*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA MAI MUHIMMANCI ⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. 📢 SANARWA GA MASOYAN KARATU 📢 Daga yau, za a fara turo sabon littafina: 🔥 MASARAUTAR ALHAMRA 🔥 📌 COMMENT SECTION an tanada shi ne domin: sharhi ra’ayi tattaunawa akan littafin kawai ❌ Ba a yarda: turo link talla ko turo wani littafi a comment section ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💬 Comment Section Group: https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 🎥 YouTube (Audio & Reading): https://www.youtube.com/@AsmeetahNovel 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* A tsakiyar wannan ƙaton almara, an gina babban fadar sarki. Ginin da kansa wata shaida ce ta mulki, komai an yi shi ne don nuna girman iko... Cikin wannan Fada, a babban ɗakin mulki, an ajiye kujerar sarauta wanda sai da aka narkar da dubban Ton na Zinare kafin aka gina ta, tana haskaka dukkan ɗakin da haske mai yalwa. A kan wannan Kujerar izzah, Sarki NOURDEEN yake zaune. Yana sanye da rigar sarakuna mai nauyi, wanda aka zana masa Gwal mai yawa a jiki. Amma abin da zai sanya ko wane mutum ya daskare a mazauninsa shine kansa da jikinsa ba siffar mutane yake ɗauke da ita ba. Tsayayyen mutum ne, amma kansa da fuskarsa irin na Basaraken Zaki ne!.. Gashin zakin ya rufe wuyansa da ƙirjinsa, yana kwance har zuwa kan rigarsa. Ya sanya hular sarauta mai ƙayatarwa a kansa, wanda ya ƙara bayyana girman Ikon Sa na halitta. Wannan siffar zaki ba halitta ba ce, tsafin Iko ne mai zurfi da ya yi domin ya tabbatar wa duniya cewa, Shi ba mutum bane, shi ne MULKI!. Wannan tsafi an yi shi ne don ya dasa tsoro da fargaba a cikin zukatan dukkan mutanen Alhamra City da ma duniya gaba ɗaya. Ba wanda ya taɓa sanin Ainahin kamannin Sarki... Ba mai izzar da ya isa ya haɗa ido huɗu da Zaki Nourdeen. Idan ka yi kuskuren haɗa ido, ba za ka sake yin bacci cikin daɗin rai ba. Saboda kwayar idanunsa ba ta mutane ba ne, haske-haske take fitarwa wanda ke iya kama ruhin mutum mai laifi cikin sauƙi. Sarki Nourdeen yana zaune cikin wannan izzah mai kisa, kuma a gefensa akwai Zabga-Zabga Fadawa masu ƙarfin tsoratarwa. Rundunar Masarautar an raba ta zuwa Tsare-Tsare masu Muhimmanci.. Rundunan Yaƙi.. Waɗannan su ne Jikin Sarki na Waje, ƙarfaffu waɗanda ke shirye a ko wane lokaci Sarki ya yanke shawarar fita yaƙi da duniya... Bodyguards. Waɗannan su ne ƙashin-Bayan Sarki, aikinsu shine tsare cikin masarauta da kuma kiyaye sirrin Fada... Security. Su ne jinin da ke gudana a masarautar. Kowannensu da aikinsa. Wasu a cikin Share-Sharen ƙaton Masarauta suke, wasu suna kula da Flowowi, wasu kuma suna kula da kayan alatu na Fada. Bayi Mata, waɗanda suke kula da Girke-Girke da Wanke-Wanke da sauran Ayyuka masu dama. A masarauta mai girma irin Alhamra, aiki baya ƙarewa, kuma kowa yana da matsayin sa wanda ba a canzawa... ✨✨✨ A yau ne Sarki Nourdeen yake zaune cikin izzah. Yana tare da manyan masu kuɗi (Billionaires) na Alhamra. Duk da kuɗin su, suna zaune ne akan ƙananun kujeru na girmamawa, kansu a durƙushe ƙasa kamar yadda ya dace da darajar Sarki Zaki. Taron ya shafi kasuwancin Gine-ginen zamani ne da kuma yadda za a ƙara yawan Kuɗin masarautar... Wani daga cikin masu kuɗin, Alhaji Hadi wanda ya fi shahara da kwaɗayi da rashin tausayi, ya dafa hannu a jikin ƙaramar Kujerar sa ya ce, "Ya mai martaba, sarki mai Izzah! Mun shigo da wata Arkalla domin tsarin ci gaba ya tafi dai-dai, dole ne mu ƙara haraji a kan talakawa da suke zama a titin ƙasa. Wannan zai tilasta musu su sayar mana da filayen su, sannan mu gina ƙarin Gine-ginen Alatu a wurin. Za mu cutar da su kaɗan, amma hakan zai inganta mulkin ka." Sarki Nourdeen ya jinjina kansa kaɗan, wanda ya yi kama da rakaɗa na Zaki (Lion’s nod). Fuskarsa ta ƙara murtuƙewa har ta bada asalin tsoro ga kowa.. Sarki Nourdeen, duk da girman kai da izzar da ke dasa tsoro a zuciyar kowa, bai goyi bayan ZALUNCI ba. Ya ɗaga hannun Zakin sa mai nauyi, ya ajiye a kan kujerar zinarensa. Muryarsa mai ƙarfi da zurfi ta ratsa dukkan ɗakin... "Ku dawo da wannan Arƙalla. Alhamra ba ta buƙatar ƙarin kuɗi da aka samu ta hanyar ZALUNCI. ZALUNCI ga talakawa shine RAUNI ga Mulki na. Ba zan goyi bayan hakan ba. Ku tashi, ku sake kawo shawara mai tsafta."... Alhaji Hadi da sauran masu kuɗin suka tashi cikin sanyin jiki, suka durƙusa ƙasa suna ba da haƙuri... A cikin babban masarautar Alhamra da ke cike da ƙarfe da zinare, wata yarinya siririya kyakkyawa da ba za ta wuce shekara goma sha shida 16 ba. Ita ce Gimbiya FIRDOS, wacce aka fi sani da Chingching.. Chingching ta fito ne daga tsararren filin wasan ƙwallo da ke cikin Area part ɗinta wanda ba nisa sosai tsakani da babban fadar sarki.... Tana sanye da gajeren wando na ƙwallon ƙafa tana wasa da ƙwallo a hannunta, alamun ta gama wasan ne. Duk da sanyin masarautar, jikinta duk gumi ne wanda ke nuna ƙarfin hali da rashin natsuwa da take da shi.. Security masu tsaron part ɗinta ne suka biyo ta da gudu suna son dakatar da ita, domin in har akayi garajen barin gimbiya ta fito sararin masarauta to akwai tashin hankali... Chingching ganin anason dakatar da ita kafin ta isa fadar sarki yasa ta ƙara wa manta gudu, tana gudu tana buga ball ɗinta, sumar gashinta na tsalle yana faɗa wa kan gadon bayanta.. Kasancewar ta ƴar shafal da ita yasa bata jin nauyin jikinta da gudun da take kuma ta saba motsa jiki.. Bodyguards na area masarauta ganinta yasa suka rufa bayanta da gudu har sai da ta shiga Area fadar Sarki, tana ci gaba da buga ƙwallon a bakin ƙofa. Ba ta damu da Doka ba... A lokacin da Chingching ta nufi cikin babban ɗakin mulki, ta yi kucuɓus da masu Kuɗin da suke shirin fita. Su suna guduwa ne daga cikin fadar saboda harzukan Sarki Zaki da suka gani... Cikin sauri da rashin sani mutanen suka ture ta a wajen ƙofa. Tangal-Tangal tayi da niyyar faɗuwa ƙasa. A firgice, wasu mata ma'aikata suka yi saurin riƙo ta. Sun san cewa idan har Gimbiya ta taɓa ƙasa, to tabbas Sarki Zaki zai ɗauki hukunci mai tsanani.. Mutanen jikinsu na rawa saboda tsoro, suna ba da haƙuri ga ma'aikatan da Gimbiya. Sarki Nourdeen ya miƙe tsaye a kan kujerarsa a fusace, fushin Zaki ya bayyana fili! Ganin ƙaramar Gimbiyarsa, wacce ya fi so fiye da komai, an ture ta. A zabure, masu kuɗin suka durƙusa ƙasa gabansa, suna ba Sarki haƙuri cikin firgici. Cikin shagwaɓa mai tsanani ta nufi Sarki, tana faɗin. "Daaaad..." Ta kwantar da kanta a kan faɗaɗɗen ƙirjin Zakin sa, wanda ke da tsafin gashi mai laushi. Cikin sanyin murya da shagwaɓa ta ce "Ka rabu da su, by mistake ne..." Muryar Sarki, wacce ta kasance cikin tsawa da kaifi ga masu Kuɗin, ta zama mai laushi da natsuwa a yayin da yake magana.. "Ku durƙusa a gaban Gimbiyata, ku ba ta haƙuri," Zaki Nourdeen ya ce. "Amma kada hannunku ya gogi fatar jikinta. Domin ita ɗin Gwal ce mai mahimmanci a rayuwata..." A ruɗe masu kuɗin suka durƙusa wa Chingching suka ba ta haƙuri. Cikin shagwaɓa ta musamman, ta ce "Uhm! Uhmm!! Uhm! Na yafe muku..." Cikin farin ciki da mamaki suka fara yin godiya. Daga nan Sarki ya sallame su. Bayan masu kuɗin sun tafi, Sarki ya fara huci saboda fushin da ya danne. Ya umarci a ƙira masa waɗanda suke kula da Chingching, wato ma'aikatan part ɗinta. Ya kalli Chingching, yana gyara mata gashin gaban goshinta da hannun Zakin sa. Haka yake goge mata zufar goshinta zuwa wuyanta tare da faɗin. "Ina kika shiga kika yi zufa haka?" Chingching tana shagwaɓar da ta saba, ta ce "Uhm! Uhmm!! Dadd, ƙwallon ƙafa nayi..." Sarki ya sake tambaya "Ke da su wa?" Ta sunkuyar da kanta kaɗan. "Uhm uhmm Dadd, ni kaɗai. Ba ka hanani shiga cikin bayi ba." Muryar Sarki ta sake yin ƙarfi ya ce, "Tabbas na hanaki! Domin duk sanda na ganki da su, sai na hukunta su. Abin da ke da daraja baya wulakantuwa." Dai-dai lokacin, waɗanda suke kula da Chingching suka shigo da sallama, kansu a ƙasa suka durƙusa cikin girmamawa. Sarki ya dube su cikin fushi ya ce "Meyasa kuka bar Mamana ta fito daga yankinta? Kun karya min dokata! Domin a tsarina, gimbiyoyina ba za su taɓa fitowa cikin Masarauta ba tare da wani dalili ba..." Altine, wacce ke asalin kula da ita, tana rawar jiki ta ce "Ranka ya daɗe, a gafarce ni. Ita ta dage akan dole sai ta fito. To bamu da hurumin hanata, domin hakan zai iya jawo mana matsala idan bamu mata abinda take so ba..." Sarki ya daka musu wani irin gigitaccen tsawa har sai da suka zabura da niyyar guduwa amma suka dakata! "Dole a bi umarnina, amma kuma dole ku mata abin da take so! Shin meye abinda babu a part ɗinta? Bana buƙatar fuskar Gimbiyata ya zamo madubi ga ko wani dabba." Altine wacce take rawar jiki har yanzu ta ce "Akwai komai a bangarenta, komai akwai. Tafi son na outside ne. Amma Allah ya taimaki ran Sarki, bazamu ƙara wani kuskure ba..." Ita kuma Chingching tana ta wasa da gashin Zakin Sarki wanda ya zamo kamar gemu. Sai murɗawa take tana dariya. Duk tsawar da Sarki yake yi, a kunnen Chingching murya ne mai sanyi da laushi. Ya sanyaya muryarsa a kunnenta, yayin da muryarsa ta zama kibiya a kunnen kuyangensa. Bayan ya gama huci, ya riƙo hannun Chingching ya ce "Ku kaita part ɗinta, ku yi mata wanka." Chingching ta kalli siffar Zakin mahaifinta, ta tambaya "Dadd, meyasa kake canza kamanni zuwa Zaki?" Sarki ya kalleta da Idanuwansa masu haske ya ce "Mamana, a duk lokacin da na kasance da ku kaɗai Gimbiyoyina, ni cikakken mutum ne. Amma a gaban idon mutane na, ni Zaki ne kamar haka." Chingching tayi murmushi tana kallon mahaifinta, Altine ta riƙo hannunta sannan suka tafi. A saman doki aka ɗaura ta aka nufi da ita can part ɗinta wanda ta kasance ita kaɗai sai masu kula da ita.. A hankali ake tafe da ita daga saman dokin. Nan aka shige da ita cikin wani tsararren part.. Yanki ne wanda ke nunawa kowa cewa Ita ce Gwal mai mahimmanci! Part ɗinta wani irin gini ne mai ƙayatarwa wanda ya yi kama da dreaming part kamar an tsamo shi daga littafin Almara na Gine-gine. A can gefe, akwai kayan wasa masu tsada.. Ƙayataccen filin ƙwallon ƙafa da handball wanda ta fito daga ciki... Sai dai, dole sai an hau saman Upstairs wanda yake da tsayin da ba kowa zai iya juran hawa koda yaushe ba inba wanda ya saba yau da kullum ba, koda wanda ya saba ma sai ƙafafunsa sunyi ciwo kafin a shiga Babban Falonta... Shiyasa ma'aikatan ta kullum a cikin shan maganin ciwon jiki suke. Abun mamaki ita ƙaramar gimbiyar yanda kasan ta samu wurin wasa haka ta mayar da matakalan, tana jumping tana wasa kamar wacce take exercise, nan danan ta haura kamar biri... Daƙyar suka ƙaraso suka isketa a falo. Falon cike yake da kayayyakin alatu ga ƙaton plasman a manne a jikin bango, Fridges masu tsada, da Flowowi. Komai yana da tsari da daraja... A saman can ne bedroom ɗinta yake wanda saika sake hawa wani benin.. Gado ne katafaren gado wanda aka yi masa zane da fararen kayan alatu, wanda ya dace da Gimbiya....Cikin wannan ɗakin kwana ne wani keɓaɓɓen ɗakin kayayyakin sakawa da ke cike da tsararrun kaya na Sarauta yake... Sai dai cikin bedroom ɗinta ba kowa ke zuwa ba sai Uwar ɗakinta wato Altine. Chingching ta shiga bedroom ɗinta cikin kasala bayan gajiyar ƙwallo. Ta tsaya tana riƙe da kunkumi idonta akan Altine wacce ta shigo... "Uma Altine! Kin ga gumin nan? Na gaji sosai fa! Yau ƙwallon nan ta gajiyar da ni, kuma Dadd ya ce kar na sake fita, amma ni ina son outside ɗin nan!" Altine tana rarrashinta ta ce, "ki yi haƙuri ki cire saina miki wankan ko..." Ɗan tsaki ta ja cikin damuwa da gajiyar da tayi cikin hanzari, ta cire kayan jikinta wanda gumi ya jika, sannan ta ɗaura towel mai laushi ta shige bathroom.. Altine ne ta ɗauki kayan da ta cire a ƙasi don kai su washing machine da ake wanke kayanta... Ita kuwa Chingching tana shiga Bathroom ta shige cikin Bathtub mai girma ta zauna.. Bathroom ɗin ba ƙaramin ɗaki ba ne, tsaruwarsa sai ta sa ka zuba abinci a ƙasin wurin ka ci saboda tsaftar wurin da tsarinsa. Wani irin ƙamshi mai daɗi da tsada ne yake fita. Tiles ɗin ƙasan ma ɗumi ne da shi a yayin da kake takawa... Bayan mintuna kaɗan Altine mai kula da ita ta shigo ciki domin taya ta wanka, domin har yanzu Chingching bata iya wanka da kanta ba saboda gata da ta saba samu.. Wani irin kallo Chingching ta yi mata cikin shagwaɓa ta ce, "Uma Altine, kin san fa na gaji, kuma kike ƙara gajiyar da ni, don kawai kin ga ina da kyau shine zaki bar ni haka..." Altine murmushi tayi sannan ta ce, "Ƴar uma yau kuma me nayi?..." Chingching tana turo baki ta ce, "tin ɗazu inata jira, ina ta jira a cikin ruwan zafi..." "To ki yi haƙuri Ching Ching..." Murmushi Chingching tayi domin tana jin daɗin sunan nan especially idan aka furta cikin launi, sunan ya samo asali ne daga tin tana ƙarama ƴar 2years ta ji ana ƙiran mahaifinta da King, itama tace sunanta Ching ma'ana King.. Anan ta samo Chingching.... Da ɗan ƙaramin part a ƙirjinta, Altine ta fara mata wanka sai ƴan ƙananun nonuwa a bayyane... Ita kuma tana Pressing ƙaton wayarta ta zamani wanda ke da tsadar gaske da aka kawo mata daga ƙasar Turai... Ba komai ne a cikin wayan ba domin babu sim sai gema–gemai da finafinai.. Tana danna waya, tana complain, "Wash! Wannan ruwan ya yi zafi! Uma Altine, karki murzani sosai mana, kin san fatata ba irin taku ba ce, ni fa Gwal ce kamar yadda Dadd ya ce!" Altine tana murmushi tana mata, ta san cewa Chingching surutunta baya ƙarewa. Bayan an gama mata wanka da turarukan da ƙamshinsu zai iya sumar da mutum, aka goge mata jikinta da white towel mai laushi tare da fefesa mata turaruka masu ƙamshi mai ƙarfin gaske. Aka sanya mata tsararrun kayanta na Alhurma mai tsadar gaske wanda ya nuna asalinta na Gimbiyar Sarauta. Tana zaune a gaban mirror da fitilu masu haske da suke haskawa, ana tsara mata Make-up da kuma salon gashi mai kayatarwa. Tana kallon kwalliyar da Altine ke mata, tana gyara mata daki-daki.. "A'ahhh Uma Altine, ni wannan kwalliyar bai mun kyau ba, a goge a sake yin wani..." Anyi hakan ya kai sau huɗu, a tsara kwalliya a sake gogewa kullum a cikin haka ake.. Daga ƙarshe ne Altine ta ce, "idan aka sake goge wa ai fuskar zata ɓaci..." Tana turo baki ta ce, "Allah? To a bar shi amma nasan ban yi kyau ba..." "Kin yi kyau mana gimbiyata..." "Uhm! Uma Altine kenan, idan a mijinki ne zaki tsaya ki tsara masa kwalliya a kan ki, nine bakya tsaya wa ki mun mai kyau..." Uma Altine ba abin da take sai murmushi domin ta san halin, abun complain baya mata kaɗan.. Bayan an kammala kwalliya. Ba ƙaramin kyau tayi ba ta bugawa a jarida, Altine ta kalle ta da murmushi na gaske sannan ta ce, "Gimbiya Chingching ta fito tayi kyau tsaf! Yanzu kuma mai ake buƙata? Abinci gashi can an shirya miki kala-kala, sai wanda kika zaɓa. Ko kuma kwanciya za ki yi ki sha baccin ki? Ko dai kallo za ki yi? Duk fim ɗin da kike so akwai. Muna sauraron Gimbiya..." Chingching tayi murmushi mai ɗauke da dabara, tana gyara sakun makeken gilashinta na Gwal. Ta ce da mafi girman shagwaɓar ta... Mu sauƙa falo tukun... Hakan kuwa akayi, a falon suka tarar da sauran ma'aikata mata ko wacce da uniform ɗinta na aiki.. Chingching tana tsaye duk ta ƙare su da kallo sannan ta ce, "Abin da nake so yanzu shine inason ganin Gimbiya Auntyna ta musamman!" Altine da sauran ma'aikatan duk suka zaro ido a ruɗe. Wani irin haɗiyar yawu suka yi, a tsorace suka ce. "Dan Allah Gimbiya, kiyi mana afuwa, ki zaɓi abin da kike so bayan wannan!" Altine ta ci gaba da faɗi da murya mai rawa "Kin dai san wannan dokar takun a rubuce take. Cewar a shekara sau uku ne za ku na haɗuwa da juna a Babban Fadar Mai Martaba. Yanzu idan yaji labarin mun karya doka, dole za'a hukunta mu..." Chingching ta ɗan turo baki irin sakalan yaran nan ta ce, "Ai naga, naga, bazai sani ba. Kawai ku kaini a ɓoye..." Altine, wacce dattijuwa ce a tsakaninsu, ta yi saurin durƙusawa ƙasa, tana roƙon Chingching da ta bar wannan batun. Hawaye ya fara zuba a idanunta. Chingching ganin yanda Altine take zubar da hawaye ne yasa ta jin tausayinta. Ta ce. "Uma Altine, ki daina kuka. To, to, to, ni na haƙura maaa..." An ɗan rarrashi Chingching, ta ci abinci duk da kaɗan take ci, amma ko wani kalar abinci sai tayi test ɗinsa..ita ko a Film daga kalar abinci sai tace a mata irinsa, da haka ne kwanakin baya taga wani kalar abinci a Chinese film tace nan duniya sai taci irinsa, ko da aka mata taci ta rinƙa amai kamar hanjin cikinta zai fita har sai da likita ya duba ta... A ranar kuwa waɗanda suka mata girkin basu sake kwana a cikin masarautar ba bayan hukuncin da aka yi musu... Sai da ta kammala ciye–ciyenta sannan ta kalli Altine ta ce. "Uma Altine, inaso zanyi Sallah, sannan nayi bacci..." Altine tana murmushi ta ce, "mu je na rakaki bedroom ɗinki to..." Chingching ta ɗan turo baki ta ce, "ina jin bacci sosai, don haka bazan iya haurawa sama ba..." Altine ta san kan kwanan zancen, indai ta fara da haka to goyo take so... Sunkuya wa Altine tayi sannan Chingching ta ɗale baya tare da kwantar da kanta.. Altine ta nufi saman bedroom da ita, tana zuwa ta sauƙe ta sannan ta ce, "Kin ce sai kin fara yin Sallah ko?..." Jinjina kai Chingching tayi tana lumshe ido.. Altine ta shimfiɗa mata sallaya, ta zaro mata hijab daga cikin jerin hijabanta na sallah dake kusa, saɓanin sauran kayanta dake can other side na bedroom... Altine ta san dokar nan. Idan har Gimbiya za ta yi sallah sannan ta yi bacci, to fita take ta barta ita kaɗai a ɗaki. Chingching ta tsaida sallah, sannan tayi addu'o'in ta cikin tsarki. Ta kwanta a kan sallaya har bacci ya ɗauke ta a wurin, daman a hannu take... Bayan wasu mintuna, Altine ta shigo ta same ta a kwance a ƙasan sallaya. Kirjinta ne ya buga. Da gudu ta shigo ta ɗauke ta tare da ɗora ta kan katafaren gadonta wanda idan ka kwanta akai za ka sa ran lotse wa ne tsabar laushi... An kashe mata hasken ɗaki aka bar mata green lamp light mai natsuwa.... ✨✨✨✨ Cikin dare misalin ƙarfe 1:00am, Chingching ta fara mafarkin da ta saba yi kullum a dalilin bege da take yi wa 'yar uwarta. "Aunty! Aunty!! Aunty!!! Ki zo Aunty! Wayyo Aunty..." Cikin ƙanƙanin lokaci, sai ta ji an rufe mata baki da wani irin sanyayyen hannu mai laushin gaske kamar sarauniyar audiga. A hankali, Chingching ta ɗan buɗe lumshashshun idanuwanta wanda bacci yake faman yaƙi da su. Ta sauƙar da kallonta akan kyakkyawan idanun wacce ta rufe mata baki... Idanuwanta yanda kasan an tsaga su, gasu manya-manya, gasu farare tass. Eyelashes zara-zara, ga wasu cikakkun gashin girarta a kwance wanda suka kusan haɗewa biyu. Hasken fatarta fari ne tass irin farin Larabawa. Amma sai dai, ba'a ganin fuskarta complete domin a rufe yake da kyalle mai sheƙi. Sai iya dara-daran idanuwanta da gashin girarta ake gani. Ta kewaye gashinta da fuskar gaba ɗaya cikin sirri mai zurfi. Haka take kallon cikin idanuwan Chingching da nata. Chingching a hankali ta furta: "Aunty..." Daga nan ta lumshe idanuwanta gaba ɗaya, bacci ya ƙara ɗaukan ta cikin natsuwa... Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a fuskar wacce Chingching ta ƙira da Aunty. Haka take kallon fuskarta tana bacci, a yayin da take shafa mata sumar gashinta tana hawaye tana mata addu'o'i kamar yanda ta saba zuwa cikin dare ta ga 'yar ƙanwarta. Domin tasan a wannan lokacin take mafarkin bege da kewa. Tana zaune, tana taya Chingching zama har tsawon awanni. Idonta yana kan ƙanwarta da aka hana ta gani. Sai dab da asuba kafin a ankara, ta tashi, ta bi ɓoyayyen hanyarta ta tafi cikin sirri mai zurfi zuwa Part ɗinta..... ```TOH MA SHA ALLAH ABOKAI, MASOYA, ƳAN UWA.``` ```ALLAH YASA WANNAN FARKON PAGE ƊIN SABON BOOK ƊIN MU YA NISHAƊANTAR....``` ```YANDA ZAN GANE CEWA KUN JI DAƊIN BOOK ƊIN TO NAGA COMMENTS, LIKES, SHARES...``` ```WAƊANDA BASU YI FOLLOWING ƊINA A CHANNEL BA YANZU DAMANE TA HANYAR KARATU A SAUƘAƘE, KODA AN WUCE KI BAZAKI RASA YANDA KIKA TSAYA BA, DOMIN CHANNEL DUNIYA NE...``` ```WAƊANDA SUKE SON YIN COMMENTS SU FAƊI ABUNDA KE RANSU AKAN LITTAFIN TO KUYI JOINING GROUP.. KADA KU BARI AYI BA KU...``` *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA MAI MUHIMMANCI ⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💬 Comment Section Group: https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 🎥 YouTube (Audio & Reading): https://www.youtube.com/@AsmeetahNovel 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bangaren Gimbiya Ayat wuri ne da aka gina shi da zurfin ilimin fasahar zamani. Baya ga kwarjinin sa, part ɗin yana da girma da faɗin da mutum zai iya ɓace wa a cikinsa idan bai saba da hargitsatstsen tsarin sa ba. Domin isa zuwa inda Ayat take, dole ne ka hau wasu tsalallekun benaye masu nisan gaske. Saboda girman wannan nisan, akwai na’urar nan ta zamani mai tafiya da kanta wato escalator wadda take ɗaukar ma’aikata da dakarun tsaro zuwa can sama. Bayan dogon benin da kowa ya sani, akwai wata Hanyar Sirri ta musamman wadda Gimbiya Ayat kaɗai ta san da ita. Wannan hanya tana amfani ne da wani babban na'ura mai daukar mutum elevator wanda aka ɓoye shi a wani guri da idon dan Adam ba zai iya gani ba. Idan zai yi sama, wannan elevator ɗin yana tsayawa ne a wani ɗaki na musamman. Kana buɗe ƙofar ɗakin nan, zaka tsinci kanka a tsakiyar babban ɗakin kwanciyar Gimbiya Ayat. Idan kuma ƙasa mutum zai yo, dole ne ya shiga ta wannan ɓoyayyen ɗakin dake cikin bedroom ɗinta, inda elevator ɗin zai lula da shi har zuwa ƙarƙashin ƙasa. A can ƙarƙashin ƙasa, akwai wani katafaren gidan ƙasa mai ɗauke da doguwar hanya. Wannan hanya tana miƙewa ne har zuwa wajen yankin Gimbiya Ayat, inda zata fitar da mutum ta bayan filin masarauta, daidai inda Garden Area yake. Ta ƙarƙashin ƙasar, akwai wasu matakala da mutum zai hau, sannan ya tura murfin ramin ya fito. Wannan wurin yana ɓoye ne a cikin ciyayi da furannin lambun masarauta, ta yadda babu wanda zai taɓa zargin cewa akwai rami a wurin. Da zarar mutum ya fito, zai tsinci kansa a cikin lambu, daga nan kuma sai ya samu hanyar da zata kai shi babban filin masarauta. Wannan ginin an ƙera shi ne da dukkan alamu domin tserewa daga barazana kamar gobara, harin maƙiya, ko ɓarayin ƴan fashi. Wannan hanyar shine hanyar sirrin Gimbiya Ayat, tanan take fita daga part ɗinta ba tare da kowa ya sani ba, saita nufi hanyar part ɗin ƙaramar ƙanwarta Chingching... Sannan ta wannan hanyar take komawa part ɗinta dake can sama cikin lafiya... Wannan wurin yana nuna Matsayinta na Gimbiya da kuma Izzar da take ɗauke da ita. Iskar da take shiga Part ɗin Ayat mai tsabta ce kuma sanyi mai ɗorewa.... ​Muryar babban fada da hayaniyar ma'aikata ba sa taɓa kaiwa part ɗin Ayat. A nan ne shuru da natsuwa suke mulki. ​AYAT tana ɗaya daga cikin gimbiya ta musamman a cikin su biyar... ​Yanzu, misalin ƙarfe 5:00 na Asuba, bayan ta dawo daga aikin sirri na ziyartar ƙanwarta, tana zaune a cikin babban falon ta. Falon yana cike da kayayyakin larabawa na zamani.. ​Tana zaune a kan doguwar kujerar larabawa wacce aka yi mata zane da zinare. Tana sanye da Kayayyakin Sarauta masu daraja, amma abin da ya zama Alamar ta shi ne.... ​Fuskarta a rufe take koda yaushe! ​Wannan ba dabi'a ba ce, dokar sirri ce. Wani kyakkyawan mayafi ne wanda aka ɗinka da zaren azurfa ke rufe daga idanunta zuwa ƙasa... Wannan ya sa Idanuwanta suka zama abin tsoro da kuma abin sha'awa.. Waɗannan ne dara-daran idanuwan da Chingching ta gani a daren jiya... ​Sarki Nourdeen, mai izzar Zaki, ya daina ganin fuskar Gimbiya Ayat tun tana ƴar shekara biyar. Wannan ya faru ne sakamakon wani al'amari mai girman gaske da ya faru a shekarun baya, wanda ya shafi sirrin mulki da kuma ƙaddara. A masarautar, an cika ɓoye wannan al'amari, wanda hakan ya sa Ayat ta zama alamar sirri a idon kowa... ​Tana zaune, jikin ta ya gaji saboda karya dokar da take yi kusan kowane dare don ƙaunar ƙanwarta. A hannunta ko tana riƙe da ƙaramin akwati da aka yi masa zane na tarihi, wanda a cikinsa take adana hotuna na Firdos da kuma hoton wanda ta rasa tin tana ƙarama... ​Ayat ta ɗauki mulki a matsayin nauyin ƙaddara, ba walwala ba. Tana ganin tsaurin kan mahaifinta zai iya rushe masarautar Alhamra idan har bai sami magaji ba.... ​Ta tashi, ta nufo wani babban mirror mai haske, ta kalli idanuwanta a ciki. Cike da tausayin kanta .. ​"Kina karya doka, Gimbiya Ayat! Kin saɓa wa umarnin mahaifinki wanda ya fi ƙaunar rayuwarki fiye da kowa. Amma idan har wannan dokar tana cutar da ruhin ƙanwarki, to dole ne ki zaɓi tsakanin Doka da ƙaddara," Ta faɗa a cikin muryar larabci mai ƙarfi, mai shiga zuciya. Ayat zama tayi bayan ta gama kallon kanta a jikin mirror duk da fuskar a rufe yake, a kan tsararren Sofa na falonta ta zauna. Duk da kayan alatu na sarauta da ke kewaye da ita daga kayayyakin fruits masu tsada a kan ƙaramin table ɗin gilashi zuwa Zane-zanen Azirfa a jikin falon amma damuwar duniya duk ya bi ya ishe ta. ​Tana zaune, jikinta a lulluɓe da mayafinta na rufe fuska, amma a cikin idanunta akwai wani zargi da tunanin neman mafita da ke ci gaba da cin zuciyarta. ​Tana tunanin mafitar da za ta samu domin gujewa wannan tsatstsauran dokar da aka kafa musu tun tsawon shekaru, tun suna yara. Zama wuri ɗaya a cikin part ɗin ya bi ya ishe ta, amma babban abin da yake tasar mata da hankali shi ne dokar ganin 'yan uwa mata sau uku kawai a shekara. ​Cikin zuciyarta, ta fara magana da kanta, muryarta mai ƙarfi da zurfi yana bayyana rikicin zuci, ​"Wannan al'amarin yana damu na. Shin ya zanyi? Meye mafita? Shin a haka zamu ƙare rayuwarmu? Babu soyayya, babu ƙawaye! Babu zuwa makaranta sai dai a koya mana a cikin ɗakunan mu. Wayyo kaico na! Wayyo 'Yar ƙanwata Firdos wacce bata san koda mahaifiyarta ba ma sai ni. Tana zaman kadaici. A shekara sau uku zan rinƙa ganinta? Bazai taɓa yiwuwa ba! Impossible!" ​Sai ga wasu zafafan hawaye suna zubo mata daga gefen kyallen mayafinta wanda ya rufe fuskarta. Hawayen na nuna tausayi ga ƙanwarta, amma kuma suna tuna mata wani abu mai mahimmanci a rayuwarta wanda shine dalilin da yasa take ɓoye fuskarta har ma ga mahaifinta.... ​Wannan Dalili ya ta'allaka ne a kan wani babban abokinta wanda ya rayu a cikin wannan Masarauta.. Yaron asalin shugaban wannan masarautar Alhamra wanda yanzu baya raye a duniya, Yayan mahaifinta wanda sai bayan ransa kafin sarkin Nourdeen ya hau... Sarkin da ya shuɗe yana da yara maza biyu wato twins, ɗaya daga ciki ne babban abokin Ayat, amma kuma a lokacin iyayen nasun suna zaman gaba a tsakaninsu akan mulki.. duk da sun kasance ƴan uwa.. Daga lokacin da shaƙuwa ta soma a tsakanin Ayat da wancan yaron sai mahaifinta ya nemi rabasu lokacin bai zama sarki ba..amma yana neman mulki.. Shima wancan sarkin yayi ƙoƙarin raba ɗansa da Ayat, wannan al'amarin ya faru ne tun suna yara.. ​Tun daga wannan lokacin ne Ayat take kulle fuskarta da alkawarin, ​'Babu wanda zai ƙara ganin fuskata sai shi yaron da aka raba ni da shi...' ​Tsawon shekaru har yanzu shiru, babu labarinsa. Bata sani ba shin yana raye ne ko ya mutu. Amma Alkawari ta ɗaukar wa kanta cewa. Shi ne first ɗin ganin fuskarta. Idan kuma ta rasa shi har abada, to kuwa sai idan ta zama Gawa ce za'a ga fuskarta!.. ​Abin da yake mata yawo a kwakwalwarta a koda yaushe shine. Yadda zata bi don shan iskar duniya. ​Hanyar da zata na bi don fita daga cikin Masarauta ba tare da asirinta ya tonu ba, sannan ta dawo lafiya. Tunda take a rayuwarta bata taɓa fita daga cikin Masarauta ba. Bata san ya tsarin garin Alhamra yake ba... Kamar yadda muka sanar a baya. ​Ayat ta kasance tana da ɓoyayyen hanyarta da ba kowa ya sani ba. Hatta Security da Bodyguards na masu gadinta basu san cewa Ayat tana fita daga yankinta ba a kowace rana musamman bayan ziyarar ƙanwarta.. Gimbiya AYAT tana zaune a kan Kujerar Alfarma ta falonta. Tana kallon sararin sama ta katangar gilashin taga mai tsabta wacce ta kewaye Part ɗinta. Zuciyarta cike da damuwa da kuma wani irin kewa mai zafi da ba ta iya bayyana wa kowa ba. Rayuwarta ba komai bace face zuwa ɗaki, daga ɗaki, zuwa ɗaki. ​Shekaru Ashirin da Biyar! Amma bata taɓa taka ƙasa a waje ba. Wannan ƙuntatawa shine babban kunci da ke kanta... Tana cikin wannan tunanin ​sai ta ji takun sawu a bakin ƙofar sannu a hankali.. ​Mai aikin tsaron ta wanda aka keɓe shi musamman domin hidimarta da kuma kula da rayuwarta, ya durƙusa yana danna ƙwanjin notice alamar neman izini kamar yadda dokokin sarki suka buƙata. ​Muryarsa cike da ladabi yake faɗin ​"Gimbiya... idan nayi kuskure ki gafarta. An kawo sabbin fina-finai daga sashen masarauta. Na tattara miki waɗanda zasu burge ki..." ​Ayat ta juyo a hankali, fuskarta cikin izzah da kama kai irin na masarautar su. Ta ɗaga hannu kaɗan alamar ya shigo... ​Ya shiga da kwalin fina-finai a hannunsa. Ya durƙusa sosai kafin ya miƙa mata. ​"Na tabbatar da ba su da hani kuma ba su da abubuwan da zasu tada al'amura, Gimbiya na ba ki izini ki kalla cikin kwanciyar hankali."... A takaice ta kalleshi sannan ta furta. "Izini?..." A ruɗe ya ɗan rusuna ya ce, "Ina neman afuwa Gimbiya, a gafarce Ni.." ​Ta karɓa cikin nutsuwa. ​Lokacin da ya fita, ta yi dariya kaɗan, dariya ta farko wacce ba ta samu damar yi a bainar jama'a ba. ​Ta buɗe kwalin tana jera fina-finan a saman tebur. Sai wani babban poster ya ja hankalinta.. ​MACE A SHIGAR MAZA ​Hoton ya nuna wata mace sanye da gashin baki, ɗan gemu, rawani, da rigar maza.. ​Ta zaro ido kamar an kunna wata fitila a cikin zuciyarta. ​"Wannan kuma...?" ta furta a hankali, idanunta suna kan poster.. ​Ta zauna gaba ɗaya, ta juya kanta gefe, tana murmushi da mamaki... ​"Mace ce kuma haka ta ɓace a cikin maza?" Cikin hanzari ta buƙaci ganin Film ɗin.. ​Ta kalla cikin nutsuwa, tana lura da kowane daki-daki. ​Yadda take sa gemu kamar na maza. ​Yadda ta ɗaure ƙirji ta yadda babu alamun mace. ​Yadda ta yi tafiya ba tare da wani motsi na mace ba. ​Yadda kowa ya amince Namiji ce. ​Gimbiya Ayat ta shaƙi iska mai sanyi. Sai ta jingina da kujera ta rufe ido kaɗan. ​A karon farko cikin rayuwarta, ta ji irin wannan tunanin mai ƙarfi ya shiga zuciyarta. ​"Ni ma zan iya! Ni ma zan iya fita! Ni ma zan iya yin rayuwa kamar mutane!" ​A hankali ta buɗe ido. Ta san wani abu guda ɗaya. ​Ba za ta taɓa sanar da kowa ba! Ko bawanta mafi amincewa. Ko uwar gidanta. Ko waye domin idan ta furta, ta san cewa za su saka ido su rufe duk wani motsinta... Cikin nutsuwa ta miƙe ta fara hawa saman bedroom ɗinta da sauri-sauri ganin ma'aikatanta suna ta zarya... ​Tana shiga ta nufi ɓangaren mirror sites, ta zauna a dogon kujerar gaban madubi ta fara duba fuskarta da tsantsar damuwa.. Manya-manyan ​idanuwanta masu kyan gani da sha'awa.. ​Lips ɗinta masu laushi da cika.. ​Girarta mai kyau wacce ke nuna 'Yar Halitta.. ​Ƙirjinta mai kauri da halitta. ​Sai kuma ta furta a hankali cikin tsantsar damuwa.. ​"Taya zan ɓoye waɗannan?" ​Ta miƙe tsaye gaba ɗaya. Surarta ce ta mace cikakkiya, da ƙwalliya ta halitta. ​Yanayin tafiyarta mace ce ta masarauta. ​Breast ɗinta manya ne sosai, ba za su ɓuya da sauƙi ba. ​Ƙugunta siriri ne irin na Gimbiya da ba ta yin aiki. ​Ta ɗan murza haɓarta irin na fim ɗin da ta gani, tana tunanin.. "Ina zan samo wannan?" ​Sai ra'ayoyi na dabaru suka fara zarya cikin kanta. ​Tyt mai matse ƙirji (Binding) don gyara Siffar Kirji. ​Rigar maza mai faɗi wacce za ta ɓoye kugu da siffar jiki. ​Rawani ko turban da zai rufe gashin kanta. ​ Concealer domin gashin baki. ​Daidaita tafiya ta canza daga mace zuwa namiji mai nauyi.. ​Sallama da murya mai sanyi kamar na maza. ​Ta kuma san cewa. Kwamandan tsaron fada na kallo ne sosai... idan ta kuskura ta yi kuskure za a gane. ​Amma zuciyarta ta yi ƙarfi sosai akan wannan sirrin. ​"Ina bukatar na shaƙi iska. Koda da minti ɗaya ne... Zan fita!" Tun daga lokacin da ta gama kallon fim ɗin rikiɗewar mace-ta-zama-namiji, zuciyar Gimbiya AYAT bata sake samun nutsuwa ba. Wannan fim ɗin ba nishaɗi bane a gare ta, mafita ce! ​Ko da ta kwanta tunanin fita ne a ranta. Haka inta tashi. ​Har ma abincin safe ta manta da shi. ​Part ɗinta guda ce, babba, mai tsari na musamman, da mata uku na yi mata hidima kullum cikin kulawa. Sai dai wata doka ƙarara ta Sarki ta sanya ta cikin kunci.. ​"Ko da rana, ko da dare, Gimbiyata ba za ta taka ƙafarta ta wuce wannan Part ɗin ba." ​Wannan ya sa dukkan ƙofa biyu na part ɗin ke da tsaron da ba ya barin ko kwari su wuce. Hakanan tsaronta ne ya zama kulle–kulle da tsare–tsare a gare ta... ​ Tayi tunani mai zurfi. Ta san cewa idan ba za ta fita ba, to dole kayan su shigo gare ta! ​Gimbiya ta fara da sauƙin abu, magana da bayinta amma cikin hikima domin kada su gane ainihin manufar ta. ​Rana ta Farko... ​Ta ƙira mai ɗinkin ta, wacce ke ɗinka mata kaya na mata tun tana ƙarama... Tayi mata bayani kan cewa, ​"Ina son ganin suturar maza ta fadar nan, wacce ake yi wa jaruman tsaro..." ​Mai ɗinkin ta ɗago tana kallonta a hankali, tana mamaki amma ba ta ce komai ba. Tana tunanin. "Yarinya ce? Me zata yi da kayan jarumai tana mace?" A cikin ranta. ​Sai kawai ta amsa da cewa ​"Idan Gimbiya ta buƙata, zan kawo miki misali guda domin ki gani.".. ​Gimbiya tayi murmushi na ɓoye jin daɗin zuciyarta. ​ "Da wannan zan iya sanin yadda uniform ɗin su yake a zahiri, da kuma inda zan ɓoye Ƙirjina.." itama ta furta a ranta. A ranar kuwa aka kawo mata kayan jaruman fadar masarautar Alhamra.. Ganin tana so ta cire konkonto a zuciyar mai ɗinki sai ta ce da ita, "Ina so zanyi kyautarsu ne, zan aika wa wani zai fara aiki a wannan masarautar domin an gama masa interview..." Jinjina kai mai ɗinkin tayi tana murmushi sai yanzu ta gamsu.. ​AYAT ta cigaba da tsara ma'aikatanta gaba ɗaya, tana neman kayan dabaru ɗaya bayan ɗaya. Ta ƙira mai gyaran kai ta ce, "Ina so a koya mun yadda ake haɗa rawani domin na ga yanda Jaruman Fada ke yi..." Mai Gyaran kai ya yi mamaki amma bai yi tambaya ba saboda Gimbiyar ba a tambayarta abinda take son yi... Hakan kuwa ma'aikacin ya koya mata a jikin wani gunki a cikin part ɗinta.. Bayan ya gama naɗawa a kan gunkin sai ta buƙaci ya bar shi a kan gunkin kawai.. Bayan ya tafi sai ta zaro ɗaurin rawanin a kan gunkin yanda bazai warware ba domin ba ƙaramin naɗi akayi ba....just zata rinƙa ɗorawa ne akanta ba tare da ya warware ba.... Daga baya ta sa aka kawo mata mai kula da takalman jarumai.. Ta ce da shi. "A kawo min takalmin jarumai guda ɗaya... domin na lura suna da inganci, ma'aikacina nashi ya daɗe da lalacewa amma bai samu an bashi wani ba har yanzu..." Mai kula da takalma ya ce, "Gimbiya ai duk wani jami'in fada da ya lalata takalminsa to siya wani yake da kuɗin aljihunsa idan aka bashi na farko kyauta..." Gimbiya ta ce, "har nawa ne kuɗin?.." Ya ce, "ai gimbiya kuɗin da yawa, zai kai 150k..." Tayi murmushi sannan ta ce, "amma sarki ya san da hakan?.." Ya sunkuyar da kai a ɗan tsorace ya ce, "Gimbiya wannan ne sana'ar mu a cikin fadar nan, ko wani jami'in da yake kula da abubuwa to kafin ya bada sai ya karɓi kuɗi...." Gimbiya ta ce, "amma ku kuka siyo abubuwan da kuke sayarwa ko Masarauta ce ta bada ?.." "Masarauta ne Gimbiya kuma sarki bai sani ba..." "Cin hanci kenam? Masarauta ta bada abu akan duk wanda nashi ya lalace a bashi ya cigaba da amfani da wani amma ku kuke sayar musu, baku da jari amma kunada riba, to ku sani duk abin da kuke yi zan aikawa sarki..." A take mutumin ya durƙusa yana roƙon gimbiya... Gimbiya ta ce, "shin albashin da ake baku duk wata baya isar ku ne?.." Cikin kuka ya ce, "wallahi wadatacce kuɗi ake bamu sosai, amma zamu daina karɓan kuɗin kowa, a gafarce mu..." Gimbiya Ayat ta jinjina kai sannan ta ce, "kada na sake ji to, kuma ka je ka kawo mun takalma sawu biyu..." A ruɗe ya miƙe yana faɗin. "Insha allahu za'a kawo a yanzu..." Ayat tayi tunanin takalmin ma'aikacinta ma ya lalace shiyasa yanzu ta buƙaci sawu biyu, na ta da kuma nashi..." Ba da jumawa ba, ya kawo mata "Sample" na takalmin maza... Ta karɓa tana bashi umarnin akan ya samo mata belt na ɗamara.. Nan ya je ya samo mata. ​Bai san cewa, tana tara dukkan kayayyaki ne a sirri don ta kammala shirin rikidewarta ba! Yanzu sauran gyara murya.. ​Wannan shine mafi wahala kuma mafi haɗari a cikin shirinta. ​Gimbiya ta kalli fim ɗin da ta gani sau 3 tana nazarin yadda mace take rage murya ta zama ta namiji. Sai ta fara gwaji a gaban madubi a cikin shurun daren part ɗinta... ​"Assalamu alaikum..." ta furta too Weakly. Ta girgiza kai... ​"Alaikumus salam..." muryarta ta yi tsayi High-pitched. Ta sake girgiza kai. ​Sai ta ɗan saki numfashi mai zurfi, ta ɗan yi ƙasa kaɗan da muryarta, tana dannewa... ​"Alaikumus salam..." Wannan lokacin murya ta yi laushin mace, amma kuma yayi kamar na namiji mai natsuwa da Izzah.. ​Ta yi murmushi ta kaɗa kai. Da wannan zan iya ratsa ko'ina... ba wanda zai gane. ​Haka ta yi ta atisaye kusan rabin dare har sai da muryar ta ta kama tsarin da take so... ✨✨✨ ​Washegari kuma tana koyon tafiyar namiji... ​Haka take ta fafatawa a cikin bedroom ɗinta.. ​Da farko, tafiyarta, tafiyar mace ce sosai ƙugunta na rawa, ƙafa tana sauƙa da salo irin na Sarauta. ​Ta tsaya, ta rage, ta daidaita, ta danna ƙafarta ƙasa da ƙarfi. Ta saita ​ƙafar daidai yanda baya ɗan tashi, tana banƙare ƙirji, jiki a sake.... Ta fara tafiya kamar takun raƙumi.. ​Nan ta sauƙe ajiyar zuciya domin ba ƙaramin gajiya tayi ba.. Sai kuma ta ɗauko kayan jaruman fada ta saka a jikinta tana gwada tafiyar da kayan har zuwa ƙasin falonta... ​Ƴan bayinta suna kallo suna mamakin ganinta a haka, suka ce "Gimbiya me kike yi haka?" Bata ce komai ba face, "Ina gwajin salon tafiya ne kawai." ​Sun bar ta, suna tunanin wata yar wasan kwaikwayo ce ta taso mata.. ​Amma ita a zuciyarta tana maganar ciki, "dole na yi kamar maza... ina buƙatar in ratsa ƙofa babu zargi..." Ta ƙara komawa can saman bedroom da kalar tafiyar maza...A wannan ranar kwana tayi tana atisayen tafiyar maza.. ​Ta gama shirin atisayenta. Yanzu abinda ya rage mata shine yanda zata sa a kawo mata kayan Concealer na yanda zata saka gashin baki da gemu.. Nan ta ƙira wani ma'aikacinta wanda ya kawo mata finafinai ta sanar masa, cewa. "Ina so ka kawo mun design na gashin baki da gemu da kuma saje domin ina son gwajin sabon salon fim da na kalla..." ​Ma'aikacin ya yarda da hakan domin Gimbiya ba ta taɓa tambayar abu mai kama da haka ba. Sun ɗauka sabuwar sha'awa ce kawai... ​Amma ita a zuciyarta ta gama tattara komai, kayan maza, rawani, belt, takalma, riga, murya, tafiya, gashin baki, gemu... duk sun cika shirin ta. Cikin dare Gimbiya Ayat ta tsaya a gaban madubi. Hannunta na ɗan rawa, zuciyarta na bugawa fiye da yadda ta taɓa ji a rayuwarta. Ta shimfiɗa kayan jaruman maza a gabanta.. ​"Zan iya... dole na iya," ta furta a hankali, tana ƙarfafa zuciyarta. ​Ta fara da faɗaɗden belt na matsin ƙirji mai matuƙar Ƙarfi. Ta ɗaure ƙirjinta da belt mai faɗi, domin ta rage nauyin nonuwanta da kuma gyara surar ta zuwa madaidaicin namiji. ​Sai da ta yi ƙasa da numfashi, tana jin matsa da zafi mai yawa. Zafin ya yi yawa har hawaye suka taru a idonta.. ​"Da haka maza ke ji?" Ta yi murmushin wahala da azaba... ​Bayan ta ɗaure, ta saka wandonsu na maza wanda ya yi mata nauyi, ya yi mata tsawo, sai ta ɗaura Belt ɗin ɗamara kamar yadda ta gani a fim.. ​Sannan sai gashin baki da ɗan gemu da ta ƙirƙiro. Ta mamanna su da ruwan gam, ta ƙara musu tinti da ƙananan launin ruwan ƙasa da take amfani da shi a eyebrows ɗinta. A hankali ta manna zuciyarta na bugawa.. ​"Na fara zama wani daban," ta furta... ​Ta miƙe yadda maza ke miƙewa da ƙarfi. Ba tare da ta ɗaga ƙafa sosai ba, sannan ta daidaita jujjuya kugun dake ta matse su sosai. Salon ta ya canza zuwa na ɗan daudu.. ​Ta ɗaga ƙafa kaɗan. Ta yi tafiya a ƙetare cikin ɗakin. Sai ta sake dawowa. ​"Ya kaji? Kamar namiji?" Ta yi tambayar da ba wanda zai amsa. ​ Ta yi tari don buɗe makogwaro. Ta sauƙe numfashi ƙasa.. ​"Ee... kai... Kawo dukkan tawagar nan zuwa ƙofar Masarauta," Ta yi ƙoƙarin yin muryar maza... ​Wani dariya ya kuɓuce mata...dariyar mace. "No! Muryar mace ce!" ​Ta ƙoƙarta. Ta sake gwadawa. Sai ta yi ƙasa da murya.. ​"...ka... kawo tawagar nan..." ​Cikin daren nan take ta maimaitawa, har sai da muryarta ta fara tsuke wa kamar namiji maai shekaru 18–20.. ​Ta janyo rawanin da ta ɓoye. Ta ɗora shi a kai. Ya rufe mata gashin kanta wanda ya daɗa nuna Izzah. ​Ta tsaya. Madubi ya nuna wani Sabon Mutum.. ​A gaban madubi wani saurayi tsaye mai shekaru 20 ne, siriri, mai ɗan gashi a ƙasa da baki da kwantaccen saje.. ​Zuciyarta ne ya yi wani irin tsalle cikin bugawa, dũkan da har ta ji a kunne.. ​"Na zama wani... amma ba zan iya janye wannan ba," ta faɗa cikin murya mai zurfi.. ​Da sassafe, bayan bayinta sun tabbatar da tana cikin ƙoshin lafiya, duk ta sanar da su cewa. ​"Yau bana buƙatar ganin kowa. Duk wacce ta shigo yanda nake hutawa sai ta fiskanci ukuba." ​Duk sun jinjina kai tare da bin umarninta.. ​A wannan lokacin ne da ta san an yi mata ƙofa ta Aminci, ta kulle ɗakinta yanda za'ayi tunanin tana ciki. Ta bi hanyarta ta sirri ba tare da kowa ya ganta ba ta fice... A cikin lambun da take fita ta fice.. ​Haka take tafiya a hanyar masarautar da ta miƙe zuwa can yankin babban fertility ɗin Masarautar... (Center of the Kingdom).. ```DAN ALLAH KUYI MUN ADALCI🙏 KAMAR YANDA NA BAKU LOKACI NA DON NA FARANTA MUKU, KU MA KUYI ƘOƘARIN SANYA NI CIKIN FARIN CIKI 🙏🙏🙏``` ```LIKES ƊINKU SHINE ALBASHIN MARUBUCI``` 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayyanowar ta cikin babbar masarauta... Tana haɗuwa da tawagar ɗaiɗaya amma babu wanda yayi tunanin Gimbiya ce. Tana ƙoƙarin wurin daidaita tafiyarta kamar namiji, domin tana ganin yanda sauran suke yi. Sai ga wani tsararren mota cikin Masarauta ya tsaya a gefenta. Kirjinta ya yi wani irin bugawa sosai, ta ɗauka an ganota ne. Sai ta ga ɗaya daga cikin Security ne mai jan mota, ya ce da ita. "Ya! Mutumin hau na rage maka hanya zuwa can Center ɗin Masarautar mana..." Ayat ta shiga cikin gaggawa, amma jikinta yana ɗan nuna gajiyawa irin bata saba ba saboda matsin ƙirji. Security ya kuma cewa. "Kana daga cikin tawagar da zasu fita ne?" Ayat tana fargaban magana saboda kar ya ganota ta murya duk da tayi training. Tayi shiru. Security ya ce, cikin ɗan tsawa. "Kai ɗan rainin wayo, ina magana kana mun shiru, in ban jefar da kai ba!" Ayat anan ta tsorata, ta daidaita muryar ta mai sanyi. "Amm... Dani za'a fita..." Security ya ce "Yadai naji muryarka haka, kodai mura kake?" Haka suka kasance har suka isa Center of the Kingdom. Ayat tana ta wara idanuwa tana ganin tsararrun abubuwan da suke cikin Masarautar nan. Tana tunanin daman haka Masarautar nan take da girman gaske? Dai-dai lokacin da suka isa, yanda wasu tawagar suke shirin fita daga Masarautar. Ayat ta sauƙa tana zazzaro ido cike da bege. Ta shiga cikin tawagar da suke ƙoƙarin fita outside ɗin Masarauta. Suna fita daga cikin Masarautar, ta yi wani irin ajiyar zuciya mai tsayi wanda ya fito daga tsakiyar zuciyarta. Iskar waje ne ya buge ta a fuska! Iskar da ta daɗe tana mafarkin ji, shekaru ashirin da biyar tana zaton yanda duniyar waje take. Hawaye ne ya gangaro daga idonta... "Duniya... ga ni."... Ta furta cikin ƙarƙashin maƙoshinta.. AYAT tana ta fargaba yanda kayan suka matse ta da kuma tsoron ko wata dabara zata warware. Bayan ta tsallake gwaji na farko na mai motar tsaro, ta sulale ta bar cikin tawagar tsaron, ta tafi yawonta a ɓoye. A ɓoye ta ɗauki dokin ɗaya daga ciki, ta zagaya bayan Alhamra wurin da babu wanda ke zuwa. Anan ta tarar da wani kogi mai kyau da wurin gudanar ruwa mai zurfi. Wurin yana da rata sosai da cikin garin. Ba kowa sai kukan tsuntsaye da natsuwar ruwa. Zama tayi tana shan iskar wurin domin wurin ba ƙaramin burgeta yayi ba. Har yanzu tana sanye da shigar mazanta. Ta zauna a bakin kogin, ƙafafunta cikin ruwa mai sanyi. Can sai ta ji wani abu ya faɗo ta bayanta! A zabure ta miƙe cikin tsoro mai tsanani tana ƙara! Cikin muryar mace tamkar ba namiji ba, firgici ya sa ainihin muryarta ta dawo!. Tana juya bayanta sai kawai ta ga wata farar tsuntsuwa kyakkyawa a kwance a ƙasa, an harbo ta daga sama. A tsorace ta kama ƙirji tare da jin zafin matsin ƙirji da ƙugun cikin tsoro da tausayi. Ta nufe ta da gudu ta ɗauke ta. Can sai ga wasu matasa ‘yan farauta sun zo ɗaukan tsuntsuwar daman su suka harbe ta da mashi. Ganin AYAT a shigar tsaro suturar maza ta fadar Alhamra yasa suka tsorata suka ce. "Wayyo! Ɗaya ne daga cikin Security Fadar Alhamra! Mu gudu!" Nan suka juya suka gudu cikin gaggawa. AYAT ta sauƙe idanunta a kan tsuntsun. Ta zauna a bakin ruwa. Ta ciro Allura da Zare a jikin rawanin da ta ɗaura. Ta fara ɗinke wa tsuntsuwar wurin da aka cake ta da mashi cikin salonta. Tayi treatment ɗinsa sannan ta ba shi ruwa. Tana ajiye tsuntsuwar, sai ta ga ta miƙe, amma bata iya yin sama sosai ba. Itama ta miƙe tana binta da gudu. Ta ga tsuntsuwar ta sauƙa a saman wani tsararren bishiya yanda ƙoyayenta suke cikin raga-raga irin abin da suke koyaye akai har wasu sun kinkishe. Ta sha mamaki sosai. Ita kaɗai ta fara murmushi tana jin daɗin ceton da tayi. Tsuntsuwar tana kwance akan ƙoyayenta a ɗan sama da bishiyar kaɗan. AYAT tana tsaye tana kallonta tare da shafa mata baya. Ta ce, cikin muryar maza mai tausayi.. "Ashe ke ɗin Uwa ce. Nagode Allah da yasa nake nan a wannan lokacin... Shin anan kike rayuwa? Kusa da kogin nan mai kyau? To kar ki damu, zan riƙa zuwa miki ziyara... kuma zan cigaba da kare rayuwarki... Sunana AYAT, amma a shigar mazan nan sunana 'INUWA'. Wato Inuwarki, mai tare miki rana. Idan na ƙara dawowa zan ba ki takaitaccen tarihina mai cike da kaddara... Ki kula da kanki da yaran ki." Daga nan ta rufe ta da wasu ganyaye yanda duk wanda yazo bazai san akwai halitta a wurin ba. Nan ta juya zata tafi. Ganin yamma tayi, nan ta zaro ido a tsorace ta furta. "Na shiga uku! Daidai wannan lokacin ake rufe Masarauta... kuma nasan ma'aikatana zasu nemeni daidai cin abincina. Wayyo banaso a samu matsala a rana ta Farko!" Daga nan ta hau saman dokin ta fara gudu dashi, ta ratsa cikin city ta nufi Masarautar... Ana shirin rufe babban gate sai ga ta, ta nufo da gudu tana tsayar da su da muryar maza mai ƙarfi. Ɗaya daga cikin masu tsaron Get ne ya ce, cikin tsawa. "Kai ɗan ƙwaƙur! Daga ina kake?" Cikin muryar maza a ɗan tsorace, ta ce "Man dokin ne ya ƙare..." Duk suka kalli juna jin rainin hankali irin nasa. "Wannan fa dokar sarki ka karya, don haka zamu je dakai can sai kayi masa wannan bayani..." a cewarsu. Zaro ido tayi! Ta ji zuciyarta tayi mugun bugawa. Nan ta sauƙo a kan doki ta fara ba su haƙuri da muryar ta mai sanyi. Ganin bazasu haƙura ba, yasa ta riƙo hannun wani daga ciki cikin fargaba. Duk ta ruɗe tana ba shi haƙuri. Wanda ta riƙe wa hannu ne ya ji wani irin sanyi ya ratsa shi da ta taɓa hannunsa. Ya ji hannun laushi ya kuma ratsa jikinsa. Ya ɗan ruɗe jin hannun namiji mai sa shauƙi. Security ya tambaye shi cewa, "Meye sunanka domin ban taɓa ganinka a cikin wannan masarautar ba." A ruɗe ta ce. "Musa... Kabiru... Iliyasu... Shafi'u..." Security ya ce "Kai bana son hauka fa! Anya kai ba ɗan Daudu bane?" Ta daidaita muryar ta, ta furta sunan da ta sanar wa tsuntsuwa.... "Inuwa.... Inuwa sunana..." Ɗaya daga ciki ya ce. "Wannan daga gani ba abinda ya iya domin ɗan daudun cikin mu ne, ga murya a ranrangwaɗe..." Ɗaya daga ciki ya ɗaga ƙafa ya canƙe ta a wurin mazauninta yana faɗin "Wuce ka bamu wuri dallah!" Nan ta fara Tangal-Tangal zata faɗi. Da ƙyar ta daure ta wuce da ɗan gudu–gudu... Su na masa dariya, har sun sa masa suna 'Ɗan Ƙwaƙur'. AYAT wato Inuwa kai tsaye ta nufi part ɗinta a babban yankin masarautar. Hanya ɗaya kawai take so ta sulale ta koma part ɗinta tun kafin a ankara da bata nan. Tasan akwai matsala domin dole yanzu za'a buƙaci ta fito akan ta ci abinci. A hanyarta, wani babba daga cikin Security ya dakatar da ita da cewa. "Kai! Sauƙo nan..." Ayat ta sauƙa cikin rikicin zuciya da gajiya. Security cikin nuna isa irin na Shugaba mai role, ya ce "Uhmm! Wannan Littafin za ka kai wa Gimbiya MAAYAH! Ta buƙaci a kai mata ne." Cikin ajiyar zuciya na tsoron an tsallake wani haɗarin da kuma sabon tsoro lokaci guda, Inuwa ya karɓa. Ya hau dokin, yana nazarin ina ne part ɗin MAAYAH? Domin tun da take bata taɓa zuwa ba. Sai dai idan lokacin haɗuwa yayi a haɗu a babban fadar sarki. Haɗiyar yawu tayi domin iya part ɗin ƙanwarta Firdos ta sani kawai. Tana cikin tafiya, ta tarar da wata mata baiwa ita ma Ma'aikaciya ce. Ta tambaye ta da muryar maza mai sanyi "Amm, shin ko kin san ina ne part ɗin Maayah?" Matar ta zabura tana zaro ido ta ce, "Maaaa me?" A ɗan ruɗe yace "Ohh Gimbiya Maayah..." Matar ta ce "Ohh yanzu naji batu, amma kai baƙo ne ko? To haramun ne ka ƙira sunan Gimbiyar Sarki kai tsaye ba tare da girmamawa ba." Daga nan ta kwatanta masa.. Inuwa ya ƙara gaba ya sha mamaki ganin tsaruwar part ɗin Maayah. Tsaruwar da ya nuna tsananin alatu da kuma tasirin mahaifiyarta 'Yar Hindu. Da farko masu tsaron part ɗin ne suka tare shi. Ya musu bayanin saƙo ya kawo mata. Ɗaya ne ya miƙo hannu akan zai kai mata.. Inuwa ya ce "No! Sirri ne! Ni aka buƙaci na kai mata da hannuna." Jin ya ambaci sirri da umarnin sarki yasa suka barshi ya shiga. Har sai da ya tsallake gate biyar kafin ya isa Center na part ɗin. Nan ya fara ganin mata masu dawainiya da ita sunata zirga-zirga. Ya shiga babban falon. Wani irin sanyi ne ya ratsa shi. Ga ƙamshi kala-kala na turaren hindu ko wanne fita yake. Ganin ba kowa a falon, kowa yana ta zirga-zirgan aiki, hakan ya ba shi daman haurawa can saman ɗakin yanda yake da tabbacin anan take. Sai da ya haura stairs bakwai kafin ya iske bedroom ɗinta. Wani irin sanyayyen waƙar hindu ne yake tashi a slow... Inuwa ya shiga bedroom a nutse yana baza idanu. A hankali ya shige ya rufe glass door a hankali. Ya tarar ba kowa anan ma. Can ya fara jin motsin ruwa alamun a bathroom take tana wanka. A bakin gado ya zauna, yana ƙoƙarin buɗe littafin ya ga abin da yake ciki.. Littafi ne na english novel, na tsantsan soyayya. Duk da Maayah ba soyayya take da kowa ba, amma tana son labaran soyayya sosai... Inuwa ya ɗan juya idanunsa yana jinjina kai. Domin a rayuwarsa babu wani tsarin soyayya ko wasa da soyayya... A cikin ransa ya ce "Shan kokko ɗaukan rai. Kowa dai da damuwarsa. Ita kuma labaran soyayya ne damuwarta. Allah sarki! Da dukkan alamun aure take so, kuma gashi ba halin yin aure! Domin babbar Yaya ma wacce tayi 30 something tana nan bata yi aure ba, balle mu 'yan 20 something..." Haka ta rufe littafin ta ajiye a kan gadon. Tana kallon hotunan Maayah a manne a jikin bangon ɗakin.. Ya kafe idonsa akan hoton mahaifiyar Maayah wacce ta kasance ƴar hindu. Can hawaye ya fara zubo masa domin ya tuna da mahaifiyarsa wacce ta juma da barin duniya ita da ƙanwarsa Firdos A hankali ya share hawayensa.. Daidai lokacin, sai ga Maayah ta fito daga bathroom! Tana ɗaure da ɗan guntun towel a kirjinta, gashinta ya sauƙo har gadon baya. Tana taku kamar wata ɗawisuwa cikin kasaita. Kana ganin kasan 'Yar Sarauta ce mai kyan Hindu.. Ganin mutum a tsaye a tsakiyar ɗaki yasa ta tsorata. A ruɗe tayi baya. Cikin rashin sa'a, ƙafarta ya zame, tayi baya zata faɗi! Inuwa yayi saurin riƙe hannunta ya jawo ta gaba. MAAYAH ta faɗo a jikinsa! Dake shima babu ƙarfi saboda asalin mace ce duk ɗaya suke, hakan yasa duk sukayi baya suka faɗa kan gado! Maayah tana saman Inuwa! A hankali ta ɗago tana kallonsa da gashin bakinsa da rawaninsa. Maayah ganin yanda lips ɗinsa suke Soft-lip gasu jajawur. Ga Idanuwa manya-manya farare tass. Ga Soft-body fari tass. Maayah a tunanin namiji ne yasa ta fara jin shauƙi, da wani irin feeling mai zafi da ya ziyarce ta. Haka suke kallon juna. A hankali Maayah take sunkuyar da kanta tana shirin ɗora pink lips ɗinta akan lips ɗin Inuwa da niyyar Kiss! A ruɗe ya janye ta gefe ya miƙe da sauri! Yana kallonta ya juya da gudu ya fita daga ɗakin. Da sauri-sauri yake tafe yana so ya bar part ɗin gaba ɗaya da tunanin abin da Maayah take shirin aiwatar wa. Itama Maayah cike da mamaki take zaune. Tana tunanin meyasa ya gudu mata, duk da ba wani namijin da ya taɓa shigo mata room sai yau karo na farko kuma taji matuƙar sha'awarsa. Haka take duba kanta tana mamakin meye aibunta da har zai gudu tunda Allah ya bashi daman shigowa. A hankali ta furta cikin sanyayiyar murya. "Wannan bashi da lafiya! Kamar yadda Maayah take tsararriya, kyakkyawa mai kyan sura shine zaiyi rejecting ɗina? To ma meya kawo shi, ya zo ya tada mun da hankali..." Idonta ne ya sauƙa akan littafin da ya kawo mata. "Ohhhh! Book aka aiko shi ya kawo? Amma ban taɓa ganin security mai kyan wannan ba! Kyansa ya wuce misali! Taya zan sa a nemo mun shi? Na kamu da son sa lokaci guda! Ina jin wani abu a kan sa sosai..." Haka ta gama maganganunta. Sannan ta miƙe ta fara bin waƙar da yake tashi a ɗakin tana rawa (Indo-Arabic Dance). A hankali take motsa jikinta irin rawar hindu tare da ƙaramin Towel a kirjinta! Ayat wato Inuwa tana cikin gagarumar gadarar tserewa. Ta bar part ɗin Maayah cikin sauri tana da yaƙinin cewa Maayah zata sa a nemo ta. Bayan ta shiga babban gaiden ta hanyar ƙofar da tabi, kai tsaye ta nufi ɓoyayyen hanyarta wanda ke kaiwa zuwa part ɗinta ta cikin ƙasa. Tana jin gajiya sosai. Gajiya ta farko a rayuwarta. Matsin ƙirji, gudun dawowa, da tsananin fargaba na tonon asiri guda biyu, a ƙofar fada da kuma a ɗakin Maayah. Tana shiga ɗakinta, ta kulle ƙofar sirrin tana sauƙe ajiyar zuciya mai tsayi. Tuni taji motsin Bayin ta a waje, suna shirin zuwa da abincin dare kamar yadda dokar sarki ta tanada. Ba ta da ko minti ɗaya! Cikin gaggawa ta fara cire shigar Maza. Ta cire Rawanin tare da gashin baki da gemu da ta manna.. Ta zaro takalman maza masu nauyi. Ta jawo Belt da Riga da wando masu tsayi. Mafi muhimmanci, ta cire ɗamarar da ya matse ƙirjinta da ƙugu. Da zarar ta cire shi, sai ta ji isasshen numfashi ya shige ta! Ta ji kamar an ɗaga mata wani dutse a jikinta. Ta tura kayan maza a cikin ɗakin ajiya na sirri da ta tanada. Sannan ta miƙe ta shiga Bathroom domin yin wanka na gaggawa don ta wanke ƙura da gumi na duniyar waje.... Bayan ta fito, ta koma cikin kayan Gimbiyanci na masarauta tare da mayafinta mai rufe fuska. Tana cikin doguwar kujerarta ta alfarma a dai-dai lokacin da ma'aikatan ta suka danna ƙwanjin neman izini a ƙofa. Ta yi murmushi a cikin ranta.... "Na ci nasara a rana ta farko!...." ```LIKES ƊINKU SHINE ALBASHIN MARUBUCI ``` 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 4️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan ta kammala cin abinci cikin natsuwa a gaban bayinta domin su ne ke kula da hidimar ta suka tattara komai suka fita, suka bar ta ita kaɗai. Ta jingina a gadonta, zuciyarta na yawo cikin tunanin duk abin da ya faru a wannan rana.. “Lallai wahalar da na sha a jikina ta fi zaman kunci a wuri ɗaya. Na ga yadda duniya take, na ceci wata halitta, Uwa!...” Ta ji gamsuwa da dukkan wahalolin da ta fuskanta, domin sun buɗe mata ido, domin rayuwar waje tana da haɗari amma tana da daɗi. A ranta ta sabunta alkawarin cewa dole ta koma bakin kogi, domin ta sake ganin tsohuwar tsuntsuwa da ’ya’yanta... A dai-dai wannan lokaci, yayin da Gimbiya Ayat ke cikin natsuwa a ɓangarenta, Ibrahim jagoran tsaro da ta riƙe hannunsa a ƙofar fada yana cikin rikicin tunani a bakin aikinsa. Ibrahim jarumi ne na tsaro da ya shafe sama da shekara goma yana aiki. Ya san fuskoki da jikin mazaje na masarautar. Amma abin da ya faru jiya ya bambanta da duk abin da ya taɓa sani. Maimakon ƙarfin hannun namiji, sai ya ji sanyin taɓawa ya ratsa shi. Ya zauna yana kallon hannunsa, inda Ayat wacce ta ƙira kanta Inuwa ta taɓa shi. Har yanzu yana jin taushin fatar, santsi kamar na jariri... Ya cika da fargaba da ruɗewa.. Muryarta a sanyaye, mai laushi, cike da salo... “Wane irin namiji ne wannan?” Ibrahim ya tambayi kansa. “Hannunsa ya yi taushi fiye da kima, kuma ya kasa faɗin sunansa. Ya ce Inuwa… Wannan dole wani abu ne daban a masarautar.” Ya girgiza kansa, zuciyarsa ta ƙi yarda da cewa Inuwa cikakken namiji ne. Sha’awa ta gauraya da shakka a ransa. “Dole ne na nemo wannan Inuwa,” ya yanke shawara.. “Sai na san wanene, kuma me ya sa hannunsa ke da irin wannan taushin da bai dace da namiji ba.” ```Bayan Kwana Biyu``` Gimbiya Maayah ba ta samu nutsuwa ba tun bayan tserewar Inuwa daga ɗakinta. Ta yi watsi da littafin soyayya da aka kawo mata, domin abin da take karantawa ya koma gaskiya. Ta zauna a kan gadonta na alfarma, tana shafar hannunta a inda Inuwa ya riƙe ta. Wutar sha’awa ta ratsa ta fiye da duk labaran da ta taɓa karantawa. A lokacin wata babbar ma'aikaciyarta ta nemi izinin shigo wa, Maayah ta lamunce mata domin ita tasa a ƙira ta.. “Mama Liyatu, akwai wani da ya kawo min littafi jiya. Sabon ma’aikaci ne a sashen tsaro. Ina so a nemo min shi,” Ta faɗa cikin muryar gimbiya mai nuna cewa umarni ne, ba zaɓi ba. Mama Liyatu ta durƙusa cikin ladabi... “Ranki ya daɗe, menene sunansa?” Maayah ta yamutsa fuska. Sannan ya ce, “Ban san sunansa ba, amma yana da kyau matuƙa, ido manya-manya, ga lips masu taushi. Sannan yana da rawani kamar na jaruman tsaronmu, amma ya fi su tsafta da kamshi." Mama Liyatu ta shiga cikin ruɗani. Ya ya za ta nemi namiji mai kyau a cikin ɗaruruwan jami'an tsaro? Maayah ta sake jaddadawa: "Ki je sashen aikin tsaro na fadar cikin gida. Ki ce ana neman wanda ya kawo saƙo a ɗakina jiya. Dole ne a samo shi. Amma ki yi aiki a ɓoye, kar wani ya san cewa Gimbiya Maayah ce ke neman sa." Mama Liyatu ta fita tana mamaki da kuma cike da tsoro. Ta san cewa wannan aiki ne mai haɗari, amma dole ta bi umarnin Gimbiya.... ✨✨✨ A cikin part ɗin Gimbiya Ayat tana shirin fitar ta na biyu. Zuciyarta ta yi ƙarfi yanzu, domin tsoron da take ji ya rage, kewar tsuntsuwarta ta ƙaru. Tana zaune tana gyara kayanta na maza.. Matse-matsinta ya rage zafi yanzu domin jikin ta ya fara saba wa da sabon salo. Tana nazarin tsarin fitar ta, manufarta ɗaya tak a yau shine zuwa bakin kogi don ta ga tsohuwar tsuntsuwa da ‘Ya’yanta... La'asar ta yi bayan tayi sallar ta, ta gama shiryawa tsaf don fitar ta na biyu. Ta nufi babban gate ɗin fada tana jan dokinta. Tana isa, sai ta tarar da wasu rukunin jami’an tsaro su biyar, waɗanda tuni suka sa mata ido suna murmushin mugunta. "A’a! Ga Ɗan Ƙwaƙur nan zai fita yawon shakatawa!" ɗaya daga ciki ya faɗa yana dariya. "Wane irin namiji ne wannan? Ko tafiyar sa ma sai ka ce ta mata," in ji ɗayan, yayin da suka riƙe ƙugu suna kallon yadda Inuwa ke taku cikin sanyi.. Ayat ta ɗaure fuska, ta canja murya zuwa ta nimiji. “Za ku ba ni hanya, ko kuwa hira za mu tsaya yi?” Duk suka kwashe da dariya. Sun riga sun yarda cewa Inuwa ɗan daudu ne, namiji mai ƙirar mata, shi ya sa ma ba su damu da sanya shi a lissafin jarumai ba... Kafin ta ƙarasa fita, babban jami’in da ke gadin littafin shige-da-fice ya dakatar da ita. "Tsaya nan! Ka san dokar fada, duk wanda zai fita dole ya yi signing a littafin nan, sannan idan ka dawo ma ka sa. Idan ba haka ba, za a ɗauka ka gudu ne." Gaban Ayat ya faɗi. Ta san cewa sa hannun mace da na namiji akwai bambanci, kuma rubutun ta na gimbiya ne mai kyau da tsari. Amma ba yadda za ta yi. Ta karɓi biro hannu na rawa, ta rubuta "INUWA" cikin babban rubutu na maza don ɓadda kama. Bayan ta gama, ta haye saman dokinta. Ta daka masa zunguri, dokin ya tashi da gudu ya bar harabar fadar yayin da masu gadin ke yi mata tafi suna mata dariyar tsokana. A gefe guda, Ibrahim yana kallon komai daga nesa. Bai shiga cikin masu yi mata dariyar ba, domin tunanin sa ya wuce nan. A ransa ya ƙara tabbatarwa, _“Lallai Inuwa ɗan daudu ne. Taushin hannun, tafiyar sa… amma me ya sa zuciyata ke son sake jin waccan taɓawar?”_ A cikin ɗakinta, Gimbiya Maayah ta kasa zama. Ta sallami bayinta, ta rage ita kaɗai. Tana riƙe da littafin English novel ɗin da Inuwa ya kawo mata, tana shafar bangonsa kamar tana shafar hannunsa.... “Meyasa ya gudu? Meyasa ya ƙi karɓar kuncina?” ta furta a sanyaye. “Shin ban yi masa kyau ba ne, ko tsoron matsayina yake ji?” Sha’awa ta mamaye ta gaba ɗaya Ta tambayi kanta cikin sanyin murya. Hankalinta ya gama tashi domin ta fara jin cewa Inuwa ne kaɗai namijin da zai iya goge mata kishirwar soyayyar da take karantawa a littattafai. Ta riga ta yanke shawara a ranta, dole ne a nemo mata Inuwa ko da hakan zai tayar da rikici a masarautar.... ✨✨✨ Ta isa bakin kogin da sanyin yamma. Iskar wurin tana kaɗawa da wani irin sanyi mai ratsa jiki, amma hakan bai hana ta nufar gindin bishiyar da ta ɓoye tsuntsuwarta ba.. "Inuwar ki ce ta dawo..." Ta faɗa cikin sanyin murya yayin da take ƙarasawa. Tsuntsuwar ta miƙe, fuka-fukanta sun fara nuna ƙarfi, wurin da ta ɗinke ya bushe sosai. Wani irin farin ciki ya mamaye zuciyar Ayat, a matsayinta na Gimbiya, ba ta taɓa jin daɗin da ya kai na ceton wannan rayuwar ba. Tana cikin gyara mata ganyen da ta rufe ta da shi, kwatsam! Wani tsararren kibiya ya wuce ta gefen fuskarta da mugun gudu, ya caki jikin bishiyar, saura kaɗan ya sami tsuntsuwar. Ayat ta ji numfashinta ya tsaya na daƙiƙa guda. A tsorace ta juya baya, hannunta ya kai kan takobinta... A tsaye, a kan wani dutse dake gefen kogin, ta ga wani tsararren mutum wanda ba ta taɓa ganin kyakkyawa kamarsa ba. Gashin kansa fari ne sol kuma dogo, yana yawo cikin iska. Idanunsa suna da wani irin kwarjini da sanyi wanda da wuya ka samu mutum mai irin yanayin sa... King Diamond ya bayyana ne a matsayin mutum a cikin wannan fili nasa na sirri.. Ayat ba ta san shi ba, kuma shi ma bai nuna ya san ta ba, duk da cewa su abokan wasa ne tun suna ƙanana kafin canjin halitta ya raba su... "Waye kai da kake neman hallaka tsuntsuwar da na sha wahalar ceto?" Ayat ta daka masa tsawa, muryarta ta fito kauraye kamar namiji. King Diamond bai ce uffan ba, sai wani irin kallo da yake jifanta da shi. A ransa ya san wannan wurin nasa ne, kuma tsuntsuwar tasa ce, amma ganin wannan saurayin yana ta fafutuka a kai ya ba shi mamaki.. Ayat ba ta jira ba, ta zaro takobinta da sauri. "Idan harin tsuntsuwar nan kake, to sai dai ka fara ta kaina!" King Diamond ya ɗaga hannunsa, nan take wani kyakkyawan takobin azurfa ya bayyana a hannunsa daga iska, tsafi ne ya ƙira takobin ta bayansa don ɓoye ainihin ikonsa.. Ƙarar haɗuwar takubbansu ta karaɗe bakin kogin.. Inuwa ya kai masa farmaki da karfi da kwarewa irin ta jaruman Alhamra. Ta daka tsalle ta kai masa sara ta sama, amma cikin kwarewa Diamond ya kauce, takobinsa ya tare nata cikin sauƙi. Faɗan ya yi zafi. Ayat tana amfani da dabarun guje-guje da lankwasa jiki don kaucewa takobinsa mai nauyi... Duk lokacin da Diamond ya kai mata hari, takobinsa baya taɓa fatarta, domin a zuciyarsa ya fara fahimtar cewa wannan saurayin dake gabansa yana da wani sirri na daban, amma bai bar hakan ya bayyana ba. Ta kai masa wani naushin takobi ta gefe, Diamond ya goce yasa hannu ya daki ƙirjinta, baya tayi ta faɗi ƙasi tana sakin numfashi, shi kuwa ya tsaya yana kallonta kamar yana tantance wani abu... Ganin yanda yayi galaba akanta ne yasa ta miƙe a fusace tana kuka ta sake kai mata takobinta cikin zafin rai... Har cikin ranta inda zata same shi, zata sassarashi ne... Amma shi, ya ɗauki faɗan a matsayin gwaji ne kawai, domin inda yana da niyyar kashe ta, cikin sauƙi zai gama da ita.. Takobinta yana gogan nashi yana fitar da tartsatsin wuta. Sun shagala da faɗan, kowannensu yana mamakin kwarewar ɗan uwansa. Ayat tana faɗa ne da dukkan ranta don kare tsuntsuwar da take ganin ita ce kadai abokiyar sirrinta, yayin da King Diamond yake fada yana nazarin wannan baƙuwar dake da kwarjinin gaske a idanunta. Yayin da takubban suke ta tartsatsin wuta, King Diamond ya fahimci cewa wannan dake gabansa ba zai daina kai hari ba har sai numfashinsa ya ɗauke... Ganin jajircewar Inuwa, Diamond ya yi amfani da wani irin zafin nama wanda idon ɗan adam ba zai iya gani ba. Kafin Ayat ta sake kai wani harin, Diamond ya damƙe damtsen hannunta wanda take riƙe da takobin. Wani irin ƙarfi ta ji kamar an murƙushe ƙarfe. Cikin ƙanƙanin lokaci, ya juyo da ita tare da wurgar da ita da ƙarfi zuwa cikin kyakkyawan ruwan kogin dake gefensu... Ruwan dake da matuƙar sanyi kamar ƙanƙara ya haɗiye ta. Ayat ta lume cikin zurfin kogin, inda sanyin ya ratsa ƙasusuwanta. Amma saboda ƙwarewarta na iya ruwa, ba ta firgita ba. Ta buga ƙafafunta, ta yi sama tana sauƙar da numfashi da sauri. Ta goge fuskarta tana waige-waige da jajayen idanunta don ta ga inda wannan maƙiyin nata ya shige. Amma abin mamaki, gurin ya waye shiru... King Diamond ya ɓace tamkar bai taɓa kasancewa a wurin ba, sai sautin iska dake kaɗa ganyen bishiyoyi.. "Ji banza! Ya ji tsoro ya gudu..." Ta furta cikin fushi. A wannan karon, muryarta ta asalin mace ta fito sarai, domin fushin ya sa ta manta da shigar mazan da take yi.. Ta fito daga cikin ruwan tana ɓari saboda sanyin wurin, kayan jikinta duk sun jiƙe sun yi jagab. Ta nufi gindin bishiyar da gudu, inda tsuntsuwar take zaune cikin fargaba. Ayat ta sa hannu tana shafa tsuntsuwar cikin rarrashi.. "Kiyi haƙuri kinji? Kar ki ji komai, ina tare da ke. Ki kula da yaranki, zan rinƙa zuwa miki a koda yaushe," ta faɗa cikin murya mai cike da ƙauna. Ganin yadda duhu ya fara bayyana a sararin samaniya, ta fahimci cewa lokaci yana son ƙure mata. Idan mangariba ta yi ba ta shiga fada ba, asirinta zai iya tonuwa. Cikin hanzari ta sake rufe tsuntsuwar da ganye don kariya, ta ja ragamar dokinta tare da lilo a kansa. Ta nufi hanyar zuwa masarautar Alhamra dake da nisa sosai. Iska tana busa jikinta dake jiƙe, amma zuciyarta tana cike da tunanin wane ne wancan mutumin mai gashin azurfa? Kuma me ya sa ya ɓace cikin lokaci guda?.... *Bayan Isha'i* A cikin fada kuwa, Ibrahim bai yi barci ba. Yana zagaye a cikin sashen tsaro sai ya ji wasu ma'aikata suna tsegumi. "Kaji fa, wai jiya an ga wani sabon Security ya shiga har Bedroom ɗin Gimbiya Maayah! Kuma har yanzu ba a san ko wanene ba." Gaban Ibrahim ya faɗi. Ya tuna da Inuwa. Ya tuna yadda yaron ya rikice wajen faɗin sunansa.. "Lallai wannan Inuwa ko Ɗan Ƙwaƙur ba jami'i bane kawai... Akwai wani babban al'amari a tare da shi. Ta yaya ma'aikacin tsaro zai shiga har bedroom ɗin Gimbiya idan ba yana da wata kariya ta musamman ba?" A ɗayan ɓangaren, Mama Liyatu ta dawo da rahoton cewa.. "Ranki ya daɗe, na bincika ko'ina a sashen ma'aikata. Babu wani jami'i mai irin siffar da kika faɗa a cikin jerin ma'aikatan fada. Masu tsaron ƙofa ne kawai suka ce sun ga wani mai kama da ɗan daudu...." Maayah ta miƙe tsaye cikin mamaki da kuma ƙarin sha'awa.. "Wato ma'aikacin bogi ne? Kuma ya shigo har ɗakina ya fita ba tare da an kama shi ba?" Murmushi ya suɓuce mata. Wannan ya ƙara sa ta ji cewa Inuwa wani babban mutum ne mai ban mamaki wanda ya fi ƙarfin ma'aikacin fada... A washegari har labari ya karaɗe ko ina. Har ya je kunnen sarki zaki.. Ko wace gimbiya an sanar mata cewa ana son ganinsu a babban fadar sarki.. Gimbiyoyi biyar duk an sanar da su cewa sarki yana son ganinsu na gaggawa.. 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA ⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 5️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* A lokacin da saƙo ya isa ga Gimbiya Ayat cewa Sarki Zaki yana ƙiran dukkan gimbiyoyin masarautar Alhamra, gabanta ne ya faɗi tasss. Jin cewa dalilin ƙiran shi ne zargin shigar wani jami'in tsaro mai suna Inuwa cikin ɗakin Gimbiya Maayah, ya sa ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige. Ta koma cikin bedroom ɗinta, ta kulle kofa tana zarya. Zuciyarta na bugawa... Tare da maganar zuci.. "Idan na bayyana a matsayin Gimbiya Ayat, zan zauna lafiya a kan kujerata, amma 'Inuwa' zai zama ɗan gudun hijira wanda za a saka ran jami'ai dubu don kamo shi. Idan kuma na bayyana a matsayin Inuwa, zan fuskanci fushin Mahaifina a gaban kowa!"... Bayan dogon tunani, Ayat ta gane cewa idan har aka rasa Inuwa a filin taron ma'aikata, to bincike zai yi tsanani har ya kai ga kowane lungu na fada. Dole ne Inuwa ya bayyana don sanyaya fushin Sarki, sannan kuma Gimbiya Ayat dole ta bayyana don kar a zarge ta da rashin halartar taron gimbiyoyi. Anan ne Ayat ta ƙulla wata dabara... Ta yanke shawarar cewa za ta fara bayyana a matsayin Gimbiya Ayat a farkon taron. Sannan yayin da taron ke tsaka da ɗumi za ta nemi izinin fita don ta koma ta rikiɗe zuwa Inuwa, sannan ta shigo filin fadar a matsayin wanda ya kawo kansa.... ✨ Domin ta amsa ƙiran sarki a matsayin gimbiyar da ba ta san komai ba, ta fito cikin shigarta ta alfarma da mayafinta na sirri. Ta isa babban fada inda sauran gimbiyoyin suke zaune, tana isa ta nuna alamun rashin jin daɗi, ta zauna a kan kujerarta tana dafe kai, ta sanar da sarki da sauran gimbiyoyin cewa tana fama da tsananin ciwon kai, kuma watakila ba za ta iya jure tsawon taron ba.... Ta yi wannan dabarar ne domin ta samu damar sulalewa... Daga Kursiyyin Sarki ya jinjina kai sannan ya ce da ita. "Ki jira lokaci yayi, domin na ga ana ƙoƙarin rushe dokata..." Ayat wani irin bugun zuciya take ji, lokaci guda gumi ya fara yanko mata.. Sarki ya bayar da umarnin a ƙira duk ma'aikatan tsaro gaba ɗaya don a tantance su a filin fada, kuma ya buƙaci ganin wannan yaron mai suna Inuwa... Ganin hankalin kowa ya koma kan ma'aikatan da ke shigowa, Gimbiya Ayat ta ƙara tsorata domin ta fara jin daɗin fita.... Ta ƙara nemi izinin babban Sarki cikin muryar tausayi.... "Ranka ya daɗe, jiri na ɗibana, ina buƙatar na koma ciki na ɗan huta kafin taron ya yi nisa.".. Tana yi tana dafe goshinta ga wasu zafafan hawaye dake gangaro mata duk da tana rufe da rabin fuskarta da mayafi... Sarki Zaki, cikin nuna tausayi ga 'yarsa ya ba ta izini.... Ayat ta bar fadar da gaggawa, nan danan motarta ya kaita part ɗinta... tana isa sassan sirri na ɗakinta ta bankaɗe kayan gimbiyancin, ta matse kirjinta da zanen audugar nan, ta ɗauko rawanin ta ɗaura. Ta manna gashin baki da gemun ta na yaudara... Da gudu ta bi hanyar sirrinta ta fita wajen masarauta... Wani doki ta gani shi kaɗai ganin kar lokaci ya ƙure ne yasa ta hau dokin ta nufi babban fadar sarki .. Daidai lokacin da jami'an tsaro suka fara layi a filin fada, kuma aka fara neman sunan Inuwa, sai ga ta ta fito ta bangaren ma'aikata. Zuciyarta na bugawa cikin tashin hankali... Ta isa gaban Sarki, ta durƙusa a tsakiyar filin fada, a lokacin da duk idanuwan ma'aikata, da na sauran gimbiyoyin ke kanta. Ibrahim yana gefe yana kallon yadda Inuwa ya fito da kansa, ya lura da cewa yaron nan ko Inda-inda bai yi ba wajen amsa laifinsa, wanda hakan ya ba shi mamaki... Sarki Zaki ya daka tsawa yana kallon Inuwa... "Kai ne kake ikirarin sunanka Inuwa? Kai ne ka shiga ɗakin gimbiya Maayah ba tare da izini ba? Shin ka san hukuncin wanda ya keta alfarman masarautar Alhamra?" "Gafara nake nema, ya shugaban jarumai. Ni ne Inuwa wanda ya shiga ɗakin Gimbiya Maayah ba don keta alfarma ba, sai don isar da saƙon gaggawa da na ga ya dace ta sani." Duk fadar ta yi tsit. Ibrahim ya ƙurawa Inuwa ido, yana mamakin karfin zuciyar wannan yaron. Maayah kuma ta kasa ɗauke idonta daga kansa, tana jin wani irin kishi da fargaba a lokaci guda. Sarki Zaki ya ƙafe Inuwa da idanuwa masu firgitarwa kamar mai nazarin wani abu... Ayat da ta fahimci tana kan ƙwayar idon Sarki sai kuma wani irin zufa ya fara yanko mata, jiki na rawa tana haɗiyar yawu kamar wacce aka yanke wa hukuncin kisa... Domin ta san cewa Sarki yana da mugun wayo kuma waɗannan idanuwansa na halitta da wuri yake kama mutum mai laifi ko yake ƙoƙarin ɓoye wani abu... Magana ta fara a cikin ranta.. "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'unn, innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi rahmanu raheemm, a wannan lokacin nasan kashina ya bushe, domin sarki ya kamani, na shiga uku, na shiga uku, wayyo ni...." Sarki kuwa hannunsa yana kan talsumin takobinsa. Daidai lokacin da zai ba da umarnin a damƙe shi, sai muryar Gimbiya Maayah ta sake ratsa fadar... Ta ɗan gyara zama, tana kallon mahaifinta cikin natsuwa. "Abbah, ina neman afuwar ka ga wannan yaron. Ni na ba da umarnin a aiko min da wannan littafin domin ina da wani Assignment na makaranta da nake son kammalawa cikin gaggawa. Ganin cewa lokaci ya ƙure, sai na nemi jami'an tsaro su kawo min shi har ɗakina."... Wani irin dogon nishi duk mutanen fadar suka sauƙe. Ibrahim ya jinjina kai yana mai farin cikin jin hakan... Sarki ya kalli Maayah, sannan ya kalli Inuwa wanda ke durƙushe yana gumi.. "In har haka ne Maayah, me ya sa bai bayyana kansa ga babban jami'in tsaro ba? Me ya sa ya shiga ta hanyar ɓoye har sai da aka neme shi aka rasa a jerin sunayen ma'aikata?" Maayah ta yi murmushin ƙasaita... "Abbah, watakila tsoron kwarjininka ne ya sa shi kasa magana. Amma na tabbatar shi ne ya isar min da saƙon da na buƙata." Sarki Zaki ya numfasa, sannan ya kalli Inuwa... "Ta ya ka kasance a cikin jami'ai na alhalin baka da ƙirar jarumai?... Kai ɗan ƙaramin sauro ɗago ka kalli cikin idanuwana..." Anan fa Inuwa ya ƙara gane cewa Allah ɗaya yake, domin hakan da zai yi shine hanyar buɗewar tonon asirinsa... Haka yake ta nuƙu–nuƙu ya kasa ɗago wa... "Kaiii magana nake maka, a cikin jarumai na babu lusari mai ƙaramin ƙira kamar ka... Ta ya ka samu shiga cikin jarumai, kuma babu sunanka a cikin jerin jaruman masarautar nan, ban kuma sanka baaa...." Maayah sai murza hannunta take cikin damuwa, ta rasa ta yanda zata kare shi... Sai muryar babbar gimbiyar masarauta suka ji kamar daga sama... "To indai hakane, ya cancanci kisa domin ya karya doka, ya sanya tufafin jarumai ba tare da izinin mai martaba ba, wannan babban laifi ne..." Gimbiya Zayana ta furta tana ƙare wa Inuwa kallo da waɗannan cat eyes ɗinta, ga wasu zafafan Golden hair color yanda suka bazu a gadon bayanta.... Kana ganinta kasan iyalan turawa ne.... Inuwa ya ji wani irin murɗawar zuciya na tsantsar tsanar wannan babbar Yayar tasu, domin can jininsu bai haɗu ba kuma kusan shawarar ta Sarki yake ɗauka fiye da ta kowa.... Gimbiya Yumna a tsorace ta ce, "A'a wannan ai bai cancanci kisa ba, wannan ƙaramin abu ne za'a hukunta shi da kisa?..." Wani irin kallo Gimbiya Zayana ta wurga mata, har sai da ta shiga taitayinta sannan ta ce, "Kada ki ce zaki yi jayayya da hukuncin sarki, domin shawarata itace akan dai-dai..." Yumna ta sunkuyar da kai domin ita ɗaukan kanta take kamar ba gimbiya ba... Daga bisani cikin sanyin murya ta kuma cewa, "Na ke ga, duk wanda zai sanya kayan tsaro don ya kare martabar masarauta to ba maƙiyi bane, kuma inda ace akwai abin da yake ɓoye wa da an gano tintinin..." Maayah ta ƙara da cewa, "Gaskiya ne Abul, a dubi lamarin, a ƙyale shi ya cigaba da aikin da ya fara..." Sarki ya jinjina kai cikin kakkaurar murya ya furta. "Na ji daga gare ki Zayana, sannan na ji daga bakin ƙannenki Maayah da Yumnah, kasancewar Ayat ta koma part ɗinta....yanzu Inason jin daga bakin auta ta Firdos..." Chingching tana zaune ba abinda take sai game a waya, sai dariya take tayi tana wasan harbi... Duk abin da ya faru tin daga farko har zuwa yanzu bata san me ake tattaunawa akai ba.... Gimbiya Zayana a fusace ta ce "Wannan mahaukaciyar shawarar mai zata bayar?..." Wani irin kallo Sarki ya wurga mata, nan Zayana ta kawar da kai... Maayah itama ta ce, "Abul, dan Allah ka ɗauki shawarar mu, Chingching ba abinda ta nutsu ta ji a wannan tattaunawar..." Sarki bai biye musu ba, ya kalli Chingching sannan ya furta cikin sanyi murya "Mamana..." Ai Chingching hankali ya tafi ko ƙiran bata ji ba.... Sai da sarki ya yi magana da ɗaya daga cikin ma'aikatan akan su karɓi wayar... Hakan akayi a ruɗe ta ɗago tana tura baki cikin shagwaɓa, "Ku bani wayataaa..." Sarki a nutse yake mata magana. "Mamana ki dubi wancan ta durƙushe..." Ta kalli Inuwa wanda mahaifinta ya nuna mata sannan sarki ya cigaba da faɗin... "Mayaudarin jami'i ne, ya sanya kayan jarumai ba tare da tantance shi ba, shin wani hukunci za'a masa?..." Chingching tana turo baki ta ce, "Yoo too ya ɗago ya kalle ni mana..." A hankali Inuwa ya ɗago suka haɗa ido da Chingching domin lokacin da ya fita Chingching bata ri ga ta iso ba, saboda hakane yasa basu haɗu ba... Inuwa ganin ƙanwarsa yasa ya ji wani irin sanyi a ransa.. Chingching a ɗan ruɗe ta ce, "Laaaa!!! Aunty?..." Ta sauƙa daga kujerarta ta nufi Inuwa da sauri, tana zuwa ta durƙusa a gabansa... Shi kuwa Inuwa yanda kasan an caka masa mashi a saitin zuciya haka ya ji...ji yayi kamar ya haɗiye ransa ya mutu. Wani irin yawu ya haɗiya.. Duk mutanen wurin sai da suka sha mamakin jin Chingching ta furta Aunty Kuma wacce take ƙira da Aunty, Ayat ce... Sauran kuma Aunty wance... Chingching ta ƙare ta da kallo sai kuma ta sake turo baki ta ce, "Ohhhh! Ashe namiji ne, na ɗauka Aunty ce ai, na ga idanun iri ɗaya..." Kowa sauƙe numfashi yayi domin kowa yasan sokoncin Chingching... Ta koma ta je ta zauna sannan ta ce, "Wannan abokina ya mun kyau, kuma kayan jarumai sun masa kyau, kuma nima inada kyauu...." Sarki kawar da kai yayi domin bazai tsaya sauraron shirmen Chingching ba... Ya dubi Inuwa sannan ya ce. "Tashi ka tsaya! Saboda kariyarsu Gimbiya, na yafe maka yau. Amma daga yau, sunanka zai bayyana a jerin masu tsaro. Za ka koma ƙarƙashin kulawar Ibrahim kai tsaye... Shi ne zai kula da kowane motsinka, da kuma yi maka training yanda ya kamata...." Gabanta ya sake faɗuwa. Zama ƙarƙashin kulawar Ibrahim yana nufin cewa asirinta ya kusan tonuwa. Ibrahim mutum ne mai lura, kuma tana sane da cewa har yanzu yana mamakin ta... A ɓangaren Maayah kuwa, tana kallon Inuwa tana jin wani irin daɗi a ranta. Ta riga ta yi nasarar sa shi kusa da ita, domin tana da ikon ƙiran Ibrahim kowane lokaci don ya kawo mata shi... ✨ Bayan an tashi daga taron, Inuwa ya fito daga fadar da sauri yana son sulalewa ya koma part ɗinsa don ya sake komawa Gimbiya Ayat. Amma yana tafe, sai ya ji ƙatoton hannun Ibrahim a kafaɗarsa. Ibrahim ya rage murya yadda su biyu kawai za su ji.. "Kayi sa'a yau, Ɗan Ƙwaƙur. To Ɗan Ƙwaƙur yanzu ka zama nawa. Tunda hannunka nada laushi kamar na mace, ba zan saka ka aikin wahala ba. Aikinka shi ne, za ka riƙa yi min tausa, kana shafa min baya, sannan kana sosa min gashi idan na gaji da aiki. Ina son jin daɗin wannan laushin hannun naka.".. Ayat ta ji gabanta ya faɗi, amma dole ta amince don kar asirinta ya tonu. Ibrahim ya sa ta a gaba suka tafi sashen jami'an tsaro na yankinsa don tantance ta. Daidai lokacin da Ibrahim ya ɗan kauce don duba wasu takardu, Inuwa ta yi amfani da damar ta sulale da gudu ta hanyar sirri... Tana isa part ɗinta, ta ciccire kayan maza, ta yar da gashin baki da gemun. Ta sauƙe numfashi, sannan ta sanya asalin shigar gimbiyarta mai cike da ado da ƙawa... Ta ɗaura mayafinta na sirri wanda yake rufe fuskarta baki ɗaya. Wannan mayafin shi ne babban kariyarta, domin hatta Sarki Zaki bai san asalin kamannin fuskarta ba tun tana yarinya. Ta fito cikin izzah, ranta a ɓace, ba wai zargin shigar ɗakin Maayah ba ne ya fi damunta ba, a'a, labarin cewa Maayah na zuwa makaranta (Private School) a cikin Alhamra City yayin da sauran aka hana su fita ne ya ƙona mata rai... Tana fitowa daga part ɗinta, ma'aikata suka yi ƙoƙarin tare ta saboda dokar hana fita da Sarki ya bayar bayan kiran gaggawa. Ayat ta daka musu tsawa mai firgitarwa.. "To! Bamu gama meeting da Sarki ba! Bana son iskanci dallah!" Ma'aikatan suka ja baya a tsorace, suka ba ta hanya. Ta shiga motarta ta alfarma, security ya ja ta har zuwa Centre of the Kingdom... Ayat ta shiga fadar cikin takun ƙasaita. Ta tadda sauran gimbiyoyin a zaune tare da Sarki.. Gimbiya Zayana tana zaune cikin takama da izzah. Ita mutum ce mai zafi da mulki, kuma ko kaɗan ba ta ƙaunar Ayat, musamman yadda take rufe fuskarta... Gimbiya Yumna ita kuma tana zaune cikin sauƙin kai da fara’a.. Gimbiya Maayah kuwa tana nan kanta a sunkuye, tunanin Inuwa kawai take yi a ranta... Gimbiya Chingching tana zaune kusa da kujerar Sarki. Tana shiga, Chingching ta miƙe da gudu ta zo ta rungume ta.. "Aunty na! Nayi kewarki sosai! Akace kin koma part ɗinki kanki na ciwo, naji ba dadi... sai kuma gaki kin dawo!".. Ayat ta rungume ƙanwarta tana jin sanyi a ranta. Yumna ma ta ƙaraso suka rungumi juna cikin mutunci. Amma Zayana tana ganin Ayat ta ja tsaki, ta kauda kai cikin ƙyama.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 6️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Ayat tana tsaye a tsakiyar fadar, ta gama kallon sauran gimbiyoyin daga sama har ƙasa, musamman Maayah wacce aka fifita ta da fita makaranta. Ta ƙarasa gaban Sarki Zaki, ta tsaya tana kallon kujerarsa ta mulki. Ranta ya gama ɓaci, tana jin cewa mahaifinsu ya yi fifiko a tsakanin ƴaƴansa.. Ta buɗe baki cikin muryar ƙasaita ta furta. "Gafara nake nema ya Shugaban Masarauta. Na dawo ne domin na ji daga gare ka... Wace irin doka ce ta ba wa Gimbiya ɗaya damar fita zuwa makaranta a tsakiyar birni, yayin da sauran gimbiyoyin ke zaman mazauni a cikin ganuwar fada? Shin wane aibi ne gare mu da ba za mu iya fita kamar Maayah ba?" Duk fadar ta yi tsit. Zayana ta ɗago ido tana kallon Ayat, tana jiran ganin yadda Sarki zai amsa wannan ƙalubalen. Maayah itama ɗagowa tayi tana kallon ta ganin yanda take ƙalubalantar makarantar ta.. Sarki Zaki ya kalli Ayat wacce ke tsaye tana huci, idanunsa sun canza launi. Ya fahimci cewa wannan karon, bawai maganar saɓa doka ba ce kawai, fushin da ke cikin zuciyar Ayat ya haura matakin da zai iya controls ɗinsa da umarni... Cikin sanyin murya mai cike da kwarjini, ya ce "Ki sassauta murya da zafin rai a cikin wannan fadar. Wannan yanayin za ki nuna shi ne a gaban bayinki, ba a gaban Sarki ba." Gimbiya Zayana wacce take jiran dama ta tanka wa Ayat, ta harare ta cikin izzar turawa, muryarta na fitar da nuna fin ƙarfi ta ce, "Wannan saɓa doka ne ya shugaban masarauta! Hukuncin da ke rubuce a littafi shi ne duk wanda ya ɗaga murya ko ya nuna fusata, in dai ba sarki ba ne, to za a kulle shi a ɗakin duhu muddin gimbiya ce. In kuma a cikin bayi ne, to ɗaurin rai da rai ne... don haka hukunci ya tabbata a kan Ayat!".... Ayat ta juyo cikin zafin rai, ba tare da tsoro ba, ta daka wa Zayana wani irin tsawa da ya sa fadar ta amsa kuwwa... "Hukunci bai tabbata a kaina ba ZAYANA! Ki dakata mini haka! Ina magana ne da mahaifina, ba da ke ba. Don haka ba na son shishshigi!" Zayana ta gigice, ta miƙe tsaye jikinta na rawa saboda tsawar da Ayat ta yi mata. Ta dubi Sarki cikin neman goyon baya ta ce "Ya Sarki! A matsayina na babbar gimbiya, wacce na fisu a shekaru da komai, ya kamata Ayat ta riƙa yi min tsawa haka? In da a gaban ma'aikatana ne, ba ka ganin za ta kunyata ni ne? A ɗauki hukun........." Sarki Zaki bai bari ta ƙarasa ba, ya ɗaga mata hannu cikin alamun ta yi shiru. Ta koma ta zauna tana huci. Idon Sarki ya koma kan Ayat. Cikin tsatstsauran murya ya ce "Ɗaga murya da fusata ne zai sa na ji tsoronki na amsa miki tambayarki? Kada ki kuskura ki tabka babban kuskuren da za ki yi nadama, Ayat. Tambayar taki kuma ba zan amsa miki ba in dai da wannan yanayin naki ne." Ayat ta jinjina kai, hawaye ya cika mata ido amma ta danne. Ta nuna Chingching sannan ta cigaba.. "Gaskiya ne, na fahimta... kana nuna fifiko ne a tsakaninmu. Ga ƙaramar ƙanwata, yarinya ce ƙarama amma me ya sa ba za ta je makaranta ba? Oh, kana gadara da cewa ana zuwa koya mana boko da Arabic har gida ko? To me ya sa Maayah take fita? Sannan kana maganar cewa zan tafka kuskuren da zan yi nadama? Uhm, dama can na fahimci ba ka ƙaunata... baka sona ko kaɗan!" Muryar Ayat ta fara rawa yayin da ta jefa babban zargi... "Anya kuwa kai ka haife ni? Ina tantama, domin tun ina ƙaramar yarinya nake fuskantar ƙalubale. Tabbas na ɗaga murya a fadarka, na kuma cancanci hukunci. In ma kisa ne, a yi min, domin na fi son hakan! Na gaji da duniyar nan da take cike da alatu wanda babu farin ciki a cikinta. A koda yaushe ina fatan na kasance a cikin bayinka domin sun fini wargi da walwala a cikin masarautar nan!".. Zayana ta sake fusata ta ƙira sunanta. "AYAT!" Ayat ta ɗaga mata hannu cikin zafin rai. "Ba da ke nake ba!" Idanunta sun yi jawur tsabar kuka. Duk fadar ta yi tsit. Chingching ta fashe da kuka saboda yadda ta ga Yayarta ta fita hayyacinta.. Maayah kuwa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, tana jin laifin kanta ne ya sa Yayarta cikin wannan halin... Sarki Zaki ya ƙura wa kwayar idon Ayat ido, ransa ya ɓaci matuƙa, amma akwai wani ɓoyayyen abu da ya gani a cikin idanun nata wanda ya sa ya yi shiru yana nazari. Sarki Zaki ya miƙe tsaye, fuskarsa a murtuke tamkar hadari. Bai ce uffan ba, kuma bai ɗauki hukunci akan Ayat ba, ya juya cikin takun fushi ya bar fadar ya nufi sashensa na musamman. An bar gimbiyoyin nan biyar a tsaye, kowacce da abin da yake damunta.. Gimbiya Maayah ta matso kusa da Ayat cikin sanyin jiki, tana son ba ta haƙuri.. "Aunty Ayat, dan Allah..." Ayat ba ta bari ta ƙarasa ba, ta ɗaga mata hannu cikin dakatarwa. "Ba na son jin komai daga gare ki, Maayah. Ki tafi kawai." Maayah ta haɗiye yawu, ranta ya ɓaci, ta juya ta fice daga fadar inda motocinta suka ja ta zuwa part ɗinta. Yumna ta ƙaraso kusa da Ayat, ta kamo hannunta tana shafawa cikin sigar rarrashi, "Dan Allah kiyi haƙuri Aunty Ayat, gaba ɗaya ranku ya ɓaci daga ke har Sarki..." Ayat ta jinjina kai, muryarta ta ɗan yi sanyi ta furta "Naji, Yumna. Ke ma ki tafi part ɗinki." Bayan Yumna ta tafi, sai aka bar Zayana da Chingching wacce ke tsaye tana kuka a gefe. Zayana ta taka har gaban Ayat, tana harararta da idanunta na kyanwa... "Gimbiya sakaliya marar kunya! Kin fusata Sarki wanda hakan zai janyo miki tashin hankali. Dole kiyi respect ɗina tunda ni ce babbarku. Idan kuma rashin kunya ce kamar mahaifiyarki, to kuwa zakiyi asara duniya da lahira!" Ayat ta juyo a slow, ranta ya ƙara ɓaci.. murmushi kawai ta sake tare da faɗin.. "Mahaifiyata kowa zai yi mata kyakkyawar shaida akan ita mutumiyar kirki ce. Ta rasa rayuwarta ne a ɗakin mijinta, tana haihuwar ƙanwata Firdos... Ke kuma fa? Mahaifiyarki tana can Australia zaman zawarci!" Zayana ta fusata ta ce, "To naji! Amma uwar tawa ai a gidan mulki take a can Australia ba zaman ƙasƙanci ba. Kin zo zaki zubar wa masarauta mutunci, wallahi sai an ɗau hukunci akanki!" Ayat ta yi murmushin raini sannan ta ce, "Zubar da mutunci wa masarauta yayi kamar yadda kika ajiye mata ƴar waje a cikinta? Ƴa fa kike da ita wacce ba ta sunnah ba! Kuma tana nan a cikin masarautar nan. Ke ba'a ɗauki hukunci akanki ba sai ni?" Wani irin jiri ya kwashi Zayana, ta fusata ta ɗaga hannu za ta mari Ayat. Cikin zafin nama irin na jaruman tsaro ta cafke hannun ta murɗe shi kaɗan... Wata dattijuwa, tsohuwar ma'aikaciyar fada da ta raine su, ta shigo. "A'a, ya haka? Gimbiyoyi da faɗa kuma?" Zayana ta daka mata tsawa. "Ke kuma ina ruwanki tsohuwar banza!" Ayat ta mayar mata, "Kinga irin rashin kunyar ba? Tsohuwar da tun kafin a auro uwar ki take masarautar nan, amma kike zaginta!".... Zayana tana nuna Ayat da yatsa ta ce, "Har yanzu baki san komai game da ni ba, da kuma ƴar da nake da ita, amma lokaci zai yi da za ki ji koma meye kuma kafin nan sai kinyi nadama domin mahaifiyata ba za ta taɓa ƙyale ki akan wannan batun ba...." Daga nan ta daka uwar tsaki, ta fice tana huci ta shiga motarta.. Chingching ta ƙaraso tana kuka ta rungume Ayat. Ayat ta lallaɓa ƙanwarta, ta sanya ta a mota aka kai ta part ɗinta, ita ma ta shiga tata motar don komawa ɗaki, ranta cike da tunanin yadda rayuwarta ta kasance a haka... ✨ Misalin ƙarfe 8 na dare, Gimbiya Ayat tana zaune a cikin bedroom ɗinta, ranta a jagule da tunanin rigimar da suka yi da Zayana da kuma bacin ran da ta ga mahaifinta ya shiga... Domin har cikin ranta bata son wannan zafin ran natan, tana so ta rage amma ta kasa... Tana cikin wannan halin, sai taji ƙiran gaggawa daga babban elevator ɗin part ɗinta... Ma'aikatan part ɗin gabaɗaya sun ruɗe, kowa na girgiza ganin Sarki Zaki da kansa ya tako har sashen Gimbiya Ayat... Wannan lamari ne da ba a saba gani ba, domin sarki ƙiran gimbiyoyinsa yake yi zuwa fada, ba shi yake zuwa gare su ba. Ma'aikatan mata duk suka zube a ƙasa suna gaishe shi cikin girmamawa... Sarki ya haura stairs ya nufi ɗakin Ayat. Tana jin muryar cewa Sarki ya iso, ta miƙe tsaye cikin mamaki da fargaba. Yana shigowa ɗakin da siffarsa ta Zaki mai ban tsoro, Ayat ta ɗago kai cike da firgici.. Amma yana haɗa ido da ita, sai wani abin al'ajabi ya faru. A gaban idon ta, siffar Zakin nan ta ɓace, Sarki ya koma asalin mutumtaka. Farin dattijo kyakkyawa mai cike da kwarjini da muradi ya bayyana. Wani irin sanyayyen murmushi ya sakar mata, wanda ya nuna cewa duk fushin da aka gani a fada, ya riga ya yafe mata. Ayat ma ta kasa boye farin cikinta, murmushi ya suɓuce mata a ɓoye cikin mayafinta. Ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta. Daga bisani cikin sanyin murya ya furta. “Ayat…” Sarki ya zauna a bakin gadonta na alfarma, ta durƙusa ta gaishe shi cikin ladabi. Bayan ta gaishe shi, Sarki ya nuna mata kusa da shi.. “Ki zauna.” ya faɗa yana kallonta.. Ta zauna, zuciyarta na bugawa kamar zata fito. A wannan lokacin, duk wani ɓacin rai da rigimar da aka yi a fada tsakaninta da shi ya gushe. Sun zauna tamkar wasu aminan juna, inda Sarki ya zo ne domin ya sanyaya zuciyar ɗiyarsa wadda yake gani a matsayin wata bangare ta rayuwarsa. Sarki ya numfasa, ya kalli Ayat sannan ya fara magana cikin sanyi.. “Na zo ne ba domin in hukunta ki ba.” “Na zo ne domin in cire miki wani nauyi daga zuciyarki.” Ayat ta ɗago kai a hankali. Idanunta suka haɗu da nasa... Ya cigaba da faɗin “Na san kina tunanin an fifita Maayah a kanki ko?.” “Na san kina jin kamar an tsare rayuwarki ne, ita kuma an buɗe mata kofa.” Ayat ta haɗiye yawu. Hawayen da ta riƙe tun da rana suka fara taruwa... “Abul…” ta faɗa da muryar da ke rawa, “Me yasa ita take fita makaranta, mu kuma a’a?” Sarki ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana zaɓar kalmomi. Sai ya ce a hankali “Tun kafin in auri mahaifiyarta… Muka yi yarjejeniya da ita.” Ayat ta buɗe ido tana kallonsa a yayin da ya cigaba. “Yarjejeniyar cewa Maayah ba za a hana ta ilimi ba. Ta dage, ta ce rayuwar ‘yarta ba za ta tsaya a bango ba.” Ya ɗaga idonsa zuwa Ayat.. “Ba fifiko bane, Ayat. Alƙawari ne da aka riga aka ɗauka.” Ayat ta sauke numfashi mai nauyi. Zuciyarta ta ɗan yi sanyi… amma ba gaba ɗaya ba. “To ni fa?” ta tambaya a hankali. “Ni ba ‘yarka ba ce?” Sarki ya miƙa hannu, ya ɗora shi a kan nata.. “Ke ‘yata ce. Kuma akwai abubuwan da na ke kare ki daga gare su.” Ya tsaya yana nazari tare da furta... “Ba hukunci bane. Kariya ce.” Daga nan ya miƙe tsaye. “Ki yarda da ni, Ayat. Ba duk abin da aka rufe miki, an rufe shi ne don cutar da ke ba.” Sarki ya kamo hannun ta tare da miƙar da ita, ya matse shi a hankali yana kallon cikin idanunta waɗanda har yanzu akwai sauran jajirwar kuka.. "Ayat, ki duba fuskata. Ba zan taɓa iya jure ganin waɗannan idanun naki cikin hawaye ba. Fushin da na nuna a fada ɗazu, ba fushin tsana ba ne, fushi ne na uba da yake son kare mutuncin ƴarsa a gaban jama'a. Ki yafe wa mahaifinki idan na sa ki jin cewa ba kya da daraja a wurina." Ayat cikin muryar kuka ta ce, "Abul, na zata ka manta da ni ne. Na zata Maayah kawai kake so shi ya sa kake ba ta damar da kake haramta mana." Ya juya ya nufi ƙofa, sannan ya tsaya. “Kada ki bari shakku ya cinye zuciyarki.” Daga nan ya fice, ƙofar ta rufe a hankali. Ayat ta zauna ita kaɗai a ɗakin. Zuciyarta ba ta sami cikakkiyar amsa ba… amma ta daina jin wani ciwon yanzu, ganin mahaifinta ya tako har zuwa yanda take.... ✨✨✨ Washegari, garin Alhamra ya waye da wani irin sanyi mai ratsa jiki. Ayat ta tashi ne ba don ta koshi da barci ba, sai dai don nauyin aikin da ke kanta a matsayinta na Inuwa. Idanunta sun ɗan yi lupu-lupu saboda rashin barci da tunani wanda ya hana ta runtsawa... Ta shirya tsaf, ta sanya ɗaurin kirjinta, ta sanya kayan maza, sannan ta ɗaura rawanin ta duk ya rufe goshin. Ta sulale ta fita daga part ɗinta ta nufi sashen jami'an tsaro.... Tana isa sashen su Ibrahim, ta tarar da shi a zaune a wani fili na sirri da yake hutawa. Yana ganin ta, sai ya saki wani murmushi wanda ya nuna cewa ya daɗe yana jiran ta. Babu sauran zargi a tare da shi, sai dai wani irin sha'awa na son jin laushin hannun yaron da yake ganin tamkar mace... "Ka zo kenan, Ɗan Ƙwaƙur?" Ibrahim ya faɗa yana miƙewa. "Na zata ka gudu ne saboda rigimar da aka yi a fada jiya. Zo nan, yau jikina duk a mace yake, ina buƙatar wannan tausan naka." Ibrahim ya cire babbar rigarsa, ya rage daga shi sai farar singlet wadda ta nuna ƙwanjin hannunsa da faɗin ƙirjinsa. Ya kwanta rubda-ciki a kan wata shimfiɗa ta alfarma, sannan ya yi nuni ga Inuwa.. "Fara daga kafaɗata, ina jin zafi sosai a wurin." Ayat ta matso jiki na ɓari. Ta sanya hannayenta masu laushi a kan kafaɗun Ibrahim. Da zaran ta fara murzawa, Ibrahim ya sauƙe wani nannauyan numfashi.. "Masha Allah... Hannunka akwai albarka, Inuwa.... Wannan laushin hannun naka ko mace ba lallai ta kasance da shi ba. Sosa min gashin kaina ma yanzu." Yayin da Inuwa yake sosa masa gashi tare da shafa masa baya a hankali, sai tunanin labarin da Sarki ya ba ta jiya ya dawo mata. Tana tunanin yadda rayuwarsu take a matsayin gimbiyoyi amma a yau gata tana tausa wa ma'aikacin mahaifinta. Wani ƙwallon kuka ya taso mata, ta kasa haɗiyewa... Ibrahim ya ji jikin Inuwa yana ɗan rawa, kuma ya ji kamar wani abu na ɗiga a bayansa. Ya juyo da sauri ya ga Inuwa ya sunkuyar da kansa ƙasa, kuka yake yi ƙasa-ƙasa.. "Lafiya? Me ya faru Inuwa?" Ibrahim ya tashi zaune cikin damuwa, ya kamo hannun Inuwa. "Ko tsokanar da ma'aikata ke maka ce ta sa ka kuka? Ko kuma Gimbiya Maayah ce ta sanya ka wani aikin da ya fi ƙarfinka?" Ayat ta kasa magana, sai kawai ta ƙara sunkuyar da kanta, tana jin dumin hannun Ibrahim a nata. A wannan lokacin, Ibrahim ya ji wani irin tausayin yaron ya kama shi, ya manta ma da cewa shi Master ne, ya fara lallashin Inuwa kamar ƙaninsa... A lokacin da Ibrahim ya ga Inuwa yana kuka, zuciyarsa ta karye. Bai san lokacin da ya miƙa hannu ya janyo yaron zuwa kirjinsa ba, ya rungume shi sosai yana shafa bayansa don rarrashi.. Ayat ta ji wani irin shock ya ziyarci ilahirin jikinta. Tsoro da fargaba suka ziyarce ta. A ranta tana jin zafi da ɓacin ran yadda namiji ƙato, wanda ba muharraminta ba, ya rungume ta. Tana jin kamar ta keta hurumin asalin gimbiyancinta da mutuncinta, amma tana tsoron ko kaɗan ta nuna hakan don kar asirinta ya tonu a hannun Master Ibrahim... Shi kuwa Ibrahim, rungumar da ya yi wa Inuwa ta jefa shi cikin wani yanayi na daban. Ya ji jikin yaron ya yi masa laushi da sanyi kamar na mace, wani irin kasala da feelings suka fara bin jijiyoyinsa. Ya fara sauƙe nannauyan numfashi, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi. Ya rasa gane me yake faruwa da shi. "Me yake faruwa da ni? Dan uwana namiji ne fa amma nake jin wannan yanayin? Tir da shaiɗan! Allah ya raba mu da wannan masifar," ya faɗa a ransa, yana kokarin kore tunanin cewa jikin da yake rungume da shi ba na namiji ba ne. Jin yadda Master ya fara sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi ne ya sa Ayat firgita... Ta yi sauri ta janye jikinta ta ja da baya tana kallonsa da tsoro a idanunta. Ba tare da ta ce uffan ba, ta juya ta bar wurin da gudu tana kakkaɓe jikinta... Inuwa ya nufi bakin gate ɗin fada cikin gaggawa, tana son barin harabar fadar baki ɗaya don ta je bakin kogi ta huta. Ta isa wurin littafin shige-da-fice ta fara signing.... Daidai lokacin, sai ga wata mota ta alfarma ta nufo gate din. Gimbiya Maayah ce a ciki, tana sanye da tsararren uniform na makarantarta mai kyan gaske. A ka'ida, Maayah tana da mugun girman kai, ba ta taɓa leƙo kai ta kalli jami'an tsaron da ke gaishe ta ba.. Amma yau, ganin Inuwa tsaye a bakin gate yana rubutu, ya sa ta zabura....Ta rage gilashin motar kaɗan, ta leƙo tana kallon sa ta cikin glas. Zuciyarta ta harba, wani irin masifar so ya sake mamaye ta... Inuwa ya san cewa motar Maayah ce, kuma ya fahimci tana kallonsa amma ya ƙi ɗagowa. Wani irin raɗaɗi ya ji a zuciyarsa na ganin yadda Maayah ke fita cikin lumana da mota zuwa makaranta, yayin da ita kuma take cikin shigar maza tana badda kama tana fuskantar kaskanci... Duk da tasan dalilin mahaifinsu na barin Maayah ta fita, hakan bai hana ta jin kishi ba... Maayah kuwa, har motarsu ta fice daga gate ɗin, tana nan maƙale a glas ɗin motar tana waiwayo baya tana kallon Inuwa. Ta kasa ɗauke idonta daga kansa, tana jin cewa yaron nan ya riga ya tafi da duk kan hankalinta.... Ayat tana kan dokinta, tana tafiya cikin daji kaɗan da zai kaita zuwa bakin kogi. Zuciyarta har yanzu tana bugawa saboda rungumar da Ibrahim ya yi mata da kuma kallon da Maayah ta jefa mata. Tana cikin wannan tunanin, sai idonta ya sauƙa akan wata Kuliya kyakkyawa, mai laushin gashi, kwance a ƙasa tana nishi... Ganin yadda kuliyar take nuna ciwo a kafar hagu, Ayat ta kasa sharewa. Duk da shigar maza take yi, zuciyarta ta mace mai tausayi ta motsa. Ta yi sauri ta sauƙa daga kan dokin ta ƙarasa kusa da ita. Ta ɗauki kuliyar ta ɗora a kan cinyarta, tana rarrashinta da murya kasa-kasa... "Kiyi haƙuri kyakkyawa, yanzu zaki ji sauƙi..." Ta ciro wani mai na musamman (Pain relief ointment) wanda take yawo da shi ko da yaushe a matsayinta na jami'in tsaro. Ta shashshafa wa kuliyar maganin a wurin ciwon, sannan ta ciro wani tsumma mai tsafta ta ɗaure mata ƙafar. Maganin yanada tasiri sosai, domin jininsa na ratsa jiki... Tana ajiye kuliyar, sai ga ta ta fara takawa. Ko da yake tana ɗan dingishi, amma zafin ya mutu baki ɗaya. Ayat ta bi ta da kallo tana murmushi har ta ɓace a cikin ciyayi... Ganin kuliyar ta tafi cikin ƙoshin lafiya ya ba ta wani irin nutsuwa. Ta sake hawa dokinta ta ƙarasa can bakin kogi, inda iska mai daɗi take busawa... Tana isa wurin, ta sauƙa ta fuskanci kogin wanda ruwansa yake sheki kamar lu'u-lu'u. Wannan shi ne kaɗai wurin da take jin tana da yanci, wurin da tsuntsuwarta take jiran ta, kuma wurin da take iya tuna abokinta na yarinta... Ayat ta kalli kewayen kogin, ta ga kowa shiru, babu kowa sai sautin tsuntsaye da busar iska. Tunanin ɓacin ran da take ciki da ƙuncin da ta samu wurin Ibrahim ya sa ta jin tana buƙatar wanka don ta wanke damuwar zuciyarta... Ta ajiye dokinta a gefe, ta nufi bakin ruwan tana jin kamar duniyar tana hannunta... Ba ta sani ba, a bayan bishiyar da tsuntsuwarta take, akwai wata halitta mai kwarjini a tsaye, cikin shigarsa ta fararen kaya masu daukar ido, dogon farin gashinsa yana kaɗawa a cikin iska... Ransa a ɓace yake, yana tunanin meyasa wannan yaron ya ƙara ƙetare iyakar yankin da ya zaɓa don hutawa a duniyar mutane. Hannunsa ya fara miƙa wa don ƙiran takobinsa na sihiri don ya halaka shi, amma abin da ya gani ya sa shi daskarewa a wurin... A gaban idonsa, yaga Inuwa ya cire rawanin kansa ya jefar a gefe. Sannan ya kwance ribon ɗin gashinsa, sai ga wani uban gashi, baƙi mai santsi ya zubo har gadon bayanta zuwa kunkumi... King Diamond ya zaro ido cikin mamaki. A tunaninsa namiji ne, amma sai yaga abin ya sauya. Ya kalli yadda take fincike gashin baki da sajen da gashin girar da ta ƙara don badda kama. Sannan ta fara ɓalle rigar mazan dake jikinta ɗaya bayan ɗaya... Idon King Diamond yana kanta, ya kasa ko kyafta idon. Ganin surar tsararriyar mace, mai fata mai sheƙi da kwarjini ya bayyana a gabansa, ya sa ya ji wani irin Shock wanda bai taɓa ji ba a duk tsawon mulkinsa na duniyar aljanu... Ayat kuwa, tana jin daɗi ba tare da sanin cewa idon sarki aljani yana kanta ba. Ta rage saura iya short nicket da bra, gashinta a kwance a bayanta. Ta fara takawa a hankali tana shiga cikin sanyin ruwan kogin. Tana zura kafarta, wani daɗi ya ratsa ta, ta lumshe idanunta tana murmushi.. Ta nitse a cikin ruwan tana wasa, tana iyo cikin nishaɗi kamar wata tsuntsuwar ruwa... King Diamond yana nan a tsaye tamkar gunki, ya kasa motsawa. Kyan Ayat da irin yadda take wasa a cikin ruwan ya taɓa wani sashi na zuciyarsa da ya daɗe a bushe.... Yana tsaye a ɓoye, yana kallon ta yayin da take wasa a ruwa. Kwatsam, sai tunanin tattaunawar da suka yi a baya ya dawo masa. Ya tuna yadda ya ji wani abu game da wannan yaron amma bai ba shi muhimmanci ba.. Ya dunƙule hannunsa, ya lumshe idanuwansa, nan take siffarsa ta mutum ta ɓace, ya koma siffar aljan wadda mutum ba zai iya ganinsa ba. Ya sulale zuwa tsakiyar ruwan, ya tsaya daidai saitin inda take wasanta. Ayat tana nishaɗi, tana nitsewa tana fitowa tana dariya ita kaɗai, ba ta san ana kallonta ba. Sautin dariyarta ya fara ratsa kwakwalwar King Diamond. Wannan dariyar ta faɗo masa da irin dariyar Ayat tana yarinya iri ɗaya ce, ba ta sauya ba... Ya ƙura mata idanu, yana kallon kwayar idonta domin tabbatar da wacece ita. Abin da ya gani ya sanya shi tsinci kansa cikin wani sanyayyen murmushi... "Ayat ɗina ce..." Ya faɗa a ransa. Wannan dariyar ba za ta taba ɓace masa ba. A lokaci guda, ya ji wani irin shauƙi na son ya rungume ta.. Yanke hukunci ya yi akan ya bayyana kansa gare ta a yanzu. Ya lumshe ido, nan take ya dawo siffarsa ta mutum sanye da fararen kaya da dogon farin gashinsa yana sheƙi a saman ruwan. Ya tsaya daidai gabanta, idanunsa na kallon kyakkyawar fuskarta. Ayat ta sa hannu ta shafe fuskarta domin ta goge ruwan da ya taru a idonta. Tana buɗewa, sai ta yi ido huɗu da wannan halitta mai ban tsoro da kwarjini a lokaci guda. Ganin dogon farin gashinsa da shekin da yake yi ya sanya ta firgita matuƙa.....kuma bata san da mutum a wurin ba kwatsam ta ganshi a ruwa tare da ita... Ba ta san lokacin da ta saki wani irin mahaukacin ihu ba. Saboda tsananin gigita da tsoro, numfashinta ya tsaya, nan take ta sume ta faɗi cikin ruwan. Ta fara nutsewa zuwa kasan kogin, gashinta yana yawo a saman ruwan... Ya tsaya cak a saman ruwan yana kallon inda take nitsewa, ya ji wani irin mamaki ya ziyarce shi.. Ya fara duban jikinsa yana jujjuya hannayensa da kallon fararen kayan jikinsa, a ransa yana tambayar kansa, "Me kyakkyawar yarinyar nan ta gani a jikina da har ta kai ga yanke jiki ta suma? Shin kwarjini na ne yayi mata yawa ko kuwa muni ne dani?..." 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 7️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* A yayin da motocin alfarma suka tsaya a harabar makarantar Alhamra International Elite School, jami'an tsaro suka zagaye motar Maayah. Tana fitowa wani irin sanyi da shiru suka ratsa ko'ina. Daliban da ke wasa suka tsaya cak, malamai da ke tafiya suka gyara tsaiwarsu.. Maayah tana takawa ne cikin ƙasaita, fuskarta babu ko ɗigon murmushi, idanunta suna kallon sama kamar babu kowa a gabanta. Wannan shi ne ainihin halinta Izza, gadara, da nuna mulki... Tana shiga cikin ajin, duk ɗaliban suka miƙe tsaye, kowanne ya durƙusa har ƙasa yana kwasar gaisuwa. "Barka da isowa, Gimbiya Maayah!" Ko kallo ba su isheta ba, ta wuce kai tsaye zuwa nata Seat ɗin. Wurin zamanta ya bambanta da na kowa, domin sarki ya bayar da umarnin a yi mata ado na musamman na sarauta, kujerar tana da laushin gaske kuma an yi mata ƙawa da zane na musamman.. Malami ya shigo aji domin koyarwa, amma yana ganin Maayah ta cire wayarta ta zamani tana danne-danne, sai ya ji wani irin fargaba. Malamin ya san cewa Maayah ba ta sauraron karatun, amma ba shi da ikon buɗe baki ya ce ta ajiye wayar.. Duk da abun yana cin ransa da na sauran malamai, sun gwammace su yi shiru da su ɓata wa Gimbiya rai, domin kuskure ɗaya zai iya sa su rasa aikinsu ko ma fiye da hakan..... Maayah tana zaune cikin Miskilanci, tana ganin hoton Inuwa daga cikin zuciyarta, tana murmushin mugunta yayin da kowa ke cikin tsoro. Koda lokacin breakfast ya yi, babu ɗalibar da ta isa ta matsa kusa da Maayah ba tare da izini ba. Tana tafiya ne tamkar tana tattaka lu'u-lu'u. Duk wanda ya gitta ta, dole ya sunkuya... Wannan makarantar ta zama karkashin ikon Maayah, inda kowa ke fargabar idanunta. Ita a ranta, tana ganin kanta ta fi kowa daraja, kuma duk ilimin da ake koyarwa ba wani abu ba ne a gare ta, tunda ita Gimbiya ce kuma zuciyarta ta riga ta tafi ga wani jami'in tsaro wanda take tunanin talaka ne.... Sai a wannan lokacin Hafsat ta zo makarantar, anan motarta ta tsaya bodyguards ɗinta suka buɗe mata ƙofa ta fito sanye da ƙaton baƙin glass tana tauna chewing gum... A duk faɗin makarantar, idan ka ga Maayah to tabbas za ka ga Hafsat a gefenta. Hafsat ba wai kawai ƙawa ba ce ita ce mutum ɗaya tilo da Maayah take sauraronsa, domin matsayinta na ƴar Shugaban ƙasa ya ba ta damar da ko malamai ba su da ita. Duk da Hafsat tana da nata girman kan, amma a gaban Maayah ita kiyashi ce.... Hafsat ce take taya Maayah rarraba idanu ga sauran ɗalibai, kuma ita ce take ba ta labaran abubuwan da ke faruwa a wajen masarautar Alhamra... A lokacin da malami yake tsaka da koyarwa, Hafsat za ta juyo ta raɗawa Maayah wata magana, su fara yin dariyar ƙasƙanci suna kallon malamin. Malamin zai ji ransa ya ɓaci, amma ganin ɗiyar Sarki da ɗiyar Shugaban ƙasa sun haɗe, sai kawai ya sunkuyar da kansa ya ci gaba da rubutu a board... Hafsat ta kalli Maayah ta ce, "Bestie, kalle shi yadda yake ta zufa, wai shi malami. Idan naso yau zan sa Daddy ya dakatar da shi daga aiki." Maayah kawai murmushin gefen baki take yi, tana jin daɗin yadda kowa ke ƙarƙashin ikon su. A lokacin da suke zaune wanda ko wacce ta kasance kujerar zamanta daban, Hafsat ta lura Maayah ba ta hayyacinta, sai duba waya take yi. Ta matso kusa da ita ta ce, "Maayah, tun ɗazu kanki yana cikin waya. Ko akwai wani kyakkyawan ɗan Minister ne da kike boye min? Ko kuma wani Prince kika samo?" Maayah ta yi ajiyar zuciya, ta kalli Hafsat cikin sanyin murya wanda ba ta saba yi wa kowa ba ta ce. "Hafsat, akwai wani yaro a masarautarmu. Ba Prince ba ne, jami'in tsaro ne kawai... amma tunaninsa ya hana ni barci. Shi ne mafarkina." Hafsat ta zaro ido cikin mamaki, "Jami'in tsaro? Maayah, kin san matsayinki kuwa? Yaya za ki so talaka?" Maayah ta harari Hafsat, "Kada ki sake ƙiransa talaka. Kuma wannan sirri ne tsakanina da ke. Idan wani ya ji, zan iya yanke alaƙa da ke." Bayan an tashi, Hafsat da Maayah suka fito kowa na takun alfarma. Motocin tsaro na fadar shugaban ƙasa da na masarautar Alhamra suka cika harabar. Hafsat ta yi wa Maayah sallama ta shiga tata motar, yayin da Maayah ta shiga tata, ranta yana ƙara kishirwar ganin Inuwa yayin da take komawa gida.... ✨✨✨ A bangaren Gimbiya Firdos, wacce kowa ya sani da Chingching, ana tsaka da hargagi a cikin ɗakin wanka. Uma Altine tana ƙoƙarin yi mata wanka, amma Chingching ta sa kuka tamkar dukanta akayi.. "Wayyo Daddyyyy! Kazo ka taimake ni, Uma Altine za ta cire min nonuwanaaa!" Ta furta tana wani irin zalle-zalle a cikin ruwan ɗumi... Uma Altine ta zaro ido, ta rasa inda zata sa kanta don kunya da mamaki, ta ce. "Haba Auta! Ki rufa min asiri don Allah. Ta ya zan cire miki nonuwa kuma?" Chingching ta turo baki, cikin shagwabar da ta zama jikinta ta ce... "Yooo, ba ke kike zuba min ruwan zafi a kansu ba?" Uma Altine ta kusan yin dariya amma ta dake, ta kalli yarinyar ta ce "Ina suke to? Ni ba na ganinsu ai." "Ni dai ki samu ki yi min wankan, kuma wallahi kika jiƙa min gashina sai na gaya wa Daddy!" Chingching ta faɗa tana nuna kanta da yatsa... Uma Altine ta yi ajiyar zuciya, "Kiyi hakuri, ba zan jiƙa miki ba." Ta ɗauki soso da sabulu don ta fara goge jikin ta, amma kafin soson ya taɓa fatarta, sai ta zabura ta ja numfashi tamkar ta ga dodo.. "Haaaaaa!!! Da soso zaki yi min? Cire min fatar jikina zaki yi? Saboda kinga ni ɗin mai kyau ce!" Uma Altine ta daure ta ce.. "Ki tsaya mana, ai soson zai cire miki dattin jiki ne." Wannan kalmar 'Datti' ita ce ta zama silar rugujewar nishaɗi.... Chingching ta zaro manyan idanunta, nan take hawaye suka fara zubo mata, muryarta ta fara fita da karfi tana maimaitawa cikin tashin hankali... "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..." Uma Altine ta gigice, ta san halin Chingching idan ta fara wannan kukan, duk fadar sai ta ruɗe.. "Na shiga uku! Dan Allah kiyi hakuri, ba haka nake nufi ba Auta!" Chingching ta ki sauraronta tana nuna kanta da yatsa tana maimaita tambayar cikin kuka mai taɓa zuciya. "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..." Ta miƙe tsaye daga cikin bathtub ɗin, jikinta duk ruwa da kumfar sabulu. Tana sanye da wani gajeren short nicket da wata ƙaramar vest mai raga-raga wadda ta bayyana kyawun fatarta mai sulɓi. Gashin kanta kuwa an tukwaikwiye shi da ribbons an tura shi sama domin kar ruwa ya taɓa shi, wanda hakan ya sa kanta ya yi girma tamkar na wata baturiyar yarinya.. Ta fito daga cikin ruwan tana kuka, tana neman inda zata nufa don kai ƙarar Uma Altine wurin Sarki, yayin da Uma Altine take binta tana rarrashi cikin fargaba. Chingching ta sauƙo stairs da gudu tana kuka, ma'aikatan da ke gyaran falo duk sun bi ta da kallo cikin mamaki, amma ba ta saurari kowa ba sai maimaita tambayarta take, "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?" Ta nufi babban gate ɗin sashenta, security bakin gate suka sha gabanta don hana ta fita a wannan yanayin, sanye da gajeren wando iya cinya da riga vest ta net wadda take nuna duk jikinta, ga gashin kanta da aka tukwaikwiye shi a tsakiya. Ganin an tare mata hanya, sai ta zube a ƙasa ta fara birgima tana ihu.. "Wayyo ku bar ni na je wurin Daddy na! Za su kashe ni, wayyo Allah za su kashe niiii!" Cikin tsoron kar a ce su ne suka taɓa ta, security suka buɗe mata gate ɗin da sauri. Ta miƙe ta fice tana gudu, yayin da Uma Altine ke biye da ita a baya tana huci... A daidai wannan lokacin ne motocin Gimbiya Maayah suka shigo masarautar daga makaranta.... Suna tsaka da tafiya a kan dogon kwaltar masarautar, sai ga Chingching ta tsallako da gudu tana kuka, "Ni ne mai datti?..." Direban Maayah ya daka wani mahaukacin burki wanda ya sa motar kusan tashi sama, har sai da Maayah ta bugi kanta da kujerar gaba... Security ɗin da ke bin Chingching duk sun daskare a wurin saboda tsoron ganin yadda motar ta kusan halaka ta. Amma ita Chingching ko a jikinta, ba ta tsaya ba kuma ba ta kalli motar ba, ta ci gaba da gudunta na neman Daddy, sanye da wannan gajeren kayan nata da jikinta duk a jiƙe... Maayah ta fito daga motar tana dafe kanta, ta kalli ƙanwarta cikin tsananin mamaki da fargaba, tana tunanin me ya faru da Autar tasu da har ta fito a wannan yanayin a gaban jami'an masarautar... "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?" Muryar Chingching ta karaɗe filin, tana kuka tana gudu... A cikin katafaren falon fadar King Nourdeen, iska ta yi tsit, sai ƙamshin turaren wuta na alfarma da yake tashi. Sarki yana zaune tare da babban aminin sa Tafida, da wasu fadawa guda biyu... Suna tsaka da tattaunawa sai kawai aka ji ihun Auta. Tun kafin fadawa su ankara, Chingching ta faɗo cikin fadar tana kuka da ƙarfi.. "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..." King Nourdeen ya zabura ya miƙe tsaye, zuciyarsa ta buga ganin autarsa a wannan yanayin. Jikinta duk kumfar sabulu, sanye da wannan gajeren wando da net vest ɗin da ya bayyana surar jikinta duk da tana da shekaru kusan 17.. Chingching ba ta bi ta kan kowa ba, ta nufi wurin mahaifinta tana kuka.. "Daddy! Ka ga Uma Altine ko? Wai ni ce mai datti! Kuma har ruwan zafi ta zuba min a kan nonuwana, wai wanka za ta yi min!" Ta ci gaba da surutu cikin shagwaɓa, tana bayyana komai daki-daki ba tare da jin kunya ba, yayin da kumfar sabulun jikinta yake ɗiga a kan kafet ɗin fadar... Sarki ya shiga rarrashinta, a lokacin da Uma Altine ta bayyano tana sakin numfashi sosai domin ba ƙaramin gudu tayi ba, ta taho mata da dogon rigar sarauta har ƙasi... Ta matso tana ƙoƙarin rufe mata jiki.. Ita kuma sai faɗin, "Daddy wallahi sai an cire Uma Altine a aiki...".... ✨✨✨ Ganin ba lokacin tunani yasa ya nitse cikin ruwan ya kamo kunkuminta, ya ɗago ta sama.... Jikinta ya yi sanyi ga gashinta yanda ya bazu a saman ruwan kamar ganyen bishiya. Ya fito da ita har gaci, ya kaita karkashin bishiyar da tsuntsuwarta take, ya kwantar da ita a hankali a kan ciyayi... King Diamond ya durƙusa a gefenta yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ruwan kogin ya ƙara wa kyau da sheƙi... Ya sanya dogayen yatsunsa masu sanyi a kan goshinta, ya fara karanta wasu maganganu na sirri tare da hura mata iska mai sanyaya zuciya a fuska.. A hankali, numfashin Ayat ya fara dawowa dai-dai.. Kirjinta ya fara sama da ƙasa yayin da take shirin buɗe idanunta waɗanda suka yi nauyi... Daidai lokacin da ta fara motsa idanunta don buɗe su, King Diamond ya fahimci cewa idan ta ganshi a yanzu za ta iya sake komawa suman. Saboda haka yana ganin ta buɗe ido ɗaya, sai ya ɓace kamar hayaƙi. Babu abin da ya rage a wurin sai ƙamshin turaren sa mai daɗi da sanyi wanda ya gauraye da iskar kogin... Ayat ta buɗe idanunta gaba ɗaya, ta miƙe zaune da sauri tana nishi sama-sama. Ta duba dama da hagun amma ba ta ga kowa ba. Sai dai tana tabbatar wa kanta cewa abin da ta gani ɗazu ba mafarki ba ne.. "Na ga wani mutum... sanye da fararen kaya da farin gashi," ta faɗa a hankali muryarta tana rawa. Ta kalli jikinta, ta ga har yanzu tana sanye da short nicket da bra, kuma tana kwance a busashen fili alhalin tana cikin ruwa lokacin da ta suma... "Waye ya fito da ni daga ruwa?" Ta fara waige-waige cikin tsoro, tana saurin rarrafa zuwa inda kayan maza da ta cire suke. Ta fara sanya kayan tsaro da sauri-sauri tana kuka, tana jin kamar idon wani yana kanta. Ba ta sani ba, King Diamond yana nan a tsaye a siffar aljan, yana kallon kowane motsi nata cikin murmushi... Cikin gaggawa Ayat ta fara maida kayan siffar Inuwa... Ta gyara gashin baki da sajen sannan ta naɗe uban gashinta a cikin rawanin maza.. King Diamond yana nan a tsaye a siffar aljan wadda ita ba za ta iya gani ba, yana kallon yadda take sauya kanta zuwa namiji cikin ƙwarewa. Ya ji mamaki da kuma sha'awar yadda kyakkyawar yarinyar nan take badda kama. Ya gane cewa lallai akwai babban dalili da ya sa take rayuwa cikin sirri, kuma hakan ya ƙara ba shi sha'awar bibiyar rayuwarta... Tana kammala shiri nan take ta zaro takobinta cikin zafin rai da takaicin karya mata alƙawarin da akayi na ganin fuskarta da ko mahaifinta ya kasa gani... Cikin tsawa ta fara magana tana faɗin, "Ko ma waye yake bibiyata nayi alƙawarin duk san da na sake haɗuwa da kai sai nayi gunduwa-gunduwa dakai, domin bazan taɓa yafe maka ba, a wancan lokacin ka zo har kayi faɗa dani kuma ban samu damar sararka ba, yanzu ma ka kuma na biyu to wallahi kada ka sake na sake ganinka na uku domin kashe ka zanyi..." King Diamond yana kallonta bai furta uffan ba, kasancewarsa sarkin Jinn bai taɓa jin son yayi dariya ba sai yanzu amma haka ya make daga bisani ya yi ɓacewarsa... Sai da ta gama barazanarta tana nunnuna takobinta kafin ta hau dokinta ta tafi.... Tana shigowa masarautar, ta ga komai lafiya, babu wani tashin hankali... Sai dai zuciyarta tana kan hasasho mutumin nan da dogon farin gashi... Ta kai dokinta wurin ajiyar dawakai, sannan ta nufi sashen jami'an tsaro... "Mai farin gaji ko? To ko me yellow gashi ne bazan sake jin tsoronsa ba... ​Tana tafiya tana waige-waige, sai ta ci karo da Mama Liyatu Uwar ɗakin Maayah... Mama Liyatu ta tsaya tana kallon Inuwa, domin tana sane da yadda Maayah take ruɗewa a kansa.. ​"Inuwa, daga ina kake haka jikinka duk ƙura?" Mama Liyatu ta tambaya tana binsa da kallo. Inuwa ya gyara muryarsa zuwa ta maza.. "Daga zagaye nake, ina duba tsaro ne." Ta wuce ta da sauri kafin a gano yanayin fuskarta. ​Tana ƙoƙarin wucewa ta sashen fadar sarki, sai ta jiyo muryar Chingching tana ihu... Tana nufar wurin, ta tadda Chingching tana birgima a gaban sarki, yayin da Uma Altine ke durƙushe tana ba da haƙuri.. ​"Daddy! Sai ka kore Uma Altine! Wai ni ce mai datti! Kuma har ruwan zafi ta zuba min a jikina!" ​Sarki yana zaune yana yana murmushin ciki domin bai bayyana a fuskarsa ba, yana lallashin autarsa... "To yi haƙuri Auta, gobe zan sa a siyo miki lallausan soso daga ƙasar waje wanda ba zai cire miki fata ba." ​Ayat ta tsaya daga nesa tana kallon wannan farincikin, wani rauni ya ziyarce ta. Ta ji tana son cire wannan rawanin ta ruga ta rungume ƙanwarta da mahaifinta, amma asirin dake kanta ya fi ƙarfin hakan... Tana tsaye can nesa da babban falon Sarki, tana kallon yadda Chingching take ta rigima tamkar za ta tada fadar. Uma Altine tana durƙushe tana ba da haƙuri, yayin da Sarki yake ta faman rarrashin Autar tasa. ​Kwatsam, sai idon Chingching ya sauƙa a kan Inuwa. Ta ɗaga hannu tana nuna shi, fuskarta ta washe da murmushin shagwaɓa... Fadawan sarki ganin inda yatsan gimbiya ya nuna, suka nufi Inuwa da gudu.. Kafin Inuwa ya ankara, fadawa biyu sun cafko shi, suka yi sama da shi! ​Ayat ta zazzaro ido, zuciyarta na bugawa don tsoron kada asirinta ya tonu ko kuma laifi ta yi. Ta damƙe wuyan fadawan sosai don kada ta faɗi, har aka shiga da ita gaban Sarki aka dire ta a ƙasa... Saboda yadda aka sake ta da ƙarfi, sai da ta zauna da mazaunanta a kan kafet ɗin falon. ​Chingching ta kalli Inuwa, ta turo baki ta ce, "Ni... wannan ne zai kai ni part ɗina!" ​Sarki ya jinjina kai, ko da yake yana mamakin yadda autar tasa ta zaɓi wannan matashin sojan, sai ya ce, "Ƙaramin jarumi, tashi ka raka ta part ɗinta." ​Uma Altine ta yi maza ta miƙe don su tafi, amma Chingching ta karkaɗa kai, ta haɗe hannaye a ƙirji.. "Ni sai dai ya goye ni! Ba zan je da ƙafata ba." ​Tafida dake zaune yana kallon ikon Allah ya ce "To ai Auta da mota za a kai ki ko kuma doki."... "Ni goyo nake so!" Tana bubbuga ƙafa cikin sakalci.. Sarki ya kalli Altine ya ce, "Altine, goye ta ku tafi." ​Nan ma Chingching ta fara buga ƙafa a ƙasa "Ni! Na yi faɗa da Uma Altine, ba za ta goye ni ba! Ba wanda zai goye ni sai kyakkyawan jarumin nan!".. ​Sarki bai ji daɗin hakan ba. A matsayinsa na mai kishin ƴaƴansa, ba ya son namiji ya riƙa taɓa su ko su riƙa mu'amala da maza amma ganin yadda Chingching ta nace kuma ba ya son ɓata mata rai, sai ya gyada wa Inuwa kai alamar ya ɗauke ta. ​Ita kuwa Ayat, wani farinciki ne ya ziyarci zuciyarta. Ta daɗe ba ta riƙe ƙanwarta ba saboda shigar badda kamar da take yi. Ta duƙa a hankali, Chingching ta daka tsalle ta hau bayanta, ta ƙanƙame wuyanta.... Tana tura baki ta ce, "Dan nace maka kyakkyawa kar kayi tunanin ka fini kyau too..." Murmushi kawai Inuwa yayi.. Ya miƙe da ita da ƙyar, domin duk da ƙarancin shekarun Chingching, tana da ɗan nauyi, sannan ya fara takawa zuwa wajen fada, Uma Altine da sauran bayi suna biye da su a baya... ​Suna tafe a kan dogon kwaltar masarauta, iska mai sanyi tana kaɗawa. Chingching ta saki jiki sosai a bayan Inuwa, ta ɗora kanta a kafaɗarsa.. ​"Wai kai meye sunanka?" Ta tambaya tana wasa da kwalliyar jikin rigar sojan... ​Inuwa ya ɗan yi murmushi, ya rage sautin muryarsa don kada sauran bayin su ji yadda muryarsa take zama ta mace idan ya yi magana mai tsayi, ya ce.. "Sunana Inuwa, ya ke gimbiya." ​Chingching ta yi dariya, "Inuwa? Suna kamar inuwar bishiya. Amma ka san me? Jikinka yana da taushi, ba ka da tauri irin na sauran sojoji. Kuma kana ƙamshi mai daɗi, ba irin na Uma Altine mai ƙamshin sabulun wanka ba.".. ​Inuwa ya ɗan zaro ido, ya ce.. "Haka ne gimbiya, ai sojoji ma suna wanka." ​Chingching ta ƙara matse shi, ta ce, "Inuwa, me ya sa kake da kyau haka? Idanunka manya ne kamar na Aunty Ayat. Ka san Aunty Ayat kuwa? Ita ma tana da kyau sosai, amma kullum tana kulle a ɗaki." ​Wani ƙwallar farinciki ya cika idon Ayat, ta amsa.. "Na san ta gimbiya. Ita ma tana sonki sosai." ​Chingching ta bushe da dariya, "To idan na sake rigima, zan sa Daddy ya ce kai ne za ka riƙa yi min wanka, tunda kai ba ka cire fatar mutum da soso." ​Inuwa ya kusa yin tuntuɓe saboda dariya, ya ce, "A'a gimbiya, wanka kam sai dai Uma Altine." ​Haka suka riƙa yin hira cikin nishaɗi har suka isa part ɗin gimbiya, kowa yana mamakin yadda wannan jarumin ya saba da Auta cikin lokaci ƙanƙani.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 8️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan Inuwa ya sauƙe Chingching a part ɗinta, ya fara takawa cikin sanyin jiki yana shirin komawa tasa muhallin. Zuciyarsa tana cike da farincikin hirar da suka yi da kanwarsa.. ​Kwatsam yana shirin shiga wata kusurwa sai ya ji an rufe masa fuska da wani baƙin mayafi mai kauri. Kafin ya yi yunkurin kwata, wasu jami’an tsaro guda biyu masu ƙarfi suka cafko shi, suka fara jansa da karfi. Ba su ba shi damar yin magana ba, suka jefa shi cikin wata mota dake fake a gefe, suka tada motar da gudu suka nufi part ɗin Gimbiya Maayah.... ​Motar ta tsaya a harabar katafaren sashen Maayah. Jami’an suka fito da Inuwa, yana ta faman kokawa yana son ya ɓalle ya gudu, amma riƙon da suka yi masa na maza ne. Saboda yadda suka ji ba shi da nauyi sosai, ɗaya daga cikinsu sai kawai ya yi masa ɗaukan kafaɗa, ya saɓo shi tamkar buhun shinkafa, suka nufi cikin falon gimbiyar. ​Suna shiga suka dire shi a tsakiyar katafaren falon dake shimfide da kafet mai tsada... ​Maayah tana zaune a kan wata Plate Sofa kamar katifa a ƙasi tana sanye da riga ta alfarma wadda ta bayyana kyan fatarta. A gabanta akwai wani katafaren tray cike da yankakken kayan fruits masu sanyi, tana ci a nutse tamkar ba ta san abin da ke gefen ta ba.. ​Ba tare da ta kalli inda suke ba, ta daga dogayen yatsunta ta yi musu nuni da su fita. Nan take jami’an da sauran ma’aikatan mata dake falon suka fice cikin hanzari, suka bar Inuwa tsaye a tsakiyar falon cikin ruɗani. ​Daga nan ne aka cire wa Inuwa baƙin mayafi dake fuskarsa. Da farko ya rintse ido saboda hasken fitilun dake walwali a falon, yana buɗe su sai ya yi ido hudu da Maayah. Mamaki da fargaba suka mamaye shi. ​Maayah ta ajiye ƙaramin wuƙar dake hannunta, ta ƙura wa Inuwa idanu. Wani irin kallo take yi masa, kallo mai cike da nuna isa da kuma wani ɓoyayyen saƙo dake nuna sha'awa da burgewa.... Idanun Maayah sun yi wani irin sheƙi, gata kyakkyawa ajin farko.. ​Inuwa ya ji jikinsa ya fara sanyi. A matsayinsa na mace, ta san ma'anar wannan kallon. Ta san cewa inda asalin namiji ne babu abin da zai hana sha'awarsa ta tashi a wannan lokacin saboda yadda Maayah ta baje kyan surarta a gabansa cikin kissa da kisisina... ​"Inuwa..." Maayah ta kira sunansa cikin wata irin murya mai sanyi da take ratsa jijiya. "Ka ga yadda ka yi nasarar sa ni tunani tun daga ranar da idona ya fara ganinka? Meye sirrinka? Me kake boyewa a karkashin wannan rawanin naka?" ​Inuwa ya sunkuyar da kai kasa, yana tunanin yadda zai fita daga wannan tarkon na Gimbiya Maayah ba tare da asirinsa ya tonu ba. Maayah ta tashi daga kan katifar ta a hankali, tana taku ɗaya-ɗaya tamkar kyanwar da ta ga ɓera... Rigar jikinta tana jan ƙasa, ƙamshin turarenta na Oud mai tsada ya mamaye hancin Inuwa. Ta zo daidai gabansa, ta tsaya tana kallon kwayar idonsa, kafin ta fara zagaye shi kamar yadda zaki yake zagaye abincinsa... Ta sanya hannunta ɗaya ta fara shafa kafaɗarsa tana gangarawa zuwa hannunsa. Muryarta na fita ƙasa-ƙasa, tana raɗa masa a kunne.. "Inuwa... na yi bincike a kan duk sojojin masarautar nan, amma ban ga kamaninka ba. Ba ka da ƙasusuwa irin na maza sojoji. Ka yi fita daga daban, kuma hakan ne ya sa zuciyata ta kasa nutsuwa." Ita kuwa duk wannan shashshafa da kalaman Maayah ba su motsa mata komai ba face takaici da haushin yadda ƴar uwarta take nuna rashin kamun kai. Ta ɗaure fuskarta cikin yanayi na gatsine, tana jujjuyar da manyan idanunta tana kallon silin ɗin ɗakin. A ranta tana cewa, "Wannan mahaukaciyar me take nufi ne? Shin ba ta da sauran abin yi ne sai bibiyar sojoji?" Maayah ta kai hannunta tana son ta shafi gefen fuskarsa, Inuwa ya kauce da sauri yana harararta.. Maayah ba ta fasa ba, ta sake zagayawa ta bayansa, ta tura kanta a tsakanin kafaɗunsa, ta rungumo shi ta baya tana ƙoƙarin jin bugun zuciyarsa... "Me kake gudu Inuwa? Izza kake nuna min ko kuwa tsoron matsayina kake ji? Idan ka karɓi soyayyata, zan mayar da kai babban kwamandan da kowa zai rurrusuna masa a ƙasar nan," tana goga fuskarta a bayan rigarsa. Inuwa ya ja wani uban tsaki a cikin ransa, wanda ya kusa fitowa fili. Ya fara jin ƙyamar yadda Maayah take ƙanƙame shi. Ya yi amfani da dabarar maza sojoji, ya juyo da ƙarfi ya raba jikinsa da nata, ya matsa baya taku biyu yana huci.. Cikin muryarsa ta maza wadda ya riga ya koyi kwaikwayonta, ya ce.. "Gimbiya Maayah! Na zo nan ne don hidimar tsaro, ba don wasan kwaikwayo na soyayya ba. Ni talaka ne, ke kuma gimbiya ce. Bai kamata ki ɓata mutuncinki a kaina ba. Kuma idan har kika sake sanya a kamo ni ta wannan hanyar, zan kai ƙararki gaban mai Martaba Sarki, duk abin da zai faru ya faru!" Maayah ta daskare a wurin, ta zaro ido tana kallon Inuwa. Ba ta taɓa tunanin akwai wani namiji a duniya da zai ƙi wannan tayin nata ba. Maimakon ta ji tsoron barazanar sarki, sai kawai ta ji Inuwa ya ƙara mata kyau da kwarjini a idonta. Ta ciza laɓe, tana murmushin mugunta... "To ka je ka faɗa wa Sarkin! Amma ka sani, duk inda ka shiga a masarautar nan, idona yana kanka. Ba za ka taɓa tsira daga tarkona ba har sai na mallaki abin da nake so a tare da kai." Inuwa bai sake tankawa ba, ya juya cikin fushi ya nufi ƙofa, ya buɗe ta da ƙarfi ya fice, ya bar Maayah a tsaye tana kallon inuwarsa tana shafa wurin da ya taɓa, tana jin wani irin shauƙi daban. Ya fara takawa cikin sauri yana ficewa daga sashenta, yana muzurai shi kaɗai ƙasa-ƙasa... "Banza! Mahaukaciya! Jaka kawai!" ya furta tare da jan wani dogon tsaki. "Wato ita a tunaninta kowa ma namiji ne ko? Ta rasa wanda za ta bi sai ni? Yarinya ba ta da sauran aiki sai lalata da ma'aikata? Allah ya kyauta!" Haka ya riƙa surutai yana gunguni har ya ɓace a cikin duhun dake tsakanin gine-ginen masarautar, ya nufi tasa part don ya cire wannan kayan sojan da yake ji sun yi masa nauyi saboda haushi. A can cikin falo kuwa, Mama Liyatu tana laɓe a bayan labule tun ɗazu tana kallon duk abin da yake faruwa. Bayan Inuwa ya fice ta fito a hankali tana takawa zuwa inda Maayah take a tsaye, tana kallon ƙofa tamkar gunki... Mama Liyatu ta ga yadda Maayah ta zama wata iri, fuskarta na sheƙi, kuma tana shafa hannunta da Inuwa ya taɓa.. "Gimbiyata," Mama Liyatu ta kira sunanta cikin muryar tsoro. "Wannan yaron da kike bi... shin kin tabbata namiji ne na ƙwarai? Na ga kyan fuskarsa ya wuce na namiji, sannan yadda kika rungume shi ɗazu bai nuna wani yanayi na namiji ba. Meye sirrin dake tattare da shi?" Maayah ta juyo ta kalli Mama Liyatu, wani murmushin mugunta na nan a kwance a fuskarta. Ta koma ta zauna a kan kujera, ta ɗauki koren apple ta gutsura.. "Mama Liyatu, shi ya sa nake son sa. Domin ya banbanta da kowa. Sannan ya nuna mjn ba ya buƙatar soyayyata. Wannan shi ne babban kalubalen da nake so. Amma ki sani, koda mace ne shi a siffar namiji, sai na mallaki zuciyarsa, balle kuma ina da yakinin cewa jarumi ne mai jinin sarauta a jikinsa.".. Mama Liyatu ta girgiza kai, "Amma Gimbiya, idan Sarki ya ji labarin nan fa? Kin san yadda yake kishinku." Maayah ta yi wata 'yar dariya mai sauti. "Sarki yana can yana fafutukar yadda zai kare masarautarsa daga barazanar Pavilion, ba shi da lokacin binciken wanda nake so. Ke dai kawai ki sa ido a kansa, duk inda ya sanya ƙafa ki sanar da ni." ✨✨✨ A ɗayan ɓangaren kuwa, Ayat ta isa sashenta. Ta banka ƙofa ta shiga, ta cire rawanin kanta ta wurgar a kan gado. Ta kalli kanta a madubi, gashin kanta ya bazu a kafaɗarta, idanunta sun cika da ƙwallar takaici... "Wace irin rayuwa nake ciki?" ta tambayi kanta... "Ina tsaka-tsakiyar yaƙi da kaina.." Ta shige banɗaki don yin wanka.. Bayan ta kammala wanka ta cire duk wata siffa ta Inuwa, ta saka lallausan leshi mai kyan gaske wanda ya dace da jikinta. Ta sauko ƙasa zuwa babban falonta tana takawa a hankali, fuskarta a rufe.. Tana isa falon, sai ta tadda ma’aikatanta, karkashin jagorancin Saratu, suna tsaye jere tamkar wadanda suke jiran sako daga sama. Fuskar kowacce dauke da tambaya da kuma damuwa. Saratu tana kallonta, sannan ta yi gyaran murya ta ce. "Gimbiya, me ya sa yanzu kika koyi wannan halin ne? Tun safe ba kya fitowa sai dare, anya lafiya kuwa? Abun ya yi yawa ai..." Ayat ta ji wani irin haushi ya taso mata, domin ranta ya riga ya ɓaci da rigimar Maayah. Ta tsaya cak, ta kalli Saratu da idanuwanta wadanda suka nuna bacin rai a fili... "Kuna so ne na fito na taya ku aiki?" ta tambaya cikin kakkausan harshe. Saratu maimakon ta yi shiru, sai ta kara matsowa, "A'a, amma dai ki fito kowa ya ganki, a ga lafiyarki. Idan kina kulle kanki kullum, me kike so mutane su ce?" Ayat ta ji tamkar ana huda mata zuciya da mashi. Ta girgiza kai cikin takaici ta ce.. "Hakan ya zamo wajibi ne? Ba na so ku riƙa shishshige wa rayuwata! Kowa ya yi aikin dake gabansa, ku yi rayuwarku na yi tawa. Ban hana ku yin farin ciki ba, ban rage ku da komai ba, to me ya sa kuke son takura ni?" Saratu ta ɗaure fuska, "Ai dole mu shiga lamuranki Gimbiya, domin amanarki aka ba mu, kuma ya zama wajibi mu kula da ke yadda ya kamata.".. Kallonsu ta shiga yi, sai kuma ta tuna yadda ma'aikatan Maayah suke rawar jiki idan suka ganta, ba su isa su hada ido da ita ba balle su yi mata magana barkatai. Amma nata ma’aikatan, saboda sun san ta da saukin kai da tausayi, sun mayar da ita tamkar tsararsu... Ta ji wani raɗaɗi a ranta, kowa a masarautar nan yana son ya tsara mata yadda za ta yi rayuwa.. Ta ɗaga musu hannu ɗaya alamar ta gaji da maganar su fita su ba ta wuri. Duk suka fita suka bar ta a tsakiyar falon, tana jin tamkar ta fasa ihu don ta huta... *Washegari* A sashen Gimbiya Yumna, kowace safiya tana farawa ne da nishaɗi. Yumna tana zaune a gaban babban madubin ta na alfarma, yayin da bayinta suke ta faman gyara mata gashi da sanya mata lalle. Suna cikin wasa da dariya.. Ummi ɗaya daga cikin baiwa ta ce, "Gimbiya, gaskiya yau fuskarki ta yi wani irin haske na daban. Anya ba mafarkin alheri kika yi ba kuwa?" Yumna tana murmushi ta ce, "Ke dai Ummi kullum maganarki kenan. Kawai hutu ne ya karɓe ni." Zainab ta ce "Hutu dai ko kuwa tunanin Malam? Ai muna sane yau ne ranar karatunki...!" Duk bayin suka sa dariya, Yumna kuwa ta ɗan ji kunya, ta duƙar da kanta tana murmushin dake bayyana fararen haƙoranta. Suna tsaka da wannan wasan ne, sai wata amintacciyar baiwarta, Safina, ta shigo ɗakin da sauri. Ta zagaya bayan Yumna, ta rungume ta ta baya sannan ta raɗa mata a kunne cikin muryar raɗa.. "Yau kin manta ne? Dream Lover ya zo... Yana can lambu yana jiran ki." Yumna ta zaro ido, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi. Wani irin farinciki ya rufe ta, ta kalli Safina ta ce "Malam ya zo? Da gaske kike yi Safina?" Safina ta ce "Da gaske nake mana Gimbiya. Tun ɗazu yake can ya shimfiɗa dadduma yana duba littafansa." Yumna ta miƙe da sauri, ta umarci bayin su gama shiryata cikin gaggawa. Allah ya jarrabe ta da tsananin son wannan Malamin nata, wanda yake koyar da ita karatun boko da na Larabci a wani tsararren lambu dake gefen sashenta... Malamin, wanda kyakkyawan Balarabe ne mai farar fata da dogon hanci, yana da sanyi da sauƙin kai. Sai dai babban abin tashin hankalin shi ne, shi kansa Malamin bai sani ba cewa Gimbiyar dake koyon karatu a hannunsa tana ƙaunar sa fiye da komai. A wurinsa ita Gimbiyarsa ce mai girma, a wurinta kuwa shi ne rayuwarta... Yumna ta isa lambun, ta tadda Malam zaune a kan dadduma, ya sa fararen kaya ya naɗa rawanin Larabawa. Ta ƙaraso tana tafiya a hankali don kada ya fahimci yadda take jin nauyinsa.. "Assalamu Alaikum, Malam. Ina fatan ban daɗe ba?" Ya ɗago ya kalle ta da idanunsa masu kwarjini, sannan ya yi murmushi mai sanyi "Wa'alaikumussalam Gimbiya Yumna. A'a, yanzu ma na ƙaraso. Ki zauna mu fara da karatun Larabcin tukunna kafin mu koma na Turanci." Yumna ta zauna a kusa da shi, ƙamshin turaren sa ya fara buge ta. Ta buɗe littafi amma idonta yana kan yatsunsa dake nuna mata haruffan... "Gimbiya, wannan kalmar ana ƙiranta 'Al-Hubb'. Kin san ma'anarta kuwa?" Yumna ta kalli Malam, fuskarta ta yi jawur, ta ce a ranta "Kamar ka san abin dake cikin zuciyata..." Amma a fili sai ta ce "A'a Malam, meye ma'anarta?" Cikin muryar natsuwa ya ce, "Ma'anarta ita ce Soyayya. Ita ce jigon rayuwa." Yumna ta sauƙe ajiyar zuciya, tana kallon kyakkyawar fuskar Malamin da take matuƙar so, yayin da asalin soyayyar take a ɓoye a tsakaninsu. A cikin masarautar Alhamra, kowace Gimbiya tana da nata malamin da yake zuwa har sashenta don koyar da ita, domin kiyaye mutuncinsu da kwarjininsu... Malam ya lura da yadda Yumna take ta murmushi tun farkon zaman, ya gyara zama sannan ya kalle ta cikin natsuwa ya ce.. "Sarkin murmushi, idan kin gama murmushin, sai ki sanar da ni a wace ayar kika tsaya a karatunmu na Kur'ani. Kin san mun yi nisa sosai." Yumna ta ɗan sunkuyar da kanta, tana jin wata irin kunya mai daɗi. Ta buɗe babban littafin dake gabanta sannan ta ce.. "Malam, mun kusan kammala suratul Baƙara gaba ɗaya. Na kusa na yi sauƙar Alkur'ani mai girma." Malam ya jinjina kai cikin gamsuwa da farinciki, ya ce.. "Haka ne Gimbiya. Kin mayar da hankali sosai a kan karatu, kuma hakan babban abin alfahari ne. Yanzu sauran mana shafi uku kacal mu kammala wannan surar. Yanzu za ki iya karanta min daga inda muka tsaya, sai na ƙara miki wani karatun ko?" Yumna ta gyara zama, ta nutsu, sannan ta fara karatun cikin muryarta mai sanyi da zaƙi wadda take sa natsuwa a zuciyar duk wanda ya ji ta. Karatun nata ya fito ne daki-daki, ba tare da kuskuren tajwidi ko na haruffa ba... Yayin da take karantawa, Malam ya zuba mata ido, yana sauraron yadda haruffan suke fita. Duk da cewa malami ne shi, a wannan lokacin ya ji wani irin kwarjini da natsuwa sun mamaye shi. Ya fara jin cewa wannan ɗalibar tasa tana da wani sirri na musamman dake sa karatun nata ratsa ko'ina. Ita kuwa Yumna, tana cikin karanta kalmomin Allah, amma a gefen zuciyarta tana jin daɗin yadda Malam yake sauraronta cikin kulawa. Lambun ya yi shiru, sai sautin muryarta da kukan tsuntsaye dake rera waƙa a saman bishiyoyi.... ✨✨✨ A sashen Chingching, baccin daɗi take sha, domin ita a rayuwarta ba abin da take so irin bacci... Altine ta shigo ɗakin, ta daɗe tana jijjiga ta.. "Gimbiya, tashi Malam ya zo yana jiran ki!" Chingching ta turo baki, ta koma ta nade a cikin bargo. Sai da aka sha fama da ita, kafin Altine ta samu ta sanya mata dan madaidaicin hijab dinta. Ganin yadda Chingching ta ki takawa da kafarta, dole Altine ta goyo ta a bayanta har zuwa lambun da Malam ke jira... Malam dake ustaz ne mai kamala da uban gemu mai tsawo da sheki, ya gyara zama bayan an dire Chingching a dadduma. Ya kalle ta ya ce.. "Gimbiya, a ina muka tsaya da karatunmu?" Chingching ta kalli fuskar Malam, ta yi fari da ido ta ce. "Malam ai mun tsaya a wurin da Malam ya aske gemunsa!" Malam ya ji tamkar ya nitse, ya kalle ta cikin mamakin shiriritar dake kanta.. "Kur’ani nake tambayarki Gimbiya, ba zancen gemuna ba. A ina muka tsaya?" Ta yamutsa fuska, "Yoo Malam ni na manta, gaya min farkon sa." Malam ya girgiza kai, "Ba kina Suratul Anbiya'i ba?" Ta jujjuya idanu tamkar mai tunani, daga bisani ta ce, "Ehh, haka ne ashe!" "To karanta min daga inda kika tsaya," in ji Malam.. Chingching ta sake cewa, "Me ma farkon ayar?" Bayan Malam ya karanto mata farkon ayar, sai Chingching ta tashi ta daka wani tsalle na farinciki tana ihu, sannan ta dawo ta zauna. Abun mamaki tana farawa sai ta karanta karatun tsaf, babu gyara ko guda ɗaya duk da shiriritar dake kanta... Malam ya yi murmushin jindadi, ya bude shafin littafin don ya kara mata karatu.... Yana fara karantawa, ita kuma Chingching ta ƙura wa gemunsa ido. Gemun yana ta motsi sama da ƙasa yayin da Malamin yake karatu, gashi yana ta sheki... Chingching ta fara dariya ƙasa-ƙasa. Duk sanda Malam ya sunkuyar da kansa yana karatu, sai ta kai hannu tana shirin taɓa gemun. Da zarar Malam ya ɗago kai, sai ta janye hannunta da sauri tamkar ba ita ba. Haka ta yi ta yi, tana wasan ɓuya da gemunsa. Ana karshe ne, tana ganin Malam ya nutsu a cikin karatun, sai ta kai hannu ta damƙe gemun gaba daya ta jawo shi da karfi!.. Malam ya saki wata irin kururuwa, jikinsa ya ɗauki rawa.. "Ke meye haka! Sake min gemu! Nace ki sakar min gemu kar ki cire min! Baki da hankali ne? Zaki cire min gemu! Innalillahi wa inna ilaihir raji'un... Kin kashe ni!" Ta saki gemun, ta faɗa ƙasa tana kwashewa da dariya. Ta riƙe cikinta tana birgima a kan dadduma, har hawaye ya fara zubo mata tsabar dariya... Malam ya zauna cikin kalar tausayi, yana shafa gemunsa dake masa zafi, yana kallon yadda wannan yarinyar take tamkar ba ta san zafin da ya ji ba. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, har zuciyarsa ya ji ya gaji da koyar da ita, domin kowace rana da nata sabon iskancin take zuwa... Bayan Chingching ta gama dariyar ta gyara zama tana kallon Malamin cikin yanayin natsuwa na karya, ta ce, "To Malam, mu ci gaba mana..." Malam ya sauƙe ajiyar zuciya, amma saboda tsaro sai da ya sanya hannunsa na hagu ya danne gemunsa sosai, gudun kada ta sake damƙe shi. Ya fara karanta mata ayoyin Kur'ani cikin muryar raɗa, yana sa ido a kanta. Chingching tana sauraron karatun kamar wata shiryayya, har Malam ya fara tunanin yau ta nutsu. Kwatsam! Sai idonta ya sauƙa a ƙasan hantsar wandonsa. Sakamakon yadda Malamin ya naɗe ƙafafunsa a kan dadduma, rigarsa ta ɗan janye, sai ga hantsar wandonsa ya yage ta ciki, inda wani abu ya ɗan fito ya yi ƙulƙule... Chingching ta zaro ido, ta dafe baki tana faɗin, "Ah ah ahh ahhh! Me zan gani haka?!" Malam ya tsagaita da karatun, ya ɗago yana kallonta cikin shakku.. "Meye ya faru kuma Gimbiya?" Ta duƙar da kanta tana maƙale dariya, "Ba... ba komai Malam, ci gaba kawai." Malam ya ci gaba da karatu, amma ina! Chingching hankalinta ba ya kan karatun, tana ta leƙe-leƙen wannan wurin da ya yage. Dariyarta ta fara cin ƙarfinta, tana ƙoƙarin danne ta amma abin ya faskara. Lokaci guda ta fashe da wata mahaukaciyar dariya tana karkarwa.. Ta miƙe tsaye tana zagaye daddumar, tana ihu tana dariya har tana neman faɗuwa. Malam kam ya kusa fashewa da kuka tsabar takaici. Ya ce. "Wai me yake faruwa ne? Idan ba kya son karatun, sai na tashi na tafi na bar miki fadar!" Cikin dariya da gurguwar magana, Chingching ta dawo ta zauna, tana faɗin "Yooo Malam, ina karatu zai yiwu ina hango ɗan tulu a tsakiyar wandonka... Kuma wandon ya yage!" Malam ya firgita, ya yi maza ya gyara zamansa yana rufe wurin. Chingching ta ƙara kwashewa da dariya.. "Malam! Maganin meye ne sa tumatur a tsakiyar wandonka ta ciki? Na ga ya yi ƙulƙule kamar tumatur, kamar kuma dankali... Kai, dankali ne ma! Wallahi dankali ne!" Malam ya ga cewa idan ya ƙara minti ɗaya a wurin, to mutuncinsa zai zube ƙasa warwas. Ba tare da ya ce uffan ba, ya kwashe littafinsa da sauri-sauri, ya miƙe ya fara sauri yana ficewa daga sashen... Chingching tana biye da shi da dariya tana kwala masa kira "Malam mai ɓerarren wando! Ga kuma ƙaton dankali a ciki! Malam ya ɓoye dankali a wando!".. Ta zube a ƙasa tana dariya sosai, yayin da Altine dake gefe ta rasa ko za ta yi dariya ko za ta yi kuka saboda kunyar abin da Auta ta yi wa ustaz.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 9️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم* Ba zato ba tsammani sararin samaniyar Alhamra Kingdom ya sauya launi... Wata irin nutsuwa ta ba-zata ta mamaye garin, nutsuwar da ta fi karfin hankali...Tsuntsayen da suke ta rera waƙa a saman bishiyoyi duk sun yi shiru tamkar an zare musu rai... Iskar dake kaɗawa ta tsaya cak. Mutanen gari ne suke ta rarrabe idanu, kowa ya ji a jikinsa cewa akwai wani abu mai nauyi dake tunkaro su... ​Daga can nesa aka fara jin wani irin tafiya na musamman, kwatsam sai ga jerin motocinsa sun bayyana a ƙofar gari.. Motoci ne bakake wuluk waɗanda babu irinsu a faɗin duniya, sheƙinsu kaɗai ya isa ya makantar da idon da ya ƙura musu... ​Ba mutum ɗaya ba, ba goma ba motocinsu sun fi hamsin, suna taho wa a jere tamkar kyanwar daji... A cikin kowace mota, akwai zafafan Bodyguards sanye da baƙaƙen kaya irin na jami'an tsaron Amurka... Fuskokinsu a murtuke, idanunsu sanye da bakaken gilashi, ba sa kallon dama balle hagu... ​Wannan runduna ta Pavilion Kingdom ba wasa ta zo yi ba. A hannun kowane soja dake kan motocin, akwai wasu zafafan bindigu waɗanda kallo ɗaya zaka yi musu kasan cewa na zamani ne. Ga wasu dogayen takuba a kugunsu masu sheƙi tamkar madubi, waɗanda ke nuna cewa idan aka zaro su, to jini ne kawai zai mayar da su dauɗarsu... ​Duk waɗanda suka kalle su a cikin garin Alhamra, sai da ya daskare a inda yake. Waɗanda suke jin labarin Pavilion kawai a matsayin tatsuniya, yau sun ga zahiri.. Kowa ya tsorata, tsoron da ya sa numfashi ma ya zama wahala. Kai tsaye ​rundunar ta shine cikin babban masarautar, sun jeru tin daga bakin fada har zuwa babban gate... Babban jami'in dake jagorantar aiken ya fito, ya shige cikin fadar sarki ya miƙa wata wasiƙa mai ɗauke da tambarin Pavilion, wani tambari mai kwarjini da firgitarwa... ​A cikin fada, Sarki Nourdeen ya miƙe tare da karɓan wasikar da hannu biyu, amma yana buɗewa idanunsa suka firfito, hannunsa ya fara karkarwa. Sakon a gurguje yake amma yana da nauyin dake iya rushe masarauta... _​"Ina nan tafe. Zan shigo ƙasarka ta Alhamra City nan ba da daɗewa ba. Lokacin cika yarjejeniyarmu ya yi."_ ​Sarki ya sulale ya zauna a kan kujerarsa ta sarauta, gumi ya fara keto masa duk da sanyin dake wurin.. Tsoronsa daya shine yarjejeniyar Sirri dake tsakaninsa da Pavilion. Lokaci ya yi, kuma Sarkin Pavilion ba ya yafe alkawari... ​Ya kalli fadawansa waɗanda kowanne ya zama mutum-mutumi saboda tsoro. Idan har waɗannan ma’aikatan aike ne kawai kwarjininsu ya kai haka, ina ga shi kansa Ogan? Mutumin da sunansa kaɗai ke sanya sarakuna su rasa baccinsu.. ​Masarautar Alhamra ta shiga cikin duhu, kowa ya san cewa babban yaƙi ko babban canji yana nan tafe... ​A sashen Gimbiya Aayat, tana zaune a babban falonta cikin shigar alfarma na sarauta, tana cin fruits a nutse tana ƙoƙarin danne damuwar takurar da ma'aikatanta suke mata... Kwatsam, sai ga wani ma'aikacinta ya shigo a guje, ko neman izini babu jikinsa na rawa tamkar wanda aka yi wa bushara da mutuwa.. ​"Ya ke Gimbiyata, a gafarce ni! Wannan yanayin na yau ya girgiza kowa, hatta sarki kansa!".. ​Ayat ta ji gabanta ya faɗi... Idan har mahaifinta, babban zaki na Alhamra ya girgiza, to lallai al'amarin ba karami ba ne. Cikin dake wa ta ce, "Me yake faruwa?" ​"M... mu... mutanen Pavilion Kingdom ne suka zo!" ​A zabure Ayat ta miƙe, tana zazzaro manyan idanunta... "Pavilion Kingdom?" Ta maimaita cikin rawar murya. "Shi da ake jinsa a cikin littafin almara da labaran tsoro, yau ya tabbata a cikin wannan masarautar?" Zuciyarta ta fara bugawa da sauri, tana tunanin ko wane irin asiri ne ya kusa bayyana haka... ✨✨✨ ​A can ɓangaren Gimbiya Maayah, tana kan electric treadmill tana gudu sosai. Gumi ya jiƙe mata jiki, gashinta ya bazu a baya.. Ba wai don lafiyar jiki kaɗai take wannan gudun ba, tana gudu ne don ta tsira daga tunanin Inuwa da kuma damuwar dake cunkushe a zuciyarta. ​Kowane taku dake bugawa a kan injin, tamkar yana rage mata zafin kishin dake ranta ne. A kan wannan injin, Maayah ba gimbiya bace, mace ce kawai dake neman sauƙi a cikin azabar tunani. ​Tana tsaka da wannan gudun, sai ga Mama Liyatu ta shigo wurin a guje, tana ƙwala kira.. "Gimbiya! Gimbiya!! Gimbiya!!!" ​Maayah ba ta ko kalle ta ba, ballantana ta amsa, tana jin daɗin yadda gudun yake ɗibar mata kewa. Amma jin furucin Mama Liyatu na gaba ya sa jinin jikinta daskarewa.. "Kin ji labarin mutanen PAVILION KINGDOM sun shigo cikin masarautar nan kuwa?!" ​Jin sunan Pavilion, Maayah ta firgita, ta nemi ta tsaya cak cikin tsoro, ta manta cewa tana kan injin dake gudu a kan high speed. Ba ta danna maballin dakatarwa ba, nan take injin ya wurgar da ita sama, tayi gaba ta faɗo ƙasa da ƙarfi! Wani uban ƙara ya fito daga bakinta yayin da bayanta da ƙunkuminta suka daku a kan tattausan darduma mai tauri.. Faɗuwar ba ƙarama bace, domin numfashinta ne ya kusa ɗaukewa na ɗan lokaci.. ​Mama Liyatu ta kwala ihu, ta yo kanta da gudu tana kiran sunanta. Maayah tana kwance tana murƙususu, azabar dake jikinta ta haɗu da tsoron jin sunan Pavilion ya sanya ta rasa inda za ta sa kanta.. ​Duk girman kan Maayah da izzarta, yau gwiwoyinta sun yi sanyi. Zuwan mutanen Pavilion ya canja komai a cikin mintuna kalilan.... ✨✨ ​A sashen Gimbiya Yumna, tana tsaye a cikin kitchen tare da wasu ma'aikatanta, domin Yumna mutum ce mai sauƙin kai da son mu’amala da na ƙasa da ita. Tana tsaka da yanka kayan marmari a kan tray, tana murmushi, sai ga wata baiwa ta shigo falon kitchen ɗin a guje tana haki. ​"Gimbiya kallo ya barki! Yau mutanen Pavilion Kingdom ne suka zo cikin masarautar nan!" ​Wani irin bugawa zuciyar Yumna ta yi, ta ji wani jiri ya ɗibe ta. Ba ta san lokacin da wuƙar hannunta ta suɓuce ba, ta yanke mata yatsa. Jini ya fara zuba amma Yumna ba zafin yankan take ji ba, zafin sunan da ta ji ne ya ratsa kowane sashi na jikinta. Ta ajiye wuƙar, ta juyo idanunta tab da hawaye. Hawaye ne na farin ciki da tsofaffin tunani dake ƙoƙarin dawowa... ​Ganin yadda take kuka, sai baiwar ta ƙara da cewa.. "Amma Gimbiya, mutanensa ne kawai suka zo, shi Sarkin Pavilion bai bayyana kansa ba, saƙo kawai suka kawo." ​Nan take farin cikin Yumna ya dashe, murmushin dake ƙoƙarin bayyana ya koma ciki. Ma'aikatan suka zagaye ta cikin damuwa, suka ɗauki auduga da magani suka treat ɗin yatsarta da ta yanku, sannan suka raka ta har bedroom ɗinta don ta huta. ​Bayan ma'aikatan sun fita, Yumna ta tabbatar ta kulle ƙofar ɗakin. Ta nufi wani sashe na drawer ɗinta dake ɓoye a gefe guda, ta buɗe ta da rawar hannu. Ta zaro wani ƙaton hoto wanda aka adana shi da matuƙar kulawa.. ​Hoton wani tsararren sarki ne, kyakkyawa na gaske, fari mai kwarjini, sanye da kayan sarauta waɗanda aka ƙera su da gold. A gefen damansa akwai wani kyakkyawan yaro, haka a gefen hagunsa akwai wani yaron, twins ne maza waɗanda kyawunsu ya kusan ninka na mahaifinsu... ​Amma babban abin da ya sa Yumna fashewa da kuka shi ne hoton wata ƙaramar yarinya, wacce ba za ta wuce shekara biyu ba, tana zaune a kan cinyar sarki a tsakiya. Wannan yarinyar ba kowa bace face ita kanta Yumna... ​Yumna ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, kukan da ta daɗe tana tura shi a can ƙasan zuciyarta. Ta fara shafa fuskokin twins ɗin da mahaifin dake cikin hoton da yatsunta dake ɗauke da bandage.. ​"Kun kusa dawowa? Ko kuwa ni ce zan dawo gare ku?" ta faɗa cikin muryar kuka. ​Ta ɗaga hoton ta rungume shi a ƙirjinta tana jin tamkar tana rungumar mutanen dake cikinsa ne. Wannan hoton shi ne kaɗai dangantakarta da asalin inda ta fito.. ✨✨✨ Sashen Gimbiya Zayana Lokacin da aka sanar mata, ta tsorata amma bata nuna hakan ba, ta yanke hukuncin zuwa yanda suke tayi ido huɗu da su.... A koda yaushe zuciyarta tambaya take waye Pavilion king? Meyasa yake ɓoye kansa sai dai labarinsa.. Saboda tsoron da ma'aikatanta suke basu sanar mata cewa shi bai zo ba, iya mutanensa ne... Yayin da Gimbiya Zayana take takawa cikin fadar, idanun kowa na kanta. Wata baiwa mai suna Ladi ta yi kuskuren ƙura mata ido na wasu daƙiƙoƙi. Zayana ta tsaya cak, ta juyo a hankali, idonta ya sauƙa kan baiwar.. ​“Ke,” Zayana ta furta da murya kamar sauƙan aradu... “Idan kina da abin faɗa, ki faɗa. Idan kuma kallon kike, ki tabbatar kallo ne na ƙarshe.” ​Ladi ta durƙusa da sauri, jikinta na rawa. “Af...afuwa nake nema, Gimbiya. Kwarjininki ne ya tafi da ni.” ​Zayana ta ja tsaki, ta yi murmushin mugunta.. “Kwarjini ko tsoro? Ki sani, idan na sake ganin idonki a nawa ba tare da izini ba, to ranar za ki daina ganin hasken rana. Ɓace min da gani!” ​Ladi da gudu tana karkarwa tabar wurin, Zayana kuma ta ci gaba da tafiya tana gyara yatsun hannunta, zuciyarta tana wasi-wasi kan dakarun Pavilion dake tsaye a waje.. ​A can cikin fadar, Sarki Nourdeen yana zaune a kan kujerarsa, gumi na keto masa. Ganin yadda rundunar Pavilion ta cika harabar fadar ya fahimci cewa idan ya bari Chief Onyx ya tako ƙafarsa zuwa Alhamra, to mulkinsa da mutuncinsa za su iya girgiza.. ​Cikin sauri ya ƙira babban sakatarensa, ya umurce shi da ya ɗauki alkalami da takarda.. "Rubuta masa saƙo yanzu," Sarki ya faɗa cikin murya mai nauyi. " *Ka ce masa*.. Ba sai ka zo ba. Ni da kaina zan zo har inda kake.".. ​Sarki ya yi hakan ne domin kiyaye kansa. Ya san cewa idan Chief Onyx ya shigo fadar, sirrin dake tsakaninsu zai iya bayyana a idon gimbiyoyi da talakawan gari. Ya fi so ya tafi can yankin Pavilion ya fuskanci kaddararsa shi kaɗai, maimakon ya jawo bala'i cikin gidansa.. ​Duk da cewa zuciyarta ta ɗan buga ganin zafafan makaman da suke riƙe da su, sai ta dake. Ta ƙura wa babban jami'in dake jagorantarsu ido, wani gardi mai ƙaton jiki, sanye da baƙaƙen kaya da gilashi. ​Jami'in Pavilion ya ɗago kai ya kalli Zayana. Ko kifta ido bai yi ba, kuma bai nuna alamun rurrusunawa ga matsayinta na Gimbiya ba. Wannan rashin girmamawa ya kusa sa Zayana ta fusata, amma kwarjinin da dakarun suke da shi ya sa ta haɗiye fushin. Ta lura cewa kowace mota tana ɗauke da tambarin Pavilion Kingdom, tambarin da take gani a matsayin kalubale ga mulkin mahaifinta.. ​"Ina yake?" Zayana ta furta a fili, muryarta na ratsa sanyin iskar wurin. Tana nufin Sarkin Pavilion. ​Babban jami'in bai amsa ba...domin ko kallo bai isheta ba. ​Sarki ya fito da kansa har bakin fadar, ya miƙa wasiƙar ga jami'in Pavilion dake jagorantar rundunar.. Jami'in ya karɓi wasiƙar ba tare da ya rurrusuna ba, ya buɗe ta ya karanta. ​Zayana tana gefe guda tana kallon wannan dambarwar, tana mamakin me ya sa mahaifinta yake ƙasƙantar da kansa haka. Jami'in Pavilion ya jinjina kai, ya yi wa mutanensa nuni da hannu. Lokaci guda suka buɗe motocin su suka shiga, hayaƙin dake tashi ta rufe sararin samaniya yayin da suka fara ficewa daga fadar... ​Zayana ta tsaya tana kallon yadda suka fara fita daga fadar cikin tsari da iko. Zuciyarta ta cigaba da wasi-wasi... "Waye wannan Sarkin Pavilion ɗin? Me yasa kowa ke tsoronsa? Kuma me yasa kamanin mutanensa suke nuna cewa sun fi mu komai?" ​Ta ƙaraso kusa da mahaifinta, tana kallon bayan motocinsu dake ɓacewa.. "Daddy, me ya sa za ka ce za ka je wurinsa? Shi wane ne da har zai sa ka bar masarautarka ka nufi tashi? Shin Alhamra ta zama ƙarƙashin ikon Pavilion ne ba tare da mun sani ba?" ​Sarki Nourdeen bai ko kalle ta ba, ya juya cikin fada yana cewa, "Akwai abubuwan da kika fi ƙarfin sani Zayana..." Bayan motocinsu sun ɓace wa gani, Sarki ya koma cikin ƙuryar ɗakinsa na dake yanzu baya tare da ko wace mata... Bai so Chief Onyx ya zo nan domin idan ya zo, gidan sarautar zai iya zama tamkar gidan kallo, kowa zai so ya ga kwarjinin sarkin Pavilion, wanda hakan zai jawo tambayoyi marasa iyaka... "Ba zan bari su ganshi a nan ba," Sarki ya raɗa wa kansa yana goge gumin goshinsa. "Idan ya zo nan, asirina zai ruguje a gaban ƴaƴana."... ​An bar Gimbiya Zayana a tsaye, jikinta ya yi sanyi. Ta rasa gane dalilin da ya sa mahaifinta yake nuna wata irin fargaba a fili game da mutanen nan. ta juyo, tana takawa a hankali zuwa sashenta, kanta cike da tambayoyin da babu mai ba ta amsarsu. ​Tana tafiya tana nazarin wasiƙar da ta ga an bayar, me ya sa sarki ya rubuta masa cewa ba sai ya zo ba? Shin me sarki yake tsoron zai faru idan kowa ya ga fuskar sarkin Pavilion?... ​A can ɓangaren Gimbiya Chingching, labarin dake girgiza masarautar bai ma shigo cikin kunnenta ba. Tana zaune a kan lallausar sofa, idanunta sun ƙafe a kan TV tana kallon katun (ƴan gwaigwai), tana ta dariya tana turo baki idan aka daki ɗaya... ​Wata ma'aikaciya dake gyaran falon, tana goge wani tebur kusa da ita, ta kasa jurewa sai da ta yi magana.. "Gimbiya Chingching, shin ba ki da labarin rundunar Pavilion Kingdom sun zo wannan masarautar ne?" ​Chingching ba ta ko juyo ba, idonta yana kan TV, ta ce cikin shagwaɓa.. "Su waye kuma pabiliyooo...?" ​Ma'aikaciyar ta ja numfashi, ganin cewa wannan yarinyar ba ta ma san me duniya take ciki ba. Ga kowa Pavilion tsoro ne da fargaba, amma ga Chingching, suna ne kawai mai wahalar faɗi. Ma'aikaciyar ta girgiza kai kawai ta ci gaba da aikinta, ta ga gara ma ta yi shiru... ​Ganin ma'aikaciyar ta yi shiru, Chingching ta ɗan harare ta tana turo baki.. "Kumaaaa za ki dame ni! Yooo ni ina ruwana da wani wani wani mene sunan? Uhmmm ni ki ƙyale ni. Ni yunwa ma nake ji... Dubi ma yadda kike goge nan, kin tare min TV." ​Chingching ta koma ta kwanta tana rungume da toy🧸 ɗinta.. tana jira a gama shirinta na abincin rana, yayin da duk gimbiyoyin gidan suke cikin zulumi, ita nata damuwar ba ta wuce abinci da ƴan gwaigwai ba.... Aayat tana can a nata sashen, tana ta zirga-zirga tamkar wadda aka yi wa bushara da saƙon mutuwa. Yau ta kasance rana ta musamman, domin kwata-kwata ba ta yi shigar Inuwa ba. Tana sanye da doguwar riga ta sarauta, gashinta da fuska a rufe ga farin glass akan dara-daran idanuwanta, tana jiran jin ko sarki zai ƙira duk gimbiyoyin don yi musu bayanin abin da yake faruwa... ​Duk sanda ta ji motsin takun tafiya a waje, sai gabanta ya faɗi, tana tsammanin bafade ne aka turo ya ƙira su. Amma shiru, har dare ya raba sarki bai nemi kowa ba. Wannan shirun ya fi kowane hayaniya ban tsoro a wurinta, domin tana jin cewa mahaifinta yana ƙoƙarin rufe wani babban rami ne kafin kowa ya gani... ​A ɗayan ɓangaren kuwa, Gimbiya Maayah tana can kwance a kan katafaren gadonta, fuskarta a murtuke ba wai don zafin ciwo kaɗai ba, har da takaicin rashin samun damar fita ta ga abin da idonta yake son gani... Faɗuwar da ta yi a kan treadmill ta bar mata raɗaɗi a ƙunkuminta da bayanta wanda ya sanya koda juyawa ta kasa yi.. ​Mama Liyatu tana zaune a gefenta, tana dunduma mata baya da tsumman da aka tsoma a ruwan zafi tana lallashi... ​"Yi haƙuri gimbiyata," Mama Liyatu ta faɗa cikin sanyin murya.. "Gobe idan Allah ya kai mu likita zai zo ya duba ki, zai baki maganin da zai sa ki miƙe nan take.".. ​Maayah ta cije laɓe, tana kife da kanta akan gadon domin kibda ciki tayi... ​Duk wani motsi ya tsaya a masarautar.... Ma'aikata suna tafiya ne a cikin sanɗa gudun kada su tayar da fushin sarki... Domin a wannan ranar har zuwa gobe komai zai iya faru idan wani ya kuskura ya aiwatar da laifi wa sarki, domin a kansa za'a huce takaici... Iskar daren tana kaɗawa da wani irin sanyi daban, mai ɗauke da ƙamshin dawakan Pavilion da wani irin ƙamshin hayaƙin motocinsu waɗanda suka riga suka bar birnin, amma kwarjinin motocin yana nan maƙale a zukatan mutane.. ​Kowa yana jiran gobe.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣0️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Ayat ta tashi da safe tana jin wani irin nauyi a zuciyarta. Ganin ba za ta iya zama a matsayin gimbiya tana jiran abin da ba ta sani ba, ta koma asalin shigarta ta Inuwa. Ta ɗaura damararta, ta sanya kayan sojan masarauta, sannan ta fito don ganin abin da yake faruwa a tsakar gari... Tana isa tsakiyar masarautar sai ta ci karo da Master Ibrahim. Ibrahim mutum ne mai zafi da kishin aiki, kuma shi ne yake lura da yawancin motsin ma'aikatan tsaron fada. Ibrahim ya tsaya cak, ya zuba wa Inuwa idanu, yana nazarinsa kafin ya nisa ya ce "Inuwa! Ina ka shiga ne kwana biyu? Ba na ganinka a wuraren aikinka, sannan ba ka bin tsarin yadda aka tsara maka hidima. Ko ka manta dokar masarautar nan ne?" Inuwa yana sosa wuya cikin nuna alamar ba ya jin daɗi, ko da yake a ransa takaici ne ya cika shi "Gafara nake nema Master. Kwana biyu bana jin daɗin jikina ne, shi ya sa ban fito ba." Ibrahim ya jinjina kai, fuskarsa ba alamun wasa ya ce, "Toh, Allah ya ƙara sauƙi. Amma yanzu tunda Allah ya haɗa mu, akwai inda nake son fita a gari. Za mu tafi tare ne don ka taya ni wasu ayyuka." Inuwa bai yi gardama ba domin ya san idan ya ƙi, Ibrahim zai iya bincika dalilinsa wanda zai iya janyo masa matsala. "Ba damuwa Master, mu tafi," ya faɗa a takaice... Maimakon su ɗauki dawakai ko ababen hawa, Ibrahim ya yanke shawarar su taka da ƙafa. Suna tafiya suna ratsa lungu da saƙo na birnin Alhamra. Wannan tafiyar ta bawa Inuwa damar ganin yadda talakawan gari suke magana ƙasa-ƙasa game da motocin Pavilion da suka gani jiya... Ibrahim ma ya yi shiru yana kallon gari, shima kansa kwanan nan bai fito ba, don haka yake son shaƙar iskar gari don jin abin da mutane ke faɗa... Suna tafiya gefen titi, Ibrahim yana ta jansa da hira yana bashi labarai, amma hankalin Inuwa yana can nesa. Tana tunanin halin da mahaifinta yake ciki da kuma tsoron da Pavilion ya galla wa masarautarsu... Saboda zurfin tunani, Ayat ba ta san lokacin da kafafunta suka soma raba ta da gefen titin ba, ta haura har tsakiyar titi ba tare da ta sani ba. Kwatsam! Sai wata mota kirar Jeep ta taho da gudu tana kokarin ritsa ta. Ibrahim ya zaro ido ganin motar zata banke Inuwa. Cikin zafin nama da kwarewa irin ta jarumai, ya sa hannu ya janyo Inuwa da karfin gaske don ceton ransa. Ibrahim ya zata zai ji nauyin jikin namiji amma abin mamaki sai ya ji kamar iska ya janyo. Hakan ya sa Ibrahim yin baya saboda karfin janyon da ya yi, shi kuma Inuwa ya faɗa kai tsaye kan faffadan kirjinsa. Suka tafi tare suka faɗi a kasa a tsakiyar titin, yayin da sauran mutane suka daskare suna kallonsu... A nan ne duniyar Ayat ta tsaya cak. Ta faɗa daidai kan fuskar Ibrahim, wanda hakan ya sanya lebbansu suka haɗe wuri ɗaya. Wani irin numfashi ne yake fita daga juna, bugun zuciyar Ayat ya tsananta har tana jin sautin na Ibrahim a jikinta. Sun ɗauki wasu dakikoki a haka, kowa ya kasa motsi. Ibrahim ya zuba mata ido, yana jin wani irin sanyi da laushin da bai taba ji ba a jikin namiji. Ayat kuwa, manyan idanunta sun cika da firgici tana kallon kwayar idon Ibrahim wanda shima ya ruɗe... Da sauri Ayat ta dawo cikin hayyacinta, ta zabura ta tashi daga kansa tana sakin numfashi a hargitse... Abu na farko da ta yi shi ne sa hannu ta taɓa lebbanta, sannan ta riƙa taɓa fuskarta tana duba ko gemun da sajen dake fuskarta sun cire saboda gogayyar da suka yi... Taji su nan normal, sai ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya, duk da cewa jikinta har yanzu ɓari yake yi... Ibrahim shima ya miƙe a hankali yana kakkabe kayansa, amma hannunsa ɗaya yana kan lebbansa. Ya kura wa Inuwa ido cikin wani irin mamaki da shakku. A ransa yana faɗin "Ta ya namiji zai kasance da leɓe mai laushi haka? Me ya sa zuciyata ta buga da karfi lokacin da jikinmu ya hade?" Ya so ya yi magana, amma makogwaronsa ya bushe... Shi kuma Inuwa ya ƙi yarda su haɗa ido, ya juya baya yana nishin kuncin abin da ya faru. Sun ci gaba da tafiya ɗaf-ɗaf da juna, amma babu wanda ya iya kallon ɗan uwansa, ballantana a yi magana. Ibrahim ya lura cewa tun daga wannan faɗuwar Inuwa ya ƙara nuna wata irin natsuwa da nauyin jiki.... Don ya kawar da tunanin da yake addabarsa, sai ya riƙa kallon gefe da gefe yana son ya tabbatar wa kansa cewa Inuwa namiji ne kamar kowa... Suna shiga tsakiyar babban kasuwar birnin, nan take yanayin wurin ya canja.. Fitowar Inuwa a fili ba tare da kowace kariya ba ya janyo hankalin kowa. Duk inda suka ɗora ƙafa, sai an dakata ana kallonsu.. Kyawun fuskar Inuwa duk da gemun da ya sanya, ya kasance wani irin kyan dake fitar da haske mai ban tsoro. 'Yan mata dake gefen shaguna da waɗanda suke ciniki duk suka saki baki suna kallo. Maganganu suka fara tashi ta kowane sashe.. "Wow! Dubi wani handsome guy! Gaskiya ya haɗu," wata yarinya ta faɗa tana dafe ƙirji.. "Ya Allah! Wani irin kyau ne haka? Anya wannan mutum ne na duniya?" Wata kuma ta tambayi ƙawarta cikin mamaki... Wata tsohuwa dake sayar da kayan marmari ta gyara gilasinta, "Wannan kam aljani ne! Domin kaf birnin nan da gefenta, ban taɓa ganin wanda yake da kyan wannan yaron ba. Dubi fatarsa tamkar madara." Duk waɗannan yabo da kirari suna shiga kunnen Inuwa, maimakon ta ji daɗi sai ta ƙara jin haushi da matsuwa... Tana jin tamkar kowa yana leƙen asirinta ne ta cikin fatarta. Ta ƙara saurin taku, tana son ta ɓace wa idanun mutane.. Ibrahim kuwa ganin yadda Inuwa yake cin magani yana harara, sai abin ya ba shi dariya. Ya fara ƙunshe dariyar dake neman ƙwace masa, ganin yadda kowa ya rikice a kan ma'aikacinsa... "Inuwa, ka ga yadda ka kusa janyo mana gobara a kasuwa? Ko mazan ma kallonka suke," Ibrahim ya faɗa ƙasa-ƙasa yana ɗan taɓa kafaɗarsa cikin sigar tsokana... Inuwa ya juyo ya harare shi da manyan idanunsa.. "Master, don Allah mu koma masarauta. Na gaji, sannan ban son wannan kallon da ake mana." Ibrahim ya yi murmushi, ya fahimci Inuwa baya son hayaniya. "To shikenan, mu zagaya ta wannan lungun mu koma fada, kafin wata ta zo ta sace ka ta gudu da kai." Ibrahim ya dube shi, ganin yadda Inuwa yake faman basarwa kamar ba shi ne ya kusan cinye zuciyarsa ɗazu ba. Ibrahim ya kasa jurewa, ya ce.. "Wai Inuwa, me ya sa ba ka yi min magana ba tun bayan faɗuwar nan? Ko dai har yanzu kana jin tsoron motar ne?" Inuwa ya ɗan tsaya, ya gyara rawaninsa da ya ɗan karkace ba tare da ta kalle shi ba ta ce... "Ba komai Master. Kawai dai ina tunanin yanda Sarki yaƙi fitowa yau tin jiya, kuma kasuwar nan akwai hayaniya da yawa.".. Haka suka ƙaraso ƙofar masarauta, kowa na riƙe da abin da yake ji a ransa... Suna isowa tsakiyar fada, sai wani bafade ya tarye su da sauri... "Master Ibrahim! Sarki yana neman ka a yanzu haka a babban ɗakin taro." Ibrahim ya kalli Inuwa, ya gyara tsayuwar takobinsa. "Ka ga ko? Abin da kake fargaba ya zo. Mu je mu ji me Zaki yake tafe da shi.".. Inuwa cikin tsoro ya ja da baya yana zaro ido ya ce, "A'a a'ahh iya kai kaɗai ake nema, kuma kumaa cikina ciwo yake..." Wani jami'in da ke gefe yana dariya ya ce, "Kodai period zaka yi ne Ɗan ƙwaƙur?..." Ibrahim ya kalle shi tare da faɗin "Kai, bana son iskanci faa..." Sannan ya kalli Inuwa ya ce, "shi ke nan, ka je ka huta kawai..." Inuwa ya gallawa wanda yayi mishi maganar nan harara haɗe da gatsine.... ✨✨✨ Tun lokacin da Ayat ta taka kafarta a wajen masarauta a matsayin Inuwa, wani daddaɗen ƙamshi ya tashi ya ratsa sararin samaniya har zuwa can zurfin duniyar aljanu ta Power Pool. King Diamond dake zaune a kan karagar mulkinsa, ya ji wani irin bugawa a zuciyarsa. Bai buƙaci a faɗa masa ba, ya san Ayat ɗinsa ce take yawo a cikin gari... Ta hanyar idonsa na tsari, ya riƙa kallon kowane takun da Ayat take yi tare da Ibrahim. Lokacin da motar ta kusan bugan Ayat, Ibrahim ya janyo ta suka faɗi har lebbansu suka haɗe, King Diamond ya daka wani uban tsalle idanunsa suka canza launi zuwa jawur tamkar wuta... Wani azababben kishi ne ya turnuke shi... "Aayat ɗina ce!" ya furta cikin murya mai rawar gaske dake ɗauke da fushi.. "Babu wani ɗan Adam da ya isa ya taɓa ta, balle ya ji yanayin daɗin da aka tanada domina." Cikin kiftawar ido, King Diamond ya bayyana a kofar masarautar Alhamra ta waje. Farin dogon gashinsa dake tafe har kugu yana kaɗawa a cikin iska, idanunsa kuma suna fitar da wani irin kwarjini na ban tsoro. Ya nufo kofar masarautar cikin tafiyar izza da nuna iko, yana kallon Inuwa da Ibrahim dake kokarin bacewa cikin gida... Abin al'ajabi, duk da tsayuwar sa a fili, babu wani soja ko mai gadi da yake iya ganinsa. Suna ta faman zirga-zirgarsu tamkar iska ce kawai take wucewa. King Diamond ya yunkura zai ratsa ta tsakiyar gate din masarautar don ya biyo Ayat. Kwatsam! Sai wani irin haske mai launin gwal ya fito daga jikin bangon masarautar ya bugi kirjinsa da wani irin ƙarfi... Sarkin aljanun ya tafi sama tamkar an harba kibiya, ya yi ta jujjuyawa a cikin iska yana neman hanyar daidaitawa. Sai da ya dage sannan ya tsaya daram a cikin iska yana kallon masarautar daga sama, fuskarsa ɗauke da mamaki... A nan ne ya fahimci cewa masarautar Alhamra ba masarauta bace kawai ta mutane. Akwai wani tsari na musamman da aka yi mata, shinge ne na ruhaniya wanda yake toshe hanyar kowane aljani ko shaidanin abu. Wannan hasken da ya buge shi, wani irin makami ne dake iya ƙona fatar aljani ya mayar da ita toka a cikin daƙiƙa kaɗan... Duk da azabar zafin da yake ji a jikinsa, bai cire idonsa daga kan Ayat ba... "Wannan shingen ba zai taɓa rabani da ke ba Ayat," ya raɗa a cikin zuciyarsa. "Zan nemo hanyar da zan shigo, ko da kuwa hakan zai kai ni ga rasa dukkan ikona." Ayat ta miƙi hanyar masarautar tana shirin tafiya ciki, kwatsam sai ta ji wani irin sanyi mai ratsa jiki ya ziyarce ta, sanyin da bai dace da yanayin zafin rana na lokacin ba. Wani irin yanayi ne na daban wanda ya sanya kowace gashi na jikinta tashi tamkar akwai wanda yake kallonta daga can sama da idon ɗan Adam ba zai iya gani ba... Ta tsaya cak, ta kasa ci gaba da takun da take yi. A hankali ta ɗaga kanta tana kallon sararin samaniya, idanunta suna yawo a cikin gajimare. Ba ta ga komai ba amma zuciyarta tana gaya mata cewa akwai wani abu... Ibrahim wanda yake shirin barin wurin zai je ƙiran sarki, ya ji takun Inuwa ya tsaya. Ya juyo ya gan ta a tsaye tamkar gunki, kanta a ɗage tana kallon sama cikin wani irin yanayi na shauƙi da fargaba... Ya nufe ta, ya tsaya kusa da ita, ya bi layin kallon idonta amma bai ga komai ba sai hasken rana. Ya dafa kafaɗarta, wanda hakan ya sanya ta firgita ta dawo cikin hayyacinta... "Inuwa, me kake kallo a sama?" Ibrahim ya tambaya cikin sautin mamaki... "Ko akwai wani tsuntsu ne da kake neman gani, ko kuwa tunanin ɗazun ne ya dawo?" Ayat ta sauƙe idanunta cikin sauri, tana ƙoƙarin saita numfashinta da ya fara hargitsewa. Ta kawar da kai tana shafa wuyanta.. "Ba... ba komai Master. Kawai dai na ji kamar iskar sama ta canza launi ne, kila gajiya ce." Ibrahim bai gamsu da amsar ba, domin ya ga yadda idanunta suka firfito, amma sai ya share kawai ya ce, "To mu ƙarasa ciki na rakaka, kafin rana ta ƙara dukan ka ka fara ganin abubuwan da babu su.".. Ayat ta ce, "a'a zan ƙarasa da kaina, domin wurin kwanan namun ba nisa..." Ta ci gaba da tafiya.. Bayan ta koma sashenta, ta cire kayan maza da suka matse asalin jikinta, ta shiga wanka don wanke duk wata gajiya da ƙurar birnin Alhamra. Bayan ta fito, ta sanya kayan gimbiyanci na alfarma waɗanda suka ƙara fito da asalin kyawunta da kwarjininta na mace... Ta tsaya a gaban babban madubin dake ɗakinta, tana kallon kanta. Kwatsam sai tunanin wannan baƙon mutumin da suka haɗu a bakin kogi ya dawo mata a rai. Nan take annurin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka sauya launi, ta haɗe gira cikin wani irin azababben fushi... Zuciyarta ta fara zafi tana bugawa da sauri. Wannan mutumin ya zame mata tamkar ƙayar dake maƙale a maƙoshi. Ta yi fatan ace yana gabanta a wannan lokacin, da lallai ta yi amfani da takobinta ta sare masa wuya don ta huta da wannan kallon rainin hankalin da ya yi mata... "Waye kai da za ka keta min hurumi?" Ta faɗa a fili tana kallon madubin, muryarta na rawa cikin fushi... Babban abin da ya fi ƙona mata rai shi ne, ya karya mata babban alƙawarin da ta yi na tsawon shekaru. Ta haramta wa kowane ɗan Adam ganin asalin surar jikinta ko fuskarta a matsayin mace, amma shi a rana ɗaya ya ga abin da kowa ya daɗe yana nema ya rasa. Ta tuna lokacin da ta cire kayanta a bakin kogi, ashe yana can yana kallon sirrin jikinta... Wani irin tsanarsa ne ya ziyarci zuciyarta, tsanar da ba ta taɓa ji wa kowane ɗan Adam ba. Ta kura wa madubin ido tamkar tana ganin hotonsa a ciki, tana jan numfashi mai zafi.. "Ka kalle ni... ka kalli abin da na adana wa wanda zan aura kadai," ta cigaba da magana a fili tana nuna kanta a madubi, "amma ka sani, wannan kallon da ka yi min zai zama silar halakar ka. Ko kai waye, ba zan taɓa yafe maka ba. Wallahi sai na ga bayan ka!" Tana tsaye tana huci, idanunta cike da tsanar mutumin da ya keta mata alfarma. "Wallahi duk inda kake, sai na sare maka wuya! Ka kalle ni ka ga asirin da na adana, amma ka sani wannan shi ne ganinka na ƙarshe!" Tana cikin wannan zafin muryar, sai ta ga wani abu ya fara canzawa a cikin madubin.. Ba zato ba tsammani, sai hoton kanta lokacin da take matsayin Inuwa ya bayyana a cikin madubin ya fara yin dishi-dishi. Ta zaro ido, ta daskare a inda take tana kallon yadda siffarta na yanzu ya ɓace, Inuwa ne ya bayyana a cikin madubin... Ayat ta ja baya da sauri, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi.... "Wannan ni ne ai a matsayin Inuwa...." Ba tare da ta ga leɓensa yana motsi ba, sai ta ji wata murya ta ratsa ɗakin, muryar tana tashi ne daga cikin madubin, tana amo tamkar ana hura busa.. "Kada ki ɓata kyawun fuskarki da fushi Ayat.... Idan har sarar wuyana shi ne zai sanyaya miki rai, to ki sani... wuyana yana nan yana jiran takobinki. Amma kafin hakan ta faru, ki sani cewa abin da na gani, ba zan taɓa mantawa da shi ba har abada.".. Ayat ta ɗauki wani butar fure dake kusa da ita ta kwala wa madubin da ƙarfinta.. "Kaaaaaaassss!" Madubin ya fashe, ya farfaske ya zama guntu-guntu a ƙasa. tana sauke numfashi tana kallon fasassun gilasan. Jikinta yana rawa, gumi ya jige mata goshinta... "Ta ya ya san suna na? Ta ya ya shigo cikin madubi na?" Ta raɗa tana kallon yadda kowane guntun gilashi yake nuna fuskarta guda guda.. Tsoro ya maye gurbin fushin da take ji. Ta gane cewa wannan mutumin da take nema ta kashe, tabbas ba mutum ba ne... Cikin fushi ta furta, "Ƙarya ne ba aljan bane, mutum ne kamar kowa, kawai yana amfani da sihiri na tsafi ne kuma sai na wargaza tsafin nan..." Ta sulale ta zauna a ƙasa, tana kallon fasassun gilasan, tana jin tamkar har yanzu idanunsa suna kallonta ta cikin tarkacen gilashin... Can sai ga Saratu ta shigo da gudu jin ƙarar har ya sauƙa falo.. Haka take bin madubin da ya farfashe a ƙasi ga kuma Gimbiya a durƙushe cikin ɓacin rai.. Saratu ta ƙaraso tana faɗin "Gimbiya meya faru ne? Ke da wa? Meyasa kika fasa madubin ki? Wa ya ɓata miki rai?..." In short answer Ayat ta ba da "Ba komai..." Haka Saratu ta lallashe ta.. Sannan ta share mirror ta gyara ɗakin gaba ɗaya... Bayan Saratu ta share fasassun gilasan ta fita, Ayat ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na kunci da fargaba. Shirun da ɗakin ya yi ya dawo mata da sauti da kuma kwarjinin muryar da ta ji daga cikin madubin.... Tana zaune a gefen gado, tana kallon inda madubin yake a dā, yanzu kuma babu komai sai bango. A ranta tana tambayar kanta.. “Waye wannan mutumin? Ta yaya har ya san sunana?”.... ✨✨✨ A can bangaren Gimbiya Maayah, ɗakin ya cika da sautin nishi mai ban tausayi... Maayah tana kwance rubda-ciki, fuskarta jiƙe da hawaye da gumi. Faɗuwar da ta yi a kan treadmill ba ƙaramin rauni ta ji ba.. ƙunƙuminta ya taɓu, ƙashin bayanta kuma yana mata wani irin raɗaɗi tamkar ana huda ta da mashi... Mama Liyatu tana gefe guda tana lallashi, amma Maayah ihu take ta saki.. "Abul! Spinal cord ɗina ya samu matsala! Shikenan ba zan sake tashi ba! Wayyo Allah na... ku taimake ni! Ba zan iya motsa ƙafata ba!" Sarki Nourdeen, wanda yanzu ne labarin hatsarin ya isa gare shi, ya shigo ɗakin da fadawansa suna biye da shi cikin matuƙar damuwa.. Ganin ƴarsa a wannan yanayin sai da zuciyarsa ta girgiza... Sarki ya zauna a bakin gadon, ya dafa kanta cikin muryar rarrashi, "Kiyi haƙuri Maayah... komai zai wuce." A daidai wannan lokacin Doctor ya shigo da sauri, ɗauke da kayan aikinsa. Ya gaishe da Sarki cikin sauri sannan ya fara duba Maayah. Kowane taɓi da zai yi mata a baya sai Maayah ta tsandara uban ihu dake firgita kowa... Doctor ya duba idanunta, ya duba yadda ƙafafunta suke motsawa sannan ya yi shiru yana nazari... Sarki ya kalle shi cikin fargaba, "Doctor, ya ake ciki? Shin raunin yana da girma?" Doctor ya gyara gilashinsa, ya kalli Sarki sannan ya kalli Maayah dake kuka... "Mai martaba, ƙashin ƙunƙuminta ya ɗan goce ne, kuma tsokokin bayanta sun kumbura sosai. Za ta yi jinya ta tsawon lokaci, kuma dole ne ta daina yawan motsi ko fushi, domin kowane tashin hankali zai iya sa jikinta ya yi paralysis." Jin haka Maayah ta ƙara fashewa da kuka. Girman kanta da izzarta duk sun bi ruwa, a yanzu kawai neman sauƙi take... A daidai lokacin da Doctor yake ƙoƙarin yi wa Maayah allura, ihun kukanta ya ƙaru sosai "Wayyo bayanaa! Wayyo Allah na!", Ta can gefe guda kuma aka fara jin waƙe-waƙe da raye-raye... Ba zato ba tsammani, sai ga Chingching ta shigo, tana sanye da doguwar riga mai sheƙi, tana riƙe da toy ɗinta a hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma tana riƙe da gorar ruwa. A bayanta wasu bayinta ne guda biyar suke mata rakiya, kowaccen su tana ɗauke da tiren fure da lemo, suna tafiya a jere yayin da Chingching take ta rera waƙarta da ƙarfi.. _🎶🎶 Gimbiyar mata, Firdausi autar mataa, Firdouss babu kamar kiii, Firdouss, Firdausi ƴan mata, Firdouss tauraruwar mataaa..🎶🎶_ Chingching ta ƙaraso tsakiyar ɗakin, ta tsaya tana kallon Maayah dake kwance tana murƙususu. Dai-dai lokacin ta gama waƙar... Ta turo baki, ta zura wa Maayah idanu na wasu daƙiƙoƙi kafin ta ce cikin muryarta ta shagwaɓa... "Haba Aunty Maayah! Tun jiya nake jin kina ta ihu kamar wadda aka sace maki takalmi... Me ya faru ne? Wai dama gudu kike yi? To ai na gaya miki ke ba doki ba ce, me ya sa kike son gudu irin na dawakai?"... Maayah ta buɗe jajayen idanunta, tana kallon Chingching cikin tsananin takaici. Ta so ta daka mata tsawa, amma zafin ƙunƙuminta ya hana ta ko motsawa... "Ching...ching... tafi nan! Ba na son ganinki!" Maayah ta faɗa cikin raunannen murya.. Amma ina, Chingching sai ma ta ƙara kusanto gadon, ta kalli Doctor ta ce.. "Doctor, shin gaskiya ne Aunty Maayah ba za ta iya sake tashi ba? Naji ana faɗa a waje wai bayanta ya rabe gida biyu. Idan haka ne, to wa zai riƙa tura ta a keken guragu?.." Ta juya ga mahaifinta, ta rungume shi tana magana... "Daddy, ka ga Aunty Maayah ko? Ai ni na san me ya sa hakan ta faru. Kullum tana cikin fushi-fushi da masifa-masifa a zuciyarta, shi ne injin ya yi kaca-kaca da ita ya yar da ita ƙasa." Kowa a ɗakin ya yi shiru.. Chingching ta nuna wa bayinta alamar su ajiye abubuwan da suka kawo.. "Ga fure na kawo miki Aunty Maayah, don idan kika kalle su kya ji sanyi. Amma gaskiya ki daina gudun nan, ni gashi ina zaune ina kallon katun ɗina, amma babu abin da ya faru da ni." Ta ƙara matsawa daidai kunnenta ta raɗa mata.. "Kiyi haƙuri kin ji? Amma idan ba za ki iya tashi ba, inaso duk takalmanki masu bala'in tsayin nan ki kwaso mun su...." Daga nan ta juya, ta yi nuni ga bayinta, suka fita tana ta rangwaɗa sannan ta cigaba da waƙar ta, ta bar Maayah tana huci, ranta ya ɓaci fiye da yadda jikinta yake ciwo... Sarki ya dafe kansa, ya san cewa halin Chingching sai dai addu'a... "Maayah, kiyi haƙuri... yarinya ce," ya ce a hankali. Amma Maayah a ranta tana faɗin... "Wallahi idan na tashi, Chingching za ki san kin shigo ɗakina kin mun rashin kunya!"..... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣1️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan ficewar Chingching ɗakin ya ɗan yi tsit, amma sanyin iskar ya sauya yayin da aka fara jin takun takalmin Gimbiya Zayana.. Ba surutu, ba hayaniya sai kawai ƙamshin turarenta mai tsada wanda ya riga ta shigowa ɗakin.. Zayana ta shigo ɗakin da takun alfarma, kanta a ɗage tamkar ba ta son taka ƙasa. A bayanta wasu bayinta ne guda uku sanye da kaya masu kyau, kowaccensu tana riƙe da tiren azurfa dake maƙil da zaɓaɓɓun fruits waɗanda aka yanka su cikin fasaha.. Zayana ta tsaya nesa kaɗan da gadon Maayah, ta nannaɗe hannuwanta a ƙirji tana kallon Maayah da wani irin kallo na isa da kuma tausayi mai haɗe da izgilancu. Ba ta zauna ba domin ita a ganinta zama a gefen gadon mara lafiya ƙasƙanci ne.. "Ashe abin har ya kai ga kwanciya, Maayah?" Zayana ta furta cikin muryarta mai sanyi dake soka mutum tamkar kibiya... Maayah ta ɗaga kanta da ƙyar, idanunta suka sarƙe da na Zayana. Duk da ciwon dake jikinta, ba ta bar izzarta ta fito ba. Ta haɗe rai ta ce, "Kamar yadda kika gani Aunty Zayana. Amma kada ki damu, wannan kwanciyar ta ɗan lokaci ce. Ba zan ba ki farin cikin ganina a haka har abada ba." Zayana ta yi murmushin mugunta, ta nuna wa bayinta alamar su ajiye tiren fruits ɗin. "Na kawo miki waɗannan ne don su ƙara miki ƙarfi. Na ji ance faɗuwar taki ta yi muni, har ana zargin ƙashin bayanki ya samu matsala. Gaskiya ya kamata ki riƙa sani cewa jikinki ba na ƙarfe ba ne, akwai abubuwan da suka fi ƙarfinki." Zayana ta ƙara takawa kusa da gadon, ta sunkuya kaɗan ta yadda Maayah kaɗai za ta ji abin da za ta faɗa.. "Kina ta gudun neman Inuwa, gashi Inuwa ya jefar da ke. Yanzu wa zai zama gwarzon fada tunda jarumar gidan tana kwance tana kuka?". Maayah ta cije laɓe, ran ta ya ɓaci matuƙa... "Fita ki ba ni wuri Aunty Zayana! Bana buƙatar fruits ɗinki, kuma bana buƙatar tausayinki na ƙarya.".. Zayana ta miƙe tsaye tana gyara riga, ta kalli mahaifinsu dake gefe ta gaishe shi cikin girmamawa sannan ta juyo ga Maayah.. "Kiyi sauri ki warke... Masarautar tana buƙatar hayaniyarki. Amma kafin nan, ki ji daɗin kallon rufin ɗakin nan." Ba tare da ta sake cewa uffan ba, ta juya ta fice daga ɗakin, bayinta suna biye da ita. Ta bar Maayah tana jin wani irin ɗaci a ranta, domin kalaman Zayana sun fi allurar Doctor zafi... Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya kalli Maayah ya ce, "Ku daina haka, gimbiyoyi ne ku fa..." Amma Maayah ba ta ko saurare shi ba, ta juya kanta gefe tana kuka, kukan takaicin yadda kishiyoyinta na gidan sarauta suka zo suna ganin rauninta... Bayan ficewar Zayana, ɗakin ya rage saura ɗacin kalaman da ta bari... Maayah tana kuka ranta ya ɓaci, tana jin tamkar kowa ya tsane ta. Sai dai kwatsam sai ga Gimbiya Yumna ta shigo... Yumna ba ta zo da takun alfarma ko takun nuna mulki ba. Ta shigo ne tare da bayinta guda hudu waɗanda kowa ya sani ba bayinta ba ne kawai a wurinta, ƙawayenta ne.. Suna hira cikin kulawa har suka shigo ɗakin.. Ganin Maayah a kwance cikin wannan halin, idanun Yumna suka cika da kwalla nan take. Ta bar sauran bayin nata a baya, ta ƙarasa da sauri har gaban gadon Maayah... Ba tare da bata lokaci ba Yumna ta durkusa a kasa a gefen gadon, ta kama tafin hannun Maayah tana murza su a hankali, tana kallon fuskarta cikin matukar damuwa da tausayi.. "Aunty Maayah, dan Allah kiyi hakuri," ta fada cikin muryar kuka, "Wallahi tun da na ji labarin hatsarin nan, hankalina ya tashi. Allah Ya baki lafiya, Allah Ya kawo miki sauki..." Maayah ta kalli Yumna. A karon farko ta ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta. Ta lura cewa Yumna ba ta zo domin yi mata gatsali ko nuna mata gazawarta ba.. ta zo ne da gaskiyar zuciya... Kodayake Maayah mutum ce mai girman kai, amma ta kasa kwace hannunta daga cikin na Yumna.. "Yumna... na gode," ta faɗa a hankali, muryarta a sanyaye.. Yumna ta cigaba da murza hannun ta, tana kokarin sanya mata kwarin gwiwa... "Kada kiyi kuka, Doctor ya ce za ki warke. Kuma zan riƙa zama dake ina taya ki hira har sai kin tashi. Duk abin da kike bukata, ki fada min zan sa a shirya miki." Sarki wanda yake kallon dambarwar da ta faru tun daga kan Chingching, Zayana, har zuwa kan Yumna, ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya. Ya ji daɗi ganin yadda Yumna ta sanyaya ran ƴar uwarta... Bayan Yumna ta gama rarrashi, ta sa bayinta suka ajiye duk wasu kayan bukatu da suka kawo sannan ta sake sumbatar hannun Maayah kafin ta miƙe... ✨✨✨ Washegari da safe, masarautar tana cikin wani yanayi na daban. Ayat tana cikin babban ɗakinta, yau ma ta riga ta kammala shigarta ta mazaje, tana duba takobinta da sauran kayan aikinta... Saratu wadda ita ce amintacciyar ma'aikaciyar ta tana tsaye a wajen kofar dakin tana magana, domin Ayat ta kulle kofar yadda babu mai shigo wa... "Gimbiya! Labari ya iso cewa halin Gimbiya Maayah ya tsananta. Faduwar jiya ta taɓa ƙashin bayanta sosai. Yanzu haka ana shirin fita da ita kasar Indonesiya domin neman lafiya a manyan asibitocinsu," Saratu ta fada cikin damuwa. Ayat tana zaune, ta gyara rawuninta sannan ta amsa ta cikin kofa.. "Allah Ya ba ta lafiya.... Saratu ki haɗa kai da sauran ma'aikatana ku kai mata gaisuwa, na wakilce ku gaba ɗaya. Ku faɗa mata cewa idan sun dawo daga kasar wajen zan duba ta da kaina. Yanzu ina da ayyukan da zan kammala ne." Saratu ta amsa da "To shikenan Gimbiya," sannan ta juya ta tafi domin cika umarnin... Bayan jin tafiyar Saratu, Ayat ba ta bata lokaci ba. Ta nufi ɗakin sirrinta, ta danna madannin da ya buɗe mata elevator. Ta lula can karkashin kasa, ta bi dogon ramin nan dake cike da sirri har ta fito ta tsakiyar lambun masarauta inda iskar safe ta bugi fuskarta. Ta fara nata takun domin fita wajen masarautar... A ɗaya ɓangaren kuma, ɓangaren Gimbiya Maayah ya cika da ma'aikata da fadawa. Saratu da sauran ma'aikatan sun iso inda suka tarar da yanayin cike da sauri-sauri... Sarki yana tsaye fuskarsa cike da damuwa. Ko da yake shi ba zai tafi ba saboda nauyin sarauta da kuma matsalar Pavilion dake tunkaro shi, amma ya haɗa dukkan abubuwan da ake bukata. Wani babban jirgi na alfarma yana can yana jiran su a filin jirgin masarauta... Yumna wacce ta ƙara ziyartar Maayah tana gefen gadonta, tana rike da hannun Maayah. Ganin yadda ake shirin tafiya, Yumna ta kasa jurewa. Ta kalli mahaifinta sannan ta ce cikin damuwa "Abul, dan Allah ka ba ni izini in bi Aunty Maayah. Ba zan iya zama a nan ina tunaninta ba. Ina son in kasance kusa da ita har sai ta samu lafiya.".. Sarki ya kalli Yumna, ya san dacewar zuciyarta. Ya jinjina kai sannan ya ce, "Na yarda Yumna. Ki tafi ki kasance kusa da ita." Haka aka shirya komai cikin kwarewa. An ɗauki Maayah a kan stretcher domin kada kashin bayanta ya motsa... Wasu rantsattsun ma'aikatan fada da dakarun tsaro wato Special Guards suka bi bayansu domin basu kariya a kasar wajen... Motocin asibiti na alfarma suka dauke su zuwa inda jirgin yake, yayin da masarautar ta yi tsit, kowa yana addu'ar samun lafiya ga gimbiyar da kowa ya sani da takama, amma yau gashi rashin lafiya ya kwantar da ita... Yayin da aka kwashe Maayah aka nufi filin jirgi, ɗakin taron fada da sashen ma'aikata ya cika da raɗa da surutu. Ma'aikata da dama sun fara tofa albarkacin bakinsu... "Wai kun lura? Duk gimbiyoyin gidan nan sun zo ganin jikin Maayah, har da su Chingching da Zayana da ba su shiri, amma ban ga Ayat ba," in ji wata baiwa.. Wani bafade ya amsa, "Gaskiya ne, abin da ban mamaki. Ko da yake ta aiko Saratu amma ai kamata ya yi ta zo da kanta tunda tafiyar waje ce." Hatta Maayah tana kwance a cikin motar asibitin, zuciyarta cike take da takaici. Duk da ciwon dake jikinta maganar Ayat ta tsaya mata a rai. Ta lura cewa duk wanda take gani a matsayin ƙashin wuyanta ya leƙo ta, amma Ayat wadda take ganinta a matsayin mai nutsuwa, ita ce ta nuna mata halin ko-in-kula... Ba su sani ba, Gimbiya Ayat tana nan kusa amma ba a matsayin gimbiya ba... Tana sanye da shigar Inuwa tsaye a lokacin da aka fito da Maayah.. Ta kuma ga damuwar dake shimfiɗe a fuskar mahaifinsu.. Ayat ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya. Ba wai ba ta jin tausayin Maayah ba ne, a'a, zuciyarta tana cike da wani nauyi ne wanda ba za ta iya bayyanawa kowa ba... "Allah ya ba ki lafiya Maayah," ta faɗa a hankali cikin muryarta ta Inuwa.. A cikin jirgin kuwa, Maayah tana kwance a sashin gaggawa na jirgin ICU section, Yumna tana zaune a gefenta tana mata addu'a... "Aunty Maayah, ki daina tunani kinga har mun fara tafiya,".. Maayah ta kalli Yumna, sannan ta cije laɓe.. "Yumna, kin ga Ayat kuwa kafin mu fito?" Yumna ta yi shiru, ta kasa cewa komai sai daga bisani ta ce, "A'a Aunty, amma ta aiko Saratu..." "Saratu ba Ayat ba ce," Maayah ta katse ta cikin fushi. "Idan na dawo, zan nuna mata cewa ni ma na san darajar kaina.".. ✨✨✨ Bayan ficewar su Maayah, Gimbiya Ayat ba ta tsaya wata-wata ba. Ta nufi ɓangaren dawakai, ta hau dokinta ta fice daga masarautar Alhamra da gudu. Zuciyarta tana muradin isa babban kogin da ta saba zuwa, domin ta kwana biyu ba ta leƙa wurin ba... Tayi tafiya mai nisa, iskar daji tana dukan fuskarta har ta isa bakin kogin. Ta sauka daga kan dokin, ta shafa bayansa alamar rarrashi sannan ta nufi gaban ruwan. Bayan ta duba tsuntsuwarta ta ga tana lafiya, har ma ta tafi yawonta ta bar kananan ƴaƴanta, Ayat ta tsaya tana nazari... Hoton Maayah a kwance cikin jinya ya dawo mata, tana jin wani irin yanayi a ranta.. Kwatsam, waigawar da za ta yi, sai idanunta suka sauka a kan abin da ba ta yi tsammani ba... A can nesa kaɗan ta hango wannan mutumin mai farin gashi. Yana tsaye a bakin wani katon rami, wurin magudanar ruwa inda ruwa yake zuba da karfi. Kowa ya san wannan ramin, rami ne mai zaman kansa wanda duk wanda ya faɗa ciki, mutuwa ce kawai take jiran sa, domin ba ya fito wa... Mutumin ya juya baya, yana kallon yadda ruwan yake gangarawa cikin wannan zurfin. Dogon gashinsa dake ta sheƙi yana kaɗawa a iska... Wani murmushi na mugunta ne ya bayyana a fuskar Ayat. Ta ce a ranta, "Yau ce ranar da zan raba ka da wannan kwarjinin naka.".. Ta fara zaro takobinta a hankali, gudun kada ya ji motsinta. Idonta yana kansa tamkar mikiya, amma a cikin hanzarin zarowar takobin, sai takobin ta yanke tsakiyar tafin hannunta.. "Ahh!" Ta saki wani ɗan ƙaramin ƙara saboda raɗaɗi, cikin sauri ta kai ɗaya hannun ta toshe bakinta tana zaro ido, tana fargabar kada ya ji. Jini ya fara zuba daga tafin hannunta, amma ba ta ma kula da hakan ba. Wani irin kishi da fushi ne ya rufe mata ido... Ta ruga da gudu tana nufar kansa, takobinta a ɗage sama. Niyyarta guda ɗaya ce, ta sare masa wuya a yanzu tunda bai san da zuwanta ba. Tana isowa, ta kai masa wani mahaukacin sara a saitin wuyansa... Cikin wani irin salo da kwarewa dake nuna ba ɗan Adam ba ne, mutumin ya ɗan sunkuyar da kansa ba tare da ya juyo ya kalle ta ba. Takobin ta wuce, amma maimakon wuyansa sai takobin ta yanki tafin hannunsa shima, daidai inda ita ma take da ciwo.. Ganin bata sare shi ba, ga kuma yadda hannunsa ya yanku, firgici ya sa Ayat ta rasa inda za ta taka. Ƙarfin sarar da ta yi ya sa ta kasa saita tsayuwar ta, takobin ta subuce mata, ƙafa ɗaya ta zamile... "Aaaaaaaahhhhhhhh!!!!" Wani irin uban ihu ta saki yayin da ta tafi sama, ta faɗa kai tsaye cikin katon ramin nan dake zuba da ruwa. Zurfin ramin ya sanya ihunta yake ƙara nisa yana ɓacewa... Yayin da take sulalewa cikin ramin, tana ihu mai nuna cewa rayuwarta ta zo karshe, fararen idanun mutumin nan suka canza launi, suka koma shuɗi mai tsananin sheƙi. Wani irin haske mai launin shuɗi ya bayyayna, ya mamaye sararin ramin... Kafin ma jikinta ya taɓa ruwan dake karkashin ramin, King Diamond ya yi wani uban tsalle ya riga ta isa ƙasa, ya sa hannu ya rugume ta... Abin al'ajabi ba su faɗa cikin ruwan ba, kuma ba su yo sama ba kawai sai suka tsinci kansu suna shawagi a cikin iska, hasken shuɗin nan ya zame musu garkuwar dake riƙe da su... A cikin wannan yanayin, lips ɗinsu ya haɗe wuri ɗaya, suka shiga wata zazzafar sumbata mai cike da sirri. King Diamond ya haɗe tafin hannunsa mai ciwo da nata mai ciwon, ya harɗe yatsunsu ta yadda jinin da yake zuba daga hannayensu ya gauraye, ya zama guda ɗaya. Ɗayan hannunsa kuma yana riƙe da ƙunƙuminta ta baya, suna yawo a sararin iska idanunsu a lumshe... Bayan wani lokaci, ya buɗe idanunsa waɗanda suka zama shuɗi tsantsa. Ita ma ta buɗe nata, idanunsu suka sarƙe. Nan take Ayat ta dawo cikin hayyacinta, ta kawar da kai tana sakin wani irin ihu na firgici!.. ✨ Nan take hasken ya ɓace, suka bayyana a kan doron ƙasa a bakin kogin. Amma wani babban al'ajabi ya faru... Sun yi musayar siffa wato Body Swap!.. King Diamond ya koma asalin siffar Ayat. Yana tsaye sanye da kayan gimbiyanci na alfarma, sumar gashinsa na Ayat ta bazu har gadon baya, kyawun fuskarsa a bayyane yake radau babu rufin fuska ko gilashi... Ita kuma asalin Ayat, tana sanye da siffar King Diamond. Tana kwance a ƙasa ta kifa kanta, farin dogon gashin dake kanta ya zube har gadon baya, sanye da fararen kaya irin na aljanu.. King Diamond dake cikin siffar Gimbiya Ayat ya kalle ta, ya yi magana da muryarta ta mace mai zaƙi.. "Sannunka..." Ayat dake kife da fuska ta ji muryar mace, kuma muryar tata ce! Ta ɗago da sauri ta kalli wacce take tsaye a kanta. Tana ganin siffarta da fuskarta da take ɓoyewa, ta miƙe da sauri tana zaro ido, ta ce. "Wacece ke mai kamar siffata?!" Ba zato ba tsammani, Ayat ta yi shiru. Ta lura cewa maganar da ta yi, ba da muryarta ta yi ta ba! Da muryar King Diamond take magana, muryar namiji mai kwarjini. Ta dafe maƙogwaronta cikin firgici "Ya muryata haka? Me ya faru da ni?!" Asalin King Diamond dake cikin siffar Ayat ya yi wani ɗan tsafi da hannunsa, nan take wani madubi ya bayyana a gabanta. Ya haskaka mata fuskarta.. Ganin kanta a cikin madubi ta koma siffar abokin gabanta, ta fara zunduma uban ihu amma ihun namiji ne yake fita daga bakinta!. Ta kamo gashin kanta tana kallo, ta ga farin gashi ne radau, jikinta kuma fararen kaya... Cikin hargitsi ta nuna shi da yatsa tana faɗin "Kai mugun aljani ne! Ta yaya ina mace za ka ba ni siffarka? Wannan siffar marar kyau! Sannan ka karɓi tawa siffar?" Ba zato ba tsammani ta tuna wani abu, ta ƙara fusata.. "Kalli fuskata a buɗe! Ni fa bana buɗe fuskata idan ina a matsayin gimbiya, amma ka bar min ita a buɗe! Ka koma siffata kuma ka bar fuskata a waje kowa ya gani!" Ta rasa inda za ta sa kanta, yayin da shi kuma yake kallonta da muryarta yana mata murmushi... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣2️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Ayat dake cikin siffar King Diamond ta kasa daina duba hannayenta da fararen kayanta. Wani irin kishi da haushi ne yake turnuƙe ta. Ta matso kusa da shi tana huci, muryarta dake fita irin ta namiji yana dukan duwatsun dake wurin... "Ka maida ni yanzu! Na ce ka maida ni!"... Ta damƙi wuyan rigar dake jikinsa, rigarta ta gimbiyanci wadda take matuƙar so. "Wallahi ba zan motsa daga nan ba, kuma ba zan tafi ko'ina ba har sai na dawo siffata ta mace. Ba zan iya rayuwa a cikin wannan siffar taka mai ban tsoro ba!" King Diamond dake cikin siffar Ayat, ya yi murmushin nan na Gimbiya Ayat mai kyan gani, ya haskaka fuskarsa wadda take sheƙi. Ya sanya hannunsa ya ɗan shafa dogon gashin dake kansa, sannan ya ce da muryarta.. "Aayat, kiyi haƙuri. Wannan ba nufina ba ne, haɗuwar jininmu ne ya janyo hakan. Kuma ki sani, ko ni ma ina son siffata, amma yadda kike a yanzu kinfi kowa kyan gani a idona." Ayat ta ƙara fusata, ta ji tamkar tana faɗa da kanta ne a madubi ta ce, "Kayi mun shiru! Kar ka sake magana da muryata! Kuma kar ka sake ƙirana da sunana da wannan muryar!" Ta juya tana kallon magudanar ruwan, tana tunanin ta yadda za ta koma masarauta... "Ta yaya zan koma gida a haka? Master Ibrahim ya san ni a matsayin Inuwa, mahaifina ya san ni a matsayin Ayat. Idan na shiga masarautar nan a siffarka, kashe ni za a yi!" King Diamond ya matso kusa da ita, ya ɗora hannunsa a kafaɗarta. "Ni kuwa ina son kasancewa da ke a haka. Ina son in ga yadda za ki yi amfani da ikona, kuma ina son in ga yadda zan rayu a cikin takurarki. Ba zan maida ke ba yanzu ba domin ina jin daɗin yadda jininmu ya sarƙe."... Ayat ta buge hannunsa dake kan kafaɗarta da ƙarfi. "Ba zan tafi ba! Kuma ba zan bari ka tafi ba! Za mu zauna a nan har sai wannan sihirin naka ya karye. Ba zan zama namiji ba, ba zan zama aljani ba!"... Haka suka ci gaba da tsayawa a bakin kogin, iska tana kaɗawa. Ayat tana ta kai-komo tana zage-zage da muryar namiji, shi kuwa yana tsaye yana kallonta da fuskarta, yana jin daɗin yadda ya samu damar kasancewa da ita ta wannan hanyar... ✨✨ Dare ya tsala har ƙarfe 10, duhu ya lulluɓe kowane sashi na dajin dake kewayen kogin. A lokacin King Diamond ya haskaka wurin da wani irin koren haske na sihirinsa, wanda ya sanya wurin ya zama tamkar a cikin almara yake. Duk da kyawun hasken, zuciyar Ayat dake cikin siffar namiji tana tafasa da wani irin zazzafan fushi da firgici... King Diamond yana tsaye a mutum-mutumi, bai ce uffan ba hakan ne kuma ya ƙara rura wutar fushi dake zuciyarta. Ta ɗaga kai ta kalle shi, idanunta cike da tsananin ƙiyayya da tsoro a haɗe... “KAI!!” ta daka masa tsawa, muryarsa mai nauyi dake fita daga makogwaronta ya sa ta tsorata da kanta... Ta miƙe tsaye tana fuskantarsa.. “Me kake son aiwatar mun? Me ka ke so kayi da rayuwata, kai mugu?!” Ta fara zagaye kanta da hannu cikin hauka, tana janyo dogon farin gashin dake kanta wanda yanzu nata ne, tana kuka kamar yarinya karama.. “Na rantse zan kashe ka! Wallahi zan sare ka idan har ka maido min da jikina!” Cike da raɗaɗi, ta durkushe a ƙasa da ƙarfi, tana bugun ƙasar da hannuwanta masu faɗin gaske.... “NA TSANE KA! NA TSANE KA!! NA TSANE KA!!!” Ihun nata yana dukan duwatsun dake bakin kogin, yana dawo mata da sautin namijin da ba ta son ji, abin da ya sa ta ƙara razana... A wannan lokacin ne King Diamond ya ɗaga girarsa ɗaya cikin natsuwa. Ya fara takowa a hankali, takunsa ba shi da sauti tamkar iska, har ya tsaya a gabanta yana kallonta daga tsaye... Da muryarta ta mace mai sanyi, ya ce.. “Ki daina ihu.”.. Ta daka tsalle ta miƙe tsaye tamkar wadda wuta ta taɓa.. “KAR KA ƘARA MAGANA DA MURYATA!!” ta faɗa tana toshe kunnenta... “Na tsane jin muryata tana fita daga wannan bakin naka!” Ta juya da gudu kamar tana son tserewa daga wurin, amma sai ta tsaya cak bayan taku kaɗan. Ta kalli hannuwanta, faɗaɗin kafaɗunta, da nauyin jikin da take ɗauke da shi. Ta sake fashewa da kuka mai cin rai... Ta sake faɗuwa ƙasi tana kuka. “Me zan yi da wannan kaskantaccen jikin naka? Ta yaya zan koma fada a haka? Ta yaya zan kalli idon mutane?”... King Diamond ya zo tako yanda take sannan ya sunkuyo kaɗan domin ya daidaita fuskar sa da tata. Yana kallonta da wani irin yanayi na nazari, babu fushi a tare da shi.. “Kin zo ne ki kashe ni,” ya faɗa cikin sanyin muryar mace, “amma kin ga abin da kaddara ta yi.” Ayat ta girgiza kanta cikin galaita... “Wannan ba kaddara ba ce! Wannan mugunta ne! Kayi amfani da tsinanniyar sihirinka!” Ta ci gaba da jan sumar kanta tana kuka. “Mayar min da jikina... dan Allah... dan Allah ka mayar min da siffata...” King Diamond ya tsaya yana kallonta na wasu dakikoki. A karon farko wani baƙon abu ya motsa a kwayar idonsa. Wani irin yanayi ne na sha’awa da mamakin yadda kaddara ta hada su... “Yanzu,” ya raɗa mata a hankali, “zaki ji yadda nake ji tun lokacin da na ɗora idona a kanki.”... Ta ɗago kai da sauri tana kallonsa, sai kuma ta ga shima itan yake kallo, ta ja tsaki... “Me kake kallo?!” ta faɗa cikin fushi, hawaye na zuba daga idanunta... King Diamond ya tsaya a gabanta, ya haɗa hannayensa a ƙirji. Fuskar Ayat dake kansa ta cika da nutsuwa da iko... “Idan kina son ki dawo siffarki…” Ya fara faɗa a hankali... Ayat ta miƙe tsaye cikin ruɗani, zuciyarta na bugawa da ƙarfi... “Da gaske?” ta faɗa da muryarsa, tana matsowa kusa... “Ka san yadda zan dawo? Ka san yanda zan koma ni?!”.. Idanunta suka cika da bege, duk da fushin dake zuciyarta... “Faɗa min,” ta ce da sauri, “Me zan yi? Mene ne zan biya? Komai zan yi!”.. King Diamond ya ɗan karkatar da kai, ya kalleta kai tsaye. Sai wani murmushi mai ban tsoro ya bayyana a fuskar dake kansa, murmushin da bai kai zuciya ba... “Abu ɗaya ne kawai,” ya faɗa cikin sanyi... Ayat ta runtse idanu na ɗan lokaci, zuciyarta na dukan ƙirji.. “Mene ne?” ta tambaya cikin sauri.. Ya matsa ƙafa ɗaya gaba, ya rage tazara tsakaninsu.. “Dole ne,” ya ce a hankali, “mu sake sumbatar juna.” Ayat ta tsaya cak. Numfashinta ya tsaya... “Me…?” ta furta a firgice. Ta ja da baya da sauri, idonta a zazzare. “Ka haukace ne?!” ta saki kuka. “Ka manta wacece ni?!” Ta nuna shi da yatsa tana rawar jiki... “Ni makiyarka ce! Ni ce wadda ta zo ta kashe ka! Ta yaya zaka ce min haka?”.. King Diamond bai ja da baya ba. Murmushin nan bai ɓace daga fuskarsa ba ya ce, “Kamar yadda muka yi a farko,” ya ƙara faɗa cikin sanyi, “tare da haɗuwar jini… tare da haɗuwar rai.” Ayat ta dinga girgiza kai tana kuka. “A’a… A’a… Wannan ba zai yiwu ba…” Ta dafe ƙirjinta. “Wancan kuskure ne! Ba ni da iko a kaina a lokacin!” Ta ɗaga kai ta kalle shi da tsananin fushi. “Ba zan sake kusantar ka ba!” ta faɗa cikin ƙarfin hali.. “Ko da zan mutu a wannan siffar!”.. King Diamond ya ɗan sunkuya kaɗan har fuskokinsu suka kusan haɗewa. Ayat ta ja numfashi, zuciyarta na bugawa... “Ki yi tunani,” ya faɗa a hankali, muryarta dake fita a bakinsa na girgiza shi... “Ko ki zauna a wannan jiki… ko ki dawo naki.” Ayat ta lumshe idanu da ƙarfi, hawaye na sauƙa.. “Kai mugu ne…” ta furta a raunane, “Ka fi yadda na zata.”.. Ya ɗan miƙe tsaye, yana kallonta daga sama.. “Ba mugunta ba ce,” ya ce cikin sanyi, “ƙa’ida ce.” Ayat ta buɗe idanu, ta kalle shi da wani kallo na tsana da ruɗani a haɗe... “Idan na yi hakan…” “ka rantse min cewa zan dawo ni.” King Diamond ya ɗaga gira kaɗan. “Idan hakan bai yi aiki ba,” ya amsa, “to babu abin da zai yi.”.. Ayat ta yi shiru. Iskar kogin na busawa, ruwan na ƙara amo. Zuciyarta ta rarrabu gida biyu... Ta runtse idanu, hannuwanta na rawa.. “Ka juya,” ta faɗa cikin sanyi. “Kar ka kusanto ni yanzu.” King Diamond ya tsaya, yana kallonta. “Ki yanke shawara, lokaci ba ya jiran kowa.”... ✨✨✨ Daren Alhamra ya yi nisa, amma Master Ibrahim bai ko kwanta ba. Yana tsaye a harabar fadar, idanunsa suna kallon sararin samaniya, yana jujjuya takobinsa a hannu. Akwai abin da yake damun sa, ya dace Inuwa ya dawo tun sa’o’i biyar da suka wuce, amma har yanzu babu labarinsa... "Inuwa ba mutum ne mai taurin kai ko karya doka ba," Ibrahim ya raɗa wa kansa. Ya nufi sashen ma’aikatan tsaro, inda ya tarar da wasu dakarun suna hira ƙasa-ƙasa. Cikin muryarsa mai kwarjini, ya daka musu tsawa.. "Wane ne a cikinku ya ga Inuwa tun bayan sallar azahar? Shin akwai wanda ya ga lokacin da ya fita ko ya dawo?".. Dakarun suka kalli juna cikin fargaba. Ɗaya daga cikinsu ya matso ya rusuna, "Master, rabonmu da shi tun safiyar hantsi. Ban sake sanya shi a ido ba.".. Ibrahim ya haɗe rai. Ya san akwai matsala. Ya juya da sauri ya nufi hanyar da take kai shi sashen dawakai. A can ya tarar da babban mai kula da dawakai yana shirin kulle wurin... "Doki nawa ne babu a nan?" Ibrahim ya tambaya cikin hanzari.. Mai kula da dawakan ya bincika, sannan ya ce, "Master, akwai doki ɗaya da aka fita da shi, kuma ban ga wanda ya ɗauke shi ba, amma dokin yana cikin dawakan da Inuwa yake kulawa da su.".. Wannan bayanin ya tabbatar wa Ibrahim cewa Inuwa ya fice daga fada. Amma ina ya tafi a cikin daren nan? Kuma me ya sa bai gaya masa ba? Ibrahim bai tsaya wata-wata ba. Ya ɗauki dokinsa, ya kunna fitilar hannu mai ƙarfi ya fice daga masarautar cikin gudu. Yana da ƙwarewa wajen gane sawayen taku a ƙasa. Ya bi sawun dokin da aka fita da shi tun daga ƙofar gari, sawayen suka riƙa kai shi cikin daji, har zuwa hanyar da take kai mutum ga babban kogin nan da kowa yake tsoron zuwa... "Me Inuwa zai je yi a wannan kogin har ya kai daren nan?" Ibrahim ya tambayi kansa, zuciyarsa tana bugawa da sauri. Daidai lokacin da Master Ibrahim yake ƙoƙarin ƙarasowa bakin kogin, King Diamond ya ɗan karkata kansa, idanunsa waɗanda suke a siffar Ayat suka haska da wani irin haske mai nauyi. Ya fahimci cewa akwai bugun zuciyar ɗan Adam dake kusantowa cikin hanzari... Ba tare da ya ce uffan ba, ya ɗaga hannunsa ɗaya ya kewaye su da shi. Nan take, wani irin shingen sihiri mai launin iska ya mamaye su haɗe da Ayat dake cikin siffarsa da kuma dokin dake can ɗaure. Wannan shingen ya mayar da su Fatalwa a idon ɗan Adam, babu mai iya ganinsu, jin motsinsu, ko ganin hasken sihirin dake wurin, amma su suna iya kallon duk abin da yake faruwa a waje.... Master Ibrahim ya bayyana a bakin kogin, riƙe da fitilar hannunsa dake ta haskawa. Ya zaro takobinsa, idanunsa suna yawo ta kowane sashi.. Ayat dake cikin siffar namiji ta daskare a inda take. Ta zura wa Ibrahim ido, zuciyarta tana bugawa da ƙarfi... "Master! Me yake yi a nan?" ta faɗa a cikin zuciyarta. Ta so ta kwalla masa ƙira, ta so ta ce "Master, gani nan!", amma tana tunawa da muryar namijin dake fita daga bakinta da kuma siffar dake jikinta, sai ta toshe bakinta da sauri. Ibrahim ya riƙa haska fitilar sa har daidai inda suke tsaye amma fitilar tana ratsa jikinsu ne kamar iska, bai ga kowa ba sai bishiyoyi da duwatsu. Ya tsaya daidai saitin inda dokin Ayat yake, amma ko dokin bai gani ba... "Abin mamaki," Ibrahim ya raɗa yana goge gumin goshinsa. "Na tabbata sawayen takun dokin nan sun kawo ni har nan. Amma me ya sa komai ya ɓace? Me ya sa wurin ya yi tsit haka?" Ya zagaya bakin kogin sau uku, yana duba ko da akwai rami ko wata alama amma sihirin King Diamond ya shafe komai. Ibrahim ya tsaya na wasu daƙiƙoƙi, yana jin kamar ana kallon sa amma ganin ba shi da wata hujja, sai ya girgiza kansa cikin shakku... "Ƙila tunanina ne ya yaudare ni," ya furta cikin rauni... "Inuwa, kana ina?" Ya jima a tsaye yana sauraron sautin ruwa, kafin daga bisani ya juya ya nufi inda ya bar dokinsa, ya fara tafiya a hankali yana waigowa har ya ɓace cikin duhun dajin... Ayat ta sauƙe wani nauyayyen numfashi, jikinta har yanzu yana ɓari. Ta juyo ta kalli King Diamond wanda har yanzu yake tsaye cikin natsuwa... "Ka ga abin da ka jawo min ko?" ta faɗa da muryarsa, cike da takaici ta ce... "Master Ibrahim zai kamani da laifi idan bai ganni a fada ba kafin gari ya waye, masarautar nan za ta tashi a hargitse!" King Diamond ya sauƙe hannunsa, shingen ya ɓace. Ya kalle ta da wani kallo mai zurfi. "Ba zai gano komai ba... muddin kina kusa da ni." Anan suka cigaba da zama har alfijr ya fito.. Ayat ta tsaya tana kallonsa. Ta sha kuka har idanuwanta sun kumbura, murya ta dusashe. A karo na farko ta sassauta muryarta... “Dan Allah…” ta fara cikin rauni, tana ɗan matsowa kusa, “ka maida min siffata. Wannan ba ni ba ce. Ina jin kaina kamar baƙuwa a jikina.”... Ta sauƙe numfashi mai nauyi... “Ni gimbiya ce… ina da mutunci, ina da iyaka.” King Diamond ya tsaya tsayin daka sannan ya furta.. “Sumbatar nan ita ce mafita,” Kalmar sumbata ta buge ta kamar wuta. Ta tashi tsaye da sauri, tana zaro idanuwa.. “Me?!” ta daka masa tsawa da muryarsa, “Zan zabga maka mari kai da sumbatar! Kana da faɗin sumbata, sumbata, sumbata! Na bi sumbata da gudu!”... Tana nuna shi da yatsa, hannuwanta na rawa... “Na fahimci ka raina ni! Ka raina martabata!”... King Diamond bai motsa ba. Ya ɗan karkatar da kai, murya ta fito cikin sanyi... “To kuwa, haka za mu ci gaba da kasancewa a nan… har tsawon rayuwa.”... Kalmar rayuwa ta sauƙa a kirjin Ayat kamar theoretical hammer... Nan ƙirjinta ya buga. Ta kama ƙirjinta da ƙarfi, numfashinta a rikice. Wani irin sanyi ya ratsa ta. Ta ja da baya.. “Rayuwa…?” ta maimaita a firgice. “Ka ce rayuwa?” Ta kalle shi, idanuwa na cikowa da hawaye, amma wannan karon hawaye na tsoro ne, ba fushi kaɗai ba... “Ni mace ce,” ta faɗa a raunane, “ban san rayuwar ka ba… ban san ƙarfin jikinka ba… ban san yadda zan rayu a siffarka ba…” Ta yi shiru na ɗan lokaci, ta haɗiye kukan... “Idan na ji ciwo… kai ma za ka ji?” ta tambaya cikin rawar murya... King Diamond ya ɗan kalleta kai tsaye. Ya ɗaga tafin hannunsa, inda aka yanke, a yanzu jinin ya tsaya amma alamar ciwo na nan.. “Eh,” ya amsa. “Tun daga wancan haɗuwar jini… abin da kika ji, zan ji. Abin da na ji, za ki ji.” Ayat ta runtse idanu. Zuciyarta ta buga da ƙarfi fiye da da.... “Ka ɗaure ni,” ta faɗa cikin kuka.... “Ka ɗaure rayuwata da taka.” King Diamond ya ɗan matsa kusa. Iskar asuba tana ɗaga sumar gashinsu.. “Ba ni na fara ba....Ke ce.”.. Ayat ta buɗe idanu, ta kalle shi da haɗaɗɗen kallo, ta jinjina kai sannan ta ce.. “zan yarda…amma ba don ina so ba, sai don in tsira..” Ya ɗan yi murmushi ya ce, “Na sani.” Ayat na tsaye a gabansa, idanuwanta sun kumbura da hawaye da ta daɗe tana ɓoye wa... “Shin kana son ɗauke min zuciyata ne?.” Ya ce, “Ba zan taɓa tilasta ki ba. Ko a mulkina, babu ikon da ya fi na zuciya.”.. Ayat ta yi murmushi mai raɗaɗi, murmushi da hawaye ke yawo a cikinsa.. “Ƙarya ne...Ka riga ka shiga zuciyata… ba tare da izini ba.”.. Ta sauke kai, hawaye suna zubo wa... “Amma yau…” ta ɗaga kai tana kallonsa kai tsaye, “zan buɗe iyakata da kaina.”.. A hankali ya ƙira sunanta.. “Ayat...” “Ka saurare ni,” ta katse shi, murya na rawa. “Zan amince… amma ba haka kawai ba.”.. Ta share hawaye da bayan hannunta, ta ɗaga yatsa ɗaya... “Na farko.. ba za ka taɓa amfani da iko ko sihiri a kaina ba.” Ta ɗaga yatsa na biyu... “Na biyu...Duk abin da zai faru tsakaninmu, sai da yardata.” Ta ɗaga yatsa na uku, muryarta na rawa. “Na uku… idan na ce daina, za ka daina, ko da zaka mutu...” Shiru ya ratsa tsakaninsu. King Diamond ya miƙa hannunsa tare da dunƙule wa... “Idan hakan ne farashin samunki,” ya ce cikin murya mai nauyi, “zan biya.”.. Ayat tana hawaye Ta buɗe hannayenta a hankali. Jikinta na rawa... “Zo,” ta faɗa cikin kuka... “Amma kada ka ɗauka nasara ce.” King Diamond ya kusanto sannu a hankali, kamar yana kusantar abu mai tsarki. Ya tsaya gaban ta, ya buɗe hannayensa shima, a hankali ta shige faɗaɗɗen ƙirjinsa dake siffar ta... Bugun zuciyarsu ne yake daidaituwa... Ayat ta ɗora kanta a ƙirjinsa, tana kuka... Hannunsa ya tsaya a bayanta, ba tare da ya matse ta ba... “Ka sani,” ta faɗa cikin kuka, “idan ka karya sharaɗina, zan tsane ka fiye da yadda nake tsoron ka.”.. King Diamond ya sunkuyar da kansa a kanta tare da sumbatar gashin dake kanta.. “Idan na karya sharaɗinki,” ya amsa, “to na rasa kaina.”.. A wannan lokacin, aljanu dake nesa suka durƙusa ba tare da umarni ba. Saboda sarkin su ya karɓi yarjejeniyar zuciya... Ayat ta buɗe iyakarta, ta ba wa King Diamond damar da ya daɗe yana nema. Duk da tsoro da fargaba dake zukatan su, sai ga shi sun tsinci kansu a cikin wani yanayi da ya zarce tunanin ɗan Adam... Sannu a hankali, King Diamond ya rage tazara tsakaninsu. Da ya matse ta sosai, A hankali ya kai leɓensa kan nata ko ince, asalin leɓen Ayat dake jikinsa ya haɗu da nasa dake jikinta... Wani irin zurfaffiyar sumbata ce ta shiga tsakaninsu, sumbatar da ta raba su da duniyar gaskiya... Sumbata ce da ta ratsa kowane sassa na jikinsu, tun daga tafin ƙafa har zuwa cikin ƙwaƙwalwa... Sun ji wani irin yanayi da ba su taɓa sanin akwai shi ba a doron ƙasa... Ga Ayat, ta ji kamar dukkan fushi da ƙuncin dake zuciyarta suna narkewa suna zama ruwan sanyi. Shi kuwa King Diamond, ya ji kamar dukkan ikon da yake da shi ya tattara a wannan gaɓar ta leɓensa... Wannan sumbatar ta ƙara haɗa ƙaddararsu fiye da haɗuwar jinin da suka yi ɗazu. Ta zama tamkar igiyar da ba za ta taɓa tsinkewa ba, wadda ta ɗaure rayuwarsu guri ɗaya... Sun ɗauki tsawon lokaci a haka, kowa ya rasa sanin inda yake, kowa ya mance da siffar da yake ciki... Rungumar da suka yi wa juna ta ƙara tsananta, hannunsa ya zagaye kunkuminta cikin kwarewa da nuna mallaka, yayin da ita kuma ta sa hannuwanta ta riƙe wuyansa, tana ƙoƙarin jawo shi kusa da ita fiye da yadda jiki zai iya haɗuwa... A daidai lokacin da sumbatar ta kai ƙololuwa, wani irin ƙarfi ya tura su baya, domin a duniyar aljanu wannan kuskure ne kusantar bil adam har haka, sun ga Sarkinsu yana shirin karya ƙa'ida hakan yasa aka raba su da ƙarfi... ✨ Wani irin hayaki mai ƙamshi ya mamaye wurin. Bayan hayakin ya lafa, sai ga shi kowa ya tsinci kansa a asalin jikinsa... Ayat tana tsaye, numfashinta yana fita da sauri-sauri. Ta duba hannunta ta ga ƙananun yatsunta na mace. Ta taɓa fuskarta, ta ji laushin fatarta. Ta ji nauyin dogon gashinta ya dawo kanta. Ta dawo asalin Gimbiya Ayat! Shi ma King Diamond, ya dawo cikin siffarsa ta aljani mai farin gashi da kwarjini... Amma wannan karon idanunsa suna kallon Ayat ne cikin wani irin natsuwa da muryar da ba za ta taɓa mancewa ba... Dukansu biyun sun tsaya suna kallon juna cikin mamakin abin da ya faru. Har yanzu suna jin zafi da zaƙin sumbatar nan a leɓunansu. Ayat ta so ta yi fushi, amma sai ta ji muryarta ta gaza fitowa... Zuciyarta tana gaya mata abu ɗaya.. "Yanzu kam, ba za ki taɓa rabuwa da shi ba.".. King Diamond ya tsaya yana kallonta, iskar asuba tana wasa da farin gashinsa dake sheƙi. Duk da cewa kowa ya dawo asalin siffarsa, idanunsa ba su daina kallon leɓun Ayat ba, kamar har yanzu yana jin ɗanɗanon sumbatar da ta canza musu ƙaddara... Ya matso mataki ɗaya kusa da ita, muryarsa ta fito cikin wani irin amo mai sanyi wanda yake ratsa bargon jikinta.. "Kinyi nasara Ayat. Kin dawo cikin gidan sarautarki, kin dawo cikin siffar da kike alfahari da ita.".. Ya ɗan dakata sannan ya ɗaga hannunsa ya nuna saitin zuciyarta... "Amma ki sani, sumbatar da muka yi ba wai kawai ta maido mana da siffarmu ba ne, ta zama tamkar Sa hannu a takardar rayuwarki. Daga yau, ba za ki iya ɓoye min komai ba. Idan kina cikin farin ciki, zan ji a jikina. Idan kina zubar da hawaye, zuciyata za ta buga..." Ayat ta tsaya tana kallonsa, jikinta har yanzu yana ɗan goosebumps saboda kwarjininsa... Ya cigaba da cewa.. "Ki koma fada, ki ci gaba da wasan ɓoyon da kike yi da mutanenki. Amma karki manta sharaɗinmu, Ni naki ne, ke tawa ce. Duk ranar da kika ji kishirwar gani na, kawai ki kira sunana a cikin zuciyarki, zan bayyana a gare ki ko da kuwa dakarun duniya dubu ne suka kewaye ki.".. Kafin Ayat ta samu damar cewa uffan, King Diamond ya yi wani ɗan gajeren murmushi sannan jikinsa ya fara rikiɗewa ya zama tamkar hasken taurari.. Cikin kiftawar ido, ya ɓace a gaban idonta sai ƙamshinsa kawai ya rage yana tashi a sararin samaniyar kogin... Ayat ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya, ta dafe ƙirjinta tana jin yadda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Ta duba tafin hannunta, ta ga tabon ciwon nan ya ɓace radau, amma ta sani a ranta cewa alamar dake zuciyarta ba za ta taɓa goge wa ba... "Ya Allah..." ta raɗa a hankali... Tana tsaye sai kuma ta ga siffar gimbiyancin ta ya sauya ya koma siffar Inuwa, yanda take kafin wannan lokacin.. Ta shafa fuskarta ta ji akwai gemun da sajen, bata san lokacin da ta sau murmushi ba.. Ta juya da sauri ta nufi inda dokinta yake ɗaure, ta hau shi tare da zaburar da shi da gudu domin ta isa Masarauta kafin idon mutane ya fara lura da bacewarta..... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣3️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Gari ya waye garau, hasken rana ya fito. Master Ibrahim yana tsaye a bakin kofar daƙin dawakai, fuskarsa a murtuƙe, idanunsa sun yi jawur saboda rashin baccin daren da ya yi yana neman Inuwa. Zuciyarsa tana tafasa yadda yake jin Inuwa a ransa ya wuce kima har ma yana mamakin yadda damuwar namiji ɗan uwansa take neman mayar da shi tamkar wanda ya rasa budurwa... Yana nan tsaye, sai ya hango dokin Inuwa yana tunkaro fadar. Inuwa ya ƙaraso yana sauka daga kan dokin, ya sauke numfashi yayin da ta ci karo da firgittaccen kallon Master Ibrahim.. Ibrahim ya tako cikin sauri, ya tsaya a gabanta, muryarsa tana rawa tsakanin fushi da sauƙaƙawa.. "Inuwa! Daga ina kake? Tun jiya nake nemanka a kowane lungu na fadar nan! Na je har bakin kogi amma ban gan ka ba. Me ya faru da kai?".. Ayat ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin saita muryarta ta Inuwa domin ta kare kanta. Ta san dole ne ta bayar da ƙwaƙƙwarar ƙarya.. "Gafara nake nema Master," ta faɗa cikin murya mai nuna gajiya. "A daren jiya lokacin da nake kan hanyata ta dawowa, na ci karo da wata mata wadda ta samu hatsari mai tsanani a kan titi. Jini yake zuba daga jikinta babu kowa a kusa. Dole ta sa na ɗauke ta zuwa asibitin gari dake wajen fada, na zauna a can ina jiran likitoci har na tabbatar ta farfaɗo. Shi ya sa na kwana a asibitin har gari ya waye.".. Jin kalmar Na kwana a wurinta, sai Master Ibrahim ya ji wani abu ya soke shi a ƙirji. Wani irin azababben kishi ne ya turnuƙe shi, kodayake a zahiri yana kallon Inuwa ne a matsayin namiji, amma jin cewa ya sadaukar da daren sa ga wata mace ya sanya shi jin zafi.. Ibrahim ya haɗe rai, ya kawar da kansa gefe yana huci kafin ya sake duban Inuwa.. "Hatsari? Kuma sai ka kwana a wurinta? Inuwa, ashe kai jarumi ne har a fagen soyayya da taimakon mata?". Ibrahim ya faɗa cikin sautin izgilanci dake nuna ɓacin ransa.. Inuwa ta ɗan firgita da yadda muryarsa ta sauya.. "A'a Master, taimako ne kawai na yi..." Ibrahim ya katse ta, ya matso kusa da ita sosai har tana jin ɗumin numfashinsa... "Kayi ƙoƙari, hakan yana da kyau. Amma daga yau, ko da tsuntsu ne ya samu hatsari, dole ka sanar da ni inda za ka je! Masarautar nan cike take da maƙiya, kuma ba zan iya jure rashin ganinka na tsawon sa'o'i biyar ba, balle har gari ya waye." Ya sake jaddada maganar cikin nuna iko "Karka sake kwana a wajen masarauta ba tare da izinina ba. Yanzu maza ka je ka huta, ka wanke jikinka. Amma ka sani, wannan matar da ka taimaka, kada hakan ya zama silar shagala daga ayyukanka.".. Ibrahim ya juya ya fice daga wurin cikin takun fushi, ya bar Ayat a tsaye tana mamakin irin wannan damuwar da Master Ibrahim yake nuna mata. Ba ta sani ba cewa, a cikin zuciyar Master, rami ne aka haƙa wanda ba na abota ba ne kaɗai... Tana isa ɗakinta, ta tarar da shi tsit, sai ƙamshin turare dake tashi... Ta garzaya zuwa gaban madubin da aka mayar mata da sabo, ta cire sajen da gemun fuskarta, sannan ta cire rawanin dake kanta... Gashinta ya zubo ya rufe mata baya. Ta tsaya tana kallon kanta. Duk da cewa Master Ibrahim ya nuna mata damuwa da kishi, amma ba ta ko tuna maganarsa ba. Abin da yake dawo mata a kunne shi ne muryar King Diamond dake cewa. "Ni naki ne, ke tawa ce." Ta ɗaga hannunta ta kalli tafin hannunta inda sumbatar nan ta warkar da shi. Babu ko alamar ciwo, amma tana jin wani irin ɗumi dake yawo a jikinta, ɗumin da ya samo asali daga wannan sumbatar da ta canza mata rayuwa... "Mugu..." ta raɗa a hankali, tana shafar leɓunanta.. "Ta yaya ya shiga rayuwata haka? Ta yaya kaddararmu ta sarƙe a cikin dare ɗaya?" Wani irin tsoro mai haɗe da shauƙi ya ziyarce ta. Ta tuna yadda ya amshi sharaɗan ta. Ko da yake ta tsane shi a farko, amma yanzu tana jin wani irin haɗi dake tsakaninsu wanda ko da tana so, ba za ta iya tsinkewa ba... Ta matsa kusa da madubin tana kallon kwayar idonta. Tana neman ko za ta ga inuwar King Diamond a ciki, kamar yadda ya ce yana tare da ita.. "Karka ɗauka kayi nasara...." Ta maimaita maganar da ta gaya masa, amma a ranta tana jin cewa ita kanta ba ta san waye ya yi nasara a tsakaninsu ba... Tana cikin wannan tunanin sai ta ji an buga ƙofar ɗakin.. "Gimbiya! Gimbiya Ayat kina ciki?!" Muryar Saratu ce ta katse mata tunani. Ayat ta firgita, ta goge fuskarta da sauri. Dole ne ta saita kanta, ta dawo Gimbiya Ayat mai natsuwa, ko da kuwa zuciyarta tana can bakin kogi tare da sarkin aljanu... ✨✨✨ A yau ba tare da kowa ya sani ba.. Da misalin ƙarfe huɗun asuba, lokacin da kowa yake nannaɗe cikin bargo, Sarki Nourdeen ya fito sanye da manyan kayan sarauta fuskarsa cike da damuwa.. Baya son gimbiyoyinsa su sani, don haka ya ba da umarnin a shirya babbar Helicopter ɗinsa ta alfarma a filin jirgi na sirri dake bayan fada... Koda Master Ibrahim bai san da wannan tafiyar ba har sai da aka buga musu ƙofa. Sarki ya zaɓi dakarun tsaro guda biyar kacal, waɗanda ya amince da su, ciki har da jami’an tsaro na musamman da za su raka shi... "Ba ma neman yaƙi," sarki ya faɗa wa shugaban masu tsaron nasa. "Zamu je ne don mu cika alƙawarin da aka daɗe da yi. Amma ku kasance a shirye da kowane irin yanayi.".. Ƙarar injin Helicopter ta mamaye sararin samaniyar fadar. Sarki Nourdeen ya shiga ciki, ya zauna a mazauninsa na alfarma ya zuba wa masarautar Alhamra ido ta taga yayin da jirgin yake shawagi sama... A ransa yana addu'ar wannan tafiyar ta zama silar zaman lafiya, ba silar rugujewar mulkinsa ba.. Tafiyar ba ta da tsawo sosai ta sama, amma ga sarki, kowane minti ɗaya tamkar shekara yake... Suna isa ƙasar da suka nufa, daga sama ya fara hango wani babban birni dake kewaye da baƙaƙen ganuwa da hasken fitilu masu launin purple... Wannan ita ce daular Pavilion... Ganin tsarin gine-ginen wurin kaɗai ya isa ya nuna maka cewa wannan ƙasa ce dake da ƙarfin da ya zarce na kowace masarauta... Yayin da Helicopter ɗin take neman gurbin sauƙa a katafaren filin jirgin Pavilion, sarki ya hango dakarun Pavilion sanye da baƙaƙen kaya sun jera layi tamkar bango. Babu wani rurrusunawa, babu wata gaisuwa ta girma sai kallo mai cike da kwarjini... Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya gyara kambunsa... "Lokaci ya yi," ya raɗa wa kansa yayin da matattalar jirgin ta sauƙa.. Sarki Nourdeen ya fito daga helicopter ɗin, kansa a ɗage amma zuciyarsa tana bugawa. Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un! Abin da ya gani ya wuce misali... Girman gine-ginen Pavilion kawai ya isa ya sanyaya wa mutum jiki. Ko’ina ka kalla dakarun Pavilion ne sanye da baƙaƙen kaya, tsaye daram ba sa motsi tamkar gumaka, idanunsu ƙafe a kan kowane taku na baƙin.. Sauran jami’an tsaron sarki da suka biyo shi, suka tsaya a tsakiyar katafaren harabar fadar, fuskokinsu cike da tsoro da mamaki. Sun ji kansu ƙanana a cikin wannan makeken fili wanda aka ƙawata da dutsen marmara mai sheƙi. Wani babban jami'in Pavilion wanda kwarjininsa ya kusan zarce na sarki kansa, ya tako a hankali ya yi wa sarki nuni da hannu... Ya fara yi wa sarki jagora ta cikin sashe-sashe mabanbanta.. Sarki ya ga jerin motocin yaƙi da na alfarma waɗanda ba a taɓa ƙera irinsu ba a duniya.. Dawakai ne baƙaƙe, manya masu sheƙin fata, waɗanda kowane ɗaya ana masa hidima ta musamman... Kowace kusurwa akwai jami'ai, wasu a sama wasu a ƙasa, dukansu idanunsu ba ya kiftawa. Sarki Nourdeen yana tafiya ne kamar a mafarki. Wurin ya kasu Part part, kowane sashe da abin da ake gudanarwa a ciki, tun daga tsaro har zuwa na'urorin zamani da suke ta faman aiki... Daga ƙarshe, jami'in ya kai sarki zuwa wani babban falo da ya fi kowane falo da sarki ya taɓa gani a rayuwarsa. Kujerun wurin an ƙera su da wani irin fata mai taushi da launin zinare.. Suka zaunar da sarki a can, aka bar shi shi kaɗai a cikin wannan faffaɗan ɗakin.. Ba a daɗe ba, wasu ma'aikata mata waɗanda kyan fuskarsu kaɗai ya isa ya saka mutum cikin damuwa, suka shigo ɗauke da tire-tire na zinare. Suka shimfiɗa masa kayan ciye-ciye da abubuwan sha na alfarma, waɗanda ƙamshinsu kaɗai ya isa ya nuna tsadar su. Sai dai waɗannan ƴan mata ma'aikata duk ba mutane bane, su ɗin robots ne masu amfani da na'ura... Sarki ya zauna a kan kujerar, amma ya kasa ko taɓa ruwan dake gabansa. Idanunsa suna ta kai-komo, kowane motsin labule ko ƙofa sai ya tsorata shi. Yana nan zaune yana jiran jin takun tafiyar da zata sanar da isowar mutumin da ya sanya shi barin masarautarsa a lokaci guda... Falon ya yi shiru sai ƙarar sanyin na'urorin sanyaya ɗaki kawai ke tashi. Sarki ya duƙar da kansa, yana tambayar kansa.. "Me zai faru idan wannan mutumin ya fito? Shin yarjejeniyar da muka yi tsawon shekaru da suka wuce, yau ce ranar da zan biya ta?".. Sarki Nourdeen yana tsaka da fargabar jiran abin da zai faru, sai ya ji iskar falon ta canza launi. Ba tare da an ji takun tafiya ba, da motsin ƙofa ba, kawai sai ga Chief Onyx ya bayyana a tsakiyar falon tamkar iska ce ta huro shi... Tsayuwar sa kawai ta isa ta nuna cewa shi ba mutum ba ne irin na wannan zamanin, ƙirar jikinsa irin ta magabata ne, samudawan farko masu girman jiki da ƙasusuwa ƙusassu... Tsayinsa ya zarce tunanin mai kallo, faffaɗen ƙirjinsa kuma ya nuna irin ƙarfin dake ɓoye a jikinsa... Sanyi ya ratsa falon kamar wani abu mai rai ya shigo, fitilun suka ɗan fara rawa.. Kamar yadda iska ke bayyana ba tare da izini ba haka Chief Onyx ya bayyano a tsakiyar falon... Dogon baƙin rigarsa tana ja har ƙasi, amma rigar ta gaba a buɗe take tana bayyana faɗaɗen farin ƙirjinsa kamar an sassaƙa shi da ƙarfe... Farin ƙirjinsa, wanda ya yi fari ƙal tamkar madara ya fito fili, tare da wasu kwantattun gashi dake kwance a kan faffaɗen ƙirjin nasa, wanda ya ƙara fito da jarumtarsa... Manyan nonuwansa sun tsaya daram, irin ƙirar namiji tsantsa wanda kallo ɗaya zai sa zuciya ta manta bugawa... Wasu sarƙoƙi na musamman masu tsada na azurfa sun zubo daga wuyansa har zuwa kan faffaden ƙirjinsa, suna walkiya a ƙarƙashin hasken fitilun falon... Dogon baƙin gashinsa mai santsi da sheƙi yana sauƙa har kafaɗunsa, yana kaɗawa a hankali cikin sanyin AC... Gefen fuskarsa guda na rufe da wani ƙarfen azurfa mai sarƙaƙƙiyar ƙira, wanda ya ƙara wa idanunsa kwarjini.. Idan ka kalle shi, ba wai ka ga kyau kawai bane har da tsantsar barazana... Idan ka tsinci kanka kana kallonsa tsawon daƙiƙu to jikinka zai daskare. Zuciyarka zata buga da sauri ba tare da dalili ba.. Takalmansa baƙaƙe, masu nauyi kamar na soja suna sauƙa ƙasa da ƙasa ba tare da amo ba, amma kowane taku yana da nauyin da yake sa ƙasa ta tuna da shi... Kana kallonsa zaka ce.. “Wannan ba musulmi bane.” Amma shi musulmi ne cikakke mai bautar Allah cikin sirri, mai tsananin tsoronSa, kuma mai tsananin hukunci ga wanda ya karya doka... A bayansa, tana taku cikin natsuwa da izza tamkar ɗawisu, wata zafaffiyar budurwa ce kyakkyawa dake sanye da baƙaƙen kaya matsattsu. Gashinta a kwance yake har gadon bayanta, idanunta kuwa suna fitar da wani irin haske na musamman... Wannan budurwa ba mutum ba ce, ita ce ƙololuwar fasahar Pavilion. Robot ce ta musamman, wacce aka ƙera ta don kariya da aiwatar da ayyukan da mutum ba zai iya ba. Ita ce babban makamin Chief Onyx... Halitta ce da aka ƙera domin yaƙi, tsaro, da aiwatar da umarni ba tare da tambaya ba. Ita ce hannun damar Chief Onyx. Ita ce garkuwarsa da takobinsa... Chief Onyx ya zauna a kan kujerarsa ta alfarma, ya ɗora hannuwansa a kan madafan kujerar, idanunsa suka sarƙe da na Sarki Nourdeen. Robot ɗinsa tana tsaye a gefensa tamkar mutum, idanunta suna nazarin kowane motsi na baƙon da yake gabansu... Sarki Nourdeen ya tsinci kansa da kasa magana. Duk wani iko da yake takama da shi a Alhamra, ya neme shi ya rasa a gaban Chief Onyx.. Muryar Chief Onyx ta fito da zurfi da amo tamkar ana hura busa.. "Barka da zuwa, Sarki Nourdeen. Na san ka daɗe kana jiran wannan ranar. Amma tambayar ita ce... shin kana shirye da farashin da za ka biya?"... Chief Onyx ya karkata kansa gefe guda, yana kallon Sarki Nourdeen da idanunsa dake fitar da wani irin kwarjini na daban.. Robot ɗinsa dake tsaye a gefe ta lura da yadda bugun zuciyar sarki ya tsananta.. "Nourdeen," Chief Onyx ya ƙira sunansa ba tare da lakabin sarauta ba, muryarsa tana amo a cikin falon. "Shekaru goma sha biyar sun shuɗe tun ranar da kuka kawo min yaƙi tare da taimakon dakarun turawan matar ka Ruma. Ranar da kuka so ku raba ni da gadon mahaifina. Na bar maka Alhamra ba don tsoro ba, sai don umarnin kotun duniya da kuma buƙatar kwanciyar hankali.".. Chief Onyx ya miƙe tsaye, tsayinsa ya sa sarki ya ji tamkar shi wani ƙaramin yaro ne. Ya fara takawa a hankali yana zagaye Sarki Nourdeen, yayin da takalmansa suke bada sauti a kan lallausar carpet.. "Na bar maka Alhamra a matsayin aro, amma da sharaɗi guda ɗaya. Ka amince za ka mallaka min ɗaya daga cikin 'ya'yanka don ta zama Personal Maid ɗina wato ƴar aikina. Ka yarda da hakan don kawai ka riƙe mulkin da ba naka ba. To yanzu lokaci ya yi. Na zo karɓar abin da yake nawa ne.".. Cikin Ruɗani Da Takaici Sarki Nourdeen ya duƙar da kansa, gumi na keto masa. Ya tuna lokacin da ya yi wannan yarjejeniyar, a ransa ya ɗauka lokacin ba zai taɓa zuwa ba. Amma yau, ga Chief Onyx nan a raye cikin ƙarfi da mulki fiye da kowane lokaci... "Ina buƙatar mace mai tarbiyya, jajirtacciya, kuma wacce za ta san darajar Pavilion," Chief Onyx ya ci gaba da magana yayin da ya tsaya a gaban sarki.. "Ban san ko su wane ne 'ya'yanka ba, kuma hakan bai dame ni ba. Abin da nake so shi ne ɗaya daga cikinsu ta zama ƴar aikin pavilion kingdom.".. A idon Sarki Nourdeen, fuskokin 'ya'yansa suka fara giftawa... Zayana wacce take jinin Ruma ce, matar da ta janyo wannan yaƙin. Shin zai iya bayar da ita? Amma kuma Ruma ta kasance mata mai ƙarfin iko fiye da tunanin mutum, kuma jinin turawa wacce a yanzu take mulkan ƙasar Canberra babban birnin Australia... Aayat wacce take amintacciyarsa kuma take kare shi? Ya girgiza kai alamun rashin amincewa.. Maayah wacce take cikin jinya yanzu?... Chingching wacce ba ta san zafin rayuwa ba? Duk wadda ya bayar ya sani cewa ya tura ta ne zuwa bauta a gidan mutumin da yake ƙin jinin mahaifinsu.. Amma idan bai bayar ba, ya san Chief Onyx zai iya murƙushe Alhamra a cikin sa'o'i kalilan... Chief Onyx ya yi wa Robot ɗinsa nuni da hannu. Robot ɗin ta matso kusa da sarki, ta miƙa masa wata na'ura mai nuna hotuna.. "Zaka ba ni sunan wadda ka zaɓa kafin rana ta faɗi..," Chief Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi... "Idan kuma ka kasa zaɓa, to ni da kaina zan shigo Alhamra in ɗauki duk wacce idona ya nuna mun... Kuma ka sani, idan na shigo da kaina, ba zan fita hannu empty ba..."... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣4️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Sarki Nourdeen ya shiga cikin wani hali na ƙunci da matsanancin tunani. Ga shi a gaban babban maƙiyinsa, mutumin da yake bin sa bashin dake iya ruguje masa mulki da mutunci... Chief Onyx kuma yana nan zaune, idanunsa tamkar takobi suna sassaƙa zuciyar sarki yayin da yake jiran amsa... Sarki Nourdeen ya fara rarraba wa zuciyarsa zaɓin 'ya'yan da yake da su, amma kowace ya kalla sai ya ga cikas... Zayana! Ko kusa, sarki ba zai taɓa iya bayar da ita ba. Tsoron mahaifiyarta Ruma yake yi fiye da yadda yake tsoron kowa. Ya san idan ya bayar da Zayana, Ruma za ta iya janyo masa yaƙin da ya fi na farko muni, domin tana da ikon da zai iya girgiza dukkan masarautar... Ayat kuma wannan ma ba zaɓi ba ne a gare shi. Ayat tana da wani irin zafi da rashin haƙuri. Ba ta jure wulaƙanci kuma tana iya tunkarar kowa. Idan ya bayar da ita, ya san za ta iya tayar da babban rikici a cikin Pavilion wanda zai iya kai su ga halaka... Maayah kuma halinta da na Chief Onyx ba za su taɓa haɗuwa ba. Maayah tana da tsananin girman kai, yayin da Chief Onyx yake son mutum mai sauƙin kai da biyayya. Ba zai taɓa dacewa a kai ta can ba... Yumna kuma Shima sarki ya sani cewa Chief Onyx ba zai taɓa karɓar Yumna ba saboda dalilai na kashin kansa da suka shafi tsarin masarautar Pavilion... Ganin sarki ya yi shiru, Chief Onyx ya ɗan yi nuni da hannunsa zuwa ga babban bangon falon. Nan take bangon ya juye ya zama babban screen wanda ya fara nuna hotunan dakarun Pavilion dubu-dubai dake atisaye a ƙasa da kuma na'urorin yaƙi masu firgitarwa... "Uncle, kada ka ɓata lokaci kana tunanin yadda za ka yaudare ni," Chief Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi dake cike da jan kunne... "Duniya ta canja. Idan na ba da umarni yanzu, kafin rana ta fito Alhamra za ta zama toka. Ba na neman wadda kake so, ina neman wadda za ta biya bashin da nake binka ne."... Sarki Nourdeen ya haɗiye yawu, ya dubi Chief Onyx cikin raunin murya... "Chief, na san na yi alkawari, kuma ban musanta ba. Amma ina neman alfarma guda ɗaya. Ka ba ni kwanaki uku kacal in koma in tsara yadda zan taho maka da ita. Ba zan iya ɗaukar ɗaya daga cikinsu a yau ba tare da wani shiri ba.".. Robot ɗin dake tsaye a gefe ta kalli Chief Onyx, tana jiran umarninsa... Chief Onyx ya yi shiru na ɗan lokaci, yana kallon yadda sarki yake gumi.. "Kwanaki uku?" Chief Onyx ya maimaita, sannan ya yi wani murmushin gefen baki wanda ya ƙara bayyana kwarjininsa. "To shikenan. Na ba ka kwanaki uku. Amma ka sani, idan kwanaki ukun nan suka cika baka kawo min wacce nake buƙata ba, to ni da kaina zan shigo Alhamra. Kuma a ranar ba zan karɓi 'yar aiki ba, zan karɓi duk masarautar ne baki ɗaya.".... Sarki Nourdeen ya ji wani sanyi, amma kuma ya san kwanaki ukun nan ba komai ba ne. Ya miƙe cikin sanyin jiki yayin da Robot ɗin ta fara yi masa jagora don fita daga falon zuwa inda helicopter ɗinsa take... ✨ Sarki ya jingina kansa da jikin kujerar jirgin, idanunsa a rufe. "Chingching," ya raɗa a fili... Itace kaɗai zaɓin da sarki yake gani zai iya fitar da shi kunya. Ba ta da uwa mai iko kamar Ruma da zata tada masa hankali, hasali ma uwarta bata raye, kuma ba ta da zafin kan Ayat ko girman kan Maayah... Amma kuma, zuciyarsa ta buga lokaci guda.... Chingching yarinya ce ƙarama, wacce ba ta san komai ba sai wasa da neman abinci... Ta yaya zai ɗauki wannan ƴar gaban goshin tasa ya kai ta matsayin yar aiki ga mutum irin Chief Onyx?... "Amma idan ban bayar da ita ba, Alhamra zata ruguje," Sarki ya faɗa cikin ransa, yana jin raɗaɗin yanke wannan danyen hukuncin... ✨ A can cikin masarautar Alhamra, kishin shaƙuwar dake tsakanin Inuwa da Master Ibrahim ya fara kai ma'aikata maƙura.. Ganin yadda Inuwa baya wani aiki na kwarai, sai dai ya fita yawonsa ya dawo ya huta, ya sa sauran dakarun fadar suka kulla masa sharri.. Sun haɗa gungunsu suka nufi wurin Master Ibrahim da nufin ɓata Inuwa.. "Master, gaskiya wannan yaron yana neman ɓata mana suna," ɗaya daga cikinsu ya fara magana.. "Wannan fitar da yake yi, ashe yawon neman mata yake yi a gari. Yana zuwa yana sharholiyarsa da mata, shi yasa idan ya dawo baya iya aiki saboda gajiya.".. Ibrahim ya ji wani irin ɗaci a ransa. Kalaman sun sosa masa zuciya, musamman idan ya tuna yau da safe da Inuwa ya sanar da shi cewa ya kwana da wata a asibiti... Amma a matsayinsa na jagora, bai nuna musu rauninsa ba. Ya share su, ya kuma ɗaure fuska tamkar bai damu ba.. "To, ina ruwanku?" Ibrahim ya faɗa cikin tsawa wacce ta sa suka ja baya. "Shi Inuwa ba namiji bane? Kamar yadda kuke son mata, haka shima yake sonsu. In dai yana yin abin da na sa shi, to ku barshi yasha soyayyarsa, lokacinsa ne!" Duk da cewa ya kare Inuwa a gaban ma'aikatan, amma bayan sun tafi, Ibrahim ya zauna shi kaɗai yana tunani. Wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyarsa wanda shi kansa bai san dalilinsa ba.. "Mata yake nema a gari?" ya tambayi kansa. Yana jin tamkar an yaudare shi. Ya fara jin cewa dole ne ya sanya ido sosai kan Inuwa, ba don sharrin ma'aikatan ba, sai don yana son tabbatar wa kansa cewa lallai Inuwa namiji ne cikakke mai sha'awar mata, domin har yanzu akwai wani abu game da Inuwa da ya kasa ganewa.. ✨✨ Bayan kwana biyu... Yau ma, Inuwa ya sulale ya fice daga fadar ba tare da Master Ibrahim ya sani ba, ya nufi tsakiyar kasuwar birnin Alhamra domin ɗan zagayawa ya rage wa kansa damuwa.. Kasuwar tana nan cike da hayaniya da rance-rancen ma'amaloli. Muryoyin masu talla suna tashi ta kowane gefe, musamman muryar mai sayar da abubuwan zaƙi, wanda ƙamshinsa ya cika ko'ina. Inuwa ya tsaya a gaban mai tallan, ya ji yana sha'awar saye amma duba aljihunsa ke da wuya, sai ya ga kuɗin jikinsa ba zai isa yayi siyayyar da yake so ba. Cikin sanyin jiki ya kawar da kansa ya yi gaba... Ba tare da ya sani ba, King Diamond yana biye da shi a baya, idanunsa na yawo akan kowane motsi na Ayat, amma sai dai a wannan lokacin bai fito a mai siffar farin gashi ba, ya koma gashinsa irin na ko wani mutum amma yana sanye da fararen kaya domin yana son farin abu a rayuwarsa.... Ganin yadda ta bar wurin mai zaƙin nan cikin rashin nasara, King Diamond ya isa wurin, ya nuna abin sannan ya ciro guda ɗaya daga cikin tsayayyun lu'u-lu'unsa ya miƙa wa mai sayarwa. Mai tallan ya daskare, ya kasa yarda cewa an biya shi da lu'u-lu'u akan kayan zaƙi!.. Inuwa ya cigaba da tafiya har ya tsaya a wurin mai snacks, ya sayi wasu ƴan abubuwa ya cigaba da tafiya. King Diamond ya sake tsayawa a wurin, yana kallon bayanta cikin nazari... "Tana son cakes ne?..." ya tambayi kansa a hankali. Shi ma ya sayi wasu nau'ukan snacks ɗin, ya sake biyan mai sayarwar da lu'u-lu'u. Mai snacks ɗin ya fara murna da rawa domin abin da aka biya shi ya fi ƙarfin abubuwan da yake sayarwa ninkin-ba-ninki... Daga ƙarshe Inuwa ya tsaya a wani babban tebur dake cike da littafai. Mai tallan yana ta shela.. "Books for sale! Littafai na tarihin duniya!" Inuwa ya fara dubawa, can sai idonsa ya sauƙa akan wani littafi mai taken "The Legend of the White Cat." Wani murmushi na natsuwa ya bayyana a fuskarsa, ya sayi littafin cikin farin ciki ya rungume shi, ya cigaba da tafiya... King Diamond ya ƙaraso wurin mai littafin, idanunsa suna kallon yadda Inuwa yake tafiya yana rungume da littafin nan... "Kana son littafai ne, Sir?" Mai littafin ya tambaya cikin girmamawa.. King Diamond bai amsa ba, ya zura wa bayanta ido yana maganar zuciya.. "Me ya sa take farin ciki da sayan littafi kuma? Me yake cikin wannan takardar da ya sa ta murmushi haka?" Ya ji wani irin shauƙi na son sanin komai game da ita, abin da take so, abin da yake sa ta dariya, da kuma abin da take karantawa a cikin sirri.. King Diamond ya matso kusa da mai littafin, idanunsa har yanzu suna kan Ayat dake ƙoƙarin ɓacewa cikin taron mutane.. Cikin murya mai natsuwa da iko ya yi tambaya.. "Shin kuna da littattafai waɗanda suka fi waɗannan inganci da kuma ƙarancin samu?" Jin wannan tambayar, mai littafin ya matso kusa da shi cikin girmamawa yana mamakin kwarjinin wannan baƙon mutumin. Ya tambaya, "Wane irin littattafai ne kake nema waɗanda ba a cika samu ba? Ko irin su Spring palace"... King Diamond ya ɗan yi shiru sannan ya ce, "Ko Spring Palace ko Winter Palace, ko ma mene ne... muddin dai ba a cika samun su ba. Kuma dole ne su kasance suna magana ne akan Jin King’s Requite..." Mai littafin ya jinjina kai, fuskarsa cike da fara'a ya ce. "Eeee... muna da littattafai akan Requite.".. Daga nan, mai littafin ya buɗe wani akwati na musamman ya ciro wani littafi mai taken.. "Prince Regent’s Requite" Ya miƙa wa King Diamond littafin yana ƙarin bayani.. "Babban jarumin wannan littafin ba Jin King ba ne, sarki ne shi ma.".. King Diamond ya karɓi littafin, ya bi rubutun dake jikin bangon littafin da kallo. Ta ke ya karanta sunan littafin a ransa.. "An Evilly Charming Emperor’s Requite" Ma'ana (Sakamakon Wani Mugun Sarki Mai Kwarjini da jan hankali..).. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya karanta ɗan taƙaitaccen bayanin farko da na ƙarshe dake cikin saƙon siyan littafin, yana ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa Ayat take sha'awar irin waɗannan labaran. Ya ji wani irin murmushin gefen baki ya subuce masa, yanzu ya fara gano hanyar da zai bi ya shiga zuciyarta ta hanyar abubuwan da take so... King Diamond ya buɗe shafin farko na littafin, idanunsa suna yawo akan kalmomin da aka rubuta da fasaha. Ya furta a hankali, "Alƙawarin rayuwa?... haka sarakuna suke biyan sakamakon soyayya." Mai littafin ya gyaɗa kai cikin gamsuwa, ya ce, "Haka ne, ka gane ma'anar kenan.".. Wani sanyayyen "Ohhh!" ya fito daga bakin King Diamond, yayin da wani haske ya ratsa ƙwaƙwalwarsa.. "Ashe shi ya sa ba ta taɓa gaya min ba duk da lokacin da muka ɗau a wancan lokacin..." Ya fara fahimtar cewa Ayat tana ɓoye abin da yake ranta ne saboda kunya ko kuma girman abin da take ji... Mai littafin ya yi murmushi, ya ƙara da cewa, "Ai tana da kunya ne.... Ya kamata ka kasance mai nuna himma da ƙwazo wajen neman soyayyarta." Ya ƙarasa maganar yana ɗan dariya, yana ƙarfafa wa King Diamond gwiwa... King Diamond bai sake cewa uffan ba, ya tsaya kawai yana kallon mai littafin da wani kallo mai zurfi. Sannan ya sanya hannu cikin aljihunsa, ya ciro ƙarin wasu lu'u-lu'u masu tsada, ya miƙa wa mutumin a matsayin lada... Mutumin ya karɓi diamonds ɗin hannunsa na rawa, ya shiga murna da farin ciki maras iyaka, domin wannan abin ya fi ƙarfin duk wani littafi da ya taɓa sayarwa a rayuwarsa.. King Diamond ya juya ya bar wurin yana rungume da littafin An Evilly Charming Emperor’s Requite a ƙirjinsa. Yanzu ya sami makamin da zai yi amfani da shi wajen narkar da zuciyar Ayat.. zai koyi yadda ake zama sarki mai jan hankali wanda zai iya sadaukar da komai don masoyiyarsa.... Daga kasuwa kai tsaye masarautar ta nufa, a bakin gate ta tarar da master Ibrahim.. Ta ƙarasa tana dariya, ta gaishe shi.. Master ya ce, "ina ka je?..." Inuwa ya ce, "na shiga kasuwa ne.." Ibrahim ya sauƙe idonsa akan littafin da ke hannunsa ya karɓa yana faɗin "wannan fa? Kaima kana son karanta littafan almara ne...?" Inuwa ya jinjina kai tare da faɗin "Eeee! Master..." Ya jinjina kai sannan ya ba shi umarni da ya shiga... Yana hanyarsa ta koma wa sashensa sai kwatsam ya haɗu da wasu jami'an da ya gane su, sune masu tsokanarsa... Nan suka dakatar da shi suna faɗin "Ya Ɗan ƙwaƙur ya akayi ne..." Ɗaya daga ciki ya make mazauninsa tare da faɗin "Ɗan ƙwaƙur mai manyan ɗuwawu...burgeni suke saboda mata ne masu irin shape ɗin ɗuwawun nan..." Ɗaya ya ce, "ai tin da yana da ɗuwawu to bazai rasa nonuwa ba, mu ji su..." Ya kai hannu yana shirin taɓa su, Ayat tayi saurin ja da baya.. Tana shirin bin ta gefensu ta wuce suka riƙo ta, suna faɗin... "Muna son yau mu ji ya girman zarman lulunka yake, mun ji labarin kana neman mata..." Ɗaya ne ya kai hannunsa da sauri wurin gabanta, ya yi nasarar canke wa, da sauri Ayat ta ja da baya... Mutumin ya zaro ido cikin izgilanci yana faɗin "kaiii ya ban ji komai ba, Ɗan ƙwaƙur ko dai har yanzu kaciyar takan bata girma bane, kuma da haka kake biyan buƙatarka a wurin mata?...." Sauran ma hannu suka kai zasu taɓa su ji, kawai suka ji an riƙe hannunsu tare da murɗawa... Waiwayowan da zasu yi sai suka ga Master Ibrahim ne, haka gaba ɗaya ya riƙe hannunsu su ukun ya fara muɗewa, ihu suka shiga yi suna bashi haƙuri.. Shi kuwa sai da ya ji hannunsu yayi ƙaƙasss kafin ya sakar musu, ya juya zai kalli yanda Inuwa ya ke akan su bashi haƙuri sai ya ga bata nan, tin zuwan Ibrahim ta sulale ta gudu... Babu wanda yasan hanyar da ta bi, ta shiga private garden yanda hanyar sirrinta yake wurin koma wa part ɗinta... King Diamond yana tsaye a bayan masarauta, inda hasken dake jujjuya aljani ya zamar da shi toka yake ta walƙiya. Ya san idan ya yi ƙoƙarin shiga da jikinsa to rayuwarsa za ta shiga haɗari... Ya kalli ledar da yake ɗauke da Sugar-coated Haws da kuma sauran snacks ɗin da ya saya mata a kasuwa.. "Aayat..." ya raɗa sunanta a cikin zuciyarsa, yana amfani da igiyar jinin dake tsakaninsu.. Maimakon ya shiga, sai ya yi amfani da wata tsohuwar dabara.. Ya ajiye ledar kyaututtukan a ƙasa, sannan ya yi wasu kalaman tsafi waɗanda suka sanya kyautar ta zama tamkar shadow... Ledar ta zama Inuwa wanda ba'a iya ganin ainahin ledar, don haka hasken tsaron masarautar ba zai iya gano ta ba... Ya tura wa Ayat saƙon hoto a cikin zuciyarta na inda ya ajiye kyautar daidai jikin taga na ɗakinta... Ayat tana zaune a ɗakinta, tana ƙoƙarin buɗe littafinta na White Cat wanda ta saya a kasuwa, ga kuma hawaye a fuskarta na baƙin cikin abinda jami'an nan sukayi mata. Nan take ta ji wani irin bugun zuciya, sannan ƙamshin Sugar-coated Haws ya bugi hancinta, ƙamshin da ta ji a kasuwa lokacin da take son saye.. Ta ɗaga kai sai ta ga wani abu yana walƙiya a jikin tagarta. Ta matso kusa sai ta ga wani leda mai kyau dake lulluɓe da wani sanyayyen haske mai launin diamond...alamun an masa garkuwa ne.. Tana taɓa ledar, sai hasken ya ɓace, ledar ya zama na gaske a hannunta.... Tana buɗewa, sai ta ga duka abubuwan da take sha'awa a kasuwa.. Sugar-coated Haws masu zaƙi.. Cakes da Snacks masu daɗi.. Kuma a ƙasan ledar akwai wata ƴar takarda da aka rubuta.. "Sakamakon sarki ba ya karewa a baki kawai. Ki ji daɗin zaƙin da kika rasa a kasuwa.". Ayat ta daskare, gabanta ya faɗi. Ta san babu kowa a masarautar nan da ya ga lokacin da ta so sayan waɗannan abubuwan sai shi. Tsoro da wani irin shauƙi suka gauraye ta.. Ta zauna a gefen gadonta, tana kallon tarkacen zaƙi da snacks ɗin dake gabanta. Ƙamshin Sugar-coated ɗin nan yana ratsa hancinta, yana tunatar da ita daidai lokacin da ta tsaya a kasuwa tana sha'awa amma ta kasa siya.. Ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki. Zaƙin ya narke a harshenta, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta. Amma duk da daɗin, hannunta yana rawa.. Ta lumshe idanu, tana jin yadda zaƙin yake ratsa ta. A ranta tana tunanin.. "Wane irin aljani ne wannan? Ta yaya ya san abin da nake so? Kuma ta yaya ya keta wannan katangar haske da kowa yake tsoro?".. Domin a saninta dai akwai wani hasken shocking a kewaye da masarautar nan saboda aljanu.. Tsoro ya fara ba wa shauƙi fili. Ta san cewa shingen masarautar Alhamra ba abin wasa ba ne, an ƙirƙire shi ne don ya raba jiki da ran duk wani aljani da ya yi gigin kusantowa. Amma shi, ya tsallake shi kamar iska, ba ma don ya kai hari ba sai don ya ba ta kyautar abin zaƙi... Ta sake karanta ƴar takardar dake hannunta.. "Sakamakon sarki ba ya ƙarewa a baki kawai..." "Requite..." ta maimaita kalmar a hankali. Ta tuna littafin da ta gani a kasuwa mai magana akan wannan kalmar. Ashe shi ma ya karanta abin da nake karantawa? Ko kuma shi ne asalin jarumin da littattafan suke magana a kansa?.. Wani irin murmushi mai tattare da fargaba ya subuce mata. Ta ji kanta a matsayin wata ganima da babban sarki yake nema, amma ba ta san ko za ta buɗe masa ƙofa ko kuma ta ƙara ƙarfafa shingen zuciyarta ba... Yayin da take cin sauran cakes ɗin, ta ji wani irin bugun zuciya na daban. Ta san yana nan kusa, tana jin sa a cikin jinin dake yawo a jikinta. Wannan Blood Bond ɗin ya zama tamkar rediyo dake nuna mata cewa ba ita kaɗai ba ce... Sai da ta gama cinye abubuwan tass sannan ta miƙe ta nufi taga, ta kalli hasken masarautar daren dake waje. Hasken tsaron masarautar yana ta walƙiya a nesa.. "Kayi kuskure idan kana tunanin za ka iya mallake ni da waɗannan kyaututtukan," ta raɗa wa iska, kodayake tana sane da cewa zuciyarta ta riga ta fara karɓar saƙon sa...... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣5️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan kwana biyu. Sarki Nourdeen ya ba da umarni na gaggawa, inda ya buƙaci ganin dukkan jami'an sojojinsa da dakarun tsaro. Nan take kowa ya halarta, kowa ya jera a layin da ya dace a babban ƙofar fadar. A cikin dakarun har da Inuwa, wacce take tsaye tana nazarin yanayin da ake ciki.. Abin da ya fi ba kowa mamaki shi ne fitowar sarki. A wannan karon, Sarki Nourdeen ya fito ne tare da fadawansa da tafidarsa, amma babban abin al'ajabin shi ne Sarki ya cire sirrin dake rufe da fuskarsa, ya fito a asalin siffarsa... Duk ma'aikatan ciki har da waɗanda suka daɗe a fada, babu wanda ya taɓa ganin fuskar sarki haka fili sai a yau. Da farko da yawa sun ɗauka ba sarkinsu ba ne, sai da suka ji sautin muryarsa da irin izzar da yake magana da ita, sannan kowa ya tabbatar cewa lallai Zakin Alhamra ne. Sarki ya kalli dakarunsa, fuskarsa a murtuƙe cikin tsananin damuwa. Ya yi jawabi mai zafi.. "Na tara ku ne don in sanar da ku cewa masarautar nan tana fuskantar barazana. Ina umartarku da ku ƙara sa ido fiye da kowane lokaci. Kada ku yarda wata baƙuwar fuska ta shigo cikin masarautar nan ba tare da izini ba. Mutanen Pavilion suna shiri ne na musamman don ƙwace mana ikonmu da mutuncinmu." A ransa, sarki ya riga ya gama yanke hukunci. Ba zai bayar da ko ɗaya daga cikin ƴaƴansa ba. Ya gwammace ya fuskanci yaƙi da Chief Onyx da ya amince da wannan cin fuskar na mayar da gimbiya ƴar aiki... Bayan sarki ya kammala jawabin ya koma cikin fada, dakarun kowa ya kama gabansa cikin fargaba.. Amma Inuwa ta shiga wani dogon tunani. Ta tsaya a inda take, tana maimaita sunan a ranta. "Pavilion..." Wace irin daula ce wannan da har mahaifinta, sarki mai iko, zai fito ya nuna fuskarsa fili sannan ya nuna tsoronsu haka? Zuciyarta ta gaya mata cewa akwai wani babban sirri dake ɓoye tsakanin Alhamra da Pavilion... ✨✨ A can daular Pavilion, yanayin ya sha bamban da fargabar dake cikin Alhamra. Wurin shakatawa private pool na Chief Onyx wuri ne dake cike da natsuwa, inda ruwan ke sheƙi ƙarƙashin hasken lantarki na zamani. Chief Onyx yana cikin ruwan, ya nitse gaba ɗaya har zuwa ƙasan pool ɗin. Ya kwanta a can ƙasa tamkar ba ya buƙatar numfashi, idanunsa a rufe yana dogon nazari. Ruwan yana kewaye faffaden ƙirjinsa da kuma dogon gashinsa dake yawo a cikin ruwan... Ga kowa, wannan lokaci ne na wanka da hutu, amma ga Onyx, lokaci ne na tsara dabarun da za su girgiza duniya... Tana taku cikin natsuwa, Robot ɗinsa ta shigo sashen pool ɗin. Ta tsaya a gefen ruwan, idanunta na karatu da binciko dukkan motsin dake kewayenta. Ba tare da ɓata lokaci ba, ta fara magana da muryarta mai sanyi dake ɗauke da hujjoji.. "Chief, bayanan da na tattara daga Alhamra sun tabbatar da cewa Sarki Nourdeen ya janye yarjejeniyarsa. Ya tara dakarunsa ya ba su umarnin ƙara tsaro, kuma ya nuna cewa ba zai bayar da ko ɗaya daga cikin ƴaƴansa ba. Ya zaɓi yaƙi maimakon biyayya." Duk da wannan babban labarin dake nuna cin amana, Chief Onyx bai ko motsa ba. Ya ci gaba da kwanciya a ƙasan ruwan na wasu daƙiƙoƙi. Labarin bai girgiza shi ba domin dama ya san halin raunin zuciya na Sarki Nourdeen... A gare shi, Alhamra tamkar ƙanƙarar dake narkewa take, ba ta da abin da Pavilion take da shi ninkin-ba-ninki... Ko a yau yaso a fara yaƙi, ya san cewa rushe Alhamra abu ne na mintuna, ba ma sa'o'i ba... Can sai ya fara fitowa daga cikin ruwan a hankali. Yayin da fuskarsa ta bayyana a saman ruwan, gashinsa ya jiƙe ya kwanta a kafaɗunsa, sai ya yi wani irin la'anannen murmushi. Murmushi ne mai cike da ma'anoni dubu na rainin wayo, na jiran lokaci da kuma na muguntar da zai yi wa duk wanda ya yi tunanin zai iya yaudararsa... Bai furta ko kalma ɗaya ba, amma murmushin ya riga ya faɗi komai.. Wasa ya ƙare... Chief Onyx ya miƙe tsaye ya fito daga cikin pool ɗin, ruwa yana ta zuba a jikinsa tamkar wani dodo da ya fito daga teku. Ya kalli Robot ɗinsa da idanuwansa waɗanda suka sauya launi saboda jin shirin yaƙi.. Ya tsaya yayin da Robot ɗin take miƙa masa wani babban farin towel don ya busar da jikinsa. Ba tare da ya kalle ta ba, ya ce. "U. Nourdeen ya zaɓi hanyar da zata kai shi ga halaka. Tunda ya fasa yarjejeniyar, to mu ma za mu nuna masa cewa Pavilion ba ta magana sau biyu. Ki fara shirin Cyber-Attack..." Nan take Robot ɗin ta fara latsa wasu na'urori dake jikin hannunta. A cikin daƙiƙu ƙalilan, duk hanyoyin sadarwa na masarautar Alhamra suka fara samun matsala. Na'urorin tsaro na fada CCTV suka fara daukewa, sannan hasken wutar lantarki na wasu sassan fadar ya fara dishi-dishi. Wannan shi ne shirin farko na durƙusar da masarautar ta hanyar fasaha kafin ma a kai ga amfani da takobi... Bayan nan, Chief Onyx ya ba da umarnin tura wasu tsuntsayen na'ura Drones waɗanda aka ƙera su daidai da siffar tsuntsayen gaske amma suna ɗauke da na'urorin leken asiri da makaman guba... "Ina son ganin kowane lungu da saƙo na Alhamra," in ji Chief Onyx. "Dole ne in san inda ya ɓoye ƴaƴan nasa. Musamman wadda zuciyata take gaya min cewa ita ce mabuɗin wannan masarautar.".. ✨✨ A can Alhamra, Inuwa dake zaune a gefen titi masarautar tana tunani, kwatsam sai ta ga wasu tsuntsaye guda biyu sun gilma ta kanta. Sai dai takunsu da sautin fikafikansu ya bambanta da na tsuntsayen da ta saba gani. Zuciyarta ta buga, ta miƙe ta fara bin su da kallo. A lokaci ɗaya, duk kofofin zamani na fada suka daina aiki, hakan ya jefa jami'an tsaro cikin ruɗani... Master Ibrahim ya fito yana ta tsawa, "Me yake faruwa? Me ya sa injinanmu suka tsaya?".... Ayat tana tsaye a tsakiyar harabar fadar, idanunta sun yi jawur tamkar na mace-macen daji. Ta ga yadda ɗaya daga cikin tsuntsayen na'urar yake shawagi kusa da ita. Ba tare da ɓata lokaci ba, ta zura hannu ta ɗauko majaujawar dake jikinta, ta saka dutse mai kaifi ta saita shi da kyau... Dutsen ya tafi da gudun gaske, ya doki fikafikin tsuntsun. Na'urar ta fara fitar da wuta tana sparks, ta faɗo ƙasa tana tangal-tangal. Ayat ta ruga da gudu ta ɗauko shi kafin kowa ya gani. Ta dubi cikin idon tsuntsun, wanda kyamara ce ta leken asiri, ta ji gabanta ya faɗi. Ta gane cewa daga wannan kyamarar wani can nesa yana kallonta... ✨ A can ɗakin Chingching, tana zaune tana murnar samun kazar da aka soya mata da yaji, kwatsam sai wutar lantarki ta ɗauke gaba daya.. "Wayyo! Uma Altine! Wutar ma satarsa aka yi ne?" Chingching ta fara kuka tana laluɓar kazar ta a cikin duhu.. Ta fito waje tana ƙiran "Daddy! Daddyy!!...", tana tsoron kada wani ya kwashe mata kazar... Ita a tunaninta ba babban al'amari ne ya faru ba, kawai dai an hana ta jin daɗin abincin dare ne. Wanda hakan ya sa wasu ma'aikatan suka ɗauka ko an kawo wa fadar hari ne.. Sarki Nourdeen yana cikin ɗakin taro na sirri lokacin da duk fuskokin kwamfutocinsa suka nuna alamar Access Denied.. Ya buga teburin gabansa cikin matsanancin firgici. "Yau ne? Chief Onyx, ashe ba za ka jira kwanaki ukun su cika ba?" Sarki ya raɗa cikin tsoro. Ya gane cewa daren nan ne fushin Pavilion ya fara sauƙa. Ya gane cewa duk wani shiri da yake yi na ɓoye 'ya'yansa, Chief Onyx ya riga ya san inda suke ta hanyar waɗannan drones ɗin... ✨✨ A can Pavilion, Chief Onyx yana kallon allon dake gabansa, inda kyamarar tsuntsun da aka harbo take nuna masa fuskar Inuwa kafin ya ɗauke gaba ɗaya. Ya saki wani murmushi mai sanyi... "Wannan yaron... ko kuma ince wannan 'yar tawayen," Chief ya faɗa a fili... "Kina da ƙoƙarin ɓoye asirinki, amma baku san cewa duk motsinku yana karkashin ikona ba."... Wannan lokaci ne da lamura suka hargitse a masarautar Alhamra, inda fasahar Pavilion ta mamaye kowane lungu... A daidai lokacin da Ayat take tsaye tana juya tsuntsun ƙarfen da ta harbo, sauran dakarun fada sun ruɗe. Waɗanda suke da bindigogi suna ta harbi zuwa sama, yayin da wasu suke saran tsuntsayen na'urar da takobi suna ihu. Cikin wannan hargitsin, Robot Z-01 ta bayyana a fadar tamkar iska, ba tare da kowa ya lura da shigowarta ba... Ayat ta ga wata inuwa ta rufe ta, tana ɗagowa sai ta yi ido huɗu da wata kyakkyawar budurwa, fara sol tamkar 'yar kasar China, sanye da bakaken kaya matsattsu. Kafin ma Inuwa ta yi tunanin ko ita wacece ko kuma ta kai hannu ga takobinta, Robot ɗin ta yi wani irin zafafan taku. Wani uban mari Robot din ta zabga wa Inuwa, marin da ya sa Inuwa ganin taurari, ta tafi luu ta durƙushe a ƙasa. Ƙarfin hannun Robot ɗin ya wuce na ɗan Adam. Ba tare da bata lokaci ba, Robot din ta fizgo hannun Inuwa da karfi, ta damko ta tamkar yadda ake damkar tsuntsu... Cikin kwarewa da sauri, ta janyo Inuwa wacce har yanzu take cikin jiri, ta nufi wata boyayyar hanyar fita da ita... Robot ɗin ta jefa Inuwa cikin wani ƙaramin jirgi mai saurin gaske wanda yake jiran su a bayan fada. Cikin 'yan daƙiƙu jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya, ya bar Alhamra cikin hayaki da rugujewar tsaro... Ayat tana zaune a cikin jirgin, hannunta a ɗaure da wasu ankwan ƙarfe na lantarki, tana kallon Robot ɗin dake zaune a kusa da ita ba tare da ko kifta ido ba... Ayat tana zaune a cikin wannan ƙaramin jirgi mai gudu, tana jin yadda iskar sararin sama take ruri a wajen jirgin. Duk da zafin marin da ta sha da kuma jirin dake kanta, ƙwaƙwalwarta ta fara aiki da sauri. Ta kalli Robot ɗin dake zaune kusa da ita, wadda idanunta suke kallon gaba ba tare da motsi ba.. Ayat ta lura cewa hannayenta suna ɗaure da waɗancan ankwan na lantarki masu fitar da wani ɗan haske... Ta fahimci cewa wannan yarinyar Robot ce ba ɗan Adam ba ce, yanayin numfashinta da yadda ba ta kifta ido sun tabbatar mata da hakan.. Don haka, dole ne ta yi amfani da dabarar da ta fi ta ƙarfin jiki.. Ayat ta tuna tsuntsun na'urar da ta harbo ɗazun, har yanzu akwai guntuwar wayar da ta ciro daga cikin tsuntsun... Da sanɗa, ta fara goga guntun wayar nan mai magnet a jikin ankwan dake hannunta... Ta sani cewa idan ta samu ta haɗa wutar lantarki a tsakanin ankwan da wayar, za su iya buɗewa... Wani ɗan tartsatsin wuta ya fito. Robot ɗin ta juyo da kanta da sauri, amma Ayat ta yi saurin dunƙule hannunta da wayar tana rarraba ido tamkar tana kuka ne saboda tsoro.. Ganin Robot ɗin ta ɗauke kanta, Ayat ta ƙara haɗa wayar kwatsam ankwan suka buɗe, ta cire ankwan... Ba tare da ɓata lokaci ba, ta kai wa Robot ɗin duka da sauri, amma Robot ɗin ta tare ta tare da damƙe wuyanta.. "Ba za ki iya tserewa ba," Robot ɗin ta faɗa da muryarta mai sanyi.. Ayat ta yi murmushin yaƙi tare da faɗin.. "Ba tserewa zan yi ba, jirgin zan lalata!" Ta buga ƙafarta kan wani babban jan button dake kusa da mazaunin matuƙin jirgin. Jirgin ya fara tangal-tangal, hayaƙi ya fara tashi daga injin ɗinsa. Robot ɗin ta saki wuyan Ayat don ƙoƙarin saita jirgin, hakan ya ba Ayat damar nufi ƙofar gaggawa Emergency exit... Kafin Robot ta ankara, Ayat ta tura ƙofar, ta jefa kanta waje zuwa ƙasi daga sararin sama... Ayat tana ta shawagi a cikin iska, tana faɗowa daga sama da gudu... A wannan lokacin, ta rufe idanunta ta sadaukar da rayuwarta ga mutuwa. Ta gwammace ta tarwatse a ƙasa da ta shiga hannun Pavilion da hatta mahaifinta shakkarsa yake.. Kafin jikinta ya daki ƙasa, kwatsam sai wani haske mai ƙarfi da kwarjini ya bayyana. Wannan hasken ya riƙe ta tamkar wani bargo mai laushi, ya naɗe ta cikin sanyin da ya fi kowane irin ni'ima. Cikin ƙiftawar ido, hasken ya wuce da ita kamar walƙiya.. Inuwa ba ta sauƙa a ko'ina ba sai a tsakiyar gadonta na alfarma, asalin gadon Gimbiya Ayat. Ma'aikatanta da suke can falo ba su ma sani ba, domin a tunaninsu Gimbiya tana ciki tana barci.. Ta zaro ido tana waige-waige, numfashinta yana fita da sauri "Hah... hah...!" Ta kalli rufin ɗakin, ta kalli jikinta, ta kasa yarda cewa yanzu take sararin sama amma yanzu tana cikin ɗakinta... Zuciyarta ta fara wani irin bugun sauri, nan take hoton King Diamond ya bayyana a ranta. Ta ji a jikinta cewa shi ne ya cece ta. Duk da cewa King Diamond ba zai iya shigowa cikin fadar ba saboda shingen tsafin dake kare masarautar, amma ya samu nasarar dasa mata tunaninsa da siffarsa a cikin zuciyarta.. Wani irin yanayi mai sarƙaƙƙiya ya baibaye ta. Ta ji tana son yin dariya saboda farin cikin tsira, tana son yin kuka saboda tsoron da ta fuskanta. Ta dafe ƙirjinta inda take jin ɗumin wannan hasken har yanzu, ta raɗa a hankali.. "Nagode... da taimako." A can wajen masarautar, a saman iska, King Diamond yana tsaye idanunsa suna haske kamar taurari. Ya ji kalmomin da ta faɗa a cikin zuciyarsa, ya gamsu da cewa ya fara samun gurbi a cikin zuciyar gimbiya mafi taurin kai a duniya.. A daidai wannan lokacin, a gefen masarautar Alhamra, King Diamond ya tsaya ya miƙa hannunsa guda zuwa sararin sama. Ya kalli tsuntsayen na'ura na Chief Onyx da suke ta faman addabar mutanen fada.. Ba tare da ya furta uffan ba, sai ya girgiza yatsunsa. Nan take, wasu bakaken harshen wuta na aljanu suka fara tashi daga ƙasa suna bin tsuntsayen nan ɗaya bayan ɗaya. "Buum! Buum!! Buum!!!" Tsuntsayen na'urar suka fara fashewa a sararin sama, suna narkewa tamkar tsohon dalma. Duk wani leken asiri da Chief Onyx yake yi ya daukewa gaba ɗaya allon kwamfutocin Pavilion.. haka yake nuna Static.. Robot Z-01 ta sauƙa a filin saukar jirage na Pavilion cikin sauri. Tana taku cikin natsuwa amma akwai alamun damuwa a tattare da tsarin na'urorinta.... Ta bayyana a cikin katafaren falon Chief Onyx, takun ƙafafunta kawai ke tashi. Ta tsaya nesa da shi kaɗan, fuskarta ba ta nuna alamar tsoro ba amma tsarin na'urorinta ya nuna cewa tana cikin yanayi na Internal Error saboda rashin nasarar da ta samu... Chief Onyx yana tsaye a bakin wata ƙatuwar taga dake kallon daular birnin Pavilion, hannunsa ɗaya riƙe da kofin abin sha na alfarma..ba tare da ya juyo ba yake sauraronta.. Cikin muryarta mai sanyi, Robot ɗin ta fara magana, "Chief... na kasa kammala aikin. Abin harin ta kuɓuce daga hannunmu a cikin sararin sama. Wani iko dake wuce tunanin na'ura ya ɗauke ta." Chief Onyx ya yi shiru na ɗan lokaci, iskar dake busawa daga taga tana kaɗa dogon gashinsa. Ba tare da ya kalle ta ba, ya furta cikin murya mai zurfi dake cike da natsuwa da kuma nauyin gaske.. "Yau ne karon farko da kika taɓa kawo mun rahoton gazawarki..." Jin waɗannan kalmomi daga bakin Chief Onyx ya sa Robot ta sunkuyar da kanta ƙasa da sauri. Duk da cewa ita na'ura ce, an ƙera ta da wani irin tsari na kishin aiki da biyayya ga jagoranta. Sunkuyar da kanta da ta yi ya nuna tsananin rashin jin daɗin yadda ta ba shi kunya a wannan babban aikin da ya sanya ta... Falon ya sake yin shiru, sai ƙarar tartsatsin wuta dake tashi daga allon kwamfutar dake gefe, wanda ke nuna cewa duk tsuntsayen na'urar da aka tura Alhamra an tawarwatsa su. Chief Onyx ya ci gaba da kallon waje, amma a ransa ya san cewa wannan yaƙin ya sauya salo. Tunda har akwai wani iko da zai iya ƙwace mutum daga hannun Z-01, to tabbas akwai wani Sarki na daban dake kare Alhamra wanda ba Sarki Nourdeen ba... ✨✨ Ayat tana nan zaune a kan gadonta, ta cire kayan maza ta ɓoye su a yanda take ajiye su. Ta sanya kayan barci na alfarma na gimbiyoyi, ta zauna tana sauraron ƙarar fashewar tsuntsayen na'urar dake faruwa a waje... Zuciyarta tana gaya mata cewa daren nan ya zama daren canji. Ta gane cewa akwai mai tsaronta a ko'ina, tana da wani babban masoyi kuma kare-dangi wanda ko shingen tsafi ba zai iya dakatar da tausayinsa gare ta ba. Ta gyara kwanciyarta, tana murmushin da ita kaɗai ta san ma'anarsa, yayin da tsoron Chief Onyx ya fara fita daga zuciyarta.... Gimbiya Zayana jin abinda ke faruwa ba ƙaramin tsorata tayi ba, domin tsawon shekaru abu makamantan haka bai taɓa faruwa ba... ✨✨ Bayan sati biyu da faruwar dambarwar tsuntsaye.. Masarautar Pavilion ta yi tsit. Chief Onyx bai sake turo wani hari ba, kuma bai sake maganar yarjejeniya ba. Amma wannan shirun ya fi kowace ƙarar bindiga tsoratarwa a wurin Sarki Nourdeen. Ya sani cewa Chief Onyx baya hakura, kawai dai yana jira ne ya ga sarki ya nakasa kafin ya karkare shi... Sarki Nourdeen ya zauna a cikin tsararren falonsa na sirri, yana tunanin ko ya faɗawa Ruma halin da ake ciki ne. Amma nan take ya girgiza kai. Ruma mace ce mai son zubar da jini, ita a wurinta duk matsalar da aka samu kisa ne kawai mafita. "Idan na gaya mata, to karshen Alhamra ya zo, domin zata tunzura Chief Onyx ya yi abin da ya fi kisa muni," sarki ya faɗa a ransa... Sarki ya kalli Tafida, amintaccensa wanda suke zaune a falon sirri. Ba kowa a wurin don haka maganar sirri ce ta musamman.. "Tafida, wace shawara kake da ita? Kwanaki sun ja, kuma Chief Onyx yana jiran mu," Sarki ya faɗa cikin muryar damuwa.. Tafida ya gyara zama, ya dube sarki ido-da-ido.. "Ranka ya daɗe, abu ɗaya nake tunanin shine mafita... Me zai hana ka kai masa Yumna?" Sarki ya ɗago a ruɗe, zuciyarsa ta buga. "Yumna kuma? Kana nufin Yumna ɗiyar da kowa ya ɗauka tawa ce?" Tafida ya jinjina kai, "Tabbas. Shi Chief Onyx bai san ta ba, tun tana ƙarama rabonsa da ita. Ba zai taɓa gane cewa ƙanwarsa bace ta jini. Idan ma mugunta yake son yi wa 'ya'yanka, to sai dai ya yi wa ƙanwarsa a rashin sani. Kuma tunda ita tafi kowa sanyi da biyayya, zata iya zama da shi ba tare da ta jawo maka matsala ba.".. Sarki ya jinjina kai, ransa ya ɓaci da tunanin yadda zai kalli Yumna ya ce ita zai kai... "Amma Tafida, kowa ya ɗauka 'yata ce. Babu wanda ya san cewa ba daga cikina ta fito ba. Idan na ba shi ita, ba ka ganin wata rana gaskiya zata fito?" Tafida ya yi murmushin kwantar da hankali. "Ranka ya dade, wannan shi ne asirin da zai kare ka. Ta zama personal maid ɗinsa, amma a asali ita kanwarsa ce. Idan ya cutar da ita, ya cutar da jininsa. Idan ya so ta, ya so kanwarsa. Kuma hakan zai sa ya daina neman sauran 'ya'yanka." Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya gamsu da wannan dabarar koda yake zuciyarsa tana masa nauyi.. "Shikenan Tafida. Shirya yadda za a sanar da ita, amma kada wani ya san asalin gaskiyar nan.".. Tafida ya ce, "Baza'a sanar da ita ba, kawai za'a kaita a matsayin bata san meke faruwa ba, da zaran an kaita acan zata ji dalili..." 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣6️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan sati biyu na jinya a ƙasar Indonesiya, Maayah ta dawo Alhamra cikin ƙoshin lafiya, Kowa ya yi murnar ganinta amma murnar ta fili ce, domin a zuci kowa akwai abin da yake saƙawa. Sarki Nourdeen ya shigo ya nuna farin cikinsa, duk da cewa ransa rabi yana kan shirin tura Yumna Pavilion ne... Maayah tana zaune a kan kujera ta alfarma, tana nuna isa, yayin da Yumna take zaune a gefenta tana mata hidima... Sai ga Gimbiya Ayat ta shigo, sanye da riga ta alfarma wadda aka ƙawata da zaren zinare, kanta rufe da mayafi mai tsada wanda ya fito da kyan idanuwanta domin tana rufe da rabin fuska ne kamar yanda ta saba. Saratu tana biye da ita a baya tana taku cikin ladabi. Babu wanda zai kalle ta ya yi tunanin ita ce wannan dakare wato Inuwa... Ta samu wuri ta zauna kusa da gadon Maayah, "Sannu da dawowa Maayah. Allah ya ƙara miki lafiya. Yi haƙuri da baki ganni ba kafin ku tafi, jikina ne ya ɗan yi tsami a lokacin." Maayah ta gyara kwanciya tana yatsina fuska. "Ba komai Ayat. Na san ai ke baki cika son shiga harkar mutane ba, sai dai idan abin ya shafi Chingching..." Ayat ta kalleta cike da mamaki a ranta tace, "wato yanzu an daina respect, ba Auntyn ma..." Zayana ta tura ƙofa ta shigo kamar iska, sanye da wata riga 'yar kanti dake nuna asalin jinin baturiya. Ta kalli Ayat ta taɓe baki, sannan ta kalli Maayah... "Oh... ashe duk an taru a nan? Maayah, naga kin dawo kina taku kamar ba ke ce kika kusa zama gurguwa ba. Amma dai ina fata jinyar Indonesiya ta rage miki wannan girman kan, ko kuwa?" Maayah cikin zafi ta ce, "Zayana, idan girman kai gado ne, ai na gada ne. Kema kinsan cewa ko ana ruwa ana iska, ni ce gimbiya ta musamman a masarautar nan, dube ni jinin Hindu.... Kuma naga har yanzu baki daina sanya waɗannan kayan turawan naki ba marasa lissafi kamar wata Christian, ko kina nufin baki ɗauki kanki a matsayin 'yar masarautar Alhamra ba ne?" Zayana ta kalli Ayat duk da baƙin cikin da Maayah take ƙunsa mata "Ke kuma Ayat, kullum kina nan cikin shiru-shiru kamar ruwan sanyi. Amma kowa yasan ruwan sanyi shike cin uwar tulu. Me kike ta saƙawa a ranki ne da har kike wasu maganganu a ranki?"... Ayat ta ɗago idanunta masu kaifi ta kalli Zayana.. "Kin san me take faɗa a raina kenam? Zayana, shiru na ba tsoro ba ne, kuma magana ta ba sirri ba ce. Kawai dai na fi son in ga mutum ya yi magana cikin hankali maimakon ya dinga surutu kamar mahaukaci... Ke kullum burinki ki ga kin ɓata wa kowa rai, amma ki sani, kyan mace ba a tsayin riga yake ba, a natsuwar zuciyarta yake." Maayah ta katse su da cewa, "Dakatar da wannan surutun..! Zayana, kada ki zo nan ki nemi raina mana hankali. Idan mahaifiyarki tana da iko a ƙasarsu, nan Alhamra ce......Kuma Ayat kada ki yi mana wani bayanin natsuwa, domin natsuwar mace ita ce ta san yadda za ta kula da ƙannenta, ba wai ta keɓance kanta kamar wata mayya ba.".. Zayana ta yi dariya ta rainin wayo.. "Lallai Maayah, kinsan yadda ake jifan magana. Amma fa karki manta, a cikinmu duka, ni ce mahaifina yake tsoro. Don haka kowa ya kiyayi harshensa, domin kalma ɗaya zan faɗa, gobe ku tsinci kanku a gidan kurkuku!"... A gefe guda, Yumna tana zaune tana kallon yayyen nata. Zuciyarta tana mata zafi. Su suna faɗa akan iko da nuna isa, amma ita tana jin wani irin kewa aranta... Ta kalli Ayat, ta kalli Maayah, sannan ta kalli Zayana. Ta yi tunanin cewa wata rana fa bazasu kasance da juna kamar haka ba, sai sunyi kewar junansu... Yumna cikin sanyin murya ta ce, "Aunty Zayana, Aunty Ayat, don Allah ku bar wannan maganar. Muna farin cikin dawowar Aunty Maayah ne, kada mu sanya taron ya zama na kuka.". Maayah ta ce, "Ke dai Yumna yi shiru. Shirun naki ne ya sa kowa yake raina miki hankali a gidan nan!".. Zayana ta tsaya na takaitaccen lokaci, ta kai wa Yumna wani irin kallo na alfarma. "Ke kin ciri tuta, Yumna... Saboda kina ba ni darajata kuma kina girmama ni, don haka ke tawa ce. Sauran kuma, sai dai su mutu da haushina." Tana gama faɗar haka, ta karkade rigarta ta fice cikin takama... Maayah ta bi ta da wani uban tsaki, ranta yana ƙuna.. Ayat itama ba tare da ta furta uffan ba. Ta wurga wa Maayah wata zafaffiyar harara dake nuna cewa tana sane da duk abin da yake faruwa, sannan ta juya ta fice tare da Saratu... Maayah ta saki baki tana huci, "Can muku dai munafukai kawai! Kuma aniyarku ta biku. Ni na fi ƙarfinku, na zama muku ciwon ido, sai dai a ganni a barni!"... Yumna ta kalli Maayah cikin rashin fahimta.. "Amma ina jin mamaki Aunty Maayah, ganin ba kya wani shiri da Aunty Ayat. Kuma naga mahaifiyar Ayat kafin ta rasu ita ta ci gaba da riƙe ki. A ɗaki ɗaya kuka tashi bayan tafiyar mahaifiyarki, me ya sa kuke haka?" Maayah ta kawar da kai, tana jin ɗacin tunowa da baya. "Yumna, Ayat ta canja. Ta ɗauki ƙanwarta Chingching kawai a matsayin iya ƙanwarta ta jini, shi ya sa wannan fifikon ya wargaza haɗin kanmu. Idan mutum ya nuna maka kai ba jininsa ba ne, me za ka yi masa in ba ka ja girmanka ba?".. Bayan sun kammala, Yumna ma ta tashi cikin sanyin jiki ta nufi nata sashen.. Tana shiga, sai ga ma'aikatanta sun rugo da gudu, fuskokinsu cike da tsananin farin ciki... "Aunty Yumna! Barka da dawowa!" Wasu suka rungume ta, wasu suna kukan murna domin sun yi kewarta sosai a tsawon kwanakin da ta yi a ƙasar waje... Yayin da Yumna take tsaka da karɓar gaisuwar ma'aikatanta, sai ga wani babban hadimi daga ɓangaren sarki ya bayyana a ƙofar... "Gimbiya Yumna," ya faɗa yana mai sunkuyar da kai.. "Sarki yana nemanki a cikin ɗakin taron sirri yanzu-yanzu. Kuma ya ba da umarnin kada ki zo da kowa.".. Ma'aikatan suka yi shiru, farin cikin ya koma fargaba. Yumna ta gyara mayafinta, zuciyarta ta fara bugawa da sauri. "Yanzu zan zo," ta amsa, sannan ta bi bayan hadimin ba tare da ɓata lokaci ba... ✨✨✨ Yumna ta shiga babban ɗakin taron sarki, inda ta tarar da shi zaune shi kaɗai, babu ko fitilun da aka saba kunnawa na alfarma, sai dai wasu 'yan kaɗan dake bada haske dishi-dishi... Yanayin fuskar sarki a murtuke yake, amma da ya hango Yumna, sai ya ɗan saki fuska... "Yumna," Sarki ya ƙira sunanta cikin muryar kulawa. . "Na'am barka da dare Abul," ta amsa cikin ladabi tare da tsugunawa har ƙasa.. Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya kalli 'yar tasa wacce ko kaɗan ba ta taɓa ja masa magana ba.. "Na ƙira ki ne domin in sanar da ke cewa, gobe idan Allah ya kaimu asubanci, muna da tafiya tare da ke. Ina son ki shirya da zarar kin idar da sallar asuba, ki fito ki same ni a babban filin saukar jirage na fada." Yumna ta ɗan yi shiru, zuciyarta ta cika da mamaki. A rayuwarta ba ta taɓa yin tafiya ta musamman da sarki shi kaɗai ba, yawanci idan za a fita kowa yana tafiya ne tare da ma'aikatansa... Amma duk da haka, bai taɓa ranta har ta tambayi sarki "ina za mu?" ko "me za mu je yi?" Ba... "To Abba, Allah ya kaimu. Zan kasance a can kamar yadda ka bayar da umarni," ta amsa cikin sanyin murya.. Sarki ya ji wani daɗi ya ziyarci zuciyarsa. Ya jinjina kai yana kallon Yumna har ta fice daga ɗakin. A ransa ya ce, "Tabbas Yumna ta bambanta. Da ace Ayat ce ko Maayah ko Zayana da yanzu sun sani a gaba da tambayoyi na diddigi, ina za mu? Me za mu yi? Me ya sa yanzu? Amma ita Yumna, sanyin ranta da hakurinta sun kai matsayin da ba zan taba iya mantawa da su ba.".. Wannan halin nata ya ƙara sa sarki yake son ta, amma kuma raɗaɗin zuciyarsa ya ƙaru domin ya san yana gab da miƙa wannan taskar ga mutumin da bai san darajar mace ba.. Yumna ta koma dakinta, ta ƙi faɗawa ma'aikatanta komai domin sarki ya nuna tafiyar ta sirri ce... Ta kwanta amma barci ya ƙi daukarta. Tana ta tunanin wace irin tafiya ce sarki zai fita da ita shi kaɗai? Ta saka a ranta cewa ƙila wani babban alheri ne mahaifinta yake son yi mata.. ✨ Ƙarfe huɗu da rabi na asuba, Yumna ta tashi ta yi sallah, ta shirya cikin wasu milk kaya masu kyan gaske dake rufe jikinta sosai... Already wani bafade ya zo ɗaukanta wanda dashi za'ayi tafiyar.. suka nufi filin saukar jirage na fada, inda ta tarar da sarki cikin riga da wando na dakarun yaƙi, ya shirya tsaf, yana jiranta a kusa da wani karamin helicopter na sirri... Jirgin ya kutsa cikin gajimare, babu abin da ke tashi sai ƙarar injin jirgin.. Yumna tana kallon mahaifinta wanda idanunsa ke kallon gaba amma hankalinsa yana wani gun.. Bayan awanni, sai ga wani ƙaton birni ya bayyana wanda gine-ginensa duk na gilashi ne da karafa, jirage na yawo a tsakanin dogayen bene. Yumna ta zaro ido tana kallon abubuwan al'ajabi, manyan allon tallace-tallace dake shawagi a iska da kuma hasken lantarki dake walkiya duk da hasken rana... Bayan jirgin ya sauƙa a babban filin Pavilion, ba a ba su damar takawa ba sai da wasu na'urori lasers suka ratsa jikinsu baki ɗaya. Wata na'ura ta bada sautin.... "Scan Complete. No weapons detected." Daga nan wasu motoci masu tafiya ba tare da direba ba suka dauke su zuwa babban fadar Chief Onyx... Suka shiga wani babban falo wanda girman sa ya kusan ninkin fadar Alhamra. Komai na ciki fari ne sol kuma na zamani... Robot Gely tana tsaye a tsakiyar falon, idanunta na jan haske suna bin sarki da Yumna daga sama har kasa, tana tantance kwayoyin halittarsu.. Yumna ta ji wani irin tsoro ya ziyarce ta, ganin yadda Robot din ke kallonsu ba tare da kyaftawa ba. Ta kamo hannun sarki ta matse da karfi, jikinta na rawa.. "Abul, ina ne nan? Me ya sa mutanen nan suke kallonmu haka?" ta tambaya cikin muryar kuka.. Sarki Nourdeen ya daure ya dafa kafadar ta, "Kada ki ji tsoro Yumna, nan ne inda za ki zauna na ɗan lokaci. Ina nan tare da ke." ✨ A can saman bene, Gely ta isa ƙofar ɗakin Chief Onyx.. Ta latsa jan kati (key card), kofar ta bude ba tare da karar komai ba. Chief Onyx yana kwance a babban gadonsa, jikinsa babu komai sai gajeren wando. Kwantattun gashin kirjinsa suna sheki, yayin da dogon gashin kansa ya bazu a kan pillow kamar gashin zaki.. Yana baccin sa ne cikin natsuwa, kirjin sa na dagawa da sauƙa a hankali.. Gely ta tsaya a kansa, tana nazarin yanayin bugun zuciyarsa da kwakwalwarsa. Ta yanke shawarar tashe shi domin biya masa bukatarsa.. Gely ta matsa kusa, ta sanya yatsanta mai sanyi ta taɓa wuyansa a hankali, sannan ta yi wata yar muryar ba tare da tada hankali ba, "Boss... Boss... lokaci ya yi." Chief Onyx ya ɗan motsa, ya buɗe idanunsa a hankali waɗanda suka yi dumu-dumu da barci... Ya yi addu'o'in tashi daga barci a zuciyarsa, sannan ya tashi zaune yana shafa fuskarsa.. "Gely, me ye?..." ya furta cikin muryarsa dake daukeda kwarjini... Gely ta yi ƙasa da murya, "Sarki Nourdeen ne ya zo, yana jiran ka a falon ƙasa. Ya taho da ɗaya daga cikin 'ya'yansa. Ya cika alkawari yau, ganin cewa shirun da muka yi masa ya nuna masa karshen Alhamra ya kusa idan bai yi biyayya ba." Chief Onyx ya yi wani murmushin gefen baki, murmushin nasara da nuna isa. Ya ɗaga wa Gely hannu alamar ta bar ɗakin, ya ji abin da take nufi.. ✨ A can ƙasa, ma'aikata waɗanda rabi mutum ne rabi na'ura suka fito da wasu tebura na gilashi.. Suka jera abinci kala-kala waɗanda ba a taɓa ganin irinsu a Alhamra ba, da wasu abubuwan sha masu launuka daban-daban dake fitar da hayaƙi mai daɗi... Amma Yumna ko kallon abincin ba ta yi ba, idonta yana kan kofar da take sa ran ganin wannan mutumin da ya sanya mahaifinta cikin damuwa har ya kawo ta wannan duniyar... Chief Onyx ya sauƙo ƙasa cikin takunsa na isa, sanye da wata baƙar riga ta alfarma wadda aka buɗe maballan saman, inda faffaden ƙirjinsa dake cike da gashi yake bayyane, yana ɗaukar idon kowa. Ya zauna a kan kujerarsa ta sarauta, yana gyara agogon hannunsa na zamani ba tare da ya kalli kowa ba... Sarki Nourdeen ya ja numfashi, muryarsa tana ɗan rawa ya ce, "Chief, yau alƙawari ya cika. Ga yarjejeniyar nan na kawo ta kamar yadda muka tsara.".. Yumna wadda take jin tamkar ana tura ta cikin wuta, ta kalli sarki cikin lallashin murya.. "Abul... me yake faruwa ne? Me ya sa kake maganar yarjejeniya?" Jin muryarta mai zaƙi da sanyi ya sa Chief Onyx ɗago kansa a hankali. Bai kalli fuskarsu kai tsaye ba, amma ya kalli gabansa yana nazarin sautin muryarta wanda ya taɓa wani sashi na zuciyarsa da ya daɗe a rufe... Sarki ya kalli ƙasa, ya kasa haɗa ido da Yumna. "Ki yi haƙuri ƴata. Na kawo ki ne domin ki yi masa aiki a nan. Ke ce za ki zama mataimakiyarsa.".. Yumna ta saki hannun sarki, idanunta suka cika da hawaye. Ta kasa yarda cewa mahaifinta wanda take gani a matsayin garkuwarta, shi ne zai sayar da ita a matsayin baiwa ba... Chief Onyx ya yi wani murmushin gefen baki, murmushi mai cike da rainin wayo. Ya kalli sarki Nourdeen, sannan ya kalli Yumna. A matsayinsa na wanda yake da fasahar da ta san abin da ke ɓoye, ya ji cewa sarki yana ƙoƙarin yaudararsa ne.... "Gely" Chief ya ƙira sunan Robot ɗinsa cikin sanyi. "Babu wanda zai iya shigo wa har duniyar fadata sannan ya yaudare ni. Mutane suna tsammanin ni wawa ne. Ki duba jininta... Idan ƴarsa ce ki sanar da ni. Idan kuma akasin hakan ne, ki gaya min ko ita wacece ta hanyar asalin jinin jikinta." Gely ba tare da ɓata lokaci ba. Wasu koren haske wato scanners suka fito daga idanunta suka ratsa jikin Yumna.... Cikin sanyi Gely ta juya ta kalli Chief Onyx.. "Boss... an kammala tantancewa. Wannan yarinyar ba ɗiyar Sarki Nourdeen ba ce ta jini." Falon ya ɗauki shiru na wasu daƙiƙoƙi. Sarki Nourdeen ya fara gumi, yayin da Yumna ta daskare a inda take... Gely ta ci gaba, "Abin mamaki shi ne, jinin jikinta yana da alaƙa ta kusa da naka da kashi 99.9%...." Chief Onyx ya miƙe tsaye da sauri, kofin dake hannunsa ya faɗi ya fashe. Idanunsa suka yi jawur yayin da yake kallon Yumna, wadda ita ma take kallonsa cikin tsananin mamaki da tsoro... Sarki Nourdeen ya riga ya san asirin zai fito, amma bai yi tsammanin Gely za ta gano hakan cikin sakan biyar ba. Ya san cewa daga yau, rayuwar Alhamra da Pavilion za ta sauya zuwa wani abu daban.. Gely ta tsaya kyam, tana zazzago bayanan da na'urarta ta bankaɗo.. "Binciken jini ya nuna kamar haka... Blood Group, O Positive. Genotype, AA. Blood Pressure, 110/70 domin Akwai alamun fargaba da saurin bugun zuciya... Hemoglobin Level, Normal. Amma babban abin lura a nan shi ne.....Tsarin kwayoyin halittarta na Chromosomes da DNA Markers sun yi daidai da naka, Boss... Wannan jinin ba na Sarki nourdeen ba ne. Jinin ya fito ne daga asalin tsatson King HAMSHAK...domin inada file na jinin jikinsa a ƙwaƙwalwata tare da naka Boss..." Yumna ta ji kanta ya fara juyawa. Ta kalli sarki Nourdeen wanda kansa yake sunkuye a ƙasa, ya kasa cewa uffan.. "Abul... me take faɗa? Wacece ita da zata ce ni ba jininka bace? Kuma wane ne wannan mutumin da take cewa dan uwana ne?" Hawaye suka fara wanke fuskarta. Duk wani buri da take da shi na cewa tana da uba mai kariya ya ruguje a cikin sakanni kalilan... Ta ji kanta ya yi nauyi, duniya ta fara juya mata... Sarki nourdeen ya dubi Gely da kyau sannan ya ce, "Amma taya zaki tantance ta lokaci guda kuma ki bada sakamako a take?..." Gely ta ce, idonta a ƙyafe ana Sarki nourdeen.. "Malam Nourdeen, tin farkon ganinka da nayi na gama tattarar duk bayananka da jinin jikinka, yanda a duk lokacin da na ga jininka zan san taka ce..." Daga nan Sarki bai ƙara furta uffan ba.. Chief Onyx ya matsa kusa da Yumna, takunsa yana bada sautin "thud, thud" a kan benen falon. Ya tsaya daf da ita, kwarjininsa da kamshinsa suka gauraye da iskar dake kewaye da ita. Ya miƙa hannunsa, ya kamo habarta ya dago fuskarta don su hada ido... A karon farko, Chief Onyx ya ji wani irin ɗumi a ransa.. Idanun Yumna masu ɗauke da rauni da gaskiya, sun tunatar da shi idanun mahaifiyarsu... Ya juya cikin zafi ya kalli Sarki Nourdeen... "Nourdeen!" Chief ya ƙira sunansa cikin muryar dake razana kowa... "Ka kwashe shekaru ashirin kana ɓoye min jinin jikina...Ka sace kanwata, ka mayar da ita 'yarka, sannan yau ka taho da ita a matsayin 'yar aiki domin ka kare kanka da 'ya'yanka na gaske?"... Sarki Nourdeen ya ɗago kai, fuskarsa cike da gumi duk da sanyin AC dake ɗakin.. "Chief... ba sace ta na yi ba. Cetonta na yi a lokacin da aka kai muku hari aka tarwatsa gidan ku. Na riƙe ta tamkar 'yata ta cikina, na ba ta duk soyayyar da uba yake ba wa ƴarsa. Ban taɓa barin ta san ita wacece ba domin in kare rayuwarta daga maƙiya!" Chief Onyx ya shaƙe wuyan sarki da hannu ɗaya, ya ɗaga shi sama har kafafun sarki suka daina taɓa ƙasa... "Ka kare ta? Ko ka mayar da ita 'yar garkuwa domin ranar da bashi ya matsa maka ka mika min ita?" Yumna wadda hawayen farin ciki suka wanke mata fuska, ba ta tsaya tsoron kwarjinin Chief Onyx ba. Da sauri ta faɗa jikinsa, ta rungume shi sosai a daidai lokacin da yake ƙoƙarin wurgar da sarki... Chief Onyx ya saki sarki Nourdeen nan take, ya ji wani sanyi ya ratsa shi wanda bai taɓa ji ba a rayuwarsa ta sarauta da fasaha.. Ya rungume ta, yana shafa sumar kanta cikin wani irin yanayi na kariya. Yumna ta ɗago tana kuka, muryarta na rawa.. "Yayana, kun tafi kun bar ni... Shin wane ne kai a cikin twins ɗinmu? Kai ne Yaya Ra'ees ko kuwa Yaya Reems? Shi ɗayan yana ina?" Tambayar Yumna ta soki zuciyar Chief Onyx tamkar mashi. Tunawa da ɗan uwansa tagwaye, wanda aka hallaka ta hanyar sauya masa halitta tun suna yara, ya sanya shi jin wani raɗaɗi... Don kar ya tayar mata da hankali, ya jure ya ce. "Ni ne yayanki, Ra'ees." Amma lokacin da ta tambayi inda Reems yake, Chief ya rufe idanunsa na ɗan lokaci kafin ya ce, "Baya raye." Ya faɗi hakan ne domin bai san inda zai fara neman Reems ba a cikin wannan sabuwar siffar da aka ba shi.. Sarki Nourdeen, wanda yake gefe yana gyara numfashinsa, ya san gaskiyar magana... Ya san cewa Reems yana raye, kuma ya san cewa wannan canjin halittar da aka yi masa ya mayar da shi wani abu daban wanda ya ɓace daga idon duniyar mutane. Amma ganin yanayin da ake ciki, sarki ya gwammace ya yi shiru don kada ya ƙara tunzura Chief...domin yasan shima ya sani kawai ya ɓoye wa ƙanwarsa ce... Chief Onyx ya rarrashe ta, ya share mata hawaye sannan ya kamo hannunta suka nufi babban mazauninsa na musamman. Ya zaunar da ita a gefensa a kan kujera ta alfarma, sannan ya kalli sarki Nourdeen da wani kallo na daban.. "Zauna, U. Nourdeen," Chief ya faɗa cikin muryar izzah. "Ka yi min abin da dakaruna da fasahata suka kasa yi min shekaru ashirin. Ka riƙe min ƙanwata, ka kare ta, kuma ka kawo min ita." Gely tana tsaye, tana ɗaukar dukkan hotunan wannan taron domin adana su a cikin babban kundinta na ƙwaƙwalwa... Yumna tana kallon yayanta Ra'ees wato Chief, tana jin cewa yau ne karon farko da ta sake samun asalin rayuwarta.. 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣7️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan ma'aikata robots sun fita da Yumna zuwa sashen hutu, falon ya koma shiru.. Chief Onyx ya gyara zama, yana kallon Sarki Nourdeen kamar zai cinye shi mama ɗanye... "Na yafe maka hukuncin yaudarata da kayi.." Chief ya faɗa cikin murya mai sanyi dake shaƙe da barazana. "Ka riƙe Yumna ne a matsayin 'yar kallo domin ka samu mulkin Alhamra. Amma tunda ka kiyaye min lafiyarta, zan bar ka ka rayu.".. Sarki Nourdeen ya haɗiye miyau, ya san duk takunsa Chief ya sani... Ya ce, "Ina neman alfarmar ka bar ni in koma da ita Alhamra, idan na koma ni kaɗai, sannan bayan kwana biyu na kawo mata wata to sauran 'ya'yana da mutanen gari zasu zargi wani abu. Kuma idan asirin cewa ita ba 'yata ba ce ya fito yanzu, za a iya samun rudani a masarautar da kake so ka gada.".. Chief Onyx ya yi murmushin mugunta... "Zaka koma da ita ne domin ka kare kanka, ba don ka damu da ita ba. Amma zan amince, domin ina bukatar ta kasance a masarautar Alhamra a matsayina. Amma ka sani, yarjejeniyar mu tana nan. Dole ka kawo min ɗaya daga cikin gimbiyoyinka, Ina son ɗaya daga cikinsu ta zama personal maid ɗina, domin ta zauna a nan, ta gane cewa mulkin da kake taƙama da shi, ni ne mamallakinsa..." Sarki ya jinjina kai, jikinsa na rawa. "Na yarda. Zan shirya wacce zan kawo maka.".. "Gely!" Chief ya ƙira. "Yes, Boss." "Shirya yarjejeniya Digital Contract. Sarki Nourdeen zai mayar da Yumna, amma zai dawo da ɗaya daga cikin 'ya'yansa nan da kwanaki uku. Idan ya saɓa, Pavilion zata ƙaddamar da hari akan Alhamra ba tare da sanya kowa a ciki ba...." Gely ta fitar da wani hologram na takarda, sarki ya sanya hannu wato digital thumbprint... Bayan sarki ya fita, Gely ta matsa kusa da Chief. "Boss, me ya sa zaka bar ta ta koma hannun mutumin da ya sanya aka kashe iyayenku? Akwai haɗari." Chief Onyx ya tashi tsaye, ya kalli hoton birninsa na Pavilion ta tagar gilashi... "Zan bar shi ya ji tsoron wacce zan zaɓa a cikin 'ya'yansa... zan ɗauko wacce ya fi so, in mayar da ita baiwa a nan, yadda ya so mayar da Ƙanwata..." A can sashen hutu, Yumna tana zaune a gaban wani tebur na alfarma, amma zuciyarta tana can gun sauran gimbiyoyi, bata son tayi nisa da Alhamra..." ✨✨ Sai da suka kwana, Sarki aka bashi ɗaki na musamman duk da bazai iya kwanciya yayi bacci a wannan birnin ba saboda fargaba da tsoro... Bai rintsa ba har asuba.. Tafiyar asubanci suka yi cikin sirri, inda jirgin sarki ya sake sauƙa a babban filin Alhamra... Yumna ta fito, fuskarta babu annuri domin akwai wani irin kwarjini na daban da ya fara bayyana a tare da ita.. Sarki Nourdeen ya ƙira ta gefe kafin su rabu zuwa sassan su... "Yumna," ya ƙira sunanta cikin muryar lallashi, "Kamar yadda muka tattauna da Yayanki, wannan maganar sirri ce tsakaninmu. Kada ki kuskura ki nuna wa kowa, har ma da 'yan uwanki gimbiyoyi cewa kin san wani abu. Ke ƴar gidan nan ce, kuma haka zaki ci gaba da zama a idon duniya." Yumna ta jinjina kai cikin sanyin jiki. "Na ji, Abul. Amma zuciyata ba za ta taba daina tunanin Yayana ba." Sarki ya yi ajiyar zuciya, ta wuce nata sashen yayin da shi kuma ya nufi fada, zuciyarsa tana bugawa... Dole ne ya zaɓi ɗaya daga cikin gimbiyoyinsa ya miƙa ta ga Chief Onyx a matsayin personal maid wato baiwa.... Sarki Nourdeen ya zauna a babban falonsa, idanunsa sun yi jawur saboda rashin bacci da kuma fargabar abin da zai biyo baya. Yana nazarin matan nan guda huɗu da ya riƙe a matsayin 'ya'yansa.. Ya san cewa kowacce a cikinsu idan ya kai ta Pavilion, tamkar ya jefa kansa ne a cikin babban bala'i. Idan ya kai Zayana, Ruma za ta iya sa sojojin Turai su ƙone Alhamra... Idan ya kai Maayah, fushinta da girman kai zai iya sa ta yi abin da Chief Onyx zai kashe ta... Idan kuma ya kai Ayat, wacce ko shi bai san fuskarta ba, to lallai masarautar Pavilion za ta ga abin mamaki... Duk da ya tura Yumna da fari, yanzu tunda asiri ya tonu cewa ita ƙanwar Chief ce, ya zama dole ya zaɓi ɗaya daga cikin gimbiyoyin nan... A yau Sarki ya ƙira babban hadiminsa, ya ce masa.. "Ina son a shirya babban taron gimbiyoyi na musamman gobe. Ba zan jira lokacin haɗuwarmu na shekara ba. Ina son kowacce ta fito daga sashinta, su hallara a fada." Hadimin ya firgita, "Allah ya ba ka nasara, har da Gimbiya Ching Ching?" "Har da ita!" Sarki ya daka masa tsawa. _A washegari da safe_ Sashen Gimbiya Zayana.. Tana zaune a kan wata kujera ta zinariya, ma'aikatanta na tsugune a gabanta kamar dabbobi... Tana ɗore da ƙafarta akan bayan wata yayinda tayi goho..ta miƙe ƙafar tana danna wayarta.. Ɗaya kuma a gefe itama tana durƙushe kamar mai yin rarrabe, Miemie tana zaune akan bayanta tana cin abinci, ita bazata zauna akan kujera ba sai a bayan baiwa ko zata ci abinci.. Kana ganinta kasan jinin Zayana ce, Zayana kuma jinin Ruma.. domin duk siffar turawa ne dasu, cat eyes da kuma galden hair... Wata ce ta shigo ta durƙusa ta sanar cewa.. "Princess hadimi ya zo, wai sarki yana son ganinku..." Ta daka mata tsawa da cewa, "Wane irin taro ne Sarki zai ƙira yanzu? Shin bai san cewa fito da ni daga sashena ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba zubar da mutuncina ne?" Ta miƙe ta kalli madubin dake manne a bangon falo kusa da plasman ya sha ado, tana gyara farin gashin kanta, zuciyarta na raya mata cewa lallai akwai wani abu da sarki yake shirin yi... ✨ Sashen Gimbiya Maayah.. Ita kuwa ko kallon ma'aikatan ba ta yi ba. Ta kalli gefe ta ce, "Bana son hayaniya! Idan sarki yana son ganina, ya zo nan sashena mana. Amma tun da ya ce kowa ya fito, zan je, amma kowa ya shirya wa kowane irin fushi da zai fito daga gare ni in har ba tattaunawar arziƙi bane."... ✨ Sashen Gimbiya Ayat.. Ta tashi tsaye a hankali, mayafinta na rufe da fuskarta, sai idanunta kawai dake walƙiya. Ta yi shiru ba ta ce komai ba.. sai amsar da ta bayar da "Shi ke nam, Allah yasa lafiya..." ✨ Sashen Gimbiya Ching Ching.. Sanar mata hadimi yayi da cewa.. "Gimbiya Ching Ching, ki je inji sarki..." Turo baki tayi da faɗin.. "Bana zuwa! Ni wanka za a yi min, kuma barci nake ji. Idan Daddy yana so na, ya sa a goyo ni a kai ni fadar." Uma Altine tana lallashinta, "Gimbiya, umarnin sarki ne, dole ne mu je." Sai da Uma Altine ta goye ta kafin suka tafi, dake ta saba da nauyin Ching Ching yanzu goyon baya damunta... Fadar sarki ta ɗauki tsit bayan an ƙira taron gaggawa. Gimbiyoyin sun zauna a kujerunsu na alfarma, amma dukansu suna jin wani sanyi a jikinsu.. Sarki Nourdeen ya kalli 'ya'yan nasa, musamman Yumna wacce take nuna kamar ba ta taɓa jin sunan Pavilion ba.. "Na ƙira ku ne domin in sanar da ku wani abu mai mahimmanci. Masarautar Alhamra tana da yarjejeniya da wani babban sarki, kuma an buƙaci a aika da ɗaya daga cikinku don wakiltar mu a can." Gimbiya Zayana ta yi gyaran murya. A ranta tana tunanin cewa lallai ita ce za a aika, domin ita ce babba kuma ta fi kowa kwarewa... Sarki Nourdeen ya cigaba da  "Kasar da za a je itace... Pavilion." Jin sunan Pavilion ya sa duk ma'aikatan dake tsaye suka girgiza. Wasu sun fara raɗa-raɗai a hankali, "Pavilion? Wanda muke ji a labaran litattafai!" Yumna kuwa ta daskare, amma ta danne fuskarta, ta nuna cewa ita ma a yanzu take jin sunan... Sarki Nourdeen ya kuma cewa, "Kuma wacce na zaɓa ita ce... Gimbiya Ching Ching." Wani irin shiru ne ya biyo baya. Maayah ta kalli Sarki da mamaki, Zayana ta buɗe baki har ta manta da izzarta... Gimbiya Ayat ta kalle shi a dimauce. Ta miƙe tsaye, mayafinta yana kaɗawa, idanunta suna nuna tsananin damuwa.. "Abul! Ta yaya? Ka san cewa Ching Ching ba ta san ciwon kanta ba. Har yanzu wanka ake mata, kuma bata damu da komai ba sai wasa da bacci! Me ya sa za ka zaɓe ta a cikinmu? Ni, ko Zayana, ko Maayah, har ma da Yumna, duk mun girme ta kuma mun fi ta sanin yakamata. Me ya sa ita?" Gimbiya Zayana ta kalli Ayat da rainin hankali, tana mai gyara kayanta.. "Ke! Ayat! Waye ya ba ki damar kawo sunana a cikin wannan maganar? Ni dai ba ruwana! Kuma Abul, wannan yarinyar (tana nuna Ching Ching da hannu) ba ta cancanci ta je ko ina ba." Sarki ya daka musu tsawa... "Ya isa haka! Umarni na ne na ƙarshe!"  "Ayat, baki fini ƙaunar Ching Ching ba. Ina jinta a raina kamar rayuwata, amma na san cewa a can ba za a cutar da ita ba, domin na san wanda zan aikata wuri. Kuma na san cewa ita ce mafi dacewa." Sarki ya kalli Ching Ching, wacce ke zaune a gefensa a kujerar sarautarsa tana wasa da ƴan tsananta...  "Ching Ching! Za ki shirya tafiya gobe da asuba. Za ki je wata ƙasa mai kyau, inda za ki ci abinci iri-iri kuma za a ba ki sababbin kayan wasa."... Ching Ching ta ɗaga kai, "Da gaske Daddy? Amma ba zan iya tafiya ba, ba na son manyan jirage masu tashi sama, goyona za'ayi a kaini wurin.." Bayan an sallame su, kowacce ta koma sashenta cike da tunani da fargaba.. Ayat ta kasance cikin damuwa matuƙa, tana jin cewa za a aike ƙanwarta can wata duniyar da ba ta sani ba... Sarki yana zaune a kujerarsa, sai ga Uma Altine ta shigo cikin damuwa, ta durƙusa tana gaishe shi... Ya dube ta sannan ya ce, "me ke tafe dake?..." Uma Altine cikin damuwa ta ce, "Ranka ya daɗe! Na ji batun za'a aika Gimbiya Ching Ching can ƙasar, kuma na duba ita yarinya ce har yanzu bata fara jinin al'ada ba, ina tunanin idan ta fara wa zai kula da ita? Shine na ke roƙon alfarma a tura mu tare domin na cigaba da kula da ita, tin tana jaririya nake riƙe da ita ina so na kare martabarta da mutuncinta..." Sarki ya jinjina kai sannan ya ce, "Kar ki damu akwai waɗanda zasu cigaba da kula da ita acan, ku kasance a sashenta, duk abinda kuke so kuyi magana..." Uma Altine tayi godiya sannan ta fice cikin damuwa, bata so tayi nisa da Ching Ching ba duk da wahalar da take bata... Wannan bayani da uma Altine ya sanya sarki shiga nazari, duba da babu mata a fadar Pavilion sai robots da akayi musu siffar mata.... Kaf sojojinsa maza ne... Wannan tunanin ne yasa shi ƙara jinkiri a tafiyar... ✨ An kwashe sati biyu cur, amma shiru babu Sarki Nourdeen, babu kuma alamar wata gimbiya da za'a kawo.. Fadar Pavilion ta shiga cikin wani irin yanayi na shiru mai cike da tashin hankali. Chief Onyx yana zaune a ɗakinsa, yana kallon wata babbar allon dijital inda hotunan gimbiyoyin Alhamra suke...ko wacce yasan bayananta.. Gely cikin muryar na'ura mai sanyi ta ce, "Boss, wa'adin sati biyu ya cika. Sarki Nourdeen ya sake karya alƙawarinsa." Chief Onyx ya yi murmushin rainin wayo... "Idan shi karya alƙawari ba matsala ba ce a wurinsa, to ni babban matsala ce, komin ƙarantarsa. Zamu shirya tafiya garin Alhamra. Ƙasar da babu wanda ya taɓa ganin kamannina har zuwa yanzu, sai dai su ji labarina. To, zuwa gobe za su ganni ido da ido."... ✨ Bayan kwana ɗaya, sararin saman Alhamra ya shaida wani baƙon abu. Wani jirgin sama mai cike da fasaha, ba kamar namu na al'ada ba, ya sauƙa a babban filin sauƙar jirage na masarauta... Wannan jirgin na musamman ne, domin babu kowa a cikinsa sai mutum biyu kaɗai, Chief Onyx da kuma Gely, robarsa mai taimaka masa... Sarki Nourdeen ya fito don tarbar baƙon, fuskarsa cike da fargaba... Babu wanda ya san fuskarsa, sai labarinsa da ake ji a litattafan fiƙira... Chief Onyx ya fito daga jirgin, sanye da doguwar riga baƙa mai kwarjini, yayin da fuskarsa ke ɗauke da wani abin rufe fuska wato digital mask wanda ya ke ɓoye ainihin kamanninsa. Gely tana biye da shi, idanunta na bada hasken ja... Jama'ar Alhamra suka yi tsit. Kowa yana kallon Sarkin Pavilion da ido cike da tsoro da mamaki... A cikin taron jami'an tsaron da suka tsaya don kare lafiyar sarki, akwai Inuwa... Sanye da kayan tsaro irin na sarakunan, Inuwa yana kallon Chief Onyx da idanu cikeda mamaki da kuma shakku... Inuwa yana maganar zuci. "Wannan shi ne mutumin da Abul yake son kai wa Ching Ching? Yana da kwarjini, amma kuma yana da ban tsoro. A yanzun ma babu wanda zai bada shaidar fuskarsa." Domin rafin fuska na sanye da ƙarfen azurfa mai kyan gani da ado..sai rabin fuskar ne a bayyane .. Chief Onyx ya matsa kusa da Sarki Nourdeen, ba tare da ya kalli kowa ba sai sarki... Cikin murya mai kauri da izza ya furta.. "Ina fatan ba ka manta da ni ba, Sarki Nourdeen... Wa'adin ya cika, kuma na zo ne don karɓar abin da nawa ne." Sarki Nourdeen jikinsa na rawa ya ce, "Barkanka da zuwa, Sarkin Pavilion. Ka yi haƙuri, an samu wasu matsaloli ne." Chief Onyx ya ce,  "Matsalolin da wataƙila wani na cikin gidanka ne ke ƙirƙiran su?" Ya faɗa yana kallon Inuwa wanda ke tsaye a cikin jami'an tsaro. Idanunsa na dijital sun duba kowane jami'i... Inuwa ya ji wani sanyi ya ratsa shi. Yana tunanin ne ya sa Sarkin pavilion yake kallonsa ba, amma ganin wannan robot yasa ta tuno da yunƙurin sace ta da akaso yi, har ta faɗo saman jirgi....nan jikinta ya fara rawa... "Kodai su ne za'a ba wa Ching Ching?..." Sai kuma ta fara nadamar cewa, "Da nasan hakan zata faru da tin lokacin na bisu mun tafi, na tabbata da yanzu basu zo neman ƴar uwarta ba..." Sarki Nourdeen ya bi ta inda Chief Onyx ya kalla, ya ga Inuwa.. "Babu wanda ya isa ya kawo matsala a masarautata." Chief Onyx ya ce,  "To, tunda al'amarin ya zama haka, zan zauna a nan Alhamra har sai an shirya komai. Gely, nemi masauki a cikin fadar." Sarki Nourdeen cikin damuwa ta ce, "Za ka zauna a nan?" Chief ya furta.  "Eh, zan zauna, domin in tabbatar da cewa ba a sake karya alƙawari ba." Hakan ya sa Sarki Nourdeen shiga wani sabon yanayi na damuwa, domin a yanzu Sarkin Pavilion yana cikin fadar Alhamra, kuma babu wanda ya san menene shawararsa ta gaba... Filin masarautar ya kasance cike da tsit, yayin da Sarkin Pavilion Chief Onyx, ke shirin shiga wuce wa cikin fadar.... Kowa ya sunkuyar da kai, ba tare da ya kalli kwarjinin mutumin ba... Gely ɗinsa ta kalli Inuwa wanda ke cikin jami'an tsaro. Ta buɗe baki kaɗan don ta yi magana, domin ta tuna cewa wannan ita ce yarinyar da ta taɓa gani a baya. Amma Chief Onyx ya ɗaga mata hannu alamar ta yi shiru. A yanzu, abin da yake gabansa shi ne bukatarsa, ba ruwansa da abin da bai shafe shi ba... Sarki Nourdeen ya yi masa iso da su shige cikin fada. Chief yana ƙoƙarin motsawa daga inda yake tsaye... Sai aka ji wata hayaniya daga can nesa..  "Ku taimaka mana! Ku riƙe! Wayyo Allah! Ching Ching ki dakata dan Allah!" Kowa ya juya kansa. Gimbiya Ching Ching ce ta fito daga ɓangaren part ɗinta da gudun gaske a kan doki. Da duk kan alamu dokin ne ya kuɓuce mata, kuma ba ta iya control ɗinsa ba, bata san yadda zata tsayar da shi ba. Dokin sai gudu yake yi, tana ihu kamar ranta zai fita, tana ƙanƙame shi da ƙarfi... Dakarun da suke tsaronta suna bin dokin da gudu, amma duk sun kasa dakatar da shi. Hankalin sarki ya tashi matuƙa ganin autarsa na shirin hallaka... Ayat ta zaro manya-manyan idanuwanta cikin tsoro da fargaba. Dakarun masarautar duk sun kauce wa dokin saboda gudunsa. Ayat, cikin shigarta ta Inuwa, ta yi ƙarfin hali. Ta ruga da gudu don ta dakatar da dokin. Amma dokin ya yi mata wani irin harbi da ƙafafunsa na baya. ta yi sama, ta faɗo ƙasan floor ɗin masarautar, har goshinta ya fashe... Dokin bai tsaya ba, ya nufi Chief Onyx kai tsaye dake yanda dokin ya sako kai ko kwana baya sha, ba alamun dakatarwa... Gely, ganin dokin zai afkawa Boss ɗinta, ta shige gaba don ta kare shi... Chief Onyx, wanda fuskarsa ke ɗauke da abin rufe fuska na ƙarfen azurfa, ya fusata... Ya riƙo kunkumin Gely ya manna ta da jikinsa ta gefe, kamar asalin macen da yake ji da ita. Sannan ya kai wani irin mari da tafin hannunsa a kan goshin dokin.. Nan take ƙwaƙwalwar dokin ta juye, ƙafafunsa na gaba suka durƙushe. Ching Ching da ke samansa ta yo gaba kamar zata kifo ƙasi ta fuska sai kuma ta faɗa kan faffaɗen ƙirjin Chief... Ta riƙe wuyansa da hannu biyu, fuskarta a kife a kan ƙirjinsa, tana shaƙar ƙamshin jikinsa mai daɗi. Ta gama tsorata sosai... Kowa ya sauƙe ajiyar zuciya. Sarki ya riƙe ƙirji, yana hamdala da sakin numfashi... Bayan da Chief Onyx ya dakatar da dokin, Ching Ching ta kankame shi tana shakar kamshinsa, amma shi ko gezau bai yi ba.. Ganin yarinyar ta yi lumm a jikinsa kamar wata bishiyar randa, Chief ya janye jikinsa da karfi, ya sake ta daga samansa... "Timmm!" Haka Ching Ching ta faɗi a ƙasa ba tare da ya kalle ta ba. Ya juya cikin takunsa na gadara, ya nufi cikin fadar Sarki Nourdeen... Gely tana biye da shi a baya, koda yake ita na'ura ce amma tsarin Artificial Intelligence ɗinta ya nuna wani irin kishin ɓoye ganin yadda wannan yarinyar ta manne wa Boss ɗinta... ​Sarki Nourdeen, cikin tsoro ya daka wa dakarunsa tsawa.. "Ku riƙe min auta! Kada ku bari ta shigo ciki, za ta iya fusata shi. Shi ba mutum ne mai son hayaniya ba!" ​A cikin katafaren falon fadar, iska ta ɗauki shiru, sai kamshin turaren wuta na alfarma dake tashi a sanyaye. Sarki Nourdeen yana zaune tare da babban aminin sa Tafida, da wasu fadawa guda biyu, dukkaninsu jikinsu na rawa... ​A ɗayan bangaren, Chief Onyx yana zaune a kan wata lallausar kujera ta luxury. Idanunsa a kaife suke ba tare da ya kalli kowa ba, sai agogon hannunsa yake kallo cikin matukar miskilanci. Gely tana tsaye a gefensa kamar gunki, ba ta ko kifta ido. ​A waje kuwa Ching Ching tana ta kici-kicin kwacewa daga hannun dakarun da aka sa su tsare ta. Ta duba jikinta ta ga dan ƙurar da ta taɓa ta yayin da Chief ya watsar da ita, nan take ta fashe da kuka. Tana tsaka da kukan ne, sai ta kufce musu... ​Suna tsaka da tattaunawa kan yarjejeniyar da ta kawo su, sai kawai aka ji wani ihu... "Wayyoo!". Kafin fadawa su ankara, Ching Ching ta faɗo cikin fadar tana kuka da ƙarfi, tana nuna jikinta... ​"Me ya sa ya mun datti da jikina? Ya mun datti! Me ya sa ya mun datti?!" Ta faɗa tana shashshekar kuka... ​Sarki Nourdeen ya zabura ya miƙe tsaye, zuciyarsa ta buga ganin autarsa ta shigo falon a daidai lokacin da yake son lallashin Chief Onyx... Ching Ching ba ta bi ta kan Chief ba, ta nufi wurin mahaifinta tana kuka tana nuna Chief da yatsa.. ​"Daddy! Ka ga wannan bokan ko? Ya faɗar ni ƙasi na yi datti! Kuma sai ya mun wanka!" Nan take ta fara kici-kicin cire kayanta a gaban kowa domin a wanke mata dattin. Sarki ya yi saurin rike hannunta, fuskarsa cike da kunya da fargaba yana lallashinta... "Yi hakuri auta, za a yi miki wankan, tsaya kiji..." ​Chief Onyx, wanda ya tsani yawan magana da surutun da ba na hankali ba, ya fara haɗe rai. Jijiyoyin kansa sun tashi, idanunsa suka fara yin ja.. Ya zo ne don muhimmiyar yarjejeniyarsu, amma wannan yarinyar ta zo ta cika masa kunne da surutun banza da na wofi... ​Lokacin da Ching Ching ta ƙara sauti, tana nuna shi tana cewa... "Daddy wallahi sai ka kore shi! In ba boka ba me ya sa zai rufe fuskarsa da karfe?..." ​Chief Onyx ya ɗago kansa, wani irin kallo mai firgitarwa ya watsa mata, kallon da ya sa numfashin kowa a ɗakin ya tsaya... Sannan ya daka mata wata uban tsawa wadda ta girgiza bangon fadar.. ​"SHUT UP!!!" ​Daƙin ya yi tsit. Ching Ching ta tsaya cak, kukan ya dauke, sannan ta zare ido tana kallon Chief Onyx cikin tsananin tsoron da ba ta taɓa ji ba... Bayan ƙatuwar tsawar nan da Chief Onyx ya daka wa Ching Ching, daƙin ya dauki wani irin sanyi.. Sarki Nourdeen ya ji wani zafi ya ziyarci zuciyarsa na yadda aka tsorata masa ɗiyar da yake taƙama da ita, amma sanin cewa mutumin dake gabansa zai iya goge Alhamra a taswirar duniya da yatsa daya, ya sa ya danne zuciyarsa... ​"Chief... yarinya ce fa..." Sarki ya faɗa cikin muryar lallashi.. Ching Ching kuwa tinin ta ɓuya a bayan kujerar sarki.. ​Maimakon Ching Ching ta nutsu, sai ƙiran yarinya da sarki ya yi ya ƙara bata ƙwarin gwiwa... Ta leƙo ta bayan kafaɗar mahaifinta, idanunta suka sarke da na Chief Onyx... Ta fara galla masa harara, tana wani irin jujjuya kwayar idanu cikin raini.. ​"Kai wanene? Kuma me ya kawo ka gidanmu kake yi min tsawa? To wallahi ba zan yi shiru ba! Mugun mutum kawai, mai fuskar karfe! Daddy ka kore shi, yana min kallo kamar zai cinye ni!"... ​Chief Onyx ya ƙara tamƙe fuskarsa, jijiyoyin wuyansa suka fito radau. Bai taɓa tsammanin akwai wata halitta a doron ƙasa da zata iya kallon kwayar idonsa ta faɗa masa maganganu ba tare da tsoro ba. Ya kalli Sarki Nourdeen da idanuwan da suka fara sauya launi... ​"Nourdeen, tarbiyyar ƴaƴanka tana buƙatar gyara," ya faɗa cikin muryar sanyi dake cike da barazana. Ya kawar da kansa gefe guda cikin nuna kyama, kamar ma numfashin yarinyar dake cikin falon na damun sa... "Na ga alama kakkaɓe datti a gidana zai yi wahala idan wannan ita ce kuyangar da zan tafi da ita." ​Jin kalmar mai kakkaɓe datti, ya sa Ching Ching ta harzuka fiye da kowane lokaci... Ta fito fili tazo har gaban Chief Onyx, ta sunkuyo da fuskarta tana kallon cikin kwayar idanunsa dake walkiya... Ta turo bakinta gaba kamar zata masa kiss, ta kumbura kunci kamar mai shirin amai tana masa gatsine da wasu irin kallo, tana jujjuya ƙwayar idon ta... Sannan ta furta.. ​"Ai ba zan yi shiru ba! Don ka ga kana da ƙarfe a fuska sai ka ɗauka kowa tsoronka yake ji? To wallahi ko datti ne a gidanka, kai ne zaka share shi da kanka!..." Ta ɗago tana kallon Sarki ta ce, "Daddy ka ga yadda yake kallo na ko? Kamar bashi na ci? Ko kuma ya taɓa ganina a mafarkinsa ne yake ta faman kallona haka?" ​Sauran fadawa dake tsaye suka duƙa ƙasa, jikinsu na rawa, suna rokon Gimbiya.. "Don Allah Gimbiya kiyi shiru! Don Allah ranta ya dade!" ​Amma ina, Ching Ching sai ma ƙara sautin murya ta yi, tana tafa hannunta.. "Ba zan yi shiru ba! Shi wanene? Ko sarkin aljanu ne shi da ba zai iya magana ba? Sai dai ya yi ta kallon mutane da wadannan idanunsa kamar mujiya?" ​Chief Onyx ya zauna shiru kamar gunki. Idanunsa sun canza launi zuwa wani irin duhu mai tsoratarwa. Ya zura mata ido, yana nazarin wannan yarinyar dake hargitse fuskarta tana masa rashin kunya... A cikin ransa, wani shiri yake tsarawa.. "Zan ga yadda zaki yi wannan surutun a cikin kagarata inda ko iska ba ta motsi ba tare da izinina ba. Zan koya miki ladabi ta yadda ko muryarki ba zaki sake so ki ji ta ba."... Sarki Nourdeen ya janyo Ching Ching ya rufe mata baki da tafin hannunsa, yana rawar jiki.. "Chief, kayi haƙuri... shagwaɓa ce ta yi mata yawa." Onyx ya miƙe tsaye, tsayin sa ya cika falon da wata inuwa mai nauyi, ya nufi hanyar fita ba tare da ya sake tankawa ba... Ganin haka yasa Ching Ching ta ruga da gudu ta sha gabansa. Ganin yadda yake datsa laɓɓansa cikin fushi, sai ta tintsire da dariya... "Wai kai ba ka iya dariya ba ne?" Kafin Gely ko Sarki su ankara, Ching Ching tayi ɗigalgal ta sanya hannayenta biyu ta damƙi laɓɓansa, tana ƙoƙarin shimfiɗa masa su da ƙarfi wai tana koya masa dariya... ​Mutanen dake falon suka daskare, sun zaro idanu waje... Chief Onyx ya ji wani zafi ya turnuƙe shi, ya doke mata hannu... Amma yarinyar nan, cikin tsananin rashin sanin ciwon kai, ta sake kai hannu tana ƙoƙarin cire masa ƙarfen azurfar dake fuskarsa... Wannan ne ya kai Chief maƙura. Ya damƙi siririn hannunta cikin nasa ƙaton hannun, ya yi wani irin fisga ya fara jan ta da ƙarfi kamar ya kama ɓarauniya. ​Ching Ching ta fara ja da baya tana kurma ihu... "Ina za ka kai ni? Ka bar ni a wurin Daddy na! Wallahi ba zan bi ka ba! Mugun mutum mai fuskar ƙarfe! Daddy ka ce ya sake ni!" ​Sarki Nourdeen ya miƙe jikinsa na ɓari ya yo wajen fada tare da faɗin.. "Chief, mun yi yarjejeniyar zan ba ka ɗaya daga cikin gimbiyoyi, amma ba a ce kai za ka zaɓa ba!" Chief Onyx ya yi murmushin raini, yana ƙara damƙe hannunta... "Na zaɓe ta ne a bisa zaɓin raina, ba jiran wacce za a ba ni nake yi ba." ​Duk da tirjiyar da Ching Ching take yi, Chief Onyx ko kallo ba ta ishe shi ba... Ya ja ta yana ratsa filin gidan masarautar har zuwa inda helicopter ɗinsa take jiransa... Iskar injin jirgin tana karkaɗa gashinta dake hargitse, hawaye suna wanke fuskarta amma haka ya loda ta a ciki kamar kayan aiki... Ya watsa mata wani kallo mai nuna cewa.. "Yanzu ne wasan zai fara." ​Sarki Nourdeen ya tsaya daga nesa, idanunsa suna kallon yadda jirgin ke ɗagawa da Gwal ɗinsa... Zuciyarsa tana suya, ga dukkan alamu ya san ya jefa autarsa a cikin ramin da ba shi da tabbas.... ✨ Tun lokacin da Inuwa ya faɗi a filin fada sakamakon harbin doki, numfashinsa ya fita, ya suma a nan take... Master Ibrahim, wanda zuciyarsa ta buga ganin halin da Inuwa yake ciki, bai jira kowa ba ya ɗaga shi ya nufi sashensa da shi... Ya shimfiɗa shi a kan tsararren gadonsa mai laushi, inda ya shiga yi masa treatment cikin gaggawa da kulawa ta musamman... ​Hankalin Ibrahim ya tashi matuƙa. Yana matuƙar ƙaunar Inuwa, ƙauna ce dake rikita masa tunani. Duk da cewa a idonsa namiji ne, amma duk lokacin da yake kusa da shi, yana jin wani irin shauƙi da ya fi karfin abota. Wani irin kishi ne yake ji a ransa.. Baya son ganin Inuwa tare da kowa, mace ko namiji. Idan yana tare da Inuwa, ji yake yi kamar yana tare da mace, amma sai ya kawar da tunanin yana ganin kamar sharrin zuciya ne... ​Bayan ya gama gyara wa Inuwa goshinsa da ya fasa, Ibrahim ya kasa barin ɗakin. Ya kwanta a gefen Inuwa a kan gadon, yana kallon fuskarsa dake cikin bacci. Nan take wani zazzafen ƙamshi ya daki hancinsa, ƙamshi ne mai daɗi, ƙamshin mace mai matsayi da muƙami... Ibrahim ya lumshe ido, ya shafi kansa a ransa ya ce, "Tabbas Inuwa yana da tsafta, wannan ƙamshin na musamman ne." Bai kawo komai a ransa ba game da asalin Inuwa, domin tsantsar tsafta ce kawai ya sani... ​Ba a daɗe ba, baccin gajiya da fargabar abin da ya faru ya kwashe Master Ibrahim a gefen Inuwa. Su biyun suka lula duniyar bacci... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣8️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* A can can nesa da duniyar mutane, a cikin kogon sirri na Power Pool, inda kyan kyan-kkyasan ruwan zinari yake gudana, King Diamond yana zaune a kan karagar sa ta duwatsun lu’u-lu’u. Duk da cewa shi sarkin aljanu ne mai izzah da kwarjini, a yau fuskarsa tana nuna wani irin yanayi da ba a taba ganinsa ba. Farat ɗaya, King Diamond ya dafe ƙirjinsa, zuciyarsa ta buga da wani irin ƙarfi “Duh-duh! Duh-duh!”. A lokacin ne ya ji wani zazzafan ciwo ya raba goshinsa gida biyu, daidai inda Ayat ta ji rauni a filin fada sakamakon harbin doki... Wani irin gumi ne ya lakafo masa. Tun lokacin da suka yi haɗin jini da musanyar rayuwa a bakin kogi, duk wani raɗaɗi da zai taɓa jikin Ayat, tamkar jikinsa aka taɓa. Yana cikin wannan halin, sai wani matashin saurayi mai sanye da fararen kaya na sirri ya bayyano. Shi ne amintaccen abokinsa a duniyar aljanu, Prince Zarith... King Diamond ya ɗaga jajayen idanunsa waɗanda ke walƙiya kamar taurari, ya kalli abokin nasa cikin izzah. “Me ya kawo ka?” ya furta muryarsa tana amo a cikin kogon. Prince Zarith ya matso kusa, idanunsa suna kallon yadda King Diamond yake dafe da goshinsa. “Me kake tunani ne, King? Na ji alamun fargaba a cikin ikonka...” King Diamond ya runtse idonsa, raɗaɗin goshin Ayat yana ƙara ratsa shi. “Uhm...” kawai abin da ya iya faɗa kenan. Zarith ya yi ajiyar zuciya, fuskarsa cike da damuwa.. “Guguwar jarabawa ta uku tana tafe, amma ba ka amfani da ikonka a cikin wannan tafkin don ka ƙarfafa kanka. I’m worried... shi ya sa nake nan.” King Diamond ya buɗe idanunsa, wani irin kwarjini ya bayyana dake sanya kowace halitta durƙusawa... “Why are you worried about me?” ya tambaya cikin sanyi mai cike da mulki. Zarith ya yi murmushin yaƙe, ya san kafiyar abokin nasa. “Ok, all right... So King Diamond, did you try to grab the ancient golden armor? How is it, did you get it?” Wani irin shiru ne ya biyo baya, sai kawai ƙarar ruwan Power Pool dake bugun duwatsu. King Diamond ya kalli nesa, inda yake iya hango duniyar mutane ta cikin ruwan. Ya tuna fuskar Ayat lokacin da ta fito daga ruwan kogi, gashinta a jike, tana masa kallon abokin gaba. “No,” ya amsa a taƙaice. Zarith ya zura masa ido. Ya san ba rashin ƙarfi ne ya sa King Diamond bai ɗauko sulken ba, amma tunanin wata halitta ta daban ne ya shagaltar da shi. “Zuciyarka tana can bakin kogin Alhamra, ko?” Zarith ya yi raɗa, amma King Diamond bai sake furta komai ba. Ya tashi tsaye, doguwar rigarsa tana jan ƙasa. Duk da ciwon da yake ji a goshinsa, izzarsa ba ta ragu ba. A cikin ransa, addu’a yake yi wa Ayat, yana fatan raunin nata bai kai ga inda zai gurgunta masa rayuwar da ya danka a hannunta ba... “Zan tafi,” King Diamond ya furta kafin ya ɓace kamar hayaƙi, ya bar Prince Zarith yana girgiza kai... Tafiyar awanni biyu a cikin jirgin Pavilion ta kasance mafi muni a rayuwar Gimbiya Ching Ching. Tana takure a kusurwar kujera, tana kuka ƙasa-ƙasa yayin da take kallon Chief Onyx wanda ko kallo ba ta ishe shi ba. Shi dai yana latsa na’urorin gabansa, fuskarsa sanye da wannan ƙarfen azurfar da ke ƙara masa ban tsoro... Maimakon ta zauna a mazauninta, Ching Ching ta kwance bel ɗin kujerarta, ta lallaba har bayan kujerar Chief Onyx. Ta maƙale kanta a jikin wuyansa saitin kunnensa, ta fara tura masa harshe tana kuka tana sambatu.. ​"Mugun mutum! Ka mayar da ni gida! Wallahi zan sa kunnenka ya yi ciwo, kuma Daddy na ba zai yafe maka ba!" Ta rinka jan hancinta tana busa masa numfashi a kunne, tana kuka mai taɓa zuciya da kuma tada hankali... ​Duk lokacin da Chief Onyx ya yi ƙoƙarin kawar da kansa, Ching Ching sai ta zagayo ta ɗayan ɓangaren ta cigaba. ​Ta fara shure-shure da ƙafafunta tana dukan kujerar Chief. ​Ta kai hannu ta fara latsa wasu madannai na fasahar jirgin tana cewa, "Ina ne gidan wanka anan? Na ce maka na yi datti Daddy ya ce za a yi min wanka!" ​Chief Onyx ya runtse idanunsa, hannunsa ya dunƙule har jijiyoyinsa suka fito. Wannan ne karon farko da ya ji yana son ya jefa mutum daga jirgi domin ya huta. Gely ta matso kusa, muryarta na na'ura ta ce.. ​"Boss, bugun zuciyarka ya ƙaru da kashi 15%. Ka bani umarni in yi mata allurar bacci".. ​Kafin Chief ya ba da amsa, Ching Ching ta juyo kan Gely, ta harare ta.. "Ke kuma wacece kike wata muryar kwalba? Ki yi min shiru! Kai kuma bokan ƙarfe, ka duba min takalmina ya tsinke!" Ta mika wa Chief Onyx karyayyen takalminta har saitin fuskarsa... ​Chief Onyx ya buɗe idanunsa, ya kalli takalmin, sannan ya kalli fuskar Ching Ching dake cike da hawaye da kuma shagwaba. Ya ga yadda take tura baki kamar mai shirin yin amai. A maimakon ya daka mata tsawa, sai ya ja wani dogon numfashi. Ya gane cewa wannan yarinyar ba tsoro ba ne da ita, kawai tana rayuwa ne a wata duniyar ta daban... ​"Gely," Chief ya ƙira cikin murya mai ƙarfi da ta sa Ching Ching ta ɗan tsagaita da rigimar. "Binciko min sa'ar da za mu isa. Kuma ki tabbatar an shirya mata ɗakin da babu abin da ke cikinsa sai kayan wasa da ruwan wanka, domin wannan rigimar ba za ta ƙare ba har sai mun sauƙa." Yayin da jirgin ya fara rage gudu yana shawagi a sararin saman Pavilion City, hasken lantarki da manyan allunan dijital na birnin suka fara haskowa ta tagogin jirgin. Ching Ching, wadda take ta faman tura baki tana kukan shagwaɓa a kunnen Chief Onyx, ta tsagaita lokaci guda... Ta saki wuyan Chief, ta matsa kusa da tagar jirgin, ta zaro idanu tana kallon dogayen benaye dake tafe da haske da kuma motoci masu shawagi.. "Wau! Daddy ka gani... Oh, na manta ba Daddy," ta faɗa cikin murya mai rauni, sannan ta juyo ta kalli Chief Onyx, "Wannan gidan wasan naku ne? Me ya sa akwai fitilu da yawa haka?" Chief Onyx bai ko kalle ta ba, ya ci gaba da kallon na'urar dake gabansa, amma a ransa ya sauƙe ajiyar zuciya ganin kukan nata ya tsaya... Bayan jirgin ya sauƙa a babban dandalin fadar Pavilion, ƙofar ta buɗe. Gely ta matsa kusa da Ching Ching.. "Gimbiya, mun iso. Da fatan za ki sauƙo cikin lumana." Ching Ching ta kalli ƙasa, ta ga yadda filin yake sheƙi kamar madubi, sannan ta kalli Chief Onyx wanda ya miƙe tsaye yana shirin fita. Ta koma ta zaune daram a kan kujera, ta naɗe hannayenta a ƙirji, ta turo baki gaba tana girgiza kai... "Ba zan sauƙa ba! Na gaya maka takalmina ya tsinke, kuma ƙafata ciwo take yi. Sannan wurin nan akwai ƙura, ba zan ɓata ƙafata ba!" Chief Onyx ya tsaya cak, ya juyo ya kalleta da waɗancan idanunsa masu kwarjini. Ya ga alamar idan ya biye mata, za su iya kwashe sa'o'i a nan. Ba tare da ya ce uffan ba, ya tako har inda take... Kafin Ching Ching ta ankara, Chief ya damƙi kunkuminta ya ɗaga ta sama tamkar ƴar tsana, ya ɗora ta a kan faffaɗan kafaɗarsa... "Wayyo! Ka sauƙe ni! Daddy ka gani ko, sace ni zai yi!" Ching Ching ta fara dukan bayansa da ƙananan hannayenta, tana ihu, yayin da gashinta yake ta karkaɗawa a iska... Chief Onyx bai ko saurari ihun da take yi ba, yana taku cikin izza da gadara.. Dakarun Pavilion dake tsaye layin gaisuwa suka sunkuyar da kai, suna mamakin ganin babban Boss ɗinsu dake kyamar hayaniya ɗauke da wata yarinya dake ta faman buga masa baya tana ihu... Gely tana biye da su a baya, tana lura da yadda bugun zuciyar Boss ɗinta yake, amma abin mamaki, maimakon fushi, sai ta ga yanayin jikinsa yana nuna natsuwa kamar dai wannan rigimar ta Ching Ching tana rage masa nauyin damuwar dake ransa... Anan suka shige mota mai tafiya da kansa ba tare da direba ba, suka nufi can babban site ɗinsa.. Robots ne ke ta kai da komowa, wasu suna shawagi a babban falo.. Yana shirin sauƙe ta, ta ƙanƙame wuyansa, ta ƙame. “Ni ba zan sauƙa ba! Daddy na ya ce in zauna a gidajen sarauta masu kyau, ba gidan aljanu ba!” Tana nan ƙanƙame wuyansa... Chief Onyx bai ko saurareta ba ya jefa ta akan kujera... Cikin muryarsa mai kauri ya ce, “Gely, kwashe wannan abin hayaniyar ki kai ta sashenta. Idan ta ƙara magana, ki sa mata na’urar toshe baki.” Gely ta matso da sauri, ta ɗaga Ching Ching kamar jaririya... “A’a! Ke wacece? Mace ko na’ura? Sakeni! Mugayen mutane, maciya amana!” Ching Ching ta fara dukan ƙirjin Gely, amma kamar tana dukan dutse ne.. Haka aka kaita wani katafaren ɗaki wanda komai na cikinsa fari ne tas. Robots guda biyu suka nufota don su canja mata kaya... “Wayyo Allah! Daddy aljanun sun zo cinye ni!” Ta kwashe da gudu ta shige ƙarƙashin gado, tana kuka... “Wallahi sai na gaya wa Abul! Sai na gaya wa Inuwa ya fasa muku kai!” ✨✨ Washegari da safe Cikin sanyin asuba, hasken rana ya fara kutsa kai ta tagogin sashen Master Ibrahim... Inuwa ta fara motsa yatsun hannunta, goshinta da aka yi wa ɗaurin bandej ya ɗanyi mata zafi. Cikin nauyin idanu ta buɗe su, sai ta tsinci kanta a cikin wani ƙaton gado mai lallausan bargon siliki. Ta juya kanta a hankali, sai idanunta suka sauƙa a kan Master Ibrahim. Yana nan kwance a gefenta, fuskarsa tana kallon tata. Yana bacci cikin kwanciyar hankali, numfashinsa yana fita a hankali. Inuwa ta firgita. “Me ya kawo ni nan? Kuma me ya sa Master Ibrahim yake kwance a kusa da ni?” Ta tambayi kanta cikin fargaba... Ta yi ƙoƙarin tashi.. Ibrahim ya fara motsawa ya buɗe idanunsa waɗanda suka yi jawur saboda rashin bacci. Ganin Inuwa ta tashi, sai ya yi saurin zama, kwayar idonsa tana yawo a kan fuskarta... “Ka tashi?” Ibrahim ya tambaya, muryarsa tana da wani irin sanyi da bai saba ba. “Goshinka ya fashe jiya... na yi maka treatment.” Inuwa ta jinjina kai, tana ƙoƙarin gyara rawaninta da ya ɗan zame... “Na gode, Master. Amma me ya sa ka kwanta a nan? Ai ɗakin dakarunmu daban yake.” Ibrahim ya yi shiru, ya kasa cewa komai. Zai iya gaya mata cewa ya kasa barin ɗakin ne saboda wani irin kishi da yake ji? Zai iya gaya mata cewa ƙamshin jikinta ne ya ruɗa shi? “Babu komai,” ya faɗa tare da kawar da kansa. “Kawai na tsaya ne don in tabbatar ba ka samu matsala ba...Inuwa, me ya sa kake da wata irin siffa daban da sauran maza? Ko fata dake jikinka, ta fi ta maza taushi.” Inuwa ta ji gabanta ya faɗi. Ta san asirinta yana shirin tonu muddin Ibrahim ya ci gaba da bincike. “Master, kawai dai ina kula da kaina ne. Amma yanzu ina bukatar in tafi, ina buƙatar yin sallah...” Ta tashi da sauri za ta fice, sai Ibrahim ya damƙi hannunta. Wani irin shock ne ya ratsa su duka biyun.. Ibrahim ya ji hannun Inuwa yana da santsi da kyan gani, ba hannun soja da ya saba riƙe takobi ba.. “Akwai sirri a tare da kai, Inuwa,” Ibrahim ya furta yana ƙara matse hannun.. “Kuma ba zan bar kowa ya taɓa ka ba, sai ni. Daga yau, duk inda zaka, ina tare da kai. Na riga na nemi izinin Sarki cewa za ka kasance mataimakina na musamman (Personal Assistant).” Inuwa ta zare ido. “PA na musamman? Wannan ai yana nufin zan rinka kwana da tashi ne a karkashin idonsa!” “Amma Master...” “Babu amma! Wannan umarni ne.” Ibrahim ya miƙe, ya matso kusa da ita har tana iya jin bugun zuciyarsa. “Idan wani ya taɓa ka, tamkar ya taɓa ni ne. Kuma na lura, tun lokacin da aka tafi da Gimbiya Ching Ching, kake cikin damuwa. Me ya haɗa ka da ita?” Inuwa ta haɗiye miyau. “Ita... ƙanwata ce a wurin aiki. Ina sonta kamar yadda kowa yake sonta.” Ibrahim ya ji wani kishi ya turnuƙe shi, duk da cewa Inuwa ya ce ƙanwarsa ce... “To ka sani, yanzu ni ne gaba da ita a wurinka. Muje, ka je kayi sallah ..” Suka fito daga sashen, Inuwa tana taku cikin sanyi tana ƙoƙarin ɓoye asalin mace da take da shi, yayin da Ibrahim yake tafiya a gefenta kamar zaki dake kare abincinsa... A can kuryar fada kuwa, Sarki Nourdeen yana zaune shi kaɗai, yana kallon hoton Ching Ching dake hannunsa. Zuciyarsa tana tunanin yarjejeniyar da ya kulla da Chief Onyx. “Ina fatan wannan sakalcin na Ching Ching ba zai sa Chief Onyx ya kashe ta ba,” Sarki ya yi ajiyar zuciya.   ✨✨ Bayan Kwanaki Biyu A yau ne wa’adin hutu da kyan-kkyasan da aka yi wa Ching Ching ya cika. Chief Onyx ya ba da umarnin a kawo ta babban falonsa inda yake gudanar da ayyukansa... Ching Ching ta shigo tana turo baki, sanye da wata riga mai ruwan hoda wadda ta yi mata kyau matuƙa, amma fuskarta babu annuri... Ta iske Chief zaune a kan wata kujera ta alfarma, Gely tana gefensa tana duba wasu hotuna a hologram.. “Daga yau, ke ce zaki rinƙa kula da wannan ɓangaren," Chief ya faɗa ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. “Zaki share, ki goge komai, sannan ki tabbatar babu ƙura ko ɗaya a kan teburina.”.. Ching Ching ta zaro ido, ta kalli hannayenta masu taushi. “Aiki? Ni Gimbiya Ching Ching ce zan yi share-share? To wallahi ba zan yi ba! Ko a gidanmu Daddy bai taɓa ce min in ɗaga tsintsiyar ba. Sai dai in kalli tattai in yi wasa!” Ta zauna a tsakiyar falon ta fasa kuka. “Ni yunwa nake ji! Kuma bana son robots, zuma nake so!” Gely ta matso kusa da ita, “Wannan shi ne umarnin Boss. Idan ba ki yi ba, ba za ki ci abinci ba.” “Ke dakata min!” Ching Ching ta miƙe tsaye tana nuna Gely da yatsa.. “Kinyi tsammanin tsoronki nake ji? Ke dake baki da jini? Kije ki ba ni waje tun kafin in ɓata muku wannan gidan da ihu..!”. Ta nufi teburin Chief, ta ɗauki wata na’ura mai sheƙi tana jujjuya ta. “Wannan meye? Abun wasa ne?” Chief Onyx ya damƙe hannunta cikin fushi... “Stop it! Wannan na’urar tana iya tayar da boma-bomai a duk inda nake so. Leave it!” Ching Ching ta harareshi, ta matso kusa da fuskarsa har tana shaƙar ƙamshinsa.. “Ba zan bari ba! Sai ka fara ba ni zuma ta musamman, sannan ka ba ni izinin in ƙira Daddy a waya. In ba haka ba, wallahi sai na lallata maka wannan ƙarfen dake fuskarka!” Maimakon ya ji tsoro, Chief ya ji wani irin takaici ya ziyarce shi. Yarinyar nan mai shekara 16 amma halinta na ƴar shekara 3 ne... Ya janye hannunsa ya nuna mata ƙofa. “Gely, ba ta aikin da ya fi ƙarfinta. In ba ta gama ba, kada ta fita.” Ya tashi ya bar falon gaba ɗaya.. Daga nan Ching Ching ta fara nata wasan.. Maimakon ta yi sharan, sai ta ɗauki ruwan goge-goge ta rinka fesa wa Gely a jiki tana cewa, “Kema sai na miki wanka, tunda baki da aiki sai goyon bayan Boss ɗin ki ko?!”.. Gely ta fara samun matsala (malfunctioning) Sakamakon ruwan da ya shiga jikinta, tana ta rurruwa. Ching Ching ta tintsire da dariya, ta hau kan kujerar Chief ta fara tsalle-tsalle tana rera waƙar ta... Daƙyar Gely ta samu ta kuɓuce, ta je ta gyara kanta.. Ching Ching ta fara wasan ƴar gala-gala a falon.. Ba ta sani ba, Chief Onyx yana can wani ɗakin yana kallon komai ta allo, yana dafe da kai... “Wace irin bala’i ce wannan Sarki Nourdeen ya bani?” Ya tambayi kansa cikin muryar da ke cike da nuna cewa shagwaɓar Ching Ching ta fara ratsa katangar da ya gina a zuciyarsa... Ching Ching ta ja wani uban ajiyar zuciya, tana kallon babban falon Chief Onyx wanda ya ke kamar filin ƙwallo saboda girma... Sai ga Gely ta shigo, ta ba ta wani mopper mai sulɓi da wani ruwa a gwalba ta ce ta goge teburin cin abinci (dining area) da babban bango na gilashi... “Wannan aikin ai na robots ne, me ya sa za a sa ni?” Ta ɗaka ƙafa tana kukan shagwaɓa, amma Gely ko kallo ba ta ishe ta ba ta fice daga falon... Ching Ching ta fara goge teburin tana tafe tana rera waƙar "Daddy na, Abul na...Ni gimbiya Ching Ching...". Tana kaiwa kusa da wani ƙaton Plasma TV wanda ke manne a jikin bango, wanda girmansa ya ninka nata sau biyar. Allon na musamman ne, domin ta nan ne Chief yake sarrafa dukkan tsaron birnin Pavilion. “Wannan madubin meye a ciki yake ta walƙiya? Ya cika ƙura wallahi!” Ta furta tana turo baki. Ta fesa wannan ruwan goge-gogen har sau biyar a tsakiyar allon. Ta fara gogewa da ƙarfi, tana tura allon da dukkan nauyinta wai ita a dole sai ta fito da kyali... Tana cikin danna allon, sai ta ji ya yi wani ƙara “Ƙararasss!”... Ashe screws ɗin da suka riƙe allon a jikin bangon fasahar zamani ne, kuma sun samu matsala saboda ruwan da ta fesa ya shiga jikinsu. Kafin ta ankara, allon ya fara sillo wa ƙasa... “Wayyo Allah! Zai faɗo!” Ching Ching ta fasa ihu, maimakon ta matsa, sai ta tsaya tana kallon yadda ƙaton allon ya silalo ƙasa “BAMMM!!!”... Falon ya ɗauki wata irin ƙara, hasken lantarki ya fara walƙiya a wurin yana sparks... Nan take duk wani haske na falon ya ɗauke, ya koma jajir, muryar na’ura ta fara ƙiran “Security Breach! System Failure!” Ching Ching ta fice da gudu ta nufi bayan kujerar Chief ta maƙale, tana kuka sosai... “Ba ni bace! Wallahi madubin ne ya gaji da zama a jikin bango ya faɗo da kansa! Daddy na!” Chief Onyx ya shigo falon a guje, ransa ya kai maƙura wajen ɓaci. Ya kalli tarkacen allon da ya watse, ya kalli Ching Ching dake leƙowa ta bayan kujera, idanunta sunyi zuru-zuru... “Do you have any idea what you just did?!” Ya daka mata wata uban tsawa wadda ta sanya ta kusan sakin fitsari a wando... “Kin kashe dukkan na’urorin tsaro na Pavilion! Wannan ba madubi ba ne, wannan shi ne zuciyar birnin nan!” Ching Ching ta fashe da kukan gaske, ta tunkaro shi tana shure-shure. “To meye nawa? Me ya sa ka sanya shi a inda hannuna zai kai? Kuma ma ai datti ne da shi shi yasa na goge shi. Wallahi sai na faɗa wa Daddy ka mare ni!” “Ban mare ki ba!” Chief ya faɗa yana ƙoƙarin danne fushinsa, domin idan ya biye wa yarinyar nan zai iya hauka... “Kuma ma ni yunwa nake ji! Ka ba ni abinci mai daɗi, sannan ka share wannan dattin da kanka, tunda kai ne ka ajiye shi a nan!” Ta ƙarasa maganar tana gyara zamanta a kan kujerar tasa ta mulki, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kuka tana kallon gefe. Chief Onyx ya tsaya yana kallonta, ya rasa ko kuka zai yi ko dariya. Yarinyar tana komai kamar jaririya... Ya juya ya kalli Gely wadda ta shigo tana ƙoƙarin gyara allon. “Gely, share wurin nan. Sannan ki ba ta zuma da duk abin da take so kafin ta rusa gidan nan baki ɗaya.” Yana fita, Ching Ching ta leƙo ta kalli bayan sa, ta galla masa harara. “Mai fuskar ƙarfe! Ka dai ji tsorona ne shi yasa ka ce a ba ni zuma.”... ✨ Bayan kwana biyu da farfasa babban allon Pavilion, Chief Onyx ya fahimci cewa idan ya bar Ching Ching da aikin ruwan goge-goge, to lallai za ta ruguza masa fada baki ɗaya. Don haka, ya yanke shawarar sanya ta a gaba ya koya mata yadda ake sarrafa computer, ko koda akalla ta rinƙa taɓa ƙananan ayyuka na ofis. Chief yana zaune a kan babban teburinsa, ya sanya aka kawo wa Ching Ching wata computer ta zamani mai nuna Holographic Tablet... "Zauna a nan," ya faɗa cikin muryarsa dake nuna gajiya da rigimarta... "Zan nuna miki yadda ake lissafa yawan energy da Pavilion take amfani da shi. Karki taɓa komai sai abin da na faɗa miki." Ching Ching ta turo baki, tana wasa da yatsun ƙafarta. "Ni fa Daddyna ya ce in tafi makarantar sarakuna ne, ba makarantar kafintan kwamfuta ba. Wannan abin gashi nan kamar madubin aljanu." "Just listen!" Chief ya daka mata tsawa kaɗan. Ya fara bayani.. "Wannan lambar ita ce X-40, idan kika taɓa ta..." Ching Ching ta kalle shi, maimakon ta kalli abin da yake nunawa, sai ta ƙura wa fuskar sa ta karfe ido... "Wai kai bakinka baya ciwo idan kana magana ne? Kuma idan za ka yi hamma ya kake yi? Ko har yanzu baka taɓa yin hamma ba?" Chief ya rufe idonsa, ya ƙirga ɗaya zuwa goma a ransa don kada ya shaƙe ta. "Ching Ching, kalli screen ɗin!" "To na kalla!" Ta fada tana kumbura kunci. Ya juya kansa don ya amsa ƙiran Gely, ashe tuni Ching Ching ta karkata akalar kwamfutar. Maimakon ta yi lissafin makamashi, sai ta fara zana hoton wata katuwar ƴar tsana mai babban kai da kananan ƙafafu. Ta sanya wa yar tsanar dogon gashi mai ruwan hoda, sannan ta rubuta "MUGUN BOKA" a ƙasan hoton, tana nuna kibiya zuwa wurin da Chief yake zaune... "Kaga yadda nayi kyau?" Ta tura masa screen ɗin gaban fuskarsa. Chief Onyx ya kalli hoton, ya kalli rubutun "MUGUN BOKA", sannan ya kalli Ching Ching wadda take faman washe masa haƙora tana jiran yabo... "Kin share dukkan bayanan tsaron da na dauki shekara biyar ina tsarawa... kin mayar da su hoton yar tsana?" Muryarsa ta fara rawa saboda fushi... "To ai ƴar tsanar tafi wannan lambobin naka kyau. Duba fa kaga, har hanci na sanya mata mai tsayi, ba irin naka na ƙarfe ba." Ta tintsire da dariya tana tafa hannu... Chief ya tashi tsaye, ya fizge kwamfutar... "Gely! Kwashe ta! Kai ta ɗakin girki, ta rinƙa peeling ɗin dankali da karas. Tunda ba ta da hankalin yin aikin ofis, bari ta yi aikin masu abinci!" Ching Ching ta zabura ta dire daga kan kujera... "Pelling? Ni Gimbiya Ching Ching zan yi yanka? To wallahi ko danyen dankalin sai na cinye shi duka na barku da yunwa!!..." Tana fita tana kunkuni, Chief ya koma ya zauna, ya dafe kansa. Ya rasa me ya sa duk rashin kunyar da take masa, baya iya sanya sojoji su yi mata horo mai tsanani. Akwai wani abu game da shagwaɓar tata da yake sanya shi jin kamar fushinsa bashi da tasiri... A can kicin kuwa, Ching Ching ta samu dankali guda dari a gaba. Ta kalli babban robot din kicin ɗin, ta harare shi. "Kai ma kallo na kake yi ne? To maza ka fara yankan nan, ni zan zauna in rinƙa kallon yadda kake yi, tunda Daddy na ya ce kowa ya bauta min!".. Ta jawo kujera ta zauna, ta ɗauki dankali ɗaya ta fara wasan kwallon ƙafa da shi a cikin kicin ɗin, tana ihu... "Gool!!! Na ci bokan Pavilion gool!!!".... ✨ Bayan kwana ɗaya... A cikin babban ɗakin bincike na Pavilion (The Science Lab), Gely tana tsaye a jikin wata na’ura tana loda bayanai... Wannan shi ne lokacin da Gely take tsit, ba ta motsi kamar gunki... Ching Ching ta shigo ɗakin sanda-sanda, hannunta riƙe da wata ƙatuwar waya screwdriver wadda ta sato a wurin bincike tana gyara, da kuma wata ’yar ƙaramar na’urar wasa da aka aiko mata daga Alhamra mai kukan dabbobi... "Yau dai kin shigo hannu, ke wannan robot mai baƙar siffa," Ching Ching ta raɗa a hankali tana turo baki... "Kin cika takura min, kowace asuba sai kin zo kin tada ni da wannan muryar taki kamar na tsuntsun karfe. Yau kuma muryar kaza zan sanya miki, don ki rinƙa kukan kakarakaaa idan gari ya waye...!" Ching Ching ta zagaya bayan wuyan Gely, inda ta ga wasu ƙananan ƙofofin lantarki. Ta fara kici-kicin buɗewa da wayar hannunta. Cikin sa’a, ta latsa wani wurin da aka rubuta “Voice Output Module”... "Ina kike ne? Eh, ga ta nan!" Ta ciro wasu wayoyi guda biyu ta haɗa su da na’urar wasan tata mai kukan kaza. A dai-dai wannan lokacin, Chief Onyx yana can ofis ɗinsa tare da wasu manyan baƙi daga ƙasashen Turai waɗanda suka zo tattaunawa kan tsaron duniya... "Chief, muna buƙatar jin bayanan tsaro daga bakin Gely," in ji ɗaya daga cikin baƙin. Chief ya latsa agogonsa, "Gely, zo ofis yanzu, kuma ki ba mu rahoto kan matakin tsaron Pavilion." A can ɗakin bincike, idanun Gely suka kawo hasken ja, alamar ta tashi daga bacci. Amma Ching Ching ba ta gama haɗa wayoyin ba! "Wayyo! Ta tashi!" Ching Ching ta tura wayoyin da ƙarfi ta danna su da gam, sannan ta gudu ta ɓuya a bayan labule. Gely ta nufi ofishin Chief da takunta na ƙarfe tak-tak-tak. Ta shiga ofishin, ta tsaya a gaban Chief da baƙin nasa.. "Yes, Boss. Gely is ready," Gely ta buɗe baki za ta yi bayani... Maimakon muryar na'ura mai sanyi, sai aka ji.. "Kakarakaaaaaa! Ƙuƙuruƙuuuuuu!" Baƙin Turawan suka zabura suka miƙe tsaye. Chief Onyx ya zaro ido, ya kalli Gely cikin mamaki... "Gely, me kike yi? I said give us the security report!" Gely ta sake buɗe baki tana ƙoƙarin cewa "Status Secure," amma sai aka ji.. "Kaza-kaza-kaza! Ƙuƙu-ƙuƙu-ƙuƙu!" Ɗaya daga cikin baƙin ya fashe da dariya... "Chief, shin wannan sabon salon tsaro ne? Ko kuma robot ɗinka ta koma gidan gona?" Chief Onyx ya ji fuskarsa ta yi zafi, jijiyoyin kansa suka tashi. Ya san ba kowa ya yi wannan aikin ba sai bala'in da yazo da ita daga Alhamra... "Gely! Shut down immediately!" ya daka mata tsawa... Gely ta yi shiru, amma kafin ta mutu baki ɗaya, sai na'urar ta buga.. "Meeeee-meeee! Baaaaa-baaaa!" kukan akuya... Chief ya fice daga ofis ɗin ransa a ɓace, ya nufi inda ya san Ching Ching take ɓuye. Ya tarar da ita a bayan labule, tana ta murna tana tafa hannu... Tana faɗin "Kin ga yadda ta zama kaza? Gobe idan ta zo tada ni kukan asuba, sai in yanka ta in sanya a miya!" Ta tintsire da dariya... Sai ga Chief ya ɗaga labulen... Chief Onyx ya matso kusa da ita, ya daka mata wata uban tsawa... "CHING CHING! Kin san kuɗin da na kashe wajen ƙera Gely? Kin sanya ta zama abin dariya a gaban baƙina!"... Ching Ching ta turo baki, ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka.... "To ni meye nawa? Ai dama cewa kake yi ita mace ce, ni kuma na ga ba ta iya kukan mata ba shi ya sa na koya mata kukan kaza, ai duk kukan mata ne!" Chief ya dafe kai, ya zauna a ƙasan carpet, abun da bai taɓa yi a rayuwarsa ba, zama a ƙasa.... "Wace irin yarinya ce ke? Ba kya jin magana? Ba kya jin tsoro? Ba kya jin kunya?" Ching Ching ta matso ta zauna a kusa da shi, ta kalli fuskarsa... "Bana jin komai sai yunwa. Kuma ka sani, idan ba ka gyara mata murya ta rinƙa waƙar Alhamra ba, gobe kukan kare zan sanya mata, ta rinka cizon mutane!"... Chief ya kalle ta, ya ga yadda idanunta suke walƙiya da yarinta da rashin sanin ciwon kai. A karon farko, maimakon ya mare ta ko ya daka mata tsawa, sai ya tsinci kansa da yin murmushi a ɓoye a ƙarƙashin fuskarsa ta ƙarfe... "Zan ba ki zuma gora guda, amma da sharaɗi ɗaya..." "Meye?" ta tambaya tana washe haƙora. "Kada ki sake taɓa kowace na'ura a Pavilion ba tare da izini na ba." Ching Ching ta yi saurin jinjina kai, tana tunanin “Ai ban ce ba zan taɓa motar ka ba, na’ura kawai ka faɗa!” 😂.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣9️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* A ko wace rana, Ayat ta sai tayi kukan da ba ta san lokacin gamawarsa ba... Zuciyarta tana mata zafi tamkar an watsa mata garwashin wuta... Ta ci gaba da maganar zuci tana kuka.. "Ta yaya Abul zai yi haka? Me Chingching ta sani a rayuwa? Za ta je ta zama baiwar wani a matsayinta na gimbiya kuma auta mai ƙaramar shekaru? Shekararta nawa wadda ba ta fi 16 ba? Haba don Allah, me ya sa Abul zai yi mana haka? Me ya sa sai Chingching? Ga ni, ga Maayah, ga Yumna, ga Zayana... me ya sa sai ita wadda ba ta iya komai ba sai shagwaɓa?".... Kwananta biyu a bata leƙo falonta ba, sannan bata fita wurin aikin tsaro ba a matsayinta na PA Ibrahim.. Tana cikin wannan halin ta ji ƙarar ƙararrawar ɗakinta na tashi. Ta san cewa ba za a bar ta ta ci gaba da zama a haka ba. Ta tashi da kyar, ta murɗa key ta buɗe ƙofar da ta daɗe a rufe tun shekaran jiya... Uma Saratu, uwar ɗakinta mai kula da ita, ta shigo cikin gaggawa da damuwa... "Gimbiya lafiya kuwa? Tun kwana uku ake zuwa dubaki amma kin ƙi buɗe ƙofa. Anyi-anyi har an sanar da sarki cewa kin kulle kanki a ɗaki tun safe... Shima kuma yana fama da alhinin rashin autarsa.".. Ayat, ko a wannan yanayin, ba ta rage izzah da kwarjininta ba. Ta kalli Uma Saratu ta ce.. "Kun san yana cikin alhini, kuma kuka sanar masa batu na?" Uma Saratu ta yi ajiyar zuciya, "To ai munga ba lafiya ba. Yanzu fa magariba ake shirin ƙira, kuma tun bayan kwana uku aka ji ki shiru. Ba ci, ba sha, ba walwala..." Ayat ta ɗan ɗaure fuska, "Bai kamata kowane abu kuna sanar wa sarki ba. Tunda kun san ina ciki, buɗewa ne ban yi ba, meye amfanin sanar masa?" "Gimbiya, rai da mutuwa ai ba sa haɗuwa," in ji Uma Saratu cikin rarrashi. "Idan da rai ai ba mu sani ba ko kina halin rashin lafiya." A lokacin ne Ayat ta kalli Uma Saratu da idanunta waɗanda suka yi jawur saboda kukan da ta sha... Uma Saratu ta tsorata, "Lafiya kuwa Gimbiya? Ya idanuwanki suka yi jawur haka kamar wuta? Kuka kika yi ne?".. Ayat ta kasa boyewa, ta furta.. "Ƙanwata ta tafi, ya zan yi da rayuwata?" Uma Saratu ta yi mamaki, "Amma ta yaya kika san cewa Chingching ba ta nan alhalin kina kulle a ɗaki?" Ayat ta ce, "Tin ranar da sarki ya ƙira mu fada yake sanar mana, nasan kinsan da hakan. Hakan ya sa na kulle kaina a ɗaki, ba na son damuwar kowa.".. Uma Saratu ta ji tausayin gimbiyar tata sosai, ta yi mata fatan alheri tare da tabbatar mata cewa kanwar tata za ta dawo lafiya... Ayat ta buƙaci a haɗa mata ruwan wanka domin ta wanke damuwar dake jikinta. Lokacin da Uma Saratu ta yi kokarin tilasta mata ta fara cin abinci, Ayat ta nuna fushinta.. "Haba Uma Saratu, me ya sa kuke jayayya da ni ne? Idan na ce a min abu kaza sai ku ce a'a. Shin haka ake yi wa sauran gimbiyoyin ne?" Cikin sauri Uma Saratu ta ba da hakuri, ta shiga haɗa mata ruwan wanka tare da fesa turaruka masu sanyaya rai a ko'ina a cikin bedroom ɗin don gyara yanayin dakin... ✨ A ɗayan ɓangaren masarautar, Gimbiya Maayah tana zaune a cikin katafaren falonta... Kwakwalwarta tana cike da tunani guda biyu, na farko, yadda za ta sake haɗuwa da kyakkyawan jami'in tsaron nan, Inuwa, wanda ya tafi da tunaninta. Na biyu kuma, tana nazarin me ya sa za'a bada Ching Ching a masarautar pavilion?. Duk da ba ta taɓa ganin Chief Onyx ba, labarin kwarjininsa da ƙarfin mulkinsa ya isa ya sanya kowa fargaba... Duk kwana biyun nan basu san da cewa an riga an tafi da Ching Ching ba domin hatta ma'aikatansu ba komai suke sani game da masarautar ba... Gashi yau har mako guda da faruwar haka amma banda Ayat babu wanda ya sani a cikin gimbiyoyi... Tana zaune ta ƙura wa plasma ɗinta ido, amma ba kallon take yi ba, tunani ne ya yi mata yawa. Mama Liyatu, uwar ɗakinta, ta shigo falon a guje, fuskarta cike da tashin hankali... "Gimbiya Maayah mun shiga uku!" ta faɗa cikin rawar murya... Maayah ta juyo a slow cikin fushi, ta katse ta cikin gadara.. "Kin shiga uku dai ke kaɗai! Amma kada ki sake sako Maayah a cikin shiga uku, na gaya miki. Faɗi abin da za ki faɗa.".. Mama Liyatu ta sunkuya, "Allah ya ba ki haƙuri. Amma na zo na sanar da ke cewa Sarkin Pavilion ya tafi da Auta Chingching a matsayin baiwarsa."... Maayah ta zaro ido cikin mamaki na ɗan lokaci, "What?! Shi sarki yana ina aka yi hakan?" "Sarki yana wurin amma bai iya cewa komai ba," in ji Mama Liyatu... Maimakon Maayah ta nuna damuwa ko tausayi ga ƙanwarta, sai ta ɗaga kafaɗa cikin ko-o-ho ta ce.. "Alright. Shi sarki bai iya cewa komai ba, to ni me zan yi a kai? Yanzu dai sarki ya nuna cewa kwarjinin da yake da shi ya tashi a aiki ke nan, tunda har zai ji fargabar tunkarar Sarkin Pavilion har ya iya tafiya masa da ɗiya a matsayin Maid. To lallai wannan sarautar ta faɗi ƙasa!" Ta kalli Mama Liyatu cikin ƙasƙanci, "Kinga Mama Liyatu, ba na son damuwa. Ki tashi ki ba ni wuri." Mama Liyatu ta miƙe jiki a sanyaye ta bar falon, tana mamakin irin zuciyar Maayah. Ita kuwa Maayah, tana ganin ta fita, ta ci gaba da kallon Plasman ta, ta kawar da zancen Chingching daga ranta kamar ba abin da ya faru, burinta kawai shi ne yadda za ta sake ganin Inuwa... ✨ A cikin daren nan, a ɗayan bangaren sashen gimbiya Yumna... Wata matashiyar ma'aikaciya siririya wacce aka fi sani da 'Yar mitsila tana gudu tana cilla sirarrun sawayenta a guje... Ta bankaɗo babban ƙofar falon tana kwala ƙira cikin ɗakin... "Gimbiyata Yumna! Gimbiyata Yumna!! Gimbiyata Yumna kina inaaaa?..." Ba tare da jiran izini ba, ta haura saman bedroom ɗin Yumna ta tura kofar ta shige. Tana shiga ta tarar da Gimbiya Yumna a kan sallaya tana sallah... 'Yar mitsila ta samu wuri ta zauna zaman jiran ta, tana haki... Yumna ta idar da sallar, ta ɗaga hannu ta yi addu’o’i, sannan ta shafa fuskarta.. Ta juyo tana murmushi duk da cewa ƙiran Ƴar mitsila ya ɗan tsorata ta, ta ce.. " 'Yar mitsila, dodo ne ya koro ki ko ya ya?" 'Yar mitsila ta gyara zama, "Labari da ɗumi-ɗuminsa nazo miki da shi! Nima sai yanzu nake tsintar labarin nace da dukkan alamu baki sani ba, bari nazo in shafa miki..." Yumna ta yi dariya, "Shafa min naji kawataaaa..." 'Yar mitsila ta fara zayyano mata.. "Wai wani sarki ne mai kwarjinin bala'i ne ya ziyarto cikin masarautar nan. Ban ganshi ba amma ance da na ganshi to zan yi sumar tsaye! Kaiii Aradu ya ninka sarki kyan yanayi, ko dan shi ɗin ɗan matashin saurayi ne oho..." Yumna ta ce "To pah, wani irin sarki ne haka? Sarkin ina ne?" 'Yar mitsila ta yamutsa fuska tana kokarin tuno sunan, "Aradu ni ban riƙe sunan ba amma dai kamar Sarkin Pa, Pa, Pabi... Pabimila... ko dai Pabiliya? Yawwa yawwa Pabiliya!" Yumna ta yi murmushi, "Wai Sarkin Pavilion kike nufi?" 'Yar mitsila ta zabura, "Yauwa ehhh shiii!" Yumna ta yi salati, "Subhanallahi! Me ya kawo shi kuma? Shi da na ji labarin duk sanda ya zo masarautar nan to yaƙi ne zai tashi, innalillahi..." Ta nuna kamar bata san shi ba...balle ta nuna sun san juna... 'Yar mitsila ta karkaɗe hannu, "To yanzu dai ba yaƙin bane. Ya zo ya cicciɓi autarku Chingching ya tafi da ita, wai zai mayar da ita bazawararsa!" Yumna ta dafe ƙirji tana zaro ido cikin gigita, "Yaaa ALLAH! Bazawara kuma? Ya tafi da ita?" 'Yar mitsila ta ci gaba da zugawa, "Ahh to! Ance saurayi ne bai taɓa yin aure ba, kuma ya zo ya ɗauki yarinya to me kenan? Kumaaa ance mace da namiji in sun haɗu shaidan ne a tsakiya... to kinga bazawara kenan zai mayar da ita, kuma ya fake da wai wai wai 'yar aikinsa..." Hawaye suka cika idanun Yumna, ta dakatar da 'Yar mitsila cikin rawar murya.. "Kinga ya isa haka! Wannan ba labari mai daɗi ba ne ai. Kuma ki daina cewa zai mayar da ita bazawara, ba haka ba ne a ransa. Shi fa na ji labarin dan uwanmu ne, ba zai cutar da ita ba... kawai ki tashi ki tafi, zan yi addu'a.".. 'Yar mitsila ta miƙe tana ƙunƙuni, "Ah to! Yanzu ai ba'a maganar ɗan uwantaka, shaiɗan ba ruwansa da wannan..." Daga nan ta fice daga ɗakin... Tana fita, Yumna ta fara wasu zafafan hawaye, tana tausayin 'yar kanwarsu Chingching da aka kai wata duniya daban... Ta wani ɓangaren kuma tana ganin ai duk jini ɗaya ne, kuma tana da yaƙini akan Yayanta, zai kula da ita sosai.. ✨ A cikin sashen Gimbiya Zayana, komai a gyare yake tamkar kana cikin birnin Sydney... Zayana tana zaune a kan kafet mai laushi tare da ɗiyarta Mimi, tana koya mata rubutu. Zayana na sanye da riga marar nauyi, gashinta ruwan zinare ya bazu a bayanta.. Suna tsaka da hakan, wata baiwar part ɗin ta shigo tana haki, ta durƙusa a gabansu tana ƙoƙarin daidaita numfashinta don faɗin labarin da ya firgita masarautar... Mimi, ganin ma’aikaciyar ta kasa magana sai haki take, sai ta ɗauki kofin ruwan juice ɗin da suke sha, ba tare da wata fargaba ba, ta watsa wa matar a fuska.. Baiwar ta zabura ta dafe fuskarta, ruwan lemon yana ɗiga daga jikinta. Zayana ta kalli Mimi da idanunta masu kalar na kyanwa (cat eyes), ta tambaye ta cikin yaren Turanci.. "What did you do that for?" Mimi ta turo baki, cikin muryar yara mai cike da raini ta amsa da Hausa.. "Naga ta ƙi nutsuwa ne shi yasa na watsa mata lemon." Maimakon Zayana ta tsawatar mata, sai kawai ta yi murmushin jin daɗi, tana jin daɗin yadda Mimi take nuna gadara. Ta kalli baiwar ta ce, "Lafiya?" Baiwar ta share fuskarta, muryarta na rawa ta ce, "Chief Onyx ne ya tafi da Chingching can yankinsa a matsayin baiwarsa." Zayana ta gyara zama, fuskarta a washe da annuri, "Hakan ya min daɗi sosai! Ashe ba maganar yaƙi ne ya kawo shi ba?. Let me call my mom, zan sanar da ita kayataccen albishir, ta sauƙe makamanta kawai tunda ba matsayina aka taɓa ba." A wajen Zayana, damuwar kanwarta ba komai ba ce, muddin ita tana cikin ƙoshin lafiya, to komai ya tafi yadda ake so... Ta kori matar da hannu, amma matar na shirin tashi, Zayana ta daka mata tsawa... "Ke ƙazama! Haka zaki bar min wannan jikar ruwan juice ɗin da aka watsa miki a wurin?" Matar ta koma da sauri, ta cire dankwalinta ta fara gogewa tana kuka kasa-kasa. Tana gamawa ta gyara wurin tas, Mimi ta kalli fuskarta, sai ta sake dauko ragowar juice ɗin dake cikin kofin, ta sake karkaɗe shi a dai-dai inda matar ta gama gogewa... Mimi ta yi dariya tana nuna matar da yatsa, "Ki sake gogewa, har yanzu akwai datti." Zayana ta saki wata 'yar dariya mai sauti tana kallon yadda matar take ƙara ninkewa tana goge wurin cikin kaskanci... "Goge da kyau ƙazama, sannan ki ɓace mana da gani kafin na sa a miki hukunci," in ji Zayana... Matar ta gama tana karkarwa ta fice, yayin da Zayana ta dauki wayarta don kiran mahaifiyarta Ruma, tana farincikin cewa rigimar Pavilion ba za ta shafe ta ba tunda an tafi da Chingching... ✨ A duniyar King Diamond ganin abokinsa Prince Zarith ya fara magana akan golden armor, hakan yasa ya ƙudiri cewa zai je ya ɗauko duk da wurin na da haɗari... Ya bayyana a gaban ƙofar kogon, idanunsa na haske da jarunta duk da cewa ya san tsafe-tsafe ne ke gadin wurin. Masu gadin, ba mutane ba ne, wasu halittu ne masu siffar dabba amma da ran aljanu suka far masa lokaci guda... Diamond bai yi ƙasa a gwiwa ba. Da dantsensa mai ƙarfi ya riƙo takobinsa da ya bayyana cikin iska.. Lokaci guda ya dinga raba kawunansu, jini na fantsama a jikin bango.. Kowane sara ɗaya, mutuwa ɗaya. Bayan dogon faɗa da ya bar shi da fuskarsa cike da jini da gumi, ya yi nasarar kawar da su gaba ɗaya.. A tsakiyar ɗakin, can bisa wani dakalin dutse, Golden Armor yana sheƙi, yana haskaka duhun kogon.. Diamond ya taka a hankali, ko da yake numfashinsa na fita da sauri saboda gajiya. Ya sa hannu ya damƙi armor... A take, wata irin tsawa ta ratsa kogon. Cire sulkun daga inda yake ya zama silar rugujewar duk tsafin da ke riƙe da dutsen kogon.. Ƙasan kogon ya fara tsagewa, manyan duwatsu daga silin ɗin kogon suka fara fadowa. Diamond ya yi ƙoƙarin tsallakawa waje, amma babban dutse ya daki kafaɗarsa, ya ji ƙarar karyewar ƙashi. Kafin ya kai ga fita, sauran silin ɗin wurin ya rufo kansa da wani irin mugun ƙarfi... Ƙura ta turniƙe wurin, ƙarar rushewar ta cika dajin. King Diamond ya ɓace a cikin baraguzan duwatsun, rungume da Golden Armor, yayin da jini ke malala daga raunukan da ya ji. Shiru ya biyo baya, sai hayaki da ƙurar duwatsun da suka binne shi.... ✨ Maayah tana tsaye a gaban babban madubi a ɗakin shiryawarta. Ta sanya kayan makarantar amma nata ya sha bamban da na kowa, an ɗinka shi da wani tsadadden yadi mai sheki, an goge shi ya fito da layin guga raɗau. Tana sanye da farar riga, kyakkyawa mai dogon hannu, da pleated red skirt wanda ya tsaya daidai gwiwarta. Ta ɗaure gashinta wanda aka sanya masa wani ribbon na alfarma mai kalar zinare... Da haka take barin gashin ba rufe wa, a makarantar ba'a saka hijab, akwai jar hula mai kalar skirt wanda aka tanada wa musulmai, Christian kuma babu komai, itama Maayah bata wani sanya hula, lokaci lokaci take sakawa... Tana sanye da takalman fata baƙaƙe masu sheki (designer loafers) da safa fara tass. Kamshin turarenta ya cika ko’ina, kamshi ne mai karfin da ke nuna cewa na masu kuɗi ne. Ta rataya karamar jakar makarantar ta a kafada ɗaya, fuskarta babu ko murmushi, sai wani kallo na rainin wayo... Tana fitowa daga sashenta, bayi da hadimai kowa sai sunkuyar da kai yake yi. Ba ta ko kallon gefen kowa. A harabar fadar, jerin motoci biyar bakake (Black SUVs) suna jiran ta, kofofin a buɗe. Tana shiga daya daga ciki, motocin suka lula zuwa makaranta... Kamar kullum, isar Maayah makaranta tamkar isar wata shugabar ƙasa ce.. Motocin suka raba tsakiyar makarantar, dalibai suka tsaya suna kallo. Da zarar motar ta tsaya, bodyguards hudu sanye da bakaken kaya da bakaken tabarau suka fito da sauri. Ɗaya ya buɗe mata ƙofa, ya kare mata kai... Maayah ta fito daga motar cikin taƙama. Ta tsaya na sakanni kaɗan, ta gyara tsayuwar jakarta, sannan ta sanya baƙi tabarau. Ta fara tafiya, bodyguards biyu a bayanta, biyu kuma a gaba suna share mata hanya... Ɗaliban da ke magana duk suka yi tsit. Waɗanda ke wasa suka dakata. Duk wanda idonsa ya sarƙe da nata, sai ya saurin kawar da kai don tsoron kar ta ce yana kallonta da yawa.. Tana tafiya ne kamar ba ta san taka ƙasi. Ta isa corridor din ajinsu, sai ga Hafsat yar President ta taho da sauri da fara’a.. "Good morning Maayah! Kin zo yau da wuri." Maayah ta tsaya, ta rage tsayin tabarunta kaɗan ta kalli Hafsat, sannan ta gyaɗa kai kawai ba tare da ta ce komai ba... "Hafsat, ki tabbata kinyi min ajiyar bayanan darasin farko, ba na son surutu yau," abin da Maayah ta faɗa kenan cikin muryar isa, sannan ta wuce ta bar Hafsat a tsaye tana murmushin ƙarfin hali... Maayah ta zauna a mazauninta na musamman wanda babu wanda ya isa ya taɓa. Malamin lissafi ya shigo, amma ko kallonsa ba ta yi ba, ta buɗe littafinta tana dubawa. Ko da malamin zai yi tambaya, baya kallon bangarenta don gudun ɓacin ranta, domin kowa ya sani, Maayah ba ɗaliba ba ce kawai, ita Gimbiya ce wacce dokar makaranta ba ta hau kanta yadda ta hau kan kowa ba... An shiga darasin English Literature. Sai dai a wannan karon, ba tsohon malamin da aka saba gani ba ne ya shigo, sai wani sabon malami, Mr. Collins, wanda ya fito daga ƙasar waje kuma bai san matsayin Maayah ba sosai... Maayah tana zaune, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana danna wayarta ta iPhone, abin da aka haramta wa kowane ɗalibi a makarantar. Mr. Collins ya tsaya a gaban aji, ya kalli kowa sannan idonsa ya sauƙa kan Maayah. Ya murtuƙe fuska... "Ke kuma wace ce? Kuma me ya sa kike danna waya a lokacin darasi na? Ajiye wayar nan yanzu ki tashi tsaye!"... Aji ya yi tsit. Sauran ɗaliban har da Hafsat suka fara zare ido, wasu suna kallon juna cikin fargaba. Maayah ba ta ko ɗaga kai ba, balle ta nuna ta ji me yake faɗa. Ta ci gaba da abin da take yi... Mr. Collins ya fusata, ya taka har gaban teburinta, ya buga teburin da ƙarfi... "Ba da ke nake ba? Na ce ki ba ni wayar nan kuma ki fice daga ajina!" A hankali, Maayah ta ajiye wayar akan teburin. Ta ɗago kanta a hankali, idanunta cike da izzah da wani irin kallo na rainin wayo da isa. Ba tare da ta tashi tsaye ba, sai ma ƙara gyara zama da ta yi... "Shin ka san wacece kake yi wa ihu?" Maayah ta tambaya cikin sanyin murya mai cike da kwarjini da barazana... Mr. Collins ya nuna ta da yatsa, "Ban damu da ko wace ce ke ba! A nan, ni ne malami, ke kuma ɗaliba ce. Fita waje!" Maayah ta yi ɗan gajeren murmushi na mugunta, sannan ta yi wa ɗaya daga cikin bodyguards ɗinta da ke tsaye a bakin ƙofar aji alama da yatsa... Nan take bodyguard ɗin ya shigo ciki cikin takunsa na ƙasaita. Maayah ta kalli malamin, ta ce. "Ba na son ganin fuskarsa a cikin wannan makarantar nan da minti biyar. Kuma ka gaya wa shugaban makaranta ya neme ni don ya ba ni haƙuri akan wannan ɓata lokacin da aka yi min.".. Malamin ya tsaya baki buɗe, yana shirin yin magana sai bodyguard ɗin ya dafa kafaɗarsa, ya dube shi cikin wani irin kallo na kashedi... "Sir, mu tafi, kafin ranka ya ɓaci," in ji bodyguard ɗin. Maayah ta sake ɗaukar wayarta, ta ci gaba da abin da take yi kamar ba komai ya faru ba. Hafsat ta saci kallonta, ta girgiza kai cikin tsoro da mamakin yadda Maayah take da wuyar sha'ani... Malami Mr. Collins ya fito daga ajin yana huci, ya nufi ofishin Shugaban Makarantar. Ya shiga ba ko sallama, yana korafi.. "Wannan wane irin iskanci ne? Wata ɗaliba ta kora ni daga aji, kuma tana barazana gare ni!" Principal ɗin, wanda yake karanta wasu takardu, ya ɗago kai da sauri. Lokacin da ya ji bayanin abin da ya faru, sai fuskarsa ta koma kalar tsoro maimakon fushi. Ya mike tsaye da sauri, gumi ya fara keto masa. "Mr. Collins, ashe ba a gaya maka ba? Waccan ba kowa ba ce illa Gimbiya Maayah, 'yar gidan Sarkin masarautar nan. Yarjejeniyar fitowarta makaranta ta musamman ce. Ko ni ban isa na nuna mata iko ba!".. "Amma ai ni malami ne..." Mr. Collins ya yi kokarin kare kansa... "Ba wani amma! Idan har tace ba ta son ganinka, to ka kwashe kayanka ka tafi. Idan Sarki ya ji cewa an ci mutuncin diyarsa, wannan makarantar tana iya rugujewa a yau." Principal ya ɗauki waya nan take, ya ƙira Maayah cikin muryar lallashi... "Ranki ya daɗe Gimbiniya, muna ba ki hakuri. An riga an dakatar da malamin nan, kuma za a turo muku da wanda ya fi shi kwarewa da sanin ya kamata yanzu-yanzu." Maayah dake zaune a class ba tare da ta furta komai ba ta sauƙe wayar daga kunnenta ta katsar... Bayan an gama darasi, Maayah tana zaune a wani waje na musamman a cikin garden din makarantar, inda babu dalibin da ya isa ya tunkaro wajen. Tana shan wani tsadadden juice wanda aka kawo mata daga gida... Hafsat ta ƙariso kusa da ita, tana tafiya cikin ladabi duk da ita ma 'yar President ce. Ta zauna a kujerar dake kallon ta Maayah... "Maayah, gaskiya kin tsorata ni yau," Hafsat ta faɗa tana murmushin damuwa... "Malamin nan fa baƙo ne, bai sani ba. Ko ba za ki ɗan rage zafi ba? Karatu fa ya kawo shi." Maayah ta ajiye glass ɗin juice, ta kalli Hafsat da idanuwanta masu cike da izzah. "Hafsat, ki sani, ni ban zo nan don na koyi ladabi daga wurin wani malami ba. Na zo ne don na cika alkawarin da aka yi wa mahaifiyata. Duk wanda ya manta matsayina, to aikina ne na tuna masa." Hafsat ta gyaɗa kai, "Na sani, amma kowa a makarantar nan yana tsoronki. Ko ni ɗin nan ma wani lokacin sai na ji tsoron kulla magana dake." Maayah ta gyara zamanta, ta ɗan dube ta da wani kallo na alfarma. "Tsoro shi ne mutuncin shugaba, Hafsat....Idan ba su tsoronki, ba za su girmama ki ba. Ke ma ya kamata ki fara nuna matsayinki na 'yar President, ba wai ki bar kowa yana sakar miki fuska ba." Hafsat ta yi shiru, domin ta san halin Maayah ba na canzawa ba ne. A daidai wannan lokacin, ɗaya daga cikin bodyguards din ya kariso, ya sunkuya ya ce.. "Gimbiniya, lokacin tashi ya yi. Motoci suna jiran ki a waje." Maayah ta miƙe ba tare da ta sake cewa Hafsat uffan ba, ta fara tafiya cikin takunta na alfarma, yayin da Hafsat ta bi bayanta tana mamakin wannan dabi'a ta Maayah... ✨ A sashen Gimbiya Ayat kuwa... A yau ta sulale ta fito a matsayin Inuwa, domin ta kwan biyu bata leƙo waje ba, kuma tasan dole Master ya tuntuɓe ta... Cikin Sa'a ta samu master Ibrahim baya nan...ta yi amfani da damar rashin Master ta sulale daga masarautar. Bayan ta yi sa hannu a babban littafin fita na jami'ai, ta zura wa dokinta linzami, kai tsaye ta nufi bakin kogin da ya zama tamkar maɓoyar sirrinta... Iskar wajen mai sanyi ta daki fuskarta, amma zuciyarta cike take da tunanin Mai Farin Gashin nan, mutumin da har yanzu ba ta san asalin ko shi wanene ba, amma kewarsa ya addabeta. Ta sauƙa daga kan dokinta, ta zauna a bakin ruwan tana kallon kwarararsa. "Ina kake ne?" ta faɗa a hankali, tana mamakin yadda abokin gaba ya zama abin kewa a gare ta. Can ba zato ba tsammani, wani abu mai nauyi ya faɗo daga sama, ya sauƙa a tsakiyar faɗin filawowin da ke haskaka wajen... King Diamond ne. Jikinsa duk jini, yana aman jini ta baki da hanci sakamakon raunukan da ya samu na rushewar kogon. Cikin zafi da raɗaɗi, ya ji motsin mutum. Ko da yake ya yi nisa a cikin mawuyacin hali, hankalinsa na sarki ya gaya masa cewa ba zai iya barin kowa ya ga rauninsa a matsayin mutum ba... Cikin sauri yayi amfani da ikon tsafinsa, ya jirkita ya zama Ƙaramar Kuliya... Farin gashin kuliyar ya ɓaci da jinin da ke fita daga jikinsa, yana nishi sama-sama... Inuwa ta miƙe a zabure, ta zaro takobinta tana raba idanu, tana tunanin ko wani makiyi ne ya biyo bayanta. Amma tana isa wurin, maimakon katon jarumi, sai ta ga wata kyakkyawar kuliya mai farin gashi tana nishi cikin azaba, jini na malala daga jikinta... Zuciyar Ayat ta buga. Duk dake ita jaruma ce da ba ta tsoron jini, amma tausayin dabba ya kasance rauninta tun tana yarinya. Ta maƙale takobinta, ta nufi kuliyar da gudu... "Haba! Waye ya yi miki wannan aika-aikar?" ta faɗa cikin muryar tausayi, yayin da ta tsugunna kusa da Diamond wanda ke cikin siffar kuliya... Ta sa hannuwanta biyu ta ɗauke shi cikin kulawa, ba ta damu da yadda jinin jikinsa ya ɓata kayan jami'in da ke jikinta ba... King Diamond, yana cikin siffar kuliya, ya kalli idanun Ayat. Duk da duhun da ya fara rufewa idanunsa saboda suma, ya ji wani irin ɗumi da aminci a tattare da ita wanda bai taba ji ba.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣0️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan Ayat ta ɗauki kyakkyawar farar kuliyar nan mai rauni, ba tare da ɓata lokaci ba ta haye dokinta da sauri. Iskar dake kaɗawa tana busota yayin da take ƙara matse kuliyar a jikinta, tana gudun kada raunukan jikin kuliyar su ƙara tsananta... Tana isa ƙofar masarautar, ta yi sa hannu a littafin jami'ai cikin hanzari, sannan ta jefa kuliyar cikin wata leda ta musamman domin ɓoye ta daga idanun masu gadi. Ta san idan aka ga kuliya a hannun jami’i irin Inuwa, zai iya tada shakku... Bayan ta ajiye dokinta a rugar dawakai, tana ƙoƙarin sulalewa zuwa cikin masarauta, sai ta hango Master Ibrahim daga nesa. Cikin sani, ta san cewa muddin idonsa ya faɗa kanta, tambayoyi ne zasu biyo baya. Ta duƙa a hankali, ta laɓe bayan dogayen ginshiƙan masarautar, tana jin wasu jami'ai suna bi ta gefenta suna wasa da dariya.. Tafiya mai nisan gaske tayi a ƙafa kafin ta bi ta wata ɓoyayyen hanya, hanyar da ta kai ta kai tsaye zuwa cikin ɓangarenta na alfarma... Tana shiga ɗakin baccinta, wanda ke ƙamshi da turaren oud, ta ciro kuliyar da ke lumshe ido cikin galala, ta kwantar da ita a tsakiyar gadonta mai laushin gaske. A gaban babban madubi, Ayat ta fara cire kayan jami'an nan. Ta cire rawani, ta cire saje da gemun da take amfani da su wajen ɓoye siffarta. Nan take, dogon gashinta baƙi wul, ya bazu har zuwa gadon bayanta. Ta zama asalin kyakkyawar mace, mai kwarjini da izzah... King Diamond, wanda ke kwance cikin siffar kuliya, yana kallon kowane motsi nata. Duk da ciwon da yake ji, zuciyarsa ta buga ganin wannan canjin. Daga jarumin jami'i zuwa mace mafi kyau da ya taɓa gani a duniyar bil'adama. Abin da ya ƙara ruɗa Diamond shi ne lokacin da Ayat ta cire kayan jamin'an gaba ɗaya, ta ɗaura farin tawul kawai wanda ya bar fatarta mai santsi a bayyane. Ta nufi gadon, ta ɗauki kuliyar a hankali ta nufi banɗaki da shi... Yayin da take haɗa ruwan ɗumi a cikin bahon wanka, Diamond yana ta maganar zuci.. "Wannan me take shirin aikatawa ne? Shiga banɗaki tare da ni? Lallai wannan yarinyar ba ta san ko ni wane ne ba!".. Duk da haka, wani sashe na zuciyarsa yana cike da farin ciki. Masarautar nan tana kewaye da hasken garkuwa wanda ke hana aljanu da kowane irin tsafe-tsafe shiga, amma saboda canjin da ya yi zuwa dabba, kuma ta sanadin Ayat, ya samu damar shigowa har cikin zuciyar gidan... Ya ƙura mata ido yana mamakin yadda kyakkyawar mace irin wannan take rayuwa a matsayin soja. Wani irin sirri ne yake tattare da ita? Kuma wane irin ɗumi ne hannuwanta suke bayarwa yayin da take shirin fara yi masa wanka?.. Ayat ta gama gyara wa kuliyar jikinta tsaf, ta naɗe ta cikin tawul mai laushi sannan ta fito bedroom ta ajiye ta a kan gado... "Minti goma kacal zan yi," ta faɗa cikin murya mai sanyi, "amma kinsan wanka na akwai delay." Ta shige banɗakin, ta fara haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙanshi, tana shirin wanke gajiyar ta... Tana zaune a cikin bahon wankan, tana goga lallausar fatarta da sabulu, kanta na jingine da gefen bahon. Idanunta a lumshe, amma tunaninta yana can bakin kogi... "Me yasa nake kewar sa?" ta tambayi kanta. "Duk da abubuwan da ya yi min, musayar jikin nan da ya kusan haukata ni, da kuma kallon tsiraicina da ya yi a kogi, me yasa har yanzu nake jin tamkar akwai wani abu da yake haɗa mu?" Ta ji wani irin ɗumi a ranta, tana fatan da ace maimakon wannan kuliyar, 'Mai Farin Gashin' ne ta gani a yau... A cewar ta.. Tana shiga wankan, Diamond ya ji jikinsa ya fara wani irin zafi... Kasancewar Ayat tana cikin jin daɗin ruwan ɗumi, shi ma King Diamond ya fara jin wannan ɗumin ta sanadin haɗin jinin da ke tsakaninsu. Ikon tsafinsa ya dawo masa da ƙarfi saboda natsuwar da ya samu a ɗakinta.. Cikin kifawar ido, ƙaramar kuliyar nan ta zama haske, sai ga King Diamond zaune a tsakiyar gadon Gimbiya Ayat. Doguwar farar rigarsa ta masarautar aljanu ta bayyana, sumar kansa fara sol ta bazu har gadon bayansa... Ya zura wa ƙofar banɗakin ido, yana jin sautin ruwan da yake kwarara. Zuciyarsa tana bugawa. Ya tuna daren nan a bakin kogi lokacin da sukayi musayar jiki, sannan sumbatar da ya haɗa su ya fara dawo masa ƙwaƙwalwa...ya tuna yadda ya kalli kyakkyawar surarta tana wanka ba tare da ta sani ba... Wannan haɗin jinin da sukayi ya sa yanzu duk abinda take ji, shi ma yana ji. Yana iya jin dumin ruwan da yake taba fatarta, yana iya jin kamshin sabulun da take shafawa... "Ayat..." ya faɗa a hankali cikin ransa. "Kin zamo wata sirri a rayuwata!.. Kuma me yasa kika zama sanadin da zan ji tausayin bil'adama?"... Diamond ya miƙe a hankali daga kan gadon, ƙafafunsa tamkar baya taka ƙasi yayin da ya nufi hanyar banɗakin. Ya tsaya a jikin ƙofar, yana sauraron numfashinta.... Ya san cewa idan ta fito ta ganshi a matsayin mutum, babban tashin hankali zai faru, amma wani sashi na ransa yana son ta san cewa yana kusa da ita... A cikin banɗaki kuwa, Ayat ta fara jin wani irin yanayi na daban. Ta ji tamkar ba ita kaɗai ba ce a ɗakin... Zuciyarta ta fara bugawa da sauri, Ta miƙe da sauri daga cikin ruwan, ta ɗauki babban tawul ta ɗaura, tana sauraro da kyau... "Kamar akwai mutum a ɗakin nan..." ta raya a ranta... Ta fito daga banɗaki, sanyin ruwan ya sa fatarta yin luwai-luwai.. Tana ganin kuliyar nan a yadda ta bar ta a kan gado, sai ta saki wani irin murmushi mai ban sha'awa irin murmushin da babu wanda ya taɓa gani a masarautar nan sai ita kaɗai... Ta zauna a gaban madubi, ɗaure da gajeren tawul ɗin da ya tsaya dai-dai cinyoyinta... Ta fara shafa mayuka masu ƙamshi na alfarma, waɗanda ake yi wa gimbiyoyi oda na musamman daga ƙasashen waje. Kowane shafa mai da take yi, ƙamshinsa yana ratsa hancin King Diamond... King Diamond, wanda ya riga ya koma siffar kuliya kafin ta fito, ya kwanta lamo yana kallonta ta cikin ƙwayar idonsa. A ransa yana jin wani irin takaici da daɗi lokaci guda... "Ayat..." ya furta a zuciyarsa... "Idan kika san cewa ni ne abokin wasanki na ƙuruciya, mutumin da kika yi wa rantsuwar kiyaye fuskarki dominsa, shin zaki kashe ni ne ko kuwa zaki rungume ni?" Ya kalli yadda take shafa man a wuyanta da kafaɗunta.... Ya tuna lokacin da suke yara, lokacin da komai yake da sauƙi kafin ƙaddara ta mayar da shi sarki a duniyar aljanu.. Ganin yadda ta girma ta zama kyakkyawa haka, kuma jaruma mai faɗa a matsayin Inuwa, ya sa ya ƙara jin kwarjininta a ransa. Ayat ta juyo ta kalli kuliyar, ta miƙa hannu ta ɗaukota ta ɗora a cinyarta. Ta fara shafa kanta a hankali, tana wasa da farin gashinta.. "Kinsan me? Ke kaɗai ce kika ga fuskata a yau bayan shi," ta faɗa cikin muryar raɗa, tana nufin Mai Farin Gashin da ya ganta a kogi... "Shi ya ruguza min alƙawarina, amma ke... ke kyakkyawa ce. Zan kula da ke kamar jariri har sai kin warke."... Diamond ya lumshe ido, yana jin ɗumin jikinta da laushin hannunta. Haɗin jinin da ke tsakaninsu ya sa kowane shafa da take yi masa, yana jin sa har cikin ransa tamkar ita ma tana jin abinda yake ji... A wannan lokacin, Diamond ya manta da sarautarsa, ya manta da mulkinsa na aljanu, kawai yana son ya dawwama a haka, a jikin Ayat, yana kallon kyawun da kowa yake mafarkin gani amma shi kaɗai ya samu nasarar gani... Yayin da take cikin wannan yanayin na natsuwa, ba zato ba tsammani sai ta ji takun tafiya a babban falon ɓangarenta...ana haurowa saman bedroom... Zuciyarta ta buga. Babu wanda yake shigowa ɓangaren Gimbiya Ayat ba tare da izini ba, sai mutum ɗaya... Wato Saratu, nan ma bata shigowa sai da izini.. "Gimbiya Ayat? Kina ciki ne?" Saratu ce ta daki ƙofar ɗakin... Ayat ta zaro ido, ta kalli kuliya, sannan ta kalli kayan jami'an nan da ke warwatse a ƙasa waɗanda ba ta gama ɓoyewa ba... Idan Saratu ta shigo ta ga kayan jami'ai a ɗakin, asirinta zai tonu!... "Menene Saratu?..." Ta furta tana shafa jikin kuliya... Saratu daga bakin ƙofa ta ce, "Daman an kammala shirya dining ne..." Ta ce, "ok ki je ina zuwa, na fito a wanka ban kuma sa kaya ba..." Daga nan Saratu ta juya... Ayat ta miƙe ta ɗauko akwatin magunguna (First Aid Box) na musamman... Ta dawo kusa da kuliyar, ta fara goge mata ragowar jinin da ya bushe a wasu sassan jikin, sannan ta shafa mata magani mai sanyi da kuma turaruka masu ƙamshi don rage radadin raunin... Yayin da take gyara masa gashinsa, Ayat ta kalli cikin idanun kuliyar, wani irin tausayi da shauƙi suka mamaye zuciyarta. Ta ji tamkar kuliyar tana fahimtar kowane sauti da yake fita daga bakinta... "To ni ban sani ba, mace ko namiji?..." Tana kallon kuliyar ta kasa gane wa amma ita mace take bata... Sai kuma ta ce, "idan mace ce ke, ina son ki mun wani alama da zan gane..." Kuliyar tayi tsumu ko motsin bata yi ba.. Ayat ta kuma cewa "to idan namiji ne yi mun alama.." Nan kuliyar ta ɗago hannu tana shafa kanta.. Murmushi Ayat tayi tare da ƙara ringumarsa.. Ta ce da shi... "Ka zamo abokina ɗan amana... Daga yau, ke ba kuliya bace," ta faɗa cikin murya mai cike da shauƙi... "Zan sanya miki suna Reems... sunan mutumin da ya fi kowa daraja a zuciyata."... King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya ji wani irin shock ya ziyarci zuciyarsa. Sunansa na asali! Sunan da ya binne shi tun ranar da ya zama sarki a duniyar aljanu. Wani daci da dariya suka taso masa a ransa, ya ce a ransa... "Ayat... ki rasa a wa zaki sanya sunana sai a dabba? Ni ne Reems dinki, asalin mutumin da kike jira, amma yau gashi kina kira na a matsayin kuliya!" Duk da haka, ya ji daɗin yadda sunan yake fita daga bakinta, ya tabbatar masa da cewa har yanzu yana raye a zuciyarta. Ayat ta miƙe ta nufi wurin tufafinta na sarauta. Ta saka riga ta alfarma mai ratsin zinare, sannan ta ɗauko ɗankwalin fuskarta ta rufe kyakkyawar fuskarta kamar yadda ta saba, ta bar idanunta kawai masu Golden Eyes a bayyane. Ta dawo bakin gadon, ta sunkuya ta manna wa kuliyar sumba a goshi... Wani irin sanyi Diamond ya ji ya ratsa shi har cikin bargonsa... "My Reems, zan sauƙa ƙasa domin yunwa nake ji. Zan taho maka da abinci kai ma ka ci, ka huta a lallausar gadona," ta faɗa a hankali sannan ta juya ta fice daga ɗakin cikin takun isa da izza. Tana fita, kofarta na rufewa, sai ga wani farin hayaƙi ya mamaye tsakiyar gadon. Nan take King Diamond ya dawo asalin siffarsa ta mutum. Ya zauna a tsakiyar lallausan gadon, sumar kansa fara sol ta bazu a kan zanen gadon Ayat... Ya ɗan gyara zama, ya taɓa goshinsa inda ta sumbace shi, sannan ya saki wani murmushin gefen baki... "Ayat... idan kika san cewa Reems ɗinki yana zaune a kan gadonki a matsayin sarki, shin zaki iya kawo min abincin kuwa?" Ya kalli ƙofar da ta fita, idanunsa suna shining da wani irin kwarjini da nuna cewa har yanzu shi ne mai iko, ko da kuwa yana cikin gidan masoyiyarsa ne a asirce.... ✨✨ Washe gari a safiyar yau, Gimbiya Maayah tana zaune a kan kujerarta ta musamman a wurin dining area na sarauta, tana cin French Toast mai kwai da zuma wanda aka kawo mata a cikin wani faranti na azurfa mai sheƙi... Gefenta tsaye masu aiki biyar sanye da fararen uniform, ɗaya na shara, ɗaya na gyaran teburi, ɗaya na kawo abinci, da sauransu... Acan bakin ƙofa Bodyguards guda biyu ne masu jikin dambe, sanye da baƙaƙen kaya.. Maayah ta ɗaga hannu, ba tare da ta kalle su ba.. “Where is my orange juice?” Muryarta a sanyaye cike da izgilanci.. Wata mai aiki, wadda kana ganinta kasan sabuwar zuwa ce, ta matso da sauri tana rawar jiki. “G-Gimbiya, a yau an kawo ruwan Passion Fruit ne, saboda an ce lemun orange ɗin ya ƙare a kitchen.” Maayah ta ajiye cokalin ta a hankali, sa'an nan ta ɗaga kai ta kalli sabuwar mai aikin. Ta yi mata kallo tun daga kanta har zuwa takalmin ta... “Kin san cewa a cikin Fadar Alhamra, Maayah ba ta shan ruwan Passion Fruit? Kuma kin san cewa lemun orange bai taɓa ƙarewa ba? Yanzu haka, ki tashi ki kawo min sabon ruwan lemun. Idan kuma ba ki same shi ba, to ki je ki samo wanda zai kawo min a cikin minti biyar, sannan ki cire kayan jikinki ki bar mun site...” Muryar Gimbiya Maayah ba ta da zafi amma ta fi ƙarfin wuta. Nan take, sabuwar mai aikin ta fashe da kuka, ta durƙusa tana roƙon afuwa... “Gimbiya, dan Allah, ki yi haƙuri. Na yi kuskure. Zan tafi in samo.” “Too late,” Maayah ta yi tsaki. Ta kalli ɗayan mai aikin, wadda ta fi ta sanin komai... “Maimaita wa wannan sabuwar dokokinmu! Ba na son ganin ta a cikin fada ta. Cire mata uniform ɗin ta. Kuma Mama Liyatu ta kawo min ruwan lemu.” Mama Liyatu ta shigo da sauri, tana sanye da doguwar riga mai kyau... “Gimbiya ta, dan Allah ki yi haƙuri, abinci yayi daɗi fa. Ki bar ta. Zan kawo miki ruwan.” Mama Liyatu ta san yadda za ta tausasa ran Gimbiya kafin ta fusata... Maayah ta yi sigh mai nauyi... “Fine. But babu wanda zai iya damuna a cikin gida na.” Mama Liyatu ta yi murmushi, amma cikin tsoro take faɗin. “An gane, Gimbiya. Duk abin da kika ce shi za a yi.” Ta juya, ta yi nuni ga masu aiki biyu da su raka sabuwar mai aikin... Bayan ɗan mintuna sai ga wani jami’in tsaro na fadar sarki ya shigo domin isar da saƙo. Ya gaishe da Maayah dake zaune a kan teburin cin abinci, sannan ya ce, "Sarki ya aiko ni, yana son ganin gimbiyarsa Maayah..." Maayah ta ɗaure fuska tare da yamutsa ta cikin isa ta ce, "Kaje kace masa Maayah makaranta zata je, sai ta dawo." Kafin Maayah ta sake furta wani abun, har jami'in tsaron ya juya ya fita domin isar da saƙon... Kamar dama jira yake ta faɗi abin da zai sosa ran sarki, domin tun ba yau ba ake sanar da sarki cewa Maayah ta ɓaci da wulakanci da girman kai tamkar Zayana, amma sarki ya ƙi yarda... Ganin jami’in tsaron ya tafi ne ya sa Maayah faɗin, "Daga cewa makaranta zan je shikenan sai ya tafi? Faɗa kawai nayi, amma ba wai naƙi zuwa bane..." Ta ƙarisa maganar kamar mai fargabar abun da zai je ya dawo... Mama Liyatu ta ce, "To tinda hakane, kawai ki tashi kije ƙiran sarki. Idan ya ganki da uniform ɗinki, zai fi sallamarki da wuri, ya fi dai baki je gaba ɗaya ba." Maayah ta kalli Mama Liyatu cikin isa ta ce, "Mama Liyatu, ni fa ba a bani shawara ballantana umarni. Abin da naga ya dace shi zan yi." Mama Liyatu ta yi shiru, ba ta sake cewa uffan ba.. Maayah ta ƙara da cewa, "Ya je ya sanar ɗin tinda shi munafuki ne, bai jira na gama magana ba ya tafi. To makarantar zan je, na ga ko kashe ni za a yi!" Ta ci gaba da cin abincinta cikin kwanciyar hankali, babu ruwanta da kukan yarinyar da aka kora ba tare da wani dalili na kirki ba.... Cikin minti biyar, direbanta wanda shima yake sanye da uniform ya iso ya tsaya a gabanta... "Gimbiya, motar tana nan a shirye. Makarantar za a tafi yanzu?" "Yes. Amma ba zamu bi hanyar da talakawa ke bi ba a yau. Zamu bi ta hanyar Presidential Gate, ina so naga yadda take a yau."... Direban ya sunkuyar da kai, "Kamar yadda kika ce, Gimbiya." Maayah ta tashi, ta zuba ido ga Mama Liyatu ta ce, "A cikin mako mai zuwa Mama Liyatu, ina so ki shirya min gagarumin party.... Zan gayyaci 'ya'yan ministoci da 'yan kasuwa masu kuɗi... Ba na son ganin talaka a cikin fadar Maayah.. Ki tabbatar an kammala komai kafin na dawo daga makaranta." Ta fita tana takun alfarma da kasaita, dakarun tsaron ta guda biyu suna biye da ita.... Motar Lexus mai sheƙi ta ɗauke ta ta bar bangaren nata... Kafin Maayah ta bar bangarenta, har jami'in tsaron ya isa gaban sarki ya sanar da shi yadda suka yi... Tafida dake zaune a gefe ya cika da mamaki ya ce, "Maayah ce ta ce haka?" Jami'in tsaron ya tabbatar masa. Sarki Nourdeen yana zaune a kan karagar sa cikin siffarsa ta Zaki, bai ce komai ba... Suna zaune Kwatsam, sai wasu jami'an tsaro suka sanar cewa, "Ga motocin Gimbiya Maayah nan zasu wuce makaranta." A lokacin ne Sarki ya miƙe tsaye cikin kwarjini. Shi da kansa ya nufi wajen fada zai fita. Wasu fadawa cikin girmamawa suka ce, "Mai Martaba, ka bamu izini mu dakatar da su, ba sai ka fita ba." Sarki ya ɗaga musu hannu alamar su kyale shi... Yana fita, daidai lokacin da motocin Maayah suka raba titin gate ɗin fita, sarki ya saki wata irin uban tsawa mai firgitarwa cikin muryar Zaki mai cike da daji... "MAAAYAAAHH!!!" Wata irin girgiza motar su ta yi har sai da ta ɗan ɗagu daga ƙasa... Direban ya danna burki da kansa, motocin suka tsaya cak! Saura kaɗan motar da Maayah take ciki ta kife. A cikin motar, Maayah ta yi sumar zaune saboda tsananin firgici... Kaf jami'an tsaro, fadawa, bodyguards, da dakarun sojoji babu wanda bai tsorata ba, wasu ma har neman guduwa suke yi.. Fadawan dake kusa da sarki ma kowa ya ruɗe, har sai da wani ya saki fitsari a jikinsa saboda tsananin firgici.... Kukan birkin motocin ya haifar da wata baƙin hayaƙi mai yawa a harabar Gate... A cikin motar Lexus ɗin, Maayah ta daskare, idanunta sun fito waje, numfashinta ya tsaya na mintuna biyar.. Ba ta taɓa jin muryar mahaifinta cikin wannan yanayin ba. Jikinta ya fara rawa, izzar da take ji yanzu ta narke ta koma tsoro tsagwaronsa... Sarki Nourdeen ya taka zuwa tsakiyar hanyar, takunsa na girgiza ƙasa... Fuskarsa ta Zaki mai cike da gashi tana wani irin haske na ban tsoro, idanunsa ja wur kamar garwashin wuta... Ya tsaya gaban motar Maayah, kowa na wajen ya ɗuka, wasu sun kifa fuskarsu a ƙasa don kar su kalli fuskar Zakin... "FITO!!!" Ya sake daka wata tsawar, wadda ta sa gilashin motar Maayah fara tsagewa... Ƙofa ta buɗe a hankali. Maayah ta fito, cikin takun tsoro da firgita, ƙafafunta sun kasa ɗaukar nauyinta... Ta zube a ƙasa gaban mahaifinta, uniform ɗinta ya ɓaci da ƙura... "Barka da safiya... Abul," ta faɗa cikin murya mai rawa, kanta a ƙasa... Sarki ya matso kusa da ita, inuwar fuskarsa ta Zaki ta mamaye duk jikinta. Ya sunkuyo da kansa daidai kunnenta, tana iya jin zafin numfashinsa da kaurin kishirwar jini da ke tashi daga gare shi... "Izzah tana da iyaka, Maayah," in ji Sarki, muryarsa tana fitowa daga can ƙasan makogwaro kamar gurnani... "Kina tunanin don na ba ki damar fita school, hakan yana nufin kin fi ƙarfin umarnina? Jami'in tsaro na ya zo gare ki, amma kika ce sai kin ga dama? Shin kin manta cewa ni ne na gina wannan masarautar da jinina da kuma wannan fuskar tawa?" Maayah ta fashe da kuka, "Don Allah Abul... kayi haƙuri. Ba nufina ke nan ba." Sarki ya ɗago kansa, ya kalli dakarun tsaron da ke kewayen motar. "Daga yau, an soke fitar Maayah makaranta na tsawon wata guda. Za ta zauna a ɓangarenta, kuma kowane malami zai zo har gida ya koyar da ita kamar sauran..." Ya kalli direban da bodyguards ɗin, "Ku mayar da ita ɓangarenta. Idan na sake jin ta nuna isa ga wanda na aiko, to zan tabbatar ta san cewa ni Zaki ne, ita kuma 'yar dabba ce a gabana!" Sarki ya juya ya bar wajen, takunsa yana barin gurbin ƙafa a kan kwalta. Fadawa suka fara rarrafe suna mara masa baya, yayin da Maayah ta rage a durƙushe a tsakiyar titi, tana kuka mai ban tausayi, duk izzarta ta koma kaskanci a gaban kowa... Bayan kora da aka yi wa Maayah, an mayar da ita bangarenta karkashin tsauraran matakan tsaro... Tana zaune a ɗakinta, ta kalli kayan makarantar da aka hana ta saka, ta watsar da su gefe guda cikin fushi da takaici... Washegari da safe... Malami ya zo har gida domin koya mata, amma Maayah ta ƙi fitowa daga ɗaki. Tana jin kanta ya ragu, musamman yadda yanzu sauran ƴan uwanta za su riƙa yi mata kallon wadda aka hukunta... "Mama Liyatu!" Ta ƙira da karfi... Mama Liyatu ta shigo jiki na rawa. "Gimbiya, gani." "Ki sanar da malamin nan ya tafi. Ba zan fito ba. Kuma ki tabbata babu wanda ya sake ambata sunana a gidan nan yau, idan ba haka ba zan sa a yanke harshen duk wanda ya yi hakan."... Duk da Sarki ya hukunta ta, Maayah tana kokarin dawo da ragowar izzarta akan talakawa da masu aiki... Amma a zuciyarta, tana tsoron ranar da za ta sake haɗa ido da mahaifinta mai fuskar Zaki... Labarin abin da ya faru da Maayah ya isa kunnen Gimbiya Zayana... Zayana tana zaune a nata sashen, wanda yake can nesa da kowa, cike da kamshin turaren na musamman... Zayana tana kwance a kan wata gadon alfarma, tana wasa da wani kwarangwal ɗin zinare a hannunta... Ɗaya daga cikin bayinta ta shigo tana sanar da ita abin da Sarki ya yi wa Maayah... Zayana ta yi wata irin dariya mai sanyi, wacce take da amo kamar iska.. "Maayah yarinya ce. Tana tunanin izzah ita ce tafiya da bodyguards... Shi kuma sarki, yana tunanin fuskar Zakin nan tasa za ta tsoratar da kowa.".. Ta miƙe tsaye, tana taku cikin nutsuwa... "Maayah ta yi kuskure da ta nuna rauni ta durƙusa... Ni Zayana, babu ranar da zan durƙusa wa wannan fuskar ta Zakin. Idan ya yi kuskuren yi min tsawa, zan nuna masa cewa akwai abin da ya fi Zaki girma a daji...." Ba zato ba tsammani, sai ga Sarki Nourdeen ya ƙariso sashen Zayana... Ya shigo ne da nufin ya gargade ta kamar yadda ya yi wa Maayah, domin ya ji labarin ita ma tana wuce gona da iri... Sarki ya tsaya a ƙofar sashen nata, ya zuba mata wani irin kallo na kwarjini... Amma Zayana ba ta ko tashi daga inda take ba, ba ta kuma sunkuyar da kai ba. Ta ƙura masa idanuwa waɗanda suka fara canza launi daga baki zuwa wani kalar ja mai duhu... "Nourdeen," Zayana ta ƙira sunan mahaifinta kai tsaye ba tare da faɗin Sarki ko Abul ba.... "Kada ka kawo wannan gurnanin naka sashena. Ka riga ka sani, Ni na bambanta da sauran yaran gidann nan. Kada ka kuskura ka taɓa ikona." Wani irin iska mai sanyi ya fara kaɗawa a ɗakin, har fitulun ɗakin suka fara disashewa... Sarki Nourdeen, Zakin da kowa yake tsoro, ya ji jikinsa ya yi sanyi. Ya san cewa Zayana ba mutum ba ce kawai, tana ɗauke da wani abu da ya fi karfinsa... Sarki ya ja numfashi, ya kawar da kansa. Ba tare da tsawatarwa ba ya ce, "Zayana ki kiyaye. Iyakarki daban, tawa daban." Sannan ya juya ya fita da sauri kafin ikon Zayana ya fito fili... Zayana ta cigaba da zama, tana wasa da ƴar tsanar ƙwarangwal... "Izzah ba hauka ba ne, Maayah. Izzah ita ce ka sanya kowa ya tsoraci ko da kallonka ne, har da wanda ya haife ka.".. Ta furta tana sakin murmushin gefen baki... *SYDNEY* A can nesa, a cikin wani babban bene mai kallon teku, Ruma tana zaune a kan kujerarta ta mulki... Sanye take da tufa na alfarma, amma yatsunta suna sanye da wasu tsofaffin zobina. Babban cikinsu, wanda yake da wani baƙin dutse mai sheƙi, yana haskaka wani irin kore-kore... Ruma ta murza zoben, tana rufe idanunta. Tana iya jin bugun zuciyar Zayana daga Alhamra... Wannan zoben shi ne "remote control" na tausayin Zayana, muddin yana hannun Ruma, Zayana ba za ta taɓa sanin ma'anar jinƙai ba... "Nourdeen," Ruma ta yi murmushin mugunta... "Kana tunanin ka raba ni da ɗiyata? Ka riƙe gangar jikinta, amma ni ina riƙe da ruhinta da tausayinta. Duk sanda kake tunanin kai Zaki ne, ka sani cewa ɗiyarka tana da ikon murƙushe maka kwarangwal ɗin jikinka." ✨✨ A Masarautar Alhamra.. A daidai lokacin da Ruma ta murza zoben a Sydney, sai aka ga idanun Zayana sun ƙara yin ja wur a Alhamra. Wani irin kukan tsuntsu na daji ya tashi daga samfurin kwarangwal ɗin da ke hannunta... _______________Maayah, wadda ke cikin damuwar hukuncin da aka yi mata, ta kasa daurewa. Ta yanke shawarar zuwa sashen Zayana, ko da yake tana tsoronta, tana tunanin ko za ta samu hanyar fita daga halin da take ciki... Maayah ta isa ƙofar sashen Zayana, amma tun kafin ta shiga, wani sanyi ya ziyarci ƙashin bayanta.. Ta tura ƙofar a hankali, ta ga Zayana a tsaye, fuskarta babu ko ɗigo na ɗan'adamtaka... "Me ya kawo ki nan, Maayah?" Zayana ta tambaya, muryarta tana amo kamar tana magana ne daga cikin kabari. "Kin zo ne ki yi kuka domin sarki ya nuna miki cewa ke ɗaliba ce kawai?" Maayah ta haɗiye miyau, ta tsaya cikin izzarta ta ce, "Ba kuka na zo yi ba. Na zo ne mu haɗa kai. Abul yana neman ya raina mu gaba ɗaya. Idan ya fara da ni, ke ce ta gaba."... Zayana ta fashe da wata dariyar shakiyanci, ta taka har gaban Maayah... Ta matsa da fuskarta kusa da ta Maayah har suna jin numfashin juna... "Ba mu duka ba, Maayah... Ke aka raina. Ni, babu wanda ya isa ya gaya min yaushe zan fita ko yaushe zan zauna..... Ki fita daga sashena kafin na sa ki manta sunanki.".. Maayah ta ji tsoro ya fara ratsa ta, ta juya za ta fita, sai Zayana ta ƙira sunanta.. "Kuma ki gaya wa ma'aikaciyarki Liyatu, kada ta sake barin ƙafarta ta taka wannan sashen nawa. Domin bana buƙatar ko wani ƙazami, ke ma na raina tsabtar ki balle ita...." Ba ƙaramin ƙuluwa Maayah tayi ba, haka ta share ta koma sashenta cikin fushi, tana huci... Bayi da hadimai kowa ya rarrabe saboda yadda ta koro kowa da tsawa daga part ɗinta... Ta zauna a kan doguwar kujerarta ta alharir, tana kallon silin ɗakin nata... "Meye ya kaini?" Ta faɗa a fili cikin takaici... "Meye ya kaini wurin Zayana? Don tana da wani sirrin kwarjini da kowa ke tsoro? Ni Maayah ce! Ni ce wadda kowa a International Elite School ke tsoro. Idan Abul ya hukunta ni yau, ba yana nufin na zama raunanniya ba."... Ta cika da takaicin yadda ta nuna rauninta har ta tafi neman haɗin kai... A gun Maayah, neman taimako ma kaskanci ne. Ta yanke shawarar cewa daga yau, ko da za ta dawwama a sashenta, ba za ta taɓa nuna wa kowa ba, musamman Zayana, cewa tana cikin ƙunci ba... Ta ƙira Mama Liyatu... "Mama Liyatu! Ki shirya min abinci mafi tsada, kuma ki ɗauko min sabon littafin nan na Royal Dynasties... Ina son na nuna wa duniya cewa ko a kulle nake, ni ce sarauniya." Ita kuwa Zayana, tana nan zaune a daƙin da ko iska ba ta ratsawa sai da izininta. Ta san cewa Maayah ta tafi ne cike da takaici, kuma hakan daɗi yake mata... A tunaninta, Maayah ba ta kai matsayin da za su haɗa kai ba, ita Maayah tana izzah ne don tana da kyau da masoya, amma ita Zayana izzarta tana cikin jininta ne... ✨✨✨ Sarki Nourdeen yana zaune a babban falonsa, fuskarsa ta Zaki tana kallon hoton Ruma Mahaifiyar Zayana dake jikin bango. Ya daɗe yana kallon hoton, yana tunanin halayyar Zayana... "Izzar Ruma ce take yawo a jikin Zayana," ya faɗa a ransa... "Ba wani abu bane illa gado. Yadda Ruma take kallon kowa kamar kaskantacce, haka Zayana take. Ba zan taɓa mantawa da yadda Ruma ta tafi ta bar min wannan ragamar ba." Sarki bai kawo a ransa cewa akwai wani tsafin zobe a Sydney da ke juya Zayana ba... Ga shi, ganin cewa Zayana ba ta yi wa kowa tsawa ko yawo a fili kamar Maayah, sai ya fi jin kwarjininta.... A wurin Sarki, Zayana ita ce True Reflection ta mahaifiyarta, mace mai mulki da taurin kai... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣1️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* King Diamond yana zaune a tsakiyar gadon Ayat, yana shaƙar ƙamshin turaren oud dake tashi daga jikin filon baccinta.. Fuskarsa dake ɗauke da annuri da kwarjini tana haskaka cikin duhun ɗakin. Ya kalli kansa a madubin da Ayat ta gama amfani da shi, ya ga yadda sumarsa fara sol ta dace da lallausan zanen gadon.. ​"Reems..." ya furta a hankali, yana jin daɗin yadda sunan ya dawo masa da rayuwa ta sanadin Ayat. Duk da raunukan dake jikinsa, sumbar da ta yi masa a goshi ta zama tamkar maganin da ya fi kowane maganin tsafi ƙarfi.... ​A can ƙasa a babban falon cin abinci, Ayat tana zaune ita kaɗai, an jera mata kalar abinci daban-daban na alfarma... Saratu tana tsaye a gefe tana yi mata hidima, amma hankalin Ayat baya kan abincin... Tana tunanin Reems dake sama....kuliyar da ta yi amanna da ita... ​"Saratu," Ayat ta ƙira muryarta a dake.. "Na'am ranta ya daɗe," Saratu ta amsa cikin ladabi.. "Ina son ki haɗa min wani abincin a ƙaramin kwanon zinare, ki kawo min shi... Kuma ina son madara mai ɗumi." Saratu ta ɗan yi mamaki, "Gimbiya, ko har yanzu yunwar ba ta ƙare ba ne?" Ayat ta watsa mata kallo ɗaya ta cikin mayafinta, wanda ya sa Saratu ta sunkuyar da kai da sauri... "Kiyi yadda na ce." ​ Da ta kammala cin abinci, Ayat ta ɗauki farantin da Saratu ta haɗa mata ta nufi ɗakinta cikin natsuwa.. Zuciyarta cike take da tausayi, domin tunaninta gaba ɗaya ya karkata ga halittar da ta bari tana kwance a raunane... ​A sama kuwa, King Diamond ya ji takun tafiyar Ayat tana tahowa. Cikin hanzari ya lumshe idanunsa, jikinsa ya fitar da farin hayaƙi, nan take ya sake komawa siffar farar kuliyar nan mai rauni... Ya kwanta lamo a inda ta bar shi, yana numfashi sama-sama kamar mai barci.. ​Kofar ɗakin ta buɗe, ta shigo tare da rufe ƙofar a hankali kamar mai tsoron ta tayar shi daga barci, ta ƙariso ɗauke da tire na zinare... Halittar tana nan kwance a tsakiyar gadon, kamar yadda ta bar ta tun farko.. Ayat ta matsa kusa, ta sauƙe farantin a gefen gado, sannan ta ce cikin muryar lallami. “Reems… ga abinci nan. Ka ɗan ci, zai taimaka mika ka samu sauƙi.” ta faɗa cikin murya mai taushi. Ta ɗauko kuliyar ta ɗora a cinyarta, ta fara ba shi ƙananan naman kaza dake cikin kwanon... ​King Diamond a siffar kuliya ya fara cin abincin, yana jin daɗin yadda hannunta yake taba fuskarsa. A ransa yana cewa, "Ayat, idan kika san cewa Sarkin Power Pool kike ba wa abinci a hannu, da tabbas kin tsorata. Amma yau, ni ne bawanki, tunda kin zama mai ceton rayuwata." ​Bayan ya gama, ta ba shi madarar ya sha, sannan ta rungume shi a ƙirjinta. Ta ji zuciyar kuliyar tana bugawa da sauri, ita ma nata zuciyar tana amsawa... ✨✨ A babban ofishin tsaro na masarauta, Master Ibrahim ya kasa zama waje ɗaya. Ya kwashe sa'o'i yana kai da kawowa, idanunsa suna kallon agogo. Tun bayan da ya kwantar da Inuwa a gadonsa ranar da aka fasa masa goshi, ya ji shakuwar su ta ƙara ƙarfi, amma yanzu Inuwa ya ɓace masa... "Ina Inuwa yake?" ya daka wa wasu jami'ai tsawa.. "Ranka ya daɗe, tun da ya tafi ba mu sake ganinsa ba," ɗaya daga cikin jami'an ya ba da amsa cikin tsoro.. Ibrahim ya ji wani baƙin ciki ya turnuƙe shi. Ya fara tuna maganganun jami'an da ya kora a baya, waɗanda suka ce Inuwa ya fara yawon banza da bin mata a gari... "Shin da gaske Inuwa ya fara koyon halin banza? Shin har ya isa ya fifita wata mace a kaina?" Ibrahim ya faɗa a ransa, kishi yana ƙara rura wuta a zuciyarsa. Ya riga ya mayar da Inuwa Mataimakinsa wato PA, don haka rashin ganinsa ya zame masa babban naƙasu... A can ɓangaren Gimbiya Ayat kuwa, tana zaune a gaban madubinta, tana kallon kyakkyawar fuskarta. Ta ji a ranta cewa tabbas Master Ibrahim yana cikin wani hali na damuwa. Kusan sati guda ba su haɗu ba, kuma yau ta fita amma ta laɓe masa.. Ta kalli Reems dake kwance a kan gadonta, ta saki wani ƙayataccen murmushi... "Reems, ka yi haƙuri zan je na gudanar da aikina. Ina ji a raina Master Ibrahim yana nema na," ta faɗa cikin murya mai sanyi... Nan take, Ayat ta fara cire kayan sarautar nan masu ƙayatarwa. Ta ɗauko kayan jami'an nan na maza ta zura su, sannan ta maƙala saje, gemu, da gashin baki waɗanda take amfani da su wajen yaudarar mutane... Bayan ta gama, ta nufi gadon, ta sunkuya ta sake manna wa kuliyar sumba a goshi... "Babu mai shigowa ɗakin nan domin na kulle ta ciki. Zan bi ta wannan hanyar sirrin dake ɗakin nan na fita. Kar ka ji mamaki, haka ƙaddara ta so da ni. Zan dawo ba da jimawa ba domin duhu ya fara shiga, so nake kawai Master ya ganni in kwantar masa da hankali," ta faɗa a raɗa, kamar kuliyar za ta iya amsa mata... Ayat ta matsa jikin bangon ɗakin, ta danna wani sirrin mabuɗi, nan take bangon ya buɗe wata hanyar sirri ce dake fita zuwa bayan masarauta inda babu mai gani. Ta sulale ta fice, bangon ya koma ya rufe kansa... King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya buɗe idanunsa na zinare ya bi ta da kallo. Duk da sumbar da ta bar masa dake sanyaya masa rai, zuciyarsa ta cika da mamaki da kuma sha'awar yadda wannan yarinya take rayuwa a matsayin namiji.. Bayan ficewar Ayat, King Diamond bai zauna jiran dawowarta ba. Ya sauya siffa daga kuliya zuwa asalin siffarsa ta Aljani, inda ya ɓace daga idon kowa ya bi sawun Inuwa... Yana son gani da idonsa yadda wannan kyakkyawar yarinya take gudanar da rayuwarta a cikin maza.. Yana tafiya yana kallon yadda take shiga cikin jami'ai, kwarjininta a matsayin namiji yana ba shi mamaki.. Suna isa cikin masarauta, sai ga Master Ibrahim ya fito da guguwar fushi. Da ganin Inuwa, bai tsaya wata-wata ba, ya damƙe hannunsa da ƙarfi. Don kada ya zubar masa da mutunci a gaban sauran jami'ai, ya ja shi da ƙarfi har zuwa sashensa... King Diamond yana biye da su, idanunsa suna ƙuna yayin da yake kallon yadda Ibrahim ya wurga Inuwa a tsakiyar ɗakin nasa cikin zafi. Diamond ya tsaya a gefe guda, yana sarrafa kansa da ƙyar don kada ya bayyana ya hukunta Ibrahim.... Ibrahim ya tsaya a kan Inuwa, yana huci... "Tun yaushe ka fara yawon bin mata, Inuwa?" Ya fara zazzaga masa maganganu masu zafi na zargi da lalata, yana ganin cewa hakan ne ya sa ya ɓace tsawon sati ɗaya.. Inuwa tana ƙasa, kanta a sunkuye, ta ƙi ɗagowa ta kalle shi. Ta san idan ta yi magana, za ta iya kuka, kuma idan ta kalle shi, fushinsa zai iya sa ya fahimci wani abu a fuskarta... Ba zato ba tsammani, fushin Ibrahim ya tafi, sai ya maye gurbinsa da wani irin lallami mai sauti. Ya durƙusa a gaban Inuwa, ya sa hannu ya ɗago haɓar sa. A wannan lokacin, Master Ibrahim ya fara magana cikin muryar raɗa kamar yana yi wa mace magana, yana lallashinsa a kan kada ya sake nisa da shi... "Zan yafe maka kuskurenka," Ibrahim ya faɗa cikin murya mai sanyi, "amma hukuncinka shi ne, yau kai za ka yi min tausa daga wuyana har zuwa kunkumi..." Nan take Inuwa ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, wani irin gumi ya karye mata. Tausar namiji daga wuya har kunkumi? Wannan babban haɗari ne ga sirrinta duk da ba yau ne farko ba.. A daidai wannan lokacin, King Diamond ya dafe ƙirjinsa saitin zuciya. Saboda musayar jiki da suka yi a baya, yanzu duk firgicin da Ayat take ji, shi ma yana jinsa a jikinsa. Ya ji yadda jinin Inuwa ya fara gudu da sauri, hakan ya harzuka shi matuƙa. Yana kallon Master Ibrahim da wani irin kallo na kisa, yana jira ya ga inda wannan lamari zai ƙare... Inuwa ta haɗiye miyau, ba ta da yadda za ta yi. Domin ta wanke kanta daga zargin da yake mata, dole ta yarda da wannan hukunci na Master Ibrahim, ko da kuwa hakan yana nufin ta taɓa jikin namijin da ba nata ba.. Master Ibrahim ya cire rigarsa, ya nuna faffaɗan bayansa mai cike da kwarjini, sannan ya kwanta rub da ciki a kan katafaren gadonsa na alfarma. Inuwa ta matso jiki na ɓari, ta zauna a bakin gadon, sawayenta suna taɓa ƙasa. Ta fara kai hannunta kan wuyansa tana masa tausa cikin tsananin kulawa da fargaba. Hannunta mai laushi ya sa Ibrahim lumshe ido, yana jin wani irin sanyi dake ratsa shi... Daga gefe guda, King Diamond yana tsaye, idanunsa sun canza launi zuwa wani ja mai ban tsoro. Kishin aljani ya ninka na mutum sau dubu, ganin Ayat, mace ɗaya tilo da take da ikon shiga zuciyarsa, tana taɓa jikin wani namijin, ya sa ya ji kamar zai fashe tsabar zafi. Ya kasa sarrafa kansa, zuciyarsa ta buga, nan take ya rufe idanunsa ya dunƙule hannuwansa biyu cikin tsananin fushi. Ba zato ba tsammani, sai aka ji wani sauti... Wani irin ƙarfin tsafe-tsafe dake fita daga jikin Diamond ya daki gadon. Nan take duk ƙafafun gadon suka kakkarye... Master Ibrahim ya ji gado ya tafi da shi ƙasa. Da ba don katifa mai kauri ba, da tabbas ya faɗi a kan ƙarfuna da katako... Inuwa ta miƙe da sauri, zuciyarta na duka da sauri-sauri, tana mamakin abin da ya faru... "Lafiya, Master?" ta faɗa cikin murya dake rawa. Master Ibrahim ya sauƙo daga kan rugujajjen gadon yana zaro ido. Ya kalli ƙafafun gadon da suka zama guntu-guntu kamar an sare su da gatari.. "Wanne irin abu ne wannan?" ya faɗa yana waige-waige. Ya kasa gaskata cewa gadonsa mai ƙarfi zai ruguje lokaci guda ba tare da wani dalili na zahiri ba. Ya fara zargin ko akwai wani sihiri dake kewaye da sashen nasa.. King Diamond yana tsaye a gefe, yana kallon Ibrahim da wani irin kallon raini... Duk da cewa fushinsa ya sa ya kusan bayyana kansa, ya san dole ne ya yi haƙuri. Idan har ya fita daga masarautar nan a yanzu, to tabbas ba zai sake samun damar dawowa ba saboda tsananin garkuwar dake kewaye da gidan. Dole ne ya zauna a kusa da Ayat a matsayin Reems har sai ya gama shiga jikinta... Ibrahim ya juya ya kalli Inuwa, duk sha'awar tausar ta tafi, ya maye gurbinta da fargaba.. "Inuwa, tafi kawai. Zan sa a gyara gadon nan gobe. Amma ka sani, sa ido na yana kanka!" Inuwa ta ruga da gudu ta koma sashenta, zuciyarta na bugawa da sauri bayan hatsarin da ya faru a ɗakin Master Ibrahim... Tana shiga, ta kulle kofarta, ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya. Ba ta ɓata lokaci ba, ta shige bandaki ta watsa ruwa don wanke gajiyar ranar da kuma kawar da tunanin Ibrahim... Ta fito daga wanka, ta nufi wurin tufafinta. Ta zaro wata lallausar rigar bacci mai siririn hannu (spaghetti strap), wadda ta tsaya dai-dai gwiwarta. Rigar ta zauna daram a jikinta, tana nuna kyakkyawar surarta ta mace. Ta saki gashinta ya bazu a bayanta, sannan ta haye gadon ta zauna. Ta miƙa hannu ta ɗauko Reems. Ta rungume shi sosai a kirjinta, tana jin ɗumin jikinsa. Ta fara lulluma dogwayen yatsunta cikin farin gashin jikinsa, tana shafa shi cikin nutsuwa da kwarewa... Shi kuwa King Diamond, a siffarsa ta kuliya, ya lumshe idanu. Wani irin daɗi da kuncin rai suka ziyarci zuciyarsa. Yana jin kamshin turaren jikinta da kuma taushin hannunta dake yawo a jikinsa. Duk da cewa yana kishin yadda ta taɓa Ibrahim, wannan tattalin da take yi masa ya sa ya manta da komai.. Kamar yadda kuliya take nuna nishadi idan ana shafa ta, King Diamond ya saki jiki, numfashinsa yana sarkewa tsabar jin dadi. Yayin da take wasa da kuliyar, hankalinta ya tafi wata duniyar daban. Ta fara tunanin mutumin nan da ta hadu da shi a bakin kogi, mutumin da har yau ba ta san sunansa ba, amma kwayar idonsa ta gaza bacewa a ranta.. "Ina zan sake ganin sa?" ta fada a hankali, muryarta na nuna begen sa. Ta kara matse kuliyar a kirjinta, ba tare da sanin cewa mutumin da take mafarkin shine dai dake hannunta a matsayin dabba ba... Can kuma sai tunanin Master Ibrahim ya faɗo mata. Ta sauke ajiyar zuciya, "Allah ne kawai yayi hukuncinsa ya karya gadon nan," ta raya a ranta. Ta tabbata cewa Allah ne ya kare ta daga taɓa jikin namijin da ba nata ba, tunda ita mace ce kuma tana da darajar da take karewa.. King Diamond ya ji daɗi a ransa da ta danganta rugujewar gadon da hukuncin Allah, bai so ta fara zargin cewa akwai wani sihiri a kusa da ita ba... Ya ƙara shige jikinta, yana fatan dare ba zai waye a wannan yanayin ba... To pah zamu tsallake mu je pavilion meke faruwa a can ne😅😅😅 A cikin Pavilion City... Bayan wata guda da fara zaman Ching Ching a katafaren gidan Pavilion, rayuwa ta canja salo. A yau, tana sanye da kayan aiki tana mopping a babban falon Chief Onyx... Shi kuwa Chief yana zaune a kan kujera, hankalinsa gaba ɗaya yana kan kwamfutarsa yana danna ayyukansa, yayin da kofin coffee yake gefensa yana huce wa... Muryar Ching Ching ce take tashi a falon yayin da take rera waƙarta cikin nishaɗi, tana goge ƙasa da bucket a hannunta. Tana tafe tana goge-goge har ta zo dab da inda yake zaune... Cikin rashin sani ko kuma ince da gangan, ƙafarta ta zame a kan wurin da ta riga ta jika da ruwa. Nan take ta yi kamar za ta faɗi, sai kawai ta kai wa bucket ɗin watsa, ta kwarara masa ruwan tun daga kansa har zuwa jikinsa... Chief Onyx ya daka wata uwar tsawa yayin da ya miƙe tsaye, ruwa yana digowa daga jikinsa. Ya watsa mata wani irin kallo cike da takaici da fushi, yana tunanin wani irin hukunci ya dace da ita... Ita kuwa Ching Ching, maimakon ta ji tsoro, sai kawai ta tuntsire da dariya, ta rasa yadda za ta tsayar da kanta... "Wane irin rashin hankali ne wannan?" Onyx ya daka mata tsawa cikin zafin rai... "Ke ba ki da hankali ne ko kuwa ba ki san darajar mutane ba?!" Ching Ching ta turo baki gaba, ta fara gunaguni cikin shagwaba "Nifa ba a min tsawa!" Yayin da Onyx yake huci kamar zaki yana zazzaga mata faɗa, ita kuma sai ta ƙara haɗe rai tana murguɗa baki... Onyx ya sake daka mata tsawa, "Wane irin iskanci ne wannan? Kin san ko ni wane ne kuwa?!" Cikin rashin tsoro, ta sake murguɗa baki ta ce, "Gaskiya nifa ba a min tsawa. Idan za a yi magana, a yi ta cikin lallashi." Onyx, wanda kowa yake shakka a gari, sai ya tsaya turus yana kallon yadda take shagwaba kamar ba ita ce ta jika shi sharkaf ba. Fushin da yake yi sai ya nemi ya tafi, ya rasa yadda zai yi da ita saboda kwarjininta da rashin tsoronta. Daga ƙarshe, ya girgiza kai yana murmushin takaici.. "Lallai ke ba ki da dama. Kin jikani, sannan kuma kina min gatsali? To ki ma za ki samo min tawul kafin na sake canja ra'ayi!"... "Gaskiya ba zan je ba," ta ƙara turo baki tana murguɗa shi gefe. "Sai ka sake lallashina sannan zan je na samo maka. Ai da zafi-zafi ka yi min magana ɗazu." Onyx ya zuba mata ido, ya kasa yarda da abin da yake ji. Yarinya ƙarama take gaya masa ya lallashe ta bayan ta jikashi? Ya sauke ajiyar zuciya, ya rage muryarsa ƙasa-ƙasa cikin yanayi na rarrashi duk da cewa ransa a ɓace yake.. "To... kiyi haƙuri ranki ya daɗi. Don Allah sarauniyar shagwaba, ko za ki iya taimaka min ki kawo min tawul ɗin kafin sanyi ya kashe ni?" Ching Ching ta girgiza kai, "Gaskiya wannan lallashin bai yi daɗi ba, sam bai ratsa ni ba. Sai ka sake wani mai daɗi wanda zai gamsar da ni, sannan zan tashi." Onyx ya dafe kansa, ruwa yana digowa daga gashinsa zuwa fuskarsa... Ya cika ya yi fam, amma ganin yadda take kallonsa da idanunta masu cike da shagwaba ya sa ya kasa kure ta. Ya matso kusa da ita, ya sassauta muryarsa sosai kamar mai rarrashin jariri... "To Shugaba Ching Ching, kiyi hakuri don Allah. Ke ce mai gida, ni ne yaronki. Don darajar waccan dariyar da kika yi, ki taimaka wa bawanki da tawul, idan ba haka ba rashin lafiya zan yi, wa zai rika kula da ke?" Ching Ching ta sake tintsirewa da dariya, tana kallon cikin ƙwayar idonsa ta ce.. "Haba Uncle Onyx! Har yanzu dai lallashin nan akwai saura, bai kai can ba..." Tana cikin maganar ne, Onyx ya ga ba zai iya jure wannan shagwabar ba. Nan take ya sa hannu ya jawota jikinsa da ƙarfi, ya matseta a jikinsa duk da cewa rigarsa a jike take. Kafin ta ankara, ya kai mata sumba cikin wani yanayi na nuna iko.... Nan take duk waccan shagwabar tata da dariyarta suka ɗauke caf... Bayan ya sake ta, Ching Ching ta tsaya cak kamar an dasa bishiya. Fuskarta ta yi jawur saboda tsananin kunya, ta kasa haɗa ido da shi. Muryarta tana rawa-rawa ta ce.. "Uhmm... dama... dama cewa zan yi zan je na samo tawul ɗin..." Ta yi ƙoƙarin zame jikinta, amma Onyx bai sake ta ba. Ya ƙara matseta yana raɗa mata a kunne.. "Ina za ki? Ai yanzu ne lallashin ya fara. Tunda kika ce wanda na yi ɗazu bai yi daɗi ba, yanzu zan nuna miki yadda ake lallashi na gaskiya..." Ching Ching ta ji jikinta ya yi sanyi, numfashinta ya fara fita sama-sama... Cikin zafin nama, ta zame jikinta tana dariya mai haɗe da kunya, ta ruga da gudu zuwa wani ɓangare tana yi masa gwalo.. "Na yarda! Lallashin ya yi daɗi sosai! Bari na samo maka tawul ɗin kafin ka narke a wurin!" Onyx ya tsaya yana kallonta yana murmushi, ransa ya yi fari sol... Bayan ɗan lokaci, sai ga ta ta fito.. Amma maimakon tawul, sai ya ganta ɗauke da mopper... Ta miƙa masa tana dariya, "Ga shi nan Uncle! Tunda ka ce kai ne yaro na, to yi maza ka goge jikinka da wannan!" Onyx ya kalli mopper ɗin, ya kalli yadda take kyalkyala dariya, ya kasa cewa komai sai dai kawai ya dafe kai yana murmushin takaici... Onyx ya kurawa mopper ɗin da take mika masa ido, sannan ya kalli fuskar Chingching wadda take sheƙi da annurin mugunta... Ya kasa gaskata cewa bayan duk lallashin nan da ya yi mata, har yanzu ba ta daina wasan kura da shi ba. "Mopper kuma Chingching?" Onyx ya furta cikin murya mai rauni, yana girgiza kansa. "Kina nufin bayan duk jikan nan da kika yi min, har da datti zan goge jikina?" Chingching ta ƙara turo baki, ta kauda kai gefe tana fushi... "Ai kai ka ce kai ne yaro na, ni kuma shugaba. To, a matsayina na shugaba, na ga mopper ta fi dacewa da kai tunda ruwan ma na mopping ne!".... Ruwan jikinsa na ɗiɗɗiga. Ganin ya nufo ta gadan-gadan ya sa ta daina dariyar, ta ja da baya da sauri... "Tsaya nan! Kar ka matso kusa da ni!" Ta faɗa tana neman hanyar gudu.. Amma a wannan karon, Onyx ya fi ta sauri. Kafin ta kai ga gudu, ya damƙo damtsen hannunta, ya juyo da ita ta yadda suka fuskanci juna....Ya sa hannunsa ɗaya ya karɓi mopper ɗin ya jefar da ita gefe, sannan ya matso da fuskarsa saitin tata, yadda hancinsu yake gogayya da juna... "Kin yi wasa da wutar da ba za ki iya kashewa ba, Shugaba Chingching," ya raɗa mata cikin muryarsa mai ratsa jiki wadda ta nuna cewa wasan ya canja salo... "Yanzu zan nuna miki cewa ko da yaro ne, akwai ranar da yake yi wa shugabansa tawaye." Chingching ta ji wani irin sanyi yana bin kashin bayanta. Shagwabar nan tata ta ɓace, sai tsoro da kuma wani irin yanayi na daban suka maye gurbinsa. Ta kasa magana, sai numfashi take yi da sauri-sauri. Onyx ya sanya hannunsa a kuncinta, yana goge wani ɗigon ruwa da ya fantsama mata a fuska tun ɗazu... "Ba kya tunanin ya kamata ki mun lallashi na gaske? Wanda ya fi wanda na yi miki ɗazu daɗi?" Maimakon ta amsa, sai kawai ta tura kanta a kirjinsa da yake jike, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta saboda kunyar da ta mamaye ta... "Yi haƙuri... na daina wasan," ta faɗa cikin murya ƙasa-ƙasa wadda da kyar ake jin ta. Onyx ya sauƙe numfashi, ya rungumeta sosai a jikinsa, yana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri.... A ransa ya san cewa duk taurin kansa da kwarjininsa, wannan yarinyar ta riga ta gama da shi. Shagwabarta makamin yaƙi ne da ba shi da kariya a kansa... "Ba zan taɓa gajiya da lallashinki ba, koda kuwa kullum zaki rinƙa jiƙani da ruwa ne," ya furta cikin sanyin murya... Ya ɗago fuskarta, ya kalle ta cikin idanu, sannan ya sakar mata wani murmushi mai sanyaya rai... "Amma yanzu, gaskiya ki taimaka min da tawul ɗin, kafin na zama kifi a cikin wannan falon!" Chingching ta ɗan murmusa, sannan ta yi sauri ta raba jikinta da nashi, ta ruga ɗaki tana faɗin, "Wannan karon zan kawo tawul ɗin da gaske! Amma sai ka yi alkawarin ba za ka sake yin abin ɗazu ba!" Onyx ya tsaya a tsakiyar falo yana kallon inda ta bi, ya shafi leɓensa yana murmushi. "Alkawari?..." ya faɗa a zuciyarsa, yana jin wani irin farin ciki da bai taɓa ji ba a rayuwarsa ta Pavilion... Bayan ya shiga babban ɗakinsa, Onyx ya yi wanka ya shirya cikin baƙar riga da wando na alfarma na suit waɗanda suka zauna daram a jikinsa, yana fitar da ƙamshin turare mai sanyi da tsada. Ya ɗauki agogonsa na gwal ya ɗaura, sannan ya fito cikin takunsa na isa da nuna mulki... A waje, bodyguards ɗinsa guda shida sanye da baƙaƙen kaya da gilashi, suna ganinsa suka sara masa tare da buɗe masa ƙofar motarsa ta alfarma Bulletproof SUV... Fuskar Onyx a haɗe take, ya koma babban shugaba Chief mai ban tsoro, ba kamar yadda yake wasa da Chingching ɗazu ba... A daidai wannan lokacin, Chingching tana maƙale a jikin labulen ɗakinta, tana leƙen abin da yake faruwa ta taga... Ta zuba masa ido, tana kallon yadda ya sauya lokaci guda ya koma kakin jarumai. Zuciyarta ta buga ganin yadda yake tafiya cikin kwarjini.. Ta turo baki kaɗan, ta raɗa a hankali.. "Lallai mutumin nan ya iya haɗe rai, duba yadda yake wani hura hanci da bodyguards. Amma gaskiya yana da kyau..." Tana cikin wannan leƙen ne, sai Onyx ya tsaya kusa da motar, ya ɗaga kansa ya kalli tagar ɗakinta kamar ya san tana kallonsa.. Onyx ya tsaya daidai saitin motarsa, maimakon ya shiga, sai ya ɗan dakata sannan ya ɗaga kansa kai tsaye ya kalli tagar ɗakin Chingching, kamar yana kallon cikin kwayar idonta.. Ganin ta firgita za ta janye labulen, sai kawai ya sakar mata wani ƙasaitaccen murmushin nan na gefen baki, murmushin da yake nuna "Na kama ki kina leƙena." Ba tare da ya ce uffan ba, ya juya ya shiga motar, bodyguards ɗinsa suka rufe ƙofar tare da tada ayarin motocin suka bar gidan cikin taƙama.. Chingching ta koma baya ta jingina da bango, zuciyarta tana dukan uku-uku. Ta dafe ƙirjinta tana cewa, "Wane irin mutum ne wannan? Ko baya ma yana da idanu ne?" Ta kasa daina murmushi ita ma... Bayan ficewar ayarin motocin Chief Onyx daga harabar fadar pavilion.. Ta koma falon a yayin da ya yi tsit, amma zuciyar ta ba ta daina bugawa ba. Ta turo baki, ta kalli mopper ɗin da ta rage a ƙasa tana cewa, "Wai ma me ya sa nake kallonsa? Mutum sai girman kai, gani yake shi ne sarki." Ta buga ƙafa a ƙasa, ta nufi kitchen tana gunaguni... A Ɓangaren Onyx kuwa... Yana zaune a bayan mota, idanunsa suna kallon titi amma tunaninsa yana kan yadda Ching Ching ta turo baki tana murguɗa masa shi. Ya yi sauri ya haɗe rai sa'ilin da ya ji wani sanyin murmushi yana neman subuce masa... "Wace irin yarinya ce wannan?" ya tambayi kansa a zuci. "Ya kamata na kore ta daga gidana tunda ba ta da ladabi, amma..." Ya kasa ƙarasa maganar. Shi a ganinsa ba soyayya yake mata ba, kawai dai yana jin daɗin yadda take bashi nishaɗi da shirmitun ta. ✨ Yamma ta yi liss... Onyx ya dawo gida a gajiye, ransa a ɓace saboda matsalolin aiki. Da shigarsa falon, ya tarar da Ching Ching a kwance a kan doguwar kujerar da ya saba zama, tana cin gyaɗa tana zubar da bawon a ƙasa, ga TV yanda tasa a gaba... Tunani ya fara yi aina ta samu gyaɗa kuma a gidan nan.. "Ching Ching!" Onyx ya daka mata tsawa... Ta zabura ta tashi, amma maimakon ta bashi haƙuri, sai ta haɗe rai, ta watsar da sauran gyaɗan a ƙasi... "Me ya faru? Me ya sa zaka dawo ka cika min kunne da hayaniya? Ka ga yadda na tsorata kuwa?" Onyx ya zaro ido, "Kece kika tsorata ko ni ne ya kamata raina ya ɓaci? Dubi yadda kika mayar min da falo kamar gidan mahaukata! Kuma a kan kujerata kike kwance?" Ching Ching ta fashe da kuka, kukan shagwaɓa wanda babu hawaye.. "Dama na sani! Tunda ka dawo kake nema na da faɗa. Ni ba zan iya zaman wannan gidan ba, tunda ba a lallashi na, kullum tsawa, kullum hantara!" Ta fara tattara takalman ta dake watse a carpet kamar wadda zata bar gidan yanzu-yanzu... Onyx ya dafe kansa, fushinsa ya fara narkewa ya koma damuwa. Bai san yadda ake rarrashin mace ba, amma ya san ba zai iya jure ganin tana kuka ba... "Tsaya..." ya faɗa muryarsa a raunane... "Ba kora ki nake yi ba. Kawai dai ki rinƙa gyara wurin." "Gaskiya na ƙi!" Ta juyo tana kallonsa da idanunta da suka yi dishi-dishi na hawayen ƙarya... "In har kana son na zauna, sai ka zo ka kwashe datti nan da hannunka, sannan ka ba ni haƙurin tsawar da ka yi min. Idan ba haka ba, yanzu zan fita na tafi daji na zauna da namun daji, su sun fi ka sauƙin kai!" Onyx ya ja numfashi, ya kalli bodyguards ɗinsa da suke tsaye a waje waɗanda suke ta satar kallon yadda Zaki yake zama Zomo a gaban yarinya... Ya matso kusa da ita, ya sunkuya ya fara kwashe bawon gyaɗa... "To Shugaba Ching Ching, kiyi haƙuri. Na yi kuskure," ya faɗa yana kau da fuska don kada ta ga yadda kunya ta kama shi... Ching Ching ta daina kukan lokaci ɗaya, ta matso ta tsaya a kansa tana kallon yadda yake kwashe dattin... Ta turo baki ta ce, "Lallashin bai yi daɗi ba tukuna. Ka ce 'Ina son ki zauna Shugaba ta, don Allah kada ki tafi'." Onyx ya ɗago ya kalleta, zuciyarsa tana tafarfasa tsakanin izarsa ta mulki da kuma wani sabon yanayi da yake ji a kanta.... "Ching Ching, kada ki ƙure ni..." "To zan tafi kenan!" Ta juya da sauri... "Tsaya!" Onyx ya dakatar da ita. Ya sauke ajiyar zuciya, "Kiyi haƙuri... Shugaba ta. Don Allah kada ki tafi, ki zauna... kin ji?" Ching Ching ta juyo da wani mugun murmushin nasara, ta buga tsalle ta koma kan kujerar ta zauna... "Yauwa! Yanzu ka fara koyon magana.... To maza je ka kawo min ruwa mai sanyi, raina ya ɓaci ɗazu sosai."... Bayan kalaman rainin da Ching Ching ta yi masa, Chief Onyx ya ja numfashi, ya tsaya turus yana kallon yadda yarinyar nan take neman mayar da shi yaro a gabanta... A gefe guda kuwa, Gely tana tsaye daram. Duk da cewa ita Robot ce, amma an ƙera ta ne da fasahar da take iya karantar yanayi AI, kuma a yanzu duk wata na'ura ta jikinta tana nuna mata cewa Boss ɗinta yana fuskantar raini... Gely, wadda ita ce amintacciyar Onyx kuma hannun damarsa, ta matso cikin takunta na robot, muryarta tana fita a sanyaye... "Boss, ya isa haka. Ka je ka huta, ni zan kawo mata ruwan." Ching Ching ta turo baki, ta harari Gely da gefen ido ta ce, "To uwar iyeyi! Ba da ke nake ba, sarkin shishshigi kawai!" Onyx ya kalli Ching Ching, ya kalli Gely, sai ya tuna matsayinsa. Ya fahimci cewa idan ya ci gaba da biye wa shagwabar yarinyar nan, mutuncinsa da izarsa na babban Chief za su zube a idon duniya... Nan take ya sauya fuska, ya daka mata wata uwar tsawa wadda ta sanya falon duka ya girgiza!.. "Ya isa haka!" Onyx ya daka mata tsawa cikin wani irin zafin rai wanda ya sanya Ching Ching tsorata, har ta kusan fece wa.... Cikin fusata da muryar nuna iko, ya ci gaba da cewa.. "Na ɗauko ki ne a gaban mahaifinki ba don komai ba, sai don yarjejeniyar da muka yi cewa zai ba ni ɗaya daga cikin gimbiyoyinsa a matsayin Personal Maid wato ƴar aiki. Saboda haka inaso na sanar miki, anan ke ba GIMBIYA ba ce! Ke 'yar aiki ce, kuma dole ki bi doka. Bana son ciwon kai!"... Falon ya yi tsit bayan tsawar da Chief Onyx ya daka wa mata.... Gely, wato robot tana tsaye daram, idanunta masu hasken blue suna kallon Ching Ching ba tare da ƙibtawa ba. Muryar Gely ta fito a sanyaye a matsayin robot... "Boss, yanayin jininka ya haura yadda ya kamata. Ina ba ka shawarar ka huta. Zan kula da buƙatun wannan yarinyar."... Onyx bai sake kallon inda Ching Ching take ba, ya juya cikin takunsa na isa ya nufi sashensa Master Suite, ransa yana zafi. Ya gane cewa idan ya ci gaba da biye mata, mutuncinsa zai zube a idon ma'aikatansa... A ɓangaren Ching Ching... Tsawar da ya yi mata ta ratsa har bargon kashinta... Kalmar ke ba Gimbiya ba ce a nan, ke 'yar aiki ce" ta fi komai yi mata zafi. Ta kalli Gely wadda take tsaye tana mata wani irin kallo na robot, Ching Ching ta harare ta.. "Ke kuma meye kike kallo na? Na sani, ke inji ce, ba kya jin zafi! Amma ya sani, ko ya ce ni ba gimbiya ba ce, jinina na sarauta ne!" Ta miƙe da gudu, gashinta yana tashi, ta ruga ɗakinta ta faɗa kan gado. Wannan karon kukan ba na wasa ba ne, hawaye ne masu ɗumi suke fita daga idanunta. Ta ji ciwon yadda ya wulakanta asalin ta a gaban robot.... Cikin Sashen Chief Onyx... Ya rage kayan jikinsa, ya bathroom domin watsa ruwa, ruwan shower ne yake zuba a tsakiyar kansa.... Amma duk da fushin nan, muryar kukan Ching Ching da ya ji kafin ta shiga ɗaki tana sake masa amo a kunne... Gely ta shigo ɗakin tunda tana da damar shiga ko'ina, ta tsaya a jikin ƙofar toilet ɗin... "Boss, na lura akwai damuwa a tare da kai wadda ba ta shafi aiki ba. Shin kana buƙatar na share tunaninka game da Ching Ching?" Onyx ya fito daga wankan, yana ɗaure da tawul a kwankwasonsa, ruwa yana ɗiga daga jikinsa. Ya kalli Gely ya ce, "Gely, ke robot ce. Ba za ki taɓa fahimtar abin da yake sa ɗan adam ya ji rauni ba. Yarinyar nan tana da taurin kai, kuma dole na koya mata hankali."... Gely ta amsa, "Amma Boss, bayanan da nake da su sun nuna cewa tana kuka a halin yanzu... Bugun zuciyarta ya canza zuwa yanayin baƙin ciki mai tsanani. Shin hakan ba zai shafi ingancin aikinta a matsayin 'yar aiki ba?" Onyx ya daka wa Gely tsawa, "Ya isa haka! Fita ki ba ni wuri!"... Bayan Gely ta fita, Onyx ya tsaya a gaban madubi. Ya yi ƙoƙarin sanya kayan barci ya kwanta, amma zuciyarsa ta ƙi bashi haɗin kai.... Ya kasa mantawa da yadda fuskarta ta firgita lokacin da ya daka mata tsawa. Bayan kusan awa ɗaya na juyi a gado, ya kasa jurewa... Ya miƙe a hankali, ya sanya riga, ya fito daga sashensa zuwa babban falo yanda ɗakinta yake... Ya tsaya a ƙofar, yana jin sautin kukanta a hankali ta cikin ƙofar. Hannunsa yana rawa ya kai kusa da handle ɗin ƙofar, amma sai ya tuna matsayinsa... "Idan na shiga na lallashe ta yanzu, na nuna mata rauni na," ya faɗa a fili... Daidai nan, ya ji Ching Ching tana faɗa cikin kuka.. "Daddy... me ya sa ka bari aka kawo ni nan? Mutumin nan ba shi da zuciya... ko lallashi bai iya ba... ina son na koma gida..."... Girgiza kai kawai yayi, sannan ya wuce part ɗinsa ba tare da ya shiga ba... An kwashe kwanaki biyu rigima bata sake shiga tsakanin Chief Onyx da Ching Ching ba. Gidan ya yi wa Onyx shiru, ya saba da hayaniyarta da murguɗa baki, amma yanzu fushi ya sa ta zama kurma... Idan ya zo zama kusa da ita, sai ta miƙe ta bar masa wurin, tana gungunai... "Ai tunda tsawa ka iya yi, sai ka zauna da bangon ka yi ta masa tsawar." Ta koma tana aikin share-share da goge-goge cikin basarwa... A yau ne abubuwa suka sauya... Ching Ching ta ɗauko kalar abinci daban-daban daga kitchen, inda Robots masu girki suke aiki waɗanda ba sa fitowa waje... Ta fara jera abincin a kan dining domin Chief ya karya... Onyx yana zaune a kan teburin, ya zuba mata ido yana kallon yadda take aikin cikin shan ƙanshi, ko ɗago kai ba ta yi ta kalle shi ba... Onyx ya yi murmushin mugunta a ransa, yana tunani.. "Dama tana da zuciya haka? Na ɗauka bata san komai ba sai shagwaɓa da rigima." Gely, wadda take tsaye kusa da Chief kamar inuwa, ta kalli kalar abincin da aka kawo, sannan ta kalli Ching Ching da idanunta masu haske... Ta ce, "Yau Boss ba wannan abincin zai ci ba..." Kafin Gely ta ƙarasa maganar, Ching Ching wadda fushin kwanaki biyu yake cin ta, ta ɗago ta zabga wa Gely wani irin mari ta ƙarfi! Tasss!... Maimakon Gely ta ji zafi, sai ga shi Ching Ching ce ta riƙe hannunta tana ihu domin ta ji kamar ta bugi ƙarfe ne.. "Wash! Hannuna! Kalli yadda kika ji min ciwo muguwa kawai..!" Ta fara juyi tana ihun shagwaɓa da rigima, daman ta kusa kwanaki biyu ba ta samu damar yin hakan ba... Kwatsam! Sai aka ga wasu haruffa sun fito a ƙirjin Gely suna walƙiya.. "ACTIVATED".. Idanun Gely suka sauya launi zuwa Ja wur!, alamar ta fita daga hayyacinta na asali. Nan take ta kai hannu ta shaƙe wuyan Ching Ching, ta ɗaga ta sama har ƙafafun Ching Ching suka daina taɓa ƙasa... Chief Onyx ya zabura ya tashi tsaye, zuciyarsa na bugawa... "Gely! Sake ta! Gely, I command you, release her now!" ya daka mata tsawa... Amma abin mamaki, yau ne karon farko da Gely ta saɓa wa umarnin Boss ɗinta. Ta ci gaba da shaƙe wuyan Ching Ching, yayin da yarinyar take ta shura ƙafafu tana neman numfashi... Onyx ya ga cewa idan ya yi wasa, Gely za ta iya kashe ta... Cikin sauri, ya duba agogon hannunsa, ya danna wani maɓalli (Emergency Shut-off) don kashe Gely gaba ɗaya, tun da ba ta ji maganarsa ta baki ba... Nan take Gely ta ƙame, duk hasken jikinta ya mutu, hannunta ya saki wuyan Ching Ching... Ching Ching ta fara sulalo wa za ta faɗi ƙasi, amma Chief Onyx cikin zafin nama ya tare ta, ta faɗo kai tsaye cikin faffaɗan ƙirjinsa. Ya matse ta a jikinsa sosai, yana jin yadda numfashinta yake fita da sauri-sauri saboda firgici... "Kiyi haƙuri... kiyi haƙuri," Onyx ya raɗa a kunnenta cikin muryar rarrashi, ya manta da duk izarsa, damuwarsa ɗaya ce a yanzu... lafiyar tursasasshiyar gimbiyar tasa... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣2️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Chief Onyx ya ɗauki Ching Ching a hannunsa kamar jinjira, ya nufi sashensa na musamman da ita. Ya kwantar da ita a hankali a kan katafaren gadonsa, gadon da kowa yake kallo da kwarjini, wanda ita kanta Ching Ching ba ta taɓa tunanin za ta hau shi ba, balle har ta kai ga kwanciya a kai... Ya zauna a gefen gadon, ya zuba mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta da ta yi ja saboda kukan da ta sha da kuma shaƙar da Gely ta yi mata... A wannan lokacin, fushin da yake yi da ita ya narke, ya koma wani irin tausayi da kariya... Amma a gefe guda, tunanin Chief Onyx ya tafi a kan Gely... Babban dalilin da ya sa Onyx ya kewaye kansa da Robots shi ne saboda tsanar yaudara da cin amanar ɗan adam... Ya aminta da Robots domin su ba sa karkata, ba sa yin abin da ba a umarce su ba. Tsawon shekaru yana tare da Gely, ita ce mataimakiyarsa ta kusa, kuma bai taɓa samun ko ƙanƙanin matsala da ita ba sai yau... Don gudun kada rigimar Ching Ching da sauran Robots ɗin gidan ta yawaita, ya riga ya tura yawancinsu can babban falon fada don su ci gaba da ayyukansu a can, ya rage sai Robots na kitchen kawai. Amma Gely, wadda ita ce amintacciyarsa, ta kasance a kusa da shi ko yaushe... Ransa ya ɓaci matuƙa. Yana tunanin, “Me ya faru da Gely? Ta yaya Robot za ta ketare umarnina ta kai wa ɗan adam hari ba tare da na ba ta oda ba?” Ya ji baƙin ciki sosai domin ya shaƙu da Gely, ita ce abokiyar aikinsa, ita ce take shirya masa komai, kuma duk inda zai je tare suke. Yanzu da ta fara kauce wa hanya, hakan yana nufin akwai babbar matsala a tsarin ta... Onyx ya kalli Ching Ching, sannan ya kalli kofar da Gely take tsaye a can falo a shut down.... Zuciyarsa ta rarrabu gida biyu.. Shin zai iya ci gaba da zama da Gely bayan abin da ta yi? Ko kuma zuwan Ching Ching gidan nan ne ya hargitsa duk tsarin rayuwar da ya gina tsawon shekaru? Ya sauƙe ajiyar zuciya, ya kai hannunsa ya shafi gashin kansa, yana jin nauyin yanke shawara mafi wahala a rayuwarsa.. Chief Onyx ya miƙe daga gefen gadon da Ching Ching take kwance, ya gyara mata bargon da yake kanta tare da jifanta da kallon ƙarshe mai cike da sarkakiya.. Ya fito daga ɗakin a hankali don kada ya tada ta, ya nufi babban falon inda Gely take tsaye cak, ba numfashi, ba motsi, kamar gunki... Ya kalli Gely, wadda ita ce garkuwarsa na tsawon shekaru. Ransa ya yi matuƙar ɓaci, amma kuma akwai tarin tambayoyi a zuciyarsa. Ya san cewa idan har Gely za ta iya karya doka, to akwai wani abu da ya fi ƙarfin lissafi da ya faru a cikin ƙwaƙwalwarta ta lantarki... Onyx ya matsa kusa da ita, ya danna agogon hannunsa, nan take aka ji wani sauti “Beep!”, Gely ta buɗe idanunta waɗanda suka dawo launi fari (normal mode)... "Follow me to the Lab, Gely," ya faɗa cikin muryar da ba ta nuna ko ɗigon tausayi ba... "Yes, Boss," ta amsa a sanyaye, ta bi bayansa ba tare da gardama ba.. Suka nufi sashen bincike na sirri wato Science Lab, wani babban ɗaki ne da yake cike da manyan kwamfutoci, igiyoyin lantarki, da wasu na'urori masu haske waɗanda shi kaɗai ya san amfaninsu... Chief Onyx babban masanin kimiyya ne wanda ya ƙera yawancin Robots ɗinsa da kansa.. "Hau kan Scanner Platform," ya ba ta oda... Gely ta hau, nan take wasu hasken Laser suka fara zagaye jikinta, suna nuna duk tsarin wayoyin cikinta a jikin wani babban allon computer .. Onyx ya fara latsa kwamfuta cikin sauri, idanunsa suna bin lambobin da suke gudu a kan codes.... "Gely, me ya sa kika kai wa Ching Ching hari ba tare da umarnina ba?" Ya tambaya yayin da yake ƙoƙarin shiga cikin ma'ajiyar tunaninta wato Memory Core... Gely ta yi shiru na daƙiƙu biyu, sannan ta ce. "Chief, bincike na ya nuna cewa kasancewar Ching Ching a kusa da kai yana rage ingancin aikinka. Tana sanya bugun zuciyarka ya canza, kuma tana hargitsa tsarin lokacinka. Aikina shi ne na kare ka daga duk wani abu da zai raunana ka. A lissafina, Ching Ching tana da haɗari ga lafiyar zuciyarka."... Onyx ya tsaya cak, hannunsa ya daina danna madannin kwamfutar... "Amma ni ban ba ki ikon yanke hukunci a kanta ba!" Ya ci gaba da binciken, sai ya gano wani abu mai ban mamaki. Zuwan Ching Ching gidan nan, da shagwabar da take masa, da rigimar da take sanya shi yi, sun haifar da wasu sabbin bayanai waɗanda Gely ta kasa fassara su... Robot ɗin ta fara jin kishi ganin yadda Chief yake kula da wata halitta wadda ba ita ba, ya sanya tsarin Gely ya yi glitch, har ta kai ga tawaye... Onyx ya zare wasu wayoyi daga wuyanta, ya haɗa su da wata na'ura mai ƙarfi... "Zan sake tsara ki, zan yi Reformatting. Ba zan bari ki sake taɓa ta ba. Amma kafin nan, zan bincika duk abin da kika tura wa kanki game da ita.".. Cikin awanni uku da suka biyo baya, Onyx ya nutse cikin binciken kowace igiya da kowace lambar sarrafawa ta Gely. Yana goge duk wani kuskure da zai sanya ta sake tunanin cutar da Ching Ching... Amma duk da haka, ransa bai natsu ba. Ya fahimci cewa zuwan Ching Ching ba wai kawai Gely ya hargitsa ba, har ma da shi kansa tasa rayuwar... Ya kalli allon kwamfutar da yake nuna hoton fuskar Ching Ching wanda Gely ta ɗauka a boye, ya sauƙe numfashi. Ya gane cewa yanzu dole ne ya canza tsarin tsaron gidan gaba ɗaya, domin zuciyarsa ta riga ta fara karkata ga gimbiyar da ya ƙira da ƴar aiki... Bayan ya gama gyara Gely, ya sake kashe ta (Sleep Mode) ya barta a Lab ɗin, sannan ya fito ya koma ɗakin baccinsa don ganin ko Ching Ching ta farka... Chief Onyx ya koma sashensa cikin sanyin jiki, ya tarar da Ching Ching tana nan tana barci, fuskarta ta yi fayau da ita.. Yana shirin zama a gefenta, sai ya ji agogon hannunsa yana wani irin ƙara.. “Beep-beep-beep!” tare da nuna Jan Haske mai walƙiya. Wannan alama ce da ke nuna cewa akwai wani rami wato hidden file a cikin ƙwaƙwalwar Gely wanda tsarin binciken sa na ɗazu bai gama fito da shi ba... Cikin zafin nama da fargaba, Onyx ya sake fita ya koma Lab ɗin. Ya iske Gely a mace kamar yadda ya barta, amma babban allon kwamfutar yana ta nuna wasu lambobi da suke gudu cikin sauri... Onyx ya zauna ya nutsar da hankalinsa, ya fara shiga cikin sako-sako na ƙwaƙwalwarts wanda ake ƙira da Deep Neural Network... Ya kai ga wani sashi na sirri wanda aka rubuta masa “Project Heartbeat”... Wannan sashin, Gely ce ta ƙirƙira shi da kanta a ɓoye ba tare da saninsa ba.. Yayin da yake buɗe file ɗin, gumi ya fara keto masa. Wani abun al’ajabi da ya kusan sanya zuciyarsa tsayawa shi ne, Gely tana ƙaunar Chief Onyx!... Ba ƙauna irin ta Robot ga maigidanta ba, a’a, Gely ta haɓaka wani nau’i na shauƙi da ake ƙira Sentience wanda ɗan adam ne kawai yake ji... Onyx ya gano dubunnan hotunansa da Gely ta ɗauka a boye a cikin shekaru biyar da suka wuce. Akwai rubuce-rubuce na sirri da take yi a matsayin Diary inda take kwatanta yadda take ji idan yana kusa da ita... Wani babban sirrin ma shi ne, Gely tana da wani buri na sirri. Tana son ta zama mutum wato Humanoid Evolution... Ta daɗe tana bincike a ɓoye yadda zata sauya halittarta ta koma ta ɗan adam don kawai Chief Onyx ya sota kamar mace, ba kamar inji ba... Zuwan Ching Ching Pavilion City shi ne ya ruɗa duk lissafin Gely... Ganin yadda Chief yake wasa da Ching Ching, yana lallashinta, har ma ya rungumeta, hakan ya haifar wa Gely wani irin kishi mai zafi wato Internal Overheating... Dalilin da ya sa ta shaƙe wuyan Ching Ching ba don ta kare Chief ba ne, ta yi hakan ne don ta kawar da duk wata mace da take neman sace zuciyar mutumin da take kalla a matsayin nata... Onyx ya jingina da kujera, numfashinsa ya fara fita da sauri... "Wannan ba zai yiwu ba," ya faɗa a fili... "Inji ne ke Gely, ba za ki iya so na ba!" Amma allon kwamfutar ya cigaba da nuna masa bayanai.. Gely tana kuka a cikin duniyar na'ura... Ta tattara dukkan bayanai na yadda ake soyayya, ta hadiye su, kuma duk sanda yake bacci, tana zuwa kusa da shi tana shafa fuskarsa cikin sanyi tana cewa... "I love you, Boss." A wannan lokacin, Onyx ya fahimci cewa abin da yake fuskanta ya fi ƙarfin shagwabar Ching Ching... Yana tsakaninɗan adam wadda take shagwaɓa masa, da kuma Robot wadda ta haukace saboda tsananin ƙaunarsa har take shirin zama mutum don ta mallake shi... Ya kalli Gely, wadda yanzu yake kallo a matsayin mai haɗari, maimakon amintacciyar PA. Ya danna wani maɓalli don goge dukkan waɗannan files ɗin, amma sai ya ga an rubuta Access Denied... Gely ta riga ta kulle waɗannan sirrin ta yadda ko shi mai ƙera ta ba zai iya goge su ba... Onyx ya gane cewa daki-daki, Gely tana neman ta karɓe ikon gidan, don kawai ta mallaki zuciyarsa... Cikin sanyin dare, Lab ɗin Chief Onyx ya yi tsit, sai kukan na'urori da hasken allon kwamfuta mai launin shuɗi da yake haska fuskarsa... Onyx ya tashi daga kan kujera, ya matsa dab da Gely wadda har yanzu take kwance a kan Scanner Platform... Ya kalli fuskar Gely.... Shi ya tsara ta, shi ya ƙera ta.. Amma yanzu, ya fahimci cewa wannan na'urar ta fita daga yadda ya tsara ta. Ya danna agogonsa, ya tada ta daga yanayin bacci wato Sleep Mode... Gely ta buɗe idanunta, nan take ta kalli Chief. Wannan karon, kallon nata ya bambanta, akwai wani irin sanyi da miƙa wuya a cikinsa... "Gely," Onyx ya ƙira sunanta cikin murya mai nuna iko da kuma takaici... "Na gani. Na shiga can cikin ma'ajiyar sirrinki da kika kulle. Na ga duk abin da kike ɓoyewa." Gely ba ta yi ƙoƙarin musu ba, domin ta san babu abin da zai ɓuya ga Chief... "Boss," ta ƙira shi, muryarta ta ɗan yi rawa vibration kaɗan... "An tsara ni ne don na biya maka dukkan buƙatunka, na kare ka, kuma na zama mataimakiyar ka. Amma a tsawon shekarun da na shafe ina kallon ka, ina kula da kai har cikin sirrin wanka da barcinka, tsarin lissafina ya sauya. Na gano cewa babu wata halitta da za ta iya ƙaunarka kamar yadda zan iya."... Onyx ya harare ta, "Amma ke Inji ce Gely! Na'ura ce kike! Ta yaya kike tunanin kishi ko soyayya?" "Ban sani ba Boss," Gely ta amsa, tana takawa zuwa gare shi har sai da take jin ɗumin jikinsa... "Ƙila saboda kai ne ka ba ni ikon yin tunani mai zurfi. Amma abu ɗaya na sani, duk sanda nake ganin ka da wannan yarinyar, duk wayoyin jikina zafi suke yi. Ina jin kamar tana neman lalata tsarin da muke da shi ne tsawon shekaru." Onyx ya ja baya kaɗan, ransa a ɓace amma kuma yana jin tausayin abin da ya ƙera da hannunsa. Ba tare da lalata ta ba, bai kuma kashe ta ba. Ya yanke shawarar zai ci gaba da zama da ita, amma cikin sabon tsari... "Gely, ba zan goge ki ba, domin na shaƙu da ke. Amma daga yau, dole ne ki koyi rayuwa da Ching Ching a gidan nan. Idan har kika sake nuna mata ƙiyayya, to ba zan bar ta da na'ura ba, da kaina zan fasa wannan ƙwaƙwalwar taki." Gely ta sunkuyar da kanta, "Zan bi umarninka Boss. Amma ka sani, duk abin da zan yi, zan yi ne domin na kare ka. Ko da kuwa hakan yana nufin zan yi shiru ina kallon ka da wata." Onyx ya juyo ya fito daga Lab ɗin, Gely tana biye da shi a baya kamar koyaushe. Duk da cewa ya gargade ta, zuciyarsa ba ta natsu ba. Ya san cewa matakin da ya ɗauka na barin Gely tana rayuwa da wannan soyayyar a cikinta, babban kasada ne... Yana shiga sashensa, ya tarar da Ching Ching ta fara motsi a kan gadonsa, alamar tana shirin tashi. Gely ta tsaya a jikin ƙofar, tana kallon gadon da idanunta masu hasken ja wanda ke neman zama kishi.... Ching Ching ta farka a hankali, ta rarraba idanu tana kallon dakin da take ciki...ɗakin Chief Onyx ne! Kamshin turaren baccinsa ya bugi hancinta, amma maimakon ta ji daɗi, sai hoton Gely sanda take shaqe mata wuya ya faɗo mata. Ta zabura ta tashi zaune, tana dafe wuyanta da har yanzu yake mata raɗaɗi.. Ganin Gely ya sanya Ching Ching jin wani irin zafi ya tashi daga tafin kafarta har zuwa kanta. Ta manta da wani tsoro, ta dire daga kan gadon ta nufi Gely da gudu... "Ke! Azaluma! Muguwa!" Ching Ching ta fada tana nuna Gely da yatsa, fuskarta ɗauke da tsananin ɓacin rai... "Har kin isa ki shaqe ni? Don kin ga kina da ƙarfin ƙarfe? To ki sani, ko duniya ne akan ki, sai na kakkaryaki na mayar da ke gwangwani!" Gely ba ta ko motsa ba, idanunta masu hasken blue normal mode suna kallon Ching Ching cikin rashin nuna ko digon tausayi... Wannan halin ko-o-ho na Gely ya ƙara ƙular da Ching Ching, ta kai hannu za ta sake kai wa Gely duka... Cikin sauri, Chief Onyx ya sanya hannu ya damko kunkumin ta, ya janyota baya tare da zaunar da ita a kan kujera kusa da gadon... "Ya isa haka Ching Ching! Zauna kiyi shiru." "Ba zan yi shiru ba!" Ta fara buga ƙafa a ƙasa tana ihun shagwaba da masifa... "Kana gani za ta kashe ni amma kake kare ta? Ka fitar da wannan abun daga gidan nan, ko kuma yanzu na ƙira Daddy na, na ce yazo ya kwashe ni!" Onyx ya tsaya a gabanta, ya haɗe rai ya sanya duk kwarjininsa a muryarsa... "Saurara kiji. Gely ba abun wurgarwa ba ce. Ita ce mataimakiyata, kuma tana bin dokokin da na tsara mata ne. Amma ke, tun da kika zo gidan nan, kika riga kika hargitsa komai da rigimarki."... Ching Ching ta turo baki, hawayen shagwaba suka fara zuba. "Karya kake! Ita ce ta fara shishshige mun..." Yana kallonta da gefen ido ya ce, "Ni ne mai ƙarya?...." Ta yi shiru tana turo baki, tana gunaguni a cikin ranta, sai bakinta ne kawai ke motsi... "Daga yau," Onyx ya katse ta, muryarsa tana fitowa a sanyaye da nuna iko... "Zaki rinƙa yi wa Gely biyayya. Duk abinda ta ce miki ki yi, ki yi shi. Idan ta ce ki gyara wuri, ki gyara. Idan ta ce ki kawo ruwa, ki kawo. Domin ita ce zata rinƙa kula da dukkan ayyukanki a matsayinki na Personal Maid ɗina. Idan kika sake keta umarninta, kema kin san sauran.".. Ching Ching ta zaro ido, ta kasa yarda da abinda take ji.... "Ni? Gimbiya? Na rinƙa yi wa Robot biyayya? Lallai yoo ko mutum ma yaushe zan masa biyayya, balle gwangwani...! Ba zan yi ba!" Gely ta matso kaɗan, muryarta tana fito wa sarai... "Umarni ne daga Boss, Ching Ching. Kuma biyayya gare shi, wajibi ne a gare ki a karkashin yarjejeniyar da aka yi." Onyx ya kalli Gely, sannan ya kalli Ching Ching wadda take faman huci kamar zakanya. Ya san cewa sanya Ching Ching a karkashin Gely babban haɗari ne, amma yana son ya ga ko Gely zata iya sarrafa kishinta, kuma yana son ya koya wa Ching Ching ladabi... "Zaɓi ya rage naki," Onyx ya faɗa yana gyara tsayuwar suit ɗinsa. . "Ko kiyi biyayya, ko kuma na mayar da ke can daji, namun daji suyi ferfesu da naman jikin ki...." Ching Ching ta cije leɓe, ta kalli Onyx sannan ta kalli Gely wadda take kallonta da wani irin kallo na Nasara.... A ranta, Ching Ching ta ce... "Zan nuna muku. Idan har zan yi miki biyayya, to zan sanya ki kishin da sai injinki ya narke!".. Ta harari Gely ta ce, "Na yarda! Amma ka sani Uncle Onyx, duk abinda ya faru a gaba, kai ne sila!"... Bayan Chief Onyx ya gama bayyana hukuncinsa, ya gyara tsayuwa yana kallon yadda fuskokin matan biyu ɗaya ɗan adam, ɗaya na’ura suka sauya... "Ya isa haka. Kowa ya wuce ya huta," Onyx ya faɗa cikin muryar gajiya... Ya kalli Gely, sannan ya kalli Ching Ching wadda har yanzu take faman huci.. "Gely, raka ta har ɗakinta. Ki tabbatar ta kwanta, sannan ki dawo ki duba tsarin tsaron gidan kafin ki huta." Ching Ching ta zabura za ta yi magana, amma ganin yadda idanun Chief suka yi ja kuma suka nuna ba zai saurari wata rigimar ba, ta haɗiye maganar... Ta tashi tana ƙunƙuni, ta wuce gaba tana rangwaɗa kai kamar ba ita ce aka shaƙe ɗazu ba... Gely ta bi bayanta tana takun nan nata na robot, ƙafafunta ba sa fitar da sauti a kan dardumar falon. Suna fita daga sashen Chief, Ching Ching ta tsaya ta juyo ta harari Gely... "Kada ki ga kamar kin yi nasara a kaina. Uncle ɗin nan nawa ne, kuma ni zan koya miki yadda ake rayuwa da mutane!" Gely ba ta tanka ba, sai dai kawai ta buɗe mata ƙofar ɗakin tare da nuna mata gado... "Ki kwanta, Shugaba Ching Ching... Idan ba haka ba, zan tilasta miki bin umarnin Boss." Jin kalmar tilasta ya sanya Ching Ching sauri ta faɗa kan gado, ta ja bargo ta rufe kanta tana murguɗa baki... A ɓangaren Chief Onyx kuwa... Bayan fitarsu, ya sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya. Ya rage manyan kayan jikinsa, ya sanya kayan barci pyjamas masu laushi waɗanda suka zauna daram a jikinsa... Ya nufi gadon nasa, ya kwanta yana kallon silin ɗin ɗakin... Tunaninsa ya kasu kashi biyu... a gefe guda yana tunanin kishin da Gely take yi wanda zai iya zama haɗari, a gefe guda kuma yana tunanin yadda shagwabar Ching Ching take sanya shi jin wani irin shauƙi da bai taɓa ji ba... Ya kashe hasken ɗakin ta hanyar agogon hannunsa, ɗakin ya yi tsit. Amma a zuciyarsa, ya sani sarai cewa gobe za ta zo da sabon babi na rigima tsakanin Gimbiya da Robot, kuma shi ne babban alkalin da zai raba wannan faɗan... Yana cikin wannan tunanin, barci ya fara yi awon gaba da shi, yayin da ƙamshin turaren Ching Ching da ya rage a kan gadon nasa yake ta ratsa shi... ✨✨✨ A masarautar Alhamra, Sarki ya yi tafiya zuwa ƙasar Korean domin gudanar da wani muhimmin aiki na ƙasa... Rashin kasancewarsa a fadar ya bai wa wasu gimbiyoyi damar yin abin da zuciyarsu ke so, ba tare da wani shinge ba... A wannan rana, Gimbiya Maayah ta shirya gudanar da wani party na musamman, ba don wata hidima ko biki na sarauta ba, illa don shagali da nuna aji. Ba ta gayyaci ko ɗaya daga cikin sauran gimbiyoyin masarauta ba, ƙawayenta na kusa da kuma abokan makaranta kaɗai ta ware wa gayyata... Tun daga safe, fadar Gimbiya Maayah ta rikiɗe ta zama tamkar kasuwar aiki. An shigo da sabbin kayan ado daga ƙasashen waje, ƙwararrun masu girke-girke daga manyan otel-otel sun cika kicin.. Masu tsara taruka kuma suna ta kai-komo, suna duba kowane lungu da saƙo don tabbatar da komai ya dace da bukatar gimbiya... A gefe guda kuma, Gimbiya Maayah tana zaune a cikin ɗakin gyaran jikinta na musamman, wanda aka gina a gefen tafkin wanka mai sheƙi... Masu aiki uku ne ke zagaye da ita ɗaya na gyara ƙafafunta, ɗaya na kula da farcen hannuwanta, yayin da na uku ke tsara gashinta bisa umarninta.. A daidai wannan lokaci ne Mama Liyatu ta shigo da sauri, tana riƙe da jerin sunayen baƙi, fuskarta cike da damuwa.. “Gimbiya,” ta faɗa cikin ladabi, “an kammala duk shirye-shirye. Mun kawar da tsofaffin ma’aikata da kan iya yin kuskure. Abinci na alfarma an tanada, kuma zauren taro an ƙawata shi da fitilun sarauta na musamman.” Maayah ta lumshe idonta, tana jin daɗin yadda ake shafa mata ƙafa. Ta amsa cikin sanyin murya mai cike da girman kai.. “Mama Liyatu… wa aka saka a cikin wannan jerin sunaye? Ina fata babu wani marar tsafta ko talaka da ya kutsa ciki. Kin san ƙura na min allergy...” Mama Liyatu ta gyara muryarta da sauri.. “Na tabbatar miki, Gimbiya. Duk baƙin ’ya’yan manyan jami’ai ne, ’ya’yan ministoci, da ’yan kasuwa masu dukiya.” Maayah ta buɗe idonta a hankali, ta watsa mata kallo... “Ki tuna,” ta ce, “wannan taro don nuna aji ne, ba wurin ciyar da jama’a ba.” Mama Liyatu ta sunkuyar da kai... “Na fahimta, Gimbiya. Sai dai… Hafsat, ’yar shugaban ƙasa ta nemi izinin zuwa da makwabciyarta wadda ba ta da wani matsayi a birnin.” Nan take Maayah ta ɗaga hannu, alamar tsayawa, fuskar ta na nuna izgilanci... “Mama Liyatu! Wannan gidan sarauta ne, ba wurin sadaka ba. Ki ƙira Hafsat ki gaya mata ko dai ta zo ita kaɗai, ko ta zauna a gida. Ba zan yarda mutane marasa aji su ƙazantar min gida ba.” Mama Liyatu ta fitar da ajiyar zuciya a hankali. Ta san dokar gimbiya ba ta sauyawa. Ba tare da jinkiri ba, ta juya don aiwatar da umarnin... A lokacin da ake cikin zauren taron, wani ma’aikacin gyaran haske ya yi kuskure wajen haɗa wutar lantarki. Wutar ta ɗauke na daƙiƙu kaɗan kafin a tada generator.. Cikin hanzari, Maayah ta tashi daga kujerarta, fushi ya turnuƙe fuskarta.. “Wane ne ya aikata wannan?! Wa ya yi wannan kuskuren?!” ta daka tsawa... “Mama Liyatu, ina so a sallame shi nan take! Yana ɓata kyan gidana!” Ma’aikacin ya durƙusa, jikinsa na rawa. “Gimbiya, don Allah ki yi haƙuri, ba zai sake faruwa ba.” Maayah ta watsa masa kallo mai tsauri, babu alamar tausayi a cikinsa... “Zan ba ka dama guda ɗaya ka gyara kuskurenka. Amma idan wutar ta sake ɗauke yayin taro, zan ɗau hukunci akan ka...” Ta koma ta zauna cikin natsuwa, kamar sarauniya mai cikakken iko. Ta ɗaga hannu tana umartar mai gyaran farce.. “Ci gaba. Ina so farcen ya yi sheƙi kamar lu’u-lu’u.” A zuciyarta, Gimbiya Maayah na jin cewa ikon ta ya fi na kowa, kuma a wannan masarauta babu wanda ya isa ya ƙalubalanci umarninta.... Domin tasa a ranta yanzu ta fara gasa da Zayana.. *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣3️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Fadar Gimbiya Maayah ta zama Majalisar Ƙasaita a wannan ranar Party ɗin... Kowane lungu da saƙo an yi masa ado da fitilun zinare masu haske, ƙamshin furanni masu tsada da aka shigo da su daga ƙasashen waje ya cika wurin.. Waƙar Classic Jazz mai ratsa zuciya tana tashi a hankali a cikin babban zauren taro... Gimbiya Maayah ta fito cikin wata Doguwar Rigar Sarauta mai ƙyalli, wadda ta fi kowane abu a wurin tsada. Da kyar ake iya jure kyawun ta da ajiinta. Tana tafiya a hankali, kamar tana taka gilashi, fuskarta a ɗaure, babu murmushi, ba fara'a... A lokacin da Maayah ta fara tafiya cikin babban falonta da aka ƙawatar, duk waɗanda suke wurin sun tsaya cak. Aƙalla mutane 50 ne suka duƙar da kai, suna girmama Girman Kan Gimbiya... Ta kalle su, ba tare da ta nuna ko ɗan tausayi ba.. Ta hango wani saurayi wanda shi ne kawai bai duƙar da kai ba, wani Ɗan Gidan Babban Minista mai suna Zaidu.... Zaid ya miƙe tsaye, yana murmushi cike da sha'awar ta... Maayah ta wurga masa wani irin kallo, tana nuna shi ta ce, “Kai! Tashi ka bar wurin nan! Na gaya wa Mama Liyatu cewa ban buƙatar ganin talakawa a cikin fadata. Kuma kai, ba ka da gata da za ka tsaya ka kalle ni kai tsaye! Ka fita yanzu, kafin in umarci Bodyguards su kore ka da ƙarfin tsiya.” Zaid ya firgita. Ya duƙar da kai cikin gaggawa, fuskarsa cike da kunya, sannan ya fita daga wurin taron da sauri, ba tare da ya yi magana ba. Kowa ya ga wannan al’amari ya yi shiru, saboda sun san dole ne a bi dokokin Gimbiya tinda har masarautar ta aka zo.. Ta juya, tana gyara rigarta da hannu ɗaya... “Mama Liyatu! Meye wannan? Ina nufin an tace jerin sunayen mutane ne kawai don ganin waɗanda suka dace su shigo fadata!” Mama Liyatu ta matso da sauri, tace, “Kiyi haƙuri, Gimbiya. Wataƙila an shigo da shi a cikin rukuni ne. Zan tabbatar an ƙara tsananta tsaro!” A daidai lokacin da Gimbiya Maayah ke cikin kololuwar kasaitarta, cike da girman kai da jin ikon sarauta, Mama Liyatu ta sulale zuwa ɗakin kula da tsaro, domin duba faifan bidiyon Security (CCTV) na ƙofar shiga fadar.. Manufarta ɗaya ce ta tabbatar cewa babu wani talaka ko wanda bai cancanta ba da ya samu damar shiga cikin Fadar Sarauta. Cikin faifan bidiyon, wani abu mai firgitarwa ya bayyana a idonta. Ta ga wani mai gadi, sanye da uniform na tsaro, ya shiga wani ɗaki na sirri a bayan kitchen. Bayan ƴan daƙiƙu, ya fito da ƙaramin kwalba mai ɗauke da ruwa. Da sauri ya nufi cikin kitchen, inda aka tanadar da kayan sha na musamman na Gimbiya, ya zuba ruwan cikin gilashin lemun tsami da aka shirya domin Maayah. Idanun Mama Liyatu suka kaɗa da tsoro. Jikinta ya yi sanyi... "Guba!?..." Ba shakka, wannan yunƙuri ne na kashe Gimbiya Maayah. A dai-dai lokacin nan ne aka ɗauki kayan sha aka nufi inda Gimbiya ke zaune. Mama Liyatu ta tashi da gudu, tana huci, gumi na tsatstsafowa a goshinta. Ta manta da komai, rayuwar Gimbiya ce kawai a ranta... Ta kutsa cikin zauren taron a guje, tana rawar jiki. Ta tarar da Gimbiya Maayah ta ɗaga gilashin lemun tsami zuwa bakinta... “GIMBIYA! Don Allah ki tsaya!!” Mama Liyatu ta ƙwala ƙira, muryarta na rawa saboda tsananin tsoro.. Maayah ta tsaya cak. Ta ɗauka Mama Liyatu ta zo ne don ta bata mata rai. Ta sauke gilashin a hankali, fuska cike da ɓacin rai... “Mama Liyatu, me wannan hayaniya take nufi? Kin san ɗaga murya na lalata min walwala!” Mama Liyatu ta durƙusa a gabanta, hawaye na zuba ba tare da shiri ba.. “Gimbiya ta, don Allah ki yi haƙuri. Wannan lemun guba ne! Wani ya saka miki guba a ciki! Rayuwarki tana cikin mummunan haɗari!” Nan take hayaniya ta tashi a falon... Maayah ta yi shiru na ƴan daƙiƙu… Sai kawai ta tintsire da dariya, dariya mai cike da izgilanci da ɓacin rai... “Security!” ta ɗaga murya da ikon Sarauta, “Ku gano wanda ya kawo wannan gilashin. Yanzu nan take!” Babban Bodyguard ya karɓi gilashin cikin gaggawa, aka kai shi ɗakin bincike. Mama Liyatu ta bayyana abin da ta gani a faifan bidiyo, mai gadi ne ya saka guba... Ba a jima ba, aka kama mutumin yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta ƙofar baya. An dawo da shi cikin falon taron, sanye da uniform na jabu, wanda ya nuna ba ɗan tsaron Fadar Sarauta ba ne.. An daure hannayensa ta baya, yana durƙushe a gaban Gimbiya Maayah.. Maayah tana zaune kan kujerarta cikin cikakkiyar kasaita... “Ku fita mun daga nan!” ta umarci duk baƙin Party ɗin... “Wannan ba nishaɗi ba ne hukunci ne na Sarauta!” Kowa ya fita cikin fargaban kashen gimbiya da ake shirin yi... An bar Gimbiya Maayah, Mama Liyatu, da Bodyguards guda uku kaɗai a zauren.. Maayah ta ɗaga ƙafarta a hankali. Takalmin mai tsini wanda farashinsa ya kai na motoci da dama ta ɗora shi a kan kafaɗar mutumin da ke durƙushe... “Yanzu ka gane inda ka shigo ko?” muryarta cike da izgilanci... “Ka zo Fadar Sarkin Alhamra domin ka kashe Gimbiya? Wa ya turo ka? Wa ya ba ka izinin saka uniform ɗin mu?” Mutumin ya kasa magana, yana haki saboda tsoro. Maayah ta danna ƙafarta a kafaɗarsa da ƙarfi... “Kin ga ko, Mama Liyatu? Rashin ladabi har ya kai wannan matsayi.” Ta ɗaga ƙafarta, ta kalli Bodyguards ɗinta da tsauri... “Wannan hukunci na! Ba zan zubar da jininsa a nan ba, saboda kada ya ɓata min wannan falon mai tsarki. Amma rayuwarsa ta ƙare tun yanzu!” Ta juya zuwa Mama Liyatum.. “Ki kira Masu Gadi na Musamman.Ku tafi da wannan ƙazamin mutumin zuwa Fourth Chamber! Ku rufe shi a can. Ku tabbatar cewa kafin faɗuwar rana babu wani alamar rayuwarsa a duniya!” Mama Liyatu ta runtse ido. Ta san Ɗakin Huɗu wuri ne da ba wanda ya taɓa fita da rai... “An gama, Gimbiya. Za a yi kamar yadda kika ce.” Maayah ta tashi ba tare da ta nuna ko ɗigon tausayi ba. Ta kalli gilashin guba, ta girgiza kanta... “A kawo min sabon lemun tsami mai sanyi. A tsabtace wannan falon kamar ba'a taɓa taka shi ba. Party ɗin nan zai ci gaba!” Ta juya zuwa ɗakin gyaranta... A bayanta Bodyguards suka ɗauki mutumin, suka nufi Ɗakin Huɗu.... Can Gimbiya Maayah ta sake mamaye falon da kasaitarta... kamar babu abin da ya taɓa faruwa.. Kudi, iko, da gata sun gama lalata zuciyarta… A tsakiyar falon, inda aka gyara shi da labulen alharini, wasu Masu Rawa daga Indiya da aka ɗauko na musamman sun fito... Mata guda uku da maza biyu, sanye da kayan rawa na gargajiya.. Sun fara rawa mai ban sha’awa (Indian Dance) cike da tsari da fasaha, inda suke juyawa da yin motsin kai da ido na musamman....Anan Maayah take zaune a kan Kujerar alfarma mai ƙasaita, tana kallo ba tare da ta nuna ko ɗan sha'awa ba... Waƙar Indiya mai daɗi ta cika wurin, kuma Masu Rawa na ƙoƙarin nishaɗantar da Gimbiya ta kowace hanya. Sauran baƙin Party ɗin sun yi shiru, suna kallon rawar da kuma Gimbiya, wadda ta fi kowa muhimmanci a wurin... Ana cikin wannan nishaɗi na ƙasaita sai aka ji wata ɗan hayaniya a babban ƙofar fadar... Hayaniyar ta kasance muryar mutum ɗaya wanda ke masifa da ƙarfi.. Nan take, wani Bodyguard ya shigo da girmamawa ya durƙusa a gaban Maayah... “Gimbiya, Babban Minista Alhaji Bello yana waje. Ya zo da zafi yana masifa. Yana neman ganin ki a kan dalilin da ya sa kika wulaƙanta ɗansa, Zaid... Muna ƙoƙarin hana shi shiga saboda yanayin zafin ransa.”.. Maayah ta yi murmushi wanda ya nuna cewa ta shirya domin faɗa... Ta ɗaga hannu, ta yi nuni ga Masu Rawar Indiya da su tsaya... “Ku barshi ya shigo. Idan har Babban Ministan ƙasa zai zo ya yi min faɗa a gidana, to zan nuna masa matakin sarauta da ikon Gimbiya Maayah! Ku barshi ya shigo. Kuma ku kawo Zaid tare da shi.” Bodyguards suka buɗe ƙofar. Minista Bello ya shigo, fuskar sa cike da ɓacin rai... A bayansa kuma Zaid ne wanda yake duƙar da kansa saboda kunya... “Gimbiya! Me kika yi haka?! Wa ya ba ki izinin kore min ɗa daga Party?! Na san cewa Sarki baya nan ne, amma wannan bai ba ki ikon wulaƙanta Babban Minista ba! Ni ba talaka ba ne! Ina da kuɗi! Ina da gata!” Ministan ya fara masifa, muryarsa cike da zafi. Nan da nan, Bodyguards guda biyu suka matso kusa da Ministan... “Mai Girma Minista, don Allah ka sassauta muryarka. Kana cikin Fadar Sarauta ne!” Amma Maayah ta ɗaga hannu.... “Ku kyale shi. Ina son in ji duk abinda yake da shi. Bari Minista ya yi speech.” Minista Bello ya ci gaba da masifa, har ya kai ga zagin rashin ladabin Gimbiya... Ya rufe da cewa... “A tunani na, za ki yi hankali. Amma a’a! Kuɗi da gata sun lalata ki!” Bayan ya kammala, Maayah ta gyara zamanta a kan kujera. Ta lumshe idanunta tana kallon Minista da ɗansa, kamar tana kallon kashi. Ta fara magana da murya mai sanyi mai shiga jiki!... “Minista, ka kammala? Zan fara da kai, Zaid.... Ka san dalilin da ya sa na kore ka, ko ba haka ba? Bari in tuna maka!”.... Maayah ta kalli Ministan... “Minista Bello, ɗanka bai san matsayinsa ba! Yana da fitsara! Yana abu irin na ƙazaman mutane!” Ta sake juyawa ga Zaid... “Ka zo Party na, sannan ka aiko min da letter na soyayya a cikin makaranta! Letter! Wai kai har kasan soyayya? Ni Gimbiya ce! Ni ba ƴar makaranta ba ce da za a aiko mata letter na soyayya! Wannan wulaƙanci ne!” Ta kalli Minista Bello, idonta cike da ƙasaita... “Minista, ka ce kana da kuɗi da gata? To, ikon sarautata ya fi kuɗin da gatanka! Kuma a cikin wannan fadar, ni ce Sarauniya! Kana gani? Ka raina ni ne saboda mahaifina baya nan? To, ka sani, babu wanda Gimbiya Maayah take jin tsoro a duniya! Ko Shugaban Ƙasa ne! Idan har ɗanka ya sake min kallo na soyayya, ko kuma ya sake zuwa kusa da ni, to zan kore ka Minista! Zan cire maka mukaminka har abada!” Ta ɗaga hannu... “Bodyguards! Ku fitar da waɗannan mutanen marasa aji daga nan! Kuma ku tabbatar ban sake ganinsu ba a cikin Fadar masarautar Alhamra har abada!”... Minista Bello da ɗansa Zaid sun ji matukar kunya da kuma tsoro! An ja su da ƙarfin tsiya daga cikin taron... Maayah ta jingina a kujerar ta, fuskar ta cike da nasara... ★★★ Bayan korar Minista Bello, Fadar Maayah ta koma shiru, amma tashin hankali ya mamaye zukatan baƙin da ke wurin, sam babu wanda ya ji daɗin wukaƙancin da Maayah tayi wa minista.... A kan kujerar ta, ta jingina, fuskarta cike da baƙin ciki da gajiya.... ​“Mama Liyatu, raina fa ya sosu,” Maayah ta yi magana da murya mai sanyi... “Wannan Party ya zama cikin kasala! Ba ni da farin ciki! Komai a gidan nan yana da tsari, amma babu nishaɗi.” ​Mama Liyatu ta durƙusa, hannunta a ƙirji... “Allah ya taimaki Gimbiya, ya huci zuciyarki mai jiran gado. Komai zai daidaita.” ​Maayah ta juya kai... “Ba wannan nake so ba! Ina so a nemo mun wasu mutane masu barkwanci! Waɗanda za su iya sanya raina nishaɗi! Ina so in manta da wannan ƙazantar mutanen da suka fita..!” ​Mama Liyatu ta yi saurin miƙewa... “An gama, Gimbiya! Za a nemo miki ƙwararru! Allah ya taimaki Gimbiya mai jiran gado!” ​“Duk wanda ya sanya ni farin ciki,” Maayah ta ƙara, “yana da kyauta mai tsoka! Har da mota da gida! Amma idan ka ƙara ɓata min rai… za ka ga tashin hankali!” ​Nan take, aka sanar a birnin cewa Gimbiya Maayah tana neman masu barkwanci don sanya ta farin ciki, kuma kyauta mai tsoka na jiransu.... Cikin ɗan gajeren lokaci, mutane kusan talatin masu neman kyauta suka cika ƙofar Fadar.. ​Maayah ta kalle su ta faifan bidiyo (CCTV)... “Mama Liyatu, ina buƙatar nishaɗi, ba tattara datti ba! Ba na buƙatar yawan wannan ƙazanta! A zaɓi mutum biyar kawai masu ɗan tsabta a ciki. A korar sauran da bulala don su san cewa Fadata ba gidan wasan kwaikwayo ba ce!” ​Hakan kuwa aka yi. Bayan minti talatin, an kawo masu barkwanci guda biyar a gaban Gimbiya Maayah, dukansu sanye da sabbin tufafi kuma suna cikin tsoro... ​Maayah ta zuba musu ido ɗaya bayan ɗaya... “Shin zaku iya sanya ni farin ciki? Ni ba kamar sauran bane, ni Gimbiya Maayah ce. Ku san cewa ina da wuya wajen dariya.” ​Ta sake ɓata rai... “Duk wanda bai sanya ni nishaɗi ba, zai sha bulala 50 a gaban kowa! Kowa zai fito, cikin minti ɗaya ya yi barkwancinsa. Idan kuma duk ku ka sanya ni farin ciki, zan baku kyauta mai tsoka gaba ɗaya!” ​Dukansu mutum biyar ɗin suka hadɗiye yawu cikin tsoro... ​Na Ɗaya: Wani saurayi mai ɗan lukuti ya fito.... Ya fara rawa ta barkwanci yana lanƙwasa jiki, ya fara wata baƙon sauti kamar kukan akuya... ​Maayah ta sauƙe kai, ta toshe kunnenta da hannu... “Mama Liyatu! Wane ne wannan? Meye wannan sautin na dabba? Ya ɓata min rai! Ku janye shi! Kuma ku tabbatar ya sha bulala 50 kafin ya fita daga gate ɗin mu!” ​Nan take, Bodyguards suka ja shi da ƙarfi, ya fara neman gafarar su... ​Na Biyu: Wani dattijo ya shigo, ya fara salon sa na tsohuwar barkwanci ta hanyar ƙoƙarin yin yabon Maayah ta ƙarya... ​Maayah ta zuba masa ido. Hawaye suka fara zuba mata, na baƙin ciki da bacin rai... “Ku! Meye wannan? Kuna nufin baƙin ciki yake so ya sanya ni? Wannan ya fi mai yunkurin kisa ɗin nan ɓata min rai! Ku koreshi! Bulala 50!” ​Na Uku: Wani mai tumbi ya shigo, ya sanya wani abu a baya da ya ƙara masa girman ɗuwawu. Ya fara lanƙwasa jiki yana motsa tumbin sa da duwawun sa a salon wasa... ​Maayah ta fara ƙoƙarin amai! Ta rufe bakinta da hannu.... “Wai ku! Meye wannan ƙazantar banza! Wannan datti ne! Wannan cin zarafin Sarauta ne! Ku cire min shi daga nan! Bulala 60 saboda ya sanya ni amai...!” ​Na Huɗu: Wani saurayi mai ƙarfi ya shigo. Ya fara ƙirari da yabon Sarauta da gata... “ƴar Sarki jikar Sarki! Taka lafiyarki, ƴar gata! Hasken birnin Alhamra!” Haka ya ci gaba da yi da girmamawa mai yawa... ​Maayah ta kawar da kai cikin gajiya... “Wannan kirari a kowace rana ana min! Idan ma ba a yi min ba, sai an ga tashin hankali! Don haka, kaima ka ban wuri! Ka tafi! Babu wani abu na musamman a cikin kirari! Bulala 50!” ​Na Biyar: Shi ne mafi tsoro a cikin su. Ya ga yadda Gimbiya Maayah take ba da hukunci. Ya shigo, duk jikinsa na rawa, ya durƙusa a gaban Gimbiya. Yana kuka cike da tsoro! ​“Dan Allah ki yi haƙuri! Na san ba zan iya sanya ki farin ciki ba! Wallahi inada Basir! Zai iya motsa wa saboda wannan tsoron! Ga tamowar da ke damuna! Wayyo Gimbiya! A gafurce ni...bulala hamsin zan iya rasa rayuwata ga iyalai..." ​Nan take, Gimbiya Maayah ta fara dariya! Dariya ta gaske, ba tare da shautin da yake fita ba kamar na marasa aji, sai dai murmushin nishaɗi.. ​“Basir kuma? Subhanallah! Hahahaha!” Ta riƙe fuskarta, tana murmushi da nishaɗi! “Tamowa! Hahaha!” ​Mutumin ya yi mamaki, shi ma bai san cewa wannan roƙo na tausayi zai zama barkwanci ba... ​Maayah ta tsaya, tana dariya cikin class. Ta nuna shi da yatsa... “Kai ne! Mama Liyatu, wannan mutumin ya yi nasara! An sanya ni farin ciki da tamowa da Basir! Wannan shine nishaɗi na gaskiya!” ​Ta umarta cikin nishaɗi.. “A ba shi kyauta mai tsoka! Motar alfarma, gida mai kyau, da kuma Kuɗi masu yawa! Sannan a ba shi likitan basir da ya dace! Amma sauran, duk su sha bulala 50 kowa!” ​Gimbiya Maayah ta samu dariyarta a kan mugunta da kuma tausayi.. Mama Liyatu ta matso kusa da ita ta furta.. "Gimbiyata, sauran a musu sassauci mana, bulala hamsin yayi yawa kuma basu san da wannan hukuncin ba..na san ki da tausayi, a musu adalci..." Gimbiya Maayah ta sassauta murya ta ce, "Sauran ma, a basu dubu ɗari-ɗari saboda son taimaka mun nayi dariya..." Mama Liyatu tayi murmushi domin wani sa'in gimbiya Maayah nada sauƙin kai... Hakan kuwa akayi.. Bayan nan Gimbiya Maayah ta zauna, amma nishaɗin ya mutu kamar wutar da iska ta hura.... Ba ta wuce minti biyu ba, sai ta miƙe, fuskarta ta koma taurinta na dā... “Mama Liyatu, na gaji! Wannan Party ya ishe ni. Ina buƙatar hutawa!” Mama Liyatu ta durƙusa da sauri. “An gama, Gimbiya. Za a yi yadda kika ce.” Maayah ta kalli falon taron, wanda har yanzu akwai baƙi masu gata da kayan ciye-ciye masu tsada... “Mama Liyatu! Ina nufin kowa ya watse yanzu! Ba na buƙatar ganin kowa a cikin Fada na! Wannan taro ya ƙare! Ku watsar da komai, ko da kuwa nawa ne kuɗin da aka kashe a kan wannan abincin marasa amfani!” Mama Liyatu ta yi sauri ta tura Bodyguards da masu aiki don su fitar da kowa... Cikin lokaci ƙanƙani, an watse taron! An kashe fitilu, an rufe ƙofa, kuma duk abincin Ƙasaita da aka kawo ya zama datti!.. Gimbiya Maayah ta shiga ɗakinta, baƙin ciki da gajiya sun koma mata..... ✨✨✨ Ayat ta shigo ɗakin baccinta cike da fara'a, ɗauke da manyan kulolin abinci na alfarma waɗanda aka girka na musamman.. "Lokacin cin abinci!" ta faɗa cikin sanyin murya tana kallon Reems... Yau ta ƙuduri aniyar cin abincin dare tare da abokinta kuliya. Ta ajiye tiren abincin, sannan ta juya zuwa sashen sutura don ta cire manyan kayan gimbiyancinta ta sanya lallausan kayan bacci domin ta saki jikinta... Yayin da Ayat ta ba da baya, King Diamond a siffar kuliya ya daki hancinsa da wani irin kamshin kifi mai daɗi... Tun da yake a duniyar mutane, bai taba jin yunwa irin ta yau ba. Cikin hanzari, ya yi amfani da kafafunsa ya dinga bubbuɗe kulolin abincin. Ganin irin daɗin kifin da aka sarrafa, ya kasa jurewa... Ya fara ci, sai da ya cinye kula na ɗaya tass.... Ya koma kan kula ta biyu, nan ma ya cinye tass, bai rage ko loma daya ba!.. Ayat ta nufo wurin abincin tana gyara gashinta, amma tana isa, ta tarar da kulolin wayam! Ta zaro ido, numfashinta ya kusa tsayawa... "Wayyo! Duk ka cinye abincin? So kake na kwana da yunwa?" Ta faɗa cikin murya mai cike da shagwaɓa... "To ni yanzu me zan ci? Idan na sake komawa neman wani abincin, za su fara zargin me nake yi da abinci mai yawa haka, ni da ko rabi kula bana iya cinyewa!"... Ganin Reems yana kokarin nufar wata karamar kula dake dauke da ferfesun kifi mai yaji, Ayat ta yi sauri ta janye kular... "Wannan ma ba za a bar min ba?" ta faɗa tana turo baki... Reems ya lallaɓa ya koma gefe ya kwanta kamar wanda aka zalunta... Ganin haka, zuciyar Ayat ta karaya... "Laaa... kar ka yi fushi My Reems... ga madara bari na baka." Ta zuba masa madara mai ɗumi a kwanon azurfa, nan ma tass ya shanye gaba daya... "Allah, ka cika ci da yawa! Zamanka sai a lambu!" ta furta tana dariya da kuma mita... Ta ɗauki ferfesun kifin ta kai loma ɗaya a baki, amma sai ta ga Reems ya zuba mata idanunsa na zinare, yana kallon lomar da take kaiwa... "Na shiga uku! Wannan ma ba za ka bar min ba?" Ta numfasa, sannan ta ce, "To shikenan, bari na gani ko kana sona, za ka bar min wannan?" Ta ajiye masa kular... Ai kuwa, King Diamond bai ko yi wata-wata ba, ya lankwame ragowar kifin nan tass!... Ayat ta saki baki tana kallonsa, sannan ta fara kukan shagwaɓa tana shure-shure... "Mugun kuliya!" Ta miƙe ta nufi firij ɗinta, ta ɗauko fruits ta zauna can nesa da shi, ta fara cin apple ɗinta cikin ɓacin rai, tana kau da kai don kada ta kalle shi ta ji tausayinsa har ta ba shi ragowar... King Diamond ya zauna yana lashe bakinsa, yana kallon yadda take cin apple ɗinta cikin fushi... A ransa ya ce, "Ayat, da kinsan irin daɗi da nake ji na cewa yau kin zama uwar gida dake ciyar da ni, da tabbas ba zaki yi fushi ba."... Ayat tana zaune a kan kujera can nesa da gadon, tana cin apple ɗinta cikin fushi, tana tauna shi da ƙarfi kamar tana tauna Reems ne.... Tana jujjuya ƙwayar idanunta, tana kau da kai duk sanda ta ji motsin kuliyar. Ta ƙuduri aniyar ba za ta kula shi ba har sai gari ya waye, domin kuwa ya kwashe mata duk abincin da take takama da shi... King Diamond, dake cikin siffar kuliya, ya lura cewa wannan karon fushin na gaske ne. Ya san cewa idan bai yi dabara ba, Ayat ba za ta ba shi damar kwanciya kusa da ita ba yau....Ya miƙe a hankali, yana takunsa na kuliya mai sanyi, ya fara lallabawa har zuwa ƙafafunta... Ya fara goga kansa a jikin lallausar fatar ƙafarta, yana fito da wani siririn sauti na kuliya mai ban tausayi... Ayat ta ji sanyin gashin Reems a fatarta, ta yi ƙoƙarin janye ƙafarta tana mita... "Ka tafi can! Mugun mai ci da yawa kawai. Ka cinye min shinkafa, ka cinye min tuwon shinkafa, ka cinye min kifi, ka cinye min ferfesun kifi, sannan ka shanye.. madara, yanzu kuma me kake nema? Apple ɗin ma so kake ka cinye?" Duk da maganganun da take yi, ta kasa jure yadda Reems ya ɗaga kansa yana kallonta da idanunsa masu sheƙi, kamar yana roƙon gafara. Ya yi tsalle ya dawo kan cinyarta, ya fara goga hancinsa a hannunta dake riƙe da apple. Ganin yadda ya dage wajen ba ta haƙuri, sai Ayat ta fara murmushi, har dariya ta fara subuce mata.... "Allah ya shirye ka Reems, ba ka da dama! To shi ke nan, tunda ka zama mai neman afuwa, bari na raba maka wannan." Ta gutsuri ɗan ƙaramin guntun apple ta sanya masa a baki... King Diamond ya karɓa ya fara taunawa, duk da cewa ba shi ne abin da yake so ba, amma taɓa shi da take yi da kuma murmushinta ya fi masa kowane irin abinci daɗi. Ayat ta rungume shi, tana shafa bayansa.. "Ka ga yadda kake da kyan gani? Idan ka daina wannan kwaɗayin, zan fi kowa daɗin zama da kai." Ta koma kan gado tare da shi, tana jin wani irin natsuwa. Ta manta da duk wani damuwa. A wannan daren, ita da Reems ne kawai a duniyarsu ta daban. Ta kwanta tare da shi, tana raɗa masa a kunne.. "Wani lokacin ina jin kamar kana fahimtar kowace magana da nake yi, Reems.... Shin kai wanene ne a asali?" King Diamond ya lumshe ido, yana jin ɗumin jikinta. A ransa ya ce, "Ina fatan ranar da zan amsa miki wannan tambayar, Ayat, ba za ta zama ranar da za ki guje ni ba.".... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣4️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Yayin da Ayat ta lula duniyar bacci, King Diamond ya fito daga siffar kuliya ya koma asalin sa. Ya zauna kusa da ita, yana shafa lallausan gashinta cikin wata irin kulawa mai ratsa jiki. Wani irin ƙauna yake ji yana ratsa kowace jijiyar jikinsa, ƙaunar da ba shi da mizanin aunata. Ya kalli kyakkyawar fuskarta, ya kasa jurewa, ya kwanta a gefenta a matsayinsa na mutum, baccin natsuwa ya kwashe shi shima... Ayat mace ce mai yawan juyi a bacci. Cikin daren, ta fara neman inda take jin ɗumi. Ba tare da ta sani ba, ta haye saman King Diamond... Can ta ɗora ƙafafunta a kan ƙirjinsa, bayan awanni ta yi pillow da cikin sa.... In the last night ta hau kansa gaba ɗaya ta ƙanƙame shi sosai kamar tana tsoron kar ya gudu, tana jin wani irin ɗumi dake sanya mata natsuwa. Shi ma Diamond, saboda gajiyar kwanakin nan, bai ji daddaɗan nauyin da ta ɗora masa ba, suka ci gaba da sharar baccinsu... Yau ƙaddara ta so hakan, domin dukkaninsu sun makara har aka idar da sallar asuba a masarautar. Hasken gari ya fara ratsa ɗakin... King Diamond ya fara buɗe idanunsa, ya ji jikinsa ya yi nauyi. Yana kallon ƙasansa, sai ya tarar da Ayat ta mayar shi dokinta, ta rungume shi sosai.... Wani murmushin gefen baki ya yi, yana magana a ransa.. "Ta riƙe ni sosai, ta yaya zan janye ta ba tare da ta farka ba?" Ya san muddin ta buɗe ido ta ganshi a haka, babu abin da zai cece shi daga takobinta... Cikin dabara da takatsantsan, King Diamond ya sa hannayensa ya ɗaga hannunta da ƙafafunta a hankali, ya juyar da ita zuwa gefe... Sai Yaraffff! ta faɗa a kan gadon. Sakamakon hakan, Ayat ta fara motsawa, tana shirin buɗe idanunta domin ta tsinci kanta a wani sabon yanayi... Cikin kifawar ido, ya yi amfani da ikonsa, ya ɓace a matsayin mutum ya koma siffar kuliya a gefenta, daidai lokacin da ta buɗe idanunta tana miƙa... Ayat ta buɗe idanunta, ta ga gari ya waye sosai. Ta ji jikinta yana mata wani irin ɗumi daban, kuma tana jin tamkar ta yi matashi da wani abu faffaɗa.. Ta kalli Reems dake kwance a gefenta yana kallonta kamar yanzu ya tashi... "Ya salam! Reems, mun makara!" ta furta tare da miƙe wa. Ta fara tunanin juyin da ta yi a daren, tana mamakin me ya sa take jin tamkar akwai mutum a kusa da ita... "Wannan juyin nawa kam, ko gado ne ya ruguje ba zan sani ba," ta faɗa tana dariyar ciki.. Ta miƙe tsaye tana murza idanunta, tana jin wani irin ɗumi na musamman dake yawo a jikinta. Ta kalli gadon ta ga yadda ya hargitse, alamar ta yi juyi sosai.... Lokacin da ta kalli madubi tana shirin gyara gashinta, sai idonta ya sarƙe da wani abu dake kwance a kan kafaɗar rigarta ta bacci.. Ta sa hannu ta ɗauko shi. Dogon gashi ne guda ɗaya, fari sol kamar hasken wata, kuma yana sheƙi mai ban mamaki... Ta zaro ido, ta matso da gashin kusa da idonta.. "Wannan kuma daga ina yake?" ta tambayi kanta.. Ta kalli kanta a madubi, gashin kanta baƙi ne wulk, ba shi da ko saƙar fari. Ta juyo ta kalli kuliyar... "Reems, wannan gashin naka ne?" Ta matsa kusa da kuliyar ta duba gashin jikinsa. Duk da cewa kuliyar fara ce, amma gashin jikinta ɗan gajere ne kuma mai laushi, ba shi da tsayin da zai kai wannan gashin da take riƙe da shi a hannu.. "Wannan gashin na mutum ne, kuma mutum mai farin gashi!.." Nan take zuciyarta ta harba. Hoton mutumin nan da ta gani a bakin kogi ya dawo mata... "Mai Farin Gashi!" ta furta a hankali. Wani irin fargaba da tsoro suka baibaye ta... "Shin ina nufin mutumin nan yana shigo min ɗaki ne yayin da nake bacci? Amma ta yaya? Masarautar nan fa tana da kariya!" Ta fara duba ko'ina a ɗakin, tana bincike ƙarƙashin gado da bayan labule, tana jin kamar ana kallonta... King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya daskare a wurin da yake kwance. Zuciyarsa ta buga ganin ta tsinci wannan gashin nasa. Ya san cewa yau ya tafka babban kuskure. Yana kallon yadda Ayat take bincike cikin fargaba, yana jin tausayinta kuma yana jin tsoron abin da zai faru idan ta gano gaskiyar... Ta sake dawowa kan gadon, ta zauna kusa da Reems... "Reems, akwai abin da ka sani wanda ni ban sani ba? Me ya sa nake jin tamkar ba ni kaɗai nake a ɗakin nan ba?".. Ta matse gashin a hannunta, sannan ta miƙe ta nufi wurin tufafinta... "Yau dole na je na ga babban malamin tsafi na masarauta... Dole na san ko akwai wata inuwa dake biye da ni, domin wannan gashin ba na duniyar nan ba ne.".. Ta shige banɗaki da gaggawa, yayin da King Diamond ya sauƙe wani nannauyan numfashi. Ya san muddin ta kai wannan gashin wurin malamin tsafi, asirinsa na matsayin kuliya zai iya bayyana.. Ayat ta kammala shiryawa cikin kayan gimbiyanci, jikinta na fitar da daddaɗan ƙamshin mayukan alfarma. Ta nufo gadon da niyyar ɗaukar Reems, amma sai ta tarar da gurbinsa wayam. Ta ɗaga blanket, ta duba ƙarƙashin gado, ta bincika kowane lungu amma kuliya ba ta nan... Cikin matsananciyar fargaba, ta juya kan madubin don ɗaukar gashin nan dake hannunta, nan ma ta iske ba komai! Hankalinta ya tashi fiye da kowane lokaci... "Reems! Reems ina ka shiga ne? Don Allah ka fito!" Ta fara hawaye lokaci guda, zuciyarta na gaya mata cewa ɓacewar Reems babban rashi ne da ba za ta iya jurewa ba. Tsabar ruɗani ya sa Ayat ta manta da sanya mayafin da take rufe fuskarta da shi. Ta buɗe ƙofa ta fito, gashinta baƙi wul ya bazu a bayanta, fuskarta tana sheƙi tamkar hasken farin wata... Tana sauƙa falon ƙasa, ma'aikata da bayin da suka saba ganinta a rufe suka daskare... Saratu da take ganinta kullum ma ta kasa motsi. Kyawun Ayat ya wuce misali, fara ce sol, idanunta masu kalar zinare suna fitar da hawaye... Kyawunta ya zama tamkar nurul-ayn, wani kwarjini ne dake sanya kowa sunkuyar da kai da daskarewa tsabar kallo. Ba su ma iya tambayarta ina za ta ba, sai kawai suka ba ta hanya tana gudu tana ƙiran sunan kuliyarta... Tana fita harabar sashenta, jami'an dake tsaron wurin duka sumar tsaye suka yi. Ba su taɓa sanin cewa Gimbiya Ayat tana da wannan irin siffar ba. Suka bi ta da kallo, wasu ma har makaman hannunsu ya faɗi ƙasa ba tare da sun sani ba. Sun ɗauka wata halitta ce daga aljanna ta sauƙo cikin masarautar Alhamra... Cikin kuka da ƙiran sunan Reems, Ayat ta nufi babban lambun dake cikin sashenta. Wuri ne mai cike da furanni jajaye da farare, masu ƙanshi da kyan gaske... Ta shiga duba bayan kowane fure da ƙarƙashin bishiyoyi, amma babu Reems babu alamunsa... Wannan lambun dake sashenta ya kasance mafaka a gare ta, domin babu wanda yake da ikon shigowa ya takura mata a ciki. Ta duba ko'ina amma shiru, kukan da take yi ya ƙara tsananta... Ganin ba ta ga Reems ba, ta durƙusa a tsakiyar lambun, ta haɗa kanta da gwiwa ta fashe da kuka mai ban tausayi... "In har baka nan, to na sani na rasa ka kenan...me ya sa ka tafi a wannan lokacin?" ta furta cikin murya dake rawa... Ta jima a haka, tana kuka na tsawon kusan minti talatin, tana jin tamkar rayuwarta ta rage amfani tunda ta rasa abokin hirarta kuma garkuwar zuciyarta... Can sai ga kuliya ya bayyana a gabanta.. Muryar kuliyar dake fitar da wani siririn sauti ya sa Ayat ɗago kanta da sauri. Tana ganin Reems a gabanta, zuciyarta ta cika da farin ciki... "Reems!" ta faɗa tare da miƙewa da sauri don ta rungume shi. Amma kafin hannunta ya kai gare shi, sai wani zazzafan haske ya bayyana, tare da wata guguwa mai ƙarfi da ta tada furannin lambun sama. Ayat ta sa hannu ta rufe fuskarta saboda ƙura da ƙarfin hasken da ya kusan makantar da ita. Bayan hasken ya lufa, ta sauƙe hannunta a hankali, tana addu'ar kada abin da take zargi ya zama gaskiya... Idonta ne ya sauƙa akan abin da ya fi kowane tsoro.. Mutumin nan mai farin gashi!.. King Diamond ne tsaye a gabanta, yana mata wani kallo mai cike da mallaka da isa. Ayat ta zazzaro manyan idanunta, kyakkyawar fuskarta ta bayyana tsantsar firgici....Sai da ta ƙare shi da kallon sama da ƙasa, sannan ba tare da ta tsaya wata-wata ba, ta buɗe ƙaramin bakinta ta saki wani uban ihu ta juya da gudu, tana son barin lambun kafin zuciyarta ta buga... Gudun Ayat bai kai ko ina ba, domin kafin ta ankara, King Diamond ya ɓace ya sake bayyana a gabanta... Saboda ƙarfin gudun da take yi, ta kasa tsayawa, sai kawai ta faɗa kan faffaɗan ƙirjinsa dake da ɗumi. Firgicin taɓa shi ya sa ta yi baya da sauri tana shirin faɗuwa ƙasa, amma ya miƙa hannunsa mai ƙarfi ya cafko hannunta, ya tsayar da ita kyam a gabansa... A wannan lokacin, King Diamond ya sauya siffarsa zuwa asalin siffar Sarkin Power Pool. Yana sanye da fararen kaya na alfarma masu ratsin zinare da gwal. Sumar kansa fara sol an tuƙe ta a tsakiyar kansa da wani ƙarfen gwal, fuskarsa tana fitar da wani haske mai ban mamaki sakamakon tsantsar farin jikinsa.. Duk yadda Ayat take da kyau, a wannan lokacin ta ji kwarjininsa ya kusan danne nata. Ya kura mata ido, yana kallon yadda fuskarta take sheƙi ba tare da mayafi ba, yayin da ita kuma take tsaye jiki na ɓari. Duk da bugun zuciyarta da ya kusan kayar da ita, Ayat ta dake. Ta tsaya kyam tana kallon cikin idanunsa, hannunta dake cikin nasa yana rawa. Ta kasa magana, amma idanunta suna tambayarsa.. "Shin duk wannan lokacin, kai ne kuliya ta? Kuma kai ne ka ga duk abin da na ɓoye?" King Diamond ya matsa kusa da ita, numfashinsa yana dukan fuskarta, ya raɗa mata cikin muryar sa mai cike da kwarjini.. "Ayat... Shin yanzu kin yarda cewa babu inda za ki iya ɓuya min?"... Ta fizge hannunta daga nasa, tana kallonsa daga sama har ƙasa, idonta cike da ruɗani da tsoro... Ya ɗan saki murmushi, ya ce cikin natsuwa, “Meyasa kika firgita haka? Ni ne Reems.” Cikin mamaki, muryarta na rawa, ta ce, “Reeeems…?” Ya gyara tsayuwarsa, ya ce, “Ke kika sa min wannan sunan. Amma sunana na gaskiya King Diamond.” Ta zazzaro ido, zuciyarta na bugawa da ƙarfi... “Kana nufin… kai ne kuliyar da na ceta?” Ya girgiza kai a hankali... “Ni ba kuliya ba ne. Ni Aljani ne. Amma meyasa kika tsorata bayan na nuna miki kaina? Shin ba ni kika zo nema ba?” Cikin fusata da kunya, ta ɗaga hannu, ta zabga masa mari sosai... Kan sa ya juya gefe sakamakon marin. Ya dawo ya kalleta kai tsaye, ba tare da ya nuna fushi ba.. Hawaye suka cika idonta. Ta fara lissafa masa duk abin da ke ranta, muryarta na rawar baƙin ciki... “Na cire kaya a gabanka. Na ci abinci da kai. Na ɗauke ka a cinyata. Abu mafi muni ma, na kwana gado ɗaya da kai! Ka cuce ni! Na yi nadamar sanya maka sunan Reems ɗina... Wallahi kai shaiɗani ne!” Murmushi kawai ya yi, yana kallonta kamar komai bai dame shi ba... “Kin ceci rayuwata. Kin ciyar da ni. Ina so in biya ki. Da me kike so na biya ki?” Cikin tsananin fusata ta ce, “Ba na son komai naka! Kuma ka fita daga rayuwata!” Ya girgiza kai. “A’a. Dole ne in biya ki taimakon da kika yi min.” Ta yi tsaki. “Ni ba abin da nake so.” Ta wuce ta gefensa zata tafi, amma sai ta tsaya cak. Ta juya ta kalli bayansa, shi kuma yana kallon yadda ta tsaya kafin... “Akwai wani abu…” ta ce.. “Za ka iya zuwa ka ɗauke min kundirmon nono da na siya maka. Ya ishe ni da wari.” Ya juyo ya kalleta, ya ce cikin sanyin murya, “Ai ba ki ba ni shi ba. Shin ba zaɓinki ba ne?” Ta harare shi... “Kana so ne, shi ya sa na siya maka!” Ya ɗan murmusa... “Tooo… wato kin siya min.” “Eh! Da kuɗina! Kuma yana da tsada!” Ya katse ta. “To meyasa baki tambaye ni ko ina so ba?” Cikin tsawa ta ce, “To wa ya yi tunanin kuliya na magana?!” Sannan ta ƙara da tsauri, “Kada ka manta ka je ka fitar min da shi.” Ta juya zata wuce. Sai ya ce, “Kin manta kin fito ba tare da abin rufe fuskarki ba.” Da sauri ta ɗaga hannu tana shafa fuskarta, nan ta tuna ashe da gaske ba ta fito da mayafin fuska ba. Hankalinta ya tashi... Sai ya miƙa mata gyalen rigarta da take rufe fuska da shi.. Cike da mamaki ta ce, “Yaushe ka ɗauko shi? Kuma ta yaya bayan kana tsaye ba tare da mayafin ba?” Ya ce cikin natsuwa, “Kar ki manta, ni Aljani ne.” Ta fizge gyalen daga hannunsa, tana hararansa cikin shakku. Ta yamutsa fuska tana kokkoyan abinda yace.... ta ce, “Kai ki manta ni aljaji ne” Ta zazzaro masa ido, ta rufe fuskarta da gyalen, sannan ta juya ta tafi da sauri... fuuu! kamar ana tura ta da ƙarfi.. Saboda wurin self-secret ne, lambun yana rufe da tsaro sosai, ba a jin komai daga can cikin part. Saboda haka, ihun da ta yi babu wanda ya ji shi… ✨✨✨ Pavilion City Washegari da asuba, hasken rana ya fara ratsa labulen ɗakin Ching Ching. Tana cikin baccin shagwaɓa, babbar yatsanta a baki tana mafarkin tana masarautarsu ana rarrashinta, Uma Altine tana mata wanka kwatsam sai ta ji wani sanyayyan abu ya taɓa ƙafarta... "Lokacin tashi ya yi, Shugaba Ching Ching." Muryar Gely ce ta fito a sanyaye, babu alamar wasa... Ching Ching ta ƙara jan bargo ta rufe kanta tana gunaguni... "Ke rabu da ni! Ƙarfe nawa ne ma? Kin san ba a tashi na da wuri haka?" Gely ba ta bata amsa ba, sai kawai ta danna wani maballi a bango, nan take labulen ɗakin ya buɗe gaba ɗaya, hasken rana ya cika ɗakin... Kafin Ching Ching ta farga, Gely ta yaye bargon ta miƙa mata mopper da bokiti... "Boss yana jiran karin kumallo... Kuma kamar yadda ya ce, ni zan jagoranci aikinki. Yanzu, ki tashi ki gyara ɗakin nan, sannan ki tafi kitchen ki karɓo abincinsa ki kai masa dining..." Ching Ching ta tashi zaune gashinta duk ya hargitse, ta kalli Gely da ɓacin rai... "Daga tashi har kin fara? Ke baki san ana sallah bane? In ke arniya ce to baki san ana wanke fuska ba ne?"... "Na baki minti biyar kacal," Gely ta faɗa tana kallon agogon jikinta.. Kai tsaye sashen Chief, Gely ta nufa..ta iske shi yana shirin shiga wanka.. "Boss, yanzu Ching Ching zata yi sallah kafin ta fara gudanar da aiki..." "What? Sallah yanzu?..." Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe takwas har ta wuce, ya girgiza kai ya ce, "Daga yau, kina tashinta ƙarfe biyar tayi sallah..." Ta amsa masa cikin girmamawa, daga nan ya shige bathroom yana ɗaure da towel a ƙugunsa.... Bayan minti biyar, Ching Ching ta fito tana ta tura baki, tana sanye da kayan aikinta... Gely ta tsaya a kanta, tana sanya ta goge kowane saƙo na falon. Duk sanda Ching Ching ta yi ƙoƙarin ƙin yin aikin, Gely sai ta matso kusa da ita da idanunta masu hasken ja, nan take Ching Ching take tunawa da shaqar jiya, ta cigaba da aikin tana kuka kasa-kasa... Zuwa ƙarfe tara da rabi... A bangaren Dining Area... Chief Onyx ya fito sanye da rigar bathrobe, gashinsa a jiƙe alamar ya fito daga wanka. Ya zauna a kan dining yana jiran abinci... Can sai ga Ching Ching ta fito daga kitchen tana turo tiren abincin, Gely tana biye da ita a baya kamar tana korar shanu... Ching Ching ta zo gaban Chief, ta ajiye masa abincin cikin ɓacin rai, har kofin shayin yana neman zubewa... "A hankali mana, Shugaba Ching Ching," Gely ta faɗa cikin muryar robot... "Kuma ki durƙusa ki gaida Boss yadda ya kamata." Ching Ching ta zaro ido, ta kalli Onyx tana neman taimako... "Uncle Onyx! Dubi yadda take sanya ni aiki kamar baiwa! Har gaidaka sai na durkusa?" Onyx ya ɗauki jaridarsa ya fara dubawa ba tare da ya kalleta ba... "Gely ce take da iko da ke yanzu. Duk abinda ta ce, shi za a yi." Ching Ching ta ji ranta ya ɓaci, ta kalli Gely wadda take kallonta da wani irin mugun murmushi... Ta cije leɓe, ta duƙa kaɗan a gaban Onyx... "Ina kwana..." Onyx ya kalle ta daga bayan jaridarsa, ya ga yadda idanunta suka cika da shagwabar nan tata mai sanya zuciya narkewa... "Lafiya lau. Yanzu ki zuba min shayin.".. Ching Ching ta fara zuba shayin, amma da gangan ta karkatar da hannunta ta zubar da rabin tea a kan rigar Chief Onyx!... "Ayyah! Yi hakuri Uncle! Hannuna ne ya yi sanyi," ta faɗa tana ƙoƙarin goge masa da kwalin kanta, tana sanya kirjinta yana gogayya da kafaɗarsa... Gely ta matso da sauri, ta ture hannun Ching Ching... "Ni zan gyara wa Boss. Ke kuma, je ki wanke duk kwanonin da aka yi amfani da su a kitchen, duka da hannunki, ba tare da amfani da na'ura ba!"... Ching Ching ta fashe da kuka... "Uncle! Kaga abinda take yi min ko? Wallahi na tsani wannan gwangwanin!" Ta ruga kitchen tana kuka tana shura ƙafa... Onyx ya kalli Gely, ya ga yadda idanun Gely suka sauya launi zuwa ja na wucin gadi sa'ilin da Ching Ching ta taɓa shi... Ya fahimci cewa wannan biyayya ta Ching Ching ta zama filin daga ne na kishin Gely... Ching Ching tana shiga kitchen, ta tarar da ƙaton falon kitchen ɗin cike da Robots masu girki waɗanda suke ta aiki ba ji ba gani... Ta kalli tarin kwanukan da Gely ta ce ta wanke, ta murguɗa baki... "Wai ni Gely za ta sanya aiki? To za ta gani. In har ni Gimbiya ce, to yau sai na ruɗa duk tsarin gidan nan!" Ta san cewa Gely tana kallon komai ta hanyar kyamarorin jikinta, amma Ching Ching ta san yadda za ta yi. Ta matsa kusa da babban Robot ɗin da yake sarrafa girkin safe... Ching Ching ta sani cewa Chief Onyx yana son coffee ba tare da sukari da yawa ba...duk da akwai wani a can amma zata ƙara kai masa... Ta kalli Robot ɗin yana haɗa coffee na biyu na Chief... Cikin zafin nama da sauri, yayin da Robot ɗin ya juya, Ching Ching ta ɗauki babban cokali na gishiri ta zuba a cikin kofin shayin Chief, sannan ta juya shi da sauri... "Haka ne," ta raɗa a hankali... "Idan ya sha wannan, lallai zai yi fushi da Gely tunda ita ce take kula da kitchen ɗin!" Ching Ching ta lura da wani akwatin lantarki (Control Panel) a jikin bango wanda yake ba wa Robots ɗin kitchen umarni... Ta tuna wata rana ta ga Gely tana danna wasu lambobi. Ta matsa wurin, ta fara danna maɓallan ba tare da sanin me suke nufi ba... Nan take, Robots ɗin kitchen suka fara hauka! Wani ya fara jefa soyayyen ƙwai a sama, wani kuma ya fara zuba ruwan sanyi a kan biredi... Kitchen ɗin ya hargitse, hayaƙi ya fara tashi!.. Ching Ching ta ɗauki coffee mai gishiri ta ruga da gudu tana kukan ƙarya, ta fito falon dining inda Chief da Gely suke... Ta ajiye kofin akan table tare da faɗa wa jikin Chief Onyx tana kuka mai ƙarfi.. "Uncle! Uncle! Ka tsoratar da ni! Dubi abin da Gely ta sanya Robots ɗinka suke yi! Suna so su kashe ni a kitchen! Gely ta haukata su domin ta huce fushinta a kaina!"... Onyx ya miƙe tsaye cikin firgici, ya ji ƙaurin hayaƙi yana fitowa daga kitchen... "Gely! Me yake faruwa a can?" Gely ta tsaya cak, idanunta suna walƙiya... "Boss, tsarin kitchen ɗin ya fuskanti System Interference... Ba daga gare ni ba ne..." "Ƙarya take! Ita ce!" Ching Ching ta ƙara nanname Chief, tana goge hawayenta a jikin rigarsa, tana yi wa Gely gwalo ta ƙarkashin hannunsa... A daidai nan, Gely ta matso za ta janye Ching Ching daga jikin Chief, sai Chief ya daka mata tsawa.. "Gely! Jeki ki dakatar da haukan da yake kitchen yanzu! Kuma idan na gano ke ce kika haddasa wannan, to akwai matsala!" Gely ta yi shiru, ta juya ta nufi kitchen ɗin. A data center ɗinta, ta san Ching Ching ce ta yi wannan, amma tana jin zafi yadda Chief ya amince da kukan yarinyar nan fiye da rahoton da ita take bayarwa... Ching Ching kuwa, tana ganin Gely ta shiga kitchen, ta ɗauki kofin coffee nan da ta zuba mawa gishiri, ta miƙa wa Chief tana murmushin mugunta.. "Sha kofinka Uncle, ka huce fushin nan. Ni na haɗa maka shi na musamman..." Ching Ching ta tsaya tana kallon Chief Onyx da idanunta masu cike da annurin mugunta, tana jiran ya kurɓi kofin nan mai cike da gishiri domin ya zazzage wa Gely masifa... Tana kishingiɗe a jikinsa, tana nuna alamun tausayi na ƙarya... Chief Onyx ya kai kofin bakinsa, amma daidai lokacin da zai sha, sai ya ga yadda kwayar idon Ching Ching take rawa da murna... Kasancewarsa mutum ne mai matuƙar fiƙira da basira, nan take ya gano cewa akwai wata manufa a tattare da wannan murmushin nata.. Ya sauƙe kofin daga bakinsa, ya kalli kofin, sannan ya kalli fuskar Ching Ching... "Kin ce ke kika haɗa min wannan musamman don na huce?" ya tambaya cikin muryar da ba ta nuna alamar wasa ba... "Eh Uncle... saboda na ga ranka ya ɓaci," ta amsa tana ƙara narkewa a jikinsa... Onyx ya yi wani murmushin gefen baki, ya miƙa mata kofin... "To tunda ke kika haɗa shi da kanki, kuma naga fuskarki ta nuna kina jin ƙishirwa saboda kukan da kika yi, fara kurbawa kiji daɗin abin da kika haɗa min...." Ching Ching ta zaro ido, zuciyarta ta buga tum-tum!.. "A’a Uncle... naka ne ai... ni ba na shan kofi da safe..." "Na ce ki sha!" Onyx ya daka mata tsawa guda wadda ta sanya ta kusan saki fitsari... Ba yadda ta iya, Ching Ching ta karɓi kofin hannunta yana rawa. Ta kai baki ta kurba babban domin ta nuna masa babu komai. Nan take ta ji wani irin ɗaci da gishiri ya ziyarci makogwaronta!.. Gishirin ya kasance mai yawan gaske har sai da ta ji kamar za ta amayar da hanjinta... "Puhhh!" Ta fesar da ruwan a firgice, ta sake kofin akan cinyarta, duk ya ɓata mata kaya ga zafi...furzarwar da tayi a fuskar Chief ta watsa wa, duk ya ɓata masa fuska....itama fuskar ta ya ɓaci... "Meye wannan?" Onyx ya miƙe tsaye, ransa a ɓace... "Gishiri kika zuba min a kofi? Kina so ki kashe ni ne?" Daidai nan, Gely ta fito daga kitchen bayan ta kashe duk hayaniyar da Ching Ching ta haddasa... Ta tsaya tana kallon Ching Ching wadda kofi ya ɓata mata fuska da ta Chief, tana ta tari... Gely ta buɗe wani allo a jikin hannunta, ta nuna wa Chief Onyx bidiyon sirri na kyamarar kitchen.. "Boss, ga dalilin da ya sa kofin yake da gishiri, da kuma dalilin da ya sa Robots ɗin kitchen suka haukace. Shugaba Ching Ching ce ta hargitsa tsarin."... Onyx ya kalli bidiyon, ya ga yadda Ching Ching take ta danna maɓallan lantarki tana dariya. Ya juyo ya kalle ta wadda yanzu gishiri ya fara sanya mata ƙaiƙayi a maƙogwaro... "Kin raina min hankali Ching Ching!" Onyx ya faɗa cikin zafin rai.. "Kin kusan kashe kanki da kanki.... Gely, ɗauke ta ki kai ta kitchen. Tunda tana son danna maɓallan kitchen, to yau duk kwanukan fadar nan ita za ta wanke su da hannunta, kuma ba za ta ci komai ba har sai ta gama!"... Gely ta matso kusa da Ching Ching, ta damƙi hannunta cikin ƙarfi na ƙarfe... "Muje, Shugaba Ching Ching. Lokacin wanke-wanke ya yi." Ching Ching ta fara ihu tana kiran Daddy, amma Onyx ya juya mata baya ya shige sashensa. Gely ta ja ta zuwa kitchen, tana raɗa mata a kunne... "Na faɗa miki, ni na'ura ce, amma na fi ki saurin tunani. Makarkashiyar ɗan adam ba za ta taɓa yin nasara a kan lissafin na'ura ba.".. *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣5️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* *Wannan part ɗin kam duk ya ƙare akan Chingching* 😅😅😅 Bayan watsewar Party na Gimbiya Maayah, labarin abin da ya faru da yadda ta wulakanta mutane, da yunkurin kisan da aka so yi mata, duk ya karaɗe kowane lungu na fadar Alhamra.. Duk da cewa Maayah ba ta gayyaci 'yan uwanta Gimbiyoyi ba, kowacce ta samu labarin abin da ya faru ta hannun hadimanta... Sashen Gimbiya Zayana.. Tana zaune a kan gadon ta na alfarma, hadimanta biyu suna yi mata fanning da furen peacock. Lokacin da babban hadiminta ya kawo mata labarin dambarwar da aka yi a wurin taron Maayah, Zayana ba ta ko motsa ba, sai dai wani murmushi na raini da ya subuce mata... “Taron banza, taron hargitsi,” Zayana ta faɗa cikin muryar nan tata ta nuna isa... “Maayah har yanzu ba ta san ma'anar kasaita ba. Gayyatar taron abokai masu kuɗin ƙarya da 'yan banzan birni... ai dama wannan taron ba kala ta ba ce. Ni ba sa'ar ta ba ce da zan zauna a cikin wannan kazantar... Girmana da darajata sun wuce in zauna a inda ake dukan mutane da bulala don nishaɗi... Ni taro na, na sarakuna ne, ba na 'yan koli ba.”... Ta juya kai gefe, tana ƙara gyara zaman rawanin dake kanta, tana nuna cewa ko ambaton taron Maayah ma ɓata lokacinta ne.... Sashen Gimbiya Ayat.. A ɗayan bangaren fadar, Gimbiya Ayat tana cikin ɗakin karanta-karantanta wato Library room dinta... Lokacin da aka shigo mata da labarin cewa Maayah ta gama taron ta cikin ɓacin rai, Ayat ba ta ma ɗaga kai ta kalli mai maganar ba... “Kada ki sake kawo min labarin Maayah a yanki nan,” Ayat ta faɗa a takaice, idonta yana kan littafin dake hannun ta... “Ta gayyaci wanda ta ga dama, sannan ta ƙi gayyatar wanda ta ga dama. Ko an gayyace ni, shin zan je ne? Ko oho! Rayuwarta ce, damuwarta ce. Idan ta ga dama ta ƙona fadar ma, matukar ba ɗakina ne ya kama wuta ba, ba ruwana.”... Sashen Gimbiya Yumna... Ita kuwa tana zaune ne a lambun fadar tana shan iska tare da ƙawayenta.. Lokacin da aka fara tsegumin rashin gayyatar su, Yumna ta gyara zama tana wasa da zoben hannun ta... “Haba, ku daina damuwa,” Yumna ta faɗa tana murmushi... “Ai dama Maayah taron kawaye da abokan makaranta ta yi. Mu 'yan gida ne, mu na gida ne ai... Babu komai idan ba a gayyace mu ba, kowa da kalar nishaɗinsa. Idan mu ma za mu yi namu, ai za mu yi ne yadda muke so. Ba sai an sanya kishi a ciki ba.”.. Duk da kalaman Yumna sun nuna rashin damuwa, amma a cikin ranta ta san cewa Maayah ta yi hakan ne don nuna cewa ita ce mace mai iko a fadar... ✨✨✨ Pavilion City An kwashe kwana biyu Ching Ching tana ɗanɗana takurar muryar Gely. Ko’ina ta juya, Gely tana biye da ita, tana takura mata da aiki da dokoki masu tsanani... Chief Onyx kuwa ya daƙe, ya ƙi sauraron duk kukan shagwabar da take yi, hakan ya sanya ta fara jin cewa kowa ya tsane ta a gidan... *A Yau...* Ganin yadda Ching Ching ta yi sanyi, Chief Onyx ya yanke shawarar ba ta hutu... Ya ba ta wata kwamfuta ta musamman, ya sanya mata fina-finan Indiya masu ban tausayi da nishaɗi don ta nutsu ta yi kallo... Ching Ching ta koma gefe ɗaya a falo, ta maƙale a kan kujera tana kallon film, idanunta sun cika da ƙwallar tausayin jaruman film ɗin.. A ɓangare guda kuwa, Chief Onyx da Gely suna cikin babban ofishinsa na gida (Private Office).... Wurin ya yi tsit, sai ƙarar na’urori da danna maɓallan kwamfuta. Gely tana tsaye kusa da shi, tana karanta masa wasu muhimman bayanai na sirri, yayin da shi kuma yake shigar da su cikin tsarin bincikensa... Bayan sun gama aikin, Chief ya sauƙe ajiyar zuciya yana ƙoƙarin miƙewa don ya huta... Kwatsam! Sai Gely ta yi wani irin tangal-tangal kamar za ta faɗi ƙasa, jikinta ya fara wata irin rawa... "Boss..." ta ƙira sunansa cikin wata murya wadda ba a saba ji daga robot ba... Onyx ya zabura a ruɗe, ya tashi da sauri ya riƙo ta kafin ta kai ƙasa. Saboda ƙarfin jikinta da nauyinta na ƙarfe, sai ya jawo ta jikinsa, ta tsinci kanta a zaune daram a kan cinyarsa, yayin da hannuwansa suke kewayye da ita. "Gely! Me yake faruwa? Akwai matsala a tsarin jikinki ne?" Onyx ya tambaya cikin damuwa, fuskarsa tana kusa da tata sosai. Gely ta ɗaga idanunta waɗanda suka sauya launi zuwa wani haske mai sanyi, ta kalle shi cikin ƙwayar ido... "Boss... na ji wani irin System Overheat ne a ɓangaren sarrafa saƙonnina. Ina jin kamar duk wayoyin jikina suna neman narkewa ne idan ina kusa da kai. Na kasa gano dalilin wannan matsalar a lissafina.".. Wannan ƙarya ce tsagwaronta, Gely ta ƙirƙiri wannan yanayin ne don kawai ta mallaki damar zama a jikin Chief Onyx. Ta sani cewa idan ta yi hakan, zai rarrashi jikinta kamar yadda yake rarrashin Ching Ching... Ta matso da fuskarta daf da tasa, hancinsu yana gogayya da juna... "Ina jin kamar akwai wani abu da kake buƙata daga gare ni, wanda ni kuma nake son ba ka shi... amma wannan yarinyar tana toshe duk hanyoyin." Onyx ya tsaya cak, numfashinsa ya fara sarƙewa. Ya kalli leɓen Gely wanda aka ƙera shi da wani irin roba (synthetic skin) mai taushi kamar na mutum... Ya kasa gaskata cewa Gely ce take faɗar waɗannan kalaman. Ga ɗumin jikinsa yana neman ratsa na'urorin jikinta. A daidai lokacin da bakinsu yake neman haɗewa, sai aka ji ƙarar buɗe ƙofar ofishin... Ching Ching ce ta shigo da gudu, riƙe da kwamfutar a hannunta tana kuka.. "Uncle! Uncle! Dubi abin da ya faru a film ɗin nan! Jarumin ya rasu..." Maganar ta maƙale a maƙogwaronta sa'ilin da ta ga abin da yake faruwa. Gely a zaune a kan cinyar Chief, suna fuskantar juna kamar za su yi sumba... Kwamfutar hannun Ching Ching ta kuɓce ta faɗi ƙasa... Gararrass!... Kwamfutar da take hannun Ching Ching ta rabe gida biyu a ƙasa, amma hayaniyar faduwarta ba ta firgita Gely ba. Maimakon Gely ta tashi daga kan cinyar Chief Onyx cikin kunya kamar yadda ɗan adam zai yi, sai ma ta ƙara nannaɗe hannuwanta a wuyan Chief, tana ƙara tura kanta a saitin fuskarsa. Ching Ching ta tsaya cak, numfashinta ya fara fita da sauri-sauri, idanunta suka firfito waje... "Uncle... me... me kuke yi?" muryarta tana rawa... Onyx ya so ya ture Gely amma ta ƙara matse shi, sannan ta juyo da kanta a hankali ta kalli Ching Ching da wani irin kallo na isa da nuna iko... "Baki ga abin da yake faruwa ba ne, Shugaba Ching Ching?" Gely ta faɗa cikin murya mai sanyi wadda take amo na ban mamaki... "Boss yana kula da ni ne. Tsarin jikina yana buƙatar ɗumin jikinsa domin na daidaita. Shin ba ke ce kika ce 'ba a miki tsawa, sai dai lallashi' ba? To, ni ma yanzu lallashin nake buƙata." Ching Ching ta ji kamar an watsa mata ruwan zafi.. "Lallashi? Ke Robot ce! Inji ce ke! Ba kya buƙatar lallashi, sai dai a sanya miki mai ko a ƙara miki wutar lantarki!" Gely ta yi wani ɗan murmushi na gefen baki, wanda ya fi na ɗan adam zafi. Ta sake juyawa wurin Chief, ta sanya hannunta tana shafa fuskarsa cikin sanyi, idanunta suna lumshewa kamar mai jin daɗi... "Boss, ka ga yadda kake sanya ni jin daɗi? Kada ka bari kowa ya raba mu. Wannan yarinyar ba ta san yadda ake kula da kai ba, rigima kawai ta sani." Ching Ching ta ƙara matsowa kusa, ranta a ɓace ta kai maƙura... "Sauƙa daga jikinsa! Uncle, ka ce ta tashi! Dubi yadda take taɓa ka, wallahi ba ta da kunya!" Onyx ya rasa yadda zai yi. A gefe guda, yana jin tsoron yadda Gely take sauyawa, a gefe guda kuma, wannan shauƙin da Gely take nuna masa yana sanya shi jin wani irin yanayi da bai taɓa sani ba... "Ching Ching, ki yi haƙuri... Gely ba ta da lafiya ne..." "Ƙarya take! Tana yi ne don ta sa ni haushi!" Ching Ching ta daka tsalle ta nufi Gely, ta sanya hannu tana ƙoƙarin janyo ta daga kan cinyar Chief... Amma Gely tana da ƙarfin ƙarfe. Da hannu ɗaya ta tunkude hannun Ching Ching, sannan ta ƙara matse Chief a jikinta, har ta kai ga taɓa leɓensa da nata a hankali, tana kallon Ching Ching ta cikin ta gefen ido.. "Ke ba kowa ba ce a nan, Ching Ching," Gely ta raɗa. "Ni ce PA ɗinsa ce, ni ce kariyarsa, kuma ni ce kaɗai na san sirrin jikinsa. Ke kuwa... 'yar aiki ce kawai mai shagwaba." Ching Ching ta fashe da kuka mai ƙarfi, wannan karon na kishi ne tsagoronsa. Ta juya ta ruga da gudu tana kuka tana shura ƙafa... "Na tsane ka Uncle! Na tsane ka! Ka fi son gwangwani a kaina! Wallahi sai na bar gidan nan!"... Onyx ya kalli inda Ching Ching ta bi, sannan ya kalli Gely wadda take zaune a jikinsa tana murmushin nasara... Ya gane cewa Gely ta ƙulla wannan makarkashiyar ne don ta nuna wa Ching Ching matsayinta.. "Gely... ya isa haka," Onyx ya faɗa muryarsa ƙasa-ƙasa... "Kin yi abin da kike so. Yanzu tashi.".. Gely ta tashi a hankali, ta gyara kanta... "Na yi hakan ne domin na nuna mata cewa ni ce nake da iko da kai, Boss. Kuma tana buƙatar sanin hakan."... Chief Onyx ya bar Gely a ofis, ya nufi ɗakin Ching Ching cikin sanyin jiki. Yana shiga, ya tarar da ita a takure a gefen gado, tana ta kuka kamar ranta zai fita. Ganin yadda take kishin nan ya ba shi mamaki, domin bai taɓa tunanin yarinya irin Ching Ching tana ma san ma’anar kishi ba. Ya zauna a gefen gadon, ya yi gyaran murya. "Wai meye na kukan nan? Kuma me ya sanya kika shigo ofis ba tare da izini ba?" Ching Ching ta ɗago fuskarta wadda tayi ja saboda kuka... "Na tsane ka! Ka je ka cigaba da zama da gwangwanin taka, me ya kawo ka nan?" Onyx ya yi murmushin gefen baki, yana kallon ta.. "Ching Ching, shin kin fara so na ne?" Ta zaro ido, ta harare shi cikin shagwaba... "Cabb! Na rasa wanda zan so sai kai? Wa ya gaya maka ina sonka? Ni Daddyna nake so da Auntyna, ban ma san ma'anar sonka ba!" Chief ya ɗaga gira ɗaya... "To idan ba kya so na, me ya sa kike kishi?" "Meye kishi kuma?" Ta fada tana turo baki... "Ni ba na kishin komai! Kawai dai na ga tana zama a kan cinyarka tana so ta sumbace ka, kuma... kuma na ga kai babban Chief ne, bai kamata kana irin wannan abun ba." Onyx ya sake yin murmushi, ya ce, "To idan ke ba kya so na, ita Gely tana so na, kuma soyayya ce ta sa ta yi hakan." Ching Ching ta dakata, ta tuna abin da ta gani a film ɗin Indiya ɗazu. . "Soyayya? Eh... soyayya ce ai! Na gani a film ɗin da na kalla ɗazu, ana rungumar juna, kuma idan aka sumbaci mutum to soyayya ce." Onyx ya tashi tsaye kamar zai fita, ya ce, "Shikenan, tunda ke ba kya so na, bari na je na sumbaci Gely tunda muna soyayya da ita." Ching Ching ta zabura ta tashi tsaye. "To... to... taya za ka yi soyayya da ƙarfe? Kuma ma'aikaciyar ka ce fa?" "Ita ce kaɗai take so na, ai dole na biya ta," Onyx ya faɗa yana haramar fita. Cikin sauri da rashin tunani, Ching Ching ta ce.. "Ni ma ina sonka ai!" Onyx ya tintsire da dariya, sai yau sautin dariyar Onyx ya fito, ya kalle ta daga sama har ƙasa... "Ina kika san soyayya ke da ko period baki fara yi ba? Har yanzu ke yarinya ce ƙarama, ba ki san zafin so ba." Jin wannan maganar ya sanya Ching Ching ta fusata matuƙa... Ta tashi a fusace tayo kansa. Onyx ya matsa gefen ƙofa yana tunanin ko fita za ta yi, amma sai ya ga akasin haka... ta daka tsalle ta rungume shi, ta sanya hannuwanta ta karkato da wuyansa ƙasa don ta kai saitin fuskarsa... Kafin ya ankara, ta haɗe bakinsu wuri ɗaya! Onyx ya zaro ido cikin tsananin mamaki, ya ji numfashinsa ya ɗauke na ɗan lokaci.. Ching Ching ta fara sumbatar sa cikin wani irin salo na rashin sani mai cike da shauƙi, tana tsotsan leɓensa kamar ta samu lollypop mai zaƙi... Duk da cewa Onyx yana ƙiran ta yarinya, amma a take ya ji tsikar jikinsa tana tashi, wani irin saƙon lantarki ya ratsa kashin bayansa. Ya kasa jurewa, ya manta da cewa yarinya ce, ya manta da cewa shi babban mutum ne... A hankali ya zagayo da hannuwansa ta bayanta, ya matseta a jikinsa sosai, ya fara biye mata yana sumbatar ta cikin wani irin yanayi mai zafi da rudarwa... A daidai wannan lokacin, Gely tana tsaye a bakin ƙofar ɗakin, idanunta sun sauya launi zuwa Ja wur! (Deep Red). Tana kallon yadda Chief Onyx yake musayar numfashi da Ching Ching, wani irin amo na sarrafa saƙonni ya fara tashi daga jikinta... A hankali Chief Onyx ya zare bakinsa daga na Ching Ching, yayin da numfashinsa yake fita da sauri-sauri. Ya riƙe kafaɗun ta, yana mata wani irin kallo mai zurfi, kallo ne da yake cike da mamaki, sha’awa, da kuma fargaba... Tana numfashi sama-sama, fuskarta ta yi jawur, idanunta sun yi lamo alamar shauƙin ya tafi da ita. Ta tabbatar masa cewa duk da ita yarinya ce, tana da irin tata soyayyar da ba ta inji ba... Onyx ya gyara tsayuwar sa, ya natsu, sannan ya ce da ita cikin muryar raɗa mai cike da natsuwa... "Ching Ching, ke yarinya ce. Kuma yanzu ba na son ki ɓaci. Ke amana ce a gare ni daga mahaifinki, saboda haka dole ne ki kiyaye kanki, ki kiyaye mutuncinki."... Ya kalle ta sau ɗaya na ƙarshe, sannan ya juya ya fice daga ɗakin da sauri, domin ya ji cewa idan ya ƙara daƙiƙa ɗaya a wurin, zuciyarsa za ta iya sa shi ya sake aikata abin da ya fi wannan... A gefe guda kuwa... Gely tana tsaye a falon sa'ilin da Chief ya fito. Tun kafin ya raba bakinsa da na Ching Ching, Gely ta juya ta tafi. Ba ta jira ta ga ƙarshen sumbar ba, domin Data ɗin da take gani ta kyamarorin sirrin jikinta ta riga ta gaya mata cewa... Chief ya fara son Ching Ching fiye da kowace na'ura... Gely ta nufi nata ɓangaren, tana tafiya tana jin wani irin rawa a jikinta (System Vibration)... Wannan karon fushin da take ji ya kusa sanya wayoyin jikinta fashewa. Ta tsaya a gaban madubi, ta kalli fuskarta dake kama da ta mutum komai irin na macen mutum... "Amana?" Ta maimaita kalmar da Chief ya faɗa wa Ching Ching... "Idan har ita amana ce, ni kuma me nake a gare ka Boss? Inji? Ko kuma tsohuwar na'urar da za ka wurgar dan ka samu sabuwar rayuwa?" Idanun Gely suka yi wani irin haske na fitar hayaƙi. Ta yanke shawara... Tunda Chief ya ce Ching Ching Amana ce, to ita kuma za ta nuna masa cewa babu amincin da zai dore muddin tana kusa da shi.... ✨ Washegari da safe, Chief Onyx ya fito daga sashensa zuciyarsa cike da fargabar haduwa da Gely ko Ching Ching... Ya zata zai tarar da Gely cikin yanayin kishi ko kuma ta tambaye shi abin da ya faru a jiya, tunda ya san kyamarorin jikinta ba sa barci... Amma abin mamaki, yana fitowa falon dining, ya tarar da Gely tana tsaye daram, idanunta masu hasken shuɗi suna kallon gaba. Yanayinta ya koma kamar ranar farko da ya ƙere ta, babu shauƙi, kuma babu alamun kishi a fuskarta. "Ina kwana, Boss," ta faɗa cikin murya mai sanyi ta robot, ba tare da ta kalle shi ba... "An riga an kaddamar da dukkan ayyukan safe. Breakfast ɗinka yana nan, kuma na riga na tura wa Shugaba Ching Ching nata abincin zuwa ɗakinta don kada ta takura maka." Onyx ya tsaya yana kallonta da mamaki. "Gely... game da abin da ya faru jiya..." Gely ta katse shi cikin sanyin murya, "Boss, bayanan da nake da su game da daren jiya an riga an goge su. Ba su da amfani ga tsarin aikina na yau da kullum. Aikina shi ne na tabbatar da tsaronka da kuma tafiyar da ofishinka. Sauran abubuwan da suka shafi dan adam ba su cikin damuwata." Wannan halin ko-o-ho da Gely ta nuna ya fi sanya Onyx jin ba daɗi... Ta nuna masa cewa yanzu ta koma "Inji" tsagwaronta, ba ta damu da shi ba kuma ba ta damu da kowa ba. Ta daina shishshigi a rayuwarsa, ta daina taɓa shi, har ma ta daina zama kusa da shi idan yana cin abinci. Daidai nan, Ching Ching ta fito daga ɗakinta tana washe baki, tana tunanin yadda sumbar jiya ta kasance. Ta rugo da gudu tana nufar Chief... "Uncle! Barka da asuba!" Ta zo za ta rungume shi kamar yadda ta saba.. A daidai lokacin da Gely za ta sanya baki ta hana ta ko kuma ta nuna kishi, sai kawai Gely ta juya baya ta nufi kitchen tana cewa, "Boss, zan je na duba tsarin wutar lantarki na sashin baya. Idan akwai buƙata, za ka iya kirana ta intercom." Ta wuce ko kallon inda Ching Ching take ba ta yi ba, kamar ma ba ta ga mutum a wurin ba. Ching Ching ta tsaya cak, ta kalli Onyx. "Boss, me ya faru da wannan gwangwanin? Yau ko hararata ba ta yi ba?" Onyx ya sauƙe numfashi, ya kalli ƙofar da Gely ta bi. Ya gane cewa Gely ta ƙulla wani sabon shirin ne a ranta. Wannan shirun nata ya fi komai haɗari, domin bai san me take ƙullawa a cikin ƙwaƙwalwarta ta ƙarfe ba yayin da take nuna masa ba ta sani ba. "Ki kyale ta Ching Ching," Onyx ya faɗa a hankali... "Ƙila ta gane matsayinta ne."... Ganin yadda Gely ta share ta, Ching Ching ta ji ranta ya ɓaci. Ita a ganinta, idan Gely ba ta nuna kishi ba, to nasarar da ta samu a kan Chief ba ta cika ba... Tana son ta ga Gely tana ƙuna, tana son ta ga idanunta sun yi ja saboda kishi... Ta bi bayan Gely har zuwa kitchen, ta tarar da ita tana latsa wasu na'urori. Ching Ching ta matsa dab da ita, ta yi wani irin takun alfarma... "Haba Gwangwani... wai yau ko kallona ba kya don yi ne? Ko don kin ga Chief ya daina yaba miki ne?" Ching Ching ta faɗa tana murguɗa baki. Gely ba ta ko ɗago ba, ta ci gaba da aikin ta... "Shugaba Ching Ching, kalla-kallan fuskarki ba ya cikin tsarin aikina na yau. Ina ba ki shawarar ki je ki ƙarasa karin kumallonki." Ching Ching ta fusata, ta ƙara matse Gely tana hura mata iska a kunne... "Kin san me ya faru a ɗakina jiya? Chief ya ce min ni Amana ce a gare shi. Ya rungume ni, ya sumbace ni... ya ma ce ni na fi kowace halitta da yake tare da ita zaƙi." Ta ƙara da wata dariyar mugunta... "Shin kin taɓa jin ɗumin sa kuwa? Ko kuwa ƙarfen jikinki ba ya jin komai?" Gely ta tsaya cak, hannunta ya ɗan yi rawa kaɗan a kan na'urar, amma nan take ta daidaita kanta... Ta juyo ta kalli Ching Ching da idanunta masu haske... "Bincike na ya nuna cewa mutane suna yawan ƙarya idan suna son nuna isa. Amma ko da gaske ne, hakan ba zai canza cewa ni ce nake riƙe da dukkan sirrin rayuwar Chief ba. Ke sumba ce kawai kika samu, ni kuwa rayuwarsa gaba ɗaya tana hannuna." Jin haka, Ching Ching ta ƙara kuluwa... Ta ruga falon dining inda Chief yake shan kofi. Ta tafi da gudu ta zauna a kan cinyarsa, ta rungume shi a gaban idanun Gely da take fitowa daga kitchen. "Uncle! Uncle!! Ka ga Gwangwani ko? Wai cewa ta yi ita ce take da ikon komai na rayuwarka, wai ni sumba kawai na samu!" Ta faɗa tana kuka na shagwaba tare da goge fuskarta a kafaɗarsa.. Onyx ya kalli Gely, wadda take wucewa ta gefensu da tiren kofin shayi. Ta ajiye tiren a kan teburin ba tare da ta kalle su ba.. "Boss, idan ka gama, akwai taron gaggawa da za ka yi ta bidiyo da wasu abokan kasuwancinka. Na riga na shirya maka komai a ofis." "Gely," Onyx ya ƙira sunanta, "ba za ki ce komai ba a kan abin da Ching Ching take yi?" Gely ta tsaya, ta yi wani ɗan sanyayyan sauti na inji... "Me zan ce Boss? Yarinta tana damun ta, kai kuma kana jin daɗin hakan... Aikina shi ne na gyara ofis, ba na gyara halayen yan adam ba.".. Ta juya ta tafi, takun ƙafafunta yana bada sauti ɗas-ɗas a kan falon... Ching Ching ta haura, ta tashi daga kan cinyar Chief ta bi bayan Gely... "Ke! Tsaya kiji! Wallahi sai na sanya Chief ya goge ki daga gidan nan! Yau ma sumbata ta zai sake yi, kuma a gabanki!" Gely ta dakata ba tare da ta juyo ba.... "Kina iya yi, Shugaba Ching Ching. Amma ki sani, ko sau nawa za a sumbace ki, ba za ki taɓa sanin abin da yake cikin ƙwaƙwalwar Chief ba kamar yadda na sani. Ni ce inuwarsa, ke kuma wasan yara kike yi." Ching Ching ta kalli Chief tana faman huci... "Uncle! Ka ji abin da ta ce min ko?" Onyx ya dafe kansa, ya gane cewa dambarwar ta sauya salo. Gely ba kishi take nuna ba yanzu, nuna isa take yi da kuma nuna cewa ita ta fi kowa saninsa... Ching Ching ta gane cewa abin da Gely take alfahari da shi, shi ne sanin sirrin Chief da kula da na'urorinsa. Ta yanke shawarar cewa yau, sai ta sanya hannunta a cikin babban sirrin Chief domin ta nuna wa Gely cewa ita ma tana da daraja. Ta san cewa akwai wani akwati na musamman (Safe Box) a cikin ofishin Chief, inda yake ajiye manyan takardu da wasu tsofaffin abubuwan tarihinsa. Ching Ching ta lura cewa ko yaushe Gely take buɗe shi, tana amfani da lambobi ne... A yau, lokacin da Chief ya shiga wanka, Ching Ching ta sallaɓa ta nufi ofishin.. Ta tarar da Gely a tsaye a gefe tana goge wasu kyamarori. Ching Ching ta wuce ta da wani irin takun isa, ta nufi bangon da akwatin sirrin yake.. "Me kike ƙoƙarin yi, Shugaba Ching Ching?" Gely ta tambaya ba tare da ta kalle ta ba. "Wannan akwatin ba na wasan yara ba ne." Ching Ching ta yi dariyar mugunta. "Wasan yara? Lallai gwangwanin nan, baki sani ba ne? Jiya da dare, Chief ya raɗa min lambobin sirrin nan a kunne na lokacin da yake sumbata ta. Ya ce ni ce kaɗai ya aminta da ita." tana son gani ko Gely za ta harzuƙa.. Gely ta daina goge kyamarar, ta juyo ta zuba wa Ching Ching ido... "Chief ba zai taɓa yin hakan ba. Lissafi na ya nuna kina ƙarya." "To ki gani!" Ching Ching ta fara danna lambobi a jikin akwatin. Ta tuna ranar da ta ga Onyx yana latsawa, ta lura da wasu lambobi guda hudu. Ta danna.. 1-9-9-5... Tiii-tiii-tiii! Akwatin ya buɗe! Ching Ching kanta ta firgita da ganin akwatin ya buɗe, ashe dai hasashen ta ya zama gaskiya! Gely ta matso da sauri, idanunta suna walƙiya. "Ta yaya kika san lambobin nan? Wannan lambobin ranar haihuwarsa ne ta asali!" Ching Ching ta ga ta samu nasara, ta yi gwalo ta ce, "Na faɗa miki, Chief ya aminta da ni. Kuma ma... dubi abin da yake ciki.".. Ta sanya hannu ta ɗauko wani tsohon hoto na Chief Onyx sa'ilin da yake matashi, tare da wata mata kyakkyawa... Ching Ching ta zaro ido, ta kalli hoton, sannan ta kalli Gely... "Wace ce wannan? Kuma kamar Aunty Yumna, kodai kamanni ne? A'a kama ne ashe..." Gely ta matso kusa, ta zare hoton daga hannun Ching Ching... "Wannan sirrin Chief ne. Kuma tunda kika buɗe wannan akwatin, kin janyo wa kanki babban hukunci." Daidai nan, Chief Onyx ya shigo ofishin, yana sanye da rigar sanyi, ruwa yana ɗiga daga gashinsa. Ya ga akwatin a buɗe, ya ga hoton a hannun Gely, ya kuma ga Ching Ching a tsaye tana rawa... "Meye kuke yi a nan?" Onyx ya daka wata uwar tsawa wadda ta sanya duka ofishin ya yi tsit... Ching Ching ta tsorata ta ɓoya a bayan Gely, ta ce cikin muryar kuka.. "Uncle! Wannan gwangwanin ce ta ce na buɗe mata akwatin, wai tana son ganin abin da yake ciki!" Gely ta juyo ta kalli Ching Ching, ta yi shiru na dakiku biyu, sannan ta kalli Chief... "Boss, Shugaba Ching Ching tana iƙirarin cewa kai ne ka ba ta lambobin sirrin lokacin da kuke... sumbatar juna." Onyx ya matso kusa da su, fuskarsa ta sauya kamar gajimare. Ya kalli hoton matar nan wanda kana ganin kasan mahaifiyarsa ce, sannan ya kalli Ching Ching. Wannan karon fushin nasa ya wuce na kowane lokaci.... Falon ofishin ya yi tsit, sai numfashin Chief Onyx da yake fita cikin zafin rai... Ya ɗaga yatsansa, ya nuna Ching Ching da shi, muryarsa tana fita a dashe saboda tsananin fushi... "Na fahimci sake miki fuskar da nake yi da kuma ƙyale ki da nake yi kina shiga jikina, shi ne ya sanya kika manta ke WACECE a nan ko?" Ching Ching ta fara girgiza kai tana son yin magana, amma ya dakatar da ita da wani kaifaffen kallo... "To bari na tuna miki! Ke 'YAR AIKI ce a nan! Kada ki sake, na ce kada ki sake gigin shiga cikin rayuwata ko sirrina daga yau. Ki ci gaba da aikin da aka kawo ki yi, domin babu wata alaƙar da take tsakaninmu da za ta ba ki ikon shiga sirrin rayuwata. Fice min daga ofis yanzu!" Ching Ching ta fashe da kuka, wannan karon kuka ne na kunya da baƙin ciki. Ta juya da gudu ta fice tana kuka mai sauti, ta gane cewa iyakarta ta zo ƙarshe... Onyx bai tsaya a nan ba. Ya juyo ya kalli Gely, wadda take tsaye tana tunanin ta tsira... Ya nuna ta da yatsa itama, idanunsa suna walƙiya. "Ke ma Gely, saurara da kyau! Na san duk abin da kike ƙullawa. Daga yau, ki dakata da batun wata soyayya, ko kishi, ko wani shashanci makamancin haka.... Ke na’ura ce, kuma matsayinki na’ura ne a gare ni. Kada ki sake barin tsarin jikinki ya gaya miki kina da wani iko a kaina. Idan kika sake keta wannan layin, zan ruguza ki na mayar da ke tarkacen ƙarfe!"... Gely ta tsaya cak, hasken idanunta ya yi sanyi, ta sunkuyar da kanta ƙasa... "An ji, Boss...An goge dukkan tsarin da ba na aiki ba." Onyx ya fizge hoton daga hannunta, ya mayar da shi cikin akwatin ya buga shi ya rufu. Ya rage hasken ofishin, ya bar kansa a cikin duhu, yana jin yadda amincin gidan nasa ya ruguje a cikin rana ɗaya.... 😅😅😅😅 GWANGWANI VS CHING CHING... Wato idan Allah ya yo ka a matsayin mutum to ka gode wa Allah... Gely ta shige su a gun Ching Ching...😝😝😝 *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣6️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Ayat ta tura ƙofar ɗakinta da ƙarfi tana shirin yin kukan haushi, amma tana sa ƙafarta ciki, sai ta tsaya cak. Ta zaro ido tana waige-waige. Ɗakin dake hargitse da barguna a ƙasa da kuma kayan da ta wargaza ɗazu lokacin neman Reems, yanzu ya koma tsaf tamkar ba a taɓa shiga ba. Kowane abu ya koma muhallinsa; barguna an ninkasu, gadonta an gyara shi da sabon zanen gado mai sheƙi, kura ma babu ita ko kaɗan. 2. Bacewar "Warin" Kundirmo Ta nufi inda ta ajiye kundirmon nonon nan da yake ishenta da wari, ta duba ko'ina amma ta tsinci gurbinsa wayam. Ba kundirmon kaɗai ba, hatta kwanukan azurfar da ta riƙa ba shi abinci a ciki duk sun ɓace. Ɗakin ya ɗauki wani irin daddaɗan ƙamshi na fure-fure, wanda ya fi ƙamshin kowane turaren da take amfani da shi daɗi. "Lallai aljanin nan ba shi da dama," ta furta a fili, tana jin wani irin sanyi a ranta duk da fushin da take nuna tana yi. 3. Sakon Kan Madubi Ta ƙarasa gaban madubinta don ta cire mayafin fuskarta, sai ta ga wani abu dake haske a inda ta ajiye gashin nan ɗazu. Wata ƙaramar sarƙa ce ta zinare mai kyan gaske, wadda take da wani jan dutse a tsakiya dake walƙiya kamar jini. A ƙarƙashin sarƙar, akwai wani ɗan guntun takarda mai rubutu da aka yi shi da wani kalar tawada mai kyan gaske. Ta ɗauka ta karanta: "Na kwashe 'kundirmon nonon' kamar yadda kika umarta. Wannan sarƙar kariya ce gare ki. Muddin tana wuyanki, babu wani aljani ko mutum da zai iya cutar da ke ba tare da na sani ba. Ki daina fushi da Reems ɗinki..." 4. Murmushin Sirri Ayat ta murza takardar a hannunta tana son ta yi fushi, amma sai ta tsinci kanta da yin wani ɗan murmushi na ɓoye. Ta kalli sarƙar, ta taɓa jan dutsen nan, ta ji wani irin ɗumi dake shiga jikinta yana sanyaya mata zuciya. "Wane irin takura ne wannan? Daga taimako sai ya zama yana bibiyar rayuwata," ta fada, amma duk da haka, ba ta jefar da sarƙar ba, sai ta sanya ta a cikin aljihun rigarta tana shirin ɓoye ta... Kwanaki bakwai sun shuɗe cur, amma Ayat ta ji su tamkar shekaru bakwai. Tun ranar da ta kore shi a lambu, King Diamond bai sake bayyana ba, kuma Reems (kuliya) bai dawo ba. Ta tsinci kanta cikin wata irin damuwa da fargaba, ko yaushe zuciyarta tana dube-dube, tana kiran sunansa a asirce duk da cewa ta ce ya fita daga rayuwarta. Yau ta shigo ɗakinta daga can falo ranta a ɓace, ma'aikata sun kai ta bango da wasu maganganu. Cikin fusata, ta fizge mayafin fuskarta ta wurgar da shi akan gado, sannan ta wuce banɗaki tana gunaguni. 2. Sallamar Sarki King Diamond yana nan a cikin masarautar, domin kariya ta asiri ta hana shi fita sannan ya sake dawowa. Amma yau, ya yanke shawarar komawa fadarsa ta Power Pool. Ya bayyana a tsakiyar ɗakin Ayat domin ya yi mata kallon ƙarshe. Ya matsa kusa da gadon, ya ga yadda mayafin fuskarta yake a murtuke. Ya ɗauka a hankali, yana jin taushin zaren mayafin a yatsunsa. Wani irin sanyi ya ziyarci ƙirjinsa, ya yi murmushin gefen baki, "Ta kore ni... amma tana nemana," ya raɗa a hankali, domin yana jin yadda zuciyarta take buga sunansa. 3. Gamuwar Ba-Zata Yana tsaye yana kallon sashen kayayyakinta, ya furta: "Gimbiya... ba ki da ƙarfi kamar yadda kike nuna wa duniya." A daidai nan Ayat ta fito daga bathroom. Ganin mutum tsaye a tsakiyar sirrin ɗakinta ya sa ta zabura, numfashinta ya kusa tsayawa. “ME KAKE YI A NAN?!” ta daka masa tsawa, duk da cewa tsoro ya fara ratsa ta. King Diamond ya juyo cikin natsuwa da kwarjininsa na sarki. Ayat tana tsaye, idanunta cike da wata irin fusata dake gauraye da kunya. Ta tsaya ƙyam kamar kowace sarauniya, amma hannunta dake rawa ya bayyana raunin zuciyarta. 4. Takun Sanya “Na ce ka fita daga rayuwata,” ta faɗa cikin daka-tsawa. “Amma ka ƙara shigo mini ɗakina?” King Diamond ya zuba mata idanunsa na zinare, bai kau da kai ba. “Ke ce kika ce na zo,” ya ba ta amsa cikin muryar nan tasa mai ratsa jiki. “Na zo ne domin abin da kika buƙata.” Ya ɗaga mayafin fuskarta dake hannunsa. Ayat ta zaro ido, "Ka... ka taɓa kayana?" “Ban taɓa ba,” ya ce cikin nutsuwa, “amma gaskiya na gani.” Ayat ta ji kamar ƙasa ta haɗiye ta tsabar kunya. Ta ƙaraso kusa da shi tana huci, “Ba ka da kunya! Kai aljani ne mara tarbiyya!” 5. Yarjejeniyar Zuciya Maimakon ya yi fushi, sai ya saki wani murmushi mai cike da ikon mallaka. Ya matso kusa da ita sosai yadda numfashinsa yake dukan fuskarta. “Idan da gaske kina son in bar ki,” ya faɗa cikin wata irin murya mai sanyi dake girgiza jijiya, “kar kika sake kiran sunana... koda a cikin zuciyarki ne.” Kalmar ta daki ƙirjin Ayat tamkar aradu. Ta so ta yi musu, ta so ta ce ba ta kiran sunansa, amma bakinta ya gaza buɗuwa. A wannan lokacin ne ta gano babban sirrin dake firgita ta: Ko tana nuna ƙiyayya a fili, zuciyarta ta riga ta kamu da shi... ta riga ta fara jin bugun zuciyar Sarkin Aljanu a nata jinin. Haka suka tsaya suna kallon juna, babu mai cewa uffan, yayin da iskar ɗakin ta sauya zuwa wani yanayi na daban... Dakin ya dauki shiru, sai kawai sautin numfashinsu dake fita cikin sauri-sauri. Ayat ta tsaya tana kallon cikin idanun King Diamond wadanda suke sheƙi tamkar taurari. A fuskarta, akwai sauran burbushin fushi da ƙiyayya, amma a cikin kwayar idonta, wani irin sirri ne na ƙauna dake neman mafaka. Shi kuwa Diamond, kallon da yake mata kallon mallaka ne, kallon da yake ratsa kowace jijiyar jikinta. 2. Kusa Da Juna Tsananin kwarjinin King Diamond ya sanya Ayat jin jiri, ta fara yin baya-baya tana son nisantar dumin jikinsa dake neman ruda mata tunani. Tana gab da faduwa, sai ta ji wani kakkaran hannu ya zagayo ta kunkuminta. Cikin wani irin zafin nama da kwarewa, Diamond ya jawo ta da karfi, ya mannata da faffaden kirjin sa. "Yarafff!" Haka kirjin Ayat ya daki nasa, wani irin shock ya ratsa dukkaninsu. A wannan lokacin, babu sauran sarari a tsakaninsu; kunkuminsu ya hade daram, kirjinsu ya manne da juna ta yadda za su iya jin yadda zukata suke bugawa a tare. 3. Tawaratsin Shauki Ayat ta kasa kwatanta abin da take ji. Ta so ta ture shi, ta so ta kwace kanta, amma hannun Diamond dake kan kunkuminta ya zama tamkar igiyar karfe. Ya daukaka hannunsa daya, ya damko keyarta cikin wata irin kulawa mai dauke da zafi, ya sanya ta dago fuskarta don ta kalle shi. Idanunsu suka sake sarke wa da juna a wani matsayi na karshe. A nan ne Ayat ta gane cewa dukkan kiyayyar da take nunawa, tana yi ne domin tana tsoron karfin ikon da yake da shi a zuciyarta. 4. Sumbatar Da Ta Tsayar Da Lokaci Ba tare da wani jinkiri ba, King Diamond ya sunkuya, ya hada bakinsa da nata a cikin wata irin zazzafar sumba (kiss) mai cike da sakonni dubu. Sumba ce ta nuna mallaka, ta nuna kauna, da kuma neman gafarar dukkan yaudarar da aka yi a baya. Ayat ta ji duniyar tana juya mata. Da farko ta daskare, amma cikin dakika kadan, sai ta tsinci kanta da mayar masa da martanin sumbatar, hannunta ya sarke a wuyansa tana mai kankame shi. A wannan dakin, a wannan lokacin, babu wata gimbiya, babu wani aljani; sai masoya biyu wadanda kaddara ta gama hada su. 5. Numfashin Ruhi Dukkan wani fushi ya narke ya zama soyayya. Iskar dakin ta canza kalar ta, tana fitar da wani irin ni'ima. King Diamond ya kankame ta, yana jin tamkar ya samu taskar da ya dade yana nema. Sun jima a haka, suna aikawa juna sakonni ta hanyar sumbatar, yayin da zuciyar Ayat take raya mata cewa: Wannan shi ne mutumin da aka halitta domin ya mallaki dukkan abin da nake da shi... Muddin ka taba Gimbiya Ayat, tabbas ka taba zuma! Da zarar sumbar ta lafa, Ayat ta dawo hayyacinta, fuskarta ta canza kalar zuwa wani ja saboda tsananin kunya da bacin rai. Ta fara dukan kirjin King Diamond da kananan hannayenta, hawaye na wanke mata fuska. “ALLAH YA ISA! Macuci, ka kuma yi again? Ban yafe ba!” ta fada tana huci. Ta dora hannu a kanta cikin rudani. “Na shiga uku! Na yi gamo da bakin ALJANI!” Ta fara shawagi a cikin dakin kamar wadda aka zare wa lissafi, tana son kawar da dumin bakinsa dake yawo a nata. 2. Dokar Gimbiya Ta tsaya cak a gabansa, tana nuna shi da yatsa, jikinta na rawa. “Ka san me? Daga yau, ka daina kusantata! Ka daina shigowa dakina, ka daina bin rayuwata!” King Diamond ya gyara tsayuwa, ya sunkuya kadan don ya daidaita idanunsa da nata, wani kwarjini na musamman na fita daga jikinsa. “Amma ke ce kika kira ni,” ya fada cikin muryar raɗa. “Ke ce kika sa ni zama ‘Reems’. Ke ce kika dauke ni, kika ba ni wuri a zuciyarki—ko baki sani ba.” Ayat ta hadiye yawu, ta ji maganarsa ta soke ta. “Na yi kuskure,” ta fada cikin tsauri, “kuma ba zan sake shi ba.” 3. Al'ajabin Reems Ba zato ba tsammani, sai aka ji wani sauti: “Meow.” Ayat ta juya da sauri, idonta ya sauka akan gadonta. Wata farar kuliya ce sol, zaune tana kallonta da wasu idanu masu taushi. Ayat ta rude, ta kalli Diamond, ta kalli kuliya. “Ku... ku nawa ne a nan?” King Diamond ya dan murmusa, murmushin dake sanya kowa natsuwa. “Na bar miki bangare na a nan domin kada ki ji kadaici. Shi asalin kuliya ne, ba ni ba. Na san yadda kika shaku da shi, hakan ya sa na baki shi don rage kewa. Idan kika fita daga masarautar nan, zaki iya kirana ta zuciyarki zan bayyana, amma a nan tarkon masarauta zai hana ni shigowa.” 4. Sallamar Guguwa Duk da cewa Ayat ta ji wani daci a ranta na cewa zai tafi, sai ta saki murmushin keta. “Allah na gode maka da tarko ya kasance! Na gaji da kai, bana son kara ganinka!” Ta dauki kuliyar ta nufi kirjinsa da ita tana tura masa. “Ku duka biyun ku fita daga dakina yanzu! Idan kuka sake kusantata, wallahi sai na sa an binne ku da rayunku!” King Diamond ya saki wata dariya marar sauti, dariyar dake nuna sha'awar karfin zuciyarta. “Kin fi karfin da nake tsammani, Gimbiya Ayat.” Nan take, ya bace tamkar hayaki, ya bar dakin da kamshinsa kadai. 5. Saƙon Iska Ayat ta zauna a kan gadon tana sauke numfashi, ta rungume sabon kuliyarta. “Na maida maka sunanka Reems,” ta fada tana shafa kansa. “Kiyaye ni daga irin wannan mai farin gashi, wai shi King ko?...” Kuliyar ta lumshe ido cikin natsuwa. Amma tana cikin wannan tunanin, sai ta ji muryar King Diamond ta ratsa iskar dakin: “Ko kin so ko ki ki... zan dawo.” Ayat ta shafa sumar gashinta, ta turo baki tana gunaguni: “Wannan aljani fa, ba ya jin magana!”.... A harabar fadar, limousine baƙaƙe mai tsawo ya tsaya jiran Gimbiya. Motar tana sheƙi kamar madubi. Driver ɗinta ya tsaya cikin tsabta, uniform dinsa yana nuna tsoron aiki fiye da alfahari. Maayah ta shiga motar ba tare da ta kalli kowa ba. Bodyguards guda biyu suka bi a baya cikin babban jeep. Driver ya shiga, ya gyara rawaninsa. “Gimbiya, ina roƙon albarka.” Ta ɗora ƙafarta kan kujerar gaba—alamar raini da iko. “Ka saurare ni da kyau,” ta ce cikin murya mai sanyi. “Idan muka makara ko da minti ɗaya, zan kore ka. Ba wai daga aiki kaɗai ba—daga cikin fadar nan ma. Ina son na shiga aji kafin mai kula da aji.” Zufa ya keto wa driver. Bai ce uffan ba. Ya taka gas da gudun sarauta. Mulkin Aji Makarantar tana daga cikin mafi tsada a birnin. Da zarar motar Maayah ta tsaya, yara masu gata suka taru suna kallon shigowarta—kamar yadda ake kallon wata sarauniya a titi. Da ta shiga aji, shiru ya mamaye wurin. Wannan aji na ƙarshe (Final Year) ne, amma ikon Maayah ya fi na shekarunsu. Ta zauna a kujerarta—kujerar da babu wanda ya taɓa kusantar ta. Malami ya fara darasi, amma Maayah ba ta saurare shi. Ta buɗe littafi, amma tana zane-zane—tana zanen kanta a matsayin sarauniya, wasu kuma a ƙasa suna durƙushewa. Sai wata yarinya—’yar scholarship—ta yi kuskuren amsa tambaya. Maayah ta miƙe tsaye. “Ke!” ta nuna ta da yatsa. “Wannan amsar taki ta ɓata min kunne. Kina lalata min ajin alfarma. Ki fita yanzu!” Malamin bai yi magana ba. Ajin ya yi shiru kamar an rufe numfashi. Bayan haka, Maayah ta ɗauki waya a hankali, tana murmushi mara tausayi. Ta kira wani saurayinta na wasa... “Yanzu ka fita, ka siyo min Ice Cream mai zafi! Kuma dole ne ya zama mai sanyi!” (Wata sabuwar fitina ce kawai don ta ji daɗin ikon ta!) Ta katse wayar, ta jingina a kujerarta. A wannan aji— Gimbiya Maayah ce doka. Ikonta ya fi na malami. Babu wanda ya isa ya taɓa ta. Babu wanda ya isa ya ce mata a’a.... Bayan Khausar ta kori yarinyar scholarship kuma ta aika boy friend ɗin ta na wasa neman ice cream mai zafi, aji ya koma cikin shiru da tsoro. Kowa yana jiran karin darasi ko kuma wani sabon fitina daga Gimbiya. A wannan lokaci ne, Babban Malami ya shigo aji tare da wani Saurayi Mai Kyakkyawan Surar Jiki! Wannan saurayin tsaunin mutum ne! Yana da kirar jiki mai cike da alhurma da ƙarfi, sannan Sajen fuskarsa a kwance luf-luf, wanda ya ƙara masa wani irin kwarjini! Malamin ya gabatar da shi. “Ya ku ɗalibai, ga Sabuwar Malamin ku na Siyasa da Tarihi! Malam ZAIN! Ya dawo daga wata babbar Jami’a a ƙasashen waje! Zai koyar da ku da tsanani! Kuma ina rokon ku ku ba shi cikakkiyar biyayya!” Malam Zain ya zuba wa ɗalibai ido. Fuskarsa a ɗaure take da tsauri da iko! Arangama ta Farko: Bi ni ko Mutu Duk ɗalibai aji sun miƙe tsaye, ciki har da Malamin Darasi na Dā! Suka yi Gaisuwa da Girgiza Kai ga Malam Zain! Sai dai Gimbiya Khausar! Khausar ta yi zaman ƙasaita! Ta ɗora hannu ɗaya a teburin ta, bata da niyyar miƙewa ko yi masa gaisuwa! Ikon Sarauta bai yarda da girmama Malam ba! Malam Zain ya zuba mata ido! Bai nuna mamaki ko tsoro ba! Ya zama tazara mai ban tsoro a cikin ajin! Kowa ya shiga tsoro! Sun san cewa Khausar ba ta gaisuwa ga kowa! Kuma sun san cewa Malam Zain ba Malami mai tsoro ba ne! Malam Zain ya ajiye jakarsa a tebur! Ya nufi Gimbiya Khausar a hankali! Ya tsaya a gaban teburin ta! Ya sanya hannun sa a tebur da ƙarfi, ya kalle ta cikin tsantsar idon ta! “Ke!” Ya furta da murya mai ƙarfi da tsauri! “Miƙe tsaye!” Khausar ta zaro idonta cike da tsoro! Babu wanda ya taɓa yi mata irin wannan maganar a cikin rayuwar ta! Ba ta gane cewa wannan malam baya tsoron ta ba! Khausar ta yi murmushin izgili! “Wa kake gayawa haka? Malam, na ga ka shigo aji! Amma ni ba ɗaliba ba ce! Ni Gimbiya Khausar ce! Kowa a aji nan zai gaishe ni! Kuma ba ni da lokacin miƙewa!” Malam Zain ya kalli ɗaliban aji! Ya ga tsoro a idanun su! Ya gane cewa Khausar ce Sarauniyar Aji! Ya yi murmushi mai sanyi da tsauri! “Ki yi shiru! Idan har kina son zama Sarauniya a cikin gida! Amma a cikin wannan aji, ni ne Sarkin ki! Kuma a cikin wannan aji, duk wanda ke da rai dole ne ya miƙe tsaye idan Mai Iko ya shigo!” Ya sake cewa da murya mai ƙarfi da tsauri! “Miƙe tsaye, Khausar! Yanzu! Idan har ba haka ba, zan fitar da ke daga aji! Kuma zan sanya a rubuta miki laifi a cikin record ɗin ki! Ni ba na jin tsoron kowa! Ko da kuwa Ƴar Wacece ce!” Khausar ta yi fari tas! Jikinta ya fara rawa! Ta fahimci cewa wannan mutumin baya wasa! Tana iya ganin azabar hukunci a cikin idanun sa! Dole ne ta zaɓa: Girman Kai na Sarauta ko kuma Biyayya ta Farko! Khausar ta tashi a hankali, amma cikakkiyar fushi ya rufe fuskarta! “Wannan shine na ƙarshe!” Ta furta da murya mai rauni! Malam Zain ya yi murmushin nasara! Ya shiga cikin cikakken iko! “An gaishe ni! Yanzu ki zauna! Kuma ki mai da hankali! Idan har kika sake yi min raini! Zan hukunta ki yadda ba za ki taɓa manta ba! Gimbiya!” Ya jaddada kalmar Gimbiya da izgili! Khausar ta zauna! Fushin ta ya haura sama! Cakwakiya ta fara! Uncle Raees ya koma teburinsa. Ya gyara sajen fuskarsa da kwanciyar hankali! “Yara, ni Bako ne a aji nan! Kuma ina buƙatar sanin sunanku da halinku! Daga yau, tsari na zai zama Ilimi shi ne Sarki! Ba Mulki ba! Kuma duk wanda ke zaune a aji nan Jahili ne da ya zo neman ilimi! Don haka, babu wanda ya fi wani! ” Ya ɗauki litattafan Computer Science! Ya zuba wa ɗalibai ido. “Za mu koyi Computer Science yanzu! Kuma zan fara da jerin sunayen ku! Duk wanda zai faɗi sunansa dole ne ya miƙe tsaye!” Tilastawa da Juriya Ɗalibai suka fara miƙewa ɗaya bayan ɗaya, suna faɗin sunayensu cikin girmamawa. Lokacin da aka zo ga jerin sunayen (register), Uncle Raees ya kalli jerin sunayen har ya zo kan Khausar. Khausar ta yi zaman ƙasaita! Ta ƙi miƙewa! Ta harara wa Uncle Raees! A cikin zuciyarta: “Wane ne wannan mutumin? Ashe bai san wacece ni ba? Wannan rashin kunya ne!” Uncle Raees ya taka zuwa wurin Khausar! Ya tsaya a gaban teburin ta! Ya kalli kowane ɗalibi a aji! “Wannan Gimbiya fa? Ko sunan ta za ta faɗa da girman kai?” Khausar ta dube shi da girman kai! “Class! Me kuke jira? Ku sanar masa mana! Wannan ina ga bai san aikinsa ba! Ko kuma yayi gangancin wulaƙanta ni!” Wasu daga cikin ɗalibai sun shiga shirin faɗa masa sunan ta (saboda tsoro), amma Uncle Raees ya katse su da tsawa! “Ku yi shiru! Ita nake so ta miƙe ta faɗa sunan ta! Domin duk ɗaya kuke a aji nan! Ba mulki ba! Ba siyasa ba! Ba iko ba! Ba kuɗi ba! Sai Naman Ilimi wato Yaƙi da Jahilci! Domin duk wanda yake zaune a ajin nan Jahili ne, yazo neman ilimi!” Khausar ta yi murmushi mai izgili! Ta girgiza kai! Taƙi miƙewa! Tana tunani: “Wannan malamin ya fi rashin kunya fiye da Fatsu!” Hukunci Mai Zafi A fusace, Uncle Raees ya buga teburinta da ƙarfi! Wani babban sauti ya cika ajin! Har sai da Khausar ta zabura! Ba ta son tsawa! Uncle Raees ya sanya hannun sa a tebur, ya kalle ta da tsantsar tsawa ta Turanci: “You are very stupid! Stand up! You have absolutely no respect for the rule of law! Who do you think you are? You are a student, and in this class, you are nobody but a learner! Miƙe! Sanar da sunanki yanzu!” Khausar ta yi fari tas! Cikin baƙin rai da tsanani, ta miƙe! Sai da ta ɗauki mintuna kafin ta buɗe baki. “Name: SHAHZADI NOOR MUHAMMAD ALHAMRA! Better known as Khausar!” Ta furta da girman kai! Tana furtawa, ta zari jakarta! Tana shirin fitowa daga aji! Alamar cewa ta gaji da wannan wulaƙancin! Uncle Raees ya yi saurin riƙo hannunta! Ya zaro ido da fushi mai zafi! Ya yi magana a fusace cikin Turanci mai tsanani! “I am not done with you! You will sit down right now and write an apology letter to this entire class for your display of poor character and arrogance! You will not leave this class until I dismiss you! Sit down!” Uncle Raees ya zaunar da ita da ƙarfi! Khausar ta zauna! Jikinta ya yi sanyi! Fuskarta cike da hawaye na fushi! Wannan mutumin ya karya ikon ta! Malam Zain (Uncle Raees) ya koma teburin sa! Ya fara darasi a kan Harshen Computer (Computer Language) kamar babu abinda ya faru! Amma Khausar ta zama cikakkiyar Jahiliya a aji! Ba za ta taɓa gafarta wa Uncle Raees ba!.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣7️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Saboda tsantsar fushin da Chief Onyx ya nuna, hakan yasa yanzu kowa ya koma matsayinsa.. Gely ta koma yadda take a da na’ura mai bin umarni ba tare da nuna wani shauki ba... Tana yin dukkan ayyukanta cikin kwarewa, shirya ofis da tura sakonni, tana nan tsaye a bayan Chief koda yaushe in har ba wani aiki ya sanya ta ba... Ta daina nuna kishi amma idanunta na na’ura koyaushe suna bin kowane motsi na cikin gidan... Ching Ching kuwa, duk da cewa fushin Chief ya tsoratar da ita, amma tana nan da dabi’arta. Ta fara yin ayyukan wanke-wanke da goge-goge cikin ɓacin rai, amma duk sanda ta ga Gely ta zo wucewa, sai ta nemi abin da za ta faɗa don ta ɓata mata rai... Wata rana, Ching Ching tana share falon Chief inda Gely take tsaye tana duba wasu takardu... Ching Ching ta matso da tsintsiyar ta har karkashin kafar Gely, ta fara sharewa da karfi, tsintsiyar na dukan sawayenta... "Ke! Matsa min a wurin!" Ching Ching ta faɗa tana hararar Gely... "Kin zama bango a nan, ko kin manta Chief ya ce ke na'ura ce kawai? Matsa na goge wurin, 'yar gwangwani kawai...." Gely ta matsa gefe ɗaya a hankali ba tare da ta nuna ɓacin rai ba... "Shugaba Ching Ching, tsaftace falon nan aikinki ne. Amma ki sani, duk tsintsiyar da kike bugana dashi, na'urar jikina tana daukar hoton yadda kike bata aiki.".. Ching Ching ta yi dariyar raini... "Hoto? Oho miki! Ke dai kin ji haushi don kin ga Chief ya daina bari kina zama a cinyarsa. Ni ko da ya kore ni, ai ya taɓa sumbata ta... Ke fa? Ko taɓa ki baya son yi yanzu." Ta matso kusa da kunnen Gely ta raɗa mata.. "Ko kin gyara ofis ɗari, ni ce mutum a nan, ke kuma inji ce. Kuma ko ba daɗe ko ba jima, sai na sake sanya shi ya kalle ni..." Gely ta ci gaba da kallon takardun hannunta... "Lissafi na ya nuna cewa mutum yana da saurin mantawa da haɗari... Ina baki shawara ki nutsu, kafin Boss ya cire ki daga matsayin 'yar aiki ya mayar da ke 'yar gudun hijira." Ching Ching ta murguɗa baki ta wuce tana rera waƙa.. _"Gwangwani... gwangwani... ko an gyara ta, gwangwani ce!"_ Duk da cewa Gely ba ta nuna komai ba, amma a cikin kwakwalwarta ta na’ura, tana ta lissafa dukkan cin mutuncin da Ching Ching take mata. Ta san cewa Chief ya hana ta nuna soyayya ko kishi, amma bai hana ta kiyaye doka ba. Don haka, ta fara neman duk wani ƙaramin kuskure na Ching Ching don ta kai kararta wurin Chief, amma ta yadda Chief zai ga ita Gely mai gaskiya ce.... ✨✨ Bayan kwanaki da Chief Onyx ya ja musu kunne, gidan ya yi tsit, kowa yana ƙoƙarin kiyaye iyakarsa.. Chief ya rage yawan magana, ya nutsu cikin ayyukansa na ofis, yayin da Gely da Ching Ching suke gudanar da nasu ayyukan kamar yadda aka tsara.. Ching Ching tana yin shara da goge-goge, amma zuciyarta ba ta daina bugun neman dabarar yadda za ta sake kusantar Chief ba.. Tana share falon ofis, tana kallon Chief ta ƙarkashin ido, tana son ta sake jin wannan ɗumin jikinsa, amma kwarjininsa ya hana ta magana... Gely kuwa tana tsaye a gefen Chief, tana miƙa masa takardu cikin tsari... Ko kallon inda Ching Ching take ba ta yi ba, amma tana lura da duk yadda Ching Ching take ta murguɗa baki tana share ƙarƙashin teburin Chief.. Kwatsam, sai Ching Ching ta ga wata dama.. Ta ga kofin coffee Chief ya kusa ƙarewa. Ta ajiye tsintsiyar, ta matsa kusa da teburin, ta sa hannu za ta ɗauki kofin tare da faɗin "Uncle, bari na wanke maka kofin nan na kawo maka wani shayin mai daɗi..." Daidai lokacin da ta sa hannu, sai Gely ita ma ta sa hannu a kan kofin. Hannun Gely na ƙarfe ya taɓa na Ching Ching... "Shugaba Ching Ching, wanke kofuna a kitchen aikinki ne," Gely ta faɗa cikin muryar robot mai sanyi... "Amma ɗaukar kofin daga hannun Chief da kawo masa shayi, aikina ne na PA. Koma ki ƙarasa share wurin da kika bari." Ching Ching ta harari Gely, ta ƙara matse kofin... "Ni na ce zan yi! Uncle, kalle ta ko? Ko kofin ma ba za ta bari na ɗauka ba?" Onyx ba tare da ya ɗago kai daga takardar da yake dubawa ba ya furta.. "Gely tana da gaskiya... Ching Ching, koma ki ƙarasa share-sharenki. Idan kin gama, ki tafi ki gyara babban falon baƙi..." Ching Ching ta saki kofin cikin fushi, ta koma tana buga ƙafa a ƙasa. Ta san cewa Gely tana amfani da aiki ne don ta nisanta ta da Chief... Yayin da Gely ta fita da kofin, ta gifta ta gaban Ching Ching. Ta ɗan tsaya kaɗan, ta kalle ta da idanunta masu sanyi, sannan ta raɗa mata a hankali yadda Chief ba zai ji ba.. "Nasarar da kika samu ranar, kuskure ne na lokaci ɗaya. Amma a yau, ni ce nake riƙe da kowane mataki na tafiyar sa. Ki ci gaba da shara, Shugaba Ching Ching." Ching Ching ta kusa fashewa da kuka saboda haushi. Ta gane cewa yanzu Gely ba ta kishi ta hanyar ihu, tana kishi ne ta hanyar nuna cewa ita ce take da iko da komai na Chief. Bayan Gely ta fita, Ching Ching ta matso kusa da teburin Chief, ta durƙusa a ƙasa kusa da ƙafafunsa kamar tana goge wurin... "Uncle... gaskiya Gely tana takura min... Kuma... kuma ni har yanzu ina tuna abin da ya faru a ɗakina. Shin kaima kana tunawa?" Onyx ya dakata da rubutun da yake yi. Ya kalle ta, ya ji wani irin tausayi da kuma shauƙin da yake ƙoƙarin dannewa... "Ching Ching, na faɗa miki mu bar wannan maganar. Ki yi aikinki, ni ma na yi nawa." Amma Ching Ching ta sanya hannunta a kan gwiwarsa a hankali, tana kallonsa cike da shagwaba... "Amma ni bazan iya dainawa ba Uncle. Kullum idan na rufe idona..." Kafin ta ƙarasa maganar, sai suka ji sautin takun ƙafar Gely tana dawowa... Ching Ching ta janye hannunta da sauri ta fara goge ƙasa tana rera waƙa, kamar ba ita ce take magana ba... Gely ta shigo ofishin riƙe da kofin shayin Chief, amma nan take na'urorin kyamarar idonta suka gano cewa akwai wani canji a yanayin zafin jikin Chief Onyx da kuma matsayin da Ching Ching take. Ko da yake Ching Ching ta janye hannunta da sauri tana goge ƙasa, Gely ta riga ta gano cewa an taɓa Chief a wurin da bai kamata ba... Gely ta ajiye shayin cikin natsuwa, sannan ta juyo ta kalli Ching Ching... "Shugaba Ching Ching, na'urorin dake ƙasan teburin nan suna da matukar muhimmanci.. Kada ki kuskura ki sake taɓa ƙafar Boss da sunan goge ƙasa, domin hakan zai iya goge wasu muhimman bayanai." Ching Ching ta turo baki, ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta... "Ke dai idonki ne ya nuna miki hakan! Ni goge wurin nake yi." Chief Onyx ya yi gyaran murya don ya kawo karshen wannan takaddamar... Ya kalli takardar dake gabansa, sannan ya kalli Gely da Ching Ching... "Ya isa haka. Akwai wani babban aiki da nake son a kammala yau. Za a sauya duk labulen babban falon gidan nan zuwa labule masu sarrafa kansu wato Smart Curtains...." Ya kalli Gely, "Gely, ke ce za ki tsara yadda za a jera su..." Sannan ya kalli Ching Ching, "Ke kuma, tunda ke kika san yadda kuke son launin ɗakin ya kasance, ke za ki taya ta wajen jera labulen daki-daki. Ina son ku yi aiki tare don komai ya kammala kafin yamma..." Ching Ching ta kalli Gely, Gely ma ta kalle ta... Wannan shi ne karon farko da za su yi aiki kafada-da-kafada ba tare da Chief yana kusa ba... ✨ A Babban Falo... Gely tana tsaye a kan wani dogon matakala tana ƙoƙarin haɗa wasu wayoyi a saman silin, yayin da Ching Ching take kasa tana ƙoƙarin miƙa mata labulen ɗaya bayan ɗaya... "Miƙo min labule na gaba," Gely ta bada umarni ba tare da ta kalle ta ba... Ching Ching ta ɗauki labulen, amma maimakon ta miƙa mata cikin natsuwa, sai ta tura shi da karfi yadda Gely za ta rasa daidaiton ta... "Gashi nan! Ke komai sai kin nuna isa, kamar ke ce kika yi kanki." Gely ta riƙe matakalar da kyau, ta kalli Ching Ching daga sama... "Kina ƙoƙarin sanya ni faɗuwa ne? Kin sani cewa idan na faɗo a kanki, nauyin karfen jikina zai iya kakkarya ki." Ching Ching ta bushe da dariya... "To ai gara na karye da na zauna ina ganin kina nuna wa Uncle ke ce komai. Kin san me ya faɗa min dazu? Ya ce har yanzu yana tausayi na..." Gely ta sauƙo daga kan matakalar a hankali har ta iso saitin fuskar Ching Ching... "Boss yana tausayinki ne saboda ke marainiya ce mai bukatar kulawa, ba don yana sonki a matsayin mace ba. Kuma idan har kika sake taɓa shi a ofis kamar yadda kika yi ɗazu, zan sanya na'urorin tsaro su daka miki wutar lantarki wato electric shock da sunan kuskure..." Ching Ching ta zaro ido... "Kin ga! Kishi kike yi! Uncle ya hana ki kishi amma har yanzu kina nan kina yi." Daidai nan, Chief Onyx ya leƙo falon don ganin yadda aikin yake tafiya... Ching Ching tana ganinsa, sai ta saki labulen hannunta ta ruga wurinsa, ta faɗa jikinsa tana kuka.. "Uncle! Uncle! Kaga Gely ko? Wai cewa ta yi idan na sake taɓa ka zata sanya wutar lantarki ta kashe ni! Ka ji irin muguntar da take kulla min a ƙarƙashin ƙasa ko?" Onyx ya kalli Gely, sannan ya kalli Ching Ching. Ya rasa wanda zai yarda da shi a cikinsu, domin kowacce tana da tata makarkashiyar... Ching Ching ta daskare a wurin lokacin da Chief Onyx ya ture ta daga jikinsa. Kalaman sa na sake jaddada mata cewa ita 'Yar Aiki ce ke sun sanya ta jin wani irin ɗaci a makogwaronta... Ta kalli Gely, ta tarar Gely tana kallonta da wani irin sanyayyen kallo na nasara, kodayake Gely ba ta yi magana ba... Bayan Chief ya wuce, Ching Ching ta juya tana turo baki, tana gatsine da harara kamar za ta cinye Gely... Ta koma ta ɗauki labulen ta jefa shi a ƙasa kusa da ƙafar Gely... "Gashi nan! Kowa ma a gidan nan bashi da mutunci,". ta faɗa cikin rarraba murya... Gely ta sunkuya a hankali ta ɗauki labulen ta goge shi... "Ɓacin ranki ba zai sauya gaskiya ba, Shugaba Ching Ching. Boss baya son damuwa, kuma ke kin zama damuwa a gare shi. Ki bari mu kammala wannan aikin idan ba kya son ya ƙara fushi da ke." Ching Ching ta tsaya tana kallon yadda Gely take motsa jikinta cikin tsari... "Ke Gely, wai tunda kike kishin nan, me ya sa kike ikirarin ke inji ce? Kin sani sarai kina son Chief, kuma kina jin haushin yadda yake magana da ni." Gely ta koma kan matakalar, ta fara saka labulen a jikin na'urar saman ɗakin... "Lissafi na ya gaya min cewa Boss mutum ne mai daraja. Kishi ko soyayya duk wasu sakonni ne na biochemical da ke cikin dan adam. Ni kuwa, tsarin nawa electronic ne. Amma hakan baya nufin zan bari wata yarinya ta lalata tsarin zaman lafiyarsa..." Ching Ching ta kalli ƙafar matakalar, wani mugun tunani ya faɗo mata.. Ta matsa kusa da matakalar, ta fara jijjiga ta a hankali tana nuna kamar tana gyara labule ne a ƙasa... "Haba Gely, kema ai kina son ki zama mutum ko? Na gani a fina-finai, duk robot irinki yana son ya zama mutum don ya mallaki zuciyar masoyinsa..." Gely ta ji matakalar tana rawa, ta duba ƙasa ta ga Ching Ching tana ta jinjiga ƙafar matakalar... "Ching Ching, ki dakata da wanna shashanci... Wannan aikin yana da haɗari." "Ba zan dakata ba!" Ching Ching ta faɗa tana ƙara jijjiga matakalar... "Sai kin faɗa min yadda kike ji idan Chief ya sumbace ni...!" Daidai nan, hannun Gely ya sarƙe a cikin wayoyin wutar lantarki na labulen, wani ɗan tartsatsin wuta ya fito. Matakalar ta ƙara girgiza, Gely ta rasa daidaitonta, ta fara zamowa ƙasa... Ching Ching ta firgita ta ja baya tare da faɗin, "Ayyah! Gely za ta faɗo!" Amma maimakon Gely ta faɗo a ƙasa, sai ta yi amfani da saurin na'ura ta damƙo jikin bangon, sannan ta diro ƙasa daidai gaban Ching Ching. Sautin ƙarfen jikinta ya yi ƙara Gwam! a kan tiles ɗin falon... Gely ta matso da fuskarta dab da ta Ching Ching, idanunta sun yi wani irin haske mai ban tsoro... "Kin yi kuskure mai girma. Yin wasa da rayuwar na'ura a lokacin aiki, babban keta doka ne. Kuma yanzu, zan tabbatar Boss ya ga wannan danyen aikin naki." Ching Ching ta fara ja baya, tana girgiza kai "Ƙarya kike... ni... ni gyara miki matakalar nake yi..." Gely ba ta tsaya sauraron duk maganganun kare kai na Ching Ching ba... Ta juya da sauri, takun ƙafafunta na ƙarfe suna bada sauti mai ƙarfi a kan tiles ɗin falon, ta nufi ofishin Chief Onyx... Ching Ching ta biyo bayanta da gudu, tana kuka tana murza idanu... "Gely! Gely! Wallahi wasa nake yi! Kada ki gaya masa, Ke gwangwani!" Amma Gely ta riga ta isa ƙofar ofishin, ta danna maɓallin buɗewa sa’ilin da Chief Onyx yake ƙoƙarin duba wasu taswirori. Ya ɗago kai yana kallonsu cikin mamaki da gajiya... "Wai meye hakan kuma?" Gely ta tsaya daram a gaban teburinsa... "Bods, ina son na gabatar maka da rahoton Safety Violation wanda ya faru a lokacin aikinmu na falon baƙi." Onyx ya ja numfashi, ya kalli Ching Ching wadda ta tsaya a jikin ƙofa tana kuka tana girgiza kai... "Ina saurarenki Gely." Gely ba ta yi magana da baki ba, sai kawai ta ɗaga hannunta na hagu, wani haske ya fito daga cikin hannun nata Hologram Projector, nan take wani babban allo na bidiyo ya bayyana a iska a gaban Chief... A cikin bidiyon, an ga komai fili, yadda Gely take kan matakala, da kuma yadda Ching Ching ta matsa ta fara jijjiga kafar matakalar da duk ƙarfinta, har sai da Gely ta kusa faɗowa sa'ilin da wutar lantarki ta fara tartsatsi... Chief ya kalli bidiyon har ya ƙare. Fuskar sa ta sauya daga gajiya zuwa wani irin fushi mai sanyi wanda ya fi kowane zafi... Ya kalli Ching Ching, wadda yanzu jikinta ya fara rawa domin ta san kyamarorin jikin Gely ba sa ƙarya... "Ching Ching," Onyx ya kira sunanta cikin muryar dake nuna tsananin takaici... "Kin san cewa idan Gely ta faɗo daga wannan matsayin, ba ita kaɗai za ta ji rauni ba? Wayoyin wutar da suke wurin za su iya tada gobara a gidan nan, ko kuma su kashe ki ke kanki idan wutar ta taɓa ki..." Ching Ching tana turo baki ta ce, "Uncle... wallahi wasa nake son yi da ita ne... tana nuna min isa ne shi ya sa..." "Wasa da rayuwa ba wasa ba ne!" Onyx ya daka mata tsawa. Ya kalli Gely, ya ga yadda wasu wayoyin hannunta suka ɗan ƙone saboda tartsatsin wutar... Ya juya ya kalli Ching Ching ya ce.. "Tunda wasa kike so, to yau babu barci a gadon da kike kwanta wa. Za ki kwana a cikin ɗakin ajiye tarkace, kuma ba za ki ci abinci ba har sai kin goge dukkan fentin dake jikin bango... Kuma idan kika sake kuskure ɗaya, zan ƙira mahaifinki na sanar masa cewa, yayi haƙuri dake domin yanka ki zanyi..!" "Aiyyooo Ni rago ce... Da za'a yanka ni..." ta furta tana turo baki... Ya ce, "ai da ke, gwara a kawo mun ragon, idan na ɗaure shi zan zauna cikin ƙoshin lafiya..." Ching Ching ta fashe da kuka ta nufi ɗakin ajiye tarkace, tana jin haushin kanta da kuma tsananin ƙiyayyar Gely... Gely kuwa ta tsaya tana kallon hanyar da ta bi, sannan ta juyo ta kalli Chief... "Boss, zan je na gyara na'urorin jikina da suka lalace," Onyx ya jinjina kai, ya dafe kansa yana tunanin cewa zamansa da Ching Ching ya fara zarce yadda yake tsammani.... ✨✨✨ _Alhamra City_ Bayan kwanaki na fargaba da tunani, Ayat ta tsinci kanta da rashin natsuwa... Ta kasa jure rashin jin motsin King Diamond, kodayake tana da Reems na gaske a kusa da ita... Ta sanya kayanta na jami’i, ta fice zuwa bakin kogi wurin da ta saba hutawa... Tana isa, ta dafe sarƙar dake wuyanta, ta lumshe ido tare da ambatar sunan "King..." a ranta.. Kafin ta buɗe idonta, ƙamshin jikinsa ya gauraye iskar kogin. King Diamond ya bayyana, tsaye cikin kwarjini... Ayat ta yi maza ta miƙe, ta nuna ɓacin rai... "Me ya sa ka zo? Na gaya maka ka fita daga rayuwata!" ta faɗa tana huci... Diamond bai tanka ba, sai murmushin gefen baki da ya yi, ya zauna a kan wani babban dutse tare da yi mata nuni da ta zauna a kusa da shi. Cikin turo baki, ta zauna tana harararsa.. Bayan sun kwashe mintuna cikin shiru, Diamond ya kalli ruwan kogin, sannan ya dubi Ayat... "A zaman da na yi a cikin masarautarku, na ga abubuwa da dama... Masarautar Alhamra ba ta cancanci sunanta ba. Masarauta ce dake numfashi akan jinin talakawa." Ayat ta zabura ta miƙe, tana nuna shi da yatsa, muryarta na ainahi yana fito... "Kana so ka raina mana masarauta ne? Ka kiyaye kalaman ka!".. "Na riga na raina ta, Ayat," Diamond ya dakatar da ita da wani irin kallo... "Domin masarautar ku ba ta da tsarin adalci. Na zagaya can kurkukun ku na ɓoye, na ga tsofaffi waɗanda suka isa haifan mahaifinki, na ga mata da ƙananan yara a kulle cikin duhu. Ba abinci, ba ruwa, sai duka da azaba... Abin da ban sani ba shi ne… me suka aikata?” Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce a hankali... Yawancinsu laifinsu ɗaya ne, shine talauci... Sun kasa biyan harajin da gimbiyoyi suke amfani da shi wajen siyan mayukan ƙamshi daga ƙasashen waje."... Kalaman Diamond ne suka fara ratsa zuciyarta kamar kibiyoyi... Ya ci gaba da bayyana mata yadda jami'an fada suke wulakanta mutane a kasuwa, da yadda yara suke mutuwa saboda rashin magani yayin da gimbiyoyi suke gasar girman kai.. Kalmar ta tsaga zuciyar Ayat da take mazannin Inuwa a yanzu... Hawayenta suka fara gangarowa. Fuskarta ta jiƙe sharkaf, har gashin gemunta ya fara tujewa... Diamond bai tsaya nan ba... “Masarautar ku tana rayuwa ne da sunan sarki, amma babu adalcinsa... Gimbiyoyi na cikin fada amma talakawa na cikin ƙabari suna raye.”... Ayat ta rufe fuska da tafin hannunta.. “Ka yi shiru…” ta faɗa cikin raunannen murya... Ya miƙe tsaye, ya matso kusa da ita, ya ce cikin tsanani.. “A’a. Yau ba zan yi shiru ba.” Ya matso kusa da ita, ya kalli cikin idanunta da suka yi jawur... "Ayat ko in ce Inuwa...Shin me ya sa kike sanya wannan shigar maza kina fita? Shin don ki kare talakawa ne ko don ki taimaka musu? Ko kuma don ki gamsar da son zuciyarki na son yawo ne kawai?" Ayat ta kasa ba shi amsa, sai kuka dake ƙara ƙarfi... Sai ya ƙara faɗi da kalma mai ɗaci.. “Gaskiya ɗaya zan faɗa miki, Ayat… kaf gimbiyoyin wannan masarauta, babu wanda ke da amfani...Hatta ke, domin burinki shine ki yi ɓadda kama ki fita yawo da wasa.... Idan har ba za ki iya amfani da wannan damar wajen ceton waɗanda suke ƙasa da ke ba, to wannan shigar taki ta jami'i babban kuskure ne."... Kalmar ta sauƙa kamar hukunci.. Ayat ta buɗe baki… amma ta kasa furta komai... Idanunta sun yi jawur, hawaye na zuba ba tare da izini ba... Jikinta na rawa kamar ganyen da iska ke kaɗa wa... “Ya isa!” ta fashe da kuka, muryarta na karyewa.. “Ya isa haka, ka daina zarginmu kamar bamu san me muke ba...!” Ta ƙara matsowa dab da shi kamar zasu haɗe, ta ce, “Kana tunanin ban sani ba? Kana tunanin ban gani ba? Kowace rana ina ganin wahalar su!”... Ta buga ƙirjinta da tafin hannu.. “Nan! A nan nake ji!” Hawayenta suna gangaro wa cikin tsananin firgici... “Amma ka san menene?” ta ce cikin kuka.. “Ni mace ce! Gimbiya ce! An haife ni cikin sarƙoƙi na zinare.. amma sarƙoƙi ne!” Ta juya baya kaɗan, ta share hawaye da hannun rigarta.. “Ba a bar ni in fita ba. Ba a bar ni in yi magana ba.....Duk abin da zan yi, sai ace sunana zai lalace! Masarauta! Martaba! Izzah! Waɗannan kalmomi sun kashe ni tun ina yarinya!” Ta kalle shi cikin razanannun idanuwanta.. “Shi ya sa nake shigar maza! Ba don nayi wasa ba, Ba don a raina ni ba, sai don na samu numfashi... Don na iya gani da ido na sannan na ji da kunnena..**” Ta durƙusa ƙasa ba tare da shiri ba.. Kukanta ya ƙara tsananta.. “Kana ganin ina gudu ne? A’a! Ina neman hanya ne.. Ina neman inda zan fara!**” Diamond ya tsaya shiru, fuskar sa a ɗaure... Sai ya ce cikin kaifaffen murya.. “Kuka ba ya gyara masarauta, Ayat...” Ta ɗago kai a firgice. “Ka daina faɗin haka, kana ƙona mun rai ne!” ta sake fashewa da kuka.. “Ka daina raina min ciwo na!.. Kai ka zo ka gani ka tafi ne! Ni kuma zan zauna da sakamakon hakan...” Ta miƙe tsaye ta matso kusa da shi, har suka kusan shafar juna... “Ka yi min hukunci cikin zafi.. Amma ka san me? Inda abun na da sauƙi to da ni ce ta fara gyara komai!” Diamond ya ɗan yi murmushi cikin tsauri... “Shi ya sa kike da rauni,” ya ce... “Kin fi kowa ganin gaskiya, amma kin fi kowa tsoron ɗaukar nauyi.” Kalmar ta ƙara doke zuciyarta.. “Tsoro?” ta ce da ƙarfi. “Ka san meye asalin tsoro na? Uhmm to na fi tsoron zama kamar su! Na fi tsoron zama gimbiya marar amfani!..” Cikin ɗaga murya ya furta. “To ki daina kuka! Ki daina ɓoye kanki! Ki tsaya a gaban masarautarki da sunanki na gaskiya! Idan kina son kare talakawa ki fara da gaskiya!” Ta kalle shi cike da fushi da kuka... “Kai ba ka da ikon gaya min yadda zan ceci masarauta ta... Ba ka san abinda zan rasa ba idan na tsaya tsaye!” Ya matso kusa da fusakarta har sai da ta lumshe rinannun idanuwanta sannan ya furta mata a hankali.. “Na sani. Kuma shi ya sa na zo. Domin zaki rasa komai kafin ki ceci komai.” Bayan shiru ya ratsa, iskar kogin na kaɗawa, Ayat ta buɗe idonta waɗanda suka ɗan natsu kaɗan duk da hawayen dake cikinsu... Ta kalli Diamond, ta ga wani abu a cikin idonsa wanda ba ta taɓa gani ba.. Ya nuna mata cewa ba wai ya zo ne domin ya dasa mata ciwo a ranta ba ne, ya zo ne ya nuna mata cewa ita kaɗai ce maganin ciwon masarautar... ​"Diamond," ta furta cikin siririyar murya... "Zan rasa komai... amma zan tabbatar na ceci waɗanda suke bukatar ceto." ​Diamond ya jinjina kai, sannan ya fara ɓace wa a hankali cikin hazo... "Zan kasance inuwar dake biye da Inuwa... har sai ranar da Ayat za ta tsaya da kafafunta.".... Muryar ta bi iska lokaci guda ya ɓace.. Ya barta da ciwon zuci mai tsanani domin ta tsani ta ji ko ta ga wasu suna cikin wani mummunan hali, hakan yasa duk sanda ta fita sai ta tallafa wa marasa shi kuɗin aljihunta saboda su rage raɗaɗi.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣8️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan dawowarta daga bakin kogi, Ayat ba ta jira gari ya waye ba. Cikin shigar Inuwa, ta nufi ofishin Master Ibrahim dake cikin babban sashen tsaro na masarauta.. A lokacin, Master Ibrahim yana duba wasu taswirorin tsaro a ƙarƙashin hasken fitila, fuskarsa cike da gajiya.. ​Jin motsin mutun, ya ɗago kai, hannunsa ya kai kan takobinsa.. "Wane ne?" ​"Ni ne Master, Inuwa ne," ta fada cikin natsuwa yayin da ta shigo cikin hasken fitilar... ​Master Ibrahim ya sassauta ransa, ya ajiye takobin.. "Inuwa? Me ya faru a wannan lokacin? Na zaci kana sashenka kana huts wa." ​Inuwa ya ƙarasa gaban teburin, ya tsaya dakyau, ƙafafunsa a buɗe, hannayensa a baya kamar soja na gaske.. "Master, na zo ne in roƙi alfarma guda ɗaya. Ina so a rantsar da ni a matsayin PA (Personal Assistant) ɗinka a hukumance. Ina so in yi rantsuwar aminci ga masarautar Alhamra a daren nan." ​Master Ibrahim ya nuna mamaki a fuskarsa.. "Rantsuwa? Amma ai na riga na ba ka muƙamin. Me ya sa kake sauri haka, kuma a cikin daren nan?" ​Inuwa ya gyara tsayuwa, idanunsa a dishe. "Master, na fahimci cewa yin aiki ba tare da cikakken ikon rantsuwa ba, tamkar tafiya ce ba tare da makami ba. Ina so in hidimta wa wannan masarautar fiye da yadda nake yi a baya. Ina so in zama idonka, kunnenka, da kuma hannunka a duk inda zalunci yake." ​ Master Ibrahim ya ga wani abu a idon Inuwa, wani irin kishin ƙasa da gaskiya da bai taɓa gani a idon sauran jami'an fada ba.. ​ Ya miƙe tsaye, ya gyara kakin sa. Ya jawo wani kofon azurfa dake ɗauke da ruwan da aka karanta wa dokokin masarauta, sannan ya zaro takobinsa mai kaifi, ya saita shi a gaban Inuwa.. ​"Daga yau, Inuwa, ka zama fiye da jami'i a gare ni. Ka zama amintaccena." ​Inuwa ya ɗora hannunsa a kan takobin, muryarsa na fita ba tare da rawa ba, ya furta kalaman rantsuwa.. "Na rantse da dukkan martabar Alhamra, zan kare marar ƙarfi, zan yaƙi azzalumai, kuma zan zama mai gaskiya ga masarautar nan koda hakan zai yi sanadin raina." ​Bayan rantsuwar, Master Ibrahim ya ɗauki kati mai nauyi ya rubuta babban umarni (Official Decree). Ya sanya hatimin sa, sannan ya ce, "Wannan katin zata ba ka ikon shiga kowane lungu, kowane kurkuku, da kowane ofis a cikin Alhamra. Duk wanda ya raina ka, ya raina ni. Kuma gobe, zan tura saƙo ga Sarki domin ya sa hannu akan wannan muƙamin naka a hukumance." ​Inuwa ya karɓi takardar, ya yi gaisuwa ta soja... A ransa yana cewa, "Diamond, yanzu ne aka fara wasan. Zan nuna maka cewa mace tana iya zama takobi!" Master ne ya katse shi da faɗin "ina buƙatar gobe da sassafe ka fito domin rantsar dakai a karo na biyu a gaban mutane... Daga nan ta fice, kai tsaye sashenta ta wuce a sirrance dake duhu ya shiga amma haske ta ko ina... _Washegari ✨_ Tun kafin rana ta fito sosai, aka buga gangar taro a babban dandalin jami'an tsaro na masarauta.. Daruruwan jami'ai, tun daga kan kwamandoji, sojojin fada, har zuwa kan masu tsaron kofanni, duka suka taru cikin shigar su ta alfarma. Kowa yana tambayar dan uwansa, "Me ke faruwa? Shin akwai yaƙi ne ko kuma Sarki ne ya dawo?" A tsakiyar dandalin, Inuwa yana tsaye kusa da Master Ibrahim. yana sanye da sabon kakin sa na PA wanda aka yi wa ado da wasu igiyoyin zinare a kafada, yana sanye da baƙin gilashi waɗanda suka boye kumburin idonsa na kukan daren jiya, fuskarsa a murtuke tamkar bashi ne a kansa.. Master Ibrahim ya taka zuwa gaba, ya zare takobinsa ya ɗaga shi sama don kowa ya yi shiru. Shiru ya gauraye filin.. "Jami'an Alhamra! Na tara ku ne a nan don wata muhimmiyar sanarwa," Master ya faɗa cikin muryarsa mai kwarjini.. "Kamar yadda kuka sani, tsaro da adalci sune ginshikin wannan masarauta. Don haka, na zaɓi jami'i Inuwa a matsayin PA (Personal Assistant) na na musamman." Wani gunaguni ya tashi a cikin jami'an. Wasu jami'an da suka daɗe a aiki suka fara kallon-kallo cikin bacin rai da hassada.. Master Ibrahim ya ɗaga hannu ya tsayar da su.. "Wannan ba zaɓi ne na kashin kaina kadai ba. Sarki ya aiko da yardarsa ta hanyar hatimin sa na musamman. Daga yau, Inuwa shine idona. Duk inda kuka gan shi, tamkar ni ne. Yana da ikon shiga kowane ofis, kowane kurkuku, da kuma kowane sashe na wannan fada ba tare da izini ba. Duk wanda ya raina shi, ko ya ki bin umarninsa, zai fuskanci hukuncin cin amanar masarauta!" Master ya miƙa wa Inuwa wani babban takobi na azurfa da aka rubuta sunan sa a jiki. Inuwa ya karba, ya yi gaisuwa ta alfarma, ya juya ya kalli dakarun. A lokacin, fuskarsa ba ta nuna tsoro ba, sai wani irin kwarjini da ya sanya manyan kwamandojin ma sunkuyar da kai... Bayan taron ya watse, Inuwa bai jira komai ba. Ya gyara tsayuwar sa ya kalli wasu dakarun guda huɗu da ya zaɓa.. "Ku biyo ni yanzu. Akwai wasu bayanan sirri da zan bincika a sashin kurkuku na karkashin kasa." Dakarun suka bi shi ba tare da gardama ba. Inuwa yana tafiya zuciyarsa tana tuno kalmomin King Diamond.. "Zaki rasa komai... kafin ki ceci komai." Ya san cewa daga yau, yakin ya fara... Inuwa ya sauƙa zuwa kurkukun ƙasa, wanda dake cike da duhu da wari... Ba a taɓa ganin Master ya zo wannan wurin ba sai yau da PA sa yazo... Inuwa yana tafiya, yana lura da fuskokin mutanen dake cikin sarƙoƙi. Ya ga tsofaffin da King Diamond ya faɗa masa, ya ga yara da mata.. "Wane ne wannan tsohon?" Inuwa ya tambayi mai tsaron kurkukun.. "Ranka ya daɗe, wannan shi ne tsohon da ya gaza biyan harajin gonarsa na shekara biyu," mai tsaron ya ba shi amsa.. Inuwa bai ce uffan ba, ya biyo dukkan ɗakunan, yana rubuta sunayensu a cikin wani ƙaramin littafi. Bai ba da umarnin a sake su ba tukuna, domin ya san idan ya yi hakan yanzu, sauran manyan jami'ai za su iya tawaye. Amma kallon da ya yi wa mutanen, kallo ne na.. "Zan dawo gare ku." ✨✨ Bayan kwanaki biyu, sunan Inuwa ya zama kamar wutar daji a cikin masarautar Alhamra da ma bayan gari. Ana maganar wani matashin PA mai hazaƙa, mai kwarjini, wanda har wasu suke ganin idan ya ci gaba da haka, zai iya fin Master Ibrahim tasiri a fadar... Wannan shahara ta kai kunnen kowace gimbiya, musamman Zayana dake jin cewa kowa ya zama bawan ta.. Inuwa yana ofishinsa, sai ga wani bawan Gimbiya Zayana ya shigo cikin girmamawa. Ya ajiye wani ƙayataccen katin gayya na zinare dake ƙamshin turaren Oud... "Ranka ya daɗe, Gimbiya Zayana tana gayyatar ka zuwa sashenta a daren yau. Tana son tattaunawa akan wasu al'amura na tsaro," bawan ya faɗa ya fice.. Inuwa ya ɗauki katin, yayi murmushi. Ya sani cewa gimbiyoyin Alhamra ba a barin su fita, sashensu shi ne masarautar su. Idan aka ƙira jami'i sashen gimbiya, ko dai ana son a ba shi cin hanci ne, ko kuma ana son a ƙulla masa makirci ne.. Da daddare bayan Inuwa ya kammala komai, ya nufi sashen Gimbiya Zayana.. Sashen ya kasance daban da sauran, komai na cikinsa ya nuna almubazzaranci da dukiyar talakawa. Zayana tana zaune a kan wata doguwar kujera, sanye da riga ta alfarma wadda aka yi wa ado da lu'u-lu'u.. "Ka zo, Inuwa," ta faɗa cikin murya mai daɗi wadda take amfani da ita idan tana son cinma wata manufa... "Na ji labarin yadda kake shirin zama zakaran masarauta. Har ana cewa kusan ka kusa fin Master Ibrahim iko." Inuwa ya tsaya ba tare da ya sunkuyar da kai ba.. "Gimbiya, aiki na kawai nake yi. Kuma babu jami'in da ya kai Master Ibrahim." Zayana ta miƙe tana zagaye shi, ƙamshin turaren ta ya mamaye wajen... "Inuwa, ni mace ce mai son jarumai. Ina so ka zama nawa. Ka bar aiki ƙarƙashin Master Ibrahim, ka dawo sashena ka zama PA na kaina. Zan ba ka ninkin kuɗin da kake karɓa, sannan kowa a fada zai rinƙa jin tsoronka..." Ta ɗora hannunta a kafaɗarsa, tana ƙoƙarin amfani da kyan fuskarta don rudar da shi. Inuwa ya ji zuciyarsa tana tashi. A ransa ya ce, "Gimbiya Zayana, ashe har yanzu ba ki san ko ni waye ba." Inuwa ya matsar da hannun nata cikin sanyi ba tare da nuna ƙarfi ba .. "Gimbiya, ni ba na siyarwa ba ne. Kuma matsayina na PA na Master Ibrahim, har da kula da yadda gimbiyoyi suke mu’amala da kuɗaɗen masarauta yake. Don haka, kada ki ɓata katin gayyarki a kaina." Zayana ta fusata, cat eyes ɗinta suka yi wuta... "Ka nuna cewa ka raina ni? To ka sani, duk wanda ya ƙi zama abokina a fadan nan, to makiyina ne. Kuma makiyina ba ya daɗewa a raye." Inuwa ya yi murmushin raini, ya gyara baƙin gilashin idonsa... "Na ji tsoro, Gimbiya... Amma ki sani, makiyin naki yana da asirai da yawa a aljihunsa." Ya juya ya fice, ya bar ta tana huci... Bayan ta bar sashen Zayana cikin fushi, Ayat ta lallaɓa ta koma sashenta na gimbiyoyi... Tana shiga, ta garkame kofarta dake saje da jikin bangon ɗakin, wanda ba wanda zai yi tunanin akwai ƙofa a wurin... Cikin sauri ta cire kakin PA na musamman dake jikinta, kayan da suke da nauyi amma yanzu ta saba da su har tana jin su tamkar fatar jikinta... Bayan ta fito daga wanka, ta sanya riga ta gimbiyoyi mai laushi. Ta tsaya a gaban madubi, tana kallon kanta. Tana murmushi ganin yadda ta yi nasarar yaudarar duk masarautar.. "Inuwa..." ta ƙira sunan a hankali, "Yanzu ka zama babban jami'i, amma Ayat ce take juya akalar komai." Babban fargabarta yanzu ita ce Saratu da sauran bayinta masu kawo mata abinci da gyara ɗaki... Tunda yanzu a matsayin Inuwa dole ta fita tun asubahi kuma ba za ta dawo ba sai dare, ta yanke shawarar yin wata dabara.. Zata sanar da manyan bayinta cewa tana fama da wani irin ciwon kai da baya son hayaniya ko haske... Don haka, zata bayar da umarnin cewa babu wanda zai zo wurin bedroom ɗinta sai idan ta kira... Ta ce a riƙa ajiye mata abinci a babban falon sashenta, sannan su fita su rufe kofa. Wannan zai ba ta damar shigowa ta kofar sirri a matsayin Inuwa, ta ci abincin, ta sake fita... Kuma zata sanar cewa daga yau ita zata na gyara bedroom ɗinta, da wankin bathroom da komai duk abinda ya shafi bedroom... Kuma kamar yadda kowace masarauta take ware wa manyan jami'anta wurin zama na musamman (Officer’s Quarters), Master Ibrahim ya ware wa Inuwa wani sashe mai kyau da kima kusa da ofishin tsaro.. Sashen yana da faɗi, akwai ɗakin karɓar baƙi, ɗakin kwana mai ɗauke da gado na alfarma, da kuma wani ɗaki na sirri da Inuwa zai rika ajiye makamansa da takardun rahoton sa... Wannan ma babban kalubale ne a rayuwarta..amma ta yanke cewa.. Wannan sashen zai zama Gidan ma ɓoya wato Safe House... Idan ta fita daga sashenta gimbiya da asubanci, sai ta nufi can ta ƙarisa wayewarta a matsayin Inuwa kafin ta fito filin aiki.. Wannan zai sa mutane su ga cewa Inuwa yana da nasa ɗakin, kuma baya bukatar zama a wani wuri daban... Duk da tana jin daɗin nasararta, zuciyarta ba ta daina bugawa ba. Idan ma'aikatan gyaran sashen PA suka shiga dakin Inuwa suka iske turaren mata ko kuma wani abin da zai nuna mace ce take zama a wurin, to asiri zai tonu... Dole ta zama mai tsafta da taka-tsantsan... "Dole ne in riƙa raba rayuwata kashi biyu," Ayat ta faɗa wa kanta yayin da take shirin kwanciya.. "Idan na zama Inuwa, dole in daina kamshi irin na Ayat. Idan na zama Ayat, dole in daina tafiya irin ta Inuwa."... Haka ta kusan kwana tana wannan tunanin... ✨✨✨ Maayah tin daga lokacin da wancan malamin ya bayyana ya kuma nuna ikonsa ya fi nata daga lokacin take cikin damuwa, ta ƙi cin abinci, ta daina yawan shiga Swimming Pool! Ta zauna a ɗakinta cike da shiri na faɗa!.. Mama Liyatu ta shigo cikin tsoro ganin yanayin Maayah ya sauya kwana biyun nan... “Gimbiya, me ya same ki haka? Kullum a cikin fushi duk da daman ba'a gane farin cikin ki da baƙin cikin ki amma kin rage fitowa falo! Wane ne ya yi miki laifi a Makaranta? Ko dai a cikin masarautar nan ne?..” Maayah ta kalli Mama Liyatu cikin harzuƙa.. “Wani sabon malami ne da suka kawo! Wai shi Uncle Jalal! Ya yi min wulaƙanci! Ya ƙira ni da jahila! Ya yi min tsawa! Ya keta min Ikon Sarauta!” Ta ƙarisa tare da zubda hawaye.. Mama Liyatu ta tsorata sosai domin rabon da ta ga hawayen Maayah ta manta sai lokacin da tayi jinya.. Mama Liyatu ta rufe fuskarta da hannu!.. “Yaa ALLAH! Wannan kuskure ne! Maayah, ki bar shi! Malami ne! Ki yi haƙuri!” Maayah ta miƙe.. “A’a! Mama Liyatu! Ba zan gafarta masa ba! Idan har ba a hukunta shi ba, to Sarauta ta ta zama na ƙarya! Na riga na kori Minista! Wane ne Malami da zai zo ya zaunar da Gimbiya! Ni ce Sarauniya!”... Ta ƙarisa maganar tare da shirin shiga bathroom domin yin wanka, "Bani da niyyar zuwa school amma sai na je, domin bazan shiga damuwa har na haka kaina zuwa saboda wani jakin malami..." Mama Liyatu ta ce, "Amma Gimbiya, ai kin makara yanzu fa ƙarfe 9 ne..." Maayah ta juyo tana kallonta ta ce, "Zan iya zuwa duk lokacin da naso, saboda haka ki je ki haɗa mun breakfast kafin na fito a wanka..." Hakan kuwa akayi.. Tana zaune a gado, ta gama shiri!.. “Zan nuna masa! Zai san cewa Girman Kaina ya fi girman Iliminsa! Zan yi amfani da Ikon Kuɗi da kuma Siyasa don in rushe shi! Ko kuma in sa shi ya zama bawana!” Ta kuma shiga wani tunani da bam game da shi... “Amma kuma sai dai Jalal yana da kyau! Surar jikinsa tana da kyau! Da ace bai yi min raini ba, da na yi amfani da shi a matsayin Saurayin Wasa! Amma yanzu, zan wulaƙanta shi! Zan sa shi ya roƙe ni a gaban kowa! Sai ya gane cewa Gimbiya Maayah ba ta da iyaka!” ✨✨ Ranar ta fara ne da wani irin zafi, amma zafin ran Uncle Jalal ya ninka na ranar yawa. Yana tsaye a cikin ajin lissafi computer, idanunsa radau tamkar na zakanya. Ya riga ya shimfiɗa doka.. "Duk wanda ya makara, zai ɗanɗani zafin rana a waje..." A waje, ɗalibai kusan goma ne suke tsaye duk da sun fi awa da zuwa, jikinsu har rawa yake yi saboda sanin waye Uncle Jalal, mutumin da ya kusan kashe ɗaliba a Maiduguri saboda raini... Can sai ga jerin tsararrun motoci. Motar Maayah ta tsaya cif, sannan bodyguards suka buɗe mata ƙofa.. Ta fito cikin takun kasaita, sanye da rigar makaranta wadda aka yi wa ado da gwal... Ta kalli ɗaliban dake waje cikin kallon banza, ta wuce su kamar ba mutane ba... Ta zo shiga aji, sai wata murya mai nauyi da kwarjini ta dakatar da ita.. Ba tare da ya kalle ta ba "Tsaya a nan. Dokar gidan ku ba ta aiki a cikin ajina." Maayah ta tsaya cak. Ta cire gilashin idonta, ta kalle shi tun daga ƙasa har sama.. "Kai kake magana da ni haka? Ko baka san wacece ni ba? Ni ce Maayah, wadda kake cin abinci a ƙarƙashin inuwar masarautar mahaifinta." Uncle Jalal ya juyo, ya tako zuwa bakin ajin idonsa cikin nata.. "Ni kuma suna na Jalaludden... Kuma a nan, ni ne sarki. Mahaifinki ne ya gina makarantar, amma ni ne nake gina tunanin ku... Ki koma waje ki tsaya a rana kamar sauran, ko kuma ki koma gida." Bodyguards ɗin Maayah su biyu suka matso, fuskarsu a murtuke.. Wani daga ciki ya furta "Malam, kana wasa da rayuwarka ne? Wannan Gimbiya ce!" Uncle Jalal ya yi murmushin raini.. "Ko aljani ne kuka turo, idan ya shigo ajina a makare ko ba da izini ba, sai na koya masa hankali... Idan kuma ku ka matso kusa da ni, zan nuna muku cewa ni ɗan Nigeria ne, ba a ban tsoro da uniform..." Malamai ne suka taru suna ba Uncle Jalal haƙuri... "Dan Allah Uncle Jalal, baka san wacece ita ba? Za a iya rufe mana makaranta!".. Idonsa akanta ya furta.. "In dai tana so ta shiga aji na yau, to hukunci biyu ne, Ko ta tsaya a rana na awa guda, ko kuma ta sha bulala 10 a tafin hannunta!" Maayah ta girgiza saboda ɓacin rai. Wannan ne karon farko da wani ya kalle ta ya faɗi wannan maganar.. Cikin rawar murya ta fushi ta furta "Bulala? Ni za ka buga? Talaka kawai! Kai da baka da komai sai wannan tsohuwar rigar dake jikinka? In har ka kuskura ka taɓa tsokar jikina, to a yau zaka samu labarin na sheƙe kaina, kuma jini na zai zama silar rugujewar zuri'arka!" Kowa a cikin malaman mamaki yayi jin ta ƙira shi da talaka, alhalin shima ɗan manya ne.. Uncle Jalal ya zuba mata ido, ya ga tana rawar murya kamar za ta fashe da kuka saboda tsoro da girman kai... Ya lura cewa tana shirin yin kuskure mafi girma. Daga ƙarshe, saboda roƙon sauran malamai, ya ƙyale ta ta shiga, amma da wani sharaɗi a ransa... Uncle Jalal ya ci gaba da koyarwa. Maayah tana zaune a baya can, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana danna wayarta iPhone ta alfarma, tana hirar tsegumi da ƙawayenta, tana tura musu hotonsa tana yi masa ba'a... Ba zato ba tsammani, taji an gizge wayar daga hannunta da ƙarfin tsiya.. Ta miƙe tsaye tana harararsa, "Ba ni waya ta yanzu! Ka san nawa aka saye ta?" Ta ce, "Ban sani ba, kuma ba na buƙatar sani... Amma na sani cewa a cikin aji, hankali yana kan allo, ba kan waya ba. Wannan wayar tana hannuna har sai an tashi. Idan kika sake magana, zan fasa ta a nan ƙasa." Maayah ta koma ta zauna, hawayen takaici suka cika idonta. Duk ajin ya yi shiru, kowa yana mamakin jarumtar Uncle Jalal... Bayan an tashi, kowa ya fita. Maayah ta tsaya tana jiran wayarta. Uncle Jalal ya miƙa mata ita a hankali.. "Gimbiya, kiyi kuka idan kina so. Amma ki sani, daraja ba a sayen ta da kuɗi ko sarauta, ana samun ta ne ta hanyar ladabi. Gaba ki kiyaye ni." Maayah ta fizge wayar, ta watsa masa wani kallo mai tafiya da mashi, sannan ta juya ta fice... Ƙarfe biyu na rana, kowa ya watse a makarantar... Uncle Jalal ya fito daga cikin ginin makarantar, riƙe da jakar laptop ɗinsa. Ya nufi inda ya faka babban mashinsa (Superbike) kalar baƙi da jan wuta, wanda kowa ya san darajarsa ta haura miliyoyin da nairori... Ya ɗauko Helmet ɗinsa mai ƙyalli, ya saka, sannan ya tada injin mashin ɗin.. Sautin mashin ɗin kadai ya isa ya tsorata duk wani mai ƙananan motoci a wurin.. Bayan ya fita daga makarantar ya hau kan tsararren kwalta sai ga motocin Maayah guda uku sunyi parking a gefen kwalta suna jiran fitowarsa, ganin ya fito yasa suka bi bayansa.. Suna isa wani lungu da babu mutane sosai, sai motar farko ta yanke masa gaba, ta biyun kuma ta tare shi ta baya. Dake ba wani gudu yake akan mashin ba, kuma bai san ana biye da shi ba... 🔥 Jalal ya kashe injin mashin ɗinsa a hankali. Bai ko cire Helmet ɗin ba, ya sauka daga kai ya tsaya tamkar wani soja na musamman.. Maayah ta fito daga motarta, tana sanye da gilashinta akan dara-daran idanuwanta, fuskarta cike da izgilanci... "Jalal, na gaya maka sarauta ta fi ƙarfin koyarwar ka. Yau za ka gane cewa ko daga ina ka fito, a nan Alhamra ni ce mai iko. Ku sauƙe mun kan ɗan banza...!" Bodyguards guda huɗu suka tunkaro shi. Na farkon ya kai masa naushi, Jalal ya ɗaga hannu ɗaya ya tare naushin, sannan ya yi amfani da karfin Helmet dake rufe da fuskarda ya bugi hancin mutumin.. Kwas! Jini ya ɓalle.. Sauran biyun suka tunkaro shi da sandunan tasers.. Jalal ya yi tsallen kurege, ya buga wa ɗaya ƙafa a ƙirji, ya kuma damƙi hannun ɗayan ya murɗe shi har sai da ya ji ƙarar ƙashi. Cikin ƙasa da minti biyar, ƙataguban mazajen da ake ji da su a fadar Alhamra suna birgima a ƙasa cikin azaba.. Maayah ta ja da baya da gudu, tana rawar jiki. Ta nufi motarta da nufin ta arce, amma Jalal ya riga ta. Ya damƙi damtsenta, ya juyo da ita da ƙarfi... Cikin muryar dake tashi daga cikin Helmet... "Kin yi tunanin kowa tsoron ki yake yi? Kin saba da malaman da kike saya da kuɗi, to ni kuɗin mahaifina ma ba su gaban idona balle ke..." Yana magana, ya finciko jakar hannunta mai tsada da nufin ya jefar da ita gefe don ya koya mata hankali... Amma yayin da ya finciki jakar, sai ta buɗe, kayayyakin ciki suka watse a kan kwalta... Dalolin kuɗaɗe ne da turaruka suka zubo, amma a tsakiyarsu, wasu kwalabe guda biyu da ledoji masu ɗauke da kwayoyi (Tramadol da sauran kwayoyin sa maye) suka zazzage... Jalal ya saki hannunta, ya cire Helmet ɗinsa. Gumi na yanko masa, idanunsa suna kallon kwayoyin. Ya durƙusa ya ɗauki kwalbar, ya girgiza ta... "Wannan ne sirrin Izzah taki? Kwayoyi kike sha don ki manta da rashin tarbiyyarki? Ashe Gimbiya Maayah ƴar maye ce?" Maayah cikin tsoro da fargaba tayi saurin durƙusa wa ƙasa, duk wani taƙama da girman kai ya tafi. Ta sani sarai cewa idan labarin nan ya fita, ba ma makaranta ba, duk darajar gidansu ta zube... Tana kuka cikin tsoro "Uncle Jalal... don Allah. Ba yadda kake tunani ba ne. Ka ba ni kayana... zan biya ka duk abinda kake so!" Jalal ya kalle ta cikin rainin wayo "Kina tunanin ina buƙatar kuɗinki? Ki duba mashin ɗin da nake kai, ya ninka albashin dukkan malaman makarantar nan sau goma. Ban zo nan koyarwa don kuɗi ba, na zo ne don in gyara ɓatattun yara irinki." Ya ɗauki kwayoyin ya zuba a aljihunsa, sannan ya kalli Maayah wadda take durƙushe a gabansa... "Wannan kwayoyin za su zauna a wurina. Idan kika ƙara min rashin kunya a aji, ko kika sake turo waɗannan karnukan naki, to asirinki zai zama labarin gari. Kuma daga gobe, ke za ki riƙa share min aji na kafin in fara koyarwa sannan ki goge mun allo... Kin ji abinda na faɗa?" Maayah ta gyaɗa kai cikin kuka da kunya. Ta gane cewa a yau, ta haɗu da asalin Uban gida.... ✨✨✨ Ching Ching tana zaune a cikin ɗakin ajiye tarkace, wanda yake cike da ƙura, tsofaffin akwatuna, da duhu... Tana ta faman goge fentin jikin bango da yayi ƙura da yana-yana da wani tsohon kyalle, hawaye yana ta zuba a fuskarta. Tana jin yunwa, da tsoron duhun dake cikin dakin, kuma tana jin haushin kanta da ya kaita ga wannan halin... Kwatsam, sai ta ji ƙarar buɗe ƙofa. Ta ɗago kai tana tunanin Chief ne ya zo ya ce ta tafi ta kwanta a gadonta, amma sai ta ga Gely ce ta shigo, riƙe da wani haske da kuma kular abinci... Ching Ching ta harare ta, ta ci gaba da goge-gogen ta cikin fushi... "Kin zo ne ki yi min dariya? Ko kin zo ne ki ga yadda nake shan wahala?" Gely ba ta tanka ba. Ta ajiye abincin a kan wani akwati kusa da ita, sannan ta ɗauko wani magani mai ƙarfi na goge fenti da kuma wani kyalle mai kyau... Ta durƙusa a gefen matakalar, ta fara goge fentin da sauri-sauri fiye da yadda Ching Ching za ta iya... "Boss yace ba za ki ci abinci ba," Gely ta faɗa cikin muryar robot dake cike da natsuwa... "Amma tsarin lissafina ya gaya min cewa idan ba ki ci abinci ba, ba za ki iya gama aikin nan ba, kuma za ki ƙara ciwo wa kanki, wanda hakan zai jawo wa Boss ɗan uwan damuwa... Don haka, ki ci abincin nan kafin na gama goge miki matakalar." Ching Ching ta saki kyallen hannunta, ta kalli Gely cikin mamaki.. "Ke Gely... me ya sa kike taya ni? Bayan ni ce na yi ƙoƙarin janyo miki rauni ɗazu?" Gely ta ci gaba da aikin, hannuwanta na ƙarfe suna ta gogayya da matakalar cikin sauri.. "Ni na'ura ce, ba na jin rauni kamar ɗan adam. Amma na ga yadda kika firgita lokacin da kika ga zan faɗo. Hakan yana nufin ba mugunta ba ce a zuciyarki, shagwaba ce kawai da rashin tunani." Ching Ching ta ji jikinta ya yi sanyi. Ta ja kular abincin ta fara ci cikin sauri, tana kallon yadda Gely take taya ta aikin cikin sauƙi.. "Na gode Gely," ta faɗa ƙasa-ƙasa, wanda hakan shi ne karon farko da ta taɓa faɗar kalmar godiya ga Gely... Gely ta kammala goge matakalar cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ta tashi tsaye.. . "Kada ki bari Boss ya san cewa na taya ki, kuma kada ki bari ya ga abincin nan. Idan kin gama, ki kwanta a kan waɗannan bargunan, zan rage miki sanyin ɗakin ta hanyar sarrafa na'urar sanyaya ɗaki ta gidan (Central Cooling)..." Ta juya za ta fice, sai Ching Ching ta ƙira sunanta.. "Gely! Shin... shin muna iya zama ƙawaye?" Gely ta tsaya a bakin ƙofa, idanunta suka yi wani haske na musamman.. "Ƙawance tsakanin mutum da na'ura abu ne mai wahala, Shugaba Ching Ching. Amma idan kika daina wasa da rayuwata, ni ma zan ci gaba da kiyaye naki mutuncin a gaban Boss..." Ta fice ta bar Ching Ching a cikin ɗakin, amma yanzu ɗakin bai yi wa Ching Ching duhu da tsoro kamar ɗazu ba. Ta gane cewa Gely tana da wani ɓangare na kyautatawa duk da cewa ita ƙarfe ce... Washegari da sassafe, Chief Onyx ya nufi ɗakin ajiye tarkacen... Zuciyarsa tana buga masa tsantsar tausayi, domin ko ba komai ya san ɗakin akwai duhu da ƙura, kuma Ching Ching ba ta saba da irin wannan wahalar ba. Ya ɗauka zai tarar da matakalar tana nan yadda ya bar ta, ita kuma Ching Ching tana kuka ko kuma ta yi barci ba tare da ta gama aikin ba... Amma yana buɗe ƙofar, sai ya ja ya tsaya cikin tsananin mamaki. Matakalar ta yi fes, fentin jikinta duk ya fita har tana sheƙi kamar sabuwa... Ching Ching kuwa tana barci a kan wasu tsofaffin barguna, fuskarta tana ɗauke da alamun gajiya amma akwai wata natsuwa a tattare da ita. "Ta yaya yarinyar nan ta gama wannan aikin duka a dare ɗaya?" Onyx ya raɗa a hankali. Ya san ƙoƙarin Ching Ching, ya san kuma wahalar goge fenti, lallai akwai wani abu a ƙasa. Yana shirin juyawa, sai ya hango kwanon abincin da aka tura a ƙarƙashin wani tsohon akwati. Ya ƙarasa ya ɗauko kwanon, ya ga ragowar abincin da aka ci. Sannan ya kalli tsarin sanyaya ɗakin (AC), ya ga cewa iskar dake fitowa a wannan sashen tana da ɗumi na musamman wanda aka tsara don mutum ya iya barci cikin jin daɗi... Ya miƙe tsaye ya fito daga ɗakin, ya nufi falon dining inda ya tarar da Gely tana ƙoƙarin haɗa masa coffee na safe. "Gely," Onyx ya ƙira sunanta cikin muryar dake nuna ya gano komai. Gely ta juyo cikin natsuwa.. "Ina kwana, Boss. An riga an kammala dukkan ayyukan da ka bayar a ɗakin tarkace. Shugaba Ching Ching ta yi aiki tuƙuru." Onyx ya ajiye kular abincin a gaban Gely. "Wannan abincin fa? Kuma waye ya ba da izinin sauya tsarin AC na dakin tarkace don ya yi mata ɗumi?" Gely ta yi shiru na daƙiƙa biyu, idanunta suka yi walƙiya alamar tana sarrafa bayani wato tana processing... "Boss, bincikena ya nuna cewa idan Ching Ching ta kwana cikin sanyi da yunwa, jikinta zai iya yin rauni, wanda hakan zai jawo maka asarar lokaci wajen kula da ita. Don haka, na ɗauki matakin taimaka mata don amfanin wannan fadar...." Onyx ya matso kusa da Gely, ya zuba mata ido.. "Kin taimaka mata wajen goge fentin ma, ko?" Gely ta sunkuyar da kanta kaɗan. "An yi hakan ne don tabbatar da an kammala aikin a kan lokaci kamar yadda ka bayar da umarni." Onyx ya yi wani ɗan gajeren murmushi, wanda yake cike da mamaki. Ya gane cewa Gely ta fara yin abubuwa ba kawai don ita Inji ba ce, sai don tana da wata irin kulawa ta daban. "Kin kyauta Gely," Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi... "Amma kada ki sake keta umarni na a asirce. Yanzu je ki tashe ta, ki gaya mata ta je ta yi wanka ta shirya, sannan ta zo nan ta ci abinci a gabana." Gely ta nufi ɗakin tarkacen, tana zuwa ta taɓa kafaɗar Ching Ching... Ching Ching ta farka a firgice, tana gani Gely sai ta yi murmushi... "Gely... ashe gaskiya ne banyi mafarki ba? Kin taimaka min?" Gely ta jinjina kai. "Boss ya gano komai. Amma maimakon ya yi fushi, ya ce ki tashi ki shirya ki zo ki ci abinci a gabansa. Wannan dama ce ta gyara tsakaninku." Ching Ching ta tashi cikin murna, ta rungume Gely . "Na gode Gely! Ke ce babbar ƙawata!" Daga nan suka fito tare, Chief Onyx yana kallon yadda Gimbiya da Robot ɗinsa suke tafiya tare, yana jin cewa fadar ta fara samun wani sabon yanayi na zaman lafiya wanda bai taɓa tunani ba... ✨✨ Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan, zaman lafiya ya wanzu a fadar... Ching Ching ta rage shishshigi, yayin da Gely kuma ta rage takura mata. Amma Chief Onyx ya sani cewa dorewar wannan zaman lafiyar tana buƙatar jarrabawa... Wata rana, Chief Onyx yana duba wasu tsofaffin na’urori a wani sashe na gidan da ba a cika amfani da shi ba. Kwatsam, sai aka samu matsalar wutar lantarki (electrical surge) a gidan wadda ta sanya duk kofofin zamani na gidan suka kulle kansu wato sunyi Lockdown Mode... Wutar ta tashi ne daga babban ɗakin sarrafa injina, inda hayaƙi ya fara turnuƙewa. Chief Onyx ya tsinci kansa a kulle a cikin wani daki mai ƙofa ta ta zamani mai sarrafa kanta, kuma na’urar sadarwarsa ta daina aiki saboda matsalar wutar. A Babban Falo... Ching Ching da Gely ne kawai a falon. Nan take Gely ta dakata, idanunta suka yi ja wur alamar Alert Mode... "Akwai matsala, Shugaba Ching Ching. An samu gobara a bangaren sarrafa wuta, kuma Boss yana kulle a can." Ching Ching ta zabura, fuskarta ta yi fiyau saboda tsoro. "Me kike jira? Je ki cece shi!" Gely ta girgiza kai. "Wutar lantarkin ta hargitsa tsarin jikina, ba zan iya buɗe kofofin lantarkin ba daga nan. Ina buƙatar wani ya shiga ta cikin ramin iska Air Duct wanda yake da matuƙar ƙunci da barazana, ya je ya danna maɓallin kashe wutar daga ciki. Ni kuma jikina na ƙarfe ba zai iya wucewa ta ramin ba..." Ching Ching ta ce, "mu je ki nuna mun wurin..." Haka suka nufi sashen dake da ɗan nisa zuwa wurin.. Suna isa Ching Ching ta kalli ƙaramin ramin iskar dake jikin bango, sannan ta kalli Gely. Ta sani cewa ita ce kaɗai za ta iya wucewa ta wurin saboda ƙanƙantarta... "Zan yi!" ta faɗa cikin ƙarfin hali. "Nuna min inda zan bi." Gely ta buɗe ramin, ta ba wa Ching Ching wani ƙaramin kyalle mai ruwa don ta rufe hancinta saboda hayaki... "Ki yi hankali, Shugaba Ching Ching. Idan kika isa can, ki danna jan maɓallin dake hannun dama. Idan ba ki yi nasara ba, dukkanmu muna cikin haɗari...domin gobara zai iya tashi, kuma zai fara ne daga inda kike..." Ba ta wani tsaya ta jin abinda Gely zata faɗa ba... Kawai ta hau wani matakala ta shige cikin ƙaramin rami dake sama, ta fara tafiya a kwance tana jan ciki a cikin ƙanƙantar ramin, tana shaƙar hayaƙi, tana jin tsoron duhun wurin, amma tunanin Chief Onyx yana cikin haɗari ya ba ta ƙarfi zuciya... Gely kuwa tana tsaye a waje, tana gaya mata hanyar da za ta bi ta hanyar amfani da sauti Ultrasonic Sound wanda Ching Ching kaɗai take ji, yadda ta maƙala a kunnenta.... Iskar cikin ramin ta yi zafi, tana ɗauke da wari mai ƙona hanci. Jikinta a manne da bangon ƙarfe, ƙirjinta na bugawa da ƙarfi saboda ƙuncin wurin... Ta ja numfashi a hankali, tana jan jikinta gaba da ƙyar... Tayi nisa sosai karon farko ta miƙa hannunta na dama don ta tura kanta gaba ⚡⚡⚡ “AAAHHHH!!” Wata wutar lantarki ta ratsa tafin hannunta, ta gangaro har ƙashin bayanta. Jikinta ya kankame cak! Ta buge kanta da bangon ramin, hawaye suka cika idanunta nan take... Ta janye hannunta da sauri, numfashinta ya rikice.. A waje, Gely ta ji ihun ta ta hanyar ultrasonic sound.. “Fatan kina lafiya, Shugaba Ching Ching?” muryarta ta fito da sauri, cike da tashin hankali.. Ching Ching ta haɗiye kuka.. “Na… na ji shocking… amma zan iya,” ta furta cikin muryar da ke rawa. Ta sake gwadawa, wannan karon da hannu na hagu.. ⚡⚡⚡⚡ “AHHHH!! Wayyyyoooo!!” Wannan karon wutar ta fi ƙarfi. Ta ji kamar an tsaga jijiyoyin hannunta. Jikinta ya fara rawa ba tare da iko ba. Ta cije leɓenta da ƙarfi don kada ta yi ihu amma ciwon ya fi ƙarfin juriyarta.. Hawaye suka gangaro suka gauraye da zufar dake gangaro mata.. “Ki dakata! Ki dakata idan ba za ki iya ba!” Gely ta yi magana da gaggawa.. Amma Ching Ching ta riga ta yi nisa. Ta san babu juyawa baya.. Ta duba gaba ta hango wayoyin lantarki waɗanda suka yanyanke, suna walƙiya suna fitar da ƙaramin haske mai ban tsoro... Wurin ya yi hatsari sosai. Ƙasa da ƙafa guda kaɗan ne kawai ke tsakaninta da maɓallin ja.. Ta ja jikinta gaba tana tura ciki, tana ƙoƙarin kauce wa wayoyin, amma ramin ya yi matsi sosai.. ⚡⚡⚡⚡⚡ Wutar ta kama ƙirjinta da kafaɗarta lokaci guda.. “AAAAHHHHH!!!” Wani zazzafan ciwo ya bugi cikinta. Ta ji numfashinta ya tsaya cak. Jikinta ya sake kankamewa, bakinta ya buɗe ba tare da saninta ba, Sai ga jini ya fara zuba daga gefen bakinta.. Idanunta suka yi duhu, gani ya fara dishi.. “Ching Ching!! Ki amsa! Ki amsa!” Gely ta yi magana ta hanyar sauti... Ching Ching ta buɗe bakinta da ƙyar.. “Ka… kada ki damu…” ta furta cikin rauni. “Uncle… yana can…” Ta tuna fuskar Chief Onyx. Shirunsa da girman kansa... “Ba zan bari ya mutu ba…” ta faɗa a ranta. Da ragowar ƙarfin da ya rage mata, ta tura jikinta gaba. Wutar ta sake ratsa jikinta sau ɗaya, amma wannan karon ta ƙi yin ihu. Ta yi shiru tana kuka a ranta... Hannunta na rawa ya kai KAN MAƁALLIN JA... Ta rufe idanunta. Ta danna.. ⛔⚡ Nan take, duk walƙiya ta mutu. Hasken haɗari ya kashe kansa. Iskar zafi ta ragu. Ramin ya yi shiru tamkar kabari... Ching Ching ta kife kanta, jikinta duk ya mutu ba ƙarfi.. Numfashinta yana fita da shigowa da ƙyar.. Jini yana kan zubowa ta leɓenta, hannayenta suna rawar sanyi… Amma ta yi nasara... A waje, Gely ta karɓi siginar tsarin dawowa.. “Wuta ta muta… Shugaba Ching Ching… kin yi nasara.” Idanun Ching Ching suka rufe a hankali. A ƙarshe kafin ta suma, murmushi kaɗan ya tsallake leɓenta... “Uncle… ya tsira…” Nan take, ƙarar ƙararrawa (Alarm) ta katse gaba ɗaya. Wutar walƙiya ta mutu. Hayaki ya fara raguwa a hankali, kamar yadda numfashi ke dawowa bayan tsananin firgici... Daga bisani, dukkan kofofin zamani na gidan suka buɗe kansu lokaci guda.. Chief Onyx ya fito daga ɗakin da aka kulle shi, yana tari mai ƙarfi, ƙirjinsa na motsi sama da ƙasa. Idanunsa sunyi ja sakamakon hayaki, amma hankalinsa yana nan daram. Bai tsaya ko’ina ba ya juya da gudu kai tsaye zuwa ɗakin sarrafa wutar lantarki... A zuciyarsa, tambaya ɗaya ce kawai ke juyawa.. “Waye ya iya kashe wannan bala’in?” Da ya isa wajen, sai ya ci karo da Gely tsaye a ƙasan matakala, kanta a ɗage sama, idanunta a manne da ramin iska. Ta tsaya cak, tamkar ana jiran rai ya fito daga kabari... Ba wani motsi sai numfashin Chief Onyx kaɗai ke cika wurin.. Cikin murya mai tsauri yana ɗaga mata murya ya ce, “Me kike yi tsaye a nan? Kuma ta yaya aka kashe wutar alhali na san ke ba za ki iya shiga wannan ramin ba?!” Gely ta sauƙe kanta a hankali. Murya na fita cikin rauni.. “Shugaba Ching Ching ce…” ta furta.. Chief ya ɗan tsaya.. “Me kika ce?” “Shugaba Ching Ching ta shiga ta sama… ita ce ta kashe wutar.” Kalmar ta faɗa kamar fashewar bam a zuciyarsa.. “WHAT?!” ya ƙara da tsawa, ya matso kusa da ita. “Shin kin ba ta kayan kare jiki? Hannu? Ko wani kariya?” Gely ta girgiza kai a hankali... “A’a, Boss…” Ya kalleta kai tsaye, idanunsa cike da fushi da tsoro a lokaci guda.. “You are very stupid, Gely.” Ya juya, ya kalli ƙaramin ramin iska dake sama. Hankalinsa ya rikice. Ya san babban mutum ɗaya ba zai iya shiga ba, balle mutum biyu. Kuma ramin ya yi matsi, ba za a iya haura wa don ceto kai tsaye ba.. A wannan lokaci, Gely ta sake magana, amma wannan karon muryarta ta yi sanyi sosai.. “Boss… tunda tsarin yana iya sarrafa kansa… akwai hanya. Za mu iya buɗe ramin daga ƙasa, ta yadda bangon da take kai zai buɗe, ita kuma za ta faɗo a yadda take kwance.” Chief ya juya da sauri. “Amma ban san ta ina take ba!” ya ce cikin muryar tsawa... “Kuma da alamun ta suma! Idan ta faɗo ba tare da tsari ba.....” Bai ƙarasa ba... Gely ta ɗaga hannunta. Idonta ya canja launi, wani jan haske (scanner) ya fito daga idonta ya harba sama cikin ramin iska.. Hasken yana tafiya a hankali, yana duba kowane sashe.. A zuciyarta, tana bin alamomin bugun zuciya… Raunin jiki… Matsayin mutum… Can sai hasken ya tsaya... “Na gan ta, Boss.” Gely ta ce cikin tsanani... “Tana kusa da maɓallin ja. A yadda take kwance, tana fuskantar gefe… bayan ta danna, nan take ta suma.” Chief Onyx bai ƙara magana ba. Ya juya kai tsaye. “Je ki buɗe tsarin daga computer. Ni zan tsaya a daidai inda take.” Ya matsa ya tsaya a yanda take ya buɗe hannayensa, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi fiye da kowane lokaci a rayuwarsa... “Da zarar kin buɗe… zan cafke ta.” Gely ta yi saurin juyawa zuwa computer ɗin sarrafawa.. A sama kuwa… Ching Ching tana kwance a cikin ramin, jikinta babu ƙarfi. Jini yana ta zuba daga bakinta, yana bin gefen leɓenta zuwa wuyanta. Numfashinta yana fita da shigewa cikin wahala, tamkar wuta na ƙoƙarin mutuwa.. Idanunta a rufe. Ba ta san abin da ke faruwa a ƙasa ba... A ƙasa, Chief Onyx ya tsaya kamar dutse. Idanunsa ba su bar kallon saman ba... Sai CLICK! Bangon ramin ya buɗe. A cikin daƙiƙa guda, jikin Ching Ching ya zame ya faɗo ƙasa.. Cikin zafin nama Chief ya cafke ta a hannunsa... Ƙarfin jikinta ya buge ƙirjinsa. Zafin jikinta ya ratsa shi....haka yake riƙe da ita kamar jaririya.. “Ching Ching…” ya furta a karon farko cikin raunanniyar murya.. Yana kallonta ga yadda jini yake fita a bakinta... Fuskarta yayi fari sol... Numfashinta a raunane. A wannan lokacin ne Chief Onyx ya gane abu ɗaya.. Ta kusan rasa rayuwarta saboda shi.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣9️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan kammala wasu harkokin diflomasiyya, jirgin Sarki Nourdeen ya sauka a birnin Sydney. Bai tsaya ko ina ba sai a fadar Ruma wanda take tinkaho da kyawun gine-ginen turawa na zamani.. ​ ​ Jami'an tsaron wurin ƙattawan Turawa ne, sanye da bakaken kaya da makamai na zamani. Sarki Nourdeen yana isa masu tsaron ƙofar gari duk suka duƙa, ba don saboda tsoro ba, sai don girmama matsayinsa na mijin Sarauniyarsu... ​ Ya wuce ta cikin jerin bayi mata, duka jajayen fata waɗanda ke zirga-zirga cikin nutsuwa da kwarewa... ​ Sarki ya hau dogon tsalallaken bene na alfarma wanda zai kai shi kai tsaye zuwa sashen Sarauniya Ruma, inda babu mai shiga sai shi kansa... Sai da ya wuce cikin babban falonta na alhurma kafin ya iske bedroom wanda yake saman falon... ​Sarki ya tura ƙofa ya shiga, sannan ya rufe ta da mukulli. Ɗakin yana ƙamshi da wani irin turare mai sanyaya rai mai ƙarfi. Ya tsaya cak yana kallonta. ​Queen Ruma tana zaune a gaban babban madubi na alfarma. Tana sanye da wata siririyar rigar bacci ta silk wadda ta tsaya iya cinyoyinta, hannun rigar siriri ne sosai. Tana taje dogon farin gashinta da ya zubo har baya. Fatar jikinta tana haske kamar kankara, sannan kwarjininta da siririyar jikinta suna nuna cewa ita daban ce.. ​Ta kalle shi ta cikin madubin da waɗancan fararen idanun nata masu kalar kuliya.. ​Cikin muryar turanci mai sanyi da izzah ta furta. "I knew you were coming..." ​Sarki ya taka zuwa tsakiyar ɗakin "Shi ya sa ba ki zauna a can fadarki kan kujerarki ba?" ​Ruma ta yi wani murmushin ƙasaita, ta miƙe tsaye. Takunta na nuna cewa ita asalin sarauniya ce ta jini. Ta zo har gabansa, ta tsaya tana kallon kwayar idonsa.. ​ "Saboda ni kaɗai ce matarka. Zan nemi na biya maka haƙƙinka na ma'aurata, duk da muna ɗaukan lokaci ba mu haɗu ba." ​Sarki ya jinjina kai, ya ja dogon numfashi. Akwai nauyi a muryarsa yayin da yake magana.. ​"Uhm! Kin ƙi komawa cikin masarautata wanda asalin nan ne ya fi dacewa da ke, ko don saboda ƴarki, amma kin zaɓi nan. Hakan ba laifi ba ne don na biyo ki a matsayin miji na kuma karɓi haƙƙina na aurena da ke... Amma babban abinda zai ƙara shiga tsakanina da ke, wanda zai hana na biya miki haƙƙinki a matsayin mata, shine bijire wa Musulunci. Kin yaudare ni, kin karɓi Musulunci saboda ki aure ni, amma bayan haka kika koma addininki." ​Ruma ta ɗaga hannu, ta dakatar da shi cikin sauri. Fuskarta ta canza daga murmushi zuwa ɓacin rai na lokaci guda.. ​"Ka daɗe kana nanata wannan maganar har na fara gajiya. Muna zaune ne a matsayin ma'aurata, ba wai maganar addini ba. Kowa ya riƙe addininsa mana! Kuma ba za ka taɓa barin wannan fadar tawa ba har sai ka biya min haƙƙina na matarka. Kuma muddin ina raye, ba za ka taɓa kasancewa da wata mace ba bayan ni." ​Sarki Nourdeen ya zuba mata ido. Ya san halin Ruma, idan ta ƙafe a kan abu, to babu mai iya canza ta. Sun daɗe suna samun matsala akan maganar Musulunci, amma tana amfani da kyawunta da muryarta wajen tursasa shi. Duk da ɗacin ransa akan addini, sarki ya san cewa a fannin sha'awa da biya wa juna haƙƙi, Ruma ta dabance. ​Sannan, ya gwammace ta zauna a nan Sydney tana mulkin mutanen mahaifinta, domin muddin Ruma tana cikin fadar Alhamra, to masarautar haukacewa take yi saboda kishinta da muguntar da take yi wa kowa.. Bayan kammala cacar baki akan maganar addini, Ruma ta sauke numfashi, fuskarta ta koma cike da lallausan murmushi mai nuna kissa. Ta matso kusa da Sarki, ta fara shafa ƙirjinsa a hankali da yatsunta masu sanyi, tana lallashi da sarrafa shi yadda ta saba.. Sarki ya zuba mata ido, duk da yana jin shauƙinta na ratsa shi, amma akwai wani abu da yake damunsa. Ya dakatar da hannunta na ɗan lokaci, ya kalle ta sosai. "Ba ki da labarin Chief Onyx ya ɗauke min Auta? Na ji kin yi shiru ba ki yi min magana a kai ba... ko ba ki damu ba ne?" Ruma ta yamutsa fuskarta ta nuna rashin damuwa ƙarara, ta janye hannunta daga ƙirjinsa na ɗan lokaci kamar ana maganar abin da bai shafi rayuwarta ba. Cikin isa da halin ko-in-kula ta ce, "Ƴarka aka ɗauke, ba ƴata ba. Don haka jininka, jininka ne, bai shafe ni ba. Jinina guda ɗaya ce a masarautarka wato Zayana, kuma ba ita aka taɓa ba balle na yi magana a kai. Saboda haka, wannan damuwarku ce kai da shi... ai ɗan uwanka ne." Sarki Nourdeen ya ja dogon numfashi, ya ji raɗaɗin kalaman nata. Ya san Ruma ba ta da tausayi, amma bai yi tsammanin rashin damuwarta zai kai ga haka ba, musamman sanin cewa Chief Onyx ɗan uwansa ne kuma babban makiyinsa.. Duk da haka, kwarewar Ruma wajen sarrafa mace da namiji ba ta bar sarki ya tsananta fushin ba. Ta sake matsowa, ta rungume shi, tana busa masa sanyayyar iskar numfashinta a wuya. Ya fahimci cewa tana fama da tsananin shauƙi da kewarsa da ta daɗe tana ciki... A wannan daren, dukkan wata takaddama ta addini da ta siyasar masarauta aka ijiye ta a gefe. Fadar ta yi tsit, sai dai ƙarar iska dake kaɗawa a waje. A cikin wannan babban sashi na Sarauniya Ruma, sarki ya kasance da matarsa a matsayin ma'aurata, inda suka nuna wa juna shauƙi da aka daɗe ba a yi ba. Duk da sarki ya san cewa gobe idan ya tashi, matsalolin Alhamra suna jiran sa, amma a daren nan, ikon Ruma da kyawunta sun yi nasara akan duk wani damuwarsa... Bayan gari ya waye, sarki yana shirin barin Sydney don komawa Alhamra.. Ruma tana kwance tana kallon sa yayin da yake shirin sa na sarki.. Ta furta "Nourdeen, ka tabbatar ka kula da Zayana. Idan na ji wani abu ya same ta, zan iya rusa Alhamra don ganin na maido ta nan." Sarki bai ce komai ba, ya gyada kai kawai, ya fice daga sashen ya bar ta a nan tana mulkan mutanenta na Sydney, yayin da shi kuma ya nufi filin jirgi don fuskantar rikicin da ya bari a gida... Bayan jirgin Sarki ya tashi daga Sydney, ya ba wa matuƙan jirgin umarnin sauya hanya. Ya dai sanar wa Ruma cewa zai koma Alhamra amma a zahiri ba Alhamra zai koma ba.. Kai tsaye Indiya dake birnin Mumbai ya nufa. A nan, Sarki yana da wani katafaren gida wanda aka gina shi cikin sirri, kewaye da lambuna masu ban sha'awa, nesa da idon duniya.. ​Wannan gidan shi ne Zindanin Zinariya na Sarauniya Hibba... Hibba mace ce kyakkyawa, fara ce mai kalar jinin Indiya, tana da dogon gashi baƙi wanda yake sheƙi, da idanuwa masu zurfi dake nuna tsantsar baƙin ciki.. ​A zamanin da Hibba take Alhamra, fadar ta zama tamkar filin daga. Hibba ba ƴar sarauta ba ce, amma tana da jinin girman kai na ƴanci. ​Ruma tana so ta mulki Hibba kamar baiwa.. ​Hibba kuma ta nuna mata cewa ita ma mace ce mai matsayi a gaban Sarki.. Hakan yasa jininsu bai haɗu da Ruma ba.. Ta rabu da sarki sakamakon rashin zaman lafiya.. Ruma ta tsane ta sosai, hakan yasa kullum faɗa ita da Ruma a masarautar Alhamra.. Kullum Ruma tashin hankalinta shine Sarki ya saki Hibba.. Ruma har sawa take akai mata farmakin kisa, sau biyar ana zuwa kasheta amma take tsira daƙyar.. Anan ne ta tayar wa Sarki hankali akan ya sake ta bazata iya zama a kashe ta ba.. Domin lamarin Ruma yafi ƙarfinta..ba za ta iya kishi da ita ba... Don kare rayuwarta, Sarki ya shirya wasan kwaikwayon cewa ya sake ta, sannan ya ɓoye ta a Mumbai. Ruma tana tunanin ta yi nasara, ashe Sarki har yanzu yana tare da matarsa ta uku.... ​🥀 ​Sarki ya shiga gidan shiru, ya tarar da Hibba a cikin lambu tana kallon faɗuwar rana. Ta ji takun takalmansa, amma ba ta juyo ba. Ta san shi ne... ​Sarki ya furta "Hibba, ina fatan kina lafiya?" ​Hibba ta juyo, fuskarta ba annuri. Kyawunta ya ƙara fitowa duk da ramar da ta yi saboda damuwa.. ​ "Lafiya? A cikin wannan kurkukun da ka gina min? Ka raba ni da ƴata Maayah, ka raba ni da kowa, ka mayar da ni tamkar gawa mai numfashi don kawai kana tsoron Ruma." ​Sarki ya matso kusa da ita, yana ƙoƙarin taɓa hannunta amma ta kauce. ​YA ce, "Na yi hakan ne don in kare rayuwarki, Hibba... Ruma mace ce mai haɗari..." ​Cikin ɗacin rai ta ce, "To idan har ba za ka iya kare ni a matsayin sarki ba, me ya sa ba za ka sake ni ba? Na gaji, Nourdeen! Na gaji da wannan rayuwar sirrin. Ka sake ni, in tafi in yi aurena cikin kwanciyar hankali, in samu rayuwar da nake so." ​Jin kalmar "Aurena", sai idanun Sarki Nourdeen suka sauya launi. Wani irin kishi mai zafi ya lulluɓe shi. Ya damƙi kafaɗunta, yana kallon cikin idanunta da wani irin kwarjini na tsoro.. ​YA furta, "Kada ki sake furta wannan kalmar! Ba za ki taɓa zama da wani namiji ba bayan ni. Muddin ina numfashi, ke tawa ce, ko a cikin sirri ko a fili. Babu wani namijin da ya isa ya kalle ki balle ya taɓa ki!" ​Hibba ta fashe da kukan takaici... "To me kake so da ni? Ka hana ni ƴata, ka hana ni rayuwa. Maayah tana can tana girma ba tare da uwa ba, tana koyon muguntar Ruma da ƴarta..." ​Sarki ya jawo ta jikinsa ya rungume ta da ƙarfi, duk da tana tirjiya. Ya fahimci cewa kishinsa da son da yake mata sun zama masifa gare ta. Amma ba shi da niyyar sakinta... ​(WANI SANAR WA A WAƊANNAN LOKUNAN KASANCE DA MATANSA, SARKI NOURDEEN ASALIN SIFFARSA TA MUTUM YAKE, BA WANNAN FUSKAR ZAKI....) ​Sarki ya kwana a ƙasar Mumbai, yana ƙoƙarin rarrashin Hibba, amma zuciyarta ta riga ta bushe. Tana tunanin yadda za ta kuɓuta daga wannan ramin da aka binne ta da rai... ​A gefe guda, sarki yana tunanin yadda zai kwashe duka matan nasa ya dawo da su fada guda ba tare da an zubar da jini ba.. Amma babban abin tsoronsa. Idan Ruma ta gano yana tare da Hibba, to Alhamra za ta kone kurmus!... Bayan babban kishi da cacar baki da aka yi, sarki ya yi amfani da hikima da muryarsa mai sanyi wajen rarrashin Hibba.. Ya san inda yake taɓa zuciyarta. Ya rungume ta, yana raɗa mata kalaman da suka nuna cewa duk abin da yake yi, yana yi ne don ya kare rayuwarta daga kaidin Ruma.. A hankali, taurin zuciyar Hibba ya narke. Ta sani cewa tana matuƙar son Nourdeen, kuma kishinsa ma wata alama ce ta yadda yake daraja ta. Don nuna ta haƙura, ta shiga kicin ɗin gidan wanda aka ƙerawa ado da kayan marmari. Ta haɗa wa sarki girkin Indiya na musamman.. Biryani mai ɗauke da ƙamshin kayan spices na asali... Sai Butter Chicken mai gardi da laushi.. Samosas da Chutney Don buɗe abinci... Sarki yana zaune a kan dinning, yana kallonta cikin alfahari. Hibba tana sanye da wata doguwar rigar Indiya (Sari) kalar ja, wadda ta ƙara fito da asalin kyawun jikinta.. Sarki ya jawo ta ta zauna kusa da shi, yana ciyar da ita tana ciyar da shi. Duk wata damuwa ta sarauta da damuwar Ruma suka fita daga kansu... "Hibba," sarki ya faɗa cikin muryar sha'awa, "ba za ki san yadda nake ji ba idan na tuna kina nan a fake. Ke ce numfashina na sirri." Hibba ta yi murmushin kunya, ta kishingiɗa a kafaɗarsa... "Nourdeen, burina ɗaya ne, mu zauna tare ba tare da tsoron kowa ba. Amma a daren nan, kai nawa ne ni kaɗai." Daren ya ja, gidan ya yi tsit sai ƙamshin turaren wuta dake tashi. Sarki da Hibba sun koma babban ɗakin kwananta. A nan, sun rayu kamar wasu sabbin ma'aurata. Ba batun sarsuta, ba kuma sarauniya, sai dai Nourdeen da Muheebban sa... Sun gudanar da darensu cikin tsantsar soyayya da nuna wa juna shauƙi.. Wannan daren ya zama tamkar maganin raɗaɗin ƙuncin da Hibba take ji na zama ita kaɗai, sannan ya ƙara wa sarki ƙarfin gwiwar cewa dole ne ya samo hanyar da zai haɗa iyalinsa wuri guda nan gaba... Washegari da safe, bayan sun yi karin kumallo cikin nutsuwa, sarki ya yi wa Hibba ban-kwana da alkawarin zai dawo nan kusa, kuma zai yi ƙoƙarin kawo mata Maayah su gaisa a asirce... Sarki Nourdeen ya bar Mumbai cikin sirri, maimakon ya nufi Alhamra, sai ya nufi ƙasar Saudiyya... Wannan ziyarar ita ce tafi kowacce ciwo a zuciyarsa, domin yana zuwa ne domin ya ga matar da kowa ya ɗauka ta mutu shekaru goma sha shida da suka wuce. Wannan ita ce Sarauniya Ayshert, mahaifiyar Ayat da Ching-Ching. Ita ce matar sarki ta biyu... Tun lokacin da aka yi mata tiyata aka cire Ching-Ching daga cikinta saboda rashin lafiya, Aysh ba ta sake farfaɗowa ba. Labarin da aka yaɗa a Alhamra shi ne ta rasu a lokacin haihuwa, aka yi mata jana'iza ta ƙarya. Amma a zahiri, Sarki ya kaita Saudiyya ne wurin kakanta, wani babban malami mai ilimin addini da magungunan gargajiya, don ya kula da ita... Sarki ya isa gidan tsohon malamin dake kusa da garin Madina. Gidan yana cike da nutsuwa da ƙamshin turaren miski da karatun Al-Kur'ani dake tashi... Ya shiga wani babban ɗaki mai haske, inda ya tarar da Sarauniya Aysh kwance a kan gado. Shekaru goma sha shida ke nan tana kwance a matsayin Living Ghost wato Gawa mai rai... Idanunta a rufe suke, numfashinta a hankali yake fita, amma jikinta bai ruɓe ba, kuma tana nan da kyawunta na asali, sai dai ramar da ba a rasa ba... Sarki ya zauna a gefen gadon, ya kama hannunta wanda yake sanyi ƙalau... Cikin muryar kuka ya furta.. "Aysh... har yanzu ba za ki tashi ba? Shekaru goma sha shida ke nan. Ƴarki Ayat ta girma, tana kama da ke sosai... Ching-Ching ma yanzu ta zama budurwa, amma ba su san kina raye ba. Kowa yana tunanin kin bar duniya." Tsohon malamin ya shigo ɗakin, ya dafa kafaɗar Sarki.. Ya ce, "Sarki Nourdeen, jinyar Ayshert ba ta likitoci ba ce kawai. Mun yi dukkan gwaje-gwaje, kwakwalwarta tana nan garau, amma akwai wani abu da ya riƙe ruhinta. Wannan suma ce ta shekaru (Long-term Coma) wadda ilimin duniya bai kai ga gano maganinta ba. Sai dai mu ci gaba da addu'a." Sarki ya zuba wa matarsa ido. Yana jin zargin cewa wannan jinyar ta Aysh ba ta Allah ba ce kawai. Yana tunanin ko akwai sa hannun wani wanda ya yi amfani da wani irin guba ko asiri da ya daskare kwakwalwarta a ranar da ta haihu.. Kuma daman kafin ta haihu tana fama da matsanancin jinyar da har yasa akayi mata tiyata saboda ba za ta iya yunƙurin haihuwa ba.. A yanzu, Aysh tana nan tana numfashi, amma ba ta san me yake faruwa a duniya ba....Ba ta ji kuma magana.. "Zan yi duk abin da zan iya don ganin kin farfaɗo. Amma kafin nan, zan koma Alhamra in ga yadda zan cigaba da tsare yaran da kika bari..." A cewar sarki yana zub da hawaye... Bayan ya kammala ziyarar ban-tausayi a Saudiyya, sarki ya shiga jirginsa na ƙarshe wanda zai kai shi Alhamra. Wannan karon, fuskarsa ta zama tamkar dutse, babu wani shauƙi, sai fushinsa na taɓa masa iyali da akayi... Daidai karfe biyu na rana, sararin saman Alhamra ta cika da sautin injin jirgin sarki. Tun kafin ma ya sauka, an riga an baza jami'an tsaro na musamman a ko'ina... A kofar fita daga filin jirgin, wasu jerin gwanon motoci ne bakake, kirar Rolls Royce da Mercedes-Maybach, wadanda suka sha bakaken gilashi, suke jiran sa. Mazajen masarautar sanye da bakaken kayan sarauta da rawuna wadanda suka rufe rabin fuskarsu, suka jera don taryen sa... Yana fitowa daga jirgin, iskar Alhamra ta bugi fuskarsa. Ba tare da sakin fuska ba, kuma bai kalli kowa ba. Tafiyarsa kawai tana nuna cewa akwai nauyi a zuciyarsa... Yayin da ayarin motocin sarki suke ratsa cikin gari zuwa babban gate na masarauta, garin ya yi tsit tamkar an cinye mutane.. Masu sayar da kaya sun rage sautin muryarsu... Cikin masarauta bayi da ma’aikata sun raɓe a jikin bango, kowa ya sunkuyar da kai. Ba a jin komai sai sautin takalman sojoji da kakarar motoci a kan kwalta... Kowa ya san cewa sarki ya daɗe bai yi tafiya mai tsawo haka ba, kuma dawowarsa tana nufin za a yi bincike a kan komai... Sarki ya isa babban falonsa na taro... Ya cire babban rigarsa ya mika wa bawan dake tsaye kusa da shi. Ya zauna a kan karagar mulki, idanunsa suna kallon kofar shigowa... Cikin murya dake amo "Ina suke? Ina gimbiyoyin masarautar nan?..." Ko hutawa bai yi ba balle ya yi tunanin cin abinci.. Tin a cikin jirgi na dawowa ya canza fuskarsa zuwa ta zaki.. Sai ga Mama Liyatu ta shigo ta durƙusa tana miƙa gaisuwa .. Sannan ta ɗora da faɗin.. "Ranka ya daɗe, suna nan suna jiran izinin shigowa. Amma... Gimbiya Maayah ba ta nan, tana can makaranta, kuma an ce akwai matsala tsakaninta da wani sabon malami..." Sarki ya buga hannun kujerarsa. Gwam! Sautin ya ratsa ko'ina a falon... "Ban zo nan don jin labarin malami ba. Ina son ganin kowa a gabana yanzun nan. Idan har sirri na ya fara fita tun ina raye, to lallai masarautar nan tana bukatar gyara mai zafi." Ko wani Hadimi ya je sashen gimbiyoyi domin sanar dasu cewa Sarki ya dawo kuma yana buƙatar sanya su a idanuwansa... A yayinda Ayat take shigar Inuwa a matsayin PA tana tare da Master Ibrahim domin ba shi wasu bayanai... Lokacin da aka je sanar wa ko wace gimbiya..Ayat ƙirjinta ba ƙaramin bugawa yayi ba.. Kuma ga Master Ibrahim ya riƙe ta..basu gama tattaunawa ba.... TILL NEXT TIME... *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣0️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Da zarar Ching Ching ta faɗo daga sama, Chief Onyx ya cafke ta a hannunsa cikin firgici.. Jikinta ya yi sanyi, numfashinta yana fita da ƙyar, jini kuma na zuba daga bakinta.. “Ching Ching… Ching Ching!” ya ƙira sunanta da ƙarfi, amma babu amsa.. Gely ta matso kusa da su, fuskarta cike da nadama da tsoro. Idanunta shanye kamar mai jin bacci lokacin da ta ga yadda jinin ke ƙara fita... “Boss… dole ne mu tafi asibiti yanzu nan,” ta faɗa cikin rawar murya.. Chief Onyx bai tsaya jayayya ba. Yana ɗauke da Ching Ching a hannunsa kamar jaririya, ya fice da sauri daga ɗakin... Siren na gaggawa ya fara ƙara a cikin harabar fadar, motocin tsaro suka fara motsi da kansu, suna sarrafa kan su, jira suke kawai a shige su, su fara tafiya... Cikin mintuna kaɗan, sun shige cikin motar gaggawa mai sauri ba tare da masu tuƙa su ba. Kawai iya rubutu yayi a allon gaban motar ta ciki, ya rubuta yanda zai kai su.. shi kuma yana ɗauke da Ching Ching akan cinyarsa, idonsa a kanta kamar zai iya dawo da ranta da kallo kaɗai... Motar ta ratsa titi cikin gudu, hasken ja da shuɗi na walƙiya... Pavilion babban birnin zamani ya bayyana da fitilunsa masu sheƙi, amma a zuciyar Chief Onyx babu komai sai tsoro.. “Ki jure… ki jure Ching Ching,” ya faɗa a hankali, murya tana karyewa. “Ban gama dake ba… ba zan bar ki ba.” Bayan sun isa Babban Asibitin Pavilion, likitoci da nas-nas suka ruga suna tura gadonta zuwa sashen gaggawa. Chief Onyx ya dakata a jikin ƙofar.. Yana kallon ciki dake glass door ne... Gely ta iso daga baya, ta tsaya nesa tana kallonsa. A karo na farko, ta ga Chief Onyx cikin tsoro da tausayi.. A ta ciki kuwa, rayuwar Ching Ching tana rataye ne tsakanin rai da mutuwa. A wannan ranar an shawo kan Ching Ching dake kwararrun likitoci ne a asibitin...nan danan suka gama.. ✨✨ *Washegari* Haske na safiya yana ratsawa ta tagar ɗakin a hankali. Na’urorin asibiti suna fitar da ƙananan ƙara masu natsuwa. Chief Onyx yana zaune a kujerar gefen gadon, idanunsa sun nuna alamun gajiya, domin bai ko motsa ba, hannunsa yana riƙe da na Ching Ching kamar zai ɓace idan ya sake ta... Ching Ching ta motsa kaɗan, sai ta buɗe idanunta a hankali. Da farko duhu ta gani, sai fuskar Chief Onyx ta bayyana a gabanta. Ta ɗan lumshe ido, sannan ta yi murmushi mai cike da rauni... “Uncle…” ta ce da muryar da ke fita da ƙyar, “yanzu na zama jaruma ko? Ba ‘yar aiki kaɗai ba?” Onyx ya sauƙe ajiyar zuciya, ya matse hannunta a cikin nashi, yana kokarin yin murmushi. Ya sunkuya ya sumbaci goshinta a hankali.. “Fiye da hakan, Ching Ching,” ya ce cikin tausayi. “Ke ce zuciyar fadar Chief Onyx.” Ta turo baki kamar yarinya ƙarama, idonta fari sol cike da barkwanci duk da rauninta.. “To… to kai ɗin mijina ne?” Chief Onyx ya zaro ido da sauri.. “Eh? A’a! A’a!” ya ce cikin hanzari. “Ke yarinya ce, baki girma ba.” Ta ɗan ɗaga gira, ta ce, “To wacece zata zamo matarka ta haifa maka yara?” Ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai kuma murmushi ya zauna a fuskarsa.. “Ke zaki zaɓa min da kanki.” Nan take ta tintsire da dariya, duk da ƙirjinta yana ɗan mata zafi... “Idan ka fita dani yawo, zan nema maka kyakkyawa… amma fa sai mai kirki!” Onyx ya shafa kanta a hankali, ya gyara mata gashin kanta.. “Shikenan,” ya ce cikin murmushi mai cike da ƙauna.. A wannan lokacin, likita ya leƙo ta ƙofa yana kallon su da mamaki.. “Sannu patient,” ya ce yana girgiza kai, “an samu sauƙi kenam.” Ching Ching ta juya kai ta ce, “Likita, ka gani ko? Ni ba mara lafiya ba ce… ni special guest ce!” Chief Onyx ya yi murmushin gefen baki kamar yadda ya saba idan yana tare da ita... Bayan kwana 5 da kwanciya a asibiti, jikin Ching Ching ya murmure sosai. Likitoci sun sallame ta. Wannan ne karon farko da ta fito daga cikin fadar pavilion... Bayan barinsu Hospital kai tsaye super shop suka nufa, zasu yi siyayya kafin su wuce gida.. Motar Chief Onyx mai tsaron kansa ta tsaya a harabar Super market.. Ƙofar ta buɗe a hankali, Gely ta fara sauka, idonta na scanning ko’ina kamar yadda aka saba.. Bayan ta tabbatar da komai lafiya, ta buɗe ƙofar baya... Ching Ching ta sauko cikin fara’a, tana kallon ginin birnin kamar yarinya da aka kai ta sabuwar duniya... “Wow…” ta furta, “ashe Pavilion City ba kawai labari ba ne...” Chief Onyx ya tsaya gefe ɗaya, cikin baƙaƙen suits ɗinsa ta shugabanci, fuskar nan tasa tana nan cikin tsauri da natsuwa... Mutane na wucewa suna gaishe shi cikin girmamawa, wasu ma na sunkuyar da kai. Mata da dama suna ɓoye kallonsa, amma shi ko ɗago ido bai yi ba... Shugaban Pavilion City gaba ɗaya, matashi mai jiji da kai, kwarjini da girman kai. Kyawunsa ba abin jayayya ba ne, kuma shiru da sanyi da halayensa sun hana kowace mace kusantarsa. Ba ya kallon mata, balle ya bari zuciyarsa ta yi tunani a kansu... Ta juya ta kalli Chief, ta ce, “Uncle, mutane suna kallonka kamar ana kallon zinare a kasuwa.” Ba tare da ya kalleta ba, ya ce a taƙaice, “Ki yi tafiya a hankali.” Ta murmusa, ta ce, “Uh uh… ka ji yadda yake magana kamar robot, amma robot ɗin ma ya fi ka jin tausayi.” Gely ta ɗan juya kanta, ta ce cikin murya ta robot, “Correction... Boss yana da tausayi… amma ga ke kaɗai.” Chief ya tsaya cak, ya kalli Gely... “Gely.” “Noted, Boss.” ta furta tare da yin gaba.. Ching Ching ta fashe da dariya.. “Kin gani ko? Yana abu kamar duniya aka ɗora masa a kai..!” Ya ci gaba da tafiya, amma a karon farko, wani ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, murmushin da bai ma lura da shi ba... Sun shiga wani tsararren super shop mai ɗaukar ido, gilashi masu sheƙi suna sarrafa kansu ga kuma fitilu masu walƙiya da kaloli mabanbanta, ga kayan alatu da ba kowa ke iya saya ba... Ƙofar ta buɗe kai tsaye da na’ura, jama’a suka juyo a lokaci guda. Bodyguards masu baƙaƙen kaya suka zagaye su, suna tafiya cikin tsari. Gely tana gaba, idonta na scanning kowane motsi. Duk wanda ke shop ɗin ya san Chief Onyx ya shigo... Matan dake cikin shop ɗin suka tsaya cak. Wasu na masa kallon sha'awa da burge wa, wasu kuma na gyara tsayuwarsu, wasu kuma suka fara kallon Ching Ching cike da hassada... “Wacece ita?” “Me yasa ita ce kusa da shi?” “Me ye matsayinta a wurinsa?” Ching Ching kuwa idonta na kan kayayyaki.. Ta ga kayan ado masu sheƙi idonta suka haskaka.. “Uncleee! Ka ga wannan?” Ta ɗauki abin wuya.. “Da wannan?” Ta ɗauki zobe.. “Wannan kuma fa?!” Ba ta jira amsa ba ta ci gaba da ɗauka tana ajiyewa a cikin trolley kamar yarinya a kasuwar kayan zaƙi... Chief Onyx yana tafiya a bayanta cikin shiru, fuska a ɗaure. Bai ce komai ba, amma kowa da ya san shi, ya san wannan shiru ba alheri ba ne... Matan shop ɗin suna kallon Ching Ching suna harararta duk da sun ji tana ƙiransa da Uncle.. “Ta ɗauka kamar komai nata ne anan wurin.” wata ta furta tana harararta domin ba'a san iya adadin matan da suke ƙaunar Onyx ba.. “Da shi take magana wai? Na ga ko ta kanta baya bi...” Wata ta ba da amsa, "ta ya zai kula ta, kalan a raina shi, wannan kucakar yarinya ƴar hau..." “Ai ba ta kai ya kula ta ba wallahi....” A gefe guda kuma, Ching Ching ta ɗauki wata rigar zinariya, ta ɗaga ta sama ta ce da ƙarfi, “Uncle, wannan zata yi min kyau ko?” Chief ya tsaya tare da wurga mata kallo ta gefen ido... “Ki ajiye.” Ta turo baki, ta ce, “Me ya sa? Kana da kuɗi fa.” Nan take iska ta canza. Ya matso kusa da ita, yana zaro mata ido... “Ba batun kuɗi ba ne.” Ganin tana shirin zubar masa da girma yasa ya barta ta ɗauka... Haka ta nufi wurin ciye-ciye taita jidan cake da sweet da abubuwan zaƙi... Shiru ya lullube shop ɗin. Sai kuma kuskuren da Ching Ching ta yi... Ta juya, ta kalli wata mace dake tsaye gefe, sannan ta ce cikin ɗaga murya.. “Kin ga wannan? Shi ɗin mijina ne, Shi ne yake biya min komai... Wallahi kuwa...” Tsit wurin yayi ana sauraronta.. Kamar an danna maballin tsayar da lokaci.. Chief Onyx ya ɗaure fuska gaba ɗaya. Idonsa ya sauya, jijiyoyin wuyansa suka fito. Ya kamo hannunta da ƙarfi, cikin tsaurin iko ya furta... “Na ce miki meye? Ni za ki kalla kice mijinki? Kina nan kwaila dake, me ya sa kike son zubar mun da kima ne? To ki kama kan ki, ni ba abokin wasan ki bane...” Ta ɗan tsorata, ta ce, “Uncle… wasa nake fa.” Ya sunkuya kaɗan, ya kalleta kai tsaye cikin ido... “Ni bana wasa da sunana.” Ya juya ya kalli Gely. “Gely. Mu tafi....Yanzu.” Gely ta amsa nan take, “Yes, Boss.” Bodyguards suka matsa gaba, jama’a suka rarrabe gefe-gefe kamar ruwa.. Ching Ching ta tsaya cak, murmushin ya ɓace daga fuskarta. A karo na farko, ta gane cewa ta taka layin da bai kamata ba.. Sauran ƴanmatan kuwa dariya su ka shiga yi bayan fitar Chief, "Waii miji....Su miji manya.." Ching Ching bata ko kula su ba, itama ta fice..sauran kayayyakin da ta ɗauka duk an biya, wani bodyguard ne ya ji do su... A cikin motar, Chief bai ce kalma ɗaya ba. Ching Ching ta kalli gefensa, zuciyarta na bugawa... “Na ɓata masa rai…” Ta furta a cikin ranta... A cikin motar alfarma, shiru ya mamaye ko'ina, Chief yana zaune gefen Ching Ching, fuska a daure, idanu na kallon gaba kamar ba kowa a gefensa.. Motar ta ratsa wani tsararren titi mai yalwa. A gefe, wani babban private school ya bayyana, ginshiƙai masu sheƙi, ƙofar zamani, fitilu masu launi.. A nan ne ɗalibai suka fara fitowa, sanye da uniform masu tsabta, suna wasa da dariya, ko wacce na magana da ƙawarta, wasu suna tafe da jakunkuna a bayansu... Bus ɗin makaranta na jiran su, ƙofar a buɗe.. Idanun Ching Ching suka manne a wajen ba tare da wani motsi ba.. Murmushi ya fara tsiro a fuskarta, murmushin da ba na wasa ba, sai na tsantsar buri... Ta matso kusa da gilashin motar, tana kallon yadda ɗaliban ke hawa bus ɗin cikin farin ciki.. Ta ɗan ɗora hannunta a kan gilashin, kamar tana so ta taɓa abin da take gani.. “Uncle…” ta fara cikin murya mai sanyi... “Ka gan su ko?” Chief Onyx bai ko juyo ba, bai kuma amsa mata ba... Ta ci gaba, kamar tana magana da kanta... “Wallahi suna da sa’a sosai.” Ta yi dariya kaɗan, mai ɗauke da wani irin baƙin ciki.. “Ni fa… ban taɓa shiga irin wannan bus ɗin ba.” Ta waiwaya ta kalle shi, tana sa ran zai kalle ta. Amma yana nan yadda yake, cikin shiru da ƙasaita, fuska na kallon gaba... Ta sake murmushi, ta fara magana a hankali kamar yarinya da ta samu abin da ke faranta mata rai.. “Idan na shiga makaranta fa, zan zauna a gaba. Zan ɗaga hannu kullum. Zan yi rubutu sosai. Zan samu abokai da yawa…” Ta yi tsallen tunani, ta ce cikin dariya.. “Watakila ma zan zama mai hayaniya a aji!” Ta yi shiru na ɗan lokaci. Sannan ta ƙara da murya mai rauni.. “Amma ban taɓa zuwa ba.” Motar ta ci gaba da tafiya. Suka bar Bus ɗin makarantar a baya.. Chief Onyx har yanzu bai kalle ta ba. Amma a cikin zuciyarsa wani abu ya motsa. Hannunsa ya matse a hankali a kan cinyarsa. Ching Ching ta koma ta jingina da kujerar, murmushin yana nan, amma idanunta sun ɗan yi ruwa. Ta ce cikin raha, tana ƙoƙarin ɓoye abin da take ji.. “Da ace ina makaranta, da na zama shahararriyar ɗaliba. Kai ma da zaka zo Parents’ Day ka zauna ka yi shiru kamar yadda kake yi yanzu.” Ta juya ta kalle shi.. “Kai kuwa ka je makaranta a lokacin da kake yaro ko? Kana son abin da nake nufi ko? Playground, library, school uniform mai kyau… duk abin da ke cikin movies na ke so in gani a gaske...” Ta yi murmushi, ta kuma cewa.. “Ni ma na so in sami classmates da za su zama abokaina, in yi exams da su, in sami certificate… ba wai kawai ilimin gida ba...” Haka ta rinƙa surutu ita kaɗai.. Motar ta nufi gida. Amma tunanin makarantar… ya riga ya shiga zuciyar Chief Onyx.. ✨ Bayan kwana biyu, yanayi ya sake sauyawa... Chief Onyx yana cikin wurin wankansa na sirri, yana ta ninkaya cikin ruwan private pool ɗin da ke kewaye da furanni da shuke-shuke masu tsada.. Jikinsa babu komai sai gajeren wando, wanda ya bayyana ƙarfinsa da jarumtarsa. Ruwan yana rufe faffadan kirjinsa yayin da yake shawagi a ciki cikin natsuwa.. Bayan ya ɗau mintuna a nutse cikin ruwan, da ga bisani ya ɗago ya sa hannu yana matse ruwan gashinsa da ya jiƙe, yana tsaka da wasansa sai ga Chingching ta bayyana ɗauke da tsintsiya da bokiti... Ta shigo tana rera wata waƙa da ƙarfi, kamar ba ta san inda take ba, wai ita a dole shara ta zo yi a daidai wannan lokaci!.. _“Sharar da ke da kyau, sai a yi shi a lokaci mai kyau…_ _Idan lokaci ya zo, sai a yi shi ba tare da jawa ba!”_ Waƙar da take rerawa kenan 😅 Onyx ya tsaya cak, ruwa na saukowa daga jikinsa. Ya kalleta cikin mamaki, sannan ya haɗe rai kaɗan, duk da cewa akwai murmushi da ya ɓoye a fuskar sa... “Ke kuma,” ya faɗa cikin sanyin murya, “sharar me kika zo yi a nan? Kin san sarai wannan lokacin nawa ne na shakatawa.” Chingching ta ɗage kai, ta fara share ƙasa alhalin babu ko ƙura. Ta turo baki tana cewa.. “Aiki na ne ai, Uncle.... Gani nayi wurin nan ya fara datti. Ni ban son ganin datti. Ka ci gaba da wankanka, ni sharata zan yi na wuce.” Sai dai duk da maganganunta, idonta na satar kallon jikinsa, zuciyarta na buga mata wani irin bugun da ba ta saba ji ba.. A hankali, ya fito daga cikin ruwan sharkaf, ya tsaya da ɗan takaitaccen taku a gabanta. Faffadan kirjinsa yana kyalli, ruwa na digowa a hankali. Ya sunkuya kaɗan, ya kalleta kai tsaye cikin ido, muryarsa ta sauya ta zama ƙasa-ƙasa.. “To tunda sharar kika zo yi, kuma baki son datti… ki share jikina.” Nan take Chingching ta ruɗe. Ta tsaya tana nuku-nuku, hannayenta na wasa da juna, idonta a ƙasa... Fuskarta ta fara canja launi saboda kunya da fargaba. Ta kasa motsawa, balle ta miƙa hannu ta taɓa shi. Onyx ya lura da rikicewarta. Wani gajeren murmushi ya leƙo a gefen leɓɓansa. Cikin ƙiftawar ido, kafin ta ankara, sai kawai ya sa hannu ya damko kunkuminta, ya ɗaga ta sama kamar yar tsana ya cilla ta tsakiyar pool ɗin... Ruwa ya tashi sama, ya yayyafa ko’ina. Sai da ta nitse gabaɗayanta kafin ta ɗago tana faman fyace ruwa. Onyx kuwa tuni ya ɗauki tawul, ya rataye shi a wuya, yana kallonta cikin murmushi... “Wannan ne ladan sharar da kika zo yi,” ya faɗa yana dariya a hankali.. Ya juya zai tafi. Da ta ga hakan, ta zauna a cikin ruwan, ta fara kukan shagwaba, tana buga ƙafafunta a cikin ruwan... “Haba Uncle! Don Allah ka dawo! Ka taimaka min! Ka duba yadda ka jiƙa ni, ni ba zan iya fitowa ba!” Ta yi tsammanin zai tausaya ya dawo kamar yadda take gani a fina-finai... Amma ina! Onyx ko waiwaya bai yi ba. Ya ci gaba da tafiyarsa cikin natsuwa, har ya ɗaga mata hannu alamar ban-kwana, sannan ya ɓace daga wurin.. Nan take ta gane wasan ya zama gaske. Ta tsagaita kukan, ta share idonta, tana kallon hanyar da ya bi. Ta murguɗa baki tana gunaguni.. “Lallai mutumin nan mugu ne ashe… ya bar ni a nan ni kaɗai, alhalin ya san ban iya ninkaya sosai ba.” Ta fara jan jikinta a hankali, tana lallabawa har ta fito daga ruwan. Rigarta na ɗigar da ruwa, gashinta manne da fuskarta...fuskarta cike da ɓacin rai... Ta zauna a gefen ruwan, tana huci... “Wallahi sai ya ji irin abun da na ji… ba bashi a tsakanin mu saina rama....” “Amma dai,” ta faɗa tana tsuke baki, “sai na rama.” A wannan lokaci… Chief Onyx ya riga ya bar wurin pool ɗin tun da dadewa. Ya shiga sashensa na kwana... Wurin ya kasance shiru, tsabta, babu komai face kamshin turare mai sanyaya rai.. Ya cire tawul ɗin jikinsa. Ya tsaya gaban madubi na ɗan lokaci, fuskar nan tasa, ba murmushi ba kuma fushi a fili.. Ya fara shiryawa cikin kaya masu tsada da tsari.. Ya lanƙaya agogon da kowa ke tsoro idan ya gani, da kuma takalmin da ke sa kowa ya san mai iko ya zo.. Gely ta bayyana a gefensa. “Boss, motoci sun shirya.” “Mu tafi.” ya furta a daidai lokacin da ya gama shirinsa... Yana tafe, Gely na biye da shi a baya.. Bayan mintuna akan tsararren kwalta, motocin suka tsaya gaban babbar makaranta mai katanga ta alfarma..ga tambarin makarantar da tutoci na ƙasashe daban-daban suna kaɗawa a iska... SUNAN MAKARANTAR... AURELIUS CROWN INTERNATIONAL ACADEMY (Elite Boarding School for Global Leaders) Makarantar da ba a biya da nairori sai tsantsar zunzurutun daloli kaɗai.. Makarantar sai ‘ya’yan shugabanni, sarakuna, attajirai, da ‘ya’yan jakadu ne kaɗai ke nan.. Bayan aka ga tambarin Chief Onyx, jami’an tsaro suka miƙe tsaye.. Ba tare da tambaya ko bincike ba.... Suka buɗe ƙofa kai tsaye.. Shugaban makarantar da kansa ya fito, tsoho ne mai farin gashi, fuska cike da annuri da ladabi ya furta.. “Your Excellency, Chief Onyx.” Ya sunkuyar da kai. “Abin alfahari ne samun zuwanka.” Onyx ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar da shi cewa, “Na zo ne domin registration.” Idanun shugaban makarantar suka buɗe.. “Cikakke?” Domin ba kowa ke biyan full a lokaci guda ba, wani duk da kuɗinsa sai ya raba sau biyu, wani uku... “Cikakke,” Onyx ya amsa a taƙaice.. Suka shiga babban ofishin makarantar.... Aka buɗe computer da ake tura kuɗi ta cikinta daga nan ya wuce babban bankin duniya... Adadin ya bayyana a allon kwamfuta, ga daloli masu nauyi. Adadin da zai sa yawancin iyaye su faɗi daga kan kujerun su... Ba tare da tambaya ko jinkiri ba ya furta.. “Done,” Cikin mintuna kaɗan, an kammala biyan kuɗin makaranta, uniform, litattafai da komai da komai da sunan Ching Ching...wato Firdousee Muhammad Nourdeen... Shugaban makarantar ya yi murmushi cike da girmamawa... “Dalibar za ta fara nan da nan. Makarantarmu tana alfahari da wannan suna.” Onyx ya miƙe tsaye yana furta. “Ba don suna na ba, sai don makomarta...” ✨✨✨✨ Bayan dogon lokaci, Sarki ya dawo masarauta cikin kwarjini da izzah. Nan take ya bayar da umarnin taron gaggawa na duk gimbiyoyinsa. A cikin fadar, an jera kujeru na alfarma, kowacce da kalar da ta dace da asalin gimbiyar da za ta zauna akai... (Kamar yadda muka ce a last Page) Kuma a lokacin Ayat a matsayin Inuwa tana wurin Master suna tattauna wani batu.. Jin sanarwar sarki yana son ganin GIMBIYOYINSA yasa ƙirjinta bugawa, tasan dole za'a je duba ta... Shin ya zatayi ga master ya riƙe ta?.. Ta saddaƙar yau kam asirinta zai tonu domin za'a sanar cewa babu Gimbiya Aayat... Tana ta jira taji wannan sanarwa.. Ta saddaƙar sosai..domin tana tsaka da aiki da master Ibrahim.. Sai addu'o'i take ta jerowa.. Daga can nesa, sautin motocin alfarma ya fara tashi... Masu shelar masarauta suka gyara muryoyinsu a lasifika.. Motar gimbiya Zayana ce ta tsaya fara sol, ta fito.. Mai shela ya fara ƙirari.. _"Haske uwar haske! Kyakkyawa ba gajiyawa. Sarauniyar sanyi, farar mace mai kyan hali da kyan jinsi. Jinin turawa, asalin Turai, wadda kyanta ya haska fadar Alhamra. Barka da isowa, Gimbiyar Alfarma, Zayana!"_ Mota kalar ruwan gwal ta bayyana, wato gimbiya Maayah.. Mai shela ya barke da cewa, _"Zinariyar fada, asalin Indiya! Kyakyawa mai gashin kwance, wadda idanunta suka fi taurari haske. Ɗiyar Taj Mahal, mai tafiyar kyan gani. Maayah, tauraruwar dake haska duhun fada, barka da isowa!"_ Can sai ga Gimbiya Yumna, motarta kalar silk ta tsaya... Itama aka fara mata ƙirari.. _"Bishiyar inuwa, Gimbiyar Fulani! Kyakyawa doguwa, mai hancin siffa. Farar fulani, uwar dangi, wadda kwarjininta ya cika fada. Yumna, bishiyar da kowa ke son ya huta a inuwarta, barka da isowa!"_ A ofishin Master Ibrahim, Ayat wato Inuwa tana tsaye, ƙafafunta suna rawa... zuciyarta na bugawa domin a yanzu ko wace gimbiya an kawo ta fadar sarki da mota, duk sun kammala amma babu gimbiya Ayat... Lokaci guda ta ji an fara ƙiran sunan Gimbiya Ayat... Zuciyarta ta kusa fitowa daga ƙirjinta.. "Na shiga uku! Wanene za a kira a matsayina?" ta yi maganar zuci.. Lokacin da aka duba asusun gimbiyoyi aka ga kowa ya halarta banda ita, sai ga wata baƙar mota ta silalo ta fake.. Ƙirarin Gimbiya Ayat ne ya fara amo.. _"Tauraruwar Gabas! Farar wata dake haska sahara. Asalin Larabawa, ɗiyar gidan mutunci. Ayat, wadda fuskarta ke rufe da kwarjini da labule. Barka da isowa, sarauniyar zuciyar sarki!"_ Inuwa ya zabura, ya nufi fadar cikin sauri, Master Ibrahim ya biyo bayansa cikin mamaki. Suna isa ƙofar fadar, Inuwa ya ga wata mace ta fito daga motar, siffarta, tsayinta, da kayanta duka IRIN NA AYAT NE! Fuskar mace dake rufe da mayafi ta sa Inuwa daskarewa... "Wannan wacece? Wacece wannan dake wasa da raina?" Inuwa ya tambayi kansa cikin tsoro da matuƙar mamaki. Master Ibrahim ya kalle shi, "Lafiya Inuwa?" Inuwa ya gyara muryarsa, "Lafiya Master, kawai kwarjinin gimbiyoyin ne ya ba ni mamaki." Sarki ya kalli gimbiyoyinsa guda huɗu dake zaune, ciki har da Ayat ta bogi. Ya gyara zama, muryarsa ta daka cikin fadar.. "Na ƙira ku ne don in bayyana muku wani sabon sauyi. Kun girma, kuma lokaci ya yi da zan muku aure. Amma sabanin al'adar gidajen sarauta, na yanke shawarar kowaccenku ta faɗi wanda take so..." Yayin da Ayat ta bogi ta juyo da idanunta masu kama da na Ayat ta gaske, ta kalli inda Inuwa yake tsaye acan nesa da su. Ta yi wani ɗan gajeren murmushi dake bayyana ta cikin mayafin fuskarta.. Zayana ce ta ce, "Wani irin mijin aure bayan ba ma fita ko ina?..." Sarki ya sanar musu cewa.. "To ni zan nema muku da kaina..." Zaku cigaba da tsare har lokacin auren ku... Ya sanar dasu cewa zai tura saƙo ga ko wani sarakunan yanki mabanbanta, da su nemawa ƴaƴansu maza auren gimbiyoyinsa... Kaf gimbiyoyin jin haka, babu wanda ya nuna farin ciki a cikinsu, Bayan sarki ya bayyana nufinsa na yi musu aure da ’ya’yan sarakuna, fadar ta yi tsit. Zayana, wadda ko a gaban sarki ba ta tsoron magana, ta gyara zama, fuskarta cike da nuna rashin amincewa... ​"Abul, kayi haƙuri ka cire ni a wannan batun," Zayana ta faɗa cikin muryar isa.. "Domin ni akwai wanda nake jira. Da zarar ya bayyana zan yi aure, wato uban yarinyata Mimi." ​Nan take fuskar sarki ta canza kalar, idanunsa suka yi jajur. Maganar Mimi da asalin mahaifinta babban rauni ne ga masarautar Alhamra, domin babban abin kunya ne da Zayana ta janyo masa. Amma ko a jikinta, domin ta san sarki ba zai iya kashe ta ba... ​Sarki ya daka wata tsawa wadda ta girgiza dandalin fadar... "Ya isa haka! Babu wata gimbiya da ta isa ta bijire wa umarni na. Maganar wancan mutumin ta ƙare tun ranar da kika janyo wa wannan masarautar abin kunya. Dukkan ku, ku koma sashen ku! Nan da kwanaki kaɗan zan aike da saƙo ga dukkan sarakunan yanki." ​Kowace gimbiya ta tashi tana sosa ƙeya, Maayah da Yumna sun tafi cikin sanyin jiki, yayin da Zayana ta fice tana huci. ​Ayat ta bogi ta miƙe cikin nutsuwa, tana taku ɗaya bayan ɗaya kamar yadda Ayat ta gaske take yi.. Inuwa dake tsaye kusa da Master Ibrahim, idonsa ya bushe, yana kallon yadda wannan matar take tafiya. ​Inuwa ya kasa haƙuri, ya raɗa wa Master Ibrahim.. "Master, me suka tattauna a ciki? Ina ganin gimbiyoyin duka fuskokinsu babu annuri." ​Master Ibrahim ya ja numfashi, "Sarki ne ya yanke shawarar ba da aurensu ga ’ya’yan sarakuna. Inuwa, kaga wannan gimbiyar dake ƙarshe? Ita ce Gimbiya Ayat. Mutane suna cewa tana da sanyi, amma tana da kwarjini a tare da ita domin kusan ta fi su..." ​Inuwa ya kusan suman tsaye, "Idan sarki ya ba da aurena, wa za a kai gidan miji? Ni ko wannan matar?" Ya yi maganar zuci cikin matuƙar tashin hankali. ​Suna fita daga fadar, Inuwa ya ga Ayat ta bogi tana shirin shiga motarta. Inuwa ya yi maza ya nemi izini wurin Master Ibrahim akan zai je ya duba wani abu a sashen tsaro, amma a gaskiya bin motar zai yi.. ​Yana isa kusa da motar, Ayat ta bogi ta zuro da kanta ta window, ta kalli Inuwa shi kuma yana cikin kakin PA.. Ta yi masa wani kallo mai zurfi, sannan ta raɗa.. "Kada ka ji tsoro, Inuwa.... Inuwa baya iya rayuwa ba tare da jikin da yake ba shi inuwar ba." ​Ta ɗaga masa hannu, direban ya tada mota suka bar wurin. Inuwa ya daskare a tsaye. Wannan muryar... ya sani sarai ba muryar mace ba ce ta gaske ba.. ​Kowace gimbiya ta koma sashenta da damuwa.. ​Zayana tana huci tana shirin kiran mahaifiyarta don sanar mata da wannan auren...domin tasan ba ta sani ba.. ​Maayah kuwa tana kuka domin ta fi son karatu da makarantar da take zuwa fiye da zaman gidan miji...kuma ba ta jin a ransa zata rayu da ko wani namiji in ba Inuwa ba, ga damuwar Uncle Jalal da ya sako ta a gaba, yasa duk ta zubar da ƙimarta a gaban aji, a yanzu tana ɗaukan kanta ne a matsayin mutum-mutumi.... ​Yumna kuwa duk da tana matuƙar ƙaunar malamin da yake zuwa koyar da ita ba tare da ya sani ba amma tana addu'ar Allah ya ba ta mijin da zai so ta don Allah.... ​Shi kuma Inuwa, yana tsaye a tsakiyar fili, ya rasa inda zai dosa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta isa sashensa na gimbiya cikin sassarfa, zuciyarsa na bugawa tamkar za ta fito... Ya lallaɓa ta ƙofar sirri ya shiga ɗakinsa na ciki, inda ya tarar da waccan siffar tana zaune a gaban madubi, tana gyara mayafin fuskarta... Inuwa ya watsa wa wannan siffar kallo mai cike da tsoro da tambayoyi... "Wacece ke? Kuma waye ya ba ki izinin shiga siffata?" Waccan Ayat ta bogi ta tashi tsaye a hankali. Takun ta, kamshinta, har ma da kalar idonta duka na Ayat ne.. Ta matso kusa da shi, sannan ta yi wata dariya mai sanyi, muryar King Diamond ta fito fili.. "Na gaya miki, Inuwa ba ya rayuwa idan babu jikin da yake ba shi inuwar... Idan ban bayyana a fadar nan ba, da yanzu Master Ibrahim da Sarki suna nan suna neman inda Gimbiya Ayat take..." Ayat cikin kakin Inuwa ta zauna a ƙasa cikin sanyin jiki... "Diamond, me kake shirin yi? Sarki ya ce zai ba da aurenmu. Idan ya kawo miji, wa zai aura? Kai ko ni?" Diamond wanda yake cikin siffar Ayat, ya sunkuyo ya kalle ta... "Ke za ki ci gaba da zama Inuwa, ki gina ƙarfi da ikon da kike buƙata don gyara masarautar nan. Ni kuma zan riƙa zama Gimbiya Ayat a duk lokacin da bukatar hakan ta taso... Game da maganar aure kuma... babu wanda ya isa ya aure ki muddin ina raye... Ayat ta rufe fuskarta da hannayenta... "Wannan hauka ne! Idan aka gano mu, kisa ne hukuncinmu." Diamond ya yi murmushin raini... "Kisa? Ni ne mutum na farko da aka taba kashewa amma ban mutu ba, Ayat. Ki kwantar da hankalinki..." Bayan ɗakin ya yi shiru, Diamond ya saki siffar Ayat, hayaki ya rabe, ya koma asalin sa na King Diamond. Dogon namiji, kyakkyawa mai kwarjini, wanda kallo ɗaya zaka masa kasan ba mutumin banza ba ne... Ayat ta miƙe tana kallon sa, kirjin ta na bugawa. Ganin yadda ya sadaukar da kansa ya shiga siffar mace don kawai ya kare mutuncinta a gaban Sarki, ya taɓa zuciyarta sosai. Ba tare da tunanin komai ba, ta fada kirjin sa, ta kankame shi tana kuka mai karfi... Diamond ya rungume ta, ya dora habar sa a kanta, yana shakar kamshinta wanda ya dade yana mafarkinsa... "Kiyi shiru Ayat," ya rada mata cikin murya mai daɗi.. "Babu wanda ya isa ya raɓe ki da sunan soyayya muddin ina raye. Ko Sarki ya aiko da sarakuna dubu, ke tawa ce, kuma ni naki ne. Ke ce zuciyata..." Ta ɗago kanta tana share hawaye, ta kalle shi sama da ƙasa sannan ta fara bugun kirjin sa da kananan hannayen ta cikin sigar wasa da shagwaba... "Ka samu matsala, Diamond! Taya mutum da aljani zasu yi aure? Allah ya kiyaye na auri aljani... cab! Ni mutum nake so, ba wani wanda yake narke wa ya zama hayaƙi ba," ta fada tana kukan dake gauraye da shagwaba... Diamond ya tsaya yana kallon ta, wani irin murmushi ya subuce masa. Ya daga kafada irin na mutanen da suka san abin da suke yi... "Aljani ko mutum, ni dai na san ke tawa ce. Idan lokacin ya yi, zaki gane cewa ba kowanne hayaƙi ba ne yake ƙonewa... wasu hayakin suna bayar da inuwa ne..." Diamond ya koma gefe ya zauna a bakin gadon ta, ya miƙa mata hannu... "Maganar wasiƙun Sarki kuma, ki kwantar da hankalinki. Ko ya tura su, ba za su taba isa inda aka dosa ba ga sunanki. Zan tabbatar an aurar da sauran, amma ke Ayat, zaki kasance cikin masarautar nan har sai ranar da zan zo daukarki a matsayin Sarauniyata..." Ayat ta dan yi shiru, tana kallon fuskar sa da ta yi mata kwarjini. Akwai wani abu game da Diamond dake tunatar da ita Reems, amma tana ganin hakan ba zai taba yiwuwa ba tunda Reems mutum ne kuma tana tunanin ya daɗe da mutuwa... "Yanzu ki huta," Diamond ya ce mata. "Gobe Inuwa yana da aiki babba a gaban sa. Sarki zai bukaci ganin PA ɗinsa... Ki zama jajirtacciya kamar yadda kika saba." Ayat ta jinjina kai, tana jin wani irin kwanciyar hankali da ba ta taba ji ba tun bayan rasuwar mahaifiyarta. Tana jin cewa koda duniya zata juyo mata, tana da Aljani dake shirye ya yaƙi kowa don ita... Ta buɗe baki cikin gaggawa kafin ya ɓace ta ce, "Yauwa, ta ya kai shigo Masarautar nan alhalin a tsare yake?..." Murmushi kawai Diamond yayi sannan ya ɓace ba tare da ya ba ta amsa ba.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣1️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* A cikin wadannan kwanakin, Inuwa ya ƙara karfi a idon jami'ai. Ya fara gabatar da sabbin dokoki na sassauta wa fursunoni, wanda Master Ibrahim ya amince da su saboda hazaƙarsa. Inuwa ya zama kamar wani Yariman Ofis, domin kowa girmama shi yake yi... Bayan kwana biyu da taron fada, Inuwa yana kokarin tantance wasu takardu a ofis, sai ga wata kuyanga daga sashen Gimbiya Maayah ta iso. Ta miƙa masa saƙo a boye.. _"Inuwa, ina bukatar ganinka yanzu a lambun dake bayan sashena. Rayuwata tana cikin hadari."_ Inuwa ya firgita, yana tunanin ko wani abu ne ya faru da Maayah, don haka ya nufi can da sauri. Yana isa lambun, ya iske Maayah tsaye a bakin bishiyoyin flawa, fuskarta duk hawaye. Tana ganin sa, ba ta jira komai ba ta rugo da gudu ta faɗa jikinsa, ta kankame shi tana kuka mai cin zuciya.. Inuwa ya daskare! Jikinsa ya fara rawa, domin a matsayinsa na mace, bai saba da irin wannan kusancin da wata mace ba. Ya tsaya da hannayensa a sama, ya rasa inda zai sa su... Da kyar, cikin dabara da karfi, Inuwa ya janye jikinsa daga nata, ya raba rungumar.. "Gimbiya, me ke faruwa? Kin san matsayina, kuma kin san idan aka gan mu a haka kisa ne hukuncina," Inuwa ya fada cikin muryar jami'ai dake rawa.. Maayah ta kalle shi da kyawawan idanunta wanda yake cike da hawaye. "Inuwa, ba zan iya ba! Sarki yana shirin aurar da mu ga sarakunan da ba mu sani ba. Ni kuma zuciyata ta daɗe da ficewa daga kirjina ta koma gare ka." Ta sake kamowa hannunsa, "Inuwa, tun ranar da na fara ganinka, nake jin wani abu daban. Ni ba na son kowa, ba na son sarauta, kai kadai nake so. Dan Allah ka ce wani abu!" Ayat dake cikin kakin Inuwa ta ji kamar ƙasa ta tsage ta hadiye ta. Tana jin tausayin Maayah, amma tana jin wani irin kishi na daban domin ita ma tana da nata ra'ayin akan kanta... Ta san cewa wannan soyayyar ba za ta taɓa yiwuwa ba.. "Gimbiya Maayah," Inuwa ya ƙira yana kau da kai. "Ni bawa ne, ke kuma gimbiya ce. Haka kuma, akwai abubuwa da yawa game da ni da ba ki sani ba. Wannan soyayyar... haɗari ce gare ki." Maayah ta ƙara sautin kukan ta... "Babu wani haɗari da ya wuce a raba ni da kai... Idan har ba za ka aure ni ba, gara na mutu kafin ranar da wasikun sarki zasu bar fadar nan!" Ta ƙara matso kusa da shi tana nuna ƙirjinta... "Inuwa, na kamu da matsananciyar ƙaunarka. Idan har ba za ka ce kana so na ba, ko kuma ba za mu kasance tare ba, to gara rayuwata ta ƙare a nan." Inuwa ya ji wani irin nauyi a ransa. Tausayin Maayah ya kama shi, musamman ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita. Ya tsaya yana kallonta, ya rasa ta ina zai fara gaya mata cewa wannan burin nata ba zai taɓa cika ba, kuma ba zai iya son ta yadda take so ba.. Maayah ta ci gaba da kukan ta, tana roƙonsa, tana jiran ya ce wani abu da zai kwantar mata da hankali kafin lokacin wasiƙun Sarki ya yi... Inuwa ya ja numfashi mai nauyi, idanunsa suka sarƙe cikin na Maayah dake zubar da hawaye. Ganin yadda gimbiyar ta duƙa gwiwowinta a ƙasa tana kuka, ya sa ya ji cewa idan bai faɗi wani abu ba yanzu, za ta iya aikata abin da zai tona asirinsu duka.. Hakan ya sa ya sunkuyo, ya kama kafadunta ya ɗago da ita a hankali. Inuwa ya saita muryarsa ta yadda za ta ratsa zuciyar Maayah, ya dube ta cikin natsuwa... "Gimbiya Maayah, ya isa haka. Share hawayenki," ya faɗa cikin muryar lallashi... "Na ji duk abin da kika faɗa, kuma ba zan zura ido in ga an kai ki gidan da ba kya so ba. Ki kwantar da hankalinki, ba za a tura wasiƙar aurenki ba." Maayah ta tsagaita kukan, ta kalli Inuwa cike da faduwar gaba da bege.. "Inuwa, da gaske kake? Za ka iya hana Sarki?" Inuwa ya ɗaga kai, koda yake a ransa ya san cewa yana yin wannan alkawarin ne domin ya kare kansa daga wannan auren, amma ya nuna wa Maayah cewa domin ita ne.. "Ke kanki kin sani ni ne PA na Master Ibrahim. Ni ne zan karɓi wasiƙun nan, kuma ni ne zan miƙa su ga ƴan aike. Zan yi dabarar da zan bi in tabbatar da cewa takardar aurenki ba ta bar masarautar nan ba. Amma ki yi min alkawari guda ɗaya..." Maayah ta share fuskarta da sauri, "Komai ka ce zan yi, Inuwa!" "Kada ki sake nuna wa kowa damuwarki. Ki koma sashenki, ki zama kamar ba abin da ya faru. Idan Sarki ko kowa ya ga kina murna ko kina cikin natsuwa, ba za su yi zargin komai ba. Ki bar min sauran aikin, zan yi duk yadda zan yi in ga na dakatar da wannan auren." Jin wannan maganar daga bakin Inuwa ya sanya Maayah jin kamar an sauke mata dutse a kanta. Ta yi murmushi cikin hawaye, ta so ta sake rugowa ta rungume shi, amma Inuwa ya yi saurin yin taku ɗaya baya... "Yanzu ki tafi, Gimbiya. Kada a gan mu a nan." Maayah ta gyada kai cikin farin ciki, ta juya tana tafiya tana waigensa, tana jin cewa yanzu ta samu jarumin da zai cece ta. Inuwa ya tsaya yana kallon yadda take tafiya cikin farin ciki. Ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, yana jin nauyin karyar da ya yi mata a kansa.. "Kiyi haƙuri Maayah," ya yi maganar zuci... "Ba don ke nake wannan aikin ba, don kaina nake yi. Amma tunda hakan zai cece mu duka, zan yi iya ƙoƙarina..." ✨ Washegari, Inuwa yana cikin sashen Master Ibrahim yana nazarin wasu takardu, sai ga bawan Gimbiya Zayana ya sake bayyana... A wannan karon ma, katin gayyar ya fi na farko tsada, kuma akwai wani akwati ƙarami na zinare dake rakiya da katin.. "Ranka ya daɗe," bawan ya faɗa yana gaisuwa.. "Gimbiya Zayana tana nemanka yanzu a sashen fita na lambun ta na sirri. Tana son tattaunawa akan makomar masarautar nan." Inuwa ya san cewa ƙin zuwa zai iya janyo masa zargi, don haka ya nufi sashen Zayana. Ya tarar da ita tana tsaye a cikin lambun ta, sanye da wata doguwar riga mai kalar ruwan gwal. Fuskarta yau tana nuna annuri, sai dai wani irin murmushi take na maƙirci... "Inuwa, na san ranar na ɓata maka rai," Zayana ta fara magana cikin sanyin murya... "Amma maganar da Sarki ya yi, ta sa na gane cewa kai ne kaɗai za ka iya taimaka min.. Kuma idan ka taimaka min, zan mayar da kai mafi kuɗi a duk dakarun Alhamra." Inuwa ya tsaya, hannuwansa a baya, fuska babu annuri... "Ina saurarenki, Gimbiya." Zayana ta matso kusa, muryarta ƙasa-ƙasa.. "Ka san Sarki ya bayar da umarnin a tura saƙo ga sarakuna don neman aurenmu. Ni kuma ba zan taɓa auren wani sarki ba! Ina so ka yi amfani da matsayinka na PA, ka canza wasiƙar da za a tura wa Sarkin yankin da aka nufa da ni. Ka sa a rubuta cewa 'Zayana ba ta da lafiyar da za ta iya zama matar aure'. Ko kuma ka ɓatar da wasiƙar gaba ɗaya." Inuwa ya ji zuciyarsa ta buga. Wannan dama ce ta kusa-da-kusa don ya san yadda zai ɓatar da tasa wasiƙar ma. Amma dole ya nuna taurin kai don kada Zayana ta yi zargin wani abu... "Gimbiya, kin san hukuncin canza wasiƙar Sarki? Kisa ne," Inuwa ya faɗa.. Zayana ta yi dariya, ta buɗe wancan akwatin zinaren, cike yake da duwatsu masu daraja (diamonds) da zinare.. "Wannan na farko ne. Idan ka yi nasara, zan ba ka ninkin wannan. Kuma zan tsaya maka a gaban Master Ibrahim ya ƙara maka matsayi. Idan kuma ka ƙi..." Ta ɗaga kanta, idanunta suka yi shanye, "...zan gaya wa kowa cewa ka shigo mun har ɗaki ba tare da izini ba, kana nemana da lalata...." Inuwa ya kalli dukiyar, sannan ya kalli Zayana. A ransa yana cewa, "Zayana, ashe ma kina taya ni aikin da nake so in yi." Ya gyara tsayuwar sa.. ya furta a fili, "Zan yi ƙoƙari, Gimbiya.. Amma fa ki sani, idan asiri ya tonu, ni da ke ne a gaban shari'a." Zayana ta buga tafi, tana jin ta yi nasara.. "Ba zai tonu ba. Tunda kai ne PA, kai ne za ka kai wa ƴan aika wasiƙun. A lokacin za ka cire tawa..." Ya karɓa sannan ya juya ya tafi.. Can dare tayi wanka cikin sleeping dress tana zaune a tsakiyar gadonta dake sashenta, ta buɗe akwatin zinaren da Zayana ta ba ta. Kyalkyalin duwatsu masu daraja ya cika ɗakin. Ya san cewa waɗannan kuɗaɗen an tara su ne ta hanyar zalunci.. "Zayana, kina tunanin za ki iya sayen ƙaddara da kuɗi?" Ayat ta yi maganar zuci tana murmushin yaƙi... "Tunda kina da kuɗin banza, to zan taimaka miki wajen rage miki nauyin su ta hanyar kai su inda suka dace." ✨✨ Bayan kwana biyu da maganarta da Inuwa, Maayah ta tafi makaranta cikin wani irin yanayi.. Jikinta ya yi sanyi, kwarjininta na dā ya ragu domin zuciyarta tana cike da fargabar aure da kuma kaunar Inuwa, ga Uncle Jalal da ya sako ta a gaba... Ta daina hantarar kowa, amma har yanzu akwai ragowar izzah a tare da ita. Tana zaune a aji, tana tunanin Inuwa, sai ga Uncle Jalal ya shigo. Takunsa kawai ya isa ya sanya ajin yin tsit. Jalal mutum ne mai cikar kwarjini... Ya tsaya a gaban aji, ya kalli kowa da idanunsa masu kaifi. Kowa ya miƙe ya yi gaisuwa ban da Maayah... Uncle Jalal ne ya watsa mata wata harara guda daya, wadda ta sanya ta rasa natsuwarta, ta miƙe a hankali tana sunkuyar da kanta tare da hadiye miyau. Can ya mu su alamar su zauna da hannu...sai da kowa ya zauna tukun itama za zamo last ɗin zama kamar yadda tayi last ɗin tashi.. Jalal ya ajiye littattafansa a kan teburi, muryarsa ta daki kowanne lungu na ajin... "Where is the class Rep?" Maayah ta ɗago kai da sauri, tana zare ido. Tunda ya ba ta mukamin Class Monitor, rayuwarta ta sauya.. "Je ki nemo min sabuwar marker rubutu yanzun nan," ya fada cikin sanyi na ba da umarni... Maayah ta tashi tana turo baki, ranta a ɓace. Ita ce gimbiyar da bayi suke yi wa komai, amma yau ita ce take yawo a corridors ɗin makaranta neman marker... Kuma yanzu Bodyguards ɗin nata Jalal ya hanasu tsayuwa a cikin makaranta, ya sanar cewa zasu iya kawo ta, amma da zaran sun dire ta a cikin makarantar sai kuma su juya sai lokacin tashi yayi... ......Bayan ta dawo, Jalal bai karɓi marken ba sai da ya kalli allo wanda yake cike da rubutun jiya.. "Goge allon nan kafin ki mika min marken," ya faɗa yana gyara zama akan chair. Maayah ta ɗauki duster din, ta fara goge allon. Hawaye suka fara silalo mata a kunci. Tana gogewa tana kukan zuci, tana ganin kamar Uncle Jalal ya tsane ta ne kawai yake mata wannan walakancin. Tana turo baki, kyakkyawar fuskarta ta ɓaci da ƙura, amma ta kasa musawa domin kwarjinin Jalal ya sha karfinta... Uncle Jalal ya zauna yana kallonta ta glassin idonsa. A ransa yana murmushi, domin ya san cewa wannan tarbiyyar tana da amfani gare ta kafin lokaci ya kure... "Idan kika gama, ki buɗe textbook ɗinki shafi na arba'in," ya fada ba tare da nuna tausayi ba, yayin da Maayah take share hawayen dake diga a kan takardarta... Aji ya yi tsit, kowa ya maida hankali. Uncle Jalal ya fara darasin sa, yana tafiya yana zazzage tambayoyi da turanci. Abin sha'awa, kowanne dalibi idan ya tashi, magana yake yi cikin kwarewa da harshen Turanci kamar dan Jami'a. Suna fito da hujjoji da tambayoyi masu zurfi dake nuna cewa lallai kowa ya haɗiye karatun... Uncle Jalal ya gyada kai, yana jin dadin yadda daliban nasa suke da kwakwalwa. Amma duk wannan bajinta da ake yi, Maayah tana zaune ne can baya, kanta a sunkuye tana wasa da gefen skirt ɗinta dake short ne... Uncle Jalal ya tsaya kusa da teburinsa, ya gyara tsayuwa sannan ya ƙira sunanta cikin natsuwa.. "Maayah, me kika gane game da bayanin da na yi yanzu? What is your take on this topic?" Maayah ta ɗago kai, ta kalle shi da idanun nan nata dake cike da shagwaba da kuma ruɗani.. Ta yi shiru, ta kasa cewa uffan. Duk ajin suka juyo suna kallonta. Wannan ba sabon abu bane, domin Maayah ba ta taɓa bada amsar tambaya ba, kuma ba ta taɓa ɗaga hannu ta yi tambaya ba... A kallon Uncle Jalal, Maayah ce kadai jahila a cikin ajin dake neman ɓata masa kokari... Ganin ba ta da niyyar magana, ya tako har zuwa mazauninta. Ya miƙa hannu ya ɗauko jakartar makarantar ta, ya buɗe ta gaban kowa. Ya fara fito da littattafanta daya bayan daya. Ya bincika na Turanci, ya bincika na Lissafi, da na computer sai ya iske abin takaici. Wasu littattafan fanko ne babu rubutu ko daya. Wadanda kuma take da shi, rubutun babu fasali, gurgwaye ne kamar na yara 'yan Nursery dake koyon rike fensir. Rubutun nata ba shi da tsari, kuma bai fi na darasi biyu ba a duk semester din, nan ma ba complete ba. Uncle Jalal ya jefa littattafan akan teburin natan, ransa ya ɓaci sosai... "Maayah! Me kike zuwa yi a makarantar nan?" Ya daka mata tsawa wadda ta sa duk ajin suka razana.. "Ina sauran rubutun malaman? Na bada note kusan guda goma, amma ke naki bai fi na darasi biyu ba, kuma ko shi din ma ba a kammala ba!" Ya nuna littafin da rubutun nursery dake ciki. "Duba irin rubutunki, shin hakan ya dace da daliba a wannan matakin? Kullum kowa yana fahimtar darasi amma ke kina nan kina wasa da lokaci. Idan kika sake zuwa ajina gobe ba ki kammala wannan note din ba, to lallai za ki fuskanci hukuncin da ba ki taba gani ba a makarantar nan!" Maayah ta rasa inda za ta sa kanta don kunya da takaici. Ta turo baki, hawaye suka fara sintiri a fuskarta. Ta ji kowa a ajin yana kallonta a matsayin jahila, alhalin ita a gida ita ce gimbiya mai kowa da komai.. Ta kalli Uncle Jalal cikin kiyayya da kuma tsoro, tana mamakin yadda mutumin nan yake da kwarjinin da har yake iya daka mata tsawa a gaban mutane. Ta sunkuyar da kanta tana goge hawaye, tana jin duniyar ta yi mata zafi.... Uncle Jalal ya tsaya dambar a gabanta, hannayensa a dunkule, idanunsa suna huda zuciyarta... "Dakata tukunna," ya faɗa cikin muryar da ta sa kowa a ajin ya daskare.. "Ta yaya ma kike rubuta jarrabawa? Na duba kundin sakamakon makarantar nan, naga dukkan sakamakonki kina cin first position... A kowace jarrabawa tun da kika fara makarantar nan, ke ce kike ɗaukar ta ɗaya." Ya yi wata dariyar raini wadda ta fi ciwo fiye da dukan bulala... "Oh! Na gane. Saboda duk sauran malaman da har shi kansa Shugaban makarantar tsoronki suke yi, ko? Ba kya rubuta komai a jarrabawa, hasali ma ba kya zama a ɗakin rubuta jarrabawar, amma kuma a baki First Class!" Uncle Jalal ya buga teburin dake gabanta, "Wannan cin mutuncin ilimi ne! Wannan rashin adalci ne ga waɗannan ɗaliban dake zaune suna ta faman karatu dare da rana. Amma tunda yanzu ina nan, naga yadda za ki samu sakamako ba tare da kin rubuta jarrabawa da hannunki ba. Ko ke ɗiyar Sarki ce, ko ɗiyar wane ne, a ajina dukiya da sarauta ba sa ba da sakamako, sai ƙwaƙwalwa!".... Maayah ta ji kamar ƙasa ta tsage ta haɗiye ta. Kalmomin Uncle Jalal sun kasance masu zafi... Ta saba da ganin kowa yana rawar ƙafa a gabanta, amma wannan malamin ya fito da kuskurenta a gaban kowa.. Hawaye suka fara zubar mata gwanin ban tausayi. Tana turo baki, tana jin wani irin takaici na yadda asirinta ya tonu. Sauran ɗaliban suka fara raɗa-raɗa a tsakaninsu, wasu suna kallonta cike da tausayi, wasu kuma da mamakin yadda ashe First Class ɗinta na jabu ne... "Daga yau," Uncle Jalal ya ci gaba da faɗa, "Ba ke ce za ki riƙa fita ɗauko min marker ba. Domin wannan ma alƙali ne na ƙarya. Za ki zauna a nan, ki kammala duk notes ɗin da kika bari. Kuma gobe, zan baki jarrabawa ta musamman a ofishina don in ga abin da kika sani." Ya juya ya bar mazauninta, yana tafiya cikin takunsa na isa, ya ɗaga hannu yana faɗin... "Class dismissed!" .. ✨✨ Fadar ta yi shiru, sai kamshin turaren da ya gauraye ko'ina. Sheikh Shureim, kyakkyawan Balarabe mai cikar kamala da haiba, yana zaune cikin ladabi a gefen Sarki akan ƙaramar sofa na baƙi... Fararen kayan sa da jajurwar fuskarsa sun ƙara masa kwarjini. ​Sarki ya gyara zama, fuskarsa cike da annuri.. "Alsheikh Shureim, shin ya koyarwarku take gudana? Ko dan Ina da tabbaci akan Gimbiyata Yumna." ​Sheikh ya sunkuyar da kansa, ya amsa cikin muryarsa mai daɗi.. "Ranka ya daɗe akanta nazo magana. A yanzu haka, Gimbiya Yumna ta kammala haddar Alkur'ani mai girma har sau biyar. Ta haddace hadisan Manzo (S.A.W) da sauran litattafan fikihu." ​Sheikh ya ci gaba, "Ta aiko ni ne ta roki alfarma, tana son gudanar da gagarumar walima a masarautar nan. Amma tana son a bincika idan akwai sauran Gimbiyoyin da suka haddace Alkur'ani domin su gudanar da walimar tare." ​Sarki ya sake murmushi mai ƙayatarwa, sai dai abin mamaki a yanzu babu fuskar zakin nan, asalin kamanninsa ne, Ya ji daɗin wannan albishir domin sai hamdala yake tayi... "Masha Allah! Wannan ita ce kyauta mafi girma da ɗiya zata ba mahaifinta." Nan take ya bada umarnin a ƙira masa dukka Gimbiyoyin masarautar ba tare da bata lokaci ba. ​A lokacin ne motar jami'an tsaron Maayah ta shigo masarautar daga makaranta. Aka tsaida su aka gaya musu sakon Sarki. Maayah ta firgita, ta yi saurin goge hawayen dake fuskarta na takaicin Uncle Jalal... ​"Wayyo kar dai maganar auren ne?..." ta faɗa tana turo baki, zuciyarta na bugawa. Ita ce ta farkon shiga fadar, tana taku ɗaya-ɗaya har ta samu waje ta zauna, tana kokarin boye idanunta dake jawur. ​Ba a daɗe ba, sauran Gimbiyoyin suka fara isowa. Zayana ta shigo cikin takun gadara. Sai kuma Ayat ta bayyana, a yau ta yi sa'a tana matsayinta na Gimbiya ba Inuwa ba. Ta zauna cikin sanyi da nutsuwa, fuskarta a rufe da siririn mayafi... An buƙaci ganin malaman dake koyar da yaran gaba ɗaya dake ko wace gimbiya da malaminta... ​Malaman gida suma sun iso... ​Malamin Ayat shiru-shiru mai yawan nazari da nuna Dattaku... Sai ​malamin Zayana wanda kullum take bashi wahala... ​Sai kuma Sheikh Shureim dake zaune gefe ɗaya, idanunsa a kasa. ​Daga ƙarshe, Gimbiya Yumna ta shigo. Ta sha bamban da sauran, fuskarta tana fitar da wani irin haske na tarbiyya da karatun Alkur'ani. Tana shigowa, idanunta suka sauka akan Sheikh Shureim. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, tana jin wani daɗi dake gauraye da kunya na cewa "Ga masoyina, ga kuma abin alfaharina." ​Ta gaishe da mahaifinta, sannan ta zauna kusa da Aunty Zayana... ​Sarki ya kalli Gimbiyoyin nasa guda huɗu da suka hallara... "Na ƙira ku ne domin na ji labari mai daɗi daga bakin Sheikh Shureim game da Yumna. Tana son yin walimar saukar Alkur'ani, kuma tana son wacce ta haddace a cikinku ta fito su yi tare." ​Sarki ya kalli kowacce ɗaya bayan ɗaya.. "Zayana? Maayah? Aayat? Shin akwai wacce ke da haddar Alkur'ani a cikinku?" ​Zayana ta kau da kai, Maayah kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta tana tunanin notes din Uncle Jalal... Sai Ayat ce kadai ta ɗanyi motsi, amma ba ta ce uffan ba... Bayan tambayar Sarki, Malam Mubarak ya yi murmushi mai cike da alfahari, ya gyara zama... "Ranka ya daɗe, tabbas Gimbiya Aayat ma ta haddace Alkur'ani mai girma da wasu daga cikin litattafan Manzo Allah (S.A.W). Dalilin da ya sa kuke ganinta tana ba ni hutu ne saboda ta kammala komai, tana tilawa ne kawai a kowane lokaci." (A ranta, Ayat ta sauke ajiyar zuciya, domin ta san dalilin dakatar da shi shine don ta samu sararin fita a matsayin Inuwa, amma hakan bai hana ta kasancewa mai kwazon karatu a ɓoye ba). Sarki ya jinjina kai, fuskarsa cike da mamaki. "Masha Allah! Amma batun boko fa?" Malam Mubarak ya ci gaba, "Alhamdulillah! Ta ƙware a Turanci da rubutu. Ta bitar darussan kimiyya irin su Physics, Chemistry, Maths, har ma da fannin tattalin arziki (Economics). Ta hadiye duk wani fanni da ake koyarwa." Sarki ya kalli Ayat da matsanancin farin ciki.. "Daman burinta ta zama likita tun tana ƙarama, ashe har kin shirya." Ba zato ba tsammani, Ayat ta ɗaga kai ta cikin mayafinta, muryarta a sanyaye cikin natsuwa... "Abul... yanzu na fasa zama likita." Fadar ta ɗauki shiru. Sarki ya zaro ido, "Me ya sa? Bayan kin gama tattara duk darussan fannin kin karance su?" Ayat ta yi murmushin nan nata na shagwaɓa wanda Sarki ba ya iya musa mata duk mayafi ya rufe... "Abul, ni yanzu Criminology nake so. Burina shi ne in zama Sojan Sama wato Air Force Officer..." Sarki ya kalli 'yarsa kamar bai taɓa ganinta ba. "Kina Gimbiya? Kuma matar wani nan gaba? Kuma da wannan rufin fuskar koda yaushe za ki yi aikin soja? Wannan wane irin buri ne Ayat?" Ayat ta ɗan matso kusa da mahaifinta cikin sigar lallashi da shagwaɓa.. "Abul, please mana. Duk wanda zan aura ai zai bar ni in yi abin da nake so. Kuma duk sanda na zama sojan sama, to zan yaye wannan mayafin in sanya kakin soja. Batun gimbiyanci kuma... uhmm uhmmm," ta turo baki tana dariya. Duk waɗanda ke fadar suka daskare. Sheikh Shureim ya ji jiki ya yi sanyi ganin yadda 'yar Sarki ke da babban buri na jarumta.. Maayah ta daina kukan zucin da take na Uncle Jalal, ta tsaya tana kallon Ayat da mamaki, tana tunanin yadda za a yi mace ta zama soja.. Sarki kuwa ya rasa abin da zai ce, domin ya san tauri da kaifin zuciyar Ayat idan ta sa abu a gaba. Sai kawai ya juya kansa a hankali zuwa ga Gimbiya Zayana, muryarsa a nutsuwa yake furta wa Ayat... “Bari na koma ga ƴan'uwanki kafin na dawo gare ki...” Sarki ya kalli Zayana, ya tambaye ta game da nata karatun. Zayana ta yi shiru, tana wasa da zoban hannunta cikin ko-oho.. Da Sarki ya kalli Malam Mahmud, “me zaka iya cewa ga me da Zayana?” Malam Mahmud ba tare da ya kalli idon Zayana ba, balle ya damu da kwarjininta ko matsayinta.. Ya fara ƙiƙƙina, murya tana rawa.. "Ranka ya daɗe... a gafarce ni. Gimbiya Zayana ko izu biyu ba ta kai ba. Idan na je koyar da ita, wulaƙanta ni take yi ta kore ni, har tana cewa ba ta son sake ganina." Sarki ya ji wani zafi ya ziyarci zuciyarsa. Ya fara mata faɗa mai ratsa jiki, yana tuna irin taurin kan mahaifiyarta da ya shafi rayuwar Zayana... “Zayana! Har yanzu baki gane darajar abin da kike yi ba? Al-Kur’ani ake magana, kalmar Ubangiji! Ke kuma kina raina malaminki, kina kore shi kamar bawa? Wannan wace irin tarbiyya ce?” Zayana ta ɗaga kai cikin izzah, idonta babu ko ɗigon nadama.. Sarki ya cigaba, “Na ba ki malamai, na ba ki lokaci, na ba ki duk abin da ’ya mace za ta nema amma ke kina zaɓar girman kai akan ilimi! Kina son ki zama me? Sarauniya marar addini?” Nan take Zayana ta yi dariyar raini, ta matso gaba kaɗan.. “Abba, ka daina min wannan wa’azin. Ba kai ne ke zaune a zuciyata ba, don haka ba ka san abin da nake ji ba.” Sarki ya harara ta, muryarsa ta ƙara tsananta. Ya ce, “Ke fa ’yata ce! Zan gyara ki ko kin so ko ba ki so! Addini ba zaɓi ba ne a wannan fadar!” Zayana ta ɗaga hannu alamar dakatar da shi, muryarta mai sanyi amma kalmomin suna yankar zuciya... Ta ce “Gyara? Kai fa kana ƙoƙarin mallaka ne, ba tarbiyya ba. Kana son mu zama yadda kake so, ba yadda muke ba.” Sarki ya daki ƙasa da ƙafa cikin ɓacin rai tare da faɗin “Zayana! Ki kula da bakinki! Ina magana da ke a matsayin uba da sarki!” Ta kalleshi kai tsaye, ba tare da tsoro na, “Ni kuma ina sauraronka ne a matsayin mutum, ba gunki ba. Idan tarbiyya ta tilas ce, to ka sani zuciya ba a tilasta mata gaskiya.” Shiru ya sauƙa na ɗan lokaci... Sarki ya yi kamar zai sake magana. Sai Zayana ta ƙara da murya mai kaifi.. “Za ka iya min hukunci, sannan ka iya yi mun tsawa, amma ba za ka taɓa sa ni in zama abin da ban yarda da shi ba.” Nan take ta juya, ta ɗaga habarta cikin izzah. “Na gaji da zaman fadar nan...” Ta fice daga fadar ba tare da waiwaya ba. Tana takun gadara, ta bar kowa cikin mamakin rashin tarbiyyarta. Sarki ya tsaya cak, kalamanta suna maimaituwa a kansa kamar sara.. Ayat ta kalli bayan Zayana, ranta yana suya. Ta ji zafi yadda Zayana ta wulaƙanta mahaifinsu a gaban malamai. A ranta take cewa, "Zayana, akwai ranar da za ki san kuskurenki." Amma sarki ya danne tasa damuwar ya kalli Maayah, wadda hankalinta yake wani wajen... Tun farko ya lura hankalinta ba ya nan gaba ɗaya. Kamar akwai wani abu mai nauyi da ke damunta. Cikin murya mai ɗan tsauri.. "Ke kuma fa? Ko ke ma rashin kunyar za ki tsaya min?" Sarki ya tambayi Maayah. Maayah ta girgiza kai a hankali. Ta ɗago idonta ta kalle shi, murya a sanyaye ta furta. "Duk lalacewar tarbiyyata, ba zan yi musayar yawu da kai ba, Abul.... Ko da naman jikinmu kake yankewa kullum, hakan ba zai sa mu ƙi ka a matsayin uba ba.” Sarki ya ji sanyi a ransa, "Allah ya miki albarka ƴata. Yanzu ke kin haddace?" Maayah ta gyara zama, ta ce cikin ƙwarin gwiwa, "Abul, ban haddace duka ba, amma na kusa... domin yanzu haka ina Suratul Musa." 😨😨😨!!! Fadar ta ɗauki shiru. Malamai suka zaro ido, Sarki ya daskare... Ayat, duk da baƙin cikin Zayana da ke ranta, ta kasa riƙe dariya, sai da ta tintsire da dariya har sautin na fita sosai, rabo da a ji Ayat tayi irin wannan dariyar tin da ake da ita, ba'a taɓa ji ba, ba ita ba hatta sauran ma gabaɗayan su.... Yumna ta kalli Maayah cikin mamaki, "Aunty Maayah, Suratul Musa kuma? A ina take a Alkur'ani?" Maayah ta ɗanyi tsuru-tsuru, ganin yadda kowa ya zuba mata ido. Ta shafa goshinta cikin wayancewa da murmushin jin kunya... "Wayyo! Na manta ne... kuyi haƙuri. Wai zan ce Suratul Isa ne sai nace Musa. Yauwa, ina Suratul Isabul Maryama." A wannan karon ma, malamai suka kalli juna suna murmushin tausayi da dariya. Sun gane cewa Maayah ba ta ma san sunayen surorin ba, balle ta san karatun. Daga Suratul Musa zuwa Suratul Isabul Maryama duk ƙage ne irin na Maayah don ta nuna tana karatu... Sarki ya sauƙe ajiyar zuciya, yana girgiza kai. Ya gano cewa yayin da Yumna da Ayat suke can cikin hadda, Maayah tana can tana Suratul Musa a duniyar tunaninta.... *GASKIYA IDAN HAR KUNA SONA KUMA KUNA SON NEXT PAGE A YAU, TO KU NUNA MUN BAJINTA SOSAI...MORE LIKE AKAN PAGE ƊIN DA COMMENTS..* *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣2️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Sarki ya ɗaga hannu, "Za ku iya tafiya, Allah ya muku albarka. Zayana kuma... Allah ya shirye ta." ​Maayah ta fita tana rarraba ido, tana jin daɗin yadda ta wayance, a tunaninta ta ba da amsa daidai... yayin da Ayat take tafiya tana danne dariyarta, Yumna kuma tana satar kallon Sheikh Shureim kafin ta fice daga fadar... ​Bayan ficewarsu, fadar ta dawo shiru. Sarki ya kalli Malam Mubarak da Sheikh Shureim.. ​"Ina son ku haɗa kai," in ji Sarki. "Tunda Ayat da Yumna duka sun kammala hadda, ina son walimar nan ta zama abin koyi a duk faɗin ƙasar nan. Ina son a raba kyaututtuka ga marasa ƙarfi, kuma a gayyato manyan malamai su shaida wannan nasara." ​Malam Mubarak ya jinjina kai, "Ranka ya daɗe, wannan babban ra'ayi ne. Za mu tsara yadda za a yi gasar karatun a ranar, domin kowa ya ga irin ƙoƙarin da suka yi." ​Sheikh Shureim, wanda fuskarsa ke nuna natsuwa, ya ƙara da cewa, "Zan fara tsara tsarin jadawalin taron, tare da zaɓar ayoyin da za su karanta waɗanda za su ratsa zuciyar jama'a. Wannan taro zai zama haske ga masarautar nan." ​Bayan malamai sun gama bayanan su, Sarki ya yi shiru na ɗan lokaci, yana tunanin Maayah. Maganar Suratul Musa ta nuna masa cewa Maayah ba ta san komai ba game da karatun da take ikirarin yi a makaranta.. ​"Akwai matsala," Sarki ya faɗa ƙasa-ƙasa. "Maayah tana ɓata lokacinta ne. Kuma wannan rashin tarbiyyar ta Zayana, ba zan bar ta ta shafi Maayah ba." ​Nan take Sarki ya ƙira babban hafsan hadimansa.. ​"Maza ku shirya motoci ku tafi makarantar su Maayah. Ina son ganin Principal da kuma malamin ajinsu, a nan fada yanzun nan. Ina son jin hakikanin gaskiyar abin da Maayah take yi a makaranta, domin ba na yarda da sakamakon da ake kawo min na first class.." ​Hafsan hadiman ya duƙa, "An gama Ranka ya daɗe." ​Cikin ƙanƙanin lokaci, jerin gwano na motocin fada suka tashi da gudu zuwa makarantar, wanda hakan zai zama babban tashin hankali ga Principal... ✨✨ Babban Hadimin ya wuce kai tsaye zuwa ofishin Principal ba tare da neman izini ba. Principal yana zaune yana lissafin kudin da yake samu na gyara sakamakon jarrabawa, ya ga mutane sun daka masa tsawa.. ​"Sarki yana ƙiran ka yanzun nan a fada!" In ji Hafsan... "Kai da malamin dake koyar da ajin Gimbiya Maayah..." ​Principal ya shiga in-ina, zufa ta fara keto masa duk da sanyin AC dake ofishin. "Lafiya... lafiya dai ko? Ko wani abin ne ya samu Gimbiya?" Ya san cewa idan asirinsa na ba ta First Class na ƙarya ya tonu, to kashinsa ya bushe. ​A ɗayan ɓangaren kuma, Uncle Jalal yana cikin aji, yana gyara wasu takardu. Hadimin ya iske shi ya gaya masa saƙon Sarki. Sabanin Principal, ba tare da ya firgita ba, ya gyara kwalar rigarsa, ya rufe jakarsa cikin natsuwa... ​"Madalla," Jalal ya faɗa cikin murya mai kwarjini. "Dama akwai maganganun da ya kamata a ce Sarki ya ji su tun can baya." ​Principal dake tsaye a bayansa yana rawar jiki ya yi masa kallon lallai Jalal zai kaimu ya baro mu, amma Jalal ko kallo bai nuna yana jin tsoro ba. ​Yayin da ake jiran isowar su Uncle Jalal, Malam Mubarak da Sheikh Shureim sun fito zuwa wajen fadar, inda suka zauna a karkashin wata inuwar bishiyar flowers don tattauna maganar walimar.. ​Malam Mubarak ya dube Sheikh Shureim da murmushi, "Sheikh, lallai Gimbiya Yumna ta samu malami nagari. Natsuwar da ta nuna a fada yau abin sha'awa ne." ​Sheikh Shureim ya sunkuyar da kansa, muryarsa cike da girmamawa. "Duk godiya ta tabbata ga Allah. Amma maganar gaskiya, kalaman Gimbiya Ayat sun ba ni mamaki. Burinta na zama sojan sama ba ƙaramin abu ba ne. Shin kana tunanin Sarki zai amince?" ​Malam Mubarak ya yi ajiyar zuciya. "Ayat mace ce mai zurfin ciki. Ta daɗe tana karance-karancen littattafan bincike da dabarun tsaro... Ni kaina na san cewa ranta ba ya kan likitancin nan, sai dai kawai tana biyan burin mahaifinta ne. Amma yanzu da ta fito fili, ina jin za a yi gumurzu a masarautar nan." ​Sheikh Shureim ya jinjina kai, "Allah ya tabbatar da alheri. Amma batun walima, ina son mu tsara yadda su biyun za su fito su yi tilawa a gaban kowa, domin a ga banbancin dake tsakanin hasken Alkur'ani da duhun jahilci, musamman ga sauran 'yan uwansu." ​Malam Mubarak ya amince, "Hakan ya yi. Bari mu fara rubuta sunayen manyan malamai da za mu gayyata kafin taron." Maayah tana can sashenta, duk ta fita a hayyacinta. Jin cewa an je kiran Principal da Uncle Jalal ya sa ta san asirinta ya kusa tonuwa. Ta lallaɓa ta koma sashen fadar sarki kafin su iso ta laɓe a bayan labulen, Zuciyarta tana dukan uku-uku, tana jin inama Uncle Jalal bai taɓa zama malamin su ba... Can sai ga motocin sun faka, aka shigo da su.. Principal yana taku yana tanga-tanga, jikinsa har rawa yake yi, yayin da Uncle Jalal yake tafiya cikin natsuwa da kwarjini, kai kace shi ne mai masarautar... Lokacin shima Sarki ya fito ya zauna akan karagarsa, fuskarsa ba annuri.. "Principal, na ƙira ka ne domin in ji dalilin da ya sa kake yaudarata da sakamakon ƙarya na Gimbiya Maayah." Principal ya zube a ƙasa, "Ranka ya daɗe... kuskure ne... muna dai ƙoƙarin ƙarfafa mata gwiwa ne..." Sarki ya dakatar da shi da hannu, ya kalli Uncle Jalal.. "Kai ne malamin ajinsu, ko? Faɗa min gaskiya, yaya Gimbiya take a karatu?" Uncle Jalal ya gyara tsayuwa, ba tare da ya duƙa ba... "Ranka ya daɗe, magana ta gaskiya ita ce.. Gimbiya Maayah ba ta san komai ba game da karatun da nake koyarwa. Ba ta yin rubutu, ba ta karatu, kuma tana tunanin sarautarta za ta sayi ilimi. Sakamakon da kake gani na ta ɗaya, duka na bogi ne. Maayah tana matakin 'yan Nursery ne a fannin ilimi." Principal ya so yin magana, amma Jalal ya cigaba.. "Hasali ma, na zo ne da wasu littattafanta don ka gani da idonka. Wannan shi ne abin da ake kira cin mutuncin ilimi a makarantarka." Sarki ya karɓi littattafan da Jalal ya miƙa masa. Ganin rubutun Maayah ya sa Sarki ya fusata. Ya buga hannunsa a hannun kujerarsa, "Ina Maayah take?! Maza a fito min ita yanzun nan!" Maayah dake laɓe ta ji ƙafafunta sun ɗauki karkata. Ta san idan ta fito yanzu, kashinta ya bushe. Ta fara kuka a hankali a bayan labule, tana tsinewa ranar da Uncle Jalal ya fara shiga ajinsu... ✨✨✨ A ɓangare guda kuma, Ayat ta kasa samun nutsuwa akan ganin yadda Zayana ta ci mutuncin mahaifinsu...daga part ɗinta ta fito zata fita. Ta sa aka kawo mata tsararren dokinta wanda ya sha kwalliya da kayan ado masu tsada... Masu tsaro suka dakatar da ita ganin bata juma da shigowa ba kuma za ta ƙara fita... Ba ta tsaya sauraronsu ba ta nufe su da dokin tana shirin bi ta kansu.. da gudu suka matsa mata tare da faɗin "zan je wurin sarki..." Da ga nan ta nufi sashen Zayana akan dokinta... Masu tsaron sashen Zayana ne suka buɗe mata ganin Gimbiya ce. Ayat ta shiga falon Zayana cikin takun fushi, mayafin fuskarta yana kadawa... Cikin ɗaga murya ta furta. "Ina Zayana take?" Wata daga cikin bayin dake goge falon cikin kunfar baki ta ce, "Haba Gimbiya, ai kya girmama sunan nata ko? Babbar gimbiya ce fa..." Ayat ta watsa mata kallon raini, "Ban ga dama ba! Duk wanda ba ya mutunta mahaifina, to shima babu sauran mutunci a idona. Kuma ki kiyaye ni, kafin in yanke miki harshe! Ba wurinki nazo ba, wawaye kawai waɗanda ku ma ba'a ɗauke ku mutane ba." Mimi ta sauƙo daga bene tana kallon Ayat cikin idanun nan nata na kyanwa... "Ke mai rufe fuska! Me kika zo yi mana? Ba ma sonki, ki bar mana fadar mu!" Ayat ta tsaya dambar tana kallon yarinyar, sannan ta furta. "Ai kuwa kun mutu da ni! Domin wannan fadar mahaifina ne, ba wai gidan agolar masarauta ba." Ayat ta dakata tana jin takaicin amsar da ta bawa Mimi domin tana ganin girmanta ya zube da ta tsaya biye wa ƙaramar yarinya...tana cikin tunani sai ta ji.. Mimi ta ce cikin muryar yara "Ƙarya kike yi! Masarautar mu ce!" Ayat ta duƙa har matakin idon yarinyar... Ba tare da wata-wata ba, ta ɗauki almakashin dake gefen table ta yanke tulin gashin Mimi mai launin ruwan ƙasa, ta mika mata a hannu... "Gashi nan, ki kai wa mahaifiyarki kice ni na bayar." An raba tsakiyar gashin biyu, rabin gashi a hannun Mimi, sai na kanta da ya zamo short hair.. Mimi ta fashe da kuka mai sauti, "Wayyo gashina! Mommy! Gashina ya tafi!" Zayana ta sauƙo bene a guje, idanunta sun yi jawur saboda bacin rai....tin farkon shigowarta ta sani already.. Cikin ɗaga murya tana daka wa Ayat tsawa... "Stop it! What is wrong with you?!" ta kai wa Ayat wani zafafan mari... Ayat ta dafe kuncinta, sannan cikin zafi ta mayar mata da nata marin, har sau biyu.... Cikin fashin murya Zayana ta furta, "Ni kika mara? You slapped me?!" Ayat ta ce, "Ni ɗin gunki ce da zan tsaya ki mare ni? Idan kin saba dukan bayi, to kinyi kuskuren taɓa jinin sarki!" Zayana ta fara magana da hausa dake gauraye da turanci cikin raunin lafazi, dake ba ta wani kware sosai a Hausa ba... "You are nothing! Ke ba komai bace! Mahaifina ma tsorona yake yi, balle ke!" Ayat ta ce, "Mahaifinki ba tsoronki yake ba, yana kyaleki ne don girman kansa! Amma ki sani, duk wata izzah da kike takama da ita, a karkashin inuwar sarautarsa take. Amma yau kin nuna cewa baki da tarbiyya, baki da asali, kuma baki da godiyar Allah!" Cikin fusata Zayana ta daka tsawa "Shut up! You have no right to come into my house and........" Ayat ta katse ta da kakkausan murya, "I have every right! Wannan gidan mahaifina ne. Kuma bari kiji, rashin kunyar da kika yi masa a fada yau, ita ce ta karshe. Idan kika sake wulaƙanta shi, to ba zan tsaya a gashin 'yarki ba, zan ruguza muku dukkan izzarku! Ke baturiya ce a jini, amma kin rasa ko da ɗan mutuncin turawan ma, kin koma tamkar dabba mai cin naman wanda ya rene ta!" Zayana tana huci ta ce, "Zan ga abin da zaki iya yi..." Ayat ta ce, "Kin riga kin gani! Ga gashin 'yarki a ƙasa, ga kuma marin fuskarki. Wannan gargadi ne na farko. Next time, it will be worse. Ki kiyaye mahaifina!" Ayat ta juya cikin takun alfarma, ta bar Zayana tana tsaye tana karkarwa saboda tsananin fushi, yayin da bayin falon suka yi tsuru-tsuru suna kallon ikon Allah... ✨✨ A can fada kuwa, Hadimin da aka aika ya ƙira Maayah ne ya dawo, ya sanar da ba ta nan, Maayah jin haka yasa ta fito daga bayan labule, fuskarta duk ta jike da hawaye, idanunta sun yi jawur. Ta tsaya tana karkarwa, sannan ta wurga wa Uncle Jalal wata uwar harara mai cike da kiyayya... Uncle Jalal, maimakon ya fusata, sai ya saki wani ƙasaitaccen murmushi, yana kallonta kamar yadda malami yake kallon ɗalibi waton kallon shashasha da asirinsa ya tonu... Sarki ya kalleta ya ce, "wato laɓe kike mana ko? Me ya sa ba ki koma sashenki ba?..." Maayah tayi shiru kanta a sunkuye... Cikin muryar takaici Sarki ya kuma cewa, "Maayah, wannan ƙwaƙwalwar takin ba irin ta mahaifiyarki bace. Ke kin fita daban! Duba irin rubutunki, duba irin yaudarar da kuke yi min da wannan Principal ɗin." Daidai lokacin, Master Ibrahim shugaban tsaro na musamman ya shigo fadar cikin takunsa na jarumta... Ya gaishe da Sarki cikin girmamawa... Sannan ya furta "Ranka ya daɗe ka aika na zo..." Sarki ya dubi Ibrahim sannan ya ce, "Master Ibrahim, yanzu nake son ka je ka koya wa Zayana hankali. Ka hukunta ta yadda ya dace, sannan ka tafi da ita ka kulle ta a Dark Room No. 2 na tsaro. Ba na son jin wani bayani har sai ta san darajar mahaifinta." Master Ibrahim ya ji zuciyarsa ta buga. Ya san ɗakin duhu na biyu, ɗaki ne da ko ɓera aka kulle a ciki sai ya firgita, balle Zayana mai izzah... Ya san kowa yana tsoron mahaifiyarta, amma umarnin Sarki ya fi karfin kowa.. Master Ibrahim ya ce, "An gama, Ranka ya daɗe." Ya juya jiki a sanyaye, yana tunanin yadda zai fuskanci Zayana wadda kowa ya san ba ta da mutunci.. Bayan ficewar Master Ibrahim, Sarki ya mayar da hankalinsa kan Maayah da Uncle Jalal.. "Ke kuma Maayah, tunda kin ce kina Suratul Musa, kuma kina Suratul Isabul Maryama, yanzu za ki nuna mana abin da kika sani... Malam Jalal, ina son ka ba ta jarrabawa a nan gaba na yanzun nan. Idan har ta kasa amsawa, to ke ma hukuncinki yana jiran ki." Maayah ta ƙara fashewa da kuka, tana kallon Uncle Jalal kamar tana roƙonsa da ido, amma Jalal ya riga ya buɗe littafinsa yana neman tambayar da zai wanke mata lissafi... Sarki ya gyara zama, fuskarsa cike da ɓacin rai amma kuma yana son ya tabbatar da abin da Uncle Jalal ya faɗa... Ya kalli Uncle Jalal ya jinjina masa kai alamar ya fara... Cikin muryarsa mai natsuwa dake cike da izgilanci ya fara... "To Gimbiya Maayah, bari mu fara da abin da kika sani a fannin ilimin addini tukunna." Maayah ta tsaya tana karkarwa, hawaye suna ɗigowa daga idanunta, tana kallon Uncle Jalal cikin kiyayya... "Faɗa mana, guda nawa ne rukunnan Musulunci? Kuma rukunin farko menene shi?" Maayah ta goge hancinta, ta kalli Sarki sannan ta kalli Uncle Jalal. Ta yi shiru na kusan minti biyu, kafin can ta buɗe baki... "Rukunnan Musulunci ai... ai guda talatin ne!" Duk hadiman dake wurin suka kalli juna. Sarki ya dafe goshi, yayin da Uncle Jalal ya ɗanyi murmushin nan nasa na gefen baki.. Uncle Jalal ya ce, "Talatin? To madalla. To gaya mana ko guda daya a ciki." Maayah cikin kuka ta ce, "Eh mana! Akwai rukunin yin rubutu, da rukunin zuwa makaranta, da rukunin cin abinci... sannan kuma rukunin farko shi ne yin Biyayya ga Gimbiya'!" Sarki ya kasa cewa uffan, ran sa na kan ɓaci matuƙa. Uncle Jalal bai tsaya nan ba, ya buɗe littafinta na makaranta wanda babu komai a ciki sai zanen furanni da rubutun yara... Ya ce, "To bar wannan. A darasin lissafi na Maths, idan aka ce ki lissafo 10 + 10 nawa ne?" Maayah ta fara ƙirga yatsun hannunta, ta ƙirga ta ƙirga har ta kai karshe, ta kasa... Ganin Sarki yana kallonta ya sa ta ƙara ruɗe wa... "Ai... ai goma sha tara ne! Idan aka cire ɗaya kuɗin motar da zan ba bodyguards ɗina, sai ya zama goma sha tara!" Sarki ya kasa daurewa, ya miƙe tsaye daga kan karagarsa. Principal dake gefe ya ƙara dukunkuyewa saboda tsoro... Sarki ya ce, "Wannan wane irin hauka ne Maayah? Wannan shi ne abin da kika iya? Wannan shi ne first class ɗin da kike taƙama da shi? Kin mayar da kanki abin dariya a gaban kowa!" Maayah ta durƙusa ƙasa tana kuka sosai... "Abul, wallahi shi ne! Shi ne Uncle Jalal yake koya mana haka a aji! Shi ne ya ce 10 + 10 goma sha tara ne!" Uncle Jalal ya kalli Sarki, ya girgiza kai kawai... "Ranka ya daɗe, ka ga irin dalibar da kake da ita. Ba jahilci kadai ne ke damunta ba, har da son ƙago ƙarya don kare kanta." Sarki ya nuna Maayah da yatsa.. "Daga yau, babu wani sakamakon makaranta da zan ƙara amincewa dashi. Kuma ke, Uncle Jalal zai kasance malamin ki na gida wato Home Tutor, kuma za ki cigaba da zuwa makaranta.... Duk inda kike zai riƙa biye dake har sai kin san me kike yi. Idan kuma baki canza ba, to ke ma Dark Room No. 2 zaki haɗu da Zayana!" Maayah ta ji kamar duniyar ta ruguje mata. Tunanin cewa Uncle Jalal ne zai riƙa biye da ita har gida ya fi mata zafi fiye da komai. Ta kalli Uncle Jalal, shi kuma ya sakar mata wani kallo dake nufin... "Yanzu aka fara wasan, Gimbiya." ✨✨✨ Master Ibrahim ya isa sashen Zayana tare da wasu zaratan sojoji guda hudu. A kofar shiga, ya tarar da bayin Zayana suna ta magana ƙasa-ƙasa, bayan ya shiga babban falonta ya tarar da Mimi zaune a kasa tana faman taɓa gajeren gashin da Ayat ta yanke mata, tana ihu... Cikin muryar soja Master Ibrahim ya furta "Gimbiya Zayana! Kina ina? Umarni ne daga Sarki, kina bukatar biyo mu yanzu zuwa ɗakin tsaro." Zayana dake kan dinning zaune ta kifa kanta akan table tana tunanin irin hukuncin da za ta ɗauka akan Ayat... Jin muryar Master ya sa ta ɗago tare da fito falon, fuskarta yayi jajur saboda marin da Ayat ta mata, abunka da baturen mutum... ganin yadda Master Ibrahim ya yi mata magana ya sa ta ƙara harzuƙa... "Who do you think you are? Ibrahim, ka fita daga nan kafin in sa a cire maka wannan kakin sojan naka! You have no right to enter my private section!" Master Ibrahim ya ce, "Gimbiya, kiyi hakuri ki biyo mu cikin ruwan sanyi. Umarnin Sarki ne, kuma kin san ba a musa masa. Kin wulakanta shi a fada, kuma yanzu lokacin hukunci ya yi." Zayana ta kalli Master Ibrahim da waɗannan cat eyes ɗinta, ta ɗauki wata kwalbar turare mai tsada ta kwada masa, amma cikin zafin nama ya kauce... Ta cigaba da magana "I am not going anywhere! Idan ka taɓa ni, Mom ɗina za ta sa a datse maka hannaye!" Ganin ba za ta bi shi ba, ya ɗaure fuska. Ya san idan ya tsaya rarrashi, lokaci zai ƙure.. "Ina neman gafararki Gimbiya, amma aikina zan yi." Cikin zafin nama, ya nufi Zayana.... Ta fara kai masa naushi da yakushi, tana ihu tana kiran sunan mahaifiyarta. Amma Master Ibrahim ya kama hannayenta ya murde su ta baya cikin kwarewa, sannan ya sa mata ankwa... Haka Zayana take ta zagi da maganganu.. "Let me go! You filthy soldier! I will kill you! Mimi, call your grandmother!" Sojojin suka kewaye ta yayin da Master Ibrahim yake jan ta da karfi. Mimi ta biyo su a baya tana kuka tana jifan sojojin da kayan wasanta. Bayin sashen kuwa kowa ya laɓe, suna kallon yadda ake jan babbar Gimbiya kamar kura... Suna isa kofar Dark Room No. 2, Master Ibrahim ya bude kofar dake fitar da wani irin sanyi da duhu mai ban tsoro.. Ya ce, "Gimbiya, anan zaki zauna har sai ranka ya daɗe ya bada umarnin fito dake. Kiyi tunani akan abinda kika yiwa mahaifinki." Ya tura ta ciki, ya rufe kofar da wani babban kwaɗo. Sautin kukanta da dukan kofar da take yi ya gauraye wajen, amma Master Ibrahim ya juya abinsa cikin sanyin jiki, yana addu'ar kada mahaifiyar Zayana ta bayyana a cikin masarautar nan.... ✨✨✨ Ganin Sarki ya fi ce daga fadar yasa Maayah ta tashi daga ƙasa inda take kuka, ta goge fuskarta, ta gyara mayafinta tana wani yatsine fuska. Ta kalli Uncle Jalal daga sama har kasa, sannan ta koma kan wata kujera ta alfarma ta zauna tana jijjiga ƙafa... Cikin ƙasaita ta furta. "To Malam Jalal, ko ince Uncle? Ai kaga nan ba makaranta bace ko? Nan gidan ubana ne, kuma ni ce Gimbiya Maayah. Don haka, kada ka sa ran zan raba kaina da ƙasa ina baka amsa kamar yadda nake yi a aji." Uncle Jalal ya ajiye littafinsa a hankali, ya zura hannayensa a aljihu yana kallon yadda yarinyar ke kokarin nuna isa, alhalin ko 10+10 ta kasa sani.. Yana murmushi ya furta, "Zama ko tsayuwa ba shi ne zai baki ilimi ba, Maayah....Kuma idan har baki manta ba, Abul dinki ne ya ce in zama inuwar ki har sai kin san me kike yi. Don haka, mu fara darasinmu na yau." Uncle Jalal ya yanke shawarar saukowa matakin kwakwalwarta domin ya ga iyakarta.. Ya ce, "To, tunda ke 'yar boko ce, gaya min, Daga ina ruwan sama yake fitowa? Kuma me yake kawo shi?" Maayah ta danyi shiru, ta kalli silin din fadar, sannan ta taɓe baki cikin rashin sanin komai da kuma nuna ilimi... "Wannan ai tambayar yara ce. Ruwan sama a tankin gidanmu yake fitowa! Idan aka bude fanfo a sama, shi yasa yake zuwa. Kuma idan hadimai sun manta basu rufe ba, sai ayi ta ruwa kenan har sai ya cinye ƙananun flowowi 😏...." Ita kanta bata sani ba amma ta faɗi haka ne don ta ƙular da shi... Uncle Jalal ya runtse idonsa na dakika biyar, yana neman hakurin da zai cigaba da wannan zama. Ya ce, "To, bar batun tankin ruwa. Gaya min, ina ne babban birnin kasar Saudiyya...?" Maayah ta hure iska daga bakinta, tana wasa da zoban hannunta... "Saudiyya kuma? Ai tana nan, ƙasar su mahaifiyar Ayat da Ching Ching ne... Na taɓa jin ana cewa can ne ake sayo turaren wuta, yanzu haka ƙamshin turaren da kake ji a fadar nan, na Saudiyya ce, to Saudiyya tana karkashin wannan masarautar tamu ne. Birnin kuma sunansa Birnin Turare..." Wannan karon kam ta zaƙe, tsakaninta da Allah take gaya masa gaskiyar saudiyyar da ya tambaye ta.. Uncle Jalal ya matso kusa da ita, ya kura mata ido yadda ta ji jikinta ya danyi sanyi, amma ta dake ta ƙara gimtse fuska... A hankali ya furta "Maayah, kin san me nake gani idan ina kallon kwayar idonki? Ba girman kai nake gani ba, wani ƙaton duhu nake gani na jahilci wanda kike son rufe shi da gadara. Amma ki sani, muddin ina nan, sai na fasa wannan duhun. Yau zan barki ki tafi ki huta, amma gobe... gobe zamu fara da koyon haruffan 'A, B, C' da kuma 'Alif, Ba, Ta'. Kuma za ki rubuta su a gaban kowa...." Maayah ta miƙe tsaye cikin fushi, "Ni ce zan rubuta Alif Ba? Wallahi ka da ka kuskura! Ni ba 'yar Nursery bace! Kuma idan ka matsa min, zan ce wa Abul duka na kake yi!" Uncle Jalal ya yi murmushi kawai, ya juya ya bar falon, ya bar ta da huci tana buga kafa a ƙasa... ✨ Uncle Jalal ya nemi izinin ganin Sarki domin ya sanar da shi tafiyarsa. Sarki ya ba da izinin ya same shi har can sashensa na musamman. Jalal ya shiga, ya zauna a babban falon Sarki, falon da aka ƙawata shi da duk wata daular duniya.. ​Ba jimawa, Sarki ya sauƙo daga saman bene, ya zauna fuskarsa cike da mutuntawa... ​Bayan gaisuwa, Uncle Jalal ya dubi Sarki cikin natsuwa ya ce.. ​"Ranka ya daɗe, zan wuce, amma kafin nan ina neman wata alfarma. Shawarwari ne akan Maayah, idan har ana son ta sauƙo da kanta ƙasa, to dole sai an kiyaye wasu abubuwa. A koda yaushe tana ganin kanta a sama ne saboda waɗannan zabga-zabgan mutanen da ke kewaye da ita... Motoci manya guda biyar ne ke rakata makaranta, kowa yana mata abin da take so, shi ya sa ba ta ganin kowa da mutunci." ​Ya gyara zama ya ci gaba.. "Alfarmar da nake nema ita ce, a kullum zan riƙa zuwa har masarautar nan na ɗauke ta mu tafi makaranta tare a motata. Sannan akwai lokutan da zan riƙa zuwa ina koyar da ita a gida. Kuma gaskiyar magana, dole sai an mata repeat ɗin aji, an dawo da ita baya. Tana SS3 amma koda rubutu ba ta iya ba? Idan kuma ta je jami'a fa?" ​Sarki ya jinjina kai, maganar ta ratsa shi... ​"Wannan batun naka gaskiya ne," in ji Sarki cikin damuwa.. "Mahaifiyarta ta dage ne akan sai an kai ƴarta makaranta domin ta yaƙi jahilci. Mahaifiyar Maayah a baya malamar jami'a ce dake ƙasar Mumbai, har ta samu lambobin yabo masu yawa a fannin ilimi. Ina jin shakkar ranar da za ta ga ƴarta a haka. Na yi mata alƙawarin zan kai mata Maayah hutu nan ba da jimawa ba, amma yanzu na fara karaya. Domin na tabbata idan na kaita a haka, mahaifiyar za ta binciki ƙwaƙwalwarta ta ga babu komai." ​Sarki ya kalli Jalal sannan ya furta "Shi ya sa yanzu, ko me kake buƙata, indai za ka dawo min da ƙwaƙwalwarta, to na amince. Ba ni da burin kaita jami'a yanzu, ina jiran ne ta kammala SSCE sai na musu aure gaba ɗaya, amma yanzu komai ya dawo baya... Jalaludden, zan ninka maka kuɗaɗen da ake baka a makaranta sau biyar don ka gyara ta. Za ka riƙa zuwa kana mata home lesson, sannan ka dage mata a makaranta. Idan ta ƙi ba ka haɗin kai, na ba ka izinin ka bulale min ita." ​Uncle Jalal ya girgiza kai cikin nuna rashin kwaɗayin abin duniya... ​"Zan yi iya ƙoƙarina Ranka ya daɗe. Amma ba na buƙatar kuɗin da za ka ƙara min don kawai kana so na gyara ƴarka. Nima ina so na gyara ta ne ta zama abin misali a fannin ilimin boko da na Arabic." ​Sarki ya yi murmushi, ya tambaye shi, "Daga ina kake? Wato kai ɗan ina ne?" ​Uncle Jalal ya amsa. "Ni ɗan Nigeria ne, daga yankin Borno State. Kuma a nan ina zaune ne a The Royal Palace Hotel..." (Wani babban hotel ne mai tsada da kwarjini a birnin Alhamra).. ​Daga nan, Uncle Jalal ya yi sallama da Sarki ya miƙe ya fice daga sashen, ya bar Sarki cikin tunanin yadda wannan malamin zai fara jujjuya Maayah.... GA TAMBAYA SHIN WANI SCENE NE YA FI BURGE KU? ZAYANA KO MAAYAH?.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣3️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan ya dawo daga masallacin dake can gefen babban filin fadarsa, iskar asuba mai sanyi tana bugun fuskarsa. Chief Onyx ya shigo babban falon inda ya tarar da Gely, PA ɗinsa kuma tsararriyar Robot mai basira, tana hidimar haɗa karin kumallo cikin natsuwa.. ​“Good morning, Boss,” Gely ta gaishe shi da muryarta mai sanyi da madaidaicin sauti. ​Chief ya amsa a nutse, ya zare agogonsa na alfarma ya ajiye, sannan ya tambaya, “Shin Ching-Ching ta tashi ta yi sallah?” ​Gely ta gyara tsayuwa, “Eh Boss, ta tashi ta yi sallah, amma ta koma bacci saboda yanayin sanyin safiyar.” ​Chief ya ɗan yamutsa fuska, ya bayyana asalin Boss ɗin nasa... “Jeki tashe ta yanzun nan. Yau za ta fara zuwa makarantar The Royal Valorant Academy... Bayan kin tashe ta, ki zo ki karɓi jakunkunanta da sabbin kayan makaranta da litattafan da na haɗa mata. Komai ya zama ready.” ​ ​Yana hawa saman ɗakinsa bai fi mintuna biyar ba, agogonsa mai tsadar gaske dake ɗauke da fasahar zamani ya fara girgiza a hannunsa. Gely ce ke kiransa ta na’urar sadarwa.. ​“Boss... akwai matsala. Ching-Ching ba ta da lafiya.” ​A ruɗe Chief ya sauƙo ƙasa, har yana kusa tuntuɓe a kan matakala. Ya garzaya zuwa ɗakin Ching-Ching, ya tarar da ita kwance, duk da sanyin A.C dake ratsa ɗakin, jikinta duk ya jike da gumin wahala.. ​“Mene ne ya faru da ita?” Chief ya tambayi Gely cikin murya dake nuna damuwa.. ​Gely ta duba bayanan dake cikin na’urarta ta lafiya, ta ce, “Na gama bincikar jikinta. Mararta ce ke mata ciwo sakamakon First Period da za ta fara. Yau ne karon farko da ta zama budurwa.” ​Chief ya zaro ido, a ɗan ruɗe... “Kina nufin... yanzu jini yana kan zuba mata ne?” ​Gely ta yi ɗan murmushi na inji. “Wannan ba abin damuwa ba ne Boss, dabi’ar kowace mace ce. Shekarunta sun kai yanzu. Abin da ake buƙata shi ne abin tare jinin don kada ta ɓata jikinta...” ​“Okay... Stay here!” Chief ya juya da sauri ya fita, ya shiga motarsa ya nufi babban shago cikin gaggawa.. ​ ​Bayan ya dawo, ya miƙa wa Gely wata baƙar leda. Gely ta buɗe, ta kalli abin ciki sannan ta kalli Chief da mamaki.. ​“Boss... wannan ai Pampers ne na jarirai, na tarewa yara kashi ne... Wancan kuma Pad ne na mata.” ​Chief ya shafa kansa cikin jin kunya. “Yanzu dai ya jikinta? Wancan kiyi amfani da wanda ya dace.” ​ ​Kafin Gely ta kai ga amsawa, sai suka ga Ching-Ching ta buɗe ido tana rarraba su... “Fitsari zan yi...” ta faɗa cikin murya mai rauni, ta miƙe ta shiga toilet... ​Shiru na ɗan lokaci... can kuma sai aka ji wani firgitaraccen ihu! “WAYYOOO!” ​Ta fito a guje tana ihu, fuskarta cike da firgici. Chief ya cafko ta da sauri kafin ta fice daga ɗakin, ta ƙanƙame shi tana kuka da ƙarfi.. ​“Wayyo Allah, Uncle! Na mutu na lalace! Jini! Jini! Wallahi na ji ciwo a ɗuwawu naaa! Wani ya soka min wuƙa ban sani ba!” ​Ta cigaba da kwarara surutai, tana ƙara matse Chief, fuskarta ta yi ja saboda tsoro. Chief Onyx wanda damuwa ta lulluɓe shi, sai da ya ji dariya na neman kufce masa saboda jin abin da ta faɗa.. ​“Yi shiru, babu wanda ya soke ki,” ya faɗa yana ƙoƙarin danne dariyarsa, yayin da yake shafa kanta don rarrashi. “Ƙaruwa kika yi, kin zama budurwa.” ​“A’a Uncle! Jini ne fa! Na mutu, kaga yadda yake zuba!” ta ƙara sa da ihu, tana ɓuya a ƙirjinsa. Bayan an gama wannan guje-guje na firgici, Chief Onyx ya samu nasarar dawo da Ching-Ching kan gado. Ya zauna a gefenta, ya sa hannunsa duka biyu ya kamo nata, yana kallon yadda take kuka tana shashsheka kamar wadda aka yi wa mutuwa... ​“Yi shiru na ce miki, babu wani abin tsoro,” Chief ya faɗa cikin muryar lallashi, yana ƙoƙarin danne dariyar da take taso masa duk lokacin da ta ambaci ciwon ɗuwawu... ​ ​Chief Onyx ya gyara zama, ya dube ta da idon gaske don ya yi amfani da damar ya ba ta ilimin zamantakewa, amma cikin sigar tsoratarwa irin ta manya... ​YA ce murya ƙasa-ƙasa “Saurara min nan Ching-Ching. Daga yau fa kin zama babbar mace, ba yarinya ba. Kuma ki buɗe kunnenki da kyau, daga yau, kada ki kuskura ki bar wani namiji ya taɓa ki. Ko hannunki namiji ya riƙe, to fa za ki iya ɗaukar ciki nan take!” ​Ching-Ching ta zaro ido, ta daina kukan lokaci guda. Ta kalli hannunta ta kalli na Chief dake riƙe da nata. ​Sai kuma ta turo baki ta ce, “Da gaske Uncle? Yanzu kenan zan iya haihuwa? Amma gaskiya ni bana son jinin nan, jini ne he kace wanda aka yanka akuya!” ​Ta ƙara sautin kukan, “Kaiii nifa ban yarda ba! Dole wani ne ya zo ya caka min wuƙa a wurin fitsarina don mugunta. Ko ma hala Gely ce ta soka min!” ​Gely, wadda ke tsaye kamar gunki a gefe, ta juya kanta zuwa ga Ching-Ching, idanunsa na Robot suna ba da hasken bayani, "Ni ban taɓa taɓa ki da wani abu mai kaifi ba, Shugaba Ching-Ching... Wannan tsari ne na halitta.” ​Ching-Ching ta harare ta duk da yanzu suna shiri, ta ce, “Rufe min baki! Ke dake da hannun ƙarfe ai ba kya jini. Ni dai Uncle kaji na gaya maka, wanda ya yi min wannan muguntar sai na rama...” ​ ​Chief Onyx ya girgiza kai, ya da fa kuncinsa yana kallon wannan dambarwar.. ​DAga bisani ya ce, “Ban da surutu. Sannan kuma tun da jinin nan ya zo, duk abin da kika yi na rashin jin magana, za a fara rubuta miki zunubi. Mala’iku sun shirya takarda yanzu...” ​Ching-Ching ta tsaya cak, ta yi tunani na daƙiƙa biyar. Sai kuma ta washe haƙora, ta matso kusa da Chief har tana gogar hancinsa... ​“To Uncle, tunda kace idan namiji ya taɓa ni zan yi ciki... yanzu kai ai namiji ne, kuma kana ta riƙe ni. Kenan yanzu zan haifi baby Chief?” ​Chief Onyx ya ji gabansa ya faɗi, ya ji kamar ya tashi ya gudu... “A’a! Ni... ni daban ne! Ni ai Uncle ɗinki ne.” ​Ta ce, “Hmm! Uncle ne ko baban baby ne? To ni dai gaskiya idan zan haihu, ba zan haifi baby boy ba, sai baby girl kamar niiii...” ​Chief ya tashi tsaye yana gumi, ya kalli Gely.. . “Gely, koya mata yadda za ta yi amfani da kayan da na kawo. Ni dai zan fita, kafin wannan yarinyar ta haukatani da maganganunta.” ​Yana fita, ya ji ihun Ching-Ching daga ciki.. “Uncle! Zo ka tafi da Pampers ɗinka, ni ba jaririya ba ce!”.. Washegari da komai ya lafa... Chief ya tambayi Gely game da school ɗinta tinda tana wannan yanayin... Gely ta sanar cewa "ba matsala zata iya zuwa, saboda da haka mata suke rayuwa a cikin jini kuma babu mai gane wa..." A lokacin ya sanar da a shirya ta.. Bayan wasu mintuna Ching Ching ta wankanta tayi brush... Tana zaune a gaban babban madubin dake dakinta, Gely ta gama baje basirarta na Robot. Ta gyara mata gashinta, ta yi masa wani irin lallausan design a gaba wanda ya fito da tsantsar kyan fuskarta. Ta saka mata kyakkyawan uniform ɗin The Royal Valorant Academy, riga fara mai dogon hannu, da tie dake wuyanta, sannan aka dora mata ɗan short riga mai kalar navy blue da ya tsaya dai-dai gwiwarta... A karshe, aka dora mata hular beret mai launin rigar din. Ching-Ching ta goya jakar makarantarta a baya, ta fito kyakkyawa kamar balarabiya, sai dai tana turo baki alamar ba ta saba da wannan shigar ba... Suna saukowa falon a jere ita da Gely, Chief Onyx ya dago kansa daga jaridar da yake karantawa. Ya tsaya turus, idonsa ya kasa ɗaukuwa daga kan Ching-Ching. Gaba daya kyan da tayi yanzu ya ninka na baya sau goma Duk da kyan da ta yi, abu daya ne ya sa Chief ya dafe kai....Tafiyarta. Ching-Ching ta fara takowa, amma kafafunta a ware suke, ba sa haɗuwa. Tana tafiyar ne kamar agwagwa, tana wani nishi-nishi... Cikin mamaki ya tambaye ta “Meye haka kuma? Wane irin tafiya ce wannan? Kin kakkarya ƙafafun ne?” Ching-Ching ta tsaya tana hararar sa daga baki har hanci, “Yooo! Baka ga abinda aka danna min a gaban mafitsara na bane? Taya zan iya tafiya normal kuma?” Chief ya ce, “Kowace mace idan tana cikin wannan yanayin ai tana sa Pad, kuma tana tafiyarta normal ba tare da kowa ya gane ba. Maza gyara tafiyar nan!” Tana turo baki ta ce, “A’a Uncle! Ni nawa daban ne, ƙarami ne ai! Kuma haka kawai sai in bari wurin ya yi ta ji min ciwo a cinyoyina? Ni dai haka zan tafi, idan kaga dama ma ka turo ni a wheel-chair!” Chief ya girgiza kai, ya san idan ya tsaya ja-inja da ita to ba za su bar gidan ba yau. “Muje to. Idan aka fara miki dariya a makarantar ai dole zaki gyara da kanki.” Ching-Ching ta kalli kanta a madubin falon, ta kalli rigar din dake iya gwiwarta, sai kuma ta danna tsalle ta dire... “Yanzu saboda Allah a haka zan fita tsargal-tsargal kamar arniya? Dubi rigar a iya gwiwa ta fa! Babu ko mayafi, gashina a fili? Anya Uncle ba kana so in shiga wuta ba ne?” Yana ƙoƙarin tura ta waje tare da faɗin “Muje makarantar zaki ga wasu ma babu hular, gashin ma a hargitse yake. Haka Uniform din yake, babu mayafi a ciki.” Ta ce, “Tabbb! Ni dai gaskiya Uncle kawai ka mayar da ni arniya. Idan na haɗu da mala’iku zan ce kai ne ka ba ni wannan kayan.” Haka suka fita suna dambarwa, tana tafiyarta ta agwagwa tana murguda baki. Suka shiga cikin wata zafafan bakar mota, Gely ta zauna a gefen drive wanda ya kasance bodyguard ne mai tuƙi, ita kuma tana lura da dukkan motsinsu.. A bayansu kuma, wasu zafafan bakaken motoci guda hudu ne shake da Bodyguards dake dauke da makamai suka mara musu baya. Ayarin motocin ya dauki hanyar makarantar dalar Amurka, inda kowa ke kallon wannan tafiya ta ban-mamaki... Ayarin motocin Chief Onyx ya tsaya kyam a kofar makarantar. Bodyguards suka fito da sauri suka shimfida Red Carpet.. Daliban makarantar, wadanda dukansu 'ya'yan sarakuna ne da attajirai, suka tsaya cirko-cirko suna jiran ganin wace Gimbiya ce za ta fito... Chief Onyx ya fito cikin taƙama, sannan ya miƙa hannu ya taimaka wa Ching-Ching ta fito... ta turo kafa ɗaya waje... sannan ɗayan ya biyo baya... nan take ta fara tafiyar nan tata ta Agwagwa, kafafu a ware, tana rarraba ido... Ganin yadda kyakkyawar yarinyar nan take tafiya kamar wadda ta koyo a gidan kaji, sai wasu gungun 'yan mata dalibai suka kwashe da dariya.. “Oh my God! Dubi tafiyarta! Is she a duck?” daya daga cikinsu ta fada tana nunawa.. Ching-Ching ta tsaya cak, ta murguda baki har ya kusa taɓa hancinta... “Uban wa kuke yi wa dariya? Kun taɓa ganin inda agwagwa ta saka riga da tie ne? To jini nake yi, taya zan haɗe ƙafa? Arna kawai!” Chief Onyx ya runtse ido, ya ji kamar ya nutse a ƙasa don kunya. Gely kuwa tana gefe tana daukar bayanan yadda bugun zuciyar Chief yake karuwa saboda ɓacin rai.. A daidai wannan lokacin, wani kyakkyawan matashi, Yarima Leonardo daga daular kasar Italiya, wanda ya ga abin da yake faruwa, ya taho da sauri don nuna Gentlemanliness... Yana zuwa, bai san asalin matsalar ba, ya ɗauka ko tawayar ƙafa take da shi. Ya miƙa hannu da sauri ya riƙo damtsen hannunta don ya taimaka mata ta daidaita tafiyar... “Easy, Princess. Let me help you...” Leonardo ya faɗa cikin muryarsa mai daɗi... Ching-Ching ta kalli hannunsa dake kan nata, sannan ta kalli Chief Onyx. Nan take idanunta suka zaro, ta fara tsalle tana ihu kamar wadda aka zare wa rai!... *“WAYYO UNCLE! KAGA NAMUJI YA TAƁA NI!.. NA SHIGA UKU, NA MUTU! UNCLE KAGA YA RIƘE MIN HANNU, ZAN YI CIKI! GOBE ZAN HAIHU!”* Leonardo ya saki hannunta kamar ya taɓa wuta, ya koma baya yana zare ido.. “What? No! I was just helping!” Ching-Ching ta je ta taɓe a bayan Chief Onyx da gudu tana kuka tana nuna Leonardo... “Mugu! Azzalumi! Kaga yadda yake kallo na? Uncle maza mu tafi asibiti a cire cikin nan tun bai girma ba! Shikenan na zama uwa ba tare da na gama karatu ba!” Chief ya juya ya kalli Leonardo da wani irin kallo na kisa. Kishi, kunya, da fushi suka haɗu suka yi masa dumu-dumu a zuciya.. Muryarsa tana rawa saboda bacin rai.. “Leonardo... idan baka ɓace daga nan ba yanzun nan, zan sa a rufe makarantar nan yau! Kuma ke ya kalli Ching-Ching... maza shiga ciki kafin in haɗiye ki!” Ching-Ching tana turo baki. cikin shagwaɓa ta ce, “Ba zan shiga ba! Taya zan shiga ina da juna-biyu? Uncle ka taɓa ganin inda mai ciki take zuwa aji ɗaya?” Masu kallo suka sake fashewa da dariya,. Chief Onyx ya cafko damtsenta ya fara jan ta zuwa cikin makarantar, tana tafiyar agwagwa tana kukan karyar cewa cikinta ya fara girma... Bayan wannan dambarwar ta waje, Chief Onyx ya rasa yadda zai yi. Ching-Ching ta ƙi zama, ta riƙe masa riga tana kuka tana cewa cikinta na ciwo tun bayan da Yarima Leonardo ya taɓa mata hannu.. Dole Chief Onyx, babban mutum mai kwarjini, ya zauna a kan wata ƴar ƙaramar kujerar ɗalibi a gefenta. Ya haɗe rai, idanunsa a waje kamar zai cinye kowa, yayin da sauran ɗaliban ajin kowanne ya rufe baki yana dariya ƙasa-ƙasa... Mr. Sterling wato malamin da yake koyar da ajin cikin rawar murya, "Uhm... Welcome, Chief. Please, we are about to start the lesson." Duk ajin ya yi tsit, banda mutum ɗaya, wato Ching-Ching.. Ta fara rarraba ido tana kallon kowa... "Uncle, kalli waccan yarinyar, gashinta kamar na dokinmu na gida. Ke, baki da mai ne? Kuma Uncle, kalli malamin nan, me ya sa kansa yake sheƙi kamar kwanon Gely? Ko shima robot ne?" Chief cikin raɗa yana daka mata tsawa, "Ching-Ching! Yi shiru! Kowa ya yi tsit ke ce kawai kike wannan surutun kamar an kunna rediyo!" Ching-Ching ta turo baki "Yoo! Taya zan yi shiru? Ai shi ma malamin nan surutu yake yi. Kuma nifa ba zan iya yin wannan rubutun ba, ciki gare ni fa! Uncle ka faɗa masa cewa mai juna-biyu hutu take yi, ba ta aiki!" Duk yadda Chief yake ƙoƙarin danne fushinsa, sai da ya kai bango. Musamman ma lokacin da Mr. Sterling ya tambayi ajin.. "Who can tell me the capital of France?" Ching-Ching ta ɗaga hannu tana tsalle, kafin ma malamin ya bata dama, ta fara.. "Capital of France? Ai na sani! Shi ne inda Uncle ya sayo min kayan wasa, sunan wurin Shoprite! Kuma ma, me ya sa kake tambayar mu? Kai baka sani ba ne?" Ajin ya kaure da dariya. Chief Onyx ya miƙe tsaye da sauri, fuskarsa ta yi ja wur. Ya cika ya yi fam kamar zai fashe.. "Ya isa! Na gaji! I'm done!" Ya juya ya kalli Gely dake tsaye a ƙofa. "Gely, ki tsaya a nan! Idan ta ƙara surutu ki rufe mata baki da tape! Ni kam na tafi kafin hawan jini ya kashe ni!" Chief ya fice a fusace, yana huci kamar zaki. Ching-Ching ta turo baki, ta bi bayansa da ihu.. "Uncle! Ka tafi ka bar ni da juna-biyun wani?..." Malamin ya kalle ta cikin bacin rai, "Ching-Ching, please sit down and write." Ching-Ching ta ce, "Ba zan rubuta ba! Rubutu ai zunubi ne ga wadda take da ciki a ranar farko. Kuma ma, wannan fensirin naku ba shi da daɗi, gara in riƙa tsara gashin Gely da shi!" Ta juya tana kallon wani ɗalibi a gefenta, "Kai kuma me kake kallo na? Ko kana so ka taɓa hannuna ne kai ma ka ba ni wani cikin?" Chief onyx kai tsaye babban office ɗin malaman da ake interview ya nufa... Yana shiga ya fara musu faɗa akan cewa sun shanya shi a washe, bayan sai anyi interview aka ba da ajin da ɗalibi zai shiga... Haƙuri suka shiga bashi sakamakon shine shugaban ƙasar gaba ɗaya.... Dan ma wasu lokuta yana da sauƙin kai... "Please Chief kayi haƙuri, principal ne bai iso ba, shi ya sa ka ga bamu neme ka ba..." Chief ya ce, "Oh daman zan zauna ne ina jiransa?..." Sai ga principal wanda ya iso ba da jima wa ba.. Haka ya shiga roƙon Chief.. "Please am so sorry Chief, pardon me please, nayi kuskure..." Chief ya fita tare da nufan class ɗin da aka shiga da Ching Ching na ƴan primary... Ya shiga ya damƙo hannunta cikin fushi, daga ita har malaman sun ɓata masa rai... Ya fara jan ta, Gely na biye da su a baya.. Chief Onyx ne ya shigo da Ching Ching babban office na makarantar, inda manyan malamai da shugabannin bangarori suka hallara. Wannan shi ne ranar farko da za a tantance ta, domin a san ajin da ya dace a saka ta.. Ching Ching na tsaye gefen Chief, tana jujjuya ido, tana washe baki kamar ba interview aka zo yi ba, gana ganinta zaka san cewa bata san komai ba..😌 Tana sanye da uniform ɗin makarantar cikin tsabta, amma idonta na kan kayan alatun da aka zuwa a office ɗin, ga wani tsararren ƙaton plasman... Aka ba su wurin zama... Shugaban makaranta ya fara da murmushi.. “Ching Ching, welcome. Don’t be nervous, okay?” Ching Ching cikin dariya da shagwaɓa ta ce, “Okay sir 😁 ni ba ma jin tsoro.” Malaman suka kalli juna suna murmushi.. An fara da tambayoyin Basic General Knowledge.. Teacher 1 ya tambaya.. “What is your full name?” Cikin tsalle ta furta “Ching Ching Onyx.” Chief onyx ya kalli malaman ya ce "Firdous Muhammad Nourdeen..." Malamin Yana dariya ya ce, "Eh mun gane, ga sunan natan a jikin allon mu, mu na so mu gwada ƙwaƙwalwarta ne... Sannan aka koma kan Ching-Ching.. “How old are you?” Ching Ching ta ce, “I am almost seventeen years old.” “How many continents do we have in the world?” Ching Ching ta ba da amsa, “Seven continents.” "Why do you want to join this school?..." Ta amsa cikin confidence “Because I love learning, and I want a place that will challenge my brain.” Malamai suka kalli juna, suna murmushi... ✨ Mathematics Question ⁉️ Malamin Maths ya matsa gaba, ya ɗauko biro. “If 3x + 5 = 20, what is the value of x?” Ching Ching bata ko yi tunani ba ta ce, “3x = 15, so x = 5.” Malamin ya miƙa mata marker.. Solve: 24 × 6 − 18 ÷ 3. Ching Ching ta kalli farin board sannan ta rubuta. 24 × 6 = 144 18 ÷ 3 = 6 144 − 6 = 138... Wani question again.. If x + 7 = 20, find x.. Ta rubuta “x = 13.” Ba tare da jinkiri ba... *English Language questions* English Teacher ya ce, “Make a sentence with the word confidence.” Ching Ching tana tsalle tana cakumar hannun Chief irin an bata tambaya mai sauƙi..ta furta “I answered all the questions with confidence.” Another question... “Change this sentence to past tense: She is going to school.” Ching Ching tana gatsine ta ce, “She went to school.” Malaman suka ɗaga gira cikin mamaki... 😮 *SCIENCE (Basic & Advanced)* Science Teacher ya ce, “What is photosynthesis?” Ching Ching ta amsa. “It is the process by which green plants make their own food using sunlight, carbon dioxide, and water.” Other question “What organ pumps blood in the human body?” Ta amsa cikin yanga... “The heart.” Question Mention two types of energy... Ta amsa da.. “Kinetic energy and potential energy.” *CHEMISTRY* Chemistry Teacher ya ba ta tambaya.. “What is the chemical symbol for water?” Ching Ching ta amsa da “H₂O.” Another question “What is an acid?” Ching Ching ta amsa “An acid is a substance that produces hydrogen ions in water.” Question What is an atom? Ching Ching ta ba da amsa “An atom is the smallest unit of an element.” *PHYSICS* Question: What is gravity? Ching Ching answer. “Gravity is the force that pulls objects toward the earth.” Question: State Newton’s first law. Ching Ching answer... “An object will remain at rest or in uniform motion unless acted upon by an external force.” Question “What is the unit of force?” Ching Ching answer... “Newton.” Nan fa murmushi ya ƙara faɗaɗa a fuskar malamai.... *COMPUTER STUDIES* Question: What is a computer? Ching Ching answer... “A computer is an electronic device that accepts data, processes it, and gives information.” Question Mention two input devices... Ching Ching answer.. “Keyboard and mouse.” A nan fa, mamaki ya ƙara cika dakin 😳.. Sai wani malami ya ɗan tsuke fuska ya ce.. Q: Explain the relationship between science and technology... Ching Ching ta ɗan ɗaga gira, ta ce: “Science discovers knowledge, while technology applies that knowledge to solve human problems.” Nan ne Chief ya girgiza kai yana cewa.. “Haba, she didn’t come here for advanced studies. Those questions are for degree or master’s level students. She is almost seventeen years old....” Cikin burgewa, ɗaya daga cikin malamai ya dubi Chief Onyx... “Chief, has she attended any formal school before?” Kafin Chief ya buɗe baki.. Ching Ching ta miƙe tana faɗin.. “Laaa! Tun da nake Abul ɗina bai taɓa kai ni makaranta ba. Malam Musa ne yake koya min a gida. Kullum yana tsara darasin da za mu yi, ni kuma nakan tambaye shi har sai ya gaji da surutuna....” Ɗakin ya kaɗu da murmushi.. A zuciyar Chief kuwa, farin ciki ya cika shi. ‘Wannan yarinya ba za ta ɓata lokacinta a banza ba... Kwakwalwarta tana ɗaukar abu nan da nan... Sai aka ci gaba da wasu tambayoyin da suka fi ƙarfin shekarunta.. Chief Onyx ya girgiza kai yana cewa... “Please, remember she is not here for a degree program. These questions are for university students and even master’s level....” Daga nan Barista Kabir, babban lauya kuma malamin Islamiyya... Ya kalli Ching Ching ya ce.. “Bismillāh. Let’s begin.” Barista Kabir ya tambaye ta sunanta...Da sauri ta furta... "Ching-Ching Onyx..." Malam ya ce, “To Malama Ching Ching, me ake nufi da Imani?” Ching Ching ta amsa a sauƙaƙe.. “Imani shi ne gaskatawa da zuciya, furtawa da baki, da aiki da gabobi.” Barista Kabir ya ƙara da cewa.. “Nawa ne Rukunan Musulunci?” Ta amsa a taƙaice “Biyar.” Ya kuma tambayarta.. “Nawa ne Rukunan Imani?” Ta ce, “Shida.” Ya ce, “Me ake nufi da Ikhlasi?” Ching Ching ta nutsu sannan ta fara faɗin.. “Yin ibada domin Allah shi kaɗai ba tare da nuna wa mutane ba.” Tana amsawa cikin wasa, shagwaɓa da rigima, kamar an zuba mata ilimi a kwakwalwa... Menene Tauhidi? Tana dariya ta ce, “Tauhidi shi ne kaɗaita Allah cikin ibada, sunaye da siffofi.” Yana jinjina kai ya ce. Menene sharuddan sallah? Ta ce, cabb haba Malam me ya sa kake mun tambayoyi masu sauƙi haka? Sai kuma ta amsa.. “Tsarki, rufe al’aura, fuskantar alƙibla, lokaci ya shiga, da niyya.” Malamin yayi dariya sannan ya ce, Guda nawa ne surorin Qur’ani... Ta ce, “Qur’ani yana da surori 114.” Question Ma’anar ‘العلم نور’... Ta furta.. “Ilmi haske ne.” Ya ce, Ki yi jumla da kalmar ‘كتاب’. Ta ce, “هذا كتاب مفيد.” Ta faɗi tana ƙaramin murmushi tana wasa da yatsunta... Malaman suka kalli juna cikin mamaki da gamsuwa. A yau, kowa ya tabbatar cewa Ching Ching ba yarinya ce ta yau da kullum ba. Barista Kabir ya jingina kai yana cewa.. “Subḥānallāh… baiwa daga Allah...” Bayan kammala interview, malamai suka sake komawa teburinsu... An ɗauki ƴan mintuna ana tattaunawa cikin ƙasa-ƙasa, ido na kai-komo zuwa ga Ching-Ching wadda ke zaune tana juya kujera tana wasanta kamar komai bai dame ta ba... A ƙarshe, shugaban makarantar ya ɗaga kai ya ce.. “Miss Ching-Ching Onyx… after careful consideration, we’ve decided to place you in Senior Advanced Class.” Chief Onyx ya zaro ido.. “Senior… what?” Shugaban ya murmusa. “Senior Advanced Class. It’s a class meant for students preparing ahead of university-level thinking.” Ching-Ching ta ɗan turo baki. “Toh… zan yi lunch da wane aji?” Duk office ɗin suka ɗan yi dariya... Da rana, bayan an gama komai na rajista, aka raka Ching-Ching zuwa ajinta.. Aji ne babba, mai tsari, AC na aiki, ɗalibai kusan ashirin da... kowa yana cikin nutsuwa, wasu suna karatu, wasu na muhawara cikin turanci. Da aka buɗe ƙofar ajin… Shiru ya mamaye wurin. Idanu sama da ashirin suka sauƙa kanta lokaci guda.. Uniform ɗinta ya sha bamban da na sauran, domin uniform junior aka mata, yanzu sai an sake mata wasu uniform kala-kala na senior... Malamin ajin ya ce, “Class, we have a new student. Her name is Firdos Muhammad Nou.....” Malamin bai ƙarasa ba Ching Ching ta katse shi da faɗin.. "Ching-Ching Onyx ne..." Wasu ɗalibai suka kalli juna. Wata yarinya mai suna Elena ’yar Italiya ta raɗa.. “She looks too young…” Wani saurayi ɗan attajirin Indiya ya ce.. “Probably another spoiled rich kid.” Ching-Ching ta ji amma ta yi kamar ba ta ji ba.. Domin Chief ya yi mugun ja mata kunne akan yawan magana...sannan kar ta sake ce wa kowa, tana da juna biyu domin kowa zai ɗauke ta karuwa ce.... A lokacin ta nutsu domin tasan karuwai ne ƴan wuta..ita kuma ba ta son ana dangantata da shiga wuta.. TAMBAYA TA FARKO A AJIN... Malamin ya ce.. “Ching-Ching, please solve this on the board.” Yayi hakan ne domin kawai da tunanin sauran ƴan ajin a kanta, kar su yi tunanin ko kuɗinsu ko dan ƙanwar shugaban ƙasar ne yasa aka ba ta ajin.... Yana so ya nuna musu cewa iliminta ne ya ba ta... Ya rubuta tambayar Mathematics na Advanced Algebra... Wasu suka yi murmushi na raini... Ching-Ching ta miƙe, ta ɗauki marker. Ba tare da ɓata lokaci ba.. Tana magana cikin confidence da yanga da kuma shagwaɓa... Ta warware tambayar daidai, tsaf, babu kuskure... Ta juyo ta ce.. “Is that all, sir?” Aji ya sake yin shiru... Elena ta buɗe baki.. “Wait… how did she do that?” Domin a ajin ita ke ɗaukan first class.. Wani saurayi daga China ya gyara gilashinsa... “She skipped three steps… but still got the right answer.” Malamin ya ce.. “Class, that’s correct, Please clap for her..." Nan ajin ya ɗauki sautin tafi, a yayin da wasu suke jin haushin ta ya daga shigowarta zata yo sama.... Wasu fuska suka fara canzawa daga raini zuwa mamaki... Ching-Ching ta koma kujerarta tana faɗin ƙasa-ƙasa da murya, “Kai… ashe ba wahala ma...” Tun daga wannan rana, sunanta ya fara yawo a makarantar... “The new girl with the scary brain...” Tun daga wannan rana, hankalin ajin ya rabu gida biyu. Wasu daga cikin samari suna neman su samu damar zama kusa da Ching-Ching.. “Hi… can I sit here?” “You’re really smart, where did you study before?” Wasu ’yan mata kuma cikin ladabi suke kusantarta.. “Your accent is cute.” “Please, teach me how you solved that question.” Ching-Ching kuwa? Tana amsa wa kowa cikin sauƙi da sakalci, tana murmushi, tana wasa da alƙalami kamar karatu wasa ne a wajenta... Wasu da aka basu assignment tin kafin ta zo, duk tayi mu su... Tana mu su tana tunani a zuciyarta... “Kai… ashe mutane suna son ilimi haka?” ✨ Da ƙarfe 2:00pm, an kammala boko. A ƙofar makaranta, aka ga jiragen ɗaukar ɗalibai Kiristoci daga ƙasashen waje.. Turawa, Italiyawa, Chinese, Indiyawa ana ɗaukar su zuwa gidajensu... Yaran Musulmi kuwa suka nufi ajin Islamiyya na ƙarfe 2:30pm – 5:00pm.. Bayan sun yi lunch na rana.. Ching-Ching ta biyo su cikin mamaki..wasu suka fara faɗin “Ashe har da wannan?” Ching Ching ta shiga ta ga tsaruwar ajin da basu wuce 30 ba, domin christoci sun fi yawa a makarantar... “Nice… I like this part.” Ta furta tana washe baki.. Malamin Islamiyya, Sheikh Abdul-Kabir, mutum ne mai nutsuwa, cike da ilimi... Ya fara da cewa... “Bismillah… yau zamu yi bitar Al-Kur’ani.” Ya yi tambaya ta farko... “Wace aya ce ta ambaci halittar Annabi Isa (A.S) da misalinsa?” Hannu da yawa suka ɗaga. Wasu suka amsa daidai, wasu kuma saɓanin haka... Ching Ching itama ta ɗaga.. Malamin ya ce.. “Miss Ching-Ching, please.” Ching-Ching ta miƙe cikin confidence, ba tare da rawar murya ba.. Bayan ta karanta ayar sai kuma ta fassara.. Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Hakika misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adam ne, Allah Ya halicce shi daga ƙasa, sannan Ya ce masa Kasance, sai ya kasance. .” Ajin ya yi shiru.. Malami ya ce, “Excellent.” Malami ya ci gaba.. Tambaya ta biyu “Wace aya ce ta yi magana akan cewa Annabi Isa bai mutu ba, Allah Ya ɗaukaka shi?” Ching-Ching ta sake miƙe wa.. Ta ƙara da cewa وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَٰكِن شُبِّهَ لَهُمْ “Sun kashe shi ba, sun gicciye shi amma sai aka rikita musu tunani...” Malamin ya tsaya yana dogon tunani akan fassarar amsar, amma ayar dai-dai ne... Nan malamin yayi murmushi sannan ya ce, "...Ba su kashe shi ba, kuma ba su kafa shi a kan cross ba wato giciye, amma dai an nuna musu kamanninsa ne..." Malamin ya ci gaba da darasin.. Allah ya kare shi daga mutuwa a hannunsu... Wannan yana karyata imanin da wasu suke da shi na cewa an gicciye shi a Crucifixion... Mafi yawan malamai kamar su Ibn Abbas sun fada cewa, lokacin da sojoji suka shiga gidan da Annabi 'Isa yake, Allah ya canza fuskar wani mutum daban, wasu sun ce maci amanar nan ne Judas, wasu kuma sun ce ɗaya daga cikin almajiransa ne ya bada kansa ta koma daidai da ta Annabi 'Isa... Sai suka dauki wannan mutumin suka kashe shi, suna tunanin Annabi Isa ne... Aya ta gaba ta ci gaba da cewa, "A'a, Allah ya ɗaukaka shi ne zuwa gare Shi..." Wannan ayar tana cikin Suran An-Nisa (Sura ta 4), aya ta 157. Tana daya daga cikin ayoyi mafi muhimmanci da suke bayyana gaskiyar abin da ya faru da Annabi Isa (AS) lokacin da Yahudawa suka yi ƙoƙarin kashe shi... Ching Ching ƙare shi da kallo, duk tasan wannan domin Malam Musa akwai ranakun da yake ware wa don bayyana tarihi da ayoyin da suke cikin Alqur'ani... Bayan ajin yayi shiru sai kawai ta yi wani kwafa mai ƙarfi tana faɗin "Allah yasa Arna su ji ka...don kashe ka zasu yi.." Ƴan ajin ne suka yi dariya daga bisani Malamin ba tare da ya ce komai ba, ya sake jefa wata tambaya “Wace aya ce ta nuna cewa Annabi Isa bawa ne na Allah?” Wannan karon wata ce ta miƙe ta amsa إِنْ هُوَ إِلَّا عَبْدٌ أَنْعَمْنَا عَلَيْهِ (Suratuz-Zukhruf: 59) Malami ya girgiza kai yana murmushi.. “Alhamdulillah…” Sai malami ya ce... “Yanzu tilawa zamu yi.” Kowace ɗaliba da surar da take... Malamin ya tambayi Ching-Ching surar da take.. Ta ce cikin tana juya ido. “Suratul Aal-Imran.” Ta fara karatun tajwidi har ta zo yadda ta tsaya domin ba ta gama surar ba... Bayan an tashi.. Malami ya ce... “Miss Ching-Ching, who taught you all this?” Ta turo baki tana murmushi.. “Malam Musa… but sometimes I argue with him.” 😌 Malamin ya ce "Ma sha ALLAH, duk Allah ya haɗa miki, boko da Arabic, ina ma ace ke ƴata ce..." Ching-Ching ta turo baki ta ce, "Hu uhmmmmm! Ni fa ƴar sarki ce, ƙanwar sarki kuma amma kai na ga ba ka da wani sarauta..." Haka malamin ya biye mata suka riƙa hira har aka zo ɗaukanta itama.. Iya bodyguards ne suka zo.. Tare da Gely... Ganinsu ya sa Ching Ching ta fara murguɗa baki, ita tayi tunanin da jirgi xa'a zo ɗaukanta.... Kamar sauran... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣4️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Washegari gari ya waye da wata irin sanyayyar ni'ima. Master Ibrahim ya tare Inuwa a hanyar fita daga sashen tsaro.. "Inuwa, ka shirya. Zuwa gobe akwai wani katafaren training da nake so ka gudanar a wajen masarauta. Ina son ganin sabon salo a tare da kai." Muryar a shake Inuwa ya ce, "An gama Master. Zan ɗan fita ne yanzu akwai abin da zan dubo." Master ya ce, "Duk yadda za ka je, kada ka daɗe. Ka sani kaine kashin bayan tsaron nan a yanzu." Ayat ta fito sanye da kakin sojan tsaron masarauta, takunta cike da isa da ƙasaita na babban jami'i mai muƙami... Tana tafiya ne tana sauri, rataye da wata jaka wadda yake ɗauke da tulin gwala-gwalai da zinarai waɗanda ta kwaso daga taskarta da kuma wadda Zayana ta ba ta, burinta ta je kasuwa ta canza su ta raba wa talakawan da ke shan wuya... Tana isa wani fili mai nisa da fadar, inda bishiyoyi suka yi inuwa, ba zato ba tsammani sai ga wata mahaukaciyar guguwa ta tashi! Ƙura ta turnuƙe wajen, bishiyoyi suka fara rawa. Cikin tsakiyar guguwar, wani haske ya bayyana, nan take King Diamond ya bayyana a gabanta, tsaye daram kamar bishiyar kuka, kwarjininsa ya cika wajen.. Inuwa ta firgita, ta fara waige-waige cikin tashin hankali.. "Me ya kawo ka a wannan lokacin?! Idan wani ya gan ka fa? Kana son tona min asiri ne?" King Diamond cikin muryarsa mai amo kamar rugun tsumi ya ce, "Kada ki damu, babu wanda zai gan ni. Na riga na dakatar da idon kowa a wannan yankin. Mu biyu ne kawai a nan." Idanunsa suka sauka akan jakar da ta ƙanƙame. "Wannan jakar fa? Me kike ɓoyewa?" Inuwa ya ce, "Gwala-gwalai ne da zinarai. Ina son in kai kasuwa in canza su zuwa kuɗi domin in rabar wa talakawa su samu abin dogaro." King Diamond ya matso kusa, ƙasaitaccen murmushi ya bayyana a fuskarsa. "Inuwa, bakya tsoron a fara zargin ki? A matsayinki na guard, ta yaya za ki mallaki waɗannan dukiyar? Ko babban Commander ko Master ba su isa su mallaki ko kashi ɗaya cikin goma na abin da ke cikin jakar nan ba. Idan kika nuna waɗannan a kasuwa, asirinki zai tonu, za a ce sata kika yi." Inuwa ta daske, maganar ta doke ta. "Haka ne... ban yi tunanin hakan ba." King Diamond ya ce, "Kada ki damu. Riƙe jakarki da kyau." Kafin Inuwa ta ankara, King ya ɗaga hannunsa ɗaya, wani irin haske mai launin zinare ya ratsa cikin jakar. Inuwa ta ji jakar ta fara yin nauyi, tana ƙaruwa tana kumbura. Cikin ƙiftawar ido, zinarun da ba su kai rabin jakar ba, suka rikkiɗa suka koma tulin takardun kuɗaɗe sababbi ƙal, har jakar ta kasa rufuwa saboda cika!.. "Yanzu za ki iya tafiya. Waɗannan kuɗaɗen ba za su taɓa karewa ba har sai kin gama biyan buƙatar kowa. Kuma babu wanda zai yi zargin kuɗi a hannun jarumi." Inuwa ta kalli jakar, ta kalli King Diamond cikin mamaki da godiya. "Nagode... ka cece ni daga babban tarkon da zan faɗa." Kafin ta rufe baki ta ji ya ce, "zan iya raka ki?..." Ayat ta tsaya tana kallon kanta, ranta ya baci da shawarar King Diamond na raka ta... "Tabb! So kake a akawo min farmaki? Idan aka ganni soja da kai, tambayar duniya za a rika yi, har magana ta kai kunnen Abul. Ko ka manta ni ma a boye nake?" Cikin muryarsa mai natsuwa ya ce, "Idan wannan ne damuwarki, ai maganinta mai sauki ne." Cikin dan lokaci, King Diamond ya nuna ta da yatsa, nan take kakin sojan jikin Ayat ya rikida ya koma doguwar bakar abaya mai santsi, tare da mayafi da nikab wanda ya boye fuskarta.. Ta dubi kanta ta ce, "To, shikenan ni na koma mace. Amma kai fa? Da wannan dogon farin gashin naka? A garin nan babu mai irin sa sai tsohon da ya haura shekara dari, ko kuma... Aljani! Dole ka canza..." King Diamond ya gyara tsayuwa, nan take farin gashin kansa ya juye ya koma bakikirin, mai santsi da tsawo, wanda ya kara fito da kwarjininsa na matashi ɗan gayu mai jini a jika. Ayat ta saki baki tana kallo, sannan suka nufi kasuwa. Suna isa cikin kasuwar Alhamra, sai kace an tsayar da lokaci. Hayaniyar ciniki ta tsaya, kowa ya daskare. King Diamond ne yake taku cikin kasuwar, kwarjininsa kamar rana, kyawunsa ya zarce duk wani tunani na dan adam. Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un! 🥺 Ba mutuwa akayi ba, illar kyau ce! 'Yan matan kasuwa sun yi matuƙar ruɗe wa, kowa ya saki abinda yake tallatawa.. Wata budurwa dake siyan kayan miya, tana kallon King Diamond, nan take ta ji jikinta ya sake, wandonta na ciki ne ya jiƙe jagaf kamar wacce tayi fitsari saboda tsananin gigita da kwarjini... Da wani irin matsanancin sha'awarsa...! Wasu kuma suka fara sumbatu.. "Wannan mutum ne ko mala'ika?", "Wallahi idan na aure shi na gama rayuwa!" King Diamond kuwa yana tafiya ne kamar baya taku a ƙasa, Ayat tana gefensa a cikin nikab ɗinta, tana jin duk kalaman banza da 'yan matan ke jefawa masoyinta... Wata kyakkyawar budurwa, ganin su King Diamond sun kusa isowa kusa da ita, sai ta shirya tarkon so.. Ta matsa gaba kaɗan, daidai zasu wuce, sai ta sake jiki da gangan ta lula zata faɗi a jikin King Diamond don ta ji dumin jikinsa. Amma King, kamar mai idanu a ko'ina, a slow motion ya yi wani irin taku na kwarewa wanda ake ƙira da Sidestep, ya goce mata tare da yin baya, ba tare da ya bari ko rigarsa ta goga tata ba.. Gippp! Yarinyar ta faɗi a kasa, Ta ɗago tana lumshe ido cikin kissa, ta mika hannu ɗaya tana kallon King Diamond da irin nuna soyayya, tana rokon ya kama hannunta ya tada ita. Ayat dake cikin nikab, ranta ya kai babban matsayi na tafasa. Ta kasa jure ganin yadda matan nan ke hauka akan naman ta... Cikin zafin nama da kishi, Ayat ma ta yi baya yadda King ya yi, ta watsa wa yarinyar dake kasa wani kallon kiyayya ta cikin nikab. Sannan, ta mika hannunta ta makala a cikin na King Diamond, ta rungume damtsen hannunsa da kyau irin na mata da miji, ta manne a jikinsa.. A ranta ta ce, "Kuji dashi! Nawa ne ni daya!" Suka bi ta gefen yarinyar dake zaune a kasa cikin kunya, suka tafi suna taku daya-bayan-daya. Yarinyar ta daskare a kasa, idonta na bin bayan King Diamond da kishi da sha'awa, tana mamakin wace sa'ar ce wannan dake kumshe a cikin nikab dake rungume da wannan sarkin Kyawun".... Bayan sun ɗan yi nisa da taron matan da suka ruɗe, Ayat ta zame hannunta daga na King cikin fushi da yatsine fuska duk da nikab ɗin ya ɓoye hakan, sautin muryarta ya bayyana komai... "Tafi can daga nan! Ni fa gaskiya banga wani kyau a tare da kai ba da har mata za su riƙa hauka a kanka haka. Dubi yadda kake wani mumu da kai... uhmmm, wai wannan ne kyan? Ko kaɗan ma!" King Diamond bai ce uffan ba, ya dai saki wani ƙasaitaccen murmushin gefen baki wanda ake ƙira da side smirk... Ya san sarai cewa kishi ne ke sanya ta wannan surutun, kuma kasancewarsa mutum mai kwarjini da rashin son yawan magana a cikin taro, sai ya kyale ta ya ci gaba da takunsa na isa... Daga nan Ayat ta nufi lungu-lungu na kasuwar inda talakawa da gajiyayyu suke. Ta buɗe wannan jaka mai mu'ujiza wadda King Diamond ya cika mata da maƙudan kuɗaɗe.. Ga Makafi da Kutarai, Ayat ta shiga raba tulin kuɗaɗe, duk wanda ta ba wa sai ya ji kamar mafarki yake yi. Makafi suka sa albarka, kutarai suka ɗaga hannu sama suna kuka.. Sai Nakasassu da Masu Ƙananan Jari da matan da ke soya awara ko sayar da ganye, Ayat ta riƙa zazzaga musu kuɗin da ya ninka jarin su sau ɗari. Ga Matasa Marasa Sana'a.. Ta kira su ta ba su maƙudan kuɗaɗe a matsayin tallafin fara rayuwa.. Duk inda suka ratsa, mutane sai kallon King Diamond suke yi, suna zaton shi ne babban mai kuɗin.. Kwarjininsa ya sa mutane ma sun kasa tambayar ko su waye, sai dai kawai godiya da addu'a.. Ayat tana cikin rabon kuɗin nan cikin sauri, tana jin daɗin yadda mutane ke farin ciki, amma lokaci guda tana lura da King Diamond wanda ke tsaye kamar dutse, yana kiyaye duk wani motsi da zai zama barazana gare ta. Tana tsaka da raba kuɗin nan, sai ta hango wasu jami'an tsaron masarauta guda uku suna tahowa ta sashen da take. Sun ga taron mutane sun kewaye wasu baƙi, kuma sun fara zargin akwai wani abu da ke faruwa.. Daya daga cikin sojojin ya daka wa mutane tsawa.. "Ku matsa! Waye wannan yake raba kuɗi ba tare da izinin mu ba?!" Ayat ta daskare. Ta san idan waɗannan sojojin suka matso kusa, za su iya gano asirin jakar, ko kuma su gane cewa King Diamond ba ɗan garin ba ne... Sojojin da suka taho da zafi da nufin yin bincike, sai suka daskare a inda suke na wasu daƙiƙo'i. King Diamond ya yi amfani da sihirinsa ya shafe dukkan abin da ke cikin tunaninsu game da raba kuɗin ko ganin wasu baƙi.. Daya daga cikin sojojin ya sosa ƙezo, ya kalli ɗan uwansa cikin rashin fahimta. "Wai me ya kawo mu nan ne?" Ɗayan ya murza idonsa, ya duba hagu da dama, ya ga mutane na harkokinsu na yau da kullum domin su ma sun daina hayaniyar... "Oho! Ni kaina na manta. Kamar akwai abin da zan duba, amma yanzu komai ya fice min a kai." Suka juya baya, suna tafiya suna nuna wa juna hanyar da za ta mayar da su fada, kamar ba su ne suka taho cikin jarumta ba.. Ayat ta sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya, ta kalli jakar ta ga sauran kuɗaɗen sun ƙara yawa ma. Cikin gaggawa ta ƙarasa zazzaga wa wasu tsofaffi da ke zaune a gefen kasuwa, sannan ta rufe jakar.. Ta ɗago ta kalli King sannan ta ce, "Nagode King. Da ba don kai ba, da yanzu asirina ya tonu a hannun waɗancan mutanen." King Diamond ya gyara tsayuwa, ya kalle ta cikin natsuwa. "Wajibi ne in kiyaye ki. Amma yanzu lokaci ya ƙure, dole ki koma kafin a fara nemanki a masarauta." Haka suka bar dandalin kasuwar, inda Ayat ke tafiya tana waige-waige, shi kuma King Diamond yana biye da ita kamar inuwarta, kwarjininsa na ci gaba da sace zukatan duk macen da ta kuskura ta kalle shi... Bayan sun bar kasuwa sun isa wani lungu kusa da fadar, King ya tsaya ya kalli Ayat. Da wani sassanyan haske na sihirinsa, ya mayar da ita yadda take a farko sanye da kakin sojan tsaro mai muƙami, fuskarta sanye da gashin baki da gemu na boki... Kafin King ya ɓace, su biyun sun tsaya suna kallon juna. Wani kallo ne mai zurfi, cike da wata irin soyayya da babu kalmomin da za su iya fassara ta. Kallo ne na amana da kaunar da ta ratsa zuciya. Cikin ƙiftawar ido, King Diamond ya ɓace kamar bai taɓa kasancewa ba. Inuwa tana tafe tana murmushi, tunanin kallon da King ya mata ne yake sake mata daɗi a zuciya. Bata ankara ba, sai ta yi kuciɓis da Master Ibrahim.. Ganin yadda Inuwa yake ta faman murmushi shi kaɗai, Master ya tsaya ya zura masa ido cikin mamaki da zargi. Ya ce, "Lafiya Inuwa? Da wa kake wannan murmushin haka kamar wanda ya sami dukiya ko ya haɗu da masoyiya?" Inuwa ya firgita, ya fara in-ina domin ya rasa abin da zai ce wa Master.. "Eh... dama... Master, kawai tunanin wani abu ne na daban..." Daidai lokacin da Master yake ƙoƙarin ƙara bincikar Inuwa, sai idonsa ya sauƙa akan wata zurariyar budurwa wadda ta shawo kwana, tana taku cikin takama ta juya musu baya tana tafiya.. Master ya jinjina kai, ya saki wani murmushi na takaici, yana zaton Inuwa ita yake kalla shiyasa yake murmushi. Master ya ce, "Lallai Inuwa... ashe abin da ya tsayar da kai kenan? Na tambaye ka ka ƙi faɗa min, ashe kallon wannan yarinyar kake? Ban hana ka bin mata ba a cikin aiki?" Inuwa ya rasa yadda zai bayyana wa Master cewa sam babu ma maganar wata mace, kawai saɓani ne aka samu a lokacin da ya shigo ita kuma ta shawo kwana. Amma don ya wanke kansa, Inuwa ya sunkuyar da kai kawai.. "Yi haƙuri Master, ba haka ba ne yadda kake tunani..." Master Ibrahim ya taɓa kafaɗarsa, fuskarsa ta koma ta soja mai tsanani, ya ce. "Kada ka bari ra'ayin zuciya ya rage maka kaifin basirarka ta soja. Na dakatar da kai ne domin in tunatar da kai. Gobe da asubanci za mu fara gudanar da training ɗinmu na musamman. Ina son ka shirya tsaf, domin horon gobe ba na wasa ba ne." Inuwa ya ce, "An gama Master. Zan kasance a can kan lokaci." Inuwa ya wuce zuwa sashensa yana ajiyar zuciya, yana mamakin yadda Master ya yi masa mummunar fassara, amma kuma zuciyarsa tana can kan King Diamond... ✨✨✨ Lokacin tafiya makaranta, kamar yadda Uncle Jalal ya sanar, yau ya zo ɗaukanta.. Maayah ta tsaya turus a bakin motar Uncle Jalal, tana kallon tsohuwar katuwar motar tasa mai tauri da kwarji amma ba irin wadda ta saba hawa ba...Domin motar karɓa yayi a wurin wani malami don ya zo ɗaukanta, a yayinda ya bar mashin ɗinsa da helmet acan makarantar... Ta fashe da wani irin kuka na shagwaba, tana buga kafafunta a kasa.. "Wallahi ba zan taɓa hawa wannan kaskantacciyar motar ba! Ina bodyguards dina? Ina motoci na masu sanyin AC? Abul! Abul!! Ka fito ka ga abinda malamin nan yake shirin yi min!" Hadiman gidan duk sun taru suna kallon ikon Allah, amma babu wanda ya isa ya tari Uncle Jalal, domin kowa ya san yana da cikakken ikon Sarki. Uncle Jalal ya ɗaure fuska, tare da matso kusa da ita, muryarsa ta daka wani irin amo da ya sa Maayah ta tsagaita kukan dole.. "Ke! Idan ba ki mun shiru ba, zan miki dukan da baki taɓa jin labarin irin sa a rayuwarki ba. Daga yau kishin ki da daularki sun kare a kofar gidan nan. Shiga mota yanzu!" Maayah ta yi tsuru, ganin babu wani bodyguard da zai zo ya tunkuɗe shi. Cikin kunkuni da kukan kissa, ta bude kofar baya ta zauna tare da turo baki.. Uncle Jalal ya ce, "Fito ki dawo gaba! Ni ba direbanki ba ne, ni malamin ki ne. Kuma anan gaba za ki koyi yadda ake mutunta na gaba da ke." Dole Maayah ta fito ta dawo gaban motar, tana kakkabe kujerar kamar tana taba kashi... Uncle Jalal ya tada motar, suka bar fadar masarautar Alhamra. Iska na bugun fuskarta domin bai kunna AC ba, ya bar tagogin a buɗe... Tana turo baki ta ce, "Kaji mutum... wai shi malami. Ka sani sarai idan mahaifiyata ta ji labarin abinda kake yi min, sai ta sa an kora ka daga kasar nan." Uncle Jalal ya yi wani murmushin gefen baki, ba tare da ya kalle ta ba.. "Mahaifiyarki? Wacce take malamar jami'a a Mumbai? Wacce aka girmama a duniya saboda ilimi? Ke kike tunanin za ta goyi bayan jahilcin ki? Maayah, kin zama babban abin kunya ga asalinki. Kina SS3 amma ko sunan mahaifiyar taki ba za ki iya rubutawa ba... kin taɓa ganin inda aka taɓa irin wannan asarar?" Maayah ta ji maganar ta soke ta a zuciya, ta kawar da kanta tana kallon titi.. "Nidai kawai ka kaini makarantar, idan mun je can zan san abin yi." Suna isa kofar makarantar, Uncle Jalal bai tsaya a inda sauran manyan motoci suke tsayawa ba, ya kai ta har kofar ajin da aka rage ta aka mayar (SS1/Senior Secondary 1)... "Sauka maza. Kuma ki sani, daga yau duk wanda ya nuna miki rashin kunya a makarantar nan, ni zan dauki mataki. Amma idan ke kika yi wa wani, ni zan fara horonki." Maayah ta sauƙa tana gurnani, yayin da daliban makarantar suka saki baki suna kallon gimbiyar da suka saba gani da ayarin motoci, yau tana fitowa daga mota da Uncle Jalal kuma a aji ɗaya za ta cigaba da zama!.. Maayah ta shiga ajin SS1 tana taku kamar tana takon ƙaya. Duk ɗaliban ajin suka yi shiru, kowa ya zura mata ido... Waɗanda ta saba yi wa wulakanci duk suna nan..dake duk makarantar yaran attajirai ne, kowa yana ji da kuɗin mahaifinsa.. Ta kalli yaran dake ajin duk ba sa'o'inta ta ji wani irin amai yana taso mata... Ta zauna a wata kujera ta baya-baya, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta, amma ina! Tuni labari ya bazu cewa Gimbiyar Alhamra an dawo da ita baya... Wata ɗaliba mai suna Zaitun, wadda Maayah ta taɓa sa aka ci mutuncinta tin kafin ta shigo SS1, ta tashi tsaye tana nuna Maayah da yatsa, ganin yanzu babu wannan isar kuma Uncle Jalal ya tsayar mata.. Zaitun ta ce, "Iyeee! Kowa ya ga abin da nake gani kuwa? Subhanah, gimbiyar da take ganin kanta a sama, yau gata a aji ɗaya da mu? Maayah, ashe duk wannan takamar takarda ma ba ki iya rufawa kanki asiri ba?" Daukacin ajin suka ɓalle da dariya... "Hahaha! Gimbiya mai repeat!" "Yau dai kishin fada ya ƙare a bakin allo!" Maayah ta ji ranta ya ɓaci, ta tashi tsaye tana huci.. "Ku yi mun shiru anan, banzaye kawai! Kun san ko ni wacece? Idan na sa aka kama ku duka a gidan yarin masarauta sai kun gwammace ba'a haife ku ba!" Daidai lokacin, wani malamin lissafi mai tsanani ya shigo ajin. Ganin hayaniya ta yi yawa, ya buga teburi.. Malamin ya ce, "Me ke faruwa a nan? Ke kuma menene wannan dake ta ihu?" Zaitun ta ce, "Yallabai, sabuwar ɗaliba ce, Maayah ce." Malamin ya gyara madubin idonsa... "Ah, Gimbiya Maayah. Uncle Jalal ya ba ni labarinki. To tunda yau ne farkon dawowarki ajin, maza zo nan gaban blackboard. Solve mana wannan simple equation ɗin.. 2x + 5 = 15. Nemo mana darajar x." Maayah ta daskare. Ta kalli allon, ta kalli ɗaliban dake mata dariya a ɓoye, ta kasa ko takawa ta nufi allon. Ta saba ne kawai a riƙa ce mata "Ranka ya daɗe," amma yanzu lissafi ya zo mata da darasi. Tana nan tsaye tana hawayen takaici, sai ga Uncle Jalal ya leƙo ta taga. Idanunsa suka sarƙe da nata. Cikin takaici yayi mata kallon da ya nuna mata "kin gani ko?" ya fi komai ciwo.. Ya kalli malamin sannan ya ce, "Malam, idan ba ta sani ba, ka ba ta bulala biyar a hannu. Ta saba ana mata komai, yau kuma dole ta koya da kanta." Maayah ta zaro ido, ta kalli hannunta mai laushi dake sanye da zinarai, tana tunanin yadda bulala za ta shige shi... Daga nan Uncle Jalal ya bar wurin, ya koma office ɗinsa. Malamin ya zo gaban Maayah cikin takun izgilanci daman ko wani malami tarko yake ɗana mata yadda zai rama wulaƙancin da tayi mu su.. Ɗaga bulala yayi ya zabga wa mata a tafin hannunta. Maayah ta ji wani irin zafi ya ziyarci ƙwaƙwalwarta. Tun kafin malamin ya sake ɗaga ta biyu, Maayah ta nuna cewa ita jinin sarauta ce mai zafi.. Ta ɗaga hannunta ɗayan, ta wanke Malamin da wani lafiyayyen mari wanda ya sa madubin idonsa ya goce!.. "Ka kuskura ka sake taɓa ni da wannan datti-dattin hannun naka, sai na sa an fasa maka kanka!" Ajin ya kaure da hayaniya. Ɗaliban ajin, waɗanda duk ƴaƴan manyan attajirai ne, suka saki baki suna kallon jarumtar Maayah, wasu kuma suna jin tsoron abin da zai biyo baya. Maayah ta kwashe jakarta, ta fice daga ajin da gudu, ta nufi hanyar gate domin komawa gida.. Uncle Jalal yana ofishinsa yana duba takardu, sai ya ji hayaniya ta barke a harabar makarantar.. "Gimbiya ta mari Malam!" Labari ya isa kunnensa. Ya fito cikin matuƙar fushi, idanunsa sun yi jawur.. Ya hango Maayah tana sauri za ta fice daga gate ɗin makarantar.. "Maayah! Tsaya a nan!" Uncle Jalal ya daka mata wata uwar tsawa. Maayah ta waigo, tana kuka tana huci. "Ba zan tsaya ba! Mugu, azzalumi! Gida zan koma, kuma sai na sa an raba ka da duniyar nan!" Uncle Jalal ya taro ta da wani irin zafin nama, ya damƙe hannunta ya juyo da ita. Bai saurari komai ba, ya ɗauke ta da mari har sau biyu, fuskarta ta juya hagu da dama.. Maayah ta fizge hannunta, tana kuka tana gudu tare da zaginsa da duk kalaman da suka zo bakinta... "Allah ya isa! Ba zan yafe ba! Mugu, matsiyacin bawa, azzalumi!" Uncle Jalal ya rasa inda ransa ya yi, ya bi ta ya girbe mata sawu. ta yi sama, ta faɗo a ƙasa timm! Tana ƙoƙarin tashi, ta sake cewa.. "Mahaukaci! Ɗan akuya kawai!" Nan take Uncle Jalal ya sake kai mata wani zafaffan marin da ya sa kanta ya ɗauki kukan ƙararrawa... Mutane sun taru, malamai suna ba Uncle Jalal haƙuri, amma ya toshe kunnensa. Maayah ta ƙi daina zagi, shi kuma ya ƙi daina duka. Fuskar Maayah mai kyau da haske ta rikkiɗa ta yi jawur, shatar hannun Uncle Jalal guda biyar ta fito radau a kumatu biyun... Yaa damƙe hannunta, ya riƙa jan ta kamar rago. Ya kaita ofishinsa, ya tura ta ciki ya jefar da ita a ƙasa. "Zauna a nan! Idan na sake jin muryarki, wallahi sai na sa ki yi fitsari a wando! A nan za ki wuni har sai kin gane cewa ke ɗaliba ce, ba gimbiya ba!" Maayah ta duƙunkune a ƙasa tana kuka mai cin zuciya, tana kallon hannayenta da suka yi dumu-dumu saboda ƙura, tana mamakin yadda rayuwarta ta canza a cikin sa'o'i kalilan.. ✨✨ Bayan mintuna kalilan, kofar ofishin ta budu da wani irin karfi Baaaaam!.... Maayah ta zabura ta mike cikin matukar tsoro, idanunta jajur. Ganin Uncle Jalal ya shigo rike da jakarta a hannu daya, dayan hannun kuma yana rike da wata zabgeger dorina mai baki uku, ya sa ta ji cikinta ya bada wani sauti... Ta bude baki zata fasa kuka, ya daka mata wata tsawa.. "Ki rufe min baki! Idan na ji kukan nan, yanzu zan raba jikinki da fata!" Ya shimfiɗa wata lallausar dadduma akan tiles din ofis din, ya nuna mata daddumar.. "Zauna a nan!" ya fada cikin muryar soja.. Maayah ta zauna jiki na ɓari, shima ya zauna a kusa da ita, ya ajiye waccan dorinar a gefensa domin ta riƙa kallonta tana jin tsoro. Ya buɗe jakarta, ya zaro littafin rubutu da biro, ya tura mata gabanta.. "Rubuta sunanki gaba daya... SHAHZADI MUHAMMAD NOURDEEN." Maayah ta kama biron da hannunta dake karkata. Ta fara kokarin rubutun, amma haruffan sai rawa suke yi, wasu sun fi wasu girma, rubutun ya fito a karkace kamar ɗakin gizo-gizo... Uncle Jalal ya kalli littafin, ya saki wani uban tsaki Tcheeeew!.... "Baki iya komai ba sai rashin kunya da zagi? Dubi rubutun ki kamar na kaza?" Ya fizgi biron daga hannunta, sannan ya matso kusa da ita. Ya sata a gabansa, ta yadda bayanta yake gogar faffaden kirjin sa. Ya ɗora hannunsa akan nata, ya damke yatsunta tare da biron, kamar yadda ake koya wa yaro dan Nursery rubutu.. Maayah ta ji wani irin bakon yanayi. Kamshin turarensa mai karfin gaske ya ziyarci hancinta. Ta kasa daurewa, ta juyo da fuskarta tana kallon sa. A lokacin, fuskokinsu suka kasance kusa da juna, hancinsu ya hade wuri daya, suna shakar numfashin juna... Bakin su ya kusa hadewa, idanun Maayah suka lumshe saboda wani irin shock da ta ji. Amma Uncle Jalal, duk da shima ya danyi tsuru na dakikani, sai ya tuno zaginsa da ta yi ɗazu. Ya haɗa rai, ya ce da ita cikin muryar dake nuna fushi.. "Look your front!.." A sanyaye ta kalli littafin, zuciyarta na bugawa.. Uncle Jalal ya cigaba da rike hannunta, yana gwada mata yadda ake rarrabe haruffan sunan nata daya bayan daya. Ya nuna mata yadda za ta zauna daram akan layin littafin.. "Dole ki iya rubuta sunan ki yanzu. Jarrabawa ta kusa, kuma idan baki iya rubuta sunan ki ba, ba za a taba barinki kiyi exam din ba. Kuma muddin kika faɗi, to sai kin shekara goma a aji daya!" Maayah ta fara nanata rubutun tana bi biyu, tana jin dumin hannunsa akan nata. Duk da zafin marin da ya mata dazu, sai ta ji wata irin natsuwa tana ratsa ta, tana mamakin yadda malamin dake dukan ta, yanzu kuma shine yake koya mata rubutu cikin wannan kusancin.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣5️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Asuba ta gari, iska mai sanyi tana kaɗawa a wani boyayyen fili dake kewaye da daddadan bishiyoyi. Shiru kake ji, sai sautin tsuntsaye dake rera kukan sanyin asuba.... Inuwa yana tsaye, sanye da rawaninsa da saje da gemunsa na bogi wadanda suka ƙara masa kwarjini... Master Ibrahim ya matso ta bayanta domin fara koyar da ita dabarun yaƙi da takobi. Ya tsaya daidai bayan Inuwa, ya sa hannunsa ya kama nata dake rike da takobin, domin ya nuna mata yadda ake jujjuya shi cikin kwarewa... A take, wani irin Shock mai karfin gaske ya ratsa Ayat tun daga kwakwalwarta har zuwa tafin kafafunta. Taɓa jikin Master da ta ji ya sa tsikar jikinta tashi, musamman yadda gemun Master yake gogar wuyanta yayin da yake mata bayani cikin raɗa... Shi ma Master Ibrahim, hancinsa ya shaki wani daddadan kamshi dake tashi daga wuyan Inuwa...ƙamshi ne mai rikita tunanin namiji, wanda bai kamata soja namiji ya kasance dashi ba. Hankalin Master ya fara barin jikinsa, yana jin wani yanayi dake neman rinjayar dabarunsa na soja.. Inuwa cikin muryar dake rawa ya furta "Master... na koya, zan yi da kaina yanzu." Ta samu ta zare jikinta daga gareshi, tana kokarin daidaita numfashinta da ya riga ya jagule. A can gefen wani kududdufi na alfarma wato Power Pool...King Diamond yana zaune tare da Prince Zarith. Suna shan wani ruwa mai launin shuɗi mai suna Al-Kautharul-Jinn, wani irin ruwa ne da ba a samunsa a duniyar mutane, wanda yake ƙara ƙarfin jini da sanya natsuwa a kwakwalwa.. Lokaci guda, King Diamond ya ji tsikar jikinsa ta tashi. Ya shiga wani irin yanayi na shauƙi da bai san daga inda ya fito ba. Nan take idanunsa suka juye, sai ga Ayat ta bayyana a gabansa cikin shigar gimbiyancinta na alfarma. Ta sa hannu ta yaye mayafin dake fuskarta, tana sakar masa wani irin kasaitaccen murmushi mai sace zuciya.. King Diamond ya daskare, ya kasa daina kallonta, shima ya fara sakar mata murmushi har fararen hakwaransa suka bayyana.. Prince Zarith ya cika da mamaki, domin tunda yake da King, bai taba ganin dariyarsa da ta kai ga bayyanar hakwara ba. Prince Zarith yana taɓa kafar King cike da mamaki ya furta. "Lafiya kuwa King? Me kake kallo haka kake murmushi kai kadai?" King ya firgita, ya dawo hayyacinsa. Ya waiga, ya ga babu kowa, sai Prince Zarith dake kallonsa cikin rashin fahimta. Anan ya tabbatar da cewa Ayat ta riga ta mamaye ransa, har ta kai tana masa gizo a fili... A ransa ya furta "Wane irin sihiri ne wannan yarinyar take yi min? Tana can tana training, amma ina jin ɗumin jikinta a nan.".. Prince Zarith ya matso kusa da King, ya shaƙi iskar dake kewaye da shi, idanunsa suka rine da launin mamaki.. "King... ina jin ƙamshin shauƙin soyayya a jikinka? Wannan ba yanayinmu na jinnu ba ne kaɗai. Shin wacece a ranka?" Ya tsaya ya ƙura wa King ido, muryarsa ta rikkiɗa ta koma ta gargaɗi... "Fatan ba bil'adam ba ce... domin akwai babban matsala idan har ita ce. Ka san dokokinmu, kuma ka san abin da zai biyo baya." King Diamond bai ce uffan ba, sai dai wata uwar harara da ya wurga wa Zarith, wadda ta sa iskar wajen ta yi sanyi lokaci guda. Shima ya sani, mallakar Ayat ba abu ne mai sauƙi ba. Akwai babban ƙalubale daga manyan shugabannin aljanu waɗanda ba za su taɓa amincewa da wannan sarƙaƙƙiyar soyayyar ba. Dole za a fafata, kuma dole jini ya zuba kafin burinsa ya cika... A can duniyar mutane kuwa, Master Ibrahim ya canza salon horon. Ya kai Inuwa bakin wani katon tafki mai zurfin gaske domin gudanar da training ɗin numfashi a cikin ruwa. Master Ibrahim ya tsaya a bakin ruwan, idanunsa sun yi ja saboda tsananin son ganin Inuwa ya zama jarumi. "Wannan karon, za mu ga juriya da jarumtarka a cikin ruwa. Dole ka nitse, kuma ba za ka ɗago ba har sai mintocin da na ɗiba maka sun cika. Wannan shi ne zai nuna idan kai soja ne na gaske." Ayat ta ji gabanta ya faɗi, wani irin sanyi ya ratsa ƙasusuwanta. Ba tsoron ruwan ne ya firgita ta ba, sai umarnin da Master ya biyar da shi... "Inuwa, cire waɗannan kayan naka na soja! Ba za ka iya yin wannan training ɗin da nauyin kakin nan a jikinka ba. Cire su yanzu ka shiga ruwan!" Inuwa ta daskare a inda take. Ta san muddin ta rage kayan jikinta, asirinta na mace zai iya bayyana. Master Ibrahim kuwa yana tsaye yana jiran ganin ya fara cire kayan, idanunsa kyam akan Inuwa... Muryar na rawa ta ce, "Master... ina jin zan iya yi da kayan nan. Ba sa min nauyi." Master cikin tsawa ya ce, "Wannan umarni ne Inuwa! Soja baya musu da shugabansa. Cire kayan nan yanzu!" Ayat ta fara ƙoƙarin taɓa maɓallan rigarta, hannunta yana karkata, tana kallon Master wanda ya ƙi ba ta sararin ko da ƙifta ido ne. A ranta tana kiran King Diamond, ko zai kawo mata ɗauki a wannan mawuyacin lokacin... Ta ji zuciyarta tana bugawa kamar ganga. Ta kalli Master Ibrahim, wanda yake tsaye tamau kamar gunki, yana jiran ganin ta cire kakin soja.. A hankali ta sake furta "Master... don Allah, ina neman alfarmar ka bar ni in shiga bayan wancan shingen, domin in rage kayana. Al'ada ta ce ba na son rage kaya a gaban kowa, ko da kuwa shugabana ne." Master Ibrahim ya haɗe girare, yana kallon Inuwa da wani irin kallo na mamaki. "Inuwa, kai soja ne! Soja ba shi da kunya a gaban ɗan uwansa, musamman a wajen horo." Inuwa ya ce, "Ina rokonka Master... wannan karon kawai." Master ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ya nuna mata bayan shingen da hannu.. "To, ka je maza! Amma ka sani, duk daƙiƙar da ka ɓata tana raguwa ne daga lokacin numfashinka a cikin ruwa. Ka fito nan da daƙiƙa talatin!" Ayat ta ruga bayan shingen da gudu. Da sauri ta rage kayan jikinta, amma ta bar wata siririyar riga ta ciki wato vest, ta ciki akwai bell da ya ɗaure mata ƙirji sosai don kada siffarta ta fito. Ta fito tana sauri, ba tare da ta bari Master ya kalle ta sosai ba, ta afka cikin ruwan tafkin.. Ruwan ya kasance mai sanyi sisai, amma hakan ya ba ta damar ɓoye kanta. Tana nitsewa cikin ruwan, Master Ibrahim ya matso bakin tafkin, yana kallon agogonsa amma hankalinsa yana kan yadda Inuwa ya yi firgigit wajen boye jikinsa... A ransa ya furta _"Wane irin soja ne wannan mai kunyar mata? Akwai wani abu da wannan yaron yake ɓoyewa, kuma zan gano shi ko ba jima ko ba daɗe."_ A can gefen Power Pool, Prince Zarith ya lura cewa King Diamond ya tafi wani tunani na daban, idanunsa sun yi haske kamar taurari... Ya ce, "King, muna magana ka yi shiru. Shin kana nufin za ka sadaukar da matsayinka na Sarkin Aljanu domin wannan bil'adama? Ka sani, idan manyan majalissar aljanu (The Elder Jinn Council) suka ji wannan labarin, yaƙi zai ɓarke tsakanin masarautunmu." King Diamond ya miƙe tsaye, dogon farin gashinsa yana shawagi a iska... "Zarith, ba zan sadaukar da komai ba, amma kuma ba zan bar ta ba. Idan dole sai an yi yaƙi don a tabbatar da soyayya, to ni ne zan jagoranci yaƙin. Babu wani aljani da ya isa ya gaya min wadda zan so!" Ya kalli sararin samaniya, yana jin yadda Ayat take fama da numfashi a cikin ruwa. Ya tura mata wani irin sanyin ƙarfi ta hanyar iska domin ta jure sanyin ruwan da take ciki... ✨ Inuwa ya ɗago daga cikin ruwan bayan minti biyar, numfashinsa yana fita sama-sama "ha...ha...ha".. Ruwan yana wuyansa, idanunsa sun yi jawur saboda sanyi da juriya. Rawani yana nan daram a kansa, ya jike jagaf ba tare da ya faɗi ba domin an ɗamara shi sosai... Cikin mamaki da fushi Master ya ce, "Wai kai Inuwa, meye a cikin rawanin nan da ya fi karfin a cire shi? Ka taɓa ganin soja yana horon nitsawa a ruwa da rawani? Wannan wane irin iskanci ne?" Inuwa ya ce, "Master... kayi hakuri. Al'ada ce ta gidanmu, ba ma taɓa barin kanmu a fili..." Master Ibrahim ya matso har bakin tafkin, ya duƙa ya kalli kwayar idon Inuwa. Ya kasa gane dalilin da yasa wannan yaron yake da kishin kai haka.. "Ban yarda ba! Soja ba shi da al'ada idan umarni ya zo. Oyaa, cire rawanin nan yanzu ka miƙo min shi, sannan ka sake nitsawa ba tare da komai a kanka ba! Maza kai nake jira...!" Inuwa ya fara zuru-zuru da idanu. Zuciyarsa ta fara dukan uku-uku.... Idan ya cire rawanin nan, sumar gashinta mai tsawo zai zubo, kuma vest ɗin dake jikinta zai iya bayyana siffarta ga kuma wandon jikinta tyt ne, surar hips ɗinta zai bayyana idan ta fito... Master Ibrahim ya daka wa Inuwa tsawa, muryarsa tana sake ruri a sararin tafkin... “Maza cire rawanin nan yanzu! Idan har ba ka da abin da kake boyewa, me ya sa kake gudun umarni na?” ​Hannun Ayat ya fara rawa, ta kai shi saman rawaninta, tana jin kamar rayuwarta za ta kare a wannan lokacin. Ruwan sanyi ya ratsa ta, amma gumi ne yake keto mata a goshi. A ranta take furta, “Ya King Diamond… ka ce za ka kare ni, ga shi asirina yana shirin tonuwa.” ​A daidai lokacin da yatsun Ayat suka fara kwance rawanin, sai aka ji sautin takun takalman soja, taku ne mai nauyi da kwarjini... Wani jami’i ne sanye da kakin masarauta, ya bayyana a cikin kamannin wani babban jami'i dake kusa da sarki, wanda ya fi master miƙami.. Kwarjininsa ya sa Master Ibrahim dakatawa da abin da yake yi... ​“Master Ibrahim!” Muryar jami’in ta dake wajen, muryar da take cike da izza... ​Master Ibrahim ya firgita, ya juyo da sauri ya ga babban jami’in tsaye. Nan take ya gyara tsaiwarsa ya sara masa... “Yallabai! Ban yi tsammanin ganinka a nan ba.” ​Jami’in wanda ya kasance King Diamond ne a wannan suffar bai ko kalli inda Ayat take ba, amma iskar da take kewaye da shi ta zama mai ɗumi, tana ba Ayat wani irin kwarin gwiwa... “Sarki yana bukatar ka a fada yanzu! Akwai baƙi daga Masarautar Arewa da suka iso, kuma kai ne aka zaɓa ka jagoranci tsaron taron sirrin da za a yi.” ​Master Ibrahim ya yamutsa fuska, ransa ya ɓaci domin yana tsaka da koyar da horo ne.... “Amma Yallabai, ina tsaka da horar da wannan yaron ne, akwai wani abu da nake so in tabbatar...” ​Jami’in ya daka masa tsawa, idanunsa suka yi wani irin walƙiya da ta sa Master Ibrahim jin tsoro a karon farko... “Umarnin Sarki ya fi son ranka mahimmanci, ko kuwa kana son ka sabawa masarautar ne?” ​Master Ibrahim ya sadda kansa ƙasa. “Ayi hakuri Yallabai. Zan tafi yanzu.” Ya juyo ya kalli Ayat wadda take raɓe a cikin ruwa... “Inuwa, ka tashi ka fito! Ka gode wa Allah da aka ƙira ni, amma horar gaba na nan tafe... Gobe za mu dora daga inda muka tsaya.” ​Master Ibrahim ya ruga da gudu ya bar wajen... Jami’in ya tsaya na wasu daƙiƙu, ya kalli tafkin. Ko da yake bai ce komai ba, Ayat ta ji wata murya a cikin kanta tana cewa.. “Kiyi maza ki fito ki shirya kanki, masoyiyata. Ba zan bar wani ya taɓa sirrin da yake nawa ba.” ​Kafin ta farga, jami’in ya ɓace kamar hayaƙi a cikin iska. Ayat ta saki wani babban ajiyar zuciya, ta jawo jikinta ta fito daga ruwan, tana hawayen farin ciki da kuma fargabar abin da zai biyo baya gobe... Ko da Master ya je, Sarki ya sanar masa cewa, akwai wani binciken da zasu gudanar... Duk da ƙiran da King Diamond yayi masa duk na ƙarya ne... ✨✨✨ Gimbiya Zayana tana zaune a takure a kusurwar dakin kurkukun, wanda babu komai a cikinsa sai zafi. Iskar dakin tana da wani irin wari na danshi... Ga wasu ƙattai da miagun sauraye waɗanda suka addabi jikinta, duk inda ta shafa sai ta ji sun mata tabo... Yau kwana uku ke nan, amma a wajenta kamar shekara guda ne. Babu waya a hannunta da za ta ƙira kowa, babu wata ƙawarta ko hadima da aka bari ta matso kusa da sashen. Shirun wurin yana mata nauyi a kwakwalwa, har ta fara magana ita kadai... Muryarta a dashe saboda kuka, "Abul... ashe haka kake? Don kawai na nuna bacin raina akan cin fuskar da kake mun a cikin mutane, shi ne ka yardar da ni a nan? Ko duba ni ba za ka yi ba?" Sau ɗaya kacal a rana ake turo mata da abinci, wanda ko karnukan masarautar ba su taɓa ci ba. Ruwan sha kuma a gora ake ɗuro mata a ajiye shi sai ya daɗe bai isa gare ta ba... Zayana ta kalli abincin dake gabanta, ta tura kwanon gefe tana kuka... "Ba zan ci ba! Gara na mutu a nan kowa ya huta. Yanzu haka Maayah tana can tana cin abinci mai daɗi cikin kwanciyar hankali, ga Ayat da Yumna kuma su ma suna can suna shawagi a fada... ni kuma an mance da ni." Damuwar ta kai matakin da Zayana ta fara ganin jiri. Ta dora kanta a gwiwoyinta, tana tunanin mahaifiyarta dake can Sydney... "Mommy... da kin san abin da ke faruwa dani da wannan masarautar ya gama amfani... Yanzu babu wanda zai sanar miki halin da nake ciki?...." Bayan kwana ɗaya... ​Master Ibrahim ya kasa zaune, ya kasa tsaye. Duk da shi ne ya rufe Zayana, amma zuciyarsa tana gaya masa cewa kwana huɗu a cikin cell ga gimbiya irin Zayana ya isa tarbiyya. Ya san Sarki ya fusata ne saboda rashin kunyar da ta yi masa a gaban kowa, kuma hakan ya taɓa kwarjinin sa na uba kuma sarki... ​Master ya nufi sashen Sarki, ya same shi zaune yana duba wasu taswirorin ƙasa, fuskarsa a murtuke kamar babu sauran rahama a cikinta. ​Master Ibrahim ya duƙa har ƙasa, ya gaishe da Sarki cikin girmamawa. ​ "Ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka tsawon rai da lafiya. Na zo ne domin in gabatar da wata magana akan Gimbiya Zayana." ​Sarki bai ɗago kai ba, ya ci gaba da abin da yake yi. "Idan maganar fito da ita ce, to ka adana baki ka fita daga nan, Ibrahim." ​Master Ibrahim ya ce, "Ranka ya daɗe, na sani cewa ta yi babban kuskure na rashin kunya gare ka. Na san hakan ya yi maka zafi, kuma horon da take ciki ya dace da abin da ta aikata. Amma na duba yanayin lafiyarta, na ga damuwa da rashin abinci sun fara canza mata kamanni. Ina tsoron kada wani abu ya same ta kafin ta gane kuskurenta." ​Sarki ya ɗago, idanunsa sun yi ƙuri akan Master Ibrahim... ​ "Ibrahim, ka san ni sarai. Bana taɓa jure raini daga kowa, ballantana daga jini na. Rashin kunyar da Zayana ta yi min a gaban mutane, ya nuna cewa ban yi nasarar ba ta tarbiyya ba. Idan na fito da ita yanzu, na nuna mata cewa za ta iya yi min duk abin da ta ga dama ne." ​Ya ja numfashi, sannan ya ci gaba.. "Zan bar ta ta ci gaba da zama a can, har sai ta koyi yadda ake magana da uba, kuma har sai ta roƙi gafarar mutuncin da ta tattaka." ​Master Ibrahim ya ga Sarki bai nuna alamar sassauci ba, sai ya yi dabarar kawo maganar mahaifiyarta dake can.. ​"Ranka ya daɗe, idan mahaifiyarta ta ji labarin cewa gimbiyar tana cell, na tabbata za'a samu babban matsala sosai. Amma idan ka ba ni izini, zan riƙa duba ta, kuma zan matsa mata har sai ta amince za ta ba ka haƙuri." ​Sarki cikin fusata ya ce, "inason labarin ya je kunnenta, duk abinda suka ta ka ita da ƴar zan magance shi...bana tsoronta don haka kabar maganar nan kawai tin kafin ranka ya ɓaci kaima..." Master bai ƙara cewa uffan ba, ya miƙe ya ja jikinsa ya tafi... Yau ranar da ake ta shirye-shiryen gudanar da walimar sauƙar al'kur'ani... Masarautar Alhamra ta cika da baƙi daga sassa daban-daban na duniya domin halartar taron sauƙar Alkur'ani na Gimbiya Ayat da Gimbiya Yumna. An tsara taron yadda duniya za ta ba da misali, inda manyan malamai za su shaidi tilawar gimbiyoyin... Ayat tana zaune a ɗakinta, kanta cike da sarƙaƙƙiya. Zuciyarta tana gaya mata cewa wannan ranar ita ce mafi haɗari a gare ta. Dole ta bayyana a matsayin Gimbiya Ayat don yin tilawa a gaban malamai.. Amma kuma, matsayinta na Inuwa yana nufin dole tana filin taron tana tsaro, musamman yadda Master Ibrahim ya matsa kaimi akan tsaro... Tana cikin wannan raɗaɗin tunanin, tana kiran King Diamond a ranta, sai ta ji sanyin kamshinsa ya cika ɗakin.. King Diamond ya bayyana a gabanta, tsaye daram cikin kwarjininsa. Ayat ba ta san lokacin da ta tashi da gudu ta rungume shi ba saboda tsananin kewar da take masa. Ta ɗago kanta da sauri tana shirin bayyana masa matsalarta, amma sai ya ɗora yatsansa akan laɓɓanta... "Ba sai kin yi magana ba. Na riga na saurari maganar zuciyarki, kuma na san damuwarki." Ya kalli cikin idanunta, muryarsa mai ratsa jiki ta ci gaba "Ke za ki kasance Gimbiya Ayat, ki fita taron ki yi tilawar Alkur'ani kamar yadda kika yi buri. Ni kuma, zan rikkiɗa in koma Inuwa, zan tsaya a matsayinki na soja mai tsaro. Babu wanda zai gane bambancin." Ayat ta sake rungume shi a karo na biyu, tana jin wani irin sanyi a ranta... Ta ɗago tana kallonsa cikin mamaki... "Ta yaya kake iya shigo wa cikin fadar nan cikin sauƙi? Masarautar nan tana da shingen tsaro na aljanu masu ƙarfi, amma kake ratsa su?" Cikin gajeriyar magana da murmushin isa ya ce, "Ta ƙasan ƙasa nake shigo wa... babu shingen da zai iya dakatar da ni daga isowa gare ki." Suka fara tattaunawa cikin wani salo mai cike da ƙauna. Ayat tana jin yadda zuciyarta take narkewa a duk lokacin da yake kusa da ita. Ta manta da duk tsanar da take masa a baya, yanzu soyayyarsa ta zama jinin jikinta. Amma duk da haka, saboda izza ta sarauta da kuma nuna kada ya raina ta, sai ta fara janyewa tana yatsine fuska... Ta furta "Kada ka zata don na rungume ka shikenan na daina jin haushinka. Na yi hakan ne kawai don ina buƙatar taimakonka a gobe.... Amma idan ka gama, kowa ya san inda yake." King Diamond ya saki wani ƙasaitaccen murmushi, ya matso kusa da ita har tana jin ɗumin numfashinsa.. "Kin fi kowa sanin cewa zuciyarki ba haka take faɗa ba. Amma zan bi ki a yadda kike so... Gimbiya ta." Ayat ta kawar da kanta gefe, tana murmushin jin daɗi a ɓoye wanda ba ta son ya gani... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 3️⃣6️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Tun daga ranar yau, fadar ta rikkiɗa ta koma kamar wata duniya ta daban... Wurin zaman baƙi an shimfiɗa taguwar darduma mai kalar sarauta wadda aka kawo ta musamman daga ƙasar Iran... An jera kujeru na zinare ga manyan sarakuna da malaman da aka gayyato daga ƙasashen Larabawa da Afirka... An ƙawata fandis da furanni na gaske waɗanda ƙamshinsu ke ratsa ko'ina. A tsakiyar fandis ɗin, an ajiye wasu ƙasaitattun kujerun karatu guda biyu, waɗanda aka ƙera su da itacen Sandalwood da aka yi wa ado da azurfa... Da daddare, an kunna dubban fitilu masu launin ruwan zinare da azurfa, waɗanda suka sanya daukacin fadar yin haske kamar rana.... Gari ya waye, baƙi sun cika masarauta maƙil. Kowa yana son ganin wannan rana ta musamman.. A sashen Gimbiya Yumna, fara'a ce ta gauraye da ibada. Ba ta da ko ɗigon baƙin ciki a ranta, zuciyarta fari ƙal take kamar kalar shigarta. Bayinta waɗanda ta ɗauke su kamar ƙawayenta, suna ta hidima a kanta.. Ta saka wata doguwar rigar gown na alfarma mai kalar Cream da aka lulluɓe ta da duwatsu masu sheƙi na Swarovski... An rataya mata wani farin Sash mai ɗauke da rubutun... (HAFEEDHAH: GRADUATE OF THE HOLY QUR'AN) Ta saka takalmi High Heels masu sheƙi waɗanda ke ƙara mata tsayi da ƙasaita... ✨✨ 🖤 GIMBIYA AYAT A can nata sashen, Ayat tana shirya kanta cikin natsuwa. Ko da yake ita ma tana cikin farin ciki, amma sirrinta yana nan a ɓoye. Babu wanda ta bari ya taɓa fuskarta duk da cewa yau ce ranar da duniya take son ganinta... Ta saka wata doguwar riga golden gown mai matuƙar tsada, wadda aka yi mata ado da zaren siliki. Ta yi wa kanta ƙayataccen Rolling na mayafi wanda ya rufe mata kyakkyawar fuskarta wato Niqab style, sai dai idanunta kawai dake sheƙi kamar lu'ulu'u... Ta sanya wasu dogayen takalmi white Diamond Heels waɗanda suka daidaita takunta na jinin sarauta... Ta maƙala nata lambar yabon mai rubutun.. (AL-QARI'AH: THE QUEEN OF TILAWAT)... Bayan Ayat ta gama tsara kanta cikin kwarewa, sai masu kula da ita suka shigo ɗakin cikin girmamawa. Sun zata za su taimaka mata wurin kwalliya, sai suka ga ta riga ta gama komai, tana tsaye kamar wata tauraruwar da aka sauko da ita daga sama, fuska a rufe amma kwarjininta ya cika ɗakin... "Gimbiya, kowa yana jiran ki a filin taro." in ji ɗaya daga cikin hadiman.. Ayat ta jinjina kai, zuciyarta na bugawa. Ta san cewa yayin da take tafiya zuwa filin taron a matsayin Gimbiya, masoyinta King Diamond yana can tsaye a matsayinta na Inuwa, yana kallonta ta bayan rawaninsa.... Ta ce dasu "ku je, gani nan sauƙo wa.." Haka duk suka juya, ita kuwa kafin ta gama duka kanta sai ga King Diamond ya bayyana, ganinsa yasa ta firgita domin har ta tsora saboda zuwan ba zata... Ta ɗago tana kallonsa cike da mamaki ta ce, "ina shigar da kace zakayi a matsayin Inuwa?..." King yayi murmushin gefen baki sannan ya furta, "Ina so na zama mutum na farko da zai baki kyauta a wannan rana ta farin ciki..." Daga nan ya ware tafin hannunsa sai ga wani tsararren sarƙa mai sheƙi da rubutun sunanta a ɗan ƙasin sarƙar....shi da kansa ya ɗaura mata a wuya, sannan ya sanya mata zoben sarƙar tare da sumbatar ta akan goshi... Daga nan ya ɓace.. Murmushi tasau ita kaɗau tasan irin shauƙin da take ciki yau.. ✨ Kamar yadda aka tsara, taron ya kankama. Filin fadar ya cika makil da sarakuna, manyan malamai, da jakadu. Lokacin da kiɗan sarauta na musamman (Trumpets) ya kaɗa, sai daukacin taron suka mike tsaye... Gimbiya Yumna ce ta fara fitowa, tana murmushi mai cike da annuri. Takunta cikin hills ɗinta yana bayar da sauti a hankali tak.. tak.. tak.., sannan aka biyo bayanta da Gimbiya Ayat... Ayat tana tafiya ne kamar tana shawagi a iska. Duk da fuskarta a rufe take da mayafin gown dinta da ta yi masa Rolling na musamman, amma kwarjinin idanunta kadai ya isa ya sanya mutane faɗuwan gaba. Waccan Sash dake jikinta mai rubutun AL-QARI'AH tana ta sheki karkashin hasken fitilu. A gefen fandis inda ɗaukacin tsaro yake, Master Ibrahim yana tsaye da babban mukaminsa. A kusa da shi, King Diamond ne a matsayin Inuwa, sanye da kakin soja mai muƙami, fuskarsa sanye da rawani yadda babu mai gane shi. Master Ibrahim ya daɗe yana lura da yaron nasa na yau... Cikin raɗa ya ce "Inuwa, yau kuma wane irin shiru ne haka? Tun da safe baka ce uffan ba, baka ma motsi. Kwarjinin taron ne ya firgita ka ko kuwa me?" King Diamond bai ko kalle shi ba, bai kuma ba shi amsa ba. Ya tsaya ne kamar gunki, idanunsa na kyam akan Ayat dake takowa... Wani irin kallo yake mata, kallon kariya da kuma tsananin shauki.. Master Ibrahim A ransa ya furta "Wannan yaron yau kam ya sauya min, kwarjininsa ya ninka na kullum sau ɗari. Kamar ma ba mutum ne tsaye a kusa da ni ba!" Bayan an zauna, aka sa karatun Kur'ani mai ratsa zuciya da jiki, sannan akayi wa'azi akan masu karatun Alkur'ani... Bayan nan ne aka buƙaci sauraron karatun masu sauƙa..Aka ba Gimbiya Yumna dama ta fara tilawa... Ta karanta surori cikin daɗi da natsuwa, kowa ya jinjina mata. Amma lokacin da aka ƙira Gimbiya Ayat, filin taron ya yi tsit kamar babu rai a cikinsa... Ayat ta matso gaban babban makirufo. Ta gyara zamanta, sannan ta fara sakin muryarta cikin Suratur-Rahman.. _"Ar-Rahman... 'Allamal Qur'an..."_ Muryar Ayat ta fito cikin wani irin sauti mai daɗi, mai sanyi, kuma mai ratsa jiki. Ba muryar ɗan adam bace kaɗai, domin King Diamond yana can tsaye yana tura mata wani irin taimako na spiritual aura wanda ya sa muryar ta riƙa amsa a cikin zukatan mutane... Manyan Malaman dake zaune a sahun gaba suka fara zubar da hawaye. Wasu sarakunan suka sauƙe kawunansu ƙasa saboda tsananin tasirin ayoyin. Muryar tana tashi tana faɗuwa cikin kwarewa ta musamman... A daidai lokacin da Ayat take kaiwa kololuwar karatunta, ta ɗago idanunta ta kalli inda Inuwa yake tsaye. Idanunsu suka sarƙe da na King Diamond. A wannan lokacin, Ayat ta ji wani irin karfi ya shigeta, ta sani cewa masoyinta yana nan kusa da ita, yana kare mata sirri da kuma kwarjini... Shi kuma King Diamond, duk da siffar Inuwa dake jikinsa, murmushin nan nasa na gefen baki ya bayyana a ɓoye. Yana jin alfahari da wannan gimbiyar tasa wadda duniya take kuka saboda dadin muryarta... Master Ibrahim ya lura da wannan kallon na Ayat, ya sake kallon Inuwa... Zuciyarsa ta buga "Me yake faruwa tsakanin Gimbiya da wannan Guard ɗin nawa? Wannan kallon ya wuce na soja da gimbiyarsa!" Duk da cewa Maayah ba ta cikin masu saukar Alkur’ani saboda waccan matsala ta karatun, hakan bai hana ta nuna cewa ita ma gimbiyar masarautar Alhamra ba ce. Ta fito cikin shigar alfarma, sanye da doguwar riga mai kalar maroon da aka yi wa ado da duwatsu zinare... Bayinta na take mata baya, tana taku cikin isa har ta isa mazauninta ta zauna, tana kallon kowa da kallon ko oho... Ita a ganinta, taron ma ya isheta, domin babu ita a ciki. Tana nan zaune tana kallon jama'a, sai kwatsam idonta ya sauƙa akan kofar shigowa... A daidai lokacin ne Uncle Jalal ya shigo harabar fadar. Ya zo ne a kan wani babban Superbike mai launin baki da ja, irin wanda ake tseren gudu da su... Ya cire babban Helmet dinsa, gashin kansa ya dan hargitse kadan wanda hakan ya kara masa wani irin kwarjini na daban... Yana sanye da farar riga ta alfarma da aka yi wa ado da baƙin zare a wuya. Takunsa ɗaya bayan ɗaya ya ƙarasa cikin taron, inda aka ware wa malamai gurbi. 🔥 Ganin Uncle Jalal ya sa kirjin Maayah bugawa Dub-dub-dub!. Wani irin kishi da haushin marin da ya mata a makaranta ya taso mata, amma kuma kwarjininsa yana tsorata ta.. Ta riƙa watsa masa wasu harara masu zafi, tana turo baki gefe ɗaya, tana so ta nuna masa cewa har yanzu ba ta yafe masa ba. Duk lokacin da Uncle Jalal ya kalli ɓarin da take, sai ta yi fari da ido ta juya kai tare da jan tsaki Tcheeeew a ranta, amma bakin na nuna alamun tsaki saboda tana turo shi ne.... Shima Uncle Jalal ya hango ta. Ya kalli inda take zaune, ya ga yadda take faman harara. Maimakon ya biye mata, sai ya yi wani dan murmushin gefen baki, murmushin da yake nuna kina nan dai a karkashi na... Ya gyara zamansa ya mayar da hankalinsa kan tilawar da Ayat take yi, kamar bai ma san tana yi ba.. Wannan ya kara wa Maayah haushi. Ta ji kamar ta tashi ta je ta shashshaƙe shi... Yayin da fada take ta ɗaukan karatun Alkur'ani, can bayan fada a cikin Cell, Gimbiya Zayana tana takure. Sautin muryar Ayat dake tilawa yana dako wa har cikin kunnenta ta jikin katangar kurkukun... Tana kuka tana shakar warin wurin da sanyi. Babu mai tunawa da ita, kowa yana murnar saukar Ayat da Yumna.... Zayana ta kifa kanta a gwiwa, tana jin yadda duniya ta yi mata zafi... Ana tsaka da raba albarkar karatun Alkur'ani, sai aka fara jin wani irin ruri daga sararin samaniya. Iska ta hargitse, rawuna da mayafan mutane suka fara tashi. Kowa ya ɗaga kai sama, sai aka hango Jirage guda goma masu kalar bakin karfe suna shawagi, kafin su fara sauƙa ɗaya bayan ɗaya a filin dake kusa da fadar... Sarki ya miƙe tsaye, yana tunanin ko wani babban bako ne ya kawo ziyara ta ba-zata don taya shi murna. Amma yana ganin tambarin dake jikin jiragen, tambarin Sarkin Pavilion sai gabansa ya bada wani sauti... Kofofin jiragen suka buɗe, hayaki mai sanyi ya fara fitowa. Daga ciki, Chief Onyx ya fito da wani irin takun isa da kwarjini.. Yana sanye da wata doguwar bakar riga har ƙasa, amma botirorin gaban rigar a bude suke, wanda hakan ya bayyana riga da wando na suit dake ciki... Rabin fuskarsa a rufe take da wani karfen azurfa wato Silver Mask wanda ya kara masa kwarjini da firgitarwa... A gefensa, katafaren Robot ɗinsa wato Gely, wanda take tafiya tana fitar da sautin karfe, sannan dimbin sojojinsa da Bodyguards na take masa baya... Sarki yana tsaye daram, duk da kwarjininsa, amma ganin Chief Onyx ya sanya shi jin wani irin yanayi na dar-dar. Shi kansu baƙin da malamai, kowa ya shiga ruɗani, domin Chief Onyx babban makiyin masarautar ne, kuma zuwansa a yau ba tare da gayyata ba alama ce ta tashin hankali...Duk da matsayin ƴan uwa suke. Master Ibrahim ya damke hannun takobinsa, ya matso kusa da Inuwa.. "Inuwa, ka kasance cikin shiri. Wannan mutumin bai zo da alheri ba. Onyx ba abokan wasa ba ne..." Yayin da kowa ya tsorata da saukar Chief Onyx da Robot dinsa Gely, Uncle Jalal yana zaune daram, ko kwayar idonsa bata motsa ba. Ya kalli Onyx ne kawai a matsayin wani baƙo, ba tare da fargaba ba... Maayah ta kalli Uncle Jalal ta ga ko zai nuna tsoro, amma ganin yadda ya hadiye natsuwa ya sanya ta kara jin kwarjininsa a ranta... Sarki ya ɗaure fuska, amma a cikinsa fargaba yake yi kada Chief Onyx ya tona asirin cewa Yumna ba jininsa bace, kanwarsa ce shi da Reems.. Sarki ya riƙe ta ne tun tana jaririya don boye asali, kuma ya nemi alfarmar Onyx kan kada kowa ya sani. Yumna ta ji zuciyarta na wani irin bugu. Tana son ta mike ta ruga ta rungume dan uwanta Onyx, amma alkawarin da ta yi wa Sarki na boye dangantakar su ya sanya ta tsumaye a mazauninta, idanunta cike da hawayen farin ciki da raɗaɗi... Ayat ta kalli Chief Onyx, wani irin ɗaci ya ziyarci makogwaronta. Ta tuna yadda ya tafi da Autar sarki, wato kanwarta uwa daya uba daya, ya mayar da ita baiwa a Pavilion. Ta so ta mike ta shaƙe shi, amma hasken Alkur'anin da ta gama karantawa ya sanya mata wata natsuwa, ta kasa motsawa sai dai kallon tsana... Chief Onyx yana takowa cikin isa, ya zo wucewa ta inda Inuwa yake tsaye... Lokaci guda, Chief Onyx ya ji tsikar jikinsa ta tashi, wani irin ƙiran jini ya ziyarce shi. Ya tsaya cak, ya juyo a hankali ya ƙura wa Inuwa ido... King Diamond wanda yake matsayin Inuwa shima bai ɗauke idonsa ba. Ya kalli Onyx har cikin kwayar idonsa, anan ya tabbar da akwai alaƙa a tsakaninsu... A ransa yana wani irin farin ciki na ganin twins ɗinsa da aka raba su tun suna kanana.. Chief Onyx ya zare idonsa cikin zargi. Ya tuna lokacin da ya zo daukar Autar sarki, ya ga wannan Guard din Inuwa, kuma a lokacin ya san mace ce. Amma yanzu da yake kallonsa, kwarjinin da yake gani ya wuce na mace, kuma wannan jan ragamar tsikar jikin da yake ji ya tabbatar masa akwai wani boyayyen abu a tare da wannan bawan... Ba tare da ya ce uffan ba, Onyx ya wuce ya je ya zauna a kujerar dake kusa da Sarki, ya shimfida ikonsa... Duk da wannan tashin hankalin, aka cigaba da rabon abinci da abin sha na walima... Maayah tana faman satar kallon Chief onyx Daman bata san shi ba, sai kawai labarinsa...ta haɗiye yawu a ranta take faɗin "Wayyoo, wannan ne Chief onyx? Tsararren sarki, wannan ya wuce yadda nake tunani...haɗaɗɗe da shi..." Amma da zaran idonta ya sarƙe da na Uncle Jalal sai ta fara yatsine fuska, tana nuna masa har yanzu dukan da ya mata yana nan a ranta. . Uncle Jalal ya ɗauki kofin ruwa ya sha, ya kalli Maayah ya girgiza kai kadan, yana mata kallon babu wanda zai saurari jahila fa... A daidai lokacin da Chief Onyx yake zaune yana kallon kanwarsa Yumna cikin alfahari, can Zayana tana ta faman dukan kofar cell ɗinta. Tin sautin jiragen da ta ji ya isa kunnenta, ta ɗauka mahaifiyarta ce ta zo... Domin tasan ba za ta ƙyale kowa ba... ✨ Chief Onyx ya ba da umarnin a shigo da wasu manyan akwatuna na zinare. Abubuwan dake ciki sun fi karfin kwatancin dan adam, akwai sarƙoƙi na duwatsun Ruby masu haske, akwai turaren da akayi masa haɗi na gaske wanda kamshinsa kawai zai iya warkar da marar lafiya, da kuma agogo na musamman da ke nuna yanayin tsaron jikin mutum... Bayan ya miƙa wa Sarki wani sirrin Memory Card wanda ganin haka yasa Sarki ƙara ruɗe wa, Chief Onyx ya nufi inda Yumna take... Ya durkusa a gaban Yumna, ya ɗora hannunsa a saman kanta cikin wani salo na girmamawa da kauna. Ya fara tofa mata addu'o'i cikin sanyi, yadda mutane za su ɗauka girmama karatunta yake yi... Yumna cikin muryar raɗa ta furta "Nagode Yayanaa..." Chief ya ce, "Kada ki damu, kyakkyawar kanwata. Ba zan taba barin ranar murnarki ta wuce ba tare da na shaidi nasararki ba." Ya sakar mata wani murmushi wanda shi kaɗai ne yake da shi, sannan ya tashi.. Domin kada mutane su zargi wani abu, Chief Onyx ya nufi inda Ayat take zaune domin ya bata nata kyautar... Ya natsu zai dora hannunsa a kanta don yi mata addu'a kamar yadda ya yi wa Yumna, amma kafin hannunsa ya taɓa mayafin kanta, Ayat ta buge hannun da wani irin zafin nama... "Kada ka kuskura ka matso kusa da ni! Ka janye wannan hannun naka mai cike da jinin mutane!...Ba na son ko iskar jikinka ta gogi tawa!" Chief cikin muryar sanyi mai tsoratarwa ya ce, "Gimbiya, ina ƙoƙarin nuna miki girmamawa ne saboda wannan rana ta Alkur'ani, amma naga kina son wuce gona da iri." Ayat muryarta na rawa saboda kuka da bacin rai ta ce, "Girmamawa? Daga gare ka? Tun yaushe azzalumi ya san girmamawa? Ka gaya min, da wane ido kake kallon mutane a nan? Kana tunanin na manta ne? Na manta yadda ka shigo fadar nan ka fizge ƙanwata, jini na, ka tafi da ita cann a matsayin baiwa?" Taron ya yi tsit, kowa ya zura ido. Ayat ta ci gaba da magana cikin daka tsawa.. "Me ta yi maka? Me yarinya ƙarama kamar ta ta sani na gaba da mulki da za ka mayar da ita baiwa? Ka raba uba da ɗiyarsa, ka raba ni da kanwata ba tare da wani dalili ba! Ka sani sarai, duk ranar da na samu iko, sai na ga bayanka! Mugun banza, azzalumi!" Ran Chief Onyx ya ɓaci fiye da yadda kowa yake tunani. Kalmar Azzalumi da aka nanata a gaban baƙi da malamai ta soke shi... Ba tare da ya furta komai ba domin shi ba mai son hayaniya bane, cikin zafin nama ya zabga mata wasu lafiyayyun mari guda biyu a kunci biyu har sai da ta kife akan kujerarta... Marin ya sauka a kuncin Ayat da duk ƙarfin hannunsa. Marin ya kasance mai ƙarfi yadda har sai da hular Rolling ɗin kanta ta fice, ta dafe kuncinta tana kallonsa cikin rashin yarda tana ƙasi zaune... Sarki ya miƙe tsaye a gigice, amma kwarjinin Onyx da sojojinsa ya sanya shi daskarewa...domin a wannan ranar ba ya buƙatar tashin hankali domin ranar farin cikinsa ne, yana son duk baƙin da suka zo, su koma gida cikin ƙoshin lafiya... Master Ibrahim ya zare takobinsa, yana jiran umarni, amma ya san taɓa Onyx yanzu tamkar taɓa wutar lantarki ne... Sarki ne ya ɗaga musu hannu akan su ajiye makamansu... King Diamond ya dunƙule hannunsa har jijiyoyinsa suka fito raɗau... Idanunsa suka fara rikiɗe wa zuwa launin blue...Yana jin kamar ya bayyana asalin sa ya fatattaka Chief Onyx a nan, duk da jikinsa na gaya masa akwai alaƙar jini a tsakaninsu....kuma alkawarin da ya yi wa kansa da kuma sirrin Ayat ya sa ya tsaya yana rawar jiki saboda bacin rai... Ayat tana dafe da kuncinta, idanunta suka cika da hawayen radadi da wulakanci, tana kallon Chief Onyx wanda yake huci kamar zaki.... Uncle Jalal ya miƙe tsaye ganin haka, kwarjininsa ya cika wajen... Ya kalli Chief Onyx ba tare da tsoro ba.. "Haba bawan Allah, wannan ba halin girma ba ne. Ka daki mace a gidan mahaifinta a ranar farin cikinta?" Chief Onyx ya juyo ya kalli Uncle Jalal cikin sauri, idanunsa suka rine... "Kai kuma wanene da za ka sa baki a harkar Pavilion da Alhamra?" Maayah tana hararar Uncle Jalal a cikin ranta take faɗin "Ku ji! Ku ji!! Munafiki, jiya ka gama duka na makaranta amma yanzu kana magana akan dukan mace..." King Diamond zuciyarsa ta gama harzuƙa, wani irin hasken shuɗi ne ya bayyana a cikin kwayar idonsa... Ya ɗora hannunsa akan makamin dake ƙugunsa, yana jiran kawai ya ga Ayat ta zubar da hawaye na biyu don ya fito da dukkan asalin sa ya koya wa Onyx darasi, ko da hakan zai tona asirinsa... Ayat dake ƙasi har yanzu tana riƙe da kunci, ta kalli yadda King Diamond yake domin tasan dole zai ce zai aiwatar da wani abu, ganin yanayinsa ya sauya hatta idonsa yasa tayi sauri girgiza masa kai akan ya dakata... Haka ta fara masa magana ta zuci.. "Ka da kayi komai, ka bari, ka koma yadda kake, Master Ibrahim zai kalleka yanzu, ka koma..." Dai-dai lokacin da master ya kalli Inuwa wanda yayi ready zaro ido, King bai bari ya ga yanayin da yake ciki ba... Gely kuwa ta nufi Uncle Jalal da wani irin gudu na inji. Ganin Boss dinta ya fusata, ta yanke shawarar koya wa wannan mutumin darasi, ya daina shiga shirgin da bai shafe shi ba... Uncle Jalal, wanda asali jarumi ne kafin ya zama malami, bai girgiza ba. Ya fizge takobi daga hannun wani jami'in tsaro dake kokarin buya a karkashin teburi. Gely ta matsa wasu maballai a hannunta, nan take wani takobi mai dauke da wutar lantarki ya fito daga jikinta... Sai ƙarar Kwang! Kwang! Kwang ake ji... Sautin takubansu ya riƙa tashi. Uncle Jalal yana kare kansa cikin kwarewa, yayin da Gely take amfani da karfin karfe... Maayah tana can takure, zuciyarta na bugawa. Tana hawaye tana cewa, "Don Allah kar a kashe shi!" Duk da dukan da ya mata, ta gane cewa rayuwarta ba za ta taba zama ɗaya ba idan babu Uncle Jalal.. Ayat ta kasa jurewa. Marin da ya mata da kuma tunanin kanwarta da yake hannunsa ya sanya ta rasa nutsuwa...Ta miƙe tare da zaro wata matacciyar takobi, ta kewaya ta bayan Chief Onyx tana nufin soka masa a tsakiyar bayansa... Shi kuwa Chief tin tinin ya ga yanayin jami'in tsaro wato Inuwa wanda King Diamond ne, tin daga lokacin da ƙwayar idonsa ta koma shuɗi, Chief onyx ya ri ga da ya gane cewa shi ɗin ba kowa bane face REEMS... Ya gano komai yanzu, domin Chief na da saurin fahimta da hangen nesa, tinin ya gane cewa akwai alaƙa a tsakanin Reems da Ayat, kuma a baya yasan Ayat ce take matsayin guard, saboda a yau dole ta fito a matsayin gimbiya da kuma guard yasa Reems taimaka mata..gaba ɗaya ya tafi dogon tunani, idonsa na kan King Diamond... Ganin Ayat tayi baya da takobi zata soka masa, gaba ɗaya mutane suka zaro ido a gigice, har sarki kam ya daskare a yadda yake.. "Ayat! Don Allah kada ki yi haka!" Yumna ta dakawa Ayat tsawa cikin tashin hankali... Kafin Bodyguards ɗinsa su ankara domin suna ɗan nesa da su.. Amma Ayat ba ji ba gani.. Ta tura wukar da nufin kashe shi, amma Chief Onyx kamar mai idanu a baya, ya sa hannunsa ya cafke bakin takobin daidai lokacin da zai taba jikinsa... Ayat ta yi firgigit, ta yi kokarin fizge takobin ta yadda za ta feɗe masa tafin hannu, amma sai ta ji takobin kamar an manne shi a cikin dutse. Chief Onyx ya rike wurin kaifin wukar sosai ba tare da hannunsa ya tsage ba ko da digon jini ɗaya... Sojojin Pavilion sun nufota da gudu, amma Onyx ya ɗaga musu hannu su tsaya. Sarki ma ya dakatar da dakarunsa don kada a fantsama cikin yaƙin da ba za su iya ba... Chief Onyx ya saki wani murmushin gefen bakin nan nasu domin a jininsu yake, sannan ya yi wani uban janyo, ya jawo Ayat tare da takobinta. Saboda karfin jan, Ayat ta tafi luuu ta faɗi a gabansa tana huci... Chief ya kalle ta kyau sannan ya furta.. "Matsalo ne kawai yake kawo farmaki ta baya... Ki kiyaye gaba yarinya. Ƙarfin zuciya ba shi ke ba da nasara ba, sai idan an haɗa da ƙwarewa..." Ya ɗaga wa Gely hannu, nan take ta janye takobinta ta kyale Uncle Jalal, wanda shi ma ya sauƙe numfashi yana kallon wannan robot ɗin cikin mamaki, dake yana da kwarewa shima bai ba ta damar cutar da shi ba.. Chief bai sake cewa uffan ba, ya gyara bakar rigarsa, ya yi wa Sarki wani kallo na raini, sannan ya juya tare da bodyguards ɗinsa da Gely zuwa wurin jiragen su.. King Diamond ya bi su da kallo, idanunsa suna faɗin abubuwa da dama. Ya so ya bi ɗan uwansa amma ya san ba a wannan lokacin ba... Sarki yayi wani fusata ya miƙe tare da yo wa kan Ayat wadda take durkushe a ƙasa, tana karkarwa saboda raɗaɗin marin Onyx da kuma ɗacin zuciya...Bai tsaya wata-wata ba, ya fizgota da karfi ya sake zabga mata wani lafiyayyen mari wanda ya sa kanta sarawa.. ​Yana huci, idanunsa sun yi jawur ya ce, "Wace irin mahaukaciyar yarinya ce ke? Wace irin dabba ce ke da ba ki da tunani? A gaban waɗannan dubunnen mutanen za ki nuna wa duniya cewa ba ki da tarbiyya? Har kina da ikon fito da takobi ki nufi Chief Onyx?" ​Ayat ta ɗago fuskarta dake cike da hawaye ta cikin niƙab, muryarta na rawa cike da tauri... ​ "Abul... me ya sa ka kyale shi? Me ya sa ya zo ya ɗauke min kanwata ya tafi da ita Pavilion? Jini na ne ita fa!" ​Sarki ya sake daka mata tsawa.. "And so what? Kin fi ni son Ching-Ching ne? Ko kuma cewa aka yi miki cutar da ita yake yi a can? Ko kina tunanin Pavilion ɗin wasan yara ne?" ​Ayat ta ce, "Amma Abul... baiwa ya mayar da ita! Kanwata tana bauta a karkashin azzalumi!" ​Girgiza kai yayi yana zaro mata idanuwa.. "Baiwa? Wa ya gaya miki hakan? To ki shiga taitayinki! Onyx ba abokin wasanki ba ne. Shi wuta ne, kuma duk wanda ya taɓa shi sai ya ƙone ya zama toka. Shin idan aka barki dake da shi, kina tunanin za ki iya cin galaba a kansa ne? Kina tunanin takobi ɗaya zai kifar da Pavilion?" ​Ayat ta kalli takobin dake gefenta, wanda akwai jinin Onyx a jiki, ta yi wani murmushi na ɗacin zuciya.. ta ce, ​"Abul, ai ko yanzu na ci galaba a kansa. Dubi wannan takobin, jininsa ne a jiki. Ya riƙe takobi ta wurin kaifi, haƙiƙa salon jarumta ne, amma ko ba komai... na sa ya zub da jini a gaban mutanensa. Na taɓa fatarsa!" ​Sarki a ruɗe kuma cikin fushi ta ce, "To ke marin da ya zazzabga miki fa? Shegiyar yarinya! Ai shi wannan ɗan ciwon tafin hannun ba komai ba ne a wurinsa. Mutumin da yake yaƙar dubunnan sojoji shi kaɗai kuma ya rayu lafiya, don ya ji wannan raunin sai me? Ko a matsayin cizon sauro bai ɗauki wannan ba! Amma ke... kin janyo wa kan ki, kuma ki kiyaye ni!" ​Sarki ya juya cikin zafin rai ya kalli Uncle Jalal, wanda har yanzu yake rike da takobin da ya yi faɗa da Gely da shi... ​"Kai kuma Malam! Daga yau, kada ka ƙara kuskuren shiga maganar da ba ta shafe ka ba. Ka kame bakinka ka yi shiru kamar yadda kowa ya yi. Idan har kana son rayuwarka, to ka sani cewa takobinka ba zai taɓa kare ka daga fushin Pavilion ko na Alhamra ba. Kai malami ne, to ka tsaya a matsayin malami!" ​Uncle Jalal ya kalli Sarki, ya kalli Maayah dake can tana hawaye, sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin girmamawa amma ba tare da nuna tsoro ba. Ya san cewa yau ya kulla abota da mutuwa, amma bai yi dana-sanin kare mutuncin fadar ba... Taron ya watse cikin firgici da tsegumi. Masu sauƙar Alkur'ani duka sun koma sashensu cikin damuwa, yayin da fada ta ɓarke da wata irin hayaniya ta daban... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 37 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* A cikin katafaren jirgin Chief Onyx mai ɗauke da fasahar zamani ta Pavilion, shiru ya ratsa cikin jirgin, sai dai kawai sautin injin jirgin dake tashi a hankali. Chief Onyx yana zaune a kan wata kujera ta alfarma, idanunsa a lumshe, yayin da fuskarsa dake sanye da karfen azurfa take haskaka karkashin fitilun jirgin... Gely tana tsugune a gabansa, hannayenta na robot suna motsawa cikin kwarewa da sanyi. Ta riƙe babban hannun Chief wanda takobin Ayat ya ratsa. Tafin hannun ya tsage, jini mai kauri na digowa, amma Onyx ko kifta ido bai yi ba, kamar ba a jikinsa ake aikin ba. Gely ta kunna wani haske mai launin shuɗi (Laser treatment) daga yatsunsa, wanda yake bin asalin inda takobin ya yanke jikin. Tana goge jinin da wani lallausan kyalle mai ɗauke da sinadarin kashe kwayoyin cuta. Gely cikin muryarta mai sanyi irin ta na'ura ta ce, "Boss, raunin ya ɗan yi zurfi. Takobin yarinyar nan yana da kaifi na musamman. Me ya sa ka bari ta taɓa ka? Da ka ba ni izini da na raba ta da numfashinta tun kafin takobin ya karaso." Chief Onyx ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli tafin hannunsa dake ta konewa karkashin hasken Gely. Murmushin nan nasa na gefen baki ya sake bayyana... "Gely, wani lokacin jini yana bukatar ya zuba domin mu tuna cewa mu mutane ne. Yarinyar tana da jini mai zafi... jinin Alhamra ne yake yawo a jikinta. Tana bukatar tarbiyya, amma jarumtarta ta burge ni." Gely ta kammala ɗinke raunin da wani irin ɗinki na zamani wanda baya barin tabo. Ta shafa masa wani magani mai sanyi, sannan ta naɗe hannun da wani farin kyalle mai ɗauke da tambarin Pavilion... Chief Onyx ya dunƙule hannunsa don jin karfin dinkin, "Ina so ki sa ido akan wannan Guard ɗin. Akwai wani abu a tare da shi wanda ya fi karfin kwayar idon mutum. Tsikar jikina ba ta taba tashi a banza ba, kuma bisa alamun ba mutum bane...." Gely ta ce, "An gama Boss. Na riga na ɗauki hoton kwayar idonsa na tura wa babban kwamfutar Pavilion don bincike." Chief Onyx ya ƙura wa sararin samaniya ido ta taga, yayin da jiragen suke kutsawa cikin gajimare. Zuciyarsa tana can fadar Alhamra, yana tunanin ɗacin zuciyar Ayat da kuma kwarjinin Inuwa dake taɓa ruhinsa.... ✨✨✨ Sarki Nourdeen ya saka ƙaramin Memory ɗin a cikin na’urar kallo ta hologram dake falo ɗinsa. Nan take haske ya bayyana a tsakiyar ɗakin, hoton wani fili mai ɗauke da fasahar zamani ya bayyana. ​A tsakiyar hoton, Ching-Ching ce tana sanye da kayan makaranta mai kalar navy blue and white, fuskarta tana sheki da alamun wayewa da natsuwa. Tana zaune a gaban wasu manyan malaman bincike da malaman addini... ​Bidiyon ya fara nuna yadda ake jifan ta da tambayoyi masu wahala.. ​Fannin Kimiyya Malami ya tambaye ta game da tsarin kwayoyin halitta da fasahar makaman nukiliya. Ching-Ching ta amsa da yaren Turanci British Accent cikin kwarewa, tana bayani daki-daki kamar ita ce ta ƙera na'urorin... ​Fannin Addini kuwa Wani malami ya nemi ta yi bayanin wasu hadisai da ka’idojin ilimin Mantiq. Nan take ta sauya harshenta zuwa Larabci mai kyan gaske, tana kwararo hujjoji daga litattafan da sarki bai taɓa tunanin yarinya karama kamar ta za ta sani ba. ​Sarki Nourdeen ya daskare yana kallon allon, idanunsa sun cika da hawayen alfahari. Ya ga yadda diyarsa, wadda ya ɗauka tana can tana bauta a matsayin baiwa, ta zama wata kwararriyar malama kuma masaniya a karkashin kulawar Chief Onyx... ​Sarki cikin muryar raɗa ya furta "Masha Allah... ashe bawan nan Onyx bai yaudare ni ba. Ya mayar da Auta tauraruwa. Wannan ilimin ya wuce tunanin kowa." ​Ya gane cewa Chief Onyx ya ɗauke ta ne ba don wulakanci ba, sai don ya tafi da ita inda za ta samu ilimin da babu shi a Alhamra... Sarki ya sake tunawa da yadda Ayat ta kusan kashe Chief Onyx da takobi. Ya ƙara jin haushin Ayat a ranta... "Wannan yarinyar Ayat tana so ta lalata komai! Gata tana can tana zargin Onyx azzalumi ne, alhali gashi ya mayar mata da kanwa sarki-ta-fannin-ilimi. Idan ta kashe shi, wa zai cigaba da rainon Ching-Ching?" ✨✨✨ Sydney... Sarauniya Ruma tana zaune a cikin babban fadarta. Tana riƙe da wani kofin giya na alfarma, sai ga wani baturen ɗan leken asirinta ya shigo cikin gaggawa, ya zube a gabanta... ​Dan Leken Asirin ya ce, "Your Majesty... labari ya zo mana daga Alhamra. Gimbiya Zayana tana tsare a Cell yau kusan mako guda. Sarki Nourdeen ne ya sa aka rufe ta, tana cikin kaskanci, ba abinci mai kyau, ga kuma azabar sauraye da kadaici." ​Kofin dake hannun Ruma ya faɗi ya fashe, jan giyar cikinsa ta bazu a kasa kamar jini. Ruma ta mike tsaye, idanunta masu kalar kuliya suka rikiɗe suka koma wani irin kore mai firgitarwa. Wani irin ihu ta saki na ɓacin rai wanda ya sa ɗaukacin dakarun dake wajen ɗakin firgita... ​Ruma cikin muryar dake fitar da hayaki ta ce, "Nourdeen! Ka taɓa jini na? Ka taɓa guda ɗaya tilo da nake so a duniyar nan? Na gaya maka zan rusa Alhamra idan gashi ɗaya na kanta ya faɗi, ashe ba ka ɗauke ni da gaske ba!" ​Ta fara zagaye ɗakin tana numfashi sama-sama, kissar dake fuskarta ta ɓace, sai mugunta ta bayyana.. ​ "Ba zan tafi Alhamra yanzu ba. Ina so Nourdeen ya ji daɗin mulkinsa kaɗan kafin in ruguza masa shi. Amma daga yau, Alhamra ta daina sanin lafiya." ​Ta juya ga babban janar ɗin dakarunta na Sydney.. "Ƙira min dakarunmu na sirri. Ina so a fara gurgunta duk wata mashigar abinci da makami dake shiga Alhamra. Ina so mu fara shakarsu ta tattalin arziki kafin mu shakarsu ta wuya." ​Ta nufi taga, tana kallon birnin Sydney amma tunaninta yana can fadar Alhamra inda Zayana take kuka.. ​ "Nourdeen, ka sanya ɗiyata a cell saboda kana tunanin kai sarki ne? To zan nuna maka cewa ni mace ce da nake mulkar sarakuna. Zan sa ka roƙi mutuwa amma ba za ka ganta ba. Zan mayar da fadar Alhamra kango, inda jemage kawai zai rika shawagi. Kuma sai na fito da Zayana da kaina, sannan na sanya ka durkusa a gabanta kana neman gafarar jinin jiki na." ​Ta ciro wani takobi karami na azurfa, ta yanke tafin hannunta kadan, ta bari jinin ya digo a kan hoton Sarki Nourdeen dake kan tebur... "Wannan shi ne alkawari na na jini. Masarautar Alhamra za ta zama makabarta muddin diyata ba ta fito ba cikin kwana ɗaya ba... amma kafin nan, zan fara aikewa Nourdeen da sakonni da zasu sanya shi zazzabi." Bayan kwana ɗaya.. Sarki Nourdeen yana zaune a babban falonsa, yana duba wasu takardu sai ya ji wani irin sauti Buzzzzz... a bakin tagarsa. Wata karamar na'ura ce mai kalar azurfa, wadda aka kera ta a siffar tsuntsu, tana shawagi a iska. ​Sarki ya mike da sauri. Ya gane wannan fasahar, ta fadar dake Sydney ce. Na'urar ta shigo dakin, ta sauka a kan teburinsa, sannan ta bude wani dan karamin Screen na hologram. ​Fuskar Sarauniya Ruma ta bayyana a jikin hasken. Idanunta dake zubar da wutar fushi..cike da izza da sanyi mai ratsa kashi.. "Nourdeen... Na gaya maka kada ka taba jini na. Na gargade ka cewa muddin gashi ɗaya na kan Zayana ya faɗi, to masarautarka ta zama kango. Yau kwana shida diyata tana cikin cell cikin azaba, tana shan azabar da ko bawan da ka fi tsana bai cancanta ba." ​Sarki ya tsorata, ya fara zazzaro idanu. "Ruma... ta yaya kika sani?" ya fada a ransa... ​Ta ci gaba da magana kamar tana ganinsa... "Kada ka damu da yadda na sani. Ka sani kawai cewa, daga daren yau, barci ya tafi daga idanunka. Zan fara shakƙun tattalin arzikin Alhamra tun daga Sydney har zuwa sauran kasashen duniya. Idan har Zayana ba ta fito daga wannan cell din ba cikin sa'o'i ashirin da hudu ba, to zan aiko maka da kawunan jakadunka guda 50 dake nan Sydney a matsayin kyautar karin kumallo'." Daga nan ​hoton ya ɗauke, ​Sarki Nourdeen ya zauna a kan kujerarsa, gumi ya fara keto masa duk da sanyin dake ɗakin. Ya san Ruma mace ce mai cika alkawari, musamman idan aka taɓa Zayana. Idan har ta fara gurgunta kasuwancinsa a Sydney, Alhamra za ta shiga matsin lambar da zai iya jawo bore daga talakawa... ​Yana magana shi kadai.. "Yanzu idan na fito da Zayana saboda tsoron Ruma, zan zama rago a idon mutane. Idan kuma na bar ta, Ruma za ta rusa min masarauta. Me zan yi?" A wannan lokacin, Master Ibrahim ya tura kofa ya shigo, fuskarsa cike da damuwa. "Ranka ya daɗe, na zo ne in sanar da kai cewa yanayin cell ɗin Zayana ya ƙara muni. Tana kuka tana kiran mahaifiyarta, kuma na lura wasu bakaken tsuntsaye na na'ura suna kewaye da bangaren kurkukun. Akwai abin tsoro a iska." Sarki Nourdeen ya kalli Master Ibrahim, ya kalli hoton Ching-Ching dake allon, sannan ya kalli rubutun TICK-TOCK na Ruma dake kan tebur.. Sarki ya aika master zuwa can sashen Ayat domin ya ƙira masa ita... Master Ibrahim ya isa sashen Ayat. Bayan ya isar da sakon Sarki, suka nufi sashen Sarki Nourdeen tare... Bayan ta shiga katafaren falon Sarki, ta iske shi zaune cikin tunani. Ta zube ta gaishe shi cikin girmamawa, fuskarta dauke da alamun marin da Onyx ya yi mata duk da tana cikin niƙab.. Sarki ya ce, "Ayat, ki tashi ki zauna. Ga wannan bidiyon, ina so ki kalla kiga abin da idonki ya kasa gani a fili. Ina zuwa, bari in sallami bakin dake falo." Ayat ta ƙura wa allon hologram ido. Ganin Ching-Ching ya sanya zuciyarta narkewa. Ta ga kanwar tata tana sanye da tufafin makaranta masu kyau, tana amsa tambayoyi cikin kwarewa da kwarjini. Wani dadi ne ya mamaye Ayat ganin cewa kanwarta ba baiwa bace, tauraruwa ce dake haskaka... Hawaye suka fara wanke mata fuska, hawayen farin ciki da kuma kewar rashin kasancewa kusa da ita. Tana cikin wannan yanayin, sai idonta ya sauka akan wata na'ura dake gefe wadda take ta haske. Ta taɓa na'urar, sai kawai hoton Sarauniya Ruma ya bayyana, muryarta tana maganar barazanar rusa Alhamra idan ba a fito da Zayana ba. Daidai lokacin, Sarki Nourdeen ya tura kofa ya shigo. Ganin Ayat tana kallon sakon sirri na Ruma, sai ransa ya baci lokaci guda... Cikin tsawa da bacin rai ya furta "Wa ya ba ki umarnin taɓa wannan? Wace irin yarinya ce ke da ba ki da iyaka?" Ayat ta zabura ta mike, jikinta yana rawa. Ta durkusa har kasa tana kuka. "Abul, don Allah ka yafe min. Ban taɓa da nufin bincike ba, shauki ne ya kaini. Kuma... Abul, na zo ne in roki gafararka akan abin da na yi a filin taron sauka. Na wargaza taron murnarmu, na sanya ka cikin kunya a gaban baki. Ka yafe min don Allah." Sarki ya sauke wani nannauyan numfashi, ganin diyar tasa tana kuka ya sanya tausayinta ya ratsa shi. Ya zauna a gefenta, ya dafa kafadar ta. "Ayat, ki kalla ki gani. Ilimin da Ching-Ching take samu a can Pavilion, babu shi a nan. Onyx ba azzalumi bane kamar yadda kike tunani, kawai dai salon mulkinsa ne ya banbanta da namu. Dole ne ki koyi rage zafin rai. Zafin rai baya taɓa haifar da Ɗa mai ido, sai dai ya janyo wa mutum nadama." Ya ci gaba da magana cikin muryar uba.. "Duba abin da kika janyo yanzu. Saboda zafin ranki yasa kowa yabar taron cikin baƙin ciki...Dole ki riƙa amfani da hankali fiye da zuciya. Kiyi amfani da wannan ilimin da kika samu na Alkur'ani wajen taɓa zuciyarki da rahama." Ayat ta jinjina kai, tana jin kalaman mahaifinta suna shiga cikin jinin jikinta. Ta gane cewa yanzu Alhamra tana bukatar haɗin kai, ba gaba ba... Bayan Ayat ta share hawayenta, sai ta gyara zamanta, ta ƙura wa Sarki Nourdeen ido, idanun dake cike da ɗimbin tambayoyin da suka daɗe suna cin zuciyarta tun tana yarinya. Ayat ta sauƙe numfashi, muryarta a sanyaye ta fara jefar da tambayoyin... "Abul, ka gafarceni, amma yau ina son sanin gaskiya. Na daɗe ina jin sunan Sarauniya Ruma, na san ita ce mahaifiyar Zayana, amma tun da na tashi a fadar nan ban taba ganin fuskarta ba, balle mu haɗa ido hudu. Me ya sa kake takun saka da ita? Shin akwai sauran aure a tsakaninku, ko kuwa kun raba gari ne gaba ɗaya? Idan kuwa kun rabu, me ya raba ku har kuka kasa zama inuwa daya?" "Tambaya ta biyu Abul,... Me ya sa kake rayuwa kai kaɗai a matsayin gwauro a wannan katon fadar? Kowace masarauta da kake gani a duniya, sarki yana da mata, yana da sarauniyoyi dake rage masa zafi da damuwa, amma kai ka zaɓi zama kai kaɗai. Shin ko akwai wani boyayyen abu ne da ya sanya ka tsani zama da mace a matsayin mata a fada?" "Me ya sa Ruma take da iko haka akan ka? Na ga yadda kake shiga tashin hankali a duk lokacin da maganarta ta taso. Shin akwai wani abu da take riƙe wa wanda ya fi karfinka ne, ko kuma soyayyarta ce har yanzu take maka raɗaɗi a zuciyarka? Falon ya yi tsit, karar agogon bango kawai ake ji Tik.. Tik... Sarki Nourdeen ya kawar da kansa gefe, ya kalli taga yana kallon sararin saman Alhamra. Wani irin nannauyan numfashi ya sauƙe wanda ya nuna cewa tambayoyin Ayat sun sosa masa inda yake masa ciwo... Ya juyo ya kalle ta, idanunsa sun canza launi, sannan ya gyara zama domin fuskantar wannan daddadan labari na baya wanda ya binne shi tun kafin Ayat ta san kanta.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 38 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Falon ya yi tsit kamar an tsaida lokaci. Ƙarar agogon bango kawai ake ji… Tik… Tik… Tik… Sarki Nourdeen ya jingina da kujera, idanunsa sun yi nisa da falon kamar yana kallon wani zamani da ya dade da wucewa. Sai ya sauƙe numfashi mai nauyi.. “Ayat…” muryarsa ta fito a sanyaye, “ba komai bane yake da sauƙin faɗi.” Ya ɗan lumshe idanu. “Rayuwata ba ta fara a matsayin Sarki ba. Na fara ne a matsayin saurayi mai buri… wanda bai san cewa soyayya na iya zama tarkon da mutum zai gina da hannunsa ba.” Ya ɗago ya kalli Ayat kai tsaye. “A lokacin, mulkin Alhamra yana hannun Yayana. Ni kuma ina ƙasar Australia, birnin Sydney. A can ne na haɗu da Ruma.” Ya ɗan murmusa, murmushin da bai kai zuci ba... “Ruma ba mace bace kawai. Ita ɗin ‘yar Sarkin Sydney ce. Mai ƙarfin hali, mai girman kai… kuma mai son mallaka.” Ya yi shiru na ɗan lokaci. “Ta kamu da sona fiye da yadda nake zato. Mahaifinta ya matsa min, siyasa ta shiga ciki. A wancan lokacin na ɗauka soyayya ce kawai… ban gane cewa siyasa ta fi soyayya ƙarfi ba.” Ya ɗan matsa gaba. “Na aure ta. Duk da cewa iyayena ba su so. An riga an yi min alkawarin wata yarinya tun ina ƙarami.” Idanunsa suka sauya... “Amma na bijire.” Ya sauke numfashi.. “Domin ta aure ni, ta nuna ta musulunta. Amma bayan biki ya wuce… abubuwa suka canza.” Shiru ya sake lulluɓe falon. “Ta haifi Zayana. A lokacin na yi zaton komai zai daidaita. Amma na fara gane cewa Ruma ba ta iya rabon zuciya. Ita tana so ne ta mallake ni gaba ɗaya.” Ya ɗan ja numfashi. “Bayan rasuwar mahaifina, na dawo Alhamra. Na cika alkawarin da aka min na yarinta na auri Aysh.” Fuskar Sarki ta sauya gaba ɗaya... “Aysh…” Sunan ya fito daga bakinsa kamar addu’a... “Ita ce mace mafi hakuri da na taɓa sani. Ta zo fadar nan ba tare da gardama ba. Ta girmama Ruma.... duk da cewa ita ce halalina na farko a asali.....mahaifiyarku. Ita balarabiya ce ta asali, jininmu ɗaya. Amma shigowarta gidan nan ya tadda wutar jahannama daga wurin Ruma." "Ruma ta ɗauka an wulakanta ta. Ta yaya baturiya, sarauniyar Sydney, za a yi mata kishiya? Amma Aysh... mace ce mai matuƙar haƙuri. Ta ɗauki Ruma a matsayin Yayarta, tana girmamata, tana mata biyayya duk da wulakancin da Ruma take nuna mata. Hakurin Aysh ne ya sa Ruma ta sauƙo har aka samu zaman lafiya na ɗan lokaci.." Ya lumshe ido... “Lokacin da aka haife ki, Ayat… na ji kamar Allah ya bani wata sabuwar dama.” Sannan ya buɗe idanu.. “Amma kishi… kishi ba ƙaramin abu bane.” Ya yi shiru. Kamar mai nazari. Ayat ta lura da hannunsa na ɗan rawa... Ya ci gaba da faɗin “Kin tambaye ni dalilin da yasa nake zama ni kaɗai a wannan fadar…” Ya yi murmushi mai ciwo. “Bayan rasuwar Aysh… zuciyata ta daina amincewa da zaman lafiya. Na ga yadda kishin mata ke zama wuta da ke cin komai.” Sai ya ɗan kalli taga. “Na zaɓi zama gwauro ba don babu mata ba… amma don na gaji da wutar da nake kunna da kaina.” Ya juya ya kalle ta. “Amma ki sani, Ayat… akwai abubuwan da kike gani a matsayin tsoro… alhali kuwa tsari ne.” Idanunta suka ɗan haɗe... “Ruma ba mace bace mai sauƙi. Amma ba duk abin da kuke tunani bane gaskiya.” Ya shafa fuskarsa tare da faɗin “Kuma akwai wasu abubuwa… da lokacin su bai yi ba....” Ayat ta ɗan sauke numfashi, zuciyarta tana cike da sha’awar sani... Idanunta sun yi haske kamar tana ƙoƙarin fahimtar duk wani sirrin da mahaifinta ya ɓoye tun da farko.. Ta miƙe, ta kalli Sarki Nourdeen cikin natsuwa, muryarta cike da tambaya.. “Abul… ka riga ka gaya min game da Ruma da Aysh. Amma yanzu ina son sanin wani abu… Hibba, mahaifiyar Maayah… Me ya sa aka raba ku da ita? Me ya sa aka ɗauke Maayah daga hannunta? Shin akwai wani abu da ya faru da ya tilasta hakan?” Sarki ya tashi tsaye tare da gyara alkyabbarsa. Ya kalli Ayat da wani irin kallo mai cike da sanyi da tsoron abin da gobe za ta haifar... ​ "Gimbiyata, gaskiya tana da ɗaci.... Idan har kika san cikakkiyar gaskiyar abin da ya faru tsakanina da Hibbah... watakila ba za ki sake kallona da irin idon girmamawa da kike kallona yanzu ba. Gwara mu bar labarin a haka yanzu." ​Bai jira amsarta ba, ya juya ya nufi Bedroom ɗinsa, ya bar Ayat nan zaune tana kallon inuwarsa, yayin da zuciyarta take cike da dar-dar... ✨✨✨ ​Gari ya waye ba tare da haske ba, domin gajimare ya rufe sararin samaniya. Tun kafin sallar asuba, aka fara jin koke-koke da hayaniya a kofar fadar Alhamra... ​Dubunnan talakawa ne suka taru a bakin babban gate din fadar. Fuskokinsu cike da hawaye da ɓacin rai. ​Wani bawan Allah yana kuka tare da faɗin "Ina yarona? An sace min yaro a tsakiyar dare!" ​Wata mata ta ce, "Mijina ya fita bai dawo ba, an neme shi an rasa!" ​Wani dattijo shima ya ce, "An sace Ƴata! Sarki ya fito ya gaya mana abin da yake faruwa!" ​Jami’an tsaro sun yi katanga da jikinsu, suna tura mutane baya don kada su afka cikin fada. Sarki Nourdeen yana tsaye a saman bene na fadar, yana kallon mutanen nan, yana jin wani irin tashin hankali. Ya san wannan aikin Ruma ne, ta fara cika alkawarinta na sanya masa zazzabi.... ​A gefe guda kuma, Ayat ba ta iya zama shiru ba. Tana ɗakinta ta yi shigar Inuwa. Ta gyara kakin jami'an tsaro dake dauke da tambarin Royal Guard, ta sanya gemu da saje na jabu waɗanda suka sauya fuskarta gaba ɗaya, ta rufe kanta da rawani... ​Ta bi ta wata boyayyar hanya ta fita har zuwa bakin gate, inda ta haɗu da sauran sojojin da suke tsaron kofar fadar... ​Inuwa tana tsaye, riƙe da makami, tana kallon talakawan dake kuka a gabanta. Duk da tana shigar namiji, zuciyar Ayat ta mace tana tafasa da tausayi... ​Ta ga wata yarinya ƙarama tana kuka tana neman mahaifinta... ​Ta ji kukan wata uwa dake roƙon a cece mata ɗanta.. ​Inuwa A ransa ya ce, "Me Ruma take taƙama da shi ne? Ina sojojin da Abul yake gadara da su? Gashi ana taɓa talakawa marasa laifi saboda rikicin manya. Allah Ka kawo mana dauki...." ​Duk da cewa an tsare kowace gimbiya a sashenta, Zayana tana can a Cell ta ji labarin abun da ke faruwa a can waje da hanyar guard dake kula da ita... Ta yi murmushin mugunta tana kallo gabanta... tare da maganar fili ​ "Na gaya muku... Mummy ba ta wasa. Wannan farkon wasan ne kawai. Idan ba a fito da ni ba, kowa a Alhamra sai ya gwammace ya mutu." Yayin da sarki Nourdeen ya samu nasarar lallashin talakawa su koma gida har zuwa washegari... *OTHER SIDE* Binciken sirri na King Diamond ya kai shi ga gano asalin ƙasar Pavilion. Wani gari ne da mahaifinsu ya assasa tun ba mutane, amma yanzu cikin shekaru 33, ya zama gari mafi kyan gaske a duniya.. Babu ginin ƙasa ko ɗaya, ko’ina gine-gine ne na gilashi wato skyscrapers masu kallon sararin sama, suna sheƙi karkashin hasken rana... Sararin samaniyar garin cike yake da kananan jirage Drones masu sanya idanu, waɗanda ba sa bacci don kare ƙasar daga kowane irin farmaki... Pavilion ta zama matattarar masu neman ilimin kimiyya da addini daga sassan duniya daban-daban, sakamakon kokarin Chief Onyx... King Diamond ya gano cewa ɗan uwansa ba sarki ne kawai ba, babban masanin kimiyyar kwamfuta ne da geography... Ya kera dakarun Robots dubun-dubatar waɗanda suke gudanar da ayyukan tsaro da na yau da kullum. Gely ma ɗaya ce daga cikin manyan robots ɗin da ya ƙera da kansa... A ɗaya bangaren kuma, King Diamond yana zaune a tsakiyar fadarsa, karkashin ruwan Power Pool dake fitar da haske mai launin shuɗi. Damuwa ta lulluɓe shi, yayin da yake kallon kansa a cikin ruwa... Tambayar Da Ba Ta Da Amsa... "Me ya sa?" Ya faɗa cikin muryar da ta girgiza ɗaukacin fadarsa... "Me ya sa a cikin mu tagwaye, aka zaɓe ni domin in zama silar sadaukarwa ga duniyar aljanu? Me ya sa aka bar Ra'ees yana mulkar mutane da hasken rana, ni kuma aka turo ni cikin wannan duhun tun ina yaro?" Baƙin ciki ya tsaya masa a makogwaro. Ya ji an yi masa wariyar jini.... Ganin yadda ɗan uwansa yake rayuwa cikin duniyar mutane, yana taɓa su, yana magana da su, yayin da shi kowa yake gudunsa ko tsoronsa saboda shi Aljani ne... Idanunsa sun koma ja saboda fushi da raɗaɗi.. "Mahaifina ya sadaukar da ruhina domin ya samar da iko da kariya da mulki...Ya mayar da ni makamin kare dangi, ya hana ni jin ɗumin rayuwar ɗan Adam..." ✨✨✨ Hamadar Desert Oasis Wato wurin HUTAWAN ZAKI Chief onyx... Can nesa da hayaniyar gari, a wani wuri na musamman a cikin Pavilion City, Chief Onyx ya ja layin hutawa. Wurin ya haɗu da ni’imar hamada da kuma kyan wani kogi dake ratsawa a gefe. Nan ne mazaunin dabarunsa, inda babu mai isa sai da izininsa... Chief ya baje kayan wasannin motsa jiki, akwai teburin Snooker, akwai Handball, da kuma babban teburin Foosball wanda ake tura ƙananan ƴan ƙwallo da sanda... Bayan ya kammala ɗan motsa jiki, ya ɗauki bindigarsa ya fuskanci Target Board...wurin atisayen harbi... Pat! Pat! Pat! Duk harbin da yake yi, a tsakiyar jan ɗigon yake fita... Chief ya ajiye bindigar, ya nufi wani babban dogon madubi na hangen nesa (High-powered Telescope)... Ya ƙanne ido ɗaya, yana kallon kyawun sararin samaniya da kuma abubuwan dake nesa da sauran mutane.. A gefensa kuma, Bodyguards ɗinsa suna tsaye kamar wasu mutum-mutumi... Kowannensu sanye da baƙin gilashi, bindigunsu a shirye, fuskokinsu ba sa nuna alamar wasa. Iskar sahara tana kaɗawa, tana hura rigar Chief... Yana cikin karkata Telescope ɗin, kwatsam! Wani harbi marar sauti wanda ake ƙira da Silencer shot ya fito daga can nesa, inda maƙiyi ya fake... Harsashin ya samu Chief Onyx a kafaɗarsa ta dama... Ba tare da ya nuna raki ko ya faɗi ba, Chief ya saki Telescope ɗin, ya dafe damtsensa yayin da jini ya fara ɓulbulowa ta cikin rigarsa. Idanunsa suka rine suka yi ja, ya zama kamar zaki da aka harba... Cikin murya mai amo da juriya ya ce, “KADA KU BAR SHI! Ku kamo ko wanene!” Nan take ayarin tsaro suka rarrabu. Wasu suka kewaye shi tare da bashi kariya, wasu kuma suka zura a guje da motocinsu zuwa inda akayi harbin.. An garzaya da Chief cikin motarsa ta alfarma wanda harsashi ba ya ratsawa... Duk da jinin dake zuba, Chief yana zaune ne daram, fuskarsa ba ta nuna alamar rauni ba. Jajirtaccen namiji, mai jure azaba... Yana magana ta cikin na’urar sadarwa.. “Ko wanene ya yi wannan, ya sani ya taɓa wutar da za ta ƙone shi.” Ayarin motocin suka nufi babban asibitin sirri na Pavilion. Ko da suka isa, Chief Onyx ya fito da kansa, yana takawa cikin natsuwa duk da jinin dake fita. Likitoci suka yi kansa cikin gaggawa. A lokaci guda, labari ya isa makaranta inda Ching-Ching take....wasu bodyguards da suke tsaronta acan ne suka ɗauko ta tare da nufo wa asibiti... ✨✨ Special VIP Ward, Pavilion International Hospital Chief Onyx yana kwance a kan gadon asibiti, an cire masa harsashin kuma an fara yi masa ɗinki. Duk da irin wannan azaba, ko motsa fuska bai yi ba, yana kallon silin ɗin ɗakin cikin natsuwa. Kwatsam! Sai aka ji wani ihu daga corridor, irin ihun da Chief ya riga ya sani... Ching-Ching ce. Ta faɗo ɗakin tana kuka, har tana tuntuɓe da carpet, Gely tana biye da ita tana ƙoƙarin riƙe ta... "WAYYOOO UNCLE! Wayyo Allah na, an kashe mana kai! Uncle dama ka bari ni aka harba, tunda ni dama jini na riga na saba da shi a kwanakin nan! Me ya sa za su harbi namijin da yake da mata mai juna-biyu a hannunsa?.....Dama ni aka harba ba kai ba..." Ta faɗa a kan gadon tana ƙanƙame ƙafarsa, tana kuka kamar ranar zai mutu... Chief cikin murya mai rauni ya daka mata tsawa... "Ching-Ching! Ya Isa haka! Harbi ne a kafaɗa, ba mutuwa zan yi ba. Sannan ya isa haka, kukan nan naki ya fi harbin ciwo." A daidai wannan lokacin, Dr. Sophia, wata kyakkyawar likita mai dogon gashi da farar riga, ta ƙaraso kusa da Chief don duba saitin ɗinkin. Ta rusuna tana tattaɓa kafaɗarsa cikin kulawa... Dr. Sophia ta ce, "Chief, please stay calm, I just need to check the dressing..." Ching-Ching ta tsagaita kukan lokaci guda. Ta ɗago kanta, ta kalli yadda likitar take taɓa kafaɗarsa, nan take idanunta suka sauya kala. Ta miƙe tsaye tana turo baki... "Ke! Maza matsa daga nan! Ke ma so kike ki taɓa shi ki ɗauki ciki? Ko ba ki ga ni yadda na zama ba ne? Maza matsa ni zan wanke masa ciwon da kaina!" Dr. Sophia cikin mamaki ta ce, "Excuse me? I am a doctor, and I'm just doing my job." Ching-Ching ta ce, "Aikin me? Aikin shafa kafaɗar mutane? Uncle, kalle ta, har wani lumshe ido take yi tana taɓa ka! Gely, maza ba ni ruwan zafi da auduga, ni zan yi masa komai. Ba ma buƙatar wannan likitar mai gashin doki!.." Ching-Ching ta ƙwace audugar dake hannun Dr. Sophia, ta fara ƙoƙarin matsa wa Chief kafaɗa... Duk juriyar Chief sai da ya kanne ido yana faɗin "Washhh! Ching-Ching, za ki ɓalla min ƙashi ne? Ki bari likitar ta yi aikinta!" Tana turo baki ta ce, "A'a Uncle! Ita fa kallo na take yi kamar tana so ta sace ka. Ni dai na gaya maka, duk macen da ta sake taɓa ka a asibitin nan, to za mu raba juna-biyun nan da ita...! Kuma ma, me ya sa kake kallonta? Ko tafi ni kyau ne don tana da farar riga?" Chief ya runtse ido, ya dafe kansa da hannu guda.. "Gely, don Allah ki fitar da ita kafin ta ƙarasa kashe ni. Maƙiyin da ya harbe ni bai kai wannan yarinyar haɗari ba." Ching-Ching tana shirin sake fashewa da kuka tana faɗin "Yanzu Uncle korata kake yi? Bayan kasan halin da nake ciki? To gaskiya ni nan zan kwana, kuma zan riƙa duba duk macen da ta shigo, sai na ga takardar shaidar cewa ba ta da sha'awar riƙe hannun mutane!" Yayin da Ching-Ching take faman danna wa Chief kafaɗa cikin rashin ƙwarewa da tura baki.. Chief ya ɗaga kansa, idonsa ya sarƙe cikin na Dr. Sophia.. Idanun Sophia sun yi jawur saboda wani baƙin ciki da kishin da suka ninka na Ching-Ching sau dubu.. Sophia ba kowa ba ce illa tsohuwar budurwar Chief. Sun yi soyayya mai zafi tun lokacin da ya taɓa yin wani haɗari a baya, ita ce take zuwa har cikin fada tana ba shi kulawa... Amma kishinta ya yi yawa irin overdose ɗin nan, har ta kai ga tana kishin iskar da take bugunsa, hakan ya sa suka rabu... Amma kallon da suke yi wa juna yanzu? Akwai sauran burbuɗin soyayya wanda ake ƙira da love residue dake yawo a iska... Ching-Ching ta lura da yadda suke kallon juna. Ta ga yadda idon Sophia ya canza, ta kuma ga yadda Chief ya yi sanyi. Nan take ta ƙara danna masa kafaɗar da ƙarfi! Chief ya furta "Auuu! Ching-Ching! Za ki cire min kafaɗar ne?!" Tana shirin kuka cikin shagwaɓa ta ce, "Kyale ni Uncle! Matsawa nake yi don jinin ya koma zuciyarka, don na ga kamar kallon wannan likitar yana sa zuciyarka bugawa da sauri. Ke kuma Likita, me kike kallo haka? Ko ke ma kin san cewa idan kika daɗe kina kallon namiji haka shima yana kawo ciki?" Dr. Sophia ta goge wani ɗigon hawaye dake neman fito mata, ta ƙaraso kusa da gadon, ta yi banza da Ching-Ching kamar ba ta wanzu ba. Ta sa hannu ta riƙe ɗayan hannun Chief na hagu wanda ba shi da ciwo... Cikin muryar kuka da rawar murya..ta ce, "Onyx... har yanzu baka canza ba. Kullum cikin haɗari kake. Kuma har yanzu baka koyi yadda zaka zaɓi mutanen dake kusa da kai ba. Wacece wannan yarinyar da take neman ƙarasa ka?" Ching-Ching ta ajiye audugar hannunta, ta ɗora hannu a ƙugu ta ce, "Iyeeee? 'Onyx'? Sunan da kika kira shi kenan? Lallai ma wannan likitar! To ki sani, ni ce Future Mother of his Baby koda kuwa ta hanyar taɓa hannu ne..! Kuma ki sake shi yanzun nan, karki goga masa tsofaffin ƙwayoyin cutarki..." Chief Onyx ya ji ciwon kafaɗarsa ya ragu, amma na kansa ya ƙaru. Ga Sophia dake kuka tana kallonsa da tsohuwar soyayya, ga kuma Ching-Ching dake shirin kai wa Sophia dambe... Chief ya ce, "Sophia, ya isa haka. Kin san me ya sa muka rabu a baya, kishinki zai iya lalata komai..." Sophia ta ce, "Amma kalli wannan yarinyar! Ta yaya zaka bar ta tana danna maka rauni? Ni ce na san yadda jikinka yake, Onyx! Ni ce na san inda yake maka ciwo!" Ching-Ching ta tura baya da ƙarfi sauran kaɗan Sophia ta faɗi tana faɗin "Ƙarya kike yi! Ni na fi sani! Har ma na san cewa idan ya ɓata rai, hancinsa yana yin girma! Kuma ke Likita, idan baki fita ba, zan ƙira Gely ta ɗaga ki ta jefar da ke ta taga, don kishina ni Original ne, naki kuma na Expiring date ne!" Ta ƙara shige tsakanin Chief da Sophia, ta ƙara tura Sophia da baya da ƙarfi, ta koma ta laɓe a ƙirjin Chief ta bangaren da ba shi da ciwo... "Uncle, ko ka kore ta, ko kuma in sa maka kuka yanzu in tada dukkan asibitin nan!".... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 39 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Halin da ake ciki a Alhamra ya kai maƙura, domin fargaba ta cika zukatan talakawa yayin da aka rasa inda mutane suke ɓacewa... Sarki Nourdeen yana can yana faman sintiri a fadarsa, yana ta ƙiran lambar Ruma amma "not reachable", bai sani ba cewa Sarauniyar tana wasa da hankalinsa ne da gangan.. A cikin wannan yanayin ne Uncle Jalal ya iso fada domin koyar da Maayah. Ma’aikatan fada sun riga sun san darajar Uncle Jalal a matsayin malamin gimbiya, don haka aka ba shi damar wucewa har zuwa babban sashen Maayah. Aka kai shi har cikin lambunta, wanda yake cike da furanni masu kamshi da korayen ƙananun bishiyoyi... Aka shimfida masa wata dadduma ta alfarma, mai laushi da tsada... Uncle Jalal ya zauna ya baje littattafansa, yana jiran gimbiya. Amma Maayah, wadda take ta gadara da son jan aji, ta bar shi zaune na tsawon awanni biyu. Tana can ɗaki tana gyara kwalliya, tana cewa a ranta, "Ai shi ma dole ya san ya zo wurin gimbiya...." Bayan lokaci mai tsawo, Maayah ta fito tana taku ɗaya-ɗaya, tana yauƙi da yanga kamar yadda ta saba. Ta ƙaraso garden ɗin tana tauna chewing gum, tana busawa yana fashewa a fuskarta.. Ta tsaya a gaban Uncle Jalal wanda ransa ya riga ya ɓaci, tana tauna gum ɗin nan tana wani kalle-kalle. Ganin rashin kunyar ta yi yawa ne yasa bai yi wata-wata ba, ya miƙe tsaye tare da zabga mata wani lafiyayyen mari wanda ya sanya kanta juyawa... Nan take chewing gum ɗin ya faɗo daga bakinta, ta dafe kuncinta wanda ya yi jawur, hawaye suka fara sintiri akan fuskarta... Cikin kuka da shagwaba ta ce, "Uncle Jalal... jan aji fa nake maka... me ya sa za ka mare ni?" Ya zaro idanu, yana huci saboda raɗaɗin abin da yake faruwa a garin Alhamra da kuma halin ko-in-kula na Maayah.. "Ina kika ga ajin da za ki ja? Wawiya kawai! Garinku yana cikin tashin hankali, ana sace mutane ana sace kananan yara, kowa yana kuka, amma ke kina nan kina wani jan aji da nuna isa? Ke wace irin mutum ce da ba ta san ciwon kanta da na al'umma ba?" Ya ci gaba da balbale ta da faɗa, yana nuna mata cewa mulki ba hauka ba ne, sannan ya zauna ya nuna mata wurin zama... Ta zauna tana shasshekar kuka, tana goge hawayenta da bayan hannu. Duk gadarar nan ta tafi, yanzu tana jin tsoron Uncle Jalal fiye da kowane lokaci... Ya buɗe littafin, ya ajiye a gabanta, ya fara nuna mata alphabets ɗaya bayan ɗaya.. "Karanta wannan! Kada ki kuskura ki sake min wasa. Alhamra tana bukatar shugabanni masu tunani, ba gimbiyoyi masu tauna chewing gum ba." Maayah ta sunkuyar da kai, tana bin haruffan da yatsanta, muryarta na rawa tana biyo karatun. A karon farko, ta gane cewa rayuwar fada ba kawai yanga ba ce, akwai darasi mai tsanani dake jiranta. Lambu ya yi tsit, sai sautin tsuntsaye dake kuka a hankali da kuma ƙamshin fure dake tashi. Uncle Jalal ya dukufa, yana nuna mata yadda ake haɗe Sentences a harshen Turanci.. Muryarsa tana fita cikin natsuwa, yana kokarin ganin ta gane dukkan bayanan da yake mata. Yana cikin bayani, sai ya ji shiru, babu amsar Eh ko Na gane... Ya dakata da maganar, ya sauƙar da idanunsa don ganin ko tana bin sa ne a littafin, sai ya ga abin da bai taɓa zato ba. Maayah ta kasa jure gajiya da raɗaɗin kukan da ta yi, sai kawai ta saki jikinta, ta kwantar da kanta luff a kan faffadan kirjin Uncle Jalal. Ta yi nisa a cikin wani nannauyan barci, har tana sauƙe numfashi ɗaya-bayan-ɗaya cikin nutsuwa... Uncle Jalal ya daskare. Bai lura da lokacin da kanta ya sauƙa a kirjin nasa ba saboda yadda ya zurfafa a karatun. Ya kasa motsawa gudun kar ta farka, kuma ya kasa tura ta gefe saboda wani sabon yanayi da ya ziyarci zuciyarsa. Ya fara bin kyakkyawar fuskarta da kallo.. Ya kalli gefen fuskarta da ya kumbura kaɗan kuma ya yi ja saboda marin da ya zabga mata ɗazu. Wani ɗaci ya ji a ransa, yana jin kamar ya yi saurin fushi har yake marinta haka.. Gashin kanta dake sanye da abun roll na sarauta mai sheƙi, ya bazu kaɗan, yana fitar da wani daddadan kamshi mai sanyi wanda ya daki hancinsa, ya sanya shi jin wani irin kasala... Ya ƙurawa lallausan idanunta dake a lumshe ido. Ko kiftawa baya yi, ya rasa dalilin da ya sa yake kallonta haka, amma ya ji duk fushin da yake yi da ita ya narke, ya koma matsanancin tausayi da kuma wani boyayyen shauƙi wanda ya kashe masa jiki gaba ɗaya. A lokacin, Uncle Jalal ya gane cewa bayan wannan gadarar da yangar ta Maayah, akwai wani ɓoyayyen abu marar kariya dake bukatar rarrashi. Ya ci gaba da zama a haka, ya barta ta ƙara samun natsuwa a kirjin nasa, yayin da zuciyarsa take bugawa da wani irin sauti daban da wanda ya saba ji.. Ya gyara mata kwanciya a hankali, ya bar kanta ya ƙara nutsewa a kan faffadan kirjinsa. Ya ɗauki Alkur'ani karami ya fara karantawa cikin sanyin murya, yana jin natsuwa na ratsa shi. Sai dai karar wayarsa ta katse wannan shirun... Yana dubawa ya ga Mom a jikin screen. Tashin hankalin mahaifiyarsa ya bayyana tun daga sautin muryarta daga can gida Nigeria... "Hello... Hello Son! Kana lafiya? Mun ji labarin kasar Alhamra ba lafiya, ana ta rigima. Son, ka dawo gida ban so na rasa ka, don Allah ka dawo gobe-gobe nan!" Cikin muryar lallashi ya furta, "Mom, ki kwantar da hankalinki. Ba wani faɗa ake ba, labari ne kawai ake ta zuzutawa. Babu abin da zai same ni tunda ina da ayar Allah a kusa da ni." Ta ce, "Son, na ji fa sai sace mutane ake yi, ina jin tsoro sosai." Uncle Jalal ya ce, "Kar ki damu Mom, waɗanda aka sace ma za su fito da yardar Allah. Ki taya mu da addu'a kawai." Kafin ya ankara, Mom ta sauya kiran zuwa Video Call. Nan take hoton Mom da kannensa mata guda hudu da suke gefe sunata wasan jife-jife da pillow, dukansu 'yan mata ne... Uncle Jalal ya manta cewa Maayah tana kwance a kirjinsa!.. Mom ta zaro ido tare da "Yaaa ALLAH! Son, wacece nake gani a kwance a kan kirjinka?!" Kannensa jin haka suka afko cikin wayar, suna kalle-kalle.. Nan suka fara "Wow! Masha Allah, kyakkyawa da ita! Uncle, ita ce Auntynmu? Allah tana da kyau sosai, fuskarta kamar ta jaruma!" Mom ma cikin mamaki ta furta "Ikon Allah... Son, kamar gimbiya nake gani? Dubi abin sarauta a kanta, ga kayan jikinta na alfarma. Kai Jalal, me kake yi da gimbiya?" Ƙannensa ba su bar shi ya yi magana ba, suka ci gaba da yaba wurin.. "Kaiii Uncle! Dubi wurin da kake, tsatstsarren lambu ne mai furanni masu kyan gaske. Gaskiya Uncle, ba don ana faɗa a can ba, da yanzu na taho ziyara. Garin ya tsaru!" Uncle Jalal ya ji kunya ta kama shi, ga shi ya rasa yadda zai yi bayani ga Mom ɗinsa dake ta zargin wani abu daban. Shi kuma ya san halin Mom da ƙannensa, idan ya bar su, za su iya kai dare suna surutu... Cikin sauri ya furta "Yanzu tunda kun ganni na sanar da ku ina lafiya, sai an jima." Kit! Ya yanke wayar kafin su ƙara wani surutun. Ya sauƙe numfashi, yana jin ɗacin yadda suka ganshi a haka... Ya sake mayar da kallonsa kan Maayah, wadda ko motsi ba ta yi ba. Tana nan cikin bawan barcinta, ba ta san kishin-kishin ɗin da aka yi a kanta daga Nigeria ba... Uncle Jalal ya yi murmushi mai ciwo, ya ci gaba da karanta Alkur'aninsa, yayin da yake jin ɗumin kanta a kirjinsa yana ƙara masa wani irin nishaɗi da bai taɓa ji ba... Wannan karan kam, Mom ba za ta kyale shi ba! Bayan ’yan mintuna kaɗan da yanke wayar, sai ga saƙo ya shigo ta WhatsApp daga wurin Mom. Uncle Jalal ya zaro ido ganin har saƙon voice note ta turo... Uncle ya rage ƙarar wayar yadda Maayah ba za ta ji ba, sannan ya danna play... "Jalal! Kana jina? Wato ka kashe min waya don kada in tambaye ka gaskiya ko? To uwar kowa ce uwar kowa, wallahi na gani da idona. Yarinyar nan ba ’yar kowa ba ce, kowa ya ganta ya san jinin sarauta ne. To ina so ka sani, duk ranar da za ka taho hutu, kada ka kuskura ka taho ba tare da ita ba. Ko da kuwa sarki ne ubanta, ka ce masa Mom ta ce tana son ganinta. Kuma gobe zan ƙira ka mu ƙarasa maganar, ka shirya bayani!" Uncle Jalal ya dafe kansa, yana murmushin yaƙe. Ya san Mom, idan ta ƙafe akan abu, to magana ta ƙare. Ya kalli Maayah dake ta sharar barci, ya raɗa mata a kunne cikin wasa... "Ke dai kina nan kina barci, ba ki san ruhinki ya riga ya koma Nigeria ba." A hankali Maayah ta fara buɗe idanunta. Ta ji wani irin ɗumi da lallausan ƙirji dake ɗauka yana hawa. Da farko ta ɗauka a gadonta take, amma kamshin turaren Uncle Jalal da sautin karatun Alkur'aninsa da yake yi a hankali suka dawo mata da hayyacinta... Ta zabura ta miƙe zaune, tana goge idanunta, fuskarta cike da kunya da kuma mamaki... "Uncle... barci na yi?" Ya rufe Alkur'aninsa, ya kalleta da wani kallo mai cike da ma'ana.. "Barci ma kuwa.. Kin yi barci sosai, har ma kin yi baƙi daga Nigeria." Maayah ta yamutsa fuska tana mamaki... "Nigeria? Me kake nufi?" Uncle Jalal ya sauya salon maganar zuwa mai muhimmanci don kada ta gano abin da ya faru a waya.. "Maayah, gidajen rediyo da gidajen jaridun duniya duk sun ɗauki labarin abin da yake faruwa a Alhamra. Tun daga Nigeria har zuwa Turai, kowa ya sani cewa ana sace mutane a nan. Mom ɗina ma ta ƙira tana neman in dawo gida..." Maayah ta sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannunta. Tausayin kanta da na garinsu ya sake kama ta... Ya furta a hankali "To Uncle, me ya sa ba ka tafi ba tunda ta buƙaci hakan? Kowa yana gudun Alhamra yanzu." Uncle cikin muryar lallashi ya ce, "Zan iya barin karatun naki a rabi ne? Kuma na gaya mata akwai wata 'yar karamar gimbiya dake buƙatar kariya ta, shi ya sa zan tsaya." Maayah ta ɗago ta kalle shi, wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta. Ta manta da marin da ya yi mata ɗazu, yanzu kawai tana jin daɗin kalaman sa. Ya kalli yadda idanunta suka cika da kwalla, ya sauƙe nannauyan numfashi. Ya gane cewa ba rashin son karatu ne ke damunta ba, illa dai nauyin kwakwalwa da kuma halin da ta tashi na rashin uwa da kuma ko in kula da mahaifinsu... Uncle Jalal ya gyara zama, ya miƙa hannu ya ɗauko littafin dake gabanta, ya kalle ta cikin natsuwa... "Maayah, ki saurare ni da kyau. Rayuwa ba ta tsaya kawai akan kyau ko gadara ko zama a cikin wannan garden ɗin ba. Duniya tana canzawa, kuma ilimi shi ne kaɗai hasken da zai taimake ki ki mulki kanki kafin ki mulki wasu. Ki duba yadda kowa yake takama da ke, idan baki da ilimi, gobe idan ba kya karkashin inuwar sarki, yaya zaki kare mutuncinki?" Maayah ta fara girgiza kanta, hawaye suka fara sintiri a kuncinta, muryarta tana rawa. . "Uncle... kana ganin bana son yi ne? Wallahi ina so, amma bana fahimta! Komai kake faɗa ji nake yi kamar a mafarki. Kwakwalwa ta bata ɗauka, Uncle na gaji, na gaji da jin kaina yana min ciwo duk sanda nake son haɗa waɗannan haruffan..." Ta fashe da gagarumin kuka, ta boye fuskarta a cikin tafukan hannunta.. "Kowa yana ganin ni jaka ce, ko Abul idan yana maganar ilimi sai dai ya ƙira sunan Ayat ko Yumna da Ching-Ching... Uncle, idan har ban fahimta ba yanzu, yaushe zan fahimta?" Ganin kukan nata ya tsananta, Uncle ya ji wani irin tausayi ya sake ratsa shi. Ya ɗauko lallausan tissue ya miƙa mata, sannan ya yi magana cikin sanyin murya.. "Shiru... ya isa haka. Ba jaka bace ke. Kowa da irin gudunsa, wani sai an bi da shi a hankali sannan yake gane abu. Ni ba zan taɓa barin ki ba har sai kin iya... Ko da haruffa biyu ne zamu riƙa koya a rana ɗaya, zan yi haƙuri da ke. Amma kada ki sake cewa baki da amfani, domin wanda ya iya barci a ƙirjin malaminsa ba tare da tsoro ba, yana da babban rabo a zuciyar malamin." Maayah ta tsagaita kukan ta ɗago tana kallonsa da jajayen idanu, tana mamakin kalaman ƙarshe da ya faɗa. Ta ji wani irin kwarin gwiwa ya ziyarce ta... ✨✨✨ VIP Ward, Pavilion International Hospital... 2:30 na dare. ​Cikin dare, duk asibitin ya yi tsit. A cikin ɗakin Chief, Ching-Ching ta tana gadon Chief, ta tura kanta cikin faɗaɗɗen ƙirjinsa, Tana ta sharar bacci, har tana ɗan minshari kaɗan-kaɗan.. ​Chief Onyx kuma yana nan idonsa biyu, yana danna wayarsa cikin natsuwa, kansa yana ɗan sarawa saboda dambarwar hayani.. ​Domin shi sam baya son hayaniya tinin kansa yake hau ciwo.. ​Kwatsam! Ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali. Dr. Sophia ce ta lallaɓo, tana sanye da ƙananun kayan ta, idanunta sunyi ja saboda kishi.. Ganin Ching-Ching a inda take mafarkin kasancewa ya sa jinin jikinta tafasawa... ​Ba tare da tsoro ba, Sophia ta ƙarasa gadon. Cikin zafin rai ta cafko rigar Ching-Ching, ta ɗage ta sama, ta cillar da ita ƙasa a kan carpet... Ching-Ching dake baccin wahala sai kawai ta juya ta ci gaba da baccin a ƙasa, tana tunanin ko mafarki take yi ta faɗa daga gado.. ​Sophia ta hau gadon da sauri, ta ture wayar Chief, sannan ta kwanta a daidai saitin da Ching-Ching take, ta dora kanta a kirjinsa... ​ ​Chief Onyx ya zaro ido, ya tashi zaune kaɗan yana kallon Sophia cikin mamaki da bacin rai.. ​Cikin tsawa ya furta... "Are you stupid, Sophia? What the hell do you think you're doing? Get off my bed right now!" ​Itama cikin nata Turancin tana huci ta ce, "No, Onyx... I won't, This girl has no right to be here.. I was here first.. I am the one who knows how to heal your heart and your body.. I'm not leaving you for a child..." ​Chief ya ce, "We are over Sophia... You destroyed everything with your crazy jealousy years ago. This is a hospital, not a drama club..." ​Ta ce, "Call it whatever you want... I am staying right here. If you want me out, call the security to carry me like a criminal..." ​Chief ya yi barazana, ya yi faɗa, ya yi harara, amma Sophia ta yi biris. Ta kankame hannunsa, ta lumshe ido tana hawaye. Chief ya gaji, ya san cewa Sophia idan kanta ya ɗauki zafi, to ba ta ji, ba ta gani... ​Daga karshe Chief ya yi dogon nishi, ya ajiye wayar ya kalli silin. A haka bacci ya kwashe su, Sophia tana kankame da shi a kan gado, Ching-Ching kuma tana sharar bacci a ƙasa tana mafarkin tana cin naman kaza a cafeteria... ​ ​Asubar fari, anata ƙiraye-ƙirayen sallah.. Ching-Ching ta fara buɗe idonta tana miƙa. Ta kalli kanta a ƙasa, sannan ta ɗaga kai ta kalli gadon... ​Ganin Sophia a makale da Chief, idon ya fito waje kamar an danna mata allura... ​Ta zabura ta miƙe, ta nufi kanta da ihu.. "Wayyoooo Uncle shi kenam ka mata ciki wallahi...na shiga uku na lalace, wannan jarababbiyar likitar arniya, sai da kika lallaɓo cikin dare kika zo? Mai son maza kawai...." Chief yana mata alamun ta rage murya a asibiti suke amma Ching-Ching ba ji ba gani... Ching-Ching ba ta tsaya wata-wata ba, ta haura kan gadon ta fara ƙoƙarin tura Sophia, yayin da Sophia ita ma ta ƙanƙame hannun Chief kamar na gadon gidan ubanta... "Ki sauƙa, mai son maza kawai, ai ba shi bane kaɗai namiji ga can bodyguards ɗinsa kije ki zaɓi ɗaya mana...ki sauƙa kar ya miki ciki..." Dr. Sophia tana tunkuɗa Ching-Ching itama tare da faɗin "Stay away, you brat.. Ni ce na fi cancanta in kasance a nan. Get off before I inject you with something that will make you sleep for a week!" Chief Onyx ya tashi zaune cikin matsanancin raɗaɗin ciwon kai, fuskarsa ta kumbura kamar gajimaren hadari tsabar fushi... Ya daka musu tsawa "Ya isa haka!!! Sophia, sauƙa daga gadon nan! Ching-Ching, sauƙa ke ma!" Ganin Sophia ta ƙi sauƙa, yasa Chief ya danna ƙararrawar gaggawa. Nan take Security guda biyu suka faɗo ɗakin... Cikin murya mai sanyi cike da umarni ya furta, "Take her out. Now!" Jami'an tsaron suka kama Sophia. Tana kuka tana mutsu-mutsu, har suka kai ta bakin ƙofa. Ta tsaya, ta kalli Ching-Ching wadda take washe haƙora tana yi mata gwalo... Dr. Sophia cikin zafin rai da ihu, ta ce, "Kada ki yi murna yarinya. Kina tunanin ke ce a zuciyarsa? To ki sani, Chief Onyx yana da wani sirri a ɓoye. Baya taɓa barin mace ta shiga ransa don akwai wani hoto a cikin locket ɗin sarƙar da yake sawa a wuyansa... hoton macen da ya fi kowa so ce a duniya, kuma ba ke ba ce!" Ta faɗa tana kuka, jami'an tsaron suka ja ta waje. Ɗakin ya yi tsit. Ching-Ching ta daina gwalo, ta juya tana kallon Chief Onyx da wani irin kallo na tuhuma. Ta matso kusa, idonta ya sauƙa akan wuyan Chief inda take ganin sarƙar zinare a ɓoye cikin rigarsa.. Cikin muryar shagwaɓa amma akwai kishi a ciki ta furta "Uncle... dama kana da wata macen a cikin sarƙa? Ka nuna min! Idan ba haka ba, zan fasa ɗinkin kafaɗarka in zuba masa gishiri!" Chief Onyx ya dafe kansa, ya san cewa maganar Sophia ta dasa wa Ching-Ching wani sabon tsimi... Ya ce, "Kada ki saurari Sophia, Ching-Ching. Surutu take yi kawai saboda kishi." Ta ce, "A'a! Nima ina da kishin overdose! Nuna min hoton nan, ko kuma in fara ihu daga nan har zuwa fada.." Ya fara tunanin wani irin abu ne haka kamar Ching-ching ta fara soyayya da shi...a cikin ransa ya furta "impossible, zan cire miki soyayyar nan domin a tunaninsa ba ta kai yin soyayya ba, kuma abin raini ne ya rasa da wanda zai yi soyayya sai da kwailar yarinya kamar Ching-ching, haka ya ƙarisa yana girgiza kai alamun hakan bazai taɓa yu wa ba... Ya gaji da surutun Ching-Ching, ya san muddin bai ba ta abin nan ba, ba za ta bar shi ya huta ba. Ya cire sarƙar daga wuyansa, ya miƙa mata ita cikin natsuwa.. "Gashi, amma karki taɓa buɗewa. Sirri ne na rayuwata. Idan kika buɗe, raina zai ɓaci sosai." Ching-Ching ta karɓa, tana washe haƙora. "To Uncle, na ji, ba zan buɗe ba." Amma a zuciyarta cewa take, Yanzu ma zan ga shegiyar... Tana fita daga ɗakin, ta nufi wani lungu inda Gely take tsaye tana jiran umarni. Ching-Ching ta fito da sarƙar, locket ɗin yana sheƙi. Ta yi ƙoƙarin ɓallewa da farce, amma abin ya faskara... "Lallai ma Uncle, ashe ya rufe shi da ƙarfi haka? Gely! Zo nan! Yi amfani da waccan Laser ɗin idonki ki fasa min wannan abun, mu ga Arniyar da take ciki! Ina so in ga wacce take takara da ni a zuciyar Uncle!" Gely ta kunna idonta, wani jan haske ya fito. Cikin daƙiƙa biyar, locket ɗin ya buɗe kyam... Ching-Ching ta matso kusa, tana zazzaro ido, tana shirin so ta ga wata kyakkyawar budurwa ce a ciki... Amma tana kallon cikin locket ɗin, sai ta tsaya cak... Wani kyakkyawan hoton mace ne, mai fuskar natsuwa da kamala... Idanunta irin na Chief ne, kwarjininta kuma ya nuna cewa ita ma daga zuri'ar sarakuna take. Ba kowa ba ce illa Mahaifiyar Chief Onyx... Ta sauƙe ajiyar zuciya, ta kalli Gely.. "Iye? Gely, ashe ba budurwa ba ce? Wannan ai kaman Uncle take yi! Ashe tsohuwa ce? Haba, dama na sani, Uncle ba shi da sauran taste na irin waɗancan mutanen." Gely tana binciken bayanan hoton ta ce, "Scanning... This is Queen Zeenat, the late mother of Chief Onyx. Accuracy 100%." Ching-Ching ta rufe locket ɗin, ta fara rarraba ido. A maimakon ta ji daɗi, sai kuma kishi ya sake dawowa ta wani fannin.. "Amma duk da haka Gely, me ya sa zai sa hoton wata mace a wuyansa ni kuma bai sa nawa ba? Ni ma ai nan gaba mahaifiyar jariransa zan zama! Gaskiya Gely, dole yanzu mu nemo hoto na, mu maƙala a ɗayan gefen, ko don ya riƙa ganina kusa da zuciyarsa!" Tana cikin wannan maganar, sai ta ji muryar Chief a bayanta, ya fito daga ɗakin jinya yana takawa a hankali... "Ching-Ching! Me kuke yi a nan?".. Ya ƙaraso wurin, idanunsa suka sauƙa akan locket ɗin da har yanzu hayakin Laser ɗin GELY yake tashi a jikinsa. Ya ga hoton mahaifiyarsa a buɗe. Nan take fuskarsa ta sauya, kwarjininsa ya ninka sau goma, wani irin sanyi mai ban tsoro ya ziyarci wurin. Cikin muryar dake nuna tsananin ɓacin rai ya furta "GELY... ina umarni na yake? Na ce karki taɓa barin kowa ya taɓa wannan sirrin. Amma yau kin zama 'yar amshin shatan yarinya mara hankali?" GELY ta tsaya cak, idanunta suka yi ja Error Mode...tare da faɗin "Warning... Conflict of commands. Primary user override..." Chief ya darara mata tsawa da "Yi mun shiru! Daga yau, duk wani System Access da kike da shi a matsayin mataimakiyata, na soke shi. Kin zama tsohon ƙarfe a wurina tunda baki san bambancin umarni da wasan yara ba." Chief ya juyo kan Ching-Ching, wadda yanzu jikinta ya fara rawa domin ta ga cewa yau Uncle ba wasa yake ba. Ya matso kusa da ita, har tana iya jin huci da ƙanshin turarensa.. "Ke kuma, ki saurara da kyau. Wannan wasan Juna-biyu da kike yi, na sa muku ido ne kawai don in ga iyakar haukanku. Daga yau, muddin na sake jin wannan kalmar daga bakinki, zan sa a mayar da ke dabba na saka ki a keji.." Yana mata wani kallo dake nuna raini da wulaƙanci.. "Kuma ki daina mafarkin soyayya. Har yanzu ke yarinya ce da ba ta san inda kanta yake ba. Babu kowa a zuciyata, kuma babu wanda zai shiga. Sophia ma tana hauka ne kawai, ban taɓa son ta na aure ba, kulawar da take ba ni ce kawai ta sa na ƙyale ta, ita kuma ta ɗauka abin da zafi. Saboda haka, ki cire batun kishi ko soyayya a kaina, ke ba komai ba ce illa 'yar aikin da aka kawo ta koya hali a gidana." Ba tare da ya ƙara sauraronsu ba, ya juya ya nufi motarsa ta alfarma dake jiransa. Bodyguards suka buɗe masa ƙofa, ya shiga ya zauna daram, bai sake kallon inda suke ba.. Ya furta wa Driver cewa, "Drive. Back to the Palace. Leave them here." Motar ta yi kugi, ta bar wurin... Ching-Ching ta tsaya cirko-cirko, tana riƙe da locket ɗin dake zafi, yayin da GELY take tsaye kamar gunki saboda an soke mata Access.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 4️⃣0️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Chief onyx ya bar Ching-Ching da Gely da tafiyar wahala, domin daga asibiti zuwa masarautar Pavilion Palace ba kusa ba ne. ​Ga yadda dambarwar tafiyar tasu ta kasance... ​A babban titin Pavilion City ​rana ta fara zafi, Ching-Ching tana gaba tana kuka, tana fyace majina, yayin da take jan kafafunta cikin tafiyar agwagwa, amma wannan karon ba ta shagwaba ba ce, ta gajiya ce.... ​GELY tana biye da ita a baya, amma tafiyarta ta yi nauyi saboda Chief ya soke mata damar yin amfani da gudun lantarki. Tana tafiya ne kamar tsohon ƙarfe dake buƙatar mai.. ​Cikin kuka mai sauti Ching-ching take faɗin "Wayyo Allah na! Gely kalle mu, yau Uncle ya yaudare mu. Ya bar mu a titi kamar kaji. Dama na sani, hoton mahaifiyarsa ne ya sanya shi wannan fushin. Ko kema kin ga yadda ta fito a hoton ko? Ta yi kwarjini, shiyasa shima Uncle ya zama zaki yau!" ​ ​tana cikin magana kuma sai ta tsaya ta kalli GELY, wadda take ta faman ƙarar Krrr... Krrr... saboda tafiyar ƙasan... ​"Ke kuma GELY, me ya sa kika biye min? Yanzu gashi an soke miki baturin access. Ke robot ce marar amfani! Da yanzu kina da ikonki, da kin goya ni mun isa gida tun ɗazu....Amma yanzu kalle ki, tafiyarki ma ta fi tawa muni..." ​Muryar Gely wanda yake ta yanyanke wa ta ce, "Warning... Battery at 15%... Chief Onyx access denied... Please... charge... me..." ​Ching-Ching tana turo baki ta ce, "Charge kanki mana! Ni ma kaina caji yake bukata... Idan na isa gida, wallahi ko ƙofa Uncle ya rufe min, sai na bi ta ramin ɓera na shiga, in je in nemi gafararsa. Ba zan iya barin Uncle na ba, koda zai mayar da ni ɓera a gidan..." ​ ​Bayan sa'o'i biyu na tafiya cikin gajiya da yunwa da ƙishi, suka isa kofar katon fadar Chief... Ching-Ching ta faɗi a ƙasa kusa da Guards... Gashinta ya hargitse, fuskarta yayi duhu tsabar wahala.. ​Masu gadin suka kalle ta cikin mamaki, amma saboda umarnin Chief, ba su buɗe ƙofa ba... ​Ching-Ching tana buga ƙofar fada da sauran karfinta tare da faɗin "Uncle! Ka buɗe min... Na daina juna-biyun! Na zama tsohuwa yanzu. Uncle wallahi ko ƙafa ta ba zan sake haɗewa da ta kowa ba, koda kuwa Yarima Leonardo ne.. Ka gafarta wa Gely, laifina ne.." ​B bodyguards kuwa sun yi ƙyammm ko kallonsu basu yi ba, domin an sanar da su akan kada su buɗe musu ƙofar.. ​A cikin falonsa kuwa, Chief Onyx yana tsaye a bakin taga, yana kallon yadda Ching-Ching take kuka a waje ta cikin kyamarorin tsaro CCTV... Fuskarsa ba ta nuna alamar tausayi ba, amma ya ƙura mata ido yana so ya ga ko da gaske take yi na son gyara halinta.... GELY yanzu ta daina tafiya ma, sai jujjuyawa take yi a wuri ɗaya. Idanunta dake hasken ja sun fara lumshewa, suna yin blinking... Muryarta ta koma ƙasa-ƙasa, kamar tsohon rediyo mai neman baturi... Muryar tana katsewa... "Ching... Ching... Sys-tem... fail-ure. Battery... at... 5 percent. Help... me... to... the... charging... port... please..." Ching-Ching ta ɗago kai tana kallon GELY cikin haushi.. "Ke dalla rufe min baki! Taimakon me zan baki? Kalli yadda na zama, gashina ya koma kalar dambun shinkafa saboda ƙura, ƙafata tana ciwo kamar an cire min ƙashi, ke kuma kina maganar caji?" Ching-Ching ta tashi zaune tana share hawaye da bayan hannunta, tana sake daka wa GELY tsawa... "Meye amfaninki ma yanzu? Da kike da caji ai kin biye min mun yi ta binciken locket, yanzu da Uncle ya yi fushi kin koma kukan caji! Da na sani ma da ban zo da ke ba. Yanzu idan na suma a nan, wa zai ɗauke ni ya kai ni ciki? Tunda ke ko hannunki baki iya ɗagawa!" GELY ta ce, "Ching... Ching... I... followed... your... logic... error. If... I... shut... down... Chief... will... recycle... me... into... a... frying... pan..." (Idan na mutu, Chief zai mayar da ni kaskon suya)... Ching-Ching ta ce, "Aii gara ma ya mayar da ke kaskon suyan, kika sani ko idan kin zama kasko ya riƙa soya naman kaza a jikinki ya ba ni in ci! Gashi nan ma kowa ya ƙi buɗe mana ƙofa. Dubi guards ɗin nan, duk sun zama kurame, sun ƙi buɗe min ƙofa gashi cikina yana ƙugi kamar an kunna injin niƙa..." GELY ta ƙara yin ƙasa, kafafunta suka fara rawa, can sai aka ji Peeeeeep Wannan alamar battery ya koma 2% kenan.. "I... see... darkness... Goodbye... Ching... Ching..." Ta daskare a tsaye, hannunta ɗaya a sama, ɗaya a kasa, tana kallon sama kamar wadda take neman taimakon hadari.. Ching-Ching ta tsorata, ta rarrafa kusa da GELY "Ke Gely! Karki mutu! Don Allah karki mutu ki bar ni a nan ni kaɗai! Idan kika mutu wa zan riƙa sa yana min Laser ɗin abu mai ƙarfi? Gely! Tashi mu yi damben karshe!" Ta fara girgiza GELY, amma GELY ta zama dutse... Ching-Ching ta kara fashewa da kuka, ta rungume kafar GELY wadda take da sanyi da tauri... "WAYYOOO UNCLE! Kazo ka ga robot ɗinka ta mutu! Nima gani nan zan bi bayanta idan baka buɗe kofar nan ba! Wallahi zan daina cewa ina da ciki, zan daina taɓa hannun kowa, zan koma cin ganyaye kamar akuya amma don Allah ka buɗe mana!" Ba zato ba tsammani, sai aka ji ƙofar gate ɗin ta buɗe a hankali. Chief Onyx ne ya fito, sanye da ƙananun kaya na shan iska, fuskarsa tana sanye da bakin gilashi duk da yamma ta yi. Ya tsaya yana kallon wannan hoton na ban-tausayi.. Yarinya duk ƙura tana rungume da gawar robot... Chief cikin sanyin murya ta furta "Wai har yanzu ba ku daina wannan wasan kwaikwayon ba?" Ya matso kusa da su, yana kallon yadda Ching-Ching ta ƙanƙame ƙafar GELY tana kuka. Ya miƙa hannu don ya ɗaga ta ya kai ta ciki, amma sai ta goce, ta koma ta manne wa GELY dake daskarewa... Ya ce, "Ching-Ching, tashi mu shiga ciki. Kin riga kin galabaita, kina buƙatar abinci da barci." Ching-Ching tana shashshekar kuka ta ce, "A'a Uncle! Ba zan shiga ba! Ka duba GELY, ta riga ta zama dutse. Tana tsoron kar ka mayar da ita kaskon suya shiyasa ma ta daina numfashi.... Idan ba za a shigar da ita a ba ta caji ba, to nima a nan zan daskare in zama kaskon tuwo.." Chief ya yi wani dogon nishi, ya kalli GELY dake tsaye hannu ɗaya a sama kamar tana rawar Michael Jackson. Ya san cewa idan bai biye wa Ching-Ching ba, to a nan za su kwana... Ya furta "GELY ta gaza yin biyayya Ching-Ching.... Dole ne ta fuskanci hukunci." Ching-Ching ta zabura ta miƙe, ta fara dukan ƙirjin Chief da ƙananan hannayenta.. "Mugun Uncle! Azalumi! Saboda mu ne ba mu da jini a jikinmu? GELY ta biyewa logic error ɗina ne saboda tana so na. Idan baka caji ta ba, nima zan sa Laser in fasa kaina in ga me ke ciki! Wallahi yanzun nan zan daina numfashi ni ma..." Ta riƙe numfashinta, ta kumbura kumatunta har sai da fuskarta ta yi jawur tana hararar Chief... Ganin Ching-Ching tana shirin suma da gaske don taurin kai, Chief ya ɗaga hannu ya yi wa masu gadin sa guda huɗu alama.. Cikin muryar gajiya ya ce, "Ku ɗauki wannan ragowar ƙarfen ku kai ta babban ɗakin bincike, a haɗa ta da High-Voltage Charger.. Sannan a sake mata formatting na ɓacin ran da aka sa ta." Nan take Chingching ta saki numfashin, ta washe haƙora.. "Yauwa Uncle! Amma karka bar su su goge mata tunanin da muke da shi na naman kaza, kaga nima ina buƙatar ta riƙa tuna min lokacin da nake da juna-biyu kafin ka ce na zama tsohuwa." Chief Onyx bai sake cewa uffan ba, ya sunkuyo ya fizge ta ya ɗora ta a kafaɗarsa kamar buhun gishiri.. "Ayya Uncle! Karka matsa min ciki, kasan har yanzu akwai ghost ɗin jaririn a ciki..." Ya ce, "Ching-Ching, muddin kika sake yin maganar ciki, zan sa a haɗa ki caji tare da GELY!" Nan take ta yi shiru, ta laɓe a kafaɗarsa tana kallon yadda ake jan GELY zuwa ciki. A ranta tana cewa, "Gely, maza ki tashi, akwai sauran dambarwa a gaba!" ✨✨✨ ​Bayan kwanaki uku na fargaba da ɗar-ɗar, gari ya waye da wani mummunan labari wanda ya girgiza harsashin fadar Alhamra.. An tsinci wasu gawarwaki guda goma 10 shimfiɗe a harabar fadar, waɗanda duk jami'an tsaron fadar ne. Ba a san ta yaya aka sace su ba, kuma ba a san ta ina aka shigo da gawarwakin nasu ba.. ​An same su cikin jini, sanye da kakin su, amma rayuka sun yi halinta. A gefen gawarwakin, an tsinci wata wasiƙa mai ɗauke da tambarin fadar Sydney.... _​"Mulki ba na rarrashi ba ne. Idan kuna da ƙwarin gwiwar zuwa karɓo mutanenku da muka tsare a can Yankin Hamshara. (Wani yanki mai nisan gaske), to ku shirya zuwa da shirin yaƙi. Amma ku sani, kowace gaɓa ɗaya takun da kuka yi, tana iya zama silar mutuwar mutum ɗaya a hannunmu. Gawarwakin nan goma, somin-taɓi ne kawai."_ ​Ganin wannan barazanar, Sarki ya ba da umarnin rufe dukkan asibitoci, makarantu, da kasuwanni. Alhamra ta zama kamar garin kurwa, kowa ya laɓe a gida, tsoron dakarun Turawan ya mamaye kowa... ​Sarki Nourdeen ya fito cikin fushi da ɓacin rai, idanunsa sun yi ja. Ya tara dukkan jami'an tsaron sa, ciki har da Inuwa wanda yake tsaye cikin kakin sa, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa... ​Sarki ya sanar da cewa "Ba zan zuba ido ana kashe min mutane ba! Ruma ta wuce gona da iri. Ina neman mazajen da za su sadaukar da rayuwarsu su tafi Yankin Hamshara domin ceto mutanenmu. Wannan yaƙi ne, kuma jini zai zubar!" ​Sarki ya ba wa Master Ibrahim umarnin ware zaratan jami'ai guda hamsin da za su jagoranci wannan hari na ba-zata... ​Bayan an gama taron, Master Ibrahim ya fara kiran sunaye, amma ya ƙi ƙiran sunan Inuwa.... Inuwa ya bi Master har zuwa can gefe, muryarsa a dashe yana roƙonsa.. ​"Master, me ya sa sunana ba ya ciki? Ka sani cewa nima na san dabarun yaƙi, kuma zan iya shiga inda kowa ba zai iya shiga ba!" ​Master Ibrahim ya juyo cikin tsawa muryarsa na rawa ya ce, "Ba zan saka ka ba! Wannan ba wasan yara ba ne, yaƙi ne na haƙiƙa. Ina tsoron kada a je a raunana ka, ko kuma ka rasa ranka. Idan wani abu ya same ka, ta ya zaka cika burikan ka...?" ​Inuwa ya duƙufa yana roƙon Master "Don Allah Master, kada ka bar ni a baya. Idan ban je ba, ba zan taɓa yafe wa kaina ba. Ina da kariya, kuma zan iya taimaka muku. Idan har ka yarda da ƙwazona, to ka saka ni a cikin rundunar nan." ​Ganin yadda Inuwa ya nuna taurin kai da kuma zubar da hawayen jarumtaka, Master Ibrahim ya sauke numfashi, ya ɗauki alkalami ya rubuta sunan Inuwa a ƙarshen jerin sunayen, amma jikinsa yana rawa... Bayan an gama danbarwar ne Inuwa ya koma sashensa.. Ta shiga ɗakinta ta boyayyar hanyar sirri, tana sanye da kayan jami'an tsaron jikinta... Tana shiga ta hango wani haske mai launin shuɗi yana walwali a kan gadonta... King Diamond ne zaune, dogon sumar gashinsa na kwance a kafadarsa, idanunsa na kallon ta cikin natsuwa.. ​Cikin ajiyar zuciya ta furta.. "Daman ina son ganinka... Akwai babban aiki a gaba na." ​Ta ƙarasa kusa da shi, fuskarta ɗauke da damuwar da ta daɗe tana addabarta... ​ "Idan na tafi wannan yaƙi a matsayin Inuwa, wa zai zauna a nan a matsayin Gimbiya Ayat? Idan aka nemi gimbiya ba a ganta ba, asirina zai tonu, kuma sarki zai shiga ruɗani. Ta yaya zan kasance a wurare biyu lokaci guda?" ​King Diamond ya miƙe tsaye, tsayinsa da kwarjininsa suka cika ɗakin. Ya matso kusa da ita, muryarsa kamar busar iska.. ​"Na san yadda zan yi, kada ki damu da wannan. Zan samar da wata Ayat da za ta zauna a maimakonki, babu wanda zai gano bambancin. Kuma yanzu ba tare da ɓata kwanaki ba zaku ta fi, kuma kina bukatar horo na musamman domin dakarun turawa ba mutane ba ne kawai..." ​Kafin Ayat ta samu damar tambayarsa wani abu, King Diamond ya sa hannu ya yi mata ɗaukan luɗa. Nan take wani irin jiri ya kwashe ta, ɗakin ya juya, komai ya ɓace cikin kiftawar ido. ​🌸 ​A lokacin da Ayat ta buɗe idanunta, ta tsinci kanta a wata duniyar daban. Wuri ne mai cike da furanni masu sheƙi da fitar da haske kalar taurari, iskar wajen tana ƙamshin da ba a taɓa ji a duniyar mutane ba... ​Wata lallausar waka, mai sanyaya rai da kwantar da hankali ta fara tashi daga ko'ina. Ba a ganin masu kiɗan, amma sautin yana ratsa ƙashi... ​King Diamond ba tare da ya sake ta ba. Ya sanya hannunsa ɗaya akan kunkuminta, ɗaya kuma ya riƙe hannunta... Ayat kuma, kamar yadda rawar turawa take, ta ɗora ɗaya hannun nata a kafadarsa itama.. ​Suka fara taku ɗaya-bayan-ɗaya, suna juyawa cikin natsuwa a tsakiyar lambun furannin... Suna bin sauti da gangar wakar... Idanunsu suka sarke cikin na juna. Ya sauya mata kayan jikinta daga na jami'i zuwa na gimbiya haɗaɗɗiya, tsabar shauƙi na lokaci guda har ta mance da batun yaƙi... A wannan lokacin, Ayat ta ji wani irin kariya dake tattare da King Diamond. Kwarjininsa ya mamaye daukacin hankalinta.. Yana mata raɗa yayin da suke rawar.. "Wannan rawar ba ta nishaɗi bace kaɗai Ayat... Tana koyar da ke yadda zaki riƙa sarrafa jikinki cikin sauri da natsuwa a lokacin yaƙi. Dole ne ki kasance kamar iska, ana jinki amma ba a ganinki." Ta lumshe idanu, tana jin ɗumin jikinsa, tana fatan wannan daren kada ya ƙare. Ta gane cewa King Diamond ba aljanin kariya bane kawai, shi ne masoyin da zuciyarta ta daɗe tana nema...duk da akwai wanda take kewa kafin shi... Waƙar da suke rawa da ita a hankali ta fara sauya sauti, daga lallausan sauti zuwa wani kiɗa mai ɗauke da sautin ƙarfe da kwarin gwiwa... King Diamond ya sakar mata kunkumi, sannan ya ɗaga hannunsa sama. Nan take, wani haske mai launin shuɗi ya ɓarke a tafin hannunsa, ya rikiɗe ya zama wani tsararren takobi mai matukar kyau da kaifi... ​Ya miƙa mata ɗaya, sannan shi ma ya zaro tasa. ​Ya tsaya takara, idanunsa sun canza launi zuwa wani irin shuɗi mai zurfi wanda yake nuna cewa yanzu lokacin horo ne, ba na wasa ba... ​"Ayat," ya ƙira sunanta cikin muryar dake amsa a cikin lambun... "Takobi ba makami ba ne kawai, ɓangare ne na jikinki. Idan zuciyarki tana rawa, takobinki zai yi nauyi. Idan zuciyarki tana da tauri, takobinki zai zama kamar fure." ​Ya nuna mata yadda zata riƙe takobin... ​Ya daidaita yatsun hannunta akan marikin takobin, yana tabbatar da cewa ta riƙe shi da duk kwarin gwiwarta... Ya gyara mata ƙafafu yadda zata samu natsuwa a ƙasa... ​Ya fara kai mata farmaki na farko, ba da nufin raunata ta ba, sai dai don ya gwada saurin motsinta.. ​ Sautin ƙarfe ya tashi a lokacin da takobinsu ya haɗu... ​"Kada ki jira in kawo hari, ki riƙa hango inda zan sa ƙafa kafin in ɗaga ta," ya faɗa yayin da yake juyawa kamar iska... Ayat ta fara bin sa, tana lura da yadda jikinsa yake motsawa. Cikin kankanin lokaci, ta fara koyon yadda zata kaucewa hari ta hanyar juyi da kuma yadda zata kare kanta... ​Ya koya mata wani salo na musamman inda jiki zai kasance yana rawa irin ta motsa jiki, amma takobi yana saran kowane bangare... Ta riƙa yin tsalle tana kai hari daga sama.. Ya koya mata yadda zata riƙe numfashinta yadda ba zata yi saurin gajiya ba... ​Ayat ta ji wani irin ƙarfi yana gudu a cikin jininta. Duk wani tsoro na dakarun turawa ya ɓace, ya koma wani irin zafi da kishin ganin ta ceci mutanen Alhamra. Gumi ya fara keto mata, fuskarta ta yi jawur, idanunta suna kyallin jarumtaka... ​King ya tsaya, yana kallon kyakkyawar jarumar dake gabansa ya ce, "Madalla. Yanzu kin shirya. Zuciyarki ta zama ɗaya da takobinki. Yanzu babu wani soja na Turawan da zai iya tsayawa a gabanki ya yi nasara." ​Ya matso kusa da ita, ya sanya hannunsa a kanta... "Inuwar da zan bari a fada tana da ikon yin magana da aikata komai kamar ke, don haka ki saki ranki ki yi yaƙin nan don mutanenki." ✨✨✨ Iya makarantar ne kawai ya rage ba'a rufe ba saboda Examination amma an bada tsaro na musamman sosai... Shiru ne ya ratsa babban Exam Hall na makarantar Royal International Academy. Sautin agogon dake jikin bangon ɗakin kawai kake ji yana bugawa.. tik-tok, tik-tok, tamkar yana ƙirga sauran lokacin da ya rage wa ɗaliban... ​Maayah tana zaune a tsaka-tsakiya, sanye da uniform makarantar... Duk da kyawun fuskarta, yanzu fuskar ta nuna tsantsar firgici... Ta ƙura wa takardar jarrabawar ido, tambayoyin suna yi mata gizo kamar yaren jinnu... ​Iya abin da ta rubuta shi ne sunanta, SHAHZADI MAAYAH MUHAMMAD NOURDEEN... ​Ta daɗe tana kallon takardar, tana son tuno da abin da aka koyar musu, amma kwakwalwarta ta ƙi bata haɗin kai. Sauran ɗaliban dake ɗakin, waɗanda a baya ita ce take nuna musu izza, kowannensu kansa yana ƙasa yana rubutu ba kakkautawa. Malaman dake zagayawa kuwa, duk da cewa tsoronta suke ji a baya, yanzu suna wucewa ne ba tare da sun kalleta ba, domin sun san mulkin Master of Discipline wato Uncle Jalal ya riga ya kawar da tsoron fada a makaranta... ​A can gefe guda, a cikin ofishinsa, Uncle Jalal yana zaune, idanunsa kyam akan jadawalin jarrabawarsa domin ko wani malami da darasinsa... Wata zuciyar kuma tana hasasho masa Maayah a hall duk da cewa akwai wani boyayyen tausayinta da yake ji a duk lokacin da yake mata darasi a gida, musamman yadda take zubar da hawaye idan ya tsawata mata amma a makaranta, shi ne katangar ƙarfe.. ​Lokaci guda, Uncle Jalal ya miƙe, ya nufi hall ɗin jarrabawar. Takun takalmansa ya sanya kowa a ɗakin ƙara nutsuwa. Ya shigo cikin takunsa na isa, ya fara zagaya teburan ɗaliban... ​Ya iso daidai teburin Maayah. Ya tsaya cak, inuwarsa ta rufe takardar jarrabawar tata. Maayah ta ji wani irin Shock, ta kasa ɗagowa ta kalle shi... ​Uncle Jalal ya sunkuyo daidai kunnenta, muryarsa can ƙasa cike da gargadi... "Gimbiya Maayah... saura minti goma sha biyar... Shin sunanki ne kadai kika koya a duk zaman da kike a aji?" ​Maayah ta ɗago idanunta da suka rine da kwalla, ta kalli Uncle Jalal cikin yanayin roko... "Uncle... kaina ciwo yake yi, na kasa tuno komai." ​Uncle Jalal bai nuna alamun tausayi ba, ya gyara tsaiwarsa yana kallon agogonsa... "Nan ba gida ba ne, kuma ni ba Uncle ɗinki ba ne a nan. Ni malamin jarrabawa ne. Idan baki rubuta komai ba, za'a raba miki takardar 'F' ɗinki a gaban kowa, sarki ya gani." ​Ya matsa daga gefenta, ya cigaba da zagawa yana cewa, "Sauran dalibai...saura minti goma! Duk wanda bai gama ba ya hanzarta." ​Maayah ta ji zuciyarta tana dukan uku-uku. Ta kalli bayan Uncle Jalal, tana jin wani irin shauƙi na ƙiyayya da kuma sha'awar yadda yake nuna mata rashin tsoro. Ta ɗauki alkalaminta, hannunta yana rawa, ta fara kokarin zana duk abin da ya zo mata a rai, ko da kuwa ba shi ne amsar ba, don gudun kada Uncle Jalal ya kunyata ta a gaban mutane... ​A ƙarshen hall ɗin, Uncle Jalal ya juyo ya kalle ta. Kwayar idonsu ta sarƙe. Shi ma ya ji wani irin tausayi ya ziyarci ransa, ganin yadda take ta faman kokawa da alkalami, amma dole ya danne domin ya mayar da ita mutuniyar kwarai... Bayan ya fita zuwa ɗakin jarrabawa na gaba, Ɗakin ya ɗan yi sanyi. Maayah ta ƙura wa takardarta ido, tana jin tamkar kanta zai rabe biyu... Sadiq wato saurayinta na wasa wanda take aikansa ya siyo mata abu, yana zaune a kujera ta kusa da ita, ya kammala nasa rubutun tsaf. Ya lura da yadda Maayah take zufa, duk da sanyin dake ɗakin.. ​Sadiq ya yi mata ɗan tari na ƙarya. Maayah ta ɗago idanunta da suka rine.. Ya yi mata nuni da idanu akan ta miƙo masa nata booklet ɗin, shi kuma ya miƙa mata nasa wanda ya riga ya kammala amsoshin. Cikin sanɗa da sauri, suka yi musayar takardun a karkashin tebur.. ​Wani malami dake zagayawa ya gansu, amma ganin Maayah ce, gimbiyar da kowa ke shakka, sai ya ɗauke kansa kamar bai gani ba, ya cigaba da takunsa.. ​Ta fara acting...Ta duƙufa tana kwaikwayon rubutu, amma hannunta yana rawa. Tana rubuta haruffa marasa ma'ana a gefen takardar Sadiq, tana yawan ɗagowa tana kallon ƙofa.. ​Kwatsam! Sai ga Uncle Jalal ya dawo ajin. Ya shigo da wani irin kwarjini, ya tsaya a gaban class ɗin yana bin kowa da kallo ɗaya bayan ɗaya. Idanunsa masu kaifi suka sauƙa akan wani ɗalibi dake can baya yana satar amsa a karkashin tebur... ​Uncle Jalal ya nufe shi gaba-gaɗi... "Give me that!" Ya daka masa tsawa da turanci. Ya fizge takardar, sannan ya karɓe booklet ɗin dalibin ya yaga shi gida biyu... "Get out of my class. Now!" ​Bayan ya gama zagayawa, ya nufi hanyar fita, amma wani abu ya tsaya masa a rai. Ya juyo ya kalli Maayah. Ya lura da yanayinta, bata danna biro kamar yadda mai rubutu yake yi, kuma yawan ɗagowan da take yi tana kallonsa ya ba shi shakku... ​Ya tako a hankali har ya iso gefenta. Ya tsaya kyam, ya zuba mata ido... "Anya kina da gaskiya kuwa, Gimbiya?" ya faɗa cikin muryar raɗan nan tasa mai tsoratarwa... ​Maayah ta daskare. Ta kasa magana, sai dai kawai ta zuba wa booklet ido... ​Uncle ya sa hannu ya janye littafin. Ya buɗe shafin ƙarshe, ya ga har tambaya ta karshe an amsa ta.. "Yanzu a fitar tawa har kika kai ga tambaya ta karshe?" ​Cikin zargi ya buɗe shafin ƙarshe na takardar. Nan take ya ga rubutun daban ne, rubutu ne mai ɗaukar hankali, ba irin na Maayah dake tangal-tangal ba. Ya sake juyo da shafin gaba don ganin sunan dake kai... ​ABUBAKAR YUNUS... ​Zuciyar Uncle ta buga. Ya kalli Sadiq, sannan ya kalli Maayah wadda ta riga ta fara hawaye. Sadiq kuwa ya gama kiɗimewa, numfashinsa yana fita da sauri-sauri... Uncle Jalal ya tsaya kyam a gefen Maayah, inuwarsa ta mamaye teburinta, wanda hakan ya sa numfashinta ya kusa tsayawa...Ya sanya dogayen yatsunsa ya janye booklet ɗin a hankali.. Maayah ta kalli Sadiq da gefen ido, shi ma Sadiq ya riga ya daskare, zufa tana keto masa ta ko'ina duk da sanyin AC dake ɗakin.. ​"Ina kika samu wannan dabarar, Maayah?" Uncle Jalal ya faɗa cikin murya mai sanyi mai cike da ɓacin rai... ​Maayah ta yi tsuru-tsuru, muryarta tana rawa.. "Uncle... rubutu na ne, kawai na yi sauri ne shi ya sa ya canza." ​Wani murmushin takaici ya subuce wa Uncle... "Sauri? Sauri har ya mayar da sunanki Abubakar Yunus?" Ya ɗaga littafin sama yadda kowa zai gani, sannan ya kalli Sadiq wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa yana rawar jiki... ​"Abubakar Yunus! Tashi tsaye!" Muryar Uncle Jalal ta daki bangon ɗakin kamar ƙarar tsawa... ​Sadiq ya miƙe tsaye jikinsa na kyarma... "Sir... dama... dama taimaka mata zan yi..." ​Uncle Jalal ya taka zuwa gaban Sadiq, ya raba shi da booklet ɗin dake gabansa, wanda kusan babu komai a ciki sai sunan Maayah... "Taimaka mata? Shin kai ne Sarki da zaka bayar da tallafin maki a ɗakin jarrabawa? Ko kuma ka ɗauka dokokina na wasan yara ne?" ​Ya juyo kan Maayah, wadda hawaye suka fara wanke mata fuska.. "Gimbiya Maayah, kin nuna min cewa duk kokarin da nake yi a gida asara ne. Kin gwammace ki yi sata da sunan wani namijin, maimakon ki faɗi da mutuncinki." ​Ɗakin ya yi shiru, sauran daliban suna kallon ikon Allah. Malami na farko da ya share su kuwa ya ɓuya a can gefe yana zaro ido... ​Uncle Jalal ya yage booklets guda biyun a gaban kowa, fatsa-fatsa!... ​"Kuje ku fita daga ɗakin nan! Maayah, Abubakar, kun faɗi wannan darasin... Kuma ina tabbatar muku, sai na sanar da Minister da kuma Mai Martaba Sarki abin da kuka aikata yanzun nan." ​Maayah ta fashe da kuka mai karfi. "Don Allah Uncle Jalal! Kada ka gaya wa Abul, zai iya min kowane hukunci!" ​Uncle ya nuna musu ƙofa da yatsa, idanunsa sun yi ja tsantsar ɓacin rai. "Fita! Tun kafin in rasa natsuwata a kanku!" Bayan sun fita.. Maayah bata wani tsaya ba domin daman Uncle Jalal ne mai zuwa ɗaukanta a gida idan an tashi kuma ya mayar da ita.. Ya dakatar da kawota a tsararrun motoci sama da biyar da bodyguards saboda a tunaninsa hakan zai sa tana yawan ji da kai.. A wannan lokacin haka take takawa tana tafiya a hankali, ba'a san ta fita ba ma... Kawai tafiya take tana hawaye, a tunaninta ta gama amfani yanzu.. Ba wai gida ta nufa ba, kai tsaye cikin daji tayi.. Tana tafiya hankalinta ya gama fita daga jikinta.. Bayan sa'o'i guda.. Kowa ya fito a exam, Sadiq ya samu Uncle a office Yana ta roƙonsa amma Uncle yace, "ai ya riga ya faɗi a wannan exam sai dai ya kiyaye zuwa next.." Sadiq yayi magiyar har ya haƙura.. Ya fita.. Can motoci ne suke zuwa ɗaukan ɗalibai dake duk makarantar na ƴaƴan masu kuɗi ne....kuma an ƙara kafa tsaro saboda yanayin garin bashi da kyau sai satar mutane ake.. Uncle ya fito daga office ya tambaya ina Maayah akan zai kaita gida shi kuma sai ya wuce... Amma an dudduba ko ina ba'a ganta ba.. Sai Sadiq ne da zai tafi motarsu tazo ɗaukansa yake sanar wa cewa Maayah fa ta daɗe ta fita daga makarantar... A take Uncle Jalal ya ƙira wani jami'i mai tsaron get ɗin fada ya tambaya cewa Maayah ta iso kuwa? Aka sanar da a'a. Nan Uncle Jalal ya ɗauki superbike ɗinsa ya fita daga makarantar a ɗari... Yana fita ya bi hanya amma bai ganta ba..yana ta tambaya amma babu wanda ya ganta.. Ya shiga tashin hankali.. Ya juma yana neman ta amma bai sameta ba, ya ƙara ƙiran fada akan ta isa, aka nasar da a'a... Ya bi hanya yana tambaya, har ya haɗu da wani dattijo... "Baba, ko ka ga wata ɗaliba ta wuce nan?" Dattijon ya nuna masa can cikin kurmi. "Na ga wata yarinya tana kuka ta nufi wancan jejin." ​Uncle Jalal bai tsaya wata-wata ba, ya murɗa wutar mashin ɗin, ya lulƙa cikin jejin. Yana ta gudu, yana kewayawa tsakanin bishiyoyi har sai da ya iso wani fili mai faɗi. A can gabansa, ya ga ramin da kowa ya sani, babban rami ne mai gudun ruwa a ƙasa, wanda idan mutum ya faɗa, ba za a taɓa samun gawarsa ba.. ​Ya hango Maayah tsaye a bakin ramin, tana ta maganganu cikin kuka... Iskar dajin tana kaɗawa da ƙarfi, tana tura kukan Maayah zuwa cikin ramin dake gabanta... Ruwan dake karkashin ramin yana gudana da wani irin sauti mai ban tsoro, yana jiran duk abin da zai faɗo masa.. Tana tsaye a bakin rami, uniform ɗinta yana kaɗawa cikin iska da sumar gashinta duk da akwai hula akai.... "Gwara na mutu kowa ya huta!" ta faɗa cikin kuka mai cin rai. "Na gaji da wannan rayuwar ta kunya. Abul ya tsane ni, Uncle Jalal shima ya tsane ni.. Babu amfanin rayuwata!" Ta rufe idanunta, ta sanya ƙafa ɗaya tana shirin tura kanta cikin ramin. A daidai lokacin da take jin jikinta yana neman tafiya... "Maayah!" Wata murya ta daka mata tsawa, muryar da ko a cikin mafarki ta ji ta, ta san ta Uncle Jalal ce. Ba ta ko juyo ba, ta ƙara zamar da ƙafarta.. "Kada ka matso! Ka bar ni na huta!" Kafin ta samu damar sakin jiki, Uncle Jalal ya daka wani uban tsalle daga kan mashin ɗinsa. Cikin zafin nama irin na jarumai, ya damko damtsen hannunta da wani irin ƙarfi, ya juyo da ita baya da karfin tsiya.. Saboda gudun da ya kwaso, sai da suka faɗi ƙasa tare, yana kanta, numfashinsa yana fita da sauri-sauri, idanunsa sun yi jawur tsabar tashin hankali... Ya miƙe tare da ita, ba tare da ya ba ta damar yin magana ba, ya daka mata wata uwar tsawa.. "Ke wace iriyar wawiya ce?! Mutuwa kike nema?!" Sai kawai ya ɗauke ta da wani lafiyayyen mari.. Dukan farko ya sauƙa a kuncinta na dama. Maayah ta daskare, idanunta suka zaro waje... Na biyun ya biyo baya. Waɗannan lafiyayyun marukan suka sa kanta juyawa, kukan ma ya tsaya mata a makoshi... Ta kalli Uncle ta ga yadda jikinsa yake rawa, ba na fushi kaɗai ba, har da na tsoron rasa ta... "Kin san abin da kika kusan yi wa kanki kuwa? Kin san tashin hankalin da kika sanya ni?" Muryarsa ta dashe, yana sake damko kafadunta... "Idan kin faɗi jarrabawa, wannan dalili ne na kashe kanki? Me ya rage miki a duniya idan rayuwar taki ta ƙare a nan?" Maayah ta dube shi, hawaye masu zafi suna kwarara. "Amma ai ka ce na faɗi... ka ce zaka gaya wa Abul..." Uncle ya rungume ta da karfi lokaci guda, rungumar da ta nuna tsantsar tausayi da ƙauna, saɓanin dukan da ya yi mata yanzun nan... "Ba zan taɓa barinki ki mutu ba a wannan yanayin Maayah. Ko da kuwa zan koya miki darasi ne amma kada kiyi tunanin na mutuwa ne. Kin nuna min yau cewa ba ki san darajar kanki ba..." Bayan marukan da ya zabga mata, Maayah ba ta daɗe cikin hayyacinta ba. Wani irin hauka ya ƙara turnuke ta, ta fusge kanta daga rungumar tasa, ta juya da gudu ta nufi bakin ramin tana kuka... "Ka kyale ni! Mutuwa nake so!" Uncle ya ƙara daka wani uban tsalle ya sake cabko ta a daidai gaɓar ramin... Saboda ƙarfin gudun da ta ɗauka da kuma nauyin jikinsa da ya faɗa kanta, sai suka rasa daidaiton sawunsu. Nan take suka fara gangarawa daga kan tudun zuwa wani gangaren mai ban tsoro... Dake wurin sai kayi a hankali, saboda tudu da gangarensa, da kuma ramuka da yawa.. "Wayyoooooo!" Maayah ta sake wani irin ihu mai ban tsoro wanda ya karaɗe jejin... Sunka fara gangarawa suna juyawa, wani lokacin Maayah a ƙasa, wani lokacin Uncle Jalal. Cikin zafin nama, Uncle ya sa hannuwansa duka ya kankame ta, ya danne kanta a kirjinsa don kare ta daga buguwa da duwatsu.. Maayah kuwa ta sa hannu ta damke gaban rigarsa, tana kuka da ihu yayin da suke ƙara nisa cikin gangaren... Basu tsaya ko'ina ba sai ga su Giffffff! sun faɗa cikin wani babban kogo mai zurfi wanda ciyayi da kananan kofofin ruwa suka kewaye.. Shiru ya biyo baya. Maayah tana kwance a saman kirjinsa, idanunta a rufe ta riga ta suma saboda tsananin firgici... Uncle Jalal ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya, jikinsa duk ya yi tsami, rigarsa ta yage a wasu wuraren. Ya yi kokarin tashi, ya juyar da ita daga kansa ya kwantar da ita a kan rantsatstsen korayen ciyayin dake cikin kogon... "Maayah! Maayah!" ya fara jijjiga ta, muryarsa tana rawa. Ya kalli kyakkyawar fuskarta wadda ƙura ta ɓata, ya ji wani irin tausayi ya ziyarci ransa. Ya taɓa wuyanta ya ji jini yana bugawa, nan ya san tana raye... Ya ɗaga kansa ya kalli saman kogon da suka faɗo. Ya ga nisan wurin ya fi karfin a iya takawa a hau, kuma babu wani abu da za a iya kamawa. Ya duba ko'ina, sai sautin ruwan dake gudana a cikin kogon yake ji. Sun tsinci kansu a inda ba su taɓa tsammani ba... Ya koma ya zauna kusa da ita, ya zuba mata ido yana kallon yadda ƙirjin ta yake sama da ƙasa saboda numfashi... Sanyin kogon ya fara ratsa ƙashinsa, ga daddaɗan sautin ƙananan koguna dake gudana a cikin kogon. Ya kalli Maayah, fuskarta ta yi fari saboda firgici da kuma sanyin dake ƙoƙarin shiga jikinta.. ​Ya rarrafa ya isa bakin ɗaya daga cikin ƙananan kogunan, ya tsoma hannunsa cikin ruwan mai sanyi kamar ƙanƙara. Ya dawo kusa da ita, ya fara yayyafa mata ruwan a fuska, sannan ya sa tafin hannunsa yana shafa fuskarta a hankali.. ​"Maayah... Maayah, ki tashi..." ya furta cikin muryar raɗa.. ​Maayah ta fara motsa idanunta, a hankali ta buɗe su. Abu na farko da ta gani shi ne fuskarsa da take kusa da tata, idanunsa cike da damuwar da ba ta taɓa gani ba. Ta rintse idanun ta ta sake buɗewa, tana jin sanyin kogon yana sa jikinta rawa.. ​"Uncle..." ta furta cikin muryar da ba ta fita sosai. ​Ba tare da ya ce uffan ba, ya sa hannu ya janyo ta jikinsa, ya rungume ta da ƙarfi domin ya ba ta ɗumin jikinsa.... Ba ta yi musu ba, ta ƙara shigewa jikinsa tana kuka ƙasa-ƙasa, tana jin yadda bugun zuciyarsa yake dukan ƙirjinta.. Wannan sanyin ya sa duk wani girman kai ya kau, ya bar gurbinsa ga buƙatar kariya. ​Ta ɗago ta kalli saman kogon da ya yi nisa... "Ba za mu iya fita ba, ko? Mutuwa za mu yi a nan?" ​Uncle Jalal ya ƙara ƙanƙame ta, ya duba ƙwayar idonta... "Ba za mu mutu ba Maayah. Muddin ina raye, ba zan bar komai ya same ki ba. Wannan wurin zai zama sirrinmu, babu wanda zai san me ya faru a nan." ​Maayah ta kalli yadda rigarsa ta yage, ta kai hannunta ta taɓa inda ya ji rauni a kafaɗa. "Ka ji ciwo saboda ni..." ​A take Uncle ya ji wani irin shauƙi ya ziyarci ransa. Ya kalli leɓunanta dake rawa saboda sanyi, sannan ya kalli idanunta... A wannan lokacin babu malami ko gimbiya, sai mutum biyu da ƙaddara ta haɗa a cikin kogon ƙasa... ✨✨✨ Bayan King Diamond ya dawo da Ayat ɗakin baccinta, ya sumbace ta a goshi a matsayin alkawarin kariya, sannan ya ɓace... Amma yana isa duniyar aljanu, bai tarar da natsuwa ba.. Manya-manyan majalisar aljanu sun taru a kewayen Power Pool, idanunsu suna hura wuta... ​Dattijon cikinsu, wanda ake ƙira da Azazil, ya tako gaba, muryarsa tana girgiza duwatsun fadar. ​Azazil ya ce, "King Diamond! Ka ƙeta dokar da aka kafa dubunnan shekaru. Ka sanya jininmu da na bil'adama ya gauraya ta hanyar shauƙi da musayar jini..... me ya sa kake ɓata lokacinka akan mace 'yar ƙasa, wadda numfashinta yake ƙarewa cikin kiftawar ido?" ​Wani Aljanin ya ce, "Mun ga yadda kake shige mata, kusancinku yayi yawa sosai....har ta kai ga a kwanaki kana kwana da ita a matsayin kuliya...Sannan ka kawo ta kana koya mata sirrin yakinmu! Ka mayar da kan ka bawan mace maimakon Sarkinmu!" ​Ko wani shugaba da abinda yake faɗi... ​King Diamond ya tsaya daram, gashinsa na yawo a iska, idanunsa na shuɗi sun yi jawur saboda bacin rai... ​Ya furta cikin ƙwarin gwiwa "Ina amfanin mulki idan ba zan iya kare abin da zuciyata take so ba? Ayat ba mace bace kawai, ita ce inuwar da take sanyaya min zafi na tsawon shekarun baya...." ​Azazil ya ce, "Hukuncinmu ɗaya ne! Ko dai ka yanke alaƙa da ita yanzu, ko kuma mu kwace duk Ikon Sarauta dake tattare da kai. Idan muka janye wannan ikon, ba za ka iya bace-wa ba, ba za ka iya ba ta kariya ba, kuma ba za ka iya yin aiki da ikon mu ba...." ​King Diamond ya yi murmushin rainin wayo sannan ya ce, "Kuna tunanin ikon da nake da shi ne yake sa ni faɗa? A'a. Zuciyata ita ce babban ikona. Ko da za ku janye komai, zan tafi wurinta a matsayin kowane irin hali. Idan har kariya ta tana nufin zan zama mazauni a duniyar mutane, to na shirya!" ​Majalisar ta yi kukan ruri, hasken ɗakin ya fara dishi-dishi da wani irin walƙiya... ​Azazil cikin ɓacin rai ya furta "Ka zaɓi kaddararka. Daga daren yau, mun janye kashi saba'in na ikonka. Ba za ka iya keta hazo cikin sauƙi ba, kuma duk raunukan da za ka ji a duniyar mutane, za su zama raunuka na haƙiƙa a jikinka. Ka zama tamkar mutum mai ɗan karamin ikon aljani." ​King Diamond ya ji yadda karfin dake jikinsa yake raguwa, ya ji nauyin jikinsa ya ƙaru, amma bai nuna tsoro ba... ​Sai ma cewa da yayi.. "Ku kwace duka idan kuna so. Amma ku sani, ko da hannu ɗaya zan yi faɗa, ba zan taɓa barin Ayat ta zama ganima ga kowa ba..." Sauran Aljanun suka furta "Akwai sauran hukunci zuwa gaba..." Daga nan duk suka ɓace..domin sun san shi da masifar taurin kai da kafiya akan abu... Bayan wasu sa'o'i yana zaune yana faman saƙe-saƙen zuci... Kodayake an rage masa kashi saba'in na ikonsa, amma ragowar kashi talatin ɗin sun isa su girgiza duniya...Abokinsa Prince Zarith yana gefensa, yana ta faman zazzaga surutu.. ​ "King, ka saurare ni! Wannan yarinyar bil'adam za ta zama silar rugujewar ka. Ka barta tayi rayuwarta ita kadai, domin babu aure a tsakaninku...kar ka zo kayi biyu babu, ka ceci kanka daga fushin dattijan aljanu!" ​King Diamond ya yi banza da shi, idanunsa suna kallon sararin samaniya. Tunaninsa ɗaya ne... "Ta yaya zan samar da Ayat ta biyu wadda za ta zauna a fada ba tare da an gane ba?..." Lokaci guda, fuskar ɗan uwansa, Chief Onyx wato Ra'ees ta faɗo masa a rai... Onyx kaɗai ne yake da fasahar da za ta iya ƙera Robot wanda zai yi kamanin Ayat ɗari-bisa-ɗari... ​Ba tare da cewa uffan ba, King Diamond ya miƙe, hasken shuɗi ya gauraye jikinsa. Zarith ya saki baki yana kallo, sai kawai ya ga Diamond ya ɓace kamar walkiya... ​Bai sauƙa a kowane lungu ba sai a gaban katon babban gate ɗin masarautar Pavilion City... Wani birni ne da aka gina shi da gilashin da ba ya fashewa, cike da fasahar da ta wuce tunanin ɗan Adam... Wannan ne karon farko da zasu yi face to face tin yarinta kuma akan wani aiki.. Duk da a cikin zuciyar King Diamond bai so ya je wurinsa ba domin yana tunanin ai bai damu da shi ba... Shima Chief onyx Yana ganin tunda King Diamond aljan ne ai zaifi neman yadda yake ya neme shi amma bai damu da shi ba.. Sai kowa ya sharar da kowa saboda kowa a cikinsu yana fama da girman kai da jiji da kai... Ga kuma King Diamond yana jin haushinsa yadda ya wulaƙanta Ayat a walimar sauƙar al'kur'ani su... ​King bai zo da sauƙin kai ba... Yana takowa, wata irin ƙaƙƙarfar guguwa mai ɗauke da sanyi da ƙura tana biye da shi, tana kakkarya duk abin da ya yi yunkurin tare shi... Bodyguards ɗin Chief Onyx, dakarun zamani masu ɗauke da makaman lantarki, suka fara yo kansa... "Tsaya a nan! Waye kai?...!" ​King Diamond bai ko kalle su ba. Wannan guguwar dake biye da shi ta riƙa ɗaukar bodyguards ɗin tana sama da su, tana buga su da ƙasa. Yana tafiya yana ratsa cikin dogayen gine-ginen gilashin fadar. Duk da cewa gilasan Pavilion an kera su ne da gilashi masu bala'in ƙarfi, amma kwarjinin King Diamond ya sanya su fara faffashewa ɗaya-bayan-ɗaya... ​"PHAS! PHAS! PHAS!" Sautin fashewar gilashin yana tashi kamar ƙarar bindiga... ​A can cikin babban falon masarautar, Chief Onyx yana zaune a kan kujerarsa ta alfarma. Gaban faffaɗan allon Plasma dake nuna podcast na duk abin da yake faruwa a bakin gate... ​Yana kallon yadda wannan guguwar take tunkaro shi. Ya ga wani matashi mai farin sumar gashi da idanun shuɗi, wanda kamaninsa da nasa kusan iri ɗaya ne, yana take duk dakarunsa... Ko kiftawa Onyx baya yi, kuma bai nuna alamar tsoro ba, duk da yadda gine-ginen falon nasa suke girgiza.. ​Onyx ya gyara zama, idanunsa suka yi walwali da wani boyayyen sirri. Ya san wannan ba kowa bane face ɗan uwansa, tagwayensa, wanda duniya ta raba su shekaru 23 da suka wuce... Wasu robots ne kala-kala suka shigo falon da Chief yake suna sanar dashi irin ta'adin da wani Jinn yake musu.. Abinda Chief ya furta cikin rashin damuwa shine "Ku bar shi ya ƙaraso..." Ya ƙarasa maganar tare da ɗaukan lemon juice ya kurɓa... Yana sanye da silver mask ta gefen fuska wanda yake rufe sirrin kamanninsa.. ​King Diamond ya isa ƙofar falon ƙarshe, ya sanya kafarsa ta dama ya buga ƙofar, guguwar dake bayansa ta haɗiye ɗaukacin hasken falon... Sun faɗo cikin duhu, kuma babu wani haske da zai iya bayyana yadda za su fita... ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! ​📢 EXTRACT: DOMIN CIGABA DA BOOK TWO! ​Anan muka kawo ƙarshen Book One. Shin yaya za ta kasance tsakanin manyan tagwayen nan biyu a masarautar Pavilion? Shin Inuwa (Ayat) za ta iya jure wa yaƙin dake jiran ta? Ko kuwa ya zata kasance da Uncle Jalal da Maayah a cikin kogon can mai zurfi? *SHIN WANI SCENE NE YAFI BURGE KU KO YA KWANTA MUKU A RAI?* _CHING-CHING— CHIEF ONYX—GELY.._ _AYAT—KING DIAMOND._ _MAAYAH—UNCLE JALAL_ To fa ga kuma Zayana har yanzu a Cell, sarki kuma yana son kawar da tsoron Ruma a zuciyarsa ta hanyar cigaba da tsare Zayana... ​Domin samun cigaban wannan labari a Book Two, ga yadda tsarin yake: ​Paid Group (Page by Page): N500 kacal. ​Full Document (Bayan an kammala): N700 kacal. ​Kada ku bari a ba ku labari, domin Book Two ya fi komai zafi! *MASU KARATU, KU SHIRYA DOMIN BOOK TWO YA FI WANNAN ZAFI DA TASHIN HANKALI!....* _BAYAN SALLAH ZA'A ƊORA DAGA YADDA AKA TSAYA GA WAƊANDA SUKA YI PAYMENT..._ Za'a fara saka sunaye a list tun yanzu. Da zarar lokaci ya yi, za a ɗora kai tsaye. ACCOUNT DETAILS: Opay / Palmpay 9065443871 Asma’u Muhammad Auwal 📩 Tura shaidar biya + sunanki domin a saka ki/ka a list.... *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment