😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇 👇 * https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 51-52*(BOOK TWO)* *Bayan wata biyar* *Ayaman* Tun daga ƙofar sashen zaka jiyo nishin mace kaɗan-kaɗan da alama tana jikin wahala. Da alama ƙarar daga banɗaki take, kuma matsawa nayi don ganin me ke faruwa, Ayaman! Tabbas Ayaman zaune a banɗaki cikin jini alamar mai naƙuda. Wani nishin ta kuma saki sai ga jaririya ta faɗo tana ra chanyara kuka, "Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." Ayaman ta faɗa a karo na ba adadi. Yarinyar ta kuma kalla kafin ta ji wani baƙin ciki ta fashe da kuka, ƙarni da kuma zafin banɗakin ya sa yarinyar cigaba da chanyara kuka . Sai da Ayaman ta kai kusan minti goma a wurin sannan taga shigowar innar Anas, "Hasbunallah wa ni'imal wakeel." Abinda innar Anas ta faɗa kenan sannan ta fice daga sashen cike da takaici. Wani kukan Ayaman ta saki kafin ta miƙe da ƙyar ta nufi hanyar kitchen, wuƙa ta ɗauko ta raba mahaifar da jaririyar sannan ta ɗauko flask daga ɗaki duk da jan ciki ta haɗa ruwa ta ɗauraye yarinyar ta ɗauraye jikinta. Ɗaki ta shiga tana ɗingisawa ta nemi zani ta rufe yarinyar ita kuma ta kwanta a gado tana jin wani uban raɗaɗi a mararta. Wani abu mai ɗumi taji yana bin ƙafarta, jini ne tabbas wannan jini ne, wasu zafafan hawaye ne suka kuma fitowa daga idanunta. Tabbas wannan ce rana mafi muni a wurinta, ranar da baza ta taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwarta ba, dan ta kasance rana mafi muni bayan ranar mutuwar mahaifiyarta. Muryar Anas taji a kanta yayin da ta lumshe idanunta, ɗago idanun tayi a hankali ta ƙure su a fuskarsa wadda da alama shima labarin ya riske shi na abin da ya faru. "Ayaman...." Sai kuma ya yi shiru sakamakon wani kuka da yaci ƙarfinsa, durƙushewa ya yi a wurin yana kiran sunan Allah. A ɓangaren Ayaman kuma duk sai taji ta takura dan bata taɓa ganin namiji yana wannan kukan ba. A hankali kuma ya tashi tsaye, sai da ya kai ƙofa sai yace "Ayaman ban taɓa tsammanin wannan sakayyar daga wurinki ba, na nuna miki ƙauna, soyyaya da kuma kulawa, ni da mahaifiyata mun amshe ki hannu bibbiyu amma kin watsa mana ƙasa a ido." Ya goge hawaye sannan ya cigaba da faɗin "Ayaman kin ci amana ta, baki ci sunanki ba, Allah zai saka min wannan sakayya da kika min, aurena da ke ya ƙare Allah ya haɗa kowa da rabonsa na sake ki saki ɗaya." Ya ƙarasa yana goge wasu zafafan hawaye. Ayaman saurin toshe kunnuwanta tayi sakamakon wannan kalaman da suka mata nauyi, kuma ƙwaƙwalwarta ta gaza fahimtar su. Kalmar ƙarshe ce tafi girgiza ta, toh ya aka yi haka? "La'ilaha illah anta subahanaka inni kuntu minaz zalumin." Sune kalmomin da suke iya fitowa daga bakinta. Tabbas ko me Anas ya yi dai-dai, dan ko addinin muslunci idan mace ta kai wata shida a ɗakin mijinta ta haihu toh ba shakka ana kyautata zaton ɗansa ne amma akasin haka na janyo cecekuce. Indai tana ƙirge yau wata biyar da kwana uku da aurensu, ga kuma jaririya wacce da alamu lafiyayya ce hakan na nufin ta cika wata tara a cikin mahaifiyarta. Sai da ta ɗau wani lokaci kafin ta tashi ta goya yarinyar da ko arziƙin ɗan kamfai bata samu ba balle kaya. Sannan ta ɗauko wani ƙaton hijabinta wanda ya rufe ko'ina ta zira a jikinta, takalmi ta saka kana ta fara tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki. Rumfar innar Anas ta nufa, sallama tayi mata ta amsa, cike da takaici innar Anas tayi wa Ayaman kallon banza sannan ta tofar da yawu. "Innata, innata ki jiyo ki kalle ni, Ayaman ce, yarinyar da kika ɗauka a matsayin ƴarki ta jini, innata wallahi ban aikata abinda kuke zargina da shi ba, ba zan taɓa iya wa ba, nima abin ya zo min bagatatan ban sani ba wallahi." Ta ƙarashe cikin muryar kuka sosai. Ƙara kawar da kai inna tayi dan bata son kallon Ayaman, wani irin kallo take yi wa Ayaman ya za'a ce mace daga zuwa gidan miji wata biyu ta haihu? Ay bazai taɓa yiwuwa ba. Ayaman ta gaji da durƙuson ta miƙe ta fice daga gidan. Tafiya take amma ji take kamar ba a duniya take ba, ina ma ace tun lokacin da mutuwa ta zo ɗaukar mahaifiyarta ta haɗa da ita, meyasa, ta yadda da Allah kuma ta yadda da ƙaddararsa, amma wannan jarabawar tayi mata tsauri da yawa. Haka dai ta ƙarasa ƙofar gidansu tana ta surutai, tsaye tayi ta rasa shiga zata yi ko kuwa, ta san ta ta ta ƙare, dan Ladiyo ba raga mata zata yi ba. "Assalamu Alaikum." Ta faɗa a hankali tana shiga gidan. Ladiyo na tsakar gida ta amsa sallamar, abin mamaki yau Ladiyo ce da amsa sallama? Durƙushewa Ayaman tayi a ƙasa tana wani kuka mai ban tausayi. "Kar dai raɗe-raɗen dake yawo a gari na cewa kinyi cikin shege har kin haife sa ne ya tabbata?" Ladiyo ta tambaya tana zazzaro idanu. Sakamakon zafi da kuma takura da jaririyar ta samu ne ya sa ta chanyara kuka wanda yasa Ladiyo sakin kwanon dake hannunta. "Hehehe wato dai ya tabbata, cikin shege ya tabbata shikenan Ayaman kin gama da mu, munafuka tsinanniya." Ladiyo ta ƙarasa tana dungurewa Ayaman kai har ya yi sanadiyyar faɗuwarta ƙasa. Wani uban kuka jaririyar ta saki, Ayaman na kuka a lokaci ɗaya kuma tausayin yarinyar na kuma lulluɓe ta. "Jama'a! Jama'a! Wayyo Allah! Ayaman tayi cikin shege ta haife sa, ta biyo halin uwarta, karuwanci taje tana yi a gidan miji." Ayaman ta jiyo muryar Ladiyo tana kururuwa tana sanar da mutanen gari. Kafin kace me gidan ya cika da mutane, yara da manya kowa yazo kallon Ayaman da tayi cikin shege. Wata maƙociyarsu ce ta buɗi baki tace "Shegiya zata janyo mana bala'i a gari, wannan hukuncinta kawai kisa ne dan in bala'i ya tashi ba ruwansa da mai laifi ko akasin haka." Haka dai kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa kafin lokacin da malam Isyaku ya shigo. Idanunsa duk sun yo waje ya tsaya yana kallon Ayaman, rasa mai zai ce mata ya yi kawai ya nuna mata ƙofa. "Fitar min daga gida!!" Shine kalmar da ta ji daga bakin mahaifin na ta. Tsugunnawa tayi tana kuka har da sheshsheƙa. "Baba...." "Ki fitar min daga gida nace!!!!" Malam Isyaku ya faɗa cikin ɓacin rai wanda kana ganin idanunsa zaka tabbatar da hakan. Jiki a saɓule ta fara jan ƙafafunta yayin da mutane ke bin ta suna tofin alatsine. A ƙofar gidan ta tsaya tana kuka mai ban tausayi amma hakan bai hana yaran dake mata ihu dainawa ba. "Shegiya uwar shegiya." Shine kalmar da yaran ke faɗa suna jifan ta da dutse wasu kuma suna tofa mata yawu abubuwa da yawa dai kuma manyansu na kallonsu babu mai hana su. Muryar maman su Tsahare ta jiyo tana kora yaran amma duk da hakan basu tafi ba, jan Ayaman tayi suka fara tafiya duk da hakan yaran basu ƙyalesu ba abin yana neman shafar ummansu Tsahare. Suna isa gidan tayi sauri ta rufo ƙofar amma sai da yaran suka san yadda suka yi suka turo ƙofar suka shigo. Da ƙyar ummansu Tsahare ta kora yaran ta rufo kofa a hakan ma sai da ta saka abubuwa a bakin ƙofar. Juyawa ummansu Tsahare tayi wurin Ayaman, "Kwanto yarinyar." shine kawai abinda ta faɗa. Ba musu Ayaman ta kwanto ta ta miƙa wa umma. Bayan ta amshi yarinyar ta tsaya kallon ta, jikinta duk jini da kuma sauran ruwan mahaifa ga ƙarni da take ga gumi da ya game jikinta. Yarinyar sai ajiyar zuciya take ta sauke wa da alama ta jigata, wuta ta haɗa sannan ta wanke yarinyar ta ɗauko wasu tsofaffin kayan jarirai duk da sun daɗe amma tsaf suke babu datti dan ana wanke su wani lokacin. Bayan ta shafa mata mai ta saka mata kayan ay kuwa jaririya ta fito fess abinta tayi kyau sosai dan ba ƙarya ta biyo bayan hasken mahaifiyarta. Shiru suka yi dan sun rasa me zasu cewa juna, ruwan zafin da umma ta ɗaura ne ta juye wa Ayaman tayi mata wanka na gargajiya dai. ******************************** *_Ladiyo_* Tun bayan lokacin da wani farin haske ya ɗauke boka babu shi babu alamarsa, wannan duhu da ya baibaye wurin yasa ta tsalla ihu, cikin ikon ubangiji ta samo hanya ta fito daga kogon. Haka tayi ta gudu a dajin Allah ga duhun dare ga kukan wasu namun daji. Tana isa cikin gari ta fara haɗuwa da mutane da yake dare ne kuma wata ba wani haske ne da shi ba kuma ba wutar nepa bace yasa ba wanda ya gane ta. Da gudu ta ƙarasa cikin gidan ta shige ɗaki ta rufo, baya-baya take yi dan gani take wannan duhun zai biyo ta, hannu taji ya taɓa ta ay kuwa ta kurma uban ihu "Wayyyyooo Allah na, dan Allah kuyi haƙuri bok...." Bata ƙarasa faɗa ba taji muryar Malam Isyaku " Lafiyarki kuwa Ladiyo?" Tsaki ta saki kana tace "Dama kaine asrarre kana aikin kenan zaman kashe wando." Ta ƙarasa faɗa cikin masifa, yayin da a cikin zuciyarta godewa Allah take da yasa bata yi wa kanta ɓaranɓarama ba dan indai malam Isyaku ya san asiri tayi mai shikenan aikin ya lalace. Zani ta nema ta rufe jikinta tana ta yiwa malam Isyaku masifa, da ya gaji da bala'inta ta miƙe ya bar mata ɗakin. Yana fita ya ci karo da wata kyakkyawar mace a dai-dai kofar ɗakin Ayaman. Kamar ya san fuskar amma ya manta a ina ya san ta, yana fara ƙoƙarin tunano ta kawai sai wani ciwon kai mai tsanani ya ratsa sa sai kuma bacci mai nauyi ya kwashesa. Hakan yana yawan faruwa da shi a duk lokacin da ya yi ƙoƙarin tunano wannan matar. Tafiya tai tafiya har ta kai ga Alhaji Gabatari ya kawo kayan aure kuma ansa ranar ɗaurin aure, shiri ba wanda Ladiyo bata yi kuma tun daga lokacin ko taje wurin boka ba ya iya sauraron ta . Tun a wurin ɗaurin aure ake mamakin Alhaji Gabatari da dukiyarsa, dan sadaki million ɗaya ya bada, mutane suna ta tuntuɓar malam Isyaku anya ya yi bincike kuwa? Dan da ayar tambaya a kan sa. A cikin gida kuwa zo kiga yadda Ladiyo ta sume domin daɗi tun da aka kawo kuɗin sadakin ta ƙanƙame su a hammata ta hana kowa gani ita a tunaninta sace wa zasu yi. A wurin ɗaukar amarya ma an sha ruwan mamaki, dan rantsa-rantsan motoci Alhaji ya turo domin ɗaukar amarya kuma a ƙalla sun kai goma sha ɗaya kuma kowacce mota babu irinta a garin. Ladiyo kuwa kasa rufe baki tayi dan abin ba'a cewa komai, haka ta shige gaban mota dan ta rantse da ita za'a kai amarya. Tafiya ake ta yi har aka shigo cikin garin Kano, kuma har aka zarce ƙarshensa wurin garin Tudunwada dake kano aka nufa. Tun da suka shiga layin babu gida ko ɗaya sai na Nabeela shi ma ɗin kamar villa dan ba ƙarya gidan ya tsaru ga shuke-shuke ta ko'ina furanni da abubuwa da dama. A cikin gidan kuwa mutuwa ce kawai su Ladiyo da sauran ƴan ɗaukar amarya basu yi ba, dan komai na gidan sabo dal kuma na zamani, kama daga italian chairs, bed set kayan kitchen komai Alhaji ne ya yi dan cewa ya yi kar su ɗauko ko cokali. Girma da kuma ƙayatuwar gidan bazai misaltu ba sai wanda ya gani a ido ne zai tantance. Sai da suka yi wa komai na gidan ɗai-ɗai suka fayyace biri har wutsiyarsa sannan suka fara shirin tafiya. Ƙiri-ƙiri Ladiyo tace babu inda zata, ga godan hutu ina zata koma ƙauye, haka dai suka janye ta suka chusa a mota dan ba hauka ake ba da za'a bar uwa ta kwana gidan ɗiyarta ba. Amarya Nabeela na cikin mayafinta ta fara jiyo hayaniyar mutane kamar ana biki. More comment more typing, ga book two nan dai fatan zaku ji daɗinsa . Khairat ce ✍️🤍 Love you all 💞 🥰 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 53-54 (BOOK TWO) *_Amarya Nabeela _* Hayaniyar kuma matsowa kusa da ita take, ƙara rufe fuskarta tayi dan ta zata abokan ango ne suka rako sa. Shiru kusan minti talatin babu wanda ya shigo ɗakin ga kuma hayaniyar ta ƙi ƙarewa kamar biki ake sosai dan har ƙarar buɗe lemuka take ji ita a tunaninta sun tsaya yin shagali ne kafin su shigo dan haka ta kuma rufe fuskarta. *_WAIWAYE_* *_Ayaman_* Ita dai a rayuwarta bata taɓa samun wannan chanjin yanayin jiki irin haka ba, cikinta ba wasa ya fara ɗagowa, ka ƙafarta da ta fara kumburi kaɗan har yanayin mamanta basu kai girman da ba. Ta alaƙanta hakan da sauyin yanayi da ta samu da kuma cima, ta sanar da Innar Anas ko wani ba lafiya ba, amma innar tace ta yiwu hutu da ta samu kwana biyu ne ya sa ta ƙiba haka amma fa chan ƙasan zuciyarta tana da abin faɗa kawai dai tana jiran lokaci ne. Haka ranar tana ji aminiyar innar ta zo suna magana, "Kice sirikar taki har ta ɗauki ciki, kai ma sha Allah." Hajiya Shafa'atu ta faɗa tana shan ruwan da aka kawo mata. Cike da mamaki Inna ta kalle ta, "Ciki fa kika ce Shafa'atu?" "Eh mana baki lura bane, kuma da alamu cikin ya kai kusan wata biyar dan ga cikin nan ya taso." "Kai Shafa'atu sai dai wasa, dududu watansu ɗaya da kwana sha tara da aure fa." Innar Anas ta ƙarasa cikin mamaki. "Toh wallahi Maryam(innar Anas) in zaki yadda ki yadda dan yarinya dai ciki ne da ita." Ayaman dake madafa tana girki taji cikinta ya bada ƙululu, ciki fa? Toh ta ina? Wata ɗaya da aure kuma tace cikin har ya kai wata biyar? Shafa cikin tayi sai taji ya yi tauri kuma ya ɗan taso ba kamar da ba. Wani uban gumi ta share a fuskarta, taya za'a ce ciki, in shaa Allah ba haka bane ta ƙarasa tana cigaba da girkinta. Wajen bayan isha suna hira ita da Inna dan Anas bai dawo ba innar take tambayar ta, "Ayaman yaushe ne baki ga al'adar ki ba?" Shiru Ayaman tayi kafin tace "Inna wancen satin ma nayi." Wata ajiyar zuciya Inna ta sauke tana bagarar da zancen cikin da Shafa'atu ta dasa mata. Kuma wani ikon Allah, cikin bashi da girma dan hakan kowa ya zata tumbi ne kuma yarinyar bata cika motsi ba balle Ayaman taji motsi, bugu da ƙari tana ganin al'adar ta. Kwatsam a wata ƙaddararriyar safiya Ayaman ta tashi da wani azababban ciwon mara da baya, innar Anas na ganinta ta tabbatar wa kanta Ayaman da ciki ta shigo gidan, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi bata taɓa tsammanin wannan sakayyar daga wurinta ba. Abinda mutane ke zargi ya tabbata, amma tambayar anan ita ce, taya Ayaman ta samu ciki? Sannan waye ubansa??? ******************************** *Delu* *WAIWAYE* Kuyi haƙuri da short page ɗin More comment more typing Khairat ce ✍️🤍 Love you all 💞 🥰 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 🤍✍️ https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 55-56(BOOK TWO) *Delu* *WAIWAYE* Ihun da ta ƙwantsama ne ya sa Mariya da Idi dake kwance suna aikin ashsha miƙewa, sauri Idi ya yi ya sa kayansa ya fece da gudu ya zo dai-dai ƙofar fita yaji an ƙwantsama mai taɓarya, juyi ya fara yi a ƙasa yana ihun neman taimako yayin da Delu ta cigaba da dukansa da hannuwanta. Da ƙyar ya samu ya fece daga hannunta yana cin alwashin komai dare sai ya rama abinda tayi mai. Kan Mariya ta juya, "Tsinanniya wato karuwanci kika fara a gidan nan? " Ta ƙarashe tana zabga mata wani mari. Bata dire hannunta ba Mariya ta mayar mata da maruka zafafa guda biyu wanda sai da Delu ta ga taurari sun ratsa mata. "Mariya nii..?" Bata ƙarasa ba wani kuka ya ci ƙarfinta, ƴar da ta haifa da cikinta ce ta mata wannan abin? Ta kasa gasgata hakan. Juyawa Mariya tayi ta shige ɗaki ba tare da ɗigon tausayin mahaifiyarta ta ba, ta bar Delu na zubda hawaye. Ta kai kusan minti ashirin a wurin kafin taji shigowar Malam Surajo, sallama ya mata bata amsa ba dan haka ya yi sauri ya fara ayyukansa dan yanzu tana barinsa ya fita. Tashi tayi daga wurin ta shige ɗaki cike da ƙunci. Ta kwanta a kan gadon ne ba wai dan tana jin bacci ko gajiya ba, kallon saman ɗakin take yi yayin da ta lula duniyar tunani. Wai Mariya ce zata ɗaga hannu ta mare ta? Har yanzu ta kasa yadda da hakan, lallai kuwa in haka ne maganar boka ta tabbata, na cewa zasu gani a kan ƴaƴansu. Ƙarar abubuwa da ake bige wa a tsakar gida ne ya dawo da ita daga tunani, "Wallahi ba ni ne ubanta ba, uwarta ce kuma tana ɗaki." Ta jiyo muryar Malam Surajo cikin tashin hankali. Wasu riƙaƙƙun ƴan daba ne suka hankaɗo yadin dake jikin ƙofar, "Ke ce Delu ko? " Wani saurayi ya faɗa wanda da alama a bige yake. Kasa magana tayi, wani uban mari ne ya daki fuskarta, kafin ta fara jin saukar wasu mugayen makamai tun tana iya gani har ta ji ƙittt bata ji bata gani. Sai da suka mata liss kafin suka fice suka bar gidan. Ko da ta farka sai gani tayi gari har ya waye dan sanda ƴan daban suka zo dare ne, ƙoƙarin tashi tayi taji ƙissss ƙashinta ya yi wata ƙara kuma sumewa tayi a wurin. A taƙaice dai sai da Delu ta kai kusan kwana biyu kafin wani daga cikin ƴanuwanta ya leƙo gidan ya tarar da ita. Mai gyaran ƙashi aka kira ya ja mata wanda a wurin Delu tayi fitsari yafi a ƙirga, da guntayen kashi da ta saki. Mariya kuma tayi ɓatan dabo, babu ita babu labarinta, duk ƴan kuɗin Delu ta kwashe da sauran kaya masu muhimmanci. *Cigaban labari* "Washhh Amina ki bini a hankali mana." Delu ta faɗa yayin da ake ƙoƙarin tayar da ita domin yin wanka. Yarinyar da aka kira da Amina ta yatsina fuska ganin fitsarin da Delu ta jibga a kan shimfiɗarta. "Wallahi na gaji, babba da ke ba yarinya ba ki rinƙa sakin fitsari a kwance, habaa." Amina ta ƙarasa cike da mita. Amina wata ƴar yar Delu ce da ke wani garin da zama, aurenta ya mutu shine aka kira ta domin ta rinƙa kula da delu har ta warke. Haka dai ana masifa ana bala'i aka kammala wanka. ******************************** *Ummu Kulsum* *WAIWAYE* Tun lokacin da ta fito daga gidan domin nemowa Nafee fruit tayi hatsari mota ta bige ta. Ɗanta Mu'ayyad take a wurin Allah ya ƙarɓi abinsa yayi da ita kuma ta samu matsalar ƙashin baya. Ta kwanta a asibiti na kusan wata uku, rashin kula daga ɓangaren danginta yasa aka mai da ita gidan gajiyayyu. Dan sai a yi sati babu wanda yazo ya ga lafiyar jikinta dan kusan kowa za'a iya cewa ya manta da shafinta da wata maƙociyarta da take ɗan zuwa akai-akai. Tana gidan gajiyayyu ba um ba um um bata iya magana bata iya motsawa. Iya takaicen da Nafee ta ƙunsa wa rayuwarta ya ishe ta komai, ta raba ta da gidanta, ta raba ta da mijinta ga shi ta raba ta da lafiyarta, wallahi Allah yana gani baza ta iya yafewa Nafee wannan tarin laifukan da tayi mata ba. Kamar kullum tana kwance a kan gado, hawaye na zuba daga kurmin idanunta, ta ƙura wa ceiling idanu, nurse ɗin dake kula da su ce ta shigo. Direct wurin Ummu ta nufa, goge mata hawaye tayi tana girgiza mata kai. Wata nurse ce ta kuma shigowa ɗakin, da yake akwai gajiyayyu da yawa kusan su shida a ɗaki ɗaya. "Wace ce Ummu Kulsum Hamza?" Kallo Ummu ta bi ta da shi idanunta duk sun zaro waje. Nurse ɗin dake gefen Ummu ce ta amsa da cewa "Gata nan." Farar takarda wannan nurse ɗin ra miƙa wa ɗayar nurse ɗin, "Saƙo ne aka kawo mata." Sannan ta fice. Buɗe takardar nurse Haleemah tayi, hawayen da bata shiryawa ba ne suka zubo mata. "Ni Farouk Aliyu Datti na saki matata Ummu Kulsum Hamza saki biyu." Abinda ke rubuce a jikin takardar kenan sai signature ɗin Farouk. Kuma kallon Ummu nurse Haleemah tayi, duk ta lalace ta fita hayyacinta, wannan yawan tunanin ma ya isa ya zugar da ita , take wani kukan ya kuma kufce mata kawai ta miƙe ta fita daga ɗakin. Tana tsananin tausayin Ummu yarinya mai shekaru ƙalilan ta shiga irin wannan masifa. Da ido Ummu ta bita haka kawai taji zuciyarta na bugawa da sauri. (Allah sarki Ummu 😭❤️‍🩹) *Nafee(p.o.v)* Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ Khairat ce ✍️🤍. Love you all 💞 🥰 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 🤍✍️ https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 57-58 (BOOK TWO) *Nafee(p.o.v)* Duniyar Allah, duniya tayi mata daɗi komai na tafiya tsaff, yanzu ma suna ƙasar Dubai a Abu Dhabi, wani wurin shaƙatawa ne ya mutane manya da yara. Sun ci sun ƙoshi ita da Farouk tana kwance a jikinsa suna taɓa hira, yanayin mai kyau ne, ga iska na kaɗawa a hankali. Tashi suka yi suka nufi wani wurin da ake ɗaura mutane a kan raƙumi suna zagaye wurin, biya suka yi suka hau kai, wayarta ta miƙa wa wasu ma'aurata dan su ɗauke su hoto. Haka suka dinga zagaye wurin cike da nishaɗi da ƙaunar juna yayin da wannan ma'auratan ke ta ɗaukan su hoto. *WAIWAYE* Tun lokacin da ta aiki Ummu Kulsum siyo fruit tayi sauri ta kira Lubna a wayarta, "Hello Nafee." Lubna tayi magana ta ɗayan ɓangaren. "Wallahi ta tsallaka maganin." Nafee ta faɗa tana leƙa Ummu da ta kusan kai bakin gate. "Ayyiriri, toh albishirinki ita da dawowa gidan nan lafiya har abada, ta tafi kenan." Lubna ta faɗa ta cikin wayar. Sakin wayar Nafee tayi tana ihun murna, shikenan, ta gama da Ummu Farouk ya zama nata ita kaɗai. Haka ta zauna cike da murna dan ji take kamar an mata hajji da umara. Tun daga lokacin Farouk ko kuma tambayar Ummu be yi ba bare ƴan uwansa su Ammi. Suka kuma shiga duniya suna yawon shakatawa da cin amarci.... *CIGABAN LABARI* Kwanan su ashirin da biyu a Abu Dhabi suka dawo gida Nigeria. *Farouk* Kwana biyu ko bacci kirki baya iya yi, mafarkin wata mata yake da yaro a hannunta suna kuka suna neman taimakonsa, yana ji yana gani suka tafi daga wurinsa. Kullum cikin tunani yake, gani yake kamar akwai abinda ya rasa a jikinsa, haka kawai yake jinsa ba dai-dai ba. Da ya matsawa kansa da tunani sai kansa ya fara ciwo, duk ya daburce ya rasa mai yake mai daɗi. Asiri gaskiyar mai shi..... *Amarya Nabeela* Shiru ba wanda ya leƙo ɗakin, kuma ga hayaniya na tashi a falon, leƙawa tayi ta kofa, maza ne danƙam a falon sai Alhaji Gabatari da ta gani a zaune kan kujera cikin babban kaya sai kuma wani saurayi a gefensa. Alhaji Aminu da Alhaji Ahmed kawai ta sani a wurin sai kuma wasu manyan mutane, fatan alkhairi taji ana ta yi ana fatan Allah ya basu zaman lafiya, duk a zatonta a kan aurensu ake yi. "Baby chakwai Allah ya baku zaman lafiya." Taji muryar Alhaji Ahmed yana dariya. Wanda aka kira da baby chakwai ne ya rufe fuskarsa alamar kunya. Kan Nabeela ne ya kuma ɗaure wa, sakamakon ganin Alhaji Gabatari ya kai wa wannan saurayin da aka kira baby chakwai kiss. Idon baby chakwai ne ya kai kan Nabeela dake tsaye, yatsina fuska ya yi kana yace " Alhaji wannan fa." Ya faɗa yana nuna Nabeela. "Ni ce nan matar gidan." Nabeela ta faɗa cike da rashin kunya. Marin da baby chakwai ya wanka mats ne ya sa ta yin shiru, Alhaji Gabatari ne ya janyo baby chakwai, " Ki kwantar da hankaliki, wannan ƴar aiki ce na ɗauko miki." Kuka Nabeela ta fashe da shi tana shigewa cikin ɗaki, su Alhaji suka cigaba da sharholiyarsu har dare ya tsala taro ya watse. ******************************** *Ladiyo* Fess zuciyarta, abinda ta daɗe tana shiryawa ya tabbata, a ƙarshe dai Ayaman tayi abinda ko kare baze ciza ba. "Yanzu aka fara wasan....." Ta faɗa. ******************************** *Ayaman* Bayan tayi wanka taji wani daɗi a jikinta amma mararta da gabanta sai zugi suke. Kuma kallon jaririyar dake hannun ummansu Tsahare tayi, ta kuma sakin wasu hawayen . Umman Tsahare tana gefe riƙe da yarinyar taji wani bugun ƙofa, a zatonta yaran ne suka dawo hakan yasa ta yi biriss da su. Muryar baban su Tsahare da ta ji ne ya sa ta saurin miƙewa domin buɗe masa. "Wannan karuwar zaki ajiye min a gida, toh wallahi baki isa ba dalla malama tashi ki fitar min daga gida." Baban su Tsahare ya ƙarashe faɗa yana kallon Ayaman. Razana Ayaman tayi ta miƙe cikin hanzari ganin yadda baban su Tsahare yake zare idanu. "Haba malam..." Bata ƙarasa faɗa ba yace "Ki ka kuma magana a bakin aurenki sai ki zauna da ita." Haka Ayaman jiki na rawa ta goya jaririyar ta fice da sauri. Ai kuwa tana fita kamar jira suke yaran suka fara bin ta suna mata ihu, ganin babu inda take da shi sai gidan mahaifinta ya sa ta nufar gidan. Tana isa ta shiga ɗakin Ladiyo in da mahaifinta yake zaune cikin tashin hankali. Durƙusawa tayi ta fara kuka mai taɓa zuciya, tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah, duk da asirin Ladiyo amma Malam Isyaku yaji tausayin Ayaman sosai. "Baba.... Dan Allah ka saurare ni, wallahi zan gaya ma waye uban yarinyar nan." Ta ƙarasa cikin kuka. Juyowa Malam Isyaku ya yi yana kallon Ayaman. Ta buɗe baki ta fara magana kamar haka..... Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ 🤍 Khairat ce ✍️🤍 Love you all 💞 🥰 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat✍️🤍 *(Posting room)* https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* .https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 59-60(BOOK TWO) _______Ihun da Ayaman ta saki be ya janyo hankalin Ladiyo wacce shigowarta kenan. Shigowa ɗakin tayi da gudu ta tarar da malam Isyaku riƙe da zuciyarsa jini na fita ta hanci da bakinsa, sai Ayaman dake gefe tana matsanancin kuka. "Kashe uban naki kika yi? Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." Ladiyo ta faɗa cikin tashin hankali. Ita ma kukan ta fara suka saka Malam Isyaku a gaba suna rusa kuka, "Allah yaaaa miiiikiiii aaallbarkaaaaa....." Malam Isyaku ya faɗa a ɗan rarrabe, kafin ya cika da imani, Allah ya karɓi abinsa. Sun kai kusan minti goma a ɗakin kafin Ladiyo ta fita ta fara kwantsama ihu. "Innalillahi, ta kashe shi, wallahi Ayaman ce, ta kashe shi, ." Haka ta rinƙa ihu. Kafin kace me gidan ya cika mutane na sauraren surutan Ladiyo wanda ko ganewa ba sa yi, wasu manya aka samu aka wanke gawar Malam Isyaku wanda da ƙyar aka raba Ayaman da ita. Haka ana rirriƙe Ayaman aka fita da gawar aka sallace ta aka kai ta gidan gaskiya. Ana dawowa aka fara tsegumi a kan mutuwar, wasu na zargin Ayaman ce ta kashe shi wasu kuma suna ganin bazai taɓa yiwuwa ba. Nan fa aka samu wasu marasa kunya daga cikin samarin garin suka shiga har gidan suka fara yi wa Ayaman video a kan cewar tayi cikin shege kuma ta hallaka mahaifinta har lahira, domin posting a kafafen sada zumunta domin samun mabiya. Washegari sai ga Yunusa da muƙarrabansa, wai sun zo gaisuwa, haka dai suka gama shirmensu suka tashi. Haka aka yi zaman makoki na ranar ɗaya, washegari Ladiyo da Yunusa suka tada bala'i wallahi sai Ayaman ta bar gidan. Kai tsaye fadar mai gari aka nufa dan Tsahare ta tsayawa Ayaman dole sai ta samu wani kashi na gidan dan tayi amanna cewa Ayaman na da gadon gidan. Ana isa mai gari ya turo da mutane domin a yanka gidan a ga wani kashi Ayaman take da shi, ay kuwa aka tabbatar da rabi da kwata na ɗakin da take ciki nata ne ƙwata ne na su Ladiyo. Nan aka ƙarƙare cewa Ayaman zata dinga biyan kuɗin hayar wannan ƙwata dan Ladiyo ta rantse baza ta bar ta kyauta ba. Ana kammala rabon gidan sai ga su Addah Asiya dan sun samu labarin rasuwar Malam Isyaku. Da gudu Ayaman ta riƙe su, jaririyar da suka gani a hannunta ne ya ɗaure musu kai. Har yanzu dai, wane ne uban yarinyar nan????? ******************************** *Ummu Kulsum* Bacci take mai daɗi, kawai taji alamar ana tashin ta, wata baƙar halitta ta gani mara kyau ga muni. Tsurawa halittar kallo tayi, ga dare ga kuma ba bakin magana, shaƙe ta wannan halittar tayi. Ta kasa motsi ta kasa ihu, sunan Allah kawai take faɗa a zuciyarta. Cikin ikon Allah ta ji shaƙar tayi sauƙi, hamdala tayi a zuciyarta ta cigaba da kiran sunan Allah a zuciyarta. Idonta biyu har asuba tayi gari ya fara wayewa, nurse Haleemah ce ta shigo fuskarta ɗauke da damuwa. "Ummu, ya kk?" Ta tambaya tana ƙoƙarin yin murmushi. Hawaye ne suka zubo mata, saurin share su tayi sannan ta ɗaga Ummu ta kai ta banɗaki tayi brush tayo fitsari sannan ta ɗauro alwala. Dawo da ita ɗakin tayi ta chanja mata kaya ta kwantar sa ita ta tayar da sallah a kwance. ******************************** *Nafee & Farouk* Kwance take a kan cinyarsa, "Babe, ka ga wata yarinya tayi cikin shege ta kashe ubanta." Ta faɗa tana nuna mai wayar. Taɓe baki Farouk ya yi, dan wallahi a gajiye yake haka jiya ta hana sa bacci kwana suka yi suna abu ɗaya har ya gaji duk da kasancewar yana da buƙata sosai. ******************************* *Nabeela* Tun da ta shige ɗaki bata kuma fitowa ba, kwanciya tayi a kan gadon abinka da ba'a saba ba duk sai ta takura ta sauko ƙasa. Shiru tana jira taji shigowar Alhaji Gabatari kasancewar yau ne daren su na farko. Har ta gaji tayi bacci. Gari ya yi haske sosai san da ta tashi, dan rana ta game ɗakin da take ciki, a hankali ta buɗe idanunta, miƙewa tayi ta fita domin samar wa kanta abin da zata ci. Alhaji Gabatari da baby chakwai ta gani a falo, baby chakwai namiji ne cikakke amma farin fata ne da shi kamar na bleaching. "Kehh!!!" Ta jiyo muryar baby chakwai yana kiranta. Tsaki ta ja ta rinƙe buɗe kofofin domin nemo ta kitchen. Tsawar da Alhaji ya buga mata ne ya razana ta kaɗan, amma da yake rashin kunya ta cika ta sai ta mai banza. Tashi Alhajin ya yi ya chafko ta, maruka ya sakar mata kafin ya fara jibgar ta kamar Allah ya aiko sa. "Wato ko kin zata ban san dan kuɗina kika aure ni ba? Na zo ina son Mariya ku ka yi asiri ke da matsiyaciyar uwarki a zaton ku zaku mallake ni, hehehe." Alhaji ya ƙarasa cikin wata shaƙiyiyar dariya. Duka suka haɗu suka yi mata ba na wasa ba dan har jini suka fitar mata. Barin falon suka yi, ita kuma ta ja jiki ta shiga ɗaki. "Allah ya isa tsakani na da ke Ladiyo kin cuce ni ." Abinda take ta maimata wa kenan cikin kuka. Wanke fuskarta tayi ta fito falon, ƙofar fita ta nufa ta fice, har ta kai bakin get wani ɗan sanda ya hankaɗo ta da ƙafa, ai kuwa ta faɗi ra bige kai. "Dan Allah ka barni na tafi gida, dan Allah." Abinda ta roƙi ɗan sandan kenan amma ko ɗigon tausayi babu haka dauko bulala zai dake ta in bata tafi ba. Ganin ga ciwon dake jikinta taya za ta kuma bari a jibge ta, hakan ya sa ta nufi ciki da gudu. Tunda ta shige ɗaki bata kuma fitowa ba, chan taji fitar Alhaji, kafin taji ana murɗa ƙofar ɗakinta. Baby chakwai ne ya shigo, wani mayen kallo yake bin ta da shi. Tuno irin dukan da ta sha ɗazu, ya sa ta fara ja da baya. Matsowa baby chakwai yake yi ita ma tana ƙara matsawa. Janyo ta ya yi da karfi, hakan ya sa ta saki wani ihu zuciyarta kamar zata fito. Yakice rigar dake jikinta ya yi, taɓe baki ya yi "Ji bi jikin naki ko kyen gani babu, duk kin yamushe sai kace tsohuwa amma bari nayi maleji." Ya ƙarasa faɗa yana kai wa na shanunta chafka. Wani ihun ta kuma saki, cire kayansa ya yi, ya juyo da ita, ɓaƙar azabar da ta ji a duburarta ya sa ta sume wa..... Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ Khairat ce 🤍✍️ Love you all 💞 🥰 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat ✍️🤍 https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *(Posting room)* *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 61-62(BOOK TWO) ________ A taƙaice dai Nabeela ba ƙaramar azaba ta sha ba a wurin baby chakwai, ko da Alhaji Gabatari ya dawo tayi yunƙurin gaya mai amma abin yaci tura! Baby chakwai ya ƙi bata dama. Haka kullum cikin Allah ya isa da tsine wa Ladiyo take dan san kuɗinsu da kwaɗayi ya kai su ga wannan halin, Allah sarki, Ayaman ɗin da suke ƙoƙarin kullum su cusguna mata ga shi tana jan tana rayuwarta. A ganinta kenan. *Ayaman* Bayan zuwan su Addah Asiya sun zauna sun yi magana ta kuma kai kukanta wurinsu, amma duk yadda suka kai ga naci Ayaman ta ƙi gaya musu uban wannan jaririyar. Haka da zasu tafi suka ce ta zo su tafi tare amma ta ƙeƙashe ƙasa tace babu inda zata, tana nan a gidansu zata cigaba da kula da jaririyarta har zuwa sanda Allah ya yi. Haƙura suka yi suka bar ta dan Ayaman mutanen nan ne masu ƙaƙƙauran ra'ayi. Rayuwa tayi rayuwa, ta fara zuwa chan wani gida tana yi aikatau domin rufawa kanta asiri, yayin da jaririyarta ta fara girma tana yo kamarta sak. Ta ɓangaren mutane ma bata daina samun ƙyama da hantara ba, ba hali ta fita yanzu za'a fara nuna ta da baki ana shegiya uwar shegiya. Ba laifi kuma tana samun taimako daga gidan da take aiki, da kuma ƙawarta Tsahare ko yaya ta samu sarari yanzu zata kawo mata kaya, da sauran kayan amfani Yanzun ma tana gidan aikinta suna aiki tana ɗan taɓa hira da matar gidan, yaran gidan ne suka dawo daga makaranta, suka taho da gudu suna rungumar mahaifiyar tasu, "Momy yau munyi karatu sosai, kuma momy ina so na zama likita babba." Babba a cikin yaran ya faɗa cike da murna. Haka suka cigaba da hirarsu ta uwa da 'ya 'ya, kafin suka bar kitchen ɗin. Hawaye masu zafi ne suka zubo mata, Allah sarki duk da ta san kowa da kalar ƙaddararsa a rayuwar nan, amma yawancin ƙaddarorinta Ladiyo na da kaso a kai, ta rasa me ta tsarewa Ladiyo a rayuwar duniyar nan, ta ƙwallafi rayuwarta, Allah zai saka mata. Haka ta share hawaye ta cigaba da ayyukanta. (Allah ya saka miki Ayaman 😔) *Ladiyo* Rayuwa fess, duniyar Allah ta fita takaba , duk da ba wani muhimmanta takabar tayi ba dan tana cikin takabar bata fasa zuwa wurin boka ba domin a duba mata taurarinta, a haka ya tabbatar mata da cewa tabbas zata ƙara aure amma wannan auren mai cike da abubuwa ne. A ɗayan ɓangaren kuma bata fasa amsar kuɗin hayar Ayaman ba duk da babu abinda yake shiga tsakaninsu. Wata rana wacce har yanzu tana ganinta a matsayin ranar sa'arta. Ta dawo daga wurin boka kenan ta ga wata ƙaramar mota golf a ƙofar gidanta. Har tazo zata wuce ta ji muryar wani mutum, fitowa ya yi daga motar, toh a haife dai ta haife sa dan wannan bai fi sa'an yunusa ba, shekara 23-24. "Ranki ya daɗe har kin dawo." Ta ji muryar wannan saurayin. Da kallo ta bishi ba tare da tace uffan ba. "Toh Hajiyata ko amsa min baza a yi ba, in ba damuwa magana nake so muyi mu shiga daga ciki." Nan ma shiru tayi kafin kuma ta shiga cikin gidan ya bi bayanta. Tabarma ta shimfiɗa kafin ta zauna a kujera chan nesa da shi. Wani kallo mai kashe zuciya ya sakar mata wanda hakan ya sa ta farat ɗaya taji yaron ya shiga ranta. Murmushin ƴan duniya Sadeek ya yi mata ganin haƙarsa ta fara cimma ruwa. Kalamai ya fara mata wanda ba ƙaramin sanyaya zuciyar Ladiyo suka yi ba dan tun da take ba'a taɓa zubo mata kalamai irin haka ba. A ƙarshe dai ya ƙarƙare da cewa zai aure ta idan ta yadda. Babu musu Ladiyo ta amince dan wani shauƙin soyayyar yaron ta ɗibe ta. *Anya kuwa Ladiyo??? Muje dai zuwa.* *Nafee* Cin karenta take yi babu babbaka, dan tana fantamawa a dukiyar Farouk, ta zama oga sai abinda tace shi ake yi, tayi sharrr abinta duniya tayi mata daɗi ta manta da batun an taɓa yin wata halitta mai suna Ummu Kulsum. Ta ɓangaren Farouk kuwa, ta ko'ina gasa mishi aya ake yi a hannu, ta ɓangaren Nafee ta sako sa a gaba indai ta tambayi abu to fa dole ayi mata shi ko rai ya ɓaci, gashi a duniyar nan in akwai abinda baya so to fushin Nafee ne, ga wurin aiki ya ci bashi duk dan biyan ɓuƙatun Nafee hakan ya sa suka basa wa'adin wata ɗaya ya tattaro da kuɗin kamfani ya dawo da su ko kuma law zata yi aiki a kansa. *Ummu Kulsum* Wannan abun da ya zo mata daren jiya shi ya ƙara zuwar mata, tabbas tata ta ƙare yau ba makawa zata koma wurin mahaliccinta, dan abubuwan da take gani ya tabbatar mata da cewa tabbas ba na duniya bane na lahira ne. A hankali ta saki wani lallausan murmushi wanda hakan ya sa kumatunta lotsawa, "Allahu Akbar." Shi ne abinda take ta maimaitawa a zuciyarta tana murmushi. Tun da dare da suka yi sallama da nurse Haleemah , jikin nurse Haleemah ya yi matuƙar sanyi dan wallahi sun shaƙu da Ummu fiye da tunanin mai tunani. Kuma tana ji a jikinta kamar haɗuwarsu ta ƙarshe kenan, haka dai ta fita ba dan ta so ba. Wuraren ƙarfe ɗaya na dare Ummu ta amshi kiran ubangijinta, ta mutu daren juma'a mai cike da tarin ni'imomi. Shikenan Ummu ta rasu, Nafee hankalinki ya kwanta ta bar miki duniyar mai cike da ƙalubale iri-iri, kin rabata da mijinta, ɗakin aurenta, farincikinta, ɗanta Mu'ayyad da sauran jin daɗin rayuwa, anya kuwa zaki zauna lafiya Nafee? Anya kuwa? Da asuba mutanen dake ɗakin suka lura da rasuwar Ummu, haka suka yi wa junansu ta'aziyya, kafin suka jira isowar nurses. Da nurse Haleemah taji rasuwar Ummu, tayi takaici tayi baƙinciki, ta yi kuka har ta gaji dan tana matuƙar tausayin Ummu irin. *( Irin wannan rayuwar mata da yawa suna fuskantarta a gidan miji, ƴaruwa dan kinzo a ta biyu kar kice ala dole sai kin fitar da ta farko, ko kuma ke ta farko kice ta biyu baza ta shigo ba, wannan rayuwar bata dace ba sam, hakan kuma baya daga cikin tsari da koyarwa ta addinin musulunci, in kinyi haka kin zalince ta kin zalinci kanki dan Allah maɗaukakin sarki baya taɓa yafe lefin wani a kan wani, yanzu ya kuke gani in Ummu Kulsum bata yafewa Nafee ba kuna ganin rayuwarta zata yi dai-dai? Ta raba Ummu da farincikin rayuwarta, kai hatta Farouk anya zai ga dai-dai ya yi abubuwa da yawa na ɓaƙantawa Ummu, gashi a ƙarshe ta bar musu duniyar, a kula kuma a kiyaye !!! Ƴanuwana mata kar son duniya da kuma miji ya ɗebe ki ki aikata shirka!)* Wanka aka yi wa gawar aka fitar da ita domin sallace ta, mutuwar tayi mutane sosai dan gabaɗaya ma'aikatan asibitin maza har da wasu marasa lafiya wanda suka ji dama-dama sun halacci wannan sallar, ga mutanen bakin asibitin ga wasu da wucewa suka zo yi haka aka tafi maƙabartar ɗan sarari aka kai ta gidanta na gaskiya kowa cike da alhini. Allah ya jiƙanki Ummu ya sa mutuwa hutu ce a gareki😢 More comment more typing *Ga masu buƙatar a tallata musu haja zasu iya magana ta wannan number 09036812206* *Ko kuma kawo shawara ko ƙorafi ko gyara ku tuntuɓi wannan number 09036812206* Khairat ce✍️🤍 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 🤍✍️ *(Posting room)* https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr * My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin swß vvvv. 1 Qwp sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 63-64(BOOK TWO) Mutuwar Ummu ba ni kaɗai ba, ta girgiza ɗaukacin masu karatun littafin MUGUNTA, tabbas Ummu ta cika ayi alhinin rashinta, amma zanso ku gane a haka labarin ya zo kuma a hakan zan rubuta sa, labarin Ummu da gaske ya faru, dan ni ganau ce ba jiyau ba, amma ku ƙara haƙuri domin jin yadda zata kaya. In shaa Allah na kusa kammala littafin nan . __________ Haka aka dawo daga kai Ummu gidanta na gaskiya kowa cike da alhini da kuma tsoron Allah a zuƙatansu. Mutuwar Ummu ishara ce ga mai hankali, ko iya binne ta da aka yi ya bawa kowa mamaki, wani danshi da sanyi-sanyi ne ke tashi a kabarin tamkar an kunna Ac, duk da yanayin zafin dake garin. Masu haƙar kabarin sun labarta wannan yanayi da suka ji, har wata kasala ce ta kama su a yayin haƙar kabarin, kamar kar su fita daga ciki. "In shaa Allah wannan baiwar Allah ta samu dacewa bi'iznillah." Wani daga cikin masu haƙar kabarin ya faɗa. Wani likita ne ya buɗe baki yana faɗin "Ay labarin wannan yarinyar ya bawa kowa tausayi, duk da bamu san akwai wani abu da ya haɗa ta da mijin nata ba amma ga dukkan alamu bai damu da ita ba." Shiru suka yi mutanen kafin ya cigaba da faɗin "Tun da aka kawo ta asibitin nan sau ɗaya ya zo ya ganta shima cikin ƙyama ya wurga mata kuɗin ya fita yana tofar da yawu, a kan ido na komai ya faru." Doctor ya ƙarashe da alamar tausayi a ransa. Dr Lawan ne ya ce " Tabbas Dr maganarka haƙƙun! Ina ga har da takaicinsa ya yi sanadiyyar mutuwarta, amma tabbas mutuwarta ta zama ɗaya tamkar dubu tunda aka gina asibitin nan, ba'a taɓa samun gawar da tayi mutane kamarta ba." Haka suka cigaba da hirarsu suna alhinin rashinta, su na kuma nemar mata gafara. Haka a cikin asibitin su nurse Haleemah sun kasa taɓuka komai banda kuka, haka nan jininta ya haɗu da Ummu ji take kamar ƴar uwarta ta jini. Sai wurin yamma ta sassauta kukan aka lallaɓa ta aka kai ta gida. *A gidansu nurse Haleemah* Mai adaidaita ne ya sauke ta ta sakko jikinta duk a sanyaye, ɗari biyar ta basa ya ɗauko ɗari da hamsin ya bata. Ƙarba tayi ta shiga cikin gidan a sanyaye. Madaidaicin gida ne mai ɗauke da ɗakuna manya guda biyu sai falo guda ɗaya wanda haɗe yake da ɗayan ɗaki, sai kitchen da sauran abubuwa. Tana shiga ta ga Gwaggo tana yanka kuɓewa a tsakar gida, tana shiga ta faɗa kanta ta fara kuka. Cike da tashin hankali Gwaggo ke kallonta, tana tambayar ta me ya faru. Gwaggo kakar nurse Haleemah ce ta wurin Uba, tun sanda ta zo karatu Kano take zaune a wurinta yayin da iyayenta ke zaune a Kaduna. Mutuwar Ummu da ta gayamata ya tada mata da hankali, dan labarin Ummu kullum sai taji sa daga wurin Haleemah. Rarrashin ta ta fara yi har ta samu tayi shiru, sannan tayi wanka ta ci abinci ta sha paracetamol dan kanta ba ƙaramin ciwo yake mata ba. Bacci ta kwanta ta fara yi.... Labarin Haleemah kuma??? Toh mu dai je zuwa. ******************************** *Ladiyo* Saurin amincewa da tayi da Sadeek ya matuƙar yi masa daɗi, haƙarsa ta cimma ruwa. Har sun saka rana a kankansi ba tare da neman shawarar wani ba. A ɓangaren Ayaman ma bata fasa abinda tayi niyya ba. A ɓangaren ƴarta kuwa Nabeela, kullum so take ta samu lokaci taje ta kai mata ziyara ta samo arziƙi. Ga kuma munanan mafarkai da take yi kwana biyu, ko taje wurin boka iya kaci yace ta tashi ta bar mai kogo bar shirya mutuwa ba. *Delu* Jikinta ya fara yin sauƙi dan yanzu tana iya tashi da kanta amma sai ta riƙe sanda. Duk sa tana jin wani zafi a tsakiyar gwiwarta amma ta alaƙanta hakan da warkewa ciwon yake yi. Ga Mariya tayi ɓatan dabo, babu ita babu labarinta kowa sai gulma yake a gari na cewa karuwa ce shiyasa Alhaji Gabatari ya fasa aurenta. Tayi kukan kuma tayi takaici, Malam Surajo ma kansa bawan Allah ya samu chanji daga wurinta, wannan masifar da take yawan yi mai ta rage ko dan cutar ne oho, amma dai ya ƙudirci a ransa sai ya saki Delu komin dade wa. *Ammin Farouk* Farar matar cike da fararen kaya ce tsaye a gabanta, murmushin budurwar take mata ita ma ta mayar mata, chan gefe kuma Farouk ne tsaye daff da wata rigiyar wuta sai tafarfatsi take. "Ammi !!! ". Muryar da taji tana kiranta kenan kafin kuma diff ta dena ji ta dena gani, ji tayi an rirriƙe mata jiki ta kasa ko motsi. Farkawa tayi daga wannan mummunan mafarkin nata, amma abin mamaki ko addu'a bata iya yi ba sakamakon nauyin da bakinta ya yi, ga shi ta kasa motsa kowacce gaɓa ta jikinta. Zuciyarta bugu take sosai kamar zata fito daga ƙirjinta, ga duhu da ya mamaye idanuwanta. Ita dai gata nan a kwance, bata gani bata ji bata iya motsi, ta kai kusan aƙalla awa biyu a wannan yanayin taji ana taɓa jikinta. Jijjigata ake yi amma tsam ta kasa motsi. Kuyi haƙuri da short page ɗin rashin comment yana karya min gwiwa. More comment more typing GASKIYA BANA JIN DAƊIN RASHIN COMMENT ƊIN KU, KU ƘOƘARTS DAN ALLAH KU RINƘA COMMENT Khairat ce ✍️🤍 *Domin shawara ko ƙorafi ko gyara ku tuntuɓi wannan number 09036812206* *Ga masu son a tallata musu haja su nemo wannan number 09036812206* 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat 💙 (Posting room) https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇 https://chat.whatsapp.com/EoTRoZq4KA0JFbynkYp9wi 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM Page 65-66(BOOK TWO) ____Mai aikin Ammi kuwa, Badi'a jijjiga Ammi take amma shiru, a guje ta fito falo, ganin ba kowa ya sa ta yi saurin fita tana kiran maigadi, "Baba! Baba! Ammiiii!" Badi'a ta faɗa cikin tashin hankali tana nuna kofar shiga falon. Saurin tashi Baba mai gadi ya yi yana bin bayan Badi'a, har sun zo shiga ɗakin ya tsaya yace "Mene ne Badi'a? Lafiya kuwa?" "Ammi ce tun ɗazu nake girgiza ta bata motsi, kuma sai kallo na take.". Ta ƙarashe cikin kuka. "Toh kinga baza ayi haka ba, bai kamata na shiga ɗakinta ni ba muharrarimta ba, bari na kira Alhaji(Farouk)." Ɗaga mai kai tayi ta shige ɗakin shi kuma ya ciro wayarsa ya nemo number Farouk ya kira shi. Yana kwance a gado Nafeesa na kwance a jikinsa ya ji kira ya shigo wayarsa, Baba maigadi ya gani a screen ɗin wayar. Cike da mamaki ya ɗauki wayar yana tunanin me ya sa zai kirasa da sanyin safiyar nan. "Assalamu alaikum." Amsa sallamar ya yi kana suka gaisa cikin mutunta juna. "Dama Alhaji jikin Hajiya ne ba daɗi, tun asuba Badi'a ke motsa ta amma shiru kuma tana nan tana kallon mutane..." Bai karasa ba Farouk ya tsayar da shi da. "Whattt???? Ammin?". Sannan kuma ya jefar da wayar ya yi sauri ya miƙe. Nafee da tayi wasarairai a jikinsa tana danna wayarta taji ya sake ta ta bige da katifa. "Baka da hankali ne zaka wullar da ni haka?" Ta faɗa a fusace. "Nafee Ammi fa? Ammi ba lafiya." Ya faɗa kamar zai yi kuka. "Koma wacece ." Ta ja uban tsaki ta kuma kwantawa. Mamakin Nafee ya tsayar da shi chak, wato koma wacece? Lallai uwarsa bata da wani daraja a idonta. Zarar key ɗin motarsa ya yi ya fita parking space, shiga motar ya yi, ya sa key kenan ta nuna masa babu mai a ciki. Dukan stiyarin ya yi jikin fushi wanda ya yi sanadiyyar fitowar hawaye a kumatunsa. Rasa me zai yi ya yi, kawai ya fita ya fara tarar adaidaita, har sun fara tafiya yaji mai adaidaitan yana cewa "Ina muka nufa ranka ya daɗe?" Sai yanzu ya tuna ko gaya mai inda zasu bai yi ba, " Hotoro tsamiyar boka." Haka suka cigaba da tafiya har suka iso. Su na isowa ko jira ya gama parking bai yi ba ya fito ya yi cikin gidan da sauri, kiran da mai adaidaita yake masa ne ya tuna ko sisi bai fito da shi ba, kawai ya shige cikin gidan. Yana isa ya shige ɗakin Ammi ya tarar da Badi'a zaune tayi tsuru tana kallon ta. Tsugunawa ya yi a ƙasa yana sakin kuka mai ciyo. Bai jira ba ya ɗauki key ɗin motar Ammi, shi da Badi'a suka kama suka fitar da ita zuwa mota. Har ya fito ya tarar da mai adaidaitan tana jiransa, laluba motar ya yi ay kuwa ya samu wata dubu ɗaya ya cilla masa. Tuƙi yake yana kuka a hankali, lokaci zuwa lokaci yana kallon Ammi dake shimfiɗe a bayan motar, asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano suka nufa, suna shiga ya tuna ko waya bai ɗauko ba bare ya kira family Doctor ɗinsu. Office ɗin sa ya nufa ya gaya mai yanayin da Ammi ke ciki, haka suka duƙufa a kanta, su kuma su Farouk da Badi'a na waje suna jiran fitowarsu... *Ayaman* Yamma ce lis ta dawo daga wurin aikinta kenan sai tafiya take tana tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki har ta iso gidan. Tana isa ta tarar da Tsahare ta zo tana zaune a ƙofar ɗakinta, da sauri ta ƙarasa kusa da ita tana rungume ta. Buɗe ɗakin tayi dan yanzu ta kwaso kayanta daga gidansu Anas, nan fa suka hau hira su ta bawa juna labarai iri-iri. Wata leda Tsahare ta fito da ita ta ajiye a gaban Ayaman, "Abban Khalifa ya yi mana kayan sallah ni da ke, shi ne nace bari na kawo miki.". Ta ƙarasa tana murmushi. Amsar kayan Ayaman tayi cikin murna tana ta sa albarka tana godiya, har da kayan yara ya siyo wa Ummi(A'isha) ƴar Ayaman masu kyau da tsada. " Chankwaɗiɗi, kice Ai'i na tsaf da ke wannan sallar kai ma sha Allah." Ta faɗa cike da murna. Haka suka cigaba da hirarsu har suka ji kiran sallah, "Har an sha ruwa muna nan muna hira." Tsahare ta faɗa tana miƙewa. "Ki cigaba da haƙuri Ayaman, na sani wannan rayuwar ba sonta kike ba, amma ki daure dan Allah." Murmushi Ayaman tayi ba tare da tace komai ba. Sallama suka yi suka rabu, Ayaman ta ɗauko abincin da aka bata daga gidan aikin nata. Dabino da ruwa tayi tayi addu'a sannan ta ɗauro alwala ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ne ta ɗauko abincin ta fara ci har sai da ta ƙoshi ta ajiye sauran domin sahur. Ta ɗan kishingiɗa tana hutawa taji ana kiran sallah, alwala tayi ta kwantar da A'isha a gado dan tayi bacci, ta saka hijab har ta zo fita taji kukan A'ishah, haka nan ta ɗauko zani ta goya ta ta kullo ƙofar domin tafiya sallar taraweeh. A tsakar gida tayi karo da Ladiyo ta bararaje ga kayan abinci da yawa a gabanta. Allah ya kyauta Ayaman ta furta a ranta , a ce mutum ko sau ɗaya tunda aka fara Ramadan bai yi abin da zai amfane shi ba? Wannan wace irin babbar asara ce? Tana isa masallacin ta tarar har an tayar, hakan ya sa tayi sauri ta shimfiɗa sallaya ta tayar. Bayan an idar da sallar ta ji gulmammaki game da yarinyarta dan har yanzu mutanen gari basu fasa abinda suke fadi a kanta ba. "Wallahi shegiyar yarinyar kyakkyawa ce, kin ganta kamar balarabiya? Chab ɗin sai kace aljana?" Wata mata ta faɗa riƙe da baki, juyawa Ayaman tayi ta watsa musu wani kallo dan yanzu ta daina ɗaukar wulaƙanci, tuni kuwa matan suka sha jinin jikinsu. Tana isa gida tayi alwala ta kullo ƙofarta ta kwanta domin tashin tsakar dare. *Delu* Rayuwa ita kam sai dai a ce babu daɗi sam, rayuwar ta fitar mata a rai kwata-kwata ta daina jin daɗin rayuwar. Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ Khairat ce ✍️🤍 Love you all 💞 🥰 *😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈* *BY* *KHAIRAT*🤍 *POSTING ROOM* https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *MY WHATSAPP GROUP COMMENT SECTION 👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/EoTRoZq4KA0JFbynkYp9wi 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM PAGE 67-68(BOOK TWO) *Delu* Rayuwarta kuwa sai dai ace babu daɗi komai ya chaɓe mata, tana cikin mawuyacin hali sosai, wannan gyaran da aka mata a ƙafarta bai yi kyau ba dan haka duk ƙafar ta chaɓe ta lalace. Amina ma dake zaune da ita ta gudu ta barta dan wani irin wari ƙafar take mara daɗin ji, ga wani baƙi da tayi na tashin hankali. Duk da ta san azabar da take sha ishara ce daga ubangiji, hakan bai hanata abinda ta ga dama ba. Malam Surajo ma yanzu ya fara gujar ta, dan sai ya ga dama yake shigowa gidan kuma ko ya shigo ɗakinsa yake nufa, ya yi kwanciyarsa, haka Delu zata yi kwanaki babu wanka sai ya ga dama yake wanke ta shima kuma a tsatstsaye. *Ladiyo* Ta faɗa soyayyar Sadeek ba da wasa ba, yanzu jira suke bayan sallah ƙarama ayi aurensu, duk da Ramadan ne hakan bai hana su aikata aikin ashsha ba, dan cin karensu suke babu babbaka. *Farouk* Sai da suka ɗau kusan awa biyu a ɗakin sannan likitocin suka fito, su biyu ne doctor Ashir sai doctor Mubarak. Su na fitowa suka tarar da Farouk ya haɗa kai da gwiwa, taɓa sa Dr Ashir ya yi, ɗago fuska ya yi ay kuwa fuskar tayi jazur da idanun sun yi luhu-luhu kamar fanke. Office ɗin Dr Ashir suka nufa, bayan sun zazzauna Dr Ashir ya kalli Farouk yace " Farouk, ni dai a sanina Hajiya bata da ciwon zuciya, bare muce heart attack ne ya janyo mata paralysis , sannan kuma ita ba ciwon suga ne da ita ba ko hawan jini, mu dai a iya binciken da muka yi babu abinda yake damun Ammi scientifically, sai dai spiritually kuwa, abin shawara a nan, ku nemar mata maganin islamic." Ya dakata kana ya cigaba da faɗin "Wannan matsalar ta ta akwai ayar tambaya, amma zamu kwantar da ita muga yanayin jikin nata." Tunda Dr ya fara magana ko motsi bai yi ba kawai ya ƙura mai ido yana kallonsa, shima Dr ɗin tsayawa ya yi yana kallon sa. Tashi ya yi ya fice daga office ɗin ya shiga ɗakin da aka kwantar da Ammi. Tsuru ya yi yana kallonta yadda take bacci hankali kwance. *Ayaman* Ibadarta take hankali kwance, zikiri ,sallah, taraweeh, tahajjud basa wuce ta a wannan watan mai falala. Yanzu ma ta dawo daga gidan aikinta kenan dan yau da wuri ta tashi dan babu aiki sosai kuma a yau ta amso kuɗin aikinta na wata, dubu sha biyar ne chiff. Kantin Sani ta nufa dan da shi kaɗai suke ɗasawa a garin shi ne baya hantararta ko ƙyamar ƴarta, har alawa yake bawa yarinyar wani sa'in. Shinkafa da sauran abubuwa ta siyo na dubu bakwai, sai ta siya gawayi da kayan miya. Tana isa gida ta buɗe ɗakinta ta ajiye kayan, ta ɗauko fulawa ta kwaɓa ta sa kayan miya ta haɗa ƙullin wainar fulawa. Tana wurin ƙofarta tana suyar waina da A'isha a bayanta tana ta wasanta taji sallamar Ladiyo kamar an hankaɗo ta, ko kallon inda take bata yi ba ta cigaba da suyar ta. Ladiyo ce ta zo ta tsaya tana faɗin "Su uwar shegiya yau kuma waina ake soyawa?" Wani baƙinciki ne ya taso wa Ayaman amma ta danne dan ganin falalar watan Ramadan. Hannu Ladiyo ta sa ta ɗauki waina ɗaya tana kai wa baki, ko kallon inda take Ayaman bata yi ba ta cigaba da suyar ta. "Hmm dama ba dole a soya waina ba, tunda ana fita karuwanci ana samo kuɗaɗe." Ladiyo ta faɗa tana tanɗe baki. Kaskon suyar Ayaman ta ɗauka ta buga wa Ladiyo a fuska, cikin fushi tace "Ladiyo uwarki ce karuwa, banza jaka, dan ina miki shiru ba wai ina tsoron ki bane kawai gudun fitina ne amma wallahi kika kai ni ƙarshe zaki sha mamaki!!!" Ayaman ta ƙarasa fuskarta ɗauke da fushi wanda sai da Ladiyo ta girgiza, saurin shigewa ɗakinta tayi cikin mamaki. Yau Ayaman ce ke da wannan ƙarfin da har zata iya dukan ta? Lallai kan mage ya waye. Ayaman kuwa ta cigaba da suyar wainarta rai na ƙuna, tana gamawa ta tattare kayanta ta shige ɗaki ay kuwa ta ci Sa'a tana shiga aka kawo wutar nefa, hakan ya sa ta rufo ƙofarta ruff. Ana shan ruwa tayi addu'oin da ta saba sannan ta sha ruwa, bayan ta idar da sallah har ta ɗauko wainar zata ci ta ji ta fitar mata a rai, hakan ya sa ta ture ta gefe. Sallar taraweeh ta tafi abinta. * Nabeela* Zuwa yanzu Nabeela ta fice daga hayyacinta, tayi baƙi dan ba ƙaramar wahala take sha daga wurin Alhaji da baby chakwai take sha ba. Tana tsaye da yanzu bata iya zama da mazaunanta , dan wasu irin tsutsotsi ne ke fitowa daga mazauninta, ga wani ruwan yauƙi mai warin tsiya. Duk karuwancin da take yi kafin tayi aure, ba'a taɓa neman ta ta baya ba, amma baby chakwai da Alhaji ta baya suke nemanta. Tana cikin tunani taji shigowar Baby chakwai, cikin tashin hankali ta dungura ta miƙe dan ta san halin baby chakwai, "Dan Allah kayi haƙuri wallahi na tuba bazan ƙara ba." Ko jin magiyarta bai yi ba, ya janyo ta, kaya ya cire mata, kallon mazaunin nata da ya ruɓe yake yi ga tsutsotsi dake safa da marwa a ciki. "Chabb, haka kika ruɓe? Lallai, amma bari nayi maneji a haka." Ya ƙarasa faɗa yana chusa d*ck ɗinsa a f*rjinta, wata ƙara ta saki kafin kuma ta sume a wurin. *Doctor Haleemah* Tabbas wannan Ummu Kulsum ce, cikin farar abaya mai ratsin duwatsu masu tsada da kyau a jiki. Murmushi Ummu ta sakar mata tana kiran sunanta, amsa mata tayi kafin taga Ummu ta ja ta zuwa wani lambu mai cike da itatuwa da shukoki daban-daban masu kyau da ƙamshi. Nan taji muryar Ummu " Haleemah zaki yi mamakin yadda na bayyana a mafarkinki, wannan wata dama ce da Allah(S.W.T) yake bamu mu mamata muna magana da rayayyu." Ta numfasa ta cigaba da faɗin, "Ina so ki taimake ni a duniya, ina so ki taimaki rayuwar Farouk dan tana cikin tashin hankali na masifa, Farouk mutum ne mai yawan ibada da bautar Allah amma haɗuwarsa da Nafee ya lalata masa rayuwa." Shiru doctor Haleemah tayi tana kallon Ummu. "Zaki yi mamaki, amma roƙo nake dan Allah akwai wani mai shago kusa da gidanmu yana bi na bashin dubu uku wanda na ara a lokacin da Farouk ya dena bani kulawa, inaso ki taimake ni a biyamin bashina, sannan aiki na biyu kuma sai haɗuwar mu ta gaba." Ummu Kulsum ta faɗa tana sakin murmushi kafin kuma ta ɓace. A lokacin doctor Haleemah ta tashi dai-dai ana kiran asuba. Tayi kusan minti ashirin tana tunanin wannan mafarki, da gaske Ummu ta gani tayi kyau tayi fess haka???. More comment more typing ✍️ Domin a tallata muku hajarku kuna iya tuntuɓar wannan number 09036812206 Ƙorafi ko gyara a tuntuɓi wannan number 09036812206 Khairat ce 💞 Love you all 💞 🥰 *😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈* *BY* *KHAIRAT 🤍* *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/EoTRoZq4KA0JFbynkYp9wi *Posting room* https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM* *PAGE 69-70* *NURSE HALEEMAH* Tsamm! Jikinta ya yi, ta kasa ƙwaƙwaran motsi, ta ɗau lokaci sosai kafin ta tashi ya nufi banɗaki ta ɗauro alwala ta tayar da Sallah. Tana sallah gaba ɗaya ta daburce, badai Ummu ta gani ba? Toh fatalwa tayi mata ko me? Chabb, kuma har da cewa ta taimaka ta gyara rayuwar Farouk? Wanene haka? Ko shi ne mijin nata? Toh ko ma dai mene zata je ta biya bashin da tace ana bin ta. Ko azkhar bata ƙarasa ba bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita. "Haleemah! Haleemah! Ke Haleemah! Ki tashi, a ce mutum rana ta fito tangararan har hantsi ya yi amma har yanzu bacci yake yi kamar kayan wanki? Maza ki tashi." Gwaggo ta ƙarasa wannan maganganun tana niyyar fita daga ɗakin, "Gwaggo!" Haleemah wacce tashinta kenan tayi saurin kiran gwaggo. "Ya aka yi ƴar gidan gwaggo?" Haleemah ta miƙe kana ta nufi wurin kakar tata ta dafa ta tana faɗin " Ina kwana Gwaggona?" "Lapiya ƙalau an tashi lapiya." "Uhm " Haleemah ta saki wata miƙa tana salati. "Gwaggo ina wannan baiwar Allahn da nake baki labarinta, Ummu?" "Ehh me ya faru da ita?" "Mafarkinta nayi Gwaggo, ta zo cikin kayan alfarma ga wani lambu wanda ban taɓa ganinsa ba tun da aka haife ni, shi ne har muka yi magana da ita." Gwaggo ta numfasa tace "Me ta faɗa miki?" "Ta buƙace ni wai na gyara rayuwar wani ko Farouk ko mene sunansa, sannan tace na fara biya mata bashi." "Allahu Akbar, ikon Allah kenan mai yin yadda ya so, ya bata damar magana da rayayyu, sannan kuma ga dukkanin alamomi tana cikin ni'imar Ubangiji, tabbas wani hani ga bawa baiwa ne." Haleemah tayi ƙuru tana kallon Gwaggo, kafin kuma ta miƙe "Gwaggo bari nayi brush sai na fito." "Yadda kika gani.". Gwaggo ta faɗa kafin ta bar ɗakin. Toilet ta nufa tayi brush ta wanko fuskarta sannan ta fito, direct falo ta nufa, ƴar aikin Gwaggo ta gani, Abidah tana ta goge-goge a falon. "Anty Abidah ina kwana?" Haleemah ta faɗa tana ƙarewa falon kallo yadda ya sha gyara. "Lafiya ƙalau likita bokan Turai, yawwa dama wannan ƙugun nawa har yanzu ya addabeni da ciwo, ki rubutan magani ba amso a chemist ɗin ɗan Bala." Haleemah tayi dariya ganin yadda Abidah ta riƙe ƙugu tana ta bayani, "Anty Abidah gaskiya sai dai kije asibiti, sau uku kenan ina rubuta miki magani amma har yanzu ƙugun bai daina ciwo ba." Taɓe baki Abidah tayi tana faɗin "Kinsan ba son zuwa asibitin nan nake ba ko." "Ay kuwa dole kije." Haka ta zauna suka cigaba da hira da Anty Abidah har zuwa wani lokaci. Tana kammalawa ta nufi ɗakin Gwaggo, karatun Alkur'ani ta same ta tana yi dan haka ta fice domin bata damar yin karatun da da kyau. Yau bata da aiki dai night duty, hakan ya sa tayi komawarta bacci tayi, da alama azumin yau zai wahalar da ita tun yanzu ta fara shan wahala. Kafin kace me bacci ya yi awon gaba da ita. *Farouk* Kwanansu uku kenan an kwantar da Ammi komai yi mata ake yi harta da tsarki. Kuma duk da wannan daɗewar tasu ko ƙafar Nafee bai gani ba a asibitin bare ayi tunanin zata zo duba Ammi. Lamarin Ammi na matuƙar bashi tsoro, haka kawai cikin dare jikinta zai ɗau zafi kanar garwashi, ga kuma zabura da take yi da alamar ana tsorata ta. Yau ma an sha ruwa kenan jikin Ammi ya rikice, banda zabura babu abinda take yi, gaba ɗaya ta rikice, Farouk ma ya shiga cikin mawuyacin hali dan har ga Allah yana matuƙar son Ammi. Ƴar uwarsa Haleemah ya kira, dan ya ga lamarin Ammi sai ƙara tabarbarewa yake yi don haka ya yanke shawarar kiran ƴan uwan nasa ya sanar da su. Tana ɗaga wayar taji muryar Farouk cikin kuka yana faɗin "Sis Leemah, Ammi! Ammi tana wani irin hali ki taimaka ki zo." Yana gama faɗin haka yaji credit ɗin wayarsa ya ƙare, innalillahi wa'inna i'laihi raji'un wai yau shine katin wayarsa ya ƙare. Kiran Anty Haleemah ne ta shigo cikin wayar, daga wa ya yi cikin sauri, nan kuwa Anty Haleemah take tambayarsa me yake faru, bai iya ce mata komai ba illa shirun da ya yi. *Ladiyo* Kwana biyun nan har shakkar ganin Ayaman ta shigo gidan take yi, dan yanzu ta banbance tsakanin aya da tsakuwa, tabbas ta yadda duk wani mai haƙuri bai iya fushi ba kuma ta san ta kai Ayaman karshe. Ita a ganinta Ayaman ko yatsa ta sa a baki baza ta iya taunawa ba amma ita ce har marinta. Ta ɗayan ɓangaren ma ta faɗa soyayyar Sadeek ba da wasa ba, dan ita tun da aka haife ta bata taɓa san wani namiji kamar shi ba. Yaro ɗanyan jini, gashi kaff ƙauyen ba wanda ya san asalinsa amma ta dage kai da fata sai ta aure sa, mutuwa ce kawai zata hana ta auren sa. Irin kalaman soyyaya da yake zuba mata ne ya sa take jin tamkar tafi kowacce mace kyau da class a duniya, dan da bata zata ita wata kyakkyawa ce ba sai da ta san Sadeek yadda yake ayyana mata tafi kowacce mace kyau a duniya. Hmmm ayi dai mu gani........ *Nabeela* Ganin ba sarki sai Allah ya sa ta koma garesa, duk da ba wani ilimin addini ne da ita ba amma ta kan iya abinda ya sawwaka tun da da bata sallah yanzu ta dawo tana yin ta yadda ta samu dan ba wani sanin hukunce-hukunce sallah tayi ba. Haka har azumi ya zo, tana daurewa tayi azumi ko ya ya ne amma fa duk da haka baby chakwai bai fasa abinda ya yi niyya ba. Sau da yawa duk da akwai azumi a bakinta hakan bai hanasa nemanta ba, daga shi har Alhaji Gabatari. Tayi danasanin wannan rayuwar, zina ƙiri-ƙiri kuma ba ta halattacciyar hanya ba, ga uban aikin da suke tula mata. Tabbas tayi nadama, namada kuma ta gaske dan yanzu bacci mai daɗi ma bata iya yi, yanzun nan zata fara munanan mafarkai ga shi ita ba addu'ar bacci ta iya ba sai dai ta tashi tayi ta tsinewa Ladiyo. Hmm Allah ya sa dai tuban gaske aka yi, dan "duk wanda ya tuba dab wuya ba lada!" *Ayaman* Rayuwarta na tafiya duk da ba wani daɗi take ji ba amma kullum ita mai godiya ce ga ubangijinta. Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ Masu buƙatar a tallata musu hajarsu su yi magana ta nan 09036812206 Ƙorafi ko gyara 09036812206 Khairat ce ✍️☺️ Love you all 💞 🥰 *😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈* BY *KHAIRAT 🤍* *My WhatsApp group posting room 👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr *My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/EoTRoZq4KA0JFbynkYp9wi 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. _With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_ BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM PAGE 71-72(BOOK TWO) *Ayaman* A safiyar ranar sai ga Tsahare a gidan, bayan sun gaisa kuma sun taɓa ƴar hira Tsahare ta buƙaci ko Ayaman zata iya bin ta suje garin da take aure, shiru Ayaman ta yi ta rasa abin faɗa. Fuskar tausayi Tsahare ta yi tana faɗin "Dan Allah mana, tunda na yi aure baki taɓa kwanar min ba sau ɗaya kawai kuma shima ranar bikina ce." Haka dai Tsahare ta kalallame ta da maganganu har ta yadda. Kayanta da kuma na A'ishah, basu ɗauki wani lokaci ba suka fito, kullo ƙofarta ta yi bayan ta tabbatar ta kwashe duk wani abu da yake mallakinta a tsakar gidan. Gidansu Tsahare suka nufa, a bakin ƙofa ta tsaya dan baban su Tsahare ya yi mata iya daga shiga gidan. Tana tsaye har ta jira fitowar Tsahare da kayanta da kuma ɗanta goye a baya. Su na tafe su na hira abinsu, kwatsam sai ga Anas ya zo wucewa a babur ɗinsa, tsayawa ya yi suka gaisa da tsahare yayin da Ayaman ta sunkuyar da kanta ƙasa ta kasa ɗago sa. Shima ganin hakan ya sa ya ja babur ɗinsa ya yi gaba ko waigowa bai yi ba, siraran hawaye ne suka zubo mata daga kwarmin idanunta. Dafa ta Tsahare ta yi tana faɗin "Ayaman ki kwantar da hankalinki dan Allah, ba komai bane rabuwarku, in shaa Allah alkhairi ce ita kuma wannan yarinya Allah ya raya ta." Shiru Ayaman ta yi bata amsa mata ba, Tsahare ta cigaba da faɗin "Amma Ayaman, waye uban wannan yarinyar?" Shiru Ayaman ta yi ta kasa magana, zuwa chan Tsahare ta kuma buɗe baki ta ce "Amma dai Ayaman na zata ko zaki ɓoye wa kowa abu ni bai kamata ki ɓoye min ba, hmmm amma dai shikenan." "Tsahare , ba ɓoye miki nake ba, wallahi ina cikin tsaka mai wuya, halin da nake ciki ba mai bayyanuwa bane." Ta yi shiri kuma kamar Malam ya ci shirwa. Haka suka cigaba da tafiya har suka iso babbar tashar garin, inda kowa ya fito a na ta hada-hada, ga masu abinci,kayan sayarwa wanda suka haɗa da kayan gwanjo, kayan koli da dai sauransu. Motar garin su Tsahare suka nema wato Madobi, babu ɓata lokaci suka kama hanya dan dama motar a cike take mutum biyu a ke nema. Tafiyar awa ɗaya da rabi ce tsakanin ƙauyen hazdabe zuwa Madobi, amma da yake sun samu mota mai kyau sai gashi cikin ƙasa da awa ɗaya sun iso tasha. Su na sauka suka kama hanya dan dama sun ri ga da sun biya kuɗin motar naira dubu ɗaya ko wanne mutum, dan haka ba ɓata lokaci suka tare mashin sai cikin unguwa Ayaman ta samu tarba mai kyau daga wurin dangin mijin Tsahare, sai nan-nan ake da ita, da yake gidan gandu ne ma'ana gida ɗaya mai ɗauke da ahali ɗaya, sai ga matan yayye da kuma ƙannen mijin Tsahare ana ta mata kara ta hanyar mutunta baƙuwarta, duk da hakan ya zama kamar al'adar gidan har dai wata a cikin matan ƴaƴan gidan ta yi baƙuwa nan fa za ki ga ana ta shigowa ana gaisawa wasu har abinci ake kawowa baƙo nufinsu ba sai kin yi girki ba tunda ki na da baƙuwa. Umaru, wato mijin Tsahare haifaffen karamar hukumar Madobi da ke ƙarƙashin jahar Kano ne, ya taso a gidan mata uku inda ya tarar da su du na zaman lafiya, duk da ba'a rasa ƴan saɓanin zaman yau da gobe ba. Haka nan duk wani matashi da ya isa munzalin aure, ake yankar mai wani ɓangare na gidan tunda gidan ya kasan cikakken gidan bahaushe mai filin gaske, da tsakar gidan kansa za'a iya gina gidaje biyu zuwa uku. A haka har shima Allah ya haɗa shi da Tsahare dalilin zamanta kenan tare da facalolinta. Bayan sun gama gaisawa, Tsahare ta ja Ayaman zuwa ɓangarenta nan suka baje, ga gajiyar tafiya ga gajiyar azumi abin dai ba'a ce wa komai, kuma sun taki sa'a akwai wutar lantarki, nan take bacci ya yi awon gaba da su... *LADIYO* Farkawa ta yi daga baccin asarar, gari ya waye tangararan sai rana da ta ƙwalle wacce fita a cikinta ba ƙaramin barazana ce ba ga lafiyar mutun. Haka ta hangame baki tana hamma, babu salati babu komai, wurin randar ruwanta ta nufa, sai dai me wayam, babu komai, ta kalli gefen ɗakin Ayaman sai yanzu ta lura da kwaɗon da ke jiki, "Hmm, ayi mutum sai dan banzan yawo? Auren fari na ya gagara ga kuma shegiya kana goyo, tabb ." Nan ta gama surutanta ta shige ɗaki ta fito da wani yagalgallen hijabinta wanda in aka ce ya yi wata bai ga wanki ba kar ka musa, waje ta leƙa ta ga kamar babu alamar mutane a layin, chab ta hango Zakariyya ɗan maƙociyarta, yaron bai gaza shekaru bakwai ba. "Kai Zakariyya! Zo nan." Ta ƙwala wa Zakariyya kira. Yana wasa da kuɗin hannunsa ya taho, askin da ke kansa ya yi solll alamar an kankare gashin sosai. Hannu ta sa ta ɗala mai duka a kan, ai kuwa yaron ya firgice ya zura a guje yana "Allah ya isa." Sakin baki ta yi lallai, wannan ɗan karamin yaron har yana da bakin mata Allah ya isa. Haka nan, ba dan ta so ba ta ɗauki bokiti ta nufi bore hole ɗin garin, kamar kullum a cike ga zafi ga azumi, ta kawo hannu za ta sa bokitinta wata mata ta hankaɗe ta sai ga ta shirim a gefe, wata ƙara ƙugunta ya yi, dan haka cike da masifa ta ɗago za ta zazzage wa matar nan buhun rashin mutunci. "Dallah malama ba ki ga kin bige ni ba? Ko ke makauniya ce ?" Ko kallo bata ishi matar ba balle ta tanka mata, hakan kuma ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba. Kallon kayan jikinta ta yi, duk sun ɓaci da taɓon wurin ga ruwan datti, haka ba dan ta so ba sai dan bata da yadda za ta yi ta bar wurin cikin fushi. Ta zo wucewa ta hango gidan Delu, sarai ta ji me ya faru da Delun dan har gida aka kawo mata gulma, amma ta yi biriss ta wuce ba tare da ta yi tunanin shiga ta yi mata jaje ba. Gidan maman Zakariyya ta nufa tunda kusa ta gidanta suke kuma su na da rijiya a gidan, dan haka ba ruwansu da zuwa bore hole. "Assalamu Alaikum." Ladiyo ta rangaɗa uwar sallamarta haɗ da kutsa kai cikin gidan. Shiru gidan alamar ba kowa, kuma sallama ta yi ta ji shiru hakan ya ba ta damar ɗaukar gugar da ke gefe ta fara cilla ta cikin rijiyar. "Kehh! Kehh me zan gani haka?" Ce war Binta maman Zakariyya. "Au ashe ki na ciki ki na ji na ki kai shiru, ruwa na zo ɗiɓa." Ladiyo ta faɗa ciki-ciki ta na cigaba da abinda ya kawo ta. "Wallahi Ladiyo ba na son neman rigima, haka kawai ki shigo gidan mutane ki fara ɗiban ruwa ba tare da izininsu ba? Haka ake?" Ganin Ladiyo ta yi banza da ita ya sa ta yi azamar riƙo gugar ta na wancakalar da Ladiyo a gefe, ay kuwa ta faɗi himm a wurin banɗakin gidan inda har wanke-wanke yi ake a wurin. Nan fa suka hau faɗa da Ladiyo ana ta rigima duk da Allah ya sa matar ita ma ba daga baya ba wurin bala'i. Haka nan ba dan ta so ba ta ja bokitinta ta yi gaba ta na sakin mugayen alkaba'ir a kan wannan rijiyar. *NAFEE* Babu abinda ya mata zafi, daɗinta kawai take ji, dan ma yanzu rashin lafiyar Ammi ya ɗaga wa Farouk hankali duk ya daburce. Ganin ba wasu kuɗi ne ke shigo mata ba ya sa ta siyar da gidanta a bisa shawarar ƙawarta Lubna. Dan haka ta cigaba da flexing ta na jin daɗin rayuwarta, ga samari da maza da take tarawa Farouk a cikin gidansa a sirrance. "Wallahi NAFEE bana son irin wannan!!! Da aurenki fisabilillah? What kind of life is this? Sai kace s*x machine? Kullum ba kya gajiya da abu ɗaya?". Farouk ya faɗa ranar da ya kama ta da Tee boy, wani saurayinta tun kafin bikinsu. Da dubara ta shashantar da Farouk da yake ga aikin boka, ga kuma kissa da kisisina iri-iri duk bata rabo da su. Da ƙyar Tee boy ya fece, ira kuma Nafee ta bawa Farouk haƙuri da alƙawarin har abada ta daina kawo maza gidan. *Nurse Haleemah* Kamar yadda Ummu ta buƙata, bayan ta farka wuraren ƙarfe tara na dare ta yi wanka ta shirya cikin wata jar atamfa me haɗe da ash color, sai ga ta ta fito ɗass abinka da farar fata. "Gwaggo sai na dawo." Haleemah ta faɗa tana kuma juyawa a gaban Gwaggo dan ta shaida kwalliyarta. Ai kuwa Gwaggo ta shaida, dan haka ta rinƙa yabon kwalliyar Haleema har da bata dubu ɗaya a bisa kuɗin siyan kwalliya. Haka ta fice cikin annashuwa da ƙaunar kakar tata, ta tare napep ta gaya mai in da zai kai ta. Direct hotoro tsamiyar boka da ke garin Kano ta nufa, babu ɓata lokaci ta biya mutumin kuɗinsa ya ja babur ɗinsa ita kuma ta shiga daidai layin da take ganin shine wanda za ta iya tunawa a mafarkin. Exactly mai shagon ta gani, ai kuwa ta yi mai sallama haɗe da gaishesa suka gaisa cikin mutunci . "Dama kuɗi ka ke bi na na zo ba ka." Haleemah ta faɗa tana ciro dubu ɗaya ta miƙa masa. Cike da mamaki mutumin ya amsa, yana ce wa "Baiwar Allah yaushe kika karɓi bashin?" Damurcewa Haleemah ta kusan yi tana inda inda ta ce "Eh, ko ka manta ne ɗari biyar na amsa amma kamar ba kai ne a shagon ba." Haka nan mutumin ya amsa ya bata chanji, ƙin amsa ta yi tana ƙoƙarin fita daga shagon. Kichiɓis ta yi da mutum, ba ta gama tantace waye ba, ta ji tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa, ta yi taga-taga zata faɗi Allah ya taimaka akwai freezer a gefe sai ta yi saurin dafe ta. Cikin fushi ta juya ko ganin mai wannan ikon, abin mamaki Farouk! Lallai ko sau ɗaya ta ga Farouk a mafarki tana zaton za ta iya tantance shi. Hayaniyar da ta ji su na yi da mai shagon ce ta juyo da ita daga duniyar tunani, "Wallahi ba zan baka ba, bashin dubu tara da ɗari biyu fa nake bin ka, kuma har yanzu shiru ba labari, shine za ka zo ka ce na ara ma har dubu biyar? Habaa ka yi lissafi mana Farouk." Mai shagon ya gama faɗa yana cigaba sa harkonkinsa, ganin ba sarki sai Allah ya sa Farouk ficewa daga shagon wanda ko tantama ba ta yi hawaye ta gani cike da idanun. "Hajiya kina buƙatar wani abun ne?" Mai shagon ya faɗa ya na kallon Haleemah ganin ta tsaya a wurin kusan minti goma. "Dan Allah waye wannan wanda ya fita?" "Hmm, wannan mutumin da ki ke gani, yana ganin jarabawa, ya auro wa kansa jaraba da bala'i, ai ba ki san wani abu ba, komai na sa yana kan idonmu..." Nan fa Musa kai shago ya saki baki yana ɓarin zance, dan tun tarewar Farouk da Ummu har aurensa da Nafee. Daga ƙarshe dai Musa ya ƙarashe da faɗin "Ai in gaya miki da girman kai babu wanda be nuna mana ba, wulaƙanci kala-kala, matarsa kafin ta ɓace kar ki so ki ga wulaƙancin da yake mata shi da amaryarsa ba, daga ƙarshe dai ko hatsari ta yi daga nan bamu sake jin labarinta ba." Nan suka ƙarƙare hirar, Haleemah ta kama hanyar gida da tunani kala-kala a ranta, "Dole na samo asalin Nafee!!!!." Ta faɗa a ranta. *Ladiyo* Tafiya take tana faɗa a ranta ƙasa-ƙasa, tana fatan wannan rijiyar ta ƙafe ko kuma wani mugun abin ta same ta. Wasu mata ne su biyu suka zo wucewa, ay kuwa ta jiyo su su na gulmarta, abinka da mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki nan ta hau surfa masifa da bala'i a kan hanya har ta kai ta gwada ƙwanji tsakaninsu da matan, abin asara a ka fasa mata bokitin gida biyu, kuma nan suka bar ta kamar za ta haukace. A daburce ta yi hanyar gida tunawa da ta bar ɗakinta a buɗe kuma akwai kuɗaɗe masu yawa a kan gadon. Tun daga nesa ta hango mutum ya fito daga gidan yana sauri, da gudu ta isa tana ihun ɓarawo, amma kash har mutumin ya ɓacewa ganinta. Tana isa gidan ta shige ɗaki, sai dai me kuɗi suka ce ɗauke ni inda ki ka ajiye, wayam ga kaya baja-baja alamun an mata bincike, sif ta buɗe, ihu ta sa haɗe da durƙushewa tana zubewa a ƙasa sumammiya.. Amma kema Ladiyo da sakacinki, toh Allah ya kyauta sai mun haɗu da ku a kashi na gaba , na gode. More comment more typing ✍️ Khairat ce 💙 Love you all 💞 🥰. 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat (SHALELEN JAJIRTATTU 🤍) Posting room 👇 https://chat.whatsapp.com/HxEIWhndU7REHF43SVBdYF My WhatsApp group comment section 👇 👇 https://chat.whatsapp.com/JNgqE1jHaacFt85y33FgDv *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM* *PAGE 73-74(BOOK TWO)* _____ "Wayyo!!! Innalillahi, ina kuɗina? Ina kuɗina?" Abinda take ta faman maimatawa kenan tana watso kayanta. Duk ihu da kururuwar da take yi a cikin gidan bai ishe ta ba har sai da ta fito waje tana birgima a cikin ƙasa. Sanin hali ya sa ba wanda ya bi ta kanta, dan ita ma in wani abu ya sami mutum daga ta yi mai dariya sai Allah ya ƙara, ko ta saka ma idonta kwalli ta balbale shi. Zuwa chan ta ta ga duk kururuwar da take ba wanda ya kula ta ya sa ta koma cikin gidan, ay kuwa tana yin arangama da kayanta ta ji zuciyarta ta ce dumm, ta kuma faɗi ƙasa sumammiya. *FAROUK* Rayuwa ta yi mai juyin-juyi, tabbas ya yadda da karin maganar da hausawa ke cewa ba kullum ake kwana a gado ba watarana dole a kwanta a ƙasa, toh kuwa ba shakka hakan ta faru da shi, bai gama girgiza ba sai da ya ga debit alert daga bankinsa alamar an cire mai kuɗi. "Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un!" Ya faɗa sakamakon ganin an ciri kuɗi daga bankinsa har naira miliyan daya da dubu ɗari takwas, wanda kaf duniya ya rantse su kawai ya mallaka a halin yanzu, bugu da ƙari ga kuɗin asibitin Ammi dan ba ta iya numfashi da kanta sai an sa mata oxcygin wanda a ƙalla a rana ana kashe mata #150, 000 kuma hakan ba ƙaramin giɓi ya yi masa a kuɗinsa ba. Ganin yawan fashinsa ga kuma sama da faɗi da ya yi da kuɗin Company ya sa suka salleme shi, inda Allah ya taimake shi ma sun haƙura basu nemi kuɗinsu ba. Abinda Farouk bai sani ba shine NAFEE ce ta cire wannan kuɗaɗen, a bisa shawarar Lubna, domin shi kansa Farouk bai san ta san pin ɗin cire kuɗinsa ba, haɗe kuma da babban sakacin da ya yi na barin katinsa a gida. Haka nan ya rasa madafa ya kira Anty Haleemah, ta na ɗaga wa suka gaisa kamar kullum, sannan Farouk ya ke gaya mata abinda ya ke faruwa. "Wallahi Farouk mu ma yanzu fama muke, kamar ka manta mijina takarar gwamna yake? Duk kuɗaɗensa ya zuba su a harkar siyasarsa, yanzu ba kamar da ba, amma turo account na sa ma ko #100,000k ne sai a sai mata magani ." Anty Haleemah ta faɗa ya yin da Farouk ke gaya mata ba shi da kuɗi a hannunsa. Cikin kuka Farouk ke faɗin, "Big sis #100,000k ya yi kaɗan, ko kuɗin oxygen ba zai siya mata na rana ɗaya ba, dan Allah ki taimaka, ki tuna fa mahaifiyarmu ce baki ɗaya." Ba tare da Anty Haleemah ta kuma ce wa komai ba ta kashe wayar, ta na banbami, "Habaa, ni kaɗai ce ƴarta? Ita Raihana da ke ƙasar waje ba za'a tuntuɓe ta ba sai ni? Wallahi abinda na yi niyya shi zan saka." Ta ƙarashe cikin masifa. Haka nan ta tura masa 100k ɗin, a ranta ta na raya irin ƙoƙarin da ta yi. Farouk bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kuma kiran Raihana, nan fa take zayyana masa halin rayuwar da suke ciki ita da mijinta, dan rayuwa a ƙasar waje ba abu bace mai sauƙi, yanzu ma shirin dawowa gida Nijeriya suke yi. Haka ya haƙura ya tura wa asibitin kuɗin a ka basa magungunan Ammi, abin mamaki haka ta yini bata buƙaci Oxygen ba, Allah kenan mai duba bayinsa a duk yanayin da suke ciki. *Ladiyo* Sai wurin isha'i ta farka, shima kuma Sadeek ne ya tashe ta dan ya shigo gidan ya same ta baje a tsakar gida. Ladiyo ta kai mai wata chafka ta na faɗin "Ina kuɗina? Kaine ka ɗauke mun kuɗi ko?" Ta faɗa kamar wata zararriya. Hannu ya sa ya bige na ta ya na faɗin "Lafiyarki kuwa Ladiyo? Anya baki haukace ba? Wasu kudi kike magana a kai?" Ay kuwa ta zabura jin ya kuma yin maganar kuɗi, "Wallahi sai ka biya ni kuɗina,na uwarka ne za ka ɗauka." Sadeek ya zuciya jin ta ambaci uwarsa, ya kaure ta da wani shahararren mari wanda sai da ya sa kwanyar kanta ta daina aiki na wasu daƙiƙu. Haka faɗa ya kaure tsakaninsu har sai da suka haɗa wa juna jini da majina. *Kwana biyu kafin sace kuɗin Ladiyo* Abinda baku sani ba shine, kwana biyu da suka wuce Yunusa ya shigo gari, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga wa Ladiyo tunani ya yi ba. Zuwansa ke da wuya ya tayar da husuma a kan shi fa ala dole sai an siyar da gidan nan tun da gadonshi ne, dan shine kaɗai yaron Malam Isyaku sai Ayaman wacce ba sa ɗaukanta a matsayin ƴa mai cikakken iko da gidan ubanta, Nabila da Nafeesa duk agololi be. Ganin Ladiyo ta tayar da nata ruwan bala'in, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba ya sa Yunusa cin alwashin komai dare dole a siyar da gidan nan. Ai kuwa kiran sallar magariba ke da wuya , Yunusa da mutanensa suka dira a kan Ladiyo, manyan makamai ne a hannuwansu wanda ba karamin firgita Ladiyo suka yi ba. Dan kare lafiyarta, dan ya san a kan siyar da gidan nan Yunusa zai iya nakasa ta har ƙarshen rayuwarta duk da kasancewarta mahaifiya a wurinsa . Wurin Alhaji Maude, babban dillalin garin suka nufa, ba tare da ɓata lokaci ba ya turo mutane a ka ga gidan kuma aka taya shi naira miliyan daya, duk da gidan na da girman gaske dan kuɗinsa na ainihi zai iya haura miliyan goma, haka nan Yunusa ya siyar. Ko da aka gama cinikin gidan ya amshi kuɗin dubu ɗari ya cilla wa Ladiyo ya kama hanyarsa. Haka ta sha kuka kuma ta yi danasanin haihuwar Yunusa, yanzu ina zata je? Sai kuma ta tuna da Sadeek... Danasani yanzu kika fara Ladiyo. *Ayaman* Cikin haba-haba da farin ciki ta tarar da matan gidan ana ta kai komo domin samar da abincin shan ruwa da kuma sahur. Girki suke yi a tare sai kowacce ta ɗiba a kularta, hadin kansu sai wanda ya gani. "Sannunku da aiki." Ayaman ta faɗa ya yin da take tsugunawa ta na daɗa ƙare wa matan aiki. Nan suka shiga amsa sannun suna faɗin me yasa Tsahare ta fito da ita daga zuwanta. Nan ita ma ta zauna aka fara aikin, kunu da ƙosai ne wanda sai tashin kamshi yake yi, ga kunun gyaɗa ga wanda ba ya son kunun tsamiya, sai kuma lallausan tuwon shinkafa miyar kuka ita ma sai kamshi take. Kafin a sha ruwa sun kammala komai,nan aka fito da kankana aka yayyanka aka shirya komai. Wato a tarihin rayuwar Ayaman za ta iya ce wa wannan rana ta 27 ga watan Ramadan shekara ta 1443 wanda ya yi dai-dai da April 27 shekara ta 2021 bata taɓa jin daɗin karya azumi irin wannan ba, ko'ina ta juya murmushi da ƙauna ake nuna mata, haka ta godewa Allah ta kuma yi salati ga manzon rahama ( S.A.W). Bayan shan ruwan nan matan da ke sallah aka nufi masallaci domin sallar isha'i da kuma taraweeh. More comment more typing ✍️ Domin talla, ko ƙorafi ko gyara a tuntuɓe ni ta wannan number 09036812206 Love you all 💞 🥰 Khairat ce ✍️🤍 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By KHAIRAT 🤍 *Ga masu son a tallata musu hajarsu ko sana'arsu, su tuntuɓi wannan lambar wayar 09036812206, in shaa Allah kuna da Khairat ba ku da damuwa🙌😁* *Assalamu Alaikum, ina shahararrun marubutan suke? Ku matso wannan magana ta ku ce. Kina rubutu amma har yanzu ba ki da tsayayyen wurin da za a miki graphic design? Toh fa ga dama ta samu, domin gwangwaje ku da graphic design mai kyau da ɗaukar ido, wanda tun kafin ma karanta su karanta littafin sun san zai yi armashi, ku tuntuɓi wannan lambar wayar 09036812206 kai tsaye domin samun na ku book cover ɗin* 😍 *Ban tsaya iya nan ba, duk dai a kan marubutan namu masu albarka ❤️, kin kammala littafi kins son a haɗa miki shi document? Wannan ma babbar dama ce domin da kuɗinki ƙalilan za'a haɗa miki document mai password ko kuma mara password, shima dai ku tuntuɓi wannan lambar wayar 09036812206* BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM PAGE 75-76(BOOK TWO) *Ayaman* Rayuwa daidai gwargwado ta mata adalci a ƴan kwanakin nan, domin kuwa, so da ƙauna wanda ba'a taɓa nuna mata a gidan mahaifinta tun bayan rasuwar mahaifiyarta ba ta na samu a gidan Tsahare, dan so suke mata tamkar ƴar uwarsu. A'ishah ta girma ma sha Allah, ga farar fatarta kamar ka latsa jini ya fito saboda haske da ɗaukar ido da take yi. "Ayaman!." Tsahare da tun ɗazu take kan Ayaman ta na mata magana amma ba ta amsa ba ta furta cikin ɗaga murya. Zumbur ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula ta na ƙare wa Tsahare kallo. "Me ki ke tunani haka? Ayaman kin ɗaurawa kanki damuwa wallahi yanzu meye na tunani kuma? Dan Allah tashi a yi harkoki da ke kin zo kin zauna a ɗaki ke kaɗai." Shiru Ayaman ta yi ta na kallon Tsahare kamar bata taɓa ganinta ba, kafin ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Ba za ki gane ba maman Auwal."(Auwal shi ne Asalin sunan ɗanta) "Dama ta ina zan gane tun da ban ɗaurawa kaina damuwar banza ba, ba ma wannan ba tashi ki shirya mu je amso ɗinki." Girgiza kai kawai Ayaman ta yi kafin ta miƙe ta ɗauko hijab ta zira haɗe da sa takalminta. Ita ma Tsaharen haka ta yi, ta kullo ɗakin saboda yara da ke hada-hada kar su je su ɓata mata. Sallama ta yi wa mutanen gidan a kan ce wa za su je su amso ɗinki. Sun fito kenan, A'ishah ta taho daga wurin yaran dake waje ta na ta surutanta, da alama dai wasa suke yi. Kuka ta dasa a kan sai ta bisu, ba yadda ta iya haka ta ɗauko ta suka nufi titi. Wurin da ɗan nisa dan haka sai da suka tare tasi suka hau suna faɗa mishi in da zai kaisu. Shagon ɗinkin suka nufa bayan mai tasi ɗin ya sauke su, da yake Tsahare mace ce mai son ƙwasƙwas da gayu, shiyasa bata kaiwa masu ɗinkin unguwa ɗinkinta a ce war ta basu ƙware ba. A bakin titi wurin yake, hakan ya sa ba shi da wahalar gane wa. Maza ne a shagon sai ƴanmata da ke zuwa koyon ɗinki a wurin. Bayan an gaggaisa telan ya fito da kayayyakin ya na nuna musu Sun nisa wajen kallon kayan suka ji ihun mutane ana salati, a razane ta ɗago ai kuwa ƙirginta ya buga dumm sakamakon ganin abin da ya girgiza kwanyar kanta. *FAROUK* Alhamdulillah, jikin Ammi sai san barka, dan kuwa yanzu ta na iya motsa wa har ta buɗe idanu. A yau ne abokansa, wanda suka haɗa da Don jezzy(Abdullahi), Kamal, da kuma Mubarak suka kawo mai ziyara ta musamman zuwa asibitin domin duba jikin Ammi. Bayan gaisuwa da addu'oi suka tura masa naira dubu ɗari tara, da niyyar a cigaba da kula da jikin Ammi. Ya yi kuka kuma ya godewa Allah, dan ba dan wannan taimakon ba ya rasa yadda zai yi. Fitowa suka yi daga ɗakin da aka kwantar da Ammi, dan su wuce masallaci dan gabatar da sallar la'asar, nan fa Kamal ke shawartar Farouk ko an haɗa da maganin gargajiya a cutar Ammi? Dan akwai lauje cikin naɗi game da wannan rashin lafiyar. Amsa masa ya yi da a'a, sa'annan suka wuce abinsu. Kafin su tafi sai da Kamal ya bada shawarar neman maganin gargajiya, in da a nan Farouk ya amince da niyyar gobe zai kama hanyar Madobi wurin wani mai bada magani. *NAFEE* Rayuwar sharr abinta, babu wata damuwa, yanzu sabon saurayin da ta yi mai yaayi da kuɗi sai kashe mata zuciya yake yi. Duniya suke ci da tsinke, babu abinda ya sha musu kai, dan ya fi Farouk komai, ita wani sa'in ma mantawa take yi da wani Farouk a rayuwarta, dan ta watsar da batun auren shi ta na shagali abinta. Karuwa kenan!!! Wai ni kam ya labarin NABEELA? Mu je zuwa. *NABEELA* Gidan Alhaji Gabatari na nufa, babban gidan mai cike da kayan alatu na rayuwar duniya taƙaitacciya! Wannan gidan saboda tsaruwarsa da kyaunsa ba za ka taɓa aiyanawa a ranka akwai wani mahaluƙi da zai sha wahala a cikin wannan gida. Ilai kuwa, Nabeela na mawuyacin hali a wannan tamfatsetsen gida. Kwance ruff da ciki na same ta a kan tiles, dan yanzu baby chakwai ya dawo da ita wani ɗaki a chan ƙarshen gidan ba tare da sanin Alhaji ba. Kallo na ƙare mata tsaff, ba dan tsayin da take da shi ba, haɗe da faffaɗan kwankwaso da wallahi na ce ba Nabeela ba ce, wata halittar ce daban, ta rame ta jeme, banda istigfari babu abinda ke iya fita daga bakinta, shima kuma ba dai-dai take iya faɗa ba. "Astangafurullah." Ta ke ta maimaitawa, sannan ta cigaba da faɗin "Kaicho duniya! Mai kyalkyalin banza, ban taɓa zaton duniya za ta juya min baya ba, duniyar da na yi sabon Allah dan in mallake ta ga shi ta juya min baya, ta rikiɗe ta zama wani abin daban! Na bi san zuciya da kuma huɗubar uwa kamar Ladiyo na yi shirka, babu ilimin addini, ban san komai game da Allah ba, ga irinta nan, yanzu zama ma ya gagare ni, wayyo ni." Ta na ƙarashewa ta kece da wani irin kuka mai cike da nadama da ciwo, tabbas a tunaninta yanzu kam rayuwarta ta zo ƙarshe ba ta da wani amfani. Ta na cikin kukan ta jiyo hayaniya mai tarin yawa daga waje, daddafewa ta yi ta miƙe sai ga wani ruwa mai yauƙi da warin gaske ya zubo daga hq ɗin ta. A hankali ta bi ruwan da kallo ta na sake fashe wa da wani irin kuka, window ta kalla, abinda ta gani ya sa ta kuma murza ido domin tabbatar da abinda take gani, ƴan sanda! Ta faɗa da ɗan ƙarfi. In kuwa ta tabbata ƴan sanda ne , lallai addu'ar ta bata faɗi ƙasa banza ba, duk da ta na da tabbacin bai dai-dai take addu'ar ba saboda ƙarancin ilimin addini. Iface-iface ta ke jiyowa daga falo, ta yi ƙoƙarin fita amma ba dama tun da ƙofar a garƙame take. Ihun neman taimako ta kurma wanda ya taimaka wani daga cikin jami'an ya jiyo ta, kofar yake ƙoƙarin buɗewa amma a kulle take, ya saita harsashinsa a wurin mabuɗin kofar ya harba, sannan ya samu bude ƙofar. Wani wari da ya ziyarce shi ne ya yi sanadiyar ja baya da ya yi, ita kuma Nabeela da jan ciki ta fito wajen. Ƙare musu kallo take yi ɗaya bayan ɗaya, jami'ai ane wanda ya tabbatar da ba yan sanda bane amma sun fi kama da jami'an NDLEA wato hukumar yaƙi da sha da kuma sufurar miyagun ƙwayoyi. Manyan mutane ne, Alhaji Ahmed , Alhaji Abubakar, Alhaji Mamman, da kuma Alhaji Gaɓatari, sai baby chakwai da ke gefensa, wata jaka ce a gabansu wadda da alama miyagun kwayoyi ne (cocaine) suna rabawa a tsakaninsu, wanda bata daɗe da shigowa ƙasar ba. Ba tare da ɓata lokaci ba aka yi motar jam'ian da su gaba ɗayansu, ita kuma Nabeela aka wuce da ita asibiti. *Ladiyo* Ladiyo ikon Allah! Tun bayan abinda ya faru, bayan sati biyun sun cika ta tattara kayanta ta nufi shagon Sadeek, bayan sun gama tattaunawa a kan hakan. Nan fa suka ɗaura aure a tsakaninsu, suke kuma cin karensu babu babbaka. *Sati uku bayan tarewar ta a shagon Sadeek.* Tafiya take a hankali kamar ƴar maye, haka dai ta daddafa har ta ƙarasa babban asibitin ƙauyen. Kwana biyun nan zazzaɓi mai zafi take yi hade da wata irin gudawa kamar ruwa, ga ciwon kai mara misaltuwa, da ciwon jiki da dai sauransu. Bayan fuskantar wulaƙanci daga wurin ma'aikatan asibitin ta samu aka ɗebi jininta, biyan kuɗin test din ta yi. Bayan sakamakon ya fito aka tura ta ganin babban likita, shima a wurin sai da ta daɗe kafin ta samu shiga office ɗin. "Wasu alamu kike ji ko sauyi a jikinki?" Likitan ya tambaya bayan ta zauna. "Likita ni kaina na fuskanci chanje-chanje a yanayin jikina, ina yawan yin amai, kasala da ciwon jiki, sai kuma zazzaɓi, sannan kuma ka ga yadda tafukan hannayena suka yi." Ta karasa ta na nuna mai tafukan hannayenta da suka sauya launi suka koma yellow. Tashi likitan ya yi ya matso kusa da idanunta, ya haske wata ƙaramar fitala, sannan ya koma. Cike da gajiya da kuma kasala Ladiyo ta buɗe baki ta fara ce wa "Likita ka gaya min me yake damuna, na zata malaria ce da na saba yi, amma da na je Chemist ɗin Hamisu ya bani maganin malaria na sha na ji ban warke ba, kawai na garzayo asibiti." (Da yawan mutane su kan alaƙanta ƙanƙantar cuta da malaria, wanda ba haka bane, kamata ya yi a daure a je asibiti a gwada kafin a sha magani, Allah ya kyauta) Ƴan rubuce-rubucensa likitan ya yi kafin ya ɗago ya kalle ta , "Ki na da aure?" Ɗago wa ta yi ta amsa mai da "ehh" Kuma rubutun ya yi kafin ya ce, "Mijinki na bin mata ne?" Banbarakwai ta ji maganar, hakan ya sa ta ɗan haɗe rai tare da furta "Wannan wace irin tambaya ce likita? Cewa na yi ka duba ni ba wai ka zo kana tambaya ta mijina na bin mata ba ko shigen haka." Furzar da iska likitan ya yi sannan ya ce "A gaskiya a iya binciken da na yi, ya tabbatar da kina da ɗauke da cutar hepatitis B." Da ayar tambaya ta ce "Me hakan ke nufi likita?." "Cuta ce da ake ɗaukar ta ya yin da wata mu'amala ta haɗa ka da mai wannan cutar, tana addabar hanta ne, kuma a iya bincikenmu ta fi cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV illa." Salati Ladiyo ta rafka ta na zubewa a ƙasa tare da fashewa da kuka, ita kalaman likitan ne ya fi daga mata hankali, ta fi HIV ILLA? Akwai tashin hankali. Likitan ya cigaba da faɗin "Wannan cuta ba wai ta na nufin ƙarshen mutum ne ya zo ba, a'a, za ka iya magance ta tun kafin ta yi ƙarfi a jikin mutum, amma ga wasu daga cikin hanyoyin da ake ɗiban wannan cuta *1- Ta hanyar kitso ko aski, wannan ƙarfen na riƙe cuta sosai, kuma wannan virus na hepatitis na zama a jikin ƙarfe na tsawon awa 7 zuwa 8, kuma da zarar jini kaɗan ya taɓa ƙarfen, shikenan dan ita ba ta raina wurin.* *2- Amfani da banɗaki mara tsafta, tabbas ƙazanta na da kaso mafi girma a wanzuwar wannan cutar* *3- Na uku kuma mafi girman hanyar da ake kwasar wannan cuta ita ce, hanyar saduwa da mai irin wannan cutar, ko yaya take kuwa.* Dan haka ku kare kanku daga saduwa barkatai da mutanen banza. Haka dai Ladiyo ta taho hanya riƙe da sakamakon gwajin a hannunta, ga yunwa ga cutar da ke nuƙurƙusarta. Siraran hawaye ne ke zuba daga kurmin idanunta, Yanzu ina mafita? Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ *SHALELEN JAJIRTATTU CE (KHAIRAT)* 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By *KHAIRAT(SHALELEN JAJIRTATTU)* *BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM* *PAGE 77-78* *LADIYO* Ganin ba ta da wata madafa ya sa ta nufi shagon Sadeek, a zaune ta tarar da shi ya na shan garin kwaki da ya ji gyaɗa da kuma madarar gari. Zama ta yi kusa da shi cike da sanyin jiki, shi kuwa gogan ko kallon in da take bai yi ba. Dama ta lura a kwanakin nan kawai dai ana rayuwa ne, amma sam Sadeek ya daina damuwa da ita, ban da danne-dannen waya ba abinda ya iya ko kallon arziƙi ba ta samu daga wajensa. "Sannu da gida." Ta furta murya a karye kamar mai shirin yin kuka. In kun tanka toh shima ya tanka, haka ya yi banza da it. Wani malolo ta haɗiye kafin ta miƙa mai takardar sannan ta ce "Dama asibiti na je ga sakamakon nan." Ta faɗa sai kuma ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi. Fizge takardar ya yi, kana ya buɗe ya karanta. Wani murmushin makirci ya saki kafin ya cilla mata takardar ya cigaba da abinda yake yi. Tsayawa ta yi ta na ƙare mai kallo, toh me yake nufi da hakan bai damu ba kenan? *Farouk* Washegari ya tashi da shirin nufar hanyar madobi tare da Kamal domin ziyartar wani mai bada maganin gargajiya musamman abinda ya shafi tsibbu ko asiri. Ya kwantar da kansa a jikin kujerar mai zaman banza yayin da Kamal ke tuƙin motar . Wani wawan birki da Kamal ya ja ne ya yi sanadiyar bige kansa da jikin motar. "Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." Da Kamal ke ta maimaitawa ya sa shi fitowa da sauri daga cikin motar. Wata kyakkyawar farar yarinya wacce ba za ta gaza shekara ɗaya ba ya gani kwance jikin jini a kwalta. Wasu mata biyu ne suka iso wurin, ɗayar da ya fi tunanin ita ce mahaifiyar yarinyar ta zube sumammiya a wurin sakamakon wannan mugun ganin da ta yi,ɗayar kuma cike da ruɗu take tashinta. *AYAMAN* Salatin da suka jiyo ne ya sa su ɗagowa daga kallon ɗinkin suka kalli wurin da mutane suka taru. Gefenta ta kalla ta ga babu A'ishah a wurin, zuciyarta ta buga dumm!!! Ta nufi wurin da ta ga mutanen Tsahare na take ma ta baya. A'ishah da ta gani kwance a kan kwalta ga jini duk jikinta ya sa ƙwaƙwalwarta ɗauke wa kafin daga bisani ta rasa in da kanta yake. *NABEELA* Tun san da ma'aikatan hukumar yaƙi da sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi wato NDLEA suka ɗauke ta zuwa asibitin ta kasa gane wani hali take ciki. Idanunta ta lumshe sannan ta ƙara buɗesu tarr a ɗakin asibitin da take ciki, farin fenti da fararen zanin gado ya daki idanun nata ta damƙe su ƙam, kafin kuma a hankali ta buɗe su ta na ƙarewa ɗakin da take ciki kallo. Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️🤍. Khairiyya ce💘🌹 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By *SHALELEN JAJIRTATTU ()KHAIRAT()* BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM > *PAGE 79-80* Wai ya labarin DELU ne? Ta ɓangaren Deluwa kuwa, abu babu daɗi sam, asirin da ta yi wa Malam Surajo ya karye sakamakon ruwan sama da aka sha a wani daren Lahadi har ya yi sanadiyyar rugujewar kabarurruka a maƙabartar ɗandolo ta garin. Ta gane hakan ne sakamakon masifa da faɗa da Malam Surajo ya shigo gidan ya na yi mata, ta tanka, ai kuwa ya hau zage-zage da tsinewa Delu, ga wasu daga cikin kalaman da yake faɗa. Lbl "In ba dan aikin asiri ba, ina ni ina ke Delu, matsiyaciya la'ananniyar Allah kawai, wallahi ki je za ki gani, dan haƙƙina da na sauran mutane ba zai taɓa barin ki ba." Sai kuma ya yi shiru ya na mayar da numfashi, Delu da tunda ya fara magana zufa take tsatstsafo mata daga dukkanin wata kusurwa ta gashi a jikinta. Da ƙyar dai ta buɗe baki dan ta tabbatar da ko asirin har yanzu ya na nan ta ce "Ka ga Malam ba fa kai matsayin da za ka zo ka na gasa min magana yadda ka ga dama ba kuma na ƙyale ka, ba ka kai wannan matsayain ba wallahi, kuma da kake maganar asiri da la'anta ta, ka san sai dai mu tsine wa juna, dan kaima waye a garin nan bai san kwartanci kake yi ba? A haka na haƙura na aure ka shi ne yanzu za ka zo min da wannan maganar? Dama an ce ɗan Adam butulu." Ta ƙarashe ta na wani gunjin kuka. Malam Surajo ya fusata jin ta kirasa da sunan kwarto, ya juya bayansa ya ɗauko muciya, ya samu ƙafarta da ta karye har ta fara warkewa ya ƙwala mata dai-dai wurin karayar, ai kuwa ta daddage ta tsala ihu "Wayyo jama'a!!! Na shiga uku zai kashe ni." Delu ta faɗa kafin kuma ta sume a zaunen da take dan raɗaɗin azaba. Kasancewar mutanen unguwar sun san halinsu, ko faɗa suke yi ka jiyo ihu da ka shiga cikin gidan za su hau kanka da masifi wai ba ruwanka da su, dan haka babu wanda ya yi gigin shiga ya tambayi me ya faru duk da sun jiyo , ya yi saurin ficewa daga gidan ta ƙofar baya, in da babu wanda ya gan shi. Bayan awa biyu. > *"Assalamu Alaikum."* Amina ta rangaɗa sallama ta na shiga cikin gidan .( kamar yadda muka gani a baya, Amina ƴar kawun Delu ce, ma'ana ƙanwarta.) Turus ta yi ganin Delu a kwance kamar matacciya ga ƙafarta da ke fitar da wani irin ruwa mai yawa. Wullar da kwanon abincin da ta kawo mata ta yi sannan ta ƙarasa wajenta a rikice. Ganin halin da yayarta ta ke ciki, ya sa ta fice da gudu daga gidan ta nufi gidansu dake farkon layin. Babanta ta kira, in da bai yi sanya ba ya ari motar abokinsa aka sa Delu a ciki suka nufi babban asibitin ƙauyen. *Ya labarin Nurse Haleemah da manufarta kuwa?* *Nurse Haleemah* Bincikenta ba laifi ya yi nisa sosai a kan Farouk, dan yanzu ƙalilan daga cikin abubuwan rayuwarsa ne bata sani ba. Ta yi ƙoƙari sosai har ta gano asibitin da aka kwantar da Ammi. Kasancewar asibitin state hospital ne, ma'ana duk matsayi ɗaya suke da asibitin da take aiki ya sa ta ƙudiri aniyar neman transfer zuwa asibitin da Ammi ke kwance. Ranar Monday da safe bayan ta gama shirinta ta yi wa Gwaggo sallama ta fito. Adaidaita sahu ta tara zuwa asibitin Aminu Kano. Bayan gaisuwa kamar yadda ta saba da masu gadin ta wuce ciki, ofishinsu na nurses ta nufa ta ajiye kayanta ta gaisa da sauran nurses ɗin da ke wurin kana ta wuce zuwa office ɗin babban likita. Ofishin doctor Lukman ta nufa, ta ƙwanƙwasa in da bata jira a bata izini ba ta ƙusa kai ciki haɗe da sallama. Rubuce-Rubuce ta tarar da shi ya na yi, ɗago kai ya yi dan ya ga wanda ya shigo mai ofice kai tsaye haka. Wani lallausan murmushi ya saki, duk da ba kyakkyawa bane amma fuskarsa ta yi kyau da murmushin. Ganin haka ita ma ta mayar mai da maratanin murmushin da ka na gani ka san bai kai zuci ba. "Ina kwana Sir." Ta faɗa sannan ta yi wa kanta masauki daga ɗaya daga cikin kujerun ofishin. "Lafiya ƙalau, Halimatus Sa'adiyyah mai tagwayen suna." Ya faɗa ya na bin ta da wani irin murmushi da ta gaza fassara wa. "Uhmm." Kawai ta faɗa kafin nan ta yi ƙasa sa kanta ta yi shiru, ganin shirun ya yi yawa kuma ta na jin idanun doctor Lukman a jikinta ya sa ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Alfarma nake nema doctor." Da sauri kamar jira yake yi ya ce "Faɗi kanki tsaye Halimatu." "Dan Allah transfer nake so zuwa ɗayan branch dake hanyar rijiyar Zaki." Ƙurr ya mata da idanu ya na jin babu daɗi a ransa, yanzu in ta tafi ina zai samu damar kallon wannan kyakkyawar fuskar tata mai cike da nutsuwa? "Transfer kuma Halima?" Ya faɗa da sigar tausayi dake sauƙaƙa zuƙatan masu sauraron sa. "Ehhhh ranka ya daɗe." Ta faɗa cike da girmamawa. "Tohh, ki rubuta takarda zuwa ofishin supervisor wannan huruminsa ne." "Okay Sir, na gode sosai." Sannan ta fice daga office ɗin ta bar doctor Lukman zuciya babu daɗi . Shi kuwa doctor Lukman da kallo ya bi bayanta, ya rasa wannan taurin kai na Halima, sai bin kanta yake ta so shi amma ta ƙi har ya haƙura da ita. Ita kuwa Haleemah da ƙaramin tsaki ta fita daga office ɗin, ita a ganinta ko maza sun ƙare ba za ta taɓa auren doctor Lukman ba.... Kamar yadda ya bata shawara haka ta yi, ta rubuta letter zuwa ofishin supervisor. Ta nufi office ɗin bayan ta ɗau break daga wurin aiki. Ta shafe kusan awanni biyar ta na jiran supervisor, haka ta wuce ba tare da ta samu abinda take so ba. *Ya labarin bokan kan tudu?* Tun ranar da yake tattaunawa da Ladiyo a ɗakin tsafinsa ya ji abubuwa ba kamar yadda ya saba ba, har wani birkice wa aljanun dake taimakawa tsafinsa suka fara yi, ilay kuwa BARQAAAN ne ya bayyana cikin haske mai ɗaukar ido. A gaban idonsa Ladiyo ta rikice ta na iface-iface shi kuma aka ɓatar da shi zuwa fadar matsafa. Durƙushewa ya yi a gaban (Uwar kowa) kamar yadda suke kiran shugabarsu. Tsawar da aka daka masa ce ta dawo da shi daga tunanin Ladiyo tunowa da ya yi a wurin da yake. Sai mun haɗu a next page. Shalelen ce © 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By *© Shalelen Jajirtattu (Khairat)* > *BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM* *Page 81-82* Tsawar da aka daka masa ce ta dawo da shi daga tunanin Ladiyo tunowa da ya yi a wurin da yake. A nan muka tsaya yanzu zamu cigaba . Buɗar bakin shugaba ya ce " Talle(sunan bokan), ba za mu zuba maka ido ka cigaba da aikin da maƙiyanmu ba, dan tabbas BARQAAAN maƙiyi ne, maƙiyin da bai chanchanci yafiya ba ta har abada.... *BARQAAAN* Shin waye wannan BARQAAAN din? Kuma meye matsayinsa a wannan littafi? Ku biyo ni.. *Takaitaccen bayani a kansa* BARQAAAN za'a iya kiransa ruwa biyu, wato rabi Mutun rabi aljan, mahaifinsa ya kasance masunci, wato masu kamun kifi, kuma ya haɗu da mahaifiyarsa a cikin ruwan ta fito shan iska. Tun ya na jin tsoro har ya dawo shaquwa ta shiga tsakaninsa da ita, wadda ba shaƙuwar hankali bace. A wata rana ya fito sunci kamar yadda ya saba, ya tsaya a bakin ƙoramar ya na kallon ta in da Suhain za ta fito kamar yadda ta gaya mai sunanta. Chanbya hango igiyar ruwa ta taho da ƙarfinta, hakan ke nuni da ita ce ta taho, ya gyara tsayuwarsa ya na jiran ƙarasowar ta. Bayan ta diro a gabansa ya tsaya ya na ƙare mata kallo, tabbas kamar yadda ake faɗa matan ɗan Adam sun fi na aljanu kyau nesa ba kusa ba, duk da a suffar mutane take zuwar kai hakan bai taɓa tsorata sa ba. Kallon diri da kuma surar da Allah ya mata yake yi, nan fa ta zo mai da labari mara daɗin ji, na ce wa a masarautarsu an tilasta mata auren ɗan uwanta kamar yadda al'adarsu ta gabatar, amma a wannan lokaci ta na jin gaskiya ba za ta biye musu ba domin ta cutu, ta gwammace ta fice daga masarautar har dai basu yadda da aurenta da shi ba. In dai abu an haramta sa a addini, Allah shi ya san dalilinshi na haramta wannan abu ko halasta shi, kamar yanzu haramun ne keɓewa tsakanin namiji da mace, dan na ukunsu tabbas sheɗan ne. Sheɗan ya taka muhimmiyar rawa wurin aikata ɓarna a wannan wurin, dan kuwa babban al'amari ya gifta tsakanin wannan matasan mutum da aljan. Haka ta wuce zuwa masarautarsu domin jiran faruwar next plan da suka shirya... *LADIYO* Galala ta saki baki ta na kallon Sadeek da ya nuna ko a jikinsa game da matsalar da ta zo da ita, sai ma maida hankali da ya yi wurin scrolling a manhajar facebook. "Sadeek magana fa nake maka." Ta furta a ɗan zafafe dan wannan hali na ko in kula da ya nuna mata ba karamin ɓata mata rai ya yi ba. Nan ma banza ya bawa ajiyarta ko uffan bai ce ba sai ma dariya da ya saki ganin wani post mai abin dariya. Da sauri ta miƙe haɗe da ƙwace wayar ta cillar da ita a ƙasa ta tsaya ta na kallan sa. Cike da tijara ta miƙe ta na faɗin "Tun ɗazu ka mayar da ni mahaukaciya sai magana nake maka da yake ga sabon kamu ko kallo ban ishe ka ba ko Sadeek? Cutar nan ma ina da tabbacin a jikinka na kwasa dan jita-jitar da nake ji a gari na neman matan banza da kake yi ashe da gaske ne, lallai kam mashahurin ɗan iska....." Ai ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ji saukar mari zazzafa a kuncinta na dama Cike da zafin rai Sadeek ya hayayyaƙo mata "Yo ai mahaukaciyar ce Ladiyo, in ba hauka irin naki ba da daƙiƙanci da dabbanci ina kika taɓa ganin saurayi kama ta ya zo wannan ƙauyen har ya aure ki ? Ƙazama da ke tsohuwa kin san dole akwai manufa, kuma tun da na kammala manufata shikenan sai kowa ya kama gabansa." Ya faɗa kafin ya fice da sauri. Zubewa ta yi daɓasss,me hakan ke nufi kenan? *Ayaman* Cike da tashin hankali ta bi bayan A'ishah dan ƙwaƙwalwarta kasa fassara komai ta yi a wannan lokacin, kafin kuma da ƙarfi ta fara faɗin. "A'isha ta! A'isha ta! A'isha ta! Aun kashe min ita, sun kashe min maraniyar Allah wayyo Allah na, A'ishah dan Allah kar ki mutu ki bar ni, ke kaɗai ce sanyin idaniyata a wannan lokacin dan Allah kar ki barni." A kiɗime Kamal ya saka A'isha a bayan motar sai Ayaman da ta shige a rikice ta na kiran a kai ta asibiti kar ta mutu, bayan mantawa da ta yi cewa mutuwa a hannun Allah take, mutum lafiyayye ma sai ya mutu mara lafiyar na nan har sai san da lokacinsa ya cika. Tsahare ma bayan motar ta shiga sai Farouk da ya shige gaban motar ya na jin kansa na wani sara masa dan har ga Allah kukan matar ya cika masa kunne. Asibitin wellness hub (wanda aka kwantar da Ammi suka nufa tun da ba wani nisa suka yi ba wannan iftila'in ya afku) Kamal ya nufa da su, in da cikin gaggawa a ka shige da A'ishah emergency ɓangaren yara. Bayan wani lokaci likita ya fito nurses na biye da shi a baya, ganin yanayin fuskar likitan ba ƙaramin kiɗima su ya yi ba. "I'm sorry to say, she's no more." Ya faɗa da ƙyar kafin ya wuce ya bar su Ayaman shiru dan basu fahimci me yake faruwa ba, yayin da Kamal ya saki wani dogon salati ya na nanata innalillahi wa'inna i'laihi raji'un. Ɗakin da likitan ya fito ta shige kamar a guje ta na baza idon in da za ta ga A'ishah. Karaf!!! Idanunta suka hango mata farin ƙyalle shimfiɗe a saman A'ishah, buɗe fuskarta ta yi, fari tass kamar za ka mata magana ta amsa. Zubewa ta yi a wurin ta fara gunjin kuka mai taɓa zuciya, yanzu shikenan ita komai na ta daga ta fara jin daɗin rayuwa sai ta katse? Mai yake faruwa ne? Mamanta ta rasu tun ta na da ƙarancin shekaru, ta faɗa uƙubar kishiyar uwa da ƴaƴanta, cikin shege ta haife shi a gidan Anas wanda hakan ya yi sanadin datsewa alaƙarsu, mahaifinta ya rasu, yanzu kuma ƴar da ta zama sanyin idanunta ta rasu? A haka za ta gama rayuwarta cikin kunci a kullum? "Ya hayyu ya qayyum ka kawo min mafita." Sai mun haɗu a next page. 😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈 By *Khairat**shalelen (j.w.a)* Page 83-84 *Ladiyo* Ta sha kuka na lokaci mai tsawo, kafin ta hakura ta ɗauki dangana. Wayyo ita kam san zuciyarta ya jawo mata masifa, yanzu ina take da arzikin magance wannan matsala da ta same ta? Ta na cikin tunane-tunane har bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita . Ta na cikin barcin ta ji motsii amma ba ta gama tantance mene ne ba, ta juya ta cigaba da sharɓar bacci. Shi kuwa Sadeek cikin sanɗa ya ɗebe kayan shi kaff, ya juya zai tafi ko mai ya tuno oho ya dawo a hankali ya buɗe lalitar Ladiyo ya kwashe kudin dake ciki bai bar mata ko kabo ba ya fice abinsa. Sai wuraren bayan la'asar ta farka daga nannauyen baccin, tsayawa ta yi ta na ƙarewa ɗakin kallo sai ta ga kamar akwai abubuwan da babu a ciki, kawai ta bar tunanin ta miƙe. Fita waje ta yi ta kalli sauran matan dake ta aikinsu, dan a gidan haya ta kama saboda ba za ta iya zaman shago ba. Ci kanki basu ce mata ba ita ma haka ta ɗauki buta ta nufi da babban ɓanɗakin tal dake cikin gidan. Gida ne babban,mai ɗauke da ɗakuna sha biyu in da mutane mabanbanta ke rayuwa a ciki, in da kowacce mata ke sana'arta domin rufawa kai asiri, wasu na suyar masa, wasu ta wainar fulawa da wasu kayan miya suke siyarwa, wasu kayan gwanjo, da dai sauransu. Kun dai san yanayin gidan haya ba sai na tsaya baku labari ba. Lukutar matar da ta gani a cikin banɗakin sai bahaya take yi ya sa ta yi saurin ja da baya ta na sakin tsaki, ai kuwa Iyabo bayerabiyar da ta kasance maƙociyar Ladiyo a cikin gidan dan ɗakinsu na kallon juna, ta fito da azama bayan ta gama abinda ta je yi, ta na surfa masifa, ita za'a biyo banɗaki ana kalla, wato gulmarsu bata tsaya iya wace ba har sai an biyo ta banɗaki. Haƙuri Ladiyo ta fara bata ta tuno banɗakin waccan gidan nata da in Ayaman ta wanke har hana ta shiga take yi yau ita ake ƙarewa tanadi akan banɗaki gidan haya. "Aikin banza!! Wallahi Ladiyo ki kiyaye ni, kuma ki kiyayi gamuwar mu ni da ke, na ji an ce baki da mutunci, ko ki sa a ranki na dame ki na shanye kuma dai-dai nake da zamaninki." Iyabo ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausarta sannan ta juya ta tafi ta na ta juya ɓaka-ɓakan mazaunanta ta na cigaba da sababi. A hankali ta shiga banɗakin, wari da zarnin da ya ziyarci hancinta ya kusa hallaka ta,anya ma ba a nan ta kwashi cutar nan ba? *Nurse Haleemah* Alhamdulillahi al'amurra suna tafiya daidai yadda nake so ta tura letter kuma an yi accepting,dan haka ta shirya komawa chan next Monday. Ko da ranar Monday ta zo ta shiga asibitin, ta tsaya suka gaisa ta kuma gabatar da kanta a gaban sabon supervisor ɗin ta. Ɓangaren adults aka kai ta dama kuma nan ne Field of study ɗin ta. *Bayan wata ɗaya* Haka ta fara aikinta ba ji ba gani, kuma ta san yadda ta yi ta fara duba Ammi, kamar wasa shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu. Ammi ta ɗauki Halima kamar ƴar cikinta, haka ma Halima ta ɗauki Ammi kamar mahaifiyarta, har Gwaggo ta ɗauko ta duba ta. "Kai Ammi, ki daure ki ƙarasa shan faten nan, kin ga saura kaɗan ko so kike Dr ya ce ba za'a sallame mu ba?" Ammi da murmushi a kan fuskarta ta ce "Halimatu ya kike so na yi ne? Ko so kike cikina ya fashe ." Ta ƙarasa faɗa suka fashe da dariya duka su biyun. Farouk ne ya shigo ɗakin riƙe da da ledojin fruits. Sai mun hadu a next page *MUGUNTA 😈😈😈* Written by KHAIRAT ✍️✨ Bismillahir rahamnir rahim Page 85-86 Bayan wata biyu... Kafin kace me soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin nurse Haleemah da Farouk, soyayya suke gudanarwa mai tsaftar gaske, komai nasu a cikin tsari kuma Ammi ma ta yi na'am da hakan, dan haka ba'a ɓata lokaci ba manya suka shiga cikin maganar. Yanzun ma Farouk ne a ƙofar gidan su Haleemah suna taɗi, magana suke a kan sa ranar da aka yi nan da wata guda, hira suke yi sosai ta masoya kafin ya ji wayarsa ta hau ruri. Ciro ta ya yi daga aljihunsa ya ga special number ce, sai ya yi tunanin ko kamfani ne amma kiran na katsewa wani ya kuma shigowa, sanin kamfani ba sa kira so biyu ya sa shi ɗaukar wayar ya kara a kunnensa. "Assalamu alaikum." Wata babbar murya mai cike da dattijantaka ta maza ta yi mai sallama, amsawa ya yi ya na son tuna a ina ya san wannan muryar amma hakan ya gagara. "Farouku ka na ina ne." Wannan sunan na Farouku ya sa shi dubar lambar da sauri, "Baba Alhaji." Ya faɗa da ƙarfi, Baba Alhaji ya amsa mai da ya zo gida ya na nan. Haleemah kam tsayawa kallansa ta yi, kafin ta ankare har ya shige cikin wata adaidaita da bata daɗe da sauke wata mata ba ya shige ya na mata bye-bye. Murmushi ta yi ta kada kai ta shige cikin gidan, ta na tunanin ko ma waye wannan ya kira Farouk toh ba ƙaramin matsayi yake da shi a wurinsa ba. Ta ɓangaren Farouk ya na shiga gidan jikinsa ya yi sanyi ganin Ammi na kuka, kuma ta na shaƙar iska a hankali daga oxygen. Baba Alhaji ya kasance babban mutum mai faɗa a ji a garin Kano, kuma ya kasance abokin baban su Farouk tun yarinta, amma Alhaji ya fi babansu kuɗi nesa ba kusa ba. Bayan gaishe-gaishe da kuma bayanin bayan rabuwa, nan Alhaji ya sauke musu sha tara ta arziƙi, ga babban gida da ya mallaka musu, ga kuma wani ƙaramin Company da yace tare suka bude shi da Alhajin su Farouk kafin ya rasu, dan haka ya yi signing a kan yanzu kamfanin ya koma hannun su Farouk da yayyensa... *Ya labarin Nafee* Bariki ta buɗe sosai a jahar Lagos bayan shawarar da ƙawarta Lubna ke ɗora ta a kai, ana cikin wannan halin wani babban Alhaji daga Abuja ya bukaci ganinta a nan garin na Abuja domin su sheƙe ayarsu da suka saba. Ta gama shirinta tsaf, ta kama hanyar Abuja ko iya kuɗin mota Alhaji Ahmed ya tura mata miliyan daya, ga kuma alƙawarin mota bayan ta je. Sun sha honeymoon din su (waiyazubillah) a garin na Abuja, duk gurin cin abinci da outing ba wanda Nafee bata sani ba, sun yi abubuwa kam abin sai wanda ya gani. Ana saura kwanaki biyu ta koma garin Lagos Alhaji ya buƙaci da ta shirya za'a zo a kawo ta guest house dinsa tunda ita a hotel take zama. Bata musa ba, ta shirya cikin danƙareren leshinta ta yi tsaf, har da bankaɗar magungunan mata kala-kala, ta zauna ta fara cin abinci kenan sai ga yaron Alhaji ya zo, suka taɓa hira sama sama sannan suka shiga Mota suka kama hanya. Ganin an kauce hanya anyi wata hanyar daban ya sa ta kalli Maude, ta ce. "Aah Maude ya na ga ka wuce hanyar?" Ko kallonta bai yi ba sai da ya faka motar a bakin titi sannan ya shammace ta ya bige mata kai da ƙarfi, nan take kuwa ta suma sai ga jini ta hanci da baki, hannunsa ya kai kan hancinta ya ji da sauran numfashi ai kuwa ya kuma dagewa ya bige ta da gwiwar hannu, nan take rai ya yi halinsa... Wata dariya Maude ya yi kafin ya chaje jakarta ya kwashe dukah kudin dake ciki, haɗe da mukullin motar da Alhaji ya bata. j ce ta ga dacewar a shiga a duba ko lafiya tunda yanzu kwanaki uku kenan bata fito ba, kar su je ta mace musu. Nan kuwa matan gidan suka yi ayari aka shiga ɗakin Ladiyo, wata mai ƙaramin ciki ce ta fito ta na faɗin hhhhh "Innalilahi wa'inna ɓhhi'laihi raji'un." Kafin kuwa ta fara amai kamar zata amayar da ƴaƴan cikinta. Nan da nan sauran matan suka fito daga mai mai amai sai bai tofar da yawu abindai ba kyan gani dan haka nayi shahada na shiga domin ganin me wannan mata suka gani suke tushe hanci. Ladiyo ce kwance cikin kashi da fitsari ga wani farin ruwa kamar kumfa dake fitowa daga gabanta. Ba shiri mutanen gida suka bazama neman ƴan uwan Ladiyo da ƙyar dai aka samo Wani kawunta, ya ce zai riƙe ta, ɗakin waje na shago aka ajiye ta dan yace kar ta shigo cikin gidan kar ta hallaka mai yara da mata. MUGUNTA 😈😈😈 By Khairat... Bismillahir rahamnir rahim Page 87-88 Ina Delu? Tabbas ta tabbatar rayuwar nan ba wurin madawwama bace, daga karshe dai sai da wata kungiya ta ɗauki nauyin aikin cire kafarta, dan kuwa Cancer ce mai ƙarfi mai hallaka mutum , da ƙyar aka cire kafar ɗaya Allah ma ya sa ɗayar bata kamu ba. Dan haka nauyin abincinta ya koma kanta, wurin kwana ne kawai yayanta yake bata dan haka sai ta fita ta yi Bara take samun abin ci. "Allah ya baku mu samu, a taimaka dan darajar Annabi masoya Annabi a taimaka ." Abinda take ta nanatawa kenan a bakin hanyar babbar kasuwar garin. Waro idanu ta kuma yi dan ta tabbatar da abinda idanuwanta ke kokarin nuna mata, "Ayaman!!!!" Ta furta da ƙarfi, Ayaman kuwa jin an kira sunanta ya sa ta juya dai-dai in da ta ji maganar . Delu kuwa kuka ta fashe da shi na ban mamaki, rayuwa kenan, tabbas duk wanda yace tukunyar wani baza ta tafasa a toh tabbas ta sa ko dumi baza ta yi ba, a ce Ayaman da suka so ganin ta gaza a rayuwa, wadda suka so rayuwarta ta lalace ta zama wulaƙantacciya sai gashi sune suke a wulaƙance, gashi nan yau tana bara ita kuma Ayaman fess da ita. "Dan Allah Ayaman ki yafe min, dan Allah wallahi na ga izina a kanki, babu kalar tsafin da bamu miki ba, da niyyar lalata rayuwarki, amma cikin ikon Allah sai gashi mune muka ƙare a haka, wallahi Ayaman nayi nadama, tun daga lokacin da muka yi miki baƙin tsafi, dan Allah kiyi haƙuri kuma akwai wani sirrin da nake son gaya miki." Ta ƙarashe cikin kuka mai ban tausayi. Tuni Ayaman da sauran matan masu saurin kuka sun fara sakin hawaye, mutane kuwa suka tsaya kallon ikon Allah. "Ki faɗa min ina jin ki." Ayaman ta faɗa tana sheshsheƙar kuka. " Ladiyo da ni mu muka yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarki, saboda son zuciyarmu, sannan cikin shegen da aka ce kin yi, Yunusa ɗan uwanki ne uban cikin!" Da sauri Ayaman ta juya tana ƙare wa Delu kallo, "Bannn gaaanneee baaa?" "Ehh kwarai abinda kika ji shine , a ranar wani asiri zaku aiwatar a kan auren Ladiyo da Sadeek, dan haka boka yace sai ɗanta ya kwanta da ke sannan auren zai yiwu." Ta numfasa sannan ta cigaba. "A lokacin wani magani aka shaƙa miki, kika fita daga hankalinki, har aka gama abinda aka yi, in kin tuna ai make ya shigo gidan yana tangaɗi." Durkushewa Ayaman ta yi, hawaye masu zafi da matuƙar ciwo suna zubo mata, "Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un, dan Allah Delu mai na muku? Na cutar da ku ne? In zan tuna bayan biyayya da girmamawa da nake muku babu komai, amma kuka cutar da ni cutarwa mafi girma, innalilahi wa'inna i'laihi raji'un ɗan uwana na jini kuka sa ya lalata ni, na haifi cikin shege, babu kalar tsangwama da kyara da ban gani ba, duk kuwa da bayan azabtarwar da na samu daga wurin Ladiyo, wannan abin shi ya yi sanadiyar mutuwar mahaifiyata da mahaifina, ribar mai kuka ci yanzu? Kun cutar da ni, kun cutar da rayuwata, Allah ya isa tsakanina da ku." Daga nan Ayaman ta cigaba da kuka mai ban tausayi, wannan wace kalar rayuwa ce, mai ta tsare wa wannan mutanen? A zabure ta miƙe, "Wallahi wallahi Delu bazan taɓa yafe muku ba, Allah zai bi min hakkina." Sannan taja hannun Tsahare da ta daskare a wurin suka nufi gida. A ranar Ayaman ko abinci bata ci ba, kuka ta yi sosai, dan ji tayi rayuwar gaba ɗaya ta fitar mata daga rai, ga kuma mutuwar mahaifanta da ta dawo sabo. Farouk Cikin ikon Allah yau aka ɗaura auren shi da Halimatu a kan sadaki 200k , an yi shagali sosai sannan aka kai amarya ɗakinta. Washegari sai ga kiran Ammi a kan yazo da sauri, yana zuwa ya tarar da wani babban mutum, sai ga Hajiya a zaune. Gaisawa suka yi, sannan mutumin ya fara gabatar da kansa ga Farouk, "Ni abokin kasuwancin mahaifinka ne, kusan shekaru 20 kenan bana ƙasar sai yanzu da na dawo nake samun labarin rasuwar tasa, Allah Ubangiji ya jikansa da rahama ya sa ya huta." Dukkan su suka amsa da Ameen. Ya cigaba kamar haka " a lokacin mun saka hannun jari a wani kamfanin wayoyi dake China, kuma alhamdulillah kuɗin sun haihu fiye da zato, ina neman yafiyarku na riƙe muku kuɗi da nayi dan bani da labari, a yanzu tunda ga babban ɗansa ai alhamdulillah, dan damƙa amanar kuɗaɗen zuwa wurinsa ya cigaba da juyawa." Nan dai suka cigaba da tattaunawa, saboda yawan kuɗin da Farouk ya gani kasa motsi ya yi, billions!!! Cikin ikon Allah aka raba kuɗin, kowa ya samu rabonsa har ƴan uwansa dake ƙasar waje, nan kuwa ya zuba hannun jari mai yawa a kamfanin Dangote, ya buɗe katafaren supermarket a garin Kano, ya cigaba da running kanfanin da Alhaji ya rasu ya bar musu. Bayan watanni uku. Kuɗi sun zauna a jikinsa, yayin da Halimatu ke ɗauke da ƙaramin ciki dan wata biyu, ta ajiye aikinta Farouk ya bata kuɗi masu kauri ta fara business da su na atamfofi, ai kuwa cikin ƙanƙanin lokaci ta karɓu ta zama hajiyar kanta. Kwatsam wata ranar Lahadi suna cikin shaƙatawa a garden ɗin dake cikin gidan, kasancewar Farouk ya danƙara uban gida mai manyan part guda biyu, ya ɗauko Ammi ta dawo gidan da zama, sai ga mai gadi ya zo da sauri ya durkushe yana kai gaisuwa. Amsa mai suka yi sannan yace "Alhaji Allah ya sa ban yi laifi ba, wata mata ce ta dage sai ta shigo wai tana son ganinka, tace nace ma ko mafi, ko Nafee ne na dai manta Alhaji." Ɗan dagowa Farouk ya yi, yace "Nafee???" Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Halimatu dake kwance a cinyarsa da cikin ta haihuwa yau ko gobe ya mike tana cewa "Nafee ce, tabbas ita ce!!" Da sauri ta mike zata fita Farouk ya riƙo hannunta, suka tafi tare. Amai ne ya kwacewa Halimatu ganin Nafee da ta yi "Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un," Runtse ido Farouk ya yi, ganin wata halitta mara kyan gani, "Wannan halittar fa? Ka fitar da ita!!!!" Ya ƙarashe a ɗan tsawace. "Farouk ni ce, Nafeesa, Nafeen ka ce." Kuma kallon ta ya yi, bayanta ta durkushe alamun ƙusumbu, ga bakinta da ya turo kamar na kare,fatarta duk ta zazzago ta zama wani abin ƙyanƙyami. " Dan Allah Farouk ka yafe min." Ta ƙarashe cikin kuka. "Na san na cutar da kai da Ummu, wallahi sharrin shaidan ne na kashe baiwar Allah da bata ji ba baga gani ba, dan Allah ku yafe min." Nan fa ta fara sumbatu, tana faɗan mugayen abubuwan da ta yi. Halimatu kuwa kuka ta fashe da shi, "Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un, yanzu meye ribar cutar da wani, kin kashe ta yanzu kina tunanin Allah zai bar ki??" "A'a wallahi na tabbata wutar jahannama ce makomata." "Hmm" Farouk kuwa mai gadi ya bawa umarnin fitar da ita daga gidan ya yar da ita a bakin titi. Halimatu tace ba za'a yi haka ba, ta sa aka ɗauko ƴar ƙurƙura aka jibge ta a nan, aka nufi garinsu da ita. Suna zuwa garin kuwa neman duniya babu wanda ya gane ta, da ƙyar aka samu wani mutumi ya gane ta yace zai kai ta wurin mahaifiyarta, wata bola suka nufa, ai kuwa sai ga Ladiyo ta taho da gudu tana wata dariyar hauka, "Gurin boka zan kai ku? Hehehehe zan kaiku wurin boka wlh, bokaaa hhhhhhhh." Haka dai ta rinƙa soki burutsu ga wani ruwa mai wari da yake fitowa daga gabanta. Ajiye Nafee suka yi, mutumin yace "Tabbas ita ce Nafeesa ƴar Ladiyo, a halin yanzu Ladiyo ta haukace hauka take yi tuburan kun ganta nan dai." Jike da jimami mutanen suka juya suka bar wurin. Washegari. Wannan gari ya tashi da wani mummunan masifa, dan kuwa Ladiyo ta mutu a cikin bola, sai da ƙyar aka samu wanda zasu mata wanka, aka yayyaɓa mata likafani, aka kai ta zuwa maƙarbarta. Sai dai wani ikon Allah duk kabarin da aka haƙa sai a ga micizai sun fito manya kuwa, a haka sai da aka haƙa kabari 5 amma duk same micizai ne suke fitowa, a haka aka haƙura aka zo za'a sa ta, amma sai dai me ƙasa ta ƙi karbanta, da an saka gawar Ladiyo sai ƙasa ta bulluƙo da ita, aka yi aka yi amma ƙasa ta ƙi ƙarbanta, da aka dage da addu'a da kuma nema mata yafi sannan aka samu kasa ta karɓe ta ga kuma micizan da suka nannaɗe ta suna saranta ta ko'ina. Kowa kuwa a garin banda faɗan munanan abubuwa a kan Ladiyo babu abinda suke, har da masu tsine mata sanadiyyar cutarwar da ta musu. *Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un 😭, ƴan uwa mu hankalta, duniyar nan ba madawwama bace wata rana dole zamu mutu mu bar ta, mene amfanin bin bokaye, wani la'ananne fasiƙi, gashi nan dai ina fatan mutuwar Ladiyo ta zamo izina a gare mu, Allah ya kyauta* Ta ɓangaren Delu kuwa tun da ta samu labarin mutuwar Ladiyo da kalar azabar da aka gani, tuni ta mayar da hankalinta wurin neman yafiyar mutane, wasu su ce sun yafe wasu kuwa suce basu yafe ba, a haka dai ta mai da hankali wurin neman yafiyar Allah, istigfhari baya wuce bakinta, sallah ma a lokaci. Bokan kan tudu Yana cikin tsafinsa wani irin ciwon kai ya dirar masa, tuni ya fara ƙaƙƙafewa kamar mai farfaɗiya, ga wata farar kumfa da take fitowa daga bakinsa, babu mai taimako haka ya mutu a wulaƙance a wurin tsafinsa. Yana mutuwa kuwa kayan tsafin suka fara jijjiga, duk suka rufto masa a kai, ga wani baƙi da ya yi nan take. Farouk& Halimatu Rayuwa suke gudanarwa mai cike da tsafta da nutsuwa, Halimatu ta haifi ƴan biyu mace da namiji, duk aka sa musu sunan mahaifan Farouk, sannan gwaggo ta koma Kaduna da zama wurin danta wato gidan su halima. Kyawawan yara ke ta wasan su a tsakar gidan, sai ga motar Farouk ta shigo cikin gidan tuni suka nufi wurin suna kiran "Daddy! Daddy!". Robar ice cream ya miƙa musu ai kuwa tuni suka nufi part ɗin Ammi suna nuna mata, bin su yayi ya yiwa Ammi sannu da gida sannan ya wuce part ɗin su ya bar twins a wurinta A parlor ya tarar da Halimatu tana sa turaren wuta, murmushi ta sakar mai sannan ta nufe sa ta rungume sa, kiss ya sakar mata a wuya yana shaƙar humrarta mai daɗin gaske. "Baby nah." Ya faɗa yana jan dogon numfashi, cakk ya ɗauke ta, sannan ya raɗa mata a kunne "Muje a yi wa twins ƙani." Ɗakinsa suka shiga suna dariya ni kuma na fita daga gidan ina musu fatan alkhairi. Ayaman. Bayan ta hakurƙurtar da zuciyarta ta cigaba da rayuwa a gidan su Tsahare, cikin ikon Allah mai kamfanin Mudassir and brothers wato Alhaji Mudassir ya ganta a lokacin da suka je siyan atamfofi a kasuwa, ai kuwa tuni ya bi ta. Ba'a ɗau lokaci ba aka sha biki dan kuwa ita ma Ayaman ya kwanta mata, biki a ka yi gagarumi wanda ya girgiza garin Kano. Ga lefe da aka danƙara mata kusan akwati 50 tare da kyautar mota. Bayan wasu shekaru... Zaman lafiya ya wanzu, Ayaman ta haifi yara biyar, akwai ƴan uku gabaɗaya maza, sai kuma mace sai wani namijin, suna rayuwa a danƙareren gidansu daga G.R.A. (Ya kamata ni da masu karatu mu je mu ga gidan dan faɗar tsaruwarsa ɓata baki ne🤭😁) Cikin falon na shiga ai kuwa na hango Hajiya Ayaman zaune a kan cinyar Alhaji Mudassir, ƙaramin yaron sai kuka yake wai zai hau cinyar Maama( Ayaman) ai kuwa sai dariya suke mai. Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Dukkan yabo su tabbata ga Allah Ubangijin talikai, ina mai addu'ar duk wani darasi da za'a ɗauka a cikin littafin nan ya zama abu mai kyau, abinda na rubuta ba daidai ba kuma Allah ya yafe min, ina godiya sosai ga masu karantawa, sharing da masu comment ku sani ku na daban ne a zuciyata🥹🤍 ina godiya Allah ya saka da alkhairi. Bye, by KHAIRAT SHALELEN JAJIRTATTU ✍️ 🎉