💞 JINAH (Matar Aljani)💞 _Sabon labarin soyayya_ Na Malik al-Ashtar *PROLOGUE* Motsi take ji, takun sawun kafafu na kara tinkaro inda take, a jikinta tana jin ko meye ke nufota zai cutar da ita ne. Amma ta yaya zata iya guduwa, ta yaya zata iya guduwa domin ta buya? Alhali ba zata iya ba, domin sai da kafafuwa ake gudu, ita kuwa bata da su. Abinda kawai take iya yi shine tayi rarrafe. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta fara rarrafawa iya karfinta, duk da haka ba zata iya kubuta daga wannan mutumin da tuni ya nufo gurinta yana tangadi. Namiji kakkausa mai girma, jiki ne ya fara yi mata rawan tsoro koda ta hada ido dashi. Kallonta yayi tare da yin wani shu'umin murmushi, ita kuwa ganin hakan ma ya kara mata tsoro, kara kusanto ta yayi tare da durkusawa daidai kafafunta. Murya na mata rawa ta tambayeshi "Me kake so dani?" Ba tare da bata amsa ba ya kara kokarin riketa ita kuwa da sauri ta kara ja baya daga zaune bisa mazaunanta. Kara yunkurawa yayi ya rikota tareda fincike mataccen zanin dake jikinta. Tayi ta kokarin ta kwaci kanta, amma hakan ya faskara domin akwai banbancin karfi tsakanin su. Wani masifaffen wari ne ke fita daga jikinshi, warin giya ne, alamar yasha ya bugu ne. Cikin muryar kuka da ban tausayi take rokon wannan mutumi "Dan Allah kayi hakuri ka kyaleni! baka ganin yanda nake? Mumuna kuma gurguwa? Kayi hakuri ka kyaleni kar kara min wata najasar!" "Ke kike ganin wannan a jikin ki, dan abinda nazo nema wajenki bayada wata nasaba da kazantarki ko gurguntarki." Kalmomin da kawai suka fito daga bakinshi, ya cigaba da abinda ya kawoshi. Bai rabu da ita ba har sai da yaga ya samu biyan bukatarshi, yayi mata fyade. Sunanta Hauwa, ita kadai ke rayuwa cikin bukkarta nesa da wani kauye mai suna Kumana dake a wata kusurwa a kasar Nijar, kauye ne da kowane gida yake rayuwa cikin farin ciki amma banda ita, kauye ne da kowane makoci yake zaune lafiya da makocinsa amma banda ita. Sanadin munin da take da shi ga kuma kasancewarta musaka na rashin kafafuwa duka biyu yasa mutanen garin suka koreta a cewar su Mayya ce. Ta kasance ita daya ke da irin wannan halittar a kauyen, ita kanta ba zata iya tuna ina mahaifanta suke ba, kawai ta tsinci kanta korarriya kamar kare daga wannan kauye tun tana yar karamarta. Bayan ya gama abinda yake so, ya fito ya barta a sume yayi tafiyarshi ba tare da ya waiwaya ba balle ya duba ko tana raye. Bayan wasu awanni Hauwa ta farka, matsanancin ciwon da zugin da tsakanin cinyoyinta ke mata yasa ta fashe da kuka mai tausayi, gashi babu wani da zai kawo mata dauki, ba dangin kusa balle na nesa. BAYAN WATA TARA (9) Wannan rana ta banbanta da sauran ranakun, Hauwa tana jin wani abu, tana jin wani abu da itama ba zata ce ga asalin abinda take ji ba. Ta tashi ne tana jinta cikin wani farin ciki, komai lafiya lau. Katon cikin dake jikinta ta shafa, jin alamar yanda dan cikin nata ke motsawa yasa ta saki murmushi. Sanadin wannan fyaden da wannan mutumi yayi mata watanni 9 da suka wuce yasa ta samu ciki,duk da ba wai kamar kowane da bane, shi ga sanadin yanda ta sameshi amma tana cikin farin ciki, ko ba komai yanzu tasan ba ita daya bace tanada mai debe mata kewa, wanda take samu tayi fira dashi duk da tasan ko dan cikin nata na jinta ba zai iya amsa mata ba. Tana jin dan cikin nata har cikin ranta, domin shine haske yanzu a gareta. Fitowa tayi da rarrafe ta nufi cikin dajin domin samo abinda zata saka ma cikinta. Bayan taje ta samu 'ya'yan itatuwa da suka fado kasa taci ta koshi, komawa tayi gindin bishiyar wani mangoro dan ta dan huta kafin ta juya zuwa gida. Bacci ne mai nauyi ya dauketa har dare yayi, sheshekar kuka ne ya tayar da ita. Inda take jin sautin kukan ta nufa tana yi tana buya. Wata matashiyar mata ta gani sanye da zallan fararen tufafi ta gani a durkushe a kasa. Kasa dauke idanunta tayi daga kan wannan mata, don wannan shine karin farko da taga irin wannan halitta. Ta raya a zuciyarta "dan mutum ba zai iya samun irin wannan kyau ba haka, gaskiya wanann Matar tanada masifar kyau." Kasada ta dauka na karasawa kusa da matar tare da tambayarta "Baiwar Allah lafiya kike kuka?" Cikin sheshekar kuka ta bata amsa "Yarona... yarona mutuwa zai yi idan ban bashi Yattaba ba, ganyen shuka da shine zai iya warwakar dashi!" Cikin tausawa Hauwa tace "Ayyah, ai kuwa akwaishi a cikin killatacciyar fadamar kauyen nan." Matar tace "Ai ba yanda zan yi na shiga fadamar domin ni Aljana ce." Gaban Hauwa ne yayi wani mumunan faduwa, tsoro ya mamayeta, cikin ziciyarta take cewa : Na shiga uku ni Hauwa, yau kuma na taro abinda yafi karfina, aljanu wadannan dai masu karfin sihiri da shan kwalwar mutum, yau gani ga daya daga ciki. Me zan yi yanzu? Idan nace zan gudu, rarrafe nake kafin nayi wani yunkuri zata kamani. Ganin yanda jikin Hauwa ke mazari aljanar ta fahimci ta tsorata ne "Kar ki damu ba zan cutar dake ba, zaki iya tafiyarki ki kyaleni na cigaba da kukan mutuwar dake tunkaro yarona (Dana)." Hauwa juyawa tayi, tayi tafiyarta sedai ba gidanta ta nufa ba, wannan fadamar mai tsaro ta kauyen ta nufa, guri da dan Adam ne kawai zai iya shiga gurin, Idan har aljani yayi kuskuren shiga wurin to fa ba zai fito da rai ba, dan fadama ce da mutanen garin suka gada daga kakanin su mai cike da tsaro na tsafi. Hauwa tana son ta taimaki wannan aljana, dan ita daya ce ta taba yi mata magana ba tare da ta nuna mata kyama ba. Cikin sanda da kulawa Hauwa tayi nasarar debo ganyen. Cikin kuka mai hade da farin ciki aljanar take ma Hauwa godiya, ta amshi ganyen da dan gudunta dan taba danta. Lokaci na farko da Hauwa ta fara jin wani mummunan ciwon ciki ya turnuketa, da alama lokacin ne yayi, Haihuwa. Har awanni masu yawa suka shude Hauwa na cikin wannan hali, har lokacin da aljanar ta tardota. "Na zo ne in maki godiya, ta dalilinki dana ya samu lafiya, ki fada min duk abinda zan yi maki ni kuma zan yi ma..." Tsayawa tayi da maganarta sakamakon ankara da tayi da halin Hauwa take ciki. "Wayyo.. ci..kina, da alama ya..ro..na ne ke zuwa...! Aljanar ta fahimci haihuwa ce zata yi, anan ta fara kokarin taimaka mata, bayan wani lokaci kadan ta haife 'yarta mace. Aljanar ta rike 'yar tana murmushi tare da sanar da Hauwa abinda ta haifa. Murmushi da hawayen farin ciki ne suka kwacema Hauwa. Wuka aljanar tasa ta yanke cibiyar yarinyar sannan ta nadeta da zani. "Ina rokonki da ki kular min da 'ya ki rike min ita,ki kawatata da kyau kamar naki, bana son ta wulakanta kamar yanda na wulakanta, ina son ki saka mata suna JINAH, ma'ana aljana da yaren mu..." Sai yanzu aljanar ta fahimci kalar kalamin da Hauwa take, alama ce ta mutumin da karshensa yazo, domin bata karasa fadin abinda take son cewa ba rai yayi halinsa. Aljanar daukar yar jinjirar mai suna Jinah tayi zuwa gidanta, kafin daga bisani taje ta bizne gawar Hauwa. "Daga ina kike da dan Adam? Kinsan hadarin da ke tattare da kawota nan da kika yi?" Cewar mijin aljanar bayan ganin Jinah da yayi. "Yar matar nan ce da ta ceci dan mu, bayan ta haifeta ne ta mutu kuma ta bani amanar 'yarta ne kuma na dauka." "Amma kin sani sarai cewa,sauran dangin mu (Aljanu) ba zasu karbi dan Adam ba a cikin mu, kuma zamu fuskanci babban hukunci idan suka gano hakan." Sanin mijinta nada gaskiya yasa bata kara cewa komai ba, dan tasan ta riga da ta dauki alkawari kuma dolenta ta cikashi. Tuna alkawarin zata mayar mata da 'ya kyakyawa yazo mata, sedai tuni Jinah mai kyau ce dan tsabar kyau itama kamar aljanu take. Jinah girma take yi a hankali a cikin wadannan halittu (aljanu), sedai ta ganin tsana a gun sauran aljanu, duk da su marikanta suna kaunarta sosai, suna jinta tamkar 'yar cikin su, kuma suna kareta daga dukkan wani sharrin aljani da yake son cutar da ita, tana samun kulawa haka daga wajen dan uwanta (dan marikanta wanda mahaifiyarta ta ceta) mai suna Fally, Fally yana matukar son Jinah dan a kullum sai yayi fada da yan uwanshi aljanu idan suka ce zasu taba Jinah. Son da yake nuna ma Jinah yayi tsananin da har iyayensa sun sanar dashi illar yin hakan, dan babu aure tsakanin dan Adam da aljani, kuma hukunci mai tsanani ga duk wanda yayi kokarin taka wannan doka a duniyar aljanu, amma ina shi Fally bai san wannan ba dan tuni har yaga Jinah ta zama matarshi, kuma itama haka sosai take sonshi. Wata rana Fally ya dauki Jinah zuwa wani kebataccen guri wanda wannan guri ya kasance anan aljanu wanda suka kasance masoya, suke alkawarin zama tare na har abada a tsakanin su. A lokacin Fally na da shekaru 18 ita kuma Jinah na da 16. "Jinah kin shirya zama dani, zama dani har abada?" cewar Fally rike da hannuwan Jinah suna masu kallon Juna. "Sosai ma, ina kaunarka kuma zan kasance koda yaushe a tare da kai." Ta bashi amsa cikin farin ciki Wata yar karamar wuka Fally ya dauko tareda yanka babban yatsanshi, itama haka Jinah tayi, sannnan suka hada yankakkakun yatsun nasu gu daya inda jinin nasu ya garwaya. Bayan sunyi hakan sannan Fally ya dauko wata kwarya mai dauke da wasu koren ruwa, ya fara sha sannan ya ba Jinah itama tasha. Jinah cire zanin dake daure kugunta tayi, sannan ta kara cire wanda yake daure a kirjinta. Kwantawa tayi akan wani jan kyalle dake shinfide a gurin babu komai a jikinta. Shima Fally dama wani gajeren wando kadai a jikinshi ya fiddashi, sannan ya zuba wasu ruwa a jikin Jinah, bayan wani dan lokaci sai ga wani maciji ya bayanna a hannunshi, sakin wannan maciji yayi yanata bin jikin Jinah, uta kuwa ko a jikinta, dan ta san wannan yana daga cikin siddabarun alkawarin nasu, kuma daman ta iya sarrafa dabbobi kamar sauran aljanu, kuma kasancewar kyawun dake gareta irin na aljanu yasa tana iya yin wasu abubuwa sosai wanda cikakken dan mutum ba zai iya ba. Macijin ya bace bayan wasu yan lokuta. Bayan wannan, cikin farin ciki Fally suka raya wannan rana kamar kowanne ango da amarya. Hakan zai nuna sun dau alkawarin zama na har abada a tare. Waje kuwa, sama tayi mugun baki, wanda hakan na nuna ba alkhairi a yau, eh babu alkhairi don saduwar mutum da aljani baya haifar da abu mai kyau. Lokacin da suka zo tafiya gida, Jinah da Fally sun lura da canjawar yanayi na garin, su kuwa ko a jikin su dan yau ta kasance masu ranar farin cikin da ba zasu taba mantawa da ita. Fally daukan Jinah yayi suka nufi gida, tin daga nesa suke jiyo kukan Mahaifiyar Fally wato uwar rikon Jinah. Fally aje Jinah yayi suka nufi dakin mahaifiyar tasu. Mahaifiyar karasowa tayi wajen Fally kafin ta sakar masa wani masifaffen mari. Dafe kunci Fally yayi kafin ya dago ya kalli mahaifiyarsa cike da mamaki. "Mama me ya faru? me nayi kika mareni?" Fally ya tambayi mahaifiyar tashi cike da mamaki. "Me ya faru mama?" Ita ma Jinah ta kara jefo ma uwar cikin mamaki. "Baku ga yanda sama tayi bane? Ko baku ji kukan dabbobi bane? Ku a ganin ku lafiya a wannan lokacin mahaifin ku baya gida?" Kallon Juna Jinah da Fally suka yi dan su har yanzu basu fahimci komai ba. "Ke Jinah tun tuni na fada maki, mahaifiyarki ta mutu, kuma mutum ce, kuma kema mutum ce, mu kuwa jinsin aljanu ne. Kuma akwai banbanci tsakanin duniyat mu da taku, wanda dole watara zaki nemi ki zama uwa, ki yi aure ki haihu, kuma hakan zai faru ne kawai idan kin auri mutum dan uwanki. Sai da na fada maki kar ki kuskura wata alaka ta hadaki da aljani!" Yanda mahaifiyar take magana zaka fahimci ranta yayi matukar baci. "Ni..Ni.." cike da i'ina Jinah ta fara kokarin ta kare kanta amma sai ta sunkuyar da saboda kunya. "Mama kinsan muna son junan mu kuma..." "Kai kuma ka rufa min baki, ai komai ma laifin ka ne! idan ba sakarci ba me ya kaika yin alkawari da ita? To ku sani abinda kuka yi babu wanda bai samu labari ba, dan yanzu haka mahiafin ku yaje amsa kira. Dama dangi sun jima suna son su ga bayan Jinah, yanzu kuwa ta sanadin abinda kuka yi kun basu hujjah kwararra da zasu batar da Jinah. Gashi bansan me zasu yi maku ba..." Tsoro ne fal ya cika fuskokin matasan, dan Jinah har ta fara zubar da kwalla. Fally ne ya riko hannunta dan tabbatar mata da ba abinda zai samun su. A take mahaifiyarsu ta fara hada kayan Jinah, dan bata son wani abu ya samu Jinah saboda ba zata yafe ma kanta ba, na rashin cika alkawarin da ta daukar ma mahaifiyar Jinah. Kuka Jinah ta fara, rabuwa da wadanda take tunanin sun zamar mata yan uwa abu ne mai ciwo garesu, mafi ciwo ma shine a rabata da abin kaunarta Fally. Wanda tun tasowarta shine abokin rayuwarta kuma dan uwanta. Gashi yanzu har sun yi alkawarin zama na har abada a tare. Shi kuwa Fally ya fada duniyar tunani, dan hankalinshi ya guje, ya kasa gane abinda ya kamata yayi. Kukan da yaci karfin Jinah ne ya dawo dashi hankalinsa, rungumeta yayi sosai sannan ya rada mata a kunne "Ina sonki Jinah, ina makk son da ba zan iya rabuwa da ke ba, son da ba zan iya samun madadinki ba. Zasu rabamu amma na maki alkawarin zan samo mana hanyar da zamu zauna har abada. Mun riga mun yi alkawarin zama na har abada. Kada ki taba mantawa da hakan Jinah, Ke tawa ce, kuma tawa ni kadai!" "Eh ni taka ce Fally, taka ta har abada." "Ki min alkawarin ba zaki taba mantawa da ni ba." "Nayi maka alkawari ba zan manta da kai ba, koda kuwa na so haka..." Mahaifiyar su ce ta rabasu, da sauri ta finciki Jinah tayi sama da ita. Fally yayi kokarin ya bisu amma mahaifinsa da ke shigowa yayi sauri rikoshi. "Ya kamata ka barta ta tafi Fally, idan ba haka ba zasu kasheta. Yanzu kaje ka dakatar da alkawarin da kuka kafin awanni 24 abun ba zai yi kyau ba." Shiru Fally yayi bai ba mahaifin nashi amsa ba. Mahaifin ya dafashi yace "Kana jina Fally kayi sauri kaje yanzu!" Juyawa yayi ya tafi, mahaifin nashi na tunanin ya tafi ya dakatar da alkawarin nasu ne. Sai dai shi a zuciyarshi ya kudura Jinah tashi ce har abada ba zai taba rabuwa da ita ba, alkawarin da yayi mata kenan kuma yasan itama ba zata taba mantawa dashi ba. Kuma dole ya nemota duk inda mahaifiyarsa ta kaita. To me zai sa yaje ya dakatar da alkawarin nasu? Inaaa! wani masifaffen ihu ya saki wanda yayi sanadin tarwatsewar manyan itacen dake kusa dashi. A bangaren su Jinah kuwa, wani nauyayyen bacci ne aljanar ta saka Jinah, Nisa sosai tayi da Jinah kafin ta kawota bakin wani kauye. Wani siddabaru ta yiwa Jinah wanda zata manta da duk wata rayuwarta ta baya, wadda tayi da aljanu, ta cirewa Jinah duk wani karfi dake gareta na iya sarrafa wasu abubuwa kamar yanda aljanu suke yi, har karfin dake ga Jinah na ganin aljanu shima ta cire mata, wanda indai ba shi aljani yaso Jinah ta ganshi ba. Jinah ya dawo kamar kowanne mutum, kuma ko ba komai zata koma tayi rayuwa a cikin yan uwanta bil'adama. Jinah ta manta da Fally, ta manta da alkawarin da suka yi, ta manta da ita matar aljani ce. --------------------------- Wannan shine prologue na sabon labarina mai suna Jinah (matar aljani), zan cigaba ne kawai idan kun ga yayi maku kuma naga comments sosai. WhatsApp Contact : +22794203632 💞 *JINAH (Matar Aljani)*💞 by _Malik al-Ashtar_ ✒️ *You'd like this New ❤️ Story* *CHAPTER 1* Sanyanyar iska ce mai dadi ke kadawa, Bishiyu ne ke rangaji daga dama zuwa hagu. Tsintsaye sai shawagi suke a sama, ga kukan dabobbi iri iri sai tashi yake a wannan jeji. Wannan yanayin ne ya kara dada wa baccin da Jinah ke yi dadi. Baccinta take cikin kwanciyar hankali bisa babbar bishiyar kuka. Haka ta cigaba da bacci har lokacin da surutun da ake yi mata a kunne ya tasheta. - Jinah! Jinah! Wani karamin yaro ne ke maimaita hakan da alama so yake ya tasheta. -humm... cikin muryar bacci Jinah ke amsawa -Ki tashi Tanti Sarah na kiran ki (Tanti na nufin kanwar uwa ko ta uba, ko matar uba a Nijar wanda haka ya samo asali daga yaren French kamar dai yanda wasu ke cewa Aunty da yaren English). Ba tare da Jinah ta amsa mashi ba ta sauko daga kan bishiyar, tare da janyo babban zanin da ta shinfida bisa reshen bishiyar, sannan ta rufe duka jikinta dashi har da fuskarta. -Tanti Jinah me yasa kike bacci kan bishiya? Baki tsoron wani abu ya sameki a wannan daren? Mama tana yawan ce mana akwai hadari zuwa cikin jeji da dare. Tsoron mutane kike yasa baki magana gaban su? Me yasa kike boye fuskarki...? Tambayoyin da yaron ke ta aiko mata ne ba kakkautawa. Da sauri ta dakatar dashi : -Dan Allah ka yi mana shiru, kai bakin ka ko gajiya baya yi irin wanann Tambayoyi haka! -To kiyi hakuri na dena... Bata tankashi ba, suka dauki hanyar zuwa gida, Gida ne wanda aka yi da bulo da siminti, hakan ke nuna mai gidan yanada dan abin hannu, dan sauran gidajen duk na kara ne a kauyen, Gidan Lasaini shi ne taken da ake yiwa gidan. Jinah ba wanda ta sani a gidan da kauyen bayan matar da ta kawota, sai kuma wannan yaron mai suna Bukari wanda shima tasu tazo daya ne sakamakon wayonshi da kuma shegen surutu dake gareshi. Lokacin da suka karaso gidan, shigewa daki Jinah tayi ta fada akan gado, kamar kullum yau ma shiru take ba magana. Tanti Sarah ce ta shigo dakin tare da yiwa Bukari da ya fita da gudu godiya. -Sannu Jinah, zaki ci wani abu? ko na kai maki ruwan wanka ne? Duk wadannan Tambayoyi da Tanti Sarah ta yiwa Jinah, Jinah girgiza mata kai kawai tayi. -Jinah! Wai sai yaushe zaki fara yimin magana, yaushe zaki fada min abinda ke damunki? Tun lokacin da na fara ganin a cikin jeji, kika ce min na taimaka maki baki iya tuna komai da dalilin da ya kawo ki cikin jejin, kawai abinda kike iya tunawa sunanki ne, tun daga ranar baki kara bude baki kin yi min magana ba, bakya magana da kowa idan ba Bukari ba. Ki je jeji kiyi kwanciyarki idan kika dawo sai ki shige daki ki ki fitowa. Yau tsawon wata daya kenan da na kawoki gidan dan uwana, amma babu wanda ya taba ganin fuskarki idan ba ni da Bukari ba. Na yiwa kowa karya akan ke diyar kawata ce ta bani rikonki.. Ki yimin magana Jinah! Ki fada min damuwarki? Kar ki sa nayi nadamar taimakonki da nayi. Ni ina daukan ki ne tamkar kanwata, kuma hakan na mani ciwo ganin halin da kike ciki. Cikin Sanyanyar murya Sarah ke fadawa Jinah haka. Jinah ta fahimci Sarah tana son tayi mata magana ne. Kuma tasan wannan matar ta cancanci ta sanar da ita duk wata damuwarta. Tasowa Jinah tayi daga inda take tareda durkusawa a gaban Sarah, kafin tace -Kiyi hakuri Sarah, ba wai nayi hakan bane, don in bata maki rai ko rashin yarda ba, abin yana min ciwo ne na rashin tuna rayuwata ta baya, ina jin kewar wasu mutanen da na kasa gane su waye, ina jin nan ba a muhallina nake ba, ina jin kamar wannan shi ne karon farko da nake rayuwa a cikin mutane kamar ku, Na kasa fahimta, na kasa fahimta Sarah. Ina son na san ta yaya hakan ta kasance, wata kil 'yan uwana basa sona ne suka jefar dani, kin fa sameni ne da kayana a cikin jaka da kuma makuden kudade a ciki, wata kil kuma guduwa ce nayi, ba zan... Kuka ne yaci karfinta, tabbas da alama tana jin abun sosai a ranta, sai dai ba yanda zata yi. -Na fahimce ki Jinah, wannan yanayi ne mai rikitarwa, shi yasa ni da ke muka kasa fahimtar komai. Amma ki ragewa kanki damuwa kar ki haifarwa da kanki wani ciwo. Ke yarinya ce, kuma akwai rayuwa mai tsawo a gabanki.Ya kamata ki fita kiyi abokai, ki sake sabuwar rayuwa kafin ki tuna komai, domin ta yiwu zai dau lokaci kafin ki tuna rayuwarki ta baya. Fadawa Jinah tayi jikin Sarah tare da fashewa da wani sabon kukan. -Ki bar kukan haka yanzu, tashi kiyi wanka sannan ki zo ki ci abincin ki. -Nayi wanka tin dazu... Jinah tayi mata karya tare da sunkuyar da kai -Oh na tuna ashe baki yin wanka sai tsakiyan dare kowa yayi bacci, me yasa kike tsoron mutane su ganki? -Kafin na hadu dake, duk wanda na gani na nufeshi da niyyar ya taimaka min sai ya gudu. Shi yasa nace wata kila akwai wani abu ne a fuskata da yake ba mutane tsoro, ko kuma kawai munina ne ke tsorata mutane. Ku kadai ne ke da Bukari baku ranci na kare ba ranar da kuka fara ganina. Abin da Jinah ta fada ne yasa dariya ta kwacewa Sarah. -Allah Sarah da gaske nake, mutumin da na fara gani, rokona yayi tayi akan dan Allah kar in cutar dashi in kyaleshi, ai kuwa ina bashi hanya ya fece kamar mashi. Dariya Sarah take tace -Ni kaina na so guduwa lokacin da na fara ganinki. Cikin mamaki Jinah ta kalleta tace -Me yasa? Hannu Sarah ta dora akan fuskar Jinah tana shafawa tace -Jinah, kina da wani masifaffen kyau ne, fuskarki har wani sheki take, ki duba ko ina a jikinki daidai ga gashin ki har ya wuce mazaunan ki. Gaskiya kyanki ba irin na mutane bane, sai dai ko na aljanu. Idan mutum ya fara ganinki dole yayi tunanin ke ba mutum ba ce, dan ko ni ban taba ganin mutum mai irin wannan kyau ba. Cikin jin dadi Jinah tace -Allah da gaske kike? -Da gaske nake Jinah, ki bari duk randa kika je bakin kogi ki duba fuskanki a ruwa zaki gani. -Kenan babu wani dalili da zan boye kaina? -A'a, zo bari in gabatar da ke ga mutanen gidan nan ba tare da kin boye fuskarki ba, daman sun sha tambayata wai don me yasa kike boye fuskarki. Kama hannun Jinah tayi suka fita zuwa tsakar gida, inda kowa sai aikin gaban sa yake. Ganin Jinah yasa kowa ya tsaya da abinda yake, suka zura mata na mujiya. Ganin haka Sarah ta katse shirun da cewa -Sunanta Jinah, itace yar kawata da ta bani riko. Wurin shiru yayi, mutanen gidan na bin Jinah da kallon tsoro. Sarah ta kara katse shirun da fahimtar dasu cewa Jinah mutum ce kamar su, kuma tana boye fuskarta ne dan ganin yanda mutane ke yawan kallonta da jin tsoronta. Ajiyar zuciyoyi ne ke tashi a wajen, wasu da yawa tsoron su ya rage, amma wasu har yanzu suna ganin wannan kyau na Jinah yayi yawa. Wasu kuwa tasowa suka yi suna ta taba jikin Jinah, wasu kuma na shafa dogon gashinta suna al'ajabin wannan abu. Ganin Jinah duk ta tsargu yasa Sarah ta janyeta. Rungume Sarah Jinah tayi tana hawayen farin ciki, domin Sarah tanada kirki, gashi dai basu hada komai da Jinah ba amma ta dauketa tamkar wata yar uwarta. Tin daga ranar komai ya koma daidai tsakanin Jinah da Sarah, suka koma tamkar wasu shakikan kawaye, duk da Sarah zata fi Jinah da kusan fiye da shekaru 10, domin Jinah tana shirin shiga shekara ta 17 ne ita kuma Sarah tanada shekaru 33. Kauye kowa ya dauka ana ta yadawa cewa ai gidan Lasaini akwai wata kyakyawar yarinya mai kama da aljanu. Mutane na ta tururuwar zuwa ganin Jinah, hakan ya dauki lokaci sosai, har ta kai idan Jinah ta fito a hanya mutane na kallonta har suna nunanta suna cewa ita ce mai kama da aljanu, har ya kai Jinah na tsarguwa da abinda suke mata. Shi yasa koda yaushe tafi son taje cen cikin jeji tayi ta wasa da dabbobi, kuma tafi jin dadin kwanciya kan reshen bishiya da kwanciya kan gado. Sai dai yanzu bata boye fuskarta kuma tana magana da mutane. 'Yan matan kauyen da dama kishi da ita suke, ganin samarin su nata rawar kafa gunta wasu har zuwa tambayar aurenta suke. Ita kuma Jinah ko a jikinta don wannan bai ma gabanta. Sarah ta fahimci hakan har wata rana take tambayar Jinah -Me yasa baki kula samarin dake zuwa wajenki? -Kawai haka nan, naji bana da ra'ayin soyayyar ne. Jinah tace a takaice. -Jinah ya kamata ace kina kulasu, dan idan da ta nice ba zan bari ki ma fara ba, domin aure shine babban kuskuren da na taba yi a Rayuwata. Amma sanin aure shine darajar kowacce mace, yasa nake son ki fidda gwani a cikin masu neman aurenki. Cike da mamaki Jinah ta kalleta tace -Amma me yasa? Ina mijinki yake? Sai yanzu wannan tunanin yazo min dan tinda nazo gidan nan ban taba ganin mijinki ba... Sarah ta katseta da cewa -Ke nifa kar ki sauya mana magana, ya maganar da muke yi amma ke kina so ki canja zancen ki kamo wani babi. Bansan daga inda kike ba amma mu nan a kauyen Mambila muna aurar da yarinya ne da wuri... Ita ma Jinah katseta tayi da cewa -Kece dai kike son canja maganar! Ita ma ta kara musawa -A'a ke dai kika canja maganar! Musu ne ya barke a tsakanin su kafin daga bisani Sarah tace -To shikenan wata rana zan fada maki. Jinah tace -Me zai hana ki fada yanzu? Sarah tace -Ke dai nace ba yanzu ba... Mikewa Jinah tayi tana kakkabe zaninta tace -To shikenan, ni dai na tafi cikin jeji. Tabe baki Sarah tayi tace -Aikin kenan! Cikin shagwaba Jinah tace -Ina jin dadin zaman ne a cen, kuma ko ba komai ina kallon yanda dabbobi ke kai kawo... Kara tabe baki Sarah tayi tace -Ina guje maki kar ki je wani aljani ya ganki, ya makale maki, kin ga sai ki dawo gida ki zauna. Fita Jinah tayi daga gidan tana dariyar maganar Sarah. Tana isa cikin jejin, kamar kullum bishiyar da take hawa tayi kwanciyarta ta dale, cikin zurfin tunani ta fada, tunani take ko zata iya tuna wani abu na rayuwarta ta baya, kamar kullum dai tana jin kewar wasu mutane da ta kasa gane su waye, tafi jin kewar wani wanda tana tunanin nata ne na kusa da ita sosai, da ta fara irin wanann sai zuciyarta ta rinka bugawa da sauri da sauri. Tana cikin wannan tunanin ne taji wata murya tana cewa -Ni fa ba zan koma gida yanzu ba, kawai kuyi tafiyar ku! Lekawan da Jinah zata yi sai ta ga wasu samari su uku ne a kasan bishiyar da take kwance. Daya daga cikin samarin ne yace -Ka dakata da taurin kan nan naka Dauda, dare fa ne ke shirin yi, kuma kaga nan jeji ne bamu san me yake dauke dashi ba na cutarwa. Dayan saurayin kuma yace -Musa fa na da gaskiya Dauda, bamu san meke akwai na hadari ba anan... Dayan saurayin mai suna Dauda wanda yake ta yiwa yan uwan nashi taurin kan ba zai koma gida yanzu ba, ya katseshi da cewa -Ku rabu da ni kuyi tafiyar ku! ku wane irin masu naci tsiya ne? na fada maku ni ba yanzu zan koma gida ba, ta yaya zamu fito farauta ko fara bamu kama ba, sannan mu koma gida haka hannu rabbana? Kuna tunanin wani abu zai same ni ne? Ai bansan cewa abokaina matsorata ne ba. -To mu kaga tafiyar mu zaka iya tsayawa, ruwanka ne wannan. Muje Mahadi idan ya gaji ya iskemu gida. Tafiya suka yi suka barshi anan, shi kuwa ko a jikinsa. Duk abinda ke faruwa Jinah na saman bishiya tana kallon su. Wata dabara ce ta fado mata, tace bari na koyama wannan dan rainin wayon hankali. Shi kuwa Dauda zaunawa yayi karkashin bishiya ya dauko Kwari da bakanshi yana gyarawa. Koda ya ida tashi yayi wai da niyyar kama wata kurciya da ya gani. Cikin Sanda Jinah ta bishi a baya ba tare da ya sani ba, boye fuskarta tayi da gashinta sannan ta dira gaban Dauda, Dauda kamewa yayi guri daya ya kasa motsi, ita kuma Jinah ta kara nufoshi... Ganin haka Dauda ya fara kyarmar tsoro yana cewa -Dan Al..lah ki..yi hakuri ki kya..leni kar ki cutar dani... Mamata zata damu sosai idan na mutu, nine dan autanta. Kiyi min rai! Dariya ta so kwacewa Jinah, kamar ba shi bane yake ta cika baki dazun. Dauda kokarin guduwa yayi ai kuwa sai ga maciji kuma gabanshi, kasa motsi yayi ya fasa ihu -Wayyo Allah! yau lokacina ne yayi!! wayyo!! Taku daya Jinah tayi gaban macijin, ta durkusa tana kallon macijin cikin ido, koda macijin ya hada ido da ita sululu ya juya ya koma daga inda ya fito. Duk wannan dramar da ake yi Dauda yana tsaye a kame yana kallon ikon Allah, dan yau ya tabbata tashi ta kare. Jinah kasa rike dariyarta tayi, ai kuwa tayi ta dariya har ta gaji dan kanta ta dena, amma har yanzu Dauda ko motsi shi kawai gani yake tashi ta kare. Jinah ta matso kusa dashi tana mai dauke gashin da ke kan fuskarta tace -Ni ba aljana bace, mutum ce kamar ka. Har yanzu shiru Dauda yayi yana kallon ikon Allah. Jinah ta kara cewa -Kamar ba kai bane kake ta kurari dazu ba, wai duk ina jarumtar taka? Kallo dai kawai Dauda ke bin Jinah dashi. Abin ya fara ba Jinah haushi tace -Tsaya da yimin wannan kallon, na fada maka nima mutum ce! Ajiyar zuciya Dauda ya sauke tare da cewa -Na kasa yarda ne... Jinah tace mashi cikin zolaya -To kayi hakuri da tsoratar da kai da nayi, kawai ina son na gwada jarumtar ka ce, ganin yanda kake ta cika ma abokanka baki dazun. Juyawa tayi da niyyar tafiya. Dauda ya dan dawo cikin hayyacinsa, tsoronshi ya ragu. Cikin zuciyarsa yace "Kuma da ita Aljana ce ba yanda za'a yi ta ceceni a hannun wannan macijin, kuma ba yanda za'a yi ta kyaleni tayi tafiyarta." Tsayawa yayi yana kallon Jinah da tayi nisa, yana kallon irin halittar da Allah yayi mata kamar wata aljana. Kuma da ya tuna yanda tayi ta kori macijin nan sai ya kasa yarda cewa ita mutum ce. Dauda bai san lokacin da ya fara bin Jinah a baya ba, lokacin da Jinah ta fahimci ana binta a baya, tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace -To kuma yanzu me kake so? Ka dakata da bina. -Nima..nima bansan me yasa nake binki ba, kawai dai ina son nayi maki godiya akan cetona da kika yi, kuma ina son nasan sunanki... A tsawace Jinah tace -Wannan kuma ba zai yiwu ba, maganar godiya kuma ni nayi haka ne dan nishadi, shikenan zaka iya tafiya. Juyawa tayi da sauri da niyyar tafiya, tuntube tayi ta fadi kasa, da gudu Dauda ya nufeta da niyyar taimaka mata -Sannu ba kiji ciwo ba? Kwalla a idonta tace -Wayyo Allah zafi! Anan Dauda yaga ya kara tabbatar ma kanshi lallai wannan mutum ce kuma akwai kurciya a tattare da ita. Lokacin da yazo da niyyar tabata, da sauri Jinah taja baya dan bata so ya tabata. Kuma me yasa zata yi haka alhali taimakonta zai yi? itama kanta bata san dalili ba. Dauda ya dan ji ba dadi yace -Kawai ina son ganin inda kika ji ciwo ne. Da sauri Jinah tace -A'a kar ka tabani! Dauda bai tsaya saurarenta ba ya kama kafar tata, dole ta kyaleshi, kaya ce yaga ta taka a kafarta ta hagu. Jin laushin kafarta da Dauda yaji yace -Masha Allah, gaskiya kinada fata mai laushi da dadin tabawa... oh yi hakuri. Kafarta kawai Dauda ya taba yana wannan sambatun ina ga... Wata bishiya Jinah ta nuna mashi tace ya debo kunnuwanta, dan ta canja maganar, dan ta fara lura dan saurayin ya fara fita hayyacinshi. Dauda yace -Shit, barni nayi aikina, ba abinda zaki nuna min dan nima haihuwar kauye ne. Cikin shagwaba Jinah tace -To kayi a hankali. Murmushi Dauda yayi yace -Kinga shi yasa raina mutane baida kyau, ki duba yanda kika nemi kasheni da tsoro kema gashi yanzu Allah ya saka min. Kallonsa Jinah tayi tace -Kana nufin dan na tsorata ka ne yasa naji ciwo? Dauda ya kara yin murmushi yace -Ni dai ban ce ba.. Turo baki Jinah tayi a shagwabe tace -Haka kake nufi ba gashi da bakinka kake fadi ba.. Fashewa da dariya Dauda yayi, kafin daga bisani wajen yayi shiru. Ciro ganyen bishiyar Dauda yayi sannan ya nika ganyen da taimakon wasu duwatsu biyu sannan ya saka dadai inda Jinah ta taka kayar. Keta zaninta tayi kadan ta bashi ya daure mata ciwon. Kamata Dauda yayi da niyyar taimaka mata ta mike, wani zafi ne yaji ya sauka a jikinsa kamar an kunna masa wuta. Ihu Dauda ya fasa kafin ya fadi sumamme ko matacce. --------------------------- To Fans ku biyo mu domin jin abin da zai faru da Dauda sanadin taba Jinah da yayi. --------------------------- Please comments dinku suna da matukar anfani domin suna karawa Marubuci karfin gwiwa... Ga link sabon Group da zaku rinka samun updates na wannan sabon labari : https://chat.whatsapp.com/JGjb07Du5N45rzy8gfOCOV Note : Amma fa ku sani Group ne wanda admin ne kawai zai iya posting, dan bamu son wani labari in ba na wannan labarin ba. 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 2 Mambila, cikin wannan kauyen mai nisa a kasar Nijar, duk da rana ta fadi, dare yayi, hakan bai hana farin wata haska kauyen ba. Kowane mutum a kauyen ya aje aikin da yake yi ya nufi gidanshi don an ce dare Mahutar bawa. Saidai ba haka yake ba a bangaren Jinah dake durkushe tsakiyar jeji da mutum kwance baya motsi, kamar babu rai a jikinsa. Tsoro da firgici ne kwance a fuskarta, haka ta cigaba da kokarin tasheshi, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Cikin kuka take fadin -Dan Allah ka tashi, bawan Allah nasan baka mutu ba. Kuka Jinah ta cigaba da yi, wata kakkausar murya taji ana cewa -Idan har kika cigaba da tabashi, to ba zai taba tashi ba! A tsorace Jinah take ta dube dube dan ganin mai magana amma bata ga kowa ba, tunani tayi wata kila kunnuwanta ne ke zaginta. Cigaba tayi da jijiga Dauda, amma ba alamar zai motsa, tsoronta ne ya karu. Ganin hakan ba zai fisheta ba, ta tashi a guje ta nufi hanyar gida domin nemo agaji. -Sarah! Sarah! Sarah! Jinah take fada, da alama har ta fara fita hayyacinta. Kusan karo suka yi da Sarah. A tsorace Sarah tace -Me ya faru kike wannan uban gudun da yimin irin wannan kiran? Jinah na haki tace tana kama hannun Sarah -Sarah zo ki gani, yaki tashi! Zo ki gani dan Allah! -Kwantar da hankalin ki, kar ki tashe da mutanen gidan, fada mani me ke faruwa? -Fa..du..wa ya..yi, faduwa yayi kasa, na tasheshi, na tasheshi amma yaki tashi. Sarah ina gudun ya mutu, wayyo Allah na... -Muje ki nuna min inda yake. Jinah kaita tayi inda Dauda yake, har yanzu dai yana nan kwance kamar gawa. Karasawa Sarah tayi kusa dashi, tana shirin tabashi suka jiwo ana cewa -Me kuke a nan? Lasaini ne, dan uwan Sarah. Karasowa yayi yana fadin -Me ya faru? Ganin mutum a kwance kusa da su. Bai jira jin amsar su ba, ya sunkuci Dauda a kafadarshi, ya nufi gida dashi. bai dire dashi ko'ina ba sai bisa gado, sannan yace a samo masa ruwa. Jinah a guje taje ta debo ruwan, ta kawo masa. Zuba masa ruwan yayi a fuska amma shuru bai farka ba. -Ya mutu ko? Jinah tace zuciyarta na bugawa. -A'a yana numfashi. Lasaini ya bata amsa. -To me yasa bai farka ba, gashi kuma ko motsi baya yi. -Ki kwantar da hankalinki Jinah Cewar Sarah. Wani mari Lasaini ya gaura masa, sai suka ga ya motsa. Ajiyar zuciyoyi Sarah da Jinah suka yi. A hankali Dauda ya bude idonshi yana binsu da kallo, kafin ya tambaya a ina yake. Basu bashi amsa ba, Lasaini ya tambayeshi -Kai dan wane kauye ne? Dafe kai Dauda yayi kafin yace -Ni dan kauyen NA GAMA ne! -Ko zaka iya tuna abinda ya faru da kai? Daga idanu yayi ya kalli inda Jinah take, sannan yace -Gamo nayi da aljana ta rikida zuwa mutum ko kuma mutum ce ban sani ba... Sarah ce tayi dariya, kafin su hada ido da Lasaini ta gimtse dariyarta. -Zaka kwana anan kafin safiya, tinda yanzu dare ya riga yayi. Cewar Lasaini kafin ya mike tareda cewa su Sarah su ma su je su kwanta. Sarah ce ta juyo tareda kiran dan uwan nata -Lasaini! A fusace ya juyo yace -Ya aka yi ne! Sunne kai Sarah tayi cikin i'ina tace -ah daman... daman.. so nake.. ba komai ma sai da safe. Tsaki yaja bai kara bi ta kanta ba, yayi gaba. Kwalla ne suka zubo mata, ta rasa sai yaushe tsakaninta da dan uwanta zai daidaita. Tana fata watara ya yafe mata, su koma kamar yanda suke da. Kama hannunta Jinah tayi ba tare da tace mata wani abu ba, suka wuce daki. Suna shiga dakin kowace ta nufi makwancinta, Sai dai bacci ya kasa daukansu. Jinah ce ta sauko daga nata gadon tana fuskantar Sarah tace -Sarah, kin san dalilin da yasa yayi kamar ya mutu? Alhali bai san abinda ya faru dashi ba, kawai fasa ihu ne fa yayi ya fadi. Daman ana irin wannan ciwon ko kuwa? Sarah ta kalleta tace -Ba wani ciwo a yanda yace ya ganki, yayi tunanin aljana ce ba dole ya tsorata ya suma ba. Ai yayi kokari ma da bai hade zuciya ba tsabar tsoro. Dariya dukansu suka yi, kafin Jinah tace -Tinda baki jin bacci, ki bani labarin ki, da abinda ke tsakanin ki da dan uwanki, naga baku cika magana ba, kuma na lura duk lokacin da zai yi maki magana fuskarsa a daure take. Dazun ma naga haka, kece babba ko shi ne? Ajiyar zuciya Sarah tayi kafin tace -Yayana ne, shekara daya ce a tsakanin mu. Tabe baki Jinah tayi, tace -Shekara daya ya baki, shi ne ya rainaki har haka? -Haba, ai kuwa sai na fada masa. Zaro ido Jinah tayi tace -Lah rufa min asiri da wasa nake, ai mutumin kirki ne. Ganin yanda Jinah take zaro ido ya baiwa Sarah dariya. Shuru na dan lokaci ya biyo baya, kafin Jinah tace -To meye musabbabin abinda ya hada ku? Shuru Sarah tayi kafin ta fara ba Jinah labarin -Hakan ya fara faruwa ne lokacin da na fara soyayya. Ni da dan uwana mun kasance tamkar jini da hanta, kullum muna tare bama rabuwa, duk inda za'a ga keyata to ki tabbata za'a ga tashi... Murmushi Sarah tayi tare da kwalla na tuno alakarta da dan uwanta a baya. Ta cigaba -Na fada soyayya... Kara matsowa Jinah tayi, cikin zumudin jin labarin soyayyar Sarah. -Na fada soyayya ne da babban makiyin yayana mai suna Kimba. Kimba kyakyawa ne ajin farko ga kuma kudi, bai cika zama a kauyen nan ba saboda mutum ne mai yawan tafiye-tafiye. Yayana ya tsani Kimba kamar rai da ajali, lokacin da ya gane muna soyayya, sai da ya share kusan sati bai min magana kuma haka shi ne ya fara zama silar wargajewar alakarmu. Yayi kokarin ganin ya datse alakata da Kimba, amma fir na kiya, na nuna masa nifa ina son Kimba. Yana yawan fada mani, Kimba ba mutumin kirki bane, yaudarata kawai zai yi. Amma ina ni soyayya ta rufe min ido. Kimba ya turo yan uwanshi neman aurena, iyayen mu suka bashi, kowa na dangi na murna da auren mu amma banda yayana. Ana gobe daurin auren mu, da yawan samarin kauyen suka yi wata tafiya zuwa wani kauye dan nesa da mu mai suna Kumana. Hankalina bai kwanta ba dan tafiyar har da Kimba da yayana a ciki. Ina tsoron kar yayana yaje yayi wa Kimba wani abu. Saidai cikin ikon Allah suka dawo kowa lafiya lau. Sai dai Yayana yazo min da wani labari wanda shi yayi sanadin datse alakar dake tsakanin mu. Ya bani labarin cewa lokacin da suka isa kauyen Kumana, Kimba yayi shaye shaye ya bugu, ya shiga cikin jeji lokacin da ya dawo sai yaji yana ba abokinshi labari wai ya samu wata yarinya a jeji ya kore kishirwarshi, wato yayi lalata da yarinyar. Bansan lokacin da na wanke yayana da mari ba, ba zan taba manta abinda yayi ta nanata min ba "Yanzu Sarah ni zaki mara akan wannan dan iskan? To ki sani daga yau babu ke babu ni, kuma ba zan kara shiga tsakanin ki da wannan dan iskan ba!" Wadannan kalaman har yanzu suna min yawo a cikin kwakwalwa, amma ko kala ban ce masa ba dan nima a lokacin haushin sa nake ji, dan kazafin da yayi wa Kimba. Da safe aka daura auren mu, shiru ban ga alamar yayana ba har aka daukeni zuwa gidan Kimba, tun daga ranar ban kara ganin yayana ba. A farkon auren mu, na kasance cikin farin ciki, na irin soyayyar da Kimba yake nuna min, duk abinda nake so Kimba yana yimin. Bayan wasu watanni Kimba ya nemi da na bishi garin da yake kasuwanci, hakan na damu sosai dan bana son nayi nisa da yan uwana, bare ma yayana, ina son na rinka ganinshi kullum koda kuwa baya min magana. Ba yanda zan yi dole na bishi, saboda mijina ne dole nayi masa biyayya. Tafiya mai nisa muka yi kafin mu kai kauyen tsakiyar dare lokacin kowa yayi bacci banda wata mata wadda da alama zata fini shekaru kadan. Bayan mun aje kayan mu, matar tazo tace min naje ga ruwa cen ban daki nayi wanka. Bayan na gama, na kwanta baccin gajiya. Hawaye ne suka zubo daga idon Sarah, shuru tayi dan ba zata iya cigaba da ba Jinah labarin ba, domin tana jin kamar yanzu ne abun yake faruwa. Rokonta Jinah tayi ta yi akan dan Allah ta cigaba. Share hawayen da suka zubo mata tayi kafin ta cigaba. -Da safe, motsin yara ne dake wasa da kuma matan gidan da ke daka ya tayar dani, dubawa nayi gefena amma ban ga Kimba ba. Fitowata daga dakin naci karo da matar jiya da dare, bayan mun gaisa nake tambayarta ko taga mijina Kimba. Budar bakinta sai tace min wai "Ya tafi wajen daya daga cikin matansa, ni sunana Mariya nice matarsa ta biyu ke kuma kece matarsa ta biyar." Jiri naji ya fara dibana, a take maganar yayana ta fado min. Sai dai ba zan yi saurin yarda da maganar wannan matar ba. Nuna mata nayi da ban fahimci me take nufi ba. Anan take bani labarin cewa ai Kimba yanada mata da yawa da 'ya'ya a wurare daban daban, wannan ma shine karon farko da ya hade matan sa biyu waje daya. Bayan ta gama bani labari komawa nayi daki nasha kukana, shine abu mafi muni da nake ganin ya faru a Rayuwata. Ban taba tunanin Kimba zai min haka ba, dan yasha fada min "Kece matata ta farko kuma kece ta karshe." Bai taba fada min cewa yanada wasu matan ba. Kuma wani bangaren na zuciyata kasa gasgata maganar matar yayi, dole Kimba ne zai fada min gaskiyar abinda ke faruwa, haka na bar abin a zuciyata na zauna jiran dawowar Kimba. Kwanaki da yawa sun shude, babu labarin Kimba, nan na fara gasgata maganar yayana tabbas Kimba mayaudari ne. Bai tashi dawowa ba sai bayan wata daya, da zuwanshi na haushi da masifa da kuka akan ni sai ya sakeni na koma gidan mu, babu tausayi ya lakada min dan banzan duka, naci kuka da neman taimako amma babu wanda yazo ya kwaceni, saka Mariya yayi ta tattara 'ya'yanta suka tafi, bansan ina ya turata ba. Kashedi yayi min akan idan har ina son zaman lafiya to dole inyi masa biyayya. Haka dan zaman da Kimba yayi na kwana biyu ya mayar dani tamkar jaka, dukan safe daban na rana daban. Gashi ya hanani zuwa ko ganin gida, idan ya tashi zuwa wajen sauran matanshi, haka zai barni ni kadai a gida gashi babu damar naje gida, dan mu a al'adar mu idan aka yi aure ko yaji ba'a yi bare saki, da kin ga aure ya mutu to ki tabbata daya ne ya mutu ya bar daya. Haka gidan Kimba ya zame mani tamkar gidan yari... Kuka ne yaci karfin ta, lallashinta Jinah kawai take yi, dan sosai ita ma ta tausaya mata. Share hawaye tayi ta cigaba -Na dauki shekaru masu yawa gidan Kimba babu wani sauyi, lokacin da ya aureni inada shekaru 18, yanzu kuma shekaruna 32. Bayan wani lokaci naji labarin matarshi ta farko a Nigeria take, kuma yafi dadewa a cen dan wani lokacin yana kwashe har shekaru 2 wajenta. Kuma yanzu cen ne zai je, ganin hakan yasa na rokeshi da ya barni naje ganin gida daga karshe ya amince amma da sharadin kafin ya dawo yana son ya tarar dani na dawo. A haka na amince akan zan zo naga dangina uwa uba yayana dan yau kimanin shekaru 5 da rasuwar Abban mu, ita kuma umman mu shekaru 3 kenan. Har lokacin yayana baya min magana, ranar da nazo, na durkusa har kasa nayi ta rokonshi akan ya yafe mani, amma ko kallon banza bai min ba. Nasan har yanzu yana sona, dan duk wata kulawa yana bani ne ta hanyar matarshi, ban rasa komai ba anan, ko ba komai ina jin dadin ganina kusa da yayana dan shi kadai ne ya rage min a dangi, gashi ban taba haihuwa ba. A wannan karon har Jinah kuka take yi, dan Sarah ta bata tausayi ba kadan ba. Bayan sun ci kukan su sun gaji, Jinah tayi mata alkawari da zata daidaita tsakanin ta da yayan ta. Hakan yayi wa Sarah dadi kuma tana fatan haka. Ganin dare yayi nisa yasa kowace ta nemi makwancinta. Asuba ta gari! Safiya na wayewa, Sarah ta tafi kasuwa yin cefane, ita kuma Jinah wanka ta shiga, bayan ta fito ta zauna taci abin karinta. Tana idawa ta kwanta da niyyar komawa bacci, wata murya taji na rera wasu baituka masu dadi a kunnenta. Baituka ne kamar na mutumin da yayi kewar masoyiyarsa. Yanda Jinah ta kashe kunne, zai tabbatar maka da lallai tana jin dadin baitukan, tashi tayi ta leka ta window da niyyar ganin mai wannan dadaddiyar murya, sai dai kafin ta karasa lekawa taji sallama a bakin kofa. Amsawa tayi tareda tambayar waye. Dauda ne ya amsa da -Nine Dauda! Fitowa tayi ta tarar dashi bakin kofa. -Nazo nayi maki sai an jima, dan tafiya zan yi. Ba tare da Jinah ta kalleshi ba tace -To sai an jima.. Kallonta yayi yace -Sai kuma yaushe zamu sake haduwa? Zaro ido Jinah tayi tace -A'ah ba da ni ba? Dauda yace -Saboda me? Tace -So kake ka mutu a hannuna? kaje kawai nagode. Dariya Dauda yayi, abin dariya yake bashi ganin yadda Jinah ta kakkahe ita dagaske take. -Ai ki kwantar hankalinki ni da nake fatan mu kasance na har abada.. Ya fada yana kashe mata ido. Irin kallon sama da kasa Jinah tayi masa kafin tace -Ban fa gane ba! -Zaki gane nan gaba kadan, kyakyawar aljanata. Ya fada yana murmushi tare da juyawa zai tafi, Jinah kuwa kamewa tayi kamar an shukata, tana ta juya maganar tashi dan ita sam bata fahimta ba. Tunawa tayi da dadaddiyar muryar nan da taji, da saurinta taje ta leka windon dakin amma bata ga kowa ba. Tunani take a zuciyarta, waye wannan mai muryar, me yasa take jin wani abu a lokacin da yake rera baitukan kuma me yasa har yanzu muryarshi ke mata yawo a kwakwalwa? Da wannan tarin tambayoyin da batada amsar su, ta nufi jeji da muryarta mai dadi tana rera daya daga cikin wakokin Umar M. Shareef. Wa zani ba kaina? in ba ke ba a cikin yan mata Wa zani ba raina? kece dai nake kira yar gata Kaunar da nake miki ban yiwa kaina, kin riga kinyi rata Kowa yazo tanka mini kan kaunarki yanzu ma fafata In zaku yimin take, bani son wata sai ke Ga masara ga wake, ni dai nace sai ke... You can watch lyrics of this song by Umar M Shareef 👉 https://youtu.be/Q0tGz9DJ1Ck --------------------------- To fah wannan shine Chapter din mu na yau. Bayyana ra'ayin ku akan labarin yana karan karfin gwiwar cigaba. Zaku iya cigaba da bibiyar labarin a wattpad ta wannan link din 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 3 Kamar yanda yake a duniyar mutane haka yake a duniyar aljanu, idan har aljani ya taka daya daga cikin dokokin al'adarsu, ana yanke masa hukunci daidai da laifinsa. Abinda ya faru ga Fally kenan, ya rasa duk wani karfi nashi da iko irin na kowanne aljani. Idan kuwa haka ta kasance ga aljani, kwanaki kadan suke rage masa a maimakon dubannin shekarun da zai yi. Aljanun da sarki ya turo sun yi nasarar cafke Fally ne, lokacin da yake kokarin bin Mahaifiyarshi da Jinah. Sanadin abinda ya aikata aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari. -Me kayi aka kawo ka wannan wajen? Cewar wani aljani da suke daki daya da Fally a gidan yarin. Ba tare da Fally ya bashi amsa ba ya cigaba da cewa -An yanke mana hukuncin daurin rai da rai ne, kuma ko ba dade ko ba jima dole zamu mutu a bayan wannan kantar, dan haka kayi amfani da sauran lokacin da ya rage ma da wannan zaman tunanin da kake... tam duk da ka ki kayi magana, kuma nasan kana ji na, bari na baka labarina da dalilin zuwana wannan waje. Na kasance daya daga cikin aljanu masu tafiye tafiye daga wannan kasa zuwa wata kasa bisa umarnin sarki. Inada mata, na kan dade ban koma gida ba, hakan yasa matata take amfani da wannan damar tana kawo kwarata gida. Nasha kamata amma bansan wane mataki zan dauka ba, har dai wata rana da na kamasu zuciya ta debeni na cire masu kai ita da kwartan nata sannan na kona gawarsu. Wannan yasa aka yanke min hukuncin daurin rai da rai. Ko a cikin aljanu ko cikin mutane, cin amana mummunan abu ne, yana iya kasancewa ga mace ko ga namiji, wannan ya zama kamar ruwan dare. Cin amanar wanda muke so yanada ciwo. Ba zaka taba sanin zafin cin amana ba sai lokacin da wanda ka yarda dashi yaci amanarka. Sai dai daukar hukunci kamar yanda wannan aljanin yayi ba abinda zai rage maka na daga radadin zuciya. Har yanzu Fally bai da alamar yin magana, dan ba lalle bane ma yaji abinda aljanin yake fada. Hankalinsa yana cen a tunanin abar kaunarsa, yana cikin kewarta sosai kuma da fama ciwon rashinta a kusa dashi. Wani aljani daya daga cikin masu gadin gidan yarin ne, yazo ya sanar dashi, mahaifiyarshi ta kawo masa ziyara. Bayan yazo daidai inda mai kawo ziyara ke haduwa da fursuna, mahaifiyarsa ya gani, take ya ji zuciyarsa ta rage zafi. Ita ma ta ji dadin ganin danta duk da akwai shamaki tsakaninta dashi. -Yaya kake dana? Tace tana mai tausaya masa -Lafiya lau nake, ke fa yaya kike? -Lafiya nake, sai dai nayi kewarka sosai. -Nima haka, yaya baba? -Lafiya lau yake, shi ma zuwa an jima zai zo ganinka. Ta fada, yanayinta na nuna alamar damuwa. Fally ya fahimci bata zo da labari mai dadi ba. - Ba zasu sake ni ba koh mama? -A'a dana... -Haba! Mama kinsan fah kwanakina kidayayyi ne anan. -Na sani Fally, na sani, hakan shi ke kara tayar min da hankali, kusan zaucewa nake ganin na samu hanyar fitar da kai! -Na sani Mama, kawai ina jin tsoron ranar da zan... -Ranar da zaka mutu? Ka yarda da ni, mutuwa ba yanzu zaka yita ba, zan fitar da kai daga wannan guri koda kuwa zan rasa raina. Haka ta cigaba da kwantar masa da hankali tare da yi masa alkawarin zata fitar dashi koda kuwa hakan zai zama ajalinta. Uwa kenan, ta kan so ta wahala akan danta ya wahala, Uwa zata iya sadaukar da komai dan ganin murmushin danta. Ga uwa farin cikin danta shine gaba da komai. Bayan tafiyar mahaifiyarsa, damuwarsa ta rage, farin ciki fal a zuciyarsa, tabbas yasan mahaifiyarsa zata fitar dashi, abinda yafi sanyashi farin ciki shine idan ya fita zai ga sanyin idaniyarshi Jinah, wadda ta dalilin ta ya rasa duk wata kima tashi ta aljanu, wadda ba zai taba daina sonta ba har abada.. -Kana ganin Jinah ba zata manta da kai ba kuwa? Wani bangare na zuciyarsa ne ke fadar haka. -A'a ba yanda za'ayi ta manta da ni... Nan fa rikici ya barke tsakanin bangarorin zuciyarshi. -Kana da tabbaci ne? Tayi fa nisa da kai yanzu! -Nisa ba abinda zai iya a soyayyar mu. -Ka tuna, tana da masifaffen kyau, kuma ba wani namiji da zai ganta bai kyasa ba. Murmushi yayi. -Baka yarda ba kenan? -A'a abokina, ni da Jinah mun riga mun yi aure, tare da alkawarin zama na har abada. Duk namijin da yayi kuskuren kusantarta, to fah jikinsa zai zama tamkar kifin da aka fiddo awa daya daga cikin ruwa. Mutuwa zata tabbata ga mutumin da yayi kuskuren yin hakan. Eh, Jinah tawa ce ni kadai har abada! A bangaren su Jinah Sarah ce ta shinfida tabarma, Jinah ta zauna. Dauko matajin kai da Man kwakwa Sarah tayi sannan ta zauna a bayan Jinah. -Bari muga yanda za'a yima wannan gashin naki, ki rage yawo dashi haka buzuzu. Sarah ta fada tana yamutsa gashin Jinah da mataji. Sarah sai da ta fara da nasanin farawa Jinah kitso, dan gashinta ba dai yawa ba, ga kuma santsi. Lura tayi da wani tabon haihuwa a bayan wuyan Jinah, tsayawa tayi, dan ta tuna mijinta yanada irinshi komai da komai shima kuma daidai da inda na Jinah yake. Abin daureta mata kai yayi, amma sai ta barshi a zuciyarta kafin ta maida hankalin ga yi mata kitson. Duk lokacin da ta kamo gashin da niyyar kitsawa sai Jinah tayi ta murkususu tana fadin "da zafi." tana turo baki. Sarah bata tanka mata ba, da abin Jinah ya isheta sai tayi mata rankwashi a tsakar ka ita kuma Jinah ta fasa kara. Haka suka cigaba da yi abin gwanin ban sha'awa. -To an kare! Sarah ta fada, mikewa jinah tayi tana ajiyar zuciya tace -Haba kin ji yanda mazaunaina suka yi kamar zasu kama da wuta. -Je ki duba madubi, zaki ga yanda na gyara maki shi, sai kin min godiya.. Dariya suka yi kafin Jinah taje ta duba a madubi, gashin yayi kamar an zatse kwarya, shi ba babba ba shi ba karami ba. Koda Jinah ta gani kasa motsawa tayi dan yayi bala'in kyau. Manyan zane ne Sarah tayi mata a tsakiyar kai tare da game jelar gashin ta dunkule waje daya ya sauka a gadon bayanta, kasancewar Jinah fara, haka fatar gashinta fara ce yasa zanen kitson ya fito da kyau. -Sarah kinyi gaskiya, yayi kyau sosai wallahi, nagode. -To idan kika tashi kwanceshi, zan sake maki wanda yafi wannan. -A'a gaskiya ba zan iya kara irin wannan zaman ba, ai sai duwawuna su fashe.. Dube dube Sarah take tana neman abinda zata jefi Jinah dashi, fahimtar abinda zata yi yasa Jinah tayi waje da gudu. -Shakiyiya! Sarah ta fada tana dariya. Bayan wasu yan mintuna suna zaune cikin daki, suka ji Bukari yana ta kwada sallama. Sarah ce ta amsa sannan tace masa ya shigo. -Wai kai Bukari, ba nasha fada maka idan kayi sallama biyu ta isa, sai ka jira a amsa ba? Cewar Jinah. -Babu banbanci idan biyu nayi ma tayi, idan kuma shida nayi ma tayi ko Tanti Sarah? Bukari ya fada cikin muryarshi ta yarinta. -Da gaskiyarka Bukari.. Sarah ta fada tana dariya, ita dai tana son Bukari, tana jinsa kamar danta. Bata samu sa'ar samun haihuwa ba gashi kuma ita mai son 'ya'ya ce. Sai dai ta dalilin Jinah da Bukari tana jinta tamkar Uwa kuma hakan yana mata dadi. -Jinah! kitsonki yayi kyau! Bukari ya fada yana kallon kitson Jinah. -Hmm nagode, Sarah ce tayi min. -Tanti Sarah kin iya kitso, fada mani kudinshi koda dubu dubu ne yanzu na biya.. Cewar Bukari, shi a dole dagaske yake, kallon juna matan suka yi. Barkoncin Bukari yasa yake da saurin shiga rai. Yaron yanada hankali da wayo, yana da cikin yaran kauyen masu zuwa school. Kwada masa kira yaji ana yi, ya amsa. -La'ilah, na manta! Tanti Sarah, Jinah mama tace na kirawoku kuci abinci. Sannan ya juya ya fita da gudu. -Duk wannan surutun da yake yi, ashe aikoshi aka yi kinji sai yanzu ya tuna. Cewar Jinah tana mikewa. Bayan sun ci abinci, kowa ya shige dakinsa, Jinah ta tarar da Lasaini dan uwan Sarah zaune tsakiyar gida. Yau tsawon kwanaki kenan tana son yi masa magana, sai dai bata samu dama ba dan bai cika zama gida ba. -Ina wuni? Ta fada, dago kai yayi ya kalleta, suka hada ido kafin ya amsa gaisuwarta. -Zamu iya magana? -Ina saurarenki. Zaunawa tayi bisa benci dake kusa dashi. -Magana ce nake son muyi akan Sarah. Yamutsa fuska yayi kafin yace -Kinga yarinya, ina mai baki shawara da kar ki shiga abinda ba ruwanki, dan baki san komai ba. -Ta bani labarin komai. -Wannan ba abinda ya dameki ba ne, dan haka ki fita daga wannan maganar kuma ki je ki kwanta dare yayi. -Ba'a gyara wata matsalar da kunno kan wata matsalar. Dakatar da ita yaso yi, amma ta rokeshi da ya saurareta. -Yanzu kamar kai, idan rana tsaka aka ce ka rabu da matarka, zaka iya?... ko kuma idan aka ce ita ta barka, ya zaka ji? Sunne kai Lasaini yayi alamar yana tunani. -Lasaini, Sarah tana son wannan mutumin sosai, ta yanda lokaci daya a nuna mata wani aibu nashi ba zata yarda ba. Wani lokacin soyayya tana hana mu ganin aibun masoyi. Ka dan yi tunanin ace kai ne ita na wani dan lokaci kaji. Tana cutuwa da irin rashin ko in kula da kake yi mata, wanda har ta kasa boye hakan, batada iyaye, batada 'ya'ya, kai ne komai nata a halin yanzu. Har zuwa wane lokaci zaka bar cutar da ita? Har zuwa wane lokaci zaka dawo yayanta na da? 'yar uwarka ce fah, kuma wajibinka ne ka kula da ita. Shiru Jinah tayi sannan ta mike da niyyar tafiya, itama tana jin tayi gangancin fadama mutumin da ya girme mata irin wadannan maganganun amma kuma tasan gaskiya ta fada. -Jinah! Kiran sunanta yayi, ta juyo tana fuskantarsa. - Wai nace shekarunki nawa? Idanu ta fiddo, tana mamakin me ya kawo kuma wannan tambayar? -Kawai naji kamar mahaifiyata ce a gabana... Ba tare da ta bashi amsa ba ta juya tana murmushi, cikin ziciyarta tace "Ashe dai maganganuna sunyi tasiri cikin dan karamin kanshi! Ai kuwa, safiyar ranar, Lasaini yaje har gun kanwarsa ya nemi gafagarta. Sarah kasa gasgata hakan tayi, dan ranar tasha kuka, tayi ta yiwa Jinah buhu buhun godiya, gashi ta sanadinta ta shirya rashin jituwar dake tsakanin yan uwa. Fita Jinah tayi, ta barsu. Ta nufi bakin kogi. Rage kayan jikinta tayi ta fada cikin kogin. Cen taji ance -Kyanki ya kara fitowa, da kika yi kitso. Sauri tayi ta fito, ta saka kayanta sanin ta gane mai muryar. -Sarkin naci! Ta fada kasa da murya. -Sunana dai Dauda ba sarkin naci ba. Ya fada yana mai nuna mata alamar ya ji abinda ta fada. Kunya ce ta kamata. -A'a ai da kin cigaba da wankanki, kiyi kamar bana wajen. Ya fada ganin ta juya zata tafi. -A'a dama na kare. -Toh, dan Allah kar ki tafi, daman yau tsawon kwanaki kenan nake ta son na ganki. -Ni kuma? -Eh -Saboda me? -Ai na fada maki, kin riga kin fada komata. -Ni kuma ai na fada maka, bansan me kake nufi da hakan ba! -Zo ki zauna dan Allah, sai na fada maki ma'anar hakan. Haka dai ta hakura ganin magiyar da yake ta yi mata. Zaunawa suka yi bisa wan dutse. -Toh ina sauraronka? Cikin wata marainiyar murya ya fara fadin -Jinaaaaah, tuuuuun lokaaacin... Dakatar dashi tayi, tace -Dauda bafa waka nace ka yimin ba. -Jinah, bana ganin komai a duk lokacin da na ganki, bana tunanin komai a duk lokacin da nake tunaninki! -Ni fah ban gane komai ba a cikin wannan waken naka, ka yimin gwari gwari. -A takaice kin fada komata ne! -Oh Allah, wai Dauda wannan kalamin naka ba fahimtarshi nake ba. -Yi hakuri, to "ay gaba ni Jinah" -Da Hausa! -Ina sonki Jinah, ina matukar kaunarki, kuma ina son ki kasance matata. Tuni ta dade da harbo jirginshi, kawai dai tana so taji daga bakinshi ne. Sai dai bata so yaji ba dadi, dan tasan amsar da zata bashi ba zata yi masa dadi ba. Itama tana son Dauda, gashi hadadde, sai dai ta bashi zuciyarta wannan ba mai yiyuwa bane. Shuru dukansu suka yi, kafin ita ta mike da niyyar tafiya gida. jiri ne ya debeta ta koma ta zauna. -Bana jin dadi Dauda! Ta fada tana dafe kai. -Sannu, me yake damunki? tashi muje na rakaki gida. Mikewa tayi yana mata sannu, suka kama hanyar gida, sai dai ba wanda ke yiwa wani magana har suka karaso kofar gida. -Yauwa ya isa nan, Dauda zaka iya tafiya nagode. Ta fada tana rike da kanta. -Kin tabbata? Ya tambayeta da alamar damuwa a fuskarshi. -Eh kar ka damu! nagode Ta juya da niyyar shiga gida, ya kira sunanta -Jinah! Waiwayowa tayi, yace -Ina jiran amsarki. Bai jira jin me zata ce ba, ya juya ya tafi. Jinah tarar da Sarah tayi ita kadai cikin daki, Sarah ta damu ganin halin da Jinah take ciki. Kwantar da ita Sarah tayi, ta kura mata ido kafin tace -Jinah, amma kwanan nan kina jin tashin zuciya ko? -Eh ina jin haka dan wani lokacin sai naji kamar nayi amai. -Tinda kika zo gidan nan, ko kin taba ganin al'adarki? -A'ah ban taba ba. -Innalillahi, Jinah kar dai ciki ne da ke? --------------------------------------- Bon, zan dakata nan a yau. Sai kuma zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Fatan dai wannan chapter ta burge ku? To ku fada min abinda kuke tunani, i want to know hahaha. 😂 Muje zuwa a wata sabuwar chapter, kuma kar ku manta da yin comment domin shi nafi bukata. 🤗 Watty : @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 4 Asubar fari na yi, Sarah da Jinah suka fito da shirin zuwa asibitin dake kauyen. Suna fitowa, suka ga Safiya ce matar Lasaini kadai ta tashi, sauran har yanzu bacci suke. Bakin murhu take tana kokarin kunna wutar dumama tuwan karin kumallo. -"Mat arango Safiya?" Ina kwana Safiya? Sarah da Jinah ne suka gaisheta da yaren zabarmanci, ko kuma dai nace Sarah, dan Jinah tana cikin tashin hankalin da magana ma wahala take mata. -"Samaï day no. Mat ni kani bani?" Lafiya lau, an tashi lafiya? Safiya ta amsa masu gaisuwar. -"Samaï day no wallah." Lafiya lau wallahi. Sarah ta fada kafin tace -"Jinah sigama inga gahamo kani, aygo ga dum loktoru koira." Jinah bata jin dadi, shine zan raka asibiti. -"Ayyah! Irkoy madi ase, ma konda aran bani." Ayyah! Allah ya koro sauki, sai kun dawo. -"Aminna, kala tonton." Amin sai mun dawo. Hanyar asibiti suka dauka. Jinah har yanzu shiru babu alamar magana, duk tsoro da fargaba sun mamayeta. Bayan yar doguwar tafiyar da suka yi suka karaso asibitin, ba wata babbar asibiti bace kasancewar kauyuka irin Mambila sun fi ganewa yin maganin gargajiya akan na bature. Bayan sun je sun ciri tikitin ganin doctor. Kusa da Jinah Sarah ta zauna, ita kuma sai ta dora kanta bisa kafafun Sarah, Hankalin Jinah a matukar tashe yake tun jiya da Sarah ta tambayeta ko ciki ne da ita. Lallai idan dai ya tabbata ciki ne da ita, ta shiga uku dan bata san waye uban yaron ba, shin ta yaya ta samu cikin kuma wanne lokaci ne hakan ta faru. Addu'a ta cigaba da yi Allah yasa ba ciki bane, duk da tasan yanayinta yana nuna mai alamar mai ciki ne. Juyar da kanta tayi jin hawaye na son zubo mata. Hankalinta ne ya kai kan maganganun wata mata da bata zata wuce shekaru 50 ba da wata matashiyar budurwa da ba zata wuce 17 ba duke tana rizgar kuka. -Me kike so na fada ma ubanki? Kin bani kunya Nana! -Wallahi Mama ki yarda da ni, ba abinda nayi! -"Ah to Nudu gunde par magie?" Ah kina nufin a ruwa kika shashi ko me? Kin bani kunya Nana, yanzu da wane ido zan kalli mutanen kauyen nan? Shikenan kin ja mutanen kauye su zageni suce na sakeki kin je kin yi ciki. To sai ki sani inda dare yayi maki dan yau kam ba dai a gidana ba, ni kinga tafiyata! Juyawa matar tayi ta tafi cike da damuwa, ta bar yarinyar durkushe tana kuka. Mutane sai kallonta suke amma ita ko a jikinta. -Bari naje na samo mana abin kari. Cewar Sarah tana mikewa, gyada mata kai kawai Jinah tayi. Bayan tafiyar Sarah, Jinah matsawa tayi kusan yarinyar dake kuka. -Yi shiru ki daina kuka, kar ki sawa kanki wani ciwon. Jinah ta fada cikin sigar lallashi, ba tare da ta dago kai taga mai lallashinta ba, ta fara ba Jinah labarin abinda ya faru. Haka na kasancewa ga kowa, idan muna cikin damuwa mu kan so mu bayyanawa wani ita ko da ba zai iya yi mana maganinta ba kawai dai hakan nasa muji damuwar ta ragu. -Na rantse da Allah ban yi komai ba, ni ban ma taba sanin yaya gaban namiji yake ba indai ba na yaro karami ba, ni ko saurayi banidashi, ba abinda na sani in ba karatu ba, ba anan kauyen nake ba, ina karatu ne a Niamey (babban birnin kasar Nijar). Nazo nan hutu ne, gashi yanzu wai nice da ciki, to wa yayi min shi? Yanda take bada labarin da yanayinta zai tabbatar maka ita iya gaskiyarta take fada, hakan ya zama ruwan dare a kauyuka ba dama yarinya tazo daga birni, abin kamar maita. Haka saurayi zai je ma yarinya da sigar yana sonta, daga nan zai yaudareta, yayi mata ciki, in ma da saninta, ko kuma yayi mata asiri, ko kuma ya zuba mata wani abu a abin sha ta sha, daga nan ya gudu ya barta da taraddadi. Shikenan fa rayuwar yarinya ta lalace, haka zaka ga wasu sun zama karuwai, wasu su kashe kansu, wasu kuma ana samun maza masu tawakkali da dogon ilimi su auresu. Allah ya kyauta! Hankalin Jinah kara tashi yayi jin labarin yarinyar gashi yana kamanceceniya da nata, sai dai ita tana ganin Sarah bata koreta bane, ganin ba a tabbatar da nata cikin ba. Lokacin da layi yazo kanta, lokacin yarinya mai kuka ta tafi, Sarah ta dawo har sun karya. Wani bugawa zuciyar Jinah ke yi da sauri sauri dan da tafiyar hawainiya ta shiga ofishin doctor. Yana zaune yana duba wasu takardu, ba tare da ya dago kai ba yayi masu izini da zasu zauna, tareda cewa -Ku dan jira yanzu abokin aikina yazo ya duba marar lafiyar. Ganin har lokaci ya dan ja, abokin aikin nasa bai zo ba, ya dago kai yace -Tinda har yanzu bai zo ba, bari ni na dubaku. Yanzu fada min me yake damunki? Ya fada yana kallon agogo. Sarah tace -Kwanan nan ne take fama da zazzabi da tashin zuciya, shine muke son sanin ko... -Ko me? -Ina son sanin inada ciki ko a'a! Jinah ta fada dan ita ta matsu taji wanne hali take ciki. Bayan yan gwaje-gwaje da doctor yayi, ya tabbatar masu da Jinah tana da ciki. Doctor ya basu shawarar suna iya sake zuwa wani wajen ayi masu gwajin dan kara tabbatarwa sai dai ita Jinah batada wannan ra'ayin. Fita tayi daga asibitin da dan gudunta Sarah ta bita a baya. Sai dai Sarah bata yi nasarar cimmata ba sai da suka kai gida. -Kalleni nan Jinah. Sarah ta fada, cusa kanta tayi cikin katifa tana kuka. Ba wai tana kuka bane dan tanada ciki, a'a tunawa ne tayi matar nan ta dazu a asibiti dake hantarar yarta dan tayi ciki. Gani take itama haka Sarah zata yi mata, tasan itama haka mutanen garin zasu rinka nunenta suna zaginta. -Ki daina kuka Jinah, nasan ke ba irin wannan yaran bane masu kai kansu ga maza. -Kinada tabbacin haka Sarah? Idan fa saboda hakan ne aka koreni daga gida? Jinah ta fada tana fito da kanta daga cikin katifa. -Me kike cewa haka? kika sani ko kinada aure ne? -Ki duba fa samari nawa suka zo neman aurena, ai ba wanda aka taba fadawa inada aure. To yanzu kina tunanin akwai wanda zai yarda idan aka ce na taba aure ko inada aure? Yanzu wane kallo kike tunanin zasu yi maki keda kika bani mafaka? Ina ga zan yi tafiyata kafin mutanen kauyen nan su gane har na ja maki abin kunya... Kuka ne yaci karfinta. -Eh na sani dole zasu yi ta fada, dan kina karkashin kulawata ne, kuma hakan ba zai yimin dadi ba. Amma hakan kasheni zai yi? ko kwantar dani zai yi rashin lafiya? A'a ba fah abinda zai sameni. dan haka ki daina wannan kukan ki natsu muyi tunanin samun mafita. Mikewa Jinah tayi tana goge fuskarta tace zata je bakin kogi. Sarah bata hanata ba don tana ganin wata kila hakan zai ragewa Jinar damuwa. Da zuwanta bakin kogi ta zauna ta hade kai da gwiwa. Zuwa cen taji kamar kana kallonta, juyawa tayi taga Dauda ne, karasowa yayi ya zauna gefenta. -Yaya kike? -Lafiya lau. Ta bashi amsa a takaice. -Anya dai? Ya fada yana kare mata kallo, dan ya hangi damuwa a tattare da ita. -Na fada maka lafiya nake. Ta fada a dan tsawace. Duk da hakan bai hakura ba ya kara tambayarta. -Fada mun me yake damunki dan Allah? -Kaga ko na fada maka ba abinda zaka iya yi a kai, kuma wai wane sani ne nayi maka da har zan fada maka damuwata? Dan haka ka rabu dani. Duk wannan maganganun da ta fada mashi, basu hanashi yin dariya ba. -Abin dariya ma ya baka kenan? Dan Allah ka rabu dani. -Fushi baya maki kyau, kanki sai ya koma wani kala abin dariya. Ya fada yana dariya. Ganin so yake ya kara bata mata rai yasa ta mike da niyyar tafiya. Da sauri yace -Yi hakuri dawo ki zauna dan Allah, duk da bansan me yake damunki ba, amma na damu ganinki cikin wannan hali. Dawowa tayi ta zauna, sannan ta bashi hakuri akan daga masa murya da tayi dazun. Ya nuna mata ba komai. Cewa yayi ta fada masa abinda ke damunta, amma taki. Rokonta yayi ta yi akan sai ta fada mashi, ganin nacin da yake mata, kuma ita kanta taji tana son ta bashi labarinta. Dan yan kwanakin da suka yi a tare ta fahimci Dauda mutum ne mai tausayi da kuma barkwanci. Sai dai tana tsoron idan yaji tanada ciki ya kasa fahimtarta. Daga karshe dai yanke sharawar ta fada masa tayi, bayan ta gama bashi labarin yace -Yanzu kina nufin babu wani abu da kike iya tunawa na rayuwarki ta baya? -Eh, abinda kawai nake tunawa ranar da na bude ido na ganni a wannan kauyen sai sunana. Kuma babban tashin hankalin shine.... -Ina jinki meye? -Inada ciki! Da sauri Dauda ya mike, cikin tashin hankali yace -Ciki? Sunne kai Jinah tayi tana hawaye sannan tace -Wallahi bansan ya aka yi hakan ta faru ba, inada aure ne ko kuwa, ban sani ba? Nasan mutane zasu ta min kallon yar iska, ita kuma Sarah suyi ta nunata. Na jawo mata abin kunya. Hada kai da gwiwa tayi ta cigaba da rera kuka. Shi kuwa Dauda safa da marwa ya fara a wurin kafin yace -Ni nasan yanda za'ayi! Da sauri Jinah ta dago tace -Ta yaya? -Abu mai sauki, na aureki kinga mutane zasu yi tunanin dan nawa ne. Duk da hawayen dake fuskar Jinah hakan bai hanata kyalkyata dariya ba tana yi tana cewa -Daman na dade ina wannan tunanin, ba isashiyar lafiya gareka ba... -Allah Jinah da gaske nake! -Gaskiya bakada hankali, ni kaga tafiyata. -Ki dakata Jinah, Allah da gaske nake, hakan ita kadai ce mafita. -Kaga, bamu san juna ba kace kana sona, haka ka cigaba da bibiyata tin daga ranar da wannan abun ya faru, a duk lokacin da nazo cikin jeji ko bakin kogi sai na tarar da kai. Yanzu kuma nace maka inada ciki ba tareda nasan ta yaya na sameshi ba, kai kace zaka aureni. Fada mani wane mai hankali ne zai yin irin wannan? -Kinada gaskiya Jinah, amma kin manta da cewa idan mutum ya kamu da soyayya, zaucewa yake yi. Saboda daga ranar ba kwalwa bace ke jagorantarsa, Zuciyarsa ce, zuciya Jinah! -A dauka na amince, idan kuma aka je inada aure, kuma na tuna komai? -Daga ranar babu aurenmu, na amince zan barki ki tafi. -Ni fah bana sonka Dauda! Duk da yaji maganar tata kamar saukar aradu, hakan bai hanashi cijewa yayi dariya ba. -Kai abin dariya ma ya baka kenan? -Ina dariya ne, dan zan aureki dan ina sonki duk da ke baki sona, amma zan zauna zaman jiran ranar da kema zaki bude baki kice kina sona. -Gaskiya ba zan iya ba Dauda, kayi hakuri. Ta juya ta tafi, ta barshi a tsaye kamar an dasashi, shi kanshi yayi mamakin kalamanta sai dai wannan itace mafitar da zai iya samun Jinah, don har cikin zuciyarshi yana sonta. Tun jiya da ya fada mata yana sonta, bai ga alamar amincewa a idonta ba, yasan taki fada masa ne dan kar yaji ba dadi. Yanzu kuma yana cikin farin ciki ganin zai aureta, sai dai sam bai ji dadin jin tanada ciki ba. Amma yana tunanin komai zai zama daidai da ya aureta. Jinah karasawa tayi gida da kuka, ita dai bata san me yasa rayuwa tazo mata a haka ba, duk da ta fara sabawa da cutar mantau din da yake damunta, sai dai yanzu abin ya dawo mata sabo sanadiyar wannan cikin. Abincinta Sarah ta kawo mata, sai dai bata cikin yanayin da zata iya cin abinci. Tunani ta fara Yanzu idan na auri Dauda, mutane zasu dauka Dansa ne, kuma hakan ba zai taba mutuncin Sarah ba, ba zan iya ja mata abin kunya ba, dan tayi min halacci kwarai. Kuma Dauda mutumin kirki ne, nasan ba zai wulakantani ba... Tana idar da tunaninta, ta duro daga kan gado ta nufi bakin kogi inda ta baro Dauda. Tarar dashi tayi a gurin zaune yana wasar jefa kananan duwatsu a ruwa. Wani dogon numfashi ta ja, kafin ta kira sunanshi. -Dauda! Ba tare da ya juyo ba yace -Oh Allah, haukacewa zanyi, har muryarta nake ji alhali bata wajen. Zaunawa kusa dashi Jinah tayi tareda cewa -Ni din dai ce da gaske. Har wata yar zabura Dauda yayi dan baiyi tunanin zata dawo ba. Sunkuyar da kai tayi kafin tace -Nayi tunani kuma na amince zan aureka. Wani farin ciki ne ya lullube Dauda, ta yanda kasa fadin wani abu yayi. Ji yake tamkar a mafarki, wanda kuma ba zai so ya farka ba. Kowannen su tunani ya fara ta yanda wannan al'amari zai kasance, sai dai basu yi tunanin me zai je ya dawo ba. Dauda yana matukar sonta, Sai dai bai san abinda zai sameshi ba idan ya auri JINAH matar aljani. --------------------------- Madallah, a nan zan tsaya a yau, sai kuma idan Allah ya kaimu a wata sabuwar chapter. Kada ku manta da fadar ra'ayinku na wannan labari...!🤗 My watty : @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 5 Kalmomi sun yi kadan wajen fayyace maku irin farin cikin da Dauda yake ciki. Har yanzu ya kasa gasgata cewa Jinah ta yarda zata aureshi, ganin kin amincewa da tayi a baya. Duk da wawanci ne auren mace da ciki, sai dai Dauda yana ma Jinah matsanancin son da idanunsa sun rufe ba zai iya ganin aibun da zai hanashi aurenta ba. Abinda yake ji game da ita kwarai ne, wanda shi kanshi ba zai iya fassarashi ba. Muna iya fadawa soyayyar wani a kowanne lokaci, ta dalilin haduwar farko ko kuma a kallon farko. Haka so yake. -Yauwa ka bani labarinka. Jinah ta fada tana mai kawo karshen zurfin tunanin da kowannensu ya fada. -Da farko dai, anawa gidan mu lakabi da gidan Malam Shehu, inada 'yan uwa maza uku da mata biyar wanda muke uwa daya uba daya. akwai kuma yan uwa maza da mata wanda muke uba daya. Mamata itace mace ta biyu cikin su hudu a gun babana. Ke a takaice dai mu mun kasance babban dangi da muke zaune a gida daya... -Kai kace babban gidane? -Sosai ma kuwa ai sai kin shiga ciki zaki gani. Murmushi Jinah tayi tana kallonsa. Cigaba yayi da bata labarin gidansu. -Babana yanada babbar masana'antar sarrafa auduga, babban mutum ne kauyen mu. Ke dai sai kinje kin ganema idonki. Jinah na murmushi tace -Naji labarin gidanku, saura naka. -Shekaruna 20 daidai, tun ina da shekaru goma na bar school na koma masana'antar babana da aiki. kinsan anan bamu baiwa karatu muhimmanci ba. Saura ke bani labarinki. Kwalo ido Jinah tayi tace -Amma wasa kake ko? -Da aka yi me? -Kai da na fada bana iya tuna komai... Ta fada cikin yanayin damuwa. -Oh yi hakuri, na manta. -bari naje gida, na fadawa Sarah. -Toh, amma ki shirya gobe zan zo muje ki gaida yan gidan mu. -Ok, Allah ya kaimu. Ta fada tana mikewa. -Ameen, ki gaida yan gidan. Koda Jinah tayi nisa, Dauda dan tsalle yayi tare da cewa "Yes!" rawa ya fara tika kamar mahaukaci. Gida ya nufa, mahaifiyarshi ce ta farko da ya fara ba labarin Jinah. Yana yan tsalle tsalle, yana fadawa mamanshi -Na samota Mama, mama na samota! -Me ka samu dana? Mamarshi ta fada tana kallon ikon Allah ganin yanda yake tikar rawa gabanta. -Na samo matar aure mama! Inda kin ganta kamar aljana tsabar kyau, sai idan ma tayi magana mama, sai inji kamar tayi ta magana kar tayi shiru. Muryarta idan kika ji kamar algaita, murmushinta wayyoh.. hakorinta sai kice na karamin yaro. Dariya mamarshi ke yi, dan idan da sabo ta saba da shirmen dan autanta. Kawai gani take giyar soyayya ce take diban dan nata yake wannan sambatun. Yana gama shirmenshi ya nufi masana'anta ya tarar da mahaifin nashi. Daure fuska mahaifin nashi yayi, kafin yace -Sai yau kayi niyyar zuwa? Yaushe rabonka da zuwa aiki? -Ai Abbah, yanzu ma ba aikin bane ya kawoni, nazo ne na fada maka wani labari kuma sai kayi farin ciki da jinsa. -Meye wannan da ya hana min yaro zuwa gurin aiki? -Abbah, na samu mata, duk wannan lokacin da na dauka ina wajenta ne, dan in san halinta sosai, in san ko matar aure ce. Kuma Abba komai ta hada, kyau, hankali da komai ma. Yanda Dauda ke ta zuba gaban mahaifin nashi zai tabbatar maka da shagwababbe ne sosai. Cike da fara'a Mahaifin nashi yace -Ah to madallah, dole kaki zuwa aiki, ashe ka fara zama mutum. Fada min yar gidan waye? -Ba anan kauyen take ba, a Mambila take. -Ah hakan yayi kyau, Allah yasa alheri. -Ameen Abbah, gobe insha Allahu zan kawota ta gaisheku, jibi kuma sai kuje ku nema min aurenta... -To ba damuwa, Allah ya kaimu lokacin. -Ameen Abbah, bari naje na kama aikin. -A'ah yau na yafe maka, kaje ka huta. -toh nagode abbah! Ya fada cike da zumudi ya nufi gurin abokinshi. Ita kuwa Jinah zuwa tayi ta fadawa Sarah. Hakan ya girgiza Sarah, dan kasa cewa komai tayi. -Dan Allah kice wani Abu Sarah! -Ni..Ni bansan me ya kaiki yin wannan gangancin ba. Kin ga na farko baki san wannan mutumin ba, ke ba sonshi kike ba, kina tunanin aure wasa ne da zaki yanke wannan shawarar ba tareda kin fada min ba? Kunya ce ta kama Jinah ta sunkuyar da kanta, dan wannan shine karon farko da taga ran Sarah ya baci. Kuma tasan Sarah tafi ta gaskiya. -Dan Haka wannan aure ba yiwu ba, dan sam ni ban amince ba. -Na fa riga nace masa na amince Sarah, kuma wannan ita kadai ce mafita, idan ba haka ba kema kinsan abinda zai faru. Shiru Sarah tayi na wani lokaci kafin tace -Wannan ba hujjah bace Jinah, ni dai ban amince ba, dan haka ki fidda wannan tunanin a ranki. Fita tayi ta bar Jinah a gurin. Kuka kam Jinah tashashi, dan daren ranar kasa bacci tayi. Washe gari, Dauda yazo daukan Jinah, ranar, ranar hutu ce, kowa yana gida, har da Lasaini da yayi mamakin ganin Dauda. Koda Jinah ta ganshi kallon kayi hakuri tayi masa, shi kuwa yayi kamar bai gani ba. Bayan ya gama gaisawa da yan gidan, ya nemi da su kebe da Lasaini ganin shine babba a gidan. Bayan sun kebe Lasaini yace -Ya sunan malamin ma? -Sunana Dauda Ibrahim. -Madallah malam Dauda, ko me yake tafe da kai? -Am.. Nazo ne daman na gabatar maku da kaina, ina son auren Jinah ne. -Ikon Allah, amma ita Jinar ta sani? -Eh ta sani, dan har ma ta amince. -To madallah hakan yayi kyau, sai dai ni banida iko da ita, iyayenta ba anan suke ba, tana karkashin kulawar yar uwata ne, amma bari na kirata dan jin me zata ce. Kiran Sarah Lasaini yayi, bayan wani dan lokaci ta zo. -Sarah, wannan saurayin da kike gani yazo ne da maganar yana son Jinah, kasancewar tana karkashin kulawarki, kuma ke kika san iyayenta yasa na kiraki dan ki ji. -Eh Jinah ta fada min, sai dai zan so muyi magana da shi, daga ni sai shi. -Ok, ba damuwa, bari na baku waje. Lasaini ya fada tareda mikewa ya tafi. -Me kake so ne da wannan yarinyar? Sarah ta fada fuska a tamke. -Ban fahimta ba, me kike nufi? -Wanne namiji ne zai yarda ya auri yarinya tana cikin wannan halin, ba tare da ita kanta tasan ya aka yi hakan ta faru ba? -Nasan kina son Jinah, kuma ba zaki so wani abu ya sameta ba, ina mai tabbatar maki ba wani abu nake so ga Jinah ba, face farin cikinta. Ina sonta har cikin zuciyata, duk da nasan ita bata sona kamar yanda nake sonta. Kuma ke kin sani, duk yawancin auren da ake yi cikin kauyen nan, auren hadi ne, daga karshe bayan aure ya juye zuwa na soyayya. Nayi maki alkawarin zan saka Jinah farin ciki, kuma ba zan taba cutar da ita ba. Nayi maki wannan alkawarin. Jin abinda Dauda ya fada yasa jikin Sarah yayi sanyi. Tayi shiru na wani dan lokaci kafin tace -Amma kasan ba'a yin aure da ciki ko? Kuma ya zaku yi da darenku na farko? dan kasan ba budurwa bace. -Kar ki damu, ke dai a daura auren, nayi maki alkawarin babu wata matsala da za'a samu. Kiran Lasaini Sarah tayi. -Lasaini, iyayen Jinah sun bani ita ne, tareda bani duk wani iko akanta, ganin ni mace ce ba zan iya bada aurenta ba, yasa nace zan baka ramagar komai, kuma kaga kai ne babba a nan. -Idan haka ne, babu damuwa, kai Dauda ka turo min magabatanka domin mu tsaida magana. Kuma a gaskiya naji dadi da zata yi aure dan na gaji da ganin samarin da ke min sintiri a kofar gida. -Naji dadin jin wannan kuma insha Allahu idan na koma gida zan turo magabatana. Amma yanzu ina son ku yimin izini muje da ita don ta gaishe da mahaifiyata. -Wannan ba matsala bace. Cewar Lasaini. -Shikenan bari nayi mata magana. Sarah ta fada tana mikewa. Dakinta ta nufa ta tarar da Jinah zaune ta kurawa window ido. -Tashi ki shirya zaku je ki gaida iyayen mijinki na gobe. Tsalle Jinah tayi bisa gado tare da cewa -Wai kin amince!? -Eh, munyi magana dashi kuma naga tsantsar sonki a idonshi. Nasan ba zai cutar dake ba. Da sauri Jinah ta shirya, ta nufi gun Dauda da ya hangota yake ta watse hakora. A tare suka fito daga gidan. Wani kyakkywan doki Jina ta gani a bakin kofa. -Kai dokin waye wannan mai kyau? Ina matukar kaunar dawakai! Ta fada tana karasawa kusan dokin tare da shafa kanshi. -Nawa ne! Cewar Dauda. -Dagaske? amma me yasa ban taba ganinka dashi ba? -Ya dan yi rashin lafiya ne, shi yasa na barshi ya dan huta. -Mace ce ma ko? meye sunanta? -Ashanti sunanta! -Suna mai dadi! Zan iya hawa? -Me zai hana? tsaya ki gani. Hawa ya fara yi sanann itama Jinah tayi kamar yanda yayi ta hau. Kada kan ashanti yayi, Sai da suka yi tafiya mai nisa kafin su kawo gidan. Jinah tayi mamakin ganin gidan, dan babban gida ne. Gabatar da ita ya fara yi ga mahaifiyarshi wadda tayi mutuwar zaune dan bata taba zaton maganar da danta ya fada gameda kyan Jinah gaskiya ne ba. Ta yaba da hankalin Jinah kuma taji tana sonta. Sauran yan gidan ya gabatar ma da Jinah, tsabar yawansu kasa rike duka sunayen su tayi. Gida ya dauka "Matar Dauda, kamar aljana." Washe gari, iyayen Dauda suka je gidan su Jinah neman aurenta, ba wata-wata aka tsaida maganar aure, domin mahaifin Dauda babban mutum ne da duk kauyukan dake yankin an sanshi. Kwanci tashi asarar mai rai, yau an daura auren Jinah da Dauda. Farin cikin Jinah kasa boyuwa yayi, har wani zumudi take. Bayan ta fito daga wanka, Sarah ta kunce mata kitso, sake mata wani tayi saidai bai kai na farkon ba, dan irin simple din nan ne tayi mata, ta dunkule gashin duka, yayi mata tozo a tsakiyar kai. Zuwa karfe goma, gidan ya cika da mutane, makada da maraya sai cashewa ake. Kasancewar abin yazo da gaggawa babu abinda Sarah ta dinkawa Jinah, sai Wani leshi madaidaici da kuma wata doguwar riga tata da bata taba sakawa ba. Da leshin tayi yinin ranar, da dare kuma Sarah ta bata doguwar rigar ta saka. Rigar tayi mata bala'in kyau. -Wow, gaskiya wannan riga ba dai kyau ba! Jinah ta fada tana juyi dan ganin yanda rigar take a jikinta. -Eh ta jima gareni, amma ban taba son sakata ba, gashi yanzu tayi rana. Rungumeta Jinah tayi, dan nuna godiyarta. Zuwa karfe tara na dare kafin a dauki Jinah zuwa gidan su Dauda, Sarah ta zaunar da ita a daki dan yi mata huduba. -Toh Sarah, yau Allah gashi yayi kin yi aure. Mijinki yayi min alkawarin babu wata matsala akan maganar budurci, kuma ina fatan hakan. Dama tsorona dangin mijinki. Dan Allah ki kasance mai yiwa mijinki biyayya, duk da nasan baki sonshi amma kuma babu wanda ya takuraki da sai kin aureshi dan haka dole kiyi masa biyayya. Kuma gashi kinyi sa'ar miji mai hankali, duk da hakan nima nayi tsammani a aurena. Dan Maza sai ana yi ana taka tsantsan dasu. Ina son dan Allah kiyi masa biyayya kamar yanda kike min, yi nayi, bari na bari. Sannan kiyi hankali da danginshi wasu zasu soki wasu kuma a'a, duk da haka ki zauna dasu lafiya. Ina son ki dauki Mahaifiyarshi da kishiyoyinta tamkar mahaifiyarki, mahaifinshi tamkar mahaifinki, 'ya'yan yan uwanshi tamkar 'ya'yanki. Sannan kuma kiyi hankali da yan uwanshi maza, dan kinsan namiji ba ruwanshi da ke sirika ce ko akasin haka, bare kuma ke ga yanda kike masha Allah. Ki tarairayi mijinki tamkar jinjiri... Tashi muje yanzu wata rayuwar na jiranki. Kuka Jinah ta fashe dashi. Dan har ga Allah taji bata son rabuwa da Sarah to amma ya zata yi. Rakata Sarah tayi har gurin yan daukar amarya. Suka tafi ana guda, wasu na waka wasu na raye raye. Bayan sun kaita kowa ya watse banda Sarah da zata kwana a gidan dan ta zama shaida idan Jinah budurwa ce. Sanin Jinah ba budurwa bace yasa hankalinta ya kasa kwanciya, bata san wace dabara Dauda zai yi ba gobe. Jinah ce zaune a tsakiyar gado ita kadai cikin wani babban daki. Ganin Dauda shuru babu alamun Dauda tayi niyyar kinshigidawa sai gashi ya shigo. A hankali ta mike zaune. Ajiye ledar hannunshi yayi tare da tambayarta gajiyar biki. Bakar ledar da ya shigo da ita ya janyo ya bude, dakwalan kaji ne guda biyu. Tashi yayi ya dauko faranti ya fiddo kaza guda ya babbaleta sannan yayi mata bisimillah. Nokewa tayi, akan ita a koshe take. Da naci da lallashi yasa ta dan ci kadan. Tashi tayi ta wanke bakinta sannan ta dawo ta kwanta. Bayan shima ya gama ci, ya tattare yaje yayi brushing. Fira ya fara janta sama sama tana biye mashi, har bacci ya dauketa, shima ganin tayi bacci ya kwanta. Da safe karar bugun kofa ne ya tashesu. Dauda yaja dan guntun tsaki kafin yace -Waye? -Sarah ce! Wani bugawa zuciyarshi tayi, dan shi sam ya manta da wani farin zanin gadon da ya kamata yan uwanshi su ga jinin budurcin Jinah, gashi bai yi tunanin yin wata dabara tun jiya da dare ba. Tsoro ne ya kamashi, dan bai san wane kallo mutane zasu yiwa Jinah ba. Karin bugun kofar ne ya karu, muryoyin biyu daga cikin aunties dinshi yaji. Cike da tashin hankali ya fara Safa da Marwa a cikin dakin yana tunanin mafita. ---------------------------- Dauda a cikin tsaka mai wuya, yanada kyau ku bashi shawarar abinda zai yi Fans ko dan ku ceci Jinah abar kaunarsa. 😀 Sai mun hadu a wani chapter🤗 My Watty : @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 6 Sintirin da Dauda ke yi a tsakiyan daki, kamar zakin da aka kulle a keji. Tunani kawai yake ko zai samu mafita. A jiya sam ya manta da alkawarin da yayi wa Sarah, dan shi hankalinsa ya karkata ne a zumudin son cikar mafarkinsa na ganin abar kaunarsa a gidansa. -Me yake faruwa ne? Jinah ta fada cikin muryar bacci. Tausayinta ne ya lullube Dauda, yayi mata irin kallon kiyi hakuri. -Me yake faruwa ne Dauda, kayi magana? Ta sake tambayarshi, amma wannan karon muryarta ram take ganin yanda mijin nata ke safa da marwa yasa dole baccin ya gudu. -Sune a waje! Ba sai yayi mata wani karin bayani ba, ta fahimci yan uwanshi ne dan Sarah tayi mata bayani. Amma ganin halin da mijin nata yake ciki ya tabbatar mata da ba wani shiri da yayi. Rawa jikinta ya fara, tsoro duk ya mamayeta. Toshe bakinta tayi kafin ta fashe da kuka. Ita ba kanta take tausayawa ba, Sarah dake waje, dan tasan tabbas sai tasha kunya ganin ita ce ta tsaya tayi sheda. -A'a kar kiyi kuka dan Allah, zamu nemi mafita! -Wace irin mafita? Ta fada hankali a tashe. Tunani Dauda yayi na wani dan lokaci kafin yace -Ko zakara nake samu na yanka sai mu zuba jinin a zanin gadon? -Me? Hauka kake yi? Kana fa fita su zasu shigo kuma ma me zaka ce masu idan suka ganka da zakara? Dafe kai yayi dan mafitar da kadai ya iya samu kenan. -Me zai hana muyi abinda suke so? Jinah ta fada tana kallon Dauda. -Toh me hakan zai samar, ai a budurwa kadai ake samun abinda suke so. Haka kowanensu yayi ta kawo shawarwari wanda ba zasu fiddasu ba. Ana cikin haka Dauda ya nufi wata yar karamar wuka da ya gani bisa dressing table ajiye. -Me zaka yi da ita Dau...? Kafin ta karasa tambayarsa, ya bude tafin hannunshi na hagu ya yanka. Zuwa yayi ya tara bisa zanin gadon a take jini ya fara zuba. -Wayyo Allah...! Cike da tsoro Jinah ta fada tana toshe bakinta da hannuwanta. -Ke, ba fa wani abu bane, kawai dan karamin ciwo ne kuma bada jimawa ba zai warke. Ya fada dan ya kwantar mata da hankali. Ganin jinin ya tsaya yasa ya goge hannunsa. Sannan yace mata ta kwanta, yaje ya bude kofa. Kusan kadashi aunties din nashi suka yi, shigowa dakin sukayi Sarah na biye dasu a baya fuska a dame. -Ka wani garkame daki kai ga mai mata ko, baka son kowa ya shigo. Daya daga cikin aunties din nashi ce ta fadi haka. -Ai ba laifina bane, kusan kasheni fah tayi... Dauda ya fada cikin rada yana wani murmushi. -Kai jah cen ko kunyar mu baka ji... Dariya suka yi, sannan suka karaso kusan amarya dake dunkule. Jan abu suka gani ga zanin gadon. Nan fa matan biyu suka hau guda. Daya daga cikinsu ce tayi kokarin daukar zanin gadon amma Dauda ya hana. -Wannan kuma ba zai yiwu ba! Nine zan ajiyeshi, dan zai zama abin tunawa na karamcin da matata ta yimin, na bani wannan kyautar. Jinah ji tayi kamar ta nutse tsabar kunya. Fita matan sukayi, suna guda suna fadawa sauran mutanen gidan Jinah budurwa ce. Nan fah gida ya dauka "Matar Dauda danya ce kamar tuffa sabuwa fil a leda".... Abinda basu sani ba, Dauda yaki basu zanin ne, dan kar suje wani dan konkonto ya gano ba jinin budurci bane. Ajiyar zuciya Sarah tayi. Ta shiga ta tarar da Jinah, Rungumeta tayi ba tare da tace wani abu ba. Haka suka kasance rungume da juna na tsawon dan lokaci kafin Sarah ta rada mata a kunne. -Nasan baku yi wani abu ba Jinah, amma ki shirya lokaci na zuwa. Dan Allah kiyi kwanciyarki daki, kar ki fita su fahimci wani abu. Kuma idan kina bukatar wani abu ki zo ki ganni zan baki, idan kin tuna da rayuwarki ta baya ki zo ki fadamin. Ki kula da kanki, zan kasance kullum domin ki kuma zan yi kewarki. Gyada mata kai kawai Jinah tayi, tana hawaye, dan itama tasan zata yi kewar Sarar. A haka Dauda yazo ya tarar dasu, ya dade yana mamakin irin wannan shakuwa tasu, gashi basu hada komai ba, amma Sarah tana jin Jinah tamkar 'yar uwarta ko kuma 'yar da ta haifa. Mikewa Sarah tayi, kafin ta tafi ta kara jaddadawa Dauda alkawarin da yayi mata na kulawa da Jinah. Bayan ya raka Sarah, ya dawo daki wajen matarshi. Babban daki ne da makeken gado a tsakiya, a gefe kuma akwai dressing table da wardrobe, sannan bathroom madaidaici. Dakin ya kawatu sosai, har da gidan ma baki daya. Saboda idan ka shigo cikinsa zaka dauka a birni kake, duk da yanzu kauyuka da dama ana ta samun cigaba amma wannan ya banbata da sauran, dan a kauyen babu irinsa. Bayan wani dan lokaci, Jinah ta fara jiwo wani sauti, wata murya, ba yau ba ne na farko da ta fara jiwo wannan sautin. Amma wannan karon taji kamar sautin kusa yake ba kamar da ba da take jiwoshi daga nesa. Shurun da tayi tana sauraran sautin ne yasa Dauda ya tambayeta. -Me yake faruwa? -Daga ina wannan sautin yake fitowa? -Wane sauti kike magana? -Saurara kaji. Saurarawa Dauda yayi kafin ya fahimci me take nufi. -Wannan kiran sallah ne! -Kiran Sallah? me hakan ke nufi? A da ina jiwo sautin ne daga nesa amma yanzu kamar... -Eh anan cikin gidan ne, muryar Buraima ce, yayana. Hakan yana nuna alamar lokacin sallah yayi. Ya fada cikin yanayin damuwa, dan ya fahimci matarshi babu abinda ta sani game da musulunci, wata kila yana daga cikin matsalar mantau da ta samu ne. Ya fahimci hakan ne tun ranar da ya fada mata yana sonta. Duk da irin wannan ba wani abin mamaki bane a kauyuka. A kauye mutane na amsa sunan musulmai ne amma basa yin komai da ya danganci musuluncin, suna yawan fadar za suyi idan sun tsufa, su a tunaninsu addinin ana yinsa ne idan aka cimma kabari wato tsufa, akasarinsu matasa ne suka yi imani da wannan da'awar. Shi kanshi Dauda a baya yana fadar hakan har zuwa lokacin da yaje Maradi wajen wani kawunsa, anan yaga yaro dan shekara 7 bakwai yana sallah abin gwanin ban sha'awa. A ranar yaji kunya ba kadan ba, tun daga ranar ya shiga neman ilimin addini. Anan ya gano muhimmanci da kuma wajibi na gudanar da addini. Yana dawowa kauyensu yasa mahaifinsa ya gina masallaci a cikin gidansu kuma da taimakon wani malami a kauyen yayi nasarar jawo hankalin yan gidansu da ma makota suna zuwa sallah. Duk da har yanzu ba wani sani gareshi sosai a cikin addinin ba, amma yasan hakkoki da kuma gujewa duk wani sabon Allah. Duk da yan kwanakin nan yana fama da muguwar sha'awa, hakan yasa yake yawaita azumi da tsayuwar dare dan gudun fadawa tarkon shedan. -Matso nan kusa dani! Ya umarci Jinah, ba musu ta matso ta zauna dab dashi bisa gado. -Kinsan addinin musulunci? Ya tambayeta. -A'a. -Ok, bari yanzu idan na dawo daga masallaci, sai muje gurin liman. Bata fahimci komai ba cikin maganar, shi kuma murmushi yayi ganin yanda take ta kyafce-kyafce. Kamar yanda yayi alkawari, yana dawowa, ya kaita wurin Liman. Liman ya biya mata kalmar shahada. Cikin yan kwanaki kadan Jinah ta iya abubuwa sosai na musulunci, haka itama ta koyawa Sarah lokacin da taje gida. Kamar walkiya lokaci yake wucewa, Jinah tana zaune lafiya da mijinta da sauran danginshi. Sai dai matsalarta daya rashin iya girki, amma cikin sa'a Dauda yayiwa mahaifiyarsa bayani. Ba tare da bata lokaci ba, a boye mahaifiyar tashi ta fara koyamata. Dan ita kanta abin kunya ne gareta sauran mutanen gidan su fahimci sirikarta bata iya girki ba. Jinah tayi sa'ar sirika, dan bayan girki har da abubuwa da dama take koya mata. A farkon watan June cikin Jinah ya fara bayyana, dan yanzu zai kai wata hudu. Dauda yana nuna kulawarsa sosai akan cikin, amma ita sam bata son cikin dan ko maganarshi bata so ana yi, wani lokacin ma shigewa daki take ta yita kuka. Kullum Dauda cikin rarrashinta yake da nuna mata ko ta wanne hali ta samu cikin, jininta ne kuma dole ta kaunaceshi. Duk zaman nan da suke, ko kuskuren tabata Dauda yayi to fa ranar sai ya kwana da jinya. Ganin haka da kanshi yaba kanshi baki, kuma shima hakan ce ta fiye masa. Wata ranar lahadi da yamma, Dauda ne zaune ya buga uban tagumi, ya fada duniyar tunani. Wanda hakan ba halinsa bane. Ganin haka, Sarah ta tambayeshi ko lafiya. Dan karamin tsaki yaja kafin yace -Ba komai, kawai bana jin dadi ne. Mikewa yayi ya nufi tsakar gida. Tarar da Kakarshi yayi ta tara yara tana yi masu tatsuniya. Wata aljana ce mai kyau da dogon gashi. Da dare yayi sai ta boye fuskarta, ta sa fararen kaya, ta shiga cikin kauye tana cinye mutanen kauyen yara da manya... Bai tsaya jin karshen labarin ba, ya juya cikin daki wajen matarshi. -Inada wata dabara! Ya fada tareda yin murmushin mugunta. -Toh, wace irin dabara? Jinah ta tambayeshi. -Kinada farar riga doguwa? -Eh... inada.. me zaka yi da ita? -Ina so ki sakata, dan yau ina son kallon drama ne. -Ban fahimta ba, me zamu yi da ita? -Kaka ce ta tara yara tana masu tatsuniya. Bata labarin abinda yaji kakar na fada yayi, sannan ta fahimta. -Ka tabbatar tsorata su zaka yi? Kar fa a samu matsala? -Ba wata matsala da za'a samu ke dai sako rigar, kawai dan ayi nishadi ne. Ya fada yana murmushi. Ba tare da tana son yin wannan wasa ba, dan kawai bin umarninsa zata yi. Saka rigar tayi, doguwa har kasa sannan ta kunce gashinta ya barbazu a fuskarta. Fita suka yi tsakiyar gida, labewa Jinah tayi, shi kuma Dauda yaje cikin yaran yayi zaune. -Kinga Kaka ki daina basu labarin aljanun nan, kinsan idan ana bada labarinsu bayyana suke... Dauda ya fada yana mai gargadin kakar tashi. Karyatashi kakar tayi sannan ta cigaba da ba yaran labari. -Shikenan ni dai na fada maku, amma baku ji ba. Ya fada yana mikewa, Jinah ce ta fito daga inda ta buya ta dunfarosu. Kaka ce ta fara kara sannan ta gudu, yaran ma suka rufa mata baya suna fadin "Da gaske Dauda yake akwai aljana", Kyalkyacewa da dariya Jinah da Dauda suka yi, sannan suka gudu suka buya. Mutanen gidan ne suka fito dan ganin meke faruwa. -Wallahi ku dai anyi yara, bansan yaushe zaku girma ba. Mahaifiyar Dauda ce ke fadar haka da ta tarar dasu suna kyalkyatar dariya. -Ai Mama ko ba komai, Kaka ta motsa jikinta. Dauda ya fada yana dariya. -Haba zaku gane kurenku idan ta gano kune, kuka yi mata wannan shakiyancin. Mahaifiyar ta fada kafin ta koma daki. -Gaskiya ka cika yarinta Dauda! Jinah ta fada. -hahaha, ai ni ba abinda nayi, kece kika tsorata su. Kinga yanda kika yi kuwa? Kin bazo gashi ga kuma katon cikin ki. Dauda ya fada yana dariya. Bata rai Jinah tayi jin yayi maganar cikin. Dan sam bata son maganar cikin. -Ke lafiya, wannan fa danki ne, ya kamata ki daina wannan abun. Me yasa baki son ana maganarshi? Wallahi ni ina jinsa kamar dana ne, duk da ba nawa bane. Dan haka ki daina wannan abun. Kinga zo muje ki dan tattaka. Suna yin taku kadan, wani ya tari gabansu. Idrisa ne, daya daga cikin yan uwan Dauda da suke uba guda. Murtuke fuska Dauda yayi, dan sam basu shiri tsakanin su, kuma Jinah ta lura da hakan tun zuwanta gidan, haka ma akwai wasu sauran yan uwan da duk basu shiri. -Zaka iya matsawa, dan muna so mu wuce. Dauda ya fada cikin yanayin bacin rai. -Naji duk abinda kuke fada, kuma nasan wannan shegen cikin ba danka bane. Idrisa ya fada yana nuna cikin Jinah tare da yin wani shu'umin murmushi. Zuciyar Jinah ce ta bada wani dum, shi kuma Dauda yi yayi kamar bai ji abinda Idrisa ya fada ba. Kama hannun matarsa yayi suka yi gaba suka bar Idrisa dashe a wurin. Idrisa baida wani makiyi duniya da ya wuce Dauda, kuma yasha alwashin ko ta wane hali sai ya yiwa Dauda illa, gashi yanzu yaji wannan labari sai dai rashin tsoro da ya gani a idon Dauda yasa ya fara konkonto. Tunani ya fara, kafin daga bisani ya tuna koda ya fallasa wannan sirrin babu wanda zai yarda dashi dan kowa yasan ba kaunar Dauda yake ba, cewa za'a yi kawai sharri ne. Rarrashin Jinah Dauda yayi ta yi, kan babu abinda dan uwansa zai ce. Sai dai ita tsoro duk ya mamayeta dan tana tsoron Idrisa ya fallasa wannan sirri. Bayan kwana biyu, zuwa karfe uku na rana kusan kowa yana wurin aiki, ciki har da Dauda. Bugun kofarta Jinah taji ana yi, budewar da zata yi taga Idrisa. -Ki biyoni dakina yanzu ko na fallasa wannan cikin naki, yanzu kowa ya sani. Ganin yanayin da yayi maganar, yasa Jinah bata yi tunanin komai ba, ta bishi a baya ba tare da tayi tunanin me zata yi a dakin dan uwan mijinta ba. Suna shiga, yaja kofa ya garkame. -Yau dan iskan mijin nan naki zai gane kurensa. Zan nuna masa shi karamin dan iska idan yazo ya tarar da abinda zan maki yanzu. Nine babba gareshi amma har yanzu banyi aure ba, shine shi har da zuwa ya auro zukekiyar mace! Kokarin bude kofa Jinah tayi, shi kuma ya janyota tareda gamata da bango, kokarin kwatar kanta ta fara, ya kifa mata wani gigitaccen mari. Ganin ba sarki sai Allah Jinah ta fara hawaye. -Dama na dade, ina fakonki! Harshe yasa yana lasar kuncinta kafin ya gaura kanta da gini ta suma. Daukanta yayi ya jefa kan gado tare da cire kayan jikinta. Ba tareda wani tunani ba yayi kokarin shigarta. Sandarewa yayi sakamakon wani addababben zafi da ya shiga jikinsa, haka yayi ta kokowa neman numfashi amma babu dama, bayan wani dan lokaci da ya dauka cikin wannan azabar Kamar buhun dankali haka ya fadi tim gefen Jinah matacce! ------------------------------------------------------------ Ko kuma nasan zaku ce, yanzu kuka san labarin Jinah matar aljani kuke karantawa. Tinda gashi Aljani har ya fara aikin kula da matarshi. lol.😂 Sai kuma idan mun hadu a sabuwar chapter. Amma fa kuyi hakuri ba lokaci, ku dai kawai sai in kun ga update. @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 7 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp A kullum dan adam yana da mafarkai wanda yake da burin wata rana su zama gaske, haka dan adam, akwai wasu abubuwa da suke faruwa a rayuwarsa wadanda zai yi burin a ce mafarki ne yake. Wannan shine abinda Dauda yayi burin a ce mafarki yake, da ganin wannan rana dan uwansa a kan matarsa. Sanadin ranar da ake yi mai zafi da sanya kishi, Dauda ya ajiye aikin da yake yi, ya nufi cikin rumfar hutu dake cikin masana'antar domin samun ruwan da zai jika makoshinsa. Yayi mamaki na rashin ganin Idrisa, bai kawo komai ba a ransa yaje yasha ruwa ya cigaba da aikinsa. Tunawa yayi da abinda ya faru tsakanin shi da Idrisa, da alwashin da Idrisa yasha na sai yayi masa abinda har ya mutu ba zai manta dashi ba. "Tabbas zai iya aikata abinda yayi niya." ya fada a zuciyarshi. Tunawa yayi da ya ganshi lokacin da yake fita daga masana'antar, alhali kuma lokacin tashi daga aiki bai yi ba. "Jinah!" yada cikin tashin hankali, bai tsaya wani dogon tunani ba yaje ya fadawa mahaifinsa zai je gida. Lokacin da yazo gida ya nemi Jinah ko'ina bai ganta ba, haka shima Idrisa bai ganshi ba. Tunani kala-kala yayi tayi, ga kuma zuciyasa dake tsananta buguwa. Dakin Idrisa ya nufa, ya tarar da dakin a kulle. Juyawa yayi da niyyar dubawa makota, amma sai ya fasa da ya tuna babu inda Jinah take zuwa. Yana nan tsaye bakin kofar dakin Idrisan, sai ga Surayya 'yar yayarshi. -Surayya baki ga Jinah ba? -A'a ban ganta ba! -Kawunki fah Idrisa? -Dazu na ganshi ya shiga dakinsa. -Yauwa to jeka abinka. Ya fada kafin ya nufi dakin auntinshi wadda ke da duk wani sifayen yan makullayen dakunan gidan. Kusan sau biyar yana kwankwasa kofar kafin ta bude, fuskarta alamar bacci. -Ya aka yi ne? Ta fada cikin yanayin bacin rai da tunanin ko wasar da Dauda ya saba yi mata ne. Dan idan yayi niyyar yi mata shakiyanci, da ya bubbuga mata kofa ta bude, sai yace mata ai yayi makuwar daki ne. Murmushi yayi da ya fahimci abinda take nufi. -Baba ne ya aikoni daukan kayan aiki da suke dakin Idrisa, sai dai na manta ban karbo makullin dakin ba, shine nake son ki bani na hannunki na bude. Yayi mata karya, ita kuwa bata yi tunanin komai ba ta dauko masa makullin. Yaje ya bude kofar gabansa na dukan uku-uku. Jiri ne ya debeshi, Da sauri ya koma ya rufe kofar, kafafuwansa kasa daukanshi suka yi, ja da baya yayi ya jingina da bango. Bai taba tunanin tsanar da Idrisa ke nuna masa zai kai ya iya aikatawa matarsa wannan danyen aiki ba. Karasawa yayi, kokarin ture Idrisa yayi daga bisa gadon, ya girgiza ganin Idrisa ya fado kasa kamar gawa. Dan tun farko bai lura Idrisa bai motsi ba. Wani mugun kunci ne ya turnukeshi ganin matarshi ba kaya, jikin da ya dade yana mafarkin gani amma bai taba tunanin a irin wannan yanayin ba. Idanun Jinah a rufe suke, alamar tana bacci, anan ya fahimci sumar da ita ne Idrisa yayi, kayanta ya saka mata sannan ya dauketa ya kaita har dakinsu ya shimfideta kan gado. Komawa yayi dakin dan uwan nashi da har yanzu yake kwance a kasa. Nan fah hankalinshi ya tashi, kunnensa ya kara a kirjin Idrisa anan yaji zuciyarshi bata bugawa. A hankali ya sakama dan uwan nashi wando, sannan ya ya barshi anan kwance. Bai rufe dakin ba, yaje ya kaiwa auntynshi makullin. Kada Ashanti (godiyarshi) yayi, nesa da gida. Yayi hakan ne ko zai manta tare da rage damuwar abinda ya faru. Abinda dan uwansa yayi ko yake kokarin yiwa matarshi, ko kuma mutuwar dan uwan nashi bai san wane ne yafi masa ciwo ba. Bayan yayi tafiya mai nisa, ya juya ya koma gida. Tarar da gidan yayi makil da mutane, dan kusan kowa yana nan, sai dai abinda ya bashi mamaki babu alamun an yi mutuwa a gidan, sauke ajiyar zuciya dan yana tunanin wata kil Idrisa ba mutuwa yayi ba. Daki ya nufa dan ganin ko Jinah ta farka. Tarar da ita yayi ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gado, sam baya jin dadin ganin matarshi kuma abar kaunarshi cikin damuwa. -Bansan me yayi min ba, ya..ya..umarceni da in bishi dakinsa, na bishi, naji tsoro, tsoron kar ya fada cikin dake a jikina ba naka bane..na..na.. Jinah ce ke fadin haka cikin kuka ba tare da ta jira ya tambayeta abinda ya faru ba. -Ki daina kuka dan Allah Jinah! -Na..naje dakinsa Dauda, hanani yin ihu yayi, ya tsoratani, san..sannan ya buga kaina a bango, sannan, sannan, sannan...Wayyoh Allah! bansan me yayi min ba. Me yayi min, ba zan iya tunawa ba... Ganin tashin hankalin da matarshi ta shiga, Dauda ji yayi yana son ya rarrasheta, ya kwantar mata da hankali, ya gusar mata da wannan tunanin da take. -Bai tabaki ba, nazo kan lokaci sannan na fitar dake daga wurin, bai yi maki komai ba. Shiru Jinah tayi da alamar rashin yarda tace -Ka tabbata? Tsareta yayi da ido don shi kam baida tabbaci, ya fada mata haka ne dan ganin ta kwantar da hankalinta. Itama Jinah tsareshi tayi da nata idon dan jin ya tabbatar mata da maganarshi. -Eh, na tabbata bai yi maki komai ba. Cikin dan kankanin lokacin da baiyi tsammani ba yaji ta fado jikinsa, ta kankameshi tana kuka marar sauti. Ji yayi zuciyoyinsu na bugawa a tare, lallausar fatarta na gugan tashi, tunda suke hakan bai taba faruwa ba, bai taba jin dadi irin na yau ba, haka bai taba jin matsanancin zafi da radadin jiki irin na yau ba. Dan ji yayi kamar an kunna mashi wuta a jiki. Lallai abu ne marar misaltuwa a wurinshi dadi da ciwo a lokaci guda. Ganin idan suka cigaba da kasancewa manne da juna to fah zai iya kamawa da wutar gaske yasa ya janye jikinshi daga nata. Ba'a dau lokaci ba kuwa ya bar jin zafin jikin. -Nagode kwarai da gaske! Jinah ta fada cike da farin ciki, murmushi kan lebenta. -Nauyina ne hakan, kuma ki kwantar da hankalinki ba zai taba fadawa kowa ba abinda yaji. Ya bata amsa kafin ta mike ta nufi ban daki. Wanka tayi da ta fito bata ganshi ba, kaya ta sake, tayi sallah sannan ta kwanta kan gado. Bata fatan ta kara haduwa da Idrisa, inuwar ma mai kama da Idrisa bata fatan sake gani dan ya tsoratata sosai, dan haka dole tayi taka tsantsan dashi. Da irin wannan tunanin bacci marar nauyi ya fara saceta. Cen cikin baccinta sama-sama taji kara daga wajen tsakar gida, zuciya na dukan uku-uku, Jinah ta fito daga daki dan ganin meke faruwa. Matan gidan ne ke ta kuka, Maza kuwa na kokarin rarrashinsu, wasu dora hannuwa biyu suka yi a kai, wasu na girgiza kai irin na anga abin alhini, Habi ta gani uwar gidan sirikinta kwance tana birgima a kasa, 'ya'yanta mata biyu suna riketa. Kasa fahimtar komai tayi, zuciyarta na bugawa kwarai. Neman Dauda ta fara yi kafin ta hangeshi kusan kofar dakin mamarshi, fuska a dame. -Wayyoh dana! me yasa Allah bai daukeni ba a maimakonsa, wayyoh Idrisana. Muryar Habi ke karade ko'ina da kukan rashin danta. Nan Jinah ta fahimci abinda ke faruwa, toshe bakinta tayi da hannuwanta ta zauna dirshen bisa wani benci dake kusa da ita. Duk abinda yayi mata, ba zata yi mashi fatan mutuwa ba. Cikin zuciyarta tace "to me ya faru dashi?" Dawowa hayyacinta tayi ganin Isa ya tunkari Dauda kamar wani mayunwacin zaki, Kanin Idrisa ne wanda suke uwa daya uba daya, wanda shima basu shiri ko kadan da Dauda kuma ya girmi Dauda da shekara biyu. -Kai ne ka kasheshi, naga lokacin da ka fito daga dakinshi, kai ne nan ka kasheshi! Isa ke fadin haka kafin ya kaima Dauda wani mugun naushi a fuska wanda yayi sanadiyar faduwar Dauda kasa, da sauri Jinah ta mike tsaye. Hankalin kowa dawowa yayi kansu. Wani kawu da wani dan uwan Dauda suka yi saurin janye Isa. -Ku kyaleni! Sai na kasheshi kamar yanda ya kashe mani dan uwa! shi... Bai karasa maganarshi ba yaji saukar wani gigitaccen mari a kuncinshi na hagu, da sauri ya dago yaga mahaifinsu ne. -Kada na kara jin wata magana makamanciyar irin wannan ta fito daga bakinka! Dan iska kawai! ta yaya zaka zargi dan uwanka da kashe dan uwanshi, baka ji kunya ba? Mahaifin nasu yake fadar haka cikin fushi hannunsa na rawa, bai gama farfadowa daga jin mutuwar babban danshi ba, yanzu kuma ga wannan abu da yake faruwa. -Kayi hakuri baba, zo ka zauna! Daya daga cikin 'ya'yansa ne ya fada yana kokarin kwantarwa da baban nasu hankali. Babu wanda ya yarda da maganar da Isa ya fada, dan sun san kiyayyar da yake yiwa Dauda komai zai iya kirkira ganin ya cutar dashi. Kuma duk sun san alakar dake tsakanin Idrisa da Isa, akwai abota mai karfi bayan yan uwantaka ma, dan haka komai zai iya cewa gameda mutuwar Idrisa, alhali Idrisan mutuwa ce yayi ta Allah da annabi ba wai kasheshi aka yi ba, abinda dai suke tunani dan babu wanda yayi tunanin akasin haka. Daren ranar babu wanda ya samu runtsawa, dan wannan shine karon farko da dadewa mutuwa bata konkwasa masu kofa ba. -Babu abinda nayi masa! Cewar Dauda yana fuskantar matarshi dake kan gado shi kuma yana zaune a kasa a lokacin da suka koma daki. -Nasan ba zaka aikata haka ba. Ta bashi amsa. -Bari tabbatar da hakan, dan abinda yayi kokarin yi maki, Abinda na kudira kenan, sai na kasheshi... -A'a, ka bar irin wannan tunanin, komin abinda mutum yayi mana, ba mu bane zamu yanke hukunci na rayuwarshi ba. Kai mutum ne na kwarai Dauda kuma dan Allah kar ka canja daga haka. Murmushi yayi mata, dan yaji dadin kalaminta. Yasan wata rana itama zata fara sonshi. Bubbuga masu kofa da ake yi kamar za'a balleta ne ya katse masu hirar da suke yi. Tashi Dauda yayi ya bude, sai dai da sauri ya ja da baya, lokacin da suka yi ido biyu da mai bubbuga kofar. Karasowa Jinah tayi wajensu, Dauda yayi mata umarni da ta koma bayanshi. Isa ne a gabansu, fuska a murtuke da kuma katuwar tabarya a hannunshi. -Dan Allah Isa kayi hakuri, ka kwantar da hankalinka, kar kayi abinda zai saka nadama. Jinah ce ke rokonshi, cikinta ya duru ruwan tsoro. -Sai na kasheka kamar yanda ka kashe Idrisa! -Na fada maka ba ni na kasheshi ba... -Karya kake yi, ai ya fada min abinda yake shirin yiwa wannan karuwar, shi yasa ka kasheshi! -Kada ka kara zagar min mata! -Dan Allah Dauda ba lokacin yin wannan rigimar bane. Jinah ta fada, ganin mijin nata shi kokarin kara kunna wutar yake. -Karuwa ce mana, idan ba haka ba, ya za'a yi ta shigo maka gida da cikin wani. Wani lafiyayyen naushi Dauda ya kaima Isa a fuska, shima Isa bai yi wata-wata ba ya kwada masa tabaryar dake hannunsa. Anan Dauda ya fadi kasa, jini na zuba kamar fanfo. Yar da tabaryar Isa yayi tare da saurin toshe bakin dake kokarin fasa ihu da hannunshi. Kuka Jinah take ganin mijinta a kasa baya motsi ga jini na zuba. Tsoro ya kama Isa, ya bar shedan yayi galaba a kanshi, so yake ya kasheshi, amma kuma yanzu da ya aikata nadama ce fal yake yi. Bai san me zai yi ba, idan mutane suka san abinda ya aikata, kashe dan uwansa na jini, kuma tabbas idan baba ya sani nima sai ya kasheni, ko kuma naje kurkuku, a'a ba zan bar hakan ta faru ba. Hakan zata faru ne idan mutane suka sani. Ya fada, yana kallon Jinah kafin ya saka hannayensa biyu ya shake mata wuya, kokarin kasheta yake yi, dan kar ta tona masa asiri. Kara makure Jinah yayi, ita kuma tari take tana kokowar kwatar numfashi, sai dai shima kamar ana yi masa hakan, shima ji yayi ya kasa numfashi, ga wata iriyar zufa da yake yi, jikinsa ya dauki wani zafi. Duk da wannan azabar kin sake Jinah yayi, dan kasheta shine mafita. Sassaucin makurar Jinah ta fara ji, iskan shaka taji ta fara samu lokacin da Isa ya fadi kasa matacce! -------------------------------- So pray for the deads lol. 😁 Ina mai barka da zuwa ga sabbin makaranta wannan labari, koda yaushe abin jin dadi ne gareni ganin sakonninku da kuma comments naku. Sannan ina mai baku hakurin lattin ganin cigaban wannan labari, hakan ta faru ne sakamakon azumi, da na bari ne sai bayan sallah to kuma wannan Monday din muke komawa school shine nace bari nayi maku ko 3 chapters ne kafin mu koma. Sai mun hadu a wata chapter din idan Allah ya kaimu. Wattpad : @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 8 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Gidan bahaushe, gida ne da zaka tarar da mace fiye da daya wato kishiyoyi. Kishiya kalma ce dake girgiza da yawan mata. Hada miji da wata matar, ko kuma ma wasu matan, hakan ba kowacce mace bace keda wannan jarumtar. Wadansu suna kallon haka a matsayin cin amana daga mazajensu idan suka ce zasu kara aure wanda har ta kaisu ga sun nemi saki. A wannan lokacin ma da muke ciki wasu matan kawo karshen rayuwarsu suke ko na mazajensu. A wajensu kishi wani abu ne da bai dace ya wanzu ba a duniya. Sai dai a wajen wasu matan ba haka bane, koda za'a auresu suna sakawa a ransu "namiji mijin mace hudu" ne dole wata rana mazajensu su kara aure. Zaman kishi yana iya zuwa da matsaloli, makirce-makirce, surkulle... kamar yanda zai iya zuwa gidan ya zama wani babban ahali, kishiyoyi su hade kansu, su zauna cikin kwanciyar hankali... Bangaren Malan Shehu baban Dauda yayi sa'ar samun mata da suka kawata masa gida da kwanciyar hankali, kuma shima yana yin adalci a tsakanin matan, a wurin matan ya kasance miji na kwarai. Sai dai matsalar tana wurin 'yan'yanshi ne, ba kamar mazan, dan ya gaza a matsayinsa na uba. Kuma hakan ta fara faruwa ne, wata rana lokacin Dauda yana cikin mahaifiyarshi, ziyara suka samu ta wani abokin mahaifin Dauda, mutumin babban malami ne, wanda yayi kaurin suna wajen warkar da cututtuka da yin duba. A ranar da malamin yazo yayi ta kallon mamar Dauda kafin yace «Wannan yaron da yake cikinki, shi zai zamo arzikin wannan ahali, yana tafe da alkhairai masu yawa, zai zamo yaro mai farin jini, ki kula dashi kamar tilon kwan kazar da ya rage a duniya.» Wadannan kalaman da ya fada, su suka yi tasiri a kunnuwan kowa dake kauyen, kowa a kauyen ya yarda da maganar malamin. Lokacin da aka haifi Dauda, malan Shehu ya samu wannan masana'antar da tayi sanadin daukaka ahalin aka sansu kowanne lungu a kauyuka. Nan fa kowa ya kara gasgata maganar malam ana fadin "lallai wannan yaron da sa'a yake tafe." Daga ranar Malan Shehu ya dauki son duniya ya dorawa Dauda, ya fifitashi kan sauran ya'yanshi. Matan sun fahimci fifikon da yake nuna ma Dauda amma basu saka komai a ransu ba, dan sun san dagaske Dauda alheri ne garesu tinda gashi yayi sanadin arzikinsu. Sai dai ga yaran wani abu ne daban, Idrisa da Isa da suka kasance diyan fari a gidan suka dauki karan tsana suka dorawa kaninsu Dauda, gani suke uban kamar ya daina sonsu tinda aka haifi Dauda. Shi kuma Dauda natsuwarshi da kyawawan halayensa suka sa yake da farin jini ga sauran mutanen gidan da ma kauyen baki daya. Kiyayyar dake tsakanin yan uwan gashi yanzu tayi sanadin mutuwar Idrisa da Isa, Dauda kuma kwance cikin jini rai a hannun Allah. Jinah zaunawa tayi kusa da mijinta jiki na mata rawar tsoro, tallabo kanshi tayi da sauri ta mayar dashi ta kwantar ganin yanda jini ya wanke mata hannuwa, ta saki wani razanannen ihu, ihun da ya yayi sanadin fito da wasu daga cikin yan gidan. Mahaifiyar Dauda ce ta fara shigowa dakin, daskarewa tayi waje daya ganin abinda ke faruwa, kafafuwanta kasa daukanta suka yi da rarrafe ta karasa wajen danta, kuka ta fara tana kiran sunan Dauda. Wata razananniyar kara tare da jan Innalillahi wa inna ilaihi raji'un suka ji a bayan su, Malan Shehu ne ganin danshi mafi soyuwa a wajenshi kwance cikin jini ya saki kara tareda faduwa kasa. Sauran mutanen gidan dake biye dashi suka yi kanshi, suka ciccibeshi zuwa dakinshi kafin su dawo dakin Jinah. Lokacin da mutanen suka lura da Isa kwance, daya daga ciki ya tabashi yaji baya numfashi tuni ya mutu, umarni yayi da kar a bar mahaifiyar Isa din ta shigo dakin, mutuwar 'ya'ya biyu a rana daya, kwalwarta ba zata iya dauka ba, amma kuma ko ba dade ko ba jima dole ta sani. Kawun Dauda, koda ya taba Dauda yaji yana numfashi yace a daukeshi zuwa wajen makocinsu mai magani. -Yana numfashi! Kawun ya fada, wata nauyayyiyar ajiyar zuciya Jinah da Mahifiyar Dauda suka sauke a tare. Lokacin da aka tambayi Jinah abinda ya faru, kasa cewa komai tayi sai hawaye da take, dan ba zata iya jure tuna abinda ya faru ba a cikin kanta, ba kamar idan ta tuna itama saura kiris ta mutu sai tsoro ya kara shigarta, sai dai tsoronta yayi yawa akan halin da mijinta yake ciki. addu'a ta fara Allah ya tashi kafadun Dauda. Kamar daga sama Kanwar Isa ta fado dakin lokacin har an dauke Dauda zuwa wajen mai magani, ganin jini a malale ga kuma gawar dan uwanta kwance, kara ta saki, ta fita a guje zuwa dakin mahaifiyarsu, sauran yan dakin da basu san meke faruwa ba suka dugunzuma dakin Jinah dan gane ma idonsu. Tashin hankali ne shimfide a fuskokinsu ba kamar Habi mahaifiyar Isa, mutuwar 'ya'yanta biyu maza wadanda take tunanin zame mata madafa a kingin rayuwar da zata yi gaba. Habi taci kuka har ta godema Allah, neman mijinta ta shiga yi bata ganshi ba, dakinsa ta nufa da shigarta ba'a fi mintuna biyar ba ta fito tareda kecewa da wata mahaukaciyar dariya da ta jawo hankalin yan gidan. Ganin abinda ke faruwa mahaifiyar Dauda da gudunta ta nufi dakin mijin nasu, tarar dashi tayi rai yayi halinsa, sai dai ita ba kamar Habi ba fitowa tayi tana jimamin rashin mijinsu. Wannan ba abu bane da ahalin zasu iya jurewa ba. Kafin kace me gida ya cika da mutane da koke-koken mata. Sai bayan wasu awanni mutane suka farga da dariyar da Habi take, mutuwar 'ya'yanta biyu da kuma ta mijinsu ya haddasa mata tabin kwakwalwa. Mahaifiyar Dauda fita tayi daga gidan, itama hankalinta a tashe na mutuwar mijinsu, abin kaunarta, mahaifin ya'yanta. Duk da tasan irin wannan ranar zata zo, sai dai bata shiryawa hakan ba, haka ma mutuwar ya'yan kishiyarta ta tabata, yaran da suka tashi a gabanta, tana son yaran duk da diyan kishiyarta ne. Ga kuma danta Dauda kwance rai hannun Allah. Gidan mai maganin ta nufa ta tarar da Dauda kwance, komawa tayi kusan kanshi tana kuka. Jinah kuwa a tsakiyar gida ta samu wuri ta rakube, tana kallon matan gidan sai rizgar kuka suke. Kukan da Jinah taci da hawayen da ta zubar yasa idanunta yanzu suka kafe babu alamar hawaye tana son yin kuka amma ta kasa. A cikin kanta kuwa tunani take yi, tana yiwa kanta tambayoyin abubuwan da suke faruwa wanda ta kasa samun amsarsu, alhali ita ya kamata a yiwa wadannan tambayoyin ta bayar da amsarsu, domin itace komai ya faru gabanta. Bayan wani dan lokaci, Jinah taji kamar ana kallonta, dagowa tayi taga daruruwan idanu a kanta. "Me nayi kuma?" tambayar da ta fara zo mata a kwanya kenan. -Itace, komai ya faru ne sanadinta, muna zaune lafiya kafin zuwanta, babu wata masifa irin wannan da ta konkwasa mana kofa. Wata 'yar uwar Dauda ce ke fadar haka tana nunen Jinah da yatsa. -Kwarai kuwa, ya za'a yi ace Isa ya mutu a dakinta kuma Dauda gashi cen rai a hannun Allah. Wata daga cikin yan uwan Daudan ta kara da hakan. -Wai ya aka yi kuka zama kamar makafi, baku ga yanda take kama da aljanu ba. Mayya mai cin kurwar maza. cewar wata makociyarsu. -Ina yawan ganinta a mafarki, duk lokacin da naso fada sai wani abu ya tokare min makoshi. Cewar wata yar uwan Dauda. -Rannan a tsakiyar dare na ganta tana magana da wani kare... Nan fa kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa na yiwa Jinah sharrin maita. Ita kuma Jinah ji tayi kamar tana gaban tv, dan binsu kawai take da idanu. Bata ko taba ganin da yawa daga cikin matan ba, amma gasu sai bada shedarta suke yi akan mayya ce kamar sun santa. Kuma hakane a duniyar nan tamu a yanzu, mutane suna jin dadin nuni da yatsa, yanke hukunci ba tareda sani ba, wato yiwa mutum sharri. Jinah bata ankara ba, taga matan sun yo kanta, wasu na kara daure zani, wasu kuma da makami irin su tabarya, itace, ludayin miya. Jinah kasa motsawa tayi dan razanar ganin wannan al'amari da yake shirin faruwa da ita. Matan na karasowa gareta, da sauri ta runtse ido tana jiran saukar duka a jikinta. Har wani dan lokaci ya shude shuru bata ji saukar dukan ba, kuma bata jin muryoyin matan, kamar ma nesa da ita suke. A hankali ta bude idonta, mamaki abin ya bata ganin kamar an tara al'amarin zuwa baya. Abun kamar ya faru mintuna goma baya (time travel). Wani makahon mari ta yiwa kanta, ta mitsiki kanta wai ko mafarki take amma kuma zahiri ne ba mafarki ba. Ganin komai tayi yana faruwa kamar a baya, sai dai lokacin da matan suke ta fadar maganganu a kanta ne aka cire a lokacin. Matan ko kallonta ma basu yi ba, bare kuma suyi mata magana. Tunani ta fara ko dai ta fara haukacewa ne, da sauri ta mike ta nufi dakinta, ji tayi ta fada kan gado, sannan ta fara wani nauyayyen bacci da bai wuce mintuna kalilan ba. Kiyi hakuri Jinah, na kasa cika alkawarina na kula dake da na daukarwa mahaifiyarki, babu yanda zanyi, nima tawa tazo karshe. Ki bar wannan gidan Jinah, kiyi nesa dashi, ba zan iya kareki ba... Ki gudu! ki gudu Jianh! Jin wannan kalaman cikin baccinta, Da sauri Jinah ta farka tana zufa, zuciyarta na dukan uku uku. "Me hakan ke nufi? Wayyo Allah me yake shirin faruwa dani?" tambayoyin da Jinah ke ta maimaitawa cikin tsoro. Tana cikin wannan halin taji wani mugun ciwon ciki ya turnuketa, wata yar karamar karar wahala ta saki, sai kuma ta fashe da kuka... Gashi ta kasa sauka daga kan gadon. Bayan tsawon lokaci da Jinah ta dauka cikin wannan matsanancin ciwo, cikinta ta gani yana kara girma, ta fara kurma ihun wahala, ji tayi a tsakanin kafafunta kamar zai kama da wuta tsabar azaba. Bayan dan lokaci kafafuwanta suka bude, saka yatsunta tayi a cikin katifa, ta cije labbanta na kasa, ta runtse idanunta. Lokacin da ta bude taga jariri ya fito daga cikinta, kara runtse idanu tayi, tana budewa taga wani ya kara fitowa. "Wannan wanne irin mummunan mafarki ne nake yi?" Ta fada cike da tsoro tana kallon halittun dake gabanta. --------------------------------- Fatan dai wannan chapter zata kayatar daku? Zaku yi saurin samun cigaba ne, idan naga adadin comments yafi na ko yaushe 🙁 My watty : @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 9 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp “Haihuwa maganin mutuwa, ba don ke ba da iri ya ƙare!" Wannan shi ne kirarin da ake wa haihuwa. Kuma sukan ƙara da cewa, “Kyan gida da magaji!” kirarin haihuwa kirari ne na ƙaruwa. Ma’anar haihuwa ita ce, yayin da miji da mata suka sami ƙaruwa ta samun ɗa ko ‘ya. Ma somin haihuwa kuwa shi ne, lokacin da mace ta samu juna biyu, wato ta sami ciki, bayan an tabbatar da igiyar aure tsakaninta da mijinta. Ƙarshen haihuwa shi ne yayin da jariri ya fito daga cikin uwarsa ta hanyar al’ada. Da zarar mace ta samu ciki (juna-biyu) sai iyayenta ko masu lura da ita su duƙufa wajen neman taimako don ta sauƙa lafiya. Akan kuma kafa mata dokokin da zata kiyaye, kamar kada ta riƙa cin abinci, ko abin sha mai zaƙi, kamar zuma da sukari ko rake ko mazanƙwaila ko alawa, saboda sauƙin nauyin fitowa abin haihuwa wanda yake faruwa da ciwon zaƙi. To, kuma akan umurce ta da ta riƙa shan magani a kai a kai, kamar sabara da bauri. Da kuma wasu tadodi na mai ciki kamar rashin fita da dare ba tare da wani makami ba, kamar wuƙa ko lauje ko ɗan makoɗi ko mashinjiri ko dagi, saboda shu’umi da aljani. Anan in an ga alamar cewa haihuwa ta kusa, sai a shiga neman maganin sauƙin guiwa, kamar shan rubutu da jiƙe-jiƙe. Sai a aika a ƙirawo wata mace, wato ungozoma, don ta kula da mai haihuwa. Kuma in ta sauƙa lafiya a kula da abin da aka Haifa. Sannan ta yanke cibiya, ta binne uwa, wato mahaifa. Kuma ba za a ba da sanarwar haihuwa ba, sai in an ga faɗuwarta, kana ungozoma ta kan ce “ Alhamdulillahi, barka da arziki!” da sauran maganganu ko addu’o’i da a kan yi bayan mahaifar ta faɗi. Daga nan farin ciki ne zai mamaye uwar a lokacin da taji kukan farko na jaririnta, abu na farko da zata so tayi shine ta dauki jaririn a hannunta, ta rungumeshi kwarai a kirjinta. Sai dai ita Jinah da ta haihu ba tare wani ya sani ba ko taimakon wata ungozoma ba, sam bata ji son daukar jariran ba a hannunta, eh tagwayen da ta kawo duniya mace da namiji. Ita abinda tafi bukata a lokacin shine ta runtse ido idan ta bude taga babu yaran ace mafarki take. Na farko dai bata san yaushe, ta yaya kuma da wanene ta samu cikin ba. Sannan ga wannan mutuwar da ta konkwasawa sirikanta kofa, kuma gashi bata samu wani taimako ba lokacin da zata haihu, sannan cibiyar jariran a yanke take, to ta yaya haka zaka ta faru? Abubawan al'ajabin da suka zo suka cunkushe mata kwalwa kenan. Cikin tsoro, tasa zani ta lullube jariran, sannan ta kwanta ta juya masu baya tareda rufe ido. Ji tayi kamar mutum a kusa da ita, zuciyarta ce ta buga. Bude ido tayi, taga Sarah durkushe gabanta. Hawaye dukansu biyu suke, dan Sarah ta karanci tsantsar tashin hankali a fuskar Jinah. -Labari yaje mana kan abinda ya samu sirikanki, abun babu dadi Jinah. Ya shi Daudan ya farka? Girgiza mata kai kawai Jinah tayi. -Kar ki damu, insha Allahu zai samu lafiya. Mikewa Sarah tayi ta zauna bakin gadon, tana shafa kan Jinah, irin ta kwantar mata da hankali. -Allah mai iko, jariran waye? kamar yan... Sarah ta fada lokacin da ta lura da yan tagwayen jarirai a bayan Jinah. -Nawa ne! Jinah ta fada a takaice cikin muryar damuwa. -Sabuwar haihuwa. Me kike... a'a wannan ba zai taba yiyuwa ba. Kasa yarda Sarah tayi. -Da gaske nake Sarah! Cikin Jinah, Sarah ta kalla taga wayam, sannan ta kalli jariran, hannu ta dora a bakinta da ya kasa rufuwa tsabar mamaki, ta kasa magana. Haka ta tsaya na tsawon wani lokaci kafin tace -Tun yaushe? -Dazu.. -Ikon Allah! Ta..ta yaya ba ki.. Me yasa jariran basu yin kuka? Gaskiya yayi wuri ace kin haihu Jinah! -Na sani Sarah, na fiki shiga razanin ganin wannan al'amari, akwai ma abubuwa da dama da suka faru da na kasa fahimta, kuma nake bukatar wani yayi min bayani. -Da taimakon wa kika haihu? -Babu wanda ya taimaka min. -Ikon Allah, Jinah! Mikewa tayi, ta yaye zanin da Jinah ta lullube jariran, nan ta lura babu kaya jikinsu. Fita tayi daga dakin ta samo bokiti cike da ruwa da kuma wani bahon wanka. Daya bayan daya tayi masu wanka, Sannan ta shafesu da mai kafin ta lullubesu da zani. -Karbi ki basu mama! Sarah ta fada, tana mikawa Jinah jariran. Hannunta na rawa ta fara karbar macen. Lokacin da jaririyar ta bude bakinta, ta tura mata kan maman, da sauri Jinah ta runtse ido, sannan taja wani dogon numfashi, wani yanayi ne mai dadi ya lullubeta, bude idonta tayi, lokaci na farko da ta jita a matsayin uwa. Murmushi tayi tana shafa kumatun jaririyar. Bayan dan wani lokaci, shima namijin tayi masa kamar yanda ta yiwa macen. -Sai kuma me zan yi? Ta tambayi Sarah cikin kasalalliyar murya. -Ban sani ba Jinah, amma tabbas idan mutanen nan suka fahimci kin haihu ba kyaleki zasu yi ba. -Na sani, zasu gane cikin ba na Dauda bane. -Toh tun wuri ya kamata mu bar gidan nan. -A'a Sarah, ni zan tsaya sai nasan halin da Dauda yake ciki. Ke kije da yaran ni na biyoku a baya. -Ba zan iya daukansu duka biyun ba. Sake Jinah tayi alamar tana tunani, kafin ta mike tana niyyar fita daga dakin. -Ina zaki je? Sarah ta tambayeta. -Ina zuwa. Fita tayi sannan ta dawo da Samira 'yar yayar Dauda. Yarinya ce da ba zata wuce shekaru 13 ba, amma Jinah ta yarda da ita sosai. Fadawa yarinyar tayi cewa wannan jariran ita ta haifesu kuma bata san kowa ya sani kuma tana son ta taimakawa Sarah taje da jariran. Yarinyar bata tsaya jin wani cikakken bayani ba, ta fita ta samo amalanke, da yake lokacin babu kowa a tsakiyar, saka kowane jariri suka yi kondon jarirai, kowacce ta dauki daya a suka kama hanyar kauyen Mambila. Jinah kwantawa tayi da niyyar rage gajiyar dake jikinta, amma bacci ya kasa daukanta, wata murya taji amma wannan karon, ji tayi ance : Kiyi hakuri Jinah. Mikewa tayi ta nufi gidan mai magani dan ganin halin da Dauda yake ciki, har yanzu bai farka ba, sai da ta dauki dan lokaci kafin ta dawo gida, wanka ta shiga tayi. Tana idawa, ba'a jima ba wata yarinya ta leko tace mata tazo inji Rashida daya daga cikin kishiyoyin sirikarta. Amsa kiran tayi, ta nufi dakin Rashidar, da shigarta ta tarar da gungun mata wadanda duk yawancinsu yan uwa Dauda ne sai kuma ita Rashida. -Me kike yi a daki, ko kina tunanin abincin karin shi zai sarrafa kanshi? Cike da mamaki Jinah ta dago tana kallonta, ba wai abinda ta fada bane ya bata mamaki, a'a yanayin yanda tayi mata maganar ne. Dan wannan shine karon farko da Rashida tayi mata irin wannan maganar cikin yanayin mugunta. Wata tsohuwa dake zaune kusa da Rashida, ta taso ta zagaya Jinah sau uku kafin ta yarfa mata wasu ruwa cikin kwarya da tsintsiyar kaba. Komawa tsohuwar tayi ta zauna tareda fadawa Rashida wani abu a kunne. Zabura Rashida tayi cikin karaji tace -Daman na sani! Ba cikakkiyar mutum bace, gashi yanzu Gwamma ta tabbatar. -Itace, komai ya faru ne sanadinta, muna zaune lafiya kafin zuwanta, babu wata masifa irin wannan da ta taba konkwasa mana kofa. Wata 'yar uwar Dauda ce ke fadar haka tana nunen Jinah da yatsa. -Kwarai kuwa, ya za'a yi ace Isa ya mutu a dakinta kuma Dauda gashi cen rai a hannun Allah. Wata daga cikin yan uwan Daudan ta kara da hakan. -Wai ya aka yi kuka zama kamar makafi, baku ga yanda take kama da aljanu ba. Mayya mai cin kurwar maza. cewar wata makociyarsu. -Ina yawan ganinta a mafarki, duk lokacin da naso fada sai wani abu ya tokare min makoshi. Cewar wata yar uwan Dauda. -Rannan a tsakiyar dare na ganta tana magana da karnuka... Girgiza kai Jinah take ko ta farka, dan ita a tunaninta mummunan mafarki take, dan ganin abinda ya faru jiya yana sake maimatuwa yanzu, kamar ana tariyar kaset. Rufe ido tayi sannan ta bude, tsoro ya kara shigarta ganin idanun wadannan matan kanta suna kallonta cike da tsana. Bata ankara ba, taji sun rufeta da duka da yakushi. Ihu Jinah take tana kuka amma babu wata mai imani da ta sassauta mata. Jinah tana kuka tana maimata : dan Allah ku fada min me nayi maku, me yasa kuke dukana? Ita al'amarin daure mata kai yake ganin yanda take zaune da sirikanta lafiya kuma suna kaunarta amma lokaci daya sun juya mata baya gashi yanzu kokarin kasheta suke. Tunani take "Anya wannan zahiri ne kuwa ba mummunan mafarki ne nake ba?" Haka matan nan suka cigaba da jibgarta babu tausayawa, kamar daga sama taji ana cewa -Baku jin kunya ne, duk abubuwan da suka faru a gidan nan. Maza ku rabu da ita! -Innalillahi! Me kuka aikata haka? Jinah bata san ko waye ya kawo mata dauki ba, amma taji an daina dukanta. Mahaifiyar Dauda ce da yayarsa. -Gwamma ta fada mana ko wacece ita, wannan yarinyar ita ce sanadiyar duk wani tashin hankali a gidan nan, Mayya ce ita! Cewar Rashida tana nishin gajiyar dukan Jinah. Wani mugun kallo Jinah taga sirikarta ta watsa mata, wanda yasa duk gwiwowinta suka sace. Yanzu kenan tana goyon bayan wadannan matan, to me yasa? Kuma wacece wannan tsohuwar da suka yarda da abinda ta fada? -Ku kyaleta, sirikata ce ni nasan me zan yi mata. Nusaiba (wato 'yarta, yayar Dauda) taimaka min na kaita dakinta. -Mama! Cewar Jinah tana kuka, lokacin da suke su uku a dakinta. -Kada ki kara kirana da wannan sunan. Ki tattara kayanki yanzu ki bar gidan nan, kafin sauran yan kauyen su san abinda ke faruwa, kuma na hanasu dukanki ne kawai albarkacin soyayyar da dana yake maki. Mahaifiyar Dauda ta fada kafin ta juya ta fita. -Yanzu Nusaiba kin yarda da abinda suke fada a kaina? Jinah ke tambayar Nusaiba yayar Dauda. -Ban sani ba Jinah, amma Gwamma bata taba karya ba ga abinda ya shafi wannan, dan tasan mayu sosai. Shuru Jinah tayi, ta cigaba da sheshekar kukanta, dan batada abin cewa. -Bari na taimaka maki, ki hada kayanki. Cewar Nusaiba. -Amma fa wannan ba shine na farko ba da na hadu da wannan tsohuwar, me yasa bata taba cewa ni mayya ce? -Nima ban san dalili ba Jinah. Zuwa karfe goma na safe, Jinah ce zaune tare da kayanta bisa amalanke zuwa kauyen Mambila. Tayi matukar galabaita, ko'ina na jikinta ciwo yake, cikin awannin da basu fi 24 ba, abubuwa da dama sun faru wadanda tsabar rashin sanin ma'anarsu tana nema ta zauce, abinda tafi kasa ganewa yanda farat daya dangin mijinta suka sauya mata. Tunaninta komawa yayi kan mijinta da yake cen kwance rai a hannun Allah, ji tayi sam babu dadi, Addu'a tayi Allah ya tashi kafadunsa, duk da tasan sai ya kara shiga wani halin idan ya farka yaji labarin mahaifinsa ya rasu. Bayan tafiyar kamar mintuna ashirin, suka karaso gidan su Sarah. -Sannu Jinah, labari ya riskemu, yanzu haka shirye shiryen tafiya muke, Allah ya jikansu yasa aljanna ce makomarsu. Gaskiya abin juyayi ne sosai ya samu dangin mijinki. Safiya matar Lasaini ke fadar haka kamar wacce aka jona a radio, kalamanta sai suka kara sa Jinah fashewa da kuka, kuma a lokacin idan aka tambayeta kukan me take, ita kanta bata san amsar me zata bayar ba. -Kiyi hakuri ki daina kuka Jinah, dama duk mai rai mamaci ne. Murmushi kuma safiya tayi lokaci guda. Dazun Sarah ta haihu, ta haifi kyawawan tagwaye. Wasu na tafiya, wasu na zuwa. Ikon Allah kenan. "Kenan Sarah wata karyar ta kuma yi a kaina?" Jinah ta fada cikin zuciyarta. -Ah Masha Allah! Abinda Jinah ta iya fada kenan, tareda kirkiran wani murmushin dole. -Eh, kuma babu wanda yasan tanada ciki. Ita kadai ta haihu ba tare da wani ya sani ba, gaskiya uwar rikonki jaruma ce. Lasaini na jirana zamu je jana'iza, ki wuce Sarah na ciki, yanzu muma mun dawo. Daman maganar ta fara isar Jinah, suna yin sallama tayi saurin karasawa dakin Sarah. Sarah ganin Jinah ta tabbatar ba lafiya ba dan duk fuskar Jinah ta kumbure. -Me ya faru Jinah? -Dukana suka yi Sarah, sannan suka yi min sharrin maita kafin su koreni daga gidan. -Allah sai ya saka maki, bani labarin abinda ya faru. Jinah labarin duk abinda ya faru taba Sarah daga lokacin da ta barota, sai dai kamar ita Sarah ma bata fahimci komai ba. Taimaka mata tayi ta kwanta, zuwa dare ta dauko man zaitun ta tattausa mata jikin, ba abinda Jinah keyi bayan kukan wahala. -Allah sai ya saka maki Jinah, kuma insha Allah aniyarsu sai ta bisu. Sarah ke fada tana kwalla, dan abin yayi matukar bata mata rai. Da taimakon tausar da Sarah tayi mata, Jinah ta samu yin bacci sai dai kafin nan sai da taji muryar nan ta rada mata : "Nagode da zama uwar 'ya'yana". Da yamma, Jinah da Sarah suna zaune a daki suna fira, suka ji ana bubbuga kofa, Yayan Sarah ne Lasaini, shigowa yayi yace Jinah ta basu wuri zai yi magana da Sarah. Fita Jinah tayi zuwa tsakar gida, inda taga mutanen gidan kowa sai yi mata irin kallon da dangin mijinta suka rinka yi mata. Tsoro ya kamata, ba tare da tace uffan ba ta jawo banci ta zauna bakin kofar dakin. Cikin dakin kuwa, rigima ce ta kaure tsakanin Sarah da yayanta Lasaini. -Ni babu ruwana da abinda wadannan mutanen suka fada maka, kawai sharri suke mata. -Ke da kanki kin sani, yanayinta yayi kama da na aljanu, dole a ce mayya ce. -Na fada maka mutum ce kamar mu. Lasaini, ka tuna da Tanti Amina, cousin din Mamarmu? -Eh na tunata! -Ba mutane sharrin maita suka lakaba mata ba. Amma ni da kai da Mama mun san ba mayya bace. Korarta aka yi daga kauye kamar karya. Kuma kai kasan daga baya abinda ya faru... Jikin Lasaini yayi sanyi yace -Eh kashe kanta tayi. -To kuma shine kake son haka ta sake faruwa ga Jinata? Wannan ba mai yiyuwa bane, ba wanda zan bari ya taba min Jinah, mutane mugaye ne Lasaini. -Kinada gaskiya, kiyi hakuri. Nan Lasaini ya lallashi kanwarsa tareda tambayar lafiyar yan tagwayen da yake tunanin 'ya'yanta ne. Bayan sati daya, aka yi bikin yan tagwaye, aka sa ma macen suna AYA shi kuma namijin AYYU KANTE. Jinah ce ta zabi sunayen sai dai ita kanta bata san dalili ba. Kawai abinda ta sani KANTE sunan mahaifin Kimba ne mijin Sarah. Wani abin mamaki ga tagwayen girma suke yi da sauri, har wani lokaci cikin raha Sarah sai tace: "Lallai wannan diyanki, suma akwai abubuwan al'ajabi a tare dasu kamar ke." Jinah tana cikin farin cikin kasancewarta uwar wadannan yan tagwaye, wani lokacin idan ta kallesu sai taga kamar tasan fuskokin a baya. Sosai suke tuna mata wani, wanda ta kasa gane waye. Matsala daya da har yanzu take fuskanta har yanzu a kauyen wasu kallon mayya suke mata, tana shan tsagwama sosai. Ganin haka Sarah ta shirya barin kauyen ita da Jinah da kuma tagwayen ba tare da taso rabuwa dan uwanta ba da kuma dan yaro Bukari, dan ba zata iya jure ganin halin da Jinah take shiga ba a kauyen. A wata safiyar Lahadi, suka dauki hanya zuwa gidan Sarah wato gidan mijinta Kimba. Basu kai gidan ba sai tsakiyar dare, amma da zuwansu sai suka tarar da alamun mutane a gidan. Ba zai wuce Kimba ne mijinta ba, amma kuma ba shi daya bane. Zuciyar Sarah ce ta buga, tunawa da tayi yace mata kar ta yarda ya rigata dawowa. ----------------------------------- Assalamu alaikum, fatan kun sha ruwa lafiya readers? I'm sorry much, nq jinkirin yin update da wannan labari. Sai kuna yi kuna hakuri dan rubutu akwai wahala bare ga sabon shiga. Kuma nasan a wannan chapter akwai wurare da dama, da sai mutum yayi da kyar ya fahimta. But everybody be cool! Sai mun hadu a wata chapter insha Allah 🤗 @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 10 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Hankalin Sarah yayi matukar tashi lokacin da ta tabbatar Kimba ya rigata dawowa gida. Tsoron nata kasa boyuwa yayi har Jinah ta fahimci halin da take ciki. Kokarin kwantar mata da hankali tayi. -Babu abinda zai yi maki, ba ce maki yayi, idan yaje cen zai dade bai dawo ba? To kenan ban ga dalilin tada hankali ba ganin ba wani dadewa yayi ba sosai. -Eh, amma... -Ba wani amma, ki kwantar da hankalinki, ni nan nasan me zan yi. -Me zaki yi? Sarah ta tambayeta tana kwalalo ido. -Ke dai ki jira zaki gani. Jinah ta fada cike da tabbatarwa, dariya Sarah take wanda har tsoron nata ya gushe. Ita kuma Jinah fuska tayi, irin yanayin ita fa ba da wasa take ba. Ta tsani mutumin nan duk da bata taba ganinsa ba, kuma lallai ya cancanci a koya masa hankali. Kokarin shiga gidan suka yi ta baya, sai dai ganin kowacce da yaro a hannunta, so ba zasu iya shiga da kayan baki daya ba. Goya Aya Jinah tayi a bayanta sannan ta dauki Ayyu a hannu, ita kuma Sarah ta shiga da kayan. Duk wani taku idan tayi zuwa cikin gidan, sai taji tana kara kusanto muryoyin dake magana cikin gidan, muryar mijinta da wasu da ta kasa gane su waye take ji. Su waye wadannan mutanen? Wata kila daya daga cikin kishiyoyina ne. Ta fada cikin ranta. Dakinta ta nufa a maimakon ta nufi inda mijin nata yake, domin ajiye kayan nasu, sai dai... -Sarah! Muryar Kimba taji ya kwala mata kira. Wani bugawa zuciyarta tayi, taji yin numfashi na shirin gagararta, Sakin Jikunan dake hannunta tayi. Kamar wata sakago, ta juya a hankali suna fuskantar juna. -Ina son magana dake, ki sameni a daki. Ya fada cikin wani yanayi da ta kasa fahimta. -Ina..ina zuwa. Kayan ta fara kaiwa daki, sannan ta yiwa Jinah da tagwayen masauki kafin taje amsa kiran mijinta. -Ina yini? Ta fara gaidashi. -An zo lafiya? Ya gajiyar hanya?...tun yaushe kazo?... Me kake so na hada maka, ko na kai maka ruwan wanka?... Duk ta rude, tambayoyi take ta yi masa ba kakkautawa, ita dai kar dai yace tayi laifi. Cike da mamaki da daurewar kai taga Kimba ya nufota tare da rungumeta. -Ta mutu Sarah, ta mutu! Kimba ya fada cikin kasa da murya, amma kuma taji abinda yake fada. Karon farko kenan da taga Kimba cikin irin wannan yanayin gashi kuma har da hawaye. Tausayinsa ne ya kamata, a take ta manta da duk wani abu da yayi mata a baya, shafa kansa take da sigar lallashi. Bayan wani dan lokaci, bakin gado suka zauna, dora kansa yayi bisa kafafunta, ita kuma a hankali take shafa sumar kanshi. Bayan ta tabbatar kamar hankalinsa ya dawo jikinsa, ta tambayeshi: -Kimba, waye ya rasu? -Aisha, Matata ta farko. Wani abu taji ya tokareta a kirji. Kenan nima irin wannan halin zai shiga idan na mutu? Tambayar da ta yiwa kanta kenan, da sauri kuma ta kauda tunanin. Fuskarta cike da damuwa, taji babu dadi na mutuwar kishiyar tata duk da basu taba ganin juna ba. -Allah yasa kwanciya hutawa ce a gareta kuma Allah yasa aljanna ce makomarta. -Ameen Shuru na dan wani lokaci ya biyo baya, kafin Kimba yace: -Akwai wani abu da nake son fada maki. -Ina sauraronka. -'Ya'ya uku muka haifa ni da Aisha, babban yana karatu ne a wajen kasa, su kuma biyun a tare muka zo. Ina son su zauna a nan, ina fata zaki kula dasu kamar ya'yan da kika haifa. Kasa gasgata abinda kunnuwanta suka jiye mata tayi, duk matan da ke gareshi, a ce ita zai zaba ta kula mashi da 'ya'ya. Wata kila yana ganin ita daya ce zata rike masa su da amana, abinda bata sani ba, sai da ya kaisu wajen sauran matan amma suka ki karbarsu. -Allah ya bani ikon rike amana, kuma naji dadin tunawa dani da kayi. -Ameen, na sani Sarah ke yar halak ce. Nagode sosai. Murmushi tayi jin wannan kalaman na yabo daga mijinta. Wata kila mutuwar matarshi ce tazo masa da shiriya. -Zan je inyi wanka, sannan na hada maku wani abun ci. -Ok, nima ina son yin wankan, amma kar ki wahalar da kanki, bana jin yunwa. -Yaran fa? -Eh, duka a koshe muke, kar ki damu. -Ok, bari na kai maka ruwan wanka. Kamar yanda tace, haka tayi, jawo ruwa tayi a rijiya dake tsakar gidan sannan ta kai masa bayi. Zuwa tayi ta tarar da Jinah da har ta fara bacci. Ta manta bata yiwa mijinta maganar Jinah ba. Sai dai akan wa zata gabatar da ita? Bata yi wannan tunanin ba ga kuma wadannan tagwayen. Zaune tayi tana tunani kafin Jinah ta bude ido. -Lafiya dai? Me ya faru? -Daya daga cikin kishiyoyina ce ta rasu, uwar gidan Kimba dake a Nigeria. -Ayyah, Allah ya jikanta, ya kyautata makwancinta! Bata lafiya ne? -Ban sani ba, amma rasuwarta ta taba Kimba sosai, dan nayi mamakin canjawarsa, wata kila dalilin rasuwarta ne, amma dai yau naga asalin Kimba da na sani kuma naso a baya. -Masha Allah, Allah ya kara dorashi bisa hanya. -Ameen, yazo tare da 'ya'yan marigayiyar, yace anan zasu zauna. -To ya kike gani? -Kema kin sani dole na karbesu hannu biyu sannan na kula dasu. Zan je in gansu, ko zaki rakani? -Eh, me zai hana? Fita suka yi daga dakin, suka bar tagwayen kwance suna bacci. Suna shiga dakin suka tarar da matasan zaune, macen ba zata wuce shekaru 15 ba, sai namijin saurayi ne da ba zai wuce 20 ba. -Sannunku, kun wuni lafiya? Sarah ta gaishesu, sai dai basu amsa ba, ko kallon tsiya bata samu ba. Kallon Jinah Sarah tayi da ta daga mata kafadu. Kara maimata gaisuwar tayi amma shuru basu amsa ba. Tashi suka yi, suka fita da tunanin wata kila har yanzu firgicin mutuwar mahaifiyarsu ne bai gama sakinsu ba. Bayan Sarah tayi wanka, itama Jinah ta shiga tayi. Kwantawa Jinah tayi gefen jariranta, ita kuma Sarah sai da ta tabbatar da diyan mijin nata sun samu wurin kwanciya sannan ta wuce dakin mijin nata. Tarar da mijin nata tayi a kwance bisa gado, tunani tayi ko har yayi bacci. Kwantawa itama tayi gefenshi. Cen cikin bacci taji hannunshi na shafa bayanta. Lebenta na kasa ta dan ciza, tana son ce masa a gajiye take, sai dai ba zata iya ba, ga halin da mijin nata ma yake ciki, kuma wannan shine karon farko da dadewa rabon da yazo mata cikin kwanciyar hankali. Juyawa tayi suna kallon juna, idanunta cike da sha'awa. Bata tsaya dogon tunani ba, ta biye mashi zuwa wata duniyar. Washe gari, Sarah ta riga kowa tashi, gyara gidan tayi. Bayan ta idar ta nufi dakin da Jinah ta kwana domin tasheta tayi sallah. Kusan suman tsoro tayi, lokacin da ta tarar da yan tagwayen zaune suna kallon juna kamar wadanda ke tsaka da hira alhali ita uwar tasu bacci take ta yi abunta. Ido Sarah ta zuba masu, suma kuwa suka zubo mata nasu. -Idan da ban sanku ba, to zan iya rantsewa aljanu ne ku! Sarah ta fada tana kallon yaran dake ta yi mata murmushi. -Gaskiya kuna da abin tsoro. Ta fada kafin hankalinta ya koma kan Jinah da ta farka. Bayan ta fito daga dakin Jinah, ta nufi dakin yaran mijinta, tayi mamakin tarar da su suna sallah domin tuni suka tashi. Fita tayi ta nufi tsakar gida inda ta ajiye gumba domin dama kokon karin kumallo. (...) Sarah na tsakar gida tana raba kokon da ta dama, sallama taji ana yi a bakin kofar gidansu. Amsa sallamar tayi tare da duba mai sallamar, da mamakinta taga Dauda, wani farin ciki ne ya lullubeta ganin Dauda a tsaye kan kafafunsa ya warke sumul. Tashi tayi da niyyar yi masa iso sai ga mijinta Kimba ya fito sanye da lafiyayyun kaya da jaka a hannu. Zuciyarta ce ta buga, ganin alamar tafiya zai yi. -Kimba, ina kuma zaka je haka? Ta fada da alamun tambaya a fuskarta. -Ina ruwanki da inda zan je! Yaushe kika fara samun dokar sanin inda zan je? Shuru tayi, domin ta tsorata da lamarin Kimba, mutum jiya take lafiya lau dashi, har ta fara tunanin zasu fara sabuwar rayuwa ganin kamar ya shiryu, ashe ba haka. Hawaye ne suka kwaranyo mata. -Ina zaka je Baba? Cewar 'Yarshi. -Ba fa zaka tafi ka barmu a wannan gidan ba! Cewar danshi. -Ban son shirme, ba jimawa zan yi ba zan dawo. Kuma kar ku kuskura ku bar gidan nan. Kai kuma Samaila ka sake yi min magana haka, kaga yanda zan fasa maka baki, marar kunya kawai... Sai a yanzu ya lura da bakuwar fuska a wurin, yace: Kai kuma waye? Me kake nema anan? -Sunana Dauda, kuma nazo wajenta ne, wato matata! Dauda ya fada yana nuna Jinah da ta fito daga daki. Inda hannun Dauda ya nuna Kimba yabi da kallo, kwalalo ido yayi cike da tsoro, baki hangame kamar wanda yaga fatalwa. Duk wannan kallon ba kowa yake yiwa ba face Jinah. Sakin jakar dake hannunsa yayi, ya nufo inda take. -Am..amma..ta..ta yaya.. kika dawo kyakyawa haka, ku..kuma kika mike tsaye kan kafafuwanki?.. Ya..yaya aka yi kika samu kafafuwa?..A'a ba haka kike ba, rarrafe kike yi a lokacin da nayi maki fyade. "Nayi maki fyade" ita ce kalmar da kowannensu ya iya rikewa. Kimba jinsa yayi zube kasa sakamakon wani lafiyayyen naushi da Dauda ya aika masa a fuska. Sarah, kasa motsawa tayi, ita kuma Jinah ba ma zaka gane yanayin da take ciki ba... (.....) Kwance yake yana kallon sama, ya lula duniyar tunanin abubuwan da suka faru, yarintarsa, iyayensa, Mahaifiyarshi, Jinah... Tunaninsa tsayawa yayi ranar da zai rabu da Jinah, kuma a ranar ne aurensa da Jinah, murmushi yayi, murmushi mai ciwo. Zai iya cewa wannan ranar ita ce rana mafi dadi da ciwo a rayuwarsa, saboda bayan an rabashi da matarsa abar kaunarsa, mahaifinsa ya umurceshi da yaje ya dakatar da alkawarin da suka yi da Jinah, amma yaki yin hakan. Irin wannan umarnin sarkin aljannu ma yayi masa amma yaki yin hakan, wanda hakan yasa dole ya biya kin bin umarnin da yayi. Auren mutum babban kuskure ne a kabilarsu, mahaifinsa yace masa yaje ya dakatar da alkawarin shi kuma zai yi kokarin ganin ba'a turashi kurkuku ba. Fally shi bai shirya yin hakan ba, dan shi a ganinsa ba wani abu bane dan aljani ya auri mutum, sai dai bai san akwai kalubale da dama a cikin auren ba... Fally yana ganin idan har ya karya alkwarinsu to dole Jinah zata auri wani, shi kuma abinda bai so kenan, yafi son Jinah tayi ta kasancewa tashi shi kadai. Kuma ma idan yayi hakan kamar yaci amanar Jinah ne, kuma ya karya alkwarin da suka dauka a tsakaninsu. Bayan awa 24 sun wuce wanda ya kamata ace cikinsu zai dakatar da alkawarin, Kaddararsa ta sauya, ya rasa duk wata kima irin ta aljanu. Sarki ya aiko a kama Fally, a duniyarsu idan aljani yayi laifi ana zuwa kamunsa ne da wata azababbiyar sarkar wuta mai dauke da kananun kwari masu cin nama, idan wannan sarkar ta taba jikin aljani, shiga take har cikin naman jikinsa, ta sakar masa kwarin sun dinga cin naman jikinsa. Lokacin farko da ta taba jikin Fally, hannuwansa a daure suke ta yanda ba zai iya anfani da siddabarunsu na aljanu ba, Babu abinda ya iya yi face ihu. Bai taba jin matsanancin zafi a rayuwarsa irin na lokacin ba. A karo na biyu da za'a lafta masa ita, runtse ido yayi yana shirin jin saukarta. A maimakon yaji saukar bulalar, sai yaji an rungumoshi ta baya. Yana bude idonsa yaga bulalar ta sauka a bayan mahaifiyarsa da ta dantse hakori tare da runtse ido tsabar zafi. Ganin abinda mahaifiyarsa tayi yace: -Me yasa kika yi haka mama? Me yasa kika zo nan? Me yasa kika bari bulalar ta tabaki? -Kiyi hakuri ranki ya dade bamu ganki bane... kiyi hakuri. Cewar Aljanun da suke bugun Fally cike da firgicin ganin bulalar ta sauka a bayan AYA mahaifiyar Fally. Domin babu aljanin da bai san da kwanan mahaifiyar Fally ba. A wahalce mahaifiyar Fally tace: -Idan har bakwa son ganin fushina, to ku gaggauta daina dukan dana, idan ba haka kuma kun san abinda zai biyo baya. -Mun daina ranki shi dade, yanzu zamu maidashi cikin kurkuku. -Karka damu Dana, zan fitar da kai daga wannan gun, nayi maka alkawari. (...) Girgiza kansa yayi domin dawowa hayyacinsa, a yanzu babu abinda ya rage masa face yin tunani domin kwanaki kadan suka rage masa. Kullum yana ji kamar ana cire wani bangare a jikinsa da wata wuta, da haka aljani ke fahimtar karshensa yazo. Juyawa yayi ya kalli inda abokin zamansa yake, tuni ya dade da mutuwa har wurin ya zama kamar sahara, babu komai da yayi saura a gawar sai kasusuwa. Shi ma lokacinsa kawai yake jira, duk da mahaifiyarsa tayi masa alkwari, amma ya riga da ya sare ba makawa sai ya mutu. Lokaci guda, idonsa suka fara yi masa nauyi, rufe idon yayi. _Lokacina yayi Jinah._ _Ina matukar kaunarki Jinah._ _Na sani bayan mutuwata, zaki zama mai 'yancin kasancewa da wani, ni kuma idan haka ta kasance, zuciyata zata zama tamkar kwalbar da aka jefo daga kan bene mai hawan dari biyu._ _Nayi imani da soyayyarmu Jinah kuma zan cigaba da yin imani, tare da fatan kasancewa da ke a wata rayuwar._ _Ki cigaba da tunawa da ni, kamar yanda ba zan taba mantawa da ke ba, kema kar ki taba mantawa da ni, kar ki manta da ni Jinah!_ Fally ke fadar haka da tunanin maganarsa ce ta karshe. Domin ya gama sarewa cewa babu abinda zai hanashi mutuwa. Sai dai kamar almara, Fally yaji wani karsashi na kara bayyana a jikinsa, fatarsa na komawa daidai, wani karfi na kara shigarsa. Kasa yarda yayi, dan ya tabbatar, gwada bacewa yayi sai gashi ya bayyana a tsakiyar dokar jeji, Fally ya kubuta, Wani ihun farin ciki ya saki, ihun da yayi sanadin tsorata duk wata dabba dake cikin jejin. *Libéré, délivré!* A rayuwa, komai yanada dalili, a bayan kowanne al'amari akwai boyayyen sirri. Idan da Fally yasan me yayi sanadin fiddoshi to da zai gwammaci mutuwa. -------------------------------- In cigaba ne? To na fara ganin likes da comments 😁 @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 11 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Rayuwa akwai dadi, kasancewa a raye, shakar numfashi, kasancewa cikin koshin lafiya, abubuwa masu dadi da ban sha'awa a cikin rayuwa da kudi basu iya siya. Mai kudi a shirye yake ya sadaukar, a lokaci daya, duk wata dukiya da yasha wahalar tarawa shekara da shekaru, kawai dan ya kasance a raye. Haka ma talaka yana iya kokari ganin yayi fafutukar yakin kasancewa a raye. Wasu kuma duk dukiyarsu, adadin kwararrun likitocin duniya ba zasu iya kubutar dasu daga wata cuta da Allah ya dora masu ba, haka zaka ga kullum suna fadi tashin neman lafiya da tunanin idan sun kwanta bacci ba za'a wayi gari dasu ba. Sannan akwai wadanda a kullum cikin koshin lafiya suke kuma a kullum fatan dawwama a haka suke. Duka wannan nau'i hudun na mutane mun kaddarantu ga mutuwa ne ko ba dade ko ba jima. Amma duk da haka muna fatan masu tsayin rayuwa, domin kamar yanda nace rayuwa wata aba ce mai ban sha'awa, kasancewa a raye wani iko ne na Allah kuma dole mu kasance masu yi masa godiya a kowanne hali. Iska daya ta numfashi da muke shaka ya fiye mana adadin dukiyar Karuna, mu kwanta da dare, mu wayi gari da safe wannan duk iko ne na Allah. Sai dai Rayuwa takaitacciya ce, lokaci yana gudu ne tamkar haske. Kuma kowanne cikinmu yanada takaitaccen abin kirgen lokacinsa, dan haka muyi anfani da wannan takaitaccen lokaci namu, mu tunkari kaddarar dake gabanmu, mu kasance masu komawa ga Allah, dan mu kamar matafiya ne da muka yada zango a wannan duniyar. A bangaren Fally a yanzu ya fahimci mecece rayuwa, domin halin da ya shiga da ganin mutuwa a kusa dashi. Yanzu kuma gashi ya kubuta, ya zama mai 'yanci sannan ya gujewa mutuwa a halin yanzu. "Nasan iyayena zasu yi farin cikin ganina idan naje gida." Ya fada a zuciyarsa cike da zumudin zuwa gida. Sai dai da karasawarsa gida, yanayin kamshin gidan ya sauya, kamar akwai abinda ke faruwa, dan ba kamar yanda yake a baya ba. A kasalance ya karasa shiga gidan, mahaifinsa ya tarar zaune cikin yanayin bakin ciki. Ido suka hada, Fally yayi mamakin rashin ganin farin ciki ko mamakin ganinsa a fuskar mahaifinsa. -Baba! Cewar Fally. -Kada ka kara kirana da wannan sunan! Kaga inda taurin kanka ya kaimu ko? Mahaifiyarka babu gwagwarmayar da bata yi ba ganin ta fiddoka, ganin cewa baka mutu ba. Gashi yanzu ta... A'a babu abinda ma zan iya fada maka dan bani da wannan karfin. Jeka! je ka kwanta kan gado. Fally ya fahimci abinda mahaifinsa ke nufi, domin idan aljani ya mutu to yana barin wasiyyarsa ne kan gadon baccinsa. Kallon mahaifinsa yayi, bai ce dashi komai ba, ya nuna yatsa a take gadon marigayiyar ya bayyana a gabansu. Tafiya Fally yake kamar wanda kwai ya fashe ma, karasawa yayi kan gadon ya kwanta tare da rufe idonsa.... Dana, da farko, bana son ka dorawa kanka laifi akan abinda ya sameni, sam ba laifinka bane. Nayi kawai abinda ya dace ne. Naje naga Hindu... Nasan me zaka ce, kamar yanda mahaifinka yace min. "Bakida hankali ne, kinsan wannan matar shedaniya ce, kullum idan aljani yaje mata da neman taimako sai ta nemi wata sadaukarwa gareshi, ke kuma shine zaki je ki nemi taimakonta?" Itace aljanar da tafi kowanne aljani tsufa a wannan duniya tamu, ta rayu tsawon zamani da yawa, mace ce mai dogon sani da kuma karfin tsafi. Da yawan aljanu idan suka samu matsala suna zuwan wajenta ne neman taimako. Ban nemi taimakonta ba har sai da na tabbatar babu wata hanya ta kubutar da kai. Domin na kubutar da kai ka rayu, dole ni na kashe kaina, eh, na kawo karshen rayuwata. Lokaci mai tsawo kenan da take son taga mutuwata amma bata samu dama ba, ita da kuma da yawa daga cikin aljanu. Ba don komai ba, sai domin nice mai gadin Jinah kuma nice wadda uwarta ta bani amanarta kafin ta mutu. Shi yasa indai ina raye to basu taba cimma burinsu akan Jinah ba. Amma nayi imanin kai da mahaifinka zaku kare min 'yata Jinah, shi yasa na yanke ni na mutu dan kai ka rayu. Nasan mahaifinka zai yi fushi da kai, amma komai zai wuce. Sannnan ina tayaka murna Dana, ka zama uba yanzu, Jinah ta haifi yan tagwaye kuma ta saka masu sunanmu, ni da mahaifinka. Yaran sun rayu, wannan wani ikon Allah ne dan hakan bai taba faruwa ba, idan irin haka ta faru yaran mutuwa suke. Wadannan yara suna tattare da wani karfin sihiri na aljanu, dan haka yanzu ba sai an jima ba rayuwar Jinah tana cikin hadari. Zasu bi kowacce irin hanya ganin sun mallaki waddan yara. Hindu ta dade da ganin wannan al'amari dake tattare da yaran shi yasa take son na mutu. Kar kayi bakin ciki dana, zan kasance kullum a cikin zuciyarka, ina yi maka ban kwana, ka kula min da 'yata Jinah da kuma jikokina. Mahaifiyarka mai kaunarka. Wasu zafafan hawaye ne suka zubo ma Fally lokacin da ya gama jin wasiyyar mahaifiyarshi, hannuwa yasa ya dafe zuciyarsa sakamakon wani zugi da take masa. Mikewa yayi ya sauko daga kan gadon sannan ya nufi mahaifinsa tare da fadawa jikinsa yana kuka kamar wani karamin yaro. Yana ji da ba dan taurin kansa ba da har yanzu mahaifiyarsa na raye. -Yanzu tunanin Jinah da ya'yanka zaka yi, ka daina kuka. Take kuma wani farin ciki ya lullubeshi jin abinda mahaifinsa ya fada, yanzu kenan shi uba ne. Ana yawan basu labarin idan aljani da mace mutum, ko kuma aljana da namiji mutum suka samu haihu tare, yaron ba za'a taba haifarsa da rai ba. Amma gashi cikin ikon Allah nasu yaran sun rayu. -Bamu da lokacin batawa, ya kamata muyi saurin tafiya kafin su farga da mutuwar mai gadin Jinah. Cewar Ayu mahaifin Fally. Goge hawaye Fally yayi tare da daukar wata jaka ya saka wasu kaya da zai bukata, suka dauki hanya shi da mahaifinsa. Ba suyi tafiyar wasu kilomitoci ba, aka harbo wani mashi ya ratsa cinyar mahaifin Fally da tayi sanadiyar faduwarsa kasa. -Baba! Fally ya kwala kara tare da durkusawa kusan mahaifin nasa. -Ka gudu! Suna nan! Cewar mahaifin nasa da ya ankare da an biyosu. -A'a baba a tare zamu je! -Guba ce, ba zan iya anfani da tsafina ba. Motsi Fally yaji, yana juyawa yaga mayakan aljanu sun kewayesu ta ko'ina. -Ka ceci kanka dana! Wasu kibiyoyin aljanun suka kara sakawo kafin Fally yayi saurin bacewa. Sai gashi ya bayyana a tsakiyar wani jeji, durkushewa yayi kasa tare da dafe kai, yana ji kamar yayi kuka, yayi kara ko kuma gurnani kamar zaki... Yanzu shi daya ya rage, shi daya, kuma dole ya kare matarsa da kuma 'ya'yansa... (.....) Jinah, Sarah, Dauda da kuma 'ya'yan Kimba ne zaune a tsakiyar gida, kowanne ya fada duniyar tunani. Duk wannan ta faru ne lokacin da Kimba ya furta shine ya yiwa Jinah fyade. -Wannan ba fa zai taba yiyuwa ba, ba shi bane. Tagwayen da ba'a dade da haifa ba, lokacin da ya kamata a samu cikin yaran, Kimba yana Nigeria. Sarah ce ke magana, kowannensu daga kai yayi yana kallonta, kamar tana maganar ne da niyyar kare Kimba, domin har yanzu kalaman mijin nata suna mata yawo a kwanya, sai dai ba yanda za'ayi ta gasgata hakan, abu ne marar yiyuwa ace Kimba ya yiwa Jinah fyade. -Ba abu ne mai yiyuwa ba ace babana ne. Cewar diyar Kimba. Jikin jinah yayi sanyi, ita kanta bata yarda shine ba, shi da ma baya cikin Nijar din, kuma bama tada hujjar cewar fyade aka mata. -To me yasa zai ce shine idan ba shi bane? Cewar Dauda. -Gashi yayi tafiyarsa ba tare da ya bamu hujja ba. Cewar dan Kimba. -Bama shi bane, na tabbata. Cewar Jinah. -Kenan ke fyade aka yi maki? Cewar diyar Kimba. -Nima ban sani ba! Jinah ta bata amsa. -Mu manta da wannan yanzu, idan ya dawo, shi zai yi mana bayanin komai. Cewar Sarah tare da juyawa ga diyan mijin nata. Baku fada mana sunanku ba? -Ni sunana Abdul. Cewar namijin, ita macen kin magana tayi. Ya cigaba. -Ita kuma Nafisa sunanta, amma muna ce mata Nafi zararra ko kuma kuce Nafi yar mahaukaciya. Dariya dukansu suka yi, banda Nafi dake ta hararar yayan nata, shi kuma yayi kamar bai gani ba. -Ina maku barka da zuwa gidan nan, kuma ina maku jajen rasuwar mahaifiyarku. Allah ya jikanta, yayi mata rahama. -Ameen. Fira suka cigaba da yi, kafin Jinah da Dauda su kebe zuwa daki. Da shigarsu daki ke da wuya Jinah ta fada jikin Dauda tare da fashewa da kuka. -Kayi hakuri dan Allah Dauda, na haifar da abubuwa da dama cikin danginku. Naji dadin ganinka ka warke. Ka yafe mani dan Allah, da cutar da kai da danginka da nayi. Mutanen nan suna da gaskiya, ni may... -Shiit, yi shuru ya isa haka... Shiru dakin yayi, babu abinda ke tashi sai sheshekar kukan Jinah. Dakatar da shurun Dauda yayi bayan wani dan lokaci. -Ko kin san lokacin ne nafi bukatarki, abinda yafi min ciwo, lokacin na dawo hayyacina ban ganki ba, da na tambaya aka ce mani kinyi tafiyarki, naji ciwon haka marar misaltuwa. Bai dace kiyi tafiyarki ba Jinah, haka nayi ta nemanki domin yayan Sarah bai so fada min inda kike ba. Yi tunani idan da ban ganki ba, halin da zan shiga. -Kayi hakuri, ka yafe mani. Jinah ta fada tana kara shigewa jikinsa. -Ban yi fushi dake ba, amma kiyi min alkwari ba zaki kara tafiya ki barni ba. Murmushi tayi, taji dadin ganinsa da tayi cikin koshin lafiya, ya warke sumul. -Ina sonki! Dauda ya fada yana kallon fuskar abar kaunarsa da ta kasa cewa komai, kallonsa kawai take itama. Kukan jariran Jinah da suka tashi bacci ne ya katse masu yanayin da suke ciki. -Ya Allah! Wai sune haka? Cewar Dauda cike da mamaki ya nufi inda jariran suke. -Wow masha Allah, kyawawa dasu! Kallon yaran yake yana murmushi, yana ji tamkar nashi. Wasa ya fara yi da yaran da har ya fara manta damuwar da ke tare dashi. Jinah ce ta katse masa nishadin da tambayar da tayi silar kawo damuwa a fuskarsa. -Dauda, me yasa ka nuna min kamar akwai aure a tsakaninmu? -Ban gane ba? -Akwai wata rana da muka je ni da Sarah wajen wani waza'i, nan naji malamin yana fadar, ba'a yin aure idan macen na da ciki, idan kuwa aka yi to auren bai halatta ba. Nasan ka sani, dan ina lura da yanda baka son tabani. Me yasa kaki fada min? Wani yawu Dauda ya hade kafin yace -Eh hakane, ina ganin wannan ita ce damar da zan samu ta kasancewa a kusa da ke. Kiyi hakuri da karyar da nayi maki. -Taimakona ne kayi, nagode sosai. Shiru ya dan biyo baya kafin Dauda yace -Jinah! -Na'am? -Zaki aureni, auren gaske a wannan karon? -Eh sosai ma! Wani kayataccen murmushi tayi tare da gyada masa kai. Ta amince zata aureshi, dan ya cancanci komai, kuma tana fata itama wata rana ta soshi. Sungumeta Dauda yayi yana ta juyin farin ciki da ita a cikin dakin. -Ba zaki san wane irin farin ciki yau nake ciki ba, ina cikin matukar farin cikin da yafi kalmar farin ciki. Nayi maki alkawarin ba zaki taba nadama ba. Gobe kenan za'a daura auren? -Gobe? Ta fada tana fiddo ido. -Eh mana gobe, ko yayi nisa? Fashewa da dariya Jinah tayi. -Dauda, ba fa guduwa zan yi ba, dan haka ka kwantar da hankalinka! Gobe yayi kusa! -To naji nan da kwana uku? Nan suka fara jayayya har dai ya yarda akan nan da sati biyu. Daukar Ayu Jinah tayi, shi kuma Dauda ya dauki Aya, suka fita dan sanar da Sarah labarin auren. -Sarah, aure zamu yi nan da sati biyu ni da Jinah! Dariya Dauda yaba Jinah ganin yanda yake maganar kamar yaro. -Ah madallah, nayi murna kwarai! Cewar Sarah tana tafa hannu. -Na tayaku murna! Cewar Abdul. -Nagode nawa (abokina) -Zan iya daukar yaron? -Eh, me zai hana? Cewar Dauda yana mai mika masa Aya dake hannunsa. -Woww! Mace ce ashe, kyakyawa masha Allah! Zo ki gani Nafi! Ko kallo bai samu ba daga yar uwar tashi, ya cigaba. -Wayyo dubi idanunta kamar Barbie, dubi lebenta duka kalan pink, har da ma dimples idan tayi dariya, masha Al... Duk yana yin hakan ne dan jawo hankalin yar uwar tashi dan ya santa da masifar son yara kanana. Ai kuwa yayi nasara, tashi tayi ta nufi wajen Jinah ta karbi Ayu dake hannunta. -Ai daman nasan ba zaki iya jurewa ba. Cewar Abdul yana mata dariyar keta. -Ni kyaleni! Nafi ta fada tana turo baki, dariya sauran sukayi. -Oh ni bari na tashi na hada mana abinda zamu ci, dan nasan kun fara jin yunwa. -Wallahi kuwa, dan cikina har ya fara yaren Chinese. Cewar Dauda. -Ai bai kai nawa ba. Cewar Abdul. -Ai kai dama cin tsiya ne da kai. Cewar Nafi, dariya dukansu suka yi. -Ba sai kin wahalar da kanki ba Sarah, zamu je ni da Jinah mu siyo abincin a waje. Cewar Dauda. -Eh bari sai muje mu siyo dan na rogo. Fatan dai kunsan meye haka? -Sosai ma, a cen akwai wata yar Nijar dake soyashi kusa damu. Cewar Abdul. -Ai na fada maku ba abinda ya sani sai ci. Nafisa ta fada. Kowa ya kwashe da dariya. Bayan wani dan lokaci Jinah da Dauda suka nufi kasuwa. (.....) Dare yayi sosai, Jinah ce daga ita sai yan tagwayenta kwance akan gado. Juyi take ta yi idanunta rufe amma ba bacci take ba. Tana jin kamar mutum a kusa da ita amma bata ganinsa. -Jinah, abar kaunata, kalleni nine Fally! Eh Fally ne, mutumin nan dake kusa da ita wanda ta kasa ganinsa. Fally ne a gabanta, farin ciki ne fal a ransa gashi ga rabin ransa, cike da zumudi ya kai hannunsa kan gashinta yana shafawa, ganin idonta a rufe hannun nasa yakai kan fuskarta yana shafawa, ita kuma Jinah ji take yi tamkar ana shafa mata wani narkakken karfen da aka sanya a wuta. Abun bai ishi Fally ba, duko kansa yayi yana sumbatar wuyanta, a hankali ta bude ido. Baki Fally ya wage kai kace gonar auduga. -Jinah abar kaunata! Ya fada, ita kuma dube dube ta fara kamar wadda hanya ta bacewa. Anan ya fahimci ba ganinsa take ba. Wani haushi ne yaji ya turnukeshi, sai dai bai ida gasgata abinda zuciyarsa ke fada masa ba, yanke sharawar ya bayyana mata kansa yayi. Tsalle daga kan gado Jinah tayi, tare da kwala wata gigitacciyar kara... Tsoro duk ya kamata, jikinta sai rawan mazari yake. -Jinah nine fa! Fally naki! -Dan Allah kar kayi min komai, kar ka cutar dani dan Allah! Dauda! Dauda! Ta shiga kwalawa Dauda kira. -Kinyi alkawarin fa ba zaki manta dani ba! -Dan Allah ka tafi, bana son ganinka! Jinah ta fada, da alama bata jin ma abinda yake fada. Kofar dakin ce ta bude da karfi, ba kowa bane face Dauda. Sai dai Fally tuni har ya bace, ko Jinah bata ganinsa. Ran Fally yayi matukar baci, ta yanda yake ji tamkar ya ciro zuciyarsa yayi jifa da ita nesa. Cikin awowin da basu wuce 48 ba, ya rasa uwa da uba, gashi kuma wadda dan ita komai ya faru wai ta kasa ganeshi. "Kawai zan kyaleta da sauran aljanun su cutar da ita ma, me yasa zan kare wadda tayi sanadin wargajewar rayuwata? A'a ba zan iya ba, taci amanata!!!!" --------------------------- Salam, miss u many, realy lol. Bon, ina fata zaku ji dadin wannan chapter. Kar kuyi tantamar fadin kowanne ra'ayi naku game da wannan chapter, haka idan ma kalamai sunyi maku karanci zaku iya bina da stickers marar iyaka. 😂 Merci de toujours vous retrouver même si je tarde a publier, je vous adore 💘 vous êtes les meilleurs. Sai mun hadu a wata chapter. 🤗 Kusha ruwa lafiya 🎈 @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 12 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp A wajen aljanu idan daya daga cikinsu ya fada soyayya da dan adam. To fa mawuyacin abu ne dan adam din nan ya manta da soyayyar dake tsakaninsa da aljanin, sai idan dai wankin kwalwa aka masa kuma hakan na faruwa ne ko daga cikin iyayen aljanin ko kuma shi kanshi aljanin wani yayi wa dan adam din wankin kwalwa ta yanda ba zai kara tuna wata soyayya da yayi da aljanin ba. Wani lokacin kuma soyayyar da dan adam din yake wa aljani idan ya samu wani masoyin da suke jinsi daya wato dan adam kuma har yaji yana kaunar wannan dan adam din to zai gama har da shaukin soyayyar da yake wa aljanin duk ya juyeta akan dan adam din, to hakan na faruwa a hankali zai fara manta soyayyar dake tsakaninsa da aljanin. Shi yasa Fally yayi tunanin babu yanda za'ayi iyayensa su yiwa Jinah wankin kwalwa, dan suna son Jinah kuma ba zasu so ta mantasu ba. Sai dai kuma hakan ce ta kasance, mahaifiyarsa tana son Jinah, saboda haka, bata son wani abu ya samu Jinah, bata son Jinah ta tuna dasu har tayi kokarin nemansu, idan da bata manta komai ba da tuni ta shiga nemansu kuma kafin ta nemosu tana iya fadawa hannun muyagun aljanun dake son cutar da ita, bare kuma yanzu da har tanada tagwayen da kowanne aljani yake da burin mallakarsu ba. Dan haka wankin kwalwa da mahaifiyar Fally tayi mata ba don komai bane face dan ta tseratar da ita. Ganin yanda Jinah take tadi da Dauda, suna yi suna kyalkyata dariya da irin kallon da suke yiwa junansu yasa Fally yake tunanin soyayyar da Jinah ke masa a yanzu ta koma kan Dauda, wato kenan Dauda ya maye gurbinsa. Tunani ya fara, yanzu duk wannan sadaukarwa da nayi a kanta! Sau da dama har sai yayi yunkurin tafiya ya barta in yaso aljanun su cutar da ita, amma sai ya kasa. Ga kuma 'ya'yansa dake hannunta, yana son yaran sosai domin da ya kalli yaran wani farin ciki ne ke ziyartar zuciyarsa. Suma kuma tagwayen suna ganin Fally amma sun kasa fahimtar waye shi, ba zasu gane matsayinsa ba har sai sunyi shekara daya da haihuwa kuma a kullum wannan ranar yake daukin jira. Kwanaki da yawa sun shude, Fally bai bar gidansu Sarah ba kuma bai bar ganin abin takaicin dake faruwa ba tsakanin matarsa Jinah da kuma wannan mutumin wato Dauda. Sai dai farin cikinsa a kullum babu yanda za'ayi wani abu ya shiga tsakanin Dauda da Jinah domin har yanzu matarsa ce. Jira kawai yake lokacin da tsautsayi zai dauki Dauda yace zai kusanci Jinah ya gane kurensa. Shima haka take bangaren Dauda, yana ji tamkar ya matso sauran ranakun da suke rage na aurensu, yau ace ga Jinah a dakinsa a matsayin matarsa. Kamar kowanne Marece tun ranar da yazo, Dauda ne da Jinah a zaune tsakiyar gida suna tadi. -Kwana biyu kawai ya rage ki zama matata... Dauda ya fada cikin yanayin farin ciki. Murmushi Jinah tayi. Shi kuma ya cigaba: -Matata! Oh har na tuna da wata waka, Sunanki mai dadin fadi, kin ratsa zuciya! Kowa yazo za ayi nadi kece Sarauniya.... Dakatawa yayi da wakar ganin Jinah ta kyalkyace da dariya. -Kushe miji fah ba kyau... Dauda ya fada yana tamke fuska, irin dagasken nan yake. -Eh koda yana waka da murya kamar gwangwani! Ta fada tana dariya. -Eh din! Dariya dukansu suka yi. Shuru na dan wani lokaci ya biyo baya, Jinah ta lura Dauda hankalinsa yayi wani gu, ya fada duniyar tunani. Hannunsa Jinah ta kama tareda kallonsa a natse cikin ido. -Har yanzu baka son fada min dalilin dake sanyaka cikin wannan dogon tunanin. Dan Allah ka fada min me yake damunka? Wani dogon numfashi Dauda yaja, wanda Jinah bata fahimci komai ba, domin shiga yanayin bakin ciki ba dabi'ar Dauda bace, mutumin da kullum cikin raha yake. -Me yasa dan Adam butulu ne? Me yasa soyayyarshi da dukiya ta wuce kima? Me yasa in dai akan kudi ne, soyayya, dangi, zumunci ba komai ba ne? Jinah da kinsan abinda ya faru bayan tafiyarki. Ya... Sauran kalaman tsaya masa suka yi a baki. Hannu yasa yana goge kwallan dake shirin zubo masa. -Kayi hakuri Dauda... Jinah ta fada cikin Sanyanyar murya. -Kinsan me yasa nake sonki, zuciyarki tsarkaka ce! Babu digon hassada ko keta a cikin idonki, fuskarki tana bayyana tsantsar gaskiya da mutuntawa. Imanina yana karuwa ta dalilinki, na kan ce koda munafukai da maciya amana ba zasu dakata da gurbata duniya ba, za'a samu mutanen kirki kamarki. Ya fada cikin murya mai nuna yakini a maganarsa, wanda kuma yasa Jinah ta yarda lallai akwai wani babban al'amari da ya faru dashi bayan tafiyarta. -Ka fada min abinda ya faru. Ta fada cikin raunanniyar murya. -Lok..loka..lokacin da na farka daga dogon suma, na samu labarin mahaifina ya rasu, anan, na tabbata bakin ciki yayi mana sallama. Yayinda dangi ke cikin jimami, Kawuna Mati, yayan mahaifina yazo, ba mutumin da na tsana kamarshi, tashi da mahaifina bata taba zuwa daya ba, shine kadai dan uwan mahaifina da ba a cikin dangi yake da zama ba. Kwana hudu da faruwar wannan masifa, kawu Mati yazo gida cike da zumudi da murmushi har kunne, ya nemi da dangi su hadu yana son magana damu. Duka muka hadu a tsakar gida, wasu takardu ya fiddo, wasu banzayen takardu wai na masana'antar mahaifinmu da kuma na gidanmu duka nashi ne. Bamu yarda da hakan ba, domin wannan ba zai taba yiyuwa ba, dattijawan garin aka kirawo da yake duk ya siyesu, har da kuma Kawunaina sai daya kawai da yace shi bai yarda ba haka yayi masa korar wulakanci shi da iyalinsa. Gashi manyan yayyena Idrisa da Isa basu duniyar, sauran kuma biyun yayyena sun tafi kasar waje gashi babu takardun dawowa a lokacin. Dayan yayan nawa kuma yi yayi kamar abun bai dameshi ba, ni kuma, nayi iya kokarina daga karshe ma korarmu yayi ni da Mahaifiyarmu da kuma kannena, inda Allah ya taimakemu dangin mahaifiyata sun karbemu hannu biyu. Na samu kuma labarin yace zai auri sauran mata biyun babana, idan basu yarda ba, zasu iya bar masa gida. Kuma kinsan mu anan, mata ba aiki suke ba, kenan ta yaya zasu iya ciyar da ya'yansu idan kuka bar gidan, kuma komawa wajen iyayensu a wannan lokacin abun kunya ne. Haka yasa biyun matan babana suka dawo matan kawuna, saboda ya kori mahaifiyata kuma Tanti Habi ta haukace. Sannan kuma ya sallami wasu kawunaina daga aikin masana'anta domin ya saka yan'yansa da kuma wadansu da suka taimaka masa wajen samun komai. Uwa daya uba daya yake da babana, amma bai ji ko digon imani ba wajen tarwatsa masa ahali. Na kudura a raina sai na yaki wannan zalunci da yayi mana, duk da mahaifiyata tace na manta komai, ba zan iya ba.. Jinah naga tsantsar rashin imani na dan adam... Shuru yayi, ita kanta bata san me zata ce ba jin kalamansa, ta razana da jin labarin kuma taji ba dadi. Rungumesa tayi dan tunanin shi daya abinda taji zata iya, amma basu dau lokaci ba. Shuru dukansu suka yi, kafin wata murya daga bayansu ta katse shurun. -Ba laifin kawunka bane, shi ne! _Yana nuna yatsa zuwa sama._ Ba shine ke da ikon komai ba? Me yasa ya bar wannan mutumin ya cika burinsa, kamar kuma yanda ya dauke min mahaifiya? Abdul ne ke fadar haka lokacin da yaji labarin Dauda. Zaunawa kusa dasu yayi. -Muna sallah, muna azumi, muna yin duk abinda ya wajaba a kanmu, muna kuma barin duk abinda aka hanemu! Toh me yasa kullum mune cikin masifa? Irin kawunka ya kamata su shiga irin wannan halin ba mu ba! -Abdul. _Cewar Jinah kafin ta cigaba cikin tausashiyar murya._ Daga Allah muke kuma gareshi zamu koma. -Amma ya kamata ya barmin ita, naso ace har na kai matsayin da zan sanyata cikin farin ciki, na bata duk wani jin dadi na duniya, na mayar da ita tamkar sarauniya, kar ta rasa komai na rayuwa kuma ta dinga alfahari dani. -Akwai lokacin da ina cikin damuwa sosai, wani ya taba fadamin, idan bakin ciki ya bubbuga mana kofa, ko ya adadinsa yake, mu kasance masu godiya ga Allah, wannan ba wani abu bane face jarabawa domin jarraba imaninmu. Kuma a lokacin da muka koma gareshi zaka ga ya saka mana da mafificin alkhairi. Komai ya samemu na dadi ko akasinsa dole mu kasance masu godiya ga Allah. Kuma mutumin da ya fada min haka ba kowa bane kai ne Dauda, to kenan kai ba zaka yi amfani da nasihar da kayi min ba? Kai kuma Abdul, uwa bata bukatar zinare, kudi ko lu'ulu'u domin tayi alfahari da danta, yanzu da bata duniya bata bukatar komai illa addu'a. Dukansu biyun jikinsu yayi sanyi da jin kalaman Jinah. Haka suka cigaba da hira da tayi sanadin gusar da duk wata damuwa tasu, har sai da dare ya tsala sannan kowa ya nufi makwancinsa. Jinah kasa bacci tayi, tunanin abinda ya faru jiya take, ganin wannan mutumin ba karamin tsoratata yayi ba, ta kasa fahimtar komai game da lamarin, yanke sharawar daukar maganar Dauda tayi kawai ba komai bane face mafarki. Haka tayi ta tunani har bacci barawo yazo yayi gaba da ita. -Babu abinda za'a yi, kawai ina son a daura auren, to wai ma wa zan gayyata, ba wanda na sani kuma la'akari da abinda ya faru kasan babu wani danginka da zai tako kafa wai da sunan zuwa wajen biki. Jinah ke fadawa Dauda ana gobe daurin aure. -Eh, na samu labari duk abinda suka yi maki, kuma har yanzu Mahaifiyata tayi imani da wannan karairayin amma idan muka yi aure, zamu je mu ganta kuma zan canza mata wannan tunanin. Kuma dan Allah kiyi hakuri akan abinda suka yi maki, ki yafe min na rashin kasancewata a wajen domin kareki. -Me zaka yi kenan? Ai ni naji dadin rashin kasancewarka a gurin, domin ba zan so a dalilina ka samu matsala da mahaifiyarka ba. -Toh yanzu manta da wannan, ya riga ya wuce, yanzu ne da kuma gobe a gabanmu. Ya karashe maganar da murmushi a fuskarsa. Ita kuma Jinah fargaba ce duk tabi ta dameta, domin tana ji a jikinta wannan auren ba karamin kuskure bane yinshi. Da sauri ta dawo daga tunanin da take jin daya daga cikin tagwaye ya tsala wani uban kuka, wani lugude zuciyarta tayi kamar zata fito daga kirjinta, tsoro duk ya mamayeta. Domin babu daya daga cikin yaran da ya taba yin irin wannan kukan. Da gudunta ta nufi gurin yaran da ta bari cikin daki tareda Nafisa, Dauda na biye da ita a baya. Tarar da Nafisa suka yi itama na kuka. -Me ya faru? Murya na rawa Jinah ta fada tare da karasawa ta dauki danta da yaki daina kuka. -Na..na..na fita ne yanzu.. naje..debo ruwan sha shine da naji kuka na rugo... shine na tarar da Ayu na kuka...ita..ita kuma Aya ban ganta ba. Jinah kalmar karshe kawai ta iya rikewa, sai yanzu ta lura da babu Aya. -Me? _Ta fada da karaji._ Ina 'yata? -Ku kwantar da hankalinku duka, bazata yi nisa ba. Ke Jinah lallabi Ayu ni zan fita waje ko zan ganta. Jinah tayi tayi amma Ayu yaki yin shuru, kokowa ma yake yana son uwar ta saukeshi. Abun fa kara ta'azzara yayi lokacin Dauda ya dawo ba tare da Aya ba. Zuciyar Jinah bugawa take da sauri ta yanda tayi tunanin ko fasa kirjinta zata yi ta fito. (.....) A waje kuwa, wani masifaffen fada ya turnuke. Fally ji yayi ya fara gajiya, ba zan bari ya tafi da 'yata ba, shine abinda yake ta maimatawa. A takaice dai, aljanun sun gano inda suke, shine daya daga cikin aljanun yake so ko ta yaya ya dauke Aya, kuma yayi nasarar dauketa har ma yayi nisa da gida da ita. Sedai Fally ya tareshi, sai gwabza fada suke tamkar wasu mayunwatan zakuna. Bayan wani dan lokaci, Fally yayi nasara akan aljanin da karfinsa ya kare da kyar ya iya guduwa yana fadar : -Zan dawo, kuma bani daya ba, ka san da wannan! A wata bishiya Fally ya zauna yana maida numfashi, Aya kusa dashi, tana masa wani irin kallo. Tabbas dole ya sake daura damarar kare ya'yansa daga waddanan miyagu. Da wannan tunanin ya dauki Aya ya kaita har kofar gida kuma daidai da fitowar Sarah da Abdul cike da mamaki suka ga Aya a waje ita daya. Sarah ta dauketa suka koma cikin gida. Suna shiga Jinah tazo da gudunta, bata tsaya amsa tambayar da Sarah da Abdul ke yi mata ba kan ya akayi Aya ta fita waje ba ta amshe yarta tareda kankameta. Kuma a take Ayu ya daina kukan da yake yi. -Wai mun gode Allah, _Cewar Dauda tareda ajiyar zuciya._ Shikenan daina kukan tunda an ganta. Da Nafisa yake da ke ta rizgar kuka tana tunanin laifinta ne. Yayanta ya matso kusa da ita tare da rungumeta yana lallashinta. Shi da Sarah basa bukatar wani dogon bayani akan me yakai Aya a waje, komai ya wuce tunda dai gashi an ganta. Washe gari, ranar daurin aure, ba tare da wani shagali ba aka daura aure a masallaci kamar yanda Jinah ta bukata. Duk da ba wani jagali ba aka yi amma kowa gidan cikin farin ciki yake. A marecen ranar ma basu yi bacci ba. Suna ta hirar duniya. Abdul da Nafi har sun saba da zaman gidan, duk da har yanzu zaman jiran mahaifinsu suke domin su koma cen asalin gidansu... -Sarah, wata alfarma nake son ki yimin. Cewar Dauda cikin yanayin dagaske yake. Shuru kowa yayi yana sauraron me zai ce. -Ina sauraronka Dauda. -Kamar yadda kuka sani, yau Jinah ta zama matata, tawa, toh shine... -Ahan muna sauraronka. -Shine... Nake son ki dauki yaran, ni kuma sai na dauki matata. Dariya Abdul yayi, su kuma matan rike baki suka yi suna mamakin Dauda... -Bakada dama Dauda, toh shikenan, dare yayi yanzu ni zan je in kwanta. Sai da safenku. -Toh yara kuma ku tashi dare yayi aje a kwanta. Dauda ke fadawa Abdul da Nafi yana dariya. Seda suka dan taba raha kafin su je su kwanta. Ya rage sai amarya da Ango. -Kinsan wani abu Jinah, har yanzu na kasa gasgata yau kece a matsayin matata, komai ina jinsa kamar a mafarki. Yanzu da nake a tare dake sai nake ji kamar babu wani abu na bakin ciki da ya faru dani a baya. Kin baiwa rayuwata ma'ana Jinah. Nayi maki alkawarin har indai ina raye, zaki kasance cikin farin ciki. Murmushi Jinah, tayi sosai kalamansa suka tabata. -Kayi min abinda ba zan taba mantawa ba Dauda, kayi abinda ba kowanne namiji zai iya yi ba. Ba zan boye maka ba, a duk lokacin da ka furta min kalmar "Ina sonki" na kanji ba zan iya baka amsa ba, amma kuma duk da haka bani nadamar aurenka, ina fatan wata rana na soka, son da yafi kalmar so. Hannu Dauda ya kai kan fuskarta ya janye gashin kanta da ya zubo a fuskarta zuwa bayan kunnenta sannan ya kai mata lafiyayyen kiss a kumatu. Mikewa yayi tsaye sannan ya mika mata hannu ta kama ta tashi tsaye. A haka har suka je daki. Ba tare da bata lokaci ba, ya fara kwabe mata kaya, zafin da a duk lokacin da ya rabeta yake ji, yanzun ma shi yake ji, sedai wannan karon zafin yafi na ko yaushe, hakan bai dakatar dashi ba domin shima sha'awar da yake tattare da ita mai karfi ce. karfi biyu ya hadu a lokaci daya, sai duka suka bayar da masifaffen zafin da yafi wuta. Da taimakon dan hasken dakin da kuma na farin wata, Dauda ke karewa kyakyawar surar Jinah kallo, zafin jikinsa karuwa yayi, idanunsa suka kafe, ya fadi gefenta matacce ko sumamme...! Da alama shi Dauda aljanin bai bari yaje ko'ina ba lol. 😂 ------------------------------ Salam, fatan kuna nan lafiya? Kuma ina fata zaku ji dadin wannan chapter kuma ta fanshe fushin da kuke yi dani na rashin posting da wuri? 😊 Ina jiran jin ra'ayinku 🤓 Mu hadu a wata chapter bayan sallah idan Allah ya kaimu. 🤗 ©El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 13 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp -'Ya'ya nawa kike son kara samu? Dauda ya tambayeta. -Ban sani ba, ta fada tare da daga kafada. Ko nawa na samu. Hudu, biyar, shidda... Duk ina so. -Amsa mai kyau. To kuwa yau zaki samu! -Marar kunya! Jinah ta fada tana boye fuskarta alamar kunya. -Me? Toh ni me nace? Ya fada da yanayin shi ba ruwansa. -Zamu kasance cikin farin ciki a tare, zo ki rungume mijinki abar kaunata. Ya fada yana bude mata hannuwansa. Bata jira komai, ta fada jikinsa kamar wata karamar yarinya. -Ina tunanin fa na fara sonka. Ta fada kamar daga sama. -Jinah! Zaki iya maimatawa dan Allah? -Ina sonka Dauda. -Wow zuciyata cike da guguwar farin ciki, naji dadin jin haka. Rufe ido Jinah tayi cike da jin dadin rungumar mijinta, sedai dan lokaci kadan komai ya tsaya, bude ido tayi ta ganta ita kadai. -Dauda? Ina kake? Tafiya take tana kiran sunan Dauda ba tare da tasan inda ta nufa ba. Jiri ta fara ji yana daukanta kafin ta fadi. Lokacin da ta bude ido, a wannan karon, cikin dakinta a bisa gadonta ta tsinci kanta. Dauda kwance a gefe. Tunawa tayi lokaci na karshe da take cikin dakin, mijinta ya fadi gefe, tayi tayi ta tasheshi amma bai tashi ba, ganin haka yasa ta juya gefe dayan gadon ta kwanta tareda rufe ido. Wanne al'amari ke shirin faruwa, daman maganar da tayi da Dauda, mafarki ne ko me? Kara rufe ido tayi, Dauda ta gani, amma wannan karon nesa da ita yake yana mata murmushi. Da gudunta ta nufeshi, amma ta kasa cimmasa, kara gudu take don ganin taje gunsa amma kuma kamar kara mata nisa yake, tsayawa tayi tana sauke ajiyar zuciya, suma ta kuma yi a karo na biyu tana farkawa ta ganta bisa gadonta, Dauda kwance a gefe. Wannan karon saukowa tayi daga kan gadon daidai ladani ya fara kiran sallah. Fitowa tayi waje ta tarar da Sarah da Abdul da kuma Nafi suna alwala domin yin sallar asuba, itama alwalar tayi. -Ina Dauda? Sarah ta tambayeta. -Yana zuwa. Jinah ta bata amsa a takaice. Shimfida babbar tabarma Sarah tayi, kowannensu yayi raka'a biyu nafila kafin Abdul yayi limanci suyi farillah. Suna idawa dukansu shiga tambayar Jinah dalilin da yasa mijinta bai fito yayi sallah a tare dasu ba. Wannan karon shuru tayi, bata amsa ba, shurun da ya dau hankalin su Sarah. Lokacin da wani abu ya zamar mamu kamar almara, lokacin da wani abu ya girgiza mu sosai, lokacin da muke tunanin wani abu na cutar damu, cutarwa mai tsanani, mun fi son muyi kokarin manta abun, muyi kamar abun bai taba faruwa ba. Sedai hakan ba wai zai sa mu manta da abun baki daya ba, a kullum yana dunkule a cikin zuciyarmu. Lokacin da Jinah taga Sarah ta fito daga dakinta baki toshe da hannu, nan ta kara gasgata mutuwar Dauda, hawaye ne suka fara ambaliya a fuskarta kafin ta fashe da kuka mai ban tausayi. Abdul da Nafisa tambayar Sarah abinda ke faruwa suke domin su har yanzu sun kasa fahimtar komai, ganin Sarah batada niyyar basu amsa suma suka kutsa kai cikin dakin Jinah, anan suka samu amsar tambayoyinsu. Abdul kasa tsayuwa yayi, yayi dishen a kasa. Ita kuma Nafi da saurin kuka, ta fara kamar an aikota. Kwanakin da suka yi da Dauda ba masu yawa bane, amma dattakonsa da kuma barkwancinsa yasa yake da shiga rai, suke jin tamkar shekaru masu yawa suka yi da saninsa. Dukansu cikin tashin hankali suke, ganin bai fi awanni masu yawa ba da suke tare dashi anata wasa da dariya. Yaya hakan zata kasance ace Dauda ya mutu? Tambayar da suke ta yiwa kansu kenan. Sedai wannan ba wani abun mamaki bane, domin mutuwa bata bukatar shiri, tana zuwa ne ba tare da sallama ba, lokacin da taso, inda taso a kuma yanda taso. Sedai wannan mutuwar ta Dauda, ba ta ajali ba ce, a yanzu Jinah ta tabbatar akwai wani babban al'amari dake tattare da ita, ta tabbata Dauda ya mutu ne ta sanadinta. Bayan Idrisa, Isa yanzu kuma Dauda, yanzu kam ta gama tabbatar da laifinta a ciki. "Dauda yayi min halacci a rayuwa, ni kuma me nayi, na kasheshi." Ta fada a hankali tana cigaba da kuka. Nan fah ta rantse kan ba zata kara barin wani namiji ya rabeta ba, bare kuma ya kusanceta. -Jinah! Firgigit tayi ta dawo hayyacinta jin Sarah ta kira sunanta. Tsabar dogon tunanin da ta shiga, bata san lokacin da har Sarah ta shiga daki ta canja kaya ba. -Zan je na sanar da yan uwansa, dan Allah ki daina kukan nan, ba yanda muka iya lokacinsa ne yayi. Sarah tace mata cikin Sanyanyar murya da tausayawa. -Ba zaki gane ba Sarah, nice..lai.. laifina ne. Jinah ta fada tana sarkewa saboda kuka. -Me kike cewa ne? Daina wannan shashancin, tashi kije ki duba ya'yanki, kila ma sun tashi daga bacci, ni na tafi. Kallon Sarah da ta fara nisa take cike da tausayinta, tasan ba abu bane mai sauki kai irin wannan labarin ga dangin Dauda. Ji tayi an dafata, daga kai tayi taga Nafisa ce. -Kiyi hakuri. Cewar Nafisa. Addu'a kawai zamu yi masa, Allah yasa aljanna ce makomarsa. Rungumeta Jinah tayi, bayan wani dan lokaci suka saki juna, Jinah ta nufi daki. Tarar da yan tagwaye tayi, cike da mamaki zaune kan gado. Yanzu har sun saba idan suka tashi basu yin wata hayaniya. Kamar sunji halin da mahaifiyarsu take ciki, zaunawa tayi itama kan gadon, rarrafowa suka yi tareda rungumeta kamar zasu koma cikinta, suka yi kamar ba zasu saketa ba. Da mamaki, Jinah taji damuwarta na raguwa. Haka suka kasance kusan mintuna 30 kafin Abdul da Nafi su kwankwasa kofa a hankali, sai a lokacin tagwayen suka saketa. -Ku shigo! Ta fada. Shigowa suka yi, sedai babu wanda yayi magana. Fita Nafisa tayi da yaran sannan ta maidosu bayan tayi masu wanka tare da sanya masu kaya. Dan uwanta da Jinah suna zaune kan gado kowane yayi shuru, ya zurfafa cikin tunani. Sai zuwan Sarah sannan suka samu damar yin magana. -Kinyi saurin dawowa, Jinah ta fara fada. -Eh na samu dan acaba ne. -Ya suka ji labarin mutuwar? Wayyo Allah nasan mahaifiyarsa zata shiga cikin tashin hankalin jin labarin mutuwar danta mafi soyuwa a gareta. Yana yawan bani labarin irin son da mahaifiyarsa take masa da kuma irin shirmen da yake yi mata, duk da ya girma bai bar kwana a dakinta ba har sai da muka yi aure, ya fada min shine abokin hirarta da kuma na rakiyarta idan zata je wani kauyen, mahaifiyarsa ita ce komai garesa... Jinah ta fada murmushi da kuma ambaliyar hawaye a fuskarta. -Eh, lokacin da taji labarin, halin da ta shiga ya tabani sosai, kasa jure kallonta nayi. Hankalin Jinah kara tashi, ta fashe da kuka tareda tashi da gudu zuwa tsakar gida tana kuka, hanyar dakinta ta nufa da niyyar zuwa ta tashe da Dauda, sai kuma ta tsaya cak sakamakon tunawa da tayi cewa idan mutum ya mutu, ya tafi kenan baya dawowa. Zaunawa tayi kan wani benci ta cigaba da rera kukanta. -Dan Allah Jinah ki dakata da kukan nan, kar ki jawa kanki wani ciwo, kukan da kike ba abinda zai anfanar. Cewar Abdul cikin sigar lallashi. Tashi tayi ta nufi hanyar fita daga gidan, tana bude murfin kofar kuma sai ta tsaya. -Ina zaki je? Abdul ne ke tambayarta. Bata bashi amsa ba ta juya da niyyar fita. -Gata nan! gata nan! ita ce mayya mai cin kurwar maza. Kafin ta fahimci meke faruwa, ta jita sheme a kasa, lafiyayyun mari biyu suka biyo baya, sannan aka rufeta da duka da itace. Cikin tashin hankalin ne ta fahimci wasu daga cikin yan uwan Dauda da kuma Auntynshi cikin masu dukanta. Bata tsaya tantance sauran matan ba, ta boye fuskarta kar suyi mata lahani. Da gudu Abdul, Sarah da kuma Nafisa suka zo domin kawo mata dauki. Sedai matan sunada yawa. Shi Abdul, nasarar kwace itacen hannun matan yayi, su kuwa basu hakura ba suka koma dukanta da hannuwa. -Ku kyalesu, ku kyalesu su kasheni, ni ce, laifina ne, ni na kasheshi. Jinah take ta fada da shakakkiyar muryarta alhali kuwa azaba take ta ci. Jinah bata ga laifin matan ba, ita tana ganin ta cancanci wannan hukuncin, da son samu ne su kasheta, domin ita ce silar mutuwar Dauda. Matan taji sun daina dukanta sakamakon suma da suka ji ana dukansu da itace, har da karin yakushi da cizo, alhali su basa ganin mai aikin. -Wayyoh Allah, mayya ce da gaske! Gashi ta fara cin naman jikinmu alhali kwance take kasa. -Wayyoh dan Allah kiyi mana rai! -Bayan kin kashe yan uwanmu, garemu zaki dawo... Ihu suke suna sambatu tsabar azabar da suke ji, ganin ba sarki sai Allah kowaccensu ta ranci na kare su kuwa su Sarah suka yo kan Jinah tareda taimaka mata zuwa dakinta. Sam matan basu ji tausayinta ba domin ta bugu sosai. Kuka kawai Sarah ke yi tun lokacin da matan suka fara dukan Jinah. -Kamata yayi mu kaita asibiti, tsinannun mata! Idan da ba mata bane, na rantse sai sun gane kurensu. Wannan ai dabbanci ne! Ran Abdul ya baci sosai ganin aika-aikar da matan suka yiwa Jinah. -Gaskiya wannan ba mutane bane, wannan rashin imanin har ina??? Nafisa ta fada, cike da tausayawa Jinah. -Zan je na nemo amalanke domin kaita asibiti. Tagwaye sai kuka suke, farko dai suna kukan halin da mahaifiyarsu ke ciki sannan suna ganin hukuncin da suka yiwa matan bai isa ba. Eh sune wanda suka hukunta matan ta hanyar yakushi da cizo da kuma taimakon mahaifinsu da yayi ta dukan matan da itace. Fally yayi takaicin rashin zuwansa da wuri, gashi duk sun illata masa Jinah. lokacin da yaji mutuwar Dauda, ji yayi kamar yayi ta tikar rawa har sai ya gaji duk da hakan keta ce, soyayyarsa ga Jinah takai matsayin da babu ruwansa da komai zai faru. Sedai Farin cikinsa gushewa yayi lokacin da ya tarar da matan nan sunan dukan abar kaunarsa da kuma irin wahalar da take sha. Hakane, idan muna yiwa mutum so na gaskiya, ba zamu iya kasancewa cikin farin ciki ba alhali shi yana cikin bakin ciki. Kasa jurewa Fally yayi ganin Jinah har ta fara kukan azabar da matan ke gana mata, cikin jeji ya shiga ya karyo wani lafiyayyen reshen wata bishiya, ya dawo yayi ta dukan matan dake dukar masa mata. Lokacin da Abdul ya tafi neman amalanke, Fally ya shigo dakin ba wanda ke ganinsa sai yan tagwaye, da karfin siddabarunsa ya warkar da duk ciwon dake jikin Jinah. -Yauwa ku taimaka ku fiddota ga amalanken nan na samo. Cewar Abdul da ya shigo a hargitse cikin dakin. Sarah, dake zaune a bakin gado, ta dora goshinta jikin gadon, hannunta cikin na Jinah, tana kuka a hankali, ta dago da sauri tare da mikewa. Nafisa dake zaune kan tabarma ta mike itama. Nufo Jinah suka yi da niyyar dagata, turjewa suka yi, suna kallon kallo. Sarah ce tayi karfin halin duduba jikin Jinah, hannu, kafafuwa, gadon bayanta amma babu ko alamar ciwo. Jinah bata ma san ana yi ba, wani nauyayyen bacci take abunta. Hannu Abdul ya kai kan hancin Jinah domin tabbatar ko dai mutuwa ce tayi shi yasa raunukan suka bace, sedai Jinah da ranta cikin koshin lafiya. -Assalamu alaikum! Suka ji ana kwada sallama a waje, fita Sarah tayi ta tarar da wasu maza, ta gane wasu daga ciki yan uwan Dauda ne, sun zo daukan gawar Dauda ne. Sarah ta nuna masu suka dauka suka tafi. -Wannan ba mai yiyuwa ba! Cewar Abdul. -Ko dai mafarki muke? Cewar Nafisa. -Mu fita mu barta tayi bacci. Cewar Sarah. (....) -A ina zamu samu bayanin abinda muka gani? Nafisa ta tambayi dan uwanta lokacin da Sarah ta tafi kasuwa, daga su sai yan tagwaye. -Ni kaina ban sani ba, domin komai ina ganinsa ne kamar almara. -Kuma ka duba matan nan da aka yita duka alhali ba'a ganin mai dukan nasu. To ko dai da gaske Jinah... -A'a wannan ma ba gaskiya bane, kawai dai akwai boyayyen al'amarin dake faruwa. Haka suka zauna cikin wannan tunani har Sarah ta dawo daga kasuwa. shiga tayi kitchen ta gyara abincin da ta siyo kasuwa domin tashin hankalin da take ciki bata ji zata iya dora girki ba, Shi ma domin su Abdul ta siyo. Haka suka zauna gidan shuru kowa cikin taraddadin abinda ya faru har zuwa lokacin da ihun Jinah ya dawo da su hayyacinsu. -Ina suke? Sarah suna ina? Jinah ta fada lokacin da Sarah ta kunno kai dakin, Abdul da yar uwarshi a bayanta kowanne rike da yaro a hannu. -Me kike cewa ne Jinah? -Raunukana, radadin da nake ji, me yasa bana jin komai yanzu? Bai dace hakan ya kasance ba. -Kwantar da hankalinki Jinah! -A'a a'a, na cancanci wannan ciwon, me yasa duka suka bace? Ina suka yi ne? Duk ta hargitse, ta fara fita hayyacinta, ta zama abar tausayi. Kara takurewa tayi cen karshen gadon tareda hade kai da gwiwa sannan ta hana kowa ya kusanto inda take, hatta yaranta dake ta kuka taki kulasu. Sarah ta rasa me zata yi, fita tayi daga dakin ta nufi kitchen ta zauna kan kujera ta shiga rera kuka mai ciwo. Duk wadannan abubuwa dake faruwa sun zo sun cunkushe mata, ga kuma halin da Jinah take ciki, rashin sanin abinda zata yi ne ya sata kuka. Ba ita ta haifeta ba, amma tana jinta tamkar mahaifiyarta, kuma cilas ne idan Da ya shiga mawuyacin hali itama uwar ta tsinci kanta. Hakama Abdul da Nafi suna cikin firgici sosai. A cen tsakiyar kwakwalansu neman duk wani abu da zai warware masu kullin dake cikin wannan al'amari suke. Abinda basu sani ba shine basu ga komai ba a kan tashin hankalin da ke gaba. ============================= Salam, fatan kowa yayi sallah lafiya? Allah ya nuna mana ta wata shekarar da ran da lafiya. Ameen Allez à bientôt pour la suite. 😍 ©El_Ashtar Oooh na manta, ku dinga hakuri da kuskuren typing, ni kaina ina ganinsu duk lokacin da nake sake karantawa.... 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 14 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Kwanaki da yawa sun shude da mutuwar Dauda, sai dai babu wani sauyi da ya samu, komai yana nan kamar a baya. Ba mai yiyuwa bane, me yasa har yanzu ta kasa ganina? Me yasa ta kasa tuna ni? Idan saboda ta fada soyayya da Dauda ne yasa ta manta ni, ai yanzu kuma baya duniyar, ya kamata ta tuna ni tunda yanzu baya nan. Maganar da kullum Fally yake maimaitawa kenan. Alhali, a cen tsakiyar kwalwarsa yasan amsar duk wannan tambayoyin, kawai dai ya kasa yarda ne. Yanzu ya tabbatar Jinah ba wai ta mantashi bane domin tana soyayya da Dauda, mahaifiyarsa ce, tayi sanadin da abar kaunarsa ta manta da duk wata rayuwa da tayi dasu. Yana jin takaicin abun sosai, domin shi bai ga wata hujja da zata saka mahaifiyarsa yin hakan ba, sanin yadda duka biyun suke son junansu, ga kuma duk sadaukarwar da yayi domin kawai kasancewa da Jinah. Wani barin na zuciyarshi yana ganin kawai Jinah amanarsa taci, ba sonshi dama take ba. -Kai ne Babanmu ko? kananun muryaoyin suka dawo da Fally daga dogon tunanin da yake. Murmushi yayi har kunne ganin yan tagwaye ne da tuni suka fara magana. -Eh! Na jima ina jiran wannan ranar da zaku fara magana, ko ba komai kadaicina zai ragu. -Idan kai babanmu ne, me yasa mama bata ganinka? Kuma bata taba maganarka ba? Aya ce tayi masa wannan tambayar, walwalar dake fuskar baban nasu ta gushe. -Labari ne mai tsawo! Fally ya fada. Matsowa Ayu yayi wajensa tare da dora hannunsa akan goshinsa. -A'a kar kayi haka! Aya ta fada tare da janye hannun dan uwan nata da sauri. -Me? Meye yake son yi? Fally ya tambayeta da mamaki a fuskarsa. -Duba rayuwarka ta baya, sanin duk wani labari na rayuwarka da kace mana mai tsawo ne. -Da gaske, zaku iya yin hakan? -Muna iya yin fiye da haka ma. Ayu ya bashi amsa. -Tabbas, ansha bamu labarin abubuwan da irinku wanda rabinsu aljanu rabinsu mutane ke yi, amma ban taba samun nasarar ganinsu ba. Sai gashi yau gaku kuma a matsayin 'ya'yana. Dole aljanu su shiga farautarku, amma karku damu zan kasance a kullum domin kareku. -Mune zamu ce maka kar ka damu, ba zasu iya yi mana komai ba. Cewar Ayu. Murmushi Fally yayi, tunawa da yayi da kuruciyarsa, kamannin Ayu da komai kamar shine yayi kaki ya zubar. -A'a Dana, yawan fariya, yana kashe yarda. Zan so ku gwada min duk wani karfin da kuke da. -A gaskiya, bamu san iya adadin karfin dake garemu ba, abubuwan suna zuwa ne lokaci lokaci. -Oh na gane, Aya fada min me yasa kika hana dan uwanki yasan labarina? -Saboda ina so ne kai ka bamu labarin da kanka! Babu ladabi idan muka bincika labarinka ba tare da izininka ba. -Dakyau 'yata haka ake so, Ayu ya kamata ka dinga koyi da yar uwarka. -Eh, ai ita a komai sai ta zake. Dariya sosai Fally yayi kafin yace: -Shikenan bari na baku labarina, Ni da mamanku tare muka taso tun muna kanana, tun lokacin na fahimci ba daya muke ba, ta banbanta da duk wanda da ke yankin mu. Da farko na fara magana, ita kuma a'a. Na fara tafiya, amma ita a'a, ina iya yin abubuwa da dama, da aljanu ke yi, amma ita a'a. Idan muka ga wani abu na cutarwa, ni zan iya bacewa amma banda mamanku, anan na fahimci nine ya kamata na kula da ita, na kareta daga duk wani da zai yi kokarin cutar da ita. A koda yaushe muna tare, zan iya fada da kowa saboda ita. Haka lokuta na shudewa, ina cigaba da zama mai bata kariya da kuma jin ina zama ita, ita ma tana zama ni. Wata rana, ba zan wuce shekara 13 ba, muka je wajen wani wasan dambe da ake shiryawa a yankin mu, akwai wani matashin aljani da ya dan fimu shekaru, ba a yankinmu ba yake, dalili kuwa ban taba ganinsa ba ko jin labarinsa ganin yanda yake ta dambe yana zubar da maza a kasa, domin da a yankin mu yake to da tuni labarinsa ya tsayawa kowa a baki. Ana cikin wasa na hangeshi ya nufi inda Jinah take zaune, zaunawa yayi kusa da ita suka fara fira. Babu mai iya yin haka a yankin mu. Duka sun san Jinah mutum ce, shi yasa babu mai rabenta idan ba cutar da ita ba zai yi. Dariya Jinah ta fashe da ita da alamu firar da suke tana mata dadi, tuni wani haushi ya turnukeni na nufi inda suke, finciko Jinah nayi muka nufi hanyar gida. Zai fi mun a ce shekara dari za'a yi ana dukana ba tare da tsayawa ba, da ganin Jinah tare da wani kuma har alakarsu ta wuce abota. Anan na fara fahimtar ina sonta sosai, ta yanda komai zan iya yi saboda ita. Haka komai ya cigaba da tafiyar mana cikin jin dadi, domin itama tana sona da dukkan zuciyarta, ina da yakini akan cewa mamanku ta gari ce, batada keta ga kowa, zuciyar zinare ce da ita, ita tilon fure ce a tsakiyar sahara, ita... -Mun gane baba, ka cigaba. Cewar Ayu yana murmushin yanda baban nasu ya fara mayar da labarin tamkar waka. -Iyayen mu basa gajiya da nuna mana kuskuren da muke son tabkawa, abu ne da ba zai yiwu ba kuma anyi hani da hakan. Sai dai mu bamu taba baiwa maganarsu muhimmanci ba. Komai yana tafiyar mana daidai ni da mamanku har ranar da muka shirya zuwa mu daurawa kanmu aure, wanda shine sanadin wargajewar duk wani farin ciki nawa, shine yayi sanadin abar kaunata ta manta dani, kallon soyayya ya kare tsakaninmu. Ta daina ganina indai ba ni na nuna mata kaina ba, kuma idan nayi haka, tsorata take. Sam ta kasa tunani. -Amma me yasa, ina nufin me ya faru ta kasa tunawa da kai? Aya ta tambaya. -Ni kaina ban sani ba, bani da tabbacin... yauwa ya isa haka yanzu ku je kuyi wasa, wata rana ma cigaba. Ganin baban nasu babu abinda zai kara fada masu suka juya zuwa gurin wasansu. Murmushi Fally yayi domin yana tunanin wannan ita ce hanyar da zai iya dawo da memorin Jinah. (.....) Tun ranar da raunukan Jinah suka bace, bata kara samun kwanciyar hankali ba, duk ta wani hargitse kamar mahaukaciya, kullum tana rakube cikin daki, idan ka ganta waje to ban daki zata shiga. Abinda yafi daga mata hankali ma, yan tagwayenta da suka fara magana, magana da kalmomi daki daki kamar manyan mutane... Cewa take ko dai ta fara cin kai ne. Yaran da basu kai ga cike shekara daya da haihuwa ba, bai dace ace suna magana daidai ba, ta kara tabbatar da ta haukace, sai ranar da taga yaran sun bace a kan idonta kuma sun bayyana, sai tace kawai duk cikin haukan da take ne kwalwarta ke shirya mata irin wannan abun. -Ina son magana da ke Jinah. Cewar Sarah tare da zaunawa kan gadon kusa da Jinah. -Ki yimin magana dan Allah Jinah. Ta maimaita ganin Jinah bata da niyyar bata amsa. -Ni ya zan yi? Ya zan yi... Na haukace Sarah! Cewar Jinah tana mai saka kanta tsakan kafafuwanta. -Me yasa kike wannan tunanin? ko saboda abinda ya faru, to ai mu ma muna a wajen, koko dan yan tagwaye suna ta saurin girma ne, suna magana kamar manyan mutane... Eh ba ke kadai bace kike ganin wannan abun ba, kinga kenan idan mahaukaciya ce ke, to mu ma mahaukata ne. Abun da tsoro na sani, amma me yasa ba zaki yarda da cewa wannan ikon Allah ba ne, ba a koda yaushe ba ne muke fahimtar abubuwan dake faruwa damu, wasu abubuwan basa fassaruwa. Mutuwar Dauda ba abu bane mai dadi garemu baki daya, fada mun wa yake iya yaki da kaddara? Zamu iya goge rubutun da bamu ma san yana rubuce ba? Wata rana kila zaki fahimta, amma kafin wannan ranar, kiyi rayuwarki kamar yanda tazo maki a yanzu. A lokacin ne Jinah ta fara yarda da wasu abubuwan. Rungume Sarah tayi na dan wani lokaci kafin taji an dafata a kafada. Nafisa ce. -Nagode. ta fada kafin ta mike ta nufi tsakar gida, tarar da yaran nata da Abdul tayi suna wasa. -Nima nazo ayi wasar da ni! Ta fada tana kallonsu tare da murmushi. Murmushin jin dadin ganinta Abdul yayi, su kuwa tagwayen a guje suka nufi uwar tasu. Abdul yace -Naji dadin ganinki. Har cikin ransa yake fadar haka, domin baya jin dadin ganin halin da take ciki, yana ganin tunda yanzu ba Dauda shine wanda ya kamata ya zama mai tallafa mata. Bayan ta gama da Abdul ta dawo kan yaranta. Rungumesu tayi kwarai kamar zata maidasu ciki tana maimaita ku yafe mani, hawaye na zubo mata kamar fanfo. Tana dana sani sosai na watsi da tayi da su kwana biyu. -Kar kiyi kuka mama, mun fahimta. Cewar Aya. Idan da yarinyar nan ta fadi haka awannin da suka wuce, to fa Jinah zata iya zundumawa da gudu, tace ta haukace, abinda taji ba gaskiya ba ne. -Ina sonku sosai, rabin raina. Nafi da Sarah suka nufi kitchen domin sarrafa abinda zasu ci, suka bar Jinah da Abdul da kuma tagwaye da kamar walkiya suka bace daga wurin ba tare da mahaifiyar tasu ta lura ba. -Har yanzu babu wani labari game da mahaifinku? -A'a, wannan ma ba wani abun damuwa bane, domin ya saba irin wannan ba tare da mun samu labarinsa ba. Abinda yafi daure mun kai yanayin da ya shiga da kuma maganganun da ya fada kafin ya tafi. -Nima haka ban fahimci komai ba. -Mu bar dai maganar a yanzu, me zai hana ki tashi mu zagaya gari? -Toh bari na dauko mayafina. -Eh gaskiya kam, ko dan kar mutane suyi ta rantan na kare ba. Dariya dukansu suka yi kafin taje ta dauko mayafinta. A hanya labarin dariya Abdul yake ta bata, tana ta kyalkyata dariya. Cikin dariya tace -Dan Allah ka dena, ba zan iya ba, cikina ya fara ciwo. Kamar Dauda kake sai ku nemi kashe mutum da dariya. Shuru tayi tana hawaye tunawa da tayi da Dauda. Kwantar da kanta Abdul yayi a kirjinsa, yana lallashinta, shi kansa yana kewar Dauda sosai. -Hum yaran yanzu ba kunya, suyi ta manne mannen juna kamar chewing-gum a kan hanya. Tirr, shi yasa a wannan zamanin 'ya'yan shegu suka yi yawa. Cewar wani tsoho da yaje wucewa ta kusan Abdul da Jinah. Dukansu Kyalkyacewa da dariya suka yi. -Kai mutane akwai kananan kwakwale, ta yuwu mu yan uwa ne, amma su basa wannan tunanin, sun saba da ganin aibu a kullum, idan basu da tabbaci akan abu, to fa abinda zasu yi ta yadawa zai zamo na kuskure ne. Abdul ya fada, sakinsa Jinah tayi tana dariyar wannan tsoho. Abdul ne ya katse zancen da cewa: -Fada min da gaske kina son Dauda... Ina son na sani ne, saboda wata rana yace min zai yi komai ganin kin soshi, ni kuma na fada masa kina sonsa ganin yanda kuke a kullum amma yace min a'a. Dogon numfashi Jinah ta sauke kafin tace: -Eh ina son Dauda, amma ba kamar yanda yake so ba. Ina jin wani abu ne a cikin zuciyata kamar ina son wani wanda na yiwa alkwarin bashi zuciyata ba tare da na hada sonshi da na wani ba. -Ikon Allah! -Hmm na sani. Haka suka cigaba da tafiya shuru ba wanda ke magana, bayan sun dan zagaya suka dauki hanyar komawa gida. Suna kawowa gida, Jinah taja burki ta tsaya, waiwaye take kamar wadda ta bata. -Me ya faru? Abdul ya tambayeta. -Ina jin alamun wasu ne anan. -Me? -Ba yau na fara jin haka ba. Kallonta Abdul yake na irin kodai ta fara cin kai ne. Sedai da gaske ne, koda Jinah bata ganinsu, tana jin alamunsu idan suna kusa da ita, wato aljanu. Har ta saba da hakan din sakamakon kasancewar Fally kullum a kusa da ita. Sai dai wannan karon ba Fally bane, tana jin alamun kamar suna da yawa. Dakarun aljanu ne da dama suka zo, sun zo ne domin yan tagwaye. Tuni yan tagwayen da mahaifinsu sun ga aljanun, ganin yawansu Fally ya karaya, yasan ba zai iya masu ba amma yayi alkwarin ba zasu taba daukan yaran ba sai bayan ranshi. -Kamar yanda nayi alkwari, gani na dawo, kuma bani kadai ba, bakada wata dama ta kubuta a nan. Ka barmu mu tafi dasu, mu kuma zamu kyaleka. Cewar wannan aljanin da yayi fada da Fally a baya. -Ku fara bi ta kan gawata tukunna! -Toh ka sani koda mu bamu yi nasarar tafiya dasu ba, to wasu zasu zo, dan haka ba zaku taba samun sukuni ba... Kafin ma ya karasa maganarsa sai ga Aya da Ayu sun bayyana a gurin. -Ban fada maku, ku buya ba? Fally ya dakawa yaran tsawa. -Mu suke son dauka baba, su gwada kamamu idan zasu iya. Gama fadin haka keda wuya, tagwayen suka arce da wani masifaffen gudu. Makwamusan da kuma mahaifin nasu suka bi bayansu. Dukansu mamaki suke na irin masifaffen gudun yaran. Tsayawa suka yi, domin basa ganin yaran. Tagwayen sun bace. -Kay gamu nan, me kuke jira ku zo ku kamamu! Cewar Ayu yana dariyar keta. -Wannan wane tashin hankali ne, double bacewa! Cewar daya daga cikin aljanun, suma sauran al'ajabin abun suka shiga yi fahimtar abinda ke faruwa. Bayan karfin dake garesu na iya bacewa idon bil'adama, tagwayen zasu iya bacewa suma aljanu. Da taimakon mahaifinsu suka yi ta shammatar aljanun. Dukansu suke ta ko'ina, aljanun duk sun jigata. Anan suka tabbatar da dalilin da yasa shugabansu ke son su kwato masa tagwayen. Da yawa daga cikinsu suna jin labarin yara rabi mutum rabi aljanu, amma basu taba haduwa ba dasu ko jin labarin irin karfin dake garesu. Bayan wani dan lokaci, wasu aljanu hudu suka yiwa Fally kawanya, kokarin kubutar da kanshi yake amma ya kasa, dirarwa biyu daga ciki yayi, su kuwa biyun suka yi kansa suna duka, daya daga cikinsu yayi nasarar shaudawa Fally bulalar nan mai fasa jikin mutum ta sakar masa kwari masu cin nama, bulalar ta sauka a kirjinsa. Wani azabataccen ihu Fally ya saki, wanda yayi nasarar jawo hankalin yan tagwayen dake cen suna fafatawa da sauran aljanun, basu lura da mahaifinsu yana bukatar taimako ba. Da sauri suka nufi mahaifin nasu, ganin wannan kwarin na cin nama jikinsa, basu san me zasu yi ba, basu san cewa kwarin zasu bar jikin mahaifin nasu ba ne idan suka dauki wani aljanin suka dora kan mahaifinsu, sannan kwarin zasu bar jikin mahaifinsu. Kuka Aya ta fara, tayi ta kokarin cire kwarin da hannunta, amma kamar tana kara masu yawa. Tashin hankalin da suka shiga yasa suka kasa sarrafa karfinsu, har suka dawo aljanun na ganinsu, Ayu kokari yake na hana aljanun kaiwa garesu, amma hakan ya faskara har lokacin da daya daga cikin aljanun yayi masa wani mugun naushi. Kara ya saki ya fadi kasa. Aya ganin dan uwanta kwance a kasa, wani ja fuskarta tayi, ranta ya baci, aljanun cigaba da karasowa kanta suka yi, ita kuma barin ran da ta shiga, ta rufe idonta tareda dunkule hannuwanta, ba tare da sanin me zata yi ba ta watsa hannuwanta daidai aljanun kamar tayi jifa, wani haske da kuma guguwa suka fito daga hannunta. Wannan guguwar tayi ta daukan aljanun tana jefarwa, wasu suka yi ta fadawa kan bishiyu, wasu kuwa a kasa. Wanda suka fada kan bishiyu, duk suka ji manyan raunuka sakamakon reshinan bishiyun. Tsoro ne ya kama Aya, ta boye hannuwanta, tareda jin tsoron ba zata sake aikata irin wannan ba. Ita ba abinda taso yi ba kenan, bata san cewa kananan hannuwan nan nata zasu iya yin wannan aikin ba. Juyawa tayi kan dan uwanta taga har yanzu bai farka ba, gashi kuma wannan kwarin sai cin naman babanta suke. Dole ne ta nemo hanyar da zata cecesu, gashi bata san ta ina zata fara ba. Tambayar kanta take wa zai iya taimakonta, tunawa tayi da mamanta. A take ta bace da dan uwanta da kuma babanta, bata bayyana ko'ina sai cikin gidansu, kwantar dasu tayi, ta nufi cikin gidan da gudu domin nemo mahaifiyarta, sai dai itama tarar da ita tayi kwance bata motsi, Sarah da Abdul na ta kokarin tasheta. Amma ina, babu alamar rai a tare da ita. -------------------------------- Hello 👋 Fatan kuna nan lafiya? Ya hakurin zaman jira? A cigaba dashi dan Allah, laifin school ne. Ga wannan kuyi maneji dashi 🤗 Insha Allahu zan yi kokari duk ranar da nake free naga na kawo maku chapter 😍 ©El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 15 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp -Banzaye marassa anfani ! Cewar Shugaban nasu cikin bacin rai. -Amma, shugaba yaran ne karfin tsiya ne dasu. -Babu abinda ya shafeni da komai ke garesu, zaku koma kuma idan har kuka dawo ba tare dasu ba, to ku tabbata zaku mutu ! -Shugaba, ba zamu iya... Mai maganar bai samu karasawa ba sakamakon nunashi da sanda da shugaban yayi, a take ya daskare a gurin kamar dutse. Tsorata duka sauran aljanun suka yi ganin irin mutuwar da dan uwansu yayi, babu wanda ya kara samun kuzarin bude baki. Umarni shugaban ya baiwa wasu da basu je da farko ba, da su raka sauran su tafi neman yan tagwaye. Dakatawa suka yi lokacin da wata murya tayi masu umarnin su dakata, ba kowa bane face dan shugaban nasu. -Me kake aikatawa haka Zumana ? Me yasa... -Saurara kaji baba, idan har suka je, zasu dawo ne kamar yanda na farkon suka dawo ko ma nasu yafi na farkon. -Toh yanzu ya kake son ayi, so kake mu rungume hannuwa har sai daya daga cikin makiyan mu yayi nasarar mallakarsu, ka sani wannan itace damarmu, domin mune kadai wanda muka san inda suke kuma ina jin tsoro idan muka kara yin sanyar zuwa, wasu su rigamu ba kamar ma Hindu, ita duk nafi tsoro, domin wannan matar... -Na sani Baba, inada wata dabara ce da zan iya kawo su cikin sauki. -Wacce dabara? -Ka barni na tafi na wani lokaci, idan zan dawo ba zan dawo ni daya ba. -Amma Dana, akwai ha... -Ka yarda da ni baba. Wannan itace hanyar da zan nuna maka, na cancanci na gajeka. Kuma ai koda mun kamasu ba yana nuna zamu iya yin abinda muke son yi dasu ba. Idan muna son duka abinda muke so, to dole su yarda da mu sosai. Idan kuwa ana son haka to dole maganar aikin ilimi ne da wayo. A haka dai mahaifin ya yarda, abinda bai sani ba tuni dan nasa ya shirya wani plan nashi, yasan duk mutanen dake tare da yan tagwayen. Yasan abubuwa da dama game dasu. Har ma cikinsu ya samu wata da ta fada tarkonsa, domin Zumana akwai rauni game da mata. Duk inda yaje sai ya samu wadda yayi soyayya da ita in ma aljana ce ko mutum. Bayan ya shirya ya dauki hanyar zuwa gidansu yan tagwaye, ba tare da wani ya rakashi ba. (....) Tashin hankali, tsoro da kuma rudewa ne suka bi suka addabi yar yarinya Aya, batagwayenta dan uwanta, mamata da kuma mahaifinta duka a kwance ba a hayyacinsu ba gashi ta rasa me zata yi. -Ayu...Ayu dan Allah ka tashi. Abinda take ta maimaitawa kenan, amma babu alamar zai motsa. A gajiye, sharce zufar dake fuskarta tayi sannan ta dauki hannun dan uwan nata ta dora a daidai saitin zuciyarta sannan ta runtse ido. A hankali, taji ya motsa, bude idonta tayi sannan ta rungumeshi. -Ka tsoratani dan uwana! Ta fada cike da murna. -Baba fah? Ayu ya tambayeta. -Wannan kwarin har yanzu basu bar jikinsa ba gashi ban san me zan yi ba. Yar uwarshi ta bashi amsa cikin yanayin damuwa. -Mama ma haka. Aya ta kara fada a sanyaye. -Me, me ya samu mahaifiyarmu? -Ban sani ba lokacin da naje ganinta, na tarar da ita ne a kwance bata motsi. Da gudunsa ya nufi inda mamar tasu take, yar uwarshi a bayansa. Sai dai da mamakinsu, zaune suka tarar da Jinah tana shan ruwa, rugawa suka yi suka fada jikinta. A tunaninsu Mamarsu kawai ta dan ji ba dadi ne. Abinda basu sani ba ta fita hayyacinta ne domin danta shi ma baya cikin hayyacinsa, basu san cewa akwai wata alaka mai karfi ba tsakanin su da uwarsu, alakar da zata iya jin duk wani zafin ciwon da daya daga cikinsu zai ji. -komai ya wuce, Allah ya kara kiyaye gaba. Abdul ya fada. Sarah da Nafisa suka amsa da ameen. Juyawa yayi da niyyar barin gurin. -Ina zaka je? Nafisa ta tambayeshi. -bandaki zan je! Ko kina da sako ne? -A'a, Allah ya kiyaye hanya. Babban aiki za'a yo koh? Yar uwar tashi ta fada cikin sigar zolaya. Kada mata hannu yayi irin haba zan kamaki kafin ya cigaba da tafiya. Yana kan hanyar zuwa ban dakin yaji kamar ana binsa a baya ko kuma ana kallonsa... Bai dai gama tantance yanayin ba. Wani mugun tsoro mai iya sa mutum ya hadiye zuciya a take ne ya kamashi lokacin da yaga mutum zaune a gefen kusurwar bandakin, zuciyarsa ce ta buga. Kamar walkiya kuma yaga mutumin ya bace, sai dai kuma yaji kamar da mutum a bayansa. Kasa samun kuzarin juyawa yayi, hakan ma baida anfani domin yanzu mutumin ya dawo gabansa suna kallon juna. Wannan mutumin kuwa ba kowa bane face Aljani Zumana da yazo domin yan tagwaye. Kasa motsi Abdul yayi tsabar tsoro. Murmushi kawai Zumana yake bin Abdul dashi, shi kuwa Abdul tunanin guduwa ne yazo masa amma sai yaji kafafuwansa kamar an sa masu siminti, tunanin yayi ihu yayi, sai dai babu wani sauti da ya iya fita daga bakinsa. Tawa ta kare! Wani bangare na kwalwarsa ya ayyana masa haka. Cikin wannan yanayin na shuru da babu abinda ake ji sai bugun zuciyar Abdul, aljanin ya karaso kusa da dashi, a hankali yake karasowa kafin daga karshe ya shiga jikinsa. -Haha, daman na sani, babban aiki kaje yi, idan ba haka ba, ba zaka dau lokaci har haka ba. Cewar Nafisa tana yiwa wanda take tunanin dan uwanta ne dariya. Ba tare da ya kulata ba ya cigaba da tafiya. Hakan ya baiwa kowa mamaki. -Ba Abdul bane! Cewar Aya. Babu wanda yaji lokacin da tayi maganar sai dan uwanta da kuma Abdul din wato aljanin dake cikin jikin Abdul. -Kai yan yarori ku zo ku taimaka min nan! Cewar Abdul yana kokarin shiga dakinsa. Yan tagwayen binsa suka yi a baya. -Waye kai? Ayu ya tambayeshi fuska a murtuke. -Nazo ne domin na taimakeku. Naga abinda ya faru da babanku! -Me yasa kake cikin jikin Abdul? -Nasan yanda zan taimaki mahaifinku, amma yin hakan, dole sai na ari jikin wani dan adam. Kuma idan har na dauki na wani daban to mamanku da sauran yan gidan ba zasu amince da ni ba. Shuru yan tagwayen suka yi suna juya maganarsa. -Domin na tabbatar maku, ku kawo min mahaifin naku. Ya fada dan ya kaudar masu da kokonton da suke. -Amma ku sani aikin zai dau dan dogon lokaci. Ya kara da fadin haka. -Mu dai muna son ya warke. Cewar Aya, amma dan uwanta bai ce komai ba, domin bai yarda da wannan mutumin ba. Amma tunaninsa ya canja lokacin da suka ga aljanin yanata fadin wasu dalasuman tsafi a tunaninsu na warkar da mahaifinsu ne, tsugunawa Abdul yayi sannan ya fiddo wani yan kananan abubuwa jajaye guda biyu. Dorashi yayi kan goshin Fally, sannan ya dauki dayan ya dannashi da karfi kan kirjin na Fally. Bude ido Fally yayi, dadi sosai yan tagwayen suka ji sunata washe baki har kunne ganin mahaifinsu ya tashi. Magana suka yi masa amma shuru ba amsa sai dai binsu da ido da yake yi kuma bai iya motsawa. Kallon Zumana suka yi cike da zargi. -Dama na fada maku aikin zai dau lokaci, amma kar ku damu zan warkar dashi. Wancan ranar a bayan bishiyu naga irin yanda kuke kaunar babanku sai dai ba zan iya kawo maku wani taimako ba, yanzu ma ya kamata mu kaishi wani guri nesa da mutane, domin nan gaba zai iya komawa mutane sun dinga ganinsa. Kamar yanda ya fada masu haka suka yi, suka dauke mahaifinsu zuwa wani wurin. -Naga mamanku mutum ce, kenan ku ruwa biyu ne? Ya tambayesu. -Eh haka ne! Ayu ya bashi amsa. Kai ma so kake ka daukemu? -Nesa dani da wannan kudirin. Amma zan iya taimaka maku ta yanda zaku yi ku iya sarrafa karfinku dakyau, mahaifina ya koyar dani sosai ilimin sanin irinku. -Da gaske? Cewar Aya. -Eh da gaske. Ya bata amsa. -Yaushe zamu fara? Wannan karon Ayu ne yayi tambayar. -Lokacin da kuke so. Murmushin jin dadi suka yi, barin dakin Abdul din suka yi lokacin da mahaifiyarsu ta kirasu. Wani shu'umin murmushin mugunta Zumana yayi, ganin komai na tafiyar masa daidai. Yana iya warkar da Mahaifinsu kyabtawa da bismillah amma da gangan sai ya kara saka masa wani abun da ba zai so ya tashi da wuri ba, domin yasan in har Fally ya tashi to zai iya wargaza masa plan. Fita yayi daga dakin ya nufi gun sauran mutanen gidan, ya zauna ba tare da yayiwa wani magana ba. -Me yake damunka? Ko wani kudan ne ya cijeka a bandaki? Jinah ta fada cikin sigar zolaya. -Rabu dashi, yan matsutsan nasa ne suka motsa. Cewar Nafi, a tunaninta yayanta ne. Sai dai abun mamaki bai tankasu ba. -Ku shafa masa lafiya, idan yana magana kuce ya cika magana kamar aku, yanzu kuma da yayi shuru kuke son saka shi dole sai yayi magana. -Yauwa nagode Sarah! Sai yanzu yayi magana yana washe baki. Wani kallo yake bin Sarah dashi, wanda yasa ta tsargu. Tunani tayi ko sau daya Abdul bai taba mata irin wannan kallon ba. Sai dai abinda bata sani ba, babu ruwan Abdul da wannan aikin. Zumana tun lokacin da ya fara zuwa leken asirin sanin inda su Jinah suke, anan hankalinsa yakai kan Sarah, wannan ma yasa ya shiga jikin mutum dan ya cimma kudirinsa. Domin yana iya yin abinda ya kawoshi ba tare da ya shiga jikin mutum ba, tunda yan tagwayen zasu iya ganinsa. Amma yaki yin haka dalilin fadawa soyayyar Sarah da yayi. Bayan sun gama cin abincin dare kowa ya nufi makwancinsa amma banda shi. Washe gari da sassafe ya kira yan tagwaye dakin Abdul domin fara yi masu darasi. Fara masu yayi da yanda zasu iya karanta tunanin wani. -Ku rufe idonku, ku ja dogon numfashi, kuyi tunanin gaku nan a wani gu, sai ku fada min abinda kuka gani. Idan kuka yi haka to kuna cikin kan wani ne, sannan ku zabi mutumin da zaku yiwa haka. To yanzu ku saki asalin tunaninku. Sannan... -Wow nawa yayi!... Kayi... Amma kuma komai ya yamutse. Cewar Ayu yana bata fuska. -Saboda baka aje hankali bane sosai. Zumana ya rada masa. Bayan dan lokaci Aya ta bude idonta cike da murna. -Ni dai bai yi ba. Cewar dan uwanta. Murmushi Abdul yayi. -Halan nawa tunanin kake son karantawa? -Eh ko ba zai yuwu bane? Sai da yayi wata munafukar dariya kafin ya bashi amsa. -Zai yuwu, amma yana bukatar lokaci kafin ku koyi karanta tunanin aljanu. Yayi masu karya, domin babu wani banbanci tsakanin karanta tunanin mutane da na aljanu, kawai dai shi ne baya son su harbo plan dinshi, shi yasa da yaga yaron na kokarin shiga kanshi yayi sauri ya birkice komai. Haka ya cigaba da koyar dasu abubuwa da dama, amma sai yace masu basa yi sai ga mutane. Kwanaki na ta shudewa, Zumana yana cigaba da koyar dasu, har yaran sun yarda dashi sosai, haka bangaren Sarah kullum cikin takurata yake da mayen kallo, har dai abun ya kai ya ishi Sarah wata rana tayi masa magana. -Wai kai me yake damunka kwanan nan? Ta tambayeshi. -Kamar ya ban gane ba? Yayi kamar bai fahimci akan me take magana ba. Shuru Sarah tayi, jikinta yayi sanyi, domin tana tsoron kar aje itace ke tunanin abinda ba shi yake nufi ba. -Shin ba kamar uwa ka daukeni ba? Shuru yayi, murmushi kan lebensa ba tare da ya dauke ganinsa daga kanta ba. -Kinada kyau sosai... Katseshi tayi da sauri ta hanyar kiran sunansa. -Abdul! -Allah da gaske nake. Mikewa tayi da niyyar tafiya, amma kuma kamar tsafi ta dawo ta zauna. Wani shu'umin murmushi Abdul yayi. -Me yasa kike son kashe kuruciyarki anan? Ya tambayeta. -Kamar ya? Ba auren mahaifinka nake ba. -Oh wannan? To me yasa baya nan? Baki dace da irin wannan ba. Ba mutumin da zai bar mace kamarki yayi tafiyarshi. Mahaifina ne eh, amma sam baku dace ba. -Duk da haka dai mijina ne, kuma indai har yana nan ba zan kalli wani namijin daban ba. -Ku din nan, me kuke tattaunawa haka, kwanan nan fa na lura kuna daukan lokaci ku biyu kuyita maganganun da na kasa fahimta. Cewar Jinah dake karasowa wajensu. -Kece dai kika fara sa'ido shi yasa kike ganin haka. Cewar Abdul. Dama Sarah ta samu na zuwan Jinah ta mike da niyyar tafiya tana cewa -Ni dai bari naje aikin gabana... -A'a karki tafi dan Allah. Cewar Abdul yana wani kashe murya. Mamaki abun yaba Jinah, binsa take da kallo. -Ya aka yi ne? Ya tambayeta. -Abdul ka canja! -Ni ba wani canjawa da nayi. Ya fada yana juya mata baya da niyyar tafiya. Kokarin tashi tayi da tabi bayansa, sai taji kafafuwanta kamar an saka mata danko, ta kasa motsawa. Ba aikin kowa bane face Zumana. Sati daya bayan wannan ranar, Kuka da ihun Sarah dake durkushe tsakar gida ta dora hannu a kai ne ya karade ga baki daya gidan, gangar jikin wani ne kwance babu alamar rai a kusa da ita. Abdul da Nafisa suka karaso wurin da sauri. -Ba..ba.baba ne! Nafisa ta fada tare da fadawa kan gangar jikin tana kuka. -Dan Allah baba ka tashi, karka tafi ka barmu, ka tashi dan Allah, kada ka mayar dani marainiya, dan Allah baba. Kokarin kamata Jinah tayi amma ta fizge, tashi tayi da gudu ta nufi dakinta, binta Jinah tayi, suma yan tagwaye suka rufa masu baya. -Ba kyau, ki daina kuka Nafi. Aya ta fada da sigar lallashi. Sai dai Nafisa ko sauraronta bata yi ta cigaba da rera kukanta. Zaunawa kusa da ita Jinah tayi, tare da rungumota, wannan karon bata yi turjiya ba, ta cigaba da kukanta. Ita kanta Jinah mutuwar ta tabata, ta kasa fahimta amma tana jin zafin mutuwar har cikin ranta. Yanda mutuwar bare bata taba mutum har haka. Hakan ne yasa ake cewa mutum ba zai ji zafin mutuwa ba har sai nashi ya mutu. A waje kuwa, wanda suke tunanin Abdul ne, murna ce fal a ransa. Matsawa yayi kusa da Sarah ya rungumota. Yana shafa bayanta da sigar lallaba, alhali shi irin wannan ya dade yana fakon samu ace Sarah a cikin hannuwansa har yana taba jikinta. Ita kuwa Sarah cigaba da kuka take, domin ita bata kawo komai ba, hankalinta yana kan jimamin mutuwar masoyinta, duk da Kimba ya cutar da ita sosai, ba zata yi masa fatan mutuwa ba, tana tunanin wata rana zai iya gyaruwa suyi zama na amana dashi. Ba masoyinka ba ma ko makiyinka baka masa fatan mutuwa. Wani sabon kukan ta shiga rerawa tunawa da tayi da sauran matansa da kuma diyansa wanda wata kila ba zasu ji mutuwarsa ba har abada, tunda babu wanda yasan a ina suke. Bata san ta yaya zata sanar dasu ba, ko a ina zata gansu, kuma ta kasa fahimtar yanda aka yi Kimba yazo gidan da kuma ta yaya ya mutu. Wadannan sune tambayoyin da suka tsaya mata a kwalwa kuma batada amsarsu. -Karka damu, nayi alkawarin zan kula daku. Sarah ke fadawa Abdul. -A'a, ni kadai ne namiji yanzu a gidan nan, dan haka nine ya kamata na kula daku. Murnushi tayi. -Har yanzu kai yaro ne. -Amma kuma kwalwata babba ce. Ya bata amsa yana murmushi. Da taimakon wasu makota a kauyen, aka yi jana'izar Kimba zuwa makwancinsa na gaskiya. Taso taje cen kauyensu domin ta sanar da dan uwanta mutuwar, amma kuma tana tsoron yayan nata yayi ko a jikinsa domin rashin jituwar dake tsakaninsu, kuma bata son tafiya ta bar diyan mijin nata da kuma Jinah da yan tagwaye. Haka kwanaki suka cigaba da shudewa, Sarah tana cigaba da kulawa da diyan mijinta da kokarin kauda masu duk wata damuwar maraici tasu. Sai dai duk lokacin da take tare da Abdul sai ya zama kamar shi ke kula da ita... Wata rana da dare, lokacin sauran sunyi bacci. Sarah ya gani ta wuce ta kofar dakinsa, da gangan ya jefar da kofin kwalba tare da sakin wata razananniyar kara. Da gudu Sarah ta fado dakin, a tsorace, bata ma tsaya tunanin konkwasa kofa ba. Da shigarta dakin, taja burki ta tsaya, sakamakon ganin Abdul zigidir babu komai a jikinsa, a idonta ba wai suffar matashin yaro take gani ba, A'a suffar babban mutum baligi wato suffar Zumana ce take gani. Kasa daidaita natsuwarta tayi kuma ta kasa dauke ido daga kallonshi. Aljanin ya fahimci halin da ta shiga, sai ya shiga dube-duben munafunci wai neman abunda zai rufe jikinsa dashi, hakan da yayi kuma dan ya kara bata damar karewa duk sauran jikin nasa kallo. -Am..ina..ka... I'ina ta fara, duk ta daburce ta kasa hada kalmomin da zata yi magana, juyawa tayi ta fita da saurinta domin ita kadai ce mafitar da ta iya samu. Wani tsallen farin ciki Abdul yayi tare da fadawa kan gadonsa. Da zuwanta daki, safa da marwa ta shiga yi, tana mai jin haushin kanta na kasa fita da tayi daga dakin lokacin da ta shiga. Ta kasa goge hoton suffarsa da ta gani a cikin kwalwarta, tunani kala-kala yanata zuwar mata a kwalwa. A matsayin dana yake tunda dan mijina ne, kuma na girme mashi nesa ba kusa ba. Abinda take ta maimaitawa kenan. Idan da farko tana cikin tashin hankali, to yanzu fa cikin tashin tashinar hankali take. Kwabe kayan jikinta tayi, tayi daure gaba da zaninta, ta nufi gado da niyyar kwantawa taji ana konkwasa mata kofa. Zuwa tayi ta bude, Abdul ta gani daga shi sai singileti da karamin wando. -Nazo ne na baki hakuri kan abinda ya faru dazu, ban yi tunanin wani zai shigo ba. -A'a ni ya dace na baka hakuri domin ban konkwasa kofar ba kafin na shiga. -Ah ba komai, sai da safe. Yana juyawa da niyyar tafiya kamar tsafi, dan karamin kadangare ya fado kan kirjin Sarah. Kwalalo ido tayi a tsorace. -Shiit, kar ki motsa. Ya rada mata. A hankali ya cire kadangaren daga jikinta, ikon Allah ne ko kuma da gangan yayi, yankewa yayi a tafin hannunsa, jini ya falsu sai ga tsakiyar kirjin Sarah. Sai dai ita ba wannan bane damuwarta, damuwarta danta yaji ciwo. -Innalillahi, kana zubar da jini! Shigo daga ciki na daure maka ciwon. Cike da jin dadin plan dinshi na tafiya ya shiga dakin, wanke masa ciwon tayi sannan ta yagi wani tsohon zani nata ta daure masa. Daukan sauran zanin yayi, gadan-gadan ya nufeta. -Me kake yi haka? Ta tambayeshi tana fiddo idanuwan tsoro. -So nake na goge maki jinin da ya zubar maki. Ya fada yana kai tissus din kan kirjinta. -Abdul! Ta fada tana kallonsa. -Gogewa kawai zan yi. Kamar wata sakarya ta barshi yana goge jinin, duk da tasan ba wai gogewar kadai yake son yi ba. A hankali yake yin kasa da hannunsa zuwa cikin zaninta. -Abdul! Ta daka masa tsawa marar sauti. -Gogewa ne fa nake yi. -Ka goge, kuma gogewa kawai mana... Ta fada cikin wata kasalalliyar murya. Da dayan hannun yake kokarin sauke zanin nata, ita kuwa Sarah tuni ta fita a hayyacinta bata san wainar da ake toyawa ba. Daidai yana kwance mata zanin ta dawo cikin hayyacinta, hannu biyu tasa iya karfinta ta ingijeshi. Ta sake daura zanin. -Abdul fitar min daga daki! -Kiyi hakuri. Ya fada kamar da gaske kafin ya fita. Fashewa da kuka tayi. Me nake shirin aikatawa? Ta fada. A wannan daren kasa bacci tayi. Washe gari, kokari tayi na ganin bata hadu da Abdul ba. -Lafiyarki kuwa Sarah? -Eh me kika gani? -Naga kamar da damuwa a fuskarki. -Ba komai, kar ki damu. -Humm to shikenan. -Wai baku lura ba, dan uwana duk ya wani sauya? Cewar Nafisa. -Wallahi kuwa, cewar Jinah, ko me yake damunsa? -Ni zan je na kwanta domin na gaji sosai. Da zuwanta daki, ta zauna kan gado, tunani ta fara yi kan abinda ya faru jiya. Hayyacinta ta dawo sakamakon bugun kofarta da taji ana yi. -Shigo! Ta fada da tunanin ko daya daga cikin yan matan ne. Sai dai da mamakinta taga Abdul ne ya shigo. -Me kake yi a dakina? -Ina son muyi magana ne. -Ina sauraronka. -Ina sonki Sarah. Fiddo ido tayi waje. -Ba zai yiwu ba Abdul, ka fara hauka ina ga. -Ba hauka ba nake Sarah, da gaske ina sonki, nasan hakan akwai rikitarwa domin ke matar babana ce. -Kuma bayan haka, na girme maka... -Sarah soyayya ba ruwanta da shekaru, kuma ni hakan bai dameni ba, ki barni na soki Sarah, ni kaina nayi yaki da hakan amma na kasa, dole na yada makamaina. -Ka fita dan Allah Abdul. A karo na biyu, yanzun ma kamar tsafi taga katon maciji kan gadonta. Tsalle tayi ta fada kan Abdul. -Maci... Ta juya da niyyar nuna masa amma bata ga komai ba. -Kwantar da hankalinki babu komai. -Amma..ni.. -Shiit, idan kina jin tsoro ne, zan iya tsayawa. -Ba zai yiwu ba! -Sarah ba komai fa zan yi ba, illa gadinki. Kwantawa tayi shi kuma ya zauna gefen gado. -Me yasa kake min duk wannan abun? -Na fada maki ina sonki har cikin raina. -Babu namijin da ya taba bani irin wannan kulawa. -Idan har namiji ya sameki kuma har ya kasa baki kulawa to shi ba namiji bane. Shuru suka yi, kowa na saka da warwara cikin zuciyarshi. Ita kanta Sarah taji ta kamu da kaunarshi amma kuma tana jin tsoro na kasancewarshi dan mijinta. Kalamanshi suna tabata sosai, tana jin ina zata samu damar dandana jikin wannan matashin. Amma kuma ta kasa daina maimaita. Zan daure, zan cije, ba zan iya ba. -Zan iya tabaki? Kamar daga sama taji tambayar tashi, zai tabani, kenan ba zai iya yin haka ba sai da izinina? Kuma yace tabani kawai zai yi, tabani din kawai zai yi kenan? Tunanin da tayi kenan. -Eh! Ta fada cikin kasalalliyar murya. Hannu Abdul ya dora kan kafarta. -Fatarki akwai laushi, zan iya shafawa? -Eh, ai shafawa kawai zaka yi ko? -Sosai ma. Wata irin shafa ya fara yi mata, wadda duk tabi ta daga mata hankali. Ganin ta fara fita hayyacinta, ya kai hannuwansa kan ruwan cikinta. A hankali hannuwansa suka kai kan kirjinta ya cigaba da shafata. Ganin kamar tana jin dadin abun, ya kunce mata zanin gaba daya. Sai gata babu komai a jikinta. Abun nasa gaba gaba ya fara yi. Tsawa ta daka masa. -Abdul ya isa haka! Ba tare da yayi magana ba ya koma dakinsa, kwabe kayan jikinsa yayi duka, sannan ya kwanta kan gado idonsa na kallon rufin dakin kamar mai jiran zuwan wani. Rufe idonsa yayi, cen yaji kamar mutum kusa dashi, bude idonshi yayi yaga Sarah a tsaye. Wani makirin murmushi yayi, ita kuma bata yi wata-wata ba ta kwabe kayan jikinta baki daya sannan ta hau gadon. Zumana ya samu abinda yake so, ya samu burin cika farkon plan dinshi. (....) -Tunanin me kake? Aya ke tambayar dan uwanta da taga kamar yana cikin tunani. -Ko kin taba lura da irin wannan abun da Aljanin nan ya sakawa baba? -A'a, me yasa kace haka? -Ni na taba ganinsa a inda muka yi fada da wannan aljanun. Ayu tun lokacin da aljanin ke warkar da baban nasu ya lura da abinda yayi anfani. Komawa suka yi shi da kanwar tashi inda suka yi fada da aljanun, anan suka ga ire iren abun a kasa, wanda aljanu suke anfani dashi wajen sankarar da mutum wuri daya ta yanda ba zai iya motsi ba. Komowa suka yi wajen mahaifin nasu, suka cire abun na kan goshinsa da kuma na kirjinsa. Wani ihun wahala Fally ya saki tare da yin tari. Bayan kamar mintuna goma, Fally ya dawo hayyacinsa, mikewa yayi. Cike da murna yan tagwayen suka rungumeshi. Daidai lokacin Zumana ya karaso wurin, ya tsorata da ganin Fally ya tashi amma bai bari suka lura da canjin fuskarsa ba. Washe hakorin dole ya shiga yi kafin ya fada cikin rada: -Muje a plan B! ©El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 16 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp A wannan rayuwar akwai mutumin da na abincin da zai ci kawai yake so, akwai mutum mai na abincin kuma yana da burin mallakar gida, akwai mutum yana da gidan kuma mota yake da burin mallaka, akwai mai gida da mota kuma kari yake so sannan akwai mai shi da yawa duk da haka kari yake so. Duk adadin samun mutum a duniya kalmar "Bai isheni ba" ba zata taba gushewa ba daga bakinsa. A kullum idan mutum ya samu cikar burinsa to wani burin ne ke maye gurbin tsohon burin. Kuma ya kan manta da cewa duk wani abu da ya tara a duniyar nan, ba mallakinsa bane haka zai wuce ya bar abun.... Haka yake a gun Hindu, tsohuwar aljana da tafi sauran aljanun tsufa a duniyar da Jinah ta taso, duk adadin karfin tsafin dake gareta, burinta a yanzu bai wuce mallakar yan tagwaye ba domin kara habbaka karfin tsafinta ta yanda zata dawo gagarabadau a duniyarsu. Domin haka su ma sauran aljanun suka dau haramar samun hanyoyin da zasu mallaki wannan yara, saidai ita Hindu a dage take kallonsu domin ita tanada nata plan da ta shirya. A ganinta sauran aljanun kawai shirmen banza zasu yi da yan tagwayen domin basu son komai ba game da asalin karfinsu kamar yanda ta sani. -Ranki shi dade Hindu! Wani Aljani daya daga cikin amintattun masu yi mata hidima ne ya kira sunanta a yayin da yake shigowa hankali a tashe. -Ya aka yi ne Manfa? Wane labari ka zo min dashi? -Labarin marar dadi ne ranki shi dade. -Haifoshi zan iya goyashi! -Zumana da ga sarki Mombi na kabilar Fomba wayon tsiya ne dashi, a yanzu haka yana tare da yaran, yana taimaka masu su san karfinsu. Shuru Hindu tayi kafin ta kyalkyace da wata mahaukaciyar dariya. Cike da mamaki Manfa ya tambayeta : -Ya naga baki damu ba, ranki shi dade? Ya kamata mu san yanda zamu wargaza masa plan. -A'a Manfa, fili kawai Zumana yake share mana. -Kamar ya? - A sannu zaka fahimta! Manfa bai kara cewa kala ba, ko daya baya tantamar fadar uwar gijiyarshi, domin shi shaida ne a kan karfin da take dashi. -Ina fata baka manta da babban aikin da zaka yimin ba? -Wane ni da zan manta, da ni da ahalina ai duk mallakinki ne, kuma ba zan taba da nasanin abinda zan yi maki ranki shi dade. -Naji dadin jin wannan! Mu tafi yanzu. Cikin kankanin lokaci suka dira a inda suke son zuwa. -Tona ramin! Hindu ta bashi umarni. A take ya tone ramin, yana gamawa ya fada mata da ya gama. Wani umarnin ta sake bashi. Shiga yayi cikin ramin, ya kwanta kan abinda suka tarar cikin ramin, wasu ruwa Hindu ta shiga zuba masa har sai da ya jike sharkaf, sannan ta shiga fadin wasu kalmomi da ita tasan anfaninsu. Da tafin hannunta take bin ko'ina na ramin tana cigaba da fadin maganganunta, a take wata wuta mai karfi ta fara ci a cikin ramin. Azabar da Manfa yaji tasa ya saki wani azabataccen ihu, ihun da kamar mala'ikan mutuwa na zare ran kafiri. Duk da Hindu bata dakata da sambatun da take ba, sai ma kara daga murya da tayi. Bayan ihun da Manfa yake yi, za'a iya jiyo ihun wasu amma ba daga wannan ramin ba ihun yake fitowa, yana fitowa ne kamar daga nesa. Wutar daina ci tayi kamar bata taba kamawa ba, kara rufe ramin Hindu tayi. Sannan ta daga hannunta sama tana maimaita : wili, wili sela! Ba bata lokaci sai ga hannuwa biyu sun fito daga cikin ramin, kamar zombie zai fito daga cikin kabarinsa. Mutum ne lafiyayye ya fito daga cikin ramin ya tashi tsaye gabanta. Wani makirin murmushi ta fara yi, kafin daga bisani ta kyalkyace da wata mahaukaciyar dariya, dariyar da ta karade ko'ina na dajin. (..........) -Ina son magana da kai, kai kadai idan zai yiwu. Zumana ya fada da damuwar karya a fuskarsa. -A'a, muma muna son jin abinda zaka fada, da kuma yanda zaka kare kanka domin kayi wasa da kwalwarmu. Cewar Ayu. -Eh, ba kamar ni da na dauki yardata na baka. Cewar Aya tana wa Zumana kallon a barni na kasheka. -Baba, ka kyalemu da shi muyi maganinsa. Cewar Ayu cike da tsana kafin ya nuna yatsa zuwa wuyan Zumana. A take Zumana ya fara kakarin amai da kokowar kwatar numfashi. Ji yake tamkar an ratayeshi ne da igiya, fara karewa karfinsa yayi, ya durkushe kasa. -Dakata Ayu, ya kamata mu fara jin me yasa yayi hakan. Umarnin mahaifin nasa yabi, ya saki Zumana. Tarin wahala ya fara yana mayar da numfashi. Fally bai ce komai ba, dakatawa yayi na dan lokaci domin ganin ko Zumana zai yi kokarin guduwa, amma da mamakinsa sai yaga babu alamun haka. Amincewa yayi suyi maganar a gefe su biyu, yaji ya yarda dashi domin da yana son ya cutar da 'ya'yan ne da tuni ya cutar dasu. -Me kake bukata? Fally ya fada bayan sun koma gefe. A wahalce Zumana ya fara fadin: -Ban zo ba da niyyar na cutar daku, na nemi nayi magana da kai ne domin nasan kai zaka fahimce ni. -Kamar yaya? -Ba ina son na kasheka bane, kawai nayi hakan ne domin ita, domin nasan ba zaka barni na rabeta ba idan lafiyarka kalau. Ina so ne na cika wani burina a kanta. -Ni fa ban fahimci inda ka dosa ba. -Na kamu da soyayyar bil'adama ce, kamar kai. Ja fuskar Fally tayi tsabar bacin rai. -Ba wai soyayyar Jinah ba, ta Sarah nake nufi. Zumana yayi saurin fada domin ya lura kadan ya rage Fally ya fizgo zuciyarshi. -Ba nazo bane domin yan tagwaye, domin ita nazo. Kuma shima na wani dan lokaci ne, nasan ba zai yiwu ba na har abada, dole zan fita daga jikin wannan saurayin. Amma... Ina son... Kasan me nake nufi... Yana fin karfina a duk lokacin da nake tare da ita. Ina rokonka gafara ka yafe mani cutar da kai da nayi. Karyar da Zumana yake ta zubawa Fally kenan, tausayinsa ne ya kama Fally domin yana ganin kamar irin halin da yake ciki ne. Yana tsananin bukatar ace Jinah ta tuna dashi, ta kasance kowanne lokaci a tare dashi, yaji ta bude baki tace tana sonsa. -Na fahimceka. Fally ya fada cike da alamun tausayi. Sai dai bai dace ka dauki jikin Abdul, Zaka haifar da babbar matsala ne tsakaninsa da matar babanshi bayan tafiyarka. -Kana da gaskiya, ban yi wannan tunanin ba ni, na kasance sakarai mai biyewa son zuciyarsa ne... -Yanzu ya tsakaninku yake? -Ina tunanin tana sona sosai, ina nufin ta fara kamuwa da soyayyar Abdul ba ni ba. Ya fada da yanayin damuwa. Shuru Fally yayi yana kare masa kallo, sai dai bai fahimci komai ba face tsantsar gaskiya a idon Zumana. Zumana yasan hakan na iya faruwa kuma da yake kwararre ne wajen iya controling yanayinsa da boye iya ainahin suffarsa ga mutane da kuma yan uwansa aljanu. -Na fahimci wani abu, uwar 'ya'yanka bata iya ganinka, alhali kuwa ya kamata a ce tana ganinka domin 'ya'yan dake tsakanin ku saboda karfin jinin dake tsakaninku a yanzu. -Eh hakane, ni kaina ban san ya zan yi ba, domin bata iya tuna komai na rayuwarmu a baya. Fally ya fada cike da matsananciyar damuwa. -Na fahimta, mahaifiyarka ko mahaifinka wani daga ciki yayi mata wankin kwalwa. Ido Fally ya fiddo waje da alamun mamaki. -Ta yaya ka... Wa ya koya maka duk wadannan abubuwan? -Mahaifina. -Ni nawa, ba mu samu lokacin da zai bayyana min komai da ya shafi duniyarmu ba. A hankali na fahimci babu komai da na sani a kan kaina. -Zan iya taimaka maka. -Taimako a kan me? -Domin matarka ta tuna da kai. -Da... Da gaske kake? -Sosai ma. -Kai, bana tunanin zai yiwu. -Ka yarda da ni, akwai wani abokin mahaifina yanada karfi sosai kan duk wani sirri na duniyar nan tamu. Yana da mafitar kowacce irin matsala. Tsoho ne da ya shafe karnika da dama. A take damuwa ta mamaye zuciyar Fally, tunawa da yayi da mahaifiyarsa lokacin da taje neman taimakon Hindu, kwatancen yayi kama da na Zumana. Wadda tayi ajalin mahaifiyarsa domin cetonsa. -A'a, ba zan je ba! Ba zan iya sadaukar da kowa ba. -Shi ba kamar Hindu yake ba. Cewar Zumana kamar ya karanci tunanin Fally. -Ka santa ne? -Waye bai santa ba, shedan ne a suffar mace! Bayan shuru da kuma zurfin tunani na dan lokaci da Fally yayi. Yace : -Yaushe zamu je? -Yanzu ma zamu iya idan kana so, wani abu kuma, za'a iya daukan lokaci baka dawo ba. -Zai fi dai a ce anyi aikin da wuri, domin na gaji da wannan rayuwar, ina kusa da matata amma bata ganina. -Na fahimceka. Cewar Zumana da tausayin Fally na karya a fuskarsa. -Ina son kayi min wani taimako. -Ina sauraronka. -Ina son ka kula min da 'ya'yana kafin dawowata, hankalina ba zai kwanta ba idan na barsu su kadai, zan fi jin dadi a ce kana kusa dasu, kuma kaga kasan abubuwa da dama kan karfinsu. Zumana ji yayi kamar ya kurma ihun dadi, ganin Fally ya kara saukaka masa plan dinshi. Kira yaran yayi, yayi masu bayani a takaice. Sai dai hankalinsu sam bai kwanta ba, domin basu yarda da wannan aljanin ba. -Kada kaje baba. Cewar yar yarinya Aya. -Dole na tafi 'yata, domin kasancewarmu cikin farin ciki ne ni da ku da kuma mahaifiyarku. -To ka dawo da wuri. Cewar Ayu. -Kar ku damu. Mu tafi! Ya karashe maganarsa ga Zumana. Ba bata lokaci suka dauki hanya. Suna zuwa wani guri, Zumana yayi masa nuni da ya shiga wani dan karamin daki dake gabansu, da saka kafarsa cikin dakin yaji saukar mashi a gadon bayansa, wata azabatacciyar kara ya saki. kokarin sa hannunsa yayi domin ganin ya cire mashin amma ya kasa. Faduwa yayi kasa. Murmushin keta Zumana yake, wani aljani ne ya fito daga cikin dakin shi ma yana murmushi, babban abokinsa ne da ya fadawa duka sirrinsa. Su biyu suka kama Fally suka daure jikin bishiya da dioru. Igiyar da ake daure aljani ta yadda ba zai iya anfani da karfinsa ba. -Da alama wannan gubar taka tanada karfi. Cewar Zumana ga Aljanin da ya taimaka masa. -Tantama ma kake a kan aikina? Cewar abokin nasa. -Ai daga yau na dena! Ni zan koma, ka tsareshi da kyau, kuma ina sonsa a raye na wani dan lokaci. Bayan fadar haka, kamar walkiya ya dira wajen Sarah. Da yan tagwaye yaci karo. -Yaushe babanmu zai dawo? Cewar Ayu. -Ban sani ba, abinda kawai na sani idan ya dawo zaku kasance cikin farin ciki ku da Mahaifiyarku. Ya fada da kudirin ko zai iya dawo da yardar da yan tagwayen suka yi masa a baya, shi yasa yayi masu magana cikin sanyi. -Idan bai dawo ba da wuri, zaka kaimu wajensa mu mu dawo dashi. Cewar Ayu cikin yanayi mai kama da gargadi. Murmushi Zumana yayi, alhali cikin zuciyarsa tsoro ne fal, domin ya fara jin tsoron yaran. Bayan yaran sun juya sun tafi, tunawa yayi da wani babban bangare na plan dinshi, wani makirin murmushi. Kyabtawa da bismillah ya dira cikin dakin Sarah. Ihun tsoro Sarah ta saki da ta ganshi. -Ta yaya ka shigo? Ka tsorata ni! -Ina ta konkwasawa amma da yake kina nan kin zurfafa cikin tunanina sai baki ji ba. Ya fada da murmushi a fuskarsa. Shuru Sarah tayi kafin tace: -Gaskiya Abdul, nayi da na sanin abinda ya faru tsakaninmu, domin a yanzu haka na kasa hada ido da yar uwarka. Ba tare da ya bata amsa ba, ya kama hannuwanta ya saka cikin nashi tare da sanya idonsa cikin nata. Wata azabatacciyar wutar sonsa taji na kara ruruwa a zuciyarta. Bata yi wata-wata ba ta hade bakunansu. Bayan wani dan lokaci ta janye bakinta tana kallonsa kafin tace : Manta da abinda nace, ba zan iya rayuwa ba babu kai, Ina sonka Abdul. Sosai Abdul yaji dadi. Ba tare da bata lokaci ba suka lula wata duniyar da sauran yan gidan basu san da ita ba. Haka suka cigaba da soyayyarsu, Sarah ta gama mutowa a kan Abdul, mutumin nan rijiya yake son jefata amma ita bata sani ba. Haka aljanin ya cigaba da anfani da wannan damar a plan dinsa. Ya Fara sawa Sarah a kai wai Jinah sonshi take, shi yasa take mata wasu abubuwan. Bata yarda da hakan ba sai ranar da ta jiyo Jinah na fadawa Nafisa : Ina son dan uwanki, yana da natsuwa sosai. Bata tsaya jin karshen maganar Jinah da take cewa : Ina jinsa kamar dan uwana, amma kwanan nan na kasa gane masa. Sai wata rana kuma da taga ita Jinah tana rungumar Abdul din. Hankalinta yayi matukar tashi, abinda bata sani ba duk cikin makircin Zumana ne. Daga ranar duk tsantsar soyayyar da take wa Jinah ta juye zuwa kiyayya. Yarinyar da ta dauka tamkar diyar cikinta, take matukar so, yau gashi ta zamar mata wata da take tunanin zata kwace namijin da tafi so a rayuwarta. Jinah lura tayi da wannan kiyayyar, take zuciyarta ta karye, ba zata iya jure ganin wadda ta dauka a matsayin mahaifiyarta na nuna mata irin wannan tsanar ba. Wata rana ta kudiri sai taji ko me ta yiwa Sarah domin ta nemi yafiyarta. -Dan Allah Sarah ki fada min ko nayi maki wani laifi ne? Nan fa Sarah ta shiga fada ba dali, inda ta shiga ba ta nan take fita ba. Daga karshe tace Jinah ta fitar mata daga gida. Kasa motsawa Jinah tayi tsabar firgicin mamakin jin wannan daga bakin Sarah. -Ki fice min daga gida! Ki fita nace! Abinda take ta maimaitawa kenan, tana tasa keyar Jinah kan taje ta kwashe kayanta. -Kayi wani abu dan Allah, baka ganin korarta zata yi daga gidan? Cewar Nafisa ga dan uwanta, bai ko bi ta kanta ba yayi shigewarsa daki. Takaici ne ya kama Nafisa domin ta lura kamar ma farin ciki yake da faruwar lamarin. Shi kuwa abinda yake so kenan Jinah ta bar gidan ita da 'ya'yanta shi kuma sai ya bisu da niyyar taimaka masu, inda zai kaisu a matsayin masauki dama cen ya zuba tarko sai su kama tagwayen suyi yanda suke so suyi dasu. Nafisa bin Jinah tayi cikin daki tana bata hakuri kan dan Allah kar ta tafi. -Ba zan iya tsayawa a nan ba, gidanta ne kuma ita taso in tafi. -Gidan mahaifina ne ai. -Ko ma yane ba zan iya ba! -To nima kuwa ba zaki barni ba, domin na gaji da halin dan uwana, kuma wai kinyi tunani a kan 'ya'yanki? -Eh, su, zasu zauna a nan, zan roketa dan Allah ta rike min su, idan naje na samu wurin da zamu zauna sai in zo in daukesu. Yanzu dai ni kadai zan je. -Na fada maka mama tana cikin damuwa. Cewar Aya da ta bayyana a tsakar gidan. -Ina zaki je mama? Tafiya zaki yi ki bar mu? Cewar Ayu cikin sigar son yin kuka. -Wa ya fada maku haka? Ba zan taba rabuwa da ku ba. Kawai na dan lokaci ne. -Mama, ba zan taba yafe maki ba idan kika tafi kika barmu, har abada. Cewar Ayu. Hawaye ne suka fara ambaliya kan fuskar Jinah na tausayin kanta da kuma 'ya'yanta. -A'a dana ka manta da akwai mutuwa? -A'a! -To ka dauka mutuwa nayi, amma kuma zan dawo. -To ai baki mutu ba, kuma ma ba zaki mutu ba yanzu. Kuma ki daina maganar mutuwa. -Ka sani dana, mutuwa tamkar kana tafiya ne tsuntsu yayi maka kashi a kai, ka shirya zuwansa ne? A'a, yana zuwa ne ba tare da sanarwa ba. Haka tana iya kasancewa a yau. Wannan tafiyar zan yita ne ba da son raina ba. -Ko ma dai meye, mu dai damu zaki tafi. Cewar yan tagwayen lokaci daya. Toshe baki Jinah tayi tana kokarin hana kanta kuka, ita sam bata son taje ta saka rayuwar 'ya'yanta cikin hatsari, haka kuma bata son su tsaneta kan tafiyar da zata yi. Mikewa tayi ta tattara kayansu. Suka nufi kofa da niyyar barin gidan ba tare da ta saurari magiyar da Nafisa ke mata ba. -Ina zamu je mama? Cewar Aya, amma maimakon taji amsar mahaifiyarta, wani dake shigowa gidan ne ya amsa. -Ku biyoni muje! Da ganin mai maganar, Nafisa ta fadi sumammiya. -D.D.D...Dau.da! Cewar Jinah kafin itama ta sume. TOOOOH ------------------------------------- Welcome back 2 duniyarmu Dauda lol. 😁 Bon week-end à vous tous 🕺 See you next chapter 😍 ©El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 17 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Idan mutum ya ciri tikitin mutuwa, to fa tikitin na tafiya ne kawai, ko alama babu tikitin zuwa da dawowa wannan wuri wato mutuwa. Mutuwa wata kaddara ce da babu daya daga cikin mu da zai iya kubuce mata, kuma idan hakan ta kasance, shikenan an gama da babin mu. Ba'a dawowa idan an mutu, ana mutuwa ne sau daya a rayuwa. Mutuwa kamar lokaci ne da ya wuce, ba za'a taba iya komawa ba. Wannan shine tunanin da Jinah da Nafisa ke yi kafin su ga Dauda a tsaye a gabansu. Firgicin da suka shiga yayi sanadiin tsunduma su cikin wani yanayi. Nafisa ce ta fara dawowa hayyacinta, da sauran yan gidan, Dauda ya basu labarin abinda ya faru dashi. Sun tausaya masa tare da girgiza da jin labarin, sai dai banda Jinah da har yanzu take a sume. Fara dawowa hayyacinta tayi, a hankali ta fara bude idanunta. Ganinta tayi kwance kan gadonta, koda ta karasa bude idanuwanta taga Dauda kusa da ita, anan komai ya dawo mata. -A'a! Kwantar da hankalinki, kar ki tsorata, da gaske nine Dauda..ban..ban mutu ba. Ganin jinah alamar har yanzu bata gamsu ba, ya kara da cewa: -Jinah da gaske nine, Daudanki, gani na dawo kuma ba zan kara barinki ba, kina tunanin zan iya tafiya na barki? Har abada kyakyawata Jinah! A wannan karon Jinah, ta fara sakin jikinta sannan ta samu damar bude baki: -Ta yaya hakan zai yiwu? na ganka fa ba rai Dauda, nayi kukan... -Ba mutuwa ba nayi Jinah, ina tunanin zuciyata ta tsaya da buguwa na wani dan lokaci. Amma yanzu gani, kuma babu inda zan kuma zuwa, nayi maki alkawari. A yanzu kam Jinah ta gama yarda da zancen Dauda, tsalle tayi jikinsa ta rungumeshi tare da fashewa da kukan farin ciki, farin ciki sosai take ciki, ba kamar mintuna ashirin baya ba da suka wuce. Yan tagwaye, Nafisa da Sarah ne suka shigo dakin, sakin Dauda Jinah tayi, tare da bin Sarah da kallo amma da mamakinta sai ta ga alamar farin ciki a fuskar Sarah. -Fada mani, ina zaku je da kayanku dazu? Dauda ya tambaya. Sarah ce tayi saurin cabewa da cewa: -Ba inda zasu je, ba wanda zai je ko'ina, yau ranar farin ciki ce. Yan tagwaye ku dauki kayan ku mayar dasu inda suke. Mamaki, Jinah ta kasa cewa komai. Sarah tana cikin farin ciki da dawowar Dauda, wannan ne dalilin da yasa ta fasa korar Jinah. Tunda mijinta ya dawo, yanzu zata shafawa Abdul dinta lafiya, sarah ta raya a zuciyarta. Tana son zaman Jinah a kusa da ita, amma kuma tana jin wani abu da yake ingizata a kan sai ta kori Jinah. Shi kuwa Abdul yana daki, ransa a bace, sakamakon duk plan nashi yabi ruwa, kuma Sarah tazo ta tabbatar masa da Jinah da tagwaye babu inda zasu je. Me ya kamata yayi, abinda yake ta maimaitawa kenan. Idan ya cigaba da bata lokaci, to fa tagwaye zasu harbo jirginsa domin dama cen ba wani yarda suka yi dashi ba. -Ko barka da zuwa ba zan samu ba? Cewar Dauda da ya shigo dakin Abdul ba tare da Abdul din yasan shigowarsa ba. Wani murmushin karfin hali Abdul din ya kirkira tare da nufar Dauda suka rungume juna. -Nayi farin cikin dawowarka abokina! Cewar Abdul. -To ai ban ga alamar farin cikin ba a fuskarka. Dauda ya fada cikin sigar zolaya. -Kawai bana jin dadi ne kwana biyu, amma da gaske naji dadin ganin fatalwarka. Abdul ya bashi amsa shi ma cikin sigar zolaya. Dariya suka yi, kafin Dauda yace: -Zaka bani labarin duk abinda ya faru bayan tafiyata. -Karka damu, zaka ji komai. A wannan ranar kowa cike yake da farin ciki banda Abdul, Nafisa ce ta hada masu lafiyayyen girki. Dauda kuwa sai fira yake da yan tagwaye, koda yazo kan labarin aljanu, tattara hankalinsu suka yi, suka zuba mashi na mujiya. -Ina da wani kawu da yake mu'amula da aljanu, yasan sirrukansu da dama kamar misali idan aljani yayi tarayya da mutum sannan suka haifi 'ya'ya to yana wahala yaran su rayu, idan kuwa suka rayu, yace yaran ana ce masu yan baiwa kuma ruwa biyu ne, suna da tsananin karfin da babu wanda yasan adadinsa, kuma zasu iya yin abinda aljanu ba zasu iya ba, misali zasu iya karanta tunanin kowane irin aljani. Hmmm kunji sai shirme nake ta zuba maku ko, ni kaina bansan dalilin da yasa nake baku labarin nan ba, wasu har cewa suke yi kawuna haka haka ne (mahaukaci ne). Shuru tagwayen suka yi suna juya maganganun Dauda kafin su fara magana tsakaninsu ba tare da bakunansu sun bude ba. Idan abinda Dauda ya fada masu gaskiya ne, kenan Zumana yana boye masu wani abu, domin yace masu basu kai girman da zasu iya karanta tunanin aljani ba. -Taso muje Aya na nuna maki wani abu, yanzu mun dawo Tonton Dauda (Kawu Dauda). -Ku dauki iya lokocin da ku so yarori. Dauda ya fada yana murmushi. -Ya kamata muje mu kure wannan aljanin domin ina tunanin ya mayar damu shawaragai, ya mana karya akan abinda muka iya. -To idan fa da gaske kawun tonton Dauda haka haka ne? -Ni bana tunanin haka, amma mu je mu bincika. -Toh muje yana cikin daki a yanzu. Tarar da Abdul suka yi kishingide da alamun tunani yake, tun da plan dinsa ya wargaje babu abinda yake yanzu face tunani. -Yaushe babanmu zai dawo? Aya ta tambayeshi domin ta dauke masa da hankali, shi kuma Ayu yana kokarin karanta tunaninsa. Ganin Ayu shuru, yasa Abdul saurin harbo jirginsu saidai kafin yayi wani yunkuri yaji kamar an saka hannu an shake masa wuya, yana kokowar kwatar numfashi, magana yake son yi amma babu dama. -Zaka fada mamu ne a yanzu inda babanmu yake, ko sai na... -Me kake kokorin yi, kashe shi zaka yi? Cewar Aya, da alamar kwalla a idanunta. Abdul ya fahimci Ayu ya gane makirin plan dinshi, tsoro ne ya dabaibayeshi domin yana tsoron abinda tagwayen zasu yi masa. -Kana son sanin me zamu yi maka? Da farko zaka fita daga jikin Abdul, sannan ba zamu yi maka komai ba idan ka bamu babanmu ba tare da komai ya sameshi ba. Cewar Ayu kafin ya saki wuyan Zumana da ya lura yana son yin magana. Rokonsu yayi da kar su kasheshi kuma yayi masu alkawarin zai kaisu inda mahaifinsu yake. Ba tare da fata lokaci ba ya daukesu zuwa inda babansu yake, domin Zumana yasan irin karfin dake ga yaran shi yasa ba zai gangancin yi masu abun da zai sa su halakashi. Kai su yayi wurin da kamar sahara, mahaifinsu kawai suka gani a daure, abokin Zumana wata kila ya buya ko kuma ya tafi wani wajen. Koda tagwayen suka yi tsalle suka rungume babansu, Zumana yayi anfani da wannan damar ya gudu. Ko ta kansa basu bi ba, domin ta mahaifinsu suke da yake cikin wani yanayi. -Bari ka gani! Cewar Aya kafin ta dora karamin hannunta kan goshin mahaifin nasu, cikin kankanin lokaci Fally ya dawo hayyacinsa, murmushi yayi na ganinsu a kusa dashi. -Ban taba tunanin zai ci amanata ba. -Eh mana, ai indai mutum taurin kai ne dashi zai gani... Kallon da yar uwar tashi tayi masa yasa ya kame bakinshi. Shi baban nasu ma bai damu ba, hasalima dariya yayi. -Shikenan baba, ba zamu kara yarda da kowa ba idan ba wanda suke kewaye da mu ba, nayi farin cikin ganinka a raye, na tsorata sosai da na gano, yana wasa da tunanin mu ne. Cewar Aya kafin ta kara rungume baban nasu. Suna komawa gida, Fally yayi matukar mamaki da takaicin ganin Dauda, a ranar haka ya wuni sukuku. A ranshi ya raya, dole yayi wani abu ganin ya raba Jinah da wannan mutumin, zai bi ko ta halin yaya ganin Jinah ta tuna dashi da kuma soyayyarsu. Bayan yan tagwaye sun bashi labarin ta yanda suka gane makircin Zumana, turasu yayi su tambayi Dauda ko ya taba jin irin makamancin labarinsa a wurin kawunshi; dan Adam da ya kasa tuna soyayyarshi da aljani. Dauda amsa masu yayi da eh, kuma har da ma tagomashin sanin yanda ake dawo da tunanin. Ya basu labarin komai da yayi masu karyar kawunsa ya fada mashi. Ba tare da wani tunani ba, Fally ya yarda da maganganun Dauda, har ya yanke shawarar da marecen nan zai aikata abinda ya fada masa. A bangaren Sarah, sauyi sosai ta gani ga Abdul, sai dai tayi tunanin wata kila saboda Jinah bata bar gidan bane ya dan dameshi. Yanke shawarar zuwa ta fahimtar dashi tayi, daman kuma sosai tayi kewarshi, da dadewa kenan rabon da ta jita manne a jikinsa, da wannan tunanin mai cike da tsantsar kunya ta karasa dakinsa. Tarar dashi tayi zaune, ya kurawa bango ido, hankalinsa na wani gu, a hankali ta rugumoshi ta baya, yayi firgigit ya mike. -Subhanallahi, ah ke ce? Wallahi har kin tsorata ni. Abdul ya fada cike da tsoro, ba tare da ya fahimci abinda Sarah take nufi ba. Sai dai lokacin da ta matso kusa dashi ta dora labbanta akan nashi, fiddo ido yayi waje kamar zasu bar cikin kurminsu. -Meye...haka...saboda.. Tsabar firgici ya kasa hada kalaman da zai fada. -Na san ka damu ne saboda ta tsaya, amma kar ka damu ba zata kara takuraka ba, zamu iya yin soyayyarmu babu shamaki. -Baki da hankali ne? Fita daga dakina yanzu yanzu, kin manta ke matar babana ce? -Daman nasan wata rana zaka ce min haka domin ba sona kake ba, yanzu na tabbatar da wawancina da na yarda da kai. -Ki fita dan Allah! Kallonsa take cike da damuwa da da na sani, ba tare da ta hana hawaye wanke fuskarta ba ta fice daga dakin. Da na sani fal a ranta, tana jinta tamkar hankicin da aka yi anfani da shi aka jefar. Abinda bata sani ba, Abdul ba zai iya tuna komai ba da ya faru tsakanin ita da shi, ko kuma in ce tsakanin ita da gangar jikinsa. Shi kanshi ya kasa fahimtar komai, yana jinsa kamar wanda ya samu tabin kwakwalwa na wani dan lokaci ko kuma wanda ya dauki kwanaki masu tsawo yana bacci. Tashi yayi da niyyar zuwa wajen kanwarsa, domin yana son suyi magana. Tarar da ita yayi tare da Jinah, ya nemi guri kusa dasu ya zauna. Kallon da yaga suna binshi dashi yake jin kamar ya aikata wani abu da shi ma bai san meye ba. -Me yake faruwa? Irin wannan kallo kamar na aikata wani mummunan abu? -Tambaya ma kake? Mtssww. Cewar kanwarshi. -Me nayi? Ganin basuda niyyar bashi amsa, ya cigaba da cewa: -Ko ma dai meye na aikata, ina neman afuwarku har cikin zuciyata, ina sonku kuma kun sani, idan na cutar daku to ba da sanina bane. Ba tare da ya jira jin ta bakin daya daga cikinsu ba, ya bar wurin, tunaninsa a wannan lokacin kawai ya koma Nigeria zai fi, ya kasa fahimtar komai a cikin wannan rayuwar, tunani yake ma idan ya zauna da wanne irin ido zai kalli matar babanshi, bordel rungumarsa fa tayi. Da marece, ya fara tattara kayansa, ya kuma ce da yar uwarshi ita ma ta hada nata. -Dan Allah Abdul, mu kara ko sati ne. Kar muyi irin wannan tafiyar ta farat daya. -A'a. Ya kamata mu tafi, kuma kinga an kusa komawa school. -Babu baba babu Mama a cen, ko ba komai nan munada yan uwa, dan haka nidai zan zauna anan. Ta fada da yar hayaniya. -Dan Allah Abdul, ku kara wasu kwanaki mana. Cewar Jinah da ta shigo. -To naji naji, kar ki wage mana wannan bakin naki. Cewar Abdul ga kanwarsa da yaga tana shirin fara kuka, tsalle tayi ta kankameshi tana murna. -Yauwa yayana na kaina, irin wanda ba kowacce kanwa ke da irinshi ba. -Eh ai na jima da sanin haka. -Banda dai girman kai. -Ai ba sai nayi ba, tuni kambun sauratana ya riga da ya mayar min shi katoto. Dariya su duka suka yi, dukansu ukun suna cikin farin ciki, matan a yanzu suka tabbatar da Abdul din da suka sani a baya ya dawo, mai raha da barkwanci. Zuwan Yan tagwaye yasa Jinah ta bar Abdul da Nafi, taja yaranta da niyyar zuwa su kwanta. Bayan ta kwantar da yaran, ta nufi hanyar zuwa wajen mijinta dake daki, sai dai akan hanyar taci karo da Sarah zaune ita kadai, ta buga uban tagumi, da yanayin damuwa a fuskarta, taso yi mata magana amma ta fasa. -Me yasa kazo ka tsabbace anan? Jinah ta tambayi mijinta. -Ba komai kawai yar gajiya ce. Dauda ya bata amsa, da murmushin tabbatarwa akan labbansa. Canja kaya Jinah tayi sannan ta kwanta kusa da mijinta, taga sauyi sosai a tattare dashi, amma hakan bai dameta ba ko ba komai yana kusa da ita. Bata jima ba tana tunani bacci yayi awon gaba da ita, wani mafarki ta fara yi mai firgitarwa. -A'a, a'a! Kar ka tabani a'aaa! Wayyooh, ka sakeni, dan Allah ka daina. Ihu da take yi kenan, a tsorace take, na ganin wannan mutumin da yake yawan tsoratata yayi mata fyade a cikin mafarkin, kuka take yi iya karfinta amma babu mai iya jinta. Ta kai har ta jika zanin gadon da zufar da take yi. Firgigit tayi ta farka, ganin duk halin da take ciki da murkususun da tayi ta yi bai iya tada Dauda daga nauyayyen baccin da yake ba, yasa ta gama kai da gwiwa, haka ta kasance har wayewar gari. Wannan tsoron kin sakinta yayi tsawon ranar. Wani lokacin ma sai ta dinga jin ana mata rada a kunne ba tare da ganin mai yi ba, wani lokacin kuma mutum take gani yana bayyanar mata yana bacewa akan idonta. Ayyanawa tayi a ranta idan haka ta cigaba da kasancewa to zata haukace. (....) -Fada min yaya plan namu yake tafiya? -Komai yana tafiya daidai! Zumana ya dade da fita daga filin tseren, shi kuwa wannan sakaran Fally tuni ya fada tarkona. Hahahah, bai san cewa yana haka kabarinsa bane. -Hahahahahaha!, ina alfahari da kaina! Zaka iya komawa, ka cigaba da aikinka. -Kar ki damu shugaba, wadannan tagwayen da ma duk wani karfinsu nan da ba da jimawa ba zasu zama mallakinmu. -A'a! Mallakina! Mallakina dai! Na kagu naga cikar burina!!!!!!!! *****************************""**** After un long moment! J'suis enfin de retour mes vrais 🤗 Ya hakurin jira? Fatan dai ba'a yi fushi da yawa dani ba? ©El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 18 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Cikin kankanin lokaci, Jinah duk tabi ta lalace, ko ina a jikinta kasusuwa ake gani, rama ta ban tausayi tayi ba tare da tasan wace irin cuta ke damunta ba, eh cuta mana me zuwa ba tare da sanarwa ba ko dalili, abar da kullum muke takatsantsan wajen ganin mun kare kan mu daga kamuwa da ita. Cuta bata bamu zabi. Muna iya wayar gari lafiya amma mu kwanta da ciwo, mu dinga jin wani yanayi da zafi da ba zamu iya misultashi ba wanda hakan zai sa muje asibiti domin a fada mana abinda ke damunmu. Sai dai ita tata cutar Jinah, har likitocin sun kasa ganota, sakamakon ganin abu yaki ci yaki cinyewa Sarah ta dauketa zuwa asibiti sedai an kasa gane sahihin abinda ke damunta. Gashi dai a jikinta da ka gani kasan batada lafiya, amma kuma sanin ciwon nata ya gagara. Ganin haka likitocin suka bata shawarar kawai taje birni domin a kara dubata amma taki a cewarta idan har likitoci sun kasa gane abinda ke damunta wata kila ciwo ne mai wucewa, ba babba ba. Sedai kuma kullum ciwon nata kara ta'azzara yake, wannan ma ne yayi sanadin jinkirin tafiyar su Abdul. Halin da take ciki ya tayarwa da kowa hankali ba kamar ma yan tagwaye da suka kasa yin komai har da karfin tsafinsu, a tsorace suke sosai. -Me kake tunanin shine sanadin rashin lafiyar mama? Aya ta tambayi dan uwanta. -Ina tunanin baba ne! -Me? Hakan ba zai yiwu ba, baka ga shima ya damu sosai ba, kuma shima yana iya kokarinshi ganin Mama ta warke. -Eh, amma idan fa shine sila ba tare da ya sani ba, baki lura ba hakan ta fara faruwa tun lokacin da ya fara abinda tonton Dauda ya fada mashi zai yi domin mama ta tuna dashi. Shuru yar uwar tashi tayi alamar tunani kafin tace: -Kuma fa kanada gaskiya. -Ya kamata muyi masa magana. -hakan za'a yi. Neman mahaifin nasu suka shiga amma basu ganshi ba, yanke shawara su jirashi suka yi. Kafin nan suka wuce wajen mahaifiyarsu. -Nan da ba da jimawa ba zaki warke mama. Cewar Aya. -Nayi kewar fadanki. Cewar Ayu. -Karya ne, Mama bata yi mana fada. -Eh gaskiya ne, Tanti Sarah ce ke yi mana fada. -Amma ita mama idan muka yi laifi, kawai zata ce : a'a rabin raina, ba kyau abinda kuke yi, ku daina kunji kuma kar ku kara sakewa. -Sannan sai ta kara da ina sonku sosai, kyawawan diyana. -Kuma abinda zamu yi matsayin hukunci, shine mu rungumeta. -Kuma ba zamu saketa ba har sai taso hakan. -Muna sonki mamamu ! Duk da halin da jinah take ciki, sai da ta jawosu jikinta ta kankamesu, sosai kalamansu suka tabata ta yadda hawaye suka kasa tsaya mata. Zuwa cen kuma ta fashe da kuka, sedai kukan nata kuma da nashi dalili, ba komai ba ta tuna face yanzu idan ta mutu a wanne hali zata bar 'ya'yanta, duk da ta tuna hakan hankalinta na matukar tashi ganin irin shakuwar dake tsakaninsu. Jinah bata daina kuka ba har lokacin da Dauda ya shigo dakin. Tagwayen fita suka yi suka barta daga ita sai mijinta. -Ni fa wannan koke koken naki sun fara isata! Cewar Dauda a fusace, idanu Jinah ta fiddo cike da mamaki. -Gaskiya na fara gajiya. -Me.. Me yake damunka? Tsawa fa kake min? Jinah ta fada tare da kara fashewa da kuka, ko sau daya mijinta bai taba yi mata haka ba. -Kiyi hakuri, ki yafe min, ba a son raina ba, ki yafe min dan Allah. Kinsan ina sonki fiye da komai. Mamaki ya kara dabaibaye Jinah ganin yanda ya koma yana bata hakuri. Zuwa cen Dauda kamar an bangajeshi yayi baya ya bugu da bango, yanayin fuskarshi ya fara canjawa, da ta nuna suffar mugun mutum sai kuma ta sauya zuwa ta nutsatsen mutum. Jinah bata ankara ba taji Dauda ya shaketa kamar zai kasheta, kokowar kwatar numfashi ta shiga yi, zuwa cen kuma ya saketa sannan ya rugumeta yana kissing dinta. Sosai Jinah ta tsorata da lamarin Dauda. Mikewa Dauda yayi, sannan ya fara buga kanshi jikin bango yana fadin : -Ka mutu ! Eh amma kuma gangar jikina ce ! Ni kuma ruhina ne ! Ba zan barka ka cutar da ita ba ! Ni ban damu da ita ba !... Juyawa Dauda yayi wajen Jinah sannan ya shiga juya kanshi hagu da dama, kuma duk lokacin da yayi hakan sai kamannin fuskarsa sun canja daga ta salihi zuwa ta mugu. Daga karshe dai ta muguntar ce tayi nasarar tsayawa, cike da mugunta ya dunfari Jinah kafin ya nausa mata wani naushin da yayi sanadin sumanta. A wancen ranar Aljana Hindu da mataimakinta makabarta suka je, sunje da niyyar kawo karshen rayuwar wannan aljanin ne domin taso da Dauda. Tayi anfani da ruhin aljanin a gangar jikin Dauda. Hakan yasa aljanin ya koma mutum ba tare da ya manta da tunaninsa na aljanu ba. Hindu tasan idan ta aika aljanin directly, tagwayen zasu iya halakashi. Amma yanzu wannan hadin da tayi shine kadai hanyar da zata iya samun cikar burinta ba tare da wata matsala ba, sedai kuma wata barazana da zasu fuskanta a yanzu shine, tsananin soyayyar da Dauda yake wa Jinah, da kuma zaman gangar jikinsa a kusa da ita, yasa kwalwar asalin Dauda ta fara aiki, a hankali a hankali yana dawowa Dauda. Gangar jikin ta fara kokowa da ruhin, da ganin ta hanashi yin duk wani abu da bai dace ba. A yanzu haka dai Aljanin ne ya dauki control din jikin ta yanda har ya sumar da Jinah, yanke shawarar zuwa ya samu uwar gijiyarsa yayi sai kuma ya tuna da yanda Hindu take ba zata yi jinkirin kasheshi ba domin bata son duk wani abu da zaya kawo mata cikas a cikar burinta. Bayan wasu lokuta Jinah ta farfado taga Dauda kwance a gefenta yana ta sharar bacci, a tunaninta mafarki tayi, ajiyar tayi tare da cewa : wannan wane irin mummunan mafarki ne nayi. (.....) Sarah ce ta shigo gidan a kasalance, Nafisa da gudunta tazo ta taimaka mata ta zauna kan tabarmar dake shinfide a tsakar gidan, dan kishigidawa Sarah tayi. -A ina kika je aunty Sarah ina nan duk na damu ? Nafisa ta fada cike da nuna kulawa. Tsantsar nuna kulawar da Sarah ke yi masu yasa a kullum take kara sonta, kuma tana damuwa idan ta ganta cikin wani hali. -Ganin likitoci sun kasa yin komai game da rashin lafiyar Jinah, shine na tafi neman mai maganin gargajiya. Sarah ta fada da muryar damuwa. -Kuma shine zaki tafi cikin wannan ranar, kema bakya tsoron wata rashin lafiyar ta kamaki ? Abdul ne ya karaso wajensu, ba tare da ya yarda ya hada ido da matar babanshi ba. Duk da abinda ke faruwa tsakaninshi da ita ba zai so ganinta cikin wani hali ba. Yar uwar tashi ce tayi masa bayanin inda Sarah taje, shiga yayi cikin kayansa ya dauko magani doliprane, da taimakon Nafisa Sarah tasha maganin, kafin wani dan lokaci taje tayi wanka, sannan Nafisa ta danyi mata massage kafin ta kyaleta tayi bacci. Haka gidan ya kasance tsit, kowa yayi bacci banda yan tagwaye dake jiran dawowar babansu. Bayan tsawon wasu awanni sai gashi ya dawo. -Ina ka tafi baba ? -Ina tunanin ai zaku iya sani. -Ai ka hanamu anfani da tsafinmu ga mutanen dake cikin gidan nan, idan ba ya zama dole ba. -Hakane. Yau tsawon watanni kenan Fally yake son ko ta yaya yaga ya dawo da matarshi, yanzu kuma da ya samu hanyar ance masa duk cikin aikin ne matar take fama da wannan ciwon. -Idan mama ta cigaba da rashin lafiya, ba zan taba yafe maka ba. Ayu ke fadawa mahaifinsu da alamar kashedi, kafin ya bar wajen yar uwar ta rufa masa baya. Shi Fally a tunaninsa ciwon nata na wani dan lokaci ne daga nan komai zai koma masu daidai. Abinda Dauda yace masa yayi shine : Sake yin wani alkwarin aure tsakaninsa da Jinah kamar a baya «Wata yar karamar wuka Fally ya dauko tareda yanka babban yatsanshi, itama haka Jinah tayi, sannnan suka hada yankakkakun yatsun nasu gu daya inda jinin nasu ya garwaya. Bayan sunyi hakan sannan Fally ya dauko wata kwarya mai dauke da wasu koren ruwa, ya fara sha sannan ya ba Jinah itama tasha. Jinah cire zanin dake daure kugunta tayi, sannan ta kara cire wanda yake daure a kirjinta. Kwantawa tayi akan wani jan kyalle dake shinfide a gurin babu komai a jikinta. Shima Fally dama wani gajeren wando kadai a jikinshi ya fiddashi, sannan ya zuba wasu ruwa a jikin Jinah, bayan wani dan lokaci sai ga wani maciji ya bayanna a hannunshi, sakin wannan maciji yayi yanata bin jikin Jinah, ita kuwa ko a jikinta, dan ta san wannan yana daga cikin siddabarun alkawarin nasu, kuma daman ta iya sarrafa dabbobi kamar sauran aljanu, kuma kasancewar kyawun dake gareta irin na aljanu yasa tana iya yin wasu abubuwa sosai wanda cikakken dan mutum ba zai iya ba. Macijin ya bace bayan wasu yan lokuta. Bayan wannan, cikin farin ciki Fally suka raya wannan rana kamar kowanne ango da amarya. Hakan zai nuna sun dau alkawarin zama na har abada a tare.» Wannan shine abinda ya faru ranar aurensu, ranar alkawarinsu. Sai dai yanzu da yake son ya sake yin haka a cikin mafarkin Jinah, komai sai ya jagule, domin ita Jinah, ta kasa fahimtar komai, ta tsorata da ganin wannan mutumin yana tursasata shan wani abu da bata san ko meye ba, da kuma yanda taga maciji na tafiya a jikinta, kuma ta firgita sosai na ganin mutumin nan ta karfi yana yi mata fyade. Komai da ya kamata suyi cikin soyayya ita gani take ta karfi ne yake mata. Shi kuma ganin yake komai zai daidaita daga baya zasu zamo a tare kuma hakan shine muradinsa. Sam ya kasa bude ido ya farka ya kwaci kansa daga tarkon aka yi masa, ya gane wannan ba soyayya bace yake nunawa Jinah, kawai yana cutar da ita ne. Dadi da kari ma, kusan kullum sai ya bayyana akan idanunta sannan kuma ya bace, hakan ma bai san dab yake da haukatata ba. A zahirance Fally bai san hakikanin abinda yake kokarin yi ba, bai san yana sanya rayuwarsa, ta Jinah da kuma ta 'ya'yansa a hadari bane. Yayi nisan da ba zai iya gane abinda Dauda ya fada masa zai kaishi ga rasa duk wani farin ciki nasa, kuma a hakan zai cigaba ba tare da yasan wadda yafi tsana a duniya wato Aljana Hindu yake taimakawa da kokarin cika mata burinta ba. ---------------------------------------------- Domin sanin abinda zai biyo baya kan abinda Fally yayi. Mu hade a Chapter na gaba. Fatan wannan chapter ta kayatar daku ? Zan yi farin cikin ganin ra'ayinku. Sannan ina bada hakuri akan kuskuren typing. *©El_Ashtar* Allez à la prochaine Readers 💪 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 19 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp A wurin mutane soyayya ba wani dogon nutsatsen kogi bane a'a, a wurin mutane soyayya dogon kogi ne mai cike da igiyoyin ruwa masu saka kogin yayi sama yayi kasa. Haka a wurin aljanu, banbancin ba mai yawa bane, sai dai akwai muhimmanci mai tsauri a soyayyarsu, suna tsananin yarda akan wanda suke so, ta yanda zasu iya sadaukar da komai akan wanda suke so, nuna kulawa da muntuntawa da gujewa duk wani abu da zai cutar dashi, wannan kenan a cikin soyayyar aljanu. Amma kuma idan aka samu akasin haka daya daga cikin masoyan wani ya cutar da dayan, alakar dake tsakaninsu zata wargaje kuma dukansu biyun da wanda aka cutar da wanda ya cutar kowanne zai biya bisa laifin dan uwan nasa. Hukuncin kuwa ba komai bane face mutuwa. Abinda Fally yayi kenan, bayan yayi magana da 'ya'yanshi, ya gano rashin lafiyar Jinah shine sila amma sai yace ai abu ne mai kyau domin dan ya gyara gobenshi ne. Bai san abinda yake aikatawa ba, a hankali yana wargaza muhimmiyar alakar dake tsakaninshi da Jinah ne kuma idan har ya cigaba dukansu zasu rasa rayukansu. Hindu tana sane da hakan, kuma wannan shine plan dinta, da kanta ta tsara komai daki-daki, kuma abinda zaifi kayatar da ita shine yayin da Fally da Jinah suka mutu haka zai sa yan tagwaye suyi rauni, ta yanda ba zasu iya anfani da karfinsu ba. Daga nan zata sa a kamosu ta barka kirjinsu ta ciro zuciyoyinsu ta cinyesu danyu. Daga wannan lokaci babu wanda zai iya kwatanta karfinsa da nata, karfinta zai karu, kuma zai mayar da ita gagara badau ki mutuwa (Immortelle). (...........) A gidansu Sarah, alfigir ya keto, duka mutanen gidan idanunsu biyu tun awowi 3 da suka shude, suna kan Jinah, sakamakon farkawa da tayi da kara, ciwo mai tsanani da kuma sambatu, wanda yayi sanadin taso Sarah, diyan mijinta da kuma yan tagwaye. Kowannensu cikin tashin hankali yake, basu san me zasu yi ba, su kaita likita? Sun riga da sun san abinda likitoci zasu ce. Sarah bayan tayi iya kokarinta na ganin ta rarrashi Jinah. Da gudunta taje ta jiko ganyen maganin da wani mai maganin gargajiya ya bata, lokacin da ta bata ta sha, Aya da dan uwanta ta dalilin karfinsu, suka saka uwar tasu bacci, su kuwa sauran sai suka dauka ganyen maganin ne yayi aiki. Fita suka yi suka barta ita kadai domin ta samu hutu. Yan tagwaye wajen babansu suka je, suka ce ya dakatar da abinda yake. Ce masu yayi, zata warke ne kawai idan ta tuna dani, a yanda na kusa cimma burina, ba zai yiwu na dakatar ba. Abinda ya fadawa yaran kenan. -Ka cika son kai baba. Cewar Ayu, kafin yaja hannun yar uwarshi su bar wurin. Shiga dakin mahaifiyar tasu suka yi, suka tarar har yanzu tana bacci. A bangare daya kuma na dakin, Dauda ne zaune a kasa hannuwansa dafe da kanshi. Matsawa suka yi kusa dashi, anan suka ji yana ta wasu sambatu. Aje hankalinsu suka yi domin fahimtar abinda yake fada. Anan suka ji yana fadar : -Ba zan iya cutar da ita ba! Me yasa nake yin haka? Amma kuma ba ni bane! Zan yi fada domin ta! Ta dalilina ne ka dawo, zan fadawa shugaba, zata batar da kai har abada! Daga nan kuma wannan karamin ahalin naka zai biyo baya. Ba zan barka ka aikata hakan ba! Ba zan barka ka cutar da... Maimata kalamansa na karshe yayi ta yi kafin ya fadi sumamme. Kallon juna yan tagwayen suka yi, ba tare da dayansu yace kala ba. Ayu ne ya saka hannunsa cikin rigar Dauda tareda dora hannun daidai kan zuciyar Dauda, shuru yayi na dan lokaci bayan ya janye hannunsa kafin yace : -Bansan ko menene shi ba. -Kamar yaya? Yar uwar tashi ta tambayeshi da mamaki. -Ban sani ba ko shi mutum ne ko aljani. -Me kake fada ne? Mutum ne mana! -Eh, da gani mutum ne, amma jin bugun zuciyarshi zai tabbatar maki da ta mutum ce kuma ta aljani ce. Kasa yarda yar uwar tashi tayi, sai da itama tayi da kanta ta tabbatar. Dukansu cikin rudu suka fada. Kokarin tayar da Dauda suka yi domin yayi masu bayanin meke faruwa dashi amma kuma yaki tashi. Kalaman Dauda ne ke ta lugude a kwakwalan yan tagwaye, kafin dukansu tunaninsu ya basu aljani ne ya shiga jikinshi. Daukar Dauda suka yi suka bace daga dakin nasu. Anan suka shiga bin duk wata hanyar da Dauda zai farfado, sai dai basu suka samu nasara ba sai da sanyin safiya. Kokarin karantar tunaninsa suka yi amma hakan ya faskara, wannan ya tabbatar masu shi ba aljani bane kuma shi ba mutum bane. -A zahirance kai waye? Ayu ne ya fara magana. -Ruhina aljani ne, gangar jikina mutum. -Ta yaya haka zai yiwu? Cewar Aya. -Ta karfin tsafin shugabata Hindu. -Wacece Hindu kuma meye dalilinta? -Hatsabibiya ce ita, Aljana mai karfin tsafi marar misaltuwa, kuma tana son kara zama gagarabadau ta hanyar samun naku karfin. -Me? Ta yaya? -Ta riga da ta fara, kuma sai ta karasa. -Tanada alaka da ciwon mahaifiyarmu? -Eh. -Kuma da abinda babanmu ke yi? -Eh. Zai yi sau 10 ne, a dare goma, daren jiya shine na dare na karshe. Zuciyoyin yaran ne suka buga duum. -Me zai faru bayan hakan? -Iyayenku zasu fada doguwar sumar da zata dauke su tsawon wasu kwankaki kafin su mutu. Kuma da hakan ta kasance zata juyo kanku. Zaku fara yin rauni, ku kasa amfani da karfinku, daga nan zata kamaku ta ciro zuciyoyinku ta cinye. Da gudu Aya ta nufi wajen iyayenta domin tabbatar da abinda Dauda yake fada, sai dai kuma da zuwanta ta tarar dasu sumammu, wurin mahaifiyarta ta durkusa ta fashe da wani azabataccen kuka wanda yayi sanadin jawo hankalin Nafisa, Abdul da Sarah. Ganin Jinah taki farkawa kuma bugun zuciyarta kadan kadan yake yi, yasa suka nufi asibiti da ita duk sun san ba lallai bane likitoci su iya yin wani abu. Shi kuwa Ayu tsayawa yayi wurin Dauda domin sanin yadda zai iya wargaza plan din Hindu. -Amma ta yaya zamu dakatar da ita? -Ba zaku iya ba, amma akwai hanyoyi biyu da zaka iya daidaita wannan matsalar. -Wanne hanyoyi ne? -Zaku iya cire zuciyar Hindu kafin ku rasa karfinku, hakan zai sa kai da yar uwarka ku rayu, amma Iyayenku zasu mutu. Ko kuma hanya ta biyu, daya daga cikinku yaci ganyen Fula, itaciya ce dake kashe aljanu. Wannan itaciya guba ce da zata sa yayi rauni, daga nan sai yaje ya nemi Hindu, ganin halin da yake ciki zata dauka ko plan dinta ne yayi aiki, daga nan zata cinye zuciyar mai guba sai ta mutu shi ma mai zuciyar ya mutu. Hakan zai sa Iyayenku su tsira, sannan mahaifiyarku zata tuna da babanku da duk wata rayuwa da tayi da aljanu. Hawaye ne suka kwaranyo daga cikin Ayu kafin yace bana son mama ta mutu. -Kuka kake yi Ayu? Cewar yar uwarshi data bayyana kusa dashi. Jin bai bata amsa ba, ta cigaba : -Ba zasu mutu ba, ba yanzu ba. Goge hawayen fuskarsa yayi tare da rungume yar uwar tashi. Yaji dadin kalamanta sosai. -Nayi miki alkawarin babu abinda zai faru. --------------------------------------------------------- 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 20 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Aya da Ayu sun shiga rudin tashin hankali na ganin halin da iyayensu ke ciki, babu wata hanya da ta rage masu ta ceton iyayen nasu. A tunanin Aya kenan, domin dan uwanta tuni ya yanke hukuncin abinda zai yi, ya yanke hukuncin tafiya ya sadaukar da rayuwarshi akan iyayenshi da yar uwarshi. -Je ki ga mama, sannan ki tsaya kusa da ita. Ayu yaba yar uwarshi umarni. Ya kara da cewa : -Ni zan je wurin baba. Sai dai karya yayi mata. Gyada kai yar uwar tashi tayi ba tare da bata lokaci ba tabi umarninsa. Shi kuwa sai ya dauki hanyar zuwa wurin Hindu tare da rakiyar Dauda. Kafin su karasa sai da suka biya ta cikin bakin tsibiri wanda mutane basu iya ganinsa, suka debo ganyen Fula, a take Ayu ya saka a baki ya tauna kafin ya hadiye. Bayan yayi hakan, suka dauki hanyar gidan Hindu. Suna zuwa kusan gidan, Ayu yayi kamar ya galabaita. Koda Hindu ta tsinkayesu tayi wata kururuwar jin dadi. Ayu sai ganin yayi ta dira gabanshi. Kyakyawa ce sosai, ba za'a kwatanta gashinta da na mahaifiyarshi ba wajen kyau. Hakoranta har wata walkiya suke tsabar haske da kyau, batada siffar miyagun aljanu. Katse masa tunani tayi ta hanyar tambayar Dauda. -Amma abin yayi sauri kuma ina yar uwar tashi? Bata samu amsar tambayarta ba, sai dai wata mahaukaciyar dariya da Dauda yayi. Hindu da Ayu cike da mamaki suke kallonsa. -Kayi tunanin na kawoka nan ne domin ka kashe shugabata? To ba komai nayi ba face saukaka mata shirinta. Ayu ya fahimci tarko ne ya fada, kokarin amfani da karfinsa yayi amma ya kasa sakamakon gubar dake jikinsa. Aljanin bayani ya yiwa Shugabar tashi da dalilinsa na yin haka, ita kuwa ta kara kecewa da mahaukaciyar dariyar jin dadi. Kawai zuciyar Ayu zata cire daga nan zata wanketa da wasu ruwan tsafi shikenan zata iya cinta ba tare da wani lahani ba. -Toh idan har na mutu iyayena zasu tsira? Ganin dariyar da suka kara kecewa da ita, ya gane zai mutu ne ga banza ba tare da ya ceci iyayensa ba. A zahirance ganyen Fula da yaci, ya kama duk wata hanyar jini ta jikinsa, sannan ya raunanar dashi ta yanda ba zai iya amfani da karfin tsafinsa ba. Kuma idan gubar ta dauki kwanaki cikin jikinsa zai mutu. -Da gaske akwai hanyar da za'a iya cetonsu? -Sosai ma. -Fada mini, ina saurare. -Babu abinda zai amfaneka domin ba zaka fita nan a raye ba. -Na sani kawai ina son na sani ne. -Kawai tasan ko shi waye kuma ta yafe masa. -Ban gane ba. -Ba amfanin ka gane. Manfa kawo min wukar nan. Cika umarninta aljanin yayi, sai dai kuma ya tsaya cak yana waswasin ba shugabar tashi wukar, a wannan karon ma, ruhin da gangar jikin suka shiga dambe, Dauda na kokarin hana aljanin dake jikinsa bayar da wukar ga Hindu. Kiran sunan Aljanin da Hindu tayi, yasa aljanin yayi nasarar daukar control din gangar jikin. -Me yake damunka ne? Hindu ta tambayi aljanin a fusace. -Babu komai shugabata. Amsar wukar tayi, ta juya kan Ayu da yake ta kallonta ba tare da karfin kokarin kare kansa ba. Kwantar dashi tayi tare da dauko wani farin gari kamar hoda ta shafa masa kan kirjinsa, sannan ta dauki wukar ta kai daidai kan bakinta a take ta huro wuta daga bakinta zuwa kan wukar, ba ita ta dakatar da wutar ba har sai da taga wukar ta koma jawur. Sannan ta nufo kirjin Ayu da ita, da ganin haka shi kuwa ya runtse idanunsa, yana takaicin mutuwar da zai yi ba tare da ya ceci iyayensa ba.... -Ki dakata! Cewar wata murya cikin karaji, Ayu ya gane mai muryar, bude ido yayi tareda ajiyar zuciya. Ba kowa bace face Aya yar uwarshi. Kallo daya ta yiwa wukar dake hannun Hindu, wukar ta fadi kasa. Ajanin dake jikin Dauda ya dauki wukar ya dumfaro Aya da ita, ganin haka Hindu ta ari wannan damar ta gudu, sosai take shakkar karfin yan tagwayen nan. Sumar da Dauda Aya tayi ta hanyar nunashi da yatsa, yayi sama ya fado kasa. Daga nan ta bace dasu duka zuwa gidansu. -Ya aka yi kika gane inda nake? -Zan iya sanin inda kake a kullum, ba kamar idan kana cikin hadari. Wannan ba shi bane mai muhimmanci a yanzu, zaka sani a duk ranar da na shiga hadari nima. Yanzu fada min ya aka yi ka tsinci kanka a cikin wannan halin? Labarin duk abinda ya faru dan uwan nata ya bata. A'a...a'a.. take maimaitawa tana girgiza kai. -Kana..kana.. kana nufin kaima zan rasaka. Da kai nake tunanin zamu ceci iyayenmu kuma shine kai ma zaka tafi ka barni. Kada ka yimin haka dan uwana. -Ki yafe mani Aya. Wannan gubar tana daukar lokaci kafin ta kashe mutum. Kar ki damu zamu samu mafita kafin lokacin. Abu mai muhimmanci dai a yanzu, mu ceci iyayenmu. A yau wannan muguwar aljanar ta bayyana mani, babu abinda ba zamu iya ba da karfin mu. -Amma ta yaya zamu san abinda zamu yi? -Dauda, ko kuma nace aljanin dake jikinsa, bawanta ne shi, dole zai san yanda zamu yi. Ruwa masu sanyi Aya ta zuba masa a jiki, firgigit yayi ya tashi tare da mikewa tsaye. Kokarin guduwa yake, amma yaji kafafuwansa kamar an saka masa siminti. -Zauna! Aya ta umarceshi, ba bata lokaci yabi umarninta, bayan ganin shugabarsa da yayi, wadda duk duniyarsu ake tsoronta ta gudu gaban wannan yarinyar, waye shi da ba zai ji tsoronta ba. -Ta yaya zan iya ceton dan uwana da kuma iyayena? -Na...na rantse miki, ban sani ba! -Kasan yanda za'a dawo da tunanin mamarmu? Cewar Ayu. -Me hakan zai amfanar ne? Aya ta tambayeshi da mamaki. -Hindu tace, domin cetonsu, kawai sai ta tunashi sannan kuma ta yafe masa. Da farko ban gane me take nufi ba, amma da nayi tunani na gane da iyayenmu take. -Kanada gaskiya. Maza muna sauraronka! Ta yaya zamu yi hakan? -Dole sai kun rushe alakar dake tsakanin mahaifiyarku da kuma uwar rikonta wato kakarku wadda ta haifi babanku. Kakarku ta mutu, naji wannan ne daga bakin Hindu. Indai har Jinah ba zata iya tuna rayuwarta ta baya ba, to saboda alakar dake tsakaninta ne da kakarku. -Ta yaya zamu iya gane menene ya hada alakar tasu? -Wannan mahaifiyarku ce kawai zata iya sani. -Amma bata cikin hayyacinta, kuma ma ba zata iya tuna rayuwarta ta baya ba. -Zaku iya bincikawa a cikin kwalwarta. -Da gaske? -Eh to ina tunanin haka, domin shugabata tace min ba abinda ba zaku iya ba. -Ta yaya zamu yi haka? -Ban sani ba. Ba tare da bata lokaci ba, Aya ta nufi inda mahaifiyarta take. Ganinta yasa taji wani abu mai radadi yabi duk ilahirin jikinta, a kwance take tamkar gawa. Tsoro ne ya kamata, na kar taje ta tabata taji babu rai a jikinta. Daurewa dai tayi, ta runtse idanunta kafin ta dora duka hannuwan nata biyu kan goshin mahaifiyar tata, da farko kasa ganin komai tayi, kafin daga baya kamar walkiya taga tunanunnukan mahaifiyarta na baya. Cigaba da dubawa tayi har ta kai ga wani wuri inda taga wata karamar yarinya zaune tare da wata mata suna magana. Tabbas wannan mamata ce da kakata. Ta fada cikin ranta. -Ina so na fada maki wani abu, domin nasan yanzu kinyi girman da ya kamata ki gane. Cewar Matar. -Menene mama? -Ni ba asalin mahaifiyarki bace, mahaifiyarki ta rasu yayin haihuwarki, kuma ita ta bani amanarki. Kuma ita bil'adama ce mu kuwa aljanu ne. Kuka yar karamar yarinyar tayi kafin tace : -Na dade ina jin sauran yara na ce mani bil'adama amma ni na kasa fahimta. Kenan shikenan daga yanzu ke ba mahaifiyata bace? -Sam ko alama, ni mahaifiyarki kuma zan cigaba da kasancewa mahaifiyarki har abada. Ke 'ya ce da banyi tunanin samu ba, ke komai ce gareni 'yata Jinah. -Nima mama, ina sonki kuma ina son na zama aljana kamarki. Murmushi uwar tayi. -Ai ba mai yiwuwa bane 'yata, sai dai zaki yi kama damu, kuma ma kyanki ba kasafai ake samunsa ba ga bil'adama. -Da gaske? -Sosai ma, matso ki gani. Matsowa yarinyar tayi, matar ta debo wani dogon gashi daga gashin kanta ta dora kan na yarinyar tare da shafa shafa gashin. Cikin dakiku kadan gashin kan yarinyar ya kara tsawo har kan mazaunanta. Yarinyar tana ta murna ganin gashinta ya koma irin na sauran 'ya'yan aljanu. Aya kara ganin wani tunanin tayi, matar dai ce da kuma karamar yarinyar. Wannan karon, matar fidda zobenta tayi sannan ta dunkuleshi a hannunta, tana budewa sai ga zoben ya zama biyu kuma iri daya. Sakawa Yarinyar tayi daya, sanann ta sakawa kanta dayan. Wani tunanin Aya ta kara gani. Sai dai wannan karon ta gane mahaifiyarta ce. Tana kwance kasa da alamun bacci take, wannan matar ce tsugunne gefenta. -Idan kika tashi ba zaki tuna komai na rayuwar da kika yi damu ba, sannan zaki rayu da bil'adama yan uwanki. Cewar matar kafin ta bar Jinah a gurin. Bayan wannan Aya bata kara ganin wani tunanin ba. A nan ta fahimci wannan tunanin su ke nuna alakar dake tsakanin Jinah da kuma uwar rikonta. Ta fahimci abinda ya kamata tayi, anan take tayi kokarin yin kudirinta. Sai dai a daidai lokacin sai ga su Sarah sun shigo dakin. Ta so ta jira har su fita, amma kuma sai tayi tunanin yanzu duk wani minti da zai shude barazana ne ga rayuwar iyayenta. Fita tayi daga dakin sannan ta sake dawowa amma wannan karon su Sarah basu ganinta. Shiga bincikar gashin mahaifiyarta tayi wai ko zata ga na kakarta, amma sai dai da yake gashin kala daya ne sai ta kasa tantancewa. Daga karshe dai yanke shawarar ta yanke gashin gaba daya tayi. Kara Nafisa da Sarah suka saki ganin gashin kan Jinah yana ta zubewa kasa. Shi kuwa Abdul fita yayi da sauri ya kira likita. Lokacin da likitan yazo, kiransu yayi duka ukun zuwa ofishinsa. Nan Aya ta samu dama ta cigaba da aikin da take. Tana gamawa ta cire zoben dake dan yatsan Jinah. Yanzu abu na uku ya rage masu, abinda ta kasa fahimta a cikin tunanin kuma bata san ko meye ba. A cikin ofishin likitan, su Sarah sun zura masa na mujiya domin jin abinda zai ce. -Ina mai baku hakuri. Ya fada, tuni Sarah taji zuciyarta kamar zata fito daga kirjinta. -Likita me yasa kake bamu hakuri, ba abinda fa muke son ji bane. Cewar Abdul da kaguwar jin dalilin likita. -Muna tsare da ita ne a banza. Babu wani abu da zamu iya yi mata. Abun yi anan shine ku mayar da ita gida ta karasa sauran kwanakinta. Domin kunga nan karamar asibiti ce mu kan mu muna da bukatar gadon domin wani majinyacin. Kuyi hakuri dan Allah. Ba tare da tace uffan ba, Sarah ta juya ta koma dakin da Jinah take su Abdul na biye da ita. Ba karamar razana suka yi ba, ganin gashin kan Jinah zube a kasa iska na dauka, kanta babu komai kamar wadda aka yiwa sabon kolo. Durkushewa Sarah tayi, ta shiga rera kuka mai ban tausayi haka ma Nafisa ta kama mata suna tayi. Abdul ne yayi karfin halin tsince gashin ya zuba a leda, da taimakon wasu ma'aikatan suka bar asibitin zuwa gida. Haka su Sarah suka cigaba da kuka har suka kai gida. -Kalleki, yarinya dake, da kuruciyarci kike shan wannan wahalar. Gashi yanzu zaki tafi. Wayyo Jinah, me zan yi ne domin ki tsaya. Ta dalilinki nasan me ake cewa samun 'ya. Kada ki rabani da wannan farin cikin tun yanzu, kiyi tunani akan yaranki Jinah. Suna bukatarki a kusa dasu... Kuka yaci karfin Sarah ta yanda har makoshinta ya fara yi mata ciwo. Haka Sarah ta zauna kusa da Jinah har lokacin da Abdul ya shigo dakin. -Na samu tayi bacci. Bayanta Sarah take dubawa domin ta tabbatar idan da ita Abdul yake. Domin sam Abdul ya daina yi mata magana. -Wa..wa kenan? -Nafisa -Ah hakan yayi kyau, ai dole tana bukatar bacci. -Ke ma ya kamata ki kwanta. -Ba.. ba zan iya ba, ina tsoron na kwanta na tashi naga bata a raye. -Nima wannan nake tsoro. -Su kuma yan tagwaye baki gansu ba? -Ah suna dakina, Ayu yayi bacci ita kuma Aya tana zaune kusa dashi. Ina tunanin basu fahimci halin da ake ciki ba. A kusa da ita ya zauna, suka cigaba da gadin Jinah kamar hakan zai hana mutuwa tazo daukanta. A bangaren yan tagwaye kuwa. Aya ta bayyanawa dan uwanta duk abinda tayi sannan ta fada masa abu na ukun da bata san meye shi ba, kuma dole sai ta ganoshi ta lalatashi kafin iyayensu su rayu. -Gara da kayi kamar kana bacci lokacin da Abdul ya shigo. Hakan zai kawar da hankalinsu daga garemu. Cewar Aya ga dan uwanta. -Toh me kika ce masu game da Dauda? -Ce masu nayi ya tafi nemo wa mama magani. -Makaryaciya! Ayu ya fada cikin sigar zolaya, murmushi Aya tayi. -To yanzu me zamu yi? Bansan meye cikon abu na uku dake da alaka da mamarmu da kuma kakarmu ba. Kawai abinda na sani ta tattare kayan mamarmu, sannan ta dauketa ta kaita nesa kafin ta sumar da ita sannan ta barta a wurin. -Kar da ki damu zamu gano ko menene. -Amma kuma lokaci tafiya yake, idan bamu sameshi ba fah, zasu mutu Ayu, shikenan zamu zama mu kadai muka rage. ------------------------- Voilaaaaaaaaaa ! Anan zan dakata sai kuma wata chapter idan Allah ya kaimu. Fatan kunji dadin wannan chapter, idan kuwa hakane ku nuna min ko da stickers ne 🤓 A tunaninku meye abu na karshe da yayi saura a alakar Jinah da uwar rikonta? Sai naji daga gareku! 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 21 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Esperanza, ban sani ba ko kun taba jin wannan sunan, duk da ba suna bane na hausawa, amma masu karance karance da kuma kallon fina finan kasar Italia ko na kasar Spain ba zasu rasa jin wannan sunan ba. Akwai mutanen wannan kasashen da dama dake da irin wannan sunan Esperanza, wanda a hausance zamu iya bashi ma'anar "Sa rai". Wannan kalmar Sa rai, tana karawa mutum karfin gwiwar rayuwa, muji mun kaunaci mu rayu, sa ran cigaba da al'amuranmu na yau da kullum, da sa ran jiran gobe mai kyau. Dan haka komai yanda yau taki yimana dadi, mu sa ran gobe zata zo da dadi. Wannan kalmar tayi tasiri sosai a gun yan tagwaye, yanda basu fidda ran ganin samun lafiyar iyayensu ba, yau gashi cikin ikon Allah sun gani. Aya da Ayu ne kwance kusa da mahaifiyarsu, tana shafa sumar kansu. Farin ciki ne marar misaltuwa akan fuskokinsu, tunda Jinah ta farfado suke like da ita ta yanda basu ma yi kokarin sanar da sauran yan gidan ba. Ganin abun nasu ba mai karewa bane, Jinah tace masu suje su kira Sarah, babu wanda ya motsa cikinsu, kowanne jiran dan uwanshi yaje yake. Jinah cewa tayi Ayu yaje, ba tare da yana so ba ya tashi zuwa aiken. -Sarah, Abdul, Nafi! Mama ta tashi! Yana fadar haka ya juya da gudu ya koma wajen mamarshi. Sarah sakin kwaryar dake hannunta tayi, kwaryar kuwa ta fashe abinda ke ciki ya watse kasa. Ko rige rigen shiga suka yi ita da 'ya'yan nata zuwa dakin Jinah. -Alhamdulillahi! Abinda suke ta firtawa kenan tsananin murna. Babu wanda ya iya tambayar ta yaya aka yi ta warke, ko ta yaya gashin Jinah ya sake fitowa wanda hakan aikin yan tagwaye ne. Dawowarta a Jinah da suka sani shi kadai ma ya ishesu. Sarah da Nafisa har da kukan murna suka yi, shi kuwa Abdul rungume Jinah yayi kamar ba zai saketa ba. Suna ganin wannan wani ikon Allah ne. Shuru dakin yayi na wani lokaci kafin Sarah tace : -Abdul, ka raki yar uwarka kasuwa ta siyo wani abun da za'a gyarawa Jinah nasan dole tana jin yunwa. Ta fada tana mikawa Nafisa Jika biyar (5000fcfa). -Yanzu kuwa Aunty! Nafisa ta fada da hanzarinta na son zuwa kasuwar. Fita tayi Abdul yabi bayanta. Bayan Tafiyarsu Jinah ta fara kuka. -Ki daina kuka mama. Cewar Aya. -Kiyi shuru Jinah, ki daina kuka! Sarah ta fada. -Na tuna komai Sarah, komai ya dawo min. Yarintata, dangina komai... Rungumeta Sarah tayi tana cewa : -Kiyi hakuri komai zai wuce, yanzu dai ya kamata ki kwanta ki huta. -Ba zan iya ba, ba zan iya ba Sarah! Take ta maimaitawa tana kuka, abubuwa da yawa ke ta dawo mata. Tana cikin farin ciki amma tunawa da rayuwarta ta baya ne ya sanyata kuka ba kamar ranar da ta rabu da dangin nata. Abinda yafi daga mata hankali shine rashin sanin halin da iyayenta suke. Yan tagwaye sun fahimci halin da mahaifiyar tasu take ciki, shi yasa da Sarah tayi masu tayin su fita su bar mamarsu ta dan huta yasa basu yi musu ba. Tana zaune ita kadai cikin daki, tun daga nesa take iya juyo alamun zuwan Fally, rarraba ido ta fara ko zata ganshi, ba bata lokaci sai gashi ya bayyana kusa da ita. Duk da ya canja hakan bai hana ta kasa ganeshi ba. -Fally! Tsalle tayi ta fada kanshi. Shima cike da murna yace : -Jinah! Masoyiyata! Nayi tunanin na mutu, ba zan sake ganinki ba, ba zamu taba dawo da soyayyarmu ba. Nayi kewarki sosai! -Ni kuwa, ban ma iya tuna rayuwata ta baya ba, amma ina jin kewarka sosai a cikin raina. A baya na dade ina jin akwai abinda na rasa, wanda ya zama tamkar cikon barin jikina. -Ba zamu kara fadar haka ba, babu abinda nake so da ya wuce ki kasance kullum a cikin hannuwana har na sauran kwanakina. Har abada, ba zamu sake rabuwa ba. Ina tabbatar maki ba zan jure ba, idan haka ta kasance, zan mutu ne anan take. Haka suka zauna tsawon wani lokaci, Jinah ta manta da abinda take son ta tambayeshi. Shi kuwa Fally, ji yake da ya matsa ko na yan dakiku ne, to zai kara rasata. Da wannan tunanin, har lokacin da su Sarah suka dawo dakin bai tafi ba amma su basu ganinshi. Kowa na gidan na nan amma banda Dauda, a take Jinah taji ba dadi, tanada wani auren da wani mutumin, anya kuwa Fally ya sani. Tambayar da take wa kanta kenan. A take kuma taba kanta amsa, Wata kila bai sani ba, tunda bata ga wata alama da ya nuna mata ba. Haka gidan suka zauna anata hira har dare ya raba tsakiya kafin kowa yaje ya kwanta. Sai dai Fally da Jinah cigaba da hira suka yi kamar ba zasu kare ba. Kamar zasu ba junansu labarin duk abinda ya faru tsayin rayuwarsu. Zuwa cen Jinah ta jero masa tambayoyi : -Wai me ya faru bayan bani nan? Ta yaya aka yi na dauki tsawon wannan lokacin ban tuna rayuwata ta baya ba? Ina su mama? Fuskar Fally juyewa tayi zuwa ta damuwa. Sai kuma ga hawaye sun zubo masa. -Mama ce, ita ce ta mantar dake komai. Domin ki rayu nesa damu kuma kar kiyi tunanin dawowa. Domin rayuwa a cikin mu hadari ne gareki. Ranar da kika tafi? Kin tuna? -Eh, a ranar da muka yanke zama na har abada tsakanin mu. -Rana mafi dadi a garemu. Murmushi kowannensu yayi. Kafin kuma fuskar Fally ta sauya. -A ranar ne kuma duk wani bakin ciki ya shigo rayuwarmu. Labarin duk abinda ya faru ya bata, har zuwa lokacin mutuwar iyayensu. Dakatawa yayi yana kallon Jinah da ta kasa dena kuka jin labarin halin da masoyinta ya shiga. Hankalinsa ne ya tashi, baya son ganinta cikin wannan halin. Sai dai yafi shiga tashin hankali da ya tuna yanda zata ji idan taji mutuwar iyayensu. Katseshi kuwa tayi da tambayar : -Su mama fah, suna ina? -S..un..sun.. -Ka fada min Fally! -Sun mutu. -A'aaaaa ba gaskiya bane! Ka fada mani ba gaskiya bane Fally! Mama tayi min alkawarin ba zata taba barina ni kadai ba, zata kasance dani har tsawon rayuwata. Kuma ita da baba zasu ga jikokinsu da zana haifa... Jin labarin mutuwar iyayenta duka biyun a lokaci guda ba karamin tashin hankali bane gareta. Taci kuka sosai kamar hawayen nata zasu kare. Fally kasa jure kukanta yayi, ya hade bakunansu wuri daya, wani zai dauka kissing dinta ne yake a'a, yana kokarin zuke duk wani zafin da Jinah take ji ne yana mayar dashi jikinsa. Jinah ta gane hakan sai tayi kokarin ta kwaci kanta amma kuma shi ya hana. Fally, har sai da ta kai zafin yayi masa yawa, kasa jurewa yayi ya kwanta kan gadon. Jinah zata yi magana ya dakatar da ita da hannu, shuru tayi tare da kwantowa kan kirjinsa, a hankali a hankali yaji zafin yana ragewa, ya gama fahimtar Jinah maganin duk wata cuta ce gareshi. Bacci ne ya dauke Jinah, shi kuwa ya kasa bacci, domin wani sabon tunani ne ya takurashi. Shin ko zata iya yafe masa idan tasan abubuwan da ya aikata mata domin memory ta ya dawo? ------------------------------------------------------ Alooooooooooooors, ya kuka ga wannan chapter? Ayi ta hakuri da typing error. See u next chapter abokai 😍 ©Al_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 22 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp "Akwai wata budurwa a wani kauye mai suna Kurya. Kauyen ya sami sunan ne dalilin wani shahararren kasurgumin barawo da ke da wannan suna, don kwarjininsa da tambaya har masu kada masa take ke gare shi, in zai je wurin fashi." Shuru wurin yayi ba abinda suke saurare face labarin da Sarah ta fara basu. Tun da rana ta fadi, Jinah da Nafisa ke ta rokonta akan ta basu labari kamar wasu kananan yara. Allah yayi masu son jin labarai, ba kamar Nafisa da ba zata iya ganin littafi bata karantashi ba, har ma tafi karfi a na tatsuniyoyi irin su na Shehu Jaha, Magana jari da makamantansu. Daga karshe dai sun shawo kan Sarah har ta amince zata basu amma sai bayan anci abincin dare. Bayan an kammala komai, babbar tabarma suka shimfida a tsakar gida, kowa ya zauna banda Dauda da kowa yake tunanin ya tafi kauyensu tun kafin farfadowar Jinah sakamakon wata wasika da ya aje masu. Sarah ta cigaba da labarinta : -A tsakanin Kurya da wani kauye Tafi-da-Kwarinka akwai wani surkukin daji, to a wannan dajin Kurya ke zuwa ya tare duk wani mai wucewa ta nan ya yi masa fashi. Kurya dai katon gaske ne, gabjeje, baki-kirin kamar gawayi, da gashin baki, da jajayen idanuwa, ga shi da kwarjini da komai karfin halinka da jarumtarka in kun yi arba sai gabanka ya fadi. To, wayewar gari duk sai ka ji an ce ya yi fashi, kuma ya kan zo da jakkai ne ya labta masu kayan da ya yi fashin, ya kora ya tafi cikin dokar daji inda ya kafa bukkokinsa, ya yi dangar kara ya kewaye ya jibge su a nan, kuma ya yi runbuna da ya kan zuba hakoran mutanen da ya kashe, watau ko mutum nawa ya kashe a ranar sai ya bi su da dai-dai ya cire hakori guda na kowanne ya kai rumbu ya jefa, da haka sai da ya yi rumbu guda guda cike da hakoran mutane. Wannan mutum sai ya zama abin hirji da neman tsari a wurin matafiya; kai ta kai intaha dai ya kashe hanyar, in kaga wani ya biyo, to bako ne cikin rashin sani. Ana cikin wannan halin ne, sai mutanen da ke kauyukan, nan biyu suka rinka kaura, sai dagatan kauyukan byu abin ya dame su, don sun ga mutanensu sun kusa kauracewa su bar kauyukan, sai su ka hadu suka yi shawara, suka zartar da cewar, kada kowa ya yi tafiya, sai cikin ayari dauke da makamai, tun da sarkin yawa dai ya fi sarkin karfi, ko Kurya zai bullo dai, sa gabza da shi, kuma suka ce duk wanda ya yi dalilin Kurya ya zo hannu za'a bashi lada mai-yawa, kuma a dauke ma sa biyan haraji, in kuma mace ce, to mijinta ko iyayenta sun huta da biyan kudin kasa muddin ransu. Wata rana sai samarin wannan kauyen suka tafi yawon tsarince a Tafi-da-kwarinka, sai wani saurayi daga cikin samarin ya sami wata budurwa a kauyen, akawala kyakkyawa, sai ya ce, yana sonta, sai ta ce, ita ma tana sonsa, ya tambayeta sunanta, ta ce masa sunata Ayashe, ta tambayeshi nashi sunan, ya ce mata Mazgau. Ayashe ta yi dariya, ta ce, wannan suna naka bai dace da kai ba, don ga alama dai sunan ya cancanta da masu karfi ne, to, amma kamar nan taka, wa za ka iya mazgewa? Hala dai sunan kakanni ne wannan. Mazgau ya amsa mata ya ce, "I" na yarda, tunda an ce alamar karfi tana ga mai kiba, toamma ba a dukkan lokaci ba, wani sai ki gan shi, ki raina, amma in wuri ya yi wuri sai ya baki mamaki, ya yi maki ba zata." Mazgau ya yi sallama da budurwarsa, ya tambayeta randa za ta zo kauyensu Kurya, ta ce masa za ta rinka zuwa a duk ran kasuwar kauyensu, don cin kasuwa, in ta kwana ta ci kasuwar, ta juyo, suka yi sallama ya tafi. Ayashe ta rike alkawarin da ta yi masa, a duk ranar kasuwar kauyensu Mazgau, sai ta je masa tsarince, to a duk lokacin da ta je, in suna tadi na hirar saurayi da budurwa, sai ta kan ce masa, Shin me ya sa ne kai baka cika zuwa kauyenmu ba, sai ni ke zuwa naku, ko don barawon nan ne dan fashi da ke tare mutane? Mazgau ya amsa mata cikin ruba ya ce, "Shi din me, ya ma isa, ji kika yi an ce maza mata ne? Ayashe ta yi murmushi ta ce masa, haba ai ko a matan ma suna kadai suka tara, amma ai akwai munam mata, akwai mataye, akwai kuma mata, kai har ma da mateku. Ashe baka da labarin wata matar ta f namiji jarunta ba ? Don kuwa ta kowace hanya ya bi, ta damashi ta shanye a nan, sai Mazgau ya ce don Allah rufe mana baki, namijin banza ba ? In dai ban da baki, da me mata suka fi maza ? Ayashe takan ce to a bar wa ranar gwaji wann sani, sai randa ta zo. Ayashe ta ci gaba da zuwa tsarance wurin Mazgau, har dai ta gaji, shi da rana daya bai taba zuwa mata can kauyen nasu ba, tun dai daga ranar da suka sadu, ashe dai shi a ransa tsoron gamuwa da dan-fashin nan ya ke yi, kuri ne kawai ya ke yi wa Ayashe ta ce masa, ko Kurya ke hana shi zuwa kauyensu ganinta. To, ana haka, har sai Ayashe ta soma shan jinin jikinta ta ce, ko baya sonta ne, shi ya sa baya zuwa, rannan data je sai ta sake tambayarsa dalilin da ke hana shi zuwa, sai ya kawo mata wadansu dalilai marasa karfi ya ce, su ne suka hana masa samun sukunin zuwa, daga nan sai Ayashe ta ce, haba Mazgau, ku maza dai kun raina hankalin mata, alhali kuwa ba ku san bakan mukan yi maku ba, don mu ga iya gudun ruwanku, kai dai kawai matsoraci ne, Kurya ke hana maka zuwa kauyenmu, ni kuwa in fada maka yau, ni fa ba matar matsoraci ce ba, daga yau in baka je ba, ni ma na daina zuwa maka. Mazgau ya murtuke fuska, ya ce haba ki dubi duk tuli na ki ce da ni matsoraci ? Yo, duk duniya akwai wanda nike tsoro, in barnda wanda ya haliccemu. To, yau in za ki koma har gida zan kai ki, in kuma dawo komai dare, kuma ta nan wajen sarkakiyar itatuwan kukkokin, inda yake labewa, ta nan za mu bi mu shige. Ayashe ta ce masa, to, in dai kai namiji ne sosai, sai ka bari sai dare ya yi tsaka, kana mu bi, mu tafi... -Wa ke son yaji karshen labarin? Sarah ta tambayesu. Dukansu suka amsa da "Ni!" -Toh, kuyi addu'a Allah ya nuna mamu gobe i warhaka lafiya, domin sai gobe zan karasa maku labarin. Cewar Sarah kafin ita da Abdul su kyalkyace da dariya. -Dan Allah Sarah ki karasa mana. Cewar Jinah da Nafisa. -A'a sai fa gobe, kunga har yan tagwaye sunyi bacci. -Dan Allah... -Nace a'a. -Ba kyau haka fa aunty Sarah. -Kuyi kamar ni kuyi imagine sauran labarin. Abdul ya fada yana cigaba da dariya. Harara Jinah da yar uwar tashi suka watsa masa. Shi kuwa kamar sun kara tunzurashi ya cigaba da dariya. Fally da shima yake wurin yana sauraron labarin ba tare da sauran na ganinshi ba, ya radawa Jinah a kunne : -Kinga muje mu kwanta, tanada gaskiya, dare yayi. Hakura tayi akan ta jira gobe a karasa mata labarin. Daukar daya daga cikin yan tagwaye tayi ta nufi makwancinta, itama Sarah ta dauki dayan ta wuce. Nafi kuwa sai da ta gama guna guninta Abdul yana mata dariya kafin taje ta kwanta. -So nake na gabatar da kai a wajensu. Jinah ta fada bayan sun koma daki ita da Fally. -Kina tunanin zasu yarda da ke? Ba zasu yi maki kallon mahaukaciya ba? -Wata kila, amma zan gwada, na gaji da boyewa idan zan maka magana. Murmushi yayi kafin yace : -Yanzu dai kiyi bacci, kinsan dare mahutar bawa ne, gobe sai muyi maganar. -Shikenan, ka tashi lafiya bugun zuciyata. -Ki tashi lafiya sanyin idaniyata. -Ka tashi lafiya masoyina. -Ki tashi lafiya rabin raina. -Ka tashi lafiya numfashina. -Ki tashi lafiya tauraruwata. Haka suka cigaba da yi, har sai da bacci barawo yayi awon gaba da Jinah. Washe gari kamar Kullum Sarah ce ta fara tashi, tayi alwala sannan ta tada sauran domin suyi sallar asuba. Bayan sun gama, ta shiga hada abin karin kumallo. Tarar da ita Jinah tayi, tana janye da yan tagwaye. -Ina son in tayaki aikin nan, amma wadannan masu kamar danko suna manne dani sunki su sakeni. Dariya Sarah tayi tare da cewa : -To ba dole ba, irin dadewar da suka yi da kewarki. -Idan muka sakeki zaki fadi kuma ba zaki bude idanu ba. Cewar Ayu, ita kuma Aya ta kara da cewa : -Eh, ai idan muka rikeki haka, ba zaki fadi ba bare ki sake rufe ido. Sosai Jinah da Sarah ke dariya, sai dai kuma lokaci guda suka shanye dariyar ganin Aya na kokowar neman numfashi, kamar an shaketa. -Aya! Aya! Me ya sameki? Yimin magana...'yata...Sarah...ta.. -Yi sauri ki bata ruwa! Jinah bata kai ga yin koda taku guda ba taga 'yarta ta zube kasa sumamma. Ba tare da shakkar komai ba, ta kwalawa Fally kira ta hanyar kiran sunanshi. Lokaci guda suka zo shi da su Abdul. -Me yake faruwa, innalillahi Aya! Cewar Nafisa. -Fally, kayi wani abu, bata motsi! Sauran kasa fahimtar ko da wa take magana suka yi, Abdul ne ya shiga rarrashinta tare da ce mata ta tashi suje asibiti. -Me yasa kaki cewa komai? Kasan abinda ya sameta ne? Cewar Jinah ba tare da ta damu da sauran basu ganin ko da wa take magana. Abdul fita yayi da gudu neman abun hawa. -Mama ta mutu ne? Cewar Ayu dake ta rizgar kuka, bayan yayi iya kokarinshi ganin ya tayar da yar uwar tashi. -A'a na tabbatar bata mutu ba, kinga Jinah ki tashi mu tafi asibiti. -Wai me kake nufi ne Fally, me yasa ba zaka yi komai ba? -Kiyi hakuri ki yafe min Jinah. Sai a wannan karon Fally ya bude bakinsa. -Hakurin me kake bani? Kayi wani abu mana! Rungume diyarta tayi jikinta tana kuka. Ta kasa gane komai, amma tasan duk abinda Fally ya kasa to ko likitoci ma walaha ce zasu sha. -Ki tashi kinji diyar mama... kada ki yiwa mama haka, dan Allah! Mama na sonki, kiyi magana Ayata. Kasa jurewa Fally yayi, ya bace daga wurin. Bayan ya danyi nesa dasu, ya fashe da kuka yana mai dana sani da jin haushin kansa. Kwanakin nan cike suke da jin dadi a gareshi ta yanda har ya manta meye silar samun farin cikin nashi. Tunawa yayi da ranar, ranar da itace silar fadawar 'yarshi wannan halin. Ranar da itace yayi wannan mummunan zabin. A lokacin da yake kwance kafin su samu lafiya shi da Jinah, yayi tunanin komai ya kare masa, rayuwarsa da ta Jinah, da kuma soyayyarsa... Babu wani sauran karfi da ya rage masa ta yanda ko idanu bai iya budewa. Wani abu yaji ya sokeshi, yayi tunanin ko mutuwa ce, amma sai yaji ana kiran sunansa : -Fally ! Fally ! Haka yake ji ana fada cikin rada, sai da mai kiran nasa ya cigaba da maimaitawa kafin ya bude ido dakyar. Kara rufe idanunsa yayi ya sake budewa domin tabbatar da ko wacece a gabansa, ba kowa bace face Hindu. Murmushi tayi masa, daman tayi alkawarin zata dawo gashi yanzu ta cika. Farawa tayi da fadin : -Zan iya fitar da kai daga wannan halin. Kokarin yin magana Fally yayi amma ya kasa. Ganin haka ta kara da cewa : -Nice kadai zan iya taimakonka. Sake iya kokarinsa yayi ganin yayi magana, amma bakinsa ne kawai ya motsa, sauti bai fita har sai da Hindu ta tsikara masa wani abu kamar allura. -Na..roke..ki...ki..taimake...ni. Wata bahaguwar dariya tayi ta jin dadi, jin ana rokonta, tasan a duk lokacin da aka roketa, to zata samu abinda take nema a matsayin na fansa. -Tabbas zan taimakeka, ina ce tsakanin aljanu akwai taimakekeniya? Ta fada tana wani dage gira, sai dai Fally ya fahimci me take nufi, tana son ya bata wani abu a matsayin fansa. -Kaga Fally, na sanka da wayo, kada kace min yanzu ka zama sakarai. -Yan tagwaye. -Yauwa ko kai fa? -Ba..zan iya yin hakan ba. -Kwarai kuwa zaka iya, kuma ai ba duka nake so, daya daga cikinsu nake so. -Jinah ba zata taba yafe min ba. -Ai zaku iya sake haihuwar wasu. -Ke kinsan ba a cika samun irinsu su rayu ba. -Ni wannan ba damuwata bace, bakuda lokaci mai yawa gara da sauri ka yanke abinda yafi. -Ba zan iya yiwa 'ya'yana haka ba. -Kana tunanin zasu yi tsawon rayuwa ne bayan mutuwarku? -Me kike nufi? -Suna rayuwa ne, dalilin alakar dake tsakaninka kai da Jinah, kuma wannan alakar ta rushe, kai da Jinah zaku mutu, bayan wasu kwanaki su ma su biku. -Ni ban yarda ba, hakan ba zai yiwu ba. -Yarda dani wannan ruwanka ne, amma ka sani zaka yi nadama. Wata kila Hindu karya take masa, domin irinsu a shirye suke suyi komai domin cimma burinsu, ko ma dai ta yaya, Fally ya yarda da maganarta, amma kuma cikin zuciyarsa yana jin kada ya yarda da wannan matar. Sai dai sonshi da yaga ya dawo da Jinah yafi komai karfi. Rufe idanunsa yayi na wani lokaci hawaye masu zafi suka zubo masa kafin yace : -Na amince. Wani murmushin keta Hindu tayi sannan tace : -Abinda ya dace kayi kenan, Jinah ba zata ki yafe maka ba. -Me ya kamata nayi yanzu? -Zaka jawo daya daga cikin yan tagwayen anan sai ka bashi wannan ruwan yasha. Ta fada tana miko masa wata yar karamar kwalba da wasu ruwa a ciki. Kasan yanda za'a yi yasha wannan ruwan ba tare da wata tilastawa ba. Zai daukeshi sa'o'i 48 kafin ya fara aiki a jikinsa. -Daga nan kuma me zai faru? -Dena hanzari, zaka gani. Ta bashi amsa da wani makirin murmushi a fuskarta. Karawa tayi da cewa : -Kuma sai kayi sauri, domin abinda nayi maka yanzu domin ya kara maka karfi ba mai dadewa bane, dole sai ka hanzarta kafin ya kare, ni zan tafi kuma idan kayi abinda nace maka ba zaka kara ganina ba. -Tsaya ki tafi da wannan fatalwar taki. Fally ya fada yana kallon Dauda. -Daina kishi, Jinah kai kadai take so. Ta fada tana dariya. -Bana son kara ganinshi, domin bansan me zanyi masa ba. -Kar ka damu, zan tafi dashi kuma ba zai kara dawowa ba bare ya kawo maka cikas tsakaninka da Jinah. Tunani Fally yake ko wannan itace mafita gareshi. Sai dai wata murya cikin kanshi na kara tabbatar mashi. "Ko ba komai Jinah zata dawo gareka, kuma komai zai koma kamar a ranarku ta farko, zata yafe maka domin zata fahimta." Kamar yanda Hindu tace, karfin jikinsa ne ya fara janyewa a hankali. A take ya rufe idanunsa, tunanin Aya yayi ta yanda har ita taji babanta yana son ganinta. Cikin kankanin lokaci sai gata ta bayyana a wurin. -Baba! Ka tashi? Nayi tunanin ko kuskure ne aka samu naji kana nemana. Yi hakuri na barka kai daya, muna tare da mama ne a asibiti yanzu muka dawo gida. -Kar ki damu 'yata, ya mama taku take? -Ba sauki, ko motsi ma bata yi. Ta fada tana kokarin yin kuka. -Kar kiyi kuka 'yata, komai zai wuce. -Ta yaya? Bamu san meye abun yi ba yanzu. A ina zamu sa kanmu idan kun tafi? Kada ku tafi dan Allah! -Zo nan. Kwantar da ita yayi bisa kirjinsa tare da kankameta, a hankali ya fara kuka. Fally har ya riga da yayi zabi, kuma Aya ya zaba ita zai sadaukar. Kuna tunanin to me yasa bai zabi Ayu ba ko? Fally yasan abun ba zai zo da sauki ba idan Ayu ne, dubban tambayoyi ne zai yi ta yi masa kuma zai ce sai ya karanci tunaninsa ko kuma ya tilastashi sai ya fada mashi gaskiya daga nan ya gano dalilin da yasa zai yi haka. Ita kuwa Aya tanada banbanci da dan uwanta. -Karbi sha wannan! Ya umarceta tare da miko mata kwalbar. -Meye shi baba? -Ki sha dan Allah. Nan take Aya ta karanta tunanin mahaifin nata, sai dai bata kai ga yin wani nisa ba ganin cewa ya bata ne domin ya cecesu gaba daya, wannan ma kawai ya isheta ba sai ta kara sanin wani abu ba, domin ita ba mai son sanin sirrin wasu ba ce. Bata yi wata wata ba ta karba ta shanye. Hannu tasa ta goge hawayen da babanta ke zubarwa ba tare da tasan dalilinsu ba. Haka suka zauna shuru suna jiran sakamako. Kamar walkiya Fally yaji wani karfi na shiga jikinsa, kowanne bangare na jikinsa na komawa kamar sabo. Ihu Aya tayi tana kiran sunan babanta : -Baba! Sakamakon bace mata da yayi bata ganinsa, tana cikin wannan dube duben taji ya kira sunanta : -Aya! Babanta ta gani tsaye cikin koshin lafiya a bayanta, tsalle tayi ta rungumeshi tana murna. -Ka...warke, baba ka warke! Wata muryar suka ji a bayansu. -Aya! Aya! Mama ta tashi! Ta... Cak Ayu ya tsaya ganin mahaifinsu a tsaye. Da gudunsa ya fada jikinsa yana murna. Ita kuma Aya ta ruga domin ganin mahaifiyarsu.... Wata sabuwa kara da Jinah ta saki ita tayi sanadin dawo dashi daga tunanin da yake, da gudunsa ya karaso wurin, kasa daukarshi kafafuwansa suka yi, tsabar rudin da ya shiga. Yanzu ba wai Aya bace kadai kwance da alamun babu rai, har da Ayu. Sai kuma Jinah da ta fara wani abu kamar zautatta. Nan fa, shi kanshi ya kasa fahimta. -------------------------------------- G day readers, ina fata yanzu masu tambayar : "Ta yaya suka farfado ba tare da Aya ta samu cikon abu na uku ba?" da kuma "Wanne irin laifi ne Fally ya yiwa Jinah?" sun samu amsoshinsu? Ganin comments dinku, ke sa na gane ko labarin yana shiga...😊 ©Al_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 23 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Fally ganin duka 'ya'yanshi kwance ba a hayyacinsu ba, ji yayi kasa ta kasa daukanshi, ya kasa yin numfashi da kyau, iskar shaka na neman ta gagareshi. Ya amince da wadda sam bai kamata ya yarda da ita ba. A cikin ransa yace ta yaya na yarda da wannan matar, matar da ita tayi sanadin mutuwar mahaifiyata. A yanzu ya gane irin kuskuren da ya tabka. A daidai lokacin ne suka dunguma zuwa asibitin kauyen, Jinah bata daina kuka ba, duk tabi ta firgice, suna zuwa likitoci suka sanar dasu yaran suna numfashi. Kallon Fally Jinah tayi anan ta tuna da hakurin da yake bata dazu. -Fally me ka aikata ne? Ta tambayeshi da alamun tuhuma. -Ina son ki dawo gareni ne, mu sake raya soyayyar mu, ina son mu koma kamar da ne. -Fally ka fada min, me ka aikata? Wannan karon muryar Jinah cike take da zafi da kuma rashin tsoro. -Dole mu hakura da daya daga cikin su, Hindu.... -Innalillahi Fally! Me yasa ita? Ta yaya kayi hakan? Ka maido min da yarana Fally! Ba ruwana da koma me zaka yi, ni yarana kawai nake so! Jinah ta fada kafin ta sake fashewa da wani sabon kukan. Kokarin rungumeta Fally yayi amma ta goce tareda furta : -Ka tafi, kada ka kara sako kafar ka anan, ba tare da ka dawo min da yarana ba! Bana kaunar ganin ka kafin nan! Bai yi wata-wata ba ya bace daga wurin, zuciyarshi na kuna ganin zai rasa daya daga cikin 'ya'yansa gashi kuma zai rasa wadda yake yaruwa domin ta, bayan duk wasu wahalhalu da yasha a baya da sadaukarwar da yayi. Yanke shawarar yaje yaga Hindu yayi, sai dai wata matsalar bai ma san ko ta yaya zai ganinta ba. Koma dai meye zai yi iya kokarinsa yaga ya nemota ta karya abinda tayi. To kuma idan yayi hakan su zasu rayu ne? Tambayar da yayi wa kanshi kenan. Koma dai meye zai je ya nemi Hindu ta san abinda zata yi. Jinah ce zaune kan benci dake madakatar jiran likita kamar jaririn da yake jiran a haifeshi haka take. Taci kuka iya kuka ta yanda har idanun nata sun kafe babu ko digon hawaye. Duk dakikar da zata shude,sai taji wani abu ya soki zuciyarta. -Zasu tashi. Abinda Sarah da su Abdul ke ta maimaita mata kenan, domin likitoci sun tabbatar masu da yan biyu ba mutuwa suka yi ba, sun fita hayyacinsu ne, kuma likitocin na sa ran cetonsu. Ita kuwa Jinah tasan ba zasu iya yin komai ba domin ba kamar kowanne irin ciwo bane. Kamar an tsikareta ta mike tare da fita daga asibitin. Da gudu Sarah tabi bayanta, ta tsayar da ita. -Ina zaki je ne? -Kar ki damu Sarah, yanzu na dawo, kawai ina son na samu natsuwa ne. -Bari na rakaki. -A'a dan Allah, ni kadai nake son tafiya. -Amma... -Dan Allah... -Shikenan kar ki dade. Sarah na nan tsaye har Jinah ta soma yin nisa, bata so ta barta ta tafi ba, amma kuma tana ganin hakan shi zai sa Jinah ta samu dan sukuni. Jinah tafiya take yi ba tare da tasan inda zata je ba, har wani dishi-dishi take gani tsabar wahala. Ganin jiri na dibanta ta samu wani gindin bishiyar kuka ta zauna. Hada kai da gwiwa tayi. Ta kai tsawon wasu mintuna a haka, kafin ta dago kai taga wani a gabanta. Da ganinshi ta tabbatarwa kanta aljani ne. Kura masa ido tayi, shi kuma sai kallonta yake da mamaki dan ganin ko motsawa bata yi ba. -Kina ganina ne? Aljanin ya tambayeta, cike da mamakin ganin yanda Jinah ke kallonsa da alama tana ganinshi ne. -Ta yaya kike iya ganina, alhali ke bil'adama ce? Jinah bata ce masa kala ba. -Gashi kuma kinada kyau irin na aljanu, zan so naji labarinki. Har yanzu dai bata amsa mashi ba. -Zan iya sanin sunanki? Sai da tayi kamar ba zata amsa mashi ba, kafin tace : -Jinah! -Eh na san kin san ni aljani ne kuma da mamaki yanda baki ji tsorona ba, kuma nasan ke ba jinsin mu bace, sunanki nake tambaya. -Sunana Jinah! -Abin dariya, na taba sanin wata bil'adama mai irin wannan sunan, tana rayuwa ne cikin aljanu, Jinah a cikin "jinni"... Shuru yayi yana kallonta kafin yace : -Jinah! Jinah ta Fally kece? Fiddo ido Jinah tayi, tana tunanin shi kuwa wannan ina ya santa. Kafin ta karasa tunaninta taji ya rungumeta. -Jinah nine, INFA! Dan Narama da Gausu! Kin tuna ni? -Infa! Kai ne? Jinah ta fada da alamun ta ganeshi, murna ce fal cikin ranta da kuma hawayen jin dadin ganin wanda ta dade bata gani ba. -Amma me kike yi anan? Ke kadai kuma ma ina Fally, da iyayenku? Yaya suke? Me ya faru duk tsayin wannan lokacin? -Abubuwa da dama sun faru Infa. Jinah ta fada yanayin fuskarta ya sauya zuwa damuwa. -Ina jinki bani labari. Ta fara da cewa : -Iyayen mu sun mutu. -Mene? yaushe? Ta yaya? Shi kuma Fally yana ina? Tambayarshi ta karshe tasa fuskar Jinah tayi ja na tsana jin ya tuna mata da Fally. -Shi, ban kaunar jin sunanshi, idan har bai dawo mun da 'ya'yana ba... -'Ya'yanki? Yaya ne wannan labarin yake?... Labarin komai Jinah ta bashi, abinda ya faru tun daga tafiyar Infa har zuwa yanzu da 'ya'yanta suke cikin wannan halin. Shi kuwa tun lokacin da yaji ta ambaci sunan Hindu, zuciyarsa ke tafarfasa na bakin ciki, tsana, da kuma son daukar fansa a gurin me wannan sunan. Shi ma Infa yana daga cikin wanda Hindu ta zalunta, lokacin da yake karami, shi ma yana rayuwa a cikin kauye daya da su Jinah, shine yaro daya bayan Fally mai son Jinah, yana shige mata fada idan wasu yaran aljanun suna son cutar da ita. Haka suke shakikan abokai, har ana masu lakabi da yan uku, duk da ya girmema Fally da Jinah na shekaru biyar. Komai yana tafiyar masa daidai har wata rana da ya dawo gida ya tarar iyayenshi da kanwarshi sun mutu, anan yaji ga makotansu cewar aikin Hindu ne, kuma idan shima bai gudu ba zata dawo ta hada dashi. Nan da taimakon mahaifiyar Fally ya gudu. Kuma har yanzu bai san dalilin da yasa Hindu ta kashe masa dangi ba. Yanzu da ya girma, ya dawo da niyyar daukar fansa, duk da cikin ranshi yasan ba zai iya galaba a kanta ba, amma duk da haka zai yi iya kokarinsa. -gaskiya nayi mamaki sosai, na kasa yarda, wai yan biyu kuma ruwa biyu. Kuma gaskiya Fally bai kyauta ba, amma kuma... -A'a Infa, kar ma ka fara nemar masa wata afuwa! -Ina tunanin a wannan karon, mu zamu yi nasara! cewar Infa cike da jin dadi. -Ban gane ba, akan me kake magana? -Yaushe yan biyu suka shiga wannan halin? -Yau da safe. -Akwai sa ran ceto yaranki! -Da gaske kake? Toh ta yaya? -Kin tuna babana yana yawan son bamu labarin kakanin mu? -Eh. -Toh wani lokacin ko daga ni sai shi ne, yana bani labarin sirrukan duniyarmu da abubuwa da dama. Kuma har da labarin yan biyu ruwa biyu yana bani. -Me yace? -Abubuwa da yawa, amma ki sani, zamu iya ceto yaranki a yanzu, domin ita ma Hindu tana cikin irin halin da suke, domin haka aikin yake idan tana son ta janye duk wani karfi nasu. Idan har aikin ya ida, yan biyu zasu mutu ita kuma karfinta zai karu. Sa'o'i sha biyu suka rage mana mu nemo Hindu mu kasheta domin a yanzu ne damarmu take ta yanda ba zata iya kare kanta ba. Jinah taji dadi sosai da Infa yazo mata da hanyar ceton 'ya'yanta, sai dai matsalar a yanzu basu san inda zasu nemo Hindu ba, nemo aljani a cikin duniyar nan ba abu ne mai wahala, amma yafi ga irin su Hindu, domin sun san a halin yanzu sai da ta boye kanta kafin ta shiga wannan halin, dan gudun kar wani ya cutar da ita. -Ya kamata mu nemo inda take. Cewar Jinah. -Nafi ki son mu nemota ko dan ta girbe abinda ta shuka na kashe min iyaye kuma ta fada min dalili. -Bamu da lokacin bata lokaci! -Mu fara daga wajenku inda taje cen wajen Fally. -Toh, amma mu fara biyawa asibiti domin na sanar da dangina. Shuru tayi kafin ta sake maimaitawa "dangina". Wannan ne karon farko da ta fadi hakan da nufin cewa Sarah da su Abdul. Suna zuwa asibitin ta sanar da Sarah zata tafi wani waje, kuma ba zata dade ba zata dawo. Nan suka fita ita da Infa neman Hindu. Sun bincika kasa da sama, suna yi suna tambayar duk wani aljani da suka hadu dashi, wasu ma basu amsa masu idan suka ji sun ambaci sunan Hindu. Kuma babu wani da yake da niyyar taimakonsu, amma duk da haka basu karaya ba. Abin tashin hankalin garesu, yau ce rana ta karshe da aikin Hindu zai kammala. Sa'o'i kadan ne suka rage. -Kiyi hakuri Jinah! Cewar Infa. -Koda dakiku ne suka rage mana, bazan fidda ran ceton yarana ba, bare kuma Sa'o'i ne suka rage mana. Mu dai mu cigaba da nema. Infa yana mamakin karfin halin Jinah, kuma fa haka ne uwa a shirye take da yin komai domin 'ya'yanta. Jinah duk yinin yau babu abinda taci ko tasha, ko kuma samun damar bacci, amma duk da haka batada alamar gajiya. Kamar daga sama Jinah ta fara kuka. Da mamaki Infa ya kalleta yace : -Me ya faru kuma Jinah? -Me yasa banyi wannan tunanin ba tun dazu? -Wane tunani kenan? -Kamata yayi ka shiga jikin daya daga cikin yan biyun domin sanin inda karfinsu ke zuwa. -Toh ai wannan mun sani cikin jikin Hindu yake zuwa. -Baka gane ba, ina nufin inda zamu ga Hindu! -Kuma fa haka ne, sai munyi sauri akwai sauran lokaci. Ba bata lokaci sai gasu sun bayyana kusa da yan biyu, shi ma haka Fally yazo a daidai zuwansu, shima da tunanin yin abinda suke kokarin yi, yayi mamakin ganin wani tare da Jinah, amma daga shi har Infa basu wani bata lokaci ba, kowanne ya shiga jikin yan biyu. Bayan wasu yan dakiku sai gasu sun fito daga asibitin, kama hannun Jinah Infa yayi suka bace, basu dira ko'ina ba sai inda Hindu take. Wuri ne dake cike da tsoro saboda duhunsa, gawarwaki da kwarangwal a ko'ina, ga kuma jini a jikin bango da kuma a kasa, sai kuma wasu maganganu da koke da basu san daga inda suke fitowa ba. A irin wannan wurin, kamata yayi ace Jinah ta tsorata, amma babu wannan alamar a gareta domin yanzu babu komai cikin kanta face ta ceci 'ya'yanta. -Karki tsaya anan Jinah, nine ya kamata na gyara kuskure na. Ki tafi daga nan, ta yiyuwa akwai hatsari anan. Cewar Fally da ya bayyana a gabansu. Ita kuwa yi tayi kamar bata jishi ba. -Ba zan taba yafewa kaina ba, idan wani abu ya sameki. Na rokeki ki koma gida. Koma kai waye ina son ka mayar da ita inda ka ganta. Ya fada yana kallon Infa. -Fally nine fa! baka gane ni ba? Infa! Yan uku! Ya karashe maganarsa yana nunasu duka ukun. Rike baki Fally yayi yana mamaki, sai da ya dau wani dan lokaci cikin mamaki kafin su rungume juna. -Dan Allah, ku aje wannan sanayyar a gefe, lokaci kure mana yake. Kai kuma Fally babu abinda zaka ce da zai sa na bar wannan wurin. Dan haka muyi sauri mu gano Hindu. Ba tare da sunce kala ba suka rufa mata baya. Basu wani taku mai yawa ba, suka tsinkayeta a kwance. Ita kadai ce a wajen, hakan ya basu mamaki, amma kuma daga karshe suka yankewa kansu ko tana tsoron kar daya daga cikin bayinta yayi kokarin kasheta ganin bata iya kare kanta. Wata zarceciyar takobi ce ta bayyana a hannun Infa lokacin da suka karaso kusa da Hindu. Rike takobin yayi da hannu biyu, yana mai setata daidai zuciyar Hindu, hawayen farin ciki na kwaranya a kumatunsa, shikenan yau zai dau fansar iyayenshi, da na sauran duk wasu wanda shedaniyar nan ta cuta. Ganin idan yayi mata na farat daya zata yi saurin mutuwa, yasa ya janye takobin zuwa kan ruwan cikinta da niyyar ya fara barka cikinta kafin ya fizgo zuciyarta.... Yana cikin wannan tunanin yaji Jinah ta kwala kara : -Yi hankali Infa!! Hindu ce ta farka tare da yin watsi da Infa gefe daya. Sake kwala kara Jinah tayi tana cewa : -A'a! A'a! 'Ya'yana! Hindu ba alamar karfi a jikinta ta sake faduwa. Su kuwa kallon kallo suka shiga yi tsakaninsu da mamaki. -Me hakan ke nufi? kenan 'ya'yana sun... Fally taimakawa Infa yayi ya mike, sannan shima ya dauki takobin da niyyar sokawa Hindu a zuciya. Ganin haka Hindu tace : -Aikin da nake yi a yanzu haka ya kusa karewa, kuma idan kuka kasheni a yanzu, zamu mutu mu uku, ni da kuma yan biyu. Ta fadi hakan ne ba tare da ta motsa ba. -Karya kike! -Kasheni ni kadai zai yiwu, amma da a tsakiyar aikin ne, a yanzu kuma idan kuka yi haka bani kadai zan mutu ba. -Bai dace mu barta a raye ba! Cewar Infa. -Amma kuma idan kuka kasheta ya'yana ma zasu mutu. -Jinah wannan matar shedaniya ce, bare kuma yanzu da zata sake karfi ta hanyar mallakar karfin yan biyu. Zata iya yin duk abinda take so damu. Ka kasheta Fally! Cewar Infa. -A'a Fally! Kar ka manta kai ma 'ya'yanka ne! kana so ka kashesu ne? Dan Allah, na yafe maka abinda kayi min, amma kuma idan kayi sanadin mutuwarsu, zan tsakaneka har abada. -Amma kuma idan muka barta a raye, dukan mu zamu mutu. Cewar Infa. -Nafi so na mutu kina kaunata, da na mutu kina tsanata. Cewar Fally yana mai sakin takobin hannunsa. -Ku biyun duka kun haukace! Ba zan kyaleku ku saka rayuwar duka mutane a hatsari ba saboda mutum biyu. Takobin ya dauka ya nufi kan Hindu. Su kuwa kwala kara suka yi : -A'a! -Inada wata hanyar bayan wannan. Cewar Hindu. Dakatawa Infa yayi sannan yace : -Me? Fadi muna jinki! -Hakan zai dawo da yarana ne? Jinah ta tambaya. -Zan iya amfani da karfina na baya, 'ya'yanki zasu rayu cikin koshin lafiya, kuma nima ba zan sake shiga rayuwarku ba, ba ma zan iyawa ba domin ba za'a iya kwatanta karfin yan biyu ba da nawa. Amma sai dai zaki manta komai Jinah, zaki koma daidai ranar da kika farka, kika tuna rayuwarki ta baya, amma wannan karon ba zaki tuna da rayuwarki ta baya ba, zaki koma kamar a baya ki kasa tuna komai, ki manta ko ke wacece, daga ina kika zo, ta yaya kika samu 'ya'yanki ko kuma waye ubansu. -Me zan yi yanzu? Jinah ta fada ba tare da ta tsaya yin wata shawara ba. -A'a Jinah! Kar kiyi haka, ba zan iya sake rayuwa cikin wancen kuncin ba! Naga wani katon yana tabaki, ki kasa tuna soyayyar da nake miki. Na rasa abubuwa da dama saboda ke Jinah kar kiyi min haka. -Toh ya kake so nayi kenan Fally? -Zamu samu wata hanyar ki taimaka Jinah! -So kake na bar 'ya'yana su mutu ko me?... Infa ne ya katsesu da cewa : -Na shirya ajiye fansata har wani lokacin, amma kuyi sauri ku yanke abunyi saboda lokaci kurewa yake. Wata yar karamar kwalba ce ta bayyana a hannun Hindu, ta mikawa Jinah da cewa tasha abinda ke ciki. Matsowa Jinah tayi, ta karbi kwalbar tareda budewa. Baki ta kai da niyyar tasha, Fally bai yi wata-wata ba ya buge kwalbar, ta tarwatse kasa. Jinah bata yi kasa a gwiwa ba, ta durkusa ta fara lashe ruwan da suka yi saura a kasa, ba tare da ta damu da tattakar kwalbar dake cikin ruwan ba. Dukansu kallonta suke da mamaki, ba kamar Fally, da yanzu ya tabbatarwa kanshi, Jinah bata sonshi, bayada wani muhimmanci a gareta, tana son tayi hakan ne domin ta fitar dashi daga rayuwarta. -Kin cika maci amana Jinah! Sai kinyi da nasanin abinda kika yi! Ganin yanda Fally ke maganar zaka gane ranshi yayi mugun baci, kuma zaka ga tsantsar tsanar Jinah a idanunshi. Ya gama yanke sai ya hukunta Jinah, babu ruwanshi da alakar dake tsakanin su, in taso ma zata iya wargajewa. -Me kake fada ne Fally, kasan... Bata kai ga karasa maganarta ba, ta sulale kasa. Tana farkawa ta ganta bisa gadonta, yan biyu kusa da ita. Da alamar komai ya dawo daidai, sai dai bala'in dake jiran Jinah yafi wanda ta gani a baya. Kamar yanda ake cewa tsakanin soyayya da kiyayya bai wuce taku daya ba. -------------------------------------------------- Bon Vendredi a vous tous readers ! 💕 Bye 👋 à la prochaine 💓 sur vous. 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 24 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Ana yawan fadar cewa duk ana haihuwar mu ne a matsayin mutanen kirki, idan kuma daga baya muka zama miyagu, dalilin irin tarbiyar da muka samu ne, da irin jarabawowin da muka gani da kuma dalilin mutanen da ke kewaye damu... Wata kila haka ne, domin muna zuwa duniyar nan ne bamu san komai ba, bamu iya komai ba, komai muna koyonshi ne anan. Ta dalilin wasu da muke ganin suna aikata abun. Nasan kun taba ganin yaro na kwarai da zuciya mai kyau amma kuma gidan da ya fito, tasu zuciyar ba mai kyau ba ce? Akwai kuma wani yaron wanda bakar zuciya gareshi, amma gidan su mutanen kirki ne. Haka akwai wani wanda cikin rayuwarshi, ya taso a na kwarai, rana daya zai juye zuwa mugu dalilin wani abu da aka yi masa, ko kuma wata rayuwa da yake fuskanta... Toh Fally yana cikin irin wannan rukunin na masu sauya halinsu, kamar an tsoma zuciyarshi cikin ruwan kwalta ta tashi daga launin ja zuwa bakakirin har taso tafi kwaltar baki. Kiyayya ta rufe masa ido, shi da ba zai iya cutar da wani ba ma, amma yau gashi yana cutar da abar kaunarshi wadda a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa saboda ita. Kamar yanda yake yi a halin yanzu. Tana son ta bude ido, amma ya sanyata cikin doguwar suma. -Baba, me yasa mama taki tashi? Ayu ya tambayi baban nashi. -Saboda tayi sadaukarwa saboda ku, saboda ita ne muke har yanzu a raye. -Kamar yaya, me ta aikata? Aya ta tambaya. -Toh zata farka? Shima Ayu ya kara jefo wata tambayar. -Eh, amma kuma dole sai na kaita wani guri mai nisa, nesa da nan. -Toh me muke jira, mu tafi mana! -Hakan ba sauki gareshi ba, ku ba zaku bimu ba. -Toh me yasa haka? -Inda zamu je, basu son da akwai ku ba, kuma idan kuka bimu, zasu ce ku zaku zama fansar ceto mahaifiyar ku. Kuma kunsan mamarku ba zata taba yarda da hakan ba, nima kuma haka. Nasan Sarah zata kula da ku har lokacin da zamu dawo. Karyar da Fally ya shiryawa yan biyu kenan ba tare da sun harbo jirginshi ba. Yasan idan yace masu zai dauki Jinah ya tafi da ita, ba zasu yarda ba har sai ya fada masu dalili. Yanzu kuwa ya riga da ya karance su, idan zai fada masu wani abu, kuma yasan karya ne, to sai ya fara fadar wani abun da yake gaskiya. Gashi kuma ya hanasu binciken tunanin mutane. -Ya kamata naje yanzu, domin duk wata dakika barazana ce ga rayuwar ta, zan shiga jikinta domin fadawa yan gidan zata je wani guri. -Baba kana da tabbacin wannan ita ce mafita? Ayu ya tambayeshi cikin rashin yarda. -Domin mahaifiyarku zan yi wannan, domin na ceto ta. Ya bashi amsa. Shiga jikin Jinah yayi tare da fitowa daga cikin dakin. Tarar da Sarah da su Nafi tayi waje sannan tace masu : -Zan fita, yanzu na dawo. -Ina zaki je ne Jinah? -Ba dadewa ba zanyi. -Bari na rakaki. Cewar Abdul. -A'a! Ta fada da karaji. -Lafiyarki kuwa Jinah? Cewar Sarah cike da kulawa. -Eh lafiya nake, kar ku damu, ina son na dan fita ne na sha iska kuma ni kadai nake son tafiya. Dan Allah Sarah ki kular min da yarana. Kalamanta na karshe sun sanyaya jikin kowa, amma ganin dai tace ba dadewa zata yi ba suka barta ta tafi ita kadai. Tana fita daga gidan, Fally ya bace da ita. Zuwa cen sai gasu sun bayyana a cikin wani surkukin dajin da babu kowa sai kukan namun dawa. Fita yayi daga jikin Jinah, wani daki ne ya bayyana a gabansu, ya dauketa ya kwantar da ita a ciki, har yanzu ba'a hayyacinta take ba. Shima zaunawa yayi dirshen a kasa yana kallonta. Yanayin dakin ne, ya tuna mashi da ranar aurenshi da Jinah, ranar da suka yi alkawarin zama na har abada, alkawarin soyayya har abada, ranar da suka yi alkawarin har abada dayansu ba zai ci amanar daya ba. -Amma kuma ita taci amanata! Ya fada da kakkausar murya kamar yana magana da wani. -Ta yaudare ni! Ya sake fada. Me nayi da na cancanci haka, shin ban sota ba fiye da yadda kalmar so take ba, ban kasance mai kulawa da ita tun daga yarintar ta ba, ban sadaukar da abubuwa da dama saboda ita ba, wace irin wahala bace ban sha ba saboda ita, meye ban rasa ba saboda ita? Me yasa ba zata iya sadaukarwa daya ba saboda ni, sadaukarwa daya... Ta cancanci ta wahala kamar yanda na wahala, ta cancanta, ta cancanta... Kalamar karshe yayi ta maimaitawa domin tabbatarwa zuciyarshi. Zafin ma abun gareshi, yanzu babu wata alaka dake tsakaninsa da ita face yan biyu. Alakar auren dake tsakaninsu ta tarwatse, eh sosai ma, domin wanann shine a matsayin fansar kasancewarsu duka hudun a raye. Wannan yake kara sa wutar dake ci cikin zuciyarshi tana kara azalzala. Cewa yake, yanzu shikenan Jinah zata iya tarayya da kowanne irin namiji da take so, ba tare da wani abu ya samesu ba kamar a baya. A takaice dai bai san me zai yi ba, amma a halin yanzu zai nisantata da kowanne namiji, sannan zata biya bisa cin amanar da tayi. (.....) Har karfe tara na dare yayi, babu labarin Jinah, hankalin Sarah duk ya tashi, tana tsaye bakin kofar gida, tana kai kawo. -Har yanzu bata dawo ba? Cewar nafisa da suka nufo inda Sarah take, ita da dan uwan ta. -A'a. Sarah ta bata amsa a takaice. -Mama ba zata dawo ba yau. Suka ji muryar Aya a bayansu. Juyawa suka yi suna binta da kallo. Ayu ne ya kara da cewa : -Mama ta tafi neman magani, ba da dadewa ba zata dawo. -Aya, fada mana ina mama? Abdul ya dan durkusa yana tamabayar Aya. -Ban sani ba, amma lafiya take. Dan uwanta ya kara da cewa : -Eh ku kwantar da hankalinku. Shuru kowannen su yayi, kowa da tunanin da yake kafin Sarah ta katse shurun ta hanyar cewa : -Toh ku tashi ku ci abinci kar yayi sanyi. Washe gari ma, shuru babu labarin Jinah. Sarah bata samun damar runtsawa ba tsawon duka daren. Rana na fitowa, bayan sun gama karin kumallo, ta fita ita kadai neman Jinah, tana tambayar makota da masu wucewa amma shuru ba labari. Haka ke ta faruwa har tsawon kwana biyu. Sarah tabi duk ta rame, bata iya cin abinci, bata samun wani cikakken bacci. Su kuwa yan biyu basu gushe ba suna fada mata, mamarsu tana nan lafiya. -Kar fa yaran nan da gaske suke? Cewar Abdul. -Jinah bata san kowa ba sai mu, bata tuna komai na rayuwarta ta baya, ta yaya zata iya irin wannan tafiyar? Sarah ta fada tana goge kwalla. Kafin wani ya kara cewa wani abu, suka ji ana kwada sallama. -Assalamu Alaikum! -Wa alaika salam! Suka amsa amsa sallamar a tare. Sarah ce ta kara da fadin : -Bismillah! Wani mutum ne ya shigo da yar karamar jaka a hannunshi. Mutumin nan ba kowa bane face INFA, wannan wanda ya kusan kashe Hindu, wannan wanda ya dawo ya dau fansar iyayenshi da ta kashe, wanda a hanya ya gamu da tsofin abokanan shi Fally da Jinah... Bayan sun gama gaisawa, nan yake fada masu shi matafiyi ne, yana bukatar wurin zama ne na kwana biyu kafin ya wuce kauyen Bayana. Yayi tafiya mai nisa ne yana son ya huta. Ba tare da wani dogon tunani ba, Sarah ta amince. Hakan yanada alaka da ala'adarsu ko kuma nace wasu kauyukan dake iya sauke bako gidansu ba tare da sun sanshi ba, har su bashi duk wata kulawa. Kuma ma da yake Sarah tanada babbar zuciya. Nafisa da Abdul kuwa mamaki ne yake neman kashe su, ganin yanda Sarah ta karbi bakon da bata sani ba, har suna ganin ma kamar tayi wauta. Koda yake su sun zo ne daga wata kasar kuma a birni suke, basu saba ganin irin haka ba. Dayan dakin da ba kowa Sarah ta gyara masa, sannan ta kai masa ruwan wanka a bayi. Bayan ya gama ta kai mashi abinci. -Ina mai gidan ko yayi tafiya ne? Infa ke tambayar Sarah yayin da takai masa abinci. -Ya koma ga wanda ya fimu bukatarshi... -Ayya, Allah ya jikanshi, yasa ya huta. -Ameen. Bayan Sarah ta fito daga dakin ta bar Infa shi kadai, ba'a jima ba, sai ga yan biyu sun bayyana a gabanshi, da ganinsu murmushi ya bayyana a fuskarshi kafin yace : -Yan biyu kuma ruwa biyu! Na dade ina son haduwa daku. Lallai Jinah da Fally sunyi sa'ar samunku. -Waye kai? Kuma me kake nema? -Ni abokin babanku ne, mun san juna tun muna yara, amma mun jima bamu ga juna ba har zuwa ranar da kuke tsakanin rayuwa da mutuwa. -Ta yaya kasan wannan? Aya ta tambayeshi babu alamar wasa. -Ina tare da su a ranar da suke kokarin cetonku. -Abinda kake yi yanzu anan muke son sani. Cewar Ayu. -Domin hana baban ku tabka wani kuskure. -Baban mu? Toh ai ya tafi da mamar mu! -Kash! Na makaro. -Me? Meke faruwa ne wai? -A wancen lokacin da muka hadu, mahaifin ku yayi fushi sosai da mahaifiyar ku, saboda ta zabi ta sadaukar dashi domin ceton ku. -Amma ai bai mutu ba! -Eh na sani, sai dai Jinah ta manta dashi da kuma labarin su, kuma yanzu babu wannan alakar dake tsakanin su. Yana tunanin taci amanar shi. Kuma idan aljani yasan anci amanar shi, dawowa yake mahaukaci. A take, Ayu ya rikida zuwa wani garsakeken mutum, maji karfi sannan yace : -Bayada hujjar taba koda gashin mahaifiyar mu. Idan kuwa ya cutar da ita, zan manta da cewa mahaifina ne. -Ka kwantar da hankalin ka. Cewar yar uwar shi, zamu nemo mama. A hankali ya fara dawowa mutum dai dai, amma bai sake hannun da ya dunkule ba. -Zamu nemo inda suke! Cewar Infa. -Zai yi wuya mu gansu. Cewar Aya da ta rufe ido da alamun tana neman wani abu. Shi ma haka dan uwan nata yayi. -Yasan zamu san gaskiya, shi yasa ya goge duk wata alama da zamu gane inda suke. -Kada mu bata lokaci, zamu iya anfani da tsohuwar dabarar mu; mu dinga bi muna tambayar duk wani aljani da muka gani. -Idan kuma yayi mata wani abun kafin mu gansu? Cewar Aya. Girgiza kai Infa yayi kafin yace : -Baban ku, yana cikin fushi, amma ina tunanin ba zai iya cutar da maman ku ba. Nayi mamakin yanda kuka yi saurin yarda da ni... -Idan da kanada wani kudirin, da tuni mun sani, babu abinda yake guje mana. Cewar Ayu. -Banda plan din baba. Aya ta gyara maganar dan uwan nata. -Dan mun yi masa alkawarin ba zamu taba karanta tunanin sa ba, shi yasa yayi mana haka. Sai da suka bari dare yayi, suka tafi neman Jinah. Sai dai babu alamar Fally bare kuma na Jinah. (.......) Har yanzu idanun ta a rufe suke, kokarin motsawa ta fara yi, ji tayi gurin da take kwance bai yi kama da gadon ta ba. Da sauri ta bude idanu, wani irin bugawa zuciyar ta tayi ganin a inda take. Ba'a gidan su ba, bare a dakin ta kuma wannan gurin ba dai ban tsoro ba. A tsorace ta tashi tsaye da niyyar guduwa amma taji kamar an rike mata kafafuwa. Ihun neman taimako ta shiga yi amma babu alamar za'a taimaka mata. Bata jin motsin kowa face kukan dabbobi da iska dake kadawa. Kokarin kwace kafafuwan ta ta fara yi, amma ta kasa. A wannan lokacin, a maimakon tayi tunanin kanta, tunanin 'ya'yan ta take. Kuka ta fara tana tunanin a yanzu duk inda suke suna cikin matsala. Tambayar kanta take : A ina yaranta suke? A wanne hali suke a yanzu? Ta kasa gane ya aka yi tazo wannan gurin da babu kowa sai kukan namun daji, kuma ya aka yi ta kasa motsa kafafuwan ta. Kara fasa wani ihun tayi tana fadin : -A taimake ni! Ku taimaka mini dan Allah! Fally kallonta yake ba tare da yace da ita kala ba, ita ma kuma ba ganinshi take ba domin ya bacewa ganinta. Yana kallon yanda duk ta tsorata, hankalin ta ya tashi, amma bai da alamar yin wani abu. Kiyayyar da ke cikin zuciyar shi babba ce, kamar ma jin dadin ganinta yake a wannan halin. Wani bangaren kuwa na zuciyar sa yana gargadin shi akan kada ya aikatawa Jinah haka. A wannan lokacin ne, soyayyar da yake mata tayi nasara akan kiyayyar. Jinah ji tayi kafafuwan ta sun dawo daidai, da ganin haka kawai sai tayi kokarin guduwa, shi kuwa kiyayyar ta sake maye gurbin ta. Jinah taji kafafuwan nata sun sake komawa gidan jiya. -Jinah!!! Zuciyarta ce taji tayi wani mugun bugawa da taji an kwalo mata kira. -Waye nan? Ku taimake ni dan Allah! Shuru Fally yayi. Sautin kukan ta gaba daya ta bude, shi kuwa abinda ya tsana kenan. Baya son jin kukan ta kuma baya son ya sake ta. Daga karshe, shiga yayi jikin ta sannan ya fito da ita daga dakin. Tafiya yayi ta yi har ya kai cikin wani kauye. Mutane suna ta kallonshi, amma fa bashi din suke gani ba a zahiri face Jinah da ya shiga jikinta. Wasu har tsayawa suke suna yaba kyawunta, wasu kuwa cewa suke suna sonta, ta nuna masu gidan su, domin su ga iyayen ta. Wannan abun shi ya kara harzuka Fally. Wani makirin murmushi yayi, lokacin da wata shu'umar dubara tazo masa. Ya raya a ransa : yau zan dandana irin shedancin Hindu. Zuwa yayi bakin wata rijiya yayi zaune. Cen sai ga wani mutum yazo wucewa, ganin Jinah bakin rijiya ya tsaya tare da matsawa kusa da ita. -Masha Allah! Baiwar Allah daga ina kike haka? Tun da aka haifeni ban taba ganin irin wannan kyan ba. A wannan lokacin, kunnuwa, zuciya, hanci da kuma bakina sun shiga hassadar idanuna sakamakon su kadai suke iya ganin wannan kyakyawar halitta taki. Kalamai sun min karanci. A kanki a shirye nake na rasa duk wata dukiyata domin ki zamo matata. Mutumin matsowa yayi dab da Jinah, shafa gashinta yayi sannan yakai hannunsa kan kuncin ta. Kalmar "fusata" ba zata iya kwatanta fusatar da Fally yayi ba. Ji yayi kamar ya shako wuyan mutumin nan ya jefashi cikin rijiya. Amma kuma da ya tuna da shirinsa sai ya kyaleshi kan a fara ta kanshi, ba zai kara yarda wani katon banza ya sake fadawa Jinah irin kalaman da wannan mutumin ya fada. -Zan so na kashe qishi na a tare da ke. Mutumin ya fada da wani shu'umin mumurshi. -Kana nufin kana bukata ta? Cewar Jinah ko kuma nace Fally. -Abinda nake bukata kenan, kuma zan mayar dake matata. -Toh ba damuwa, amma mu fara zuwa kaga iyaye na domin su sanka. -Yanzu kuwa, babu bata lokaci sarauniya ta. -Aha biyo ni. -Dakata, bari na je na debo wani abu daga cikin dukiyata domin so nake nayi saurin shiga zuciyar iyayen ki. -Toh, ina jiran ka. Bayan wasu yan mintuna sai ga mutumin ya dawo da wata 'yar jaka a hannun sa. Suka dauki hanyar zuwa gidan su Jinah, yana ta zumudin zai auri wadda zata kece masa raini a wajen mutanen kauyen su. Sun yi tafiyar da ta kai mintuna talatin, mutumin ya fara gajiya. -Bamu kai bane? Ya tambaya. -A'a, mun dai kusa. Sun taka yar tafiya kenan, sai gasu a daidai dakin da Jinah take kwance dazu. -Anan kuke? Toh ina iyayen naki? Mutumin ya jerowa Jinah tambayoyi cike da mamaki. -Sun tafi gona, amma ka zauna, yanzu sun dawo. -Zan iya zaman jira har illa masha Allahu, idan har zaki zamo matata. Ya tsorata sosai lokacin da suka shiga dakin, ganin yanayin dakin da kuma duhun dake gareshi. Juyowa yayi da niyyar yiwa Jinah magana, amma babu alamarta sai fuskar Fally da yayi tozali da ita. Kokarin guduwa yayi, amma yaji kamar an sakawa kafafuwansa siminti. Bayan kuma dan lokaci, yaga fuskar Jinah ta dawo daidai. Murza idanunshi yayi domin ya tabbatar ko sune ke zagin shi. -Zamu iya yin wani abun kafin iyayena su dawo. Cewar Jinah. Shuru yayi yana tunani, kafin ya yankewa kansa cewa wata kila gizo ne kawai ya gani dazu. Jinah ta kara da cewa : -Kana son ganin abubuwan dake boye a cikin kayan nan? Ta fada tana nuni da kayan dake jikinta. Shi kuwa wani bude idanu ya shiga yi kamar tsohon maye, cike da sha'awa. -Na fara ganin wannan lafiyayyan jikin naka tukun. Cewar Jinah. Cikin kyaftawar ido, sai ga wannan mutumin ya kwabe kayan jikinsa baki daya. Idanun Jinah suka fara zubar da hawaye, da alama yanzu tana cikin hayyacinta amma ba duka ba, hakan na nufin kwalwarta na aiki amma jikin ba ita ke controlling dinshi ba, ta zama tamkar yaron da ake koyawa tata..tata. Duk wani motsin ta wani ke yi mata shi ba ita ba. Wuka ta dauka, ta rike hannu, ta dumfaro wannan mutumin. -Me..me kike yi haka? Mutumin ya fada cike da tsoro, kokarin ja da baya yake. Kuka Jinah take cigaba da yi, bata son aikata abinda take kokarin yi, shi kuwa Fally abinda yake so kenan. Ta sha wahala, yana son ganin ta wahala kuma yayi nasarar hakan. Jinah tana kuka, tana girgiza kai, ta kama mazantakar wannan mutumin tasa wuka ta yanke gaba daya. Wata razananniyar kara ta saki, ta cutu iya cutawa, ta yanda take jin kamar zuciyarta zata fasa kirjinta ta fito. Ita da ko kaza bata taba yankawa ba, yau gashi tana aikata wannan danyen aikin. Fita Fally yayi daga jikinta gaba daya. Sakin wukar tayi da sauri, ta dora hannu a ka, jikinta ko ina rawar tsoro yake. -Me na aikata haka? Meke faruwa da ni? Wayyo Allah na! Ba tare da taji an rike mata kafafuwa ba, ta ari na kare ta fito daga dakin da gudu. Tayi ta gudu, sai da tayi nisa, sai gata kuma ta dawo gaban kofar dakin. Haka tayi ta yi, idan tayi tafiya mai nisa sai ta sake tsintar kanta a daidai dakin. Ta gaji sosai, kwantawa tayi a kasa, tare da rufe idanu da tunanin ko zata farka ta ganta gida tare da yaranta da su Sarah. Domin wannan abun ya wuce hankalin ta, sai dai ko mummunan mafarki! -Mafarki ne nake! Mafarki ne nake!... Ta shiga maimaitawa ba kakkautawa har sai da taji wata murya tace mata : -Wannan gaskiya ne ba mafarki ba, kuma yanzu kika fara gani...! ------------------------------------------------------------ Idan naga comments mai yawa zan yi saurin update 😡 domin naga da alama babu readers a yanzu. ©Al_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 25 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Kwanaki da dama sun shude, har yanzu babu wani labari akan Jinah. Yan biyu har sun fara fidda ran sake ganin mahaifiyar su. Sarah da su Abdul kullum cikin neman ta suke, amma shuru, babu alamun ta. Wata rana da yamma, sun dawo daga neman Jinah, kamar kullum babu wani labari mai dadi. Yan biyu da Infa suna cikin dakin da ya sauka, su kuwa sauran yan gidan suna zaune tsakar gida, sun yi shuru kowa da tunanin da yake. Suna cikin wannan yanayin ne suka ji an budo kofar shigowa gidan. "Jinah" kowane da tunanin ita ce, sai dai Dauda suka gani ya shigo. Hankalin Dauda ya tashi ganin yanayin da yan gidan suke ciki, kuma babu alamun Jinah da yan biyu. -Ina Jinah ta take? Ina kuma yan ta...... Abinda ya fara fitowa daga bakin sa kenan. Sai dai bai kai ga karasa maganar shi ba, yaji wani ya rike kafar sa, idanun shi ya saukar a kasa, Aya ya gani. Rage tsawo Dauda yayi, sannan ya rungume ta, anan yaji a jikin shi irin damuwar da 'yar tashi take ciki. -Me ya faru gimbiya ta? Me yasa kike kuka? Ya tambaye ta cikin sanyayar murya, duk da cen cikin ran shi, zai iya cewa ya cenki amsar tambayar sa. -Mama ce, ba mu ganta ba, mun nema ko'ina amma bamu ganta ba. Ka nemo mana ita dan Allah. Nayi kewar ta sosai. Dan janye ta yayi daga jikin sa, yasa hannun sa ya goge mata hawaye, sannan ya sake rungume ta, tare da yi mata alkawarin nemo mahaifiyar ta. Karawa yayi da cewa : -To ki daina kuka kin ji, kin san bana son ganin yar karamar gimbiya ta na kuka, kin sani ko? Goge hawaye ta shiga yi tana gyada kai, dan uwan ta ne ya karaso wajen, Infa a bayan shi. Ayu shi ma yaji dadin ganin Dauda, kuma shi ma kamar Aya, yayi masa alkawarin zai nemo mahaifiyar su. Hakan ya sakawa Ayu, digon kwarin gwiwa, domin yana tantamar wai Dauda zai yi abinda su suka gagara yi. Amma da yake suna son ganin mahaifiyar su, sai basu raina ta Dauda ba. Dauda juyawa yayi ga bakon gidan, gaisawa suka yi, sannan Dauda ya tambaye shi daga ina yake kuma ya aka yi ya samu kan shi a cikin wannan gidan. Nan Infa ya fada masa, yana kan hanya ne, shi ne ya sauka anan domin ya dan huta kafin ya wuce. Hankalin Dauda bai kwanta da Infa ba. Tantamar tashi bata karu ba, har sai da suka yi musabaha, hannuwan su suka hadu. Nan kowane yaji wani abu game da dan uwan nasa. -Nasan akwai gajiya gareka Dauda, je ka huta. -A'a Sarah, ba zan iya ba, zan je na aje kayana sannan na fita neman Jinah. -Amma ai dare yayi yanzu Dauda... Cewar Sarah. -Ba zan iya runtsawa ba da sanin cewa bansan inda Jinah take ko halin da take ciki ba. Da fadar haka, ya nufi dakin su shi da Jinah, amma kafin nan sai da ya wuce gurin su Nafi ya tabbatar masu da zai nemo Jinah. Dauda bai jima cikin dakin ba, Infa ya shigo. -Waye kai? Infa ya tambayi Dauda. -Kai ma, kai waye? Ya bashi amsa da irin tambayar shi. -Kai ba mutum bane, kuma kai ba aljani ba ne. Cewar Infa. -Kuma kai ma, ba mutum bane. -Kana da gaskiya. Cewar Ayu da ya fado cikin dakin yar uwar shi a bayan sa. Aya ta kara da cewa : -Wani tsohon abokin baban mu ne. -Amma kai Dauda, ya aka yi kasan haka? Ya aka yi kasan shi ba mutum bane? -Tambaya mai kyau, wannan mutumin ko ma waye a gare ku, yana boye muku wani abu, bani da tabbaci amma ina jin akwai aljani a jikin sa. Dan haka ka fada mana kai waye? Duka hankalin su ya koma kan Dauda jin me zai ce. -Ni aljani ne a cikin gangar jikin mutum. Wani lokacin aljanin ne ke nan, wani lokacin kuma ni. Shi yasa gangar jiki na da kuma ruhin aljanin kullum cikin kokowar wanda zai dauki control suke. Kuma sau tari aljanin ke cin nasara, amma wani abu da na gano da zan tsaya a ni, shine mahaifiyar ku, tunanin ta yana sa nayi nisa sosai da aljanin, a lokacin da na fahimci haka, sai naki tunanin komai idan ba nata ba. -Amma ta yaya haka zata yiwu? Kuma ta yaya ka iya dawowa hayyacin ka? -Hindu! Ita ce sanadin komai. -Shedaniya! Cewar Infa cikin bacin rai. Kuma shine ta iya barin ka ka taho a haka? -Eh. Infa cike da zargin Dauda yake, domin yasan ba yanda za'a yi Hindu ta barshi ya zo ba tare da wani dalili ba, haka kawai cikin sauki. -Dare yana kara yi, ya kamata kowa yaje ya kwanta, in yaso gobe mun fita neman Jinah. Cewar Infa. Dakunan baccin su kowanne ya nufa, banda yan biyu da suka wuce dakin Sarah, inda suke bacci tun ranar da mama su ta bata. (.....) -Me kake yi anan? Bana tunanin kayi nasara kan plan din mu a wannan dan lokacin. Ta fada da mamakin ganin shi. -A'a, nazo ne domin wani abun daban. Ya bata amsa. -Ina sauraron ka! -Daya daga cikin su kike so ko ba haka ba, idan fa kika samu duka biyun? -Zan zamo shedaniyar duka shedanu. -Ki taimake ni, ke kuma ki samu duka biyun. -Me kake so? -Kema kin sani, ita nake so. -....... -...... ........ ************** Washe gari da sassafe, dukan su, suna a tsakar gida, za'a iya cewa tun batan Jinah basu sake samun bacci mai kyau ba. Bacci ma ba mai yiyuwa bane, ga yan gidan da suka san daya daga cikin su, basu san a ina yake kuma a wane hali yake ciki ba. Sarah ita, tana cen tana hada karin kumallo, domin duk abinda zai faru, kowanne hali zata tsinci kanta, ba zata gushe tana kulawa da sauran yan gidan ba.... Kowanne dare, wata kila sauran ba bacci suke ba, suna kwance ne kan gado, tunanin halin da Jinah take ciki suke yi, ita kuwa tana zaune ne, bisa tabarmar sallar ta, tana rokon Allah ya dawo mata da Jinah. A wajen ta, Jinah tamkar 'yarta ce ta bata, kuyi tunani halin da mahaifiya zata shiga idan ta wayi gari bata san halin da 'yarta take ciki ba. -Ki goge min hawayen nan. Cewar Dauda ga Sarah, da ya tarar da ita cikin cuisine (kitchen) ita kadai tana kuka. -Su kadai suka rage min a halin yanzu Dauda. -Zaki yi murmushi, idan nace maki nan da kafin faduwar rana zaki ga Jinah? Zuciyar ta ce tayi wani irin bugawa. -Da...da..gaske kake? Kasan inda Jinah'ta take? Gyada mata kai kawai Dauda yayi, yana murmushi har kunne, hawaye na kwaranyo masa, shi ma yana cikin farin ciki kamar ita. -Amma bana son ki fadawa kowa, ina son na basu mamaki. Sarah bata bashi amsa ba, illa rungume shi da tayi, tana kukan farin ciki. Bayan wannan, Dauda ya dauki hanyar neman Jinah. **** Kwanaki na ta shudewa, wahalar yau daban ta gobe daban Jinah ke sha a gurin Fally. Har ta kai ga babu digon hawaye a idanun ta. Jira kawai take idan ya gama abinda zai yi da ita ya kashe ta. Wani abun ma da Fally yake mata, kusan kokarin maida ta mahaukaciyar karfi da yaji yake yi. Sai ta dinga jin wasu muryoyi, motsi da abubuwa na ban tsoro wanda ba ganin mai aikatasu take yi ba. Bugu da kari, kullum sai ya tara da ita, duk da ba ganin shi take ba amma tasan wani yana amfani da jikin ta, abun akwai ban tsoro, ba kamar rashin iya kare kanta da bata yi. Sai dai wani abun gun Fally, kwanaki na shudewa, azabar da yake ji tafi ta Jinah, adadin cutar da ita da yake yi, ninkin zafin da take ji, yake ji. Idan tana kuka, shi ma haka zai yi ta kuka. Idan tana jin zafi, sai yafi ta jin zafin. Amma duk da haka baida niyyar daina azabtar da ita, idan kuma wani bangare na zuciyar sa yana bashi shawarar ya daina, sai wani bangaren yace masa ai ita ta jawa kanta, dan haka ta cancanci hukunci. -Me yasa kake min haka? Jinah ta fada cikin wata shakakkiyar murya. Gaban Fally ya fadi. Dawowa yayi yana fuskantar ta, kamar suna kallon kallo. Bude baki yayi yana son yayi magana, amma ya kasa. Ya kasa ganewa. Shin tana ganin sa ne? Shin tasan ko shi waye? Alhali shi bai bayyana mata kanshi ba a yanzu. -Fada min, ka fidda ni a duhu, nayi wani abu ne da na cancanci duk wannan? Jinah ta fada, ba tare da ta jira jin amsar ta, ta baya ba. Hankalin Fally ya tashi, domin bai shiryawa irin wannan ranar ba, ko kuma bai yi tsamanin ta ba tun yanzu. -Nasan yanzu dangina da 'ya'yana sun fidda rai da gani na, na dade da mutuwa a tunanin su, ba zan iya cigaba da jure wannan azabar ba. Fally bai taba jin ya tsani wani a duniyar nan, kamar yanda yake jin tsanar kan shi a yanzu ba. Sai a yanzu yake jin bai kyautawa Jinah ba, yaji a jikin sa yayi halin karanta. -Dan Allah ka daina, ina rokon ka, ka taimaka ka kashe ni. Akwai zafk abinda kake min. Kai na da ko'ina na jiki na zafi yake min. Akwai zafi! -Akwai zafi! Fally ya maimaita, ba wai zafin da Jinah take ji ba, a'a shi ma irin abinda yake ji kenan a jikin sa. -A... a ina kake? Jinah ta fada, tana dudubawa ko zata ga wanda yayi maganar. Anan ya fahimci ba ganin sa take ba, durkusowa yayi kusa da ita ta yanda har yana iya jin numfashin ta, sannan yace : -Jinah... Ita kuma, sai ta ce : -Dauda? Ta sake maimaitawa Dauda! -Ji...Jinah! Jinah ta! Juyawa Fally yayi, da mamakin sa wa zai gani in ba Dauda ba. Mamaki yake ta yaya simple mutum zai iya kawo kan sa nan. Kafin ya dawo hayyacin sa, har Jinah ta fada jikin Dauda. Wani irin jan takaici kan Fally yayi, kafin yayi wani yunkuri, sai ga yan biyu da Infa sun bayyana a gurin, Ayu ne yayi surkullen da baban nashi ya kasa ko motsi. -Mama! Cewar Aya. Jinah ji tayi kamar an tsomata cikin tekun farin ciki. -'Ya'yana! Allah na gode maka! Dauda sakin Jinah yayi, ta rungume yaran ta. Jinah da yan biyu kuka suke, ita Jinah na kukan farin cikin ganin ya'yanta, su kuma suna kukan ganin halin da mama su take ciki. Kasa sakin junan su suka yi, kamar zasu rama duk lokutan da suka shude basu tare, ta hanyar runguma. Ba su suka saki juna ba, har sai da Infa ya fara magana. -Ta yaya ka iya aikata haka? Me ya shiga kwalwar ka, anh Fally? -Na tsaneka baba! Yan biyu suka fada lokaci guda. Jinah da Dauda basu fahimci meke faruwa ba, amma suna tunanin akwai wani anan kuma shine silar duk wannan abun. -Daga yau, kai ba baban mu bane! Babu wata alaka da ta hada mu da kai yanzu. Na tsane ka, kuma zan cigaba da tsanar ka har abada, ba zan yafe maka zaluntar mama da kayi ba. Cewar Aya cike da tsanar mahaifin nata. Dan uwan ta, ya kara da cewa : -Har abada! Wadannan kalaman a kunnuwa basu wuce iya kalamai ba, amma abinda basu sani ba, kalaman nan suna wargaza wani abu, wata alaka... Faduwa Jinah tayi sumamma, ko kuma mu ce ta fada cikin wani abu mai kama da mafarki. {{{ -Fally tsoro nake ji. -Kar ki ji tsoro Jinah, ina tare da ke! Macecin ki, mai gadin ki! Murmushi tayi har kunne. -Mai gadi na! Ta maimaita. -Eh mai gadin ki! -Haha, daga yau, zan dinga kiran ka da wannan sunan! -In dai zai saka ki farin ciki Jinah. **** -Mama, me ya samu Jinah? A rikice Fally yake tambayar Maman sa. -Kasan nan ba son ta suke ba, ta fita yin wasa, sai... Mama shi ta fada tana share kwalla. -Mama, nayi nadamar yin nesa da ita, daman ban so zuwa wannan kauyen ba, ba tare da ita ba. Ki yafe min Jinah'ta, daga yau ba zan sake tafiya na barki ke kadai ba. Mama, ki duba yanda suka ji mata ciwo, sai sun biya abinda suka yi mata. Nayi miki alkawari Jinah. -Lafiya ta kalau Fally, kar ka damu. -Ba lafiya ba kike Jinah, dubi abinda suka yi miki. -Na roke ka, kayi hakuri, ba zan sake fita ba, kai kadai zan dinga wasa da shi daga yanzu. Murmushi ne ya bayyana a fuskar Fally. **** -Fally, na gaji da tafiyar kasa, me yasa ba zamu iya bacewa ba muyi saurin zuwa gida, kamar yanda muke yi kullum? -A'a, cikin wannan dajin, ba zan iya anfani da karfi na ba, amma me yasa tun dazu baki fada min kin gaji ba? Hawo baya na, na goya ki. -A'a, bana son kai ma ka gaji! -Jinah, hawo ko na dora ki ta karfi, kin san ba da wasa nake ba. -Amma Fally...! Bata karasa abinda take son fada ba, ya sunkuce ta kamar wata gimbiya, sannan suka cigaba da tafiya. **** -Wash, wash! -Jinah, Jinah, me ya same ki? -Na yanke ne da wuka, wash kuma akwai zafi. -Ha..har yanzu, ban san ya ake warkar da ciwo ba, gashi kuma mama da baba basu nan. -Kar ka damu, zan daina jin zafin. -A'a, ba zan iya barin ki a haka ba, tsaya ki gani... -Kar ka yi haka Fally! Shi ma wukar ya sanya ya yanka hannun sa. -Kin ga yanzu sai muji zafin a tare. **** -Ko kin san meye "taken soyayyar Fally"? -Ikon Allah, meye kuma haka nan, kai kullum baka rabo da kayan shirme? -Kina so, ki sani ko kuwa? -hmm to ina jin ka, majnun! -To, bari na fahimtar da ke : Taken soyayyar Fally, wannan soyayyar ce da batada karshe, tsabar girman ta, ba za'a iya kwatantata ba da komai saboda ita kadai ce, tana rayuwa ne domin farin cikin Jinah, soyayya ce da ko jirgin kasa mai tsananin gudu ba zai iya kamo ta ba. Soyayyar da hasken ta, ba zaya taba gushewa ba domin babu wanda yasan adadin sa. Soyayyar dake rayuwa cikin zuciya ta. Soyayyar dake sa ina rayuwa, tana kara min karfi, dake sa zuciya ta, a maimaikon ta dinga bum bum, sai ta dinga bumbumbumbumbum.... Fadawa jikin sa, Jinah tayi tana hawaye. }}} -Mama ki tashi! Cewar Yan biyu, suna girgiza mahaifiyar tasu. -Jinah, Jinah! Dauda da Infa ke ta maimaita haka. Bude ido Jinah tayi, sannan ta mike ta nufi inda Fally yake tare da durkushewa gaban sa. -Fally. Ta kira sunan sa cikin disashiyar murya. Anan dukan su, suka fahimci Jinah ta tuna komai. -Fally. Ta sake fada, amma hawayen dake zubo mata sun kasa bari tayi magana. Kana tune da ranar da na kwanta rashin lafiya? Kowa na ta murna, amma kai kana a kusa da ni. Ka tuna abinda kace min? -E..eh Jinah. -Koda kowa zai tsane ni, koda kowa zai so ya cutar da ni... Amma kai kace min, ba zaka taba yin hakan ba, mutuwa zata fiye maka ganin ranar da zan ji ciwo kuma ya zama kai ne silar shi. Kuma zaka mayar da duk wata damuwa tawa zuwa farin ciki. Ka yi min wannan alkwarin, ka yi min wannan rantsuwar Fally! ...to..toh me yasa? Me yasa baka cika alkawarin ka ba, me yasa ka cutar da ni Fally? -Nayi nadama Jinah, na roke ki, kiyi hakuri ki yafe min! Cewar Fally yana kuka. -Har abada! Ta fada cikin daga murya, hawaye na ambaliya a fuskar ta. -Jinah! -Muje mama! Cewar Ayu. -Yanzu na gane irin cutar dake da nayi, kuma nasan lokaci ya kure min, na bari shedan yayi galaba a kai na, kuma nayi nadama, na makance ba tare da na san abinda nake aikatawa ba. A cen cikin rai na, ina son ki dawo gare ni, amma nasan hakan ba mai yiyuwa bane. Duk lokacin da muka bar kiyayya tayi nasara a kan mu, mu kan bude kofar kwakwalan mu ta yanda duk wani mugun tunani zai shiga, ni kuma hakan ce ta kasance da ni. Duk da wannan Jinah, abu daya nake da tabbacin sa a cikin kai na, soyayya ta gare ki, ita ce kuma zata cigaba da zama "taken soyayyar Fally". Ina son ku, ke da yaran mu, kuma na gwammace na mutu, da rayuwa da sanin cewa kun tsane ni kuma na cancanci haka. Na barku lafiya! Duk wannan doguwar maganar da yake fada, Jinah ta juya masa baya ne, ta nufi kofar fita. Amma kalaman Fally na karshe sun sa ta tsaya cak, wannan yasa ta juyo tana fuskantar sa. Sai dai kuma tuni ta makara, domin Fally ya cakawa zuciyar sa wukar da ita kadai take iya kawo karshen aljani. Kafafuwan Jinah kasa daukar ta suka yi, ta zube kasa kamar wacce aka datsewa kafafun. -A..a'a...! Take fada tana kokarin rarrafawa inda yake. *************************** ©Al_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 26 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Lokacin da Jinah ke kallon Fally a kwance, jini na malala, gangar jikin sa na bankwana da ruhin sa. Wani zafi taji da yafi duk wata azaba zafi na kwanakin da suka shuɗe. -A..a'a Fally, ba zaka mutu ba, nayi nadamar abinda na faɗa maka, na yafe maka, amma kar ka tafi dan Allah. -Ki daina mama, ya riga da ya mutu. -Ku tashe shi! Kuyi duk abinda zaku yi, ina son ya tashi! -Su tashe shi? Ai wannan ba mai yiyuwa ba ne! Cewar Infa cike da mamakin abinda Jinah ke kokarin sanya ƴan biyu. -Saboda me? Nasan zamu iya yin hakan da karfin mu! Cewar Aya. -Koda muna iyawa, ba zamu yi ba, domin abinda yayi wa mama! Ba... Cewar Ayu, wanda da alama mutuwar mahaifin nasa bata taba shi ba. Kallon da mama tashi ta watsa masa ne yasa yayi shuru. -Ko ma me ya aikata, shi ne kuma zai cigaba da kasancewa mahaifin ka. Kada ka bari kiyayya ta rinjaye ka. Ka..kada ka maimaita kuskuren mahaifin ka. Shuru tayi kafin ta cigaba. I..idan da kun san wani lokaci a baya, lokacin muna yara. Ni nasan shi a wancen lokacin, babu wani mai zuciya mai kyau irin mahaifin ku. Ta faɗa da alamun ta tuna abubuwa da dama. -Sai dai kuma yau, babu mugu irin shi, kalli fa irin azabtar dake da yayi mama! Cewar Ayu cike da wani yanayi mai kama da tsana. Sai dai akasin haka ne, bangaren yar uwar shi, mutuwar mahaifin ta ta taɓata sosai, ita ma tana son ya dawo, domin ba zata so rashin mahaifi ba, a irin wannan yanayin, duk da mintuna kadan baya da yana raye, babu abinda take fata face mutuwar sa. -Ni ina son ya tashi! Cewar Jinah. -Jinah, cewar Infa. Ina tunanin baki san wannan ba, tayar da aljanin da ya mutu abu ne da ba'a taba yin sa ba. Domin ba zai koma kamar yanda yake a baya ba, kuma a yanda zai tashi, hakan ba zai yiwa kowa daɗi ba. Domin zai iya tashi a sheɗani. Kamar bata ji ko kalma daya daga abinda ya faɗa ba, Jinah ta umarci ƴaƴanta da su tashe da baban su. Kokarin tashe shi suka shiga yi, ba irin karfin da basu yi aiki dashi ba, ganin sun tayar da shi amma sun kasa. Bayan ɓata lokaci mai yawa da suka yi, daga karshe suka ce mata ba zasu iya ba. Cigaba da rizgar kukan ta tayi. Daƙyar suka iya bamɓare ta, suka bar wurin. Jikin Dauda yayi sanyi, tun lokacin da yaga Fally ya mutu. Da farko saboda bai fahimci abinda ke faruwa ba, na biyu kuma ganin halin da Jinah take ciki. Sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa bai taɓa samun soyayyar da yake fata ba daga gare ta, ashe wani take so, kuma ba kowa ba face Fally. Kuma yaga irin girman soyayyar da take nunawa Fally : ta yafe mishi duk da irin cutarwar da yayi mata. Murna marar misaltuwa sai gida gun Sarah. Kuka take yi ba kakkautawa, ta yanda duk wanda ya gani zai yi tantamar anya na farin ciki ne kuwa, amma sai dai ganin irin murmushin da ke shimfiɗe a fuskar ta zai bayyana maka kukan farin ciki ne. Haka take ga sauran yan gidan. A ranar farin cikin su ya kasa boyuwa. Zamu iya cewa Jinah ta manta da duk wata wahala da tasha a bayan nan, ganin yanda take cikin farin ciki. -Nagode Dauda, ban san da me zan biya ka ba, kayi min alkawarin zaka nemo min ta, gashi ka cika. Cewar Sarah kafin hawaye su kwaranyo mata. Murmushi Dauda yayi mata, ko kuma mu ce yake mai kama da kuka, wanda ba kowa na wurin ba ya lura. Zarewa yayi daga wurin, ya shige ɗaki, hankalin sa duk a tashe. -Ta yaya har ka iya gano inda Jinah take? Faɗa mana gaskiya! Infa da ƴan biyu ne suka yiwa Dauda wannan tambayar. Ba tare da yaga shigowar su ba, kamar ma sun rutsa shi. -Zan faɗa maku komai. Dauda ya faɗa a fusace. -Nayi yarjejeniya ne da Hindu. -Ni fa na sani, ba yanda zata iya barin ka, ka taho haka. Cewar Infa. -Sati ɗaya ta bani, na kawo mata ɗaya daga cikin ƴan biyu, ta barni a raye. Mamaki ne ya dabaibaye fuskokin su, suna bin sa da wani kallo. -Kuma ma ba shikenan ba, lokacin da naji labarin Jinah ta ɓata, na tambaye ta, ta faɗa min yanda zan ga Jinah, tare da yi mata alƙawarin duka ƴan biyun... -Innalillahi! Jinah ta faɗa a gigice jin abinda kunnen ta ya jiwo mata daga shigowar ta. Kwalar Dauda ta shaka tana faɗin : -Me..me ka aikata ne Dauda... ƴaƴa na?! -Kin manta wani abu Jinah, ni dolo ne! Kuma dolonci na, shi ne son da nake miki, fiye da kowa. Har abada ba zan taba cutar dake ba da sani na. Kuma ni ba sakaran Fally'n ki bane, da bansan me nake yi ba. Nayi wannan yarjejeniyar ne da Hindu saboda... -Saboda me? Me hakan zaya haifar, kai kasan irin son da nake wa ƴaƴana kuma nafi ƙaunar mutuwa ta da na rasa su! Toh saboda me?! Saboda me kuke son cutar da ni? Fushin Dauda raguwa yayi ganin halin da Jinah ta shiga. A hankali yace : -Nayi wannan yarjejeniyar ce kawai dan na gudarwa Hindu, kuma dan na karashe sauran kwanaki na a tare da ku, idan da ban yi wannan ba, da ba zata taɓa bari na na dawo ba, ko kuma ma ta kashe ni, har abada ba zan taba bayar da ƴaƴan ki ba, suna cikin cikin ki lokacin da na muka fara haɗuwa, ƴaƴana ne nima Jinah, soyayyar da nake musu ba mai ƙirguwa bace, zan iya bada rayuwa ta domin su, domin ke. -A'a..a'a..Dauda. Jinah ke faɗa tana riƙe da fuskar Dauda. -Idan har lokacin da ta ɗibar min ya cika, kuma ban kawo mata ƴan biyu ba, to zata kashe ni. Ni kuma abinda ba zan taɓa yi mata ba. Shi yasa na zaɓi nazo na ƙarashe kwanaki na da ku cikin farin ciki. Wannan shi ne kawai buri na. Jinah, ƙafafuwan ta kasa ɗaukan ta suka yi, sai gata ta durƙushe a kasa. -A'a kada kayi min haka Dauda, bana son kai ma na rasa ka. Jinah ta faɗa cikin wata ƙaramar murya. Ƴaƴanta kuwa tsabar sun girgiza, sun kasa motsa koda bakin su, domin basu shirya zuwan irin haka ba. Dauda ya kasa cewa komai, shi ma zauna yayi a kasa, ita kuwa Jinah ta haɗe kai da gwiwa. Shuru wurin yayi kamar na wasu mintuna kafin Infa ya katse shurun da cewa : -Bai zama dole sai ka koma wajen ta ba, ni da ƴan biyu zamu yi ƙokarin kare ka. Kowa a wurin sai da yasa rai a kan plan din Infa kafin Dauda ya sare musu gwiwa da cewa : -Tana controlling duk wani motsi na ne daga nesa, sau da yawa nasha kokarin guduwa, amma bansan ta yaya ba, sai na ga na kara komawa gare ta. -Shedaniya! A hannun ta kake! Cewar Infa. -Lokacin da baba na ya mutu, ban ji wata damuwa ba domin nasan ina da kai, a gare ni, kafi baba na, kar ka tafi ka barmu baba. Cewar Ayu, cikin yanayin nuna tsantsar kaunar da yake wa Dauda. Shi ma Dauda cikin bakin cikin zai rabu da su yake, amma ba yanda zai yi. Dauda rungume Ayu yayi, sannan yayi wa Aya nuni da ta taho. Ita ma kamar mahaifiyar ta, tashin hankalin da take ciki marar misaltuwa ne, ta yanda daƙyar ta iya buɗar bakin ta tace: -Bana son ka tafi, kar ka barmu dan Allah. Kara ƙanƙame su sosai Dauda yayi, shi kanshi baya son rabuwa da su. -Jinah! Jinah! Jinah! Suka yo kan Jinah gaba ɗayan su, ganin ta zube kasa bata motsi. Cak Dauda ya ɗauke ta, ya kwantar da ita kan gado, su kuwa yaran suka yi waje kiran Sarah da sauran. Dubawa suka yi, suka ji tana numfashi. Kumatun ta ya dan tattaɓa, a hankali ta buɗe ido. -Sannu Jinah, duk wannan mai wucewa ne wata rana. Nasan kin gaji, kin sha wahala sosai, amma ina son ki sani komai yana da karshe. Dauda ke faɗa mata haka, yana mai shafar fuskar ta. Wahala ta rayuwa dai Jinah ta ganta, kuma fiye da haka na tafe. ***** -A ina nake? Kuma ke wacece? Sannan ni waye? Farkawa yayi, ganin wata mata da bai san ko wacece ba, Gashi shima kuma bai san ko waye shi ba. -Ni shugabar ka! Ta bashi amsa a taƙaice. -Ina jin ƙishi! Ya faɗa yana taɓa makoshin sa. Miƙo masa tandu biyu tayi, dayan ɗauke da ruwa, ɗayan kuma da jini a ciki domin ta tabbatarwa kanta a yanayin da ya tashi. Eh Fally ya dawo daga duniyar matattu, ƴan biyu sun ɗauka karfin su bai iya tayar dashi ba, amma ba haka bane, domin da sun ƙara hakuri na wani dan lokaci toh zai tashi a gaban su. Hindu kuwa tana laɓe lokacin da suke ƙoƙarin tayar dashi, kuma tasan sun iya, sai ta ƙyalesu, suna bada baya tazo, anan taga zuciyar sa na bugawa. Farin ciki ne fal a ranta. Idan aljani ya mutu, sannan aka yi kokarin tashe shi, toh fa yana tashi ne tamkar jariri, babu komai cikin kan sa, toh daga nan zai fara daukar sabbin abubuwa, walao sharri ko alkhairi. Fally mika hannu yayi, ya karbi tandu mai dauke da jini, ya shanye a take. Hindu kuwa daɗi ne ya lulluɓe ta. -Zamu je mu ɗauki fansa! Hindu ta fada cikin karaji. -Fansar wa? -Ta makiyan mu, da suka cutar da mu, kuma dole su biya. -Dole zasu biya! Shi ma ya sake maimaitawa. -Ina son ka san wani abu, ni shugabar ka ce, kuma dole ka bi umarni na. -Yanda kike so Shugaba, zan iya samun ƙari? Ya faɗa yana nuni da tandun jini. -Zaka samu, kuma sai ya ishe ka, mu je lokaci na ƙurewa! Jinah da dangin ta zasu ji daɗin ganin mu. Cewar Hindu da sigar sheɗanu. Kamar kyaftawar ido, suka bayyana a ƙofar gidan su Jinah. Sai dai basu shiga ba, suka tsaya bakin ƙofar, domin tasan ko su waye ƴan biyu. Don haka dole sai sun yi taka tsantsan. -Infaaa! Infaaa! Fally ya shiga ƙwalawa Infa kira bisa umarnin Hindu. Kiran kuwa ya isa kunnen Infa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya bayyana gaban su, ba tare da ya fahimci meke faruwa ba. Fally ne a gaban sa, bai gama mamakin ganin Fally ba, sai ya tsinkayi Hindu a bayan Fally, nan ya gama yankewa kansa wannan ba alamu bane mai kyau. -Fally...am..amma ta..yaya.. -Kai Fally bamu da lokacin yi masa bayani ka kashe shi! Hindu ta umarci Fally, murya cike da karaji. Ba tare da wani tunani ba ya cika umarnin ta. Infa bai samu lokacin maida martani ba, bare kuma ya kare kansa, sai lokacin da yaga jinin sa na zuba sannan ya fahimci meke faruwa, Hindu nada babban makami, kuma Fally ne makamin nata. -Mun gama da wannan! Ɗauke gawar ka jefar, sannan ka dawo. Cewar Hindu. Ƴan biyu ne suka karaso wajen, ganin mahaifin su yasa suka kwaso a guje suka nufo shi, ba tare sun yi tunanin ta yaya mahaifin nasu ya tashi ba, har da Ayu da tuni mutuwar baban nashi ta fara taɓashi. kafin su karasa jikin sa, tuni Hindu ta tsikarawa kowannen su, wata allura a gadon baya, fadawa jikin baban nasu suka yi summamu. -Yauwa! Yanzu ka shiga gidan, kaji daɗin ka, kayi yanda kake so da mutanen gidan, ka sha jini iya son ran ka. Bata jira jin amsar shi ba ta ɓace da ƴan biyu. Ɗaki na farko da Fally ya tarar shi ne na Jinah, tana kwance ita kaɗai bisa gado, idanun ta a rufe, da alama sauran sun fita ne sun barta domin ta huta. Matsowa Fally yayi sosai kusa da Jinah, santin kyawun ta ya shiga yi, kasa motsawa yayi kamar bai taɓa ganin halitta mai kyau ba irin Jinah. Yatsun sa, ya tura cikin gashin kanta, sannan yabi tsawon gashin, tare da janye wani daga gashin da ya rufe mata fuska, anan ya kara shaida kyan da take da shi. Kasa controlling kan sa yayi na son taba jikin ta, anan ya shiga yawo da hannun sa kan fuskar ta. A hankali ta bude idanun ta, idanun ta cikin idanun sa, numfashin su ya hade, shuru ya mamaye ko'ina, ba tare da bata lokaci ba, Fally ya tsinci laɓɓan sa cikin na Jinah, ita ta fara sumbatar sa, kafin shi ma ya biye mata. A hankali sumbatar ta kara karfi, daga nan suka lula wata duniyar, sun sha soyayya kamar ba zasu dena ba. Duk wasu sassan jiki na Fally magana suke, yana jin tamkar ana saka masa lantarki. Bai fahimtar meke faruwa, amma yana jin abun da karfi sosai da haɗuwa iya haɗuwa, zuciyar sa na wani irin bugawa da za'a iya jiwowa daga nesa, numfashin sa na yin sama-sama. Yanayin ya dauke su wani dogon lokaci, dukan su biyun suna jin su tamkar a wata duniyar da su biyu kaɗai zasu iya rayuwa a ciki, kuma domin rayuwa a cikin ta, dole sai sun rayu tamkar a gangar jiki daya. Ƙarar da Jinah ta kwalla ne ya kawo karshen yanayin da suke ciki, Fally ne ya gatsa mata wani cizo a gadon baya, ba da gangan ba. Jin ɗanɗanon jinin a bakin sa ya dawo dashi duniyar mu. Jinah tambayar kanta take : -Me yasa nake jin zafi alhali mafarki nake? ************************ 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 27 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Ganin Jinah da kuma yanayin da suka shiga a yanzu, yasa Fally ɗorawa kan sa wasu tambayoyi da ya kasa samun amsar su : "Me yasa nake jin damuwa akan wata halitta da ko sanin ta ban yi ba? Me yasa nake jin ina bukatar ta a kusa da ni? Me yasa zuciya ta ke jin zafi domin na cutar da wadda kasheta nazo zan yi? Me yasa bana jin sheɗancin dake jiki na domin ina kusa da ita? Me yasa lokacin da jikin mu ya haɗu, nake jin zuciya ta kamar zata fashe? Me yasa ganin hawayen ta, nake jin tamkar ana zuba min ruwan zafi a jiki?" Zafin da Jinah take ji ne ya dawo da ita hayyacin ta, iya karfin ta tasa ta ture Fally, sannan ta jawo lullubi ta rufe jikin ta, zuciyar ta na wani irin bugu. Kallon kallo suka shiga yi, nan Jinah ta gasgatawa kan ta da ba mafarki take ba. -Fally? Cewar ita cike da mamaki. Shi kuwa bai bata amsa ba. -Wai mafarki nake ne? Ta sake maimaitawa. -Ke wacece a gare ni? Ya bata amsa da wata tambayar. -F..Fa.. Wannan karon rawan tsoro take, domin ta gasgata Fally ne da kan shi, sai dai ya manta ko wacece ita. Nan kalaman Infa suka dawo mata : "Zai iya tashi a sheɗani." Tsoron ta kara daɗuwa yayi. Fally rage dan nisan dake tsakanin su yayi, ita ta ƙwalla kara sosai, wadda ta janyo hankalin Sarah, ƴaƴan mijin ta da kuma Dauda. Ba tare da wani tunani ba, suka kwasa zuwa dakin Jinah, nan suka ganewa idanun su, wani ƙato na kokarin cutar da Jinah. Kafin suyi wani ƙwaƙwaran motsi, ya ɓace da Jinah akan idanun su, Sarah da Nafisa zubewa suka yi sumammu. Jinah da wannan mutumin da basu san ko waye sun bace a gaban idanun su. Shi kuwa Abdul kasa motsawa daga inda yake yayi. Dauda ne kawai, ya karasa daidai wurin, hankalin sa a tashe. Nan ya shiga dukan bangon, da sa ƙafa yana kutufo da duk abinda ke kusa da shi. Yau ne yake bakin cikin rashin karfin kwato Jinah, baida wata dabara ta sanin inda zai ga Jinah, babu wanda zai iya taimakon sa a yanzu. A take ya tuna da ƴan biyu su zasu iya taimakon sa, sai dai daga baya jikin sa yayi sanyi, domin yasan da ƴan biyu na cikin gidan da su zasu fara kawowa mahaifiyar su ɗauki, ko kuma Infa yana ina? Rashin ganin su, bai nuna masa alamu mai kyau. Fita yayi daga ɗakin ya bar sauran cikin yanayin rudu. A bakin ƙofar gida, Dauda ya shiga dukan kan sa da hannayen sa. Idan ka gani zaka ɗauka mahaukaci ne sai dai shi yasan me yake yi, domin yanzu wannan hanyar ce kaɗai zata sa ya samu wata solution; yana son ya fitar da Jinah daga kan sa, domin aljanin dake jikin sa ya dawo aiki. Yasan akwai haɗari yin hakan amma wannan ita kaɗai ce damar sa. Sai dai hakan ba sauki gare shi ba domin ya kasa fitar da hoton aljanin da ya gudu da Jinah daga cikin kan sa. Daga karshe cuisine (kitchen) ya nufa, ya ɗauki wata ƴar ƙaramar wuƙa, ya saita daidai hannun sa, ya rufe idanu tare da cije hakoran sa, sannan ya cakawa hannun sa wuƙar. Wani ihun wahala ya saki, sai dai ya ci nasarar abinda yake son yi, zafin da yaji na dan lokaci yasa ya manta da Jinah, a take aljanin jikin sa ya ɗau aiki. A nan yaji babu alamar aljani cikin gidan. Babu Infa, babu ƴan biyu a cikin yankin gaba ɗaya. Tunanin sa na farko ya kai kan Hindu, ba ɓata lokaci, sai gashi ya bayyana a maɓoyar ta. Bai yi mamakin ganin ƴan biyu kwance a wurin, ba a hayyacin su ba. Ƙoƙarin zuwa yayi inda suke, Hindu ta daka masa wata tsawa : -Me kake yi a nan? -Ba ni nayi miki alƙawarin zan kawo miki su ba?! -Na samu wata hanyar da tafi take. Wai ya ma aka yi bai kawar min da kai ba? Waro idanu Dauda yayi, da mamaki. -Wa kenan? Wani kika tura ya kashe ni?! -A'a ya kashe ku dai! Domin baka da wani sauran amfani gare ni. -Kenan shi ne ya ɗauke Jinah? Waye wannan? -Hahah, sheɗani na, Fally! -M..me? Bai mutu ba? -Eh, amma kai yanzu zaka mutu. Wani irin bugu zuciyar Dauda tayi. Tunani ya fara : A'a ba zan bari ta kashe ni ba, wa zai ceci Jinah da yaran ta? Hindu zata haɗa musibu da dama idan har tayi nasarar mallakar karfin ƴan biyu. Hannu yasa ya danna ciwon da ya jiwa kan shi dazu, take zafi yasa ya manta da Jinah, aljanin ya sake dawowa, Dauda ya ɓace daga wurin, sai dai cikin rashin sa'a yana dira inda yake tunanin ya gujewa Hindu, sai gata itama ta dira a wurin. -Na roƙe ki kar ki kashe ni! -Na ƙyale ka, kaje ka aikata wani abun a bayan ido na ko, ai nasan yanda ka damu da Jinah da ƴaƴanta. -Zan fitar da su daga tunani na, sai aljanin dake jiki na ya dawo aiki, kuma kinsan irin biyayyar da yake miki. -Bari nayi tunani... Jim tayi kaɗan kafin tace "A'a!". Yatsu kawai ta ƙyasta sai gasu sun dawo maɓoyar ta. Tattaɓa jikin sa Dauda ya shiga yi, domin ya ɗauka ko har ta gama dashi ne. -Kar ka damu, zaka jira na dan lokaci, zan ji da kai daga baya, yanzu zan ji da waɗancen ƴan biyun, domin gubar da na basu ba mai daɗewa bace. Cewar Hindu. Kokarin motsawa Dauda yayi, amma yaji kamar an riƙe masa ƙafafuwa, nan ya fahimci tayi hakan dan kar ya sake wani yunkuri. Wani jan ƙyalle Hindu ta shimfiɗa a kasa, sannan ta zuba wasu ruwa dake cikin wata kwalba da ta bayyana a hannun ta. Matsawa tayi kusan ƴan biyun, sannan ta dauko Ayu. Roƙon ta Dauda ya shiga yi da kar tayi, amma kamar ma yana zuga ta. Kwantar da Ayu tayi kan jan ƙyallen. Sannan ta shiga karanto wasu kalaman tsafi, wanda dakyar na iya gano kalmar : "Uwar gijiyar sammai da kassai!" -Ki dakata Hindu, ki daina na roƙe ki! Dauda bai yi kasa a gwiwa ba, yana cigaba da roƙon ta, yana kuka kamar jinjiri sabon haihuwa dake jin yunwa. Duk da namiji ne shi, amma bai damu da irin kukan da yake ba, domin zafin biyu ya zamar masa, na farko saboda shi, yana ganin za'a kashe masa ɗa, sai kuma Jinah, wayyo Allah, idan aka fada mata ɗanta ya mutu, ba lallai bane ta iya jurewa ba. Da taga ya fara isarta da raki. Wani surkulle Hindu tayi bakin Dauda ya rufe, ta mayar dashi kurma, babu abinda ya iya yi yanzu face hawaye. Wata ƙar karamar sanda ta ɗauko, wadda take da tsini kamar mashi. Hannun ta ta kai kan tsinin, nan take ya soketa sai ga jini. Wata mahaukaciyar dariya tayi. Da wannan karamar sandar ta zana croix (cross) bisa kirjin Ayu, kafin ƙyaftawar ido ta cakata a tsakiyar cross din dake kirjin Ayu. Ba ɓata lokaci sai ga wani bakin hayaki na fitowa daga ƙirjin Ayu zuwa jikin Hindu da ta ɗaga hannuwa sama cike da jin dadi. ***** -Ka taimake ni, ni kuma zan amsa maka duk wasu tambayoyin ka. Cewar Jinah. Mamaki ne ya kama Fally, tambayar kan sa yayi, ko dai karanta tunanin sa tayi. Sai dai ba haka bane, Jinah ta yiwa Fally farin sani, tasan idan har Fally yana da tambayoyin da ya kasa samun amsar su, ya kan yawaita motsa yatsun sa kamar mai jan carbi. Duk da yanzu alaƙar dake tsakanin su ta rushe, amma akwai wata alakar da tun kafin su je suyi aure akwai ta. Sun so junan su kafin aure, ya kula da ita tun kafin ta iya rarrafe, shi ya taimaka mata ta iya rarrafe, ya taimaka mata ta iya tafiya, ya kula da ita, ya saka kan sa a haɗari domin ta, ya sadaukar domin ta, ba sau ɗaya ba. Yanzu ya manta da ita, amma kuma zuciyar sa da ruhin sa sun san ita ko wacece. Akwai alaƙa mai girma tsakanin Jinah da Fally kuma babu abinda zai canja hakan. -Ta yaya kike son na taimake ki? -ƴaƴana, kafin ka shiga ɗaki na, nayi mafarkin suna cikin haɗari. Gashi yanzu ina tunani, kuma ina jin tsoron abi..abinda zai same su. -ƴaƴan ki? -ƴaƴan mu, ƴan biyu, Aya da Ayu! -Su..suna tare da shugaba ta, Hindu. -Mene? A'a! Ka cece su, nayi maka alƙawarin, zaka samu amsoshin tambayoyin ka. Hindu tana amfani da kai ne, kada ka yarda da wannan sheɗaniyar. -Ke ma ba zan yarda da ke ba. -Kalle ni cikin ido Fally, ka yarda da ni, dan Allah. Dan jim Fally yayi kafin yace : -Shikenan! Da falar haka, ba'a dau wani lokaci ba, sai gasu sun bayyana a maɓoyar Hindu. Da isar su wurin, kasa ta fara girgiza, sama tayi jawur. Duk da wannan bai tayar da hankalin Jinah ba, dalilin tsinkayo ɗanta da tayi a kwance, jini na zuba, ga kuma wani mashi soke a daidai zuciyar shi. Numfashi ne ya fara gagarar Jinah, yin ƙarar ma ta kasa, lokaci guda ta koma tamkar marar baki. Ɗanta ya mutu, bata gasgata hakan ba, sai da taga ya koma normal yaro, da ba zai wuce shekaru uku ba. Idan jin zafi yana kashe mutum a take, toh da tuni Jinah ta jima da mutuwa domin zafin da take ji, ya wuce na misali. Dauda yana nan a wurin, yana kallon ta, ba tare da ya iya matsowa kusa da ita ba, bare ya rungume ta, ya tayata bakin ciki, domin kafafuwan sa tamkar an saka siminti. Ba kuma zai iya faɗa mata : Kada kiyi kuka Jinah, kwantar da hankalin ki, kiyi juriya, Allah yana tare da ke, komai zai wuce, ke jaruma ce... saboda babu murya. Shi kuwa Fally, ba tare da sanin dalili ba, wata shawara ta zo masa a kai, ya kashe wannan Hindun, abinda bai sani ba, shi ne : Karfin ta ya karu, ta yanda lokacin da yayi ƙoƙarin kai mata farmaki, naushi ɗaya tayi masa, sai gashi ya bugu da bango, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake kai mata wani farmakin. Wannan karon, a daidai ƙafafuwan Jinah ta jefo shi. -Ki bar nan! Ni zan ji da ita! Ki gudu! Cewar Fally, kafin ya sake miƙewa; Aya! Jinah ta shiga kiran sunan ƴarta, idanu ta shiga rarrabawa, cen ta hango ƴar tata a kwance. Wani karfi ne yazo mata, ta ɗauka a guje ta nufi wajen ƴarta, ɗaukan ta tayi ta rungume. Gudu Jinah take iya karfin ta, ba tare da tasan inda take nufa ba, hawayen kuwa sun kasa daina zubo mata. Wata iriyar faɗuwa tayi, lokacin da Hindu ta dira gaban ta. -Ita! Babu inda zata je! A yanayin yanda Hindu tayi maganar, zai iya fasa kunnen mutum tsabar rashin dadi da tsoratarwa. Ita kan ta Jinah sai da taji zuciyar ta, ta canja bugu tamkar ana buga ganga. Fally ne ya bayyana a gurin tare da kaiwa Hindu wani mahaukacin naushi, a nan take su biyun suka bace, ita kuwa Jinah ta cigaba da gudun ta. Hakan ce tayi ta faruwa, kuma a ko da yaushe sai Jinah tayi tunanin tasu ta ƙare. Fally ya gaji, kawai ya riƙe wuta ne, kuma kare kai kawai yake yi, domin ba zai iya hada ƙarfin sa da na Hindu ba, sake taso shi daga mutuwa, shi ya kara masa ƙarfi, sai dai ita Hindu nata ninkin ba ninkin nasa ne, domin cen dama ita mai ƙarfi ce, gashi kuma ta ƙara da na ɗaya daga cikin ƴan biyu, duk da ba duka ƙarfin Ayu ba ta kwashe, domin sai an ɗau lokaci kafin ta same shi baki ɗaya. Fally kam yayi ƙoƙari tunda har ya iya kai wannan lokaci yana gwabzawa da ita. Amma yanzu, Karfin sa ya ƙare, ganin tsayuwa na shirin gagarar sa, ya shammaci Hindu, ya ɓace da Jinah, ya kaita gida. Sannan ya haɗa wata katangar tsafi a bakin kofar da ta hana Hindu shigowa. -Gata nan zuwa! Gata nan tafe! Sheɗaniya! Yo kan Jinah su Sarah suka yi, cike da ruɗu da farin cikin ganin ta, tuni suka dawo hayyacin su, sai dai yanzu kuma wani sabon tsoron ne ya shige su, jin abinda Jinah ta faɗa. -Ku mu gudu daga nan, za.. Sauran kalaman nata suka tsaya a baki, ganin Fally ya faɗo daga sama a kan idon su. Kafin suyi wani yunƙuri tuni Surayya ta dira gaban su, cikin wata mummunar shiga. Jinah kara ƙanƙame ƴarta tayi cikin ƙirjin ta, Nafisa ta ɓoye bayan Sarah da Abdul. Ita kuwa dan ta ƙara tsorata su, sai ta ɓacewa ganin su. Jinah ji tayi ana ƙoƙarin ƙwace mata ƴa ba tare da tana ganin ko waye ba, faɗa ta shiga yi iya ƙarfin ta domin ganin ƴarta tata bata bar jikin ta ba. Sake bayyana Hindu tayi rai a ɓace. -Ya..ya aka yi na kasa raba ku?! Hindu ta faɗa cike da ƙaraji da jin haushi. -Ki bani ita, ni kuma zan rabu da ku! Hindu ta sake faɗa, ita kuwa Jinah taƙi sakin ɗiyar. Hindu kallon Sarah kawai tayi, ita kuwa ta shiga kokowar ƙwatar numfashi kamar an shaƙe ta. -Ki rabuta da ita, dan Allah! Jinah ta shiga roƙon Hindu. Abdul ne ya taƙarƙare, ƙawadawa Hindu wani benci dake kusa da shi. Hakan da yayi kuwa, yayi nasar dawo da numfashin Sarah. Sai dai kuma hakan ya ƙara fusata Hindu, nuna hannu kawai tayi sai ga Abdul yayi sama, kanshi ya gauru da bango, ya faƙi sumamme. -Abdul! Dukan su, suka kira sunan sa a tare. Da gudu yar uwar shi tayi kan sa tana jijjiga shi, tana kuka. -Kin raba ni da ɗana, ki ƙyale min ƴata, ki bar min ita! Ki bar min ita! -Ta kashe min dan uwa, mama! Aya ta faɗa da wata ƙaramar murya, ta faɗi hakan ne ba tare da bakin ta ya buɗe ba. Da alama gubar ta fara raguwa. -Ayu ya mutu mama, na sani, kuma naji a jiki na. Aya ta sake faɗa, har wa yau tana kwance jikin maman ta. Hakan yasa Jinah ƙara shiga cikin ƙunci, kalamn ƴarta sun taɓa ta. -Bani da lokaci! Ki bani ita yanzu kafin ta wartsake daga gubar, ko kuma na kashe su duka. Hindu ta fada a fusace tana nuna su Sarah, Jinah kuka take iya ƙarfin ta, zaɓi tsakanin ƴarta ko Sarah, wadda ta zame mata kamar uwa, ƴar uwa, babbar aminiya... a taiƙace ita komai ce gareta. Sai kuma Abdul da Nafisa, mutanen nan biyu da take matuƙar so, waɗanda take jin kamar akwai wata alaƙa mai ƙarfi tsakanin su... Ta yaya zata iya wannan zaɓi. -Ni ki ɗauke ni, ki rabu da su. Cewar Sarah. Wata mahaukaciyar dariya Hindu tayi. -Babu wani amfani da zaki min! -Mama, ki barta ta ɗauke ni. Cewar Aya, wadda maman ta ce kadai taji hakan, jin maman tata na shakku tace : -Ki yarda da ni mama, komai zai tafi daidai. -Ki ɗauke ta, amma kafin nan ki barsu su tafi, ki barsu su kai Abdul asibiti. Cewar Jinah cike da dauriyar zuciya,tana mai miƙawa Hindu Aya. Ita kuwa Hindu tsabar murna, kamar ƙyaftawar ido, ta kai su Abdul asibiti, sannan ta dawo ba ɓata lokaci, ta ɗauki ƴar yarinya Aya, sai dai farin cikin nata bai wani ɗauki lokaci ba, domin Aya tuni ta ɓacewa ganin ta, daga kan hannayen ta. -A'A! AHHHH!!! Hindu rai a ɓace, tayi wata kururuwa, ƙasa ta shiga girgiza, tuni guba aikin ta ya ƙare a jikin Aya, Hindu bata yi tsamanin abun ba zai mata sauki ba kamar yanda tayi fata. Ƙoƙarin kama Jinah take domin tayi garkuwa da ita, kafin Aya tayi wani yunƙuri, bata kai ga kudirin ta ba, taji wani abu na mata tafiya cikin jiki, kafin tayi ƙoƙarin kakkaɓe wannan abun, tuni har ya kai ga zuciyar ta. Wani masifaffen zafi ne taji da yabi kowanne sassa na jikin ta, razananniyar kara ta saki, kara mai bala'in karfi, karar da tafi wacce bokanya Karaba tayi, lokacin da Kiriku ya saka hakorin sa domin cire ƙayar dake a gadon bayan ta, wadda ta mayar da ita matsafiya. Hindu durkushewa tayi kasa tana cigaba da ihun azaba, lokaci kaɗan Jinah ta hangi ƴarta, haƙoran ta datse kan ƙirjin Hindu, da take ta ihun neman taimako. -Ki dakata Aya, cewar Jinah, sai dai bata da alamun dakatawa, kamar wani shedani ya shiga jikin ta. Da hakoran ta, ta yage duka fatar jikin Hindu, sannan ta saka hannun ta, ta fizgo zuciyar Hindu da tuni ta jima da mutuwa. Kuma Aya ta sani amma duk da haka bata dakata ba, kuma bata daina maimaita :"Ita ta kashe min dan uwa!" ba, hawaye na zubo mata. Ganin haka, Jinah ta taso ta janye ta, tare da rungume ta, tana lallashin ta. -Jinah. Dauda ne da ya karaso wajen ya kira sunan ta. Hannayen sa dauke da gawar Ayu. -A'a, a'a, ba zan iya jure kallon sa, ba zan iya ba! Jinah ta faɗa tana kuka, ganin gawar ɗanta. Ɗaki Dauda ya wuce, ya kwantar da shi. Sannan ya dawo da niyyar lallashin Jinah. Kukan Jinah ƙaruwa yayi da ta tsinkayi Fally a kwance dan nesa da ita, rarrafawa tayi wajen sa, ta shiga kokarin tashe shi. -Ka tashi Fally, kar ka barni, ba yanzu ba, ɗan mu ya mutu, kar ka tafi ka barni! -Bai mutu ba, cewar Aya. -Toh me yasa yaki tashi? -Gangar jikin sa ce ta mutu, amma shi yana raye. "Toh meye banbanci ya mutun kenan." Jinah ta fada cikin ranta, tana mai shashantar da maganar yar tata, kafin ta cewa Dauda ya tafi da Aya, su ɗan barta ita kaɗai na wani dan lokaci. Dora kanta tayi kan ƙirjin Fally, ta shiga magana magana ita kaɗai : -Ku biyu a rana ɗaya, ta fada tare da jan dogan numfashi. Ka kula min da Ayu na idan kuka haɗu, na san shi da taurin kai, amma kar ka dukan min shi, yaron kirki ne, ka faɗa masa ina son shi, da dukan zuciya ta, ba zan taɓa manta shi ba, ba zan taɓa mantawa da ku ba. -Har yanzu ina nan! Kamar daga sama taji anyi maganar. -Fally? Ta shiga waige waige. -Ruhina har yanzu yana nan Jinah! Ya sake maimaitawa, gangar jikin da ke gaban ta, babu alamun rai a tare da ita, bata numfashi, bata magana, amma gashi tana jin muryar sa. -Toh ka tsaya a nan dan Allah, kada ka tafi, jin alamun ka ya ishe ni, ka tsaya a tare da ni. -Ba zan iya ba, ko ba jima ko ba daɗe dole zan ɓace na har abada. -Kada kace haka, b..ba..bana son.. -Ina tune da komai Jinah, ta yaya zaki so kara kasancewa da ni bayan abubuwa nai miki? Kamata yayi ki tsane ni. -Ban sani ba, kuma bana ma son na sani, idan ba soyayya ba, babu abinda nake ji game da kai... -Jinah! Bata karasa abinda take son faɗa ba, sakamakon jin Dauda da ya ƙaraso wajen shi da Aya, ya kira sunan ta. Lokacin da Jinah ta ɗaga idanu ta kalle shi, ya riƙe ƴar wuƙa a hannun sa, ya saita ta daidai zuciyar sa. Yanayin fuskar sa ya canja, kafin tayi wani yunkuri tuni ya cakawa zuciyar tashi wuƙar. -Dauda!!!! Jinah ta ƙwalla ƙara, alhali kuwa ƴarta, murmushi ne akan laɓɓanta, tana wani mo-motsa hannuwa, bakin ta na faɗar wasu kalamai, ba tare da Jinah ta fahimci wani abu ba. "Kar dai ita ma ta koma sheɗaniya bayan abinda ta yiwa Hindu". Tunanin da Jinah ke yi kenan. -Fally! Fally! Shi ma shuru ba amsa, ta rasa su baki ɗaya. ------------------------ A très long chapter, ina fata zaku ji dadin ta!!! Mu hadu chapter ƙarshe idan Allah ya kai mu. Merci de toujours être là 💪💪 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story END ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Jinah dafe kan ta tayi sosai da hannayen ta, kamar tana tsoron ya tarwatse, zaune take a kasa, kafin kuma tayi kwance tare da rufe idanunta. Ta gaji sosai, babu wani sauran ƙarfi a jikin ta. Sosai take fatan ace duk wannan abun, mafarki ne ba zahiri ba. -Na gaji, na gaji da wannan rayuwar, zuciya ta na ƙuna, jiki na ya gaji. Shin yaushe duk wannan zai ƙare, wata ƙila sai ranar da na mutu. Me yasa Allah ba zaka ɗauke ni ba? Ina roƙon ka ka ɗauke ni..! Jinah ke faɗar haka, idanun ta a rufe, cikin murya mai ban tausayi. Tana magana ne ita kaɗai, sai dai bata karasa kalaman ta ba, taji an ƙatse ta da cewa : -Astagfirullah! Kada ki ƙara faɗar haka! Idan ba so kike na sake mutuwa ba. -Fally! Jinah ta faɗa tare da miƙewa da sauri tana mamaki. Eh muryar Fally ce, sai dai lokacin da ta buɗe idanu, Dauda ta gani. -Me..m..me.. Kalamai suka gagara fita daga bakin ta, ƴarta ta gani tana mata murmushi. -Mama, su ne! Cewar ƴar tata. Baba da uncle Dauda! -Zo nan , matso kusa da ni. Cewar shi. Jinah kasa motsawa tayi. Matsowa yayi ya kama hannun ta, take Jinah taji wani abu. Janyo ta yayi jikin sa, sannan ya dora bakin sa kan nata, nan taji wani lantarki ya ratsa ko'ina na jikin ta. Fally ne kaɗai ya iya saka ta a irin wannan yanayin, kuka ta fara sosai, kukan farin ciki sannan ta rungume shi sosai kamar zata tsaga shi ta shiga. Zuwa cen ta sake shi, sannan ta rungume ƴarta tana kukan farin ciki. Bata san ta yaya hakan ta yiwu ba, bata san ina gangar jikin Fally dake wurin take ba, ko kuma ta yaya Dauda da ya cakawa kan sa wuƙa ɗazun, yake a gaban ta yanzun, bata san ta yaya duk hakan ta faru ba, kuma bata damu da ta sani ba. Gashi sun dawo mata su duka biyun, a cikin gangar jiki daya : Kyakyawar fuskar Dauda, murmushin sa mai sanyaya rai, murɗaɗɗen jikin sa, namijin gaske, namijin da ya cece ta lokacin da take tsaka da neman taimako, namijin da ya juyawa duka dangin sa baya domin ta, namijin da ya dawo mata da murmushi a lokacin da take cikin ƙunci, namijin da ya sota duk da yasan tana son wani, namijin da bata fatan ta rasa shi. Da kuma daɗin ƙarin ruhin Fally, namijin da idan zata tsaya ta ɓata lokacin bada labarin abubuwan da yayi domin ta tun yarintar su da kuma girma, to ba zata gama ba, namijin da bugun zuciyar sa yafi tsananin gudun jirgin kasa domin sonta, namijin da ta dinga jin kewar sa, alhalin bata ma iya tuna ko shi waye ba. Samun wannan mazajen, ba karamin farin ciki bane a gare ta, duk da zata yi kewar fuskar Fally, yana nan, tana jin sa a kusa da ita, hakan ma ya wadace ta. Ƴarta, rabin ranta, tana nan bata sauya ba, bata koma sheɗaniya ba. Wannan farin ciki ne marar adadi gare ta! -Ina son ki, mama! Cewar Aya, kamar tasan tunanin ta mahaifiyar tata take. Murmushi Jinah tayi mata, sannan ta bata amsa : -Nima haka gimbiyata, nima haka... ƙarasa kalaman nata tayi tare da fashewa da kuka, kafin ta nufi dakin ta inda ta tarar dashi a kwance, Ayu. Shine ya faɗo mata a rai, ƙarasawa tayi kusan shi tare da rungume shi, ƙara fashewa da wani sabon kukan tayi lokacin da ta haɗa jikin ta da nashi. -Kiyi shuru, ki daina kuka Jinah. Cewar Dauda ko kuma muce Fally, da ya shigo ɗakin yana ɗauke da Aya, da ita ma take cikin damuwa, na rashin wani ɓare nata, kuma abokin ta. Langwaɓar da kanta tayi jikin baban nata, tare da rufe ido, domin bata son kallon gawar ɗan uwan nata. Daƙyar Fally ya shawo kan Jinah, ta aje gawar ɗan nata, tare da komawa wani ɗakin daban. Sauka Aya tayi daga jikin mahaifin nata, ta kwanta kan gado kusa da mahaifiyar ta, tare da sauya kamanni zuwa na ɗan uwan ta. Murmushi Jinah tayi tana hawaye tare da shafa fuskar ɗan nata. Sunan sa ta kira, duk da tasan ba shi bane. Ƙara janyo shi tayi tare da ƙanƙame shi jikin ta. -Duk lokacin da kika yi tunanin sa, ki faɗa min, ni kuma zan zama shi, mama. Hakan zai sa ba zaki yi kewar sa ba. Cewar Aya, cikin kamannin ɗan uwan ta. Murmushi Jinah tayi tare da gyaɗa mata kai. Ƙoƙarin barin ɗakin take, tunawa da tayi da su Sarah. Amma Fally/Dauda ya tabbatar mata da zai kula da su, ta koma tayi kwanciyar ta. Ba a jima ba, Jinah bacci ya ɗauke ta, tana rungume da ƴarta, ita ma Aya bata jima ba tayi baccin. Fally ya dan jima a ɗakin yana kallon su, cike da jin zafin ganin halin da suke ciki ba tare da iya yin wani abu ba. Yana jin zafi domin yasan haƙƙin da ya gagara saukewa na daga cikin wahalar da Jinah take ciki. Fita yayi daga ɗakin, shi kaɗai, ya shiga rera kuka. A gaban Jinah ya iya riƙe hawayen sa, a gaban ta, bai son ya nuna mata gazawar shi. Amma mutuwar ɗansa ta taɓa shi. Durkushewa yayi a ƙasa, ya jingina da bangon ɗakin, ya haɗa kai da gwiwa, yana zubar da hawaye. Abubuwa da dama sun saka shi kuka, bugu da ƙari mutuwar Ayu. Yanzu ya gane iyayen shi sunyi gaskiya. Da bai auri bil'adama ba da duk wannan bai faru ba. Fally yayi nadamar abubuwa da dama, abubuwa da dama yaso ina basu faru ba; kamar kowannen mu. Sau tari muna aikata kuskure, wanda daga baya mu zo muna da nasanin aikata shi. Sai dai da na sani, baya wani canja babban abu, idan har bayan mun yi nadama, bamu daina aikata kuskuren ba. Gyara kuskure, shi ne mantawa da shi da sakawa a rai ba zamu sake aikata shi ba. Fally ya ɗaukar wa kansa wannan alƙawarin, Jinah ba zata sake cutuwa ba, ta dalilin sa, har abada, ba zai sake maimaita kuskuren da yayi a baya ba, tare da yin alƙawarin zata zama macen da tafi kowacce farin ciki a duniya. Goge fuskar sa yayi, sannan ya ɓace daga wurin zuwa asibiti, Sarah ya tarar a zaune, Nafisa na kwance bisa ƙafafun ta. Ƙarasawa yayi kusa da su. -Sarah ya kira sunan ta a hankali. Lokaci guda Nafisa ta ɗago. -Yaya Jinah da ƴan biyu? Suka tambaya a tare. -Suna nan lafiya, kar ku damu. Dauda ya basu amsa a taƙaice, ba tare da ya faɗa masu halin da Ayu yake ciki ba. -Ita..i..ita kuma mayyar, tana ina? -ku kwantar da hankalin ku, har abada ba zaku sake ganin ta ba. -Alhamdulillahi! Cewar Sarah. -Ban..ban.. ban taɓa jin tsoro da ganin irin wannan halittar ba. -Nima haka, amma me ya kawo ta, daga ina take? -Zaku ji komi idan muka koma gida. Ina Abdul yake? Da jin wannan tambayar, Nafisa ta fara zubar da hawaye kamar fanfo. Dauda ne ya shiga lallashin ta. -Ina tsoron kar na rasa ɗan uwa na Dauda. Ta faɗa cike da fidda rai daga samun lafiyar ɗan uwanta. -Zai warke, cewar Dauda. Nayi miki alƙawari! Miƙewa yayi, Sarah tace : -A wancen ɗakin suka kai shi. Ta faɗa tana nuna masa ɗakin da yatsa. -Ina zuwa. Cewar Dauda kafin ya bar wurin. Ɓacewa yayi, sannan ya bayyana cikin ɗakin da aka kwantar da Abdul, ba tare da likitocin na ganin sa ba. Iya ƙoƙarin su suke ganin sun ceto ran Abdul. -Ina ga sai an wuce da shi birni. Cewar ɗaya daga cikin likitocin. -Kana da gaskiya, idan ba haka ba, zamu rasa shi. Cewar wani likitan. Matsowa Dauda/Fally yayi kusa da Abdul, tare da ɗora hannun sa bisa goshin Abdul. Ya shiga karanto wasu kalamai, idanun sa a rufe. Bayan wasu yan mintuna, ɗaya daga cikin likitocin yace : -Allah mai iko! Bugun zuciyar sa ya dawo normal. Kallon kallo likitocin suka shiga yi, na mamakin ganin Abdul ya dawo hayyacin sa ba tare da sun yi masa wani taimako ba. Dauda fita yayi ya koma wajen su Sarah, ya bar likitocin cikin ruɗu. -Har yanzu likitocin basu fito ba? Ya tambaye su. -A'a... Basu ƙarasa ba faɗa ba, sai ga wani likita ya fito. Miƙewa suka yi, suka tarbe shi. -Ya ake ciki likita? Cewar Sarah. -Yaya ɗan uwana yake doctor? Cewar Nafisa. -Zan iya ce maku, yau mun ga ikon Allah, ɗan uwan ku yana nan lafiya, zamu riƙe shi zuwa gobe idan babu sauaran wani abu sai mu sake shi. Tsalle Nafisa tayi, ta rungume Sarah cike da farin ciki. -Ko zamu iya ganin sa? -A'a, ku ɗan ƙara jira, har mu canja masa ɗaki. Bayan wani lokaci, suka ga Abdul, a hayyacin sa, yayi farin ciki sosai da ganin su cikin ƙoshin lafiya. Tambayar ina Jinah da ƴan biyu yayi, suka tabbatar masa da suna nan lafiya. Sannan hankalin sa ya kwanta. Komawa Dauda yayi gida, ya tarar da Jinah kwance, amma ba bacci take ba, matsawa yayi tare da zaunawa kusa da ita. -Yaya Abdul ɗin yake? Jinah ta tambaye shi. -Lafiya ƙalau, sun ce zuwa gobe zasu iya sallamar shi. Ya bata amsa yana mata murmushi, ita ma murmushin tayi cike da farin ciki. Washe gari, aka sallami Abdul. Da shigar su gidan, Sarah da Dauda da ya koma asibitin da safe, suka nufi ɗakin da Jinah take ita ƴarta. Sarah ita ce ta riga shiga ɗakin domin ita ce a gaba kuma tafi su sauri, da zumuɗin son ganin Jinah. Da shigar ta ɗakin, ta rungume Jinah sosai. Sauran su ma haka suka yi, Nafisa da ɗan uwanta, bayan sun gama da Jinah suka koma kan Aya. Bayan wasu mintuna na farin cikin ganin juna. A tare duka ukun suka tambayi : -Wai ina Ayu? -Ta kashe shi. Jinah ta basu amsa a taƙaice. Abdul dake bakin gadon zaune yayi da jin abinda Jinah ta faɗa, ita kuwa Nafisa ta ƙwalla kara tare da fashewa da kuka, Sarah kuwa hannu tasa ta dafe bakin ta, hawaye na zubo mata, tana maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Kowannen su ya shiga ruɗu, babu wani dake da niyyar lallashin wani. Washe gari aka kai Ayu makwancin sa. Jinah da Fally suka fayyacewa yan gidan asalin ko su waye ƴan biyu, abinda Hindu take so, yanda Dauda yake a zahiri, a taiƙace dai komai suka basu labari. Sun girgiza, amma kuma basu sha wani wahalan gasgatawa ba, bayan ganin abinda idanun su suka gane musu a cikin gidan. A yanzu sun bar abinda ya faru a matsayin sirrin gidan nasu. Kwanaki na shuɗewa, kewar Ayu na daɗa damun su. Akwai zafi rasa makusanci, domin kuwa ya tafi kenan, zamu cigaba da rayuwar mu ba tare da shi ba, zamu goge shi daga duk wani program na gobe da muka shirya da shi, zai zamana mun yawaita ambaton sa yayin da muka tuna baya. Akai akai muna ɗorawa kan mu irin tambayoyin nan : idan da wane yana nan, da abu kaza da kaza ga yadda zai kasance, da wane na nan, da zai ce kaza ko kuma yayi kaza. Mu kan yawaita jin rashin sa a kasan zuciyoyin mu. Ga duk wadanda suka rasa makusantan su, Allah ya ƙara maku hakuri da juriyar rashi. Sarah ce a cikin kitchen tana haɗa karin kumallo, lokacin da Abdul ya shigo. Gaishe ta yayi, ta amsa a takure. Tun bayan faruwar abinda ya faru tsakanin su, take jin wata matsananciyar kunya, ba kamar kunyar Abdul din, shi yasa take gujewa duk wani wuri da zasu haɗu daga ita sai shi. -Nazo ne, ina son muyi wata magana. Benci dake kusa da su suka zauna. Abdul ya fara da cewa : -Nazo ne na baki hakuri kan duk wani abu da ya faru, na rantse miki ba zan iya tuna komai ba na wata alaƙa da ta shiga tsakanin mu. Amma ina ji a jikina na aikata, ban san yaya zan fahimtar dake, ki gane gaskiya nake faɗa miki. Ba zan iya cigaba da kasancewa da wannan nauyin ba, shi yasa na yanke shawarar komawa Nigeria. Ina son duka mu koma a tare, ni kuma daga cen zan wuce Canada karatu. Ina son ki cigaba da kular min da ƴar uwa kamar yanda kike yi a yanzu. Dan Allah kar kice min a'a, ki sayar da wannan gidan, hankali na zai fi kwanciya idan duka kuna cen. Ina tsoron abinda ya faru da mu, ya sake faruwa. Sarah ta yarda da maganar sa, kuma bata wani bata lokaci ba ta amince domin gidan nan yana tuna mata da abubuwa marasa kyau. Sai dai ta fara jin ta bakin sauran kafin ta yanke hukunci. Godiya Abdul yayi mata cikin farin ciki. -Amma ta yaya zaka iya biyan kudin karatun ka a ƙasar wajen? Sarah ta tambaye shi. -Akwai gadon da muka gada ni da Nafi na mama mu. Kuma zan nemi scholarship, kar ki damu dama ina da wannan wannan program tun da daɗewa. -Shikenan. Cewar Sarah. Mikewa yayi, ya barta. Tarar da Dauda yayi zaune ya tsunduma cikin tunani. -Kai kuwa, tunanin me kake? Oh ba sai ka faɗa ba ma, na sani na Jinah! Dariya dukan su suka yi. -Lallai, ka canka! -Cikin sauki ma, domin shi kaɗai ka iya. Dariya suka yi. -Da gaske, ina son ka faɗa min, naga kwana biyu kana wani nesa nesa da Jinah. -Na cutar da ita sosai, kuma ina tunanin ba lallai bane ta yafe min. Shi yasa nake ɗan nesa da ita, domin ina tsoron tace bata sona. Ni kuwa ba zan iya jurar hakan ba. -Ko ma me zai faru, ka fara yi mata magana, ba zaka iya gane me take ji game da kai ba. -Baka yi karya ba. -Never man! Dariya suka yi, kafin ya tashi ya tarar da Jinah cikin daki. Jinah murmushi tayi da ganin shi, tace a ranta yau ya gaji da gudun. Zaunawa yayi bisa gadon, kusa da ita. Sannan yace: -Zaki iya yafe min wata rana? Zan iya sa ran haka? Shin zaki iya kallo na wata rana ba tare da kin tuna mutuwar ɗanki ba? Na rantse miki, nayi nadama Jinah, ki yafe min, na tsani kaina ni Fally, irin cutar da Jinah da nayi. Ni... Sauran kalaman sa, suka tsaya masa a maƙoshi, sadda kai yayi ƙasa, hawaye suka zubo masa. -Fally, cewar Jinah cikin sanyayar murya, tana mai dago kan shi. Yi tunani ace zafin da nake naji yakai girman tekun maliya, lokacin da naga ka dawo gare ni, baka tafi ba, ina jin kasancewar ka a kusa da ni, na kwanta na tashi kana gefe na, wannan girman tekun maliyan, yana ragewa a duk lokacin da kake kusa da ni. Saboda kai da Aya, yasa bana jin zafin mutuwar Ayu sosai. Ban manta Wata rana lokacin da muna yara, ka fita kai da baba, ni kuwa ina gida tare da mama lokacin tana bacci, na fita da niyyar na ga gari kuma kasan irin son da sauran aljanu ke min, ta faɗa tana murmushi, domin tasan akasin so suke mata. Naga irin hantara a ranar, da kuka na koma gida. Raina a bace, naji na tsane su, ta yanda ba zan taba yafe musu ba abinda suka min. Bayan mama ta lallashe ni, nayi shuru, tace min : Jinah, yafiya ita ce babban magani ga zuciyar da aka cutar, yafiya tana haskaka zuciya da ruhi, yafiya tana ƴantar da bawa, yafiya tana gusar da mummunan tunani, yafiya tana saka farin ciki. Kada ki kasance marar yafiya Jinah, idan an cutar dake, ki kalli abu mai kyau cikin cutarwar, idan baki ganshi ba, ki nemeshi zaki ganshi, idan kika yi hakan zaki samu salama da kwanciyar hankali a zuciyar ki. Da jin haka, nace : Kin yi gaskiya mama, da ba'a yimin haka ba yau da ban samu wannan kyakyawar hudubar ba daga gare ki. Dariya tayi sannan ta rungume ni, a wannan lokacin ne, na fitar da duk wani mummunan tunanin da na saka a zuciya ta. Shuru tayi domin tuna mahaifiyar tata (uwar riƙon ta) da tayi. -Bana ƙin ka Fally, ta cigaba. A baya da na faɗa maka munanan kalamai, kawai dan ina cikin fushi ne, ina farin ciki na ganin ka kusa da ni, na yanda baka tunani. Ka daina damun kanka Fally, na daɗe da yafe maka. Da gama faɗin haka, ta rungume shi, Fally kuwa ya riƙe ta sosai kamar zai sanya ta cikin jikin sa. -Ina sonki Jinah, ina sonki sosai, sosai... -Nima ina son ka Fally, nayi kewar ka sosai,... -Za.. zaki iya maimaitawa dan Allah? -Ina sonka. Dariya suka yi. -Fally. -Hum. -Zaka iya saki na yanzu, domin bana numfashi da kyau. -Haha, yi hakuri habibty. Daga wannan rana, suka fara sabuwar rayuwar soyayya, Jinah da Fally. Sun fara da barin wannan kauyen, wannan kasar, Niger zuwa wata kasar Nigeria. Dukan su baki daya. Fally yana kula da Jinah tamkar wata jinjira, baya barin wani abu ya same ta na cutarwa, duk wani abu da zai zo masa a kai, kuma yasan zai daɗaɗa ran Jinah, shi yake yi. Yana rayuwa ne kawai domin ta, farin cikin ta, shi ne nashi. Sanin Jinah tana son zaga duniya, yasa yake nuna mata hotunan wurare masu kyau na cikin duniya, kawai da ta nuna wuri, a take zai ɗauke ta ya kai ta. Cikin kwanaki kaɗan, ya kaita wurare da dama, irin su : Bahamas, pyramids of Giza a kasar Egypte, Hawaii, Paris, Dubai, The Colosseum, Ha Long Bay, Grand Canyon... da sauran su. Yau ma a wannan lokacin, suna a Pamukkale, ɗaya daga cikin kayataccin wurare a ƙasar Turkey. Jinah kamar ƙaramar yarinya, Fally sai dariya yake mata. Bayan sun gaji da yawo, suka dawo bakin kogi suka yi zaune, ta dora kanta bisa kafadar shi. -Ina cikin farin ciki sosai Fally. Bata jira jin me zai ce ba, ta ƙara laɓewa cikin jikin sa. -Yanzu dai mu koma gida, nayi kewar princess ɗita. Da fadin haka, sai gasu a Nigeria, da gudu Aya ta ƙanƙame maman ta, lokacin da ta ganta. -Ina kuka tafi yau? bani labari mama. -Toh ƴata yanzu kuwa. Murmushi tayi, mamar ta ta shiga bata labarin duk abubuwan da ta gani a Pamukkale, shi kuwa Fally yana gefe ya zuba masu na mujiya. Bayan wasu yan mintuna, Nafisa ta shigo, ta basu labarin sun fita ita da Aya, mutane na ta kallon ta kamar sun ga aljana, har yau ma wasu sun nemi da ta zamo ambassador ta wani brand na yara. -Dan Allah Jinah ki amince, my little princess ta zamo tauraruwa. Tuni har nayi suna cikin anguwar nan dalilin ta, toh ya kike gani idan aka fara ganin ta a social media, wow! -Ashe dai princess din tawa haka take da kyau! Cewar Jinah tana murmushi. -Kamar ke mama! Cewar Aya. Kuma da gaske tana da kyau sosai ita ma, ko ma taso tafi Jinah, duk da gashin ta bai kai tsayin na mahaifiyar ta ba, amma yana da tsawo shi ma. Idanun ta irin na baban ta ne, a taikace dai ita ma zubin aljanun gareta. A yanzu, ta iya controlling karfin ta sosai, kuma ta daidaita shekarun ta ba kamar da ba, yanzu da ka ganta yarinya ce yar shekara bakwai kuma tana cigaba da girma kamar kowanne lafiyayyen yaro. -Kai ya kake gani? Jinah ta tambayi Fally. -Idan kin amince, toh nima na amince. Ya bata amsa murmushi kan laɓɓan sa. -Ke kuma Aya? Ta tambayi ƴar tata, Nafisa na mata irin kallon dan Allah ki amince. -Nima ina so mama! -Toh shikenan -Cooool! Nafisa ta daka tsalle. Ina da number daya daga cikin su. Brand din su yafi zama popular, bari na kira shi yanzu. Akwai wani abu kuma. Cewar ita Nafi, da murmushin mugunta a fuska. -Menene? -Na.. na nuna mishi pic din ki, kema yace yana son... -Ba zai yiwu ba! Bata kai ga ƙarasawa ba, Fally ya katse ta. -Kin ji amsar ki. Cewar Jinah, tana ƙyalƙyata dariya. -Wai irin namijin kishin nan! Cewar Nafisa tana masa hararan wasa. Dariya suka yi su duka. Kafin ta kira mutumin, sai da taji ta bakin Sarah tukun, kuma ta amince. Cikin kwanaki kaɗan ƴar yarinya Aya ta zama Star. Wata rana da yamma, suna a falo suna fira, wani ya ƙonƙwasa ƙofa. Nafisa ta tafi ta bude, sannan ta dawo tare da wani mutum, da ba zai wuce shekaru 40 ba, irin mai ƙasaitar nan, da kyakyawar fuskar shi daidai gwargwado. Da alama ta san shi. -Aunty Sarah, uncle Ahmad ke son ganin ki. Sarah abin yayi matuƙar bata mamaki, bata ƙarasa mamakin ta ba sai gashi ya shigo falon, sauran tashi suka yi suka basu wuri. -Kin san shi? Fally ke tambayar Nafisa. -Eh, maƙocin mu ne, gida mai kallon namu. -Kin san ko me ya kawo shi? -A'a, ban sani ba. -Ina da wata dabara! Cewar Jinah. -Nima haka cewar Aya. -Aya! Ban faɗa miki ki daina karanta cikin kawunan mutane ba. Ki daina bana son haka. -Amma mama, bamu san shi ba, kinga dole muyi takatsantsan. -Kada ki sake, babu kyau. Da alama Aya bata so maman tata, ta taka mata birki ba. komawa tayi wajen baban ta tana zumɓuro baki. -Ba maman ki hakuri. Baban ta ya raɗa mata a kunne. -Kiyi haƙuri mama. Ta faɗa. Gyaɗa mata kai Jinah tayi da alamar ta haƙura, sannan ta buɗe hannayen ta, yarinyar bata yi musu ba, tazo ta rungume ta. Cigaba da hirar duniya suka yi, har lokacin da Sarah ta dawo. -Me ya kawo shi? Cewar Dauda cikin nuna kulawa. -Matar aure yake nema! Sarah ta faɗa ba tare da ta kalle su. Washe baki Jinah ta shiga yi. -Matar aure? Kamar yaya? ke kuma ya faɗawa haka? Ohhhhh ko dai keh..., na gane. Aunty Sarah ki ce kin amince, Uncle Ahmad, mutumin kirki ne, matar shi ta rasu da daɗewa, kuma kinga kyakyawa ne, kuma ga kudi, ina tunanin ƴaƴa biyu kawai gare shi. Nafisa ce ke ta zuba wannan surutun. -Toh me kika ce masa? Cewar Jinah. -Nace masa sai nayi tunani. -Da alamun mutumin kirki ne, amma ki ɗauki lokacin nazartar shi kafin nan. Cewar Fally. -Ni tuni ma yayi min! Cewar Jinah. -Nima haka! Nafisa da Aya suka haɗa baki. Dariya dukan su suka yi. Bayan wasu makonni, Sarah ta amince zata auri Ahmad, ta kuwa ɗauki lokaci tana nazartar shi, ta gano mutumin kirki ne, kuma sosai ƴaƴan shi suka shaƙu da ita. Suna jin daɗin kasancewa tare da ita, ba kamar idan Aya na gida suyi ta wasa. Wata rana, Fally da Jinah su kaɗai a zaune suna fira, Jinah ta kawo zancen da Fally ya tsani jin sa. -Zan mutu kafin kai. Ni kaga mutum ce, kiyasin shekarun da zan yi ba zasu wuce saba'in ba, wata kila tamanin, nayi masu yawa nayi ɗari. Kai kuma dubunnai ne a gaban ka. Wace kalar mace zaka sake a madadi na? Jinah tayi masa wannan tambayar domin ayi dariya, sai dai tuni taga yanayin Fally ya canja. -Ah habiby da wasa fa nake. -Toh bana son irin wannan wasa, ina shiga damuwa idan na tuna haka Jinah. -Toh yi hakuri na daina daga yau. Ta faɗa tare da shigewa jikin sa. Fally ya tsani ayi masa irin wannan zancen, domin yasan dole wata rana haka zata faru, shi yasa yake shiga damuwa sosai. Duk inda ke da rayuwa, akwai mutuwa, kaddara ce da babu mai iya guje mata. Sau tari, mu matasa, bamu cika tunawa da ita ba, mun fi tunanin tafi daukan tsofaffi. Abin dariyar ma, muna ganin yanda take ɗaukan matasa, yara kanana, hatta da jarirai, amma mu kullum tunanin mu mutuwa ta tsofaffi ce, har mamaki muke idan aka ce ta ɗauki matashi wane. Ya kamata mu daina yaudaran kan mu, mutuwa ba ruwanta da matashi, tsoho, talaka, mai kudi, mai kyau ko mai muni ne. Tana ɗaukan mu ne a lokacin da ta so ko a yanda ta so. Abinda da Sarah da wannan ahali nata suka fahimta kenan. A wata yammar litinin, dukan su suna gidan Ahmad, gidan da a yanzu Sarah take ciki tun bayan auren ta da Ahmad. Fally, Jinah, ƴarsu, Nafisa da kuma ɗan uwanta da ya daɗe da dawowa bayan wasu shekaru. Sun haɗu domin taya Jinah murnar cika shekaru 27. Suna cikin fira, cikin nishadi, lokaci guda suka bar jin muryar ta, bayan mintuna da yawa, alhali da ita ake ta surutu. Fally ne ya kai hankalin sa gare ta, mamaki yayi da ya ganta da alamun tana bacci, wani irin bugu zuciyar sa tayi. Aya dake waje tare da ƴaƴan Ahmad, ta shigo falon a gigice, da shigowar ta ta durkushe kasa, ta riga da taji a jikinta tun kafin ta shigo falon. Sauran mamaki ne a fuskokin su ganin halin da Aya take, har zuwa lokacin da suka ga Dauda na kokarin tashe da Jinah ya kasa. Falon yayi tsit, suna tunanin ta yaya hakan zai yiwu. Eh tabbas, Jinah rai yayi halin sa, Fally mikewa yayi tare da ɗaukan ta. Sauran basu fahimci komai ba, sai dai jikin su yayi sanyi duk da sun kasa gasgata abinda suke tunanin shi ya samu Jinah, sautin kukan Aya kawai ke tashi a falon. Fally nufa yayi da Jinah gidan su da ba nisa da na su Sarah, yana shiga ya kaita ɗakin su, ya kwantar da ita bisa gado. Shi ma kwantawa yayi kusa da ita, a take shi ma rai yayi halin sa. Amma kafin ruhin sa ya karasa fita daga jikin sa baki daya, yace : -Me kike tunani Jinah, dubunnan shekarun da suka rage min na rayu ba tare da ke ba, ba zai yiwu ba. Nima dole na mutu, yayin da nasan kema baki duniyar. Zuciya ta tana bugawa ne a tare da taki, babu abinda zan yi a wannan duniyar babu ke, ni da ke mun haɗu mun zama ɗaya, kuma ɗaya bata taɓa bada biyu ba. Sai mun haɗu a duniyar matattu, Habibty. Jinah was, is, kuma forever will be matar aljani. ----------------------------------------- ALHAMDULILLAHI, c'est fini lol. Bye bye matar Aljani. Ina fata kun faɗakartu, nishanɗantu, kun kuma ilmantu da wannan dogon labarin nawa. Sannan ina mika sakon gaisuwa ta ga masoya wanda suka jima suna bibiyar wannan labari. Allah ya bar hannu da kaifin ido. Ameen ya Allah