daya kai hatta da zobe na zallar ruwan azurfa iri daya ne sai dai stone din jiki da ya ban-banta hassan shine stone din shi "ja" sai hussain nashi stone din fara kowa an sanya mishi a yatsan shi na tsakiya hannun yayi kyau kamar dan su aka yi zoben Atamfofi aka zuba wa sumayya guda biyu sai lasuna biyu shadda daya material guda biyu da mayafi sai hijabi jalbab guda biyu sarka da dan kunne d abun hannu ,gaskiya babu laifi Amir yayi bajinta kaya sunyi babu karya adai dan talaka a wannan zamanin sai dai muce Alhamdulillah . Yau take suna an yanka manyan raguna guda biyu an radawa yara suna hassan shine Ibrahim sai Hussain shine Abdullahi za'a kira su da hassan da hussain din su. Can na hango mai jego da yaranta ana daukan pic da sauran mutane maijego ta dankara wani hamshakin lace wanda Amir ya siye su a gun mom hibba don kayan ta indai ka siya to babu dana sani domin kaya ne na daukan wanka duk wanda ya kalli sumayya yasan ta sa suttura mai kyau da tsada ta zama big mama hannun ta da wuyan ta yasha kayan alatu ita kanta sarkar a gun maman Afrah ya siye ta gaskiya bb laifi maijego ta yi kyau ita d yara sai dai muce allah ya raya mana Kyautattuka ta same su a gun mutane da dangin su an raba kayan suna da calendar mai dauke da hotunan 'yan biyu a jiki su karima musa anxo gidan Amir anyi wankin ciki domin taci ta koshi tasha lemuka San ranta tayi guzirin wasu domin bb a House. Taro ya watse anbar mai jego da yaran ta sai mai mata zaman wanka kanwar baban ta Aunty saratu mace mai kirki da dattaku tana kula da sumayya da yaran bata gajiya da hidimta musu Amir yana yawan cewa ki rage ayyukan nan Aunty saratu nima fa na iya wasu abubuwan sai dai tayi dariya tace aikin ai danshi na zauna da babu ai da na tafi gidana nima [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA Na mmn Annur Page(5) Wannan page din dukan shi na sadaukar wa mutane biyu mutanen Amana masoya a gare ni baki na bazai iya ba zai iya wassafo kaunar su a gareni ba,Fa'iza Abubakar (mmn Afrah) marubuciyar littafin 'YAR ZAMAN WANKA d KAZAMIN MIJI' Sai Hajjaju mutanen saudiyya Bilkisu Badamasi (mmn meenal) Allah yasa Amintar mu ta dore har gidan Aljannah. ASLAMIYYA Aslamiyya likkafa taci gaba inda ta samu wani Alhj Adnanu yake kashe mata 'ya'yan banki nan fa take cin karan ta babu babbaka domin har kayan daki ya canja wa innar ta karima irin matan nan ne masu dagawa musamman da taga an canja musu kayan daki sai ta fara feleke idan tasan kai ba mai kudi bane to fa ba zata saurare kaba kai ko a cikin kawaye ba kowa take hulda da shiba ita a cewar ta masu kudi sune da duniyar talaka kwa yana duniyar ne amma ba jin dadin ta yake ba. Yau dai sun shirya da Alhaji Adnanu domin kaita shop rite don yin siyayyar kwalam d makulashe,anan ne ta hadu da tsohon saurayin ta Kasim yana xaune a kofar shop rite din inda kasim yake sanye da uniform na shedar cewa gadi yake musu a nan din Wani kallo ta bishi dashi wanda shi bai ma san tana yi ba kallon kurar da ta dauko su ma bayyi ba aiko ta shaka da yawa ita anata tunanin zai gigice ya shiga wani hali idan ya ganta d Alhajin ta. Bata san cewa Kasim shi baya zafafa abu idan ya janye a kan abu to ko da zai shiga damuwa baya waiwayar abun duk yanda ya kai da son Aslamiyya kwata kwata ta fice masa a ranshi Shiga ciki sukayi sukayi siyayya ta kece raini har innar ta ta daukarwa kayayyaki gun biyan kudi suka karasa aka musu total din kudaden kayan Atm ya zaro daga aljihun shi ya mikawa cashier ya dau kudin tare da mika masa Atm din sa fitowa suka yi kowa hannun sa dauke da ledoji na kayayyakin makulashe,a bayan motar ya zuba kayan kana ya bude mata murfin motar ta shiga saida ta zauna sosai ya dan leko da kansa kadan "yace ranki ya dade kin xauna sosai na rufe motar? " Kanta ta daga alamar ta zauna daram ,rufe kofar yayi tare da zagayowa ya shiga maxaunin driver ya bawa motar wuta suka tafi.hmmm su karima an samu duniya ba 'a tunanin me gobe xata haifar. A kofar gidan su yayi paking sun dade a cikin motar kafin suyi sallama ya fito ya , tsegumi da shiga shara ba shanu. Yara ta samu suka shigar mata da kayan kana ta juyo tace da shi "Baby sai munyi waya ko"? Gyada kanshi yayi tamkar namijin kadangaruwa ,mota ya shiga ya ja da gudu yana tuki yana murmushi Aranshi yana ayyana yanda lkc daya yarinya karama ya sace zuciyar ta da kudi Alhalin tana da mai kaunar ta tsakani da Allah. Bata san shigo shigo babu zurfi yayi mata ba. Aslamiyya kwa tana shiga cikin gida ko sallama babu ta fara kwada wa Innar ta kira cikin isa da kasaita,inna tana jin kiran ta fito da sauri tace "a a 'yar albarka kindawo? Sannu sannu Allah ya kare min ke 'yar nan " murmushi Aslamiyya tayi ta fada cikin daki sannan innar ta ta shigo da kayayyakin suka shiga dubawa inna sai yaba kayan take yayin da taci gaba da daga kayan . Kalubale Ya kamata iyaye mu sani wannan kwadayin da muke nunawa ga abun da yaran mu 'yan mata suke bamu to hakika ba hanya mai 6ullewa bace domin hausawa sunce "somi,somin hauka zubda yau" to mu yiwa kanmu karatun ta nutsu tun kafin duniya ta koyar damu, Maza fa a wannan zamanin wllh basa yin babbar kyauta haka kurum ba tare da sun fanshe da wani abun ba don hk iyaye hattara wai dan yarinyar ki ta fita zance ta shigo miki da wani nau'in kayan kyale-kyale sai ki hau murna ke yarinyar ki ta ciri tuta ta kerewa sa'an nin ta. Da haka² zaki rushe ginshikin ginin da kika dau shekaru kina gina wa,to yarinya in ta shigo gida da kaya baza ki tuhume ta ba dan gudun 6acin ran ta.wai ni kam me muke son maida yaran mune karuwan gida ? Shin kina da tabbacin yarinyar ki saurayin nata mutuman kirki ne ? Ita fa tarbiyya rainon ta ake bawai wasa ake da ita ba wallahi duk uwar da tasan yarinyar ta tana da biye biyen samari to tun wuri tayi kokari ta dage ta cirewa yarinyar ta yawan kule kulen mazan nan ki xage dantse kiyi ta addu'a ubangiji xai amsa miki rokon ki domin shine yace"Ku rokeni zan amsa muku " Wllh mutane da dama rushewar tarbiyyar yaransu ta kai su ta baro su karshe sun sami bad result.Allah ya tayamu kula da tarbiyyar yaran mu Amin. Inna ta kwashi sauran kayan ta kai daki na sawa a fridge shima an sanya shi gudun lalacewa. Aifa Alhaji Adnanu bayan ya samu gurin yin parking a gefen hanya murmushi yayi mai dauke da ma'anoni daban daban,sannan ya furta "yaro yaro ne "banda abun yarinyar nan ta yaya xan kashe mata kudi a banza ,sai kace tare muke fita neman ? Yayi wa kanshi tambaya gami da girgiza kai yana wani shu'umin murmushi.hmmmm ya furta sannan ya ce "yaro man kaza". Innar Aslmiyya irin mutanen nan ne da babu ruwan su da Addini don ita takanyi shekara ba tare da ta dauki Alqur'ani ta karanta ba,in kaga tayi karatun to tabbata a cikin sallah ne shima dai gashi nan don ba wani nisa tayi da karatun ba balle 'yar tata Aslamiyya ita dai ga tanan babu ishashshen addini balle bangaren bokon, sukam rayuwar su sai a hankali kwata kwata 6acin ran su ne ya kashe mahaifin su Aslamiyya. Akwai yayan Aslamiyya Awwal mutumin kirki yana bakin cikin mugun halayen mahaifiyar tasu da kanwar shi yana iya bakin kokarin sa wajan kyautata musu amma su agun su baya musu, yana na'ibawa da zama shida matar sa sa'adatu da yaran shi guda biyu, Alhaji Adnan yayi wa Aslamiyya waya akan zata rakashi unguwa da yamma ta shirya zai biyo ta gidan nasu ya dauke ta. Murna tayi sannan ta tashi ta shiga wanka bayan ta fito a wankan ne ta zauna a bakin dressing mirror ne ta fara kalkale jikin ta da mai da turararruka masu dadin kamshi sannan ta shafa powder d lipstick mai danko ai fa nan tafi to a manyan Mata. Aslamiyya ba baya bace gun tsara kwalliya shiyasa ta sace zuciyar Alhajin nata. Yanzu wai abinda ya ke bani mamaki shine sai ki ga mace a gidan ta amma kojai kojai da ita babu kwalliya babu kunshi balle kitso kullum tana yawo da kodaddun kaya wai ita ai ta girma shekara talatin ko kasa da haka wai ba xata yi kwalliya a cikin gidan ta ba sai za taje unguwa,Abun yana daure mun kai sosai itafa 'ya mace 'yar kwalliya ce da kwalliya aka san mu amma haihuwa biyu uku zuwa hudu sai ki saki jiki kice ke hidimomin cikin gida sun miki yawa shiyasa bakya samun lokacin yin kwalliya. Nace ba" iya ki kauce ki bawa masu jini a jika su shigo suyi hidimomin sannan su dora da kwalliyar da tsafta ,wllh idan bamu gyara ba to muna zaune za muke kur6ar 6acin rai " hajiya a zamanin nan na yanxu kana gyara ma da ya aka kare balle ba 'a gyarawar Allah yasa mu dace. Aslamiyya na hango ta sha makeup na garari ta kashe kala jikin ta sai tashin kamshi yake na turare kala daban daban hmmm irin su aslamiyya idan mijin ka yana zuwa gunsu wllh sunan ta gidan sorry domin tayi kyau sosai sai dai muce masha Allah. Motar ya bude mata fuskar shi a sake sai murmushi yake yi kamar wanda yaga jaririn watan ramadana, sallama ta mishi sannan ta ce dashi"barkan ka yalla6ai ya garin?" Amsa mata yayi da "lfy klau baby ykk?"bai jira amsawar ta ba ya ja mota suka tafi Sunyi tafiya mai tsawo kafin yayi parking a gefen titi ya juyo da fuskar shi gareta ya kura mata idanu, "kinyi kyau baby ina ma a daura mana auren nan a yau" yace mata yana binta da wani malalacin kallo, "Fari tayi da idanun ta ta rausayar da kanta tace mishi "yalla6ai saurin me kake yi kaida kake da hajiya a gida?" Murmushi yayi yace mata" ba zaki gane ba shiyasa " hmm Alhaji Adnanu shi kadai yasan me yake kullawa wai akace mugu shi yasan makwantar mugu Kashe idon shi daya yayi sannan yace mata "ina so a cikin satin nan ki bani dama zan kawo kudin auren mu saboda nagaji da gararam ba a kan titi gara in killace ki kinga hankali na sai yafi kwanciya" Murmushi tayi sannan ta furta "yallabai ai duk lokacin da ka shirya ni ashirye nake domin nima nafi son in ganni a guri daya ma'ana a cikin gidan ka to hakika zan fi samun nutsuwa" Sosai zan tukan na Aslamiyya suka shiga Alhaji amma fa shi kudirin sa na daban yana kasan zuciyar shi "to" yace da ita kana yaja mota sukayi gaba. Basu fi mintuna biyar ba suka yi parking a daidai wani gida yace ta taho suje su kar6i sakon, da yake ta yarda da Alhajin nata 100% ta bishi suka shiga cikin gidan da yake gate ne kuma a bude da dukkan alamu an bude shi ne don ansan da zuwan nasu. Harabar gidan suka shiga gida ne na bugawa a jarida domin gidan ya hadu sosai dan bayanin gidan ma 6ata lokacine to dan haka mai karatu ka fasalta shi, ainahin cikin gidan suka dosa mutuniyar kwa ta bude baki ta kwada sallama sai jin shiru tayi tace "yallabai ko dai babu mutane a gidan ne"? Shiru yayi kamar bai jita ba ya daga wayar karya yace "yawwa na shigo gidan to,to,gani nan bari in karaso." Kofa ya nufa ya bude ya ce mata "zaki jirani anan ko kuma zamu shiga tare ne baby"? Jimmm tayi sai kuma tace mishi "muje babu damuwa" amma fa ita ta fara tsorata gaskiya shiga sukayi cikin falon gidan wanda yake dauke da kayatattun kujeru na alfarma mai dauke da labulaye masu kyau kalar purple sai chines carpet a tsakiyar falon wanda shima falon kasan shi yasha tiles fari da video 'yar bango irin babbar nan sai wani 6angare wanda yake dauke da kananun kujeru na xaman cin abinci, daga ganin gurin dai kasan 6angaren dining ne, haduwa tayi haduwa Aslamiyya sai kallon gida take aranta tana ayyana in itace a cikin gidan nan gaskiya xata tsula tsiyar ta zata huta kai har wani lumshe ido take sanyin ra6ar Ac na ratsata aran ta tana fadin "dadi kashe ni Allah ka mana tsari da talauci "shiko gogan nata ya tsaya ya kura mata idanu shedan na ayyana masa abubuwa da dama. Gyaran murya yayi yace mata "baby ki zauna kana" Zama tayi shi kuma ya shiga ciki kana ya fito hannun sa dauke da gorar ruwa da glass cup a hannun shi. Zama yayi a kusa da ita yace mata "bismillah ga ruwa 'yan mata na sarauniyar kyawawa gimbiya Amarya a gidan Alhaji Adnanu" Karba tayi ta kur6i kadan tace "yalla6ai wai nan ina muka zo"? "Kisha ruwan mana baby idan kinsha mayi magana" [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA Na mmn Annur True life story Page (6) Aslamiyya fa jiki yayi sanyi domin hankalin ta ya fara tashi gaskiya da lamarin yalla6an nata Ruwan ta dan kur6a kadan kana tace dashi " yakamata ka kar6i sakon ka mu juya saboda yaya Awwal zai shigo gidan namu da wuri to ina tsoron fadan shi" Kashe mata ido yayi yace mata "baby gidan da zan ajiye ki ne fa!" "Dan kar in ce miki zan kai ki duba gida ne kice baza ki xo ba shiyasa na miki dubara" Murmushi ta saki mai idon cin naira zagayen palon ta shiga yi tana yaba kyanshi da tsaruwar shi gaskiya komai yaji babu ce kawai babu a gidan nan Tashi yayi ya biyo ta yace "muje ki duba dakunan kiga ni kayan cikin su sun miki" Shiga tayi kanta tsaye KO fargaba babu a ranta tunda taji gidan mallakin ta xai zama Hannun ta ya kamo ta warce hannun,Kara kamota yayi ita ko tayi baya sannan tace "Wai yallabai meye hakan? Nifa na gaji ma muje ka sauke ni a gida" "OK" yace cikin nuna dakiya akan abunda yake san cimmawa buri . Rungumo ta yayi ta baya yana wani sinsinar ta so take ta kwace amma ta kasa yana neman kaita gado allah ya bata sa'a tayi wani juyi wanda saura kiris ta fadi,ai da gudun ta ta fito waje tana maida numfashi a kasan ranta tana mai tsinewa Alh Adnanu shege dan iska Alh Adnanu tsaki yayi yace" wannan 'ya kwai ja'ira wllh ,ita tunanin ta a banxa xan ke mata dawainiya ?" Gyagygyara wa yayi ya karkade rigar shi wadda tumbin sa ya samu muhallin xama aciki. Fitowa yayi compound din gidan bai ganta ba da saurin sa ya fito kofar gidan ganin ta yayi a tsaye tana wani ciccin fuska Shima daure tashi fuskar yayi ya shiga mota ya kunna ko kallon ta bai yiba da taga haka da sauri ta bude murfin motar ta shiga ta rufe . A sukwane ya ja motar kai da ka ganshi xa kayi tunanin saurin nan da yake yi gyatumar sa aka aiko ta rasu,amma tsabar dacin da ransa yake masa ne na hana shi cimma burin da tayi . Babu Mai magana a cikin su kowa akwai abun da yake ayyanawa a ransa da haka har suka zo dai dai unguwar su Aslamiyya pakinga yayi ta fito ko sallama bata mishi ba ta sa kai ta fice a motar ranta a mutukar 6ace . Haka suka rabu babu dadi. Alh gida ya koma yana muxurai don shi gani yake Aslamiyya ta cuce shi ta hana shi cikar muradin sa. Lyaqk yayi kwafa yana ayyana abubuwa a ransa . Aslmiyya Ana ta bangaren itama gidan ta nufa ranta duk babu dadi ita fa babu abun da ya 6ata mata rai yanda ya nuna zulamar shi akan ta sannan ko hakuri bai bata ba gashi dan bakin ciki yaba ta 'yan kudaden ma da ya sabar mata amma kirmisisi ya hanata aiko zai ga rashin mutunci dan ko yazo ba xata fita ba. Alh Adnanu motsi kadan a cikin gidan yayi ta harare harare ga fada na rashin dalili kai hatta yaran shi basu tsira ba suma hantarar su yake sai umman su ce ta kira su daki ta sanar musu cewa baban su baya son damu baya jin dadi shiyasa . Addu'a suka mishi d ftn samun lfy a gun Allah. Sosai Aslamiyya ta shiga damuwa domin ita fa tsakanin ta da Allah take son Alhajin nata sa6anin shi da yake da manufa akan ta. Waya ta dauka ta kira shi da kamar ba xai daga ba amma tunda shi yake neman wani abu a gunta to tabbas ya sassauta don fishi ma ba nashi ba ne Daga wayar yayi ya kara ta a kunnen shi ,shiru yayi sai ita ce tayi karfin halin ce masa "hello yallabai" Amsawa yayi yace "ya akayi kike kira na a wannan lkcn? " Shiru tayi kana can kuma ta nisa tace "gani nayi kusan tun jiya da safe rabon da ka kira ni " Shine naga ni ya dace in kira ka inji ya ka isa gida? "To ai kinji lfyr tawa ko? Yanxu ina tare da iyali na lokacin sune dan haka shikenan sai da safe kitt ya kashe wayar " Dalalo tayi da waya a hannun ta,wato yanxu duk girman namiji idan har dan iska ne to babu ruwan shi da jin kunya. Lallai ma ji girman laifin da yayi mata amma shi ko a jikin sa . Kusan satin su daya suna gaba da juna shi Alhaji Adnanu yana fushin banza ita kuma tana fushin ta mai dalili. Duk macen kirki wadda tasan kima da darajar ta to tabbas ya kamata idan namiji yana neman wani abu wanda bai dace ba a gunta to tabbas ya kamata ta taka mishi burki don ita ba hajar da aka kasa a kasuwa bace .Allah Ya yi mana sittira wadda babu halittar da aka mutunta a ka yiwa gata da gatan tawa kamar halittar mu ta 'ya'ya mata ,to don haka ya dace mu yi kishin kanmu don kaucewa tarko irin na Alhaji Adnanu. Alhaji Adnanu da kanshi ya zo ya nemi bikon mutuniyar tashi don ya kasa hakura da ita shifa burin shi kawai ta bashi kanta ba wai auren ta yake son yiba. WAIWAYE Hausawa suka ce "waiwaye Adon tafiya " Shin ya labarin su uwar biyu? Wato Sumayyar Amir. Mashaa Allah zaku so kuga yanda sumayya jego ya amshe ta domin tayi 6ul6ul da ita da yaran ta 'yan biyu,yanzu haka sun shigo wata na hudu da haihuwa amma idan ka gansu zaka iya cewa sunyi wata bakwai- bakwai don suna samun kula ta musamman a gun iyayen nasu musamman Amir yana ji da matar shi da yaran shi. Alhamdulillahi kasuwa fa ta budewa Amir sosai Allah ya azurta shi daidai gwargwado gashi da taimakon musulmi 6angaren iyayen shi ma sosai yake hidimta musu da 'yan uwan su kai hatta da jama'ar gari yakan yi musu ihsani dai dai da iyawar shi. Shiyasa Allah yake kara ninkamishi. Amir ne ya ke yiwa sumayya zancen tsarin iyali yana so ta huta kafin ta kara wata haihuwar don asamu 'yan biyun shi su warware. "Allura kike ganin za a miki ko kuma inplant kike so?" Shiru tayi sai can kuma ta ce mishi "Habibi duk wanda kake ganin saukin shi to shi nake so" Amir ne yace da ita "to ke banda abinki ina nasan wanda yafi a cikin su amma za muje asibiti in yaso su zasu san abinda ya kamata su miki" Washe gari da safe misalin karfe goma na safe ya dauketa a bayan mashin da goyon hassan din a bayan ta shi kuma hussain a hannun ta suka kama hanyar asibiti kati suka yanka sannan suka doshi hanyar da zata sadasu da dakin Awo. Sallama suka yi aka amsa musu sannan Amir din yace da nurse din "a nan ake tsarin family planning?" Amsa mishi tayi tace musu "Ku shigo mana anan ake yi" Bayan sun shiga ne sai nurse din tace musu "wanne tsari za'a muku?" Amir ne yace "wanne ne kuke ganin bashi da matsala?" Nurse din ce tace mishi "oga ai duk planning yana da side effect to sai dai wanda bashi d damuwa sosai shine tsinke wato inplant" "Amma a alluran ma Akwai depo,norester ,ciyana " Sumayya ce tace mata "kawai a samun inplant din don shi din naji ance bashi d damuwa akan sauran planning din" Test din fitsari a ka sanya ta don tabbatar da ciki ko babu . Bayan anga babu ciki ne aka ce ta kwanta akan wani dan karqmin gado sannan aka yi mata allura can bayan an yi allurar sai nurse din ta tambaye ta "shin kinji abunda na miki a hannun ki?" Tsinkon ta tayi a hannun shi yasa take tambayar ta. Amsa Mata tayi da "a a" Inplant din ta dauko tasa Mata a hannun nata sannan aka like gun da plaster akace Mata kar tqyi aiki da hannun har tsawon kwana uku sannan ya warke gun sai tacigaba d amfanin ta d shi hannun [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LjAKkRsTETX6WFnnZ3fnpl ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur Page (7) INA BARAR ADDU'A A GAREKU KANWATA BATA DA LFY INA ROKON ALLAH YA YAYE MATA ITA DA SAURAN MARASA LFY. Bayan an sanya Mata implant dinne su fito don tafiya gida to anan sai Amir ya hadu da Farida wata class mate din shi ce,karasawa gunta yayi don su gaisa "A a hajiya farida ikon Allah yau she a Cari?" Amsawa tayi da "lfy kalau Amir ykk y iyalin?" Shima Amsawa yayi da "lfy klau. Ya naki yaran?" Murmushi tayi kana tace masa "yara kam babu,baka san mun rabu da mijin nawa ba ?" Amir Kai ya jinjina yace "wllh ban san kun rabu ba,Allah ya za6a miki wanda yafi shi alkhairi " "Amin" tace masa. Amir ne ya kalli inda ya bar sumayya d goyon daya sannan daya a hannu,inda ya duba sai ganin wayam yayi bata gun ta fita daga harabar Asibitin,a sukwane ya hau mashin din shi yabi bayan ta inda ya ganta a karkashin wata bishiya tana tsaye da yaran ta wanda duk sunyi bacci. Karasawa gun nata yayi yace "haba sumy taya zaki fito nan ki xauna kowa in zai wuce sai ya kalleki?" Itama cikin kufula tace masa "Kai ya dace ne muna tare kawai dan kaga wata can sai ka tafi bayan muna tare ? Ina laifin ma kace dan Allah jirani ina zuwa " Shiru yayi inda yasan gaskiya ta fada bai dace ba saboda ita zuciya bata da kashi ,yanxu sai zargi ya shiga tsakanin su. "To kiyi hakuri gimbiyar Mata " Murmushi tayi tace "ya wuce ai bb komai" Gida suka dawo ya ajiye Mata 2k kudin cefane duk da ba wani abun zata siya da kudin ba sai kayan miya da zata ba almajirin ta kudi ya siyo mata da yake a nan cikin unguwar su akwai mai kayan miya. Godiya ta mishi tare da ftn samun nasara a cikin rayuwar shi . Amir ya na jin dadin wannan godiya ta sumayya shi ma godiyar yayi Mata sannan ya fita zuwa gun kasuwan cin sa. Namiji kenan Amir fa bai zame ko ina ba sai asibitin da ya hadu da fareda ,magana yasa aka mata sun dau lkc suna fira sannan ya kar6i number ta yayi saving da (fararu) Fareda irin matan nan ne kamar 'yan bariki akwaita da rawar kai. Bayan Amir yaje shagon sa ne ya zauna ya kira number fareda ( fararu) sun dan ta6a fira sannan yace Mata "shin zaki iya aure na?" Jimmm tayi sai kuma tace "ai Amir kai zan yiwa wannan tambayar tunda ka ga ni bazawara ce " Shima haka yace Mata "indai zata yarda ta aure shi to shifa a shirye yake don ganin ya mallake ta" Babu 6ata lkc suka kulla soyayya sosai suka dau lokaci suna fira. Wasa wasa soyayya tayi karfi inda sumayya baiwar Allah ita bata san wainar da ake toya waba Amir ya saba dawowa da rana karfe 2:00pm shine lkcn dawowar shi daga shago,idan yaci Abincin rana yayi bacci to ana yin la'asar zai koma shagon nashi bazai dawo ba sai karfe 8:00 pm na dare haka yake yi. Wasa-wasa Amir ya fara canjawa daga Amir dinsa ya zama shima baya gane kansa wani lkcn. Yanxu baya dawowa gida sai wajan 11 pm gashi duk ya fara janye jikin sa daga sumayya tun bata damuwa har taxo tafara magana akan canjin halayen nashi amma sai dai yace mata sha'anin kasuwanci ne sai dai tayi hakuri shima yanxu baya baiwa kansa kulawa. Wannan kalmomin da ya fadawa sumayya sun bata mamaki kwarai da gaske Fareeda ta riga da ta yiwa Amir dabai bayi ta masa kamun kazar kuku domin sai da ta hada shi da malamai tukunnan take samun kulawar shi ita yanxu duniyar ta tadawo mata sabuwa. Yanzu Abun na Amir sai dai Allah ya kyauta domin ko gidan mahaifiyar shi sai yayi sati uku bai lekata ba balle yasan halin da take ciki. Ita da kanta tazo gidan nashi take tambayar "ko lfy kwana biyu bai zo ba ?" Sai yake cewa da ita "lafiya klau kasuwar ce ta dau zafi" Hhhuuhhuhu "haba Dan nan nifa na haifeka bawai kai ne ka haifeni ba duk budin da kake samu a gun Allah amma butulci xaka mishi kace wai kasuwa ta dau zafi ? A a to wuta ta dauka ba zafi ba" Shiru yayi, Kiran sunan shi tayi har sau uku tace "to ko sumayyar ce ta hana ka zuwa gidan uwar taka?" Girgiza Mata kai yayi yace "wllh babu laifin sumayya itama complain dina take yi akan wai na canja " Iyyy gqskiya inji iyar Amir tace "samun guri ne yayi mata yawa ni da nake gefe sai inyi kwanaki ban gankaba amma ita kuna rayuwa gida daya shine xata ke korafi?" Amir ne yace "iya kiyi hakuri Dan Allah zanxo kije kawai Jinjina Kai tayi tace"ba shakka Dan nan " Bayan ta tafi ne Amir shima yasa Kai ya fice daga gidan. Yana fita sumayya taje ta rufe gidan ta dawo gun yaran ta tana mai zubda hawayen takaici,a ranta tana fadin "mai tayi wa Amir ne ? Kallon kirki baya mata idan zai fita ba zaice na tafi ba ta mishi Addu'a,sannan idan ya dawo ba zai amsa sannun da take mishi ba,dai dai gwargwado tana yi mishi biyayya amma shi baya gani" Rayuwar sumayya abin tausayi duk tayi baki ta lalace ga 6acin ran yau daban na gobe daban Abin yayi mata yawa . Karima kawar ta ce tazo take tambayar ta "wai sumayya lfy naga kin canja ko dai laulayi kike ne?" Murmushi tayi tqce wa kawarta ta"babu komai zazzabine yake damuna na dare". "Ayya sannu kawata zazzabin dare bashi da dadi ya kamata kije asibiti"inji karima. "Sai da yamma Amir zai kai ni "inji sumayyan. Fareda ta makalewa Amir koda yaushe suna cikin yin waya ko chatting,Kai hatta a cikin gidan sa bata barshi sai dai ya mata dubara yace bacci yake ji ko kuma bandaki zai shiga to fa shine zata sama mishi lfy. 'Yan biyu ma shaa Allah sun girma sosai sun gane iyayen su duk da yqnxu bbn su ya rage basu kulawa amma duk da haka yakan yi musu wasa amma ba kamar da ba. Yau sumayya gidan su Amir din take son zuwa anci sa'a ya amince idan zai fita zai sauketa a can din, inda ta aika aka siyo mata klin da sabulun wanka dana wanki,turare man shafawa haka ta hada kayan xata kaiwa iya. Ta shirya yaran nata itama ta shirya cikin doguwar riga ta Atamfa anyi mata dinkin zamani caftain rigar ta mata kyau matuka yaran kuma an sanya musu riguna 'yan kanti da jeans rigar milk sai wandunan blue color sunyi kyau kamar ka dauke ka gudu Kallon su ya tsaya yi hakika sumayya kyakkyawa ce gashi ta iya daukan wanka da yake ma'abociyar san kwalliya ce amma fa ba na fente fenten fuska ba yaran yaje ya yiwa photo sannan ya daga kowanne yayi mishi wasa . Ita kanta sumayyan sai da ya zolaye ta yace "gimbiya ta bakya tsufa kamar bake kika haifi yaran nan ba duk kin yi wani kyau meye sirrin?" Murmushi tayi tace masa " kwanciyar hankali da rashin kulawar da muka rasa a gunka shine ya janyo wannan kyawun da muka yi nida 'YA'YA na," kallon ta yayi tare da murmushi akan fuskar shi yace "ke kam babu dama akwai korafi" Itama tace "babu wani korafi da nayi tunda kai ma kasan baka kyauta mana ka canja mun sosai wanda har na fara tunanin wani abun a raina " "To menene a ran naki ummm 'yan mata? " "Nikam muje kawai ni bani da riko duk abinda mutum yayi in dai dai ne ai yasani" Fita sukayi daga gidan Amir ya rufe gidan ya mika mata key suka tafi. Suna hanya fareda ta kira shi a waya "wai lfy bai kira ta ba yau ?" Kashe wayar yayi Dan kar sumayya taji babu dadi aranta . Sun isa gidan iya suka shiga da sallama gidan su duka har Amir din Amsa musu sallamar akayi iyan ta fito daga daki ta musu sannu da zuwa babu yabo babu yabawa ma'ana dai fuskar ta kadaran kadahan haka suka bita dakin suka nemi gurin zama akan cafet . Sumayya ce tace "iya ina kwana mun same Ku lfy ya gida ya zafin nan?" Amsawa tayi iyan da "lfy klau ya yaran naku ?" "Lfy iya gasu nan" inji sumayya. Amir ne ya gaisheta ta amsa gami da tambayar kasuwar tashi tace " kasuwar taku tayi sanyi kenan shiyasa kaxo?" Kunya yaji tunda yasan karya yayi mata lkcn da yace kasuwa tadau zafi. Tsaraba sumayya ta mikawa iya tace "iya ga dan kadan babu yawa" Iya anga kaya aka saki fuska ake godiya tace "iyy lallai kasuwa tayi sanyi su Amir har da dawainiya haka" "Ai iya bani na siya ba sumayya ce ban san dasu bama" "To Allah ya saka muku da alkhairi Allah ya hade kanku ya tsone idan makiya nag ode" Amir kudi ya baiwa iya har 5k iya yau dadi ya cika ta ta daina jin haushin su godiya tayi musu sannan Amir ya tashi ya tafi shago ita kuma sumayya ta zauna .tashi tayi bayan ta kwantar da yaran ta fito daga dakin tace "iya bari inyi miki aikin ki zauna ki huta ga mazajen ki nan kusha fira dasu" Dariya tayi tace " a a dawo sumayya ki huta babu aikin da za'ayi yanxu sai dai anjima,kanwar taki kafin ta tafi makaranta sai da tayi wqnke wanke da shara tukun . Zama sumayya tayi suna dan ta6a fira inda iyar take tambayar ta babu matsala a zaman nasu ko shine sumayya tace mata "babu matsala iya lfy muke zaune. Bayan fitar Amir gidan su fareda yaje ya bata kudin cefane don shi tunda tace masa xata aureshi shikenan ya dau kawa kansa dala babu gammo kudin cefane yake bata ko kuma ya iyo ya kai mata gidan nasu Su iyayen ta suna murna sun sami dami a kala babu ruwansu da shin yana da wani mugun halin babu bincike suka amince dashi su walkam gaba ta kai su cefane a wanga xamanin ai abune mai zaman kansa wanda mutum ko a gidan sa ne sai ya jure . Kudin ya Kai mata 2k da naman miya sun dade suna fira tukun na ya tafi shagon nashi yana ce mata "yau a gunki xanci abincin rana saboda madam bata nan" fari tayi da kananun idanun ta tace tom kar ya damu tana marhabin lale. Karfe 2 dai dai yazo gidan su fareda ya kira ta a waya yace mata "nazo ina jiran ki" da "to" ta amsa. Tasha kwalliya ta feshe jiki da turare fareda katuwa ce ko shape din nan irin na mata bata dashi ga te6a duk tayi mata yawa kamar mai cikin wata tara,shimfida tayi masa a zauren kofar gidan su tace "ya shigo " shiga yayi ya zauna yana fadin " Amaryar Amir" dariya ta saki irin ta maanyan mata shiga tayi ta dauko abincin ta taho da rangwada ita a dole ga mace bata san matar shi ta gida ba ta doke ta a kyau d tsari ga kyan jiki da iya sarrafa jikin. Zuba mishi abincin tayi shinkafa da taliya da miya da naman miyar da ya kawo sai zobo da pure water bismillah yayi lomar farko da yakai bakin sa da kyar ta tafi ga wani masifaffan yaji da karni da ya doki hancin sa azaba ci yake kamar yayi kuka kadan ya ci "yace mata to Alhmdllh ni dama bana cin abinci in cika ciki na saboda koshi ta kura ni yake." Godiya ya mata yace shi zai wuce ana jiran sa. Fita yayi kafin ta fito ta rakashi gun mashin din shi ai a sukwane ya tada shi da gudun shi sai da yayi nisa da gidan nasu ya tsaya a gefen titi ya fara sharara Amai kamar 'ya'yan hanjin sa zasu fito sai kolon amai yake,tass sai da ya amayar da abincin nan tukun yasamu salama Tofa a gaba Amir Kai da zaka kawo ta gidan ka tayi ta girka maka hadaddun girki Hmmmm muje zuwa. Meenatu Amjuf ce ( mmn Annur) [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LjAKkRsTETX6WFnnZ3fnpl ZAMAN 'YA'YA NA. Na mmn Annur Page (8) Ina kuke mata kuna ina kina zaune kin kasa gyara kanki kin tsaya sai an baki kin zama cima zaune ? To karkade kunnuwan ki kiji idan zaki iya sana'ar turaren wuta na garwashi to matso musa labule kizo ki sara muna bayar da sari ke in so kike ahada miki to ki sai kayan ki bada mu hada miki sai dai kibiya kudin aiki kawai Sana'a aba ce wadda take kankaro da kima da mutunci a idon miji da ma sauran Al'umma baki daya . Muna saida Atamfofi shaddodi material Labulaye zannuwan gado takalma hijabai mayafai na yr d manya .laces kamfala da dai sauran kayan kyalekyale na mata Mai so ga number ta man 09069615587 Nagodeeeeee Amir yana gama amai ya samu gurin zama ya zauna yana maida numfashi tamkar wani wanda yayi tseran gudu na kilo mita goma. Ji yayi cikin sa ya fara murdawa alamun yana gab da sakin gudawa a wando ai a 360 ya tashi ya hau mashin din shi ya tada shi kan kace kwabo ya yi nisa kamar wanda yaga mutuwar shi haka yayi ta tsula gudu duk inda ya fice sai dai ace "wannan mai gudun kamar wanda zaije lahira " gudun yayi yawa. Gidan iya ya nufa da kyar ya iya kashe mashin din bayan ya sauka a zafafe ya shiga gidan iya da saurin sa ko sallama bai yi ba haka yasa kai ya shiga gidan ya nufi hanyar bandakin gdn,yaci sa'a babu mutum a bandakin ruwa ya dauka a buta ya shiga ko Addu'ar shiga bandaki bai samu damar yi ba ai yana tsugun nawa ji kake 6iyttttt burrrrr kukkkkk da ya saki wata tusa mai kara wadda ta taho da 'yar mitsitsiyar gudawa ji kake 6uttttttt kikikikikkkkkcusssss sai kace tahuna taso hardama ( injin nika) Abin tausayi abin dariya shikadai a bayan gida duk ya hada zufa sai nishi ya keyi gurin yin kashin nashi sai zafin Attaruhu ya keyi. Tsarki yayi ya fito a bandakin yana mere Kai kamar wani wanda yayi kwanaki yana yin gudawa. Dakin iya ya shiga ya taraddasu suna zazzaune suna kallon film din Tere bina (jiya ja yena) basu san ya shigo ba sai ji suka yi yace "kallo ake yi?" Firgita suka yi to su dai basu ji sallama ba sai jin mutum suka yi ya yi magana. Sumayya ce tace mishi "sannu da zuwa" "Yawwa "ya ce mata ,yace "ina twins"? "Gasu can a kan gado sunyi bacci" Gun yaran sa yaje yayi musu kiss kowannen su a goshi.Amir yana son yaran shi sosai dan ko a gida in suna rigima to shi yake lalla6a yaran,don sumayya sai dai tasa su a gaba tayi ta kuka ta rasa ya zata yi dasu. Rainon 'yan biyu akwai cin rai da zarar daya ya fara kuka shima daya sai yayi Kai ko jinya dayan yayi to yana warkewa dayan zai kamu. Abinci sumayya ta kawo mishi jallop din taliya da kifi tasha kayan lambu irin su Kabeji karas pies da curry sai kamshi take yi Sumayya ce tayi musu girkin,ita kam ba daga nan ba gwana ce gun sarrafa Abinci. Ci yake yi yana gyada kan shi tamkar wani tuzurun kadangare.Tass ya cinye Abincin nan har mamaki iya tayi tace "amma dai yau ka kwaso yunwa da yawa irin wannan caccaka haka"? Dariya yayi yace" kuma a haka bana jin dadin jikina wllh duk kafafu na sai zugin rashin ruwa suke " Ruwa sumy ta mika mishi ya kar6a ya sha, Hamdala yayi a ransa yana mai cewa"haba ga Abinci mai dadi amma naje na dirkawa cikina poison Ace wannan 'yar lukutar ko girki bata iya ba kaii dole mijinta ya kore ta.amma ni dai a haka zan aure ta don sumayya zansa ta koya mata" Sai bayan sallahr magrib ne suka tafi gidan su.Sumayya wanka ta shiga bayan ta fito ne ta shirya cikin wata farar vest mai tattara a tsakiyar wajan brest din ta sai 3quatern wando baki da hula baka irin mai net din nan jikin ta ta shafawa turare da humra sannan ta fito ta dauki hassan ta fara yi mishi wankan sannan shima hussain ta dauke shi ta yi mishi. Akan gado ta kwantar da su ta shirya su cikin kananun kaya sai pampers d ta sanya musu,gwanin sha'awa dasu sai tashin kamshi suke kicin ta shiga dan sama musu abincin dare ,kuskus ta dafa da miya sai naman zabuwa da ta gasa a oven tare da yi musu lemon mango. Gaskiya na jinjinawa sumayya a dan takaitaccen mintuna har ta gama ayyukan ta ta wanke wadanda ta 6ata sannan ta fito daga kitchen din. Sallahr Isha'i aka Kira ta shiga daki ta daura zani sannan ta dau hijabi ta sanya ta tada kabbara. Amir ne ya shigo gidan da sallama jin shiru yasa ya shiga bedroom din nata anan ya tarar da twins har sunyi bacci addu'a yayi musu ya shafa wa kowa a jikinsu. Ta idar da sallahr ne tace mishi "sannu da zuwa habibi" Amsa mata yayi babu yabo babu fallasa ma'ana ciki ciki. "Akawo abincin nan ko kuma a falo zamuci"? "A a ki barshi muci a falon kawai" Tashi tayi ta shiga kitchen ta hado kayan abincin a basket taxo ta ajiye a kasa yayin da ta dauko babban cafet ta shimfida musu sannan ta jejjera kayan akan cafet din. Shima fitowa yayi yazo ya zauna ta zuba musu a plate daya suna ci yana danna wayar shi tun tana mishi fira yana dan kulata kadan kadan har yaxo ma yayi shiru ya kyaleta al'amarin nan yana ciwa sumayya tuwo a kwarya. Kyaleshi tayi taci abincin ta ta kora da mango juice "Alhamdulillah"tace ta tashi ta barshi da waya yana danne danne da ita ga cokali a hannun sa sai jujjuya shi yake yana ta doka wani lalataccen murmushi. Sai can a shelake tukun na ya gama cin Abincin tazo ta tattare kayan ta koma dakin ta tana tunanin halin da ta tsinci kanta a ciki kuka ta fara yi tana ta Addu'a akan Allah ya yaye mata damuwar ta ya juyo mata da hankalin mijinta gareta Allah ya bata ikon cin jarabawa ko wacce iri ce. Shigowa dakin yayi ya hau gadon ko wanka bai yi ba amma ya zo zai kwanta ,ganin tana kuka yasa shi tambayar "baki da lfy ne"? Shiru tayi ta rabu dashi sai can har ta fara bacci ma tukun na ya tashe ta yace "tashi zamuyi magana" Tashi tayi ta zauna tace "ina jinka" "Sumayya me ya faru naga kina kuka dazu"? "Hmmmm Kai yanxu habibi baka san me kake yi mun ba ? Duk ka canja mu ka daina kulani kayi fira dani kwata kwata baka da walwala indai acikin gidanka kake me yasa me nayi maka? Yanzu ka auri rikon waya alhali wannan ba dabi'ar ka bace ,yanxu gashi kana neman ka sanya ake ta zargin ko jinya ma nake yi,duk na rame nayi baki kuma wllh ba komai bane illa canjawa da kayi." "To da farko dai kiyi hakuri wllh nima yanxu hakuri nake da wasu halayen da nasan ba nawa bane ada amma yqnxu ni kaina har mamakin kaina nake dan haka kiyi hakuri." Sannan ina so in baki hakuri akan wani Al'amari da yake son zuwar mana cikin rayuwar mu ,duk da abun nima na haka naso ba sumayya kaddqrar mu ce tazo da haka sai dai kiyi hakuri da abinda xan fada miki ." "To ina jinka ka sanar dqni duk wani lamari duk girman shi duk kankantar sa to ba zai tada mun hankali ba domin rayuwa cike take da kalubale kuma duk mai imani yasan Allah zai iya jarrabar sa duk lokacin da yaso dqn haka fada mun kanka tsaye" "Yawwa naji dadi da kika fahimci hakan naji dadi da Allah ya azurta ni da ke hakika kin cancanci yqbo da mutuntawa duba d yanda kika fito daga gidan mutunci da karramawa." Sumayya Aure nake son karawa,ba don kin mun laifi ba ko dan na gaji dqke ,KO daya zan kara ne saboda koyi da sunnar ma'aikin Allah.S.A.W." Dummmmmm kirjin sumayya ya buga ta dafe saitin inda yake mata radadi tace "Alhamdulillah naji dqdin jin wannan furuci naka habibi Allah yasa abokiyar arziki ce Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Mamaki ne gami da al'ajabi suka yi matukar daure kan Amir wani haushi yaji ya taso masa aran shi yake cewa "wai dama sumayya bata kishina? Ni zance mata xanyi aure amma KO a jikinta irin ta nuna damuwar ta akan batun ma bata yi ba lallai yarinyar nan yo me take nufi ne? Wllh tabani mamaki ni din zata nunawa bata damu da niba wato ba zata yi kishi naba kenan"? Hmmmm MAZA KENAN SUNFI SON AYI KISHIN SU SANNAN SUCE BAMU DA HANKALI .AMIR KENAN AI BAKA GA kuyi hakuri da wannan ciwon kai nake fama dashi. Kuyi manage Ngd 'Yar mutan Gumel [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur Page (9) Alhaji Adnanu yau shiri ake yi za'a je gun Aslamiyya don neman cikar buri don yau dinnan ya Qudurta a ransa cewa sai ya yi abinda ransa ke so, Wayar shi ya dauka tare da kiran Aslamiyya,mutuniyar fa duk san kudin ta to fa tana da Aji,don saida ta kusa tsinkewa kana ta daga ta kara a kunnen ta sai da ta dau wasu 'yan sakanni sannan tace "hello" Inda sabo ya saba da haka shima da ta daga kiran KO magana bai tarki yiba sai da yaji hello dinta, "Ummmm 'yan mata na yakike? Yau dai zanzo don haka ayi mun kwalliya ta rikitarwa gani nan a hanya" "Huhhhh to babu damuwa jarumina sai ka iso" Innar ta ce ta kwarara buda ( Ayyyiririyiriiii) yau tarko zai kama kurciya domin duk abinda yaso yayi mata ta fadawa innar ta,anan innar tace mata"to tsaye ya kamata mutashi don ba sonki yake ba wani abun yake nema a gunki,don haka zanje gun wani malami ya taimaka ya bamu abinda zai janyo hankalin sa kanki ke KO matar sa ta gida bana so ya nuna mata soyayya fiye da ke,nafison ace ke ce daya tamkar da dubu a cikin ranshi" "Aslamiyya ce ni inna nima hatsabibiya ce wllh da in bashi kaina a titi yaki aure na gara inje in samo soyayyar shi KO ta halin kaka,don haka kisa a ranki tamkar na aure shi na gama". Alhji Adnanu ya iso gidan su Aslamiyya ya tura yaro ya sanar mata. Shimfida tayi masa a cikin dakin su na zaure (tsohon dakin yaya Awwal ne) Food flask ne a hannun ta da jug sai 'ya'yan kofi guda biyu,Ajiye su tayi ta leka kofar gida ta mishi iso zuwa cikin dakin. Zama yayi babu KO bismillah tamkar ya samu dakin gyatuma tai,sannu da zuwa ta mishi sannan ta zuba mishi kunun aya wanda yaji hadi sai tashin kamshi yake. Mika mishi tayi tace "yalla6ai gashi a jika mako shi" Kar6a yayi yana mata godiya kafa kanshi yayi a bakin kofin tass ya shanye shi ta kuma kara mishi ya shanye,murmushi tayi don ganin hakarta ya fara cimma ruwa. Abinci ta zuba mishi a plate dambun shinkafa ne yasha zogale da gyada sai attaruhu d albasa da suke tashin kamshi gashi yasha curry ya bada wata kala ta musamman. Alhji Adnanu ci yayi ya koshi kamar ba gidan sirikai ba ya kara korawa da kunun Ayar nan geeetssss kike jin wata basamudiyar gyatsa d yasake ta. Kwanciya yayi a kan katifar dakin yace "tazo tamishi tausa" Hararar shi tayi tace "babu kyau fa matukar ba muyi aure ba " "Hhhhhh yarinyar nan za kiyi bayani" "Ni kam babu bayanin da zanyi yalla6ai ni yanxu so nake ka turo gidan mu azo ayi maganar auren mu duba da yanzu duniya gudu take kar mu tsofe a titi " wani lalataccen fari ta yi da idanuwan ta ta kashe masa daya idon kamar dai yadda indiyawa suke yi. "Kai yarinyar nan baki da dama ni yanxu sai abinda kika ce haka za'ayi don kin riga da kin zame mun jini da hanta" "Hmmmm tace" Akasan ranta tana mai ayyana irin abubuwan da zata tafka in taje gidan shi za taci karenta babu babbaka domin sai ta mantar dashi tsohuwar wannan wadda yake aure sai ta shayar da ita mamaki domin tana ganin mijin amma zaifi karfinta 'ya'yan shi kwa sai dai su zame mata bayi. Maganin Malamin da inna ta je ta kar6o yayi aiki ajikin Alhaji Adnanu domin shi ji yake yanxu in bai auri Aslamiyya ba to za'a iya samun matsala. Yayan shi ya samu da batun neman auren nashi anan yayan nashi yace dashi "gaskiya Adnanu baka kyautawa wllh yanzu ita matar taka duk irin fadi tashin da tayi akan ka duk baka gani ba sai ka saka mata da bakin cikin da zai zame mata illa ita da 'ya'yan ta ko "? Shiru Alhaji Adnanu yayi sai da yayan nashi ya kai aya a zancen nashi tukun na yace "yaya nifa bada wata mqnufa nake son karin auren nan ba don in raya sunnar ma'aiki (s.a.w.) ne kawai" "Haba Adnanu halinka kwa ai sai Kai,baka adalci a rayuwar ka,ga shi kai din butulu ne me karasa a gun matar na"? "yaya idan fa ba zaka nema mun aure ba to shikenan,sai fada mun bakaken magana kake akan hurumin da ba naka ba" "Yanzu Adnanu ni kake kallon kwayar ido na kake fada mun maganganu ,ni ba gaba nake da Kai ba,Karka manta ni din yayan ka ne ba wai kanin kaba" Fuuuuuuu yaja manyan sandunan kafafuwan shi yayi gaba ,Adnanu kenan Mutanen bogi Alhaji Adnanu ya samu a zuwan baffanin shine,inda suka tattauna da 'yan uwan baban Aslamiyya,shi a yanda Alhaji Adnanu ya tsara musu yana so a sanya bikin ne duka a cikin wata biyu. Haka suka nemi wannan alfarma a gun iyayen nata inda suka dora da cewa "ba sai sun yi wasu hidimomi ba shi matar shi yake so akai masa ita kadai din ta,baya bukatar kayan daki,gara,da sauran wahalhalun nan da ake yi" Godiya suka yi iyayen Aslamiyya sannan aka mika musu kudin auren ta 500,000000.inda ranar daurin aure zasu taho da sadakin ta,shima sun yanke kudin sadakin 200,000,000. Bayan sun tafi ne inna tace da kawun nan Aslamiyya "to kudi dai zata basu dubu dari,saboda ita ce da hidimomin cikin gida,dubu darin ma ta basu ne amma bai cancanta ta basu ba.Duba da yanda suka sakar mata dawainiyar marayu a hannun ta KO kunyar Allah ba suji ba suka wofintar dasu." Daya daga cikin baffan nin nasu ne yace ma ta"ke juwaira ki kiyaye mu wllh yanxun ma ba kudin ku zamu kar6a ba balle ki nuna mana halin karanta,kedai ba zaki canja hali ba Allah ya ganar dake " "Amin kuzo kuje Ku tafi gida maza kar dare ya muku a hanya don ina tunanin baku fito da ko sisi a cikin aljihun ku ba" Awwal ne yace "haba inna wannan abin da kike yi fa bai dace ba 'yan uwan mahaifin mu ne fa koba dangan taka ai bai dace ki wulakanta dattijan nan ba,kefa kika kira wosu kuma sunxo amma da abinda zaki saka musu kenan"? "A a Awwal bar ta tayi lokaci ne muke da laifi tunda mune muka zo inda take amma babu komai tayi rayuwa ce wata rana in ance juwaira tayi baza tayi ba " "Yo me kake nufi ne dani? To bari kaji Dan juma wllh ni da kake gani mace ce mai kamar maza,Allah na tuba don kar kuce bamu nemo kuba a auren 'yar Dan uwanku shiyasa na gayyace Ku Ku zanta d dangin mijin to tunda babu arziki a ciki kuxo Ku tafi kawai zan nemo mata wasu sabbin dangin, yanzu haya ma yi ake ta dangi in mutum bashi dashi yayin da zaiyi aure har kwa daga mun hankali kuje can gayyar na ayya gayyar tsiya" "Innalillahi yanzu inna iyayen namu kike zagi gaskiya bai dace ba inna ki daina kefa kika kirasu sunzo amma baxa ki yi musu magana mai dadi ba " "Awwalu rabu da ita,muntari kutashi mu tafi Allah ya sanya alkhairi Allah ya bada zaman lafiya" cewar kawu Dan juma. Tafiya suka yi dukkan su ransu a 6ace,gaskiya juwaira ta wulakanta su,sufa suna raga mata ne saboda 'Ya'yan ta da take zaune dasu ,ko gidan da suke ciki na kawu dan juma ne yace su bashi gidan shi su sai wani anan fa ta tada rigima wai saboda dan uwansu ya rasu shine zasu tozar ta iyalan sa,sunce ta basu yaran su rike tace a'a ita ZAMAN 'YA'YAN TA za tayi. Wannan kadai suke dubawa amma da tuni sun fitar da ita a cikin gidan. Rayuwar su Abin dai ba'a magana Aslamiyya sai daga kai ake in anfito waje ko a cikin kawaye,wai ita tayi zarra ankawao mata kudin aure . Gidan sumayya taje take sanar da ita labarin bikin nata,wanda zata auri mai mata. " wato sumy ina tausaya mata wannan matar ta shi don sai na nuna mata ya auro mace,tunda ita ta kasa yi masa abubuwa da yawa shi yasa zai nemi aure" Sumayya ce ta yi murmushi sannan tace "Aslamiyya wai kina nufin idan namiji zai kara aure ke a tunanin ki matar shi ce ta gaza masa"? "Ehh mana sumy in ba haka ba sai kiga mazan wannan zamanin wai da sunyi aure shekara uku shekara biyar sai kiga duk sun daga hankalin su suna neman aure to in ba sakacin matan ba taya ko dadewa ba kuyi da miji ba amma zai fara jajube jajube? Ai kawai ki yarda sakacin mata ne,ni wllh da ni ya fara aura to tabbas bai isa yayi sha'awar kara aure ba don ni da kike ganina nafi karfin namiji ya mun kishiya wllh.To dayake bani ce a farkon ba zanje matsayin ta biyu to ki tabbata ita dai sai dai ta zama 'yar kallo don ni ba lallai inyi sharing miji da ita ba" "Lallai Aslamiyya kinyi nisa banda kiyayyar talaka,harda kiyayyar kishiya a ranki? To kisani babu macen d take son a kawo mata kishiya amma idan Allah ya Qaddara akwai zama da kishiya to dole mace tayi hakuri don ta taya shi raya sunnah amma bawai ki tada makaman yaki ba ,tsaya kiji Aslamiyya duk matar da take daga hankalin ta akan namiji don zai kara aure to wllh fita take aranshi,kinga dai kishin sane yasa ta daga hankalin to tsaff xai korata gidan su kinga shikenan kin gyarawa wata mijin ki kin bashi gurin da zai sake ya wala ya sha amarcin sa" "Sumayya kenan kefa har yanzu tamkar kinci dqnkalin hausa kike.Waike kam yaushe zaki waye? To ai kishiya ba 'yar uwa bace,a harkar kishi babu sassauci duk kishiyar da kika ga tana bin kishiyar ta a sannu sannu to halayen ta take son ganewa tsaff idan ta gama sanin ta to daga lokacin zaki ga an fara samun sa6ani,nidai tsakanina da kishiya to tamkar tsakanin wuta d ruwa ne to nima hakan nake" "Allah ta kyauta Aslamiyya,yanzu yaushe ne bikin? Don mu fara shiri " " nan da wata biyu ne don haka ki fadawa mijin ki akwai anko kala biyu namu na kawaye da na gama garin mutane,kuma kowanne dolene yayi miki su" "To Allah ya nuna mana lokacin da alkhairi muxo mu rakashe .kinje gidan karima ne?" " a'a daga nan can zan nufa,bari na kira yalla6ai yaxo ya dauke ni ya kaini can din" "Gaskiya ne Aslamiyya matar manya kina sha'anin ki kawata amma fa ake yi ana tsoron Allah ,don mutuwa ake yi ta bazata ake safafawa kadan kada a zara jiki da yawa" "Hnmm sumayya kenan ni dai zan wuce sai munyi waya,yarana Ku gaida bbn Ku sai na dawo" " to nagode Aslamiyya sai mun hadu" Sallama suka yi sumayya ta zauna tana tunanin ita ma fa yanzu haka tata kishiyar ta iyu tana can tana rawar kafa tana samun mazuga zaman kishiyoyi,to Allah dai ya hada mu da ta gari wadda zamu zauna lafiya Amin Mmn sumayya ce aka zo aka sanar da ita labarin auren Amir,anan ra kira ' yarta ta.Tambayar ta tayi mene ne gaskiyar lamarin? "Haka ne umma ni ma shi yake sanar dani,bikin ma baifi wata daya ba yanxu." "Ikon Allah to Allah ya tabbatar da alkhairi ubangiji ya bada zaman lfy yasa abokiyar alkhairi ce.kiyi hakuri kada ki tada hankalin ki sumayya kinji kada ki fasa yi mishi duk abinda kika san yana so ,kici gaba da yi masa biyayya insha Allah baza ki ta6e ba " " to imma nagode in sha Allah ,ina baba?" "Baban ki lafiyar shi kalau zan fada masa kina gaishe dashi,Allah miki Albarka ya raya miki yaran ki yasa mahaddata qur'ani ne" "Amin ya rabbi umma nagode sai anjima" Shiri sosai Aslamiyya take yi 6angaren gyaran jiki ita dama ba daga nan ba magunguna irin na mata ta siye su sosai Kamar ba gobe. Maman Afrah tayi wa magana akan tana son kayan mata na gyaran jiki ciki d waje,aiko maman Afrah ta bata mamaki domin hajiya MEERAH mai kayan mata da gyaran jiki aka yiwa magana ta hado mata. Kaya ne na garari domin ita kanta Aslamiyya ta ga kyan kayan musamman na gyaran jiki,fatar ta tayi kyau sosai kamar mai rayuwa a cikin gidan hutu ,gaskiya kayan hajiya MEERAH karshe ne indai haka ne to kwa ita taga guri Sumayya ta yiwa waya akan zancen ankon inda sumy tace "ki kawo mun duk ka ankon zai min " "Yawwa sumy akwai kayan gyaran jiki wanda mmn Afrah ta yi mun hanyar su a gun hajiya MEERAH xan taho miki da wasu in kinga kyan su to sai ki siya kema " "Kai amma fa naji dadi sosai Aslamiyya Allah ya saka da alkhairi nagode sai kinzo" Bangaren gidan su fareeda shiri suke babu kama hannun yaro wai inji 'yan magana suka ce "abari ya huce shike kawo rqbon wani" Sosai suke shiri tamkar auren budurwa gashi tasha siyayyar kayan kitchen kamar wadda za'a jerawa a daki,sunje gun wani malami wai suna so ya basu maganin mallaka mai zafi,shiko malam yace musu"Kar su raina mishi hankali don sun ganshi a zaure shine za suyi tunanin malamin banza ne to sutashi su tafi mutanen banza" Tashi suka yi suka nufi wani layi suna tafe suna zagin wannan malamin wai ya yiwa arziki kafa. Basu zame ko'ina ba sai gidan wani malamin shima,bayan sun shiga cikin zauren nashi ne suka zauna zasu fara mishi bayani sai yace dasu "ai tun kan Ku dosu inda muke aka bamu labarin ku,ba mallaka kike so ba ? To kin samu indai akan Amir ne sai yanda kika yi dashi" Magunguna ya basu wanda zata yi hayaki da wanda zata zuba mishi a lemo to matukar yasha shikenan aiki ya gama. Fareda Allah ya bata sa'a ranar Amir ya je zance ta kawo mishi juice na Fineapple da dambun nama inda makociyar su ta yi mata aifa mutumin ya samu guri yaci yasha yayi hani'an. Kwana biyu sumayya ta rasa kan mijin nata abubuwa sai kara gaba suke ba wai su ragu ba. Umma ce tayi mata waya tace mata " yau zanzo sumayya idan da abin da kike bukata ki fada zan taho miki dashi" "Umma ki taho mun da Aya d gyada mai gishiri idan kinyi kantu shima a hado da shi. Umman ta tazo tayi ta mata nasiha akan muhimmancin hakuri d kauda kai "Sumayya kiyi hakuri ki kauda kanki akan su sannan ki zauna dasu d alkhairi,dole sai kinyi hakuri domin zama d kishiya akwai ciwo musamman in aka yi rashin dace an samu marar kirki,to amma kiyi kyakkyawan zato akan abokiyar zaman ki kici gaba da yin addu'o'i da sallar nafilfili d karatun Alqur'ani duk da nasan kina da kokari akan addinin ki.Ki ya waita yin sadaka,domin ita din maganin masifu ce kiyi tawassuli da ita ki roki Allah bukatun ki in shaa Allahu rabbiy Allah bazai bari ayi galaba akan kiba.sannan kiyi masa biyayya ki bashi hadin kai wajan wanzar da zaman lfyr gidan ku ki mu'amalanci abokiyar zaman ki da kyakkyawar dabi'a,kiso Ahalin ta kike musu kyauta da abin da Allah ya hore miki,kiyi kawaici ga duk mutumin da zai 6ata miki rai wllh sumayya duk mai nufinki da sharri bai isa ya cutar da keba sai dai Abinda Allah ya kadarta.ki yarda Allah ya tsara mijin ki mijin mace hudu ne in kika cire kishi a ranki zaki sami salama d kwanciyar hankali.ki yiwa mijin ki Addu'ar samun zaman lfy a tsakanin ku,Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin ku." "In shaa Allah umma zan kiyaye sannan ni bana damuwa d auren shi saboda Allah bazai bari a cutar da niba" "Yawwa 'yar Albarka ubangiji Allah ya miki albarka ya kare ki ya daga darajar ki ya daukaka minke sumayya tare da zuri'ar ki Allah ya raya miki 'ya'yan ki Allah ya daukaka darajar ki a idon mijinki d zuciyar shi .Allah ya baku zaman lfy." Sallama suka yi da umma ta tafi.kuka sumayya tazauna tana yi saida tayi mai isar ta har sai da taji kuncin da yake zuciyar ta ya ragu. Muje zuwa labari yana gaba [6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LskntU56JpKIS3kUZmcwPV ZAMAN 'YA'YA NA. Na mmn Annur Page (10) MUNA ROKON ALLAH YASA MAHAJJATA SUYI HAJJI KARBABBIYA,MUDA MUKE GIDA NIGERIA ALLAH YA KARBI TAMU IBADAR YASA WATA SHEKARA DAMU ZA'AYI Amin ya rabbi Matar Alhaji Adnanu suwaiba bata san wainar da ake toya wa ba,tunda mijin nata shi ko da yaushe ba shiri yake da matar tashi ba. Maganar auren shi ma bata ji labari ba,samun mace irin suwaiba sai an tona,mace ce ta kirki macen arziki wadda tasan kima da daraja ta mutane,musamman dangin mijin ta. Duk wanda zaizo inda take to kokari take ta faranta mishi. Da kudin ta Alhaji Adnanu ya samu arziki,daga "bani rancen kudaden nan naki suwaiba zan saro kaya idan Allah ya nufa zan maida miki kayan ki" Haka ta hada kudaden ta na hannun ta da wadanda suke banki ta bashi kudi kusa dubu dari tara da hamsin haka ta bashi wanda har yau bai bata ba gashi nan yana fantamawa da ire-iren kudin nata.tana son yin amfani da kudaden ta amma ya hana ta,wannan mugunta ta Alhaji Adnanu tayi yawa sai dai ya amfanawa 'yan matan shi amma ita da yaran ta sai dai suyi hakuri. Akwai babban dan shi Abduljabbar yana bakin cikin irin wannan halayen mahaifin nashi wasu lokutan yana ganin giftawar bbn nasu a mota da mace,wanda in mahaifiyar su bata da lafiya ko daya daga cikin yaran nashi ba lfy to sai dai su fita suje su hau Adaidaita sahu. Lamarin kam sai Addu'a Suwaiba mace ce mai addini da sanin ya kamata shiyasa yaki ya sake ta .don Acewar sa lokacin da ta nemi saki saboda ukubar da take sha haka yace "ki zauna zaman 'Ya'Yan ki don babu mai rike miki su nima in kin tafi wllh idan na tafi to ki tabbata wani muhimmin abu ne zai dawo dani amma ba kula da 'YA'YAN ki ba" Kai jama'a wato wannan mutumin ba karamin marar mutunci bane wai "ya'yan ta shi ko ba nash 'ya'yan bane oho masa Bikin Amir ranar Lahadi za'a daura masa aure da amaryar sa fareeda,bayan an daura kuma xata tare a ranar, Ana jibi biki sumayya ta kira mmn Afrah kawar hajiya MEERAH akan tana so tayi mata bucking din kunshi da kitso sai gyaran kafa da gyaran jiki. Gobe daurin aure don haka sumayya ita da kawarta aslamiyya suka je shagon na hajiya MEERAH wanda yake a zoo road Amana plaza kusa da shoprite opposite sufi mart shagon HAJIYA MEERAH B HERBS .aiko sunga tarba ta musamman domin ma'aikata ne birjik a shagon nata kowa da aikin sa akwai maryam a shagon ita ce ta yiwa sumayya kitso na fita kunya sai mai kunshi itama data tsantsara mata gashi anyi mata gyaran jiki d kafa kafin ayi mata kunshin wllh mai karatu da zaku ga sumayya baza kuce ta haifi twins ba domin ita jikinta ba irin wannan jikin da mace tana haihuwa zai nuna ba ne,tayi kyau sosai. Bayan sun dawo gida ne da daddare sai ga Amir da kaya niki niki na fadar kishiya sai cefanen ta tunda tace taro zata yi ya kara mata da 20k sai lemuka da yasiyo su katan katan 'yan biyu ma siyayya ya musu ta kayan sawa sai takalma iri daya sai abin wasa da ya kwaso musu da madarar yara,godiya sumayya tayi mishi tana murna tace " a amarya dai alamu ya nuna abokiyar arziki ce gashi har da wata siyayya ta musamman gaskiya naji dadi sosai don ni na matsu tazo ko ma kara shan wata jar miyar" Shiru yayi jikin sa duk yayi sanyi ganin sumayya tana dokin auren shi ,shi mamaki take bashi babu kishin sa a fuskar ta kwata². Bai San dannewa take ba shiyasa.Da zata tada hankali tabbas Amir sai yayi ya mididi da ita amma da yake ta iya kissa shiyasa ta ki nuna masa ko a fuska ,illa sai ya fita take samun damar yin kuka. Ayau ne aka daurawa Amir aure da fareeda inda dare nayi aka kawo amarya sai guda akeyi ita dai sumayya tana daki ita da kawayen ta da wasu daga cikin 'yan uwan ta sai ji suka yi ana amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida amarya kece da fada yau amarya uwar farin jini.ayyyriririyiriiii haka aka samu wata ta rangada buda ,kirjin sumayya sai zafi yake mata karfin Addu'a ne yasa ta zauna lfy amma tabbas taji wani iri a ranta bata jin dadi ma ita yanzu kwata² . Dakin sumayya aka kawo amarya aka samu kanwar bbr ta tacewa mutanen dakin"barkan ku dai bayin Allah ina uwargidan"? Inda sumayya take aka nuna mata tasha kwalliya cikin wani dakakken leshi tasha dauri ta yanda babu wanda zai iya kallon ta ya kawo mata wargi. "To uwargida ga amanar amarya nan ku zauna lafiya duk da kishiya ba abun yarda bace to amma mu dai ga amana mun bani" Aslamiyya ce tace iya ki rike amanar ki tunda kishiya ba abun yarda bace to maza kaita dakin ta kizo da wannan abin kamar mutanen basamudiya kice zaki bawa wannan baiwar Allah amana? To maza dauki amanar ki tunda ba mutunci a cikin tafiyar" "Yar nan meye na fadar magana kuma iyi? Kodai kishi kike taya 'yar uwar takine? To bari kiji ita tayi sake har mijin ta yayi mata kishiya in ta cika mace ta hana shi,ba gyara take ba yo ina ga ko girkin kirki ba lallai ta iya ba shiyasa aka nemo wadda ta iya* "Baiwar Allah munji kutashi ku fita Allah ya bada zaman lfy" " Amin idan da gaske kuke zama daram sai dai mutuwa zata fitar da ita" Tashi suka yi suka koma dakin Fareeda wanda yake shima ciki da falo sai toilet da kitchen a cikin dakin Ziga ta suke yi akan duk abinda tayi mata kar ta raga mata tunda kishiya ba ' yar uwa bace,ita ma faredar da yake duk jirgi daya ya kwaso su da "to " take amsawa. Bayan kowa ya tafi sai aka bar Amarya da uwar gida su kadai can anjima sai ga Ango yasha farar shadda wadda tasha dinki mai kyau anyi kwalliya da bakin zare yayin da ya dora bakar hula akan nashi. Da sallama ya shigo gidan sumayya ta amsa tana mai jifan shi da murmushin ta mai sanyaya zuciyar mai kallo,shiga yayi dakin tare da zama akan kujera yana mai fuskantar sumayya. "Habibi ina yini ya hidima ya gajiya ? To Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba" "Lfy kalau mmn twins ya taku gajiyar ? To ina fata kina lfy" "Lfy kalau.ya kamata ka tashi ka tafi dakin amarya bai kamata ace kazo ka zauna ba ita tana can kabar ta da kewar ka,katashi" "Ikon Allah sumayya bakya kishi na ban san meyasa ba har korata kike yi" " a a ni ba korara ka nake ba ina so ne ka zama adali tun daga yanxu" Tashi yayi bayan ya ajiye mata kunshin ledar ta guda biyu wanda suke dauke da San yoghurt guda uku,akwai strawberry, Banana , Sai yoghurt. Dayar ledar kuma wata hajjajun kaza ce aciki wadda ta gasu tayi laushi tasha Albasa da koren tattasai. Murmushi sumy tayi tace to Aalhmdllh bari inyi wanka inzo in sauka akan ku. Bayan tayi wanka ne ta sa kayan bacci ta sahiga kitchen ta dauko plate da wuka ta dawo ta zauna hakar kari ta yanka ta zauna tana ci sai da taji ta koshi da naman tukunna ta bude jarkar yoghurt tasha ta koshi ai nan da nan taji ta war tsake gajiya ashe dai da yunwa a tattare da ita . Dakin ta ta kulle yayin da tayi Addu'a ta tofa ajikin bangon dakin ta doshi 'ya'yan ta ta kara musu addu'a itama ta shafa a nata jikin ta kwanta ai ko waya bata samu damar dannawa ba bacci yayi awon gaba da ita. Asuba nayi Amir ya buga mata kofa ta tashi tayi sallah, tashi tayi ta shiga toilet tadaura alwala bayan ta fito ne ta samu doguwar riga ta sa a jikin ta da hijabi ta fara gabatar da raka'atanul fajr ,sannan ta yi sallahr asuba. Bayan ta idar tayi azkar dinta ta dauki alqur'ani tana karatu sai cana wajan 6:30am ta tashi ta shiga kitchen ta dora musu abin kari ,doya ta fere ta yi musu yamballs sai kunun gyada da tayi musu da yake tana son kunun gyada shiyasa ake siyo mata markadaddiyar gyada ta ajiye ta bata lalacewa.sai shayi da ta dafa yasha kayan kamshi bayan ta gama ne ta gyara gun da ta 6ata ta shiga wanka bayan ta fito ne ta shirya cikin doguwar riga T BUBU tasha stone sai kyalli take sharrr da ita don tayi bacci sosai ba ta tsaya kishi ya hana ta bacci ba. Nata ta dauka wanda zai isheta sannan ta zuba musu nasu ta ajiye musu a kofar dakin su. Sai can wajan 8:30 am ,sannan suka fito daga daki bayan sun shirya shi gogan dakin uwar gida ya shiga don canja kaya, sai ji yayi ance "habibi barka d safiya ya amarya ?" "Lfy kalau amarya ta" "Amarya kuma ? a'a kace dai uwar gida,ai in kace mun amarya to ka rage mun daraja fa,ato sarauta ce Allah ya bani kaga ai bai kamata a kwace ta ba gara kace uwar gidan sai yafi armashi" Wato sumayya da gangan ta fada mishi magana don ta nuna ita fa basa gabanta . "Sumy kinyi kyau sosai wllh kamar in zauna inyi ta kallon abata.Meye sirrin wai?" Dariya tayi tace masa"kwanciyar hankali ce da nutsuwa,yo ba abinda yake damuna shiyasa kaga nayi fresh.a gaba ma zan kara canjawa tunda kaga mu biyu ne hutu ya zo mun ai ALHMDLLH. Sai mu huta" Ya shaka mutumin fa don ficewa yayi bayan yasa kayan shi, dakin fareeda ya shiga ya taradda ita tasa kananun kaya sun matseta sosai gata wata kata6ar6ara kai sai kayi tunanin bayerabiya ce ya auro ga fuskar nan tayi mata wani jibgaga kai gata nan dai ita adole tayi wankan gayu bata san sai ta fito zata ga sarauniyar kyawawa ba . Cewa yayi da ita " ki tashi mu karya ko amarya ta,fari ta mishi da kananun idanun ta tace to honey Abincin suka ci suka koshi tukun na fareeda tace" honey wai restaurant kaje ka siyo abincin nan ? Gaskiya sun iya wllh" Dariya yayi mata yace"ai Abokiyar zaman ki gwanace gun yin girke girke ba siyo wa nayi ba." Shiru tayi don babu bakin magana tunda ita bata iya girki ba gaskiya "Kitashi ki canja kaya ina son yin magana daku a dakin sumayya" Kaya tasa babu laifi Riga da skirt aka mata na Atamfa,dinkin yayi mata dass a jiki saidai matsalar te6ar ta duk tayi mata kamar mai cikin haihuwa. Dakin sumayya suka shiga lokacin tana chatting da Karima kawar ta tana bata hakuri akan rashin zuwan ta saboda bata jin dadi. Wayar ta ajiye tace "sannun ku dai Amarya da Ango" Bayan sun zauna a kan manyan kujerun ta ne sai kuma kowa yayi shiru. Ita fareda tana jira sumayya ta gaishe da ita ,itama sumayyan tana jira fareeda ta gaishe da ita Shirun ne yayi yawa sai Amir yayi gyaran murya yace " to Alhamdulillahi ina wa Allah godiya da ya kaddara za muyi rayuwa a inuwa daya.sannan ina kara godewa Allah da ya bani sumayya a matsayin matata domin duk wasu abubuwa tana yi mun ba kasawar ta bace tasa na kara aure ,a'a kawai dai nayi sha'awar karawa ne don koyi da sunnar Manzo (s.a .w).don haka sumayya kece babba bana so ace fitina ta tashi a cikin gidana sannan ga fareda nan ina so ku hade kanku kuba wa marada kunya inaso ku zamo 'yan uwa kada a kawo wa dayar ku gulmar dayar ku ku yarda ,don Allah ku zauna lfy. Fareeda ina so ki girmama min sumayya domin ta min halacci a rayuwa ta bana so ace raini ya shiga tsakanin ku ina son matata bawai bana sonta bane yasa na aure ki ,yawwa kema ina sonki to kamata yayi ku mutunta junan ku tunda a karkashin abu daya kuke" "In sha Allah zamu zamo masu bin umarnin ka sannan kuma babu wata fitina da za kaji a tsakanin mu" inji sumy. "Fareda ke ba abinda zaki ce?" "A a honey ai duk abinda zance 'yar uwata ta fada" Da haka suka yi sallama kowa ya kama gaban sa. 'Yan biyu ne suka tashi a bacci ,wanka ta musu ta shirya su cikin kananun kaya yellon Riga da blue jeans iya gwiwa yaran nasu sunyi kyau ma sha Allah dasu.dadyn sune ya shigo gun 'ya'yan shi suna ganin sa kowa ya fara dariya suna daga masa hannu alamar a daukesu.ya dade suna wasa da twins sannan ya tashi ya shiga dakin fareda da su kwantar dasu yayi a kan gadon ta itama ta taya shi yiwa yaran wasa sai da suka nemi uwar su tukun na fareda ta kai mata yaran .hakika tayi sha'awar su sosai taji kaunar yaran a ranta . "Mmn twins ki bani su ina son su wllh" "To banda abinki auntyn twins ai kema 'ya'yan kine babu damuwa in kika ce ma acan zasu ke kwana ai duk daya kunfi kusa ni 'yar kallo ce " Dariya suka yi dukkan su . Yaran ta kar6a ta basu nono suka sha sannan ta dama musu abincin su sai da suka koshi ta dora su a kafadar ta sannan sukayi gyatsa ta sauke su ta sanya su akeken su na koyar tsayuwa Rayuwar gidan su gwanin sha'awa a yanxu dai kam zaman lfy suke yi sai dai dan abin da ba'a rasa ba amma dai shima Amir hankalin sa a kwance domin ya yarda da sumayya ita ce jigon tafiyar da kwanciyar hankali a cikin gidan sai dai muce Allah ya raba su da masu tsegumi da hadin rikici Meenatu Amjuf ( mmn Annur baby) [6/11, 6:13 AM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA Na mmn Annur Page(11) Aslamiyya A marya. Yau ake shirye-shiryen daurin Auren Aslamiyya da Alhaji Adnanu Akan sadaki naira dubu dari biyu. Daurin Auren da ya tara manyan mutane da kananu,Bayan An daura ne, Amarya da ango sun sha photuna kowa ka kalla fuskokin su akwai walwala saboda buri ya cika. Saboda an gama da Alhaji Adnanu an mallake shi saura mallaka mai karfin ma idan amarya ta tare a gidan shi. "Umma kinga wani ikon Allah shin Abba Aure yayi ba tare da mun sani ba?" Inji babban dansa Abduljabbar mika mata wayar yayi ta duba ta gani tabbas mahaifin su ne. Wayar shi ta bashi tace"Allah ya kyauta"yayin da zuciyar ta take mata radadi wani bangaren na zuciyar tata yake ganin rashin adalci irin na Alhaji Adnanu,mutumin da tayi wa dare yanzu gashi nan shine yake neman kaita rana. Tashi tayi ta daura Alwala tayi nafila sannan ta roki ubangiji ya mata maganin abinda ya fi karfin ta. Zuwa karfe biyun rana Alhaji Adnanu ya shigo gidan nashi fuskar shi a washe kana gani kasan yana cikin farin ciki domin wannan rana yake jira,duk da ta wani 6angaren Aslamiyya ta juyar da tunanin sa ne tun lokacin da ta fuskanci da zarar ya sameta a titi tofa rigar sa zai cika da iska ya gudu shiyasa sukaje akayi musu mallaka ta kut da kut. Sallama yayi wa suwaiba ta amsa mishi cikin kulawa ta yi masa sannu da dawowa " suwaiba ina so anjima kisa yaran nan su dan gyaggyra dakin can saboda zan yi amfani dashi" "To "tace dashi sannan ta kara da fadin " Alhaji lfy yau na ganka cikin walwala sa6anin wasu lokutan da baka shigowa gida fuska a sake?" " Anxo gurin suwaiba Aure nayi,yau aka daura min aure da yarinya danya sharaf yau kuma za'a kawo ta gidan nan kinga ai dole kigan ni cikin farin ciki" " to Allah ya sanya alkhairi yasa abokiyar zama ce" "Amin " yace yasa kai ya fita. Gyara dakin akayi duk da ba wani datti gareshi ba amma sun goge ko'ina yayi fess. Dakuna biyu ne acikin falon sai kuma wani dakin daga gefe alamu sun nuna kamar bedroom ne da toilet sai gefen falon gun dining sai kitchen daga gefe sai kuma wani dan lungu da zai kaika sashen mai gidan. 'Yan kawo Amarya sun xo cikin mutunci da mutun tawa,gurin uwar gida suka fara zuwa aka gaisa sannan suka ce mata " amarya ce suka kawo don Allah gata nan amana idan tayi ba dai dai ba to ta nusar da ita" Allah sarki suwaiba sarkin hakuri haka tace musu" ai karsu damu gidan wannan wani abun damuwa acikin sa,illa farin ciki da annushuwa tare da zallar hadin kai ga ma'abota zaman gidan don haka basu da damuwa ai da na kowa ne ita ba kishiya bace a gunta sai dai 'ya,tunda a haife ta haife ta sai dai fatan samun zama lfy da hadin kai" Godiya suka mata ta musu jagora zuwa 6angaren Amarya. Shiga suka yi kowa sai rarraba ido yake yana kallon irin dukiyar da aka kashe. Suwaiba fita tayi daga dakin ta koma nata 6angaren,sai can wajan 10:00pm tukun mai gdn ya dawo bayan 'yan kawo amarya sun gaji da jira bai zo ya bada kudin siyan baki ba. Da sallama ya shigo gidan ko dakin suwaiba bai kalla ba ya wuce dakin amarya direct shiga yayi yana doka wani shu'umin murmushi yace " Amarya bakya laifi ranke dade baby" Shiru bata amsa ba leka fuskar ta yayi yace amarsu ta ango mai dadin tuwo" Murmushi tayi ta kada masa idanuwan ta tace yalla6ai me yasa baka dawo da wuri ba?" Dariya yayi yace " banda abinki ai sai an sallami baki tukun ai zanzo na taho gida abokai na na wasu garin ai baza suji dadi ba amma yanxu kowa ya tafi ,yau dai ranar kice baby" Sallah suka yi raka'a biyu ko dafa kanta baiyi ba balle ya yi addu'ar nan da aka umarci wanda yayi sabon aure ya yita ( ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA KHAIRI HA WA KHAIRA MA JABALTAHA ALAIHA WA' A' UXU BIKA MIN SHARRIHA WASHARRI MA JABALTAHA ALAIHA) Dayake ba wani cikyakken ilimi ne dashi ba ko akansa ita kanta aslamyyan bata san ana wata Addu'a ba. Washe gari da safe bayan sun tashi,suwaiba ta yi makari ta mika musu na su ita ma da nata yaran suka zauna suka ci.ka'idar ta indai Abinci za'aci to ita da yara suke ci don neman albarka da hadin kan iyali a gun Allah ta'ala. Aslamiyya ce ta fito tsakar gida tana rarraba ido,a sannan Abdul jabbar ya fito daga dakin maman shi zai tafi makaranta da yake yau litinin,kallon sa tayi ta watsar tace masa" Kai yaro ina mutanen gidan naku ne?" "Ban gane ba?" "Kai gidan ku ,kai manya suna magana ka wani tsaya mun getsetse a kai. Kai baka san ni din wace ce a gidan naku ba?" "Wacece kwa banda 'yan uwan Amaryar baba na. KO bayan nan akwai wani abun ne?" "Lallai yaron nan kai tunanin ka banyi kama da matar gidan ba?" "Auuuuuu wai kina nufin kece Amaryar wucin gadin da aka kuma jajubowa? Lallai yarinya an kashe miki rayuwa da aka baki dattijon nan wllh" Aslamiyya dariya ta saki wadda tafi kuka ciwo " to yaron nan me yake nufi ne da wannan bakar maganar da ya ya6a mun?" "Hmmmm yaro yaro ne za kayi bayani in dai Aslamiyya ce" Tafiyar shi yayi yana mai bakin cikin wannan halin na yawan aure-auren mahaifin sa. Yana cutar da maman su amma bata isa tayi magana ba yanzu cibi zai zama Qari. In bai mantaba sau biyu a gaban shi bbn shi ya duki mmn shi,shiya yake kara jin tausayin mnn nasu duba da yanda ta jajirce ta hakura da farin cikin ta da jin dadin ta ta zauna ZAMAN 'YA'YAN TA. Allah ka kawowa mmn mu dauki ka shiryar da bbn mu yasan daraja da kimar mahaifiyar mu. "Alhaji Adnanu ne ya tara matan nashi a falon shi inda yake cewa " suwaiba ga baby nan kar inji kar in gani ba zatayi girki ba zaman aure take ba ZAMAN 'YA'YA ba don haka ki gargadi 'ya'yan ki akanta banda rashin kunya domin akan baby zan iya hakura da komai da kowa ciki kwa har daku" "To in sha Allah bbn Abdul za'a kiyaye" "Kin taimaki kanki" "Baby ba abinda za kice?" "Yalla6ai ai ka gama fadar komai,sai dai ina da sharadi, bana son idan ina baccin safe kwarafniyar yara ta tashe ni bana so a kiyaye" "Kinji me tace KO suwaiba?" "Eh naji Bbn Abdul" Bayan wasu kwanaki aslamiyya ta tsiro da wani salo wai Abdul shi zai ke yimata wanki da guga ,yaro yace" ba zai yi ba sai dai taba bbn su ya yi mata tunda shine ya ajiye ta" Aslamiyya tace " nasan da bbn naka ai shiyasa na baka wankin ,shima wankin underwear na shi yake yi" Ranshi kam ya 6aci sosai da wannan maganar da ta fada masa akasan ranshi yana cewa" duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ka duka" Yana azabtar da suwaiba gashi nan ya afkawa mallaka ta har abada inda sai abin da tace a gidan shi akeyi Suwaiba ta koyar da yaranta addu'o'i sosai da azkar itama yi take yi shiyasa duk wani kulle kullen Aslamiyya bai kama suba. Alhaji Adnanu fa ya susuce akan Aslamiyya don ita take juya gidan kamar yanda taso. Azabtar dasu take ta 6angaren Alhaji Adnanu don wani lokacin sai ta hana a basu Abinci Agidan ita kwa suwaiba abin tun baya damun ta har yazo ya fara damun ta.ita suke yiwa mugunta saboda 'YA'YAN ta.sai dai ta yi 'yan dubaru ta sama musu abin da za suci ita da yaran ta,don ko rabon kwana ba'ayi ba KO da yaushe suna tare,ita kwa ko takan ta basa bi. Abduljabbar ne yaje gun wani kafinta ya rokeshi akan don Allah yana so yazo gurin shi ya koya masa aikin kafintan,da yake mutumin na Allah ne amincewa yayi yace "kaxo ka koya kaji dan samari,ka burgeni sosai da kaxo kake neman abinda zaka rufawa kanka asiri wllh, don yanzu samari suna nan sunki sana'a sun zauna jiran gobnati ta dauke su aiki" Godiya yayi masa bayan mutumin ya tambaye shi sunan sa ya sanar dashi. Mahaifiyar shi ya samu ya sanar da ita ,murna tayi masa kana ta bishi da addu'a sannan ta nuna mishi muhimmancin rikon amana da biyayya wa na sama dashi. Alhaji Adnanu yana kwance yana bacci Aslamiyya ta tashe shi tace mishi " yalla6ai ka tashi ka samo mana Abinci ni wllh yunwa nake ji" Tashi yayi cikin azama har jikinsa karkarwa yake yi ya fita daga dakin inda yaci karo da suwaiba "Ina kwana" tace dashi amma ko kallon arziki bata isheshi ba. Daki ta shiga da sauri ganin kuka yana neman kwaace mata,Addu'a ta shiga yi tana yiwa Allah kirari tare da godiya a gareshi bisa jarabtar ta da yayi ,ba don baya sonta ba, A'a don ta samu babban rabo a duniya da lahira. Aslamiyya ce ta fito da kayan wankin ta, ta cewa suwaiba "ina wannan yaron?" Banza tayi da ita taci gaba da aikin ta dama gugar unifoam take yiwa Abdurra'uf da Abduljabbar na islamiya, Shigowa cikin dakin tayi tace "wai suwaiba ba magana nake miki ba?" Dagowa tayi tare da ajiye iron din tace" ke ki kiyayeni zan sa6a miki ni ba irin wannan sakarkarun matan bane da zasu zauna kishiya ta juya su,a haife na haife ki to ki juya ki fice min a daki in ba haka ba wllh zane ki zanyi yanzun nan fitsararriya marar tarbiyya" Akan kunnen Alhaji Adnanu ji yake kamar ya je ya mata duka to bari ya shiga ya gani tun kafin ta dukar masa baby Dakin ya shiga ya same ta yake mata fada kamar ya samu 'yar shi,gwalo Aslamiyya ta yiwa suwaiba tare da nuna ta da yatsa tana nunin zata san matakin da zata dauka akan ta . [6/8, 6:52 AM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LskntU56JpKIS3kUZmcwPV ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur. True life story Gajeran labari Ina ma'abota san su kyalkyale jikin su fatar su tayi smooth,hajiya ta kina so ake miki kallon kina rayuwa a in da babu rana? Hajiya kizo kiyi oder shower gel din mu domin gyara fata tana cire duk wani datti da ya makale miki a jikin fata ko matse_matsi,irin su glass, pimples ,kyasbi,makero,nankarwa.zata gyara fatar ki zata maida ki kalar hutu koda ba hutun kike ba,tana da auki sosai ga kamshi mai dadi jikin ki yy tsantsi kiyi glowing. Muna bayar da sari ga mai siyan daya ma muna maraba daku Maiso ya min magana ta wannan number, 09069615587. Page(12) Sumayya mutuniyar kirki duk da Amir ya canja mata amma bata fasa yin biyayya a gare shi ba,duk da wani lokacin yana dan yin takar takar wajen son kyautata mata. Wannan tasa Fareeda kara kaimi wajan yin amfani da magungunan ta na wajen malamin su Yau dadi gobe babu dadi a haka umman ta take yi mata nasiha ta zauna da mijinta da abokiyar zaman ta lfy sannan tasa a ranta bautar Allah take yi ba wai don Amir ba,to in dai don Allah take yi ba wai don a yaba mata ba to zata ji dadin zaman auren ta,babu Abin da wani bawa zai yi mata sai dai Abin da Allah ya kaddara zai same ta shima don a gwada imanin tane. Da wannan shawarar take zaune lfy a gdn mijin ta,Fareeda ruwa biyu ce domin idan Amir yana nan to zata ke yin biyayya wa sumayya amma da zarar baya gida to fa da kyar wata mu'amala ta kirki take hada su da ita.iyayen sumayya sun dage suna yi mata Addu'o'i na neman tsarin Allah akan ta duk wani mai binta da mugun nufi to fa ba zaiyi nasara akan taba duk da itama ba baya ba wajen dagewa da Addu'a. Duk wani kulli idan fareeda tayi wa sumayya to a banza yake domin jikin ta kullum yana tare da alwala sannan tana tofa Ayatul shifa a cikin ruwa ta shafawa jikin ta tasha ita da yaran ta wannan shi ya hana asirin da fareeda take yi yin tasiri a jikin sumy. Fareeda sai ta tsiro da in suna zaune da fareeda sai ta kunna ringtone idan yayi kamar zai tsinke sai ta daga tace" hello sweety y kk?" Can kamar ance mata wani abun sai ta kara yin magana sai daf ta jima tana waya a matsayin da Amir take sai ta kara cewa " sweety idan zaka taho ka taho mun da wannan gasashshiyar kazar irin ta kwanaki,ita nake marmari,yauwa sweety har da ita ehh rufaida ba,a'a vanilla ba strawberry ba,yawwa sweety nagode sqi ka karaso uhmmmm to byeee" sai ta saki kiss ta wayar ta. Kullum da salon da take yi kai abin fa har ya fara damun sumayya duk kawaicin ta. Yau din ma hakan ce ta kasance da ita sumayya tun dare ta samu Amir da zancen madarar yaran ta kare sai yace " zan siyo in shaa Allah idan da wani abun ki fada" Haka tace " mai na da turare na ya kare sannan gashi waya ta ta dan samu matsala" " gaskiya bani da kudi sai dai wani lokacin" Shiru tayi ranta yana Mata kuna.a cikin ranta tana tambayar kanta "shin wai me yasa Amir ya canja ne,kwata- kwata yanzu ba ya girmama abin da yake ita take so,duk abin da tace ya mata bazai yiba sai dai tana gani zai yiwa fareeda siyayya" daki ta koma ta kwanta kusa da twins din ta,kallon su take tana kuka tana fadin"yara na kune farin cikina tabbas ba don ku ba to da na dade a gidan mu,to saboda na ganku cikin farin ciki shiyasa na zauna a gidan ku ,yanzu gidan ku makabar ta tafi dadin xama fiye dashi ,babu wani farin ciki ba walwala gashi wasu hakkokina suma ba duka ake sauke wa ba" Kai sai kayi tunanin da wasu manyan yara take zancen nata. Washe gari da safe fareeda ta kar6i girki,bayan sun karya ne Amir zai fita ko kallon ta bai yi ba tace masa"Allah ya kiyaye hanya" "Amin"yace a takaice har zai fice sai kuma ya dawo ya shiga dakin ta ya duba yaran shi kana ya sa Kai ya fice. Fareeda ce ta fito daga daki hannun ta dauke da takarda da robobin lemo tana wani taku dai-dai taje ta zuba su a dustbin tana wani hamma da mika tana fadin "kaiii wllh sweety ba dai iya soyayya ba,ka hanani bacci gashi yanzu dolena in je in rama shi don ba'a cin bashin bacci a zauna lfy" Murmushi sumy tayi ta kauda kanta,don bata son irin wannan zan tukan. Fareeda tana shiga daki ko minti biyar bata yiba ta daga wayar karya ta kara a kunnen ta tace "sweety har kaje shagon ?" Sai ta kara fadin"ehhh sweety nagode sosai Allah ya barmu tare ya kauda idon makiya masu barin kashi aciki wanda baya maganin yunwa ,ai ka gama min komai maigida na rabin raina,ehhh itama tayi nagode,kaga wannan sai in baiwa iya tayi manage da ita kafin a siyo mata itama tecno ce ko? To ina sonta babu damuwa sai ka karaso byeee" Hmm makira ce fareeda tabbas sadakin ta ne ta hada tace ya siyo mata waya babba mai kyau,to an Samu ne fa shine wai take wannan barikin. Kai jama'a kishiya kishiya ce sai dai muyi ftn Allah ya mana tsari da sharrin su musamman na wannan xamanin sai kiga budurwa har budurwa amma ta bayar da budurcin ta tun a titi,hajiya in dai haka kike to kin zama jakar gayu ,don duk iskancin namiji to baya son auren 'yar iskar mace ,ke kina ganin kin burge saurayin ki tunda kin bashi damar ta6a ko ina a jikin ki to ki sani da zaiga kanwar sa ciki daya tana tare da saurayi matukar saurayin in ba na kirki bane to zakiga ya taka masa birki don yasan abinda yake yi da waccan budurwar tashi ba a bune mai kyau ba. Amir ne ya shigo gdn bakin sa dauke da sallama sumayya ce kadai a tsakar gidan ita ma zafi ne ya dame ta shine ta fito tsakar gida take shan iska,Amsa mishi sallamar tayi sannan tace mishi"sannu da zuwa Bbn twins ya hanya?" *lfy klau yawwa" A takaice ya amsa mata ko kallon inda take ita da yqran ta suna ta mika mishi hannu alamar sun gane shi amma ko ta kansu bai bi ba. Carpet din fareeda ya gani a kofar dakin ta sai ya zauna akai ita kuma hamshakiyar tana daki tana shafa jan baki da aishadow,sai kace matar kauye,ita fa idan ta shafa gani take ai ta cinye ba ya ita . Kiran sunan ta yayi sai gata ta fito tana karairaya tace "sweety har ka dawo?" "Ehh na dawo gimbiya ta sarauniya ta ruhin Amir bangaren jikin mijin ta,to ya kike?" Kanta taji ya kumbura tayi farrrr da ido ta dan juya kadan in da sumayya take zaune wai ko zata ga sumayyan tana kallon su ta kular da ita ,ita ko sumayya ko kallon in da suke ma ba tayi kunnen ta dai ya dauko mata maganar da Amir yake fada wa Fareeda. "Uhummmm sweety na barni da kewar ka ina ta jiran ka baka dawo da wuri ba ko abinci kasa ci nayi saboda ina jiran ka" Ina ruwan shahararriya inji sumayya lallai matar nan kamar ba dazu ta narki Abincin nata ba,Amma ji yanda take shara karya ,ummmm Allah ya kyauta. "Ayya sorry beauty tuba nake kai na bisa kasa ina neman Afuwar ki" "Uhmmmmm ni dai sai ka goye ni sannan zan hakura" "Kaiii rigima yau ake ji beauty to maza yi shiru kinji muna gama cin abinci zan goye ki" Abincin suke ci suna shiririta wanda basu suka gama cin Abincin ba saida suka kusan yin minti 40 tukun na. Ita fareeda da gangan take abubuwa duk don ta kular da sumayya,to amma ita sumy kwata-kwata bata nuna tasan me take yi ba don 'yan biyun ta take yiwa wasa,amma fa kasan zuciyar ta radadi yake so take tayi kuka amma ta danne ta barwa Allah mai kowa mai komai wanda ya san abinda yake wakana a fili ko a 6oye. Suna gama cin Abincin Amir ya danyi goho yace " fareey baby zo ki hau bambu " Tana dariya ta hau abin ta suka yi ta zagaye a tsakar gida karshe sai ya kaita daki suka zauna a can. Sumayya tana ganin ikon Allah don wannan zama da tayi da fareeda yqsa duk ta tsani kishiya sai dai ba yadda za tayi mai kowa mai komai ya tsara dole sai ta zauna da ita. Kwanci tashi Asarar mai rai inji 'yan magana to dai yau 'ya'yan sumayyan suka cika shekara daya a duniya,maa shaa Allah yara sun yi wayo 6ul6ul dasu gwanin sha'awa,matsala daya sun rasa gatan uba wanda kowa ya rasa uba ya koka, to su dai gasu da uban su amma baya ta tasu kwata-kwata,shifa ya zauna ya ce wannan sumayya ce matar shi abin ya gagara domin kusan kullum mallaka ta har Abada dirka masa ake a cikin lemo sannan tayi inserting da wata mallakar kai wannan masifa tayi yawa. Ita dai kullum tana kaiwa Allah kukan ta akan ya kawo mata dauki ya juyo musu da hankalin Amir kansu ita da 'YA'YAN ta haka za ta raba dare tana Addu'a da karatun Alqur'ani cikin hikima ta ubangiji sai take jin salama da aminci a ranta ga wata nutsuwa da take zuwar mata . Hakika babu Abin da yafi sanin Addini dadi ,duk wayewar mutum matukar bai san wani abu a cikin Addinin sa ba to gaskiya wannan mutumin ta can canta a Kira shi da bagidaje ba kauye. Sabuwar wayar ta da ta bashi kudin ya siyo mata ya bata ta duba ta murna ta shiga yi ganin ta faso gari itama zata rike waya irin ta sumayya a daina daga mata kai. Daukan wayar tayi ta nufi inda sumayya take tace" mmn twins kinga wayar da sweety ya siya min yace na rage kadaici in ya fita" Sumayya wayar ta kar6a ta gani tace mata"kai gaskiya waya tayi kyau sosai Allah ya sanya alkhairi yasa rayuwa ta amfana,Amma fareeda ai wannan wayar ta zama old modern me zai hana ya siyo miki irin wadda ya siya min washe garin kawo ki?" Fareeda wani shock taji don a tunanin ta ita tazo ne ta dagawa sumayya hankali sai gashi ita nata hankalin ne ya tashi. Da yake itama ba baya ba wajen kissa sai tace mata "a a ni nace dashi ga irin wadda zai nemo min saboda ina jin dadin amfani da ita" "Hmmmmmm haba amarya kawai dai kice ango ya samo miki mai kyau wadda ko taro kika shiga an San ke din ta dabance amma wannan nikam kunyar riketa zanji" Hhhhhh ramin karya kurarrene inji 'yan magana. Fita tayi daga dakin na sumayya ranta fal bakin ciki. Tana shiga dakin ta ta shiga tace"wato ni ina musu kallon basa zaman lfy ashe in suka shiga daki diff kake ji,ni Amir zai ha'inta ? Tun washe garin zuwa na gidan ya siya mata wayar ashe? To nima ai nima tunda ina nan ya siya dole nima ya siya min,amma da yake namiji ne sai ya munafince ni,zai dawo ya same ni ta ruwan sanyi" Tana fita daga gun sumayya tayi dariya tace"shu'umanci nima na iya bake kadai kika iya kinibibi ba,yaje ya siya miki mana ai duk abinda zai miki to ni ya min dubun sa,don haka ke ce akasa,domin saura na kika samu" Hmmmm to kunji fa sumayya ta fara yin baki itama. Tunanin fareeda sumayya zata daga hankalin ta tayi korafi a gun mai gidan,ba ta san sumayya duk ta san matakai na zama da kishiya ba,ita ta dau alkawarin ko me fareeda za tayi mata ba zata kai korafi gun mijin suba;saboda yawan korafi yana sa mace ta fita a ran mijin ta ko da ita daya ce a gun nashi balle kuma in akace sun biyu ne ko sama da haka,don haka fareeda tayi ta jira ko sumayya zata yi wa Amir zancen amma shiru kakeji tamkar shirwa ya ci dan shaho. Abin da sumayya tayi ya kular da fareeda sosai saboda haka ta zauna ko kwalliyar da take ca6awa in mijin zai dawo yau kam ba a yi ba,jaraba na cin ta so take Amir ya dawo ta sauke masa,don me zai ha'ince ta ya siyawa sumayya waya ita kuma ya barta da keypad sai ita ta gaji da tsammanin ko zai siya mata yaki siyan shine dan munafirci ya barta ta siya wato ya maida ta wata shashasha kenan. Amir yana shigowa gidan da sallama yayi toxali da gimbiya sumayya uwar gida sarautar mata yarinyar da bata tsufa ba zaka ce ta haifi tagwaye ba. "Sannu da zuwa hayatie" sororo yayi da ya ga sumayya tayi wankan kananun kaya tayi kyau sosai kamar ya tanka mata amma da yake ba a hayyacin sa yake ba wuce ta yayi ko magana bai mata ba Dakin fareeda ya shiga yayi sallama ta amsa mishi tsaya wa yayi yake kallon ta don babu kwalliyar da ta saba mishi kayan da ya barta da safe shine dai yanxu a jikin ta tayi wujiga wujiga ,tambayarta yayi " lfy kike sweety babu tarba babu kwalliya me yake damun ki?" " dole kace haka mana Amir ashe kai ba adali bane ? Shine ka zagaye ka siya wa sumayya waya amma ni ka barni da keypad sai ni na gaji na siya,wllh ka bani mamaki a hakan kake ikirarin kana sona? " Lallai sumayya ta zama kanwa uwar hadi Don jin yadda zata kaya mu hadu a bayan sallah in shaa Allah Ngd taku meenatu Amjuf [6/10, 6:19 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur Page (13). Free book Gidan Alhaji Adnanu zaman ya yiwa suwaiba tsanani domin yanxu ko girki an hanata sannan ba'a bata Abinci,sai dai Abin da dan ta Abdul ya samo a gun aikin su to da shine za suyi manage ayi amfani dashi.Al'amarin yayi tsanani gare su kullum suwaiba tana fadi tashi akan yaran ta,Amma duk d haka tsakanin ta da Alhaji Adnanu Babu tausayi kwata Aslamiyya ta juyar da tunanin sa akan iyalin shi.hakika suwaiba abar tausayi ce in ka kalleta ba zaka ta6a cewa suwaiba ce ba wannan 'yar gayun mace hadaddiya bafulatanar usuli Amma duk wannan kyawun ya rozaye sai wata rama da bakin dole da tayi. Abduljabbar shine cin su da shan su yaro maa shaa Allah ya taso cikin gata da kulawar mahaifa Amma shigowar Aslamiyya cikin rayuwar su duk ta Sanya ya zamo tamkar bai ta6a dandanar dadin rayuwa ba Wake ya siyo musu gwangwani biyu da shinkafa kwata sai barkono da manja da sauran mahadin Abinci,mahaifiyar shi ya kawo wa kayan cikin ladabi yana mai rusunar da kansa kasa "Abduljabbar ubangiji Allah yayi maka albarka ya daukaka ka ya bude maka kofofin samu na alkhairi Allah tsare mun ku ya shirya Mana ku ya hade mun kawunan ku ya baku Abokan zama nagari" Dadin Addu'ar mahaifiyar tasu yaji yace mata "Amin ya rabbi nagode da wannan Addu'ar taki wllh dadin ta nakeji sosai,domin idan na tuno da ita to ina kasancewa cikin azama da son neman na kaina hakika ke din uwa ce jajirtacciya wacce ta sadaukar da jin dadin ta da farin cikin ta duk saboda mu,don kika mun zama wasu,Allah yayi miki sakayya da gidan Aljannah umman mu " Hawayen idon ta ta share ba tare da Dan nata ya gani ba. Tashi tayi ta fito daga dakin tare da nufar wani sashe daga cikin gidan inda ta maida gurin wajen madafar Abincin su,don tun tuni ya kwace kitchen din tsakar gida ya ce" kada ta kara shiga ciki tayi girki yana so zai sanya wa Aslamiyya wasu kaya da ta saro a cikin kitchen din" Girki ta musu bayan ta gama ne ta zuba musu ita da 'ya'yan ta suka xauna suna ci,Sallama ya yi Alhaji Adnanu tare da bankada kofar dakin ya shiga kallon su ya tsaya yi cikin wani kaskantaccen kallo yace musu" uban waye yace ta dafa musu Abincin sa ?" Kallon kallo aka shiga yi sai can ta budi baki tace mishi " Alhaji ba Abincin ka na dauka ba Abduljabbar ne ya siyo muka dafa" "A gidan uban wa ka samo kudi da har ka siyo wannan kayan?" "Baba ai gurin wani kafinta nake zuwa nake masa aiki shine yake biyana wani Abun" "Karya kake yi ja'irin yaro yau saika fada mun waye ya baka kudi, wato kudin da narasa jiya ashe kaine ka shiga daki na ka dauka ko ?" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wllh Alhaji ba shi ya daukar ma kudi ba ,Alhaji kaji tsoron Allah mana kai kanka ka San irin tarbiyyar yaron nan bai dace ka masa irin wannan kazafi ba " "Ni zaki cewa kazafi na mishi? to ki sani ni bazan iya zama da barawo a gida ba,matukar bai nemo min kudi na ba to kisa a ranki sai dai ya bar min gidana " Abduljabbar kuka ya fara yana cewa" Wllh Baba nan dauki kudin ka ba ni rabona da in shiga dakin ka wllh tun kafin Amaryar ka tazo gidannan, Baba kai da bakin ka kake cewa zaka koreni a gidan ka baba? Idan ka kore ni ina zanje ban San kowa ba bani da wanda zanje gurin sa sama daku, Don Allah baba kayi hakuri wllh bani na dauka ba" cikin kuka yake yiwa mahaifin sa magiya akan bashi ya dauka masa kudin sa ba,Amma inaaaa da yake Alhajin ba a hayyacin sa yake ba ko tausayin yaron bai ji ba. Fita yayi daga cikin dakin ya nufi dakin Aslamiyya,wadda tayi saurin dawowa daki ta zauna bayan taje tayi musu la6e ranta fari kal. Suwaiba ce ta ke rarrashin Abduljabbar akan yayi hakuri ya daina kuka Allah yana tare dasu kar ya sake yasa wani abun a ranshi. Abincin ma kasa ci suka yi saboda 6acin rai, ba abin da yafi bakin ciki a dauki laifin da ba naka bane a kakaba maka wannan sharrin yana ta6a zuciya. Suwaiba tashi tayi ta umarci 'ya'yan ta da su tashi suyi Alwala suyi nafila don neman mafita Agun Allah tare da neman tsarin Allah akan kowace musifa da zata tunkaro su. Sallah suka yi raka'a hudu cikin kowacce sujjada tana mai kaskantar da kanta a gun ubangijin sammai da kassai Wanda ya gagara a misaltashi Wanda ya ya dai dai ta akan al'arshi,Allah mahaliccin mutum da aljan tare da dabbobi kanana da manya, kirari take yiwa Allah tana mai yakinin Allah zai warware mata dukkan matsalolin ta. Bayan sun idar ne tace su dauko Alqur'ani su karanta. Suna gama karatun dukkan su kowa yaji sassauci da salama a cikin zuciyar shi. Aslamiyya tana daga daki tana shan dariya domin kuwa burin ta ya fara cika na lallai dole sai ta tarwatsa gidan Alhaji Adnanu in yaso ita ta zauna ita daya daga nan sai ta saki jiki ta fara hiahuwa domin ita ba zata jera da suwaiba ba yanzu ita yanda take jin ta tafi karfin jerawa da kucaka irin suwaiba banda jaraba irin ta da namiji me zaiyi da suwaiba duk ta tsufa ta jeme ga sabon jini ai sai ayi waje da tsohon jini. Fadakarwa 'yan mata kuji tsoron Allah wllh duk bulalar da ta daki uwar gida to sai ta dawo ta Zane Amarya, kar kiyi tunanin wai ko don mai mata yazo gunki da zummar auren ki kiyi tunanin ko ta gidan tayi condem ba haka bane ,shi karin aure raya sunna ne sannan zuciyar namiji duk yanda ta Kai ga son ki to wllh da za a jera masa mata sama da biyar sai ya ce kowacce yana son ta don haka ki sa a ranki yana son matar sa ke din yana so ne ya kara auren kine ba wai don ya rasa wasu abubuwan ba, ta iyu sai namijin ya karo auren tukun zai San muhimmancin matar gidan musammman in ya hadu da marar tarbiyyar Amarya wadda bata ganin kan kowa da gashi to a sannan ne zakiji yana dana sani ,don haka muji tsoron Allah musa a ranmu zamu zauna lfy d abokan zaman mu Babu cuta babu cutarwa. Al'amarin Aslamiyya sai dai Allah ya shirya abin nata ya kara yin gaba, ta samu wani boka ta yi mishi bayanin abin da take so anan ya nemi yayi lalata da ita nan take ta amince bayan ya hada mata magunguna ta dawo gida sai da tayi kwana biyu tana jinyar kanta.Allah ya kiyaye. Aiki ne ya mata kan da zarar tayi hayaki da hadin to fa mijin ta zai like mata sannan ita kuma borar gidan zata yi waje ma'ana za' a koreta duk nacin ta da kwawar ta,aikwa anyi anci nasara domin Alhaji Adnanu da kansa ya shiga dakin Suwaiba ya kore su tare da cewa" suwaiba na koreki da ga gida na babu ku babu ni ki tattara kayan ku keda 'ya'yan ki ku bar min gida" Tana kuka ta tsugunna ta rike rigar shi " Alhaji kar ka min haka don Allah ka barni in zauna ko da ZAMAN 'YA'YA NA ne ina so in rayu dasu a gidan uban su bana so su taso da jin haushin ka a ransu don Allah ka tausaya mana ,bani da kowa a garin nan sai Kai kaine ka kawo ni garin nan iyaye na sun rasu bani da kowa 'yan uwa na duk babu yaki ya tashi da su an kashe mun su Alhaji kasan halin maraicin da nake ciki bai kamata kamin haka ba" Bige hannun ta yayi ya fi ce daga dakin ko minyi daya bai yi ba ya shigo dakin hannun sa dauke da wani katon karfe yace " wllh idan baku fice ba saina rotsa miki shi akan ki in yaso sai ki mutu su kuma 'ya'yan naki sai su shiga duniya ,uwar jaraba ki fice mun a gida " Haka suwaiba ta tashi ta har hada musu kayan su a cikin Akwati sannan ta shiga makota ta ce don Allah su taimaka mata za ta kawo a jiyar muhimman kayan ta gidan da ya ke sun San irin zaman ukubar da take sha a gun mijin nata sai suka ce mata ta kawo babu damuwa akwai spare daki sai a shigar mata da kayan. A kwati biyu ta hada musu sannan ta nufi gidan yayan shi ta sanar dashi halin da suke ciki tana kuka tana sanar dashi. Ya tausaya mata matuka gaya a nan ya basu daki sannan ya sa Abduljabbar ya shiga da kayan su cikin dakin da yake dakin a share yake . Hakuri ya bata sannan yace mata"ni yanzu mijin ki ko a hanya in muka hadu ba ya nunawa ya sanni saboda na hana shi karin aure,nasan halin Adnanu sarai duk biye biyen da yake na mata duk ina da labari to shi ba'a isa a gyara mishi ba sai abin da yayi niyya" Tashi tayi ta shiga cikin dakin bayan sun kintsa kayan su zama tayi ta tafi dogon tunani akan rayuwar su ta baya. SUMAYYA Gidan sumayya rayuwar sai Alhmdllh domin rayuwa ce yau fari gobe baki,fareeda ta samu ciki sai laulayi yake Sanya ta. Tana nan tana fama da Amai da zubar da yawu,Kai ana ganin kazan ta agidan kai hatta da dakin ta bai tsira ba duk jikin bangon dakin jirwayin yawu ne wani lokacin har warin yawu dakin yake yi Amma duk da haka bata hakura da yin girki ba. Sau tari wani lokacin sumayya zata ce da ita "fareeda kibar wahalar da kanki in dai girki ne zan miki in yaso sai ki kwana da mijin,ya kamata ki zauna ki huta idan cikin ki yayi kwari sai ki kar6i girkin" Amma ina ta ki yarda ita kwa sumayya ta zuba musu ido. 'yan biyu Masha Allah don sun girma sosai har sun fara tafiya. Wani lokaci fareeda tayi tuwon masara ta bar shi a bude don yasha iska aikwa Hassan ya tafi da tafiya irin ta 'yan koyo yaje ya fada ciki,jin ihun sa suka ji ai a kusan tare suka tafi da gudu har suna cin karo da kawunan su Amir ne yayi saurin ciro hannun shi daga cikin tuwon, Innalillahi suke fada ganin hannun duk yayi Ja yaron ya rasa in da yake masa dadi kuka kawai yake yi, hamshakiyar tana zaune a falon ta ko ci kanku bata ce ba illa haushin su da taji don jin wanxuwar su a guri daya . Ai gogan dakin ya shiga ya daga hannu ya sharara mata mari har sau biyu.mikewa tayi a fusace tace masa" uban me nayi ka mare ni?" "Ubanki kika yi shi yasa na mare ki" Barkan mu da sallah Allah ya maimaita mana Allah yasa ibadun mu kar6a66u ne. Meena2 Amjuf☺️ [6/13, 7:15 AM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur Page(14) Fareeda zafin marin ya shigeta sosai gashi sumayya ta biyo shi dakin da niyar kar6ar Hassan sai kuma a kayi mari a gabanta, Dan take kiciniyar kar6a ya hana ta yace mata"muje Asibiti" Ranshi a matukar 6ace gashi yaron sai wani irin kuka yake mai ta6a zuciya Hussain ta goya a bayan ta suka hau mashin don tafiya asibiti Suna tafiya a cikin layin su suka hadu da makocin su ya tsayar dasu yake tambayar lfy da yake yagan su wujiga wujiga sanar dashi halin da Hassan yake ciki suka yi shawara ya basu akan su tafi wajan ofishin 'yan kwana_kwana domin su masa maganin hausa in yaso sai su siya masa magungunan asibiti,na'am suka yi da shawarar da yake ofishin ba wani nisa ne dashi ba suka juya suka tafi I sar su ofishin 'yan kwana_kwana suka musu bayanin yaro ne ya kone shine suka kawo shi wani mutum ne ya fito daga ofis din hannun sa dauke da magani sai pure water guda daya hannun ya duba ya gani yace da Amir ya rike yaron sosai. Hannun ya kama ya ke dai daye fatar da ta ya mushe yana ciccirewa tamkar ya samu kazar da za'a figewa gashi,yaron sai kuka yake ita kanta sumayya kukan take yi ga Hussain da yake baya shima kuka yake yi. Saida ya 6are wannan fatar tass sannan ya dauko garin maganin ya lika mishi a hannun aikwa yaron nan ihu yake don maganin tamkar wuta yake shima aka yayyafa ruwa mai sanyi a hannun sai ya zuba maganin ya lullu6e gun da ya kone sai can yaron ya saki a jiyar zuciya Amma dai gaskiya yasha wahala. Maganin ya basu Wanda kullum zasu ke barbadawa akan kunar sannan suka bashi kudin aikin shi 2k. Godiya suka mishi suka tafi ran Amir duk a jagule yana ayyana irin rashin kirkin da zai yiwa Fareeda shi a rayuwar shi baya son yaga yaro yana kuka balle har ta Kai ga jin ciwo shi kanshi dauriya yayi Amma lokacin da ake dayewa sosai yaji kamar jikin sa ne ake ciccirewa. Sun iso gida direct dakin sa ya wuce da yaron ya kwantar da shi a kan gadon sa,shafa bayan yaron yake yi a hankali tuni har yayi bacci. Fitowa yayi ya kira sumayya yace da ita ta shiga ta kula da yaron yayi bacci, dakin fareeda ya shiga ya sameta a kwance fuskar nan tayi mata dam6ar 6ar. "Fareeda me yasa da kika gama girki baki dauke kayan ki a gun ba sai da kika yi sanadin da yarona ya kone"? " Ban sani ba mallam kuma Marin da kayi min wllh sai hukuma ta kwatar min 'yanci na" "Au haka zaki ce wato Dan nawa ya kone da wani shegen ruwa ruwan tuwon ki baki damu ba sai Marin da na miki ko to shi yaron an gaya miki shi ba mutum ba ne"? " Ina ruwa na ni na kone ne da zan damu ai ni wutar tuwon ma bata birge ni ba wllh so nayi ta kone shi dukan shi aikin banza akan wani karamin yaro kake min rashin mutunci" " Yanzu fareeda ni kike fada wa wannan maganar har kike fadin cewa kin so yaro na ya kone ?" "Na fada din don mai wanke wa uwar ka mayafi kuma wllh sai kayi Dana sanin abin da kamin wllh sannan zama daram a cikin gidan nan babu inda zani banza kawai solobiyo" "Ni kike zagi fareeda ni mijin ki ? Tabbbbb to kije ki tafi gidan ku sai na neme ki" "Hhhhh ai ni da Kai mutu ka raba takalmin kaza,kasa a ranka ni fareeda matar Amir ce aure ne babu saki babu yaji a tsakanin mu idan kaga na bar gidan nan to gawa ta ce za'a fitar Amma karya kake yi,mu zuba mu gani naga kanka rawa yake yi saboda dan ka ya kone to ka jira ni nan da wasu 'yan dakiku baka isa ka daga min hannu ba " "Me kika isa ki min ? Dana fa kika a jiye tuwo ya kone dashi kice min ma tsautsayi ne baki fada ba saboda kina kishi da uwar su sai ki koma kansu me sukai miki daga su har uwar su wllh sumayya ta fiki tsarkin zuciya 'yar gidan mutunci wadda ta gaji mutunci da tarbiyya tun daga tushe" "Yo sumayyar banza idan na ga dama wllh sumayya sai kashi ya fita daraja kasan da haka ka auro ni? Ai da saika zauna da 'yar mutuncin" Sumayya ce ta fito daga dakin nashi sai ta tarar suna cacar bakin nan shiga dakin tayi tace dashi " haba bbn twins bai kamata ace kana sa'in sa da mace ba kar ka manta haka Allah ya Kaddara ko ma a ina ne sai Hassan ya kone ,to ka rabu da ita mana ba da gangan ta ajiye ba kamata uziri Mana" Fareeda kiyi hakuri don Allah nasan tsautsayi ne yasa kika a jiye tuwon har yaron nan yaje ya kone ki daina biye masa kin San shi da son 'ya'ya da kin bashi hakuri da yanzu komai ya wuce,don Allah ki sassauta kalaman ki mijin kine sai kin masa biyayya kin jure tukun xaki samu aljanna ta kar kashin sa" "Munafuka makira ni zaki yiwa nasiha to ke baki da matsayin da zan dau shawarar ki don haka fice mun a daki banza bora mijin da ba ya ta taki baki da wani muhimmanci a gurin shi da zaki yiwa mutane fi'ili waike mace ta gari,nima ta garin ce rainin wayo ne bazan dauka ba " "Allah ya baku hakuri " Sumayya taji ciwon a binda fareeda ta fada mata duk da gaskiya ne to Amma furicin nata ya yi mata ciwo,tabbas gaskiyar fareeda da ta ce bata da muhimmanci a rayuwar Amir. Dakin ta koma don jin tashin hassan,A cikin dakin ta taradda Amir kallon ta yake yi tamkar ya samu TV. Share shi tayi taci gaba da uzirin ta sai can da yaga bazata yi mishi magana ba sai yace da'ita" Sumayya kada ki yarda da zancen matar can don Allah,domin kin San Ni dake soyayya ce ta hada mu ba zamu ta6a rabewa ba kuma zancen baki da muhimmanci a rayuwa ta wllh karya take ni kaina ban San me yasa wasu lokutan nake ganin ki a siffa marar kyau ba,Sumayya duk abinda yake faruwa wllh ba da sani na ba kiyi hakuri. Ni kaina ban San me yake damuna ba" Kuka take haikan Wanda ba wani abu take tunawa ba illa soyayyar su da suka gudanar kafin shigowar fareeda rayuwar su. Tasowa yayi ya zauna kusa da ita ya rike hannayen ta yana share mata hawayen fuskar ta cikin tausayawa da kalamai masu dadi,kukan ta daina ta tsayar da kanta a kan fuskar shi suka shiga kallon_kallo,gira ya daga mata yace "kiyi hakuri ki tayani da Addu'a Allah ya yaye mun abinda yake damuna" Kanta ta gyada alamun zata taya shi da Addu'ar. Hmmmm fareeda ce ta taho dakin Amir tana shiga ta taradda masoyan suna kallon love kana ganin su kasan sunyi missing junan su.Tsayawa tayi tayi turuss ranta duk ya 6aci har wani hazo-hazo take gani a cikin idon ta saboda tsabar kishin jaraba yana cinta. Sumayya tana ganin kallon da fareeda take musu ai itama sai ta narke a jikin Amir ta fara nuna masa nata salon a wani hargitse fareeada ta fito daga dakin ta shiga dakin ta ta dauki hijabi da wayar ta sai mukullin dakin ta da ta dauka ta fice a gidan. Bata zame ko'ina ba sai gidan su inda ta jewa mahaifiyar ta da zancen abinda ya faru har da Marin da Amir yayi mata,mahaifiyar ta ce tace mata su tashi su tafi gurin malamin su don da zafi-zafi akan daki karfe,tafiya suka yi mai nisa tukunna suka samu gidan malamin nasu,bayan ya musu iso suka shiga cikin zauren nashi. Sun yi bayanin yanda suke so su samu nasara anan yace musu" to yanzu akwai wasu bayani da zan muku sai ku za6i daya a ciki" "To ranka ya dade muna sauraro" "Na farko dai a kwai lakanin da za'a masa zai zama jani talau ko mahaifiyar shi bata isa dashi ba sai abinda kika ce tukunna, sai kuma Wanda za'a yi musu su duka kowa ya tsani kowa,sai Wanda za'a yiwa yarinyar a Sanya mata warin ja6a" "To malam kawai a yiwa yarinyar asaka mata warin ja6ar ta yanda ko ra6ar ta bazai yi ba" Wasu surutai ya shiga yi tare da basu kullin magani Wanda zata zuba a ruwan wankan sumayya Amma saita yi dubara don in har wadda za'a yiwa sihirin ta gani da idon ta to ya karye abun zai koma wa maishi" Godiya suka mishi suka ajiye masa kudi har kimanin naira 50k. Cikin farin ciki suka dawo gida,sai can a shelake tukunna fareeda ta tafi nata gidan. Tana shiga gidan ta taradda sumayya daga ita sai daurin kirji ta yafa tawul xata shiga wanka ai a sukwane tace mata "don Allah taimaka min zan kama ruwa kafin ki shiga wankan" "Bismillah ki shiga" Shiga tayi da sauri ko Addu'a bata yi ba saboda sharrin da take son bibiyar sumayya dashi. Kunce kullin tayi ta zuba mata a ruwan yanda baza ta gane ba ta jima a tsaye sannan ta fita daga bandakin. Sumayya shiga tayi ta fara zuba ruwan a jikin ta.tana gama wanka ta fito ta koma dakin Amir anan ta shirya yana kwance har barci ya fara daukan sa sai ji yayi acikin baccin sa wani abu marar dadi ya ziyarci hancin sa,bude ido yayi kadan sai yaga sumayya tasha kwalliya Amma wari yana fitowa a jikin ta "Sumayya wai turare kika shafa ko kuma wani abu daban?" "Hmmmm bbn twins kenan turaren da kake so ne na shafa ai" " To wllh Ni dai bana jin kamshin turare ko daya illa warin mushen 6era da nake ji" Gaban ta ne ya fadi tace furta Innalillahi.......,sannan tace masa"wari kuma ?" Idon ta yana mai zirarar da hawaye,aran ta take cewa Wannna wace irin rayuwa ce daga wannan sai wannan Allah ka kawo mun dauki . Hassan ta dauka takai daki sannan ta dawo ta dau Hussain shima ta Kai daki zama tayi ta ke tunanin me yake faruwa da ita ne? Ta yi tunanin yau matsalar ta takare ashe a yau din wata matsalar zata fito sabuwa. Alqur'ani ta dauka ta fara karantawa tana yi tana kuka har dai taji ta ji salama a ranta,tayi addu'o'in ta tayi tawassuli da karatun da tayi akan Allah ya shiga lamarin ta Allah ya tsare su da yaran ta da mijin ta wannan wari da mijin ta ya shaka Allah yasa anjima kadan ya shaki kamshi a jikin ta.ta dade tana Addu'a sannan ta kwanta a kan gado sai bacci. A cikin baccin ta ne tayi mafarki da fareeda tana janta kofar gida ita da yaran ta wai sai amir ya taho zai kwace su anan fareedar ta watsa masa wani bakin ruwa a fuskar shi ai nan da nan sai suka hadu suna Jan su sumayya sai da suka kaisu har karshen layin su sannan suka koma gida. Farkawa sumayya tayi bakin ta dauke da Addu'a Kanta taji ya Sara mata Addu'a tayi ta shafawa kan nata ta tashi zaune ta jingina da fuskar gado Allah ka rabamu da sharrin fitinar kishiya 👏🏻👏🏻👏🏻 https://chat.whatsapp.com/LskntU56JpKIS3kUZmcwPV ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annurr Page(15) Suwaiba ta dage da neman kudi domin hakan ta fadawa Dan ta Abduljabbar " Babu maraya sai rago Abduljabbar mu dage mubaiwa mara Da kunya zanyi ko wacce sana'a matukar za mu samu rufin asiri a cikin ta kaima ka dage ku karasa karatun ku in shaa Allah a gabanmu a kwai nasara wacce za muji dadi har wanin mu shima ya ra6u damu yaji dadi" "In shaa Allah Maman mu lokacin nasarar mu ya kusa zuwa yana daf damu" "To 'yan Albarka Allah ya nuna Mana lkcn da Alheri" "Amin" suka ce yaran nata. Akwai wata makaranta a kusa da gidan kawun su Abduljabbar din in da suke da zama kenan to taje ta Kai takardunta ko zasu bata gurbin da zata ke koyar da yaran koda Allah zai sa lokacin daukan ma'aikata in tana da rabo sai asanya sunan ta. Cikin ikon Allah headmastern ya amince aikwa godiya tayi masa sosai don taji dadi sosai. Ta fara zuwa makarantar cikin ikon Allah da suka ga tana da himma da kwazo ga shi tana kula da aikinta yanda ya dace aikwa ana sanarwar za'a dauki ma'aikata headmaster ya kar6i takardun ta shine ya shige mata gaba akan komai har aka yi musu jarabawa da Ikon Allah sunan ta ya fito suka je akayi musu screening. Kafin a basu offer ma sunsha wahala har ta fitar da rai sai gashi ankira su an basu offer su a hannu,zo kaga murna agun su don har Azumi suka yi su ukun na nuna godiyar su ga Allah madaukakin sarki wanda duk ya dogara da Allah ya yi yakini mai kyau to hakika Allah zai shiga lamarin sa. Anyi posting din ma'aikata in da aka kaita makaranatar da take zuwa take bolontary.sosai ta dukufa wajen ganin ta tafiyar da aikinta yanda ya dace shima karamin danta ta maido shi makarantar da take saboda mahaifinsu ya daina biya musu kudin makaranta,sati biyu daya wuce Abduljabbar yaje ya sanar dashi kudin makarantar su ya kare gashi har an korosu. Budar bakin shi sai cewa yayi ai shi yanzu ya zare hannunsa daga lamarin su suje suwaiba ta biya musu.haka Abduljabbar ya dawo jikinsa duk a sanyaye yake sanar da ita abinda bbn su ya fada masa hakuri ta bashi tace dashi "kajure ka shanye duk wani wahalhalun rayuwa don cikar burin ka in Sha Allah ubangiji zai taimakeka duk wani Wanda kagani yana cikin daula to hakika in dai ka bibiyi tarihin rayuwar sa to zakaga yawanci sai ansha wuya tukunna ake jin dadi daga karshe don haka bana so zuciyar ka ta mutu katashi ka nema don gudun 6acin rai musamman yanda mahaifin ku yake da kudi Amma gashi ya kasa kula damu sai sharholiyar sa yasa a gaba mu hadu muke masa Addu'a Allah ya dawo dashi hanyar kwarai" Karan message ne ya tashi suwaiba daga barcin da take na safe wayar ta dauko ta duba ganin sakon daga banki ne yasa tayi hanzarin dubawa Alert ne na 90k Albashin su na farko,hamdala take yi sannan ta daga murya ta Kira Abdurra'uf da yake tsakar gdn nasu yana wanke uniform din shi na islamiyya. "Zo nan Dan Albarka kaga Albashi aka Mana yanzun nan kudin ya shigo mini" "Mama kice yau akwai sha'ani a gidannan hhhhhhhh wayyo dadi maman mu tayi kudi muma munyi kudi" Dariya take mishi ganin murnar da yake yi don yaji batun kudi "Mama wai nawa ne kudin ma?" "Abdurra'uf 90k ne" "Wayyo Allah mama naji dadi wllh yau zamuci dadi a gidannan hohoho yaya baya nan sai ya dawo mu kasafta kudin" "Hmmmm yaro ni kuma ina ina to mai Dan uwa da zaku kasafta kudin " tana dariya take tambayar shi. "Ai wllh Mama kudin nan kawai sai da kisa ido kiga yanda zamu yagalgala shi nida yaya domin shopping za muje muyi " "Hhhhh to Allah ya kawo shi lfy sai kuje kuyi Mana shopping din maybe aljihunku a cike yake da kudi bansani ba" "Kiji mama da wani zancen to ina nufin albashinki dashi zamuyi bishasha" Suna cikin wannnan firar ne Abduljabbar yayi Sallama ya shigo, amsa mishi sallamar sukayi sannan Abdurra'uf ya labarta masa labarin jin Alert.shima murna yayi sosai kana yace mata "mama kinga sai a siyo kayan Abinci da sabulun wanki Dana wanka sai Dan abinda ba a rasa ba" Itama ta goyi bayan shawarar da ya bada,Abinci ya ci ta bashi ATM din tace suje shida Abdurra'uf su yi siyayyar yanda ya dace . Sun tafi wani shago da yake a tsohuwar unguwar su anan suka yada zango don sun saba da mutumin yana da kirki yakan Dan taimaka musu da bashi wasu lokutan,siyayya sukayi suka hada da manja karamar jarka,mahaifin su ne yazo shagon zai siyawa Aslamiyya pad bai kula dasu ba sai da ya kar6i pad din zai bada kudin sai Abduljabbar yace ba sai ya bada ba zai biya,kallon su yayi sannan ne ya kula dasu. Hada baki sukayi wajan gaishe dashi" Baba ina wuni?" "Lfy kalau ku daga ina kuke? Kar ku sake ku kar6i bashin sa saboda ni yanzu ba biya muku zanyi ba saboda haka kuje kuce mata kada ta kara turo ku shagon nan kar6ar bashi" Mai shagon ne yace masa" Alhaji baka ji yaron wajen naka yace kabar kudin pad din zai biya ba? To ai ba bashi suka kar6a ba kaga duba nan duk siyayyar nan daka gani to kudi zasu bani yanzun nan" Alhjai Adnanu mamaki yayi yana tsaye suka mikawa mai shagon ATM ya zari kudin sa ya basu ATM din su. "Baba ka gaida gida mu muntafi" Su Alhaji Adnanu antafi duniyar tunani ko ji baiyi ba sai juyowa yayi yaga wayam har sun 6ace masa.mamakin da yake yi shine to waya basu kudin nan da sukayi wannan uwar siyayyar haka,lallai suwaiba kar fa ta fara bin maza saboda cikar burinta na Zama da 'ya'yan ta. Pad din ya kaiwa Aslamiyya aikwa fada tashiga yi mishi akan ya dade bai kawo mata ba don wulakanci yasa ta zauna zaman jiran shi.shidai shiru yayi mata don abinda yake damun shi ma ya isheshi,wani lokacin in ya zauna tunanin 'ya'yan sa da yake kauna to kwa ranar zai wuni da ciwon kaine Amma wani lokacin idan taga kamar asirin jikin shi yana neman karyewa to itama kara kaimi take yi. Sun isa gida lfy suka bata labarin sun hadu da baban su wai yake cemusu kada su kar6i bashi don ba biya zaiyi ba,dariya tayi tace in Sha Allah yanxu kam muda cin bashi wai don muci Abinci in Allah ya yarda takau.kayan ta shiga budawa sarai kaya sunyi domin kwa ko ita ta je da kanta iya abin da zata siyo kenan,canji ta dauka a cikin Jakarta har na 5k tace su kaiwa kawun su yasha fura,aikwa suna kawowa yazo da kanshi yamata godiya yace "suwaiba bayan Abinci da kuke bani kuma harda dawainiyar kudi haka? Gaskiya yayi yawa da an rage" " A a kawu ba za'a rage ba muma fa ka taimake mu a lokacin da muke bukatar taimako don haka ko nawa zan baka ban fadi ba" " To nagode suwaiba Allah ya saka miki da alkhairi ya shirya miki yaranki ya juyo da hankalin mijin ki gareku " "Amin ya rabbil alamina nagode kawu" Nama ta aika aka siyo musu na 2k suka ci."oo mama yau dai wllh wani gata kike nuna mana" "To banda abinka Abdurra'uf in ban nuna muku gata ba wa zan nunawa? Ku kadai gareni fa kuma ni kadai gareku to ba dole mu hadu mu hade kanmu ba " "Hakane wllh mama Allah ya nuna Mana lokacin da zamu jiyar dake dadi maman mu " "Amin " Alhaji Adnanu yau dai ya wuni sukuku bashi da kuzari,domin akan kanshi yasan bai kyauta wa suwaiba da yaran ta ba gashi bai tambaye su inda suke da zama ba balle yaje ya dubasu duk da wani 6angare na zuciyar shi yana hana shi hakan "Gaskiya ban kyauta wa suwaiba ba kudin nan da nake facaka dashi ba nawa bane na suwaiba ne Amma bata ta6a tambaya ta ba akan in bata kayan taba,Amma dai zan nemeta ta dawo gidan nan saboda 'ya'ya na ina kaunar su sosai " Bai San a fili yake zancen ba ashe Aslamiyya taji duk abinda yake fada,"to ba saikaje ka dawo da itan ba da kasan da haka ka koresu don munafunci shine zaka zauna kana wani zantuka marasa amfani" "To laifi nayi don na zauna ina tunanin iyalina? " "Bakayi laifi ba Adnanu Amma ka kusa daina tunanin su " Aslamiyya gurin bokanta ta koma ya sake juyar mata da hankalin mijin nata aka dasa masa tsanar yaran nashi da suwaiba,al'amarin dai babu dadin kallo. Sumayya dai yanayin da ta tsinci kanta babu dadi domin mafarkin da tayi to shine ya faru a gaske wai fareeda tana neman yi mata duka ita ala dole sai ta zane sumayya, sosai abin ya daurewa sumayya Kai ganin fareeda ta nufo ta da bulala wai saita Zane ta wllh indai bata bar mata gida ba."lallai fareeda baki da tunani ke yanzu ke ce yakamata ki fadi hakan ko kuma Ni yakamata in fada ? Kada ki manta ni kika tarar a cikin gidan nan don haka wllh wllh wllh kika kuskura wannna gajirabil din hannun naki mai kama da hannun samudawa ya ta6a Ni to kwa jikin ki zai gaya miki ,ina kyaleki ne saboda wasu dalilai to amma tabbas ya kamata in fyato dake daga hancina " "Sumayya ke kinsan Ni ba sa'ar ki bace ko to kiyi a hankali wllh Zane ki zanyi a cikin gidannan banxa bora wadda bata da zuciya miji yana wulakanta ki Amma kin nace kin zauna" "Hhhhhhhh fareeda kenan to ai ke ce banxar wadda bata ramin kanta sai dai na wani ke fa mugun halinki ne ya rabaki da tsohon mijin ki to amma da yake kanki na dankaline shiyasa ba zakiyi hankali ba ki San Annabi ya San duniya ,a a sai dai kici gaba da Abinda kika ga dama ,to kiyi watarana wllh ko ance kiyi baki isa kiyi ba domin abinda kike takamar dashi ya koma gidan sa Wanda yafi jin dadin zama aciki" "To muzuba mu gani shege ka fasa" Suna cikin yin fadan ne Amir ya shigo gidan wani kallo da ya aikawa sumayya Saida hanjin cikinta ya kada"wai hayaniyar me nake ji haka acikin gidana ?" "Baby wannan yarinyar ce zata Raina min hankali zagina take yi,wai saina bar mata gidan ta tunda ita na tadda a cikin sa" " Wllh bbn twins ba haka akayi ba wai bulala ta dauko zata dake Ni" "Ke dalla malama kimana shiru kina bude baki kina cika Mana gida da wari wllh sumayya idan kika kara buda wannan tsatstsaman bakin naki sai na Zane ki din tunda kin Raina mutane,don Allah ji ta wai wannan macece jiki duk wari sai mugun hali da bakin kishi tasa a gaba Amma bazata gyara jikin taba kina mace Amma kina barin jikin ki da wari?" "Innalillahi yanzu irin cin mtuncin da zaka min kenan Amir nice nake warin ? Sakayyar da zaka min kenan?" "Wllh idan baki tafi dakin kiba to tabbas zan iya 6allaki haka kurum ki zauna kina mana wari a gd sannan ga warin baki gaskiya inaga gara inje in sanar da 'yan gidan ku abinda kike yi na kazanta mace har mace Amma kin zauna kina mana warin ja6a a cikin gida" Daki ta shige take kuka tare da ambaton Allah."Allah kasan abinda ake min acikin gidan nan ya rahmanu ya rahima ya hayyu ya Qayyum kaji tausayina ka tallafa min ka yaye mun abinda yake damunaYa rabbi ka warware duk wani kulli da yake jikina da jikin mijina" Tashi tayi ta dauko ganyen magarya da tazargade ta hada su a guri daya ta shiga karanta ayatul shifa baya ta gama ne ta rufe dakin ta da mukulli ta cire kayan ta, addu ar ta fara Sha cikin hannun ta sau uku,sannan ta shimfida wani Zane ta hau kanshi tayi wanka da wannna ruwan maganin da tayi addu'a acikin sa,hatta da cikin gashin ta Saida ta zuba wannan maganin bayan ta gama wankan saita bari jikin ta yabushe da wannan tsakin maganin aikwa nan take jikinta ya fara kaikayi kamar tayi kuka Saida ta bari ta daina kaikayin sannan ta goge tsakin maganin ta sa kayan ta ta kwanta bacci. Kuyi hakuri da wannan ina busy ne shiyasa kwana biyu kuka jini shiru ZAMAN 'YA'YA NA NA MMN ANNUR WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA AMINI TA, MUTUNIYAR KIRKI ALHERIN ALLAH YA ISAR MIKI A DUK INDA KIKE ALLAH YA KARA MANA DANKON ZUMUNCI INA GODIYA DA NUNA KULA DA KAUNA DA KIKE MIN MMN AFRAH. Page (16) Da yake idan har akwai sihiri a jikin mutum ko kuma sammu to da ikon Allah indai mutum yabi irin wannan matakan dana zano to da zarar ya shafa wannan hadin zaiji jikin sa ya dau kaikayi, to indai mutum zai jure da amfani da Ayatush-shifa da hadin ganyen magarya da tazargade duk wani kulli na jikinsa zai warware da yardar Allah. Baccin da ta kwanta ne tayi mafarki da wani katon mutum baki fadin sa yafi buhun gero(hatsi) tsayin sa ma kamar haka yake,wai sai ya ke tambayar ta "shin anmiki askin suna(askin da in aka haifi jariri ake mishi ) ?" Sai tace dashi"ba'a min ba" Anan ya dauko wani bakin magani mai yauki tamkar danyen ku6ewa ya zuba mata akanta,tabbas a zahiri taji zubar wannan ruwan acikin kanta sai kuma taga mutumin ya nufi inda yaran ta suke kwance zai zuba musu,tana daga nesa dasu ta fara tofa musu Addu'a,wani ikon Allah kafin Addu'ar ta je wa yaran bakin ta nauyi yake yi wajan kokarin tofawa da take. Atake mutumin ya zagwanye burinsa bai cika akan yaran ba. Farkawa tayi bakin ta dauke da Addu'a yayin da taji ciwon Kai mai tsanani,da kyar ta tashi ta dauro Alwala tayi sallah. Washe gari da safe girkin tane da tayi ko kallo bata samu na arziki ba itama fareeda kinci tayi.haka aka bar mata Abincin karshe sai almajiri taji yana bara ta kaimasa. Da rana ma tayi girkin haka suka ki ci,karshe dai duk ranar girkin ta ba'a cin Abinci a gdn sai dai yaje yayi musu takeaway su zauna a gabanta suna ci suna fira wadda zata sosa mata ruhin ta. Tun bata damuwa har tazo ta Sanya abin a ranta duk tayi baki ta lalace gashi ta kasa fadawa ko 'yan gidan su. Mahaifiyar Amir itama ta juya mata baya sun koma gurin fareeda tana ganin su zasu shigo gidan Amma ko kallo bata ishesu ba idan iyar tazo haka zata gaishe da ita Amma da kyar take amsawa. Taja jikin ta daga garesu tunda su yanzu basa yin ta.ko 'yan biyun da take so yanzu ta daina tambayar su shi kanshi Amir din yanzu ya daina daukan su, idan ya shigo gidan za suyi ta mishi gwaranci suna oyoyo Amma ko kallon inda suke baya yi. Abin duk ya taru ya yiwa sumayya yawa duk sai tazama wata kamar marar 'yanci a gidan mijin nata,to ai dole ta tsinci kanta a haka Mana duba da yadda mijinta ya wulakanta ta to waye ma bazai wulakanta ta ba? . Fareeda ta siye iya itace yin girki mai rai da motsi ta aika mata Kai hatta da wanki iya bata yi saidai fareeda tasanya kanwar Amir ta harhado wankin a kawo mata duk da itama tana fama da laulayi,Amma don kissa da munakisa a haka take yi. Sumayya ta rasa soyayyar miji data mahaifiyar shi uwa uba 'ya'yan ta da yake wofantarwa shima yana haddasa mata bakin ciki. Yau da gobe kayan Allah cikin fareeda ya shiga wata na shida,sai take fadawa Amir ya kamata ya bata kudin siyayyar kayan jariri duba da yanxu za'a ce mutum yana da kudi yanzu za'ace babu kudi sun Zama sai kace wutar kara. Aslamiyya an samu ciki don cikin ta baya Sanya ta laulayi gashi yabi jikin ta yakara mata haske ,Alhaji Adnanu murna yake yi Amarya ta samu ciki,inda suka shiga kula da cikin,shidai tamkar ba'a ta6a masa haihuwa ba haka ya zama.Tsakanin sa da suwaiba kwa har yanzu babu wani ci gaba don shi ko yaran ne suka hadu dasu to haka zasu durkusa su gaishe dashi amma bazai amsa musu ba cikin sakin fuska sai kace ba 'ya'yan da yafi kauna ba 'ya'yan da in mahaifiyar su tayi musu fada baya jin dadi karshe ma sai dai ita yayi mata fadan.'ya'yan sa basa gajiya wajen gaishe dashi insuka hadu duk da baya amsawar Amma ahaka suke gaishe dashi din. Wata rana suwaiba tazo unguwar barakar haihuwa gidan makociyar ta Fatima da yake sun zauna zaman mutunci da ita akwai aminci da shakuwa a tsakanin su shiyasa ma da ta haihu ta Kira suwaiban take sanar da ita haihuwar,shine tace gobe zata shigo unguwar tayi mata barka ba sai taje suna ba saboda mutanen unguwa masu tsegumi. Ta fito daga Adaidaita sahu kenan sai ga Alhaji Adnanu yazo wucewa ta gefen Adaidaitar cikin rashin sani ta fito ita bata lura dashi ba Amma shi ya ganta, kallonta ya tsaya yi Amma bai yi mata magana ba,itama dago kan da zata yi suka hada ido dashi take gabanta ya shiga dukan uku_uku bayan ta sallami Dan sahun ne tayi karfin halin gaishe dashi Amma da kyar ya amsa ta wuce ta barshi a gun yana sake_sake. Idan zuciyar shi tayi masa kyakkyawan tunani akan suwaiba da yaran sa to sai yaji kansa yana Dan Sara wa,yayin da ya tuna cewa yana da babyn sa a gida to sai yaji hankalin sa ya kwanta . Amma dai yanayin da yaga suwaiba ya nuna tana cikin rufiin Asiri,to shin waye ya taimakesu ya basu gurin Zama tunda ita suwaiban ba 'yar garin kano bace ita asalin ta 'yar jigawa ce ,to kodai kule kule take ko kuma yaran dauke dauke suka fara suke samo musu na Abinci? Shi kadai yake zancen shi tamkar wani mai ta6in hankali. Bayan ta dawo daga gidan barkan ne ta zauna tana tunanin inda ace da ne lokacin Alhajin yana tattalinsu to bata isa tayi yawo a Dan sahu ba sai dai yayi driving din ta ita da yara,Amma yau ita ce tazama abar kora a gareshi amma za tayi maganin sa tabbas duk abinda yake mata bata jin ciwo fiye da yau din nan da suka hadu ya nuna mata cewa kashi ya fita daraja. Lokacin data aure shi bashi da arziki illa dukiyar ta da ya ara zai juya har sai da yace mata ga lokacin da zai bata Amma ji yanda yaci ya tada kai da kudin har yake mata cin mutunci saboda Allah ya ara masa dama. Bayan wata daya da haduwar suwaiba da Alhaji Adnanu a unguwar su,sai ta zauna tana tunanin gara ta neme shi akan ya bata kudinta in ba haka ba za tayi karan shi akan kudin ta. Amma bari yaran nan suzo za tayi shawara dasu. Bayan sun dawo daga makaranta ne take sanar dasu shawarar data yanke akan mahaifin su.yaran ne suka shiga kallon-kallo,saboda basu ta6a tunanin da kudin ta yake bishasha ba. "Mama kar kiyi karan sa kawai kice masa wannan kudin naki zai baki saboda uziri ya taso miki,idan kuma yayi gardama to saiki ce masa kin dauki lauya zaki shigar da kara kotu" "Kwarai haka ne mama" Da wannan shawarar ta dauki wayar ta takira shi da yake ta haddace number sakawa tayi. Can kamar zata tsinke ya daga ta gaishe dashi ya amsa a dakile,inda ta zayyano masa bukatar kudin ta,aikwa nan ya rikice yace mata shifa wllh so yake ta dawo gdn da zama. Wata dariya tayi wadda kana jinta kasan irin ta rainin hankali ce,bayan ta gama dariyar ta sai tace dashi " Abinda bazai ta6a yiyuwa ba,kaje ka zauna da babyn ka nima inzauna da'ya'ya na kasan hausawa ma sunce "kwarya tabi kwarya inta hau akushi bata moruwa" don haka ka nemo min kudina ka sauwake min igiyoyin ka da suke kaina Ni kam yanzu tunda kace damu mu fitar maka daga gidan ka wllh kwata- kwata ka fita a raina bana kaunar sake Zama dakai a matsayin miji da mata don haka ka kula da matar son naka nima ka sauwake mun inje in samu dai dai ni in aura Wanda zan zauna dashi in rayu dashi cikin mutunci da kulawa tare da kaunar juna, ba irin kaba Wanda mace ta gama illata masa rayuwa ba" " Subhanallahi suwaiba mijin ki kike fadawa maganganu na rashin kyautawa?" "Anfada maka Adnanu abinda yasa kaga lokacin in gidan ka nake kawaici to hakika lokacin ina maka kallon miji (maji6incin al'amura na) Wanda zai iya sadaukar da farin cikin sa domin goben shi('ya'yan shi) Amma yanzu tunda ka nuna nida 'ya'ya na bamu da darajar da zaka ji tausayin mu ka mutunta mu to nima Adnanu nagaji da zama da Kai kuma kasa a ranka kotu ce zata rabamu,in ko kana son rufin asirin ka to ka bani dukiya ta sannan sarkar gwal dita data ke hannun ka ka maido min da ita" Zufa ce ta ketowa Alhaji Adnanu domin shi a tunanin sa ta manta da kudin nan da sarkar ta.sai gashi lokaci daya tana neman zautar dashi akan kudin ta. Kittt ta kashe wayar,ita daya take surutai akan Raina mata hankali da yake son yi,wato saboda ta masa zancen kudin ta shine zaice yana son ta dawo gidan shi.yaje ya zauna da 'yar mulkin nashi duniya ce ai ta isheshi. Fareeda ciki ya shiga watan haihuwa sai tsirfa take yiwa mutanen gidan yau ciwo gobe ciwo tayi wani baki bakin ta duk ya zazzago hanci duk ya baje mata ga wasu kuraje da suka 6ata mata fuska,idan ka kalleta bazaka yi tunanin fareeda bace mai kwalliyar nan da take cika fuska da powder;Aishadow,jagira da janbaki Kai fareeda fa tamkar za'aje tashe da ita. Ummar sumayya ce tayi Sallama gidan,hamshakiyar tana zaune ko kallon ta bata yiba bare tasa ran zata amsa sallamar, sumayya tana kwance a daki taji muryar umman ta ai da sauri ta fito ta tarbi umman tana mata sannu da zuwa. Daki suka shiga bayan ta zauna ta dauko mata ruwa itama ta nemi guri ta zauna tace "umma ina kwana ya gida ina Abba?" "Lafiya kalau sumayya. ya kuke ya maigidan naki ya yaran?" "Lafiyar mu kalau umma" Sai tayi shiru can dai umma ta kula da yanayin sumayya sai take tambayar ta "wai ni sumayya wannan ramar ta mecece ko dai jinya kika yo bamu sani ba ?" "A a umma lafiya ta kalau kawai dai tsotsa ce da wadannan yaran duk sun sa na rame" "Hmmmm haba 'yar nan nifa na haifeki ba wai ke kika haifeni ba. kina nufin wannan bakin da ramewar da kika yi duk tsotsa ce ummm ?" Shiru tayi yayin da zuciyar ta take bugun tara-tara, tana so ta sanar da mahaifiyar ta halin da take ciki amma tana tunanin me gobe zata haifar. "Kinyi shiru kin kyale ni ina magana" "Dama dama ummmm dama"sai kuma tayi shiru ta kasa fada. "Dama me ki fada mun Mana sumayya ko kina so in tafi a hanya inke wasi-wasi ne?" Fareeda ce ta taso cikin azama da nuna isa da rashin mutunci ta shigo dakin na sumayya tace wa umma"wai ke tsohuwa dole sai kin binciki abinda ba'a so ki sani ne? To 'yarki taji ta gani zata zauna ZAMAN 'YA'YAN ta don haka kin isheni da surutu kizo ki tafi saboda Dan cikina baya son hayaniya,itama 'yar taki baki ga a daki kika taradda ita ba?" Azuciye sumayya ta tashi da niyyar ta sharara mata mari sai ko ga Amir ya shigo gidan a matukar mamaki ya buga mata tsawa yace mata "kada ki kuskura ki dakar mun mata wllh in kika sake kika kara gigin Marin ta to tabbas sai na yanke alakar da take tsakanin mu dake ,ko don kinga ina sauarara miki saboda na miki alfarma kina zaune a gidan nan shiyasa zaki 6ullo da wani salon ko?" Umma ce tayi karfin halin fitowa wajen tace "sannu Amir kuna lafiya ko?" Da kyar ya iya buda baki ya amsa saboda baiyi zaton tana cikin dakin ba durkusa yayi a gun ya sunkuyar da kanshi yana son yin magana Amma ya kasa. Takalman ta tasanya tace "sumayya Ni zan tafi Allah ya kiyaye" Sumayya tana kuka ta raka umma bakin kofar gida anan umman take cemata " kiyi hakuri kinji duk wani tsanani to yana tare da cin nasara kiyi hakuri zan sanar da baban ki abin da yake wakana a gidan Auren ki.sannan kada ki kuskura ki kula yarinyar nan koda zata zagi iyayen kine shima Amir din kiyi hakuri da canjin da kika gani a tattare dashi ki dage da Addu'a da salloli na nafilfili in shaa Allah komai zai warware" Gyada mata Kai tayi ta dawo cikin gidan inda ta taradda Amir din ya nemi guri ya zauna a tsakar gida ya rasa me yake damun shi. Ta gaban sa ta gifta ta wuce daki ta nemi guri ta zauna ta shiga tunani akan anya inta bari wadannan abubuwan suna faruwa da ita shin a gaba kwa ba zatayi kuka ba duba da yanda yanzu an maida zaman aure tamkar zaman bariki yanxu sai kaga mace tana yiwa mijin ta rashin kunya Kai wata ma har zagi in zaga suke yi. Allah ya tsare mu da aikata hakan. Meena2 Amjuf🥰 ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur Page (17) Dakin sumayya ya shigo ya tsaya yana kallon ta Amma fa ya toshe hancin sa da kasan rigar shi,tunda shi dai tsakanin sa da Allah wari yaji tana yi to Amma sauran mutane baji suke ba. Kunsan aikin da akayi don mutum to don shi din ne domin babu mahalukin da zaiji wannan warin sai Wanda akaso yaji. Magana yake son yi mata Amma ya kasa sannan a kasan zuciyar shi yana maijin tausayin ta akan Abubuwan da yake faruwa da ita,shima kansa baya jin dadin kansa sai dai muce Allah ya warware muku kullin da aka muku. Fitowa yayi ya shiga dakin fareeda ya zauna Ajiyar zuciya ya shiga yi saboda nutsuwar data zo mishi,duk duniya baya samun kwanciyar hankali idan ba fareeda ce a kusa dashi ba. Ta shiga ta fita ta cire masa son mata da kule kulen su a ransa tayi asirin da indai mace ya gani to zai ganta ne kafafuwan ta a sama kanta a kasa koda tafiya take ahakan yake ganin ta. "Matso ka danna mun kafafuwa na ciwo suke min" Kafafuwan ya mikar ya shiga matsa mata a hankali har tayi bacci,cikin baccin nata ne taji kamar an daure mata ciki marar ta ana tsunkon ta a firgice ta tashi babu Addu'a sai wani gantsare wa take ita a dole mai ciki. Can dai ta kara ji an tsikare ta ta gefen damar ta ai bata San lokacin da ta Mike tsaye ba saboda taga abin ba irin Wanda zata yi shagwa6a bane. "Amir wllh bani da lfy nakuda nake" "Yau kuma babu sunaye masu dadin da kika saba kirana dasu sai kuma kice Amir gatsai gatsai babu dadin ji" "Don Allah malam ka kyaleni ka dameni ,ko don baka San ya nake jiba ne" Ihu ta saki abinka da girman rashin ilimi,ciwo gadan gadan kafin kace me faya ta fashe mata sai kuma nakuda ta kirkin ta tashi. ta kira sunan babar ta yafi cikin carbi akan tazo ta taimaketa Amma ina ciwo ne babu Wanda zai kar6a maka shi dole kaine dai zakaji radadin ka. Asibiti suka tafi saboda ta galabaita,sumayya tana zaune ko kallon ta basu yi ba suka tafi.da taga an dauki tsawon awanni shine ta dauki wayar ta da bata karasa lalacewar ba ta Kira Amir din riging daya ya dauka tace mishi"Assalamu Alaikum " "Waslm" "Bbn twins ya mai jikin?" "Da sauki tana labour room har yanzu hankalina duk ya tashi ,bana so in rasa fareeda a rayuwa ta gara ace na rasa Dan cikinta da inrasa ta" "Subhanallahi kadaina fadin haka in Sha Allah zata haihu lfy" "To Allah yasa" "Yawwa kuna wane Asibitin ne?" "Muna Asibitin nassarawa" "To Allah ya bata lfy. Tashi tayi duk da bata jin karfin jikin ta a haka tayi musu girki na musamman tare da ruwan Lipton da madara sai Milo data hada musu,yaran ta dauka daya a baya daya a kafada sai basket data dauka da dayan hannun da kyar taje bakin layi ta tsaya tana jiran Adaidaita sahu.da kyar ta samu saboda kowa sauri yake yaje ya tafi masallaci kasancewar yau juma'a. Inda zai kaita ta sanar dashi.suna sauka ta bashi kudin shi ta shiga cikin farfajiyar Asibitin da yake tasan labour room din haka ta fara tinkistu da kaya da daukan Yara,Amir ne ya hangota da sauri yaje ya kar6i kayan da hussain,gaishe dashi tayi ya amsa Amma fa akwai tazara a tsakanin su da yake har yanzu akwai sihirin nan na wari a jikin sumayya.bata damu ba haka ta maje ta shiga dakin haihuwar acan ta hango Amarya fareeada a kwance an wani bararraje tamkar kan Dan ne ya dungo sai wani nishi take ita ala dole nishin ta ne zai fito da dan. Sumayya murmushi tayi. Aranta take cewa baki san dawan garin ba shiyasa kika wani jejjeme ke ga mai nakuda a gaba ma sai Dan ya taho zaki fadawa 'yan garin ku. Karsawa tayi kusa da ita tace mata " sannu fareeda ya saukin jikin?" "Yawwa sumayya da sauki nagode" Juyi take tana murkususu anan sumayya tace mata "fareeda kiyi hakuri ki daina juye juyen nan kada ki jiwa babyn ciwo" "To sumayya na rasa yanda zanyi ne shiyasa.baki San yanda nake jiba shiyasa" "Na sani Mana fareeda nima ai na haihu ko kin manta?" Can data kwara wani ihu Saida Amir ya jiyo ta a sukwane ya taho zai shiga labour room din nurse's din da suke bakin kofa suka da katar dashi. Kan Da ne ya doko gashi nan kana ganin sa muraran, ai da sauran jikin zai taho sai da ta kusa fadowa daga kan gadon domin sumayya tana ganin kan Dan ya taho ta matsa daga kusan ta saboda ana bata labari akan mai nakuda in ta kama ka wllh sai kayi jinya ,shi yasa ta matsa daga kusa da ita tace mata "fareda ki kama karfen nan na gefen gado ki rike shi sosai za kiga kin haihu cikin sauki. Abinka da mai nakuda ita a tunanin ta duk abinda akace mata tofa ta dau haihuwar ce za a bata da sauki,hmmmmm Masha Allah 'yar ta mace ta samu gata nan katuwa sai carara kuka take yi alamun tazo da koshin lfy. Nurse din ce ta gyara babyn da maijegon fess dasu, dakin hutu aka maida su inda sumayya ta dauki babyn ta kaiwa Amir ita Hussain ya ajiye a kasa ya kar6i sabuwar babyn shi yana tofa mata Addu'a. Yayin da sumy ta dauki Danta ta rungume shi barka ta mishi ta koma ciki ta tambayi nurse din zai iya shigowa kwa sai tace mata "ya shigo babu damuwa" Shiga dakin yayi sai raba ido yake yaga ta ina fareedar shi take ido suka hada ya sakar mata murmushi ita kwa ta ki dariya,haushin sa take ji da taga shi dariya ma yake saboda ciwon ba ajikin shi yake ba shiyasa. Kusa da ita yazo yayi mata sannu tare da jinjinar kokarin da tayi na haifa masa baby Girl,kwa6e fuska tayi wai ita shagwa6a take son yi mishi aikwa biyata yayi sukayi ta rashin kunya a gaban mar'atussaliha Sumayya. Sallamar su a kayi suka tarkata kayan su suka koma gida ko Abincin da sumayya tayi basu samu damar ci A Asibitin ba sai da suka dawo gida. Sumayya ce ta dora babban tukuya irin ta Alminium din nan ta tafasa mata ruwan wanka takai mata bayi sannan tazo ta hada na babyn anan fareeda ta dakatar da ita akan ta bari kada ta shaka mata sabulu a hanci idan maman ta tazo zata yiwa babyn wankan an hutar da ita, haka sumayya ta fita da ruwan wankan babyn jikin ta duk yayi sanyi ita tsakani da Allah take mu'amalantar su Amma su kwata-kwata basa ganin karar da take musu sai dai ma cin mutunci da yake biyowa baya . Amir ne yaje ya dauko mmn fareeda a bayan mashin tazo da dokin ta na son ganin jikar ta ta Sallama tayi ta shigo gdn sumayya tana mata sannu da kyar ta amsa mata inda sabo ta saba da halayen uwar da 'yar. "Maijego irin Albarka madalla ansauka lfy to Allah ya raya Mana yarinya tubarkallah da ke inyee kaga Diyar Amir jikar iya ma takama da Ayar Allah wannan 'ya taki fareeda in Allah ya ya amince itace 'yar so A gidannan sai abinda take so shi za'a yi" Sumayya tana daga waje tana sauraron ta murmushi tayi tace to ai duk daya da babyn da 'yan biyu tunda abu daya ne ya yisu don haka ni ko 'yan ubanci bazan bari yarana su yi ba, zan sa su kaunaci junan su tamkar ciki daya suka fito ni wannan jahilcin ba daniba. Dakin ta ta shiga da yake 'yan biyu sunyi bacci itama kwanciya tayi don ta huta Fareeda da mmn ta ne suke zancen ingancin maganin malamin nan nasu "Wllh maganin nan akwai kyau yanzu fa ko miji bata dashi a gidan nan ta zama 'yar kallo ga hantarar ta da yake yi a gaba na Kai in takaice miki ma yanzu ko 'yan biyun ta baya son dauka ga warin ja6ar nan yana tare da ita" "Yar nan ai malamin nan na yarda dashi duk abinda nace yayi mun yana yi mun shi nikam na yarda da malam sosai" "Gaskiya kam yanzu bayan suna zan sa a kar6o min na soyayyar 'yar wannan da uban nata so nake ace duk duniya yaji babu 'yar da yake so sai ita ko su Hassan d Hussain ma kada yaji kaunar su a ranshi " "Yo dama ai haka za a yi, ke nifa in San samu ne a kori wannan kishiyar taki daga gidan nan kawai mu huta don ni na tsani in shigo gidan nan in ganta " "A a mama a bar ta tayi ta ganin bakin ciki Amir dai na kwace shi daga gurinta" "Hmmm kema kin San takan tsiya Aradu fareeda" Dariya suka hau yi Kai sai kayi tunanin abin kirki suke kitsawa. Umman sumayya tazo musu barka inda suka gaisa da uwar fareedar Amma fa mmn fareeda sai wani shamata kamshi take yi,Kai sai kace Wanda suke Auren miloniya. Jaririyar ma yanata suka yi acewar su likita ya hana jagwalgwala ta"la babu komai wllh a barta ta huta" Tashi tayi ta shiga dakin sumayyan suka gaisa inda take kara jaddada mata akan taci gaba da dagewa da Addu'a in Sha Allah ubangiji zai saukaka mata halin da take ciki,sannan sallahr dare da walha sai sadaka indai mutum zai dage dayin su to zai samu mafita. Godiya tayi mata sannan take tambayar ta Abubuwan da suke faruwa a gdn,anan sumayya take sanar da ita warin da akace take yi kuma babu maijin warin sai Amir gashi iya ma ta juya mata baya. Hakuri take bata yayin da zuciyar ta take radadi da tausayin 'yar ta ta. Kwanci tashi asarar mai rai yau take suna yarinya taci sunan babar fareeda sahura taro yayi taro sumayya bata da sukuni a gidan duk inda tayi sai anyi da ita idan ta zauna a daki ace mata ta fito ayi aiki ai 'ya tayi, sai dai tayi murmushin nata na gado Da yamma ta shirya ita da yaran ta sunyi kyau duk da bai musu dinkuna ba amma ita mai jego yayi mata har kala hudu, jaririya ma akwati akayi mata Amma su 'yan buyu ko yadi bai siya musu ba, daya ke tana da adani kayan da suka Sanya a jikin su tamkar sabo sai suka fi maijegon kyau . Taro ya watse mai jego tace ita ba zata bar girki ba dole sai dai ayi baki-baki ita tana son mijin ta akusa da ita. Rayuwa ta Mika yayin da twins aka taye su umman sumayya ce ta dauku yaran Wanda hakan sai ya saukakawa sumayya don taji dadin daukan yaran da akayi don haka indai ba bakin girkin ta bane to bata fitowa tsakar gidan sai wajejen 11:am. Har tayi kyau saboda samun hutu babu dawainiyar yara babu ta miji sai dai taci ta yi ibada ta kwanta. Al'amarin Amir kara gaba yake yi domin tunda aka dauki twins bai ta6a tambayar yaran suna ina ba,Amma. Khairat 'yar fareeda kullum yana makale da ita indai yana cikin gida.Kai hatta da wankin kashin yarinyar shine yake yi haka zai goye 'yar sa a baya ko kunyar masu shigowa baya yi. Akwai wani lokaci fareeda ta shiga wanka sai tabar yarinyar a daki tana daga kafafu sama tana wasa dai irin na Yara to yarinya taji daki shiru sai tafara kuka ganin ba kowa adakin sai sumayya ta shiga don daukan ta tasa hannu zata daga ta sai ga uban yarinyar ya shigo da sauri da yake ya jiyo kukan yarinyar tunda ga kofar shigowa cikin gidan,ganin sumayya yayi akan yarinyar zata dauke ta sai yace "me kike shirin yi mata kina so ki illata mun yarinya ne ko?" Yayin da yake binta da wani mugun kallo Idanun ta har sun kawo ruwa tace "Amir wai me yasa baka adalci a furucin ka ne ? Yarinyar nan kuka take yi mmn ta ta shiga bandaki shine nazo zan dauke ta in lallashe ta Kai kuma kashigo gidan" "Karya kike domin kishi kike yi da ita akan an haifi mace ke kuma kin haifi maza" "Haba Amir kasan halina kasan abinda zan iya kasan Wanda bazan iya aikatawa ba,to Amma me yasa duk ka tsaneni me nayi maka?" "Dalla matsa ki bani guri duk kin hargitsa mun kai da wari mace ba zata gyara kanta ba sai dai ayi ta Zama da kazanta" "Na gode Amir da irin tukwicin da zaka saka mun na gode sosai, sai dai ka sani duk abinda kake yi Allah yana kallon ka" Ficewa tayi a dakin ranta yana kuna.ta shiga magana ita kadai "hakika kishiya takan Zama alheri ko sharri ga mata, to nidai abin yazo mun a bai bai domin ni kam ta zame min sharri amma in Sha Allah zan jure don ganin sakamako mai kyau a duniyata da lahira ta". Kuyi manage da wannan muna fama da matsalar nepa kwana ✌🏻 [6/25, 3:58 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annurr True life story Gajeran labari Page (18) Alhaji Adnanu ya rasa yadda zaiyi yayi gabas ya dawo yayi yamma Amma ina abin kam tamkar almara wai ace kudin da kar6ar sa ma ya kai shekaru 25 da ranta sannan gwal dinta kusan shekarun shi 20 da kar6a, wayyo Allah ka fitar dani wannan mata tana son tozartani. Gida ya shiga ko Sallama babu haka ya fada dakin sa ya kwanta ruf da ciki yana tunanin halin da zai shiga nan gaba saboda kudin suwaiba hakika sun rufa masa asiri don kudin nan da shi yazama abin kwatancen da ake kwatanta irin su a unguwa. Aslamiyya ce ta shiga dakin nashi tayi Sallama Amma baiji ba har saida ta ta6a kafafuwan shi sannan ya tashi a firgice. "Lafiya kake Alhajina?" "Ummmmm lfy sai dai bana Dan jin dadi Amma fa ba wai jinya bace kada ki damu kanki" "Ah to yalla6ai ai kasan dole In damu tunda rabin Raina bashi da lfy" "To ki kwantar da hankalin ki na wartsake kawai dai gajiya ce" "To shikenan ka kwanta ka huta bari inje nima inwatsa ruwa a jikina" Bayan fitar ta daga dakin zancen zuci ya shiga yi shine har da zubar da hawayen bakin cikin rabuwa da kudin suwaiba,rayuwar nan tana neman juya masa baya da wuri ya rasa wane irin lissafi zaiyi ma. Suwaiba hankalin ta kwance tunda ta yi zancen kudin ta,abinda yasa tunda dadewa ma bata tambaye shi ba kawaici ne take masa a matsayin sa na mijinta duk da ba wani hakki nata yake saukewa ba sai dai Dan abinda ba arasa ba. Yaran ne suka shigo ta sanar dasu yanda sukayi da baban su da matakin da zata dauka matukar bai bata hakkin taba, yaran tamkar hadin baki suka ce mata to ai gara su koma gidan kawai Amma maganar kudi ta kar6i Abinta. "To ku bari kawun ku ya dawo sai insanar dashi, Abinda yace to" Addu'a suke a ransu Allah yasa su koma ko babu dadi dai namiji garkuwa ne sannan kuma duk abinda zaije ya dawo to suna karkashin mahaifin su ne koda bazai basu kulawa ba. Tunda maman ta samu aiki ai komai zaizo da sauki. Kawun su ne ya shigo take fada masa abinda suka yi da Alhaji Adnanu,da kuma matakin da zata dauka akan kin bata kudaden ta da sarkar ta. Bayan ta gama yi masa bayani sai yace mata" suwaiba ina so in ari bakin Dan uwana in baki hakuri,tabbas Adnanu bai kyauta miki ba saboda kece silar samun cigabansa duk wadakar da yake yi da kudi kece silar hakan,to Amma wani hanzari ba gudu ba,kiyi hakuri ki koma gidan ki ko don goben 'ya'yan ki,ki sani duk inda za kije da niyyar aure to ayanzu a wannan zamanin ba kowa ne namiji bane zai rike miki 'ya'yan ki ba,karshe sai kiga ke kinyi auren don samun maslaha to sai dai ki dawwama a cikin 6acin rai tunda babu uwar da za'a wulakanta mata 'ya'ya ka ganta a cikin walwala,to kinga da kije ki kare rayuwarki a kunci da 6acin rai gara ki koma gidan 'ya'yan ki. Hakkin ki kwa dole sai anyi Zama a kansa koda a ofishin 'yan hizba ne don ba zan bari kiyi Karan mijinki ba saboda yaran da suke tsakanin ku abin zai iya 6aci suka kansu yaran ba zasu ji dadi ba ace yau babu wata mu'amala mai kyau a tsakanin iyayen su" "To kawu naji batunka Amma gaskiya ina son ya bani kudina nima inke kasuwanci saboda Zama a haka na yishi naji babu dadi tunda ba nauyin mu yake saukewa ba,idan har ya bani kudina to zan koma gidansa in zauna tare da 'Ya'Ya na" "To shikenan zanje anjima in sameshi" "Yo kawu na gode Allah ya kara lfy da nisan kwana mai Albarka" Bayan yaje ya samu Adnanu da zancen kudin ta da sarkar ta sai yace masa dike kafin tadawo anemi kudin a bata in ba haka ba to ta samu lauyan da zai tsaye mata a kotu. Ai nan da nan Adnanu ya amince nan da karshen wata zai tattaro mata kayan ta. Gida ya koma ya sanar da Aslamiyya yanda suka yi da yayan shi Wanda suwaiba take gidan sa, anan Aslamiyya take cewa "ita da aka kora bata tafi gidan su ba shine ta tafi gidan yayan miji Amma gaskiya ta bada mata wannan ai sai ace kwawa ce ta zaunar da ita" Shidai gogan shiru yayi ya rabu da ita don yaga bata damu da zancen kudin da zai maida wa suwaiban ba. Shifa duk ba haka yaso ba,matukar ya maida dukiyar suwaiba gare ta to fa zata iya fin karfin shi don ba lallai yake bata umarni tana bi ba,shiyasa ma ya rike kudaden nata bai bata ba. Gidan kawun yaje gurin suwaiba don su tattauna akan batun kudaden nata sai dai anyi rashin sa'a tana bacci,don da Abdurra'uf ya fada mata bbn su ne yake mata magana yana tsakar gida haka tace "kuce masa bacci nake yi bana son ina bacci ana takura mun" Mamaki gami da al'ajabi suka hana shi magana saboda lokacin tana gdn sa ba bacci ba ko suma take yi da zarar yayi magana a matukar sauri zata zo kuma kanta a kasa alamar girmamawa, Amma ji wai tasan shine yazo Amma tace masa wai bacci take yi. Kai duniya juyi-juyi wai ni suwaiba da datake shakkata Amma yanzu wai Ni zan mata magana har take wani firfirta. Hmmmmm Su Adnanu ai ba kullum ake kwana a gado ba, dadin tama kai ba sakin ta kayi ba,to da sakin ta kayi ai wllh wulakancin da zaka kur6a sai kaji inama inama. Itafa mace daga lokacin da ta fitar dakai daga xuciyar ta to kuwa zaiyi wahala ta waiwaye ka shi yasa kullum ake cewa ake hakuri da juna saboda matukar saki ya gifta a tsakanin ma'aurata kuma daga baya kazo kana neman biko to za kasha mamaki don zaginka ne kadai bazata yi ba awannan lokacin don haka mu kiyaye muyi hakuri da junan mu saboda goben yaran mu. Sai can wajejen karfe uku da rabi ta tashi daga baccin ta fito tsakar gidan ne ta taraddshi yana kishingide akan tabarma yaransa suna kusa dashi amma fa ba wata fira suke ba duba da yanda aka shiga tsakanin su. Alwala tayi zata shiga daki yace mata " suwaiba ko baki ganni bane ?" Juyowa tayi irin a kidime dinnan wai ta nuna masa cewa bata San da wanzuwar shi a gurin ba. "To su Alhaji Adnanu ne a gdn namu ina fata lfy dai?" "Eh gurin ki naxo idan babu damuwa" "Ok kajira inyi sallah, kasan bana wasa da Addini" "To shikenan nima bari inje inyi a masallaci" Bayan sunyi sallahn sun zauna yaran ma sun zauna to sai suwaiba tace dasu su tashi su shiga ciki. "Ina jinka " "Yawwa suwaiba haka nace maganar kudin nan don Allah ko zaki daga mun kafa nan da wata biyu sai in ke biyan ki da kadan kadan" Wani kallo ta aika mishi mai kama da ka raina mun hankali. Shi kansa ganin kallon. Sai da hantar cikin sa ta kada saboda sosai ta bashi tsoro kuma sai yaga tayi masa kwarjini. "Kai haka mukayi da Kai lokacin da zaka ari kudin ? Kudi har tsawon shekara kusan ashirin da dori Amma kace wai za kake biyana da kadan kadan" "Don Allah suwaiba kiyi hakuri na sanki ke din damo ce sarkin hakuri ki duba Mana ko don yaran da suke a tsakanin mu kiyi hakuri" "Lallai baka da ta ido wllh Kai har kasan yaran da suke tsakanin mu? Ai a tunani na baka da Yara a gurina sai 'ya'yana na kaina, kasan da haka ka wulakanta mu ka ke barin mu da yunwa ? Baka San cinmu da shan mu ba balle uwa uba sittira.don haka babu daga kafa ka dawo mun da kudina udan kuma ba haka ba to kasa aranka kotu ce zata kwata mun hakkina " Tashi tayi da niyyar tafiya sai yace mata " Dan har na dawo da kudin naki zaki yarda ki koma gidana ?" "Idan nayi ra'ayi ba" Aransa yana ayyana yanda zai mata indai ta koma wlh sai ya bi duk hanyar da zaibai don rama wulakancin da ta masa. Shi Alhaji Adnanu da take tsoron sa Amma ji yanda take fadar magana babu taunawa tabbb zaki gane shayi ruwa ne suwaiba, naga fitowar da kika yi kin samu wani wayewar Kai Wanda shine zai wahalar dake zan baki kudin ki Amma ki sani ke da kanki zaki bani kudin. Lokacin da aka dauka masa ya cika don haka ya tattaro mata kudin ta da kudin sarkar ta kimanin naira DUBU DARI BAKWAI DA HAMSIN. Yace anbiyo shi dubu dari biyu da HAMSIN. Dakyar ta amince shima sai da kawu yasa baki ta hakura in yaso karshen shekara zai bata. Haka ta tattara takoma ita da yaranta sun share mahallin su sun gyara ko'ina duk wata kura sun goge gidan yayi kyau tazo ta Sanya turaren garwashi mai kamshi,ita kanta Aslamiyya taji dadin kamshin turaren don rabonta data ji kamshin turare tun kafin ta samu ciki duk ta daina gayun ta zauna ta Zama inna rajab Alhaji Adnanu shi ma kanshi yaga canji a gidan nashi don rabon da yaji kamshi a gidanshi to tun kafin suwaiba tabar gidan sai yau da Allah yayi dawowar ta,cikin dakin nata ya shiga da Sallama bayan ta amsa masa ne ta gaishe dashi a dake tamkar ba suwaibar da in zata gaishe dashi sai ta tsugunna tukunna har sai ya bar gurin take mikewa Amma yanzu ji yanda ta wani gaishe dashi a dake sai kace wata ishashshiya. Shi wlh yanzu har ta fara bashi tsoro ma,kodai Aljannu ne suka shiga jikin ta take wannan abu kanta tsaye. Zama tayi a kan kujera ta ce masa"akwai wani abun ne da kake bukata?" "A'a na shigo ne kawai mugaisa kafin ajima inshigo dakin don bacci nake ji yau dinnan jira nk ayi sallahr isha'i" ",Ummmmm" Gidan da ta bada Ajiyar kayan su ta aika su Abduljabbar suka kar6o mata kayan ta, tana cikin jera kayan ne ya shigo dakin da sallamar shi. Amsawa tayi ta mishi sannu da zuwa, bayan ya zauna a bakin gado yace mata"sannu aiki akeyi ?" "Ummm shi nakeyi" Da ga haka yaja bakinsa yy shiru.girkin da tayi musu ita da yaran ta je ta zubo mishi,aikwa yaji dadin ganin Abincin don rabon sa da yasa Abinci a cikin sa yaji ya koshi tun ana ya gobe zai ji labarin hada kudin suwaiba.Ci yayi ya koshi ya kora da ruwa,godiya yayi mata yace " Allah ya saka miki da Alheri suwaiba nagode" Rabuwa tayi dashi saboda taga take taken shi wani neman magana yake neman ta dashi ita kwa tayi alkawari sai ta shayar dashi mamaki. Aslamiyya ce ta kwankwasa musu dakin bayan suwaiba ta bude dakin kawai sai gani tayi ta bigeta tasa Kai ta wuce dakin,bin bayanta tayi tana ganin ikon Allah har sai da Aslamiyya ta karasa bedroom din taja ta tsaya.wani kallo take aikawa Alhaji Adnanu na ka rainawa kanka hankali.suwaiba ce tace mata" lfy kika shigo min daki babu Sallama?" "Kamar ya?" "Kamar yadda kika ji nace" "Hhhhhhh banda abinki suwaiba ai ni nake da miji kullum a gidannan, ko kinmanta?" "Ke fice mun a daki bana son shirmen banza kina jiko,. Ga mijin nan ki goyashi ku tafi,ko kinji nace miki ina bidar shi ne?" "Meye hakan suwaiba?" "Bansani ba koma meye ba Kai ka janyo mun rainin ba, kutashi ku fice mun a daki" " Aslamiyya kije ga ni nan zuwa" "Babu inda zani wlh kafarka kafa ta" Aransa yana cewa lallai mata shu'umai ne. "Ki fice mun nace wllh zan sa6a miki idan baki fita ba fitsararriyar banza kawai" Hakuri yake basu wai sudaina ba girman su bane. Shidai Alhaji Adnanu yana son Zama a dakin sannan yana son bin Aslamiyya duk da yanzu alkadarin ta ya fara warwarewa. Ayi manage da wannan. [6/26, 12:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur INA KUKE? NACE INA KUKE? KIN KARANTA SANADIN KISHIYA NE KO KIN KARANTA 'YAR ZAMAN WANKA NE KINA DA LABARIN LITTAFIN NAN NA KAZAMIN MIJI KO DAI KINA ZAUNE BAKI KARANTA BONONO BA SHIN KINA DA LABARIN LITTAFIN NAN MAI SUNA RU6A66IYAR IGIYA? TO KI HANZARTA KI NEMESU DOMIN KI NISHADANTU KI WA'AZANTU DA LITATTAFANTA YANZU HAKA TANA NAN TANA GWANGWAJE KU DA LABARIN NAN NA MALAMIN BOGI. MAI SON SHIGA GROUP DINTA YAYI MIN MAGANA TA NUMBER TA KAMAR HAKA,09069615587. page (19). Kukan zuciya take yi Wanda ya fi kukan fili ciwo da radadi,salati da hailala tare da hauqala sune take ta maimaita wa can dai taji zuciyar ta ta Dan sassauta mata halin kuncin da take ciki. Shawara ta yanke akan zata je ta sanar da iya mahaifiyar Amir abinda yake faruwa, washe gari da safe ta tambayi Amir zuwa unguwa bai tambayi inda zata je ba ya barta sai kace baya kishin ta,haka ta shirya duk ranta a dagule ta fito bakin titi don samun abin hawa. Tana tsaye wani mai mota yazo ya gifta ta kusa da ita sai kuma taga ya dawo baya dai dai inda take,ya sauke gilashin motar yace mata "madam Bismillah kizo in rage miki hanya naga Rana ta Dan fara fitowa kuma da zafin ta, in babu damuwa ki zo in kaiki inda zaki je din" "Mallam kayi hakuri matar aure ce ni" "Kai 'yan mata ban yarda ba gaskiya, ko rowar ganin naki kike mun?" Mallam don Allah ka rufa min Asiri wllh ni matar aure ce" "Shikenan nagode nayi tunanin baki da aure shiyasa na miki magana" Adaidaita ta shiga ko bayanin mutumin bata tsaya saurara ba tace da mai adaidaitan "muje mallam" Ya tada mashin din yana shirin tafiya mai motar nan ya Mika mishi 5k yace "mallam ka dauki kudin ka sai ka bata canjin" Ita kam ba tasan me yake faruwa ba da yake fuskar ta a rufe da hijabi sannan hankalin ta yana ga Abinda Amir yake yi mata. Tambayar ta yayi inda zai kaita ta mishi kwatance, bayan sun sauka ne ta bude jakar ta ta fito da 500 zata bashi, sai yace mata "hajiya ai anbiya miki ga canjin ki nan ma" "Waye ya ya biya mun bawan Allah?" "Wannan mutumin mai mota da na ganku tare" "Ikon Allah to nagode, canjin ta kar6a ta shige gida" Yo dama bata da kudi sai wannan 500 din ta cikin jakarta.godiya tayi duk da baya gurin ta shige cikin gidan iyan. Da sallama ta shiga gidan iya tana zaune tana yankan farce ta amsa mata sallamar. Karasawa tayi gurin iya tace "iya sannu da aiki mun same ku lafiya ya gida ya aiki?" "Lafiya klau ina su khairat?" " Lfy kalau iya" Shiru tayi na Dan lokaci kana tace"iya zuwa nayi gurinki akan yanayin zaman mu, iya don Allah ki samu Amir ki tambaye shi laifin me nayi mishi duk ya tsana ni,iya wllh ina cikin matsala a cikin gidan wannan, Amir yanzu baya ta tawa dukkan shi ya karkata ne agurin fareeda. Ba laifi bane don ya nuna kulawar sa ga mace Amma abin nashi yana wuce makadi da rawa. Ina ji masa fadawa halaka Allah ya kiyaye" "To ikon mai sama,sumayya ni dai banga abin da Amir yake miki ba Wanda har zaki iya kawo karar sa gurina, hausawa fa sunce "mutuwa ma tana tsoron idon mahaifi" ke matsalar ki mita da korafi uwa uba kishi, ko wacce mace da kika ganta a gidan mijin ta tana zaune lfy to hakuri tayi don haka kema kije kiyi hakuri ki rike 'ya'yan ki" "Amma iya nifa maslaha ce ta kawo ni ba wai korafi nazo miki ba" Tana kuka Amma iya ta kekashe ido ita fa bata ganin laifin Amir da fareeda. "Sumayya kishi ne yake damun ki ba wani abun ba don haka kije ki tafi gidanki ki zauna, Zama da kishiya fa dolene tunda mijin ki yayi auren nan kullum bashi da kwanciyar hankali indai a dakin ki yake ni gaskiya indai karar Dana zaki ke kawowa gidan nan to kisha zamanki a gdnki ba sai kinxo ba" To iya fa rai ya 6aci saboda anzo da zancen shalelen danta da matar sa. Haka ta tashi ta tafi ko Sallama bata yiwa iyan ba.haka ta dawo gidan ta Kara taradda wani mugun wulakancin. Shigowa gidan tayi sai ga Amir yazo zai fita fareeda tazo zata rakashi bakin kofa, tana ganin sumayya ta wani narke a gefen Amir tace masa"sweety wllh wani wari nake ji kaga cikina har ya fara hautsinawa" Shima ranshi a 6ace ya toshe hanci yace mata"wuce ki tafi daki ki kwanta ki huta nima sauri nake yi don idan na tsaya na shaki warin nan ta yiyu yau na kwanta a gadon Asibiti" Gwalo ta yiwa sumayya ita kwa tayi mata murmushi ta nuna mata ko a jikin ta. Fita yayi ita kuma ta shigo gidan ta tsaya a kofar dakin sumayya tace mata"wllh babu zuciya a kirjin wata mutum ba'ayi dashi amma kwawa ta hanashi tafiya, yo anzo an samu shinkafa da miya da ruwan leda" Banza tayi da ita ta dauki wayar ta ta shiga group WhatsApp tana duba Abubuwan da aka turo a wani group mai suna JARUMAR MACE, wani post ne ya dauki hankalin ta inda taga anyi dogon rubutu akan zaman takewa da iya Zama da kishiya da yanda zaka gyara jikin ka da irin Addu'o'in da ya kamata mu mata mu yawaita yin su musamman idan muna cikin kalubalen zamanta kewa. Sosai ta karu da wasu Abubuwan haka ta yini sukuku da ita sai wajen 11 am ta tashi ta fito tayi alwala taje tayi nafila raka'a hudu bayan tayi Sallama ne ta zauna zaman Addu'o'i kana ta tashi ta hada maganin karya sihiri da ta saba yi tsawon kwana shida yau ne zata yi na karshe na kwana bakwai kenan. Tana zuba maganin taji jikin ta kaikayin ya ragu ba kamar na jiya ba alamu sun nuna sihirin jikin ta ya karye ba tare da taje gurin malami ko boka ba, tunda yaudara ce suke yi suci kudin mutum . Haka ta fito tayi ayyukan ta Wanda tasan ita za tayi tayi girkin ta Wanda za taci zuwa anjima.can barci ya fara fisgar ta ahaka dai ta kwanta tayi baccin, mafarki tayi da wani mutum shiba mutum ba shi ba aljani ba yazo mata a siffa marar kyau yana kuka yana cewa tafi karfin sa ta kone masa rabin jiki ta jikkata shi ta raunata shi,don Allah yana rokon ta akan ta daina amfani da maganin wannan xai rabu da ita zai cire mata mushen ja6ar da ya rataya mata a wuyan ta mijin ta yake jin wari tayi hakuri ta daina kona shi. Tashi tayi da salati a bakin ta cikin kidima ta zabura ta dauro Alwala ta zauna tana tuna mafarkin da tayi da wannan mutum na cikin baccin ta,hannu ta daga sama tana cewa" yaa rabbi yaa rabbi yaa rabbi ya hayyu ya Qayyum ka taimake ni ka yi mun maganin duk abinda yake damuna yaa Allah na gode maka akan dukkan abinda ka jarrabe ni dashi ya Allah Alhamdulillah ala kulli halin ya sami'ud du'a'i ka ji6inci al'amura na ya hayyu yaa Qayyum birahmatika astagithu aslihli sha'aniy kullahu wala takilni ila nafsi darfata aini. Cikin kudura ta ubangiji sumayya taji ranta ya mata fayau dashi babu damuwa da 6acin rai ga karfin jikin ta ya samu. Karfe 2:30pm Amir ya shigo gidan sa da sallama yaji an amsa masa da muryar da ya dade baiji sautin taba,sai ya tsaya yana kallon ta tamakar wata 'yar baby da yake jikin sumayya yana da kyau shi ake Kira da'daki bari' sannu da zuwa ta mishi ta kar6i jakar hannun shi da ledojin da ya shigo dasu sakar mata yayi kayan yana mamakin ina sumayya ta shiga ne kwana biyu bai sani ba sai yau ya ganta Kai ai kuma yasha ganin ta a cikin halin rashin lfy sai ya yi yunkurin zuwa gare ta sai yaji juwa ta kwasheshi to me hakan yake nufi ne? Fareeda fitowar ta daga daki ne taga oga Amir a tsaye ya kafe wani guri da kallo , itama idanun ta ta Kai kan abin da yake kallo sumayya ce take tafiya tamkar hawainiya a nutse sai juya mazaunai take yi. "Kut....... Kai yaushe abin nan ya ke faruwa nayi bano ban sani ba to ai dazu ma Amir yaji warin ta to me hakan yake nufi ? Lallai nayi sake da yawa kamata yayi inke yiwa malamin nan gewaya saboda akara kaimi wajen yin aiki. Indai ina numfashi sumayy sai kin bar gidan nan keda tarkacen yaranki " a kasa kasa take fadar haka. Ruwan wanka sumy ta hada masa tace dashi ta Kai ruwa yaje ya watsa sannan yaci abunci, a ranta tana jinjina karfin halin ta data iya makewa taje ga Amir din da to ya amsa ya ra6a ta wajen fareeda ya shige dakin shi bayan ya fito a wankan ne fareeda ta shiga dakin ta tsaya ta cewa sumay" ke sumayya me kike nufi da nine wai eyeee in ma wata manakisa ce kika zo da ita wllh sai nayi maganin ki boyi boyi kawai " Sumayya tashi tayi ta tsinkawa fareeda mari tace mata "wllh koba yau ba yau ba idan kika kara shiga sha'anina sai na nuna miki bake kadai kika iya shegantaka ba banza haure kawai wadda bata ginawa kanta rami mai kyau saidai mummuna ki tari sakayya a gaba zakiyi kuka da idanun ki shashasha kawai marar tarbiyya ballagaza matar cushe kawai wadda bata da class sai biye biyen banza da wofi . Kisa a ranki daga yau na daina raga miki wlh tsakanina dake shege ka fasa don gidan ku muzuba" Diff fareeda tayi tana mamaki me yake faruwa yau din nan kodai malamin nan ya karya asirin da yayi wa sumayya ko dai sumayya ta samu bokan da ya karya mata sihirin jikin ta ne? Amir yana wanka ya jiyo hayaniya sai kwara ruwan yayi ya fito yake tambayar ba'asi akan fadan nasu shiru kowa yayi da yaga ba zasu fada mishi ba yace "to kutafi dakin ku ina so in huta tunda ban isa ba inyi magana aji maganar tawa" Su duka fita sukayi ba tare da sun fada masa ba.ita sumayya tasan cewa yawan korafi akan kishiya yana Sanya miji yaji kafita a ransa ,to itama fareeda da taga sumayya taki magana sai tayi shirun itama Amma fa a ranta tana ji daga sumayy har Amir wlh saita yi maganin su Meena2 🥰 [6/30, 8:07 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/LskntU56JpKIS3kUZmcwPV?mode=r_c ZAMAN 'YA'YA NA Na Mmn Annur True life story Gajeran labari. Free book Page(20) Gidan iya mahaifiyar Amir ta tafi bayan sun gaisa ne take sanar da ita halin da take ciki a gidan da yacce ya juya mata baya shida matar sa sun maida ta saniyar ware,baya zuwa inda take baya cin Abincin ta duk wata hanya da zai cusguna mata ya sani,shi ya mata matar sa ta mata ta rasa yadda za tayi kwata-kwata bata da kwanciyar hankali ta nemi sulhu a gurin shi duk da bata San laifin da tayi masa ba Amma yaki sauraron ta. Anan take kara sanar da ita don Allah ta taimaka ta shiga maganar. Iya kememe ta zubawa idanun ta toka tace" kiji tsoron Allah sumayya ni dai a iya sanina Amir yana kokari baya son damuwar ki amma ke kin sanyawa kanki kishi marar tushe kin ki ki kwantar da hankalin ki ki zauna da abokiyar zaman ki lfy,yarinyar nan babu ruwanta ga nutsuwa da kawaici bugu da kari ga kyauta da kyautatawa na kusa da ita, idan baki saki ranki kin zauna da ita lfy ba to kina gani zaman gidan zai gagare ki" "Yanzu iya abinda nace miki daban fa ba wai karar fareeda na kawo miki ba, ina sone ki tambayi Amir me yasa ya juya min baya ne" "Haba 'yar nan na San halin Amir sai dai ko kece mai laifin" "Haka ne iya Amma iya kiduba ki ganni kowa ya kalleni ya San bani da lfy, Amma Amir bazai dube ni da idanun rahama ba ya zauna yaji menene damuwa ta ba?" "Kije zan same shi Amma ki sani yanzu a wannan zamanin duk matar da ta sake namiji ya sake ta to zawarci ba dadi bane, idan ma ta koma zaman gidan to raini ma kadai na kannen ta shima babban kalubale ne ga hantara daga iyaye da zata ke fuskanta,sannan Abincin kirki ma ba lallai ta samu ba sai abin da aka ya fita mata da ta koshi da kar ta koshi duk babu ruwan mutum" "Iya me ya kawo zancen saki kuma?" "Bawai mugun fata na miki ba tuna miki nake da kalubalen da zaki shiga matukar kika bari mijinki ya sake ki. Ai duk rashin dadin zaman gidan miji to yafi alheri da zaman gida (zawarci)." "Allah ya kyauta iya sai nake ganin kamar baki fahimci me nake nufi ba" "'yar nan ba zan fahimce kiba, yanzu fa kowa dansa yake so ina miki Kara ne saboda Dana Amma ke bakya gani.Allah na tuba me kika ta6a yi mun a matsayina na babar mijin ki? Amma abokiyar zamanki duk lokacin da ta samu faraga sai ta Dan yimin ihsani " "Kiyi hakuri iya nima kam ai bai kamata ace kin fadi haka a kaina ba nima fa 'yar kice sannan kuma......" Kuka ne ya ci karfin ta ta yanda kawai ganin ta tayi ta shi ta fito daga gidan iyan, wani guri ta samu a gefen hanya ta tsugunna tana share hawayen da ya cika mata ido. Hakika na tausaya wa sumayya halin da take ciki, wani lokacin idan jarabta tayi yawa sai mutum yake tunanin shin wai shi kadaine ake jarbta? Musamman idan yaga mutane suna walwala sai yayi tunanin basu ta6a samun kansu cikin damuwa ba. Abin ba haka bane kowa yana da damuwa sai dai ta wani tafi ta wani , sannan kowa yana kokarin danne damuwar shi saboda halin yau da kullum. Musamman idan mutum yana zagaye da makiyan sa to Ni dai a nawa tunanin kada yake barin damuwa a kan fuskar shi saboda makiyin ka kullum so yake ya ganka a damuwa. Haka ta share hawayen ta ta hau Adaidaita sahu ta koma gidan ta, daki ta shiga ta kwanta wani bacci wahalalle ya dauke ta idan kaga a yanda take baccin ma ya isar maka kasan a wahale take yinsa ba wai dadin sa take jiba. La'asar mai kyau ta tashi tayi sallah bayan ta idar ne ta dauki Alqur'ani ta fara karanta suratul baqarah yayin da tazo dai dai (Wattaba'u maa tattlushshayaadinu ala mulki sulaiman,wama kafara sulaimanu walakinnashshayadina kafaru yu'allimunan nasassihir,wamaa unzila alalmalakaini bibaabila haruuta wamarut,wamaa yu'allimaani min ahadin hattaa yaqulaa innama nahnu fitnatuun fala takfur fayata'allamuna minhumaa maa yufarriquna bihi bainal mar'i wa zaujih,wamaahum biduaarrina bihi min ahadin illa bi'izinillah,..............,lau kanu ya'alamun.) Aya ta (102) Cikin hukuncin ubangiji sai taji kamar wani abu yana gewaya wa a jikin ta da kyar dai ta Kai karshen shafin na Wattaba'u, kwanciya tayi a gurin a take bacci ya dauke ta anan ne tayi mafarki da wani katon mutum baki Wanda ya ta6a zuba mata bakin abu a kanta,shine ya fara mata magana" don Allah ki daina karanta baqara a gidan nan saboda kin kona mun kafata ki daina bama so duk lokacin da kike karatun qur'ani a cikin gidan wannan kina azabtar damu nida yara na, kidaina kidaina " Yana kuka yake fada mata wannan kalmomin tare da nufo in da take zai ta6a ta a cikin baccin take tofa addu'a yayin da zata tofa addu'ar to bakin ta da kyar yake buduwa tana tofa masa a lokacin ya 6ace mata a cikin duniyar mafarkin ta. Tashi tayi cikin tsoro da Addu'a dauke a bakin ta,sannan ta tashi kanta yayi nauyi yayin da ta shiga tuna mafarkin nata. A zahiri ta furta "bazan daina karatun Alqur'ani ba kuma suratul baqarah yanzu na fara karantawa " Amir ne ya leko dakin nata yaga ko lfy bai ganta a tsakar gidan ba, da yake ba shiga dakin taba yake sai taji wani banbarakwai shi ma a nashi 6angaren hakan ta kasance sai ya ganta kamar wata sabuwar halitta. "Kitashi kiyi sallah lokaci zai kure" "Nayi" tace masa yayin da ta kauda fuskar ta daga kanshi, shima fita yayi daga gidan ma gaba daya. Fareeda ce ta shigo dakin tace mata " sumayya ki fito ki Dora Mana girkin dare Dan ni ba lafiyar kirki gareni ba" " Karki Raina mun hankali Mana ke har kin kai ki bani umarni in bi ne ? To ko Wanda ya ajiye ki bai isa ya Sanya In miki girki ba" "Haka kika ce?" "Haka nace ,fareeda sai me? Kiyi abinda kika ga ya dace in zaman ki nake a gidan" "Kanbu ni kike fadawa haka?to kisa aranki sai nasa kinyi kuka a gidan nan za kuma kiga abinda zai faru" "Hhhhhh me kika isa kiyi fareeda? Babu abinda zai faru sai alheri don haka ina jiran ki inga me zai farun, shashasha kawai wadda bata ramin kanta sai dai in wani yayi ta shiga" Khairat ce ta tashi a barci shine ya kawo karshen takaddamar, yarinyar ta dauko tazo tsakar gida ta fara yimata kirari" khairatun Abban ta khairatun umman ta kinci dubu sai ceto,kinfi na fari kinfi uwar na fari yarinya ta 'yar kirki yarinyata kin Zama ciwon ido, kin Zama kabewar kan kabari bakin cikin mai taushe " "Hmmmm Allah ya raya Mana ita khairat din Allah yasa kada ta biyo hali irin naki"sumayya tace daga daki duk da fareeda ba zata jiba. Zama tayi ta baiwa yarinyar nono Amma kirmisisi yarinya taki kar6a, da yake kan fareeda tamkar mai kan dankali ba ta da dubarar da zata yiwa yarinyar Addu'a saboda kukan karshe ma sai cewa take" kurwar "ya ta Daci gareta ba ciyiwa za tayi ba gara a saka mun ita" Sumayya ta San da ita take Amma sai ta rabu da ita ko kulata ba tayi ba.fitowa tayi daga daki tace mata "ya kamata ki tofa mata ko fatiha ce saboda tana tashi daga bacci da kuka ta tashi, baki sani ba ko wani abun ne yake damunta" " Sai dai in kece kika mata abun Amma 'yata lfyr ta kalau" "To madallah ki zauna karki mata addu'ar kin zauna ba abinda kika iya sai kishi" Shiru tayi ta rabu da sumayyan saboda hankalinta gaba daya yana ga yarinyar ne.Fatiha ta tofa mata da kula'uzai ,can kwa yarinyar ta fara sakin ajiyar zuciya sai kuma tayi shiru. Daki ta koma ta kwanta da yake jikinta bb kwari,tunanin duniya ta shiga yi da halin da ta tsinci kanta da irin maganganun da iya mahaifiyar Amir ta fada mata abin bai mata dadi ba kwata-kwata. Hakika tana son Zama da 'ya'yan ta, to wani lokacin da abin da ake mata din gara rabuwar Auren nasu saboda gudun fadawa halaka. Hakika saki halal ne Amma Allah ta'ala baya son yin shi.takan tambayi kanta "shin idan muka rabu da Amir zan samu namijin da zai aure ni ya rike min 'ya'ya na?" Wani 6angaren na zuciyar ta shi yake ankarar da ita akan a yanzu a wannan zamanin da kusan kowa a sare yake ba lallai ki samu mai rike Miki suba, doke rikon Da sai gidan ubansa, ana samun masu rikewar a mazan yanzu Amma fa idan tafiya tayi tafiya to gazawar su tana fitowa karara. ZAMAN 'YA'YA yana da wahala musamman idan akayi katari da yara marasa jin magana sai abin ya taru ya yiwa mace yawa ga azabtarwar namiji ga rashin jin yara. Sai dai muce Allah ya shirya Mana mazan da yaran da mu kanmu baki daya. Dare mahutar bawa inji hausawa Amma a gun sumayya ba haka bane domin ita a wannan lokacin da gari yayi shiru to nutsuwa ce ta lullu6e ta tare da gabatar da ibada acikin daren kana ta Dora da karatun alqur'ani sai can kusan 4:00 dai dai ta samu ta kwanta kafin ayi sallahr asuba. Mutumin nan fa yana shan bakar wahala a baccin nan na sumayya sai da ya Kara dawo wa da niyar ya shake mata wuya Amma bai samu dama ba sai kuka da yake mata akan ta daina kona shi tana bashi wahala yanzu haka gefen jikin sa duk ya silli6e kofaton sa ma ya dan ta6u, acikin baccin suke fira dashi akan me yasa yake ra6arta to, har take kona shi shine yake sanar da ita " kishiyar ki ce tasa a tura Miki wari jikin ki to shine nazo na rataya Miki mushen ja6a a jikin ki duk inda zaki ina tare dake don kar wannan mushen ya bushe shine nake zuba masa ruwa yake jikewa kullum yana fitar da wani wari marar dadi" Anan sumayyan take cewa dashi " ka rabu Dani don Ni ba zaka Sanya min shakku a cikin imani na ba ko Dan kaga muna Dan samin sa6ani da ita shine kake son hadani da ita?" "Ba haka bane dazu da yamma nine na bige 'yar ta itama taji zafin da naji lokacin da kika kona mun kafa ta shine 'yar take kuka" Doka mata dakin da akayi shi yasa bata karasa firar dashi ba ta tashi, Amir ne yace mata "anyi sallah ki tashi" Tashi tayi tana mai mamakin mutumin nan wai shi bazai shigo dakin taba Amma zai tsaya daga kofa ya tashe ta yin sallah,hakan din ma ta gode. Da safe bayan ta yi aikin ta na shara da goge daki sai ta fito da kayan 'yan biyu tana gyarawa shi kuma Amir zai fita shago sai ya hangota ta jikin glass din windown daki shine ya tsaya ta window yana tambayar ta ina suke yaran baiji motsin suba "Suna gidan umma yau satin su biyu inaga yau za a maido su" Cikin mamaki yake kallonta yace mata "yanxu yaran nawa basa gidan nan Amma ba zaki fada mun ba har tsawon sati biyu ?" "To tayaya zan sanar da Kai tunda ba harkata kake shiga ba ko ganin su baka kaunar kayi shiyasa nima na ga dacewar kin fada maka din" Jikin sa ne yayi sanyi tunda gaskiyar ta rabon da ya kwana a dakin ta yau kusan wata daya da rabi, amatsayin sa na mijin ta to Amma shima fa kasa gane kansa yake yi .ficewa yayi daga gidan baki daya a ransa yana maijin rashin dadin kyautata mata aransa. "Kai ka jiyo ni yanzu insha Allah zan jure in keyin hakuri ko hawaye zan jure rike su ba tare da sun zubo ba Allah ya shirye ka Aslamiyya ana labour room ido duk ya Raina fata sai Kiran sunan Allah take yayin da suwaiba take kwantar mata da hankali ta hanyar yi mata sannu tare da fada mata Addu'o'i da zata keyi zata haihu lfy in Sha Allah. Aikwa carab ta kama take maimaita "yaa hayyu yaa Qayyumu birahmatika astagithu aslihliy sha'aniy kullahu wala takilni ila nafsiy darfata aini" Haka tayi tayi har Allah yasa ta haifo 'yar ta mace a hannun suwaiba ta haihu. "Ma Sha Allah aslamiyya kinga 'yar ki kyakkyawa da ita" "Na ganta mmn Abdul, mutuwa zanyi ki yafe min duk abinda na Miki don Allah ga 'yata nan ki rike min ita ta rayu agidan baban ta kada abaiwa kowa yarinyar nan ke na mallakawa" "In shaa Allah ba zaki mutu ba da hannun ki zaki reni 'yar ki" "Kayya baki San ya nake jiba Mmn Abdul kiyi hakuri da duk abinda na Miki wllh sharrin shaidan ne" "Kada kidamu ni na yafe Miki tunda dadewa Allah ya yafe mu baki daya " Alhaji Adnanu aka Kira sakamakon Kiran da aslamiyya tayi mishi , yayi daidai da zuwan 'yan gidan su a tare suka shiga dakin hutun. "Mama ki yafe min mutuwa zanyi sannan ki nemi yafiyar su mmn Abdul, Alhaji ka yafe min mun cutar da ku mun so raba ku kaida matar ka hakika munyi kuskure ku yafe Mana Ni kam tawa tazo karshe" Kuka mahaifiyar aslamiyya take tace mata "ki daina fadar haka ba zaki mutu ba ki kwantar da hankalin ki" " Ni inaji a jikina mutuwa zanyi" Alhaji Adnanu shima kukan yake yace mata" ki daina fadar mutuwar nan cuta fa ba mutuwa bace zaki sa hankalin mu ya tashi" "Hmmmm" tace tare da rufe idanun ta don ita kadai tasan me take ji. Tofa shin Aslmiyya tana mutuwa kokwa? Meenatu Mamu Amjuf🥰 [7/2, 4:21 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA NA MMN ANNUR Page(21) Kuka suke su duka domin duk rashin imanin ka in kaga Aslamiyya zaka tausaya mata, wani Abu take tamkar mai shirin barin duniya hannun ta ya kudundune kafarta ma ta kanan nade bakin ta ya juye.ganin haka yasa akaje aka Kira doctor don ya dubata, gefe daya yarinyar ta ce ke kuka tamkar ana tsinkon ta duk ta rikita iyayen alamu sun nuna yunwa take ji gashi kuma mmn ta akwance abin kam sai Wanda ya gani. Shigowar doctor ne ya sa suka matsa daga jikin gadon,umarni ya basu akan su fita zai duba ta.bayan fitar su ne ya duba ta shi kam baiga wani cuta da ya haddasa mata hakan ba, Amma an Sanya mata karin ruwa kana ya fito yace musu kada a dameta da hayaniya sannan ayi kokari a samu wata taje tayi dubara ta Kara yarinyar a jikin mamanta saboda ta ji dumi na jikin mahaifiyar ta a ciro mata mama ta tsotsa za ta daina kukan in Sha Allah. Hakan akayi kwa can yarinyar ta saki maman duk da bai zo da yawa ba Amma ta samu yellow din nan da ake so asha. Bayan awa uku aslamiyya ta farka sai dai ta kasa daga hannun ta da kafafuwan ta ya Zama komai sai an mata Amma tana iya yin magana sai dai da kyar take daga bakin ta. Suwaiba gida ta koma tayi musu girki tare da dafa ruwan dumi saboda mai jegon za'a goge mata jikin ta sai shayi da ta hada mata ta tafi dashi. A yau ne aka maido da 'yan biyu gida, lokacin da umma ta kawo su Amir yana gidan yana zaune akan tabarma a tsakar gida yana shan iska,sai jin sallamar umma yayi amsa mata yayi yace mata "Bismillah shigo umma" Shigowa tayi tace "sannu Amir ana gida?" "Ehh wlh umma sannu ki karasa tana ciki " Shiga dakin sumayyan tayi tare da yin sallama,sumayya tana gugar kayan ta taji shigowar umma tace mata" sannu umma karaso " Da yake yaran bacci suke da ta shigo gdn ma ba suga bbn su ba Hassan a baya yayin da Hussain yake a kafada kwantar dasu tayi tace "Kai ma Sha Allah wannan yara ai sai ku 6alla ni haka kurum" Dariya sumy tayi, sannan tace "umma ina wuni?" "Lfy kalau sumayya, ya gida ya zafi zafi ya mai gidan da sobar taki?" "Lfy kalau wllh umma" "Ma sha Allah haka ake so, to ga yara nan na maido dasu Allah ya raya aci gaba da hakuri wata rana sai labari zaki tsinci alkhairin hakurin da kike a gaba sumayya koda bana a raye" "To umma na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara muku tsawon kwana mai amfani Allah ya kara lfy" "Amin sumayya" Amir ne ya shigo dakin ya tsugunna ya gaishe da umma, anan yake fada mata baya jin dadi ne shi yasa baije ya duba su 'yan biyu ba. "Subhanallahi sannu sumayya baki fada mana ba ai da munxo mun duba shi" "Ai umma shi yace kar a fada saboda halin rayuwa yanzu kuna ji sai kuce sai kunzo dubiya kuma ga kudin Adaidaitan sun kara shiyasa" "To abinda ya zama dole ai shi akeyi" Amir ne yace "ina twins din ne banji duriyar su ba" "Yan albarka ka gansu nan bacci suke ai" Tashi yayi ya fita daga dakin, inda umma ta dora da yiwa sumayya nasihohi da yanda za taja hankalin mijin ta gareta da yanda zata zauna da kishiyar ta lfy koda ita waccan din tana neman ta da tashin hankali ne to da siyasa zata jata a jiki sannan kada ta bari kimar ta da darajar ta ya zube a idon mijin ta bugu da kari kuma kada ta biyewa kishiya suna kace nace da ita yin hakan zai rage mata kwarjini ne a idon kishiyar ta. Da haka umma ta bata 20k tace mata inji baban ta ta siyawa twins biscuite, godiya tayi tace zata kira bbn nata a waya ta mishi godiya. Bayan umma ta tafi ta je gurin yaran ta tafara shinshinar yaran ta gwanin sha'awa tayi missing din su sosai.kwanciyq tayi a tsakiyar su inta jiyo ta karewa wannan kallo sai ta juya ta karewa dayan kallo shima tana kara godewa Allah sarkin sarakuna da ya mallaka mata yaran nan a mtsayin 'ya'yan ta, gaskiyar hausawa da suka ce" 'yan biyu kyuatar Allah" Sai dab da magariba suka tashi ta tofawa kowa Addu'a sannan ta hada ruwan wanka a toilet dinta na cikin daki ta musu wanka ta shirya su cikin kananun kaya best da dan karamin wando kowanne farare an yi rubutu a gaban rigar da bakin zare inda aka rubuta( √ boy) ma sha Allah yaran sunyi kyau sosai har takalmi tasa musu tace "maza kuje Daddy yana daki " Allah sarki yara basu manta da bbn su ba da saurin su suka tafi suna zance da gwaranci. Shiga dakin baban nasu sukayi yana ganin su ya rungume su yace "twins din daddy i miss u" kai sai kayi zaton ko yaran sun san abinda yake fada. Dariya suke kowa yana so ya hau cinyar daddyn nasu. Wani dogon tsaki fareeda ta saki don ita fa bata kaunar yaran kwata-kwata, bata san an maido suba ma sai yanxun da ta gansu. Kallon ta yaran suka yi suka lafe a jikin daddyn su sakamakon wani kallo da ta jefesu dashi. Uban bai kula da ita bama ta yaransa yake yayin da zuciyar ta ta cika da tsanar yaran da mmn su, taci alwashi sai ta daidaita rayuwar yaran nan saboda ba zai yiyu ba tana zaune azo a ke nuna wa yarinyar ta wariyar launin fata ba don ita tana mace bazai yiyu ba. Kai jahilci bai yi ba wllh to da mace da namiji dukan su Allah yasan manufar da ya sa aka rarrabawa kowa amma wasu matan da mazan sukan bani mamaki babu wanda akayi shawara dashi lokacin da za'a masa kyautar haihuwa amma kaji mutum yana ta mita akan ana haifa masa 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza, wasu fa suna nan suna neman haihuwar amma Allah bai basu ba, kai kuma Allah ya baka shine kake mita akan ambaka jinsin da baka so. Allah ya kyauta. Alhaji Adnanu dakin ya koma don ganin jikin Aslamiyyan saboda hankalin sa yaki kwanciya gani yake kamar mutuwar za tayi. Shiga dakin yayi ya ganta a kwance tayi wani fayau da ita, dai dai hancin ta yaje ya kara hannun sa a saitin hancin amma baiji numfashin ta ba a tsorace ya fito yaxo gurin su mmn ta yace musu suje su kirawo doctor yanzu. "Lfy dan nan?" "Lfy aje a kirawo shi dai kawai" Da sauri suwaiba taje ta kirawo doctor din haka ya taso ya taho duk da yana da marasa lfy a gaban sa. Dakin ya shiga ya dudduba ta yaga bata numfashi kwata kwata ruwan ya duba na hannun ta yaga ya tsaya baya shiga jikin ta, numfashi ya fesar yace musu"kuyi hakuri fa Allah ya kar6i abinsa" Daga haka yasa kai ya fice daga dakin bayan ya rufe mata fuska da zanen ta da yake gefen gadon. Innalillahi kawai suke maimatawa dukkan su sunji abun a ba zata musamman mamanta da ita saida ta tafi hutun dakika kusan goma tukun na ta dawo hayyacin ta. Wani kara ta saki ta sulale kasa ta suma, suwaiba ce mai karfin halin shafe mata idanu tare da tofa mata Addu'o'i, sannan ta harhada kayan su tare da daukan jaririyar tafita waje ta ajiye tarkacen nasu a can, dakin ta koma ta shiga lalla6a Alhajin tare da fada masa maganganu sanyaya wanda nan take yaji wata irin dakiya ta lullu6eshi. Mota aka kawo aka sanya gawar fareeda a ciki sai alhajin da ya shiga itama mmn fareedan bayan an yayyafa mata ruwa ta farfado aka shigar da ita ciki. Suwaiba tare dasu Abduljabbar sukayi gaba hannun ta dauke da babyn, kallon yarinyar take tana tausaya mata tare da jinjina kudura ta ubangiji. Sun rigasu isowa gida da yake motar gawa ba'a son ake gudu so sai hankali suke tafiya shiyasa basu iso da wuri ba. Makota ta tura a fadawa kafin kice me gida har ya fara daukan jama'a. Mutuwa tambari gareta duk nisan guri takan zuwa matukar da wanda yasan mai mutuwar a unguwar. Gawar aka shigo da ita bayan 'yan uwan su sunzo sai aka dauko ruwa za'a yi mata wankan gawa an fara kenan aka ga babban Yatsanta ya fara motsi, takusa da gawa ta gani sai take cewa ta kusa da ita" kamar motsi naga kafarta tayi" "A haba ai in an mutu babu zancen wata ga6a ta motsa" Sai tace mata "anya kwa mutuwa tayi ba suma bane tayi?" Ai kafin ta rufe bakin ta sai ji sukayi tayi atishawa da kyar aka samu dayar mai wankan gawar tayi ta maza ta dake ta tsaya tana ganin ikon Allah. Itama fitowa tayi tace "bayin Allah aslamiyya ba mutuwa tayi ba ta tashi, inaga dogon suma ne tayi" Haba ai kafin kace kwabo gidan makoki ya 6alle da hayaniya ana ta barka da arziki tunda ba mutuwa tayi ba suma ne. 'yan kofar gida aka sanarwa da labarin farfadowar Aslamiyya, sai murna ake yiwa Alhaji Adnanu da aka auna arziki. Allah sarki mutuwa rigar kowa, ba'a son mutuwa Amma ta Zama dole. Da sannu wata rana kowa zai zamo a kushewa ftnmu Allah yasa muyi kyakkyawan karshe Amin. Wankan jego aka mata Wanda hakan yasa taji dadin jikin ta aka dauko mata yarinyar ta aka Sanya mata maman ta a baki ta kama ta fara tsotsa ahankali har aka samu tasha ta koshi. Asibitin aka maidata don a binciki lfyr ta anan doctor yake zolayar ta yace mata"kin tsorata mutane da yawa lallai ki godewa Allah kina da masoya da yawa"murmushi tayi duk da bakin ta ya Dan karkace Amma hakan ba zai hana a gane murmushin da tayi ba. Lab aka tura su don yin gwaje-gwaje a inda sakamako ya nuna tana dauke da cutar calcium sannan jinin ta ya Dan hau kadan sai kuma magunguna da aka rubuta mata da ruwan gishiri d sugar saboda kafafuwan ta d hannayen ta. Gida suka dawo,mahaifiyar ta itace ta zauna da ita a cewarta zaman wanka za ta yimata saboda wankan farin nan da za'a yi mata a gargasa mata jikin ta duk da ba wani wankan jego za tayi ba saboda jinin ta da ya hau. Suwaiba tana kokari matuka duk da irin kuncin da suka Sanya ta a baya Amma hakan bai hana yi mata hidima ba. Shi kanshi Alhaji Adnanu duk sai kunyar suwaiban yake ji duba da yanda take hidimtawa Aslamiyya da mahaifiyar ta. Duk da wannan kokarin hidima da take yi kwata-kwata mmn Aslamiyya bata gani ita fa bata ki ace suwaiba bata gidan ba saboda ita ma bata zauna da kishiya ba saboda haka bata son ganin aslamiyya da kishiya tafi son 'yar ta ta zauna ita kadai a gidan ta ita da 'ya'yan ta. Kai jama'a kuji min mata keda 'yar taki ta aure mata miji duk bata ji ciwo ba sai ke da 'yar ki ta kasance haure, yo haure mana tunda sama taka taxo gidan ta fara baza bazarta . Maman Aslamiyya ce take son kara maida Aslmiyya kan keken 6era "wai ta tashi tsaye wannan kashe-kashen kudin da matar nan take yi duk fa mijin ne yake bata don ayi amfani a cikin gidan Amma ke kina zaune baza'a tambayi me kike so ba haka kawai sai dai komai ace ita ni gaskiya bana son irin haka kina zaune za'a mai daki bora ita ta Zama mowa" "Mama mmn Abdul fa tana kokari ni kuma banga laifin yin hakan ba duba da itace uwar gida sannan ko itace ta haihu to ni za'a baiwa kudin cefane da duk wani abun da ya dace a gidannan don haka ni daidan hakan na gani" "Ke gidan ku nace ana nuna Miki Annabi kina rintse idanu, to ke bazai tambayi ra'ayin ki ba saboda itace uwar gida, toke yarinyar gida ce? Ki tashi ki farka daga nannauyan barcin da kike yi in ba haka ba wllh kina zaune zasu jone da junan su su koma kamar da, ke kwa sai dai kallo shawara ce nake baki a to" "Hmmmm mama kenan bai kamata kice haka ba yanzu da na mutu me zanje in cewa Allah akan kuntata wa matar nan da muka yi ?karki manta fa dalilina har korar su yayi ita da 'ya'yan shi Amma hakan duk bai ishe mu ba sai mun sake fito da wata kitimirmirar kuma " "To salamatu shikenan kin Zama sallamammiya na haifawa suwaiba kishiyar ki ke in ba haka ba ina fada Miki gaskiya kina kaucewa to shikenan nidai in ta kwa6e Miki kada ki nemeni tommm" "In Allah ya yarda ma ba zata kwa6e mun ba" Suwaiba tana daki ta kwanta don ta huta da Rana sai jin karar massage tayi a wayar ta aikwa tana dubawa taga daga bankine budewa tayi ai tana kwance sai gata a zaune domin albashin tane ya fado na wannan watan murna tayi sosai, Alhaji ne ya shigo dakin da sallama ya zauna ta ce masa"Bbn Abdul kaga Alert ne ya fado min" "Alert kuma suwaiba?" "Ehhh albashin mu na wannan wata" "Ikon Allah aiki kika samu ban sani ba?" "To fa wai dama ban fada maka ba kafin in dawo lokacin muna gidan kawun yaran nan na samu offer a wannan makarantar ta kusa d gidan sa" "Ma Sha Allah ubangiji ya Sanya alkhairi Allah yasa mai amfani ne" ."Amin ya rabbi kayi hkr wlh mantawa nayi ban sanar d Kai ba" "Babu komai ai yiwa kaine" Da yamma ta shirya taje wani shago a nan kusa d su ta yi siyayya ta siyo atamfofi guda biyu sai rigunan jaririya guda biyu da yadi na maza ta siyo wa su Abdul , gurin tela ta wuce da yake yasan size din su Abdul din sai ta bashi ya dinka musu ita na da nata dinkunan guda biyu. Gida ta dawo ta nunawa Alhaji rigunan yarinyar sosai yaji dadi yayi mata godiya. Bayan tayi sallahr isha'i ne ta fito daga dakin ta ta nufi dakin Aslamiyya da sallama, amsa mata sukayi akace ta shiga. Shiga tayi dakin suka gaisa ta mata ya saukin jikin sannan ta Mika mata rigunan jaririyar kar6a tayi ta fito dasu daga cikin ledar tana dubawa cikin farin ciki ta dubi suwaiba tace mata "na gode mmn Abdul Allah ya saka Miki da alkhairi Allah ya jikan mahaifa na gode sosai" " Babu komai ai nima 'ya ta ce babu godiya a tsakanin mu" Maman Aslamiyya aka nuna wa kayan tace "kai kinyi kokari 'yar nan yanzu a zamanin nan da kaya suke tsada har kika iya ciro kudi kika siyo wannan rigunan 'yan dubu uku uku gaskiya mun gode Miki Allah ya saka Miki d alheri" "Babu komai mama nima na gode" Bayan fitar suwaiba daga dakin Aslamiyya ta dubi maman ta tace "haba mama wannan fa bai dace ba tsakani da Allah idan ba zaki mata godiya cikin farin ciki ba ai bai dace kice mata wai rigunan 3k ba, to wannan rigunan da na shiga kasuwar kwari kwanaki na taya zan siya lokacin da aka mun scaining aka ce mace zan haifa ita na fara taya wa rigunan kudin su kowacce 10k ce kinga ta je ta kaso Mana kudi har Dubu Ashirin bai kamata a wulakanta ta ba fisabilillahi " " Ummm to wancen rigunan sune original wadanda kika gani Amma wadannan daga ganin su jabu ne ba kwari za suyi ba" Shiru tayi ta rabu da ita don wlh ba taji dadin abinda maman ta yiwa mmn Abdul ba, ita fa ta janye makaman yakin ta don Zama lafiya yafi Zama Dan sarki" Fareeda ce ta shirya taci gayu zata je unguwa, tana taunar cingum ta fito daga daki ta fara wake-waken habaici har ta fita daga gidan murmushi sumayya tayi don inda sabo ta saba da gidadancin fareeda. Bata zame ko ina ba sai gidan malamin su inda taje masa tana yi masa magiya akan ya taimaketa ruwa yana neman 6alle mata. "Fareeda kin yi abin da Aljanin da ya Miki aiki ransa ya 6aci sosai don haka Ni bansan me zan yi Miki ba" "Ran malam ya dade ka taimaka mun Kai kadai nake da yardar zaka mun abinda nake so " "Hhhhhhhhh kin makaro Amma bari in tambayi Dan kunama idan zai Miki aiki" . "Yawwa mallam a taimaka mun ko nawa ne zan bada" "Angama" Wasu dalasimai yake karantawa a haka har ya shafe kusan mintuna biyar. Sai da ya gama kirarin da yake wa aaljani Dan kunama tukunna ya dago kansa yace mata"kinci sa'a yace zai Miki Amma da sharadin sai kin kawo masa jinin jikin ki a jikin tsumma tare da jinin kishiyar taki shima a tsumma ko wanne ki kulle daban-daban don kar ayi kuskure" Godiya tayi masa ta ce babu matsala sai ta dawo . Gidan su ta wuce ta sanar da mahaifiyar ta yanda suka yi da malamin nasu murna tayi tace mata" haka nake son ki 'yata mun Sha wahala na zauna ZAMAN 'YA'YA NA a baya yanzu kwa ai dole mu shana mu fito gari ke dai kice ya baki mallakar da yake hadawa da kan maciji da kuma karin kunama ta yadda in dai ya hada Miki shikenan kin mallake Amir da uwar sa. Gida ta koma don bata son Amir ya dawo bata nan saboda za tace masa ne bata fitan ba sai gobe saboda bata jin dadi yau din. Washe gari da safe ta tashi ta ciro tsumman da tasanya a jikin ta don tarar jini saboda jinin da ya zo mata a daren jiyan, kulle shi tayi a leda sannan ta adan sai kuma ta shiga ko kwanton ina zata sami na sumayya jinin ita da ba shiri suke ba, to koma suna shiri ta yaya zata samu Amma za ta jira anjima tayi shawara da zuciyar ta. Da yamma sumayya tana zaune a tsakar gida kusa da kicin din su na waje tana Shan iska kasancewar yau ana zafi kawai saiji tayi wani kamar an jefo mata mashi tarewa tayi da hannun ta aikwa sai gani tayi ashe wuka ce har ma ta yanke ta a hannun ta. "Innalillahi wannan wukar daga ina haka?" Fareeda ce ta fito daga kicin tace mata "subhanallahi wlh ban gani ba naje in jefa ta a cikin kwando ashe nan ta iyo kiyi hakuri ba da gangan na Miki ba. Ganin fuskarta ta nuna kalar tausayi sai sumayya tace " babu komai ai tsautsayi ne" Kyalle ta dauko ta goge mata hannun tayi hanyar inda suke zuba shara kamar ta jefar Amma sai ta linke tasa a ljihun rigar ta ta wuce daki, ranta fari kal domin cikar muradin ta ya kusa. A leda ta Sanya taje tasa a jakar ta gudun karta manta shi ma. Washe gari da safe ta shirya ta fita gidan malamin ta wuce tace mishi "gashi mallam naka sauran aikin ya rage" "Kai ashe kema shedaniya ce ta lamba daya ma to kinyi kokari" Dalasimai ya karanta sai ga wasu layu da garin magani a hannun mallam ya bayyana , bata yayi yace mata "wannan garin maganin ki tabbatar kin zuba mata a cikin ruwa Tasha to zata rikice don da kanta zata bar gidan ki shi kuma wannan layar ki binne a inda kika San ita da mijin zasu tsallaka idan kinyi wannan aikin sauran duk mai sauki ne" Godiya tayi ta ajiye mishi 50k ta tafi gida ko gidan su bata je ba burin ta kawai taje ta aiwatar da kudirin ta . Karku manta free book ne. [7/4, 9:12 AM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA NA MMN ANNUR YAA HAYYU YAA QAYYUM ina rokon ka da sunayen ka tsarkaka da suffofin ka kyawawa yaa rahmanu yaa raheem ka cikawa mmn Afrah burikan ta na Alkhairi ka shirya mata yaran ta ka basu ilimi mai Amfani ka jikan mahaifan ta kasanya su a cikin Aljannar ka madaukakiya. Ameeen yaa rabbi. Page(22). Alhamdulillah sauki ya fara samuwa jikin Aslamiyya yayi kyau tunda har nannadewar hannu da kafa dinnan babu duk sun koma dai dai, A haka maman ta tace taron suna za suyi saboda su samu kudin suna dama fatara take. Kai kaji tsiya wai da kudin suna za tayi arziki dadi na da talaka wani lokacin bai iya samun guri ba, in banda abun mmn aaslamiyya ita ba ta jinyar 'yar ta take ba,hmmmmmm takamar ta kudin Alhaji Adnanu to mai kudin ta kar6e sai muga yanda zaman zai kaya. Gobe ne za suyi taron suna inda yarinya taci sunan babar Alhaji Adnanu wato Rukayya za ake Kiran ta da Ummy. Yarinya Masha Allah kamar ta da Abdurra'uf sak hatta yatsun kafar ta Dana hannun ta iri daya ne, suwaiba idan ta kalli yarinyar sai taga kamar lokacin da ta haifi Abdurra'uf, jini ba karya ba kamar ta 6aci . Shi kanshi Abdul din zuwa yake ya dauki kanwar tashi yayi ta kallon ta musamman da mmn shi tace mishi kamar su daya da kanwar tashi. Yau take suna maijego ta tafito fess da ita ga Ummy an Sanya mata rigar wajen suwaiba sosai rigar ta mata kyau har da bandana aka Sanya mata kalar rigar, Milk ce da pink color tabarakallah kamar a sace. Yayin da Aslamiyya Tasha wani dakakken leshi ja Wanda tayi order a gurin mmn Annur Tasha sarka da Dan kunne da Abin hannun ta mai kyau Wanda ta siya a gurin mmn Afrah, gaskiya maijego tayi kyau. Kunsan ance maijego tafi Amarya kyau saboda ita sabon jini ne yake gudana a jikin ta. Can na gano suwaiba ta fito cikin dinkin ta da ta bada aka mata doguwar riga ce aka mata dinkin zamani wato na manyan hajiyoyi su ma su Abduljabbar sun Sha nasu gayun da dinkin su. Sai uban jagorar mai gayya mai aiki yasha shadda blue tayi masa kyau harda babbar riga sai walwala yake Musamman abokan sa suka zo taya shi murna inda suka masa kyautattuka na kudi. Taro yayi taro masu aikin girki sai fama suke a gurin tukunya masu suyar nama suma sai aiki suke, raguna biyu ya yanka manya, can na hango mmn Aslamiyya tasha atamfar ta an mata riga da zani rigar tasha stone babu laifi tayi kyau itama.Amma duk da haka kyashi da hassadar ta sai da ya bayyana akan suwaiba da 'ya'yan ta, Wanda su basu San tana yi ba. Anci ansha an koshi kowa ya watse inda maijego ta rattara kudaden ta data samu da kayayyakin barka ta je ta nunawa Alhaji Adnanu yayi mata ftn alkhairi sannan taje ta nunawa suwaiba itama tayi mata Allah ya Sanya alkhairi ya raya ummy akan sunna. Fareeda ta aiwatar da duk shirin da malam ya bata kuma an samu nasara domin sumayya tana tsallakawa taji jiri yana neman kayar da ita, Zama tayi tana salati fareeda tana kusa don taci burin koma meye zai faru sai dai ya faru Amma dole ayau takeson burin ta ya cika. "Sumayya lfy kwa naji kina salati?" "Jiri nake ji" "Sannu bari in dauko Miki ruwa kisha,kinsan wani lokacin karancin ruwa a jiki yana Sanya jiri, shiyasa ake son muke yawaita Shan ruwa" Ina sumayya fa jikin ta ya fara rikicewa don har wata karkarwa take you kamar mai ta6in Aljannu . Ruwan ta bata nan da nan ta ma manta ba tayi Bismillah ba haka ta kafa kofi a bakinta ta fara kwankwadar ruwan kamar wadda tayi kwana daya bata hadu da ruwan ba. Bayan ta Sha ne sai kuma taji hankalin ta ya tashi bata son zama a wajan da take, dakin ta ta koma ta zauna ,tana Zama amir shima ya shigo gidan ya nufi inda ta zuba maganin nan ya tsallaka yana tsallakawa ya nufi hanyar dakin sumayya ya daga labulen dakin ya kalleta ta kalleshi,tana son yi mishi sannu da zuwa Amma bakin ta ya gagara buduwa sai kauda Kai tayi daga kallon shi. Dakin sa ya nufa ya zauna yana tunanin wannna zaman kwawar da sumayya take ya isheshi shifa baya son ganin ta a gidan sa ya tsaneta. Ruwa da abinci fareeda ta Kai mishi tare da yi masa sannu da zuwa cikin kissa da kisisina sai da yaci Abincin ya koshi sannan ya karkace jiki ya kwanta a wajen saboda wannan maganin da ya tsallaka kansa yaji yana juyawa don haka yayi tunanin ko gajiya ce da bacci. Yana kwanciya bacci awon gaba dashi sai mafarki yayi wai ga sumayya nan ita da wani kato a dakinta suna zaune suna fira suna dariya kamar dai mijinta, aikwa yana shiga dakin ya cakumi wuyan mutumin yace "masa ka tashi ka fice min daga gida,mema ya kawo ka gidana kana gardi dakai?" "Kai da baka damu da sumayyan ba, ka sani sumayya tawace, jiran wani Abu guda daya nake yi da ba haka ba da tuni na dade da dauke ta " Farkawa yayi saboda xungurin da fareeda ta mishi ganin yana bacci yana ambatar sunan sumayya,tunanin ta ko maganin bai ci jikin sa ba shiyasa. Bayan kwana biyu taga masoyan sun rage azar6a6i akan junan su shima yanzu baya ma tambayar twins,Kai rabon da ya gansu ma kwanan shi uku don haka ta shirya don Kara kaiwa malam ziyara ta musamman sannan ya Kara mata wasu aikin da yace zai yi mata bayan tayi amfani da wannan layar da maganin. Da yamma bayan Amir ya fita daga gidan sai ta shirya ta fita ba tare da ta tambaye shi ba saboda yanzu yazo hannu shi yasa duk inda take son zuwa za ta tafine ba tare da ta tambaya ba. Zuwan ta gidan malam sai da ta jira saboda layi kusan mutum biyar ne a gaban ta, tana zaune har layi yazo kanta ta shiga gurin malamin nasu suka gaisa take sanar da shi tayi amfani da maganin kuma taga kyan sa domin yanxu ko 'ya'yan sa baya tambaya balle uwar 'ya'yan. Maganin ya harhada mata da Wanda za ta Sanya a gabanta da danyen nama ake hada shi sai ayi inserting dashi idan yayi kwana biyu a jikin ta sai ta dafa masa ta bashi yaci sannan da wani kullin magani baki a leda amfanin sa idan dare yayi zata turara gaban ta dashi to da zarar Amir ya shigo dakin ta shikenan zance ya kare domin mallaka ce tayi masa da daurin baki sannan ta ce a hada mata da wannan maganin da ya ta6a bata Wanda idan ta shafa masa a jikin sa yayin da zata taya shi shafa mai ajiki to duk macen da zai gani zai ganta tana tafiya da kanta ne kafafunta a sama wannan lakanin kawa har sumayya aka yiwa saboda ya daina ganin ta daya da fareedan ya zamana ita da babu duk daya. Haka ya hada mata su ta taho a hanya ta siyi danyen nama na 1k ta karaso gida ta za6i tsokoki kamar guda uku dai dai yanda zasu shiga jikinta ta bade su day maganin nan ta cusa a jikinta, sauran ma duk tayi amfani da su a daren ranar sai da ta aiwatar da aikin malam hatta da Wanda zata ahafawa Amir a jiki saida ta yi masa dubara yana fitowa daga wanka ta shafa maganin a hannun ta ta dauko mai ta shafa masa a kansa da bayan sa sai sauran jikin sa. Wani ikon Allah da yadda ya tsarawa bayinsa rayuwa a lokacin da yaso a take a gurin sinadaran maganin suka fara aiki a jikin sa har sai da ya ce mata ta kwanta a dakinsa shi tsoro yakeji kada ta tafi ta barshi, haka akayi kwa kwana tayi a dakin washe gari haka ta fito ta Sanya sumayya aikin tsakar gida kuma tayi saboda aikin sihirin jikin ta. Yau ne danyen nama ya cika kwanakin da aka diba masa fito dashi tayi taga duk yayi kore har wari yake yi Amma ahaka don rashin imani da kazanta ta dafa shi ta zuba akwanon miyar Amir ta bashi yaci harda sanya mata albarka tayi masa girki da nama. Wayyo Allah masoya sumayya da kungan ta a halin da take da kun tausaya mata domin sumayya ta Zama kantace yadda kusan bawa da mai gidansa haka ta Zama shi kanshi Amir din ya Zama kan tace mijin hajiya domin sai abinda tace musu a gidan suke yi haka za ta hada wanki tabasu kuma dole suyi wannan yana sa6i wannan yana dauraya rayuwar dai abin tausayi. Umman sumayya ce ta zo gidan don duba 'yan biyu aikwa tayi mummunan gani domin yaran tagani duk sun kazance babu wanka kayan su duku -duku ita kanta sumayyar ta wani fige ta lalace gashi an hado mata uban wankin kaya kuma daga ganin kayan kasan ba nata bane na fareeda ne.Umma har kuka tayi ganin yadda aka maida mata 'yar ta kwaya daya tilo jikokin ta ta kalla taga yadda sukayi baki dasu . Kiran sumayyan tayi daki tace "sumayya zo zanyi magana dake Mana" Fareeda ta kalla so take ta bata izinin zuwa Amma tayi shiru ta rabu da ita. "Don Allah inje umma ce take kirana ?" "Kije minti biyar na baki ki fito ki karasa mun wankina" Da sauri taje ta dakin ta gaishe da umma wacce kawai ta tsaya tana karewa 'yar tata kallo tana son gano me yake damun ta Amma ta rasa abun da yake damun na ta. "Sumayya me yake damun ki ? Yanxu har abin naki ya Kai ki zauna ana gasa ki bazaki tafi gida ba sumayya so kike ki kashe kanki ne? Sumayya wanki naga kina yiwa fareeda fa me yasa ? Ji yanda kika koma keda yaran ki ji dakin ki babu gyara ke kanki kin zama wata kazama sumayya me kike son zama ne ? To maza sa hijabin ki ki wuce mutafi gd daga yau auren ya kare tunda ukubar da kike shaka har takai kike yiwa kishiya wanki" Kuka take tana baiwa umma hakuri akan ita fa babu inda zata je a gidan nan zata zauna . Suna cikin haka fareeda ta ce "lokacin da na baki ya cika ki fito ki karasa mun aiki na" Da sauri ta fita daga dakin umma ta tsaya tana ganin ikon Allah wai kishiya ce ke azabtar da kishiya. Tambayar kanta ta shiga yi "wai dama haka kishin yake ko kuma dai ita nata salon kenan anya kwa ba wani mugun abun ba ta yiwa 'yata ?" Tana ciki. Wannan tunanin bata ankara ba taji muryar Amir yana cewa "kinga wannan bakin zanen naki bata dirje da kyau ba ta zuba mun a ruwan kumfa ta" Lekowa umma tayi ta window don ganin abin da yake wakana,Amir tagani fa ya zage daga shi sai wando three-quarter a jikin sa ya zage sai tikar wanki yake yi kai kace sana'ar wankau din yake you da sauri da sauri kafin kace meye har sun gama wanki.Umma hawaye take yi a ranta tana ayyana irin zalunci na wasu matan wato mijin ma ba'a barshi ba saboda son Abin duniya. Lokar su 'yan biyu ta buda ta hada musu kayan su ta ja hannayen su suka fita daga gidan yayin da fareeda ta rakasu da wata malalaciyar harara tare da wani madaukakin tsoki Wanda har umma Saida taji Karan tsokin, ranta ya 6aci matuka Amma zata je ta sanar da bbn sumayyan da kuma kanwar umman taji wace shawara suka yanke game da zaman auren sumayyan. Aslamiyya ta zubar da wanka yayin da ta kar6i girki to ta saba ada sai dai ta girka musu itada mijin to ta rasa ya zatayi da abuncin da zata dafa duba da bata San yaya ake dafawa ba shine ta Kira suwaiba da take wajen aiki ta tambaye ta "kamar Yaya ake dafa Abincin duka gidan?" "Ki dafa shinkafa kofi uku sai taliya rabin leda shine kinga zai isa tunda muna da abin tuwo sai ayi da daddare kinga mijin naki yana son tuwo Dan haka ki zage ki masa don yaji dadi ,ko ya kika ga?" "Kai mmn Abdul mijin ki dai ai ni tare na ganku" Dariya suwaiba tayi tace "to ai duk daya da Ni da nayi shekarun dashi dake da kika zo kwanan nan duk daya duk matan shi za'a Kira mu" "To na gode mmn Abdul sai kin dawo" haka zaman lfy ya wanzu a gidan Alhaji Adnanu duk da arxikin nashi yanzu ba kamar na da bane Amma suwaiba ta ce ta bar masa cikon kudin ta data ke binsa har ma ta kara masa da 100k har kukan dadi yayi yace"yanzu da baki zauna zaman 'ya'yan ki ba lokacin da nake wulakanta ki da yanzu fa wani zancen ake ba wannan ba, na gode suwaiba hakika kedin 'yar Aljannah ce Allah ya Miki Albarka ya shirya Mana yaran mu hakika 'ya'ya ma wata baiwa ce da Allah yakan baiwa iyaye Wanda bazasu gane muhimmancin hakan ba sai sun shiga irin yanayin da na tsinci kaina aciki. Ki duba fa irin abin da na Miki Amma haka kika jure kika ce in barki ki zauna da 'ya'yan ki Amma naki ,a lokacin gani nake yi ai idan na zauna ai na Miki alfarma ne ashe Ni kikewa alfarmar ban sani ba tunda kince ZAMAN 'YA'YAN KI za kiyi ashe gata kike mun da baki zauna da 'ya'yan naki ba da shikenan na rasa ki na rasa yarana tunda indai yara suka lalace shi kenan ka jefa rayuwar ka a hadari ka jefa ta 'ya'yan ma a hadari, na gode suwaiba Allah ya Miki Albarka " "Babu komai bbn Abdul nima na gode . Haka suke gudanar da rayuwar su cikin farin ciki da kaunar junan su,sun hade kansu ita da aslamiyya gashi yaransu suna kaunar junan su ita kanta ummy yanzu tafi yarda da Abdurra'uf saboda yana kula da ita sosai Abduljabbar an sama mishi gurbin karatu a jami'a baya kammala secondary dinshi da yayi ana ya fara karatun sa na Art. Suwaiba tana kokarin taimakon bayin Allah yayin da in tayi sadaka takan yi tawassuli tace "Allah ka Kai ladan wa iyaye na" Kai kuyi manage da wannan in Sha Allah zuwa dare zan yi muku wani idan na samu dama, idan kunji Ni shiru to sai dai zuwa gobe in Sha Allah. Mmn Annur [7/5, 8:54 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA NA MMN ANNUR. Page(23). Al'amarin sumayya da Amir yanzu sun Zama kamar ba mata da miji ba kowa ya tsani kowa musamman Amir,anyi-anyi sumayya ta koma gidan su taki yanda Kai kace cibiyar ta ce aka binne a gidan Amir din, itace wankin kishiya tun daga kan wankin manyan kaya har kananu irin su;pant, braziya,skirt underwear. Wanke-wanke girki share-sharen gidan hatta da dakin fareeda ita take gyarawa, Idan ruwa yazo a rijiya ita zata cika dukkanin randunan gidan gashi har aikenta ake yi cefane. Kai hatta da rainon khairat ita takeyi wankin kashin ta d fitsarin ta, har ya zamana yarinyar bata yadda da uwarta sosai sai dai sumayyan.Ita kanta iya an rufe mata baki akan yanda aka maida mata Danta janitalau,Amma fa a kasan ranta tana jin babu dadi yanzu har tausayin sumayya take ji duba da yanda ta lalace tayi baki babu gayun wannan da tsafta ga tsoro kamar farar kura, hakika sumayya tana azabtuwa a gidan nan . A da fareeda taso sumayya ta bar gidan Amma daga karshe sai taje ta sa aka rufe mata baki aka kafeta akan babu inda zata je sai dai idan har fareedan ce ta bata umarni to wannan kam yanzu ne za kaga aiki da cikawa. Abban ta da kanshi yazo ya ganewa idon sa abin da ake fada masa anan ya yi mata fada akan idan bata jin dadin zaman gidan to ta harhada kayan ta Auntyn ta kanwar umma za ta zo ta tafi da ita, Amma kirikiri tace masa tafi son Zama a gidan mijin ta, mahaifin ta ya tausaya mata sosai tashi yayi ya tafi. Gida yaje ya sanar da umman ta yanda sukayi da 'yar tasu,ran umma ya 6aci sosai har take ikirarin sai tayi Karan fareeda akan yanda take azabtar mata da 'ya sai da Abba ya lallashe ta tukunna tayi hakuri tabar zancen.Shima yana shiga dakin sa ya kwanta ya shiga tariyo yanayin da yaga 'yar tashi daya-daya, Addu'a ya shiga yi mata Akan Allah ya kawo mata dauki da mafita a acikin zamantakewar su.Umma da kanta taje gidan Aunty kanwar ta ta sanar mata halin da sumayya take ciki tana zubda hawaye take fada mata, auntyn sumayya fada tayi tace "yaya me yasa tunda wuri baku zo ba kun sanar da ni ko kuma lokacin da zakije gidan sumayyar ai da kin biyo ta nan munje? Wllh yaya sai na koyawa kishiyar ta hankali ta yadda kowani taji zai aikata abinda take aikatawa za ta bashi shawara akan kada ya tarki aikatawa" "Ta ya ya zaki 6ullowa al'amarin?" "Zanje akarya sihirin a maida mata kanta ta yadda sumayya zata rama abin da ta mata" "A'a gaskiya kada kibi wannan hanyar mu ba halinmu bane rama cuta da cuta, sai dai kawai aje akar6a mata Addu'o'i da magunguna ta yadda sihirin zai karye ita kuma fareeda ita da Allah". "Tom shikenan Yaya Amma wllh ko wannan yarinyar ummmm Allah dai ya kiyaye da tare mukaje gidan sumayya da ita tabbas da sai dai hukuma ta kamani don saina sassa6a mata kamanni" "To uwar gajen hakuri, abinda tayi ai kanta tayiwa ita kuma sumayya Allah ya bata lfy ya karya sihirin da yake jikin ta" "Amin yaya, shine illar aure-aure wasu mazan( LITTAFIN JAMILA LAWAL ZANGO) ai suna cutar mata,haka kawai kana zaune lafiya da matar ka kaje ka jaji6o mata masifa bata jiba bata gani ba" "To ya za'a yi haka Allah ya tsara tun tuni" Bayan kwana biyu Auntyn sumayya taje gidan Malam isiya mai rukiyya ta mishi bayanin abinda yake damun 'yar ta kanwar ta, shine ya hada mata magunguna sannan yayi mata Ruqya Amma a cikin ruwan faro ya hada mata da turaren hayaki sannan da Jan miski da turaren joda na shafawa, kamar man shafawa yake. "Aje ayimata amfani dasu muga yadda Allah zai yi" "To malam muna godiya, nawa zamu bada mallam?" "Eh to sai dai in fada muku kudaden magungunan ku bada Amma ai ko rukiyya akayi wa mutum ba'a kar6ar komai a gurin mutum tunda Kai don Allah kayi ba wai don abin duniya ba" Godiya suka mishi suka kama hanya sai gidan sumayya inda acan za su kaddamar da yin maganin. Sunje su suka taradda ita a kwance tana ta juyi ta rike kanta da yake neman fashewa saboda tsananin ciwo ko bude ido kasawa tayi tana jin sallamar iyayen nata Amma ta kasa buda baki ta amsa saboda azabar da take ji . Fareeda tana dakin ta sai ji tayi sun shigo gidan direct babu neman izini a gurinta a matsayin ta na matar gidan, fitowa tayi tace "wai su waye ne suka shigo gidan mutane babu neman izini?" Kanwar umma ce wadda dama kiris take jira ta fito daga dakin cikin tafiya ta irin manyan matan nan Wanda suka amsa sunan su tace mata"su mu ne wadan da muka isa da gidan dama mai gidan baki daya balle wasu da suke karkashin mai gidan, ko da ja a maganata ne?" Ta tsattsare ta da ido tana kallon ta so take taga karyar rashin kunyar tata Amma sai taji tayi shiru taki magana sai ma juyawa da tayi ta koma daki kirjinta yana dukan uku-uku saboda gaba da gabanta Aljani ya taka wuta. Ita matar ma tsoron ta taji wllh tayi mata kwarjini da yawa har ta ke tambayar kanta "shin wai nice?" Hhhhh kece mana fareeda ai duk rashin kunyar ki dole zaki samu wadda ta doke ki a fagen nan don haka ki taka a hankali wlh auntyn sumayya da niyar dukan ki ta zo gidan nan ato ki bisu a yanda suke so. Ruwan addu'ar suka shafa mata tare da shafa mata turaren joda, sai umman ta ta cewa Auntyn sumayya ta shafa mata jan miskin a marar ta da cinyoyin ta. Bayan an dau wasu lokuta sai aka dauko garwashi aka zuba garin turaren hayakin a ciki suka lullu6e ta har sai da ta fara atishawa sannan suka cire mata abin lullu6ar. Barci tayi sai da ta shafe awa daya tana bacci sannan ta farka,tana farkawa suka ce ta tashi su tafi gida. Babu musu ta tashi suka hada mata kayan ta a cikin akwati sannan suka rufe dakin suka bar gidan. Can da aka dade fareeda taji shiru alamun sun tafi sai ta fito kofar daki ta kama tsantsa tace "sumayya uwar biyu ! Sai da tayi sau uku taji shiru bata fito da saurin da ta saba ba, aikwa afusace ta tafi kofar dakin ta tura taji gamm kofar alama dai a rufe take .tunanin ta ne ya dawo dai-dai na cewa kodai tare suka tafi? . Babu mai bata amsa Amma a haka don karfin hali take cewa matukar sumayya ta dawo sai ta gane kuren ta. Gidan Alhaji Adnanu gidane Wanda aka samu ci gaba saboda taimakon uwar gidan shi suwaiba, don tayi rawar gani duk da tarin wulakancin da ta fuskanta a gurin mijin ta da abokiyar zaman ta duk don ta zauna ZAMAN 'YA'YA to gashi dai tana samun ci gaba sanadin hakuri da ZAMAN 'YA'YAN ta da tayi a baya. Matukar ka jure ka taka rawa wajen rikon amanar da Allah subhanahu wata'ala ya baka to tabbas ba zaka wulakanta ba. Abaya sun so su wulakanta suwaiba sun so su jefa rayuwar ta data 'ya'yan ta acikin matsala. Amma yanzu Alhamdulillahi taga amfanin hakuri da juriya. Shi yasa Allah ya 6oye ladan da zai baiwa mai Hakuri da mai Azumi ,don haka 'yan uwa ya kamata muyi koyi da halin manzon Allah (s.a.w). Duk abinda Allah ya yi umarni da yi ko hani da shi to yana da fa'ida don haka kada mu Raina kankantar hakuri ko kuma muce muce wai hakurina ya kare, a' a hakuri baya karewa sai dai mai yin hakurin ya kosa, to kada mu kosa da yin hakuri don Wanda muke hakurin Dan shi to yana sane sannan akwai tanadin da yayiwa mai hakuri domin sa. Sumayya tana son zaman gidan mijin ta Amma gashi sun tafi da ita ranta in yayi dubu to ya 6aci ,hakika tana tsoron haduwar su da fareeda wadda ta kasance mata tamkar zaki. Bayan sunje gida ne aka bude mata dakin ta na da lokacin tana gida, share shi akayi a ka yayyafa masa ruwan Addu'a tare da yin hayaki a cikin sa, wanka aka Sanya ta tayi ta Kara shafa maganin nan a jikin ta, tana gama shafawa a take ta Mike a gurin tana wasu surutai marasa kai da kafafuwa. Can sai ji akayi ta saki ihu da karfi Wanda karar ihun nata ne ya farkar da twins da suke barci Ayatul kursiyyu aka tofa mata saiji sukayi ta ce" ku daina konani ku daina zamu rabu da ita wayyo Allah kuna kona mu" Jin hakan da sukayi sai hankalin su ya tashi Abban ta aka Kira a waya sai gashi ya shigo gidan da sauri. Karatun Alqur'ani ya fara mata ai sai aljanin ya fara magana " kana yiwa Allah da manzon sa ka daina kona Ni na tuba na bi Allah kuna kona ni kuji tausayi na Mana " Abban sumayya ne yace " kasan da tausayin ka shiga jikin baiwar Allah kake bata wahala? Ba zan kyale ka ba har sai ka girbi abin da ka shuka " Kuka yake aljanin nan yana kururuwa saboda Ayoyin Allah da ake kona shi dasu aljanin nan har sai da suka ga ya daina kururuwa da karfi tukun na Abban sumayya ya ke tambayar shi "menene dalilin da yasa ya shiga jikin ta yake bata wahala?" "Turo Ni akayi akan in sanya mata tsanar mijin ta sannan kuma in Zama hijabi tsakanin ta da mijin ta ta yadda zan hura wutar tsanar junan su a zukatan su, sannan na maidata tamkar baiwa a gurin kishiyar ta sannan tasa muka kafe ta agidan ta yadda duk wahalar da zata Sha ba zata iya tafiya daga gidan ba har sai karshen rayuwar ta" Wannan wane irin rashin imani ne kishiya ta sa amaida mata kishiya kamar baiwa ya kamata muyi hankali da duniya, saboda duniya tamkar cin kasuwa ce lokacin da kasuwar za ta watse to lokacin ne zamu riski abinda muka aikata. Yan uwa musulmai muji tsoron Allah mu sani cewa akwi kwanciyar kabari Wanda idan aka Sanya mutum a ciki babu damar ya juya ya gyara kwanciyar shi yanda aka kwantar da Kai haka zaka kasance har karshen rayuwar ka ta barzahu. Haka ma mu sani akwai hisabi duk kan nin mu ya kamata muyiwa kanmu hisabi tun kafin a yi mana.Hisabi dole ne ko ya ya ka cuci mutum dai dai da kwayar zarra sai Allah yayi maka hisabi akan abin da kayi na kirki ko akasin haka.Allah yasa mu dace Amin. Haka aka tambaye shi waye ya aiko shi ya wahalar da baiwar Allah budar bakin Aljanin sai cewa yayi ai Malamin fareeda ne kishiyar ta ya turo shi, shima kuma fareeda ce tasa malam ya tura shi jikin ta . Tashin hankali Wanda ba'a sa mishi Rana , Anan suka umarce shi da ya sanar dasu in da aka ajiye asirin, kwatan ta musu yayi inda fareedan ta binne layu sannan yace musu su bata ruwan da aka karanta fatiha kafa bakwai garin maganin da Tasha na cikin ruwan zai karye . Sunyi yadda akace din domin anje an tone layun a tsakanin cikin gida da kofar gida tsabar masifa layun duk sunyi bakikkirin dasu sai fatiha da aka tofa mata a cikin ruwan zamzam ta Sha aikwa nan da nan ta fara wani amai mai wari gashi wani jaja baki baki kore kore, karshe dai tana gama aman ta Mike a gurin take baccin wahala. Ana tone wannan kayan sihirin a take fareeda ta fadi sumammiya ba kinta ya juye sai surutai ta shiga yi. Amir yana dawowa gida daga shago ya nufi dakin sumayya, tura kofar yayi yajita a rufe mukullin hannun shi yasa ya bude dakin gani yayi dakin kamar mamallakin sa bata nan domin dakin bayyi kama da ana zaune a cikin sa ba ma yayi kura ga tarkace aciki. Dakin fareeda yaje ya ganta a kwance bakin juye fuska ta mata bakikkirin sai Jan ido kamar tsohuwar mayya , tambayar ta yayi "ina sumayya kwa?" Da kyar ake gane zancen nata tace "ba kaga halin da nake ciki ba kake tambaya ta sumayya sai kace wata yarinyar goye?" " Me yake faruwa ne naga bakin ki ya juye bigewa kika yi?" "Ummmm ummmm lokashi daya na gyannni a ka" Da yanayin zancen nata take yin maganar baki ya juye zancen ma ba ganewa ake sosai ba . "Ina sumayya take?" Kunsan dalilin da yasa ya tambayi sumayya? To ba komai bane yasa wannan sihirin da aka karya ne na jikin sumayya yayi tasiri a jikin sa,kar ku manta tare aka musu sihirin da niyyar mutum biyu ta binne layoyin to tunda an tone shi agurin shi tamkar yayewar wata masiface.ana tonewa shi kuma tunanin sa ya dawo dai dai. " Sumeyye sun tefe gedin su de beberte" Maimaita abin da ta fada yayi yace "sun tafi gidan su da babar ta?" Gyada mishi kai tayi shi kuma ya tafi gidan su sumayyar . Da Sallama ya shiga gidan ko izini ba'a bashi ba ya shiga cikin gidan, yana shiga ya gaishe da umma yace mata "umma ina sumy?" Suma yanda suka ga Amir din a wani birkice sai ya basu tausayi Amma duk da haka a kasan ransu suna Dora laifin da shi ya jawa sumayya ko ma menene. "Tana dakin ta "inji umma, dakin ya shiga ya taradda ita tana kwance Amma ta tafi duniyar tunani ."Sumayya" shiru yaga bata kalle shiba,Kiran sunan ta ya Kara yi Amma still bata jiba ,ta6a mata kafa yayi sai ta zabura ta Mike tsaye, kallon kallo aka shiga yi tsakanin su ,sun dau lokaci mai tsayi kafin s Sumayya ta zauna ta juya masa baya tace masa"me ya kawo ka gidan mu?" "Kamar ya ya za ki tambaye Ni dalili ?bacin kin San ke na biyo tunda kin fita ba da sani na ba" "Kai har kana da bakin da zaka fadi haka eyee? Baka damu Dani ba babu ruwanka da yanayin da nake ciki kabi ka tsaneni to ka sani nima bana sonka Amir kaje ka rubuto min takaddar sakina ina jiran ka saboda Ni bazan iya Zama da mutumin da baisan kima da darajata ba, don haka kafita min a daki tunda ba da kudin ka a ka Gina ba". Tashin hankali Amir ya ganshi yau din nan da idon sa, ace wai sumy ce zata budi baki tace bata son shi to shi me yayi mata haka da zafi har take ikirarin bata son shi? "Wllh ba zan sake ki ba kuma ki sani Zama a gidana ya zame Miki dole domin Ni bazan iya rayuwa babu ke ba don haka ko ki koma gidan ki ko kuma in tattaro kaya na in dawo gidannan da Zama kinga shike nan idan muka Kara haihuwa an huta neman mai zaman jego gaki ga umman mu" Banza tayi dashi ta kwanta saboda ranta kara 6aci yake yi . Kuyi min Afuwa wllh saboda ku na ajiye uzirina mai muhimmancin don na faranta muku . Kun san matsalar bakwa comment shiyasa nake muku Dan kadan . [7/7, 9:38 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA NA MMN ANNURR INA KUKE MA'ABOTA KYAU DA KYAWUN GANI KUN SAN DA KU NAKE MACE DAI 'YAR KWALLIYA CE DON HAKA NAKE SO IN SANAR DAKU CEWA MUNA DA; ATAMFOFI SIYAN DAYA KO SARI,SHADDODI,LACES, MATERIAL,MAYAFAI,ZANNUWAN GADO MANYA DA KANANA, SLEEPING DRESS,DOGAYEN RIGUNA MASU MAYAFAI,TAKALMA, KAYAN FITAR BIKI NA AMARE(CORDNET),KANANUN KAYA,JAKANKUNA NA 'YAN GAYU, SHOWER GEL SIYAN DAYA KO SARI MUNA AIKAWA KO'INA DA YARDAR ALLAH. IDAN KIN SHIRYA KIMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER , kamar haka. 09069615587 Sumayya sai da ta shafe wata biyu a gidan su ana mata magani, shi kanshi Amir din idan yazo umma takan zuba ruwan Addu'ar a cikin zo6o idan ta hadashi sai a bashi yasha cikin ikon Allah duk wani sihiri na jikin su duk ya warware, Amma fa sumy taki da dadi tace ita ba zata koma ba yana ganin ta samu lfy shine zai maidata akara salwantar da ita.rikici suka Sha domin ita ta kafe iyayen ta sunyi-sunyi Amma taki,karshe dai tace duk Wanda ya Kara yi mata zancen gidan Amir sai ta bar gidan ta bi duniya kowa ma ya huta. Amir ya rasa yadda zaiyi da ita saboda sumy akan gaskiyar ta take,ya hadu shida matar sa sun wulakanta ta sun maidata kamar baiwa ya hantare ta a gaban mutane akan warin da bata San tana yiba har takai ta maida daki gurin da zai zamo marufin asirin ta duk zafi haka za ta zauna acikin daki koda babu wutar nepa a gari.basu damu da cinta da shantaba hatta suttura tana gani zai yiwa fareeda Amma ita ba zai mata ba 'ya'yan ta da suka zamo wani sashe na jikin ta suma baya kula dasu an dau tsanar duniya an Dora mata, mahaifiyar shi da kanwar shi sun koma gurin fareeda ita sun wareta babu ruwan su da yin wata kyakkyawar alaka da ita , to me za tayi a gidan Amir ai gara ta zauna a gidan su ta rayu cikin farin ciki ita da 'ya'yan ta su samu kulawa a gurin mahaifan ta. Gidan iya yaje ya sanar da ita abin da yake faruwa, hakuri ta bashi tace "kayi hakuri Amir don ni wlh ina jin kunyar iyayen sumayya da ita kanta mai dakin naka duba da yadda muka wofintar da ita muka fifita abokiyar zaman ta akan ta kaga ko wacece aka mata irin abinda aka yiwa sumayya to dolene taji ta tsani duk wani Wanda ya yi mata abin nan. Don haka ka koma gida kuje gidan su matar ka Kai da 'yar gaban goshin naka ku bata hakuri ta yiyu taji sanyi da zuwan ku tunda mai cutar da ita din tayi nadama " "Ai fareeda iya bata da lfy tana kwance tun ranar da sumayya tabar gidan ta kwanta jinya" Cikin mamaki iya tace "Kai Dan nan ai dole ka susuce, dube ka duk ka lalace ka zabge" "Yo ba dole ba iya, Ni wllh ban San me ya kaini yin auren nan ba ma,ina Dan zamana da matata da yarana naje na jaji6owa kaina tashin hankali, kullum Ni ina cikin fargaba da zarar gari ya waye. Wllh iya idan dare yayi har bana son gari ya waye saboda tashin hankali da bauta da muke yi nida sumayya ga wahalar wankin matar nan da take Sanya mu" "Kai ne ai ka jawowa kanka munq zaune lfy da baiwar Allahn nan ka dauko Mana tashin hankali da hannun ka ka kawo mana cikin dangi, bari anjima zan je gidan naka daga nan in wuce gidan su sumayyar". Tashi yayi ya tafi gidan nasa fareeda ya tarar ta tashi tana kicin wai xa ta dafa Shinkafa da ka ganta kaga sabon shiga, to itq da can ma ba girkin ta ke yiba sosai sai dai tasanya 'yqr mutane tayi kojai kojai da ita, tana ta kanta bakin ta akarkace ta doka masa wata tsawa "daga gidan wa kake har ka dauki tsawon lokaci baka shigo gidan ba ? Ga wanki cen yana jiran ka kaje kasanya three-quartern ka kafito kafara tunda kaki kaje ka taho sa sumayya daga gdnsu" Haka ya tu6e ya tsugunna ya fara tikar wankin nan, da yake sihirin jikin sa ba duka bane ya karye, kada ku manta yaci kwanannen nama Wanda yayi kwana biyu acikin jikin fareeda sabosa tsabar masifa naman har kala kala yake yi. Har yamma yana aikin wanki ita kuma tana zaune tana baiwa khairat mama don karfin hali ba dadi take jiba Amma take azabtar da Dan mutane saboda rashin tsoron Allah. Iya ce ta shigo gidan Amir din don ta duba jikin na fareeda, shigowar ta kenan taji fareeda na cewa Amir "kasan zanen can bai fita ba ka sake dirzawa" Haka ya dauko zanin ya goga sabulu ya dirza shi sosai, yana cikin matse zanin ne iya ta taho a 360 tayi ball da robar wankin tace "Amma ke wannan yarinyar kwa za kiga Annabi, ki rasa Wanda zaki sa wanki sai mijinki ?" Shiru tayi ta rabu da ita, tace masa"ka dauki kayan nan da tsohuwar nan ta zubar ka Kara sa6awa" Haka ya dauka yana rawar jiki zai maida kayan cikin wani botiki Wanda yake da ruwan kunfa a ciki, iya ta warce kayan ta kuma watsar dashi tace "ki tattara kayan ki ki bar gidan nan wllh tun kafin hukuma ta zo ta ka maki " "Babu inda zani,Zama daram acikin gidannan. Lokacin da ya auro Ni Ni kadai nazo to yanzu kuma na haihu kinga ba zanje gidan mu da 'ya ba tunda Ni kadai suka kawo gidan danki don haka Ni ba zan iya baki 'yata ki rike min ba Ni kuma bazan tafi da jikarki gidan mu ba,to kinga ai dole na hakura na zauna a gidan uban 'yata" "Shasha Sha ke har wata haihuwa kika yi a gidan nan ne? Ba kiga mai 'ya'ya maza ta tafi gidan su ba balle ke mai 'ya mace 'kwallin 'kwal" Amir dai dadi yaji da ganin mahaifiyar tashi ko banza zata Zama makari a gareshi saboda tsoron fadan Fareeda ya keyi. "Kinga tsohuwa Ni ba sumayya bace da zaki zo har gidana ki nemi fada mun bakar magana ,don kina surukata ai ba wai kin haife Ni bane" "Yan zu Ni fareeda kike fadawa wannan maganar ?? Ni na haifa Miki mijin da kike ta kama fa, iyyy lallai irin sakayyar da zaki yimun kenan?" "Ba wani sakayya dama ai ba wai Sona kike ba Abin hannu na kike kwadayi, kuma da kike ikirarin in tafi gidan mu to idan na tafi kinsa an sake Ni zaki iya rainon 'ya'yan da za muke haifa a kwararo? To ko kin raba mu bamu rabu ba sai dai kiyi abinda za kiyi" Iya tana ji fadan ya fi karfinta tasa Kai ta fice daga gidan kuma dole kanwar naki Amir yaci gaba da yin aikin sa na wanki. Iya tana komawa gidan ta ta rushe da kuka tana tuna alkhairin sumayya a gare ta, wato lokacin da sumayya tazo ta domin maslaha taki da dadi dama haka sumayya taji babu dadi a ranta? "Allah na tuba ya Allah ka yafeni kamin aikin gafara" A sace Amir yana zuwa gidan su sumayya ba tare da sanin fareeda ba, yayi -yayi sumayya ta dawo gidan ta Amma taki ta nuna masa fa ita yanzu baya gabanta ya rabu da ita kawai.haka ya hakura yace mata "zan baki lokaci kiyi tunani ki dawo ki zauna tare da "ya'yan ki da mijin ki" Bayan wata uku iya ta dage wa Amir da Addu'a tare da neman wani magani wai shi karya tambaya tana zuba mishi a girki da ruwan wanka cikin hukuncin ubangiji yaji shi tamkar an yaye masa ciyawa a jikin sa, duk wani tunani nashi ya dawo fresh. Wani lokaci bai nuna wa fareeda cewa ya dawo normal ba sai da ta kirashi cikin tsawa tace masa "Kai Amir ka fito ka Dora mun ruwan wanka" to anan ne fa yace mata "ke don rainin hankali Ni zan zuba Miki ruwan wankan? To Dan iyayen ki kada ki yi wankan daga nan har shekara guda kar kiyi kiga idan zan damu" Jikin ta ne yy sanyi a ranta tace "yau alkadari na ya karye Amma bari a jima idan ka fita nima zan fita" Haka kwa akayi yana fita ta fice itama bata zame ko'ina ba sai gurin malamin nata, bayan sun gaisa take sanar dashi halin da take ciki. Tambayar ta yayi ina jaririyar ta tace masa"tana makotan mu, bana so Tasha wahala ne shiyasa na barta a gida ban taho da ita ba" Malam yana jin haka yace mata "da wani sashe na jikin 'yar ki za'a hada ayi aikin da za'a miki." Ai fareeda bata San lokacin da ta kunduma wa malam zagi ba tace masa"Amma malam kanka yaci dankali da yawa? In ba haka ba 'yar tawa zan bada ayi tsafi da ita Dan kazakazan ka?" Kafin ta rufe bakin ta sai gani fareeda akayi bakin nan ya Kara juyewa tayi wani iri da ita malam ne ya dauko garin magani ya hura mata a jiki yace mata"kije kya gani fitsararriya keda wari kun daura aure dashi, dama aljanun da suke Miki aiki duk kin janyo an kona su don haka kema ki girbi abinda kika shuka" Ai malam yana fadar haka fareeda ta fara soshe soshe da wasu irin surutai jikin ta sai Kai Kai yake. Gida ta koma ta shiga bandaki don yin fitsari tsugunnawar da zata yi sai ganin wasu halittu tayi koraye sai fitowa suke yayin da fitsarin yake zuba, "na shiga uku na lalace Ni fareeda me zan gani haka ?" Fitowa tayi don ko tsarki ta kasa yi saboda bata son ta ta6a tsutsotsin nan masu motsi da suke jikin ta. Shigowar Amir yayi dai dai da fitowar ta a bandaki wani irin wari ne ya bigi hancin sa yace "ke malama ki tafi kiyi ploshing din kashin ki da kika yi kinbar gida sai wari yake yi" Ba kashi nayi ba fitsari ne" tace cikin sanyin murya. "Matsa Ni ki bani guri" yace mata lokacin da zai shige dakin sa, biyo bayan shi tayi ta mishi sannu don tunda taga alkadarin ta ya karye ta ceto daga yau zan yi biyayya wlh Ni bana son komawa gidan mu Wanda babu cimar arziki balle wutar nefa ga jarababben sauro kamar su goyi mutum. Wani wari ne ya doki hancin sa yace mata "wai wannan wace jaraba ce ta zo Mana gida ne haka kawai ake neman Sanya mutum yin amai menene yake warin nan?" Shiru tayi domin ita ma warin jin sa take yi amma bata kawo akan itace mai yin sa ba. Dakinta ta tafi ta zauna gami da yin ta gumi tace wa kanta" Anya ba warin jikin sumayya bane ya dawo jikina ga shi bakina ya karkace ga wasu halittu da suke kasana kuma masu rai, ya ya zanyi?" Hawaye take zubarwa Wanda ba na nadama bane, a'a hawaye ne na bata so ganin halittun nan da suke jikin ta ba. Za bura tayi lokaci Daya ta Mike tsaye ta rasa yadda za tayi halittun nan ne suke cizon ta baya da haka kuma tana jin doyin kasan nata, bandakin ta Kara komawa domin dubawa har da tafiya da madubi don duba gurin, " wayyo na lalace na gama yawo" kuka take yi ta fito da gudunta yayin da ta nufi dakin Amir tace masa"Amir wlh asiri aka mun kaga wasu halittu ne a jikina har wani kore kore suke ga ruwa da gurin yake fitarwa" Amir dinne ya budi baki yace mata" Alhaki ne yake bibiyar ki, tun guri bai 'kure Miki na kije ki nemi gafarar Allah sannan da gafarar wadanda kika zalunta musamman sumayya 'yar Aljannah" Hmmmm wato mai aikata shirka shi gani yake yi kowa ma aikata wa yake yi Allah ya kiyashe mu aikata aikin Dana sani Amin. "Babu wani alhaki Amir Ni ban aikata komai ba" "To ai shikenan nidai ki fice mun daga daki tun kafin cikina ya fara birkicewa don Amai nake son yi ma dalla malama ki fita mun a Daki " Kuka ta rushe dashi ta shiga dakin ta ta sa6i 'yar ta sai gidan su sumayya in da ta musu dirar mikiya Kai kace laifi aka mata ko Sallama babu haka ta fara sakin bakaken maganganu " ina sumayya ki fito kizo muje inda kika yi mun asiri a karya idan ba haka ba na tashi ramawa wllh sai kin gwammace kida da karatu domin Ni haukata ki zansa ayi" Auntyn sumayya ce da tazo lalla6a sumayya domin ta koma gidan ta saboda ta ga Amir yayi laushi yayi nadamar wulakanta ta da yayi, jin furucin fareeda yasa ta fito tace mata " ke don iyayen ki ba'a koya Miki tarbiyya a gidan kuba ? Ke idan da sumayya tana bin malamai ke kin isa ki shiga gidan ta ne da zummar Zama kishiyar ta? To ki je ki koma gurin malaminki kice masa ya yi karya idan shine ya turo ki mu da kika ganmu bama bin malamai bama hulda da masu biye-biyen malamai kina ji ko ? To ki tafi tun kafin in Miki duka shasha Sha kinxo kin cika wa mutane gida da wari banza jahila dabba kawai" Wani ihu ta saka tace "wlh idan baki Duke Ni ba bakya kaunar babar ki" Dauuuuuu taji saukar mari ta kuma Kara mata ai kafin kice me bakin ta ya hayo ya kumbura sannan wasu taurari da ta gani har sai da tayi suman tsaye. "Idan baki ji a jikin kiba to ki zauna in Kara Miki da bulala" Yarinyar ta sai kuka take yi ,ita kanta khairat din warin damunta yake you to Dan dai yarinya ce babu bakin da zata fada ne shiyasa take kuka. Fita tayi da sauri, lokacin sumayya tana wanka har sai da ta tafi tukunna ta fito domin kwata_kwata bata kaunar sake ganin fareeda a rayuwar ta. Daki ta shige ta fara kuka saboda ita bata kaunar zuwa wajen bokaye Amma ji yadda Amir ya janyo mata aka zo har gidan su aka ci mata mutunci wai tayi asiri Kai Allah ya kyauta . "Wllh na tsani kishiya irin fareeda,muna zaune lfy cikin so da kaunar junan mu Amma lokaci Daya fareeda duk ta rusa mana, wannan wace irin mace ce wadda bata jin tsoron haduwar ta da Allah? Yanzu ita ko tunanin mutuwa ba ta yi ace ka shiga tsakanin masoya guda biyu ka raba Da da mahaifi wannan ma kadai ya isheki zunubi don wlh ba zan yafe wa fareeda ba" Cikin kuka take surutan nan Kai kace da wani take tsabar 6acin rai ne da tunanin makomar ya ya rayuwar 'ya'yan ta za ta kasance ita da ta dau alkawarin Zama da mijin ta da 'ya'yan ta har karshen rayuwar ta. Gaskiya Fareeda kam gurin malam ta wuce akan ya yi hakuri ya karya sihirin da ta yiwa sumayya ko ita ma za ta samu sassaucin wannan halin da take ciki, Amma me ? Tana zuwa ta tarar ana zaman makoki a kofar gidan alamu sun nuna dai malam ya mutu. Tambaya tayi a gurin ta samu wani yaro take ce masa "Don Allah yaro wanene ya rasu a gurin nan naga taro?" Budar bakin yaron sai cewa yayi da ita" ai malam ne ya rasu yau kwanan sa biyar ba'a ga ya fito ko kofar gida ba to jiya da daddare sai akaji tsami a unguwar da aka bibiyi inda tsamin yake sai aka gano ashe a gidan sane ana dubawa aka ganshi a mace duk yayi kore ga wasu halittu sun fito masa a kunne da hanci da bakin sa, halittun ance wai kamar tsutsa kamar wutar ola-ola( doguwar tsutsar nan mai haske da daddare) cikin sa duk ya kumbura saura kadan ya fashe" Kai jama'a kaji saurayin yaron nan da shegen surutu kamar an kunna shi sai zuba yake you kamar 'ya'yan kanya. Jikin fareeda duk yayi sanyi ta tsorata da jin labarin rasuwar malam da yadda yaron ya fasalta mata halittun da suka fito a jikin malam din sak irin halittun jikin ta, ita dai ji take kamar tayi hauka ga tafiyar halittun babu dadi wani iri take jin jikin ta, idan tana so ta sosa gurin don ta ji sawaba sai dai ta Kara hannun ta a jikin zanen ta ta sosa ta waje to shine zasu Dan lafa Amma da zarar sunji an dena ta6a ta zasu fara mata tafiya. " Allah ya jikan sa". "Amin " inji Dan saurayin. Gidan babar ta ta tafi ta sanar da ita halin da ake ciki ai ita kanta maman nata dauriya tayi data saurari fareedan domin wani hamami da taji bata San lokacin da ta fita ta bar mata dakin ba tace mata" fareeda wannan wane irin wari ne naji kina yi! Kuka fareeda take yi tace mata "kema kina jin warin ko mama?" Hakika maman ta taji tausayin ta matuka Amma me warin tamkar guba yake. " Ina ji mana" " To mama daga gidan malam nake" haka ta zayyane mata labarin mutuwar malam din da yadda halittu suka fito masa a jiki. "Mama nima kaina kinga halittun sun fito min a kasana sun hanani sakat na rasa me yake mun dadi" " Asibiti za mune yanzu ki tashi ki dauraye jikin ki ki sa turare mu tafi" Haka ta shirya jikin ta suka tafi asibiti suka yanki kati,sunje gurin likita sun mai bayanin abinda suka fito mata a jikin ta ana likitan ya tura su dakin haihuwa.suna zuwa aka ce ta shiga cikin wani daki ta hau gado, nurse dince ta shiga ta haska da fitilar waya taga ikon Allah tsutsa manya da kanana a jikin Dan Adam. "Innalillahi wannan wane irin magani kika yi amfani a jikin ki ? Ko irin masu magungunan matan nan ne suka baki wani abun kika sa?" "Wllh likita banyi amfani da maganin mata ba a jikina,nima haka kawai na wayi gari na ga sun fito min" Nurse dince ta tafi taje ta sanar da 'yan uwanta abinda yake faruwa ta bukaci dasu fada mata me za tayiwa patient din, anan wasu daga cikin su ne suka bukaci dole sai sun gani tukunna za su San wani mataki za'a dauka. Tafiya sukayi domin suga wannan ikon Allah Wanda wasu daga cikin su tsegumi ne zai kaisu Dan su sami na ya ya tawa a gari, suna shiga suka ganta ta bubbude kafafu alamar ta gaji da tafiyar tsutsar sai mutsu mutsutu take da jikin ta, gani suka yi kowa yaja baya Daya daga cikin su ce tayi karfin halin tambayar ta " baiwar Allah ki fada Mana gaskiya meye silar faruwar wannan abin da suka fito Miki a jikin ki?" "Ban sa komai ba ajikina ba Amma" sai tayi shiru dayar ta hantare ta tace mata "Amma me?" Shiru tayi don wlh kunya take ji tace musu a bibiyar malamai ta samu wannan jinyar Wata tsawa da aka daka mata sai da ta tsorata ai babu 6ata lokaci ta zayyane musu abin da tasa ajikin ta wato danyen naman da ta barbade shi da garin magani. Salati suka yi kowa da Abinda yake fada. Dettol suka dauko da handgluf da kyar aka samu wadda tace zata dubata. Tana ji tana gani aka zuki dettol da wani magani aka fesawa tsutsotsin nan ai nan da nan suka fa ra komawa cikin jikin ta yayin da take ihu domin tsunkon ta suke a cikin jikin nata mamaki gami da al'ajabi suka Sanya nurse din kusan mutuwar tsaye Dan wllh ta tsorata da ganin wannan abin mamakin, doctor aka Kira Wanda shima da kyar yazo da aka bashi labarin abinda matar take fitarwa a jikin ta. Kayan aikin aka bashi yayin da ya bude mata jikin ta ya gansu halittun sun Kara kadowa waje, wani babban sirinji aka bashi irin Wanda ake yiwa dabbobi allura ya zuki wannan dettol da wani ruwan magani mai zafi da radadi aka cusa mata sirinjin a cikin jikinta ya fesa maganin ai nan take tsutsotsin suka yiyo waje suka murmutu sai da ya kashe kusan tsutsa 500 sannan ya mata allura yace mata"gobe ma kisa mu danyen kifi kisa ba danyen nama ba " aikwa kunya duk ta lullu6eta aka rubuta mata magunguna da allurai suka biya kudi sannan suka wuce gidan fareedan. Ai ko khairat bata saurara ba ta kwanta sai bacci, Wanda rabonta da yinsa tun ranar da ta gansu a jikin ta. Wai ina labarin hajiya suwaiba ne uwar gidan Alhaji Adnanu da Aslamiyya Amarya a gidan Alhaji Adnanu????? Mmn Annur Babyyyy nah [7/13, 3:27 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA NA MMN ANNURR Page (25) Alhaji Adnanu Allah ya rufa masa asiri don kwa ya fada siya da sayar da dabbobi kama daga manya da kananu yayin da in ya siya yakan yi lodin mota akai mishi lagos, sosai yake samun Albarka a ciki. Abinda ya samu yana tsakurar wani abu ya yiwa matan sa ihsani tare da "ya'yan sa hatta da Ummy karamar yarinya ana mata siyayya dai dai gwargwado, yakan zauna yayi tunanin rayuwar sa ta baya yaga ai yayi wauta da ya biyewa kudi suke neman halaka shi, wato Allah ne ya tarfawa garinsa nono ya dawo kan dai dai da yanzu sai dai ya janyo wa kansa zagi ya janyowa 'ya'yan sa abin kunya, Allah ya ganar damu baki daya. Daga cikin kudaden suwaiba ta ware wani abun ta rantawa Aslamiyya domin ta juya ,a cewar ta Zama haka ba shi da amfani koda kwa ace mijin ka ya dauke maka dukkan bukatun ka na rayuwa. Kai ma za kaso ace yau ka amfanawa iyayen ka da 'yan uwanka da mabukata Kai dama jama'ar dake kewaye da Kai, Sana'a dadi ne da ita musamman idan Allah yasa Albarka a cikin ta. Zama sukayi suka shawarci mijin nasu akan wace irin Sana'a ya kamata suyi, anan yace musu"me zai hana ku fara harkar kayan tufafi na maza da mata duba da yanzu Kai ya waye a online ma ciniki ake yi musamman idan mutum ya iya tafiyar da dubarun sa akan kasuwancin, na'am su kayi da shawarar mijin nasu. Bayan kwana biyu suka shiga kasuwa suka yi sarin kaya;Atamfofi manya da kanana,shaddodi,yadiddika, material,dankunnaye,sarkoki,hijabai da mayabai masu beadwork,Kai har kayan yara da takalma sai da suka saro dai dai kudin su. Bayan kwana biyu suka yi lissafin kudin kayan da yadda za su Saida Kai hatta da abin da suka samu asaman kayan sai da suka rubuta a takarda ,Alhmdllh da yake kowa yana da babbar waya sannan suna da groups da dama a nan suka fara tallata kayan da Dora kayan a status dinsu kan kace me mutane da dama sun nuna suna son kayan da yadda za'ayi kayan ya iso garesu, bayani suke yiwa mutane idan har akwai garin da mota take zuwa to insha Allah zasu aika musu kayan su. Wani ikon Allah sosai kayan nasu ya samu kar6uwa a gurin jama'a nan da nan suka fara saro masu yawa idan kaya sun kare sai a ware riba a Sanya ta a banki sauran kudin sai akara juyawa. A Lagos ne Alhaji Adnanu ya hadu da wata inyamura suka kulla abota har takai ga sun fara soyayya, shidai a nasa 6angaren baya sha'awar Kara aure domin karin auren da yayi da ma dakyar ya tsallake rijiya da baya, don haka sai ya sanar da ita cewa tayi hakuri bashi da muhallin da zai Sanya ta aciki, Amma fafur taki da dadi ta makale masa don har barazana ta masa akan wlh zata je har garin su ta nemi gidan sa ta sanar da matan sa inyaso kome ne ne ma sai dai ya faru,bai isa ya yaudareta ba. Abu ya taru ya yiwa Alhaji Adnanu yawa yana tsoron fitinar da ta ta6a faruwa dashi a baya ta Kara dawowa, Amma zai tun tu6i matan sa da batun sannan zaije gurin kawu suyi maganar. Bayan ya dawo daga Lagos ne yayi wa matan sa tsaraba ta musamman da Yara Kai hatta da kawu shima sai da ya masa siyayya,inda yaje wa kawu da zancen Kara auren nashi,kawun yace masa" Adnanu Ni ba kin aurenka nake ba bana son abinda aka yiwa suwaiba a baya azo a maimaita mata wani gaskiya shi ba zai goyi da bayan rashin adalci ba" "Yaya wllh nima auren nan ba son yinsa nake ba to matar tace wlh sai taxo gidana ta sanar da mata na idan su suka hana ma to su shirya sai ta shigo, Ni kuma da tazo ta wulakanta mun mata na gara kawai ayi maganar auren a wuce gurin" Murmushi yayi kawun yace masa"haba Adnanu kamar ban San ka ba ? Ai nayi alkawari wlh in dai ka wulakanta suwaiba sai nasa kotu ta sawwake mata auren ka gara ta samu ta zauna da 'ya'yan ta cikin rufin asiri a wani gurin na daban, Aure Ni ba hanaka na yiba Allah ya Sanya alkhairi" Bayan wata Daya da zancen auren Alhaji Adnanu da kawu,sunje an tsaida lokacin biki nan da sati uku, yayin da kawu yace "Adnanu to ka gama da wannan fagen da kake tsoro na inyamura sauran ka na hausawa suma aje a lalla6asu da tausashshen lafazi ka sanar dasu zancen auren naka" "To Yaya in Sha Allah zanyi duk abinda kace" Cikin jin dadi kawu ya tafi gidan sa, yayin da Alhaji Adnanu ya sanar da matan sa zancen karin auren,ya Kara da fadin"kuyi hakuri ba wai zan auro ta bane ko Dan ta fiku, a'a zan Aure ta ne in yi koyi da sunnah, kuma in Sha Allah zanyi kokarin inga ban tauye muku ba ko da da kwayar zarra don haka kuyi hakuri ku taimaka mun in sauke nauyin ku da yake kaina, babu matar da za tazo ta wulakanta mun ku a gidan nan in kyale ta,Allah yayi muku Albarka ya hade mun kawunan ku". Da "Amin"suka amsa,yayin da yace musu" babu mai magana?"suka ce "babu" Akwan A tashi hausawa sukace jariri zai Zama ango,yau aka daurawa Alhaji Adnanu aure da Zainab ( madam). A yau din aka kawo masa Amaryar sa, ya hadasu a dakin shi yayi musu nasiha sosai akan suji tsoron ALLAH su zauna lfy kada su yarda a shigo musu gidan su a cutar da su. Bayan ya sallame su kowa ya tafi dakin sa yayin da madam Zainab ta ce"Alaji wlh yawuna duk ya tsinke na kosa da ka gama nasiyar ka muci kazar nan mai kamshi,gaskiya hausawa kun iya gashi tun kafin in Kai bakina har jin dandanon nake a bakina saboda iya gashi" Aransa ya furta "Ikon Allah mace sai kace mayya lallai inyamura da San samu take" Haka ya turo mata kazar sannan ya dauki ta 'yan uwanta ya Mika musu nasu suma. Dawowa dakin yayi don cin wani Abu daga cikin kazar Amma me?? Yana shiga dakin ya tarar da ita tana sude hannu alamun taci ta koshi yace mata" miko min sauran nima inyaga na kora da lemo yau Kam ban samu na ci Abincin kirki ba" "Hhhhh Ai ina Gaya maka Alaji kazar nan na gama da ita wollayi saboda dadin gashin Ni sai naji ban koshi ba Alaji da zan samu Kari ma ba ki zanyi ba" Wani ashar da Alhaji Adnanu ya mulmulo wa inyamura sai da ta tsorata yace mata"yanzu kazar ko dandanata banyi ba daga fita in kaiwa yayunki ta su har kin cinye sai kace wata wadda bata cin nama?" "Ikon Allah yanzu Dan Amarya ta cinye kazar ta laifi tayi?? Ina cewa kazar don Ni ka siyo? To wllh kasa a ranka dole daga gobe a fara girki da kaza agidannan" Cikin hargowa take fada masa wanda sautin fadan nata har dakin Aslamiyya. Murmushi tayi tace "Tun a daren farko har an fara rigima da bayerabiya wannan ai in aka kwana biyu da mu zata fara" Da kyar ta bari yayi bacci saboda mita da jaraba akan yayi maganar ta cinye nama. Washe gari Aslamiyya tayi breakfast aka warewa Ango da Amarya nasu ,yayinda su kuma suka dauki nasu suka ci har yaran gwanin sha'awa kana ganin su kasan akwai hadin kai. Amarya sai wajen 12 pm. Ta fito waje tana wata tafiya tana bada fadi ga wasu kaya ajikin ta kai kace samudawa ne za su sa, sai kuma sikert din da ya kasance iya kar sa gwiwar ta, haka ta fito tana ciccin magani yaran ne suka gaishe da ita, ta amsa musu cikin sakin fuska tana ware musu baki tamkar gonar masara, Zama tayi kusa da suwaiba tace musu"iyayen gida kun tashi kolau" da hausar ta irin ta gwarawa, "lafiya muke " suka hada baki gurin maida mata martanin tambatar lfyr tasu. "Ina so ku fada mun ya tsarin gidan naku yake?" "Tsari kamar ya ya?"inji Aslamiyya "Yanda kuke tafiyar da sha'anin gidan naku nake nufi" "Ammm kinga ki bari idan mai gidan yazo sai aji ta bakin sa, Amma mu yanda muke tafiyar da kwanakin girkin mu shine kwana 2 ne kowacce" inji suwaiba uwar gida uwar katarere "Cabbbbb gaskiya tsarin naku bai yi ba kamata yayi ace kwana daya-daya ne shine Wanda ba zaka dau lokaci ba kana tare da mijin ka Amma Kwana biyu biyu ai da kwaruwa, yanzu kuna nufin idan ya gama Yi mun kwanaki uku na kafin in ganshi sai nayi kwana hudu ? Gaskiya bazan lamunta ba" "To kada ki lamunta Mana mu haka muka tsara don haka idan kinga za ki bi yanda muke yi kalas mafi mushkila, idan ba zaki iya ba to ki cikawa bujen ki iska ( sikert )"inji mai dakin tsakiya wato Aslamiyya. Haka ta tashi ta tafi dakin ta buguzum buguzum kana jin Karan takunta kasan wannan mata ta ginu domin a koshe take. Alhaji Adnanu ya dawo gidan sai amarya ta tareshi a gaban Yara da matan gidan ko kunya haka ta dauke shi duk da yana katon shima Amma a haka ta sungumi abunta tana masa sannu da zuwa da yarbanci. Mutsumutsu tu yake yi na kwatar Kai saboda babu da'a agaban Yara da su suwaiba ta yi masa haka da kyar ya sqmu ya kwaci kansa yace mata tayi gaba ga shi nan shigowa dakin. Abdurra'uf ya tura dakin ya kar6o ledar da ta kar6a a hannunsa. Kar6owa yayi ya kawo wa mahaifin nasu, mikawa suwaiba ledar yayi yace mata" ga tsaraba nan ku karkasa sai a baiwa madam nata itama " Bayan an karkasa aka Kai mata nata, sai maidowa tayi tace ai ita ke da miji don haka ita ya kamata a bawa ta kasa ta baiwa kowa nasa, mamaki ne ya Hana kowa magana sai suwaiba tace mata" tayi hakuri daga yau ba zasu Kara ba" "Wai maman Abdul meye hakan kike bata hakuri ?? Daga shigowar tata gidan kwana Daya har za ta kafa Mana wasu banzayen dokoki? To ba da niba kuma kema bata Isa kibi abinda take so ba " Aslamiyya take fada cikin 6acin rai. Bayan wata Daya inyamura ta juyar da hankalin Alhaji Adnanu kanta don yanzu ya koma Adnanun sa na da lokacin da ya auri Aslamiyya. Suwaiba ta saba da halin sa dama ita bata damu ba Amma ita Aslamiyya abin sai yake mata ciwo take ayyana wa a ranta " wai dama haka suwaiba take ji duk lokacin da suka wulakanta ta itada Alhaji Adnanu? Gaskiya in haka ne Mmn Abdul tana da hakuri da kawaici" Dai dai da abin kwadayi Alhaji idan ya siyo sai dai ya kaiwa inyamura ban da su Aslamiyya, abun yana konawa Aslamiyya Rai sosai da sosai Dan sai yanzu take kara jinjina wa suwaiba da hakurin da tayi lokacin Aslamiyyan tana tata rashin mutunci ta. Hakika kafin a samu mace mai kirkin suwaiba za'a dade, saboda irin matannan ne masu kauda Kai da kawaici duk yanda za ka 6ata mata Rai ba zata ta6a nuna maka ba sai dai ka gaji ka daina. Mahaifin sumayya ya takura ta akan dole sai ta koma gidan Amir, shine yake shawartar akan cewa" sumayya kiyi hakuri wlh duk yadda za mu nuna Miki soyayya to tabbas dole muso ki shiga Aljannah,ita kuma Aljannar mace dole sai tayi hakuri da halayen abokan zamanta musamman miji tunda ta karkashin sa za ki samu to kiyi hakuri Ni kqina nasan kina hakuri kuma bana goyon bayanki akan rashin Da'a , nasan bani da matsala akan tarbiyyar ki daidai gwargwado kina da akwai. Don haka ki daure ki Zama jaruma abar alfaharin yaranta da mijin ta da mu kanmu za muyi alfahari da ke" In Banda kuka ba abinda sumayya ta keyi, tana tuna rayuwar da za ta sakeyi a gidan Amir da fareeda, idan ta tuna wahalar da Tasha agidan nan sai taji duk ta bi ta tsani kanta. Hakika wata kishiyar alkhairi ce, wata kwa sharri ce, musamman kishiya irin fareeda wadda babu abinda ta sani sai mugunta, duk mutumin da zai rabaka da jin dadin rayuwar ka to hakika wannan mutumin ya cika azzalumi makiyi. "Ki daina kuka sumayya Allah Yana tare da ke, kada ki biyewa abokiyar zaman ki kice za ki rama cutarwar da data miki, idan har kika yi hakuri kika maida lamuranki ga Allah in Sha Allah ubangiji zai kasance Yana tare dake" "To Abba in Sha Allah zanyi duk abinda kuka ce , Amma Abba ku sameshi shima Amir din ku gargadeshi akan abinda suke min Abba wlh ina hakuri a gidan nan, na Zama kamar baiwa bani da kata6us daga shi har matar sa wulakanta Ni suke yi, bani daraja a gidan sh" kuka ne ya kubce mata saboda alkawari ta daukarwa kanta akan ba zata koma gidan Amir din ba sai gashi Abba ya umarceta da ta koma. Ankira Amir an sake danka masa amanar Sumayya sannan Abba yace "Amir ga sumayya a karo na biyu,ka rike min ita da kyau kada kasake ka wulakanta min 'ya ,sumayya yarinya ce mai hakuri da nutsuwa ta nuna ba zata koma gidanka ba saboda Abubuwan da suka faru da ita ,to na same ta na mata nasiha akan tayi hakuri takoma gidanka Amma Ni bazan bari a sake wulakanta mun ita ba akaro na biyu ,sannan ka fadawa matar ka indai ba zaman lfy za suyi ba to idan har ta Kara cutar da ita wllh kaji na rantse maka sai nayi shari'a da ita, Kai dama duk Wanda zai Kara cutar da ita saboda itama 'Ya ce kamar kowa yanda ko wani iyaye suke son 'ya'yan su nima haka nake son 'Yata, don haka a kiyaye a zauna lfy , Allah ya hade kanku ya baku zaman lfy ya buda maka abinda zaka ciyar dasu, Allah ya kade fitina ya say zauna lfy. Shikenan ku tashi ku tafi " Da kyar sumayya ta tashi daga gurin Abbanta zuciyar ta tana mata kuna sai dai tana yiwa kanta fatan dacewa . Gida ta shiga ta hada kayanta da na Yara har cin_cin da meatfie umma tasa kanwarta ta mata, aka zuba mata shi acikin botiki babba Abba ya bata 10k yace gashi ta siyawa jikokinsa Alewa. Godiya tayi wa iyayen nata suka tafi, a hanya ya tsaya ya siya musu kaza da Yoghurt suka tafi gidq, suna karya kwanar da zata sadasu da gidan suka ci karo da fareeda ta fito daga dayan layin sai kace mahaukaciya tana tafe tana soshe soshe ga wani dumus da yake tashi a jikin ta, kallon su tayi ta zabura tace "kan uba me nake gani haka ?" Sumayya ce tayi karfin halin ce mata "a'a Amarya kece da wannan yammar a tafe sannun ki khairat ana baya?" Banza tayi da sumayya tace wa Amir "Amma ka cika munafiki maci Amana dama za gayewa kake kana zuwa gurinta ko? Lallai namiji babu tabbas to wllh sai dai ka za6a koni ko Sumayya" Rabuwa yayi da ita suka karasa cikin gidan nasu sumayya dakin Amir ta shiga ta ajiye kayan ta da yake twins acan ta barsu sai gobe Amir zai dauko su. Dakinta ta bude da bismillahi tare da tofa Ayatulkursiyyu aciki ta dauko tsintsiya ta share ta goge ko ina ta fesa Air freshener a dakin nan da nan gida ya sauya shi kanshi da ya tsaya sallahr magariba a waje da ya shigo gidan sai da ya saki ajiyar zuciya, wata nutsuwa ta saukar masa ya karasa dakin nata yace mata "sannu da aiki da kin bari nazo na tayaki" murmushi tayi tace masa "a'a ka huta kawai ai aikin ba mai yawa bane" dakin sa ya shige yaga botikin nan na cin_cin da meatfie ya zauna ya janyo shi ya fara ci, sai da yaci ya koshi ya rufe botikin yasha ruwa ya kwanta. Fareeda ce ta shiga dakin ta rike 'kugu tace masa "ka za6a koni ko Sumayya a gidan nan don ni ba zan zauna da sumayya ba a cikin gidannan" "Amsa kike so in baki ?" Ya tmabaye ta cikin daurewar fuska tare da nuna ta da yatsa, ai tana ganin haka jikin ta yayi sanyi a ranta tace "asirin nan ya karasa karyewa kenan" Fitowa tayi daga dakin ta shiga nata dakin da ya Tara kayan datti sai wani hamami yake yi babu gyara balle shara,ita kanta 'yar ta duk ta maida ta kazama har wani guru aka daura mata a wuyan ta wai maganin baki ne da mayu,don kazanta. Sumayya ce ta shirya cikin wasu kaya masu kyau Tasha gayu ta nufi dakin Amir, sallama tayi ta shiga don daukan kayanta sai ta samu har ya adana mata kayan ta shiga dubawa bata gani ba dagowar da za tayi ta tambaye shi sai ganin fareeda tayi ta shigo dakin ta wani mangaje ta tace mata"ki fice mun daga dakin mijina ke ai kin dade baki da muhalli a gidan nan, ko kin manta Wanda kike zaune Dan shi din baya ta taki?" Sumayya bata San tana da karfin da sai data daga fareeda ta damfara da kasa sannan ta halbe ta da kafa tace mata"sakarya kazama wadda bata ramin kantq sai dai na wani ke baki da hankali, ko kin manta ke kika zo kika taraddani a gidan nan ? To kisa a ranki Zama daram babu inda zani daga gidan nan nida 'ya'ya na dole mu zauna mu wala gidan mu ne ba gidan ki ba shashasha wadda bata San inda kanta yake mata ciwo ba" Mamaki ya Hana Amir motsawa balle ya musu magana a ranshi yace "lallai sumayya ita ma da shirin ta tazo gidan nan wato mai hakuri idan aka kureshi yafi mai fada iya fadan " Bai ta shi yin mamaki ba sai da sumayya tace masa" my heart fito min da kayan nan kazo ka kaimun daki na Ni bazan iya dauka ba" da wata murya ta shagwa6a66u tayi amfani aikwa nan da nan taja ra'ayin sa ya dauki kayan ya kqma hannun ta yace "muje baby" Wani ihu fareeda ta saki tace"ba ku Isa ba wallahi, Ni za'a nunawa karuwanci a gida? to ku da zaman lfy a gidan nan har a bada,ma gani". To fa ina masoyan sumy ne ya kukace shin sumayya ta daure ta koyawa fareeda hankali kokwa??. Ina masoya fareeda ne ta ci gaba da kokari wajen bin malamai ko kuma ta hakura ta maida lamarin ga Allah kamar yadda Aslamiyya matar Alhaji Adnanu tayi ta hakura ta zubar da makaman yakin ta ???? Shin Amir ya rabu da fareeda ya kyaleta taci gaba da haukar ta ko kuma ya dau mataki a kanta ta yadda za tayi ladab su zauna lfy????. Sai naji ku . Adaure ayi share don Allah . [7/13, 3:27 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA NA MMN ANNURR FREE BOOK Page (26). Haka fareeda tana ji tana gani Amir ya rufe dakin na sumayya ya leko ta window yace mata" to Amarya sai da safe" Wani Ashar da tunda sumayya tazo duniya ba ta ta6a jiba shi ta saki taci gaba da surutan ta marasa kan gado har take ikirarin sumy da Amir ba zasu gama da duniya lfy ba. Sumy kuka take yi saboda ikirarin fareeda a zuciyar ta take cewa"wannna wace irin mata ce ke a rayuwa babu abinda kika iya sai kishi, Amma ba ki San yanda za ki sarrafa kanki ba da mijin ki ba?? Anya wannan matar ta yi karatu kwa??? " Sumy mu dai bamu da amsar wannan tambayar taki don zama da irin su fareeda marasa imani da tawakkali gara zama da Bakauyiyar mace wadda dama ba tasan komai ba sai ci da kashi. Washe gari sumy ta shiga kitchen ta hada breakfast hadadde ta gama ta zubawa fareeda nata ta ajiye mata a kofar daki ,itama ta dau nasu ta shiga dashi daki, bayan yayi wanka ne ya shirya suka zauna suna cin Abincin cikin so da kaunar juna, duk wani laifi da ya mata a baya duk ta watsar ta yafe masa . Gara ta zauna ta rungumi mijin ta ta bashi kulawar da ya rasa a baya duk da fareeda ta musu katanga da kasancewa koda yaushe . Amir yana fita bai zame ko ina ba sai gidan umman sumy yaje ya taho da yaran sa,a hanya ya tsaya ya musu siyayya har khairat suka dawo gida,na khairat din ya Mika wa fareeda suma nasu ya Mika wa maman su. Fareeda saboda rashin godiyar Allah ko godiya bata masa ba karshe ma sai cewa tayi " a ke jin tsaoron Allah dai ake yin adalci shine aka ciko musu leda Ni kuma tawa 'yar shine aka tsakuro mata Dan kadan to wllh bamu yafe ba marar adalci kawai" "Kai wannan wace irin mata ce wadda ba'a iya mata ? Ke ba Aikena ki kayi ba,ba da kudin ki aka siyo ba Amma ko ba zaki gode ba bai kamata ace kinyi korafi akan abun ba" "An yi korafin aikin banza kawai mugu marar adalci in Allah ya yarda mota ce za tayi ajalinka" "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, wannan wace irin masifa ce daga wannan sai wannan ke fareeda ba'a iya Miki ne Ni kike yiwa mugun fata saboda na siyo wa yarana kayan kwalam da ma kulashe? To ke me kike so a yi Miki Wanda za'a burgeki?" "Ka saki wannan matar taka kawai shine Ni bana kaunar ta bana kaunar 'ya'yan ta, idan kamin haka ka gama mun komai" "Lallai na tabbata ke dabba ce baki da hankali ,saboda ke sai in saki mata ta uwar yarana wadda ta kasance farin ciki na?" "Fareeda ki sa a ranki nida Amir mutu ka raba Ni bana yaji kuma Auren mu na zobe ne sai dai mutuwa ta raba mu don haka in za ki zauna da sumy ki zauna ,inko ba zaki iya ba to sai dai kiyi hakuri domin Ni nan da kika ganni kabewar kan kabari ce bakin cikin mai taushe, nida Amir mun Zama Daya tamkar hanta da jini muke, kika sani ma ko ina dauke da cikin sa nan da 'yan wasu watannin kiga na zankado 'yar budurwar 'ya ta inyiwa khairat kanwa" "Uban khairat za kiyi wa kanwa ba khairat ba aike da haihuwa sai dai kiga muna yi ba dai ke ba wllh" "Sumy ki rabu da ita kije gurin yaran can Ni zan wuce kada inji labarin kin kulata kunyi min tashin hankali a gidan nan,sai na dawo" "To Allah ya kiyaye hanya ubangiji Allah ya sadaka da halal duk kankantar ta Allah yayi maka tsari da haram duk yawanta da kankantar ta,Allah ya Sanya alkhairi da Albarka a cikin kasuwar ka da neman ka mijina ilove u with all my heart" Daskarewa yayi a gurin yana mata wani kallo na musamman,sosai ya ji dadin Addu'ar ta ta da kalamanta na karshe. "Hakika samun mace ta gari sumy akwai wahala,ga mata nan burjik a titi Amma na garin ne sunyi karanci ba kowa yake da kyawun zuciya ba sumy na na gode da kasancewar ki mata a gareni,hakika naso yin wauta a baya sai dai da yake Allah Yana Sona shi yasa ya kaddara zaman mu aguri daya na gode wa Allah" "Hmmm bbn twins nima ina godiya da kasancewar ka miji a gareni maji6incin al'amura na sannan uba ga 'ya'ya na,hakika samun irinka wahala gareshi, ina jinjina maka abisa dukkan dawainiyar da kake damu,muna godiya sahibi na, Ni sumayya ta Amir ce babu wata barazana da wani zai kawo ta gareni da za'a iya Rana Ni da Kai in Sha Allah duk tsanani muna tare" Amir bai San sanda ya isa ga sumy ba ya rungume ta yana mai jin kamar ya maidata cikin sa saboda so da kaunar dake majaujawa dashi akanta. Har da hawayen shi ya mata kiss a goshi ya ce mata "bye my wife" Da hannun ta masa alama da kalmar love you too har saida ta yiwa hannun ta kiss ta watsa masa hannun biyu. Fita yayi Yana maijin ransa fayau don 6acin ran fareeda ya ma manta dashi sai murmushi yake yi har ya isa shago, kalamanta ne suke amsar kuwwa a kunnen shi da gangar jikin sa. Khairat ce ta fara rigima, uwar tana daukan ta taji wani wari ya bigi hancin ta, ai da ta takar kare sai jin Karan mari kake tassss, ta dauke yarinyar da wani mari wanda Karan marin ne ya sa sumy fitowa daga nata dakin cikin sauri ta shiga dakin fareeda ta tsaya take ganin ikon Allah, "shegiyar yarinya dangin jaraba daga kwantar dake a kan gado na sai kimin kashi ji yanda kika 6ata mun zanin gado Dan ubanki" Sumy ce tayi karfin halin cewa "haba fareeda yanzu saboda khairat tayi kashi akan gado shine kika mata wannan Marin? Yanzu sabida Allah me yarinyar nan tayi Miki nawa take yarinyar da sai yanzu ta cika shekara daya a duniya Amma kika mata wannan Marin da ko ke akayiwa sai kinji ajikin ki, me yasa??" Ran sumy ya 6aci matuka ko da yake khairat ba sumy ce tayi nakudar taba Amma darajar Amir da ta zaman guri Daya shi yasa taji zafin Marin da fareeda ta yiwa yarinyar, hakika wasu iyayen suna ganganci wai Dan kun Sami sa6ani da uban Yara sai kayi ta hantarar Yara da zagi da duka,wannan ba dabi'ar kirki bace gaskiya su yaran babu ruwan su basu San me ya hada ka da ubansu ba Amma uwa wai saita huce akan Yara. Idan aka Sami uba mai matukar San Yara wlh to daga ranar Aure zai ita mutuwa saboda Ni banga dalilin da zai sa in samu sa6ani da miji ba kuma in sauke akan Yara , a'a ai daga ranar zan janyo yaran ajiki na ta yadda zasu dauke mun kewa zasu mantar da wani Abu daga cikin 6acin ran da na shiga, shima idan yaga haka zaice to ita wannan babu abinda yake 6ata ranta wato hade min kai za suyi ita da yara to gwara na sauko don fishin mutum daya ciwo ne dashi. "Ko zaki rama mata ne ? Naga 'yata ce Ni nayi nakudar ta Dan haka kada ki Kara shiga sha'anin na tsakani na da 'yata" "Kiyi hakuri gani nayi yarinyar bata San komai ba fareeda kada zafin kishi yasa ki illata rayuwar ki data yarinyar ki" Banza tayi da sumy ita ma sai ta fito daga dakin na fareeda ta koma nata dakin ,gurin yaran ta taje take musu wasa sai jin Karan dariyar su fareeda take yi,ranta kwa in yayi dubu ya 6aci haka ta fito da yarinyar ta zuba ruwa mai sanyi ta shiga wanke mata jikin nata, khairat din sai kuka take saboda Marin ba na wasa bane ga shi ruwan kansa da ke mata tsarkin mai sanyi ne ga yanayin garin akwai sanyi don har hazo-hazo garin yayi. Make mata baki tayi tace "don ubanki kimin shiru ubanwa yace kiyi kashin da wannan sanyin?" Kuji fa wai yarinya ake yiwa wannan tambayar,fareeda tunda ta haihu bata San yadda zata tsara gidan ta ba,bata sabar wa da yarinyar ta zama akan fo ba sai dai idan tayi fitsari a Daki ko akan gado sai dai a yayyafa ruwa a haka har katifa ta bushe, dakin ta duk zarni yarinyar ta babu gyara ko da yaushe cikin kazanta suke ga wani guru da aka daurawa yarinyar a wuya wai kafin mayu ne, Kai wani abun wlh jahilci baiyi ba. Nifa duk tsakani na da yaro indai a wuyan sa akwai layu ko guru wlh bana daukan sa,saboda Ni kam tsantsani nake yi . Kananun halittun nan sun Kara dawowa ta rasa yadda za tayi sai susa take yi. Mamar ta ta bata shawara akan take shiga ruwan dumi, haka tayi kwa da yamma ta dafa ruwan dumi ta zuba gishiri a ciki ta shiga, innalillahi kawai take Kira wasu tsutsotsi ne suka dinga fitowa daga jikin ta abun babu dadin gani haka ta fito daga cikin robar ta yi ploshing din su ta Kara maka ruwa don kar su fito. Kwana tayi tana mutsu-mutsu tu ga khairat sai kuka take saboda kwanan ta biyu babu wanka, Abin ya yiwa su fareeda yawa. Kuka take yi cikin dare tsutsa ta hanata sakat tun tana shiga ruwan dumin har tazo ta gaji da shiga ta kwanta. Sumayya bata San me ke faruwa ba sai da ta sanar da Amir cewa "Anya kwa fareeda lfy? take naga sai shiga bandaki take yi ya kamata ka tambaye ta idan bb lfy sai ka kaita asibiti" Tashi yayi ya shiga dakin fareedan ya tambaye ta " Amarya me yake damunki ne na ga kina kuka?" "Wlh Amir tsutsa ce take fito min a jikina kwanaki munje Asibiti nida mama aka wanko ta to har ta daina fitowa Amma yanzu ta dawo" sai kuma ta kifa Kai akan cinyar ta take ta rera kuka abin tausayi. Amir yaji tausayin ta ganin kukan da take yi sai kuma ya tuna da ita tajawa kanta ta'iyu ko Alhaki ne ma yake bibiyar ta. "To ki kwanta gobe za muje Asibitin sai akara wankota" Iya abinda yace mata kenan, shima kawai ya fada ne Amma idan ya biya ta halayenta ko kallonta ba zai yi ba Sumayya ya sanarwa da abinda yake damun nata ,ta tausaya mata matuka saboda ciwon macce na macce ne, Gari na wayewa ya dauke ta abayan mashin duk da tashin warin da take yi haka yayi shahada yayi ta maza ya hakura suka tafi don khairat ma a gurin sumy aka bar ta. Ruwa ta dafa ta mata wanka sosai ta shirya ta tasanya mata wata rigar sanyi ta twins da safa ta mata kalaba guda hudu akan nata da yake yarinya ce mai gashi akanta. Ma Sha Allah yarinyar tayi kyau matsalar kawai gurun layar da yake wuyan ta, haka ta dama musu checkers suka Sha sai bacci,ita kuma ta fito tsakar gidan ta hada musu breakfast tayi share-sharen ta bayan ta gama ne ta shiga wanka . Bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin doguwar riga wadda aka mata dinkin dai dai da yadda zamani yake tafiya,tayi kyau ma Sha Allah Abincin ta taci ta kwanta tare da daukan wayar ta ta kunna data wani post ne akayi a cikin wani group mai suna DUBARUN ZAMA DA KISHIYA . sosai abinda aka turo ya Sanya ta cikin rudani, wata mace ce aka yi mata kishiya sai mijin ya fifita amaryar akan uwar gidan kusan shekara 15 suna Zama a haka,ita uwar gida yaranta shida duk maza sai Amarya 'ya'yan ta hudu mace biyu namiji biyu, ahaka uwar gidan ta zauna take kunsar bakin ciki da 6acin Rai bata ta6a fada wa kowa ba ko tayi marmarin ya sake ta mijin bata ta6a yi ba,a haka har yaransu suka taso ita nata 'ya'yan aka kaisu government school ita kuma Amarya aka Kai nata yaran private school haka har suka kammala karatun su. Mahaifin su yazo ya talauce saboda baya sauke hakki da nauyin da ya rataya a wuyan sa, da Allah ya tashi Sakawa uwar gida sai Allah yasa dukkan yaranta suka samu aikin yi ita kuma 'ya'yan ta mazan dukan su shaye_shaye, matan kuma sata da bin maza. Abin babu dadin ji, haka yaran nan suka gyarawa iyayen su gidan har 6angaren matar baban nasu shima suka bude masa babban shago a kofar gida aka zuba masa kayan provition.mamar su ita take sanya wa suke yiwa amarya komai na rayuwa ga shi yaran da aka daukaka sun lalace ita nata da aka wulakanta ga shi nan sun zama abun kwatance. Jikin sumy duk yayi sanyi sai taji gara mutum yayi hakuri ma ko ya samu ribar Abun a gaba. Zuwan su Amir Asibitin suka tafi inda aka yiwa fareeda wankin gaban ta kwanaki katin suka Mika aka ce ta shiga daga ciki, Amir dinne ya tambaye su zai iya shiga tunda ita kadai ce a dakin babu masu haihuwar da aka kawo,ya shiga suka ce masa, wadda za tayi mata wankin ce ta shiga dakin suka gaisa take ce masa ya kamata ya Hana matar sa cushe cushe a jikin ta ga shinan ya janyo mata larura . Bude wajen akayi sai tashin tsami yake haka aka Sanya mata Abubuwan da zai sa tsutsar su kado,aikwa nan da nan suka yiyo waje ai Amir tsorata yayi ganin irin bala'in da suka fito daga kasan fareeda Amma a haka take Rashin mutunci . Sai da suka wanko mata tass suka rubuta mata magunguna suka taho gida. Akan hanya suka siyi magani sannan suka karasa gidan ,Sallama suka yi suka ji gidan shiru da yake da mukulli yayi amfani saboda sumy za tayi bacci ta rufe gidan daga ciki, dakin ta ta wuce yace ta fito tayi wanka har za tayi musu sai ta ga babu fuskar da za ta kawo masa raini Na gaji wlh kuyi hakuri da wannan A daure ayi share [7/14, 6:47 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA Na Amina Mamu Gumel (Mmn Annuur) Page (27). Madam Zainab ta tursasa Alhaji Adnanu akan dole sai sunje ganin gida tunda shiru har yanzu bata haihu ba to ya kamata suje su ganin gida tana son ganin iyayen ta da 'yan uwanta. Haka ya tattara matan da yaran nashi yace musu za su je ganin gida shida madam ta gaji da zaman nan din gashi ba haihuwa tayi ba, suwaiba ce tace "Allah ya kaiku lfy ya dawo da ku lfy" Aslamiyya tace "Ai gara ku tafin ma ko ma samu fili a gidan tunda mu dai da kuna nan da bakwa nan duk daya,ba ka da lokacinmu daga mu har 'ya'yan ka to kaga ai gara kuje can ku karasa cin amarcin da baku karasa anan ba,mace har shekara guda tana juya ka kamar wani karamin yaro" "Aslamiyya Ni kike fadawa wannan maganganun? Saboda na auro kabila wadda ba ta da dangi a gari? To idan ban bata kulawa ba me kike so na mata ? Kada kimanta fa tun daga uwa duniya na auro ta na kawo muku ita, kuka hade kanku keda suwaiba ita kuka ware ta,to idan ban hade Kai da ita ba dawa kike son ta zauna taji dadi a cikin gidan?" "Alhaji duk fa wannan abun bai Kai ayi tashin hankali akan sa ba, maganar hade Kai kuma laifin ka ne Kaine ka ware ta daga cikin mu ka fifita ta,to so kake muke bibiyar ta tana wulakanta mu? Don muna son zaman lfy ba zai Zama muna kallo a wulakanta mu ba. Yanzu Kai kana Adalci a tsakanin mu? Ina cewa abubuwa kake siyowa sai dai ku kule a Daki ku cinye ?sai dai muga an jefo leda tsakar gida,muna muku fatan alheri kuje lfy ku dawo lfy,idan acan ma za ku zauna to umma ta gaida Ashsha 'ya'yan ka idan suka tasa sake zuwa ganin ka,tunda Kai din dolen su ne" Alhaji ne yaje doguwar ajiyar zuciya yace"suwaiba nifa iya daidai gwargwado ina adalci a tsakanin ku sannan baku fahimce Ni ba Amma idan har kun kullaceni ku yafe Mana nida madam" Banza suka yi dashi kowa ya tafi dakin sa. Suwaiba tana shiga daki ta fara magana a fili cewa"wai wannan rayuwar haka take dama? Kana girma matsaloli suna Kara karuwa,matsalar yau daban ta gobe daban,nasha wahalar Aslamiyya yanzu kuma muna kan shan ta inyamura ,kai wllh idan naga abin ba zai canja ba gida zan siya ginanne in koma da Yara na don ba za'a maimaita mun abinda aka mun a baya ba" A yau ne su Abduljabbar da Abdurra'uf suka kammala karatun su na secondary,har walima aka shirya musu Wanda uban bai San da zancen kammala karatunsu na secondary din ba, sai gani yayi ana shigo da lemuka da biscuits katan katan saboda suwaiba tace walima za ta hada musu su day abokan su. Karfe hudu na yamma gida ya fara cika da abokan su maza kowa ka gani yasha kwalliya, suka Dan yi photuna sannan aka zuba musu abinci Wanda Aslamiyya ta dauki nauyin dafawa fried rice ce tayi musu sai cowlslow Wanda yasha kwai a cikin sa,anci ansha anyi hani'an, kowa aka bashi lemo da biscuits a leda thank you. Karfe biyar da rabi aka kammala walima Aslamiyya da suwaiba Anko suka yi na dogayen riguna na Atamfa da takalman su iri daya sunyi kyau madam ce ta fito jikin ta sanye da dogon wando na jeans blue da farar t-shirt mai zanen love a jiki, tafiya take duk a takure saboda matsetan da kayan yayi, ta je dakin Alhaji Adnanu tace masa"karfe bakwai na safe za su tafi don haka ya fito ya hada mata kayan ta ita ta kasa hadawa". Aslamiyya tana dakin tana dauko taliyar da zata dafawa Yara saboda Babu Abincin dare madam ta hada da na yaran ta cinye tass, bakin ciki ya Hana Aslamiyya motsawa kawai gani tayi Alhaji Adnanu ya bi bayan ta suna tafe suna dariya. Aslamiyya kuka ta saki ta dade tana matsar hawaye da kyar ta hakura ta fito Abincin da bata dafa ba kenan ta wuce dakin ta ta kwanta ta shiga tunanin rayuwar ta ta baya a gidan Alhaji Adnanu . Ada Aslamiyya sai abinda ta ce ake yi agidan dole abi abinda tace ko kuma Rai ya 6aci,ta juya Alhaji tasa ya wulakanta suwaiba da yaran ta ankore su daga gidan saboda ita, daga baya Kuma Allah ya juya lamarin ta shiryu to gashi nan dai tana kar6ar nata gashin ,duk da suwaiba ta yafe mata to gashi nan ita ma ana mata abinda tayi. Ai dama duk abinda ka shuka shi za ka girba, kuma duk wanda ya daka rawar wani, wata Rana sai ya rasa turmin daka nasa. Ba zai yiyu ba ka cutar da wani kuma kace kaci biliss ba a'a ko yaya ka cutar sai Allah ya Sakawa Wanda ka cutar din. Allah yasa mu dace Amin. Washe gari karfe shida na safe har sun shirya sun fito tsakar gida hannun Alhaji Adnanu dauke da akwatin kayan su ita inyamura hannun ta dauke da jakar ta ta rataye, sallama suka yi ya basu 20k yace sati Daya za suyi, Addu'a da fatan alheri suka musu sannan suka tafi. Gaban suwaiba ne yake faduwa babu dalili tun safe har yanzu da ake sallar magariba, wayar ta ta dauko ta Kira layin Alhaji Adnanu taji a rufe sai ta sanar wa da Aslamiyya ,itama haka tace mata ta Kira a rufe layin nashi. Addu'a sukayi da fatan Allah yasa lfy. Da safe wajejen karfe goma na safe sai ganin madam inyamura suka yi ta shigo gidan ko Sallama bata musu ba ta shiga dakin Alhajin sai suka ga ta fito hannun ta dauke da takardu,tamabyar ta suka yi sukace" ina Alhajin?" "Yana Tasha ya aiko nine saboda munyi mantuwa akwai takardun sa zai bawa abokin kasuwancin sa to ya manta shine ya aiko Ni in dauko masa" Sauri tayi ta fice daga gidan ta Kara waya a kunnen ta tace"yawwa ciyamaka a tafi dashi Benin kawai saboda so nake nimain bar garin" Alhaji Adananu suna kan hanya a mota sai ganib basawa yayi sun tsaida motar su suka firfito dasu,madam da Alhaji Adnanu aka ware guri guda sai suka ce mai motar ya tafi idan ba haka ba zai rasa ransa shida mutanen cikin motar, ai da sauri driver ya ja mota ya tafi aka bar inya mura da Alhaji Adnanu, mutanen ne suka tirsasa shi akan ya saki madam kana suka Dora masa bindiga a kansa dayan kuma ya Dora masa a saitin kirjin sa, haka yace musu"ba zan iya sakin taba kunawa Allah ku rabu Damu kada ku cutar da mu" Wata dariya suka saki sannan babban yace masa"wannan ba kalar matar ka bace idan baka sani ba ka sani daga yau Zainab ta was ce ni kadai don haka ka sake ta tun kafin in fasa maka Kai da bullet". Wani wahalallen fitsari ya saka yace "kuyi hakuri don Allah karku min haka wlh Ina son matata " Inyamura taga Alhaji Yana beman 6ata musu lokaci tace da shi "Alhaji ka sawwake min in kama gaba na " Mamaki ne ya kama shi ganin wai madam dinsa da kanta tace ya sake ta.tashi tsaye tayi daga knildown din da tayi tace "kana mamaki ne to wannan duk shiri na ne don haka ka sake Ni za mu wuce nida su, nice nan na kirawo su saboda Ni na gaji da zama da Kai Ni ba 'ya'ya ba ba wani na ajiye a gidan kaba da zan zauna haka kurum abin da nake yiwa na riga da na same shi to kaga gara ka sawwake min kada in tafi da igiyar ka" "Haba madam ki mare Ni ko mafarki nake in tashi don Allah" Wani mari da ta kifa masa da katon hannun sa ai sai da yaga taurari sannan ya yarda cewa gaske ne ba wai mafarki take ba . "Adnanu ka sake Ni saboda daga nan ma wani garin zansa a kaika kafin kaje gida na koma na kwashi rabona a gidan naka in yaso saika nemi yafiyar matanka daka cuta kake bani kulawa su kuma kake azabtar dasu " Yana ji yana gani ya furta mata cewa.ya sake ta saki uku.murna tayi tace" a kaishi Benin kafin ya koma gida ta je ta har hada kadarorin sa ta fece". Benin suka kaishi a mota suka yaddar dashi a gefen titi da yake shigar dare suka yi a hanyar su ta dawowa ne suka yi hadari motar ta kama da wuta. Alhaji gari na wa yewa ya tafi gurin wani famfo yayi alwala yayi sallah ya dade Yana neman yafiyar ubangiji akan cutar da matan sa da 'ya'yan sa da yayi,ga sakamako ya gani tun ba'aje ko'ina ba. Kuka yake yi Yana tuna halaccin matar sa da ya yi ta cuta gashi Allah sai rama mata yake yi ta kowacce hanya . Tashi yayi ya karasa gurin wani bawan Allah daga ganin sa za kasan musulmi ne,Sallama ya mishi suka gaisa yace masa"bawan Allah don Allah tamabaya nake yi?" Mutuman yace "Allah yasa na na sani " "Nan wani gari ne?" "Benin ne, Amma lfy kake tambayar garin da kake ciki ba Kai kazo garin ba ko kawo ka akayi?" Kuka ya saki yace masa" wlh kawo Ni aka yi ta karfi" anan dai ya kwashe labarin yadda suka yi a hanya ya fada masa, mutumin mai suna musa ya tausaya masa sosai da Allah ya taimake shi shima Dan kano ne ana ya kwantar masa da hankali yace masa wani satin zaije ganin gida za su tafi tare amma shi sana'ar sai da manja yake yi idan zai iya to sai ya saro masa ko jarka biyu ne ya gwada a cikin wani kauye dake cikin garin na benin. Godiya yayi masa yace "indai zan Sami na mota wlh zanyi koma wace irin Sana'a ce " Bayan fareeda ta tashi daga bacci ta fito waje ta shiga bandakin tsakar gida bayan ta tsugunna ne abin mamaki baya karewa afili ta furta "wai Ni wannan wace irin masifa ce an je Asibitin ma mai makon tsutsar nan ta ragu sai dai karuwa da take yi". Fitowa tayi tana tafiyar 'yan ta ta ta, dakin sumy ta nufa don kar6o khairat tana shiga ta ga yaran dukan su akan gado sai bacci suke yayin da idanun ta suka yi tozali da 'yarta ta cikin shiga ta kamala tayi kyau da take kyakkyawa ce kalar gayu sai ta saje da 'ya'yan sumy Kai kace ita tayi nakudar ta. Fitowa tayi daga dakin saboda basu tashi ba, kunu ta dama ta Sha tare da maganin ta kwanciya tayi sai bacci ba tare da tayi sallah ba, wai za ta hada da la'asar . Jama'a kinyin sallah akan lokaci babban kuskure ne yakan janyo fishin ubangiji ,ina mamakin masu hali irin na fareeda wai sallah sai a shelake tukun za'a yi, mutum fa da ya rasa sallahr la'asar a kan lokacin ta gara ya rasa dukiyar sa dukkan ta ,wani Qaulin kuma akace da ka rasa sallahr la'asar a lokacin ta gara ka rasa danginka dukkan su(iyaye' 'ya'ya, mata ,da sauran makusan ta) ALLAH yasa mu dace Amin. Alhaji Adnanu yau za su taho gida. Da wuri ya shirya ya zauna yana jiran musa mai manja, ba'a dau lokaci ba suka tafi Tasha suka Sami mota ana jiran mutum uku suka shiga ba'adau lokaci ba cikon na ukun ya shiga shima, tafiya ce suke kamar ta Saida rai, tun suna fira a mota har ya zamana kowa ya gaji masu bacci nayi wadanda suke kalle-kalle nayi shi dai Alhaji Adnanu shiru yayi Yana tunanin rayuwa yadda take garashi kamar wani kwallo. Sai wajen 12 na dare suka sauka a garin kano yayin da musa ya bashi address din shi ko Allah zaisa su hadu kafin ya koma, Alhaji Adnanu ya hau Dan sahu ya tafi gidan shi . Yana sauka a kofar gidan ya tarar da gidan a rufe ya kwankwasa Amma babu Wanda yazo ya bude mishi ga yunwa da yake ji ga gajiya, haka ya zauna kofar gidan yana jiran ayi asuba idan yaran suka fito za su masallaci sai ya shiga gidan. Suwaiba taji buga gida tunanin ta irin 6arayin nan ne nakan layi shi yasa taki taje ta bude. Aslamiyya sarkin tsoro tana jin bugun gidan tayi lamo saboda jiya a gidan biki taji ana bada labarin 'yan fashi masu bubbuga gidan mutane. Aikwa cikin ta ya duri ruwa har saida ta kusan yin gudawa a kwance da Allah ya taimake ta a cikin toilet dinta na daki akwai gurin yin ba haya, anan taje ta ragewa cikin ta farashi. Wasu 'yan sanda ne da suka fito patrol su hudu saboda kama 6ata gari suka hangi Alhaji Adnanu da wata riga 'yar shara fara sai wando Dan gwanjo baki, basu saurari abinda yake fada musu ba suka tasa keyar sa a cikin mota bayan sun bubbuge shi da kulki, saboda bakin cikin abinda yake bibiyar sa har kuka yayi, yayin da jami'an tsaro suka ce masa "kuka Yana gaba dattijo, irin kune masu tura Yara su haura gidan mutane lokacin da sawu ya dauke ko?? To jikin ka zai Gaya maka, za kayi bayani" Iniji wani figaggen Dan sanda wa da yake Dan yanayi da kofur Audu na dadin kowa. "Wllh yalla6ai daga Benin nake ganin da kuka min a kofar gidana nake na buga gidan matan sunki budewa saboda basu San da zuwa na ba yau din" "Karya kake dattijo" inji sajen bala mai tanayi da kofur Audu yana wani zazzare ido. Cikin kanta aka tura Alhaji Adnanu tare da datse wa da mukulli. Ba'a waiwayi Alhaji Adnanu ba sai da yamma D.p.o ne ya shigo cikin station din yake tambayar su "babu matsala dai ko?" "Sai oga ga wani nan jiya da misalin karfe 12 na dare muna patrol muka ganshi a kofar wani gida a zaune,to bamu sani ba ko irin masu tura Yara sata ne, shi ya zauna yana musu gadi sai an farauto a kawo masa" "A bude shi azo min da shi" d p.o ya bada umarni. Haka aka tisa keyar sa har gurin d.p.o, dagowar da d.p.o yayi don ganin Wanda aka tsare sai ya yi tozali da Abokin sa Alhaji Adnanu, tare sukayi primary har secondary school." Ikon Allah Adnan" Shima mamaki yayi da ganin Abokin nasa "mika'ilu garba" Shima ya ambata, yayin da ya tsare mai dutyn da tambaya akan wani dalili za su tsare mutum tun jiya da daddare har ya wayi gari ya wuni a gurinsu ba tare da sun yi masa bayani ba tun da wuri,haka ya karaci fadan sa sannan ya waiwayo gurin Abokin nasa yake tambayar a garin yaya yakai har 12 na dare a titi,anan yake bashi labarin abin da ya faru dashi tun daga tafiyar su lagos har ya zuwa kaishin da akayi Benin da dawowar su yau. Hakuri ya bashi yayin da yace masa "kayi hakuri Abokina tabbas ka kusa tafka babban kuskure a rayuwar ka,a yanzu a wqnnan zamanin samun mace mai hakuri da biyayya da tsoron Allah irin matar ka wllh sai an dade ba'a samu ba. Mata ga su nan birjik Amma na garin ne sunyi karanci ,yanzu ya wanci a wannan zamanin ya wanci 'yan mata duk sun koma zawarawa suna gidan su ba tare da an musu auren ba, idon su a bude suke kar suke ganin mu, don haka ake hakuri da iyali, kuma kaje ka roki gafarar Allah sannan ka roki yafiya a gurin matan ka da yaran ka" Anan ya Kira Daya daga cikin yaran sa yakai Alhaji Adnanu gida, har da bashi 10k ya siyawa Yara zigege. Sallama yayi cikin gidan nasa suka amsa kowa yana kallon bayan sa aga ta inda inyamura zata 6ullo, sai kuma suka ga shiru dakin sa ya wuce ya zauna a kan kujera, yayin da matan da yaran suka nufi dakin nasa suna masa sannu da zuwa. Amsawa yayi yace "don Allah a cikin ku wata ta hada min ruwan wanka mai zafi sosai sabida Ina son in gasa jikina". Aslamiyya ce ta tashi ta hada masa, bayan yayi wanka ne aka kawo masa Abinci dakyar yake ci sai kace ya samu Panadol, a haka dai dakyar ya ci rabin abincin, yayin da suwaiba tace masa"Alhaji Ina madam din taka ko acan ka barota sai ta huta ta dawo?" Innalillahi wa'innna ilaihi raji'un sumy take ambata lokacin da taji wani ihu daga dakin fareeda, da sauri ta nufi dakin don ganin me ke faruwa , fareeda ce ta ke ihun nan duk ta ya mutsa dakin da tarkace ta cire dankwalin kanta gashi tana neman cire zanin jikin ta sai wata dariya take da ihu, kana ganin ta kaga sabon kamu a hauka. Da gudu sumy ta je ta rufe dakinta ta dauki waya ta Kira Amir ta sanar dashi abinda yake faruwa, ba a dade ba sai gashi yana kallon ta ya San hauka ce ta fara yi rufe ta yayi a dakin ya je ya dauko maman ta, tana zuwa ta fara kuka tace "ko dai asiri aka yiwa fareeda saboda anga tana zaune lfy da mijin ta?" Amir ne yace "babu wani asiri kije ki ganta tana daki" Tana shiga dakin ita kuma ta ta ho da gudu ta fice daga dakin za ta doshi kofar gida Amir yayi sauri yaje ya rufo gidan, zanin ta taja da karfin ta a take zanin ya yage daga ita sai Dan kamfan ta (wando) Wanda tsabar dauda tasa ya Zama kamar brown kamar ash kala, Kai kazanta ba ta yi ba wllh.ihu take tana tsigar gashin kanta tana jefarwa, yayar ta aka kirawo wadda suke uba Daya ita ce tazo aka samu aka maida ta dakin ta aka rufe, zuwa gobe idan Allah ya amince zasu kirawo mai rukiyya yayi mata ko shedanu ne. Maman ta a gidan ta kwana a wani daki na daban, sumy taga ikon Allah wato Dan Adam ba komai bane ji dai fareeda a dazu da safe ma da hankalin ta Amma yanzu wai ita ce a wannan yanayin ,gaskiya Allah abin tsoro ne. Alhaji Adnanu sai da ya samu 'yar karamar nutsuwa ya basu labarin abinda ya faru, sun tausaya masa suka jajanta masa Akan Allah yasa haka shi yafi alheri. Anan suke sanar dashi ai ta dawo ta dauki sakon da kace tazo ta dauka maka wai kayi mantuwa baka dauka ba. A razane yace "mantuwa kuma to me ta dauka ?? Me yasa ba ku kira Ni a waya kun sanar dani ba ?" Salati yake yayin da ya shiga bedroom din sa ya buda lokar da ya ajiye wasu takardu na filaye guda uku da ya siya kusan 5millions babu takardu babu labarin su anyi nema an rasa, "tabbas takardun filayen nan inyamura ta zo ta dauka" Salati matan suke yaran ma salatin suke saboda kaduwa Alhaji Adnanu kwanciya yayi Yana kuka Yana rokar matan da yaran gafara akan su yafe masa saboda hakkin sune yake bibiyar shi. Washe gari da safe ana kokarin aje a kirawo malam mai rukiyya aka duba dakin da aka rufe fareeda aka tarar da dakin a 6alle ta fice ma daga gidan gaba daya anyi nema an rasa ta . Wuni guda babu labarin fareeda har sunje ofishin hizba da Police station an bada cigiyar ta ko Allah zaisa a dace, maman ta sai kuka take. Hakuri sumy take bata akan za'a samu fareeda kuma har ta samu sauki in Allah ya yarda . khairat kwa ko akanta da yake tana cin abinci sosai kuma ana dama musu checkers da sauran ciye ciye na Yara Alhamdulillahi bata rigima domin tana samun kulawa. Allah ka biya Mana bukatun mu na ALKHAIRI duniya da lahira. [7/17, 7:12 AM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA Na Amina Mamu Gumel (Mmn Annuur) Page (28). Alhaji Adnanu kuka yake kamar an saci tsohuwar shi ya rasa yadda zaiyi ya ji dadi, suwaiba ce ke karfafa masa gwiwa a mtsayin sa na namiji bai kamata yake kuka a gaban su ba, ya kamata ya maida lamarin sa ga Allah Wanda ya bashi, indai ya kyautata wa Allah zato akan dukiyar sa hakika Allah maji rokon bayin sa ne dalilin kyakkyawann zaton da yayi sai Allah ya dube shi duba irin na tausaya wa ya maido masa dukiyar da madam ta dauka ko kuma Allah ya bashi dukiyar da tafi wadda madam din ta dauka masa. Da wannan aka samu ya Dan samu nutsuwa. Aslamiyya ce tace "wlh wannan inyamurar ba Alkhairi bace a gidan nan daga zuwa ta tarwatsa Mana gida babu zaman lfy tsakanin mu da mijin mu yaran mu ma ba'a wani kula dasu shegiyar mace ashe da abin da ta shirya shi yasa ta dawo gidan nan ita kadai har da cewa wai mai gidan yana Tasha shi ya aikota daukan sako" "Ban da abunku kuyi hakuri Mana yanzu fa kuke lallashina to kuma ku lallashi zuciyoyin ku domin wannan sakayya ce nagani akan kaina, na tauye ku na juya muku baya Amma karshe gashi da abun da ta saka mun. Ni ma tsautsayi ne yasa na auro ta, in Banda tsautsayi ka auri mace ace kuma ita za ta bada goyon bayan a kama ka har akaika wani gari, garin da tunda uwata ta haife Ni ban ta6a zuwa ba sai ta dalilin ta, da kyar na samu nake sana'ar Saida manja tukunna na samu kudin motar dawowa garin nan" Yana bada labari Yana hawaye da yadda ta gaura masa mari da wannan kuttu6in hannun nata shine yake Kara 6ata masa Rai. Madam zeee inyamura bata zame ko'ina ba sai Delta inda taje ta baje kolin San cin duniyar ta da tsinke. Ta Kira ciyamaka akan sun Kai Alhaji Adnanu Benin din sai taji wayar su akashe kusan sati biyu kenan har ta hakura ta karya layin nata ma saboda gudun matsala. Gida ta kama na kuzo mu gani Wanda unguwar da take din duk karuwai ne masu zaman kansu, wata kawar ta da tayi a makotan ta mai suna pretty itace tasu tazo daya, pretty irin mutanan nan ne masu shegen wayo da bin diddigin mutum, haka ta makalewa madam har sai da ta bayyana mata sirrin ta, itama ta sanar da ita musulma ce sunan ta Daharatu Amma anfi kiranta da pretty kasancewar ta kyakkyawa kuma ga rawar kai. Ahaka suka dinke da zee inyamura har suka fara fita Shan ice cream da kudin inyamura, mutunci suke sosai har takai pretty ta dawo gidan madam inyamura sosai suke hulda sai dai ita inyamura bata kule kulen maza a cewar ta ta girmi hakan sai dai ta Sami miji tayi aure inko ta samu irin Adnanu shi kenan sai ta Kara wankar gara ta fece. Yayin da pretty kuma ta kware wajen bariki saboda har hotel take zuwa adauke ta haya ta kwana acan bata tsoron Allah kasancewar ta musulma bata kishin kanta, irin wannan rayuwar Allah ya Mana tsari da ita ya shirya Mana gaban mu da bayan mu Amin. Jinya Alhaji Adnanu yake sosai Wanda har takai shi ga kwanciya a asibiti ga Babu kudi duk ya tatike ya sai filaye, hatta kudin motar da za suyi a gurin inyamura ya barsu saboda yarda haka tace ya bata ta ajiye soyayya ta rufe masa ido da kwakwalwa a fagen kaunar da yake nuna wa inyamura ya samu damsil basirati. Fareeda bata zame ko ina ba sai wani kango anan ta yada zango ta shiga bola take ta tsince-tsince , wani gayan 🍞 baread ta gani a bolar yunwa ta sa ta dauka tana ci tana ta dariya ta samu nama mai dadi tana ci tana susar kasanta inda tsutsar nan take mata wata irin tafiya marar dadi, Yara ne suka za gayeta suna zolayar ta "kazama mai cin kayan bola mahaukaciya ta ci bredin bola" suna mata waka tana rawa abin gwanin tausayi fareeda 'yar kwalisa fareeda matar Amir itace a wannan yanayin. Allah kasa muyi rayuwra mu mu gama ba tare da mun zalinci wani ko wata ba Amin. Nema dai su Amir sun yi shi Amma shiru kake ji babu labarin ta har hoton ta aka bayar a police station sannan aka Dora hoton a kafafen yada zumunta ko za'a dace. Wani bawan Allah ne ya ganta sai kuma yayi tunanin dazu da zai wuce yaga Yara suna zolayar wata baiwar Allah mai cin bredi a bola har ya koresu shine ya gane ta a jikin hoton ai kwa da sauri ya Kira number da aka sanya akasan sanarwar ya Kira ring Daya aka dauka "Assalamu Alaikum" ya fada "Wa'alaikumussalam, dawa nake waya ?" "Wani bawan Allah ne mai suna isah naga ana cigiyar wata mata mai suna fareeda,to dazu zan shige na dawo daga masallaci naga Yara suna zolayar wata mata shine yanzu naga sanarwa ana cigiyar ta to nidai na ganta a unguwar mu yanzu haka tana kan juji tana ta dikar rawa" Innalillahi suke Kira 'yan gidan saboda Amir a hands free yasa wayar, kwatan cen inda yake ya musu akwa suka tafi a Adaidaita sahu, sunje sun Sami mutumin suka tafi inda fareeda take Amma me ?? Suna zuwa suka tarar bata nan sai Dan kwalinta a gurin. Salati suka shiga yi saboda al'amarin Yana da sarkakiya. Godiya suka masa suka yi gaba suna tambaya,sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka tarar da Yara a wani guri sun kewaye wata mace akwance, yaran suka tambaya me yake faruwa shine suka musu bayani, "wata ce aka kade da mashin kuma mai mashin din ya gudu" Amir ne yaje da sauri Dan ganin ko wace ce,tozali yayi da fareeda kwance kafar ta tana mai fidda jini gata dai kamar ta suma. Daukan ta yayi suka shiga adai daita sahun yace masa"muje Asibiti" Asibiti suka je aka dudduba ta jikin ta Babu wani babban ciwo sai dai kujewa da tayi. Magunguna aka rubuta mata ciki kwa har da na bacci, bayan sun dawo gida ne aka kwanatar da ita a waje yayar ta ta shiga dakin nata ta gyara mata sannan aka shiga da ita dakin aka wuce da ita toilet tana baccin aka kwantar da ita a cikin komi na ban dakin yayar ta ta ta mata wanka da ruwan dumi, tana gama mata aka duba kayan ta aka dauko doguwar riga irin mai fadin nan ta Shan iska aka sanya mata sannan aka kwantar da ita Washe gari da misalin karfe takwas na safe aka Kira malam mai rukiyya, bayan ya zo ne aka fito da ita palour sannan aka fara mata karatu, can kusan minti Ashirin sai ji aka yi ta yi dariya wadda Amir sai da ya tsorata saboda firgici, shi kam bai ta6a ganin ana rukiyya a gaban shi ba. Aljanin ne ya yi magana yace "ku daina kona mu bama son wannan karatun da kuke Mana kuna kona mu yiiiiiiiiiiiiwiiiiiiiii ku daina ku daina bama so" Malam mai rukiyya bai saurari jinnun ba ya ci gaba da karatun sa, sai da ya yi mintuna talatin tukunna ya tsaya yace musu"su waye ku? Menene dalilin da yasa kuka shiga jikin ta kuke bata wahala? Ku fada mun idan ba haka ba kuma mu wuni anan Ina ragargazar ku" Taurin Kai sai jinnu da kyar akayi magana shima sai da suka ji malam din ya buda baki ya kama( Wassaffati saffa) sannan suka ce "za muyi bayani" Kuka suke saboda jikin su duk ya kwaile an kona musu wasu sassa na jikin su. " Laifi tayi mana, ta bamu aiki ne akan kishiyar ta, tace mu saka mata warin ja6a, haka muka je muka nemo ru6a66iayar ja6a muka daura mata a jikin ta, sannan muka shiga tsakanin ta da mijin sannan mu cire soyayyar yaran a zuciyar uban nasu, da muka yi aikin bayan kishiyar ta ta ta zama abin gudu a gurin mijin ta, ta Kara sanyawa muka maida mata kishiyar kamar baiwar ta da mijin shima haka za tasa su wanki da duk wani aikin gida bata jin tausayin su, daga baya 'yan gidan su kishiyar suka zo suka tafi da kishiyar tata suka nema mata magani suka karya sihirin da yake jikin ta da Wanda yake jikin Amir din, an kona mu sosai acan din, saboda San duniya har sai da aka bata kashin bakin aljanu ta hada da danyen nama tasa a gaban ta. To da taje gurin malam ta masa rashin kunya shine ya hura mata garin maganin da ya bata ta maida kishiyar ta mai wari sannan ya tura mata iskokai masu launin tsutsa, to shine take warin wannan sannan kuma gaban ta yake fitar da tsutsa, duk maganin da za'a mata a asibiti baya maganin tsutsar, a idon malaman asibitin tsutsar fita take Amma mu a gurin mu tsutsar cikin jikin ta take komawa. Da taje gurin malamin domin neman sulhu sai ta tarar da malam ya mutu" Wannan bayanin da Aljanin nan yayi sai da ya daga wa mutanen dakin hankali matuka sun tsorata da halayen fareeda, yayin da sumayya ta ke share hawaye aranta take fadin "me nayi wa matar nan take neman illata rayuwa ta ?" Tun tana kuka a hankali har ta fara yi da karfin ta, Amir ne ya zo kusa da ita ya dafa ta yace mata "kiyi hakuri sumy na , babu Wanda ya isa ya rabamu kinji " Shiru tayi saboda ganin mutane a dakin kuma har yayar fareeda tana kallon su. "Za ku cire mata warin jikin da tsutsar jikin nata kokwa?" "Mu sai mun rama abin da ta Mana tukunna" "Wattaba'u maa tattlushshayaadinu ala mulki sulaiman" malam ya fara karantawa , ai kafin yakai karshen ayar har sun ce masa ya tsaya. Tsaya wa yayi yace musu "za ku fita kukwa ?sannan kuma ku cire mata haukar wannan idan ba haka ba nan gana karon mu da ku ba zaiyi dadi ba Dan haka ku fita" "Za mu fita, kuma ko yanzu muka barta ai taji jiki tunda har hauka muka Sanya ta ga wari ga tsutsa, mune da riba ba ita ba" Inji Aljanin . "Munji ku fita kafin Raina ya 6aci" Atishawa tayi sai kuma tayi lamo da ita aka yayyafa mata ruwan addu'o'i sannan aka ce a siyo mata turaren za'afaran take shafawa a jikin ta da cinyoyin ta da marar ta,sai kuma turaren joda shima tayi amfani dashi Amma a goshin ta za take shafawa kullum sau biyu safe da dare. Godiya suka yi malam ya tafi,Amir ne yabi bayan shi ya bashi abin sadaka malam din yace "a'a ba zan kar6a ba mu ai don Allah muke rukiyya ba wai don a biya muba" Godiya yayi mishi ya koma cikin gida yayin da ya wuce dakin sumayya ya tarar da ita akwance tana kuka,bai Hana ta kukan ba saboda wani lokacin kuka rahama ne bubbuga bayan ta ya shiga yi aikwa sai tayi shiru ta fara ajiyar zuciya. Hakuri yake bata yace mata "hakika fareeda muguwa ce tabbas ta zalunce mu Amma idan muka yi hakuri to hakika Allah zai Mana sakamako mai kyau, don haka muyi hakuri sumy kinji?" "Babu komai na yafe mata muma Allah ya yafe mana" Da Amin ya amsa mata yace ta kwanta saboda kanta kar yayi ciwo. Alhamdulillahi jikin Alhaji Adnanu yayi sauki saboda matar sa suwaiba ita ce ta dauki nauyin kudin magungunan shi har ya fara takawa,Amma fa ya ji jiki. Madam inyamura ta shi da sassafe tana shirin Kiran pretty a waya tazo su tafi shopping , sai jin wayar tayi akashe, tun jiya da yamma rabon ta da ita acewar ta yi kamu a hotel tayi sabon saurayi acan za ta kwana. Wanka tayi ta shirya cikin kananun kaya ta dau wayar ta da mukullin gidan sannan ta shiga bedroom Dan dauko A.t.m da wasu kudade kimanin 100k, da ta ajiye saboda shopping, kudin da atm suka ce dauke mu inda kika ajiye mu . Innalillahi take Kira ga wani uban gumi da ya zubo mata ajikin ta Kai har da wani alamun zazza6i-zazza6i ma ja6ar ta nemi gurin Zama ta zauna a kasa tana mai mamakin ina kudin ta suka shiga da A.t.m din ta, kunsan inyamurai da kudi to haka take ta sumbatu da yarabanci tana kuka har da hawaye. Tunowa tayi jiya da pretty za ta fita tace mata "zee sai Allah ya kaddara saduwar mu a yafi juna saboda nema gidan 6arawo ba sata bace" Bata kawo komai a ranta ba tayi dariya tace sai "kin dawo cikin gur6atacciyar hausar ta" Lallai pretty ta takaita zee inyamura ko naira dari biyar bata ajiye mata ba saboda wulakanci Dan ba zance saboda rashin imani ba domin ita ma zee inyamura rashin imanin ta ne ya dauko mata filayen na Alhaji Adnanu har ta sayar dasu,da yake sa hannun ma ita tayi mishi don tare suka je inda suka siyi filayen saboda jarabar soyayyar da yake nuna mata yasa ta tasa hannun ta akan takardun. Haka ta cire kayan jikin ta ta zauna daga ita sai riga iya kar ta gwiwar ta saboda shan iska. Haka dai ta wuni cikin bakin ciki da 6acin rai. Shawara ta yanke akan ta fita ko Allah zai sa su hadu da pretty in yaso ta kaita gurin hukuma a kar6a mata hakkin ta. Abduljabbar da Abdurra'uf sunje gurin kawun su day zancen suna son a nemo musu Admission a b.u.k. yayin da suwaiba tace musu idan sunje su hada ta dashi a waya, Kiran layinta su kayi ta daga sannan suka mikawa kawun nasu tare da sanar dashi maman su ke son magana da shi. Kar6a yayi ya Kara a kunnen sa yace " Assalamu Alaikum malama" Amsawa ta yi ta ce masa " kawu barka da yamma, da ma so nake a nemo musu Admission a nan B.U.K saboda bana son suyi nisa damu, kaga ga halin da mahaifinsu yake ciki to bai kamata ace sunyi nisa da mu ba" "To shikenan malama zanje in samu abokina lecturer ne a B.U.K. din " Nan dai suka gama maganar akan gobe zaije saboda an fara sai da foarm. Godiya ta mishi ta kashe wayar. Kawu sai Albarka yake Sanya wa suwaiba saboda ta yi namijin kokari tayi fadi tashi akan yaranta hatta da mai gidan da bazarata yake takawa har ya Zama shi shine,Wanda dalilin kudin ta ne ya siya masa daraja da kimar da mutane suke ganin sa da ita. Hakika suwaiba ta Sha gwagawarmayar rayuwa babu uwa babu uba ga wulakancin namiji gashi yaranta lokacin ba wasu manya bane haka ta jure tayi hakuri da irin kalubalen da ta fuskanta a gidan auren ta har kawo lokacin da aka auro mata Aslamiyya ita ma ta Dora daga inda Alhaji Adnanu ya tsaya. Haka aka musu horon kin basu Abinci ita da yaran ta sai dai Abduljabbar ya fita yayi buga buga ya nemo musu shinkafa da Wake su dafa suci Amma ba Dan wai sun koshi ba,wahala iri iri sun Sha a gidan nan har ta Kai an koresu daga gidan bata a za6i dole ta sa ta koma gidan Dan uwan mijin ta kawu, shima anci sa'a mutumin kirki ne, baya duba uban yaran, da Yana dubawa tabbas da ba zai barsu su zauna masa a gida ba duba da yadda Alhaji Adnanu ya watsar da zumuncin su tun yana bibiyar shi Yana wulakanta shi shima har ya hakura ya zubawa sarautar Allah ido. Washe gari da safe kawu yaje ya samu abokin sa da batun yaran sa yake nemawa Admission, da Allah ya taimake su an sama musu yayinda suke dab da rufe kar6ar sabbin dalibai sai kuma wata shekara idan da kwanaki. Ancike musu foarm din shi Abduljabbar engineer, shi kuma Abdurra'uf 6angaren Arabic ( Arabic & Islamic studies). Alhamdulillahi sun fara zuwa makarantar sai dai a hankali duba da yadda suke sabbin dalibai ga ba'a saba ba, to Amma duk da haka suna fahimtar karatun su dai dai gwargwado. Khairat kanwar su yarinyar gurin Aslamiyya ita ma ta girma ma Sha Allah yarinyar har ta shiga primary school, da yake ita ma mai kokarince sai ya zamana duk wani position dinsu ita take musu na daya, idan bata gane Abu ba to takan zo gurin yayun ta ta tambaya har sai ta gane tukunna suke barin ta. Kasuwancin su suwaiba da Aslamiyya Yana ta ha6aka don yanzu haka Aslamiyya ta sai sabuwar freezer wadda take sai da kayan sanyi irin su; mango, so6o, kunun Aya, Ginger,sannan kuma tana sayar da nono da fura, idan aka saro mata nonon A wata rugar fulani sai ta bada gero (hatsi) a mata fura dakan man shanu mai kyau a haka ta dage take samun kudin ta don mantawa suke yi ma su din kishiyoyi ne saboda sun hade kansu sun kori shedanu sun baiwa marar da kunya. duk wani mai gidan kirki zaiso ace yau gidan sa da hadin kai Wanda hakan zai wanzar masa da zaman lfy a cikin iyalin sa, sa6anin yanzu da muke wani zamani Wanda shi namijin ma shine baya son yaga matansa suna zaune lfy, da zarar yaga sun zauna lfy to zai fara tunanin ko sun hade masa Kai ne suna neman cutar dashi, Wanda ba haka bane zaman lafiya hausawa suka ce wai yafi Zama Dan sarki, ya kamata maza ku dage ku wanzar da zaman lfy a gidajen ku saboda hakan shi zai baku damar da kwanciyar hankali da hadin Kai tsakanin yaran ku, wasu kuma matan sune da laifin namiji Yana kokarin ya samar da zaman lfy a gidan sa Amma Inaaaaa basa son zaman lfy sai dai suyi ta tadawa maigida hankali har wani namijin baya son dawowa gidan sa , duk lokacin da ya dawo zai shiga gidan sa to fa gaban sa Yana faduwa haka zai daure ya shiga. To wannan wace irin masifa ce kishi ya Hana ku ku samar da kwanciyar hankali ga mijin ku, Wanda wannan kishin wani namijin ba so yake ba ke mai nuna masa kina kishinsa ta iyu a banza kike yi shi kam kin fice masa a Rai kina ta wahalar da kanki karshe ma ya sake ki tunda kinki kwantar da hankali ku zauna lfy keda abokiyar zaman ki. Fareeda jiki yayi lakwas sai dai zuciyar ta ina ga ko irin ta kafirai ce, ita fa ba taki ba sumy ta bar gidan ita kam bata kaunar sumayya da yaranta itama sumy da taga haka sai ta janye jikin ta daga gare ta idan ummi ta zo gurin yaran suna wasa sai ta fito daga daki ta Duke ta ta dauke ta tana sakar maganganu marasa dadi, tun Amir Yana kyale ta har yazo ya fara mata magana "kada ki Kara raba mun kan yarqna bana son wannan mummunan halin naki idan kika kuskura wlh zan dau mataki akan ki" Sai dai ta rabu dashi domin ita tana tsoron ace yau Amir ya sake ta, gani take ba zata iya rayuwa a gidan su ba. Ya kusa zuwa karshe fa 😎 [7/21, 3:18 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA Na Amina Mamu Gumel (Mmn Annur) Page (29). BAYAN SHEKARU UKU. Abduljabbar da Abdurra'uf sun gama karatun su Alhamdulillahi har sun kar6i results din su,results din yayi kyau sosai sai fatan Allah ya kawo aikin yi na Alkhairi. Khairat ce na hango ita ma ta dawo gida ita da kawayenta suna ta murna an gama primary school, fuskokin su fal farin ciki saboda gani suke kamar sunyi rabi a karatun nasu ba su San ko hannu basu Sanya ba duba da yadda zamani ya canja yanzu kowa ilimi yake nema. Sumy ta hada mata walima ita da kawayenta ta yayin da suma twins suka yi junior candy haka aka taru ana farin ciki agidan , fareeda ta so Hana khairat zuwa gurin walimar tasu sabida ba ita ta hada mata ba a cewar ta wai makiyar su ce ta hada, budar bakin khairat sai cewa tayi " haba mammy yanzu duk kokarin mommyn su Yaya Hussain bakya gani ? Ki ga fa komai tana mun har dinki take mun mammy wllh mommy tana kauna ta" Bige bakin ta fareeda tayi tace " wlh kika kuskura kika je khairat sai na canja Miki kamanni" .yayin da taci gaba da surfa mata ruwan bala'i da nema mata masifa iri iri kamar ba 'yar ta ba. Hakika maza yayin da za kuyi Aure kuke dubawa wllh, idon ku Yana rufewa yayin da kuka hadu da mace bakwa duba quality na ta a'q sai dai ku duba kyalkyal banza karshe kuma kuzo kuna Dana sani marar amfani, yanzu menene ribar ka ka auro wadda bata da tarbiyya sannan babu kamun Kai babu ilimi bata San Yaya zata tafiyar da al'amuran ta ba a gidan mijin ta balle har tasan yadda za tayi mu'amala da abokiyar zaman ta ko makwabtan ta wani lokacin sai namiji ya Kara aure tukunna yake sanin darajar matar sa ta farko (uwar gida) musamman idan akayi rashin dace da cewa Amaryar bata da kirki yayin da ya kasance uwar gidan ita kuma Allah ya yi mata hakuri da kawaici to daga nan zai San kimar ta. Amma idan akayi rashin dace sai kaga uwar gidan ce bata da kirki bata San kimar mijin ba to yayin da ya Kara neman Aure sai Allah ya sa yayi dace da Amarya ta gari wadda za ta zame masa sanyin idaniya. Allah ya ganar damu Amin. Haka Ameer ya ce wa khairat" maza tashi ki shirya mommy tana jiran ki a gurin walima kada ki 6ata lokaci" "Ba zata je ba Malam Kai wani irin sakarai ne har da zan kafawa 'yata doka ka wani kwaso sandunan kafafuwan ka kazo kace wai ta tafi ? Makiyar tawa za'a jewa Kira? To ko bana numfashi sumayya bata Isa ta rike min 'ya ta ba, don haka Babu inda za taje" "Ni kike Kira da sakarai? To ki sani khairat 'yata ce ba da ita kika zo gidan nan ba, saboda khairat nake daga Miki kafa kema ki zauna da 'yar ki a gidan mijin ki, to Amma ki sani daga yau na baiwa sumayya rikon khairat domin ba zaki 6ata mun tarbiyyar yarinya ba itama ta kwafe muna nan dabi'unki taje take yiwa mijin ta kamar yadda kike min, Ni mahaifin khairat daga yau khairat tabar dakin ki ta koma na mar'atussaliha Sumayya 'yar Aljannah" "Wlh Ameer baka Isa ba ko kana yawo da uwar ka baka Isa ka yi kyauta da 'yata ba don haka karyar makaryaci wallahi ko ma wane irin asiri sumayya tayi to ba zaiyi nasara a kaina ba domin idan junan ta sammako to Ni acan na kwana" Tana masifa tana nuna mijinta da hannu Kai sai kayi tunanin ko Dan ta ne. "Haka kika ce? To bari in sanar dake abun da baki sani ba sumayya bata biye biyen bokaye kamar yadda ke kike yi, sannan kullum zuciyar ta a wanke ta ke kamar farar takarda don haka kinji na rantse Miki da Allah wlh khairat tabar hannun ki ta koma wajen sumayya" "Da kasan da haka ka auro ni naga ta kasa kulawa da Kai ne shi yasa ka Kara auren, da kasan 'yar Aljannar ce ka mata kishiya?" "Fareeda sumayya ba kasawa tayi ba asalima nayi sha'awar Karin Aure ne domin koyi da sunnar manzon rahama s.a.w. Amma ba Dan haka ba wllh sumy ta ishe Ni rayuwa nagartacciyar mace aka samu sumy an dasa ayah" "Karya kake wllh Dan kutt" ai kafin ta karasa Ameer ya dauke ta da mari. Sannan ya Kara da cewa "kije ki tafi gidan ku Ni Ameer na sauwake miki, ma'ana na sake ki saki dai dai har saki UKU ." Wani Kara ta saki tace "wllh ban saku ba baka Isa ka sake Ni ba nida Kai tamakar Hassan da hussaini ne ka taimaka Ameer ka dawo Dani dakina wllh zanyi maka yadda kake so ka taimaka ko Dan 'yata nima in zauna in raini abata " Tana kuka tana magiya Amma ina Ameer ko kallo bata ishe shi ba karshe ma hannun yarinyar sa ya kama yace taje ta shirya su tafi gurin walima. Sumayya jin shiru khairat bata karaso ba yasa ta Kira Ameer a waya ta sanar dashi khairat suke jira ga kawayen ta nan duk sunzo. Sauri tayi ta shirya da yake a handsfree yasa wayar tana jin abin da sumy take fada kwalliya tayi amma bata Sanya janbaki ba ta shafa powder da lipstick sai doguwar rigar da sumy tayi musu ita da khairat din ta leshi, tayi kyau sai ta yafa mayafi kalar zanen fulawar lace din, rakata yayi inda suke da yake a unguwar ne Babu nisa da gidan wani kango ne da Ameer ya siya ya zagaye shi to aciki suke gudanar da walimar. Gida ya dawo yace "ki fito ki tafi gidan ku wllh kika sake na dawo na tarar dake a gidan nan sai nasa an koya Miki hankali da sanin ya kamata" Kuka take ta fito daga daki ta tsugunna tace "kayi hakuri Ameer ka barani inyi idda" "Babu wata idda da za kimin a gida tsakanina da ke aure ya kare,da saki Daya ko biyu ne na Miki to wannan zaki iya yin idda a gidana Amma ban da yanzu da na ratta ba Miki saki uku." A yau ne aka tashi da tashin hankali da bakin cikin rabuwa da Alhaji Adnanu domin kuwa Allah ya yi Ikon sa a kansa ya kar6i abinsa. Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un shine abinda Suwaiba take ta na na tawa ita da yaran da Aslamiyya domin kuwa basu tsammata ba mutuwar ta zo musu a bazata ta musu shigar sauri yayin da kawu shida kqnin sa Wanda suke uba Daya dashi sune a kan gawar Alhaji Adnanu suna gyara shi, haka Al'amarin ubangiji yake ya dauke maka abin da kake so a lokacin da kafi bukatar sa kusa da kai, ba wai don baya son kq ba a'a sai dai dama can haka ya tsara rayuwar sa ta zo karshe bashi da sauran ci ko Sha a rayuwa. Tabbas mutuwa wa'azi ce kuma sai mai imani yake kokawa kansa, duk dakiyar ka duk jarumtar ka idan kaga anyi mutuwa a gaban ka to dole sai ka koka dole kaji Babu dadi a ranka, fatan mu Allah yasa muyi kyakkyawan karshe Allah yasa Alhaji Adnanu a Aljannar sa Allah ya shirya masa zuri'ar sa Allah ya dubi abin da ya bari. Hakika mutuwar shi ta daki mutane da dama inda kuma suke farinci da cikawa da yayi da kyakkywar kalma wadda ko wani musulmi kuma mumini yake fatan kasancewa ya mutu da kalmar shahada a bakin sa. Hatta da matan sa da yaran sa sai da ya nemi da su yafe masa kan kurakuran sa da yayi musu shima ya yafe musu. Kuka suwaiba take yi tana mai masa fatan Alkhairi da fatan haduwa da mala'ikun rahama Allah ya bashi ikon amsa tambayar kabari dai dai . Yaran sa abin tausayi matuka duk da ana samun matsaloli na rashin adalci yayin da mutum ya Kara aure, to su gaskiya akwai shakuwa da soyayya a tsakanin su da mahaifin su, da kyar aka lallashi yaran. Bayan kwana bakwai kowa ya watse yayin da aka bar suwaiba da Aslamiyya domin zaman takaba, akwai makociyar su malama Hauwa'u Aminu ita ce tazo ta musu bayanin yadda ake yin takaba. Tace " idan mace mijin ta ya rasu to za ta kame kan ta daga barin duk wasu nau'i na kyale-kyale kama da ga kan Sanya tufafi masu kwalliya da Sanya turare a jiki ko a Daki da Sanya kwalli ko da kwa na ciwon ido ne, shafa mai mai kamshi, shafa powder ko lipstick, Sanya Dan kunne ko warwaro yin kitso Wanda zai nuna kyan mace, a matsayin ki na mai takaba ya kamata ki nisanci wadannan abubuwan, sannan da fita unguwa, mai takaba ba zata fita ko nan da can ba sai dai idan da larura kamar zuwa asibiti shima idan San samu ne to ta lullu6e fuskar ta ko da da nikabi ne, ko kuma bata da kowa har kuma yunwa take neman illatar da ita, to wannan ya halatta ta fita domin neman lfyr ta da abincin da zata ci, kuma ta tsare mutuncin kanta har sai tayi wata hudu da kwana goma. Bai halatta ba ace wai idan za kiyi takaba wai sai kin zauna da wuka sabuwa a gurinki ko kuma naga wasu 'yan gargajiya wai idan mace ta shiga takaba sai an mata wankan shiga takaba asiyo sabuwar wuka sannan a dauko mata Zane falle a zuba toka a ciki tayi kunzugu tasa a gaban ta, wai saboda da mamaci kar ya dawo, kiji wani jahilci musulunci ba bagidajen Addini bane da zai koya Mana shirme da shiririta. Allah ya ganar da mu yasa ayi a sa'a Allah ta'ala ya shirya muku yaran ku ya taimake ku akan tarbiyyar su ya basu ilimi mai Amfani ya jikan Alhaji Adnanu yasa Aljannah makomar sa" Yayin sa da malama Hauwa'u Aminu ta gama fadakarwar ta ta rufe taro da Addu'a. Bayan sun gama takaba ne a cikin mazan unguwar su ya fito ya nuna sha'awar auren suwaiba sai take sanar da Dan Aiken yaje ya fada masa ba za tayi aure ba za ta zauna ta kula da yaran ta yayi hakuri. Da kanshi ya zo mutumin matar sa Daya da 'ya'ya goma, yake fada mata cewa "ki daure ki Aure Ni suwaiba naga kina da duk wani quality da namiji zaiyi sha'awar auren ki, idan kin amice min nikam a shirye nake" "Gaskiya malam kayi hakuri domin Ni a yanzu ZAMAN 'YA'YA NA nake ba zan yi aure yanzu ba saboda so nake na inganta goben Yara na" Kwawar mutumin tasa ta ce masa " shin idan na yarda na aure ka za ka iya rike min Yara na guda uku" A zabure ya juyo yace mata " yaran ki ai sai ki baiwa dangin baban su in yaso muyi auren mu" Wata zawarar dariya tayi tace masa "to malam hausawa ma sunce ' maso uwa yaso 'ya'yan ta' don haka Ni ba zan iya zuwa inyi aure ba in bar yarana suna watan gaririya a titi ba sannan inje inke kula da 'ya'yan wasu, idan Babu damuwa kayi gaba kila ko za ka samu wadda kanta ya toshe ta aure ka" "Ban gane wadda kanta ya toshe ba?" "Ina nufin wadda ta za6i farin cikin ta na duniya ta wulakanta ta tarbiyyar yaran ta da amanar da Allah ya bata ta kula dasu, Kai ko kunya ba ka jiba ka nuna baka kaunar Zama da 'ya'ya na Ni kuma na amince na aureka inje in kula da naka yaran ? Shin haka adalci yace ?" " A a ni fa ba dole na Miki ba shikenan zance ya wuce,Ni zan tafi " "Madallah a sauka lfy". Cikin gida ta shiga take labartawa Aslamiyya abinda yake faruwa suka Sha dariya anan Aslamiyya take ce wa"maman Abdul yanzu fa maza basa son rikon Dan wani sai dai Kai kaje ka bautawa nasu 'ya'yan Amma badai su rike wa mace Dan da ba nasu ba , to Allah na tuba yanzu fa wahalar 'ya'yan su ma ba so suke ba balle Wanda basu haifa ba" Haka su kayi ta tattaunawa a tsakanin su kar she ma Abdurra'uf ne yace " mama idan za kiyi auren kije kiyi Amma fa mu wllh ko Garba sunan mijin ki garban za muce masa ba zamu ce dashi Baba ba, muma muna kishin mahaifin mu ai da zaice ba zai rike Miki yaran ki ba dama ba sonki yake ba gadon mu zai cinye in yaso sai ya gudu ya barki da 6a6atu" " Kai gidan ku mamar kake fadawa haka? Ashe ba zan bar khairat ba inje inyi aure ko Abdurra'uf?" " Hhhhh aunty kenan mu fa mu hakura kwa hadu da baban mu a Aljannah kuyi rayuwar ku a can" Bige shi maman sa ta yi tace "tashi ka bamu guri Dan Albarka kawai " Dariya suka yi su dukan su. Pretty bata zame ko ina ba sai gidan da ta kama ta zauna tana tunanin ya za tayi da kudin nan na madam zee, so take sai ta isarwa mai kudin kayanshi tayi alkawari ba zata ci kudin nan ba da yake inyamura ta sanar da ita address din gida da tayi auren shima bugar cikin ta tayi aikwa da yake bata da tunani sai da ta fada mata komai na rayuwar gidan Alhaji Adnanu da tayi. Pretty tayi alkawari sai ta kaiwa Alhaji kudin sa ita kuma ta roke shi ya Aure ta ta huta da zaman barikin da take yi, ta gaji da bariki nema take ta yi aure ko ma wanenne mijin so take yi to idan ta Kai wa Alhaji dukiyar sa sai ta roki alfarma ya taimaka mata ya Aure ta Washe gari da safe ta shirya cikin shiga ta mutunci tasanya hijabi tayi kyau kasancewar ta a cikin shiga ta mutuncin haka ta hada kayan ta kala biyu ta yiwa saurayin ta waya akan yazo ya kaita kanon ta shirya, da yake sunyi dashi zai kaita ganin gida a cewar ta. Haka ya shirya ya dauke ta suna fira har sai da ya kawo ta kano yace shi ba zai iya kwana a kanon ba idan ta gama ta Kira shi a waya zai koma gida ne, haka ta nemi unguwar su Alhaji Adnanu har sai da aka kaita kofar gidan sa sannan tayi Sallama ta shiga gidan Amsa mata aka yi sannan aka bada umarnin a shigo,bayan ta shiga suka gaisa Aslamiyya ta kawo mata ruwa da Abinci suna zaune a tsakar gida domin hutawa da yake kullum da yamma sukan fito tsakar gidan ne domin Shan iska, tashi tayi ta bata guri domin ta samu ta sake taci abincin, suwaiba ce tace mata "bakuwa daga ina?" Aslamiyya tace mata "nima fa ban gane taba naga dai da Alama daga nesa take duba da yadda alamu suka nuna na gajiya a tattare da ita" "Ikon Allah nima dai ban santa ba to Ina ga ko daga cikin dangin su Alhaji take na nesa din nan ko gaisuwa tazo ta Mana" "Eh to Babu mamaki" inji Aslamiyya. Bayan pretty ta gama cin Abinci ta zauna ta ce a ranta" shin mai gidan ma kwa Anya zai soni ? Duba da yadda yake da kyawawan mata haka ga iya girki ga tsafta" dube -dube ta ke yi Dan ganin makusar gidan Amma bata samu makusar ba, tashi tayi ta ce musu tana son yin Alwala,nuna Mata gurin alwalar aka yi yayin da suwaiba ta zuba mata ruwa a buta toilet aka nuna Mata ta shiga, bayan ta fito ne aka shimfida mata dadduma ta gabatar da sallolin da ake binta. Magana ta musu tace "don Allah ko mai gidan yana nan?" Baki suka hada wajen cewa "ikon Allah,baiwar Allah daga ina?" "Ni bakuwa ce to nazo gurin mai gidan ne idan Babu damuwa ko za ku ta6o shi a waya nazo ne da wani batu mai muhimmanci " "To fa Amma kinyi 6atan Kai ina ga baiwar Allah, meye sunan Wanda kike nema din?" "Babu zancen wani 6atan Kai ba nan ne gidan Alhaji Adnanu ba Wanda ya auri madam zee?" "Hakika nan ne wani abun ne ya faru da zee din haihuwa tayi ne ?" Suwaiba ta jefo wannan tambayar. "Ko Daya nazo ne dai da batu na Alkhairi a gareshi da ma ku baki Daya" " To dai da farko Allah ya yiwa Alhaji rasuwa tun kusan wata shida da ya gabata" Sanar da pretty mutuwar Alhaji Adnanu ta doki zuciyar ta hakika ta girgiza har sai da hakan ya bayyana a fuskar ta Wanda ya baiwa matan sa damar yin mamakin wannan matar da ba dangin su ba ba na Alhaji ba. Tambayar ta sukayi "shin lafiya kike neman sa? Taya kika San Alhaji mu kuma bamu da labarinki" "Haka ne, da farko dai Ina muku ta'aziyya Allah ya jikan sa. To amma matar sa zeey madam ita ta bani labarin irin cutarwar da ta muku hatta da kadarar Alhaji da ta dauke ta Saida sai da ta bani labari, Ni kuma nayi dubara na dauke kudaden da A.t.m din da ta sanya kudin a asusun bankin ta gashi to kafin na taho nayi nasarar zuwa na ciro kudaden ciki duka kafin ta je ta Kai report bankin , ga kudaden ku nan duka sannan kuma ta ta6a wasu kudaden Wanda tare muka ci da ita,to bansan adadin me ta bani a ciki ba tunda ba zunzurutun kudin ta dauka ta bani ba siyayya take Mana shine nace ku kintata yawan kudin sai na biya ku idan Babu damuwa" Murna suka yi yayin da suka yiwa Allah godiya ga shi kudin Alhaji ya dawo wannan ma kadai ya ishi bawa ya ji tsoron haduwar shi da Allah. Sai dai bakin ciki Daya kudi ya dawo Alhaji ya tafi tafiya ta din din din, Babu ranar dawowa sai lokacin da Allah yaso a hadu a Aljannah. Kawu aka Kira a waya aka masa bayanin abinda yake faruwa Sosai shima ya yi murna ko babu komai iyalan kanin nasa za su samu sassauci daga cikin halin rayuwar nan da ake fama.anan ya ce musu "ya kuke ganin hakkin da suka ci tare din ? Ni dai a nawa mahangar ku yafe wa wannan baiwar ALLAHn nan tunda ita ta dawo muku da hakkin ku , amma ya kuke gani?" "Ai kawu mun yafe mata wlh matar da ta taso tundaga uwa duniya ta kawo Mana dukiyar mu ai bamu da bakin da za mu gode Mata sai dai muce Allah ya Mata tukwicin da gidan aljannah". "Amin " suka ce gaba ki dayan su. Da kyar aka samu fareeda ta tattare kayan ta ta koma gidan su yayin da ta tarar da damuwa da 6acin Rai domin kuwa matar yayan ta ta dawo gidan sakamakon gidan su da ya rushe,haka yayan nasu yace su koma kafin ya samu kudin da zaiyi aikin ginin nasa. Da kyar take samun abincin kirki saboda yayan nasu idan yayi cefane to har maman su ake hadawa ayi girkin a cewar shi ba saita Sha wahala ba tayi girki tunda ga matar sa nan sai ta musu duka Abincin gidan. Da wannan yasa fareeda take samun rashin wadatuwar Abinci , ta saba a gidan mijin ta taci iya yanda take so tayi a binda ta ga dama Amma yanxu ta dawo karkashin matar yayan ta. Matar tana kokari Amma fareeda bata gani tayi ta tsegumin ta a gurin maman su Amma inaaaa maman su bata ganin laifin surukar tata, tunda irin masu kissar nan ne ita take yiwa maman nasu wanki gyaran daki, Kai hatta da kitso da yankan farce matar yayan fareeda ita take yi wa Maman su shi yasa bata ganin laifin ta. Tun fareeda tana tsegumi har ta hakura ta daina ta fawwalawa Allah ta rungumi kaddara. Sumayya taji bakin cikin sakin da Ameer ya yiwa fareeda saboda ko ba komai ya kamata ace taci darajar khairat, sai dai Ameer yayi murmushi yace "da kinsan a irin masifar da ta Sanya Ni da baki ce haka ba, ko da yake kema ai bata barki ba duk tare ta Sanya mu a ukuba Amma yanzu shine za kice wai da ban sake ta ba?" Kada ki manta a gaban ki akamata rukiyya Aljani yayi magana akan irin abin da tasa aka Mana Ni da ke Amma saboda ke zuciyar ki tamakar auduga take za ki tausaya Mata Ni kam da na rabu da ita wllh ji nayi tamkar na rabu da kaya a jikina sai yanzu nasan Ina rayuwa mai dadi Amma da akam a kuntace nake bani da 'yan cin kaina wai Ni Ameer Ni da sumayya muke yiwa mace wanki da sauran aikin gida tabbbb lallai ansha Ni na warke Ni kam yanzu da inyi marmarin Karin Aure gara inje in yi ta aikin lada a masallaci shima kanshi hidimawa masallaci Raya sunnah ne ba wai saina Kara aure bane yake Zama Raya sunnah" Ita dai sumy dariya take masa ganin yana ta bayani da gaske har wani nuna alhini yake saboda sunsha yin wankau shi da ita. Na ce ba saura one page a gama labarin nan Shin ya samu karbuwa a gurin ku ko kuma dai bai samu ba ???? Daga 'yar mutan Gumel Allah ya jikan musulmai baki Daya [7/22, 2:26 PM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA NA Amina Mamu Gumel (Mmn Annuur) Page (30). Wani bawan Allah ne ya fitowa fareeda da sunan zawari domin tsakanin sa da Allah shi son ta yake da aure yayin da ta amince masa saboda ta gaji da zaman gidan su a zuciyar ta take fadin wai "Abinci wai sai dai a sammaka baka da 'yan cin da za kayi magana yanzu sai amaka gori ace ka kasa zaman aure ka kaso aure ka dawo gida kayi badagargar a tsakar gida , Babu damar ka fito daga daki ka kwanta a waje sai a fara gasa maka magana idan ka koma dakin ka kwanta sai ace maka boka sarkin zaman daki Kai dai in ka Zama zawara sai dai addu'a wlh haka kurum kamar ba maman ce ta kaini ta baro ba ita ta koya mun bin malamai kawai dai yanzu ta saduda taki ta nemo Mana wani malamin aje a gyara Mana aure nida Ameer a jiyo hankalin sa kaina yaji duk duniya babu wacce yake so sai ni a cusa masa tsanar ko wacce diya mace ciki kwa har da babar sa da kanwar sa , Kai wannan lamarin dai na gaji gara inyi aure ko na huta" Haka suka tsaida ranar da za'a daura aure ita ce ranar da za ta tare a gidan mijin ta. Tana son gyara jikin ta Amma inaaaa Babu kudi, don ko kudin siyayyar nan da ango yake baiwa Amarya ma bai bata ba ya ce Mata idan ta shiga gidan sa zai bata 200k. Haka ta yadda ta aminta dashi ana gobe daurin aure ne suka je aka musu test a asibiti, bayan sun fito ne ta kalli gurin da suka ta6a haduwa da Ameer da gurin da sumy ta tsaya yayin da Ameer din yaje suka gaisa da fareeda, Allah sarki rayuwa nan gurin shine gurin haduwar mu ta farko da Ameer ba zan ta6a mantawa da gurin nan ba , hakika sumayya ta cuceni da tayi asirin da ta raba Ni da mijina ta shiga tsakanin mu. Bayan sun koma gida ne ya bata sadakin ta 100k. Murna tayi" ta ce duk da aure na uku zanyi amma har yanzu Ina da tsada, ba irin su o'o ba da sai dai abiyo miji bashi daga karshe ace an yafe masa " Dariya matar yayan ta tayi tace Mata"ke dai naga ranar da za kiyi hankali banza bagidajiya to ba kince yace Miki kudin siyayya zai baki ba yayin da kika shiga gidan sa to Allah yasa ba dadin baki ya Miki ba" "Akan ki mai mugun nufi kawai ke da bakya neman Alkhairi ga Dan uwanki musulmi sai dai kiyi hassada" cewar fareeda. Ita ma bata sassauta Mata ba haka ta biya ta sai da sukayi cancaras. Da yamma duk ta gama wasu shirye_shiryen ta hatta da kitso da kunshi duk tayi abin ta gobe ake jira a daura aure ta wuce ta huta da kayan bakin ciki da rashin wadataccen Abinci. Pretty ce take shirya wa domin komawa garin su yayin da ta yi wa saurayin ta waya yazo ya dauke ta. Haka suka hada Mata Sha Tara ta arziki suka Mata alkawari indai bikin ta ya kusa to ta fada musu za su je in Sha Allah tunda yanzu an zama Daya. haka suka kama hanya suka tafi yayin da sukaji Babu dadi rabuwar tasu. Alhamdulillahi sumayya ta samu aiki a wata makaranta da take unguwar su privet school ce duka duka ko shekara ba tayi ba da budewa Ameer ne ya bada sunan ta yayin da ake neman malamai a makarantar, tayi murna sosai iyayen Tama sunji dadi. Su Hussain sun girma ma Sha Allah sai fatan rayuwa mai kyau. ZAMAN lafiya ya wanzu a gidan Ameer har wata kiba ta musamman yayi, kudi ya zauna masa ya yin da ya Kai 'ya'yan shi shagon shi domin su koyi kasuwanci bayan haka gobnati ta bukaci da duk wasu iyaye da suka San da 'yan biyu ko 'yan uku ko 'yan hudu to suje su bada sunayen yaran saboda za su bude musu wata gidauniya ne domin dogaro da kai, Alhamdulillahi an samu wasu mutane a unguwar su sun Kai sunan su day sukaji labarin Ameer ya ce ba zai Kai sunan yaran ba saboda dai dai gwargwado Yana da rufin asiri gara a nemi masu kananun karfi a taimaka musu, to hakan da suka ji kawai suka bada sunan ba da sanin sa, hatta neman su da akayi number Ameer aka Kira aka yiwa yaran interview saboda nauyin karatun su gobnati za ta dauka komai nasu kyauta ne. Alhamdulillahi gobnati ta kawo ci gaba a jahar tamu domin ko mabarata masu goyon Yara biyu zuwa uku sun daina yawo, Amma da kana tsayawa a mota saboda cinkushewar motoci za su fara kawo maka Kai kusa da windown mota za su fara cewa "a taimaka Mana sadaka 'yan biyu kyautar Allah , 'yan biyu na gaishe ku" Amma yanzu alhamdulillahi radadin talauci ya fara tafiya. Amarya fareeda ta tare a gidan ta yayin da aka Hana ta Zama da Miji a inuwa daya, Kai duk wani motsin mijin akan idon uwar gidan ta Hana su sakat. Bayan kwana uku ta damkawa fareeda girki tace Mata " mu yaran gidan nan suna da ka'ida dole sai suna nan tukun na ake Dora girki domin ko nice dole sai na jira sun dawo daga inda suka tafi, su basa cin Abincin da ya dade da dafawa,sannan kuma sai an tambaye su abinda za su ci tukunna a dafa, kuma dole mai girki ita ce za tayi wankin Yara kinga kafin ki haifi to dole ne ki yi wankin yaran nan saboda ki ci gaba da Zama a gidan nan don haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya" Fareeda tsoro ne ya kamata ta tsaya tana kallon matar mijin ta tace Mata "aure nayi fa domin na huta ba wai don inzo inyi bautar 'ya 'ya ba" Mijin ne mai suna falalu yace Mata "kull fareeda ba'a maida magana a gidan wannan sannan ai na aure ki ne domin ki zauna kiyi ZAMAN 'YA'YA NA a gidan wannan ba wai don Ina son ki bane, ban da abinki Ina da mace kamar ta'iba me zanyi da wata macen? aiki ne ya Mata yawa a gidan shi yasa na auro ki domin in taimaka miki" Innalillahi kawai fareeda take ambata saboda tayi gudun gara ta tadda zago, wato taki sharar masallaci ta zo za tayi ta kasuwa yanzu to me yakamata tayi abinda take fada kenan. Daki ta tafi ta kwanta tana tunanin rayuwar ta ta gidan sumy lallai taci Karen ta Babu babbaka "wato yanzu ita za'a yiwa cin mutunci wai ita za tayi wankin Yara ga girki sau uku a Rana sannan kuma a matsayin ta'iba na uwar gida ita za ta kasa abinci, Karin bakin ciki wai sai anjira Yara sun dawo tukunna za a tambaye su me za ayi a gidan sannan sai suna nan za a Dora abinci, Kai wannan wani irin gidane na shigo ?" Babu mai baki amsa fareeda sai mijin ki. Ai dama karshen azzalumi baya kyau sai ya girbi abinda ya shuka don haka ki zage ki kama aiki tun kafin ki fara kar6ar gashi. Fareeda tana Shan wahala sosai duk wani nau'in aikin bauta ita take yinsa a cikin gidan Falalu, Ta'iba bata raga Mata ko kadan babu tausayi ga bata da bakin miji, za tayi aiki ranar kwanan ta Amma fa miji da ita da shi sai dai kallo domin kuwa kullum suna tare da ta'iba uwar gida. Haka za ta shiga daki ta yi ta kuka sai yanzu hankalin ta ya dawo jikin ta ta fara Dana sani marar amfani wadda lokacin yin ta ya kure Mata da ta hakura ta zauna a gidan mijin ta da duk haka bata faru ba, gashi yanzu tazo tana wahala da mutanen da basu San darajar ta ba. JAN HANKALI. Hakika duk abin da ka dauka da zafi to Babu makawa da zafin zai zo maka, Amma idan ka dau abin da sassauci to Allah zai sa abin yazo maka da sauki, wani lokacin Dan Adam muna da shagala bama tunanin za mu koma matabbata wadda take rayuwa ta dindin din, Allah shi ne ya halatta Karin aure bai fara da Daya ba sai ya fara da biyu-biyu, uku-uku, hudu_hudu, sai yace " idan ba za kuyi adalci ba to ku zauna da guda daya...... Har zuwa karshen ayar. Allah ta'ala ya Hana zalunci kamar yadda ya fada a cikin hadithi Qudusiy yace "inni harramtuz-zulma ala nafsiyy, waja'ala bainahu muharramun.....Allah ya haramtawa kansa zalunci sannan ya haramta shi a tsakanin mu. Kamar yadda yazo a cikin hadith inda Annabi yake cewa" Azzulmu zulmatun yaumul Qiyamati" hakika zalunci duffaine a ranar alkiyamah. To ya kamata muji tsoron Allah mu daina zaluntar junan mu sabida rayuwar duniya,koda da lafazi ne mukayi wa junan mu na 6atanci hakika sai Allah ya yi hisabi a tsakanin mu matukar bamu nemi yafiyar junan mu ba. Allah ta'ala yasa mudace Amiin. Duk Wanda ya San fareeda a da to yanzu idan ka ganta za kayi tunanin ko wata kanwar babar ta ce ta zo daga kauye, shima fa kauyen inda babu wayewar kai. Duk ta rame tayi baki ta jeme sutturun ta masu tsada da Ameer yake musu duk sun mutu sai dai ka ganta a cikin mummunar shiga duk ta kazance Babu kwalliya Babu shafa powder da Jan baki duk Babu , to Ina za'a samu tunda ranar da ta shafa powder ta'iba ce to Sanya ta dole sai taje ta wanke fuskar ta saboda Babu macen da za ta yi kwalliya a cikin gidan ta bata Isa ba ita take da damar yin kwalliyar wannan ba fareeda ba. Za ta ci abinci ya ishe ta Amma fa Babu sauran jin dadi na gidan aure bata da 'yanci ko kallo bata ishi falalu ba tsakanin sa da ita ta gaishe dasu shida matar sa ta musu wanki ta dafa musu abinci, to wannan shine tsakanin ta dasu Amma ko dakin ta da sunan ya kwana bai ta6a yiba. Ya hanata fita ko nan da can, daga daki sai bandaki sai ko kicin yayin da za ta Dora girki. Sumayya likkafa taci gaba domin ta girbi Alkhairin da ta shuka komai na jin dadi Ameer yi musu yake yi hatta da gidan su sumayyan yasa an gyara musu ya zuba musu komai na jin dadi ita ma tana kokarin kyautata wa mahaifiyar shi, duk kudin sumayya haka za ta zage dantse tayi wa iya aiki idan taje gidan, in za ta hanata sai tace "iya nima fa 'yar ki ce kamar baban twins don Allah ki barni in samu ladan da Da yake nema a jikin iyayen sa" sai dai iyan ta yi murmushi tace "sumayya kin zamo min tamkar lu'u lu'u saboda da taimakon ki da hakurin ki da jajircewar ki akan gidan ki Dana Ameer ya zamo abin kwatance hakika ke din matar da za'a yi alfahari ce, tabbas yaro na yayi dace da mace ta gari Wanda da bamu San da haka ba sai da makirar matar sa ta bar gidan nan tukunna, fareeda ta cutar da mutane tayi abinda ko kuda ba sai lasa ba ta cuci 'yar ta khairat, sai dai Allah yasa ta gane itama a Mata abin da tayiwa mutane tunda naji labarin tayi aure" " Babu komai mama duk abin da zai samu bawa to bai Isa ya canja wa rayuwar sa abinda Allah ya tsara masa ba don haka hakuri yake da dadi , tunda Allah yayi bushara ga masu hakuri, kuma Yana tare da masu hakuri sannan kuma Allah shi kadai yasan ladan da zai bawa mai hakuri da mai Azumi . Allah ya bayyana ladan da zai bawa mutum yayin da yayi masa wata bauta Amma bai fadi ladan masu hakuri da masu azumi ba" " Haka ne sumayya Allah ya dawwamar da zaman lafiya a tsakanin ku ya raya muku yaranku yasa su muku abinda kuke Mana na kirki" Sumayya tasanya Ameer a gaba akan suna son suje su gidan fareeda saboda khairat kada a shiga hakkinta a matsayin ta na 'ya ga fareeda, da kyar tukunna ya yarda akan suje Amma kada abar masa 'yar shi a gidan ta, haka suka shirts suka je da taimakon matar yayan su ita ta rakasu gidan. Sallama suka yi aka amsa musu suka shiga gidan Ta'iba ce a tsakar gida a zaune tana Shan iska, tace "lale marhabin da baki bismillahi ku shigo" karasawa suka yi kan tabarmar da take zaune ta tashi ta dauko musu ruwa, gaisawa suka shiga yi tace "sai dai ban gane kuba" tana cikin tambayar tasu ne fareeda ta kawo Kai ta fito daga kicin hannun ta dauke da katuwar ta6arya za ta Kai ta ajiye a ma'ajin ta, khairat ce ta kula da ita tace "mama kece?" Jin an ambaci mama yasa ta'iba ta dago da Kai don taga maman, aiko idanun ta ne ya sauka akan fareeda wadda khairat ta tafi da gudu ta rungume, mamaki ya kama ta'iba ganin wannan kyakkywar yarinyar ta nufi fareeda tana fadin wai mama to a'ina suka santa 'yan gayu dasu? "Sumy ce ta yiwa maigirma uwar gida ta'ibar falalu bayanin su din ko su waye Amma bata ce Mata ita kishiyar ta ce a da ba. Karasowa gurin su tayi tace musu "ku shigo daki Mana sumayya" tashi suka yi suka karasa dakin nata Babu laifi dakin a gyare yake sai dai yanayin ta ya nuna a cikin matsala take musamman yadda shigar ta ta kasance da yanayin ta duk ta jeme kamar ba fareedar da ta sani ba. Sosai sumy ta tausaya Mata . Fareeda ce ta zamo daga kan gado da yake dakin nata guda daya ne gado ne da madubi sai sif(drower) tace "sumayya ki yafe mun hakika nayi kuskure da abin da nayi muku ku tausaya mun ku yafe mun don Allah". Sannan ta dubi sauran yaran tace "'ya'ya na kuma kuyi hakuri ku yafe mun duk abinda nayi muku hakkin kune yake bibiyata wllh, matukar baku yafe mun ba to ba zanji dadi a rayuwata ta duniya da lahira ba, sannan sumayya ki taimaka kice wa Ameer shima ya yafe min dukkan cutarwar da na muku" kuka ne yaci karfin ta yayin da suka suke zubar da hawayen karfin hali sumy tayi tace "na yafe Miki fareeda shima Ameer ya yafe Miki dukkan mu Babu Wanda ya rike ki dai dai da kwayar zarra " Godiya ta Mata sannan ta tambayi yaran ya karatu suka yi ta surutu da yaran, can kamar kusan mintuna goma sai jin ta'iba tayi tace Mata "da kika zauna zaman surutu wani ne zai karasa Miki girkin ne ko so kike mai gidan ya dawo ya tarar da ba a gama girki ba ne ?? To maza fito idan za su jira to su jiraki ki gama yi mun aikina sai ki zo ki zauna kuyi ta shirmen ku" Suamyya ce ta ce da yaran "ku tashi mu tafi dama oga ya ce kada mu dade" Tashi sukayi sumy ta zuge zip din rigar ta ta dauko kudi ta bata, kar6a tayi ta Mata godiya sosai harda zubda hawayen farin ciki . Babu komai sumy tace sannan ta ce Mata "za kiga sako in Sha Allah, kina da waya ne?" Amsa Mata tayi da "babu waya a hannu na wannan matar ta kwace ta kuma na fada wa mai gidan sai yace inyi hakuri in rabu da ita tunda itace babba" Kai jam'a kuji wani bazawrin tashin hankali ko to ai dama hausawa sunce "Duk Wanda ya daka rawar wani to sai ya rasa turmin daka tashi" Haka suka tafi bayan sunje gida suka sanarwa da Ameer halin da fareeda take ciki, ko ajikin sa domin harkar gaban sa yake "kwandama" yace. Anan sumy take sanar dashi tana rokon yafiyar shi ya yafe Mata yace Amma abinda ta shuka ne take girba shi Babu wani taimako da zai mata, to idan ya taimaka Mata kuma mijin ta yaji labari fa me mutane za su dauke shi Yana bibiyar tsohuwar matar sa bayan ya sake ta? To ba zaiyi ba Allah ya yafe Mata abin da ta musu shine kawai magana. Kayan ta ta tattara wadan da ta gaji dasu Amma fa kar suke basu lalace ba haka ta hada Mata kusan kala biyar da sabon hijabi da turare ta aika gidan su ita kuma babarta ta Kai mata, lokacin da taje gidan ta kokawa yanayin da 'yar tata take ciki haka dai ta taho jiki duk a sanyaye. Su suwaiba arziki ya ha6aka ko ina aika kayan su suke alhamdulillahi sai godiyar Allah yayin da suka bude gidauniya ta Gina famfo har guda uku akan suna son ladan Allah ya kaiwa mijin su Alhaji Adnanu Allah ya gafarta masa. Maman Aslamiyya ta dawo gidan su suwaiba a cewar suwaiban za ta zame musu garkuwa sabida zaman su su kadai Babu dadi ita ma mamar tata gidan haya ne to mai biyan kudin hayar Allah ya yi mishi rasuwa Awwal Yayan aslamiyya, ga rayuwar ba irin ta da ba , haka ta dawo ta hada kawunan su suka Zama tsintsita madauri daya. Madam ta shiga halin 'ka'kani kayi ta rasa yadda za tayi karshe dai bara ta fara sannan ta samu ta dawo Lagos da kudin bara don masifa, taga rayuwa domin duk Wanda zaici hakkin wani sai Allah ya Sakawa wancan din Pretty ta koma gida sai dai ta tarar da labarin inyamura ta koma garinsu aikwa har can ta bita da yake tana da address din gidan su anan ta tarar da ita tana gashin masara a kofar gidan su,da farko bata gane zee din ba sai da kanin zee ya nuna Mata yace "ga aunty zee nan a kofar gida tana gasa masara " Karasawa tayi gurin ta ta ce "madam " A zabure ta Mike tsaye tace "pretty kece ? Pretty kinci amanar yadda da take tsakanin mu pretty kin cuceni, me kike nema agurina da kika biyo ni garin mu har gidan mu?" "Babu abinda nake nema a gurinki face na sauke Miki nauyin da kika dorawa kanki sauran kuma sai kije ki nemi yafiyar bayin Allah " Anan ta fada Mata yadda tayi da kudin ta da rasuwar Alhaji Adnanu da dalilin rashin lafiyar shi sanadin ta dauke masa kudi ta gudu ya shiga halin rashin lafiya har Allah ya sa ya mutu" Kuka zee take yi tace "yanzu alaji ya rasu na shiga uku na lalace me yasa na aikata mishi haka ? Ga shi ya mutu ban nemi yafiyar shi ba, Allah ka yafe mun " Kuka take anan mutanen gidan su suka fito suka ji abinda yake faruwa aikwa maman ta duka ta Mata tace "segiyan yarinya mai bakin hali kin cuci mijinki mai kaunarki kin sace masa kuttti kije keda Allah tunda ya mutu baki nemi afuwar Shiba segiya "ta Kai Mata duka. Alhamdulillahi Ameer ya biya musu kudin tafita aikin hajji shida sumy yayin da yaran za su koma gidan iya. Bayan sunje kasa mai tsarki sun dawo sumy tayi yiwa mutane da dama tsaraba ciki harda fareeda da kawarta Aslamiyya da karima musa. Kai harda Fatima kanwar Nasir tsohon saurayin ta . Rayuwa tayi dadi Babu wata hayaniya da hauragiya komai lafiya. Sumayya an zama babbar mace yayinda ta Kara haihuwar 'ya mace wadda taci sunan ta sumayya ana kiran ta da NOOR . Alhamdulillahi Anan na kawo karshen wannan gajeran labarin mai suna a sama wato ZAMAN 'YA'YA NA Abinda yake dai-dai Allah ya hada mu a ladan kuskuren da nayi a cikin sa Allah ya gafarta min Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anlaaaailaha illa anta astagfiruka wa'atubi ilaika Amina Mamu Gumel Mmn Annur Mu hadu a wani book din. Sakon gaisuwa ta a gareku 'yan ZAMAN'YA'YA NA FANS, DA MALAMIN BOGI GROUP HAUSA NOVELS. INA GODIYA MUSAMMAN GA HAPSA , SANNAN DA AYSHA🥰🥰🥰 da duk mabiya zaman 'ya'yan na . .Ina godiya Meenatu Amjuf.