[10/18, 5:33 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: https://chat.whatsapp.com/LimnMeG0kWvIfT6JQvVMh1 ☆❁ 𝗛 𝗨 𝗥 𝗜 𝗬 𝗬 𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 *©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠* Wannan Littafin Sadaukarwa ce ga. Zainab A Baba Abokiyar Hira. Asma'u Badamasi Bauchi And Hafsat Muhammad Betuwa Maman An-noor i appreciate your love 🥰❤ H U R I Y Y A -Labari ne mai ban tausayi da taɓa zuciya. Story of the 2nd October 2023 𝐑𝐚𝐧𝐚𝐤𝐮𝐧 𝐏𝐨𝐬𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐌𝐨𝐧𝐝𝐚𝐲 𝐓𝐮𝐞𝐝𝐚𝐲 𝐖𝐞𝐝𝐧𝐞𝐬𝐝𝐚𝐲 𝐓𝐡𝐮𝐫𝐬𝐝𝐚𝐲. Idan kina da wani abun da kike so a tallata miki you can chat me on 08036126660 or https://wa.me/qr/3D4THFJXLUGTM1 Bismillahi Rahmanin Rahim... 𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣ Babban gidan sama ne mai dauke da bangare biyar, na farkon da na biyu zuwa na uku da hudu sukansu suna facing din babban gate din gidan. Yayinda dayan wanda shi ne na biyar yake dama da part din hudun, dukannin part din suna da karamin gate da zaka iya hango wanda zai shiga ko ya fita, haka zalika ko wane part yana da gurin aje mota kamar uku sai kuma karamin filin da za a iya wata hidimar idan da bukata. An kawata kowane entrance na parts din da fulawowayin na kasko, a ko wane bangare akwai kujeru da aka tanada domin hutawa ko shan iska. Babbar harabar gidan wani katon fili ne da za a iya gina kananan gidaje hudu ko biyar, ko wace kusurwa da ginin na jikin gidan an dasa masa dagayen itatuwa, tsakiyar compound din kuma an yi masa round da flowers. Ko masu gadin gidan kadai ka kalla ka san ba kananan kudi suke samu ba, balle kuma ka sauke idonka akan manyan  motoci da aka jere a harabar da aka tanada domin aje motocin Alfarma, bayan mota biyu wasu daya wata uku da suke aje a kowane bangaren uku da suke gidan. End of discussion shi ne sunan da mafi akasarin jama'ar unguwar suke kiran gidan da shi, ba a unguwar Millions Quarters ba kawai, kusan duk wanda yake cikin garin Gusau ya san gidan Alhaji Haruna Mai Yadi, saboda yadda jama'a suke yawan labarin gidan da irinsa a rare a garin Gusau. Kasancewar ba kowa yake damuwa ya gina gida mai kyau da fasali kamar yadda shi ya zabi ya bayyana nashi arzikin ba a fili ba. A cikin part hudu da suke gidan uku ne suke dauke da iyalai yayinda dayan da ya banbanta da saura kuma ya kasance na Alhaji Haruna Mai Yadi, part din farko na Hajiya Kaltume ne uwargida ran gida, wato Uwargidan Alhaji Haruna a yanzu, sai mai bi mata Hajiya Nafisa da ake kira da Momy, sai ta ukunsu wadda ta zama turmin tsakar gida hausawa suka ce sha luguden mahassada wato Hajiya Iyami ake kira da Amma. Dayan part din wanda shi ne cikon na hudu, part ne da ba a taba zamansa ba, kasancewar matansa uku ne a yanzu tsabanin hudun da ya ci burin yi. A kowane part akwai dakin yara na maza dabam na matan dabam, akwai sitting room har biyu karami da babba, sai bedrooms din ko wace mata dake dauke da mayan furnitures na alfarma, dukannin furniture din parts din iri daya ne sai dai kala ta banbanta. Na dakin Hajiya Kaltume red color ne tun daga kan kayan dakin kujeru har zuwa curtains dinta, sai dai an yi musu ado da ratsin golden hakan ya kara musu kyau gashi yaranta na taya ta gyara bangarenta kasancewarsu yan mata masu wayo da son kwalliya domin yan matanta hudu, Umm Kultoon wadda ta ci sunan mahaifiyarsu ake kiranta da Maama, sai mai bin ta Umm Salma, Umm Khairi, da kuma yar auta Umm Ruman, sai dai dukansu suna bin bayan babban ďanta Yassar ne da ya kasance namiji daya tilo a yayanta. Bangaren Hajiya Nafisa kuma wato Momy ta kawata nata bangaren ne da ash color, white curtains dinta ne kadai suka banbanta da Turkish cushion din da suke falon ita ma tana da yaya uku mazanta biyu Musib, Miwan sai auta mace Namra. A dayan part din kuma wanda ya kasance na Hajiya Iyami wato Amma ya fita dabam da sauran dakunan domin komai nata na daki da falo fari ne fol, irin farin nan mai kyau da burge idon mai kallo, duk kuwa da kasancewar nata yaran kanana ne Hurriya sai mai binta Hamad sai kuma cikin da take dauke da shi a yanzu, ita ce karama a cikin matansa kana kallon Alhaji Haruna ka kalleta ka san ya kusa haihuwarta ko ma ace ya haifi kamar ta. Bayan wadannan iyalan Alhaji Haruna Mai yadi yana da wata yar da ya haifa da matarsa ta farko mai suna Maryama, sun yi zama a tare tun a lokacin da yake amsa sunansa na Haruna Mai Yadi, kusan duk wata wahala da fadi tashin rayuwa tare da ita aka yi, kamin daga bisani ya auro Hajiya Kaltume wadda ita ce uwargida a yanzu sakamakon rasuwar da uwar yarsa ta farko ta yi wato Sapna wadda take a gidan aurenta a yanzu, sai dai kulawarta da ta mijinta duk yana karkashin mahaifinta ne, abun da hausawa ke cewa an siyar da akuya ta dawo tana cin danga, domin an aurar da ita ne ga talaka kuma a lokacin da mahaifinta yake talaka kamin arzikin ya bude masa, hakan ya saka a yanzu gidansa ya cika da ƴaƴan yan'uwansa da na yan'uwan matansa. Daga uwargidansa mai rasuwa Maryam har Hajiya Kaltume irin matan nan da ake cewa auren fari auren talauci, ya auresu sun kamin yayi arziki ba tare da duba kyau hallita ba, kyau hali dai abu ne da yake a bayyana domin uwargidansa ta farko da kuma Uwargidansa ta yanzu basa ga maciji da juna, basa da aiki sai yawan fitina da fada da juna, har Allah ya dauke rayuwar Maryamu. Arziki kashi inji hausawa, bayan rasuwarta ne Haruna mai Yadi ya fara samun daukaka kofofin arziki suka bude masa gabas da yamma, a cikin lokacin ne ya auro Hajiya Nafisa yar mai gidansa, kasancewarsa mutum ne da ba shi da ra'ayin zama da mace daya, ba laifi tana da nata kyaun kuma ya dauko mace yar gidan mutunci da karamci sai dai ko kadan albasa ba ta yi halin ruwa ba, domin tana zuwa gidansa ta fara yi masa gorin arziki duba da nata mahaifin ya ninka Alhaji Haruna Mai Yadi kudi ta ko'ina, a lokacin da ya auro ta nasa arzikin be kai kamar yanzu ba, abu kadan idan aka taba ta sai tace ita yar Alhaji Garba kudi Kasa ce, hakan yana daya daga cikin abubuwan da suke yawan hada ta fada da Hajiya Kaltume da kuma Mijinta Alhaji Haruna, domin tana yi ma Hajiya Kaltume gorin arziki Hajiya Kaltume kuma tana mata gorin anga mijinta da kudi an aure. Ta bangaren Alhaji Haruna kuma ba sha da dadi a hannunta domin so take komai sai ya banbanta mata da Hajiya Kaltume saboda ita yar masu hannu da maiko ce, shi kuma a gurinsa yana ganin hakan kamar rashin adalci ne, kuma be yarda ya aikata abun da zai hana shi zaman lafiya bayan mutuwarsa ba. A haka dai aka yi ta zaman da dadi ba dadi har Allah ya kara buda masa ya tashi daga Alhaji Haruna Mai Yadi zuwa Alhaji Haruna Mai Motoci. Duk wanda ke garin Gusau ya san Mai Yadi Motors a ciki da wajen Zamfara, domin babban kamfani ne mai kawo manyan motoci na zamani, ba a iya nan ya tsaya ba, ya raba hannu ta bangaren shigo da kayan masarufi da gine gine na zamani a garin Gusau, Kaduna da kuma Abuja. A lokacin da ya zama cikaken mai kudi ne Hajiya Kaltume ta nemi daukar masu yi mata hidima ta komai a gida miji, domin Momy da nata masu aikin ta zo tun daga gidansu tsabar nuna isa da gata. Sai dai ko kadan surukarta kuma mahaifiyar Alhaji Haruna Mai Yadi bata so haka ba, Wato Hajiya Binta, Hajiya Kaltume har Momyi ba su saurareta ba saboda rashin ganin kimarta da girmamata, ita ma kuma tana taka tsantsan da matan ďan nata gudun kar suce ta shige musu hanci domin mace ce mai gudun fushi da kiyayyar zuciyar kowa. Wannan ya saka a lokacin da Allah ya buda masa ta nemi yayi mata nata gidan dabam, ta zauna tare da nata yayan idan sun zo da kuma jikokinta. Balkisu ce farkon mai aikin da aka fara kawowa a gidan a bangaren Hajiya Kaltume, Balkisu yarinya ce mai tsabta da iya aiki ga far'a da son aiki, hakan ya saka Hajiya Kaltume ta riketa da kyau ta sakar mata ragamar komai ciki har da kula da yayanta da kuma girka abincin mijinta. Daga lokacin da ta karbi girki komai ya canja ko yaranta sai da suka yaba da canjin da aka samu domin Balkisu wadda ake yi wa inkiya da Iyami tun tashinta yarinya ce yar zamani ce da ta san kan kalolin girki da ďanďannonsu, shi kansa Alhaji Haruna sai da ya yaba da girkin sabuwar mai aikin tasa tun kamin ya yalla idonsa a kanta. A lokacin da idonsa suka yi arba da ita kuma sai kimarta da kwarjinta suka karu a idonsa, kasancewarta kyakkyawa mai kurciya fiye da matansa ga jiki daidai ba mai ƙiba da baƙi kamar Hajiya Kaltume ba, fara doguwa ba guntuwa da kiba kamar Momy ba, jikinta be yi yawa ba kuma be yi kadan ba, yar bulbul da ita, haskenta mai kyaun ne cikin ma bata samu hutu da jindadi ba. Ga tarbiya da girmamawa idan zata gaishe shi sai ta kai har kasa, idan ya bata abu hannu biyu zata saka ta karba, da haka ta fara siye zuciyarsa har ta kai ya fara ninka albashinta kamin ya fara nuna mata alama, daga baya kuma ya fito fili ya fada mata burinsa bayan ya san komai a akanta. Tsoron Hajiya Kaltume da duban level din arzikinsa da nata ba daya ba, ya karya mata guiwa gurin amsa masa bukatar da ya zo mata da ita. Sai dai kuma rabo idan ya rantse dole komai sai ya afku, rabon samun Hurriyya da Hamad da kuma karamin cikin dake jikinta ya saka Alhaji Haruna yayi nasarar lurar da ita cewar tana cikin irin matan da yake so tare da nuna mata shi ma a da can talaka ne kamar ita, kuma a yanzu zai saka zane ya tare duk wata ƙura da zata taso. Kwadayi irin na talaka ya leka gidan mai arziki da kuma burin son taimakon iyaye da samun rayuwar jindadi ya saka Iyami ta amince da bukatar Alhaji Haruna. Sai aka shirya auren a boye sai bayan da da Hajiya Kaltume ta tafi Ummara sannan aka daura auren, Amarya ta tare da Mahaifiyarsa Hajiya Binta, daga lokacin ne sunan ya tashi daga Iyami wanda ta taso da shi tun kirciya ya koma Amma domin a lokacin ta wuce ƴaƴansa su kirata da sunanta Iyami dole su sakaya saboda mahaifinsu. A lokacin da Hajiya Kaltume ta dawo sai zaman lafiya ya gagari Amma da mijinta saboda fitina irin ta Hajiya Kaltume da gori da wulakanci saboda tana ganinta yar aikinta, gashi kuma Momy ma da take ganin kamar ita aka yi kishiyar bata raga mata, ba ita kadai ba kusan duk wanda ya san ta yi aiki a gidan kuma ya ji ta aure mai gida zai jefeta da kalmar cin amana. Wannan abun ya tabata matuka sai dai samun Hajiya Binta wato mahaifiyar Alhaji Haruna ya wanke mata rabin damuwarta domin tana sonta fiye da yadda take son abokan zamanta Hajiya Kaltume da Momy, domin Amma tana yi mata biyayya gwargwadon hali, ta dauke ta tamkar uwa da ta haifeta, ta rike da mutumci abun da sauran matan suka gagara yi mata. Tana jin dadi zama da ita kamin Hajiya Kaltume da Momy su ta da fitinar cewar sai dai ya hade su guri daya, suna ganin kamar ita Iyami da ya ware dabam ya hade da mahaifiyarshi ya fi bata jindadi fiye da su, hakan ya saka shi gina babban gida a unguwar Millions Quarters cikin rukunin manyan gidajen da ake ta gasar ginawa a unguwar. Na shi gidan ya fita dabam saboda kyau da tsari da aka yi ma katon gidan. Bayan haihuwar Hurriya Alhaji Haruna ya tare a gidan tare da Iyalinsa, a lokacin Amma tana da tsohon cikin Hamad, bayan tarewa gidan da wata daya ta haifo ďanta Hamad mai shekara goma da daya a yanzu, tun daga lokacin kuma sai haihuwar ta yi mata shiru tun tana damuwa har ta daina, ta rumgume yayanta biyu da Allah ya bata Hurriya da Hamad. Amma ba mace ce mai yawan shige shige ba wannan ya saka a duk lokacin da aka ce ta nemi taimako sai ta ki, domin bata san gurin waye zata duka ta tara hannu ya bata magani ba, sai Allah. A yanzu kuma da Allah ya tashi bata haihuwar sai ya kawo cikin na uku daman da kurciyarta a yanzu ne take cin nata lokacin ba kamar abokan zamanta da mijinta da suka bata kusan shekara goma sha biyar biyar ba, mijinta kuma ya bata kusan shekara ashiri. Domin yarta ta farko Hurriya a yanzu tana da shekara goma sha biyar ne, a yayinda ita kuma take da shekara goma sha shida da auren a gidan Alhaji Haruna Mai Yadi wanda shi ne mijinta na farko. Hajiya Kaltume da Momy kuma duka last born dinsu shekarunsu goma sha bakwai ne a yanzu. Iyami ta sha wahala sosai a gurin abokan zamanta na makirci da tukgu irin na kishiyoyi, yarta Hurriya kuma ta sha wahalar yan'uwa wadanda suke uba daya tun tana karama har girma, suna yawan hantararta da gori ga duka kamar ita din ba ďaya take da su ba. Hurriya kyakkyawa ce sosai irin kyau nan mai matukar daga hankalin wanda ya san kyau da sirrin kyau, irin kyau da ke shiga cikin ido ya afka a kwakwalwa ya zauna a zuciyar mai yinsa, irin kyau da idan ka kalleta sai ka sanar da zuciyarka tabbas tana da kyau, irin kyau da sai bakin ya bawa dan'uwansa labarin kyauta, ko kadan bata dauko mahaifinta a baki da muni ba, domin kowa ya san Alhaji Haruna ya san ba kyakkyawa ba ne, wasu har kirari suke masa ba dan kudi ba da sai bola, shiyasa a lokacin da aka yi aurensu da Iyami kowa yake cewa ta bi kudi shi kuma ya bi kyau. Hurriya mahaifiyarta ta dauko sai dai ta dara mahaifiyarta kyau nesa ba kusa ba, ta fita haske ta fita komai hakan ya saka ta fita dabam kamar ba yar gidan ba, domin yaran Momy ma da suke da kyau ba su kai Hurriya kyau ba balle kuma yaran Hajiya Kaltume da suka dauko ta wasu kuma suka biyo mahaifinsu, ba laifi suna da nasa kalar kyau, domin ko wace halitta ta Allah kyakkyawa ce. Duk tarin kyau da haibar da Hurriyya take da shi tana da wata lalura da aka haife ta da ita ta rashin gani, bata iya tantance komai sai da gilashi, idan babu gilashin ido a tare da ita wato medical glasses bata iya banbance fuskar kowa sai dai ta yi amfani da murya, tana iya ganin abun da ke gabanta ko gefenta haka ma ta kan iya banbance mace da namiji ta hanyar sifar da tufafin jiki, sai dai ba zata iya fadar yadda fuskarsu take ba, domin dishe-dishe take gani, kusan eyeglasses shi ne rayuwarta bata iya komai sai da shi idan yana a idonta tana ganin komai clearly kamar yadda kowa zai gani ko ma fiye da haka, idan kuma babu bata iya karatu bata iya ganin kyau ko munin mutum, hakan ya saka bachi kadai ke rabata da gilashi. An nema mata magani har an gaji amman babu sauki babu alamarsa, wani gurin ma a madadin samun sauki sai idon ya kara dishewa, tsoron kar ta rasa idon gaba daya ya saka aka daina nema mata magani Alhaji Haruna ya saka likita kwarare ya duba idonta ya fadi kalar gilashin da zai dace da ita mai kyau da tsada, mahaifinta ya saka aka kera mata har guda biyar a lokaci daya. Biyu daga cikin gilasan da mahaifinta ya saka aka kera mata ne suke hannunta, sauran ukun suna gurin Yayanta Yassar ya aje mata a bangarensa gudun kar su bata, domin tasu ta zo daya shi kadai ne take jin sanyinsa a cikin Yayan Hajiya Kaltume ya ke sonta da nuna mata kulawa tsakani da Allah kamar kanensa da suke uwa daya uba daya, Yassar kam ya fita dabam kusan ya fi sabawa da Hurriya ma fiye da sauran yara da suke gidan, yana sake mata fuska tana wasa da shi kamar ita da shi din abokan wasa ne. Idan yana gidan bata da hutu ga tsokanarta da yake yawan yi. Yassar yaro ne mai mutunci da kamanta gaskiya, domin yana ba wa Amma da Momy dukanin girmansu sam baya biye hudubar da mahaifiyarsa take masa, be taba yarda ya hau turbar da take dorashi ba, Munib da Miwan suke kan gaba gaba gurin taya Momy kishi dama da hagu har sun fi yar'uwarsu maace taya mahaifiyarsu kishi. *** *** *** Wannan Kenan, shimfida ce da share fagen yadda labarin zai tafi, labari ne mai ƙayatarwa da sarkakiya da kuma ƙulla-ƙulla sannan yana dauke da darasi na rayuwa. Allah ya sa mu amfana da shi kuma ya ba ni ikon gamawa lafiya kamar yadda na fara. Sannan ina son ku sani labarin nan ban yi shi dan wani ko wata ba, idan ma ya yi daidai ko ya ci karo da rayuwar wasu, to arashi aka samu. Tare da fatar za ku tara hannu biyu ku karɓa kamar yadda kuka saba karɓar labaraina cikin farinciki da ɗauki, sai a taya ni da addu'a na baku abun da kuke so, ma'ana na faranta ranku fesss 😀 Masoyana Asallamu Alaikum mun sake haɗuwa a wata sabuwar tafiya, Allah ya sa mu wanye lafiya kuma mu kai karshenta cikin farinciki da Amince. Sakon gaisuwa da fatan Alheri daga taku mai son farincikinku Khadeeja Candy🥰 08036126660. [10/18, 5:33 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: https://chat.whatsapp.com/LimnMeG0kWvIfT6JQvVMh1 ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝗣𝗮𝗴𝗲 2️⃣ Ta aje plate din hannunta da sauri ta zari tissue ta goge bakinta. “Amma na tafi kar na yi latti” Amma dake kokarin jefa tawul a ruwa ta ce “Kya ji da shi, kullum ke ce uwar yan latti sai an jiraki, ga kokari ga buga latti” Hurriya ta dauki jakarta ta makaranta da sauri ta goya tare da daukar lunch box dinta ta fice daga falon da gudu, kamar zata fadi haka ta isa bangaren Appanta sai haki take kamar wadda aka yi yakin duniya tare da ita. Hannu ta mika jikin window falon kamar yadda sauran yan mata sa'aninta da wandanda suka girmeta suke mika na su hannu suna karbar karamin hollandia da chocolate da yake raba musu, tana son karba yan'uwanta na tureta tana yin baya har sai da suka gama karba sannan ta samu karba daga gurin mahaifinta, kyautar wani abun ci da ko abun sha a kowace safiyar week days wani abu ne da ya sabawa yaransa da shi tun suna kanana. “Na gode Appana” Ta fada tana murmushi jindadi, shi ma murmushin yayi yana kallon kyakkyawar yarsa, mai yawan yi masa godiya da nuna masa jindadinta a duk lokacin da yayi musu kyauta komai kankantar kyautar domin haka mahaifiyarta Amma ta koyar da ita, kusan ita ce karama a cikin yayansa mata a cikin maza kuma kanenta Hamad ne karami ƴaƴansa na jini amman ya fi sauran yayansa godiya da yabawa idan yayi musu abu. “Allah ya miki albarka Hurriya, ga ladabi ga basira” Ta yi yar siririyar dariya mai sauti. “Appa haka Uncle dinmu yake cewa, har da cewa yayi wai akwai wata gasar da zan sake shiga” “Da kyau ni ma ya fada min haka, kuma yace wannan gasar ma mai tsoka ce, suna kyautata zaton idan kika yi ta daya za su dauki nauyin karatunki domin haka suke yi ma duk wadda yayi na daya, ni kuma na kara musu da cewa ko da ba su fitar da ke ba, zarar kin kallama makarantar da kike yanzu zan fitar da ke waje ki yi karatu mai kyau, duk kuwa da bana sha'awar fitar da ƴaƴa mata waje yin karatu amman ke zan fara akanki” Ba shiri Hurriya ta bude baki tana mamakin jin furucin mahaifinta. “Appa da gaske?” “Da girmana zan yi karya?” Ta saki chocolate din da hollandia ta rufe baki tana zaro ido kamar zai fado. Sai kuma ta daka tsalle ta dire. “Appa i love you i can't wait” “Ki dage da karatu Allah ya taimaka ina alfahari da ke, Allah ya miki albarka” Ya fada yana murmushi yana nuna mata alamar lokaci a hannunsa da babu agogo, sai ta duka ta dauki abun da ta zubar ta. “Ameen ina sonka Appana, na tafi sai na dawo” “Allah ya kiyaye,” Ta amsa da Ameen already ta sauka entrance din tana hadawa da gudu domin yan'uwanta sun kusa isa gurin bus din dake kaisu makaranta ta maido su. Tana daf da isa ta ji an fisge chocolate din dake hannunta kamin ta juyo aka fisge madarar hollandia din dake dayan hannunta. Suna hada ido ta bata fuska ta buga kafa kasa, shi kuma ya saka dariya yana kokarin bude ledar chocolate din. “Yaya Yassar dan Allah ka ba ni” “Wallahi ba zan baki ba” Ya fada kai tsaye yana mata dariyar keta, juyawa ta yi cikin yanayin damuwa ta koma bangaren Appanta wannan karon bata tsaya gurin windows din ba ta murda kofar falonsa ta shiga, sanin talkamin makaranta ne daure a kafarta sai ta fadi kasa tana rarrafe dan kar ta taka masa carpet. “Appa Appa Appa” Alhaji Haruna ya fito daga dakinsa da sauri jin yarsa na kiransa. “Hurriya baki wuce ba?” “Appa YaYa Yassar ya kwace min abun da ka ba ni, na kowa yana nan ni ya karbe nawa” Appa yayi murmushi ya juya ya koma ciki, be dade ba ya fito rike da wani chocolate din da hollandia ya mika mata. “Appa dan Allah ka kora Yaya Yassar daga gidanka ka ce ya tafi ya bar maka gidanka, Wallahi takura min yake yi da yawa” Tana fada tana saka hannu biyu ta karba. “Idan kin hadu da shi a yanzu ki fada masa na ce ya hada kayansa ya bar min gidana, saboda ya cika takuraki ke da gidan Appanki” “Appana na gode, zan fada masa haka a yanzu kuwa” Cikin shagwaba da jindadi ta fadi haka sannan ta mike tsaye shi kuma ya kai hannu ya shafa kanta dake cikin hijab domin ya fahimci a bakin gaskiyarta take fadar Yassar ya bar gidan. Tana kokarin juyawa Amma ta shigo falon dauke da tray, bata yi mamakin ganin Hurriya a sitting room din mijinta ba, daman ta fi kowa yin latti zuwa makaranta ko fita unguwa. Musamman idan mahaifinta yana gari, a dole sai ta ganshi sannan zata fita, idan kuma bata zuwa ko'ina to tana zaune tare da shi a bangarensa babu ruwanta da ranar girkin Amma ne ko na Hajiya Kaltume ko Momy, ko da bata shiga har inda yake ba indai ta san yana nan zata zauna a part dinsa ne, hakan ya haifar da shakuwa sosai a tsakaninsu. “Daman ai duk wanda yayi shiririta a garin Gusau a bayanki yake, ke kam Allah ya shiryar da ke Hurriya” Dariya kawai ta yi ta fice tana fadin. “Appa ka fada mata abun da Yaya Yassar yayi min. . .” Daga mahaifiyarta har mahaifinta binta suka yi da kallo jindadi da farinciki har ta fice, sannan Amma ta girgiza kai ta maida dubanta ga Appa. “Bismillah Appan Hurriyya muje ka karya” Kamar wanda aka jefo a wata duniyar haka yanayin fuskarsa ya sauya daga murmushi da jindadi zuwa bakinciki da bacin rai da be san dalilinsa ba, ba dan komai ba sai dan jin muryar Amma a bayansa. “Zan shigo” Ya amsa ba tare da ya jiyo ba, domin baya son kallonta a yanzu, fuskar dake masa kyau da kwarjini, mace da yake gani yana jin kamar shi da ita sa'anin juna ne, a yau ita yake kyamar gani, muryar da ta fi kowace murya yi masa dadi a duniya yau muryar ce yake jin kamar tana sanar masa mutuwa. Cikin hikima da kokarin danne damuwa ta sauke ajiyar zuciya domin ta san shekaru da aka fito da watanni mijinta ba haka yake ba, a da idan ta kawo masa abinci jiki na rawa yake tarbarta ya fara zuba santi tun kamin ya ci, ba zai ma bari ta fara isa bedroom dinsa ita kadai ba sai ya rika mata tray ko ya dauki wani abun yana zolayarta, amman a yan kwanakin da idan aka a hada su aka kirga zai bada wata daya ya sauya mata gaba daya. Sai da ya tabbatar ta shige sannan ya juyo ya kalli kofar dakin, hannu ya saka a kirjinsa ya danne tashin hankalin da yake jin yana kusantoshi. Cikin wani yanayi mai kama da nauyin jiki da na zuciya ya cira kafarsa ya fara takawa tare da maida hannayensa baya ya rumgume yana tafiya a hankali. Yana shigowa cikin dakin Amma ta juyo ta kalleshi da damuwar da ta gagara boyuwa a fuskarta. “Ranka ya dede waya canja Bedsheet din nan?” Tsaye yayi yana kallonta kamar mai tunanin kalar amsar da zai bata, kana kallon idinsa zaka karanci damuwar dake tare da shi. Can kuma ya kawar da fuskarsa ya dawo da hannayensa dake rumgume a bayansa ya zuba su cikin aljihu. “Kaltume ce ta canja” Da matukar mamaki Amma take kallonsa, domin al'adarsu ce duk wanda ke da girki ita zata gyara bangaren mijinta kuma zata tafi da Bedsheets dinta ta shimfida, idan wata zata karbi girki sai ta kwashe kayanta wadda ta karba ta shimfida nata ta kula da bangaren, hakan ya saka ko wace mace da kalar kamshin turaren dake fita a part dinsa idan girkinsu ya zo. “Ban gane ta canja ba? Jiya na shimfida shi fa, kuma jiya da yau girkina ne, ai ta jira har sai girkinta ya zagayo tukuna ta canja” “Ni na saka ta canja kuma na karya zaki iya dauke abincinki” Kamar an watsa mata ruwa sanyi a jiki haka ta ji duk wata kusurwa da logo dake jikinta ya saki, lakkar jikinta ta yi kasa. “Gaba daya na daina gane maka a yanzu Appan Hurriyya ka canja min” Ta matsa inda yake tsaye ta risina kasan guiwowiyinta ta hade hannayenta kamar mai rokon gafara. “Wannan shi ne karo na biyar da zan sake rokonka idan wani laifi na yi maka ka fada min na nemi yafiyarka, ka dubi girman Allah ka yafe min, ka daina hukunta ni da wasu dabi'u da halayya da ban sanka da su ba, kuma baka saba yi min ba” “Baki min laifin komai ba Iyami, Wallahi ban rike ki da wani abu ba a zuciyata ba” Ta daga kai ya kalleshi. “Toh me yasa kake min haka? Akan wani dalili zaka saka Hajiya ta canja zanen gado kuma ta kawo maka abun karyawa bayan ni ce da girki?” “Saboda zata karbi girki a yau” Kamar an tsinke wutar cikin jikinta haka ta ji, sai ta mike tsaye tana kallonsa ta kasa sake furta komai. Hannayensa ya cire aljihu zuba ya nufi kusa da inda ta aje masa tray ya zauna gefen gadonsa sannan yayi mata alama da ta zo ta zauna. Ta kalli gurin da ya nuna mata amman ta kasa cira kafata ta isa gurin. “Zo ki zauna Iyami” Sai a lokacin ta ji kuzari ta cira kafarta ta taka har ta isa gurin ta zauna jiki a sanyeye tana kallonsa. Ajiyar zuciya ya sauke kusan sai uku sannan ya kai hannunsa ya bude bedside drawer ya dauko wata yar karamar jaka ya bude ya dauko wasu takardu ya mika mata. “Wannan takardun gidana ne da yake a Samaru, na saka lawyer na ya canja komai daga sunana zuwa naki, na kafa shaida da lawyer na kuma ta bangarenki na yi magana da Bappa shi ma ne shaida domin a gabansa aka yi komai, sai dai na bukaci kar ya fada miki saboda ina son ya zama ni zan fara sanar da ke, saboda haka yanzu gidana dake Samaru mallakinki ne halak malak...” Ta mika hannu biyu ta karba cikin yanayin mamaki da faduwar gaba, ta kasa godiya haka kuma ta kasa jin farinciki ko kishiyarsa. Wata karamar Envelop ya dauko a cikin jakar ya mika mata. “Wannan Cheque ne na Naira miliyan Ashiri, ina son ki yi amfani da kudin ta hanyar da ya dace ki yi kasuwanci ki rike kanka dan Allah” Ta karba idonta na cika da hawaye. “Wannan duk na minene?” Yayi shiru ya kasa ce mata komai, sai ya sake saka hannunsa ya dauko wani envelop din ya mika mata. “Ki yi hakuri Iyami, ina jin rashin natsuwa da faduwar gaba da tashin hankali a duk lokacin da girkinki ya zagayo, idan na tuna kina a cikin gidana karkashin kulawata sai na ji kamar zan mutu, na yi ta daurewa ina ganin kamar abun nan zai wuce amman ban ga alamar haka ba, a kullum sai kara yin gaba abun yake, akan hakan na yanke hukuncin yin abun da zai zame mana mafita gudun kar na cutar da ke, domin idan muka daure a haka ban san a gaba yadda zama zai kasance ba” Kasa mika hannu ta yi ta karba kuma ta kasa ta kasa cewa komai, ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa, hawaye kuma suka ce mata ga rabarsu. Ganin haka ya saka ya aje mata takardar a saman takardun da ya mika mata. “Bana son ki bar min komai duk wani abun da na siya miki tun daga kayan daki har tufafi da duk wani abun more rayuwa, mallakinki ne zan saka a kawo miki har gida, amman dan Allah ki bar min Yayana a hannuna ban yarda ki tafi da ko daya ba, cikin dake jikinki ma idan kin haihu zan dawo da abu na a gidana” Sai a lokacin ta samu kuzarin bude bakin da yayi mata nauyi ta yi magana. “Babu uwar da zata so wasu yayan kamar nata, kuma babu yayan da za su jidadin wata uwar kamar ta su, musamman a gida irinka” “Kin fi kowa sanin yadda nake son ƴaƴana, da uwa ko babu uwa za su jidaɗin zama a gidan mahaifinsu, zan kula da su” Ta haɗe wani abun da ya tsaya mata ta miƙe tsaye da tunani kala kala, ta bude takardar ta duba me ke ciki saki ne ko akasin haka? Idan sakin ne saki nawa ne? Ko kuma dai ta faɗi a ƙasa ta yi masa kuka ta roƙi ya maida ita bayan ya faɗa mata baya jin natsuwa da kwanciyar hankalin a zamansa da ita yanzu? “Allah yasa hakan shi ne alheri, kuma ya baka ikon kula da su Hurriya da Hamad” Ita kanta sautin murya mai kama da tata take jin tana fita a bakinta, domin bata da tabbacin tana da kuzarin furta masa wani abu a yanzu. Tana jan ƙofar ɗakin nasa ta ji ƙafafuwanta sun yi nauyi, mararta ta murɗa wani irin tashin hankalin da bata taɓa samun kanta a ciki ba ya baibayeta. Da gaske Appan Hurriya sakinta yayi? Anya zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta? Ko dai wasa yake mata wata ƙila kuma wunin yau gaba ɗaya be faru ba. Tana tafiya jini na mata zuba amman bata sani ba zafin zaton sakin da bata tabbatar ba ya manta da ita zafin mararta dake murɗawa, ya hana hankalinta kusanto jikinta ya juya tunaninta a gurin abun da bata taɓa mafarkin faruwarsa ba. Arzikinta ɗaya, ko wane part an yi masa corridor da zai sada ɓangaren da ɓangaren Alhaji Haruna ba sai ta gaban gidan ba. Kuma zaka iya fita ko shiga ba tareda sanin kowa ba, har sai idan mutum ya isa part ɗin. Kamar wadda ta sha giya haka ta isa ɓangarenta ta zarce bedroom ɗinta ta zauna a kan gadonta. “Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un” Ta furta daker tana kokarin dawowa hayyacinta. “Haka ake ji? Haka saki yake? Ko dan ina da kurciya ne? Ko kuma saboda ban saka tsammanin zuwan sakin ba ne gaba daya a zaman rayuwata? Ko kuma saboda ina tsoron barin ƴaƴana ne? Allah ka sassauta min, ka saka min natsuwa da kwanciyar hankali, ka hallata aure ka hallata saki, Allah ka yaye min wannan damuwar da zata rufe ni, Ubangiji ka tsaya min” Rahamar Allah ga bayinsa, da kuma dace ya ƴan amin a kusa, tana gama addu'ar ta ji natsuwa ta sauko mata, numfashin da take jin kamar zai danne mata kirji ya daga mata, mararta ta sake murdawa har sai da ta lumshe ido ta kai hannunta ta taba cikin dake jikinta na wata shida. Kamar wadda aka yi ma allurar kuzari haka ta tashi ta aje takardun hannunta ta shiga bandaki ta gyara kanta ta fito ta gyara dakin inda ta ɓata ta cire Bedsheet din ta bar gadon a haka, ta dauki ruwa da tsumma ta bi tana goge jinin da bata san ya zuba ba sai a lokacin. Kamar mai shirin yin sata haka ta shiga ɓangaren ta goge jinin sannan ta juyo gabanta na tsananta faɗuwa ta fito daga ɓangaren. Ganin jinin yaƙi tsaya mata ya saka ta sake tsabtace jikinta ta saka pant da pad ta tare sannan ta kwanta saman gadon tana sauraren zuciyarta da ke bugawa da karfi, mararta kuma na cigaba da murdawa. “Me na yi ma Appan Hurriya?” Shi ne abun da take ta tambayar kanta, tambayar da bata da amsarta, mulmulawa ta yi saman gadon tana karewa katon dakinta kallo kamin ta tashi zaune ta fashe da kuka mai karfi, a rayuwarta bata taba fuskarta wani abu na tashin hankali irin yau ba. Cikin kuka da bakinciki ta dauko akwatunanta ta fara zuba kayanta ba tare da ta tsaya shiryasu ba, wani abun ma sai dai ta gwamatsa shi cikin wani talkaminta da atamfa ta saka su a kwati daya, sai da ta gama ta rufe ta kaisu gurin kofa ta aje ta dawo cikin dakin ta zauna kasa ta rasa me ya rage mata ta yi, kuma ta kasa fita daga dakin. Misalin Karfe biyu da mintuna Bus dake dauko yaran makaranta ta shigo gidan, a harabar da aka tanada domin aje motoci direban ya faka motar. Sai da manyan suka fara fita sannan Hurriya ta fito, Hamad kan cikin manyan yayyunsu ya kutsa ya fita, daman shi yana daga cikin sarakunan kiriniya da rashin kunya na gidan, babu kalar dukan da basa masa ko hantara amman kowa yace masa kule zai ce chasss, Amma ta yi fada har ta gaji, Appa ma har baya son a kai masa kararsa domin ko ya masa fada ba zai hana gobe ya sake ba, Hamad irin yaran nan ne da ko kallonsu ka yi a karkace sai sun rama. Hurriya na shiga part dinsu ta jefar da jakarta a kan kujera ta nufi bedroom din mahaifiyarta, a hankali ta tura kofar dakin ta shiga tsaye ta yi bakin kofar tana kallon kanenta Hamad dake ta fadawa Amma abun da ta yi masa a makaranta. “Amma karya yake, karfe 1:30pm aka tashe mu shi ne na ce nasa yaje yayi sallah saboda bus din mu sai 2pm take zuwa ai, shi ne ya taso min fa masifa har zai yi dambe da ni gaban yan makaranta har da yan ajinsu fa” Hamad ya juyo ya kalleta a fusace. “Toh ina ruwanki da ni da zaki ce na tashi na yi sallah, kafiri ne ni ko bana sallah aka ce miki? Salon friends dina su fara tsokana ta suna cewa bana son sallah” “Na ji ba zan sake maka magana ba, amman ni ma karka sake zuwa class dinmu ka ce na ara maka wani abu, ba ruwana da kai karka sake taba min komai kuma safata da ka saka yau ban yafe ba karka sake min taba min komai” Amma ta mike tsaye tana kallonsu kowane zuciyarsa ta kawo kamar abokan gaba. “Wannan fadan duk na minene wai? Ku kullum baku zaman lafiya? Kai kake binta amman kai da ita babu zaman lafiya, abinci ma ba zaku ci a plate daya ba, magana mai dadi babu tsakaninku kullum sai fada?” Hamad ya ce. “Ita ce bata ba ni respect ai” “How? Kai ne babba or ni? Ni ce babba ai kai ya kamata ka ba ni respect” “Ni ba zan taba baki respect ba i hate you kuma kika sake min wata maganar banza sai na ballaki” Hamad na kaiwa nan ya juya ya fice rike da jakarsa har yana bankade Hurriya. “Amma kin ga ko? Imagine” Amma ta dafe kanta ta zauna bakin gadon tana fashewa da kuka. “Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un” A take jikin Hurriya yayi sanyi ta bar jikin kofar ta karasa inda Amma take ta zauna kusa da ita, domin suna yawan samun tsabani da Hamad saboda rashin jituwa dake tsakaninsu su yi fada wani lokacin har dambe suke, Amman Ammansu bata taba kuka ta zubar da hawaye ba akan haka ba sai yau. [10/18, 5:34 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: https://chat.whatsapp.com/LimnMeG0kWvIfT6JQvVMh1 ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝗣𝗮𝗴𝗲 3️⃣ “Amma I'm sorry laifin fa duk na Hamad ne shi ba a masa magana ya ji” Amma ta dago da idanuwanta da suka kumbura ta kalleta. “Ke ai kina ji? Kuma ke ce yayarsa ki daina biye masa mana, ki zauna lafiya da dan'uwanki dan Allah, kullum ina fada muku haka amman baku ji, Hurriya ki daina biye masa kina kallon ba sonku ake a gidan nan ba, a madadin ku so kanku kullum sai rigima da junanku” Amma na magana Hurriya na yawo da idonta akan akwatunan da suke tsaye gefen kofar dakin da bata lura da su ba sai a yanzu. “Amma kayan miye a akwaitinki?” “Tafiya zan yi” Hurriya ta dubeta da sauri tana kallonta da ya kumbura sosai. “Amma ina zaki je?” “Gida zan koma gurin Gwaggo” “Saboda me?” Amma ta yi murmushi hawaye na sauko mata. “Hurriya abincina ya kare a gidan mahaifinku” “Kamar Yaya? Toh ba sai ya kawo wani ba? Amma me ya faru kika yi kuka? Me yasa zaki tafi?” Amma ta rufe ido ta dantse baki. “Je ki kira Hamad” Hurriya da bata gama fahimtar abun da yake faruwa ba idonta ya cika da hawaye har ya zubo ta kasan gilashin da shi ne rayuwarta. Ta mike tsaye ta fice daga dakin kamin ta isa dakin Hamad ta cire hijabin dake jikinta ta rike a hannu tana tafe tana hawaye har ta isa bakin kofar dakin. Murda kofar dakin ta yi ta tura ta shiga, Hamad dake sanye da short yana kokarin cire safar kafarsa ya kalleta. “What? Amma ta miki fada ko? That's good next time sai ki sake shiga min hanci” Ya fada azatonsa Amma ta yi mata fada ne sosai, daman haka take sometime idan aka yi mata fada kuka take. “Ba saboda haka ba ne, Amma ta ce na kira ka kuma kuka take yi, ban san abun da aka yi mata ba” Be tsaya ya karasa cire safar daya ba ya sauko da kafar ya biyo bayan Hurriya da tuni ta juya bayan ta isar masa da sakon Amma. Hamad na shiga dakin ya karasa inda take zaune ya zauna bakin gadon babu abun da zuciyarsa take nuna masa sai fadan da suka yi da Hurriya. “Amma saboda Hurriya ne ko?” Amma ta share hawayenta ta kalleshi, sannan ta kalli Hurriya ta mika mata hannu. Hurriya dake tsaye jikin kofar dakin ta karaso da sauri hawaye na sauko mata ta kasan gilashin dake idonta. Amma ta kama Hamad ta dauki hannu Hurriya ta dora a saman hannun na Hamad. “Dan Allah ku zauna lafiya, ku so junanku ku kaunaci junanku, kai baka da wata yar'uwa da ta fi Hurriya, Hurriya ke ma baki da wani dan'uwa da ya fi Hamad, wannan yawan fadan da kuke yi ku daina anyi ance da rashin bawa juna girma duk ku aje shi a gafe, musamman ma kai Hamad idan baka canja wannan hallayar ba zaka sha wahala a gidan nan kana kallon yadda kake rayuwa ma yanzu balle kuma idan bana nan” “Amma ina zaki je?” Hurriya ta tambaya daman ta kagu ta ji domin hankalinta yayi matukar tashi akan hawayen da ta gani a idon mahaifiyarta ga kuma tufafinta a shirye. Amma ta kalli Hurriya sai ta rasa ta ina zata fara amsa mata tambayarta, at her age it's too early ta fada mata sakinta mahaifinsu ya yi, ita kanta kalmar tana mata nauyin furtawa a yanzu balle kuma yadda ƴaƴanta za su ji idan ya sauka a kunnesu har su fahimta. “Gida zan tafi gurin Gwaggo ba na fada miki ba? Sai na haihu zan dawo, za'a rika kai ku kuna duba ni” “Me yasa ba zaki haihu a nan ba? Kuma kike kuka?” Hamad ya tambaya ya tambaya yana kallon cikin idonta kamar mai kokarin kure karyarta. Amma ta yi murmushi ta share hawayenta. “Saboda bana jindadi a yanzu, bayan kun fita rashin lafiya ta taso min, kuma ina yawan yin haka a duk lokacin da kuka tafi makaranta, kuma kin fi kowa sanin bana son mai aiki na fi sha'awar na yi komai da kaina, ni da mahaifinku muka yanke shawarar zan koma gida na zauna har sai na haihu na samu lafiya, shiyasa ban tafi ba na jiran har sai kun dawo na sanar da ku, kuma na ja muku kunne dan Allah ku zauna lafiya” Kalaman da Amma ta yi a yanzu sun sanyaya zuciyar Hurriya har ta samu kuzarin cire gilashin idonta ta goge hawayenta ta maida abokin rayuwarta. “Allah ya baki lafiya Amma, zamu rika zuwa kullum” “Ba kullum ba dai sai a lokutan da mahaifinku ya zaba, kuma ku masa biyayya dan Allah ku zauna lafiya da kowa, ke dai na san baki da rigima Hamad ne mai matsala” Hamad dai be sake cewa komai ba sai kallon mahaifiyarsa yake zuciyarsa na raya masa wani abun na dabam. “Ku rike karatunku, boko da Islamiya karku saka wasa” “In Shaa Allah Amma zamu zama yara masu kirki” Hurriya ta fada da murmushi a fuskarta. Hamad kam kallonta kawai yake kamar wadda aka cewa mutuwa zata yi anjima. “Je ka saka tufafinka ku rika min kayan na kai mota” Ya mike tsaye ya fice daga dakin cikin wani yanayi kamar ba shi ba, yadda ya natsu a lokaci daya wani tunani ya zo masa sai ka dauka wani babban saurayi ne. “Amma wa zai rika ba mu abinci?” “Haka ne na manta ma yau ban girka muku komai ba, sai da ku sarrafa wani abun ku ci, ko kuma ku sha tea, idan mahaifinku ya dawo zai fada muku gurin da zaku karbi abinci, gurin Momy ko Hajiya Kaltume shi zaku tambaya” “Toh Amma Allah ya dawo mana dake lafiya” “Ameen” Ta amsa tana danne abun da take ji a zuciyarta, sannan ta mike tsaye ta dauki hijabinta ta saka ta fara fitar da kayan Hurriya na taya ta kamin Hamad ya fito shi ma ya saka hannu suka dauka suka kai mata gurin mota. Ta saka wasu a bayan mota wasu kuma a back seat sannan ta shafa kan ƴaƴanta tana murmushi Hurriya ma murmushin take Hamad kuma ya hade rai kamar wadda aka yi ma laifi. “Allah ya muku albarka ya tsare ku, kuma na fada muku zan kara jaddada muku ban da fada ku daina fada dan Allah” A nan din ma Hurriya ce ta amsa Hamad kuma yayi kamar be ji ba, shi dai sai kallon mahaifiyarsa yake fuska babu annuri. “Toh Amma” Amma ta kalli Hamad tana jin wani yanayi na rashin jindadi. “Hamad ba zaka ce komai ba?” Juyawa kawai yayi ya shige cikin falon ba tare da ya ce mata komai ba. Sai ta lumshe ido hawaye suka sauko mata. “Hurriya shiga ciki idan ina ganinku ba zan iya tafiya ba” Ta fada still idonta na rufe, babu abun da take a zuciyarta sai ambaton Allah. “Amma ko mu rakaki mu dawo” Ta bude idon da sauri. “Aa zan tafi da kaina ku kula da kanku” “Toh Amma Allah ya baki lafiya ya dawo dake lafiya” “Ameen” Ta bude motar ta shiga tana share hawayenta. Hurriya ta daga mata hannu tana murmushi a tunaninta Amma na kewar rabuwa da su ne shiyasa take kuka, a kurciya da rawarkai irin nata bata damu sosai da tafiyar da Amma zata yi ba a yanzu, domin a ganinta gidan Gwaggo da gidan Appanta duk daya ne kara ma gidan Gwaggo tana musu gata tana barinsu su yi duk abun da suke so, ba kamar nan ba da wani abun Hajiya Kaltume ko Momy zata hana, wani abun kuma Amma ce da kanta zata hana. Juyawa ta yi ta koma cikin falon tana rufe kofar ta nufi dakinta ta cire uniform dinta ta dauki na islamiyarsu ta saka sannan ta sauko ta shiga Kitchen ta dauko cornflakes ta jika a two cups daya nata dayan kuma na Hamad, sai dai wanda yake na Hamad ya fi yawa domin shi baya wasa da cikinsa komai sai ya ci ya ji baya iya tashi yake bari, ita kuwa abinci be dame ta ba, bar ta ma ga kayan kwalama, ko abu mai ruwa dangin tuwo da shimkafa ba babinta ba ne shiyasa kullum gata nan kamar wadda ake diba ana miyar gidan. Jiki na rawa ta dauki cup din Hamad ta nufi dakinsa ta shiga sai ta same shi kwance ruf da ciki yana kuka. “Hamad ga cornflakes na jika maka, ka ci mu tafi Islamiya...” Yana jin sautin muryarta sai yayi tsif numfashi ma a hankali yake fitarwa dan kar ta ji. “Hamad kuka kake yi?” “Ina ruwanki bana shan ki dauke abunki ki fice daga dakina” “Na maka kirki ne fa, Amma ta ce mu zauna lafiya amman baka ji ba, miye laifina dan na kawo maka abu” “Ba zan sha ba bana so” “Kar Allah yasa ka sha din, wanda baya jin maganar Mamanshi ya ji haushi ai, ko Sallah be yi ba kalleshi” Sai a lokacin ya dago daga saman gadon ya sauko fuskarsa shabe-shabe da hawaye ya yi kanta, sanin dukanta zai yi ya saka ta saki kofin cornflakes din ta kama shi da kokawa daman sun saba, abu kadan idan ta yi masa sai ya ce zai daketa saboda ya fita girma jiki da karfi, idan ma ba wanda ya sani ba zai dauka ita ce kanwar shi ne yayan. Suna fara kokawa ya buga kanta ga kofar dakin sai kawai ta saka kuka ya fisge glashin idonta ya jefar a kasa ya saka kafarsa ya taka haka be masa ba sai da ya dauko talkaminsa ya saka ya bubbuga glass din ya fasa shi, domin zuciyarsa ta kawo idan kuma yayi fushi sai ya ji kamar ya tashi gidan, gashi baya tsoron kowa har Appa, idan za a masa dukan mutuwa sai yayi magana, sai dai yana da wata dabi'a na baya shiga safgar kowa sai idan an shiga ta shi. “Wayyo Allah na...” Hurriya ta fada tana kuka tana lalaba kofar fita dakin, domin ta daina ganin komai da kyau a yanzu sai dishe dishe saboda Hamad ya cire gilashin idon dake bata damar banbance fari da baki. Ta bude kofar ta fita tana lalaben hanya irin yadda makafi suke yi tana kuka har ta sauka kasa, da lalaben ta isa kofar falon ta bude ta fita tana kuka, dishe-dishe ta fita daga part din ta shiga part din Hajiya Kaltume har lokacin kuka take kuma ta san by that time Appanta baya gidan balle ta kai masa karar Hamad, idan kuma Appa baya gidan Yassar ne mai yi ma Hamad hukunci yadda take so, wani lokacin ko Appanta ta fadawa cewa yake ta fadawa Yayanta. Da kuka ta nufi bangaren Hajiya Kaltume ta isa har bakin kofar falon ta tura ta shiga. Hannu ta kai tana kokarin lalabawa ta ji waye a tsaye jikin kofar, sai ta ji an sauke mata lafiyayyen mari a fuska. Tsaye ta yi cak kamar wanda aka daukewa wuta tana kallon kasa, ta san kowa zai iya marinta a bangaren Momy ko Hajiya Kaltume, saboda suna ganin abun da take kamar da gangan take yi, shiyasa dole kawai ke kawo ta bangaren Hajiya, bangaren Momy kuma ko shiga bata yi idan ta shiga sai da wani kwarran dalili, domin Hajiya Kaltume na sake mata fuska irin na munafurci, Momy kam bata sakewa kowa fuska a gidan, har gobe ganin take level dinta ya fi na kowa a gidan, wannan na daga cikin dalilin da ya saka komai nata ko na ƴaƴanta take banbanta shi da na sauran, komai nata is unique and Expensive, gashi bata son ganin ƴaƴan Amma da Hajiya ko kusa da ďakinta, sai dai ita Hajiya tana karbar Ƴaƴan Momy har so take suje a gurinta yanzu da suka girma. “Haba Musib Haba Musib miye haka?” Musib dake rike da wayarsa a hannu ya kalli Yassar da ya doso inda suke tsaye cikin bacin rai. “Baka ga abun da ta yi min ba?” “Amman dai ka san idan kana gani ba zata maka haka ba? So take ta gane waye a gurin, me yasa kuke kyarar yarinyar nan ne please? Ku ba ku tausayin halin da take ciki? Ba ku ganin lalura da take tare da ita?” “Tana tare da lalura take yawo babu glass? Ni fa bana daukar wannan iskanci” Ya amsa a fusace sannan ya saka talkaminsa ya fice daga falon, har lokacin Hurriya na tsaye bakin kofar ta kasa yin komai sai hawaye, a nan ta gane wani abun ake iya yi ma magana ko kuka, ta sani sarai tana kuka ko furta wani abun zai iya kara mata ko ya rufeta da duka, domin ba yau ya saba ba. Ko kwakkwaran motsi bata yi ba sai da ta ji ta a jikin Yassar ya rumgune yana bata hakuri sannan ta fashe da kuka. “Yi hakuri Allah zai saka miki” Hajiya Kaltume dake saukowa rike da plate ta soma fadin. “Ya saka mata ga wa? Wai Yassar ba zaka daina wannan bakin shisshigin ba? Yadda kake da alaka da ita fa haka yake da alaka da ita, idan ma kwantar da ita yayi ya yanka ina ruwanka?” Dagowa Yassar yayi ya kalleta. “Haba Hajiya ai ko mai aikin gidan nan wani abu ba zai same ta na yi magana ki ce ina ruwana ba balle kuma Hurriya, marinta fa yayi kamar ya samu babbar mace” Hajiya Kaltume ta yi fuskar tausayi kamar gaske yadda ta tambaya sai ka rantse bata san abun da ya faru ba, bayan kuma tana sama a tsaye stairs tana magana da Umm Khairi lokacin da Hurriya ta shigo. “Ayya ah gaskiya be kyauta ba, me ta yi masa?” “So take ta tantance waye a gurin kawai ya sauke mata mari” “Oh Subhanallahi, Sannu Hurriya ina glass din naki?” Cikin wani irin kuka mai tsarke numfashi Hurriya ta soma magana. “Hamad.... Hamad... Hamad.. Ya fasa.. Shi..” “Saboda me? Kai Hamad akwai mugun hali ita Iyami tana aikin me yayi miki haka?” Line by line ta fada musu abun da ya faru tun a school har dawowarsu gida, ciki har da tafiyar Amma da hudubar da ta yi musu. Ciki wani yanayi na damuwa da rashin fahimta da kuma faduwar gaba a lokaci daya Yassar ya kalli Hajiya Kaltume, Hajiya Kaltume kuma ta juya ta kalli ƴarta Umm Khairi, suna haɗa ido fuskarsu ta soma fadada da murmushi, tunawa da Yassar na dakin ya saka Umm Khairi ta fara tarin karya, Hajiya Kaltume kuma ta daure fuska. Yassar da ya tattara hankalinsa gaba daya gurin kanwarsa Hurriya ya ce “Kamar ya sai ta haihu zata dawo?” “Haka tace mana, kuma bata jima da tafiya ba, har ya fara min duka, Wallahi kashe ni zai yi idan muka zauna a can mu kadai” Ya kalli Hajiyarsa cikin yanayin damuwa sai ta girgiza masa kai alamar bata san komai ba, hannun Hurriya ya rika. “Zo muje part din na ku” Har lokacin kuka Hurriya take tana biye da yayanta dake rike da hannunta suka fice. Umm Khairi ta sauko da sauri tana murmushi ta dafa Hajiya Kaltume da ta kai zaune baki har kunne tana mamakin jin kalaman Hurriya. “Hajiya Appa ya saki Amma kenan?” “Ina kyautata zaton haka, domin dazun da safe shi ya kira ni da kansa ya ce min na dauke Bedsheets dinta na kawo masa abun karyawa, har na ce masa bana son ta ga kamar ina shigar mata hakki, sai ya ce min baya son digon zance zan karbi girki a yau” Umm Khairi ta rumgume Hajiya Kaltume da sauri tana murna. “Wayyo Allah na dadi, amman me yasa ba ta fadawa Hurriya gaskiya ba?” “Waya sani? Toh ko ganin take zata dawo? Zama be gan ni ba ungo wannan kai min Kitchen bari na kira Hajiya Fatee” Ta mike tsaye da sauri, daga ita har yarta Umm Khairi kallo daya zaka yi musu ka fahimci farinciki dake zuciyarsu, da rawa Umm ta karasa kitchen ta aje plate din ta fito ta shiga dakinta ta dauki wayarta ta fara kiran yan'uwanta da basa gidan tana musu albishir domin sun dadi ba su samu wani labari mai dadi da faranta zuciya ba irin na yau. Hajiya Kaltume na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta saka key dan tabbatar da ita kadai ce a dakin sannan ta nufi wayarta cikin nauyin jikin dake hana masu kiba da teba hanzari a duk lokacin da suka yi yunkurin yin haka. Sai da ta fara zaunawa sannan ta dauki wayar ta lalabo number aminiyarta Hajiya Fatee duk kuwa da kasancewar ta girme ta nesa ba kusa ba, sai dai friendship be duba age ko level idan jini ya hadu, cikin natsuwa Hajiya Kaltume ta aika mata da kira, zuciyarta har wani bugawa take irin na jindadi da farinciki da tun da aka auro Iyami rabonta da irinshi. “Assalamu Alaikum Hajiya Kaltume” “Na'am Hajiya Fatee ke kadai kike?” “Ni kadai nake yanzu yar iskar yarinyar nan ta fita” “Ba dai Afra ba?” “Ita fa” “Ikon Allah yaushe kuma ta fara zuwa gidanki?” “Yanzu fa, ina zaune sai gata ta zo ita da yara wai an zo a gaishe ni, waya sani ko wani mugun abun aka kullo min a kawo min, ta mallake ni kamar yadda ta mallake min ďa” “Tsab kuwa zata iya shi, indai magani ne wannan yarinyar babu inda bata sani ba, gashi ta tsaneki ko maganin mutuwa ma zata iya miki” “Kamar an yi a gabanki, ai an sha fada min ta yi ta yi samun sa'a ne bata yi ba, shiyasa na tsaya a kafata bana wasa kar ta jedar da ni a zuciyarsa kuma Wallahi idan ina da rai sai Fadil ya kara aure” “To ke Hajiya Fatee anya wannan shedaniyar surukar ta ki zata yarda ta bar Fadil yayi aure?” Hajiya Fatee ta yi dariya. “Hajiya Kaltume kenan kina magana kamar baki san wacece ni ba, ai idan ta kwana da shiri wani a hanya ya kwana, daga ita har uwarta sai sun kyale min ďana, komai shige shigensu da tsafe tsafe da yardar Allah sai hankalin Fadil ya juyo kaina ni ma sai na sarrafa ďana yadda nake so” Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana kara yarda da zancen Hajiya Fatee. “Na yarda da haka, domin a yanzu na sarawa lamarinki, ni yanzu ma kira na yi na yi miki albishir, dazun da safe Alhaji yake ce min na kawo masa abun karyawa na cire Bedsheets din da Iyami ta saka, ni tun a lokacin na san wani abu zai faru, kuma na tambaye shi lafiya be fada min ba, yanzu kuma Hurriya ta shigo tana kuka wai Hamad ya daketa a nan take fada mana Amma bata gidan wai ta tafi gidansu har sai ta haihu zata dawo” Hajiya Fatee ta daki cinyarta da karfi ta kyalkyale da dariyar ƙeta da jindadi. “Ke daga jin haka ai kin san abun da muke nema ya samu, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha, kuma gadon ari sai fanna, sirrin iya sai marɗibo, yanzu kam sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai yayi kallo, ai na faɗa miki kowa yace zai iya haɗeye gatari to sakar masa ɓota, kuma idan ta sha mu ba mu karya ba, yaro baya ja da mu muja da ubansa...” Haka Hajiya Fatee ta rika jero kirari da karin magana cikin alfamari da tinƙaho. Hajiya Kaltume ta miƙe tsaye ta fara yawo a ɗakin tana jin kamar ta taka rawa. “Wallahi sai a yau na ji wannan ƙunci da nauyin da ya tsaya min a zuciya ya sauka, tun da Alhaji ya auri Iyami farinciki ya gagareni, duk wani abun da zan samu a duniyar nan farincikina raggage ne, saboda Iyami, yarinya daga zuwa aiki kin aure mai gida har da su ƴaƴa gashi ya murje ido ya nuna kamar ya fi sonta da kowa, ƴaƴanta ma kamar ya bude ciki ya saka su ya rufe haka yake ji” “Toh daman ina ke ina kwanciyar hankali da farinciki Hajiya? Mai aiki ta aure miki miji? Ai haka suke shiyasa ake cewa ďan iska na birni shege na kauye sai tsoron ɗansa, ai da zarar sun yalla ido sun ga ana jindadi a gida to sai sun aure miki miji, ita wannan shegiyar gorar Afra da ta fahimci duniya kin ga duk bokonta bata son ko mai raino balle kuma wata mai aiki” “Tana da gaskiya Wallahi, sai dai haka kuma ba zai hana ďan mu kara aure ba” “Aure kadai? Ai sai ta bar gidan nan matukar ina raye, duk wata mallaka da ta yi ma ďana sai na kwance ta, kuma ki zuba ido ki gani ba dai wannan Malamin ya iya aiki ba zaki sha mamaki” “Yanzu so nake ki shirya mu kai masa sallama kuma na sake fada masa bukatar domin ina gudun kar ya maida ita” “Karki damu, bari sai kura ta laba zamu sake komawa, daman ai na fada masa duk abun da aka ba shi karin alkalami ne kawai, biya sai bukata ta biya” “Lallai kuwa zan masa biya mai kyau, domin ya yaye min bakincikin da nake kwana na tashi da shi, a kullum burina Iyami ta tafi ta bar min miji, yau kuma wannan burin ya cika Alhamdulillah” Dariya suka yi a tare sannan Hajiya Kaltume ta yi mata sallama ta sauke wayar tana jin kamar an mata bushara da gafara. [10/18, 5:34 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝗣𝗮𝗴𝗲 4️⃣ “Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un” Shi ne abun da Hajiya Binta take ta nanatawa idonta a rufe domin danta be zo mata da labari mai dadi ba, a cikin matansa daga wanda ta rasu har wadanda suke a gidansa yanzu babu wanda take so irin Iyami, domin macece wadda ta san kanta take bata girma take rawar jiki da ita tana kyautata mata kamar uwarta. “Subhanallahi Tsoho baka kyauta ba, ka yi gaggawa kuma daman gaggawa aikin sheidan ne, ina ma baka aikata ba ka dan daga mata kafa ko kuma na turata gidansu har sai ka samu natsuwa” Cikin wani kalar rauni da rashin sukunin abun da ya aikata ya sake noce kansa kasa ya sauke ajiyar zuciya. “Hajiya natsuwar ce ta gagare ni samu, ba yau na fara jin bana da sukuni idan bana tare da Iyami ba, ji nake kamar wani abu ne a saman kaina, sai a yanzu da na sauwake mata sannan na ji nauyi ya sauka, ni kaina ina son Iyami amman bana jin natsuwa a zamantakewarmu yanzu, kuma na yi ta addu'a ina fatan samun sauki abun amman hakan ya gagara wata kila sakin shi ne mafi alheri daman aure rai ne da shi” “Har saki nawa ka yi mata tsoho?” “Daya na yi mata Hajiya” “To da sauki idan abubuwa suka daidai wata kila za a iya gyarawa, ko dan yan diyanta Tsoho, dubi Hurriyya da Hamad ga cikin dake jikinta yaran nan ba za su taba jindadin zama a gidan idan bata ciki ba, ko ma kallon iyayen kowa na nan ta su bata nan sai ya saka su jin wani iri” “In Sha Allahu zan ba su duk wani jindadi da farinciki da yaya suke bukata a gurin uwa da uba, ban taba fadar maganar nan a gaban kowa ba sai yau a gabanki, Hajiya duk cikin yayana na fi kaunar Hurriya, saboda kokarinta ga kuma lalurar da take tare da ita, Allah ya saka min tausayin yarinyar nan, fitowa daga gida zuwa nan Wallahi yaran nan kawai nake ta tunani a raina” “Tsoho” Ta kira sunansa sai ya dago ya kalli mahaifiyarsa da fatar jikinta ta fara zazzaga saboda tsufa. “Dan Allah idan ka samu sukuni ka dawo da Iyami dakinta, ko ba komai ta saba da rayuwar jindadi ga kuma ciki ga tunanin yaranta be kamata ka saka mata da haka a irin wannan lokacin ba, idan ma baka yi hankali ba tana cika idda wani zai dauke ta mace mai kyau da kurciya haka nan, ka kusan haihuwarta fa amman tana zaune gidanka gwanin sha'awa ga girmama mutane yarinya mai hankali da tarbiya” Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi. “Hajiya ban sake ta sai da na bata kyauta gidana da yake samaru, kuma na bata kudin da zata iya rike kanta da su naira miliyan ashiri, kuma babu abun da zan karba daga kyautar da na taba mata, kayan dakinta da komai ma gobe zan saka a kwashe a kai mata har gidansu, wata kila dai zaman auren ya kare gaba daya, dan Allah karki cilasta ni aikata abun da zai hana ni samun natsuwa ki yi mana addu'a kawai” “Toh Tsoho Allah yasa hakan shi ya fi alheri, ya kawo mafita a tsakaninku” Hajiya ta fada muryarta na rawa hawaye na cika idonta har suna kokarin zubowa, mikewa ta yi tsaye ta shige dakinta ta bar shi a katon falon dake cike da sanyi ac. Hannu ya saka ya dage kansa yana jin wani karin rashin natsuwar da bakinciki na kusanto shi, ada yayi tunanin idan ya rabu da ita zai samu sakewa, sai dai bakinciki rabuwa da ita ba dan zuciyarsa na so ba, da kuma tunanin damuwar da yaransa za su shiga ya hana shi samun natsuwa, arzikinsa daya a yanzu ya daina jin wannan nauyi da yake ji a lokacin da yake tare da ita. Ya dade zaune a cikin falon kamar wanda ya rasa makama sannan ya tashi ya fice yana gyara babbar rigarsa. Yana fitowa direbansa ya fito ya bude masa motar ya shiga ya maida kofar ya rufe sannanya zagaya ya shiga mazaunin tuki ya tashi motar suka fice daga gidan, kamin ya isa gurin da yake gudanar da kasuwanci kiran Bappa ya shigo wayarsa ya fi a kirga amman yaki ya daga saboda ya san maganar Iyami za su yi masa. HURRIYA POV. Yassar na riga da hannunta har suka isa part dinsu, shi ya fara tura kofar falon ya shiga sannan ya rikota ta shigo. “Careful” Ya fada yayinda take saukowa kan karamin stairs din dake bawa mutum damar shiga cikin falon. “Hamad....!” Yassar ya kira sunansa a tsawace sai ya juyo rike da kofin kankara yana kallon kofar falon fuska babu annurin ido sun masa ja alamar yayi kuka sosai. “Akan me zaka daki Hurriya kuma ka fasa mata glass?” Yassar yana fada ya saki hannun Hurriya ya nufi inda yake tsaye cikin bacin rai, a maimakon Hamad ya gudu kamar yadda sauran yara ko kuma kanen Yassar suke idan zai dake su, shi sai yayi tsaye yana jiran isowar Yassar idan ma yanka shi zai yi sai dai yayi, amman taurin zuciyarsa da jin zai iya karawa da kowa a gidan ya hana shi tsoron kowa. “Ba magana nake maka ba?” “Ita take shiga min hanci” “Ba hanci ta shigar maka ba ido, ko laifi ta yi maka ba ita ce Yayarka ba? Kana namiji zaka rika fada da mace? Kuma macen ma yar'uwarka? Sannan duk abun da zaka mata be isa a fatar baki ba sai ka kai ga fasa mata gilass gashi nan ai ka ja Musib ya mareta” Yassar na kaiwa ayar karshe Hamad ya ji ransa ya yi mugun baci zuciyarsa ta kawo kamar wani babba. “Me ta yi masa to?” “Ba a sani ba, da baka fasa mata gilashin ba zata tafi tana lalaben fuskarsa ne har ya kai ga marinta? Haba Hamad kai baka jin tausayin yar'uwarka ne? Kowa yana zaune lafiya amman kai ban da kai? Gidan ka fitini kowa? Ita din ma ba zaka raga mata ba?” Yassar ya juya ya kalli Hurriya. “Hurriya zo nan” Daga inda take tsaye ta fara takowa cikin abun da Allah ya yassare mata na gani har ta iso gurin ta tsaya daidai inda Yayanta yake tsaye. “Ka bata hakuri” Hamad ya kara murtuke fuska. “Ita zata fara ba ni hakuri ai ita ta fara taba ni” Kasancewar Hurriya mai son zaman lafiya ce ta tsoron fitini ko tashin hankali yana rufe baki ta bude nata. “I'm sorry” Yassar ya kai mata duka a saman kai “Waya aikeki shi ya kamata ya fara baki hakuri ai, ba ki ce babba ba” “I'm sorry too” “Okay bata hannu ku gaisa” Yassar ya fada, nan kam ba musu Hamad ya mika mata hannu, sai ta mika hannayenta duka biyu ta lalabo hannunsa ya mika masa nata suka yi musabaha. “Good ba fada daga yau kun yarda” Hurriyya ta daga kai, shi kuma goga ya ki cewa komai. Yassar ya juya yana fadin “Bari na dauko miki glass dinki da yake dakina” Yassar na fita falon, Hamad ya kama hannun Hurriya suka isa dinning yaja mata kujera ta zauna, ya aje kofin kankarar dake hannunsa sannan ya juya ya nufi sama, kai tsaye dakinta ya shiga yana shiga ya bude gurin da take aje kayanta ya dauko box din glass din daya daya rage dakinta ya sauko da saurinsa ya tsaya gabanta ya bude glashin ya saka mata da kansa, sai gata tana murmushi ganin ganinta ya dawo da kyau kamar kowa. “Thank You” “Ki sha cornflakes dinki zamu tafi Islamiya” “Kai ba zaka sha ba?” “Na sha zobo” “Amma ta ce... ” Tunawa da ta yi da cewar idan ta fada masa Amma tace su daina zama da yunwa zai iya rufe da fada wata kila ma ya hada mata da duka ya saka ta fasa fadar hakan. “Toh” Hannu ta mika ya janyo kofinta na dazun da ta jika cornflakes din ta fara sha, bata juyo ba sai da ta ji karar bude kofar falon. “Kin dauko wani?” “Hamad ya dauko min, daman shi daya ya rage” Yassar yayi murmushi daman ya san masu saurin fushi da fitina sometimes sun fi kowa zuciya mai kyau. “Ya kyauta bari naje na aje wannan” Ya juya sai Hurriya ta kira shi. “Yayana” Ya juyo “Thank you” Yayi mata murmushi. “Ur welcome” Ya fada sannan ya fice daga falon ita kuma ta juya ta cigaba da shan cornflakes dinta. Yana rike da box din glass din ya shigo part dinsu, stairs ya hadu da Hajiya Kaltume tana saukowa shi kuma yana kokarin hawa, kiran sunanta yayi sai ta tsaya tana kallonsa. “Hajiya me kika fahimta da maganar Hurriya?” “Wace maganar?” “Cewar Amma zata tafi gida har sai ta haihu” “Ikon Allah Yassar ina ce dai ni da kai duk kunne biyu muke da shi kuma kai ma ka ji maganar nan, bakin halin ne da tashi da zaka ce me na fahimta? Ina ruwanka da fahintata? Aunata fahimtata akan wane dalili?” “Haba Hajiya magana ce kawai fa, tsoro nake ji kar dai a wani abu ya faru?” “Koma minene ai idan ta yi tsami zamu ji, miye a hannunka?” Ta tambaya a kokarinta na kawar da maganar. Ya kalli box din. “Gilashin Hurriya ne” Hajiya Kaltume ta yi murmushi. “Sai ka yi dan gatan Hurriya, gar yanzu kana ajeye da gilasanta” “Uku ne kawai a hannuna, biyu suna hannunta Hamad ya fasa dayan yanzu sauran hudu” “Yayi kyau ka cigaba da aje su da kyau, Allah ya raya maka yar kanwar nan taka Yassar” “Ameen” Ya amsa sannan ya wuce ya haye sama, Hajiya Kaltume ta bishi da harara. “Kai kan ba dan a cikin gida na haife ka ba, sai na ce canja min kai aka yi, yaro sume sume sai munafurci fal a ciki oh ni Kaltume” Ta ja tsaki sannan ya karasa saukar ta nufi kitchen dinta, tana shiga hannunta ta fara wankewa sannan fara juya miyar dake kan wuta, da gudu Umm Salma ta shigo kitchen da wani irin murna har haki take. “Hajiya Khari ya kira ni tace Appa ya saki Amma?” Hajiya ta yi mata alama da ta yi shiru da sauri tana nuna mata kofar kitchen din. “Bari sai Yayanki ya fita kume farincikinki” Salma ta daga kai cikin murna ta fice daga kitchen din tana tsalle saboda jindadi. Sai da Hajiya ta gama miyarta tsab sannan ya kwashe ta kawo ta a dinning kana ta nufi stairs tana kwalawa yaranta kiran “Umm Salma ko Umm Khairi waninku ya zo ya jera mana abinci a dinning” Salma ce ta fito har wani tangadi take tana rawa kunneta na makale da ipod, Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta dauke kai ta shige dakinta, da sauri ta karasa gurin gadonta cikin nauyin jiki irin nata ta dauki wayarta da kiran ke daf da tsinkewa. “Hello Hajiya ina wuni” Daga dayan bangaren Hajiya Binta ta amsa. “Lafiya Kalau, Kaltume ke kadai kike?” Hajiya Kaltume ta yamutsa fuska daman a gurinta uwar miji bata da wani muhimmanci. “Eh Hajiya ni kadai nake, Lafiya dai?” “Toh Lafiya ba kalau ba, magana nake son yi dake akan yaran nan Hurriya da Hamad” “Me ya faru da su?” Hajiya Binta ta sauke ajiyar zuciya. “Dazun mijinki ya zo nan ya fada min hukuncin da ya yanke akan Iyami, ba mu san abun da Allah zai yi a gaba ba, amman kamin nan Kaltume ina son ki ji tsoron Allah ku rike Hamad da Hurriya amana, domin su da marayu duk daya a yanzu” Hajiya Kaltume ta kai zaune saman gadonta farinciki a mamaye ta, domin dazun hasashe take yanzu kuma gaskiyarce zaharan Hajiya Binta zata fada mata. “Hajiya ban fahimce ba” “Ai kin san komai Tsoho ba zai rasa fada muku ba” “Wallahi be fada mana komai, wata kila dai ita Nafisa ya fada mata, amman ni ban san komai ba” “Dazun ya zo nan ya fada min cewar sheidan yayi nasara akansa ya sallami Iyami, sai dai saukin abun saki daya yayi mata, kuma be sallame ta ba sai da ya damka mata gidansa dake samaru area kuma ya bata kyautar naira miliyan ashiri, duk da haka dai ina kyautata zaton zata dawo dakinta kamin lokacin ke da Nafisa duk ina son ja muku kunne akan yaran nan” Hajiya Kaltume bata san lokacin data mike tsaye ba ta daki kirjinta da karfi. “Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un... Amman Alhaji yayi kuskure abun da ba ayi da kurciya tun can da ba za'ayi yanzu bayan ga yara” “Ni dai na kira na ja muku kunne ne kawai, domin na san ko na nemi ya bani yaran ba zai aminta ba saboda yana son yayansa kamar yadda yake son uwarsu, Allah ya tabbatar mana da alheri” Hajiya Binta na kaiwa nan ta katse kiran. Wani irin bille baki Hajiya Kaltume tayi ta kube shi. “Munafurcin banza da wofi, wato ga Kaltume makiyiyar Iyami da yayanta har da wani kira ki bani amanar yara, ko mutuwa ta yi ai ba zan karbi amanar yayanta ba balle tana da rai, idan kin isa ki saka ya dawo da ita mu gani, har kina fada min yana son yayansa kamar yadda yake son matarsa tsabar kin raina ni” Duk wani farinciki da walwala dake zuciyarta da fuskarta ya gushe tun daga lokacin da ta ji cewar sakin ďaya aka yi ma Iyami kuma an bata kyautar kudi da gida. “Wallahi Iyami kin cuce ni, ko a haka dai kin ci ribar mijina, kin haihu da shi dan ki ci gado, kuma yanzu ya sake ki ya dauki gida da miliyan ashirin ya baki, waya taba yi ma kyautar gida a cikinmu matansa, sai dai ko wace ta siya da kudinta” Password din wayar ta cire ta duba kiran dake kasam na surukarta Hajiya Binta ta taba na Hajiya Fatee. Kamin ta amsa duk ta kagu har ta fara saba da marwa a dakin. “Assalamu Alaikum Kaltume” “Hajiya Fatee zama be gan ni, tsugune bata kare ba, Saki daya Alhaji yayi ma Iyami, kuma wani abun da ya fi ko wane bakin ciki kudi ya dauka ya bata har naira miliyan ashiri” “Million ashiri?” “Ai ba nan haushin yake ba, ya bata kyautar gidansa dake samaru, yanzu uwarsa ta kira tana fada min har wani gargadi take min saboda ya san gatan jikokinta, kin san ba jikokin da take so irinsu, kuma tun da saki daya ne zata iya buga kafa a kasa tace sai ya maida uwarsu” “Tsab kuwa wannan shegiyar tsohuwar zata iya, saboda ba sonki take ba” “Ina fa, kuma ba ba zancen dawowarta kina ganin zan yarda Iyami ta bar gidan mijina kuma ta yi arziki da dukiyar mijina? Wallahi bata isa ba ai yadda ta ci amanata haka ni ma zan nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne, sai an koya ma Iyami hankali, dan haka ki shirya tafiya gobe goben nan nake son mu tafi ba sai wata rana ba, kar mu sake ayi mana sakiya, domin ita ma zata iya shiga nata malaman ta janyo hankalinsa” “Maganarki haka take Kaltume, karki damu zan kira shi tun yau na fada masa gobe zamu zo, amman fa ki zo da wuri saboda kin san dajin nan babu ďan mutum ga halin da ake ciki kara mu yi tafiyar safe kar mu yi mugun gamo” “In Sha Allah karfe 8am a gidanki zata yi min, sai na zo” Daga haka suka yi sallama, Hajiya Kaltume tana kwafa tana jinjina lamarin. IYAMI POV. “Ban san me ya hana shi daukar wayata ba, kunyar abun da ya aikata yake ji ko kuma rainin wayo ne da raina talaka” Gwaggo ta kalli Bappa dake maganar ta girgiza kai. “Alhaji Haruna ba shi da dabi'ar raina talaka, domin be taba mana haka ba wata kila dai yana jin kunyar abun da ya aikata ne, wata kila kuma baya son ka yi masa magana komawarta ne” Iyami ta kalli Bappa cikin karfin hali ta ce. “Bappa da dai zaka kyale shi da ka kyauta min, domin na yi ta tambayarsa ko na masa wani laifin ne, amman ya ce ban masa komai ba, kawai dai bana jin natsuwar zaman aure da ni ne a yanzu” “Tun da can be san da wannan ba sai yanzu? Kuma be tashi sakinki sai yanzu da ciki wata shida?” “Ba saki yayi mata na wulakanci ba, ya kyautata mata daidai gwargwadon yadda ake son kyautatawa a saki da zaman aure, kuma aure rai ne da shi ko babu komai idan lokacin rabuwa yayi dole sai an rabu, mu dan bashi lokaci har ya dawo hayyacinsa ni na tabbatar Alhaji Haruna yana son Iyami akwai dai abun da aka yi” Wannan karon Gwaggo ce take maganar. Bappa ya mike tsaye yana ja tsaki. “Akwai yadda aka yi na me? Ku yi komai ba za su bar shi ga Allah ba sai kun ci wani abu, yanzu zaki iya cewa asiri aka yi masa, kar ma ki kawo wannan maganar, ni na fita” “Toh Allah ya dawo da kai lafiya” “Ameen” Ya fice yana sake gwada kiran number Alhaji Haruna Mai Yadi. Fitarsa da kamar minti uku Hindu ta shigo dakin tana sallama, Gwaggo ta amsa mata. A bakin kofar dakin ta saki jakar hannunta tana kallon amiyarta. “Iyami da gaske Alhaji ya sake ki?” Iyami na kallonta sai hawaye suka zubo mata, Gwaggo na ganin haka ta mike tsaye ta fice daga dakin domin bawa kawaye damar tattaunawa. ________________ Masu karatu kuna ganin Alhaji Haruna ya yi ma kansa mai kyau kuwa? Ya Hurriya zata ji idan ta san cewar Appa sakin Ammanta ya yi? [10/18, 5:34 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: https://chat.whatsapp.com/GJ9hOtbWbfDKmq8NrKsDIG ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝗣𝗮𝗴𝗲 5️⃣ “Akwai matukar mamaki ace duk son da Appan Hurriya yake miki ya sake ki, saki fa Iyami?” Amma ta saka hannu biyu ta share hawayen fuskarta. “Ni ma dai ganin nake kamar ba sakin ba ne, saboda ban saka ran ba mutuwa ce zata raba ba, har yanzu tunani nake ko dai boye min yayi? Wata kila na masa wani laifi ban sani ba” “Bayan kin ce ya fada miki baki masa komai ba?” “Hindu namiji na sakinka haka nan? Ai na ga sai da dalili” “Dalili daya ne Iyami sa'ar da matansa suke nema sun samu, kin mata a cikin manyan mata kuma tsofin mata kike zaune? Matan da sun kusa sa'ar gwaggo? Wace ce warinki a cikinsu? Iyami babu kalar kazafi da kage da ba su miki ba duk dan saboda ki bar gidan amman burinsu be cika ba sai a yau, maganin ma na san sun gwada Allah dai ne be ba su sa'a ba sai yau” “Hindu Waallahi ina son mijina, mijina kuma yana so na amman yau komai ya kare” Amma ta fashe da kuka. “Har sai kin fada? Ai kowa ya san yadda kuke zaune ya san mijinki yana sonki kuma ke ma kina sonsa, sakin ma da zai miki Iyami na musamman yayi wane namiji ne zai saki mace ya dauki dukiya ya danka mata? Ai sai zababbu cikin mata, kuma ko yanzu karki yanke kauna In Shaa Allah zaki koma dakinki ki cigaba da addu'a nima kuma zan taya ki kuma ki saka ayi miki a islamiyayo nima kuma zan zaka ayi miki” Kasa cewa komai Amma ta yi sai kuka take kukan da da zaka iya rantsewa mutuwa aka yi mata, idan ta tuna da sakinta Appan Hurriya yayi sai ta ji zuciyarta ta narke ta rasa me ke mata dadi a duniyar nan da ace mutuwa yayi sai ta dangana amman tunawa cewar yana raye kuma shi da kansa ya zabi rabuwa da ita ya fi komai daga mata hankali. “Toh wai a can kika bar su Hurriya?” “Ya ce zai rike su” Ta amsa mata cikin kuka. Hindu bata wani dade a gidan ba ta mata sallama ta fita domin komawa nata gidam ta dora girki. Haka ta wuni a daki idan Gwaggo da jikokinta suka shigo sai ta boye fuskarta ta danne kukanta har sai idan ta kadaita ita kadai, tunanin yaranta ya tsaya mata a rai, tana ta auna lokacin dawowarsu makaranta da kuma irin abubuwan da suke idan sun dawo, da dare yayi sai ta kasa bacci domin wannan ne daren farko da zata kauna a gidansu tun bayan aurenta shekara goma sha shida. Ko biki ake a gidan ko wata hidima Appa baya barin ta kwana ko da kuwa ba girkinta. Daren sai ya zame mata wani dare na dabam da bacci ya gagara kusantar idonta ma balle har ya sace ta, kukan ma sai ta neme shi ta rasa wata zuciyar nata raya mata hanyoyin da zata bi ta shirya da mijinta sai ta saka zaren idan ta karshe sai ga ba hanya ce mai bullewa ba, dare ne da yayi mata tsawo fiye da sauran dararen da suka gabata, karfe biyu da rabi ta doro alwala ta fara raya daren da sallah nafila a haka aka kira sallah asuba akan idonta. HURRIYA POV. Da murna ta shigo dakin Appanta ta zauna kusa da shi a kasa kamar yadda ta saba, sai ya kai hannu ya shafa kanta zuwa bayanta yana murmushi irin murmushin nan dake dauke da so da kauna da kuma farincikin abun da idanuwa suka yi arba da su. “Hurriya toh yaya?” “Lafiya kalau Appa, ka dawo lafiya?” “Lafiya Kalau, ina can gurin aiki zuciya na nan tare da ku sai tunaninku nake Ina Hamad” “Shi ya ce ba zai zo ba?” Ta amsa tana kai hannu ta gyara gilashin idonta. Hajiya Kaltume dake zaune kan carpet ta yi murmushi, irin murmushin nan da ya zame mata dole ne, domin ta kasa hadeye maganar da Appa yayi cewa yana gurin aiki zuciyarsa na gurin yayansa ta ce. “Hamad ai ba zai zo ba, dazun ma dukanta yayi ya fasa mata gilashi sai da Yasir ya shiga tsakaninsu” Appa ya kalli Hurriya cikin yanayin damuwa. “Me ya hada ku?” Ta zayyana masa abun da ya faru daga karshe ta rufe da fadar Yasir ya shirya su. Appa ya sauke ajiyar zuciya “Ina ganin yaran nan za su koma gurin bangarenki sa zama Kaltume, saboda a rika saka musu ido, kar wata Hamad ya ji ma yarinyar ciwo, daman ko dan kula da abincin da wasu abubuwan dole su koma can” “Gurina kuma Alhaji? Ni da nake da yan mata cike da daki? Kuma ka san yadda bama jituwa da uwar yarinyar nan yanzu nan Hurriya ko kaya ta taka na cire mata cewa za ayi na cutar da ita, ba zan hana ta zama ba idan haka kake so, amman dai da zaka barta a hannun Nafisa wata kila zamu samun zaman lafiya, daman Nafisa bata da yara da yawa uku ne kawai kuma mazan fita suke Namra ce kawai ka ga ta samu yar'uwa a kusa ko? Amman ni Hajiya ma sai tace na mata ba daidai ba domin ta kira ni tana ja min kunne akan yaran nan” Ko kadan maganar da Hajiya Kaltume ta yi bata yi ma Appa dadi ba, sai yake jin kamar bata son zaman yaransa a gurinta ne, hakan kuma sai ya kara jefashi a cikin damuwar sakin mahaifiyarsu da yayi gashi nan ya koma nema musu gurin zama domin ba zai iya barinsu a katon part din uwarsu su biyu kawai ba babu mai kula da su. “Hurriya yata ina kike son zama?” Ya tambaya yana kallon fuskarta, Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume sannan ta kalli mahaifinta ta ce. “Gurin Hajiyarka ko Gwaggo” “Ba zan iya bari ku zauna hannun kowa ba matukar ina raye, na fi sonku a kusa da ni na rika yaran wasu ma ta ina zan bada nawa riko? Idam har ba zan iya bari ku zauna gurin Iyami ba to ba zan iya hakurin ku zauna a gurin kowa ba, je ki kira Hamad” Hurriya ta tashi ta fice, Hajiya Kaltume ta bita da kallo Appa kuma ya sauke ajiyar zuciya. “Yaran nan sun zamar min kamar wasu marayu, Wallahi yau saboda tunanin abubuwan da suka faru na kasa sukuni” “Akwai damuwa kam sosai, na da zaka hakura ka dawo da mahaifiyarsu da duk yafi wannan nema musu gurin zama da kake, idan ma wani laifin ta yi maka ka yafe mata dan Allah ko mu da muka kwana biyu aka saki a yanzu ai sai mun ji dabam balle kuma ita da take da sauran kurciyarta” Appa be ce komai ba bayan sauke kai da yayi kasa, domin baya jin dawowa da ita mafita ne kamar yadda sakin ma ya kasa zame masa mafita domin ko yanzu jin yake kamar akan ƙaya yake saboda tunaninta domin yana matukar son matarsa ga kuma tunanin makomar yaranta. Hajiya Kaltume ta tsare mijinta da ido ganin ya noce kai kasa sai zuciyarta ta raya mata zai iya dawowa da ita kenan ganin yadda ya zurfafa a tunani ga kuma son yaranta da yake. Sai a lokacin da Hurriya ta dawo dakin tare da Hamad sannan Hajiya Kaltume ta kawar da kai tana kwafa a zuciyarta, Appa kuma ya dago ya kalli Yayansa. Hurriya ta zauna a inda ta zauna dazun Hamad kuma ya tsaya jikin kofa fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Hamad ka ci abinci?” “Aa” Ya amsawa Appa da kai. A take Alhaji Haruna ya kalli Hajiya Kaltume. “Ba a basu abinci ba Kaltume?” “Tuwo na girka, ka san Hamad ba ya cin ciwo kuma basa cin abinci da ake girkawa masu aiki” “Idan shi baya ci ita Hurriya bata ci? Haba Kaltume kin san uwar yaran nan bata cikin gidan nan a matsayinki na babba ki kasa kiran yaran nan ki ba su abinci?” “Ban yi tunanin ba su ci ba, ranka ya dade ayi hakuri ba za a koma ba In Shaa Allahu” “Hurriya zaki ci tuwo?” Hurriya ta daga kai a hankali daman tuwo is one of her favorite saboda abincin Appanta ne ita kuma duk abun da Appanta yake so tana sonshi, kuma yawan girka shi da Amma take ya saka ta saba da cinsa, domin Alhaji Haruna ba shi da wani abinci da ya fi tuwo duk arzikinsa ya fi son agirka masa tuwo a gidansa domin abun da ya saba da shi tun kamin zuwan arzikin. “Zan ci tuwo Appa” Ya kalli Hamad da ko a yau ko sannu da zuwa be masa ba kuma be gaishe ba, abun da be saba ba domin duk tsaurin kansa yana gaishe da Appa yana masa sannu da zuwa kamar yadda Amma ta koya masa. “Kai kuma me kake son ci? Je ka kira Dahiru ko Bello ya kaika Restaurant ka siyo abun da kake so” “Bana son komai” Ya amsa kai tsaye ba tare da ya kalli kowa ba. Appa ya kalleshi da kyau. “Hamad zo nan” Ya shiga cikin dakin sai ya zauna nesa da Appa kamar wani bakonsa ko wanda be saba da shi ba, bayan kuma a da can ba haka yake masa ba idan yayi nesa da shi to yayi laifi ne, amman idan babu laifi baya zama nesa da mahaifinsa kuma sukan zauna su yi hira da juna ayi wasa da dariya sai dai ba kamar yadda suke yi da Hurriya ba. “Me aka yi? Waya taba ka?” “Babu ba ayi min komai ba” Hajiya Kaltume ta tabe baki tana murmushi. “Kai ma dai Alhaji, a gidan nan ba zai taba Hamad ya kwana lafiya? Idan ma an fi karfinshi ai kasan yadda yake yi ma mutane ruwan duwatsu ko kuma ya shammaci mutum yayi masa wata ƙetar” Hamad ya dago ya kalli Hajiya Kaltume da irin kallon da ya fi kama da harara, daman can shi ne mai taya Amma kishi wani lokacin, Hurriya kam team babu ruwanmu ce. “Toh na ga yana ta bata rai ne kuma yace ba zai ci abinci ba?” “Uhm. Hmm” Kawai Hajiya Kaltume ta ce ta cigaba da kallon Appa dake tambayar Hamad ina yake son zama. “Ina Hurriya zata zauna?” “Gurin Momy” Appa ya amsa masa. “Nima zan zauna a can” “Toh yayi kyau, amman dai ka saki ranka Hamad ka ji? Kuma ka ci wani abun yaushe rabonka da abinci?” “Na sha zobo da rana” “Zobo ai ba abinci ba ne, zaka sha tea da bread a hada maka?” “Bana son komai Appa bana jin yunwa” “Shikenan zan yi ma Nafisa magana sai ku maida kayanku part dinta” Appa ya fada cikin yanayi na rashin jindadin dansa be saka komai a ciki ba. Hamad ya mike tsaye ya juya. Appa ya bishi da kallo yana fadin. “Hamad babu ko sai da safe?” “Sai da safe Appa” Ya fada ba tare da juyo ba har ya fice. Hurriya ta mike tsaye domin yunwa ta matsa mata lamba. “Appa ina tuwon?” Appa take tambaya sai Hajiya Kaltume ta amsa mata. “Je bangarena ki zuba ki ci, mahaifinki ya rima ci balle ku ci tare” “Toh” Ta nufi kofar fita da saurinta. Sai da ta fice Appa ya kalli Hajiya Kaltume ya ce. “Dan Allah a rika kula da yaran nan, su da marayu duk daya yanzu” “Alhaji, dan Allah na ci wannan alfarma dan Allah ko dan yaran nan, mahaifiyarsu ma tunaninsu sai ya isheta kuma kai yanzu baka lura Hamad fushi yake da kai ba?” “Fushi me?” “Ka kore mahaifiyarsu mana” “Ba kin cw bata fada musu ba?” “Eh amman ka san shi ya yafi yar'uwarsa wayo, ba mamaki ya gane, ita kanta Hurriya idan ta fahimta ba zata jidadi ba” Appa ya sauke ajiyar zuciya. “Ba zan iya ba ne Kaltume, gobe za a zo da motoci akwaishe mata kayanta” “Subhanallahi Alhaji har saki nawa ka yi mata ne?” “Daya” “Amman za akwashe kaya da wuri haka? Wai me yayi zafi ne shi ba wuta ba? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un” Ta fashe da kuka ta mike tsaye ta fice daga dakin tana rusar kuka kamar gaske. Appa ya busar da iskar bakinsa shi kansa ya san it's too early ace an kwashe kayan Amma a gidan daga sakinta, sai dai kiran da Bappa yake masa yake son amfani da damar ya nuna musu babu sauran zama tsakaninsada Amma, domin ya kasa amsa wayarsu tun jiya saboda be san abun da zai fada musu ba. Kai ya gigirza sannan ya tashi tsaye ya fice daga part dinsa zuwa part din Hajiya Nafisa wato Momy. HURRIYA POV. Hurriya na shiga bangaren Hajiya Kaltume ta samu Umm Khairi zaune a dinning tana cin nata abincin daren, da a bangaren mahaifiyarta ne sai da ta bude ta zuba amman a nan dole ta tsaya a zuba mata ko kuma a bata izinin zubawa. “Yaya Khairi Hajiya ta ce na zuba abinci” “Gashi nan ai dauki plate ki zuba mai isarki” Hurriya ta dauki plate ta bude manya warmers din ta ta dauki mulmular tuwon da aka nade a leda ta raba uku ta zuba daya a plate ta rufe ta bude dayan ta zuba miyar kubewa ďanye ta saka nama da man shanu sannan ta rufe ta ja kujera har ta zauna ta tuna bata wanke hannu ba ta tashi ta shiga bandakin dake falon ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin tuwon, sai da ta yi nisa da cin abincin sannan Khairi ta kalleta. “Hurriya” Hurriya ta dago a hankali ta kalli yayarta Khairi wadda ta kira sunanta. “Na'am?” “Me Appa yace miki da ya aiko a kira ki?” “Tambayarmu yayi ina muke son zama” “Toh ina kika zaba?” “Ni dai na ce gurin Gwaggo ko Hajiya, amman yace aa sai dai gurin Momy” Khairi ta yi fuskar tausayi. “Allah sarki, Wallahi na tausaya muku babu dadi rayuwa gidan babu uwa a gida, da ma dai Appa zai yi hakuri da ya dawo da Amma, Hurriya na ga Appa yana jin maganarki why not ki roke shi ya dawo da Amma idan ma wani laifin ta yi masa ya yafe mata” Hurriya ta yi mata wani kallo na rashim fahimtar inda zancenta ya dosa. “Amman zata dawo idan ta haihu ai” “Toh Allah yasa ya maida ita, wata kila akwai gyara ai Wallahi duk ban jidadi ba dazun har da kukana” Hurriya na jin haka sai kwakwalwarta ta dauka sarai ta gane karatun Khairi a take wani irin tashin hankali ya same ta, idonta dake cikin farin gilashi suka cika da hawaye ta kasa hade lomar tuwon dake bakinta. Slowly ta mike tsaye taja kujera baya ta fara tafiya zuciyarta na buga kamar zata fasa kirjinta ta fito, tana fita falon ta watsa da gudu bangarensu da karfi ta tura kofar falon Amma ta shiga. Hamad na kwance kan kujera yana kallon remote a hannunsa. “Hamad wai Appa sakin Amma yayi? Wai rabuwa suka yi? Yaya Khairi ta fada min” Tana maganar yana kuka even though bata gama tabbatarwa ba. Hamad ya tashi zaune yana kallonta. “Ai ke ce mahaukaciya shiyasa baki gane ba” A nan Huriyya ta samu damar fashewa da kuka mai karfi, ta juya da sauri ta nufi bangaren mahaifinta. *** *** *** “Ah Ah Alhaji ina ce Kaltume ce Babba a gidan nan? Me zai hana su zauna a bangarenta?” Appa ya mike tsaye. “A nan nake son su zauna, kuma nan za su zauna ko kin yarda ko baki yarda ba, domin ke da su duk a karkashin ikona kuka kuma a gidana” “Aa Alhaji gaskiya ban ci ƙashi ba ba zan ci aman tsoka ba! Har ina? Yara da girmansu da komai a kawo min su? Da wani abun arziki ne ai matarka take tarewa ta karbe sai a yanzu da yake wahala ce za a kawo min” Appa ya nuna kansa. “ƴaƴane wahala Nafisa? Ke dai har abada ba zaki taba zama matar kirki, har abada mai hali be taba fasa halinsa ba, kowa yana girma yana kara hankali da hali na gari amman ban da ke” “Daman ni ban taba haske a idonka ba, masu haske Iyami ce da Kaltume, ka san ni ka san halina ni bana son a shiga sabgata ina bangarena babu ruwana da kowa, akan me yanzu za a dauko yayar sarauniyar gida mace da ta hana ka ganin martaba a kawo min” Alhaji Haruna ya nuna ta da yatsansa. “Sau daya tak bakinki ya sake furta wata magana marar dadi akan Iyami da yayanta sai mugun saba miki, ni na zabi su zauna a nan kuma a nan din za su zauna, idan baki son zama da ƴaƴana jinina ƙofar gidan a bude take..!” Momy ta aje numfashi da karfi. “Bismillah ga dakuna nan su zabi wanda suke so su zauna, gidan naka ne yaya naka ne ni ma taka ce Allah ya ba mu hakurin zama” Fuuuu! Appa ya fice daga falon nata cikin mugun bacin rai. Namra da Musib suka bishi da kallo su kansu sun manta when last su ga mahaifinsu a cikin bacin rai irin wannan sai yau. “Tsakani da Allah takurawa ce dawowarsu a nan, musamman ma dan iska yaron nan Hamad ni ubansa zan ci Wallahi” Cewar Musib yana jin haushin hukuncin da mahaifinsu ya yanke. Bakinciki ya hana Momy sake cewa komai ta kai hannu ta dauki sarkar zinarinta dake kan aje a hannun kujera ta mike tsaye ta nufi upstairs, kamin ta isa dakinta ma wani aiki ne saboda izza da isa kamar wadda bata son taka kasa haka take tafiya. Bakin gadonta ta zauna ta rike da sarkar sai cika take tana batsewa, ita dai ta san tana daga kafa akan kishi da matan Alhaji Haruna domin ganin take babu sa'arta a cikinsu Hajiya Kaltume dai yar talakawa ce arzikin na Alhaji Haruna Mai Yadi ne, Iyami ma haka rufin asirinsu na Alhaji Haruna ne domin har gidan da iyayenta suke ciki a yanzu shi ya siya musu shi yake dauke da nauyinsu. Kuma Iyami ba sa'arta bace a shekaru, kuma ta fi Hajiya Kaltume zama makaskanciya a idonta domin ita ga aiki ta zo yi a gidan ta aure Alhaji Haruna, ba dan ma da kaddarar aure ta hana ba kuma yara sun shiga tsakani ba wata kila da ba zata iya hakurin sharing miji daya da yar aikin gida ba, kallon da take yi ma Amma bata da ajin da zata yi kishi da ita sai idan abun ya motsa. Ita dai abun da ta fi tsana shi ne a shiga sabgarta, idan ta shiga sha'aninta na masu arziki har mantawa take da Hajiya Kaltume da Amma, a yanzu kuma kawo mata Hurriya da Hamad da Appa ya dage sai shi ne abun bacin ranta a yanzu, domin da su zauna a gurinta kara ya dawo da uwarsu ta rainin abunta, sam sam Momy bata son yayan kowa idan ba nata ba, bata mutanta kowa sai masu kumbar susa, idan baka da arziki har ganin take kamar baka cika mutum ba. [10/18, 5:34 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: https://chat.whatsapp.com/GJ9hOtbWbfDKmq8NrKsDIG ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝗣𝗮𝗴𝗲 6️⃣ Da tunanin Amma Appa ya dawo apartment dinsa, tsansar biyayyarta da yadda take gujewa bacin ransa da nuna kulawa akan duk wani abu da ya shafe shi. Ya tabbatar da ita ce ba sai ya bukaci a bawa Hurriya abinci ba, matukar ta san uwar yaran bata gidan zata yi kokarin kwatantan kyautata musu kuma ta ja su a jiki, haka ma da ita ce ya zo mata da zancen dawowa ƴaƴan abokiyar zamanta a bangarenta zata yi marhabun ta karba da hannu biyu ko da kuwa bata son haka ba zata nuna har ya gani ba, duk wani abu da Amma ta san Appa yana son kokarin raya shi kaunar abun take ba ta bata masa rai ba. Hannayensa hade a bayansa yake tafiyar fuskarsa a yanutse zuciyarsa a hargitse yana jin kamar ya fashe da kuka gaba daya ya rasa me ke samunsa ya rabu da matarsa rabuwar ta haifar masa da rashin kwanciyar hankali da bacin rai, zamanta a gidan kuma masifa ce a gidansa masifar da be san ta micece ba domin shi dai ya san matarsa bata masa laifi ba, be san dalilin da ya saka ya tsane ta ba. Kukan Hurriya ne abun da ya fara masa maraba da zuwa a lokacin da ya kunna kai cikin falonsa, kuka take sosai irin kukan nan da ya hana gilashin idonta tsaya saboda hawayen da ke cika shi, ta rike gilashin a hannu lipa dinta da jikinta sai rawa suke, dishe-dishe ta ga alamar shigowar mutum bata bukatar saka gilashi domin tantance waya shiga, ta san tsayinsa da yanayin tafiyarsa ta haddace komai. Shi ya taho da sauri ita ma ta nufo inda yake da sauri tana rike da gilashin dayan hannunta kuma yana lalabensa. “Appa. ..apa... Appa... Appa wai ka rabu da Amma?... Sakin Amma ka yi?” “A gurin wa kika ji wannan maganar Hurriya? Waya fada miki haka cikin daren nan?” “Yaya Khairi.... Appa da gaske? Appa why? Yanzu mu kadai ne zamu rasa uwa a nan Appa! Me Amma ta yi?” Tambaya take tana wani irin kuka numfashi na fitar mata da karfi kamar ranta zai fita. Idon Appa ya cika da hawaye “Bata yi komai ba Hurriya, be kamata ki shiga cikin magana irin wannan ba, zauna a nan ina zuwa” Ya nufi kujera da ita ya zaunar da ita, ya juya ya fita gaba daya abubuwa sun rike masa har ji yake wani abu na juya masa cikin kai, kamar za a haukata shi haka yake ji. Bangaren Hajiya Kaltume ya nufa tun a tsakar falon ya fara kiran Khairi rai a matukar bace daman ciwon sakin Amma da ya kama shi, ga bacin ran da Momy ta saka masa yanzu kuma Khairi ta kara masa wani ta hanyar batawa Hurriya. Umm Khairi ta fito daga dakin Hajiya tare da Maama Umm Ruman na biye da su a baya, Umm Salma da Yasir kuma suka fito a nasu dakuna duk suka sauko kasa. “Alhaji Lafiya?” Cewar Hajiya Kaltume da ta riga su saukowa gabanta har faduwa yake. “Akan wane dalili Umm Khairi zata fadawa Hurriya sakin mahaifiyarta aka yi? Ita mahaifiyar bata fada ba sai ke yar iya? Wannan ba rashin hankali da rashin tarbiya ba ne? Ki shiga cikin maganar iyayenki?” Ya juya gurin Hajiya Kaltume. “Kin ga abun da kika hanyo ko? Kin maida yaran nan kawayenki da maganar da ya dace da wanda be dace ba duk fada kike a gabansu, har suna jin sun isa sun kai su saka baki a zaman takewar mahaifinsu, sai na koya miki hankali sai na koya miki hankali Ummul Khairi” Jikinta ya dauki rawa domin ta san halin Appansu idan hau yana wuyar saukowa. Yasir ya karbawa Appa. “Iskanci ne da rainin hankali, ta fi uban kowa baki da bakin iyayi a gidan nan kamar wata babbar mace, yau sai kin fadi wanda ya aike ki” Hajiya Kaltume na jin haka ta yi saurin zunguje Khairi. “Ba zaki bada hakuri ba yar iskar yarinya? Idan kuma ba haka ba ne sai ki fadi yadda aka yi ai ko?” “Appa Wallahi karya take min, yarinyar nan munafukace sai dai idan labe ta yi, ko kuma so take ta hada min sheri” Tana rufe baki Yasir ya fara dukan bakin nata ya saka hannnunsaya kama lips din ya jan sai da ta ti ihu sannan ya rufe ta da duka gaba daya, Hajiya Kaltume ta fara kokarin kwatar yarta Appa kuma ya fice daga falon ba tare da ya hana Yasir dukan Khairi ba. “Ai fa an taba yar gata yar gaban goshi yar lasa da halshe, kai dan Allah karka kashe min ƴa saboda ƴar wasu da ba zata amfana maka komai ba” Hajiya Kaltume na masifa tana kwatar Khairi dake ta rusar ihu, Maama da Salma sai haushi suke ji saboda ana dukan yar'uwarsu Ruma ce kadai take jin abun da yayarta ta yi bata yi daidai ba. A bangaren Hurriya Appanta na fita sai ta tsagaita kukanta ta share hawayen da suka ki tsaya mata ta saka gilashin da zai bata ganin kofar fita dakin daidai ta mike tsaye ta fito daga bangaren mahaifinta ta dawo na su bangaren tana tafe tana hawaye har ta isa. Sai ta ta tura kofar falon ta bude sai kuma ta kasa shiga domin jin take kamar Amma ma mutuwa ta yi ba barin gidan ba bata taba sanin haka kewa take ba sai yau da ta yi kewar mahaifiyarta. Kusan da ita da wanda ba shi da lakka a jiki duk daya domin tun a yanayin tafiyarta zaka fahimci zuciyarta ta karaya salulu ta shigo falon ta zauna kan kujera har lokacin Hamad na zaune a inda ta barshi, sai dai a yanzu fuskarsa na nuna danuwar dake zuciyarsa domin ya bata rai sosai ba kamar dazun ba d ya bar abun a cikin zuciyarsa. Fashewa Hurriya ta yi da kuka tana girgiza kai ji take kamar ace mata ba gaske ba ne, da ace ta san sakin Amma Appanta yayi babu abun da zai hana ta binta, da ba zata yarda ta zauna a gidan ba, a yanzu kam ta yarda ita wawuya ce da bata yi saurin ganewa ba, domin tana da saurin yarda idan aka fada mata abu dauka take ko da kuwa ba gaskiya ba ne. Kukanta ne ya saka Hamad hawaye yana ta dantse baki yana boye cikarsa domin zuciyarsa kawowa take kamar wani zaki, amman sai duk da hakan sai ya gagara rike kansa shi ma ya fasa kuka, ita da shi suka zama kamar wadanda aka cewa Amma ta mutu ta bar su. “Hurriya Hamad” Kusan a tare suka dago suka kalli kofar gefen Dinning din kofar da Appa ke tsaye, kofar cikin falon Amma ce dake basu damar shiga bangaren Appansu. Hurriya ta tashi da sauri ta nufi inda yake tana kuka sosai Hamad kuma ya dauke ido alamar baya son ganin Appa. “Wannan kuka sai kace an yi mutuwa? Haba karku saka kanku a damuwa tsakanin halshe ra hokora ma ana basawa balle kuma mutum da mutum, dan tsabani muka samu shi ne Amma ta tafi gida, amman da zarar al'amurra sun daidaita zata dawo” Hurriya ta kasa magana sai kuka take, Hamad kuma ya mike tsaye ya share hawayensa ya nufi sama. “Karka shiga, ba a nan zaku kwana ba, na yi magana da Momynku a can zaku kwana ku zo muje” Be jira cewarsu ba ya kama hannun Hurriya zuciyarsa na masa babu dadi, daman can shu baya son kukan wani ko ganin wani a damuwa balle kuma yaransa, sanin cewar shi ne silar damuwar ya saka shi jin babu dadi gaba daya abubuwan sun zo masa ta yadda be yi zato ba. Ganin Appa ya nufi kofar fita falon tare da Hurriya ya saka Hamad ya bi bayansu, sai da suka fita harabar gidan gaba daya, sannan Appa ya tsaya ya tsayar da yarsa ya daga kanta ta kalleshi. “Haka zamu shiga bangaren Momynki kina ta kuka Hurriya? Dan Allah ku yi hakuri idan ba so kuke ni ma na yi kukan nan ba, ba ku san abun da yake cikin zuciyata ba, ina cikin wani irin tashin hankali da rudani marar misaltuwa” Kai kawai ta iya daga masa ta saka hannayensa ta share hawayenta tana ta aikin hade kukan dake neman ya gagari tsayawa a iya bakinta da idonta. “Ammanku ba mutuwa tayi ba, zaku iya zuwa ku ganta a duk lokacin da kuke so, ita zata iya zuwa ta ganku, Hamad na san kai ne mai zuciya ka sakawa kanka hakuri dan Allah ko dan yar'uwarka” Ko saitin gurin da Appa yake tsaye Hamad be kalla ba, yadda ya dauke kai yana kallon wani gurin sai ka rantse da Allah ba da shi Appa yake magana ba, domin a yau kam ba shi da abokin tsana kamar Appansa saboda sanin cewar ya rabu da Amma, ko da kuwa ba zai iya fadar abun da ya faru tsakaninsu ba, hausawa suka ce mai lalabe a duhu balle an haska masa, a banza yayi fushi balle an taba shi. Appa ya dauke kai ya rika hannun Hurriya suka cigaba da tafiyar, da kansa ya shiga falon, be zarce ko ko'ina ba sai Stairs kai tsaye ya nufi dakunan da suke gefen bedroom din Momy kamar yadda suke a kowane bangare, ya san dakin Namra da na Musib da Miwan dan haka be taba dakunansu ba ya nufi wani dakin ba dabam ya tura kofar dakin sannan ya saki hannun Hurriya daki ne dake dauke da furniture na mutum daya domin Appa ya saka an zuba furniture an gyara ko wane daki duk kuwa da kasancewar wasu dakunan babu kowa, ba dan komai ba sai dan irin haka ko kuma idan an yi baki ko ma idan yaransa sun yi sha'awar canja daki daga wani zuwa wani. Hurriya ta daga kafarta ta shiga cikin dakin ta isa bakin gadon da zai wadaci mutum daya ta juyo ta zauna ta a hankali tana kallon Appanta dake jan kofar dakin. Gam... Kofar na amsawa gabanta ya yanke ya fadi, gaba daya sai ta ji kamar wata duniyar aka kawo ta, sai ta ji kamar wani gidan da bata san kowa ba kuma bata da gatan kowa a ciki aka kawota. Rabon da ta shiga bangaren Momy ma an dade, babu ruwanta da bangare sai da dalili ita ma Momy bata shiga nasu bangaren ita ta ware kanta dabam a gidan. Dayan dakin dake kusa da na Hurriya Appa ya budewa Hamad “Nan zai mana Hamad?” Ya daga kai sannan ya saka kai ya shige dakin da kansa ya turo kofar dakin ba tare da ya jira mahaifinsa ya rufe masa ba. Appa ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya sauka, Namra da Musib suka hada ido suna mamakin yadda Appa ya shigo da Hurriya be ma bari ta zo da kanta ba. “Musib ina Miwan?” “Ya fita da magariba nan Appa” “Namra da Musib dan Allah a zauna lafiya, yaran nan kanenku ne, jini daya ne ku da su, bana son na ji wani tashin hankali ko fada, Hamad dai kun riga kun san halinsa ba sai an fada muku ba, duk wani abun da zai yi ku kawar da ido ni kaina da nake mahaifinsa hakuri nake da shi, Hurriya kuma kun san babu ruwanta da fita dan Allah a zauna lafiya” Nasiha yake musu amman zuciyarsa cike take da kunci da damuwa narar misaltuwa. Appa ya amsa cike da ladabi “In Shaa Allahu Appa” Ya dan motsa kansa kadan alamar gamsuwa sannan ya nufi kofar fita. “Sai da safe Appa mu kwana lafiya” “Allah yasa” Ya amsa sannan ya fice. Yana sakin kofar falon Musib yayi kwafa ya mike tsaye ya nufi stairs Namra ta bi bayansa, ita ta shige dakin Momy Musib kuma ya nufi dakin da zuciyarsa ta raya nasa Hurriyya na ciki. Ya tura kofar dakin kamar abun arziki ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta idonta shar da hawaye. “Yar gatan Appa, da kansa ya riko hannunsa ya kawo ki, kuma saboda ke yayi ta fada da Momy” Uffan Hurriya bata ce masa ba, har ya gaji da tsayuwa ya bar mata kofar a bude yayi tafiyarsa. Runtse ido ta yi tana jin wani sabon kuka na zo mata, ta dawo a rakube gurin ta ta san cewar zata sha azaba da wahalar zama, da ma ace bangaren Hajiya Kaltume aka ajeta ko ba komai zata samu sauki ta wani bangaren saboda Yasir, amman a na bangaren ta san babu mai sonta, gaba daya sai ta ji ta zama wata marainiya ashe ba sai da rashin uwa da uba ake maraici ba. Musib na barin kofar dakin Hurriya ya nufi dakin Hamad ya tura, kwance ya hango shi saman gadon ya baya kofar baya, kuma budewar da Musib yayi be saka Hamad juyo dan ya duba ko waye ba. Wani mugun kallo da tsana irin ta yan uba Musib ya jefi kanensa da shi, sannan ya bar kofar dakin shi ma be rufe masa ba, Hamad na jin alamar an tafi ya juyo ya sauko saman gadon ya iso gurin kofar ya rufe ta da karfi ya saka key, Musib da be jima da barin bakin kofar ba ya juyo ya kalli kofar jin yadda aka bugata da karfi. “Zaka sha wahala yaro” Yayi kwafa ya nufi dakin Momy sai wani huci yake kamar mace, daman shi ne mai kishin da matan ubansa a gidan sai dai yana boye abun a zuciyarsa, yadda yake jin kiyayyar Iyami da Hajiya Kaltume ko Momynsa bata jin kiyayyarsu haka domin ita sai idan kishin ya motsa mata ne take kula su ko kula wani abu da ya shafesu. Daren sai ya zamewa Hamad da Hurriya dabam, sanin cewar rabuwa mahaifiyarsu ta yi da mahaifinsu ya hana Hurriya rutsawa har safe, sai ta raya daren da kuka Hamad kuma bayan ya gama nasa fushin bachi ya sace shi. Ta bangaren Appa ma yadda ya ga rana haka ya ga dare, kwanan Hajiya Kaltume ta bangaren be kuranye masa damuwarsa ba, sai ma ya kasa kwantar daga karshe ya koma falo ya zauna ya kunna Tv sai dai kuma babu mafitarsa a cikin kallon kamar yadda babu shi a cikin bacci sai ma karin damuwa, me yasa ya aikata shi ne abun da ya tsaya masa a rai yake ta tambayar kansa, idan kuma ya tuna da abun da yake ji idan tana gidan sai ya ga kamar yin haka shi ne daidai. Washe gari da wuri Hajiya Kaltume ta tashi, daman duk ranar girkinta da wuri take tashi ta shirya masa abun karyawa, kasancewar bata da mai aiki tun bayan da ta dauki Iyami aiki ta aure mata miji bata sake yarda ko mai sharar gida ta sake dauka ba, sai dai ta yi komai da kanta ba kamar Momy ba da masu aiki ne suke mata komai sai dai ta ci idan kuma ranar girkinta ne sai dai ta dauki na Appa ta kai masa. Ko da bakwai ta yi ta gama hada masa ruwan zafin tea da gasa masa bread dan ya fada mata tea kawai zai sha baya son cin komai. Yana shan tea yana hamma saboda bachi da ya gagareshi da dare da alama yana neman fansa a yanzu da safiya. “Wai dazun ina barin bangarenka Hajiya Fatee ta kira ni” Ya dan juyo kadan yana kalleta alamar ina saurarenki. “Wai danta Fadeel ya samu tsabani da matarsa shi ne take son na zo” “Allah ya kyauta...” Yadda ya amsa mata ya karantar da ita izinin zuwa ne, daman kuma ta san ba zai hanata ba. “Ameen zaman auren ne na su, zaman lafiya ta gagara Allah ya shirya tsakaninsu” Appa dai be sake cewa komai ba, har ya shaye tea ya aje cup be taba bread ba. Hakan kuma be yi ma Hajiya dadi ba domin ta san damuwar ba zata wuce ta ƴaƴan Iyami ba ko kuma ta Iyamin ma gaba daya. Ta dauke cup din ta fita ba tare da ta fada masa yanzu ta tafi ba da safen nan. Ta isa bangarenta rike da cup din. A dinning din da duka matansa suke fara cin karo da shi a kowane falo idan suka fito daga bangarensa ta aje cup din sannan ta nufi dakinta, tana shiga ta raba jikinta da tufafin da ta saka da safen nan ta daura tawul ta shiga bathroom, a gaggauce ta yi wanka gudun kar ta yi latti sanin cewar inda za su je kaune dake gaba daji baya daji. Ko da ta fito ta samu Khairi zaune akan gadonta fuska a kumbure musamman bakinta. “Subhanallahi haka Yasir ya fasa miki baki saboda yar iskar yarinyar nan?” “Ba laifin Ya Yasir ba ne Hajiya, laifin Appa ne yana mugun son yarinyar nan, ya fi kaunarta da duka sauran ƴaƴansa, dubi yadda ransa ya bace saboda na fada mata gaskiya bayan kuma gaskiyar ce” “Hmmm ai ni ganin nake kamar ba banza uwar yaran nan ta bar Alhaji ba, ita kanta ai ba a banza ta aure min miji ba, yanzu kuma saboda yaran nan Allah kadai ya san ran mutun nawa zai ɓace a gidan nan” “Wallahi sai na rama komai ta dade” “Toh ki rama dai ta sigar lalama, in ba haka ba Alhaji ko Yasir su ci ubanki kin san jira kawai suke” Ta tashi ta fice dakin tana wani zakuɗa ita ga balagaggiya. Hajiya ta shirya cikin koriyar Atamfa ta saka farin mayafi ta sauki jakarta mai kala daya da gyalen da kuma talkaminta ta saka sannan ta dauki wayarta ta kira daya daga cikin drivers din gidan ta sanar masa fitarta. Gurin da take aje kudi ta bude ta dauko kudi mai yawa ta zuba a jakarta sannan ta rufe ta rataya jakar ta fito rike da wayarta sai kamshi take zubawa irin na manyan matan masu kudi kuma masu miji da ikon gida. “Hajiya fita zaki yi?” Maama ta tambaya. “Eh wani guri zamu je da Hajiya Fatee” “Allah ya tsare, Hajiya kin ga yadda Ya Yasir ya fasa bakin Khairi” “Na gani, ku ma sai kun yi taka tsantsan ai, ni ba dan ubansu daya ba ai sai na tsora ta na ce aurenta yake son yi” “Lallai ya fi sonta da mu ma” “Hmmm Allah dai ya kyauta, ki tashi sauran yan 'uwanki kar su yi latti makaranta, ni na fita” Daga haka ta fice daga falon Maama na yi nata Allah ya tsare. Ko da ta fito direban har ya tashi motar ya juyata tana fuskantar gate domin ya san uwargidan Alhaji Haruna Mai Yadi bata daukar raini. Tana shiga motar be tsaya da ita ko'ina ba sai gidan aminiyarta Hajiya Fatee, yana aje ta ya juya a can ma ba su bata lokaci ba, Hajiya Fatee ta kira direban dake kai su kauyen ta sanar masa sun shirya, ba su yarda su tafi da motarsu ba saboda tsoron masu kidnapping da kuma tonon asiri, sai dai su dauki shatar motar kasuwa ta zo ta dauke su har gidan Hajiya Fatee ta kaisu inda za su je, kasancewarsa mijin Hajiya Fateen ya dade da rasuwa ita kadai ce a katon gidan sai yan matanta biyu da kuma masu aiki da danta Fadeel ya zuba mata. Misalin karfe tara da rabi na safe suka kama hanyar kauyen gidan zalla dake cikin local government din Kwatarkwashi. Suna tafe suna hira Hajiya Fatee na kara fada mata yadda matar danta Afrah ke son mulkar mata ďa ta saka shi ya manta da ita. Idan ta kai aya sai Hajiya Kaltume ta dauko nata zancen na abun da ya faru tsakaninta da Alhaji a jiya. Sanar da shi da suka yi cewar suna nan tafe ya saukaka musu wucewa kai tsaye dakin da yake gabatar da tsiface-tsifacensa. Sai da ya fara yi musu maraba da zuwa sannan Hajiya Kaltume ta ciro kudi 300k ta aje masa tana masa godiya. “Aiki yayi Malam, dan haka na zo da kaina na kawo maka goronka, kuma na yi maka godiya” Malamin da hakoransa ke daskare da jan goro ya yi dariyar jindadi da farinciki ya jinjina kai. “Hajiya ai na fada miki, indai muka yi aiki ba a dawo mana da shi, kuma kar tunanin kin yi kin yi baki dace ba yasa ki karaya a gurinmu, idan kin ji ana malam anjima da nisa ba ma gobe da nisa ba to kika zo nan kakarki ta yanke saka kawai” “Na gani ai Malam Wallahi na gode, domin shekara da shekaru ina neman yadda matar nan zata bar min mijina amman abu ya garara sai an yi kamar za a rabu sai kuma ka ga ba rabuwar bace, sai yanzu Allah ya kawo karshen abun, sai dai ko yanzu ni ina jin tsoro domin na lura ya shiga damuwa matuka gaya saboda sakinta da yayi, ina jin kar ya ce zai dawo da ita domin saki daya yayi mata” “Ina ko alama! Karki damu Hajiya, idan har mutum zai mutu ya dawo to kishiyarki zata dawo gidan, ai farraqu muka musu ita tana gabam yana yamma har abada ba zama a tsakaninsu” Wani kalar dadi ya lullube Hajiya Kaltume. “Haka nake so, kuma ina son a koya mata hankali so nake ka yi mata wani aikin da ba zata sake aure ba har abada, tun da ta zabi kishi da ni to ko bayan ta bar gidan mijina sai ta dandana bakincikin da nadanar auren Alhaji da ta yi, sannan be sake ta sai da ya damka mata kudi har miliyan asirin, Malam ina son a lalata duniyar da ya bata, har da gidan da ya mallaka mata idan akwai yadda za'ayi a ruguza gidan ko ma ya karbe abunsa, kuma a daureta ko kare kar ya sake sha'awarta balle har ta yi aure” “Wato so kike a lalata duniyar da ya bata, ba wadda ya bata kawai ba, har tata duniyar da ta mallaka za a iya lalatawa idan kina so” “Aiko idan ka yi min haka, ina mai tabbatar maka aikin Hajji bana da kai za'ayi, kuma zan maka kyautar kudi har naira miliyan daya” Malamin ya sake yin dariya yana gyara babbar rigarsa. “Hajiya na miki alkawari akaifa kishiyarki ba zata sake amfana da ita ba, ba duniyarta ko ta mijinki da ya bata ba, har dukiyar wani idan ya dauka ya bata ba zata taba amfanarta ba, ita da aure ko sai lahira idan ana yi, kuma yadda ba a mutuwa a dawo haka ba zata sake dawowa a gidan mijinki ba” “Alhamdulillah” Hajiya Kaltume ta fada tana daga hannu sama ta yi ma Allah godiya, sannan ta kalli Hajiya Fatee suka taba suna dariya. Daga bisani Hajiya Fatee ta kora masa da nata bayanin. “Malam nima da tawa mtsalar na zo yau, suruka ce ta saka ni a gaba, ta mallake min ďan yaki ya kara aure kuma baya jin maganar kowa sai ta matarsa, ga kudi yana da shi amman ko kyauta zai yi sai abun da ta so yake bayarwa, ni so nake a raba su ya sake ta saki uku idan da dama” Malamin ya amsa mata da kai. “Ya sunanta, ya kuma sunan ďanki?” “Afrah ake kiranta, shi kuma Fadeel” Ya dauko kasa dake cikin farantin katako ya dora a cinyarsa yayi zane zane ya jinjina kai ya dago ya kalli Hajiya Fatee. “Lallai sai kin tashi tsaye, ta mallaki danki Mallaka bata wasa ba, kuma idan ba ki yi da gaske ba abu ne mai wahala ya sake yin aure ko da kuwa ta mutu” “Ka ji irinta ba, shedaniyar yarinyar na sha wahalar yarinyar da can babu ruwansa da ni ma, sai da na tashi tsaye, dan abun da ubansa ya bar min duk a can ya kare, ba dan Allah yasa nasa gadon yayi albarka kuma ya samu babban aiki ba da yanzu mun kade” “Toh lallai dai gata nan ko yanzu a tsaye take akan danki” “Dan Allah a zaunar da ita, idan da dama ma a kwantar da ita a saka ta bacci ko a sumar da shegiya” Malamin yayi dariya “Ai tun da kika zo nan komai zai zama tarihi Hajiya, ki bada kudin karan alkamin kawai a saka aiki” Da sauri ta bude jakarta ta dauko kudin da ba zai wuce 30k ba ta aje masa. “Ga wannan ban zo da kudi mai yawa ba, amman dai a fara saka aiki da wannan idan zan dawo zan ciko jaka da yardar Allah” “Toh shi ke nan ba matala idan na gama aiki na hada abubuwa zan kira na fada muku sai ku zo ku karba ko kuma ku aiko ko kuma ni da kaina na aiko muku” A bisa wannan suka yi masa sallama suka fito suka dawo cikin motar. Direban ya a kama hanya, ba su yi nisa da garin ba suka rage gudu ganin an tsayar da motocin dake gabansu a zatonsu sojoji ne, hankalinsu be tashi ba sai da suka fara jin harbe harbe wasu na ihu. “Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Bandits ne” Direban ya fada, da sauri Hajiya Fatee ta kalli Hajiya Kaltume da cikinta ya soma murdawa. “Mun shiga uku mun lalace, ya zamu yi?” “Shiyasa bana son shigowa dajin nan gari gaba daya ya lalace a yanzu” Cewar Hajiya Kaltume ido na raina fata. “Kai direba ya zamu yi?” “Hajiya ni ba ku kuka kawo ni nan ba, kuma gashi motoci a bayanmu balle mu juya” Maganar yake yana leken motocin dake bayansu ga karar bindigar sai matsosu take. “Toh ko dai mu kira Malamin nan mu fada masa” Hajiya Fatee da fitsari ya fara zubo mata ta kalli Hajiya Kaltume. “Ya mana me? Soja ne shi ko dan sanda?” “Ya turo aljannu su dauke mu mana, Hajiya mutanen nan suka kama mu ai mun shiga uku, kuma na cewa Alhaji me? Daga zuwa sulhun aure!” Cikin tashin hankali Hajiya Fatee ta ce “Aljannu suka dauke mu ai shikenan mun bar duniya kuma kara ma wadannan da aljannu dan su kai mu za su inda babu kowa su aje, ko su kai mu China aljanni ai ba zai dauke ka ya aje ka nan kusa ba sai wata duniyar” Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana neman agajin Allah. “Allah ka yafe mana Allah ka dube mu Allah Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, ni har na bata zane” Direba ya bude kofar a hankali ya sulale ya yanki daji cikin ciyayi. Hajiya Kaltume ta saka kalma shada, Hajiya Fatee ta kama mata suka karasa suka kallon juna kowacce na kai hannu ta taba yar'uwarta. domin sun san yadda suka ci suka koshi nan ba za su iya gudu ba ko sa sun gwada hakan. ____________________ Hmmmmm masu karatu kun taba gani ko jin mugun kishi da bakar hassada irinta ta Hajiya Kaltume? Ni dai Hurriya ta ba ni tausayi domin rayuwa gurin da baka bukatarka yana da wahala, musamman idan babu uwa a kusa. Ta wani bangaren kuma Iyami tana da laifi daga zuwa aiki sai ki aure mijin mata? Ina laifi ki rumgume talaucinki ki shafawa kanki lafiya, yanzu wa gari ya waya...? Mu hadu da ku page din gobe, amman kamin nan ina son na ga Comments baza-baza line by line in ji Bature... [10/18, 5:35 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝗣𝗮𝗴𝗲 7️⃣ Ana kiran sallah asuba ta sauko daga kan gadon ta nufi kofar dakinta ta bude ta fito, a hankali ta sauko downstairs, tana isa bakin kofar falon bata tsaya komai ba ta kai hannu zata bude kofar. “Ina zaki je?” Ta juyo da sauri domin bata yi tsammanin wani zai iya fitowa at this early ba. “Fita zan yi” Ta amsawa Namra. Cikin mamaki Namra ta wara ido. “Asuba ne fa” “Na sani, Hijab zan dauko na yi sallah” “Haba Hurriya shiga dakina ki dauko nawa mana, saboda Hijab sai ki fita tun a asuba ki koma part dinku kamar wata bakuwa, ke a gida kike fa” Hurriya ta dan sauke kai kasa daga barin kallon yayarta wadda ta bata shekara uku da haihuwa. Namra bata sake ce mata komai ta nufi kujerar da ta zauna a jiya ta dauki agogonta da assignment din da ta yi, sai da ta kusa hayewa  sannan Hurriya ta rufa mata baya, cikin ladabi da natsuwa ta shiga dakin Namra ta tsaya jikin kofa, haka Hurriya take bata sakewa da mutane tana da wahalar sabo, musamman idan ta san zaka tsangwame ta ko ka yi mata fada. Namra ta juyo ta jefo mata hijab din cikin hanzari Hurriya ta cafke. “Akwai carpet din Sallah a can?” “Aa babu” Namra ta dauki nata ta jefa mata Hurriya ta sake cafkewa ta juya ta fice daga dakin zuwa dakinta. Bata shiga nata dakin ba sai da ta kwankwasa kofar dakin Hamad tana kiran sunansa. “Na tashi” Ya amsa mata daga can ciki, sannan ta wuce dakinta ta maida kofar ta rufe. Tun bayan da ta yi Sallah bata sake fitowa ba sai da ta auna lokacin makaranta yayi mata, sannan ta bude kofar a hankali kamar wata bakuwa ta rufe ta nufo hanyar saukowa kasa gabanta har faduwa yake kar ta hadu da Musib ko dan'uwansa Miwan balle kuma Momy da ta san bata ishe ta kallo ba. Sai dai ta yi rashin sa'a Momy da duka yaranta suna falon zaune, abun da bata saka tsammani ba domin Momy bata tashi da wuri sai idan tana bangaren Appa shi ma da zarar ta kai masa abun karyawa zata sake komawa bachi kuma babu mai tashinta sai gidan maigidan ne da kansa if not kowaye ya tasheta zai gane kurensa a ranar. “Baka fada min zaka zo ba, ai da na saka an shirya mana abinci mai kyau” Cewar Momy tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune a kujerar dake facing nata, kyakkyawan saurayin farin saurayin mai jini a jika ya girgiza mata kai yana duba agogo hannunsa. “Noo Momy na gode tafiyar ta gaggawa ce, yanzu zan kama hanya, kawai na ce bari na biyo mu gaisa ne” Momy ta yi murmushin kasaita irin na manya mata. “Daman na sani, abinci idan ba na Hajiya Turai baka ci na kowa” Ya dan fadada fuskarsa da murmushim da ya kara masa kyau da haiba yana daga kai ya kalli Hurriya dake saukowa. Momy ta dan juya ta kalleta kadan ta dauke kai irin ba ki isheni kallo ba din nan. “Momy ina kwana” Hurriya ta gaisheta cikin ladabi Momy har ta yi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ci albarkacin bakonta amsa ciki ciki kamar an mata dole. “Yaya Musib ina?” Ya amsa, ta juya gurin dan'uwansa shi ma ta gaishe shi, sai ya amsa mata fuska a sake kamar dan'uwansa, ta kalli Namra ta gaishe ta kamin ta rufe baki Namra ta amsa tana mata an tashi lafiya, daga karshe Hurriya ta cike gaisuwarta da bakon da take kyautata zaton yana da muhimmanci a gurin Momy da yaranta ganin yadda suke ta murna da ganinsa kuma suka fito dukansu da sanyin safiyar nan suka zauna a falo just because of him. “Ina kwana” Ya d'auki 'yan dak'ik'u kafin ya amsa gaisuwarta, shi ma kuma ba da baki ba kai kawai ya daga mata and light smile. Binta yayi da kallo har ta wuce ta gabansa ta nufi kofar fita. “ƴar Mijina ce, kanenta ne ka ga ya fita dazun” Momy ta fada masa domin ta san ba zai tambaya ba, ta san kallon da yake mata be wuce na neman sanin wacece ba, dan zuwan da yake gidan jefi jefi be taba ganinta ba, haka ma bata yi masa kama da masu aikin Momy ba balle yace ko yar aiki ce, ba zai ce ya san kowa a gidan ba, amman yadda ya san familynsu musamman Momy idan har ta bawa wani damar shiga ma a falonta to yana da muhimmanci a gareta, sai dai abun da be sani ba wannan shigar ta dole ce ta cilastawar Appa ba dan Hurriya tana da muhimmanci a gareta ba. “Yaya ance an daga bikinka” Miwan ya tambaya yana kallonsa. Mutumen da Miwan ya kira da Yaya ya juyo ya kalleshi. “Ka aje wannan Yaya aside ka kira ni da real sunana Jamal” Momy ta yi murmushi mai sauti. “Haba dai Captain dukansu fa kanenka ne ta ina  za su iya kiranka da sunanka kai tsaye, dole sai da girmamawa” “Wallahi na tsani wannan Yayan na fi son a kira ni da sunana na gaskiya” Ya amsa mata da murmushi sannan ya mike tsaye sai zuba kamshi yake. Namra ta mike tsaye kamar sauran yan'uwanta tare da fadin. “Tafiya nan da nan Yaya ba zaka dade ba” Da hannu ya nunata. “Yanzu na gama yi ma Miwan gargadi shi ne ke ma zaki ďana ko?” Sai duk suka saka dariya ban da shi da ya nufi kofar fita yana yi ma Momy sallama. Momy ta mike tsaye ta rako shi har bakin kofar falon Miwan da Musib suka karasa gurin da ya faka motarsa suna masa a sauka lafiya, Momy da Namra kuma na tsaye jikin kofar har sai da ya shiga motarsa yayi musu horn ya fice sannan suka dawo cikin falon. “Captain baka iya masa, Allah kadai ke masa daidai, komai ka yi sai yace ba haka ba ga zuciya abu kadan ya fusata shi” “Ai gaskiya Ammy tana hakuri da shi” Cewar Namra Momy ta ce. “Toh ya zata yi haka Allah yayi shi, kuma shi kadai ya bata daga ita har Yayana magajin da suke da shi kenan” “Kuma Allah ya hada jininsa da ke, duk ya zo garin nan sai ya zo nan” “Kin ji Namra da wata magana, uwa daya uba daya ai ta wuce wasa, ko kin manta alakata da mahaifinsa ne, ga kuma Hajiya Turai a bata da kawa a familynmu sai ni” “Duk da haka dai Momy, Wallahi idan baya ra'ayinki ba zai zo ba, ba ke kadai kuke uwa daya uba daya da mahaifinsa ba amman ke kadai ce yake zuwa gurinki, duk ya zo gurinsu Hajjo sai ya zo nan, waya ma akai akai yana yawan kiranki” “Haka kuma da maganarki, je ki taso masu aikin nan yau muyi tashi dole su zo su fara aiki, ke kuma ki shirya ki wuce makaranta” “Okay” Ta amsa sannan ta nufi sama, Momy ta dasa hirar da su Miwan. “Ku yaushe zaku koma hutu ne wai?” “January nan zamu koma, ni ai gaba daya na samu na bar garin nan na huta” Musib ya ce. “Kai gari kake son bari, ni Wallahi kasar ce ya isheni, ba dan halin Appa ba kamar mu zai hana a fitar waje, maza ne mu fa kuma yawanci yayan sa'ainsa duk suna waje suna karatu amman ya hana a fitar da mu kuma shi ba zai fitar da mu ba” “Jami'ar nan kawai zaku kare a nan, amman masters da duk wani abu da zai biyo baya a waje zaku yi shi, na gaji da halinsa shi har yanzu be gama jefar da wannan halin nasa na da can ba, kuma a yanzu tun da na fahimci baya bin ra'ayi toh kowa yayi nasa ra'ayin kawai, duba yadda ya daga mana hankali jiya saboda kawai Hurriya ta zauna a nan” “Wai me yasa ba zata bi mahaifiyarta ba?” “Kai kana ganin uwarta zata yarda ta bita su zauna a can? Ai ba zata yarda ba tana ganin ga gidan arziki” “Toh ai ko da sun koma Appa zai mata komai” Musib ya sake fada. “Amman dai ba kamar idan tana gidan nan ba, kuma Kaltume ba zata yarda Alhaji ya yi haka ba, yadda ba ta bar shi ya kula da yarsa Sapna ba haka ba zata bar shi ya kula wadannan yaran ba matukar suka bar gidan nan” Miwan ya ce. “Wai Momy saki nawa yayi mata ne?” “Ina ruwana? Balle na tambaya can ta matse musu idan uku ne sun hutu, idan daya ne ma ya dawo da ita duk ruwansu ne ba nawa ba, ni ta harkokin gabana nake shirya ba a kaina take zaune ba, daga ita Iyamin har Kaltume babu wadda zata nuna min komai gaba da baya, mu da talauci sai a baki shi ma dan ambata kawai, su ko babu wadda bata tashi a cikinsa ba, ni ko babu wadda be san ubana ba a garin nan ba” “Ai shiyasa Hajiya take shakkarki, yadda take ma Amma da yayanta bata mana haka” “Ai bata ga fuska ba ne, ita kanta ta san na fi karfinta ta ko'ina, kuma ni bana jiran abun Alhaji ita da Iyamin dai suka dogara gareshi” Hira sosai suka yi ta yi Momy na koda kanta a garin gusau ma jin take ba ko wace matar mai kudi ce sa'ar yinta ba balle kuma cikin gidan Alhaji Haruna Mai Yadi. HURRIYA POV. Tana shiga part dinsu sai kewar Amma ya kara daduwa a ranta, ta san da a jiya ne da kwanakin baya da Amma take gidan sai dai ta fito daga dakinta ta sauko kasa ta yi breakfast ba dai taje wani bangaren ta kwana ba har tana fargabar arba da Momy. Kujera ta nufa ta zauna ta rike hannayenta hawayen dake idonta suka zubo mata. “Huriyya...” Ta kalli kofar kitchen din da sauri tana zabura domin ta tsorata ba yi zaton akwai mai kallonta ba. Da sauri ta cire gilashin idonta ta share hawayenta da hannu biyu ta mike tsaye. “Ya Yasir yaushe ka shigo?” “Tun dazu abun karyawa muke hadawa da Hamad” Ta fara takawa ta nufi kofar kitchen din da yake tsaye. “Kuka kika kwana kika yi jiya ko? Idonki har ya kumbura, kuma kin san matsalar idonki why zaki jawa kanki wata matsalar” “Yaya idan na tuna Amma bata nan sai na ji babu dadi, kukan zo min yake” “Addu'a zaki yi, kuma ki daina damuwa Amma zata dawo da yardar Allah” “Haka Appa yace maka?” Ta tambaya tana kallonsa wasu hawayen na sauko mata zuciyarta kuma cike da daukin ya amsa mata da eh zai haka yace. “Aa haka dai nake sashe, kuma ni na san haka zai faru ko dan ku, baki ga yadda hankalinsa ya tashi ba jiya saboda fada miki da Khairi ta yi, karki so ganin fuskarta yau sai da na kumbura mata baki” Hamad dake can cikin kitchen yana juya plantain yayi murmushin jindadi jin cewar an kumburawa Khairi fuska. Hurriya kuma zuciyarta ta cika da tausayinsa. “Da baka doke ta ba Yaya ai gaskiya ta fada min” “Ba haka ya kamata ta yi ba, kuma be kamata daga ke har ita ace kuna shiga maganar manya ba, dan haka ke ma ki kiyeye kar na cire miki ido” Ta yi dariya tare da maida gilashinta bayan ta share hawayenta. Saboda ya dauke musu kewar Amma ya zo part din ya fara hada musu abun karyawa yana cikin hadin ne Hamad ya shigo sai ya kira shi suka cigaba da yi tare, bayan sun gama suka hadu a dinning har Hurriya suka soma karyawa tea kawai Hamad ya sha sai yankan bread daya ya ce ya koshi, Yasir ya kalleshi sai dai be ce masa komai ba domin ya fi kowa sanin ba a cilasta Hamad yin abun da be tashi yi ba a kwashe lafiya, zai iya cilasta masa kuma ya ci amman kuma za su yi fada su rabu da bacin rai. “Jiya ma haka yayi be ci abinci ba” Hurriya ta fada tana tauna bread din dake bakinta. “Ya saka tunanin abun da ya faru ne a ransa, kina ganinsa kamar be damu ba ko? Ya fiki damuwa daman mu maza haka muke muna boye abu a ran mu babu mai sanin muna da damuwa sai idan an bincika ko kuma an saka mana ido” Hurriya ta dan yi murmushi kadan. “Amman mazan ba kowa yake da zuciya kamar Hamad ba, ya cika fushi” “Akwai su, wasu sunada fushi sosai a mata ma ana samu balle kuma maza, baki dai taba haduwa da su ba ne, ai halitta ce za a iya samunta a gurin mace haka ma gurin namiji, shi ma Hamad zai daina idan ya kara girma yayi wayo” Bata sake cewa komai ba har ta gama karyawa sannan ta tashi da sauri ta nufi upstairs. “Bari na yi wanka na saka uniform” “To sai ki yi sauri domin kusa latti” Ya mike tsaye ya fice daga bangaren zuwa bangaren mahaifinsa domin gaishe, kamin ya isa bangaren mahaifinsa ya hango shi tsaye waya a hannunsa yana dannawa, hakan ya saka Yasir ya cira kafa ya karasa gurin mahaifinsa sai yaja ya tsaya yana sauraren wayar da Appa yake. “Kamar da karfe goma dai, amman ina son a kwashe komai kamin yara su dawo daga makaranta”’ Yasir ya dan kalleshi zuciyarsa na raya masa kayan Amma za a kwashe. Ashe kuwa ya canka daidai domin a karshen zancen sai Appa ya karasa da fadin “Zan turo address din da kuma number wayarta ko da ba ku gane gurin ba” Ya sauke wayar ya shiga message dinsa ya fara rubutu location din. Yasir ya mika gaisuwa cikin girmamawa kamar yadda ya saba. “Lafiya kalau an tashi lafiya” “Lafiya kalau Appa” Daga haka Appa be sake cewa komai ba shi ma kuma be ce ba, daman baya tunanin Appa yayi maganar Amma ko wani abun da ya shafe ta da shi idan dai ba umarni zai ba shi akan wani abun ba, shi kuma be isa ya daga kai ya kalli mahaifinsa yayi masa magana akan lamarin aurensa ko wani abun da ya shafi matansa ba. “Hurriya sun tashi kuwa” Appa ya tambaya, domin tun tashinsa zuciyarsa take son zuwa duba yaransa sai dai gudun kar ace ga nuna banbanci ko kuma su ya fi kaunarsu da sauran yara ya saka ya danne ya boye abun. “Sun tashi tare muka karya ma, amman Hamad be ci wani abun kirki ba?” “Ba shi da lafiya ne?” “Lafiyarsa kalau Hurriya tace jiya ma be ci komai ba” Appa ya sauke ajiyar zuciya a hankali ba tare da ya bari sautin saukar numfashin ya fito ba. Har lokacin kuma be kalli Yasir dake tsaye gefensa ba kamar mai jin kunyarsa. Suna tsaye gurin har yara suka fara zuwa karbar chocolate da juice din da ya saba raba musu idan za su tafi makaranta, Appa ya koma ciki sai Yasir ya bishi ya riko masa suka fito da kayan waje sannan ya zauna a one of kujerarun dake gurin, ya fara raba musu suna karba yaran Hajiya Kaltume ne a gaba, Khairi kam baki ya kumbura gashi ta turo shi gaba ita ala dole an mata ba daidai ba fushi take, sannan Namra ta zo ta karba, a da can Hurriya da zumudi da far'a take zuwa karba kuma a kullum Hamad sai ya rigata karba, domin shi baya bata lokaci a komai ba kamar ita ba sarkin latti, cin abinci ma sai kowa ya cinye ita bata cinye nata ba. “Appa ina kwana” “Lafiya kalau Hurriya an tashi lafiya?” “Alhamdulillah” Ta mika hannu biyu zata karba, Yasir ya rigata ya karbe yana dariya kamar yadda ya saba, kasancewar bata a cikin yanayin farinciki sai kawai ta yi murmushi ta hade hannayenta. Appa ya dauko wani ya mika mata. “Karbi, ina Hamad?” Ta saka hannu biyu ta karba taba ba shi amsa. “Yana bus ya ce shi ba zai karba ba yau” Appa ya ji babu dadi sai dai be nuna ba kuma be sake cewa komai ba, Hurriya har ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Appa. “Appa yaushe Amma zata dawo?” Kallonta kawai mahaifinta yake, kamar yace me yasa kika min wannan tambayar domin be gama saka kalar amsar da zai ba su ita da Hamad, musamman ma ita da take da shakuwa da shi sosai wata kila Hamad zai bar abun a zuciyarsa dai dai yayi ta fushi da shi. Yasir ne yayi hanzarin tarewa Appa numfashin da ya rasa ina sauke shi. “Hurriyya idan zaki yi magana mai tsada da Appa, daga ke sai shi ya kamata ku yi, ki daina yi a gaban mutane kin ji” Ta amsa masa da kai, sannan ta kalli Appa “Na gode Appa Allah ya saka da alheri” Ta juya ta fara tafiya zuciyarta babu dadi. Godiya ce ta yi masa irin wadda ta saba masa a duk lokacin da ya bata chocolate din ko kuma yayi mata kyauta kasancewar abun da Amma ta koya musu kenan, amman a yau sai ya ji godiyarta a wata sigar ta dabam, yake jin kamar abun da ya aikatawa mahaifiyarsu ne take masa godiya a kai, gashi dan murmushi da far'a da kuzarin da yake gani a fuskar yarsa yau ya kau, dan'uwanta kuma ko ganinsa be yi ba. “Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un” Shi ne abun da ya iya furtawa yana binta da kallo zuciyarsa na masa zafi, tunanin dama da hadu na kokarin hade masa su rikita masa kwakwalwa. Yasir ya kalleshi sai dai be ce komai ba. “Idan sun dawo makaranta kai ko daya daga cikin direbobin gidan nan wani ya kai su gida su duba Amma” “Toh Appa In Shaa Allah” Appa ya juya ya koma ciki, Yasir na binsa da kallo kansa a daure yana mamaki wane kalar laifi Amma ta yi masa da har ya yanke wannan tsatsauran hukunci haka. *** *** *** Ruma ta turo kofar dakin ta tsaya daga jikin kofar ta kalli Khairi dake zaune gaban madubi tana shafawa bakinta magani ta ce “Khairi wai Ina Hajiya tace miki zata tafi?” “Ba ni ta fadawa ba, Maama ta ce gidan Hajiya Fatee zata tafi” “Toh amman har yanzu zata dawo ba? Na kira wayarta be shiga” “Maybe can zata wuni, ai dole dai idan dare yayi kin san zata dawo” “Khairi karfe 6:30pm ake magana fa, kuma ta fita tun safe” “Aa Ruma kin cika matsala, Hajiya ai ba yarinyar ba ce idan lokacin dawowa yayi ai ita zata dawo, kika san abun da ya saka ta dade? Kin san dai Hajiya Fatee aminiyar Hajiyarmu ce, waya san me taje yi a gidan” Khairi ta amsa mata da kamar fada domin ta hana ta shafa maganin da take cikin salama sai damunta take da tambayoyi. Ruma ta tabe baki ta fito taja mata kofar tana sake gwada line Hajiya domin ita idan Hajiya bata a gidan duk jinsa take ya zama dabam wannan ya saka wani lokacin ma har bin Hajiya take idan zata fita, kusan duk kawayen Hajiya sun san yar autar Hajiya Ruma saboda yawan lake mata da take. Har ta isa dakinta gwada line take amman kiran yaki shiga baturiyar sai tabbatar mata take da ba a samun Hajiya. [10/18, 5:35 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝗣𝗮𝗴𝗲 8️⃣ Suna shigowa cikin gidan Gwaggo Hurriya ta shiga dakin da sauri tana neman Amma. Gwaggo ta yi dariya tana daurawa jikarta dankwali “Maraba da Hurriya yanzu ake tafe” “Eh Gwaggo ina wuni” “Lafiya kalau ina Hamad?” “Shiga nan shigowa, Gwaggo Ina Amma?” “Tana dayan dakin dake kusa da na su Rukayya” Da sauri Hurriya ta tashi ta fice daga dakin Kakarta zuwa dakin da Amma take, tana shiga dakin ta fada jikin Amma kamar bata san tana dauke da cikin kanensu ba, sai kuka ya biyo baya ta kankame Amma sosai kamar za a kwace nata ita. Cikin karfe hali da dauriya irin na uwar da bata son raunin yayanta ya kamata har ta yi kuka a gabansu ta shafa bayan Hurriya tana dariyar da sautinta yaki fitowa, hakan kuma ba karamin taimakawa idonta yayi ba gurin zubar da ruwan hawayen da a da su kwana a idonta. Kanwarta Rukayya ta bata fuska sosai kamar ta fasa kuka. “Amma da baki nan gidan babu dadi, kuma Appa ya kwashe kayanki daga gidan” “Na sani, ya aiko min da su nan ai, suna nan a zuba a gareji, wasu an saka a falon waje” Hurriya ta dago tana kuka ta kalli Amma. “Ba zaki dawo ba kenan? Khairi ta fada min Appa ya rabu dake?” “Na fada miki tun ranar ai, abincina ya kare a gidanku, ina Hamad” Amma na rufe baki Hamad ya karaso gurin kofar sai ya tsaya yana kallonsu kamar wani bako. “Hamad shigo mana ya ka tsaya a jikin kofa” Rukayya ta fada, sai ya nufo cikin dakin yana jin wani irin tausayin mahaifiyarsa da ya kasa nunawa a fuskarsa, sai dai sanin halinsa da Amma ta yi ya saka ta fahimci akwai damuwa a tare da danta domin fuskarta babu walwala kuma ba hade rai yayi ba alamar fushi, yana a wani yanayi ne da ita kadai take gane damuwarsa. “Hamad kuna nan kuna ta fadan ko?” “Ba mu yi fada ba, ba mu yi fada ba Amma, amman dai gidan babu dadi...” Dorawa ta yi da labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan ciki har da komawarsu bangaren Momy da suka yi. “Daman gidan ko da ina ciki ya kuke zaune balle bana nan, sai dai ku yi ta hakuri karku saka komai ranku” “Ni dai na ce Bappanku ya tafi gurinsa yayi magana da shi, yaran nan ya bar su zauna a gidan nan idan ba haka ba, wannan matan uban na su za su iya saka musu guba su mutu ma” Cewar Gwaggo a lokacin da take kokarin shigowa dakin. Sai Amma ta amsa mata tana hawaye. “Allah ya fi su Gwaggo, na san Allah baya bachi kuma baya son zalinci, zai kare su, amman abu ne mai wahala Alhaji ya yarda yaran nan su zauna a gidan nan” “Amma me yasa Appa ya sake ki?” Hamad ya tambaya kai tsaye yana tsare ta da ido. “Ban sani ba Hamad, Wallahi ban sani ba, da ace na san laifin da na yi masa wata kila da zan fi jin sanyi fiye da yadda nake ji a yanzu, shi kan shi ya ce ban masa laifin komai ba” “Saboda Hajiya ne? Ko Kuma Momy” Amma ta kama hannunsa ta rike “Ba saboda kowa ba ne, kar kaje ka yi ta fada da mutane wahala zaka sha a gidan nan, dan Allah ka zauna lafiya da kowa Hamad wannan fushin da saurin kai hannu ka daina, ku kenan Allah ya ba ni sai wannan idan na haifa, ban sani ba ko zan kara wani ko kuma iyaka kenan, dan Allah ku hada kanku ku zauna lafiya, ina gidan nan amman tunanina yana can tare da ku saboda na san yadda kuke yawan samu tsabani da juna, ba ku mai raba ku a yanzu idan kuka yi fada ma dadi za su ji” “Be ci abinci Amma tun da kika bar gidan nan, da safe ma tea kawai ya sha” Amma ta dauke idonta daga barin kallon Hurriya dake fada mata ta kalli Hamad. “Saboda me? So kake ka jawa kanka wani ciwo kuma?” Kamar an zunguro idonsa haka ya fara hawaye yana kallon mahaifiyarsa, duk yadda ta so ta daure sai ta kasa ita sai da kukan ya ci karfinta balle Hurriya da ke da raunin zuciya. Rukaiyah ta share hawayenta. “Kai Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, Wallahi idan raba ku aka yi an ci amanarki an ci amanar yaran nan, mu ma kuma anci amanarmu an daga mana hankali” Gwaggo ta girgiza kai cike da tausayawa. “Toh Allah ya kyauta, arzikinsu ma suna da wayo da ace kanane ai da sai sun fi shan wahala, kuma ubansu yana sonsu za su samu sauki ta wani bangaren” A gidan suka wuni har dare, abincin da Hamad ya kasa ci a gidan Ubansa sai gashi ya ci a gidan kakarsa kasancewar Amma ce ta dafa masa da kanta, kuma ta saka shi gaba ya zauna ta cinye abincin tass ya dora da lemu, tukuna hira ta biyo baya, sai da dare yayi misalin tara da rabi sannan Yasir ya zo daukarsu daman ya fada musu a lokacin da direba zai kawo su cewar shi zai dauko su. Nasiha sosai Amma ta yi musu sannan ta aika Hamad ya shigo da Yasir ya zauna saman kujerar karamin falon suka gaisa. “Yasir ga kanenka nan, na san kana kokari amman Dan Allah a kara, a rika ja musu kunne idan suka yi ba daidai ba, kuma a rika duba su dan Allah” “Amma dan Allah ki daina wannan maganar, ko minene Allah ya kawar da shi ya kawo maslaha ki dawo gidan kamar yadda aka saba” “Toh Ameen, duk da haka dai a kula da su musamman Hamad” “In Shaa Allah” “Allah ya taimaka ko a kawo maka abinci” “Aa idan na koma gida zan ci, yau Rukayya bata gidan” “Tana ciki karatu take yi kasan idan suka samu littafan nan na hausa basa son tashi, yanzu haka bata ma san ka shigo, bari a kirata ku gaisa” “No kyaleta Amma, a gaisheta dai, bamu mu tafi kar dare ya kara yi” Yana rufe baki wayarsa ta bude nata ta fara kuka, hannu ya saka aljihu ya ciro wayar ya duba ganin mai kira ya saka ya amsa da sauri. “Hello Appa” “Yasir Hurriya bata dawo ba?” “Gasu na zo dauko su” “Sai yanzu? Kasan bana son ana kaiwa dare a waje ko? Me yasa direba be je dauko su tun wuri ba?” “Affuwan Appa, laifina ne ni nace zan dauko su kuma yanzu haka ina gidan” “To ku dawo yanzu nan, karka sake yaran nan su ce zasu kwana a nan” “In Shaa Allah, yanzu zamu taso” “Sai kun iso.....ka gaishe da Mamansu” Ya fada daga karshe bayan yaja dogon numfashi, da mamaki Yasir ya amsa masa da toh sannan ya sauke wayar. “Appa ne, ya ce na gaishe ki” Wani irin faduwa gaban Amma yayi, mutumen da ya sake ta ya kwaso kayanta ya yace a kawo mata kuma shi zai ce a gaisheta. “Ina amsawa” Mikewa yayi tsaye yayi mata sallama Hamad da Hurriya suka bi bayansa, Amma kasa raka su ta yi har suka fice daga gidan. Daga gidan Gwaggo Yasir be tsaya ko'ina ba sai gidansu ya faka a bangaren Hajiya Kaltume, Hamad ya riga fitowa motar sannan Hurriya, Yasir kuma ya tsaya gyara parking din. “Me yasa baki fadawa Amma na fasa miki gilashi ba?” A jere suke suna tafiya Hamad ya tambayeta domin abun da ya tsaya masa a rai kenan tun a lokacin da ta boyewa Amma cewar sun yi fada. “Idan ta ji zata ji ba dadi ba, baka ji tana cewa mu zauna lafiya ba? Idan kana yin fada ran Amma zai bace” “Ni dai bana son Hajiya bana son Momy bana son kowa a gidan nan” Yana fada yana wani cin magani kamar wani babban saurayi, Hurriya ta tsaya kallonsa da mamakin furunci, shi kam tuni ya juya ya fasa shiga bangaren Hajiya Kaltume ma ya nufi na su bangaren duk kuwa da ya san Amma bata gidan. Hurriya ta cigaba da tafiya har ta isa bakin kofar falom ta muda kofar ta shiga da sallama farin gilashin dake kara mata kyau yana fuskarta. “Wa'alaikassalam” Fadeel ya amsa mata yana zaune daga gefen kujera yana gwada kiran Hajiya Fatee. “Ni yanzu hankalina ya tashi sosai, ace har karfe goma Hajiya bata dawo ba? Ga wayarta baya shiga, daman tun da Ruma ta dawo makaranta take ta damu na da ina Hajiya” Cewar Maama tana gwada kiran Hajiya Kaltume. “Amman fa ce mana ta yi gurin Hajiya Fatee zata je” Fadeel ya ce “Bata gidan, domin daga can na fito masu aikin suka ce min tare suka fita da Hajiya, shiyasa na zo nan ko tana nan domin wayarta har yanzu bata shiga” Yasir ne ya shigo falon yana motsa keys din dake hannunsa. “Hurriya ke da Hamad Appa yace na kira ku, Ina Hajiya?” Ya karashe zancen yana kallon Maama da hankalinta ya tashi sosai kamin ya karasa ya mikawa Fadeel hannu su gaisa. “Ita muke ta nema?” “Ban gane ita kuke nema ba?” Tambayar Fadeel dake fadar haka yake da mamaki. “Dazu na shiga na gaishe da Hajiya aka ce sun fita tare da Hajiyarka, yanzu kuma na dawo masu aikin suka ce min bata nan, na gwada kiran wayarta kuma ba a samu shiyasa na zo nan ko zan sameta sai kuma na tarar nan din ma kanenka neman Hajiyarka suke” “Wai tun fitar da ta yi da safe bata dawo ba? I thought ta dawo ba fa, yanzu ma Appa ne ya ce a kirata” Maama da tuni ido ya raina fata ta fara kuka ta ce. “Wallahi bata dawo ba har yanzu, ni hankalina ya tashi” “Subhanallahi, to ina ta ce zata je?” Maama da Salma suka amsa masa, duk abun da ake Hurriya da ido kawai take binsu, Fadeel kuma yana jefa mata kallo time to time, farar fatarsa sai daukar masa hankali take kasancewarsa baki, ba shi kadai ba har Yasir da duka yan matan Hajiya Kaltume babu fari ko daya, sai wanda ya dara wani baki, domin an yi gadon bakar fata ta uwa ta uba, kamar yadda shi ma yake baki sai dai nasa bakin mai kyau ne irin mai shaike da ya dace da fatarsa ya karawa hancinsa fa fararen hakoransa da idanuwa kyau. Hurriya ta mike tsaye ta nufi kofa domin amsa kiran mahaifinta Fadeel ya bita da ido yana kallonta kasa kasa har ta fice, ba wannan ne karon farko da ya fara ganinta ba, amman a yau ta tafi da shi, domin ta kure iyakar ganinsa ta cika idonsa. *** *** *** Wasa-wasa aka nemi Hajiya Kaltume aka rasa babu amo babu labari, duk inda ake saka ran za'a gane an bincika bata nan, haka ma Aminiyarta Hajiya Fatee ita ta bangaren danta Fadeel babu inda be bincika ba amman be same ta ba, gashi be san direban da ya daukesu ba balle ya neme su, wayoyinsu kuma idan an kira ba mai shiga, shi kansa Appa sai hankalinsa ya tashi balle kuma yayanta da bachi ma ya gagaresu, Hurriya ma da ba yarta ba sai da nata hankalin ya tashi domin bata son ta ji wani abu marar kyau ya same mutum. Tun ana maganar kwana daya, biyu har aka yi sati, sai da Hajiya Kaltume da Kawarta Hajiya Fatee suka yi kwana goma cif sannan aka kira wayar Appa ana neman ya fada miliyan dari, domin sun tambayi Hajiya kuma ta fada musu waye mijinta, ta bangaren Hajiya Fatee ma haka suka nema gurin ďanta. A lokacin Appa ya zo musu da labarin yana mamaki su ma mamakin suka yi, ba su mamakin jin cewar tana hannun kidnappers ba daman sun saka tsammanin haka domin sun bincika ko'ina ba a same ta ba, kuma su kai report gurin police an saka addu'a amman duk shiru, kudin da suka bukata ne abun mamaki. “Miliyan dari kuma? To a ina suka samu number ka Appa?” Yasir ya tambaya cike da mamaki da kuma tashin hankali a lokaci daya. “A gurinta suka samu, na yi magana da ita na ji murayarta?” “How taya suka kama su? Wannan abun sai idan da na gida aka hada kai” “Ban sani ba, amman dai mai maganar yace sun kama su a wani kauye dake kusa da gidan zalla nan kwatarkwashi” “Ikon Allah, amman dai tana lafiya ko Appa” Ruma ta tambaya tana kuka. “Ba mu sani ba dai, ba mu gama magana ba suka yanke wayar kuma na kira bata shiga” “Kamata yayi a sanar da police tun wuri” “Zan kira yanzu na sanar musu” Appa ya juya ya fice, cikin wani karin tashin hankali sa be gama warkewar daga na Amma ba an kara masa wani. HURRIYA POV. Hurriya na zaune falon Momy plate din shimkafa a gabanta tana cin abincinta na dare, Namra zaune saman kujera tana duba dogayen rigunan dake zube gefenta kan kujera. Momy ta shigo daga bangaren Appa. Namra ta mike tsaye da sauri tana nuna mata rigar da ta zaba. “Momy wannan nake so, Hurriya ta dauki bakar” Momy ta tsaya kallonta. “Idan ta dauka ke zaki biya? Ka ji min wani rainin hankali” “Momy toh ai na ga na shagonki ne” “Idan na shago ne mutuwa na yi balle ki ci gado har ki dauka riga mai tsada ki ce abawa Hurriyya?” Namra ta juya ta kalli Hurriya sannan ta juyo ta kalli Momy tana mana alama da zata iya ji. “Ta ji mana, tsoronta nake? Ke ce baki san ciwon kanki ba har kika hada kanki da ita, kina kallo a gidan nan duk kudin da mahaifinsu zai bada na siyen abu sai na ciya na siyo muku wanda ya fi na sauran yan'uwa, amman yanzu har kika maganar ki saka riga Hurriya ta saka irinta” Da kamar mamaki Namra ta ce. “Ubanmu daya da ita fa, kudin da Appa zai bata su zai ba ni duk daya ne” “Eh amman ai ina kara miki? Tufafin da kuke sakawa wake sska su a gidan nan? Karki sake min wani abu makamancin wannan, rai na a bace yake kin kara min wani” “Me ya faru Momy” “Kaltume ce wai kidnappers sun kamata suna neman milyan dari” Momy ta fada tana kiran sunanta domin ita kadaice a gidan bata sakawa Hajiya Kaltume ta ce Hajiya sai dai ta ce Kaltume kawai. Hurriya ta juyo da sauri jin abun da Momy take fada, Namra kuma ta zaro ido. “Innalillahi daman sai da na fada tana ina yanzu?” “Ke kin yarda? Ai talaka babu abub da ba zai iya ba, wannan Kaltume zata iya kidnapping din kanta da ta karbi wannan kudin gurin Alhaji, balle tana ganin yadda nake tafiyar da kasuwanci ai abun yana tsone mata ido” “Haba Momy taya? Kuma har wannan kwanakin bata fito ba?” “Ke makira ce wannna matar fa, ni na san yadda na zauna da ita, kin ji ta a waya sai kukan munafurci take wai wani idan ta kara sati a gurin mutuwa zata yi, tana cikin bala'i da masifa a Alhaji ya taimaka ya kawo kudin da wuri hmmm” Momy har wani kwaikwayon muryarta take tana nufar hanyar Kitchen Namra ta rufa mata baya dan kara jin labari, ita sam bata yarda an sace Hajiya Kaltume ba ta fi yardar Hajiya Kaltume ce ta sace kanta. Hurriya mamakin ya hana ta cigaba da cin abinci mamakin jin cewar an sace Hajiya Kaltume take, da dayan bangaren kuma tana mamakin yadda Momy take ganin kamar ita da Namra suna da banbanci bayan uba daya ya haife su, tana mamakin yadda Momy take duban Hajiya Kaltume ma dake da tarin rufe asiri a gidan tana ganinta talaka. Da sauri Hurriya ta cire hannunta a abinci ta fice daga falon zuwa bangaren su Khairi. [10/18, 5:35 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Hello Habibaties 😍🥰 Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy 𝗣𝗮𝗴𝗲 9️⃣ Hurriya na shiga falon Hajiya Kaltume ta fara rabon ido ganin yadda kowa yayi jigun, wasu daga yayanta kuma suna amsa waya suna kuka. Gurin da ta tafi wayo ta nufa wato gurin yayanta ta tsaya kusa da shi tana kallonsa har ya gama wayar sannan ta ce. “Yaya wai garkuwa aka yi da Hajiya?” Kamin ya bata amsa Khairi ta watsa mata harara. “Tsohuwar munafuka, hala dadi kika ji?” “Dadi dai? Me ye abun jindadi a ciki da har zata ji dadin? Wace irin magana ce wannan?” “Toh Yaya idan ba haka ba, me yasa take tambaya?” “Bata da hakkin sani ne? Ni kuna bani mamaki a gidan nan Wallahi, miye laifi a ciki idan ta tambaya? Karki bata min rai yanzu na fara dukanki” Yasir ya karashe maganar yana nunata da yatsa, sai ta dauke kai domin ta sani sarai zai iya, ba wani jutuwa suke da juna ba. Ya dubi Hurriya dake gefensa tsaye. “Eh sace ta aka yi, mu ma yanzu Appa ya zo mana da maganar sun ce za a ba su miliyan dari” A take hankalinta ya tashi, tana son ta sake cewa wani abu tana tsoron kar Khairi ko Salma su kwatseta, dan haka ta ja bakinta ta yi shiru tana cigaba da sauran yadda ake ta kiran yan'uwa ana fada musu. ****       ****         **** A haka sai da Hajiya ta kara sati daya a hannun mutanen nan ita da Hajiya Fatee domin police aka saka a lamarin su kuma suka hana a aika da kudin, suka ce za a gano inda take, sai da Appa ya ga abun na su ba mai yi ba, ga hankalin yaransa da yan'uwan Hajiya Kaltume ya tashi ya nemi sassauci suka rage kadan ga miliyan dari, a sake neman sauki, daker da addu'a da sudin goshi aka samu suka sauko a miliyan goma, bangare Hajiya Fatee ma haka suka karba, Appa ya hada kudinaka rasa wanda zai kai, sai da wani kanen Hajiya Kaltume yayi jihadi yace shi zai tafi kai musu kudin, ranar da zai tafi suka fadi inda zai tsaya a dajin su zo su tafi da shi, haka kuwa aka yi Fadeel ya kawo nasa kudin aka hada da na Appa suka shiga mota aka kaishi har inda suka bukata suka fito suna masa addu'a, su kawo wajen gari suka tsaya. Ba zan wani jima ba suka kira suka ce aje a dauke ta a wata gona dake nan dogon dutse a nan za su aje su. Abun ka da mai nema Yasir da Fadeel da Uncle din Fadeel din suka nufi gurin da moto suna gudu kamar ba za su je su same su a gurin ba. Kamin su isa kowannensu hankalinsa ya tashi kuma zuciyarsa ta cika da zullumi, domin suna tsoron kar su je su tararda gawarta domin sun saba haka wani lokacin sai su ce aje a dauka sai an tafi a tararda mutum a mace. A bakin titi suka faka motar suka fita suka shiga cikin gonar domin dubawa, Yasir da waya a kunne yana fadawa Appa sun isa gurin Appa kuwa sai gargadi yake masa. “Yasir ku kula da kyau, zai iya yiyuwa dabara suka muku saboda idan kun shiga gurin su sace ku” “Aka yi mana Addu'a Appa In Shaa Allah babu abun da zai faru, fatanmu dai a samu Hajiya da rai” Yana rufe baki ya ji muryar Fadeel yana fadin ya karaso nan gasu a nan, da sauri Yasir ya katse wayar ya nufi gurin, Hajiya Fatee ce da Hajiya Kaltume daure jikin itace, kansu babu ko dankwali sai wani zane atamfa kala daya da suka yafa kamar wasu yan kauye sun yi yaushi kai kace allayahun da yayi sati ne a daure, fuska ta yi burun-burun kana ganin kasan an dade ba a sadu da ruwa ba, baki ya bushe idanuwa sun kode kamar wadanda suka kusa kusantar rame. Hajiya na ganin Yasir ta fashe da kuka, Hajiya Fatee kuma ta fara zubar da hawaye. “Alhamdulillah Alhamdulillah” Shi ne abun da sukr ta fada bayan sun kwance su. “Ku yi sauri muje kar su biyo sawunmu, Sannu Hajiya” Fadeel ya fada yana kallon mahaifiyarsa cike da tausayawa. “Bana iya tafiya Fadeel bana iya komai” Tana maganar tana nishi hawaye na mata zuba, Hajiya Kaltume kam kuka take riri domin da yanzu da aka sako su da kuma lokacin da aka kama su duk yayi mata kamar mafarki, ita kadai ta an bakar azabar da suka sha. Duk yadda Yasir ya so su yi sauri hakan be samu ba saboda Hajiyoyin duk basa iya sauri tafiyar ma sai daker gashi jikin ba kadan ba balle yayansu su ce za su taimaka musu, a haka dai suka isa gurin motar, Hajiya Fatee ita ce mai tafiya kamar mai tatata, Hajiya Kaltume ce mai dan kuzari shi ma ba wani da yawa ba sai na karfin hali. Hankalin kowa be kwanta ba sai da suka isa gida, domin kin amincewa suka yi da maganar Appa da kuma na yaransu cewar a tafi da su asibiti a duba lafiyarsu, Hajiya fatee ce ta fara nuna karfiya sannan Hajiya Kaltume ta rufa mata baya. Daga gidansu Yasir Fadeel ya dauki mahaifiyarsa ya fice da ita zuwa family house dinsu bayan ta yi wanka, sai dai ta kasa saka komai a baki duk kuwa da irin lallabata da Fadeel yake. Be isa gida ba Yasir ya kira wayarsa yana fada masa wai sun kira sun ce shi ma wanda aka aika yana da mai da alama za a samu wani abu dan haka sun rike shi sai an bada miliyan 20. “Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, mutanen nan ba su da imani ko kadan, kai yaushe aka gama wannan kuma ace sun kama wani? Wai anya ana son mu cigaba da rayuwa a kasar nan kuwa? Wannan wane irin bala'i ne?” Haka yayi ta fada, Hajiya fatee tsabar tsoro ji take kamar ta rufe masa baki, domin ta ga tashin hankali da bata taba mafarki ba. “Ka rufawa kanka asiri da zagin mutanen nan, ba au da imani ko kadan, su hanyar da imani ya bi ma ba su santa ba” Fadeel ya juyo ya kalleta a daidai lokacin da ya faka motarsa a harabar gidan, yan'uwa da abokan arziki suka fito da gudu suka yo gurin motar domin taron Hajiya Fatee ciki har da Afrah da Hajiya Fatee take zagi wato matar Fadeel da kuma yaranta masu aure. “Wallahi Hajiya Kaltume ce taja min, ita na raka a kauyen” “Toh me kuka je yi kauyen?” Bata samu amsa masa ba sakamakon bude gambun motar da aka yi ana murna da zuwanta, daman kuma tana neman dalili da zai hanata yi masa wani bayani dan bata shirya tonawa kawarta asiri ba. Ta bangaren Hajiya Kaltume after ta samu ganawa da mutane ta huta zuwa dare danta Yasir ya dauketa zuwa asibiti kamar yadda mijinta ya umarta. Sun dubata suka mata duk wani gwaje gwajen da ya dace sannan suka bata maganin zafi domin kafarta na ciwo sosai saboda tafiya, sai kuma na ciwon jiki da ciwon kai da na ido saboda kukan da suka sha har kammaninta sun sauya. BAYAN KWANA BIYU.... Hajiya Kaltume ce zaune kan kujera Maama na matsa mata kafafuwan da har yanzu ba su daina mata zafi ba, domin bata taba gwada yin tafiyar da ta yi daga inda yan fashin dajin suka kamata ba zuwa sansaninsu, ko a lokacin da take da kurciya balle yanzu da girma ya fara kamata. Momy ce ta yi sallama ta shigo falon tana sanye da wada tsadadiyar shadda yar mali sai sheki take kamar an watsa mata ruwa, kana kallon shaddar ka san ranar ta fara sakata, wuyanta na cike da sarkar zinarin da ba ko wace matar mai kudi ce zata iya sakawa ba, gamshin da take ma na dabam ne domin Momy bata yarda ta siye turaren irin wanda Hajiya Kaltume ko Iyami za su iya siye ba ko da kuwa kudin da take da shi zai kare. Idan kana neman dake ji da kansu asalin ji da kai da nuna isa idan ka yi arba da Momy ka kai karshen aya. Maama ce ta amsa mata sallamar tana hada baki da Khairi dake fitowa daga kitchen rike da bowl din kankana. Hajiya Kaltume tun da ta kalli kofar falon ta ga Momy ce bata sake sha'awar kallon gurin ba. Tsaye Momy ta yi kusa da kujerar da Hajiya Kaltume take zaune abun ka da matan da tsibbo ya waya kuma suka wayance shi sai Hajiya Kaltume ta zame kafafuwanta daga hannun Maama ta matsa daga inda Momy take tsaye, jiki be bata banza ta kawo Momy bangaren ba, tunani take wani abun ta zo yi mata. “Kaltume ashe an dawo” Momy ta fada cikin izza tana Kiranta da Kaltume kai tsaye kamar yadda ta saba, tun zuwanta gidan taba taba kiranta da Hajiya ba balle kuma Yaya kamar yadda wasu matan suke yi idan za su kira uwargida ko da kuwa da sunan yaranta ne. “Eh Allah ya nufa Nafisa” Hajiya Kaltume ta amsa kamar an mata dole tana wani kashe ido. Momy ta tabe baki kamar wadda ta manta a falon Hajiya Kaltume take idan ma Hajiya bata ganinta kuma yaranta suna kallonta, amman tsabar raina uwarsu da ta yi da kuma rashin tsoron anyi an ce ya saka ta yin haka. “Toh Allah kyauta gaba” Maama da Khairi ne suka sam da Ameen, sukan tsoronta ya dade da cika musu ciki ba kamar mahaifiyarsu da take jin zata iya karawa da ita ba. Momy ta juya ta fara takawa kamar wanda bata son tafiya, haka yanayin ya ke tun tashi, sai dai lamarin ya samu promotion ne a lokacin da ta auri Alhaji Haruna Mai Yadi, saboda ta nunawa Hajiya Kaltume da Iyami ita yar sarauta ce kuma yar masu kudi ba Kamarsu. “Mtsssss” Hajiya Kaltume taja guntun tsaki tana bin bayanta da harara. “Wallahi matar nan ta raina min hankali, wato na fahimci so ta yi na mutu gaba daya idan ba haka ba ace ma samu na kubuto hannun azzaluman mutanen nan da ba su san Allah ba, amman bata shigo ta min barka da dawowa sai yau da aka kwana biyu?” Khairi ta mika mata bowl din watermelon din tare da fadar “Hmmm Hajiya ai da baki dawi ba sai matar nan ta zuba ruwa kasa ta sha” “Ai ni bayan Iyami bana da makiyiya irin Nafisa, kuma ita ma sai ta bar gidan nan da yardar Allah, komai sai ya dawo karkashin ikona sai na bata mamaki, ai Wallahi da ban dawo ba da sai Iyami ta ci ubanta dan sai ta gane kuskurenta, duk saboda ita na sha wannan bakar wahalar, duk dalilinta ne da bata aurar min miji ba da yanzu ban san wadannan yanta'adda da ba su da imani ba, yanzu na fito ga kanen can a daure” “Hajiya ba su da Imani ko?” Maama ta tambaya. “Ina fa, ai babu imani a tare da su, abinci sa mun ji yunwa suke ba mu, idan dare yayi muna nan cikin hudu sai idan sun haska mu, sun dauremu sai kace awaki, sannan a ciyayi muke bacci, baba kalar kwaron da be cize ni ba, shi kam sauro ya samu abun nema style style yake mana na cizo, kuma duk ranar da aka yi waya ba a samu daidaituwa ba sai sun mana duka, kuma a kafa muka yi tafiyar nan har ciki daji, yara kanana na haife su amman haka suke juya ni kamar waina, Allah dai ya isar min akan Iyami kawai zan ce, kuma kiyayya yanzu na fara, dacan ina boyewa  Wallahi yanzu a fili zan nuna bana sonta bana son yaranta, duk sai na ga bayansu” “Hmmm Hajiya karki ga yadda Hurriya ta shigo falon nan tana ta zumudi ta ji dadi an kama ki har tambaya take” Khairi ta shimfida mata fahimtarta akan Hurriya. Hajiya Kaltume ta cize baki. “Shegya bakar dagga, daman idan bata yi murna ba ai bata cika yar kishiya ba, aiko sai ta gane shayi ruwa a gidan nan, ke shiga dakin yayanki ki kwaso min gilasan yarinyar nan gaba daya ki boye min su” Kamar mai jiran umarni haka Khairi ta tashi da zafinta da murnarta ta nufi hanyar stairs. Maama ta tashi daga kasan da take zaune ta zauna kan kujera. “Amman Hajiya Yaya Yasir zai iya gane dauka kika yi fa?” “Ta ina zai gane fada masa zaki yi? Ko ma ya gane ai ba bayarwa zan yi ba, idan ya matsa min har shi ba zan ragawa ba, dan ni mai kaunar mai kaunar Iyami da yayanta ma bana kaunarsa, arzikinta daya ma dawo Wallahi da na mutu can da sai ta gane kurenta, kuma ita da Alhaji har abada” Sosai ta hade fuska tana maganar irin hadewar da ya kara mata muni da bakin fata. “Hajiya ai ba ita kadai ba, Hajiyar su Appa ma fa bata zo ba sai a waya ta kira, amman Wallahi da Amma ce da tun ranar zata iso gidan” “Hmmm ita ai bata da wata power yanzu, ko ba komai a bakin rame take, kuma babu yadda zata yi da ni, bugu da kari kuma na kore matar da take so, sai na ga uban da zai dawo da ita a gidan nan” Sun dade suna hirar Hajiya Binta da Maama kamin Khairi ta fito daga dakin Yasir da gilasan har uku ta nunawa Hajiya. “Kin gansu Hajiya cikin closet dinsa ya saka su” “Je ki yi musu mugun boyo idan ma bala'i yayi bala'i ki ce masa ni na dauka da kaina” “Ba sai ance haka ba, kawai kowa yace be shiga dakin ba kuma babu wanda ya dauka” “Shi ke nan, ya ma fi sauki” Khairi ta fada a ganinta shawarar da yayarta Maama ta bada ta fi, sama da ta Hajiya Kaltume. Kamin Khairi ta isa stairs aka dauke wuta, a take hankali Hajiya Kaltume ya tashi domin har yanzu bata gama wartsakewa daga tashin hankali da azabar da ta sha a dajin ba. “Innalillahi Maama kunna haske, na shiga uku... ” Kamin Maama ta kunna fitilar wayarta Mekano dake aikin bada hasken wuta a gidan ya fara aikinsa, haske ya cika ko'ina. Hajiya Kaltume ta dafa zuciyarta tana sauke gajiya. “Kai Allah raba musulmi da wahala, har yanzu ji nake kamar ina kusa da dajin nan, shiyasa ko waya bana son karba, mun ga tashin hankali mun ga shiga uku duk saboda bakar Iyami” Hajiya ta karasa tana fashewa da kuka, domin Iyami ta hana ta zaman lafiya ta hana ta rawar gaban hantsi. *** *** *** Ta dayan bangaren Iyami tana ta fama da nata, tunanin da damuwa sun hana ta walawa ko da kuwa tsakar gidan ne, ga wani sabon lalurar laulayi da ya same ta bayan dawowarta gidan iyayenta, iyakar kokarinta tana yi na nunawa Gwaggo da Bappa ta karbi kaddara, sai dai a kasan zuciyarta tana fama da tunani domin kuwa tana son mijinta, domin tana zaune lafiya a gidan tana rumgume da yayanta ciwonsu lafiyarsu duk ta sani, ba kamar yanzu da tunanin halin da suke ciki yake hana ta sukuni ba. Gashi a duk lokacin da Hamad ya zo gidan sai ya fada mata abun da aka yi musu, Hurriya ce bata fada saboda bata son tashin hankali Amma kuma tana da zurfin ciki. Gwaggo ma tana iyakar kokarinta na kwantar mata da hankali ganin cikin dake jikinta gudun kar ta jawa kanta wata matsala. Addu'a kuma su dukansu suka dukufa da yinta ta neman Allah ya daidaita tsakaninta da Appa, sai dai ta bar kyau tun ranar haihuwa domin bata damu da yin azkar din neman tsari ba, tana ta tawaya a wannan babin, duk kuwa da ta san tana cikin kishiyoyi irinsu Hajiya Kaltume da Momy. [10/18, 5:35 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Hello Habibaties 😍🥰 Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy 𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣0️⃣ Washe garin ranar... Hurriya na cire uniform dinta na makarantar boko ta dauki bakar abaya ta saka, ta bude gurin da take zuba hullunata tun bayan da ta kwaso kayanta daga bangaren Amma ta dawo da su bangaren Momy a dakin da aka bata, ta dauko farar hulla ta saka a kanta. Sannan ta fara gyara dakinta ta kintsa komai, cikin natsuwa ta fito daga dakin ta shiga dakin Hamad da ya watsar nasa uniform din akan gado ta dauka ta aje masa ta gyara masa dakin, daman shi be kula da gyara daki ba ko a lokacin da Amma na gidan balle kuma yanzu da tufafinsa ma sai da Hurriya ta kwaso ta dawo masa da su dakinsa dake bangaren Momy. After ta gyara nasa dakin ta sauka kasa domin dauko abun shara da mopper haka take kullum idan ta dawo take gyara nata dakin da na Hamad domin Momy ta hana masu aikinta share dakin Hamad da Hurriya haka ma ta hana ko cokali suka aje masu aiki su dauka, kamar ya yaran gidan ba haka Momy take treating dinsu, musamman ma Hurriya da bata iya budewa kowa cikinta, Hamad kuma idan ya ci abinci a nan yake bari sai dai Hurriya ta dauke masa, ba kowane rules and regulations na Momy ya sani ba, ko na ya sani ba amfanin da za su masa domin ba bi zai yi ba. Gurin da ake aje kayan taje ta dauko ta hauro sama a hankali, domin Momy ta jaddada mata bata son jin karar tafiyar kowa a saman, hakan ya saka take kokarin ganin ta kiyaye dokokinta, ta san ba dan komai take nata haka ba sai dan ta takura mata idan kuma ta fadawa Appa wata kila zata iya jawa kanta matsala a gurin Momy. Dakin dan'uwanta ta fara gyarawa sannan ta shiga nata dakin ta fara sharewa. Cikin ɗoki Hamad ya shigo dakin nata. “Hurriya za mu je dauko Hajiya yanzu” Ta juyo ta kalleshi da sauri. “Wace Hajiya” “Hajiyar Appa tace zata zo, Appa ya kira ni yace na zo muje daukota yanzu nan” Hurriya ta daka tsalle tana murna, daga ita har Hamad suna matukar son zuwa gurin Hajiya Binta kuma suna daukin ganinta a gidan ubansu, al'adace ta Alhaji Haruna, duk ranar da mahaifiyarsa zata zo gidansa da kansa yake zuwa ya daukota idan kuma ta tashi tafiya shi zai maidata gidanta, komai yake zai aje ya dauko ko ya kaita gida matukar gidansa zata zo, wannan ya saka tun ana sauran kwana biyu ta zo gidan take sanar masa, shi kuma ya sanar ma matansa a shirya mata tarba mai kyau. Murmushin da murnar da Hurriya ta gani a fuskar dan'uwanta Hamad ya ninka farinciki zuwan Hajiya Binta da take a gidan, domin tun tafiyar Amma bata san wata rana da Hamad ya sake fuska yana far'a kamar yau ba. “Zan mata wanka mai kyau kin san ta iya tsokana ta tana cewa ban iya wanka mai kyau ba, tufafi zan canja yanzu nan” Da karfi yake maganar, kamar yadda ya saba yi a bangaren Amma idan yana cikin farinciki. Hurriya ta yi saurin yi masa alama. “Yi a hankali kar Momy ta ji ta fara maka masifa?” “Saboda me?” “Bata son hayaniya kuma tace idan zamu hauro ko sauka stairs mu yi a hankali kar mu yi making sound bata son ana hawa mata da karfi” “Yaushe tace haka?” “An dade, kai ai ba zama kake bangaren ba sai idan zaka kwanta shiyasa baka sani ba” “Sai na fadawa Hajiya duk abun da ake mana a gidan nan” Hurriya ta saki mopper dake hannunta ta nufo kofar dakin gun da Hamad yake tsaye. “Hamad kar ka yi haka, kasan zata yi ma Appa fada shi kuma zai yi ma Momy, idan aka yi Momy kuma kan mu zai dawo” “Sai na sake fada mata, Appa ma dan ina fushi ne da shi shiyasa ba zan fada masa ba, ni ba zan ma iya zama bangaren nan ba i hate them” Ya saki kofar ya nufi tasa kofar ya bude, Hurriya ta dora hannu daya akai tana jin ina ma ace bata fada ba, tsoro take kar ace daga dawowarta bangaren ta fara hada munafurci, kuma ta san at the end abun gurinta zai dawo. Hamad na canja tufafi ya dauki turare ya saka ya canja shoes ya fito daga dakin ya sauko kasa ya fice daga falon daga Miwan har Namra dake falon be cewa kowa komai ba. Miwan ya bishi da harara “Yaro nan fa ya raina mutane, idan zai shigo haka zai shigo babu sallama idan ya tashi be iya gaishe da kowa” “Yaya idan ka ce zaka biye ta Hamad za ku yi ta samun matsala ne fa, Amma ma da tana nan fama take da shi balle kuma mu” “Ba ruwana da rashin jinsa ko rashin kunya ni ubansa zanci Wallahi” Ya amsawa Namra yana ayyana yadda zai yi ma Hamad mugun duka idan ya shiga gonarsa. Namra dai bata sake cewa komai ba ta shiga ta jera warmers din da masu aikin Momy ke ajewa a kasan dinning, Hurriya ce ta fito rike da boket din da ta yi mopping da mopper ta nufi hanyar tsakar gidan dake ta cikin falon Momy ta bude kofar baya ta fita ta wanke komai sannan ta dawo cikin falon, a daidai lokacin da aka turo kofar falon aka shigo wata doguwar mace ce tana sanye da bakar abaya da aka kawata da blue stone ta daura dankwalin atamfa saman kanta sannan ta dora mayafin abayar a sama ya sauko mata, hannunta na rike da Gucci bag, tsalle Namra ta saka ta kwala ihu ta nufi matar da alama ta nuna murmushi sai ma sai yayi yaki yake samun mazauni a fuskarta, kallo daya zaka masa ka fahimci ta ninka Momy kasaita da ji da kai. “Ammy sannu da zuwa” Cewar Namra cikin zumudi tana rumgumeta, Miwan ya mike tsaye yana gyara rigarsa tare da yi mata barka da zuwa. “Namra...ana gida” Ta fada kamar mai jin wahalar magana. “Eh Ammy sannu da zuwa, tun safe muke duban hanyarki” “Toh gani na iso, Ina Hajiya Nafisa?” Ta tambaya tana kallon Hurriya da ta yi tsaye da ta fito daga dakin da da ake aje mopper. “Momy Momy Momy...” Namra ta daga murya tana kiran Momy, Hurriya kuma ta dan risina kamar yadda ta saba ta gaisheta. “Ina wuni” “Lafiya...” Ta amsa tana binta da kallo tare da dan yamutsa fuska. “Ita ce .....” “Hurriya” Namra ta karasa mata, sai ta watsawa Hurriya wani kallo daga sama har kasa ta yamutsa fuska kamar wadda ta yi arba da wani abun kyama. Hurriya ta kalli jikinta sannan ta kalli matar da tuni ta kama hanyar stairs gurin Momy dake saukowa da saurinta tana mata lale marhabun. Da alama Namra bata ji dadin abun da matar da take bakuwa a idon Hurriya ta yi ba, sai ta kama hannun Hurriya ta nufi kitchen da ita suna shiga ta rufe kofar kitchen din ta kalli Hurriya da har lokacin mamakin yadda matar ta yi mata kallon wulakanci take, bayan kuma bata da wani abun wulakantawa a jikinta ko suturarta, gashi alama ya nuna ta santa ita kuma bata wayanci wacece matar da Izza ta cikawa ciki har ta bayyana a kamaninta ba. “Hurriya dan Allah kar abun da ake miki a gidan nan ya dame ki, kin san dai matsayinki a gidan nan, dan haka karki kula komai kin ji?” Hurriya ta amsawa yar'uwar tata da kai. “Wacece wannan Matar Yaya Namra?” “Big Brother din su Momy to natarsa ce wannan, ba a nan suke ba, a Kaduna suke zaune ta zo duba mahaifiyar mijinta ne da bata jindadi maybe shiyasa ta biyo ta nan saboda suna good time da Momy sosai” Nan ma da kai ta amsa mata sannan ta juya zata fice daga kitchen din. “Kin ci abinci?” “Aa Hamad ya ce Hajiyar Appa zata zo, ina jiram ta zo ne sai mu ci abinci tare” “Yayi yar gidan Hajiyar Appa” Hurriya ta yi murmushi ta bude kitchen din ta fito tana rike da hannayenta ta nufi upstairs, Miwan ya wurga mata harara yana jin haushin yadda Namra take mata sanyi ko a lokacin da Amma take nan balle kuma yanzu, hakan ya saka suke mata kallon munafukar cikinsu, domin ita halinta dabam da na su, kishi da ya kamata ace tana taya Momy bata yi ta bar musu sai dai su yi. Hurriya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta nufi gadonta ta kwanta ta takure gurin daya kamar wanda aka tsare sai hawaye ya fara saukowa a idonta, tunanin barin gidan da Amma ta yi ya dawo mata sabo. **** **** **** Cikin annashuwa da ďaukin gani Momy take kallonta. “Ai har ina cewa maybe ba zaki biyo ba, na ga Yamma ta yi” Matar dake kawar da kai daga barin kallon aikin Momy dake jera mata kayan da aka shirya mata ta kalli Momy. “Ai kin san halin Captain shi ya fi son tafiyar dare” “Tare da shi kuka zo kenan? Amman be shigo ba?” “Yana waje, waya yake” “Oh Soyyayar da bata karewa, ai dai an kusa auren nan a huta, ke ma ki samu hutawa Ammy” “Toh sai a taya mu da Addu'a Allah ya daidaita tsakaninsu” Tana maganar tare da kai hannu ta dauko plate din grapes din da aka rolling ta cire ledar ta fara ci. “Tsabani suka samu ne?” Cikin mamaki Momy ta bukaci sani. Kamin ta bata amsa sai da ta juya ta kalli kofar dakin Momy da daya daga cikin masu aikinta taja. “Wai har cikin daki kike barin masu aikinki suna shigowa?” “Toh ya zan yi Hajiya Turai? Kin san dai ba zan yi aiki da kaina ba, dole su zan saka” “Ai ni iyakacina da mai aiki falo sai kitchen da haraba, har yaushe mai aiki ta yi matsayin shigo min bedroom? Kina gani ai idan kika je gidana, su Larai ke kula min da daki” “Toh ni wa zan saka? Ke ai kina rikon su Larai da Aliya” “Wannan yar mijin na ki da kika fada min ta dawo nan hutu ta zo yi? Idan ma baki sonta sai ki duba a cikin dangi ki dauko wadda zata iya kula miki da daki, amman ba dai masu aiki ba” “Zan duba a dangi, yar miji ina sakata za ace bana kaunarta” Hajiya Turai ta yi murmushi mai sauti tana mamakin sakarcin Momy domin a gurinta abun da Momy take fada ko take gi sakarci ne. “Ke ma dai ban da abun ki Hajiya Nafisa waya taba son ɗa ko ƴar kishiya? Ai ba wani boye boye, ba zan hana ka aure ba amman fa ba zan so matarka da ƴaƴanta ba” “Ai Wallahi Hajiya Turai ba karamin sa'a kike yi ba, da yayana baya sha'awar aure-aure, ba kamar nawa mijin ba, domin ni ko a yanzu da ya saki Iyami tunani nake ko dai ta dawo ko kuma ya auro wata” “Shi ne banbancin tashi a gidan arziki da kuma cintar arzikin, da ace mijinki ma kamar tashin Engr ne, da ba zai yi wannan aure-aurenba, ai talauci mugun abu ne, da zarar sun ga sun yi kudi sai su ga babu abun da ya dace da su kamar aure, amman Engr kam ai rayuwarta turawace da shi, babu ruwansa da wannan hange-hange” “Wallahi ya huta, da alama ma ďana halinsa zai gado” Hajiya Turai ta tabe tana girgiza kai cike da kasaita. “Hmmm Captain? Ai idan ba Allah ya sauya masa hali ba, da wahala ma ya iya zaman da mata, yanzu ma addu'a muke kar ya ce ya fasa auren, shiyasa na ce ban yarda ya zauna ko'ina ba sai a kusa da ni” Momy ta kasa dariya. “Haba dai Hajiya Turai” “Hajiya Nafisa kin manta halin ďan naki? Wannan mugun fushi da bakar zuciyar ta Captain tsoro take ba ni, komai aka yi masa a duniya ba a masa daidai, ko kallonsa kika yi zai iya cewa kallon ya wuce kima ya fara masifa ko ma ya ce hararasa kika yi, yadda kika san shaidan aka nade aka saka masa a zuciya haka, abu kadan sai masifa sai fushi baya iya controlling kansa, ga zafin hannu a family babu wanda be san halinsa ba, ita kanta yarinyar da zai aura yanzu, ba dan tana hakuri da shi ba da yanzu rabu da ita, da inda abun ya zo da sauki ita mai sanyi hali ce kuma tana gudun zuciyarsa” “Toh ai sai a kiyaye, haka Allah yake son ganin kayansa, Captain murdaden mutum ne iya masa sai Allah” “Ina ta addu'a dai Allah ya sauke masa wannan mugun fushi da bakar zuciyar, idan ba haka ba zaman auren ba zai jima ba, kuma ya fada min idan yayi wannan auren ba zai sake yi ba har abada, wai ko matarsa mutuwa ta yi ko suka rabu a haka zai zauna har karshen rayuwarsa, ni kuwa ba fatan haka nake ba, ni da nake son na yi ta ganin jikoki a makwafin ƴaƴan da Allah be ba ni ba” “Gaskiya kam, muma muna son gani ai balle kuma ke da shi kadai kika haifa...” Hajiya Turai na taba kayan marmarin suna hira da Momy har time ya fara ja, hakan kuma be saka sun yanke hirar ba har sai da Namra ta shigo turo kofar dakin ta shigo. “Momy Hajiya ta iso” Momy ta yatsina fuska domin ta san wace Hajiyar ake magana, wato Hajiyar Binta surukarta uwar da ta haifi mijinta. “Toh shi ne kuma sai an fada min? Kin san ai ba nan take fara zuwa ba sai ta gama da ko'ina take lekowa nan, to miye damuwata da ita, je ki fadawa masu aiki su kai mata abinci” "Okay” Ta juya ta fita. Momy ta yi tsargi da fuska. “Idan ban je na gaisheta ba, sai ki ga ya shigo yana ta bala'i, alhalin ba so take ba, idan ta zo bata sauka bangaren kowa sai na Iyami, kuma sai ta fara shiga bangaren Kaltume sannan take leko nan” “ikon Allah haka take ita kuma! Allah kyauta rayuwarku sai ku Hajiya Nafisa” Cewar Hajiya Turai da kamar gatse tana jin ita duk ba zata iya daukar wannan ba, domin kowa yana da yancinsa. Namra na fitowa bedroom din Momy ta nufi dakin Hurriya ta tura kofar dakin, Hurriya na ji an taba kofar ta yi saurin juya fuskarsa ta boye kukanta. “Hurriya Hajiyarki ta iso, Appa ya aiko Ya Musib ya fadawa Momy” Hurriya ta share hawayenta da sauri ta juyo, sai gata ta sauko daga saman gadon bata ko kula Namra ba ta ratsa gefenta ta fice da gudu, duk wata dokar sauka ko hawa stairs na Momy manta su Hurriya ta yi a lokacin saboda zumudin zuwan Kakarta Hajiya Binta a gidan, kamar yau ne zata fara ganinta a gidan haka Hurriya ta ji. Da sauri ta bude kofar fita falon Momy bata kula komai ba ta saka kai zata fice, da mugun karfi ta ji kanta ya daki wani abu mai karfi har sai da ta yi baya kamar zata fadi. Dagowar da zata yi ta duba me ta buga domin be yi mata kama da karfe ko icce ba, ta ji an wanke mata fuska da lafiyayen marin da ya haddasa mata ganin wadansu kananan taurari, gilashin da yake mafaka ne a idonta ya fadi kasa, sai hudu da buji suka mamaye ilahirin idanuwanta. Sai ta tsaya cak irin tsayin da ta saba yi a duk lokacin da wani bakon al'amari ya ziyarceta. Gafen fuskarta ya hau zugi yayi ja, idanuwanta suka masa tantance mutunen da ke tsaye a gabanta, fafadane ta ga hakan a cikin hudun idanuwanta, dogo ne irin tsayin da ta tsaya iyakar kirjinsa. A hankali ta sulale ta kai kasa ta saka hannayenta tana lalaben gilashinta hawaye na kwankwaso mata kofa. Lalabe ta yi ta yi amman ta kasa jin gilashin, kamar yadda ta duka haka ta mike tsaye a hankali ta juya ta lalabi kofar falon ta fara tafiya. “Hurriya... Me ya same ki” Namra ta tambaya tana nufota da sauri ta kama hannayenta ta rike domin hawaye take kamar an bude kofar fanfo. “Ya... Ya... Namra... Gilashi... Na...” Namra bata tsaya komai ba ta rika hannunta ta juya da ita suka fita tana janye da hannunta, har lokacin Mutumen da ya mareta yana a gurin tsaye ko yatsansa be motsa ba. Namra ta kalleshi kamin ta sako hannun Hurriya ta fara duba gilashin, can gefe ta hango shi ta nufi gurin da sauri ta dauko mata. “Har gefen ido daya ya fashe daga sama, me ya faru Hurriya” Ta saka mata gilashin da kanta, lokaci daya ganinta ya dawo fashewar da gilashin yayi ba irin wadda zai hanata gani ba ne, daga sama ne ya fashe shi ma kuma kadan. Hurriya ta daga ido ta kalli mutumen da be mata uzuri ba ya wanke fuskarta mai tsada da mari. Hawaye be daina mata zuba ba, hakan kuma be hana idanuwanta ganin mutumen da kyau, dubansa ta yi ta dube shi, ta sake dubansa sannan ta sauke idonta kasa ta ratsa gefensa ta fara sauka kasa. Slowly ya juya ya kalleta kamar mai son gasgata wani abu ko karyatawa. “Bata gani sai da gilashi, me ya faru Yaya?” Ya juyo ya kalli Namra a fusace. “Aza min bindiga sai na fada miki” Jinin jikinta ta sha ta kauce ta ba shi hanya ya shiga ciki, ita kuma ta ja kofar sannan ta bi bayan Hurriya domin gaishe da Hajiya Binta, kamar yadda Appa ya sabarwa kowa a gidan ko baka cikin gidan idan mahaifiyarsa ta zo matukar kana cikin garin sai ka zo ka gaisheta... [10/18, 5:16 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy 𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣3️⃣ Da kallo ya bi Hurriya da Hamad har suka fice sannan ya kalli Hajiya Kaltume ya dauke kai ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa abun da ya fara yi shi ne duba gurin da ya aje gilasan Hurriya, amman be ga ko daya ba, a nan ya fara tunanin ko ya canja musu gurin ajiya ya manta, haka ya bi komai na dakin ya duba ba gilasan babu alamarsu, fitowar yayi mamaki duk ya cika fuskarsa ya sauka kasa sai ya samu mahaifiyarsa a gurin da ya barta zaune sai dai wannan karon waya take amsawa, gefenta ya zauna a hannu kujera har sai da ta gama wayar sannan ya tambaye ko ta dauka. “Me zan yi da gilasai kuma? Komai dai ni, ubanka ya dora min laifi matan ubanka su adabe ni kai kuma yanzu ka zarge ni da satar gilasan Hurriya saboda ga Kaltume makiyiyarta ko?” Maganar Hajiya bata masa dadi ba kuma ya san duk wani kalami da zai dora bayan nata a yanzu ba zai fahimtar da ita. Dan haka ya tashi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi dakin yan'uwa daya bayan daya ya bi yana tambayarsu kowacce tace masa bata dauka ba, Khairi har da hadawa da rantsuwa saboda ta fi kowa rashin tsoron Allah. ‘Toh ko Hurriya ta zo ta dauka ko Hamad ban sani ba?’ Ya tambayi kansa, sai dai ya san ba su taba masa haka ba, idan tana bukatar abu zata yi masa magana kuma idan ma ta dauka zata fada masa. Fitowa yayi daga bangaresu ya nufi bangaren Momy, kamar ance masa juya ka gani, yana juya ya kalli bangaren Appa sai ya hango Hurriya tsaye tare da Appanta ta rike hannunsa tana ta bata rai da alama makiya take masa kan wani abu. Fasa nufar bangaren Momy yayi sai ya nufi bangaren mahaifinsa domin tambayarta ko ta dauko gilashin be sani ba. “Appa dan Allah daga wannan ba zaka sake yi ba” Ta fada cike da shagwaba tana kara rike hannunsa. “Haramun ne, ba kyau Hurriya ni bana sha'awar irin abubuwan nan” Appa ya fada yana kallon Yasir da ya iso gurin fuska a sake. “Me take so Appa?” “Birthday kuma ka sa be da kyau ba al'adar mu ba ce hausawa wannan dabi'un turawa ne” “Oh Appa yanzu kai ya waye fa, ba wani abun ba ne kawai dai ana samun tsabanin fahimta ne ga mutane, kuma yanzu zamani ya canja ba kamar lokacin baya ba” “Ko zamani ya canja ni ban canja ba Yasir, abun da duk ba tarbiya ba bana sha'awar” “Appa sau daya zamu yi fa, daga wannan ba zaka sake ba? Appa please kawaye na duk ana musu sai ni” Tana maganar tana son yin kuka Appa yayi murmushi. “Shi ke nan na ji, za a dafa shimkafa fara ayi sadaka” Ta buga kafa daya a kasa tana kukan da babu hawaye, Yasir kuma ya saka dariya. “Appa dan Allah dai Appa” Ba kasai Hurriya take zuwa masa da bukata ba, kusan duk wata bukata da take gabatar masa da ita kidayayyyiya ce, hakan ya sak idan ta zo masa sai ya biya mata ko dan tausayinta da yake na lalurar dake tare da ita, balle kuma yanzu da tausayinta ya ninku a zuciyarsa saboda rashin Amma a gidan, sai yake ganin yaransa kamar wasu marayu da uwarsu ta mutu ta bar su. “Na ji amman daga wannan ba za'a sake ba?” Ta amsa da sauri tana tsalle. “Na yarda Appa na yarda Allah ya saka da alheri, Appa Allah ya biya maka bukatunka na alheri ya rabaka da Hajiya Lafiya ya kara buda maka a kasuwanci ya kyautata karshenka” Ta masa kwatankwacin addu'ar da Amma take masa idan yayi mata wani abun kyautata da ta ji dadi. Appa ya shafa kansa yana jin zuciyarsa da tausayin da be san na minene ba. Yasir ma murmushi yayi yana taya ta murna yadda Appansy ya amince da wuri. “Bari mu fara neman Gift din da zamu bawa mai birthday” “Har da kyauta ake badawa?” Appa ya tambaya sai Yasir ya amsa masa. “Eh Appa idan mutum yayi birthday ana ba shi kyau sosai ma, kowa da kalar abun da yake ba shi” “Oh toh saboda ki ci kudinmu kike son yi birthday kenan?” Cewar Appa yana kallonta da zolaya, sai ta saka dariya kamar ba ita ta rufe idonta. “Appa ba da kai ba an yafe maka” Shi ma dariyar yayi, ya bita da kallo domin tuni ta nufi bangaren Momy domin labartawa Hamad cewar Appa ya yarda zai mata birthday kamin ya isa gurin hawaye ya cika idonta domin ta saba idan aka mata albishir Amma take fara fadawa sai dai a yau babu Amma a gidan kuma ta san babu wanda zai taya ta farinciki da murna sai dan'uwanta. Tana ahiga falon sai ta ja ta tsaya tana kallon Musib da ya hada hannayen Hamad ya rike yana zabga masa mari. “Ba zaka yi magana ba? Waye yaje ma fadawa Appa karya da gaskiya ya zo ya rufata ta fada? Tsakanin kai da Hurriya” “Ni ce” Ta amsa kai tsaye domin ba zata jure ganin ana duka dan'uwanta ba da yaki yayi magana kuma ya ki yayi kuka sai dai idanuwansa sun kada sun yi ja sosai sai wani cika yake yana batsewa alamar zuciyarsa ta gama kawowa. “Okay zo nan bakar mufuka wato daga dawowarku za ku fara hada Momy fada da Appa ko?” Bata zo ba kamar yadda ya bukata sai dai kuma bata matsa daga inda take tsaye ba ssi hawayen da ta shigo da su suka fara sauko mata, Hamad ya juya ya kalleta har lokacin be ce komai ba, daman tun shigowarsa falon Musib ya rike shi wai sai ya fada masa waya fadawa Appa gulma har ya shigo yana mata fada ta yi kukan, Hamad ta kafiya ya ki magana hakan ya saka Musib dukansa. Musib ya saki hannun Hamad ya nufi gurin da Hurtiya take tsaye ya fara kai mata duka sai ta boye fuskarta ta fara kuka, yadda Hamad ya nufo gurin da suke tsaye sai ka dauka zai yi dambe yayansa Musib ne, ficewa yayi daga falon Musib na kokarin rikoshi ya fisge ya fice da gudu, be zame ko'ina ba sai gurin da Garden din gidan yake ya samo manya manyan duwatsu ya dauko har uku ya fito da su ya nufi gurin da Motar Momy take ta fara jefan gilashin a take ya fasa mata gilashin mota ya koma dayan bangaren ya sake jefawa. Kamin yayi na uku Appa da Yasir da suke tsaye a gurin da Hurriya ta bar su, suka iso gurin da sauri domin sun lura da lokacin da ya dauko duwatsu sun san ba za'ayi mai kyau ba, Yasir yayi saurin rike Hamad. “Kai miye haka?” Sai a lokacin Hamad ya fashe da kuka yana maida magana. “Ya Musib ya yi min mari hudu, kuma gashi can yana dukan Hurriya, wai ya ce mun yi munafurci mun hada Momt da Appa fada” Appa da ransa ya bace saboda abun da Hamad aikata, a take abun da ya fada ya gusar da bacin ran abun da Hamad yayi. Ya nufi falon fuska a hade Yasir dake rike da Hamad har lokacin yana ta zillo sai ya sake kwaso wasu duwatsun ya fasa motar ya bi bayan Appa. Da karfi Appa ya tura kofar falon ya shiga sai ya samu Hurriya duke kusa da kofar ta rufe fuskarta tana kuka marar sauti. “Musib...!” Appa ya aika masa da wani irin kira da karfin murya mai razanarwa. Musib dake boye kitchen ya fito baki kofar kitchen din yana amsa kiran muryarsa na rawa. “Na'am...” Appa ya taka ya karasa har inda yake ya dauke shi da mari. Daidai lokacin da Momy ta sauko tare da Namra. “Akwai wanda na taba duka cikinku? Akan wani dalili zaka dokesu? Kai da ya kamata ka ga wasu musguna musu ku shigar musu kai zaka saka hannu da kanka ka dokesu? Karka sake! Ina gargadinka ba su ba Hurriya da Hamad kadai ba duka yayana kar ka sake saka hannu ka dake su” Appa ya juyo ya kalli Momy dake tsaye kamar hoto tsabar mamaki ya ce. “Na rantse da Allah idan wani ya sake dokar min ƴaƴa sai na masa abun da zai yi bakinciki da na kasance ubansa, ban doka ba ba zan yarda wani ya dokar min ba” “Saboda ƴaƴan Iyami ne?” Momy ta tambaya tana jin wani tuƙuƙi a zuciyarta, shi kuma ya amsa mata ba dan suna ƴaƴan Iyami kaɗai ɓa sai dai baya daukar a zalinci kowa, amman saboda ta ji haushi sai ya amsa mata da haka. “Eh saboda suna Ƴaƴan Iyami...” Yana fadar hakan ya juya ya fice daga falon, a nan ma Yasir da har lokacin yana rike da Hamad dake ta jan numfashi da karfi saboda zuciya, ya rufa masa baya tare da Hamad din, Hurriya kuma da ta tuni kuka yayi mata bankwana ya tafi ya barta tsaye tana kallon dramar da ake ta bi Appa da kallo kamin ta juyo ta kalli Momy. “Ba hakka, haka ne... Daman ance maza ke bude wata kofar wani lokacin yau na gani, kuma ya bude muku kofa, za ku wahala a gidan nan. Musib yi hakuri” Ta juya ta fara hawan stairs din daman bata sauko gaba daya. Musib ya watsawa Hurriya wani mugun kallo ya dauke ido ya bi bayan mahaifiyarsa. Zaunawa Hurriya ta yi a gurin ta rafka uban tagumi, gaba daya kwakwalwarta ta rike ce ji take kamar ba zata iya dauka ba. *** *** *** BAYAN WATA UKU.... Tun daga lokacin sai Hurriya da Hamad suka samu salama, ta duka Hamad kuma ya samu ta magana, ba a dukansa ba a fada masa magana marar dadi, saboda ana tsoron ya fadawa Appa, Musib da Miwan ma sai duk suka shafa musu lafiya, sai dai tsanar da Hajiya Kaltume take mata sai ya karu, har ta kai a gaban Hurriya Hajiya Kaltume take zagin Iyami sai dai ba zata yi a gaban Hamad ba, Hurriya tana jin zafin abun sosai sai dai bata taba fadawa kowa ba sai dai ta bar abun a zuciyarta. Hurriya na tsaye ita da Hamad suna wanke motar Yasir Hajiya Kaltume ta fito rike da jakarta Yasir din yana bayanta rike da makullin mota. “A gaishe da ku, amman idan Appa ya gani karku ce ni na saka ku ku ce ku kuka saka kanku dan kar ya fara fada ya ce ban kai wankin mota ba na saka ku yi” “Hamad ya fada masa zamu wanke maka mota ai kamin mu fara, ya ce mu je mu yi Allah ya mana albarka” Hurriya ta amsa tana watsawa motar ruwa, domim wankin mota yana daga cikin abun da yake matukar burgeta, kuma ta taba yi sau daya a motar Appanta tun a lokacin da Amma take gidan. Hajiya Kaltume ta kallesu irin kallon nan na rasa ya zan yi da ku ta dauke kai ta nufi motar da za su shiga, tana nufar motar gabanta na kara tsananta faduwa har sai da taja ta tsaya. “Yasir anya ba za mu fasa tafiyar nan ba? Gabana sai faduwa yake Wallahi tsoro nake ji ganin nake kamar wani abun zai sake faruwa” Yasir ya ce. “Babu abun da zai faru Hajiya dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi imani da Allah, kuma kin ga tun da abun nan ya faru baki sake fita ba, yau kusan wata uku kenan dole ki ji haka” Ta girgiza kai domin bata gamsu da kalaman Yasir ba. “Ko dai mu hakura har wani lokacin?” “Hajiya idan baki kawar da komai a ranki ba, babu ranar da zaki sake fita, rasuwa nawa aka yi baki je ba, ga haihuwa ba an yi ba daya ba amman baki fita ba, Hajiya Fatee ma tare abun nan ya same ku amman zuwanta biyar gidan nan, dan Allah ki daina tsoro babu abun da zai faru da yardar Allah” “Toh Allah yasa” Ta amsa tare da bude motar ta shiga ba dan ranta ya so ba, sai dan fitar ta zame mata dole ne saboda kiran da Hajiya Fatee ta yi mata tana kuka ba zata fita ba, balle kuma da ya kasance gidanta na farko da zata fara zuwa tun bayan da aka yi kidnapping dinsu, sai take ganin kamar hakan zai sake faruwa ne. A hankali Yasir ya rika jan motar suna tafiya yana dan taba mata hira, ita kuma ta kasa cewa komai sai kallon gari take har lokacin tsoro be fice ta ba, garin kuma tana ganin kamar ya sake saboda dadewa da ta yi bata fita ba. “Bismillahi” Ta furta yayin da ta bude motar zata fita, zuciyarta nata rawa, Yasir ya rakata har cikin falon Hajiya Fatee, yan aikin Hajiya Fatee suka fara gaisheta. “Lafiya Kalau Ina Hajiya Fatee” “Tana dakinta” Hajiya Kaltume ta juya ta kalli Yasir. “Bari na kirata ku gaisa” “Okay” Ya nufi kujera ya zauna, Hajiya Kaltume kuma ta nufi dakin Hajiya fatee ta tura kofar ta shiga da sallama. Kuka ya hana Hajiya Fatee amsawa sai dagowa da ta yi ta kalleta da idanuwanta da suka gama kumbura. “Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Hajiya Fatee abun har ya kai haka” “Ya wuce, Hajiya Kaltume ina cikin bala'i da tashin hankali” Hajiya Kaltume ta juya ta leka falon saitin da yasir yake zaune. “Yasir ka tafi kawai idan zaka dawo daukata sai ku gaisa, amman fa da zarar na kiraka ka zo da sauri” “Toh Hajiya” Ya tashi ya fice cike da ladabi. Sannan Hajiya Kaltume ta koma dakin ta zauna kusa da kawarta da rabin kibar jikinta ta zube saboda tashin hankali. “Wannan abu be yi dadi ba, yanzu miye abun yi?” Hajiya Fatee ta share hawayenta ta kalli aminiyarta. “Ban sani ba Hajiya Kaltume, wannan shi ne likita na uku da ya fada min haka” “Hajiya Fatee duk laifinki, da tun farko kin yarda anje asibitin an duba lafiyarki da duk be kai ga haka ba?” “Haba Hajiya, ina zan yarda aje asibiti a fadawa ďana abun da mutanen nan suka min? Tsoron kar ya kalleni da abin kuma kar bakinciki ya zauna masa a zuciya ya saka na ki amincewa da zuwa asibitin, kuma ni ma na san idan har ya sani ba zan samu salama ba” Hajiya Kaltume ta rafka tagumi. “Wallahi duk wannan Iyamin ce ta ja mana, ba zan tana yafe mata ba, ni kaina yanzu sanadinta har tsoron fita nake” “Ni yanzu ba ta Iyami nake ba Hajiya ta kaina nake, kar asirina ya tonu, ga ni ta surukar da bata kaunata, ga makiyi babban tashin hankali kuma rashin auren nan, yau shekara goma da rasuwar Alhaji me zan fadawa duniya idan abun nan ya fito da shekaru na haka har da jikoki” Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya. “Hajiya ko dai daurewa zamu akara yin allurar nan ne? Ko Allah zai saka abun ya zube” Hajiya Fatee ta dauki robar yawu ta tsargar da yawunta cikin ta aje ta kalli Hajiya Kaltume. “Likita nan fa ya fada min, ta farko ma da na auna arziki ne, da yanzu na wuce, ni kadai na san azabar da na sha lokacin da aka min allurar nan kuma gashi bukata bata biya ba, kuma cirewar sun ce ko na mutu ko na yi rai ne” Hannu biyu Hajiya Kaltume ta dora saman kai ta fashe da kuka tana taya aminiyarta alhini. “Kai wayyo Allah wannan Iyami wannan Iyami Allah ya isar mana gareki, kin aure min miji kin fitine ni yanzu kuma sanadin nan mun fada cikin bala'i, ni Wallahi ma rasa ya zan yi da matar nan da yaranta, kin ga cikinta ya shiga wata na tara kenan wani zata haifowa Alhaji, yayanta da suke gidan ma be hada kowa da su ba, birthday nan da Hurriya ta yi sarkar zinari ta miliyoyan kudi yayi mata kyauta, ni da nake matarsa be taba siya min ba, sarkar da Nafisa take ta kuri da ita yau Alhaji ya siya irinta ya mallakawa Hurriya, ga birthday Hamad tafe waya san iya abun da zai masa shi ma, kuma saboda ita yanzu ya budewa kofa kofar birthday, abun da da ya hana” Hajiya Fatee ta daki kirji. “Sarka Hajiya? Lallai Iyami ba zata gama da duniya lafiya ba, ta mallake shi yanzu ta bar gida ta bar muku ya ku yi kishi da ita” “Hmm abun nan ya ishe ni, ai saboda na san kina cikin taki matsalar ne ya saka ban kawo miki kukana ba, amman ciwon matar nan yana nan a kirjina, a yanzu bana da burin da ya wuce na ga Alhaji ya fita lamarin yaran nan, kuma dukiyar da ya bata ta lalace” “Ba ke ba, ai ko ni ba zan iya yafewa Iyami ba Hajiya, sanadinta yara kanana sana'in yayana suka daure mu a daji babu kalar wulakancin da ba su min ba, yanzu kuma ga wani abun bakinciki ya sake biyo baya, ban san ya zan yi ba” Ta karashe zancen tare da fashewa da kuka. “Toh ni dai ina ganin abun da ya kamata kawai mu saka a nemo mana malamin nan ko Allah zai saka mu dace” Hajiya Fatee ta mata wani kallo galala. “Waya zai koma a wannan dajin? Ko gawata ba za a kai ba” “Aa ina fa? Ni ma ai ba zan yarda ba, ba komawa zamu yi ba nemansa zamu yi idan ya so shi sai ya zo ya same mu” “Ta ina? Duka wayoyin mu suka karbe fa, ba ni da number ba, kuma da aka yi welcome din Sim din har yanzu be kira ni ba, waya sani ma ko shi ya turo a dauke mu? Mutanen nan kauye nan fa ba su da kyau” “Kai bana tunani haka, kin ga ni fa na ga kyau aikinsa domin shi kadai ne yayi min aiki kuma aikin yayi yadda nake so har Iyami ta bar gidan nan, shekara nawa ina kashe kudi a banza ban dace ba sai a gunsa, sa zaki yi a nema mana shi waya nuna miki gurin Malamin” “Wata kawata ce Salame” “Toh ita zaki saka ta je ta dauko mana shi, sai mu saka gurin haduwa da shi ba dole sai ya san gidan mu ba, mu gabatar masa da bukatanmu mu basa kudin aiki, daga nan ma sai na tambaye shi ina aka kwana zancen aikin Iyami, ke kuma sai ki saka yayi miki na wannan mugun abun da yake cikinki” Kallon rashin fahimta Hajiya Fatee ta yi mata “Ya danne miki shi mana, ba zai taba tashi ba har ki mutu, ko baki san ana haka ba? Na Iyami ma so nake a danne shi kar ta haifa ma Alhaji mugun abu, dan na san duk wayonta be wuce Alhaji ya mutu ta ci gado ba” Hajiya Fatee ta kalleta wata rahma na saukar mata a ruhi, jin kamar ta samu mafitar masifar da take ciki. “Kuma kina ganin hakan zai yi?” “Me zai hana? Ki dai ki zuba masa kudi kawai, ni ma kudin zan zuba masa, kuma a hannun Alhaji zan karbe su, kudin sarkar zinarin da ya siyawa Hurriya da kudin da ya bawa Iyami duk sai na fanshesu a hannunsa, yanzu ne za su gane sun yi kuskuren taba mace kamar ni, kuma Wallahi sai na malleke Alhaji ko ta halin yaya, sai ya dawo a tafi hannuna Iyami da ƴaƴanta sai sun ɗanɗana kuɗarsu, Iyami sai ta gane kuskuren da ta aikata na aurar min miji, sai ta yi nadamar hada shimfida da Alhaji, matsayin da ta taka a baya na tana Matar Alhaji ina Matar Alhaji sai na saka ta yi nadamar haka... Ba ita ba har Nafisa sai na sake mata sabon karatu na goge mata hadda. Dukansu sai sun dawo a tafin hannuna” Ya daki tafin hannunta tana kashe ido alamar yanzu ta shiryawa rashin imani, da kuma fada da Iyami da Momy. ________________ Hmmmmmm Allah yasa kuna hango abubuwan da nake hangowa 🤔 Tafiyar fa duk duka yanzu aka fara.... Ku daura ɗamara ku zage damtse domin domin alkalinmin da zafinsa ya zo 😁 Kar a manta idan an karanta ayi sharing 🥰 [10/18, 6:15 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Hello Habibaties 😍🥰 Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy 𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣2️⃣ Musib ya aje ma Captain keys din motar Momy da ta bada umarnin a dauko masa. Kallon Keys din yayi sannan ya mika hannu ya dauka ya mike tsaye. Tsabar bacin rai zuciyarsa har zafi take kamar zata fashe, baya jin yana da sauran wata magana a yanzu kuma baya bukatar yi ma Momy sallama bayan an bata masa tayun mota a gidanta. Shi ya fara fita sannan mahaifiyarsa ta bi bayansa Momy da Musib suka biyo shi suna ba shi hakuri kamar su suka masa laifin shi dai be ce uffan ba ya matsa key hannunsa motar ta fita key ya sannan ya nufita har suka bar gidan kalma daya bata sake fitowa daga bakinsa. Ran Momy be yi dadi ba ganin ďan ďan'uwanta da take ji da shi ya fita cikin bacin rai. “Ni abun nan ya ba ni mamaki, wai waye yayi wannan aika-aikar” “Zai wuce Kaltume? Ai bata son kowa da alheri a gidan nan kuma ta ga mota mai tsada ina za so haka, ballantana fitowar nan da ta yi dan uwa ko daya be je ya mata barka da fitowa ba” “Amman Momy Yasir dai ba zai yi haka ba kin san ko da ta saka shi” “Su matan fa? Kuma shi ma ba munafurci ba ne da nuna soyayyar ido, ai ta ciki na ciki dan'uwa be taba son dan'uba ba har abada” “Ko kuma ta aiko wani yayi ba” Ta juyo tare da Musib suka shigo falon, ko zama ba su yi ba motar Appa ta faka a harabar ya bude ya fito ya shigo cikin falon fuska a dauke. “Ku ba mu guri zan yi magana da mahaifiyarku” Appa ya fada immediately after ya rufe kofar falon, Musib ya dubi Miwan sannan suka tashi suka haura sama, Momy kuma ta zauna ita ma nata ran a bace tana sauraren da wacce Appa ya zo. “Nafisa ina son na tambaye ki, akwai laifin da Hurriya ta yi miki ko kuma Hamad?” “Wani abun aka fada kuma?” “Akan wani dalili zaki nemi banbanta su da sauran yayanki? Fada min banbanci dake tsakinsu da Namra ko Miwan, dukansu ba Yayana ba ne? Akan wane dalili zaki ce Hurriya sai dai ta share dakinta da kanta kuma idan zata hau stairs ko ta sauka ba ta hau kamar yadda Namra ko Musib suke yi ba?” Momy ta rike baki. “Oh Allah na ni Nafisa, yaushe aka yi haka? Kuma shi kenan daga fada maka zance karya da gaskiya sai ka hau ka zauna har da zuwa gurin fada ba tare da ka tsaya ka bincika ba? Shiyasa ka dauko su ka kawo min? Me yasa ba a kaiwa Kaltume ba? Ita da yake tsoronta kake sai Nafisa da aka raina itace mai dadi hawa, gashi sai mulki take mana ciki gidan ita da yaranta” “Daga ke har ita karkashin kulawata kuke kuma karkashin ikona, dan haka duk gurin da nake ra'ayi a can yarana za su zauna, kuma ina gargadinki wannan ya zama na karshe da zan sake jin wani abu marar dadi akan Hurriya da Hamad, zan iya canja mata ban zanja yaya ba, gaba daya yarana babu na yarwa kuma bana son a batawa kowa” “Eh amman ai ka ware wadanda kake so kake kauna, na tabbatar da nawa yayan Kaltume ko Iyami take yi ma wani abu ba zaka yi magana ba, amman da yake yayan mowa ne ai gashi nan ka shigo falo cikin bacin rai saboda an taba yan gold, ni da zaka nuna musu kauna ka dawo da uwarsu ai da duk yafi wannan nema musu yanci da kake, idan ya so sai ta rike yayanta na rike nawa” “Abun da na ga damar aiwatarwa shi zan aiwatar, babu mai fada min gabas, na san Allah, daman ke haka kike banta zuwa da wata magana ba ki musa min ba, ban taba fada kin yi shiru kin saurareni ba sai kin fada, sa'insa da ni ba yau kika fara ba, daga ke har Kaltume babu wadda nake jin sanyinta kowacce ku da lagon da take matsawa ta bata min rai” Momy ta fashe da kuka domin kalaman Appa sun mata zafi, ta san abun da Appa ya fada akam Iyami gaskiya ne, domin ya saba yi mata fada ko a gabansu kamar yadda su ma zai iya musu a gabanta ko kuma ya tara su gaba daya yayi musu fadan idan wani abu ya faru, su kan tanka shi su kare kansu ko maida martani amman Iyami bata cewa idan yana fada har yayi ya gama, ko daga kai ba zata yi ta kalleshi ba, wannan ta saka suke yawan yi mata kallon munafuka, hawaye shar Momy take yi daman kuma bata gama hucewa daga bacin ran abun da aka yi ma Captain ba. “Eh sai Iyami, abar kaunarka, yanzu gashi nan ka rufe da fada akan yayanta, matarka Kaltume kuma ta takura min ta takurawa bakina, yanzu Captain ne ya zo, ka san dai yadda nake da Captain amman haka matar nan ta saka aka fasa mata tayun mota saboda bakin ciki, ban gama huce wannan haushin ba gashi nan kai kuma ka zo ka rufe ni da wani, toh Wallahi ka jawa yayanka kunne su daina munafurci, kuma ka jawa matarka matarka kunne ta fita safgata da ta bakina babu ruwanta da ni idan ba haka ba Wallahi za 'ayi tashin hankali da ba taba yi ba ko a lokacin da ka auro karamar yarinyar can Iyami” “Ni dai na fada miki, karki sake banbanta min to ƴaƴa duk daya suke a gurina, babu wanda ya fi wani, zan iya canja mata ban canja ƴaƴa ba bana ni da kamar ƴaƴana!” Yana kawai nan ya juya ya fice, cikin motarsa ya koma yaja ta zuwa bangare ya ajeta ya fito ya taka da kafa ya nufi bangaren Hajiya Kaltume yana shiga ita ma ya salllami yaranta suka haura sama ban da Yasir da baya gidan ma a lokacin ya fita gurin safgoginsa, Namra kuma ta fita zuwa bangarensu. Fada yayi mata sosai yana ja mata kunne akan abun da ta saka aka yi ma Momy. “La'ilaha Illallahu ni Ummul Kultoon, yaushe kuma aka yi haka? Ni miye ruwana da Nafisa balle kuma bakinta, yanzu Fisabillahi na rasa me zan saka ayi mata sai fashe tayar baki? Abu dai kamar karamar yarinyar? Ni da nake ta kaina ma? Yaushe na fito daga daji? Kofar daki ma bana sha'awar fita balle kuma har na saka ayi wani abun, shigowar nan da ka yi ma hankalina sai da ya tashi” “Ni dai na gargadeku, bana son wani tashin hankali kowa ya zauna lafiya kuma ya tsaya a iya matsayinsa, ku bar ni da abun da yake damuna, kullum ni ne cikin fitina kamar akaina aka fara mata aure da mata biyu” “Mata uku dai Alhaji, yaushe ka saki yarinyar can Iyami da har zaka dawo kanmu nu kadai, musamman ni, taya za a ce na fasa tayar mota? Yara ma wa zan saka yayi wannan aiki? So take ta zugaka ka koreni a gidan kamar yadda ka kori Iyami, to Wallahi ni kam zama daram dam dam dam sai mutuwa, kuma Alhaji dan Allah ka rika bincike kamin ka fara fada, Wallahi sheri ne kawai na kishiya da neman hada mata da miji, abun da ba ayi ba da kurci ayi shi yanzu” “Na dai ja muku kune, kowa ya tsaya iya matsayinsa bana son sake jin wata fitar” Har Appa ya fice Hajiya Kaltume bata gama mamakin jin irin kagen da Momy ta yi mata ba, Salma ce ta fara saukowa sannan Khairi suna tambayar me ya faru domin sun lura da yadda mahaifinsu ya shigo cikin fushi. “Wai munafurci matar nan ta hada, wai na tura an fashewa bakinta tayun mota, shi kuma babu tsayawa bincike da yake ta mallake shi komai ta fada masa shi yake yi kawai ya zo ya rufe ni da fada, ai bari Wallahi ita ma sai ta bar gidan nan Kamar yadda Iyami ta fitar da ni, waya sani ko gurin tsafinta ta tafi aka bata wani asirin ace ta zo ta hada mu, gaba daya ta mallake Alhaji ta juye masa kai komai ta fada sai ya hau ya zauna” “Tab Lallai Momy ta yi nisa, wane irin fasa tayun mota kuma?” Hajiya Kaltume ta kalli Salma dake maganar. “Sheri ne kawai a samu yadda za a hada ni fada da Alhaji sai ya sake ni” Haka Hajiya ta yi ta jininin maganar tana ta masifar har yamma. *** *** *** Hajiya Binta dake gidan baya tana shafa kan Hurriya dake kwance jikinta ta ce. “Tsoho kamin ka kai ni gida, ina son ka biya da ni gidansu Iyami na dubata yaranta ma su ganta” Kamar wadda aka cewa ya shiga ramen wuta haka Appa yaji, ko kadan be son abun da zai kusantashi da Iyami gashi kuma be isa ya musawa Hajiya ba. “Toh Hajiya amman idan na aje ki Yasir zai zo ya dauke ki ya maida ke gida su kuma yara ya dawo da su” “Toh zamu tafi gidan makiyiyarka ba, Allah ya kyauta” “Haba Hajiya irin wannan maganar be dace ba a gaban yara ban da alheri me iyami ta yi min da zan dauki kiyaya na bita da ita” Hajiya dai bata sake cewa komai ba har Appa ya canja hanya ya dauki hanyar gidansu Iyami. A bakin gate din ya faka, ya fito ya budewa Hajiya ta fito tare da Hurriya sannan Hamad ya bude front door ya fito. “Ba zaka tsaya ta fito ku gaisa ba?” “A gaishe ta dai Hajiya” Ya amsa yana kin hada ido da Hajiya Binta, girgiza kai kawai Hajiya ta yi ta cira kafa suka karasa bakin madaidaicin gate din da tuni Hamad ya bude har ya shiga ciki. Yanayin yadda Hajiya Binta ta tararda Iyami be mata dadi ba, daman kuma ta san za'a rine wai an saci zanen mahauciya, mai ciki ba a rabata da laulayi balle kuma ita da take cikin damuwa, sai dai ganin Hajiya Binta ya saka ta ji kamar an dauke mata ciwo, suka ta yi hira kamar yadda suka saba. “Jiya muke zancenki da Gwaggo na ce ina tuna haihuwar Hurriya da irin hidimar da kika yi” Hajiya Binta ta yi murmushi. “Abu kamar jiya, yanzu Hurriya ta cika sha shida cif” Hurriya ta wara ido tana mamaki yadda ta manta birthday dinta. “Eh fa Hajiya amman ai sai October 10” “To October ba ya kusa ba? Miye rage yan kwanaki ne kawai” “Hajiya zaki yi ma Appa magana yayi min celebration please” Iyami ta ce. “Kin san halin Appanki ba son irin abubuwan nan yake ba, shi gaba daya rayuwarsa irin ta mutanen da ne” “Zan masa magana da kaina, maybe zai yi min gashi ma dazun ya fada mana a falon Hajiya ya ce ni da Hamad a waje zamu yi karatu” Mamaki ya cika Amma har sai da ta bude baki ta kalli Hajiya dake murmushi. “Shi da kansa?” “Shi da kansa fa, sai dai ki yi ta addu'a kuma ki yi musu, ai maso uwa ya so yayanta, abu dai ne idan ya zo babu yadda za'ayi sai hakuri kawai, amman sakin nan ba karamin mamaki ya ba ni ba” Amma ta sauke kai kasa tana jin wani rashin dadi yana ziyartar zuciyarta. Hurriya ta tashi ta fice zuwa dakin Anty Rukayya haka take jjnta kamar wata sa'arta saboda tana wasa da ita sosai kamar yaya da kanwa, wannan ya saka Hurriya bata kallon Rukayya a matsayin kanwar Amma sai idan babin girmamawa ne, ba ita ba ko Hamad wasa yake da ita, daman kuma hausawa sun ce karamar uwa madaukar zunubi. Amma ta ce “Haka Allah ya so Hajiya komai Allah ne yake tsarawa Allah dai ya ba mu ikon cinye jarrabawar wannan jarabarwar” “Toh Ameen ina nan ina ta addu'a, da yardar Allah Iyami sai kin koma dakin domin sakin nan naki har hawan jini yake son tasar min, Allah ya sauke ki lafiya, da na shiga gidan ma sai na ji duk yayi min dabam” “Ameen” Amma ta amsa tana jin zafin barin gidan Appa da ta yi, ba tare da laifin komai ba. Gwaggo ce ta shigo suka suka ta hiran kowa yana fadin abun da ya fahimta game da lamarin, Amma kuma tana fadar yadda Appa ya canja mata tun kamin sakin. Cikar da cikin Hajiya Binta yayi a gidan danta be hana ta cin abinci a gidan Amma ba, saboda tana son Amma kuma ta san idan bata ci ba Amma zata ji babu dadi domin abinci Amma take fara ci kamin ta ci na kowa wani lokacin ma bata taba abincinsu sai ta ce ta koshi. Bayan sallah la'asar Yasir ya iso gidan daukar Hajiya Binta kamar yadda mahaifinsa ya umarce shi, cikin gidan ya shigo suka gaisa da sannan ya fito tare da su Hurriya a daidai lokacin da Rukayya ta sallami bakonta ta nufo karamar kofar shiga tsakar gidan da suka fito. “Yasir ya gida” Ya sake mika masa gaisuwa a karo na biyu bayan gaisuwar farko da suka yi a lokacin da ya shigo. “Mutumen da na gani saurayinki ne?” Wani kallo ta yi masa jin yadda yayi mata tambayar kai tsaye kamar da zolaya kuma kamar gaske, domin murmushin dake fuskarsa ya hanata fahimtar komai. “Dan makarantar mu” “Dan makarantarku har cikin gida? Lallai yana da matsayi da alama” Murmushi kawai ta yi ta maida dubanta gurin Hajiya da Amma ta rakota suna tafiya suna hira. “Allah ya kiyaye hanya, Hurriya sai kun dawo” “uhmmm za a shiga a cigaba da karatun ko? Ko last time da na zo har na fita baki sani ba tsabar karatun littafan soyayya, to aje a karasa kar a manta page din da ake” Ta girgiza kai still tana murmushi. “Yasir ka cika shiga min hanci fa... Haka kemin idan na je gidanku ko zama na yi sai ka ce ba daidai na zauna ba” “Toh ki fyato ni mana idan kin isa” A nan ma murmushi ta yi ta shige ciki, shi ma ya bita da kallo yana murmushi Hurriya da Hamad kam tuni sun kai cikin mota, inda sabo sun saba da ganin tsokanar yayansu akan kanwar Mamansu ba sabon abu ba ne a gurinsu Amma ma ta saba gani balle kuma su. Amma da kanta ta budewa Hajiya mota ta shiga ta rufe sannan ta juya ta koma ciki Yasir ya shiga ya fara jan motar. “Yasir na ce ko a fara sabunta kayan dakina ne na kusa samun kishiya?” Hurriya ta saka dariya Hamad kuma yayi murmushi tare da cewa “Hajiya yanzu kuma kin fasa aurena?” “Eh ga babba me zan yi da yaro! Yasir ya ishe ni gashi har yana nema min kishiya, ko da yake Kaltume ai ba zata yarda ka dauki wannan ba sai dai wata” “Ke tsohuwa waya fada miki har yanzu ana irin zamaninku da ake yi ma mutane auren dole? Ni zan zabo wadda nake so na yi aurena” “To Allah ya nuna mana, kuma ya bada ta gari” “Ameen” Ya amsa yana cigaba da jan motar. Sai da ya fara isa gidan Hajiya ya sauketa sannan ya juyo ya kama hanyar gidansu, a harabar Hajiya Kaltume ya faka motarsa ya bude ya fito Hamad ma ya fito tare da Hurriya gaba dayansu suka nufi hanyar falon Hajiya Kaltume. “Hurriya me ya samu gilashinki?” Yasir ya tambaya domin tun zuwansa daukarsu ya lura da fashewar gilashin nata. Ta kai hannu ta taba gilashin. “Faduwa na yi” Karaf Hamad yayi ya ce. “Karya take wani bakon Momy ne ya mareta ni kuma ya na fasa masa tayun mota gaba daya” Daga Huriyyar har Yasir tsayawa suka yi kallonsa da mamakin furucinsa. “How?” “Wuka na saka wukar Momy ta yanka ƙashi na yi ta cakawa ina yanka har da sai da na fashe duka tayun” Maganar yake yana nuna yadda yana yana cize baki alamar ƙeta. Cikin mamaki Yasir yayi dariya ya bugo kan Hamad. “Baka da kyau yaron nan bura'uba” Hurriya ta yi murmushi for the second time ta sake jin Hamad ya burge ta a yau, bayan da ya fadi cewar zai zama likita saboda yayi mata aikin ido yanzu kuma ya fasa tayun wani saboda ya mareta, ita dai ta san bata jituwa da Hamad suna yawan yin fada da samun tsabanin amman kuma yana nuna damuwarsa da kulawa a duk wani abu da ya shafeta, idan wani ya taba ta yana jin zafi fiye da yadda shi idan aka masa yake ji. Yasir ya shiga tambayar me ta yi ma bakon yayi mata marin da ya saka gilashinta fashewa. “By Misteke na fito... ” Shi kansa be ji dadin jin karami dalili da be taka kara ya karya ba ya saka bakon marinta marin kuma mai zafi. “Mutane ba su da hakuri kuma ba su da hakuri...” Ya rufe baki yayinda yake tura kofar falon ya shiga. “Toh Wallahi ba zan dauka ba, wannan wulakanci da rainin wayon da Nafisa take min yayi yawa” “Me ya faru?” Yasir ya tambaya domin shi kadai ne be san wainar da ake toyawa ba. A take ta amaye masa cikinta tana wani cika domin ba karamin cin mutunci ne a gareta ba Momy ta zargeta da haka duk kuwa da irin rashin zama lafiyar da suke. Yasir ya kalli Hamad, Hurriya ma ta kalli Hamad Hamad ya kalleta kowa yayi shiru, shi dai Hamad ba zai yi laifi yace shi yayi ba, kuma idan an gano shi yayi hakan ba zai dame shi ba, Hurriya kuma ba zata tonawa dan'uwanta asiri ba, balle kuma Yasir da ko da yaushe yake kashe wutar fitina. “Toh Hajiya Ki yi hakuri, dan Allah ku daina wannan fadan, bana jin dadi haka Appa ma ba dadi yake ji ba, kuma dai ba yara kuke ba be kamata ace kuna biye zuciya ba” Hajiya ta daki cinyarta “Wallahi ba zan hakura ba, sai ta dandana kudarta, kuma Wallahi na fi karfinta bokanta yayi karya Wallahi, Iyami ma ta kara da ni ta bar ni balle ita bukkar banza, mai karyar arziki sai ka ce kanta farau arziki duk ta fi ta cikawa mutane gida da bakin kuri da iyayi ita diyar mai kudi, mun ji karuna duk arzikin ubanta be kai karuna ba, ni kuwa sai na zame mata fir'auna a cikin gidan nan” “Subhanallahi Hajiya dan Allah ki daina irin maganar nan haba” Yasir ya fada cike da damuwa, domin baya jin yadda matan ubansa suke samun tsabani a gidan. “Babu ruwanka babu ruwanka idan ba zaka taya ni yaki ba karka sake shiga tsakanina da kowa, dan iya. Ke kuma yar gadon munafurci bace min da gani” Ta karasa tana watsawa Hurriya dake tsaye tare da Hamad harara, babu bata lokaci Hurriya ta juya ta fice daga falon, Hamad kuma ya tsaya a gurin kamar ba zai tafi ba, irin yadda yara masu fama da rashin kunya suke yi, sannan ya fice yana wani tukuki saboda saka sunan uwarsa a fadan da Hajiya Kaltume ta yi kuma ta kira Hurriya da yar gadon munafurci. ____________________ Masu karatun suna hango abun da nake hangowa? 😳 Akwai Bomb fa ba karami ba? Fatan dai kun shiryawa tafiyar? 😁 Idan kun karanta ku yi sharing 🥰 [10/18, 6:16 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Hello Habibaties 😍🥰 Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy 𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣1️⃣ Hanya Hurriya ta hadu da Hamad ya zo zai kirata domin ita Hajiya Binta ta fara tambaya daga isowarta gidan. “Me ya same ki? Hajiya na kiranki tana bangaren Appa” Ya tambaya kamar irin hankalinsa be tashi ba dan ya ga hawayenta. “Momy ce ta yi baki shi ne namijin ya mare ni” “Me kika masa?” “Ban masa komai ba, kawai saboda na je fitowa da sauri shi kuma zai shiga na buge shi, shi kuma ya mare ni gilashina har ya fashe, da jikinki kamar itace mugu kawai” Ta farasa tana kuka ita ma kanta ciwo yake an karon da suka yi, balle kuma shi da bata san yadda ya ji ba. “Ina yake?” “Yana bangaren Momy” Ta bashi amsa ta bar shi a gurin tsaye yana kallon apartment din Momy kamar mai tunani tafiya, ita dai ta yi gaba abinta, har Namra ma ta zo ta wuce Hamad na tsaye a gurin yana kallon part din. Hurriya na shiga bangaren Mahaifinta ta rungume Hajiya ta fashe da kuka. Hajiya Binta da tsayi ke neman gagararta sakamakon rikon da Hurriya ta yi mata kalli Alhaji Haruna. “Kalli abun da ka yi” Appa ya sauke kansa kasa ba tare da ya ce komai ba. “Allah ya kyauta” Hajiya Binta ta fada sannan ta taka a haka ta isa gurin kujera ta zauna Hurriya na rike da ita, har jikokinta da matar ďanta Momy suka shigo suka gaisheta, suka fita Hurriya bata dago daga jikinta domin ji take kamar Amman ce ta rumgume, wani gatan ma da kakanin suke mata Hajiya Binta da Gwaggo Amma bata mata irinshi. “Kullum idan na zo gidan nan bangaren Iyami nake sauka, amman yau ka raba wannan a dole na sauka a nan, mace mai hankali da girmamawa, wannan matar ta san kimata, har abada ba zaka taba samu mace mai irin tarbiyarta ba tsoho” Appa ya sauke ajiyar zuciya domin ya san gaskiya Hajiyarsa take fada, iri irin Iyami masu son iyayen miji da girmamasu kadan ne a duniya ba su da yawa. “Hajiya ga abinci ki bari na zuba miki” “Aa Hurriya zata zuba sai mu ci tare ai kasan da ita na saba cin abinci idan na zo” Appa yayi murmushi. “Hurriya dago haka Hajiya ta ci abinci mana” Hurriya ta dago ta bude kulolin ta dauki plate ta fara zubawa. Sai a lokacin Appa ya lura da fashewar da gilashinta yayi. “Me ya sami gilashinki Hurriya?” “Faduwa na yi” Ta yi karya kai tsaye. Hajiya ta kalli Hurriya sannan ta kalli Appa ta ce “Kana da dai jin abun da Hamad ya fada min a mota, idan ba zaka dauki mataki ba ni zan zo da kaina na dauke yaran nan na maida su gidana, domin ba zan bari a rika wulakanta kamar wasu bare ba” Appa ya shiga mata rantsuwa domin kare kansa. “Wallahi Hajiya, ban san da duk wannan ba, ai kin san idan na sani ba zan bari ba, ni kaina sai a yanzu nake ji a gurin Hamad din, kuma In Shaa Allahu zan dauki mataki, Hurriya me yasa baki fada min abubuwan da suke faruwa ba?” Hurriya ta kalli Appanta ta sauke kai ta cigaba da zuba abinci, daman ta sani ko da Hamad be yi ikirari ba zai iya fada balle ma har yayi. “Wallahi ban sani ba, amman zan dauki mataki yanzu da yardar Allah” “Na dai fada maka, dan ba zaka saki uwarsu ba, kuma ka barsu ana musguna musu kamar wasu ba yi, har dokoki ake saka musu a gida, kuma duk tarin masu aikin gidan nan ace Hurriya sai ta share dakinta da na Hamad su sauran yaran ai ba haka take musu ba, shiyasa tun a lokacin da na ji ka saki Iyami na kira Nafisa da Kaltume na ja musu kunne akan yaran nan ashe na yi a banza, da Iyami ce ko ba zata jefar da magana ta ba” “Za a gyara Hajiya, amman dan Allah ki aje maganar daukarsu ko maida su gurinki, tun da Iyami ta bar gudan nan yaran nan kawai nake gani ina jin sanyi, idan kika dauke su karin wata damuwar ne a gareni” Hamad ne ya shigo falon rike da karamar wuka a hannu ya zauna kusa da Hajiya Binta ya aje wukar gefe. “Me ya hadaka da wuka Hamad?” “Apple na yanka” Ya amsa tare da daukar spoon ya saka a abinci da Hurriya ta zuba. “Hamad abinci Hajiya ne fa kana ganin na saka nama da yawa shi ne kuma zaka saka spoon” A take ya daka mata tsawa. “Toh ina ruwanki da ni, ba zaki daina shiga min hanci ba ko? Hajiyar ta ki ce ke kadai” Hurriya ta kalli Hajiya tana turo baki alamar ta fusata. “Hajiya kin gani ko?” “Kyale shi zuba mana wani” Hamad yayi kwafa, Hurriya ma ta yi kwafa daman tana da haushin marin da aka yi mata zuginsa be gama wucewa a kuncinta ba. Ai a take Hamad ya daga hannu zai kai mata duka Appa yayi saurin rikewa. “Kai Kai Kai Kul daga magana sai ka ce zaka duketa, ita ce yayarka fa, ba zan daukar maka wannan ba Hamad, haka Iyami ke ta fama da kai kai baka san ka ragawa kowa ba?” “Amman Appa ai ita ta fara” “Yi mata hakuri kyaleta ai yar'uwarka ce baka da kamar ta, kyaleta” Ba dan kakarsa Hajiya Binta ta saka baki ba zai bar Hurriya ta zauna lafiya ba, hakan kuma be hana shi sake yin kwafa ba sannan ya fara cin abinci. “Ni wannan zuciya ta Hamad ban san gun da daukota ba, fushinsa har tsoro yake ba ni” Appa ya fada yana shafa kan dansa, Hajiya ta ce. “Zai daina kurciya ce, da zarar ya girma ya mallaki hankalin kansa zai daina, wani lokacin yara idan suna jin tashin balaga haka suke jin kamar daidai suke da kowa, ka bar shi ya cike 20 ko 18 fushin nan duk zai hauka” “Allah yasa, ya shirya mana” Hajiya ta amsa da Ameen. Sai da suka gama cin abinci sannan Hajiya ta tashi tare da jikokinta Hamad da Hurriya Appa na gafenta suka fito daga bangaren na Appa zuwa bangaren Hajiya Kaltume domin yi mata jaja da kuma barka da kubuta. Ko da suka shigo falon na Hajiya Kaltume yana cike da yayanta da kuma yayan yan'uwanta da ma ita kanta sai hira ake har da Namra. Kamar ta Allah haka Hajiya Kaltume ta washe baki tana maraba da zuwan Hajiya Binta. “Sannu da zuwa Hajiya, ai da ma baki zo ba, ga kafafuwa suna ciwo ni kaina idan na warware ai sai na zo na gaishe ki, kuma ai kin kira waya haka ma ya wadatar” “Aa kara dai na zo, fatar na same ku lafiya” “Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya ciwon kafafuwan yayi sauki?” “Alhamdulillah” Sama sama dai suka yi ta gaisawa Appa na zaune kusa da Hajiyarsa daga kasa, Hajiya Kaltume kuma na daga kan kujera ita da duka yaranta, Hurriya da Hamad ne kadai a kasa domin haka Amma ta koya musu idan babba yana kan gado ko kujera to su kuma su zauna a kasa, kar su zauna tare da shi ko kuma a yadda yake zaune. Da hira ta yi hira ne Hajiya Kaltume ta dauko zancen wahalar da suka sha a dajin tana fadar yadda aka rika mistreated dinsu kamar wasu dabbobi. “Shiyasa ake son a samu soji masu kishin kasa da za su iya yakarsu idan ba haka ba, kasar nan da wahala ta gyaru domin Shugabannin ma sun zama sai a hankali” Cewar Yasir. Cikin murmushi Hajiya Binta ta kalli Hamad ta ce. “Da yardar Allah Hamad soja zai yi, wannan fushi da zuciyar ta soja ce” Hamad ya girgiza kai. “Aa ba soja nake so ba?” Namra ta ce. “To me kake so? Wannan zuciyar taka Hamad ai soja ya dace da kai” “Aa ni Likitan idanu nake son zama, idan na kware zan yi ma Hurriya aiki ta, ita ma ta rika gani kamar kowa” Tsit katon falon na Hajiya Kaltume yayi domin babu wanda ya za ci abun da zai fito daga bakin Hamad kenan. Hurriya ta yi murmushi tana masa kallo irin na so da kaunar dan'uwa, ita kanta ba yi zaton Hamad yana sonta kuma ya kula da damuwarta har haka ba. “Come here my friend” Yasir ya mika masa hannu, sai ya taso ya iso gurin Yasir din Yasir ya rumgume yana buga bayansa. “Yayi kyau babban mutum” Cikin jindadi da alfahari Appa ya kalli Hamad ya ce. “Da yardar Allah da yardar Allah, Hamad ba zaka yi karatu a kasar nan ba, waje zan kai ka ka sha ilmin akan idanuwa har ka gaji, da ikon Allah wannan kudirin naka sai ya cika ko da bana raye” Hajiya Kaltume da ta rasa abun da zata yi ta kalli Appa da murmushin dole. “Za a karya dokar fitar da yara waje karatu kenan Alhaji akan Hamad?” “In Shaa Allah, ba shi kadai ba Hurriya ma ba zata yi karatu a kasar nan ba, yadda take da kokarin nan waje ya kamata ta yi karatu, kuma ko ba ni ba Principal dinsu ya fada min suna sa ran da zarar ta gama secondary school zata samu scholarship mai kyau a manya kasasshe saboda kokarinta da yadda take cin gasa ta bangaren lissafi” “Maa Sha Allahu, Allah ya nuna mana yara masu albarka Allahu akbar Allah dai yayi albar....ya bar zumunci” Sai ta kasa karasa da Allah yayi albarka ta canja zuwa Allah ya bar zumunci, domin ta san hausawa sun ce addu'ar makiyi karɓaɓɓiya ce, ita ko ba zata so su yi albarka ba. Gashi abun da Appa ya fada cewar yaran Iyami za su karatu a waje ya daki zuciyarta mugun daka irin dakan da ace mashi ne, babu abun da zai hana ya bullo ta bayanta, yanayinta ma gaba daya sai ya sauya hankalinta yayi mugun tashi, ba dan ta yaki zuciyarta ba wata kila ma da ta rasa sukuninta har kowa ya gane halin da take ciki. “Allah sarki dan'uwa mai kaunar yar'uwarsa, duk da fadan nan da kuke da rashin jituwa wannan soyayyar da kaunar tana nan a zuciyarsa, Allah ya kara hada kanku, ya shirya mana” Kowa ya amsa addu'ar da Hajiya Binta ta yi da Ameen ban da Hajiya Kaltume da gume ma ya karye mata kamar wadda aka kwancewa zane a kasuwa. Daga bangaren Hajiya Kaltume Hajiya Binta ta fito ta shiga bangaren Momy suka gaisa sannan ta fito tana jin kewar Iyami. Sai addu'a take ma Appa idan dawowar Iyami alheri ce Allah ya daidaita tsakaninsu, ya kasa amsawa da ameen bayan kuma abun da yake nema kenan a zuciyarsa. Mota daya suka shiga Hurriya bayan ta dauko mayafinta, ita da Hajiya suka zauna a back seat, Appa da Hamad kuma suka shiga gaba, Appa yana jan motar suka fi daga gidan. After mintuna goma da tafiyar Hajiya Binta, Momy ta fito tare da bakuwarta da kuma ɗanta da be ci komai ba a cikin abubuwan da Momy ta saka a shirya musu, Miwan na bayansu tare da dan'uwansa Musib sun yi ma bakuwar Momy da ďanta rakiya ban da Namra da har yanzu tana can bangaren Hajiya Kaltume. “Captain ai yana yawan zuwa nan, duk lokacin da zai zo garin na ba ya tafiya sai ya shigo, ina jindadin haka Wallahi” Hajiya Turai ta yi murmushi. “Ai danki idan yana son mutum to ya huta, Allah ya hada jininku” “Sosai kam, Allah dai ya nuna mana lokacin auren nan mu rakwashe” Cewar Momy, Mutumen da aka ta maganar akansa be ce uffan ba ya fara sauko Entrance din hannu dafe a kirjinsa yana murza a hankali domin ba karamin zafi ya ji ba a lokacin da suka yi karo da Hurriya, taku daya biyu uku hudu yayi kamin ya ja ya tsaya yana kallon yadda tsaddadiyar motarsa ta yi ta kasa gaba daya, saboda tayun motar da aka succe duka hudu. Ya juyo ya kallesu. “Waya taba motar nan?” “Wace motar?” Kusan a tare suka kalli motar Musib yayi sauri sauka ya karasa gurin motar da mamaki. “Lafiya kalau kuka zo da ita?” “Idan bata da lafiya zamu zo da ita ne? What kind of stupid question is this!” “Subhanallahi, garin ya haka ta faru!” Cewar Momy tana saukowa ta nufi gurin motar. Miwan ya ce “Gaskiya wannan succe tayun aka yi” “To waya aikata haka? Wannan dai rainin wayo ne da neman mutum yayi magana ace ya cika masifa” Ya fada da karfi wani karin bacin dai na tunkarosa, cikin bakinciki ya sauka ta isa gurin motar. Momy ta kai hannu ta dafa karjikinsa. “Kwantar da hankalinka Captain, a cikin yaran nan dai wani ba zai yi gigin yi maka haka ba, akwai dai matsalar da aka samu” Momy na rufe Hajiya Turai ta miko masa hannu kamar wani karamin yaro dan yaye. “Captain shigo ka zauna, sai mu shiga wata motar” Ya sauke ajiyar zuciya tare da jan dagon numfashi ya fi sau goma, sannan ya shuri motar da kafarsa da karfi. “Duk wanda yayi min haka da gangan yayi, saboda a bata min rai” “Toh waye zai maka haka Captain? Dan Allah karka bata ranka, na gano, yanzu haka ba zai wuce bakar matar can ba Kaltume, domin na dade da lura da yar bakinciki ce ta karshe” Momy tana maganar tana jin kamar ta yi tsalle taje ta shake wuyan Hajiya Kaltume. “Oh kekam baki zaune cikin mutane kwarai Hajiya Nafisa, rayuwa a gidanku tana da wahala” Momy ta amsawa Hajiya Turai tana kwafa. “Barta na san yadda zan yi maganinta, da ni take zancen, Captain yi hakuri shigo ka huta sai ka dauki motata ku tafi da ita, idan an gyara wannan Musib zai kai maka ita gida” Jameel ya juyo ya nufo hanyar falon, sai duk suka dugunzuma suka biyo bayansa, ban da Hajiya Turai da bata matsa daga inda take tsaye ba tun bayan da suka fito daga falon. Cikin natsuwa da kamala ya shiga falon, sai ka rantse ba shi ne ya gama bacin rai a waje ba, zaunawa yayi ya hade hannayensa ya sadda kai kasa ya rufe ido yana motsa bakinsa a hankali, kokari yake na ganin be bar bacin ransa ya ninku a zuciyarsa ba... [10/20, 6:25 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy 𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣4️⃣ Namra ta dago ta dubi kofar shigowa falon tana amsa sallama, sai ta mike tsaye da sauri tana kallon Captain da mamaki, zuwansa a yanzu ya bata mamaki tsabanin baya da bata mamakin zuwansa domin ya saba zuwa gidan a duk lokacin aiki ya kawo shi ko ziya, tana mamakin zuwansa ne kasa da wata uku da faruwar abun da ya fusata shi, wato fasa masa tayun mota da Hamad yayi suke zaton Hajiya Kaltume ce ta saka aka aikata haka. Ba kasafai yake sake zuwa gurin da aka bata masa rai ba, idan ma zai sake komawa a gurin sai ya dauki lokaci mai tsawo har an manta da shi yake sake zuwa, wannan ya saka duk wani makusancinsa da yake son alaka da shi ta daure ko da iyayensa yake kokarin kiyaye duk wani abu da zai batawa dan gatan Ammy kuma ďa daya tilo ga Alhaji Aliyu Turaki. Wata kila haduwar jinin da Allah ya saka tsakanin Momy da ďan Yayanta ya wuce yayi mata haka. Fuska ba yabo ba fallasa ya shigo falon hannayensa duka biyu suna bayansa. “Sannu da zuwa Ya... Captain” Tunawa da ta yi baya son ace masa Yaya ya saka ta kasa karasa sai ta kiranshi da sunan da kowa yake kiransa. “Yauwa hutawa kike?” “Eh bari na kira Momy tana ciki” Tana juyawa ya dakatar da ita. “No Wait... Ina yarinyar nan take Namra?” Ta juyo tana wara alamar bata fahimce wadda yake tambaya ba. “Wata fara haka mai dan tsayi marar jiki, mai saka glasses” “Oh Hurriya, tana bangaren Hajiya a kirata” Ya daga mata kai, sai ta aje remote din hannunta ta nufi kofar fitar ta fice da sauri, da mamaki da tunanin dalilin kiran Hurriya ta isa bangaren Hajiya Kaltume, sai ta ci karo da Hurriya tana rike da tiyo tana watsawa motar Yasir ruwa, Hamad kuma na ta kada kumfa. “Hurriya” “Uhmm” Ta juyo ta kalleta. “Wai ki zo ana kiranki Captain...” “Waye Captain...?” “Ina wani wadda na ganku tsaye a bakin kofar Momy har na dauko miki glashinki da ya fashe? Kin tuna” Hurriya ta yi shiru ta dan bata fuska, kuma ta kasa amsawa Namra da ta tuna ko ba ta tuna ba. “Wanda ya mareki?” Hamad ya tambaya, Hurriya ta daga masa kai Namra ta zaro ido domin bata saka ran marinta yayi ba, ta san dai akwai abun da yake faruwa. “Au daman marinki yayi? Ikon Allah me kika masa?” “Wucewa na zo yi ban gani ba muka yi karo shi ne ya mare ni har gilashina ya fashe” “Ni kuma na fasa masa tayun mota duk biyu da wuka” Namra ta rufe baki with mamaki. Hurriya ma masa kallon rashin jindadi fadar da yayi a yanzu. “Daman kai ka fasa tayun nan? An kusan yaki a gidan nan fa saboda an fasa tayun Captain, Allah ya tsare ka Momy bata sani ba, da sai ka zama abun tausayi” “Ni ina ruwana” Ya fada yana turo baki. “Captain akwai zafin zuciya ko shi zai iya maka hukunci babu ruwansa da alakarka a gidan nan, to yanzu dai shi ya ce a kiraki” Hurriya ta ake tiyon kasa ta nufi fanfon ta kashe sannan ta bi bayan Namra, Hamad kuma ya cire hannayensa daga cikin kumfan da yake kadawa ya bi bayan Hurriya. Ita dai bata san ta masa laifi a yanzu ba balle ta yi zaton mari ne ko cin mutumci, sai idan kuma cewa za'ayi ta haifar masa da ciwon kirji saboda kanta ya bugi kirjinsa. Namra ce ta fara shiga sannan Hurriya sai kuma Hamad dake bayanta. Yana tsaye a gurin da Namra ta barshi sai dai wannan karon gefen kujerar da Namra ta tashi yake kallo ma'ana kofar falon ta koma gefensa na dama sabanin dazun da ya bata baya. “Gata nan” Namra ta fada, sannan ta zauna Hurriya ta karaso inda yake ta tsaya gabansa ta kalleshi sau daya ta sauke kai kasa, Hamad kuma yake tsaye kusa da kofar falon yana kallon ya ga abun da za'ayi ma yar'uwarsa. Captain ya maido ta hannayensa gaba ya mika mata box din da ke hannunsa da hannunsa na dama ba tare da ya ce komai ba. Ko be fada mata ba, ta san box din glasse ne domin shi dabam yake ta ka ganshi kana ganewa balle kuma ita da take 5&6 da glass. A hankali ta dago ta kalli fuskarsa bayan ta kalli gilashin sannan ta kalli Hamad ya watsa mata harara duk ya bi ya bata rai, domin har yanzu haushi Captain din yake ba shi, daman kuma shi be iya tsana ba idan ya tsane ka sai Allah ke kasa ku sake shiri da shi. Captain ya karkarata da kansa kadan ya kalli Hamad da sai a lokacin da ya san da shi tsaye a gurin sai kuma ya kalli Hurriya. Ita ma ta kalleshi ta dauke kai ta nufi kofar fita daga falon ba tare da ta ce masa Komai ba balle kuma har ta karba, sai da ta fara ficewa sannan Hamad ya bi bayanta yaja kofar falon ya rufe. Captain ya matse box din gilashin dake hannunsa da mugun karfi ya daga kansa sama ya rufe ido. “Allah ya sassauta min kar na kashe yarinyar nan....” ‘Tab ka kasheta Wallahi kai ma sai an kashe ta dan gata be fi gata ba, ita ma yar gatan banbanta ce’ Namra ta fada a ranta a fili kuma sai ta ce. “Glasse ne?” Ya sauke kan ya kalleta. “Wuka ce” “Gilashin da Appa yake siya mata mai kyau ne daga waje ake kawo mata” Ta fada a zahiri a badini kuma sai ta ce. ‘Captain dai kamar ka fi kowa iya bakar magana’ Kamar ta san zai kara mata. “Wannan a bula na dauko shi” “Tambaya ce kawai, daman ai na san Hamad ba zai bari ta karba ba, amman ka ba ni zan bata hakuri sai na bata daga baya” Ya kai dayan hannunsa yana zagayen gilashin da shi. “Waye Hamad?” “Kanenta ne wanda ka ga ya tsaya jikin kofa har ta kalleshi, shi ne ya fasa maka tayun mota saboda ka mareta, ni ma ban sani ba sai yanzu yake fada” Murmushi yayi mai sauti, ya dago ya kalleta ya sake yin murmushi mai cike da mamaki. “Wow... Nice...” “Haka ya kamata dan'uwa ya zama, mai kokarin kare yan'uwansa i like him” Ya fada after yayi taking few seconds yana kallon wani bangare na falon, because he know yayi missing wani part na shi da be taba samu ba, wato yan'uwa da suka hada uwa ko uba ko ma uwa da uban gaba daya. “Amman haka ba zai hana a hukunta shi ba, they have to pay for what they did” Ya juya ya fice daga falon ba tare da ya nemi a kira masa Momy ba, daman kuma ba dan ita ya zo ba wannan karon, ya zo ne domin baya Hurriya gilashin da ya siyo Saudiya saboda ya fasa nata, and that slap da yayi mata ya tsaya masa after ya bar gidan saboda lura da yayi da bata gani sai da gilashin kamar yadda Namra ta tabbatar masa tun a wacan ranar. Namra ta san me yake nufi they instead of he, wato Hurriya saboda ta ki karbar gilashin Hamad kuma saboda ya fasa masa tayun mota. Sai da ta leka ta ga tashin motarsa sannan ta saki curtains din tana fadin. “Ban da kai Captain ana kyauta dole ne, ko ni ce ai ba zan karba ba, ka yi zafin hannu ba wani uzuri da an maka abu sai zafin zuciya” Ta nufi upstairs, sai da ta fara leka dakin Momy ta ga har lokacin bachi take sai ta ja mata kofar a hankali ta nufi dakinta. HAJIYA KALTUME POV. “Yanzu kina da number Salame?” “Eh ina da ita, ai ko shekaran jiya ta zo gidan nan, har take min zancen Malamin ni dai ban tanka ta ba, domin damuwata ta isheni kar na yi abun kunya” “Kunya Hajiya fatee? Tofar da yawu, har abada ba zamu taba kunyar duniya ba lahirar ma muna fatan nasara, saka number ki kirata ki ce ta turo miki number Malamin ko kuma idan ta samu lokaci ta shigo sai ku yi magana” Hajiya Kaltume na rufe baki Hajja Fatee ta dauki waya ta shiga laleben number Salame. Knocking aka yi har sau biyu sannan Hajiya Fatee ta amsa. “Waye?” “Hajiya Yaron nan ne ya sake dawowa fa, kuma mai Baba mai gadi ya ce yayi yayi da shi amman ya ki tafiya shi sai ya ganki” Hajiya Fatee ta hanye wayar ta rafka tagumi. “Oh wannan fitinanne yaro ba zai bar ni da abun da ya ishe ni ba” “Waye haka?” “Wallahi wani yaro ne na dauka aikin ba fulawa ruwa, ashe barawo, ni ban sani ba, irin yaran nan yan sare sare, wata rana suka zo nemansa har da fasa mana gida aka ayi, tun daga lokacin sai na sallame shi, amman yaron nan ya ki ya rabu da ni, duk lokacin da wani abun ya same shi sai ya zo ya fada ko mai dadi ko marar dadi, ko kuma ya ce ya zo gaishe ni, yanzu ya bi ya fitine ni yau sati biyu kullum sai ya zo wai mahaifiyarsa bata da lafiya ni yake son gani” “Ikon Allah toh ke Hajiya irin wadannan yaran ai suna da amfani wata rana” “Hmmm baki san yadda suke fitinar mutum ba ne, ga su da shegen na ci idan sun ga samu” “Bari na yi magana da shi, ki kira Salame yanzu” Hajiya Kaltume ta mike tsaye tabur tabur ta fice daga dakin, Hajiya Fatee kuma ta shiga kiran Salame da wayarta. “Ina yake?” Hajiya Kaltume ta tambayi one of masu yi ma Hajiya Fatee aiki da ta zo sanar da Hajiya. “Yana can gate” “Muje na ganshi” Mai aikin ta wuce gaba Hajiya ta sauko tana bin bayanta har suka fita falon suka isa gate ta tambayi mai gadin ina yake. “Yana waje Hajiya kullum sai ya zo kuma ita Hajiya ta ce kar a barshi ya shigo” Ya bude mata karamar kofar gate din ta leka waje ta ganshi zaune daf da gate din, a take gabanta ya yanke ya fadi domin ya tuna mata da lokacin da suke cikin daji hannun yan ta'adda, ga fuskarsa duk tambo alamar ya sha sara har ya gaji, bakinsa baki kirin ido kamar an daka tarugu tsabar ja, jiki a murda kamar gashin kansa, kana ganinsa ka ga rikakken dan ta'adda. “Kai ne kake neman Hajiya Fatee?” Hajiya Kaltume ta tambaya cikin karfi hali domin zuciyarta har wani zillo take. “Ni ne Allah ya taimakeki, Hajiya Wallahi ina cikin matsala ne, su kuma wadan nan watsatsin masu aikin kullum na zo sai su hana ni shiga, ba dan ina ganin mutumcin Hajiya Fatee ba da yanzu na farka cikin mai gadin nan Wallahi, sai dai Hajiya tana da kima a idona kamar uwa take a gurina ba zan iya haka ba” Magana yake da irin muryar mazan nan da shaye shaye ya gama canja kalar muryarsu ta koma mai ban tsoro. Hajiya Kaltume ta yi murmushin karfin hali. “Ka kyauta haka ake so ai, ya sunan ka?” “Sunana Isiyaku, amman dai wasu kan ce min Danja yan sunanayen nan dai na zamani Hajiya” “Toh Amman me kake so gurin Hajiya?” A take ya fara kuka kamar wani yaro ko wawa kukan da babu hawaye sai zallar iskanci. “Hajiya Gyatuma aka kwatar a asibiti, kuma ba ni da ko sisin na magani, ita Hajiya Fatee ta sani ba na wani aiki bana sana'ar komai tun da na bar gidan nan ban sake samun wani aikin ba, ina cikin matsala bana da gata sai Allah sai Hajiya Fatee so nake ta taimaka min da kudin magani, kar gyatuma ta mutu Wallahi Allah akwai matsala idan ta mutu ba a taimaka min ba, duk mai hannu a ciki sai na ci uwatar...” Yana fada yana hada hannu biyu ya buga, Hajiya Kaltume ta dan ja baya sannan ta kalli mai aikin ta ce. “Zaki iya tafiya” Sai da mai aikin ta yi nisa sannan ta taka kafarta ta fito daga cikin gidan ta taka nesa da gate din yadda mai gadin ba zai ji abun da zata fada ba. Sannan ta tsaya ta kalli Danja ta ce. “Nawa ne kudin maganin?” “Toh Hajiya dubu talatin ne, amman dai ko dubu biyu ko biyar aka taimaka min da su duk taimako ne” “Kana da account” “Akwai account Hajiya amman bana da shi aka Wallahi, kwanyar ce mun sha miyar kuka, daddawa duk ta kwashe basirar, tuwon dawa ma haka ake baza mana shi a ture, kai mun ci wuya Wallahi ga talaucin nan har yanzu be bar mu ba” Hajiya Kaltume ta yi dariya har lokacin tsoro be fice ta ba, domin muryarsa ma abar tsoro ce balle kuma ka kalleshi. “Kana da waya?” Ya dan sosa kansa ya shafa aljihu. “Wayar ce Hajiya ko an siya idan ka ji eh ya ne tana damun cikinka dole mu siyar mu siye abinci, line ma dari da hansi na siyar da shi shekaranjiya” “Toh yanzu idan ina son magana da kai za mu yi kenan?” “Ki fada min gidanki kawai zan zo na sameki har dakinki” “Aa ni da Hajiya Fatee duk ba mu gama warkewa daga damuwar da muka shiga ba, baka san yan ta'adda suka kama mu ba?” “Kai na ji Hajiya, zuwana talatin gidan nan sai ace min bata nan, wai wasu ne suka kamata, da an fada min ba za a biya sisi ba zan karbota ni sai a ba ni kudin, akwai mutanenmu fa masu harkar kuma ni Wallahi jan wuya ne, bana inda bana iya shiga, karfe be fasa ni bundiga bata kama ni sai dai ayi min tambo, danjar nan da kika ji ance Hajiya ni fa danja ne, uban fitina kuma bana tsoron kowa” “Kai zaka iya aikata komai kenan Danja?” “Zan iya komai Hajiya mun zubar da hannaye mun cire kafa, rai ma mun wulgar da shi barzahu, Allah dai ya shirya mu kawai” “Shiyasa Hajiya take tsoron ka, ni ma ina gudun na janyo ka jiki na jawa kaina matsala” “Kai... Kuturi” Ya rike baki. “Wai Hajja Fatee tsorona take? Ita din ai uwa ce ba za a mata komai ba, wani ma be isa ya mata ba balle kuma ni, ba dan ita ba da yanzu na barar da hanjin masu aikin nan nata, alkur'ane da yanzu ka ga hanta ya lilo shushushushushuuuuuuu” Ya nuna yadda hantar zata rika raea idan ya sareta. “Toh yanzu dai zan shiga gida, zan aiko mai aiki da number wayata idan ka samu waya sai ka kira ni mu yi magana, amman dan Allah ka daina damun Hajiya Fatee da yawan zuwa” “An gama amman Hajiya yanzu akwai wani abu nan? Ina fatar ke ma kina da yan abubuwa yan timatinmai eh... Eh.. Kin dai gane” “Zan aiko mai number tare da kudin da zaka hau babur ka koma” Tana fadin haka ta yi gaba tana nufi gate zata koma ciki, shi kuma ya bita da kirari yana daga mata hannu. “Chau chau chau chachachau lafiya lau ne Hajiya, Allah dai ya kara miki kwanciyar hankali ya kara miki ƙiba kai kana ganin Hajiyar nan ka san akwai manyan kaya, Allah ya kara sutura” Cikin gidan Hajiya Kaltume ta koma ta shiga dakin Hajiya Fatee ta samu biro ta mikawa Hajiya Fatee domin ita bata iya rubutun ba. “Rubuta masa number ta a nan” “Numberki kuma? Me ya faru? Karki jawa kanki matsala fa irin wadannan ba su jin magana” “Ke dai rubuta babu komai, ke na ke yi ma jihadin ai, wayo yake masa” Hajiya Fatee ta karba ta rubuta mata number ta mika mata. Hajiya Kaltume ta bude jakarta ta dauko 3k ta hade ta takardar ta fita falo ta bawa mai aikin ta umarce ta da ta kai masa. Sannan ta juyo ta dawo dakin tana tambayar Hajiya Fatee ya aka karkare da Salame. “Na kirata na mata bayani, ta ce ai ya canja line saboda rufe masa wacan da masu gidan line suka yi, amman yanzu zata turo min sabuwa numbersa kuma zata kira ta masa bayani” “Haka nake son ji, to yanzu ki kwnatar da hankali ki kira ki fada masa ya shirya komai na sa ya zo garin nan zamu aika da mota a dauko shi a kawo mana har gida, daga nan sai mu gabatar masa da matsakarmu” “Amman kina ganin zai yarda ya zo?” “Hajiya Fatee miye kudi ba zai yi ba? Muradi dai abashi kudi shi kuma ya biya mana bukata kawai” “Ni dai Allah yasa cikin nan ya tausu, idan ba haka na zan shiga uku ga shegiyar suruka zata ji dadi” “Komai zai wuce Hajiya Fatee ki kwanatar da hankali” Cewar Hajiya Kaltume ga aminiyarta tana murmushi. IYAMI POV. . “Iyami ba a zama haka, ke kanki kin san mijinki yana sonki, ga yaya yanzu kuma ga cikin nan da kika shiga watan haihuwa, kamata yayi ki nemi taimako idan ma wani asirin aka yi masa aka rabaku a karya shi, ki koma dakinki bana son ki haihu a gida Wallahi” Amma ta yunkura da katon cikinta ta tashi zaune daker tana kallon Hindu dake maganar. “Hindu, Wallahi ban taba yi ba, su kansu da suke ganin kamar asiri na yi ma Alhaji yake ta so na ko na malleke shi, ban taba bada naira biyar na ce a mallake min Alhaji ba, tsantsar biyayya ne kawai da kawar da kai da kuma jin maganar duk abun da ya fada, ni yanzu ko zaki dora wuka a wuyana ba zan iya fada miki sunan Malami daya da na sani ba a garin nan, ban taba yi ba, Gwaggo ma bata taba ta yi ba mu ba mu da kowa sai Allah” “Na sani, to ai tambaya ake kin ga har na tsarin jikinki sai ki sha kuma ki bawa yayanki, domin su ma ba barinsu zata yi ba” “Ni dai ba zan iya ba, na kai kukana ga Allah shi zai min magana, ko yanzu ai ba yadda suke so suka samu ba, duk wata sai ya aiko min da abinci da kudi saboda cikin nan, yanzu kuma kina ganin yadda aka cika harabar gidan nan da itace saboda na shiga watan haihuwar, na san idan ra'ayinsu za a bi ba zasu so haka ba, yarana kuma idan ya auna lokaci ya kan aiko da su su gan ni na gansu, an rabu ne kawai amman kamar ana tare, idan Allah yayi zan koma sai ki ga na koma kamar yadda ban saka ran auren Alhaji ba Allah yayi kuma aka yi auren” “Toh Allah yasa haka shi ya fi alheri, amman dai da kin tafi ba a san inda za a dace ba” “Allah ya hada mu da dacewar” “Ameen” Ta amsa ba dan ta jidadin yadda Iyami ta ki amincewa da zuwan ba. [10/20, 6:26 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆                   𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy 𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣5️⃣ Salame na turo number Malamin Hajiya Fatee ta kira shi a waya, suka gaisa ta fada masa abubuwan da suka faru ya jajanta mata, ya kara mata da cewar shi ma layinsa aka rufe shiyasa bata ji shi ba. Hajiya Kaltume ya karba suka gaisa sannan ta dora masa da banin abun da ya sami Hajiya Fatee, daga karshe suka yanke ranar da zai shigo garin. Sannan Hajiya Fatee ta iya fita dakinta ta samu ruwan tea ta sha domin bata iya cin komai. Hajiya Katume bata jima a gidan ba Fadeel ya shigo gaishe da mahaifiyar, da zai fita Hajiya Kaltume ta bukaci ya sauke ta gida. *** *** *** Ba kadan ran Momy ya ba ce ba, jin cewar Captain ya zo gidan tana bachi, kuma ya fita da bacin rai saboda Hurriya. “Oh to wai miye na siya mata gilashin ma?” Namra ta aje spoon din hannunta. “To nidai ranar da ya zo last na ganta da shi cirko cirko, gilashinta a kasa tana lalabe to shi ne yau take fada min ai marinta yayi saboda sun yi karo” “Ai gara da mareta ma, yarinyar nan bata da hankali, sannan yanzu ya zo ta ki ta karbi box din wata kila ba zai sake dawowa gidan nan ba kuma, ta ja min ya fara fushi da ni kenan” “Shi ma fa Captain din nan ya cika zuciya ga zafin hannu, amman dai bata kyauta ba da bata karba ba” “Bar yar iska bata san su waye iyayensa ba ne shiyasa, shi ma dai miye na kawo mata glass ko makancewa ta yi iya ruwansa” “Kila ya ga be kyauta ba, ko kuma...” Momy ta kalleta da duba kyama. “Ko kuma me? Allah ya kiyaye ai ko mata sun kare duniya Captain ba zai yi komai da wannan yar tatsitsiyar yarinyar na duka ma nawa take shekaranjiya ta yi 16yrs fa, kuma shi da yake da matar da zai aura” “Toh ba sai idan anyi auren ba, wannan me bakar zuciyar? Ba kowa ce zata iya zama da shi ba” “Ai ko fasawa aka yi sai dai ya aureki, daman Hajiya Turai ta so a hada wannan zumunci shi din ne ya ki, kuma kin san basa masa dole ” “Ni” Namra ta nuna kanta domin bata taba jin makamacin haka daga bakin Momy ba. “Ke fa mun sha yin maganar da Hajiya Turai ai, amman shi Jameel din ne be yarda ba, yanzu dai ya samu wadda yake so an huta” Namra bata ce komai ba ta maida idonta kan abincin da take ci tana motsa shi a hankali kamar mai tunani. Momy kuma ta tashi daga dinning din tana ta masifa saboda Namra bata tasheta daga bacci ba. “Kiransa zan yi yanzu Allah yasa ya daga, kar wannan yar filfilwar ta jazamin masifa ni Nafisa” Nan ma Namra bata ce komai b ta cigaba da motsa abinci tana tauna wanda yake bakinta ta kasa hadewa sai tunani take. Kamin ta juyo ta kalli falon da aka bude, Hurriya ce ta shigo kanta ba dankwali rabin kan nata a tsire. “Yi sauri ki dauki abun da zaki dauka ki fice kamin Momy ta fito, dan na san sai ta miki fadan kin karbar box din da Captain ya baki” “Abinci zan zuba” Ta nuna abinci tana kallon stairs gabanta sai tsananta faduwa yake. “Zo ki zuba” Ta nufi dinning din da sauri ta dauki plate ta zuba abincin mutum biyu ita da Hamad ta saka naman kaza a sama ta dauki spoon biyu ta saka. “Ke da Hamad zaku ci?” “Eh” “Dazun shi ya hana ki karbar glass din ko?” “Na ga ya bata rai yana hararata, na san idan na karna zai iya min masifa kuma yayi fada ni, ko ya dukeni” “Ke dai Hamad ya raina ki ya maida ke kamar kanwarsa, ko dan ya ganshi babba ke kuma ba ki ba” Hurriya ta yi dariya mai sauti ta shiga Kitchen ta dauko tray ta dora ruwa da lemu a kai sannan ta fito ta dauki plate din abincin ta dora a tray ta dauka ta fice da sauri. A harabar Apartment din Hajiya Kaltume ta dawo ta zauna a balcony kusa da Hamad ta aje tray. “Hamad zo mu ci abinci” Ya kalli abinci sai ya bata rai. “Waya ce ki hade? Waye zai ci abinci da ke to?” “To ai ni ina sauri ne, Yaya Namra ta ce Momy nemana take zata min fada saboda ban karbi abun da bakonta ya ba ni ba” “Toh ina ruwana ki je ki zuba wani” Ya saka hannu ya dauke abincin da ba zai iya cinyewa shi kadai ba ta dora a cinyarsa. “Idan ba zaka ci da ni ba, ba sai ka je ka debo na ka ba?” “Ba zan ce ba, ni ki daina ba ni umarni” “Wannan dai nawa ne ka ba ni abinci na Hamad” Yayi mata kunne ne shege yana ta cin abinci ko kallonta be yi ba. Har ta tashi zata tafi debar wani sai kuma wata zuciyar tace mata Momy na nan falo, sai ta koma ta zauna ta dauki lemun ta sha tana ta kallonsa yana cin abinci. Ita ma dai kamar mantawa ta yi Hamad be cin abinci da kowa kuma be cin ragin kowa har da na Appansa da na Amma. Hakura ta yi ta saka masa ido ta can kuma ta ji ba zata iya ba tunawa da ta yi baya son gashi idan yana cin abinci sai ta cigaba da sifar kan tana kallonsa wai ko zai ji kyama ya aje abinci. Instead of yayi haka sai ya kifar da plate din ya riko gashin kan nata a daidai lokacin da Mota ta faka harabar Hajiya Kaltume. Da wani irin karfi yake fisgar gashi da karfi bata san lokacin da ta fara ihu tana rike hannunsa ba. Da sauri Fadeel ya bude motar be ko tsaya kashewa ba ya fito ya nufi inda suke daker ya banbanre hannun Hamad Hurriya ta koma bayansa da sauri tana kuka. “Kai wannan ai sai ka tsinke mata gashin ka rage mata sadaki, miya hada ku?” Hurriya bata iya magana saboda kuka, Hamad kuma ba gwanin maida magana ba ne daman sai cika yake kamar wani zaki. Hajiya Kaltume tana kawowa kusa da su ta ce “Ai haka suke, uwa daya uba daya amman baya raga mata, basa zaman lafiya kamar Annabi da Kahiri suke” Cikin mamaki Fadeel ya kalli Hamad. “Wai kanwarsa ce yake mata wannan jan gashi haka?” “Ita ce yayar ai, dan ka ganshi da girma shi ne kanen ai, baya ragawa kowa a gidan” Hamad ya juyo yana watsawa hara Hajiya Kaltume dake korawa Fadeel bayani saboda ta tabo shi tun da ta ce be ragama kowa. “Idan ba kai ba, wake fada da mata? Ba yayarka ba ce?” Ya juyo ya kalli Hurriya da ta boya bayansa. “Ke kuma ki rika kiyaye, yi hakuri ki daina zama babu dankwali ba kyau” “Ai Allah yasa ma aljannu da ifiritai da shaidan duk su tattara su shige a cikin kan nata, ita ma ai ba karamar marar jin magana ba ce” Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume dake fadar haka tare da yin gaba da bar su a gurin. Ta share hawayenta ta kalli Hamad sannan ta kalli Fadeel. “Ina wuni” Dariya yayi. “Lafiya Kalau, Allah ya tsare gaba Hurera ko?” “Hurriya” Ta gyara masa. “Yeah ki rufe kanki” “Toh” Ya juya ta sauka balcony din ya nufi motarsa dake kunne har lokacin sai da ya shiga motar daga mata hannu sai kallonta yake sannan yayi reverse ya fice. Two Week Later.... Hajiya Fatee ta gyara zama ta kalli kawarta kamin ta kalli Malamin da suka sauka a garage din gidan. “To yanzu Malam akwai yadda za'ayi a danne cikin nan kar ya bayyana? Kuma wannan tofe tofen yawun da kin cin abinci da nake ga kasala duk na daina shi?” Malamin dake sanye da babbar riga ya kalli Hajiya Fatee yana murmushi. “Za'a iya sosai kowa, ba yau na saba ba, za a iya danne cikin nan har tsawon shekarun da kike so” “Alhamdulillah, ina son a danne min shi har nan da shekara dari, na san dai ba zan yi shekara dari a duniya ba” “Ko kuma nan da lokacin da zaki yi aure ba, Hajiya yadda kike da surar nan Maa Shaa Allah, ai sai idan mutum be samu dama ba, shekarunki ba ba za a ce kin yi ba, ai na san ba za a rasa namema ba ko?” Maganar yake yana dariya kamar wata abokiyar wasarsa. “Aa kai aure kuma? Wake ta aure yanzu? Aa mun bar wa yara, ni dai yanzu bukatata a fara danne cikinki, idan an samu nasara hakan yayi sai a shiga yi Farraqu tsakanin yaron nan Fadeel da Matarsa Afrah domin ina kwana da bakincikinta a kullum Wallahi” .“Babu Matsala Hajiya, za a danne ciki, matukar ba a daga dutsen da zamu saka layar mu rufe ba, cikin nan ba zai taba tashi ba har abada, amman fa zaki zuba kudi kam” “Karka damu zan biya ka ko nawa ne, ammam dan Allah a saka dutsen a inda ba za a iya dagawa ba” “Aljannu za mu saka su yi aikin, karki damu” Hajiya Fatee ta kalli Kaltume suka yi murmushin jindadi sannan Hajiya Kaltume ta kora da nata bayanin. “To ni Malam na ji shiru, kasan na baka kudi akan za ayi ma Iyami aiki ina son komai nata ya lalace amman har yanzu ba labari, kuma ni yanzu so nake a mallake min kowa a gidan nan daga mijina har Nafisa ikon kowa ya dawo karkashina, ina son Alhaji ya zama be iya aiwatar da komai sai abun da na fada masa, kuma ina son a shiga tsakaninsa da yaran nan, ya maida su banza a cire masa su a rai, ya ji baya bukatar ganinsu ma, domin na ji yana zancen fitar da su waje karatu, kuma ko be fitar da su ba, ita wannan da take da kokari na san gwanati ko wasu za su iya kaita waje karatu, so nake a lalata karatun nata, kai ni duk wani abu da zai saka Iyami farinciki bana sonshi a toshe komai Malam” “Hajiya, aiki ai mun aiwatar jefa muka mata kuma yana nan yana tafiya kin san jifa wani lokacin tana dauka lokaci kamin ta isa, amman kuma da zarar ta isa zaki sha mamaki ba dan karami ba, sai kin tabbatar da ba ki min biyan banza ba, mijinki kuma zaki mallake shi a hannu, sai dai wannan Nafisa kishiyar taki fitinanniyar mace ce akwai yan ƙwanƙwanmai a kanta, kin san mai yawan masifa da mai addu'a asiri be cika saurin kama su ba, amman zamu gwada” “A gwada Malam zan biya ko nawa ne karka ji haufi” Malam ya san washe baki. “To Mallada ai mu haka muke so” Hajiya Fatee ta ce. “Toh ni Malam ya za'ayi na gane idan cikin ya dannu?” “Idan na yi aiki, zaki ji motsi sosai a cikinki idan motsin be daina ba har safe, to cikin ne dannu ba wata kila sai mun sake yi, idan kuma kin ji motsin kadan to aiki yayi kuma zaki daina duk wasu dabi'u da kike na masu ciki, cikin kwana biyu” “Alhamdulillah, ni da zaka cire cikin ma ni ka dauki cikin na bar maka, ko ina da aure me zan yi da mugun iri? Balle kuma an kwana biyu har na kai ga jikoki” “Komai zai wuce Hajiya karki samu damuwa” A ranar da farinciki Hajiya Kaltume ta dawo gida, saboda ta samu fadawa bokanta abun da take so kuma ya tabbatar mata da zai iya. Wani karin abun farincikin ma sai da babbar yarta Mace mai bin Yasir wato Umm Kaltoon da ake ma inkiya da Maamata saboda sunan Hajiya Kaltume mata albishir da mai cewar mai son ta zai zo ya gaishe da Hajiya da Appanta sai Hajiya ta rasa ina zata saka kanta dan dadi, daga ita har Hajiya Fatee sun kwana da farinciki a daren kowa da bukatarsa da kuma burinsa, Hajiya Fatee bata da burin da ya wuce a danne cikin nan kuma a raba Fadeel da matarsa Afrah saboda ta tsokane mata ido. Washe gari... A tare da Hamad Hurriya ta fito bangaren Momy da far'arta tana hira da Hamad, kai ka rantse ba sa fada da juna labari take ba shi na wata class mate dinta da ya sani sai dariya yake. Sai da suka fara zuwa gurin Appa suka karbi na na su lemun da Chocolate Hurriya ta masa godiya, sannan suka nufi box din dake kai su makaranta suka shiga. A makarantar ma sai suka wuni kamar ba su ba, daman tare suke breakfast amman kowa da abincinsa dabam, a ranar duk abun da Hamad ya siya sai ya iskota har cikin ajinsu ya bata, kasancewar ajin maza dabam na mata dabam. Misalin karfe daya da rabi suka tashi suka tafi Masallaci suka yi sallah sannan suka tsaya jiran direbansu dake zuwa karfe biyu daukarsu gaba dayansu yan gidan. Biyu da mintuna ya iso suka shiga box Hurriya tana can baya Hamad kuma yana a inda ya saba zama, wato front seat babu mai zama a gurin sai shi kuma baya zama da kowa sai shi kadai. Kilometers kadan ne tsakaninsu da Family house dinsu wata bakar motar ta shiga gabansu ta tara musu har sai da direbansu ya tsaya gashi gurin babu mota ni motoci ma ba kasafai fa, shi ma direban yana biyo hanyar ne saboda ta fi saurin kawo su gida. “Malam baka gani ne?” Ya fada cikin tsawa ganin yadda yake masa ganganci kamar ba akan titi suke ba. Bude motar aka yi wasu maza hudu suka fito fuskarsu a rufe biyu daga cikinsu na rike da bindiga suka bude ma direban da tuni ya fara salati ya fito Hamad ma ya bude ya fito jikinsa na rawa suka sa ya zagayo gurin direban sannan suka bude gambun bus din. “Kowa ya fito” Kowa ya fito cikinsu na rawa suna ihu. “Ku yi shiru ko na halbe mutum yanzu” Dayan ya fada sannan biyun da ba sa rike da makami suka iso gurin dayan ya rika Hurriya dayan kuma ya rika Ruma suka fara jansu zuwa motar. Hamad ya fashe da kuka sosai yayi saurin riko Hijabin Hurriya da ita ma kukan take, kamin ta kai bakinta ta gantsawa wanda ya rike mugun cizo a hannu, aiko ba shiri ya sake ta sai ta ranta ana kare, abun ka da marar jiki kamin dayan ya rikota ta yi nisa, sai yayi wuf ya cafke Hamad dake kokarin guduwa, suka dauke shi tare da Ruma sai motarsu. Suka shiga da sauri suka fisgi motar sannan Salma da Khairi suka fara ihu tare da Namra suna kuka, Hurriya kam tun da ta sa gaba bata dawo ba sai da direban ya wasu mutane da suka tsaya bayan bata garin sun gudu suka bi sawunta, sai suka same ta tsakanin wani gida da kwararo ta duke a gurin ta runtse idon ta saka hannayensa ta danne kunnuwanta. “Hurriya” Ta razana ta bude ido jikinta da zuciyarta na rawa, gilashinta ya fadi gurin gudun da dake, shiga kwararon ma da ganinta dishe-dishe ta shiga lalabe ya taimka mata, shi ne silar tsayarwa a gurin ma, domin da tana ganin hanya da kyau ba zata kusa ba guduwa zata yi. Jin muryar direbansu ne ya saka ta fashe da kuka, tana lalabensa shi ya rikota yana matsar kwalla suka fito gurin. Kin yarda ta yi su koma gurin saboda tsoro sai da direban ya janyo motar ya kawo gurin sannan ta yarda zata shiga. “Ina Hamad?” Ta tambaya yana taimaka mata ta hau bus din har lokacin kowa kuka yake, ita kuwa bata ji kukan dan'uwanta ba kuma bata ji muryarsa ba. “Sun tafi da shi” A take ta saki hannun direban ta yi shiruuuuu kamin ta fara haki. “Wayyo Allah na Hamad” Ta dora hannu akai ta fadi a gurin ta fashe da kuka mai karfi. ______________________ Masu karatu shin suwaye wadannan mutanen da suka dauki Hamad? Me suke so? Za su dawo da shi ko kuma yaya? Anya Hajiya Kaltume da Hajiya Fatee za su nasara akan kudurinsu? Wai ni kam me Afrah ta yi ma Hajiya Fatee ne ta tsane ta har take neman raba aurenta da danta? Anya ana samun uwar mijin dake neman raba auren danta ta hanyar asiri? Anya asirin da Hajiya Kaltume ta saka aka yi ma Iyami akan karta sake aure zai yi kuwa? Amma zata dawo gidan mijinta Appa ko kuma wani auren zata yi ko kuma dai ba zata auru ba kamar yadda Hajiya Kaltume take fata? Waye wannan Captain din? Waye Wannan Fadeel din? Anya Momy zata daina halinta na kyamar Iyami da yayanta kuwa? Akwai tsabtataciyar Soyayya a cikin littafin mai taba zuciya ta zauna a ruhi, ku dai kun san ba mu fara komai ba. Kuma da yardar Allah ba zan ba ku kunya ba. 😀 Duk amsoshin wannan tambayar tana nan ƙumshe a cikin littafi na biyu da zamu fara ranar Litanin mai zuwa In Sha Allah. Sai dai shi Book two din ba free ba ne na kudi akan 500 only. If you want subscribe biya 500 to 2451879008 Zenith Bank Hadiza Abubakar Sai ku turo shaidar biyan ta wannan number 08036126660 Ƴan Nijar kuma za su turo katin Zain ko Orange na 500 ta wannan number 08036126660. Za ku iya bibiyar Litfafin nan a Arewabooks ga wadanda basa ra'ayin karantawa a Whatsapp. A username dina @khadeejacandy ko kuma ku yi searching book din Hurriya. Sai mun hada ku a Paid Group Real Masoya masu Patronizing dina a ko da yaushe.🥰 Ku huta lafiya, Allah ya bawa masu niyar siya kudin biya. 🤲