https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section*👇👇👇👇 👇https://chat.whatsapp.com/JL5uulBkRqf3E8JFFxJm8v MUGUNTA 😈😈😈 by Khairat 🖤🖤🖤 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Allah ya sa yadda na fara lapiya na gama lapiya.. Allahumma Ameen🙏 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Page 1-2 Dare ne sosai, dan a lokacin kusan karfe biyu na dare, a cikin kungirmin dajin hazdabe da ke garin dan masaki a ƙarƙashin karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano. Zaune ta ke gaban mutumin dake gaban ta,tsohone mutumin kuma kato, shirgegen ,baƙin mutum. Jikinsa butubutu wanda idan aka gaya ma bai taɓa wanka ba tsaf zaka yadda saboda baqinsa har sheƙin dauɗa ya ke , ya dago ya kalle ta cike da mamaki yace "Kin binne layar da na baki?" Da kai ta amsa mai alamar "Ehh" cike da tsoro da Kuma firgici a tattare da ita, zufa duk ta gama rufe mata fuska,ya kalli wani kwano a gabansa wanda ƙoƙon kan jaki ne,aka ɗinke sa da wani baƙin zare. Dagowa ya yi ya kalle ta, buɗe bakinsa wanda da alama bai taɓa ganin wani abu wai shi brush ko asuwaki ba. Ƙyalƙyalewa da dariya ya yi a lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai kamar ba shi ya yi dariyar ba. "BARQAAANNN!!!!!!" Ya faɗa cikin murya mara daɗin sauraro wadda cikin amo ya yi ta har sai da kogon da suke ciki ya amsa wanda duk cike yake da kayan tsaface - tsaface,kawunan dabbobi da kuma zanen mutane a jikin bangon dutsen. Wata ƴar tsana ya ɗauko mai kama da mutum sak, "kalli wannan ƴar tsanan ki gani." Ya miƙawa Ladiyo wannan ƴar tsanan. "Tabbas kamar yadda kike so, Ayaman zata wahala a rayuwa, amma kuma zata yi kyakkyawan ƙarshe." Ya faɗa cikin alamar gargaɗi. Baki buɗe ta karɓi ƴar tsanan tana kallo, kalmar da boka ya faɗa na cewa zata yi kyakkyawan ƙarshe shi ne ya tsaya ma ta a rai, lallai bata ga ta zama ba........ ******************************* "Wasshh Allah na, na gajiii." Wata kyakkyawar budurwa da aƙalla ba zata wuce shekara 20 ba ta faɗa ta na zama a kan ƙaramar kujerar dake tsakar gidan, karkashin bishiyar mangwaro. Gida ne mai tsarin ginin bahaushe na asali, tsakar gida mai ɗauke da ɗakuna biyu sai ɗakin soro(wanda yawanci na samari ne). Sai banɗaki babba na amfanin kowa, da madafa babba , a ƙarƙashin bishiyar mangwaron mai bada wata ni'imatacciyar iska mai dadin gaske, ta zauna. Duk da gidan talakawa ne amma ko Ina na cikin gidan a sha re yake tsaf. "Kulululu" cikin wannan budurwar ya yi Kara a lokacin da ta kalli madafar tasu , flask ne a ciki na jollop din shinkafa da taji attaruhu da manja a ciki,sannan kuma ta kalli gefen tulin kayan wankin dake tsakar gidan. Tuno kalaman inna ladiyo kafin ta fita ta yi, ta ce ko da wasa kar ta taɓa ma ta abinci Kuma ta yi wankin da aka kawo aikatau wanda ko sisi bata samu daga kuɗin aikin . Taba idonta ta yi taji damshin hawaye,kallon tsakar gidan da ta yi ne ya tuno ma ta da lokacin da aka shimfiɗe gawar innar ta, nann take wani hawaye ya zubo ma ta a idanu . Mutuwa bata ma ta adalci ba, ta ɗauke ma ta mahaifiya a lokacin da ta ke tsananin buƙatar ta. Kuma har yau bata daina mamakin Ladiyo ba , kasancewa Ladiyon aminiyar innar ta ce wadda a lokacin da ta ke da rai ta ga gata da ƙauna a wurin Ladiyo, bayan mutuwar innar ta komi ya chanja. Tashi tayi ta fara wankin tunda tasan bata da wata mafita da ta wuce wannan ,zafin da ta ji hannunta ya yi shi ya tuno ma ta da ciwon da taji da safe a lokacin da ta ke haɗa wuta. Durƙushewa tayi ta fara tunani, shikenan ita rayuwar ta a haka zata ƙare, cikin yiwa Ladiyo da ƴaƴanta bauta? Ganin tunanin ba shi ne mafita ba ya sa ta tashi ta nufi madafar tasu ta buɗe flask din, tuni yawun ta ya tsinke dama rabonta da abinci tun jiya da yamma da tsahare kawarta,ta kawo mata abincin bikin da su kayi har yanzu gurin magriba ake neman kira,wanko hannunta ta yi tazo ta zauna ta fara cin shinkafar nan ko zafi bata ji, "AYAMAN" taji an daka ma ta tsawa daga bayanta juyawar da zatai ta hada ido da inna ladiyo tana hura hanci kamar zakanya ...... Masu karatu ya kuke ganin wannan sabon labarin kuwa? Meye ra'ayin ku? Ku ajiye min a comment section. Muje zuwa 🏃🏃🏃🏃🏃 https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/JL5uulBkRqf3E8JFFxJm8v 😈😈😈MUGUNTA 😈😈😈 by Khairat 🖤🖤🖤 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 3-4 AYAMAN!!!! Ta ji an daka ma ta tsawa daga bayanta juyawar da za tai ta hada Ido da inna ladiyo tana hura hanci kamar zakanya "Uban wa yace ki taɓa min abinci bayan na ce miki kar ki taba?" Inna Ladiyo ta fada, fuskar nan kamar hadari, kame-kame AYAMAN ta fara yi a kokarin ta na kare kanta amma sai dai jin saukar lafiyayyun maruka ta yi a duka kunchin nata guda biyu ,kuka ta fashe da shi tana ji tana gani inna Ladiyo ke jibgar ta kamar Allah ya Aiko ta . Dayake inna ladiyo irin matan nan ne jibga-jibga. Ayaman kuwa tun tana kuka da iya karfin ta har muryar ta ta dashe. Sai da Ladiyo ta gaji dan kanta sannan ta ƙyale Ayaman, ta tashi ta shige dakin ta, ba jimawa ta fito ,ta shige bandaki ta yi wanka ta fito wanda duk jiqa-jiqa ne ,tana fitowa ta ji sallamar malam isyaku baban Ayaman,kuma mijinta, ya shigo. Koh kallon inda yake Bata yi ba tai shigewar ta daki,malam isyaku kuwa ya kalli inda Ayaman ta ke kwance duk ta jigata ,kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya shige dakin inna Ladiyo... ******************************** Zaune yake gaban halwar tsafin sa,wadda wata kwarya ce sai farin abu kamar ruwa a cikin ta,can yana cikin tsaface-tsafacen sa, a cikin wannan abun mai kamar ruwa,sai ga wasu dokuna farare biyu sai kuma baqi guda daya sun zagaye sa,ta ke wannan fararen dokunan suka rikide suka koma wata halitta mara kyaun gani. Tsugunawa wannan halittun sukayi , sukayi sujjada a garesa (wa'iyazubillah) wani yare suka fara ma junansu kafin wannan halittun suka bace baaattt!!! basu ba alamunsu,dariya ya kece da ita yana faɗin "BARQAAANNN kayi kaɗan kayi jayayya da ni kafin kuma ya dakata da dariya sakamakon ganin wani baqin hayaki yana fitowa daga wannan kwaryar. Sai ga wata mummumar mata ta fito ta cikin qwaryar,kamar ta daya da wannan bokan,"me ya hada ka da BARQAAANNN? Ta fada fuskar nan kamar hadari, hade fuska ya yi ya cigaba da aikin sa,matar kuma buɗe baki ta yi zata tambaye sa sai Kuma ta fasa ta yi wasu irin surqulle ta koma siffar tsaka ta bi bangon kogon ta fice.... ******************************** "Ladiyo? Wai Ina ladiyon ne?" Wata mata wacce baza ta wuce shekara 35-40 ta faɗa tana karasa shigowa dakin,inna Ladiyo ce ta fito daga dakinta tana masifa yayin da malam isyaku ke biye da ita, "Mallam wallahi yau ba kai ba abincin nan, wannan shegiyar ƴar ta ka ta ci da rabonka." Inna Ladiyo ta faɗa tana tura daurin kanta gaban goshi irin ba mutuncin nan, Delu ce ta tsaya tana kallon ikon Allah kafin ta kuma rangada sallama,sai a sannan ne Ladiyo ta lura da ita , "Ahh deluwa sannu da zuwa." ta faɗa tana washe dashashun hakoranta , "Yawwa Ladiyo ta faɗa tana kallon malam isyaku a wulaqan ce , Ladiyo ce ta jata zuwa dakin ta da sauri suka rufo kofa. "Ya ake ciki ne kawata?" Ladiyo ta fada tana zama akan gadonta na ƙarfe, cike da murna da kuma MUGUNTA delu ta ce "Wallahi yau nake jin an fasa bikin lamin binta,." " Kai Amma ma sha Allah haka muke so." Ladiyo ta faɗa fuskar nan kamar anyi ma ta bushara da gidan Aljanna, "Toh yanzu da usainan za ayi bikin koh kuwa ? " Ladiyo ta tambaya. "Bamu tabbatar ba gaskiya amma dai ko ma mene ne bokan nan ya iya aiki wlh." Delu ta ƙarasa cikin mamaki. " Ay aikinsa kamar yankan wuqa haka yake ." ladiyo ta faɗa,ta numfasa sannan tace "Ni yanzu babbar matsala ta wannan yarinyar, Ayaman , kinga duk bayan wahalar da mukasha da zuwa gurin boka aikin nan be yiba,har yanzu samari sai zuwa suke ita kuma Nabila(yar ladiyo) har yanzu shiru sai mazan banza da suke bin ta ga kuma rashin kunya wlh gaba daya ta raina ni a gidan na." Ta ƙarasa cikin yanayin damuwa. "Toh Ina inusa( ɗan inna ladiyo )yanzu?" Delu ta fada tana kallon ladiyo, "Hmmm wannan yaron ay sai a hankali,yanzu fa har dai ya shigo garin nan shike nan na shiga uku daga sata,sai dabanci da yake koyawa yaran mutane yanzu dai har mai garin be kyale ba fah." "Chabb Ladiyo Anya ba uwar yarinyar nan Ayaman ce ta yiwa yaran ki tsafi ba?" Kinga fah duka ƴaƴan ki su ukun ,Nabila yawon banza,Inusa dabanci,ga kuma nafisa da ta shiga yawon duniya,gaskiya ya kamata ki duba lamarin nan Anya ba sa hannu?" Delu ta ƙarasa tana kallon Ladiyo... Sa hannu Kuma delu? Toh masu karatu ya kuke ganin wannan labarin? Khairat 🖤 🖤 🖤....🖊️🖊️🖊️ Nagode,love you all 😘❤️ https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 by Khairat 🖤🖤🖤 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM. Page 5-6 _____________"Gaskiya ya kamata ki duba lamarin nan Anya ba sa hannu?" Inna delu ta fada tana kallon Ladiyo,shiru Ladiyo ta yi sannan tace"Lallai biri ya yi kama da mutum,amma indai haka ne, nasan matakin da zan dauka." Ladiyo ta faɗa sannan suka cigaba da firar su wacce duk yawancin ta munafunci ne da irin sharrin da suke haɗawa a gari.. *AYAMAN (p.o.v)* Tana nan a gurin har aka kira sallar isha sannan ta samu da tashi daga wurin ta rarrafa zuwa akurkin dakinta wanda ko arzikin plaster bai samu ba. Zama ta yi ta fara kuka me ban tausayi,sai da ta yi me isar ta sannan ta tashi ta dauro alwala,ta dawo dakin ta tayar da sallah,bayan ta idar ne ta daga hannunta sama tana kuka ta fara miqa kukan ta ga Rabbil Arshil Azeem sai da taji zuciyarta ta fara yi ma ta sanyi sannan ta rakuɓa ta kwanta a kasan dakin wanda duk kasa ne,ta lulluba da Wani zaninta. "Hasbunallahu wani'imal wakeel" Ayaman ta faɗa sakamakon jin saukar wani ruwan sanyi a jikinta, "Dan ubanki Zaki tashi ko sai na qara zuba miki ruwan?" Inna Ladiyo ta faɗa tana zaro idanu, rarraba idanu Ayaman ta shiga yi kafin ta bi kofar dakin da kallo wanda Inna Ladiyo Bata Dade da fita ba. Saukar hawaye taji a fuskarta, ta yi sauri ta goge su tana girgiza kai tana faɗin "Ba wannan ne lokacin da ya dace nayi kuka ba." tashi ta yi da sauri ta fita daga dakin inda suka yi kichibis da inna ladiyo da bokitin ruwan sanyi zata ta shigo ɗakin saurin tsugunawa kasa ta yi hadi da cewa"Inna ina kwana?' Harara Ladiyo ta watsa mata mai cike da tsana sannan ta ce "Da ban kwana ba Zaki ganni ne? Munafukar Allah da manzonsa sai wani sim-sim ta ke da kai,ki wuce kije ki ɗebo ruwa Nabila zata yi wanka kuma kinsan ba ruwa a gidan kika kwanta kikai ta sharar bacci." "Toh inna". "Keh! Ni fa ba innar ki bace,innar ki ta daɗe da macewa ta bar mana ke annoba kawai." Ladiyo ta faɗa tana tofar da yawu kamar taga wata ƙazanta a wurin. Ayaman ta kalli kanta sai asannan taga yadda kayanta suka jiƙe ga sanyin asuba me razana gangar jiki,a sanyaye ta tashi ta nufi gurin randar su ta ruwa,ruwa ta ɗiba ta shiga banɗaki ta fito ta yi alwala ta koma dakinta. Tsayawa ta yi tana kallon dakin da duk ya jiƙe,rakubawa ta yi a gefe ta buɗe ƙullin kayanta, ta ciro wata doguwar riga ta atampa wacce duk ta koɗe,sakawa tayi sannan ta mayar da hijabin da ke jikin ta,ta tayar da sallah. ******************************** Tafiya take tayi a jikin bango, a siffar tsaka har sai da ta karaso wani gida,madaidaici ne gidan mai shegen kyau duk da kasancewar sa ƙarami. Shiga ta yi cikin gidan,ta shige har ɗakin matar gidan wacce bata daɗe da haihuwa ba,ɗan jariri ne sabuwar haihuwa a kusa da ita,wannan tsakar ce ta lallaba har sai da ta kusa zuwa kusa da jaririn sai kuma ta koma baya da gudu kamar wacce wani abun ya kawo wa hari. Ƙara yunƙurin zuwa kusa da yaron ta yi Amma kamar dazu ta kuma yowa baya,sai da ta yi hakan yafi a kirga kafin ta koma gefe ta tsaya tana kallon matar,charaff ! Suka hada Ido, murmushi wannan matar tayi kafin ta dauke yaron ta fita a dakin,tsakar ce ta tsaya tana kallon matar kafin wani lokaci Kuma ta bace baaattt..... ******************************** Tafiya take cikin nutsuwa,hannun ta riqe da bokitin ruwan data debo daga borehole din garin. "Wallahi ita ce,kin ganta nan duk ta tsufa a gida har yanzu kusan shekarar ta 20 ba mijin aure." wasu mata suka faɗa yayin da suka zo wucewa. A ranta taji zafin abun sosai,amma in ta tuna aure lokaci ne sai hankalinta ya kwanta. "Assalamu Alaikum." ta faɗa yayin da ta ke shiga cikin gidan nasu inna Ladiyo da Nabila ta gani a tsakar gidan suna zaune. Kamar jira Nabila ta ke yi ta hau zaginta, ta uwa ta uba wai tun dazu ɗebo ruwa sai kace an aiki bawa garinsu,ita dai Ayaman bata da tacewa sai dai ta yi kasa da kanta dan tasan koh hauka take baza ta iya faɗa da nabila ba saboda nabilan irin jikin inna Ladiyo gare ta, saboda haka tasan duka zata sha kuma koh bakomi Nabilan ta girme ta. "Ba zaki wuce ki ƙarasa ɗeban ruwan koh kuwa kin tsaya kina kallon mutane kamar kin ga wasu sabbin halittun?" inna Ladiyo ta fada tana kallon Ayaman, wucewa ta yi ta ɗauki bokiti ta fice daga gida. Toh fah!!! Lallai inna ladiyo,toh Allah ya kyauta,masu karatu mene ne ra'ayin ku a kan wannan littafin??? More comment more typing...... Khairat 🖤🖤🖤🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ .... https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈. by Khairat 🖤🖤🖤 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ This page is specially for you zainabu ta 😅❤️ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 7-8 Tana tafiya hannunta riqe da bokitin da zata debo ruwan,har ta iso gurin borehole din garin, duk gurin ya cika, saboda manya da yara haka ake diban ruwa tsayawa ta yi tana kallon su yayin da wasunsu ke faɗa akan diban ruwa . "AYAMAN!!" Taji muryar tsahare babbar ƙawarta tana Miko ma ta hannu,miƙa ma ta bokitin ta yi ita kuma ta ɗebo ma ta ta bata. Gaisawa suka yi kafin suka fara tafiya,tsahare babbar ƙawar Ayaman ce duk da Ayaman din ta girme ta dan tsahare bata fi shekara 15 ba. Amma a haka suke ƙawance da yake tsahare yarinya ce mai hankali da halin manya. Tafiya suke su na hira sama-sama " Ina ladiyo har yanzu tana nan tana gallaza miki ke kuma kina ƙyale ta koh?" Ay na sani ko baki fada dan ganin ki da sanyin safiyar nan nasan akwai lauje cikin naɗi tsahare ta fada tana kallon Ayaman. Numfasa wa Ayaman ta yi kafin tace cikin sanyin muryarta " wallahi tsahare abun yana damuna yanzu jiya da naci abincinta baki ga dukan da ta yi min ba, gashi in nayi aikatau ita ta ke karbe kudin ,ga rashin tausayi duk abubuwan sunyi min yawa tsahare yanzu wallahi ba kiji ciki na yadda yake min ciwo ba saboda yunwa." Ayaman ta fada tana zubar da kwallar da ta taru a cikin idonta,haƙuri tsahare ta bata kafin suka yi sallama. Tun daga kofa take Jin kamshin ƙosai yana tashi,da sauri ta shiga gidan ta tarar da Inna Ladiyo tana suyar kosai a tsakar gidan. "Assalamu Alaikum. Ayaman tayi sallama tana karasa shigowa cikin gidan,hararar da inna Ladiyo ta aika ma ta ne yasa tai ƙasa da kai ta fara cewa " dama inna layi na tarar a gurin diban ruwan shiyasa... " "Shiyasa kika yi uwar ki koh ?" Inna Ladiyo ta faɗa tana kallon Ayamam, rasa me zata ce Ayaman ta yi tsuru-tsuru a gurin,can da ta gaji ta shige dakin ta.... Zan cigaba in Allah ya kaimu gobe... Nagode BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Continued to page 7-8 Tana shiga dakin nata taji muryar inna ladiyo cikin masifa tana fadin " Dan ubanki da kika shiga dakin waye zai karasa miki aikin? Sauri tayi ta fito ta dauki tsintsiya ta share tsakar gidan tass, ta janyo ruwa a rijiya ta fara wanke kwanikan da ba da ita aka ci abincin ba, bayan ta gama ne ta tafi wurin dabbobin inna ladiyo ta share wurin su,tana cikin Sharan ne yaro yayi sallama ya kawo aikatau na surfe kwano 3,inna ladiyo ta amsa ta amshi kudin. Tana fitowa daga wurin dabbobin inna ladiyo ta kalle ta sama da kasa sannan tace "ga surfe nan kwano 3 kiyi sauri kiyi musu zasu dawo yau su amsa". Da "toh" AYAMAN ta amsa mata kafin ta kalli gefen kwanon kosan dake ajiye har ya fara bushewa,inna ladiyo tace "wannan kosan sai kin gama surfen dawar nan sannan Zaki ci" kin jima na gaya miki. Daukar surfen tayi zata fara har ta fara debo ruwa daga cikin randar su taji inna ladiyo na cewa"wannan ruwan bana surfe bane na amfanin gida ne Dan haka kije ki debo Wani" "Toh" AYAMAN ta fada tana daukar bokitin ta fita daga gidan,"saura ki tsaya yawon iskancin ki kar kiyi sauri ki debo ruwan". AYAMAN dai fita tayi ta kama hanyar da zata sada ta da borehole din garin,ta tarar da borehole din ba mutane Dan haka tayi sauri ta dibi ruwan ta kama hanyar gidan,tana cikin tafiya taji muryar Anas, Anas wani saurayi ne da yake tausayin AYAMAN matuka,saboda irin halin da take ciki, "ahh yau ko nema na ba kiyi ba AYAMAN? Idrees ya fada yana murmushi. Murmushi AYAMAN tayi Mai kafin tace "Ina wuni". "lapiya kalau AYAMAN" ya gida? Idrees ya amsa mata gaisuwar tata, "lapiya kalau alhamdlh" AYAMAN ta fada tana kokarin wucewa kar inna ladiyo ta ga ta Dade, Anas ne yace "AYAMAN ya maganar mu ta ranar nan? Kina so na? Rasa me AYAMAN zata fada tayi kawai tayi sauri ta wuce tana murmushi,shima murmushin yayi kafin ya wuce. Inta ce Bata son idrees toh wallahi tayi Karya,Dan Anas ya cika namiji,ka hankali da nutsuwa ga Kuma neman na kanshi,a haka tayi ta tunanin Anas har ta qarasa gida. "Assalamualaikum "AYAMAN tayi sallama,shiga cikin gidan tayi Amma Bata tarar da kowa ba a tsakar gidan ajiye ruwan tayi sannan ta leka dakin inna ladiyo ta tarar ba kowa Dan haka tayi sauri ta debi ruwa tayi wanka da tokar da ta Tara ta shiga dakin ta shirya sannan ta fara surfen Wanda sai da ya dauke ta awa 4 ba tsayawa sannan ta kammala. Ruwa ta Sha, sannan tayi alwala tayi sallah, karar da cikin ta yake mata ne yasa tai saurin fita zuwa tsakar gidan ta dauko busheshen kosan ta zauna ta fara ci, ta cinye Ta sha ruwa ta gode wa Allah,ta zauna tana tunanin rayuwar ta.... Love you all 😘 ❤️ Khairat 🖤 🖤 🖊️ 🖊️ 🖊️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 Written By Khairat 🖤🖤🖤 Na sadaukar da wannan shafin zuwa ga babbar yayata, happy birthday my dearest sister ❤️ ❤️ 😘 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 9-10 Ruwa ta Sha sannan ta yi alwala ta yi sallah, ƙarar da cikinta yake ma ta ne ya sa tai saurin fita zuwa tsakar gidan ta dauko busheshen kosan ta zauna ta fara ci har ta cinye. Ta sha ruwa ta gode wa Allah ta zauna ta fara tunanin rayuwar ta.. Anan muka tsaya yanzu zamu cigaba.... Tuna wa ta yi da rayuwar da sukai ita da innarta da babanta. Sannan kuma tana mamakin halayya irin ta inna ladiyo. Tana mamakin wai aminiyar innar ta ce ta ke Bata irin wannan azabar,kuma mahaifinta yana kallo ba tare da yace komai ba. Tana nan zaune ta ji kiran sallar laasar, tashi ta yi ta gabatar da sallar ta tunda tana da alwala,sannan ta Kai kukan ta ga Allah mabuwayi. Karar bige kwanuka da ake yi a tsakar gidan ne yasa ta tashi daga lazumin da ta ke yi ta leqa ta yagallallan labilan dake jikin kofar dakin. Yunusa ta hango a tsakar gidan a halin maye yana ta tambele, yana magagi irin na yan giya. Tuno abinda ya faru ranar nan ta fara yi, "dimm" taji zuciyar ta ta buga,fara faɗan sunan Allah ta yi a cikin zuciyarta cike da firgici. " Kehh! Shegggiiiyyar yarrriiinnnnyaa." Yunusa ya faɗa cikin muryar maye, "Kin zata bannn gannkii baaannneee! Hhhhh. " ya sheqe da wata irin dariyar ƴan duniya. Ayaman tana daki ta yi tsuru-tsuru,ta ji shigowar mutum dakin, kukan da take riqewa ne ya kufce mata, "Wayyyyooo, dan girman Allah kayi hakuri, ka sani fah idan babu wanda yake kallon ka ka sani Allah yana kallon ka kuma akwai ranar hisabi ." Ayaman ta fada cikin muryar kuka. Sannan ta cigaba da fadin" kada kayi sanadiyyar lalata rayuwar marainiyar Allah, wacce Bata da kowa sai Allah." Ganin duk wannan jawabin ba jinta yake ba, sai dai ma kuma matsowa da yake, damkar kasar dakin ta yi ta watsa mai a Ido sannan ta hankaɗe shi ta fice daga ɗakin. Tsakar gidan ta fita tana Neman abin da zata kare kanta, murhun da suke girki da shi ta dauko, yana fitowa ta daidaici wurin goshinsa sannan ta maka mai wannan murhun. Da gudu ta zura ta fice daga gidan, bata tsaya ko ina ba sai gidansu tsahare. Tana shiga ta tarar da tsahare tana tankade garin tuwo, ganin a yanayin da Ayaman ta shigo ko ɗan kwali Babu a kanta yasa ta kama Ayaman suka zura zuwa cikin ɗakin tsahare suka rufo kofar. ******************************** *LADIYO da DELU* Zaune suke gaban bokan kan tsauni sun rusuna kamar masu neman yafiya, " Na gaya miki ba abunda zamu iya yiwa yarinyar nan,saboda akwai wani babban kariya a tattare da ita." bokan kan tsauni ya fada yana kallon inna ladiyo. Sannan ya cigaba da fadin,sai dai akwai hanya daya,matso kiji, inna ladiyo ta matsa kusa da shi tana kara kunnanta kusa da bakinshi. "Toh shikenan fatan dai ba matsala." , Ladiyo ta fada. "Idan kinga baza ki iya ba ki barshi." boka ya fada yana zazzare idanu. " A'a zanyi boka ." inna Ladiyo ta fada tana mai ƙara russunar da kai kasa. " Ke kuma." boka ya juya yana kallon Delu, mece matsalar ki?" "Na gaishe ka ɗan gidan uwar kowa,bokan da yake ɗaya tamkar dubu."inna delu ta cigaba da yi ma boka kirari har sai da ya dakatar da ita. " Dama akan maganar mijina ne, Ina son a mallaka min shi ya zama babu me iko da shi sai ni." Delu ta numfasa sannan ta cigaba da cewa, "Sai kuma maganar auren diyata , a taimaka boka." , inna delu ta gama fada tana ƙara russunar da kai. " Akan mijin ki, yau da dare misalin karfe uku na dare kije maqabartar dan dolo, akwai sabon kabari da yau aka binne gawar, mutane ma zasu ke su ajiye Wani kullin magani a cikin kabarin, ki je ki dauko maganin daga cikin kabarin ki barbada shi a kan shimfidar ku ke da mijin ki yau da daddare kuma ki tabbatar Kun kwanta a Kai, sannan Kuma kiyi tsarki da shi , ba yannan ki sa a ruwan wankan mijin ki, sannan Kuma kiyi amafani da kwalli da Kuma turaren da na baki kwanaki, sannan Kuma ki tabbatar kin gama komai kafin giftawar alfijir" bokan kan tsauni ya gama fada yana kallon inna delu. Ya numfasa ya cigaba da fadin, "batun diyar ki kuma akwai layar da zan baki ki Saka akan hanyar da mutane ke wucewa,daga nan samari zasu yi ta zuwa" boka ya fada yana kallon inna delu wacce tuni ta fara washe dashashun hakoran ta. " Ku tashiiii ku bani guri la'anannun Allah,tsinannanu" boka ya fada yana kallon su, zumbur suka mike suka kama hanyar fita, kafin su gama fita ya ce " ku kawo min ladan aiki na ranar lahadi da misalin karfe Sha biyu na dare " , " toohh boka",mun gode a Mika mana sako gurin uwarkowa" inna delu da ladiyo suka hada bakin wurin fada sannan suka fice daga kogon" . Suna fita daga cikin kogon suka dauki kayan su suka Saka, saboda dama dokar bokan kan tsauni ce cewar ba'a shigar Mai da kaya cikin kogon, suna saukowa daga kan tsaunin Dan kogon Yana Saman tsaunin. Suna ta tafiya su biyu a cikin dajin ga dare Dan a lokacin kusan karfe Sha biyu na dare,ga Kuma sanyin da ake busawa a garin. Har suka shigo cikin garin suna ta firar su, " delu tace ay ladiyo Muna gama aiwatar da aikin nan sai yadda nayi da malam" ta karasa fada tana washe baki , "toh kafinnan muje gidanki mu huta kafin lokacin yayi mu tafi maqabartar,ko ya kika gani"? Inna ladiyo ta fada tana kallon delu. " Yayi Hakan ma da na gaji wlh" delu ta fada kafin suka cigaba da tafiyar su har gidan delu. BAYAN AWA BIYU DA RABI Delu da ladiyo. Sun fito daga gidan delu sun fara tafiya, hanyar maqabarta suka nufa. Isar su ke da wuya suka durfafa akan sabon kabarin dake farko farkon maqabartar, wuqa delu ta fito da daga jikin ta, ta fara haqa kasar kabarin, ladiyo na gefe tana haska mata hade da kallon delun. Wani hayaki Mai ban tsoro da kauri ne ya fito daga kabarin Wanda yasa suka toshe hancin su. Wani qullin magani ne ya fado daga cikin kabarin ya fada hannun delu, tashi su Kayi zasu tafi, yayin da kasar kabarin ta koma yadda take kamar ba'a taba bude wa ba. Sauri suka yi suka fita daga maqabartar zuciyar delu fess, a hanya suka tsaya suka binne abin da boka ya basu, wacce hanyar zuwa kasuwar garin ce A marrarrabar hanya suka rabu inda ladiyo ta kama hanyar gidan ta ita Kuma delu tayi ta ta hanyar. LADIYO Tana Isa gida ta tura kyauren kofar Wanda ba'a rufe ba saboda mutanen garin kowa yasan kowa ne ba Wanda zai shiga gidan Wani yayi sata. A tsakar gidan tayi kichibis da yunusa kwance jikin jini, sakamakon wata yakai tsakiya shiyasa take iya ganin sa Dan gari yayi haske, razana tayi da ganin shi a Hakan, sai da ta debo ruwa ta watsa mai taga ya farka sannan hankalin ta ya kwanta. Ruwa ta dafa Mai zafi ta taimaka mai yayi wanka ya gasa jikin shi Kuma ta wanke Mai ciwon sannan ta fito daga bandakin, dakinshi dake sauron gidan ta kaishi ta kwantar sannan ta koma tsakar gidan ta zauna. Bata Ankara ba tana ta tunanin waye yayi ma yunusa wannan abin sai ji tayi an kira sallar asuba, tsaki taja kafin ta miqe ta nufi dakin AYAMAN domin tashin ta ta fara bauta. Tana kutsa Kai cikin dakin da ruwa a hannun ta, ta ga ba kowa a cikin dakin, ta duba ko Ina Bata ga kowa ba sannan ta fito tsakar gidan tana mamakin Ina AYAMAN taje..... DELU Tun bayan rabuwar su da ladiyo a kan hanya ta nufi gidan ta, tana shiga ta dauki maganin tayi amfani da shi hade da turaren Dan kwallin sai da safe, ruwa ta tafasa ta barbada maganin a ciki ta Kai bayi. Dakin mijin nata ta nufa,tashin shi ta fara yi har sai da ya Farka, " wai ke delu meye haka ne? Saboda rashin ...... Sai Kuma yayi shiru sakamakon Jin Wani luuuu a kansa da yayi , jansa tai zuwa dakin kafin ta rufo kofar tana tuna gargadin boka na kar ta sake asuba tayi Bata aiwatar da abinda ya sa suba.... Nima anan zan dakata sai mun hadu a shafi na gaba...... Nagode ❤️😘 https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 Written By Khairat 🖤🖤🖤 Wannan page ɗin ma sadaukar da shi zuwa ma karanta littafin MUGUNTA da masu comment, ina godiya I love you lodi lodi🙈❤️‍🩹💋♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️. BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 11-12 Bayan wayewar gari * LADIYO * Tun bayan fitowar ta daga ɗakin Ayaman ta shiga dakinta cike da mamakin inda Ayaman ta tafi, "Ko ba komai dole ta dawo gidan ay." inna Ladiyo ta faɗa tana tashin malam isyaku cike da masifa, " Toh asararrare sai ka tashi asuba ta yi, ko so kake a sake ma wani daren?,kai da ba aikin fari kake yi ba bare baki shine har ka samu damar shan bacci haka." ta karasa faɗa tana kallon malam isyaku. Tashi malam isyaku ya yi saboda kansa da yaji ya fara Sara masa, salati ya yi sannan ya miqe ya fita daga dakin ya bar Ladiyo tana ta sababi. Malam isyaku yana tafe yana tunanin yadda akai Ladiyo take fada masa magana baya daukan mataki a kan ta, sai dai koma meye ya barma Allah dan a gareshi yake kai kukansa. * DELU * "Delu! Delu! Delu! Ke ki tashi mana lokacin sallah ya yi,malam surajo mijin delu ya faɗa yana tashin ta daga bacci. " Malam ga ruwa a bayi na aje ma fah, da shi kayi wanka dai koh?" Delu ta tambaye shi tana mitsika idanu irin na wanda ya tashi daga bacci. "Ehh naga da dumi shiyasa nayi amfani dashi, ki tashi fah." ya gama faɗa yana fita daga dakin. Delu kuwa wani farinciki ne ya cika ta saboda ganin aikin su ya fara aiki dan malam surajo ko da wasa baya shigowa dakinta, wai shi ne yau har da tashin ta daga bacci. Fita tsakar gidan ta yi ta wanke fuskarta ta dau tsintsiya ta fara shara dan sallar asuba ba wani damun ta tayi ba. *AYAMAN* Tun bayan shigar su ɗakin tsahare, ta zauna ta fara maida numfashi sannan ta labarta ma tsahare abinda ya faru. Tsahare sakin baki tayi tana kallon Ayaman"Toh yanzu yana gidan ne?" "Eh Yana chan." "Amma dai Ayaman kinyi min daidai, yanzu Ladiyo ta gane ba tsoro kike ji ba." Tsahare ta faɗa tana jan Ayaman zuwa tsakar gidan. "Taho muje in karasa aikina, ba kowa a gidan." taja Ayaman suka fita, suka cigaba da girkin wanda tuwo ne na masara da miyar busheshen kuɓewa wanda ta ji daddawa da sauran kayan kanshi. "Wai gidan ba kowa ne" Ayaman ta tambaya yayin da suke wanke kwanikan da suka yi amfani da shi. "Ehh duk basa nan, sun tafi biki, ni ce kawai a gidan." Haka suka cigaba da aikin su har suka kammala gab da lokacin da ake kiran sallar magriba. Sallah suka yi suka ci abincin da suka dafa har suka kammala. Mahaifiyar tsahare na dawowa , tsahare ta labarta mata abin da ya faru tsakanin Ayaman da Yunusa. "Kai jama'a, umma ta faɗa (mahaifiyar tsahare) yanzu shi yunusa har lalacewar tasa takai haka?"Gaskiya Allah ya kaimu gobe muje gurin maigari ya dawo da ke hannun mu tunda abu yaqi ci yaqi cinyewa, Ladiyon ba imani ba ga ƴaƴanta marasa ji kuma baza ta tsawatar musu ba." "Badai a gidana ba." mahaifin tsahare ya faɗa yana ƙarasa shigowa cikin gidan, haka kawai, yarinya ba dangin ku ba kun bi so kuke ku liƙa mana ita, yarinyar da ta qi auruwa? Salan ta zo gidana ta shafama yayana baqin jini, toh wallahi baku Isa ba." Ya numfasa ya cigaba da cewa "Yau ne kawai zan barta ta kwanan mun a gida amma zuwa gobe zata tafi." Jiki a sanyaye tsahare ta kalli mahaifin nata tace "Dan Allah baba, wlh Ayaman tana shan wuya gurin Ladiyo kuma naga aure ay lokaci ne in yazo zata yi." Tsahare ta gama faɗa kamar zata yi kuka. Ɗaki umman su tsahare ta umarce su su shiga, Tsahare ta ja Ayaman suka shige ciki. Suna shiga dakin, Ayaman tace "Da kin barni na tafi tunda kinga baba baya so." "A'a Ayaman, gobe kya tafi." tun daga haka suka cigaba da hirar su har dare ya tsala suka kwanta abubuwa da yawa a cikin zuciyar su. *Bayan wayewar gari* A bangaren su Ayaman tun da suka tashi ita da tsahare suka yi sallah suka kama aikin gida basu suka kammala ba sai wajen bakwai na safe sannan sukayi karin kumallo suka shirya domin zuwa gurin maigari. Bayan mahaifin tsahare ya gama shiryawa suka fito daga gidan suka ɗauki hanyar fadar maigari su uku dan umma tana gida bata biyosu ba. *A bangaren LADIYO* Bayan ta tashi Bacci taga rana ta taake sosai, tsaki ta yi ta tashi ta fita daga ɗakin. Tana fita tsakar gidan taga yadda rana ta fito sosai kamar ba sanyi ake ba. Botiki ta dauko zata debi ruwa a randa taga ya qare, tsaki ta kuma yi, ta zauna akan botikin cike da jin haushi ta furta "Zaki dawo ki same ni ne." kafin ta ja kuma jan wai tsakin ta fita da botikin ta ɗebo ruwa ta yi wanka ta dafa taliya. Ta zauna tana ci kenan bafade ya yi mata sallama, amsawa tayi kaana ta dauki mayafi ta leqa. " Lapiya malam?" Ladiyo ta tambaya ganin ba fade a qofar gidan Kuma tasan ita ba laifin da tayi. " Lapiya kalau, maigari ne ya aiko ni ana neman ki a fada." ba faden ya fada yana kokarin tafiya. "Dan Allah tsaya ta tsayar da shi, me nayi? " " In kinje fada kya sa ni." wannan ba faden ya fada kamin yayi wucewarsa ya bar Ladiyo tana tunanin me ta aikata har ake neman ta a fada. Komawa gidan ta yi ta ƙarasa cin taliyar ta sannan ta saka hijabi ta fito ta kama hanyar fada... *Bangaren delu* Bayan ta kammala gyaran gidan ta chanchada kwalliya da kayan sallan ta, doya da kwai ta soya wacce tasa malan surajo ya siyo. Suna zaune a tsakar gidan tana bama mijin nata abinci a baki a lokaci daya kuma wani farinciki ne fal a zuciyarta. "Gaskiya dole na koma wajen boka na kan tudu domin aikinsa yana yi sosai." Delu ta faɗa a zuciyarta tana kallon yadda malam surajo yake nuna ma ta kulawa, mutumin da bai sakin fuska da murmushi shine yau har da fara'arsa . "Ahh ah."inna wannan dabgen ake ja a gidan nan." Mariya ta fada tana fitowa daga ɗakin, nima a zuba min nawa." ta faɗa tana miqo kwano. "Sai yanzu kika tashi mariri yar baba." malan surajo ya fada yana washe baki. Cike da mamaki Mariya ta amsa da "Eh baba na tashi." " Toh sannu da tashi, delu a zuba mata abincin mana." malan Surajo ya faɗa yana kallon delu wacce ta ke ta washe baki dan ji ta ke kamar yau sallah a gurin ta. A haka delu ta yini cikin annashuwa da farinciki Dan Gani take kamar wahalar ta ta yanke..... Sai mun hadu a next page ... Love you all 😘 ❤️ Khairat 🖤 🖤 🖤 🖊️ 🖊️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 Written By Khairat 🖤🖤🖤 Dedicated to MUGUNTA hauda novel readers. BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 13-14 A haka delu ta yini cikin annashuwa da farinciki Dan Gani take kamar wahalar ta ta yanke.... *LADIYO* Tana tafiya tana ta faman tunanin me yasa ake neman ta a fadar maigari. Tana isowa cikin gidan maigari aka yi mata iso zuwa inda maigari yake, zuwan ta wurin ke da wuya ta hango su Ayaman zaune cikin ɗakin. Wata uwar harara ta aika wa Ayaman wanda yasa cikin Ayaman ya kaɗa. Zubewa ta yi ta kwashi gaisuwa kamar ba abinda ta gani wurin maigari, bayan an amsa gaisuwarta ne, maigari ya nemi sanin ko wacece ita a wajen Ayaman. Bayani ta yi akan cewa ita ce abokiyar zaman maman ta tun kafin ta rasu. "Ina mahaifin ta?" Maigari ya kuma tambaya. "Ranka ya daɗe, mahaifinta yana wajen zaman banzan da ya saba, ba aikin fari bare baƙi." ladiyo ta fada tana qara russunar da kai. Maigari ne ya yi umarni da a je a kira mahaifin. Bayan malam isyaku ya iso ya miqa gaisuwa wurin maigari sannan ya yi bayanin matsayin sa a wajen Ayaman. Ayaman aka bukaci tayi bayani akan me yasa batason zaman ta tare da su Ladiyo, ta fara bayani kamar haka: "Allah ya baka yawan rai, inna Ladiyo ta kasance kishiyar uwa mai mara tausayi da imani a gareni, tun bayan rasuwar mahaifiyata wacce aminiyar inna ladiyo ce." Ta numfasa kafin cigaba kamar haka. "Inna ladiyo da ƴaƴanta sun daɗe suna cizguna min a rayuwa kuma na dade Ina jurewa, ina neman alfarmar a nema min wani gurin zama ba wai gidan mu ba." Ayaman ta karasa fada cikin muryar kuka. Maigari ya numfasa kafin ya kalli Ayaman da take ta sheƙar kuka tsahare na rarrashin ta. Maigari ya kuma kallon Ladiyo da malam Isyaku da suka yi tsuru-tsuru a gurin, sannan yace" malam isyaku kaji abinda ta fada ko"? . "Naji ranka ya dade, muna neman afuwa kuma zamu gyara insha Allah ." Maigari ya koma kan Ladiyo yace "ke baki ce komai ba." "Ranka ya dade ay malam ya gama magana, muna neman afuwa kuma baza mu ƙara ba." ta karasa fade tana russunar da kai. "Ayaman, kinji me iyayen naki suka fada, zaki haƙura ki koma gidan da zama ko koh, ki bi ra'ayin ki." "Na hakura ranka ya dade" AYAMAN ta fada tana ƙara matsar kwalla. "To Masha Allahu, dama maslaha muke nema Kuma tunda kin ce kin yafe Kinga shikenan komai yayi daidai" maigari ya fada yana washe baki. Anan wurin su AYAMAN suka kammala sulhu suka koma gida, a hanya ne tsahare ta fadawa AYAMAN abinda tayi bata kyauta masu ba, kamata ya yi taqi hakura har sai an hukunta su ladiyo. AYAMAN dai shiru tayi tana kallon tsahare na masifa dan ta rasa abin fada, dama chan bata so aka kai su Ladiyo gaban Mai gari ba. Haka suka karasa kan hanya inda tsahare da baban ta suka kama hanyar gidan su, ita ma Ayaman suka shige gida... *DARE* Tun komawar su AYAMAN gida ladiyo ke ta nan nan da ita tana lallaba ta har dare ya yi suka kwanta. (An ya kuwa ladiyo) *DELU* A bangaren delu kuwa sai mulki ake zubawa a gidan, dan yanzu malam surajo ya zama tamkar bawan ta (wa'iyazubillah Allah ya cigaba da tsare mu). A yanzu ma kuwa zaune ta ke kan tabarma da nama gashashshe a gaban ta tana ta cillawa baki, hade da lemo na kwalba da ta ke kurba a hankali, yayin da malam surajo ke zaune gaban ta Yana mata firfita. Yaro ne ya shigo gida ya gaishe su kafin ya ce ana sallama da Mariya, baki delu ta washe kafin ta ce " wane yake sallamar da ita? "Alhaji gabatari ne." Fara'ar ta ce ta qaru, kafin tace " je ka ce tana zuwa." "Toh" yaron ya fada yana fita. "Mariya! Mariya! Ina kike be yar baba?" Delu ta daga murya tana Kiran Mariya. "Gani inna." "yawwa maza je ki shirya alhaji Gabatari ne ya zo." "Dan Allah mama" Mariya ta fada tana daka tsalle kafin ta shige ɗakin da gudu. Dariya delu ta yi sannan ta juya ta kalli malam surajo, "Kai kuma ka wani zauna kana kallo na , dallah ka tashi ka bani wuri ka wuce kayi bacci." Sumsum malam surajo ya tashi ya shige dakin ya kwanta kamar wani wanda ake controlling, delu shewa tayi kafin ta ce "lallai malam na kan tudu ba wasa ba." sannan kuma ta ƙara sheqewa da wata dariyar. Mariya ce ta fito cikin shaddar ta blue da mayafi red hade da takalmi da jaka duk red, ga shi ta ci Wata uwar kwalliya da acuci. "Kai, Ma sha Allah, wannan kyau haka maririn baba, kinyi chass abinki." Mariya cike da jin dadi ta kalli uwar ta ta kafin tai ma ta sallama ta fita. Tana fita kofar gida ta tarar da alhaji gabatari jingine gaban motar sa kirar golf irin ta kayan miyan nan. Wata farar shadda ce a jikin shi, sai gilas da ya ƙwama a fuskar shi. Cike da zumudi Mariya ta karasa kusa da shi, Dan ba'a taba kiran Mariya ba wai ana sallama da ita ba. Alhaji gabatari ne ya bude bakinsa wanda in ban da warin sigari ba abinda yake, yace "Barka da fitowa gimbiya sarautar mata, fatan kina lapiya." Wani farrr Mariya ta yi da Ido, kafin ta bude dashashun hakoran ta tace "yawwa alhaji , Ina lapiya ya kasuwa." "Lapiya kalau mariri." alhaji gabatari ya kuma fade. A haka suka cigaba da hirar su har dare ya tsala suka yi sallama. Mariya na shiga gida ta ga delu ta dade da bacci, ita ma ta shige dakinta ta kwanta ba tare da ta damu ta sauya kaya ba. Asuba ta gari!!! *AYAMAN* MAFARKI Wata mata ta hango, zaune akan wata kujerar karfe wacce duk ta yi tsatsa ta lalace, kallon qurilla matar ta ke yi wa Ayaman wanda ya sa tai maza ta tashi ta fara gudu. Tana cikin gudun ta fara hango wani haske mai matukar kyau, ta nufi hanyar da zai kaita wurin hasken ne wannan matar ta riqo kafarta da wata kaca ta qarfe, ihu ta fara yi tana neman taimako. Yayin da wannan matar ke dada janyota, kusa da ita , tazo gab ta ita ne ta farka daga mafarkin. "Hasbunallahu wani'imal wakeel." Ayaman ta fada tana tashi a firgice, kanta ne taji ya sara mata. "innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." ta faɗa cikin tashin hankali, addu'ar da taxo bakin ta kawai take yi kafin ta ji ciwon kan ya ragu. Kiran sallar asuba da taji ana yi ne yasa ta tashi ta fita tsakar gidan nasu, hasken farin wata, da Kuma niimatacciyar iskar asuba ne yasa ta lumshe Ido. Ta Dade a tsaye a wurin kafin ta shiga bandakin da ko arzikin fitila bai samu ba, tsarki tayi kafin tayi alwala ta fito. Dakin ta koma tana tuna mafarkin da tayi. Raka'atanul fajir ta fara yi kafin taji iqama a masallacin unguwar tasu sannan ta tada sallah. Bayan ta idar da sallah ta yi azkhar sannan ta fito tsakar gidan, randa ta duba Taga da ruwa a ciki . Kwanika ta debo ta fara wanke wa, tana yi tana mitar kazantar Ladiyo dan wasu kwanikan har sun bushe ba'a wanke ba. Shara tayi bayan ta kammala wanke-wanken, sai da ta sha re gidan tsaf sannan ta zauna ta huta dan a lokacin takwas ta kusa . Bokiti ta dauko zata debi ruwa, Taga ruwan ya qare, "ya salaam." ta fada tana dafe kanta da hannu. Harga Allah bata son debo ruwa Dan wannan ranar safiyar da zafinta. Ba yadda ta iya, haka ta dauki bokitin ta fita debo ruwa. Kamar kullum gurin borehole din nasu a cike yake da mutane manya da kanana ana ta diban ruwa. "Wallahi na riga ki baki Isa ba" wata yarinya wacce bata wuce shekara 10 ba ta fada tana ture wata budurwa wacce ta Kai kusan shekara 15. "Ni sa'ar ki ce Amina? Iyi ." wannan budurwar ta fada tana hararar yarinyar. "Ehh din ay ke kika zubar da girman ki shiyasa muka bi muka ta ke shi." yarinyar ta fada tana murguda baki irin na marasa kunya. Nan fa fada ya kaure tsakanin yarinya da budurwa. Ayaman ta tsaya tana kallon I kon Allah taji an fincike bokitin hannun ta. "Anas?" "Ayaman." Kallon shi take kafin ta gaishe shi , amsawa anas ya yi kafin ya amshi bokitin yace taho muje, "Ina zamu kuma? " Binshi tai suka tafi, Mai ruwa ta samo mata ya kai shi har gida, amsar ruwan ta yi ta rinqa cika ko Ina na gidan har sai da ya cika taf. Fitowa ta yi Taga anas har ya sallami mai ruwan, " nagode sosai ." Ayaman ta fada da wani murmushi a fuskarta. "Bakomi, yiwa kaine" Anas ya fada yana mayar ma ta da martanin murmushin. "Bari na shiga gida sai anjima" "Dan tsaya Ayaman." tsayawa ta yi kafin ta cigaba da cewa "ya maganar mu ta waccan ranar"? Rufe fuska ta yi ta shige gida da gudu, yayin da anas yayi tafiyar da Yana dariya. Tana shiga gidan ta bige inna ladiyo wacce ke wanke fuskar ta, Dan da alama daga bacci ta tashi. " Kam bala'i!! , tass !! inna ladiyo ta wanke fuskar Ayaman da Mari, " ba Kya Gani ne da Zaki buge ni?" "Kiyi hakuri inna" Ayaman ta fada tana ƙasa da kai . Tsaki ladiyo ta yi sannan ta wuce ta shige dakinta, sum sum AYAMAN ta wuce ta shiga dakin ta ta zauna akan zanin dake shimfide a kasa... More comment more typing ✍️✍️ Love you all 😘 ❤️ Khairat 🖤🖤🖊️ 🖊️ 🖊 ️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 🖤🖊️✍️ This page is dedicated to aunty Reemah ❤️ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 15-16 Tsaki Ladiyo ta yi sannan ta wuce ta shige dakinta, sum sum Ayaman ta shige na ta dakin, zama ta yi a kan shimfidar zanin dake shimfide a kasan dakin. Tunanin Anas ne ya fado ma ta a rai, wani lallausan murmushi ta saki tana qara jin soyayyar Anas a ranta, wadda bata ta'ba sanar Mai ba. Tun mahaifiyar ta na da rai Anas ke hidima da ita,yana nuna ma ta ƙauna da so wanda bata fahimta ba a wannan lokacin, a gaskiya in ta yi rashin Anas ta yi babban rashi, Amma taya Ladiyo zata bari ya aure ta. Tana yawan mamakin irin qeta ta ladiyo, qiri-qiri ladiyo ke dakile maganar auren ta da zarar ta taso, kusan Maza uku ne suka zo neman auren ta, ladiyo ke zuga malam isyaku ya hana auren. Haka bayan rasuwar mahaifiyar ta, dangin ta su adda asiyah ƙanwar innar ta, tana iya tuna me ya faru sosai a ranar. "Nifa babu inda za'a kai min 'ya, haka kawai, ku barmin ɗjya ta Ina da matar da zata kula da ita." malam isyaku ya karasa fada yana kallon su addah Asiyah ɗaiɗai. "Haba malam isyaku, ay abun bai kai haka ba, naga Ayaman duk diyar mu ce, tunda ay 'ya'yan Zainab (mahaifiyar Ayaman) duk 'ya'yan mu ne koh koh?" Adda suwaiba, babbar yayar inna ta , ta numfasa sannan tace "batun matar ka ay ba wanda bai san halin ladiyo ba, auren ta na farko, ta kori kishiyar ta, ta gallaza ma mijin nata daga karshe ya mutu wanda mutane ke zargin ita ta kashe shi, gashi wani irin uƙuba ne bata bawa Zainab ba duk da cewa ita ta ma ta sanadiyyar shigowa cikin gidan?" "Wallahi ƙarya ce,munafikan banza da hofi kawai, wannan wace irin jaraba ce , habaa." Ladiyo da ta fito daga dakinta tana riqe da zani a hannu ta fada tana tura daurin dankwali gaban goshi. Ta cigaba da fadin "Kuma yarinya tana nan, ko yanka naman ta zamu yi mu ci dole ku bar ta a nan." ta tsaya a kan tabarma da su addah asiyah da addah suwaiba da sauran yan uwan mahaifiya ta ke zaune. "Kehh Ladiyo ki shiga tai tayin ki wallahi, Dan ruwa ba sa'an kwando bane, yawwa."Addah Asiyah ta fada tana miqewa daga zaman da take. Yatsina fuska ladiyo ta yi sannan tace"wannan Kuma matsalar ku.", ta cigaba da baƙaƙen maganganun ta. Addah asiyah ce ta tashi cikin fushi ta sabi jakar ta da takalmi zata fice addah suwaiba ta dakatar da ita. "Wlh Yaya ki barni na tafi kar ayi abin kunya." addah Asiyah ta karasa fada cikin wata irin murya ta fushi. "Munga Zaki ma karshen fushi, yarinya ce dai ba za'a bada ba tana nan gidan ubanta." ladiyo ta fada cikin izgili. Shiru addah Asiyah ta yi ta tsaya suna bama malam isyaku baki amma biriss yaqi karshe ma ficewa ya yi daga gidan bisa umarnin ladiyo. Tashi suka yi da niyyar tafiya gida dan ba gari daya suke da garin su ladiyo ba. Tashin su ke da wuya ladiyo ta sheqe da wata munafukar dariya, tace "Allah ya raka taki gona." tana wani watsa yatsu a iska kamar ana kora awaki. Addah Asiyah ce ta juyo ta mata magana wadda ta sa ladiyo hankada asiyah kusa da bakin rijiya. "Dama haka nake so." ladiyo ta fada a zuciyar ta. Addah Asiyah kuwa ta bige da bakin rijiyar, addah sadiyah karamar kanwar inna ta ce ta Kai ma ladiyo duka ta kufce. Kafin kace me gidan malam isyaku ya kacame da fada, ta ko'ina, Dan ladiyo dama Masha Allah, akwai jibgegen jiki, ga addah asiyah ma mai karfin hali. Kaf cikin ƴan uwan mahaifiyar tawa addah suwaiba ce kawai ke gefe riqe da kanta da aka buga ma karfe. Ni kam da ban wuce shekara 10 ba na tsaya tsuru-tsuru Ina kallon wannan tashin hankali. Malam isyaku ne ya shigo da fadawan Maigari aka tattara mutanen aka kai su gaban maigari, bayan bayanai da yawa maigari ya zartar da hukuncin su addah Asiyah ne marasa gaskiya tunda har gida suka je. Sannan batun Ayaman tana nan gidan ubanta ba inda zata tunda Yana da halin riqe ta, kuma haka addini ya tabbatar. Bayan an dawo daga wurin maigari ne su addah Asiyah suka kama hanyar gida ba tare da sun kalli ko inda Ayaman take ba, Amma a zuciyoyin su tausayin Ayaman da kuma alhinin rashin ƴar uwar su ne ya dawo musu sabo. "Ayaman! Ayaman! Ina kike ne?" Firgigit AYAMAN ta yi daga duniyar tunanin data Lula . "Na'am " ta amsa kiran ladiyon tana fitowa daga ɗakin. "Ungo abincin rana ne Maza ki cinye." Ladiyo ta fada tana miqa mata kular abinci hade da lemon kwalba. "Toh, nagode." Ayaman ta fada cike da mamaki qarara a fuskar ta . Ladiyo ta lura da mamakin nata ne yasa tace "ko baki yafe min bane Ayaman?" Ta ƙarasa fada cike da makirci. "A'a ba haka bane inna na hakura." "Yawwa diyar albarka nagode." Tashi Ayaman ta yi ta shiga dakin ta, yayin da ladiyo ta bita da kallon tsana ta ja tsaki kasa-kasa. AYAMAN na shiga dakin ta , ta zauna tana ta mamakin halin Ladiyo, dazu fah ta gama hantarar ta ita ce yanzu har da abinci, "Allah ya kyauta" ta fada tana daɗa jinjina lamarin. Bude kwanon ta yi taga shinkafa da miya ne har da salak a kai, mayar da murfin ta yi ta ajiye kwanon gefe dan har ga Allah tana tsoron cin abincin nan duba da daga hannun wacce ya fito. ******************************** *DELU* Ta bangaren delu kam likafa sai cigaba take dan yanzu har ta kai Mariya kullum tana kofar gida da wani saurayin an zo zance. Haka ma malam surajo ya yi wani kala da shi duk ya firgice, banda umarnin delu ba abinda yake bi, sai hidima yake mata ita da diyar ta. Yanzun ma zaune suke a tsakar gidan suna shan iska,Dan cikin ya yi zafi da yawa. Mariya ce ta fito daga daki tana fadin, inna wai Ina abincin ne? Cike da muryar shagwaba. "Laaa malam, waken tun dazu bai kammala dahuwa bane?" Delu ta fada tana kallon mijin nata. "Na manta ne, Amma nasan yanzu ya yi kam." malan surajo ya karasa fada cikin sauri dan baya son fadan delu. "Shi ne kazo nan ka rashe, ka saki baki kana surutu , Amma dai anyi lusari wlh." delu ta karasa fada tana riqe haba. Ta koma kan Mariya tace "yi hakuri 'yar mama, yanxu abincin zai kammala, kinji." "Yawwa inna na manta ban gaya miki ba, su ladiyo dazu aka kaisu fadar maigari akan wannan shegiyar Ayaman din." " Ke habaa! " Delu ta fada tana bude baki kamar taga wani abin mamaki. "Wlh fah, dazu da iliya yaxo yake fada min." "Kuma banji maganar ba." delu ta fada, sannan ta cigaba da fadin. "Wannan iliyan bana son alaqar ki da shi wlh, dan ba wani abin arziki yake tsinana miki ba." "Toh shikenan." Mariya ta fada. "Wai inna alhaji gabatari ne? kwana biyu Bai shigo ba. " Wlh ban San masa ba, Amma qila yau yazo." "Toh shikenan. " Sai mun hadu a next page, thanks love you all 😘 ❤️...... Khairat 🖤🖤✍️✍️ https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 🖤✍️ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 17-18 Hira delu da diyarta suka shiga yi,har malam Surajo ya kammala girkin ya miko musu. Shinkafar da ya dafa ta chabe duk ta yi ruwa ta yi kamar tuwo, fuskarsa cike da tsoro kamar wanda ke gaban Zaki, ya rusuna ya aje shinkafar hade da kallon ladiyo. " Har ka gam... " Bata karasa maganar ba ta kalli inda shinkafar ta ke. " La'ilaha illallah, abinda ka girka kenan, lallai ma malan." delu ta numfasa sannan ta cigaba da fadin "haka ma jiya ka yi mana wannan iskancin, wai meye a kanka ne? Tunanin uban me kake?". Ta ƙarasa fada kamar zata kaiwa malam surajo duka. "Hehehehe" mariya dake zaune ta sheqe da dariya, "wato ada in ni ce nayi wannan girkin ay duka da zagi ba wanda baka min baba, amma yau wai kaine da girki, waii giwa ta fadi, hhhhh." Mariya ta ƙarashe da dariya. Umarni delu ta yi ma malan Surajo akan ya zubar da shinkafar ya ɗebo wata sabuwa ya dafa. Ta bangaren malam Surajo kuwa, ya rasa me ke mai daɗi, wani ciwon kai na azaba yake yi, ga shi ya rame ya kanjame tamkar wanda ya yi cuta. Yana mamakin yadda Mariya ta gayamai magana har ya hakura ya yi shiru, dan ba damar ramawa, koma dai mene ya san duk inda aka je aka dawo dole ya bi umarnin delu. "Baza ka tashi bane." delu ta faɗa a ɗan tsawace. Zumbur ya miƙe ya nufi madafar tasu, takaici cike a ransa ya dauko wata shinkafar ya wanke ya dafa. Yana girkin yana jiyo hayaniyar delu, "Saura kuma ka kuma lalata shinkafar, wallahi kaji na rantse kayi ta dafa sabuwa kenan." Delu ta fadi cike da daga murya wanda mutumin dake waje zai iya jiyo ta. Cigaba da girkin sa ya yi har ya kammala, "alhamdulillah ." ya faɗa ganin shinkafar bata chabe ba. "Assalamu alaikum. "Muryar Ladiyo ta karade gidan . "Waalaikumus salaam ƙawar arziki, yanzu nake son zuwa gidan naki." Ladiyo ta watsa ma ta wani kallo, sannan tace "dama kin samu duniya ba dole ki sha re ni ba". "Wallahi ba haka bane, ƙawas." delun ta faɗa tana wani fari da idanu. "Waya ga fara, hhhh." ladiyo ta faɗa sannan ta cigaba. "Ni ba wannan ba ma, kinsan gobe zamu koma wurin bokan....." . Bata karasa ba delu ta yi azamar rufe ma ta baki, alama ta yi mata da ta yi shiru. Janta ta yi zuwa dakinta, matsar da tulin kayan dake kan gadon tayi sannan suka zauna. "Mene? Naga kin jayo ni daki." "Zaki ɓallo min ruwa, malam fa yana nan." "Dan malam na nan shi ne kika wani jayo ni, mchteeww." ta karasa da jan wani uban tsaki. "Ladiyo kar yaji fa aikin ya lalace." "Yanzu dai ba wannan ba kin shirya koma wa wurin bokan kan tudu?" Ladiyo ta katse maganar. "Ehhh, ina abubuwan da ya buƙata?" Delu ta tambaya. "Ni kinsan aiki na daban, dan haka tsakani na da shi ne, sannan kuma wannan yarinyar kin san har gaban maigari ta kaimu Ni da malam?" "Hmmm", delu ta ja numfashi sannan ta cigaba da fadin "ay dazu mariya ke gaya min, amma kwa in haka ne Ayaman ta fara sanin kanta". "Ke dai bari delu, yanzu jiran lokaci nake ƙanƙani, na fara musguna ma ta wanda ya fi na da . "Haka nake so muniya ta. " hannu suka tafawa sukayi sannan suka cigaba da hirar har malam surajo ya kammala girkin ya kawo musu. Ladiyo dai tayi dariyar ta har ta gode Allah, sannan ta chachakali abincin. Sai wurin magriba ta fito daga gidan delu, akan alƙawarin gobe zasu koma kogon boka. *Ayaman* A bangaren Ayaman kam tun lokacin da Ladiyo ta kawo ma ta abincin nan ta kasa ci, sai tunani da ta ke ta fama da, da kuncin rai. Da ta gaji da tunanin, ta miƙe ta fita zuwa gidan su tsahare, ta yi rashin sa'a tsaharen bata nan, dan an sa ranar auren ta da Umar dan ƙanin baban ta, dan haka ta koma gidan babbar yayar ta domin horon aure. Abinci babar su tsahare ta zuba ma ta, godiya ta yi,ta hau cin abincin su na ɗan taɓa hira. Bayan wani lokaci ta tashi ta nufi gidan, Anas ta tarar yana kofar gidan da niyyar aika yaro yayi kiran ta. "Assalamu alaikum." ta faɗa cikin sassanyar muryarta. "Waalaikumus salaam ." Anas ya amsa ma ta cikin murmushi. "Ya gidan?, naji abinda ya faru,me yasa kika kai su baba gaban maigari?" "Lpy kalau, wallahi yaya(dama haka ta ke kiran Anas), ni ma ban so ba , tsahare ce ta bani shawarar hakan, duba da yanda inna ke azabtar da ni". Ta ƙarasa maganar kamar za ta yi kuka. "Toh meye kuma na kuka, shikenan na bar maganar. " Shiru ta yi bata amsa masa ba. "Amma ba'a son kai iyaye kara, saboda darajar da Allah ya yi musu, ko ba komai inna Ladiyo ay ta haife ki, dan Allah kar na ƙara ji". Ya karasa da alamar jan kunne. "In sha Allah, yaya" ta amsa mai. Hirar su suka cigaba da yi irin ta masoya har ladiyo ta ƙaraso, sakin baki tayi tana kallon su, ko me yazo mata a rai kuma ta saki wani murmushi. "Ahh ah , su Ayaman ne anan, sannun ku toh." ta faɗa tana washe baki hade da russunar da kai kamar mutuniyar arziki. "Inna Ina wuni." Anas ya gaishe ta cike da ladabi. "Lafiya kalau ɗan albarka, ya mutanen gidan?" "Alhamdulillah inna ya gida ya yau?" "Wallahi qalau." "Toh Ma sha Allah." "A gaida mutanen gidan. " Ladiyo ta faɗa tana wucewa. Har ta je bakin kofa kuma, "Ayaman ki shigo da shi ciki mana." Ayaman dake tsaye tana kallon dramar ladiyo, ta amsa ma ta da "toh". Kallon Anas ta yi ta kalli kofar da Ladiyo ta shige ciki, tace "tabb". Sallama sukayi, Anas ya wuce ita kuma ta shige gida. Tana shiga ta ɗauki buta ta shige banɗaki, tana fitowa ta daura alwala, ta nufi daki dan gabatar da sallar magriba. Ladiyo ce ta shigo dakin ta tarar da Ayaman kan zanin da ta ke sallah. "In kin idar da sallah ga garin tuwo nan ki tuƙa mana da miyar kuka." "Toh inna." ta amsa ma ta sannan ta bita suka fita tare. Garin ta fara tankade wa sannan ta daura ruwan a kan murhun. A ƙasa da awa ɗaya ta kammala girkin kasancewar da iska a garin. Tana gamawa ta wanke kwanonin ta tattare murhun wuri ɗaya. Ladiyo ce ta fito daga ɗakin ta, "yawwa, sannu ƴar albarka". "Yawwa inna". Kwano ta dauko ta bawa Ayaman din ta zuba nata har da man shanu da yajin daddawa mai matukar kamshi . A tsakar gidan ta shimfida tabarma ta yi zamanta ga hasken watan da ya haskaka ko ina tarrr kamar rana. Iskar dake kadawa hade da kamshin abincin, da kuma hasken watan ya bada wani yanayi na daban, tunanin rayuwar su ta baya ta fara. Kwance ta ke a kan cinyar innar ta tana shafa mata kai, yanayin yayi dai-dai da wanda take ciki yanzu, ta tsuniya ta ke bata a lokacin. Abban ta ne ya shigo da sallama, sannu da zuwa sukayi mai, bayan ya nitsu innar ta gabatar da abincin dare wanda tuwon masara ne da miyar kuka. Tsire da fura abbanta ya fito da, daga jakarsa. Bayan sun kammala cin abincin ne innar ta ta dauko furar tana damawa suna taɓa hira har ta kammala suka cinye kayan su... Firgigit ta dawo daga tunanin, hawaye taji yana sauka daga idanun ta, kallon tuwon ta yi, ji tayi gaba daya ya fitar mata daga rai. Rufe abincin ta yi ta kai ɗaki ko dan da safe, alwalar bacci ta ɗauro, kichibis ta yi da Ladiyo tana fitowa daga ɗakinta, sallama ladiyo tayi mata. Ita kam tana ta mamakin ladiyo da dabi'ar ta ta ke. Daki ta shige ta yi shafa'i da wutiri sannan ta yi addu'arta ta kwanta don bacci...... Ladiyo kam sai da ta raba dare tana tunani da kuma jiran shigowar Nabila. Sai wurin sha biyu na dare sannan Nabila ta shigo gidan, da gasashiyar kaza, zama sukai suka tadar wa kazar har sai da suka cinye sannan sukai kwanciyar su... Love you all 😘 ❤️ ❤️ Khairat ✍️✍️✍️🖤https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈*MUGUNTA*😈😈😈 By Khairat ✍️🖤 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 19-20 Sai wurin sha biyu na dare Nabila ta shigo gidan,da gasashiyar kaza, zama sukayi ta re da cinye kazar,sannan suka mai da haƙarƙari suka kwanta. *5 star hotel* Hausawa suka ce dare mahutar bawa, amma a wannan wurin hakan ya bambanta. Hotel ne na manyan mutane, iya tsaruwa wurin ya tsaru, amma kash! Ba abinda ake aikatawa a wannan wurin sai alfasha da saɓawa Allah (wa'iyazubillah). Babban hall ne dake cikin hotel din, fitilu sun haskaka wurin sai ya yi kamar rana ce ba dare ba, cikin hall din kuwa fitilu ne masu mabanbantan kaloli wanda ya haɗa da jar kala, kore, shudi(blue), da sauransu. Waƙa ce ke tashi a wurin, wanda tun daga harabar hotel din ake jiyo wa, samari da ƴanmata ne chakude a wurin kowa da abinda yake . Wasu na zaune a kujerun sofa din dake wurin su na shaye-shaye, yayin da wasu ke tsaye suna kwasar rawa, wasu ko na abinda bai kamata ba. Wani kyakkyawan saurayi ne ke zaune a ɗaya daga kujerun sofar dake cikin hall din, ya sha giya ya yi tatil, ga matan banza zagaye da shi, surutan banza yake ta yi wanda ke nuna a bige yake. Wata matashiyar budurwa dake ta tiƙar rawa tun dazu ce ta taho zuwa inda yake, kallon matan da suka zagaye shi tayi sannan ta watsa musu kallon banza. "Dallah ku tashi ku bani wuri, sai kace mayu kun zo kun sa shi a gaba." ta karashe maganar cikin yatsina fuska gami da kallon banza. Sumsum suka tashi daga inda yake, dan sunsan halin Nafee. Amrah ce kaɗai ta zauna saboda sun saba faɗa da Nafee. "Baki ji me nace ba?" Nafee ta tambayi Amrah hade da ƙare ma ta kallo. "Ehhh, bazan tashi ba, in ubanki ne wanda bamu san asalin sa ba, ya sayi kujerar sai ki tashe ni." Amrah ta gaya ma ta tana kauda kai gefe. "Kut....... Nafee ta auno wata uwar ashariya ta danna wa amrah, sannan ta chakumo wuyanta, tai ma ta wata irin shaƙa wanda da ƙyar amrah ke numfashi. Da yake mutanen banza ne a wurin, ba wanda ya yi yunƙurin raba su faɗan, sai ma waya da suka ciro suna musu video inda wasu ke ihun "ku chasu mata ku chasu." suna faɗin sun samu videon posting a social media dan samun mabiya. Sai da Nafee ta tabbatar amrah taji jiki a hannunta sannan ta ƙyale ta , sakin ta ta yi kasa, yarap! Kake jin Amrah ta faɗi a kasa. Duk wannan diramar da ake sha wannan saurayin na nan zaune yana kallon su, tsaki ya yi ya tashi ya fice daga hall ɗin. Sai da ya kai kofar motar shi ƙirar honda accord 2019, sai ya tsaya, aljihun shi ya duba ya ga ba mukullin motar, "oh shit!" Ya fada yana riƙe kanshi. Guards ɗin dake tsaye bakin kofar hall ɗin ya yi wa umarnin su ɗauko mai mukullansa da wayoyinsa. Amsa mai sukayi , ɗaya a cikin su ya tafi dauko mukullan, bayan wasu daƙiƙai ya dawo da mukullan da wayoyin . Ƙarɓa ya yi ya bude motar ya shiga wurin mazaunin driver, Nafee ce ta bude gidan gaba ta shiga ta zauna, kallon ta ya yi duk ta wani firgice, tsaki ya yi yace "'Fitar min a mota.'" shiru ta yi taƙi fita, "I said get outt!!!" Ya fada cikin karaɗi. Buɗe murfin motar ta yi ta fita, riƙe murfin ta yi tana kallonsa, jan motarsa ya yi da gudu ya fice daga harabar hotel ɗin. Tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, bige ta da ya kusan yi ne ya sa matsa da sauri, "Lallai ma Farouk, ita zai ma haka?". Gajiya ta yi da tsayuwar ta koma cikin hall ɗin, wurin Meenah (ƙawar ta) ta nufa, amsar mukullin motar ta ta yi ta fice , motar ta tada ta fice daga hotel ɗin. Gudu ya ke zabgawa akan titin, Allah ma ya sa babu motoci akan titin dan a lokacin wurin ƙarfe uku na dare ne. Ikon Allah ne kawai yakai shi gidansa dake hotoro tsamiyar boka. Horn ya shiga danna wa ba ƙaƙƙauta wa, baba Hassan maigadi da ya fara gyangyaɗi ne ya taso da gudu don bude wa ubangidan nasa kofa. Ko ƙarasa bude get din bai yi ba , Farouk ya danno hancin motarsa cikin gidan, wanda ya kusan bige baba Hassan. Ko ƙarasa parking ɗin bai yi ba ya fito daga motar, gidan babba ne duk da duplex ne (mara bene) amma ya ƙayatu, flowers kala-kala masu bada kamshi na musamman da niimatacciyar iska. Kofar parlorn ya nufa wadda ƙatuwa ce mai kauri, bullet proof ce, kalar brown wadda ake ya yi a wannan lokacin. Buɗe kofar parlorn ya yi, babu haske sai na wasu ƙananan fitilu marasa haske sosai, sai suka bada wani haske mai sanyi a parlorn. Wucewa ya yi zuwa ɗakinsa, ya kunna fitila. Babban ɗaki ne mai ɗauke da danƙareren royal Italian bed, gado ne babba sosai wanda mutane biyar za su kwanta har su wataya. Ajiye wayarshi ya yi sannan ya fara rage kayan jikinsa, banɗakin ya buɗe, ba wani babba bane sosai,ya wuce wurin shower ya sakar wa kansa ruwa, "oh God!" Ya fada yana ɗaga kansa sama. Sai da ya kammala wankansa sannan ya fito daga banɗakin, gaban madubi ya tsaya ya shafa mayukan shafawa sannan ya saka kayan bacci ya nufi ƙofar fita. Kashe fitilar ɗakin ya yi, sannan ya fice daga ɗakin. Ɗakin Ummu Kulsum (matarsa) ya nufa, buɗe kofar ya yi, har zai shiga sai kuma ya tsaya a bakin kofar kusan minti goma yana nan tsaye yana kallon ta, kwance take cikin kayan baccinta sai jaririn da ke gefen ta tana shayar da shi. Shiga ya yi ya rufo kofar. Nima kuma na rufe page ɗin😅 kuyi hakuri da small page ɗin ... Love you all 😘 ❤️ Khairat ✍️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 *MUGUNTA *😈😈😈 By Khairat ✍️🖤💙 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 21-22 Shiga ya yi ya rufo kofar ɗakin. gaban gaɗon ya tsaya, suffar nasa sak sai dai kalar da ta bam banta su, nata fari ne ƙal, ya yin da na shi ya ke golden color. Kwance take ta lulluɓa da bargo sai jaririn da ke kusa da ita tana shayar da shi, da alamu rigimar dare ya yi ma ta har ta farka yanzu kam ta fara gyan gyaɗi bata sa ni ba. A hankali ya zare yaron daga jikinta, ɗan riƙe shi ta yi cikin magagin bacci, "ubansa ne." ya raɗa ma ta a kunne. Sakin yaron ta yi sannan ta kuma jan bargon mai tsananin laushi. Yaron ya riƙe a hannunsa, ya tsaya yana ƙare ma sa kallo , mamakin tsananin kamar da suke yi shi da yaron ya ke, kama sosai kamar an tsaga kara. Ba wani fari ne shi ba amma za'a iya kiran sa ruwan tarwaɗa, kalar fatar yan yanƙin Senegal,Egypt da maka mantan su, hakan ya samo asali ne daga kasancewar mahaifiyarsa ƴar Morocco ce, sa shin baƙaƙen larabawa kenan, inda mahaifinsa buzu ne dan asalin ƙasar Niger. Hanci kuwa, gadon sa ya yi daga mahaifiyarsa , dan ta kasance mace kyakkyawa me kyakkyawar zuciya . Cigaba da tsurawa yaron ido ya yi kafin ya ajiye shi a gadon shi na yara mai net. Kan gadon ya koma kusa da matarsa, ya matso da ita kusa da shi, ɗan hura ma ta iska ya yi sannan ya raɗa ma ta a kunne, "momyn Mu'ayyad, ga dadyn Mu'ayyad ." Sannan ya yi murmushi kamar tana ganin sa. ******************************** *AYAMAN (P.O.V)* *Mafarki* Wannan matar ta ranar nan ce ta kuma zuwar mata, kamar yadda ta saba da gudu ta biyo ta har ta zo kusa da farar matar nan wadda haske ya dabaibaye ta. Wannan karan, matar nan mai kama da zinariya har jariri ne riƙe da ita tana miƙo ma Ayaman, ita kuma ɗayar matar bata fasa biyo ta ba. Bayan wani lokaci kuma, wani abu kamar labule ya lulluɓe ta, ta rasa gane hanyar fita daga wannan labule , farar matar nan ce ta miƙo ma ta hannu ɗon ta fito da ita daga wannan labule, sai ɗayar matar ta cillo wani abu mai kama da maciji ya raba tsakanin ta da farar matar. Firgigit ta farka daga baccin tana kiran sunan Allah, ta daɗe tana tunanin wannan mafarkin nata mai cike da abun mamaki, ba tun yau ta fara wannan mafarkin ba amma na yau ya fi ruɗa ta. Ɗaga hannun ta sama ta yi ta roƙi Allah ya kawo ma ta ƙarshen wannan mafarkin mai abin mamaki. Wani abin mamaki shi ne, a kullum in ta yi mafarkin nan a lokaci ɗaya take tashi, shi ne ana kiran sallar asuba, "koma dai mene ne , Allah ya na sane da ni." ta faɗa a ranta. Tashi ta yi ta ɗauro alwala tazo ta fara gabatar da raka'atanul fajir kafin liman ya tada sallah. Bayan ta idar da sallah ne ta zauna yin azkar na safiya saboda muhimmancin sa, sannan ta yi addu'ointa har gari ya fara haske . Fita ta yi tsakar gidan, ta fara sharewa, sannan ta dauki botiki ta fara ɗiban ruwa har ta cika robobin gidan, bayan ta kammala ayyukan ta ne ta yi wanka, ta zauna jiran Ladiyo ta fito. Yunwar da ke azalzalar cikinta ne ya sa ta tashi ta dauko ragowar tuwon jiya, ta cinye. Tana nan zaune har rana ta fito tarr, alamar hantsi ya kai bayan ludayi kenan, wurin ƙarfe sha ɗaya kenan. Ladiyo ce ta fito tana ta rabka uwar hamma, kallon tsakar gidan tayi , sai ta buɗe baki tace " ahh ahh Ayaman ƴar albarka, har kin gama gyaran gidan kenan." "Ehhh inna, ina kwana?" "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau. " "Kin karya kuwa?" Ladiyo ta tambaya cikin kulawar munafirci. "Ehhh na ci ragowar tuwon jiya." "Toh ya yi kyau". Ladiyo ta cigaba da faɗin " Ayaman magana nake son muyi." Ayaman sai taji abin wani ban bara kwai, dan bata saba ba, ita fa wannan sabuwar ɗabi'ar ta Ladiyo ba ƙaramin mamaki take bata ba . Ta dai daure tace "ina ji" a taƙaice. "Jiya nayi magana da babanki akan wannan yaron Anas, shin kina sonsa?". Ta karashe tana kallon ta. Shiru Ayaman ta yi ta kasa furta komai saboda mamakin da Ladiyo ta bata, tuna ranar da Anas yazo gidan Ladiyo ta fito ta ci mai mutunci kuma ta haɗa ta da babanta har ya so hallaka ta da duka. Ɗaga kai ta yi taga Ladiyo ta tsura ma ta idanunta wanda ke matukar tsorata Ayaman ɗin. "Zamu yi magana da Anas ɗin.", ta faɗa tana kauda kai gefe. "Yawwa ko kefa Ayaman? Ai hakan yafi kinga azo ayi abin nan kowa ya huta, muma mu huta da ƙananun maganganu." Ta ƙarasa tana tafiya zuwa banɗaki, sannan ta cigaba da faɗin "Kinga ƙawarki tsahare, an sa ma ta rana da ɗan uwanta , bikin saura ƴan watanni." Ita dai Ayaman tana nan zaune bata ce uffan ba sai kallo da take bin Ladiyo da shi. Nabila ce ta fito daga dakin tana hamma gami da miƙa, "Wai Ladiyo(haka suke kiran uwarsu da shi)naji kina maganar wai Anas ya turo a musu aure da wannan abar?" Ta karashe tana kallon Ayaman a banzance. "Har kin tashi kenan ƴar albarka" Ladiyo ta faɗa tana washe baki. "Ni fa ba shi na tambaye ki ba, ki ban amsa." Nabila ta faɗa kamar wadda ke magana da sa'arta ba uwarta ba. Abin ka da uwar da batasan ciwon kan ta ba sai ta amsa ma ta da "eh, Ayaman da Anas ake so asa ma ranar aure." Yatsina fuska Nabila ta yi , sannan ta ja tsaki, "kinga Ladiyo ga indomie chan da kwai ki dafa mana." tana gama faɗa ta koma ɗaki. "Ayyiriri, ɗiyar arziki, Allah ya tsare gabanki da bayanki ya miki albarka." Ladiyo ta ƙarasa faɗa cikin shewa da san abin duniya. Ayaman dai na zaune karkashin bishiya tana kallon wannan san abin duniya irin na Ladiyo. Yaro ne ya shigo gidan da kayan wanki a kansa, "wai gashi babar mu tace zamu samu wanki?" Ya faɗa ya na ajiye kayan a ƙasa, a gaban Ayaman. "Kala nawa ne?" Ladiyo ta yi charaf ta amshe kuɗin wankin, Aa "Kala ashirin ne." yaron ya faɗa ma ta. "Kuɗinku ya kama naira ɗari biyar kenan", Ladiyo ta ƙarasa faɗa tana amshe ɗari biyun dake hannun yaron sannan tace "wannan kuɗin sabulu da ruwa ne ko?" "Eh" yaron ya amsa ma ta. "Toh ka dawo bayan magriba ka amsa.", Ladiyo ta faɗa mai. "Toh", yaron ya faɗa a takaice. Duk wannan abin Ayaman na gefe tana kallon Ladiyo, a mamakinta sai taga Ladiyo ta miƙo ma ta kuɗin, sannan tace "gashi Ayaman ki siyo sabulun kiyi wankin in su zo amsar wankin sai ki amshi kudin". Karɓar kudin ta yi sannan ta tashi ta saka hijabinta ta fita. Shagon shafi'u ta nufa, tana zuwa taji wurin anyi tsit alhalin tun daga kan layin ake jiyo hayaniyar samarin unguwar masu zama a shagon nashi. Sallama ta yi , ta shiga cikin shagon suka gaisa da shafi'u sannan ta karɓi sabulun ta fita. Tana fita daga shagon taji samarin sun kwashe da dariya, juyowa ta yi ta kallesu, har wa yau kuwa kallon ta suke suna ɓaɓɓaka dariyar su. Kwalla ce ta zubo ma ta daga idanunta, saurin tare ta ta yi har ta isa gida. Ruwan da ta ji yana kwarara a banɗakin ne ya tabbatar ma ta da Ladiyo na sheƙa wankan ta. Ɗakinta ta wuce ta yi zaman ta a kan zanin tana sha re kwalla.... ******************************** *Nafee* Tun da ta amshi mukullin ta fice daga harabar hotel ɗin bata zarce ko'ina ba sai gidanta dake Nassarawa GRA a Kano, maigadinta ne ya bude ma ta ƙofa ta shiga da motar harabar gidan. Kofar parlorn ta fara budewa ta shiga ciki, a wurin shoe rack ta ajiye takalminta, mai aikinta asabe ta tarar a parlorn har ta fara baccin ta, tashin ta ta yi ɗan tafi ɗaki tunda ta dawo. "Hajiya sannu da zuwa, an dawo lafiya?" Asabe ta gaida uwar ɗakinta. "Lafiya kalau." Nafee ta amsa a takaice tana wani yatsina. Ɗaki ta wuce ta kullo kofarta ba tare da ta tsaya amsa sai da safen da Asabe ke yi ma ta ba. Cire top ɗin jikinta ta yi, ta ƴar a ƙasan ɗakin, sauran kayan jikinta ta cire duk ta zubar da su a ƙasa kamar asabe bata gyara ba. Watsa ruwa ta yi ko ta ji sanyi a ranta na wannan wulaƙancin da Farouk ya yi ma ta. Bayan ta kammala wankan ta shafa kayan skin care ɗinta sannan ta sa kayan bacci ta yi kwanciyar ta ba tare da tunanin sallah ko addu'ar bacci ba. ******************************** *Farouk* Sai wurin sallar asuba tukunnan ya sauko daga kan gadon, kallon Ummu Kulsum ya yi , samun kanshi ya yi da sakar ma ta murmushi, ita ma ta mayar mai da murmushin. "Tashi muyi wanka." ya raɗa ma ta a kunne. Tashi sukayi, banɗaki suka nufa, tare sukayi wankan sannan kowa ya yi na tsarki suka fito daga banɗakin. Jallabiya ya dauko ya sa sannan ya dauki sallaya ya shimfiɗa musu su biyu, raka'atanul fajir ya fara gabatarwa kafin aka kira sallah ya ja su tare, bayan sun idar ne ya yi azkar ɗin sa , sannan yadauko ƙur'ani ya fara karantawa, kamar wasa ya ji wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi. Ummu Kulsum na ganin haka ta gyara mai kwanciyar sa akan sallayar sannan ta ɗauki mu'ayyad ta fara shayar da shi saboda rigimar da ya ishe ta da shi. Tana kammala ciyar da yaron ta mayar da shi keken su irin na yara wanda ke taimaka musu wurin koyar tafiya. Kitchen ta nufa ta kunna fitilu yayin da Mu'ayyad ke biye da ita akan keken shi yana ta wasan shi. Dankalin turawa ta ɗebo ta fara ferewa, tana yi tana lura da yaron, bayan ta gama fere dankalin ta yi mai yankan farfesu. Cikin ƙasa da awa ɗaya ta kammala girkin wanda faten dankalin turawa ne wanda yaji kayan lambu da kifi. Baba maigadi ta miƙa wa nashi sannan ta koma ɗakin ta kunna heater har ta tafasa ta juye ta fara yiwa yaron wanka, tana kammala mai wankan ta yi nata wankan , tana gama shirya yaron ya yi baccinsa , ita kuma ta fita falo ta kunna tv tana breakfast. Tana nan zaune ƴar aikinta Maryam ta shigo, gaisawa sukayi sannan ta fara aikinta. Tana nan zaune har Farouk ya tashi bacci ya fito ya same ta a falon, gaishe shi ta yi ya amsa ciki-ciki, dinning ya nufa ya fara breakfast ɗinshi kafin ya yi wanka ya fice daga gidan.... Ya kuke ganin labarin du Farouk? Love you all 😘 ❤️ Khairat ✍️💙🖤 https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️💙 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 23-24 Miƙe wa ta yi da ta gaji da zaman, ita kam ta na mamakin halayyar Farouk, kullum da sabuwar ɗabi'ar da zai bijiro da ita, yau kam ko kula ta bai yi ba ya fice. Ɗaki ta shiga ta kwanta, ta rasa me ke ma ta daɗi, tana kwanciya ta hango wannan tsakar ta ranar nan, babba ce sosai dan zata iya kaiwa girman wani ƙadangaren. Tsura ma ta ido ta yi ta na kallon ta, idanu taga tsakar ta zaro kamar zata haɗiye ta , ga wani harshe mai lankwasa kamar na maciji. Addu'oi ta fara karantawa a ranta, ita kam wannan tsakar tun lokacin da aka kawo ta gidan take ganin ta, gashi kullum daɗa zama abin tsoro take yi. Ta yi shiru tana tunani ta jiyo muryar Saratu dillaliya, fitowa ta yi taga har ta yi ma kanta masauki a ɗaya daga kujerun falon. Saratu na ganin Ummu Kulsum ta yashe baki ta fara ma ta kirari kamar ƴar maula, gaisawa sukayi da Ummu Kulsum sannan ta fara fito da kayan dake cikin jibgegen buhun ta. "Ay in gaya miki Hajiya wannan atamfofin ƴan cotouno ne, ga kyau ga sauƙi." Saratu ta ƙarasa maganar tana washe baki. Duba atamfofin Ummu Kulsum tayi kafin ta zaɓi guda biyu ta chake wa Saratu kuɗinta a hannu. Bayan sunyi sallama da Saratu ta dauko Mu'ayyad wanda ke gurin mai aikin ta, abincinsa ta ba shi sannan ta kuma miƙa ma ta yaron ita kuma ta koma ɗaki ta kwanta zuciyarta duk ba daɗi. ******************************** *Ayaman(p.o.v.)* Bayan ta gama kukan nata ta tashi ta kama wankin nan ba ji ba gani, har sai da ta kammala sa cikin mintuna ƙalilan. Abincin da Inna Ladiyo ta dafa ta bata , ta zauna ta ci ta koshi ta yi wa Allah godiya. Tana nan zaune har Ladiyo tayi ficewar ta ɗan Nabila na yin wanka ta fice sai ya zamana ita kaɗai ce a gidan. Tunanin maganar da suka yi da Ladiyo ce ta dawo ma ta, Anas dai mutumin arziki ne ga hankali da nutsuwa, kuma yana da rufin asirinsa daidai gwargwado, dan da shi da mahaifiyarsa ne kaɗai aka sani shiyasa ba wanda ya bashi ƴarsa aure. Gashi mahaifiyarsa ba lafiya ce ishashiya ce da ita ba, tana buƙatar taimakon wani, gaskiya zata amince ta aure shi ko dan taimakon baiwar Allahn nan . Da ta gaji da tunanin ta fara karanto ƙur'ani wanda ke kanta dan rabon ta da islamiyya tun mahaifiyarta na da rai, bayan rasuwar ta Ladiyo ta katse islamiyyar. ******************************** *Farouk* Yana fita daga gidan, gidansu ya nufa, a falo ya tarar da Hajiyarsu ana ma ta tausa, tana kallo tana cin kayan marmari. Gidan kam dan tsaruwa ya tsaru, dan ya fi gidan Farouk girma da tsaruwa wanda bayan rasuwar mahaifinsu ne aka ƙara tsara gidan, su uku ne a family ɗinsu, babbar mace ce sunan ta Halima tana New York City da zama ita da iyalanta, sai mai bi ma ta , Raihana, tana garin Abuja da zama, sai Farouk ɗan auta, wanda ke zaune a Kano kusa da mahaifiyarsa. Da sallama ya shiga falon, zama ya yi kusa da Ammi , murmushi dattijuwar matar ta yi, sannan ta shafa kanshi, "Babana (haka take kiransa dan sunan mahaifinta ne da shi)ya aka yi ne?" Matar ta tambaya tana sakin sabon murmushi. "Ina kwana Ammi" Farouk ya gaishe ta cike da ladabi. "Lafiya ƙalau babana, ya Iyali?" "Suna lafiya" "Masha Allah." "Bari na tafi office ana jira na" "Toh babana, Allah ya bada sa'a." "Ameen, zan dawo zuwa dare" "Toh, Allah ya kaimu." "Ameen ya faɗa yana ficewa." Ammi ce ta ƙura masa ido san da yake fita, sai ya yi ma ta kama da ubansa sak , "Allah ya maka rahama Aliyu" ta faɗa tana tuna lokutan su tare. Farouk ya na fita bai zame ko ina ba sai gidan Nafee, horn ya yi mai gadi ya buɗe mai, gaisawa suka yi da mai gadin sannan ya nufi cikin gidan. Ya na shiga falon ya tarar da Nafee zaune ta na breakfast, daga ita sai wata yaloluwar riga a jikinta. Baba Asabe ce ke ta kai kawo a falon ta na gyaran gidan, ya na shiga falon ya tsaya ya ƙura wa Nafee ido kamar tsohon maye. Idanunta sun kumbura alamar ta yi kuka har ta gode wa Allah, matsawa kusa da ita ya yi ya rungumo ta jikinshi yana faɗin "my love fushi kika yi ne naga ko kallo ba ishe ki ba?" Kawar da kanta gefe ta yi ta na turo baki gaba, murmushin gefen baki ya saki ya na matsawa gefe, ya ce "tunda ba zaki hakura ba bari na je wurin Amrah ita zata lallaɓe ni." Zumbur ta juyo jin ya yi maganar Amrah, "kar ka sake min maganar wannan ƴar iskar a gida na , kaji na gaya ma." Ta faɗa cike da jan kunne da masifa. Suna nan wurin ya bata hakuri suka jima suna hira kafin ya tashi ya nufi office ɗinsu. Nafee kuwa rai ya yi ƙal , dan Farouk ya gaya ma ta yau zasu tattauna da mahaifiyarsa a kan batun auren su, haka nan ta wuni cikin farin ciki. ******************************** *Ladiyo da Delu* Ladiyo na gama wankan ta shirya ta nufi gidan Delu, a tsakar gida ta tarar da su ita da Mariya sun zube soyayyar kaza wadda aka baɗa ma yajin tafarnuwa a kai. "Duniyar Allah." Ladiyo ta faɗa ta ƙarasa shiga cikin gidan. "Ladiyo kece tafe?" Delu ta faɗa ta na yagar cinyar kaza. "Ni ce fa Delu." Ta amsa ma ta tana ɗaukar naman ta kai baki, "waii wannan daɗi, Allah turo min da naira in more arziki na." Ladiyo ta faɗa kamar ta taka rawa. Mariya da Delu kam ban da dariya ba abinda suke yi. Zama Ladiyo ta yi da kyau, sannan suka haɗu su uku suka cinye kazar, bayan sun gama ci Delu ta yi ma malam surajo umarnin miƙo musu da lemu a ɗaki. Ba musu ya tashi ya nufi ɗakin, duk ya wani susuce , ya rame ya fita hayyacinsa Delu sai abinda taga dama take yi. Lemu biyu ya miƙo musu, ya na komawa inda ya ke zama, wanda bakin kitchen ne. "Naga ka miƙo lemu biyu ka aje, da yawa zaka miƙo ay." Delu ta faɗa mai tana kallon sa . "Ya ƙare ne " malam Surajo ya faɗa kamar zai yi kuka. "Sai kaje ka siyo." Delu ta faɗa cikin halin ko in kula. "Wai dan Allah Delu ta kike so na yi ne, duk kuɗin dake wuri na sai da na kashe su a kan ki da wannan yarinyar, sannan kin hanani fita in samo, sai bauta da na zauna nake miki a gida, hatta gonar gadon mu da aka raba kuɗin na hannunki kin hanani, ya kike so na yi ne?." Malam Surajo ya ƙarasa faɗa cikin kuka wanda duk wani mai imani zai taya sa , dan a halin da ya ke ciki ya gwammace mutuwa a kan rayuwar da ya ke. "Wannan kuma matsalar kace ba tawa ba, matsala ta ita ce ka nemo min lemu na sha." Delu ta faɗa cikin halin ko in kula. Ladiyo da ke zaune kam , lemun ta dauka tana shan kayanta, dan duk wannan batun ba damunta ya yi ba. More comment more typing....... A taya mu sharing please. Khairat ✍️ https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈* MUGUNTA* 😈😈😈 By ~Khairat~🖤💙 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page ~25-26~ Sai da ta dire kwalbar lemun sannan ta kalli inda Delu take tace "ke kam ki kyale shi haka mana, da wanne zai ji, habaa deluwa." "Kin ga fa Ladiyo babu ruwanki a harka ta, wannan matsalata ce da mijina dan haka ba ruwanki." Iya ƙuluwa Ladiyo ta ƙulu, ranta ke tafarfasa wai ita Delu ke gaya ma haka. Mariya da ta gaji da diramar ta tashi ta shige ɗakinta tana mitar wannan lamarin. Su Ladiyo kuwa saboda rashin zuciya, zama ta yi ta cigaba da cin kazar har sai da ta koshi, sannan suka ɗau hira ita da Delu. Malam Surajo na gefe yana kallon su, gaba ɗaya ya rasa me ke mai daɗi duk ya susuce ya fita hayyacinsa. Hira tai hira har suka kai wurin la'asar suna hira dan dama sallah ba damun su ta yi ba. Abinci suka nema suka, bayan sun ci suka dasa hirar tasu hade da fatan yau da dare zasu kai wa a bokan kan tudu ziyara. *Ayaman(p.o.v)* A bangaren Ayaman kuwa zamanta ta yi tana harsaso irin rayuwar da zasu yi ita da Anas, tabbas in tace bata san Anas ta yi ƙarya, rayuwarsu mai cike da nishaɗi da kaunar juna take harsashe. Kwatsam tunanin mafarkinta ya dawo ma ta a rai a lokacin da ta yi ido biyu da wata murtukekiyar tsaka mai girman ƙadangare ta ƙwalalo ma ta idanu. "A'uzu bi kalmatil lahi tammat min sharri ma kalaq." Ta faɗi a ranta saboda ba ƙaramin razana ta yi da ganin wannan halittar ba. Tsoro ne ya kamata sosai ganin tsakar bata daina kallonta ba. Hijabinta ta dauko a ɗaki ta saka ta fice daga gidan. Tana fita bata zarce ko'ina ba sai gidan su tsahare, da sallama ta shiga gidan, Innar su tsaharen ce ta fito daga banɗakin tana amsa sallamar. Dire butar hannunta ta yi tana faɗin, "Ayaman kece tafe, sannu da zuwa." "Ni ce inna, ina wuni?" "Lafiya ƙalau ya mutanen gidan?" "Su na lafiya." "Toh ma sha Allah." Zama ta yi a tabarmar dake tsakar gidan su na taɓa hira da Inna, "Inna yaushe tsahare zata dawo?" Ayaman ta tambaya ta na tsince shinkafar da Inna ta auno. "Ta kusa dawo wa Ayaman, nan kusa." Inna ta bata amsa. "Toh Allah ya kaimu." "Amin." Hirar su suka cigaba da yi har Ayaman ta daura ma ta girkin dare , su na cikin girkin Ayaman ke neman shawarar Inna a kan maganar auren Anas. "Ya kike gani inna?" Inna taja numfashi sannan tace "Ayaman, a rayuwar nan in kana abu dole ka nemi zaɓin Allah domin shi ne mai kowa mai komai, sannan Anas ba shi da wani aibu, yana da sana'ar sa, ba sata yake ba ko cutar wani, ga mahallin da zai aje ki , gaskiya a gani na ki amince da maganar auren nan, ko kin huta da rayuwar da kike fuskanta a yanzu." Inna ta ƙarashe maganar tana kallon Ayaman. Shiru Ayaman ta yi tana nazarin maganganun inna, tabbas haka zancen yake in ta yi auren zata huta da rayuwar gidansu. Nan Inna ta cigaba da bata shawarwari har ta kammala girkin suka ci tare sannan Ayaman ta yi ma ta sallama ta tafi. Tana fita daga gidan aka kira sallar magriba, dan haka kanta a ƙasa ta fita daga gidan sakamakon mazan da ke wucewa domin shiga masallaci. Wasu maza wanda aƙalla zasu yi sa'anin mahaifinta ne suka zo wucewa ta gaishe su, "yanzu ace malam Isyaku ya bar yarinya ta riƙa ta zama riƙaƙƙiyar kubewa, duk ta zama wata uwa a unguwa wannan ai bai dace ba." Ɗaya daga cikin mutanen ya faɗa, ɗayan kuma yace "Hmm, wa ya sa ni ko akwai abinda suka shirya shiyasa suka ƙi aurar da ita, koma dai mene muna nan muna zuba ido." Wucewa ta yi ba tare da ta kalli ko inda suke ba duk da ta san da ita suke kuma taji me suke cewa. Tana mamakin yadda mutane ke ma ta wata fahimtar daban, ita a ganinta aure ay lokaci ne kamar yadda mutuwa take . Da sallama ta shiga gidan duk da ba kowa, ta tsaya a banɗaki ta yi alwala ta zo ɗaki ta dauko zanin da take sallah da shi. A tsakar gida ta shimfiɗa ta yi sallar kasancewar akwai wutar lantarki dan sun ci sa'a an gyara musu. Tana zaune a kan zanin har aka kira sallar Isha'i ta yi sallar ta. Tana idarwa kam bayan ta gama zikiri ta shige ɗaki ta yi kwanciyar ta dan cikinta a koshe yake bata jin yunwa kuma tunda Ladiyo ta fita ta san sai sanda ta ga damar dawowa. ******************************** * Nafee(p.o.v)* "Ke wallahi aikin mutumin nan yana ci, yau gashi da kansa yazo yake faɗa min zai yi magana da mamansa a kaina, kinsan mun daɗe muna fama da shi a fara maganar auren sai yau dai Allah ya yi." Nafee ta ƙarasa maganar cike da jin daɗi. Ta ɗayan ɓangaren Lubna tace " ai ke kike wasa da tsafi, baki ji me bahaushe yace ba tsafi gaskiyar mai shi." Hira suka cigaba da yi a kan yadda zasu shirya abubuwa dan Nafee ji take kamar an yi ma ta hajji da Umrah. ******************************** *Farouk(p.o.v)* Yana isa office ya tarar da aiki ya yi mai yawa, dan mataimakin nasa bai yi abinda ya dace ba dan tafiyar da harkokin kamfanin. Sai da ya gama mitar kuma ya fara aikin, har wurin la'asar yana abu ɗaya, sallah ce kawai ke tayar da shi. Gidansa ya wuce bayan sallar la'asar. A falo ya tarar da Ummu Kulsum tana turaren wuta, dan bata bari mai aiki ta yi ma ta. Gaishe sa ta yi ya amsa ciki-ciki, dinning ya nufa ya bude kular abincin, masa da miyar taushe ya gani. "Oh shit!!, wai me yake damun ki ne, jahilcin da baki gama ba a kauye shi zaki zo ki dasa min a gida? Mtcwwww." Wullar da kular ya yi, sai ga waina ta yi ɗaiɗai a ƙasa, miyar ta biyo bayanta. Fuuu ya wuce ɗakinsa kamar iska, kallon dinning ɗin Ummu Kulsum ta yi tana zama turuss a kan kujera. Kuka ta fashe da shi mai ciwo, ita meye laifinta? Dan kawai daga ƙauye aka kawo ta shi ne ta yi jahilci? Ace kusan shekara ɗaya kana rayuwa da mutum amma baka taɓa samun farin ciki ba? Sai yaushe kenan?? Ta tambayi kanta cikin kuka. A gaskiya ta fara gajiya da halin Farouk, ba zata ga murmushinsa ba sai in dare ne ya yi yana nemanta? "Na jure da yawa wallahi." Ummu Kulsum ta kuma faɗa tana kuka. Mop da tsintsiya ta dauko ta gyara gurin dan Allah ya sa ta aiki ƴar aikinta wani wuri da tuni a gabanta zai yi wannan abin. Bayan ta gama gyara gurin ta shige ɗakinta ta kullo ƙofa, tana tunanin raba ta da aka yi da masoyinta aka aura ma ta Farouk da sunan zumunci. *Asalin su Farouk* Love you all 💞💋 ❤️ More comment more typing ✍️ Khairat ✍️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈* By *Khairat 💞💙* BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 27-28 *Asalin su Farouk* Mahaifin Farouk Alhaji Aliyu Umar Datti ɗan asalin garin Katsina ne a kaita local government. Ya taso cikin gata inda ya kasance shi kaɗai ne ɗan Fateema da Umar, dan shima sai da aka jima sannan aka haife sa. Ya yi karatunsa na boko da Arabi a nan kaita inda ya tafi babbar University a lokacin wadda ita ce University of Lagos. A nan makaranta ya hadu da Amina, har ta kai su da fara soyayya mai karfi, Amina ƴar asalin garin Lagos ce inda aka haife ta take. Bayan kammala karatunsu ne Farouk ya gabatar da kansa a wurin iyayen ta har ta kai ga ya tura manya domin nemo mai auren Amina. A lokacin an sha gumurzu kafin iyayen Amina su amince da auren dan sun so Amina ta auri wani ɗan uwanta. An daura aure da kimanin sati biyu aka dauko Amina daga Lagos zuwa gidan Aliyu dake Katsina bayan nasihohi masu ratsa zuciya da iyayenta suka yi ma ta. Watan Amina biyu a gidan Aliyu ta fara laulayi inda bayan cikin ya cika wata tara da ƴan kwanaki ta haifo santaleliyar ƴar ta mai kama da ubanta, aka raɗa ma ta suna Halima wanda sunan mahaifiyar Amina ne. Halima taga gata iya gata a wurin iyayenta da kakkaninta kasancewar ta jikar farko a family ɗin. Halima na da shekara biyar Amina ta kuma haifar ƴa mace wadda taci suna Raihana. Bayan haihuwar Raihana ne suka koma garin Kano da zama saboda sauyin wurin aiki da Aliyu ya samu. Amina sai da ta jima dan sai da Raihana ta kai shekara goma sannan ta haifo ɗa namiji wato Farouk. Amina da Aliyu suka haɗa kam ƴaƴansu suka raina har suka kawo karfi, Halima ta yi aure da kwanaki kaɗan Allah ya amshi ran Aliyu sai gidansa na gaskiya. A lokacin sunyi baƙin cikin rashin uban nasu amma suka yi tawakkali suka rumgumi ƙaddararsu. A haka rayuwa ta cigaba da nisawa har Raihana ta kammala karatunta ta yi auri inda ta auri ɗan mataimakin shugaban kasa su na zaune a Abuja. Lokaci zuwa lokaci Fateema tana kawo wa jikokinta ziyara, a wannan zuwa ta taho da wata budurwa wadda tace jikar aminiyar ta ce wacce mahaifiyar ta ta rasu tana da tarbiyya da hankali dan haka take son haɗa ta da Farouk. A lokacin hauka ne kawai Farouk bai yi ba dan ya gama shirinsa zai auri Nafee sai ga Ummu Kulsum ta shigo. Hajjo (Fateema) ta yi amfani da ƙarfin ikonta har aka ɗaura auren Farouk da Ummu Kulsum. Tun daga lokacin Farouk yake ƙullace da Ummu Kulsum na ganin ta yadda an daura auren bayan jan kunnen da ya yi ma ta. Tana zaune an lulluɓe ta da mayafi ta yi shiru tana tunanin wannan sabuwar rayuwar da zata shiga, kawai taji an ja ma ta mayafin aka cillar a ƙasa. A yatsine yake kallon ta kamar ya ga wani abin ƙi, ya buɗe baki da kyar yace "Finally kin yadda an daura auren, har an kawo ki gidan nan, ya yi kyau..." Ya faɗa yana cilla ma ta kaza wadda bisa umurnin Ammi ya siya. Ɗago kai ta yi ta ga yana ficewa daga ɗakin, "Ikon Allah." Ta faɗa a ranta. Tashi ta yi tana kallon ɗakin, gaskiya iya tsaruwa ya tsaru amma dimm gabanta ya faɗi sanin ba wani zaman daɗi zata yi a gidan ba. Haka ta yi ta hakuri da zama da Farouk, wata ranar ya dawo a bige ya neme ta ta ƙarfi, wata rana ya kawo matan banza har sai da abin ya dame ta ta gaya wa Ammi sannan ta tsawatar mai, shi ne ta ɗan samu sauƙin matan da yake kawo wa. A haka har ta haifi Mu'ayyad, a haka kuma Farouk bai daina abin da yake ba sai dai ma ƙaruwa da yake. Wannan kenan... *Cigaban labari* A karo na ba adadi Ummu Kulsum ta kuma fashe wa da wani kukan tuno rayuwar ta da ta yi a garin su, ga masoyinta da aka raba ta da shi ganin shi ba kowa bane . Da ta gaji da kukan ta tashi ta ɗauro alwala a banɗaki ta yi nafila tana kai ƙaran Farouk wurin Allah. ******************************** *Ladiyo* Tana nan har bayan sallar Isha'i a gidan Delu, sai wurin ƙarfe tara na dare sannan suka yi shirin zuwa wurin boka Barqaan. A hankali suke hawa kan tsaunin gudun kar wata ta fado wani abu ya same ta. Kamar yadda al'adar da kuma tsarin Barqaan yake, ba'a shigar mai kogo da kaya dole ka cire su , ka ajiye har sai ka fito. Babu tsoro ko kunya su Ladiyo suka aikata abinda aka umarce su kafin suka shiga cikin kogon. Boka Barqaan yana nan cikin kogon zaune cikin kazanta da ɗoyi wanda su Ladiyo basa ji sakamakon rufewa da idanunsu ya yi wurin neman taimako. Bayan ya gama ƴan tsubbace tsubaccen sa ya juyo ya kalli su Ladiyo, kamar wanda suke bautamai haka suka fara russunar da kai hade da kirari a garesa. Maganganu suka yi na lokaci mai tsawo sannan ya dauko wata ƙaramar baƙar laya a cikin ƙoƙon jakin da ke wurin ya miƙa wa Ladiyo yana faɗin "Wannan shi ne ƙarshen matsalar ki, ki yi aiki da shi zaki bani labari." Ya juya wurin Delu yace, "Duk abinda kike aikatawa ina ganin ki ta ƙwaryata, abinda zance shi ne ki bi a hankali ." Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru. Sumsum suka fice daga kogon bayan biyansa da suka yi da mutuncinsu. ******************************** *Ayaman* Baccinta take cikin kwanciyar hankali kawai taji alamar ana tashin ta daga bacci, a ɗan razane ta ja bargon ta rufe kanta tana karanto ayoyin Alkur'ani. Kuma jin ana jan zanin da ta rufa da shi ta ji ana yi, da sauri ta ja ta kuma tofa addu'a kusa da ita. Again aka kuma jan zanin, ta yi ta maza ta miƙe zaune, wayam babu kowa a ɗakin, chan ta hango wani abu kamar mutum a tsaye ya tunkaro ta. Duk addu'ar da ta zo bakinta take yi har wannan abin ya cimma ta.... Love you all 💞 💙 More comment more typing ✍️ https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 💞💙 Page 29-30 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Lokaci na ta shuɗewa, abubuwa na ƙara haɓaka, ta ɓangaren Ayaman ma haka. Lamura sai ƙara gaba suke dan yanzu Ladiyo ta yi yadda ta yi aka sa ranar aurenta da Anas, har yanzu bata gama mamakin Ladiyo ba har sai da ta ga saura watanni uku bikinta da Anas. Tashi ta yi daga kan zanin da take sallah, tsayawa ta yi ta na kallon tsakar gidan, gari ya waye tangararan, rana ta fara fitowa alamar za'a yi rana mai zafi. Ruwa ta ɗebo a randa ta shiga banɗaki, bayan ta fito ta fara aikin gidan, ta gama ta yi wanka tasa kaya. Abin kari Ladiyo ta miƙo ma ta dan ba laifi ta ga sauyi sosai daga wurin Ladiyo wanda bata gama yadda da shi ba. Ta kammala cin abincin ta fice zuwa gidan su tsahare dan bikin saura kwanaki uku. Ta na shiga gidan ta tarar da tsahare ana shafa ma ta kurkur dan shi ne abinda yawancin ƴan garin ke amfani da domin gyaran amarya. Bayan ta gaisa da Innar su tsaharen da wasu daga cikin ƴan uwansu tsahare, ta zauna aka fara fira tana taya su ayyuka har aka kammala gyaran jikin. Wuraren ɗaya na rana suka fita rabon katin biki , sun zagaya gidaje da yawa na ƴan uwa da abokan arziki sun raba kati. Sai ana kiran magriba suka shiga gidansu tsahare a gajiye. Innar su da sauran ƴan uwa da suka fara zuwa na ɗaki su na gabatar da sallar magriba. Bayan sun idar da sallah suka ci abinci sannan Ayaman ta yi ma ta sallama da niyyar gobe da wuri zata fito domin za'a yi sa lalle. ******************************* *Farouk* Ta ɓangaren Farouk da Ummu Kulsum abu sai ƙara tabarbarewa yake, dan yanzu an sa ranar auren Farouk da Nafee. Ummu Kulsum ta yi kukan har ta gaji, har ga Allah ta gaji da rayuwar gidan Farouk, ga Amminsa ma kamar shi ta daina bata kulawa kamar da. Dan akwai ranar da ta je gaishe ta, ta amsa ma ta ciki ciki kuma ta tashi ta bar falon. A ganin Ummu Kulsum ba laifi ne ba dan ta shiga ɗakin Ammi dan ta saba da hakan, mafi yawancin lokuta Ammin da kanta take jan ta ɗaki tai ta bata haƙuri saboda ta san zaman da suke ita da Farouk . Amma a wannan lokacin tana shiga ɗakin,Ammi ta hau ta da faɗa da masifa, "Banda tsabar munafirci, meye kuma na shigo min ɗaki? Tsaya kiji bazan dauki wannan abin ba dan haka fitar min a ɗaki!." Ammi ta ƙarasa cikin faɗa. Cikin tsoro Ummu Kulsum tace "Kiyi haƙuri Ammi, na zata ba laifi ne dan na shigo ɗakin ki ba." "Tunda na uwarki ne ay dole baza ki ɗauka laifi ne ba, fita kafin ki ƙarasa ɓata min rai." Ammi ta faɗa tana rufe idanu irin na wanda ke masifa. Sumsum Ummu Kulsum ta fita daga ɗaki tana mamakin me ya samu Ammi. Ta ɓangaren Ammi kuwa, hakanan taji ta tsani ganin Ummu Kulsum a kusa da ita, babu dalili ko ɗaya. Ummu Kulsum ta zauna a falon cike da zullumi, dan dama ta zo ne domin gayama Ammi halin da take ciki sai gashi ta tarar da Ammi a wani yanayi da bata taɓa ganin ta ba. ******************************** *Nafee* Yanzu kam Nafee ranta fess an sa ranar aurenta da Farouk sai bankar magungunan mata take ita ala dole sai ta koma budurwa, ga Lubna dake gefe tana ƙara zuga ta. Su na zaune a falon Nafee, Lubna na kallon wayarta sai ƙawar Lubna Zainab tana cin kayan marmari, ita luma Nafee ta na jujjuya wani abu a hannunta. "Lubna anya kuwa?" Nafee ta faɗa cikin rashin yadda da tantama tana juya maganin a hannu. "Nafee, kina tantama ne? Tsaya kiji wannan maganin sai da na tsallake rijiyoyi biyar kafin na amso miki su." Lubna ta numfasa sannan ta cigaba da faɗin, "Wannan ɗan ƙaramin, hmm." Ta faɗa ta a ɗaga sa sama. "Cika aiki kenan, in dai kika yi amfani da shi, hmmm wai inji mai ciwon haƙori ba'a magana kawai." Lubna ta ƙarasa faɗa tana yin alamar rufe baki kamar zip. Haka suka cigaba da hirarsu,su na ta shewa kamar an yi musu hajji da Umrah. ******************************** *Ladiyo* Abubuwa su na tafiyar ma ta yadda take so, dan yanzu ta sa malam Isyaku a gaba har sai da aka sa ranar auren Ayaman. Matsalarta, Nabila sai Yunusa amma wannan bai dame ta ba kamar Ayaman, ta tsani ganinta cikin farin ciki ko walwala. Ita da Delu ne suke kiɗansu suke rawarsu.. Love you all 💞 💙 More comment more typing ✍️ Khairat ✍️🤍https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 💞 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 31-32 Ita da delu ke kiɗansu su na rawarsu... Dan ayanzu haka, alhaji Gabatari ya nemi auren Mariya kuma Delu ta yi uwa ta yi makarɓiya sai da aka yadda da shi. Rayuwa ta yi ma ta sumul, bata da wata damuwa, dan yanzu ma Alhaji Gabatari ya aiko masu aikin gini zasu rushe gidan ayi musu sabo dal. Ta ɓangaren Malam Surajo kam ba'a magana, dan yanzu duk ya susuce duk wanda ya sanshi a baya ya ganshi yanzu sai ya kasa gane shi. Har ranar auren Mariya da aka sa bai da masaniya a matsayin sa na mahaifinta, sai lemu da Delu ta bashi tace an saka rana. Yanzu ma masu aiki ne ke ta fama da aiki, dan an ruguje gidan tass , Delu ta shigo gidan da yake a gidan wasu ƴan uwanta suke zaune kafin a kammala aikin. Washe baki ta yi tace "Sannun ku da ƙoƙari , kuna ta fama, kai sannunku sannunku." Ta ƙarashe maganar tana kallon ma'aikatan. Wani saurayi ne ya amsa ma ta suka gaisa cikin mutunci. Bayan ta gama zagaye gidan, ta fito tana mamakin wannan duniyar da ake ƙoƙarin gina musu. Kichibis ta yi da Ladiyo a hanya tana ta zabga sauri kamar ƴar maula. "Ahh ah , Ladiyo sai ina kuma?" Delu ta tambaya tana tsare Ladiyo da idanu. "Gidanki na yi niyyar zuwa, sai...." Sauran maganar ta maƙale ma ta a maƙoshi sakamakon ganin gidan Delu a ruguje dai aiki ake. "Wallahi da gaske ne, wayyo!" Ladiyo ta faɗa kamar zautacciya. Delu kam tsayawa ganin ikon Allah ta yi, dan ganin Ladiyo ta yi kamar mahaukaciya sai ɗaura hannu a kai take. Koma dai mene Delu tasan baƙin ciki ne Ladiyo ke nuna wa ƙarara. Wucewar ta ta yi ta bar Ladiyo na ta kwasar drama ita da leburorin. Gida Ladiyo ta koma zuciyarta cike da baƙin ciki, taya Delu zata samu wannan duniyar ita kuma ta na nan zaune? "Kai bazai yiwu ba!" Ta faɗa a karo na ba adadi. Nabila ce ta shigo gidan, kallon Ladiyo ta yi wacce duk ta susuce saboda ruɗewa. "Toh fah, Ladiyo lafiya kika zauna anan kike ta surutai kamar sabuwar kamu?" Shiru Ladiyo ta yi tana kallon Nabila, kai duk yadda za'a yi ma sai dai Nabila ta auri Alhaji Gabatari ko kuma kowa ya rasa. Gaya ma Nabila abinda ke faruwa ta yi suka tsaya suna shawarwari, a ƙarshe dai suka yanke cewa Ladiyo zata samu bokan kan tudu su zanta. *Ayaman* Shirye shiryen biki suke ba abinda ya dame su, dan yanzu ma kiɗan kwarya ake ta zabgawa a tsakar gidan su tsahare ana ta rausayawa. Sai wurin la'asar aka kammala kiɗan ƙwaryan, mutane sun fara raguwa tunda an kammala bikin yau saura kuma gobe da za'a ɗaura aure. Bayan sun gama hutawa suka kama hanyar gidan yayar tsahare, su kusan tara dan ba laifi ƴan uwan tsahare sun zo da dama. Hirarsu suke cikin kwanciyar hankali har dare ya tsaga, dan Anty Nusaiba ba ruwanta akwai hira. Da asuba da suka farka basu koma bacci ba suka shiga shirye shirye, gidansu tsahare suka nufa dan a chan ne amarya zata shirya. Wurin ƙarfe goma na safe aka ɗaura auren tsahare wanda asalin sunanta Fatima ita da angonta Usman. Biki kam ya yi biki dan kofar gidansu tsahare ya cika tanƙam da mutane ana shaida daurin aure yayin da mata ke cikin gida suna ta hidimar abinci. A ƙuryar ɗaki Ayaman ta sami tsahare ta yi shiru kamar mai tunani, kallonta Ayaman ta yi kana ta girgiza kai hade da murmushi. Zaunawa kusa da ita ta yi ta fara lallaɓa ta , kamar jira take tsahare ta saki wani kuka mai ban tausayi. Da ƙyar Ayaman ta rarrashe ta, ta ɗauko ma ta kayan da zata saka, girgiza kai tsahare ta yi sannan ta miƙe ta dauko wata atamfa mai ruwan toka da ja , ta miƙa ma Ayaman guda ɗaya ita kuma ta saka ɗaya. Riga sa skirt ne wanda ake ya yi tsahare ta ɗinka musu, ga ɗinkin ya yi matuƙar kyau, shiryawa suka yi aikuwa atamfar ta zauna daram a jikin Ayaman abin ka da farar fata. Fitowa sukai kamar ƴan biyu kowa sai yabawa yake, wata mata ce ta bude baki tace "kai ma sha Allah, Asma'u(babar su tsahare) wannan ƴan biyun naki kamar turawa, kai ma sha Allah, Allah ya nuna mana naki." Ta ƙarasa faɗa tana kallon Ayaman. Sunkuyar da kai Ayaman ta yi , suka cigaba da gaisawa da ƴan uwa. Wuraren ƙarfe shida na yamma, motar daukar amarya ta iso, duk da ba wata mai tsada bace amma babu laifi. Haka aka kwasa aka tafi kai amarya bayan nasihohi masu ratsa zuciya daga iyayenta da danginta. Ayaman da tsahare sun sha kuka iya kuka, dan da ƙyar aka raba su, ita a ganin tsahare barin Ayaman da zata yi, kamar zai bawa Ladiyo damar cigaba da cisguna ma ta. Ita kam Ayaman tana tunanin kewar ƙawarta mai ɗebe ma ta kewa a duk lokacin da taji duniyar ta yi ma ta zafi. An kammala biki lafiya an kai amarya gidan mijinta wanda babu karya Usman ya yi bajinta, dan ɗaki falle ɗaya da madafa sai tsakar gida da banɗaki wanda a wannan kauyen irin wannan ginin sai ƴar gata. Ga kayan ɗaki da aka ma ta daidai gwargwado anyi ƙoƙari, dan akwai samiru kusan ishirin da sauran kayan amfani na ƴa mace. ******************************** *Bayan wata biyu* *Ayaman* Kwana biyun nan ta rasa mai ke damunta, ta yi wani fari na ban mamaki da qiba, ita dai ta alaƙanta hakan da abubuwan da Ladiyo ke bata. Yanzu ma Ladiyo ce ta shigo ɗakin ɗauke da wani kwanon rubutu a hannunta, miƙa ma Ayaman ta yi "Maza shanye ki bani kwanon." Karɓar kwanon ta yi , ta sa dai-dai bakinta ta furta Bismillah a hankali, "Dan ubanki ba na hanaki wannan Bismillahn ba? Ko ke daƙiƙiya ce da baki gane hausa?". Ladiyo ta faɗa ta na kwace kwanon. Matse bakin Ayaman ta yi ta ɗura ma ta rubutun har wani yana zubowa. ******************************** *Farouk* Farouk kam yanzu kwata kwata ya daina kwana a gidansa, ya tare a gidan Nafee wacce yanzu ita kaɗai yake gani a duniyar shi. Yanzun ma kuwa shirye-shiryen biki suke yi abinsu. "Kalli wannan dress ɗin bae." Nafee dake kwance kan cinyarsa ta faɗa tana miƙa ma sa wayar. Amsa ya yi ya kalla, ya ɗan taɓe baki kaɗan yace "Ta yi." A takaice. Cigaba da kalle kalle a wayarta ta yi har zuwa wani lokaci ta tashi ta shiga ɗaki. Sai mun haɗu a next page, more comment more typing ✍️ 💙. Love you all 💞 Khairyy ✍️🤍https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB *(Posting room)* My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈 😈 By Khairat 💞 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 33-34 **Ummu Kulsum** Ta ɓangaren Ummu kuwa, ta mayar da al'amuran ta zuwa ga ubangiji dan ta yi imani shi zai kawo ma ta mafita. Yanzu ma tana zaune a ɗakinta duk abun duniya ya ishe ta, muryar wata mata ta ji a bayanta, "Kar ki damu Ummu, damuwar da kike ciki kaɗan ce ga wacce zaki fuskanta nan gaba...." Saurin juyawa ta yi domin ganin mai magana, sai taga wayam babu kowa. Saurin tashi ta yi ta fita daga ɗakin, shiru ta yi ta kasa taɓuka komai, ƙwanƙwasa gidan da ake yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula. Leƙawa ta yi taga baba maigadi baya nan, slippers ta saka sannan ta fita ta buɗe gidan. Masu aikin gini ta gani, bayan sun gaisa ne suke sanar da ita cewa maigidan ne ya aiko su. Shiru ta yi na wani lokaci kafin taji horn ɗin motar Farouk. Bayan ya shigo gidan ya bawa masu aikin umarnin fara abinda ya kawo su, wurin bayan gidan suka nufa suka fara aiki. Kangon dake kusa da su aka ruguje katangar aka hade da cikin gidan. Ummu na gefe tana kallon ikon Allah, dimm zuciyarta ta buga kar dai ace auren Nafee Farouk zai yi, "Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." Ta faɗa cike da tsoro, bin bayan Farouk ta yi cikin gidan, ɗakinsa ta nufa bakinta da sallama. Kofar ta ƙwanƙwasa kafin ta tura ta shiga ciki. A zaune ta tarar da shi a kan gado, "Sannu da zuwa Abban Mu'ayyad." Ko kallon iskar da ta kwaso ta bai yi ba bare ya amsa. Shiru ta yi sannan ta cigaba da magana, "Nace wannan masu aikin lafiya dai naga sun fara ruguje katangar gidan nan." "Tunda ubanki ne ya siyamin filin sai ki hanani kinji." Farouk ya dakatar da ita . "Kuma ki shirya, nan da sati biyu za'a ɗaura min aure da Nafeesa." Shiri Ummu ta kasa mayar mai da amsa, wani baƙin ciki ne ya taho ya tare ma ta maƙoshi, kafin ta tashi jiki a saɓule ta fice daga ɗakin. Tsaki Farouk ya yi kafin ya cigaba da danne danne a wayarsa..... ******************************** *Ayaman(p.o.v)* Mamakin yadda jikinta ya yi wani sumul ya yi haske take yi, ga wata ƙiba ta ban mamaki da ta yi. Indai tana lissafi yau saura kwana sha uku bikinta da Anas. Ladiyo ce ta shigo gidan kamar an hankaɗo ta, Nabeela na biye da ita. Ɗaki suka shige ko kallon inda Ayaman take basu yi ba, wannan halin Ladiyo na bin bokaye yana matuƙar damun ta , shirka ƙiri ƙiri kuma baka da bakin magana. Haka dai ta zauna a wurin na wani lokaci kafin nan ta shige ɗaki. ******************************** *Nafee (p.o.v)* Ta ɓangaren Nafeesa kam sai bankar magungunan mata take yi, duk ta bi ta rikice akan dole sai ta mallake Farouk, ga kuma ƙawayenta da ke gefe suna zuga ta . Ga shirin biki da take yi babu kama hannun yaro abubuwa dai ba'a cewa komai. *Bayan sati ɗaya* *Nafee da Farouk* Yau take ranar dinner kamar yadda suka tsara , amarya Nafeesa an sha kyau cikin wata bridal gown fara mai duwatsu a jiki, sai ango Farouk cikin shaddar shi fara ƙal wadda taji aikin yan Niger. Bayan shigo da amarya da angonta aka fara shagali kamar yadda aka tsara. Biki ya yi biki dan mutanen banzan da suka halarci bikin sun yi abinda ya kaisu, dan hotel ne guda aka yi renting domin shagalin biki. An sha giya da sauran kayan shaye shayen da aka gabatar a wurin da kuma sauran saɓon Allah wanda baza su ƙirgu ba. ******************************** *Ummu Kulsum (p.o.v)* Ita dai tun ranar da Farouk ya sanar da ita ƙarin aurensa bata kuma jin daɗin rayuwarta ba. Tsaye take a gaban ɗaya daga cikin falon, ƙare wa gidan kallo ta yi, wani ɓangare daban aka gina a gefen ɓangarenta. Wata aljannar duniya Farouk ya gina a wurin, dan danƙareren apartment ne mai ɗauke da ɗakuna uku kamar nata sai falo babba guda biyu da kuma kitchen babba a takaice dai part din Nafee ya fi na Ummu komai da komai. Wallahi ta yi dana sanin amincewa sa auren Farouk wanda Ammi ce ta roƙe ta akan ta amince. Shiru ta yi tana cigaba da tunani kafin taji muryar Maryam tana miƙo ma ta Mu'ayyad. Amsar yaron ta yi, Maryam ta yi ma ta sallama da niyyar tafiya gida tunda yamma ta yi. Bayan ta amshi yaron ta goya sannan ta daura abincin dare dan kanta da baba maigadi dan ta manta yaushe rabon da Farouk yaci abincinta. Ga tarewa da ya yi a gidan Nafee sai yaga dama yake shigowa gidan idan zai ɗauko wani abin. Ita wannan rayuwar tasu tana bata mamaki . ******************************** *Ayaman (p.o.v)* Yau dai ya rage kwana uku bikinta da Anas amma duk wani shirye shirye da akr yi wa amarya bata ga anyi ma ta ba. Ladiyo ce ta shigo gidan kamar an hankaɗo ta, wata baƙar leda ta cillo ma Ayaman kafin ta shige banɗaki da gudu. Bayan ta fito ta ajiye butar take cewa Ayaman "Gashi nan , mahaifiyar Anas ce ta bayar a baki, kinsan ba shi da wasu yan'uwa bayan mahaifiyarsa." Ladiyo ta ƙarasa cikin isgili kamar zata yi dariya. Ledar ta buɗe taga atamfa leda guda biyu, ɗaya riga da skirt sai ɗaya doguwar riga ɗinkin simple ne ba wani ado. Sai hijab guda ɗaya da takalmi guda ɗaya, sai man shafawa da hoda da kwalli guda ɗaya. Guɗa Ladiyo ta saki kafin ta kyalkyale da wata dariya , "Yanzu dai a taƙaice wannan ne lefe? Hehehehe lefe iya lefe." Ladiyo ta ƙarasa cikin dariya har da riƙe ciki. Ɗaki Ladiyo ta shige tana wata dariyar. Ayaman kam kayan ta ɗauka ta shige ɗaki, gaskiya taji daɗi dan Anas ya yi ƙoƙari, dan rabonta da sabon ɗinki kusan shekara goma kenan a lokacin da mahaifiyarta ke da rai. Sai mun haɗu a page na gaba, domin jib wannan auren zai yiwu kuwa🤔, . Khairat ✍️ 🤍 https://chat.whatsapp.com/BozyCwTPDOt1Lh4BxMMKq4 *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 35-36 Hausawa suka ce rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Ranar jumm'ah da misalin ƙarfe goma na safe ɗaruruwan mutane suka shaida ɗaurin auren Farouk Aliyu Datti da amaryarsa Nafeesa Ishaq a masallacin markaz imam Sadik dake rijiyar zaki Kano. Ango Farouk ya sha shaddarsa ruwan madara wacce ta ji ɗinki na gani na faɗa, mutane da abokan arziki har ma da mutanen banzan da suka halarci taron sun taya sa murna. Bayan an gama ɗaurin auren a kan sadaki naira dubu ɗari biyu, ango da mutanensa suka wuce five star hotel domin gudanar da reception. Kalolin abinci da dama sai wanda mutum ya zaɓa ga kuma abubuwan sha kama daga lemuka namu na gargajiya, giya da sauran kayan shaye shaye. An ci an sha an yi nak kuma an aikata ɓarna a wannan taron. ******************************** *_Amarya Nafee_* Ta ɓangaren Nafeesa kam, tun daga lokacin da Farouk ya sanar da ita ɗaurin aurensu taji kamar an mallaka ma ta duniya da abinda ke cikinta, dan farin cikin da take ciki ba zai misaltu ba. Kyaututtukan abubuwa da dama ta rinƙa yi kama daga kuɗi , kayan sawa, turarurruka da sauransu. Bayan haka ta tara mutane dankam a cikin gidanta ana ta budiri dan har masu kiɗan ƙwarya suka hayo domin a chashe. ____________________________________ *_Ayaman_* Yau tun da ta tashi da asuba jikinta yake ma ta wani yarrr. Da ƙyar ta tashi ta ɗauro alwala ta yi sallah a ɗakinta. Bayan ta idar da sallar ta zauna tana kallon ɗakinta, "Kamar ba gidan biki ba." Ta furta a hankali. Ita dai a ganinta ba haka gidan biki yake ba, dan da bikin Tsahare tun asuba ake fara hidima. Shiru ta yi na wani lokaci ki kafin ta buɗe bakinta ta ce "Ko da yake ni ba kamar koya nake ba, bani da gata mahaifiyarta ta rasu ta barni a lokacin da nake tsananin buƙatar ta." Kuka ne ya kufce ma ta, sai da ta yi kuka mai isar ta sannan ta miƙe. Ta fita tsakar gida , kofar su Ladiyo ta kalla , a kulle alamar su na ciki su na sharbar bacci. Tsintsiya ta ɗauka ta fara share tsakar gida, bayan ta kammala ta ɗauko kwanuka ta fara wanke wa. Sallama ta ji ana rapkawa a kofar gida, muryar da baza ta taɓa mantawa ba a rayuwarta. "Addah Asiya!!!!." Ta furta da ƙarfi tana wani irin tsalle. Faɗawa jikin ƙanwar mahaifiyar ta ta ta yi tana wani kukan farin ciki. Addah Suwaiba da su Addah maimuna ƴanuwan mahaifiyarta ne suka ƙarasa shigowa. Haɗasu Ayaman ta yi ta rungume su kamar za'a kwace ma ta su. Hawayen farin cikin dake tsere a fuskarta ne Addah Asiya ta goge ma ta da mayafinta. "Menene na kuka kuma ɗiyar mu?." Addah Asiya ta furta ita ma kamar zata yi kuka. Tabarmar Ladiyo Ayaman ta ɗauko ta shimfida musu, bayan ta dawo kusa da Addah Maimuna ta kwanta luf a jikinta, ji take kamar a jikin mahaifiyarta ta ke kwance. Shiru ne ya biyo baya na wani lokaci kafin Addah Asiya ta buɗe baki ta ce "Ina Ladiyo?" "Tana ɗaki basu tashi ba.". Ayaman ta bata amsa sannan suka ci-gaba da hirar su ta yaushe gamo. Ayaman ta zauna ta fara basu labaran abubuwan da suka faru tun daga zuwansu na ƙarshe. Kowannen su ba wanda bai zubar da hawaye ba, a lokacin Adda Asiya ta ke tambayar Ayaman ina kayan ɗakinta. Shiru ta yi dan ko cokali ba'a kawo ma ta ba. Ladiyo ce ta fito a firgice babu salati bare addu'a sai uwar hamma da take zuba wa. "La'ilaha illah , Asiya! Suwaiba ! Maimuna! Kune a gidan." Ladiyo ta faɗa tana washe dashashun haƙoranta. Ta buɗe baki ta cigaba da faɗin, "Sannunku da zouwa." Ko kallon iskar da ta kwaso Ladiyo basu yi ba, idon Ladiyo ne ya kai kan tabarmar da suke zaune. "Kam bala'i, uban wa yace ki ɗauko min tabarma ki shimfiɗawa wannan matsiyatan?" Kalmar matsiyata shine ya daki kunnen Addah Asiya. Zabura Adda Asiya ta yi zata yi kan Ladiyo Adda Maimuna ta tare ta. "A'a Asiya kinga dai mai ya faru kwanakin baya." Tsaki Ladiyo ta saki ta fara zuba waƙar habaici iri iri. Tashi suka yi Ayaman ta kai su gidan su Tsahare, umman su Tsahare cike da murna da mutunci ta karɓe su hannu bibbiyu. Sai mun haɗu a next page . Love you all 💞 🥰 Pls more comment more typing ✍️ 🤍. Khairat ce ✍️🤍https://chat.whatsapp.com/KTQQxgEVbju3BpJCQ2YBMu *{Posting room}* *[ My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇]* https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 37-38 Bayan su Addah Asiya sun zauna a kan tabarmar da umman su Tsahare ta shimfiɗa, nan suka fara mai da zance. Ran Adda Asiya in ya yi dubu toh ya bace, sai a sannan ne Ayaman take jin babanta bai sanar da su Addah Asiya a kan ɗaurin aurenta da za'a yi yau sai wani saurayi da ke zuwa cin kasuwa garin ya sanar da su. Nan suka fara tunanin haka da za'a kai yarinya babu ko cokali, nan dai suka gama shawara da umman Tsahare a kan zata raka su wurin dillaliya su siya kayan kitchen da sauransu. Suna isa wurin dillaliya suka fara kwasar kaya dan dama da uwar kuɗinsu a ƙugu. Duk abubuwan da ƴa mace take buƙata na aikin gida su Adda Asiya sun siya mata shi, kama daga flask din abinci zuwa na shayi da ruwan zafi, cups , cokula, tukwane, ɗan karamin gas , plate da dai sauransu. Su na gama biyan dillaliya kuɗinta suka bawa yara kayan akai gidan su Tsahare su kuma suka wuce kasuwa. Gado suka fara taya wa a wurin wani kafinta, gadon ya yi kyau duk da ba wani quality ne da shi ba, sai wata sabuwar katifa mai haɗe da pillow guda biyu. Ganin lokaci zai ƙure ya sa suka siya gadon da mudubi da wardrobe mai guda uku sai kuma wani set ɗin kujerun ƙarfe kalar brown da suka siya. Direct suka wuce gidan su Tsahare da kayan, yara da manya kowa ya tsaya yana kallon ikon Allah sai da Addah Asiya ta fara rashin mutunci sannan kowa ya watse. Shiga cikin gidan suka yi suka tarar da Ayaman an shafa mata kurkur a jiki, Tsahare na gefe tana tsokanar ta,guda Adda Asiya ta saki kafin ta ɗan taka rawa. Kiran sallar azahar ce ta tasar da su, bayan sun idar da sallah aka shirya amarya Ayaman cikin atamfa doguwar riga. Tsaff amarya Ayaman ta fito cikin atamfar da tayi matuƙar kama jikinta. Kafin kace me ƴan gulma da munafirci sun fara shigowa gidan da sunan yinin biki. Karfe biyu na rana bayan an sakko da masallacin juma'a aka ɗaura auren Fateema Ishaq (Ayaman) da kuma angonta Anas Mustafa a kan sadaki naira dubu talatin. ******************************** *_Ummu_* Ɗaya daga cikin window dake falon ta leƙa, motar baffi furnitures ta gani pake a daidai kofar sabon sashen da Farouk ya gina. Wata mata ce ta fito daga sashen kanta yaji ƙarin attachment ga hannayenta kamar an yi babbaka alamar ta yi bleaching har ta gaji. Zuciyar Ummu ce ta buga dimm, yanzu ta ina za ta iya kishi da karuwa? Tana nan tsaye aka fara shigar da kayan ciki, cikakkun royal bed set da royal chairs ne masu matuƙar ɗaukan hankali. Gajiya ta yi da tsayuwar ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun. Ta rasa me ke mata daɗi, sam duniyar ta fita daga ranta, kar dai ta fara son Farouk da har take irin wannan kishin? Mu'ayyad ne ya taho a irin keken yara wanda suke koyar tafiya ya ƙaraso wurinta, surutansa wanda ta kasa gane mai yake faɗa ya fara yi mata. Kunna TV ta yi ko takaicin da take ji a zuciyarta zai ragu.... ******************************** *_Nafee_* Sanye take cikin dakkaken lace ɗin ta mai kalar maroon da yaji danƙareren ɗinki na gani na faɗa. Zaune suke a falonta ita da sauran ƙawayenta su na chapkewa. Ringtone ɗin wayarta ne ya sa ta ɗauka domin ganin mai kiran, Farouk ne, da sauri ta miƙe ta nufi ɗakinta. Tana shiga ta tarar da wasu ƴanmata a kwance alamar sunyi shaye-shayen har sun gaji. Ɗaka musu duka ta yi kafin kowacce ta fice a hankali tana tamɓele irin na masu shaye shaye . Kiransa ta yi da kiran ya riga ya katse, "Hello." Farouk ya faɗa daga ɗayan ɓangaren. "Hello angon Nafeesa." "Ya taro moonlight (haka yake kiranta) ?" "Mun gode Allah.". Nafee ta faɗa tana wani karya murya. "Good, dama kira nayi na gaya miki na turo motaci za'a zo a ɗauko ki." Shiru Nafee ta yi na wani lokaci kafin taji ƙittt Farouk ya kashe wayarsa. Wallahi wannan miskilancin na Farouk yana bata mamaki, duk da cewa aikin boka yana ci amma har yanzu sai yaga dama yake yin abinda take so. Fita ta yi ta tarar da su Hajiya Turai da muƙarrabanta sun iso. Da gudu Nafee ta faɗa kan Hajiya Turai tana faɗin "Hajiyata sannu da zuwa." Hajiya Turai na murmushi ta amsa wa Nafee. Lubna Nafee ta kira ta sanar da ita Farouk ya aiko da motocin amarya. Cikin gaggawa suka nufi ɗaki ita da Lubna. Su na isa ɗakin Lubna ta yi sauri ta tara ruwa a banɗaki ta barbaɗa maganin da boka ya basu. Bayan Nafee ta yi wanka da ruwan, Lubna ta fito da wani turare kai daga ganinsa kasan ba alkhairi bane ta miƙa wa Nafee. Shafa turaren ta yi sannan ta yi hayaƙin da boka ya basu hade da shafa kwallin mallaka wanda suka amso a wurin boka. Tsaff Nafee ta shirya cikin atamfa mai matuƙar tsada da kyau sannan ta lulluɓe cikin lifaya kamar yadda ake yiwa amare. Sai gidan Farouk.......... (Mu dai namu fatan alkhairi ne, Allah ya bada zaman lafiya) ******************************** *_Amarya Ayaman _* Gidan su Tsahare ya cika tanƙam da mutane dan sai hidima ake kamar nan ne gidan bikin. Ladiyo ce a tsaye a kan matan da ke aikin abinci kamar wata isasshiya sai bada unarni take. A cikin ɗaki kuwa Ayaman ce zaune ita da Tsahare su na hira sama-sama, "Wallahi Ayaman naji miki daɗin auren nan da za kiyi, kinga kema kin huta da uƙubar Ladiyo." Ayaman bata ce komai ba sai murmushi da ta yi. Sallamar su Addah Asiya ta jiyo sun dawo daga jere. Guɗa ake ta saki kamar ba gobe duk gidan ya ɗauka. Nan dai suka yi zamansu har aka yi kiran magriba, umman su Tsahare ce ta shigo da sauri tana faɗin "Ayaman tashi maza maza ga masu ɗaukan amarya sun zo." Cikin sanyi jiki Ayaman ta miƙe , wanka ta yi da ruwan da umman su Tsahare ta haɗa , tana wankan tana jin wani irin yanayi da ta rasa na mene ne. Bayan ta kammala wankan umman su Tsahare ta shafe ta da turarurruka sannan ta saka wata doguwar rigar atamfa sai dogon mayafi da aka naɗe ta da shi. Ladiyo ce kan gaba wurin tare amarya tana faɗin "Yi nayi bari na bari, kar naji kar na gani." Kamar wata mutuniyar arziki. Motoci ne guda uku, ɗaya wato ta amarya Toyota ce sai sauran golf . Ladiyo ce ta yi charaf ta shige gaban mota tana washe baki sai Delu da ta bi bayanta tana ƙoƙarin shiga bayan motar inda aka sa Ayaman, Adda Asiya ta yi saurin janyota. Watsar da ita gefe ta yi kafin suka yi shigewarsu suka bar Delu da ƙunar rai......... Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ 🤍 Love you all 💞 🥰 Khairat ce ✍️ 🤍https://chat.whatsapp.com/KTQQxgEVbju3BpJCQ2YBMu *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 39-40 __________ Su Ladiyo ne a gaban mota sai washe baki take yi, "Malam direba ka hanzarta mana." Ladiyo ta faɗa tana kallon direban. Cikin mintinan da basu wuce talatin ba suka ƙarasa gidansu Anas inda Ayaman zata zauna. Shiga cikin gidan suka yi da sallama , su na shiga suka tarar da innar Anas da wasu aminanta guda biyu dan duk ƴanuwan su Anas ba'a garin suke da zama ba. Gaisuwa aka shiga yi cikin mutunta juna kafin aka buɗe ɓangaren Ayaman, ɓangaren ciki da rumfa ne ma'ana falo ɗaya sai ɗaki a ciki. Ta hagu kuma ɗanƙaramin kitchen ɗin ta ne wanda kayan kitchen ɗin da su Addah Asiya suka siya ma ta ne a ciki. Ta dama kuma ɓanɗaki ne sai ɗan tsakar gida ƙarami. Shiga cikin ɗakin suka yi da amarya, zo kuga yadda Ladiyo baƙin ciki ya fito ƙarara a fuskarta. Ƴan kujerun ƙarfe ne a falon masu kalar brown masu kyau duk da ba masu tsada bane. Sai wasu adon ɗaki da suka sa falon ya haskaka . Ƙuryar ɗaki aka shigar da amarya aka zaunar da ita a kan gado, shima dai ɗaki ba'a cewa komai dan ya yi kyau kalar dai mai ƙaramin ƙarfi. Har da wardrobe mai guda uku da mudubi ƙarami. Ladiyo tsaye ta yi tana kallon dakin bakinta cike fal da tambayoyi. ******************************** *_Amarya Nafee _* Zaune take a kan gadonta wanda kana gani kasan an narka naira wurin siyansa. An lulluɓe ta cikin lifaya mai kalar ja da baƙi mai matuƙar tsada da kyau. Lubna ce ta shigo da gudu ta tarar da Nafee da wata ƙawarsu zee a kan gadon. "Kuyi sauri ga tawagar ango." Ta faɗa tana miƙar da Nafee. Turaren da kwallin da boka ya basu suka kuma bulbulawa Nafee. Sannan suka kimtsa kafin suka bar ango da abokansa shigowa. Da sallama suka shiga ɗakin, Farouk na shiga yaji dimm zuciyarsa ta buga babu dalili. Addu'oi da fatan alkhairi ne suka biyo baya kafin abokan ango suka sallami ƙawayen amarya sannan suka wuce. Fita Farouk ya yi dan ya raka su sannan ya kullo kofar, a kitchen ya tsaya ya taho da plate da cups. Yana shiga ɗakin ya tarar Nafee har ta miƙe ta cire lifayar, bata ce mai ƙala ba ta shige banɗaki ta yo wanka. Kayan baccinta ta ɗauko wata yaloluwar riga da ita gwara babu dan duk wani abu na jikinta ya bayyana. Shima cire rigarsa ya yi ya watsa ruwa sannan ya sa kayan bacci. Yana fitowa ya tarar Nafee har ta buɗe kazar ta fara ci, sai a sannan suka haɗa ido. Wallahi tun da yake bai taɓa jin wannan tsoron ba a ransa, sai ya ga Nafee duk ta canza ta zama wata zakanya. Shiru ya yi dan ji ya yi kamar an kulle mai baki, sannan shima ya zauna . Kazar ta miƙo mai ya buɗe baki kamar ƙaramin yaro yana ci. Chan kuma ta ture kazar ta miƙe ta yo brush a ɓanɗaki, ta fito ta tarar baya ɗakin. Kwanciyar ta ta yi kafin taji shigowar sa ɗakin ya rufe ya kashe fitila. Yana hawowa kana gadon ta jawoshi jikinta, "Angon Nafeesa." Ta faɗa cikin wata siririyar murya. Bata jira ya amsa ma ta ba ta haɗe bakinsa da nata...... More comment more typing ✍️. Love you all 💞 Khairat ce ✍️ 🤍 https://chat.whatsapp.com/KTQQxgEVbju3BpJCQ2YBMu *(Posting room)* *(My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇)* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 41-42 Sai da ta daɗe tana masa wani irin rikitaccen salo kafin ya yi sauri ya ture ta. "Pls mana my dear." Nafee ta faɗa tana wani kashe murya. Gaskiya shi gani yake baze iya barin wani abu ya shiga tsakaninsa da Nafee ba, dan Allah na gani yasan Nafee karuwa ce, tun ba yau ba, amma shi kansa ya rasa yadda zai hana aurensa da ita . Cikin fushi ta kuma jawosa ya kufce, kamar wani yaro ya rasa mai zaiyi ma, tsaki ta yi kafin ta daka masa wata irin tsawa kamar uwarsa. Haka ya biye mata har ta biya buƙatarta, ko hauka yake yasan Nafee ba budurwa bace amma ya rufe bakinsa tsit!!! (Su Nafee wannan iko ) ******************************** *_Ayaman_* Bayan wani lokaci Adda Asiya ta kora mutane ganin dare ya yi , sannan aka bar Ayaman ita kaɗai tunda ba wasu ƴanuwa da ƙawaye take da su ba. Su na tafiya Ayaman taji shigowar su innar Anas, bayan sun gama bata haƙuri duk a ganinsu kukan rashin gida take ita kuwa tasan kukan me take. Bayan sun fita ta miƙe ta leƙa ta taga, hasken farin wata ne tarr ya fito ya haskaka ilahirin garin. Ƙarar wutar nefa ce ta bugi kunnenta kafin taji mutanen unguwar sun ɗau kuwwar "Nepa!!!" Da alama sun daɗe basu ga wutar nefa ba. Ƙare wa ɗakin kallo ta yi , banda "Ma sha Allah." da "Allah ya saka da alkhairi." babu abinda take faɗa. Ta leƙa kitchen da banɗakin, gaskiya sun mata kyau bata taɓa tsammanin haka su Adda Asiya suka kashe kuɗi ba. Ta koma ɗakin ita dai komai ya yi mata wallahi, agogon dake jikin bango ta kalla, da yake ba sabawa da agogo tayi ba sai bata gane ƙarfe nawa bane. Alwala ta ɗauro kafin ta rama sallar isha'i da ake bin ta. Muryar Anas taji yana gaisawa da mahaifiyarsa kafin ya yi mata sallama . Ya shigo sashen nasu bayan ya rufo kofa. Ƙara ɗuƙufar da kanta ta yi jin muryarsa a ɗakin, "Waalaikumus salaam." Ta amsa masa sallamar. "Amarsu ta ango." Ya faɗa yana ƙara washe baki. Shiru suka yi na wani lokaci kafin ya tashi ya umarce ta da su gabatar da raka'a biyu dan su godewa Ubangiji ga wannan ni'ima tasa. Bayan sun idar ya fito da ledar tsirensa wanda sai tashin kamshi yake ga ɗumi alamar bai daɗe ba, sai kuma lemon zaƙi da kuma fanta guda ɗaya. Buɗe fantar ya yi ya miƙa wa Ayaman, girgiza kai ta yi alamar a'a, takura ta ya yi har ta amsa ta kurɓa ta ajiye. Tsiren ya ɗauko zai kai bakinta, kamshin turarensa da kuma kamshin tsiren ya haɗe mata sai jin tashin zuciya ta yi kafin kace me ta fara amai....... ******************************** *Ladiyo* Cike da tunani kala² ta koma gida, kanta duk ya yi zafi, wai taya za'a ce Ayaman ta tafi gidan ni'ima haka? "Wallahi bazai yiwu ba, ko zan tafi tsirara sai na hana Ayaman zaman lafiya!!" Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ Khairat ce ✍️ 🤍 Love you all 💞😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 *(Posting room)* https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *My WhatsApp group comment section 👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 43-44 _____________Haka Ladiyo ta gama surutanta har ta jira shigowar Nabila gidan. "Toh ni mai kike so nace Ladiyo?" Nabila ta faɗa tana kurɓar yoghurt ɗin hannunta. "Bangane mai zaki ce ba? Kin manta alwashin da naci a kan Ayaman? Wallahi bazan bar ta ta zauna lafiya ba." Ladiyo ta ƙarashe cike da takaici. "Ba ma wannan ba, kinsan Alhaji Gabatari yana so ya turo a fara maganar auren mu." "Ayiririri , lallai ne kice su Nabila sai gidan Alhaji." Ladiyo ta ƙarashe cikin shewa. Firarsu suka cigaba da yi kafin dare ya tsala suka nufi makwancin su. ******************************** *_Ummu Kulsum _* Tun da ta zauna a falon bata kuma motsawa ba illa kallon tv da take wanda shima ba ganesa take ba. Kukan Mu'ayyad ne ya tasar da ita ta nufi ɗaki, dan kwantar da shi. Ta kwantar da shi a gadonsa kenan tana tofa mai addu'oi sai jin shewa da kuma muryar masu kawo amarya. Ita a ganinta ana kawo amarya gurin uwargida domin sanin juna amma ko hauka take tasan ba zai yiwu ba. Chan taji muryar wata mata da alama irin maroƙiya ce sai kirari take yiwa amarya Nafeesa wacce ta laɓe luff a cikin lifayarta purple color. Tsaye tayi tana sauraron matar ta window tana faɗin "Ki shiga ki fito da munafuka Nafeesa, kin ci dubu sai ceto mata ƙwalli ɗaya a gidan Farouk Datti, yanzu Farouk zai san ya yi aure wallahi." Matar ta ƙarshe cike da tsiwa da kuma shaƙiyanci. Haka suka sallame ta da kuɗaɗe kafin aka shigar da amarya sashinta. Haka ta zauna a ƙasan tiles ta rasa me ke mata daɗi, wani yanzu Farouk zai san ya yi aure, hawayen da bata shiryawa ba ne suka taho ta kuncinta. Wannan kalaman sun mata zafi, ita kanta ta san ta kamu da son Farouk tunda ba tun yau suke tare ba, bugu da ƙari Farouk mugun ɗan wanka ne wanda a kallo ɗaya zai iya sace zuciyar mace. Tana nan a zaune a wurin har taji shigowar tawagar ango da abokansa, leƙa wa ta yi ta taga ta hango Farouk sai sheƙi yake cikin dakakkiyar shaddarsa ruwan madara mai kyau da tsada. Tana tsaye har ta ga fitowar su tare da ƙawayen amarya sun wuce sai Farouk da ya biyo bayansu. Karaff suka haɗa ido da Farouk, sakin wani makirin murmushi ya yi kana ya mata blowing kiss. Alwala ta ɗauro ganin zaman bai da wani amfani sannan ta tayar da sallah. Ita kanta bata san adadin raka'ar da ta yi ba ta fara jin bacci. Kayan bacci ta sauya sannan ta kashe fitila ta kwanta. Ihun da Nafee take yi duk ya bi ya takura ta,da take bangon dakinta da na Nafee katanga ɗaya ce dan a manne suke. Mamaki falll a ranta, "Dama haka amarya take a daren farko?" Tambayar da ta yi ta sako wa kanta kenan babu mai amsa mata. Gaba ɗaya ta kasa baccin ga Mu'ayyad da ya dame ta da rigima ta rasa ta meye, tashi zaune ta yi duk ta rasa me ke mata daɗi da yaron zata ji ko da wannan mutanen? ******************************** *_Delu_* Cikin kuka Mariya ta shigo gidan tana bubbuga ƙafa, "Wallahi Inna sai na aure Alhaji Gabatari, taya zai ce ya fasa aure na?" Ta ƙarasa maganar cikin kuka. "Ya fasa aurenki kamar ya?" Delu ta zabura tana tambayar ta. "Wallahi cewa ya yi ya fasa aure na wai da Nabila zai yi auren." "Wace.. Nabeelan...?" Delu ta tambaya a ɗan tsorace. "Nabeelan Ladiyo mana, wannan munafukar ƙawar taki." Mariya ta faɗa cike da rashin kunya. "Kam bala'i Ladiyo......." Delu ta saɓi mayafinta ta fice daga gidan. ******************************** *_Ayaman_* Haka suka kwanta cike da tantama a ranta, amai? Ta ya ya? Sune tambayoyin da take ta yiwa kanta. Anas kuwa banda lallaɓata ba abinda yake dan har ga Allah ya na matuƙar son Ayaman. Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ Khairat ce ✍️🤍 Love you all 💞🥰 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 45-46 --------------------------------------------------- Ƙarar bige kwanikan ne ya fito da Ladiyo babu shiri, "Wani ɗan...." Sai kuma tayi shiru sakamakon ganin Delu tana huci kamar zakanya. "Aw Delu, kece kike wannan ɗayan aikin sai kace taɓabɓiya?" "Uwarki ce taɓabɓiya Ladiyo, ni za ki yi wa wannan rashin amanar? Ki juyar da hankali Alhaji ya koma kan ƴar ki? Toh wallahi ko sama da ƙasa zata haɗe ba zai yiwu ba." "Hehehe." Ladiyo ta kece da wata irin dariya kana ta cigaba da faɗin "Ashe a kan wannan ƴar ƙaramar maganar kika kwaso jiki kika zo min gidan da tsohon daren nan, toh bari kiji gobe in Allah ya kaimu Alhaji Gabatari zai turo a nemar masa auren Nabeela." In ran Delu ya kai dubu to ya gama ɓaci, ta juya bayanta taga tunkunyar da suke girki ta ɗauko ta tayo kan Ladiyo. Cike da dabara Ladiyo ta juya bayan Delu ta kwace tukunyar ta rafka mata a kai. Kafin kace me faɗa ya kaure tsakaninsu, ita Ladiyo ga girman jiki ga ƙarfi, ita kuma Delu ga ƙanƙantar jiki ga kuri. Mutane ne suka fara shigowa gidan duk da dare ya yi dan ganin mai ke faruwa, Baba Lami ce wata dattijuwa a layinsu ta shigo tana faɗin "Ku rabu da karnuka su cinye kansu, ji kaina wannan munafukan sun addabe ni haka ina ji ina gani suka daƙile auren Binta saboda tsabar munafinci." Haka kowa ya fara ja da baya yana tofa albarkacin bakinsu, a ƙarshe dai Delu ganin Ladiyo na ƙoƙarin kashe ta ta samu hanyar tsira ta fice tana faɗin "Allah ya isa kuma sai ta rama." Ladiyo kuwa ranta fess ta doke shegiya haka ta rufo kofarta. ******************************** *_Farouk da Nafee _* *Bayan wayewar gari* Taɓa sa da taji yana yi ne ya tasar da shi, "Good morning angona." Nafee ta faɗa tana shirin kai mai kiss. Saurin tashi ya yi daga gadon ya shige banɗaki ya kullo kofar. Brush ya fara yi kafin ya yi wanka, sai da ya kammala wankan ya ga babu towel bare wasu kayan, gashi wallahi mugun kunyar Nafeesa yake ji dan jiya ta shayar da shi ruwan mamaki. Tsayawa ya yi na kusan minti goma sannan ya mayar da kayansa ya fito. A kan gadon ya tarar da ita tana ƙoƙarin magana ya yi saurin ficewa daga ɗakin. Direct sashen Ummu Kulsum ya nufa, ƙwanƙwasa ƙofar ya yi dan a kulle take kuma babu mukulli a hannunsa. Ummu ce ta zo buɗe masa sai Mu'ayyad da ke bayanta yana tafiya a keken koyon tafiya, "Ina kwana." Tayi saurin gaishesa haɗe da russunar da kai. Bai amsa mata ba ya ɗauki Mu'ayyad suka nufi ɗakinsa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kullo ƙofar. Aikinta ta cigaba da yi a kitchen har ta kammala, shigowarsa kitchen ɗin ta ji shi da yaron a hannunsa ya na ta mai wasa. Ya sauya kaya ya sa wasu ƙananan kaya na shan iska. "In kin kammala abincin ki kai ɓangaren Nafeesa muna jiranki." Abinda ya faɗa kenan sannan ya yi ficewarsa daga sashen. A falo ya tarar da Nafee ta na kallo, kallonsa ta yi kafin tace "Wannan yaron fa?" "Ai kin san ɗa na ne ko kuwa." "Ko ma jikanka ne wallahi mayar da shi wurin uwarsa zaka yi, dan baze zo ya ɓata min sababbin kujeru na ba." Shiru Farouk ya yi, dan Nafee kam tsoro ta fara bashi. Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ne ya ja hankalinsu zuwa wurin, "Waye?" Farouk ya tambaya. "Ni ce." Ummu ta mayar mai cikin sassanyar muryarta. Buɗe ƙofar ya yi ya bara damar shigowa falon, "Ina kwana?" Ummu ta gaisar da Nafee. Ko kallo bata ishe ta ba ta cigaba da kallonta. "A ina zan ajiye abincin?" Ummu ta kuma tambaya. "A kan uwarki, baki ga dining ba?" Nafee ta bata amsa a zafafe. A hankali Ummu ta tashi daga tsugunon ta nufi dining ta ajiye abincin. Har ta yi hanyar fita ta ji muryar Farouk "Zo ki ɗauke yaron." Ɗaukar Mu'ayyad ta yi suka fice daga sashen. Tana shiga sashenta ta zauna tana tunani, yanzu da wannan mutanen zata zauna? ******************************** *Ayaman* Da asuba ta farka, alwala ta ɗauro kafin tazo ta tashi Anas, ya shirya ya fice zuwa masallaci, ita kuma ta tayar da sallah. Ta na cikin azkar taji shigowar Anas, "Ina kwana?" "Lafiya ƙalau Ayaman, ya kwanan sabon wuri?" "Alhamdulillah." Komawa ɗaki ya yi ya kwanta, ita kuwa Ayaman ta yi tsuru dan ba saba baccin safe ta yi ba. Kan kujera ta koma ta kwanta ta na tunanin wai ita ce a kujera yau, tunda take a rayuwa bata taɓa ganin kujeru na falo a gidansu ba sai dai wani gidan amma yau ita ce a nata kujerun. Ikon Allah kenan kowacce irin ƙaddara Allah ya baka akwai sakayya in dai kayi haƙu. Bacci ne sama² ya fara ɗaukarta, ta gyara kwanciyarta ta fara bacci. Taɓa ta da taji ana yi ne ya yi saurin tayar da ita, Anas ne ya na sakin wani lallausan murmushi a fuskarsa. Tabbas Anas kyakkyawa ne mai kyakkyawar zuciya, "Ayaman!" Taji ya ambaci sunanta. "Na'am." Kallon kallo suka tsaya yi kafin ta yi saurin janye idonta ta miƙe, wani uban jiri ne ya kwasheta yarap ta faɗi a kan kujera. Anas ne ya bita da sannu kafin ya ɗebo mata ruwa a zatonsa ko rashin ruwa ne. Muryar mahaifiyarsa taji ta na ƙwallamai kira, ya na isa ta miƙa mai flask ɗin ruwan zafi da na abinci. Ɗauka ya yi ya na godiya, buɗe kular ya yi a gaban Ayaman tuni yawunta ya tsinke kafin kace me ta fara jin soyayyar doya da ƙwan ko jiran tayi brush balle shan tea ko cikinta ya warware ba. Tsayawa Anas ya yi ya na kallonta, shi duk a tunaninsa yunwa ce take kuwa yaji wani tausayinta ya ratsa shi. Ruwan lipton ɗin ya ɗebar mata a kofi ya sa sugar, sannan ya miƙa mata. Sai da ta tayar da doyar tass sannan ta juya ta ga yadda Anas ke kallonta. "Sannu." Ya faɗa cikin tausashiyar murya. Ƙasa ta yi da kai dan sai yanzu ta ga aika²r da ta yi, flask ɗin wayam babu komai ita kanta tayi mamakin yadda ta iya cinye wannan uban abincin. Kitchen ɗin ya shiga yaga babu komai na gara da aka kawo wa Ayaman, shiru ya yi dan ya san ba zai iya komawa yace wa mahaifiyarsa babu abinci ba. Wurin idi mai shayi ya nufa, "Ahh ahh ango? Kaine da safiyar nan ina amaryar?" Idi mai shayi ya tambaya cike da munafinci. "Bacci take bata tashi ba." Anas ya basa amsa. "Ah ya kamata ta huta kam da wannan gajiyar ay sai da hutu." Idi mai shayi ya ƙarasa ya na wata shaƙiyiyar dariya. Ayaman kuwa wanka ta yi ta saka wata sabuwar atamfa duk da leda ce amma kuma ta yi kyau, fita ɓangaren mahaifiyar Anas tayi suka gaisa cikin mutunta juna. Hira suka fara sama-sama kana Anas ya shigo ya tarar da su, zama ya yi a kan bokiti yana faɗin "Nima ayi hirar da ni." Anan zamu dakata sai Allah ya kaimu, more comment more typing ✍️ Khairat ce ✍️ 🤍 Love you all 💞😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 47-48 ----------Hira suka fara yi sama-sama kana Anas ya shigo yace "Nima ayi hirar da ni." Ƙasa Ayaman tayi da kanta ta kasa magana, ta na jinsu su na hira iya kaci in abin dariya suka yi ta yi in na girgiza kai ne shi ma ta yi. Chan zuwa hantsi Anas ya shirya ya fita nema, yayin da Ayaman ke ƙoƙarin taya mahaifiyarsa wasu ayyukan. Su na kammala girkin innar Anas ta umarce ta da ta ɗauko flask ta zuba musu nasu, haka kuwa aka yi bayan sun gama komai da komai suka zauna ƙarƙashin rumfar innar Anas su na taɓa hira. Kayan saƙa Inna ta ɗauko tana yi yayin da Ayaman ke kallon komai kuma ta fara yunƙurin iya wa. ******************************** *_Ladiyo_* Gari na wayewa ta fara kichiniyar yadda zata gyara gidan da kuma girki domin tarbar baƙi. Wurin Habu mahauci ta nufa domin siyo nama, ai kuwa ta samu anyi sabon yanka dana haka aka zuba mata namanta ta yi gaba. Tayo sauran chefanen kama daga lemukan kwalba, kayan miya, shinkafa da sauransu. Tana isa gida ta ɗaura tunkuya ta hau aiki gadan-gadan. Nabeela na ɗaki tana kwance ko tunanin taya mahaifiyarta aiki bata yi ba, hasali ma ita ba iya wani aikin gida tayi ba dan tun tasowarsu da ƴanmatanci Ayaman ce baiwarsu dan ita take komai a gidan, dan its Nabeela bata ƙi wanka ma Ayaman tayi mata ba. Zuwa bayan azahar Ladiyo ta kammala wasu daga cikin ayyukan, shinkafa da waken da tayi duk ta chaɓe tayi ta ruwa, miyar kam ƙarni kamar me ita s ganinta tayi komai dai-dai. Sabuwar tabarmarta ts ɗauko ta shimfiɗa a ƙarƙashin bishiyar mangwaron da ke tsakar gidan, ra ɗauko komai ta ajiye sa inda ya dace. Tana aiki tana magana ita kaɗai, "Ay wallahi Nabeela tayi goshi, kai kai kai ." Sai kuma ta cigi yatsa kamar taɓabɓiya. Wuraren la'asar Malam Isyaku da amininsa sai wani ƙaninsa da sai da aka sha gumurzo kafin ya yadda yazo dan Ladiyo ba irin wulaƙancin da bata musu, daga tace ɗangin matsiyata sai tace masu ƙashin tsiya abubuwa dai iri-iri. Wani yaro ne ya shigo ya same su a kan tabarma su uku, "Ina wuninku, wai ana sallama da malam Isyaku." "Toh maza je kace yana zuwa." Ladiyo tayi charaf ta amsa mai. Haka kuwa aka yi, Malam Isyaku ya mike ya fita, manyan mutane ne su huɗu sun sha babbar riga wadda daka gani kasan sai an sa kuɗi mai yawa za'a iya siya. "Assalamu Alaikum." Malam Isyaku ya faɗa ya na miƙa musu hannu domin suyi musabaha. "Waalaikumus salaam." Suka amsa suna gaisawa cikin mutunta juna. Iso ya yi musu zuwa cikin gidan, suna shiga suka zazzauna a kan tabarma suka gaisa da su kawu Bello. Bayan wani lokaci sai ga Ladiyo ta fito a cikwikwiye cikin gumi da alama ko wanka bata yi ba. Tana fitowa ta fara washe musu baki tana gaishesu, amsawa suka yi sannan suka fara gabatar da abinda ya kawo su. Kawu Bello ne ganin rashin dacewar zaman Ladiyo a wurin ganin duk masu gemu ne a wurin ya sa shi faɗin, "Ladiyo ki shiga daga ciki mana ay bai kamata ki tsaya anan ba." Kallon banza ta bishi da shi kafin tace "Ƴar ka ko tawa? Ina ruwanka da ni? Wato salon ana bada kuɗin ku yagi rabonku ko? Toh wallahi ina nan sai an yi komai a gabana." Ts ƙarashe tana wani juyar da kai haɗe da murguɗa baki. Rasa mai kawu Bello zai ce ya yi, kawai ya ja bakinsa ya yi shiru. Malam Isyaku sam bai ji daɗin abinda ya faru ba, amma ganin baƙi yasa sa ya yi shiru dan yanzu Ladiyo ta faɗa mai maganar da ta so. Buɗe taron da addu'a aka yi sannan aka fara gabatar da abinda ya tara su a wurin, Babban yayan Alhaji Gabatari, wato Alhaji Aminu ne ya nemar wa Gabatari auren Nabeela. Ladiyo tayi charaf tace"Ay an riga da an gama kawai ku gayi nawa kuka zo da shi da kuma ranar da kuke son ayi bikin." Sakin baki Alhaji Aminu ya yi da sauran mutanen wurin dan ganin wannan lamari na Ladiyo. Kallon juna Alhaji Aminu da Alhaji Ahmed abokin Alhaji Gaɓatari. Ganin yadda Ladiyo tayi babakere a kan lamarin, yasa suka amince a kan nan da kwana ishirin da ɗaya za'a ɗaura aure, sannan kuma suka bada kuɗin tambaya naira dubu ɗari biyar. Suma ne kawai Ladiyo bata yi ba sakamakon ganin wannan zunzurutun kuɗi, ai kuwa suna ajiye wa tayi saurin ɗauke kuɗin ta maƙe su a hammata. "Ai Alhaji kuje kawai, auren Nabeela da Alhaji kawa an riga da anyi ne." Ta faɗa tana miƙe wa har da taka rawa sannan tayi cikin gidan da kuɗin. Alhaji Aminu da Alhaji Ahmed ne suka kalli juna suna murmushi. Sallama suka yi kafin kowa ya tafi harkokin gabansa, shi dai kawu Bello cike da takaicin matar yayan nasa ya tafi yana Allah wadai da abinda tayi. Shi kuma malam Sani aminin malam Isyaku ya same shi yace "Kaga dai yadda tayi komai ba tare da ko kunyar idanunmu ba, dan haka ya kamata ka gyara ɓarakar da take gidanka, na bar ka lafiya." Ya ƙarashe yana barin wurin. Ladiyo kuwa a cikin gida hauka ne kawai bata yi ba, sakamakon ganin wannan zunzurutun kuɗaɗe. ******************************** *_Nafee da Farouk _* Ko kaɗan Nafee ta ƙi barin Farouk ya fita, ko sallah ma s gida ta umarce sa ya yi shi kuwa da yake an riga an shanye shi, ba abinda ya isa ya yi. Yanzun ma tana jikinsa ta maƙale mai kamar mayya, shi ya rasa wannan jaraba irin ta Nafee ace kusan duk bayan wasu awanni sai ta buƙaci namiji? Gashi ita kamar ba mace ba haka yake jinta, wallahi a ƴan kwanakin nan ya yi missing ɗin Ummu Kulsum, ga kyau ga hankali ga shi ta san ta yadda take gamsar da shi ko ba tare da sun yi sex ba. Ita kuwa Nafee banda muguwar ƙazanta da rashin sanin ya kamata ba abinda ta iya sai kuma yawan buƙatarta kamar me. Wallahi har ga Allah ya fara gajiya da Nafee, kwana uku da aure har ta ɗauko ƴar aiki dan ita tace ita ba baiwa bace dan haka ba ruwanta da wani aiki. Haka ma ta ɓangaren girki ko cokali bata ɗaga wa, Ummu ce ta zama kukun sun ita take girka musu na safe, na rana da na dare har na da wasu tsirface-tsirfacen Nafee duk ita take yi. (Kaɗan ma ka fara gani Farouk) ******************************** *_Ummu_* Lallashin Mu'ayyad take ta faman yi dan kwana biyu ya sako ta a gaba banda rigima ba abinda ya iya. Dare ne ga wata uwar gajiya da ta tara dan Nafee yau girke-girke ba wanda bata sata ba, har meat pie ta sata yi duk dan ta wahalar da ita. Gashi dare ya yi maimakon ta huta sai ma wata sabuwar gajiyar da Mu'ayyad yake son ɗaura mata, ringing ɗin wayarta ne ya tayar ta ita taje ta ciro ta a chaji, number Farouk ce wadda ta yi saving da Abban Mu'ayyad. Ɗaga wa ta yo kafin tace komai taji muryar Nafee, ki dafo min tea ki kawo min yanzu. Kamar zata kurma ihu haka ta dafa tea ta juye a flask ta dauki hijabi da Mu'ayyad ta nufi sashen Nafee. Su na zaune a falo su na kallon wani American film ta shiga ta samesu, Nafee ta yi luff a jikin Farouk wanda ya lulluɓe ta a bargo da alama ko kaya babu a jikinsu. Ajiye tea ɗin ta yi ta miƙe da niyyar fita, "Ɗumamamin meat pie a microwave ki kawo min nan." Taji muryar Nafee cike da izza. Kitchen ta nufa ta aikata abinda aka sa ta kafin ta bar sashen. Tana fita ta shaqi wata iska mai daɗi, dan indai tana sashen Nafee bata iya numfashi da kyau dan ba ƙaramin tsoronta take ji ba. Tana shiga sashenta ta lallaɓa Mu'ayyad ya yi bacci finally ita ma dai ta samu lokacin kanta. Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ Khairat ce ✍️ 🤍 Love you all 💞 🥰😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr. (Posting room) My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇 👇 https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN Wannan page ɗin ma sadaukar da shi zuwa ma karanta littafin MUGUNTA da masu comment, ina godiya I love you lodi lodi🙈❤️‍🩹💋♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️. 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 49-50 *END OF BOOK ONE* Haka ana kiran asuba ta farka kamar birkitacciya, alwala ta ɗauro ta tayar da sallah. Tana jin Mu'ayyad na maganganunsa tayi mai shiru. Ko ƙarasa azkhar baya yi ba ta fara gyangyaɗi, ay kuwa ta koma gado taja blanket tayi baccinta. ******************************** *_Ladiyo_* "Ayiririri nanaye." Abinda take ta faman faɗa tana juyi kamar mahaukaciya, "Nabeela? Kinga rabo ko? Hehehe dubu ɗari biyar ba wasa ba." Ta ƙara faɗa tana shinshina kuɗin. "Wallahi ƙamshi suke, amma wallahi ko zanyi yawo tsirara sai kin aure Alhaji, ga gidan hutu? Ay gwara kawai ko me za'a yi ayi." Ladiyo ta faɗa tana kallon Nabeela. Nabeela dake zaune tana danna waya ko kallon Ladiyo bata yi ba bare ta amsa mata. Haka dai Ladiyo ta ƙarasa shirmenta ta kwashe kuɗin ta sa a wata ƙaramar jaka ta rataya a ƙugunta. Gyale ta saka ta fice daga gidan, Bata wuce ko ina ba sai kogon bokan kan tudu. Tana isa ta tarar da Delu na fitowa daga kogon tana saka kayanta, kallon banza suka bi juna da shi kafin ko wacce ta nufi inda zata. Ladiyo ta cire kayanya ta ajiye a wurin kamar yadda dokar wurin ta tanadar, ita kuma Delu ta nufi hanyar barin dajin. "Ma gaishe ka ɗan gidan uwar kowa, bokan da babu kamar sa duk faɗin duniya." Ladiyo ta faɗa tana shiga ciki. "La'ananniyar Allah da Manzonsa , tsinanniya ƴar wuta kuma kafira, me ke tafe da ke." Boka ya faɗa yana wata ƴar ɗariya. "Boka ƴar wuta kuma, ay baka san tsakanin bawa da ubangijinsa ba." "Haba Ladiyo, ni da ke fa duk munsan ƴan wuta ne, meye na mai da zance kuma?" Shiru Ladiyo tayi kafin tace, "Boka ka san me ke tafe da ni ay, babu wata mafita?" Boka ya yi shiru kafin yace "Kinga Delu da ta fita daga nan? Toh ƙarar ki ta kawo, tana so a lalata auren yarinyar wajenki, a dagargaza miki rayuwa, amma tunda kin zo sai ki fanshi kanki." Ya ƙarasa da wani makirin murmushi. Shiru Ladiyo tayi ta rasa me zata ce kafin chan kuma sai tayi kamar zata yi magana sai tayi shiru. "Baza ki fanshi kanki ba? Ni zan fara aikin da aka sa ni tohm." "Da me zan fashi kan nawa?" Wata ƙofa ya nuna mata, babu musu ta tashi ta shiga shi kuma ya bi bayanta. ******************************** *Ayaman* Ayaman kuwa sai ma sha Allahu, dan rayuwa tana tafiyar mata yadda take so, yanzun ma zaune suke su biyu a rumfar inna suna ta hira, dariya take yi sosai dan innar Anas akwai abin dariya ga kuma uwa uba ƙaunar da take nuna mata. Jikinta yayi luff alamar hutu da kwanciyar hankali sun tabbata, ga wata ƙiba ta ban mamaki da tayi, haske kam ba'a magana dan dama tun chan Ayaman fara ce sai dai Ladiyo da taso ta kawar da farin sakamakon ɓaƙar azabarta. Sallamar Anas taji, bayan sun gaisa da Inna Ayaman ta gaishe sa, wani kallo ya bita da shi ko ba komai zai samu ladan wannan baiwar Allah r dan ganinta ma kawai na sa shi farin ciki, ledar tsire ya miƙa mata. Amsa tayi sannan ta miƙa wa Inna, "Ay ni bana cin tsire ko kin manta ciwon sukari da nake da shi." Cewar innar Anas a lokacin da Ayaman ta miƙa mata tsiren. Innar Anas ce tace "Ku tashi ku bani wuri dare ya yi." Ta faɗi hakan ne ganin yadda Anas ke bin Ayaman da kallo. Da sauri Anas ya miƙe yana yiwa mahaifiyarsa sallama dan dama ya ƙagu, rufo ƙofar gidan ya yi ya yi mata sallama sannan ya shige sashensu. Sai da safe Ayaman tayi wa Inna kana ta shiga sashen. Tana shiga ta ga Anas a bakin ƙofar kamar jiranta yake, ay kuwa ya yi wuff ya chafe ta ta faɗa jikinsa. Saƙonni suka fara aika wa junansu kafin suka rufo kofa. ******************************** _*Nafee*_ Ita kuwa Nafee sai san barka dan rayuwa tayi dai-dai, sai fachaka take yi a dukiyar Farouk a gefe ɗaya kuma tana tunanin raba Farouk da Ummu. Yanzu ma shirin tafiyarsu yawon cin amarci suke inda zasu ziyarci ƙasar Dubai daga nan su wuce Spain. A ɗayan ɓangaren kuma ta kama duk wata ragamar gidan a hannunta, babu mai yin wani abu sai da izininta, ta kori ƴan aiki ta mai da Ummu a matsayinsu, yayin da ta shanye Farouk bashi da bakin magana ko mai tayi dai-dai ne. _*Ummu Kulsum*_ Baiwar Allah, tana kitchen sai aiki take ga Mu'ayyad a bayanta sai rigima yake dole yasa sai da ta goya sa. "Ummu" ta jiyo muryar Nafee. Amsa wa tayi sannan ta fita zuwa wurin ta, tana falo duk ta birkita wurin kamar ba yanzu ta gama gyarawa ba. "Ina fruit salad ɗin?" Kame-kame ta fara yi kafin tace "Baba mai gadi bai kawo ba." Cillo mata ɗari biyar Nafee tayi kafin tace "Ki je ki siyo." Sannan ta cigaba da abinda take. Ɗaukar kuɗin tayi ta zira takalminta ta fice. Tsuru tayi a ƙofar get ta ma rasa ta ina zata fara neman fruit, kallon jikinta tayi , jaga-jaga kamar ƴar aiki, ko da yake ƴar aikin ce. Hawayen da bata so fitowarsu bane suka fara zirya a lallausan kumatunta, ta gaji har ga Allah ta gaji, gani take dama kar ta koma cikin gidan wace irin rayuwa ce wannan? Haka ta cigaba da yiwa kanta tambayoyi kafin ta fita bakin titi dan bata san inda zata nufa ba. Ƙiiiiiiiiiiiiiiiii ƙarar mota ta bigi kunnena a lokacin da na juya zan bar wurin. *Ladiyo* Sai wurin tara na dare suka fito daga wannan ɗakin, tafiyar talala ta ke yi yayin da boka ke ƙyalƙyala dariya. Wani farin haske ne ya fito daga bangon kogon na dama, neman mafaka Ladiyo ta shiga yi dan jikinta ko ƙyalle babu. Wannan hasken wurin boka ya nufa , kafin kace me babu boka babu alamarsa a wannan kogon. Duhu mai tsanani ne ya baibaye wurin wanda ko tafin hannunka baza ka iya gani ba. Wata uwar ƙara Ladiyo ta saki kafin kuma diff kamar anyi ruwa an ɗauke, kogon ya yi shiru kamar babu wani ɗan Adam da ya taɓa rayuwa a wurin. _*Delu*_ Tana dawowa daga wurin boka ta shigo gidan da aka fara gyara musu amma ba'a kammala ba, duk da haka suke zaune sai ɗan zani da aka yafa a ƙofar gidan. Da masifa da banbami ta shigo gidan babu ko sallama, ta ajiye mayafinta ta shiga ɓanɗaki. Sai da ta fito sannan ta lura da fuskarta da ta gani a cikin ruwan. " Wayyo!" Ta saki wata uwar ƙara tana taɓa wurin, fuskar ta kumbura kamar fanke sai idanunta da suka yi jaa alamar taruwar jini. Ɗakin Mariya ta nufa da gudu dan ɗauko mudubi ta kuma tabbatar wa fuskar tace ba ta aljana ba. Abinda ta gani ne ya tsayar da ita chakk, "Mariya?" Ta faɗa cike da mamaki, waje tayo da gudu tana salati da sallalami. Alhamdulillah a nan muka kawo ƙarshen book one, book two zai fara zuwa gobe in Allah ya kaimu domin jin wannan chakwakiya, shin waye ya ɗauke boka? Me yasa Ladiyo tayi ƙara? Me Delu ta gani har ta firgice? Sannan wannan zaman lafiya na Ayaman zai daure? Kar ku manta da alwashin da Ladiyo ta ci a kan Ayaman, na gode da gudunmawar da kuke bani a ko yaushe Allah ya saka da alkhairi. Khairat ce ✍️ 🤍 Love you all 💞 🥰