[09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️* *°S-Reza✍️* _First class writers association_ _My Whatsapp chanel_ *JAN HANKALI!* Abarwa rai abun da take so shine daidai a gareta koda kuwa wannan abun bashi da inganci a tare da ita. Shin kun taɓa ganin yadda ake yin soyayya da rai bada zuciya ba? Shin da gaske idan aka hana rai abun da take so ana iya samun matsala!?. Labarin Abarwa rai labarin soyayya ne mai ɗauke da abun mamaki da kuma kuskuren so. Ina wanda suka karanta littafin Amera da Adam? Ina fatan dai baku manta da wacece Haura ba, wacce take zaune a gidan su Adam da Amera bayan ta musulunta kuma ta rasa gaba ɗaya iyayenta. To ina muku albishir cewar labarin ta ne da wani malamin makarantar su. Shin yaya zaman Haura a gidan su Amera da Adam? Shin Adam na sonta da gaske? Idan haka ne Amera zata yarda? Muje zuwa cikin labarin domin jin yadda zata kasance!. *GARGAƊI⚠️* Kuskure ne yin amfani da wani sashe daga cikin wannan labarin ba tare da neman izini ba. Wannan littafin ƙirƙirarran labari ne, ban yi domin cin zarafin wani ko wata ba, idan yayi daidai da labarin ka/ki to arashi ne. _Bismilahi rahamanun Rahim!_ *ABARWA RAI!* *Chapter 1️⃣* Da hanzari ya fito daga cikin ɗakin nasu yana gyara zaman hular kansa alamun dai sauri yake yi sosai. Yana ƙarasowa cikin palon ya saki murmushi ya nufo gurin da matar tasa take zaune tana jiran fitowar tasa. Ya na zuwa kusa da ita ya ce "Yauma na makara baki tashe ni da wuri ba, sauri nake yi sai na dawo" Ya manna mata kiss a koshi bai jira komai ba ya nufi hanyar barin gidan. Binsa tayi da kallo har ya kama ƙofar palon zai buɗe tayi ƙarfin halin faɗin "Yauma ba zaka ci abinci ba kenan ko?" Ta faɗa da wata murya mai nuni da rashin jin daɗin hakan. Juyowa yayi ya kalleta ya ce "Abinci kuma, kin duba lokaci kuwa, kiyi hakuri idan na dawo zanci nayi alƙawari" ya ƙarasa yane buɗewa ya sa kai. Ya buɗe kenan zai fita ta sake cewa "Ga wayarka ka manta da ita" ta faɗa tana miƙewa ta nufo gurin da yake riƙe da wayar fuskar tata a haɗe na rashin jin daɗin abincin da ta sha wahalar girkawa domin sa amma a banza. Da sauri ya fara shafa jikinsa yana mamakin yaushe har wayar tasa tazo palo shida yasan a ɗaki ya ajiye abarsa. Hannu yasa ya amsa bai tsaya cewa komai ba ya bar gidan harda haɗawa da gudu. Yana zuwa ya buɗe motar ya shiga ya bar gidan da gudu domin kuwa yayi latti. Saida taga tafiyarsa kafin ta shafa ɗan ƙaramin cikin jikinta sannan ta dawo tana addu'ar Allah ya ƙara tsare mata mijinta, idan akwai abun da yake ɗauke masa hankali akan komai Allah yayi masu maganin ko menene. Gaba ɗaya ta kasa gane masa a cikin wannan sati ɗayan. Ba haka ya saba mata ba, a kwai abun dake damunsa, kuma ta dubu wayarsa bata ga komai ba. Zama ta yi a palon ta kunna kallo tana yi tana danna waya. Habib na isa school ɗin har dalibansa sun gama cika class ɗin nasa, shida yake zuwa da wuri domin kawai duk ɗalibin da ya ƙara ko minti ɗaya ne sai dai ya koma gidan babansa amma yau shine ya makara. Hakan yasa bai ko bi ta ofishin sa ba ya shiga cikin ajin da zai koyar ɗin. Yana shiga suka tashi suna gaida shi ya ɗaga musu hannu yana raba idonsa a cikin ajin. Yana satar kallon yadda ɗaliban suke kus-kus kuma yasan akan makarar da yayi ne. Yau sau biyu zaiyi koyarwa na karfe takwas ɗin safe zuwa tara da rabi da kuma na yamma karfe huɗu. Hakan yasa yake ta addu'a a ransa cewar Allah yasa duk tana cikin wannan lokutan na sa. Saidai haka ya gama koyarwar safe bai ganta ba, hakan yasa ya gane bata da ajin safe sai na yamma. Bayan ya kammala ya koma ofishin nasa ya dafe kai yana ta tunani. Bai san yaya zanyi da wannan yarinyar ba, karfi da yaji ta saka masa tunaninta na dole, gashi yau bata zo ba duk yabi ya damu, sai ya tsinci kansa da addu'ar Allah dai yasa lafiya lafiya take. Ada idan yana da koyarwar sau biyu a rana to idan ya gama na safe gida yake komawa sai kuma yamma ya dawo, amma yau tsabar zumudi sai ya ke jin idan ya bar school ɗin yaje gida zai iya ɓata lokaci, hakan yasa ya fita ya sayo abinci ya dawo ofis ɗin ya zauna yaci, sannan ya miƙe ya ɗan shiga zagawa a cikin school ɗin yana kallon yadda dalibai wasu na fita wasu na shigowa, wasu kuma a zaune. Kusan duk inda ya wuce sai sun bishi da kallo domin kowa yasan wulaƙancin Malam Habib. Misalin ƙarfe huɗu ya shiga cikin ajin ya ɗaure fuska babu alamar annuri ko kaɗan. Idonsa ne ya sauƙa a kanta tana sakar masa murmushin nan nata mai tafiya da imaninsa, bai san lokacin da tari ya sarƙe shi ba. Yan aji dai sun zuba masa ido ganin ya tsaya shi bai shigo ba kuma bai fita ba. Tana zaune a inda ta saba zama wato kujerar gaba. Bayan sun gaida shi ya amsa ya ƙarasa gaban allun karatun ya fara rubutu yana yi yana satar kallonta ita kuwa sai murmushi takeyi. Yauma sanye take da doguwar riga baƙa samfarin abaya, kanta babu kitso tana yafa ɗan kwalin a kanta ba tare da ta ɗaure ba. Juyowa yayi zai fara jawabi sai dai abun da ya gani ne yasa ya shiga wani jawabin da bashi yayi nufin yi ba. Hakan yasa ajin ya cika da surutu suna tambayar lafiya kuwa Malam yake yau. Kaman yadda ta saba masa ƙafafuwanta ta shiga ware masa dukda cewar akwai dogon wando a jikinta amma hakan da tayi yasa ya rasa control ɗin sa. Gyaran murya yayi ya ce musu yana zuwa. Ofis ya koma ya ɗauki ruwa yasha ya dafe kirji yana jin wani irin abu na jansa game da yarinyar. Babu abun da yake buƙata kaman ya jita a jikinsa kaman yadda ta sabar masa, bai taɓa yin zina ba amma yana jin tabbas zai iya yi akan wannan yarinya domin yana jin hakan a duk lokacin da ya haɗa ido da ita. Komawa ajin yayi yaci gaba da bayani har lokacin tashi yayi yanayinsa bai sauya ba. Ofis ɗin ya sake komawa yana addu'ar Allah yasa yau ma ta biyo shi ciki, da tabbas yadda yake ji ɗin nan akanta komai ma zai iya faruwa. Ya kai minti biyar amma bata shigo ba hakan yasa ya fito ya nufi cikin ajin nasu yana tafiya a hankali domin yasan ba zata iya tafiya ba har sai ganshi. Yana shiga class ɗin kuwa ya sameta zaune ita ɗaya da alamar itama shi take jira. Tana ganinsa ta mike tsaye tana kwallonsa cikin ido. Da Karfi ya haɗiye yawun bakinsa yana ƙarasa kusa da ita. A hankali ta ce Sir" yayi saurin ɗora hannunsa akan leɓenta ya ce "Shiiit" yana jin wani irin abu na na jansa zuwa gareta. Sai ta lumshe ido ta buɗe a hankali, hakan yasa bai san lokacin da ya haɗe bakinsu ba. Izuwa lokacin babu kowa a makarantar har duhu ya fara yi. Haka ya shiga kissing dinta har ya rabata da rigar jikinta ya kwantar da ita a ƙasar gurin duk hankalinsa naga abun da ransa ke so. Ita kanta ranta na son abun hakan yasa take ta bashi haɗin kai, babu abun da ke fita sai nishin su. Dogon wandon nata ya zame shima ya cire nasa ya mata rumfa ya fara ƙoƙarin cika umarnin ziciyoyinsu. Har ya kusa cimma burin ran nasa ya jiyo muryar mai gadin makarantar yana tambayar waye a ana. Hakan yasa ya tsaya daga yunkurin da yake yi, jin alamar ana zuwa ne yasa ya rufe mata baki da hanci kuma ya danneta domin ya tsayar da wannan nishin da take yi. Sosai take murƙususu domin bata samun damar shaƙar numfashi kasancewar har da hanci ya toshe mata, shi kuma yaƙi sakar mata hanci domin kar tayi magana akama su. Daidai lokacin mai gadin ya turo kofar ajin yana hassakawa da fitilar sa mai hasken gaske. A wannan lokacin ne kuma take shura ƙofa hakan yasa ya haɗe ƙafafun nata da nasa ya danne yana ƙara matseta a ƙasan. Idanunsa suyi jaa sai addu'a yake a ransa akan kar a kama shi. Haka mai gadin ya gama duba ko'ina kafin ya jawo ƙofar ajin ya fita. Yana fita Habib ya ɗaga Haura yana mayar da wandonsa da ya zame duk ya rikice. Sai dai me ganin batayi motsi bane yasa ya shiga kiran sunanta "Aisha Adam" ya kira sunan a hankali. Jin shiru yasa ya sunkuyo da sauri yana ɗagota jikinsa yana taɓa ta. Amma ko alamar numfashi babu a jikinta, sai ma wani langwaɓewa da take yi alamun bata numfashi. Cikin tashin hankali ya sake jijjigata yana kiran ta, lokaci ɗaya wani irin tsoro ya shigeshi da ya aiyana ko dai mutuwa tayi. Sai lokacin yake tuna yadda take ta murƙususu tana shure-shure amma yake ƙara danneta. Rigarta ya fara ƙoƙarin mayar mata, sai wandon da ya zame mata, gaba ɗaya ya fita a cikin haiyacinsa ya rasa me zaiyi. Fuskanta ya sake kalla ya ganta fayau sai ya tashi da sauri domin yaje ofis ɗin sa ya ɗauko ruwa ya watsa mata ko suma tayi. Haka ya shiga ofis ɗin ya ɗauko sauran ruwa a gora ya fito. Saidai yana fitowa daga ofis ɗin nasa mai gadin nan ya haske shi da fitilarsa yana tambayar waye anan. Lokaci ɗaya Habib ya saki robar ruwan tsabar tsoro ya rasa mai zai ce , kamar ya kwaɗa ihu ya fita a guje. Amma haka ya daure ya ce "Emeka nine, barci ne ya ɗaukeni a ofis sai yanzu na tashi" ya karasa maganar a rarabe wanda kana ji kasan ba'a cikin natsuwarsa yake ba. Emeka mai gadi ya ce "A a Malam Habib ne kika daɗe har wannan lokacin baki tafi gida ba?" Habib ya ce "Barci ne ya ɗauke ni" yana faɗa yana bin Emeka ɗin izuwa waje. Emeka ya ce "Ina ta jin motsi ne ta cikin wancen ajin yasa take ta dubawa kasan yaran nan wasu sai su ƙi tafiya ɗakunansu sai zauna anan har safe. Habib ya ce "Um um haka ne" haka Emeka keta zuba masa surutu har suka zo bakin get. Shi dai sai leƙe ta ya keyi har ya shiga motar ya kasa kunnawa kusan minti biyu Emeka ya leƙo yana sanar dashi cewar zai rufe get ɗin. Yana tafiya a mota shi ɗaya yana tunani ga wani zufa da yake karyo masa. Jin ana kiran sallar magriba ne yasa ya kalli agogon hannunsa yaga shida da arba'in. Sai lokacin ma ya tuno ya bar wayarsa a ofis ɗin sa ga hularsa da itama ya barota a ciki. Dole ne sai ya koma school ɗin nan to amma ta ina zai bi ya shiga makarantar bayan babu hanya dole sai ta get. Kasa tsayawa yayi ya nufi gida duk a rikice. Lokacin da ya shiga palon Nadiya ce zaune tayi wankanta sanye da atanfa riga da sket, cikin nan ya ɗan taso kaɗan ɗan wata biyar. Kallo ɗaya tayi masa gabanta ya faɗi, hakan yasa ta mike da sauri ta na faɗin "Beb lafiya dai ko?" Ta faɗa tana kama hannunsa. Habib ya ɗan saki fuska kaɗan ya ce "Kawai bana jin dad'i ne, tun ɗazu kaina ke ciwo barci ma nai tayi a school ɗin" ya ƙarasa yana riƙe kansa. Nadiya ta ce "Aiya sorry, bari na haɗa maka ruwa kayi wanka sai kaci abinci kasha magani, amma ina hularka ko a mota ka barota?" Ta tambaya kuma ta bashi amsar da zai bata, ta ƙasara duk a tsorace domin tun auransu bata taɓa ganin lokacin da ciwon kai ya mayar da shi haka ba. Habib yayi ƙarfin halin faɗin "Eh tana mota" ya ɗora cewar "ki bari kawai idan na kwanta ma zai tafi" ya faɗa yana zama a kan kujerar palon. Da sauri ta sake kamo hannunsa da ta sake ya mike suka nufi ɗakin sa, ta shiga toilet ta haɗa masa ruwa mai zafi. Koda ta fito ta samu ya dafe kai yana tunani har bai ma san ta fito ba, ta ɗan kafe shi da ido na minti ɗaya sannan ta ce "Beb me ke damun ka ne, anya kuwa ciwon kai ne kawai?" Firgigit ya dawo daga tunanin ya miƙe tsaye ya ce "Na'am to zanje ina ne?" Ya haɗa maganar duk a rikice. Nadiya ta ce "Toilet zaka shiga ruwan wankan na ciki" Sai ya nufi toilet ɗin ba tare da ya cire kayan jikinsa ba. Zama tayi a ɗakin ta na ta nazarin yanayinsa, to wai me ke faruwa da shi ne, ina yake yawan zuwa yanzu ne, ko dai ya fara shaye-shaye ne, to amma bata ji warin komai a jikinsa ba. Shekara daya da wata ɗaya kenan da auransu, bata taɓa ganin irin wannan sauyin daga garesa ba, hasali baya ɓoye mata komai nasa, bashi da gurin hira sai gida, amma a cikin wannan satin gaba ɗaya ya sauya mata. Tana zaune shiru bai fito ba, sai ta tashi ta koma ɗakinta ta ɗauko masa maganin ciwon kai ta dawo ɗakin har lokacin bai fito ba. Ta sake fita ta haɗo masa abinci da ruwa ta kawo har lokacin bai fito ba. Sai ta shiga fiddo masa da kayan da zai saka na barci. Har ta gama bata ji alamar zai fito ba domin daga inda take tana jin zubar ruwa. Tashi tayi ta nufi toilet ɗin tana zuwa ta murda murfin ta leƙa. Ƙamewa tayi a tsaye tana kallon sa. Tsaye yake bai ko cire kayan nasa ba ya sakarwa kansa ruwan sanyi bayan ga na zafi da ta haɗa masa a gefe. Mamaki ne ya kamata gami da tsoro ganin bai ma san ta buɗe ba kansa na ƙasa. Da ƙarfi ta ce "Habib" ai kuwa ya ɗago yana sauke ido a kanta. Cikin kuka ta ce "Wai me ke faruwa ne, meye matsalar ka, shin ban kai ka faɗa min abun dake damun ka ba ko, na sani dama tun ba yanzu ba kana ɓoye min abu amma babu komai laifi na ne da nake son naji damuwar ka. Tana faɗa ta juya ta bar ɗakin tana kuka. Habib kuwa kayan jikin nasa ya cire ya ɗaura tawul ya fito ya saka wasu kananan kaya jinss da ƙaramar riga ya fito falo. A tunaninta hakuri yazo bata kuma ya faɗa mata abun dake damun nasa, hakan yasa ta sake haɗe rai tana juya masa baya. Amma sai taga ya nufi hanyar waje. Ya ce "Ina dawowa yanzu" yana faɗa ya kama ƙofar ya buɗe ya fita. Ta bisa da kallon mamaki, wannan fa abun nasa ya fara wuce tunaninta, ina kuma zaije bayan sallar Isha, gashi ko abincin ma ba lallai yaci ba, bare ma yayi Sallah. Da sauri ta leƙa shi ta window taga ya fita a ƙafa. Ɗakinsa ta koma taga komai a yadda ta kai masa su, ko maganin ma bai samu ya sha ba. Lokacin ne kuma hankalinta ya sake tashi da wannan sabon al'amarin. Shi kuwa Habib gaba ɗaya hankalinsa ne ya kasa kwanciya, yana jin dole ne ko ta kan katanga ya haura yaje ya duba yarinyar nan, idan mutuwa tayi ya san yadda zaiyi da ita, idan kuma suma tayi ya farko da ita ya kaita har ƙofar gidan su. Lokacin da ya ƙaraso bakin makarantar ya sallami mai mashin ɗin da ya kawo shi, sai ya tsaya yana duba ta ina zai iya bi ganin katangar tayi tsayi ga kuma irin wannan wayar wutar nan a zagaye jikinta...✍️ S Reza... Sabon labarin mu kenan, mai taken abarwa rai abun da take so, farko kenan kuma soman taɓi. Kude ku kasance da S Reza domin jin yadda zata kaya. [09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI❣️* *°S-Reza ✍️* _First class writers association_ *Chapter 2️⃣* Har bakin katangar ya ƙarasa ya na shiga duba wa ko zai iya samun ƙaramar hanyar da zai iya kamawa ya haura amma babu dama. Haka ya dinga zaga wa har ya zagayo ta gaban get ɗin, ya tsaya daga nesa yana jin gabansa na faɗuwa kar Emeka ya hango shi. Haka ya sunkuya ya na tafiya a duƙe kamar ɓarawo har ya ƙaraso bakin get ɗin. Nan ya tsaya ya na sauke ajiyar zuciya.  Kama bakin get ɗin yayi ya leƙa sai ya hango ƙofar ɗakin Emeka a buɗe amma baya gurin. Hakan yasa ya kama bakin get ɗin kenan ya ga hasken fitila ta haske masa ido, hakan yasa yayi saurin sakin get ɗin sai gashi a ƙasa tim ya faɗo, kuma bai tsaya ta zafin da yaji ba dalilin jin muryar Emeka ɗin da yayi ya na nufowa gurin da sauri domin ganin waye. Da gudu yasha kwanar makarantar yana jin yadda bayansa ke masa zafi. Bai tsaya a nan kusa ba domin yasa zai iya bin bayansa. Sai da yayi nisa kafin ya samu guri ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya. Bayansa ya dafe ya na haki sai kuma ya riƙe ƙirjinsa ya na jin takaicin kansa. Take zuciyar sa ta shiga aiyano masa suffar Haura da ya gani yau, ya na yin ƙirjinta da yaja hankalinsa yanzu gashi baiyi komai ba yasa kansa a matsla, alhalin yana da matarsa ta Sunnah a gida halak ɗin sa da zai iya yin komai da ita. Take ya shiga tsinewa zuciyarsa da ta raya masa wannan masifar da bai ma kai gayi ba kenan. Haka ya kama hanyar gida a ƙafa yana tafiya ya na tunanin tsawon lokacin da Haura take manne masa akan tana sonsa, kullum idan har tana da class ɗin sa haka zata dinga masa abubuwan da dole hankalinsa ya kai gareta, wasu lokutan har ofis ɗin sa take binsa, tun baya biye mata har ya fara yarda yana ɗan taɓa ta idan sun keɓe ko ya shafa ta. Daga fara mata haka kuma ta sake samun dama sosai domin ita har zuciyarta sonsa takeyi, shi kuma hakan da take masa yasa sheɗan ƙawata masa ita har yake aiyana yadda zai ji daɗi Idan ya samu burin ransa a kanta, gata yarinya ƙarana mai kyau ga tsafta, kuma daga gani yar manyan mutane ce, domin kullum cikin shigar kaya masu ɗan banzan kyau da nauyin kuɗi take. Saida Habib yayi doguwar tafiya kafin ya tare mai ɗan sahu ya ƙarasa da shi gida. Yana shiga gidan yaga wutar palon a kashe hakan yasa yaji daɗi domin yasan Nadiya tayi barci kenan. Yana zuwa tsakiyar palon yaga haske ya karaɗe palon hakan yasa ya tsaya ya na juyowa ya sauke idonsa akan nata da tayi tsaye tana binsa da wani irin kallon tuhuma. Duk yadda Habib ya kai da ya ɓoye halin da yake ciki sai ya ƙasa domin ba zai taɓa iya samun kwanciyar hankali ba muddin bai san halin da Haura ke ciki ba. Yana tsaye yana kallon Nadiya amma ya fara tunanin yanzu idan ta mutu za'a zarge shi ne ko yaya, to an sanshi da ita ne ko wani yaga  lokacin da suka rage a school ɗin, lokaci ɗaya ya tuno da Emeka yasan dole ne sai an zarge shi, hakan yasa bai san lokacin da ya furta "Innalillahi wa inna'ilaihi rajiun ba" Nadiya da fitar sautin salatin nasa ya sake haifar mata da wani irin tsoro da fargaba ta ce "Beb daga ina kake? Wai me yake faruwa da kaine?" Ta ƙarasa tana sakin kuka domin iya abun da tasan zata iya yi kenan a halin yanzu, gashi ba yaro ba bare ta zane shi ya faɗa mata wacce irin masifa ya tabo musu haka da ya kasa samun natsuwa. Sai a lokacin ya kula da cewar ashe fa a gida yake kuma a gaban Nadiya. Jin kukan da take yi ne yasa ya ƙaraso kusa da ita ya rungumeta da karfi yana jin ina ma shima zai iya yin kukan kaman yadda takeyi, sai yake jin ita ai kuka mara dalili takeyi shine ya dace yayi kuka mai dalili. Ta na jiran taji ya fara lallashinta kuma ya faɗa mata matsalar sa amma sai ta lura kamar ma hankalinsa baya tare da ita, sai ma wani irin matsa da yake mata kamar ya manta da cewar mutum ce kuma mace a jikinsa, macen ma mai juna biyu. Ƙarar da tayi ce tasa yayi saurin sakinta yana ja da baya yana kuma kafeta da ido. Sosai tsoro ya sake baiyana a fuskarta ta na furta Innalillahi a ƙasan maƙoshin ta domin lamarin nasa ya fi ƙarfin tunaninta. Juyawa yayi ya nufi cikin daki sai idonta ya sauka akan bayan wandonsa da ya faɗi ɗazu ya kwashi jar ƙasa. Binsa tayi da kallo har ya ɓacewa ganinta. Gaba ɗaya ta rikice to ko dai faɗa yaje yayi ne. Bata san lokacin da ta zauna daɓas a tsakiyar palon ba tana sake rushewa da kuka. Kusan minti ashirin tana kuka amma kamar babu kowa a gidan, haka dole ta tashi ta shiga cikin dakin da yake ta sameshi kwance, yana jin shigarta ya yi saurin lumshe ido kamar mai barci. Toilet ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta dawo ɗakin ta hau kan gadon ta kwanta ta juyo tana kwallonsa. Kasancewar a kwai hasken wuta yasa ta kafe shi da ita, tana kallon yadda yake buɗe idon yana rufe wa kamar munafuki. Ta ce "Beb nasam ba barci kake ba, dan Allah ka faɗa min me yake faruwa, me ya kawo ƙasa a bayan wandonka a cikin wannan daren?" Ai da sauri ya mike tsaye ya duba wandon nasa sai ga nan alamun kasan. Hakan yasa ya cire wandon ya na faɗin "Faduwa nayi, kuma ki kwantar da hankalinki komai lafiya" ya faɗa yana shigewa Toilet ba tare da yasan mai zaiyi a ciki ba sai dan kawai ya gujewa tambayoyin wannan ƴar jaridar da ya samu yau. Yana shiga toilet ya sake haɗe kansa da bango yana ta tunanin yanzu gobe haka za'a je school a samu gawarta. Sai lokacin ma ya tuna bai duba gobe karfe nawa yake da class ba. Tuno da haka yasa ya fito da sauri kamar ma harda gudu ya hada a ganin Nadiya. Sai lokacin ya tuna da cewar ya bar wayar tasa a cikin ofis ɗin sa, sai ma lokacin wani tinani ya fado masa, anya kuwa a ofis ɗin ya bar wayar tasa. Take gabansa ya bada wani rass da ya tuna cewar tabbas da wayar a jikinsa ya zame wandonsa lokacin da yake ƙoƙarin yin abun. Da karfi ya furta "Na shiga uku na lalace" ya furta yana dafe koshi. Nadiya ta tashi zaune tana kwallonsa. Da sauri ya karasa gurin da laptop dinsa take June a jikin chaji. Ya buɗe ta hannunsa na rawa ya kunna. Tana daga gurin da take tana kallon yadda hannayensa ke rawa sun kasa bashi haɗin kai akan abun da zaiyi. Yana dubawa yaga yau class ɗin sa na yamma ne kawai babu na safe. Sai ya rufe laptop ɗin yana kuma jin ai dole ne ma gobe yaje school da wuri kafin kowa yaje, to amma idan kuma aka kama shi fa, to amma idan bai je ya ɗauke wayarsa daga gurin bafa har aka zo aka gani. Sai kawai ya bari akan gobe yaje da wuri ko iya wayar ya dauke koda kuwa mutuwa tayi. Yana kashe laptop ɗin ya juyo sai ya ga Nadiya zaune tana kwallonsa tana hawaye. Shi wallahi har mantawa ma yake yi da tana dakin. Danne abun da yakeyi yayi ya hau kan gadon ya rumgumota jikinsa ya ce "Please I'm sorry, matsala ce ake so sai an dora min ita a makaranta wacce ban san da ita ba, hakan yasa gaba ɗaya na kasa natsuwa" ya ƙarasa yana jin shi da kansa ƙaryar bata samu gurin zama a bakinsa ba bare kuma zuciyar Nadiya da ya sani da saurin gane gaskiya ko ƙaryar da zai mata. Yana ji tace "Hum" daga haka kuma bata sake cewa kuma bai, kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba domin bai son yin wata maganar kuma. Daga haka ta kwanta sai dai ta kasa barci tana ta hasaso abubuwan da zasu iya firgita mata miji kamar haka, amma duk tunanin da tayi sai ta kasa yarda, harda tunanin ko dai ciki yayiwa wata amma tasan ba halinsa bane. Sai kusan ɗaya yaji alamun barci ya ɗauketa hakan yasa ya ɗan leƙa fuskarta yaga da gaske barci takeyi. Sai ya tashi zaune yaci gaba da zaman jiran wayewar gobe. A kunnensa a kayi kiran sallah sai a lokacin ya tuna da ko magriba da isha bai samu yayi ba. Ya shiga toilet ya ɗauro alaula ya tada sallar magriba bayan ya idar yayi Isha. Ita kanta sallar yana yi ne yana tunani domin bai yi ta a cikin natsuwa ba. Sallar asuba ma a cikin ɗakin yabi jam'i duk da kuwa yasan illar yin hakan, yasan irin asarar da mutum ke yi idan ya rasa jam'i salla musamman salar asuba da Manzon Allah saw yake cewa "Tabbas munafuki baya iya tashi domin yin sallar asuba a jam'i, duk wanda ka ga yana iya tashi ya je masallaci domin yin sallar asuba to tabbas ba munafiki bane. Amma dukda wannan sanin haka ya danne har aka idar da sallar tare da shi. Daidai lokacin Nadiya ta farka tana furta addu'ar tashi daga barci wato "Alhamdu lillahil lazi ayana ba'adama amatana wa'ilaihin nushur. Ta bishi da kallo ganin yana salla a gida domin bata saba ganin haka ba. A cikin wannan satin ne ma yake makara har sai an tada salla zata tashe shi kuma haka zai yi alaula cikin sauri ya tafi, kasancewar taga baya barci da wuri, to idan ya dawo ne kuma zai ta barci har sai tayi da gaske zai tashi ya shirya ya tafi makaranta. Haka take ta fama kwana biyun nan. Ta ce "Beb salla a gida kuma kamar Mace?" Ta faɗa tana sauka daga kan gadon cikin muryar barci. Ya ce "Bana jin dadi ne" ya faɗa yana fita daga dakin ya dawo Palo. Haka ya kishingiɗa a kan kujera mai ɗaukar mutum uku yana ta alla-alla gari ya ƙarasa wayewa. Yana zaune har shida da rabi lokacin gari yayi haske sai ga Nadiya ta fito bata ce masa komai ba ta shiga kichin. Sai lokacin taga kwanukan abincin sa da baici ta dawo dasu. Na safe ma sai almajirai ta bawa, haka na rana ma da taga bai dawo ba. Wannan kuwa shi zata ɗumama sai ta haɗa musu shayi tunda suna da bredi koda ƙwai huɗu ne sai ta soya musu. Tunda Allah yasa yau ya tashi da wuri itama bari ta haɗa komai da wuri sai ta kai masa kar ya sake fita barci komai ba. Bata fito daga kichin ɗin ba saida ta soya ƙwai guda huɗu ta hado ruwan zafi. Ta kawo dainintebul ta ajiye, sannan ta koma ta zubo jalof ɗin taliyar da waken da ta ɗumama a flet ɗaya ta ajiye. Ta kwaso kayan shayi harda biride ta ajiye duk tana yi tana satar kallon ganin hankalinsa baya gareta. Saida ta haɗa masa shayin kafin ta ƙarsa gurin da yake tana kiran sa. Firgigit ya dawo hankalinsa yana kallonta. Ta ce "Breakfast na gama ka tashi kaci da wuri kafin ka fita" ta ƙarasa tana barin gurin. Ya kalli a gogon palon mai irgen biyar-biyar sai yaga ya bashi karfe bakwai harda minti biyar ga kuma ɗan ƙaramin tsinken ya kusa hawa kan ɗaya number mai nuni da cewar da minti goma ya kusa. Ya kalli Nadiya ya ce "Bari na shirya nazo" ya shige daki yana jin shi har ma ya manta da batun abinci, baya ko iya tunawa da shi bare kuma yaci. Ko minti biyar bata ce yayi ba ya fito cikin shigar ƙananan kaya, yau ko samun damar gyara ma gashin bai samu ba, ta kalleshi ganin ya nufo gurin da take zaune tana jiransa. Tun kallon farko da tayi masa ta gane baya cikin haiyacinsa har yanzu, domin ba haka ya saba fita ba. Ya sunkuya ya ɗauki kofin shayin gabanta ya kurɓa sai ya ajiye. Sai ta kalli wanda ta haɗa masa a kusa da shi, ko bai ga wannan ɗin bane oho. Tayi tunanin zama zaiyi sai taji yace "Thank you Beb I'm okay, sai na dawo" yana faɗa kuma ya ja mata hanci ya bar gidan yana sauri. Har ya fita ta ƙaranin get ɗin sai ya tuna da bai ɗauki motar ba. Haka ya dawo ya tada motar ya fita daga gidan. Kamar kar ya dawo ya rufe get ɗin amma haka ya fito ya rufe yana kama hanyar school. Sosai yake gudu yana addu'ar Allah yasa shine mutum na farko da zai fara shiga cikin makarantar duk da kuwa yasan bashi da class ɗin safe. Amma sai me zai faru tun daga nesa ya hango get ɗin makarantar a wangale ga kuma dalibai har sun fara shiga. Ya kalli agogon motar ya bashi karfe bakwai da rabi harda minti ɗaya. Gabansa ne ya shiga bada wani irin sauti mai kamar ana dakan sakwara, dukda safiya ce sai ya ji kamar zufa ce ke ƙoƙarin karyo masa, musamman da yazo kusa da get ɗin yaga kamar mutanene a tsaitsaye ana kallon wani abu, wanda zuciyarsa ta raya masa cewar gawar Aisha Adam ce aka gani shine kowa ya tsaya kallo...📝 Muje zuwa a kwai ƙura a gaba. S Reza... [09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️* *°S-Reza✍️* _First class writers association_ _My Whasop chanel_ *Chapter 3️⃣* Tsabar fargaba da saurin da yake na ganin ya shigo cikin makarantar domin ganewa idonsa abin da ke faruwa har ƙoƙarin bi ta kan wasu ɗalibai mata ya yi ba tare da ya ankara ba. Tsakanin get ɗin da cikin makarantar ma a kwai tafiya mai ɗan tsayi, hakan yasa yana shiga ciki da motar tasa sai yaga wani malami ne a gefe yana magana da wasu dalibai shine dalilin da yasa yaga sauran ɗaliban suna leƙawa. Yana gyara pakin ya fito da sauri ya nufi cikin makarantar ba tare da yayi wa kowa magana ba. Ofis ɗin sa ya fara shiga ya duba baiga wayar tasa ba, hakan yasa ya fito da sauri ya nufi class ɗin da abun ya faru. Koda ya shiga ɗalibai uku kawai ya gani a ciki, suka tashi suna gaida shi cike da mamakin ganinsa a irin wannan lokacin da sunsa ba shine zai karantar dasu ba. Bakin allon karatun yaje ya tsaya yana satar kallon gurin da abun ya faru a yammacin jiya. Sai dai bai ganta ba kuma bai ga wayarsa ba. Sake mayar da hankalinsa yayi izuwa gurin nan ma babu ita babu wayar. Duk da haka bai gamsu ba sai ya nufi gurin ya ɗan wayance harda sunkuyawa yana dubawa. Daidai lokacin kuma ɗalibai kusan su goma suka shigo cikin ajin mata da maza ana dariya, wasu ma zancen banza sukeyi. Jin haka yasa ya ɗago da sauri yana mamaki to me ya faru. Yana ji suna gaisuwa amma yasa kai ya fita duk jikinsa yayi sanyi. Ɗaliban suka bisa da kallo suna ta mamakin yanayinsa, ko dan irin wankan da suka saba gani a tare da shi yau babu. Ofis ya koma ya zauna sai ya fara tunanin to ko dai ba mutuwa tayi ba, ai kuwa idan bata mutu ba dole yau zata zo school kenan. Hakan yasa faɗuwar gaban nasa ya ragu yana so sai karfe goma zai koma class ɗin ko zai ganta. Haka yaci gaba da zama a cikin ofis ɗin har karfe goma sannan ya fito ya nufi class ɗin amma yaji an kira sunansa ta baya. Kaman a tsorace ya waigo yana sauke idonsa akan wani malami wanda tun zuwansa school ɗin dashi suke ɗan gaisawa sama-sama. Ya ce "Malam Habib dama class ɗin safe kake dashi yau?" Habib ya ɗan sosai kai ya ce "Amm da kawai na zo gurin wani malami ne zan amshi abu, yanzu zan tafi" ya faɗa kamar a rikice. shi kansa Malam Ali ya fahimci kamar dai wani abu na damun sa. Ya ce "Ok Tom bari na shiga nawa class ɗin lokaci yayi sai na fito zan zo ofis ɗin na same ka" yana faɗa suka sake yin hannu Malam Ali ya tafi, shima Habib ɗin ya kama hanya. Yana zuwa bakin class ɗin shi kuma malamin dake ciki zai fito hakan yasa ya yi saurin mika masa hannu suka gaisa. Ya shiga ɗaliban suka gaida shi. Nan ya fara raba ido ko zai hangonta. Gurin da take zama ya kalla yaga babu kowa a gurin, sannan ga wannan ƙawar tata da suke zuwa makarantar tare. Kaman ya kirata ya tambaye ta amma yana tsoron kar yaje daga yin tambaya ya tono wani abun. Haka ya wayance da tambayarsu wani abun daban sannan ya fita daga class ɗin. Wannan karan kam saida suka buɗe faken hirar Malam Habib, wasu na tambayar me yake damunsa, ko dai yana neman wasu dalibai ne jiya. Duk ya koma wani iri daga jiya zuwa yau, ya kasa sakewa yayi komai. Gashi bai san gidan su ba, shi babu ma abun da ya sani game da ita. Cikin motarsa ya koma ya shiga yana dafe kan motar yayi shiru kusan minti biyar bai ko rintsa ido ba. Sai kuma ya tada motar ya bar cikin school ɗin. Hanyar gida ya nufa sai kuma ya nufi gidan iyayensa domin tun jiya da yau duk bai jeba kuma ko kiransu bai samu yayi ba. Haka kawai zuciyar sa ke raya masa in sha Allahu bata mutu ba, ai kuwa idan haka ta tabbata shida ita kuma har abada, ko kallonta ba zai sake yi ba, bare akai ga yayi yunkurin aikata wani abu da ita. A ƙofar gidan ya ajiye motar tasa ya shiga da sallam. Mahaifiyarsa ta amsa ya ƙarasa ciki da ɗan rashin kuzari. Ita kadai ce a gidan sai ƙanwarsa da yasan tana school yanzu haka. Zama yayi akujera yana ta kokarin ganin ya kawar da komai dake kan fuskar tasa. Ya ce "Mama ina uni ya ƙarfin jiki?" Ya faɗa yana ɗan ƙirƙirar murmushi. Mama ta amsa tana tanbayarsa lafiya dai taga ya ɗan zube ko baiji daɗi ba ne. Ya ce "Eh Mama zazzaɓi ne ya ɗan dameni tun jiya, amma dai yanzu da sauki" ta ce "To Allah ya ƙara afuwa, ya ita Nadiyar da jiki, yanzu haka kake fita ka barta ita ɗaya a gida ga tsohon ciki?" Habib ya ce "Ai ina koma gida idan bani da karatun safe, yauma sai biyar zan shiga class ɗin duk muna tare da ita. Yana rufe baki sallamar Nadiya ta karade palon. Kasa amsawa yayi sai Mama ce ta amsa tana mata maraba. Itama tsaye tayi ganinsa a gidan sai tayi kamar bata gansa ba ta gaida Mama ta samu guri ta zauna fuskar nan a haɗe. Ƙanwarsa ce domin su ɗin ƴan ya ne da ƙanwa. Mama itace tasha nono ta sakarwa mahaifiyar Nadiya ɗin da Allah yayiwa rasuwa shekaru biyar kenan. Hakan yasa Nadiyar ta dawo gidan da zama, kuma dama tun kafin rasuwar a kwai shaƙuwa a tsakaninsu, da ta dawo gidan ne kuma ta koma soyayya har akayi aure. Nadiya na sonsa sosai, domin bata haɗa son da take masa da komai, sannan ita ɗin mace ce mai kishi sosai hakan yasa take godiya ga Allah da ya bata Habib domin shi mutun ne da bashi da lokacin mata, hakan yasa take ƙara alfahari da shi a ko ina. Tana iya bakin kokarin ta wajen rufa masa asirin gidan sa, domin tunda suka yi aure ba'a taɓa jin kansu ba, bata taɓa cewar yayi mata abu, tana da hakuri sosai wanda ya haɗu da son da take masa. Duk abun da yace ta bari to babu shakka ta bar wannan abun kenan, haka idan ya saka ta. Yanzu haka zuwan nan da tayi tazo ne domin ta bigi cikin Mama ko taji abun da yake damun sa saboda ta kasa natsuwa kuma gashi yaƙi ya sanar da ita, domin tabbas ta lura akwai abun da yake ɓoye mata kuma ko menene ba karamin abu bane. Mama ta ce "Yanzu kuwa nake tambayarsa cewar haka yake barinki ke ɗaya a cikin gidan?" Nadiya ta ɗan yi murmushi ta ce "Ai kusan muna tare dashi a gida, yanzu ma ban san nan zai zo bane yasa bamu zo tare ba. Mama ta ce "To ma sha Allah, Allah dai ya raba lafiya Kinga kema kya samu abokiyar hira ko abokin taya hira. Habib ya ɗan saci kallonta suka haɗa ido yayi saurin kawar da idonsa yana jin gabansa na faduwa da zuwan nata. Dukda yasan bata saba kawo ƙararsa sa ba, amma yana jin kaman sauyin da ta gani ne yasa taxo ta sanarwa da Mama. Tashi Mama tayi ta barsu a palon. Ya dawo kusa da ita ya ce "Wa kika tambaya kika fito? Kuma me kika zo yi a wannan lokacin kamar an koroki?" Ta ce "Ai koroni ɗin kayi, kuma ba zan koma ba har sai ka faɗa min abun da yake damun ka, na gaji, gaba ɗaya ka sauya min, baka zama kaci abinci, jiya ina kula da kai ko barci ba kayi ba, yau da safe ka fita babu ko magana, ko ka gaji dani ne, idan ka gaji ka faɗa min sai na bar maka gida?" Ta ƙarasa da kamar faɗa. Habib sai rufe mata baki yake tana ture shi. Ya ce "Haba Beb ina ce na faɗa miki cewar wani sharri ake son ƙulla min a makaranta kuma Allah ya ƙwace ni komai ya wuce" ta ce "To mai yasa baka koma gida ba?" Ya ce "Ai daga nan gidan zan koma" ta ce "Ka min alƙawarin cewar komai ya wuce ba zaka sake yimin irin abun da ka min ba?" Ya ce "Nayi alƙawarin komai ya wuce"  Ta ce "To kayi dariya kuma kace beb ba zan sake ba harda riƙe kunne?" Ya ce "Idan kuma Mama ta shigo fa, kizo muje gida har doki sai nayi miki?" Ta ce "No ni yanzu nake so kuma anan" Habib ya sunkuya ya kama kunne ya ce "Beb ba zan sake ba" ya faɗa yana miƙewa. Ta yi dariya tana jin daɗin hakan. Ta kalleshi ta ce "Ya Allah duk masu son ganin sun tonawa Beb asiri Allah ka tona musu?" Ya amsa da amin. Ta ce "Mu dage da addu'a Allah na tare da mai gaskiya, duk yadda suke son ganin bayanka Allah ya fisu. Kusan karfe sha ɗaya suka koma gida bayan ya biya sunyi siyayya na kayan kwalliya harda abubuwan sha da take so. Suna komawa gida suka shiga kichin tare yayi kokarin kawar da komai ya tayata sukayi girkin rana, kuma suka zauna suka ci. Suna ci suna hira amma hankalinsa naga agogo domin baya so ya makara, so yake biyar tayi masa yana cikin class ɗin yadda zai kori duk wanda ya shigo daga baya. Kamar daga sama yaji Nadiya ta watso masa tambayar da sai da ta hautsuna masa kayan cikinsa, har abincin da yaci na yunkurin dawowa tsabar tsoro. Ta ce "Na kira number ka ɗazu naji an ɗaga ina ta magana naji shiru, hakan ne yasa hankalina ya tashi, kuma ina ta kira ba'a ɗagawa, lafiya dai ko?" Ta faɗa tana zama kusa da shi. Tsabar firgita bai san lokacin da ya furta cewar "Ta ɗaga?" Nadiya ta kalleshi cike da rashin fahimta ta ce "Ita wa ɗin, number ka fa nake magana?" Sai lokacin ya kula da abun da yayi. Gaba ɗaya abun ne yayi masa biyu, farincikin bata mutu ba, da kuma tsoron abun zatayi da wayar gashi babu security a wayar. Ya ce "Eh ita wayar nake nufi, yanzu haka take min sai ta ɗaga kanta da kanta ko tana aljihu ne" ya faɗa ba tare da yasan lokacin da ya shirya karyar ba, kawai dai yaji tana fitowa ne daga bakinsa. Ganin kamar ta yarda sai ya ɗora da cewar "Faɗuwar da nayi jiya ne na zauna a kanta, to shine ɗazu da na fita na kaita gurin gyara, to ko tana gurin ne kika kira, yanzu ma haka zan biya ne na amsota idan zan tafi makaranta". Ya faɗa yana kuma jin ko shi ya gamsu da wannan batun. Ta ce "To Allah ya ƙara kiyaye wa beb. Ya amsa da amin. ƙarfe huɗu ya baro gida ya tsaya a wani masallaci yayi sallar la'asar. Yana fitowa ya nufi school ɗin. Bai shiga ajin ba sai biyar yana ta mamakin yadda Nadiya tace an ɗaga wayar to kenan ita ce ko yaya. Koda ya shiga class ɗin ya tarar an zo da yawa, amma ga guraren wasu nan da yawa basu zo ba. Nan take ya fara yin abun da ya kawo shi, duk wanda yazo sai ya kora shi waje. Sosai ya ya haɗe ransa Kamar kullum baya ko bada fuskar raini ga kwanni ɗalibi. Ya gama bayani kenan ya juyo yana neman ƙarin bayani a gurin ƴan ajin yaji ana shigowa, yana ɗaga kai ya ganta tana tafiya kamar mara lafiya, sanye da wani sket ɗan ƙarami ya ɗangale mata, fuskar nan tata babu ko kwalliya sai ma wani ɗan haske da tayi, jakar school ɗin ta rataye a kafaɗarta ta dama. Tsayawa tayi tana kwallonsa shima ya shagala da kallonta har ya manta da cewar a gaban dalibai yaƙe. Bai san lokacin da yace mata "Get in" ya faɗa har lokacin yana jin yanayin nata har cikin ransa. Lokaci ɗaya dalibai suka fara kallon-kallon, bayan kowa yasan halinsa na hana kowa shiga idan har ya shigo class. Ganin haka yasa ya yi saurin yiwa na waje alama da hannu akan suma su shigo. Haka suka shigo yaci gaba da jawabi amma hankalinsa na gareta. Ita kanta shi take kallo domin ko rubutu ɗaya batayi ba, yana ɗago kai sai ya samu shi take kallo. Dogayan ƙafafuwanta dake waje masu haske suna daga cikin abun da suke ɗauke masa hankali idan ya kalleta. Idan bai yi ƙarya ba har kanne masa ido yaga tana yi tana murmushi, zuciyar sa ce ke harbawa da karfi yana ta ƙoƙarin ganin ya natsu sosai. Haka ya gama koyarwar ya fita ya ya nufi ofis ya yi mata alama da ido akan ta same shi a cen. Yana shiga ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai zagaye yake yi yana ta alla-alla ta shigo ya amshi wayarsa ta ƙara gaba shima yasan inda dare yayi masa, tunda Allah yasa bata mutu ɗin ba. In sha Allahu ya ɗauki darasi daga wannan abun, ko kallonta bai zai ƙara ba. Yana cikin haka yaji ta turo ƙofar a hankali kuma ta rufe tana kwallonsa, shima kallonta yayi har yana haɗiye yawu ba tare da ya sani ba. Jakar hannunta ta jefar gefe ta nufo gurin da yake tana masa wani irin kallo mai tafiya da imanin mutum. Habib sai ya tsinci kansa da kasa daina kallonta. Ta tsaya a gabansa ta ce "Sir" sai kuma tayi shiru ta dafa girjinsa sai kuwa gashi ya zauna a kan kujerar dake kusa da shi...📝 S Reza... [09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️* °*S-Reza✍️* _First class writers association_ _My whasop chanel_ *Chapter 4️⃣* Cikin wata siririyar murya ta ce "Sir i miss you, ina ta tunaninka ko barci na kasa yi ina ta son nazo school kawai saboda na ganka, shin kaima ka yi kewa ta?" Ta ƙarasa ta na zama a kan cinyarsa. Kasa magana Habib ya yi sai binta da kallo kawai ya ke yi, ga shi duk ta cika masa ofis ɗin da wani almurin turare mai shegen ƙamshi. Tambayoyi ne da ya wa a bakinsa da yake so yayi mata amma ya kasa samun damar yin ko guda ɗaya. Bai san mai ya sa idan baya tare da ita yake jin zai iya rabuwa da ita ba, amma daga lokacin da suka yi ido biyu sai komai ya kama gabansa, sai ya ra sa wannan ƙwarin gwuiwar da yake tunanin yana da ita na rabuwa da ita. Jin ya yi shiru ta sake faɗin "Sir baka yi kewar tawa ba ko?" Ta faɗa ta na tura hannunta cikin rigarsa kan ƙirjinsa. Wani irin ajiyar numfashi ya sauke ya na lumshe ido. Iska ta hura masa a fuskar sa hakan yasa ya buɗe idon da sauri ya sauke a kan nata. Sai ta sakar masa murmushin nan na ta mai narkar da shi. Shi kuwa idanunta ya kalla masu ɗan girma sai yaga yadda suka bada wani irin kala kaman jaa kaman kuma fari. Gabansa ne ya faɗi, domin sai yanayin idanunta suka yi kaman ba na mutane ba. Sai lokacin ya samu damar yin magana kamar mara lafiya ya furta "Ina waya ta?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye bayan ya ture ta ta sauƙa daga jikinsa. Kawar da kai gefe ya yi ganin ƙirjinta a waje lokacin da ta tashi, har tsoron haɗa ido da ita yake yi. Ita kuwa sai ta tsinci kanta da son rungume shi domin da gaske tayi kewarsa, hakan yasa bata tsaya yin tunani na biyu ba ta rungume shi na kusan minti ɗaya kafin ta sake shi jin bai hanata ba kuma bai taɓa ta ba, ya dai tsaya kamar gungume a tsaye ƙiƙam. Ya sake ce wa "We're is my phone?" Ta ce "Sir wayarka na mantota a gida saboda saurin da nakeyi, amma idan ka na so yau kazo gida anjima sai na baka, ko ka bari ranar Monday na kawo maka school" Da sauri ya ce "What akan me zan zo gidan ku, saboda me?" Haura ta ce "Sir baka sona kenan?" Ta faɗa kamar tayi kuka da wannan malalaciyar muryar tata. Habib ya kalleta da mamaki a zuciyarsa ya furta so kuma dani!. A fili kuma ya ce "Soyayya kuma?" Ya faɗa da mamaki. Domin shi dai bai jin sonta, amma yana jin tana burgeshi, yana son ya ganta, kuma yana jin daɗin magana da ita, muryarta na masa daɗi sosai. Ya na faɗa ta juya da sauri ta ɗauki jakarta ta gyra rigarta, ta ɗauki biron gabansa tayi rubutu a wata karamar takarda ta ajiye masa ta juya har zata fita sai kuma ta juyo ta ce "Idan kana son wayarka kazo ka amsa ko ka kira wannan number". Ta na faɗa ta bar ofis ɗin ya bita da kallo. Da sauri ya ɗauki takardar yana dubawa. Sunan unguwarsu ne da number gidan su, kuma ga number waya nan da alama tata ce. kaman ya yayyaga takardar amma ya fasa ya saka a aljihu ya shirya ya fito daga ofis ɗin yana kallon yadda har aka kusan watsewa daga school ɗin. Yazo zai buɗe motar ya shiga yaga anyi rubutu a murfin motar da farin abu. Ya tsaya yana karantawa kamar haka. Sir I'm waiting for u in my dream, Sir don't forget about your phone, Sir I'm in love with you, Sir i love You to moch Bay". Yana gama karantawa ya shiga waige-waige ko zai hangonta, amma ko mai kama da ita bai hango ba. Da sauri ya shiga goge wa da hannu, ganin yana goguwa ne yasa ya buɗe motar ya ɗauko sauran ruwa ya shiga wanke wa. Yana gamawa ya buɗe matar ya shiga, ya ɗwuke ki zai kunne kenan yaga rubutu akan sitiyarin motar da wata farar takarda ƴar ƙarama. Gabansa ne ya bada wani rass, zuciyar sa tayi wani irin tsalle kamar zata fito, waro ido waje yayi yana dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya, sannan ya shiga duba takardar da kyau. "Sir I love you" Shine abun dake jikin takardar, sosai ya shiga duba cikin motar, to ta ina ta shigo, shida kansa ya buɗe motar da zai shigo fa. Sosai hankalinsa ya tashi ya rasa ma to wani tunani zaiyi domin wannan lamarin a kwai ɗaurewar kai sosai. Ya na hanyar gida ya na ta mamakin yarinyar, amma ta ɓangare ɗaya kuma ya na jin sanyi da Allah yasa ta na nan da ranta kuma babu abun da ya sameta. Gaba ɗaya ma ya manta bai iya tanbayarta yaya aka yi ta fita daga cikin school ɗin ba bayan an rufe get, to ko dai a cikin school ɗin ta kwana. Shi kadai dai yake ta tunani har ya iso gida. Bayan ya faka motar ya koma ya rufe get ɗin ya nufi cikin gidan da sallama. Jin ba'a amsa bane yasa ya nufi ɗakin sa domin ya ɗauro alaula jin an ta Sallah. Lokacin da ya fito ya samu Nadiya ta na salla a palon hakan yasa ya wuce ta izuwa masallaci, har lokacin tunanin abun ya ƙi barin kansa. Koda ya dawo bata palon hakan yasa ya nufi cikin ɗakin na ta. Ya na shiga ya sameta zaune da waya a hannu. Yana shiga ta ce "Ina wayarka?" Ta faɗa babu wasa a muryarta, kuma ga wani kwantancen rigima da ya hango a kan fuskar tata. Habib ya kalleta da mamaki kuma duk rashin gaskiya sun baiyana a fuskar sa, da gyr yayi ƙarfin halin faɗin "Ta na ta ta na ta gurin gyra ai na faɗa miki"  Sai ta miƙe tsaye wanda hakan yasa saida ya ɗan ja baya domin ya tsorata da yanayinta. Ta ce "Beb ina wayarka, bana son ƙarya wacce shegiyar ce ka bawa da har take turo min sako ta whasop, kuma har take kirana sai na ɗaga taƙi yin magana ?" Daram dararam! Gaban Habib ya bada wannan sautin. Da Karfi ya fisge wayar yana kallo kamar zai shiga cikin ta. Gashi nan har yanzu ana online a wayar, ga saƙo nan kusan guda biyar ana turowa harda kira da akayi. Sai kawai ya tura kira shima ta whasop ɗin yana jin wani sabon tashin hankali da wannan yarinyar ke son jefa shi, shi ina zai iya da rikincin Nadiya gata da ciki dama ya ya aka ƙare. Ya gama karantawa amma ya kasa ɗagowa su haɗa ido, gashi har kiran ya yanke ba'a ɗaga ba. Fizge wayar ta yi ta ce "Baka faɗa min ba wacce?" Ta faɗa cikin tsawa wannan karan ma. Habib ya auro dauriya ta mazaje ya ce "Wai mata suna gyaran waya ne, nace niki gurin gyara na kaita, kuma ɗazu naje bai fito ba, shi yasa da kika ce an kira ki abun ya bani mamaki. Tayi masa wani irin kallon rainin hankali ta ce "Tun fa ɗazu nace maka an kira ni, Ok ita wayar sai ta zaɓi iya numbar na ta kira, kuma sai ta hau whasop nan ma ta zaɓi iya numbar na ta turawa message irin wannan ko? Shin Habib wai ka fara kula-kulan mata ne ban sani ba, na rantse da Allah idan har na sameka da cin amana ta zaka sha mamaki, kasan wacece ni, kasan abun da zan iya da wanda ba zan iya ba. Ta na faɗa ta bar masa dakin ya bita da kallon mamakin jin yadda ta ambaci sunansa ɓaro-ɓaro a bakinta wanda rabon da yaji ta faɗa tun da suka fara soyayya. Da sauri ya bi bayanta ya samu bata palon. Sai ya bita kichin ɗin ya samu tana juye abinci a kula sai turiri abincin yake yi. Da saurinsa ya nufo gurin ta zaiyi magana tayi saurin nuna shi da chokalin hannunta ta ce "Karka ce min komai Wallhi idan kamin magana zan kwaɗa maka wannan chokalin. Ta faɗa tana kawar da kai tana cigaba da abun da takeyi. Juyawa yayi bai ce komai ba ya bar gidan gaba ɗaya da motar sa yana jin wani irin ɓacin rai, mai yasa zata dinga kiran matarsa, bata da hankali ne, sai kawai ya nufi unguwar da ta rubuta masa yana jin yau sai ya wanke mata fuska da mari sau babu adadi, kuma yayi mata ƙargaɗi akan ta fita daga sabgarsa. *°HAURA* Aisha Adam sunanta kaman yadda ku ka sani, amma ta na amfani da sunanta na asali a school. Ta na zaman ruƙu ni a gurin Amera da Adam wanda suka ɗauketa kamar ƴar su. Su biyar ne a gidan Adam sai Amera sai ƴan biyunta da ta haifa Salim da Salma sai ita Aisha ɗin Wato Haura. Tun lokacin da ta zama ƴar gida basu taɓa nuna mata wani banbanci tsakanin ta da Salim ko Salma ba, hatta su kansu basu taɓa sanin cewar ba Amera ce ta haifi Haura ɗin ba. (Duk mai son jin asalin labarin Haura yaje ya naimi littafin Amera da Adam) Sun tashi cikin soyayyar juna sosai, domin babu laifi Adam na da rufin asiri sosai, dukkanin bukatunsu ya na ƙoƙarin sauƙe musu. Anan hannunsa ta yi secondary har izuwa yanzu da take matakin diploma shekara ta karshe. Bata da matsla dasu haka suma suna jin daɗin zama da ita. Ta na musu biyya daidai gwargwado haka kuma ta na jan ƴan ƙannen nata a jiki sosai domin duk inda take suna nan. A wannan shekarar zata kammala karatun ta daga nan kuma zata cigaba kaman yadda tace musu kuma suka bata goyan baya, dukda cewar su ɗin suna son yi mata maganar aure amma suna tsoron kar taga ko da wata manufa ne, kar tayi tunanin ko sun gaji da ita ne. Haura yarinya ce karama sosai kuma a kwai rashin wayo sosai a tare da ita, sannan hausarta bata fita daidai har wannan lokacin. Bata tsayawa da samari kwata-kwata duk da yadda suke yawan tsayar da ita, haka take yin rayuwarta ita ɗaya bata son shiga mutune, kuma hakan ya samo asali ne tun daga farkon rayuwarta da inda ta taso da kuma irin mutanen da tayi rayuwa dasu a baya, har wannan lokacin bata iya sakewa da mutane sosai, kana ganinta zaka mata kallon mara wayo kuma yarinya, sai dai hakan bai sa ta zauna babu ƙawaye ba. Ta na da ƙawaye kusan uku amma wacce kusan kullum suna tare itace Maryam Kabir. Babbar kawarta kenan wacce har gida ta na zuwa, Adam da Amera duk sun san da Maryam, kuma sun yarda da ƙawancen su. Ita kanta Maryam ba sanin cikin Haura take yi ba, domin haka take bata yawan magana sannan tana da wahalar yin fushi. Bata iya faɗin abun da ya dame ta, amma idan kai ka faɗa mata naka zata tayaka neman mafita harda shawara mai kyau. Wani guda ɗaya kuma shine bata da tsoro a rayuwar ta, sam-sam bata tsoron komai ciki harda mutane, zata iya kallon cikin idonka ko idonki ta faɗa miki duk abin da kikai mata wanda bata ji daɗi ba, kuma daga lokacin ya wuce kenan. A rana ta biyu da Habib ya fara zuwa class ɗin su a matsayin sabon malami ne tazo a makare, hakan yasa koda tazo zata shiga ya tsayar da ita, kuma gashi ita ɗaya ce kawai ta makara duk class ɗin, haka wannan ranar ta rasa wannan text ɗin nasa, kuma abun yayi mata ciwo sosai. Abun ya ɓata mata rai domin koda ta koma gida saida Amera ta tambaye ta abin da ke damunta ta ce babu komai, a ranar haka ta uni abun nata dawo mata a rai. Haka washegari ma tazo school ɗin wanda sai ta tsinci kanta da son ganinsa ko hararsa tayi ko zata huce, amma ranar bai zo ba. Washegari ma haka bai zo ba, haka har kwana biyu bata sake ganin sa, gashi ta kasa tambayar kowa ko an sauya masa class, Kuma ko sunansa bata sani ba, amma ba zata iya tambaya ba, duk sai ta damu da hakan, ta kasa sakuni. Abun da bata sani ba kuwa shine, kullum yana zuwa kawai dai suna yin katari ne na rashin haɗuwa. Rana ta uku ce take da class karfe takwas na safe hakan yasa ta fito da wuri lokacin Maryam ta mata kira ya kai uku. Tana ganinta ta ce "Ni Wallhi Haura duk lokacin da zamu fara exam sai dai mu raba hanya, haka kawai bayan kin san idan muka makara ba ƙyalemu za'ayi mu shiga ba sai ki zauna a gida kamar wata mai aure, ko uwar me kike yi oho!" Ta ƙarasa ranta a ɓace domin har lokaci ya kusa yi. Haura bata ce komai ba sai murmushi da tayi kawai suka tare mai keke suka shiga. Daidai sun nufi class ɗin nasu ne Maryam ta hango Habib ɗin shima ya nufi class ɗin, kuma ga wasu ɗaliban suma suna gudu domin kar ya riga su shiga. Hakan yasa  ta ce "Haura ga shi cen wallhi zai shiga" ta faɗa tana kama hannun Haura domin su yi gudu. Sai haura ta kalli gurin da ta nuna mata sai ta kwace hannunta ita kuma Maryam taci gaba da gudun ba tare da tabi ta kanta ba kar tayi mata a sarar wannan karatun nasa da zai taimaka mata a exam ɗin ta. Haka taci gaba da tafiya har yanzu kusa da ita, bai ko nu na ya san da ita ba zai wuce sai ta tsinci kanta ta faɗin "Good morning Sir?" Ta faɗa ta na ɗan sauri ta kamo shi domin su jere tare. Sosai taji daɗin ganinsa, gashi kuma tayi niyyar idan ta gansa ta haharesa ko tayi masa rashin kunya amma sai ta kasa, sai ma wani irin daɗi da taji, ga ƙamshin sa da yakeyi ya tafi da ita. Habib ya ɗan juya ya kalleta sai kawai ya ɗaga mata hannu alamun amsawa yaci gaba da tafiya. Ita ma bata ce komai ba ta ce gaba da jerawa dashi ta na jin yadda saurin nasa ke son fin ƙarfinta. Shi kuwa da mamaki yake ta satar kallon ta, shi bai ma kawo cewar class ɗin sa zata shiga ba, har saida yaga ta biyo bayansa. Da Karfi ya daga mata tsawa sannan ya nuna mata hanyar fita daga class ɗin yana jin wani irin ɓacin rai da rainin wayon yarinyar. Kowa dake class ɗin saida ya tsarota balle amma banda ita da ta kafe shi da ido. Kallonsa ta yi ganin yadda har wani ɗaga jijiyoyin wuya yake kamar wata uwar a kayi masa. Juyawa ta yi kaman zata fita ɗin sai da ta tabbatar ya juya ya shiga sai ta shigo da gudu, kasancewar gurin zamanta a gaba yake yasa har ta zauna bai kula ba.  Saida ya ajiye abubuwan hannunsa sannan ya juyo ya fara musu jawabi cike da ƙwarewa da iya koyarwa. Rubutu yayi sannan yayi tambaya sai Haura ta ɗaga hannu yace ta tashi. Nan ta bada amsa sai ya bita da kallo. Yana so ya tabbatar da cewar kamar itace wannan yarinyar da ya kora fa yanzu amma ya kasa gano wa, hakan yasa ya fito ya leƙa waje amma baiga kowa ba. Dawawo yayi ya sake kallonta da mamaki a fuskarsa ita kuma tana tsaye har lokacin domin bai bata izinin zama ba. Ganin dai ya rasa mai zai ce ne yasa yace ta zauna, yana ta satar kallon ta da kuma mamaki. Sai dai duk lokacin da ya leƙo sai ya tarar tana kwallonsa harda murmushi. Haka duk lokacin da yazo haka zata dinga masa dariya ko murmushi harda ɗaga masa gira. Tun ya na kawar da kai, abun na basa mamaki har ya fara ankara da abun. Watarana bayan an tashi ne ya kirata ofis ɗin sa yana so ya kankara mata worning akan idan bata daina masa wannan shirmen ba zai zane ta... S Reza...✍️ [09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️* *°S-Reza✍️* _First class writers association_ _My Whatsapp chanel_                        *Chapter 5️⃣* Bayan ta zauna ya ce "Ke baki da hankali ne? Baki san nan school bane da zaki dinga mana wasa da shirme, to daga yau idan na ƙara shiga class naga kina dariya saina zane ki a gaban mutane, wawiya mara kamun kai kawai" Ya na faɗa bai bata damar yin magana ba ya koreta daga ofis ɗin ya na mamakin yadda take iya kafe shi da ido. Tun daga lokacin Haura ta gane son Habib take yi, kuma daga ranar kullum idan tazo sai ta dinga jin kamar ta je ta faɗa masa cewar ta na sonsa, ita dama a yanayin rayuwarta babu kunya bata ma san cewar abun kunya ne mace tace wa saurayi ta na sonsa ba, haka ita a irin rayuwar ta bata jin zata ji kunyar abun da take so, kuma a yanayin yadda take jin Habib ranta ko kanta ne zata iya bashi. Hakan yasa yanzu take yin duk mai yiwuwa domin taga ta jawo hankalin sa, ana haka Maryam ta gane halin da take ciki, babu irin maganganun da bata faɗa mata ba tace babu ruwanta ita dai tana sonsa. Tun Habib baya yana ɗaure fuska har ya fara damuwa da ita. Haka zata ja sket ɗinta har cinya tana kuma kanne masa ido. Ta na sonsa sosai domin shine mutum na farko da take jin tana so har haka a rayuwarta.  Haka watara ma ya sake kiranta ofishin sa domin yaga abun nata ya fara wuce gona da iri. Saida lokacin tana shiga ta ƙarasa gabansa ta rungume shi ta ce "Sir me kake so nayi maka?" Ta faɗa da wata shegiyar muryarta mai laushi. Habib ya kasa cewa komai sai ma biyeta da yayi har sukayi shafe-shafe. Tun daga lokacin yake ta kokarin ganin ya gujewa abubuwan da take masa amma ya kasa, har ta kai ta kawo shima yana damuwa da rashin ta, idan yazo school bata nan ya dinga damuwa kenan. A haka ne ranar suka so aikata wa amma ta suma. Lokacin da ya bar class ɗin a daren itama ta farka da tari, amma taga duhu amma ko a jikinta. Miƙewa tayi ta na mayar da kanta ta fara neman hanya zata fita sai ta taka wayarsa. Hakan yasa ta sunkuya ta ɗauka. Hotonsa ne shida Nadiya a gaban wayar, hakan yasa gabanta ya faɗi ganin yana da mata. Dafe wayar tayi a ƙirjinta ta na jin wani irin haushi da kishin ganin su a tare. Zama tayi a class ɗin domin ita dama ko kaɗan bata san tsoro ba, domin ita ko magana ce bata jin tsoron yiwa mutum bare kuma zama a cikin duhu ko kuma yin tafiya cikin dare. Ta kai minti uku ta na danna wayar sannan ta kama hanyar fita daga class ɗin. Haka tazo bakin get Emeka ya taso ya na tambayar waye. Tace masa itace. Ba tare da doguwar tambaya ba ya buɗe mata ƙaramar ƙofar ta fita ganinta da ƙaramar jaga ga shi kamar barci tayi. Dukda haka bai tsaya ba saida ya koma ya sake duddubawa. Koda ta isa gida lokacin hankalin Adam da Amera harda suna Salim duk a tashe yake sun kasa zama, gashi kuma bata tafiya da waya school, kuma Adam yaje har school ɗin ance babu kowa. Amera ta ce "Ina kika je haura?" Ta faɗa da ɗan ɓacin rai ganin lafiyar ta lau. Haura ta ce "Anty babu ko ina fa, na tsaya yin rubutu ne har dare yayi" ta faɗa ta na zama a kujera mai cin mutum Uku. Salima ta karasa kusa da ita tace "Anty Daddy ya na ta faɗa harda mommy ki daina dadewa haka kinji?" Haura ta ce "To ba zan sake ba, amma kunyi sallah?" Ta ce "A'a yanzu zamuyi" ta ce "To kuzo muje muyi?" Ta faɗa ta na kamowa harda Salim ɗin da shima yake zaune kusa da ita. Amera ta kalli Adam ta ce "A kwai matsla fa, tun ba yanzu ba na fara lura da yarinyar, anya kuwa ba soyayya ta fara ba, nifa ina tsoron kar wani ɗan iskan saurayin ya yaudareta kasan ba wayo gareta ba. Ta ƙarasa ta na jin tsoron har zuciyarta. Adam ya ce "Soyayya kuma, a'a kawai dai zuwa gobe sai mu zauna da ita muji meye ya faru. Haura na shiga ɗakin suka yi alaula kowa yayi Sallah sannan suka fito palo domin cin abinci. Haka suna cin abincin suna ta satar kallonta, ita kuma ganin haka yasa ta mayar da hankalinta ga cin abinci da kuma wasa da sukeyi da su Salim. Suna gamawa ta kwashe kwanunkan ta kai kichin ta fito ta raka su Salim ɗaki bata fito ba sai da sukayi barci. Ta na fitowa ta samu adam da Amera a palon suna kallo. Har zata wuce Amera ta kira sunanta. Ta dawo ta zauna kusa da ita tana kallonta. Har zatayi magana Adam ya ce "Ba nace ki bari sai da safe bane, Kinga Haura je ki kwanta sai gobe kinji" ya ƙarasa yana bata umarni. Haura ta mike ta shige ɗaki. Kwance tayi ta na kwallon saman ɗakin. Abun da ya faru dasu yaune keta dawo mata, kenan guduwa yayi, to ko ya na tunanin mutuwa tayi shi yasa ya gudu. Ta na sonsa zata iya masa komai, amma sai ta tabbatar da cewar zai aureta, lokaci ɗaya kuma ta tuno da cewar yana da mata fa. Da sauri ta mike ta dauko wayar tasa ta na kallon hoton nasu. Gwada jan wayar sama tayi sai taga babu password. Da sauri ta gyara zama ta shiga gurin hotuna, babu hotonansu da yawa domin daga shi har ita ba masu son yin hoto bane. Jin kamar motsin mutum yasa ta kashe wayar ta kwanta. Washegari bata da class sai na yamma hakan yasa bata fita ko ina ba, ta ɗauki wayarta ta' shiga Whatsapp tana chatting sai taga ana kiransa. Dubawa tayi taga an rubuta Beb da Hoton zuciya. Kaman ta ɗaga sai ta fasa, ganin an sake kira ne yasa ta ɗaga amma tayi shiru. Haka Nadiya ta gama hello hello amma babu amsa. Number Nadiyar ta saka a wayar ta tayi seving bayan ta kira itama ta masa seving. Ajiye wayoyin tayi jin Amera na kiranta. Ta ce "Me kike yi a ɗaki ne tun ɗazu, kin duba lokaci kuwa?" Haura ta ce "Aunty yanzu fa dama zan fito" Amera ta bita da kallo sai kuma tayi shiru ta ce "Mai zamu dafa da rana?" Ta tambaye ta domin dama wasu lokutan ita ce ke zaɓar musu abun da zasu girka. Haura ta buɗe baki zata yi magana suka ji sallama. Juyawa sukayi a tare suna amsawa. Nana ce tare da mijinta Nasiru suka shigo. Amera ta ce "Ai da gida ma kika wuce nima yanzu nake son tafiya" Haura ta ce "Anty Nana maraba" ta samu guri ta zauna ta na faɗin "Idan baki son zuwan nawa ai sai na koma ina da gurin zuwa. Kafin tayi magana Nasiru ya shiga gaida Amera cikin girmamawa, ta amsa ta na masa maraba. Da sauri Haura ta buɗe friji ta kawo masa ruwa. Sannan ta koma kichin. Bata fito ba sai kusan biyu na rana lokacin ta gama komai. Har lokacin kuma Nana ta na nan, hakan yasa ta zobo mata abincin ta kawo mata. Itama Amera ta ce ta zubo mata. Bayan ta ajiye musu ne ta koma ɗaki domin ta shirya. Amma sai ta dauki waya ta shiga dube-dube, daga haka ta shiga whasop sai taga number beb ɗin nan tayi magana. Hakan yasa ta mayar mata. Daga haka kuma ta shiga toilet domin yin wanka.  Koda ta fito ta shirya da sauri lokacin taji muryar yaran sun dawo. Fita tayi ta cire musu inifon ta zuba musu abinci suka ci tare sannan ta ƙarasa shiri ta nufi school ɗin tana ta addu'ar Allah yasa yazo. Lokacin da ta bar ofis ɗin sa bayan tace masa wayarsa na gida kuma alhalin tazo da wayar kawai bata so ta bashi ne, kuma yau bata so tayi dare ne yasa ta fita. Tun a hanya ta sake fito da wayar ta kunna data ta sake ganin number Bebb tayi magana, hakan yasa suka fara chatting ta nayi tana dariya. Kafin magriba ta isa gida lokacin adam ya dawo. Ta na shiga suka mata barka da dawowa ta faɗa wanka ta saka kayan gida ta fito palo ta samu har an gama abincin daren. Homework ɗin yaran ta fara nuna musu, sannan tayi musu wanka suka zauna suna cin abinci. Bayan sun gama suka zauna a palon ana hira Adam na basu labarin rashin jin yaran Khadijah ƙanwarsa da yaje gidan yau. Haura ta ce "Ai kawai Daddy wannan yaron a kaishi aikin soja domin zai fi bada gudunmawa acen.  Amera ta ce Salim da ya girme shi amma duka yake wa Salim harda kuka. Adam ya ce "Ai dama ko zubin halittar su ai ba ɗaya ba ne, ai wannan yaron idan ya girma ba ƙaramin mai zuciya za'ayi ba. Adam ya buɗe baki kenan suka ji ana buga ƙofar palon. Adam ya ƙarasa gurin yana tambayar waye bayan ya buɗe. Yaron ya ce "Wai wani ne a waje mai Mota yace a kira masa Aisha Adam Haura" yaron ya ƙarasa yana juyawa. Adam yabi yaron da kallo yana tuna maganar Amera da tace ko dai Haura Soyayya ta fara. Kaman ya fita yaga waye amma kuma ya bari sai ya fara jin ta bakin ita Haura ɗin. Amera ta ce "Waye ke sallama?" Adam ya ce "Wai wani ne a mota yazo gurin Haura" ya faɗa yana kallon ta. Da sauri ta ɗago tana kallon daddyn nata. Ta ce "Daddy ni?" Ya ce "Wacece Aisha Adam Haura?" Cike da fara'a da kuma addu'ar Allah yasa shine ta ce "Daddy waye shi ɗin?" Amera ta ce "Ban gane wani yazo gurinta ba, ka fita kaji waye, kuma me yazo yi ne?" Adam ya ce "To kin san ko tasan da zuwan nasa ne?" Amera ta kalli Haura ta ce "Kunyi da wani zai zo gurinki ne?" Haura ta ce "Eh Anty" Da sauri Adam ya ce "Waye shi?" Amera ma ta ce "A ina kika sanshi, kuma me yazo yi?" Suka jera mata tambayoyin a lokaci ɗaya. Haura da gaba ɗaya hankalinta ya tafi da son ganin ko shi ɗin ne ko ba shi ba ne ta ce "Anty bari na fara dubawa na gani ko shine ko bashi bane?" Ta faɗa tana tashi ta nufi ɗakin ta, sai gata da hijabi bayan ta sake fesa turare, suna zaune ta wuce su suka bita da kallo. Tun daga nesa ya hangota hakan yasa ya kafe ta da ido har ta ƙaraso. Buɗe motar yayi ya fito yana cigaba da kallonta. Kafin tayi magana ya ce "Bani waya ta yanzu ko na kwakƙwaɗa miki mari?" Ya faɗa ransa a haɗe. Haura ta ɗan saki murmushi ta ce "Sir naji daɗin zuwanka gidan mu, bari na kawo maka ruwa kaji?" Ta ƙarasa tana komawa cikin gidan. Tana ji yana kiranta amma bata ko juyowa ba. Tana shiga palon Adam da Amera suka tsayar da maganar da suke yi suna binta da kallo ganin tana ta murmushi abunta. Haura ta ce "Anty shine yazo hira" ta ƙarasa da dariya. Amera ta ɗan yi dariya itama ta ce "Shine wanda ya hana ki sakewa kwana biyu kenan ko?" Haura ta shiga kichin ta haɗo masa ruwa da ɗan abun taɓa wa. Ta fito ta sake wucewa waje. Gaba ɗaya Habib mamakin yarinyar ya keyi,ita wai ma murmushi yake yi abun ta. Bata nufi gurin da yake tsaye ba, sai ta ƙarasa gefe da gurin motocin Daddy ta ajiye tren sannan ta kawo kujeru guda biyu ta zauna a ɗaya ta na kwallonsa. Haka ya nufo gurin ya zauna ya ce "Bani waya ta? Mai yasa aka kirani kika daga? Kuma kika buɗe min whasop harda chatting da matata, wai baki da hankali ne ko menene?" Ya ƙarasa ransa da faɗa sosai wanda ita kanta sai da ta sake kallonsa. Haura ta ce "Ban san cewar kana da mata ba, kuma bayan na sani hakan bai dame ni ba, ni dai kawai nasan ina sanka Sir, dan Allah kace kaima kana sona, wallahi ban taɓa son kowa ba sai kai, kaima ban san lokacin da na fara sanka ina jin ba zan iya rabuwa da kai na sir". Ta faɗa da iya gaskiyar ta har muryarta na rawa. Ya ce "Bana son shirme da hauka, bani waya ta zan tafi gida, mata na tana jirana, kuma daga yau karki ƙara min wannan shirmen. Haura ta ce "Kana son matarka sosai ko Sir?" Ya ce "Fiye da komai ma kuwa, bana haɗa ta da kowa" ta mike tsaye ta ce "Tom nima ina sonta fiye da komai Sir tunda kana sonta, kuma watarana zan kawo mata ziyara, domin na ɗauki number ta a wayarka. Habib ya kalleta da sauri zaiyi magana ta ce "Sir bari na kawo maka wayar, kuma dan Allah ko ruwa ne ka sha idan ba haka ba ba zanji daɗi ba, kuma ka gaida min da Anty Bebb kace ina sonta ina kaunar ta. Tana faɗa ta nufi cikin gidan ya bita da kallo. Ya na tsaye zaune a gurin ta dawo riƙe da wayar. Saida ta zauna kafin ta ce "Sir ga wayar taka" Habib ya ƙarɓa ya miƙe zai tafi. Tasowa ta yi ya matso kusa da shi ta ce "Bari na raka ka zuwa motar Sir" Har suka karasa bai ce komai ba sai wayarsa da yake dubawa. Bayan ya shiga motar ne ya ajiye wayar zai rufe motar yaji ta riƙe murfin. Kallonta yayi ya ce "Wai ke mai yasa baki da zuciya ne, dan Allah ki fita daga sabgata nace miki ni ina da mata. Haura ta kafe shi da ido har saida ya janye nasa. Ta ce "Sir ka manta abin da nace maka ɗaxu cewar zan iya mutuwa idan ka rabu da ni? Da gaske baka sona?" Sai kuma jikinsa yayi sanyi har ya ji wani irin tausayinta...📝 S Reza.... [09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI❣️* *°S-Reza✍️* _First class writers association_ _My whasop chanel _ *Chapter 6️⃣* Rau-rau ta yi da ido kamar za ta yi kuka kuma har lokacin shi ta ke kallo. Ya ce "Kamar yadda na faɗa miki cewar inda aure to dan Allah ki fita daga sabgata, bani da burin ƙara yin wani auren". Ya na faɗa ya rufe motarsa ya mata kii ya bar gidan. Ta kai minti uku a tsaye kafin ta juya ta shiga cikin gidan. Ta na shiga palon ta tarar babu kowa hakan ya sa ta shige ɗakinta, sai da ta cire hijjab ɗin jikinta sannan ta shiga toilet. Koda ta fito doguwar riga kawai ta saka ta ta barci sannan ta kashe wutar ɗakin ta kwanta. Wani irin abu take ji game da Malam Habib wanda bata san yaya zata masalta shi ba. Fuskarsa da gemunsa da yanayin murmushin sa harda ɗaure fuskar sa duk burgeta ya ke yi, tafiyarsa da ƙamshin sa, maganar sa da fushin sa. Gaba ɗaya komai nasa kyau yake mata, ta na sonsa ita kanta ta san da hakan. Sai kuma ta fara tunanin yadda zata saka shi shima ya so ta, domin ta lura yana son matarsa sosai kamar yadda ya ce mata. Haka haura ta raba dare ta na tunanin yadda za ta ɓullowa Habib har ya fara sonta. Da asuba kiran sallah ya tashe ta Kamar kullum. Bayan ta tashi ne ta ji jikinta a jiƙe hakan yasa ta yi saurin tashi ta shiga toilet ta na mamakin faruwar hakan a mafarkinta a karon farko. Bayan ta idar da salla ta sake komawa barci kasancewar ranar juma'a ce bata da class har sai Monday hakan yasa take son ta biya bashin barci. Wata karamar riga ta saka wacce ko guiwa bata wuce mata ba, ta ja bargo ta fara barci. Ta na barci Salim ya shigo ɗakin ya na kiran sunanta da karfi kamar an turoshi, ta buɗe ido zata yi magana taga haske ya cika ɗakin. Da sauri ta duro daga kan gadon ta ɗauƙi wayar ta domin duba lokaci. Ganin takwas harda minti biyar ya sa ta kama hannunsa suka fito ta manta da iya rigar barci ce ajikinta kawai. Ta na fitowa palon da nufin shiga kichin gurin Amera saboda jiyo motsinta da tayi a cikin shi kuma Adam ya fito cikin shirin sa na zuwa gurin aiki riƙe da hannun Salma. Kallo ɗaya ya yi mata ya yi saurin kawar da kai ya na jin wani irin kasala na son kama shi. Haura da bata kula da yanayin ta ba ta ce "Daddy good morning?" Ta faɗa ta na ƙarasowa har gabansa. Muryarsa na rawa ya amsa ya na ƙoƙarin ha na kansa sake kallonta amma ina zuciyar sa ta yi rinjaye akan son ganin abun da bai dace ba. Ya sake ɗaugo kansa a karo na biyu ya sauke a kanta sai yaji natsuwarsa ta kau, ya tsinci kansa da karewa halittar jikinta kallo kasancewar komai a bayyane suke, ya na shagwaltuwa da hakan har ya na jin wani annashuwa na son kama shi, zuciyar sa na raya masa cewar lokaci yayi da zai ƙarasa aikin ladan da yayi niyya. Muryarta ce ta dawo da shi zahirin sa. "Daddy har ka shirya zaka tafi kenan, kaci abinci ne?" Adam ya ɗan sosai kai ya ce "Am a am ai na dawo tun ɗazu, ai sorry eh yanzu zan tafi sai na dawo" Ya karasa ya na barin gidan Salim da Salma suka shiga mata Bye-bye suna bin Daddy a baya. Haura ta ƙarasa kichin ɗin ta buɗe ta shiga ta na godewa Allah ma da yasa yau bata da class. Amera da ta juyo jin an shigo. Suna haɗa ido ta ce "Meye haka haura, a haka kika fito babu kaya a jikinki, ko kin fara hauka ne?" Ta ƙarasa ranta a mugun ɓace. Da sauri ta kalli jikinta sai ta toshe baki ta ce "Haba Anty babu kaya kuma, rigar barci ce fa, bari na je na sauya to". Ta na faɗa ta juya ta koma ɗaki domin sauyawa. Binta da kallo Amera ta yi ta na mamaki Allah dai yasa lokacin da ta fito Adam ya fita bai ganta a haka ba. Har zata cigaba da aikin amma sai ta kasa ta fara tunanin wannan iya shegen, sam ba zata saɓu ba, dole ta taka mata burki, ba zata juri wannan karuwancin ba, ko kuma tunda dai har an samu wanda ta fara so kawai ta turo shi yazo a faɗa masa ita ɗin wacece idan zai iya auranta a haka ya aureta ta kama gabanta, ai sunyi wanda zasu iya. Ajiye aikin ta yi ta fito palo har lokacin ta na jin haushin abun da ya faru, dama kwana biyu ta fara lura da yarinyar kamar ta na son tsoro da sabon salon rayuwar da bata santa da shi ba, to dole ta dauki mataki tun yanzu. Zaune ta samu Haura ɗin ta zuba abinci amma ta kasa ci sai kallon guri ɗaya kawai ta keyi bata ma tasan ta zauna ba. Amera ta ce "Magana nake son yi da ke Haura?" Zumbur ta dawo daga tunanin da take yi ta kalli Amera sai taga fuskar nan tata a ɗaure. Ta ce "Anty ina kwana?" Amera ta amsa da cewar "Lafiya, magana nake son yi da ke?" "Tom ina jinki Anty" Haura ta faɗa ta na bata hankalinta gaba ɗaya. Ta ce "Shi wannan da yazo gurinki yaushe kuka haɗu, kuma sanki yake yi ko dai kawai Soyayya ce ta kawo shi?" Ta faɗa ta na kuma kafe haura ɗin da kallon da ta kasa gane masa. Haura ta ce "Anty saurayi nane" ta faɗa iya haka kuma tayi shiru. Ran Amera ya ɓaci domin bata son shiru-shirun wannan yarinyar. Dama tasan ba zata taɓa faɗa mata gaskiya ba. Ta ce "To idan da gaske auranki yazo yi kice masa ranar Sunday Daddynki na son ganinsa" Haura ta ce "Mai zai zo yayi masa?" Ta ce "Yazo ayi maganar aure mana, ko ba auranki yazo yi ba?" Da sauri ta ce "Eh aure ne amma kuma ai" sai tayi shiru. Ta faɗa tunanin yadda ma take sonsa shi kuma ko a jikinsa. Amera ta ce "Koma meye kice yazo idan yazo ai Daddy ɗin zai masa magana. Yanzu dai ki gama cin abincin ki haɗa wannan sauran kwanunkan ga cen sauran tukwanan da na fara wankewa, sai ki haɗa ki wanke tunda yau soyayya yasa kin makara baki fito kin yi aiki ba. Ta na faɗa ta mike ta bar gurin Haura ta fara cin abincin ta na tunanin maganar Amera. To ita da bai ma ce ya na sonta ba ina batun zuwa ayi maganar aure. Ita bata san cewar da hakan zai faru sai ta fi kowa murna ba. Bata gama cin abincin ba ta kwashe ta kai kichin ta gama wanke komai kafin ta koma ɗaki. Waya ta ɗauka ta danna kiran number sa, wanda tun ɗazu take ta saurin tazo ta kirasa ko Allah zai sa ya ɗauka taji muryarsa kawai. Sai dai har ta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kira tayi shima ba'a ɗaga ba. Sai ta tura masa saƙo. Bayan ta tabbatar da ya shiga sai ta nemo number Bebb ta danna kira ta na sakin murmushi. Saida ta kusa tsinkewa kafin aka ɗaga. Ta cikin wayar Nadiya ta yi Sallama. Haura ta amsa. Ta ce "Wacece?" Haura ta ce "Aisha ce" Nadiya ta ɗan shiga tunanin wacce Aisha ce haka. Kafin ta yi magana ta ce "Ina zuwa" ta na faɗa ta kashe wayar. A ranar babu inda taje dama ita idan ba school ba bata fita ko ina, sai dai idan Amera zata aikata gidan Umma ko gidan Nana ko kuma gidan su Anty Khadijah. Haka ta uni a cikin ɗaki tana ta chatting da Nadiya wacce har suka ɗan saba, so take ta san har gidan Malam Habib yadda zata bashi mamaki ta nuna masa tabbacin ita fa sonsa take yi. Sosai suke ta shan hira da Nadiya kaman dama sun san juna, a cikin hirar ne Nadiya ta gane Haura bata jin Hausa sosai, domin ko a rubutun ma a kwai kurakurai sosai, haka idan tayi mata voice not shima zata ji Hausar bata fita sosai. Bangaren Adam kuwa yana fita daga gida ya nufi school ɗin su Salim ya ajiye su kafin ya nufi gurin aikin Najib gaba ɗaya ya na ta saƙe-saƙe a ransa game da lamarin Haura. Bayan sun zauna Adam ya ja dogon numfashi ya busar da iska daga bakins ya na ƙoƙarin ganin ya samo makamar zancen da zai yi domin najib ɗin ya fahimci halin da yake ciki. Najib dai sai kallonsa yake yi ya na mamakin ko me yake damunsa har haka da kasa sakewa. Adam ya shafo daga tsakiyar kansa har gemun sa ya ce "Najib I'm serious about it, please karka ɗauki maganata da wasa dan Allah?" Ya ƙarasa ya na haɗa masa hannu alamun roƙo. Najib ya ɗan yi dariya mai sauti ya ce "To ai ba sai ka faɗa ba, kowa ya dubeka yasan cewar you're serious friend. Adam ya ce "Aure zan ƙara Najib, kuma Haura nake son aura"  Ya faɗa yana kallon Najib kaman shine zai bashi auran Haura ɗin. Najib ya kafe shi da ido ya tunanin abubuwan da suka faru a baya, zuciyar sa ta shiga tariyo ma wacece Haura ɗin. Kusan minti biyu bai iya cewa komai ba har Adam ya kaji da jiran amsar da zai bashi. Ya ce "Kayi shiru kuma kasan shawara nake nema?"  Najib ya ce "Adam wallahi baka da hankali, yarinyar da sanadiyyar ta har ta kusa raba ka da matarka, yarinyar da ta sakawa matarka aljanu gaba ɗaya ta addabi kowa, ita ce kake cewa zaka aura, to kai yanzu zaka iya kwallon idon Amera kace mata zaka auri Haura, wato saboda kaga ta na da hakuri ta yarda yarinyar ta zauna a gidanta ko, to bari kaji wallahi muddin kajewa Amera da wannan zancen sai ta dawo Amera mai ciki har ma fiye da haka, wannan wani Irin cin amana ne. Da sauri Adam ya mike tsaye ya ce "Allah ba zai nuna min wannan Ameran ba in sha Allahu, kuma ai duk wannan abun ba ita ba ce tayi, ita bata ma san tayi ba. Najib ya ce "To yanzu kuwa zata yi wanda tasan tayi, haba Adam, ko kai a kayiwa wannan abun ba zaka ji daɗi ba, nifa bari kaji maganar gaskiya wallahi har yanzu ban gama yarda da wannan yarinyar ba, tsoron ta nake ji dukda dai kace yanzu bata tare da komai amma dai ni ban yarda ba. Adam ya ce "Haba Najib meye kuma na dawo da abun da ya wuce, shekara nawa muna zaune da ita amma bata nuna komai ba, wallhi bata tare da su, ta musulunta ta dawo kamar kowa bata tsafi bata komai normal take kamar kowa, please ka fahimce ni?"  Najib ya ce "Idan shawara kake nema to dan Allah Adam ka rabu da wannan yarinyar, iya wannan taimakon da kayi mata ma ya isa haka, haba wannan yarinyar ita kaɗai ce mace ne Adam, idan da asiri akayi maka kenan yanzu iya shege ne ko me. Adam ya ce "To idan na barta waye zai aureta a haka, muddin ina son cika aikin alkairin da nake yi shine auranta, Karka manta fa yanzu bata da kowa sai mu, kuma duk wanda yazo da nufin auranta idan yaji asalinta ba zai aureta ba. Najib ya ce "Wai ita yarinyar ta na sonka ne, kuma kaji ta bakin Amera akan hakan?" Adam ya ce "Bangaren yarinyar babu damuwa, sai dai ita Amera ɗin ce ban san yadda zata karbi maganar ba, shine nake so kaje ka fahimtar da ita dan Allah. Najib yayi masa wani irin kallon baka da hankali. Ya ce "Amma dai baka da hankali ne ko, ok Kai da ka shirya abun ba zaka iya ba sai ni, to ko ni ban goyi baya ba bare baje na fahimtar da ita, ni ma ban fahimta ba. "Adam ya sauke ajiyar zuciya. Najib ya ce "Adam kenan, inaga ka manta bura'uban da ya faru a gidan ka ne a baya shi yasa kake son dawo da wani sabon domin ka huta yanzu, to ni dai na baka shawara saboda haka Allah ya bada sa'a ubangiji yasa ayi a sa'a. Adam ya amsa da amin. Ya ce "Dan Allah karka sanarwa da Khadijah wannan maganar yanzu?" Najib ya ce "Au itama tsoronta kake ji kenan" ya ce "Ina son bin komai a hankali ne. Haka Adam ya bar gurin ya nufi gurin aikin sa. Har lokacin shi bai ga wani abun tashin hankali anan ba, ai yasan itama Ameran zata so zama da haura ɗin domin bata da matsla komai zata taimaka mata sosai, gashi yara sun saba da ita, ga maganar aihuwa da har yanzu babu labari kuma shi yana son yara sosai. Gaba ɗaya haka ya uni yana ta ƙarawa kansa ƙwarin gwuiwa domin yasan Amera bata da matsla. Haka ya tashi a gurin aiki ya nufi gida yana jin Gara tun yanzu Amera ta san halin da ake ciki, kuma zai fara nunawa Haura ɗin cewar yana sonta domin ta san da abun, idan ma akwai wanda ta fara so sai ta tsayar da shi. Da sallama ya shiga gidan lokacin Salim da Salma da Haura ne a palon suna kallo. Salam ce ta fara amsawa ta nufi gurinsa da gudu, Salim ma yabi bayansa, Haura kuma ta mike tsaye tana masa maraba da zuwa. Adam ya amsa yana kallon yadda duk kalar doguwar rigar da ta saka sai tayi mata kyau. Ya ce "Happy juma'at Mubarak" ya faɗa yana kallon ta. Ta ce "Daddy yau baka dawo ka tafi da Salim masallaci ba?" Adam ya ce "Na manta yau ba anan nayi Sallah ba ne. Yana faɗa ya na shigowa cikin palon. Saida ya zauna kusa da ita abun da bai saba yi ba kafin ta ce "Daddy sannu da dawowa ya aiki?" Ta faɗa kamar kullum idan ya dawo, kaman yadda Amera yake yi, kuma suma yaran suke yi. Kafin ya amsa sai ga Amera ta fito daga daki itama sanye da doguwar riga ta atamfa mai adon ƙananan duwatsu a ƙirjin rigar. Sosai Amera ta iya ɗwukar wanka wanda shibkansa ya shida hakan. Ta yi masa kallo ɗaya ganin gurin da ya zauna, sai ta kawar da kai ta ce "Yau da wuri haka ka dawo ne haka honey?" Ya ce "Eh mun tashi da wuri shine nace tunda ban dawo gida ɗaxu ba kawai bari nazo sai a sha hira" ta zauna nesa dasu ta na sake masa sannu da aiki. Adam ya amsa yana satar kallon Amera da yaji yanayin muryarta kamar ta sauya. Haura ta mike tsaye zata bar palon Amera ta tsayar da ita. Ta sake haɗe rai sosai domin ranta ya ɓaci. Ta ce "Honey nayi magana da yarinyar nan akan wanda yake zuwa gurinta, kuma ta tabbatar min da cewar suna san juna shine na ce mata ta ce masa ranar Sunday yazo kana son ganinsa domin aji idan da gaske yake a tsayar da lokaci. Ta ƙarasa tana tuno maganar da sukayi da Nana ƙanwarta ranar da tazo. Nana ta ce "Anty Mera a duk lokacin da na shigo gidan nan naki naga wannan yarinyar wallahi sai gabana ya faɗi, idan na tuno da cewar arniyar daji ce kuma ba musulma ba, sannan idan na tuna da cewar a baya adam ya kusa ya aureta, sai nake tsoron kar fa watarana yazo miki da maganar zai aureta, tunda kinsan halin sa da son taimako, ko a baya ma abin da ya faru kenan daga taimako, kuma kinga yanzu ta ƙara girma ta zama budurwa ko ina ya ciko masha Allah, gata kuma da kyau babu laifi. Amera ta ce "Nana wani irin tunanin rashin hankali ne wannan, amma kinsan haramun ne kiran wanda ya musulunta da arne ko, kuma duk abin da ya faru a baya ba'a sanin sa bane asiri a kayi masa, yanzu kuwa mun riƙe addu'o'i da Azkar na safe da na yamma in sha Allahu babu abun da zai iya faruwa da mu sai ikon Allah. Dan haka Please ki daina wannan tunanin na san waye mijina, ko a yau Haura ta fito da miji zai aurar da ita, mun sha yin wannan maganar da shi akan auran nata, kuma ya tabbatar da cewar duk wanda ta kawo shi zai bawa. Nana ta yi murmushi ta ce "Anty Mera kenan, to waye zai aureta ɗin idan yaji labarin ta, ina rantsuwa miki da Allah Anty babu namijin da zai iya aurantn sai dai ƴan garinsu, amma duk namiji ɗan dangi ba zasu yarda ya kwaso musu arnan daji ba, kinga kuwa Adam babu wanda zai iya hana shi, domin bashi da wasu dangi nan kusa, dan haka Wallhi Anty ki farka komai zai iya faruwa, ni dai shawara ce na baki. A haka Nana ta tafi ta barta ta shiga nazari m Tun lokacin gaban Amera ya shiga faɗuwa ta na ta tunanin maganganun Nana. Hakan yasa tun lokacin da Nana ta bar gidan ta shiga sakawa Haura ido har ma ta sameta da maganar saurayinta, a kwana biyun ta lura da wani irin kusanci da Adam ɗin ke son samarwa tsakanin sa da ita, wanda hakan baya mata daɗi, amma dole ta dakatar da komai kafin a kai ga abin da take tsoro. Adam ya ɗago da sauri yana kallon Amera, ya ce "Wani turowa kuma ita da take karatu, kuma ma har yaushe suka haɗu da yaron, idan ma suna son juna sai a bari ta ƙarasa karatun nata kafin ayi wannan maganar turowa ko?" Ya ƙarasa yana kallon Haura ɗin da take tsaye tana jinsu...✍️ S Reza.... [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *°S Reza ✍️* _First class writers association_ _My Whatsapp chanel_ *Chapter 7️⃣* Amera ta ce "Karatu kuma, wa yake ta wani karatu yarinya ta samu wanda yake sonta, to idan ma karatun ne ba sai ta yi a gidan mijin nata ba" Ta ƙarasa maganar da muryar da ke nuni da ɓacin ran da take ta ƙoƙarin danne wa. Adam ya ce "Honey wai me kike nufi ne, ko kin manta yanzu haka yarinyar nan ta na shekarar karshe a makarantar ne, kuma yanzu haka text suke yi, suna ganawa kuma sai exam, so kike a katse mata karatun nata ne saboda wani yazo ya ce ya na sonta?" Ya faɗa ya na miƙewa tsaye shima da alamun ransa ya fara ɓaci da abun da ta yi. Amera ta miƙe tsaye itama ganin zai bar gurin. Ta ce "Adam faɗi abun da yake ranka?" Ta faɗa muryarta na yi kamar zata yi kuka, domin tabbas ta gama tabbatar da maganar Nana. Shi kansa Adam ɗin sai da yaji sautin muryar tata kamar daga cikin kwakwalwar sa ta fito. Sosai gabansa ya faɗi ya shiga tunanin ko dai ta gano shirin nasa ne, sai kuma ya fara tunanin anya kuwa ba dama ya samu da zai faɗa mata gaskiya ba. Kafin yayi magana Haura ta ce "Please Daddy Anty kuyi hakuri dan Allah ku daina irin wannan abun" Amera ta kalleta ta kalli Adam ta ce "Faɗa mata gata nan, idan kuma so kake na baku guri tom" ta ƙarasa maganar da ƙyar ta na barin gurin kuka na ƙwace mata. Adam ya bita da kallo har lokacin zuciyar sa na harbawa, ya dawo da kallonsa ga Haura. itama ta juya ta bar gurin ta na mamakin akan ɗan wannan abun ne za suyi faɗa, da zasu kwantar da hankalinsu ma Habib nata ne, zai sonta har ma fiye da yadda take sonsa, idan Aure ne zata yi, kuma da shi Habib ɗin in sha Allahu. Ta na shiga ɗaki ta ciro wayarta a chaji ta danna kiran number Habib ɗin ta na addu'ar Allah yasa ya ɗaga ko muryarsa taji. Har kiran ya katse bai ɗaga ba. Sai da ta kira sau uku bai amsa ba kafin ta hakura ta na tunanin ko dai ta shirya ne taje school ɗin amma kuma ai yamma ta yi ko taje ba lallai ta same sa ba, gashi bata san gidan sa ba ta daje, lokaci ɗaya ta tuno da number matarsa da ta ɗauka. Data ta kunna ta hau online ko zata same shi a online. Haka ta tara masa messages da yawa sannan ta nemo number Bebb da ta ɗauka a wayarsa. Har zata tura mata saƙo sai kuma ta sauƙa daga whasop ɗin ta kirata darekt call. Kira ɗaya Nadiya ta ɗaga da Salam. Haura ta amsa sai kuma ta ce mata pls ina zuwa yanzu". Ta na faɗa ta kashe wayar. Ta fara dariya ita ɗaya kamar wata mai jinnu. A fili ta ce "Muryarta a kwai daɗi babu laifi, in sha Allahu sai kin faɗa min sunan unguwar da kika da kanki. Ta na cikin haka ta jiyo muryar Adam da Amera na tashi a palo, dukda bata jin abinda suke cewa amma dai tasan faɗa ne suke yi, hakan yasa ta ajiye wayar ta nufo palon gabanta na faɗuwa, ta na fara shiga damuwa domin tasan dai duk akanta ne wannan faɗan nasu. Abun da bai taɓa faruwa a gidan ba tun bayan aihuwar Amera ɗin, ita abun nasu ma ya fara bata tsoro Wallhi, wai ko sun fita son yin auren ne ko meye. Ta na fitowa palon kuma taga babu kowa sai ta ji muryoyinso daga cen cikin ɗakin. Hakan yasa ta koma da baya ba tare da ta bi ta kan su ba. *°Habib* Da sallama ya shiga cikin palon gidan nasa muryarsa a sake hannunsa riƙe da baƙar leda. Ganin babu kowa yasa ya nufi ɗakin Nadiya. Ya na shiga ya sameta ta na shirin kwanciya ta saka riga ta zauna a bakin gado ta na saka soss ɗin ƙafa, fuskar nan ta ta fayau kamar babu abun da ya faru, harda murmushi ma yaga ta na masa. Shima saboda ya tabbatar mata da cewar ya amso wayar tasa ya sa ya fiddo da wayar ya kunna karatun Alqur'ani mai girma ya ajiye a kusa da ita ya na bin karatun cikin Suratul Kafiron. Bata ce masa komai ba sai ƙoƙarin kwanciya da ta ke yi. Ya ce "Bebb abinci fa, kuma ga apul na zo miki da shi?" Ya faɗa a hankali duk da ba wai yunwa yake ji ba, kawai dai ya na so ta yi masa magana ne. Miƙewa ta yi, bata ce komai ba ta fita da ledar ta kai friji sai gata ɗauke da abincin nasa da ruwa. Ta ce "Gashi?" Ya ce "Kizo muci Please?" Ta ce "Na goshi". Ɗan kaɗan ya ci abinci ya tattara komai ya mayar kichin ya shiga toilet ya sake yin wanka kafin ya kwanta a bayanta ya rumgumota yana shafa cikinta. Duk yadda Nadiya ta kai da kin basa haɗin kai a wannan ɓangaren amma ta kasa, haka dole ta bada kai bori ya hau. Sosai ya nuna mata jin daɗin sa harda mata godiya da saka mata albarka. Ita kanta taji daɗin hakan har cikin ranta. Ɗaukar ta yayi suka shiga toilet suka sake yin wanka. Bayan sun fito ne ya fara bata labarin da zai kwantar mata da hankali har barci ya ɗauketa. Yau juma'a ya na da class ɗin safe hakan yasa bai koma barci ba, ya bita kichin domin ya taya ta aiki kamar yadda ya ke yi a baya. Ita kanta sai da ta tsaya kwallonsa domin taji daɗin yadda ya ke kokarin dawowa. Ai kuwa tun kafin takwas da rabi sun gama komai, suna yi suna hira. A kwano ɗaya suka zuba abincin suka ci, sannan ya tashi domin fara yin shirin tafiya. Ya na shiryawa ya na addu'ar Allah yasa Haura bata zo school ba, Allah yasa kar ya sake ganinta, ya na yin addu'ar amma wani ɓangare daga zuciyarsa na kin amsawa da amin. Har zai fita Nadiya ta ce masa idan ya dawo ya sameta a gidan Mama sai su dawo tare. Ya ce "Gidan Mama kuma Nadiya, lafiya dai ko?" Ta ce "lafiya lau kawai abu zan karɓo kuma ma ai yau juma'a zan mata gaisuwar juma'a ne. Kamar ya ce karta je amma ya ce tom sai na dawo. Ofis ya fara shiga ya ajiye wayarsa da jakarsa Kafin ya ɗauka abun da zai bukata ya nufi class ɗin. Ya na shiga class ɗin idonsa ya fara sauƙa a gurin da take zama. Dukda ya yi addu'ar Allah yasa karta zo, gashi bata zo ɗin ba, amma sai ya tsinci kansa da jin rashin daɗin hakan. Yaso tazo ko ganinta ne kawai ya samu yayi amma ba sai mata magana ba. Haka dai yau gaba ɗaya yayi karatun jikinsa a sanyaye, duk ɗalibin da ya zo latti ma baya korarsa a tunaninsa ko itama zata zo. Amma haka lokacin sa ya ƙare ba tare da tazo ba. Bai bar school ɗin ba har kusan ɗaya sannan ya nufi masallaci yana jin babu daɗi a ransa. *°Nadiya* Misalin ƙarfe goma ta gama komai na gyaran gidanta kafin ta shirya ta tafi gidan Mama. Lokacin da ta isa babu kowa a gidan sai Mama kawai. Ai kuwa taji daɗin zuwan nata, domin ta samu abokiyar hira. Karfe sha biyu ta tashi ta shiga kichin ta ɗora girki. Ita har ga Allah magana ne a bakinta game da Habib kuma tayi nufin tazo suyi maganar da Mama ne, amma bata san ta yaya zata iya sanar da ita ba, sannan taga alamar kamar komai ya wuce hakan yasa ta kasa yin maganar da Mama har ta gama girkin. Misalin ƙarfe uku ya zo gidan, ta zuba masa abincin ya ci ta na lura da yanayinsa jikinsa duk yayi sanyi. Sai da Nadiya tayi sallar la'asar shima ya fita waje yayi kafin suka bar gidan. A hanya ya tsaya ya saya musu tsiri da Yorgot harda naman kaza, ya na ta ƙoƙarin nuna mata cewar komai ya wuce dukda kuwa zuciyar sa cike take da son ganin Haura ko jin muryarta. Ganin haka yasa itama ta sakar masa fuska sosai harda dariya ta na rungume shi. Wanka suka sake yi tare kafin suka baje naman nasu apalo suka fara ci. Ta ce "Bebb cikina fa yau sai motsi yake tayi wallhi, anya kuwa ba wata matsalar ba ce". Ta karasa ta na ɗora hannunsa akan cikin. Habib ya kai naman kaza bakinsa kafin ya ce "Ai wannan shine alamar lafiya jin motsin nasa, ki kwantar da hankalinki babu komai" Ta ce "Kaifa motsi sosai ne fa kamar zai fito" Bai san lokacin da dariya ta kubce masa na ya ce "To ko dai fitowar zai yi?" Har zata sake magana wayarsa ta hau ƙara. Ya ciro ya duba yaga number Haura. Ta ke gabansa ya bada wani irin sauti, da sauri ya dafe ƙirjin nasa yana jin kamar ya daga. Ya ɗan kalli gurin da Nadiya take yaga shi take kallo, nan take yayi saurin dawowa natsuwarsa. Ya saka wayar a silent ya cigaba da sauraron Nadiya da take nazartar yanayin da ya shiga. Ya na ji kira na shigo masa ya na son ɗauka amma yana tsoron abun da zai iya faruwa, hakan yasa ya hakura. Wayar Nadiya ce ta hau ƙara ta miƙa hannu ta ɗauka ta ɗaga a gabansa. Gaban sa ne ya sake yin wani mummunan faduwa jin kamar Muryar Haura ta cikin wayar. Hakan yasa ta na sauke wayar ya ce "Wacece?" Ta ce "Nima ban santa ba, baƙuwar number ce, kuma ta ce tana zuwa. Yayi shiru yana tunani, wai me wannan yarinyar take nufi ne dole ne fa yasan yadda zai ɓullo mata, domin baya son wannan alaƙar da take kokarin ƙullawa da matarsa. Lokacin da Nadiya ta buɗe whasop sai taga an ajiye mata saƙo da number ɗazu. Da sauri ta buɗe tana karantawa. Dariya kawai tayi ta bata amsa. Ganin ta na online ne yasa ta tanbayeta a ina ta samu number ta. Haura ta ɗan yi dariya itama kaman ta ce mata a wayar mijinta amma ba yanzu ba, so take sai ta je har gidan nata kafin tasan burinta. Ta ce "Nima a wayata naga numbar shine yasa na kiraki naji ko ke kin sanni. Nadiya ta ce "A ina kike? Kuma yaya sunanki? Haura ta ce Sunana Haura. Ta ɗora da faɗa mata unguwar da take. Nadiya ta ce "Kai gaskiya ban taɓa zuwa unguwar nan ba. Ta ce "Ke yaya sunanki?" Itama ta faɗa mata sunanta harda unguwar da take kuma ta sheda mata cewar tana da aure. Haura sai farinciki takeyi jin abun yazo mata da sauƙi. Ita kuwa Nadiya yanayin Hausar yarinyar ce ke burgeta, gashi daga ji yarinya ce ƙarama ko daga yanayin maganar ta babu tunawa. Haka suka sha hira da ita kamar dama sun saba. Washegari ma da safe saboda ita ta buɗe online ai kuwa ta sameta nan ma suka ɗan taɓa hira harda turawa juna hotuna. *°Habib* Tashi yayi zaune cikin dare yana salati gaba ɗaya ya tsorata. Wutar ɗakin ya kunna tsoro na mamaye sa. Mafarki yayi wai Haura ta shigo gidan nan har cikin ɗakinsa suna cikin aikata abun Nadiya tazo ta ritsa su, kuma Haura ɗin ta daɓawa Nadiya wuƙa a cikin ta. Da sauri ya nufo gurin wayarsa yana duba lokaci. Ganin biyu da arba'in yasa ya faɗa Toilet. Koda ya fito ya ɗauki wayarsa domin komawa dakin Nadiya sai yaga 3 miss calls. Hakan yasa ya duba. Kaman ya kirata amma ya fasa. Sai ya kasa komawa barci yayi zaune yana tunani ya dafe kai. Shi kansa zuciyarsa na son ganinta amma yana danne wa. Yana cikin haka barci ya ɗauke shi, babu abin da yakeyi sai mafarki da ita, mai kyau da mara kyau, mai hankali dama marasa hankali. Haka yau ko sallar asuba bai samu ba, ya tashi duk jikinsa a sanyaye, ga wani irin ɗokin son ganinta da ya tashi da shi kamar wanda aka dasa masa a safiyar nan. Haka ya ke komai babu kuzari kamar mara lafiya, ko abinci kaɗan yaci ya kwanta a kan doguwar kujerar palon ya na ta tunanin yanda zai samu ganinta yau. Itama Nadiya bayan ta gama komai ta zauna a kusa dashi tana chatting tana dariya domin ta tambaye shi ko bashi da lafiya ne ya ce mata lafiya lau yake. Yana cikin kallonta wayarsa ta fara ƙara. Da sauri ya duba ganin itace yasa har jikinsa rawa yake yi ya ɗaga yana barin palon. Nadiya ta bisa da kallo har ya turo ƙofar. Shiru Habib yayi yana sauraron kukan da take yi na Ratsa zuciyarsa kamar ya ce mata dan Allah tayi hakuri karta nakasa masa zuciya da wannan kukan nata. Ta ce "Sir ina ta kiranka tun jiya baka daga ba, gaba ɗaya jiya da yau ban ganka ba babu school, Please ina son ganin ka?" Ta karasa da kukan da takeyi. Ya sauke ajiyar zuciya muryarsa na rawa ya ce "Zaki iya fitowa yanzu?" Ya faɗa wanda shi kansa bai san ma ya faɗa haka ba. Sai da yayi furricin kuma ya yi saurin toshe baki ya na katse kiran. Da ƙarfi ya daki kansa ya na faɗin Meye haka me nake yi haka ne, me nake nufi. Ya na cikin haka Nadiya ta bubbuga ƙofar ta na kiran sunansa. Kafin ya amsa kuma sakon Haura ya shigo wayar tasa. Kallon ƙofar ɗakin yayi kafin ya kalli wayar da wani sakon ya shigo. Ya ce "Yes Bebb I'm okay" ta ce "Ka buɗe min kofar zan shigo?" Ya mike ya buɗe mata ta shigo ta na bin sa da kallo. Ta ce "Bebb ko dai asibiti ne zamu je Please?" Ya girgiza mata kai ya ce "Idan na sha magani nayi barci komai zai wuce, dama fa kawai ciwon kai ne kaɗan. Nadiya ta ce "Ciwon kan shine kaɗan, amma ɗazu kace lafiya kake, ai ni nasan a kwai abun dake damun ka, amma kace babu komai, waye ya ce maka ana wasa da ciwo, bari na kawo maka magani. Ta na faɗa ta fita da sauri ya bi ta kallo. Ta na fita ya buɗe sakon ya fara karantawa. Ya fito ya karanta na biyun. Shiru yayi ya na sake karanta saƙon da kyau, yana son rubuta mata amsa amma wata zuciyar na hana shi, haka ya shiga gurin yin reply ya fara rubuta mata sunan gurin da zasu haɗu ɗin kamar yadda ta tambaya. Ya na gamawa ya danna send ya na kallo har ya shiga. Minti ɗaya da shiga sai ga kiranta. Da sauri ya ɗaga yayi shiru. Ta ce "Ban san gurin ba, kawai kazo ƙofar gidan mu sai ka ɗaukeni mu tafi tare" ta faɗa da wani irin annashuwa a muryarta, shi kuma yayi shiru ya kasa magana zuciya da ransa na azazzala shi. Zuciyar ce ke zaiyano masa surar ta, da irin kyawawan fuskantar ta, da yanayin surar jikinta har yaji yana son sanin su yau ɗin nan, a hankali ya ce "Naji zan zo yanzu" ya faɗa yana kashe wayar sai kuma ga Nadiya ta shigo ɗakin riƙe da ruwa da maganin ciwon kai. Zama tayi kusa da shi ta ɓallo masa maganin ta ce ya buɗe bakin kaman yadda akewa yaro ƙarami. Ya buɗe yana kallonta. Ta saka masa maganin sannan ta miƙa masa ruwan ya sha. Ta ce "Zaka kwanta anan ne ko palo zaka je?" Tayi maganar tana kwallonsa. Ganin ya na ta kallonta kuma bai ce komai ba ne yasa ta ce "Bebb lafiya kuwa, irin wannan kallon ai sai ka tsorata ni" Ganin bai daina kallonta bane kuma bai ce komai ba sai ta miƙe tsaye ta ce "Bebb dan Allah ka bari wallhi tsoro kake bani, har zuciya ta fara harbawa. Ta ƙarasa tana rufe masa ido. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Nima ban san me yasa nake jin ina son kallonki ba Bebb. Da sauri ta buɗe masa ido ta ce "To kayi addu'a sai ka kwanta. Ya ce "Zan kwanta a palo. Suna zuwa palo ya kwanta ita kuma ta zauna kusa da shi ta ɗora kansa akan cinyarsa . Ya lumshe ido kamar mai barci yana ta Allah-allah ta ɗan matsa ya samu ya bar gidan. Ai kuwa kamar tasan abun da ke ransa ta ce "Bebb bari na haɗa Maka farfesu mai ɗan yaji idan ka tashi sai kaci ta miƙe ta shiga kichin duk a tunaninta barci ne ya ɗauke shi, shima ya tashi da sauri dama ƙananan kaya ne a jikinsa. Ya fita daga palon ya kunna motarsa ya bar gidan zuciyar sa na ƙara kwaɗaita masa ita da surar jikinsa...✍️ Hammm, A bar wa rai! [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *°S Reza* _First class writers association_ _My Whatsapp chanel_ Chapter 8️⃣ Bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su, yayi pakin a ɗan nesa da gidan su kafin ya kirata. Ya na sauke wayar ya ɗora kansa a jikin sitiyarin motar ya yi shiru ya na tunani. Har ga Allah zuciyar sa bata son aikata wannan abun da yake ƙoƙarin yi, amma kuma ransa na yaba wa sosai, idan zuciyar sa ta ce Allah na ganinka sai ransa ya raya masa cewar ai sau ɗaya ne kawai zai yi, kuma idan yayi zai tuba, Allah zai yafe masa. Kansa ne ya ƙara sara wa kaman zai fita, hakan yasa ya sake ƙanƙame kan ya na salati a fili, har ya fara tsoron karfa mutuwa ce zata zo masa gashi kuma ya na ƙoƙarin aikata aikin zunubi, sai kuma ya girgiza kai ya na tabbatarwa da kan sa cewar ba zai mutu yanzu ba. Kusan minti biyar bata fito ba hakan yasa ya ɗauki waya ya sake kiranta amma no amsa. Har zai sake kira yaga ta turo saƙo, jikinsa na rawa ya buɗe. Ta ce "Ina zuwa yanzu shiryawa nake yi" Ajiye wayar yayi a gefe ya kwanta a jikin kujerar ya na jiranta har lokacin kansa na sara masa. Ya lumshe ido ya na hango Nadiya a kichin ta na masa farfeso mai yaji kaman yadda ta ce masa. *°Haura* Sosai ta rasa ma wanne kalan kaya zata saka tun bayan da ya ce ta fito su haɗu. Idan ta ɗauko wannan sai ta mayar ta ɗauko wannan. Haka ta dinga fama har dai ta saka riga da wando ƴan kanti wanda suka matseta sosai, rabonta da kayan har ta manta amma suna mata kyau idan ta saka su. Bayan ta saka rigar ta feshe jikinta da turare sannan ta ɗauki hijjabi ta ɗora akai ta ɗauki jakar ta ƙarama ta sa waya a ciki ta fito da niyar fita. Ta na zuwa palon ta samu Amera da Salim zaune suna kallo. Ta ƙaraso cikin palon ta ce "Aunty sannu da hutawa zan je waje ana kirana. Amera ta kawar da kai gefe ta ce "adawo lafiya". Salim ya ce "Anty zan rakaki?" Ta ce "No yanzu zan dawo kaga magriba ta yi" Har zata fita Amera ta ce "Haura"  Haura ta dawo da baya ta amsa ta na kallonta alamun sauraronta. Ta ce "Wanda yazo ranar ne yazo?" Ta ɗaga mata kai. Sai ta gyra Zama ta ce "Idan kinje kice masa Daddynki ya ce idan har da gaske ya ke yazo gida a ganshi, kuma kice ke an hana ki tsayayuwa da mutum muddin ba aure ne ya kawo shi ba. Kafin ta yi magana kiransa ya shigo wayar amma sai bata ɗaga ba saboda Amera na mata faɗa. Ta ce "Tom Anty zan faɗa masa" Ta na faɗa ta na rubuta masa message ta tura masa. Amera ta sake cewa "Kin dai ji abin da nace miki ko? Kuma duk abun da ya baki ki amsa, sannan ki dage masa ke dai aure kike so, karki yarda koda ya na da mata kice kina sonsa a haka. Haura dai sai to da to kawai take cewa ta na sauraronta. Sai lokacin Amera ta yi mata kallon tsaf ta ce "Je ki cire wannan hijjab ɗin ki saka gyale yadda zai ganki da kyau" Haura ta buɗe baki zata yi magana Amera ta ce "Ke har yanzu baki da wayo, waye ya ce miki ana zuwa hira da hijjabi yanzu, su kansu samarin ba son sa sukeyi ba ya na rage miki daraja a idonsu, sunfi so su kalleki da kyau domin susan abun da zasu aura. Suna shiga ɗakin ta shiga duba mata gyale ita dai Haura ta na tsaye ta cika da mamakin wannan sabon salon kulawar daga antin tata. Amera da ta samo gyalen har guda uku ta zarosu ta kallettta ta ce "To ki cire hijjabin mana kin tsaya kina kallo na kamar wata bakuwa. Haura ta cire hijjabin jikinta Amera ta yi tsaye ta na kallonta. Ita kanta sai da ta ɗan haɗiye yawu domin ganin yadda kayan suka kamata, komai nata ya baiyana a fili kamar wata ƙatuwar ashawo. Sai ta rasa mai zata ce mata domin dai ta sani bai dace ta fita a haka babu hijjabi ba, kai ko a cikin gida ne bai dace ta zauna a haka ba bare kuma ta fita zance gurin saurayi, ai wannan bada damar aikata iskanci ne. Amma da ta tuno da cewar mijinta fa zata ƙwace mata ai sai cewa ta yi "Gashi kinyi shiga mai kyau amma kin wani ɗaura hijjabi ta yaya zaki burgeshi, yanzu yafa wannan abun ki ga yadda zaki koma" Ta yafa mata wani ɗan ƙyamurmirin gyale sannan ta shiga zuzutata tana koɗa ta. A haka suka fito har palon gidan. Ta ce "Idan kinje kuma karki manta da abun da na faɗa miki akan aure kike so, sannan kuma karki manta fa gobe Lahadi kice ya zo inji Daddy. Haura ta ɗaga kai ta na jin wani ƙwarin gwuiwa na zuwar mata, in dai akan Malam Habib ne har fiye da haka ma zatayi. Ta na fita Amera ta samu guri ta zauna ta na sauke ajiyar zuciya. Wata zuciyar ta ce "Yanzu hakan da kika yi kin kyuta kenan, shin idan ƴarki Salma ce zaki iya barinta ta fita waje da irin wannan kayan da nufin hira, shin meye laifin Haura, itafa har yanzu bata san komai ba. Jikinta ne yayi sanyi sai take tunanin waima tun farko mai yasa ta yarda ma suka riƙe ta ne, kuma tunda suke da ita bata taɓa cutar da ita ko kuma ta mata wani abu na rashin kunya ba, gashi ta na jin maganar ta, shin koda Adam ya aureta meye nata aciki, mai zata ragu da shi. Ai tana zuwa nan da tunani ta miƙe tsaye ta ce "Wallhi ƙarya ne, ba zata saɓu ba, bata isa ba, da ta auri mijina Gara ma ko tsirara ne ta dinga fita waje wallhi. A hankali ta ke tafiya har ta fito daga cikin gidan, ganin bata ga motarsa ba ne ya sa har ta ciro wayarta zata kira sai taga ya haske ta fitilar motar sa. Hakan yasa ta nufi gurin cikin takunta mai ɗaukar hankali. Babu kowa a unguwar kuma gashi duhu ya fara yi, tafiya ta keyi cike da iyawa da ɗan sanyin ta da yake a zubin halittar ta. Haka take ita, bata da tsoro, haka kuma bata da kunya sannan bata da riƙo, ta na da sanyin jiki harda ta magana, shi yasa sam bata ko ji komai ba sai rashin daɗin yanayin nata amma ba tsoron kar wani ya ganta ko kunya ba. Ta na zuwa bakin motar zata shiga motar Adam tazo ta wuce ta kusa da ita a hankali. Ai kuwa ta na ganinta ta buɗe ta shige, shi kuwa Habib ya figi mota a tamanin ya bar unguwar. Tun lokacin da ta fito ya kafe ta da ido, komai nasa ya tsaya chak da aiki ciki kuwa harda tunanin sa da hankalinsa, ganin ta tsaya ne bai san lokacin da ya haske ta da fitilar motar ba. Duk taku ɗaya da take yi wani abu ne ke ɗarsuwa a ransa game da ita, babu inda yake kallo sai kan girjinta da suke a tsaye kamar zasu tsone masa ido. Jikinsa har wani rawa yake yi halittar sa kuwa ta gama amsawa ji yake kamar ya haɗiyeta kowa ya huta, a yanayin da yake jinsa komai ma zai iya faruwa dashi akanta . Wani irin abu ne mai kamar da idan bai santa ba zai iya mutuwa tsikar jikinsa har tashi sukeyi, har wani sanyi-sanyi ne ke kama shi ya na hango shi tare da ita a wani yanayi. Shi bai taɓa jin irin abun akan wata mace ba ciki kuwa harda Nadiya matarsa, shin wannan so ne ko sha'awa ko kuma me. Sosai ya rikice ya kafe ta da ido har ta shigo motar. Ya na jin ta rufe bai ce mata komai ba ya figi motar suka kama hanya. Saida suka bar cikin unguwar kafin cikin wata matsiyaciyar Muryar da ta ƙarasa illata sauran kuzarin nasa ta ce "Sir ina zamu je?" Ta faɗa ta na kwallonsa cikin so da ƙauna da shaƙi irin na wanda yaga abun sonsa a tare da shi. Sosai take son Malam Habib, idan bata gansa ba har wani zazzaɓi ne ke kamata, ta na sonsa domin Allah, kuma da zuciya ɗaya, yanzu haka da suke tare sai take jin kamar a cikin aljannar duniya take. Habib da ya ƙarasa rugujewa ya ce "Wani guri zamu je" ta sake cewa "Sir kayi kewata kuwa?" Ta faɗa ta na ɗora hannunta akan nasa wanda yake kan gurin saka giya. Ai da sauri ya taka burki ya kallettta, ji yake kaman ya rungumeta a cikin motar ko zai daina jin abun da yake ji. Ido ɗaya ta kanne masa sannan ta sakar masa murmushi ta na ƙara matse hannun nasa. Ji yayi kaman zai narke a gurin, gaba ɗaya ya naimi kuzarinsa da ƙarfinsa ya rasa. Ta ce "Sir akan hanya fa ka tsaya, Please mu tafi". Haka ya zame hannunsa ya tada motar ya fara gudu ya na jin ko magana ba zai iya yi ba, bai tsaya a ko ina ba sai wani ɗan ƙaramin gida. Saida ya sauƙa ya buɗe Get ɗin kafin ya shiga da motar ya yi pakin sannan ya dawo ya rufe get ɗin. Ya buɗe mata ta fito yayi gaba ta bishi abaya ta na tunanin ko gidan waye nan, gashi dan ƙarami yayi mata kyau. Babu wani tsoro ta bishi a baya har cikin gidan. *°Adam* Haka suka kwana da Amera kowa na fushi da kowa abun da bai taɓa faruwa tsakanin su ba, koda sun samu saɓani baya shafar mahallinsu amma wannan karan kowa ya hau dokin naƙi. Washegari asabar baida aiki haka ya uni a gida bai ce mata komai ba haka itama bata ko bi ta kansa ba, sannan yau gaba ɗaya ta hana Haura zaman Palo ganin ya hakaikance a gurin, bayan yaci abincin rana ne ya bar gidan ya nufi gidan Najib. A cen ya zauna suna ta hira da Khadijah ya na son ya faɗa mata batun Auran nasa amma yana tsoron tijaranta, domin ai yasan bakinsu a haɗe yake da Amera, haka ya hakura da sanar mata idan komai ya tabbata zata ji. Bayan sun fito ya kalli Najib ya ce "Wallhi har yanzu na kasa sanar mata wannan maganar fa, kuma abun da zai baka mamaki shine ta gano cewar ina son yarinyar, domin yanzu haka da nake baka wannan labarin fushi take yi da ni, kuma ta fara zuga yarinyar akan ta cewa yaron da yake zuwa gurinta ya turo gida, sannan yau gaba ɗaya ta hana ta zaman Palo sabo da ina gida" Adam ya ƙarasa maganar kaman wani abun tausayi. Najib ya ce "To ka hakura mana fisabillahi, kana zaune lafiya da matar ka sai kace dole?" Adam ya ce "Eh kusan dole ne ai, domin ina sonta kuma ina tausayinta sannan kuma ina son na ƙarasa aikin alkairi na". Najib ya ɗan yi murmushi ya ce "Gaskiya ne, to tunda dai kace ta gano kawai ka faɗa mata gaskiya mana. Adam ya ce "kamar yaya gaskiya?" Ya ce "Ka ce mata kana son ka aureta saboda kana tausayinta" Adam ya ce "Najib sai anjima har yanzu ba zaka fahimci abun da nake nufi ba". Ya na faɗa ya shige motarsa ya bar gidan. Ganin magriba ta kusa ne yasa ya ƙarasa gurin masu biredi ya sayo musu ya haɗo kayan shayi harda su Yorgot holandiya da shawarma da fiza da naman kaza. Sosai yayi siyayya mai yawa lokacin har an fara sallar magriba. Haka ya ware na Amera ya ware na Haura da na yaran sannan ya kamo hanyar gida, a ransa ya na fatan su shirya da Amera a wannan daren, ita kuma Haura daga yau zai fara nuna mata gaskiyar nufinsa yasan ba zata ƙi ba, dama shi bada matsla da ita, Amera kawai yake tunani. Ya na tuƙin ya na tunanin yadda zasu kwashe da Amera duk da yasan bata da kafiya, ta na da hakuri da sauƙin hali. Tun daga nesa ya hango wata figigiyar yarinya cikin wata shegiyar shiga wacce idan da ƴarsa ce babu abun da zai hana bai zane mata mazaunai ba dan ubanta. Tsabar yadda ta ɗauki hankalinsa ma bai tsaya duba fuskantar yarinyar ba sai jikinta da surar ke ɗaukar hankalinsa a kallon farko. A zuci yake tunanin wacce sabuwar yar duniyar ce kuma suka samu a wannan unguwar haka da bata tsoron idon mutane, ko dai bakuwa ce suka samu. Saida yazo kusa da ita kafin ya kalli fuskarta. Kallo ɗaya yayi mata kuma gabansa ya faɗi ganin kaman Haura kaman kuma ba ita ba. Sai dai bai mata kallo na biyu ba ta shege cikin motar da sauri kuma suka bar gurin. Sosai gabansa ke faduwa kaman yabi bayansu amma ya nufi gida yana addu'ar Allah yasa ba ita ba ce, amma dai tabbas ita ce ya gani. Ya na pakin ɗin motar bai ko bi ta kan su shawarma ɗin ba ya shiga gidan kaman an koroshi da sanda. Lokacin babu kowa a palon ita da yaran duk sun shiga sallah. Da Karfi ya shiga kiran sunan Amera har ya na cin karo da kujera. Jin bata amsa ba ya nufi ɗajin ta. Ya na shiga ya samu ta na sallah. Hakan yasa ya fito ya nufi ɗakin Haura harda gudu. Tun daga nesa yaga ɗakin a rufe amma sai da ya ƙarasa ya tura ƙofar ɗakin da karfi. Ya shiga ya na kiran sunanta cikin wani irin ɓacin rai, haka ya shiga duba ko ina har cikin toilet harda ƙarƙashin gado kaman mai neman kaza. Lokaci ɗaya ya tabbatar da cewar ita ce ya gani kenan da wannan shigar kuma ta shiga motar wani. Ya fito daga ɗakin ya sake nufowa ɗakin Amera lokacin ta idar itama ta fito falo domin yanayin nasa ya bata tsoro. Ya ce "Ina Haura?" Ya faɗa da ɓacin ran da yazo masa har wuya, wani irin kishi ne da bai san ya na da shi ba yayi masa karan tsaye a maƙogaro. Ta ce "Dama ajiyar ta ka bani ne?" Itama ta bashi amsa a haɗe domin ta shirya masa, yau zata ga karshen rashin kunyar sa. Da karfi ya ce "Kece kika barta ta fita da wannan shigar kamar wata karuwa, kuma ta shiga motar wani suka tafi?" Ya ƙarasa muryarsa na rawa, ya na jin muddin ta ce eh to tabbas zai iya marinta a yanda yake jin zuciyarsa. Ita kanta saida gabanta ya faɗi jin cewar ta shiga Mota harda tafiya. Itafa tayi tunanin hira ne za suyi a nan ƙofar gidan ba wai mota zasu shiga su je wani guri ba, to ina zasu je. Ta ce "Wai Adam ita wannan Haura ɗin yarinya ce da bata san daidai da rashin sa ba, saurayinta yazo hira ta shirya ta je me kake so nayi, kana so na ce karta je ne alhalin kuma ta isa yin hirar?" "Bance karta ƙara fita ba?" Ya sake faɗa yana matsowa kusa da ita. Ta kalle shi ganin kamar marinta yaje son yi. Ta ce "Mai yasa baka faɗa mata ba?" Adam ya ce "Na lura baki da hankali ne da zaki barta ta fita a haka, ke mahaukaciyar ina ce, idan da ƴarki ce zaki yarda ta fita a haka,?" Amera ta ce "Adam nice mahaukaciyar kuma mara hankali?" Ta tambaya cikin muryar da bai taɓa jin ta da ita ba. Ya ce "Eh! Ai kinfi haka ma, akan wani kishinki na banza da hofi wanda ba zai hana ni abun da nayi niyya ba, kina son ki cutar da rayuwar yarinya wacce bata zauna dake da komai ba sai kyautatawa da biyayya, amma kin fara ɗorata a hanyar banza saboda da kawai mugunta da son zuciya, wallahi kinji kunya". Amera ta yi mutuwar tsaye ta na share hawaye, ta rasa me zata ce sai kwallonsa ta keyi hawaye na ƙara zubo mata. Ya ce "Wallhi Muddin wani abu ya samu wannan yarinyar ke ce, kuma ba zan bari ba" ya na faɗa ya yi hanyar ɗaƙin sa. Amera da maganar ta suɓuto daga bakinta ta ce "Ai har yanzu baka faɗi abun da kake son faɗa ba, kuma in sha Allahu ba zata dawo gidan nan lafiya ba sai naga abun da zaka yi. Ta faɗi maganar har cikin zuciyarta, sai take addu'ar Allah yasa ma yaron karya dawo da ita sai yayi mata fyade ya wulakantata, kai idan ma ta kama ta dawo da ciki domin taga abun da zai yi. Adam ya juyo har zai shige ya dawo da baya ya ce "Mene ne ban faɗa ba, cewar ina sonta zan aure ko me, ai naga babu wani bukatar sanarwa domin kin sani, kuma bari kiji ko me nene ya faru da ita sai na aureta, kuma sai dai mugun nufinki ya ƙara a kanki lafiya ƙalau zata dawo" ya na faɗa ya mata wani harara sannan ya wuce ɗakinsa yana ji tana magana amma ya rufo ƙofar ɗakin ya kulle ya zauna a bakin gado ya na tunani. Anya a kwai namijin da zai ganta a wannan yanayin ya kasa jin wani abu, to ma wai waye yaron zai mata, daga ina yake, yaushe suka haɗu, shin tana ma sonsa, sannan ina suka tafi mai za suyi mata. Kishi da baƙin ciki ne ke nuƙurƙusar sa, ya kasa zama ya miƙe ya fito ya bar gidan?...📝 S Reza...✍️ [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *°S Reza* _First class writers association_ _My Whatsapp chanel_ *Chapter 9️⃣* Bai fita da mota ba haka ya dinga yawo a ƙasa ya rasa ina zai je, har bakin babban titi ya zo ya tsaya ya na ta bin motocin mutane da kallo. Ganin dai kaman ya na neman mayar da kansa wani mai motsi ne yasa ya kama hanyar gida ya na tafiya ya na tunanin rashin wayon Haura da rashin hankalinta, idan ba haka ba ta yaya zata shiga motar saurayi da irin wannan shigar, ko shi da yake uba a gare ta ai bai dace ta shiga motarsa a haka ba, bare kuma wani ɗan iskan saurayi. Sai kawai ya shiga tunanin farkon kawota gidan sa ita da mamarta a matsayin ƴar aiki. Irin wahalar da Amera ta bata, duka zagi da cin mutuncin da aibatawa da wulaƙanci kuma ta na da ikon ramawa a lokacin amma ta jure. Zuwa lokacin da Amera ɗin ta kashe mata mamarta sannan kuma suka yi masa asiri har ya ce zai auri ita haura ɗin. Har zuwa lokacin da aka je gurin ɗaurin auren amma Auran bai ɗauru ba. Sai yake jin ina ma a lokacin bai dawo gida ba sai da aka ɗaura auran ai da shikenan ya huta, shi idan bai yi karya ba tun lokacin da ya fara ganin Haura a tsirara a gidan sa farkon zuwanta yaji yana sonta, gashi yanzu ta musulunta mai zai sa ba zai aureta ba, gashi bata da kowa. Haka ya dinga tunanin komai har zuwan da ƴan garinsu suka yi aka yanke wa kanwar mamarta Ɓultuwa hukunci kisa, sannan Haura ɗin ta zaɓi zama da su anan, kuma aka karya mata duk wani asiri da ke jikinta, har kawo yanzu da ta zama musulma kuma mutum mai ilimi, shine kuma ba zai aureta ba duk da wannan sadaukarwa da tayi. Tabbas ko waye wannan mutumin daga yau ya daina zuwa ƙofar gidan nan kenan har a bada. Haka ya koma gidan yana jin ita kanta Haura ɗin yau sai ya zane ta, ya tabbatar mata da cewar tana da iyaye wanda suka damu da ita. *°Habib* Suna shiga cikin palon kaman wanda aka turoshi ya rungumeta ya fara kissing dinta ta ko ta ina. Ita tsoro ma ya bata har ta na faɗuwa a tsakiyar ɗakin. Haka ya bita har ƙasan ya na ƙara jin wani sha'awar ta da son kasancewa da ita na ƙara taso masa. Cikin Wata murya ta ce "Sir Please" ta na rufe baki ya dora bakinsa akan nata Duk ya fita a haiyacinsa. Ta ƙwace bakin ta, ta sake faɗin "Please Sir ka na sona da gaske? Muddin kana sona zan iya maka komai, zan baka kaina idan har kamin alƙawarin zaka aure ni, ina sonka da rai ba da zuciya ba, amma ina tsoron ka samu abun da kake so kuma ka guje ni" duk maganar da take yi ya na ji, kuma shi kansa ya san yana sonta, ba zai iya rabuwa da ita, shi da yake jin ma zai iya mutuwa a kanta, shi kan sa har ransa yake jinta. Ta buɗe baki kenan ta ce "Sir" yayi saurin faɗin "Ina sonki ba zan iya rabuwa da ke ba, i love You with all my heart" ya karasa ya na ƙoƙarin cire rigarsa. Wani irin farinciki ne ya saukar mata, take wani so say soso ya mamaye mata ƙalbi, ta mike tsaye ta na kallon cikin idonsa wanda sai da ya kawar da kai domin wani haske da ya gani. Da kanta ta shiga cire kayan jikinta, sai da ta rage iya rigar mama da wandonsa, sannan yayi saurin ɗaukarta ya yi cikin ɗajin da ita. Ya na ajiye ta a kan gadon ya karasa rabata da sauran kayan jikin nata shima ya cire nasa. A daidai wannan lokacin babu abin da Habib ke bukata kaman ya jishi a jikinta, haka itama take da burin mallaka masa gaba ɗaya rayuwarta da zuciya ɗaya, da amincewar rai da gangar jikinta. Sosai ta bashi haɗin kai ya fara aiwatar da burinsa cike da shauƙi da jin dadin abun. Sosai hankalinsa ya bar jikinsa ya samu gamsuwa sosai wanda bai taɓa jin irinta ba a tare da Nadiya. Dukda cewar shine na farko da ya fara saninta amma ba tayi kururuwa ba kaman lokacin da ya samu Nadiya. Ƙasa da minti arba'in komai ya faru, ga jini da ya fitar mata mai yawa amma idanunta a ƙeƙyashe duk da cewar yaji kukanta amma ba mai hawaye ba. Gefe ɗaya ya koma ya na jin kansa wasai, sai kuma wani irin abu mai kama da rashin daɗi da ya ratsa zuciyarsa, juyowa yayi ya kalli gurin da take kwance ta na kallon sama. Da sauri ya tashi ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa. Sosai kansa ya daina ciwon amma ya kasa samun natsuwar zuciya, sai ma wani irin kyamar abun da yayi yake yi, har ya fara jin kunyar sake haɗa ido da ita. A fili ya furta Astagfulrullah mai na yi haka, da aure na, innalillahi wa inna'ilaihi rajiun. Ya dafe kansa da lokaci ɗaya ya sara masa. Ya daɗe a cikin toilet ɗin kafin ya iya fitowa. Sai ya tsinci kansa da jin wani irin haushin ta da haushin kansa. Bai ko bi ta kanta ba ya saka kayansa ya dawo Palo ya zauna yayi shiru. Wani faifan karatun porf Ibrahim maƙari ne ya dawo masa kamar yanzu yake saurara. Inda malamin ya ke cewa "Shi fa mazinaci daga lokacin da ya ɗarsa a ransa cewar zai yi zina, suna shiga daki shida ita mazinaciyar, za'a ɗaye wannan fatar dake jikinsu, sai sun gama kafin za'a mayar musu da ita, wato abun nufi shine zunubin zina baya taɓa wankuwa domin ba'a wajen jiki yake ba. Ita Zina bashi ce, idan kayi sai an maka, sannan mazinaci maƙaryaci ne, sannan daɗin zina baya wuce na minti talatin". Ihu Habib yayi yana gasƙata maganar malamin domin gashi ya faru a kansa, mai yasa kafin yayi bai tuno da wannan wa'azin ba sai da ya gama. Nadama da tsoro da fargaba sune suka cika masa zuciya. Ji yake kaman ya gudu ya barta anan, tabbas da hotel ne wallhi ba zai bi ta kanta ba domin ya tsani ganin fuskarta ko jin muryarta. Haka dole ya tashi ya nufi cikin ɗakin domin ya mayar da ita gida ya kama gabansa. Lokacin da ya shige toilet tayi ƙoƙarin tashi zaune amma taji zafi a ƙasanta, amma haka ta daure ta zauna a bakin gadon ta na jira ya fito itama ta shiga wankan. Tunani ta keyi akan abun da taji, tabbas ta sha wahala taji zafi wanda bata taɓa jin irinsa ba, amma idan ta tuno da cewar Habib ne kuma zai aureta sai komai yayi mata daɗi saboda ta na sonsa. Ya na fitowa ta shiga itama, dama tasan yadda ake yi, ta na karantawa a cikin littatafan da take karantawa Amera, idan haka ta faru ana wanka da ruwan zafi domin samun sauƙi. Hakan yasa ta haɗa ruwan zafi ta shiga ciki, ta sake haɗa wani ta shiga, sannan ta mayar da ƙaramin wandonta da rigar mama. Tana ta mamakin abun da yasa bai dawo ɗakin ba, sannan gashi a irin labarin da take karantawa mazan ne ma suke ɗaukar matan suyi musu wanka, amma shi ya kasa shigowa, sai ta bari akan ko dai kunyarta yake ji. Ta janye zanin gadon da ya ɓaci ta kai toilet. Ta fito kenan sai gashi ya shigo ɗakin. Bai ko kalleta ba ya ce "Saka kaya zamu tafi" ya faɗa ya juya ya bar ɗakin. Ta bishi da kallo wani sonsa na ƙara shigarta, sai ta saki murmushi kawai. Haka ta fito izuwa palon. Yana ganinta ya tashi da sauri ya fita gurin Mota. Ta tsaya ta na kwallonsa, bata ce komai ba ta saka kayan nata, ta naimi gyalen da tazo dashi ta rasa. Haka ta ɗauki jakarta ta buɗe ciki ta ɗwuko wayarta taga tarin miss calls ɗin daddy. Gabanta ne ya faɗi taji wani irin tsoro mai dalili na Daddy, sai take jin kamar zai gane abun da ya faru. Da sauri ta mayar da wayar jaka ta fito daga palon ta ja ƙofar ta iso bakin motar. Budewa tayi ta shiga wanda bata gama gyara zama ba ya ja motar kamar zai tashi sama ga fuskar nan a haɗe. Kallonsa ta yi tana mamakin kuma me ya sa yake ɓata rai bayan ba haka ya dace yayi ba, shida zai yi farinciki da godiya. Ta ce "Sir me ya fa" tayi tambayar cikin rashin jin daɗin yanayinsa. Shiru yayi kamar bai jita ba. Ta sake faɗin "Sir ko dai".. da ƙarfi ya daka mata tsawar da sai da ta jita har ƙwaƙwalwar kanta. Ya ce "Please kije gida zamuyi magana gobe kaina ciwo yake yi" Haura ta sake kafe shi da wannan mayun idanun nata, amma ya ki yarda ya kalli gurin da take. A daidai lokacin kuma maganar Amera ta fado mata Ta ce "Sir gobe Lahadi Daddy ya ce na sanar da kai ya na son ganinka?" Da sauri Habib yayi mata wani kallo, shi fa gaba ɗaya muryarta ma tashar masa da zuciya take yi, har sauri yake ya kaita unguwarsu ya kama gabansa. Jin yayi shiru ta ce "Sir ka j..." Da sauri ya ce "Naji Allah ya kaimu" ya faɗa ya na mayar da hankalinsa ga tuki. Haura tayi murmushi ta ce "Sir da gaske zaka zo?" Ya ɗaga mata kai. Ya na mamakin to mai yawa yanzu muryarta bata masa daɗi, mai yasa baya jin wannan abun mai kama da so da yake mata. Suna zuwa bakin babban titin unguwar so ya tsaya ya kalleta a wani irin yanayi kamar dole ya ce "Ki sauƙa ki ƙarasa kar a ganni kuma ayi tunanin wani abu ne, zamuyi waya idan kin shiga gida" ta ce "Tom sai goben idan kazo ko Sir?" Bai ce komai ba tana fita yaja motarsa ya bar unguwar. Bin motar tayi da kallo har ta daina ganin ta. Kallon kanta tayi ganin babu ko gyalen da ta tafi da shi, gashi har lokacin ƙasanta na mata zafi sosai, haka ta fara takawa a ƙasa har ta iso bakin get ɗin gidan nasu. Haka ta tura ƙaramin ƙofar ta shiga, ta na ta ƙoƙarin ganin ta saita tafiyar ta tayi daidai. Lokacin da taje ƙofar shiga palon sai da ta duba lokaci taga tara da kusan arba'in kafin ta shiga palon da sallama. Ganin bata ga kowa ba yasa ta nufi ɗakin ta babu ko alamar tsoro a fuskar ta. Har ta kusa barin palon ta jiyo muryar Adam na tambayar ta. *°Adam* Haka ya cigaba da zama ƙofar gidan ya na jiran yaga ta ita zata shigo, har takwas zuwa da rabi, har tara, hakan yasa ya koma cikin gida yana jin gabansa na faduwa haka kawai. Har zai shiga gidan ya tuno da abubuwan da ya sayo ɗazu. Ya buɗe motar ya kwaso ya shiga dasu gidan. Lokacin Amera na zaune a palon itama abun duniya ya ishe ta, ganin har lokacin Haura bata dawo ba yasa ta shiga damuwa, sosai abun ya dameta ita ba haka tayi zato ba. Adam ya ajiye mata ledar ta, ya ɗauki ta Haura ya kai mata ɗakinta, sannan ya fito ya zauna a palon ya yi shiru. Amera ta ce "Ga abinci fa?" Ta faɗa cikin murya mai sanyi. Bata ji dadin abun ba, sannan sai yanzu ta gane cewar ba haka ya kamata tayi ba. Adam bai ko nuna yaji taba, sai da ta sake magana kafin ya kalleta ya kawar da kai. Ta ce "Honey Wallhi ban san cewar fita za suyi ba, ina ce kawai hira ce yazo kaman yadda ya saba" Adam da zuciyar sa ke tafasa ya ce "Bayan kin gama addu'ar Allah yasa karta dawo lafiya, wallhi kin bani mamaki". Amera ta yi shiru. Ta ce "Kaina kasa ni yin wannan furricin amma wallhi ba zan so wani abu ya samu Haura ba, ina jinta kamar Salma da Salim, kawai banji dadin abun da kake son yi bane, idan kayi haka baka kyauta min ba, ba zan ji daɗi ba, dan Allah honey karka lalata rayuwar gidan ka da kanka Please?" Adam ya ja dogon tsaki ya tashi ya bar palon. Amera ta bishi cikin ɗakin bayan ta kwashe ledojin da ya shigo da su. Babu yadda batayi da shi ba amma ya ce shi ba zai ci abinci ba domin bashi da wannan natsuwar. Haka ya sauya kayan jikinsa ya dawo palo ya zauna, itama ta dawo suka zauna tare. Ganin tara harda rabi yasa ya tashi ya leka waje ya dawo ya wuce ɗaki itama ta bishi. Yana zama yaji alamun buɗe ƙofar hakan yasa ya tashi da sauri ya fito, sai kuwa ya ganta tana har ta kusa shiga Palo. Cikin Wata murya mai kamar an shaƙe shi ya ce "Daga ina kike Haura?" Ya faɗa ya na nufowa gurin da take. Juyowa tayi suka haɗa ido, lokaci ɗaya Komai da ya aiyana zai mata suka fara zama tarishi a cikin zuciyarsa. Kanta tsaye ta ce "Daddy shine fa yazo, kuma na fadawa Anty, sannan na masa magana akan yazo gebe kana son ganinsa kuma ya ce zai so?" Ta ƙasa da sakin murya. Adam yayi jim, zuciyar sa na jin wani ɗaci. Ya ce "Yanzu Haura a haka kika fita da Namiji baki ji kunya ba?" Ta ce "Daddy ba zan ƙara ba" ta ƙarasa kamar mai roko. Adam yaji wani sanyi jin yadda tayi maganar. Sai kawai ya tsinci kansa da tausayinta, ya kasa ma yin wata tambayar. Ya ce "Karki sake fita babu hijjabi, sannan ki je ki kwanta gobe idan yazo zamuyi magana, kuma daga yau karki ƙara fita gurin kowa har sai kin kirani kin sanar min. Ta ce "Tom Daddy na ji". Har ta fara tafiya ya ce "A kwai shawarma da Yorgot da na kawo miki a ɗaki ki sha kafin ki kwanta". Ta amsa cike da farinciki da jin dadi. Ya na juyowa yaga Amera tsaye ta na kallonsa. Ta ce "Shikenan faɗan da zaka yi mata dama? Hakan shine matsayi uban da yasan ciwon ƴarsa? Ko kunya baka ji yarinya na kiranka Daddy Daddy amma kana tunanin auranta, yarinyar da zata iya bin saurayi a haka kana tunanin babu soyayya a tsakanin su ne, to Wallhi tun wuri muddin baka son zubar da mutuncinka a idon ta ka barta da wanda take so, kar daga kiran ka Daddy a koma kiranka da Dade domin wallhi tana son wannan saurayin nata, amma idan ka ɗauki haka a matsayin kishi daidai ne, idan kuma kayi tunani akai shima daidai ne. Ta na faɗa ta juya ta nufi ɗaki ta kwanta abunta, tana yadda da irin wannan hanyar da zata bi akan ta tsaya ta na tashin hankali da shi, ai in sha Allahu ko ya furta mata ba zata so shi ba, ita zata kara tsoratar da ita da nuna mata yin hakan zata cutu ne...📝 [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *°S Reza* _First class writers association_ _My Whatsapp chanel_                          *Chapter 1️⃣0️⃣* Bai ce mata komai ba shima ya shige nasa ɗakin a ransa yana jinjinawa kishin Amera, domin yasan dai idan ba kishi ba yaya za'ayi ta ce wai Haura zata iya cewa bata sonsa, ai wannan maganar banza ce, ta san yadda kuwa haura ta ɗauke shi da har take tunanin zata iya cewa bata sonsa, Allah dai ya kaimu gobe zai bata mamaki, idan ma ta kama kawai auran za'a ɗaura ko a cikin satin nan ne, ba sai ya bawa kansa wahala ba, domin dai shine mai ba da auren kuma shine mai karɓa. Ɓangaren Haura kuwa ta na shiga ɗakin ta zauna a bakin gado ta shiga cire kayan jikinta domin sun daneta kamar ta saka ƙaya. Ta na gamawa ta shiga toilet ta sake yin wanka da ruwan ɗumi kafin ta fito ta saka rigar barci ta nufo kichin domin ɗiban abinci saboda wata azabbabiyar yunwa da take ji kamar an mata sata a cikinta. Haka ta zuba kaɗan domin taji Daddy ya ce mata ya kai shawarma ɗakinta, ita dama bata wani iya cin abin ba sosai baya mata daɗi a baki, shi yasa ma ta je zubo abincin. Ta haɗo da ruwan gora ta dawo ɗaki ta zauna. Ta jawo ledar ta buɗe taga shawarma harda nama ga Yorgot. Murmushi tayi ta na jin dadi a ranta da wannan ɗawainiyar na Daddy, sosai take alfahari da daddynta saboda abubuwan da yake mata, ya zama dole ta daina duk abun da ya ce baya so. Ta na ci ta na tunanin abun da ya faru tsakanin ta Habib. Ita ko kaɗan bata yi nadama ko kuma tsoron wani abu ba, ita har cikin ranta daɗi take ji, wani irin shauƙi ne ke kamata idan ta tuno da abun. Sosai ta ci abincin da naman, ta bar iya shawarmar ta kai kichin ta ajiye. Ta na dawowa ta ciro wayarta ta shiga kiransa. Amma number a kashe, kira uku ta yi bata shiga sai ta kunna data ta shiga online. Sakon Bebb ta fara cin ƙaro da shi har guda uku. Da sauri ta shiga ta na karantawa, gashi minti biyar da sauƙar ta a online ɗin. Ganin bata kai ne yasa itama ta fara mayar mata da amsa, Dama tambayar ta tayi akan ya karatu, yau bata ganta ba lafiya dai ko. Bayan ta gama ta kamo number Habib shima ta ajiye masa saƙo da yawa. Har zata sauƙa taga sakon Maryam, ta na dubawa taga ta na online, hakan yasa suka fara hira. *°Habib* Lokacin da ya iso get ɗin gidan sa, ya kai minti uku a cikin motar ya kasa shiga cikin gidan, nadama ne fall ransa, hakan yasa yake ta tunanin hanyar da zai bi domin ya goge haɗuwa da ita, domin haushinta yake ji da hasken gaske. Wayarsa ya ɗauko, yayi blocking din number ta har ta whasop. Sannan ya cire layin ya karya shi ya yar. Ya ja motar sa ya ƙarasa cikin gidan. Budewa yayi ya fito daga cikin motar ya na jin wani irin fargaba na haɗa ido da Nadiya. Matarsa ta Sunnah gashi ta na ɗauke da juna biyu, mai kula da shi, mai masa biyayya, bata rage shi da komai ba amma ya tsallake ta ya je ya aikata zina! Abun da baiyi tun ya na saurayi ba sai da yayi aure. Sai yanzu ya fara tunanin ma a yadda ya baro gida, ya ce mata bashi da lafiya ta bashi magana ya sha, sannan ta shiga kichin domin ta haɗa masa farfeso duk saboda ta damu dashi. Sauke ajiyar zuciya yayi ya na jin kaman kar ya shiga gidan. Haka ya tura ƙofar palon ya shiga da wata siririyar sallama. Kasancewar hankalinta naga ƙofar domin taji shigowar sa gidan, hakan ne ma yasa taji sallamar tasa. Ajiye wayar tayi ta amsa sallamar ta na kwallonsa yadda ya ke a sanyaye sai itama jikinta yayi sanyi, kuma fargabar da take ciki ya ragu dalilin ganinsa. Miƙewa tayi da sauri ta na tambayar ina kuma ya je shida bashi da lafiya kuma bai faɗa mata ba, ta kira shi kuma bai daga ba. Zama yayi a kan kujera ya dafe kansa. Itama tazo kusa dashi ta zauna ta kama kan nasa ta ce "Bebb jikin ne dai? Nayi mamakin da na fito na samu baka nan, kuma baka faɗa min zaka fita ba?" Ya ce "Sorry na je kemis ne an min allura domin sosai zazzaɓi ya sake kamani". Cikin Muryar tausaya wa ta shiga masa sannu, ta na faɗin "Bari na kawo maka abinci?". Haka ta shiga kichin ya bita da kallon so da tausayawa. Har ta kawo masa abincin tunani ya keyi. Shinkafa ce da wake da miya, sai kuma farfeson da tayi masa, sai apul da kankana da ta yanka tun ɗazu. Sai abun sha. Haka yake ta kallonta har ta gama haɗawa. Dama tasan baya iya cin abinci idan baida lafiya, haka take kasawa ta tsare sai ya ɗan ci ko babu yawa. Hannunsa ta kama ta saƙƙo da shi ƙasa ta na masa sannu. Ta fara zuba masa shinkafar ta mika masa. Sannan ta zubo naman shima a wani plet ɗin ta miƙa masa. Baya jin yunwa ko kaɗan, amma saboda taji daɗi yasa babu musu ya ƙarɓa ya na godiya ya fara ci. Shi shida ne ta bangaren iya girkin Nadiya, amma na yau sai yaji shi salam, babu ɗanɗano ko kaɗan a bakin shi. A zuciyarsa ya ce "To dama bakin mazunaci ai baya gane ɗan ɗano mai daɗi da mara daɗi kaman yadda farjinsa baya iya banbance haram da halak. Tsayawa yayi da cin abincin yayi shiru ya na jin kamar ya fara kuka. Nadiya ta ce "Please Bebb Dan Allah ka ci, ko abincin ne baiyi daɗi ba?, yanzu fa ka ce allura a kayi maka, kuma ko da rana ba wani abincin kirki kaci ba, dan Allah ka daure ka cinye wannan abincin sai ka haɗa da kayan cikin nan kasha wannan sai ka kwanta. Ta ƙarasa ta na jin a ranta inama ya iya cinyewa. Ya ce "Amm Bebb cikina a cunkushe ya ke ba zan iya ƙara cin komai ba". Ya faɗa da muryar rashin lafiya. Ta ce "To ka ƙara ko kaɗan ne ka daure" Ganin yana girgiza kai yasa ta taso ta ɗauki kwanon abincin ta ɗebo ta kai masa baki. Tsayawa tayi ta na kwallonsa jin wani ƙamshin turare mai daɗin ƙamshi dake fita daga jikinsa. Bata zargin mijinta hakan yasa ta sa masa abincin a baki, ta na mamakin a ina ya samo wannan turaren shi da ya je yin allura, jin zuciyarta na kasa haƙura ne ya sa ta ce "Bebb ka sake samo wani kalan turaren ne?" Ta faɗa tana kuma sake ɗebo abincin ta nufi bakinsa. Da sauri ya buɗe bakin ta saka masa yana zare ido kamar munafuki. Haka ba tare da yayi magana ba saida ya cinye wannan abincin tass harda naman da ta zubo masa. Ya na gamawa ta shiga ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga ya watsa ya fito ya saka kayan barci, ya kwanta ya na addu'ar Allah yasa kar Nadiya ta sake masa tambayar. Ya na cikin tunanin ta shigo ɗakin ta kashe wutar ta kwanta a bayansa ba tare da ta ce masa komai ba, yana jin yadda ɗan cikin nata ya tokareshi ta baya. Haka Habib ya ta juye-juye ya na ta tunani akan hukuncin da yake son yanke wa, babu mafita dole ne yayi hakan muddin ya na so ya manta da wannan yarinyar. Haka sai wajajen asuba barci yayi gaba da shi, kuma ana kiran sallah ya tashi. Haka ya wayi gari wasai kansa ya daina ciwo, zazzaɓin ma babu, sai kawai rashin natsuwar zuciya. Ya na zaune a palo sai tunani ya keyi, yau ko zuwa ya taya ta aiki ma ba ta samu ba. Ita kuma tayi tunanin ko ciwon kan ne har yanzu. Bayan so yaje ya aika abun da zai lalata masa rayuwa, shi yasa yake ta shawara da zuciyar sa akan wannan hukuncin. Sai ya saƙa ya kwance hardai ya yarda da shawarar zuciyarsa duk da cewar gabansa na faɗuwa da abun da zai biyo baya. Sosai yayi ƙoƙarin sakin jikinsa suka karya ya nuna mata ya warke, harda wasa da dariya. Bai bar gidan ba sai sha biyun ra na, ya je ya sayi sabon layi ya sa aka yi masa welcome back, ya saka a wayarsa. Yaje yayi aski ya aske kansa gaba ɗaya yayi malolo ya bar iya gemun nasa shima yasa aka rage masa shi. Gaba ɗaya ya sauya kama kamar ba shi ba. Ya nufi makaranta duk yau Lahadi ne kuma bashi da class. Kai tsaye ofis ɗin shugaban makarantar ya nufa ya mika masa takardar barin aiki gaba ɗaya. Shugaban makarantar ya kalleshi bayan ya gama karanta takardar. Ya ce "Malam Habib wani irin ciwo ne ke damun ka da har zaka bar aikinka saboda shi?". Habib ya ce "Shine kawai mafita domin kar ya taba aiki na". Malam ya sake kwallonsa ganin yadda ya sauya kama, sai ya fara tunanin ko dai ciwon taɓin hankali ne yake son kama shi shine ya bar aiki. Tunanin hakan yasa ya ce "Tom Malam Habib Allah ya sawaƙe, kuma za'a tura maka albashin ka na wannan watan harda wani tallafi daga hukumar makaranta domin kula da lafiyar ka. Kuma duk lokacin da ka samu lafiya muna maraba da kai a kowani lokaci. Nan take ya sa hannu na barin aiki, ya na yi zuciyar sa na faduwa idan ya tuna irin wahalar da suka sha shida Mama kafin su samu wannan aikin. Bayan ya gama ya je ofishin sa ya kwashe komai nasa sannan ya bar school ɗin. Duk inda ya wuce sai an sake kwallonsa domin ba'a gane shi ba. Haka ya ja motar sa ya bar school ɗin ya na jin hawaye na son zubo masa. Dole yayi nesa da ita, ya tsaneta baya son ko jin muryarta. Haka ya dawo gida ya samu Nadiya ta sake wanka ta haɗa kayan wankin su tana jira yazo ya kai musu gurin wanki. Ya na shiga kuwa tai masa magana sai ya kira mai wankin akan yazo ya kwasa ba zai iya zuwa ba. Zama yayi palon ya na son ya sanar mata da cewar ya bar aiki amma amma ya kasa. Yana kallon yadda take chatting ta na dariya abunta. A ransa ya ce "Yanzu ita babu abin da yake damunta saboda ita ba mazinaciya ba ce, gashi dai hankalinta a kwance. Haka ya uni a gida, dama shi ba wasu a bokai ne gareshi ba, haka yake rayuwarsa daga gurin aiki sai gida sai gidan Mama. A bokai sai irin na school ko wanda suke koyarwa tare. Ya ce "Wai ni me kike kallo ne haka da kika ta dariya tun ɗazu?" Habib ya faɗa ganin dariyar Nadiya ɗin kaman da gaiyya takeyi yi, kaman tasan halin da ya ke ciki ne ta ke masa dariya. Ta ce "Wallhi Bebb wata friend ce da muka haɗu ta na bani labarin matar babanta lokacin da take da ciki, shine fa abun yake bani dariya, taji nace mata ina da ciki shine take tambayar wai ni cikin baya sani masifa irin na matar ne, shine da nake tambayar ta ita matar meye ta ke yi haka na masifa, shine take bani labari, wai masifaffiya ce ta bugawa a jarida a lokacin da take cikin, wai hatta mijin nata bata barshi ba, kowa ya shigo gidan nan ba'a wanyewa lafiya da shi, ko waje ta fita bata dawowa sai anyi faɗa da ita, mijinta kuwa ya sha duka da kashe kuɗi duk saboda ita. Habib ya ce "Wannan kam iskanci ne, duk a kan tana da cikin sai kace mai ɗauke da cikin aljannu?" Nadiya ta sake fashewa da dariya ta ce "Wa ya ga nima na fara yiwa Bebb haka, sai kawai na kalleka na ce bana son ganinka a cikin gidan" Habib ya ce "Sai na tashi na fita ai wannan ba komai ba ne, ta fifiyata zanyi rabda kika neme ni sai na dawo" Nadiya ta ce "Shima wai mijin nata da yaji bala'in yayi yawa sai ya tattara kayansa ya bar mata gidan ya tafi chan wani guri. Habib ya ce "Lallai ya na da hakuri wannan mijin" ta ce "Idan kai ne ba zaka iya ba?" Ya kalleta sai ya ce "Anya kuwa, amma zan iya ai ina sonki".  Sosai take bashi labarin rikicin cikin Amera wanda shima tsabar nishadi sai da ya samu kansa da jin dadi. Har ya na manta wa da batun gaya mata barin aikin nasa. Ita kuwa Nadiya har video call suka koma da Haura ana ta hira. *°Haura* Ta na idar da sallar asuba ta sake yin wanka da ruwan zafi, bayan ta fito ta saka doguwar riga da hijjabi haf Sunnah ta shiga kichin. Nan ta fara tunanin abun da zata dafa musu mai ɗan sauƙi domin ta na jin jikinta babu daɗi kaman zazzaɓi ke son kamata, gashi ta na so yau ita ce zatayi musu girki ko dan saboda laifin da tayi musu jiya. Haka ta fere dowa ta dafa, sannan ta fasa ƙwai ta fara soyawa, ta na aikin ta na sauraron waƙar soyayya cike da jin dadin baitocin cikin waƙar kamar da ita a kayi, ta na bin waƙar cikin sauƙi harda ɗan juya kanta Amera ta shigo kichin ɗin ta na binta da kallo. Sai da ta tsaya ta gama ƙare mata kallo sama da ƙasa sannan ta ƙaraso ciki ta na mata magana. Haura ta ce "Aunty good morning?" Amera ta amsa ta ɗora da "Yau da soyayya aka tashi kenan?" Haura ta yi shiru ta na dariya. Ta sake cewa "Kin gama komai ne ko na kama miki?" Haura ta ce "Na gama saura kaɗan, amma naga kamar babu biredi dama ina so a haɗa da ruwan shayi ne" Amera ta ce "Ok bari na faɗa masa sai ya samo mana yanzu kafin ki gama ko?". Tana faɗa ta bar kichin ɗin Haura ta cigaba da bin waƙarta ta na jin daɗi a ranta, barin ma idan ta tuna da cewar yau Habib zai zo a tsayar da magana. Bakwai da minti goma ta gama komai, ta jera musu a gurin cin abinci ta shiga ɗakin su Salim da Salma ta taso su, bata fito ba sai da tai musu wanka ta sawa kowa kayan zaman gida kafin ta fito dasu zuwa gurin karyawa. Suka zauna suna wasa kafin masu gidan su fito. Sai kusan takwas saura suka fito a tare. Da sauri Haura ta miƙa musu gaisuwa suna yaran suka gaida su. Adam ya dafa su gaba ɗaya ya na amsawa. Ya kafe Haura da ita a ɓoye. Nan suka zauna Amera ta zubawa Adam sannan ta zuba nata, itama Haura ta zubawa yaran nasu itama ta zuba nata suka fara. Gurin yayi shiru kowa ya mai da hankalinsa ga cin abincin, yayin da Adam ya ta tauna maganar da zai yi. Ita dai Amera hankalinta na kansa, yayin da haura kanta ya ɗan fara tsananta da ciwo...📝 Habib Zai zo kuwa? [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *°S-Reza* _First class writers association_ _My Whatsapp chanel_ *Chapter 1️⃣1️⃣* Sai da suka gama cin abincin kafin Adam ya kalli Haura da tun ɗazu ta gama cin nata abincin ta na dai zaune ta na kallon Salim. Ya ce "Karfe nawa ne ya ce zai zo?" Haura ta amsa da "Sai dai na sake tambayar sa amma bai faɗa min ba" Adam ya ɗan saci kallon Amera sai suka haɗa ido, ya kawar da kai. Ya ce "Ki ce masa yazo da wuri domin a kwai gurin da nake son zuwa yau" Haura ta amsa masa. Ya tashi ya bar gurin ba tare da ya sake cewa komai ba. Amera ta kalli Haura ta ce "Da gaske kina son wannan mutumin kuwa Haura?" Amera ta tambaya ta na kallon yanayinta. Ta ɗago kai ta na kallon ta ba tare da ta ce komai ba, kanta ne ke sara mata tun ɗazu, wanda izuwa yanzu har da zazzaɓi ne ke son kama ta, sai kuma taji tambayar tayi mata wani iri. Jin bata ce komai bane yasa Amera sa ke faɗin "Yanzu idan Daddynki ya ce miki baya son ki da shi saurayin naki zaki iya hakura da shi?" Ta yi mata tambayar domin sanin ko da gaske take son mutumin. Haura ta ce "Anty nasan ma Daddy ba zai hana ba, domin ina sonsa kuma shima yana sona" ta ƙarasa maganar a hankali. Amera ta saki wani murmushi mai lankwasa harshe. Ta sake cewa "To tsakanin shi da Daddy wa kika fi so?" Kafin tayi magana Salim da Salma suka haɗa baki gurin cewa "Daddy muke so" itama ta ce "Nafi son Daddyna akan kowa ai Anty" Amera ta ce "Kenan idan ya ce karki ƙara kula shi zaki daina?" Ta ce "Anty kaina na ciwo, idan kina da magani ki bani, ko naje na sayo?" Amera ta ce "Sorry ina da shi, bari na zo. Haka ta shiga ɗaki ta ɗauko mata maganin ciwon kai ta bata ta sha. Amera ta ce "Kije daki idan kin gama waya da shi kin faɗa masa cewar yazo da wuri sai ki samu ki kwanta ki ɗan samu barci ko ciwon zai tafi ko?" Haura ta miƙe ta nufi ɗaki Salim da Salma suka bi bayanta amma Amera ta dawo dasu akan su barta ta huta. Ta na shiga ɗakin ta ɗauki wayarta ta kira shi amma bata shiga, sosai ta dinga jera masa kira amma shiru. Jefar da wayar tayi a kan gado ta kifa cikinta ta na tunanin to mai ya samu wayar tasa ne, shi bai san tayi kewarsa bane, tun fa jiya bata sake jin maganar sa ba. Ta na cikin haka Amera ta shigo ɗakin ta ce "Yauwa na manta ban faɗa miki ba, wani irin abinci yafi so sai kawai mu fara shirin kafin lokacin ko?" Haura ta ce "Anty ban san abun da yafi so ba, kawai ayi koma meye zai ci" ta ce "Kin tabbatar?" Ta ɗaga mata kai. Amera ta ce "Kunyi waya ɗin?" Haura ta amsa da "Yanzu zamuyi" Amera na fita haura ta fara rubuta masa saƙo dan gajere ta tura. Sannan ta sake kwantawa tana tura kanta cikin filo ta na tunanin Habib da yadda suka kasance jiya, har yanzu ta na ɗan jin zafi, ta na tunanin ma abun da ya ke ƙoƙarin haifar mata da zazzaɓin kenan. Haka ta dinga tunani har taji wayanta na ƙara. Da sauri ta ɗaga ta na duba sunan mai kiran. Ido ta waro ta na mamaki, ai kuwa da sauri ta ɗaga ta na sallama. Ta cikin wayar Nadiya ta amsa ta na tambayar ta bata hau online ba, ta na ta jiranta. Haura ta ce "Yanzu dama nake shirin hawa" take ta kashe kiran. Ta buɗe Data. Haka suka dinga shan hira har bata san lokacin da ciwon kan ya tafi ba domin hira sosai suka sha ta na bata labari, karshe ma aka koma Vedo call. Babu laifi Nadiya na da kyau daidai gwargwado, kuma bata rasa komai ba, sannan ita Haura bata jin komai game da ita wai na kishi, hasali ma harga Allah ta na son Nadiyar so sosai kuwa, ko dan saboda Habib na sonta ne, haka kawai take jinta rai, kuma take jin dad'i hira da ita. Ta bangaren Nadiya itama haka ne, yarinyar na burgeta, tana son yarintarta da kuma yanayin Hausar ta, ta na son kulawarta, hakan yasa bata gajiya da hira da ita. Suna ta hira har bata san lokaci yaja har haka ba. Hakan yasa ta ce mata tana zuwa zatayi abu ne. Koda suka kashe ta duba shi a Whatsapp amma bata ma ga karshen hawansa ba. Ta sake kiransa baya shiga. Izuwa lokacin ta fara damuwa, sai taje jin ko dai ta tambayi Bebb ne ko ba lafiya ba. Domin haka tayi seving number Nadiya da Bebb saboda haka Habib yayi a wayarsa. Tashi ta yi ta fito waje, ta samu yaran suna wasa abun su, ta shiga kichin ta samu Amera na girki har ma ta kusa gamawa. Ta ce "Anty sannu da aiki?" Amera ta amsa ta na murmushi. Haka ta kama mata aikin suna ta hira har suka gama. Izuwa lokacin ɗaya da wani abu, hakan yasa Amera ta ce taje ta shirya tunda ta mata ƙaryar cewar wai karfe huɗu ne zai zo. Amera ta shigo ɗakin sai ta rasa ma to wani kaya zata saka. Sai da tayi wanka kafin ta fara fiddo da kayan da zata saka. Ta na cikin haka kira ya shigo wayarta. Da sauri ta ɗaga tana karawa a kunne. Nadiya ta ce "Ina ta jiranki na nuna miki wani abu" haura ta ce "Da gaske?" Ta ce "Buɗe Whatsapp ki gani" Nan take ta buɗe suka haɗa video call. Abinci ne tayi take nuna mata shi kasancewar sunyi maganar abincin ɗazu da haura ɗin take cewar tana son ta gwada irinsa. Sosai abincin yayi mata kyau a fuska, ta shiga santi tun ma kafin ta ci. Haura ta ce "Zaki koya min yadda ake yi fa Anty, domin ina so na gwada a gida?" Nadiya ta ce "Duk lokacin da kika kawo min ziyara zan koya miki. Haura ta ce "Da gaske kike?" Ta amsa da cewar da gaske. Suna wayar Haura na ta leƙa ko zata hango shi ta cikin wayar amma ko motsi ma bata ji. Sai ta ce "Anty yanzu wannan ke ɗaya zaki ci ko tare da shi zakuci?" Nadiya ta yi dariya ta ce "Ni da yaron cikina ne, baki san masu ciki suna da cin abinci ba, ko baki ga haka a lokacin cikin Amera masifaffiya bane?" Ta faɗa ta na dariya. Haura ta ce "Antyna ɗin ce masifaffiya ko, ai da na, yanzu ta na da kirki sosai" Nadiya ta tsayar da dariyar ta ce "Na sani wasa nake miki, ki gaida min da ita kice Nadiya tana gaishe ta, bata jira komai ba ta kashi kiran. Haura ta yi shiru tana tunanin mai yasa bata so su dinga magana akan mijinta, ko dai ta santa ne. Har ƙarfe biyu number Sir bata shiga, har zuwa uku, haka dai ta ci uban kwalliya na doguwar riga jikinta a mace musamman ma lokacin da Adam ya dawo daga masallaci ya sake tambayar ta. yadda suka yi. Har huɗu da rabi babu Sir babu wayarsa. Har karfe biyar babu labarin sa, izuwa lokacin Najib yazo gidan dalilin kiransa da Adam yayi. Domin shi Adam har ya shirya yadda zai masa idan ya zo, zai ce masa an mata miji ne, dan Allah karya ƙara zuwa, kuma karya ƙara kiranta a waya. Karfe biyar da rabi Adam ya zo palon ya sameta a zaune ta sunkuyar da kai. Ya ce "Haura bai zo ba ko?" Ya tambaya cikin tausasa murya. Ai kuwa ta na ɗago kai sai ga hawaye. Lokaci ɗaya ta fashe da kuka. Adam ya tsaya yana kallonta. Kuka takeyi sosai domin abun yayi mata zafi, yaya za'ayi ya ce zai zo amma yayi mata haka, ko ba komai ko saboda abun da ya faru jiya ai ya dace yazo saboda ya faranta mata. Adam ya ce "Haura wannan mutumin ba sonki yake yi ba, muna fuki ne, yaudarar ki kawai dama ya ke yi, ina so ki fita daga sabgarshi kinji?" Ya faɗa ya na kallonta. Da sauri ta tsayar da kukan na ta ta ɗago itama ta na kallon sa. Sai ta fara girgiza masa kai, ta kasa magana domin bata ma san mai zata ce ba. Ta na son ta ce masa ba zata iya daina son sa ba, kuma ta fada masa cewar Sir yana sonta, domin shi da kansa yayi mata alƙawarin yana tare da ita har abada kafin ta bashi kanta. Amma tana buɗe baki sai kuka. A haka Amera ta fito ta same su. Adam ya ce "Idan da dagask ne yana sonki da yazo anyi magana Haura" tun kafin ya sauke numfashi Amera ta ce "Kaman yaya baya sonta, ka bar yarinya da abun da yake damunta mana, shi ya faɗa maka cewar baya sonta, kasan wani irin uzuri ne ya tsayar da shi bai zo ba, yanzu haka ma yana kan hanya ko kuma sherin ƙarfe ne. Ta na zama haura ta tashi ta bar gurin domin taji haushin maganar Daddy. Ta na shiga ɗaki ta sake fashewa da kuka, kuma tana sake kiran number sa. Wasa-wasa har sallar magriba babu Sir kuma har lokacin number sa bata shiga. Izuwa lokacin tayi kuka har ta gaji, haka kuma ta kira number sa har bata san adadi ba. Kasancewar gobe class ɗin ta na safe ne yasa ta bari akan zasu haɗu a school Allah yasa lafiya. A daren ma sai da sukayi chatting da Nadiya, kusan na minti talatin kafin ta kashe wayar ta kwanta. Washegari haka ta tashi babu daɗi, tayi mafarkin wai yazo sunyi magana da Daddy har an saka musu rana. Haka take yin komai sukuku babu kuzari, bata iya cin komai ba sai ruwan zafi, ta riga kowa fita a gidan. Ta na shiga class ta zauna ta dafe kai tana tunani a gurin da take zama. Haka suka gama karatu bata ganshi ba. Amma bata koma gida ba har Maryam tazo da yake ita na yamma ne nata, haka ta jiranta har aka tashi. Har ofishin sa taje ta gan shi a rufe, hakan yasa hankalinta ya tashi. Haka ta dawo gida kamar mara lafiya, sai ta kasa natsuwa, idan ta kira number bata tafiya har lokacin, gashi ta kasa fadawa kowa halin da take ciki. Ranta zafi yake mata na rashin ganinsa da ji daga garesa, har wani abu take ji mai yaji a zuciyarta. Washegari ma haka taje school tun safe har yamma babu shi babu labirinsa, sannan ofis ɗin nasa a rufe hau yau ɗin ma. Izuwa lokacin ta fara saduda, to me ke faruwa, kuma idan suna waya da Nadiya sai ta kasa mata maganar sa, kuma ko sunyi vedio call bata jin motsin sa. Abun da ta lura kaman Nadiya irin matan nanne da basa wasa da mazajensu a gurin mata, domin bata taɓa yarda ta sako mata zancen sa, wasu lokutan ma idan haura ta nuna tana son ganin hoton mijin nata sai ta share da wani zancen. Duk wata dabara da take tunanin tana da ita akan ta samu labarin sa tayi amma shiru. Bata sake shiga tashin hankali ba sai a rana ta huɗu da tazo school ta ga wani sabon malami a gurbin sa, kuma a cikin ofis ɗin sa, kuma gashi kowa na maganar wai Malam Habib ne ya bar school ɗin aka kawo wannan. Sosai students kowa ke murna banda ita da hankalinta yayi mugun tashi. A ranar bata zauna a school ba haka ta koma gida ta sha kuka harda rashin lafiya. Ta kasa fahimtar kenan saboda ita ya bar school ɗin ko dai me, to ma mai yake nufi. Tuni ta gane cewar blocking dinta ya yi, domin yanzu ta daina ma gwada kiransa. Ta rame sosai wanda kallo ɗaya zakayi mata ka gane hakan. Babu yadda Amera batayi da ita ba amma ta ƙi sanar da ita halin da take ciki. Bangaren Adam kuwa yaji daɗin rashin zuwan yaron, kuma idan ya kula har yanzu bai sake mata maganar ba. Yana so ya shiga da maganar sa yadda zata manta da wancan ɗin sai dai ganin halin da take ciki yasa ya ɗan sarara. Sosai wata dabara ta fado mata, ranar Alhamis wato gobe bata da aji gaba ɗaya, kuma ta na son ganin sa, domin ji take kamar idan bata gansa ba zata iya yin hauka, hakan yasa ta shiga bugar cikin Nadiya. Ta ce "Gobe muna da biki a unguwar ku?" Kasancewar ta faɗa mata unguwar, kuma bata taɓa zuwa ba, amma babu nisa sosai da tasu unguwar. Nadiya ta ce "Ke dan Allah, ashe dai zaki zo min kenan ko?" Haura taji Kamar ta ce eh lokaci ɗaya amma ta ce "Ai ba lallai Antyna ta barni ba, saboda tare zamu zo". Nadiya ta ce "A haba dai, sai kace wata yarinya ƙarama" Haura ta ce "To ai yarinyar ce, ni da ko fita ba'a barina nayi" Nadiya ta ce "To ni idan kun zo sai ki haɗa ni da ita nayi mata magana, ina dai Amera ce ko?" Haura tayi dariya ta ce "Itace amma fa babu ruwana idan ta balbale ki". Sukayi dariya suka ɗora da wani hiran. Haura ta sauke wani ajiyar zuciya lokacin da suka gama wayar. Ta ke wani farinciki ya cika mata zuciya harda murmushin son ganinsa. Ta na zuwa gida ta tarar Amera bata nan, babu kowa a gidan domin ta tafi da yaran. Kichin ta shiga ta fara musu girki, ta na cikin yi ne taji tsayuwar motar Adam. Cen kuma ta ji sun shigo gidan gaba ɗaya harda yaran. Jin haka yasa ta fito falo tana musu maraba da dawowa. Salim da Salma suka zo da gudu suna ɗaneta. Adam ya amsa ya na mata sannu da gida. A ranar su kansu sun lura da sauyin da ta samu, yau tana ta fara'a har dare. Ai kuwa washegari tun safe ta kira Nadiya ta ce suna hanya. Karfe goma na safe tace mata suna gidan bikin amma ita sai karfe biyu zata zo. A lokacin ne kuma take shirin fita daga gida, ta saka jar abaya ta shafa janbaki ta yafa mayafin a kanta kaman yadda ta saba. Haka ta bar gidan izuwa unguwar su Nadiya ta na hanya ta kiranta akan cewar ta turo mata da number gidan domin gata a hanyar gidan ita ɗaya. Nan take kuwa ta tura mata. Cikin lokaci kaɗan kuwa mai kekenapep ya kawota har ƙofar gidan bayan ta bashi wayar ya duba address ɗin. Bayan ta sauƙa ta bashi kudinsa sannan ta nufi cikin gidan kanta tsaye, zuciya da gangar jikinta na azalzalar ta...📝 S Reza... [09/07 à 14:07] S Reza: A BAR WA RAI!❣️ S-Reza Chapter 12 Ta na shiga da motarsa ta fara cin karo a ɗan madaidaicin harabar gidan wanda ya yi mata kyau gashi ɗan ƙarami amma a wadace. Sai da ta tsaya ta ƙarewa motar kallo sosai ta na jin yadda ta yi kewar motar har cikin zuciyarta, jakarta ta buɗe ta fiddo da abun rubutu ta fara za na abun da take son zanawa sannan ta wuce ta na jin wani irin farinciki na ratsa ta, har wani lallausan murmushi take saki ita ɗaya. Tabbas ta tabbatar nan gidan Sir ne domin irin wannan daɗin da farincikin dole sai a gurin da ya dangance shi. Number Nadiya ta kira ta ce mata gata a ƙofar palon ta zo ta buɗe mata. Minti biyu da yin wayar sai ga Nadiya ta buɗe ƙofar. Ido biyu suka yi, yayin da bakin Nadiya har kunne tsaɓar farinciki da murnar ganinta, ta ware hannunta alamar tazo ta rungumeta. Haura kuwa lokacin da ta haɗa ido da ita sai gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, haka kawai taji zuciyarta ta harba da ƙarfi, wani mugun abu taji a zuciyarta mai wahalar fasaltawa, musamman ma ganin wannan cikin na jikinta. Sai take jin kamar itace ta tare mata hanyar da zata bi domin cikar burinta, sosai zuciyarta ke bada wani irin sautin fat-fat da sauri da sauri kamar zata fito daga ƙirjinta. Batayi tunanin zata iya jin hakan a tare da Nadiya ba, ko dama saboda basu taɓa haɗuwa bane yasa taji tana sonta, kenan dama kawai tana sonta saboda bata ganta a gidan Sir ba. Haka Nadiya ta ƙaraso da ita cikin palon ta zaunar da ita tana cigaba da mata maraba har lokacin shinfiɗar fuskar nan tana shinfiɗe da annuri. Dole ta kawar da kai ta shiga amsawa ta na murmushin da iya karsa fatar baki. Kafin ka ce wani abu sai ga shi ta fara cika mata gaba da abubuwan sha da ci wanda tayi musamman domin ita, sai janta da hira takeyi. Ta ce "Ina so na shiga toilet Please?" Haura ta faɗa a hankali, domin har ta gaji da hirar da take mata, ina wallahi ba zata iya ba, Gara kawai tayi abun da ya kawota, tana jin tsaf zata iya mutuwa idan ta cigaba da sauraron ta. Nadiya ta nuna mata toilet ɗin dake palon. Ai kuwa ta tashi da sauri ta shiga. *°Habib* Sosai barin aikin da yayi ya fara damunsa musamman lokacin da yaje gida ya faɗawa Mama. Bayan ganin askin da yayi ne yasa take tanbayarsa lafiya dai yake ko, ya amsa mata da cewar lafiyarsa lau. Saida suka gama gaisawa kafin ya shigar mata da maganar dukda cewar ya ɓoye mata asalin abun da ya faru. Sosai Mama ta fara Salati ta na kama baki, sai kuma ta fara tambayar sa mai yayi musu da zasu koreshi, amma haka yace mata babu komai kawai shari ne na wasu mutanen. Haka ya bar gidan bayan ta masa faɗa sosai sannan ta ke tambayar sa wani aiki zaiyi yanzu ya ce zai sake neman aikin koyarwar ne, nan ta masa fatan alkairi ya bar gidan, har tana cewa idan za'a iya zuwa a basu hakuri to ya fadawa Nadiya sai ta samu mai makarantar domin ta inda aka hau tanan ake sauka. Amma yace mata ko anje ba zasu hakura na. Daga nan gida ya koma domin fuskantar Nadiya, tun a hanya yake tafiya yana tunanin mai ma yasa bai tsaya ya yi dogon nazari ba kafin ya ajiye aikin, ai ko tana school ɗin zai iya koyarwa, kawai zai ɗwuke kai da ita ne ya dinga korar ta ko ya kaita ƙara gurin shugaban makarantar wataƙilla ma a koreta, kuma gashi ma wannan shekarar ita zata fita daga school ɗin gaba ɗaya. Take nadama da tausayin kasa ya cika shi, yanzu a ina zai samu aiki yadda aiki yake da wahalar samu a Nigeria. Haka ya dawo gida duk ransa babu daɗi, sai tsinewa abun da ya haɗa shi da Haura ya ke yi, ta cuceshi ba zai yafe mata ba ta bata masa rayuwa. Yana shiga gida ya samu Nadiya na waya, bai ce mata komai ba ya wuce ta ya shiga daki. Da sauri ta kashe wayar tabi bayansa da sauri. Ta na shiga ta samu ya bata baya, hakan yasa ta karewa askinsa kallo, ita a ranta yayi mata kyau dama haka zai koma yin askinsa ma da taji daɗi, tun lokacin da yayi askin ita kadai ce tace yayi kyau, kuma ko lokacin da ta faɗa kawai ya jita ne, amma yasan dalilinta na faɗin haka, amma in ba haka ba, tana ganin yadda ya koma kamar wani soloɓiyo amma tace yayi kyau, tabbas yin aski mamalo yana ragewa mutum kwarjini da cika ido. Kamar daga sama taji muryarsa ya na faɗin "Bebb an koreni a gurin aiki" ya faɗa ba tare da ya juyo ba. Yau Litinin ne, kuma tun safe bata ga alamar zai tafi aiki ba, domin tunda suka karya yake gida, bai fita ba sai kusan goma, kuma da zai fita ya faɗa mata cewar gidan Mama zaije, idan bata manta ba duk ranar da bashi da school yana faɗa mata domin su zauna a gida suyi hira harda game da daidai abubuwan da zasu ɗebe musu kewa. To amma yau bai faɗa mata cewar yana da class ko babu ba, bata kawo komai ba, ta bari akan ko sai yamma zai shiga school. Ko yanzu ta zo ne da nufin tanbayarsa sai gashi ya na sanar da ita da kansa. Kuma ko kafin ta sake cewa komai ya ɗora da faɗin "Dama kwanakin baya na faɗa miki cewar ana so a ƙulla min gadar zare ne, kuma sun yi nasara, amma Allah yasa hakan shine mafi alkairi, na yarda da kaddara a duk yadda tazo min" ya karasa ya na karasa cire dogon wandon jikinsa ya ɗauko wani gajere ya saka. Nadiya ta tsaya ta na ta kallonsa, da yake ya santa da dogon tunani gata mai amfani da ilimi, ko daga maganar Nadiya kawai zaka san tana da hankalin magana, ya sani zata iya karya masa zuciya da tambayoyin ta masu gama da tuhuma. Hakan yasa ya buɗe baki zai yi magana amma ta riga shi ta ce "Bebb ban gane kora ba, kora fa gaba ɗaya kenan kabar school ɗin ko yaya?" Ta faɗa ta na jin wani irin tashin hankali mai lasisi na tirar mata, aikin da shine rufin asirinsu, aikin da kafin a samu sun sha wahala, aikin da sanadiyar sa ne rayuwarsu ta sauya, aikin da saboda shi ne yasa yanzu suka fi ƙarfin komai na rayuwa, aikin da bata mantawa ita kanta sai da ta sha wahala kafin sabuwar sa. Ya ce "Eh Bebb kora gaba ɗaya" ya faɗa shima yana tuno irin rayuwar da suka yi a baya. Kamar daga sama yaji ta watso masa tambayar da bai zata zatayi masa ba, kuma ta ɗora da cin albashin da yasan Wallhi sai tayi domin yasan ba zata ɗauki lamarin da wasa ba, itama ta sha wahala Kafin ya samu wannan aikin. Ta ce "Wai ma wani laifi ne ake tuhumar ka da shi ne?" Ta tambaya ta na kallonsa. Lokaci ɗaya ya rikice. Ta ɗora da faɗin "Gobe zan je school ɗin kuma in sha Allahu komai zai warware karka damu, gaskiya zata fito muddin shirri ne aka yi maka to za'a gano gaskiya". Ta ƙasa da tabbacin da shi kansa ya san zata je ɗin. Ya sani zata je ɗin, kuma da sharri ne aka yi masa zata iya wanke shi saboda ta na da alfarma a school ɗin, asalin mai makarantar abokin mahaifinta ne na sosai, ko lokacin da za'a bada aikin akwai sa hannunta dan zai iya cewa saboda ita ne ma aka ɗauke shi, kuma ko yanzu idan tayi magana za'a duba. Duk yadda Habib ya kai da doje mata amma ya kasa, komai ya faɗa sai ta ce itafa wallhi sai taje, ko ya manta da yadda aka samu aikin ne. Haka ya hakura ya barta har zuwa washegari. Ai kuwa kaman yadda ta faɗa haka ta shirya zata fita Habib ya tare mata hanya akan babu inda zata je. Ta kalleshi sama da ƙasa ta na rasa mai zata ce masa. Shi wai bai san cewar ta gane ƙarya yayi mata ba ne, tun lokacin da ya ke ta wannan surutan cewar ya ɗauki gaddara da meye meye ta gane ƙarya ne, wanda aka kora daga aiki duk yadda ya kai da ita yarda da yadda da gaddara ba haka ya kamata aga fuskarsa da kalamansa ba, babu damuwa a fuskarsa, kuma babu tsoro da fargaba da tashin hankali a kalamansa. Sai kawai ta ce "Faɗa min gaskiyar abin da ya faru?" Ta faɗa cike da ɓacin rai. Ita tunda taga yana ta hana ta zuciyar ta ta ɗarsa mata cewar Habib baida gaskiya, kuma ta sake tabbatar da hakan ɗin ne yanzu. Tabbas yana ɓoye mata abu tun ba yanzu ba, kuma tasan yadda zata yi da shi. Ya ce "Ban gane gaskiyar abin da ya faru ba?" Ya faɗa cike da mamaki. Ta ce "Kai ba yaro bane, kasan abun da nake nufi, maganar korar da kace an maka ba haka bane Habib, faɗa min gaskiyar Abin da ya faru?". Habib ya ce "Tabbas gaskiya ne, nine na bar aiki da kaina, kuma dan Allah karki tambayeni dalili, ban san mai zan ce miki ba, amma namiki alƙawarin zan samu wani aikin nan kusa. Dan Allah karki ce komai idan kina ƙaunar Allah da Manzonsa, kuma idan har kina sona saboda Allah Please Bebb?" Ya karasa harda risinawa har ƙasa. Nadiya ta share hawayen da ya zubo mata, a hankali ta ce "Haka kake so?" Ya ce "Eh bana son kimin maganar ban san mai zance ba". Ta ce "Ba zan yi ba, in sha Allahu ba zan ce komai ba". Ta na faɗa ta koma ɗaki ta cire hijjabin da ta saka ta zauna a bakin gado ta fashe da kuka. Habib ya sauya mata, ya shigo da halin da bata san shi da shi ba wato ƙarya, mai yasa zai dinga mata karya, ko dan ta damu da shi, ko yana tunanin samun aikin wasan yara ne, sannan gurin da zasu iya biyan sa kamar wannan ma ba wasa bane, sosai tunaninta ya tafi tariyo mata farkon auransu da shi yadda suka yi zaman hakuri. Duk yanda take son jin abun da ya faru haka ta kawar da kai bata ƙara ce masa komai ba shima haka. Kullum yana gida, daga ɗaki sai palo sai Kuma masallaci, wasu lokutan ne ma yake ɗan fita. Nadiya dai bata kara masa maganar komai ba kamar yadda ya roka, shi kuwa yana ta binciken makarantar da zai fara zuwa domin neman aiki. Daidai da minti ɗaya bai taɓa mantawa da Haura a zuciyarsa ba, sai dai yanzu ya tabbatar da cewar dama kawai sha'awar ta ya keyi, yanzu ko ya tuno ta baya jin Komai sai ma tsanarta da wani irin haushin ta da yake ji, kullum sai ya tsine mata ya kuma roƙi Allah akan karya haɗa shi da ita har abada. Yau harda mafarkin sun haɗu a hanya ta ganshi ta biyo shi da gudu yayi tana ta cewa "Sir Sir", hakan yasa yana farkawa ya fara salati domin baya ko son tunowa da ita. Haka kawai yaji jikinsa ya mutu sai yake jinsa wani iri kamar mara lafiya. Palo ya fito ya zauna yana ta bincike a makarantu kusan guda huɗu. Ya ce "Bebb zo ki gani ina sa ran in sha Allahu zan samu aiki anan?" Ya faɗa yana kiranta akan tazo ta ga makarantar. Ta ce "To Allah ya bada sa'a" ta faɗa tana cigaba da danna wayarta. Ya sake cewa "Bebb zo dan Allah a cikin wannan da wannan wanne ya kamata na yi applying, ko wannensu suna da tsari ga shi ba laifi suna da tsoka?" Ta ce "Ka zaɓi duk wanda yayi maka kawai" Ya ɗago da sauri ya ce "Bebb wai miye haka ne dan Allah, wani abu nayi miki ne?" Ta ce "Mai ka gani kuma?" Ya ajiye laptop ɗin a gefe ya dawo kusa da ita ya ce "Bebb ban sanki da fushi ba, dan Allah komai ya wuce?" Ta ce "Wai wani abu ne dama ya faru? Kana ta cewa ya wuce meye shi zai wuce ɗin ne?" Ta karasa harda dariya. Habib yayi shiru ya cigaba da aikin sa yana satar kallonta. Yana ta kokarin sako ta a hirar amma tana basarwa, abun da ya lura magana idan har ta shafi aiki ne bata so, shi yasa ya daina mata maganar. Sosai yake ta satar kallonta ganin yadda take ta aiki kamar ba mai ciki ba. Shi dai yana jin labarin yadda masu ciki ke bawa mazajensu wahala, ko na laulayi kona rashin lafiya ko iya shege, amma dai shi Nadiya kamar ma son aiki aka ƙara mata da ta samu ciki, kaman ya tambayeta ko baƙi zatayi ne ganin yadda ta dage amma ya waske. Ta ce "Bebb zaka iya komawa ciki da aikin nan zanyi baƙi yanzu Please?" Ta faɗa ta na kallonsa. Ya ɗago da nufin yin magana amma ganin yadda ta haɗe rai, kuma shine mai neman shiri, sannan dama haka take yi, shi zai ce bai taɓa ganin kishi irin na Nadiya ba, muddin zatayi baƙi yana gida to zata ce ya koma daki kar ya fito sai sun tafi, sannan bata taɓa iya haɗa shi da wata ko da kuwa kawarta ce bare kuma wacce bata sani ba. Bata da hayaniya amma tana iya hukunta shi da fushinta mai sanyi ba tare da tayi magana ko ta hana shi wanni hakkinsa ba. Ya tashi ta ce "Idan sun tafi zan faɗa maka". Ya ce "Kin san dai lokacin sallah ya kusa gara dai su tafi da wuri?" Ya na faɗa ya wuce yana jin wani kasala da kuma tuno da abun da ya faru tsakanin sa da Haura, abun da take tsoron ai ya faru, shure-shure baya hana mutuwa. Haka ya koma daki yaci gaba da aikinsa. Yana cikin aikin ne ta shiga ta kawo masa irin abun da tayi harda Yorgot mai sanyi da soyayyen naman kaza. Bata ko tsaya ba ta koma tana jin yana mata godiya. Haka dai har ɗaya da rabi ya na ta aiki. Ya samu makarantu guda huɗu da zaiyi applying wanda dukkansu ya yarda da tsarin su, kuma fatan nasara. Ya ɗauko takardusun ya shigar da baya nan sa nan take kuwa ya tura gaba ɗaya. Daidai lokacin kuma aka kira sallar azahar. Da farincikin ya shiga toilet ya ɗauro alaula ya fito ya sake duba laptop ɗin yaga da gaske ya shiga sai ya nufi masallaci. Yana buɗe ƙofar palon gabansa ya fadi wanda bai san dalili ba, da sauri ya dafe gurin ya fara karanto addu'o'i domin sosai gaban nasa ya fadi. "Good afternoon Sir?" Ya tsinkayo muryar ta kamar daga cikin kansa ko daga sama, kuma kamar daga zuriyar sa ta fito. Sautin muryar ya dinga masa yawo a kunne, kuma kamar a mafarkin da yayi da ita ɗazu. Ya juyo da sauri ya hangota zaune a gurin cin abinci ita ɗaya sanye da irin kayanta wannan karan jar abaya tana masa murmushin nan nata mai tsaya masa a zuciya. Wani yawu ya hadiya mai kauri yana kallonta. Ta ce "Kaje kayi Sallah ka dawo ina jiranka, idan ka daɗe zan iya kwana saboda kai Sir, kasan bana iya jure rashin ka" ta ƙarasa ta na kanne masa ido ɗaya, kuma maganar a hankali wanda ba dan hankalin sa na gareta ba ba lallai ya ji ba. Habib yaji kamar zai kasa tsayawa. Yana cikin haka yaji alamun tafiya ai da sauri ya fita ba tare da yace komai ba. Yana fita ya tsaya yana kallon cikin palon daga waje, ya mutsutsuka idonsa da karfi ya buɗe. Lokaci ɗaya ma ya rasa me ma yake faruwa. Saida yaji an fara sallah ya tuno da abun da ya fito da shi. Ya nufi masallaci yana tafiya yana yana leƙen baya. Yana kusa da saitin motarsa yaga anyi rubutu da irin abun da aka taɓa yi masa da shi a makaranta. "Sir I miss You, I come over u Sir, I come to see u Sir, Sir I'm in your house Sir. Gaba ɗaya haka ta dinga rubutawa a jikin motar. Da sauri ya shiga sharewa yana jin wani sabon masifa da tashin hankali har cikin gida, yana ganawa ya nufi masallaci kamar yayi kuka. Koda ya fito sai ya tsinci kansa da tsoron shiga gidan, kuma yana tsoron ƙin shiga ɗin. Wai ma to a ina ta santa, wama ya nuna mata gidan nasa?...📝 S-Reza... [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*               _FCWA_              _Whasop chenal_ https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a                 *Chapter 13* Dole ya danne zuciyar sa ya koma cikin gidan domin kuwa rashin komawar babbar matsala ce a gareshi. Da sallama ya shiga gabansa na faɗuwa, zuciyar sa na raya masa abubuwan da bai ma san adadi su ba, babban abun da ya ke tsoro bai wuce Haura ta tona masa asiri ba, kuma ya lura yarinyar bata da hankali sam-sam, kanta rawa yake yi. Hauran ce ta amsa sallamar sai ya kasa ɗaga kai ya kallesu dalilin ganin Nadiya a gurin. Kasa tafiya yayi sai kawai ya samu guri ya zauna domin so yake yaji wacce irin hira suke yi, kuma ma yaushe ne har Nadiya ta san haura, ko dama sun san juna ne. Tambayoyi ne furjik a kansa wanda dole ya ɓoye abansa domin babu wanda zai tambaya a wannan lokacin. "Nadiya ce ta miƙe ta zuba masa abinci sannan ta kalleshi ta ce "Ga abincin bari na kai maka ɗaki ina tare da baƙuwa ne?" Ta ƙarasa ta na wucewa ɗakin. Ya sani bata son ganinsa a palon ne saboda baƙuwa, shi kuma yau ba zai bar palon nan ba har sai wannan da take kira da baƙuwar ta tafi. Nadiya kuwa bata san cewar Habib ya fita ba, sai da taga ya dawo yanzu. Sai da gabanta ya fadi lokacin da ta ji sallamar sa, bata ƙara cika da mamaki ba sai da taji Haura ta amsa masa sallamar da wannan muryar tata wacce ita ma da take mace sai da tayi mata daɗi, bare kuma Namiji kamar Habib. Hakan yasa ta ƙara jin wani iri a ranta na rashin daɗi da tsoro, bata wasa da miji ko kaɗan, bata sakin fuska ta wannan bangaren. Ta na cikin haka taga ya zauna a palon kuma ya kunna tv ya raƙe ƙara ya na kallo, wato dai anan zai zauna. Abun da ya fara zuwar mata shine ya ganta kuma yaga ta burge shi, shine yasa ya zauna domin ya dinga kallonta. Hakan yasa ta zuba masa abincin ta wuce da shi ɗaki domin kawai ya zauna yaci a ciki. Har ta kusa shiga dakin da abincin ta tsinkayo muryar sa ya na faɗin "Bebb a koshe nake, ki bari zuwa anjima sai naci, kin manta ɗazu kika haɗa min kayan ciye-ciye, to har yanzu ban cinye ba". Ya faɗa yana kallon tv show ɗin da bai ma san mai suke yi ba. Juyowa tayi ta na so su haɗa ido amma yaƙi yin hakan, ta kalli gurin da haura take zaune taga su take kallo. Babu yadda ta iya saboda kar ta bada shi a gaban bakuwa yasa ta dawo da abincin. "Ina uni" Dukkanin su suka tsinkayo muryar Haura tana gaida Habib cike da salo mai jan hankali. Kasancewar hankalinsa na gurinsu yasa ya san da shi take. "Am um umm la laa lafiya lau, ya gida ya karatu to madalla" ya amsa a rikice tsoro fall muryarsa. Daga haka kuma kowa yayi shiru suna cin abinci shi kuma ya kallo biyu. Jin shirun yayi yawa ne yasa Haura faɗin "Anty gidan nan naku yamin kyau sosai, Allah yasa saurayina ya gina min irinsa". Nadiya ta ce "Amin" ta faɗa kamar bata so, domin ta cika sosai, sai hararar Habib take yi, kuma hankalinta duk yana kansa. Haura da ta lura da hakan sai taji daɗi, ai kuwa sai cewa tayi "Bari na ɗan zazzaga naga gidan da kyau" Nadiya ta ce "Ba yanzu zaki tafi ba ko?" Ta tambaya da wata irin siga da saida Habib ya kallosu. Haura ta ce "Anty ai babu damuwa na fadawa Anty Mera cewar sai yamma zan koma, nace idan ta gama ta wuce kawai zan dawo da kaina. Nadiya ta yi shiru bata ce komai ba. Sai mamakin ƙarfin halin yarinyar da take yi. *°Haura* Miƙewa tayi ta fara zazzaga cikin palon ta na yi tana cigaba da jan Nadiya da hira game da cikinta ta na tambayar yaushe ne zata aihu. Ta bi ta bayan kujerar da yake zaune tana tafiya kanta a sama ita a dole saman ɗakin take kallo. Ta na zuwa saitin inda yake, ta shafa masa wuya ta wuce. Ta sake dawowa ta gabansa tana tafiya tana yabon palon da kayan cikinsa. Ganin haka yasa ya nade ƙafafuwansa domin karta taka shi, a tsorace yake sosai, ya na jin rashin daɗi ace Nadiya tasan abun da ya aikata. Ta shiga kichin ta dubo ko ina tana ta yabon gidan. Ta dawo ta zauna tana kallon Nadiya ta ce "Anty gida fa yayi kyau, yanzu idan na tafi sai kuma suna ko?" Nadiya dai sai murmushin yaƙe takeyi domin lamarin ta ya fara fitar mata akai, gashi yarinyar sai kwarjini take mata. Haura ta ce "Anty bari nayi miki wanke-wanke yau na hutar da ke ko dan saboda Baby". Nan take ta fara haɗa kayan ta kai kichin ta ce "Shikenan abun da za'a wanke?" Ta tambaya domin ta na so ko dai tace ita ta shiga ɗakin habib ta kwaso ko ita Nadiyar ta shiga. Nadiya ta ce "Ai Aisha da kin bari ma, babu komai zan iya yi fa" Haura ta ce "Ba komai anty ai yaune kawai kinga sai ki huta. Nadiya na shiga ɗakin ta ƙaraso gurin da yake da sauri ta ce "Kace mata kaine zaka kaini gida domin ina son magana da kai, idan kuma ba haka ba wallhi zan kwana ana kuma zan faɗa mata komai dake tsakanin mu" Ta na faɗa ta koma gurin ta da take ta tsaya. Habib kuwa wani irin sabon tsanarta ne ke ƙara taso masa idan tayi magana, tabbas shima zai so yayi magana da ita domin ya faɗa mata matsayinta yanzu, dole ya zazzage ta idan ta kama ma harda duka domin ta fita daga sabgarsa, ta fita a rayuwarsa. "Bebe "Bebb "bebbbb!?" Ta faɗa da ƙarfi ganin kamar hankalin sa ya yi ɓatan dabo. Amsa yayi yana kallon Nadiya tsaye a gabansa ashe har ma ta fito daga ɗakin bai sani ba. Ya ce "A ina kika samo wannan yarinyar mai ido a tsakar ka, mara kunya mara kamun kai haka?, tazo sai zazzaga mana gida take tana ta surutu?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye sai zare ido yake yi, kuma haɗe da borin kunya. Nadiya ta kafe shi da ido tana jin faɗuwar gaban nata na ƙaruwa. Tsoro ne ke son kamata amma ta dake ta ce "Shi ne yasa ka zauna a palon bayan kasan bana so?" Sannan ina ruwanka da ita?" Ya ce "Okay haka zaki ce, to tazo ta bar min gida, karna sake ganin ta, kina kallon idon ta kinsan bata da kunya, kuma ni ban ma yarda da ita ba wallhi, kawai ta bar min gida yanzu". Ya ƙarasa yana nufar kichin ɗin kamar gaske. Har ransa yana so ta bar gidan ko dan ya samu ya warware mata komai. Ita kuwa Nadiya taji daɗin abun da yayi, kuma har ranta Itama tana so ta tafi ɗin amma ba zata so ayi mata haka ba. Da sauri ta tsayar dashi ta ce "Zan mata magana Please ka bari?" Haka ya dawo palo ya zauna, dama borin kunya ne, sai kuma ya tashi ya shiga ɗaki. Wani tinani tayi domin ganin kamar hakan zaifi, bata so ta bari a wulakanta mata baƙuwa ba, musamman ma Haura da yau ne suka fara haduwa. Haura kuwa duk abin da sukeyi tana jinsu. Hakan yasa tana shigowa ita kuma ta gama wanke-wanke sai kawai ta ce "Anty zan tafi, Anty Mera wai Daddy na faɗa yace mudawo tare?". Nadiya ta ce "Kuma tun yanzu ki bari ayi sallar ƙarfe huɗu mana ko?" Ta ce "A'a anty Daddy yana da faɗa, idan kin aihu zan zo suna". Tana faɗa ta fito daga cikin kichin ɗin bayan ta wanke hannu kuma ta na dariya. Nadiya ta ce "Ina zuwa?" Ta shige ɗaki. Habib yayi mata wani irin kallo ya ce "Wawiya mara kamun kai! Wallahi kinji Kunyar rayuwarki, ace kina bin namiji har gida saboda tallan kai, to bari kiji wallhi ni na fi karfin ƙazamar mace irinki stupid kawaii". Ya ƙarasa yana ja da baya ya kawar da kai. Haura ta yi shiru tana sauraronsa. Bata iya cewa komai ba har Nadiya ta fito. Ta miƙa mata baƙar leda tana mata Allah ya kiyaye hanya. Ƙasa ƙar ɓar ledar tayi domin zuciyarta da tayi mata zafi, ji take kamar a mafarki irin kalaman da suka fito daga bakinsa, sannan ga irin kallon da yake mata. Ta ce "Anty kisa uncle ya ajiye ni a gida Please ban san Daddy ya min faɗa idan ya ga na koma gida ni ɗaya?" Nadiya ta ce "Bebb pls aje min ita a gida dan Allah?" Ya kalli Haura kallo irin na tsana ya ce "Ina ne unguwar?" Ta juya ta bar palon ba tare da ta bashi amsa ba. Nadiya ta ce "Please Bebb babu ruwanka da ita dan Allah?" Yana shiga motar ya sameta zaune ta ɗaga kai sama hawaye na zubo mata. Yana shigowa ta dawo da kallonta ga reshe ta ma rasa mai zata ce. Sai da ya bar gidan ta iya yin ƙarfin halin faɗin "Kayi blocking dina, kaƙi zuwa gidan mu, kabar school, baka nemana, yanzu nazo gidan ka kana faɗa min wannan maganar mai kake nufi da ni ne sir?" Ta faɗa da muryar kuka. Da Karfi ya gangara cen gefen titi ya buɗe motar ya fita, itama ta fita ya zagayo yana zuwa ya ɗauke ta da mari ya ƙara mata a ɗaya jumatun, shi kansa yaji yadda marin ya shigeta sosai. Ya ce "Ga abun da yasa nan dan uwarki! Wai ke wacce irin jakar mace ne, ana soyayya dole ne, me nene dalilin da zai sa ki biyo ni har gida, tun ba yau ba na faɗa miki ina da mata, kuma ni ba aure zanyi ba, ko ma aure zanyi sai na rasa wacce zan aura sai ke mara kamun kai mai bin maza har gida". Ya ƙarasa ya na jin kamar ya shaƙeta ma ta mutu kowa ya huta. Babu abun da take yi sai kuka, ta riƙe gurin da ya mareta. Ta ce "Kenan saboda baka son haduwa da ni yasa kabar aiki kuma kayi blocking dina? Sannan saida ka lalata min raruwa shine kake cewar na fita a sabgarka, kenan dama abun da kake so daga gareni kenan kuma ka samu, shine ka guje ni?" Ta karasa tana fashewa da wani kuka mai karfi, wanda ke fita daga cikin zuciyarta. Ya ce "Wallhi ban taɓa sonki ba ko sau ɗaya, kuma ba zan taɓa ba, ko abin da ya faru tsakanin mu tsautsayi ne da sha'awar ki da kuma ke da kike ta chusa min kanki, kuma nayi nadama, daga yau karki ƙara nuna kin sanni, babu ni babu ke har a bada, idan kuma ba haka ba, wallhi zan baki mamaki na faɗa miki". Lokaci ɗaya Haura ta ɗan saki wani irin murmushi mai ciwo a zuciyar wacce irin wannan abun ya taɓa faruwa da ita ne kawai zata ji irinsa. Ta ce "Kalalat min rayu, ka zageni, ka kuma mareni, ka kirani da jaka ƙazama mara kamun kai mai bin Maza, kuma kace na rabu da kai, sai dai kasan me Wallhi ba zan iya rabuwa da kai ba, ko mai zaka ce min ka faɗa zan jure, kuma zan sake faɗa maka cewar ina sonka Sir?" Ta ƙarasa tana fashewa da wani sabon kuka sannan ta faɗa a jikinsa. Sonsa ne ke ƙaruwa duk zagi ɗaya da zai mata, ba zai gane ba ne, ita da rai take sonsa, zata iya haukacewa muddin yayi mata haka. Da karfi ya cireta daga jikinsa ya sake falla mata mari, ya ƙara mata. Ya ce "Ba dai ke mahaukaciya ba, yar isa karuwa ba, ina daidai da ke, Allah sai nayi ajalinki anan, kowa ya huta, kin bata min rayuwa kin sa na aikata abun da ban taɓa yi ba, nayi Wa mata na da iysyena karya, na rabu da aiki na, na kasa samun kwanciyar hankali. Ta sake fashewa da kuka ta ce "Ka kirani da komai ma amma ina sonka kuma ba zan daina sonka ba har abada, kuma dole sai ka aureni wallhi". Habib ya ce "Sai na aureki ko, zan kuwa babi mamaki, sannan ma a ina kika san mata na?" Ya faɗa yana matse mata baki, domin shifa har ga Allah ya tsaneta wanda bai san dalilai ba. Haura ta kwace da kyra ta sake fashewa da kuka. Sai da tayi mai isar ta Kafin ta ce "Saboda ina sonka yasa na nemo number ta, kuma karka manta kai da kanka kafin na yarda na baka kaina kamin alƙawarin zaka aure ni, Sir wallhi ina sonka sosai, zan iya mutuwa idan na rasa ka, raina ne ke barazanar fita idan na rasa ka, ban taɓa son kowa ba sai kai, Sir ka taimake ni ka Aure ni domin kar Na shiga wani hali pls Sir?" Habib ya tofa mata yawi tsaɓar takaici sannan ya shiga motarsa ya ja ya bar ta a duke tana kuka. Ta daɗe a haka kafin ta share hawayen ta tare mai mashin ta faɗa masa inda zai kaita. Tana hanya tana ta kuka tana tunani, zuciyarta tayi mata zafi sai take jin kamar mutuwa zatayi. Suna ƙarasawa ta sauka kenan sai ta kasa tsayuwa da ƙafafunta ta zube a gurin sumammiya. Tana buɗe ido ta ganta a Palo Amera tsaye a kanta. Ta sake fasa wani irin ihu tana kiran sunan Anty? Ta ce "Waiyoo Anty zuciyata na min zafi, please kira min shi yazo kar Na mutu?" Amera ta ce "Waye ne, me ke faruwa ne, ina kika je mai ya faru da ke?" Ta jera mata tambayoyin cikin tashin hankali. Ai da sauri ta ɗaga waya ta kira Adam ta sanar da shi halin dake faruwa. Haura ta ce "Anty zan mutu, zuba min ruwa anan please Anty?" Ta faɗa tana nuna mata zuciyarta. Amera ta ce "Bari Daddy yazo muje asibiti ko?" Haura ta kafe Amera da ido ta ce "Aunty ya yaudare ni, wai she ba sona yake ba, wai baya sona Anty wai bai taɓa sona ba Anty dan Allah ki taimaka min ki kira min shi dan Allah Anty?" Ta karasa tana sakin wani tari sai ga gudan jini ya faɗo ɗan ƙarami. Amera ta fasa uban ihu tana rike ta, lokaci ɗaya ta fara wani irin jijjiga tana juya wuya da cikinta, ana haka Adam ya shigo gidan a rikice. Yana ganin halin da take ciki ya saɓe ta izuwa asibiti. Itama ta biyo bayan su...✍️ S Reza... [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI❣️* *FCWA* *Chapter 14* Har suka isa asibitin ihu take yi ta na faɗin zata mutu, waiyoo ƙirjinta zafi, ya cuceta, ya ce baya sonta. Sannan har lokacin jini na fitowa daga bakinta, gaba ɗaya ta fita a haiyacinta shi kansa Adam a tsorace yake ganin yadda take yi kaman zata mutu. *°Adam* Zaune yake a gaban likitan yana sauraron bayanin da yake masa. Sai da ya gama gaba ɗaya kafin yayi ƙarfin halin faɗin "Ciwon zuciya fa likita? wannan ƙaramar yarinyar ita ce ciwon zuciya zai kama? To a garin yaya?" Yayi tambayar da tsoro da mamaki. Likitan ya ce "Wannan ba ƙaramar yarinya bace allaji, kuma nima tambayar da nake son na maka kenan a matsayin ka na mahaifinta, me nene yake damunta har haka da zai lalata mata rayuwa?" Adam ya ce "Babu abun da ke damunta likita, hasali ma ita bata yin rashin lafiya, bamu taɓa kawota asibiti ba, bana tunanin da gaske ne wannan ciwon da ka faɗa ne yake damunta". "To akwai abun da yake damunta domin tabbas zuciyar ta ta kamu da ciwo wanda daf take da bugawa, yanzu munyi mata allura an saka mata ruwa, zuwa anjima zata farka, mun mata wannan ne domin ta samu hutu da ƙarfin jiki, idan ta farka zaku iya tafiya domin maganin ciwon ƴarku yana tare da ku muddin kuna son rayuwarta, dole wai abu ne tasa a ranta kuma yake ƙoƙarin gagararta shine ya haifar mata da hakan, ina mai sake jaddada maka cewar idan har baku zaunar da ita kun ji damuwarta ba, zaku iya rasa ta". Likitan na gama faɗa ya miƙa masa hannu alamun ya gama dashi. Adam ya fito daga ofis ɗin duk ya na rasa tunanin mai zaiyi. Kenan dai Haura Soyayya ce ta saka mata ciwon zuciya ko dai wani abu ne daban. Lokaci ɗaya wani irin mahaukacin kishi ya ɗarsu a zuciyarsa, sai kawai ya dinga nazarin abun da ya dace yayi a wannan gaɓar, a garin yaya har ya bari Haura ta fara Soyayya har tayi irin wannan nisan a ciki. Shiru ne ya ratsa palon gidan nasu na ɗan daƙiƙa kaɗan yayin da kowa ya shiga tattauanawa da zuciyarsa akan wannan lamarin. Babu abun da ya tsayawa Adam arai kaman ciwon zuciyar da likita ya tabbatar masa da cewar ya kamata kuma a kan s, son ma son wani ba shi ba. Yanzu gashi ita da kanta ta sake tabbatar masu duk abun da ya faru tsakanin ta da shi, kuma ta na faɗa tana kuka akan dan Allah Daddy ya taimaka ya kira mata shi, gashi ya mayar musu da yarinya kamar wacce ta samu taɓuwa, yau ɗaya duk ta rame sai kuka. Wani ƙatoton abu ne ya tsayawa Adam a wuya ya kasa tafiya kuma ya kasa dawo da shi. Idan ya kalli Haura sai ya rasa mai zai ce mata. Amera ta ce "Yanzu fa dole ne zaka tashi keje gurin wannan yaron kaji gaskiyar abun da ya faru, idan ma ta kama hakuri zaka bashi to sai ka bashi haƙuri domin dai kana ganin halin da take ciki" Amera ta katse shurun da palon yayi da wannan maganar. Adam ya mata wani kallo ya ce "Kina ji ta ce harda dukanta yayi, harda barin aiki dauk dan baya son ganinta, to ana soyayya dole ne, wani irin zubar da mutunci ne wannan ace wai ni uban yarinya naje ina bawa saurayi haƙuri yazo ya auri ƴata?" Amera ta ce "To ai dole ce tasa, wallahi kamawa tayi, idan ma har fiye da Haƙuri ne ai za'ayi, kaga idan ma kai ba zaka iya zuwa ba ni zan iya takawa har gidan na bashi hakuri, ai risinawa wasa ba gajiyawa bane,meye a cikin bada hakuri dai kawai Allah natuba!. Haura da tun ɗazu take sauraronsu tayi shiru a palon ta na ta tunanin abubuwan da suka faru tsakanin ta da shi. Lokacin da ta fara ganinsa, lokacin da tazo shiga class yayi mata tsawa, lokacin da suka jero tare da shi kawai ta na kallonsa, lokacin da ta sameshi a ofis na farko, lokacin da ya fara shafa jikinta, lokacin da take masa murmushi idan ya shigo class, lokacin da take ware masa ƙafafuwanta, lokacin da suka rage a school daga shi sai ita har komai ya kusa faruwa har ta suma ya gudu, lokacin da suke waya tana masa shagwaɓa, lokacin da yazo gidan su, lokacin da ya zo ya ɗauketa ya kaita wani gida, lokacin da ya rabata da budurcinta, lokacin da taje gidansa yau da abubuwan da suka faru. Hannu tasa ta dafe ƙirjinta hawaye na zubo mata, ba zata iya yin rayuwa babu Sir ba, Wallhi mutuwa zatayi, ƙirjinta zafi ga cikin jikinta da gaba ɗaya shima zafi yake mata. Adam ya ƙaraso gurin da haura take ya dafa ta ya ce "Haura kiyi hakuri ki manta da shi, Wallhi wannan yaron ko auranki yayi wahala zaki sha, sannan ni zan aura miki wand..." Da sauri Amera ta ce "Wai honey wannan wacce irin magama ce fisabillahi!? Kana ganin halin da yarinya ke ciki amma kai ba damuwarka ta samu lafiya ba, ita ga wanda take so, kuma taji ta gani shi take so, kawai hakuri da zaka je ka bayar ka kasa yanzu kana mata zancen wani, yaya kake so tayi da ranta dan Allah?" Ta karasa har tana miƙewa tsaye. Adam ya ce "Wallhi Amera kimin shiru, na rsante da Allah ranki zaiyi mugun ɓaci muddin baki min shiru ba, na san duk take taken ki, kuma wannan abun ba shi zai hana faruwar komai ba idan Allah ya so" ya faɗa da mugun ɓacin rai! Amera ta ce "Take taken na na me? To mai zan taka, ai ko yanzu wallahi ka..." Maganar da Adam ɗin yayi ce yasa ta tsaya da maganar tata. Wani irin shiru ya sake ratsa palon yayi da gaba ɗaya palon kowa ya ɗauke wuta, daga kan Haura zuwa Adam da ita Amera ɗin. Saida Adam gama tattara dukkanin ƙwarin gwuiwar sa kafin ya ce "Haura kina sona zaki aure ni ki zauna tare damu har abada, domin ki manta da wannan yaron?" Sai da ya faɗi maganar kuma kunya da tsoron amsar da zata bashi ya cika masa kirji. Kallon kallo aka fara yi a palon yayin da haura ta tsayar da kukan nata, ta kafe Daddy da ita, Amera ma sai kallon Adam takeyi domin abun ya bata mamaki. Kawai sai fashe da wani sabon kuka ta kasa magana. Adam da yake jin ina ma shima zai iya kukan ta ce "Baya sonki ba zauna dake sa mutunci ba, ba zai..." Da sauri ta ce "Ni ina sonsa a haka Daddy, Please Daddy ka kira min shi, wallhi bana son kowa sai shi. Adam ya ce "Harda ni ba kya so?" Haura ta ce "Eh Daddy Wallhi shi nake so" Adam yaji kaman ta kira sunan uwarsa da ubansa ta zaga. Amera da an gama cika ta da mamaki da irin wannan kafcen kamar wani shirin Film. Gaba ɗaya ma ta kasa magana domin har ga Allah Adam ya gama shayar da ita mamakin da ya ce, a gabanta babu ko kunyar idonta. Adam da ransa ya ɓaci cikin tsawa ya ce "Kaman yadda na faɗa miki cewar ba zan je gurin shi yaron domin na bashi haƙuri ba, Kuma aure tsakanina dake dole sai an daura, zanyi haka ne domin na tseratar dake daga sharrinsa. Sai a lokacin Amera ta ce "Wallhi girma dai ya faɗi, kuma anji kunya, yarinyar ta ce bata sonka amma tsabar rashin sanin ciwon kai har kana faɗin zaka aureta a haka, Kenan Auran dole kenan, saboda bata da iyaye, saboda ita ba yar gata ba ce ko, saboda ba kaina ka haifeta ba ko, yarinya ta nuna ga abun da take so har ranta amma zaka mata isa da nuna cewar kaina ka isa da ita, to Wallhi babu wanda ya isa yayi mata auren dole, ai ba kai ɗaya ne kake da iko da ita ba" Tana rufe baki ya ɗauke ta da mari, ya ɗora da faɗin "Nafi ƙarfin ki tsaya kina ɗaga min murya har haka, ni mijinki ne ba ɗan ki ba, dake da haura duk kuna ƙarƙashin iko nane, kuma kaman yadda na faɗa na sake faɗa gobe za'a ɗaura auran Haura kuma dani, idan kuma kin isa ki hana?" Ya ƙarasa yana sake nuna ta da hannu. Amera da marin ya shigeta da kyau, ta dafe gurin idanunta sun cika da ruwan hawaye, ta ɗago tana kallonsa. Ta ce "Adam ni ka mara?" Tayi maganar hawayen na gangaro mata. Ya ce "An mareki, ko zaki rama ne?" Ya tambaya yana kafe ta da ido. Amera tayi shiru amma ta zuba masa ido, shima idonsa na cikin nasa, shi kansa idonsa kama wanda yayi kukan sun haɗu sunyi jaa sosai, fuskarsa har wani karkarwar ɓacin rai take yi. Sun kai minti ɗaya a haka ziciyoyinsu na tafarfasa. Juyawa tayi ta koma ɗaki. Shi ma ya dawo da kallonsa ga haura ya ce "Kinji duk abun da na ce ko? Gobe za'a ɗaura miki aure, ina so ki manta da wancen yaron ba sonki yake ba" yana gama faɗa ya bar gidan gaba ɗaya. Number Najib ya nemo ya kira yana tanbayarsa ina yake. Kasancewar yamma tayi lokacin ya dawo gida yasa ya sheda masa cewar ya na gida. Ai kuwa ya ɗauki mota ya nufi gidan. Yana hanya yana jin har lokacin ransa a ɓace yake, sosai Amera ta ɓata masa rai, ita kuma Haura ta bashi mamaki, kaman shi zata ce bata so, ita bata san cewar tun ba yau ya ke sonta ba, ita bata san cewar son da yake mata tafi wanda ita take wa yaron ba. Ko sallama babu ya shiga palon ya samu suna zaune suna kallo. Khadijah ta ce "Yayi ina uni?" Ya amsa da lafiya ya kalli Najib ya ce "Ina so zaga zamarwa Haura wakili gobe za'a ɗaura mata Aure Please" Najib ya ce "To kai fa ba zaka iya tsaya mata ba ne?" Ya ce "Haba mana Najib, kaman baka san komai ba, nine zan aureta, kuma a gobe" na faɗa maka ne domin ka zauna da shiri, gobe juma'a. Khadijah ta ce "Ko dai wannan mutanen na garin nasu sun sake dawowa ne, sun zo sun sake asirce mana kai ko yaya?" Khadijah ta faɗa a tsorace. Adam ya ce "Idan kina sake sa baki a wannan maganar sai na tattakaki mara kunya kawai" Adam ya faɗa kamar ya kai mata mari. Najib ya ce "Ikon Allah wai Adam lafiyarka kuwa, me ke faruwa ne, karfa kazo ka aikata aikin da ka sani, ya kamata ka faɗa min abun dake faruwa?" Cike da faɗa ya ce "Kamar yaya na faɗa maka abun da ke faruwa, ina ce dama na faɗa maka cewar zan aureta, ko yau ne kawai kasan da maganar ne, please bana son wani dogon tambaya idan zaka zame mata wakili na sani idan ba zaka zama ba to na samu wani. Ya na rufe baki Najib ya ce "Ka samu wani, amma ni kam babu ruwana wallhi" Khadijah ta gyada kai alamar amincewa da maganar mai gidan nata. Adam yayi musu kallo ɗaya ta girgiza kai ya bar gidan. Bai tsaya a ko ina ba sai gurin wannan malamin da ya taɓa zuwa gunsa a wancen lokacin domin ya daura musu aure. Koda yaje ya samu malamin baya nan. Haka ya kamo hanyar gida yana tabbatarwa kansa cewar zai dawo gobe, ai dama gobe juma'a. Ya na son Haura sosai, kuma wannan ita ce hanyar da zai bi domin ya sameta, yasan bayan auran zata fara sonsa. Ya na zuwa kofar gidan yaga get a buɗe, da sauri ya shiga da motar ya dawo ya rufe. Yaga ƙofar palo ma a buɗe. Gabansa ne ya faɗi ya karasa yana jin wani irin tsoron da bai san na meye ba. Ɗakin Amera ya leƙa yaga bata nan, ga drowan kayanta duk a buɗe, tsaki yaja aransa yana jin taje duk inda ta ga dama. Zama yayi apalo sai kuma ta tashi ya nufi dakin haura, nan ma ya ganshi a buɗe itama ga drowan kayan nata nan a buɗe. Nan ya fara kiran sunanta, jin shiru yasa ransa ya ɓaci, kenan dai Amera ce ta ɗauketa suka tafi gida. Ai kuwa yanzu zaije ya dawo da ita Haura ɗin, ita kuma idan taga dama ta shekara a cen. Saida aka yi sallah kafin ya nufin gidan su Amera ɗin, yana zuwa kuwa sai ga Abba zai shiga, suka tsaya suka gaisa. Abba ya ce "Lafiya dai ko Adamu?" Adam ya ce "Lafiya lau, dama nazo ne gurin Amera?" Abba ya ce "Au dama tana ciki ne?" Ya tambaya kasancewar sai yanzu zai shiga gidan. Adam ya ce "Eh suna ciki" Minti biyar ya kwashe a gurin sai gata ta fito. Ta na zuwa "Je ki fito min da ita yanzu nan?" Ya faɗa babu wasa. Amera da ya bata mamaki, ita a tunaninta biko yazo. Ta masa kallo ɗaya ta kawar da kai. Ya sake faɗin "Ba magana nake miki ba ne, idan ke kin dawo gidan ku saboda kin isa, to ita a wani dalili zaki ɗaukota Ku zo tare?" Ya sake faɗa a fusace. Amera da sai yanzu ta fara gane abun da yake nufi, sai kuma ta fara tunanin kenan Haura bata gidan ne ko yaya. Adam ya ce "Amera zan ɓata niki rai fa Wallhi, kije ki kira min Haura mu tafi?" Ya sake faɗa ganin tayi shiru. Ita kuwa ranta ne ke baci idan ya faɗa haka. Ta ce "Kaje ka naimi inda yarinya take, domin ni ban tafi da ita ba...📝 S Reza... [09/07 à 14:07] S Reza: A BAR WA RAI ❣️ Amera na faɗa ta shige gida ta bar shi tsaya. Adam ya cika da mamaki, to me take nufi, basa tare da Haura ko yaya! Kaman ya shiga cikin gidan da kansa amma ya fasa. Ya na tsaye sai ga wani yaro yazo zai wuce, ya tsayar da shi ya ce "Shiga gidan nan ka ce Adam ya ce wai Haura ta zo" ya faɗa ya na tura yaron. A fili ya ke faɗin "Wallhi duk abun da Amera take nema dani zata samu, ba dai gidansu tazo ba, zata nuna masa cewar ta na da gida ba, ai kuwa zata cigaba da zaman gidan nasu domin dai shi ba zai taɓa zuwa da nufin dawo da ita ba. Ya na tsaye sai ga Salim da Salma sun fito daga cikin gidan da gudu suna kiran sa. Bai ko amsa ba ya ce "Salim je ka kira Anty Aisha mu tafi gida" (Haka yaran duke ce mata ) Kafin ma Salim yayi magana dan aiken nasa ya fito ya ce wai ance babu Haura a gidan. Adam ya ce "Tom na gode tafi abunka. Salim ya ce "Daddy Anty Aisha bata gidan tana gida inji Mommy" Adam ya ce "Mommy da wa suka zo gidan?" Salim ya ce "Ita ɗaya ce, kuma tana ta kuka. Adam yayi jim kaɗan ya ce "Anya kuwa Salim ka tabbatar Anty Aisha bata gidan?" Ya ce "Eh Daddy bata zo ba. Adam ya ce "No shiga ka sake dubawa" Salim ya shiga gidan da gudu, ita kuwa Salma dama tuni ta nufi gurin motar ta buɗe ta shiga. Adam dai na tsaye sai ga Salim rike da jakar makarantar su ya ce "Daddy ba ta nan, kuma Mommy ta ce ka tafi damu gida"  Adam da abun ya fara bashi tsoro ya nufi mota da sauri ya kunna ta, Salim da bai shiga ba ya zagayo zai bude amma Adam ya ce "No ku koma gida gobe zaku dawo da Mommy". Ya na jin zasu fara rigima ya sauƙo da Salma ya ja motar sa ya bar unguwar ransa a haɗe. Koda ya koma gidan bai ganta ba. Haka ya shiga duba ko ina. Karshe ya kira number ta amma a kashe, ya kira number Amera itama tun ta na shiga har ta daina. Ya shiga tura mata sako akan Wallhi duk inda ta kai Haura tazo ta fito da ita. Haka Adam har bayan sallar Isha. Karshe gidan su Maryam kawarta ya je amma nan ma tace yau gaba ɗaya ma basu yi waya ba. Wasa-wasa har karfe goma na dare babu Haura babu dalilinta. Haka ya sake komawa gidan su Amera wannan karan da kansa ya shiga har cikin gidan. Lokacin har Umma tayi barci, Abba dai yana Palo yana kallo, Amera ma tana ɗaki amma batayi barci ba. Shi kansa Abba yayi mamakin ganin sa. Bayan sun gaisa Abba ya ce "Ko dai matsala kuka samu ne da ita Adamu, ta ce wai kasan da zuwanta amma kuma yanzu naga ka dawo, lafiya dai ko?" Adam ya ce "Amma Abba babu komai, dama ita ɗaya yarinyar ce nazo ɗauka, ba Amera ɗin ba". Abba ya ce "Wacce yarinya, Salma kenan?" Adam ya ce "A'a Abba babbar dai wacce muke ruƙo, tare suka zo nan ɗin". Ya karasa a ɗan rikice. Abba ya ce "Ikon Allah, amma ai ni ban ganta anan ba, daga ita sai yaran na gani, kuma yaran ma ai ba yau suka zoba" Adam ya ce "Ka kira Amera ɗin Abba Allah suna tare" ya faɗa kamar a fusace. Abba da ya cika da mamaki ya ce "To ai yanzu ne sunyi barci, to ka bari zuwa safiya mana ko?" Adam ya ce "Am dama saboda a kwai..." Abba ya ce "To bari na kira ita Amera ɗin. Zama yayi apalon yana jira su fito. Ji yake kamar tana fitowa ya haɗa su duk su biyun ya musu shegen duka. Jin an buɗe labulen palon yasa ya mike tsaye. Kallon-kallon a ka fara yi. Adam ya ce "Shiga ki fito min da ita?" Ya faɗa kansa tsaye. Amera da tun da ya tafi take ta tunanin maganar sa, ita kanta abun ya bata mamaki jin wai bata nan, yanzu haka wani mamakin ne ya sake kamata jin wai har yanzu bai ganta ba, ita dai tasan ta tafi ta bar Haura a gidan, kuma kan kujera ta wuce ta. Ya sake faɗin "Nan shine gidan ku, kina da ikon da zaki zo ki zauna har tsawon lokacin da kike so, amma banda Haura, ita nine uwa da ubanta, zuwa wani lokaci kuma mijinta, dan haka tun kafin ta kaimu izuwa wani mataki ki fito da ita" Amera ta ce "Gara ma da ka dawo, bari na fito maka da yaranka su tafi gidan nasu uban kaman yadda nima na dawo gidan ubana, domin nan ba gidan ubansu bane" ta na faɗa ta Kama Hanyar zata koma. Taku ɗaya yay ya kamota ya ce "Wai Amera me kike nufi da nine, ya ina miki magana kina kawo min wani shirme banza da hofi?" Amera ta ce "Karka sake taɓa ni, nan gidan ubana nane ba gidan ka ba, kuma maganar da kake yi naga bata shafeni bane shi yasa ban saka baki ba, ita Haura ɗin nan gidan ubanta ne da zanzo da ita, ina yanzu kace kaine uwa da ubanta, to ai sai kaje ka nemeta a gidan naka". Ya ce "Me kike nufi?" Ta ce "Abun da kaji shi nake nufi". Ransa ya ƙara ɓaci ya ɗan busar da iska da baki ya ce "Nasan duk inda Haura zata je kece zaki saka ta, dan haka ko bata gidan nan kinsa inda ta tafi, saboda haka ina kika aikata, domin babu inda ta sani?". Har ta buɗe baki zata yi magana Abba da Umma suka shigo palon domin muryoyinsu ne ya tada Umma, shi kuwa Abba tun farkon maganar su yake sauraronsu, yana tsaye Umma ta zo, ganin abun nasu na son ya ɓaci ne yasa suka shiga palon. Abba ya zaunar dasu ya tambayi Adam abun da ya faru. Nan take ya kwashe komai ya faɗa masa harda maganar auran Haura ɗin da zai yi da kuma ɗaukota da Amera ɗin tayi a cewar sa. Dukda Abba ya cika da mamaki amma ya tambayi Amera abun da ya faru. Itama ta faɗi daidai da abin da ya faɗa amma ta ce ita ko magana ma batayi wa Haura ba lokacin da zata fito. Adam ya ce "Wallhi Abba karya take yi, saboda kishi ne yasa ta boyeta". Amera ta ce "Kishin wa kai, Allah ya tsare ni Wallhi, daga kai har ita baku isheni kallo ba bare nayi kishi". Umma ta daka mata tsawa ta ce "Idan kin san ke ce kika boye masa yarinya ki faɗa masa inda take kafin ranki ya ɓaci?" Umma ta faɗa cike da takaici. Amera ta fashe da kuka ta ce ita Wallhi bata san inda take ba. Shi kansa Adam din izuwa yanzu ya tabbatar da cewar ba ita bace ta boye ta, amma to ina zata je. An daɗe ana abu ɗaya kafin Adam ya hakura zai tafi, Abba ya ce Amera ta tashi ta bishi, Amera ta ce babu inda zata je, shi kansa Adam ya na fita yaja motarsa ya bar unguwar. Ya koma gida ya cigaba da zaman jiran amma har sha biyu, har karfe ɗaya karshe dai dole ya hakura. Washegari ma babu Haura babu labarin ta, izuwa lokacin kam ya tabbatar da a kwai matsala, ko dai gidan saurayin ne ta tafi, tuno da hakan yasa jikinsa yayi sanyi, sai kishi ke danunsa, gaba ɗaya gidan yayi masa wani shiru babu kowa. *°Habib* Lokacin da ya koma gida ya samu Nadiya a Palo har ta sake wanka. Ya ce "Wai a ina kika san wannan yarinyar?" Yayi tambayar kaman a fusace. Gaban Nadiya ne ya faɗi a ranta tana jin tsoron ko dai ta masa kyau ne, domin tun da suka fita ta kasa samun natsuwa. Ta ce "Ka kaita gidan ne?" Ta faɗi haka domin taji ko ya ga gidansu. Ya ce "Bani wayarki?" Ya faɗa har yana jan tsaki. Wayar ta miƙa masa ya shiga Whasop, ya ga number Haura a farko an rubuta Aisha. Goge numbar yayi ya ce "Bana son alaƙarki da wannan yarinyar domin ban yarda da ita ba, kuma ba mutuniyar kirki bace". Ta ce "Wai me ya faru ne, duk ka tsorata ni, ka santa ne da har ka gane ba mutuniyar kirki ba ce?" Habib ya ja tsaki wanda yanzu ya zama masa farulla magana ɗaya biyu sai ya yi. Ya ce "Ana ruwa yaci makadi kina ganga ta jiƙe, wani abokina ne ya ganni da ita shine yake faɗa min wai ƴar isa ce, tana bin maza, shima ya taɓa kamata da abokinsa, kuma ta zubar da ciki har sau biyu". Nadiya ta dafe girji ta ce "Ita Aisha ɗin, wannan yarinyar da gaba ɗaya ma nawa take?" Habib ya ce "Haka tace miki sunan ta Aisha? To karya ne sunanta Haura". Nadiya ta ce "Haura kuma? Wani irin suna ne wannan?" Habib yace "Oho dai, idan zaki yi hankali da ita kiyi ni dai na faɗa miki gaskiya bana sonki da ita kwata-kwata". Haka ya shiga ɗaki ya bar Nadiya da tashin hankali, nan take ta goge number Haura tayi blocking din ta a ko ina. Sosai komai ke dawo mata tun farkon alaƙar ta da ita, sai take ganin wata killa ma Habib ɗin ne yayi mata kyau shine ta biyo ta wannan sigar domin ta haɗu da shi. Haka ta uni gaba ɗaya lamarin ya tsaya mata a rai.  Habib kuwa wanka yayi ya sake kaya ya ɗauko laptop ɗin sa ya shiga duba inda ya tura neman aiki, ya tabbatar da komai daidai. Sai kuma ya faɗa tunanin lamarin Haura, sai yanzu yake kara yin da ya sanin barin aikin sa, ai ko a haka ba zai yarda ya sake bari ko magana ya haɗa su ba. Lokaci ɗaya yayi shiru yana tunanin irin kukan da yaga tana yi, ta na faɗin wai zata mutu, zuciyarta na mata zafi, ko kaɗan bai ji tausayinta ba, har ma ji yake ina ma ta mutu ɗin da yafi kowa murna. Daga yau zai fara tuba akan abun da yayi in sha Allahu. Haka suka uni a gidan suna ta mayar da lamarin Haura. Misalin ƙarfe takwas suna zaune suna cin abinci suka ji ana buga ƙofar palon nasu, Nadiya ta miƙe ta je ta buɗe tana tambayar waye?" Tsayawa tayi chak kamar wacce ta suma a tsaye tana kallon Haura janye da ƙaramin a kwati. Daga gurin Habib ke tambayar waye, amma Nadiya ta kasa magana, gefe ɗaya kuma ga wani irin rama da ya baiyana a jikin Haura ɗin. *°Haura* Ta yi mugun mamaki jin abun da Adam ke faɗa wai ya na sonta, kuma wai da aure, duk irin zafin da ƙirjinta ke mata a lokacin sai da taji komai ya tsaya mata. Daga kuma lokacin ta fara masa kallon wanda baya son ganin cigaban rayuwarta, shi bai san so bane, shi bai san Habib kawai take jin zata iya rayuwa da shi kawai bane, bai san bada zuciya kawai take son Sir ba sai da rai!. Lokacin da taji maganar da Amera take faɗa na cewar ko saboda ba shi ya haifeta ba, ko saboda yaga bata da Kowa, wannan kalmar ce tasa ta shiga tunanin to wai ita ɗin ma wacece tun farko, mai ya faru da ita, gaba ɗaya komai na rayuwarta na baya ta goge shi tun lokacin da ta karbi musulunci, amma a yau sai ta fara tariyo komai, ciki kuwa harda garinsu na Garuk da mutanen ciki da irin rayuwar da suke yi, sosai ta tuno da irin gatan da take da shi a garin, domin dama ko a baya Ɓultuwa ce kawai matsalar su ita da Aminta, da kuma laifin da suka yi, idan bata manta sarki da yazo gidan Adam an wanke ta daga laifin, kuma Ɓultuwa ta mutu. Ta na cikin haka taga Amera ta wuce da jaka, hakan yasa ta miƙe tsaye ta shiga ɗakinta ta jawo akwatin ta, zuciyar ta kawai ta raya mata cewar gidan Sir zata je, akan dai Daddy ya aureta gara taje gidan Sir ta zauna, idan kuma yaki ta faɗa wa matarsa gaskiyar abun dake tsakanin ta da shi to ita da kanta zata faɗa mata. Da wannan tunanin ta fita daga gidan Adam ta iso gidan Habib. Babu ko tsoro ta buɗe ƙaramin get ta shigo har cikin harabar gidan, sannan ta tsaya ta fara buga musu palo. Murmushin dole Haura ta aro ta na sakarwa Nadiya ganin ta tsaya tana kallonta. Jin muryarsa yasa ta jawo jakar zata shiga shi kuma lokacin ya ƙaraso gurin ya na kallonta. Gabansa ne ya bada wani rass zuciyarsa tayi tsalle ta tafi shawagi na wasu lokuta. Ganin zata shigo yasa Nadiya faɗin "Ke ina zaki shiga ne munafuka maƙaryaciya?" Ta faɗa ta na tare mata hanya. Haura ta dago ta kalleta jin abun da tace, to ko dai ya faɗa mata abun dake faruwa ne, to idan ya faɗa mai yace mata. Ta na cikin wannan tunanin taji Nadiya ta sake faɗin "Munafuka ki ka ce min sunanki Aisha ashe ƙarya kike yi Haura ne sunanki?" Ta sake faɗa ta na kuma tare hanyar. Kafin Haura ta yi magana Habib da har ya fara zufa domin shi ganinta da jaka ne ma ya ƙara rikita shi. Ya ce "To wai ma gidan uban wa zaki je ne harda jaka, kuma ba yanzu kika bar gidan nan ba da zaki dawo? Bebb kin ga abun da nake faɗa miki ko, Wallhi wannan yarinyar munafuka ce" ya ƙarasa ya na kallon cikin idon Haura da ke bashi tsoro a duk lokacin da ta ɗora masa su. Haura da har lokacin zuciyar ta zafi take mata, gashi babu wani ƙwari jikinta, hasali ma harda jiri take ji sosai. Ta ce...📝 S Reza [09/07 à 14:07] S Reza: A BAR WA RAI ❣️ FCWA Chapter 16 "Sir ka faɗa mata abun dake tsakanin mu ne Da kai ko? Ta yarda zaka aureni?" Haura ta faɗa hawaye na zubowa daga idanunta, sannan yanayin muryar da tayi maganar kana ji kasan bata jin dadi, ji take inama ya ce mata eh Nadiya ta yarda zai aureta. Kafin ma Habib ya magantu Nadiya ta ce "Abun da ke tsakanin ku! Dama kin san shi ne?" Nadiya ta faɗa cikin wata murya mai sanyi domin abun da take ji game da haura ba zai faɗu ba. Habib yayi saurin faɗin "Bebb Kinga abun da nake faɗa miki ko, kin dai gani da idonki ko, to wallahi babu ruwana duk abinda ya faru, ko ɗazu da na tafi Kaita gida idan kinji irin maganganun da take yi babu daɗin faɗa, kuma gashi a gabanki ta na sake faɗa, ƴar isa ce fa sosai ta bugawa a jarida ina faɗa miki Bebb". Habib ya faɗa kaman a rikice wanda da Nadiya ta lura da kyau zata gane ya fita daga haiyacinsa. Nadiya ta kalleshi ta kalli Haura. Sai kuma ta ce "Da gaske sunanki Haura?" Ta tambaya ta na kallon Haura ɗin da ta rame mata daga ɗazu zuwa yanzu. Haura ta ɗaga mata kai, sannan ta ɗora da faɗin "Ya faɗa miki komai ko?" Nadiya ta ce "Kin bani mamaki Aisha au sorry Haura, ashe kin shiga jikina ne saboda mummunan manufa a kan mijina ko, to in sha Allahu mijina yafi karfin ki, kuma ki bar min gida yanzu kafin nasa yayi miki shegen duka anan gurin, bana son ganinki na tsaneki Allah ya isa tsakanina da ke". Ta ƙarasa ta na zubar da hawaye domin da gaske ta tsorata da haura, yarinyar ta fitar mata a kai, ta na son mijinta, duk wani abu da zai sa wata mace ta nuna cewar tana son mijinta to tabbas ko wacece zata yi tsayuwar daka sai taga wannan matar ta hakura. Haura da izuwa lokacin ji take kamar ta samu guri ta zauna tsabar ciwon da jikinta ke mata, ga gajiya da zazzaɓi duk sun haɗar mata, maganar ma dole ce tasa yake yi, ga wani irin maradin son ganinsa a kusa da Sir ɗin ta da ya cika ta, ji take da ya zo ya dafa ta ya lallashinta zata ji duk wannan ciwon ya tafi. Ita yanzu abun na da ya ƙara bata tsoro shi ne, ya faɗa mata ne ko dai yaya. Ta buɗe baki a hankali ta ce "Anty dan Allah kiyi hakuri ba laifina ba ne, kuma..." Da sauri Habib ya daga mata tsawar da sai da ta tsayar da sauran maganar bakinta. Ya turo kai ya fito daga cikin palon ya ɗauketa da mari mai karfi wanda sai da ta kifa a gurin. Ita kanta Nadiya ta tsorata da ganin irin wannan marin da ko Namiji a kaiwa dole ya san ammaresa bare kuma mace, macen ma wannan yarinyar, sannan yanayin ta ya nuna kamar bata da lafiya, take taji wani iri a ranta, lokaci ɗaya cikinta ya murɗa mata da karfi. Habib bai tsaya anan ba ya ɗakota ya shiga zare mata ido ya na faɗa mata maganganun da sam bata jin mai yake cewa. Batayi tunanin zai iya marinta a irin halin da take ciki ba, ko dai bai kula da yanayinta ba be, shi yasa marin yayi mugun shigarta da kyau. Jikinta ne gaba ɗaya ya ɗauki zafin marin wanda lokaci ɗaya ciwon nata ya sake tashi. Ta na jin lokacin da ya ɗagota, amma bata san mai yake cewa, jinta da sauraronta ne yayi ɓatan dabo na wasu yan daƙiƙu. Ji tayi ya sake ta sai kuwa gata a ƙasa shafar kamar kayan wanki, hakan yasa ta faɗi ta gefe kanta ya fashe jini ya fara zuba. Nadiya na ganin haka ta koma ciki tana riƙe cikinta ta ya sake murɗa mata, sai kawai ta fashe da kuka mai ƙarfi tana dafe cikin nata. Habib ganin ta zube ne yasa ransa ya ƙara ɓaci. Sai kawai ya kama hannunta da hannu ɗaya, ya riƙe a kwatin kayanta da hannu ɗaya ya fara janta. Sai da ya kaita har ƙofar gidan nasa kafin ya watsar da ita a gurin. Kasancewar dare ne yasa ya zagayo ta kanta ya sake mata gargadi da kuma faɗa mata wallahi idan ta ƙara dawowa gidan sa sai ya ɓatar da ita. Ya na gamawa ya rufe get ɗin gidan ya koma ciki ya samu Nadiya na ta murƙususun ciwon mara. Tun lokacin da ya fara janta a ƙasa ta dawo zahirinta amma ta kasa magana, sosai ko ina na jikinta ke mata ciwo. Koda ya jefar da ita duk tana jin abun da yake faɗa, har ya koma ciki ya rufo get ɗin. Ta kai minti biyar a haka kafin ta iya tashi zaune ta na kallon ƙofar gidan. Wani irin sanyi ne ya fara ratsata, ga kuma gefen kanta hagu da dama da ta bugu amma ɗaya bai fashe ba, gurin dai yana mata zafi sosai, dayan gurin kuma jini na fita kaɗan-kaɗan. So take ta tashi amma ta kasa, hakan yasa kawai ta fashe da kukan da babu sauti domin shi kansa kukan babu ƙarfin yin sa. Kaiwa sunan Aminta take kira a cikin kukan ta na cewa tazo ta taimaketa zata mutu tazo ta tafi da ita. Tayi kuka sosai kafin kuma tayi wani abu da hannu yadda take yi a baya kafin a ƙwace mata tsafin ta. Sai dai duk yadda tayi abun yaƙi yin aiki, haka ta dinga gwada abubuwan da ta iya amma kowanne baya aiki, dama tunda aka rabata da komai bata taɓa gwada yin wani na tsafi ba sai yanzu da take cikin wannan masifar kuma wai akan son wani. Lokaci ɗaya ta tuno lokacin da Sarkin garin Garuk yake tabbatar mata da cewar muddin zata zauna anan kuma zata amshi addinin musulunci to dole sai an karya mata duk wani asiri da tsafin da yake jikinta, kuma a lokacin batayi tunani sau biyu ba tace ta yarda. Kuma take aka karya komai da komai ciki kuwa harda rage wa nesa kusa da suke yi, da kuma warkar da ciwo nan take harda tsayar da jini da dai duk wani abu da ya shafi tsafi da suke yi. Sosai take kuka tana jin ta kamar wata mara gata ƙaskantatciya a cikin mutane, mara galibu. Sai kawai ta sake kwantawa a gurin ta na addu'ar ina ma ta mutu kawai anan sai taje ta haɗu da Aminta. Cikin kukan nata ta tuno da daddynta da kuma anty Amera. Idan ta tuna da maganar Daddy na cewar zai aureta sai ta ji cewar ba zata iya ba, ai gara ma ta mutu batayi aure ba akan ta auri Daddy, ita Sir take so, kuma har yanzu bata ji ko sau ɗaya son da take masa ya ragu, idan akansa ne sai dai ya kashe ta, amma tabbas sai ta rayu da shi kuma dole ya cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata. Ta kai minti ashirin a gurin kafin ta iya miƙewa tsaye kamar ƴar maye, ta buɗe akwatin kayan nata ta ciro wani ɗankwali ta ɗaure gurin ciwon nata, sannan ta ciro wayarta da wata ƙaranar jaka. Ta zuba kuɗin ciki a jakar sannan ta ɗauki wata rigar sanyi ta saka. Ta na ganawa ta kalli gidan Habib na tsawon minti ɗaya kafin ta fara barin gurin a hankali cike da karfin hali. Ta na tafiya ta na rawar ɗari har ta bar unguwar. Bata iso bakin titi ba sai kusan sha biyu na dare. Anan ta tsaya a bakin titi duk motar da ta gani sai ta tare amma babu wanda ya tsaya. Har ta hakura sai ga wata farar mota kamar ma sabuwa. Tana ɗaga mata hannu ta tsaya. Ta ƙarasa gurin mai motar ta ce masa Katsina zata je. Ya kalleta sama da ƙasa kafin ya ce "Nima cen zanje, amma zan kwana a hotel zuwa biyar na safe zan tafi, zaki iya jira na?" Ya faɗa yana kallon yanayinta, ba dan ya na son kuɗi ba shi ina ma zai tsaya neman fasinja. Ta ce "Dan Allah kayi hakuri kawai mutafi zan biya ka ko nawa kake so". Ya ce "Hanyar ce ina tsoron bi kuma motar ba tawa bace" ta ce dan Allah ka taimaka min bani da lafiya ne Please" ta faɗa da ƙyar, wanda mutumin shi kansa ya lura da bata da lafiya ne. mutumin ya ɗan yi jim sai ya ce "Zaki biya dubu sha biyar?" Haura ta ce "Zan baka dubu ashirin". Ai da sauri ya buɗe mata gidan baya ta shiga. Suna fara tafiya ta ce "Please kafin mufita anan ka sama min maganin zazzaɓi da abinci da ruwa kaji?" Ta faɗa har lokacin rawar sanyi ta ke yi, ga yunwa da take ji. Mutumin ya ce "ina kuɗin?" Kafin ma ya rufe baki ta miƙo masa dubu biyar. Ya amsa suka ci-gaba da tafiya. Saida suka iso wani guri kafin ya tsaya ya saya mata komai da tace ya kawo mata, ai kuwa take ta ɗan ci abincin kaɗan, ta sha maganin ta kwanta ba tare da ta ce masa komai ba ta na jin har lokacin sanyin na ratsa ta, haƙwaranta sai haɗuwa sukeyi. Mutumin dai yana tuƙi ya na juyowa ya na kallonta, har ga Allah ta fara bashi tsoro, gashi har yanzu bai ga asalin fuskantar ba, gashin kanta ya rufe mata fuska, sannan ga rigar jikinta itama mai gashi ce. Haura kuwa kasa ma yin barcin tayi sai tunanin yadda yan garinsu zasu tarɓeta take yi, inama Aminta na raye, ina ma Ɓultuwa na raye, inama babanta na raye, yanzu idan ma taje garin sai dai taje gidan dangin babanta, ko na mamanta, sosai take tariro komai na garin da al'ummar cikin garin. Wata zuciyar na cewa kar taje wata zuciyar na cewa ta haka ne kawai zata iya mallakar Sir dinta, dole ta cikawa ranta burinsa na samar masa da abun da yafi so koda kuwa zata rasa ran nata. Idan ta tuno da abubuwan da suka faru sai ta ƙara jin ƙwarin gwuiwa na zuwa musamman yadda yake nuna mata cewar ya tsaneta, bayan kuma ya lalata mata rayuwa. Amma idan ta tuno da rayuwar ƙazanta da dabbanci da rashin ƴanci da kuma jahilci da suke yi a garin Garuk sai taga anya kuwa zata iya zama a garin. Hatta cimarsu ma ba irin wannan ba, hatta shigar da sukeyi. Haka take ta tunanin har suka iso cikin garin Katsina, izuwa lokacin ta fara yin zuffa alamun zazzaɓi ya fara sauƙa. Koda ta duba a gogo wayarta ƙarfe biyu da minti uku. Har lokacin gurin da ta bugu yana mata ciwo, kuma bata jin karfin jikinta kwata-kwata. Mai motar ya ce "Munyi sauri ko?" Ya faɗa yana kallon fuskarta a karon farko. Ta ce "Nan Katsina ne?" Ya ce "Eh kin ga an samu cigaba ko? Hanyar ta zama kamar a Abuja ko? Da alamu kin kwana biyu baki zo ba ko?" Ya shiga jera mata tambayoyi duk saboda ya samu alkairi. Haura ta ce "Ga kuɗin ka" ta miƙa masa dubu ashirin ɗin sa. Ya ce "Ina zaki je a daren nan?" Ya faɗa ganin ta bi hanya ta fara tafiya. Bata tanka masa ba, ta cigaba da tafiya. Bata manta komai ba, kuma ba zata iya kasa gane hanyar garinsu ba, domin a ƙwaƙwalwarta komai yake. Haka ta nusa cikin dajin nan ta fara tafiya, baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye, tafiya kawai take yi tana tunanin rayuwar da tayi a garin kafin su fita gaba ɗaya ita da Aminta. Ganin kaman bata sauri ne yasa ta fara haɗawa da gudu. Har karfe huɗu tana cikin dajin, ji take kamar ma acikin dajin take, duk da ciwon da jikinta ke mata bai hana ta zage ba, tana haska ko ina da wayarta. Lokacin da ta fara cin karo da tarko irin nasu, kuma ta hango wani ƙaton dutsen dake kusa da garin nasu, sai wani daɗi da sanyin daɗin ya fara Ratsa ta, take ta naimi wannan gajiyar ta rasa. Bata ƙara jin dad'i ba sai da ta ganta a kan wannan dutsen kuma tana hango cikin garin Garuk. Batayi mamaki ba ganin garin yana nan yadda ta sanshi, sai ma wasu tsare-tsaren da suka yi na hana baƙuwar fuska shiga garin nasu. Ta na cikin tafiya taji an shaƙe mata wuya ana mata magana da yaren garin nasu. Kafin ka ce me an zageta wasu mazaje su biyar. Sun saitata da kifiyoyi. Sai da yayi mata ƙamshin mutuwa kafin ya sakar mata maƙogaro. Nan take ta shiga tari tana kakarin amai domin ta shaƙu. Ta ɗauki minti ɗaya tana tari kafin cikin yaren masu ta ce "Meye haka Haura ce fa, baku gane ni ba ne?" Ta faɗa ta na zare musu ido, domin duk babu wanda bata gane ba a cikin samarin, a lokacin da take garin duk ta take su gagara da iya tsafi. Lokaci ɗaya suka kalli juna. Wanda ya shaƙeta ɗin ya ce "Haura tiii attt chuhhh azzt kit ataaau butullitu (Wato Haura dama kina raye baki mutu ba?) ya na faɗa suka kurma wani uban ihu suka yi sama da ita suna kiran sunanta suka yi cikin gari da ita, duk inda suka wuce sai an bar abun da ake yi an biyo bayansu, dukda dare ne amma ga al'umma kamar safiya, ba'a ajiye Haura a ko'ina ba sai gaban sarkin garin Garuk. °*Adam* Wasa-wasa har kwana uku babu Haura babu Amera babu kowa a gidan nasa, yaje har gidan su Maryam akan ta kaishi gidan su saurayin Haura din amma ta ce masa bata sani ba, ya ce To a ina suke haɗuwa ta ce masa makaranta dai ta sanshi. Haka ya je makarantar aka ce masa ai ya daɗe da barin aiki anan. Ya ce To dan Allah a bashi address ɗin sa, amma aka hana shi akan basa yin haka. Gaba ɗaya Adam ya zama wani kala kamar mara lafiya, bai taɓa tabbatar da cewar yana son Haura har haka ba sai yanzu. Ji yake ina ma bai faɗa mata ba, sai dai kawai yaje a ɗaura, shi san bai ma damu da rashin dawowar Amera ba domin shi dai ya sa a ransa cewar ai ba shi ne ya koreta ba. Bangaren Amera kuwa babu yadda Abba da Umma ba suyi da ita ba amma ta ce ba zata koma ba har sai yazo da kansa ya ce ta koma kuma ya fasa maganar auran Haura da yake da niyya, hakan yasa Abba ɗin ya shiga buɗe mata wuta saboda shi yafi ganin laifinta, ai shi Adam ɗin ba shi ya ce ta tafi gida ba da zata ce sai yazo zata koma. Ya ce "To idan kin mata waye Adam bari na tuna miki, lokacin da kike da cikin yaran nan wani irin iya shege ne bakiyi masa ba, kin zagi uwarsa, kin zagi ubansa, kuma duk suna kabari kwance, amma yaron nan bai taɓa koroki gida da nufin yaji ba bare aje ga yin saki. Haka kika fasawa ƙanwarsa kai dan kawai tazo gidan ki. Sannan shi kansa har wuƙa kin chaka masa, kin sa shi asara marasa lissafuwa duk wai saboda kin yi ciki, ita kanta wannan yarinyar da yace zai aura har kika dawo gida ke ce silar mutuwar uwatar, haka ya sha samo miki masu aiki duk kina dukansu kina kora, daga karshe ma shi da kansa ya bar miki gidan saboda kawai baya son ya ce ke kitafi, saboda yana sonki, to ke idan kina da mutunci da tunani dan ya ce zai auri wannan yarinyar ke ba mai goya masa baya bane, gashi yarinyar ma da kin san halinta kin san abun da zata iya, kuma gata babu ruwanta, yarinya ma mara son hayaniya. Abba na ajiye wa Umma ta ɗora da nata. Ta ce "A lokacin ma babu irin rigimar da bata haɗa wa Nana da Nasiru ba, ta ce wai ba sonta yake yi ba, yanzu gashi tun da a kayi auran Nana bata taɓa dawowa gida ba, ke yanzu ma ba abun kunya ba ne ace kin dawo gida saboda mijinki zai ƙara aure, bayan kowa yasan irin abubuwan da kika yi lokacin da kina da ciki. Umma ta ƙarasa itama tana goyon bayan Abba. Babu abun da Amera ke yi sai kuka. Sosai komai ke dawo mata, ita kanta ta na mamakin abubuwan da tayi a wannan lokacin, to amma ai an ce ba ita kadai bace lokacin, amma dukda haka Adam yayi ƙoƙari. Hakan yasa ta shirya kayanta ta haɗa kan yaranta ta ci alwashin ita da kanta zata shawo masa kan Haura ya aura ko bata so, domin tunda haka ta faru ko bai auri Haura ba zai auro wata wacce bata san halinta ba, amma Haura fa, kishiya ce Amma bata da maraba da ƙanwa koma ta ce ƴar cikinta, ta sanan Haura ba zata cutar da ita ko yaranta ba, hasali ma yaran sunfi sabawa da ita, tun farko ma mai yasa bata danne zuciyar ta ba, mai yasa bata tumo da abubuwan alkairin Adam a gareta ba, mai yasa bata tsaya ta bashi gudun mawa ba, shi za'a samu irin Adam a duniya kuwa, tabbas bata kyauta ba, kuma ko ba komai itace dai sanadiyyar rasuwar ita mamar haura ɗin, mai yasa ta bari kishi ya mantar da ita komai, lokaci ɗaya ta tuno da cewar marinta fa yayi, sai kuma tayi murmushi tana tuno ita mari nawa tayi masa lokacin. Sai da ta gyara jikinta sosai harda sabon kitso da lalle sannan ta nufi gidan nata...📝 S Reza.... [09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* FCWA                           Chapter 17 Kasancewar yamma ne tayi sa'a baya nan. Haka ta shiga gyara gidan ta na hawaye, ta shiga tuno lokacin da take da ciki da suka je supermarket yin sayayya har faɗa ya haɗa ta da yarinyar soja, karshe Adam ne ya sha dukan. Ta sake tunowa da mai sayar da kwai inyamuri na ƙasan layin su da shima rigama ya haɗa, a ranar idan bata manta ba Adam ya mareta, amma itama ta rama. Bata manta lokacin da tace masa ya tashi ya tafi aiki ƙarfe shida na safe ba. Bata manta lokacin da ta hana shi zuwa gidan Khadijah ƙanwarsa ba, bata manta lokacin da ta biyo shi da wuka har suka fadi ta chaka masa a wuya ba, bata manta lokacin da ta naushi Ammin Haura a haƙarƙari har ta mutu ba. Bata manta lokacin da tsabar masifa da tashin hankalin ta har ya rubuta mata wasika ya bar mata gidan na wasu kwanaki ba, bata manta lokacin da ta kusa illata masa mazantakar sa ba. Ta na cikin wannan tunanin taji ya turo ƙofar palon ya shigo. Kallo ɗaya ta yi masa gabanta ya faɗi ganin kamar yayi shekaru yana jinya, duk ya rame ya koma kamar ba shi ba. Cikin muryar kuka ta ce "Sannu da zuwa honey" ta faɗa kuka na kufce mata.  Adam kuwa yau a gajiye ya dawo daga gurin aiki, izuwa yanzu ya tabbatarwa da zuciyar sa cewa Haura gurin saurayinta ta tafi, kenan dai da gaske bata sonsa. Ransa ya sosu ainun kuma yayi ƙoƙarin ganin ya takaice ta amma zuciyarsa taƙi bashi goyan baya, haka dole ya cigaba da jinyar zuciyarsa akan Allah ya dawo da ita kuma ya tsare masa ita. Haka yayi aikin yau kamar bashi da lafiya, a ransa ya bari dole ne ma ya koma school ɗin nan domin a bashi number Habib, idan ma sun ƙi zai faɗa musu abun dake faruwa, kuma gashi za su fara exam a sabon wata. A lokacin da ya buɗe palon da Salim ya fara cin karo a cen gefe yana danna waya, lokaci ɗaya zuciyarsa tayi wani sanyi ganin yaron. Har ga Allah yana son Haura, kuma da zuciya ɗaya yake sonta, amma baiyi tunanin Amera zata iya zaɓar rabuwa da shi akan hakan ba, shi dai yayi alƙawarin ba zai dawo da ita ba duk abin da take ganin shine daidai kawai tayi. Ya na cikin haka yaji muryarta hade da kuka ta na masa barka da zuwa. Sosai ya tsorata, domin bai kawo cewar zata dawo nan kusa ba, yayi tunanin yaran kawai tasa aka kawo. Ya so ya kawar da kai, ya nuna ko a jikinsa, amma ba zai iya ba, kukan Amera illata masa natsuwa yake yi, baya taɓa iya jure wannan bangaren, sannan gashi yaga tai masa wani haske, ga kayan da ta saka sun matse ta, kanta babu ɗan kwali, ga lallan da tayi nan jazirr a hannunta. Lokaci ɗaya raunin sa ya baiyana. Ya ce "Honey" ya faɗa a hankali. Muryarsa ce ta ankarar da Salim da ya nufo gurin sa da gudu yana kiran sunansa. Itama Salma ta fito da gudu suka rungume shi. Amera ma ta ƙarasa gurin ta rungume shi ta na kuka. Shi kansa bai san lokacin da hawaye suka fara gangaro masa ba. Cikin muryar koka ta fara faɗin "I'm sorry honey, I'm sorry" haka kawai take faɗa tana share hawaye shi kuma yana bubbuga bayanta. Salma ta ce "Daddy ina Anty Aisha?" Ta faɗa ta na ɗagowa daga jikin daddyn nata. Shima Salim ya tambaya suna kallon daddyn nasu. Adam ya ce "Tayi tafiya zata dawo" ya basu amsa ya na ɓoye hawayen nasa. Yaran suka shiga tambayar yaushe zata dawo. Amma yayi kamar bai jisu ba ya nufi ɗakin sa da sauri. Ya na zama Amera ta shigo ta na share hawaye. "Ta ce "Har yanzu ba'a ganta ba ko?" Adam ya kafe ta da ido ganin yadda ta damu kamar ba ita ba, yaso ya nuna mata cewar shine mijin kuma gidansa ne, sannan yana da ikon da zai iya yin aure a duk lokacin da yake so, amma dai ganin nadama a fuskar ta sai ya ce "Ban san ina ta tafi ba, dan Allah idan kece kika turata wani guri ko kika mata wani abun ki faɗa min please honey, wallhi ba wai zan aureta saboda ke kin gaza min bane, ko saboda wani abun bane, a'a honey, ina yin haka ne saboda Allah, kuma na taimaka ta, amma kin kasa fahimta ta?" Ya ƙarasa yana zuwa har kusa da ita. Lokaci ɗaya Amera ta sake fashewa da kukan abun da tayi. Ta ce "Yanzu shikenan ka daina yarda da ni honey, wallhi ban san inda ta tafi ba, dan Allah nima kayi hakuri da tafiyar da nayi please I'm very sorry for everything" ta ƙarasa ta na fadawa jikinsa. Adam yayi shiru yana sauraron irin kukan da take yi. Ya ce "Ya isa kiyi shiru ya wuce, bana son wannan kukan, na yarda da ke, kuma har abada yardar da na miki ba zata goge ba" ta tsayar da kukan ta ɗago ta ce "Baka cancanci haka aguri na ba honey, kuma itama Haura ban kyuta mata ba, in sha Allahu zan tayaka neman ta duk inda ta shiga, sannan kuma na yarda ka k ka k ka aureta" ta na faɗa ta bar ɗakin da gudu tana sakin wani kukan. Adam ya bi bayanta da ido bai ko iya cewa komai ba. Tun daga ranar komai ya wuce, suka fara neman Haura, babu yadda baiyi ba ya rasa number Habib. kwana ɗaya biyu Amera bata jin daɗi ana zuwa asibiti likita ya tabbatar da cewar tana ciki sati biyu. Tun daga asibitin ta fara kuka shi kansa Adam ɗin tsoro ne ya cika shi. Ai kuwa suna zuwa ta shiga rera kuka ita dai kawai a cire bata so. Shi kansa idan a sonsa ne kawai a cire. Da ya kalli irin kukan da ta ke yi kuma tana cewa a cire sai ya dinga ganin kamar fa an fara ne. *°Habib* Sosai Nadiya ta shiga ihu ta na faɗin cikin ta. Haka ya ɗauketa izuwa asibiti. A cikin daren aka samu ciwon ya lafa, aka saka mata ruwa da allura. Haka Habib ya kwana a tsaye duk ya shiga damuwa. Ai kuwa da safe ya kira Mama ya faɗa mata, ba'a daɗe ba kuwa sai gasu ita da ƙanwarsu Zainab ɗauke da abinci da kayan shayi da ruwan zafi. Suna ajiye wa Zainab ta juya kasancewar zata tafi school. Ko minti biyar basuyi da zuwa ba Habib ya tafi gida domin yayi wanka ya kuma kwasowa Nadiya kayan da zata saka. Ya na fita ita kuma ta farka. Ganin Mama yasa ta fashe da kuka na gaske. Hankalin Mama ya tashi, babu irin tambayar da batayi mata ba amma sai kuka ta keyi ta ƙi cewa komai. Gashi ance ta ci abinci taƙi ci, haka Mama ta dinga fama da ita amma sai kuka. A haka Habib ya dawo ya same su. Ya na shigowa ta tsayar da kukan ta na kallonsa. Tun kafin yayi magana Mama ta ce "Wai me ke damunta ne, tun ɗazu tana ta kuka lafiya dai ko, me likitan ya ce?" Habib ya karasa gurin da take ya ce "Bebb ya jikin?" Tayi banza da shi sai ma harara da ta bishi da. A haka likitan yazo ya samesu ya kira Habib ɗin ya faɗa masa cewar ya lallaɓa ta har lokacin aihuwar ta yayi idan ba haka ba zai iya rasa cikin dama uwar gaba ɗaya, domin ko yanzu ma Allah ne yasa sun kawota asibiti da sauri, sannan abu na gaba ta dinga samun huta, a daina yawan ɓata mata. Sosai likitan ya faɗa masa abubuwan da za'a kiyaye mata. Sannan ya rubuta musu sallama. Koda suka dawo gida sai yamma Mama ta koma sannan kuma ta ce Zainab zata dawo nan gidan da zama har lokacin da zata aihu domin ta rage mata aiki. Haka suka yi kwana biyu Nadiya bata ce masa um ko um-um ba. Duk irin tambayar da yayi mata sai dai ta kalleshi ta kawar da kai. Har maganar Haura yayi mata ya ce shi wallahi babu abun da yake tsakaninsa da ita, karta bari zuciyarta ta raya mata karya akan Haura. Duk abinda ya ce sai dai tayi hawaye ko ta kawar da kai. Yanzu kullum sai ta tashi cikin dare tai ta yin Sallah wanda shima ganin haka yasa ya tashi ya bita. Gaba ɗaya ta sauya, magana bata iya yin mai tsayi koda kuwa da Zainab ne, kullum cikin shiru da tunani. Bangare daya kuma Habib shima bai tsaya wajen tuba akan abun da yayi ba, bashi da addu'a sai Allah ya yafe masa, kuma karya ƙara haɗa shi da haura ko a mafarki. Yau sati biyu kenan da tura takardun neman aikin sa, amma yayi rashin sa'a duk babu wanda suka kira shi. Izuwa lokacin cikin Nadiya ya shiga wata na takwas, yanzu komai na gidan Zainab ce ke yi, shi kansa Habib ɗin baya zama sosai, kullum cikin fita neman aiki amma gaba ɗaya babu sa'a, izuwa yanzu sun gama haɗa komai na kayan aihuwa domin dama tun lokacin da suka tabbatar da cikin suka fara shiri. Izuwa yanzu hankalin Habib ya fara tashi na batun rashin wannan aikin, babu irin fadan da Mama batayi masa ba na sakin aikin da yayi, duk da kuwa ya ca masa sharri aka masa. Nadiya kuwa kaman yadda tayi masa alƙawarin ba zata ƙara saka baki a maganar aikin sa ba, haka ko yaje mata da maganar sai tayi banza da shi ko tace Allah ya bada sa'a to ta ce ma to. Wannan lamari nata ya fara ɓata masa rai. Yau misalin ƙarfe takwas bayan sun gama cin abinci ya riga ta shiga ɗaki, yana jiran tazo ta faɗa masa wai me yayi mata ne da ta sauya haka. Ta na shiga kuwa ya fara magana ta inda ya ke shiga da fita daban. Ita kuwa ko magana bata masa ba ta shinfiɗa dadduma ta tada salla. Haka abun ya cigaba da tafiya, shi a ransa yaso ace Kafin ta aihu ya samu aiki amma abun babu sauƙi. Dole shima ya ci gaba da binta a yadda take so ɗin, idan ta tashi cikin dare tana sallah sai yayi ta mamakin ta, watarana ya tashi watarana kuma yayi kwanciyar sa. *°Haura* Mamaki da tsoro da firgice ne suka kamata lokaci guda saboda abun da ta gani. Wani irin ihu ta saki mai karfi wanda daga haka bata sake sanin inda take ba sai yamma liss lokacin rana tayi jaa zata fadi. A hankali ta buɗe idonta, bata sauke shi a kan na kowa ba sai kan na Aminta. Da Karfi ta kira sunan Ammin tata ta amsa itama hawaye na zubowa daga cikin idonta na murna da farinciki. Ganin daga ita sai ita ne a ɗakin yasa Haura tashi zaune da kyau, tana ta kallon Uwar Tata, tana jin wani abu mai kama da kafi daɗi daɗi, ji take kamar ta tashi ta goyata tayi ta rawa, amma hawaye da kukan dake cinta na murna ta kasa aiwatar da ko ɗaya. Kafin ta iya samun damar magana aka buɗe ɗakin wani kyakkyawan saurayi ya shigo ɗakin ya na tambayar Ammin da rayensu wai hauran ta farka, kafin ma ya karasa yayi ido biyu da ita. Haura na ganinsa ta kira sunansa da ƙarfi tana nufar sa. Ta ce "Guber Ammi ce wannan, dama bata mutu ba?" Ta faɗa tana chakume wuyan Guber wanda babu riga a jikinsa ko wando, sai wata fata da ta rufe masa alaura. Ita kanta Ammin haka take zaune amma ita ta daure girjinta da wani tsimma, sai kuma wata farar mayafi da Haura ɗin ta kasa gane a ina ta samo shi ta yafa a kanta. Ya ce "Eh Haura bata mutu ba tana raye" ya amsa shima hawaye na zubo masa na kewar ta da yayi. Guber shine abokinta na yarinta, kuma wanda ake cewa zai aureta a lokacin. Sosai Haura ta sha kuka har saida Ammin ta rarrasheta, Guber ma ya bata hakuri, da ƙyar ta daina kuka tana ta tambayan abubuwa ana bata amsa suna ta hira. Mutane wannan yazo wannan yazo, sai take kallonsu kamar wasu halittun da ban ba irin nata ba, tun daga haka ta tabbatar da cewa zata iya zaman garin nan ba. Ganin dai Haura na da tambayoyi da take son mata ne yasa Ammin ta tambayeta mai ya dawo da ita. Kallon Guber ta yi. Ammin ta ce ta fadi komai babu damuwa. Guber yayi dariya yana tsokanarta da ko ta dawo suyi Aure ne. Cikin wata iriyar murya Ammin ta daga mata tsawa bayan ta gama jin komai da take son ayi mata, kuma ta basu labarin rayuwarta da abun da Habib yayi mata, amma banda abun da suka aikata, kaman dai yadda ta fadawa su Adam. Ta ce "Yanzu-yanzu ki tashi ki koma muddin wannan abun ne ya kawo ki". Haura ta kalli Ammin nata, tabbas wannan ba ita ba ce, idan ma ita ce to a kwai abun dake faruwa, aminta da take goyan bayanta akan komai, bare kuma irin wannan cin amanar da aka yi mata. Guber ya ce "Haura Ammi musulma ce yanzu haka, ta na yin Sallah ba tare da kowa ya sani ba, kuma ko yanzu muna shirya yadda zata bar cikin garin Garuk ne saboda taje cen tayi adininta. Ammin ta ce "Bana son naji kinyi maganar nan da kowa, sannan shi wannan mutumin da kike so bana son taraiyar ki da shi, Adam nake so ki aura shine ya taimake ki, a lokacin da baki da kowa, shine mutumin da ya samar miki da ilimi da wayewa da komai na rayuwa, sannan karki ƙara batun ƙarɓar tsafi. Da sauri Haura ta toshe kunnenta ta ce "Ammi bana sonsa, shi Daddy na ne, ba zan iya auransa ba, ni Habib nake so, kuma shi zan aura, wallahi bana son daddy". Kwanan Haura goma sha shida a garin Garuk, izuwa lokacin sun sanar da cewar kawai ziyara ne tazo, kuma har wannan lokacin babu yadda ba tayi da Ammin akan a dawo mata da tsafinta ba amma Ammin ta ƙi. Kuma ta ce ta bata labarin yadda ta musulunta amma ta ce mata sai ranar da ta shigo cikin gari zata bata labari. Haka Haura ta shirya komawa ba tare da ta samu komai ba, taje tayi sallama da Sarkin garin Garuk ya saka mata albarka irin tasu, shima sai da yayi mata tayin sake karɓar tsafin amma ta ce bata so. Guber ne zai rakota wanda har cikin gari zai kawo ta da izinin Sarkin garin. Bayan tayi sallama da yan garin da Aminta ne suka kama hanya. Sai da suka gangara ƙasan dutsen bayan garin kafin Guber ya ƙyalƙyale da wata shegiyar dariya. Itama Haura ta bushe da dariya, sai da suka yi mai isar su, domin sun tuno da lokacin baya, haka suke yi shi da ita, komai nasu ɗaya, duk inda zasu je tare, ayi wanka tare aci abinci tare, hakan yasa yafi kowa sanin damuwarta a lokacin da kuma yanzu da abun da ya faru da ita ɗin ya tsaya masa a rai domin ta faɗa masa cewar harda fyaɗe yayi mata. Guber ya ce "Bayan duk wannan abun da ya miki kuma yace ba zai aure ki ba, ita kuma Ammi wai a rabu da shi, to wallahi sai ya mutu ko kuma ki aure shi ko dai matar sa da cikin jikinta su mutu, wa ya faɗa masa ana yiwa ƴan matan Garuk fayɗe dan ubansa, ba dan ma Allah yasa bani da ikon shiga gari ba da yau zai mutu a daren nan wallahi". Ya ƙarasa da mugun ɓacen rai.   Haura ta daka masa tsawa ta ce "Bana so ya mutu, domin ina sonsa, idan ya mutu nima mutuwa zanyi, kawai kai dai bani abun da zaka bani, aure nake so muyi, bana so matarsa ta mutu domin tana da kirki". Guber ya kama hannunta na dama ya chaka ƴan yatsansa guda biyu kaman wanda zai ƙwaƙulo wani abu. Sai kuwa ga wani haske yana fitowa daga cikin idonsa yana shiga nata, wani abu kuma mai kamr blue (kore ) yana fitowa daga yatsun hannunsa yana shiga hannunta. Ƙasa da Minti ɗaya ya gama shiga sai ga Haura ta zube a ƙasa kamar wacce aka ɗaga aka maka da ƙasa. Guber ya busa mata iska sai kuwa gata ta miƙe tsaye. murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa ya buɗe mata hannunsa ta zo da gudu ta shige suka fara masayar maganganu da yaransu na alƙawarin zata dinga sanar dashi komai. Sai da ya rakota har bakin dajin kafin ya koma. Ita kuma ta shiga Motar Abuja bayan an saka mata akwatin ta a baya, ana tafiya tana tunano yadda zata kasance da abun sonta. Ana ajiye ta a tasha ta kama hanyar gida a ƙafa, wanda ko minti biyar batayi ba ta iso unguwar tasu hannunta riƙe da a kwatin kayanta da ta tafi da su. Ta tura get ɗin gidan ta shiga da sallam. Lokacin rana ne Adam baya nan Amera ce sai yaran da yau babu school. Salma ce ta fara hangota hakan yasa ta kira sunanta da karfi tana nufarta. Amera da barci ya fara tafiya da ita ta fara da mamaki. Dukda gabanta ya faɗi amma sai da ta nuna farinciki. Haura ta nufota da sauri ta rungumeta. Nan take Amera ta ɗau waya ta kira Adam ta faɗa masa. Ko minti biyar baiyi ba sai kuwa ga sallamarsa a palon...📝 S Reza... [09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *FCWA* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Chapter 18* Bai ko jira an amsa masa sallamar ba ya shigo cikin palon da sauri ya na kiran sunanta. Ya na zuwa kusa da ita ya tsaya ya na kallonta, itama shi take kallo idanunta ƙur a kansa babu alamar tsiro ko nadama akan abun da tayi. Kafin yayi magana ta ce "I'm sorry Daddy please kayi hakuri" Ta faɗa ta na marairaicewa alamun abun tausayi. Adam da gaba daya jin daɗin ganinta ya kawar da ɓacin ran da yake ciki. Ya ce "Ina kika je?" Ta ce "Daddy ina makaranta fa, cen na koma da kwana amma yanzu na dawo Please I'm sorry kaji" Ta ƙarasa ta na yi kamar zata yi kuka. Ajiyar zuciya ya sauke yana rasa mai kuma zai sake ce mata. Amera ta ce "Shiga ɗaki ki huta ko?" Ta faɗa ganin sun tsaya cirko-cirko kowa ya ƙi magana. Ai kuwa da sauri Haura ta nufi ɗakin ta Salim da Salma dai suna manne da ita. Ta na shiga daki Adam ya samu guri ya zauna yayi shiru. Amera ta ce "Sannu da dawowa" ya amsa ya na kallonta. Ta ce "To sai ga shi dai Allah ya dawo da Haura gida lafiya, sai mu godewa Allah" Adam ya ce "Kin yarda da inda tace taje? Idan da makaranta ta je Maryam zata sani, kuma ko da naje school ɗin na tambaye ta amma an ce bata zuwa". Amera ta ce "To yanzu dai ba ta dawo ba? Sai kawai ayi abun da ya da ce" Adam ya ce "Zuciyata bata kwanta ba, ba zan ɓoye miki ba kawai ta na faɗa min cewar gurin saurayin nata taje". Amera ta ɗan kawar da kai gefe kafin a hankali ta ce "Kasan idan zuciya ta na son abu to bata cika ganin aibun wannan abun ba, sannan zuciya ta na yin uzuri ne wa wanda take so koda kuwa akan ƙarya yake" Amera ta ƙarasa ta na kallonsa. Adam ya ƙura mata ido kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce "Tabbacin soyayyar gaskiya shine kishin abun da kake so, tabbas idan baka jin kishi idan wani ya raɓi wanda kake so to babu shakka ba sonsa kake ba, Honey ina son Haura sosai son da ban san iya adadin sa ba, idan da kinsan yadda zuciyata ke zafi da wannan abun da tayi da kin tausaya min" ya ƙarasa ya ne dafe saitin zuciyarsa. Amera ta ce "Na sani kuma..." Ta ke kuka ya kufce mata, ta kasa ƙarasawa. Ai kuwa tayi cikin ɗaki da sauri, ya bita ya na kiran sunanta. Haura na shiga ɗakin cikin minti ɗaya ta gyara ko ina harda cikin toilet. Ta kwanta a kan gadon tana kallon sama. Tana ji su Salim suka fita bayan sun ɗauki wayar ta. Marmarin ganinsa take yi, tayi kewarsa, ta matsu ta sake ganin sa. Wanka ta shiga bayan ta fito ta saka ƙananan kaya da hula ta fito ta shafe jikinta da mai, ta aiyana banbancin dake tsakanin garin Garuk da kuma nan inda take. Kallon makeken gadon ta tayi, da irin kayan da ke cikin ɗakin, ga A.C ga fanka, ga toilet mai kyau harda mashin ɗin wanke kaya, ga sabulai masu ƙamshi da gyara fata. Dariya kawai tayi tana jin gaskiya ba zata ma iya zama a garin Garuk ba kwata-kwata ko mai zai faru, gara ma ta dage ammi ta dawo nan da zama. Palo ta fito ta samu yaran ne kawai suna ta wasa abun su. Ta amshi wayarta ta samu guri ta zauna ta fara kiran Maryam. Ta na ɗagawa Maryam ta fara mata masifa da tambayoyi, Haura ta ce "Kizo gida ina gida" ta na faɗa ta kashe wayar ta na dariya. Bata dade da zama ba sai ga Adam ya fito. Yayi nufin yayi mata magana amma ya share kaman yadda Amera ta ce masa zata ji da komai. Haka tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita. Ta na zaune Maryam ta shigo gidan. Sosai suka sha hira, anan ne Maryam ke sanar mata da cewar ta godewa Allah ma an ɗaga exam ɗin yau kwana uku da farawa, badan haka ba da yanzu an gama. Babu yadda ba tayi da ita ba amma ta ce mata wani guri ta ce, ta shiga faɗa mata yadda Adam ya dinga sintirin zuwa gidan su da kuma makarantar su, harda tambayar ta gidan Malam Habib. Haura ta ce "Kin kai shi?" "To na san gidan ne da zan kai shi?" Ta faɗa da afusace. Haura ta ɗan yi dariya, ta tashi ta shiga kichin. Ganin babu komai yasa lokaci kaɗan ta haɗa lafiyayyar taliya da wake ta sha kifi, ta zubo musu ta haɗo da abun sha. Ta zo zata fita suka ci karo da Amera. Haura ta ce "Anty Maryam ce ta zo, shine nayi mana girki, ga sauran chen a ciki. Ta faɗa kamar a ɗan firgice. Amera ta ce "Ok tom, kin kyauta" ta faɗa ta shige kichin ɗin. Washegari ta shirya ta tafi school bayan ta gama musu girki. Lokacin babu wanda ya fito a gidan, basu ma yi tunanin zata je school ɗin ba, sai da suka fito suka ga komai ta jera a dainintebul. Cike da wani mamakin Amera ke kallon abubuwan da aka dafa. Bata ce komai ba suka fara ci, amma dai tabbas ta shiga kokwanton, domin wani abun ma basu da shi a gidan, kuma ita bata ji motsin ta a kichin ɗin ba. Sai tayi tunanin ko ita ce ta sayo domin tana so. Koda Adam zai fita sai da ya ƙara tuna mata da maganar Haura. Ai kuwa ya na fita ta gyaran gidan ta hau karatun sabon littafin da ta saya jiya a gurin S Reza mai suna Tsinuwar uwa. Sosai labarin ke mata dadi, wanda bata san lokaci ya ja ba, sai da taga Haura ta shigo gidan. Haura ta zauna ta na kallon yadda Amera ke ta dariya. Ta ce "Anty wannan dariyar fa?" Ta tambaya. Amera ta ce "Please zo ki karanta min wannan littafin" Haura ta amshi wayar tana duba labarin. Ta ce "Anty kina son littafin wannan S Reza ɗin" Amera ta yi dariya kawai bata ce komai ba. Haura ta fara mata karatun, sai ga haura itama ta fara dariya, sosai suke dariya idan an zo gurin dariya. Duk abun da suke yi Haura an ankara da lokaci domin ta na lura. Hakan yasa sha ɗaya na yi ta ce ta gaji. Amera sai taji kamar da isa tayi maganar hakan yasa taji wani abu kamar na raini dai haka. Ta ce "Ina so zamu yi magana?" Haura ta ce "Tom Anty amma idan na dawo ko?" Amera ta ji ranta ya ƙara ɓaci ta ce "Yanzu" Ta faɗa a dake. Haura ta ce "Tom ina jinki anty?" Amera ta ce "Mai yasa kika ce ba kya son Daddy?" Haura ta ɗago da sauri ta kalle ta, sai kawai ta ɗan yi murmushi ta ce "Anty ke kin yarda ya aure Ni?" Ga ban Amera ya fadi, amma ta dake ta ce "Eh zan so domin yana sonki" ta faɗa a hankali. Haura ta ce "Anty Ni kuma bana sonsa da aure amma ina sonsa a matsayin Daddy" ta faɗa tana dariya domin ita har ranta bata son Adam da aure sai Habib. Lokaci ɗaya Amera ta ji wani abu ya tsurkuleta a zuciya, taji kaman ita kaman ba ita ba. Eh tabbas abun ya mata dadi, amma idan ta tuno da irin son da Adam ke mata sai abun ya bata tsoro. Amma kuma ta kasa samun natsuwa, ita ai ba tayi zaton Haura zata ƙi yarda ba, amma yanzu meye abun yi. Adam kuwa ya na fita gidan su Amera ya fara zuwa kasancewar sunyi da Abba cewar idan har ta dawo shi zai zama wakilin haura wajen ɗaura auran, hakan yasa yaje har gida ya samesa. Sai da ya fara masu albishir da cikin Amera kafin ya sanar da abun da ya kawo shi. Abba ya shiga hamdala da Allah ya dawo da ita, sannan ya tambaye shi yaushe nei za'a ɗaura. Adam ya ce ya ɗan bashi zuwa nan da gobe za suyi magana da yarinyar. Haka ya bar gidan ya nufi gidan Najib, shima dai sai da ya fara faɗa masa maganar cikin kafin ya sanar da su dawowar Haura. Najib ya ce "Yanzu dai dole sai ka aureta ko?" Adam ya ce "Please bana son kana dawo da abun da ya wuce, Please ban ce ka min komai ba dan haka babu ruwanka. Najib ya ce "To batun cikin Amera fa, Kasan dai yadda take yi idan ta na da ciki ko?" Adam yayi saurin fadin "Aniyar ka ta bika, in sha Allahu ba zamuga wannan ɗabi'ar ba". Ya na faɗa ya bar gidan. Itama dai Khadijah abun da tace kenan amma dole suka zuba masa na mujiya. Koda ya koma gida ya samu Amera ita ɗaya a gida, kuma gata duk a sanyaye, nan dai ta faɗa masa yadda suka yi da Haura, amma bata ce masa bata so ba, ta ce dai sun fara maganar da ita. Ai kuwa sai Gashi yana fsrinciki harda godiya ga Allah. Nan ya shiga yi mata alƙawarin ba zai bata kunya ba, kuma tasa a ranta ita ce ta farko kuma ita ce ita ce itace. Haka dai ita sai duk maganganun nasa ma suka fara ɓata mata rai. Jin yaƙi yin shura ne yasa ta kasa daurawa ta ce "Dan Allah naji, haba ni ka ishe ne, ai naji duk abun da kake cewa" ta na faɗa ta bar masa palon. Ya bita da kallo bai ce komai ba. Ta shiga daki ta fashe da kuka tana jin zuciyarta na zafi ga wani irin ɓaci da ranta yayi da abun da tayi, wai ita da kanta. Wanka tayi mai ɗaukar hankali da irin kayan da ta saba sakawa wato doguwar riga. Ita kanta tasan tayi kyau, ko waya bata ɗauka ba. Sannan ko jaka babu a hannunta. Ta saka wani ƙaton glas a idon ta. Lokacin da ta ƙaraso ƙofar gidan Habib sai ta dinga bin gidan da kallo, ta na tuno irin ƙorar da aka yi mata a gidan. Kanta tsaye ta buɗe get ɗin gidan ta shiga cikin gidan ta na sallama. Jin babu kowa ne yasa ta shiga palon ta zauna. Minti ɗaya, biyu,uku, huɗu, biyar. Ganin babu motsin kowa ne yasa ta miƙe tsaye ta shiga duba gidan. Ganin babu kowa yasa ta shiga kichin ta samu babu komai na abinci wanda yake a dafe. Sai kuwa tayi musu girki, ta shiga ɗakin sa ta gyara ta koma na Nadiya shima ta gyara. Sannan ta zubo abincin da tayi ta zauna ta na ci tana kallo, a ranta tana jin koma ina suka tafi zasu dawo. *°Habib* Ganin get ɗin gidan a buɗe ne yasa ya ɗan yi mamaki domin koda zasu tafi asibitin shi da kansa ya rufe, sai kuma yayi tunanin ko dai Zainab ta dawo daga school ne, amma idan ita ce ai ya mata faɗa akan rashin rufe masa gida. Da haka ya shigo da motar ya zagayo ya budewa Nadiya ta fito da ƙyar domin cikin ya tsufa sosai da ƙyar take tafiya ga kasala kullum ciwo, hakan ne ma yasa kusan kullum suna hanyar asibiti. Sai da ya rufe get ɗin kafin yazo ya kamata suka nufi gidan. Ganin palon a buɗe yasa ya tabbatar da cewar Zainab ce ta dawo, ai kuwa zai saɓa mata tunda bata jin magana. Haka ya shiga lallaɓata har suka shigo cikin palon ya na mata sannu, ita kuma tana taku da ƙyar tana yatsinewa. "Innalillahi wa'inna'ilai rajiun! Ya faɗa da ƙarfi har yana sakin Nadiya tsaɓar tsoro, ita kanta Nadiyar ta tsorata sosai domin sai da ta fadi a tsakiyar palon. Haura kuwa sai murmushi take yi tana kallonsu ganin yadda tsoron ganinta ya rikita su. Ganin sun kasa magana ne yasa ta ce "Sannunku da dawowa?" Habib ya kasa magana, Nadiya kuma ta samu guri ta zauna domin ba ƙaramin jin jiki take yi ba, kuma yaɗuwar da tayi ma taji shi amma ta daure tana ta kallon haura ɗin. Sai lokacin ma suka kula da abinci take ci, ga gidan duk a gyrare har yana tashin ƙamshi. Habib dai ya kasa zama kuma ya kasa ko motawa. Da ƙyar ya nufi gurin Nadiya ya na son kamata domin ya Kaita ɗaki amma ta ɗaga masa hannu alamun ya barta. Haura ta ce "Sir nayi kewarka sosai, ina fatan kaima kayi kewata ko?" Ta faɗa tana nufar gurinsa. Suna haɗa ido ya ji kamar an zare masa lakkar jikinsa, yaji wani sanyi ya shigesa. Ta zo har kusa da shi ta ce "Sir Mai yasa baka sona bayan kuma ka koya min sonka, bayan ka min alƙawarin zaka aure ni, ko matarka bata yarda ba ne?" Ta faɗa tana sha masa fuska. Habib ya ce "Wa ya faɗa miki bana sonki, ina sonki sosai har cikin zuciyata" ya ƙarasa yana sakin fuska. Ta ce "Sir Aure nake so zamu yi na dawo gidan ka da zama" ya ce "Nima zan so hakan baby" yana faɗa yana ta sakin murmushi. Nadiya ta yunƙura da nufin tashi ta bar gurin amma ta sami mistake ta zame. Har Habib ya tashi da sauri zai je gurin ta amma Haura ta riƙe masa hannu ta ce "Sir wannan ai lokaci na ne, nazo ne fa kawai domin na ganka na samu muyi hira". Sai kuwa ya ce "Haka ne fa, yau ranar ki ce gaba ɗaya". Ganin ya na ta kallon gurin da Nadiya ke kwance ta na ihu ne yasa Haura kama hannunsa ta na fadin "Sir zo mu shiga ciki zan baka labari. Ai kuwa sai ya miƙe yabi bayanta, suka bar Nadiya kwance tana murƙususu a gurin. Sun kai minti biyar da shiga dakin Zainab ta dawo. Daga ɗakin da suke Haura ta hangota, hakan yasa ta tambaye shi wacece ya ce ƙanwarsa ce. Hakan yasa ta ce masa yaje ya hana ta shigowa cikin gidan. Ai kuwa tare suka fita har palon, kuma har lokacin Nadiya na kwance a gurin har ɗankwalinta ya fita. Ganin Habib ya fita Haura ta dawo kusa da ita ta ce "Idan har mutuwarki itace zata bani damar shigowa gidan nan to Allah yaji ƙanki, zan iya miki alfarma ɗaya, ko dai kiyi hakuri na shigo Mu zauna tare ko dai na fitar da ke Ni na shigo. Saboda babu abin da ba zan iya ba akan damuwar burin zuciyata, karki wahalar da kanki akai na, domin wallahi sai Sir ya aureni. Ta na faɗa ta tsalleketa ta koma bakin window tana kallon Habib da Zainab suna ta muhawara. Cen dai sai Gashi ya shigo gidan ya ce "Ta tafi, amma dole zata dawo saboda kayanta suna nan" Cikin wata murya mai kamar ta bankwana Nadiya ta kira sunan Habib wanda yaji sa har cikin zuciyarsa. Ya kalleta sai kuma ya kalli Haura da ta kafe shi da ido. Ai da sauri ya tsallake ta ya dawo gurin Haura yana murmushi. Haura ta ce "Kama ta ka Kaita ɗaki" ai kuwa da sauri ya saɓeta Haura na binsa a baya har ɗaki, yana ajiye ta suka baro ɗakin suka dawo palo...📝 Wai me ke faruwa S Reza... [09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *FCWA* *Chapter 19* Bayan sun zauna a palon Haura ta dube shi ta ce "Ina so yau muje gurin Daddy tare da kai kuma ka tabbatar masa da cewar zaka aure ni, kuma ka bashi hakuri akan abun da ya faru wancen lokacin da baka zo ba?" Ta faɗa ta na shigewa jikinsa. Habib ya amsa da sauri kamar mai tsoro. Ya ce "Zan bashi hakuri kuma ba zan baro gidan ba sai da alƙawarin auren mu" ya faɗa cike da shauƙin jinta a jikinsa. Ta ce "Sir ba kayi kewata ba ko?" Ya ce "Nayi sosai ma, baki san yadda naji bane kwana biyu da bana ganinki" Ta ce "To ba kai ne kake korata ba harda duka na saboda matar ka ba?" Ta faɗa da shagwaɓa a muryar ta, har tana cuno baki gaba. Habib ya ce "Ba laifi na bane, kuma ai na baki hakuri, yanzu dai a fuskanci gaba baya ta wuce. Ta ce "Yanzu ni da matarka wa zaka saɓa idan an ce ka ɗauka?" Habib ya ce "Wacce mata kuma idan gaki, ai ni kin fiye min kowa da komai a duniyar nan, dan Allah ki daina ma haɗa kanki da ita" Ta sake cewa "Da gaske kake Sir?" Ya ce "Da gaske nake ina mutukar sonki" Haura farinciki kamar zai hallaka ta, sai yanzu take jin cewar tana yin soyayya, domin kaso a soka ai shine so, tabbas ko mai zai faru sai ta auri Habib ɗin ta. Sai kuma ta mike tsaye ta kama hannunsa suka shige ɗaki ta na masa kalaman da suke ƙara hargitsa shi. Suna shiga ita kuma ta fito ta nufi ɗakin Nadiya. Ta tura ƙofar ta shiga sai ta sameta a kwance kamar mai barci duk ta fita a haiyacinta, har lokacin tana numfashi sama-sama. Sunkuyawa tayi kamar mai duba wani abu a bakin kofar, amma ta ɗago bata ga abun da take nema. A hankali Nadiya ta buɗe ido jin an shigo tana kallonta, sai ta fara karanto addu'o'i a zuciyarta, domin dai ita ta tsorata da yarinyar. Duk yadda Haura taso da tayi mata abun da tayi nufi sai ta kasa, taso tayi amfani da cikin jikinta domin ta furgitata har ta haukacewa Habib yayi mata shegen duka ya sake ta amma ta kasa hakan. Daga karshe ma ɗakin ta bari tana jin haushin Nadiya ɗin, tana tunanin kawai ta fita a sabgar Nadiya kawai tayi ta amfani da Habib. Duk yadda taso akan su aikata zina a karo na biyu amma yaƙi yarda ya ce shi auranta zai yi, itama saboda tafi son auran yasa ta haƙura ba tare da tayi masa dole ba. Sai kusan magriba suka bar gidan bayan yayi wanka ya saka manyan kaya. Lokacin da suka iso ƙofar gidan Adam an fito daga sallar magriba. Ya shiga da motar har cikin gidan ya paka. Ta ce "Karka ji tsoron komai kawai kai dai kace masa da gaske kake sona kaji?" Habib ya amsa yana fitowa daga cikin motar. Tana gaba yana binta a baya har bakin palon. Ta buɗe ta shiga da sallama. Lokacin gaba ɗaya suna palon, yaran ne kawai a cikin ɗaki suna Sallah. Da gudu haura ta kara so gurin Amera ta faɗa jikinta ta na faɗin "Anty gashi na kawo shi, yazo ya bada hakuri akan wancen lokacin, kuma ya tabbatar da aure na zai yi" Amera ta kalli Adam da ya kafe Habib da ido. Amera ta ce "Sannu da zuwa ga guri ka zauna?" Ta nuna masa kujerar dake kusa da shi. Habib ya zauna. Haura ta ce "Daddy ga shi yazo ya baka hakuri?" Kafin Adam yayi magana Habib ya fara miƙo gaisuwa. Amera ta amsa ta na cewa Haura taje ta samo masa ruwa. Haura ta tashi tana kallon fuskar Daddy. Adam ya ce "Me ya kawo ka gidan nan bayan dukan da kayi mata da kuma ƙin zuwa da kayi a lokacin farko da aka nemeka, ka manta sanadiyyar abun da kayi mata har kwanciya a asibiti tayi, shine yanzu ka dawo ka sake karya mata zuciya ko?" Habib ya ce "Duk abun da ya faru kuskure ne shi ne yasa nazo yanzu na bada hakuri, wallahi yanzu a shirya nake domin nayi komai akan ta, saboda ina sonta, kuma auranta zanyi wallahi" Adam ya ce "To ka makara domin an riga ka, yanzu haka auranta ya kusa saboda haka ina so ka fita daga sabgar ta, kar na ƙara ganinka da ita, idan ba haka ba zan baka mamaki?" Habib ya zamo ƙasa ya fara roƙo harda magiya yana cire hular kansa kamar zai yi kuka. Ita dai Amera ta kasa magana, abun ya ɗaure mata kai, ita tunanin ma da ta fara yi shine dole ne fa sun san ina Haura ta je tayi wannan daɗewar, shin suna tare da shi ne ko dai yaya. Ana cikin haka haura ta ƙaraso gurin tana kallon yadda Habib ke ta rikon Daddy kamar zai masa sujjada. Ta na ajiye ruwan Habib ya ce "Ki taya ni bashi hakuri wai an kusa miki aure, dan Allah kice yayi hakuri zan iya shiga wani hali idan ban ganki ba" Haura ta ce "Aure kuma?" Adam ya ce "Eh aure! Kaman yadda na faɗa miki kuma Amera ta faɗa miki to haka ne za'a ɗaura miki kwananan" Haura ta yi dariyar ƙarfin hali ta ce "Daddy nifa bana sonka da aure, ga wanda nake so, kuma ni shi kaɗai nake jin zan iya aura, saboda haka kawai a bar maganar wani aure ga wanda nake so shi kadai". Ta ƙarasa tana zama kusa da shi. Adam ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya ji ƙirjinsa yayi masa nauyi kamar an tara masa abu a gurin, ya sunkuyar da kansa ƙasa ya dafe kan. Amera ta taso tana masa sannu, itama Haura ta fara masa sannu. Ya ɗago kai har idanunsa sunyi jaa sosai. Ya kalli Habib ya ce "Tashi ka zauna" Habib ya zauna yana kallon Adam da gaba ɗaya yanayinsa ya sauya. Anan palon aka tsayar da magana akan Habib ya turo magabatansa nan da juma'a mai zuwa. Amma Haura tayi caraf ta ce ina sai dai su zo gobe. Shima Habib ɗin ya ce goben yayi masa zasu zo. Haka aka bari akan gobe zasu so ɗin. Haura ta rakashi har mota ya shiga suka yi sallama akan yana zuwa gida zai kirata. Suna fita Adam ya kwantar da kansa a kan kujerar da yake zaune yayi shuru. Amera ta zo kusa da shi ta ce "Honey ya kamata musan ina wannan yarinyar taje tsawon wannan lokacin, domin ni ina tunanin tana tare da shi ne fa, sun shirya komai ne, ku..." Adam ya ɗaga mata hannu ya na tashi ya bar palon. Habib kuwa gidan Mama ya wuce darigt, yana zuwa suka gaisa ta tambayi Nadiya da jiki ya amsa. Ta ce "Sai kuma naga Zainab ta dawo wai kace ta dawo gida, bayan kuma a kasan jikin Nadiyar dole sai da wani a kusa da ita, domin ta shiga watan ta?" Habib da har ya manta da cewar ya koreta ya ce "Ni ɗin Mama, ƙarya take min ni bamuyi haka da ita ba. Mama ta ƙwadawa Zainab kira tana zuwa ta ce "Kika ce shine ya ce Ki tafi gida ashe ƙarya kike masa, wai mai yasa Zainab ba kya son zaman lafiya ne?" Zainab ta kalli yayan nata suka haɗa ido ta ce "Allah Mama shi ne ya ce na dawo gida, ko ciki bai bari na shiga ba" Adam ya ce "To naji yanzu kizo mutafi" ya na faɗa ya miƙe domin bai so a cigaba da maganar, kuma maganar ma da yazo da ita ya fasa. Haka suka tafi da Zainab ya sauketa a ƙofar gidan, shi kuma ya koma da matarsa baya. Gidan kawunsa ya je ya faɗa masa abun da ya ke so yayi masa na zuwa gidan su Haura gobe. Kawun ya kalle shi da kyau ya ce "Tambaya ko dai ɗaura aure?" Habib ya ce "Kawu gaba ɗaya ma duk wanda a kayi?" Ya ce "To ai ita mamar taku bata min maganar ba, ko ita ce ta aikoka, domin yau ma naje gidan, Sannan kuma har yaushe ma kayi auran na ka, shekara ɗaya ne fa gaba ɗaya habibu, kuma gashi yarinyar nan ciki ne gare ta, da ka bari ta sauƙa lafiya ko?" Habib ya dage shi dai kawai aje. Hakan yasa ya ce zai yi magana da Mama amma Habib ya ce baya so ya ta sani. Jin hakan yasa kawun nasa gane cewar a kwai iskanci a lamarin. Sai kawai ya ce "Allah ya kaimu goben". Da haka ya koma gida. Ya na shiga ya samu babu kowa a palo, hakan yasa ya shige ɗakinsa ya cire manyan kayan da ya saka ya sa kanana ya fito palo yana nemo number Haura. Dama welcome back yayi nan take ya cireta daga blocking ɗin da yayi mata ya kirata. Zainab ta fito daga ɗaki ta ce "Yaya Nadiya fa har yanzu jikin ne, ni sai nake jin kamar aihuwa ce". Ya ce "To kije ki taimaka mata mana, ko ni kike so naje gurin aihuwar?" Ta ce "To bani waya na kira Mama, ni na manta tawa a gida?" Habib ya mike tsaye kaman zai mareta ya ce "To ke meye amfanin ki da ba zaki taimaka mata ba har sai kin kira Mama a cikin daren nan, to ba zan bada wayar ba, kuma karki kuskura ki kira Mama a daran nan na faɗa miki?" Zainab ta ce "Wai yaya lafiya kuwa kake, ko ma me Nadiya tayi maka ai ciwo ba wasa ba, kuma ma na ce maka aihuwa ce fa, Dan Allah yaya ka zo ko..." Marin da ya kai mata ne yasa ta bar gurin da gudu ta koma ɗakin da Nadiya take kwance. Zainab na barin gurin Haura ta ɗaga kiran suka fara hira. Bangaren Nadiya kuwa sosai ta fita a haiyacinta, ita kanta Zainab ta tsorata kaman wacce zata mutu irin wannan shure-shure, hakan yasa itama ta fashe da kuka domin bata san me zata iya mata ba. Ganin dai abun ba na ƙare bane yasa ta sake zuwa palon ta same shi yana waya harda dariya abunsa. Ta na kuka ta ce "Yaya asibiti Nadiya zata mutu wallahi!" Ta faɗa da wani irin kukan da sai da gaban Habib ya fadi, ya danyi jim kaɗan kamar zai fahimce ta, sai kuma ya ce "Na rantse da Allah Zainab idan baki bar nan ba zan mugun saɓa miki, wai ina wasa dake ne, dan ubanki ke ba zaki iya taimaka mata ba, ba zaki tsaya tare da ita ba kina mace wawiya kawai". Zainab ta juya izuwa cikin dakin ta na tafiya tana waigawa tana kallonsa, ita dai bata ga laifin da mace za tayi har a shareta a irin wannan halin ba. Shi kuwa ta cikin wayar take tambayar sa cewar ya yi wa iyayen nasa magana, ya ce ai gobe suna hanya. Ta ce "Sir ko nazo na taya ka hira ne?" Ya ce "Da kuwa naji dad'i wallahi?" Ya faɗa ya na ce ko wasa take yi. Ta ce "Tom bani minti ɗaya?" Yayi dariya ya na cewa ya bata. Minti ɗaya kuwa ta ce ya shigo ɗaki tana ciki ta na jiransa. Yayi dariya har yana riƙe ciki. Ya ce "To ai ko aljana ce ba zata iso yanzu ba, bare kuma ke" Haura ta ce "Wai kana ce da wasa nake ne, ka shigo ina ciki a kwance?" Habib ya ce "Ni ba wannan ba, wai dama Daddy ba shi ne ya haife ki ba, kuma dama shima sonki yake yi shi zai aureki?" Ya tambaya domin shi tun ɗazu abun ya tsaya masa a rai. Haura tayi shiru tsoro na son kamata, har yaushe ya samu damar yin wannan maganar. Jin shiru yasa ya ce "Hello" har zai sake cewa wani abu yaga an bude ƙofar ɗakin nasa an fito. Duk da a zaune yake amma sai da yayi tsalle sama ya dawo kan kujerar yana yin wurgi da wayar hannunsa. Ta ce "Meye haka? Tun ɗazu fa nazo ina ciki ne fa" ta faɗa ta ƙarasowa kusa da shi. Habib dai har lokacin a tsorace yake gabansa na faɗuwa, haka yana ji ta zauna a kusa da shi sai kuma ta kama hannunsa. Ɗaki suka koma suka cigaba da hira, ta sake yin amfani da wannan damar ta rufe masa baki. Sai kusan karfe sha biyu kafin ta bar gidan. Bangaren su Nadiya kuwa sai kusan sha biyun suma ciwon ya lafa, hakan yasa Zainab dole ta kwanta a ɗaki, ashe ba aihuwa ba ce, kawai abun da ta gani ne ya furgitar da ita. Cikin dare ta miƙe ta shiga toilet da ƙyar domin sai da ta dafa bango. Kuma har lokacin jiri na kamata, amma kaman yadda ta sabarwa da kanta haka ta ɗauro alaula ta fara Sallah a zaune. Sosai take ta yin Sallah tana kaiwa Allah kukanta, domin tabbas ta yarda cewar Haura ba haka ta bar Habib, bayan ta idar taji kamar ta je ɗakinsa ta duba shi amma ba zata iya ba. Maganin da aka basu a asibiti ma yana cikin motar basu kwaso ba. Haka ta kwanta tana ta tunani, tana tuna to kenan gurin boka taje aka yi masa a siri ko me, kenan dai da gaske ne abun da ya faɗa akan ta. Dama ace mutuniyar kirki ce, da ita da kanta zata bari Habib ya aureta saboda irin son da yake mata, amma irin waɗannan matan masu zuwa gidajen bokaye ba'a taɓa yarda da su. Kuka take yi sosai, wai yau itace bata da lafiya aka haɗa Bebb zuwa kusa da ita. Washegari Zainab bata da class sai na yamma, hakan yasa ta tashi da wuri ta ɗora musu abin kari. Bata gama ba sai kusan takwas da wani abu. Ta jera musu a gurin cin abincin tannan ta shiga ɗaki ta kira Nadiya. Haka ta fito daga ɗakin sai da Zainab ta kama ta domin da ƙyar take tafiya, cikin yayi ƙato yau ko gobe. Ta ce "Ina Habib ɗin?" Tana rufe baki sai Gashi ya fito waya a kare kuma cikin shirin fita saboda haura ta ce masa yazo ya Kaita school karfe tara take da takarda, ya ce zai ci abinci ta ce yazo zata girka masa, hakan yasa ya shirya da sauri ya tito. Zainab ta ce "Yaya ina kwana?" Ya ɗaga mata hannu alamar amsawa. Nadiya ta ce "Bebb!" ta faɗa a hankali, itama ya ɗaga mata hannu ya nufi hanyar fita. Zai buɗe ƙofar kenan yaji an turo an shigo. Da sauri ya cire wayar a kunnensa yana kallon mai shigowar. Itama Nadiya kallon ƙofar palon tayi, Zainab ma gurin take kallo domin da ƙarfi aka turo ƙofar. Mama ce ta shigo sai kawunsa biye da ita a baya. Da sauri ya ce "Mama ina kwana?" Ya faɗa a rikice. Ta ce "Ban kwana ba, koma ka zauna?" Ya ce "Mama bari na dawo sauri nake yi ana jira na nane, wallahi yanzu zan dawo?" Mama ta ce "Wallahi idan baka koma ba sai na ɗauke ka da mari wawa kawai mara hankali". Habib ya riƙe Kamatu yana kallon Mama jin batun mari. Ta ce "Ko Ba zaka zauna bane?" Ta faɗa da tsawa. Ya koma ya zauna. Ta kalli Nadiya da hawaye suka wanke mata fuska. Ta ce "Wai me ke faruwa a gidan nan ne? Ke Nadiya dake nake, nasan ke ba zaki min karya ba, me kika masa?" Nadiya ta fashe da kukan da tun ɗazu take son yi, tana jin kamar ta haɗiye zuciya ta mutu zaɓar zafin da take ji. Ganin dai kukan nata yaƙi tsayawa ne yasa ta dawo da kallonta ga Habib ta ce "Ne ke faruwa a cikin gidan ka? Wacce yarinya ce kace aje tambaya maka auranta yau?" Gaban Nadiya ya faɗi jin batun aure, take kukan nata ya tsaya ta ƙurawa Habib ido da yake ta cika yana batsewa. Mama ta daga masa tsawa. Ya ce "Eh Aurenta zanyi Saboda ina sonta...📝 S-Reza... [09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *FCWA* *20* Mama ta ce "Saboda kana sonta?" Habib ya ce "Eh Mama ina sonta kuma yau muka yi da iyayenta akan zan tura aje gidan su a tsayar da magana" Mama ta kafe Habib da ido ta rasa me ma zata ce masa, sai ta dawo da kallonta ga Nadiya da itama shi take kallo. Ta ce "Habibu Lafiya kuwa kake?" Ya amsa da cewa "Mama lafiya nake mana, me kika gani?" Kawunsa ne ya ce "A ina yarinyar take, kuma yaushe kuka haɗu da ita da har za kai nema maka aure ba tare da anyi bincike kanta ba?" Habib ya ce "A makarantar da nake koyarwa muka haɗu da ita, kuma har gidan su na sani zan raka ku idan zaku tafi sai muje tarw". Mama ta ce "To ba zaka aureta ba, na ce ba zaka aureta ɗin ba, muddin nice na haife ka to wallahi ba zaka ƙara aure yanzu ba, saboda baka da hankali kalli halin da matarka ke ciki, amma kai tunanin ƙara aure kake yi, ko wani abun ta yi maka wanda bai dace ba shine za ka yi aure domin ka rama, to ban yarda ba na faɗa maka". Habib ya ce "Nifa ina sonta, kawai kiyi hakuri amma dai sai na aureta wallahi, zuciyata ta kamu da sonta gaskiya ayi hakuri a bar wa rai abun da yake so?" Ya faɗa ya na mikewa tsaye dalilin kiransa da take ta yi. Daga Mama har kawun da Nadiya da Zainab sake baki sukai suna kallon sa har ya bar palon. Zainab ta ce "Mama Allah yaya tsoro yake bani yanzu, haka fa jiya ya dinga min ihu kamar zai mareni". Nadiya kuwa marar ta ce ta ƙulle tun ɗazu da taji batun aure, hakan yasa ta kasa cewa komai sai fama da take yi da marar. Zuciyarta na raya mata yanzu kuma auranta zai yi, har yake iya faɗin irin wannan maganar a gaban mama, tabbas wannan abun azumin ne, ta ƙara yarda da cewar Haura asiri tayiwa mijinta, hakan yasa ta ƙara jin irin radade na ratsa ta. Ganin abun yafi ƙarfinta ne yasa ta kurma ihu tana durƙushewa a gurin. Wani irin azaba ne ya fara ratsata wanda bata ma san cewar ihu take yi ba. Sunan Allah kawai take kira tana kuma dafe bayanta ta na fadin "Innalillahi Mama baya na, zai tsage mama, mara ta, cikina, Mama ki taimaka min Zainab, mara ta mama Waiyoo Allah innalillahi wa inna'ilaihi rajiun". Lokaci ɗaya palon ya rikice da salati suna kama ta. Mama ta ce "Zainab je ki duba ko bai tafi ba ya kaimu asibiti da motar tasa kaman aihuwar ce ta zo". Zainab ta fita da gudu amma tana zuwa har ya bar gidan, haka ta dawo ta sanar musu. Dole Kawu ya fita ya samo musu mai dan sahu suka nufi asibiti. *°ADAM* Zazzaɓi ne mai ƙarfi ya riƙe shi tun jiya, hakan yasa bai ko iya fita ba yana ɗaki yana ta tunani shi kadai. Babu yadda Amera bata yi da shi ba akan yaje asibiti ba amma ya ce babu komai kawai ɗan ciwon kai ne zuwa an jima zai daina. Ganin yadda yake ta rawan sanyi ne yasa ta kira Khadijah ta faɗa mata. Ai kuwa ba'a fi minti goma ba sai gata tare da Najib duk hankalinsu a tashe. Suma babu yadda ba suyi da shi ba amma ya ce ba zai je asibiti ba. Haka dole Najib ya kira masa abokinsa likitan da suke zuwa asibitinsa. Nan take kuwa ya duba shi ya bashi magani ya saka masa ruwa, sannan ya bar sauran maganin da za'a dinga bashi. Da Najib ya tambayi abin dake damunsa sai ya ce kawai damuwa ne da gajiya da kuma yawan tunani, dan Allah kwantar masa da hankali koma me nene ke danun sa. A haka likitan ya tafi. Duk yadda Najib yaso jin abun da ya faru har ya shiga wannan damuwar Amera ta ce bata sani ba. A gidan suka uni har bayan sallar magriba, har ruwan ya gama shiga kuma babu laifi jikin nasa ya ɗan yi kyau amma har lokacin yana jin jiki. Gaba ɗaya a kusa da shi suka uni, daga Amera har Haura da su Khadijah, suna ta jansa da hira yana amsawa sama-sama. Ita dai Khadijah haka kawai bata son wannan haura ɗin, ko yanzu bata cika amsa mata magana, kuma tasan wannan ciwon bai wuce nasaba da ita ba, itama Haura ɗin da ta fahimci haka sai ta manta da ita, bata ko shiga sabgar ta. Washegari Haura ce tayi musu girki wanda ko kichin ɗin ma bata shiga ba, Amera dai yau sai bin ta da kallo take yi lokacin da take jere abincin. Sosai take nazarin yarinyar, tun da ta dawo take yin abubuwan kaman farkon zuwanta, karan farko da Amera ta zargi ko dai har yanzu bata bar yin tsafin bane, wata zuciyar kuma ta ce kodai wannan tafiyar da tayi cen gurin ƴan uwanta taje ne. Take Amera ta miƙe tsaye ta nufi gurin abincin ta buɗe tana kallonsa. Ta ce "Haura yaushe har kika girka wannan abincin?" Haura tayi wannan murmushin nata mai shigawa mutum rai ta ce "Kina barci lokacin da nayi" Sai kawai ta kawar da wannan maganar ta ce "Haura zo?" ta faɗa tana kamo hannunta. Haka ta jata har cikin ɗakin da Adam ke kwance. Sosai Amera ta tausaya masa, tasan duk saboda yana son ta ne yasa wannan ciwon. Tabbas ta yarda yana son Haura, kuma zata taimaka masa domin dama tayi masa alƙawari. Suna shiga ɗakin Adam ya mike zaune yana binsu da kallon mamaki. Amera ta ce "Gashi nan a gaban ki haura sabo da yana sonki ne kwanta rashin lafiya, mutumin da ya mayar dake mutum lokacin da baki da maraba da dabba, mutumin da ya shiga damuwa da matsaloli duk saboda ke, wanda ya toshe kunne daga maganganun mutane akan ki ya riƙe ki, wanda ya bar..." Adam ya ce "Amera meye haka?" amma ta ɗaga masa hannu ta ce "Barni na faɗa mata ko ita wacece idan ta manta" ta cigaba da fadin "Ke duk duniya kina tunanin akwai wanda ya dace ki aura da ya kai Adam nagarta, yanzu kina da tabbacin masu zuwa auranki idan suka ji ke wacece zasu aura wa ɗansu? Haura wallahi muddin wani abu ya samu mijina zan nuna miki iyakar ki, nafi son mijina fiye da komai, ina baki shawara akan ki rabu da wannan mutumin domin ki rufawa kanki asiri, ba wai ina tallata miki mijina bane domin bana sonsa, ina son abun da yake so ne saboda irin halaccin da yamin a rayuwa" Amera ta ƙarasa ta na kuka mai karfi. Haura kuwa idanunta a ƙeƙashe sai dai tausayi sun baiyana a fuskar ta ganin irin kukan da Amera ke yi. Kaman zata yi kuka ta fara magana kamar ba ita ba da bata wani yin dogon magana a gaban su "Anty na sani na san komsi, Adam shine yamin komai tun ban san kai naba. Amera ta kalli Adam shima ya kalleta jin sunansa ɓaro-ɓaro a bakinta, abun da bata taɓa yi ba tun da tazo gidan tun ma lokacin tana ƴar aiki ƴar mabaraciya. Ta cigaba da fadin "Wallahi ina son Habib ne, zuciyata shi take so, bana jin zan iya zaman aure da Adam dan Allah ku saurarwni kumin uzuri, amma ina sonsa Adam so irin na ƴa da uba, dan Allah kuyi hakuri ku bar wa rai abun da yake so" Adam ya ce "Ya isa haka, abar wannan maganar daga yau, bana son a sake yinta" Adam ya faɗa a hankali. Amera ta ce "Kin bani mamaki, kuma ki sani wallahi idan har iyayen sa basu zo yau ba, sai dai ki kaishi cen garinku a ɗaura miki aure, ba dai kin ce a bar wa rai abun da yake so ba, an bar masa, an bar shi da abun da yake so ɗin" Adam ya ce "Amera ya isa haka na ce ko?" Haura ta ce "dan Allah Anty kiyi hakuri, raina ne ke so kuma ba zan iya hana ta ba, zan iya mutuwa idan ban auresa ba" Daga haka suka bar ɗakin. Abincin da kowa baici ba kenan. Adam na toilet yana wanka ya hango motar Habib ta shigo gidan, sai ga haura ta fito riƙe da kular abinci ta shiga motar sun tafi. Ya na fitowa yaga Amera zaune a ɗakin ta kawo masa abinci da ruwa. Duk yadda ya ke cewa ya ƙoshi amma haka dole sai da yaci ta bashi magani ya sha ta ce "Ina so na faɗa maka wata magana amma ban san yadda zaka karɓeta ba?" Ya ce "Kar kimin wannan maganar domin ta wuce a gurina" ta ce "ba ita ba ce" ya ce "Ina ji?" Ta ce "Kayi hakuri kabar Haura ta auri wanda take so kaman yadda ta ce, domin yau kwana uku ina yin istahara akan lamarinka da ita bana ganin alkairi, kar kayi tunani ko kishin ta ne yasa nake faɗa haka, a'a ko ɗaya domin Ni kaina a yanzu zan so kayi auren domin samun natsuwarka, idan har ka hakura da ita ni da kaina zan nemo maka matar da zaka aura mai nagarta da asali, amma dan Allah ka cire Haura a ranka, tabbas ba alkairi bace. Adam yayi shuru a ransa yana jin ba zai iya daina son Haura ba, sai dai kawai ya daure zuciyarsa har Allan da ya saka masa ya cire masa. Ya ce "Honey ki kwantar da hankalinki babu komai kuma na yarda ta auri wanda take so. Kuma na gode da ƙoƙarin ki a gareni, Allah ya sauke ki lafiya?" Ta ce "Sannan ina zargin wani abu, amma ina so kawai ka dage da addu'a da karatun Alkur'ani mai girma domin Allah ya tsare mu, kai sheda ne akan abun da ya faru damu a baya na sakaci da addu'a, dan haka yanzu dole ne mu dage da karatu a kowani lokaci da addu'o'i" ta na faɗa ta tashi ta ɗauko masa Alkur'ani ta kawo masa itama ta ɗauko. Dama yaran tun ɗazu suka tafi school abun su. Sai da ta fara karantawa kafin shima ya fara. Sun Dade suna yi kafin su kayi addu'a ya sakar mata murmushi yana jin wani natsuwa na shigarsa a karon farko. Ta ce "Naga barci zaka yi to kayi addu'ar kwanciya barci" bata bar ɗakin ba sai da barci ya ɗauke shi dalilin maganin da ya sha. Sai da ta sake masa addu'a kafin ta fita. *°HAURA* Koda ya zo kusa da school ɗin ya ce shi ba zai ƙarasa ba, saboda baya so a ganshi. Haka ta sauƙa ta ƙarasa a ƙafa ta ce idan ta gama zata kira shi sai ya mayar da ita. Ta na shiga school Allah yasa da sauran lokaci. Nan take ta shiga ta zauna tana tunanin maganar Amera, wallahi ba dan tana tausayin Adam ba sai ta sa zaman gidan ya gagari Amera, amma yanzu ma tasan yadda zata yi da ita. Ta na cikin tunanin Maryam ta shigo class ɗin ta zauna kusa da ita tana mata magana. Ƙarfe goma suka tashi, tayi nufin kiransa amma tabi Maryam suka tafi gida, Maryam na tambayar ta batun Malam Habib amma take ta kawar da maganar. Koda taje gida ta samu ko ina fess, ga wani irin turaren wuta mai yaji da ya fara shiga mata hanci da ido. Da sauri ta shige ɗakinta tana tari tana zagin wanda ya kunna wannan abun. Ta na shiga ta kira Habib sai dai bata shiga. So take ta tambaye shi yaushe zasu zo domin tayi musu girki mai rai da lafiya wanda basu taɓa cin irinsa ba. Wanka ta shiga tana fitowa ta saka kayan zaman gida doguwar riga da gajeran wando. Ta sake gwada kiran number sa, ta na shiga ya ɗaga. Ta ce "Sir yaushe zasu zo ne baka faɗa min ba?" Ya ce "Wai sai da yamma zasu so" ta ce "Na dawo gida kuma ina son ganinka?" Ya ce "Nima ina gida yanzu ma na tashi a barci kuma babu kowa a gidan ban san ina suka tafi ba" ta ce "Sir ko nazo na taya ka hira?" Ta faɗa domin dama tana son barin gidan nan saboda wannan turaren wutar ya fara shigowa ɗakinta. Shi kuwa Habib dama kawai yana son ganinta ne, shi fa a yadda yake ji baya son yana yin nesa da ita ne kwata-kwata. Ya ce "Eh Please kizo yanzu" ta kashe wayar tana dariya. Ba suyi minti biyar da wayar ba ta iso cikin gidan nasa. Tana zuwa yaji kamar an masa kyautar yanke talauci tsabar farinciki, harga Allah shi kullum ƙara sonta yake yi, kuma kullum ƙara yi masa kyau take yi. Wannan karan kam ba iya hira suka tsaya ba, sai da suka yi romantic sosai, dan har kaya sun cirewa juna, amma bai yarda ya shigeta ba. Bayan sun gama suka dawo palo suka zauna ta yi musu girki suka fara ci. Shi idan yana tare da ita har mantawa yake da kowa da komai a rayuwarsa, yana jin idan babu ita ba zai iya rayuwa ba. Ta kwanta a ƙan cinyarsa yana shafa gashin ta, suna hira sam-ama. Sallamar da suka ji ce tasa suka mike tsaye. Mama ce da Zainab sai Nadiya a bayansu wacce itace karshen shigowa. Dama tun da suka je asibitin suke kiran number sa, amma baya ɗagawa, cikin ikon Allah Nadiya ta haifi yarinyarta mace mai kama da ubanta. A asibitin suka samu kayan jarirai suka saya na sanyi, ganin babu wata matsala ne yasa aka salamesu domin da kanta ta aihu. Kawu ne ya biya komai na asibitin suka kamo hanya. Tun a asibitin Nadiya ta faɗa musu iya abun da ta sani tsakanin ta da Haura da kuma Habib da Haura. Hakan yasa mama ta ce ba lallai idan asiri bane amma idan ma haka ne zasu taimaka da addu'a, sannan kar kawun ya yarda yaje nema masa auran kowacce yarinya. Suna tafiya tana faɗa musu labarin farkon haɗuwar ta da Haura ta online har lokacin da Adam ya koreta, anan ne Mama ta yarda da cewar aikin asiri ne. Lokaci ɗaya suka haɗa baki wajen kiran sunan Allah saboda abun da suka gani. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Suka faɗa suna ɗorawa da Auzibillahi mina-sheɗanun rajin . Mama ta ce "Habibu me zan gani haka, iskanci a gidan aureanka?" Habib kuwa a karon farko da yaji wata iriyar kunya, ya shiga kare jikinsa. Haura kuwa a bayansa ta shiga ɓoyewa tana jin itama kunyar na kamata, ko babu komai ai Mama suruka ce bai dace ta ganta a haka ba. Mama ta ce "Wacece wannan?" Ya ce "Itace yarinyar da nake faɗa miki ɗin?" Mama ta shiga tafa hannu, sai kuma kuka ya biyo baya. Nadiya ta kalli Haura ta ce "Duk abun da kika yiwa mijina in sha Allahu sai ya dawo kanki". Habib dai ya kasa magana domin ji yake kamar yaje ya rungume Nadiya, sannan ganin Zainab riƙe da jariri yasa zuciyarsa har tsalle take yi, ga kuma babu ciki a jikin Nadiya, idan ya haɗa lissafin daidai to Nadiya ce ta aihu, amma wata zuciyar ta na nuna masa Haura a kusa da shi. Mama ta ce "Ke kuma shegiya kafura tsinanniya idan baki zo kin bar gidan nan ba sai na sa an karya min ke?" Habib ya ce "A'a Mama dan Allah kiyi mata a hankali wallahi ina sonta?" Ya faɗa yana riƙe Haura da sai yanzu ta samu ƙwarin gwuiwa. Mama ta ce "Habibu karuwar kuma sheɗanuyar mai bin bokaye ita kake so?" Ya ce "Wallahi ba ƙaruwa ba ce, kuma bata bin bokaye, Allah mama Haura mutuniyar kirki ce kuma tana sona". Haura ta ce "Wallahi Mama ina sonsa babu abun da ke zuciyata sai alkairi dan Allah ki bar wa rayuka abun da suke su dan Allah Mama?". Zainab ta ce"Wallahi Mama ba haka kawai ta bar yaya ba, anya ba za'a kira malamai ba ko zasu taimaka mana, ni dai ban yarda da ita ba?" Nadiya ta fashe da wani irin kuka mai ratsa zuciya jin abun dake faruwa kamar shirin flim, wai Habib da babu ruwansa da mata shine yau yake faɗin hk. Mama ta ce "Ina alkairi a gurin wacce take bin maza a waje har cikin gida?" Adam ya ce "Mama nine fa na kirata, kuma aure zamu yi, ni na yarda da ita zuciyata na so, haka raina ma, dan Allah mama a barni da ita, a bar wa rai na ita idan na rasa ta zan iya mutuwa...📝 S Reza ... [09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *FCWA*                                *21* Mama ta ce "To kuwa sai dai ka mutu ɗin, domin ba za'a bar wa ran abun da yake so ɗin ba dan ubanka" Ta na faɗa ta na ƙaraso wa gurin da yake, ta ci gaba da daɗin "Sakar mata hannu ta bar gidan nan na ce ko na saɓa maka mutumin banza mutumin hofi kawai?" Habib ya ce "Dan Allah Mama kar ki..." Kafin ya ƙarasa ta ɗauke shi da mari wanda sai da Haura ta rintse ido domin ji tayi kamar ita aka mara. Tun da su Mama suka shigo take ta ƙoƙarin ganin ta rufe mata baki amma kaman yadda ya faru akan Nadiya itama haka Mama. Babu yadda batayi ba amma sai abun ya tafi sai kuma ya dawo. Habib ya ce "Mama kimin duka amma dai wallahi ina sonta kuma sai na aureta" Haura ta shige cikin ɗaki da sauri ta saka kayanta. Gabanta ne ke ta faɗuwa taji kamar ana kiran sunanta. Haka ta fito daga ɗakin zata fita amma Habib ya riƙe mata hannu. Ta ce "Sir ina sonka babu wanda ya isa ya raba mu, kai dai ka tabbatar ka turo anzo gurin Daddy yau kaji?" Habib ya ce "Idan ma basu zo ba ni zan zo da kaina" su dai suna tsaye suna kallon ikon Allah. Haka Haura ta fita. Mama ta bi Habibu da kallo ganin ya shige ɗakinsa bai ko ƙara bi ta kansu ba. Ta ce "Tabbas wannan ba Habibu na bane" Ta faɗa tana sakin kuka. Ta ce "Zainab shiga ki haɗa mata ruwan zafi, ta samu tayi wanka, sannan ku saka na jinjirar idan na dawo zan mata wanka". Haka Mama ta fita Nadiya kuwa a gurin ta zauna ta fara tunanin abun yi, tana kuka tana tunanin yadda zata dawo da mai gidan ta cikin hankalinsa. Kusan minti ashirin sai ga Mama tare da wani malami sun shigo gidan, har cikin ɗakin habib ta kai shi lokacin yana kwance yana kallon rufin ɗakin hawaye na kwaranyo masa. A wannan lokacin wani irin kewar haura ce ta dame shi, jira yake lokaci ya ɗan ƙara ja ya tashi yaje gidan da kansa ayi magana, domin yadda yake ji idan bai aure ta zai iya zaucewa. Jin anyi sallama yasa ya mike zaune da sauri yana zare ido ganin baƙon fuska a ɗakin sa. Kallo ɗaya malamin yayi masa ya tabbatar da cewar a kwai sihiri a jikinsa. Hakan yasa ya ce a basu guri. Mama ta fita ta koma palo ta kama Nadiya suka shiga toilet tayi mata wanka sannan ta wanke jinjirar. Malam ya fita da kansa ya samo maza guda biyu majiya karfi wanda zasu riƙe masa Habib domin yi masa aiki. Haka suka dawo palo suka yi jikun suna jiran ikon Allah. Haura ta na fita taji kanta na sarawa, hakan yasa ta saka hannunta a cikin bakinta ta gogo yawun bakin nata ta goga shi a goshinta take komai ya tsaya. A haka ta ƙaraso gida ta samu Salim da Nana a palo zaune suna hira. Dama tsakanin ta da Nana har yau babu shiri domin muddin Nana ta zo gidan ta dinga binta da kallon banza kenan. Hakan yasa ko magana babu wanda ya yiwa wani sai Salim ne ya mata Barka da dawowa. Ta na shiga ɗaki ta ware tafin hannunta domin tayi magana da Guber amma duk yadda tayi baya baiyana, take ta shiga tashin hankali, lokaci ɗaya ta tuno da maganar Aminta akan Adam, cewar auran Habib ba alkairi bane Adam ta ke so ta aura. Tsaki tayi a fili ta shiga toilet a ranta tana jin auran Habib shine alkairi ba Adam ba. Tana fitowa ta saka kayan zaman gida ta fito ta samu yanzu harda Salma da Amera duk suna karatun Alkur'ani mai girma. Wanda ganin shigowarta ne yasa amera ɗauko musu domin su karanta, Ita dai bata yarda da ita ba, ba zata manta wahalar da ta sha a irin wannan sakacin ba. Tsayawa tayi tana kallonsu da mamaki ganin suna karatu kuma a fili. Ita da sai yanzu ma ta tuna da cewar rabonta da yin Sallah tun da ta dawo bare kuma karatun Alkur'ani, sosai zuciyarta ke mata wani irin Abu kamar mintsini kamar tafiyar tsutsa, a ranta tana jin bata son wannan karatun da suke yi. Sai kawai ta koma ɗaki ta zauna ta ci gaba da lalubo Guber amma shiru. gaba ɗaya gidan yayi mata zafi ta ɗauki waya ta kira Habib taji a kashe, sai taji kamar ta kurma ihu. Ta sake fitowa ta nufi ɗakin Adam da sauri. Ta na shiga ta samu ya na barci abunsa, ga fuskar nan tasa fayau, har zata zauna taji an buɗe an shigo. Ido biyu sukayi da Amera tsaye tana kallonta. Ta ce "Bayan kince baki sonsa mai kuma kike nema a gurinsa?" Haura ta ce "Anty dama fa akan maganar masu zuwa ne, kawai mun yanke idan sun zo za'a ɗaura auran shine nake so na faɗa masa" Amera ta ce "Idan ya tashi za'a faɗa masa" haura ta ce "Dan Allah Anty.." Amera ta katse ta da fadin "Idan ya tashi na ce Zan faɗa masa dan Allah ki bar shi ya wuta mana?" Tana faɗa ta nuna mata hanyar fita. Haura ta fita tana waigawa kuma tana mamakin sauyin da amera ɗin ke mata yanzu, ko dai ta fara zarginta ne, ta aiyana a ranta. Amera ta dawo ta sake tofe Adam da addu'a ta fita. Nana ta bi Haura da kallo har ta shige ɗaki. *°HABIB* Sosai kansa ya fara juyawa yana jin kamar ana yin sama da shi, lokaci ɗaya ya daina ganin kowa da komai sai wani abu mai kama da gajimarai na sararin samaniya. Shi kuwa Malam sai karatu yake yana kallon yadda Habib ɗin ke ta muzurai yana ƙoƙarin ƙwacewa amma yasa maza majiya karfi sun danne shi yana yin wasu surutai marasa kan gado. Sosai yake ta kararo karatun ayoyin Alkur'ani yana yi. A daidai wannan lokacin kuma a cen garin Garuk Guber ya yi nasara tseratar da Ammi, sai dai abun da bai sani ba shine an ganshi, hakan yasa tun kafin ya dawo aka sanar da Sarkin garin. Ai kuwa dokar garin ce duk wanda aka samu da cin amanar garin to sare masa kai ake yi nan take. Sannan shi laifinsa ma biyu ne, na ɓoye Ammi da kuma na tsera tar da ita, sannan a ka samu tabbacin cewar ya bawa Haura tsafi a ɓoye, bayan kuma ta bar addinin da suke yi, hakan yasa aka gurfanar da shi a gaban fada. Kuma a tsarin dokokin garin Garuk ba'a musu akan abun da kayi, domin komai da kayi za'a nuna maka shine ba wai zargi ko hasashe bane, hakan yasa Guber bai ja ba ya ce tabbas anyi haka, sannan aka nuna komai kamar ana kallon Film. Nan take aka fara karya duk wani tsafin dake jikinsa, wanda hakan na nufin na jikin Haura ma zai karye. Wannan dalilin ne yasa ɗazu Haura ta kasa samunsa, sannan taji kanta na sarawa, kuma taji kamar ana kiran sunanta. A daidai lokacin da aka fille kan Guber, a daidai lokacin ne Habib ya saki wani atishawa mai karfi, ita kuma Haura ta suma a gurin da take. Malam yaci gaba da karatu har sai da ya kai aya kafin ya tsaya. Ya ce "Ku sake shi?" Ya faɗa yana kallon samarin da suka danne Habib. Suka sake shi. Malam ya ce "Alhamdu lillh, tsarki ya tabbata ga Allah buwayi gagara musali!". Kowa yabi Habib da kallo ganin ya ɓingire da barci. Malam ya kalli Mama ya ce "In sha Allahu yana farkawa zai dawo yadda yake" ta ce "Ba zai sake yin maganar ta ba Malam?" Malam ya ce "In sha Allahu babu shi babu ita, dama aljani aka saka masa ajiki yake amfani da shi, ana bawa aljanin umarnin yin abu wanda za'a ga kamar shi ne yake aikatawa, kuma aljanin yanzu haka ba ya tare da shi". Mama ta fashe da kukan farinciki, itama Nadiya kukan ne ya cika mata baki. Malam ya ce "Zan je na dawo kafin ya tashi, zan zo masa da rubutu, kuma ina so nayi muku tunatarwa idan ya farka?". Mama ta ce "To malam muna godiya Allah ya saka da alheri, mun gode sosai sai ka dawo ɗin" Malam ya ce "Kar kowa ya tashe shi da kansa zai tashi". Suka ce to. Haka Malam ya fita ya bar su tsaye a ɗakin sun zuba masa ido. Gashi anyi aihuwa amma tsabar tashin hankali babu wanda aka sanarwa. Haka sukayi cirko-cirko kowa na ta saƙa da warwara a zuciyarsa. Bayan kamar minti arba'in Malam ya dawo, kuma har lokacin bai farka ba sai barci yake yi yana ta sauke ajiyar zuciya. Malam ya shiga har cikin ɗakin ya kunce gorar maganin da yazo da shi ya shiga yayyafa masa ruwan. Ai kuwa da ƙarfi ya zabura ya miƙe tsaye yana riƙe ƙansa. Malam ya shiga tofa masa addu'a na tsawon minti biyu kafin ya dawo hankalinsa. Ya fara bin ƴan ɗakin da kallo. Ya sauke ido akan Mama sai ya nufeta da sauri ya na daɗin "Mama lafiya dai ko? Me ya faru mai kuke yi anan? Ina nadiya? Ya faɗa yana haɗa ido da ita ta take ta kuka. Da sauri ya ƙarasa gurin da take ta rungumeta yana daɗin "Wai me ke faruwa ne? Ina cikin jikinki ya shiga?" Haka ya dinga maganganu amma duk sun kasa amsa masa sai kuka da kuma tausayin sa suke ji. Malam ne ya masa magana wanda sai lokacin ya kula da shi. Ya ce "Ka ce "Alhamdu lillhi?" Habib ya kalli malamin ya kalli Mama, sai ta ɗaga masa kai. Nan ya ce "Alhamdu lillhi" ya na faɗa ya fashe da kuka. Sai da Malam ya bari yayi mai isar sa kafin ya fara bashi labarin abun da ya faru da shi ya ɗora musu da tunatarwa. Ya ce "A matsayin ka na musulmi da Allah ya baka takobin kariya daga mugayen sheɗanu da aljannu har mutane, amma kayi sakaci har aka ci galaba a kan ka, kunyi sakaci na barin gidajen ku babu kariya, sannan kuna barin kawunanku babu kariya, ku daina raina addu'a duk yadda take, idan zaku kwanta kuyi, idan kun tashi kuyi, idan zaku fita kuyi, idan kun dawo ma haka. Sannan ko da kuna aiki ne ku dinga kunna karatun Alkur'ani ku ajiye in sha Allahu sheɗanu ba zasu iya shigowa cikin gidanjenku ba. Wannan azkar ɗin na safe da yamma ku daure ku riƙa yi domin shine takwabin mumini. Sosai Malam ya tunatar dasu wanda suka yi alƙawarin daga yau zasu cigaba, shi kansa Habib ɗin kuka yake yana sake yin na damar abun da ya aikata. Ya taka Malam har waje sannan ya ce da Malam ɗin zai zo har gida ya same shi domin zasu yi magana. Haka ya koma gidan ya samu Zainab ta kunna ƙira'a ta ajiyar wayar a Palo. Lokacin da Habib ya ga jinjirar da aka nuna masa a matsayin tasa sai kawai ya fashe da kuka yana rungumeta. Ya sunkuya har ƙasa yana kuka yana daɗin ta yafe masa. Itama ta sunkuya suka saka yarinyar a tsakiya suna kuka. Ya ce "Ba'ayi mata huɗuba ba" Ya ɗago da sauri yayi mata kiran Sallah sannan yayi mata huɗuba. Ta ce "Sunan Mama ko?" Ya girgiza kai ya ce "Nadiya" Jin haka yasa ta sake fashewa da sabon kuka tana girgiza kai shima ya shiga girgiza nasa kan, ta kasa magana sai kuka shima ya kasa cewa komai kuma. Ita kanta Mama da take bayansu hawaye ne ke mata zirya. *°ADAM* Jin shuru-shuru har bayan sallar la'asar babu masu zuwa neman auren ne yasa ya kira amera ya tambaye ta ina Haura. Ta ce "Gata a baya na a goye" Adam ya ɗan yi murmushi ya ce "Haura fa amanar mu ce kin sani, bana son ki sauya mata da ga yadda kike Please?" Amera ta ce "Ban sauya mata ba, kuma ba zan sauya ba, amma dole nayi nesa da ita domin ban yarda da ita ba, nifa har ga Allah da zaka ji shawara da gida ka kama mata ta koma da nafi sakewa wallahi" Adam ya dawo bakin gadon ya zauna ya ce "Duk akan tace bata son mijinki ko?" Ya faɗa da sigar wasa. Ta ce "Allah na roƙa da ya zaɓa mana alkairi, kuma ya zaɓa mana rashin amincewar tata" Adam ya miƙe tsaye suka fito palo tare. Ya ce "Kira min ita?" Haka dole ta shiga dakin ta sameta a yashe a ƙasa. Ai da sauri ta kira Adam ya shigo yana kallonta. Ruwa ya ɗebo ya watsaa mata. Ai kuwa yana taɓa jikinta ta miƙe zaune. Sai ta fara raba ido. Ta ce "Guber ina Ammita?" Ta faɗa ta na fashewa da kuka. Sai kuma ta ce "Daddy suzo, an ɗaura ko?" Adam da amera dai sai binta da kallo suke yi jin wai Amminta da kuma wani Guber. Take tayi yunkurin yin wani abu amma taji jikinta ya sake, nan take ta gane ba lafiya ba. Ta na kallon tafin hannunta taga babu komai hakan ya tabbatar mata da cewar mafarkin da tayi gaskiya ne. Ta ce "Daddy sir yazo ko?" Adam da tausayinta ya cika sa, kamar ya rungumeta ya rarrasheta. Ya ce "Basu zo ba" ya faɗa a hankali. Amera ta kama hannunsa suka bar cikin ɗakin domin gaf take da wanke fuskar Haura da mari. Sai kuwa ta ɗauko wayarta ta biyo su palon. Ta ce "Daddy dan Allah muje gidan su, Please Daddy help me, yanzu haka ba lafiya ba tunda ai ya ce zai zo?" Ta faɗa tana jin wani tashin hankali domin gaba ɗaya shi take son gani, tsoro da kuma wani madaran san ganinsa ne ya taso mata, babu abun da take hangowa sai yadda Habib ya tsaneta kafin taje Garuk, kenan yanzu ma zai tsaneta, wannan dalilin yasa duk ta fita a haiyacinta. Adam ya ce "Honey please bari na Kaita?" ya faɗa yana jin wani mugun tausayinta. Amera ta ce "Babu inda zaka je wallahi, yau kwananka nawa baka fita, kuma waye sila, sai yanzu daga fara tashin ka, to babu inda zaka je" Haura ta kalli amera ta ce "Anty Please dan Allah ki..." Amera ta ɗaga mata hannu. Ta ce "Daddy to bani aron motar ka Please?" Da sauri ya ɗauki makullin ya bata, ai kuwa ta fita da gudu kamar zararriya. Adam ya ce "Da gaske tana son wannan gayan, Allah ya dawo da ita lafiya, kuma Allah yasa dai lafiya shima yaron, domin naga yana sonta shima" Amera dai bata ce komai ba, domin bata ma so ya bata motar ba, duk da tasan ta iya. Jikinta har rawa yake mata lokacin da ta shiga cikin motar, ta yi mata kii ta bar gidan a guje. Tana barin titin unguwar tasu taje hawa babban Titi bata tsaya duba komai ba ta shiga a guje, hakan yayi daidai da ɗaga wani mai mashin da goyo a bayansa zai karyo kwana ya shiga unguwar ta yi sama da shi ta buga. Lokaci ɗaya jama'ar gurin suka ranƙayo gurin suna salati, domin ta daki mashin ɗin da ƙarfi, kuma sai da yayi sama kafin suka zubo a kan titin, kuma cikin ikon Allah Mai tuƙawar ne ya iya miƙewa wanda aka goye ɗin kuma ko shurawa bai yi ba jine ya malale gurin...📝 S Reza..... [09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️* *FCWA* *22* Da wani irin gudu Haura ta fito daga cikin motar ganin kamar Amminta ce a kwance cikin jini. Ai kuwa ta na ƙarasowa taga ita ɗin ce. Hakan yasa ta kurma ihu tana ja da baya tana kallonta, sai kuma take mata gizo kamar ita kamar ba ita ba. Sai Kuma ta dawo da gudu ta faɗa kanta tana kiran sunanta tana jijjigata. Mutane suka rirriƙeta ganin dai kamar ta na da alaƙa da gawar da ta buge ɗin. Duk yadda suka kai da tayi shiru taƙi sai ihu take yi tana kiran sunan Amminta. Wani ne ɗan unguwar taso da ya gane ta ya nuna har gidan Adam cewar yarinyar ƴar gidan ce. Hakan yasa aka ɗauki gawar aka yi gidan da ita. Ita kuma ta zabura da sauri kamar wacce ta tuna da wani abu,ta hau motar ta sake ɗaukar hanyar gidan Habib. Tana tafiya tana kuka. Lokaci ɗaya ta tuno da abun da Guber ya faɗa mata kafin ya bata wannan tsafin. Ya tabbatar mata da cewar muddin wani daga cikin garin Garuk yasan tana ɗauke da wannan tsafin halhalin kuma ta musulunta to tabbas daga shi har ita sai aljanun sun dawo kansu, yayi mata misali da wani da irin haka ya faru da shi har yanzu ba'a san inda yake ba. Hakan yasa gabanta ya fadi take tunanin Allah yasa Amminta bata ganta, ko kuma Allah yasa ba wani abu ne ya samu Guber ba. A ƙofar gidan ta faka tana tura ƙaramar ƙofar ta buɗe ta shiga. Ƙofar palon ma a buɗe take, hakan yasa ta tura labulen ta shiga ta na kiran sunan sa a karon farko. "Habib!" Ta faɗa da karfi murya ta har wani diri take yi tsabar tsoron da ya cika ta. Lokacin kuma Habib ya fita, daga Zainab sai Nadiya sai wasu daga cikin masu zuwa barka ƙawayen Nadiya ɗin. Ai kuwa suna ganinta kowa ya miƙe jin yadda ta kira sunan da ƙarfi, Nadiya kuwa sai da gabanta ya fadi lokacin da ta haɗa ido da ita, ta shiga karanto addu'o'in neman tsari. Ta ce "Ina Habib?" Ta faɗa ta na kallon Nadiya da take shayar da jinjirar ta. Kafin Nadiya tayi magana Zainab ta wanka mata mari, Haura ta riƙe kumatu tana kallonta zuciya na ɗibanta. Sauran matan suka riƙe baki suna kallon ikon Allah. Zainab ta ce "Itace wannan sheɗaniyar mai bin bokayen da na baku labari" ai kuwa suka ce "Ita ce?" Ta ce "ita ce shegiya" take suka hau jibgarta kamar an aikosu, duka suke mata kamar zasu kashe ta. Ita dai Nadiya bata sa su ba kuma bata hana su ba, domin itama da lafiyar gareta da ta taya su, domin irin su Haura basu da amfani a cikin al'umma. Sai da suka mata shegen duka kafin suka turota har wajen get suka rufe gidan. Ta dinga kuka tana bubbuga get ɗin tana kuma zargin su. Anan ma babu yadda batayi ba domin tayi tsafin saboda ta rama amma babu komai. Nadiya ta kira Habib ta faɗa masa abun da ke faruwa, wanda a lokacin yana gurin Malam ya faɗa masa asalin laifin da yayi tun farko. Malam ya bashi shawara akan ya dage da tuba, kuma babu ruwansa da ita, kar ya sake dukanta koda tazo inda yake kawai dai ya naimi tsari da ita, idan SO samu ne yaje har gidan iyayenta ya faɗa musu abun da ya faru. Tana tsaye a gurin tana ta kuka sai gashi ya ƙaraso. Tana ganinsa ta tsayar da kukan ta nufo shi da sauri tana ka sa ko yin magana tsabar farin ciki. Wannan wani irin so ne take masa, anya kuwa zata moru idan bai aureta abu, take duk wannan zafin jibgar da tashi suka tafi saboda da murnar ganinsa. Tana zuwa kusa da shi ya tare ta hannu ganin tana son rungumeshi. Ta ce "Sir ina ta jiranka, dan Allah kaxo muje a ɗaura wallahi na yiwa Daddy magana ya ce ko kai ne kawai kazo za'a ɗaura, kuma na shiga gidan ka matarka da wasu sun min duka duk saboda da kai" ta faɗa tana ta ƙoƙarin ganin sun hada jiki ga kuma wani sabon hawaye na gangaro daga ido guda ɗaya. Shi kuwa sai addu'a yake yana ta fatan Allah yayi masa tsari da ita, a ransa yana mamakin wai har wannan ya iya zuwa gidan boka. Ya ce "Haura na dawo hankalina, yanzu na san mai nake yi, kuma zan sake faɗa miki, bana son ki, bana son ki, dan haka ki fita daga sabgata dan Allah, wallahi ko mata sun ƙare a duniya ba zan taɓa auranki ba?" Ya faɗa kamar zai yi kuka domin ko maganar da yake yi da ita ji yake kamar dole, ya tsaneta tsana mai yawa. Ta ce "Sir ba zan iya ba, wallahi ina sonka kuma duk abun da nayi saboda kaine Please Sir, kar ka manta kaine ka fara sanina a matsayin Mace, kuma kamin alƙawarin zaka aureni, amma Sir sai yanzu kace ka fasa? Ka manta irin sadaukarwa da nayi maka, na baka komai harda rai na? Wallahi sai da rai nake sonka, idan ba'a bawa raina abun da yake so ban iya mutuwa sir please?" Lokaci ɗaya yayi wani tunani, tausayinta ya tsargu masa idan ya tuno da cewar tabbas shine mutum na farko da ya sameta a budurwa. Ya ce "Shiga motar taki muje gidan naku yanzu" ya faɗa a ɗan sakewar fuska. ta ce "Sai dai kaima ka shiga tawa motar mu tafi tare?" Ya ce "Sai na fasa zuwa" ai da sauri ta shiga, tana tuƙi tana kallon sa har suka iso ƙofar gidan Adam. Yayinda Habib ke cigaba da addu'a da kuma tattauna abun da ya kawo shi. Sai yanzu ma ta tuno da abun da ya faru ɗazu na Amminta, amma lokaci ɗaya sai taga abun kamar fa a mafarki ne ya faru, kawar da wannan batun tayi, ta bari idan na da gaske ne ai zata ga gawar Amminta ɗin a gidan idan ta shiga. Hakan yasa ta sauƙa ta buɗe get ɗin da kanta ta shiga da motar shima haka. Ganin bata ga kowa bane yasa ta fara tunanin to ina aka kai Amminta ɗin, ko har an binne ta. Tana gaba yana baya har cikin palon. Habib ya samu guri ya zauna, haura ta shiga ciki ta kira Adam wanda tare suke da amera suna hira akan fitar Haura ɗin da mota. Bayan sun gaisa Adam ya ce "Sai kuma muka jiku shiru Allah dai yasa lafiya?" Habib ya ce "Lafiya Alhamdu lillhi" ya gyara zama ya kalli Adam da Amera da ita kanta Haura ɗin da take zaune ta zuba masa ido birninta kawai taji anyi zancen aure. Ya ce "Zan so sanin shin kune kuka haifi Haura?" Suka kalli juna. Itama ta lalle su da mamaki. Amera ta ce "A'a ba mu bane gaskiya?" Habib ya ce "Su waye iyayenta?" Adam ya ce "Lafiya dai ko?" Habib yayi murmushi ya ce "Gata nan ta faɗa muku komai da bakinta?" Suka kalleta sai ta ce "Sir dan Allah a ɗaura auran yanzu daga baya sai ayi maganar?" Tayi maganar kamar mai shirin fashewa da kuka. Habib ya ce "Idan kin faɗa musu gaskiya zan yarda a ɗaura mana aure" ta ce "Kayi alƙawari?" Ya daga mata kai. Ai kuwa nan take ta fara basu labarin abun da ya faru, daga lokacin da ta tabbatar da cewar Habib ya gujeta sai ta tafi garinsu. Shi kansa Habib sai yanzu yasan ita ɗin wacece. Amera kuwa tsabar tsoro yasa ta miƙe tsaye tana mata kallon mamaki. Shi kansa Adam bai taɓa kawo cewar zata iya komawa garinsu har ta karɓi tsafi ba. Habib ya ce "Dama ita arnan daji ce?" Amera ta ce "Kaman yadda kaji ta faɗa da bakin ta" Ya ce "Innalillahi wainnailaihi rajiun! astagfurulla! Take ya shiga salati yana tuba har da kuka. Shi kasan Adam hawaye yake yi domin Haura ta goge masa hadda. Amera ta ce "Tsintanciyar mage kenan, akan soyayya, kin bar Musulunci, sannan kin cutar da bawan Allah da matarsa harda mu gaba ɗaya, wallahi kinyi asara Haura, Allah ya wadaran ki, ai dama ni tunda kika dawo naƙi yarda dake, na faɗa masa ya ce wai ba komai saboda shi Man of God ne! Yafi kowa son kyautatawa, ai gashi yanzu kaji da bakinka". Adam ya rasa ma me zai ce. Ta ce "Dan Allah Daddy ka ba shi hakuri, wallahi yanzu bana tare da komai please a ɗaura auran ina sonsa har raina" Amera ta ce "Waye zai ƙara yarda dake Haura, yanzu haka dole ki bar mana gida domin ba zamu taɓa zama dake ba kina mushirika kafura sheɗaniya. Habib ya miƙe zai fita ta yi saurin kama masa Kafa, ya kalleta, sai kawai yaji wani irin ƙyamar kansa da tsanar kansa da jin haushin kansa na kusantarta da yayi, dole ne ma yaje asibiti a duba shi. Ya rasa mai zai ce mata. Sai kawai ya shiga kwace ƙafarsa ya ture ta ya fita. Tabi bayansa tana kuka tana faɗin zuciyarta zata mutu. Wani irin mari ya sauke mata wanda ke cike da ɓacin rai da zuciya da haushi da tuƙuƙin ɓakin ciki, bai ko bi ta kanta ba ya shiga mota ya nufi gida. Yana shiga gida yasa Nadiya ta haɗa duk abun da take bukata su koma gidan Mama. Haka a wannan yammacin ya haɗa komai nasa suka koma. Ya karya layinsa, ya toashe duk wata ƙofar da zata iya samunsa. Sai da ya bar gidan kafin ta iya dawowa cikin haiyacinta. Ta fita waje ta bishi da gudu har bakin babban titi. Daidai gurin da ta bige Amminta ta tsaya tana dube-dube. Ta ƙarasa gurin mutanen da ta gani ta tambaye su ina aka kai matar da aka bige ana. Suka ce "yaushe?", ta ce "ɗa zu". Suka ce ai ba'a bige Kowa anan ba. Haka ta dawo gida duk ta rasa me zata yi. Ta na shiga gidan taga Amera ta na watso mata kayan ta harabar gidan akan ba zasu zauna da ita ba ta tafi garinsu taci gaba da tsafin ta. Adam ya fito da sauri ya kwashe kayan ya shigo dasu yana kamo hannun Haura ɗin suka koma ciki. Ya zaunar da ita a palo har zai yi magana ta miƙa masa makullin motar sa ta na jin kanta ya fara sarawa ga har yanzu ana kiranta. Ta ce "Daddy kayi hakuri ina son Habib zan iya mutuwa idan na rasa shi, ka taimaka min ka kira shi ya dawo?" Duk yadda yaso yayi mata magana ya kasa. Ya kalli Amera ya ce "Zaki iya zama da ita a haka a matsayin kishiya Honey?" Adam ya faɗa har cikin ransa. Amera ta tsaya chak tana kallonsa, wani abu mai kama da sarewa da kuma tsoro ya shige ta. Ya ce "Eh idan har zaki yafe mata zan aureta a haka, Amera nasan zuciyarki mai kyau ce, kuma kin san halin Haura ko wannan abun gaddara ce yasa da kuma yarinta, amma nasan ita kanta tayi nadama" Haura ta ce "Daddy ina son Habib shi kawai zuciyata ke so dan Allah ka taimaka min na same shi, Daddy ka taimakawa rai a bashi abun da yake so Daddy please?". Amera ta riƙe kai ta rasa abun cewa, har ga Allah a wannan matakin muddin yace zai auri Haura to tabbas ta haƙura da auransa wallahi wallahi ko shine autan maza ta bar shi kenan, ai so ba hauka bane, me ya rasa, mai ya gani a jikinta, abu kamar dai shima asirin tai masa. Adam ya ce "Haura Habib ba zai aure ki ba, domin baya sonki, abun da kika yi masa ya sake shi ya dawo hankalinsa, Haura Daddynki yana sonki, shima ransa na sonki ki daure ki ba wa ran Daddy dama da lokaci Haura?" Lokaci ɗaya ta sake fashewa da kuka da ƙarfi ta tashi da sauri ta shiga ɗakinta tana ta ihu zuciyarta na mata zafi. Shima sai ga kukan nan ya fara zuwar masa da hawaye. Ya kalli Amera da itama kukan ya fara biyo kumatunta. Ya ce "Honey zuciyata zafi take min, rai na na sonta ba domin kin gaza a komai ba, haka kawai nake son na taimaka mata. Please ki bani goyon baya na cikawa zuciyata burinta dan Allah ki yarda a bar wa rai abun da yake so please Amera kiyi jahadi?" Amera ta fashe da kuka mai karfi ta ce "A bar wa rai abun da yake so koda mai cutar da shi ne? A bar wa rai abun da zai hallakar da al'ummar da suke tare da shi? A bar wa rai abun da baya sonsa, Honey yarinyar nan ba alkairi bace, wallahi babu alkairi a tare da ita, a hakan zan haɗa miji da ita?" Adam ya ce "Ba halinta bane, nasan wacece haura ta tuba har abada Please Honey?" Amera ta sake rungume shi ta ce "Sai dai ka sauwaƙe min sai ka zauna da ita, wannan shine adalcin da zan iya maka daga kai har ita" Adam ya ce "Ba zan iya ba, kuma ba zan iya ƙin aurenta ba" Amera ta ce "Honey na yarda ka aureta na yarda" Ta faɗa har tana zubo da majina daga hancinta tsabar kuka. Adam ya matseta a jikinsa yana rarrashinta. A cikin daren bayan sallar ishe Adam ya kira Amera ya kira Haura wacce har lokacin kuka yake yi. Babu abun da take kira sai Habib da cewar zuciyarta na mata zafi. Sai da Adam yayi da gaske kafin tayi shiru, gaba ɗaya ta rame tayi baƙi duk ta sauya kama, kamar ma bata cikin haiyacinta. Ya faɗa mata cewar abun da tayi kuskure ne, kuma shirka ne, saboda haka ta tuba kuma ta sake ƙarɓa Musulunci kuma tayi alƙawarin ba zata sake fita ba, kuma ko garin nasu ba zata sake zuwa ba. Anan taso ta faɗa musu abun da ya faru na Amminta amma taga ba amfani domin ta tabbatar hakan ya faru ba anan bane. Haka tayi alƙawarin aka bata kalmar shahada. Sannan Adam ya ce gobe da safe za'a ɗaura musu aure. Tana jin haka ta fashe da kuka. Daga haka Amera ta tafi ɗakinta bata san yaya suka ƙare ba, tayi alƙawarin ba zata sanarwa kowa ba, ta cigaba da addu'a tana kaiwa Allah kukunta akan idan har ba alkairi bane kar Allah ya tabbatar da wannan auran, idan kuma da alkairi Allah ya sanyaya mata zuciya. Ranar batayi barci ba, haka ta kwana tana Sallah harda kuka da hawaye. Ba ita tayi barci ba sai bayan da tayi sallar asuba. Ihun su Salim da Salma ne ya farkar da ita. Jin kukan nasu kamar bana lafiya bane yasa ta kwaso da gudu ganin har rana ta fito. Maza ta gani su biyar Najib kawai ta iya ganewa sai Adam da ya zauna ya dafe kai yana hawaye, sauran kuma da baƙaƙen kaya an luluɓe gawa a palon gidan. Hakan yasa zuciyarta ta yi sama da ƙasa. Take taji kanta na juyawa ta kasa fahimtar abun dake faruwa. Ta ƙyr ta iya fadin "Innalillahi wa inna alaihi rajiun tana nufar gawar da ta buɗe da ƙarfi taga Haura kwance fuskarta tayi baƙi kanta babu gashi, gaba ɗaya a harƙitse take. Abun da ya faru shine... A cikin daren nan shima Adam bai iya barci ba ya tashi ya dinga Sallah yana kaiwa Allah kukansa akan idan Haura alkairi ce ya tabbatar masa. Duk yadda yake jin sonta amma bai manta da zabin Allah ba. Itama Haura haka batayi barci ba, a daren ta fita izuwa gidan Habib wanda zuciyarta ke janta. Duk da nisan gidan haka ta taka a ƙafa a cikin daren. Sai dai koda taje gidan a rufe, anan ta zauna ta dinga rusar kuka tana bubbuga musu ƙofar, ganin kamar a rufe yake ta gaba sai ta kamo hanya tana tafiya tana kuka har gida. Lokacin da ta shiga ɗakin ta ɗauko waya ta shiga kiran sa. Lokaci ɗaya taji an shaƙe mata wuya, take kuma maganar da Guber ya faɗa mata ta dawo mata akan muddin wani abu ya faru zata haukace. Babu abun da take ji a kanta sai sunan Habib hakan yasa itama ta fara kira sunan nata, nan take aka fara abartar da ita, a turata nan a jawota nan. Sanin abun da zai faru da ita ne yasa da hannunta ta ɗauko wuƙa ta daɓa wa kanta. Nan take ta fara shure-shure, duk da haka sai da suka mayar da ita kamar ba ita ba kafin ta mutu. Sosai mutuwar ta taɓa su, musamman ma yaran da suka saba da ita sosai. Shi kuwa Adam sai da yayi jinyar zuciyarsa kafin ya iya saduda. Amera ta ce "Tabbas duk abun da zaka yi ka riƙa saka Allah a ciki domin ya zaɓa maka mafi alkairi" Adam ya ce "Allah ya saka miki Matata ya sauƙeƙi lafiya. Ta amsa da amin. Haka suka cigaba da rayuwa har cikin Amera ya tsufa ta haifi namiji mai kama da babansa. Alhamdu lillhi, tammad bihamdilla, anan littafin A bar wa rai yazo karshe, kurakuran dake ciki Allah yayi mana abuwa ya yafe mana. Abun da ke na faɗakarwa da ilmantar wa Allah ya bamu ikon yin aiki da shi. Yan uwa ayi min afuwa wannan littafin tunatarwa ne gare mu akan sakaci da addu'a, da kuma illar biyewa zuciya, da rai, son zuciya bakinta inji hausawa. Ina muku fatan alkairi daga S Reza....