[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE Sadaukarwa ga Aminiyata Sadiya Abbakar Maru (Ƴar gatan royal star) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* PAGE 1. Cikin Natsuwa jerin gwanon Motoci kusan guda biyar kirar Mercedes Benz , farare ne sol gwanin sha'awa, suke tafiya, duk in da motocin suka wuce ɗaga musu hannu da jinjina ake, wanda hakan ma ya isa ya shaida maka, ba ƙaramin mai daraja da ake ganin mutuncin shi bane a motar, sai da suka zo gurin wani Babban hospital kafin su fara rage gudu, a hankali suka fara sulalawa cikin Asibitin, sai da suka shiga cikin tafkeken parking space din cikin Asibitin kafin su tsaya. duk fitowa mutanan da suke cikin motocin suka yi, sai wata mota daya da go budeta ba'ayi ba, a hankali aka bude murfin motar, kamshin turaren Huge Boss da ya daki hancina ne ya tilasta min ɗago da idanuna, hankan kuma yy dai-dai da zuro fararen ƙafafunshi fararw tass, wanda suke cikin takalmi half cover fari mai kyau, yana yin zubin takalmin kawai zaka kalla kasan cewar na Sarakai ne. tun daga ƙafafunshi na fara ƙarewa kallo, har izuwa kwaurinshi wanda farar Alƙyabba mai torch din Golding da ta mammaye gaba daya jikinshi, wanda har fuskarshu ba'a iya gani, sai dai hannayenshi da ya zuro, wanda ya ke gyara igiyar Alƙyabbar jikinshi. A hankali ya sanya kyawawan fararen hannayenshi, ya dan jaaa hular Alƙyabban da yake jikinshi, Masha Allah, kyakyawa ne sosai, duk kuwa da ban ga fuskarshi da take nannaɗe da rawanin da yake a kanshu ba, idanubshi kawai da gefen fuskarshi na samu nasarar gani, idanunshi manya ne dan kai tsaye za'a kiransu da Lu-lu Eyes ko ace Oil Eyes, dan har wani mai-mai ko in ce ruwa-ruwa ne a cikin idanun nashi, farare ne tas, sai dai maimakon back eyes ball , sai nashi y kasance royal blue. lumshe idanun nashi yy, wanda hakan yy nasarar bayyanar da zara-zaran Eyes lashes dinshi, da suke baƙaƙe sidiƙ, idanunshi y bude tare da dan juyasu a hankalin, kafin ya fara tafiya, cikin yalwatacciyar natsuwa da kamalarshi. Sauran Fadawan da suke bayanshi ne suka fara take mishi baya, cikin natsuwa duk suka nufi cikin Hospital din. shigarsu kuma tayi dai-dai da shigowar motar Ambulance da take ta ihu, cikin gaggawa gaba daya nurses din da suke cikin Asibitin da Drs duk suka nufi waje in da Ambulance din ta tsaya. cikim gaggawa aka fara fitowa da Majiyatan da suke cikin Ambulance din wanda kallo daya zaka musu kasan cewar Haɗarine Hadarin ma mugun haɗari wanda baya kalluwa, daga gaba dayan su bb wanda bai rasa wani sashe na jikinshi ba, duk jini jikinsu bb kyan gani, masu rauni zuciya ma daga cikin nurses din sai kuka suke, Drs din kuwa dama su sun saba gani, hakan yasa abun bai wani ɗaɗarasu da ƙasa ba, sun damu amma bawai kamar nurses din ba.fiffito dasu aka yi, amma sai suka yi cirko², ba'a shiga da su ciki ba. Mutanan da suka shiga ciki ne suka fito , gurin da mutanan suke tsaya suka nufa, abin ya mugun ɗaga musu hankali, wanda yasa da damarsu suka fara zubar da hawaye,daya daga cikin Drs din ne ya ce "wannan sai dai ku shiga dasu Amma bb alamar rai a jikinsu", ya fada yana niyyar juyawa, hannunshi mutumin ya kama, idanunshi da dago tare da tsurasu akan mutumin da sauri cikin ƙanƙan da kai yace "Allah ya taimaki Sheikh Arman wannan Haɗarin ya munana, bashi da kyan gani, bana tunanin za'a iya fitar da mai a ciki", ya fada cikim zallar jimami. sakin hannunshi yy ya ƙarasa gurin motar, yana zuwa idannshi ya sauka akan wata Yarinya da take sharɓe gaba daya jikinta jini ne, wanda yasa bama a iya ganin fuskarta sa boda jinin da ya wanke gaba daya illahirin jikinta, ga wani farɗeɗan ciwo da ya zagayo tun daga kanta har tsagin fuskarta ɓangaren haggu, gaba daya Yarinyar ba zata wuce 7years ba, royal blue eyes din shi, ya juya a kam Yarinyar da kallo daya yy mata ya gane tana numfashi, a hankali ya furta "Yah Subhanallah", ya fada yana kutsa kanshi cikin tarin Jama'ar gurin. yana zuwa bai ɓata lokaci ba ya dauketa chaak tare da nufar cikin Asibitin da ita, cikin wata Golden Voice mai dadin gaske, wadda kamar ana busa sarewa ya fara kiran "Doctor! Doctor!! Doctor!!!", ya ƙarasa faɗa cikin gajiyawa da rashin son magana, Dr din da ya mishi mgn Ɗazun ne y fito da sauri jikinshi na rawa, miƙa mishi Yarinyar yy , da ido ya mishi alama da a duba ta, da sauri ya karɓi Yarinyar da bb alamar rai a jikinta, Accident and Emergency room ya nufa da ita da sauri. Yana shiga ya shimfiɗeta kan gadon da aka tana da domin masu rashin lpy mai tsanani ko haɗari, gaba daya gadon yana kewaye da na'u'o'i , na ceton ran Dan Adam, da sauri Dr din ya dauki stethoscope da yake ajiye a saman wani dan table in da anan ne ake ajiye duk wani abu mai muhimmanci da Drs suke buƙat amfani da su domin ceto ran marar lpy. cikin Sauri ya juyawa Yarinyar baya tare sa zage zip din yar rigar jikinta, ya ajiye a gefe, kwantar da ita yy tare da daura stethoscope din a kirjinta ɓarin dama, domin jiyo sauti bugun numfashinta, a hankali ya jiyo bugun numfashinta da yake chan ƙasa sosai wanda in baka saurara ba ba zaka iya jiyowa ba, da sauri ya dauki ya matsa gurin Ventilator, (Na'urar hura iska ita ce injin da ke shaka wa mutum yayin da huhu ke samun waraka. Yana aika iskar oxygen ko iska zuwa cikin huhu ta cikin bututu mai bakin ciki kuma yana ba da damar carbon dioxide ya tsere. Ana sanya bututun a cikin bututun iska ta hanci ko baki), cikin Jaddada wannan lamari ya ci gaba da gyara mata jikinta, sai dai irin manya-manyan rauni kan da suke jikin Yarinyar ya bashi tsoro, domin raunika ne wanda ba lallai in mutum ya jisu a jikinshi ya iya rayuwa ba. jinin da yake ta zuba a tsakiyar kanta ya fara tsayar mata, ganin wani kwasheshen ciwo yasa, ya dauki scissor ya fara iske mata gurin da taji ciwon, tsorata yy lokacin da yy arba da ciwon da yake kanta, wanda yasa har ya matsa ba, yanka ce sosai wadda ta shiga cikin kanta, wanda har naman kanta ana iya hangowa. bai san lokacin da kwalla ta zubo mishi ba, sa boda zallan tausayin Yarinyar, a hankali ya shiga mata ɗinki a kan, har ya gama yana hawaye, duk in da ta ji ciwo ya wanke mata, ya gyara mata karayar da tayi, kafin ya fara gofe mata jinin fuskarta, bayan ya gama da ya kalli fuskarta, sai da zuciyarshi tayi wani kyakywan bugawa, sa boda ganin yarda fuskar Yarinyar take, wadda jini duk ya dan bubushe mata, Fara ce sosai, yana yin zubin halittar fuskarta da farin fatar jikinta kaɗai ya isa shaida maka cewar ba cikakkiyar yar Ƙasar Nigeria bace, dan tafi kama da Larabawa ko Turawa. bayan ya gama ya shiga duddubata, domin ganin in ta samu wani Internal Injury, abun da ya gani yy bala'in girgiza mishi tunaninshi, wanda yasa sai da ya dago ya kalleta,na wasu minutes kafin ya ci gaba da aikinshi, bayan ya gama, ya fidda sakamakon Gwaje-gwajen da aka mata, tare da fitowa yana goge idanunshi da fuskarshi da suka yi jaaazir tsabar tashin hankali. ko da ya fito wayam yaga ƙofar, ko ha'a faɗa ba yasan Sheikh Arman-Maleek Abdul-azeez Sarki ya tafi , domin lokacin Sallar Juma'a yy wanda kuma yana da tabbacin duk lokacin da ya shigo Ƙasar shine yake Limancin Central Mosque din da yake cikin Abuja . da sauri ya shiga cikin Office dinshi domin shirin tafiya shima, sai da ya gama kafin ya fito, kiciɓis yy da wata nurse cikin harshen turanci ya fada mata ta kula da Patient din da take ER(Emergency room), jinjina mishi kanta tayi, kafin ya wuce , yana hawa kan titin da sai kai shi Asokoro Central mosque da yake cikim Abuja, ya fara jin daddar muryar Sheikh Arman-Maleek tana tashi ta cikin abun ƙara karfin saurin maganar da yake cikin Masallacin wanda ya ƙaraɗe gaba daya Unguwar ta Asokoro, cikin dadda kuma sanyayya tattausar muryarshi yake huɗuba , tare da nusar da jama'ah da baiwar da Allah ya bashi ta iya magana. har ya ƙaraso harabar tankamemen Masallacin da yake cike da Al-umman Annabi yana jin Muryar Sheikh din na ratsa cikin kunnuwanshi, a hankali cikin natsuwarshi shima ya nufi cikin Masallacin in da ya fara tara jama'a, sosai wanda da ka kalli yawansu ma zaka san ba mutane ne kawai ba, dole ma akwai ƙarin wasu jama'ar. Cikin Masallacin da ya kusa cika ya shiga, kusan gaba daya Masallacin ta kusa cika da mutane, hakan yasa sai kusan sahun karshe ya samu , yana shiga bai fi sa 2 minutes ba aka kabbara Sallah,cikin tsari da tausasa harshe yake karatun Al-qur'ani mai girma a cikin Suratul Khafi, cikin zaƙi da dadin muryarshi yake karatun har aka idar da Sallah, mutane ne suka fara fita, bayan idar da Sallah Juma'an, kusan kowa da yake cikin Masalacin sai da ya fita, kafin Sheikh Arman ya fara takowa domin fita, ta wata ƙaramar kofa da take gefen kusa da gurin da Liman yake, bakishn dauke da Tasbhi yake tafita, yana yi yana lumshe idanunshi, har ya fito daga cikin masallacin. Escort dinshi da suke a waje suna jiranshi je da Fadawa suka take mishi baya, har gurin motarshi,, bude mishi akayi, sai da ya tattare Alƙyabbar jikinshi kafin ya shiga, rufewa aka yi,bayan duk tarin mutanan da suka rakoshi sun shiga mota , kafin aka fara tafiya , a jere cikin tsari. Direct Hanyar Garin Gombe suka nufa, idanunshi na lumshe bakinshi bai gushe da Ambaton Allah ba har suka yi nisa sosai suka raba dai-dai tsakanin Abuja da Gombe, A hankali ya fara bude Royal Eyes dinshi, tare da kallon wayar da take gefenshi wadda take ta vibrating , ga kuma haske da take kawowa. a hankali ya kai zara-zaran fararen yatsun hannunshi, ya dauki wayar tare da yin Receiving call din, a hankali ya kara wayar a kunnenshi ba tare da sanin mai kira ba, Wata Muryar ce mai sanyi da dadi ta daki dodon kunnenshi wadda tasa ya dan lumshe ido, yarda ya dan saki jikinshu ne kawai zai fahimtar da kai wanda yake kiran nashi yana da matuƙar muhimmanci a gareshi,a hankali cikin halin rashin son magana yace "l'll call you late ",yana fadar haka ya kashe wayar . ko Ajiyeta a in da take bai yi ba, wani call din ya ƙara shigowa cikin wayar tashi, ```Jaddi``` sunan Mai kiran nashi ya bayyana a kan screen din wayar, sai da ya lumshe idanunshi kafin ya dauki kiran, A hankali yace "Assalamu alaika", daga cikin wayar muryar wani tsoho ta fara magana cikin harshen turanci , sai da na ƙarewa fuskar wayar kallo kafin na gane ashe number bata Nigeria bace, number ƙasar waje ce. shi din ma da ya dauka ba wata maganar kirki ce ta haɗashi da shi ba, daga uhmm sai uhumm, shi kenan abun da yake ce mishi, har suka yi Sallama. 4hours ne ya kai su Gombe daga Abuja, direct titin Abdul-azeez Arman-Maleeek Sarki roaud suka nufa, basu tsaya ko ina ba, sai gaban wani tankameman get din gidan Sarauta wanda gaba daya gidan fenti ne irin na daɗɗiyar masarauta, fentin da ba'a samunshi a ko wace Masarauta sai masarautar da ta Haura shekara ɗari biyu da wani abu, tsarin gini da shigar mutan gidan ma ya isa kara tabbatar maka da dadewar Masarautar, a hankali ya bude idanunshi da suka dan zurma sa boda wahalar tafiya, dan tunda ya shigo ƙasar bai samu ya huta ba. Get din gidan aka bude, in da motacin suka fara shiga a hankali, suna shiga ƙaramin get wanda zai sadaka da cikin gidan in da mutane suke, aka saki wani Algaita da busa wanda ba ko wace Masarauta ake yinshi ba, sai Masarautar da suke da Kambun Sarauta, sanan Algaitar nan da Busar ba wani ne yake yinsu ba, suna busa kansu ne a duk lokacin da wani wanda yake da Haƙƙin Mulkar Sarauta idan ya biyo ta ƙofar wanda bama kowa ne ake budewa ita ba. matse idanunshi yy sosai, dan baya son busar nan da Algaitar dan a duk lokacin da za'ayisu to gaba daya tsikar jikinshi na zubuwa ne, sai ya rasa Natsuwarshi har sai yata Addu'o'i, yanzun ma hakan ce ta kasance, har suka ƙarasa parking space aka bude mishi mota bai bude idanunshu ba, kuma bai yi wani abu da zai nuna cewar zai fito daga motar ba. kusan 10 minutes da bude mishi ƙofar motar kafin ya fito, A hankali, cikin kamala da cikar Zati yake tafiya, yana babbazar Alƙyabbar da take jikinshi, hannun na rike da wani dan sada irin na sarakai ko kuma wani gawurtacce a cikin gidan Sarauta. Ƙofar Fada da ta fi ko ina tsaruwa da shan Ado a cikin gidan Sarautar ya nufa a hankali, kafin ma ya iso, har an shiga An mishi iso da Sarki, yana zuwa ya shige, duk sauran mutanan da yake tare da su , suka tsaya a waje. Laɓɓansa dauke da Tasbhi da Addu'o'i ya shiga, yana mai yin Sallama ciki-ciki, wata sanyayyiyar murya ce ta Amsa mishi Sallamar daga ciki , a hankali ta ci gaba da tafiya zuwa ciki, Kishingiɗe ya samu Sarki akan kujerarshi, yana shiga ya tashi ya zauna, har ya ƙaraso cikin Fadar idanunshi na cikin kanshi, shi kuwa idanunshi na ƙasa dan baya kallon mutane, kullum idanunshi a ƙasa........ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️. SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR ) ```WANDA YAKE SON A TALLATA MISHI HAJARSHI. ZAI IYA TUNTUƁATA TA NUMBER NA KAMAR HAKA. 07033371851 ZAMU TALLATA MAKA HAJAR KA CIKIN SAUƘI DA RANGWAME``` *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* PAGE 2. A hankali ya ƙarasa gurin kujerar da yake zama a kullum da ko Yaushe in ya shigo cikin Masarautar, zama yy tare da dan Zamowa with full respect yace "Sannu da hutawa Lamurɗe", ya fada a hankali cikin natsuwar da ta zame mishi jiki, dan murmushin da ya tsaya mishi iya kan fuskarshi yy tare da cewa "Sannu da sauka Arɗo", jinjinw kanshi yy bai ƙara cewa komai ba,sai da suka nisa kusan 5 minutes kafin Ahmad Arman Maleeq(Ƙanin Mahaifin Arman Maleeq), yace "Ya Barkindo da jiki ?", ya fada maganar na tsaya mishi iya laɓɓanshi. a hankali cikin natsuwa da kamala ya bude laɓɓansa tare da cewa "Alhamdulillah", ya fada tare da mayar da idanunshi ya lumshe, tsureshi yy da ido na dan wani lokaci kafin ya juya idanunshi, ya dade sosai a gurin Ahmad Sarki kafin ya miƙe, A hankali yace "zan shige", bai ji Amsar da Allaraini ya bashi ba ya fice a binshi. har ya shige ta gaban wani side mai kyau da tsari, sai kuma ya dawo baya, a hankali ya doshi cikin palon sashen, tura ƙofa yy a hankali yy Sallama, cikin palon yana tura kanshi ciki. cikin Kaɗuwa da razani Hamshaƙiyar tsohuwar matar da take zaune nannaɗe cikin wata ƙasaitacciyar shiga, mai kyau irin ta Masu fada a ji, ƙarasowa yy cikin palon, ya zauna fuskarshi bb walwala ko kaɗan, fuskarta ta haɗe fiye da Yarda take baya, kyakyawa ce fara tasss da ita, tana da manya idanu, da hanci har baka, sai dan ƙaramin bakinta, yana yin kallon da take bin Sheikh Arman maleeq kawai zai gamsar da cewa akawai wani abu mai kama sa ƙiyayyaeshi a cikin ranta. Cikin Yar isa da taƙama tare da jin kanta a Sama tace "sannun Isasshe Saukar yaushe ?, yau kuma daga wata duniyar ?, Ya Ubanka yaji da jiki?", ta fada cikin gatsali , idanunshi ya bude ya watsasu akan fuskarta a ƙaro na farko tun da ya shigo cikin palon. Harshen shi ya taune kafin cikin ƙarfafa harshenshi da kumbura bakinshi, ya ce "Uhmmmm", abun da ya furta kenan bai ƙara kallon in da take ba, ita ma din bata damu da maganar tashi ba, bata kuma damu da lafiyar Mahaifin nashi ba. a Hankali ta miƙe tayi cikin bedroom dinta ba tare da ta ko kalleshi ba, Sheikh kuwa haka ya gaji da zama ya miƙe tare da barin palon, zuwa sashenshi da bayan na Sarki da Sayya(Mahaifiyar Ahmad Sarki , tsohuwar da ya fita daga sashenta) bb sashen da ya kai shi kyau a cikin Masarautar. Fadawan da suke a ƙofar shiga cikin sashen ne suka bude mishi, ya shiga cikin palon bakinshi dauke da Kamilalliya kuma cikakkar Sallama kamar yarda Addini ya tanadar, bb kowa cikin palon, sai dai hakan bai hana komai da yake cikin palon yin aiki ba kama daga kan Fankokin da suke kunne da AC har kan hasken da ya mamaye gaba daya palon , wadda ya haska ko ina tanwar kamar rana. kuma ko ina ƙal-ƙal bb alamar ƙazanta ko wani najasa, a hankali ya fara taka ƙafarshi tsakiyar palon, idanunshi a dan janye, har ya ƙarasa kan kujera 2 siter ya zauna , a hankali ya ƙarasa jaanye idanunshi gaba daya ya lumshesu, yana sauke numfashi a hankali cikin natsuwar da ta zame mishi jiki, a hankali ya dan sanya hannunshi ya fara zare half cover din da suke ƙafarsa, yana sauke numfashi a hankali,har ya gama zarewa a hankali yajaa numfashi tare da furta "Subhnallah wal-hamdulillah waa laaa'illaha'illalahu wallahu Akbar, Suhbanallah", ya furta yana ƙara rumtse idanunshi. nauyin da ya ji kanshi ya fara mishi sakamakon ciwon kan da ya riskeshi, yasa ya sa hannunshi tare da fara zare farin rawanin da yake kanshi ,bakinshi na kiran sunan Allah har ya gama zareshi. kyakyawar sumar kanshi da take a barzaze mai kala biyu, ƙasa baƙiƙƙirin irin sumar Asalin Fulani, sai kuma Sama Brown kalar sumar turawa, wadda ta kasance kamar an rinata, sai dai ba rinatan akayi ba, zallar sumar kanshi ce a haka , a hankali ya dago kanshi, tsura mishi idanu nayi , sai dai na kasa ganin fuskar tashi, wadda sumar kanshi ta sauko ta rufe mishi gaba daya fuskarshi, sai dai kyakyawan cute lips dinshi da suka ƙasance pink irin na mata ake iya gani, da kyakywan sajenshi wanda ya haɗe da gumenshi, mai mugun yawa, san har kusan kirjinshi , baƙi sosai irin gemun larabawa. a hankali yasa hannunshi ya fara zame gashin kanshi da ya zubo mishi akan fuskarshi, da sauri na matsa dan na mugun firgita da yana yin zubin tsarin fuskarshi, dan kallo daya in ka mishi baza ka gamsu cewae mutum bane, abu na farko da Zuciyarka zata fara raya maka shine ba mutum Bane Aljani ne, dan sam baya kama da mutane, sa boda tsananin kyanshi. yana da kyan da ba kowa ne ya taɓa ganin irin kyan ba, kyanshi Ainahin kyau ne marar Algus , fari ne sosai wanda farin nashi ya sirka da jaa - jaa wanda ba'a cika ganin irin wannan farin a mutanan Nigeria din mu ba,sai dai mutanan waje, yana da yar faffaɗar fuska da bata cika fadi ba, sannan bata cika tsayi ba dai-dai misali. yana da siririn hanci da ya dace da kyakyawar fuskarshi, uwa uba bakinshi da Idanunshi, wanda su zaka kalla ka tabbatar da cewar ba Asalin dan ƙasar bane, sa boda yarda suke, idanunshi ba za'a kirashi da blue ba ba za'a kirasu da light blue ba sai da ace musu royal , wanda suka ƙarawa fuskarshi kyau, bakinshu kuwa dan mitsitsi mai dauke da pink lips , a hankali ya bude bakinshi, jerarrun fararen haƙoranshi farare tas masu kyau da daukar ido wanda har fuskarka kana hange ta cikinsu ne ta bude , kafin a hankali yace "Alhamdulillah", wanda na lura da cewar hakan ya riga ya zame mishi jiki, dan duk motsawar da zai yi sai ya kira sunan Allah. Wayarshi da take ring yasa hannu ya dauja ba tare da ya duba wanda yake kiran ba, a hankali ya ƙara wayar a kunnenshi, daga chan ɓangaren aka ce "Assalamu alaika Yah Sheikh", a hankali ya Amsa Sallamar har lokacin bai shaida wanda ya kirashi ba, sai dai yana ji a jikinshi kamar ya san muryar ko kuma ya taɓa jinta a wani guri. Cikin sauke Ajiyar zuciya Dr din yace "Ranka ya dade Yah Sheikh ", ya fada a ƙasalance yana gyara amanshu kan kujerar da yake zaune,a hankali ya furta "Uhmmm!", wanda shi din ma na lura ya zamar mishi jiki, ya fi ganewa yy hakan da yy magana. A hankali yace " ni ne Dr din da ka bawa Marar lpy Ɗazun", a hankali yace "hope everything is fine", ya haɗa yana lumshe idanunshi da sauke numfashi, jinjina kai Dr din yy tare da cewa "to lpy ba lau ba, dan gaskiya ta samu babbar matsala ga kuma dama matsalar da take fama da ita, sai abun ya haɗu ya ƙara dagula lissafin jikinta", gyara zama yy tare da sauke numfashi, kafin yace, "ina bukatar duk wani information a kan ta, send me"ya fada yana kashe wayar. A hankali ya mike ya shige ciki , wata ƙofa ya nufa, yana budewa wani kyakyawan bedroom mai dauke da bed da wadrobe sai carpet , bedside drower , sai wata doguwa kujera 3siter wadda za'a iya kwanciya kai, gefe kuma wani dan lugun ne mai dan faɗi, wanda yake dauke da table wanda litattafan Addini ne kawai a kai, sai wata Yar kujerar zama, wadda da alama ita ce wadda ake zama ayi karatu, Sallayarshi da Chasbharshi Agefe a ajiye . A hankali ya ƙarasa gefen babban bed din da ya mamaye kusan rabin bedroom din, bai zauna ba, sai ta nufi wani ƙofa in da anan wani kyakyawan bathroom mai tsaro irin na wayyayu ya bayyana, wani katon mirror da yake ajiye a gefen bathroom din ya dan tura, wanda take wata ƙofa ta bayyana , da mamakina naga ya murɗa hannun ƙofar ya shiga ciki, wani rantsatsen bedroom da ya fi na baya haɗuwa ne ya bayyana. gaba daya kayan bedroom din green ne da white, wanda kalar tayi mugun fito da bedroom din, gefen bed din da ya sha shimfiɗa da green and white bed sheet ya nufa, bai zauna ba daga tsaye Shehi ya fara warware igiyoyin Alƙyabbar jiknshi, sai da ya kunce kafin ya zameta daga jikinshu a hankali, cikn natsuwa ya ajiyeta a gefen bed din, lokacin kuma na ƙare mishi kallo, babban mutum ne sosai dan a kalla in bai yi 33 years ba zai iya yy 29 to 30 years, yana d dan faɗi ba sosai ba yana da tsawo da faffadan kirji, ba za'a kirashi mai jiki ba ba kuma za'a kirashi marar jiki ba,bashi da ƙiba yana tsaka tsakiyar jiki, irin na Jarumai ko in ce sadaukai. bayan ya zame Alkyabbar ya ajiye, wani farin boyel ne mai kyau da taushi ya bayyana , ya ji dinkin surfani da ya kasance Golding , sosai dinkin yy kyau kuma ya dace da jikinshi, wata ƙofa naga ya ƙara nufa, nan kuma wani Bathroom din ya ƙara bayyana wanda shima komanshi ya kasance green da white gwanin kyau. bottom din gaban rigarshi ya shiga ballewa, bayan ta cire rigar wata rigarce ta ƙara bayyana, haka bayan ya cire dogon wandon Boyel din wani wandon mai dan tsayi da ya kusa rufe ƙafarshi ya bayyana, ajiye kayan da ya cire yy a jikin hanger, matsawa yy jikin shower ya sakar wa kanshi ruwa, a hankali ya furta "Subhanallahi", ya fada yana lumshe lu-lu eyes dinshi, wanda hakan yy sanadiyar kwanciyae eyes lashes dinshi, wanda suka kwanta a ƙasan idanunshi suka yi zaro-zaro sakamakon ruwan da take sauka a kanshi wanda yake gangara har cikin jikinshi gaba daya . gashin kanshi kuwa gaba daya ya rufe mishi fuskarshi ya zamana ba'a iya ganin fuskarshi, sa boda gashin kanshi da ruwa ya jiƙa ya zubo, ya dade sosai ruwan na dukan jikinshi, kafin ya dauki wani soso mai taushi da Sabulun Dove mai gyara fata da sanyata taushi ya fara gogawa jikinshi ba tare da ya cire kayan jikinshi ba, while ruwan da ya kunna yana dukan kanshi. duk kuwa da ga komin wanka nan amma bai damu da yin wankan ciki ba, domin yana koyawa kanshi rashin jin dadi, domin yana duba wanda basa da dukiya ya suke, shin lokacin da Allah ya yanke maka wani jin dadi ya zaka yi?, hakan yasa wani lokaci yake dan nuna wa jikinshi ba fa kullum ake kwana gado ba dolle wata ranar a kwanta a ƙasa. har ya gama wankan mai matsa daga ƙasan shower din da take dukan jikinshi ba, sai da a ko wane lokaci yana ƙara rumtse idanunshi da kiran sunan Allah har ya gama wanka. yana gamawa ya nufi wata Yar kofa ya bude, ya shiga tsarin jararrun kaya ne musu kyau da tsari tare da tsada suka bayyana a cikin gurih, wanda hakan ya tabbatar min da cewar gurin Adana kaya ne. dan sakaya ƙofar yy..kusan 10 minutes kafin ya turo ƙofar ya fito kamshin turaremshi na Huge boss din da na shaƙa ne ya tabbatar min da fitowarshi, cikin wani shigar ta Ash din Jallabiya har wa yau kanshi na nannaɗe da rawani , a haka ya fito yana ta baza kamshi, kafarshi sanye da wani slippers mai taushi a hankali yale takawa har ya fita dayan bedroom din , zama yy kan bed, tars da daukar wayarshi da take haske alamar shigowar saƙo, a Gmail dinshi ne aka turo mishi saƙon. hakan yasa ya zauna cikin bawa Saƙon muhimmanci , a hankali ya bude saƙon, Abun da ya gani yy mugun girgiza mishi tunaninshi, tare da sanya duniyarshi cikin wani, firgitaccen yana yi, a hankali yace "Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un, Allahumma Ajrni fiii masibati ", ya fada yana ƙara duba saƙon Dr din . kafin ya gama banbance halin da Yarinyar take ciki a lokacin Dr y kira, a hankali ya ƙara mishi bayani, "kamar yarda na rubuta maka, gaskiya tana buƙatar ganin Manyan Likitoci domin su dubata da kyau tare da bata duk wani treatment da ya kamata, babbar Jijiyar dai da take riƙe da jinta tare da maganarta ne ta samu matsala domin tama zaro daga in da take sakamakon mumunan haɗarin da sukayi, sannan ta ko ina jikinta raunika ne, gashi kuma tana dauke da Asthma mai karfi sosai, gashi kuma wani sashe daga zuciyarta yana da matsala, kodarta ma daya tana da matsala, wadda in ba'a gaggauta mata aiki ba zata iya rasa Rayuwarta, gaskiya Yarinyar nan tana ciikin haɗari domin ta shiga cikin Critical condition. wanda bayanin shi zai yi wuya, da mugun wahala ta rayu",ya fada cikin wani yana yi. wani zazzafan breath Shehi ya sauke, cikin kamilalliyar muryarshi mai tattare da gaji yace "Uhmm", yana fadar haka, ya,kadhe wayar dan ya tabbatar da cewar Dr din ya gaɓa duk bayanan da zai mishi. Agogon bangon da take maqale a jikin bangon bedroom din ya kalla, ganin lokacin Sallar Magrib ya gaba to, ya sashe miƙewa, dan in dai yana nan bb mai Limancin Masallacin Masarautar sai shi. A hankali ya...... Littafin nan na kuɗi ne #400 ne kuɗinsa,ga mai so zai iya tuntuɓata domin sanin ta yarda zai biya kuɗinsa. 07033371851 DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI YAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️ SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR) ```MASU SON A TALLATA MUSU KASUWANCIN SU ZASU IYA TUNTUƁATA AKAN NUMBER NA KAMAR HAKA. 07033371851``` *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Page 3. A hankali ya miƙe, tare da daura baƙar Alƙyabba mai dan saukin nauyi a jikinshi, tare da ƙara gyara Rawanin kanshi, sai yy fito A Ahmad Sudeis sak. cikin Kamala da natsuwa yake tafiya, yaba ta ƙara baza kamshin turarem Huge boss da, ya kama mishi jiki sosai dan har ko bai sa ba, to zaki ji kamshi a jikinshi. yana Zikirin maraice ya fito daga bedroom din, zuwa palo, kasantuwar yana da Alwala yasa bai tsaya yin wata ba, ya nufi hanyar fita, a ƙafarshi yy shiga tattaki zuwa Masallacin da yake faron Masarautar in da anan kowa dan cikin Ahlin masarautar yake gabatar da Sallarshi. yana tafe yana zikirinshi, har ya ƙarasa Masallacin, gaba daya Jama'ar da suke bakin Masallacin suka miƙe, tare da fara mimmiƙa mishi hannu, suna gaiswa, wani ɗan tsoho ne yace "Yah Shehin Malamin mu ka guji Ƙasarmu , bayan lokaci mai dan tsawo da ka bar nan sai a cikin Talabijin muke ganin ka, fatan dai komai lafiya?, Ya Mai martaba Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki da jiki?", ya fada yana dunƙule hannayeshin. karo na farko da tunda ya shigo cikin Masarautar da yy amfani da tattausar murya mai dadin Sauraro yy tsohon magana a hankali cikin rashin son maganarshi, ganin lokacin Sallah na shigewa Yasa ya nufi cikin Masallaci duk mara mishi baya suka yi suna Addu'ar Samun Sauƙin wa Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki , gurin Liman ya tsaya tare da kabbara Sallah cikin zazzaƙar muryarshi, gaba daya garin sai yy tsitttttt ana saurarar sautin karatunshi. Masallacin kuwa kowa ya natsu, zukatansu gaba daya sun narke da jin Muryarshi da suka dauki tsawon wattanni basu ji ba, haka har Aka ƙarasa Sallah, gyara zamanshi yy, tare da nannade ƙafafunshi ya juya gurin dubban jama'ar gurin, wanda bb wanda ya fita duk suna zaune, suna jiran karatunsa. Manyan Littatafan Addini ya dauka, dauka tare da fara koyae da su, cikin harshen fulatanci in yy da hausa yy da fulatanci yy da turanci, dan kusan rabin mutansn basa jin hausa, wasu kuma basu ciks fahimtar fulataccin ba, kasantuwar garin ya haɗa ƙabila biyu, hausa da fulani. har lokacin Isha yy yana zaune yana koyar da su, sai da A kayi Sallar Isha kafin ya mike zuwa cikin gida, bakinshi yana ambaton sunan Allah,haka ya ratsa dukkan parts din da suke gidan har ya isa nashi part din,yana shiga ya zauna a palo tare da lumshe idanunshi, da suke dauke da tsananin gajiya , da barci. bai fi 10minutes da zama ba, aka turo ƙofar Pallon, bai ɗago da idanunshi ba har wanda ya shigo ya iso tsakiyar palon, bb ko Sallama haka ta tsaya mishi a ka, a hankali ya fara bude idanunshi har ya saukesu akan Jadda da take tsaye. mayar da idanunshi yy ya rufe, san dama yasan wani kayan sai Amale, cikin zazzaƙar muryarshi yace "ke baki iya Sallama ba ?, ko ke Arniya ce ?", ya fada cikin rashin damuwar cewae Ita Jaddar Babbar mace ce dan A kalla zata iya yin 95 a shekaru,sai dai yarda ta zubar da girmanta, sa boda yar da take babbar da batasan girmanta ba, ta tsaneshi bata son shi, bata kaunar Mahaifinshi da Mahaifiyarshi Da Yan uwanshi kullum neman abun da zai cutar da su take nema. wani kallo ta mishi tare da cewa "ai kasan ni dangin Maimoon ne Uwarka sune basa Sallah dan Ubanka", ta fada cikin harzuƙa... taɓe bakinshi yy bai ce mata komai ba, ita kuwa haushin rashin kulatan da yy yasa ta fice a faɗace tana zazzaga mishi zagi, sai da ta bar gurin kafin ya miƙe, ya nufi hanyar Upstairs dinshi, yana zuwa ya tura ƙofar ya shiga, bai zauna a na dayan ba sai ya shige chan na biyun, bathroom ya shiga yy wanka tare da dauro Alwala ya fito, Shafa'i da Wuturi yy, yy Addu'o'i da karatun Al-qur'ani, kusan 11pm yana karatub cikin muryarshi mai dadi kafin ya miƙe daga in da yake. gefen bed ya zauna, tare da dan daura hannunshi akan cikinshi, ya lumshe idanunshu, fuskarshi ya dan yamutsa tare da dan shagwaɓeta, kaɗan irin na Shagwaɓaɓɓun da in suka samu wuri to zasu zuba shagwaɓa, a hankali ya miƙe ya nufi fridge din da ke kusa da bed din. budewa yy , tare da fitar da peak milk mai sanyi sosai, tare da wata gorar zuma mai kyau, cup ya dauka ya daurayo, ya dawo tsakiyar carpet din da yake walale bakin bed din shi,zuba madarar yy ya sanya zuɓa, tare da sanya Spoon ya fara jujjuyawa sai da ya tabbatar ya haɗe jikinshi. kafin ya dauka da Bissimillah..!, dauke a bakinshi ya kafa kanshi, sai da ya shanye tasss kafin ya ajiye cup din, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da lumshe idanunshi. gefe ya mayar da cup din da gwangwanin ya, matsa ya jingina kanshi da jikin bed din yy shiru, idanunshi a lumshe kamar msi barci, a zahirin gaskiya kuwa ba barcin yake ba,tunanin rayuwa kawai yake.. A hankali guraren 1 ya miƙe daga zaunan da yake, ya nufi bathroom, alwala ya ƙara daurowa, yana fitowa ya sanya wata lafiyayyiyar Dubai Jallabiya mai masifar kyau black da tayi asalin fito jishi da tsantsae farin fatarshi. gurin pray met dinshi ya matsa, tare da kabbara Sallah, cikin zazzaƙar muryarshi ya ringa rairo karatun Al-qur'ani, har guraren 4 sai da aka fara kiran Sallah Subhi kafin, ya tsagaita ya koma gefe yana karatu da Tasbihi 4:30am ya miƙe , Sabon Wanka da Alwala yy, tare da chanja kaya, ya nufo hanyar waje. Shi daya ya fara takawa daga cikin Masarautar zuwa Masallaci , a hankali yake tafiya, bakinshi kuma har lokacin bai gushe da ambaton sunayen Allah ba da Addu'o'i tare da Tasbhi , haka har ya fita daga part dinshi, ya fara ratsawa ta cikin masarautar da bb kowa, bb motsin kowa, sai sanyayyiyar Iska Asuba da take kaɗawa, wadda take dauke da ni'imomi da wani yalwataccen nishaɗi, iska ce mai sanyaya zuciya, da sanya ruhi cikin natsuwa, iska ce mai dauke da iskar hadari wanda ya gangamu garin yy baƙiƙƙirin kamar za'a kece da ruwa. haka yake tafiya cikin rashin tsoro, har ya ƙarasa Masallacin da bb kowa a ciki, A hankali ya ƙarasa cikin Masallacin, sai da ya dudduba komai kafin ya fito, tsayawa yy daga dan gaba cikin rumfar Masallacin, ya kauɗa kiran Sallah cikin sanyayyiyar muryarshi mai dadin gaske. wadda tayi sanadiyar tashin kusan dukkan Al-ummar Masarautar tashi daga barcin da suke yi, gaba dayansu zuciyarsu tayi wani irin taushi jikimsu duk ya saki, kwaɗa kiran Sallarshi na biyu ne yy Sanadiyar tashin duk wani mai gigga-giggan masu Jinnun da suke cikin Masarautar, dan dama aje ne, duk lokacin da zai sauka masarautar, yy kiran Sallah to , duk wani mai gigga-giggan Aljannu da suke cikin Masarautar sun tashi. cikin Azama gaba daya Ahlin Masarautar maza gaba dayansu suka yo Masallaci domin gabatar da Sallah Subhi , kafin kace Kwabo Masallacin da bb kowa ya cika damkam da Mutane, wanda cikarsu ma har tayi yawa, hakan zai shaida maka ba mutane ne kawai ba, cikin Nishaɗin da ya tsinci zuciyarshi a cikinshi, ya fara karatuh Al-qur'ani cikin Surarul Maryam, wanda gaba daya dadin Surar da Daddin Muryarsa yasa illahirin Aljannu , Mutane , Dabbobin da suke cikin gidan suka yi tsiiiittttt suna saurararshi, hatta da iskar Hadarin da take kadawa da karfi sai ta daina kaɗawa da karfin, sai sanyayyyiyae iska da take ratsa ko ina, har sai da ya idar da Sallah, gaba daya wata iriyar iska mai karfi ta fara kaɗawa. kan kace wani abu ruwa ya fara dan sauka a hankali, duk da haka sai da yy musu karatu sosai kafin a tashi, shine last din fita daga Massalacin sai da ya rufe kafin, ya fara tafiya cikin natsuwa . lokacin 6am tayi, a hankali yake tafiya yana sauke numfashi, sai da ya kusan shiga cikin part dinshi, kafin ruwan ya fara sauka sosai kamar da bakin kwarya, har sai da yasa Shehi ya dan kara takun tafiyarshi da yake yi, duk kuma da haka cikin natsuwa yake tafiya,har ya ƙarasa. palon ƙasa ya zauna, yana zama wata Babbar mace da zata iya kai wa 60years fara ta fito daga wata hanya fuskarta washe da murmushi, cikin dan farin cikin da ya mamaye gaba daya fuskarta da zuciyarta tace "Assalamu alaika...!",a hankali ya bude idanunshi,jin muryar da ta daki dodon kunnenshi. wani murmushi da ya kusa kasheni ya sakar mata, kafin ta mayar da kamilalliyae fuskarshi kamar yarda take yace "Wa'alaikissalama...!", ya fada cikin sanyayyiyar muryarshi, idanunshi yy ƙasa da su kafin ya dan murya zoben Zinarin da yake cikin hannunshi da yake fitar da wani kyalli na musamman. cikin bada girma da rissinawa, tace "Barka da Asuba Shehi..!", a hankali ya furta "Uhmmm Coffee..!", ya fada a hankali ba tare da yace komai ba , miƙewa tayi tare da cewa "bari na haɗa maka" tana fada ta bar gurin shi kuwa ya lumshe idanunshi. bata dauki wani lokaci mai yawa ba ya dawo hannunta daure da ƙaramin tray mai dauke da wani flask ƙarami, da cups da tea spoon sai sugar, dan tasan zalla ake haɗs mishi shi yake aa sugar da kanshi. Stool ta jawo ta ajiye gabanshi, kafin ta dan rusunar da kanta tace "Shehi an gama", tana fada ta matsa chan ta zauna, kan kujera ta zauna, tana dan kallonshi,shi kuwa a hankali ya bude idanunshi, tare da dan rankwafawa, ya dauki cup din ya dan tsiyayi rabin cup ya zuba Sugar tea spoon huɗu, tare da fara dan gaurayaww har ta narke, kafin ya matsa gefe, da Bissimillah ya fara dan sipping dinshi har ya shanye tass, ya ajiye cup din. A hankali ya dan kalleta da idanunshu, yace "Ngd ..."', ya fada yana dan mayar da kanshi akan kujerar, jinjina kai tayi ba tare da tayi magana ba. Dan Jim sai ga wanu kyakyawan matashin Sarauyi ya shigo cikin palon, cikin dan murmushi yace ''Barka da safiya Shehi . barka da safiya Umma Jakadiya", murmushi tayi tare da cewa "barka Zayn-Maleek . fatan kun sauka lpy ?", dan shiru yy tare da cewa "Qlau Umma", jinjina kanta tayi. kallon Shehi Arman_Maleeq , Zayn-Maleeq yy tare da cewa "Yaa Shehi komai fa ya gama kammala. kayan suna wajen Masarauta zuwa Anjima za'a shigo da su." shiru Arman_Maleeq yy bai cewa Zayn_Maleeq komai ba... daga karshe ma miƙewa yy ya haye sama, duk binshi da kallo suka yi, kafin Zayn_maleeq ya koma inda ya tashi, tare fara haɗa Coffee sai da ya gama ya kallin Umma Jakadiya yace "Umma An jima Shehi zai raba kayan Azumi, dan wannan karon ba zamu jima ba zamu koma,na ji kuma kamar Ammie tace a taho da ke ", ya fada yana surɓar Coffeen, murmushu tayi tare da cewa "Zayn_Maleeq baki abin magana, Allah ya kai mu, " dariya yy tare da cewa "Su Umma za'a hau jirgi a tafi Madina", dariya itama tayi cikin sabo da irin rahar Zayn_maleeq tace "Oh Zayn_maleeq baka gajiya. abin da ba zuwana na farko bane wannan, bari na tashu na shige", ta fada tana miƙewa.. ****** Gaba daya kusan Drs Biyar ne a kanta bayan Nurses dukkansu sun rufa a kanta, suna dubata, dan gaba daya numfashinta daukewa yy , yana sama da ƙasa, sai shasheƙa take, gaba daya jijiyoyin jikinta sun fito, jikinta ya dauki wani rawa. Gaba daya Drs din su fara sarewa da lamarin Yarinyar, cikin lokaci dan kaɗan zata birkice , sai kuma jikin ya dai-daita, yanzu ne abun ya fi ko yaushe gaba daya, ta birkice sun kasa yarda zasuyi da ita. Dr Aslam wanda ya fara daukarta , ya fito yana sharce zufa idanunshi sunyi jaaazir, hatta kayan jikinshi sun jiƙe da zufa, Office dinshi ya shiga, ya zauna ya dafe kanshi... sai kuma ya ɗago kan tare, da daukar wayarshi. lallatsawa ya shiga yi kafin ya karata a kunnenshi. sautin ring din Wayar Shehi ne ya fara tashi cikin bedroom din nashi, lokacin 9am ,a hankali ya dan mirgina da Addu'ar tashi daga barci cikin bakinshi, ya miƙa hannunshi, ya dauku wayar, sai da ya duba sunan mai kiran kafin yy picking call din ya ƙara a kunnenshi. Zallar tashin hankalin da ya ji a cikin muryar Dr din ne yasa ya dan muskuta ya gyara zamanshi,cikin gaggawa yace "Shehi a gaggauta fitar da Yarinyar nan domin yi mata dashen nan,dan jikin gaba daya ya rikice bb sauƙi gaba daya, numfashinta ma baya fita, gaskiya tana cikin hali, in da hali ayi duk abun da za'ayi a yau din nan zuwa gobe a fitar da ita,"sauke numfashi yy . kafin yace "akwai abokina da yake irin wannan ....... Wannan littafin na kuɗi ne , game buƙata zai iya tuntuɓata ta number na kamar haka. 07033371851 DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* PAGE 4. Akwai wani Abokina da yake irin wanna Surgery din a chan garin Madina yake zaune, in kana so zan iya magana da shi sai ya shirya muku duk abun da ake baƙata", Ya fada yana dan sauke numfashi. dan jaaan ajiyar Zuciya Shehi yy kafin yace "okay..!", yana fada ya kashe wayar, tare da yin baya ya koma in da ya tashi, barcinshi ya koma sai guraren 1pm kafin ya tashi, wanka da Alwala yy ya fito, yana ta baza kamshi, tare da ƙoƙarin sanya agogon Rolex diamond da yake tayi a hannunshi. kamar kullum yana sanye ne da Turkey Jallabiya fara sol,sai takalminshi da ya kasance half cover, ya lulube gaba daya jikinshi da irin Alƙyabbar Manyan Malamai baƙa mai kwalliyar Golding , ga wani kamshin Huge Boss da yake tashi, yy wsni sihirtaccen kyau, kamar a boyeshu, ƙasumbarshi da sajenshi gaba daya sun kwanta luf,dogon Gemunshi kuwa sai motsawa yake a hankali kyawawan lips dinshi suma suke motsawa,tare da Ambaton Ubangijin Talikai. Downstairs ya nufa, yana ƙara baza Alƙyabbarshi, da gyara Agogonshi. tun kafin su ƙaraso cikin palon, kamshin turarenshi ya shidawa su Zayn_maleeq da suke zaune cikin palon zuwanshi. cikin ladabi duk suke kallonshi, har ya ƙaraso cikin palon, duk duƙar da kansu suka yi ƙasa cikin bafa girma suka zube tare da cewa "Barka da fitowa Yaa Shehi", tsantsar kauna da kulawa, ya shafa kawunansu . tare da lumshe ido kafin yace "kuna lpy ?", gaba dayansu suka Amsa da "Alhamdulillah", jinjina kanshi yy kafin ya zauna kujerar da ta kasance ta zamanshi, bayan shi bb mai hawanta sai Zayn_maleeq shima kuma ba ko yaushe ba. Umma Jakadiya ce ta fito daga wata ƙofa, kallom Shehi tayi tare da dan rausayar da kanta tace "sannu da hutawa Shehi...!", a hankali ya bude jikirtattun idanunshu, akan Umma Jakadiya, kafin ya jinjina kanshi, yace "Alhamdulillah..!", cikim tsananin kula ya mata maganar, wanda yake nuni da Zallar kularshi a kanta. kallonshi tayi , tare da cewa "Shehi a kawo Abin ci ne ?", dan tsura mata idanu yy na wasu seconds kafin ya jujjuya kanshi, yacr "ah'ah lokacin Sallah...!", yana fadar haka ya miƴe, gaba daya Ƙannenshu suka mara mishu baya izuwa Masallaci. ko da suka je Shi yana gurin Liman su kuma suna Sahun bayanshi, haka har aka idar da Sallah, bayan an idar duka fito, yana jere da Lamurɗe suna dan tattaunawa Zayn_maleeq da Abdul_Maleeq tare da Sayyid_Maleeq na bayansu tare da Ayman Yaron Lamurɗe, suna tafiya suma suna fira,sai dai Zayn_maleeq duk ya fi zuba, sauran Triplet dinshi kuwa Abdul_Maleeq da Sayyid_Maleeq basu cika surutu ba, duk ya fisu labari, dan su kusan zubin tsarin halittarsu daya da Shehi basu damu da duniya ba ayi ko kar ayi bb ruwansu, su dai kawai suna rayuwarsu. In da aka tsayar da Motocin Rarrabar Azumi suka nufa, motoci ne Dav guda Biyar, daya Sugar ne ciki,daya gyero, daya wake, daya shinkafa sai dayar Mai ne ciki. ga kuma jerun mutanan da duk suka hau hali suna jiran Shehi, bude motocin aka yi, fiffito da kayayyakin aka fara yi, Zayn_maleeq na gefe kasantuwarshi na mai son jiki yasa duk wani aikin wahala baya ciki.. Sayyid_maleeq da Abdul_maleeq kuwa suna bayan Shehi suna taimaka mishi, su da kansu suke dauka su bawa Shehi shi kuma ya miƙawa mutanan, bayan an gama rarrabawa, sai kuma ya bi kuwa da 10k , wanda wannan kyauta ta tsoma gaba daya yan Masarautar Baihan cikin murya da jin dadi, dan in ba shu ba sai Babanshi sune kawai suke bautawa Masarautar, da jikimsu da kuɗinsu, basa gajiya da dukkan buƙatun mabiyansu. duk halin da mutun yake yaje ya fada musu sube masu kafadar dauka, wanda tausayin da Allah ya daurawa Lamido Abdul-azeez Arman Maleeq na talakawan garin shine mussababbin ciwonshi, yanda Al_umma suke kaunarshi shine mafarin ciwonshi, yarda yake da zaratan Mazaje wanda suka kasance Yaranshi ha cikinshi shine ya zama tubalin ciwonshi, wanda shekara day-daya har shekara 20years cif yana kwance bashi da lpy. rashin lpy mai muni, wadda kwata-kwata baya iya aiwatarwa da kanshi komai, konai sai dai a mishi. sai guraren 3:30 o'clock suka gama rarrabar cikin gajiyawa, Zayn_Maleeq ya taso daga in da yake zaune ya nufosu, yana zuwa ya riƙe hannun Shehi da yake cikin Alƙyabbarshi , cikin kulawa ya dan kalleshi, da ido ya mishi mgn . fuskarshi ya dan ɓata kafin yace ,"Yaa Shehi akwai gajiya", ya fada yama kallon sauram Yan uwanshi, Abdul_maleeq yace " wa mai gajiya ??", a hankali yace "Shehi Zayn yake da gajiya..!", ga fada yana dan yin luuuu da idanunshi.. kallonshin Shehi yy cikin dan nuna hukunci ya rike yatsun hannunshi, tare da matsewa, yar ƙara ya saki, cikin dan yana yi yace "Ayya Hamma Shehi na tuba na bi Allah na bika,ba ni da Uwa , Uba ba lafiya Adda na bata kusa Kai ne kawai Babana Mmna , Addana, ka gafarce ni", ya fada yana shagwaɓe fuska. tuni raunin Shehi ya bayyana, triplets din da suke jere masu bala'in kama da juna ya kalla, numfashi mai karfi ya sauke, tare da dan shiga tsakaninsu gaba daya ya rungumesu . suma riƙeshi suka yi, dan sun san duk lokacin da yake kewar Mahaifiyarsu ne kawai yake musu haka. sun dan jimaa a haka kafin ya sakesu, ya kama hannayensu , suka nufi masjid. sai da ya tsayar da su bayanshi, kafin ya matsa gurin Liman ya zauna, Al-qur'ani ya dauka duk ya mimmiƴa musu, shma ya dauka, cikin ƙira'a mai dadin gaske suka fare karatu gaba dayansu. bama sa kallon Al-qur'anin saboda suna da haddarshi a kansu, dan sittin ta zauna musu daram a kansu. sun san yi karatu mai yawa kafin lokacn Sallah yy, miƙewa yy ya ajiye Al-qur'anin, suma ajiyewa suka yi suka kiƙe, kabbara Sallah yy, duk mutame suna shishigo cikin Masjid din, bayan sun idar suka fito, yana jere da Ƙananshi dukkansu Ukkun dan Dsn Lamurɗe baya tare sa su tuni Lamurɗe yy mishi wata Uwar harara da tasa bb shiri ya barsu. suna tafiya Zayn_maleeq ma duƙewa, sa boda tsananin yunwar da yake ji, sun kusa shiga part din Shehi ya dan yi yar ƙara tare da dafe cikimshi, da sauri suka jujjiyo gareshi, kafin suyi taku daya ya isa in da yake da sauri ya taroshi, karashi yy da jikinshi, tare da tsura mishi kyawawan idanunshi, yana kallonshi. sai kuma ya kalli Abdul_maleeq da Sayyid_ Maleeq, kallon sa yy musu kawai ya fahintar da su mai yake nufi, da sauri suka tarairayi Dan Uwansu, suka kakkamashi zuwa part din su, har sun gilma part din Jadda, Zayn_maleeq yace su shiga da kyar, su sama mishi abun da zai ci. ba suyi musu ba suka shiga, zaune suka samu Jadda ƙafa daya kan daya tana kallon TV , zaunar da shi suka yi, cikin irin maganarshi yace "Jadda ina son a bani Abin ci", ya fada yana dan riƙe ciki, yarda ta dan washe fuska ta miƙe, kitchen dinta ta nufa da sauri, kallon juna suka yi, kafin su kalli Zayn_maleeq da ya dawo ƙasa yana jiranta . bata jima da shiga ba ta dawo , baiwarta na bayanta hannunta dauke da babban tray mai dauke da wormers marasa girma sosai, da plates da spoons , sai dan jug mai dauke da juice . ajiyewa tayi gaban Zayn_maleeq tana washe bakinta, kai da ganin irin murmushin da take zakasan akwai wata a ƙasa, dan farkom shigowarsu palon ko kallo basu isheta ba. gyara zama Zayn_maleeq yy tare da bude katuwar Wormer din gabanshi, kyakyawan tuwan shinkafa da yake fari tass an mulmuleshi a cikin fararen ledoji ya mayyana, tuwo daya ya dauka, tare da bude wormer din miyar. haɗaɗɗiyar miyar Egusi , da tasha kifi banda ta bayyana, plate ya dauka ya zuba miyar a plate. a hankali ya fara ci yana jin wani dan karci a bakinshi, sai dai bai kawo komai a kanshi ba, har ya kusan cin rabi. kallon Abdul_maleeq da Sayyid_maleeq tayu, tare da ɓalla musu harara tace "ku ba zaku ci ba ...?", ta fada tana kallonsu da idanunta da suka ji bakin kwalli jail. taɓe baki suka yi basu ce komai ba, tsaki ta jaa tare da cewa "Shegu ni zaku wa kwanere, ni na ci Uwarku har da Ubanku a Iskanci", ta fada tana kwata, tari ne ya dan tsarke Zayn_maleeq a hankali ya fara tarin, har ya fara yi sosai. tari ne ya tsarkeshi sosai, har idanunshi suka fara kakkafewa,, a tsorace Sayyid_,maleeq da Abdul_maleeq suka nufeshi, suna jijjigashi, sai dai baya jin su dan ya fita a hayyacinshi. da sauri Abdul_maleeq ya fiddo wayarshi da take cikin pocket din shi, ya fara kiran Number Yaaa Shehi, kira daya ,biyu, a na ukkun Shehi Arman ya dauki Wayarshi, a hankali ya dan yi jim kafin yy Sallama. bai amsa Sallamar cikin ba, a ruɗe Abdul_maleeq ya fara magana cikin ruɗu ya ce "Yaaa Shehi Zayn! Zayn!! Zayn_maleeq Yaa shehi ", ya fada kamar zai yi kuka,cikin rashin fahimta yace "mai yake damunsa ...?", cikin sauri yace '" gamu a part din Jadda baya hayyacinshi, wani abu yake makamar wanda zai mutu, Yaaa Shehi ka taho", ya fada cikin wani yana yi. cikin sauri Yaaa Shehi ya fara daga ƙafarshi zuwa sashen Jadda, yana zuwa ya samesu, suna kan Zayn_maleeq Jadda kuwa tana zaune kan kujerarta . sai tauba chewing gum take kamar wata budurwa, da sauri Sayyid ya nufeshi yana cewa "Abin ci Jadda ta bashi yana cikin ci ya fara haka", ya fada yana nuna shi. kallon Jadda da take zaune yy, wadda ganinshi yy mugu-mugun razanata,nunawa ne kawai bata yi ba . takawa ya fara yi zuwa gareta, da sauri ta miƙe , tana jin wani futsari na ƙulle mararta, tana tafiya yana bin bayanta, har sai da ta kai karshe gurin bango, ta fara zazzare idanu take. idannunshi da suka yu jaaazir tsabar ɓacin rai ya watsasu akan fuskarta, cikin wata kakkasar murya yace "ke..! , ke !!, ke!!! ki roƙi Allsh kar wani abu mummuna ya faru da Zayn, in kuwa ya faru da shi uhmmmm...", cije lips dinshi na ƙasa yy da karfi Alamar, koma mai zai aika ba zai mata kyau ba, sosai ta tsorata wanda tsoratar tayi sanadiyar zubowar Futsari daga mararta.. Wannan littafin na kuɗi, game buƙata ya tuntuɓi number ta kamar haka . 07033371851. DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️. SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA,SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹 ) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *P. 5* Hannunshi ya juya mata, kafin ya juya gurin Ƙannanshi, idanunshi jaaazir, Umarni yy musu da su daukeshi, Part dinshi, suka nufa da shi. Kan kujera suka ajiyeshi, Umarni ya ƙara musu da su dauko mishi Madara peak da cup a fridge, da sauri suka dauko suka dawo, karɓar madarar yy,ya ɓula bakinta da Key din mota , gaba daya madarar ya juye cikin cup din, Sayyid-maleeq ya kalla kafin yace "Zuma and Spoon", ya fada yana daura tafin hannunshi a goshin Zayn_maleeq , da ta dauki wani mugun zafi sosai. da sauri Sayyid ya je yy abun da Shehi ya Umarceshi da yy, bayan ya kawo ya haɗa Zumar, ya jujjuya , tare da tallafar kan Zayn ya fara zuba mishi haɗaɗɗiyar madarar da Zuma , a bakinshi cikin ikon Allah yake shiga cikinshi, har ya shanye tasss. tafin hannunshi, ya kama ya matsa, zazzafan numfashi ya sauke, tare da ƙaƙarin Amai, dagoshi Shehi yy ya ƙarashi da jikinshi,amai ya shiga kwararawa baƙiƙƙirin . shafa mishi bayanshi ya shiga yi , yana fesar da iska mai zafi, sai da Zayn ya amai gaba daya abun da ya ci kafin ya koma jikin Shehi, yana sauke numfashi, cikin kakkausar murya da gargadi yace "kai kunnen kashe ne da kai ko ??,ba na haneka da karɓar wani abu ba hannun yan cikin masarautar nan?,ka ci gaba da shishige musu kana karɓar abu a hannunsu kana ci, ba mutuwa ake tsoro ba wahalar da zaka sha ita de abun gudu", dafe kanshi yy yana jin yana wani mugun sara mishi. zameshi yy daga jikinshi ya wucewarshi Upstairs. dai-dai nan Umma Jakadiya ta shigo palon a tsorace, da sauri ta isa gurin Zayn , tana tattaɓashi a firgice take cewa "fatan dai bb abun da ya sameke ko ?" ta fada a firgice, idanunshi da suka kasance irin na Shehi ya dan bude tare da yin luuuu da su irin dai yarda Shehi yake yi, idan baya son hayaniya ko baya jin dadi. taɓa wuyanshi yy, jikinshi bb zafi, numfashi ta sauke tare da cewa "Alhamdulillah", kallon Sayyid da Abdul tayi, tace "ku kamashi ku kai shi Bedroom ya kwanta, ya huta, kafin na sama mishi abin da zai ci", ta fada tana miƙewa. Yaa Shehi na shiga bedroom dinshi, ya kwanta kan bed, yana sauke wani wahalalan numfashi,cikin rashin yake ayyana tunda sun gama abun da ya kawosu garin dole su tattara su barshi, kafin ayi Sanadiyar rai abu mafi soyuwa a gareshi. zazzafan numfashi ya sauke yana jin wani zafi tun daga cikin jikinshi, har saman gashin kanshi,a hankali ya miƙe ya zare Alƙyabbar jikinshi, ya zame rawanin kanshi ya ajiye akan bed din, tare sa nufar bathroom, tsakiyar shower ya tsaya, tare da kunnawa. ruwan sanyi ne ya fara dukan kanshi, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tura yatsun hannunshi tsakiyar kanshu, yana barbaza gashin kanshi . ta yarda ruwan ya ke shiga dukkan jikinshi. sai da ya tabbatar da cewar zafin ranshi, har ma da zafin jikimshi yy ƙasa kafin ya fito kashe shower din, ƙaramin towel ya daura a kanshi, yana tsane gashin kanshi da yake lirif da ruwa,a hankali yake takowa . sai da ya zo gurin ƙofa kafin ya zare lallausa kuma tattausar ƙafarshi daga cikin bathroom slippers din, bude kofar yy ya fito, yana fitowa ya daura ƙafarshi akan welcome carpet da yake shimfiɗe a ƙofar fitowa bathroom din. da Sunan Allah ya fito ya fara shiryawa cikin Arebiyan Jallabiya Back mai kyan gaske, gaban dressing mirror ya tsaya, hand dryer, ya fara busar da gashin kanshi, da har rufe mishi fuska yake, tsabar yawa da sulɓi, a hankali ya tattare gashin ya mayar da shi baya , yana fesar da sanyayyar ajiyar zuciya, turarenshi na Huge boss ya dauka, ga fara feshe jikinshi da shi. har sai da ya fara hawar mishi kai kafin ya ajiyeshi, yana juyawa daga gaban mirror, gurin Pray mat ya matsa, tare da zama, ya tankwashe ƙafafunshi , Al-qur'ani ya dauka ya fara karantawa. Yaa Shehi bai fito ba sai gabanin Magrib, a hankali ya fara saukowa, wannan ƙaron yana sanye da Jallabiya Fara ƙarr sai hula fara, ƙafarshi na sanye da wasu tausasan slippers masu kyau da sukawa ƙafarshi ɗas. A hankali yake saukowa daga Upstair yana cewa "```Allahummaj al fiy kalbiy nu`ran, wa fiylisa niy nu`ran, wafiy basari nu`ran, wamin fauki nu'ran, wamin tahti nu`ran , wa an yami`ni nu`ran , wa an shima`liy nu`ran, wa min ama`mi nuran, wa mankhalfiy, waj al fiy nafsiy nu`ran, wa aazim liy nu`ran , wa azzimliy nu`ran , waj al liy nu`ran , wa nu`ran , Allahumma aadiniy nu`ran , waj alfiy asabiy nu`ran, wafiy lahmiy nu'ran , wafiy damiy nuran , wafiy shaariy nu`ran , wafiy bashariy nu`ran```" , bai ko yi musu magana ba sai nuni da yy musu da su tashi lokacin Sallah yy. har ya kuaa fita Umma Jakadiya tace "Yaa Shehi mai za'a haɗa maka ??.", hannu ya ɗaga mata alamar yana dawowa, Zayn_Maleeq da ya warwarw ne yace "Ummu Tuwan Shinkafa da miyar Kase", yaba fada ya bi bayan Yan uwanshu haka suka fice yana gaba suna binshi a baya, har suka ƙarasa Masjid din bb wanda yy wa wani magana. ko da suka ƙarasa bakin Masjid din, suka yi Addu'ar shiga Masallaci, lokacin Yaah Shehi har ya shige ciki, kasantuwar lokaci ya tafi da yawa. kafin su ƙarasa shiga cikin Masjid din har ya ƙwala kiran Sallar Magrib cikin zazzaƙar muryarshi mai dadin Sauraro , cikin yar Azama suka shiga Masjid din, suka tsaya a sahun gaba daga bayanshi. cikin Zazzaƙar muryarshi ya fara karatun Al_qur'ani mai girma, har ya idar a cikin Suratul Ma'eedah , Ƙarin karatun da ya soma yi musu jiya yy musu ,har lokacin Sallar Isha yy , Bayan ya Jasu Jam'in Sallar Isha, suna idar wa, ya miƙe tare da yin hanyar waje, ganin hakan yasa da sauri Sayyid_Maleeq da Zayn_maleeq da Abdul_Maleeq suka biyo bayanshi. jerawa suka yi su huɗu a bunsu suna tafiya, ko wane tasbhi yake, haka har suka ƙarasa sashen Matan Sarki da tun zuwansu basu leqa ba, sashen Babbar Matar Sarki Hajiya Lami suka fara shiga,ba laifi ta sakar musu fuska sosai, dan kusan Ƙawar Ammiensu ce kafin ta bar duniya, bayan sun gama gaisheta, suka nufi sauran sassan gidan. duk in da suka shiga bb wani sakin fuska hakan, yasa basu wani damu ba, san sun saba da yana yon gidan Sarautar nasu,Asalin Sarautar tasu ce, amma gaba ake musu da mugun kwulli a kanta. su basu ma damu da Sarautar ba kwata-kwata amma an damar musu rayuwarsu, hakan yasa basa jin dadin zama cikin gidan ko kaɗan, wanda har zaman Abroad ya fiye musu zaman gidan , dan ta ko wane ɓangare hari ake kawo musu, duk kuwa da cewar Sarautar ba hannunsu take ba sun riga da sun Miƙata ga Ƙanin Mahaifinsu. daga nan Ɓangaren Sarki suka nufa, cikin sanyayyiyar muryar Shehi yy Sallama cikim palon Lamurɗe,cikinshi ne yy wani mugun murɗawa, zuciyarshi tayi wani mugun bugawa, tunaninshi ya so gushewa daga cikin jikinshi, dakyar ya tattare gaba daya natsuwarshi guri daya, har suka ƙaraso cikin palon shi bai amsa Sallamarsu ba kuma bai dauke idanunshi daga kallon da yake musu ba. har suka ƙaraso su Zayn suka zauna ƙasa Yaa Shehi ya zauna saman kujera, amma Lamurɗe bai dauke ganinshi garesu ba, da alama ma baya cikin cikakken natsuwarshi, gyara murya Yaa Shehi yy, tare da cewa "Fatan Lafiya Abba ..?", da sauri ya dauke idanunshu daga garesu yana sakin dan ƙiƙirarran murmushi, tace "Uhmm hhhhmm lpy lau Yaa Shehi", ya fada yana dai-daita natsuwarshi. Haɗa baki su Zayn suka yi gurin cewa "barka da dare Abba ", dan murmushin da iyakarshi laɓɓa yy tare da cewa ''barka dai Yaran Albarka", jim suka dan yi kafin Yaa Shehi yace "Uhmmm na zo faɗa maka cewar gove zamu koma", ya fada yana dan sauke numfashi. ɓoyayyiyar Ajiyar Zuciya Lamurɗe ya sauke tare da cewa "to..to...to. Madallah Allah shi kai mu goben", ya fada yana dan murmushi. sun jima a gurin Lamurɗe yana jaansu da fira su kuwa suna san biye mishi, har dai ya gaji shima ya tsuke bakinshi, sai da Zayn kawai yake Yar fira , dan Zayn din shine Uban surutu. amma sauran da dan su za'ayi surutu da ba'ayi ba, dan ko mai zaka ce musu a gajarce suke amsa maka. sai gurin 9pm kafin suka miƙe gaba dayansu suka fice, part din Yaa Shehi da dama nan suke gaba dayansu suka koma, lokacin da suka shiga Umma Jakadiya na ƙarasa shirya Wormers akan dining table, da murmushi kan fuskar Zayn Maleeq yace "Yawwa Umma kamar kin san da yunwa nake tare", girgiza kanta tayi, dan tasan gogan dama baya wasa da tunburƙumarsa. kan dining ya wuce ba tare da ya tsaya cikin palon ba, tsayawa yy yana ƙarewa Dining din kallo, su Sayyid kuwa suna tsaye cikin palo, in da Yaa Shehi yy Upstairs . Kallo Umma Jakadiya yy yace "Umma taho ki haɗa min Yaa Shehi", tun da ta ji haka tasan tare zai ci Abin cin da Shehi dan wani lokacin tare suke ci, matsawa tayi dining din ta shiga haɗa mishi cikin babban tray mai kyau sosai. miƙa mishi tayi tace "gashi na gaban goshin Yaah Shehi", ta fada tana murmushi, murmushin shima yy, tare da ƙarɓa ya haye Upstairs din zuwa palon Yaa Shehi. Zaune ya sameshi, ya tanƙwashe ƙafafunshi, idanunshi a lumshe yana ta Istigifari , da Sallama a bakinshi ya ƙarasa gaban Yaa Shehin da ya lumshe idanunshi, a hankali ya amsa Sallamar Zayn chan ciki, wanda in ba ka saurara da kyau ba ba zaka ji sadda ya amsa Sallamar ba. gaban Shehin ya ƙarasa tare da ajiye tray din a ƙasa, yace "Sannu da hutawa Yaa Shehi..!", bai bude idanunshi ba, kuma bai Amsa mishi ba. gefenshi Zayn_Maleeq ya zauna ya nannaɗe ƙafafunshi ya dan jaaa numfashi, yana kallon Shehi. kusan 10minutes Yaa Shehi bai bude idanunshi ba,bai kuma yi mgn ba, kallonshi yy yace "Yaaa Shehi Yunwa",ya fada yana dan yatsina fuska,bude idanunshi yy tare da jaan tray din, ya fara bude plate tare da ajiyewa a ƙasa. wormers din ya fara bubbudewa, Tuƙaƙƙen Tuwon shinkafa da ya haɗe jikimshi yana daure a leda ya bayyana, daya ya dauka tare da budewa ya daura akan plate, dan bowl ya dauka, tare da bude ƙaramar Wormer kalar babbar Wormar din da ya fiddo tuwon. buɗe Wormer din yy lafiyayyiyar miyar Kase ce ta bayyana,sai kamshi take ta ji name zuƙul-zuƙul sai turiri yake, hannu Yah Shehi ya dauraye cikin wata yar tasa, tare da gutsiro tuwon, ya sanya cikin miyar ya fiddo tare, da nufar bakin Zayn_Maleeq, da sauri Zayn ya gyara zamanshi, ya dawo gaban Yaa Shehi sosai, bude bakinshi yy, cikin soyayyar Yan Uwantaka ya fara bashi tuwon yana ci, har ya cinye leda daya, kallonshi yy tare da mishi lamar ya ƙoshi girguza kanshi yy . hakan yasa ya kara bude wani, tare da gutsirowa, jin da zafi yasa ya dan busa mishi da iskar bakinshi, ya ci gaba da bashi,zufa ce ta fara tsatsafowa Zayn_maleeq na ƙoshi, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da cewa " ```Alhamdulillahi Ala kullu Halin ...!``` ", ya fada yana dan jaaa baya, sanyayyayen Lemun Kwakwa da yaji madara Yaaah Shehi ya zuba mishi , dauka yy ya sha, yana lumshe ido sa boda sanyin da ya ratsa maƙogwaronshi. baya ya Jaaa tare da jingina kanshi da jikin kujerar da Yaa Shehi yake zaube ya fara sauke numfashi, tuwon shima ya ci kaɗan dan ko loma biyar bai yi ba, duk kuwa da cewar yana jin yunwa dan tun Coffeen safe bai ƙara cin komai ba. Amma kasantuwarshi na ba ma'abocin cin Abin cin mai nauyi bane, musamman in zai kwanta bai iya cin Abin cin ba. bayan ya gama ya tattara komai cikin tray din ya miƙawa Zayn_Maleeq , ba tare da yace komai ba, ganin ya miƙa mishi gabanshi yasa ya dauka yy Downstairs domin mayar da kayan abin cin. bayan ya ajiye ya zauna gurin Sayyid da suke zaune suna kallon ball.... sai guraren 11pm kafin ya miƙe yy Sama suma bin bayanshi suka yi, yana zuwa ya tarar da Yaaa Shehi na Bathroom hakan yasa suka kwanta akan bed dinshi, sai da suka yi Addu'o'i kafin su rufe idanunsu, suna Tasbhi kamar yarda Yaa Shehi ya koyar da su dan basa barci matsawar basu yi Tasbhi ba, barcin ma gaba daya baya zuwa amma da sun fara sai ya daukesu. har suka yi barci bai fito ba, sai da ya ɓata kusan 1 hour kafin ya fito, cikin Jallabiya Maroon da tayi mishi masifar kyau, idanunshi da suke cike da gajiya da barci ya dan jaanye tare da lumshesu, ƙarasawa yy gurin bed din, sai da ya sake musu wata Addu'ar ya shafe musu jikinsu, ya jaaa musu duvet kafin ya kwanta a gefensu, kashe glove yy tare da fara karanta "```SUBHANALLAHIWA BI HAMMADIHI SUBHANALLAHIL AZEEEM```", haka ya ringa mai maimatawa, hae barci mai dan nauyi ya daukeshi. ```Washe gari``` wannan book din na kuɗi ne, ki dage ki siya domin karantawa, dan na tabbarar zaki fa'indantu da wani abu. 07033371851 Wanda ya shirya siya kawai pls. DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️. ```SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA . SADIYYA ABBAKAR MARU(ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹)``` *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *P. 6* ``` Washe gari``` Gurin 9am Yaaa Shehi ya fara takowa daga Upstairs zuwa Downstairs , sai baza kamshi yake, har kullum yana sanye da Alƙyabbarshi ruwan ƙasa ciki kuma ya sanya wata Milky din Shadda Gizna sai wani irin maiko take, yana tafiya yana barbaza Alƙyabbar jikinshi. Umma Jakadiya ce ta dan tsareshi da idanunta, tana dan murmushi tace "barka da hantsi Shehin Malamin mu..!", ta fada cikin bada girma, dan kallonta yy tare da jinjina kai, sai da ya kusan ficewa kafin ya tsaya cikin Yar daga murya yace "Umma kin shirya ?", cikin girmamawa tace "da izinin Allah", jinjina kanshi yy tare da ficewarshi. A hankali cikin natsuwa da ciƙar kamala yake tafiya, bakinshi kuma na motsi, dan saurarawa nayi, sai da nayi dan shiru kafin naji yana cewa " ```SUBHANALLAHI WA BI HAMMADUHI ADADU KHALƘIHI```" haka yake ta maimaitawa har ya fito wajen Masarautar , Jerin Gwanon Motocinshi duka suna parker a ƙofar shiga part dinshu, wanda kuma duk shi suke jira,wannan jaron 4Matic GRL 350, aka bude mishi. shiga yy tare da hakimcewa, ya baza Alƙyabbar jikinshi, Sayyid-maleeq Abdul-maleeq da Zayn-maleeq kuma suka shiga motar bayanshi, wadda itama ta kasance 4matic din sai Motar bayansu kuma ita Ummu da wasu Kuyangu Ukku suke ciki,a hankali motocin suke tafiya, har suka fita daga get din Masarautar. bayan fitarsu daga Masarauta Abuja road suka nufa direct dan sai sun koma ta chan jirginsu zai tashi, fira ce ta barke tsakanin Zayn da Yan uwansa, dan dama in kaga firar su Sayyid to da Zayn ne ko kuma Shehi ko Yayarsu Babba da Yaranta. haka suke fira har suka ƙarasa cikin garin Abuja, basu zarce ko ina ba sai wannan Asibitin dai. A mota duk suka tsaya Shehi ne kawai ya fito daga motar zuwa cikin Asibitin, Office din Dr din ya nufa direct,bayan gama Yan maganganun da zasuyi ya miƙe ya fito , Dr din na bayanshi har suka fito daga cikin Asibitin, direct gurin motarshi ya nufa, sai da suka ƙara yin musabha da Dr din kafin ya shiga motarshi suka wuce International Airport din da yake nesa kaɗan da Asibitin. lokacin da suka ƙarasa bai fi saura 10 minutes jirginsu ya tashi ba, hakan yasa suka shishiga suka zauna zaman jiran tashin shi, lokacin tashin jirgin nayi, ya fara tafiya, tare da lulawa sama. Lumshe ido Yaa Shehi yy yana fesar da sanyayiyyar iska daga cikin bakinshi. tasbhi ya fara tare da kirari wa Mahaliccin Sammai da Ƙassai , har zuwa wani lokaci, VIP side. Umma Jakadiya ma idanunta lumshe suke kamar mai yin barci, Zayn-maleeq na gefenta kunnenshi manne da Ear pie, yana sauraron karatun Al-qur'ani mai girma , sai su Sayyid-Maleeq da suke kujerar gefensu, kowa ya natsu yana abu mai muhimmanci. 4 hours chif ta saukesu, a cikin birnin garin Madina, bayan sauƙar jirgin da wasu mintoci, aka bude ƙofar jirgin, a hankali ciƙe da gajiyawa da zaman cikin jirgin mutane suka fara fitowa daga cikin jirgin, kowa fuskarshi washe da murmushi,kusan sai da kowa ya gama saukowa kafin Yaa Shehi ya fara taka Steps din jirgin a hankali cikin natsuwa da kamalar da ta zame mishi jikinshi, kanshi a ƙasa, yana baza Alƙyabbar jikinshi mai kyau da tsari, har ya gama saukowa daga kan Steps din, yana diro da ƙafarshi daga kan steps din, Yan Jaridar Ƙasar Madinah suka mishi Caaaaa, a kanshi,lafiyayyu kuma firgitattun idanunshi masu dauke da kwarjini tare da zallar haiba ya watsa musu, yana ci gaba da tafiya a hankali. Ciƙe da murnar dawowarshi suke mishi tambayoyi, Amma ya gagaraa Amsa musu ko Tambaya daya, su ma kansu sun san halinshu ba mutum bane mai yawan magana, in kaga maganarshi to Karatu yake, mafi aka sarin maganarshi da ido yake yinta ko da hannu. "Fatan Yaa Shehi ya sauka lafiya..?" , duk suka dauka bakin dayansu, gentle ya lumshe idanunshi, tare da dai-daita kyawawan lips dinshi masu taushi da sheƙi, ya furta "Alhamdulilah..!", ya fada chan ciki, wanda sai kayi dagaske zaka iya jin mai yace, sai dai motsin kyawawan lips dinshi ne zai nuna maka alamar mgn ya yi. jinjina kansu suka yi cike da tsananin gamsuwa tare da kaunarshi, haka suka rakashi har gurin manya-manyan motoci kirar Benz da aka zo daukarshi da su, Zayn-Maleeq ne ya bude mishi ƙofar motar. ciƙe da dattaku tare da zallar natsuwa ya kimtsa kyakyawar fuskarshi, shi bai saketa ba, shi kuma bai daureta ba, yana yi mai wuyar fassarawa, wanda ba kowa ne ke iya fassara irin wannan fuskar ba, sai wanda ya karanci ilimin Halayyar Dan Adam. dai-daita zamanshi yy tsakiyar nack site din, tare da jinginar da kanshi jikin kujerar ya lumshe idonshi, a hankali ya furta, "Subhanallah wal hamdulilah wa laa'ila ha illalahu wallahu Akbar", ya furta yana dan jaan igiyar wuyan Alƙyabbar jikinshi, ya sassauta matsewar da ya mishi. Zayn-Maleeq da Umma Jakadiya motar bayan Yaa Shehi suka shiga, ya yin da Sayyid_Maleeq da Abdul-Maleeq suka shiga ta bayan tasu Zayn, bayab tasu motar akwai biyu toyota a bayansu, da kuma ukku gaban motar Yaa Shehi, wanda gaba dayansu Escort dinshi ne a ciki. a jere motocin suja fara tafiya a hankali har suja fita daga tafkeken Airport din wanda ya zama International Airport , kan titi suka hau, tare da fara tafiya cikin wani kalar speed , a hankali Yaa Shehi ya gyara zamanshi, tare da dan gyaran murya. gane nufinshi yasa Driver da ya kasance Balarabe sanye da baƙin rawani ya fara sai-saita gudun motarshi, ganin hakan yasa gaba daya sauran motocin suka shiga taitayinsu, tare da dai-daita tafiyarsu, dan Yaa Shehi bai fiye son gudu da mota ba , sakamakom in ana gudu sai yaji kanshi na juya mishi. har suka shiga cikin garin Makka yana lafe jikin kujera idanunshi lumshe, har suka zo cikin gari ss. Hanya ce ta rabu ukku, daya wadda zata kai ka Massalacin Makkah, daya gidan Sarkin Makkah dayar kuma cikin gari, hanyar cikin gari sauran motocin suka yanke suka bi, ta Yaa Shehi kuma direct hanyar da zata sadasu da gidan Sarkin Makkah suka nufa, dan suna da babban taro na Manya-Manyan Malaman. da Limaman garin Makkah. bai ko motsa ba sai sa suka ƙaraso tafkeken get din gidan, da Jami'an Tsaro suka daddaɓe suna zagayanshi ko da zasu ga wani abuj cutuwa, tsayar da motar Yaa Shehi suka yi, ko da suka leqa ta win door suka ganshi, da sauri suka basu hanyar wucewa, dan Yaa Shehi sananne ne a cikin Ƙasar har ma da kewayenta . Kai tsaye Driver ya shige da motar cikin gidan, sai da ya dai-daita Parking a cikin manya-manya motocin da suke tsakiyar gidan , sai da ya fito ya budewa Yaa Shehi nota, kafin ya juyo ya kalli Yaa Shehi da idanunshi suke lumshe yace "Mun ƙara so..", ya fada a hankali . bude idanunshi ya bude tare da fesar da numfashi a hankali, ya zuro zara-zaran kafafunshi waje, kusan 5 minutes kafin ya zaro gangar jikinshi daga cikin motor, ya fito baki dayanshi, yana dai-daita zaman Alƙyabbar jikimshi ya bazata. A hankali ya fara takawa, yana fesar da numfashi, har ya ƙarasa wani tafkeken ƙofa, da wasu manya Sojoji suke tsaronta, ganinshi yasa suka wangale mishi ƙofar shiga, a hankali ya zare Cover shoes dinshi na Alfarma, kafin ya zira kyakyawar ƙafarshi cikin palon da Bissimillah akan harshenshi, a hankali ya furta "Assalamu alaikum..!", ya furta yana dago da zara-zaran Eyes lashes dinshi, da manyan kyawawan idanunshi farare masu dauke da nau'in blue din eyes ball. ciƙe da tsantsar mutunta juna suka Amsa mishi, da dan murmushi kan fuskokinsu, "Haaaaa..!", ya furta a hankali ba tare da bari sautin ya fita ba. ƙarasawa cikin palon yy , hannu ya fara binsu daya bayan daya yana basu suna musabha, tare da side hug na al-adar larabawa, ko da ya ƙarasa gurin Sarkin Makkah sai ya dan risinar da kanshi alamar ban girma, murmushi yy , yana son Wannan girmamawar da Yaa Shehin yakw mishi, shi yasa yake ƙara kaunarshi, domin shi mutum ne mai son mai girmamashi tare da girmamashi shima. Kujerar da take kusa da Sarkin ya nuna mishi, tare da cewa "ga gurin Zama Yaa Shehi Maleeq..", kallon kujerar yy , tare da mishi dan godiya da murmushi, kafin ya zauna. gaba daya Sauran Limaman kansu daurewa yy , dan su sun dauka kujerar ta Sarki ce, domin dukkansu, bb wanda ya zauna a irinta sai shi. A hankali, Sarkin ya shiga Gabatar da Abun da ya tarasu a kanshi, bayan gama maganarshi , suka dan yi maganganu da suka danganci Azumin watan Ramadan, bayan gama tattaunawa ne , aka zaɓi wanda zasu gabatar da Sallar Tarawidhi, an Zaɓi mutane da yawa wanda aka tabbatar da Babu wani Babban Uzuri a kansu lokacin, bayan gama zaɓarsu aka zaɓi wanda zasu gabatar da Sallah Ƙhiyamullal . shima aka zazzaɓa Yaa Shehi dai na Zaune ban da yamutsa fuska bb Abun da yake, dan ya ƙaragara a tashi taron Sa boda gajiyar da take ɗawainiyya da gangar jikinshi. Bayan gama komai, kowa ya Natsu domin Sarki zai fitar da wanda zai zama Special Imam, wanda shine mai Jaan Sallah sai dai in da wani Babban Uzuri kafin wanda aka zazzaɓa su maye gurbinshi, ba Tarawidh kaɗai ba har Ƙhiyamullal, manyan Limamai duk sun Natsu , kowa na fatan Zama wannan Imam din, sai dai Yaa Shehi ko a jikinshi ma, dan idanunshi a lumshe suke yana ta kirari ga Allah, wanda in ba ka lura da yarda yake sauke numfashu ba zaka rantse barci yake. Azahiri kuwa duk Abun da suke yana sauraransu, yana kuma kallonsu ta ƙasan Ido, sai dai Uffan bai ce da su ba, tun bayan gama gaggaisawa da suka yi, ya zauna,bai ce komai ba. kallonsu gaba daya yy, kafin yace "A wannan shekarar Yaah Shehi Arman_Maleeq ne zai zanto Shugaban Limamai, shine zai dunga fitar da tsare-tsaren da za'ayi Amfani da su, sannan shine Special Imam, muna roƙon Allah ya taya shi Riƙo", ya furta idanunshi akan saurarn Imam's din. kallan-kallo sukawa junansu, kafin su taya Yaa Shehi da idanunshi suke lumshe murna, bayan gama taya murna, Sarki ya musu kyauta, kafib suyi Sallama su fice, sai da duk suka fice kafin Yaa Shehi ya sauke nannauyar Ajiyar zuciya, kallon Sarki Tajjudeen Abdulgaffar Ya yi, tare da cewa "Shukran laka Yaa Sayyadi", ya faɗa yana mai fadada fuskarshi, sai dai ba murmushi bane akan fuskar. Dukan Kafadarshi yy, kafin su miƙe, yana dan mishu Jawabai , ga mai da shirye-shiryen, bayan gama maganganunsu, aka ƙara mishi Escort da motoci, Sannan aka bashi lafiyayyiyar mota, Kirar Campanyn Audi, tare da kyautar babban gida a kusa da Babban Masaalacin Makkah wanda bazai mishi wahalar zuwa ba daga Masallaci. godiya Sosai yawa Sarkin kafin ya wuce, direct ........ NA KUƊI NE, DUK MAI SO ZATA IYA MIN MGN SAI NA TURA MATA ACCOUNT DETAILS. 07033371851 IN KIN SAN BAKI SHIRYA SIYA BA PLS KAR KI MIN MGN MU BATA LOKACINMU. DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR. RUWA NE KAWAI YAKE MAGANIN ƘISHI🤙🏾 [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *P.7* Godiya yy sosai, kafin ya wuce tulin Escort dinshi na binshi a baya,kafin ma ya ƙarasa gurin Moto din shi an buɗe mishi mota, yana zuwa ya shiga da Bissimillah, rufewa aka yi, kafin suma duk suka shige motocin da suke bayan tashi da gaban tashi, a hankali suka fara tafiya cikin ƙwarewa. Asalin gidanshi da yake babbar Anguwar Shara-Mansir da take cikin Makkah suka wuce da shi, idanunshi na lumshe har suka ƙarasa tafkeken gidanshi da yake cikin Anguwar, gida ne babba na gani na faɗa,gaba daya gidajen da suke kewayen Anguwar gidan shine the number 1, z gurin kyau da tsari, har da wasu akwakun fitilu , masu kyau sai kaloli suke badawa. Sun danno kai gurin gidan gaba daya get din gidan mai kyau da tsari ya yaye yy sama, cikin natsuwa suka sulala da motocin cikin gidan , sun dan yi tafiya mai dan nisa kafin su iso Asalin cikin gidan wanda shima take dauke da wani get din, hon suka yi , wanda yasa da sauri Get man din gidan ya rugo ya bude musu get din. sulalawa suka yi ciki, suna shiga wani babban parking alot mai kyau da tsari wanda yake cike da motoci masu kyau kala-kala ya bayyana, gaba daya motocin a wajen parking alot din suka tsaya motar Yaa Shehi ce kawai ta samu guri cikin parking alot din. bayan Driver ya dai-daita parking a cikin parking alot din, aka bude mishi mota, a gajiye yake sosai, hakan yasa bai ɓata lokaci ba gurin fitowa daga mota, A hankali ya fito yana baza Alƙyabar jikinshi, cike da tsantsar gajiya yake dan lumshe gajiyayyayun idanunshi, tare da fesar da sanyayyiyar iska,haka har ya zo daf da ƙofar shiga cikin palon part din. tsayawa yy na yan mintuna, sai da ya ji takun Driver din shi kafin ya juyo, tattausan hannunshi ya miƙa mishi, brief case din shi ya miƙa mishi, karba yy kafin yace "Jazakhallahu bi khair..!", yana fadar haka ya juya ya shiga ciki. chan ciki yy sallama cikin muryarshi sanyayyayiya mai dauke da zallar gajiyawa, "Wa'ailaika Salama..!", wata Babbar Mace da zata iya kai wa 29 years ta furta cikin sanyin hali, idanunshi ya sauke akan fuskarta mai dauke da murmushi, ta gefenta ya wuce yana sauke numfashi, bata yi mgn ba har ya haye Upstairs. A hankali ta miƙe, kitchen ta nufa, bata jima ba ta fito da madaidaicin flask , da Ƙananan Cups sai kwalin Sugar da Tea spoon, saman ta haye, ƙofar farko ta kwanlwasa tare da tura ƙofar , haɗaɗɗen palo mai kyau da tsari ya bayyana, sanyayyan kamshi tare da sanyi ACn cikin palon ne ya haɗu ya gauraye Palon tare da bada wani ni'imtaccen kamshi mai sanyaya zuciya, tare da sanya natsuwa. kan daya daga cikin royal chair din palon ta zauna, tare da jaawo Center table ta daura tray mai dauke da flask da cups, jiranshi ta shiga yi, ganin an share 1 hour, bai fito ba yasa ta miƙe ta fita, tana fita ba da jimawa ba, ya turo ƙofar bedroom din ya fito, yana ta baza kamshi, yana sanye da Jallabiya fara tass da wando, kanshi yana luluɓe da hirami red da ɗigon fari, hannunshi zube cikin Aljihun Jallabiyar , sai zuba kamshi turaren huge boss yake, fuskarshi na fitar da wani Annuri da haske mai daukar hankali , yy wani fitinannen kyau , yana tafiya kanshi a ƙasa, yana tasbhi da baya rabuwa da bakinshi. zama yy kan kujera yana fesar da numfashi, jinginar da kanshi yy , tare da zame lips dinshi na kasa ya zamana yana cikin bikinshi, a hankali ya fara tsotsa cikin wani salo na musamman, wanda za'a kiranshi da Sexy moment , shi kuwa zallar gajiya da yunwa ce ta sanyashi yin hakan, dan rabonshi da abin ci, tun jiya war haka. Wayarshu ƙirar Iphone 13 pro, ya dauka a hankalin tare da daddana number, ring daya biyu a na ukku ta dauka cike da natsuwa tace "Assalamu alaika..!", "Wa'alaiki salam..!, Yunwa", ya furta da daddare. Yana ajiye wayar ta shigo sanye da hijab dark Blue , ta ziro siraran hannunwanta ta cikin hannun hijabin, fara ce sosai, sai dai tana da dan jiki ba laifi a shekaru ba zata gaza 16 years ba, colour ba Hijab din shi ya fidda Asalin kyan fuskarta, zagayayiyyar fuskarta ta fito rass ta cikin dan wuyan hijab din, tana tafe tana fitar da kamshin humra mai masifar kamshi. Sallama tayi,chan ciki ya amsa mata ba tare da ya bude idonshi ba, tana ƙarasowa tsakiyar palon ta cire zunbuleliyar hijab din jikinta, ta ajiye akan kujera 1 sitter, kyakyawar surar jikinta mai kyau da tsari da ta gama haɗewa cikin ɗamammum kayanta, masu kyau. sanye take da riga fara body hug , sai black din wando skin tight ya bala'in dameta shima iya cinya. gaba daya surar jikinta da ta kasance coca-cola a bayyane, jikinta sai glowing yake. ƙarasawa tayi kusa da shi, tare da dan zama ta shige jikinshu, a hankali ta furta"Shehi..!", idanunshi ya dan matse a hankali ta daura yatsun hannunta da suka sha jaan lalle akan fuskarshi tana bin sajenshi da yatsunta, tare da jaa mishi gemunshi. kyakyawan murmushi ya sakar mata tare da riƙe hannun yy kissing nashi . yana bude idanunshi akam hannun, idanunshi ƙirrr akan yatsun na wasu mintuna, yana kallon jaan lallen da yy masifar yiwa hannun kyau sai sheƙi da ƙyalli yake, turo bakinta ta dan yi, tare da gyara zamanta sosai, gaba daya rabin jikinta ya zamana yana nashi, ta daura kanta akan kirjinshi, tana dan shagwaɓe mishi. "Waya miki..?", ta tsinci maganarshi a sama, "Ayyana..!", ta fada kanta tsaye, bai ƙara cewa da ita komai ba sai sakin hannun nata da yy yana gyara mata hular kanta mai gashi, wadda take kamar ta sanyi. zamowa yy da ita , tare da zama akan carpet, miƙewa tayi ta dawo gabanshi, tare da fara warware cups din da Ayyana ta haɗe gurin daya, daya ta ajiye, tare da bude flask , ta fara tsiyayo coffee sai tiriri yake, sai da tayi rafin cup din kafin ta barshi haka, sugar ta dauka kwara ukku ta zuba, tare da jujjuyawa. sai da ta gama ta kalleshi, shima ita ya kalla, sai ta kyarkyace da dariya, taɓe bakinshi yy bai ce mata komai ba, sai jawowa da yy shima ya fara haɗawa, sugar daya tal kawai ya sanya ciki tare da jujjuyawa, a hankali yy Bissimillah tare da fara skipping coffee . tana gefenshi tana shan nata itama kafin ya gama sha tuni zufa ta wanke mishi fuskarshi, handkerchief ta dauka tare da fara goge mishi goshinshu, da yake fitar da zufa, sai da ya shanye tas kafin ya saki sanyayiyyar gyatsa, Hamdallah yy lokacin da ya tabbatar da cewar cikinshi ya cika . Sannu ta mishi, gyara zamanshi yy a inda yake zaune, kanta ta daura akan kafadarshi tace "Boɗɗi am ba zamu je gurin Affa ba ?", ta fada tana wasa da gashin kanshi, da yake har bayanshi, shiru ya mata , jaan gemunshi tayi, wanda hakan yasa ya lumshe idonshi, tare ƙara buɗesu sa boda zafin jaaan da ta mishi. Miƙewa yy, yana mikewa itama ta mike, da sauri ta nufi bedroom dinshi, bata tsaya ko ina ba sai gaban wardrobe dinshi, budewa tayi tare da zaɓo mishi wata baƙar Alƙyabba mai torch milk , fitowa tayi da ita a hannunta, tana zuwa ta rataya mishi, tana kallonshi, ƙarasa sawa yy , yana sauke numfashi bb karya ya gaji, amma idan bai wa wannan Yar rigimar tashi abun ya take so ba, baza ta bar shi kwanciyar hankali ba. trayn ta dauka , sai da suka zo in da hijab ɗinta take, ta dauka ta sanya suka fito, a kitchen din sama ta ajiye kayan suka fito, suna fitowa suka tarar da Zayn - Maleeq , tsaye da alama shigowarshi kenan, "na rigaka ai", ta fada tana dariya, tana ƙarasowa gurinshi suka yi shaking hands, shiru Yaa Shehi yy yana kallonsu, kafin cikin faɗa yace "ban hana ku wannan ɗabi'ar ba..?", ya fads cikin kakkausar murya, shiru duk suka yi, "uhmmm ya fada tana wucewa , da sauri ta bi bayanshi suka fita yana baza Alƙyabbar jikinshi. suna zuwa aka bude musu mota suka shiga, sai da aka fara tafiya, kafin ta zame daga in da take zaune ta koma kan jikinshi ta zauna, sai da suka dan yi nisa da gida yace ,"Ɗabi'ar banza ko.?, sau nawa ina miki gargaɗi akan hakan.? shi bake tuna cewar ke matar aure ce.? in ƙara ganin hakan zaki ga hukuncin da zan miki.", ya fada fuskar a kamile, "ba zamu ƙara ba, kuma gaskiya ni ba Matar Aure bace," ta fads cikin rigima. yana kallon bakinta yace "wace ke..?", tura bakinta tayi kafin tace "Yarinya mana, sai na girma zan aure", ta fads cikin zallar Yarinta, "Allahu yahdiki",da sauri tace "Ameeen", tare da lafewa akan jikinshi tayi shiru, har suka ƙaraso. ROYAL INTERNATION HOSPITAL da yake cikin garin Makkah bata ƙata cewa komai ba, dan hannunta ma na baki tana tsotsa, tuni na tuna da Munkhair dan kusan, Attitude dinsu iri daya ne. har mannewar konai kala daya, suna tsayawa ya zareta a jikinshi, tare da dan matsawa, ana buɗe mishi ya fito, cikin kamala da cikar zato, itama zagayawa akayi aka bude mata ta fito . Zagayawa tayi gurinshi, suka fara tafiya a tare,bayan ta gyara hijab dinta, ta rufe idanunta da niƙaf din jikin hijab din, idanuwanta kawai akr iya hangowa,haka suka shiga cikin Asibitin. bayan shigarsu cikin Reception din Asibitin suka nufi wani sashe na daban , sun dan yi tafiya , ƙafin su ƙaraso wani haɗaɗɗen sashe mai kyau, ƙofar Room 2, suka tura suka shiga bakinsu dauke da Sallama, Ayyana da bata jima da zuwa bace ta Amsa musu Sallama tasu, ƙarasa shiga suka yi cikin room din mai kama da gida , dan palo da bedroom ne , Zama Halimatu tayi kusa da ita tana mata magana, Yaa Shehi kuwa ciki ya wuce Abinshu ba tare da ya ko zauna anan din ba. duk da yasan ko yy Sallamar bb wsnda zai Amsa mishi amma haka yy Sallamar, tare da shiga ciki, bed din ya nufa, tare da raɓawa gefe ya zauna, wani kyakyawan Tsohon mutum dan ba'a ƙirashu da matashi ba dan zai haura 70years na kwanxe akan bed din, fari ne sosai wanda kalli daya zaka mishi kawa Yaa Shehi kasan suna da dangantaka ya jini sosai. ko dai Mahaifinshi ko kuma Yayanshi dan kamarsu har ta ɓaci, sai dai yana kwance ne , yadda kasan butun butumi, baya motsi, ban da idanunshi farare tar da suke jujjuyawa bb wata jijiya ta cikinshi da take harbawa, riƙe hannunshi Yaa Shehi yy, tare da mishi magana a hankali, duk da baya iya mgn Amma fuskarshi ta fallasa Asirin jin dadin ganin Yaaa Shehi da yy, dan sosai fuskar ta washe duk da va murmushi bane kan fuskar, kuma ya kafe guri daya da ido. Ayyana da Haleematou ne suka shigo cikin bedroom din, Yaa Shehi ne ya kalli Ayyana , cikin girmama Yayar tashu yace "Zaytun", ya fada ya a rike hannun Affa, matsawa tayi kusa da Drawer din da kaya yakw jere, ta dauko kwalbar Zaytun ta miƙa mishi, ƙarɓa yy tare da budewa ya tsiyaya, ya fara shafa mishi a hannunshi da yake tubus bb gautsi bb komai . kamar bayan kifi tsabar sulbi, na dauka hannun ne kawai, sai da naga har ƙafafunshi da yana shafa mishi haka yake taushi tuɓus, sai yanzun na gane dadewa ne a guri daya zaune, da tsabar gyaran da yake samu. sai 10pm suka shirya wucewa, suna fitows su Zayn na zuwa dan sune suke kula da mahaifin nasu da daddare, har za suyi shaking hands shi da Haleematou sai kuma suka tuna da gargadin Yaa Shehi suna juyawa suka ga ya tsaresu da ido kuwa...... Kar ku manta wannan Book din na kuɗi ne, duk wanda yake so zai biya domin ya sha karatu. 07033371851 Don Allah duk wanda yasan ba siya zai yi ba kar ya min mgn, domin kar ma mu ɓata lokacinmu a banza please. DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *P.8* Tsaki yy A hankali dan ya lura Ɗabi'ar ta hi jikinsu, sai ya ci mutuncinsu zasu daina , sum-sum ta dawo bayanshi ta tsaya, wani kallo ya makawa Zayn-maleeq kafin ya wuce, shi kuwa sosa kanshi yy dan yasan shirun na Yaaa Shehi mai yake nufi. har suka Fito reception , tana maƙale a bayanshi tana binshi a baya, gefen hijab dinta a hannunta tana tafiya tana wasa da shi. kai ka rantse yar 8 years ce , tsabar shiriritar ta, da wauta, wani ɓangarwn suka ƙara nufa, ita dai tana bayanshi, har suka isa wani ɓangare sak shigen na su Affa dan dai wannan word din Yara ne. Wani Ɗaki ya tura ya shiga da Sallama a bakinshu,kamar yarda yy itama haka tayi da Sallamatar ta shiga ciki,bb kowa a ɗakin sai Yarinyar nan dai da take kwance akan bed, fuskaeta manne da Oxygen , babban yatsar hannunta an sa mata wani abu mai kama da kilif din matse shanya , hsnnunta daya na dauke da ledar drip . gaba daya jikinta an yane mata shi da mayafi, gashin kanta kuwa an mata cover dinshi da wata kalar hula sharara blue. har suka ƙarasa gurn gadon Haleematou bata ankare da Yarinyae da take kwance kan gadon ba, tsayawa tayi a gaban Yaa Shehi zata yi mgn, sai lokacin ne ta lura da Yarinyar da take kwance akan bed. kafe Yarinyar tayi da ido na wani lokaci kafin tace "Yaa Shehi.!", bai kalleta ba haka kuma bai Amsa mata maganar tata ba, matsawa tayi ta rike hannun Yarinyar daya, tace "Yarinya mai kyau, ina sonta.!" ta fada tana kallonta, ganin ko matsowa bata yi ba, yasa tace "Yaa Shehi bata motsi fa ?. ka ganta kamar wadda ta mutu, ko dai bata da rai ne ?" ta jera mishi tambayoyin a jere, rasa wadda zai Amsa mata yy, hakan yasa yy tsut da dan bakinshi, yana kallon yana yin fitar numfashin Yarinyar. basu jima a Ɗakin ba ya fice, ganin ya fita yasa itama da sauri ta bi bayanshi, har tana haɗawa da gudu-gudu, sai da ta cin masa kafin ta dai-daita tafiyarta, haka suka jera suna tafiya, har suka fito compound din Asibitin, inda jeren motocinsu suke, ganin motocin b wanda ta saba gani bane yasa tace "Shehi ina ka samu wannan motocin da yawa kuma ba naka bane.?", izuwa yanzu ya gama gajiya da tulin tambayoyinta da yasa fara sanya kanshi ciwo, cikin yana yin kama kai da kamala , yace "satosu nayi ", ya fada ba tare da ya ko kalli inda take ba. tsayaww tayi ta riƙe bakinta , ganin ya kusa shiga mota yasa ta kara kwasa da gudu zuwa gurinshi, bai fi sauran taku biyu zuwa ukku ta ƙarasa gareshi ba, zunbulelen hijab dinta ta harɗe mata ƙafarta, tayi gaba zata kifu, cikin jadadda Sunan Allah da ya kama bakinta tace "Innalillahi wa'inna'ilaihi ra'un..!", ta furta da karfi,kafin ta kifu ya riƙe hannunta tare da jawota jikinshi ta kifu akan kirjinshi, al-amarin da yasa tayi gajeruwar Ajiyar zuciya kenan, lamarin kuma da ya haddasawa Yaa Shehi wani yana yin na, a lokacin da sam bai shiryawa lamarin ba, dan lokacin da ta tashi sauka gcikin jikinshi sai ta sauka a bahagon yana yi, gaba daya ta zuba hannayenta kan waist sunshi tare da rungumowa very tight . zareta yy daga jikinshi ya fara yarfa mata ruwan faɗa cikin sanyayyiyar shi , wadda sam bb hayaniya a cikinta balle kuma fusata, "baƙya kula ko, ? bana hana ki gudu ba ? duk ranar da kika ƙara gudu har kika yi attempting faɗuwa bazan tarekii ba, sai dai ki faɗi ki karye", ya fada yana zareta daga jikinshi. tura baki tayi tana magana ciki, duk da yaji abun da take cewa amma bai kulata ba, sai da ya shiga mota ya zauna kafin ta shiga itama, bata fasa hayewa kan jikinshi ba, shi kuwa lumshe idonshi yy yana kiran sunan Allah, ya yin da gaba daya sassan jikinshu suke saku, wani baƙon Al-amari na mamaye gaba daya yana yinshi na Asali . zamar da ita yy daga jikinshi, ya matsa , yana kafeta da idanunshimasu firgitarwa, cuno mishi ƙaramin bakinta tayi, idanunta nayi narai-narai kamar wadda zata yi kuka, akan kafadarshi ta daura kanta. zame mata kanta ya yi, tare da matsar da ita dan nesa da shi, shiru ta yi dan tasan wannan alama ce da take nuna cewar fushi yake da ita. har suka ƙarasa gida bai ƙalli inda take ba, dama kuma shi ba mai yawan magana bane, hakan yasa bai ce Uffan ba, hasalima idanunshi na lumshe, bakinshi kuwa bai gushe da Ambaton Allah ba, wanda da dukan alamu jikinshi da haka ya gino har ya saba,shi yasa baya gushewa da hakan. suna zuwa suka tarar da Yaran Ayyana su ukku daya Namiji sai Twins dinra dukansu mata , Namijin bazai wuce 8 years ba, matan kuwa dukka ba zasi wuce 3 years ba, yana fitowa daga mota suka rugo dukkansu, suna cewa "Oyoyo Uncle M ", suka fada suna fadawa jikinshi, fuskarshu ce ta faɗaɗa, a hankali haɓarshi ta shiga dan motsawa alamar murmushi, sai dai bai bayyana akan fuskarshi ba, shafa kan Yaran ya yi,cike da tsantsar kaunarsu. A ranshi yake fatan Allah ya kare mishi su, ya Albarkacesu da tarin Albarkarsa, tambayoyi suka shiga jera mishi, kasantuwar sun kwana biyu basu ganshi ba, hakan yasa suke tambayar in da ya je, Haleematou ce ta matsa tare da riƙe hannuwansu tace "Uncle M ya gaji ku barshi ya shiga ciki ya huta" ta fada tana musu murmushi. Amatul-azez ce tace "Anuty Sadiyya ki goya ni." ta fada tana dira ƙafa irin na Shagwaɓaɓun Yara, Duƙawa tayi ta haye bayanta , girgiza kai Yaa Shehi yy dan yasan bata rabuwa da shiriritar Yaran, yana ji bayan wucewarshi Amatulrahman na cewa ta dauketa, haka ta goya daya ta dauki daya, tana nishi da komai haka take takawa da su zuwa cikin gidan. bata zauna a Downstairs ba sai tayi sama , palon Yaa Shehi ta tura ta shiga,baya palon hakan yasa ta tabbatar da yana bedroom, ajiye Yaran tayi ta kwanta kan carpet tayi ruf da ciki tana hutawa, idanunta na lumshe, dan mararta take mata ciwo, Amatul-azez ce ta dawo kan bayanta tace "Anuty ki min goyo - goyo." bb yarda ta iya miƙewa tayi da Amatul-azeez din a bayanta ta shiga zagaya palon da ita. Daga chan ciki yana jin ƙarar hayaniyarsu da dariyarsu, Addu'ar shiriya ya fara karanto musu cikin ranshi, dan suna buƙatar shiriya, bayan gama shirinshi yy duk abun da ya dace, ya gama. Amma har lokacin da hayaniyarsu cikin palon , Agogon da take manne da Bedside drowar ya kalla, idanunshi ya dan fitar kadan cikin ɗunmin mamaki, ganin lokacin 1 saura. bedroom slippers dinshi masu taushi da tudu ya zura, tare da miƙewa ya fito palon, zaune ya tarar da Hakimar ta kunna musu MBC 3 suna kallon Cartoon sai kyarkyata dariya suke, suna maganganu a tsakaninsu, tsayawa yy kawai yana kallonsu, girgiza kai yy, tare da matsawa gurin kayan kallon, cable din TV ya zare, wanda hakan yasa da sauri suka kalleshi. shanyanyun idanunshi ya watsa musu kafin yace "in ce ko gobe bb School.?" ya fada yana tsaresu da idanunshi, Haleematou ce ta sosa kasan gashin kanta da ya zubo baƙi siɗik, girgiza kai yy kafin yace "Allah yasa nazo tashin mutum da Asuba na tarar bai farka ba yaga yarda zan yi da shi", ya fada yana shigewa, da sauri Amatul-azeez suka miƙe. dan sun san kashedin wa su aka bugawa, duk da Yara ne sosai, Amma an horesu da ibada, tare da karatu sosai, dan Sallah Asuba baya bari ta wucesu. kullum da Asuba sai ya tashe su,bayan gama Sallah su daura da karatun Al-qur'ani da sauran litattafan Addini, sai da safe sukawa Haleematou kafin su wucewarsu part dinsu. ta dan jima a gurin tana tunanin faɗan da Yaa Shehi zai mata, dan tasan tilas ne fadan nan sai ya mata shi, gashi ita a rayuwarta bb wanda take tsoro da fargaba irin ɓacin ranshi da faɗanshi,rashin samun madafarta yasa ta sauke nannauyan numfashi dan ta kasa samun wata gamsashiyar hujja, jiki a Saɓule ta nufi bedroom dinshi . ko da ta shiga kwance ta tarar da shi kan bed dinshi kamar mai barci, a Zahirin gaskiya kuwa idanunshi biyu, itama kuma tun shigowarta ta ga alamun hakan, to amma bb yarda ta iya, Wata Wardrober ta bude, towels ne kala-kala suka bayyana, fari, pink, baƙi, blue, green , kala kala, pink din da yake sama ta zame, tare da daukar ƙarami ta nufi bathroom, Ruwan wanka mai zafi ta tarar a haɗe da turaren wanka mai kamshi sosai, ga flowers a ciki, murmushi tayi dan tasan wannan aikin Yaa Shehi ne, madamar yana gari to ruwan wankanta a haɗe take zuwa ta sameshishigewa ciki tayi tana lumshe idanunta, ta jima sosai kafin ta fito, towel ta daura a jikinta kafin ta daura wani akanta. a hankali ta leƙo ta yar kafar key din ƙofar , numfashi ta sauke kafin ta fito, tana sanɗa ta ƙarasa gaban mirror, lotion din ta mai kamshi ta bude tare da fara murtsukawa jikinta bayan ta gama shafawa, ta shafa humra, turare ta mai matuƙar kamshi da daukar hankali, ga sanyin kamshi dauka ta fara fesawa, har sai da ta ji yana hawar mata kanta, kafin ta ajiye. A hankali ta fara takawa zuwa gurinshi, har ta ƙarasa gurin bed din, tana tafiya a hankali ba tare da ta bari wani sautin taku ya fita ba, a hankali ta ƙara kunneta gurin hancinshi, domin tabbatar da cewar barcin yake, kafin ta ankare sai ta ji tayi, ya sakar mata lamuntaccen cizo a kunnen wanda yasa tayi zillo . fisgota tayi ta faɗo jikinshi, bargo ya bude tare da sanyata ciki, ya haɗa hannayenshi ya rumtse , kallonshi tayi tana cuno baki...... 07033371851 DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *P.9* miƙewa tayi tare da fara yunƙurin guduwa, Kanshi ya fara jujjuyawa yana mai miƙa hannunsa ya kashe wutan ɗakin. A take duhun daren da ya tsala ya mamaye ɗakin gaba ɗaya. Cike da tsoro ta fara kiciniyar sauƙowa daga kan gadon. Tana sauƙowo, shi kuwa yana isa gab da ita, haka yasa bayanta ya manna da ƙirjinsa, da sauri yasa hannunsa duka biyu ya ruggume da ƙarfi jin yadda take mutsu-mutsun kwace kanta ne, yasa cikin cool voice dinshi yace "Sadiyyerh!", ya furta cikin sanyayyiyar murya mai nuna zallar fushi, wanda hakan ya tilasta mata zama kan kafarshu cike da fargaba. sakinta yy ya koma kan bed din ya kwanta, da kanta ta gangara gareshi, tare da shigewa cikin jikinshi ,a hankali tace "Afwan Yaa Zauj.!", ta furta a hankali, banza yy da ita, tasan halinshi, dama ba lallai he ya mata mgn ba , amma ita da wannan shirun nashi gwara ma in dukanta zai yi ya duketa, dan ta tsani shirunshi, hannunta ta sanya cikin tattausan gemunshi ta dan shafa, tare da sanya yatsunta biyu tana dan jaaa a hankali, cikin sigar shagwaɓa tace "ina fa Zauj bana son shirunka , na gwamma ce in ma duka na ne kayi . da kayi shiru", ta fada tana cuno baki gaba. banza ya kuma yi da ita, dan bai ma san ta in da zai fara ba, ace matar Malam gudu, Shehi, Alaramma, Sheikh amma tana abubuwan da basu dace ba, "don Allah..! " ta fada cikin marairaicewa. Ajiyar zuciya ya jaa tare da cewa "Uhmmm..!", "Uhuum uhummmm", ta fada tana tirza kafafu a jikinshi, zameta yy daga jikinshi ya juya mata baya, riƙe bakinta tayi kafin tace "Laaaa'ilah Abun ya ƙaura har haka, innalillahi don Allah Yaa Shehi ko faɗa kamin in ta kama da duka, Allah kuwa bazan iya fuskantar fushin nan naka ba, domin ban san mai yake nufi ba, fushinka a gareni babban bala'i ne, don Allah ka sauko " ta fada tana haɗa hannayenta tare da komawa dayan side din da ya mayar da fuskarshi. Numfashi ya ja kafin cikin harshen Fulatanci yaren da yasan zata fi fuskanta fiye da ko wame Yare a duniya, Yaren Uwa da Uba, yaren duk Ahlinta ya fara cewa " D'un wod'a gorko me ma debbo mo tegal nasti shaka ma66e e dow andal, bo d'un gotun e memuki don nanki beldun e bo memuki nontan. Sai dai to wodi larura nyawu, a d'on gorko wa wai mema debbo to wodi koltan a shaka, ko b'awo waduki god'd'un iri ba majun. Ko e d'un warti dole sai d'un wad'ama, ko ittiku d'er diyam, da dun watta gam non d'un mema 6andu ko d'un nyid'u ko dun nyid'a. Ko yidaki tinaki, to wala wakkati te fuki koltal koo d'un hendirta shaka bo to memuki kin warti na der shiri ko andal, ko majjuki heftiki dina, to wala god'd'un e dow do'o..... Gam non, har joni memuki bandu na dow jawu dun wod'a, d'un dole bo d'un tubana dun, sannan dun hotana jomirawo tagud'o tagu . (Haramun ne taɓa jikin juna a tsakanin mace da namijin da ba Muharraman juna ba bisa sani, kuma duk ɗaya ne taɓawar da nufin jin daɗi ne ko kuwa ba da wannan ƙudurin ne ba. Amman a cikin yanayin larura kamar Magani da Jiyya babu makawa sai ya zamo wannan taɓawar da tufafi a Tsakani, ko kuma bayan sanya safar hannu ta roba da ire-irenta, in banda a yanayin da yake keɓantacce idan ya kasance maganin ko jiyyar ko kuɓutar da wanda ya dulmiya a cikin ruwa ba zai taɓa yiwuwa baya tabbata ba sai an taba jikin kai tsaye, ko kuma ta lalurar gaggawa zuwa maganin ko kuɓutarwar ta fuskar gaggawa da rashin lokacin da za a sami safar hannun ta robar da ire-irenta nan kusa". Hakanan idan ya kasance taɓawar ba cikin shiri ne ba kuma ba cikin sani ba, ko kuma ya kasance bisa jahiltar hukuncin shari'a ne to babu komai a cikin hakan. Duk da haka dai ita taɓawar juna bisa sani ba bisa lalura ba Haramun ce, kuma wajibe ne yin istigfari daga aikatawa da yin Tuba zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki. cikin sanyin harshe ya kai karshen mgnr tashi, numfashi ya jaa dan ya manta rabon da yy mgn mai tsawo haka, ita kuwa shiru tayi tana saurararshi ,chan tace "Astagfiroullah wa atubu ilai..! ³ Astagfiroullah.!³", ta furta a hankali tana ƙara maƙaleshi, tare da sauke ajiyar zuciya mai sanyi , tana jin natsuwa na saukar mata cikin ruhi da gangar jikinta, tana Alfahari da samunshi a cikin rayuwarta dan a duk lokacin da ratuwarta zata shiga tangal² shi yake tarota.ya mayar da ita kan hanya mai-daiciya. "Jazaqallahu bil khair Yaa Zaujilkhair", ta fada tana hug nashi very tight har sai da ya dan yi nishi kafin ta sassauta riƙon da ta mishi, a hankali ya fara biya mata karatun Al-qur'ani mai girma cikim zazzaka sanyayyiya lallausar muryarshi, haka ya ringa mata karatun a kunnenta, har sai da ya ga barci ya dauketa , dan yasan a irin wannan lokacin har idan ba haka ya mata ba, to haka zata yi ta surutu har lokaci yazo ya ƙure bata yi barci ba. sai da ya tabbatar da yin nisan barcinta kafin ya zameta a jikinshi a hankali, sai da ya jaa mata blanket tare da sanya mata pillow a ganta ya runguma mata,kafin ta miƙe ya nufi bathroom,wanka ya yo kafin ya fito, da Jallabiyarshi Ash colour wadda tayi Asalin fito da kalar fatar jikinshi da take ta walƙiya , ya mannu a jikinshi ta lafe, sai hularshi wadda ta rufe mishi gaba daya kanshi, wanda hakan yy sanadiyar zubowar sumar kanshi da take ɗigar da ruwa, "Fa Tabaraqallahu Ahsanul khaliqin ", bb abun da za'ace da ya wuce wannan . duk in da ake neman cikakken namiji mai haiba da kamala, kwarjini da kasaita , mulki da dukiya, to duk ya wuce yanan, ilimi Allah ya bashi both Arabi da Boko, duƙiya yana da ita wadda har bai san iyakarta ba, ƙarewae mulki shine kanshi Sarkin gobe wanda mulkin Yau din ma yake karkashin ikonshi, shi dai bb abun da zai ce da Allah sai godiya, dan irinsu ne ake cewa 1 in world ma town ba. Lungun da kayan Ibadarshi suke ya nufa, yana zuwa ya dai-daita tsayuwarshi kan pray mat din gurin,tare da Kabbara Sallah, yy nafilfili kamar yarda ya saba, kafin ya fara karatun Al-qur'ani da Hailala tare da salati, a takaice dai haka ya gama raya wannan daren gangar jikinshi da ruhinshi basu samu wani hutu ba, sai bautar Allah da suka nitso a gurin yi,sai ƙarfe 4 saura kafin ya tashi daga gurin da yake, gurin da ake ijiye kayanshi ya nufa, bai wani jima ba ya fito sanye da Jallabiya sai kuma Babbar Alƙyabbarshi haƙa mai golden din zane , irin wadda yake yawan sawa, kafarshi sanye da takalmi Gucci baƙi da yy wa ƙafarshi gwanin kyau, kanshi na nannaɗe da hirami fari, sai siririn glasses din da ya sanyawa kyawawan idanunshi, wanda ya sanya ne sa boda ya tashu baya jin dadin idonshinshi sosai, yana jin kamar zai mishi kyau, amma ba ƙaramin kyau yy mishi ba dan sai ka rantse irin samarin nan ne yan 20 something, Al halin kuwa ya bawa 30 ma baya dan ya fara hararar 40, turarenshu na Huge Boss da ya zauna a jikinshi ya dauka tare da ƙara faffaseww yarda ba zai yi yawa ba, shi bai yi yawa ba shi bai yi kaɗan ba dai-dai misali, ya sanya, sai da ya gama shiryawa kafin ya kalli Haleematou da ta ƙara nannaɗewa cikin blanket sakamakon sanyin Subhi da ya fara busowa kamar za'ayi ruwan sama , dan da wasu ƙasashen ne da ake ruwan ƙanƙara to da ba makawa irin sanyin nan da ake zugawa da sun sa ran ko ruwan dusar kankarar za'ayi. matsawa gefen bed din yy , yasan idanunta biyu dan a irin wannan lokacin yasan rabi da kwatar mutanan gidan nan idanunsu biyu, sai dai Yara haka suma kuma kiran Sallar fari zasu mafarka. "tashi..!" yana fadar haka ya ficewarshi hankalinshi kwance bakinshi kuma na fitar da sautin Ambaton Allah, lokacin da zai fito gaba daya Driver din gidan da Escort idanunsu biyu, suna ganinshu suka fara gaisheshi, bai iya amsa musu ba sakamakon Abun da yake bakinshi, sai dai jinjina musu kai da yy , mota aka bude mishi da sauri, ganin lokaci na kurewa yasa ya shiga, A hankali Driver dinshi ya fara jaan motar , cike da kwarewa da sanin ya kamata....... tafiyar da suka yi ba zata wuce ta 5 minutes ba suka ƙaraso Harami, Kofar shiga ta gaba nan motar Shehi ta tsaya, bude mishi aka yi, a hankali ya fito yana raira karatun Al-qur'ani cikin zuciyarshi, shiga yy cikin masallacin , lokacin da zai shiga lokacin Sallah ya cika, bayan saqala Microphone din a jikin rigarshi ya fara ƙwala kiran Sallah, wanda yasa Haleematou tashi zumbur dan, bayan fitarshi wani barci mai masifar dadi ta fara jin ya dauketa, Umma Jakadiya ma da ba barci take ba ta miƙe ta zauna, haka Ayyana da dukan sauran yan cikin gidan, ba cikin gidan kawai ba duka yan cikin garin in da sautin muryarshi zata iya ratsawa,cikin gaggawa maza har ma da wasu matan ƙwala kiran Sallah, wanda yasa Haleematou tashi zumbur dan, bayan fitarshi wani barci mai masifar dadi ta fara jin ya dauketa, Umma Jakadiya ma da ba barci take ba ta miƙe ta zauna, haka Ayyana da dukan sauran yan cikin gidan, ba cikin gidan kawai ba duka yan cikin garin in da sautin muryarshi zata iya ratsawa,cikin gaggawa maza har ma da wasu mataan,cikin natsuwa da kamala tare da tattausan harshe da karyashi yake rero karatun Al-qur'ani mai girma cikim bawa ko wane harafi haƙƙinsa. gaba daya zuciyoyin masu sauraranshi sun tsumu, sun shiga bege da shauƙin karatun nasa, domin muryarshi na da taushi da dadi ga wani sarewa da yake cikinta, ba zaka karaa jin dadin muryar tashi ba sai ma ka ji yana rairo karatun Al-qur'ani kai girma, anan zaka ƙara sanin cewar Ehhh lallai Allah yy baiwa anan. bayan idar da Sallah ne , ya fara gabatar da Tafsiri da hatahohi , sai misalin 6am, yy Sallama zai miƙe wani daga cikin Ɗakibzn gurin ne yace "Yaaah Shehi muna son ka kara mana gayani game da rabon gado , tare da cij duƙiyar marayu ma baki daya",shiru yy yana jin yarda lokaci daya mutumin ya ɓaro mishi gaggatumin jawabi mai girma, wanda baknshi sai ya kusa ciwo a kanshi, Amma zai taƙaice kusu bayanin kawai. ```NIMA ANAN NIKE CEWA BARI NA TAƘAICE MUKU KAWAI , SAI ZUWA GOBE IN SHA ALLAH``` ```GAMAI BUKATAR BOOK DIN NAN ZAI BIYA KUƊI SAI NA SANYASHI CIKIN GROUP DIN DA ZAI RIGA SAMU KULLUM BAYAN GAMA FREE PAGES IN SHA ALLAHU ``` 07033371851 ```WANDA ZASU SIYA KAWAI DON ALLAH, IN KIN SAN BA ZAKI SIYA BA TO KAR KIYI MGN PLEASE``` DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Second to the Last Free page *P.10* Gyara zaman Alƙyabbar jikinshi yy, tare da fesar da numfashu cikin lankwasa harshe , ya fara cewa "Abinda muke son fitarwa cikin karatunmu na yau game da al'amarin rabon gado a muslunci shine mu qara nunawa mutane masu hada Uwa da 'yan'uwa cikin gado cewa babban kuskure ne, domin matuqar akwai Uwa ko 'ya, to, 'yan'uwa ba su da kason komai cikin abinda dan'uwansu ya bari, sai dai suna yiwa Uwa babbar illa wacce ke hana mata cin kaso daya bisa uku (1/3) na danta, ta koma cin kaso daya bisa shida (1/6) na daga abinda dan nata ko 'yarta ta bari. Bari dai mu kawo aqalla misalai uku cikin mas'alar mutuwar Ɗa ya bar magada tare da abinda za su gadan, domin idan ya zama babu abinda ya bari to, babu abinda zasu gada kenan. Abinda aka bari na daga cikin sharadin gado. تفسير القمي‏ يُوصِيكُمُ اللَّهُ فِي أَوْلادِكُمْ لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏ قَالَ إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ تَرَكَ بَنِينَ وَ بَنَاتٍ- فَلِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏- فَإِنْ كُنَّ نِساءً فَوْقَ اثْنَتَيْنِ فَلَهُنَّ ثُلُثا ما تَرَكَ‏ يَعْنِي إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ تَرَكَ أَبَوَيْنِ وَ ابْنَتَيْنِ فَلِلْأَبَوَيْنِ السُّدُسَانِ وَ لِلِابْنَتَيْنِ الثُّلُثَانِ وَ إِنْ كَانَتِ الِابْنَةُ وَاحِدَةً فَلَهَا النِّصْفُ وَ لِأَبَوَيْهِ لِكُلِ‏ وَاحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ وَ بَقِيَ سَهْمٌ يُقْسَمُ عَلَى خَمْسَةِ أَسْهُمٍ فَمَا أَصَابَ ثَلَاثَةَ أَسْهُمٍ فَلِلِابْنَةِ وَ مَا أَصَابَ اثْنَتَيْنِ فَلِلْأَبَوَيْنِ فَإِنْ كَانَ لِلْمَيِّتِ إِخْوَةٌ وَ أَخَوَاتٌ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَ الْأُمِّ أَوْ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَحْدَهُ فَلِأُمِّهِ السُّدُسُ وَ لِلْأَبِ خَمْسَةُ أَسْدَاسٍ فَإِنَّ الْإِخْوَةَ وَ الْأَخَوَاتِ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ هُمْ فِي عِيَالِ الْأَبِ وَ تَلْزَمُهُ مَئُونَتُهُمْ فَهُمْ يَحْجُبُونَ الْأُمَّ عَنِ الثُّلُثِ وَ لَا يَرِثُونَ‏. Ya zo cikin Tafsir na Qummy (R. A) game da inda Allah (T) ke cewa : " ALLAH NA YI MUKU WASIYYAH CIKIN 'YA'YANKU, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA 'YA MACE. " yace : " Idan mutum ya rasu yabar 'ya'ya maza da 'ya'ya mata, to, namiji na da kaso biyu na 'ya mace. " IDAN KUMA 'YA'YA MATAN SUN FI BIYU, TO, SUNA DA BIYU BISA UKU (2/3) NA DAGA ABINDA AKA BARI. " Abin nufi shine idan ya rasu ya bar mahaifa biyu (Uwa da Uba) da 'ya'ya mata biyu, to, iyayen na da biyu bisa shida (wato kowanne daga cikinsu na da daya bisa shida kenan), su kuma 'ya'ya matan na da biyu bisa uku (2/3). Idan kuma ya kasance 'ya daya (1) to, tana da rabi 1/2, kowanne daga cikin mahaifan na da daya bisa shida (1/6), abinda ya rage (bayan kason) sai a kasa shi gida biyar, abinda aka samo kaso uku na 'ya ne, abinda aka samu na kaso biyun na iyaye ne. Idan ya zama ga mamaci yana da 'yan'uwa maza da 'yan'uwa mata ta bangaren Uwa da Uba ko kuma ta bangaren Uba kadai, to, Uwa na da daya bisa shida (1/6), Uba kuma na da biyar bisa shida (5/6). Domin su 'yan'uwa maza da mata ta fuskar Uba suna cikin iyalan Uba, dawainiyarsu ta hau kansa. Su suna tsare Uwa daga (samun) daya bisa uku (1/3), amma ba za suyi gado ba. " تفسير عليّ بن إبراهيم ج 1 ص 132- 133. Ga misalan nan biye kamar haka : (1)- Mutum ne ya rasu ya bar Uwa da Uba da kuma 'ya'ya mata 2 tare da dukiya #1,200,000. YADDA KASON ZAI KASANCE Uwa Uba 'Ya'ya 1 1 2 -------- ------ --------- 6 6 3 1 + 1 + 4 = 6 ---------------------------- 6 KASON UWA 1 #1,200,000 ----- * -------------=#200,000 6 1 KASON UBA 1 #1,200,000 ---- * -------------=#200,000 6 1 KASON 'YA'YA MATA 4 #1200,000 ----- * -------------=#800,000 6 1 Idan muka hada jimlar za muga #1,200,000 ta fito, shi wannan kaso na 'ya'ya sai a kasa musu daidai-wa-daida, wato kowacce za ta sami #400,000 kenan. (2)- Mutum ne ya rasu ya bar Uwa da Uba da kuma 'ya guda daya (1) tare da dukiya #2,000,000. YADDA KASON ZAI KASANCE Uwa Uba 'Ya 1 1 1 ------ ------- ------- 6 6 2 1 + 1 + 3=5 --------------------------- 6 KASON UWA 1 #2,000,000 ---- * --------------=#333,333 6 1 KASON UBA 1 #2,000,000 ---- * ---------------=#333,333 6 1 KASON 'YA 3 #2,000,000 ---- * ------------=#1,000,000 6 1 Idan muka hada jimlar abinda aka raba za muga an raba #1,666,666, abinda ya saura a qasa bayan kaso shine #333,334. To, wannan sauran shine aka ce a raba shi kaso biyar, abinda aka samu na kaso uku sai a bawa 'yar, sauran kaso biyun kuma sai a bawa Iyayen, wato kowanne daga cikin mahaifa zai sami qarin #66,666 kenan, sai ya zama kowa ya tashi da #399,999 kenan, ita 'ya kuma ta sami qarin #200,000, sai ya zama ta tashi da #1,200,000. Idan muka tara jimlar zai zama: #1,200,000 +# 399,999 # 399,999 --------------------- #1,999,998 Abinda ya rage shine #2, wacce ba za ta rabu ba. Saboda haka maimakon ayi wahala biyu bayan anyi kaso na farko azo ana qara kasa sauran abinda yayi saura sai a kasa shi kawai kashi kashi biyar, a bawa 'ya kaso uku, iyayen kuma kowa a bashi shi kaso daya daga cikin biyar din. Ga shi kamar haka : KASON UWA 1 #2,000,000 ---- * --------------=#400,000 5 1 KASON UBA 1 #2,000,000 ----- * --------------=#400,000 5 1 KASON 'YA 3 #2,000,000 ---- * -------------=#1,200,000 5 1 Idan muka tara wadannan kaso za mu sami jimla kamar haka : #1,200,000 # 400,000 # 400,000 -------------------- #2,000,000 -------------------- -------------------- (3)- Mutum ne ya rasu ya bar Uwa, Uba da kuma 'yan'uwa maza da mata tare da dukiya #900,000. YADDA KASON NASU ZAI KASANCE Uwa Uba 'Yan'uwa 1 5 --------- ----- ------ 6 6 1 + 5=6 ------------------- 6 KASON UWA 1 #900,000 ---- * -----------=#150,000 6 1 KASON UBA 5 #900,000 ----- * -------------=#750 000 6 1 'YAN'UWA Su 'yan'uwa ba su da komai duk da cewa samuwarsu ya yiwa Uwa illa, domin illar kawai suka iya amma ba su da wani abu cikin kaso, domin matuqar akwai Uwa ko Uba ko kuma daya daga cikin 'ya'ya ba za suyi gado ba. Idan muka tara jimlar kason Uwa da Uba za mu sami jimla kamar haka : #150,000 +#750,000 ----------------- #900,000 ----------------- Shi kenan kaso ya fita", ya fada yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, wanda yasa gaba dayansu suka ƙara natsuwa, cikin zallar gajiya, idanunshi akan Agogon da take daure A tsintsiyar hannunshi, tace "Idan Allah ya kai mu gobe zamu daura akan Cin Dukiyar Marayu", ya fada sautinshu chan ciki, godiya suka mishi tare da ficewarsu , sai da aka samu saukin hayaniya kafin ya bude idanunshi da ya rufe, a hankali ya ƙara tattara Alƙyabbar jikinshi ya miƙe,cikin gajiyawa yake taka ƙafarshi har ya fito inda motocinshi suke, har zai shiga ya dan tsaya, yana kallon gefe in da Yaga rabi da kwatar Limaman Massalacin sun tsaya. jim yy kafin ya nufi in da suke, ganin cikin gayyar har da su Sarki, yana zuwa ya mimmiƙa musu hannu suka yi musabaha, "Yawwa Shehi game da batun ganih Wata muna sa ran Yau In sha Allahu a ganshi, dan haka za'a fito dubanshi da misalin karfe 3pm "', jinjina kai Yaa Shehi yy kafin ya musu sai An jima ya wuce, halinshi wanda da yawansu suka tsana, wanda basu san nature dinshi ne haka ba, bashu da hayaniya baya sonta kuma, Amma su kallon mai girman kai suke mishi. A hankali ya shiga takawa daga parking Space zuwa cikin gidan, yana tafiya yana sauke sanyayyayen numfashi, idanunshi masu dauke da gajiya yake lumshewa a hankali , yana budewa, cikin kamilalliyar muryarsa yy sallama cikin palon gidan, Hayaniyyar Surutunsu Amatul-azeez da Amaturrahman da Haleematou ya jiyo cikin kitchen, sai kaya kayya suke, Umma Jakadiya na ta faman magana, Amma sun ƙi suyi shiru, daya daga cikin kujerun palon ya zauna, tare da ɗago Tsintsiyar hannunshi, 7:30am ya gani, lafiyayyen numfashu mai cike da zallar gajiya ya sauke. A hankali cikin natsuwa , ya furta "Amah.! Amah!!", ya fada yana lumshe ido, a hankali hayaniyarsu ta fars yin ƙasa, kafin daga bisani Haleematou ta fito , tana sanye da riga da wando da suka ɗameta, rigae iya cibi fara sai wandon bakita yane kanta da bakin siririn mayafi, idanunshi da ya lumshe ya bude, gently cikin natsuwarshu da kamala ya miƙe yy sama, da sassarfa ta bi bayanshi da tray din coffeen da cups a sama. ko da ta shiga nan ma a zaune ta sameshi kan kujera, bakinshi na Ambaton sunan Allah, da sauri ta ƙarasa tare da jaan center table gabanshi ta ajiye tray din , tsugunnawa tayi gabanshi tace "Sabahul khhair Yaaa Zauj!, ta fada idanunta na kan haɗa mishi coffeen da take cike da kwarewa, shi kuwa fuskarta ya tsurawa ido, ƙasa ya ringa yi da idanunshi har ya sauka akan kirjinta da suka cika masha Allah, lumshe idanunshi yy, yana jin wani chanji na daban wanda a iya tsawon rayuwarshi ya manta rabon da ya ji irin wannan chanji a jikinshi, wanda da har yake tunanin koma bashi da lafiya, "Zauj.!" , ta dawo dashi daga tunanin da yake, miƙa mishi cup din tayi, A hankali ya karɓa, hakan yasa ta miƙe, hips dinta da suke kamar zasu faso wandon jikinta su fito ya tsuraww ido, yana mamakin girman da Sadiyyerh tayi lokaci daya, ta cika ta ko ina, iskar da ya shaƙa ya fesar cikin wani yana yi, kallonta yy ganin tana shirin juyawa, "Yaa Subhanallah" ya furta lokacin da yy Arba da Mazaunanta da suke so masha Allah kawai, tuni zuciyarshi ta Ayyana mishi wani saƙo. har ta juya yace "Sadiyyerh!." a hankali ta juyo tace "Zauj..!", har cikin ranshi yake jin sunan in ta faɗa dan tayi mugun iya sarrafa harshenta ta lankwasashi ta yarda in ta faɗi magana zata jaa hankali, "Zo!" ya furta ba tare da ya kalli fuskarta ba, a hankali ta tako zuww gareshu, jikinshi ta fara ƙoƙarin shigewa , ganin hakan yasa ya bubbuga gefenshi da hannunshi, gane abun da yake nufi yasa ta zauna a gefenshi, tare da daura kanta a kafaɗarsa, hannunta cikin gemunshi tace "Zauj Azumi gobe ko ?", ba tare da ya kallets ba yace "In sha Allah !", idanunta akan yatsun hannunshi da suke zara-zara farare tass suna dauke da kyawawan kumba, ga wani siririn duhu da ya zagayesu wanda ya ƙara ƙawata hannun, kumbarshu fatt , sai sheki take. hannunshi yasa ya shafi wuyanta har zuwa gurin kirjinta, zabura tayi tare da kankame hannun, dan danan jikinta ya dauki rawa, kamar wadda aka haɗawa Electric current , idannunshi akan yatsunta, yace "me.?", cikin fisgo maganar daga ƙasan maƙoshi ta ce "Allah hannunka Current", kallonta ya danyi , ido cikin ido suka kalli juna, da sauri ta dauke idanubta tare da yin ƙasa da su, dan ba zata iya jurar kallon cikin idanunshi ba, shi kuwa abun da ya gani cikin idanunta ya sanyashi sauke ajiyar zuciya mai karfi , yana da ɗumbin ilimi sosai, ciki kuwa har da Ilimin nazartar halayen Dan Adam da ɗabi'unsu har ma da wasu sassan nasu, shi yasa cikin abin da ba zai wuce second biyu zuwa ukku ba ya gama fuskantar yana yinta, har ma da zubinta. kafadarta ya rungume tare da lumshe idonshi, chan ciki tace "Zauj Coffee ", ta furta cikin sanyi da kasalar da suka risketa cikin lokaci ƙanƙani, matsawa tayi daga jikinshi, ta miƙa mishi tea din, a gurin karɓa hannunsu ya goge juna, da sauri ta saki, cikin zafin nama ya damki cup din, idanunta da suka fara chanja kala cikimsu yy jaa-jaa ga hawaye kwance ciki ya kalla, da sauri ta dauke idanunta , dan yau din in ya kalli cikin idanunta wani abu take ji cikin jikinta. gefenshi ta koma ta kankame jikinta kamar mai tsoron a taɓata, wannan sauyin nata a yau ya matuƙar bashi mamaki, abun da ya gani cikin idanunta ya matuƙar gigitashi, bai taɓa tunanin har haka ba, bata taɓa abu makamancin haka ba. duk ya yarda take duduma akan jikinshi amma bata taba haka ba, ko yanzu girma ya fara kamata, da buƙatar mijinta?. shin akanshi kawai abun yake faruwa ko kuwa hae ma akan kowa, ya zama dole kuwa ya mata hijabi da sauran maza , kuma dole ya tabbatar da ita a matsayin katangarsa,wadda zai ringa raɓa a duk sanda yake da bukatar hakan, a hankali ya fara shan coffeen yana kallonta har ya ƙarasa shanyewa tas, ƙafarta da gashi suka mimmiƙe ya tsurawa ido yana kallon yarda matsirar gashin tayi burɗum-burɗum. Alƙyabbar jikinshi ya cire tare da yafa mata a jikinta dan yama fuskanci sanyi take ji, shigewa bedroom dinshi yy domin ya dan kwanta ya huta, yana shiga ya wuce bathroom sai da yy wanka kafin ya shirya ya fito, cikin Jallabiyarshi, bed ya nufa direct yana zuwa ya haye tare da jaaan blanket ya rufe jikinshi, idanunshu a lumshe har ya gama Addu'a kafin ya fara kiran sunnan Allah, dan-dan barci ya daukesa, barci mai dadi..... iya kuwa cikin wasu yan mintuna gaba daya jikinta ya gauraye da zafin zazzaɓi zafi sosai , jikinta na ta rawa, tuni ta ƙara ƙudundunewa cikin Alƙyabbar da ya bata, sai guraren 12 pm kafin zazzaɓin ta zamu ya dan barta har barci ya dan dauketa, amma duk da haka da zafin zazzaɓin a jikinta. 12:30pm ƙamshin turaren Huge Boss ya karaɗe gaba daya palon har ma da kewayen palon, yarda kamshi yake ƙara shiga hancinka ne kawai zai ƙara jadadda maka cewar mamalakinshi yana kusa ko kuma yana doso gurin, takun takalminshi yasa na dagon da kai na, kamar kullum yana nzn dai cikin shigarshi ta kamala da ya saba yi,idanunshi a kanta har ya ƙaraso cikin palon har gurin da take, yana mai mamakin yarda aka yi har lokacin bata tashi daga in da take ba, ko wuyanta ba zai mata ciwo bane ?, ya tambayi kanshi , a hankali ya yaye kanta da yake cikin Alƙyabbar, gashun kanta ya fara tozali da shi wanda ya zubo kan fuskarta, wanda da alama wahala ce ta mayar da shi kan fuskarta, hannunshi mai ɗumi yasa ya fara tattare mata gashin kan nata, tare da gyara mata shi yy baya. hannunshi ya daura kan wuyanta, numfashi ta jaaa , jin jikinta da zafin zazzaɓi yasa, ya ƙyaleta tayi barcin may be zai ƙarasa sauka duka in tayi barcin........ KAR KU MANTA KU TUNTUƁI NUMBER TA KAMAR HAKA. 07033371851 PLEASE IN KIN SAN BA SIYA ZAKIYI BA KAR KIMIN MGN, MU ƁATA LOKACINMU . DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️ [2/22, 11:58 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼 *DAGA ALƘALAMIN* SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️ SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* LAST FREE PAGE👯‍♀️ *P.11* Ficewa yy ya barta anan, ko da ya sauka palon ƙasa, Ayyana da su Amah. ya gani zaune suna wasa sai Umma Jakadiya, da take ta faman list din abubuwan da basu da shi wanda za'a siyo kafin kamun Azumi, zama ya danyi kujerar da take fuskantarsu, A hankali cikin sanyinshi da ya zame mishi jiki yace "Ayya.!" Ayyana ce ta juyo ta kalleshi, ba tare da tace mishi komai ba, "Sadiyyerh bata jin dadi ki kula da ita , sanan ki haɗa mata kayanta zamu koma chan dayan gidan", ya fada idanunshi akan su Amah. "mai yake damunta.?", watsa hannuwanshi yy ba tare da tace komai ba, Su Amah ne suka mike zasu yi sama, da sauri yy kusu nuni da su dawo, ai kuwa da saurinsu suka koma suka zauna "please kar ki bari su tasheta She need rest!.", ya furta yana miƙewa, kai tsaye yy hanyar fita, sai kuna ya dan dawo da baya, "Umma Jakadiya kema ki haɗa kaya", yana fada yy ficewarshu ba tare da ya ko juyo ba. yana fita Asibiti ya nufa, sai 1pm kafin ya nufi Masallaci. Haleematou kuwa tun da ya fita ya barta sai kusan Asr ta farka, Ayyana ta gani kusa da ita, ita ta taimaka mata kafin ta bata tea da magani tasha, dan danan ta wartsake bama kama da su Amah suke zuba mata surutu ai sai ta zage. yinin ranar hala suka yishi, ta kasa cin Abin ci hakan yasa ta dan faɗa kaɗan, bayan idar da Sallah Isha aka sanar da ganin wata, wanda hakan na nuni da cewar gobe za'a tashi da Azumi gaba daya duniya, Yaa Shehu bai koma gidan ba sai mota da ya tura a daukosu da ita, nan suka tarar da su Zayn, tana zuwa suka zauna suka fara rantafa fira, har bata san sun zauna kan kujera daya ba, Sallamar Yaa Shehi zai ta ankarar da ita, ranshi yy matuƙar ɓaci da ganinsu kan kujera daya, tazarar da take tsakaninsu ba wata mai yawa ba, fada ya farawa Zayn kamar zai ari baki duk da bawai ya iya fadan bane, dan cikin sanyi fada yake fita ba tare da wata hayaniya ba, dan in ma ba ka tsaya ka fuskanci maganar tasa ba sai ka dauka magana ce kawai yake ba fada ba. Bayan ya gama balbalesu yy sama abunshi, har 11 tayi kowa yaje ya kwanta Amma Sadiyyerh na in da take, ta kasa motsawa, yanzu dun fadan da ya mata jiya yau ta ƙara aikata abu kamakancin hakan, har 12am bata tashi daga gurin ba. Umma Jakadiya ta fito zata dauki ruwa kawai ta ganta zaune tayi tsuru, "lafiyarki baki je kin kwanta ba", kwaɓe fuskarta tayi tare da cewa "Ina tsoro kar ya min faɗa", ta fada hawaye taf idanunta, "ai kece bakya kyautawa , sam bakisan kin girma ba,uhmmm bana jin zai miki faɗa tunda ya miki ɗazun kin san bashu da mitar magana " da jin hakan jikinta ta samu ƙarfin guiwa ta miɗe izuwa saman, daki daya ne saman, hakan yasa ta tura da Sallama bakinta. Zaune ta sameshi kan kujera, tuni tsoro ya luluɓeta dan gani take kamar ita yake jira, ɗurkusawa tayi kan ƙafafunta zata fara bashi hkr, da sauri ya miƙe yy shigewarshi ciki, bin bayanshi tayi kirjinta na dukan ukku-ukku. tsaye ta ganshi, nufo inda take yy. Da sauri ta haura kan gadonsa, tana jujjuya mishi kai. Shi kuwa Yaa Shehi maida ƙofar yy ya rufe ba tare da yasa key ba, Da sauri ta rumtse idanunta ganin ya nufi gadon, kana yana zare jallabiyar dake jikinsa. Cilla jallabiyar yayi can gefe. Cikin yanayin tsoro da mmkin ganinsa hakan tace."Don Allah Zauj kayi haƙuri bazan sake ba" Ta kare mgnar tana jawo towel din da da ta samu a gefen gadon tana ƙara kare kanta dashi. Kanshi ya fara jujjuyawa yana mai miƙa hannunsa ya kashe wutan ɗakin. A take duhun daren, da sanyayyiyar iska ya mamaye ɗakin gaba daya. Cike da tsoro ta fara kiciniyar saukowa daga kan gadon. Tana sauƙowo, shi kuwa yana isa gab da ita, haka yasa bayanta ya manna da kirjinsa, da sauri yasa hannunsa duka biyu ya ruggume da ƙarfi jin yadda take mutsu-mutsun kwace kanta. Cikin narkekkiyar murya, tace "don Allah Zauj ka bari" ta ida mgnr hawayen da bata san dalilin zuwansu ba suba, suna kwaranya, cikin yanayi rauni tace, "please" Cikin rawan jiki, ya fara murza siket din ta ƙasa kana murya na rawa yace."oooh ba kece kika sa ba, na fuskanci kina buƙata ne" Da sauri ta kankame jikinta cikin fidda nannauyan numfashin jin ya zame siket ɗin ta ƙasa murya a raunace tace. Zaauj sanyi, Please ka bari" Da sauri ta manna kanta a kafaɗarsa sa boda jin yadda yasa hannunsa daya ya zuge, zib din gaban rigarta, a take sai ga ƙirjinta ya fito fili. Janye rigar yayi ya wurgar ya zama daga ita, sai pant da ko bra babu a jikinta. "Yah Subhanallah"ya faɗaa a fili kuma da karfi lokacin da yaji fatarsa da nata sun haɗe wuri ɗaya, wani gigitaccen abu na fusgarshi, lumshe idanunshi yy, bai taɓa tunanin haka ba, bai taɓa zaton zai tarar da wannan lamarin ba, ya hankali ya shimfiɗar da ita, jikinta na mugun rawa ta riƙe hannunshi, hawaye na zuba a idanunta, yunƙurawa tayi zata miƙe da sauri fa mayar da ita ta kwantar, hakan kuma ne ya ƙara rawar da jikinta yake, tuni wani tsoro ya mamayeta firgici da tashin hankali suka dabai-bayeta. tun da take da shi, wani abu makamancin haka bai taɓa shiga tsakani su ba sai yau, shi yasa sihirtaccen tsoro ya kamata, rasa yarda zata yi tayo, kawai sai ta kankameshi tare da nutsar da fuskarta cikin kirjinshi , ɗago kanta yy, ya jima yana kallon kyakyawar fuskar tata, lios dinta da suke sheƙi ta cikin dan hasken da ke shigowa , ta waje sakamakon labulayen da suke dagawa, iska ake sosai wadda take kama da ta tashin hadari, wani abu yake ji yana fusgarshi,a hankali cikin wani salo ya manna lips dinshi da nata, wanda hakan yy sanadiyar sumar da su na wucin gadi. Abun da ko a mafarki bata taɓa ji ba balle a ido biyu shi take ji, wanda yasa numfashinta ya fara shiɗewa, kirjinta ya fara dagawa sama da ƙasa kamar wadda ke da Asthma ,shesheƙa ta fara yi, Yaa Shehi ma ya rasa yarda zai yi, abun ka ga farin shiga gaba daya ta daburce ya raasa in da zai tsoma rayuwarsa, ga hannuwanshi sun ƙi tsayuwa guri daya, sai yawo suke a cikin jikinta, wasu salon kisses yake aika mata da su, wanda tun da take duniya ko a labarai bata taɓa jin labarinshi ba, balle a ido biyu, abun da bata taɓa tsammaninshi a gurin kowa ba, yau gashi Yaa Shehinta yake mata, tuni ta fara dan ƙaramin hauka , alamar saƙon da yake son aikawa, yaje in da yake bukata, hannaenta tasa ta zagaye bayanshi, a hankali ta fara yawo da su a bayanshi, wanda ya ƙara fitar da Yaa Shehi cikin tunaninshi, zafi da zugin da taji lips dinta ya dauka ne yasa gaba daya ta dawo hayyacinta, hawaye suka fara ambaliya kan fuskarta, dan ji take lips din kamar zasu cire sa boda tsabar yarda Yaa Shehi ke tsotsarsu har wani tattaunasu yake kamar wanda ya samu wata Alawa mai zaki. ƙoƙarin raba lips dinta da naji ta fara yi amma ina, ƙara riƙeta yy gam, numfashunta ne ya tsaya, lokacin da ta ji saukar hannunshi, kan cikinta, a hankali ya shigayin ƙasa da shi, har yy sanadiyar fadawar yatsunshi cikin ramin cibinta, nannauyan numfashi ta ja, lokacin da ta ji yatsunta na mata tafiyar tsutsa, hae kan mararta, da ace tana da baki, bb Abun sa zai hanata kurma Ihun Salati, saboda abun abun da take ji yafi karfin tunaninta, ya shige tunanin-duk wani mai tunani, hannayenta ta shiga bubbugawa ko zata samu sauƙi daga abun da take ji cikin jikinta, na daga abubuwan da Yaa Shehi ke mata. wanda ko idanunta ya nuna , to fa sai ta ƙaryata balle kuma ace wani ya fada mata, sai gashi akan kanta yake faruwa, idanunshi da suka yi matuƙar jaaa tare da kankancewa, har wasu hawaye-hawaye suke tarawa , ya bude blanket ya jaaa musu . hannunsa da suke ƙaikayin son taɓa kirjinta, ya kife a kai, tare dayi musu wani irin shafan da yasa sukaja mataccen numfashin a tare. Wani irin miƙa Sadiyyerh tayi tare da ɗaga hannunta sama sa boda amsar saƙon sa da tayi a duk hudar gashin jikinta. Shi kuwa Yaa Shehi cikin rawan jiki ya zauna kan gado tare, da riƙon hannunta, Bo........... MASHA ALLAH..! , ALHMDULILLAH..!, DUKA DUKA ANAN NA KAWO ƘARSHEN BOOK 1 NA ARMAN MALEEQ, DOMIN SAMUN BOOK 2 AND 3 SAI KUMIN MGN DOMIN KO SAMU CIKIN SAUƘI DA RAHUSA, INA KARA JADADDA GODIYA GAREKU MASOYANA, ALLAH UBANGIJI YA BAR KAUNA DA TARE, HAƘIƳA KUMA MATUƘAR SANYANI ALFAHARI, ALLAH YA DAURAR MANA DA KAUNARMU YA HAƊA KANMU, YA KUMA BAR ZUMINCINMU HAR IZUWA ALJANNATUL FIRDAUSI, NA GODE! NA GODE!! NA GODE!!! 07033371851 PLEASE WANDA ZAI SIYA KAWAI IN KINSAN/KASAN BA SIYA ZAKA YI BA TO KAR KA YI MGN PLEASE, KAR MA MU ƁATA LOKACINMU DA NI DA KAI. DAGA ALƘALAMIN ƳAR LELEN ROYAL STAR🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️