K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 *EPISODE* 1 FACHANKAN wani K'auye ne dake k'aramar hukumar Jigawa, rayuwar K'auyan abun sha'awa ce, sai dai suna da k'arancin addini harda ma na boka, bawai babu Makarantun ba, a'a sunfi ba sana'arsu mahimmanci, da yawan y'an matan garin talla suke yi, sai kaga budurwa tana tallar abinci da dai sauransu, sana da kin kai shekara sha uku ko hud'u za'a fara shirye-shiryen aurar dake, da yawansu suna durkusar da yaransu, sai kiga yarinya k'arama ta tsofa da wuri, gara ma mazan garin idan suka dage suka gama secondary, tofa shikenan yaro ya gama karatu, wasu iyayan su tura yaro neman kud'i Kudu ko sauran garuruwa, ko a kai yaro almajiranci. Kai tsaye mu kutsa cikin labarin. Haka ce take kasancewa a gidan Alhaji Sani Mai Goro, Babban gida ne wadda ya kasance ginin k'asa ne mai d'auke da d'akona Takwas, ko wanne d'aki da akwai mamallakinsa, Sani mai Goro yana da mata uku, Inna Suwaiba, sai Inna Khande, sai kuma Inna Indo, Inna Suwaiba ta kasance macece mai son kud'in tsiya bata da hakuri dan duk wadda ya tab'a ta gidan sai an jisu tana y'ay'a biyu Hamza, sai Binta, wacce tayi aure wajan K'auyan, sai ko Inna Khande, ita bata shiga harkar kowa a gidan da wuya ana abu a gidan ta tanka, idan ba an tab'o yaranta ba, yaranta uku Ismail, wadda suke kira da Ilo, sai Sule sai kuma Abubakar, wadda suke kira da Abu, Inna Indo kuwa y'ar rigima ce itama ga habaicin tsiya, ko baka tab'a ta ba idan tasu sai kunyi rigima da ita, itama tana da yara biyu Iro, sai Mamman. Cikin yaran nasu Iro dana mata d'aya, Sa'ade da yaron ta namiji wadda ya fara zama saurayi, mai suna Hamisu, Hamisu baya jin magana son matan tsiya ne dashi kamar mi ga bin matan banza tun yana k'arami yaso ayi mai aure, saboda muguwar sha'awar da yake da ita, iyayan sunki mai auren sunce sai yaje neman kud'in idan ya dawo yayi auren shine ya fetsare yak'i zuwa neman kud'in, ya tsaya a gari a jan magana. Sai kuma matar Mamman mai suna Maryama macece itama makirar gaske baka gane gabanta bare bayanta, duk abinda take ciki da ita sai yaranta mata su biyu, Bishira da Habiba suma basa jin magana ga rashin kunyar tsiya ba wadda suka ragamawa a cikin gidan koda kuwa Kakanin su ne, wadda suke d'an shakkarsa shine Kakansu Sani mai Goro. Sai ko Abubakar shi yana da Mata d'aya shima mai suna Hadiza, itama dai y'ar rigima ce ga cika bakin tsiya, idan ta ganka da abu tofa ta kama jin haushi da hassada kenan itama sai taga tayi irinsa, tana da d'iya mace guda d'aya duk duniya tana son Na'ima ta d'ora burin duniya akan d'iyar ta Na'ima, saita auri mai kud'i kuma a birni, bata cika shiri da matan gidan ba. Sai kuma sule wadda yanzo yaran suke kiran su Kawu kamin su kira sunan nasu, shi kuma shine kadai Allah ya d'an d'aukaka shi ya fita daga gidan yana aikinsa a can birni yana samun kud'i sosai yana da shigo a katin Kwari Baban shago ne har abun ya hab'b'aka sosai yanzu haka yana da shago sama da guda biyar sosai arzik'insa ya k'ara bunk'asa, shi yasa gidan Sani mai Goro suna ji dashi iyayansa sunsu su had'a shi aure da y'ar dangi, sai dai mai gidansa wadda ya fara bashi tsaron shigo ya bashi d'iya mai suna Bilkisu ya aura, babu yadda suka iya akayi auran, kuma ya gina gidansa a birnin Kano mai shegen kyau na gani na fad'a, yanzu haka Bilki ta haifa mai yara biyu mata sai namiji d'aya, Khairat, sai Ifteesan, sai ko Babban yayansu wadda suke kira da Ya Khaleefa, Bilkisu bata son y'an K'auye shi yasa bata cika zuwa ba tana da yawan kyauta amma tana mugun son yaranta kamar mi suma yaran sun taso cikin gata kuma suma basa son y'an K'auye sun raina so gani suke ai kamar su d'in basa da gata, Ya Khaleefa yanzu haka baya ma k'asar yana Engila yana karantar Lor ne yaro ne kyakkyawan gaske miskili ne na gidan gaba, dan duk gidansu ba wadda ya kaishi kyau, shi bashida wulak'anci sai dai baya son yawan magana idan ya fad'i magana da wuya ya maimaita ta, shi yasa K'annansa suna mugun shakkarsa. Shi yasa da yawan yaran Bilki basu san y'an uwansu dake K'auye ba. Su duka yaran Sani mai Goro sun tara iyali. Shi yasa Ahalin gidan Sani mai Goro suna ji da Sule, dan ko yanzu kusan shi ke rik'e da su, danma ayyika sunmai yawa sai ya d'an dad'e baizo K'auyen ba, kuma harda had'i daya samu mace wacce bata damu da danginsa ba, nata kawai ta sani. Sai kuma Hamza yayi aure Matansa biyu a gidan suke zaune Matarsa ta farko ita ce Aysha, wacce suke ma lak'abi da A'i, macece mai marar san hayaniya gata da kawaici, tunda ta auri Hamza ta tsinci kanta a gidan Sani Mai Goro, take fuskantar K'alu bale daban daban, saboda shigowarta gidan ta dad'e bata haihu ba, har sai da uwar mijinta ta fara yada mata magana a bisa zugar mutanan gidan, suma kuma sauran mutanan gidan suka had'e kai suka jefa mata karantsa, har sai da Inna Suwaiba taba Hamza umarnin k'ara aure, ba'a dad'e ba Hamza ya sake auro Hajara y'ar garin Fachankan d'in ce itama, sai dai fa tunda Hajara ta shigo gidan A'i abubuwa suka sake chab'e mata, saboda Hajara munafuka ce ta gidan gaba, duk wani abu da tasan zata k'ara jefa tsanar A'i a zuciyar mazauna gidan tofa sai tayi, saboda ta tsane A'i tana mugun kishi da ita, ga bin Malamai da Bokaye, duk wasu kud'in Hajara da buga-bugar da take duk akan Bokaye suke k'arewa, tana zuwa gidan bata dad'e ba ta samu ciki, iya murna sunyi murna an nunama Hajara gata, inda aka k'ara taso A'i gaba da habaici, wani lokacin kwana take kuka. Haka ta raini cikinta ta d'ora ma wannan ciki buri taso ta sami d'a namiji, sai dai Allah baiyi ba, dan ko mace ce ta haifa, duk da haka taga gata kamar mi, amma ita ba haka ta so ba, hakan yasa ta k'ara shiga Malamai da Bokaye domin haihuwa ta gaba ta samu d'a namiji, sai dai haihuwar ce tayi mata dogon zango dan ko tunda ta haifi Asma'u, wacce suke ma lak'abi da Nana, haihuwar ta tsaya cak. A dai-dai wannan lokacin ne kuma Allah ya azurta A'i da samon ciki itama, wai wai karkuso kuga irin tashin hankalin da Hajara ta shiga a wannan lokacin, sosai Hajara ta shiga tashin hankali wadda fad'ar shi ma b'ata baki ne, sai ya kasance bata zama a gidan kullum tana kan hanyar zuwa wajan Boka da Malamai, akan duk yadda za'ai kar A'i ta haifi cikin dake jikinta, koda kowa A'in zata rasa ranta ne. Sosai ta kashe mak'udan kud'i dankar A'i ta haifi abinda ke cikinta, a wajan A'i sosai take ganin tashin hankali tunda samu cikin take yawan wasu mugayan mafarkai masu ban tsoro, ga cikin yazo mata da laulayi mai wahalar tsiya, gashi anyi mata ture da aljanu sosai suke firgita, danma tana yawan addu'a duk addu'ar ba wani iyawa tayi sosai ba, saboda garin basu damu da ilimin ba. A'i ta rame ta fige dan har an fara mata surutu Inna Suwaiba duk da haka bata kyale ta ba, kullum ita da Hajara suna jifanta da mugayan kalamai dan Inna Suwaiba har cewa take, "tunda A'i kika shigo gidan nan d'ana bai k'ara tara abun arzik'i ba, ke tunda ma kika samu cikin nan komai ya samo sai kin yamoshe mai, haba ciki sai kace wacce take rainon cikin aljanu". kullum idan Inna Suwaiba ta fad'i haka A'i sai dai ta shige d'aki taci kukan ta. Da zarar dare yayi kuma babu ita bayin bacci, ba k'aramar fargitata ake ba duk don cikin ya zube, sai dai Allah baiyi ba, cikin kuwa saima wani girma da yake ita kuma tana tsotsewa ta koma kamar mai ciwon K'anjamau, a inda Hajara ta k'ara fantsama wajan Bokayanta dan taci burin itafa kodai A'in ta mutu ko kuma abinda ke cikinta ya mutu. Sadda cikin A'i yakai watan haihuwa, a dai-dai wannan lokacin ne Hajara ta amso wani mugun asiri, tsaye take a d'akinta cikin talatainin dare, zindir take tsaye haihuwar uwarta tasa wani kasko a gabanta tana wasu irin surutai da wani irin yare, kaskon yana ci da wuta ga wani irin hayak'i dake fita ta cikin kaskon, hayak'in mai matuk'ar warin tsiya kamar na bori, wasu irin darussan tsafi take karantowa, kamin kace mi d'akin ya d'au wata irin girgiza da wasu irin koke-koke, wani irin hayak'i ne na dunk'ule waje d'aya, can Hajara ta ware idonta dayayi jawur kamar garwashin wuta, tana zare ido, kwata-kwata ba d'igon tsoro ko imani a ranta, ta bud'e baki ta ce. "ina so kar A'i ta haihu lafiya kodai ita ta mutu ko kuma abinda ke cikinta, danna rantse sai A'i ta bar min mijina ni d'aya". Tana gama maganar wannan hayak'in yabi k'ofar d'ankin Hajara ya fice kai tsaye d'akin A'i ya nufa, A'i dake kwance da k'aton cikinta bata dad'e da samun bacci ba dama hayak'in na gama shiga d'akin ya dunkule ya zama wata irin halitta mai ban tsoro, hannunsa yayi anfani dashi yayi tsayo kai tsaye goshin A'i ya nufa wani haske ya fito daga hannun aljanin nan ya shigi A'i. Dan da nan A'i ta farka a firgice, idonta ne yayi mata tozali da wannan mummunar halitta, ba shiri ta kulle idonta tana sakin wata irin gigitacciyar k'ara, cikinta ne yayi wata irin juyi tare da muguwar murd'awa kamar mararta zata rabe gida biyu, wata irin k'ara ta k'ara saki tana juye-juye, ga muguwar halitta dake kanta. Jin ihun A'i sai k'ara yawa yake yasa Hajara dake d'akinta tana jiran tsammani, ta rarami zaninta ta d'aura tana dariyar mugunta, cike da makirci ta fito tsakar gida, tana sakin salati tana cewa, "kuna ina mutanan gidan nan wai bakwa jin A'i ne kamar fa nak'udarta ta tashi?", da yake mijinsu Hamza baya nan sunje fatauci ne. Ba shiri ta k'ara matsawa kusa sa d'akin A'i dake ihun azaba har yanzu Inna Suwaiba ce ta fara fitowa tana sakin wani shegin tsaki tana cewa "wai nikam duk an cika mana gida da karaji haba" Hajara ce ta kalleta ta ce "wai fa kamar nak'uda take" "Sai kuma aka ce ta damu mutane da shegen ihu, ko ko mu haka muke yi idan haihuwar tazo mana ita bazata iya yin hakurin da mukayi ba, sai rakin tsiya, ko nufinta mu d'auke mata ciwon, sadda taje ta kwanta da mijin tana jin dad'i uban wani yasa ni" Inna Suwaiba ta idasa maganar tana kunfan baki. Inna Khande ce ta ce "shin zamu matsa mu taimaka mata ko ko tsayawa zamuyi maganar da bata da anfani ne?". Ba wadda ya sake magana gaba d'ayansu suka shige d'akin A'i, dake kwance ta galabaita sosai ga mummunar halittar dake tsaye tana firgitata duk da shigowar su Inna Suwaiba, hakan baisa Halittar nan b'acewa ba, ba wadda ke ganinta sai ita A'in da kuma wacce tayi sanadiyar shigowarta d'akin. Wani murmushin mugunta Hajara tayi tana matsawa jikin A'i sosai dai-dai kunnanta ta rad'a mata yadda ba wadda zaiji ta ce "hmm A'i kenan ke nufin zan barki ki haihu lafiya ne saura ki haifi namiji ki gaje komai ko mu?, ai inahh A'i dole yau sai kin bak'unci lahira wallahi". Wata irin zabura A'i tayi hawaye masu zafi na d'iga ta idonta tana bin Hajara da kallo, wani murmurshi ta sakar mata ta fara magana abun tausayi cewa take "innalillhi A'i ki daure kin kusa sauka ki daure kinji", Kallonta kawai A'i take bakinta ya kasa furta komai tsabar makirci ji yadda take nuna mata, abunda ke damunta d'aya abunda zata haifa ta bari a wannan murd'and'an gida, lallai duk abunda zata haifa ta bari ba k'aramar hawala zaisha ba, shi yasa ba shiri wasu hawayen suka sake zubo mata, suna bin kumatunta. Wata irin juyawa mararta ta sake yi wadda yasa tsabar azabar da take ji yasa ihun ma ta kasa sai dai jujjuya kai da take, ta damk'e janin dake jikinta da mugun k'arfi, sosai tasha wahala kamar zata mutu da abunda ke cikin nata sana Allah yasa ta sillab'o d'iya mace, kyakkyawar gaske su kansu Inna Suwaiba sun girgiza da ganin kwawun yarinyar kamar y'ar aljanu yarinyar, tunda ta fito duniya ko tari batai ba bare kuka, sai ido da take bin su dashi Hajara ita kanta ta girgiza dan har kusan sakin layin tayi, taso abunda ke cikin ne ya mutu amma jin shuru yayi yawa ta b'angaran A'i yasa suka kai dubansu gareta, ba shiri suka saki salati ganin babu alamar rai a tare ita, jikinta ya saki idonta na kallon sama fuskarta na fitar da wani annuri kamar tana murmushi, Hajara kuwa wani irin mashahurin farin ciki ne ya ziyarce ta, ganin cewa fa A'i rai yayi halinsa.............✍️✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 *EPISODE* 2 DA SUNAN ALLAHU MAI RAHMA MAI JIN K'AI Hajara ji tayi kamar ta saki shewa amma saita maze, tana sakin wani irin salati, tana fashewa da kukan k'arya, sosai fa hankalin su Inna Suwaiba ya tashi ganin A'i fa babu rai a jikinta. Jikinsu ne yayi mugun sanyi Inna Khande ce ta amshi yarinyar da har yanzu bata yi koda tari bane. Dan da nan Inna Khande ta had'a ruwan zafi ta wanke d'iyar tas, sai a lokacin tayi d'an kuka kad'an, ana gama mata wanka kuma bacci yayi awan gaba da ita. Inna Khanden ce dai ta goyata saboda mutane da suka fara cika gidan, har an fara ma yarinyar surutu ganin irin kyan da Allah ya zuba mata. A wajan Hajara ko sosai ta k'ara jin tsanar yarinyar da A'in ta haifa ganin irin baiwar da Allah ya zuba mata na kyau, da yadda taga mutane ke son daukarta yasa ta k'uduri aniyar saita sa kowa ya tsani yarinyar. A sadda mazan suka dawo ba k'aramar girgiza Hamza yayi ba, dan har yaso ya fita daga tunaninsa dan Allah ya sani yana bala'in son matarsa, kuma uwar gidan sa. Ganin haka yasa Hajara dake zaune kusa dashi ta banka mai hararara k'asa-k'asa, ganin yadda aka kawo mai yarinyar ya wani k'ak'k'ameta, yana kuka sai kace ba namiji ba, haushin su Inna Khande ta k'ara ji ganin yadda suke wani k'ara tausarsa, y'ar gwal ta mutu. Wani murmushin mugunta ta saki, cike da makirci, ta kai hannunta zata amshi d'iyar tana sakin kukan munafurci tana cewa, "Allah sarki A'i wallahi yarinyar nan har taban tausayi zan rik'e ta, zan kula da ita kamar ni na haife ta" Wani kallo su Inna Khande suka bi Hajara dashi can Hadiza ta banka mata harara a zuciyarta tana cewa "kaji makirar mata, wallahi wannan Hajarar y'ar san a sani ce" Can ta bud'e baki ta ce "a'a Hajara keda kike cewa baza ki iya rik'e d'an wani ba, ina kuma gana kishiyar ki..... Kamin ta idasa maganar Hajara ta tashi a zuciye tana nuna Hadiza da yatsa tana cewa, "Hadiza ki kiyayeni ni ba sa'ar yinki bace karki bari na juyo ta kanki, mi kike nufi ne ina za'a kai yarinyar to nufinki kasheta zanyi?", Cike jin haushin Hajarar dan kwata-kwata gidan ba wani cika shiri sukai da junansu ba kowa burin sa yafi d'an uwansa ko kuma ya ga d'an uwansa cikin iftila'in rayuwa, ta ce "yo Ohho miki waya sani ma", "Mi kike nufi wai Hadiza?" Cewar Hajara dake tsaye kanta kamar zata kai mata naushi a fuska. Hamza ne ya tashi cike da b'acin rai ya ce "shin zaku barni da abunda nake ji ne ko kowa halin naku zaku nuna a gaban mutane?, kuma yarinya dai tawa ce sai inda naga dama ta zauna, dan haka bana son irin haka", Shuru wajan yayi Hadiza taja Na'ima cike da jin haushin su gaba d'aya suka shige d'aki. Maryama ce ta tab'e baki tana jan Hajara gefe ta ce "wallahi karki yarda ki bari dangin A'i su amshi yarinyar nan dan ko idan kika bari hakan ta faru to tabbas wannan yarinyar sai ta zama abun kwatance" Dafe k'irji Hajara tayi tana cewa "ke Mmn Bishira, maganar kifa abar dubawa ce, tabbas naci alwashin a cikin gidan nan zata girma, bauta ce saita yi mana saita koma kamar jaka a cikin gidan nan" Tafawa sukai Maryama na cewa "da kyau ai nasan bakya wasa". Habiba ce ta jawo Maman nasu tana cewa "shin wai Mama miye ruwanki da shiga harkar adda Hajara ne?", "Ke nasan abunda nake yi kinji, wannan yarinyar da kuke gani kamar y'ar aljanu, kun fara tasowa a gidan nan duk wani aiki zai iya dawowa kanku, to ni kuma wallahi babu abunda ya isa ya takura muku, ita bakuga Hadiza yadda take nunawa ba, ita tsabar bak'in hali ne da hassadarta ta ta motsa, shi yasa ta amayar da abunda ke cikin ta tun yanzu, gara ta girma a cikin gidan nan ta zama jaka dan nasan wallahi ko sama da k'asa zasu had'e tofa Hajara bazata bari a matsa da ita ko ina ba", Haka ta gama masu karatun da kullum take yiwa yarin nata shi yasa suka raina kowa basa ganin mutumcin kowa. Da safe tunda aka kai A'i makwacinta na gaskiya yarinyar data haifa take kuka mai ban tausayi, kamar tasan mike faruwa, har sai da aka mik'ata wajan Kakanta Sani yayi mata tofi sana ta sarara da kukan, inda ana dawowa aka rad'a ma yarinyar sunan Mahaifiyarta wato Aysha, Hamza yayi mata lak'ani da Marmah. Babu wadda ya ce masa danmi ya maida sunan A'i dansu gansu muta nan sun ga abinda yayi dai-dai ne, koda a cikin gidan aka fad'i sunan yarinyar ba wadda ya tanka bare ayi cecekuce. Hajara ko tunda sanyin safiyar ranar ta fice ta tafi wani mugun K'auye dake kusa dasu wajan Bokanta. Wani irin daji ne mai duhun gaske tana tafiya ko d'igon tsoro babu a fuskata tana tafiya dajin na canzawa yana koma wani irin yadda kasan ba'a k'asar take tafiya kamar akan iska, ga wasu irin bishiyoyi masu ban tsoro, amma haka Hajara take k'ara danna kai cikin dokar dajin, har takai wata buka dake zagaye da wasu irin jajayan kyalle, ga wasu irin koke-koke dake tashi cikin dajin. Zubewa Hajara tayi tana d'ukawa kanta har k'asa, kamar tana sujjada, ta mik'a hannunta gaba, tana wasu irin surutai, da wani irin yare, marar dad'in sauraro, wasu darussan tsafi ta k'ara dagewa da fad'i, da k'arfi, wata irin mahaukaciyar guguwa ce ta tashi, ta turnuk'e wajan, da wata irin mahaukaciyar dariya wacce take fitowa a rarrabe, yadda dariyar ke fitowa da amsa kuwwa, sai yasa mutum sumewa bai shirya ba, amma Hajara ko a jikinta, tana nan a duk'en da take. Har sai taji wata murya mai kama da ta basamudan k'ato tana fitowa a rarrabe itafa da k'arfin gaske, har dajin na d'aukar maganar bishiyoyi na wata irin girgiza, tsabar k'atowar muryar dake tashi ana cewa. "Ke la'ananniyar Allah wannan kira haka na gaggawa, wata muguntarce ta taso kike son ganinmu" Da sauri Hajara ta tashi tana k'ara zubewa k'asa cike da girmamawa yadda kasan tana a gaban sarki ko shugaban k'asa, zata fara magana aka dakatar da ita da cewa, "Hhhhhhh basai kince komai ba indai akan yarinyar da aka haifa ne tabbas za'a baki ita kuma sai yadda kikayi da ita, sai dai ki sani yarinyar nada wata irin baiwa, dan mu kanmu mun kasa ganin wacce irin baiwa ce, idan muka ce zamu matsanta da yi mata mugunta to tabbas, abun zai shafe mu, amma burinki zai ciki na rik'e yarinyar a hannunki, sai dai sai kinyi taka tsantsan" Ana gama maganar Hajara ta nemi Bukar nan sama ko k'asa ta rasa guguwar nan ta b'ace babu ita. Hajara da ba haka taso ba, ta so ta fad'i abunda ke ranta amma Boka bai bata dama ba, kuma ta sani ba'a kiran Boka Sank'are sau biyu, dan k'a'ida ne dashi, sai dai ta sake dawowa a irin wannan ranar a wani watan dai-dai kuma kwanan watan yazo d'aya, haka k'a'idarsa take, yatsanta ta d'an ciza tayi kwafa, ta juya ta fara komawa, tana tunani a ranta. Koba komai ta cika burinta na bata Marmah a wajanta tabbas yarinyar saita gane shayi ruwa ne, indai, tana da rai Marmah bazata tab'a jin dad'i ba, tabbas yarinyar zata ga mugunta kala-kala, idan taji matsi ma ta mutu mana ina ruwan wani, ta tabbas Marmah kin shiga uku watan shiga K'angin rayuwarki ya kama. Hajara ta fad'a da k'arfi, zuciyarta cike da tsanar yarinyar, a yanzu duk wata tsanar A'i da kishinta da take ji yasa dawo kan Marmah...........✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 *EPISODE* 3 Tunda Hajara ta shiga cikin gidan nasu, ganin har yanzu mutane keta shiga da fita, yasa ta saki wani shegen tsaki. Dubanta ta kai gefe inda ta hangi mijinta Hamza da dangin A'i kamar suna cece kuce yasa ba shiri ta matsa kusa dasu cike da makirci ta tsoma musu baki. "Ko kuwa in banda abunku ina Marmah za'a rik'e ta taji dad'i inba gidan ubanta ba, saura nan gaba a rink'a mata gori", Adda Khareema ce yayar A'i wadda suke uba d'aya da A'in saboda ita A'i bata da Wa ko K'anwa ko Yaya, a d'akinsu ita d'aya ce sai ko wadda suke uba d'aya da juna Mahaifiyarta ta rasu tun tana budurwa. Ta ce "kee Hajara ki rufe ma mutane baki an sako ki a ciki ne?, makira al'gunguma, so kike abar miki Marmah ki azabtar da marainiyar Allah, waye bai san yadda A'i tasha wuya wajanki ba, sai yanzu kuma dan tsabar makirci zaki wani ce abar y'arta gidan nan naku mai kama da gidan Gandu" Ta idasa maganar tana hararar Hajara. Hajara dake tsaye tana jijjaga tsabar munafurcin dake cinta ta fashe da wani irin kuka tana cewa, "Yanzu Abban Asma'u kana ji wa'innan maganganun da Khareema ke gaya min mi yasa zanki rik'e jinin A'i mita tsare min, kuma Marmah ce dai babu yadda kuka iya saita girma a gidan nan duk yadda zakuyi kuyi" Kawu Baffa ne Yayan A'in yayi saurin tare lumfashin Kharima ganin tana niyar maida ma Hajara da magana dan yasan ko kwana za'ai ana zancan nan idan Hajara ta fad'i goma tofa sai Kharima ta maida mata da dubu. Ya ce "ya isa haka nan" Ya kai dubansa wajan Hamza dake tsaye ko ci kanku bai ce ba. Ya sake cewa "shin kai muke sauraro d'iyar nan dai taka ce idan ka yanke hukunci a kanta ya yanku babu wadda ya isa tursasa ka, shin zaka bamu yarinyar nan mu tafi da ita ko kuwa?, tunda dai Allah ya sani babu abunda zata nema ta rasa a wajanmu" Wani kallo Hajara dake bin Kawu Baffa dashi na raini tana sauraron mi Hamzan zai ce, ai koda zatayi yawo tsirara bazata tab'a bari su tafi da Marmah ba, bare ma sunyi kad'an suyi jayya da ita, yanzu kam tasan ko Hamza bai isa ya musa mata ba, tasan abunda ta taka. Hamza daya nisa yana kallonsu d'aya bayan d'aya can yayi maganar da Baffa ya girgiza da jinta yana cewa, "To Baffa mi kake nufi ne?, mu a wajan namu zata nemi wani abu ta rasa ne?, kuma a nan gidan nayi wayo a nan na girma dan haka itama a nan zatayi rayuwa na gama magana ta" Yana idasa fad'ar haka yayi ficewar shi waje yana mik'a Marmah a hannun Hajara, Marmah ko kuka ta saki jin yadda aka mik'ata da k'arfi harta firgita. Hajara data saki wani makirin murmushi tana matsawa kusa da Adda Kharima tana dubanta ta ce "ai duk wadda yaci tuwo dani miya yasha ni nan da kike gani kabaiwar kan kabari ce bak'in cikin mai taushe, ni d'uwawu ne dole a zauna dani" Murmushi Kharima ta saki tana matsawa kusa da ita ido cikin ido ta ce "hmm indai yarinya ce har abada anbar muku ita, baza muyi jayya daku ba, kuma Marmah ce dai Allah yana tare da ita, babu abinda kika isa kiyi mata face Allah ya rubutasa, a k'undun k'addararta, daga yanzu idan kinga wani cikin danginmu yazo wai da sunan a bashi Marmah ko miye zaki iya yi an bar muku d'iyarku, ko kuma na ce d'iyarsa" Wata shewa Hajara ta saki kamar ba gidan mutuwa ba, da yawan y'an gidan sun saki baki suna kallon ikon Allah masu murna nayi masu jin haushin Hajara nayi. Ta sake cewa "yo kunma isa kuyi jayya da mai abu da abunsa, ai kunyi kad'an k'ana nan kwari". Girgiza kai Kawu Baffa yayi yana jan Kharima gaba yana kallon Marmah dake kallon sama tana tsotsar hannu baiwar Allah, yana matuk'ar tausayin yarinyar, akwai babban K'angin rayuwa da zata shiga nan gaba, koma ya ce a yanzu zata fara gani, zama a wajan matar uba wacce koda uwarta nada rai ba raga mata take ba, bare yanzu da ba idon Mahaifiyarta, ai sai abunda Allah yayi, yana mata addu'ar kariya daga Ubangiji. Bayan fitar su Kharima Sa'ade dake tsaye cikin matan gidan ta tab'e baki ta ce "ni ko Hajara banga anfanin amsar wannan yarinya da kika dage sai kinyi ba, dan nasan tabbas babu abunda zaki iyayi mata sai tsabar mugunta da makirci da kike shirin aiwatarwa, da kinbar yarinya taje inda za'a kula da ita, am.... Cike da jin haushin ta Hajara ta fara mai da mata magana tana cewa, "Kinga Malama babu ruwanki a ciki, da kike maganar bazan iya kula da ita ba, ai naga ke kin kula da d'an naki, kin kasa basa tarbiyar data dace yaro ya fitsare ya gagari uban kowa, ke har kina da bakin magana wajan cewa ba'a iya ba yara tarbiyar ba" Zage-zage suka farayi suna faman tunama junan asiri. Su Inna Suwaiba sunyi-sunyi amma yadda kasan k'ara tura su sukeyi kamar zasuyi danbe da juna. Hamisu ne ya shigo gidan a buge yasha yayi mak'is yana tangad'i, ganin abunda ke faruwa yasa ya matsa zai d'auke Hajara da mari ba shiri Hajara tayi kukan kura ta hankad'e shi, tana ba Inna Khande Marmah dake hannunta tana nuna Hamisu da yatsa. Ta ce "wallahi kul d'inki ahir d'inki nafi k'arfin kasa k'azamin hannunka ka tab'a lafiyar jikina, banyi sanadiyar nakasa rayuwarka ba, yaron banza kawai wadda uwarsa ta kasa basa tarbiyar data dace" Wata irin hargowa Sa'ade ta saki tana kunfan baki wajan cewa "eh ban basa tarbiyar ba, ai ke naga kinba yarinyar taki tarbiyar, Asma'u, waye take ganin mutumcinsa a gida nan, idan kika d'ora mata talla dan da nan take kawo miki ciniki, idan yarinya ba iskanci take da mazan banza a waje ba, ubanmi take da zata rink'a kawo miki kud'i haka, saboda tsabar son kud'inki, kike amshewa ki lamushe, garani na godewa Allah namiji ne dani, koda yayi iskancin nasa ado yayi kefa duk randa ta kwaso miki abu..... Maganar Sa'ade ce ta mak'ale jin saukar mari a kumatunta. D'ago kanta tayi tana duban Hajara dake ihuce gaf da ita ta zafga mata mari ko a jikinta, tana nunata da yatsa ta ce "insha Allahu abun kunya da kike min fata a kanki zai k'are nafi k'arfin ki wallahi, Sa'ade ki bini a hankali idan ba to tabbas zakiga mi zan miki" Hamisu daya taso a zuciye shima yana shirin sake kaima Hajara mari yaji an rik'e hannunsa, ana d'auke sa da wani mari tasssss tassss kake jinsa. Ba shiri mutanan gidan suka kai dubansu ga wadda yayi wannan mari ganin Hamza dake tsaye rik'e da hannun Hamisu ya nuna sa ya ce "kaiiii rashin mutumcin naka har ya kai haka rashin kunyar taka akan matata zaka sauke ta, kaje kayo shaye-shayen banzarka zako zo ka tada ma mutane hankali, to tabbas ka kusa daina shigowa cikin gidan nan". Wani bak'in ciki ne ya hana Sa'ade tankawa sai bin Hajara take da kallo da Hamza. Can suka tsinkayi muryar Iron yana cewa "kamar ya Hamza mi kake nufi ne?, na cewa Hamisu ya daina shigowa gidan nan, ai bata yiwuwa yadda kake da gado a cikin gidan nan shima haka yake da shi, dan haka bana son maganar banza" Hamza zai sake magana suka ji gyaran muryar Mahaifinsu wadda suke kira da Malam yana kallonsu cike da takaicin abunda ke yawan faruwa da ahalin gidan a yanzu, tunda mata sukai ma gidan yawa munafurci ya sake k'aruwa. Cike da kakkausar muryar ya ce "saboda matanku da yaranku kuke shirin yin fad'a da sa'insa, matanku suna so su raba kawunan ku, wannan ai rashin tunani ne, daga yau bana son na sake jin irin haka, bana son ganin kowa a nan bare naji tashin wata maganar, anyi mutuwa ma bazata zama izina a gareku ba?, dan haka gaba d'ayanku ku b'ace min da gani, karna sake jin tashin maganar wani, idan ba haka ba, ran mutum zaiyi mummunan b'aci". Yana gama maganar ya juya ya shige turakarsa cike da damuwa a ransa, yasan tabbas baza su tab'a dainawa ba, koda yayi gargad'i kuma yasan ba laifin yaransa bane laifin matansu ne, duk su ke had'a wannan husumar. Kowa na tsakar gidan watsewa yayi suna nufar d'akonansu wasu na jin haushin Mlm daya katse musu kallon fad'a wasu na dariyar mugunta. A wajan Kawu Sule bai tashi jin mutuwar matar d'an uwansa ba sai washe garin da akai mutuwar Mlm yasa Abubakar kiransa ya shaida masa, sosai fa mutuwar ta shigesa inda ya ce insha Allahu gobe goben nan suna nan tahowa tare da iyalansa. Bilkisu dake zaune akan wata kujera mai kyan gaske tasha gayu ga y'an aiki dake ta mafan hidima dasu, da yaranta dake zaune wadda basu wace shekara shidda ko biyar ba, Khairat da Ifteesan. Fuskarta da walwala amma jin yana waya da dinginsa na K'auye, har take jin wai gobe yake shirin su tafi yasa fuskarta ta canza. Yana aje wayar ya juyo wajan Bilki dake kallonsa ya ce "kinji mutuwa akai mana matar d'an uwana Hamza ce ta raso uwar gidansa, dan haka ku shiri gobe gaba d'ayanmu nake so muje zamu kwana biyu a can" Wata irin zabura Bilki tayi tana cewa "Allah ya jik'an musulmi, amma maganar muje mu kwana Daddyn Khairat ai nake ganin bata taso ba, tunda kaga yara suna zuwa school nake...... Dakatar da ita yayi da hannunsa, ba tun yau ba ya fuskanci Matar tasa bata son y'an uwansa bata son tushansa a inda ya taso. Ya ce "babu ruwa na da school d'insu gaisuwa ce saifa sunje kinji na gaya miki" Tashi ta k'ara yi a kansa tana cewa "haba Daddyn Khairat ya zaka ce haka yaran nanfa basu saba kwanan K'auye ba, mi zai hana mu dawo ranar, ko abincin can baza su iya ci ba wallahi bare mutanan can da basu saba dasu ba". Ran Daddy idan yayi duba ya b'ace tashi yayi shima yana cewa "lallai Bilki kinban mamaki, ni ba'a can na taso ba?, ko kowa ni na rasa raina da nayi rayuwa a can, can d'in da kika raina kika tusama yaranki tsanar y'an K'auye, karki manta nima d'an K'auyen ne, mi yasa baki gaya masu uban nasu wadda suke tak'ama dashi shima d'an can bane?, Bilki na riga na yanke hukunci saifa sunje, kinma sa na k'ara kwanaki akan wadda nayi niyar muyi, wallahi sai munyi sati d'aya kinji na rantse kuwa". Yana idasa maganar ya haura sama yana jan dogon tsaki yana ayyana wani abu a ransa tabbas sai yayi maganin Bilki. Su Ifteesan da tun d'azo suka bar parlon suka koma Babbn parlon gidan, dan k'a'idar gidan ce haka indai iyayan nasu na magana basu isa tsaya masu a kai ba, sunma sani dasun fara, ko basu ce su fita su basu waje ba, sun sani zasu fice. Y'an aikin dake aiki a parlon Asabe da Tala sukai saurin barin parlon, dankar ta dawo kansu, suna addu'ar yasa ma ya ce sai sunyi fin sati d'ayan ma, suna matukar hakuri zaman gidan domin kuwa Bilki ta sani duk wani Talaka ko d'an K'auye, shi yasa suka shige suna murmushin abunda Daddyn yayi mata, yayi dai-dai wallahi. Su Ifteesan ne Suka k'araso kusa da uwar tasu suna faman tab'e baki saboda sunji Daddynsu na cewa sai sunje K'auye. Ifteesan ce ta ce "Mami wai da gaske Daddy yake K'auye zamu wai?, nidai gaskiya bana son zuwa K'auye", Ta idasa maganar tana tab'e baki kamar zata fashe da kuka. Da sauri Mami ta ce "kuyi hakuri ai ba dad'ewa zamuyi ba, kuma koda munje da abunda zamu ce zan tafar mana dashi, kuma babu ruwanku da duk wadda kuka gani, zan d'au mataki a kansu ne gaba d'aya dangin nasa, sunga shine mai abun duniya abu kad'an an bugo mai ana neman maula y'an wahala kawai..............✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 *EPISODE* 4 Mami ta idasa maganar tana sakin wani shegen tsaki, ta juya tana kwad'ama Tala kira. Da rawar jiki Tala tazo tana zubewa k'asa ta ce "Hajiya gani", Sai da ta d'au mintina kamin ta ce "ina so kiyi mana kayan ciye-ciye please a soya mana harda kaji ayi mana miya ta soyu sosai, zamuyi tafiya ne, kin gane mi nake nufi?" Da sauri Tala ta k'ara sadda kanta k'asa ta ce "eh Hajiya na fahimta insha Allahu yanzu za'a fara ma" "Zaki iya tafiya" Tashi Tala tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta nufi kitchen dan da nan suka fara aikin data sasu ita da Asabe. A parlo Mami dake zaune duk zuciyarta babu dad'i, ta nisa cikin tunani, ringing d'in wayarta ne ya fargar da ita, Ifteesan ce ta mik'o mata wayar tana cewa, "Lahh Mami Ya Khaleefa ne" A yadda yaran suka shiga hankalin su suka nutsu dan da nan kamar Ya Khaleefan ne zai fito daga cikin wayar, sunyi shuru sun natsu. Mami data yi picking d'in wayar tana kaiwa a k'unanta ta ce "Khaleefa ya karatun fatan dai kana lafiya?, wai yaushe ne ake muku hutu ne?, munyi kewarka gaskiya, ya kamata kad'au hutu ka dawo" Daga cikin wayar wata sansanyar murya mai cike da kamala da zaki ya ce "Mami nima ina miss d'inku ai, ina yaran nan?, sun daina rashin ji ko?, I hope dai kuna lafiya?, Mima naji Daddy ya ce zakuyi tafiya ne, naso ina nan ina son yanayin garin su Daddy wallahi", Sakin baki Mami tayi tana sake cewa "wai mina ji kana cewa ne?, wannan banzan garin kake so?" "Haba Mami wane irin banzan gari kuma garin su Daddy ne fa" "Kai da'aAllah rufe min baki ni na rasa wane irin hali ne da kai nikam sai kace ba wadda ya fito daga cikina ba, wannan garin kake cewa kana wani so, ai garama da baka nan, haka kawai in kwashe yaran nawa mu nufi wannan gari dasu, aje a lashe min ku, kaga ka daina min irin haka kaji na gaya ma" Shuru Khaleefa yayi yana lumshe idonsa cike da miskilancinsa da rashin son hayaniya cikin call voice nasa mai sanyin dad'i ya ce, "Shikenan Mami am sorry Allah ya kaiku lafiya" Wani tsaki ta saki tana cewa "nifa kaga My son ba'a san raina zamu ba, wallahi da nasan yadda zanyi wallahi saina ruguza tafiyar nan" "Tohm Mami kayi hakuri mana ai ba wani dad'ewa zakuyi ba, yanzu dai bani su Ifteesan zanyi magana dasu" Tashi Mami tayi tana mik'a ma masu wayar tayi cikin Bedroom tana faman mita, bama ta lura da halin dasu Khairat d'in suka shiga, cike da tsoro sukasa wayar a amsa kuwwa. Can cikin wayar Ya Khaleefa ya fara magana ba wasa. "Kunsan Allah kuka sake kuka je garin nan kuna nuna wannan halin naku na rashin son mutane, zan sani ne kuma kunsan mi zan muku" Jin sunyi shuru yasa Ya Khaleefa a harzuk'e ya sake cewa "wai bakuji mi nake fad'a bane?", Har suna rige-rigen cewa "eh ehh Ya Khaleefa munji bazama muyi ba" "Good kun cece kanku" Yana fad'in haka ya tsinke kiran. Wata irin ajiyar zuciya sukai suna aje wayar a hankali yadda kasan wayar ce Ya Khaleefan. Khairat ce ta furzar da wata iska tana k'ara sauke ajiyar zuciya ta ce "na rantse Ya Khaleefa d'an rigima ne, karkiji yadda zuciyata ke harbawa, ita kuma Mami harda cewa wani munyi kewarshi, nidai wallahi bana so ya dawo, kwata-kwata komi kayi shi a wajansa kayi laifi" Ifteesan ta amshe da cewa "hmm ai ni abinda yake ban tsoro ma a tare dashi idan ya fad'i magana koda baki ji ba, tofa kin kad'ai dan bazai maimaita miki ita ba, sai ya mula ya munmule tukun, gashi Mami tasa shi ya kusa dawowa" Ifteesan ta kwab'e baki duk jikinsu yayi sanyi, ga zuwa K'auye da aka tilas tasu zuwa gobe. HAJARA POV Shigewa d'akinta tayi da Marmah a hannunta tana zuwa ta dungure ta waje guda, yarinyar ta saki kuka domin yinwa take ji, kallonta Hajara tayi cike da tsana tasa d'an yatsa ta dungure mata kai, tana cewa "kee jarababbiya kin ishemu da kuka, Allah ji nake kamar na shak'eki ki mutu kibi uwarki kowa ma ya huta, shegiyar yariya da kyau kamar y'ar aljanu" Ta idasa maganar tana sakin tsaki tashi tayi tana harkar gabanta duk kukan da Marmah keyi hakan baisa ta aje abunda take yiba, baiwar Allah tun tana kukan har wani wahalallan bacci ya d'auke ta, jin shuru Hajara ta saki tsaki tana k'ara cewa "da karda ma kiyi shurun ko mutuwa zakiyi da yinwa sai ubanki ya kawo abinda za'a baki, nidai ba nono zan baki ba, a'ato". Bishira ce ta fito daga d'akinsu ita da y'ar uwarta Habiba ance wata shegiyar kwalliya za'a fice talla, daga yin mutuwa amma su ko a jikinsu daga su har uwarsu, Maryama dake masu kirari tana kod'asu har suka shiga zaurar gidan suna faman washe baki. Hamisu ne ya taho bai lura dasu ba kawai yaji an bangaje, tsayawa yayi yana nuna Bishira da yatsa cike da jin haushin yaran ya ce "keee dabbar ina ce bakya gani ne?, kuna tafiya sai kace mahaukata", Wata uwar hararara Habiba ta banka mai tana murgud'a mai baki, Bishira dake mai wani kallo na raini ta rik'e k'ugu ta ce "to sannu mai hankali kai akwai ma wadda ya kaika rashin hankali, ai cikin mahaukatan garin nan kaine lanba d'aya, mai shaye-shaye har an gaya mai rashin hankali". Batai aune ba ya matso kusa da ita yana d'auke ta da wani kyakkyawan mari tasssss tassss, wata irin mahaukaciyar chafka ta mai ta chakumo wuyan rigarsa, itama kamin ya sauke hannun nasa itama ta wanke shi da nata marin, tana sakin shi ta hankad'eshi gefe, kamar wani kayan wanki. Wata shewa Habiba ta saki tana cewa "kai amma y'ar uwata na rantse kinmin dai-dai, shashasha kawai marar hankali", Tasowa yayi a zuciye yana nuna kanshi da cewa "kaiii ni ne marar hankalin?". Wata shewar suka sake saki suna cewa a tare "yo kaine mana akwai wani ne dake tsaye a nan bayan kai?, hankalin ne da kai?, ai kowa yasan mai shaye-shaye da neman mata basu cika hankali ba, ni wallahi kama cucuni dana had'a jiki da kai Allah ya isa na kuma wallahi bari ma ka gani". Bishara ce ta idasa maganar ta k'arshe tana sakin wani uban kuka tayi cikin gidan nasu da gudu, tana kururuwa, yadda kasan ana yankan naman jikinta. Dukansu mutanan gidan ba shiri suka fito, Maryama ko har tuntub'e take wajan fitowa, tana tayi saurin isa kusa da Bishira tana jijjaga tana dudduba jikinta sai faman tabbayarta take miye ya same ta. Habiba dake shigowa tare da Hamisu daya saki baki yaga wane irin shirri, Bishira ke son k'ulla mai. Itama Habiba kukan munafurci ta saki tana nuna Hamisu. Ba shiri Maryama ta matso kusa da Hamisu taci kwalar rigarsa tana cewa "to tanbad'and'e ubanmi kayiwa yara na?, na rantse da sarkin dake busan lumfashi zan sharara maka mari idan baka gaya min abunda kayi musu ba, haka nan dai baza su shigo gidan nan a haka ba, zaka yi magana ko kowa d'an iskan yaro kawai" Sa'ade ce tazo ta bangaje Maryama tana cewa "keee Malama dagata na ce abun ya isa haka, ban haifi d'an iska ba, na gaji da irin abubuwan da ake ma yaro na a cikin gidan nan gaskiya, mi yasa ba zaki iya tabbayar yaran naki ba sai shi?". Hajara dake tsaye ta rik'e k'ugu tana murmushin jin dad'i tana so taga ya za'a k'are. Bishira ce ta k'ara sakin kuka tana cewa "Mama wallahi Hamisu d'an iska ne, munzo fa fita zaure shine na d'an bigeshi ban gani ba, na basa hakuri, amma kawai ya mare ni yana rungume ni yasa hannunsa cikin rigata yana matsa min nono Na........ "Innalillhi", Gaba d'aya suka d'auka da cewa. Wani kukan kura Maryama tayi tana zanfga ma Hamisu wani gigitaccan mari, ba shiri yayi baya-baya zai fad'i, da mugun sauri Sa'ade ta taro shi, tana taroshi ta matsa kusa da Habiba itama tana zafga mata mari tasssss tassss kake ji...........✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *EPISODE* 5 "Kutumar uba, keee shine kika mareta?" Cewar Maryama dake rungume da yaran nata sai kuka suke kamar wasu yaran goye. Sa'ade dake tsaye kansu ta ce, "An mareta d'in ko zaki d'au mataki ne?, ashe babu dad'i, ni da kika mari nawa d'an" Tana gama fad'ar haka taja Hamisu cikin d'aki tana mai mitar ya daina shiga shirgin wannan gidan. Watsewa akai sai Hajara dake tsaye ta saki wani tsaki "mtswwww aikin banza kawai, kai amma fa, Maryama kin ban mamaki, harki tsaya waccan kucakar matar ta mari Habiba, ai wallahi da ni aka tab'o da tawa d'iyar, yau da ansha kallo hmm" Ta idasa maganar tana yin kwafa tayi shige cikin d'akinta. Inna Khande dake tsaye har yanzu ta matsa bakin murhu domin d'ora sanwa, dan Daddy yayi mata waya suna tafe, shi yasa bata cika shiga dama harkar gidan ba, su Inna Suwaiba ko danba da nasu ake ba shi yasa sai dai suka tsaya kallo, dan basu cika shiga harkar jikokin nasu ba. Da yawan mutanan gidan jin labarin Daddy na hanya yasa kowa fitowa suka fara taya Inna Khande aiki, sai nan nan ake da ita, kallonsu kawai Inna Khande keyi tana murmushi, dan tasan da biyu suke mata wannan abun, saboda sunsan mudin Daddy yazo garin kowa sai bashi kud'i masu yawa, su k'ara jan jari, bata tab'a hanasa ba, ita kawai idan aka zagi yaranta ne ko aka tab'a su, nanne fa zakuyi bata kashi da ita. A wajan Marmah baiwar Allah da kyar Hamza ya sayo mata madara saboda Kwata-kwata an kauda hankalinsa daga gareta, madarar ma da aka kawo sai da Hajara ta fara ba Nana d'iyarta tasha ta more tukun sauran data rage, ta d'akko Marmah dake tsutsar hannu, ta dungura mata madarar, tana bata tana faman zaginta, ji take kamar tasa mata guba taci ta mutu kowa ma ya huta, yadda kasan ta rik'e garwashin wuta haka take ji. A sadda su Mami suka iso suka shiga cikin gidan, Mami da yaranta ba abinda suke sai yatsine baki suna tafiya a hankali cikin gidan suna bin mutanan gidan da wani d'an iskan kallo, suma kansu mutanan gidan duk d'okin zuwansu sai suka sha jinin jikinsu, kai tsaye d'akin Inna Khande suka sauka ba laifi d'akin Inna Khanden an gyara shi sosai har ban d'aki anyi mata cikin d'akin nata, kuma duk aikin Daddy ne, babu abinda baya ma uwarshi, duk wani kayan more rayuwa yasa mata a d'akin, shi yasa koda su Mami suka shiga d'akin sai suka saki jikinsu sunata labari da Kakarsu, Mami ko sai danna wayarta take, mutanan gidan sai shigowa suke suna gaida ita, da kyar take amsa gaisuwar, harta gaji da amsawa sai dai ta d'aga kai kawai tana yatsina. Hajara ko tana fitowa ta saki wani shegen tsaki tana mita a fili tana cewa "Kaji y'ar iskar mata sai wani d'agin kai take, tana ma mutane iskanci, kai jama'a dama fa mutanan birnin nan basu cika mutumci ba, aka ce, ai ko na shaida wajan matar Sule" Hadiza dake zaune akan dakalin d'akinta ta amshe da cewa "hmm Hajara kema kya fad'a, kuma da take wannan d'agin kan mijin nata dai shima d'an K'auyen ne, baki ga yaran Sulen ma ko kallo basu ishi mutane ba, suma an koya musu wulak'anci da tsirfa da iyayin tsiya" "Sayi ma wadda ya shiga harkar su ai, dan wallahi nikam bana d'aukar wulak'anci a'ato, harsu gama kwanakinsu basai in ta k'ara gani na bama, shegiyar mata ita ba kyau ba sai wani faman tab'e baki take, tana cika tana batsewa", Cewar Hajara dake tsaye ta rik'e k'ugu, sosai fa abunda Mami tayi musu bai mata dad'i ba. Hadiza ko dariya ta saki tana cewa "kai Hajara karfa ajiki a'ato, dan kinsan gidan nan saboda abun duniya ai ake mata wannan biyayyar, da ace bata dashi ko mijin nata baida shi, ai ko kallon su baza'ayi ba". "Yo dama waze kalle su Hadiza?, ai dan abin duniya yanzu ake abu, anayin abu ne dan son a sani, ni da nice a matsayin Mamin na rantse miki k'ila sai nayi abunda yafi nata ma, ko ina d'ayan yaron nan nata mai shegen miskilancin tsiya?, da shegen kyau kamar aljani shima kamar ba cikin tsatsun nan ya fito ba, Allah yadda kasan bature wannan yaro" Hajara ta idasa maganar tana ayyana ina ma Ya Khaleefa ya kasance siriki a gareta dan dukansu mutanan gidan sunsan waye Ya Khaleefa, yana matuk'ar birgesu, sosai ba kad'an ba, shi yasa indai zaizo K'auyen da yawan y'an matan garin ke tururuwa zuwa kallonsa, shi kuma gashi baya son hayaniya, sai dai ya shige cikin mota yana faman tsaki. Itama kanta Hadiza shuru tayi tana hasaso abinda Hajara take tunani itama tana ma d'iyarta fatan samun miji kamar Ya Khaleefan. Da safiyar ranar su Mami suka je suka gaida Mlm, sai jan yaran yake a jiki. Da kyar da kyar dai suka idasa sati d'ayan suka wuce Kano inda Daddy ya cika mutanan gidan da alkhairin daya saba, musu, suna ta murna, inda sosai yaso ya amshi Marmah amma fufur Hamza ya k'i, inda Mami ma ta bigi k'irji tana mai surutu, danmi ma zai ce ya wani d'auki yarinyar mutane, wai ruk'o, itafa bata jin zata iya rik'e d'an wani, ba nata ba, kawai dai yarinyar ta bata d'an tausayi kad'an, kamin Daddy ya fara cewa wai zai d'auketa, yana furta haka taji ta tsani yarinyar, dan idan akwai wa'inda ta tsana to dangin mijin nata ne, bata so su rab'eta ko kad'an, bare susan wane hali suke ciki, daga yaranta sai danginta, Daddy ko kallonta kawai yake cike da takaicinta, yayi alk'awarin koba yanzu ba, saifa ya d'auke Marmah koda ta fara girma ne sai dai Mamin tayi duk yadda zatayi...................✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 6 A kwana a tashi har shekaru Goma sha uku sun waci inda a wannan shekaru abubuwa, da yawa sun faru, sosai Marmah ta fuskanci kalubale daban daban a wannan shekaru, tunda ta fara tasawa tana da jikin girma idan ka ganta saika rantse tayi shekara goma sha tara ko sha takwas ne, amma shekaru sha uku ne da ita, jikinta ya k'ara murjewa ga uban Hips dake gareta ga cikakkun nonuwa wadda suka cika k'irjinta, tubarkalla, kota ina Marmah ta zama cikakkiyar budurwa, ga tsananin kyanta dake k'ara fituwa, danma wahalar da take ciki tana b'oye wani kyan nata. Tana shan wahala wajan Hajara dan ko, waje d'aya suke kwana da Narnah, zata malala fisarin kwance tun suna shekara uku zuwa hud'u, mai yawa har ya tab'a Marmah da safe idan Hajara ta gani saita kama Marmah da uban bugu, har sai taga bata iya d'aga hannunta, tana zaginta tana kwashe mata albarka tana cewa ai ita ce tayi fitsarin, duk sanyi duk zafi aka zata wanke kayan fitsarin tana kuka. Duk wasu ayyukan gidan sai dawo kanta, da Inna Suwaiba ta fara tausaya mata, tunda Hajara ta fuskanci haka, ta fantsama wajan Bokanta, ya rufe ma Inna Suwaiba baki kwata-kwata bamai tausayin Marmah, an shafa mata bak'in jini, gata tunda ta taso ta fuskanci Mahaifiyarta bata a raye dan kuwa Hajara saita kira sunan A'i sana ta dark'ara mata zagi, shi yasa tun tana goye ta fuskanci Hajara ba ita ce ta haife ta ba, duk gidan a waje d'aya ne take jin dad'i wajan Kakanta. Tsaye Marmah take a bakin turmi tana wani uban surfe na masara da za'ai tuwon dare da ita, kusan tiya uku, tsayawa tayi da dakan, tana rik'e k'ugunta, duk'ewa tayi tana dafe k'irjinta yadda taji yana mata ciwo kamar zai rabe gida biyu, daka kalleta danma tana da tsawon k'afa girman jiki, dan ko girman jikinta yafi k'arfin shekarunta. Batai aune ba taji maganar Hajara kanta tana cewa, "Kee tsayawar uban mi kike?", Da masifar tsoro da bugawar zuciya ta mik'e tana cewa "a'a Umma bana jin dad'i ne shi yasa na d'an tsaya na huta", Wata muguwar hararara Hajara ta makama Marmah kamin ta ce "to makira kin wani langwab'e, wai baki jin dad'i, to ubanwa kejin dad'i nufinki?, to aiki ne dai ke jiranki ga wanke-wanken gidan nan can na jiranki, idan kin gama kuma ki maza-maza ki d'ora min sanwa idan ba haka ba kuma jikinki ne zai gaya miki", Wasu irin hawaye ne suka shiga zuboma Marmah akan kyakkyawar fuskarta, tana duk'awa har k'asa kusa da Hajara ta kama k'afafunta tana cewa, "Dan Allah Umma kiyi hakuri wallahi bazan iya d'ora k'atuwar tukwainyar can ba, shi yasa k'irjina ke ciwo saboda d'aukarta da nakeyi", Wata shegiyar hanb'ara tayi mata da k'afarta, Marmah har saida ta wuntsila ta kifa a k'asa, Hajara ta d'an duka inda Marmah take yashe a k'asa tana hawaye, tana cewa "to bari kaji na rantse koda k'irjin naki zai rabe gida biyu sai kinyi sanwar nan, makira al'gunguma harda wani kukan munafurci, da'aAllah tashi ki kama abinda ke gabanki ko kija ma kanki mugun duka yanzun nan wallahi", Da sauri Marmah ta tashi tana goge hawayen dake sintiri akan kumatunta ta fara dakan cike da k'arfin hali, ga gadda-gaddan y'an mata a cikin gidan, babu abinda suke sai zaman banza, da yawan banza, wadda sun girme ta nesa ba kusa ba, amma baza a iya sasu aiki ba sai ita. Cike da k'arfin hali take aikin harta gama surfen ta d'ora ruwan tuwon, ta d'au masarar ta nufi wajan nik'a. Tana tafe tana faman tunanin rayuwar da take yi ace Babanta bai damu da damuwarta ba, sai dai ta y'ar uwarta, komai ya samu ko ya sayo to na y'ar uwarta ne, tunda ta taso da kyar yasa ta a makaranta itama wani lokacin da kyar Hajara ke barinta zuwa ita kad'ai dama ke zuwa, y'an matan gidan nasu dama tuni sun daina zuwa suna idasa furamari karatun naso ya katse, sai yawan tallah da suke yi da tsayawa da samari, ko wacce aure take so, dan har ana shirye-shiryen auran da wasu. Batai aune ba taji muryar Abbas saurayinta mai k'aunarta tun tana y'ar mitsitsiyarta d'an Sarkin garin ne Abbas shi kad'ai ne a gidansu ana ji dashi dan har birni aka fidda shi yayi karatunsa mai tsawo, da yawan y'an matan garin suna mugun sonsa, suna burin ace sun aure shi, amma ita Marmah Allah yayi mata farin jini ko a makarantar boka ko Islamiya, saboda Marmah tana mugun kok'ari, da anyi abu ta hadda ce kenan tun tana shekara uku ta sauke Al'qur'ani mai girma, duk fad'in garin kusan ita ce kad'ai ta tab'a dagewa harta tayi karatun addini mai zurfi, ba irin wahalar da bata sha ba, dan Kakanta Sani ya tsaya mata dan yana mugun tausayinta, wani lokacin idan ya shigo cikin gidan yaga an tsareta da uban aiki, dan kar taje makaranta, shike rufe mutanan gidan da fad'a ya tasata gaba har Islamiya, tana jin dad'in haka, shi yasa take bala'in son Kakanta. Inda Hajara ke mugun jin haushinsa tayi-tayi Bokanta yayi maganinsa amma uban ya gagara, domin ko Mlm yana da ruk'o da addu'a, shi yasa ta kasa galaba a kanshi. Abbas daya tsaya a kanta yasa hannunsa yana ja mata hanci, da sauri ta dawo hayyacin ta d'an matsawa gefe tana jefa mai murmushin nan nata mai kashe mai zuciya da ruhi, dariya yayi yana sa hannunsa ya amshi buhun dake kanta dake d'auke da masara. Ya ce "kaii bakya jin nauyin masarar nan, ai ta miki nauyi, ina sauran y'an gidan naku da baza'a aike su ba sai ke?" "Hmm Ya Abbas kenan, kana yawan maimaita min irin haka kuma kasan ai dai ba aiken nasu ake ba saini ya kamata ka rik'e hakan a ranka" "Kinsan Allah na k'agara na aureki ko na d'auke ki daga gidan nan naku, kina ban tausayi wallahi" Dariya Marmah tayi ta ce "kaii Ya Abbas duka nawa nake?, duka fa shekara ta sha uku fa ai ban isa aure ba, kuma kaga ina da burin yin karatu mai zurfi, ko zaka barni nayi karatun?", Dariya ya saki shima yana cewa "eh man zan barki mana, ai tunda nayi karatu kema sai kinyi insha Allahu, kuma da kike cewa baki isa aure ba a hakan?, hmm idan aka kawoki gidana zan nuna miki kin isa ai" Dariya ta sake saki tana sa tafin hannunta ta rufe fuskarta. Haka suna tafiya suna raha har sukaje inda ake nik'an sukayo suka dawo, a hanyar su ta dawowa ne, Narnah ta dawo daga tallar shinkafa da take yi a bakin tasha dake garin, kamar ance Marmah ta juya taga Narnah a k'ofar gidansu tana kallonsu tana girgiza kai, cike da bak'in ciki a ranta tasa d'an yatsa a bakinta tana cizawa, cike da tsananin kishin Marmah a ranta, dan Allah ya gani batun yau ba ba tun yanzu ba Narnah ke nuna tana son Abbas, kai bama shi kad'ai ba duk wadda zai nuna yana son Marmah itama saita ce tana sonsa, Marmah tasha barma Narnah abu koda tana so, idan ma bata barmata ba, koda tsiya koda arzik'i sai Hajara ta rabata da abun. Gaban Marmah ne yayi wata irin mahaukaciyar bugawa, har sai da ta dafe k'irjinta. Ganin Narnah ta k'araso kusa dasu tana jefama da Marmah wani d'an iskan kallo, ta nunata da yatsa tana cewa, "Algunguma, dama abunda kikeyi kenan idan an aike ki, kina yawo da samari suna lallatse ki, to na rantse da sarkin dake busan lumfashi, yau sai kin gane shiyi ma ruwa ne, y'ar iskar yarinya kawai...... Kamin ta idasa rufe baki, taji an d'auke ta da wani gigitaccan mari, da wani irin sauri Marmah ta d'ago tana duban Abbas dake huci, jikinta ne ya kama kyarma cike da tsananin tsoro, Marmah har bakinta na kyarma wajan cewa, "Na shiga uku Ya Abbas mi yasa ka mare ta, kasan mi wannan marin zai jamin kuwa?, daka barni da bala'in dazan fuskanta na gani na da kawai tayi da kai, innalillhi wa'innan ilaihar raju'un". Ta fad'a tana sakin wani marayan kuka, tana bin Narnah da kallo ganin yadda take murmushin mugunta ta rik'e fuskarta dai-dai inda Abbas ya mareta, kallonsa tayi ido cikin ido ta ce "hmm wannan marin da kayi min kaci darajar ina sonka, duk cikin sonka ne da nake yi kai da baka isa tafiya wajan nan salin alin ba, wallahi kaci darajar ina sonka, amma wacce kake ikirarin wai kana so, a kanta zai k'are, danna rantse baka mari banza ba, kuma ka rubuta aje ni d'in nan nice wacce zaka aura...............✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 7 "Kee ni sa'anki ne zaki tsaya kina gaya min wannan maganganun?, banzar naki" Abbas daya idasa maganar yana tsare Narnah da ido, ko kallonsa batai ba, ta juya da sauri ta shige cikin gidan nasu. Juyowa yayi ganin yadda Marmah ke kuka duk'e a k'asa, da sauri ya d'agota, ba shiri ta ya tashi tana goge hawayen dake sintiri akan kumatunta, tana nuna sa ta ce, "Ya isa haka, Y Abbas dan Allah kabar wajan nan yanzu, tun kamin wani ma ya k'ara ganinmu, in k'ara jama kaina wata masifar", "Amma ya za'ai na tafi na barki a haka nasan dole sai anyi miki wani abu na b'acin rai, ni gaskiya bazan iya tafiya na barki a wannan yanayin ba, nina ja miki komai ina ganin bai kamata na tafi na barki a wannan halin ba" Da sauri ta ce "Y Abbas zan iya d'aukar komai duk wani wulak'anci naso, na saba da hakan, amma shedar da aka fara min ta neman maza tana sa zuciyata a wani mugun bak'in ciki, ka tafi kawai" Ganin yadda take kuka kamar mi yasa Abbas juyawa ya fara tafiya yana yi yana waigenta, yadda kasan daga lokacin bazai sake ganinta ba, harya b'ace ma ganinta. Juyowa tayi ta nufi zauran gidan zuciyarta na lugudan bugawa, ta kusa shiga harabar gidan kawai taji tayi garo da mutum, wata irin zabura tayi tana komawa baya, ganin Hamisu a gabanta yana jefa mata wani d'an iskan kallo, yana lashe baki. Kallonsa take k'irjinta na bugawa sosai, tsabar tsorantar da tayi. Can ta tsinkayi muryarsa irin ta gaggun y'an iska yana cewa "Ohhh wato dama abunda kiki yi kenan?, yawon banza a aike ki, shine sai kin lab'e wajan maza su latse ki, ai daba sai kinje wani waje ba, kawai ki taho waje na, ni nan sai na biya miki buk'atar ki, ba tare da kowa ya sani ba" Ya idasa maganar yana kamota ya had'ata da jikinsa, wani shegen wari ne ya ziyarci Marmah kamar warin giya kamar kuma warin taba ko wiwi, ba shiri ta k'ara sakin kuka, tana son turesa iya k'arfin tana cewa "ka cika ni Y Hamisu bana so irin haka, ni ba y'ar iska bace, ban tab'a iskanci ba, dan Allah ka kyale ni bana so" Ta idasa maganar bakinta na rawa da wani irin kuka mai tab'a zuciya, ba tai aune ba taji hannunsa akan k'irjinta yana shafawa iya k'arfinsa yana murzawa, yana faman cewa "ke y'ar iska a hakanne kike ikirarin cewa wai maza basa latsa ki, dan uwarki, to ko kink'i ko kinso na rantse sai na ratsaki, saina d'and'ana zumarki". Wani irin tuk'ukin bakin jiki ne ya ziyarci Marmah har bata san sadda ta ware hannunta ta hankad'e shi tasa tafin hannunta tana d'auke sa da wani gigitaccan mari har guda biyu ji kake tasss tassss. Wata irin zabura yayi yana ware idonsa a kanta yana nuna kansa, "Keee ni kika mara?" Kuka kawai Marmah keyi ba bakin magana bak'in ciki ya hanata magana ma kwata-kwata. Batai aune ba taji ya kama gashin kanta da k'arfi, ya gwara kanta da bango, wata irin azaba ce ta ziyarci Marmah har k'okan kanta, wata irin k'ara ta saki wacce bata fita sosai, jefar da ita yayi k'asa, yana sa hannunsa, a k'ugunsa ya kwanto bel, d'in dake d'aure a waddonsa, bai tsaya wata-wata ba ya fara jifgar Marmah baji ba gani. Ihu take tana birgima k'asa sune har tsakar gida yana mata wani shegen duka, ai da saurin mutanan gidan suka fiffito, ganin irin dukan da yake mata hakan baisa wani ya ce danmi ba. Hajara data k'araso wajan, itama cike da jin haushin Marmah saboda Narnah ta gaya mata komai, yasa ta d'akko wani dutse ta buga mata shi a kai, da sauri Marmah ta rik'e wajan ganin jini na zuba dan da nan goshinta ya fashe, ya kunbura. Hajara ta ce "ai wallahi kamin dai-dai dama kaine wadda nake nema yau ya lallasa min wannan y'ar iskar yarinyar shegiya ballagaza kawai, y'ar iska mai bin mazan banza, tunda aure kike so to sha kumurin ki za'a miki, ni nan zan kawo miki mijin daya dace dake", Ta k'ara matsawa kusa da ita amshi bulalar dake hannun Hamisu, ta daddage iya k'arfin ta a dai-dai gadon bayanta ta zafga mata bugu, harsai da Marmah ta gantsare tana sakin wani irin kuka. Hajara ta k'ara cewa "amma ki bud'e kunnanki ki jini, ko zanyi yawo tsirara, na rantse da Allah Marmah, bazan tab'a bari ki auri wani ba a rayuwa, kuma Abbas keda shi har abada daga yau, na sake jin an ganki da wani namiji ba wadda nice nan na zab'a miki ba, na rantse miki, sai kin gwammace dama ba'a haife ki ba" Tana gama maganar ta jefama Hamisu bel d'insa ya amsa yana cewa "waifa ganinta nayi zauran gidan nan da wani saurayi yana latsa mata nono, shine na fara mata fad'a, shine da yake y'ar hannu ce harda sa hannu ta mare ni, ni ko shine na nuna mata nima d'an tashan ne" Tashi Marmah tayi tana girgiza kai hawaye sai zuba suke, gaba d'aya jikinta rad'ad'i yake mata, duk Hamisu ya fasa mata jiki. Inna Suwaiba dake kallon komai ba damar tayi magana dan yanzu gaba d'aya gidan shakkar Hajara suke idan aka cire Inna Khande, da ita bama ta wajan danko fitowa bata yi ba, bare tasa baki, ayi mata rashin kunya. Marmah zatai magana, domin kare kanta daga wannan bak'in sharri da Hamisu ya mata, bata kai ga magana ba, Hajara tasa hannu ta buge bakin tana cewa "imin shuru makira miye zaki ce mana?, al'gunguma, wacce ta iya tsaro zance, ke har kina da abunda zaki ce ma mutane, kuma yau baza ki kwanar min a d'aki ba, d'akin uwarki data zauna zaki koma dan bazan zauna da mazinaciya ba, y'ar iska" Wasu hawaye ne suka k'ara zuboma Marmah bakinta na rawa muryarta na kyarma tana cewa "Um..Um....Umma wallahi ban tab'a iskanci ba, Umma d'akin itace ne fa aka maida shi" Ta fad'a tana jin wani bak'in ciki a ranta yadda aka maida d'akin Mahaifiyarta wajan aje itace, da tsunmokara. Hajara dake zafga ma Marmah hararara cike da tsana da kyara ta ce "kware kuwa, ko baza ki koma ba?, ai ko ban d'aki ne ya koma sai kin tare a can sai kin koma wallahi, kinji na rantse miki, inba ni ba ma, ubanwa zai iya rik'e ki, dan haka maza-maza kizo ki kwashe kwamutsanki ki kai so can, kuma kazo ki tankade garin nan wallahi yau ke ce zaki tuk'asa, koda zaki fad'a a cikin tukwanyar ne" Kuka Marmah ta k'ara saki, kukan da ba hawaye, tsabar yadda take kuka tun d'azo yasa hawayen ma k'afewa babu so, sai idonta da yayi jawur. Hajara dake kallonta ta ce "baza ki tashi ba?, kai Hamisu k'ara mata wani dukan, dan Allah kabarmin ita kwance na ce". Hamisu kamar jira yake ya fara jifgarta kamar Allah ya aikosa, dama da biyu yake mata wannan uban bugun, tak'i basa had'in kai, amma yaci alwashin wallahi saifa ya d'and'ani zumar wannan yarinyar, tun tana k'arama yake kwad'ayinta, bare yanzu da yaji luntsuma-luntsuman nonuwanta masu taushi kamar auduga, ga yarinya da bazaune kamar ita ta k'era kanta. Tun Marmah na iya kare kanta wajan dukan da Hamisu yake mata harta kaiga ko d'an yatsa bata iya d'agawa, tun tana kukan neman ceto harta gaji, sai wata ajiyar zuciya da take saukewa Narnah dake tsaye itama wajan dariyar mugunta kawai take ma Marmah, Bishira da Habiba duk da ba wani shiri suke ba, ba k'aramin tausayi ta basu ba, kwafa Habiba tayi tana kallon Hamisu, tana magana a zuciyarta. "Kenan Hamisu so yake ya lalatama Marmah rayuwa, kamar yadda ya ribace ta ya lalata tata rayuwar ya manta mike tsakanin su ne, tabbas idan baiyi a sannu ba, wallahi ta gaf da tuna mai asiri, ita zai yaudara" Ta idasa maganar zucin tana fad'awa cikin tunani a sadda Hamisu ya ribace ta. Kwanakin baya da suka wuce. Habiba ce tsaye a harabar gidan nasu, babu kowa a gidan sun tafi wata barka, dake wajan K'auyan su, dan lokacin harda Bishira aka tafi sai ita d'aya aka bari tana wankin kayan Mamansu, daga ita sai wani guntun zani, ta duk'a tana faman wanki, dan idan ta duk'a har k'asanta kana iya hangowa, gashi ko wando babu a jikinta. Hamisu ne ya shigo cikin gidan yana hard'e kafafuwa waddonshi ya cika yayi fam abar girmansa ta mik'e samb'al, dama ya kwaso jarabarsa tun a waje, yana zuwa ya hangi Habiba dake duk'e tana wanki, baiyi wata-wata ya matsa kusa da ita, yana sa hannunsa a dai-dai k'asanta a dai-dai y'ar tsakarta ya matse yana shafawa yana luliyawa, wata irin tsabura Habiba tayi tana juyowa tana shirin kwasa mai mari, wata shafa da yayi ma nonuwanta, yasa ba shiri ta k'ara rungumesa tana lumshe ido, zatai magana yasa d'an yatsa ya tushe mata baki yana cewa, "Shittttt ai kina so kiji dad'i ko, ni zan rink'a biya miki buk'ata" Turesa take sonyi tana cewa "kai yaushe kaji na ce ina son jin dad'i?" "Hhhhh yarinya kenan na tab'a ji mana kuna zancan keda Bishira, kinga yanzu kin samu a gida, babu wadda zai san tsakaninmu, kawai ki manta muji dad'in mu" Sauke ajiyar zuciya tayi shed'an na k'ara zugata, dama gashi Hamisu ya kanainayeta sai faman shafa sassan jikinta yake, duk inda yasan zai taso mata da sha'awa, nan ne yake tab'awa, har bata san sadda ta k'ak'k'amesa ba, ya sureta sai zaure inda d'akinsa yake. Tun daga wannan lokacin ya lalata Habiba, koda yaushe suna tare suna shek'e ayarsu, sun manta da Allah na kallonsu, har basu ankara ba, ciki ya shiga, sosai suka shiga tashin hankali, inda daga nan suka fara fad'a Hamisu ya ce su zubar dashi ita kuma tana tsoro, dan taji ance har mutuwa ake, inda da kyar ta amince, a zatonsa ta zubar da cikin ne shi yasa ya fara baya-baya da ita, yana nuna mata halin ko in kula, shine yanzu yake shirin b'ata Marmah. "tabbas Hamisu ka d'akko dala ba gammo, tunda ka lalata ni na rantse da sarkin dake busan lumfashi saika aure ni, babu mijina a duniyar nan sai kai, ni nasan abunda zanyi" Ta idasa maganar zucin tana dawowa tunanin data lula, tana nadamar biye ma son zuciya da tayi, da kuma biye ma Hamisu da tayi, Allah kad'ai yasan irin tashin hankalin da za'ayi a wannan family, idan wannan abu ya fito, babu yadda zatai ne dole Hamisu ya girbi abunda ya shuka, wallahi.............✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 8 Sallamar Mlm ce ta tsayar da Hamisu daga bugun da yake ma Marmah. Da sauri Mlm ya k'ara so kusa da Marmah, yasa hannunsa yana d'aga ta yana cewa "subhalllahi, Hamisu miye tayi maka haka, kake mata wannan uban dukan?", "Yo Mlm taddata nayi da wani k'ato a zaure yana shirin b'ata mata rayuwa" Da sauri Marmah ta shige jikin Mlm tana girgiza kai bakinta yayi mata nauyi. Kallonsa Mlm yake yi cike da tsananin mamaki yana cewa "Hamisu Marmah ce ka kama da k'ato?, anya baka sha wani abun ba yauma?, to ni dai nasan jikata bazata tab'a iya aikata abunda kake fad'a ba" Ya sake juyowa ga mutanan gidan ya sake cewa "dan bakwa sonta gidan nan shine ko a samu wadda zai tsawatar mai, saboda Allah dubi irin bugun da kayi mata, kayi dai-dai kenan?, kai wake bugunka haka iyee?, kai akwai wadda ya kai ka rashin ji a cikin gidan nan ne". K'unk'uni Hamisu ya fara yi yana sa k'afa ya fice daga gidan, yana ai kama da Marmah wani kallo, na ina nan hak'e dake, kuma zamu gamu ne. Da sauri Mlm ya fice da ita daga cikin gidan suka nufi kyamis, suna isa shi kansa mai kyamis d'in ya girgiza da ganin irin bugun da akai ma Marmah, cike da tausayi ya bata magunguna, ya wanke mata ciwokan da aka ji mata, yana mata addu'ar samun lafiya, haka suka taho cike da tausayinta Mlm keta bata hakuri, yana cewa, "Jikata kiyi hakuri kinji komai mai wucewa ne zaki ga watan wata rana kamar ba'ayi ba, ki daure ki cinye jarabawarki Allah ya k'ara miki hak'uri", Hawaye Marmah ta share bata ce komai ba, sai faman had'iyar zuciya da take, haka har suka k'arasa gida Mlm sai da ya biya ya sai mata lemo da kilishi, suka shiga sashin sa ta k'ofar waje, da yake zaka iya shiga sashin Mlm ta wata k'ofa dake waje harka b'illa cikin gidan, shi yasa bai cika sanin mima tsakar gidan nasu yake ciki ba, saboda ko fita zaiyi ta k'ofar waje yake fita ta cikin sashinsa. Sai da Mlm ya tabbatar ta cinye abinda ya sai mata, tasha magani, sana ya k'ara mata nasiha akan hak'uri, sana ya barta ta wuce cikin gidan. Koda ta shiga gidan kayanta taje ta kwaso daga d'akin Hajara tana kaiwa d'ayan d'akin Mahaifiyarta wadda yanzu ya zama na ajiye itace, d'akin duk yayi k'ura ga warin kayan wanki da ake tumawa a ciki, da kyar ta daure ta d'an gyara wani wajan inda zata samu ta kwanta, ga cinna ku duk sunma d'akin yawa, haka nan tasa wata yagaggar tabarma ta aje kayanta a kai. Fitowa tayi waje jin Hajara na kwala mata kira da k'arfi. Da bugawar zuciya ta fito ta ce "gani" Wani kallo tayi mata na sama da k'asa ta ce "tunda bakiyi tuwon rana ba, maza ga shinkafa can da wake, kije ki dafa ta, kizo idan kin gama ki wuce tallah, dan Narnah ta gama zuwa tallah wallahi, daga yau kece wacce zaki koma zuwa, kamin a aurar daku a tare, ko wacce ta gama gabanta" Wata irin fad'uwar gaba ce ta ziyarci Marmah, cike da k'arfin hali taje ta kama aikin data sata, tana yi tana hutawa, ga wani hakki dake taso mata, zuciyarta tayi nauyi, haka dai harta gama ta d'au tallar ta wuce. Habiba ce duk'e tana kwarara wani uban amai ba k'ak'k'autawa, Maryama dake tsaye kanta cike da tashin hankali ta d'agota tana faman mata kallon tsaf, wata irin kururuwa ta buga, da yasa mutanan gidan fitowa ba shiri. Hadiza dake tsaye ta tab'e baki tana cewa a hankali, "Komi ke shirin faruwa ne yau kuma yau zamu sha kallo da alama" Maryama tada rik'e Habiba tana zare mata ido ta ce "keee d'ago ki dube ni nan", D'agowa tayi tana zubawa uwar tata ido duk ta galabaita ta rame, Bishira dake tsaye ta ce "haba Mama baki ganin bata da lafiya ne?, kike mata ihu" Bata tankama Bishira ba ta sake kallon Habiba ta ce "ubanwa yayi miki wannan abun kunyar dake jikinki?, Gaba d'aya mutanan gidan suka d'auki salati, suna cewa, "Innalillahi abun kunya kuma" Inna Indo da gabanta ke lugudan bugawa ta matso kusa tana cewa "ke Maryama wane irin abu kike haka?, a bainar nasi miye kike tuhumar y'arki dashi haka?," Maryama dake tsaye cike da bak'in ciki ta ce "kinga Inna ki barni da ita yau wallahi ciki ne da ita ba tun yanzu na fara lura da ita ba, yau saita gaya min Ubanda suke shashanci dashi" Kuka Habiba ta saki ta duk'e k'asa sai uban kuka take mai cin rai, cike da bak'in ciki Maryama tasa hannu ta shak'o wuyanta tana cewa "zaki gaya min uban waye yayi miki cikin nan ko kuwa, sai nasa wuk'a na yankaki kowama ya huta?" Hamisu dake shigowa gabansa ne yayi wata irin mahaukaciyar bugawa ganin abinda ke faruwa, yana shirin komawa da sauri, har yana tuntub'e, da azama Habiba ta kwace daga shak'ar da uwarta tayi mata ta ce "gashi can shine wallahi yayi min cikin, kuma ba laifi na bane dole yayi min" Wani irin salati suka sake saki Hajara ta rik'e k'ugu tana cewa "babbar magana ai da yake Kakarku d'aya kuma duk tsatso d'aya yayi ku, abun zaizo da sauk'i" Ba wadda ya tankama Hajara Sa'ade tada kusa suman tsaye ta matsa kusa da Hamisu batai wata wata ba, ta fara bashi maruka ba k'ak'k'autawa, tanayi tana kuka, tana cewa "Hamisu abunda zaka samin dashi kenan?, Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un, Hamisu ka cuceni ina zamu kai wannan abun kunyar har haka" Duk jikin su sai yayi sanyi ganin yadda Sa'ade ke kuka. Maryama itama data share hawaye ta ce "na rantse da Allah Hamisu saika aure ta ko kak'i koka so" Da wani irin mahaukacin sauri ya d'ago yana kallon Maryama. Shigowar su Mlm da Mahaifin su Habiba dana Hamisu, kai harma da Hamza, yasa su yin shuru, sai dai aikin gama ya gama sunji komai. Iro tsabar bak'in ciki bai san sadda ya rarumo wani uban itace ya makama Hamisu ba, yana Allah wadai da halinsa, yana cewa "ai Maryama basai ma kince ya aureta ba, wallahi dolanshi ne, tunda shi ya lalatata, kuma ciki gara da baki zubar dashi ba, sai an haife shi, kuma tana haihuwa, za'a d'aura auran" Mlm ya rasa bakin magana Mamman ko yana shirin kamo Habiba ya rufeta da duka, da sauri Mlm ya dakatar dashi, yana cewa "dukanku mazan ku biyoni sashi na ina son ganinku, harda kai Hamisu" Gaba d'aya Mlm suka rufama baya, a tsakar gidan ko sai maida magana ake, ganin abun zai dawo na b'acin rai da gori yasa Maryama jan yaranta suka shige d'aki. Zaune suke gaban Mlm ya kalli Hamisu tsaf ya ce "Hamisu miye kaje kayi haka?, da kasan kana son aure miye yasa bazaka zo ni ka gaya min ba?" Zunburo baki Hamisu yayi yana k'unk'uni wajan cewa "yo Mlm ba sai da na nuna cewa auran nake so ba, anyi min ne?, ni kuma shine yasa naje na nemarwa kaina mafita..... Wani mari da Iro ya kaima Hamisu yasa shi yin shuru da sauri Mlm ya d'aga mai hannu, Da sauri kuma Iro ya ce "Mlm daka kyale ni nama yaron nan hankali, wallahi mu zai zauna yana gaya ma maganar banza haka" Mlm dake kallon Iro ya ce "ai gaskiya ya fad'a, ni ai bansan wannan zancan ba, da tsaf ba'a zo ga wannan halin ba, mi yasa daya nuna yana son aure bakuyi masa ba?, yanzu rashin yin hakan mi ya jawo?" Shuru gaba d'aya parlon yayi, Mlm ya gyara zama yana cewa "tabbayar ku nake?", Iro ne yayi k'arfin halin cewa "Mlm ayi hak'uri, tabbas muma munyi kuskure" Mlm ya ce "abinda zance yanzu dole a bari ita Habibar ta haihu, idan yaso sai a d'aura auran, kai gaba d'ayama y'an matan dake gidan nan, za'a had'a a ranar ayi bikinsu kowama ya huta, yanzu daba abun na gida bane, ina kukasan abun zai kai?, sana abu na gaba, karna sake naji maganar nan ta fita koda nanda k'ofar gida ne, kai hatta Sule (Daddy) ban yarda an sanar dashi ba" Mamman ne ya d'ago ya ce "amma saboda mi Mlm?" "Saboda bana so ma matarsa taji, dan nasan kunsan ba son danginsa take ba, a hakan ma ya aka k'are bare taji wannan abu daya faru" Hamza ne ya ce "hakane kuma Mlm amma kasan komin dad'ewa yana iya sani, kamar zaiji babu dad'i ana waresa" Shuru Mlm yayi can ya nisa ya ce "da wannan dan wannan amma dole ce tasa za'a b'oye masa, kuma insha Allahu abun zamuyi shi a sirrance ne, Allah zai kawo mana mafita, dan haka ko wannan ku, ya sanar da yaransa mata, su tabbatar sun fiddo da mijin aure, nanda lokacin da Habiba zata haihu" Hamisu dake k'unk'uni shifa bazai auri Habiba ba, dan yanzu jin wata tsanarta yake har cikin ransa. Mahaifinsa ne ya k'ara kaimai wani marin cike da jin haushinsa ya ce "ai ko mutuwa zakai na rantse saika aureta, mutunan banza kawai" Tashi yayi ya fice yana ayyana yadda zaici uban Habiba mudun ta bari aka kaita gidansa..........✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 9 Tun daga wannan lokacin aka hana Habiba fita koda tsakar gidan nasu ne, idan ba wani abu daya zamu dole saita fitan ba, saboda tana fita wasu daga cikin mutanan gidan zasu fara zund'inta suna magana k'asa-k'asa. Marmah ko tafe take a hankali kamar wacce bata son taka k'asa, ta dawo daga bakin tasha daga tallar da Hajara, ta nace sai ta rink'a yi. Yamma tayi sosai dare ya fara k'unnu kai sauri take ta isa gida kamin a fara kiran sallah. Tazo dai-dai k'ofar gidan nasu, kamar ance ta d'aga kanta ta hangi Narnah tsaye da Abbas d'inta suna tad'i, a yadda ta gansu suna dariya suna murmushi, kai daga ganso zaka ce masoya ne. Saura kad'an tayi tuntub'e ta fad'i, tsabar yadda take binsu da ido, cike da tsananin bugawar zuciya ta k'ara matsawa kusa dasu, wani irin zazzab'i ne taji na neman rufeta, ta tabbata an rabata da Y Abbas kenan, mutunan da take matuk'ar so, duk fad'in garin, duk yawan wadda suke cewa suna sonta, shine kad'ai ya tsiri tuta a zuciyarta. Batai aune ba taji Narnah ta buga mata tsawa tana cewa "kee mayya karki cinye mu, ai dama na ce miki duk duniya Abbas baida matar da zai aura sama da ni, dan haka Abbas ya miki nisa, sai kije ki nemi dai-dai dake, koda yake Umma ta ce wadda ta zab'a miki na nan zuwa gobe da safe, dan haka da'aAllah Malama kallon ya isa haka, karki cinye mu nida Honey na" Wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga bin kumatunta Marmah, ganin yadda Abbas ya nuna halin ko in kula da ita, gani ma take kamar nunawa yake bai san tsayuwarta a wajan ba, "k'alu Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un" kawai take mai-maitawa a zuciyarta. Ba shiri tayi cikin gidan, danjin kuka na neman kwace mata. Tana shiga gidan ko tsayawa ta kaima Hajara cinikin tallar da tayi mata bata yi ba, kai tsaye d'akin daya zamo a nan take kwana yanzu ta shige, bayan ta aje sauran kayan tallar data dawo dasu. Tana shiga ta zube akan tabarmar da take kwana a kullum, wani irin kuka ya sark'eta, tana tushe bakinta, k'ank'ame jikinta tayi, ta cigaba da kuka marar sauti mai matuk'ar cin rai, tayi kuka sosai har taji kanta kamar zai rabe gida biyu, tsabar yadda yake sara mata. Jawo zani tayi ta lullub'e dashi dan wani irin sanyi take ji, wani zazzafan zazzab'i ya rufeta, danda nan jikinta ya d'au wani zafi rau kamar wuta, sai rawar d'ari take. Mahaifiyarta ta tuna, da ace ta nan da wani abun bai sameta a yanzu ba, sai dai tasan Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i, kuka ta k'ara saki, mai sassayan sauti tana matuk'ar kewar Mahaifiyarta. Wani irin wahalallan bacci ne ya d'auke ta, tana cikin yin baccin daba dad'in shi take ji ba, taji saukar ruwan sanyi a jikinta mai bala'in sanyi, wata irin zabura tayi, danda nan jikinta ya kama kyarmar sanyi, gafgaf, har hak'oranta na had'ewa waje d'aya, kallon Hajara tayi dake tsaye kanta tana jijjiga, tsabar tsanar Marmah da take ji har bata san sadda ta kai mata wani mangari ba. Marmah daba wani k'arfi jikinta ta tafi ta bige da wani kututturan icce ta bige kanta dashi, daya sata sakin wata uwar k'ara, kanta dake ciwo ya k'ara yin wani dum, ji take kamar kan nata ba'a jikinta yake ba. Hajara ta buga mata tsawa tana cewa "to makira al'gunguma, ina kud'i na?", Da sauri Marmah ta raromo k'unshin kud'inta ta mik'a mata, kwata-kwata halin data shiga ne ya mantar da ita, bata je takai mata kud'inta ba. Sai da k'irga su ya kai sau uku tukun ta maido dubanta wajan Marmah ta nunata da yatsa tana cewa "da nufinki ki cinye kud'in komi?, makira, kuma ki bud'e kunnanki da kyau kiji ni, gobe wadda zai aureki ko na ce wadda na zab'a miki zaizo, saura idan yazo ki nuna masa halin akuyancin naki, kuma na rantse miki mudun iyayanki maza suka tabbaye ki, shin kina sonsa, kika tsake baki amsa da eh kina sonsa ba, hmmm Marmah kenan, kinsan Allah na rahira saiya fiki jin dad'i, dan rantse miki sai kin gwammace dama uwarki bata haifeki ba" Shuru Marmah tayi zuciyarta na wata irin bugawa, kamar zata tsaga k'irjinta ta fito, ta kasa cewa k'ala. Sai Hajara dake mata kallon tsana ta sake cewa "baki jin abinda na ce ne?, kikeyi k'unnan uwar shegu dani, y'ar iska marar tarbiyya" Ba shiri har bakin Marmah na rawa ta ce "naji Umma" "Yo karda ma Allah Ubangiji yasa kiji mana, jikinki ne dai zai gaya miki, kika sake kikai min ba dai-dai ba, dan wallahi sai na k'ara d'ai-d'aita rayuwarki, a K'ANGIN RAYUWAR nan dana saki, to wallahi kikai min shirme, sai na k'ara saki wadda yafi wannan da kike ciki, idan k'unne yaji gangar jiki ta tsira" Tana gama fad'ar haka ta fice tana jan dogon tsaki. Marmah share hawayen dake zubo mata tayi, duk da tana sharewa wasu ne ke faman zubowa ba k'ak'k'autawa, sauke ajiyar zuciya tayi tuna ledar maganin da Mlm ya sai mata, yasa da sauri ta jawota ta b'alli magani tasha, Allah yaso harda na zazzab'i da ciwon kai ya sak'o mata, hakan yasa danda nan tasha, kamin wani d'an lokaci zazzab'in ya fara sauka zufa ta fara rufeta, ciwon kanma ahankali-ahankali yatai sauka, wani bacci na neman d'aukarta, har yanzu idonta na hasko mata Abbas d'inta da Narnah, a yadda suke soyayya suna tad'i, girgiza kai tayi, tana saurin rufe idonta da k'arfi, tana ma Mlm addu'a dan idan badan shi ba, da K'angin rayuwar da zata shiga sai yafi haka, saboda yawanci shike sai mata sabolun wanki dana wanka, wani lokacin wajansa take zuwa idan an hana ta abinci, shike sai mata, da abubuwan da ba'a rasa ba, shi yasa daya ganta yake karantar wane hali take ciki, wani lokacin ba sai ta tabbaya ba yake sai mata, shi yasa take matuk'ar son Kakanta, Mlm tun yana ma Hamza fad'a akan rashin kulawar da yake ba Marmah harya gaji ya daina sai dai ya bisa da addu'a, dan a yanzu yasan an shiga tsakanin Y'a da kuma Uba. Washe gari da safe Marmah ta tashi ta fara ayyukan gidan nasu, duk fad'in gidan haka take zagewa ta share shi tas, tun bata sababa harya bi jikinta, tana gama sharar kuma ta fara uban wanke-wanken gidan yadda kasan shagon saida kwanoni, tana yi tana hutawa saboda zazzab'in da tayi jiya, so har yanzu ba wani k'arfi a jikinta. Tana cikin yi Habiba ta fito, cikinta harya fara tasawa, tabi Marmah da kallo, kamar na tausayi, tana tsaye saiga Hamisu ya fad'o gidan ko sallama babu, ai ko yana hango Habiba ya nufi wajanta yana nunata da yatsa yana cewa, "Yauwa dama tuni nake son ganinki, kinga Habiba kika sake aka d'aura auran nan dani dake, wallahi Allah na rahira sai ya fiki jin dad'i, dan sai kin gwammace dama baki tab'a sanina a rayuwa ba, tun wuri ya kamata kije ki zubar da cikin nan, dan bazan tab'a son abinda kika haifa ba wallahi" Habiba dake kallonsa sama da k'asa ta aje butar dake hannunta, dama band'aki zata shiga, shine yasa ma ta fito. Ta nuna sa itama da hannunta ta ce "to sannu ubana, na ce sannu ubana, ka bud'e kunnanka da kyau kaima kaji ni, kaga wannan cikin nan gani nan bari ne wai an kama kazar mayya, sana idan na aurekan an kaini gidanka domin Allah karka barni da rai kaji?, dai-dai nake kai fa Hamisu, na fika d'anyan kai duk yadda kake tunanina na wuce nan, dallah matsa ni kaban waje kona hanb'arar dakai a wannan wajan" Marmah dake duk'e tana wanke-wanke sosai fa abun yabata mamaki domin ko bata san mike faruwa ba, addu'ar shiriya kawai tayi masu ta ci gaba da yin abunda ke gabanta, duk da can cikin zuciyarta abun ya tab'a ta, wannan abun kunya har cikin family naso, "kai Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un" kawai take anbata a cikin zuciyarta. Hamisu dake kallon Habiba ya kasa ce mata komai, sai binta yayi da ido harta shige b'an d'aki. Juyowa yayi zai fice ya hangi Marmah dake wanke-wanke, baiyi wata-wata ba, ya rarumo dutse ya saita goshin Marmah ya jefa mata shi. Ai ko ya sameta a dai-dai goshin nata, da wani irin sauri ta tashi tana dafe goshin nata, sai hawaye shaaaa, tana kallon Hamisu, miye tamai haka zai mata wannan muguntar?, take tabbaya a zuciyarta. Can taji muryarsa yana son huce haushinsa a kanta yana cewa "to tsananniya makira, shine kin wani kasa kunne kina sauraran abunda muke cewa, ai dama ke na durka ma cikin aka bani ke" Da azama ta k'ara ware idonta akansa bata san sadda bakinta ya furta "Ubangiji Allah ya kiyashe ni, da fad'awa irin wannan k'addara, kuma aniyarka tabika wallahi, wannan ai mugun fata ne......... Shuru tayi ba shiri tana tushe bakinta, dan bata san ta fad'a bama, ganin yadda Hamisu ya cika yayi fam, ganin yana nufo wajanta, yasa da azama zata juya domin guduwa, sai dai charaf ya ruk'o................✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 10 Kuka Marmah ta saki tana ba Hamisu hak'uri, ganin yadda ya kama tsintsiyar hannunta, batai aune ba ya sakar mata wani gigitaccan mari, yana murd'e hannunta ta baya. Wata irin k'ara ta saki ta azaba. Kawu Mamman dake shigowa cikin gidan, ganin abinda Hamisu ke shirinyi yasa ba shiri ya matsa kusa dasu, Hamisu baisan da tsayuwarsa ba, sai dai yaji saukar mari shima a kumatunsa, ai ko ba shiri ya saki Marmah dake kuka, sauke ajiyar zuciya tayi tana komawa gefe, tanama Allah godiya daya kawo mata Kawu Mamman, dan Allah ya gani yanzu tsoron Hamisu take ji, tunda yayi mata jakin duka. Hamisu ne ya juyo yana bin Kawu Mamman da wani irin kallo. Kawu Mamman daya tsaya akansa yana cewa "ko zaka rama ne?, marar kunyar banza marar kunyar wofi, ai duk ina kallon mike faruwa, ubanmi tayi maka zaka kama bugunta?, ko tsabar cin zali ne, kai gaka tsohon mugu, wai kai ko kunya ma baka ji ne?, dallah b'ace min da gani ni, dan idan ina ganinka na rantse wani bak'in ciki nake ji, duk irin halin daka sa mutane baka dubaba ka daina abunda kakeyi, wato saima abinda yayi gaba kenan?, to Ubangiji Allah ya shiryeka, idan kana da rabon shiryowar" Ya idasa maganar yana nufar sashin Mlm. Hamisu dake daskare waje d'aya, yak'i motsawa bak'in ciki ya dabaibaye mai zuciya, yana nan tsaye, Marmah ta lallab'a ta fad'a d'an d'akin da take kwana. Har Habiba ta gama ta fito Hamisu na nan tsaye, kallonsa tayi tana tab'e baki, duk taji abunda ya faru bayan shigarta band'aki tana tafiya ta kusa shiga d'akinsu ta ce "idan bakai wasa ba dai, a haka zaka k'are solob'iyo kawai, kai in banda k'addara mi zanyi dakai fisabilillahi, ai ka cuce nima wallahi" Tana fad'in maganar tayi shigewarta d'aki ta barshi da jin haushi biyu, juyawa yayi buguzin-bugunzin ya fice daga cikin gidan. Marmah na zaune a d'akinta tana faman linke y'an suturinta daba wasu bane, ta tsinkayi muryar Hajara na faman kiranta. "Kina ina ne wai?" Cewar Hajara dake shigowa d'akin Marmah. Marmah dake saka hijab, ta ce "gani Umma" "Yauwa kinga abinda nake so dake, ki fita waje, ga Dangana can yazo, shine wadda ya nuna yana sonki, kuma shine wadda zai aureki, dan haka maza ki fice yana jiranki k'ofar gida" Marmah dake tsaye a daskare tayi mutuwar tsaye, bakinta na kyarma wajan furta, "Dangana kuma?, Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un badai Danganar data sani ba, mai mata biyu, gason y'an matan tsiya ne dashi, ga gidansa da garda-gardan mata da maza, ga matansa y'an bala'i ne, ita ko ina zata kai Dangana" "Kware kuwa au ashe ma kinsan sa har haka, harkika karanci irin rayuwarsa haka, kinga abun zaizo da sauk'i ma" Hajara ta idasa maganar tana mata kallon raini wayo. Hannu Marmah ta d'ora a saman kai, tana zubewa k'asa ta kama k'afafun Hajara tana cewa, "Dan girman zatin Allah ki taimaki rayuwata Umma ina zankai rigimar iyalansa, Dangana ba sa'an yina bane, indai Abbas ne wallahi na rantse miki na barma Narnah shi ai tuntuni, ki taimaki rayuwata karki had'ani aure da Dangana" Ta idasa fad'ar haka tana sakin kuka. Wani murmushi Hajara ta saki tana cewa "yarinya kenan ai idan kinga baki auri Dangana ba, sai dai idan bana raye, a wannan duniyar, amma mudun ina duran duniya sai kin shiga gidan Dangana, karma ki b'ata bakinki wajan bani hak'uri, domin ko bayi zanyi ba, kuma banza janye k'udurina ba, kuma da kike cewa, wai kin barma Narnah Abbas, ke kin isa ki bar mata shi, inahh ai da k'arfin ikona nasa Abbas ya dawo da soyayyar da yake miki akan Narnah, domin ke baki dace da irin su Abbas ba, irinsu Dangana ne suka dace dake" "Innalillahi dan Annabi Umma karki bari a aura min Dangana, bana sonshi wallahi, ki kawo min wani zan aura amma banda Dangana dan Allah" "Keee ki rufe min baki na ce, ai ko mutuwa zakiyi saifa anyi auran nan, idan yaso ki mutu da auran Dangana a kanki, amma auransa ba fashi kinji na gaya miki, tunkan na hanb'arar dake a nan wajan ki tashi kije yana can yana faman jiranki, sauran idan kinje ki gaya mai maganar banza, ni kuma maganar ta dawo waje na kiga yadda zanyi dake, a cikin gidan nan" Marmah ta dage sai kuka take wiwi kamar ranta zai fita, shikenan za'a tarwatsa mata rayuwa, itakam mita tsarewa Hajara ne?, a rayuwarta, take son sata a K'ANGIN RAYUWA har hakane?. Can ta tsinkayi muryar Hajara tana k'ara cewa "zaki tashi ki wuce ko kuwa, saina lakad'a miki na jaki?". Ba shiri Marmah ta fice daga d'akin tana share hawayenta wasu na k'ara zubowa. Hajara dake fitowa itama tana faman mitar cewa "kaji mun y'ar iskar yarinya, da kilbibi, ai tukun na ma yarinya, dan baki san yadda nak'i jinin bud'e idona na kalleki bane, da baza ki tsaya ma rok'ona ba, babu abinda zai canza a zuciyata dangane da irin tsanar da nayi miki". Haka Marmah ta fita k'ofar gida, tana fitowa kuwa ta hangi Dangana tsaye bakin wata bishiya dake k'ofar gidan nasu. Yana hangota ya fara washe jajayan hak'uransa, yana dariya, a zuciyarsa yana cewa "kai amma fa Hajara na gode miki, wannan zuk'ek'iyar budurwa haka, na tsinci dame a kala" Marmah data tsaya nesa dashi tana makamai wata uwar hararara, da manyan idonta kamar zasu fad'u tsabar yadda take hararar sa. Washe baki yayi yana cewa "ki k'araso mana masoyiya", Cike da tsiwar da bata san ta iya ba ta ce "bazan k'araso d'in ba, wai kai baka ji kunya ba, kike shirin aure na, ni ka dubeni da kyau, kafa yi jika dani, Dangana kaji tsoron Allah ka fita daga rayuwata, na rok'eka" Marmah ta idasa maganar tana had'e hannayenta waje d'aya alamar rok'o. Wata y'ar iskar dariya Dangana ya saki yana cewa "yarinya kenan ai idan kinga na fasa auranki, to mutuwa ce ta dauke ni, amma mudun ina lumfashi, yarinya sai kin zama tawa" "Au haka ka ce?, to bari na daina lallab'aka amma ka sani, na rantse komi nayi ma kaine ka sayeshi da kud'inka, kuma bazaka tab'a samun abunda kake kwad'ayinsa akai na ba, insha Allahu" Ta idasa fad'ar haka ta juya tayi shigewarta gida tana jamai dogon saki, bata tsaya jiran mi yake cewa ba. Shiko sai b'ab'atu yake yana murna ya samu y'ar shila, duk abunda ta gayamai baiji wani haushi ba...............✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 11 Tana shiga gidan ta taradda Hajara k'ofar d'akinta tana zaman jiranta. Hajara ganin Marmah ta shigo hannu rabbana, yasa ta tashi tana maka mata hararara, tana cewa "ke ya zanga haka?, ina y'ar k'unshin ledar, da ake yoma y'an mata, idan sauri yanzo zance, ko kuwa bak'in hali kika nuna kik'i amsa?" Da sauri Marmah ta girgiza kai tana cewa "a'a Umma wallahi nidai bai bani komai ba" "Ke dalla rufe min baki, bama sai kin tsaya kin saurare shinba tukunna, waike mi yasa bazaki daina bak'in hali da bak'in ciki ba?, tona rantse da Allah duk sadda ya sake zuwa baki tsaya da kyau kin saurare shi ba, harya baki abun duniya, kika shigo gidan nan hannu rabbana, zaki sani ne" Girgiza kai kawaii Marmah tayi hawaye sun cika idonta, ita ba wannan ke damunta ba, wannan kaddararran auran da Umma Hajara ke shirinyi mata shi yafi komai tsaya mata a zuciya, haka tana tunani harta k'arasa d'akinta tana shiga ta rakub'e waje d'aya, yadda taga Dangana, waishi zata aura yasa ba shiri ta fashe da kuka, tana tusa kanta a tsakanin cinyoyinta. Rayuwa na tafiya da gudu kwanaki na komawa kamar wuni watanni na komawa kamar sati, sati na komawa kamar kwana d'aya. Haka ce take kasancewa a ga Marmah gani take kamar ranar mutuwarta na k'ara matsowa ne, saboda yadda taga anata hada-hada a gidan naso, na shirye-shiryen auran dasu, kowaccen su ana mata gyara amma ita banda ita, saima tallar da take zuwa har yanzu, sai ko fargabar da take ciki, na auran Dangana, da kullum yake ci mata rai, shi yasa a wannan tsakanin dukta fita hayyacinta, ta rame ta figi, gashi kullum ya dameta da zuwa, yana mata wasu maganganun shirmensa, gaba d'aya iyayansu maza kamar an kauda hankalinsu daga gareta bare wani ya lura cewa bafa san Dangana take ba, kowa ya kasa ganin aibun Dangana, dan har an amshi kud'in auran y'an matan gidan nasu harda nata ma, dama Mlm ne take sa rai shi kuma hidima sunmai yawa, ga kwana biyun nan baida ishishshiyar lafiya, gashi tana tsoron gargad'in da Hajara tayi mata, shi yasa kullum cikin kuka take, da tsananin fargaba. Inda Mlm ya kira Daddy ya sanar dashi auran yaran da za'ai, Daddy yayi mamaki sosai kuma yayi fad'a danmi ba'a sanar dashi tun wuri ba, gashi yanzu baya k'asar shida iyalansa dan har ayi bikin basa nan, dan bikin bai wuci saura wata d'aya ko biyu ba, domin Habiba ta shiga watan haihuwarta, kuma tana haihuwa da sati biyu ko d'aya akeso ayi bikin, inda Mlm ya ce ba matsala karya damu, daga baya yazo, idan suka dawo, inda shi kuma Daddy kwata-kwata baiji dad'i ba, haka nan dai ya turo kud'i masu yawan gaske ya ce ayi ma y'an matan kayan d'aki, zai sa kuma a kawo kayan abinci da za'ayi anfani dasu a bikin, sosai Mlm yaji dad'in hakan yana tasa mai albarka. Yauma Marmah na zaune tana aikin tunanin da yanzu ya zame mata jiki, ita ba wata k'awa gareta ba bare takai mata kukanta, shi yasa abun yayi mata yawa, zuciyarta tayi nauyi da yawa, ta rasa inda zata amayar da abinda ke cikinta kota samu sassauci. Jin muryar Hajara a kanta tana cewa "ke wai bakiji ana miki magana ne?" Tashi Marmah tayi gabanta na fad'uwa, yanzu indai taga Hajara gabanta muguwar fad'uwa yake. Har bakinta na kyarma ta ce "Umma banji bane wallahi" "Keni ki tashi da'aAllah Dangana ne yazo yana son ganinki, ance dama yana zuwa kwana biyu sai kice ace mai baki zuwa, ke gaki mai kunnan k'ashi ko?", Shuru Marmah tayi dan Allah ya gani ta tsani Danganar nan ko ganinsa bata sonyi, ya addabi rayuwarta. Bata ce komai ba ta fice ranta babu dad'i. Ai ko yana tsaye yana hangota ta fito, ya fara washe mata baki kamar yadda ya saba, nesa dashi ta tsaya kamar yadda takeyi aduk sadda yazo. Da kyar ta bud'e baki ta ce "wai kai da'aAllah Malam, baka da zuciya ne a k'irjinka?, tunda kake zuwa ban tab'a sauraranka ba, saima k'ara tsanarka da nake ji a zuciyata, kai bazaka hak'ura ka fita a rayuwata bane?" Dariya ya saki yana cewa "ai duk abunda zakiyi min bana tab'a jin haushi, saboda ina matuk'ar sonki" Da sauri Marmah waigo tana bankamai wata uwar hararara tana cewa "kai ko kunya ma bakaji kake fad'an irin wannan kalaman, toni kaji da kyau bana sonka, kuma bazan tab'a sonka ba, mai budurwar zuciya kawai" Ta idasa maganar tana niyar juyawa ta wuce cikin gida. Ba shiri ya matsa kusa yana aje mata ledar dake hannunsa yana cewa "masoyiya kenan ai bazan tab'a jin haushinki ba komi zakiyi min kuwa, sana ga wannan ki shiga dashi, sana biki fa sai k'ara matsowa yake, har yanzu baki fara tabbayar dame-dame kike buk'ata ba" Juyowa tayi a fusace ji take kamar ta wanke shi da mari, ta ce "bana buk'atar komai, daga gareka indai akan wannan bikinne, kuma wannan abun dakake kawowa ma, ka sani ban tab'a anfani dashi ba, dan haka ka daina wahalar da kanka wajan kawowa" Ta idasa fad'ar haka kawai taji wani abu ya tsaya mata a wuya na bak'in ciki, har bata san sadda ta fashe da kuka ba. Kallonsa take ganin shi ko a jikinsa saima wasu surutai da yake mata, yasa ta fisgi ledar tayi cikin gida, danta lura Dangana baida zuciya a k'irjinsa. Koda ta shiga cikin gidan inda Hajara ke zaune tana kwashe shinkafa da wake ta sana'arta da takeyi, ta aje mata ledar tana niyar barin wajan, Hajara ta maka mata hararara tana cewa "ke zo nan ina kuma zaki?" Marmah da bak'in ciki ya cika mata zuciya ta ce "Umma ba inda zani mana" "To kuma naga kina niyar tafiya, ko nufinki ba zaki tallar bane?, ubanwa zaije min tallar nufinki?, ai idan kinga kin daina zuwa tallah to satin bikinku ne ya kama, kinji ma na gaya miki" Shuru Marmah tayi bata k'ara cewa komai ba, dama kwanakin nan rashin maganarta ya k'aru, dama ita ba gwanar magana bace. Tana gama had'a mata komai ta d'auki tallar ta fice, tana cikin tafiya kawai taji an tsaya mata a gaba, da sauri ta d'ago tana duban y'an matan dake kallonta suna jefa mata wani shegen kallo, kallo d'aya tayi musu ta shaida Y'ay'an Dangana ne, y'an mata ne guda biyu, sun girmeta nesa ba kusa ba. Suna jijjiga tsabar rashin kunyar dake cinsu, wata ta nunata da yatsa tana cewa "ke kece wadda Babanmu yake son aurowa?, ke wacce irin zuciya ce dake?, ki dubemu da kyau kina tunanin kishi da Iyayanmu mata damu kanmu abu ne mai sauk'i, to ki bud'e kunnanki da kyau kiji mu, tun wuri kije ki soke auran nan idan ba haka ba kuma, kika sake kika bari wallahi kika shigo cikin gidanmu, wallahi kinji na rantse saiya fi miki kabari dad'in zama, dan haka tun wuri kasan abunyi" D'ayar ce ta amshe da cewa "ke Hansa'u kema ke tsayawa lallab'ata, dan Allah idan kin cika ke y'ar rigima ce, to ki shigo gidan namu, wallahi sai mun lallasaki, shi Baba baccin ma baida zuciya mi zaiyi da wannan kwailar domin Allah" Marmah dake musu kallon mararsa tarbiya, sai da suka gama tsaf sana ta ce "ni da zakuje ku sami uban naku ma ya hak'ura da nemana da yake, da naji dad'i, ku kalleni da kyau nayi sa'ar auran ubanku ne?, ai kusan hanyar jirgi daban ta mota ma daban, dan haka bani zakuyi ma wannan gargad'in ba ubanku zakuje ku sama, danni in banda k'addara da kuma anfi k'arfina, na rantse kunsan nafi k'arfin ubanku" Wata irin kururuwa d'ayar tayi tana shirin kaima Marmah mari, da azama Marmah ta rik'e hannun tana mata kallon baki isa ba wallahi. Marmah dake kallonta ganin sai wani huci take tana kallonta, Marmah ta ce "ki shiga hankalinki da alama nima baki san wacece ni ba, duk abunda kuke tak'ama dashi, na damaku na shanye, tabbas inada hak'uri amma aka kaini bango, ban iya rigima ba, dan haka ku shiga hankalinku, ni ba sa'ar yinku bace" Tana gama fad'ar haka ta zagaye su ta wuce, ta barsu sake da baki, cike kuma da mamakinta, suda akeba labarinta, bata magana, hak'uri ne da ita. A wajan Marmah ko k'arfin hali ne kawai ta aro tasama kanta, bata tab'a tunanin zata iya yin maganar nan mai tsawo har haka ba, dan tana wucesu sai da ta sauke ajiyar zuciya, wasu hawayen ba'kin ciki na zub'o mata. Harta gama tallar ta dawo gida ba wani walwala a fuskarta, abunda Y'ay'an Dangana sukai mata ya tsaya mata a zuciya. Sai gashi tana shiga gidan ta k'ara taradda da abunda yasa mata bugawar zuciya............✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 12 Domin tana shiga ta taradda mutanan gidan sunyi ciccirundo a kusa da d'akinsu Habiba da alama nak'uda take. Dan yadda Marmah taji yadda Habiba ke ihu tana kuka, samun waje tayi ta zauna zuciyarta na faman bugawa, yanzu da Habiba ta haihu shikenan bikinsu ya kusa kenan?, Can kuma sai tausayin Habiba ya kamata, tana zaune saiga Hajara ta nufo wajanta tana cewa, "Bani kud'i na ke" Marmah dake zaune ta mik'a mata bata ce komai ba, saida ta k'irga kamar yadda ta saba sana ta saki wani tsaki tana cewa "Ohhh ni haba Habiba kin cika raki da yawa sadda kikaje kika lik'ema k'aton banza kuna kwasar dad'i a tare wani ya sani ne" Ba wadda ya jita bare harya samu mai biye mata, Marmah dake kallonta, ta girgiza kai, ganin Hajarar ita ko a jikinta, sab'anin mutanan gidan, da yawansu fuskarsu cike take da tausayin Habiba. Habiba dake cikin d'akin Mahaifiyarta ta kwance tsakiyar d'akin, tana murk'ususu, Maryama na rik'e da hannunta, tana, mata sannu, Inna Indo dake taimaka mata tana cewa "daure kinji, ki daure kiyi nishi mai k'arfi" Jujjuya kai Habiba tayi maganarta bata fita sosai tsabar wahalar data sha tana cewa "Inna bazan iya ba, k'arfi na ya k'are, wayyo Allah mutuwa zanyi" Sosai fa hankalin mutanan dake d'akin ya sake tashi can Bishira dake share hawaye ta ce "wai Mama baza'a kaita asibiti bane?" "Ke wane irin asibiti kuma?, ana zaune k'alau, Allah ya rufa mana asiri wannan abun kunyar data yi bai fita cikin gari ba, yanzu idan aka kaita asibiti ai asirinmu ne zai tuno" Maryama ta idasa maganar tana sharce gumi itama, duk da ta fara sarewa da Habibar yadda ta kasa iya tab'uka komai, tun tana nishan iya k'arfinta har k'arfin nata ya k'are. Tunda yamma ake abu d'aya har dare ya fara kutso kai, iyanzu Habiba kod'an yatsa bata iya d'agawa, ga kan yarinya ya fara fitowa, itakam Habiba harta sare da wannan duniyar, Maryama sai kuka take ita sa Bishira, jin Habiba na cewa su yafe mata. Cikin wani ikon Allah kuma, wani k'arfi yazo mata, tana yin wani uban nishi jariraya ta fad'u macece, sai dai kana kallon yarinyar zaka san bata zo da rai ba, domin ba kukan nan da jarirrai keyi babushi, su Inna Khande har d'an bugun yarinyar sukai, ko da ranta, sai dai tuni yarinyar dama ta mutu a ciki, saboda an raini cikin ba shan wani magani bare zuwa asibiti awo, dan yarinyar harta fara sandarewa, Allah nema ya taimaki Habibar da bata rib'e mata a ciki ba, shi yasa ita kanta Habibar tasha wuya wajan haihuwarta, domin yarinyar bata motsi, bare ta taimaka mata wajan fitowarta duniya. Mutanan gidan sunyi farin ciki da mutuwarta, bare da aka gaya ma mazan hamdala ma sukai suna ma Allah godiya, a cikin gidan akayi rami aka sallaceta aka binneta ba wadda yaji ba wadda ya gani, daga su sai su. Ta b'angaran Habiba ko kuka tayi shi dan Allah ya gani taji tana son komiye ma ta haifa tunkan yazo duniya, tana kuka tana rok'on Mahaifiyarta ta yafe mata, itada Mahaifinta, duk ta zama wani iri tana nadamar biyema son zuciya da tayi, gashi nan tun kan aje ko ina ta fara gani, ko wannan azabar wahalar data sha ai izina ce a gareta, ashe haihuwar ba sauk'i ne da ita ba, ashe haka iyayansu suka sha irin wannan wahalar wajan kawosu duniya, ai ko dole Allah yayi fushi da kai, idan har ka sab'a musu. Haka dai ta ture komai aka fara shirye-shiryen biki sosai Maryama ke gyara y'ay'anta, bare Habibar inda Allah ya taimaketa sati na zagayowa taga jinin haihuwar ya d'auke. Inda Hajara ma ke gyara d'iyarta, Marmah ko ba wadda ma ya damu da ita bare har a gyarata, y'an uwan Mahaifiyarta sunzo, sai dai Hajara ta hanasu koda ganin Marmah ne, saima ta amshe kayan da suka kawoma Marmah na bikin babu abinda basu saya mata ba, na dangane da abunda uwa take ma y'arta idan auranta ya tashi. Sai dai Hajara ta handame komai ta had'ama Narnah da shi, koda ta sami labarin kayan d'akin da akai ma y'an matan gaba d'aya da kud'in da Daddy ya turo, sai da ta had'a munafurci, a ranar da za'aje jere, ta hana a nufi da kayan Marmah gidan Dangana kai tsaye, aka wuce dasu wajan masu yin Furnitures, aka sauya su aka bada mararsa kyau, wadda basu da k'arko, sauran kud'in kuma, aka k'ara saima Narnah wasu kayan dasu. Haka akaje jere gidajan y'an matan kowacce gidanta ba laifi bare na Narnah nanne fa aka sha kallo irin gidanjan y'an birni Abbas ya gina, kuma yana so bayan bikin ya d'auki matarsa su wuce Kano, inda yake aikinsa, sosai yake rawar k'afa a bikin, kai daka kallesa kasan ma baya cikin hayyacinsa, domin yadda su Hajara da d'iyarta ke tatsarsa kud'i, da bashi umarni, jikinsa na kyarma yakeyin komai. Gidan Habiba ko bayan layinsu ne Mlm ya bada gidansa su zauna, a nan akayi mata jeranta, sai ko Bishira, da aka je wani gari dake hayin K'auyen, ita ce kawai aka fidda daga garin duk sauran cikin garin ne, gidan Marmah shine k'arshe, ansha tashan k'ananun maganganu a wajan matan Dangana, ba wadda ya biye musu, akayo jere aka dawo, d'aki d'aya ne dai, da kyar ma kayan suka amshe d'akin, har wasu na cewa "gara da Hajara ta canza mata kayan d'akin, dama tasan talaka zata aura, da haka za'a kawo wa'innan kaya masu mugun tsada, da kyau, a wannan K'urk'uk'un d'akin. Sosai aka dawo gida ana maganar gidan da za'a kai Marmah, duk bidirin da ake banda sanin Iyaye maza, dan har kayan da aka canza ma Marmah basu sani ba. Marmah kuwa kwana take kuka, sosai ta k'ara fita daga hayyacinta, kowacce cikinsu na murna amma banda ita, idan ta kallesu sai taji sha'awa inama ace itama, masoyinta zata aura wadda take so, duk da baza tai damuwar nan ba, sosai idonta ya zurma ta rame sosai dan idan ka kalli ramar da tayi sata baka tsoro, sai ido tayi zuru-zuru. Ana gobe d'aurin aure aka kawoma kowacce lefe, Habiba kuma Mlm ne yayi mata komai, cikinsu babu wacce lefenta baiyi ba, saima na Narnah ya d'ara na kowacce, sai na Marmah shine k'arshe, akwati biyu ne, bama wadda yake tashi. Anata bud'a ana shewa, su Hajara ganin komai aka kawo na d'iyarta sai yafi na kowa, nanfa ta k'ara d'agawa tana sakin maganganu da habaici. Marmah ko y'ar uwar Mahaifiyarta Kharima tazo tana ta lallashinta ta kawo mata kayan da zata sa da bikin tana bata hak'uri ta daure ta amshi k'addararta hannu biyu-biyu, sai sana Marmah tad'an samu sauk'i, amma duk da haka kullum cikin kuka take, gashi dama Kharima tunda tazo Hajara ke yab'a mata bak'ar magana, sukayi kaca-kaca, tun ranar bata sake dawowa ba, taba dai Marmah hak'uri, tayi mata nasiha sosai. *WASHE GARI RANAR D'AURIN AURE*.......✍️ *Mu ha'du a gobe idan Allah ya kaimu*🙄🤪 *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 13 Washe gari ranar d'aurin aure Marmah na k'udinddine a d'an d'akinta, jikinta yayi zafi rau, zazzab'i ya rufeta, gashi sai faman kuka take, ita d'aya, tana iya jiyo hayaniyar y'an bikin da suka cika gidansu, sauran amare an ware masu wajansu daban a cikin gidan kasancewar babban gida ne, sai basu je ko ina ba, duk a nan cikin gidan suke komai nasu, inda zasu zauna, ita ko lek'a wajan ma batayi ba. Dan harta ji an fara mata surutun girman kaine da ita, tak'i fitowa cikin jama'a, sai dai sam ba haka bane, auranne yazo mata a yadda batayi zato ba, bata tab'a tunanin zata rasa Abbas ba, sai gashi a d'an k'ank'anan lokaci komai ya ruguje mata. Tana tunanin zuci hawaye masu zafi na bi mata fuska. Kowa na gidan nata hada-hada su Hajara k'irjin biki, sai nan-nan ake an kasa zaune bare tsaye, kwata-kwata tama manta da wata Marmah, ta yarinyarta kawai take, yadda kasan ita kad'ai ce wacce ake bikinta, su Narnah a shiga waccan kaya a cire waccan, tasa kaya sun kai kala biyar, a safiyar ranar dai, anata tsokanar amare, ko wacce na shiga da fita. Habiba ce ma ta lura bata ga Marmah ba, ai ko da hanzari ta nufi d'akin da take, tana zuwa ta ga irin halin da take ciki, cike da tausayi, ta tada ta, tana cewa "Marmah mike damunki ne haka, ko wacce amarya ta shirya cikin kaya masu kyau, amma ke shuru, gashi har an kusa d'aurin auran ma, dan k'arfe sha d'aya dai-dai ake daurawa" Gaban Marmah ne yayi wani irin bugawa dassss, har sai da wasu irin hawaye suka sake bin kyakkyawar fuskarta, data rame kamar ba ita ba, tama kasa cewa komai, domin ko babu abunda zata iya cema Habiba, saboda ta tuna mugun gargad'in da Hajara ta bige mata, ba abunda keci mata rai irin wannan auran. Haka nan dai ta lallab'a tayo wanka, tazo ta zab'i cikin kayan da Kharima ta kawo mata, wata shadda ta d'auka wacce tasha ado da duwatsu, shadda kallo d'aya zakayi mata kasan ta d'inku, kuma mai tsada ce, ita kanta Habiba sai da ta kalleta ta sake kallonta, tana yaba kyan da tayi mata, danma duk ta rame, tayi duhu, ita kanta Marmah sai ta k'ara jin k'aunar dangin Mahaifiyarta, tasan da ace wajansu ta taso, tabbas da zata gata iya gata. Koda ta fito waje, suna gaisawa da mutane, sai tsukanarta ake itama, sai dai tayi murmushin yak'e kawai, Hajara ko tana kallonta cike da jin zafin ganinta ta warware, so tayi ta ganta ranga-ranga, harda sa wasu kaya, bata san da kayan ba, ai da wallahi saita amshe su. Jawota Hajara tayi tana mata kallon sama da k'asa tana cewa "keee munafuka, ina kika samo wa'innan kayan kuma?" "Umma Aunty Kharima ce ta kawo minsu" "Ahh lallai cewa zakiyi munafuka ce ta kawo miki su, inba munafurci ba, mi yasa ba'a nuna min ba, kema harda ke munafuka ko?, ko da yake ai gadon munafurcin kikayi can wajan dangin uwarki" Runtse ido Marmah tayi tana jin zafin maganganun Hajara bata ce komai ba, zata juya ta tafi taji maganarta tana cewa "kuma ki kwaso kayan gaba d'ayansu ki kawo min d'aki na wallahi baki sake sasu, kinyima kanki, ni za'a munafurta" Ko ci kanki Marmah bata ce ba, bare tasan ran zata ce dan Allah tabar mata kayan, taje ta d'akko kayan taje d'akinta ta aje mata su, a d'akin taga Narnah ana sake sa wasu kayan. Narnah dake kallon kayan jikin Marmah cike da jin haushinta ta kalli Hajara dake shigowa yanzu ta ce "Umma ita kuma wannan banzar ina ta samo kaya haka?" "Inafa zata samo su inbadda munafukan dangin uwarta sune suka kawo mata, itama da yake munafuka ce ai kinga bata nuna min ba" Wani dogon tsaki Narnah taja tana sake cewa "to kuma ubanmi kikazo yi a d'akin nan?" Juyawa Marmah tayi domin ficewa taji muryar Hajara naba Narnah amsa tana cewa, "Cewa nayi ta kwaso duka kayan data kawo mata ta kawo min su nan" "Tohm saboda mi Umma ai da kin bar mata tsiyarta kawai" "Inbar mata a ina?, ai wallahi tunda ta munafurce ni bata ba k'ara sasu, sun kuma zama haramiyarta, gara naje na zubar dasu kona bayar dasu, dana bari ta sake sakawa, nifa na tsani naga yarinyar can cikin warwala ko cikin sutura mai kyau, bare har ta rink'a jin farin-ciki nafi son ganinta kullum cikin K'ANGIN RAYUWA" Dariya Narnah tayi tana cewa "ai Umma nima nan wallahi na tsani yarinyar can, ji nake dama ba ubanmu d'aya da ita ba". Haka dai sukayi ta zagin Marmah da bata san sunayi ba, dan tana fita ta samu waje ta rakub'e ta zauna, tana tunanin data sabayi a kullum. Gaba d'aya gidan ne ya d'an d'auki shuru, jin mai shalar d'aurin aure ya fara sanar da wadda aka fara d'aurawa, danda nan gidan ya kaure da bud'a, shalar k'arshe ce ta girgiza jama'an gidan, hatta Marmah sai da ta mik'a a zabure, Hajara ko afujajan ta fito daga d'aki, ita da Narnah. Narnah ce tayi k'arfin halin cewa "Umma kodai banji dai-dai bane, da waye kuma aka d'aurama aure da Marmah" Mai shalar ne kamar yasan suna wasuwasi ya k'ara wage baki wajan k'ara cewa, "D'aurin aure na k'arshe shine an d'aura auran Khaleefa Suleman Sani Mai Goro, da amaryarsa Aysha Hamza Sani Mai Goro, akan sadaki naira na gogar naira dubu d'ari uku cif lakadan ba ajalan ba" Gaba d'aya fa gidan sunyi muguwar girgiza anma rasa bakin magana, Marmah ko ba abunda zuciyarta take sai muguwar bugawa kamar zata tsak'e k'irjinta ta fito, wani irin masifaffen tsoro ne ya rufeta. Hajara da tayi suman wucin gadi sai da mutane suka jijjagata ana watsa mata ruwa, tana dawowa hayyacinta ba inda ta nufa sai wajan Marmah, batai wata-wata ba shak'e mata wuya tana cewa "wato da had'in bakinki aka canza wannan d'aurin auran ko?, to gara na kashe ki da inga wannan ranar wallahi" Ba shiri y'an uwan Hajara suka b'anb'are ta daga jikin Marmah da idonta ya fara kakkafewa, tana shirin sumewa, tari ne ya sark'e Marmah bayan Hajara ta sakar mata wuya, ta duk'e a wajan tana sakin kuka mai cin rai, tana tunanin waye kuma Khaleefa?, waye haka ya fanshi auranta a wajan Dangana?, Da kyar aka janye Hajara y'an uwanta sukayi d'aki da ita, wata y'ar uwarta ta kalli Hajara tana cewa "Hajara kanki d'aya kuwa?, ya za'ai ki rink'a nuna wannan k'iyayya a gaban mutane, ki bari ki fuskanci abun mana daga baya kin d'au mataki" Sauke ajiyar zuciya Hajara tayi tana girgiza kai tana cewa "Inahhh wallahi bazai tab'a yuwu ba, wannan yarinyar ce za'a ce ta auri Khaleefa" Y'ar uwar Hajara wacce ta tayi magana daga farko mai suna Halima, ta sake cewa "wai waye Khaleefan nan ne?, daya sa duk kikabi kika tada hankalinki haka ne?" "Kinsan kuwa waye shi?, d'an gidan Sule ne, yanzu duk garin nan waye baisan Sule ya tara dukiya ba, shi kanshi yaron nasa yana da abun duniya, kinganshi kuwa?, gashi da kyau dan birni, gashi da iliminsa, babu abunda yaron nan ya rasa a nan gidan duniya dai, kinga yadda y'an mata ke rubibinsa a can birnin ma, wai amma a rasa wacce za'a bashi aure sai waccan y'ar iskar yarinyar, shin mi yasa ba'a bashi Narnah bane?, wai yama akai hakan ta faru ne?" Halima ce ta dafa Hajara jin sai zaro zance take har tana son sakin layi yasa Halima cewa "shin koma dai wanene ki nutsu ki kwantar da hankalinki, mazan gidan su shugo ai zakuji ya akai auran ya dawo kansa ko?" "Ya za'ai na kwantar da hankalina iyee Halima, kinsan mi kike fad'a kuwa" "Tohm ya kike so na ce miki Hajara anfa riga anyi d'aurin auran nan, ki kwantar da hankalinki daga baya sai ki d'au koma wane irin mataki ne, amma yanzu idan kina nuna haka, ai zaki iyasa shakko a zukatan mutane" Ba yadda Hajara ta iya haka yasa tayi shuru tana sharce wani uban gumi, zuciyarta cike take da mugunta da tsanar Marmah tsantsa, wacce ta linka ta da, sai had'iyar zuciya take. Ai ko su Inna Khande sukam sunji dad'in wannan had'i kawai sunja bakinsu sunyi shuru ne gudun tashin hankali, dan sunsan Hajara y'ar bala'i ce. Hamza suna shigowa ta jawoshi ko kunyar mutane babu ta sashi a d'aki ta kori kowa dake d'akin ta rufesa da tabbaya. Tana cewa "Mai gida shin ya akai auran haka naji Marmah an maida mata aure da wani sab'anin Dangana?" Hamza ya gyara tsawuyarshi yana murmushi daka kalleshi kasan yana cikin farin ciki ya ce "eh hakane abunda ya faru shine, wajan d'aurin auran ashe Sule (Daddy), ya wakilta Khaleefa zuwa d'aurin auran nan, saboda shi kad'ai ne bai biso k'asar waje ba, yana aikinsa a Abuja, amma Daddy ya sashi zuwa domin ya wakilce sa, ana cikin d'aurin aure Khaleefa ya kira Daddy a waya video call yana kallon komi ke wakana, a sadda aka zo gana Marmah Daddy na ganin angon, shi duk daukar Daddy ma banda Marmah ga masu yin auran, nanfa ransa ya b'aci ganin wadda zamu ba auranta, inda ya nemi alfarmar a maido auran akan d'ansa Khaleefa, shi kansa Khaleefan ya girgiza dajin haka, amma da yake yaro ne mai biyayya yasa ya amince, duk da bai san ko wace yarinyar ba, inda Dangana yaso tada tarzoma, a wajan d'aurin auran, shi kuma Daddy ya basa mak'udan kud'ad'e wadda suka linka hidimar da yayi ga auran, ai ko danda nan Dangana yayita washe baki, yana cewa yabar ma Khaleefa, ganin irin kud'in da aka basa, nan take aka d'aura auran, inda Daddy shine ya bada sadakin Marmah, dan Mlm shi kansa sai lokacin yaga Dangana kwata-kwata bai dace da auran Marmah ba, Mlm yayi farin ciki sosai da wannan had'in" Hamza ya idasa maganar yana kallon yadda Hajara ke mai wani shegen kallo, wata uwar hararara ta banka mai tana cewa "kai kuma sai kai tsaye ka amince mai makon a maida auran Khaleefan ga Narnah, idan yaso ita Marmah sai a bata Abbas d'in dama ai tana sonsa" Da sauri Hamza ya ce "mi kike cewa?" Da sauri Hajara ta rik'e bakinta jin tayi katob'ara, sauke ajiyar zuciya tayi jin bai fahimceta ba. Murmushin yak'e tayi tana cewa "a'a babu abinda na ce cewa nayi abun yayi" Murmushi kawai Hamza ya saki yana ficewa daga d'akin dan mutane nata jiransa a waje. Yana fita Hajara ta zube a k'asa tana sabbatu tana cewa "Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un, kai jama'a wai mi yasa bance Narnah ita ta auri Danganar ba, da nasan auran Khaleefa zai iya dawowa kanta, da sai mu nuna kamar auransa zatai da gaske, itama fa da yanzu Daddyn ya tausaya ma Narnah ya bata auran d'ansa, kai wayyo Allah na ji uban sadakin da aka sa ga auran waccan Marmah banzar" Sai surutai take wata maganar ma bata san tana zarota ba, har saida Narnah ta shigo d'akin itama kanta jikinta yayi sanyi ganin uwarta a haka, lokaci guda duk ta fita hayyacinta...........✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 14 Narnah ta dafa Hajara tana cewa "Umma dan Allah ki kwantar da hankalinki, tunda kinga nima wadda na aura mai kud'i ne, tunda babu abinda ya rasa" "Kee in kwantar da hankalina fa kike ce?, mi Abbas d'in yake dashi?, ke kinsan waye Khaleefa kuwa?, ai bazaki tab'a had'asu da Abbas ba, ai tazarar ma tayi waya tsakaninsu, inahhh ai wallahi ko zanyi yawo tsirara na rantse da sarkin dake busan lumfashi, sai na raba auran Marmah da Khaleefa tabbas tunda baki sameshi ba, sai dai kowa ya rasa wallahi" Narnah dai bata k'ara cewa komai ba, danta lura Mahaifiyarta tayi nisa bata jin kira. A wajan Khaleefa ko tunda aka d'aura auran yake jin zuciyarsa wani iri, yana cikin mota zaune ana d'aura auran ya baro wajan ya dafe kansa, dake sara mai, ya d'ago kyakkyawar fuskarsa da take cike da damuwa, Khaleefa kyakkyawan matashi ne ajin farko k'ak'k'arfan namiji, tsayayye ingarma daka kalli jikinsa yadda yake a murd'e, k'irarsa daka kalla kasan yana motsa jikinsa, fari ne amma ba can ba, ga wani saje daya kewaye fuskarshi wadda ya k'ara mai kyau da cikar zati, sanye yake da bak'in yadi wadda ya k'ara mai wani mugun kyau, mai fisgar mutum, lumshe idonsa yayi masu zara-zaran gashi ga girarsa dake da yawa kamar zata had'e da y'ar uwarta, idonsa ne ya d'anyi ja kad'an saboda damuwar daya shiga, sosai fa yake shakkar Mami idan taji wannan zancan yaya zata d'auke sa. Yana cikin tunani yaji ringing d'in wayarsa, da sauri yakai dubansa ga wayar a hankali ya d'au wayar ganin Daddy ne ke kiransa. Da sallama ya amsa wayar, daga cikin wayar Daddy ya ce "Khaleefa ka kwantar da hankalinka nasan abun yake damunka akan Maminku ne ko?, ni nan insha Allahu idan lokacin sanar da ita yayi ni zan sanar da ita, karka damu, ai ni nasaka kayi auran, bawai yin kanka bane, so hakan karya dameka kaji" Sauke ajiyar zuciya yayi cikin muryarsa mai sanyi ya ce "to Daddy insha Allah amma ita yarinyar yaushe zata bar nan d'in?" "Karka damu insha Allah sati mai zuwa zamu dawo idan mun dawo zanmu zo da kai garin mu taho da Marmah, a matsayin rik'eta zanyi dan har yanzu nasan yarinyar bata gama karatu ba, ba lallai ma tayi karatun ba, idan yaso a sadda ta gama karatunta ta k'ara zama budurwa sai ayi bikin tarewarta gidanka" Lumshe idonsa yayi yana jin sanyi a zuciyarsa, da ba yanzu Mami zata san zancan ba, sallama sukai inda yake shaida ma Daddy shima yanzu yake shirin barin garin zai biya ta Kano, zai hau jirgi zuwa Abuja, inda yake aikinsa. Sai da yaje wajan Mlm sukai sallama ya gayamai sati mai zuwa zasu zo da Daddy domin tafiya da Marmah, ya gayamai kad'an daga abunda suka tattauna da Daddyn, shima Mlm yayi na'am da abunda Daddy ya ce, sai da Mlm ya tsareshi yaci abinci sana sukai sallama, yaso yaga Marmah a ranar, sai dai jama'a sunyi yawa a cikin gidan, dama wajan gidan. Sai wajan dare aka kai ko wacce amarya d'akinta, sab'anin Marmah dake rakub'e a d'akinta tana kuka kamar ranta zai fita, bata san makomar auran nan, da akai mata ba, bata san waye angon ba, tana addu'ar Allah yasa shine mafi alkhairi a gareta. Tana ji tana gani aka fitar da kowacce amarya daga gidan aka nufi gidan kowacce, Habiba ce ma k'arshen kaiwa, su Mlm ne suka bata mota aka kai Habiba, wadda angon ma yana can yawonsa, kwana biyu ba'a ganinsa a gidan. Haka taji sun dawo suna ta zancan gidan Narnah yayi kyau sosai, ko wacce ma dai sai san barka, amma na Narnah ya zarce na kowacce, amma duk da haka, Hajara bata farin ciki, ba abunda take ma Marmah sai fatan tsiya, tana zaginta, da kwashe mata albarka, sai kace ita tasa aka aura mata Khaleefan. Washe garin ranar tunda asubahi Hajara ta fice daga cikin gidan ta nufi wajan Bokanta, koda taje Bokan ya tabbatar mata da cewa "bazai iya raba auran ba, amma yarinyar akwai sauran k'alubale a gareta domin Mahaifiyar yaron bazata sota ba, kawai ta rabo da irin k'alubalen da zata fuskanta ma a can" Ai ko jin abinda Boka ya ce yasa Hajara cikin farin ciki, tunda dai Marmah bazata tab'a jin dad'in uwar mijinta ba, ai ko bata ba kwanciyar hankali, wahala kawai zata sha, shi yasa Hajara ta baro wajan Boka cike da farin ciki. Tunda aka kai Narnah Abbas bai shigo ba, sai wajan sha biyun dare, kuskuran da Narnah tayi tana waya da Hajara ta furta sunan Marmah, Abbas yaji, yana ji yaji kansa yayi wata irin sarawa, yana son tuna ina ya san mai sunan nan?, ganin kansa ya matsanta masa da ciwo idan yana son tuna wacece mai wannan sunan. Kwata-kwata Narnah a daran ta kasa gane kansa, da akazo wajan ma'amular aure kuwa, da zafi-zafi Abbas ya rink'a tafiyar da Narnah ba wata nuna soyayya tasha azaba iya azaba, kuma yana gamawa ya sauka daga kanta ko ci kanki baice ba, tana kuka da neman ceto, duk yadda take kallon Abbas zai bata kulawa ya riritata sai taga sab'anin haka. Haka nan dai ta daure ta gyara jikinta, zuwa safiya jikinta da kasanta sunyi tsami, dan ko tafiya da kyar take yi, da kyar ta fito parlo, ganin Abbas yashe a k'asa yana ta sharar baccinsa, kamar an tsikare shi ya tashi, tana ma Narnah wani kallo kamar yau ya fara ganinta, sai can ya ce "ke ina kalacin safe na?" Wani kallo Narnah tayi mai tana cewa "kamar ya daga aure jiya nifa amarya ce kuma ma bana jin dad'i bazan iyayi ba, jiya duk ka gajiyar dani" Tashi yayi yana dafe kansa jin yadda ya sara mai, dan jiya wani abokinsa ya basa wasu kwayoyi yasha wai na rage damuwa ne, don tun ranar da akace an kauda hankalinsa daga Marmah ya shiga wata matsananciyar damuwa, shi yasa ya had'u da wani abokin banza yake d'orasa a harkar shaye-shaye, shi yasa jiya ya afkama Narnah ba wani tausayi. A ranar da daddare ma Narnah abunfa ya fara bata tsoro, da rana komai ta ce mai yi mata yake, koda zata gaya mai magana ne kuwa, bazai ce komai ba, amma da zaran yasha yayi mak'is zaizo mata a buge. Tushe hancinta tayi jin wani warin giya na feso mata ganin Abbas ya nufo inda take, tana shirin guduwa ya chafkota, ya had'ata da bango, yana faman shinshinar ta, wani irin mai ne ya taso ma Narnah jin Abbas na niyar kai bakinsa cikin nata, ai ko ta kwararamai shi a fuska, bai san sadda ya kwasheta da wani gigitaccan mari ba, ya rufeta da duka baji ba gani, ya kuma taushe ta a nan tsakar d'aki ya haye kanta, saida yayi mata kaca-kaca saida ya tabbatar ya biya ma kansa buk'ata sana ya sauka daga kanta ya zubewa a jikinta ya kwarara mata wani amai itama mai shegen wari, Narnah ta kasa koda d'aga hannunta ne sai uban kuka take, ga k'asanta dake mata zafi kamar ana yankarshi, dama ba wani warkewa tayi ba, jiya daya fara saninta, dama bata dad'i ya biyar da itaba. A cikin kwana biyu Narnah duk ta rame saboda azabar da Abbas yake gana mata, mundun yana cikin maye, ubanta yake ci la'ada waje, harsai mayen ya sake shi ne, take yin yadda taso dashi, ta rasa yadda za'ai ta hanashi shaye-shaye. Irin wannan rayuwar ke faruwa a gidan Narnah, gashi auran ba wani dad'ewa yayi ba, bare tasa ran fita taje wajan uwarta, kota samo mata mafita. A wajan Habiba ko, itama dai babu wani jin dad'i saboda tunda aka kaita bata ga Hamisu ba, sai a kwana na biyu yazo mata a buge shima, amma da yake tasan kansa rufe d'aki tayi ta barsa a waje sai faman d'ora mata ashar yake yana zaginta, bata damuwa ba, tayi kwanciyarta, sai washe gari tana fitowa ta gansa yashe a k'asa, aiko bata tsaya komai ba ta d'ebo ruwa masu sanyi ta watsa mai a jiki. Wata irin zabura yayi yana tashi yana d'ora mata zagi, dariya ta saki tana kallonsa ta ce "kai ko kunya baka ji jibeka da'aAllah kamar wani d'an bori" Cike da b'acin rai ya dubeta yana cewa "kee dankin rainani ni zaka watsa ma ruwa?, kuma jiya shine kika rufe min d'aki, d'akin na uwarki ne da zaki rufesa?" "Kai Hamisu dakata karka sake karka soma k'ara zagar min uwa, kuma d'aki na rufe indai zaka rink'a zomin a buge wallahi bazan tab'a bari ka shigar min d'aki a haka ba" "Ke dalla rufe min baki an zageki d'in ko akwai abunda zaki iya?, y'ar iska kawai wacce ta gama tanbadewarta a waje, har wani abun arzik'i ne a d'akin naki?" Dariya Habiba ta saki tana shewa da cewa "y'ar iska ko y'an iska, ka rink'a sa munjaye Malam, waya b'ata ni d'in inba kai ba, ai kaine babban d'an iska" Tana rufe baki ya d'auketa da mari, ai ko shima baiyi aune ba, ta d'auke shi da nata marin, kallon juna suke ido cikin ido, nuna kansa yake yama kasa magana, sai Habibar ce ta ce "kware na mare ka mana, ubanwa yasa ka fara mari na, kaifa bari kaji na gayama, nice dai-dai dake dama, idan kayi min dubu saina rama, kasan dai ba fin k'arfi kayi ba, saboda k'arfin naka duk ya k'are wajan shaye-shaye, taba da wiwi, da giya duk sun tsotse sa, to ka bini a sannu, dan banza tab'a bari kayi min wulak'anci ba ban rama ba wallahi" Zage-zage sukai tayi har makwafta sun fara jiyo su, k'arshe Habiba ta shige d'aki tana bugamai tsaki. Hakace take kasancewa a gidan su Habiba itama, cikin kwana biyu babu wani jituwa a tsakaninsu, kullum tunda akai auran kwana uku kenan, kullum cikin rigima suke, idan yaso samun wani abu daga Habibar saiya kama lallab'ata, to tsakanin mata da miji sai Allah, saita yarda su biyama kansu buk'ata, itama da yake tana son kasancewa tare dashi, saboda Hamisu yasan takan mace wajan kwanciyar aure, shi yasa yake gigita Habiba, daya zo yake mata wayo, su sha sha'aninsu, sai kaga a kwana ba rigima rana d'aya kuma, suyita rigima, da zage-zage da tunama juna asiri wani lokacin har sai makwafta sun shigo suna basu hak'uri. Ko wanne gida dai ana zaune k'alau amma banda gidajan nan guda biyu, na Narnah da Habiba...........✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 15 Sati na zagayowa Daddy da Khaleefa sukazo d'aukar Marmah, sosai Mlm yayi mata nasiha tana zumda hawayen rabuwa dashi, domin bata san miye zata taras ba, a can, tana ji a jikinta akwai sauran k'alubalen a tare da ita, tunda tun kan tasan wacece ita, take samun labarin Matar Daddyn yadda ake cewa girman kaine da ita, bata son y'an K'auye. Tunda suka d'au hanya ba wadda ya sake cewa uffan, gara ma Khaleefa tunda ya kalleta sau d'aya bai sake koda duban inda take ba, a zuci yake tunanin, yanzu wannan yarinyar harta isa wani aure?, yana da tabbacin k'annansa mata sun girmeta nesa ba kusa ba, su ba'ai musu auren ba sai ita, koda yake haka al'adar K'auye take, tab'e baki yayi yana k'ara kallonta ta k'asan ido, a hakanma yana da tabbacin girman jiki ne da ita, shi yasa kallo d'aya baza a iya cewa, ga shekarunta ba, itama tun a wajan Mlm data ji ya kirasa da Khaleefa, saida ta girgiza da ganin dama shine ya amshi auranta?, shin ina zata kai wannan d'an gayun mai ji da kansa, tana gani fa ko kallo bata isheshi ba, tana da tabbacin, ko kalar fuskarta bai sani ba, gaskiyar magana tana da aiki ja a gabanta. Shi ko bata san ya kalleta tsaf ba, har kallon ya wuce misali, shi kansa saida yayi zargin kansa, yana jan dogon tsaki, har saida Daddy ya dube shi, murmushi Daddy ya saki, yana basarwa shima, danshi ya lura da irin kallon da yake ma Marmah, shi kansa Daddy yasan bata inda Khaleefa zai iya cewa Marmah batayi ba, saboda yarinya ce, mai shiga rai. Tunda Marmah taga sun shigo Kano taji wata irin fad'uwar gaba, bawai fad'uwar gaba wacce wani abu zai sameka nan take ba, a'a fad'uwar gaba ce, wacce tajita can k'asan zuciyarta, kallon garin Kano take, cike da sha'awa da birgewa, tunda take bata tab'a fita tabar garinsu ba, koda wajan K'auyensu ne, bare ta shigo birni, sai dai taga y'an gidansu na fita suna zuwa, ita wake gareta ma bare ta ce zataje wajansa?, koda akwai ma, tasan Hajara bazata tab'a bari taje inda suke ba. Tunaninta ne ya katse dai-dai sun iso wata unguwa mai d'auke da gidaje masu mugun kyau, daka kalli tsarin unguwar kai kasan ta masu hannu da shuni ce, wani rantsatstsan gida wadda ya amsa sunansa gida taga sun nufa, shi kanshi get d'in gidan abun kallo ne, tasbihi take a zuciyarta, tana ayyanawa a zuciyarta dama akwai irin wannan gidajan a duniya?, bata k'ara tsinkewa da lamarinba saida suka shiga harabar gidan, sosai Marmah tasha mamaki ganin irin tsarin gidan, kamar na turawa, har suka tsaya ta fito daga cikin motar tana kallon gidan, danba k'aramin birgeta yayi ba, tsarinsa da kyansa. Daddy ne ya kamo hannunta yana k'ara tuna mata yadda zata zauna gidan, saifa tayi hakuri, saboda shi dai ba mazauni bane har Khaleefan, tana jinsa gabanta sai fad'uwa yake. Har suka shiga rantsatstsan parlon gidan wadda yaji kayan alatu, da kayan more rayuwa, ga parlon na fitar da wani sahihin k'amshi, mai kwantar da hankali, ba abunda Marmah take sai bin Parlon da kallo, cike da d'unbin mamaki a ranta, dama haka Daddy yake da kud'i?. Tunaninta ne ya katse, a sadda ta wurga ido, taga wasu mata matasa wadda suke ji da wanka, da gayu, suna zaune akan kujerun parlon, d'aya na danna waya, d'aya kuma computer. Sai sana Khairat, da Ifteesan, suka lura da shigowarsu, ai ba shiri, suka saki k'arar murna suna zuwa suka rungume Daddynsu, bama su nufi Y Khaleefa ba, saboda wani shegen kallo daya watsa masu. Marmah dake gefe, tana masu kallon sha'awa, inama itama, haka suke da Mahaifinta. Daddy daya sake su, yana murmushi, yana tabbayarsu ina Mami?, kallon Marmah suke cike da rashin sani, sai kuma taga sun tab'e baki, suka koma suka zauna, suna ba Daddynsu amsar cewa Mami na sama. Kamin su rufe baki, ma saiga Mami na sakkowa daga kan bene, tundaga sama Mami ta lura da Marmah dake zaune yanzu a rakub'e waje d'aya, Daddy na zaune akan kujera, sai Y Khaleefa daya fice ya nufi part nasa, Daddy na ma Marmah magana, ta saki jikinta, ai nan kamar gidansu ne, ta tashi ta zauna kan kujera, Marmah da kanta ke a k'asa ta girgiza kai kawai, danta lura mutanan gidan sai mata kallon banza suke. Mami data idasa sakkowa tana faman jefama Marmah wani kallo, wadda Marmah kallo d'aya tayi mata ta hango tsanar y'an K'auye a idonta, kai harda ma fuskarta data nuna. Tana idasa k'arasowa kanta a k'asa ta gaida ita, maimakon ta amsa saita jefoma Daddy tabbaya da cewa, "Daddyn yara wannan fa wacece?" "Ki zauna mana ai zanyi miki bayani" Zama tayi tana d'ora kafa d'aya kan d'aya tana cewa "ina sauraranka" Gyara zama Daddy yayi yana fuskantar Mami, fuskarsa ba wasa. Ya ce "wannan dai yarinyar da kike gani y'ar uwata ce domin ko d'iyar k'anina ce, wacce can baya naso amsarta tun tana jaririya, to yanzu ma na taho da ita ne domin na rik'eta, ta samu ilimi, a takaice dai ta dawo nan da zama dundundun" "Daddy kamar ya ta dawo da zama dundundun ban fahimce ka ba?" Murmushi ya saki yana harbo jirginta yana cewa "kamar yadda kikaji na fad'a, ai ba wani yare nayi miki magana dashi ba, kuma nasan kin fahimce mi nake cewa, dan haka na gama yanke hukunci, ai dai gidana ne, kuma y'an uwana suna ikon duk sadda sukazo su zauna a cikinsa" "Amma dai gaskiya ba'a nan gidan ba, haka kawai bansan yarinya ba, bamu san halinta ba, kawai ka wani kwasota wai ta zauna tare mu" Mami ta fad'a cike da jin haushin Daddy, tana banka ma Marmah dake jin komai harara, zuciyarta sai bugawa take cike da tsoro. Daddy daya tashi yana sake jaddada mata cewa, "na gama maganata, ku kuma" Ya nuna su Ifteesan dake zaune wajan har yanzu sun kasa kunne suna sauraro, ya nunasu da yatsa yana cewa "karna ji wani abun wulak'anci ya fito daga wajanku, a tare da Marmah, kuma ku nuna mata, d'akinta dake kusa da naku, a sama" Yana gama fad'ar haka ya juya yana hayewa sama, yana cema Marmah ta shirya da anjima, zaisa driver ya kaita tayo sayayya. Ai ko yana shigewa, Khairat tayi saurin cewa "wai Mami kinji mi Daddy yake cewa, wai a bata d'aki kusa damu, kenan kamar matsayinta d'aya damu, gaskiya ni bazan zauna waje d'aya da ita, jibeta fa wata y'ar K'auye k'azama da ita" "Kema kenan ni gaskiya bana had'a hanya da irinsu, dan ina kallonsa kamar zubar da daraja ne" Ifteesan ta idasa fad'ar haka, tana makama Marmah harara. Marmah tayi saurin kallon jikinta, ita dai bata ga wata k'azanta ba. Mami dake kallon Marmah ta ce "dalla ku rabu dashi, ba gidan ubanda zata zauna min a sama, d'akin dake k'asa na saukar bak'i a nan zata zauna, ina laifi ma" "Yauwa Mami hakanma yafi wallahi, ke tashi ga d'aki can ki shiga nanne d'akinki" Khairat ta fad'a tana jefama Marmah wani banzan kallo. Marmah tashi tayi jikinta a mugun sanyaye, tana son b'oye hawayen dake neman zub'o mata, tana gaf da shigewa, Mami ta dakatar da ita da cewa, "Kee ki bud'e kunnanki da kyau kijini, ba hutu ya kawoki gidan nan ba, aiki zaki fito duk abunda yarana suke so ki tabbatar kinyi shi, karki sake a kawo min k'ararki, dan haka saiki kiyaye, idan kinyi masu laifi kuma, bazan hana su hukuntaki ba, babu ruwana dan haka saiki kiyaye, and kuma ki tsaya iya matsayinki, bana son shishshigi, a harkar gidana, zaki iya wucewa ki ba mutane waje" Da sauri ko Marmah ta shige d'akin, tana sauke ajiyar zuciya, dan Allah ya gani ma wata irin shakkar Mami take, dan Mami tunda take mata magana fuskarta a murtuke, babu wasa, ga wani kallon k'ask'anci da suke jefa mata, duk sai taji ta muzanta. Kallon d'akin tayi ita harga Allah, d'akin yayi mata shegen kyau, tunda ga katifa babba a k'asa da waduruf harda madubi, sai toilet, ita gani take wannan ma ya isheta, ba abunda ya mata dad'i ma irin yadda Daddy yayi mata albishir d'in sata makaranta, yafi komai mata dad'i, shi yasa data tuno saita manta da abunda su Mami sukayi mata. Sai wajan yamma Daddy yasa akai Marmah shopping, yasa Tala ta raka ta, mai aiki, ai ko a cikin motar, Tala da surutun tsiya sai labari take ba Marmah, har suka d'an saba, koda sukaje shagon sayayya Marmah kasa daukar komai tayi, saita zama bak'auyar k'arfi da yaji, ita dai ba sanin wasu kaya tayi ba, bare harta zage ta zab'a, sai Tala ce ta zage tana zab'ar mata kaya masu mugun kyau da tsada, tunda saida Daddy ya gaya mata y'ar uwarsa ce, ai ko ta zab'ar mata kaya masu mugun yawa, dan har saida Marmah ta kwab'eta da cewa ta barso haka, ai sunyi yawa ma kayan, tukun Tala ta dakata, da jidar kayan. A gajiye suka dawo gida kai tsaye d'akin Marmah aka wuce da kayan. Bayan Marmah ta huta, tana zaune tana kallon kayan cike da farin ciki take d'agasu, sai murna take, kawai taji an banko d'akin ko sallama babu, Mami ce da y'ay'anta biye da ita, zabura Marmah tayi ta tashi tsaye gabanta na fad'uwa. Marmah bata san hawa ba bata san sauka ba, taji Mami ta tsinka mata mari tana nunata da yatsa tana cewa "wato kinga kud'in banza kenan?, shine yasa kikaje kika jido wa'innan uba-uban kaya, saboda kud'in bana ubanki bane, baki san ciwonsu ba" Kuka Marmah ta saki tana girgiza kai, kamar ta sani take ma Tala fad'an kayan sunyi yawa. Canta ta tsinkayi maganar Ifteesan dake d'aga kayan tana cewa "kan uban can, Mami, wai kinga tsadar kayan nan kuwa?, ai komu iya kayan da muke sawa kenan" "Kwasu min rabin kayan masu tsadar ciki, ku barma matsiyaciyar, sauran, na rantse baki sa kayan nan duka, idan ba halin tsiya zaki nuna ba, miye na daga zuwa, har kinsan ki zab'o wa'innan kayan, wato ke idonki a bud'e yake kenan, munafuka, kin wani tsare ni da ido" Mami ta idasa fad'ar maganar tana jefama Marmah wata uwar harara, Marmah dake girgiza kai tana son yin magana, domin kare kanta, Mami ta kwatsa mata tsawa da cewa, "Dalla rufe min baki munafuka, ubanmi zaki ce min?, ke gaki kinga dukiyar banza ko?, to ta Allah ba taki ba, duk wani mugun sharrinku ya koma muku, idanma turoki danginsa sukai, kiyi barbad'anci dasa ido" Har suka gama mata wulak'anci suka kwashe kayan Marmah bata k'ara yunk'urin magana ba, suna fita ta zube kan katifa tana rusa kuka..................✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 16 Da kyar Marmah ta tashi ta shiga toilet ta wanke idonta daya kunbura saboda kukan data sha, bata k'ara fita koda parlo bane, tana rakub'e a d'akinta, abinci ma sai dai Tala ta kawo mata, tana nuna tausayinta danta ji abunda su Mami sukayi mata, taita ba Marmah hak'uri. Marmah ko murmushi kawai tayi, inda sabo ta saba da irin wannan wulak'ancin tun a garinsu, tunda inda ta fito d'inma da yawan mutanan can kyararta suke, to danmi zata ji haushi?, kawai zuciyarta mai saurin rauni ce, kuma dama tana da saurin kuka. Washe garin ranar Marmah wani mugun bacci ya d'auke ta, bata san ma gari ya waye ba, saboda taji dad'i canjin wajan kwana data samu, da a k'asa take kwana, laushin katifa yasa ta makara, tunda tayi sallar asuba ta koma bata tashi farkawa ba, sai da taji saukar ruwa a jikinta. A zabure ta mik'e tana bin Ifteesan data watsa mata ruwa da kallo, itama dake mata kallon wulak'anci. "Ke kwanciyar ubanmi kike har yanzu?, Ohho an samu katifa mai laushi, abunka da ba'a sababa, to bari kiji na gaya miki, daga yau bacci bai kama ki ba, gyaran d'akinmu da wankin toilet ya dawo gareki, kamin mu tashi a gyara mana toilet a wanke sa sosai, domin bamu son k'azanta, and abu na biyu, ki tabbatar kin shiga kitchen kina taya so Tala aiki, yanzu ma nazo ne in sanar dake, na tarar dake kina bacci kega isassa, maza kije ki wanke mana toilet, kin wani b'ararraje kina sharar bacci, ai bacci ba naki bane yarinya" Ifteesan ta idasa maganar tana juyawa zata fice tana gaf ficewa ta k'ara wace "ki tabbatar kin wanke toilet d'in nan da kyau, idanma baiyi ba, wallahi sai kin mai-maita sa" Marmah bata ce komai ba, da sauri ta shiga toilet d'inta ta wanke bakinta, ta fito da hanzari, ta haura sama, inda take da tabbacin nanne d'akinsu, ta shiga, kallon d'akin take, duk had'uwar d'akin a hargitse yake, ko ina kaya a watse, ba kintsi, sai kace ba mata ke kwana a d'akin ba. Bata tsaya komai ba ta fara gyaran d'akin, tukun tana gamawa ta shiga toilet shima ta wanke sa tas, a d'an k'ank'anan lokaci ta gama gyara masu d'akunan su, dan ita irin wannan aikin baya d'aga mata hankali tana yin wadda yaci uwarshi a garinsu. Koda ta sakko ba kowa a parlon kitchen ta shiga suka gaisa dasu Tala, suna labari tana taya su aiki, har suka gama suka jera a darning table, ita kad'ai ce a parlon bayan ta kawo wata kula ta ajiye a darning d'in, taji sallamar Y Khaleefa, cikin siririyar muryarsa. Sanye yake da wasu farin yadi sai hula dake kansa sunyi mai masifar kyau kwarjinisa ya sake fitowa, tunda taimai kallo d'aya suka had'a ido, tayi hanzarin janye nata, shi ko idonsa na a kanta, yadda yake karantar tsanin nutsuwarta, gaida sa tayi, bakinta na rawa, saboda jikinta ya bata har yanzu kallonta yake. Zuwa yayi ya zauna kan darning d'in, sana ya amsa gaisuwarta, can ya dube ta ya ce "wannan d'in aikinki ne?, waya saka ki?, kin manta matsayin ki ne?" Shuru tayi mai, kallonta yayi ya tsareta da ido. Ya sake cewa "Hajiya am talking to you fa?" "Aikin ne nake sonyi amma babu wadda ya sani" "To daga yanzu karki sake yi, ki rink'a tunawa da ko wacece ke" "Amma fa na sabayi a gida, wannan d'an aikin ai ba komai bane, bana jin dad'in zaman haka nan" "To ubanta ina ruwanka da aikin da take yi?, baka ji mita ce bane?, ta saba wahala a can K'auyen nasu, kuma ni ce nan na sata" Cewar Mami dake sakkowa k'asa, bayan taji wani abunda Khaleefa yake cewa, karasowa tayi ta zauna akan darning d'in. Tana sake duban Khaleefa tana cewa "wai tsaya inama ruwanka da ita?, kaida ba shiga harkar mutane kake yi ba, dan haka bana son wannan shishshigin da ka fara yi mata" "Amma Mami" Shuru Khaleefa yayi ganin ta d'aga mai hannu. Ta ce "amma mi?, bana son jin komai" Daddy dasu Khairat ne suka iso wajan darning d'in a tare, kowanne ya samu waje ya zauna. Marmah dake tsaye ta gaisar da Daddy yana amsa mata cikin fara'a, yana tabbayarta ya kwanan bak'unta. Mami sai kallonsa take cike da jin haushi ganin yadda yake wani sakar mata fuska, yana wani washe mata baki. Mami takai dubanta ga Marmah ta yatsine baki tana cewa "to Malama tsayuwar mi kike mana a kai?, ki wuce kiba mutane waje, kin wani tsatstsare mutane da ido" Daddy dake kallon Mami yayi sauri cewa "ban gane tsayuwar mi take mana ba?, ke Marmah zu ki zauna tare damu, na ce miki kamar gidanku ne nan" "Kamar ya Alhaji ta zauna kusa damu taci abinci?" Cewar Mami dake jefama Daddy kallon takaici. Su Khairat suma jin haka yasa suka tsayar da cin abincin suna sauraron mi Daddy zai ce, Khaleefa ko daga kallesa zaka gane baiji dad'in abunda Mamin take ma Marmah ba, ko banza ai yanzu matarsa ce, anya ma Mami zata amita da Marmah a matsayin matarsa kuwa?, yana tsoron ranar da zata sani ne, Allah kad'ai yasan rigimar da za'ai, duk da baya jin komai game da Marmah, bare yaji yana sonta, kawai tausayinta yake ji, dan yaji labarin irin wahalar data sha wajan Mlm, inda yake mai nasihar ya kula da ita, yaji tausayinta, tunaninsa ne ya katse jin abunda Daddy yake cewa. "Kamar yadda kikaji na fad'a" Ya sake kallon Marmah dake shirin barin wajan, karma ace ita ta had'a su fad'a, Daddy ba wasa a fuskarshi ya ce "ke Marmah dawo ki zauna, kici abinci damu, duk wadda yaga bazai iya zama tare da ita ba, yana iya tashi" Ba yadda ta iya ta dawo taja kujera, a hankali kamar mai tsoron duka, kwata-kwata sai taji ta takura tama kasa cin abincin, ita da Daddy ya kyaleta wallahi, bata saba zama irin haka taci abinci ba, ga kallon da su Ifteesan ke jefa mata, duk sai ta sargu. Ganin yadda Daddy yasha mur yasa ita kanta Mami bata sake cewa komai ba, haka dai suka ci abincin ba walwala a fuskarsu, ita ko Marmah da kyar tayi loma uku kwakwkwara. Su Ifteesan na shirin tashi domin wucewa school, da yake BUK suke yi, sun kusa had'a degree d'insu, suka ji Daddy na cewa, "Yauwa Khaleefa ina so yau kaje kasa Marmah islamiyar su Ifteesan, inda suke zuwa, boko kuma, sai kaje secondary d'in da su Ifteesan suka gama ka sata, nasan za'ayi mata enter biyu, idan sukayi mata, sun son class d'in daya kamata su ajiyeta" Da to Khaleefa ya amsa. Sosai fa abunda Daddy ya ce yaba su Khairat haushi, islamiyarsu kuma, wannan ai sai dai ajeta a ajin y'an koyo, ko a bokon ne kuwa, ficewa sukai suna hararar Marmah, da bata san sunayi ba, ita ko sai murna take, itama ta tashi ta shige d'akinta, domin shiryawa. Daddy yaga d'akin da Marmah ta shiga tuni kawai yayi shuru ne, dankar yaja ma Marmah wata tsanar wajan Mami. Mami data cika tayi fam, ta kalli mijinta, cike da takaicinsa yadda ya fifita wata akan yaransa, yana son saiya maidata matsayi d'aya dasu. Ta ce "haba Daddynsu Khairat wane irin kuma makarantar da y'ay'anka sukayi zaka ce a sata, ina laifin a sata ta gwamnati, wannan school d'in da kake biyan kud'i da yawa haka" "Hmmm Bilkisu kenan, itama ba y'ata ba ce?, kamar yadda zan iya kashe musu ko wana ne dan suyi karatu, to itama haka zan iya kashe, ko wana ne domin ta samu ilimi, kin mata wai matsayinta a waje na ne?, dan haka Bilkisu bana son irin haka" Shuru tayi cike da jin zafin amsar daya bata, ba yadda ta iya, domin tunda taji ya kira sunanta, kai tsaye tasan ba wasa yake ba..............✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 17 Marmah ce ke fitowa da sauri saboda zumud'in za'a kaita school, ta taho da sauri bata lura ba, Mami ma ta taho, itama tana tafiya da k'arfi kamar zata tashi sama, kawai sukai karo. Cike da tsananin tsoro Marmah taja baya, zata bud'e baki domin bata hakuri, kawaii taji saukar mari, hakan fuskarta, runtse idonta tayi, tana sa hannunta ta dafe inda ta mareta, wasu hawaye suka wanke ma Marmah fuska. Jin wata tsawa data buga mata tana cewa "keeeee dabbar ina ce?, ni sa'arki ce da zaki bangaje ni?, na taho kin taho, bazaki ban waje na wuce ba, saboda dama marar tarbiyya ce ke?, shashasha marar kunya kawai, mai ido a sakar ka" Daddy dake kallon komi ke faruwa, ya had'e wani abu mai d'aci a zuciyarsa, hucewa tayi kanta kenan, kallon Khaleefa yayi yana mai alamar yaje ga Marmah so wuce. Tashi Khaleefa yayi cike da tausayin matarsa, ya matsa kusa da ita, yasa hannunsa ya kama nata hannun, suka fice daga gidan, kai tsaye mota suka hau suka fice daga gidan. Suna tafiya a mota, Marmah na share hawaye, ba tayi tsammani ba, taji hannunsa cikin nata, yana d'an murza y'an yatsun hannunta, wani irin abu taji ya fara yawo a jikinta, lumshe idonta tayi, wasu sabbin hawaye na sake zubowa, baice mata komai ba, saboda shima ba gwanin magana bane, idan kinga yayi magana mai tsawo to Mami ce, take ja, domin Mami irin matan nanne masu saurin fushi da fad'a, sai ko idan magana da wani ta zama dole yake yi. Islamiya suka fara zuwa, nanma saida akai mata enter biyu, sosai Malaman sukai mamakin iliminta da k'ok'orinta, inda har suke tabbayar Khaleefa, cewa "gaskiya wannan k'anwar taka akwai hazak'a, wannan ai sai dai a d'auketa Malama, idan an bamu dama, dama gashi bamu da Malamai mata da yawa, domin gaskiya tana da sani sosai akan karatun addini, zata bada gudunmuwa, ga d'alibai, dan enter biyun da nai mata, tana da sani akan sauran littatafai addini" Sosai shima Khaleefa ya cika da mamaki, ashe dama da iliminta har su Khairat ke mata kallon sama-sama, sosai ya cika da farin cikin samun mata kamarta, lokaci d'aya yaji zai iya zama da ita ko a yanzu ne, lokaci d'aya yaji ta shiga zuciyarshi ta zauna, yana son mace mai ilimin addini, sosai, tabbas maganar Mlm da yake cemai bazai tab'a dana sanin auran Marmah ba, domin ya yarda da Marmah d'ari bisa d'ari. Ai ko nan take Khaleefa ya bada damar zata rink'a zuwa domin koyawa d'alibai, amma sai asabar da lahadi, ranakun dasu Ifteesan ke zuwa suma, za'a rink'a kawosu tare, sosai Malaman sukai godiya, inda za'a rink'a biyanta, albashi, ko yaya ne, da Khaleefa yaso subar wani albashi, kyauta zata rink'a koyawa, sai dai Malaman sun nuna basu yarda ba, dole tasa ya amince haka. Wajan Marmah ma sosai abun yayi mata dad'i, dama tasan k'ila suce hakan, domin bata zauna haka ba, babu inda bata zuwa domin daukar karatu, hatta Mlm tana zuwa wajansa domin sanin wasu littatafan addini. A bokon ma dai taci enter biyun domin su kansu Mlmn sun jijjina mata, inda kai tsaye aka ajeta SS2, aka mata komai daya danganci school hatta kayan school d'in komai da zata buk'ata sai da aka bata, sana suka taho gida, basu isa gida ba, sai da ya biya wani shago da ita, yayi mata sayayyar kayan ciye-ciye, ai ko sosai tayi murna tana mai godiya, shi ko sai kallon kyakkyawar fuskarta yake yadda take murmushi mai zautar mai da zuciya, sai yaji shima yana cikin wani irin yanayi, yadda ta sake dashi sai surutu take mai, bai hanata ba, bai kyareta ba, itama sai yasa ta k'ara sakin jikinta dashi, tana bashi labarin rayuwar data yi, harta gangaro labarin Abbas da yadda aka rabasu, tana kai iya ta fashe da kuka mai cin rai, daya sa Khaleefa tsayar da motar, ya gangara bakin titi, jawota yayi jikinsa, ai ko ta kwanta luf tana sauke ajiyar zuciya, k'ak'k'amesa tayi tana jin wani irin abu a zuciyarta game dashi, d'agota yayi, ganin hawaye na zuba har yanzu, batai aune ba yasa harshensa ya fara lashe mata shi tas, lumshe ido tayi, sai da ya gama yabi fuskarta da kallo, wani abu na fisgarshi gareta, har baisan sadda ya had'e bakinsu waje d'aya ba, Marmah jin sabon abu a gareta yasa jikinta fara rawa, hannunta dake jagaye da jikinsa tasa ta k'ara damk'e rigar dake jikinsa, tun tana mutsu-mutsu harta daina jikinta ya mutu, sai da ya gaji dan kansa ya saketa, suna suke ajiyar zuciya a tare. Komawa yayi ya jingina da kujerar motar, yana suke lumfashi, idonsa harya suke launi, kallonta yayi da idonsa masu kaifi da suka fara shiga wani yanayi, da sauri ta sauke idonta a k'asa tana wasa da y'an yatsun hannunta, wata irin kunyarsa ta saukar mata. Can taji muryarsa mai matuk'ar sanyi da dad'in sauraro yana cewa "ki kwantar da hankalinki, ki daina tunanin wani, yanzu aure ne akanki, kuma insha Allahu zansa ki manta da wai ma kin tab'a son wani, idan bani ba, zansa miki sona a zuciyarki insha Allahu rabbi, kamar yadda zan koyawa kaina sonki, dan har na fara jin wani abu dangane dake" Ya idasa maganar yana suke lumfashi, saboda dogowar maganar da yayi, itama kanta tayi mamakin maganar dake fitowa daga bakinsa. Suke ajiyar zuciya tayi a hankali tana cewa "ai ni tuni na fidda Abbas a cikin rayuwata bare kuma a cikin raina, kawai na tuna da abunne harna baka labari" Shuru yayi bai k'ara magana ba, saima tadar motar da yayi suka cigaba da tafiya, itama kama bakinta tayi ta tsuke, dan tasan ba lallai ya sake magana ba, kuma, ai tama yi mamakin doguwar maganar da yayi yau a tare da ita, lallai yau ta ciri tota. Har suka isa gida, ita ce ta fara fita, ta nufi babban parlon gidan, koda ta shiga da kayan school d'inta a hannunta tayi karo da su Khairat na zaune a parlon, daga ganin alama sun dawo school ne, suka zube a parlon. Kallonta sukai Ifteesan ta ce "kee zo nan" Zuwa Marmah tayi ta ce "gani" "Yauwa ina so ki shiga kitchen ki had'a min abinci kala uku, da lemo mai dad'i, zanyi bak'o ne wadda zai aure zai zo, dan haka karki sake kiyi min shirme, kin gane ko?" Amsawa da kai kawai Marmah tayi. Ifteesan cike da jin haushinta yadda ta wani amsa mata da kai yasa cikin fad'a ta ce "baki da baki ne?, da bazaki amsa min ba?, ko tsabar kin fara raina mutane?" "To baza tayi ba, marassa kunya kawai, ke bazaki iya shiga kitchen d'in kiyi masa girkin ba, tunda kece wacce zatayi bak'on, idanma bazaki iya ba, kisa su Tala suyi miki mana, dole sai Marmah ce zatayi, ko kun manta matsayinta a gidan nan ne, matsayinku fa d'aya ne, babu wani babbanci, ai ba y'ar aiki bace dan haka bazata yi ba, wallahi kafin nabar garin nan na koma wajan aiki, k'ila sai na koya muku hankali, kun girma amma gaku nan babu tunani" Y Khaleefa ya idasa fad'ar maganar da shigowarsa kenan yaji maganar da suke mata, yana jefa masu harara, ai ko ba shiri suka tsuke bakinsu suka yi shuru. Tsaki yaja zai juya ya tafi, Marmah dake shirin barin wajan gabanta na fad'uwa, dan Allah ya gani ita tana jin tsoron taji suna fad'a a kanta. Suka cinkayi muryar Mami na k'arasowa wajan tana nuna Marmah tana cewa, "tsaya na ce munafuka" Tsayawa Marmah tayi gabanta na dukan uku-uku, shima Khaleefa ba shiri ya dagata da fita. Mami ta juyo wajan Khaleefa tana cewa "wai kai ban gane mi kake nufi da wannan yarinyar ba, mi yasa kike shiga harkarta ne haka?, ko akwai wani abu a zuciyarka dangane da ita?, ko kyanta ne ke rud'arka?, to bari kaji na gaya maka, wallahi idan ma akwai wani abu ne, a ranka, zuciyarka ta fara d'arsa maka a kanta, tun wuri ka gargad'i zuciyarka to, domin bazan tab'a lamunta ba, ka sani basai na sake fad'a maka ba, kuma daga yau karna sake jin ka shiga harkar wannan yarinyar, kuma aiki ne saita yi shi a gidan nan, tunda ba gidan ubanta bane, kuma da kike cewa wai matsayinsu d'aya, ta ina suka zama matsayi d'aya?, sufa gidan ubansu ne, itafa?, daga cin arzik'i" Mami ta sake juyowa ga Marmah da kanta ke k'asa tana had'iye wani abu mai d'aci a zuciyarta, taji muryar Mamin na sake ce mata "ke kuma daga yau dan Allah su saki aiki bakiyi ba, kiga yadda zanyi dake a gidan nan, sana kikai kayan nan naki, kizo ki wuce, ki fara aikin data saki" Da sauri Marmah tayi ciki tana aje kayan ta fito ta wuce kitchen domin fara aikin, itafa dan aiki baya b'ata mata rai, da Y Khaleefa zaiji maganarta daya barta tayi masu aikin, bafa raguwa tayi ba, saima k'aruwa da tayi, suda basu iya komai bafa, a haka za'aje gidan miji, ai ko tana tausaya musu, domin mazan yanzu sunfi son matansu su rink'a masu komai, bawai y'an aiki ba, ba komai zaka sa y'an aiki suyi maka ba, bare kuma hidimar mai gidanka. A parlo kuwa Khaleefa ji yake kamar ya bud'e baki ya ce ma Mami ai yanzu matsayinta ma ya d'ara naso, tunda matarsa ce, amma saiya taushi zuciyarsa, tunda dai Mahaifiyarsa ce, ya bata hakuri, yana ficewa daga parlon. Su Ifteesan ko dad'i ne ya rufe suna rungume Mami. Mami ce ta kalli Ifteesan ta ce "ya akai baki sanar dani zakiyi bak'o ba?, da bansa anyi shirya wani abu wadda yafi wadda kikasa ayi masa ba, mi yasa baki sanar dani tun wuri ba?" "A'a wallahi Mami nima sai muna hanyar dawowa daga school ya kira ni yake shaida min, wai zaizo ya gaida ku ne" "To ai kinga Daddynku ma baya nan, da kin sanar tun wuri, ai bazai fita ko ina ba, dama burinsa ku fidda miji kuna gama school ayi bikin" Sauke ajiyar zuciya Ifteesan tayi tana gyara zama tana kallon Mami ta sake cewa, "Eh kuma hakane, bai sanar dani da wuri bane, amma Mami ki kira Daddyn mana zai baro wajan aikin yazo" "Eh kuma hakane bari naje sama na kira shi, namai albishir, ke kuma Khairat sai yaushe ne naki zai kawo gaisuwar?, so nake asa muku rana a tare" Mami ta idasa maganar tana kallon Khairat dake latsa waya. "Hmmm Mami shima yana nan zuwa, kinsan Abuja yake aiki, daya shigo Kano to danni yake zuwa, zai zo very soon" "To shikenan Allah ya nuna mana" Da amin suka amsa, tayi sama domin kiran Daddy ta sanar dashi................✍️ *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 18 Marmah na gama girkin, su Tala suka taimaka mata suka jerasa darning table, saboda basu san inda zasu ajeshi ba. Shiga d'akinta Marmah tayi tana zama tad'an huta domin ta gaji sosai, tashi tayi kawaii ta shiga wanka domin jin kiran salar la'asar, tana cikin yin wanka taji kamar shigowar mutum. Can taji muryar Ifteesan tana cewa "wai kina ina ne?, ya za'ai ku aje min abincin bak'o a babban parlo, parlon bak'i ya kamata aje min abincin" Ta idasa maganar dai-dai Marmah na fitowa daga toilet, wata harara Ifteesan ta watsa mata, da yasa da sauri Marmah ta ce "kiyi hakuri, bamu san inda ya kamata mu aje bane, shine yasa ana gamawa aka ajeshi akan darning" "Mine-mine, sai ana magana, kiyita sukuyar da kai, kega munafuka, to idan kin gama sai zo ki kwaso su, ke d'aya nake so ki kawo minsu parlon bak'i, domin bana son ana min shiga da fice bak'o na ya iso, fatan kin saurari mi nake cewa?" "Eh naji kuma yanzu zan fito" Marmah ta k'are maganar cike dajin haushin ce mata munafuka da tayi. Su Ifteesan anci uban wanka, ana zaune a parlon bak'i, da wani saurayi, yaci uban wanka da manyan kaya, sai wani shishshige mata yake, suna zaune kujera d'aya da juna, kamar zasu had'e da juna, sai jefa mata wani shu'umin kallo yake, kai ka rantse da Allah bai saba ganinta bane, yadda yake binta da kallo. Harsai da Ifteesan cike da yanga ta ce "Ohh my Abdul, wannan kallo haka, sai kace yau ka fara gani na" "Yaushe rabon dana ganki, ai na dad'e sai dai ta waya fa, muna gari d'aya amma bakya son gani na" "A'a fa ba haka bane kasan yanayin Daddynmu ne sai a hankali, baya son wasa, yanzu ma dan ka shirya aure ne, yasa na barka kazo, idan ba haka ba, Daddy zai tamin tabbayoyi ne, idan yaga zuwanka, shi yasa ba wadda muke ba damar zuwa gidanmu, wai da sunan zuwa zance" "Hakane kuma yana da gaskiya, kuma very soon na shirya auran ki" Ya idasa maganar yana jefa mata murmushi yana kamo hannunta yana murza y'an yatsun hannunta. Suna cikin haka Marmah tayi sallama ta shigo kanta a k'asa tunda ta shigo idonta yayi mata tozali da yadda suke zaune kamar zasu manne da juna, ga hannun Ifteesan dake a hannun saurayin. Marmah ta girgiza kai tana ganin hakan ba waye wa ba ce, a yadda suka zauna ma kwata-kwata bai dace ba wallahi, koda yake daga ganinsa da tayi idonsa shima a bud'e yake, daga shi har Ifteesan d'in, su gani suke nan waye wa ce. Haka dai ta gama kawo abunda zata kawo ta gaida shi, ya amsa yana binta da kallo harta fice. "Amma dear wannan kuna kuma, ko y'ar uwarki ce? ban santa ba" Yamutse fuska Ifteesan tayi tana cewa "wallahi y'ar aikinmu ce" "Kai amma nayi mamaki batai kama da y'an aiki ba bare y'an K'auye" "Ai ko y'ar K'auyen ce, kaga dan Allah dai min zancan ta" Basarwa yayi ganin ranta ya b'aci danda nan ya sakko da ita, suka cigaba da soyayyarsu. Koda aka gayama Daddy da farin ciki ya iso, Ifteesan tayi mai iso shida Y Khaleefa, suka gaisa sosai da Abdul, Daddy yayi mai tabbayoyi yana basa amsa, inda Ifteesan ta basu waje domin su tattauna. NARNAH POV Zaune take a parlonta, tayi uban tagumi, yau kusan wata uku da auransu da Abbas amma kullum ba ranar banza da bai zai zo mata cikin dare a buge ba, kuma kusan kullum saiya mata dukan kawo wuk'a, duk jikinta tab'on duka ne, duk ta rame ta lalace, kuma kwata-kwata ya hanata fita koda k'ofar gida ne, shi yasa yau da gobe asirin da suka mai ya sake shi, sai dai abunda ba'a rasa ba, gashi kayan abinci sun k'are dama tun na auransu ne, garar da aka had'a mata ce, ta k'are kuma yak'i kawo kayan abinci, kullum sai garin kwaki da take ci shima yau ya k'are. Hawaye ne ke mata zuba a fuska, dafe cikinta tayi dake kukan yunwa. Jin motsin mutum yasa a zabure ta tashi dan tasan bamai shigo mata a yanzu sai shi, domin ya hana kowa ya rab'eta. Shigowarsa yasa ta zube a k'asa tana ruk'onsa cewa "dan Allah ka bani abinci wallahi yunwa nake ji, sana ka barni naje na gano Umma ta, tana cikin wani hali bata da lafiya fa" Wani banzan kallo yayi mata, baice mata komai ba ya fice ya dawo, sai gashi ya shigo rik'e da kofi a hannunsa, zama yayi kan kujera, yana mik'a mata kofin. Kallon cikin kofin tayi ganin garin kwaki a jik'e harda gyad'a ciki, yasa ba shiri ta fara sha, sai dai mi?, loma d'aya takai bakinta ta furzo da ita, a gigice tana kallonsa. Ta ce "Abbas garin kwaki da gishiri ne fa" "Kuma a haka zaki shanye sa tas idan ba haka ba, kinsan sauran wallahi, kuma da kike cewa wai uwarki bata da lafiya, duk ba ita ce ta raba ni da Marmah ba, abar k'aunata, bazan tab'a yafe muku ba, ke baccin ina son d'aukar fansa a kanki, da tuni na sake ki, domin babu digon sonki a raina, kuma bazan tab'a sakinki ba, haka zaki zauna, cikin K'ANGIN RAYUWAR dana saki, itama Mahaifiyar taki abunda ta shuka ne take girbewa tun a nan gidan duniya" Shuru Narnah tayi tana jin wata nadamar auran Abbas data yi, tana nadamar kwace ma Marmah shi data yi, yanzu wa gari ya waya?, yanzu data je ta sami wadda yake sonta tsakani da Allah da duk hakan bata faru da ita ba. Wata tsawa daya daka mata yana cewa "maza ki cinye sa na ce, kuma aure zan k'ara domin bazan iya zama dake ke kadai ba, wacce nake so zan auro" Wani sabon tashin hankali ne ya ziyarci Narnah, ba shiri ta fara tusa garin kwakin tana ci tana kuka, bakinta ba abunda yake sai zafi da zugi, ga cikinta dake murd'awa yana mata ciwo kamar zata shid'e, danda nan ta fara amai, har a jikin Abbas, tashi yayi ba shiri baiyi wata-wata ba, ya tsinka mata mari mai zafin gaske, har saida ta wuntsila, sai gata cikin aman dame-dame, tana kuka, wani dogon tsaki ya kuma ja, yana tsallake ta ya fice da gidan, nan barta tana rusa uban kuka, ta rasa inda zata fara, ga ciwon Mahaifiyarta, da y'an gidansu suke zuwa, domin kawo mata tsegumi, ta rasa inda zata sa kanta taji sanyi. Ita kanta Hajara hankalinta a tashe yake, abubuwa sun taro sun mata yawa, kullum tana aika wa aje aga wane irin hali d'iyarta take ciki, dan duk wacce tayi aure a gidan, tazo gida, kuma da abun arzik'i ga iyayansu mata, sosai fa hankalin Hajara ya tashi da irin labaran da ake kawo mata dangane da irin zaman da Narnah take yi a gidan Abbas, ga wasu irin k'uraje dake feso mata a gabanta, wadda yasa Hamza gudunta ko inda take baya son zuwa, duk wani tsoronta da yake ji yanzu babu shi, shi yasa data bi ta tada hankalinta, dole saita je gidan Narnah, ya hanata ya ce mudun taje bada yawunsa ba, indai taje daga nan karda dawo gidansa, shi yasa hankalin uwa da d'iyarta a tashe yake kullum, ga ciwo dake cin Hajarar a tsaitsaye, k'uraje kullum k'ara fesowa suke a gabanta, ko a gaban waye sai kiga tasa hannu a gabanta, tana sosawa tana kartar gabanta, wajan harya fara rub'ewa ya fara jagwalewa, wannan ciwon yasa Hajara fara sakin maganganu barkatar, kanta ya fara samun tab'uwa, duk wani laifi da ba'asan tayi ba,ta fara bankad'o shi, yau hankali gobe babu, mutanan gidan yanzu kam basa shakkarta, saima kyararta da suke suna gudunta, data zo waje za'a tashi saboda warin da take, gashi Hamza na shirin yin aure, abunda ya k'ara hargitsa kwanyarta kenan, kuma Mlm ne ya hana Hamza sakinta da tuni ya saketa saboda, bazai iya rab'arta da irin warin da take yi ba. Hamisu ko ba laifi Habiba ta d'an canza shi, sai abunda ba'a rasa ba, amma sun rage rigimar da suke sosai ada can................✍️ *And ina so na sanar daku duk wadda yake son ayi tafiyar book d'in nan dashi book 1 ya kusa k'arewa, daga na 20 za'a shiga book 2, tohm gsky book 2 na kud'i ne naira #500 ne kacal game buk'atar book 2 akwai sa complete a yanzu haka d'aya turo kud'insa zan tura masa ni kuma Kai tsaye idan kana so zaka iya min magana ta wannan number d'in* 👇 08130479973 Ko kuma ka turo kud'inka ta wannan account number d'in 👇 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Saika turo shaidar biya a number Dana aje sama. *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* 19 "Ke bakya gani ne wai?" Cewar Khairat dake sakkowa sukayi karo da Marmah tana shirin zuwa school. Marmah tad'an matsa kad'an ta ce "Ohhh kiyi hakuri dan Allah please banga ni bane" "Ki dai rink'a tafiya a hankali idan ba haka ba, zaki sami mai wanka miki mari ne, mtswwww aikin banza kawai yarinya sai k'iriniyar tsiya, kina tafiya ba kintsi" Ita dai Marmah da sauri ta rab'a ta wuce domin Y Khaleefa ne yake jiranta. Tana fita ta hango shi jingine jikin mota, kallonsa take cike da birgewa, yasha shadda ruwan k'asa tayi mai bala'in kyau, manyan kaya namai kyau sosai kamar mi, k'arasowa tayi tana jefa mai murmushi. Shima murmushin ya sakar mata yana ware mata hannu alamar ta rungume shi, waro ido tayi tana waige-waige, mik'e k'afad'a tayi tana mai alamar kar wani ya gansu. Dariya ya saki yana k'ara mata alamar ta taho gare shi, ganin alamar da gaske fa yake yasa, Marmah ta tafiya a hankali ta isa gareshi, tana k'arasawa ta kwanta a jikinsa, masauki yayi mata akan faffad'an k'irjinsa ya zagaye hannunsa a k'ugunta, tare suka sauke ajiyar zuciya, d'agowa tayi tana kallonsa, bata san sadda ta ce "Y Khaleefa kayi kyau manyan kaya nama kyau sosai" Ja mata hanci yayi na fad'ad'a murmushinsa ya ce "da gaske?", d'aga mai kai tayi, ya sake sakar mata murmushi yana rabata da jikinsa ya ja hannunta suka shiga mota, har suka d'au hanyar school d'in hannunsa na cikin nata. Suna isa dai-dai k'ofar school d'in zata sauka, ya jawota jikinsa yana mata rad'a a kunnanta, yana cewa "kiyi karatu sosai, sana ki rink'a tunawa ke ba kamar sauran y'an matan school d'in bane, ki rink'a tunawa kina da aure, ina da kishi sosai, bare a kanki, ina jin wani irin kishi a kanki, ki kiyaye kinji, y'ar albarka?" Murmushi tayi itama cike da d'unbin son mijin nata, wadda bata san sadda ya shigeta ba, shima kuma haka, lokaci d'aya suka fad'a son juna. Ta ce "tohm insha Allah d'an albarka na" Tana idasa fad'ar haka ta b'alle murfin motar ta fita da sauri, tana d'aga mai hannu, murmushi ya saki yana shafa kansa, girgiza kai yayi yana jin wani irin nishad'i idan yana tare da ita, shifa gaskiya da za'a bashi matarsa su tafi tare, dan gobe ne yake shirin komawa wajan aikinsa, yana buk'atar matarshi kusa dashi, amma yasan hakan bazata yuwu ba, Maminsa ce babbar matsalar. Washe garin ranar da zai tafi da daddare Marmah tasha kuka, duk ya jagwalgwalata da soyayyarsa mai yatsawa a zuciya, dan sashinsa yasa ta kawo mai shayi, yake sanar da ita, ita kanta bata san sadda ta saki kukan rabuwa dashi ba, a daran ya nuna mata so da k'auna kamar ya had'iye ta, shi yasa da kyar suka rabo idonsa yayi jawur shima, duk miskilancin Y Khaleefa ita kam yanzu baya mata shi, kusan zata iya cewa daga ita sai Daddy suke ganin hak'uransa, sai ko Mami, da safe da zai wuce Marmah bata yarda ta fita ba, bare a gane da wani abun, shi ko Y Khaleefa yaso yasata a idonsa kamin ya tafi, gashi ba waya ne da ita ba, sai su Khairat da Mami da suka fito raka shi harya tafi. Kwananshi biyu da tafiya, sosai Marmah take kiyaye duk wani abu dasu Ifteesan zasu kyareta, da wuri take gyara masu d'aki sana driver ya kaita, school, satin Y Khaleefa uku da tafiya yazo garin Kano, ba wadda yasan zai shigo garin yaje har school d'in su Marmah sai dai kawai ta ganshi. Ai ko gaban kowa ta ruga da gudu cike da matsanancin farin ciki ta rungume sa da k'arfi, ta sauke ajiyar zuciya, shima rungume ta yayi yana jin wata sabowar k'aunarta ta rufesa, a yadda yaji bugun zuciyarta kad'ai zai basa amsar tayi kewar sa sosai, da yadda take sauke ajiyar zuciya kad'ai ya isa ya tabbatar ma tana matuk'ar k'aunar mijinta. Kai tsaye hotal ya kama masu, Marmah ta kallesa cike da tsoro ta ce "Y Khaleefa karfa aga na dad'e fad'a za'ai min a gida" "Ba wadda zai miki fad'a insha Allah, nima ke kad'ai nazo gani, daga nan zan juya na koma Abuja" Zaro ido Marmah tayi tana cewa "kamar ya baza ka je gida bane wajan su Mami?", "Yeah ke kad'ai na zo gani" Ya idasa maganar yana jawota ta fad'a jikinsa, wani irin sihirtaccan kallo yake jefa mata, itakam da sauri tayi k'asa da kanta tana kwantawa akan k'irjinsa. Magana ya farayi cike da wata shu'umar muryar mai kamar yana mata rad'a. "I really need my wife by my side, and I feel like I'm gone" Tashi da sauri tana kallon kyakkyawar fuskarsa, hannunta tasa tana shafa sajen fuskarsa, danta kawar da maganar da yayi ta ce "This sergeant is beautiful, I love him" Murmushi yayi yana cewa "mai wayo, hmm ai naki ne ki tab'a yadda kike so" Murmushi tayi tana k'ara fad'awa jikinsa, d'agota yayi suka fad'a kan gado, ya had'e bakinsu waje d'aya. Ganin abun zaiyi nisa, danta lura shi yama manta a inda suke, yasa da sauri Marmah ta kwace jikinta tana sauke ajiyar zuciya. Khaleefa da yayi nisa ya bud'e idonsa yana kallonta, da sauri Marmah ta runtse idonta ganin idonsa yayi ja, tsabar jarabar dake taso masa, ga wani ciwon mara dake taso masa, sai zufa ke yanko masa, duk sanyin AC dake d'akin, shima kansa yafi so a kawota gidansa abun sai ya fi mai dad'i. Kallonta yayi yana had'e wani abu a mak'oshinsa ya ce "Please come and find peace, I have nothing to say to you, but please find peace for your husband" Tausayi ya bata ba shiri ta matsa kusa dashi, da kyar ta cire kunya, amma wani abun saita runtse idonta saboda bata sababa kwata-kwata da wannan irin abun, saida ta tabbatar ta samamai natsuwa sosai, sai albarka yake sa mata. Da kansa ya maida ta har k'ofar gida ya bata wata waya iPhone 7 ta rik'e ko sun rink'a waya. Daga cikin motar ya lek'o yadda yaga idonta ya ciko da hawaye yasa yasa ya jawota cikin mota. Yana ce mata "Oh my baby, don't cry and here's the phone, we'll say hello and if you want to see me, tell me and see me, and bana son na ganki haka" A shagwab'e ta ce "I won't cry because you don't want me, but I will miss you so much" "Wow da gaske zakiyi Miss d'ina" Cewar Y Khaleefa yana jan hancinta, yana kallon yadda take mai shagwab'a, yana matuk'ar son mace mai shagwab'a. Da kyar suka rabu, sana ya juya ya koma, ji take kamar karya tafi, shima a wajansa hakane, daurewa kawai yayi. Wayar tasa a school bag d'inta sana tayi sallama a parlon gidan, birki taja ganin Mami na jefa mata wata irin harara. "Ke daga gidan ubanwa kike?, tun d'azo aka tashi daga school driver yaje d'akko ki aka ce kin taho" Ifteesan dake sakkowa daga sama ta ce "kuka sani ko tayi saurayi shiya zo ya d'auke ta" "To bari kiji mu nan gidan ba y'an iska bane, yarana basa yawon banza, dan haka sai kiyaye dan baza'a kaso mana abun kunya a gida ba" Mami ta idasa maganar tana komawa ta zauna tana jefama Marmah harara. Ifteesan dake danna computer ta d'ago tana ma Marmah kallon tsaf ta ce "to tsayuwar uban mi kike kuma, marar kunya, ke nan har kinsan bin wani saurayi?, bar wajan nan ko yanzu nazo na sharara miki tafi wallahi" Marmah da idonta ya cika da ruwan hawaye bata bari sun zubo ba tayi d'akinta, tana jin sadda Ifteesan ke cewa, "Ni wallahi Mami na tsani yarinyar can, wai mi yasa ma Daddy zai wani d'akko mana ita ne?" "Ohho mai shima k'ila wani mugun abun sukai mai, sunga ai shi kad'ai keda abun hannu, shi yasa kullum suke mak'alemai, nima nan basan yarinyar can nake ba, dandai ba yadda zanyi ne" Ranar asabar dasu Marmah sukaje ismilya, su Ifteesan sunyi matuk'ar mamakin wai Marmah ce aka d'auka Malama, ai ko haka suka dawo gida suna sanar da Mami cike da bak'in ciki a ransu, suna mata kallon marar ilimi ashe sune ma take ma kallon sakarkaru, duk da sun fahimci haka, basu daina musguna mata ba, harsai idan Daddy na gidan, ko Y Khaleefa yazo garin suke d'aga mata k'afa. Rayuwa na gudu, cikin k'ank'anan lokaci Marmah ta gama secondary d'inta inda Daddy yasa mar mata, wata school of hygiene, shekara biyu, zata gama, dai-dai su Ifteesan suma sun kammala karatun nasu, yana so gaba d'aya a had'a ayi hidimar bikin a tare, kuma a lokacin ne zai sanar da Mami..........✍️ *And ina so na sanar daku duk wadda yake son ayi tafiyar book d'in nan dashi book 1 ya kusa k'arewa, daga na 20 za'a shiga book 2, tohm gsky book 2 na kud'i ne naira #500 ne kacal game buk'atar book 2 akwai sa complete a yanzu haka d'aya turo kud'insa zan tura masa ni kuma Kai tsaye idan kana so zaka iya min magana ta wannan number d'in* 👇 08130479973 Ko kuma ka turo kud'inka ta wannan account number d'in 👇 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Saika turo shaidar biya a number Dana aje sama. *K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR 08130479973 Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe. *Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.* *EPISODE* *END END END* *IT IS THE LAST PAGE I WILL TYPING A LOT* Duk wata wahalar RAYUWA da tsangwama Marmah ta gansu, a shekaru biyun data yi a gidan Mami, amma data jure ta kauda kai, sai gashi komai ya kusa shigewa ya wuce. Cikin nasarar rayuwa ta gama school d'inta inda tana gamawa ta samu aiki asibiti, sai dai Y Khaleefa ya nuna baya ra'ayi kuma ya nuna mata ba'a Kano zasu zauna ba, zai samar mata wani aikin a can Abujar. Gaba d'aya an fara shirye-shiryen bikin su Ifteesan, kwana biyun ta samu sauk'in bak'ar maganar da suke yab'a mata, domin kullum basa gidan, suna gyaran jiki, gobe suna kasuwa, a sayo wannan a sayo wancan, gida ya fara d'aukar harami, Marmah itace suke sa duk wani aiki, Y Khaleefa yana jin ciwon abun, amma babu yadda zaiyi ne, saboda yana sa baki Mami ke gwalashe shi, ya zuba musu ido kawai, domin Daddy yaune yake shirin sanar da Mami, ita kanta Marmah a firgice take, tun safiyar ranar bata fito daga d'akinta ba, saboda tana jin sadda Daddy yake cewa yana son ganin Mami a sashinsa. Cike da farin ciki ta shiga sashin Daddy ta d'auka ko wani abu zasu tattauna wadda ya danganci bikin su Khairat d'in. Zama tayi kusa dashi tana cewa "Daddyn yara ina cikin mutane ka aika a kira ni, ko wani abunne ya taso kuma?" "A'a ba wani abu bane, dama akwai abunda baki sani ba, kuma ya kamata ki sani, wadda zan sanar dake yanzo, za'a kawo wani lefe akwati goma sha uku za'a kaishi can garinmu domin dangi su gani" Dakatar dashi tayi da sauri tana cewa "lefe kuma?, kuma akai shi garinku, to akan mi?" "Shine nake so ki tsaya ki saurare ni ko" "To ina jinka ai" Sosai Daddy shima ya canza fuska babu wasa ya fara sanar da ita duk abunda ya faru dangane da auran da Khaleefa yayi da kuma wacce ya aura. Tunda ya fara magana harya kai aya, Mami ke kallonsa, sake da baki, ko motsi ta kasayi bare ta ce wani abu. Kawai gani yayi ta tashi ta fice daga part d'in ta nufo part d'inta da mugun sauri yabi bayanta. Mami tana shiga parlonta tayi hanyar d'akin Marmah, da k'arfi ta banka k'ofar d'akin ta shigo, su Ifteesan da dawowarsu kenan daga wankin kai, sukaga Mami tayi d'akin Marmah kamar bata cikin hayyacinta yasa suka rufa mata baya suma. Sai dai Mami tana shigowa d'akin ta iske Marmah zaune kamar tasan sai tazo d'akin, ba shiri Marmah ta mik'e tana kallon Mami a tsorace. Mami bata b'ata wani lokaci ba, ta matsa kusa da Marmah tana d'auketa da wani gigitaccan mari, tassssss, ta nunata da yatsa bakinta na kyarma tana cewa "wato abunda nake zargi akanki ya tabbata kenan?, akwai manufar zamanki a cikin gidana kenan, kinsan komai kenan?" Girgiza kai Marmah keyi tana ja baya amma duk da haka sai da Mami ta k'ara kai mata wani bahagon mari, wadda har yasa Marmah zubewa k'asa. Wata tsawar ta kuma buga mata tana cewa "harda had'in bakinki kika aure min d'ana, ki dube ki da kyau, d'ana ba sa'an auran irinku bane, to na rantse da Allah sai ya sake ki yau-yau d'in nan" "Idan kike sake kike k'ara furta kalmar Khaleefa ya saki Marmah to tabbas kema, ki rubuta ki aje sai kin barmin gida na" Ja da baya su Ifteesan suke ba shiri jin muryar Daddy a bayansu, cike da d'unbin mamaki suke kallon abun, yanzu wannan yarinyar ce matar Y Khaleefa, duk cin mutumcin da sukai mata dama da auran Y Khaleefa akanta, amma bata nuna komai ba, bare ta nuna d'agawa, jikinsu ne yayi sanyi, lokaci guda daga Ifteesan d'in har Khairat suka ji Marmah ta basu tausayi, da sune a matsayinta da yanzu wata maganar ake ba wannan ba. "Kamar ya ban gane ba Alhaji, akan wannan abar kake cewa wai yau na barma gidanka akanta?" Cewar Mami tana nuna Marmah cike da b'acin rai a fuskarta ji take kamar ta shak'e Marmah, saboda tsabar yadda take jin tsanarta a ranta. "Kware kuwa kuma idan kina ganin wasa kisa Khaleefan ya sake ta kiga matakin dazan d'auka, kuma a ranar da za'a kai su Ifteesan gidajan mazajan su a ranar Khaleefa zai d'au matarsa su wuce Abuja, dan acan na basa gida, kamar yadda nayi ma y'ay'ana hidimar biki itama haka zanyi mata, dan haka tun wuri idan zaki samawa zuciyarki ruwan sanyi ma kiyi, domin mudun ina raye, ke koda na mutu ma, ban amince Khaleefa ya saki Marmah ba, idan ko yayi haka ban yafe masa ba". Wani irin juya ido Mami tayi tana kallonsa lallai ta k'ara yarda dangin Mijinta sun wanke sun bashi yasha yo idan ba haka ba, ubanwa yake ma irin wannan gatan idan basu ba. Fuuuuu Mami ta wuce kamar zata tashi zama, su Khairat jiki a sanyaye suka fice daga d'akin sai Daddy dake ba Marmah hakuri, yana ce mata komai ya kusa zuwa k'arshe. Marmah dake kuka ta d'ago tana cewa "amma Daddy sai yaushe ne Mami zata soni?" Shafa kanta yayi yana samata albarka yana cewa "zata soki, insha Allah very soon" Yana fad'ar haka yabar d'akin zuciyarsa babu dad'i. Mami zarya kawai take a d'akinta ta kasa zaune bare tsaye, su Ifteesan ne suka shigo suna cewa "Mami dan Allah ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai-dai" Kallonsu tayi cikin fad'a ta fara cewa "wai ni Daddynku yau yake cema na bar gidansa idan na k'ara magana akan na tab'a danginsa" "Amm.... D'aga musu hannu tayi tana cewa "ku tashi ku bani waje naga alamar kuma ta gama daku, maganar banza zaku gaya min, tama k'ara b'ata min rai" Tashi kawai sukai suka bata waje. Khaleefa kuwa ta fuskar Mami kawai ya gane akwai matsala, Daddy ya sanar da ita kenan, dan ko gaida ta yayi bata amsawa saima ta d'auke kai, duk da haka bai fasa bata hakuri da gaishe ta ba, amma duk sadda zai mata magama saita yarfa shi, kota danna mai ashar duk akan Marmah. Haka dai aka fara biki ba wani sakin fuska ga Mami koda akazo kai lefen Marmah y'an uwan Daddy su gani, tunda ba'ayi mata lefen tun time d'in ba, Mami ta hana kowa cikin danginta zuwa, sai d'ai-d'aiku sukaje kai lefen. Inda Marmah taga canji wajan su Ifteesan, duk wani gyara sai suka rink'a jawota jikinsu anayi da ita, duk da haka dai, bata wani sakewa dasu. Tofa tunda aka kai lefen gidansu Marmah, nanfa kallo ya koma sama, ba wadda bai girgiza da ganin irin uban lefen da aka narkama Marmah ba, a sadda aka kawo lefen Hajara lokacin y'an hankalin na kai, ta girgiza ainon, bak'in ciki ya kusasa zuciyarta bugawa, danda nan ta fara sakin maganganu barkatar haukan ya motsa, tana tunama kanta asiri duk abunda tayi ranar saida ta fad'eshi kaf, da kyar aka janyeta daga wajan a ranar Hamza ya saki Hajara, furincin daya sata ta k'ara hartsewa, tana cire kayan jikinta, tana fisge gashin kanta, y'an kawo lefe sunga tashin hankali, da kyar aka d'aure Hajara wani d'aki. Koda wa'inda suka kawo lefe suka dawo suna bada labarin Hajara, sosai Marmah ta girgiza dajin abubuwan da Hajara ta aikata mata wadda bata sani ba, sosai ta rink'a kuka kamar ba gobe, koda Mami taji ta ga yadda Marmah ke kuka, da irin abunda taji yarinyar ta fuskanta a cikin rayuwarta, duk sai jikinta yayi mugun sanyi. Shi kanshi Khaleefa yayi mamakin jin abunda aka kaita ma Marmah, zuciyarsa ta k'ara kamuwa da tsananin tausayin matarshi, sai kuma ganin Mami ta dawo tana amsa masa gaisuwa, ta rage kyarar Marmah da take yi, sai dai ba wani sosai take sakar mata fuska ba, amma dai tana mata magana cikin dad'in rai, a hakan ma Marmah ba k'aramin dad'i taji ba. Ranar juma'a aka d'aura auran su Ifteesan, kuma a ranar kowacce aka kaita gidanta, Khairat Abuja sai Ifteesan cikin garin Kano, a tare aka je kai Marmah da Khairat, da wasu dangin Marmah y'an uwansu na gida, dan harda Habiba aka je Abuja. Sunsha kallo fa gidan Marmah sun girgiza da ganin irin kayan da Daddy yayima Marmah, komai iri d'aya da y'ay'ansa yayi mata, kusan d'akuna hud'u ne sai parlo biyu, sai kuma wani parlo na sakar bak'i, gida fa yayi masha Allah sai san barka, su Habiba haka aka baro Abuja Marmah ta cikasu da abun Arzik'i naban mamaki.. Haka suka dawo gida suna bada labarin irin dukiyar da daular da Marmah take ciki a yanzu, da garin da aka kaita, garin masu kud'i. Koda labari yaje ma Narnah kuka ta rink'a yi tana sake nadamar abunda tayi ma y'ar uwarta, a ranar ma sai da Abbas yayi mata shegen duka, yana mata gorin, ai gashi sunyi mata bak'in ciki, sai kuma gashi Allah ya maida mata mafiyin wadda suke ganin ai yafi k'arfin Mamarh. Marmah sosai take ba Mijinta kulawa yadda ya kamata, shima haka yana riritata kamar kwai, yana nuna mata so, ji take kamar ita kad'ai ce tayi dacen miji a duniya. Sati uku da yin auran su Ifteesan, matsaloli suka fara k'unnu musu kai, ita Khairat mijinta ya ce taje ta koyo girki, da dabarun zama da miji, danya lura bata iya komai ba, ita kuma Ifteesan tunda aka kaita ta lura ashe mijin data aura d'an k'arya ne duk wasu kud'in da yake zuzutawa yana da su ashe k'arya yake mata, to itama dai bata iya komai ba, ta ce ya d'akko masu y'ar aiki, shi kuma ya ce baida halin d'akko y'ar aiki sai da taje ta koyi yadda zata kula dashi, bazai iya da irin halinta ba, idan ba haka ba kuma ya sake aure, tana ji tana gani. Tunda suka gaya ma Mami hankalinta yake tashe, sai dai Marmah data ji wajan Mijinta yake gaya mata, ta ce mai ya kawo mata su suyi wata d'aya a wajanta zata koya masu komai da ikon Allah. Koda Mami taji haka, taso tayi wata magana amma saita basu damar tafiya gidan Khaleefan. Cikin ikon Allah dama sun samu fahimtar juna da Marmah, cikin farin ciki da kwanciyar hankali ta rink'a koya masu komai, da yake iyawar suka zo yi, sai suka mai da hankali wajan koya, kamin ma wata d'aya ba laifi sun iya wasu abubuwan, nanfa sukai ta k'ara ba Marmah hakuri dama ashe haka masu aiki suke wahala, amma da idan sukai masu aikin basa ma ko gode masu, lallai sunyi kuskure babba, ashe da ba gata ake nuna musu ba, da sai dai su ci su kwanta, inda Marmah ta nuna musu ita dama bata rik'e su a ranta ba, Aunty sama Aunty k'asa suke kiranta dashi yanzu, ba abunda Marmah keyi sai godiya ga Allah. Koda suka koma gidajan mazajan su sosai suka ga canji, sosai suka k'ara ganin kulawa daga wajan mazajan nasu, inda suka kira Mami suna fad'a mata, sosai Mami ta kira Marmah tana mata godiya harda sa albarka. Itama Marmah cike da farin ciki take amsa mata tana cewa "ai babu komai yiwa kaine" Sosai ta k'ara ganin darajar ta, ta k'ara jin sonta a ranta, saboda ta kyautata ma yaranta. One year later........ A wannan shekara d'aya data wuci abubuwa da yawa sun faru, ciki harda mutuwar Mlm, sosai Marmah taji mutuwar Kakanta dan har suma tayi, da kyar Khaleefa ya shawo kanta, koda suka je garin, saita zama abar kallo, wacce ake ji da ita, kowa so yake ya rab'eta, kuma dama Marmah bata da ruwa bare wulak'anci, tayi ta kyautata ma y'an uwanta, data ji irin zaman da Narnah take da mijinta da kanta ta rok'i da Khaleefa ya barta taje gidan Narnah, ya kuma barta taje sai da tayi kuka ganin yadda Narnah ta koma, Narnah itama tana kuka tana rok'on ta yafe mata, Marmah ta ce dama ita tuni ta yafe mata, ta sake rok'on ta yafe ma Mahaifiyarta Hajara, sai dai Marmah ta kasa cewa komai, hakan yasa Narnah tayi shuru tasan dama ba lallai ta yafe mata dan yanzu ba. Koda Abbas yazo shima sai da yayi kukan jin Marmah na rok'on sa ya sassauta ma Narnah haka nan kodan ita, inda ya ce insha Allahu zai sassauta mata, abunda yake mata, kamar yadda ta nema, amma ta sani darajarki taci. Abbas ya rage wasu abubuwan da yake ma Narnah, yanzu har yana barinta fita, taje gidansu, taga Mahaifiyarta dake cikin hauka tuburan, inda Abbas ya sake auro wata matar wayayya y'ar boko nanfa sai dai Narnah ta zama y'ar kallo. Zaune Marmah take a jikin Khaleefa a babban parlon Mami sunzo Kano kawo ma Mami ziyara, da yake duk k'arshen wata suna zuwa Kano, su duka suna had'uwa a gidan Mami su Ifteesan, Khairat nada ciki, sai Ifteesan dake goyan d'anta namiji. Kallonsa Marmah tayi cike da shagwab'a ta ce "nima Y Khaleefa ina so" Kallonta yayi yana ja mata hanci ya ce "mi kake so?" Ta nuna cikin Khairat. Dariya yayi ya ce "insha Allah kema very soon zaki samu naki, amma sai kin bari na k'ara dagewa da abun nan, kin yarda mu rink'a yi sau uku a rana uhum?" Da sauri ta ce "eh wallahi na yarda indai zamu samu baby muma" Dariya ya saki yana cewa "kai wannan yarinyar waya koya miki rashin kunya wai?" Rufe fuskarta tayi tana dariyar itama. Haka wannan ahali suke kasancewa a kullum cike da farin ciki wata rana kuma akasin hakan, yau da gobe sai Allah, har Allah yasa itama Marmah ta samu tana rabon. Sosai cikin ke wahalar da ita laulayi take mai wahalarwa komi ta ce saita amayar. Duke take a toilet tana kwarara amai, da sauri Y Khaleefa ya shigo toilet d'in yana kamata ya wanke mata baki, yana mata sannu, d'aukar ta yayi kamar baby yayi d'aki da ita, yana faman mata sannu. Suna shiga ya shinfid'eta a gado yana d'akko mata abinci ko zata samu ya zauna, tab'e baki tayi cike da zallar shagwab'a ta ce "bazan iya ci ba" "Ki daure ki ci kinji baby na?" "Wallahi banzan iya ci ba ko k'amshinsa bana sonji fa baki na d'aci yake" Da sauri ya maida abincin ya d'akko zuma yana lakuta mata a baki da haka yad'an samu ta samu bacci, bayan ta samu bacci yana kallonta cike da tausayin mata a ransa, lallai mata sun cancaci a jinjina masu. Sosai wannan cikin da Marmah ta samu ya k'ara mata fitina da rigima, haka dai Khaleefa ya rink'a biye mata, har Allah yasa ta sauka lafiya, ta haifo d'anta namiji mai kama da ubansa sak, karku so kuga irin farin cikin da wa'innan ahali suka shiga, bare Mami ji take kamar ta goya Marmah danso, dama ga Mami da son yara, inda yaro ya ci sunan Mlm wato Sani, amma an b'oye sunan ana kiransa da Mubeen, a gidan Mami tayi wankan arba'in d'inta ta samu kulawa sosai, tayi kuma wayon arba'in amma da kanshi Khaleefan ya kaita, basu kwana ba, suka wuce Abuja. Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu cike da son juna da zuminci da y'an uwa, Marmah bata tab'a mantawa da y'an uwanta ba, kullum cikin kyautata masu take, haka ma dangin mijinta su Ifteesan sosai suke zuminci, babu nuna kyashin juna ko hassada.....................✍️ Alhamdulillah Thumma Alhamdulillah Yabo da godiya su tabbata ga Allah tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Annabi Muhammad Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam. Alhamdulillah na gode Allah da ya bani ikon rubuta wannan labarin ina addu'ar Allah ya sa mu amfana da shi. *NICE DAI TAKU ZAHRA ROYAL STAR INA K'AUNAR MASOYA NA A DUK INDA SUKE* *SAI MUN HAD'U A BOOK 2 AKWAI SAURAN LABARI A GABA AMMA BOOK 2 NA KUD'I NE, KUNDAI JI YADDA BOOK 1 YAYI ARMASHI, KARKA BARI KARKI BARI A BAKU LABARI, AKWAI SAURAN RINA A GABA, KU DAI KU KASANCE TARE DA NI* *And ina so na sanar daku duk wadda yake son ayi tafiyar book d'in nan dashi book 1 ya kusa k'arewa, daga na 20 za'a shiga book 2, tohm gsky book 2 na kud'i ne naira #500 ne kacal game buk'atar book 2 akwai sa complete a yanzu haka d'aya turo kud'insa zan tura masa ni kuma Kai tsaye idan kana so zaka iya min magana ta wannan number d'in* 👇 08130479973 Ko kuma ka turo kud'inka ta wannan account number d'in 👇 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Saika turo shaidar biya a number Dana aje sama.