بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* 🔥BAJININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Bismillah Rahmanir Rahim Allah kayi dad in tsira da aminci ga shugabanmu jagaba fiyayye annabi muhammadu S A W tareda dukan ahalin gidan sa da sa habbansa baki d'aya Wannan shafin naku ne JININA ABDU WAHAB ABDULAZIZ TARE DA ADAMU ABDULAZIZ Ina matuk'ar farin cikin tayaku murnan k'aruwan yara maza da kukayi Ahmad Adam da muhamma Sani Abdul WAHAB Allah ya albarkaci rayuwar su yasa cikon addinin musluncine Amin Page 1 "Ke Maryam naji wata ’yar matashiyar budurwa tana kira cikin muryar rad'a" da sauri naga yarinyar da aka kira da Maryam ta waigo fatabarakallahu asanulkalik'in shine abinda na fad'a lokacin da idanuna suka arba da zankad'ed'iyar kuma matashiyar budurwar aka kira da MARYAM wani shegen murmushi tasaki tace "ba saikin fad'aba Halima nasan abinda yasa kike wannan kiran sai kace makauniya' a d'an dame Halima tace "kinsan halin wannan bros d'in nakifa baida mutunci yanzun saiya b'ata mana shiri" Wani d'an iskan kallo Maryam ta sakarwa Halima tace "ke ya dama ni kam banga wanda ya isa hanani abinda naga damar yiba uwata da ubana basu ta kuraniba sai wani can daban, kinga malama aje acigaba da shirya wajen ayi yadda zamufita kunyar abokanmu" kai kawai Halima ta jinjina batare da ta ce komai ba domin tasan halin Maryam da shegen taurin kai idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya juyata sai YAYA MUHAMMAD daya daneta ya shanye a taurin kai gashi bala e en sojan dana k'asansa suke masifar tsoronsa gashi miskili ne shi na gaban kwantace inba ta k'ureba zai wuya kajishi yana yawan magana hatta abokansa da abokan aikinsa sun saba da halinsa sau tari da ido yake basu umarnin abinda zasuyi kuma su aikata domin sun riga sun saba da halinsa. Ta juya kenan zata gidan su anwar wani mate d'inta ne yayansu yana d'inki to duk kayan da zata buk'ata shi tabama d'inkinsu, saiga Nasser ya k'araso da gudu yace "Adda Maryam kizo inji Ammyna" wata shegiyar harara ta galla masa tace "kaje kace tazo tajani bazan zoba inkuma zata iya tazo tajani" Shima hararan ya maida mata dan babu ragayya a tsakaninsu ko kad'an yace "kada Allah yasa kizo d'in banza wacce batasan darajan nagaba da itaba" Cikin b'acin rai tayi Kansa tace kai dan uwarka ni kake zagi?" "Anzage kin ni uwata sa ar wasanki ce da zaki zauna kina aikena da wannan banzayen zantukan?" Kansa tayi da nufin mammake shi ya d'ebi sauri tabishi tana cigaba da gaya masa bak'ak'en maganganu akan mahaifiyar sa, shi kuma koda wasa bai saurara mata ba duk zagin data masa Sai ya maida mata martani acewar sa tunda ita Allah baiyota da ruwan mutunci ba baiga dalilin da zaisa ya kyaleta ba. Yana bud'e get ya hango bros wani shu'umin mirmushi ya saki sannan ya tak'ark'are ya zunduma wani uban ihu har Sai da bros ya to she kunnensa ya juyo afirgice dan jin wannan ihun tayi zaton kunama ne ya d'alleshi ganin shi yai yana nufoshi yana cigaba da kukansa wata uwar harara ya maka masa wadda tasa nan take ya had'iye kukan ya k'araso kusa dashi, da ido yake tambayar shi abinda akayi masa yace "Ba Adda Maryam bane kawai dan Ammyna tace na kirata shine ta hau zaginmu nida Ammeyn danna ce badai Ammeyna ba shine ta mareni kuma ta biyoni wai zataje gaban uwar tawa ta takamin kai taga inda abinda ta isa tayi" Kafin yace wani abu saiga maryam d'in ta shigo a fusace kuma har lokacin bata bar fad'ar bak'ak'en maganganun da take fad'awa Nassar ba, abinda ya dad'a b'ata ran bros kenan yayi mata wani mugun kallo wanda sam bata kula daahi ba Sai da tashigo tsakiyar gidan itama had'e rai tayi ta bala in d'auke kai tai kamar batasan da zaman su awajen ba. . "Ke zo nan" ya fad'a cikin dakakkiyar muryarshi da babu alamun wasa aciki had'e rai tayi tare da kuma galla masa harara sannan ta saki tsaki tayi cikin gidan abinda yai masifar k'ona masa rai kenan ya kama hannun Nassar suka nufeta ai tana ganin ya nufota ta taka aguje tayi ciki' mamanta da Ammey suna zaune afalon suna d'an tab'a hirar su dake babu laifi basu cika fad'a da junansu ba saboda hak'urin haj. Amina da kuma tsantsar biyayyar da take wa abokiyar zamanta haj. Lubabatu hakanne yasa ba ajin kansu indai ba Maryam aka tab'owa haj. Luba ba yanzun zakaji ruwan masifar ta da bala I. Suna cikin hirar Maryam ta shigo da gudu ta shige bayan mama cikin shagwab'ar daya zame mata jiki tace "mama kinganshi ko zai dakeni " "Wa kenan?" mama ta tambaya tana duban hanya ai tana ganin wanda ya shigo tai masifar had'e rai dan a duniya idan da wanda taiwa masifaffiyar tsana to Muhammad ne dan ya riga da ya hana ta sakat ya shige mata hanci da k'udundune tarasa yadda zata fyato matsiyaci ta huta. Sosai tai masifar had'rai tace "dan ubansa idan ya isa yazo ya tab'aki tsabar masifa da jaraba abi a hana yarinya sakat to wallahi ni na gaji bari alhajin ya dawo dole yayi mana tsakani dakai dan 'yata na baiwa bace" Kafin takai ga dire jarabar da take Muhammad ya shammace ta ya fisgo Maryam ya d'auketa da wani gigi yaccen mari wanda yasa nan take ta shid'e numfashinta ya tafi yajin aikin hucin gadi kafin tasaki wata azababiyar k'ara, karar ce ta ankarar da mama ai har mayen ya damk'eta sunan da tasaka masa kenan dan duk inda takai da bala I matuk'ar yayi niyyar mata hukunci babu wanda ya isa ya hanashi sai Baffa wato mahaifinsu Ranta yai masifar b'aci cikin bak'in ciki tace "matukar ka kuma dukanta Allah ya isa ban yafe makaba shege mugu azzalumi ta Allah batakaba munafiki wallahi bari alhaji ya dawo sai yayi mana tsakani dakai tunda kai Allah yayi ka da zuciyar kafurai. Duk zagi da munanan kalaman da take binsa dashi bai saurareta ba saida ya tabbatar ta turarawa Maryam jikinta sannan ya wulla mata ita jikinta ya juya ya fice yana huci yayin da mama taci gaba da zagi tana la antarsa. Rungumo maryam tayi wacce take rusar kuka na fitar hankali domin ba k'aramin dakuwa tayiba jikinta kuwa banda azaba babu abinda yake mata abinka da farin mutum fatar nan tayi jajur tayi rud'u rud'u, suna had'a ido na Nassar tayi mata gwalo ta hayagagar ta tace " wannan munafikar uwar taka ita kayima gwalo dan uwarka shege mai kama da d'iyan aljanu🤣🤣🤣🤣dole na dara domin duk wanda yaga Maryam yaga Abdul Nassar yaga JINI Tana dire zagin bros yana dad'a danno kai daman a bakin k'ofa yatsaya domin ya San da cewa dama bazatayi shiru ba dole zata fad'i wani abun. Comments and shere Maman isi ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Goron Taya murna Ga Shugaba ummy khaleel tasamu k'aruwan baby girl Allah ya rayata yasa cikon addinin musluncine amen Ina gaidaku daukacin y'an kungiyata ta first class Allah ya k'ara daukakamu ya yabamu ikon rubuta abinda za a amfana dashi dan fiyayye Annabin rahama Amen Page 2 Tana ganisa ta shige d'aki da gudu ta datse k'ofar da key dan tasan k'aramin aikinsa ne ya biyota har d'akin yacasa kayarsa. Sai da taci kukanta ta gaji sannan ta mik'e ta shiga wanka fasa amsar d'inkin da tai kenan, bayan ta fito a wankan ta zauna ta d'and'asa kwalliyar ta tai matuk'ar kyau dan dama maryam mayyar kwalli yace duk da tsantsar kyawun da Allah yai mata akwaita da son kwalliya. A can b'angaren Halima kuwa ad'ari d'ari take komai domin ba ta da tabbacin fitowar Maryam tunda wannan mayen bros d'in nasu mai fad'an tsiya ya dawo. Sosai masu docuration d'in suka k'ayata wajen sai kace wani bikin aure ba walima ba. Maryam kuwa duk da tsamin da jikinta yai mata saboda azabar dukan datasha bata fasa shirye shiryenta ba dan bata tsoron bros ko kad'an acewar ta ai dukane kawai guda zai daka kuma guda zai bari. Bata samu damar karb'o kayan ba sai wajen k'arfe hud'u da sauri tazo ta shirya cikin wani d'anbanzan swess mai azabar kyau da tsada ita da kanta tasan cewa babu k'arya tayi masifar kyau ba na wasa ba. Tana shirin fita suka kicib'us damama tana shirin shigowa galala tayi da baki tana kaonta da irin kyaun da tayi rumgume maman tayi tace "mamana na shirya, nayi kyau kuwa?" " fad'a ma ai b'ata bakine 'yata kyawun da kikayi bazai fad'uba fatana dai ki kula da kanki kinji ko karki bari wani abin yasamar min ke in hakan yafaru bazan yafe ma kainaba?" Wani lallausan murmushi ta sakar mata tareda manna mata kiss a goshi tace karki damu mamana insha Allahu babu abinda zai faru, yauwa ansaka min duk abubuwan da nace amitar?" " komai ya kammala kije driver ke yake jira kar ku b'ata lokaci" Had'e rai tayi tayi kicin kicin da fuska, take naga hankalin maman ya tashi tajawo ta jikinta tace "me kuma ya faru baby? muna maganar mu lafiya yanzun kin canja?" Cikin shagwab'a tace "mama nafa ce miki da kaina yau zanja shine zakima driver magana gaskiya nidai ni da kaina zanje" murmushi maman ta saki tace "yanzun ke da wannan shine zaki b'atamin ranki abanza gashi" ta fad'a tana mik'a mata mukullin ta amshe tare da kuma rumgumeta ta sakar mata kiss a kumatu tace "ina k'aunar ki mamana sai na dawo" ta fad'a tare da yin waje aguje. A d'an farfajiyar gidan ta tarar da Ammey tana kiranta amma ko kallon banza bata isheta ba balantana na arzik'i, tun kafin ta tada motar ta saki wani d'an banza hom ai baba mai gadi yanajin haka yataso aguje ya bud'e mata k'ofa dan yasan order ta ya fita daban dana kowa acikin gidan. Ammey na tsaye har tafice sannan ta girgiza kai aranta tana mata addu ar sauka lafiya. Ba d'an k'aramin gudu maryam take ba domin acewar ta wai ta b'ata lokaci abokanta na cen suna jiranta ga wani uban kid'a data k'ure wanda zai sa Sam bazata fuskanci ko gane abinda zai fad'a mata ba, wannan tabi ar tace sam maryam bata da mutunci ko kad'an bata sami tarbiyar kwarai daga maman tata ba ta nuna mata kudi sune komai na rayuwa dan haka tayi komai babu komai kud'ad'en mahaifinta zasuyi mata maganin duk wata damuwa. Cikin k'ank'anin lokaci ta isa wajen, tasami gu tayi parking saida ta fara manna arnan glass d'in daya dace da kwalliyar tata kafin ta zuro kyakyawar farar k'afar ta waje ahankali take takawa, yayin zuciyar ta ya falfala da gudu cikin wajen saboda kid'an data ke jiyowa awajen da maryam gwana ce wajen rawa gata mayyar rawar ce biki ko batasan maishiba taje sai ta taka. Tunda ga sanda ta faka motar yakafe wajen da ido har zuwa lokacin data fito cikin yauk'inta datakun ta mai tafiyar da hankalin 'yan maza kai har ma da matan bak'aramin mummunar fad'uwa gabansa yaiba ganita gashi babu damar shiga wajen domin lokacin shiga meeting d'in da zasuyi yayi dole ya wuce amma aransa yana fatan har sugama bata bar wajen ba tunda yaga wajen data shiga yasan cewa wani bikinne tazo. Ita ko maryam tana ganin ta shiga wajen har ta fara wata irin rawa da juyi karab idanunta suka sauka akansa, take ta aro wata irin nutsuwa ta arawa kanta dan tana masifar gudun abinda zai b'arar da ajinta wajen masoyin nata kuma abin k'aunarta Muhseen. Abokanta na hangota suka saki shewa da ihun murnan ganin ta da sauri suka k'araso wajen wasu na d'aukar ta pic yayin da wasu ke suka take mata baya har suka k'arasa cikin wajen. Kujerar da aka tanada mata wacce ta kasance kusa da Muhseen ta zauna kamar wasu amarya da ango tunda shigo wajen akan idanunsa har rawa data soma amma sam bai nuna ya gantaba domin maryam ba k'aramar 'yar disgi bace shi yasa yake masifar kame kansa agabanta. Ba tare da b'ata lokaci ba aka fara gudanar da abinda ya Tara su awajen sukaci suka sha sannan ta rarraba kyautukan data tanada domin abokanta duk Halima ce ta kula da wannan yayin da maryam ta masifar kame kanta agaban Muhseen sai da za ayanka cak ne ma ta d'an dubeshi k'asa k'asa ta gaida shi murmushi ya sakar mata ba tare da ya amsaba ya tashi suka k'ara wajen, wa ashe na murnan zagayowar haihuwar muhseen abin ya k'ayatar dashi yadda ya kamata yadda maryam take 'yar bidiri to shi har ya dameta ya shanye bayan gama yanka cak ne aka bud'e musu filin rawa suka shiga suna wani irin taku mai ban shi' awa da burgewa, juyowar da zatayi kawai idanunta suka sauka hakansa yana tsaye sanye cikin kakinsa dayake masifar yi masa kyau ya hard'e hannayensa a k'irjinsa ya kafeta da fitinannen kallonsa, take gabanta yai masifar fad'uwa hankalin ta yai mugun tashi ba dan komai ba sai dan gudun kar ya disga ta agaban saurayinta da abokanta musamman da ta kalli idanunsa taga sunyi wani irin rinewa sabo da b'acin rai, amma dan k'arfin hali irin nata kawai sai ta basar taci gaba da rawarta, abinda yai masifar k'ona masa rai yafara takawa cikin tafiyar sa na ingarman namiji batasan ya isota ba sai dayayi mata wani mugun damk'a kamar zai karyata saida ta saki k'arar wahala Muhseen kuwa yana ganin haka ya cika wandon da iska dan yasan sojoji ba imanine dasu ba yanzun sai suyi masa walmakalifatu. K'ok'arin kwacewa ta soma ai kuwa yana juyowa ya d'auketa da wani azababben mari wanda a take hancinta ya balle da jinitayi luuuu zata fad'i saboda tsabar gigita ya fisgota ta fad'o jikinsa ya dad'a d'auketa da wani marin har guda biyu tsabar wahala da azaba bai barta ta gane inda take ba ya fincike ta daga jikinsa ya hau janta har jikin motar sa ya wullata ciki har Sai da ta gwaru da murfin motar saura kad'an ya had'e da hannunta wajen rufewar mukullinta ya jefawa driver da ya kira shi kuma ya tada tasa yabar wajen da masifaffen gudu yayin da yabar k'awayen ta da abokanta da jimami da tausayinta Allah ya had'ata da jarababben d'an uwa mara mutunci d'an hana ruwa gudu. Daga yanayin order dayake ma mai gadi yasan cewa babu lafiya wannan jarababbiyar yarinyar ta tab'oshi, da sauri ya bud'e masa get yai saurin matsa gefe dan yasan cewa ba shigowar dad'in rai zaiyi ba ilai kuwa saida yayi wani irin masifaffen cin taya sannan ya danna hancin motar ciki, Nassar da dawowar sa kenan daga masallaci ya kwasa da gudu yai cikin gida domin yasan indai yayan nasa yana cikin zafi to kan mai uwa da wabi yake duk wanda yasamu bi yake ta kansa. Maryam kuwa zuwa lokacin ta gama shiga wani hali tsabar wahalan dukan data sha haka ya kuma fincikota yajata ciki keeee ya gwara da kujera yana huci sai kace mayunwacin zaki a idanun haj. Luba ya watsar mata da 'ya kamar kayan wanki nan kuwa ta hau jaraba tana tsine masa ko kallon ta baiyi ba yayin da sai da ya kuma lallasata sannan ya d'ago yana huci ya kalli Ammey dake karatu cikin wayar ta bata ko kalli inda suke ba yace. " Ammey yakama ta ace kinsa ido akan yarinyar nan domin kuwa kema 'yar mijinki ce dan haka kina da hakki akanta bai kamata ace kinsa ido ana watsa tarbiyyar yarinya ba idan ba haka ba idan Baffa ya dawo zan fad'a nasa irin rashin d'ar da yake faruwa agidan kamilin mutum kamar sa" "Uaban Kane ya koya mana bad'alar nace uban kane bad'alalle d'anb iska mara mutunci kai dan ubanka tarbiyyab'ace da kai kai dazaka zauna kana gayan magana d'an iska mara zuciya dakana da zuciya da tuna ka fita harkana da 'yata amma dake kai zuc..................take ta had'iye sauran maganar saboda wani matsiyacin kallo daya watsa mata duk bala inta tana tsiron Muhammad domin ba shi da mutunci idan ransa ya b'aci MD kenan kamar yadda abokansa suke masa lak'abi. Sai data yi jinyar jikin ta na kwanaki biyu kafin ta samu ta warware har ta iya shiryawa ta fice gidan su Ammey ta nufa wajen malam Babba mahaifin Ammey hakanan Allah ya nufeta da son tsohon saboda shi mutum ne dayasan kansa ya iya zama da mutane abinda ya kamata ace uwa zatayiwa d'anta shine malam Babba yake ma maryam cikin hikima da dabarun su irin na tsofaffi domin ya kula Luba banzar Uwa ce irin iyayyen nannan da basu son b'acin ran 'ya'yan su dan haka komai yaro zai basa tsawatar wa. Tun daga nesa ya ta hango wani kamar bros a kusa da malam d'in take kuwa tai bala in had'e rai da k'yar ta iya yin sallama ta k'arasa kusa da MALAM d'in ta durk'usa har k'asa ta gaida malam sai wani ciccin magani take murmushi malam yasaki yace. Idan naga zan iya zan dinga yin posting safe da dare idan na Gama daukiin Kuma sai abinda Allah yayi 😂😂😂😂😂😂😂😂 Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 3 "Maryamu kenan maryamu sarauniyar mata me ya faru ne naga maryam d'in tawa tana wani ciccin magani?" Murmushi ta d'an saki batare da ta shirya wa hakan ba yadda yai maganar ne dole abin yabaka dariya cikin shagwab'a yace "har ga Allah bazan yafe abinda ake minba malam kawai dan anga ubana baya gari shine ake neman kasheni ko akassaramin rayuwa nidai nabar mututm da Allah gaskiya" Ta k,are maganar tare da zubowar hawaye. "Subhanallahi wake neman kassara min rayuwar uwa ina raye a duniya da lafiyana?" Had"e rai ta k'arayi tana hararan MD k'asa k'asa sarai ya ganta ya basar yayin da malam ya d'an kalleshi yace "kodai kaine muhammadi kake takurawa uwata?" Murmushi kawai yayi yana shafa kansa yayin da malam yace "ashe kuwa kaine gaskiya muhammadu karka k'ara dukar min uwata shifa duka baya shirya mutum sai daima ya dad'a kangara shi dan haka naaiha itace kawai zatasa mutum ya rusuna ba wai dukana kaji ko muhammadu" "Shikenan malam yafad'a cikin sanyin sa" yayin da maryam ta tsagal tace "tab waye zaimin nasihar ai wallahi sai dai yaiwa kansa mutanen da suke zama cikin bariki suna k'arewa matan abokan aikinsu kallo har su kyasa ne zaimin wata nasiha" ta k'arasa tana manna masa wata shegiyar harara dan har ga Allah ta tsanesa saboda gana mata azabar da yake. Murmushi malam yayi yace "haba uwata shid'infa yayanki ne bai kamata ace kina masa raahin kunyaba" "Tab' ai wallahi sai dai ya nemi k'anwar sa ni babu abinda na had'a dashi' Malam yace "gidanku nace gidanku ai ko ke kika had'a hanya da shi kuma alak'arku ba mai yankewa bace har k'arshen rayuwar ku" "Ai kuwa ni zan Malku wannan bak'ar alak'ar kuma zakace na fad'a maka malam babu ni babu shi wallahi yadda baya sona baya k'auna ta nima haka" Ta k'arasa maganar yayin da idonta yake nuna gaskiyar abinda yake kenan har k'asan ranta, malam yace "uwata idan zakiyi so kiyi so dan Allah haka idan zakiyi k'i kiyi domin Allah domin bakisan me gobe zai haifarba dan haka nake so ki cire duk abinda kika sanya aranki game da d'an uwanki" "Malam alkhairi goben zai haifar ta fad'a idanunta yana cikowa da kwalla taci gaba da cewa malam dukanfa dayaimin ne yasa kayi kwanaki baka ganni ba ina can ina jinyar jikina, ni bama dukan ne ya fi b'atamin rai ba irin yadda ya disgani a gaban saurayina da k'awaye na dan haka wallahi ni babu ruwana da shi" Malam yace "saurayi kuma maryamu shi Baffan naki bai sanar dake yayi miki miji bane?" Da mamaki Maryam tace miji kuma malam? Ni bai fad'amin ba yadai ce na kasance mai kula da kaine kuma bai amince na saurari kowa ba har sai ya bani izini iya abinda na sani kenan" "Yanzun bai isaba kenan shiyasa har kika fara kula wani batare da izinin saba"malam ya tambaya babu alamar wasa atare dashi, tace" bafa haka bane malam shid'in fa yayan k'awata ne wallahi yana da nutsuwa" "Ke zaki fad'a mana hakan ko kuma mu zamu gano da kanmu?" "Kune malam ta fad'a asanyaye ganin babu alamar wasa atare daahi. Ranan dai hiran da malam batayi armashi ba ta sallame shi ta wuce, tana barin wajen malam ya dubi MD yace "akwai matsalafa muhammadu MD ya kafe malam da manyan idanunsa batareda ya furta komai ba, gane me yake nufi ne yasa malam cigaba da cewa kamata yaifa ace kaja maryam ajiki ba wai kadasa mata tsanarka a zuciyar taba kasanfa meke faruwa tsakanin ku dan haka nake neman alfarmar ka rik'a janta a jiki ba wai ka rik'a tsan gwamar taba hakan zai iya haifar da Marsala" "Insha Allahu zanyi yadda kace malam cewar MD cikin sanyin jiki dana murya sannan ya d'ora da cewa " yarinyar ce batajin magana ko kad'an malam" "Tunda haka Allah yayi ta dolene mu rik'a hak'uri da ita my bita da addu a. Ita ko maryam bayan tabar wajen malam gida ta dawo ranta babu dad'i domin ko a hanya tak'i jinin su had'u bare su had'a inuwa guda da shi, abakin get tayi kicib'us da Nassar ya rugo da gudu yace "Adda maryam albushir" tace "sweet" hannu ya mik'a mata yace to bani?" Tace "ai kasan tunda nace zan baka ko" yace Baffa yayo waya aje a d'aukoshi inaji Ammey tana Kiran bros tace yaje ya d'aukoshi" manyan idanun ta ta wara akanshi tace na fara wasa da kaine ABDUL Nassar?" "Allah da gaske nake kuma idan nayi k'arya kimin duka" hannu ta bashi suka tafa sannan ta kama hannunshi tace "muje nabaka sweet kai yau har wannan ball d'in da ka nunamin jiya kace na sai maka to yau insha Allahu yanzuma zanje na siyo maka wani tsalle ya doka ya rungumeta yace na" gode Adda maryam wallahi wata ran kina da kirki, dan Allah ki daina zagin Ammey na kinga nima bana zagar miki mama" kallonsa ta d'an yi sannan ta shafa kansa har ga Allah ta na son d'an uwanta mama ce bata son mu amalarta dashi wanda duk iya nacinta ta kasa gano dalilin. Maman islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 4 Tana rik'e da hannunsa suka shiga cikin gidan lokacin mama tayi shirin fita ganinsu tare da Nassar mama tayi kicin kicin da ranta tace"bana hanaki hurd'a da wad'annan annobar ba?" Itama had'e ran tayi tace ni wallahi k'anina ba annoba bane haka kawai arik'a batamin sunan d'an uwa ubanmu fa d'aya sannan bani da wani k'ani bayan shi ni har ga Allah daga yau na daina hanayarar shi dan bazan masa abinda bros yake mana ba" Murmushin dole mama tayi tace "haba shalele ba fa haka nake nufiba kawai dai ina gudar miki raini ne amma tunda kina son mu amalantar su ai bazan tab'a hanaki kome kike soba shalelena" Ita kam maryam kama hannun d'an uwa ta tayi suka shige tana fad'in ina zuwa ne haka da yamma mama?" "Gidan haj. Fauziyya zani zan amso wasu sak'o" tab'e baki maryam tayi tace "wato duk randa Baffa zai dawo sai anje amsar wannan sak'on da baya k'arewa tun ina yarinya nake ganin wannan sak'on daya k'i ci yak'i cinyewa" ta fad'a suna shigewa d'akinta da Nassar yayin da mama ta fice cikin sanyi jiki. Suna shiga d'akin Nassar yace "wow Adda dama haka d'akin ki ya had'u gaskiya yafi nawa kyau sosai" yafad'a yana sufa agadonta, murmushi tayi tace "to ai kaine baka tab'a ahigowa d'akin nawaba" aikece Adda kullum cikin hantara ta kike kuma ni ina sonki tunda Ammey tace duk duniya bani da kamar ki dan ke kad'aice 'yar uwata JININA" jikinta ne yai sanyi ta k'arasa bakin gadon ta jashi jikinta ta rungume tace "kayi hak'uri kaji d'an uwa na nima daga yau na daina biyewa mama ina cin zalin tilon k'anina a duniya kaji ko" "To Adda dan Allah Ammey nama ki daina zaginta kinga wallahi tana sonki sosai ko sallah nayi saita ce nayi miki addu a itama tanayi miki" yanzu kam jikin maryam yagama sanyi tajashi jikinta ta rungume tace "na daina insha Allahu k'anina kaji ko?" "To Adda naji yanzu dai bani sweet d'in dan bazaki min wayoba sauri nake zanje muci gaba da ball d'inmu da su boy" murmushi ta saki ta d'ebo sweet d'in mai d'an dama ta bashi domin itama gwana ce wajen shan kayan zak'i 6:15 pm Dai dai lokacin motar bros ta shigo gidan ya dawo daga airport d'aukar Baffa Nassar daya dawo yanzun daga sallah magrib yasan cewa andawo kenan daga d'aukar mahaifin nasu ne ai kuwa wani ihun murna ya saki ya taho da mugun gudu. Yayin da MD yai saurin fitowa ya bud'e masa k'ofar nan naga wani farin dattijo kal kal ya fito daga motar fuskarsa k'awace da kyakyawan murmushin daya k'arawa fuskarsa kyau, farine sosai d'an siriri kyakyawan bafulatani nasha mamakin ganinsa na kuma fara hasaso haj. Sailuba dan ita bak'ace irin k'irin d'innnan koda wasa maryam batayo kamar Sailuba uwar taba saima kamar da sukeyi da haj. Amina matuk'a kamar itace ta haife ta. Da sauri Nassar ya rungume Baffa yana murnan ganin sa wanda ihunsa ne yasa maryam fitowa a miliyan har tana bangaje MD ta afka jikin Baffa tana "oyoyo Baffana gaskiya Baffa munyi kewar ka da yawa ko Nassar?" Ta k'are maganar da tambayar sa, yayin da Baffa da MD suka bita da kallon mamaki dan sunfi kowa sanin cewa kwata kwata Maryam da Nassa basa zama inuwa guda, basu k'ara mamaki ba saida sukaji Nassar yace "eh Adda kuma gaskiya inya tashi komawa saidai yaje damu tunda ku kunyi candy ni kuma zan tafi secondry kinga sai musha hutunmu kusa da Baffan mu ko?" Hannu ta bashi suka tafa sannan sukaja Baffan nasu zuwa cikin gidan yayin da MD wanda ya daskare da mamakin had'in kan daya gani tsakanin maryam da Nassar ya bi bayanau, aransa yana ayyana ina ma zasu d'ore a haka da sai yafi kowa jin dad'i sannan wahalarsa na son ganin had'in kan su zai k'are lallai zaici gaba dayi musu addu a kamar yadda ammeyn nasu ta buk'ata ya tabbata wata rana maryam zata bar abinda takeyi wanda kowa yasan cewa zugar uwar tane yake tasiri aranta. K'yale Baffansu sukayi ya shiga fat d'insa yai wanka yai sallar magrib yana idarwa ana shiga isha dan haka ya fito suka wuce masallaci da MD da Nassar, Yayin da maryam da mama suka gabatar da tasu hakama Ammey tayi tata anata d'akin sannan suka fito dirning domin cin abincin dare basu tab'a zaman cin abinci mai dad'in wannan ba tunda suka zauna ba babu fad'a da hayaniya tsakanin maryam da Nassar shi kanshi MD satar kallon ta yake tare da mamakin abinda ya sauyata cikin sauk'i haka. Aban garen iyayen kuwa Ammey hakan ba k'aramin dad'i yayimata ba domin bata da burin daya wuce ganin had'in kan 'ya'yan nasu Yayin da mama kuwa hakan yai masifar k'untata mata tayi wani kicin kicin da rai tana hararan maryam wacce ma batasan tanayiba domin sha aninsu kawai suke sha ita da d'an uwanata, yayin da zuciyar ta yake fad'a mata cewa lallai idan bata d'auki matamin gaggawa ba to shirinta na shekaru zai lalace dake ita ba mutum ce mai iya b'iye damuwa ba hakan yasa ta tashi a fusace tabar wajen tana dad'a d'aure fuska duk suka bita da kallo yayin da Baffa yatam bayi maryam ko anwa maman ta wani abunne" Kagad'a ta motsa kafin tace "itafa mama bak'in cikinta dan taga mun shirya da Nassar ne mun daina fad'a ita kuma bataso shine kawai" dake maryam 'yar gatsal gatsal ce kuma duk inda gaskiya take fad'a take kai tsaye batare da shakka ko tsoron wani abuba. "Ungo nan" cewar Ammey tana ma maryam irin zagin nan nabaza yatsu tace "yanzun dan gidan ku mamar takice 'yar bak'in ciki?" "Eh mana Ammey muguwar 'yar bak'in ciki ma kuwa itafa koda wasa bataso taga na rab'i k'anina tafiso na zauna bani da kowa bani da abokin ahawara ni kuma daga yanzun na daina lamunta randa babu wani acikin ku kenan bazanyi huld'a da d'an uwana ba ina bazai yiyuba" Baffa yace "ga wannan indai kina neman abokin shawara kika same shi ai kin gama dan haka ki daukeshi d'an uwa amini zai baki ki d'aukeshi yaya aboki kuma aminin ki zakiji dad'in hakan wata rana" "Tab ina wallahi bazan iya ba wannan mai kama da maka ikan d'aukar ran kullum fuska babu annuri ni wallahi ina masifar tausayawa matar sa domin ta shiga uku da bak'in rai wallahi" duka Ammey ta kawo mata ta goce yayin da Baffa tace "Kika san inda rana zata fad'i?" "Nassar taso muje muci gaba da buga was an nan idan har kabari nayi winning d'inka saina zazzage bankinka ka yarda?" Tak'are da tambayarsa "Eh na yarda amma fa idan nina cinyeki zaki sa Baffa nima ya sai min computer irin naki" ita ma tace ta yarda suka bar wajen tana hararan MD k'asa k'asa, wani b'oyayyen murmushi MD ya saki Binta da kallo k'asa k'asa ta yadda zai wuya ka gane ita yake kallo. Baffa ya d'an dube shi da damuwa yace 'Muhammad kafasan alak'ar dake tsakanin ka da ita dan haka ina so ka kawo k'arahen wannan bak'ar kiyayyar dan Allah na rok'eka" Baffa ya k'arasa yana had'e hannayen sa alamun rok'o iaka ya fesar batare dayace komai ba ya ture kujerar yabar wajen ba tare da yace komai ba, duk suka bishi da kallo, yayin da Ammey taji wani irin abu yana taso mata saiga idanun ta sun cika da kwallah Baffa ya dafe hannunta yana girgiza mata kai. Sunan Baffa yasamo asaline tunda ga sunan kakan sa da yaci iyayen sa suka mak'ala masa Baffa shike nan Baffa ya bishi har zuwa yanzun da yaransa ma duk da hakan suke kiransa Baffa d'an gatane sosai awaken iyayen sa kasancewar sa shi d'aya rak hakan yasa yasami gado mai d'umbin yawa daga mahaifinsa bayan ya rasu gata da kulawa babu irin wanda bai samu daga iyayen saba yayi karatu tundaga matakin pir har zuwa dgreen sa na biyu duk afannin likitanci duk da kasan cewar su 'yan k'auye hakan baisa Inna da baba hana d'ansu karatun boko dana zamaniba yanzun haka yana da ilimi mai train yawa daga na zamanin har na wajibin. Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 5 Tun bayan raauwar mahaifin sa ya samu aiki acikin gari ya baro k'auyen su babu yadda baiyi Innar sa ta dawo kusa dashi ba mursisi tace ita tafijin dad'in zaman can tunda da nan tasaba saidai ta had'ashi aure da d'iyar k'anwarta SAILUBA wacce ta rika tun bayan rasuwa k'anwar tata wacce ta rasu awajen haihuwar ta ta biyu lokacin Baffa yana matakin secondary dake bording school ce hakan yasa sai lokacin daya dawo suke had'uwa da ita. Allah ya jarabci Sailuba da matuk'ar son Baffa saidai bata nunaba kasancewar ansa 'ya mace da kunya dan haka ta barwa ranta amma ta dage da addu ar neman zab'in Allah, itama tana danata ilimin daidai gwargwado domin ta kammala aji uku na wato k'aramar secondary sannan afannin addinin ma ta d'anyi nisa, Koda wasa Baffa bai tab'a nunawa Sailuba cewa aurensu auren had'ine ba domin tun mahaifinsa sa na darai baya iya k'etare duk wani umarni da zasu bashi haka ma yanzu da ya kasance baya raye duk abinda mahaifiyar shi tasaka shi komai wahalar sa baya k'inyi mata Dan haka yake shan albarka da addu o I kala kala daga mahaifiyar sa wanda yake ganin ci gaba arayuwar sa. Tunda akayi auren su da Sailuba basu tab'a jin kansuba domin suna matuk'a zaman lafiya komai tare suke yi su kashe su binne tare yayin da Sailuba ta ganta a birni idanunta ya bud'e tafara k'awaye matan abokansa wanda daga baya takejin kanta ta wuce da ajinsu bazata iya alak'a dasu ba saboda d'aukakar da Allah yaiwa mijinta lokaci guda ta hanyar kasuwancin daya somo wannan kenan. Matsalar farko da suka fara fuskanta shine rashin haihuwa lokacin da Inna taga an kwashe kimanin shekara biyar babu amo babu labari sai abin yafara damunta kullum bata da magana sai na son ganin 'yan jikokinta, tun Baffa baya damuwa shima har abin yasoma damunsa, magani kuwa suyi na gida suyi na asbiti, Wata rana Sailuba ta kaima babbar aminiyar ta ziyara wacce tun zuwanta garin bata da aminiya sama da ita bayan sun gaisa tasa ankawo mata kayan motsa baki mai aiki ta gabatar mata dashi ta d'an dubi aminiyar tata Zakiyya tace "ni kuwa ina DEEDAH" babbar 'yar haj. Zakiyyan kenan murmushi tayi tace "humm Deeda rikici zakice min tana can d'akin ta tana faman kumbure kumburen banza wai sai nasa Abban ta yacanja mata mota, ni kuma banga abinda motar ta yayi ba shiyasa nayi banza da ita ta cika fitina yarinyar nan wallahi" 'Yar dariya Sailuba tayi tace haba Zakiyya tilon 'yar taki kikasayi mata wani abu gaskiya baki kyautaba tana ina ni tazo ta fad'amin duk kalar data ke so kiga aiki da cikawa" suka yi dariya yayin da haj. Zakiyya tace "kina shagwab'a yarinyar nan da yawa Sailuba ya kamatafa ace tasan cewa ba komai ne mutum yake so arayuwarsa yake samuba" "Yauwa Sailuba ni kuwa ya batun maganin andace kuwa?" "Wanne kenan cewar haj. Sailuba tana duban haj. Zakiyya na haihuwa mana" ta bata amsa cikin gaakiya da gaskiya wata 'yar banzar dariya ta saki tace "wai ke anfad'a miki duk wahalar da su Inna suke amfani nake da maganin?" Kallon rashin fahimta haj. Zakiyya tayi mata sannan tace "ban fahimce kiba k'awata kina so kicemin duk wahalar banza mukeyi bakya amfani da maganin?" "To mai zai dameni dan ban haihuba kuma ni gaskiya koda zan haihun ma ban shirya yanzun ba saboda haka kuma daina wahalar da kanku da kud'ad'en ku wajen nema min magani domin ba na amfani daahi" "Ke kuwa mai yakaiki aikata wannan d'anyen acikin k'awata kuma naga ko ba komai ai 'ya'ya rahama ne bakisan wanda zaki moraba sai Allah" "Nifa kin fara takuramin da wani wai haihuwa haihuwa ki k'yaleni mana dan Allah a a haka kawai nifa babu abinda na nema na rasa mijina bai tauyeni ba haka mahaifiyarsa nima uwata ce bata d'aukeni suruka ba dama can ni 'yar k'anwar tane kuma rainonta dan haka banga abinda zaisani wahal da kaina dole sai na haihu ba" "Bakya tunanin wata rana idan mijin naki ya gaji yace zai auro wacce zata Haifa masa yara kinsanfa babu wanda bayason ganin kwansa a duniya?" "Ke dallah saurara taya kike tunanin zan bari hakan yafaru"? Baffa bashi da wata mata a duniya bayan SAILUBA kisawa ranki haka sannan kisa aranki cewa duk yadda yakai ga son yara dole ya hak'ura tunda mahad'in rayuwar sa bata buk'ata kin gane? Haka rayuwa tayi ta tafiya Sailuba da mai gidanta Baffa ana cin uwar soyayya yayin da inna taci gaba da damun kanta akan rashin jikoki shi kuwa Baffa ko ajikinsa acewar sa haihuwar ma lokacine. Ana haka ya kammala k'asai taccen gidansa an an wata unguwa tsaka tsaki yabar jerin gidajen ma aikata ya koma nasa, hakan kuma yasa yasamu cigaba sosai dan yakan d'auki wasu daga matasan unguwar irin maau zaman ban zan nan ya bud'e musu wani kasuwancin hakan ba k'aramin kima da daraja yajawa Baffa a idanun iyayen yara ba suna matuk'ar ganin girmansa. Ganin lokaci yana taja yasaka Inna tace lallai lallai dole Baffa ya nemo mata ya k'ara aure domin bazai yiyu ace suyi ta zama babu aure ba tofa sai lokacin hankalin Sailuba yay masifar tashi dan batayi tsammanin hakan daka ta wajen innan ba. Muje zuwa Plss commmen and shire Takuce maman islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MANAN ISLAM Page 6 Takasa zaune takasa tsaye dole ta bazama gidan haj. Zakiyya neman shawarar ta, karfa kuyi tunanin haj. Zakiyya yarinya ce kamar sai luba ko d'aya kawai dai irin k'awancen nanne na yanzun dan ak'allah Deedah d'iyar haj. Zakiyya zatayi kusan shekara ashirin sannan bayan ita tana da manyan 'ya'ya guda biyu da suke karatu a waje yayin da Sailuba a lokacin batafi irin shekaru ashirin da kwai zuwa da takwas dinnan ba domin lokacin da aka yi aurenta da Baffa duka batafi shekara sha takwas ba kunga kenan ak'alla yanzun suna da shekara goma da aure. Tunda ta gama karanto mata damuwar ta tayi shiru tare da zubawa haj. Zakiyya wacce tai shiru tana buga k'afafunta ak'asa idanu, wata ajiyar zuciya ta sauke tace "kin yi shiru bakice komai ba k'awata kinsan cewa fa wannan ba maganar wasa bane domin nafi kowa sanin cewa duk abinda Inna ta zartar ya zartu domin Baffa baya iya tsallake maganar ta" "Kuskuren da kikayi kenan Sailuba tun farko saida nace miki ki tashi tsaye ki kama Baffa a hannun ki kikace aike daga shi har uwar sa suna tafin hannun kiyanzun ai kin gani dama wacce uwace bazata so ganin jikokinta a duniya ba kika ce ke duk abinda kike so shi kike samu dan haka bazaki komai ba ai yanzun gashi nan naga ikonkine yake sama da umarnin innan awajen Baffa ko?" "Dan Allah k'awata duk mubar wannan maganar naji nayi kuskure yanzu dai so nake mu samo hanyar da zan gyara kuskure na kuma mu to she duk wata hanyar da zata kuma b'ulluwa mai kama da wannan" wani shu'umin murmushi haj. Zakiyya ta saki kafin tace komai saiga mijinta ya shigo da sallama kamar mara gaskiya ya soma sand'a zai wuce "kai" ta buga masa tsawar da sai da tasaka Sailuba ta zabura tace "kai wanne irin dak'k'ine dan Allah me yasa bakajin magana duk abinda zan fada maka baya shiga kunnen ka wallahi alh. Lawan duk randa ka kaini bango agidannan bazamu kwashe ta dad'i dakai agidannan ba" "Jiki na rawa alh. Lawan yace " dan Allah haj kiyi hak'uri ban kula daku awajen bane" sannan ya k'araso gaban haj. Sailuba ya durk'isa har k'asa ya gaida ita a sanyaye ta amsa idanunta har sun kawo ruwa tsabar tausayinta daya kamaahi sannan ya tashi sum sum ya wuce sama "kuma ka gyara min d'akin kafin na hawo" "To" kawai yace mata ya wuce. Dafa Sailuba tayi tace " kinga k'awata muddun kikace zaki saka tausayi aranki to aikin ki bazai tafi yadda kike soba kuma ko sune suka samu dama abinda zasuyi miki sai yafi wannan domin sai sun kacaccala rayuwarki" Haka dai haj. Zakiyya tayi nasarar yi mata hud'ubar shed'an akan su maida Baffa rak'umi da akala akan komai kamar dai yadda taga tanayiwa mijinta, cikin k'ank'anin lokaci aka rushe maganar auren da Inna ta da Baffa basu k'ara d'aga zancen ba har zuwa wani lokaci yayin da Sailuba tasamu hanyar sarrafa Baffa iya son ranta baya aiwatar da komai saida umarnin ta hatta abu idan zaiwa inna sai ta amince inbata yardaba anbarshi. Akwai wani malam Babba anan k'asan layin da suke shi mutum ne na kwarai wanda yake amfani da ilimin da Allah yabashi shiyasa yasa yake da matuk'ar kima da daraja a idon mutanen unguwar duk lalacewar yaro badai kaji mummunar kalma daga bakin malam babba ba saida fatan shiriya da sanya albarka wannan yasu masa farin jini sosai wajen yara da iyayen su yana damatuk'ar kima a idanun matasan earia dama na kewayen hakan yasa ya bud'e makarantar ialamiyya wanda ake zama daga magriba zuwa sallar esha ranan alhamis da juma a yara da manya haka suke cika amakarantar. Baffa yana d'aya daga cikin d'aliban makarantar haka kuma bashi uban dayafi malam babba kaf unguwar domin shine mutumin da baya duba girma ko matsayinka zai fad'a maka gaskiya kai tsaye komin d'acin ta kuwa, haka duk sanda Baffa yake gari bashi da wajen hiran yamma sai wajen malam babba haka nan cikin hikima yake dad'a yiwa duk Wanda suke tare nasiha da hak'uri da zaman lafiya da kowa tare da rok'awa duk Wanda ka gani ba akan daidai ba shiriya bawai ka rik'a zaginsa ko la antarsa ba domin hakan ayace wata rana sai ya faru akan ka ko akan d'anka. Cikin matasan da alh. Baffa ya bawa aiki akwai 'ya'yan malam Babba guda biyu Kamalu da kuma Usman yana matuk'ar jin dad'in aiki dasu saboda ingantaciyyar tarbiyyar da suka samu daga mahaifin su. Oh na manta ban muku bayaniba tun lokacin Baffa yana k'auyen su yana da aminiya gsai d'aya Hassan Wanda suka kasance tamkar uwa uba d'aya koman su tare sukeyi hatta wajen kwana ma idan ya sun kwana agidan su Baffa to gobe agidan su Hassan zasu kwana Wanda har hakan yaja wa iyayen su kusanci suka zamo kamar 'yan uwa na jini. Sai da aka shafe shekara guda Inna bata kumayiwa Baffa maganar k'arin aure ba saboda danne tan da akayi da k'arfin asiri sai lokaci guda yaje garin Wanda alokacin ma rabon data sanyashi idanunta ma an d'ebi wata kusan biyu mutumin da duk k'arshen sati sai yaje ya ganada mahaifiyar ta ya kai mata abubuwan bak'ata yanzu kuwa sai gimbiya Sailuba tabada umarni wannan kenan Taku maman islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASA MAMAN ISLAM Page 7 Bayan sun gaisa da tare da tambayar juna bayan rabuwa yabata uzuirin cewa baya zama ne shiya sa ta d'an jima bata ganshiba da mamaki ta rik'a kallon sa domin bata tab'a ganin uzurin daya hanashi gaida itaba Sai a wannan lokacin sai dai ta alak'anta hakan ne akan maganar auren data dameshi da ita hakan yasa tace "Allah ya kyauta" Gyara zaman ta tayi tace "Baffa kamar dai yadda na takura maka na matsa maka har hakan yasa kake ganin kamar na matsa maka dayawa to Baffa inaso kasani 'ya'ya suna k'arawa mutum martaba da kima idon al'umma kuma 'ya'ya rahama ne sannan ni'emane da ba kowa Allah yake yiwad,,,irin wannan baiwar ba, kai yanzun ba abin alfaharinka bane ace yau ga sanyin idaniyar kaba kana dubansu kanajin dadi? to inaao ka saurareni da kyau yau muna biyar ga wata dan haka na baka daga nan zuwa k'arshen wata kafito da mata ka aura ko kuma ni na zab'a maka kamar yadda nayi maka na Sailuba" Shiru yayi yana sharce gumin dayake tsiyayar masa har saida Inna ta kula da halin dayake ciki amma sai tai kamar bata ganiba gyara zaman sa yayi yace "dan Allah Inna ki d'an k'aramin lokaci zanyi yadda kike so amma Inna taya zan fara fad'awa sailuba wannan labarin?" Sosai inna ta hasala abatunsa ta lura saboda bayason bacin ran Sailuba ne baya so dan haka ta had'e rai tace "au saboda b'acin ran Sailuba ne kai baka son barin baya to wllh kaji na rantse muddun ka bari k'arshen watannan yazo baka nemo matar aure ba ni zan nema maka ance maka ita Sailuban haihiwar take sone da tana so ai bazata rik'ka to she mahaifa tana d'inketa ba ko ance maka bansan halin da kuke ciki bane to ita aminan nata da tad'auki amanar zuciya da rayuwanta ta damk'awa sune suke kewayowa suna kawomin labarin komai dan haka ni na gama magana idan kuma ka isa kai d'ane ka k'etare magana ta kagani duk duniya babu wanda yakaini son Sailuba domin ita d'in 'yatace halak malak kuma JININA CE sannan rainona ce sai dai a irin tarbiyyan da nabata babu wanda take amfani dashi sai na banzayen aminanta da suke d'orata a keken b'era har nagaji da fad'a mata gaskiya ta nuna bata buk'ata Allah yasani na sauke hak'k'in ta da yake kaina nabata kula da tarbiyyan da ko uwar data haifetane iyaka kenan dan haka na fita hak'k'inta sannan inayi mata fatan shiriya" Tunda yake baitab'a ganin fushin mahaifiyar tasaba sai wannan karon domin daga shi har Sailuba lallabasu Inna take amma yau kam yaga tsantsar b'acin ranta dan haka ya rik'a lallab'ata har zuwa sanda yabaro garin. Sai dai babban tashin hankalin sa yadda zai fuskanci gimbiyar tasa da wannan batun yasan cewa ba abune mai sauk'iba ya tunkareta da wannan babban al'amarin, koda yadawo gida haka abin yay ta damun sa arai har gimbiyar tasa tay ta tambayarsa damuwarsa yace babu. Sau tari idan abubuwa suka sha masa kai yakan nemi shawarar malam Babba wannan karon ma yazo wajen malam d'in kamar ko yaushe neman shawara tare da baran addu a kamar yadda yasaba abin Allah kuma masu Karin magana sukace kaddara ta riga fata anan suka had'u da Amina d'iyar malam wacce tunda yake Allah bai tab'a sawa sun had'uba sai ranar dan dama ba wani sanin yaran malam d'in mata yayiba domin basu cika fitaba sai da babban dalili kuma bayan haka ma dole bazai san Amina domin ko acikin gidan ma abune mai wahalar gaske kayi katarin ganin ta atsakar gida domin koda yaushe tana d'aka. Tunda yay arba da Amina ya nemi nutsuwar sa yarasa bai tab'a katarin had'uwa da abinda lokaci guda yai tsalle ya shige zuciya lokaci guda ba sai Amina, itace tayi masa kamun dashi da kansa ya kasa daurewa har saida ya furtawa malam Babba hakan, take batare da wani jinkiriba yace ya bashi Amina halak malak yaje ya sanar da mahaifiyarsa kuma insha Allahu k'arshen watan da muke ciki za ad'aura auren haka nan Allah yasanyawa malam Babba k'aunar baffa saboda Baffa mutum ne dayasan darajar manya haka nan ya iya mu'a mala da duk wanda suke tare daahi. Cikin tsantsar farin cikin daya kasa b'oyuwa ya k'arasa gidansa fuskar nan d'auke da annuri haka ya dinga abubuwa har dai Sailuba ta kasa daurewa ta tambayeshi yace mata babu komai kawai dai yajishine fresh shiyasa yake farin ciki. Bata k'ara tsinkewa da lamarin ba sai washegari dataga yana shiri ta tambaye shi inda zashi yabata amsa da wajen Inna take taji 'yan hanjinta sun kad'a tace "naga yau dukafa kwananka biyu da dawowa shine zaka kuma komawa?" Dakatawa yayi da fesa turaren da yake ya dubeta yace "yanzu dai kina so kice dan na dawo daga gaida uwata shekaran jiyaifi ne kenan dan na koma yau?" "Ba lafi bane amma gaskiya bazaka koma yauba ina laifin ka bari zuwa koda k'arshen watane amma daga dawowa sai ka wani kwashi jiki kace yau zaka koma nidai gaskiya ban amince ba" Ta k'arishe da irin yaudararrun kalaman da malamain su yace su d'an rik'a had'awa dasu dan ba ko dayaushe ne aiki yake amfaniba wani lokacin sai an had'a da kissa. Wani banzan kallo ya watsa mata kafin yace "to uwata ai tunda kin isa sai ki hanani zuwa tunda naga alama kin kai har kin wuce wuyanki yayi kauri" mts yaja dogon tsaki ya juya batare da ya kalli inda takeba ya fice. Sau tari wasu abubuwan dayake mata sai yaga kamar cikin tsoronta yake ga wani d'an banzan Shankar ta dayake wanda indai zata bashi umarni sai ya bi. Ita kanta Inna tasha mamakin maganar dayaje mata dashi ba k'aramin farin ciki tayi da irin da ya nemoba dan ita kanta ganau ce akan irin tarbiyyan Yaran malam Babba dan haka batare da b'ata lokaci ba ta tashi 'kaninta d'aya da k'anin Baban Baffa suje suka kai dukiyar aure da kayan nagani ina so har da nasakun rana. Babu yadda malam baiba akan su barshi ai shima Baffa d'ansa ne suka k'iya cikin mutuntawa suka baro gidan malam Babba suna ta yaba karamcin sa. Sanda Sailuba tayi ido biyu da kawun ta dana Baffa saida tasha jinin jikinta domin tasan cewa banza baya tab'a kai zomo rafi. Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 8 Haka nan dai ta yi musu sannu ta kawo musu ruwa da abinci kasan cewar dare yakawo kai domin tsakanin garinsu da nan akwai d'an nisa hakan yasaka dole suka kwana dan ason ransu so sukayi subi motar 'yan kasuwa. Duk naci da son jin kwakwaf na Sailuba babu abinda ta fahimta dan babu wanda ya tanka mata har zuwa wayewar gari da suka shirya Baffa ya kuma maida shi har gida anan ne Inna take masa maganar dawo da Muhammad d'an amininsa dayake rik'o tunda shima Hassan shikenan d'an nasa k'wara d'aya kamar rai tundaga haihuwarsa da matar ta rasu bai k'ara haihuwa ba duk kasancewar shima alokacin matansa uku kuma uwar Muhammad itace amarya kuma da ita Allah ya bashi haihuwa wanda shima Innan ce ta raineshi da madara bayan ya isa yaye kuma k'iri k'iri Babba ya d'auke shi ya hana uban shi wanda saboda kara baiko kara waiwayar Baffa akan maganar ba dama matansa ba wani son sa sukeba sun masifar tsanarsa saboda tarin dukiyar da Allah ya horewa Hassan gashi duk cikinsu babu wacce ta haihu hakan yasaka ko k'aunar ganinsa basayi tun yana zuwa gidan idan Baffa ya kawoshi hutu har dai ya gane ba a buk'atar sa shikenan idan yazo sai dai yasamu Abbansa akasuwa suyi wuninsu anan susha hiransu. Tsanar da Sailuba tayiwa Muhammad kuwa ta ninninka wacce matan babansa sukayi masa domin acewar ta akansa shi kad'ai Baffa ya tare baya kula kowa baya ganin kowa indai yana tare da Muhammad wanda bata da damar musguna masa dan akan yaron tayi imanin zai iya sakinta ga ubansa malamin k'auye injita koda tabi tak'asa babu nasara dan haka ta koma ci masa mutunci da wulak'anci iri iri ga d'an karen gori wannan ne yasamo asalin tsanar da Muhammad yaiwa Umma kamar yadda Baffa yasashi dole yake kiranta dan da farko Sailubanta yake kiranta dan Muhammed tayayyen mutum ne kaifi d'aya kuma mara tsoro sannan baida shakka duk abinda yayi India yasan shine kana tambaya zai ce shi ya aikata wannan abun sai dai kome zai faru ya faru ganin kima da darajar Baffan shine yasa har yake kiran sailuba da umma. Ak'alla Muhammad yakai shekaru sha biyar a hannun Baffa tun baifi shekaru hud'aba ya d'aukko shi yanzun haka yana shirye shiryen turashi waje karatune dan atsarinsa yafison shima d'ansa yazamo likita kamar shi. Bayan tafiyar Muhammad da sati biyu aka d'aura auren Baffa da Amina auren da yai mutuk'ar girgiza rayuwar Sailuba domin koda wasa bata tab'a kawowa Baffa aure nan kusa ba domin malaminta ya tabbatar mata da cewar an kawar da tunanin Baffa akan wata maganar aure kujifa wani shirme. Lokacin da falonsu yake karb'ar bak'uncin 'yan garinsu, ita kuma sannan tafice a matuk'ar gigice zuwa gidan k'awa aminiya kuma babbar mai bata shawara haj. Zakiyya. A haukace ta shiga gidan lokacin mijimta yana durk'ushe yana mata matsar k'afafu yayin datake hakimce asaman kujera tana faman shan k'amshi yayin da shi kuma bawan Allahn yake tasharb'ar gumi abin dai gwanin tausayi kamardai yadda ta sharad'anta masa duk sanda wata k'awa ko 'Yar uwa tata suka zo kuma hakan yazamar masa dole ko ya shiga tashin hankali da masifar ta. Yau kam baisamu amsa daga haj. Sailuba ba domin a hargitse take dan tundaga bakin k'ofa take kiran "nashiga uku na lalace shikenan k'arshene yazo, yau ni Sailuba naga takaina" yayin da hawaye suke rige rigen zubo mata daga wannan ya fito wani zai tunkud'oshi. "Lafiya k'awata naganki haka saikace wacce aka aikowa cewa iyayenta sun mace rana d'aya irin wannan tashin hankali haka?" "Ai wallahi gwanda ace iyayena ne suka mace rana d'aya wannan tozarci da wulak'ancin da Baffa yayimin, baffa tozartani ya nunawa duniya ni ba komai bace Baffa yagama da rayuwata k'awata" tafad'a tareda rushewa da wani shegen kuka wanda yasake d'aga hankalin haj. Zakiyya tai k'uri tana binta da kallo kafin daga bisani ta sauke ajiyan zuciya tace "Wai duk mai yai zafi kike irin wannan maganganun k'awata?" Majina ta fyace sannan tace "Baffa k'awata shine" ta rik'a maimaitawa babu k'k'kautawa, "Naji shine, me yayi miki mai zafi haka?" ta katse da tambayarta "waini Baffa zaiwa kishiya?" "Hmmm shine me?k'awata yanzun ke akan wannan kike d'aga hankakalinki indan wannan ne ai basai kin d'aga hankalinki abanzaba yau d'innan ma Baffa yana iya dawowa yace miki anfasa" "Daga baya kenan k'awata aure kuma saidai wani amma wannan yafi mintuna talatin da d'auruwa" A firgice haj. Zakiyya take kallon k'awar tata "aure Kuma? Aurefa kikace shi Baffan neyayi mana wanna cin mutuncin lallai yatarowa kansa dala ba gammo dan wallahi sai yayi nadamar abinda ya aikata manata Kinga yanzun dare yayi babu damar mufita amma gobe da asbah zaki fito mu kama hanya dole ne mu ladaftar da Baffa amma kafinnan zokiji" ta fad'a tare da rad'a mata wani abu a kunne duk da cewa abinda tace ya d'an sanyaya mata rai amma hakan baisa ta saki rantaba domin bak'aramin shammatar ta Baffa yayi ba amma tayi alk'awarin saita shayar dashi ruwan mamaki saita sa yayi nadamar abinda ya aikata mata wallahi _________________________ Duk da cewa ranta ajagule yake hakan bai hanata yima kawunna nan nata sauka ta musamman ba kuma Saida tayi k'orafin auren da akayi batare da ansanar da ita ba Suma sun amsa laifinsu sai dai sunbata uzurin cewa basa sone su d'aga mata hankali wai idan abin yazo lokaci guda zai wuce ba kamar afad'a mata tunda wuriba abin yayi ta damunta. Maman islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 9 Haka dai ta daure tayi musu karb'a ta musamman har zuwa lokacin da suka wuce, cikin k'awayenta babu wanda yasan da maganar auren sai haj. Zakiyya dan haka da itakad'ai suka zauna har zuwa bayan sallahr magriba sanda 'yan kawo amarya suka fara shigowa. Haj. Zakiyya ce ta rik'a tausarta da k'yar tasamu ta hak'ura dan da cewa tayi wallahi saitayi musu hauka sai sun ganecewa mijin mahaukaciya 'yarsu ta aura haj. Zakiyya tace "haba k'awata waishin duk abinda na fad'a miki tun muna gidana baki d'aukaba? na sani da ciwo amma idan kika daure zakiyi dariya harda shewa kinga yanzu idan kikayi wani abu to duk abinda yasamu 'yarsu to kaitsaye zasuce kece dan zaki aikata amma idan kika bi yadda na fad'a miki zakiga yadda zasuga kima da darajanki" Da k'yar haj. Zakiyya tasamu ta lallab'a haj. Sailuba a wannan gab'ar har ta hak'ura ta karb'i bakin amarya yadda ya kamata har suka tafi suna yabon kirkinta ganin yadda ta karb'i amarya cikin farin ciki da walwala, tare da ita aka raka amarya har d'akinta suka tafi suna godiya Bayan ta tafiyar sune haj. Zakiyya ta dubeta tasaki shu'umin murmushi tace ba'a faraba k'awata sharar fage ake kafin wasan ya fara" "Allah ko k'awata?" "Ai ke d'ince bakya ganewa baki da aiki sai fushi Kuma babu inda wannan zai kaiki sai na dama" "Abinne ya masifar d'amin hankali k'awata amma yanzun ya zanyi?" "Shi nake son ai ki nutsu ki fahimta domin abune da zakiji dad'insa kuma zai amfaneki batare da kowa ya fahimtaba, Kinga yanzu angon yana hanya abinda nakeso dake goben ya kasance kin gama musu duk wani aiki har abin kari kafin ki fito, kidai fito da wuri kinsan wajan yana da nisa sosai" "Angama amine zanyi yadda kikeso insha Allah" _________________________ Ranar dai ango ya gwangwaje agwancinsa shi da amaryar sa Amina yayin da Sailuba ya yadda taga rana haka taga dare batako runtsaba tsabar masifaffen kishin dayake cin ranta. Koda gari ya waye tun bayan da ta idar da sallar asuba bata komaba ta zauna ta had'a musu had'ad'd'an break wanda rabon data girka irinsa har ta manta tsab ta gyare gidan tsab aranta take cewa duk wani abu da zanyi agidannan na bankwana ne domin nima lokacin hutawana yazo. Sanda Baffa suka fito daga d'akinsa shida Amina tuni Sailuba sunyi nisa a hanyarsu ta zuwa wajen shahararren malamain da yai k'aurin suna aciki da wajen garin wanda ake kira da kowa naka. Sosai yaji dad'in yadda ta gyare ko ina tayi musu girki duk da cewa yaji babu dad'in fitar ta arana irin tayau daya kamata ace ta tsaya ta Kula da komai na gidan kodan bak'in dayasan cewa bazasu rasayi ba aranar irin ta yau d'in. Bayan gama cin abincinsu babu dad'ewa kuwa saiga yayar Amina wacce takasance ita kad'aice 'yar uwarta mace dan duka yaran malam Babba mata biyune kawai sai maza guda goma Sha uku yayin da ad'akin su Amina ita kad'aice mace sai kuma d'aya d'akin nanma guda d'ayar ce shamsiyya. Matan malam suna da matuk'ar had'in Kai yadda zai wahala a yaransu ma kaban bance na wannan da na wannan. Yini su anty shamsiyya sukayi kamar yadda Amina take kiranta tare da bata shawarwari da buga mata misali akan gidansu da kuma nuna mata yadda umman ta take bin nanne mahaifiyar shamsiyya sau da k'afa duk da kasancewar Nanne wacce ainihin sunanta Zahra u irin matan nanne masu fad'an tsiya, hakan bai hanata jin dad'in zama da Mariya ba (Umma) domin ita mutunce mai mugun hak'uri dan zan iya cewa duk wani hali na Amina da shiru shirunta a wajenta ta gadosu, tun bayan da aka kawota gidan malam Babba ta kama yaran nanne ta runguma tamkar nata dake tana da matuk'ar ilimi haka take dad'a fahimtar dasu duk wani abu daya gagaresu a makaranta hakan ba k'aramin dad'i yayiwa malam da Nanne ba gaba d'aya tasakarwa Mariya ragamar yaran hatta kayansu d'akinta suka koma sannan itace ta aurar da Shamsiyya yayin da tunda aka haifi Amina Allah ya jarabce ta da masifar k'aunar yarinyar wacce tun tana k'aramar ta take da wannan hak'urin abin har tsoro yake bawa Nanne takan cewa malam kodai yarinyar bata da lafiyane.murmushi yakeyi mata a duk lokacin datayi masa irin wannan tambayar yace "Zahra'u kenan ai kowane bawa da kikegani yana da kalarsa ita wannan kalar ta kenan hak'urinta har ya zarta na uwar ta" Baki Nanne takan tab'e tace "sam ni wallahi hakan bamin dad'iba wani hak'urin idan yayi yawa a cutane" shima dariyar yake mata baya k'ara tankawa. Sosai shamsiyya ta d'an bata kad'an daga tarihin gidansu da irin ribar da Umman take ci na irin tsantsar hak'urin da Allah ya hore mata Basu bar gidanba sai bayan sallar la'asar kuma har lokacin haj. Sailuba bata dawoba. _________________________ Tunda haj. Zakiyya tafara jan sailuba wajen malami bata tab'a kaita waje mai wahala da ban tsoron wajen ba dan haka ta matuk'ar wahala tun kafin ma su kai wajen domin tafiyar k'afa ce wacce koda tayi rayuwar k'auye bata tab'a, sai dai abinda ya matuk'ar k'ayatar da ita shine yadda suna zuwa malamain ya hau zayyano mata dukan abinda ya kawosu, sannan shi da kanshi yafara dace"kinyi babban kuskure da har kika k'i yarda ki haihu da mijinki Kuma d'an uwanki Baffa domin dakin haihu dashi shine samun nasarar rayuwarki ni bana fad'awa mutum abinda zai kasance karya dan haka nake tabbatar miki da cewa ita wannan mata zata haihu itace uwar 'ya'yansa sai dai kuma ke kin riga kingama da rayuwarki domin keda haihuwa har abada kin gama lalata mahaifarki da k'wayoyin hana d'aukar ciki shekara goma shabiyar ba kwana goma sha biyar bane babu ke babu haihu amma zaki mulki mijinki da kishiyarki yadda ranki yake so. Duk inda wani abu mai suna tashin hankali yake sailuba ta shige shi dan tun kafin malam ya k'arasa mata jawabi ta fashe da wani fitinannen kuka domin wani iko da k'udura na ubangiji a lokacin sai taji babu abinda take buk'ata sai haihuwar sai dai ta riga ta gama da rayuwarta tun farko a tunaninta Baffa da yake d'an boko me zaiyi da tarkacen yara su hanashi sakat. Ranar dai bata tsaya amsar sak'on komai a wajen malaminba saboda tsantsar tashin hankalin data ke ciki wujiga wujiga ta dawo ba ita ta shigo gidan ba sai bayan sallar Isha dan lokacin Baffa yana massalaci Amina tana d'akinta tana sallah, dan haka duk basu san da dawowar taba. Tayi kuka kuka dana sani da nadama mara amfani domin bakin alk'alami yariga ya bushe Saida tayi jinya saboda tsabar bak'in ciki tareda cin alwashi iri daban daban duk akan abinda ita tajawa kanta Muje zuwa daga taku Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JINANA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 10 Sai bayan kwana shida suka koma wajen malamin wanda Sailuba tace so take daga mijin har amaryar tasa su zamo a k'ark'ashin ikonsa sai abinda tace zasu Kuma su kasance suna matuk'ar jin tsoronta duk abinda ta basu umarni suyi mata shi jiki na rawa. Sosai malam ya had'a mata mugun asirin da ta dawo gida ta aiwatar dashi cikin ruwan sanyi ta soma azabtar da Amina batare da wata tsangwama amma bauta iri iri hatta wankinsu sailuba sallamar maiwankin tayi Amina ce wankinsu da guga girki shara wanke wanke da duk wani aiki na wahala tana daga zaune zata bawa Amina umarni ita kuma babu musu zata aiwatar. Cima mai kyau sutura mai kyau da tsada want bacci mai kyau babu abinda ta nema tarasa agidan Baffa ga kulawar dayake da ita amma uban aikin da ake jibga mata asiyasan ce yasa tafara wata irin rama wadda 'yan uwanta suke tunanin ciki ta had'u dashi mai laulayi tunda basu tab'a katarin zuwa sun tarar da ita cikin wannan uban aikin kamar jaka ba dan boka yace mata ta kiyaye sannan kuma ya tabbatar mata da cewa duk sanda Amina tasamu ciki to aiki ya lalace sai an sabunta. Haka Amina taci gaba da bautuwa a hannun haj. Sailuba a siyasance batareda ita kanta ta lura da hakan ba domin hatta abinci tare suke ci kuma zasu yi hira suyi wasa da dariyansu koda wasa bata tab'a nunawa Amina wani abuba duk da kasancewar bata k'aunar koda bud'ar idanunta taganta a gidan. Bayan wasu'yan watanni saiga Amina tana zuba laulayi mai masifar wahala hankalin sailuba kuwa idan yayi dubu to atashe yake domin tunda Amina tafara zazzabi Baffa yakaita asbiti aka tabbatar masa da cikine da ita ya tsinci kansa cikin tsantsar farin ciki ga wata kula ta musamman dayake Bata duk da yana iya bakin k'ok'arinsa wajen danne farin cikinsa dan gudun kada Sailuba taji babu dad'i. Tunda taji labarin cikin hankalinta yai masifar kad'awa lallai tasan cewa aiki ya lalace kamar yadda boka ya fad'a mata gaahi haj. Zakiyya basa k'asar ita da mijinta ya rakata ganin likita zafine ya had'ar mata dan dole ta danne damuwar ta tacigaba da bawa Amina kulawa ta musamman wanda ya d'auke hankalin Baffa akansu ganin ko baya nan ai sailuba tana nan. Da k'yar ta samu lambar haj. Zakiyya cikin taahin hankali ta sanar mata da abinda yake faruwa itama ba k'aramin kad'uwa tayi ba dajin wannan labarin sai dai ganin irin halin da k'awar tata ta shiga yasa ta kwantar mata da hankali ta tabbatar mata da nan da k'arahen wata zasu dawo. Haka dai haj. Sailuba ta daure tacigaba da bawa Amina kulawa na musamman yayin da aranata take kiyasta iya kwanakin da cikin ya rage ajikin Amina Baffa kuwa ba k'aramin Jin dad'in yadda sailuba take kula da Amina yakeba sai ta k'ara wani martaba da kima a idanunsa. Saboda tsabar iya kissa ko aikin da take azabtar da ita dasu ta daina dan acewar ta lokacin guda zata kwabar da d'anbanzan cikin kowa ya huta, yanzun dai bari ta tayasu raino yadda ko wani abun yafaru babu wanda zai zargi dasa hannunta. _________________________ Haka sukaci gaba da tattalinta har zuwa sanda haj. Zakiyya ta dawo a lokacin har ya shiga wata na uku yayin da Baffa kullum cikin take tsantsan da tsantseni yake shima dama can shi mutum ne Mai yawan kyauta samun cikin Amina yasa ya k'ara sosai akan yadda yakeyi. Kwana biyu da dawowar ta suka d'aga wajen boka sosai suka sha mamakin ganin yadda suna zuwa bai saurara da daga garesuba yabasu wani kullin magani yace "Susan yadda zata Shashi ashayi ba Madara ko gama Sha bazata yiba cikin zai soma murd'a maya ina tabbatar miki wannan cikin bazaya kwana dashiba ajikinta" Tace "ranka yadad'e inaso ayi mata abinda bazata k'ara d'aukar cikinsaba" "Bazai yiyuba domin tun farko na fad'a miki akwai yara atsakaninsu Kuma dole zata haifesu sai dai zaki iya yin yadda kikaga dama dasu shine kawai abinda nasani" Bayan sun baro wajen boka suka dawo gida nan ta ninka kulawar datake bata har zuwa kusan sati tana tunanin yadda zata aiwatar da shirinta batare da wani abu mai kama da zargi ya ahiga tsakaninsuba wannan kenan. Yau kam Amina tashi tayi sam batajin dad'i sai dai dauriya data rigayi dan kar ta d'aga hankalin mutanen gidan ganin yadda suke dai dai bakin gwargwadonsu akanta. Tana zaune afalo saman dugowar kujera hah. Sailuba ta rako k'awarta Zakiyya har inda take haj. Zakiyya ta k'araso suka gaisa tayi mata sannu da jiki, da ido tayima sailuba alamar kawai ta aiwatar yau. _________________________ Koda ta rakata ta d'an Jima suna tattaunawa da k'awar tata kafin suyi sallama inda ta barta nan ta dawo tasame ta sai dai sab'anin d'azu yanzun idanunta alumshe suke alamun barci yafara fisgarta wani kayataccen murmushi ta saki ta wuce kicin dake ranata d'anyi dan d'aya ya wuce abincin mutum biyu ta dafa mai rai da lafiya daga ita sai Baffanta dan tasawa ranta yau abincin nan bazai ciyu awajen Amina ba. Hakan cewa kuwa yafaru bayan ta gama dai dai lokacin ana kiran sallah ta fito da nufin tashinta sai k'eyar ta ta hango tana shigewa d'akinta, tabita da wani shegen harara aranta tana fad'in zanyi maganinki ne, daga haka itama ta wuce nata d'akin danyin tata sallar bayan sun idar kusan atare suka fito da Amina wacce takejin wata mahaukaciyar yumwa har hautsina cikinta yake saboda tsabar yunwar dake d'awainiya da ita ganin haka yasa Sailuba shigewa kicin da sauri ta had'o mata ruwan lipton ta kawo mata tace "Kinga k'anwata fara da wannan naga yau du bakici komai ba bazai yiyu ki farada abinci Kai tsayeba" sosai hakan yayi mata dad'i dan tana da buk'atar hakan, batare da wani tunaniba ta kafa kai tashanyen tas tun kafin ta dire kofin cikinta yai wani irin masifaffen murd'awa wanda tun jiya takejin hakan, da mugun k'arfi ta dafe cikin gami da fad'in washhh, wani b'oyayyen murmushi tasaki ama azahiri k'arasowa tayi da sauri ta kamata "lafiya kuwa k'anwata?" Ta bud'a baki kenan zatayi mata magana kenan cikinta yayi way irin fitinannen murd'awa sai cewa tayi"babu" cikin pretanding tace "babu me?" Kasa magana tayi saboda azaba Saida ta Jima kafin ya lafa mata ta dubi Sailuba tace "dan Allah anty ki taima kamin ki Kira Baffa yazo yakaini asbiti mutuwa zanyi" Da sauri ta nufi hanyar d'akinta tana fad'in "to bari na kirashi gwanda yazo kar wani abun yazo yafaru mushiga uku" Tana shiga d'akin tasaki wani uban tsalle tana d'ebo shoki farin ciki fal ranta yau burinta zai cika zatayi kwanan farin ciki wannan alak'ak'an cikin zai bar gidansu ta huta daganin tashin hankali. Muje zuwa بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDU AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 11 Anan ta k'yaleta tana ta faman murk'ususu yayin da tai kwanciyar ta saman gado tana waya da haj. Zakiyya a maimakon Baffa sosai suke shewa, Jin kamar motsi yasa tayi saurin katse Kiran tana laluben wayan Baffa. Anty shamsiyya ce ta shigo arud'e domin sanda ta shigo har Amina ta sume ga uban jinin dayake malala ta k'asan ta tana ganin haka tayi d'akin haj. Sailuba arud'e, sai dai tashin hankalin data gani akan fuskar sailuba yaci uwar nata dan hawaye tagani shab'e shab'e a fuskar ta tanama Baffa bayani halin da Amina take ciki. Cikin tsantsar tashin hankali yabaro kamfaninsa wanda yake ziryata a irin ranan dan ganawa da manya da k'ananun ma aikatansa. _________________________ Wuya ita wuya Amina tacishi kafin tasan inda kanta yake sai da tayi kusan sati guda acikin asbitin kafin tasan inda kanta yake ciki dai Kam babu shi domin ya riga da ya zube tun aranar. Sosai haj. Sailuba ta rik'a bawa Amina wata irin kulawa dan hatta Nanne wacce Sam bata yarda da Sailuba kuma tana nusar da Amina ta kula da takun matar dan dai sunk'i d'aukan abinda mahimmanci ne saida tazuba ido wannan karon ta k'yale sailuba da Amina amma duk wani takunta tana ankare gane hakan yasa Sailuba matuk'ar taka tsantsan. Babu wanda yakai Inna takaicin rashin cikin sai dai tayi musu addu'ar Allah yabada na aike tareda yiwa Baffa nasiha mai kamar jirwaye cewa ya kula da matansa ya sanya ido akansu da takunsu, duk da cewa bai gane me take nufiba yayi mata godiya ya maidata har gida dan bai tab'a yarda Innarsa tahau motar haya. _________________________ Kusan sau hud'u hakan yana faruwa wanda hakan yasa Baffa ya rufe ido yanama Amina bala'i da tambayarta nufinta akanshi ya lura haihuwane batasonyi dashi daga baya har k'asa ya durk'usa mata yana rok'on data taimaka ta haifa masa koda d'a d'aya ne yamata alk'awarin duk abinda takeso zaiyi matashi amma dan Allah kada ta k'ara yimasa asaran gudan jininsa. Hawaye hawaye fa take gani a idanunsa Baffa ne yake mata kuka da rok'on ta haifa masa 'ya'ya yana nufin ita ke zubar masa da yara idan tasamu ciki. Itama fashewa tayi da kuka mai k'arfin gaske zuciyar ta yana wani irin suya take kalaman anty shamsiyya suka shiga dawo mata akaro na hud'u data sake rasa cikin dayakai kimanin watanni biyar wanda har sunfara saka rai da shi tunda yafi sauran ukun jimawa. "Amina nifa nafara zargin kishiyarki akan wannan b'arin dakike yi ajere ajere duk dana san cewa komi dayake faruwa daga Allah ne kuma dama can Allah ya hukunta wannan cikin da suka lalace bamasu taka k'asa bane amma akwai sula kuma Koda ba haka bama idan kin zauna kinyi tunani taya ita bata haihuba zata bar wata tazo da daga baya ta cika gidan aikinsan dole zatayi wani abun akai duk wannan soyayyar da kulawar datake baki duk na banzane ga uban bautar dake da take a siyansace tunda kikazo gidannan baki gaba baki baya kullum ak'are ya kud'in guzuri inzaki farka ki gane ki farka sannan maganar gaskiya Amina ta inda zaki gane cewa magana na gaskiya ne idan kin sake samun wani cikin ko Baffan kada ki sake ki fad'awa sai dai su ganshi tunda na lura ke ba mai girman ciki bane irin girman cikin bane irin cikin Umma ne dake wanda inda anganshi to bazai k'ara sati guda ba zai fito duniya dan haka duk irin wahalar da zakici ki daure ki cije ki raini abinki dan tun mahaifarki tana iya d'aukan ciki zata zo ta gaza kema azo ana samun wata matsalar kinga kunyi duro kenan burinta ya ciki ke babu ita kinga anyi one one kenan daman abinda take so kenan. Ganin tayi tsaye ga hawaye na tafaman shatatowa daga idanunta yasa ya kamo hannayenta ya zaunar da ita asaman cinyar ta yana cigaba da hawayen tare da rok'on ta daure ta daina Yi Masa ganganci idan tasamu ciki, ganin cewa ko me zata ce ba fahimta zaiba yasa ta tsuke bakinta amma ranta banda suya babu abinda yake mata. _________________________ Wannan karon Saida tayi wajen wata hud'u kafin Allah yabata wani cikin mai d'an Karen laulayi dan haka kamar yadda 'yar uwarta ta bata shawara ta rik'a daurewa tana shanyewa dan tanaso ta tabbatar da abinda ta fad'a mata akan wannan kareemar matar ma kula da ita da damuwa da al'a muranta Hakan kuwa akayi duk yadda taso ganewa bata bata damar hakan ba haka ta rik'a daurewa tana nuna babu komai duk da kuwa irin bak'ar azabar datake sha wajen cimaka da kuma rashin son wani k'amshin haka ta dinga daurewa har zuwa lokacin da cikin shiga wata bakwai bai fitoba amma komai nata ya k'aru domin Amina macece mai matuk'ar kyau da diri gata fara tas babu ta inda ta baro mahaifiyar ta bafulatanar asali mazauna wani daji. Bayan wata guda lokacin cikin ya shiga wata na bakwai Kuma cikin kariya da k'udura na Allahu S W T A daga Baffa har Sailuba babu wanda Allah yasa ya gane cewa Amina tana da ciki, yayin da Baffa yadamu sosai har yana cewa kodai wani abun tayi dan karta haihu dashi? Tun bayan da cikin ya shiga wata na biyar ta daina duk wani laulayi sai dai dan banzan kwad'ayi kasancewar Koda yaushe itace a kicin tana bauta da aiyukan gidan hakan yasa duk abinda ranta yake so shi take dafawa taci son ranta kayan kwalam kuwa Baffa baya rabo da kawo musu dake ita Sailuba tafi ganewa ta narki abinci aci kaji da su kifi duk wannan abubuwan basu dameta ba haka Amina zatayi taci ta kuma bawa duk mai rabo dan itama mutum ce mai yawan kyauta kamar Baffa, sannan kuma duk wani irin kyau da shek'i data k'ara hakan baisa Sailuba ta ganeba kasancewar dama can ita d'in Mai kyaun ce, Baffa ne kad'ai ya kula da hakan saidai bai tankaba domin ya lura da ita a y'an kwanakin wani bin sai tayi ta k'unci irin dai abubuwan da ba a raba mai tsohon cikin dashi. Ranan wata laraba Amina ta tashi da matsanan cin ciwon mara cikin dare Allah yasa Baffa ad'akin ta yake ganin irin murk'ususun wahalar datake yasa yayi tunanin ko wani cikin tasamu zai fita dan haka yadda take kuka tana fad'in ya taimaka mata haka shima yake rok'on dan Allah karta bari wannan karon ma yayi asaran cikin dakyar ta iya bud'an baki tace"dan Allah ka taimakamin Baffa ba bari bane wannan karon haihuwa zanyi d'a zan haifa Baffa da sam bai gane abinda take cewaba ya fita da gudu zuwa d'akin Sailuba dagashi sai gajeran wando ko riga babu ajikinsa haka ya fice yatasota tasha mamakin ganin yadda Amina take murk'ususun ciwo wani b'oyayyen murmushi ta saki tana fad'in aranta magani yabi jiki Kennan, ita ta taimakawa Baffa yasa kaya yasunkuci Amina da gudu yayi waje sam kasancewar sa na likita bai kamata ace har irin haka yafaru a gidansa ba matarsa da suke kwana su tashi tare har tasamu ciki ya kai tamakin haihuwa duk bai saniba, amma idan mukayi duba da cewa Allah shine me yadda yaso Kuma asanda yaso sai muga hakan ba abin mamaki bane. Labarin yafara sauyawa ne daga lokacin dayagama dubata ya tabbatar da abinda ya gani bai k'ara tabbatarwa sai da yayi mata scainin, tashin hankali yatad'a a rud'e domin ganin dan mutum muraran yana neman hanyar isowa wannan duniya mai cike da abin al'abi da mamaki. Kasa control d'in kansa yayi yafashe da wani k'arkarfan kukan dayasa Sailuba danno kai cikin d'akin da mugun gudu zuciyar ta kamar takarda tsabar haske tasani wannan kukan na Baffa yana nufin wannan karon ma sunyi messing babynsu saidai kuma abinda tagani ba k'aramin kad'uwa tayiba domin har lokacin bai kashe na'urar ba ga babyn nan wanda basu gane wane jinsi bane na ta wutsulniya sosai ta daskare a jikin k'ofa zuciyar ta yana wani irin masifaffen bugu. Wani irin juyi Amina tayi gami da sakin wani k'arkarfan nishi da gudu Baffa yatarota dan saura kad'an ta fad'o daga gadon tarotan yayi daidai da sallamar babyn izuwa duniya wadda ta fad'o ita da mahaifar gaba d'aya rasa yadda zaiyi yayi sai kawai ya zube gwaiwoyinsa ak'asa yayi sujjada shukuriyya kafin yayi saurin Kiran ma aikata suka shigo dakayan karbar haihuwa shi ya gyara matarsa da 'yarsu takafin ya rungumeta ajikinsa yana tofe ta da addu o I kala kala. Wani abin mamaki tun kafin Baffa ya sanarwa kowa haihuwa Muhammad yafara sanarwa haihuwar Wanda a yanzun yake shekara ta uku amatakin karatuntasa Wanda yakeyi Kuma zab'in Baffansa yayin da ak'asan ransa Kuma yasha alwashin bayan ya gama zaije yayi na soja wanda shine zab'i da ra'ayinsa amma yanzun kam zab'in mahaifinsa yabi yake Wanda ya zabar masa. Hakanan ya tsinci kansa da wani irin farin cikin kasancewar ganin Baffansa cikin tsantsar farin ciki, haka ma Inna ana fad'a mata haihuwar da kanta ta taso abinda bata tab'a yiba wato kwana agidan Baffa wannan karon cewa tayi ita zata kula da maijegon da'yarta wannan karramawa ta Inna ya k'ara mata kima da mutunci a wajen iyayen Amina. Ranan suna kuwa Saida Muhammad ya yabaro makaranta yazo suna yasha fad'a wajen Baffa domin a lokacin suna shirin jarrabawane, a lokacin murmushi yayi yace kasa daurewa ne. Tunda yai arba da kyakykyawar yarinyar yaji ta masifar shiga ransa shikenan Kuma ya tare a d'akin domin kullum ya fito daga b'anga rensa yana d'akin Ammey kamar yadda itama Baffa yasashi fad'a mata har zuwa sanda yakoma makaranta dakewar MARAYAM kamar yadda taci sunanta wanda take Ammey tace sunan mahaifiyar malam ne hakan kuwa yayiwa malam dad'i kulawa ta musamman yake bawa yarinyar kullum sai ankai Masa ita ya tofeta da addu o in tsari Sailuba kuwa Takuce maman islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ BA JINANA BACE 2021 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 12 Haka rayuwa taci gaba da tafiya, yayin da Sailuba sukayi amanna da malaman tsubbu wani lokacin suyi sara kan gab'a wani lokacin kuma sai b'ata lokaci da nesan ta kai da mahalicci. Wata rana Sailuba takaima k'awarta haj. Zakiyya ziyara anan ne take cewa "k'awata ni kuwa me zai hana ki karb'i Maryam?" Wani d'an iskan kallo ta watsa mata tace "amma k'awata basiranki ya gude ne ko?kirasa yar da zakice na karb'a na raina da hannayena masu albarka" "Hum k'awata kenan inbaki saniba ki sani rainon wannan yar shine zai baki duk wani abu da kike nema kuma ta hakane zaki cimma burinki akanta sannan zokiji" tajawo tayi mata rad'a, bushewa sukayi da dariya suka tafa sun jima suna kulle kullensu kafin su sallami juna. Haka Maryam taci gabada samun kulawa daga ta ko wane fanni kamar yadda Nanne ta buk'ata haka dole Ammey ta cire kunya take kula da yarinyar ta domin ta kula abokiyar zamanta ba irin wannan matan bane da suke son jan d'an wani jikinsu. Sai dai abinda yai masifar d'aga hankalin Amina shine sanda Maryam ta isa yaye kawai tace ita Maryam takeso abata tunda ita an tabbatar da bazata k'ara haihuwa ba, ita kuma Amina yanzune ma ta soma Kuma babu wanda yasan iyaka ci sai Allah dan Allah ya rok'ar mata ita ta temaka tayi mata wannan sadaukarwar. Wani irin masifaffen tashin hankali ne yakawowa ziciyarta farmaki take tafashe da wani fitinannen kuka mai mugun k'arfi wanda yasa duk suka maida hankalinsu kanta yayin da Baffa yake dubanta da masifar mamaki Sailuba kuwa wani b'oyayyen murmushi take saki azahiri Kuma hawayene yake ta rige rigen fitowa daga idanunta ta bala in kalar tausayi ta taso ta durk'usa agabanta tareda rik'o hannayenta tana wani irin kuka mai cin rai tace. "Dan girman Allah badan halina ba dan soyayyar da kikewa annabinmu muhammadur rasulillah (S A W) ki taimaka kiyimin wannan sadaukarwar na miki alk'awarin Maryam bazata tab'a sanin zafin cewa bata tareda mahaifiyar taba zan rik'eta da gaskiya da Amana zan kula da ita fiye da yadda bakiyi tunaniba kiyimin wannan temakon 'yar uwata" ta k'arashe tareda zubowar wasu hawayen Mai uban yawa. Wani irin tausayin tane ya rufe Baffa yasawa ransa Koda wannan ce kad'ai kwansa a duniya ya baiwa Sailuba ita halak malak ko ba komai Sailuba 'yar uwarsa ce jininsa Koda baya raye ita mai rik'e masa 'yarsa ne. Ta ko Amina wani mugun kallo ta watsawa Amina kuma tasaki wani mugun tsaki mai k'arfin gaske tace"Allah ya baki naki kema maman Maryam shine sunan data rad'a mata tun bayan haihuwar Maryam amma kisani kome zai faru bazan iya baki 'yata ba domin wannan ai zakunci ne ace an rabani da d'iyata wannan sam bazai yiyuba wallahi" ta k'arashe tana kuka bil hak'k'i domin yanayin kallon dataga Baffa yana mata shi yake nuna jin d'acin kalamanta, batareda ya k'ara duban inda takeba yacewa Sailuba "Karki damu insha Allahu babu wani abu dazaki nema kirasa shi matuk'ar yayanki Baffa yana raye dan haka bazakiyi kuka rayuwarkiba" daga haka ya tashi ya d'auko Maryam dake d'akin uwarta tana baccinta hankali kwance ya dawo inda suke har lokacin Sailuba bata bar kukan datake ba yace. "Gata nan na baki amanar ta ki kulamin da ita karki bari wani abun yasameta Kinga itake nan abinda Allah ya mallakamin a halin yanzu wannan kyautar ba kowa Allah yakewa irintaba nasan ko babu raina ke mai rik'e min 'yatane dan haka bana so kisawa ranki cewa bake Kika haifi Maryam ba haka banaso tasan cewa bakece mahaifiyar taba" Cikin wata irin razananniyar k'ara Amina ta sulale awajen ta fad'o k'asa sumammiya take suka yo kanta cikin tashin hankali suna jijjigata Baffa ne ya tashi da sauri ya kawo ruwa suka shafa mata take ta kawo ajiyan zuciya, zumbur ta mik'e tana wani irin kuka mai cin rai d'akinta ta shige da gudu yayin da Sailuba ta kalleshi tace " Baffa ko mu maida mata da 'yarta kar wani abun Kuma yazo yana dasamun jifa abinda takeyi" "Karki damu zata rage kinsan dole ne taji babu dad'i ace 'yarta guda d'aya tak an kyautar wanda bamu da tabbacin cewa tana da wani Kwan takakke bayan wannan musamman idan Kika duba irin yadda ta ringa samun cikin yana zubewa" Ita ko Amina tana shiga d'akinta ta fad'a saman gado tana wani irin masifaffen kuka mai matuk'ar cin rai tasawa ranta kome zai faru wallahi bazata bawa wannan matar yar taba matar da bataso zuwan yarinyar duniyaba duk wani irin tuggu da ta dinga had'a mata wanda ya dinga sanadin zubewar gudan JININTA tana sane mutumin kuwa da baya son ganin kwanka sanyin idaniyarta a duniya ai baka da mak'iyi sama dashi mayafinta ta zara kawai ta fice agidan tana kallonsu har lokacin suna dining Baffa yana rarrashin Sailuba datace zata dawo mata da yarta. Kai tsaye gidan su ta nufa tsabar rud'anin data shiga bai barta ta kula da malam dake zaune saman dakalin k'ofa ba ta shige d'akin Nanne wace fitowar ta kenan a wanka tana shirin zuwa duba surukar shamsiyya wacce ta sha ciwo Umma taje ta sake zuwa ita sai yau Allah ya nufa dake a tsarin malam baya yarda su fita rana d'aya sai dai d'aya taje d'aya ta jira. Tagama zura hijabinta Kennan juyowar da zatayi taji fad'owa Amina jikinta tana wani irin mugun kuka mai masifar cin rai, take jikinta ya kama rawa ta rik'e ta da kyau tana tambayarta ta abinda ya same ta cikin tashin hankali domin tasan duk abinda yasaka Amina kuka to lallai abin yakai intaha. Amina ta kwashe duk yadda sukayi da su Baffa ta fad'a mata cikin kuka ta k'ara da cewa 'Kuma Baffa yace ko kallon yarinyar kar na K'ara you amatsayin 'yata. Wani fitinannen kallo Nanne ta kafe Amina dashi yayin da ziciyarta yake wani irin tasa tace Taku ce maman Islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JINANA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 13 "Yanzun shi Baffan ne ya d'auke 'yar yabawa kishiyarki akan me shi ya haifa Miki yar ko su sukayi Miki rainon da nak'udar wallahi bazai sab'uba bindiga a ruwa" sosai Nanne ta hau fad'a ta inda suka shiga bata nan suke fitaba sosai ranta yai azabar b'aci ganin fad'an bazai fisshe taba ta finciki hannun Amina tana fad'in"zo muje gidan dole su baki yarki haka akeyin kyauta da abun wani mugunta" Tana bud'e labulan suka gabza karo da malam dayagama jin komai tayi saurin ja baya tana had'e rai danma kar ya dakatar da ita dan daga kallon irin kallon dayake binta dashi tasan cewa yagama jin komai " muje ciki ko?" Shine kawai abinda malam yace yana rab'a gefenta ya wuce had'e rai ta k'ara yi tana hararan bayan sa sai dai babu ikon musu dashi dan tun farko basu sabar Masa da hakan ba. Waje ya samu ya zauna saman kujera mazaunin mutum d'aya yayin da Amina ta zauna agabansa ta sunkuyar dakanta k'asa ita Kuma Nanne ta zauna gefen gado fuskar nan babu alamun annuri ta masifar cin magani dan ma kar malam yace zai hanata zuwa d'aukar ma 'yarta mataki. Gane take takenta ne yasa malam sakin murmushi yace "Zahra kenan Zahra'u manya Zahra'u sarkin rikici dan Allah Zahra in kin girma kisan kin girma inbanda abinki ina ruwanki da harkar yara 'yar nanfa tasace yana da iko akanta dan me Zaki goyi bayan rashin gaskiya to ban amince Miki zuwa ki zubar min da kima a inda nake da Martaba da daraja dan haka na kashe wannan maganar ke Kuma" ya fad'a yana nuna Amina karna sake hanin kinsa k'afa kin baro d'akin ki akan wani dalili mara tushe 'ya dai tasace Kuma yayi abinda yake so da ita ace danme kar naji kar na gani kinji ko" sosai malam ya rik'a yi musu nasiha har zuwa sanda yai shiru Nanne ta sauke ajiyar zuciyata tace "nifa malam bawai ina goyon bayan Amina bane saboda anbama kishiyarta yarta ba domin da ace suna zaune lafiyane to da hakan mu kanmu saiyafi Mana dad'i amma kishiyarta muguwar makirace datasan kan kissa ta mugunta" nan Nanne ta rik'a bawa malam irin labarin da shamsiyya ta fad'a mata da irin bautuwar da Amina take a siyasance a hannun Sailuba. Ajiyar zuciya malam ya sauke yace "karku damu domin komai na Allah ne Kuma duk abinda yake damuwa hukuncin Allah ne dan haka kusa aranku duk abinda zai samu mamana daga Allah ne domin babu wani abu dayake samun bawa face da sanin Allah" Sosai nanma ya kwantar musu da hankali sannan yayima Amina nasiha da hak'uri a duk halin data tsinci kanta hak'ik'a Allah baya barci, yace Nanne taje ta rakata Kennan Baffa yayi sallama' bayan sun gaisa da malam kafin yace komai malam ya soma bashi hak'uri abisa shirmen Amina har Saida kunya ya kama Baffa ya dinga sunne Kai yana dad'a bawa malam sannan yace adad'a bawa Amina hak'uri domin ansan anyi mata ba daidai ba amma yayi hakanne dan samun had'in kansu. Malam yace babu komai Allah yabada wasu masu albarka. Tunda suka dawo gida Amina tayi masifar d'auke kanta daga garesu ta daina kulasu duk wani aikin gidan ta ajeshi tsakanin ta dasu sai ido hatta kicin na falonta take shiga, sosai hakan yake sosa ran Baffa shi da kanshi yasan cewa basu kyauta mata ba sun nuna son ransu kuma zata na ganin cewa dan Sailuba 'yar uwarsa ce shiyasa ta nuna son Kai acikin al'amarin. Da k'yar yasamu yasha kanta suka koma dai dai haka ma mama kamar yadda ta rad'a wa sailuba suka koma daidai amma Kuma bata Kara yarda tayi mata wannan uwar bautar ba. Wata irin sangartacciyar rayuwa aka koya Maryam wani irin mugun gata ake gwada mata wanda babu wanda ta ragawa rashin kunya wa kowa sai anyi magana Sailuba tace ai yarinyace haka rayuwa taci gaba da tafiya an mugun tab'ara Maryam duk girman mutum bai wuce ta zageshiba. Koda Nanne ta kula da yadda Amina ta watsar da Maryam da al amuranta fad'a ta Mata tace yau idan akace Maryam ta lalace kafin kowa yaji ciwon haka kece zakiji domin kece kika san zafinta ita adirenta ta ganta dan haka ita hakan bazai tab'a damunta ba domin batasan ciwontaba haka Nanne tayi ta mata maganganu tare da nuna mata illar kawar da kanta da tayi daga kan Maryam. To Kuma duk yadda taso Jan yarta ajiki tareda nusar da ita hakan ya faskara see domin Sailuba ta wuce tunanin mai tunani akan komai musamman ta fannin makirci ta kware fiye da zaton me karatu. Haka rayuwarta yacigaba a tab'arb'are babu kwab'a babu harara duk abinda take so shi ake mata a ta gefe guda kuma tun bayan da ta Kuma haifar yara maza guda biyu duk basu zo da raiba bata sake Koda b'atan wataba sosai abin ya dameta ga matsalar Maryam da Allah yayita da fitinar tsiya ga shegen rashin kunya ga d'an banzan tsokana abin ya masifar damunta amma sai takema yarta addu ar Allah ya shirya. A b'angaren Sailuba kuwa tunda taga daga Kan wannan yara anja kusan shekara bakwai Amina bata k'ara Koda b'atan wataba hakan ba k'aramin faranta ranta yayiba dan haka ta watsar da duk wani nema da take akanta ta maida dukan wani asirinta akan iya Baffa shi kad'ai riba biyu ga Baffan ta ga Kuma Maryam data b'atar da duk wata hanya da zata gane cewa Amina ce mahaifiyar ta. Lokacin da MD ya dawo ya tarar da irin tab'arb'are war da rayuwar Maryam yayi ga fitsara ga raini wa kowa ba k'aramin tashi hankalinsa yayiba ya dinga bin Ammey yana fad'an bata kyautaba databar rayiwar Maryam awajen wacce batasan ciwon haihuwaba amma sam Ammey tak,'i kula hakan tama daina sauraron say domin tasan cewa kotayi magana babu abinda hakan zai haifar sai fitina Kuma tun wataran da taga abin yana yawa tayi ma yarinyar fad'a ta zageta ta kuwa kamata ta zane ai kuwa ranar taga ruwan bala I a wajen Baffa dan rufe ido yayi ya tujareta har da mata iyaka da yarta abin ya k'ona mata rai sosai har Saida tayi zazzab'i saboda bak'in ciki shi kanshi Baffa da yaga kamar bai kyautaba yasa ya dinga rarrashin ta daga baya. Da farko MD yaso jan Maryam ajiki amma Sailuba bata bada damar hakan ba domin da kanta ta dinga tusa tsanar Muhammad a zuciyar Maryam har taji duk duniya babu wanda ta tsani ta bud'a ido ta gani irinsa. Tun yana daurewa halayyar tata har abin yafi k'arfinsa domin halin yarinyar ya wuce tunanin mai tunani, hakan yasa yai masifar tsanar wannan mugun halin nata yarinyar da ya ginu da tunanin yadda zai jata jikinsa ya gwada mata Koda gutsuren k'aunar da mahaifinta yake nuna masa amma ina makircin uwar rik'onta bazai bari hakan ya faruba. Sanda Maryam ta cika shekara goma dai dai Amina ta Kuma haifo yaronta katon gaske sak Maryam har yaso yafi Maryam fari da manyan idanu, wannan haihuwa ba k'aramin gigita tunanin haj. Sailuba yayiba domin ta rigada tagama sawa ranta cewa Amina tagama haihuwa ita da k'ara haihuwa har abada, kamar yadda sabon bokan da suka sake ya fad'a Mata. Tun kafin suna take tunanin hanyar dazata b'ullowa wannan yaron dan bata tab'a jin abinda ta tsana sama da wannan yaron ba duk iya yanda taso had a makircin ta akan yaron idanun Baffa ya rufe abinda ya k'ara d'aga hankalin Sailuba yadda atake Baffa yayiwa Amina kyautar wani kat'on gidansa na G R A sannan Kuma yaron wanda yayima hud'uba da Abdul Nassar yabashi companyns na takalma company data gama cin buri akai tagama tsara duk yadda zata yi ace anbarwa Maryam shine yau ake bama wani banza da uwar banzan lallai Baffa ya tarowa kansa Ba k'aramin murna MD yai da haihuwar Abdul Nassar ba dan ko ba komai yasamu aboki duk da kasancewar sa mutum mara son hayaniya hakan bai hana sunyi wata irin shak'uwa da yaron ba. Haka rayuwar Nassar yaci gaba da tafiya cikin tsantsar so da kulawar Ammey sa da Kuma bross d'in sa kamar yadda Baffa yasa su dinga fad'a masa. Sosai Nassar yataso yaga yadda akema uwarsa cin mutunci a fakaici shima ya kuwa yace baisan wannan ba dan haka duk abinda akasa Maryam taiwa Ammey sai ya rama akan Mama tun suna had'uwa suyi ma yaron duka har zuwa lokacin da Maryam din ta fara rage wasu abubuwan domin daga yanayin yadda Ammey take tafiyar da al amuranta yasa ta gano nagarta da kyaun halin Ammey yasa ta sassauta mata duk da cewa ba wai ta dena dukabane. Haka dai rayuwar yacigaba yayin da agefe guda MD yakasa jurewa fitsaran Maryam yasa duk abinda Masa yake kamata yayi Mata d'an banzan duka tun tana zaginsa idan ya daketa har azaba yasa ta daina sai dai tayi ta fad'a masa bak'ak'en magan ganu shima Kuma sai ta tabbatar databa da tazara mai yawa atsakaninsu ga wani tsinannen d'abi a da aka koya Mata na yawon club wanda mama takance tayi komai ba komai ubanta ya tara mata Hakanne yasa Maryam take abinda taga dama kud'i kuwa ko nawa take buk'ata za a bata batare da bin ba asin abinda tayi daauba Kuma Koda an bata yanzun anjima ta buk'ata wanda suka fisu Bata za ai batare da wani bin diddigiba. Hakanne yasa Ammey dauk'e kanta akansu har zuwa yanzun da Maryam ta fara jan d'an uwanta ajiki ta dai ce aun daina fad'a to bari mu gani da gaske ne ko Kuma wani shirin ne Maryam da uwarta suka Kuma yowa Muje zuwa Daga taku Maman Islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 14 Cigaba Suna shiga d'akinta Nassar yace "Adda ni nafasa game muje muyi kwallo kawai, kawai ko muyi basket kallonsa ta d'anyi tace "a a nak'i wayon saboda kasan kafini kwarewa anan ko" yace "to naji buga game d'in Allah yabawa mai rabo sa a" "Hello k'awata akwai matsala fa wallahi ina cikin damuwa"ta d'aya b'arin haj. Zakiyya tace "mun shigesu wane irin matsala Kuma kinsanfa bana juran irin wannan k'ananun zantukan yanzun sai kisa cikina ya murd'a" "Hmmm kedai bari k'awata wannan tsinanniyar matar Saida tasan yadda tayi ma Maryam asirin da gashi tana neman sawa Maryam tafi k'arfi na zokiga yadda take wani jan wannan shegen yaron ajiki wallahi karkiji zuciya na" Itama Zakiyyan ajiyar zuciya ta sauke idan bata manta aikinsu na farko ba bokan ya tabbatar musu da cewa ba ko yaushe ne suke da nasara ba dole wani lokacin a jarrabisu da rashin nasara dan matar atsaye take itama bata sanya wajen addu a sannan babanta ma tsohon mugun matsafine" kujifa? Sosai suka shiga neman mafita wanda daga k'arshe dole suka yanke komawa wajen tsohon bokan da suka daina zuwa tun tuni. Maryam kuwa suna d'akin har lokacin suna buga wasa da Abdul sai rinto take masa da ya cinye saita ce ba hakaba tun yana hak'ura har shima yai zuciya ya tashi ta dubeshi "ina zaka?" "Wallahi na daina wasan sai na cinye saikice ke baki yardaba kuma ke kike min rinto nadaina shike nan" yafad'a kamar zaiyi kuka tace "to shikenan k'anina zokaji wani abu" ya rank'wafo kamar zaijin ya kuwa d'auke wayarta daya gama fakonta ya haddace password d'inta, ai kuwa ya zuba da gudu ko takan Baffa da Ammey da har lokacin suke dining bai biba ya arce waje, can saiga Maryam d'in ta biyoshi tana fad'in "wallahi inbaka bani wayana ba saina fasa baka wannan abinda nace" ganin har ya fita itama tabishi da gudu yayin da iyayen suka bisu da kallo cikin sanyin rai. Da gudu ya shige lambu itama ta rufa masa baya sam idanunta bai kula da dutsen ba sai data taka santsi ya d'ebe ta tafi zata fad'i tasaki k'aran firgita jinta ajikin mutum yasata sakin wani irin ajiyar zuciya. MD wanda tun shigowar Abdul da gudu ya dawo daga duniyan tunanin daya tafi ganin Maryam ta biyoshi tana hayaniyan data saba indai antab'ota yasa ya maida hankalinsa kansu baisan ya akayi ya isota lokacin datayi sufa zata fad'iba shidai kawai yaganta ne kwance saman kirjinsa Maryam wacce sai lokacin ta bud'e idanunta ganin jikin wanda take tayi saurin tashi tare da sakin wani d'an uban tsaki, abinda yafi tsana a rayuwarsa ya fincikota da mugunta ta Kuma fad'owa jikinsa Saida tasaki k'ara saboda bigewan datayi da gwaiwar hannunsa, cikin b'acin rai yace "dawa kike? ni sa ankine da zakimin tsaki?" Dubansa tayi taga har idanunsa ya sauya tasani Sarai idan tashiga hannunsa bazataji da sauk'i ba d'auke kanta tayi tana hararan gefe tace "ni ai ba dakai na keba da wancen nake" ta fad'a tana nuna dutsen daya tad'eta, duk da yanayin dayake ciki sai da abin yaao dariya yadan murmusa ya tun kud'eta daga daga jikinsa sai data kai k'asa ta na tashi kuwa ta galla masa harara da murgud'a baki tace dakai nakeyi me ka isa yimin yi yayi kamar zai kamota ta taka da gudu ta wuce cikin gidan. Da yamma suka fito domin zuwa gidan malam gaba d'aya har Baffa wannan k'aida ne idan ya dawo sai yajema malam tare da dumbin alkhairansa mai tarin yawa. Bayan sun gama gaisawa da malam Amina da Nassar sukayi cikin gidan yayin da Baffa ya tsaya anan suke dad'a gaisawa da malam anan malam yake tambayarsa ya kuwa lek'a Inna? D'an sunkuyar da kansa k'asa yai yana sosawa cikin ladabi yace "ban Sami zuwaba har yanzu amma ina mata aike akai akai" Malam yace "zancen banza kenan ance maka wai abin hannunka ne maganin matsalar ta karfa kamanta Kai kad'ai ne d'an da Allah yabata a duniya ina mai tabbatar maka tafi buk'atar ka akan duk wani abu da kake da Kuma Allah ne kad'ai yasan halin datake ciki akan hakan, dan haka nake umartarka daka daure kaje" Shiru yayi cikin d'acin rai yarasa wannan masifa yarasa abinda yake damunsa shida mahaifiyarsa amma zuwa inda take ya gagaresa meke nan meyake faruwa da rayuwansa ne? Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JINANA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 15 Sun jima sosai a wajen malam yana dad'a fad'a masa maganganu masu sanyaya jiki da karyar da zuciya sosai yaji babu dad'i shi da kanshi yana matuk'ar kewan mahaifiyarsa tsohuwar Allah ta ala amma ya kasa sauke hakkinta dayake kansa tsayin lokaci, har hawaye Saida yayi malam ya rik'a lallashinsa tareda nuna masa kuskurensa. "Adda zo muje gidan su anty Halima dan Allah" hararansa tayi tace "bazanjeba ka manta dazu kasa Baffa ya hanani zuwa sayan kayan kwalliya Kaine kace na cika ta adin kud'i" "Kiyi hak'uri dan Allah Adda na daina" da k'yar yasamu yasha kanta suka fito, yamma ce sosai ga uban hadari bak'i k'irin har tace su koma Nassar ya nace suka fito dai dai nan motan MD ya shigo sanye cikin kakinsa da alama ya dawo atafiya ne d'an tun ranan data k,wace suka had'u alambu basu k'ara had'uwa ba sai yau da murna Nassar yai wajensa yayin da Maryam ta d'auke kanta kamar bata gansa ba. Kanta na k'asa batasan ganinsa, duk da kasancewar Nassar ya d'auke hankalin Shi da surutu amma dukkan motsinta yana ankare ta gefen ido yake k'are mata kallo yana mamakin yadda take da d'an Karen d'aukar Kai da mai da kai ba komaiba an riga an gama da ita ranan dayabar garin yanaji ana fad'a da ita akan ta zagi mai gadin kusa da su mama tana goyon bayanta akan wai da abin daya mata hakanan Maryam bazata zageshiba sai da dalili wannan abu ya bala in b'ata masa rai. Sai dai masu Karin magana sunce hannunka baya rub'ewa ka kayanke ka yar dole zai koya Mata tarbiyyan da aka gaza bata tun farko amma yasani fitsara ne zaisha kala kala ita Kuma taci bak'ar wahala. "Kira min Addanka Nassar" yafad'a cikin rashin sonaganar sa, sai da Nassar ya k'ara kallon MD dan mamakin aiken daya masa "bazaka bane" yafad'a cikin daka tsawa da gudu ya k'arasa "Adda kizo inji bross" wani banzan kallo Maryam ta watsawa Nassar kafin taja tsaki tace "ina wasa dakai ne dazaka zomin da wannan banzan sak'on? To ka koma kace bazan"""""""""kafin tak'arasa taji d'all asaman leb'b'an ta da mugun k'arfi da sauri ta dafe bakinta tana kallon sa yadda yai bala in daure fuska saitaji wani irin shakkarsa ayau d'in, shikam k'ara tamke fuska yayi yace "wato ke maraya kunya ko kullum iskancinki k'ara gaba yake to ni d'in nan sai na gyara miki zama ke k'aramar mara kunyace wallahi kuma ku koma babu inda zaku fita da wannan hadarin" Maryam wadda har idanunta ya fara ciki da kwalla ta juya batareda ta kalleshi ba har yana mamakin rashin mai da raddinta dan yasan hali saidata tabbatar takai tsakiya kafin ta juyo ta galla masa harara tace "kuma sai Allah yasakamin ban yafe ba" ya d'an taka kamar zai bita ta shige da gudu, Murmushi ya d'an sosa kansa aransa yace wannan saitata ba k'aramin aiki bane andai riga da an cuci uwarta ne an lalata Mata tarbiyyan d'iya. Tana shiga falon taci tuntub'e da k'afar Ammey da ta mik'e tana zaune saman kujera saura kad'an ta fad'i Ammeyn ta tarota "ke lafiya kike wannan uban gudun saikace wata wacca aka biyo?" Maimakon amsa saita fashe da kuka Ammey ta d'ago kanta saita ga lebanta a kumbure gashi har sun d'an tsatstsafo da jini "waya dakar miki baki har ya kumbure haka?"kasa bata amsa tayi sai sabon kukan data fashe da. Nassar ne yace "wallahi Ammey bross ne ya dakar mata baki da k'arfi saikace yasami sa ansa" Hararan Nassar Ammey tayi tace "haka nan dai bazai daketaba da abinda tayi masa inba hakaba bazai tab'a taba" Hararan Ammey Maryam tayi sannan taja tsaki tabar wajen dama rashin kunyar ta bawai ta dainayi mata neba in babu Nassar awajen tana d'an tab'awa da kallo duka suka bita yayin ta shige d'akinsu mama tana can gidan haj. Zakiyya ta rasa tsiyar da suke k'ullawa agidan wannan haj. Zakiyyar hakanan ta tsani matar ko gidan ta zo sai maman tayi da gaske take gaidata. Bayan wata uku Sakamakon jarrabawan su ya fito ba k'aramin farin cikin sakamakon Baffa yayiba haka Kuma haj. Sailuba tasa dole yasai mata mota matsayin gift d'in cinye jarrabawan datayi ko kad'an hakan baima Ammey dad'i ba amma bata da ikon magana tunda anyi mata iyaka da hakan amma kullum tana kaiwa mahalicci kukanta ba dare ba rana tana sane da cewa baya bacci tana fatan ya bimata hakkinta akan yadda ake d'ora mata rayuwar d'iya. Haka ma muhammad baiso akaba Maryam sarkin rawar Kai motaba ta mama datake fita da itama bason ransa bane amma Baffa yace yayi hak'uri ya riga da yayi mata alk'awarin intaci jarrabawan duk abinda take so zai sai mata. Hakama b'angaren cigaban karatunta Baffa yace ta zab'i duk k'asar datake son yin karatu' tace ita tace ita Dubai take so tana son gadon Baffa amma Islamic medicine sosai hakan yayiwa Baffan dad'i sai dai wannan karon Muhammad yayi nasara Dan cewa yayi k'anwarsa mace bazataje wani k'asa karatuba anan kusa dasu zatayi. Wai Maryam batasan sanda ta fashe da wani mugun kuka ba tace "ai dama na dad'e da sanin cewa baka k'aunar mu nida mamana wai ma ina ruwanka da rayuwana ne da zakabi ka takura ka addabeni ni bana shiga huriminka amma ni duk kabi katakurawa rayuwata yadda ka tsane ni haka nima NA TSANEKA NA TSANEKA NA TSANEKA haka maganar ta yayi ta amsa kuwwa a kunnen tunda yake bai tajin maganar daya masa d'acin wannan ba sosai abin ya dake shi da sauri ya tashi da nufin binta Ammey ta dakatar dashi haka ma Baffa sukace ya k'yale ta yanzun tana cikin zafine. Maryam bata san kukan rashi ba a rayuwarta an d'ora tane akan cewa ubanta yana da komai dan haka duk abinda take so zata samu hakan ne yasa tai masifar saka ranta da tafiya Dubai yayin da Mama take dad'a ingizata wannan dalilin yasa taji ta Kuma tsanar MD aranta fiye da yadda ta tsanesa abaya. A b'angaren MD kuwa tunda ya koma d'akin sa maganar Baffa yake tayi masa Kai kawo "Muhammadu ka taimakemu kaja Maryam a jikinka ka rage wannan 'yar tsamar dayake tsakaninku domin duk duniya baku da kamar junanku Kai kafi kowa sanin haka sannan in Mai k'ara jadadda maka alk'awarin d'an uwana Hassan bazai tab'a tashi a banza babkoda k'asa ta rufe idonsa babu abinda za a fasa. Sosai abinda Maryam d'in ta masa ayau yai masifar tsaye masa arai bai tab'a jin d'acin abinda take masa irin na yau d'in ba ya jima yana Kai kawo kafin ya samu Kiran gaggawa daga office dan haka ya shirya cikin sauri ya fice Tunda ga ranan bai k'ara had'uwa da itaba dan ko fitowa tayi ta jangoshi komawa take da gaske bata son ganinsa wani b'acin rai take tsintar kanta a ciki duk lokacin data yi arba dashi. Shi da kanshi ya nema mata makarantar da ransa yake so sai da ya gama mata komai sai sa hannun da yazama dole ita zatayi da kanta sannan ya kawowa Baffa komai sannan yacewa Baffa indai yana gari to shine zaina kaita ya kuma d'auko ta hakan yasa hankalin Baffa ya fara kwanciya. Maman Islam CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM 16 Koda Baffa yazo musu da maganar makarantar tsalle sukai suka dire kamar had'in baki sukace su indai abu daga hannun MD ya fito basa sonsa, ranan haj. Sailuba taga ruwan bala i wajen Baffa bata tab'a tunanin ya iya jaraba hakaba sannan a k'arshe yace matuk'ar tasaka Maryam ta bijirewa makarantar sai tasha mamakin sa badan tasoba ta lallab'a Maryam ranan Monday tayi shiri cikin tsananin fushi. Cikin tashin hankali ta Kira haj. Zakiyya take fad'a mata yadda sukayi da Baffa da irin wutar daya bud'e mata abinda bai tab'a yimata ba tace "ni abinda yasa bana son kusancinta da wannan tsinannen yaron saboda" banji abinda tace mataba saijinai haj. Zakiyyar tana cewa"muci gabada shirinmu k'awata komai zai tafi yadda ya kamata itama Deedah can zataje dole ko bata so domin aikinmu yafi tafiya dai dai Kuma dole zasu zama k'awaye na irin mamakin nan ta hakanne aikinmu zaifi tafiya. Haka dai sukaci gabada kulle kullensu wanda su kad'ai sukasan abinda suke shiryawa. Zaune suke afalon suna d'an tab'a hira jefi jefi dan matuk'ar Baffa yana gari bazaka tab'a gane asalin halin Sailuba ba shiyasa Baffa yake ganin har tafi Amina son Maryam baisan irin wainar da ake toyawa agidansaba kuma bai tab'a ganewa ta kalan halayen yarinyar ba domin son dayake mata da kuma muguwar kisisinar haj. Sailuba bai bashi damar gane abinda take tafiyar dashi na rayuwarta ba domin ta toshe duk wata hanya da zai gane hakan da asirinta da kuma kissa. Koda tagama shirin ta cikin wani bluen swiss mai matuk'ar kyau da tsada kasancewar ta mayyar kwalliya ba k'aramin ado ta tsarawa kantaba saikace wacce zata gidan biki. Kanta tsaye b'angaren Baffan ta wuce dan har yagama shirinsa yau zai koma wannan karon China ya nufa dan shigo da wasu kaya dan haka shima cikin shiri tasame shi, ta d'an had'e rai tace "Baffa ina kwana?" "Kin tashi lafiya merona?" "Lafiya tace ganin shi cikin shiri tace Baffa tafiya zakayine?" "Eh Maryam Kinga wannan karon na dad'e dayawa ga kayan dana zo dasu saura kad'an dan haka daga China zan wuce Dubai dan shigo da sauran kayan harda dogayen rigunan dana tab'a kawo miki to suma na d'an gwadasu suma naga sun tafi har ana ta cigiyarsu dan haka suma zan siyosu" sosai hakan yaima Maryam dad'i arai sai dai wannan karon bata nuna rawan kantaba tace "Allah ya k'ara bud'i da d'aukaka Allah ya kare mana ku Baffa daga dukkan abin ki dan fiyayyen halitta amen" Sosai Maryam ta d'auko wasu daga hallayar mahaifiyar ta na yaba kyauta duk kankantar abu da kuma kyauta ga duk wanda take tareda dashi sannan bata da k'yamar wanda take ganin tafishi ko natane wannan halayyar yana matuk'ar burgesa. "Baffa ya maganar motana kaga yau zan fara zuwa school Kuma bani da ko sisi a account d'ina mama ta rance bansan abinda mama take da kudiba ita bata ajiyeba kuma bata barni na ajiyeba saikace mai caca" Sosai maganar ta yabawa Baffa dariya yace karki damu my dear zan bud'e miki sabon account komai da komai da sunana ATM kawai Zaki amsa duk sanda kikaso ciran kud'in sannan yanzun zan miki transfer dubu d'ari biyar sai ki kiyi amfani dashi kafin na dawo motarki kuma so nake ni da kaina na zab'o miki mai kyau da tsada" tace "Baffa ni kaga kalar da nake so ta fad'a" tana nuna masa fuskar wayarta zaro ido Baffa yayi sannan yace "wannan kikeso MAMAN malam tab' wannan koni bazan iya lale million 25 nasai mota dan fariyaba anayi wutar duniya Maryam nasai miki ta 5 million inba hakaba sai dai ki hak'ura wallahi" Ganin bazatayi nasaraba tace to Baffa amma kud'in dakace zaka zuba min yayi kad'an kaga wancan karonma kafin ka dawo har na dawo abin tausayi" "Naji zan k'ara Miki d'ari biyu akai" tace "na gode Allah ya tsare mana kai kaje lafiya ka dawo lafiya" "Amen ya Allah dota" daga hakan Baffa ya sallameta bayan ya bata dubu dari a hannunta kafinma ta k'araso ta b'oyesu ajakar ta har sanda ta sakko suna falon ta d'an kalli mama tace "mama bani kud'in makaranta zan wuce" Maman ta d'an dubeta tace"Baffa bai baki bane?" "Ya bani sun min kad'an" "Je cikin jakana inajin baza a rasa canjiba" da sauri ta shige d'akin ta fito tana k'irga kud'in, sannan ta dubi maman tace "mamana na d'auka duka dubu ashirin da biyar ne" jin abinda tace sai da Ammey ta d'ago ta dubeta suka had'a ido ta kuwa galla mata harara ta d'auke kanta, mama tace "to Maryam ki kula da kanki kiyi abinda yakaiki domin babu mamaki ya kasance wannan shine zai kasance gatanki anan gaba" "Ban gane me kikeson ceminba mama banason irim wannan maganan dan Allah mama" Irin wannan maganan ya zama dole Maryam domin da sannu zaki iya rasa wani abu mai muhimmanci arayuwarki ko mu ko dukiyar ko dukanmu" Yanzun ba iya Maryam ce take kalloan maman tata ba harda haj. Amina dataji gabanta ya tsinke take ta hau karanto hasbinnallahu aranta yayin da Maryam tabar gidan cikin sanyin jiki. A jikin mota ta hango MD sanye cikin kakinsa da alama shima daganan office zai wuce ganin yadda yai masifar had'e rai sai da gabanta ya fad'i amma dake itama jan wuya ce sai ta had'e nata ran tak'arasa zata bud'e bayan motar tsawan daya buga mata yasa batasan lokacin data bud'e gaban ba sai tsintan kanta tayi kawai a zaune jikinta na rawa. Sai da ya daidata zamansa sannan ya dubeta yace "ke baki iya gaida mutane bako, ita mahaukaciyar 'yar rainon naki bata koya miki girmama manya bane?" D'auke kanta tayi gefe tana k'unk'uni tare da hararan waje ya wani fincikota da k'arfi har Saida kanta ya bugu da gwaiwar hannunsa "me kike cewa ina wasa dake ne ko?" Shiru tayi batare data tankasa saima hawayen daya ciko mata abinda tunda yake da Maryam bai tab'a ganina, karaya a tare da ita lallai duk abinda yasanya ta a wannan yanayin ba dan k'aramin abu bane. Tunda yaga haka sai ya fasa hukuntatan ya tunkud'eta ta koma mazaunin ta ko kallonsa bata kumayiba har suka Isa makarantar ya fito itama ta fito har lokacin jikinta a sanyaye duk da rashin jinta sai yaji tausayin ta ak'asan ranshi amma Koda wasa bai bari hakan ya nuna akan fuskar Saba, har ta juya ya kirata ga mamakinsa saiyaga ta dawo ta tsaya a kusa dashi sosai yasan cewa da abinda yake damunta domin ya jima da sanin cewa indai tana cikin yanayin damuwa to ita d'in rak'umi da akalace sai yadda kayi da ita. Dubu biyar yabata kamar bazata karb'a ba sai Kuma ta karb'a batareda ko kallon inda yake ba bare yasa ran zata gode tayi gaba abinta murmushi kawai yayi yabi bayanta suka jera yayin da idanu sukayi kansu duk inda suka gifta sai an kallesu an k'ara saboda tsabar kyau da kwarjinin su. Sai da ya rakata ta gama komai kafin ya karb'i wayarta zaro ido tayi tana kallonsa nombobinsa ya saka ya kira ya d'auki nata daga haka ya mik'a mata wayanta yace "Allah yabada sa a" Har ya shige motarsa tana tsaye tana kallonsa yana shiga ya juyo ganin tana wajen harara ya galla mata kafin yaja motar yabar wajen ajiyar zuciya tasaki tana juyowa wata matashiyar budurwa wacce batafi sa artaba tana tana k'arasowa inda take, tayi tareda mik'a Mata hannu sukayi musabaha tace "ni sunana Maryam Abdullah Abubakar kefa?" Zaro ido Maryam tayi tana kallonta kafin tasaki wani k'asaitaccen murmushi tace "ni Kuma sunana Maryam Baffa Abubakar" itama Maryam kallonta tayi da mamaki tace mata" badai Baffa Abubakar mai gidajen mai ba?" Jinjina mata kai Maryam tayi sannan tace "shine kina wane b'angaren ne?" Tace "Islamic medicine" itama Zaro ido tayi tace ai nidake b'angaren mu d'aya tace suka tafa tareda rik'e hannun juna suna murmushi Maryam Abdullah Abubakar tace "da alama kema sabuwace ko?" "Eh yau na fara zuwa " "Ni kuma jiya Kinga Ashe bani kad'ai nayi missing 2 weeks ba" Maryam tace "au ke jiyama kikazo Kennan?" "Eh wallahi" haka dai sukayi ta hira har suka k'arasa cikin ajin. Ranan basu hutaba daga wannan malamin ya fita wani zai shiga wuni gudana na ranan farkonta amakaranta bata da wani huta, Koda ta koma gidama agajiye take wanka kawai tayi ta fito neman abinci dan wata fitinanniyar yunwa takeji ko samun damar cin abinci basuyiba. A dining ta had'u da Nassar shima shigowarsa Kennan dan shima nasu makarantar tun safe sai karfe shida suke dawowa shine makarantar da Maryam tagama wanda acan tayi sauka tareda sauran litattafai na addini Arabic ne da boko a had'e amma akwai mugun tsada. Sun fara cin abincin kenan MD ya k'araso wajen sanye da kayan shan iska tree queter wando da riga mai yankakken hannu irin iya kafadan nan farare kar. Zama yai yana opposite d'in Maryam yace "d'an zubamin abincin nima yunwa nike ji sosai" yayi hakanne ak'ak'arinsa nason janta ajiki kamar yadda Baffa ya buk'ata, kallonsa tayi da mamaki dan a saninta ko abinci yazo ci yagansu ita da mama a dining d'in ya hak'ura yau Kuma ya da ahaka sai dai ko kallonsa batayi ba taci gaba dacin abincinta. MAMAN Islam CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 17 Kafe ta yai da manyan idanunsa yayin datai bala in d'auke kanta tayi kamar bata san da zamansa awajen ba ganin haka yasa yajanye nata abincin yafara ci shima cikin d'aure fuska. Dagowa tayi ta dubeshi ta ko ina bataga alamar wasaba dan haka takai hannu zata d'auki ruwa shima ya dafe hannun batareda ya kalleta ba haka Kuma bai daina cin abincin saba janye hannun ta tayi ta mik'e batare data tanka Masa ba tabar wajen' bin bayanta yayi da kallo har ta shige d'akin ta, kai tsaye toilet ta shige ta d'auro alwala tazo tagabatar da sallar magriba bayan tayi addu o i sosai sannan tafara karatun alqur ani mai girma har zuwa lokacin da aka kira sallar isha sannan ta rufe qur anin tayi ta addu o'i har zuwa sanda aka shiga masallaci tabi jam 'i daga nan cikin d'akin ta duk abinta bata sanya da addu a sam bata da wasa a wannan fannin. Nassar ne ya lek'o ganinta ninke sallaya ya koma da gudu tana kiransa amma bai dawo ba, can kamar wajen mintuna uku sai gashi ya sake dawowa da sallamar sa ya shigo ta d'ago tana mallonshi tace "da gulmane yasa ka lek'o ka koma kamar w""""""""""" ragowar maganar ne ya mak'ale sakamakon ganin wanda ya biyo bayansa take ta maida kallonta ga Nassar tana hararan sa murmushi ya mata tareda salute nata ya juya jin kiran da Ammey tayi dan haka ya wuce da d'an tsallensa. Juyowa tayi asanyaye har yayiwa kansa zauni asaman kujeran gefen gadonta "k'araso ki zauna hira nazo tayaki" wani kallo ta watsa masa amma batace komaiba sai uban bugu da ziciyarta yakeyi sai kawai taci gabada gyaran kayanta data soma tunda safe batasan tashinasba sai jin hucin numfashin sa tayi daf da ita a d'an firgice ta juyo saura kadan ta fad'a jikinsa saboda yadda ya matsota kamar zai shige jikinta tana k'ok'arin janye jikinta yayi saurin dafe kafad'unta ya kafeta da idanunsa mai firgita masu kallonsa d'auke kanta tayi gefe tana tura baki tareda k'unk'uni "me kike cewa nida nazo muyi hiranmu nayaya da k'anwa shine zaki shareni ki hau aikin nasan ba dan Allah kikeyinsa ba" Bata iya tace masa komaiba saboda kusancin dayake tsakaninsu hakan yasa takasa wani kwakwaran motsi har jikinta ya soma d'an rawa rawa, wani murmushi ne ya kwace masa ganin tsoro k'arara kwance cikin idanunta,sakinta yayi ya koma inda ya taso yace "zoki zauna labarin abinda ya faru a makaranta yau zaki bani, sannan me da me aka koya muku duk abinda baki gane ba Kuma ni zakizo ki tambaya" Ita dai tsabar mamakinsa ya hanata tankawa domin tasani cewa duk duniya babu wacce yatsana sama da ita da mamanta gashi yanzu Kuma yazo yana wani shige mata anya ba wani muguntar yake shirya mataba Kai ita Kam tana kokwanton wannan shige matan da yake. Shi Kam duk yadda yaso janta da hira takasa sakewa dashi saima shakkunsa dayake hangowa a kwayan idanunta amma babu komai shima duk da badason ransa yake biye matanba zai daure yaci gaba har sai yaga ta saki jiki dashi. Washe gari da wuri tayi shiri ko Kari bata tsaya tayi ba duk a shirinta na tserewa MD bata son abinda zaina had'a dashi dan ta bala in tsanar say wallahi har cikin zuciyar ta, sai dai ta makaro domin tana fitowa ta hangoshi jikin motarsa a tsaye ga draiver agefensa shi Kuma hankalinsa yana kan wayarsa yana faman latsawa. Har ranta taji sanyi dan tayi tunanin shi zaisa yakaita dan haka a nutsenta ta k'araso tazo d'an gefensa taja ta tsaya batareda ta tankawa kowa cikinsu ba mai gadin ma datake gaidawa yau dan karta gaida Muhammad yasa taki gaidashi, shi Kam ko ajikinsa saima mota daya bud'e mata yace shiga, babu musu ta shiga driver ya shiga ga mamakinta sai gani tayi ya zagayo tadayan b'arin ya shigo', d'ago kai tayi da niyyar kallonsa suka had'a ido d'age mata gria yayi "ya dai?" ya yace yana kallonta d'auke kanta tayi kamar bataji me yace ba tunda suka shiga ya maida hankalinsa Kan computer yanason k'arasa wani aiki kan ya isa office. Yau ta riga Maryam zuwa dan da wuri ta fito yau ma kamar juya 5k yabata batason dogon magana yake had'a ta dashi dan haka yauma amsa kawai tayi ta wuce yabi bayanta da kallo har ta b'acewa ganinsa ajiyan zuciya ya sauke sannan ya juya ya shiga mota driver yaja. Tafiya take a nutsa tana tuna maganar da sukayi da mama yanzun kafin ta fito inda take ce mata"Maryam kiyi yadda kikeso kiyi abinda kikaga dama rayuwa bashi da tabbas inke kece yau gobe wanin kine abinda yake hannunka zai iya kwacewa ya koma hannun wani sannan rayuwa takan sauya mai bud'i ya koma talaka, shi kuma talaka ya koma me k'udi dan haka kiyi amfani da lokacin ki sannan kiyi amfani da damarki dan duk lokacin daya kubce miki bazaki sake samun irinsaba" sosai maganganun maman yake tsinkar Mata zuciya tabbas tafi kowa sanin halin mama bata maganan banza tunda ta dage akan wannan akwa k'arkarfan dalilinta haka nan yauma dazata fito dubu hamsin ta bata duk da wannan ba komai bane awajen maman amma tana mamakin yadda take bata kud'ad'e akai akai har dubu d'ari biyar tana bata musamman intasan tana da wani casu ko shagalin k'awayen ta' tana tsaka da wannan tunanin wanda yai matuk'ar d'aukan hankalinta taji tayi karo da abu kafin ta d'ago dan ganin waye an d'auke ta da wani matsiyacin mari wanda yasa saida tasaki jakarta da wayarta suka tarwatse awajen amatukar fusace ta d'ago sukayi ido biyu "me na maka dazaka mareni?" tayi masa tambayar hannunta dafe da kuncin ta "ubanki Kika yimin dan uwarki hanyar ta ubankice da zaki taho kina mana rangaji har ki buge mutane" Itama fusata tayi tace saidai ubanka dan uwarka hanyar ta inaga naka ubanne ya ginata d'an iska wawa jaki dabba kuma wallahi ina mai tabbatar maka sainaga waye ubanka ak'asar nan sanaga g"..........kafin ta k'arasa ya Kuma d'auke da wani mugun marin take jini ya balle mata ta hanci da gefen bakinta durk'ushewa tayi awajen saboda jirin daya fara kwasar ta shima tsuganawar yayi agabanta ya d'ago hab'ar ta ya kalli cikin kwayar idonta yace kije ki turo duk uban da kike tak'ama dashi" Duk da bak'ar azabar daya gauraye mata fuska haka bai hanata "furta cewa zaka gani ina mai tabbatar maka cewa saikaga gatana wallahi zakasan ni katab'a saikayi nadamar zuwanka duniya yau" ina jira 'yan mata ya fad'a tareda barin wajen take duk mutanen da suka cika wajen suka watse basuyi mamakin d boy ba domin takadirin d'an iska ne ya addabi kowa amakarantar gaba d'aya kowa tsoronsa yake hatta da malamai ma basu da ikon hukunta KAMAL ABBA AL HASSAN d'a d'aya tilo ga mahaifinsa alh. Abba AL HASSAN wanda yasamu dukkan dama da sake yake yadda yadda dama arayuwarsa. Saida kowa ya watse sannan Maryam ta k'araso wajen d'ago fuskar Maryam tayi yadda taga yayi kaca kaca da jini ga gefen idonta har yayi kwanciyar jini batasan sanda ta fashe da kukaba tace "ke kuwa name sake me ya had'a ki da wannan azzalumin d boy d'in wanda bashi da mutunci ko kadan jifa yadda yadda ya mayar miki da fuska?" Bakin ciki bai barta ta ce komaiba sai wayanta data Mik'o mata bayan ta cire code "kiramin mamana" shine kawai abinda Maryam ta iya cewa daga haka ta yanke jiki awajen ta fad'i a sume, take Maryam ta Kuma rud'ewa jikinta ya kama rawa garin ta kira mata maman ta dannan no MD wanda yai save da MY LOVELY BROSS yayi hakanne dan tsokana sai akayi rashin sa a ko dubawa ma batayi ba. Shiganea office kenan babu dad'ewa kiran yashigo saida yai matuk'ar mamakin ganin kiran nata domin yasan ba k'aramin abune zai saka Maryam kiransa zaima iya cewa tunda suke da ita bata tab'a kiransa ba, kamar kada ya d'aga sai Kuma yace baisan dalilin kiranba bari ya d'aga yaji ko wani abunne. Memakon muryanta muryan wata daban yaji tana kora Masa abinda ya faru cikin tsantsar tashin hankali ransa ne yai wani irin mummunan b'aci take jijiyar kansa tayi wani irin rud'u rud'u tsabar azabar fushi mik'e wa yayi a fusace yana kiran waya yai waje ko takan driver bai biba ya figi motar da mugun gudu yayin dayai magana cikin d'acin rai ta waya. Cikin kankanin lokaci ya isa makarantar har lokacin tana jikin Maryam tana faman girgizata yayinda mutanen da suka dad'a dawowa ganin Maryam ta sume wasu na bada shawarar akaita asbiti wasu na fad'in akaita gida tunda ansa mata ruwa a fuska bata farko ba. Cikin takun izza da isa ya k'araso wajen fuskar nan tasa babu d'igon rahama ya k'araso mutane suna ganinsa sanye da kaki tare da rubutun matsayin sa ajikin wannan d'an k'arfen da suke rubuta matsayin mutum ajiki an rubuta LIEUTANANT GANERAL MUHAMMAD BAFFA ABUBAKAR kafin kice me mutanan sun watsa, bai tsaya bin ba asiba ya sab'i 'yar uwarsa Maryam ta rufa masa baya. Daga taku har kullum MAMAN Islam CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMANA ISLAM Page 18 Asbiti mafi kusa ya nufa da ita ransa amasifar b'ace aransa yana ayyana irin hukuncin da zaiwa wannan yaron dan yasha alwashin saiya gane kurensa tunda ya tab'a masa 'yar uwarsa. Acan makaranta kuwa anfita da Maryam Kennan wani abokinsu ya k'araso wajen su d boy yace "abokina kaga yawan sojojin da sukazo suka tafi da wannan yarinyar kuwa?" Wani banzan kallo d boy ya watsa masa "to sai me dan tasan wani daga cikin sojoji Allah yasa bakin bindiga tasani kafa riga kasan koni waye Man kaf k'asar nan mutum bai fi biyu zuwa uku ba suke da damar iya hukuntani dan haka zanci haba da yin yadda naga dama ni kad'ai ne awajen ubana kuma yatara min shegun so kaga dole na warwasa son raina" "Kasan d'ayar wa daka kuwa?" "Koma 'yar uban waye dole gobe taji tsoron bin hanyar danabi" Man bai tsaya sauraron ba yace "yar gidan BAFFA ABUBAKAR ce fa" Duk da cewa gabansa yayi mugun fad'uwa amma Saida yace "wane banza ne haka har girman ikonsa yakai na ABBA AL HASSAN be?" Kafin ma Man yabashi amsa moticin da suka shigo na sojoji kusan guda shida suka faka agefensu ak'alla sunkai su ashirin ko ma sama su kansu malaman makarantar tunda sukaga wannan gangamin sannan ba wani taro suke ba suka tabbatar babu lafiya. K'arasowa sukayi inda su d boy suke wani daga cikinsu yace "waye kamal d boy anan wajen?" "Lafiya kuke nema na ko naci ban biyaba ne har aka yo mun gayyar masu gadi haka" Wata irin damk'a d'aya daga cikinsu yayi masa turoshi gaban sauran da mugun k'arfi har saida yai baya zai fad'i suka wani talle masa k'eya suka cakume gefen wandansa suka jashi zuwa jikin motarsu. "Kunsan koni waye kukema wannan wulak'ancin? wallahi zakasan ni kuka tab'a dukanku sai kun rasa aikinku sai kunyi nadamar abinda kukayimin" duk cikinsu babu wanda ya tankashi har suka figi motocinsu da mugun gudu sukabar wajen take hayaniya ta kaure kowa da abinda yake fad'a wanda ya raina kuwa hakan ya musu mugun dad'i ko ba komai an karya alkadarin sa. "Ba wani mummunan rauni tajiba b'acin raine yasa ta suma amma mun shawo kan matsalar sai dai gaskiya ku dunga kiyaye shigarta irin wannan b'acin ran dan zai iya jawo babbar matsala" wannan shine bayanin shine bayanin da Dr yaima MD. Bayan ya fito a office d'in Dr d'akin dataken ya dawo tana zaune ta jingina bayanta da d'an k'arfen gadon har lokacin bak'in cikin abinda d boy yai mata bai gama sakinta ba sannan taci alwashin saita rama Koda hakan zai haifar da ko wacce irin fitina. Hannu kawai taji yana yawo saman fukarta tayi saurin d'ago kanta' ganin MD tayi cikin wani irin masifaffen fushi wanda bata san yana da irinshi ba, saida yagama share mata hawayen da suke ta faman gudu sannan ya maida hannun inda yatsun d boy sukayi rud'u rud'u wajen yayi wani irin ja "me ya had'a ku da har zai kamaki yayi miki irin wannan dukan saikace wata yarsa" Jin yanayin da yai maganar yasata d'ago ta d'an kalleshi ganin babu wani alamun wasa yasa ta kwashe duk abinda yafaru ta fad'a masa jikinsa har wani tsuma yake tsabar b'acin rai. Mik'ar da ita yayi yabata mayafinta da takalmanta ya kama hannunta sukayi waje basu zame ko inaba sai inda yasa aka kai d boy kafin yaje yayi mugun laushi mari uku kacal yayiwa Maryam amma shi yasamu mari kala kala fiye da kala d'ari tuni kamannimsa suka sauya banda bulalar dayashi dan cewa yayi karsuyi masa dukan wasa dama yana ciki da ubansa Abba AL HASSAN wanda suke ta fafatawa dashi akan wani case da suke zarginsa. Sanda suka shiga wajen tuni d boy ya jima da suma domin ba k'aramin jin jiki yayi ba duk da mugun haushin sa akan abinda yayi mata saida yabata tausayi ganin yanayin daya shiga balle itama mace mai matuk'ar tausayi da rauni take ta fashe masa da kuka tace ita tayafe dan Allah ya rabu da d'an mutane kar su masa illah, ganin yadda ta d'aga hankalinta yasa yace kar tadamu dama d'an gargad'i ne kawai sukayi masa dan gaba ya kiyaye yasan cewa duk matsayinsa duk abinda yake tak'ama bakowa zai tab'a ya kwana lafiya ba. Daga nan gida ya wuce da ita lokacin haj. Sailuba ta fito haraba tanama driver magana zasu fita motansa ya ahigo sarai tasan motarsa ne yasa ta d'an dakata dan tanason masa gargad'i akan 'yarta duk da cewa Baffa ne ya bashi dukkan dama. Ganin Maryam ce tafara fitowa daga motar yasa tai bala in had'e rai mugun kallo ta rik'a binta dashi har ta k'araso inda take tsaye ganin irin shatin marukan dake kwance saman farar fatar fuskar ta yasa a rud'e takamo fuskar da duka hannayenta tace "baby wanne azzalumin mara imaninne yayi miki wannan d'anyen aikin, wane la'anannen ne wanda bazai gama da duniya lafiya ba, nan dai ta zage tana ta zuba ruwan rashin arzik'i duk a tunanin ta MD ne yayi mata domin dama shine yake iya mata dukan dabata isar d'aukan mataki ba sai dai ruwan tujara da rashin mutunci koda taji cewa bashi bane hakan baisa tayi shiru ba sai datayi mai isarta ranan fitar dabata samu tayiba Kennan. Ita kanta Ammey ganin irin zaluncin da akayiwa Maryam d'in sai da taji ajikinta amma bata tankaba kamar ko yaushe idone nata amma har kullum bata fasa yiwa 'yarta Adda a ba. _________________________ B'angaren abokan d boy kuwa ana barin wajen dashi d'aya daga cikin abokansa ya bugawa alh. ABBA AL HASSAN waya ya sanar masa, take ransa yai masifar b'aci cikin tsawa yace"wane me zarrar ne yake da k'arfin gwaiwar kama d'ana wanene shi wane me tsautsayin ne lallai inason sanin wanene shi" "Dad yar gidan BAFFA ABUBAKAR ya daka yau amakaranta shine yayanta ya turo aka kamashi" innalillahi,wa inna ilahi raji'un shine kawai abinda Abba AL HASSAN ya iya fad'a kafin ya zube saman sofa dake office d'in lallai yau Kamal ya janyo masa wata sabuwar masifar da baisan ta hanyar da zai magance ta. MAMAN Islam CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 19 Yajima yana gabza bala e kafin ya fice daga office d'in cikin tashin hankali,kai tsaye gidansa ya nufa lokacin haj. Maimuna tana hakimce saman kujera ta d'ora kafa d'aya saman d'aya mai aikinta tana durkushe agabanta da alama wani umarnin take bata. Tana ganin shigowarsa ta sallami mai aikin sannan "sannu da zuwa alhaji lafiya naganka tun kafin lokacin tashin yayi" "Na gaji nagaji nagaji haba dan masifa wallahi maimuna kin haifi masifa kin haifi fitina haka kawai ina zaman zamana zai je ya d'auko min masifar da bazan iya magance taba wallahi ba ruwa d'an iskan yaro haihuwar asara t""''"""''''''' dakata malam Kaine haihuwar asarar ba d'ana ba me yai maka zaka zo kasashi gaba da masifa ai duk wannan tsinannen bakin nakane yake binsa" "Zanci" ya lailayo wani katon zagi ya lafta mata,nanfa rigima ta balle wannan ba sabon abu bane agidan Abba AL HASSAN indai ransa zai b'aci ta ranar babu zaman lafiya. Washe gari bayan tagama shirinta a dining ta tadda Nassar yana kari ta harareshi tace " um su acici har an fara afawa Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 21 Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin data ganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi, yayinda wani irin shak'uwa mai ban mamaki ya shiga tsakaninsu da name sake d'inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima. Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d'aukan fansa Abban sa ya taka masa burki yace"kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K'are ba wannan yaron da kake ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad'a maka nagaban kwatance dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba 'yar kowa bace face'yar Baffa Abubakar" Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d'umin karamcin sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok'on yayanta da ya k'yale shi haka duk da yadda ake fad'an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan d'aukan fansa ya ruguje saima k'ok'arin son kulla alak'a da ita. Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d'aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab'a sanin wainar da suke toyawaba. Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d'in duk abinda zai rik'a faruwa akaf gidan ta ko ina har d'akin Ammey batare datasan anyi hakanba. Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan lokacin tashinsu yayi ta fad'a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k'ala batace masaba kuma dama yasan basatace d'in ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen. A hankali tafara takawa zuwa bakin get d'in tunda tafara zuwa makarantar shekara d'aya kenan da d'an wani abun bai tab'a ajeta anan d'in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k'ofar kamar yadda ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya. "Hey hey" taji muryan wanda bazata tab'a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko da babu wanda ya tab'a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun fusace ta d'ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar. Yana k'arasowa bata bari ya fad'a mata wani abuba tayi saurin cewa "wai kai wane irin mutum ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa? Yau kuma takeni kake sonyi komai? Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine? Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira. Duk abinda take fad'a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace 'Amincin Allah yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai dan na k'ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss d'in yayan naki ya k'yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk'awarin ko kallon banza bazai k'ara had'a ni dakeba pls pls pls" ya rik'a maimaitawa yayin da tayi masifar d'auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok'on yafiyar ta bai ko damu da yadda mutane suka fara taruwa awajen ba. Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu kad'an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa "meye haka dan Allah jifa har an fara taruwa anan katashi" "Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin" "Tashi dan Allah" ta fad'a cikin sanyin murya "zantashi ne kawai idan kince kin yafemin" "Na yafe maka amma bisa wani sharad'i to tashi" tasake fad'a can k'asan mak'oshi da sauri ya tashi yana fad'in"na gode na gode sosai ko wane irin sharad'i ne ki fad'a na miki alk'awarin tunda dai kin yafemin" fad'a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa d'aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa. "Gaskiya yakamata ka gyara halinka da d'abi unka ba abune me kyau ba kowa ya rik'a maka shaidar baka da mutunci babu wanda ka ragawa har akai ga matakin da kowa zai fara jin tsoronka sam wannan zalunci ne babba dan Allah ka gyara kaga ni d'innan dakake gani duk abinda kake ji dashi nafika ko ranan ma shammata na kayi banda haka bazakayi nasara akainaba sai dai ni bana shiga harkan wanda bai shiga nawaba dan haka kaga ko makarantar nan banda kawa sai A A" "Nasani sam ban kyautaba kuma na miki alk'awari insha Allah daga yau nima babu ruwana da sabgar kowa" " Allah yasa" ta fad'a atakaice tana wucewa department d'insa. Yana tsaye har ta shige murya k'asa k'asa yace "tamin Allah yasa tasoni nidai tamin badan komai ba sai dan nutsuwa da ajinta Abba kayi suruka irin wacce kake so 'yar wani wanin ma wanda yai suna aciki da wajen k'asar nan" (Su Kamal d boy daga sannu sarkin fawa lol🤣🤣🤣) Yau kam da wuri suka koma gida dake lacca d'aya ke garesu suna gamawa babu wani jinkiri Maryam ta nemi da A A ta rakata banki tana son bud'e sabon account, da mamaki AA take dubanta kafin tace "ke kuwa name sake duk yawan asusanku wanda ba ayi miki iyaka dasuba sai kin bud'a wani?" Bazaki gane bane sam mama bata barina da k'udi ita zata bani kuma ita zata dawo ta rance na rasa abinda mama take da k'udi duk yawan kyauta irin na Baffan mu wallahi A A Saida mama ta kureshi" haka dai suka tafi tana bata bad habits d'in mamanta wanda abin yake masifar damunta ta kuma rasa dawa zata zanta taji sanyi saifa yanzun dataji ta aminta da ita. Har sukaje suka bud'e account kud'ad'en da Maryam ta zuba a account d'in saida abin ya bata tsoro yayin da Maryam ta dinga mata dariya daganan tace Maryam ta rakata kasuwa zatayi siyayya sai da suka fara zuwa tasiyi kayan kwalliya da turarukanta dake Maryam mayyar turarece zai wuya ka kusance takaji bata k'amshi domin ita d'in 'yar gayuce tagaban kwatance hakan yasa take da masifar farin jini Saidai halinta bai barinta shiga sabgar mutane domin bata da kirki ko kad'an. Daga nan Kuma suka nufi wajen masu saida kayan abinci A A taga Maryam ta d'auki babban buhu na shinkafa da k'arami sannan ta d'auki taliya carton biyu haka makaroni da cous cous da semonvita irin buhunnan mai guda sha biyu shima guda biyu manja man gyad'a Maggi kanshi saida ta d'auki carton guda banda sauran spacies data d'iba ita dai A A kasa daurewa tayi tace "name sake nasandai abincin gidanku trela ake kawoshi me zakiyi da wannan abin da kike ta loda?" "Ba damuwarki bane" cewar Maryam datakewa mai shinkafar maganan ko zasu samu motar da zai kwashe musu dukan kayan? dan adaidaita yayi musu kad'an. "Akwai 'yar k'ur k'ura wanda shi dama aikinsu Kennan d'iban kaya sukai maka duk inda kakeso' ya fad'a yana kwalawa wani kira. Tun tambayar da tayi mata tace ba damuwanta bane bata k'ara tofa nataba abinda ya Kuma d'aure mata kai shine ganin motar bai faka ko ina ba sai k'ofar gidansu da mugun mamaki ta rik'a kallon Maryam wacce ta d'auke kanta batare data bari sun had'a ido ba. Suna tsaye har aka gama shiga da kayan abinci sannan ta sallami mai motar suka bi mai d'aukan kayan na k'arshe, shima ta sallame shi yayinda suna shiga suka tadda Umma da Abban Maryam da shima shigowarsa Kennan gidan aka fara shiga da kayan daya fara tunanin ko b'atan kai masu kai kayan sukayi amma yana ganin Maryam da Maryam sun shigo ya dingabinsu da kallo fuskarshi da alaman tambaya. " Ku zauna mana Abba" Maryam ta fad'a tana zaran buta tayi bayan gida, sam Maryam batada k'yamar mutane musamman inkana da tsabta dake it's mutum ce mai tsananin tsabta da k'yamar k'azanta, tana fitowa tayi alwala tayi d'akin Umman su A A ganin haka yasa itama Maryam tayi alwalar tabita d'akin. Tana fitowa tanemi waje ta zauna tana gaida Umma da Abban kafin ta kalli Umman tace "nifa yunwa nake ji Umma yau bross ko kari bai bari nayi agidaba wai ya makara a office" Kallon mijin nata tayi yayin da yayi mata alamar data bata abinda suke dashi,shi kuma ya saka takalmansa yayi waje Umma Kuma ta nufi kicin ta kawowa Maryam wake da shinkafar da suka dafa da salak da tumatur da cocomber, ta aje mata ta koma domin kawo mata ruwa sai ga Abba ya shigo da ruwan roba da lemo harda dafaffen kwai tunda yasan me aka dafa agidan. Sam bata wani nuna bak'unta ba taja abincin taci ta k'osh har tana santi ita kam Maryam zuba mata ido tayi tana kallonta batareda data iya cewa uffan ba saida ta gama ta wanko hannunta ta dawo tasha lemon da ruwa sannan tace. "Abba wannan kayan abincin nakane kai na siyowa dan Allah Abba kada ka k'ara zuwa kayi dako insha Allah idan Baffana ya dawo zansa yabaka jari ka fara business kaima insha Allah Allah zai dafa maka" Rasa bakin magana Abba da Umma sukayi suka rik'a kallon Maryam da tsabar mamaki dama Maryam taji sanda yake cewa saida yai dako ranan sannan ya samo musu abinda zasuci? Sosai Abba ya gode mata sannan yayi mata fad'an abin yayi mugun yawa tace "Abba wannan ba komai bane akan idan da ace Baffana na fad'a wa shi ya doramu akan wannan tsarin nida 'yan uwana" addu'ar da Abban Maryam ya rik'a yiwa Maryam da zuri arta harsaida yasata hawayen farin ciki itama. Sai bayan la asar ta baro gidan ta kamo hanyar nasu gidan dake suna da tazara sosai sai yamma ta dawo maimakon Kuma ta shiga gida sai kawai ta shige gidansu MM wani class mate d'inta wanda har yau suna mutunci dashi kasancewar su unguwa d'aya. MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JINJINA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 20 Suna fita wajen ta fauce hannunta daga nashi ta nufi motar ta bud'e har ta shiga ta zauna bai k'araso ba daga inda take tana hangoshi yana magana da wani. Wayarta dake k'ara ta zaro Maryam ce ta d'anyi murmushi tareda d'agawa "ya akayine besty?" "Yau Kuma yada makara beaty malamin nan fa kinsan bashi da kirki kuma gashi saura 10 min mushiga kuma kinsan Koda 1min ya rigaki bazai bari ki ahigaba" cikin damuwa tace "ganinan besty" "Wai kina ina need?" "Zan fad'a Miki idan na shigo" "To kiyi sauri dan Allah" "Insaha Allah" Tana kashe wayar yana k'arasowa yana duba agogon hannunsa ta wani kalleshi tayi kicin kicin da rai, murmushi ya d'an yi batare da yace komaiba ya tada motar lokacin da suka isa tuni malamin ya fara da kusan 10 yana faking tace " maidani gida" Kallonta yai da son k'arin bayani tayi masifar had'e rai tace "to meye amfanin barina tunda anriga an shiga kuma malamin baya barin kowa ya shiga muddun ya riga ka shiga" ta fad'a tareda zubowar hawaye sai da ya d'an kalleta na kusan 7 second kafin yama hannunta har department d'in nasu yayi sallama abakin hall d'in wanda ya lek'o ne yasa MD rik'e baki yace "kana ruwa yaro dama Kaine kake furgita mana kanne haka?" Shima da mamakin yace "MD kana duniya gaskiya bamuda kirki zumunci yayi karanci me yafaru kake cewa ina firgita muku k'anne?" Maryam MD ya nuno masa "na d'an biya da ita office amsar wani muhimmin sak'o ina ajeta ta fashe min da kuka wai na maidata gida kariga ka shiga" dariya m Bash yayi yace "Yarran ne koya sukaga wallenka sai su rainaka" ya fad'a yana dosar inda Maryam take yayin da MD ya biyoshi yana magana a waya. Da sauri Maryam ta d'an russuna tace "good morning sir" ga mamakinta taji yace morning dear how fa maza wuce aji karki k'ara biyewa wannan yayanki ya makarar dake" ya fad'a bayan ya tambayi ya take batareda ya bari ta bashi amsa ba da alama yadda yai maganar akwai sanayya tsakaninsu da yayannata. Da sauri ta doshi ajin inda ta hango Maryam tana ta faman lek'e ta window ta d'an kai mata dundu tace "me kike nema haka kamar zaki tsinka wuya tsabar lek'e?" Ajiyar zuciya Maryam ta saki tace "ya akai yabarki kika shigo?" "Uhm bross nefa ya makarar dani yana direni nasa masa kuka""""" nan ta kwashe yadda sukayi ta fad'a mata. Bayan sun fito a lacca ne Maryam ta d'an dubi k'awar tata tace "besty yau ni naga masifa da tashin hankali ganin ido na,kai soja bala I ne wallahi besty" "To yau kuma me ya had'aku keda sojan naki nasan dai dashi kike wannan maganar" "Uhm besty wai ashe jiyan nan da muna hospital bross turowa yayi aka kama d boy karki ga yadda yasa yaransa suka mai dashi wallahi sai da nayi kuka" "Ke banza ce wallahi besty mutum yayi miki irin wannan yarfin dan an bi miki hakkin ki shine har zai baki tausayi? bakisan d boy ba' bakisan waye shiba wallahi da bross bai masa hakaba ya rik'a tunda yaga yayi na farko yaji dad'i haka halinsa yake" Ajiyan zuciya ta sauke tace Allah ya kyauta,yauwa dear kikace Abba yana harkan dillancin gidaje ko?" "Eh me yafaru?" "Gida nake son siya besty" " Ke kuwa besty duk yawan gidajen ku me zakiyi da wani gidan?" "Bakiji me kikace ba beaty a maganar ki, kinsaka jimlar ku nawa ni kad'ai nakeso" "To shikenan kamar yaushe kike buk'ata sai muje" "Ki kira wayarsa idan da dama mu wuce daga nan idan babu damuwa tunda Kinga yanzun bamu da wata lacca" "Yadda Kika ce besty hakan za ayi" Daga nan direct unguwar su Maryam dake tayima Abbanta waya ya dawo yana jiransu sai da suka fara gaida mamanta kafin tayi mata iso har d'akin Abbanta sosai kwarjinin sa yaima Maryam dan daka ganshi kaga kamilin mutum mai cikar Kamala da mutuntaka bayan sun gaisa Maryam ta fita ta basu waje. Kallonta malam Abdullah yace "yarinya me sunan kine?" Tace "sunana Maryam Abba murmushi Abba yayi yace "d'iya tace ashe" itama murmushin ta saki wanda ya k'ara mata kyau. "Maryam tace kina son ganina Allah yasa lafiya?" "Eh Abba lfy dama ina son siyen gidane to shine nakema Maryam magana tace kana harkar gidaje" Kallonta Abban Maryam yayi na d'an lokaci yana nazarinta sannan yace"ke yar waye ne 'yata?" "Baffa Abubakar" ta fad'a atakaice sosai ya jinjina take mamakin yadda akai tasamu k'udi ya d'auke tunda yanajin irin labarin jita jita cewa yarinyar tana mugun b'arin k'udi sannan akwaita da kyautar girma irin na mahaifinta sannan ansakar musu k'udi suyi yadda suke so, kasancewar su Kennan yaransa. Kallonsa ya mayar kanta yace "to 'yata kamar wanne kike buk'ata?" Abba na baka zab'i mai kyau nake so wanda bai gaza 7 million ba" da mamaki yake kallonta kafin yace "shikenan 'yata insha Allah zanyi miki kamar yadda zanyiwa Maryam" daga haka Maryam ta bashi dubu goma tace "Abba ga wannan ayi cefane" Da k'yar tasamu ya karb'a dan shi d'in ba irin masu zarmewar zuciya bane. Ba a wani dad'e ya samo mata gida mai kyau aka yi ciniki ta biya batareda sanin kowa nataba tabar komai awajen Abban aminiyar tata. Tunda ga ranan dataganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi sai tasai abinda tasan duk lokacin data tashi zata siyar ta samu k'udinta. Shin wai duk meye dalilinta nayin hakan muje zuwa daga 'yar mutan YAKASAI MAMAN Islam CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 21 Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin data ganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi, yayinda wani irin shak'uwa mai ban mamaki ya shiga tsakaninsu da name sake d'inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima. Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d'aukan fansa Abban sa ya taka masa burki yace"kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K'are ba wannan yaron da kake ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad'a maka nagaban kwatance dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba 'yar kowa bace face'yar Baffa Abubakar" Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d'umin karamcin sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok'on yayanta da ya k'yale shi haka duk da yadda ake fad'an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan d'aukan fansa ya ruguje saima k'ok'arin son kulla alak'a da ita. Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d'aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab'a sanin wainar da suke toyawaba. Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d'in duk abinda zai rik'a faruwa akaf gidan ta ko ina har d'akin Ammey batare datasan anyi hakanba. Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan lokacin tashinsu yayi ta fad'a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k'ala batace masaba kuma dama yasan basatace d'in ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen. A hankali tafara takawa zuwa bakin get d'in tunda tafara zuwa makarantar shekara d'aya kenan da d'an wani abun bai tab'a ajeta anan d'in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k'ofar kamar yadda ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya. "Hey hey" taji muryan wanda bazata tab'a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko da babu wanda ya tab'a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun fusace ta d'ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar. Yana k'arasowa bata bari ya fad'a mata wani abuba tayi saurin cewa "wai kai wane irin mutum ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa? Yau kuma takeni kake sonyi komai? Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine? Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira. Duk abinda take fad'a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace 'Amincin Allah yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai dan na k'ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss d'in yayan naki ya k'yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk'awarin ko kallon banza bazai k'ara had'a ni dakeba pls pls pls" ya rik'a maimaitawa yayin da tayi masifar d'auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok'on yafiyar ta bai ko damu da yadda mutane suka fara taruwa awajen ba. Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu kad'an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa "meye haka dan Allah jifa har an fara taruwa anan katashi" "Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin" "Tashi dan Allah" ta fad'a cikin sanyin murya "zantashi ne kawai idan kince kin yafemin" "Na yafe maka amma bisa wani sharad'i to tashi" tasake fad'a can k'asan mak'oshi da sauri ya tashi yana fad'in"na gode na gode sosai ko wane irin sharad'i ne ki fad'a na miki alk'awarin tunda dai kin yafemin" fad'a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa d'aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa. "Gaskiya yakamata ka gyara halinka da d'abi unka ba abune me kyau ba kowa ya rik'a maka shaidar baka da mutunci babu wanda ka ragawa har akai ga matakin da kowa zai fara jin tsoronka sam wannan zalunci ne babba dan Allah ka gyara kaga ni d'innan dakake gani duk abinda kake ji dashi nafika ko ranan ma shammata na kayi banda haka bazakayi nasara akainaba sai dai ni bana shiga harkan wanda bai shiga nawaba dan haka kaga ko makarantar nan banda kawa sai A A" "Nasani sam ban kyautaba kuma na miki alk'awari insha Allah daga yau nima babu ruwana da sabgar kowa" " Allah yasa" ta fad'a atakaice tana wucewa department d'insa. Yana tsaye har ta shige murya k'asa k'asa yace "tamin Allah yasa tasoni nidai tamin badan komai ba sai dan nutsuwa da ajinta Abba kayi suruka irin wacce kake so 'yar wani wanin ma wanda yai suna aciki da wajen k'asar nan" (Su Kamal d boy daga sannu sarkin fawa lol🤣🤣🤣) Yau kam da wuri suka koma gida dake lacca d'aya ke garesu suna gamawa babu wani jinkiri Maryam ta nemi da A A ta rakata banki tana son bud'e sabon account, da mamaki AA take dubanta kafin tace "ke kuwa name sake duk yawan asusanku wanda ba ayi miki iyaka dasuba sai kin bud'a wani?" Bazaki gane bane sam mama bata barina da k'udi ita zata bani kuma ita zata dawo ta rance na rasa abinda mama take da k'udi duk yawan kyauta irin na Baffan mu wallahi A A Saida mama ta kureshi" haka dai suka tafi tana bata bad habits d'in mamanta wanda abin yake masifar damunta ta kuma rasa dawa zata zanta taji sanyi saifa yanzun dataji ta aminta da ita. Har sukaje suka bud'e account kud'ad'en da Maryam ta zuba a account d'in saida abin ya bata tsoro yayin da Maryam ta dinga mata dariya daganan tace Maryam ta rakata kasuwa zatayi siyayya sai da suka fara zuwa tasiyi kayan kwalliya da turarukanta dake Maryam mayyar turarece zai wuya ka kusance takaji bata k'amshi domin ita d'in 'yar gayuce tagaban kwatance hakan yasa take da masifar farin jini Saidai halinta bai barinta shiga sabgar mutane domin bata da kirki ko kad'an. Daga nan Kuma suka nufi wajen masu saida kayan abinci A A taga Maryam ta d'auki babban buhu na shinkafa da k'arami sannan ta d'auki taliya carton biyu haka makaroni da cous cous da semonvita irin buhunnan mai guda sha biyu shima guda biyu manja man gyad'a Maggi kanshi saida ta d'auki carton guda banda sauran spacies data d'iba ita dai A A kasa daurewa tayi tace "name sake nasandai abincin gidanku trela ake kawoshi me zakiyi da wannan abin da kike ta loda?" "Ba damuwarki bane" cewar Maryam datakewa mai shinkafar maganan ko zasu samu motar da zai kwashe musu dukan kayan? dan adaidaita yayi musu kad'an. "Akwai 'yar k'ur k'ura wanda shi dama aikinsu Kennan d'iban kaya sukai maka duk inda kakeso' ya fad'a yana kwalawa wani kira. Tun tambayar da tayi mata tace ba damuwanta bane bata k'ara tofa nataba abinda ya Kuma d'aure mata kai shine ganin motar bai faka ko ina ba sai k'ofar gidansu da mugun mamaki ta rik'a kallon Maryam wacce ta d'auke kanta batare data bari sun had'a ido ba. Suna tsaye har aka gama shiga da kayan abinci sannan ta sallami mai motar suka bi mai d'aukan kayan na k'arshe, shima ta sallame shi yayinda suna shiga suka tadda Umma da Abban Maryam da shima shigowarsa Kennan gidan aka fara shiga da kayan daya fara tunanin ko b'atan kai masu kai kayan sukayi amma yana ganin Maryam da Maryam sun shigo ya dingabinsu da kallo fuskarshi da alaman tambaya. " Ku zauna mana Abba" Maryam ta fad'a tana zaran buta tayi bayan gida, sam Maryam batada k'yamar mutane musamman inkana da tsabta dake it's mutum ce mai tsananin tsabta da k'yamar k'azanta, tana fitowa tayi alwala tayi d'akin Umman su A A ganin haka yasa itama Maryam tayi alwalar tabita d'akin. Tana fitowa tanemi waje ta zauna tana gaida Umma da Abban kafin ta kalli Umman tace "nifa yunwa nake ji Umma yau bross ko kari bai bari nayi agidaba wai ya makara a office" Kallon mijin nata tayi yayin da yayi mata alamar data bata abinda suke dashi,shi kuma ya saka takalmansa yayi waje Umma Kuma ta nufi kicin ta kawowa Maryam wake da shinkafar da suka dafa da salak da tumatur da cocomber, ta aje mata ta koma domin kawo mata ruwa sai ga Abba ya shigo da ruwan roba da lemo harda dafaffen kwai tunda yasan me aka dafa agidan. Sam bata wani nuna bak'unta ba taja abincin taci ta k'osh har tana santi ita kam Maryam zuba mata ido tayi tana kallonta batareda data iya cewa uffan ba saida ta gama ta wanko hannunta ta dawo tasha lemon da ruwa sannan tace. "Abba wannan kayan abincin nakane kai na siyowa dan Allah Abba kada ka k'ara zuwa kayi dako insha Allah idan Baffana ya dawo zansa yabaka jari ka fara business kaima insha Allah Allah zai dafa maka" Rasa bakin magana Abba da Umma sukayi suka rik'a kallon Maryam da tsabar mamaki dama Maryam taji sanda yake cewa saida yai dako ranan sannan ya samo musu abinda zasuci? Sosai Abba ya gode mata sannan yayi mata fad'an abin yayi mugun yawa tace "Abba wannan ba komai bane akan idan da ace Baffana na fad'a wa shi ya doramu akan wannan tsarin nida 'yan uwana" addu'ar da Abban Maryam ya rik'a yiwa Maryam da zuri arta harsaida yasata hawayen farin ciki itama. Sai bayan la asar ta baro gidan ta kamo hanyar nasu gidan dake suna da tazara sosai sai yamma ta dawo maimakon Kuma ta shiga gida sai kawai ta shige gidansu MM wani class mate d'inta wanda har yau suna mutunci dashi kasancewar su unguwa d'aya. MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 22 Bata zauna ba data tadda jm bayanan nayi b'ata last page jm zance na manta nace mm, tana zuwa bakin get taji mai gadi yana cewa "gatanan yallab'ai" MD daya gama rud'a driver da bala i saboda kawai yace tun biyu saura su Maryam suka bar makaranta kuma alhalin ba ama turashi ba sai wajen biyar saura shine fa MD ya hana shi sakat da masifa sai da ya koma makarantar har sau biyu. Sannan kuma Ammey ta tabbatar masa da cewa tun fitar da sukayi tare bata dawoba amma kar ya damu wannan ba komai bane a wajen su dan takan fi hakama awaje, sosai ransa ya b'aci da jin abinda Ammeyn ta fad'a masa ya fito Kennan cikin wannan halin mai gadi da ba shine driver ba da ya had'a ya hasu sakat yace ga Maryam d'in nann Duk zubawa get d'in ido sukayi yayin da Maryam ta shigo hankalin ta kwance babu wani damuwa tattare da ita, tana tafe cikin nutsuwar da Koda yaushe ka ganta zaka ganta tattare da ita. Ran MD ne yai mugun b'aci cikin bak'in ciki ya k'arasa inda take wato shi yana nan hankali tashe ita Kuma tana can yawon gantalin ta hankalin ta kwance' wata irin fincika yayi Mata da mugun k'arfi har saida ta saki k'aran azaba, jakarta da wayarta sukayi nasu waje yayin tayi taga taga zata fad'i yayi saurin tareta ta fad'a jikinsa. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke jin ta cikin jikinshi take ya ji wani irin abu ya tsarga masa tundaga tsakiyar kansa har zuwa babbar yatsarsa ta k'afa. Ita kam Maryam wani irin takaicin jinta ajikinsa ne ya kamata batasan sanda hawaye ya sulalo mata ba saboda bak'in ciki kwace jikinta tayi daga nasa tace murya k'asa k'asa "ban yafe ba d'an iska kawai aidama Halima tace duk wanda yake irin aikinka to manemin mata ne anje neman na bariki ba asamuba shine akazo latsa k'anwa dan abin kunya tur" ta fad'a tare da fashewa da kuka. Tunda ta juya tabar shi nan tsaye yake cikin suyar ran kalamanta tunda yake babu wanda ya tab'a fad'a masa maganar daya k'untata masa irin yau ba,amma sosai abin ya rik'a sukar k'irjinsa temakon da Allah yayi masa cikin rad'a tayi masa duk wannan wulak'ancin da cin fuskar. Sai dai hakan baisaka yajanye alk'awarin da yayiwa Baffa da Ammey ba yayi musu alk'awarin zai ja Maryam ajikinsa yanda zasuyi sabon da duk abinda zaisa ta bazata tab'a Musa masaba ta hakane Ammey take ganin zasu samu hanyar gyarawa Maryam zama. Bayan an idar da sallar issha suna d'akinta ita da Nassar tana tayashi assignment d'in da yazo dashi saiga sallamar shi abakin k'ofar ba k'aramin fad'uwar gaba ta tsinci kanta aciki ba d'azu bayan tagama masa fitsaran ta dawo d'akin tace sam saitaga bata kyauta masa ba kome ya mata ya kamata yaci darajan shi na d'an uwanta JININTA. Bata samu damar amsa masa ba sai Nassar ne ya amsa masa ya k'araso gefen da take ya zauna daf da ita tanaji Nassar yana gaidashi takasa had'a ido dashi bare wani gaisuwa ya had'asu. "Nine d'an iska mai bin mata ko?" Ya tambaye ta cikin wani irin murya mai kashe jiki wanda hakan yasata jin wani irin babu dad'i "kayi hak'uri bross dan Allah" maganar ya kwace mata batare data shiryawa hakan ba. Sosai ya kafeta da idonsa wanda sukayi wani irin kyalli saboda kwallan daya cikasu, tunda yake babu wanda ya tab'a gasa masa bak'ar magana irin nata. Jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago idanunta dake duk'e kan littafin Nassar daya jima da ficewa daga d'akin,ba k'aramin fad'uwa gabanta yayiba ganin kwallan daya ciki idanunsa sai dai bai basu damar zubowaba saboda nayasan taga logonsa amma maganar gaskiya yaji zafin maganar ta ainun wanda dama dan yaji zafin tayi masa. Rasa yadda zatayi masa wani maganar tayi sai kawai ta fashe masa da kuka wanda zan iya kiransa da kukan shagwab'a, take ya k'arasa zaman durshen agabanta tareda kamo hannunta yace "haba k'anwarta me kuma nayi miki banfa yi miki ko mai ba" ya k'arasa maganar cikin rawar murya domin har ga Allah jiyai kukan yana mugun tab'a masa zuciya. "Kayi hak'uri" ta k'ara fad'a masa cikin muryan kuka "nayi" yafad'a mata da sauri cikin rawan murya sannan ya d'an dubeta yace "k'anwata na miki wani tambaya mana amma ina son dan Allah ki fadamin gaskiya tsakaninki da Allah" "To" kawai tace masa tana faman goge hawayen da suke zubo mata har lokacin "to ki daina kukan haka mana dan Allah kinji" yafad'a yana share mata hawayen data rasa dalilin k'in tsayawarsu. "Wai me yasa kika tsaneni ne?" Yayi mata tambayar dayafi komai ci masa rai tun ranan data furta masa ta tsanesa har yau baidaina jin amsa kuwwar abin cikin kunnen saba sosai abin ya tab'a shi. "Ai nima baka sona nida mama ka tsanemu kafi son Nassar da Ammey kanawa mama rashin kunya agabana baka dukan Nassar agaban Ammey amma ni kamar jaka haka kake jubgata ko dan kaga Nassar d'an d'akinku shiyasa ni kake nuna min 'yan ubanci" ta fad'a cikin zubowar sabon hawaye, maganar ta na k'arshe ya mugun bashi tausayi har baisan sanda yasa hannu yajata jikinsa ba kamar jira take kuwa ta fad'a tareda sakin kuka irin mai cin rannan. Dagajin yanda take kukan yasan akwai abinda yake damunta wanda ta barshi aranta takasa fad'uwa kowa, saida yabari ta d'an yi kukan da d'an yawa kafin ya soma d'an bubbuga bayanta har saida yasamu tayi shru da k'yar. "Me yasaka ki kuka?" ya tambaye ta cikin sanyin murya, "ku kullum Ammeynku tana tareda ku tana kulawa daku duk abinda kukeso tanayi muku bata yawan fita unguwa bare tabarku cikin kad'aici, amma ni kullum mamana tana gidan k'awarta haj. Zakiyya danayi magana sai tabani k'udi ko tace bari ta had'a min wani d'an party bathday d'ina kuwa ko manta date d'in batayi dan Allah bross k'udi ne yake maganin ko wane matsala?" Ta K'are maganan da tambayar abinda yake matuk'ar damun ranta, "A a" yabata amsa cikin tausaya mata domin shima ya fahimci wannan abun yafara damunta hakan kuma ba k'aramin dad'i yayi masa a rai ba ko babu komai tunkafin ya fara tunanin hanyar da zaibi dan shan kanta ta yadda zajata jikinsa su kulle har akai ga maganar da ake son k'ullawa wacce babu wanda yasani dagashi sai Baffa sai kuma Ammey da Baffan yake jin tana da hak'k'i akan tasan komai. "Amma Maryam bamune muka tsaneki ba kece Kika tsanemu bakya mutantamu da Ammeynmu ko kad'an har zaginta fa kikeyi taya kike tunanin zamu mutuntaki bayan bakya mutanta mana mahaifiyar mu?" K'are maganar dayi mata tambayar wanda nan take ta gano kuskurenta amma Kuma sai tace "ai mama tace kada nasake nayi sabo da 'yan uba dan muddun nace zan dinga mu amalantar ku to babu abinda zaisa baku kashe niba tunda Kuna ganin agabanku Baffa yake nuna yafi k'aunata akan ku, kuma tace Ammey muguwace tun ina jaririya taso kashe mata ni kuma tace Ammey ce take asiri take had'a ta fad'a da Baffa shiyasa kullum yake mata fad'a baya bata k'udi saidai inya ajiye ta turani d'akin sa na d'ebo mata mai yawa amma baya isarta saita had'a danawa. Tsabar tashin hankalin jin wannan mugun zantukan baisan sanda ya zube ak'asan wajen yace "maman?" Yafad'a gamida zaro ido har saida yanayin sa ya mugun tsoratata. Pls manage data taku har kullum MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Wannan shafin nakune gaba d'aya kuyi yadda kuke so MUHAMMAD KAREEM HAYATU BABA ZUBAIRU (YAYA HAYAT) ITS ABBAS Allah yabar kauna Page 23 Jikinta take ya hau rawa tace "wa lla hi haka tace min, shi yasa kaga nima bana son Ammeynku. Kasa magana yayi da hannunta da ya kama ya rik'e gam cikin nashi, idanunsa kuwa kad'awa su kayi suka yi wani irin ja, Me wannan matar take nufi? Takasa kula da amanar data dauka, Kuma tana son raba hanta da jini wannan ba adalci bane, zalunci ne babba, ke baki kula da yarinya ba, sai ma d'ora ta da kikayi akan wata turba mara b'ullewa. "Zaki abota dani?" Ta tsinci muryarsa cikin wani irin yanayi batasan lokacin data d'ago kai ta dubeshi ba sai dai bata iya tace masa komai ba ganin yadda ya kafeta da runannun idanunsa "Uhm?" Ya k'ara tambayar ta again babu amsa sai faman murza idanunta take da d'aya hannun da bai rik'e ba. "Kema Ammey mamanki ce, ta tsinci muryar shi yana rad'a mata a kunne daga yau zamu rik'a shiga d'akin ta muna hira tare dake, kuma kema duk abinda kike so ki tambaye ta zata baki, kuma tama fi sonki damu idan kina musu ki gwada". Ya fad'a yana cigaba da murza hannunta dake cikin nasa. "Mama bazata barni ba ta tsaneku" ta fad'i abinda tasan kullum maman tana tusashi agabanta, wanda tasan hakanne har cikin ranta. "Ai bazata sani ba saboda kinga kullum bata zaman, gida Kinga kafin ta dawo munyi hiranmu, bawai ki rik'a shigowa d'aki, ke kad'ai ba, Kinga tunani sai ya miki yawa" Ya fad'a yana kallon ta, tabbas abinda ta fad'a gaskiya ne, tunani yana damun sosai wani lokacin har sha daya mama tana kaiwa agidan hajiya zakiyya. Shi kam zama ya gyara tareda zuba tagumi ya kafeta da idanunsa, yayin da tausayin ta ya game mai jiki,yana mai jin haushin kansa, na yadda tun farko bai jata a jikin sa ba bare har yasan damuwar ta. "Zaki iya abota dani inzama amininki wanda zaki dinga fad'awa dukkan wani damuwar ki wanda zai dinga magance miki duk wani matsalar ki da yardan ubangiji?". Ya sake mata tabayan shi na farko, "Idan mama tagan mu tare akwai matsala" ta fad'a masa haka, matsayin ta na wacce tafi kowa kusanci da mama dan haka tafi kowa sanin halinta. "Karki damu Baffa bazai bata damar raba masa kanmu ba, kinsan burin ko wanne ubane ya ga kan yaransa ya had'u" ya fad'a yana d'ago hab'ar ta yana kallon, cikin idonta. "Shi kenan na amince ta fad'a cikin sanyin murya" Ihun murna ya saki tareda rungumeta"na gode my happiness na gode my Lovely sis dan Allah daga yau ki daina wannan had'e min ran baya min dad'i" Ya fad'a mata a hankali "to" tace masa daga haka ta maida hankalinta kan aikin da suke da Nassar, tayata yayi suka gama aikin, daga haka ya rik'a janta da hira. Waahegari motar ta ya iso, motar da Baffa yace bata gift idan taci jarrabawa, tun tana maganar motan har sai datayi fushi ta daina maganan bata san cewa mak'alewar motar daga MD bane shi ya hana saboda rawan kanta, yanzun ma sai yana yi yana sa mata ido sosai. Washe gari kuwa tun kafin ya fito tuni ta shirya ta bar gidan a sabuwar motan ta sai da ya fito yaga Abdul Nassar yana shiga cikin motar da yake kaishi makaranta. "Kai ina Adda?" Nassar ya tambaye shi "tab'Adda yanzun ai ta jima a schl, kasan cewa tayi bari tayi sauri ta tafi kar ka fito ka hanata kace Kai zaka kaita". Murmushi MD yayi Yana shafin sumar kanshi daya sha gyara, daga haka ya juya ya shiga motarsa security d'insa yaja shi suka wuce. Uhm su o o anyi abun kai yaushe rabon duniya tunda bross ya dawo ya hanata sakat hatta motar mama da take hawa sai da ya hana ta k'arfin bala i, dan haka yau take jinta cikin wani irin farin ciki. Tunda ta doshi cikin makarantar ido ya koma kanta domin motar tayi mugun d'aukar hankalin mutane, da yawan su basuyi mamakin ganin wacce ta fito daga motar ba domin ansan tafi k'arfin, wacce ta ninninka wannan ma, dan da yawa wasu suna mamakin yadda bata da motar kanta sai dai akawo ta. Maryam kuwa da gudu tazo ta rungumeta tace "eye had'uwa ta iso kenan" ta fad'a tare da k'arasawa tana shafa motar, wani k'awata taccen murmushi Maryam ta saki tace "humm kinga wannan bross d'in namu sai a hankali, nasan wallahi shiya hana akawo min motar amma Baffa yafi shekara da biyan k'udinta" Itama murmushin tasaki "ina ganin akwai wani abu tsakaninki da bross d'in nan" "Kamar ya? "Kamar yadda na gani bross sonki yake Maryam" Manyan ta bata amsa "Humm baki da hankali kin tab'a ganin inda akayi aure uba daya shifa d'an Ammey ne" "Ammey shekarunta baikai ta haifi kamar bross dinku ba ki dai k'ara bincike" "Humm kawai tace batare data d'auki abin serious ba. Haka dai abubuwa suka cigaba da faruwa cikin k'aramin lokaci Maryam tayi wani mugun sabo da 'yan gidansu batare da sanin maman taba wacce ta mik'a dukkan yarda da imaninta wajen malaman tsubbu da 'yan bori dan haka bata da masaniyar cewa tufkar da take yi ta cikin gida ya gama warewa tas. Wata rana kamar yadda akasaba "Zakiyya takaiwa Sailuba ziyara akan yadda suka kasa fahimtar jina ta waya, "Nifa nagaji da wahala so nake na watsata tabi duniya ta lalace ta zama k'asaitacciyar karuwa bana buk'atar akai ga d'aura wannan auren" "Humm Sailuba kenan wani lokacin kwwnyar ki atoshe yake wallahi, banda ke da abinki idanmma zatayi auren taya zamu bari tayi auren hutu?" "Ni auren ne ma bana son tayi kwata kwata, so nake rayuwar ta ya wulak'anta fiye da duk wani wulak'antacce a duniya. Tofa Muje zuwa Daga taku maman islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Shafinki ne wannan'yar laleta SA'ADATU USMAN MUSA (ISLAM) Allah ya rayamin ke tareda dukkan yayan musulmi badaya Almustapha Usman Musa shalele na kenan kuma nagaban goshi Allah ya tsaremin ku. Page 24 "Kina bani ciwon kai Sailuba nifa komai da kike gani da mugun shiri nakeyin sa, Kuma bana bawa na kusa dani damar gane akwai wani abu a cikin raina dan haka zai wuya kiga idan nayi, abu ayarda ni d'in ce nayi saboda babu fuskan da za a gane hakan, ke kuwa gajan hak'urin ki kawai ya isa tonaki, Kinga alhajina da kike ganinsa bansa me shi da sauk'i ba saboda mugun taurin Kai da Allah ya d'ora Masa, shi yasa kuma kikaga bana masa ta dad'i, domin naci bak'ar wuya kan nasame shi, sannan Kuma kina ganin har yau tak'i amincewa ta saurari Deedah shegiya mai kafirin wayon tsiya na rasa dalilin da yasa bata Sona" Ta K'are dogon sharhin ta da k'orafin yadda Maryam take masifar d'auke mata kai 'yar dariya haj. Sailuba tayi kafin tace" ashe kin manta da cewa nonon wannan shegiyar 'yaalaman tasha, kai wannan mata ta zame min annoba a rayuwata nasa ta yadda zanyi maganin tsinanniya" "Hum ai irin su idan dubunsu ya tashi cika saikin ji kamar kiyi musu kuka wallahi" cewar haj. Zakiyya cikin ya tsina fuska Sun jima suna k'ulle k'ullensu. Tana tunkaro gidan ta tuna da yadda bross ya rik'a kwala mata kira tanaji ta d'iba da gudu dan kar ya hanata fita, tunda suka sam d'an hutun nan ya wani sa mata ido yanzun ta lura aikin ma ba sosai yake zuwa ba sai jifa jifa damma yanzun Allah yasa ko ba kowa zata shiga d'akin Ammey suyi ta hira yadda Ammeyn take mata ne yasa ta jinjinawa k'aryar mamanta da tace Ammey muguwace ko kad'an bataga hakan ba saima wani irin mugun shak'uwa daya soma shiga tsakaninsu da Ammeyn ganin yadda take mata. Sam ta manta da yadda ya rik'a kiranta ta gudu kanta tsaye ta shigo gidan har da yar wakar ta, daman tun fitar ta yake dakon dawowar ta. Tana shigowa taji anyi ram da ita ya damk'e ta a bazata taji an rik'o ta sai abin yabata tsoro ta bud'e baki zatayi masa ihu yayi saurin toshe bakin da hannunsa yace "wa na kama?" Sam ta manta da abinda ya farun dan haka ta hau rarraba ido tana neman hanyar gudu, gane hakan da yayi ne yasa yaja hannun ta zuwa Pat d'in shi. Dan" Allah bross kayi hak'uri banjika bafa" "To in bakiji ba taya kikasan mai ya faru wato bakijin magana ko my happiness?" ya fad'a yana kallon yadda tayi tsuruvtsuru shi wallahi dariyama take bashi, yadda duk ta koma kamar wadda ta aikata wani babban abu tun ranan da suka shirya yake kiranta da wannan sunan hakama Nassar ya daina kiranta da Adda ya koma my happiness. Shiru tayi ba tare da ta tanka ba dan in bata ga dama ba itama wani lokacin muguwar muskila ce sai kayi ta magana tak'i tankaka. "Kina jina ko?" Ya k'ara sanda yake bud'e k'ofar falonsa, Maryam da take shirin bashi amsa kasawa tayi saboda ganin irin had'uwa da tsaruwan falon kasa daurewa tayi tace "wow gaskiya nima bari Baffa ya dawo wajena daban nima nake so kamar naka" Ta fad'a tana shigewa cikin falon tana lumshe ido saboda daddad'an k'amshi da sanyin da ya bugi hancin ta sai da ta gama k'arewa falon kallo sannan ta juyo ta dubeshi"waye yake gyara maka wajennan?" Ta tambaye shi saboda yadda taga wajen kalkal kamar d'akin mace. D'an murmushi ya saki ya shafi fuskar ta "Ni nake gyara abuna indai ina so yamin yadda nakeso amma yanzun tunda gaki na dunga maleji danaki ko?" Ya K'are da tambayarta, d'an tura baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "hum um ai tunda maneji ne kawai kaci gaba da abunka, Zo kiga ya fad'a yana jan hannunta zuwa saman benan dake falon, ta bishi har zuwa d'akin baccin shi take taga gado lafiyayye mai kyaun gaske "gyaramin zakiyi yau bani da lafiya" ya fad'a mata yana kallon yanayin ta, kafin ya juya ya fita, tana ganin fitar sa tayi wani irin sufa ta haye gadon tana wuntsilawa, wani irin taushi taji kamar auduga aranta kuwa fad'i take wallahi da sake bari Baffan ya dawo nima komai irin na bross na ke so ji gadonsa dan Allah kamar na wani yar sarkin ta k'ara nutsewa akan gadon. Shi kam Muhammad har ya sauka ya tuna wayarshi da yabarta tun d'azun saman madubinsa dan haka ya koma ya dan d'aukowa nan ya shagala da kallon yadda take ta faman tsalle tsalle sam bataji motsin shigowarsa ba sai dai maganar sa taji. "In kin gama Ammey tana kiranki" yafad'a yana d'aukar wayar shi datake saman meerrow ya juya ya fice ya barta batare da ya Kuma kallon inda take ba, Ita kam sai da ta gaji dan kanta kafin ta gyara har bandaki sai da ta wanke masa kafin ta fito baya falon wani d'aki data gani ak'asan ta lek'a kawai sai taga computers da yawa aciki Maryam da Karam bani sai kawai ta shige kafin takai ga tab'awa sai gashi ya shigo kamar an jeho shi. Ganin abinda take k'ok'arin yi yasa yai masifar had'e rai yace "me kika ajiyemin aanan" ya fad'a cikin dakakkiyar muryasa data sanshi da ita tun asali. Maryam da kwata kwata bataji motsin saba sai maganar sa yasa ta juyo a d'an firgice ganin yanayin sa yasa jikinta ya kama rawa tace "nazo ne naga ko kana nan sai banganka ba shi ne shi ne "Shine kika zo duba ajiyar da kikayi anan ko?" Ya tambaya a dake take jikinta ya kama rawa ganin yadda yanayin sa ya koma kamar bai tab'a dariyaba Muje zuwa MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 25 "Ni ka dai na min irin wannan Kal lon" ta fad'a a d'an tsorace cikin rawan murya, k'ara tamke fuska yayi yace " tambayar ki nake me kika ajiya anan?" "Dan Allah bross ka matsa na wuce kar Mama ta dawo bata ganni ba" ta fad'a idanunta na cikowa da kwalla tana nadamar shigo masa d'akin data lura kamar na sirri ne. "Kar ki min kuka idan ba hakaba tattaka ki zanyi yanzun anan" ya fad'a cikin dakewa. Take ta had'iye kukan, tana jiran yabata hanya ta wuce, Saida ya gama hukuntata da mayun idanunsa kafin yaja kunnenta da d'an k'arfi yajata zuwa bangarensu. Fashewa tayi da kuka domin bada wasa yaja mata kunnen ba sannan Kuma ya k'ara da muguntar murd'ewa, ai Nassar yana hangosu yayi saurin ficewa daga gidan daman ya lura yau yayan nasu akan tsini yake. Shigan su yayi dai dai da sallamar Mama wadda dawowar ta kenan taga yanda yake ja ma 'yar ta kunne cikin bala i tace "kai bak'in mugu azzalumi mai tayi maka' ko kuma muguntar daka saba ne ya motsa sakar mata kunne kar ka tsinka azzalumi mugu" Ta fad'a tana daga bakin k'ofar atsaye dan tana masifar shakkar sa domin idan ya juye bashi da mutunci acewar mama kenan. Shi kam yi yai kamar baijiba saida yagama jigata ta kafin ya hankad'a ta jikin uwar ta ya juya ya fice, yana jiyo yadda take ta surfa masa ashar tana tsine masa ya saki wani murmushi mai ciwo yana shafa kwantacciyar suman kansa. Alwala yayi ya fice masallaci domin lokacin anfara kiran sallar magriba. Acikin gida kuwa bayan Mama tagama tujaranta ta juyo Kan Maryam tace "ke kuma me kika Masa yake neman lahanta min ke?" Cikin kuka Maryam tace "wai dan na shiga d'akin compute sa shine fa yazo ya kamani shine tun acan yafaramin bala I" A firgice tace "na shiga uku ni Sailuba me yakaiki d'akin wannan d'an iskan? Baby me had'inki dashi dazaki je d'akin shi? Kodai kin fara shiga sabgarsa ne baby ki rufamin asiri kada ki ruguzamin shirin daya kusa kammala" Da mamaki Maryam take duban maman nata ganin yadda ta fita hayyacin ta daga cewa ta shiga d'akin MD anya babu wani mugun abinda maman take k'ullawa kuwa? Girgizata haj. Sailuba tayi da k'arfi tace "Maryam ki fad'a min yaushe kika fara mu'amala da Muhammad? "Mama ba d'an uwana bane? Maryam tayi mata tambayar cikin mamaki kafin taci gaba da cewa mama dan Allah ki fad'a min illar hakan naga kin rud'e ko zai iya cutar danine?" Tayi mata tambayar tana mai wani irin kafeta da ido, take haj. Sailuba ta dawo hayyacin ta tace "ba haka bane baby kinsan in mace da namiji suka keb'e to na ukun su shed'an ne shiyasa kikaga ina kaffa kaffa dake" Cikin k'osawa da zancen tace "babu ma abinda zai faru insha Allah mama, kuma ni ban tab'a shiga d'akin ba sai yau" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tace "to kar ki k'ara" "Naji tafad'a tana shigewa d'akin ta domin harga Allah zancen ya gara gundurar ta. Itama haj. Sailuba tana shiga d'akin ta ko maganar salla bata tsayiba ta lalubo no haj. Zakiyya ya doka mata kira,jim kad'an bayan ta daga babu sallama babu komai tace, "Na shiga uku na na lalace" cikin rud'ewa haj. Zakiyya tace "lafiya k'awata me kuma ya faru daga rabuwanmu yanzu yanzun? "Zakiyya'yar iskar yarinyar nan tana neman lalata mana shiri, nace zanyi maganin ta kin hana wallahi zata rusamin shirina na shekara goma sha bakwai adai dai lokacin danake hango nasara na kusantoni" "Wai duk me yafaru kike irin wannan zantuka kamar na sambatu?" Haj. Zakiyya ta tambaye ta cikin sauri domin tanason tasan abinda ya firgita k'awar tata haka. Batare da wani jinkiri ba haj. Sailuba ta kwashe duk abinda yafaru daga dawowar ta gidan ta fad'a mata ta k'ara da cewa "inajin tsoron kar su rusamin tsohuwar gabar da na dasa atsakaninsu tsayin shekaru,adaidai lokacin da nake son yarinyar ta kasance mara"""'''' da kata haj. Zakiyya tayi saurin katse ta "wai kina tantama akan aikin sabon bokannan ne?" Haj. Zakiyya tayi mata tambayar cikin son karfafa mata gwaiwa" bana shakka amma ina tsoron tugun uban shegiyar matar nan kinsan shima tsohon d'an tsubbu ne" "Karki damu k'awata idan yanzun yatashi mu atafe muka kwana" nan taci gaba da karfafa mata gwaiwa akan mugun shirin su. Tana shiga d'akinta ta yi gaggawar shiga wanka domin ana shirin shiga massalaci ne lokacin, wanka tayi ta d'auro alwala ta fito d'aure da tawul bata tsaya wani shafe shafe ba ta zura doguwar riga ta saka hijab ta haye saman abin salla. bayan ta idar da sallar ne tayi zikiri da sauri ta tashi ta cire rigan ta hau shafe shafe kafin tagama har an kira Isha kasancewar lokacin magriba ya kwace mata sosai. Sai da ta gabatar da sallar tayi karatun alqur ani mai girma kafin ta shirya cikin wasu riga da wando masu masifar kyau da daukar hankali farare kar, sai wani bluen rubutu da aka yi agaban rigar ONLY FOR YOU shine abinda aka rubuta, wandon kuma da kad'an ya wuce gwaiwar ta kayan sunyi masifar yi mata kyau ta taje dogon gashin kanta tayi parking d'inshi takawo wani bluen Vandana ta sakawa kanta ba d'an k'aramin kyau tayi ba haka nan ta hauyiwa kanta salfie da wayarta. Tana cikin d'aukan kanta a hotunan MD da Nassar suka shigo d'akin tana ganin MD tayi masifar d'aure fuska, saboda abinda yayi mata d'azu, murmushi ya saki yana shafar gefen face d'inshi. K'arasowa yayi kusa da ita ganin haka yasa ta maida kanta kasa tana wani cin magani, kafeta yayi da ido yanajin kamar ya had'iye ta tsabar masifar kyuan da tayi masa, Hannu yasa ya d'ago habanta ya manna mata kiss a goshi kafin amshe wayan ya d'an rab'a ta da jikinsa kad'an ya soma d'aukar su hotuna. Nassar yace "wow gaskiya bross kunyi kyau sosai kamar wasu masoya" da sauri ya dafe bakinsa saboda kallon dayaga MD yana masa fuskansa d'auke da wani irin murmushi. "Nima ayi dani Nassar ya fad'a yana shiga tsakiyar su haka suka kasance ashiriri ce yayin da halin na Maryam ya motsa dan bata kula MD ba saboda abinda yayi mata. Suna haka wayan Muhammad yai k'ara yana ganin layin Baffa na nageria yai saurin d'agawa"Allah ya temaki Baffa na" cewar MD yana sakin wani k'awataccen murmushi, duk shiru Nassar da Maryam sukayi jin MD ya ambaci Baffa "Kuzo ka d'auke ni ina airport" shine abinda Baffa yace wa MD ya katse kiran "yeee" MD yafad'a da d'an tsallensa,duk suka kafeshi da ido kafin Nassar yace "Baffa ne ya dawo?" Hannu ya mik'a masa suka tafa "dad'i na dakai gane wa" inji MD yana murmushi "zo muje mu d'auko shi" yafad'a yana kama hannun yaron "Nima zani" ya tsinkayo muryanta d'an juyowa yayi ya kalli kayan dake jikin ta sai kuma ya d'an girgiza mata kansa "gaskiya bazamu iya jiran har ki canja kaya ba yafad'a yana d'aure fuska" "Dan Allah after kawai zan d'ora akai" ta fad'a cikin marairaicewa " Minti biyu ya fad'a suna ficewa rik'e da hannun Nassar. Taku ce MAMAN Islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 26 Jikin mota ta same su sai zance Nassar yake zuba masa yayin da shi kuma hankalinsa yake kan phone d'insa yanata faman latsawa. Kamshinta ne yasa shi saurin d'agowa ya kafeta da ido yayin da zuciyar sa ya hau wani irin bugawa har d'an rawa rawa jikinsa ya soma abinda bai tab'a faruwa dashi ba. "Muje" ta fad'a cikin fad'uwar gaba saboda shegen kallon dataga ya kafeta dashi, aranta tana bitar kalaman Mama anya ba wani abun ta hangoba kuwa? Take raya hakan aranta sanda take shiga cikin motar, "my princess dan Allah kintaho da wayarki ki aramin?" Cewar Abdul Nassar da ya zuroda kansa ta b'angaren datake, "Kayi me dashi?" ta tambaye shi batare da ta d'ago ta kalleshi ba "Boy zan kira anty dan Allah" Kafin tace mai wani abu wayan yayi k'ara hakanan taji gabanta ya fad'i ganin no ba suna da mamaki aranta tace waye Kuma yake kirana ? "Ki daga mana" take tsinkayo muryansa, Dagawar tayi ba tareda ta k'ara kallonshi ba kafin tayi magana taji ance " Amincin Allah yatabbata agareki yake saurauniyar kyawawa" wani irin murmushi ne ya sub'uce mata, zuwa yanzun ta fara sabawa da halin d boy wanda yabi ya mak'ak'ale mata ga d'anbanzan iya kalami me sanyaya Rai" "Tareda kai ma aboc...........wani irin burki da MD ya take ne yasaka tayi wani tsalle ta gwaru da murgin motar wayar Kuma bata fad'i ko ina ba sai saman cinyarsa. Hannu yasa ya d'auke wayar ya zurata acikin aljihun sa ya ya zagayo a zuciye yace "zoki ki fice min a mota" da mamaki ta tsaya kallonsa domin bataga abinda tayi masaba da zaiyi irin wannan fusatar haka lokaci guda "zoki fita nace malama" ya fad'a cikin wani irin buga tsawa, ai batasan lokacin data fito cikin wani irin rawar jiki ba, tana kallonsa ya koma yaja motar sa da wani irin matsiyacin gudu ya bud'e ta da qura, agogon hannunta ta duba tara saura batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba ta daga kai tana kallon sama yadda wani irin hadari ya murtuke bak'i k'irjinta ta dafe dayake wani fitinannen bugu tace "na shiga uku ni mero, me kuma nayiwa wannan mugun mutumin da zai ajeni anan" ta fad'a afili cikin muryan kuka yayin da aka wani irin kece da ruwa mai mugun k'arfi ga Maryam da mugun tsoron hadari bare ya sauketa a wannan wajen da babu kowa sannan babu gida kusa, jitai wani irin tsanar shi ya dawo mata sabuwa dal, tafara takawa a hankali yayin da take kuka sosai jikinta na wani irin rawa. Nassar kuwa ganin yadda bross d'in nasu yake wani irin tuk'in ganganci yasaka yai tsuru abayan mota yayin da tausayin Maryam ya cika ransa domin baiga abinda tayi masaba zai ajeta wajen da babu kowa sam bai kula da hadarin ba sai zuban ruwa yaji wanda yasa MD ta ka burkin dole. Fashewa da kuka Nassar yayi da mugun k'arfi kafin yace fili "shikenan Addana ta mutu" yafad'a yana kuka sosai kafeshi MD yayi sosai kafin yajawo yaron jikinsa yana cewa "kai me kace?" Memakon ya amsa masa sai cewa yayi"me tamaka bross zaka ajeta inda babu kowa ita kad'ai idan wani mugun abin yasameta fa? Gashi kuma tana tsoron ruwan sama sosai idan ana ruwa babu inda take fita" Sosai gabansa ya fad'i da maganganu yaron har baisan sanda ya tada motar batareda ya Kuma cewa komai ba ya figeta yana maijin haushin kansa akan abinda yay mata duk da cewa har lokacin zuciyar sa masifar zafi yake masa na yadda yaji tana magana da wani wanda yarasa me yasashi jin hakan? Ita ko Maryam fara takawa tayi a hankali cikin wani irin tsoro jin yadda wajen yai tsit babu komai sai k'aran zubar ruwa yayin da zuciyar ta yake wani irin bugun dayasa jikinta rawa sosai tayi nisa da inda ya ajeta sosai tana tafi tana share ruwan dayake feso mata afuska wanda yake wanke hawayen dayake tafaman zubo mata babu ka'k'k'autawa. Yana cikin tuk'in kiran Baffa ya k'ara shigowa faking yayi a gefe kafin ya d'aga "karka zo naga garin da hadari na hau tixi" abinda Baffa ya fad'a kenan ya kashe wayar batare da yace komaiba, saboda kar Baffa ya gane halin da yake ciki. Sanda yazo inda ya sauketa ta ya rage gudu sosai zuciyar sa ya buga dan ganin bata wajen yayin da Nassar ya kuma fashewa da kuka dan a tunaninasa wani abun ne yasamu 'yar uwarsa. "Dalla malam ka karka damemu ka rufe mana baki d'if ya d'in ke bakinsa saboda yadda yaga bross d'in yai wani irin canza kama fuskar nan tayi wani irin ja yayinda ya soma zargin kansa akan abinda yayi mata sam baiga kyautawar saba ko kad'an. A hankali ya cigaba da jan motar yana d'an duddubawa ko zai ganta Maryam wacce taci kuka ta k'oshi ga d'an banzan dukan da ruwa yake mata wanda yasa wani mugun zazzab'i ya saukar mata lokaci guda ta sami gefen hanya ta zauna tana ta faman shashshek'a. "Gata can bross" Nassar wanda shima yaci kuka ya k'oshi ya fad'a yana nunota tana zaune kan wani dutse data gani abakin hanya jikinta yana wani irin rawa. Da mugun gudu ya bud'e motar ya fita yana cewa Nassar kar ya fito a cikin ruwan nan, bak'aramin sanyin jikinsa yayi ba ganin yadda ta had'e Kai da gwaiwar ta tana faman shashshek'a, a hankali ya durk'usa agabanta ya dafa kafad'anta. D'agowa tayi a mugun firgice domin batayi tunanin ma zai dayiba asanin datayi mai na tsantsar rashin mutunci sannan kuma tasan ba wai yana sonsu bane kamar yadda mamanta ta fad'a Mata. Wani irin kallo ta watsa masa da idanunta da sukayi wani irin ja wanda har lokacin basu daina zubo da ruwa "sorry" ya fad'a can k'asan mak'oshi cikin d'an rawa rawan murya "sorry for what?" ta tambaye shi cikin tsantsar b'acin rai da bak'in cikin abinda yai mata. "Zo mu tafi" ya fad'a yana kallon yadda ruwa yake tsiyayo Mata tundaga kanta yana kwanrawa kayan jikinta duk sun wani lafe mata ajiki dake ruwa ake tsugawa bana wasa ba, banza tayi dashi kamar bataji me yace ba. "Dan Allah" ya k'ara fad'a kamar maijin tsoro, yayin da shima sanyin ruwan yafara ratsashi " ba ruwana da kai kar ka k'ara shiga harkana babu ni babu kai mugu kawai" ta fad'a cikin rawan murya sosai yayin da wani irin sanyi yake k'ara shigarta hatta hak'orinta yana jin yadda suke bugan juna "Dan Allah" ya k'ara fad'a kamar zai mata kuka mak'e mai kafad'a tayi tace "um um na tsan..........wani irin fisgota yayi kafin ta k'arasa ya had'e bakinsu waje guda yana mata wani irin shan mugunta sai da ta raina kanata kafin ya sakar mata bakin cikin wani irin b'acin rai yace "sai wancen dan iskan saurayin naki ne baki tsanaba ko? Ni kikewa wannan abun akan na nuna b'acin raina akan kina kula wani banza can daban ko na gode" ya fad'a muryan shi na d'an rawa kad'an. Sai yanzu ta gane dalilin dayasa ya gane mata wannan bala in yabarta a cikin tashin hankali da tsoro jitai ranta ya dad'a mugun b'aci zuciyar ta ya wani irin dakewa ta mik'e kawai ta kama tafiya dan taci alwashin bazataje a motarsa ba "ke meye haka?" ya fad'a cikin d'an tsawa tsawa ko kallon inda yake batayi ba taci gaba da tafiya. Duk irin yadda yaso rarrashin ta abin gagara yayi hakan yasaka shi tattare hannun riga ya sunkce ta tana wuwulla k'afa tana komai ya nufi mota da ita Plss manage MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 27 Bud'e motar yai ya wulla baya kusa da Nassar sai uban kuka take jijiyan kanta sunyi wani rud'u rud'u fuskar nan tayi jajur tsabar kukan da takeci. Shiru Nassar yayi yana kallon yadda Adda nashi take kuka ga ruwan dayake ta faman diga daga jikinta rawan da jikinta yake kawai ya tabbatar masa da akwai zazzab'i atare da ita. MD tuk'in yake amma ba acikin nutsuwa ba domin ba k'aramin bugun zuciyar sa kukanta yake ba ko kad'an baiji dad'in abinda yayi mataba sai dai ko kad'an zuciyarsa ta kasa amsar laifin ganinsa bai kamata ace ta tsaya magana da wani k'aton agabansa sosai abin ya masa zafi aransa, wata zuciyar Kuma cemai tayi inbanda abinka kasan waye da har zakayi saurin fushi haka "zai wuce d'an iskan mate d'in nan nata" ya fad'a asarari Kuma da k'arfi, duk suka bishi da kallo har Maryam datake kuka sai data tsagaita jin yadda ya bugi sitiyarin da mugun k'arfi. Suna zuwa gida taba tsaya amsar wayanta ba ta balle murfin motar tayi cikin gida da gudu tana shashshek'a ta wuce mama da Ammey a falon duk suka bita da kallo, saida tasawa d'akin key tasan sarai sai Mama ta biyota jikak'k'un kayan ta cire ta shiga ta had'a ruwa mai mugun zafi har lokacin rawan sanyi take sosai ta shige cikin ruwan tana faman sauke ajiyan zuciya sai da ta gasa jikin ta sosai kafin tayi wanka ta fito ta shafa mai ta haye gado ranan bata had'u da Baffanta duk da irin yadda tayi kewansa. Washe gari ma bata fito da wuriba sai da ta gama duk nuk'u nuk'un ta sannan ta salla wanka ta ta tsara kwalliya mai kyau da d'aukan hankali ta fito cikin nutsuwar ta duk suka bita da kallo har tayi wani fayau da ita. Baffa ya dubeta yana murmushi ya mik'a ta hannu"zonan ki zauna, ya fad'a yana nuna mata gefensa nayi kewan ku sosai yarana" ya fad'a yayin da tasako hannunta cikin nashi ya zaunar da ita a kujeran kusa dashi. Tunda ta fito ya kafeta da ido sai yaga ta k'ara masa wani fitinannen kyau, gaida iyayen nata tayi, kamar ta share shi sai kuma ta gaidaahi cikin sanyin murya amsawa yayi yana k'ureta da ido, tai masifar had'e rai tana had'a tea. Su Mama suna gama karyawa suka bar wajen suka koma falon Baffa da akwai abinda suke son tattaunawa. Yana ganin fitar su ya ture nashi abincin ya kwantar da kansa saman tebur d'in yana binta da wani fitinannen kallo Nassar na ganin haka ta d'auke ragowar abincin sa yabar wajen. Gaba d'aya ya takura da wannan banzan kallon nasa sai dai bata son tayi abinda zai gane hakan, kasa cin abincin tayi sai ruwan shayin da take ta karb'a tashi yai ya dawo kusa da ita kofin shayin ya karb'a daga hannunta ya zauna ya kai bakin ta, d'auke kanta tayi tareda k'ara tamke fuska. "Kiyi hak'uri dan Allah, ya jikin naki?" ya fad'a yana shafar gefen fuskar ta, banza tayi da shi idanunta yana cikowa da hawaye ko abinda d boy yai mata bai sosa mata rai kamar na MD ba. Juyo da fuskar ta yayi kusa da shi yana k'ara kai mata abincin bakinta "karki min kuka, kiyi hak'uri dan Allah" ya fad'a cikin sanyin murya, batare da tace k'ala ba ta yunk'ura zata bar masa wajen ya daka mata tsawar dayasa ta koma ta zauna batare da tasan tayi hakan. "Wallahi yanzu sai na tattaka ki dan kinga ina lallab'a ki shine kike neman ki kawo min rainin hankali karb'i dalla malama" ya fad'a yana kai mata abincin baki ganin yanda yai kicin kicin da rai yasa ta bud'e bakin ya zuba mata abincin haka ya dinga bata tana karb'a tana hawaye har saida ya tabbatar ta k'oshi kafin ya bata ruwa tasha ya kama hannunta ta suka nufi part d'insa. Duk jiya bai iya runtsawa ba saboda tunanin abinda yayi mata iya binciken sa nason gano dalilin yi mata haka amma amsar d'aya ne tayi waya da wani agabansa dalilin fushin sa akan hakan simple words INA SON TA duk ta yadda ya juya al'amarin amsar d'ayace abin ya masifar tayar masa da hankali bai tab'a tunanin hakan daga zuciyar saba sam batayi masa adalci ba kuma ta zalunce shi tayi mai abinda zai hana shi cika alk'awarin daya daukarwa Baffa, dan iya jiya kawai ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba ganin halin data shiga sosai ya bama kansa laifi akan abinda yayi Mata. Suna shiga falon ya zaunar da ita saman kujera ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta yana murzawa a hankali wanda hakan yasa taji wani irin yarrrrrrrr ajikinta da k'arfi ta k'wace hannunta ga mamakinta sai ji tayi yace "bani da lafiya" shine abin taji ya fad'a cikin wata irin murya wadda take taji wani irin kasala ya rufeta saboda salon dayai maganar kasa ce masa komai tayi sai ma k'asa da ta maida kanta tana faman cukwaikwauye gefen d'ankwalin doguwar rigan da yake jikinta "Ni kaina bansan abinda yasa nayi miki hakan ba princess nasan ban kyautaba abinda nayi, abin yayi mugun damuna na rasa yadda zanyi na kasa runtsawa saboda neman dalilin da yasaka nayi miki hakan, sai dai dalilin dana samo bai min dad'i ba ko kad'an Maryam" ya k'arasa da kiran ainihin sunanta wanda sai yaune ta tab'a jin ya kira sunanta iya tsawon rayuwar ta, sai taji wani iri aranta sai dai bata d'ago kaiba bare tace wani abu. Ga mamakinta sai ya kamo fuskar ta ya juyo da ita saitin tashi ta d'an kafe shi da ido yadda taga yayi mugun yin kalar tausayi idanunsa da ta kalla kuwa sai da gabanta yai masifar fad'uwa da sauri ta mai da kanta k'asa. Abinda ya k'ara bata tsoro yadda ya zame ya durk'usa agabanta yana kallon cikin idonta yace "dan Allah princess in rok'i wani alfarma a wajen ki?" Yadda yayi matan ne yasaka batasan sanda ta d'aga masa kai ba alaman shi take sauraro " dan Allah princess ina so na zama amininki na k'ut da k'ut yanda komai zakiyi sai kin sanar dani nima duk abinda zanyi sai na sanar dake sannan dan Allah yaron jiya kar ki k'ara d'aga kiran shi namayi blocked d'insa dan Allah kimin wannan" "Aini bazan iya abota dakai ba kai mugune baka da tausayi daman ai su sojoji basu da imani shi yasa na tsan"..........bai bari ta k'arasa ba yayi saurin rufe mata baki da hannunsa cikin sanyin murya yace "zokiji Allah na daina daga yau bazan kara b'ata miki rai ba" Idan na tabbatar da hakan sai na zama friend d'in naka amma ni yanzun banyin abota dakai yasin dan zaka iya kashe ni wata rana ai dama Mama tace komai dad'in ka da 'yan " ke" Ya buga mata wani shegen tsawa "wallahi kika Kuma min zancen d'an ubannan sai na sab'a miki kammani yanzun nan haba kin ishe ni da wani'yan uba'yan uba'yan uban............ya dank'aro k'aton asher ya dank'ara kafin yaci gaba da fad'in duk wanda yasa miki wannan tunanin jakine shi dabba ne mai kwakwalwan kifi Kuma daga yau ina so kisa aranki cewa baki da wani d'an uba duk uwa d'aya uba d'aya muke agidannan tashi ki fita" ya fad'a cikin daka mata tsawa yana nuna mata k'ofa ai da gudu ta fella cikin rawan jiki dan yanayin sa ba k'aramin firgita ta yayiba. Komawa yayi saman kujeran da ta tashi ya zauna tare da kwantar da bayansa yana fitar da wani mugun huci me azabar zafi aduniya bai tab'a ganin matar daya tsana kamar Sailuba ba ya tsane ta ya tsane ta ya tsane ta har baisan yadda zaiyi ba MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM . page 28 Tana shiga d'akinta ta mai da k'ofar ta rufe kamar ance ya biyota ne, k'arasawa tayi bakin gado ta zaune tareda dafe k'irjinta da har lokacin bai bar bugawa ba ta "jarababbe kawai mutum babu abinda ya aje sai masifa ta fad'a tana kwanciya akan gadon bata jimaba kuwa bacci yayi awon gaba da ita. Tunda ya zauna ya lumshe idanunsa zuciyar sa na masa zafi, so yake kota wane hali sai ya raba Maryam da haj. Sailuba domin wannan matar bata da maraba da matar shed'an muguwar hatsabibiya ce tasan takan mugunta shi kansa yana tsoron shirin da take kan 'yar mutane domin yafi kowa sanin cewa ba rainon banza haj. Sailuba tayi wa Maryam ba dan bata aikin banza shi yasa yake son ko ta wane hali ya yakice Maryam daga jikinta kafin ta kai ga halaka ta. Ganin zaman sai k'ara bijiro masa da wasu irin tunaninka yake yasa yai wanka ya bar gidan. A falon Baffa kuwa bayan sun gama d'an tab'a hiransu kamar yadda suka saba Baffa ya d'an dubi matan nasa yace "yau ina so naje k'auye ba kuma zan dawo yau d'in ba sai Allah ya kaimu gobe" A matuk'ar firgice haj. Sailuba ta d'ago tana duban Baffa cikin tashin hankali yaushe tayi wannan saken ca take ta riga da tagama da babin wannan tsohuwar me shegen taurin kan tsiya ai kuwa zata gyara mata zama yanzu dai ba ta ita take ba ta wannan 'yar matsafin mutumin da aiki baya cinta take. A fuska ma nunawa tayi tafi kowa murnan zuwansa a bad'ini kuwa ji take kamar tayi ta ihu domin har ga Allah tun lokacin da Inna ta bada shawarar ayi mata kishiya ta sha alwashin sai ta d'an d'ana mata guba fiye da wacce ta d'an d'ana mata. Sai da ya fara zuwa wajen malam Babba kamar yadda ya saba yauma saida ya bashi rubutu yasha ya shafe jikinsa sannan yake bashi a duk lokacin dayake gari, kafin ya sanar dashi zaije ganin gida ba k'aramin dad'i malam yajiba domin hasashen shi yazama gaskiya cewa Baffa rabashi ake son yi da mahaifiyarsa shi yasa yaji sam baya son zuwa, amma duk wanda yake wannan abun sam bai kyautawa kansa ba. Bayan fitar Baffa babu jimawa itama ta shirya ta fice bata zame ko ina ba sai wajen bokanta kasancewar haj. Zakiyya sunbar k'asar da mijinta yasa batama tsaya b'ata lokacin tab'a ta wuce abin ta. Bayan tagama korawa bokan ta bayanin aikin da take son yayi mata ya jima sosai yana zane cikin k'asa kafin ya d'ago ya dubeta yace. "akwai abubuwa da yawa wanda kika jima kina k'ullawa duk tunaninki basa yiyuwa?" Ya fad'a yana kallonta, shiru tayi domin batayi tunanin aikin da take yana ciba dan bata ganin nasara a ciki. Aikin ki yana ci kuma abubuwan da kike sunyi yawa kuma duk ta sigar da kika d'auko hanyar wargaza komai tanan zai wargaje zaki sha mamakin rana da lokaci da waje amma kuma akwai cin amana da bayyanuwar asirinki daga baya daga wajen mutum mafi kusa dake wannan shine ki tashi kije da baya banda waiwaye daga yau bazai k'ara zuwa wajen uwarsaba sai dai ita tazo shi da garin nan sai dai yaje gaisuwar ta bayan ta rasu. Tunda takwanta take waau irin mafarkai marasa kan gado sosai take jujjuya kai tana gumi babu abinda yafi rud'a ta sai tsintar kanta da tayi a wani a hali mara dad'i tana cikin jujjuya kai kamar wacce aka tasa ta bud'e ido a firgice, sai da tayi addu'ar tashi a bacci kafin ta mik'e cikin tashin hankali ta hau karanto hasbinnallahu wani imal wakil sosai abin ya tsaye Mata arai. D boy ne a office d'in babanshi suna hira yake sako masa maganar Maryam Abba AL HASSAN yace " 'yar waye?" " 'yar Baffa Abubakar ce" " Kai k'arya ne wallahi badani ba ka rasa wa zaka d'auko min a matsayin suruka sai k'anwar wannan bom d'in wallahi ba isa ba baka isa ba nace dan ubanka" "Ni wallahi Dad ita nake so dan haka banga wanda ya isa hanani aurenta ba waima Dad meke tsakaninka da yayannata ne naga ko sunan su kaji saika firgita?" "Ban sani ba dan uwarka kuma muddun nine ubanka ban yafe maka auren wannan irin masifar ba" " Muddun kaga ban aure taba ka tabbatar mutuwa nayi amma kai baka isa hanani auren taba wallahi" ya fad'a cikin dukan teburin tsakiyar su cikin murgud'a baki kamar wani sa 'ansa, Wannan ba komai bane a wajenshi dan al amarin gidan Abba AL HASSAN babu tarbiyya ko kad'an da gaba d'aya sun gama sangarta d'an nasu kasancewar shi kadaine d'an da suke da. "Tunda haka kace to wallahi babu ruwana duk abinda ya biyo bayan ka kar kasawa ranka cewa na san ka dan wallahi ko kallon inda kake bazanyiba. "Ba damuwa" Kamal ya fad'a yana ficewa daga office din Plss manage Daga taku MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 29 Wanka tayi ta tayi alwala dake lokacin an fara kiran Azhar dan haka tana gabatar da sallar ta shirya tareda daukar bag d'in ta ta fito babu kowa a falon sai Ammey. "Ina zaki haka?" Ammey ta tambaya tana kallon fuskar ta dayake cike da damuwa' kamar bazata tanka mataba sai kuma tace "shopping" kamar maijin tsoro tayi maganar" "Zonan" Ammey ta kirata kallon Ammeyn tayi kamar tayi mata gardama sai kuma ta karasa kusa da Ammeyn ta zauna ta d'an jingina jikinta dana Ammeyn,abinda bata tab'a yiba iya tsawon shekarun datayi a hannun haj. Sailuba batama samu anbar ta taje inda take ba bare ta rab'etan. Wata irin ajiyar zuciya Maryam ta sauke mai k'arfin gaske lokacin da ta kwantar da kanta jikin mahaifiyar ta ita kanta Ammeyn sai dataji wani iri aranta bata san sanda wasu irin hawaye suka zubo mata ba tayi saurin gogewa dan kar tagani. Duk inda uwa take ko a ina ne ko a wane hali take ta fita daban hakanne ya kasancewa Maryam jitai wani irin nutsuwa na shigarta tareda wani d'an Karen sanyi da ya dirar mata lokaci guda alamun zazzab'i keson kamata. Haka nan batasan dalil ba kawai taji ta kama hawayen da batasan ko na menene ba tun iya hawayen ne har tafara shashshek'a, a rud'e Ammey ta d'ago fuskar ta tana kallon yadda take shashshek'a kallon lips d'inta tayi yadda suke rawa sosai batasan sanda ta k'ara k'ank'ame ta ba tana d'an buga bayanta kad'an kad'an batare da tace komai ba domin tasan tabbas itama idan tayi magana nata kukanne zai fasu. Sai da suka shafe ak'alla mintuna uku kafin Ammey ta d'ago ta ta fara share mata hawayen "me yake damunki?" Ta tambaye ta ahankali kamar tana jin tsoron wani yajita tace "Ammey jikin yafi na Mama dad'in kwanciya kuma ga d'umi,dan Allah Ammey nima ki rik'a rungumeni kamar yadda kike wa Nassar" "Naji amma sai kin fad'a min abinda yake damun ki kwanakin nan, na lura kina da damuwa keep ki fad'a min koda ahawaran da zan baki" kallon Ammeyn ta dingayi babu k'ak'k'autawa yayin data ta dinga jin wani abu mai sanyin gaske yana ratsa ta, tunda take da maman ta bata tab'a tambayar ta damuwanta ba sai dai idan taganta a damuwan ta d'ebi manyan kud'ad'e ta bata tace taje ta kore damuwan ta. " Ina jinki'yar albarka maza ki fad'amin ki d'auka cewar kina fad'awa mahaifiyar ki ne kima sa aranki cewa ni mahaifiyar kine zan miki maganin duk wani damuwaki a duniya,wanda kuma yafi k'arfi na zan fad'a wa ubangiji na" Ammey ta fad'a tana saurin goge hawayen daya zubo mata dan kar ta gani Muhammad dayake tsaye bakin k'ofar tun sanda Ammey ta kira Maryam ya saki wani boyayyar ajiyar zuciya aransa yana fatan Allah ya karya ak'adarin haj. Sailuba. "Ba komai" ta fad'a a hankali "kwai baby command fad'a min kinsan babu kyau d'a ya rik'a wa mamansa k'arya" batasan sanda ta rushe da kukaba tace "Ammey k'udi sune maganin ko wane matsala?" Ta tambaye ta abinda yafi komai damunta a rayuwarta " Injiwa? Duk wanda ya fad'a miki wannan k'arya yake ko waye yana yaudarar kine kawai, amma akwai abinda k'udi bai isa yayi maka shi ba da yawa ma a duniya dan haka duk wanda ya fad'a miki hakan yayi karya ya fad'i son ransa ne kawai" Ta fad'a tana shafa kanta nan "Mama ce koya ta ganni a cikin damuwa sai ta d'ebi manyan kud'ad'e ta bani tace zasuyi min maganin ko wace irin matsala a duniya" duk da cewa tasan zata iya jin abinda yafi haka daga d'iyar tata ma amma hakan sai yayi masifar d'aga mata hankali tace "Tana iya miki kyautar nawa lokaci guda?" Ta tambaye ta cikin tsantsar tashin hankali "har dubu d'ari biyar cash tana bani tace muje mu kama waje muyi d'an kwarya kwaryan walima wai na jikina ma su mori arzik'in ubana" "Kina yi?" Ammey ta k'ara jefo mata wani tambayan "da inayi amma yanzun tara k'udin nakeyi da sukayi yawa na sai gida kuma da wasu kusan 7 million a d'akina har sani fa take na d'ebo mata k'udin Baffa kinsan baya k'irga wa yake ajiyewa" "Innalillahi wainnailahi raji un" shine abinda Ammeyn ta fad'a cikin tashin hankali "Allah sarki Nanne da Anty shamsiyya yau ga abinda kuke fad'a min yana shirin faruwa tayi maganar cikin zubowar wasu zafafan hawaye. Da sauri ta share hawayen tace"kin yarda dani zaki iya bani ajiyar duk abinda kika mallaka?" Ta tambaye ta cikin rawan murya " Eh Ammey me zai hana ta bata amsa yayin da wani irin sanyi yake kwaranya aranta "Yayanku fa?" ta k'ara tambayar ta "Tab'ni bazan bashi ba mugu ne gashi masifaffen tsiya ta fad'a tana hararan gefe. Murmushi Ammey tayi shi kanshi Muhammad dake bakin k'ofar maganar ta ya bashi dariya dan haka ya d'an murmusa yana shafar k'irjinshi a hankali kamar wanda wajen yake masa ciwo "Kece baki gane halinsa ba amma yana da kirki sosai kuma zai kula daku sosai koda ace yau babu Baffa baku da sama dashi SHINE GATANKU" Tab'e baki tayi ta mik'e tana cewa "anjima zan kawo miki A T M d'ina Mama bata san dashi ba saboda shegen kashe k'udin ta idan ta sani duk saita rance kuma ba biyana take ba, tunda kince kin yarda dashi sai ki bashi zan had'a shi kuma da na siyi gida ta hanyar sa wallahi ya cinye kwandala ta bazai yi ciwon kai ba biyana zaki" Duk yadda yaso dauerwa saida ya fashe da dariyan maganta domin ta bashi dariya sosai wallahi, ita kanta Ammeyn murmushi take kafin tace "yanzun to ina zaki naga ko abinci baki ciba" Eh banjin yunwa zanje shopping, ina Nassar ya rakani?" "Za daiki siyan kayan zakin da kika saba maza muje yau nima na fanshi hajiyan tunda bata nan muje na baki da kaina tunda ta gama shagwab'a ki" Sai taji ta kasa yi mata musu tana zuba mata abincin kafin ta fara bata MD ya shigo wajen da sallama Ammey ta d'ago ta dubeshi ganinsa da kayan gida tace "yau kuma ina uniform d'in?" "Banje office ba yau?" Ya fad'a yana zama facing d'in Maryam datai wani kicin kicin da rai, murmushi ya saki lokacin da ya juyo da hannun Ammey santar bakin sa ya amshe abincin da ta d'ebo zata kaima Maryam baki, bata san sanda ta b'alla masa wata shegiyar harara ba ta juya ta kalli Ammey a marairaice tace Ammey" "K'yale shi baby in yasa tsiya yanzun zan korashi amshi maza kici ki k'oshi kinji yarinyar kirki ta fad'a tana bata, sosai taci abincin, tunda take zata iya runtsawa cewar bata tab'a samun farin ciki irin na yau a rayuwarta ba sai taji Ammey ta bala in kwanta mata arai. tana gamawa tasa tusio ta goge bakinta ta zari mukullin motar ta"sai na dawo Ammey" "Baki ba Ammeyn ta fad'a tana mik'ewa ta k'arasa kusa da ita kanta ta dafa tayi mata addu'a sosai kafin tace "Allah ya tsaremin ke ki kula da kanki ki kare mutuncin ki domin shine Martaba ki" Wani irin sanyi Maryam taji aranta ta rungumeta ta tace "na gode sosai Ammey dan Allah ki rik'a min haka please" "Kullum nake miki haka amma ba kusa da kusa ba amma ko yaushe kece farkon wacce nake fara yiwa addu'a kafin nida kaninki da sauran makusanta na" "Allah Ammey?" Maryam ta tambaya ciki farin ciki tare dajin yadda matar tak e k'ara bin dukan jikinta, dama haka halin Ammeyn yake amma mama tace muguwa ce. MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 30 Rungumeta ta k'ara yi tace "na tafi Ammey na" "Sai kin dawo'yar albarka" "Nima zan rakaki zaki siyamin chocolate?" Yayi mata yadda Nassar yake mata, batasan sanda ta saki murmushi ba ta fice a daga wajen cin abincin, binta yayi shima domin yi mata rakiya. Tayi zaton shi zai jasu, sai kawai taga ya bud'e wajen mai zaman banza ya k'ame abinsa, tura baki tayi tana d'an hararansa ta gefen ido, sarai ya ganta sai ya mai da kansa gefe yana d'an murmushi hakanan yanzu komai tayi burge shi take. Sai da ta zauna ta sakarwa mai gadi k'aton hon wannan ba sabon abu ba ne awajenea sam indai zatayi tuk'i batayin na nutsuwa tun lokacin data ke a matsayin Maryam ba yanzun da ta zama mero ba lol🤣🤣🤣 Shi kanshi Muhammad sai da yai mamakin ganin yadda ta wani figi motar da masifar gudu bai san sanda ya juyo yana kallonta ba "ke baki da hankali ne?" Ya fad'a lokacin dayaga ta kusa fad'awa wani d'an rami dake tsakiyar titin data hau tayi wani irin kaucewa ramin "Princess tsaya" ya da sauri yana dafe kan sa da duka hannayensa. Babu musu ta nemi waje ta faka dama da biyu ta keyi dan ya amsa banda son banza tana tare dashi d'in zata zauna ta jashi🤣🤣🤣 Canjin wajen zama sukayi ya amshi tuk'in yana fad'in"naga alamun ke kin shirya mutuwa ni kam gaskiya bana so na mutu banyi aure ba" Ya fad'a cikin barkwanci. Murmushi kawai tayi bata tanka masa ba, sai ma wayar ta data d'auko ta bud'e data tana chat da friend d'inta tana duba no d boy babu shi kwata kwata a jerin contact d'in ta da gaske yake ya goge. D'an kallonsa tayi sai akayi sa a shiama ya wago yana kallonta ta gira ya dage mata alamun ya dai? D'auke kai tayi tana tuna hargagin sa na d'azu akan mama wani lokacin bata cika ganin lafim su ba domin halin mama sai mai hak'uri. Kusan sau uku tana kamashi yana kallonta kuma duk sanda zasu had'a ido sai yamata alaman yadai? Sai kawai ta hak'ura bata k'ara kallonsa ba har suka isa sper market d'in da yawanci anan suke siyayya duka 'yan gidansu. Bayan ya samu waje ya faka ya bud'e ya fito sannan ya zagayo ya bud'e mata bayan tagama gyara mayafinta ta fito a hankali ya Mai da motar ya rufe ya kama hannunta suka fara jerawa cikin wajen. Duk inda suka gifta sai idanu sun bisu saboda masifar kyawunsu da kuma yadda sukayi macin d'in da mutane sukayi da juna. Sunzo shiga shi Kuma d boy sun zo fita shi da abokansa ya gansu sai da gabansa ya fad'i ganin ta tare da wannan gwaskan yayan nata ya wani kafesu da ido har suka k'araso inda suke, sai lokacin ma Maryam ta kula da d boy ta d'an saci kallon MD wanda gaba d'aya hankalin sa yake kan wayar sa. Sai da tagawa d boy hannu ne shi kuma kamar wanda akace ya d'ago sai kawai yabi hannunta da kallo lokacin shima d boy ya d'ago mata tare da wani irin mumushin farin cikin ganin da yayi, kafesu yayi da wani fitinannen kallo zuciyar sa ya hau wani fat fat fat ko ko kad'an bai damuwa da labarin mutane amma ko cikin miliyan sai ya fidda d'an jakin mutumin can, kuma ko da ace shi bai son Maryam wallahi datayi mu 'amala da wancen gwamm ace masa ta mutu ne shi zai fi masa sauk'i. Sam bata kulla da kallon da yakafe d boy da shi ba amma shi d boy yana ankarewa take jikin sa ya hau rawa ta ina zai manta da wannan basumuden mutumin wanda babu abinda ya ajiye sai mugunta tsantsar ta, kafin Maryam tayi wani motsi d boy ya b'acewa ganinta, ta d'ago kai da zummar yiwa MD magana yadda taga yayi kicin kicin da rai sai da gabanta ya fad'i ta d'auke kai aranta tana tunanin anya wannan bashi da aljanu? Duk abubuwan data siya shine ya biya k'udin, suka fito daga wajen har lokacin babu annuri atare da shi dan haka taja bakin ta ta tsuke bata k'ara kallon inda yake ba. Mai makon ya wuce gida kai tsaye taga ya d'auki wani hanya daban amma dake haushin sa take ji bata dube shi ba bare tayi masa tambayar inda zai kaita, har suka isa wani d'an madaidaicin gida mai kyau ya faka motar a k'ofar gidan ya fita ya kwankwasa aka bud'e masa wanda m Bash ya ganine yasashi hangame baki "Amma dai b'atan hanya kayi ko MD" m Bash ya fad'a yana d'an rik'e baki, harara MD ya zafga masa yace "aini gwanda ni na kawo maka ziyaran kai yaushe rabonka da inda nake? Kuma yanzun ma ba wajenka nazo ba wajen madam nazo tana dai ciki ko?" " Hum tana ciki mana ina zata bayan gani yawo ai sai ku manyan gwaraye" Harara ya galla masa batare da yace masa koma mota, har lokacin bata saki ranta ba hannunta kawai ya kama batare da yace mata komai ba ya nufo gidan. Ido ta d'an waro lokacin da suka tunkaro gidan, yayin da shi kuma ya sakar mata murmushi,itama murmushin tayi masa ta d'an rusuna ta gaida shi kafin ' yace ta wuce ciki, Kallo MD ya bita dashi har ta shige kafin ya maida hankalin sa kan m Bash da yafe shi da ido' " Muje man munafiki ka wani zubamin ido kamar zaka cinye ni" murmushi m Bash yayi kafin yace "SON TA KAKE KO?" "Na fad'a maka" "Sai ka fad'amin gashi nan ina ganin sa acikin idanunka" " Hum abokina ban san sanda yarinyar nan tayi tsalle ta daki zuciya naba lokaci guda sonta yamin wani irin kamu wanda har ya fara tab'a wasu daga cikin al'amurana na yau da gone" "Ka fad'a Mata?" "Ban fad'a mataba" "Me yasa?" " Inajin tsoron kar tace bata sona duk da nasan cewa idan nace ina sonta ko bata so sai an bani ita" "To kajarraba Mana" Ta yaya bazan iya ba ina matuk'ar jin tsoron kada tace a a" ya fad'a cikin tsananin damuwa sosai Sosai m Bash yaji yana jin tausayin abokin nasa dafa kafad'ar sa yayi yace "abokina kada ka bari ya huce" daga haka yaja hannunsa zuwa cikin gidan. Har Hajara matar m Bash ta tarb'eta duk da cewa bata santa ba amma ta cika mata gabanta da kayan makulashe suna d'an tab'a hira sama sama dake Maryam bata da bak'unta sam. Kusa da ita MD ya zauna yana kallonta tare da tunanin ta yadda zai fara taranta da maganar musamman idan ya tuna irin kallon da take masa. Ji ta ta takura da kallon daya takura masa dashi d'agowa tayi ta d'an kalleshi kafin ta kauda kanta tana hararan gefe Taku ce MAMAN Islam بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 31 Kayan da Hajara ta aje mata ya kalla yaga babu abinda ta tab'a, sai ya d'an dubeta yaga yadda take ta faman hararan gefe ta wani turo baki gaba baisan sanda ya saki murmushi ba, yasa hannu ya d'ago hab'an ya kafeta da wani shegen kallo. Ganin haka yasa m Bash ya janye matarsa suka bar musu falon, kasa daurewa kallon nasa tayi sai kawai tayi saurin rufe idanunta. "Waye shi?" Ta tsinci muryarsa yana mata tambayar da bata san inda ya dosa ba kallonsa take da alaman tambaya a fuskar ta itama?. "Wanda ya d'auke miki hankali a sper maket?" Yanzu kam kallon shi take da madaukakin mamaki, yadda yai bala in d'auke mata kai har kawo zuwansu nan batayi tunanin zai kula da hakan ba. "D boy ne yaron daya dakeni a schl" "Meye hadinki dashi?" Sai data d'an K'are Masa kallo, irin kallon dayake binta dashi sai kace wani tsohon maye yasa tayi saurin d'auke kanta. "Mutunci ne tsakanina dashi?" Ta amsa tana jan tsaki aranta ganin yadda ya fitineta da kallo. Juyo da fuskar ta yayi saitin tasa ya k'ura mata ido yana mamakin furucin ta lallai ta sauya ba dan kad'an ba tunda har ta kula d boy wanda yagama wulak'anta ta a bainar jama'a. "Amma baki da zuciya princess, mutumin da ya gama gurza miki rashin mutuncin a tsakiyar makarantar ku ke yamzun har akwai wani mutunci da zai had'a ki da shi?" Shiru tayi saboda kallon da yake mata ya masifar ta kurata dan har jikinta ya d'an soma rawa rawa. "Ni kadaina min wannan kallon" ya tsinci muryanta da yayi can k'asa sosai tana fad'a, kallon ya cigaba da binta dashi yayin da ya dad'a kusanto da fuskarta daf da tashi wanda har suke iya jin saukar numfashin juna. Take jikinta ya kama rawa ta soma k'ok'arin kwace fuskar ta daga hannunsa, sai dai bai bata damar hakan ba dan ya rik'e ta gam "Babu abinda yafi min dad'i kamar kallon ki kuma hakan yana saukar min da nutsuwa sosai, dan Allah Kar ki haramtamin kallon fuskar ki yin hakan zai cutar dani sosai. Yanzu kam gaba d'aya ta ware idanunta akanshi Al 'amarin bross d'in nasu ya fara bata tsoro anya bai samu wani ciwon ba kuwa? Yadda yake mata d'innan gaskiya ya kamata a bincike shi "Zaki iya min wani alfarma?" Ya tambaya yana cigaba da kallon ta kuma har lokacin bai saki fuskar ta ba, "To kasakar min fuskana sai muyi maganar" Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa ya sake tan kamar yadda ta buk'ata, ya kwantar da kansa jikin kujeran da suke kai yana maida numfashi. Kafe shi tayi da ido aranta tana mamakin yadda yake da zallar kyau da mugun kwarjini. Tana tsaka da kare masa kallon ne ya ware idonsa akanta yadda take binsa da kallo ya bashi mamaki "Yadai yarinya? Irin wannan kallo haka ai sai kisa naji kunya" ya fad'a yana d'an gyara zamansa. Ai kuwa wani irin fitinanniyar kunya ne ya kamata yadda ya kamata dumu dumu tana K'are masa kallo da k'arfi ta runtse idonta gam gam, yasaki wani murmushi ya d'an matsa daf da ita batayi aune ba sai ji tayi ya sakar mata wani kasalallen kiss a idanunta ai da sauri ta yunk'ura zata gudu bisa ga tsausayi sai taci karo da kayan da Hajara ta ajiye mata tun d'azu, saura kad'an ta kife wajen yayi wani irin fisgota ta fad'o jikinsa, wani irin ajiyar zuciya suka sauke atare. K'ank'ame ta ya kumayi acikin jikinsa yana sauke wani irin numfashi wani irin abu na mai yawo acikin jikinsa ji yai wasu irin hawaye suna k'ok'arin zubo masa wanda bai san dalilin faruwar su ba. "Zaki aure ni?" Ta tsinci muryarsa da yayi wani irin mugun sanyi, a wani irin firgice ta d'ago kai tana kallonsa, har lokacin idanunsa a rufe suke gashi ya wani irin cukwaikwauye ta, shikenan hasashen ta ya tabbata yayanta yana da matsala banda haka ina aka tab'a auren JINI D'AYA? K'ok'arin kwatar kanta ta soma amma ko gezau saima k'ara rik'e ta da yayi "Ki bari mu fahimci juna dan Allah princess ina son na aureki zaki aure ni?" Ya kuma k'arasa zancen da tambayarta, jitai hankalin ta yai masifar tashi take maganganu Maryam wanda su yi dad'ewa ya soma dawo mata inda take ce mata "Da kyar inba sonki wannan bross d'in naku yake ba yadda yai mugun saka miki idonnan da alama dai bazai bawa wani daga waje damar d'auke masa wannan tsaleliyar budurwar ba" Sanda maryam tai maganar hararan ta tayi tace "da alama kin sami b'acewar tunani name sake banda haka babanmu fa d'aya da kike wannan zancean aman babu tashin zuciya" ta k'arasa tana wani irin kallon Maryam d'in da kuma yin kamar da gaske aman zatayi. A lokacin murmushi Maryam ta sakar mata tace "ai lokaci zai nuna kuma kinsan lokaci baya k'arya" "Hmm amma wallahi name sake ban tab'a tunanin kina da tab'in hankali ba sai yau" "Zaki ce na fad'a miki wallahi kallon SO bross yake miki bana sister ba kuma zaki tabbatar da magana na wata rana" Ji tai wani irin fad'uwar gaba ya rikito mata lokaci guda ta ware idanunta akanshi tayi wani mugun tureshi da k'arfi ta mik'e daga jikinsa, ta doshi hanyar fita hankali tashe. Shima ji yai hankalinsa yayi mugun tashi ya bita yana kuranta bata ko juyo ba bare yasa ran zata amsa sai ma wani maganar na Maryam da yake dad'a dawowa kanta a yanzun. "Ki duba da kyau Ammey batayi shekarun da zata haifi mutum kamar bross ba sai dai ko k'aninta kuma idan kinje gida ki tambayi Mama" Tsayawa tayi a jikin motar MD ya k'araso yana kallon ta hankali tashe' yayin da Hajara da m Bash ma suka fito domin yadda MD yake kwala kiran Maryam princess princess ba na lafiya bane sai dai duk nacin m Bash wajen son jin abinda ya had'a su babu wanda ya tanka musu Da k'yar Maryam ta iya d'ago idanunta da sukayi mugun ja tsabar damuwar daya kawo mata farmaki lokaci guda ta kalli Hajara ta daga mata hannu har da murmushin k'arfin hali tayi mata. Shi ko MD bai iya yace komaiba ya figi motar da mugun k'arfi,duk da yadda hakan ya kad'ata yadda taga yana musu ganganci da rayuwa, amma bata d'ago ba saima mai da kanta datayi k'asa batare data shiryawa hakan ba wani fitinannen kuka ya kwace mata, wani irin wawan burki ya taka wajen wasu bushiyoyo ya faka ya kafeta da ido kafin a hankali ya d'ago da kanta yana kallon yadda take rusgar kuka sai kace wacce aka ce mata Baffa da Ammey ne suka mutu "Ki rufamin asiri dan Allah ki tausayawa zuciya ta ki daina kukan nan haka" Kallonsa ta kumayi yayin da kukan ya dad'a kwace mata wanda shi kukan nata yafi komai d'aga masa hankali "Pls" ya fad'a a hankali amma ina bata saurare shi ba "dan Allah" ya kuma fad'a a hankali yana d'an janta kusa dashi ya soma share mata hawayen da k'yar yasamu tayi shiru amma bata ce masa kanzul ba. Har sukaje gida bata k'ara yarda ta tanka masa ba duk irin yadda yake rarrashin ta kuwa, Yana fakawa ta balle murfin motar tayi cikin gida da sauri ko kayan da suka siyo bata tsaya d'auka ba, binta yayi da kallo har ta shige kafin yasaki wani irin ajiyar zuciya mai k'arfin gaske. Har lokacin Mama bata dawo ba dan k'ofar ta yana nan a yadda ta barshi da zata fita wani irin mugun tsaki tasaki wanda yasa Ammey dake fitowa daga d'akin ta zata shiga kicin, da kallon mamaki Ammey ta bita ganin yadda tayi mugun fita a hayyacin ta. "Ke lafiyar ki 'kalau ina yayan naki?" Ammey ta k'arasa tana tambayarta ta fad'awa tayi jikinta tare da fashewa da kukan da yake ta cinta, rik'o ta Ammey ta yi hankali a tashe tajata zuwa d'akin ta zaunar da ita tayi abakin gado ta d'ago kanta tana share mata hawayen kafin tace "Me yafaru, ko wani abunne ya samu yayan naki?" Girgiza mata kai Maryam ta yi " to me ya faru?" ta k'ara tambayar ta hankali tashe " Ammey kece kika haifi Muhammad?" Maryam ta tambaya tana kafe Ammeyn da idanunta da suka kad'a sukayi jajur, "Me ya faru da har ya daga hankalin ki haka kike min wannan tambayar? ji dan Allah yadda ki koma ji yadda idanunki yadda suka kubura tsabar kuka, bana san haka karki karamin irin haka ji yadda kika tashi hankalin ki nima kika tayar min da nawa?" Duk abinda yafaru ta kwashe ta fad'a wa Ammey, wani irin sanyi ne ya kwaranya mata arai ta rungumeta tana fad'in "yanzu ke dan wannan abun kike tayar da hankalin ki ai wannan ba abun tada hankali bane Kinga shikenan zai samu mai kula dashi ko"? Ammey ta d'igawa dogon sharhin ta aya "kamar ya zai samu mai kula dashi ban gane ba Ammey?" Eh kinsan Abban ku Hassan?" Na garin su Inna?" Itama ta tambaye ta "Yauwa d'iyar albarka shifa ina d'an sa da matarsa ta haifa ta mutu ta barshi?" "Ba ance yana k'asar waje karatu ba?" "An fad'i hakane kawai saboda wasu dalilai amma ba kowa bane face Muhammad" Idanu Maryam ta zaro duka waje tana kallon Ammeyn da madaukakin mamaki " Hum shine" Ammey ta fad'a tana daga mata kai ganin irin kallon da Maryam take mata. Nan ta bata labarin MD kamar yadda Baffa ya bata tundaga haihuwar sa da mutuwar mamansa wanda ko abinda ta haifa bata sani ba da yadda Inna ta raune shi har ya girma da yadda matan banansa suka soma azabtar da shi duk da cewa ba gida day'a suke ba har dai MD ya fara wayo ya daina zuwa gidan har zuwa d'auke shi da Baffa yayi har yanzun da yazama wani abun sosai Maryam taji tausayin sa yayi wani irin kamata Allah sarki bawan Allah shi baima tab'a ganin mahaifiyar sa ba ta ayyana aranta "Allah ya jikanta da rahama" ta fad'a tana share guntun hawayen da ya zubo mata "Amen" Ammey ta fad'a tana shafar kanta kafin tace "maza jekiyi wanka kiyi salla kinga lokacin ta ya shiga Kuma yanzun hajiya zata iya shigowa tunda magriba yayi kar ta ganki anan" Batace komaiba ta fice a d'akin. Taku ce MAMAN ISLAM بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 32 Tana fitowa daga d'akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k'yar abakin k'ofar Ammey dan sam bata son had'uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b'aci babu makawa wannan la'a nanniyar yarinyar ta b'ata mata shiri. Tsawa ta buga mata tace "ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a'mala da wadannan matsiyatan ba?" Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango tsantsar tashin hankali atareda maman tata. "Lafiyan ki kalau mama?" Kallonta mama ta d'an yi cikin alamun rashin gaskiya kafin ta wuce b'angaren ta cikin tsantsar tashin hankali. Tana shiga bata bi ta maganar sallar magriba da ake ta kwad'awa a masallaci ba ta zari waya jikinta har rawa yake ta dannawa haj. Zakiyya wacce ita shigarta nata gidan kenan kira da mugun mamaki ta d'aga kiran tana cewa. " Ya akayine k'awata ko zama banyi ba sai ga kiranki?" " Na mutu zakiyya, shikenan kuma nawa ya K'are na shiga uku zakiyya da wannan la'ananniyar yarinyar na fara karo wacce boka yace har gwanda naga kowa dana fara ganinta?" Ta fad'a cikin rushewa da wani fitinannen kuka cikin tashin hankali. Ita kanta wani irin fad'uwar gaba ne ya rufeto mata agigice tace "Ke kuwa Sailuba wanne gangancinne yasa kika bari kuka had'u?" "Cikin kuka tace wallahi nima bansan zamu had'u da itaba kawai ina shigowa mukayi kicib'us" "Allah yasa bakice zakiyi mata fad'a ba dan gudun kar kija mana matsalar kuma" "Nayi, sai dai kafin na dire na gano kuskurena nayi saurin fuskewa" Nan dai suka fara tsara yadda zasu sabunta shirin su tunda wannan ya ruguje. Ganin yadda maman ta d'aga hankalinta har tayi hanyar d'akin sai kuma ta fasa aranta tace ai kina da kud'i zaki sha kan matsalar, ta juya ta shige d'akin ta batare da wani damuwa ba ta shiga wanka a gurguje tayi wanka ta fito ta kabbara salla bayan ta idar ta d'an yi kwalliya sama sama ta fice, duk suna wajen cin abinci kamshinta ne ya sanar dasu zuwanta, duk suka bita da kallo babu MD awajen duk sai taji babu dad'i dan tun d'azu take ta faman juya labarin da Ammey ta bata nasa tana da tausayi duk da kasancewar ba wai yasha wani wuya na azo agani ba amma rashin mahaifiya ba d'an k'aramin gib'i bane ga rayuwar yaro. Tana shirin zama Baffa ya dakatar da ita yace taje ta dubo yayanta ko lafiya dan tunda ya shigo bai ji motsin saba, jitai gabanta ya wani buga da k'arfi take abinda ya faru agidan m Bash ya dawo mata sai dai bata da damar yiwa Baffa musu hakan yasa ta fasa zaman ta juya kamar kazar da kwai ya fashe wa aciki tayi waje duk suka bita da kallo yayin da Mama ta saki wani arnen tsaki tsanar yarinyar yana k'ara tasiri aranta, duk suka bita da kallo, basu kawo komai aransu ba tunda sunsan yadda ta tsani MD. Tana tunkaran wajen bugun zuciyar ta yana k'ara yawaita sai da tashafe kusan 5 mint kafin tayi k'arfin halin kama mabud'in k'ofar ta tura a hankali kamar mai jin tsoron wani abu, Tunda ya dawo salla yake zaune saman doguwar kujera ya jingina bayansa jikin makarin kujeran idanunsa a lumshe bai tantan ce halin dayake ciki ba abinda kawai zai iya ganewa itace ta cika masa zuciya duk inda zai motsa ta tokaresa. Jin motsin bud'e k'ofar yasa ya maida hankalin sa wajen k'ofar shima bugun zuciyar sa yana kara yawaita bugu ya wani irin kafe k'ofar yay da kallo, a hankali ta shigo bakinta d'auke da siririyar sallama da k'yar ya iya dai daita kansa ya amsa yana dad'a binta da kallo ta d'an kalleshi suka had'a ido bata san sanda ta galla masa harara ba sai ya saki murmushi ya sani sarai takura ta yayi gashi ita kuma babu hak'uri shi yasa. Bata san tasowar saba sai tsintar sa tayi agabanta ya dafa kafad'anta "babyna me kike sone kika ja kika tsaya anan ki shigo mana?" Kallo ta bisa dashi mai kama da harara kafin tace "ni ba babyn ka bace, Baffa ke kiranka yace tunda ya shigo baiji motsin ka ba lafiya kuwa?" "Inafa lafiya an shake min wuya da mugun k'arfi na kasa koda hadiyar yawu" binshi tayi da kallo mai kama da na tausayi dan sam bata gane me yake nufi ba tace "kasha magani me yake damun ka bross? "Ke ce, ya bata amsa cikin bazata kece damuwa ta, kece tunani na, kece jina, gani na, walwala na, kuma jin dad'i na, Maryam kece komai na" yafad'a cikin muryan daya mugun karyewa ta daga kai tana kallonsa duk yayi wani iri ga damuwa nan kwance acikin idanunshi " Kazo muje" "Kije zanzo yanzu" "Ni dai Baffa yace k'afa na k'afar ka" "To jira nayi wanka" Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya haye saman sa da gudu. Cikin 20 mints ya sauka sanye cikin blue jeans da riga ruwan toka kayan sun mugun amsar sa kunsan farin mutum kuma mai kyau duk shigan da yay amsar sa yake. Tana can yawon kalle kallen ta a falon taji ya rik'o hannunta binshi tai da kallo yadda yayi mata kyau ga wani fitinannen k'amshi dayake yi ma mugun dad'i, har sukaje bakin falon babu wanda yace da d'an uwansa komai sai itace ma da suka zo bakin falon ta warce hannunta daga cikin nasa ta wuce ciki abinta murmushi ya d'an saki kafin ya rufa mata baya Duk su Baffa suka bisu da kallo yayin da zuciyar haj. Sailuba kamar zaiyi bindiga tsabar fitina da tsanar ganin Maryam daya Kuma mamaye ta Baffa yace "maman malam daga aike kuma sai najiki shiru?" Rasa me zata cewa Baffa tayi sai ta d'ago ta dubeshi shima ita yake kallo, kafin ta lalubo abin fad'a yay saurin cewa "sanda taje ina wanka" "To ku gama cin abincin akwai maganar da zamuyi daku duka" "Nima Baffa akwai abinda nake son fad'a maka tun kafin kaje wajen Inna kuma naso binka sai bansan katafi ba" Dafa kanta yay yace kar ki damu wannan zuwan ma sai da Inna tai fad'a sosai na rashin ganinki, laifin mamanki ne da tafiya ya tashi sai ta kawo uzurin da dole ake fasa tafiyan dake shiyasa Nassar kawai Inna tafi sani. Yay maganar yana kallon haj. Sailuba da tayi wani kicin kicin da rai zuciyar ta nayi mata mugun sak'a. Shima daga haka ya wuce falonsa Ammey ta tashi ta rufa masa baya dake yau ita ce da girki. Suna barin wajen ta juyo da niyyar zuba abincin dan har ta k'agu taji neman da Baffa yake mata sai karaf idanun ta suka sauka cikin nasa ya wani yi tagumi ya kafe ta da ido, a ranta tace gaskiya wannan mutumin da bansan shi ba babu abinda da zai hana nace maye ne yadda yake da jarababbe kallon nan. Azahiri Kuma abincin da zata ci ta d'iba a flat ta mik'e zata bar masa wajen, gane hakan da yayi ne yasa yayi saurin dafe hannunta yana binta da wani marai raitaccen kallo "dan Allah kar ki tafi ki barni" Ya fad'a kamar zai mata kuka, binshi tayi da kallon mamaki, yayin da shi kuma ya k'ara wani marai raice mata sai ta samu kanta da kasa yi masa musu ta koma ta zauna, shima tsulum ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita "lafiya?" Tace dashi tana kallon yadda yake wani faman shafa cikin sa d'an marairaice mata yayi yace"yunwa nakeji nima" Abincin da ta zuba zata ci ta tura masa ta d'auki wani flat d'in yay saurin dafe hannunta yana girgiza mata kai ta d'an kafe shi da ido dan neman k'arin bayani "ki bani mana" ya fad'a yana kallonta ta d'an had'e rai shi kuma ya kafa mata naci sai da ta bashi haka kuma shima yabata suka ci suka k'oshi. Da alama nacin MD ma kawai zai sa yasamu yadda yake so lol🤣🤣🤣🤣🤣 Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 32 Tana fitowa daga d'akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k'yar abakin k'ofar Ammey dan sam bata son had'uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b'aci babu makawa wannan la'a nanniyar yarinyar ta b'ata mata shiri. Tsawa ta buga mata tace "ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a'mala da wadannan matsiyatan ba?" Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango tsantsar tashin hankali atareda maman tata. "Lafiyan ki kalau mama?" Kallonta mama ta d'an yi cikin alamun rashin gaskiya kafin ta wuce b'angaren ta cikin tsantsar tashin hankali. Tana shiga bata bi ta maganar sallar magriba da ake ta kwad'awa a masallaci ba ta zari waya jikinta har rawa yake ta dannawa haj. Zakiyya wacce ita shigarta nata gidan kenan kira da mugun mamaki ta d'aga kiran tana cewa. " Ya akayine k'awata ko zama banyi ba sai ga kiranki?" " Na mutu zakiyya, shikenan kuma nawa ya K'are na shiga uku zakiyya da wannan la'ananniyar yarinyar na fara karo wacce boka yace har gwanda naga kowa dana fara ganinta?" Ta fad'a cikin rushewa da wani fitinannen kuka cikin tashin hankali. Ita kanta wani irin fad'uwar gaba ne ya rufeto mata agigice tace "Ke kuwa Sailuba wanne gangancinne yasa kika bari kuka had'u?" "Cikin kuka tace wallahi nima bansan zamu had'u da itaba kawai ina shigowa mukayi kicib'us" "Allah yasa bakice zakiyi mata fad'a ba dan gudun kar kija mana matsalar kuma" "Nayi, sai dai kafin na dire na gano kuskurena nayi saurin fuskewa" Nan dai suka fara tsara yadda zasu sabunta shirin su tunda wannan ya ruguje. Ganin yadda maman ta d'aga hankalinta har tayi hanyar d'akin sai kuma ta fasa aranta tace ai kina da kud'i zaki sha kan matsalar, ta juya ta shige d'akin ta batare da wani damuwa ba ta shiga wanka a gurguje tayi wanka ta fito ta kabbara salla bayan ta idar ta d'an yi kwalliya sama sama ta fice, duk suna wajen cin abinci kamshinta ne ya sanar dasu zuwanta, duk suka bita da kallo babu MD awajen duk sai taji babu dad'i dan tun d'azu take ta faman juya labarin da Ammey ta bata nasa tana da tausayi duk da kasancewar ba wai yasha wani wuya na azo agani ba amma rashin mahaifiya ba d'an k'aramin gib'i bane ga rayuwar yaro. Tana shirin zama Baffa ya dakatar da ita yace taje ta dubo yayanta ko lafiya dan tunda ya shigo bai ji motsin saba, jitai gabanta ya wani buga da k'arfi take abinda ya faru agidan m Bash ya dawo mata sai dai bata da damar yiwa Baffa musu hakan yasa ta fasa zaman ta juya kamar kazar da kwai ya fashe wa aciki tayi waje duk suka bita da kallo yayin da Mama ta saki wani arnen tsaki tsanar yarinyar yana k'ara tasiri aranta, duk suka bita da kallo, basu kawo komai aransu ba tunda sunsan yadda ta tsani MD. Tana tunkaran wajen bugun zuciyar ta yana k'ara yawaita sai da tashafe kusan 5 mint kafin tayi k'arfin halin kama mabud'in k'ofar ta tura a hankali kamar mai jin tsoron wani abu, Tunda ya dawo salla yake zaune saman doguwar kujera ya jingina bayansa jikin makarin kujeran idanunsa a lumshe bai tantan ce halin dayake ciki ba abinda kawai zai iya ganewa itace ta cika masa zuciya duk inda zai motsa ta tokaresa. Jin motsin bud'e k'ofar yasa ya maida hankalin sa wajen k'ofar shima bugun zuciyar sa yana kara yawaita bugu ya wani irin kafe k'ofar yay da kallo, a hankali ta shigo bakinta d'auke da siririyar sallama da k'yar ya iya dai daita kansa ya amsa yana dad'a binta da kallo ta d'an kalleshi suka had'a ido bata san sanda ta galla masa harara ba sai ya saki murmushi ya sani sarai takura ta yayi gashi ita kuma babu hak'uri shi yasa. Bata san tasowar saba sai tsintar sa tayi agabanta ya dafa kafad'anta "babyna me kike sone kika ja kika tsaya anan ki shigo mana?" Kallo ta bisa dashi mai kama da harara kafin tace "ni ba babyn ka bace, Baffa ke kiranka yace tunda ya shigo baiji motsin ka ba lafiya kuwa?" "Inafa lafiya an shake min wuya da mugun k'arfi na kasa koda hadiyar yawu" binshi tayi da kallo mai kama da na tausayi dan sam bata gane me yake nufi ba tace "kasha magani me yake damun ka bross? "Ke ce, ya bata amsa cikin bazata kece damuwa ta, kece tunani na, kece jina, gani na, walwala na, kuma jin dad'i na, Maryam kece komai na" yafad'a cikin muryan daya mugun karyewa ta daga kai tana kallonsa duk yayi wani iri ga damuwa nan kwance acikin idanunshi " Kazo muje" "Kije zanzo yanzu" "Ni dai Baffa yace k'afa na k'afar ka" "To jira nayi wanka" Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya haye saman sa da gudu. Cikin 20 mints ya sauka sanye cikin blue jeans da riga ruwan toka kayan sun mugun amsar sa kunsan farin mutum kuma mai kyau duk shigan da yay amsar sa yake. Tana can yawon kalle kallen ta a falon taji ya rik'o hannunta binshi tai da kallo yadda yayi mata kyau ga wani fitinannen k'amshi dayake yi ma mugun dad'i, har sukaje bakin falon babu wanda yace da d'an uwansa komai sai itace ma da suka zo bakin falon ta warce hannunta daga cikin nasa ta wuce ciki abinta murmushi ya d'an saki kafin ya rufa mata baya Duk su Baffa suka bisu da kallo yayin da zuciyar haj. Sailuba kamar zaiyi bindiga tsabar fitina da tsanar ganin Maryam daya Kuma mamaye ta Baffa yace "maman malam daga aike kuma sai najiki shiru?" Rasa me zata cewa Baffa tayi sai ta d'ago ta dubeshi shima ita yake kallo, kafin ta lalubo abin fad'a yay saurin cewa "sanda taje ina wanka" "To ku gama cin abincin akwai maganar da zamuyi daku duka" "Nima Baffa akwai abinda nake son fad'a maka tun kafin kaje wajen Inna kuma naso binka sai bansan katafi ba" Dafa kanta yay yace kar ki damu wannan zuwan ma sai da Inna tai fad'a sosai na rashin ganinki, laifin mamanki ne da tafiya ya tashi sai ta kawo uzurin da dole ake fasa tafiyan dake shiyasa Nassar kawai Inna tafi sani. Yay maganar yana kallon haj. Sailuba da tayi wani kicin kicin da rai zuciyar ta nayi mata mugun sak'a. Shima daga haka ya wuce falonsa Ammey ta tashi ta rufa masa baya dake yau ita ce da girki. Suna barin wajen ta juyo da niyyar zuba abincin dan har ta k'agu taji neman da Baffa yake mata sai karaf idanun ta suka sauka cikin nasa ya wani yi tagumi ya kafe ta da ido, a ranta tace gaskiya wannan mutumin da bansan shi ba babu abinda da zai hana nace maye ne yadda yake da jarababbe kallon nan. Azahiri Kuma abincin da zata ci ta d'iba a flat ta mik'e zata bar masa wajen, gane hakan da yayi ne yasa yayi saurin dafe hannunta yana binta da wani marai raitaccen kallo "dan Allah kar ki tafi ki barni" Ya fad'a kamar zai mata kuka, binshi tayi da kallon mamaki, yayin da shi kuma ya k'ara wani marai raice mata sai ta samu kanta da kasa yi masa musu ta koma ta zauna, shima tsulum ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita "lafiya?" Tace dashi tana kallon yadda yake wani faman shafa cikin sa d'an marairaice mata yayi yace"yunwa nakeji nima" Abincin da ta zuba zata ci ta tura masa ta d'auki wani flat d'in yay saurin dafe hannunta yana girgiza mata kai ta d'an kafe shi da ido dan neman k'arin bayani "ki bani mana" ya fad'a yana kallonta ta d'an had'e rai shi kuma ya kafa mata naci sai da ta bashi haka kuma shima yabata suka ci suka k'oshi. Da alama nacin MD ma kawai zai sa yasamu yadda yake so lol🤣🤣🤣🤣🤣 Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Godiya ta musamman gareku masoyan gaskiya hak'ik'a ina jin dad'in yanda kuke min ina ina sonku domin Allah musamman ma ku d'in nan MAMAN Jani Ammeyn Sadik Antyn muhseen Ya Rahman Mare Jidda MAMAN Abul Mom Irchad Ummey Idris yakub MAMAN sayyadi Shamsan Maman sultan Umm nawaad MAMAN Raees Safiya Sopy Aisha munir MAMAN jabir Xeeyyah Rashida Muhammad Afra Fauzi Ummukurthum Aishatu k sani Zainab autar mm Jannat Aliyu Barira Aminu Hykarianeg 17 Ameenatu Khadija Muhammad Hafsat Bala kawu Maman Arif Ikilimatu D Baraya Ummu Abul Mr maimunatu Aisha ibarahim ummi Zainab Muhammad sambo Juwairiyya Lawal Maman twins Mama Khadija Isa Dari Duk wanda bai ji sunan sa ba yamin afuwan mutara a text fage ina k'aunar ku nima son so fisabilillahi. Page 33 Tusio tasa ta goge bakinta kafin ta mik'e " ina zaki?" Kallon yadda ya wani lafe jikin kujeran dining d'in tayi kafin ta wani tab'a baki tace "ina kaji Baffa yace yana son ganinmu?" Kai ya d'an dafa alamun ya manta sai kuma ya tashi yace "muje" batareda tace komai ba ta mik'e ta wuce yabi bayanta suka nufi part d'in Baffa. Tun kafin su shiga suke jiyo b'ab'atun haj. Sailuba sai faman bala i take zubawa Baffa wani mugun tsaki MD ya saki har ga Allah ya mugun tsanar matar nan haka nan, abinda ya dad'a d'aure musu kai shine yadda suka shiga suka tarar tana zuba ruwan tujara shi kuma Baffa yana lallab'a ta yana bata hak'uri, da dai yaga abin yak'i k'arewa ne ya dubi Ammey yace. "Aminatu dan Allah na rok'eki ke ki hak'ura taje tunda ita ban isa da ita ba baza tayi min alfarma koda sau d'aya na sauke hak'k'in ki ba" Cikin wani irin yanayin da bazaka tab'a iya fassara shiba Ammey tace "ai dama Baffa ni ba matar gida bace 'yar zaman jiran gida bace da kula da gida ko ba haka ba? Gaskiya Baffa wannan karon bazan yarda ba nima duk abinda zai faru sai dai ya faru amma nataji wallahi haba dan masifa da bala i shekara da shekaru abu yak'i k'arewa nima wannan karon bazan hak'ura ba Baffa sai dai duk abinda zai faru ya faru. Nan fa Ammey itama ta bud'e wuta ta rik'a zubar da maganganu masu d'aci kunsan ance mai hak'uri bai iya fushi ba to haka ne yafaru ga haj. Amina yau duk irin yadda Baffa yaso rarrashin ta botsare masa tayi. Dai dai shigowar su MD da suka gama sauraran komai MD ya kafe Baffa da ido kafin yace "Baffa mai yake faruwa ne nakejin abinda ban tab'a jiba game daku?" ya fad'a yana kallon Ammey cikin yanayin da bai tab'a ganinta aciki ba. "Kamar yadda aka saba ne Muhammad yauma nayi magana ne akan kujeran hajji danake fitarwa duk shekara, Sailuba bata tab'a bari na bawa Amina tabawa wani nata ba sai sau d'aya kuma ni bansan me take da kujeru har guda goma ba tunda ko ta b'angaren mu nike biyama dangi, to itama mai hak'urin yau ta botsare min tace sam bata amince ba itama na rasa yadda zanyi yanzun" "Kawai kabawa wanda kake ganin yafi cancanta" "Baza abawa wanda yafi cancanta d'in ba wallahi ko zata mutu wannan kujeru nawa ne dan haka banga wanda ya isa hanani wannan kujeru ba ehe, idan kuma tak'ama ce naga ubanka ma acan k'auye raba kujerun nan yake kamar babu gobe" "Ni bana harka da jahilai marasa ilimi dan haka bani da lokacin da k'ik'ancin ki* "Uwar ka ta kabari itace dak'ik'iya baniba dan is...........kafin ta k'arasa taji wani irin fitinannen zafi ya karad'e fuskar ta ta d'ago a firgice dan ganin wanda yayi mata wannan d'anyen aikin sai da ta wuntsula daga kan kujeran ta ganin Baffa ya kafeta da kallo yana huci, yayin da MD ya mai da kansa k'asa cikin tsantsar b'acin rai da wani irin tsanar haj. Sailuba. Da wani irin tashin hankali ta bar wajen domin wannan ne karon farko da hakan ya tab'a faruwa iya tarihin rayuwar su dan haka abinda yayi matan yai masifar gigitaya ta sani hakan yana nufin aikin ta yana rawa kenan ai kuwa ya zama dole ta sabunta shiri Tana barin wajen Baffa ya dubi MD yace "Muhammad na fad'a maka ka fita hanyar Sailuba matar nan jahila ce amma bakaji" da mamaki MD yake duban Baffa to shi mai yace dan kawai yace Baffan yayi abinda yake ganin daidai shine ya shiga sangarta? Da wani irin fushi MD ya bar wajen yayin da duk suka bishi da kallo sai Maryam ma ta rufa masa baya dan sam bataji dad'in abinda maman nata tayiba. Ammey ma tashi tayi yayin da Baffa itama ya bita da kallo haka dai duk suka watse kowa zuciya babu dad'i Nassar ne kawai ya zauna ya ci ya koshi abimsa ya kama gabansa ya tafi gidansu boy abokansa. Sanda Maryam ta isa part d'in MD har ya gark'ame k'ofar da key babu irin bugan da batayi ba yai banza da ita kamar baikita ba. Haj. Sailuba kuwa tana shiga d'aki a gigice ta nemi wayar ta ta kira haj. Zakiyya kamar wata k'aramar yarinya haka take kuka wurjanjan cikin tsantsar tashin hankali ta kora mata duk abinda yafaru. Sosai ta rarrasheta tace tunda abin haka ne kawai ta shirya cikin satin nan su wuce India can ne za ayi musu aiki mai kyau sun jima suna tattanawa kafin suyi sallama, sai lokacin ta d'an samu sassauci Maryam kuwa d'akin ta ta koma cikin damuwa tasani cewa Mama bata kyautaba ko kad'an amma Kuma ita meye laifin ta da zai wani rufe mata k'ofa. Ganin zaman bazai mata ba kawai ta mik'e ta saka mayafinta da niyyar taje wajen Halima ko zata d'an rage damuwa, daidai bakin get suka had'u da Baffa ya hanata fita dole ta dawo gida cikin k'unci. MD kuwa tunda da yake babu Wanda ya tab'a zagar masa uwa ido da ido sai yau hakan ya masifar k'ona shi da k'yar yasamu ya rarrashi kanshi ya baro falon shi yasa ya kulle kanshi domin a halin dayake ciki baya buk'atar kusanci ga kowa atare dashi. Ammey kuwa cikin fushi ta koma d'akin ta ranta a masifar b'ace tasha alwashin bazata k'ara yarda Sailuba ta rik'a juya ta ba tunda babu adalci a lamarin itama ya zama dole ta zage ta kwatar wa kanta yanci. Haka da ranan mutanen suka kwana kowa zuciya babu dad'i da safe da zasu wuce islamiyya hankalinta yana kan k'ofar sa bata taba alamun ya bud'e k'ofar ba, sai ta tab'e baki a k'ok'arin ta nasan yakice tunanin shi aranta tunda shima fushi yake da kowa na gidan. Sai dai duk irin yadda taso kore tunaninasa aranta hakan yak'i samu sosai tayi sanyi dan ko k'awayen ta na islamiyya sai da suka gane tana da matsala, sanda suke dawowa daga islamiyya shi kuma ya fito daga d'akin dake lokacin an yi kiran Azhar ne sai da ta d'an razana ganin har ya d'an fad'a daga jiya zuwa yau kacal bata kulashi ba ta d'auke kanta, Nassar ne kawai ya gaida shi, ya bita da kallo har tashiga ciki kafin ya juya ya wuce masallaci. Koda ya dawo shima cikin gidan ya dawo lokacin har sunyi zaman cin abinci banda haj. Sailuba datake d'akin ta tun juya shima wajen ya tunkaro duk suka bishi da kallo har Baffa wanda yay mamakin ganin shi hakan Ammey tafi kowa shiga damuwar ganinsa a hakan. K'arasawa yayi ya gaida su kafin shima su Maryam suka gaida shi Ammey ta zubawa kowa nasa abincin amma MD da kanta ta fara bashi dan ta riga tasan halinshi muddun yana cikin damuwa baya iya cin abincin sai dai yayi ta fama da tunani tana cikin bashi ya tsinci muryanta tana fad'in. "Muhammad yakamata ka gane halin wannan matar ina rok'on ka daga yau komai zai faru kada ka k'ara cewa komai ka barta komai lokaci ne dan haka wata rana sai labari" sosai taci gaba da da tausar shi har ya kammala, itama Maryam ta tubure sai da ta bata itama kafin su bar wajen ta bisu da kallo. Hannunta da Baffa ya kamo ne yasa ta juyo babu wannan walwalan dayaga tana yima yaranta yanzu, ya d'an murmusa yace "haba maratussaliha dan Allah ki saki ranki tun jiya ake fushi dani na takura da yawa" ya fad'a yana murza hannunta dake cikin nashi. "Ai Baffa na lura baka Sona ko dan ni ba yar uwarka bace shiyasa kake nuna babanci muraran atsakanin mu" "Dan Allah ki daina wannan batun Amina ta wallahi nima wani lokacin karkiga yadda abin yake damuna kawai dai tashin hankali ne bana so yasa kikaga ina biye mata" Amma Baffa shekara ashirin sau d'aya ka tab'a bani kujeran nan ban tab'a cewa dan me ba yanzun ma nagane abin ba na K'are nane dan haka wallahi akan wannan komai zai iya faruwa" "Dole na baki Amina tunda baki tab'a yi min haka ba sai yau dan haka komai zai faru kece da wannan kujeru na bana" nan dai yaci gaba da tausarta har yasamu ta d'an sakko sukaci abincin tare. Kai tsaye suna fitowa d'akinta ta dosa dan yau tana buk'atar zuwa gidan su Maryam tana shiga suma suna shigowa yi tayi kamar bata gansuba sai da ya k'araso kusa da ita ya d'an dafa kafad'anta ta juyo ta harareshi. Murmushi ya d'an saki ya sumbaci goshin ta bai ce komai ya juya ya fice daga d'akin ta raka shi da ido kafin ta juya tacigaba da shirinta. Taku ce MAMAN ISLAM بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 34 Cikin atamfa riga da sket kamar ajikinta aka dinka rigar tsabar yadda tayi mata d'as a jikinta, bata wani yi kwalliya mai yawa ba duk kuwa da yadda take da son kwalliyar, mayafin da ya dace da kayan ta dauka ta saka ta saka takalmi mai mugun tsini Allah yayi mata son takalma masu tsini ta fito d'as abinta. Dukansu juyowa sukayi suka kafeta da ido ba k'aramin kyau tayi ba,kasa daurewa MD yayi sai da ya taso ya d'an matso kusa da ita yace, "Bakiyi kyau ba" dan hararan sa tayi tace " ai daman badan kai nayi kwalliya na ba bare ka kushe" murmushi yayi tare da mata gwalo domin yasan taji haushi ai kuwa ta k'ufula ta wani had'e rai, ta juya ta wuce d'akin Ammey karab sai a idon mama da ta fito zata fita jitai wani irin fitinannen tashin hankali yakawo mata farmaki da k'arfi tace "ke gidan uwar wa zakije ne" ta fad'a tana kafe Maryam da wani irin kallo. Ba Maryam ba hatta MD da Nassar sai da suka zabura suka zuba mata ido, ita ko Maryam babu wani shakka ko tsoro tace "haba Mama wallahi har kin bani tsoro irin wannan ihun haka kamar aradu?" Wani irin tuk'uk'i ne ya tokare haj. Sailuba ta kafe Maryam da wani shegen kallo zuciyar ta yana suya yaushe Maryam ta sami damar fad'a mata magana haka lallai in batayi wasa ba wata rana sai Maryam ta zageta anata haukan tunanin kenan. Amma azahir cewa tayi "ni nake ihun bab? wai ma tukun me zakiyo ad'akin matar nan bana hanaki mu a'mala dasuba?" "Hummm mama kenan ai duk randa babu ke dole itace uwata, ko baki tab'a tunanin hakan bane? kuma kadafa ki manta mama ba a raba hanta da jini mun riga mun had'u babu yadda zakiyi tunda ta haifa kin haifa dole ne itama ta sarara agidanna dan Allah mama ki daina irin wannan abun bashi da amfani ko kad'an haba" Fashewa kawai haj. Sailuba tayi da kuka saboda tsabar tashin hankali da bak'in ciki kasa yi mata magana tayi har ta shige d'akin Ammey tana kallon ta. MD kuwa wani irin annushuwane ya kamashi sanda Maryam ke fad'awa haj. Sailuba magana wani arnen murmushi kawai yake saki, yana ganin Maryam ta shige d'akin Ammey ya k'arasa kusa da haj. Sailuba yace "hajajju makkatu me kike tunanin zai faru duk ranar da wannan yarinyar tagane cewa ke ba uwarta bace uwar rik'o ce? Ya zakiji lokacin da tasan cewa mahaifiyar ta kike sawa tanawa cin mutunci da wulak'anci Me zai faru idan tasan cewa ba dan Allah kike rok'on taba kina rik'on tane saboda wani banzan dalili naki mara amfani? Hhhhhhhhhhhh kad'an kika gani Sailuba domin Allah baya bacci" Babu kunya haj. Sailuba ta kuma fashewa da kuka tana kallon MD kafin tace "hummmm Muhammad kenan na maka alk'awarin bazan bar hakan yafaruba sannan kuma ina Mai farin cikin sanar dakai cewa komai ya kusa zuwa k'arshe rayuwar Maryam zaiyi wulakantar da babu wani rayuwa da zata kai tata lalacewa zata bi maza zata yi shaye shaye zata yi sata zata zama abin kwatance da misali na miyagu da munanan halayya" Sosai gabansa ya fad'i da jin furucin ta domin yasan zata aikata fiye da hakama jiyai hankalinsa yai masifar tashi ya dubeta da tsantsar b'acin rai yace "Allah ya fiki yafi waninki Sailuba kuma duk abinda kike tak'ama dashi insha Allah hakan ki bazai cimma ruwaba" Wata shegiyar dariya ta saki tace "zaka gani zaka kuma tabbatar muzuba nidakai shege ka fasa" daga haka tayi waje hankali a tashe. Sosai maganganun ta suka tsaye masa rai sai dai kamar yadda yake tsaye wajen yiwa Maryam Adda a ya zama dole ya k'ara zage damtse. Maryam kuwa tana shiga d'akin Ammey ta rufeta da fad'a akan maganganun da taji tana sakarwa haj. Sailuba tace mata koba komai matsayin uwa take awajen ta dan haka ta rik'a sanin irin maganan da zata fad'a Mata. "Nifa Ammey indai akan kune babu abinda zaki fad'a min na fahimta matar da bata da lokacina sai na gantali kullum tana tafe a hanya ita ba kasuwanci ba ba komaiba, ai wallahi duk laifin Baffa ne da yasake mata haka dayawa shiyasa take iskancin ta son Rai" "Ungo nan Ammey ta yiwa Maryam tace "idan har da gaske kina ganin mutunci na kamar yadda kika fad'a to kada ki sake kinji ko?" "Naji Ammey, ina Baffa shi nazo nema" "Lafiya kike neman Baffa?" Bata b'oyewa Ammeyn komai ba ta fad'a mata tana son bawa baban k'awarta jarine ya fara sana a, sosai hakan yayiwa Ammeyn dad'i arai taji dad'i ya kasance yarta tana da zuciyar tausayi dan haka Ammeyn ce da kanta ta bawa Maryam dubu d'ari tace "gashi idan Kuma bai isaba kimin magana sai na k'ara miki?" Rungumeta maryam tayi tace "na gode Sosai Ammey na Allah yaja da rai ta sumbaci Ammeyn tayi waje da sauri tana fad'in saina dawo" Sosai Ammey ke jin dad'in yadda yarinyar ta soma sakewa da ita ta rage wannan d'an banzan yawon dayake sanyata fargaba da damuwa musamman idan haj. Sailuba ta dawo taga bata nan ko zata kwana basata tuhumeta taji inda taje ba. Tana fita suka gabza wani uban karo da MD ai kuwa taji zafi sosai shima haka duk suka dafe wajen suna kallon juna kafin Maryam ta galla masa harara ta wuce tana sosa goshinta. Da sauri yasha gabanta ya tsaya yana d'an diddira k'afa irin na shagwab'a yace"ni Allah Allah Allah sai ki bigeni kuma ki wuce babu hak'uri ni sai na rama" yadda yayi maganar dole abin yabata dariya batasan sanda ta saki murmushi ba tace "sorry" Daga haka ta wuce kuma shan gabanta yayi yace "ina kuma zaki?" "Gidan su Maryam ta bashi amsa dan har ga Allah sauri take ta tsai da baban Maryam yau baifita nema ba dan haka yakamata taje akan kari "Wanda kike siyayyar nan awajensa?" Ta tsinci muryarsa tana shirin fita "Eh shi" Ta bashi amsa tana ficewa da sauri ya bita ya rik'o hannunta yana kallon ta tace "dan Allah yaya sauri nake sai batamin lokaci kake" "Muje mana naganshi idan ya cancanta da amanar da kika bashi saiya cigaba da kula da su idan Kuma ba haka ba sai na amso ko?" Sanin cewa sunyi maganar da Ammey yasa bata musa masa ba suka jera suka shiga motar yaja suka bar gidan. Maman Islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 35 Saida tasa kashi suka biya wani spermaket ta d'an musu siyayya, dan Allah yasani hakanan Allah yasaka mata tausayin iyayen Maryam, saboda yak'i nin su da kamewar su hakanan sun iya babun su, dan malam Abdullah mutum ne jajir tacce tsayayye, akan iyakansa bai yarda da zubar da daraja da kimar gidansa ba, haka kuma baya daukar raini ko kad'an dan haka hatta iyalinsa suna shakkar sa saboda sam bai yarda da wulakanta kai ko zubda mutunci ba. Yadda suke shiga cikin lungunan unguwar yasha mamakin yadda Maryam tasan wajen dan koshi dayake namiji bai tab'a yowa ta area dinba sosai ya rink'a binta da kallo yana mamakin ta. Sai yanzu yake gane asalin halinta mai kyau ne irin na mahaifiyar ta wancen halin na aro ne wanda aka d'ora ta akai bisa wani dalilin mara tushe da makama. Ita duk wannan kallon dayake binta dashi sam bata kulaba dan hankalin ta yana kan wayar ta suna chat da Halima sai yanzun ta d'ago dan taga ko sunkai inda ta kwantato masan ai batasan sanda tasaki kara ba ta maida hankalin ta kanshi ganin suna shirin taka wani k'aton dutse, shima da sauri ya taka burkin da sai daya janyo hankalin wasu daga cikin masu wucewa dake cikin unguwa be. Harara ta galla masa kamar idanunta zasu fad'o tace "to kasheni ka huta tunda ka gaji da ganin rayuwata" Murmushi ya d'an saki kafin ya d'an shafi fuskar ta yace "ina son ki princess dan Allah ki soni my happiness" hararan ta kuma masa kafin ta d'auke kanta yasa hannu ya kuma juyo da fuskar nata saitin sa ya kafeta da ido, ."dan Allah ki kalle ni nasan zaki yadda da abinda nake fad'a miki har zuciyana ne" bata musa masan ba ta d'an kalleshi na kamar 1 mint take taji ta fara d'an tsuma tsuma tasoma k'ok'arin kwace fuskar ta amma ya hanata damar hakan da sauri ta runtse idonta dan bazata juri kallon wannan fitinannun idanun nasa ba. Murya na rawa tace ni kaina ya k'age ka sakar min fuskana, kuma ka daina yimin wannan kallon mayun" murmushi ya d'an saki kafin yace "indai akanki ne baby ki kirani lasan ma ba maye ba da da yadda zanyi na tsaga jikina na sakaki da tuni na jima da yin hakan na huta' dan Allah baby karki gujeni, idan kika gujemin hakan yana nufin abubuwa da yawa ciki harda rayuwana" Yanayin da yayi maganar yasa dole ta kara bud'e idanunta akanshi yadda taga idanunsa sun koma ba k'aramin tsoratata abin yayi ba sunyi wani irin mugun ja ga wani kyalli kyalli alamun ruwan hawaye ne suka kwanta masa aciki, wani irin tausayin sa ne ya kamata tace "Zaka iya aurata koda ace bana sonka? Sosai maganar ta ya dakeshi, zaka iya aurata koda ace bana sonka? ya sake maimata tambayar a zuciyar sa kenan akwai wanda take so Kennan tunda bata son shi? Wani irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Baby wa kike so? "Babu" Ta bashi amsa atakaice sannan ta d'ora da fad'in ba kaine kakori muhseen ba yaron dayake masifar Sona kamar zaiyi hauka tundaga ranan yake masifar tsorona bama kaiba ko a hanya ya ganni wallahi canja hanya yake" Sosai maganar ta ya masa zafi a zuciya amma sai ya daure tunda shine mai nema dole ya sauke duk wani zafin ransa gefe ya nemi masalaha "Kina son muhseen d'in? Ta tambaye ta cikin tsantsar zafin rai dana zuciya. "Ni babu wanda na tab'a jin ina so arayuwata shima muhseen d'in saboda nacinsa da rashin zuciyar sa yasa na tausaya masa na fara kulashi" baisan sanda ya wani fisgeta ta fad'a jikinsa ba ya wani k'ank'ame ta atare suka sauke wata irin ajiyar zuciya kafin yasoma magana cikin sanyin da shi kansa baisan zai riskeshi a wannan lokacin ba yace "Na amince baby zan aureki koda ace bakya sona nasan dole wata rana zanyi nasara zan mallake ki KE DA ZUCIYAR KI" "Ya jima yana zubar mata da sak'onnin da suka cunkushe masa zuciya suka hanashi sukuni, bai tab'a sanin da akwai rayuwa irin wannan ba rayiwar da zaka kasa katab'us ka kasa sukuni ba sai da ya had'u da jarrabar SO wanda ya hanashi sakat yake sanyashi kasa baci cikin dare ya kasa runtsawa tsawon dare ya zubda hawaye ba adadi duk asanadin SO" Tun bata fahimtar maganganun sa har ta fara fahimta sanadin da jikinta yayi sanyi bata san da cewa akwai ranan da MD zai iya kallon idanunta ya furta mata tsadaddun kalamai irin wannan ba musaman idan tayi tunanin yadda suke da shi. "Bross muje na tsaida bawan Allah yanata jira" tayi maganar cikin sanyin jiki dan kalaman sa sun mugun kashe mata jiki sai da ya sumbaci goshin ta da idanunta da suka fi komai d'aukan hankalin sa kafin ya saketa ya tada motar suka k'arasa gidan su Maryam d'in. A mota ya tsaya ta shiga kamar yadda ta zata Abban yana nan yana jiranta kamar yadda ta nema Umma ce tayi mata shimfid'a ta kawo mata ruwa da lemo, sai da ta gaida su sannan ta sanar musu ai tare suke da yayanta Abba yace "kuma kika barshi awaje kai wannan yara Allah ya shirye ku da rashin wayo" Ya fita ya shigo da MD duk da kasancewar basu dashi amma yayin gidan kad'ai zai nuna maka mutanen gidan suna da tsananin tsabta, sosai suka gaisa da su kafin Maryam tayiwa Abban bayanin dalilin zuwansu, hakan ba k'aramin dad'i yayi wa Abban na ya zauna yayiwa MD bayanin duk abinda aka sai mata da kud'ad'en da take kawowa harda shanu da yaje can garinsu yasai mata da yake shi ba d'an garin bane. Yanayin sa kawai yasa MD yaji hankalinsa ya kwanta da shi dan haka suka d'anyi shawarwari akan abubuwan nata yace "tunda shanun sun kai har guda goma kuma duk Yan k'anana wanda basu fara haihuwa ba kawai asai na mijin sa kamar guda biyar a had'a sai abada kiwo ga wanda ya amincewa.sannan gidajen kuma anemi yan haya masu mutunci da amana asaka su aciki" "Nima tun farko shawaran da nayi da ita kenan tace in dakata tukun" murmushi MD yayi yace "kasan yar k'auye ce babu abinda ta sani sai k'auyanci" shima Abban murmushin yayi yace " banda abinka d'ana ai k'auye tushen kowa ne shima MD murmushin yayi suka ci gaba da tattanawa, sun jima a gidan har sanda Maryam ta dawo suka suka shige d'aki dake sanda sukazo bata nan Umma ta aike ta. Umma ce ta lek'a tacewa Maryam ta fito zasu wuce sai da zasu tafi sannan Maryam ta kawo k'udin da Ammey ta bata ta mik'ewa Abba tace "Abba gashi nan ka nemi wata sana ar ka fara Allah ya taimaka. Tsabar mamaki Abba kasa magana yayi gashi kuma ta toshe duk wata hanya da zai mata godiya sai addu'ar da yay ta zuba Mata har suka bar gidan MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 36 Suka shiga mota ya tada suka bar wajen saida suka d'an yi nisa da tafiya kafin ya d'an juyo ya kalleta " enye enye ashe yarinyar tana da hankali, to nima aban jarin mana" Murmushi kawai tayi tasan tsokanar ta yakeyi dan haka ta d'auke kanta suna cigaba da chat da Halima wacce take zaman jiranta a gida. "Ko bazaki baniba?" Ya sake tambaya, hararan wasa ta d'an yi masa ta dauke kanta tana d'an murmushi. Haka dai yai ta janta da hira har suka koma gida kai tsaye d'akin ta ta wuce shima fat d'in sa ya nufa dan duk sun gaji. Ita kam tana shiga falon ta tadda Halima tana zaman jiranta hararar wasa tayi mata tace " to hajiyata shanyar taki ta bushe Allah badan gobe zan koma ba da tuni nayi tafiyata" "Sorry dear gidan su name sake mukaje bamu tadda taba har sai da muka jira ta dawo" "Naji kina jam u kedawa?" "Tare da bross mana" wani irin waro ido Halima tayi tace "kedawa?" Kunsan fa Halima bata da masaniyar shirin Maryam MD domin bata da yawan surutun mara dalili. "Ai kinji abinda nace kema neman zance ne kawai irin naki" "Ai abunne dole yabani mamaki yadda baku shiri da bross kuma kice tare kuka fita ai kinsan dole mamaki yamin illah" "Humm wai kinsan ma wani abu kuwa?" "A'a" "Wai sona yake karkiga yadda yakemin naci kamar bashi ba duk ya wani susu ce" "Ke dan Allah dena fadaymin dama ba babanku d'aya ba?" Ta fad'a duk idanunta awaje tsabar mamaki "To ni tsabar tsorata ranan da yace yana sona ihu na dinga zunduma masa nayi tunanin kwakwalwan sa ne ya tab'u wallahi" Jinjina kai Halima tayi tace "haba wallahi wani lokacin nakan zauna nayi tunanin yadda Ammey take ba wata babba ace ta haifi kamar bross da ace kece akace yarta babu wanda zai yi mamaki ammafa bross abin yana d'aure min kai, ke amma kinsami dami akala wallahi na miki murna bross ai miji ne na yaw........ "Ke dalla rufewa mutane baki zaki fara halin naki babu fullstop ba qommer nace miki ina son sane da zaki wani fara yyyyyyyy murya kamar ta yan China" Harara Halima ta galla mata tace "ank'i a rufe banza mara mutunci ai dama inka shekara dubu bakaga mutum ba tambaya halinsa ni zakiwa iskanci koda yake ni na kawo kaina bari nay tafiyana" "Jeki mana seme dama duk kin isheni kin saka min ciwon kai" Sai da sukayi halin naau da suka saba duk had'uwa kafin su daidaita su hau zance na gaskiya da gaskiya, wannan halin nasu tun suna yara suka taso fashi Halima surutu ratata Maryam kuma fad'a. Sun jima sosai Maryam ta fad'awa Halima gaskiya itafa bata son MD Halima tace "karki damu yar uwa wata rana zakiso shi har kiyi kishin sa kawai dai mudage da addu'ar Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi amen" Sosai Halima tabawa Maryam shawarwari masu kyau yayin da sukayi sallama dake hutunsu ya kare zata koma schl itama Maryam d'in sati mai kamawa zata koma. Tsakanins Maryam da Halima akwai so da k'auna akwai yarda da amana akwai shak'uwa mai tsanani wanda yasamo asali tun suna yan yara alokacin basa rabuwa kullum suna tare ay fad'a a shirya kullum basa gajiya da dambe da f basa b'oyewa junanau duk wani abu har kawo wannan lokacin. Name sake d'in ta kuwa k'awance ne irin na makaranta sannan babu abinda tasani akanta banda mahaifinta da tasan mai k'udi ne dan har yanzuma bata bata damar zuwa gidansu ba dan Maryam bata jan mutum ajiki sai ta gama karantar waye shi, itama dai bata da wani aibi tana da kirki ga kamewa wanna neyasa Maryam k'ulla kanwace da ita har takai ga tafara temakonta. Bayan tafiyar Halima Maryam tayi wanka ta fito duk a dining room ta samesu har Baffa sai mama da har wannan lokacin bata dawoba, kujeran kusa da Baffa ta jawo ta zauna suka sakashi atsakiya ita da Nassar yayin da Ammey tata kujerar ke kallon ta Baffa "ke uwar taki bata fad'a miki inda ta tafi ba yau gashi har anyi issha?" Dan yamutsa fuskar ta tayi itama yawon na mama yana mugun damunta tace "zai wuce gidan waccen haj. Zakiyyar ni bata fad'a min inda zata" Kwafa Baffa yay cikin b'acin rai kafin yace komai MD ya shigo wanda gaba d'aya kamshinsa ya cikasu kujeran dake kallon ta Maryam ya ja ya zauna ya wani kafeta da ido ko kunyar su Baffan bayaji. Tana ganin haka ta wani tsare gida yayin da Baffa yace "zamu yi magana daku keda Sailuba idan ta dawo a yawon nata" Had'e rai Ammey tayi amma bata tanka ba yayin da Maryam ta sunkuyar da kanta k'asa tak'i yarda koda wasa ta kalli inda MD yake shikam ko ajikinsa ya fitineta da kallo yana cin abincin sa, bata wani ci abin kirki ba saboda yadda ya takurata ta mik'e , Ammey ta dubeta tace "ya haka baby banason fa zama da yunwa" Had'e rai tayi tana hararan MD k'asa k'asa tace "k'oshi nayi ne" daga haka bata jira cewar suba ta bar wajen, duk suka bita da kallo, shima MD kad'an ya k'ara ya mik'e direct d'akinta ya wuce ilai kuwa ya sameta tayi d'ai d'ai asaman gadonta da ice cream tana faman sha sam bai ma kula da abinda takeyi ba sai da ya buga uban sufa ya fad'a kusa da ita sannan ya kula da kayan sanyin da take sha k'ala bai ce mata ba ya zare robar a hankali ya kai saman frich ya aje ya dawo ya kuma kwanciya tareda d'ora kansa saman kafafunta a wani firgice ta kai idanunta saman fuskar shi idanunsa ma shi a lumshe suke take jikinta ya kama wani irin rawa cikin tsantsar tashin hankali da rawan murya tace me mey meye ha ka ni fa ban a son is Kan ci tayi maganar a rarrabe tsabar tashin hankalin data shiga, wani muskilin murmushi ya saki yace Muje zuwa daga MAMAN ISLAM بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Gaisuwa ta musamman gareku hazikai kuma jajurtattu a kungiyata Princess Aisha Miss flower Maryam H Allah ya kara muku juriya da hak'uri. Allah ya kara had'e kanmu first class mu dad'e muyi k'arko 💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿 Page 37 "Nine d'an iskan princess?" Ya fad'a yana kallonta ko k'ibtawa bayayi had'e rai tayi tareda fashe wa da kuka maimakon ya saketa kamar yadda take buk'ata sai kawai ya rungumeta take zuciyar ta yayi wani irin mahaukacin buga ta fara k'ok'arin tureshi amma ina k'arfin ba d'aya bane. "Na tsaneka" ta fad'a cikin kuka sakinta yayi a firgice yace "ni d'in baby ni Muhammad dinki kike cewa kin tsana?" Harara ta galla masa da idanunta da suka koma launin ja ta murgud'a masa baki ta fice daga d'akin tayi d'akin Ammey wacce itama bata d'akin ta fat d'in Baffa. Bata jima ba Ammey ta shigo hannunta d'auke da Leda da kaya aciki Nassar na biye da ita yana mitar ta hana Baffa siya masa ways. Da kallo tabi Maryam wacce ta takure waje d'aya asaman gadonta, kana kallonta kasan akwai abinda yake damunta "Ammey zoki zauna dan Allah muyi magana" tayi saurin katse Ammey tun kafin tayi mata tambayar da bata da amsa, A hankali Ammey ta tako kusa da Maryam tasamu ta zauna ita kuma tayi saurin d'ora kanta ajikinta tana sauke ajiyan zuciya sannan tace "Ammey zan iya auren MD?" ta fad'a kamar yadda ta tab'a jin m Bash ya kirashi da sunan Gaban Ammey ne yai masifar fad'uwa a d'an razane ta dubeta tace "waye kuma hakan?" Ganin yadda tayi saida tai mugun bata dariya kafin tace "Muhammad dinki nefa MD nima abokansa naji suna fad'a shine na d'ana" ta fad'a tana b'oye face d'inta ajikinta. Wani irin sanyi Ammey yaji har batasan sanda ta rungumeta ba tace "zaki iya mana baby me zaihana ai bazaki tab'a samun kamar saba kamilin mutum managarci wanda yasan darajanki" "Oh ji Ammey saboda shi d'in na wajen kine kike irin wannan zuzuta shin?" Dariya Ammey tayi ta lakace mata hanci tace ba haka bane baby ai d'ana d'aya ne tamkar da dubu nasan shi nasan halinshi yana da halin kwarai zakiji dad'in rayuwa da shi domin yana da kyautawa" "Shikenan Ammey tunda kema kin amince da nagartar sa naji na amince zan aureshi kamar yadda ya buk'ata amma fa na sanar dashi cewa bana sonshi hasali ma ni ban tab'a jin sonsa araina ba kamar yadda babu son kowane d'a namiji a zuciyana, to yace yaji ya amince shikenan magana ya kare" daga haka ta mik'e dan fita daga d'akin Ammey ta bita da kallo har ta fice ba k'aramin farin ciki ta tsinci kanta aciki ba duk da cewa maganar ta na k'arshe bai mata dad'i ba. Ba k'aramin mamaki tasha ba ganin har lokacin MD yana d'akinta akwance ya wani yi mata d'are d'are asaman gado kafeshi tayi da ido tana k'arewa baiwar ubangiji kallo MD ba k'aramin mai kyau bane ta ayyana hakan cikin ranta. A hankali ta k'arasa rufe k'ofar ta tafi cikin sand'a tana lek'a fuskar shi ya kuwa fisgota da k'arfi ta fad'a kanshi ta bud'a baki zata zunduma ihu yayi saurin toshe mata bakin da hannunsa, tashi yai ya zauna itama ya zaunar da ita suna kallon juna yadda tayi wani tsuru tsuru da ita abin yaso bashi dariya sai kawai ya murmusa baice komaiba ba sai faman kallonta yake. Yadda yake faman kallonta ba k'aramin takura ta yayi ba ta wani had'e rai tana tura baki bakin ya sumbata ta wani zaro idanu tana kallonsa da k'yar tace "Allah saina fasa aurenka idan kanamin irin wannan abun" "Yi hak'uri my happiness na daina, amma kisani iya hakan ma ba k'aramin kokari nake ba princess sonki yamin illah bansan lokacin da sonki yayi min irin wannan kamun ba yabi jinin jikina ya mamaye JININA ba dan Allah ki zauna dani koda bakya sona zanfi samun nutsuwa idan kina kusa dani" daga haka bai jira cewar ta ba ya sumbaci goshin ta ya sauka yafice daga d'akin, binsa tayi da kallo kafin ta saki murmushin dabata san ko na menene ba asarari Kuma tace "maye kawai" sai kuma ta shek'e da dariya tana buga cinya. Cikin sauran kwanakin hutunsu ba k'aramin hanata sakat MD yayi ba tun tanajin haushin sa har ta fara sabawa ya masifar nanuk'e mata duk inda zata sai ya bita matuk'ar yana gida idan ya fita office kuwa kafin ya dawo tana samun kiransa fiye da ashirin tun tana jin haushin sa har ta daina saima wani mugun shak'uwa da yafara shiga tsakaninsu sosai ta fara kamuwa da son MD batare da tasan hakan ba ita dai tasan cewa muddun yana nesa da ita ta rik'a kewar sa in yana kusa da ita kuma tana samun nutsuwa da farin ciki bata gajiya da daddad'an kalaman shi masu sanyata nishadi. Cikin haka hutunsu ya kare suka koma makaranta karatu suke babu sauk'i kasancewar suna shekaran su na k'arshe hakanne yasa Maryam bata da sukuni har rama ta somayi duk da kasancewar tana samu temako daga MD dan shima idan baku manta ba saida ya fara karatun likita kafin ya koma ya zama soja. "Na fad'a miki kiyi hak'uri ta k'arasa karatun kafin na tarwatsa komai" "Bazan iya ba boka itace fa ta wargatsa min shirina na shekara ashirin da d'aya shirina na tundaga ranan haihuwar ta har zuwa yau boka badan ina tsoron rayuwar kurkuku ba da wallahi da hannuna zan kashe ta kamar yadda ta kashe min farin ciki na" Shi kenan tunda kince haka amma kada kiyi kuka dani duk abinda yafaru ki kuka da kanki kasancewar idanunta sun riga da sun rufe tace taji ta gani kuma ta amince. "Boka ana gama mata aikinta nima nawa yasamu kamar yadda muka alk'awarta" "Ke zakiyya burinki zai cika kuma Deedah bata da irin halin ki gaskiya tana da wankakken zuciya amma fa wannan buri naki ba makawa zai cika sannan kuma komai zai wargatse" Maguguna ya had'a musu tare da fad'a musu yadda za ayi kamar yadda aka saba sosai taji dad'in shirin su na wannan lokacin. Suna fitowa haj. Zakiyya ta dubeta tace "maganar mu na zuwa India?" "Yana nan amma ba yanzu ba sai komai ya kammala sai kawai nayi b'atan dabo aneme ni arasa koya kikaga?" Suka shek'e da dariya haj. Zakiyya tace Allah k'awata kinsan takan tsiya kina ta sha'aninki hankali kwance" "Inafa kwanciyar hankali buri bai cika ba ai CIKAR BURINA shine kwanciyar hankali na" Haka suka tafi suna hiransu na mugun abu har suka cimma inda suke faking idan sunzo Wannan karon zuwan bazata Baffa yay musu sai ganinsa kawai sukayi ranan ma Sailuba taje yankan busa dan tafiyar su yana ta matsowa kai ranan Baffa ba k'aramin ruwan tujara ya zubar ba ya addabi Ammey da fitina wai duk laifin tane da bata sanar masa abinda ke faruwa. Cikin b'acin rai Ammey tace "kaga malam kada ka isheni ni nake aurenta da zan samata ido? Tsayama da zakace haka naga agaban kama ficewar ta takeyi kataba cewa dan me saini daka raina zakasa agaba da bala i wallahi nagaji kar ka k'ara sakani a shirgin ku da matarka matuk'ar kana son zaman lafiya a tsakaninmu idan Kuma tashin hankalin kake so nima na iya" Daga haka ta bige zaninta tabar masa wajen cikin b'acin rai, shima yasani k'ureta yayi shiyasa ta zage yau take mayar masa da martani. Muje zuwa MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 38 "Dad dan Allah ka taimaka min na rasa yadda zanyi na fad'awa yarinyar nan irin son da nake mata gashi saura sati biyu mugama karatun mu kasan tare zamu gama dan Allah dad kayi min rai" Wani mugun kallon Abba AL HASSAN ya jefawa d boy kafin yace "kaga Kamal ka fita daga idona na rufe karaba ni da wannan shed'anin yaron dan wallahi ko mata sun kare a duniya bazan bari ka auri wannan yarinyar ba yayanta da kake gani ba k'aramin aljanin mutum bane bashi da mutunci ko kad'an d'an iska kamar mai gani har hanji duk sanda kayana suka shigo saya yajamin babbar asara" Fashewa da kuka d boy yayi dan har ga Allah yana masifar son maryam ga Dad d'in sa idan yakafe akan abu shegen taurin Kaine dashi. Mahaifiyar sa ya kalla yana kuka sosa yace "mammy dan Allah kisa baki dad ya barni da wacce nake so" "Uwata ce ita da zatasani yin abinta banga dama ba dagakai har Maimunan wallahi sai na had'a ku naci kaza kazanku" ya antayo musu wani zagi mai rai da lafiya. Take ran haj. Maimuna ya b'aci ta kasa daurewa tace "ka daici naka uban me na maka kaji nashiga maganar ku bare ka dagamin hankali tsabar neman fitina kasan bazaka tab'a min in k'yale kaba wallahi tunda kai mutumin banza ne mara mutunci kawai" "Iyayen kine marasa mutunci yar marasa tarbiyya wadda batasan girma da martaban na gaba da ita ba" "Iyayen kadai sune iyayen banza suna kallon d'an su yana hark'allar miyagun k'wayoyi amma basa iya tab'uka komai tur da iyaye irin naka wallahi, ni kuwa iyayena sun bani tarbiyyan da har ka gani ka yaba kuma ka aure" Nanfa rigima ta balle harda mare mare dan haj. Maimuna bata ragawa Abba AL HASSAN ko kad'an tunda ta fahimci tantirin d'an duniya ne ga zagi nacin mutunci. Cikin fushi d boy ya fice yabar musu gidan yana hawayen bak'in cikin wannan halin na iyayen sa wanda ko kunyar idanunsa basaji idan fitinar su ya motsa. Tun bayan da ta shige d'akin ta Baffa bai karajin d'uriyar taba ya tabbatar da fushi tayi, maganar gaskiya yana mugun tsoron fushin Amina dan bata iya fushi ba idan tayi masa fushi yana matuk'ar shan wahala. Yana shirin tashi yabita har d'akinta haj. Sailuba tana shigowa fasa tashin yayi ya koma ya zauna ya kafeta da ido, ganin irin kallon dayake binta dashi yasa ta d'an sha jinin jikinta sai ta wayance da fad'in "La Baffa yaushe ka dawo irin wannan dawowa haka babu sanar wa? sannu da zuwa" nan dai tahau masa borin kunya. Shi kam k'ala baice mata ba kafeta kawai yay da Ido hukunci yake mata da haka, yayin da ta rasa yadda zatayi, sai da ya tabbatar da yagama sanyaya mata jiki sannan yace. "Waye naki agarin nan da har kullum bakinan me kike fita yi ko me kike nema wanda baki sameshi anan gidan ba?" Shiru tayi ta kasa magana sai faman rarraba ido take yayin da Baffa yaci gaba da cewa "maganar gaskiya Sailuba wannan shegen yawon gantalin naki ya isheni haka idan kuma baki gyara ba zan d'auki mummunan mataki akanki" Hak'urin munafurci taita bashi har da kukan k'arya kafin yace ya hak'ura sannan ya d'ora da fad'in "tunda gobe weekend ne ki sanar da Maryam ta shirya zamu wajen Inna" A mugun firgice ta d'ago tana duban Baffa yayin da maganar boka yafara kara kaina cikin kunnen ta kamar yanzu yake fad'a mata kar ta sake ta yarda Maryam ta had'u da Inna domin akwai babbar matsala ga had"uwar ta tasu domin Inna zaya ruguje musu komai ta yadda har abada bazasu tab'a nasara akanta ba kamar yadda har yau har gobe suka kasa akan Nassar domin akwai dafa in datake bashi yake sha. "Lafiya wai me kike nufine Sailuba da hana maryam kusantar mahaifiya ta idan ke kin gujeta so kike yata ma ta guje rabon Maryam da taje garin nan tunda aka yayeta sai dai idan Innan ce tazo ta ganta so kike ki raba yata da mahaifiyata be?" Cikin dauriya da k'arfin hali tace "a a Baffa ni wacece da zan raba baby da Inna naga nima Innan nan uwatace dan Allah ka daina yimin irin wannan bahaguwar fahimtar" Nan dai ta kalalleme shi da dad'in baki har ya sauka daga fushin daya dauka sannan ta wuce d'akinta da tarkacen da tazo dashi daga wajen bokanta. Karfe shida daidai ta dawo daga makaranta a mugun gajiye ga d'an banzan yunwar da ta kwaso tsabar yunwar har wani jiri jiri take gani ta fito a motar ta tana had'a hanya, shima MD shigowar babu dad'ewa wanka yai ya fito ya hango ta tana takawa kamar mai koyon tafiyar murmushi ya d'an yi kafin ya taka a hankali zuwa inda take ya d'an hura mata iska a fuska a d'an tsorace ta juyo dan bata ji zuwansa kusa da itaba tsabar bata nutsuwar ta jarrabawan yau ya azabtar da su fiye da tunanin mai tunani. Kallonsa tayi da lumsasun idanunta wanda tsabar yunwa yasa suka wani d'an shige "me yafaru happiness naganki haka?" "Yunwa" tace dashi tana dafe cikin ta da ya isheta da k'ugi "ayya baby muje ciki maza Ammey tagama tuwon dare" da sauri ta kalleshi "Allah tuwo tayi? kasanfa ina son tuwo sosai" d'an murmushi yayi danshi tsokanar ta yakeyi yayi zaton irin Nassar ce itama batason tuwo kamar sa. "Tsokanar ki nake Baffa kawai Ammey tayima" " Ai kuwa nima tuwon zanci yasin" ta wuce kanta tsaye dining room d'in, saida ta fara had'a ruwan zafi ta gasa cikin ta kafin ta bud'e tuwon Baffa da Ammey tagama shiryawa gwanim ban shi'awa ta d'auki malmala tasa aflat ta zuba miya ta soma ci a nutse, duk da bak'ar yunwar dake damunta hakan baisa ta rud'a kanta tayi irin cin yunwar nan ba, Ammey da ta shigo dan daukar abincin Baffa tsayawa tayi tana kallon Maryam dake aikawa da tuwo batare da tasan cewa Ammeyn tazo wajen ba, sai data k'arasa wajen Maryam ta ganta tayi wani wuri wuri da ita can kuma tace "wallahi Ammey bross ne yace kinmin tuwo" "Na tambaye kine?" Ta fad'a tana wurgawa MD harara wanda yake gefe yana d'an murmushi wayarsa a hannu yana faman daddannawa, bata k'ara magana ba ta d'auki d'an kwandon data jera abincin tayi waje MD ya dungure mata kai yace" da so kikai ki had'a ni da uwata ko?" Bata ce komai ba sai harara data galla masa taci gaba da cin abincin ta sai data jita daidai kafin ta mik'e tana hamdala tawuce kai tsaye d'akinta ta nufa wanka tayi ta yo alwala tayi sallar la 'asar da ya k'wace mata tun a hanya ta jima tana addu'o'i kafin ta kama karatun Al qura ani mai girma da fita tasoyi d'akin Ammey ganin lokacin magriba ya karato yasa bata fitan ba ta jima tana karatun kafin a kira magriba tayi addu a ta tashi kawo sallar magriba bata bar wajen ba saida tayi issha Nassar ya shigo da murnan zasu gidan yayar Ammey wacce take sonshi "Adda zaki?" Harara ta aika masa tace "bazani ba d'an rainin hankali da dani kuke zuwa?" Nan dai ya fitineta da hiran anty shamsiyya wacce suke kira da momma har dai ya ja arayinta tace itama zata cikin farin ciki ya daka tsalle yay waje kaiwa Ammey labari, itama ba k'aramin dad'i hakan yayi mata ba ko ba komai anty shamsiyya zatasan cewa ansami cigaba kenan. Ita ko Maryam Nassar yana fita ta mik'e ta wuce d'akin Mama mamaki ne ya kamata ganinta cikin damuwa ta k'arasa ta kwantar da kanta saman kafad'ar ta tace "Mama lafiya na ganki cikin damuwa ko baki da kud'i ne?" Wani k'ululu ne ya tsayewa haj. Sailuba jin tambayar da Maryam tayi mata, amma sanin cewa ita ce silar d'ora ta akan hakan yasa tace mata "eh kina dasu ki bani?" Girgiza mata kai tayi tace "ai tunda naga yanzu Baffa ya bud'e miki bakin aljihu fiye da kima yasa na daina tambayar sa k'udi domin nasan cewa idan kina dasha nima inada shi kuma wanda kike bani ma yanzun baya isana saboda wani saurayi danayi d'an talakawa ne sosai shi nake kashewa" da gayya tayi mata wannan zancen dan son gane asalin gaskiyar batun MD dayace wai maman ta uwar ta bata ki taga ta saida mutuncin ta ba,kimar tafa tak'amar kowacce budurwa mai ji da son kara Martaba da kimar ta har zuwa gidan aurenta. Ga mamakinta ta kuwa bud'ar bakin mama sai cewa tayi "ni dai duk abinda Zaki aikata kada kisake ki kwaso ciki ki rik'a amfani da matakan kariya" A matuk'ar firgice Maryam take kalloan haj. Sailuba jikinta har rawa rawa ya soma dan tsabar mamaki kasa magana tayi saima tunanin da ta soma aranta na "anya wannan uwa tace kuwa?" Da k'yar ta iya ce mata daman nazo ne dan Allah Mama ki barni naje garin da momma take Nassar yace kwana d'aya kacal zasuyi dan Allah......katseta Mama tayi cikin sauke ajiyar zuciyar samun mafita na kaucewa tafiyar ta da Baffa zuwa wajen wannan jarababbiyar tsohuwar tace "sai kun dawo" mik'ewa tayi k'udin da takawo mata sai da ya girgiza ta ta amsa yau ko godiyar batayi mata ba ta fice kai tsaye d'akin Ammey ta nufa har MD ma yana can ta mik'ewa Ammey k'udin ta fashe da kuka tace "wai mama ce take cemin duk abinda zanyi kada na d'auko mata ciki anya uwata ce kuwa dan Allah Ammey ki fad'a min itace ta haifeni?" Ita kanta Ammeyn ba k'aramin girgiza tayi ba musaman da suka k'irga k'udin miliyan d'aya da dubu d'ari da hamsi itama Ammeyn fashewa tayi da kuka ta kasa magana ganin haka MD ya kasa cewa komai ya rungume maryam yana rarrashin ta ransa na masa wani irin suya sun jima a haka kafin Ammey ta janyo maryam daga jikin MD ta kasa magana saima sabon kuka daya kwace mata. Muje zuwa بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 39 "Innalillahi wainnailahi raji un" kawai Ammey take ta maimaitawa, ta kasa magana, hakanan kukanta yak'i tsayawa, jikinta har rawa yake, tsabar damuwa takasa cewa komai sai fad'a jan yar ta take cikin jikinta tana shafar ta. Can kuma kamar wacce aka tsikara zumbur ta mik'e tayi b'angaren Baffa a mugun fusace, da k'yar ta iya yiwa Baffa sallama yanayin da yaji muryanta yasan cewa lallai akwai gagarumin matsala dan ba komai Ammey take d'aga hankalinta akai ba. Da kallo ya bita tana takowa kamar me koyon tafiyar yayin da Baffa ya kafeta da ido gabansa na fad'uwa, har ta k'araso cikin rawan murya tace " Baffa yau ina so abani 'yata tunda ba kune kuka yimin nakudar taba" Da kallon mamaki ya bita, me kuma ya faru take irin wannan maganar? Ya sani sarai rashin kunya ba halinta bane tana da hak'uri da sanin ya kamata yau kuma me ya tab'ota har take irin wannan zancen?" Ammey da ranta yai mugun b'aci akan abinda taji yau abakin 'yar tata yasa ta rufe ido ta rik'a fad'awa Baffa magana Kuma maganar duniya tak'i sauraran sa ga wani irin kuka da take yi mai cin rai. Tun bayan fitar Ammey MD yaji wani sanyi aransa ya sani cewa shi zai fasa kwan dubuce ta cika yau shi kad'an sa sai murmushi kawai yake saki da maryam ta juyo zata kalleshi zai basar. Gajiya yay da kukan nata ya matsa kusa da ita yace "kinsan wani abu?" Tsaida kukan tayi ba tareda tace komai ba, ta dai zuba masa ido shikuma gane cewa shi take jira yasa yace "akwai abinda in kika sanshi sai kinji dad'i ranki zai miki sanyi zakiji cewa babu d'an gata kamar ki amma ina so kidaina min asarar wannan tsadaddun hawayen naki ki adana min su sai ranan da aka mik'a min ke a matsayin matana" Ya fad'a yana d'age mata gira tareda murmushin da bata gane ko na meye ba, hararan sa tayi ta maida kanta can gefe tana shashshek'a, kafin ya k'ara magana aka kira wayarsa da sauri ya d'aga harda d'an russuna wa kamar yana gabansa, bataji abinda akace masa tadai ga ya amsa da to ya fice da sauri. Lokacin da zai shiga d'akin dan amsa kiran Baffa sannan kuma Ammey ta fito daga d'akin cikin tsantsar tashin hankali da b'acin rai taci alwashin koda hakan yana nufin rabuwarsu sai an maido mata yar ta wallahi, ko kulawa da MD batayi ba ta fice ta ta wuce d'akin ta ta zari mayafinta rabonta da kwatanta yaji tun akan bada Maryam sai gaahi yauma ta k'ara kwatawa. Yanayin da MD yasami Baffa na b'acin rai yasa MD ya k'ara nutsuwa ya k'arasa kusa dashi ya zauna kansa a k'asa Saida ya nutsu Sosai ya gaida Baffa wanda tsabar damuwa yasa ya kasa amsawa saboda tsabar tashin hankalin data jefashi. "Muhammadu zan tambayeka ka dubi girman Allah ka fad'amin tsakani da Allah nake so kafad'a min iya abinda ka sani' karka min k'arya, kar ka min k'arya, karka min k'arya, Muhammadu kada ka duba halin da kuke ciki kai da Sailuba asalin gaskiyar nake buk'ata" Shiru MD yayi na d'an wani lokaci yana son tuna komai ko abu guda baya son ya manta (🤣🤣) MD fa ka fad'i gaskiya banda heri😂😂 Kallonsa Baffa yake yana jiran amsa, dan haka ya kwashe iya abinda ya sani komai bai rage ba kafin ya k'arasa jikin Baffa yayi wani irin sanyi wata irin nadama ta saukar masa take ya hau zufa jijiyar kansa tayi wani irin tashi, waima me ya hau kanshi da har ya manta halin Sailuba ya d'auki tarbiyyan gudan JININSA ya bata matar da ita kanta tarbiyyar take buk'ata take ya kama hawaye abinda ya firgita MD kenan ya rik'a rarrashin sa tareda kwantar masa da hankali Wasa ya fara MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 39 "Innalillahi wainnailahi raji un" kawai Ammey take ta maimaitawa, ta kasa magana, hakanan kukanta yak'i tsayawa, jikinta har rawa yake, tsabar damuwa takasa cewa komai sai fad'a jan yar ta take cikin jikinta tana shafar ta. Can kuma kamar wacce aka tsikara zumbur ta mik'e tayi b'angaren Baffa a mugun fusace, da k'yar ta iya yiwa Baffa sallama yanayin da yaji muryanta yasan cewa lallai akwai gagarumin matsala dan ba komai Ammey take d'aga hankalinta akai ba. Da kallo ya bita tana takowa kamar me koyon tafiyar yayin da Baffa ya kafeta da ido gabansa na fad'uwa, har ta k'araso cikin rawan murya tace " Baffa yau ina so abani 'yata tunda ba kune kuka yimin nakudar taba" Da kallon mamaki ya bita, me kuma ya faru take irin wannan maganar? Ya sani sarai rashin kunya ba halinta bane tana da hak'uri da sanin ya kamata yau kuma me ya tab'ota har take irin wannan zancen?" Ammey da ranta yai mugun b'aci akan abinda taji yau abakin 'yar tata yasa ta rufe ido ta rik'a fad'awa Baffa magana Kuma maganar duniya tak'i sauraran sa ga wani irin kuka da take yi mai cin rai. Tun bayan fitar Ammey MD yaji wani sanyi aransa ya sani cewa shi zai fasa kwan dubuce ta cika yau shi kad'an sa sai murmushi kawai yake saki da maryam ta juyo zata kalleshi zai basar. Gajiya yay da kukan nata ya matsa kusa da ita yace "kinsan wani abu?" Tsaida kukan tayi ba tareda tace komai ba, ta dai zuba masa ido shikuma gane cewa shi take jira yasa yace "akwai abinda in kika sanshi sai kinji dad'i ranki zai miki sanyi zakiji cewa babu d'an gata kamar ki amma ina so kidaina min asarar wannan tsadaddun hawayen naki ki adana min su sai ranan da aka mik'a min ke a matsayin matana" Ya fad'a yana d'age mata gira tareda murmushin da bata gane ko na meye ba, hararan sa tayi ta maida kanta can gefe tana shashshek'a, kafin ya k'ara magana aka kira wayarsa da sauri ya d'aga harda d'an russuna wa kamar yana gabansa, bataji abinda akace masa tadai ga ya amsa da to ya fice da sauri. Lokacin da zai shiga d'akin dan amsa kiran Baffa sannan kuma Ammey ta fito daga d'akin cikin tsantsar tashin hankali da b'acin rai taci alwashin koda hakan yana nufin rabuwarsu sai an maido mata yar ta wallahi, ko kulawa da MD batayi ba ta fice ta ta wuce d'akin ta ta zari mayafinta rabonta da kwatanta yaji tun akan bada Maryam sai gaahi yauma ta k'ara kwatawa. Yanayin da MD yasami Baffa na b'acin rai yasa MD ya k'ara nutsuwa ya k'arasa kusa dashi ya zauna kansa a k'asa Saida ya nutsu Sosai ya gaida Baffa wanda tsabar damuwa yasa ya kasa amsawa saboda tsabar tashin hankalin data jefashi. "Muhammadu zan tambayeka ka dubi girman Allah ka fad'amin tsakani da Allah nake so kafad'a min iya abinda ka sani' karka min k'arya, kar ka min k'arya, karka min k'arya, Muhammadu kada ka duba halin da kuke ciki kai da Sailuba asalin gaskiyar nake buk'ata" Shiru MD yayi na d'an wani lokaci yana son tuna komai ko abu guda baya son ya manta (🤣🤣) MD fa ka fad'i gaskiya banda heri😂😂 Kallonsa Baffa yake yana jiran amsa, dan haka ya kwashe iya abinda ya sani komai bai rage ba kafin ya k'arasa jikin Baffa yayi wani irin sanyi wata irin nadama ta saukar masa take ya hau zufa jijiyar kansa tayi wani irin tashi, waima me ya hau kanshi da har ya manta halin Sailuba ya d'auki tarbiyyan gudan JININSA ya bata matar da ita kanta tarbiyyar take buk'ata take ya kama hawaye abinda ya firgita MD kenan ya rik'a rarrashin sa tareda kwantar masa da hankali Wasa ya fara MAMAN islam ce بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 40 Bai saurare shi ba ya tashi a fusace ya fita, yana fita MD ya mik'e ya buga uban tsalle yana rawa har da d'ebo shoki a aransa yake fad'in yau wata zata kwashi kashin ta a hannunta yadda Baffa ya fusata dinnan. Wani abun ta kaici Baffa a fitinensa ya shga d'akin Sailuba ya balbaleta da ruwan bala i amma tana d'agowa suka had'a ido sai ya nemi tashin hankalin ya rasa saima rarrashin ta da ya somayi ita kuma tayi wani kicin kicin da rai. Sanda haj. Amina ta isa gidansu malam Babba yana k'ofar gida da daliban sa tsabar idonta ya rufe bata gansuba kanta tsaye d'akin Nanne ta wuce cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara, ita kanta Nanne ganin ta haka sai da gabanta ya fad'i da k'yar ta rarrasheta ta daina kukan da takeyi. Ganin halin da yarsa take ciki yasaka ya sallami mutanen nasa ya taso kai tsaye d'akinsa ya wuce yasa aka kira masa duka matan nasa harda Amina wacce tai wani wujuga wujiga tsabar tashin hankalin data tsinci kanta a ciki. Sai da malam ya fara yimata fad'an fitowa da tayi batare da sanin mijinta ba dan duk wanda yaga yanayin ta yasan ba fitowar lafiya tayi ba sannan ya tambaye ta abinda yake damunta. Cikin zubar da hawaye ta kwashe tun daga ranan data fara jan Maryam har zuwa yau ta fad'a musu komai, ba matan ba hatta shi kanshi malam Babba saida hankalin sa ya tashi danjin masifar da ake son d'ora masa jikar tasa akai sosai ransa ya b'aci ya rik'a maimata innalillahi wainnailahi raji un sosai yaiwa haj. Aminatu nasiha sannan yace tacigaba da jan yarta a jikinta ta kuma rik'a nusar da ita cikin hikima ta rika sata a hanyar data dace kada tace zata yi mata hayaniya shi yaro da dabara ake tarbiyyan sa ba da hayaniya ba. Sunan zaune sai ga Baffan yazo hankali tashe tun bayan da ya fito daga d'akin Sailuba ya fara tuhumar kansa dalilin da yasa yakasa yimata bore kamar yadda ya fita da niyyar yi mata. Bayan sun gaisa da malam ne yake bashi hak'uri kuma yake rok'on abawa Amina hak'uri sannan yace koda yaje da niyyar daukar mataki akanta sai tayi masa kwarjini ya kasa tab'uka komai. Malam yace" babu komai kaci gaba da addu a kuma kadaina sake wajen yin azkar insha Allah komai zaizo maka da sauk'i yanzu dai maganar gaskiya Baffa ya zama dole kasa ido akan tarbiyyan yarinyar nan" Komai ya kusa karewa ma malam dan na tsaida auren Maryam da MUHAMMAD k'arahen watan nan da muke ciki insha Allah" ba malam Babba ba hatta Ammey ba k'aramin sanyi taji aranta ba sai taji duk abinda yake damunta ya kau, sosai malam yayi musu nasiha, kafin su baro gidan. Acan gida kuwa suna fita haj. Sailuba ta fito nan ta sami MD da Nassar a falon ta saki wani wawan tsaki ta k'arasa kusa da su tace " su agola ansami wuri kana tunanin d'an k'aramin makircin ka zaisa kay nasara ne? ni kumurcin kan dutse ne ban fito ba saida na shirya" "Haba Sailuba karfa ki manta rana dubu na b'arawo rana d'aya na mai kaya ne yanzun dai ki mai da hankali kici lokacin ki amma ki sani komai lokaci ne karshen ki ya kusa fajirar banza" "Kai dan ubanka ko Hasan ya isa ya zag........ " Ke tsohuwar banza gyara kalaman ki kada ki kara zagin bawan Allah yana kwance a raminsa yana hutawa kinsan wanda yasami shaidar mutane ya dace dan haka ya fi k'arfin ki shi d'in bawan Allah ne ba masoyin duniya bane dan haka na k'ara jin kin zage shi wallahi saina gurji bakin ki" Ganin yadda ya rikice mata idanunsa sunyi wani irin juyewa tsabar b'acin rai yasa tai gum da bakinta sai d'an uban harara da take aika masa shima dataga ya d'ago zatayi saurin k'asa da kanta. Sai da ya gama masife ta tare da zubar da ruwan rashin mutuncin son ransa kafin ya buga wani d'an uban tsaki tare da sakar mata hararan da yasa 'yan hanjin ta kad'awa babu shiri ta shige d'akin ta tana tsine masa a ranta. Su Ammey suna dawowa gida tasa maryam ta hau shiri dan tasawa ranta cewa 'yarta tabar hannun wannan azzalumar matar, hakan yasa ko Baffa baisan da Maryam akai tafiyar ba sai da yagama shirinsa yasauko yana tambayar haj. Sailuba maryam ta gama shiri shine take sanar masa tare da Ammey suka tafi ransa ba k'aramin b'aci yayi ba ya rufe ta da fad'a domin yasan dan kar ya kaita w ajen mahaifiyar sa yasa ta bari aka tafi da ita yasan Sailuba yasan waye ita, yasan abinda zata iya aikatawa da wanda baza tayi ba, ya rasa mai Inna tayi mata da zafi haka da ta daina zuwa inda take kuma ta hana maryam ta kusance ta matar da ta rik'e ta ta kula da ita bata bari tayi kukan maraici ba yau itace abar wulakantawa awajen ta kwafa yayi ya fice cikin tsantsar b'acin rai da bak'in cikin yadda yake kasa d'aukar mataki akan abinda take masa ko yaso hakan sai tayi masa wani irin kwarjini yaji tausayin ta ya baibaye shi. Maryam kuwa yau cikin wani irin farin ciki ta tsinci kanta bakin ta yak'i rufuwa tsabar jin dad'i, baza tace ga lokacin da sukayi doguwar tafiya irin wannan ba. D'an d'ago kanta tayi daga kafad'ar Ammey ta dubeta "Ammey wai me yasa Mama bata son naje wajen Inna kinga fa bansan garin ba gashi Baffa yana yawan zuwa da Nassar amma ni sai ta hana me yasa bata zuwa kuma bata so naje?" Wani irin abu mai mugun tauri yayin da taji zuciyar ta babu dad'i ta rasa bak'ar zuciya irin na haj. Sailuba matar nan fa k'anwar mahaifin tane uwa d'aya uba d'aya sannan kuma mahaifiyar mijinta amma wofintar da ita irin haka ta rasa wane irin mugun hali ne da matar nan haka. "Ammey dama kece kika haife ni ba Mama ba wallahi na tsani halinta" Gaban Ammey ne yay wani irin fad'uwa ta k'ara jan maryam cikin jikinta hakanan take jin zuciyar ta yana yawan tsinkewa, tsoron ta d'aya kar wani abun ya samar mata 'ya dan 'yan kwanakin nan mafarkin da take da maryam ba mai dad'i bane hakan yasa bata runtsawa kullum tana nemar mata sassauci wajen lillahi. "Allah yasa ta gyara halayen ta" Mayarm data gane inda Ammeyn ta dosa tace amen. Na fara ganin sauyi yawan comment yawan typing dan haka inna ruwan comment zan kara yawan page na gode masoyana ina alfahari daku MAMAN ISLAM CE بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 41 Ammey ta rik'a jan ta da hira cikin hikima take nuna mata aibun mugun halin da haj. Sailuba take son d'ora ta wanda ba mai b'ullewa bane, tacigaba da cewa. "Mutuncin ki shine martaban ki darajanki a wajen mijinki shine ki rik'e Martaba da mutuncin ki karki yarda ki zubar da kimar ki ta d'iya mace duk randa akace kin rasa martaban ki wannan abun zaiyi ta bibiyarki har jikoki, bayan haka kuma ita kanta zina tana da mugun illah kuma yad'o abin yake yay ta binka dan haka ina so ki rik'e min Martaba da kimar ki na d'iya mai tarbiyya hakan zaisa na samu salama har cikin kabari na" Gaban ta ne yay wani irin fad'uwa jin Ammey na kiran mutuwa sai take jin kamar mutuwar zatayi ta d'an dubeta a sanyaye tace "Ammey bangama jin d'umin ki ba ban gama sabawa dake ba insha Allah bazaki mutu yanzu ba sai mun tsufa kin ga 'ya'ya da jikoki na" "Kayya'yar nan ita mutuwar ai intazo bata sallama sai dai kawai kiji tayi wuf da mutum fata dai Allah yasa muyi kyakykyawan k'arshe" Jiki a san yaye tace "amen" duk sai taji hiran yafita daga ranta dan haka ta lumshe idanunta kamar mai bacci yayin da k'irjinta yake d'an bugawa sai ta kasa nutsuwa daga hiran da sukai da Ammeyn. Ba k'aramin farin ciki momma tayi da ganin Ammey da maryam ba lallai ta ga sauyi tattare da 'yar uwar tata rungumeta tayi tsantsan a jikinta duk k'arfin zuciya irin na momma sai da tani hawaye ya cika mata idanu ta d'ago Maryam a jikinta ta manna mata kiss a goshinta da gefen fuskar ta tana jin wani irin farin ciki da k'aunar 'yar k'anwar tata. Tana rike da hannun maryam suka shiga k'aton falon momman wanda ke d'auke da wasu had'ad'd'un kukeru masu kyau da numfashi. Shigar su yayi dai dai da ahigowar yaran mamma 'yan mata guda biyu saiga k'aramar sun nanma ta shigo tana kukan wai sun barota amota babu wanda yabi ta kanta suka shige da gudu suka rungume maryam dan sun santa sosai a hoto duk da cewa tun tana yarinya ne irin wanda Ammey take fakar idon haj. Sailuba tayi mata, amma Kuma ai ga kama nan domin babu ta inda Maryam tabar Ammey. Ita kanta Maryam tayi matuk'ar farin cikin had'uwar ta da su yayinda wani irin so da k'aunar su yayi ma zuciyar ta kamun farat d'aya. Nanfa falon ya gauraye da hayaniyan su dan maryam dama can bata da bak'unta dan haka ta sake a cikin su suna kwasar shafta sannan Kuma duk wanda yay mata ta mangare shi kunsan babyn ba hak'uri😂😂 Hakan ba k'aramin nishad'i yasaka momma ba hatta abinci ita ta rik'a bata a abakin ta da k'yar su mardiyya sukayi nasaran janye maryam zuwa dakinsu. Haj. Shamsiyya yayar Ammey ce inajin nayi muku wannan bayanin tun farko itama mijinta babban d'an kasuwa ne yana da rufin asiri mai yawa dan shima Allah yayi masa farcen susa Yaran ta biyar na farkonta 'yan biyu ne duk maza Abdul Malik, da Abdul jabbar, dukan su sanyi aure da yaransu, sai Fadeela itama yanzun haka yaranta biyu dan tun kafin auren Ammey aka haifesu da wayon suma akayi bikin Ammey da Baffa. Daga bayan sun fidda rai da sake samun haihuwar ne kuma Allah ya sake bata wasu 'yan biyun duka mata Mardiyya da Fauziyya sai autar su Hanifa wacce itama ak'alla su mardiyya sun bata kusan shekara goma dan duka yanzune suke shirin zana jarrabawan su na shiga jami'a. Suna barin gidan Ammey ta dubi haj. Shamsiyya sai hawaye shar shar haj. Shamsiyya ta dubeta tace "a yada haka Kuma? Memakon ki farin ciki ki godewa Allah 'yarki ta dawo gareki" rungumeta Ammey tayi tace anty sai kuma ta kuma fashewa da kuka. Sai da taci kuka sosai kafin ta d'ago daga jikin'yar uwar tata kafin tace "anty dan Allah idan na mutu kada kibar Nassar a hannunta zata gur b'ata masa rayuwa" K'are zancen cikin zubowar wasu sababbin hawayen. Had'e rai haj. Shamsiyya tayi tace me kuma ya kawo zancen mutuwa ana zaune kalau kadama ki sake wannan maganar insha Allah tare zaku girma da yaronki har kiga auren shi" "Karki ga yadda ta tsaneni tana yarinya karkiga halin dana shiga akan ta naci wuya anty yau zan fad'a miki abinda baki sani ba, INA DA CIWON ZUCIYA, duk a sanadin halin danake ganin'yata a ciki kuma bani da ikon magana yarinyar tayi wata irin rayuwa ne mara dad'i mara ma'ana. Sosai haj. Shamsiyya ta kafe Ammey da ido jikinta yana rawa sosai tace "CIWON ZUCIYA Amina wannan wane irin mugun hali Allah yayi miki na barin abu arai bazaki fitar dashi kiji sanyi ba haba Amina" ta karasa maganar cikin fashewa da kuka sosai, taci gaba da cewa "ashe duk fad'an da nake miki na ki janye 'yarki bakiyi hakan ba kikayi tasa abu aranki har ya zamar miki ciwo arai, kar kimin haka Amina dan Allah" momma take maganar cikin gurshek'en kuka dan tasan tunda har Ammey ta furta tana da ciwo to abinne ya girmama. "Ki yafemin dan Allah anty bana son sakaku adamuwa ne banda ke babu wanda yasan ina da ciwon dan Allah kar ki bari su Baffa suji hankalin su zai tashi" Rungumeta momma tayi cikin tsantsar tashin hankalin da tausayin 'yar uwar tata yayin da Ammey kuma taci gaba da bawa yayar tata labarin irin rayuwar da maryam tayi tare da irin halin da ta rik'a kasancewa a ciki a duk lokacin da Baffa ya juya mata baya, akarshe kuma dad'a jadaddawa antyn tata take ta kular mata da yaranta idan ta mutu, nan kuma ta kuma bata labarin irin mugun mafarkan da takeyi mara dad'i wanda tasawa ranta akwai abinda wannan makirar matar take shiryawa. Sosai hankalin haj. Shamsiyya ya tashi amma sai ta danne nata damuwar ta rik'a tausar 'yar uwar tata har sai da taga ta samu nutsuwa, anan take sanar mata Baffa ya tsaida lokacin auren Maryam d'in da Muhammad, ai kuwa ba k'aramin dad'i hakan yayi mata ba dan ta jima tanayi wa Maryam d'in shi'awar auren MD saboda nutsuwar yaron. Acan d'akin da su Maryam suka bajakolin hirar su kuwa Fauziyya ce ta dubi Maryam tace "dan Allah sis ki rik'a biyo Ammey kuna zuwa wallahi munji dad'in zuwanki ke d'in fa JININ muce" murmushi Maryam ta sakar mata tace "shikenan sis zan rik'a zuwa dan nima naji dad'in kasancewar mu tare Allah ya bar k'auna. Acan gida kuwa MD ji yai hankalinsa yayi wajen Maryam kamar ya bita sai dai yana binta Ammey zata gane saboda Maryam ne hakan kawai yasa ya yanke shawaran yakai ma m Bash ziyara. Kar ku manta Baffa bai sanar da MD maganar aurensa da Maryam ba hakanan haj. Sailuba bata sani ba, bawai kuma saboda wani abu yak'i sanar da ita ba sai dan b'ata masa ran da tayi na barin Ammey ta tafi da maryam d'in alhalin yana son zuwa da ita wajen Inna wanda dama zai jene dan sanar da ita maganar auren Maryam da MD d'in ne. Ku muje dai masoyana Ina alfahari daku duk inda kuke a fad'in duniya MAMAN ISLAM taku ce mai matuk'ar k'aunar ku بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *________________________ 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 42 Bayan ya gama shirin sa ya fito cikin k'ananan kayan da suka matuk'ar amsar sa,ya fito yana baza k'amshin sa mai kwantar da zuciya. Yana sako kai haj. Sailuba na fitowa daga lambum kusa da Pat dinsa cikin wani irin sauri tana wage wage gudun kar wani ya ganta da ganinta ba abin arzik'i ta shuka a wajen ba, wani mugun kallo ya bita dashi cikin tsana sannan ya yaja wani uban tsaki ya shiga lambun dan haka nan yaji yana son ganin meta aikata awajen. Da kallo ya rika karewa wajen kallo har idanunsa suka sauka kan wajen da aka hak'e da alama wani abun aka bunne awajen, gabansa ne yai mugun fad'uwa ya taka a hankali cikin nutsuwar sa ya karasa yana nazartar wajen kafin yayi Bismillah ya durk'usa dan tsabar saurin da take hatta abin hakar bata d'auke ba ta manta da shi a wajen. Sai da yai addu a sosai kafin ya fara hak'a ramin da tayi, yayi mamakin yadda ta iya hak'a rami mai uban zurfi haka, yajima yana hak'a dan har ya fara tunanin babu abin da ta binne kafin yaji hannunsa ya caki wani abu mai mugun tsini da sauri ya janye hannun saiga jini yana bin hannun nasa wanda jini ya fara bi ga wani mugun radadi da ya zuyarci har kwakwalwar sa, mamakin hakan yasa kashi saurin lek'a ramin haba da sauri ya janye kansa yana sauke wani irin wahalallen numfashi sabo da wani fitinannen wari daya daki hancin sa, sai dai abinda ya gani yasa shi saurin komawa tare da dauke numfashi dan tabbas wannan masifar zai iya masa illah. Mikewa yayi ya koma d'akin sa hankali a tashe ya d'auko hanglob jikinsa har wani rawa rawa yake sosai yazo ya hau fito da abin bakinsa d'auke da addu'a, yanzu kam rawa jikinsa ya kama sosai saboda tsabar mamaki. Kan mujiya ne jikinsa duk wasu irin manyan allurai sai kuma wata 'yar k'aramar benu da aka sa wata katuwar allura aka caki daidai zuciyar ta sai numfashi take fitar wa da k'yar ga wasu irin curin layu masu yawa suma a saman wata tsuntsu da baisan ko ta mecece ba itama daga gani ajikace take tama kusa mutuwa. Idanunsa da sukayi wani fitinannen ja ya runtse da mugun k'arfi ya zauna dab'as a wajen cikin ciyayin gun ya dafe kansa da yake mugun sara masa da k'arfi yace "innalillahi wainnailahi raji'un Maryam ko Ammey zata kashe?" Dan shi abinda ransa ya bashi kenan na ganin wannan masifar alluran dake jikin tsuntsayen da suke da rai ya fara zarewa kafin ya cire na jikin mujiyar gaban sa na wani irin mugun fad'uwa hankalin sa a masifar tashe bai ma yarda da kona kayan kai tsaye ba sai da yayi musu fitsari kafin yasa fetur ya Kone. Tunda taga Ammey ta fara shiri tace itafa sai gobe zata dawo dan gajiyan hanya bai gama sakinta ba sosai Abdul jabbar da yake ta binta da kallo yasaki murmushi yace "kawai ki k'yale ta Ammey ma kawota nida Abdul Malik" "Rufamin asiri Abdul jabbar Baffanku baisan nazo da itaba, kabari tunda bikin ta za ayi tazo tayi muku kwana biyu" sai da gabansa ya fad'i da yaji wai bikin ta za ayi dan har ga Allah tayi masa sosai. "To 'yata sai kinzo gyaran jikin ni da kaina zanwa 'yata gyara na musamman, dake sana 'ar tane gyaran amare da haka sukayi sallama. Tana zaune cikin jin dad'in cikar burinta haj. Zakiyya ta kira tana d'agowa tace "ba nutsuwa ba kwanciyar hankali ita ba mahaukaciya ba kuma ba mai hankali ba sannan ita ba rayayya ba sannan kuma ba matacciya ba" hhhhhhhhh suka saki wata muguwar dariya haj. Zakiyya tace an aikata ke nan?" Me zan jira k'awata kinajifa boka yace uban yatsaida aurenta da wannan tsinannen yaron dana fi tsana fiye da komai a rayuwata wallahi bazan bar wannan banzan auren ya faru ba na rantse kuma" ta k'arasa maganar tana huci Har lokacin MD yana d'akin sa cikin tsantsar damuwa da nazarin son gane shin cikin Ammey ko Maryam wa akayi wannan bak'in asirin dayai masifar d'aga masa hankali? Ya sandai wannan tarkacen bala in ba abin arzik'i aka shuka a cikinsu ba. Kamar wanda aka tsikara ya mik'e zumbur domin kaiwa haj. Sailuba fatanyar ta da ta manta. Yana fitowa ana budewa motar su Ammey gidan, dan haka ya dakata har driver ya shigo ya faka motar duk suka fito da gudu Nassar ya k'araso ya rungume MD wanda yai kasak'e yana kallon su, yana mai murnan ganin yayan nasa. Da wani irin kallon mamaki Ammey tabi kayan hannun MD yayin da Maryam ta wuce ciki tana mai dok'in ganin mamanta. "MUHAMMAD wannanfa me kayi dasu naganka futu futu haka?' " Ammey" sai kuma yai shiriu zuciyar sa na wani irin zafi yay saurin dafe kansa kafin yace "wa take son kashewa Ammey ke ko ZUCIYA TA? Muje dai DAGA MAMAN ISLAM 🔥 BA JININA BACE🔥 2021 NA HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI MAMAN ISLAM Page 43 Kallon Ammey yake dafe da kirjin sa wanda zuciyar sa take barazanar fitowa, itama kallonsa take da son k'arin bayani. Dak'yar ya bud'a baki yace "Ammey wani aikin nayi mai wahalarwa Ammey me waccen matar take nufin yi ne akan ni da matata Ammey na rantse da Allah wani abu yasamu matata ni da kaina zan d'auke kanta da wu'ka da wadannan hannayen nawa. Ya fad'a yana d'aga hannun nasa wanda suke wata irin rawa sama. Da wani irin rawa Ammey ta danki hannun MD jikinta na kakkarwa tace "wayyo Muhammad rik'e ni zan fad'i" tayi luuuuuu da wani azababban zafin nama MD ya rik'o ta cikin wani irin rikitaccen yanayi yace "Ammey lafiya kuwa"? "Kaini d'akina Muhammad banida lafiya" da sauri ya d'auke ta akafad'unsa yayin da jikinsa yake wani irin rawa jikinsa kuwa ta ko ina gumine yay masa wanka. Da sauri ta janye wayar daga kunnenta tana fad'in "zan sake kiranki anjima k'awata" nakamakon juyowa da tayi sukayi ido biyu da Maryam da tajima abakin k'ofar tanajin irin mugun abun da maman tata take k'ullawa tambayar da Maryam take wa kanta shine "Shin waye za'a haukata? Waza a tozarta ya wulak'anta? Waye zai zama abin k'yamar al'umma? Me yaye mata take son ya zamo kamar mujiya? Akan me take so yayi warin jab'a? Shin dama mama tana yawon bin malamai ko yanzun ta fara? Ta yarda da daukar wannan babban zunubin ko kuwa? Dawa take wannan Killin?" Inda haka ne mama baki da imani baki da tausayi baki damutunci matsayin ki na musulma ki rink'a had'a mugun k'ulli haka? Duk tayiwa zuciyar ta wadannan tambayoyin, yayin da zuciyar ta yake wani irin bugawa sai taji hankalin ta yai masifar tashi wani irin tsoron maman tata ya mugun kamata da gudu ta juya ta fice daga d'akin cikin tashin hankali gaba d'aya idanunta ya rufe. Tazo shiga d'akin suka gwabza karo da MD wanda yazo neman ta ta tsaya da Ammey wacce ya gama duba zai nemo mata magani, take tayi baya zata fad'i da sauri MD ya taro ta ya rik'e ta yana kallon yadda jikinta yake rawa Suna had'a ido da shi ta fashe da wani irin kuka har da shashshek'a, ina ma ace Ammey ce maman ta ba wannan matar mai bak'ar zuciya ba, inama ace hannun agogo zai dawo baya data rok'i ubangiji ta fito a tsatson Ammey, sai dai Kash d'an Adam bashi da damar zab'a ma kansa rayuwa sai yadda ubangiji yayi da bawan sa, "Allah kaza gatana Allah kazama gatana Allah kazama gatana" take ta maimaitawa cikin tashin hankali da wani irin fitinannen kuka, baisan lokacin da yajata jikinsa ya rungumeta da mugun k'arfi hannunsa na wata irin rawa ya d'ora abayan ta yana shafawa a hankali. Jabbar Mama ta koma saman gado ta zauna tare da d'ora hannunta saman kanta tace "shi kenan na shiga uku taji komai wayyo Allah yau dubana ya cika innalillahi asiri na zai tonu" Jiki na rawa ta ja waya ta kira haj. Zakiyya tun kafin ta d'aga tace "shi kenan k'awata yau taji komai dakanta ta kamani muna waya dake shikenan zata had'a ni da Baffa na shiga uku na lalace" "Ke taya akayi kika san tajiki ba kince sun fita da Amina ba?" "Wllh taji karkiga mugun kallon da take bina dashi dana ganta ma zan wayance bata saurare ni ba juyawa tayi da gudu ta fice" Kinsan ya za ayi?" "A'a" "Zuwa zakiyi kiji idan kin tabbatar da taji abinda muka tattauna sai kibi duk hanyar da zakini nuna mata cewar kunnenta bai juyo mata daidai ba" daga haka suka yi sallama ta mik'e tayi d'akin Maryam. Tana d'aga labulan tayi wani irin baya cikin girgizar zuciya batasan sanda ta kurma wani mugun ihu tace" jama'a kukawo min d'auki kwarto zai lalata min 'ya" A firgice duka suka juyo suka kafeta da ido yanayin sa ba karamin firgita ta yayi ba tayi saurin k'asa da kanta jikinta yana wani irin masifaffen rawa,bata san sanda ya k'arasa kusa da itaba yace adaidai kunnen ta yace "ajiyar ki tananan acikin lambun na bar miki" A firgice ta d'ago tana kallonsa kafin tayi wani luuuuuu ta zube awajen tsabar tashin hankalin jin abinda yace mata Plss manage MAMAN ISLAM CE *بسم الله الرحمن الرحيم* *☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️* FCWA *Home of qualities and trusted writers of the nation* https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17 ______________________________________ 🔥 *BA JININA BACE* 🔥 *2021* NA *HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI* *MAMAN ISLAM* PAGE 44 Da sauri Maryam ta nufeta, yay saurin tareta yana kallon cikin idonta da kallon kar ki soma. "Mama nace fa" ta fada a raunane "maman naki ban lamunta ba kibar ta zata tashi ga Ammeyn ki cen ciwon zuciyar ta ya tashi" da sauri ta kafe shi da ido gabanta yana wani irin dokawa tace "ba yanzun muka dawo daga unguwa ba?" "Eh kinsan al'amarin ubangiji babu yadda baya juyawa bawa kuna shigowa bayan shigewar ki ciki ta yanke jiki ta fad'i, yanzun ma magani zan amso mata na gama dubata. A hankali ta juya ta kafe mama da wani irin kallon tuhuma da tsoro tace "kece ko?" Mama da tun da ta fad'i take wani irin kukan zuci mai azabar radadi tayi saurin girgiza kai, alamun babu ruwanta. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da kwafa ganin yaja hannunta sun fice,. "Sai naga bayanka wallahi Muhammad tunda kayi sanadin rusamin shirina saikayi nadamar yin hakan dan haka nice ajalinka wallahi saikayi nadamar shiga rayuwana da kayi" ta mik'e tashige d'aki tana sakin kukan bak'in ciki. Yanayin da taga Ammey yasa ta k'arasa da sauri ta rungumeta tareda fashewa da kuka tace "Ammeyna me ya sameki daga dawowar mu? Kodai akanki ne naji mama na waya?" Kafeta da ido Ammey tayi batare da tace mata komai ba yayin da zuciyar ta yake mata wani irin fitinannen suka, batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba mai mugun cin rai. Ita ma maryam fashewa tayi da kuka tare da k'ara k'ank'ame Ammey tana fad'in "sannu Ammey yana miki zafi ko zai daina kinji dan Allah ki bar kukan nan haka yana Kona min rai. Wani mugun kukanne ya kuma taho mata tayi saurin toshe bakinta da hannun ta tana jin wani mugun tausayin Maryam yana kamata, ta sani rayuwar Maryam yana cikin gagarumin matsala, tasan Sailuba tasan wacece ita muguwa ce azzalumar matar da batasan Allah ba babu d'igon tsoron Allah a tareda ita makira ce ta ajin k'arshe bata da imani ko k'ank'ani. "Maryam kiyi hak'uri da rayuwa ki gyara d'abi'unki duk da kasancewar naga sauyi mai yawan gaske atare da ke, amma ina so kisani rayuwa bashi da tabbas, idan yau mune gobe ba mu bane, dan Allah zan rok'eki duk halin da kika tsinci kanki, ki kasance mai yawan godewa Allah, ki kare Martaba da kimar ki na d'iya mace k""""'''''''''ya isa dan Allah ya isa Ammey ki daina min irin wannan zantukan masu kama da wasiyya, daga kinyi d'an zazzab'i sai ki kama wasiyya kamar mai shirin barin duniya yanzu yanzu, insha Allah sai kinga jikoki na" ta fad'a cikin matsanan cin rawan jiki ga kukan da take ya kasa tsayawa tsabar tashin hankalin da kalaman Ammey suka saka ta a ciki. Wani irin murmushi tayi mai ciwo sannan hawayen ta basu bar zuba ba, sannan bata fasa yiwa Maryam nasiha ba akan rayuwa da zaman takwar mutane tare da fad'a mata yau da gobe kai ranan dai babu wani jin dad'i a wannan gida. Acan k'auye kuwa bayan Baffa ya isa ba k'aramin farin ciki Inna tayi da ganin tilon d'an nata ba, sai dai shi kad'an sa ta ganshi babu maryam kamar yadda yadda ta buk'ata, hakan bai wani bata mamaki ba tunda tafi kowa sanin halin Sailuba "kai wannan yarinya Allah dai ya shirya, Allah kanaji kuma kana gani na fita hakkinta na bata tarbiyya gwargwadon iyawa ta Allah karka kamani da laifin gurbacewar halinta dan alfarmar fiyayyen haltta (S A W). Nan falon ta tayi masa shimfida ya zauna takawo masa ruwan randa mai sanyi da fura wacce taji lafiyayyan nonon shanu zuryan, kasan cewar tasan da zuwan sa. Sai da suka gama gaisawa sannan ya soma furar kasancewar yana sonta sosai yana sha suna d'an tab'a hirar duniya da Inna wanda duk rabin sa nasiha ne da shawarwari cikin hikima. Bayan ya kammala ne ta dubeshi tace "kaje kasamu kawun Muhammadu dan a tsaida daidai lokacin da za a d'aura auren Maryama da shi Muhammadun dan insha Allahu jibinnan za'ayi babu jinkir tawa" Da sauri Baffa ya dubeta yace "jibi kuma Inna?" K "Ko ban isa zartar da hukunci akan jika ta bane?" "A haba Inna kin isa har kinyi yawa" "To katashi kaje ka dawo kazo ka amshi naka iv da zaka rabawa 'yan uwa da abokan arzik'i, saboda nasan shiriri tarka shiyasa nasa aka buga har kai, sannan magana tagaba Baffa koda wasa Sailuba kar tasan jibi daurin auren Maryama domin na fahimci ita d'in fitina ce arayuwar Maryama, kai wannan yarinya Allah dai ya ganar da ita" Daga Baffa ya fita zuwa gurin yan uwan marigayi aminin shi Hassan MAMAN ISLAM CE *بسم الله الرحمن الرحيم* *☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️* FCWA *Home of qualities and trusted writers of the nation* https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17 ______________________________________ 🔥 *BA JININA BACE* 🔥 *2021* NA *HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI* *MAMAN ISLAM* PAGE 44 Da sauri Maryam ta nufeta, yay saurin tareta yana kallon cikin idonta da kallon kar ki soma. "Mama nace fa" ta fada a raunane "maman naki ban lamunta ba kibar ta zata tashi ga Ammeyn ki cen ciwon zuciyar ta ya tashi" da sauri ta kafe shi da ido gabanta yana wani irin dokawa tace "ba yanzun muka dawo daga unguwa ba?" "Eh kinsan al'amarin ubangiji babu yadda baya juyawa bawa kuna shigowa bayan shigewar ki ciki ta yanke jiki ta fad'i, yanzun ma magani zan amso mata na gama dubata. A hankali ta juya ta kafe mama da wani irin kallon tuhuma da tsoro tace "kece ko?" Mama da tun da ta fad'i take wani irin kukan zuci mai azabar radadi tayi saurin girgiza kai, alamun babu ruwanta. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da kwafa ganin yaja hannunta sun fice,. "Sai naga bayanka wallahi Muhammad tunda kayi sanadin rusamin shirina saikayi nadamar yin hakan dan haka nice ajalinka wallahi saikayi nadamar shiga rayuwana da kayi" ta mik'e tashige d'aki tana sakin kukan bak'in ciki. Yanayin da taga Ammey yasa ta k'arasa da sauri ta rungumeta tareda fashewa da kuka tace "Ammeyna me ya sameki daga dawowar mu? Kodai akanki ne naji mama na waya?" Kafeta da ido Ammey tayi batare da tace mata komai ba yayin da zuciyar ta yake mata wani irin fitinannen suka, batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba mai mugun cin rai. Ita ma maryam fashewa tayi da kuka tare da k'ara k'ank'ame Ammey tana fad'in "sannu Ammey yana miki zafi ko zai daina kinji dan Allah ki bar kukan nan haka yana Kona min rai. Wani mugun kukanne ya kuma taho mata tayi saurin toshe bakinta da hannun ta tana jin wani mugun tausayin Maryam yana kamata, ta sani rayuwar Maryam yana cikin gagarumin matsala, tasan Sailuba tasan wacece ita muguwa ce azzalumar matar da batasan Allah ba babu d'igon tsoron Allah a tareda ita makira ce ta ajin k'arshe bata da imani ko k'ank'ani. "Maryam kiyi hak'uri da rayuwa ki gyara d'abi'unki duk da kasancewar naga sauyi mai yawan gaske atare da ke, amma ina so kisani rayuwa bashi da tabbas, idan yau mune gobe ba mu bane, dan Allah zan rok'eki duk halin da kika tsinci kanki, ki kasance mai yawan godewa Allah, ki kare Martaba da kimar ki na d'iya mace k""""'''''''''ya isa dan Allah ya isa Ammey ki daina min irin wannan zantukan masu kama da wasiyya, daga kinyi d'an zazzab'i sai ki kama wasiyya kamar mai shirin barin duniya yanzu yanzu, insha Allah sai kinga jikoki na" ta fad'a cikin matsanan cin rawan jiki ga kukan da take ya kasa tsayawa tsabar tashin hankalin da kalaman Ammey suka saka ta a ciki. Wani irin murmushi tayi mai ciwo sannan hawayen ta basu bar zuba ba, sannan bata fasa yiwa Maryam nasiha ba akan rayuwa da zaman takwar mutane tare da fad'a mata yau da gobe kai ranan dai babu wani jin dad'i a wannan gida. Acan k'auye kuwa bayan Baffa ya isa ba k'aramin farin ciki Inna tayi da ganin tilon d'an nata ba, sai dai shi kad'an sa ta ganshi babu maryam kamar yadda yadda ta buk'ata, hakan bai wani bata mamaki ba tunda tafi kowa sanin halin Sailuba "kai wannan yarinya Allah dai ya shirya, Allah kanaji kuma kana gani na fita hakkinta na bata tarbiyya gwargwadon iyawa ta Allah karka kamani da laifin gurbacewar halinta dan alfarmar fiyayyen haltta (S A W). Nan falon ta tayi masa shimfida ya zauna takawo masa ruwan randa mai sanyi da fura wacce taji lafiyayyan nonon shanu zuryan, kasan cewar tasan da zuwan sa. Sai da suka gama gaisawa sannan ya soma furar kasancewar yana sonta sosai yana sha suna d'an tab'a hirar duniya da Inna wanda duk rabin sa nasiha ne da shawarwari cikin hikima. Bayan ya kammala ne ta dubeshi tace "kaje kasamu kawun Muhammadu dan a tsaida daidai lokacin da za a d'aura auren Maryama da shi Muhammadun dan insha Allahu jibinnan za'ayi babu jinkir tawa" Da sauri Baffa ya dubeta yace "jibi kuma Inna?" K "Ko ban isa zartar da hukunci akan jika ta bane?" "A haba Inna kin isa har kinyi yawa" "To katashi kaje ka dawo kazo ka amshi naka iv da zaka rabawa 'yan uwa da abokan arzik'i, saboda nasan shiriri tarka shiyasa nasa aka buga har kai, sannan magana tagaba Baffa koda wasa Sailuba kar tasan jibi daurin auren Maryama domin na fahimci ita d'in fitina ce arayuwar Maryama, kai wannan yarinya Allah dai ya ganar da ita" Daga Baffa ya fita zuwa gurin yan uwan marigayi aminin shi Hassan MAMAN ISLAM CE *بسم الله الرحمن الرحيم* *☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️* FCWA *Home of qualities and trusted writers of the nation* https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17 ______________________________________ 🔥 *BA JININA BACE* 🔥 *2021* NA *HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI* *MAMAN ISLAM* Masha Allah kungiyata kungiyar albarka ce kungiyar da babu irin ta d'aya tamkar da dubu ina matuk'ar alfahari da first class tare da dukkan 'yan uwa masoya na cikin ta Allah ya k'ara had'e kanmu Allah sarki islamiyya ta Allah ya k'ara shiryamin ke ya sanya miki nutsuwa da jin tsoron sa Allah ya tsarkake min zuciyar ki tareda kullum yayan musulmi baki d'aya D'an auta na Al'mustapha d'an rikici na yanzun an girma ya kamata a daina rigimar banza da wofi. PAGE 45 Bai wani jima ba ya dawo haka ma Inna yana dawowa tace ya koma gida yaci gaba da shiryen sa ita tagama nata haka nan gobe zata iso da tawagar ta, sannan ta kawo wani rubutu ta bashi tace yana shiga get d'in gidan sa kafin yakai ciki yayi Bismillah ya sha daga tsaye, ta jaddada masa hakan sau ba adadi har ya daga yana mamakin wannan wane irin rubutu ne me muhimmanci haka. Sanda ya isa sai da yafara zuwa gidan malam lokacin yana tare da bak'i ganin Baffa yasa ya sallami bakin yace "k'araso mana Baffa kamar wani bak'o zaka tsaya daga nesa". K'arasa wa yay yana d'an murmushi yace "barka da yamma malam" Yauwa Baffa, ya kuma na ganka fasa zuwa wajen Innan kayi?" "Naje malam sai dai bata barni na kwana ba saboda tace auren Maryam jibi ne, gama iv ta bayar wai araba tun yau tunda abin ya kure". Cikin madaukakin farin ciki malam yace " a a to Abu yayi kyau gaskiya naji dad'in hakan sosai Allah ya tabbatar mana da alkhairi" amen amen sun dan jima da malam suna tattaunawa kafin ya sallame shi ya taho gida. Kafin ya shiga gid saida ya kira Halima dake yar abokansa ce Kuma makocin sa na amana yabata iv na daurin auren masu dan dama yace ta kaiwa Abban ta sannan ya bata na 'yan mata yace dan Allah yau ta fara rabawa k'awayen saboda Maryam bata nan su sosai tayi mamakin auren na Maryam yadda yazo musu babu shiri yadda sukaci burin wannan ranar, take ta kira Maryam k'awar Maryam ta jami'a suka sha mamakin su kafin su sannan suka fara rabo tunda lokaci ya riga da ya k'ure. Wannan tsaye tsaye da Baffa yayi shi yasa ya manta da rubutun da Inna tace lallai lallai yasha kafin ya shiga gida Dake yau Ammey ce da girki kuma yasan yadda suka rabu akan sai anbata 'yarta dan haka d'akin ta ya fara nufa sai dai yadda ya tadda ita ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba ya k'arasa kusa da ita yana tambayar Maryam abinda ya faru shida ya fita basa nan. Cikin kuka tace itama bata sani ba bayan sun dawo MD ya kirata yace tazo ta kula da ita kafin ya kawo magani, daga haka ta fice ganin yadda Ammey take kalloan Baffa tasan akwai abinda take son fad'a masa. Tana fita sukayi kicibus da MD wanda da k'yar ya samu maganin da Ammey take sha yace "ya kika fito?" "Baffa ya dawo yana ciki" Da mamaki yake kallon ta yace "bai kwana ba?" "Inaga ya fasa ne" Ta bashi amsa tana wucewa ciki saboda jin ana kiran sallar isaha, dan haka shima ya nufi part d'insa dan yayi tasa alwalar dan kar ya rasa jam i. A b'angaren Mama kuwa tunda ta shiga d'aki ta kasa nutsuwa sai zarya take daga k'arshe ma kai tsaye bokanta ta kira ba aminiyar tata ba ta sanar masa duk halin da ake ciki, Yace "kin lalata komai Sailuba dole ne abinda kike gudu zai faru, sannan bazaki samu komai da kike buk'ata ba, idan kina son cikar burinki dole ne kizo nan mu kadaice dake na kwana biyu dole nayi kwana biyu ina saduwa dake da wannan maniyin da zai fita a jikin ki zan miki aikin da zai baki mamaki bayan haka banida wata hanya ta samun nasarar ki". Idanunta ya rufe, Zuciyar ta ya toshe Tunanin ta ya b'ace Imanin ta ya barta Bata da wani buri ko fata illah tarwatsa rayuwar yarinyar da babu abinda tayi mata wanda ya wuce yi mata biyayya da gwada mata k'auna irin na uwa mahaifiya da 'ya mai mutukar biyayya agareta. Hakkan ne yasa Baffa yana shigowa ta fice dan boka yace kar ta bari su had'u dama dakon dawowar sa take wannan kenan. Bayan Maryam ta idar da sallar tana shirin komawa b'angaren Ammey kiran name sake d'in ta ya shigo wayar ta ta d'aga tana fad'in 'yar halak wallahi jikin Ammey ne ya hanani kiranki" "Eh kyace haka mana saboda rainin hankalin da kika saba, yanzu sahiba ace jibi jubi daurin auren ki amma sai yau muke sani kin kyauta ai" Dakatar da ita Maryam tayi ta hanyar cewa " dake yar tsana ce ni shiyasa aurena zai kasance jibi har na kasa sani, ko shirin film ko kuma a littafi wanda suke shirya abu nan take" "Idan kina musu ki bud'e data ki duba status dina mana ko muna da wata MARYAM BAFFA ABUBAKAR ne bayan ke?" Ai bata tsaya jin k'arshen labarin ba ta katse kiran tana katsewa kiran Halima yana shigowa ta daga asanyaye saboda bazata iya katse kiran Halima ba amma bataso Kiran ba sai ta fara duba sak'on Maryam. "Ba zaiyiyu mu zaga duka k'awayen mu yau ba dan haka waso duk ta whatsoapp muka tura musu katin gayyatar, idan Kuma kina da wani wanda zaki bawa idan kun dawo daga unguwar saina kawo miki sauran" Da mamaki Maryam tace "ke nifa bangane inda wannan dogon sharhin naki ya nufa ba katin gayyatar me?" Yadda tayi maganar ya tabbatar wa da Halima cewa Maryam bata san da maganar aurenta jibi ba dan haka tace mata "kun dawo ne?" "Eh "kawai tace mata tana dafe kanta da ya soma k'ullewa da maganganun Halima da maryam "Bari nazo yanzu" ta fad'a tare da katse kiran. Ba a rufa cikakken minti uku ba Halima ta shigo d'akin ta karasa kusa da Maryam ta dafata tunda tayi sallama bata jitaba ta fad'a duniyar tunani. Ba tare da ta ce mata komaiba ta mik'a mata iv mai d'auke da sunanta baro baro da sunan MD tareda tabbatar da d'aurin auren su ranan 2/3/2021 Sosai mamakin ganin katin ya kamata yaushe nema har tace tana son MD da za ayanke mata d'anyen hukunci haka? Dafatan da Halima tayi ne ya maidota hankalin ta a hakanli tace "nayi matuk'ar farin cikin kasancewar wannan abun kuma nasan cewa kema baki san da maganar ba Maryam nasan wannan shirin Baffa ne dan Allah karki bujere" "To" shine kawai abinda Maryam ta iya fad'a tana tunanin yadda MD zai d'auki abin yadda yake nacin soyayyar ta d'in nan bai samu gamshashshen amsa ba gashi yanzun ya sameta a arha, arha mana tunda tasan cewa wannan ba shirin Baffa bane na Inna ne dan Baffa duk abinda zaiyi sai yai shawara da ita da MD daga haka sukayi sallama da Halima bayan tayi mata nasiha ta bata ahawarwari sannan tace yanzun maman Niger zatazo tunda abin yazo a kurace ta d'an yi mata gyara sama sama Umma ne tasa a kirata. Tana fita MD yana shigowa d'akin cikin wani irin sauri ya k'araso kusa da ita ya tsaya yace "my happiness kinga abinda nagani kuwa?" "Eh na gani" ta fad'a a sanyaye haka nan maganar take sa mata wani irin fitinannen bugun zuciya "me kika ce akai to?" A dan sanyaye ta kalleshi kafin lumshe idanunta ta bud'e akanshi zuciyar ta na wani irin fitinannen bugu har tana dafewa tace "me kake so nace to? So kake naje nacewa Baffana ban amince da zab'in saba?" Sam bai kula da yanayin ta ba ya duka ya d'an tsotsi tattausan lab'b'an duk kuwa da irin yadda take nuna masa bata son hakan ya dafa kanta yace "miki alk'awarin insha Allahu bazaki tab'a nadamar kasancewa na mijinki ba ya kuma manna mata wani kiss d'in a goshinta kafin ya fita da d'an gudun sa dan kar tayi masa magana, gane hakanne yasa ta saki murmushin da bata shiryawa zuwansa ba. Bayan Baffa ya dawo daga massalaci ya shigo d'akin Ammey yaji dad'in ganinta akan sallaya itama tayi sallar tana jingine a jikin gado tana jan carbi. K'arasawa yayi kusa da ita ya zauna dab'as yana dubanta kafin yakai hannun saman fuskar ta ya d'an shafo "ya jikin babyta?" Ya fad'a da salon tsokana wanda rabon da hakan ya kasance an d'an jima sai abin ya bata dariya sosai, sai ta d'an murmusa tace "da sauk'i kafin takai hannunta saman nashi tace "Baffa" "Na am" ya amsa mata cikin sanyin jiki D'an Allah kada ka bari abinda yake faruwa da rayuwar Maryam yaci gaba da faruwa dan girman Allah, saboda kaga rayuwa ba tabbas idan yau mune gobe fa jibi fa haka wata rana bama nan an gina rayuwar 'yata cikin wani irin gurbataccen yanayi wanda sam bai min dad'i ba Baffa, kasancewar Sailuba na 'yar uwar ka bai kamata ace tayiwa 'yarka irin wannan tarbiyyan ba, kasan mai yafi d'aga min hankali?" "a a" ya fad'a yana kafe ta da wani irin kallo gabansa na mugun fad'uwa ya saboda yadda yaga ta koma kamar babu jini a jikinta, yayin da taci gaba da cewa "ce matafa tayi taje tayi duk abinda zatayi itadai karta sake ta d'auko mata ciki" "Ita Sailuban?" Baffa ya tambaye ta a fusace nan ta kwashe duk irin abunuwan da maryam take fad'a mata idan sun keb'e ta fad'a masa tas. Ran Baffa ba k'aramin b'aci yayi ba ya nufi part d'in Sailuba a fusace, sai dai abin ta kaicin yana shiga ya tarar bata nan a gogon hannun sa duba tara da rabi na dare, yaushe har nayi saken da Sailuba takeyin yadda taga dama a cikin gidannan? Ni kuwa nace an maka dabaibayi ne malam Baffa shi yasa take yadda taga dama hhhhhhhh. Tun yana saka ran dawowar ta har k'arfe daya ta buga wanda ya tabbatar masa cewa Sailuba bazata dawo daga yawon gantalin ta yau ba, ai kuwa ransa ya kai k'ololuwar b'aci yasha alwashin sai ya sab'ar mata fiye da kima. Acan wajen boka kuwa irin yadda ya rika durza Sailuba ko Baffa bai tab'a yi mata irin wannan durzar ba iya bak'ar azaba awannan daren Sailuba tasha a hannun katon kafirin da babu Allah ko kad'an a zuciyar sa haka ya kwana abu d'aya da ita ga abin nasa mai mugun tsayin da ya wuce tunanin ta gashi mugun fitinanne ka masifar warin da yasa ta rik'a yunk'urin amai amma ta kasa yi bashi ya k'yale ta ba sai da garin Allah ya waye tangaram Kuma ya hanata yin sallar yace ita da salla sai in ta koma gida tayi, dake idanunta ya riga da ya rufe cikar burinta kawai take buk'ata ba wani ja ta amince hakanan ya wuni sa suk'ar ta kamar ya samu abinci. Ganin k'arfe uku ya buga yasa Baffa komawa d'akin Ammey cikin tsantsar b'acin rai ga mamakinta saman dadduma ya tadda ta tana lazumi duk da kasancewar k'arfin hali kawai take hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba. K'arasawa yayi kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta yace "ki kwantar da hankalin ki Amina ta addu'ar ki ya amsu jibi daurin auren Maryam da MUHAMMADU inji Inna" Wani irin kafe shi tayi da ido kafin ta fad'a jikinshi ta k'ank'ame tace "na gode na gode ba ka gama min komai naji duk wani fargabana ya kau Baffa Allah ya sakawa Inna da mafificiyar Aluannah. Ta fad'a cikin fashewa da kuka yace "to meye kuma na kukan 'yan mata na kunya ne ta kamata dan haka ta b'oye fuskar ta a k'irjinshi, ranan dai haka suka karasa wannan daren cikin farin ciki da nishad'i wata irin hira sukayi mai dad'i da tsayawa a rai Sosai Baffa ya samu sauk'in b'acin ran da Sailuba ta dasa masa. Abangaren MD kuwa tunda ya fita daga d'akin ya koma part d'insa ya zauna cikin wani irin farin ciki duk shafukan sa na sada zumunci babu inda bai d'ora sanarwar auren su da Maryam ba yayin da itama maryam kwana tayi saman abin salla saboda halin da ta kasance ya k'azanta ba ita ta samu ta hutaba sai bayan anyi assalatu. Rana baya k'arya sai dai uwar diya taji kunya yaune d'aurin auren Maryam da MD wanda yau tun safe ake shirye shirye wanda yasa duk damuwar da take ji tsayin kwanakin ta nemeshi ta rasa. Ta bangaran Ammey 'yan uwanta sunzo sosai sai hidima ake, haka b'angaren ango cike tab da abokansa ana ta zuba masa shakiyan ci, haka dai aka shiryawa auren abokin nasu wanda har lokacin ya karato, idan ka kalli MD kuwa wani irin annurin farin ciki ne kwance a saman fuskar shi yayi kwalliya cikin bluen shadda wacce akayiwa riga da wanda da babba riga kayan sun yi mugun amsar jikin sa yayin da ya dinkawa Maryam nata ita kuma ruwan hoda tayi wani irin fitinannen kyau itama ba k'arya. Hum zo kaga Baffa uban amarya shima yasha wanka iya wanka duk da kasancewar yana cikin halin damuwa na rashin sanin inda Baffa ya tafi hakan bai hanashi sakin fuskar ta shi ba da farko yaso a d'aga auren a tunanin sa Sailuba b'ata tayi amma Inna wacce ta k'araso da tawagar ta mota kusan biyar tace babu abinda zasu fasa haka aka cigaba da shagalin batare da sanin uwar amarya ba🤪🤪🤪🤪 Haka haj. Sailuba tayi kwanan wahala kwanan tashin hankalin kwanan masifa, a yadda takejin k'asan ta da k'yar idan mutumin nan bai farkata ba, amma idan ta tuna cewa muradin ta ya kusa cika sai taga hakan ba komai bane, kafin ta baro wajen boka sai da ya shaida mata yau za adaura auren Maryam da MD dan haka ta yi k'ok'arin ganin ta isa gida kafin agama shafa fatiha domin idan an d'aura bazai kuntu ba, haka ta baro wajen sa hankali a tashe tana fatan ta tadda ba a d'aura ba. Tana shigowa dakin wani butu butu da ita suka fara ido hudu da Baffa wanda shigowar sa kenan daga wajen daurin auren a fusace yayo kanta cikin bala' i amma suna had'a ido ya nemi fushin nasa ya rasa sai ma washe baki da yayi yace "a a Sailuba, Sailuba, hajajjuna daga ina haka?" Yai mata tambayar cikin sanyin jiki yayin dayake jin wani irin d'aci can k'asan ranshi. Ganin yadda aikin yayi saurin tasiri yasa tace "ban sani ba daga inda ka aike ni" "A a Allah ya baki hak'uri nifa badan na b'ata miki na tambaya ba ganin yadda hankali na ya tashi ne yasa na ke tam""''""' kai dan Allah karka cika min kunne da surutun ka na banza" sai kuma ta bi 'yan falon da wani kallo kafin ta maida hankalin ta kanshi tace " Me ake yine naga an wani cika mana gida da wannan kazaman k'auyawan?" Washe baki Baffa ya sake yi da dariya yak'e yace "d'aurin auren yarki ake " 'yata kuma wacece hakan?" Ta tambaya tana tamke fuska a hankali yace "Maryam nake nufi Mana" Sai tayi wani shu' umin murmushi tace auho " cemin zaka kayi shegiyar da akayo cikin ta a waje aka halarta maka" Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara Baffa ya kafe Sailuba da ido yayin da duka 'yan taron bikin suka kewaye su da hayaniya da son jin kwakwaf wasu kuwa fad'i suke ji tsinanniya saboda bak'in cikin ke baki haihu ba shine zaka sheganta masa 'ya shi kuwa Baffa ji yai kansa yayi wani masifaffen sara masa take jikinsa ya kama rawa, yay saurin dafe kannan nasa da yake wani jin kamar ana buga masa gudu da sauri yayi saurin durkushe wa a wajen, yayin da itama Sailuba tayi saurin durkushe wa a gabansa ta bud'e dukan muryar ta da mugun k'arfi tace "EH BAFFA ABUBAKAR BA K'ARYA NAKE BA CEWA MARYAM BA YARKA BACE BA JININ KA BACE AN KAWOTA NE KAWAI DAN A GURBATA MAKA ZURI A KATAMBAYI UWAR TA WANENE UBANTA? Da k'arfin gaske Baffa ya dafe kansa dayake bara zanar rabuwa da gangar jikinsa, yayin da kalaman ta sukayi wa Maryam da Ammey wani irin duka wanda atare suka shigo babban fakon Maryam tare da k'awayen ta dan amsa kiran Inna yayin da Ammey kuma tazo kawowa su Inna abincin su. Tab Cha kwakiyar fa kenan To masu karatu shin an d'aura auren Maryam da MD? Baffa yana yadda da da maganar Sailuba? Wane hali MD yake shiga idan yaji wannan mummunan al'amarin? Da gaske ne Maryam BA JININ Baffa bane ko makirci ne? Sannan wane hali Ammey take shiga sakamakon jin wannan mummunan al'amarin? Duka wannan amsoshin dama wanda baku nema ba suna cikin littafin BA JININA BACE kashi na biyu wanda zai zo muku nan bada jima wa ba insha Allah ga mai buk'atar cigaban sai ta nemeni a lamba ta kamar haka 09030311095 Daga taku insha Allah MAMAN ISLAM CE maiyi muku fatan alkhairi a koda yaushe Thank you so much Allah yabar zumuch