[11/06 à 20:13] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔 *INUWATA DA TA GABATA*🕸️ 🦔🦔🦔 ```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)``` MRS SADAUKI💫✍️ FCWA ☀️ Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa) _____________________________________________________________________________________________ *Wani sashen ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina* Page 1 “Inyaaa! Inyaaa” kukan jinjiri ya karaɗe ɗakin,na ja wata wahaltaciyar ajiyar zuciya tare da sakin murmushin da ko second biyu ba a yi ba wani mummunan furicin da kunnuwana suka jiye min ya maye gurbinsa da ƙunci. “Wannan ɗin ma ya koma ! Allah ya karɓi abinsa! Maryam ke kam ƙaddara ta aure ki” Wacce ta yi furicin goggo Dije ce ƙanwar mahaifiyata,ko minti biyu ba a yi ba ta fito hannunta riƙe da jinjirin jikinsa da kumfan jini ta miƙo min shi ta na cewa “Ungo je ka rufe shi Ja'afar ” hannuna na rawa na karɓe shi,ban damu da farar gizner ce a jikina ba kawai na manna yaron a ƙirjina wanda yayi bala'in kama da ni. Wasu zafafan hawaye masu ɗumi suka zubo min,babu yadda na iya haka na je na yi masa wanka na kira abokaina da ba su wuce biyar ba aka yi masa sallah aka rufe shi. Jikina duk babu ƙwari na isa ɗakin matata Maryam,a kwance na tarar da ita ta na kuka.Ta na ganina ta ƙara ƙaimi,kukanta ya fi komai tarwatsa min zuciya don wani irin sihirtacen so da ƙauna nake yi mata jarumi ne ni a ko wane fage amma akanta ina da nakasau.Da sauri na ƙarasa na je na rungumo ta,wani kalar sautin kukan ta sake saki kafin ta soma magana cikin shaƙaƙar murya. “Ja'afar don mi ni ? Duk abokaina su na da ƴaƴa ,in sun ɗauki ciki normal suke haihuwa amma ni kamar wacce ta yi wa Allah laifi kullum a mace suke zuwa wannan ɗin da ya ɗan koka har na sa rai shi ma ɗin ya bi sauran ƴan uwansa” “Yi shiru mana Riam,ki yi wa Allah godiya a duk halin da kika tsinci kan ki shi ɗin ya fi mu sanin dai....” ta katse ni da “ na gaji! Ni dai kam na gaji wallahi ba zan sake ɗaukar wani cikin ba ƙarshe a je a binne shi cikin ƙasa ba” “Ya Salam!” na furta da sauri ina jin kaina kamar zai tsage gida biyu tsabar yadda yake sara min,ina kallon Maryam ta tashi ta fara haɗa kayan ta cikin trolly. “Wai ina za ki je ne?” na yi mata tambayar ganin ta na shirin jan akwatin kayan nata ta fice. “Gidanmu zan je Ja'afar! Wallahi a yadda nake jin zuciyata na min ƙuncin nan komai zai iya faruwa in ina ganin ka a gabana” “Wane irin zance ne kuma wannan Riam? Ni ɗin ne kuma yau a ba ki son gani?” na yi furta ina shirin kamo hannunta amma ta wani ja da baya,ta buɗe baki za ta yi magana kenan na ga ta yi luuu za ta faɗi na yi saurin taro ta sai kawai ta faɗa ƙirjina.Jijigata na soma amma idonta na ga su na birkicewa yayin da kuma halshenta ke zalzalowa. “Goggo! ” na furta da mugun ƙarfi ina ciciɓo Maryam na fito da ita daga ɗakin,step ɗin ma bibbiyu nake taka shi.Kan kujera na sauke ta,likitocin da na ɗauka domin kula da lafiyata da ta iyalina suka fara bata taimako an ci wuya sosai kafin ta koma normal. Na yi baya ina dafe goshi kafin na zube gwiwaina ƙasa ,daidai saitin kanta na zauna ina shafar fuskarta wacce ta ƙara yin haske fayau. “Ta na buƙatar hutu,sannan kamar jininta ya so wuce ƙa'ida ya kamata a bata kulawa ta musamman a guji abin da zai ƙara mata wata damuwar kan wacce take ciki” Dr ta faɗa wacce ita ɗin ƙwararriya ce sosai wacce ta yi fice. Idona har wani zugi suke min ina kallon Maryam abar ƙaunata wacce nake jin da dai ta suɓuce min gwara ace na rasa komai da na mallaka. “Goggo a shirya mana tafiya zuwa Dubai” “An gama” ta faɗa kafin ta soma shiri,kamar abun wasa tuni komai ya tafi cikin tsari .Ni da Maryam ne sai likitarta Dr Hannah wacce ke kula da duk wani motsin ta muddin ya shafi lafiyarta ne,maƙudan kuɗi muraren na zuba don ɗaukar ta aiki. Kasancewa ta agent jirgi ,ɗan kasuwa fitacce babu ɓata lokaci komai ya kammala muka ɗau hanya. Har lokacin da muka isa Dubai Maryam na bacci,da kaina na yi mata wanka da ruwan ɗumi na kimtsa ta sannan na saka mata wasu riga da wando masu taushi da sulɓi masu kamar jikin mage.Kan lafiyayen gadon na shimfiɗeta wanda ya sha shimfiɗa ta alfarma,sai yanzu ma na tuna da ban yi wa PA ɗina zancen ya soke duk wani zaman da zan yi da mutane da kuma taron da na tsara zan je.Text na tura masa bayan na yi wanka na shirya iya cikin gajeren wando kawai ko riga ban saka ba,na je na yi tsaye ina kallon beautiful fuskarta.Hawayen tausayinta ne suka zubo min,duk da ni ma ɗin ba baya ba wurin mugun son yara amma Maryam ta fi ni sannan a ƴaƴa ukun da duk ta haifa suka mutu ta fi sa rai a wannan na huɗun sai dai shi ma ashe ba zai tsaya ba. Duniyar tunani na tsunduma ina mai lumshe idona,‘ Allah ni ɗin bawan ka ne mai yawan bautar ka,na rabu da iyayena lafiya,ina sada zumunci,ina kyautata wa maƙwabta da marayu da maras ƙarfi.Allah ban san abin da yasa kake jarabtata ta wannan fannin ba,sai dai kai masani ne akan komai ba zan tuhumeka ba .Ya Rabb in akwai wani laifi da na yi maka ka yafe min ka bani haihuwa mai albarka,Allah ba don halina ba sai don RahamarKa na da yawa’ duk a zuci nake yin wannan jawabin,wanda ba kowa nake yi wa shi ba sai maƙagina wanda ya hallice ni.Sam kasa samun nutsuwa na yi na miƙe na je na ɗauro alwala na soma jero nafiloli a nan bacci ya ɗauke ni mai ɗauke da mafarkin da ya kamata na tsaya na yi nazari don zai taimaka min wurin warware matsalolin gobena,amma kasancewar kukan Maryam ne ya tashe ni sam ban wani maida hankali akai ba.Na zabura na miƙe na je gare ta ,“Ja'afar ka kai ni gida wurin Mama” “Ba mu fa Kamaru muna Dubai,ki ƙara haƙuri na san da ciwo rasa abin da ka haifa” Ta soma waige-waige ta na ƙarewa ɗakin kallo,ban san mi ya ja ra'ayinta ba ta bar rigirmar kawai dai ta yi lamo a ƙirjina. “A kawo miki Lipton ki sha?” na tambaye ta shiru ba ta amsa ba,na ɗago haɓarta na ce “ki daure ki sha kin ji?” ta lumshe ido kawai hawaye na yi mata shatata,na kai bakina a hankali ina shanye ruwan hawayen kafin na fake da sumbatarta.Ba wai don shauƙi ko sha'awa ba sai don kawai ya na ɗaya daga cikin abin da nake cin nasara wurin rarrashinta.Ban bar abin da nake yi ba sai da na ji yanayin bugun zuciyarta ya fara gudu,ya kuma koma normal.Na gyara pilow na kwantar da ita kafin na fita zuwa kitchen na haɗo mata tea,sai da na yi da gaske sannan ta sha rabi ni kuma na shanye sauran. “Ina jin kamar pad ɗina ya cika” ta faɗa cikin sanyin murya,ba wai wannan ne karon farko da nake taimaka mata wurin kimtsa wa ba.Sau tari in ta na period ina yi mata wannan gatan don ta na mugun son haka,sannan na yarda kuma ya na ƙara danƙon soyayya. Na sure ta ina cewa “mu je to na gani in ya ɓace sai na canza miki ” ta ɗan saki fuska kaɗan amma ba ta yi murmushi ba.Bayan mun fito daga toilet ne take cewa “Ja'afar ina jin daɗin yadda sam ba ka tsantsani na” Na shafi gefen fuskarta na ce “to miye don na yi wa matata hidima ? Ni fa komai naki ina so kuma ban jin ƙyamar ki a kowanne irin hali” “Na gode! Na ɗan ji sauƙi amma har yanzu ina jin ciwon rasa babyna” sai kuma idonta ya cika da ƙwalla. Na ce “Haka Allah ya tsara ƙaddararmu ki ƙara haƙuri in da rabo za mu dace” Ta girgiza ta ce “yaushe kenan? Haihuwa huɗu a jere amma babu ko ɗaya a gabana,yayin da mata dayawa ga su nan da ƴaƴansu...” Na yi saurin katse ta da cewa “kin manta abin da Allah subhanahu wata'ala yake cewa a cikin Suratul Zhukur ? أَهُمۡ يَقۡسِمُونَ رَحۡمَتَ رَبِّكَۚ نَحۡنُ قَسَمۡنَا بَيۡنَهُم مَّعِيشَتَهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَرَفَعۡنَا بَعۡضَهُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَتَّخِذَ بَعۡضُهُم بَعۡضٗا سُخۡرِيّٗاۗ ```Shin ku kuka bawa kan ku wannan ni'imar da kuke ciki ? Mu su Allah mu muke raba wa kowa kason shi mu tsara wa kowa irin rayuwar da zai yi,sannan ita kanta ni'imar da hawa-hawa ce ta wani ta fi ta wani daraja.....” yadda ta wani faɗo jikina irin da ƙarfin nan yasa na yi shiru . Cikin kuka take cewa “na ji Baby J na ji na ɗauka,amma ka yi min alƙawari ba za mu bar nan ba sai na samu wani cikin”......... [13/06 à 05:46] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔 *INUWATA DA TA GABATA*🕸️ 🦔🦔🦔 ```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)``` MRS SADAUKI💫✍️ FCWA ☀️ Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa) _____________________________________________________________________________________________ *Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina* 2 Na jinjina wa Maryam na ce “na yi miki alƙawari my Ryam in sha Allah sai kin samu wani cikin za mu koma Kameru,amma ya zancen zuwan ki aikin hajjin za ki fasa ne?” “Ina matar Ejan jirgi guda? Kar fa ka manta kamfanin zuwa Makkar naka ne” ta furta a wani yanayin taƙama,zan iya cewa a kaf halayen matata wannan ne na fi tsana ta na da mugun alfahari. “Za mu duba mu gani dai,kar ku gaji ke da abin ƙauna mai zuwa” na furta ina mai shafar mararta.Ta saki murmushi mai ɗan sauti ta ce “ni kam Shalele ƙarfe nawa yanzu?” “Kusan ɗaya na dare fa” “Ina son yin magana da Mama,zan sanar da ita halin da ake ciki kafin labarin ya karaɗe duniya” “Ok babu matsala bari na haɗa ki da ita ” na faɗa ina mai shirin tashi amma ta riƙe min hannu ta na aiko min wani irin mayen kallo “Ryam zan ɗauko waya ne” sai ta yi saurin sakin hannun nawa ,na je na ɗauko waya na kira mata mahaifiyarta amma ba a ɗaga ba har sau uku.Ta yi wani zuru da ido alamun damuwa kafin ta ce “ka jaraba kiran wayar gida” Na ce “Ryam irin wayoyin da ake ajiye wa a falo wani sa'in duk kiran da za a yi ana tsare da shi ko kin manta Baban ki shi ne Ministan Kamaru?” “Don Allah Shalele ka kira ko ba ta nan ba doli mutane sai sun san da labarin nan,dama idon kowa na kanmu” Babu yadda na iya haka na kira wayar,tsawon lokaci kafin ƙanwarta ta ɗauka na yi saurin miƙa mata. “Allo Marfuwa ina Mama take?” “Ta na ɗakinta mana, tun da safe ta ce ba ta jin daɗin jikinta ” “Ayya! Je ki sanar da ita ina son yin magana da ita” “Ga ta nan ma ta fito,Mama karɓa Maryam ce” “Allo ƴata fatan dai ki na lafiya?” cewar Mamar cikin wani irin yanayi. “Eh lafiya! Mama...” “Lafiya mine ne?” Mamar ta tambaya,sai Ryam ta kalle ni duk da ba a hand free take ba ina jin duk tattaunawar tasu. “Mine ne ya faru?” Mama ta sake tambaya . Ryam ta fashe da kuka ta ce “wannan ɗin ma ya mutu Mama! Yanzu haka muna Dubai ni da Daddyn Abrar” Salati kawai Mamar ke yi kafin ta yi furicin da ya fizgi ruhina “ Maryam ni fa na fara jin tsoro kar dai ace maganar da mutane ke yi kan mijin ki gaskiya ce” Ban tsaya ida jin ƙarshen hirar tasu ba na bar wurin na dawo falo na zauna ina nazari.Maimakon na ɗauki mafarkin da na yi kan Mahaifiyata na auna shi da maganar da Mamar Ryam ta yi sai na shashance kamar kullum can ƙasan zuciyata na raya min ‘ita ma hassadar ka take yi kamar sauran mutanen garin shi yasa ta zargi haka’ Tsawon lokaci ina saƙa da warwara kafin in jin an lanƙamo hannuwa ta wuyana an rungume ni,“Akhee!” na ɗan lumshe ido game da sunan da ta kira ni,Ryam na mugun sona ita ma yanayin da take ciki to da irinsa take zaɓar sunan da za ta kira ni da shi.Kamar dai yanzu da ta kira ni da Akhee ta na son yi min nuni ne ita duk rintsi ta na tare da ni don ba a sauya ɗan uwa,in kuma ta kira ni da Shalele to irin ta na cikin farin ciki ne,faɗar sunan Ja'afar kuma in ranta a ɓace yake ne kawai. Na kamo dogayen yatsunta na riƙe na ce “ƙanwata ya jikin naki?” “Yunwa nake ji” Da sauri na miƙe jin dai ta yarda za ta ci abinci, kitchen na shiga na ɗauko mata abin da ba a rasa ba a frigo. Kan cinyata na ɗora ta na soma bata a baki,bayan ta ƙoshi ita ma ta ciyar da ni.Wannan romantic moments da muka yi mai cike da tattali da kallon bege yasa raina yayi sanyi ,sai da muka yi brush kafin mu hau bed.Tsam a ƙirjina na manna ta a haka muka yi bacci,kiran sallar farko na farka na je na yi wanka haɗi da alwala na bar Ryam ta na sharar bacci ba tare da na san hakan shi ne mafarin muguwar rayuwar da za mu fuskanta a gaba ba. Maryam na bacci ,ƙofar ɗakin da Ja'afar ne ya rufe ta kafin ya fita amma ƙiiii ta buɗe kanta ƙarar ba ta taka kara ta karya ba amma abun mamaki ita ta tayar da Maryam ɗin.Idonta dishi-dishi take gani saboda nauyin baccin,a sannu a hankali ta ga kamar shigowar wani haske mai silki da iska ya shigo ta ƴar hanyar da ta buɗe. Numfashinta ya soma canzawa,haka ma yanayin jikinta ya ɗauki wata irin muguwar kasala.Ba ta san mi ya ja ragamar jikinta ba izuwa toilet ta yi wanka abun mamaki jinin haihuwar ya ɗauke cak.Ruwan ɗumi ta tara ta gasa kanta,ta yi wankan tsarki ta zo ta soma yin sallah cike da rabkanuwa saboda wani mugun desir da ke bijiro mata.Ta na gama salamce sallah ko istigfar ba ta yi ba ballantana aje da zancen Azkhar kawai sai ta cire hijab ta je ta wani kwanta kan bed a haka nan . Bayan mun gama sallah cikin sauri na taso sanin na bar Ryam cikin halin da take da buƙatar kulawa.A kan hanya na soma jan casbi da niyyar in na zo gida duk sauran Azkhar zan yi ,sai dai ina kutso kai na tarar da Ryam cikin halin da duk wani namiji mai lafiya in ya ga matarsa doli ya je gare ta. Na saki casbin na isa inda take ido rufe, wannan ya na ɗaya daga cikin raunina ban da haƙuri ta fannin kwanciya zan iya cewa ma shi ke daɗa min ƙaunar Ryam a rai don ban taɓa zuwa da buƙatata ba ta hana ni. Duk da ƙololuwar sha'awar da nake ciki bai hana ni tambayar Ryam ba gudun kar na faɗa hallaka na saɓa wa Ubangijina. “Ryam jinin ya tsaya ne?” Ba ta bani amsa ba saboda na lura kamar ta fi ni shiga yanayi,da taimakonta muka samu nutsuwa. “Yau na ji wani mugun daɗi sosai” ta furta idonta a rufe,cike da mamaki nake ƙara dubanta karon farko kenan da Ryam ta taɓa faɗa min ta ji daɗin kasancewar da muka yi.A kullum ni ne ke faɗa har in tsaya yi mata comments daki-daki,abun mamaki yau ita ce ta ɗauki place ɗina ta soma zuba kamar kanya.Zantukan da take faɗa uwanda sam kunnen da ba na babba ba to ba zai iya ɗaukarsu ba,su suka rinjaye ni suka sa na ƙara janta birnin ma'aurata. Ta na dariya na sure ta zuwa toilet muka soma wanka,“baby J please mu shiga cikin bahon wanka” ta furta min cikin kunne.Wannan duk ya na cikin abubuwan da nake so nake kuma roƙonta mu yi,sai ga shi yanzu ita ce ke yin duk wannan.Da muka shiga bahon nan Allah ne kawai ya san irin yanayin da muka tsinci kamu,dakyar muka iya bai wa kanmu haƙuri muka fita muka shirya tsab kafin mu je falo mu ci abinci. Yadda Ryam ke nuna min soyayya da ƙauna da tattali ko farkon auren mu albarka,dama babu abin da namiji ke so irin haka wannan yasa na ƙara sakin jiki ina kwasar romon love. A satin biyun farko Maryam ta zama ƴar gari,da kanta ta sallami Dr Hannah kan ta koma Kameru duk da ita ɗin ba ta ji daɗi ba amma haka ta tafi.Rayuwa mai cike da jin daɗi da farin ciki muke gudana,a kullum ina haɗa Ryam da Mamarta don kusan ita ce ƙawarta.Farkon wata na biyun mu a Dubai Ryam ta soma laulayi,da zuwanmu asibiti aka tabbatar mana da shigar ciki ne.Ra'ayinta shine mu ɓoye labarin cikin kar kowa ya sani sai bayan ta haihu. “Ryam ciki bai ɓoyuwa fa ko yaya ne sai ya fito” shine abin da na ce mata. “Zan zauna a nan na raini cikina hatta Dr Hannah ban so ta sani” “Babu damuwa yadda kike so haka za a yi,yanzu dai kwanta ki huta zan fita na dawo” Da sauri ta tambaye ni “ ina za ka je?” “Na yi baƙo Ba'amurike ne,za mu tattauna kan harkar kasuwanci ” na bata amsa. “To ” “Ya na ga yanayin tsoro a tattare da ke?” Sai da ta ɗan waiga ko ina kafin ta ce “ wallahi Shalele ji nake kamar ana kallonmu,yadda ka san ba iya mu biyu ne a nan ɗin ba” Na saki murmushi mai ɗan sauti na ce “uwanda za su dinga kula da ke ne fa ,motsin su ne kika ji” Ta ja ajiyar zuciya ta ce “ to ai ba ka faɗa min ba saura ƙiris fa cikin jikina...” ba ta kai ga idawa ba wani ɗan kofi mai ɗauke da flowers ya faɗo daga kan table ya fashe. Ta yi sauri ta riƙe ni ta ce “ ka gani ko? ” “ To mine ne kuma yanzu? ” “Ka na gani fa shi ya faɗo da kansa babu wanda ya je ko kusa da shi” na laƙace hancinta na ce “lokacinsa ne yayi” na sumbaci goshinta “sai na dawo” na furta ba tare da na bai wa lamarin da ya faru muhimmanci ba. Maryam na daga tsaye ta na kallon Ja'afar har ya fice sai ta dinga jin motsi,a hankali ta sauke idonta sai ta ga abin saka flowers ɗin na haɗe kansa da kansa tamkar ba shi ne ya fashe ba.Da mugun sauri ta kai hannu za ta dafe mararta da ke murɗawa sai dai kuma ta ji kamar wani hannun ya rige ta. Ta fasa wani uban ihu ta na kiran sunan Ja'afar,ma'aikatan ne suka shigo da sauri su na tambayarta lafiya ganin ta kasa yin magana sai suka kira ogansu amma bai ɗaga ba. JA'AFAR Cike da ƙwarewa nake tuƙin har na isa babban hotel ɗin da za mu haɗu da shi.A hanya ina ganin kira na ta shigowa amma ban ɗauka ba saboda muhimmancin abin da zan yi,sai bayan mun gama meeting ne na duba waya sai na ci karo da saƙon wai an kai Ryam asibiti.Hannuna na rawa na kira lambar na tambayi asibitin da suke,a tsiyace nake gudu har na isa.Da taimakon Dr asibitin na je ɗakin da aka shimfiɗe Ryam,ta na kwance ta na bacci .Wani irin tausayi ta bani,na je na zauna kusa da ita tsawon lokaci kafin ta farka ta na ganina ta fara yi min kuka haɗi da yi min bayanin abin da ya faru. “Yanzu dai alhamdullah tun da cikin jikin ki bai samu komai ba” na furta bayan na tayar da ita zaune.Likita ya shigo ya duba ta,na je na biya kuɗin magani kafin mu dawo gida ina ɗora ƙafata cikin falo idona ya sauka kan abin saka flowers ɗin ya na tsaye ƙyam babu alamar ma ya taɓa fashewa amma ko kafin na ƙyabta ido sai kuma na gansa a tarwatse zube akan capet kamar yadda na bar shi ɗazu.Na jawo Ryam na rungume ƙyam zuciyata na ɗan harbawa,duk da ba gwani ba ne wurin yarda da maganar aljanu sai na ji sam zuciyata ba ta aminta da gidan ba..... [13/06 à 17:56] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔 *INUWATA DA TA GABATA*🕸️ 🦔🦔🦔 ```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)``` MRS SADAUKI💫✍️ FCWA ☀️ Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa) _____________________________________________________________________________________________ *Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina* 3 Na so tsagaita tashinmu daga wannan gidan mu canza wani,sai dai sam Ryam ta ƙi yarda duk inda na yi ta na maƙale da ni ta na kukan tsoro take ji gidan aljanu ke yi mata gizau.Da ta yi waya da mahaifiyarta kuwa cewa ta yi kar ta jinkirta kawai ta dawo ko da kuwa ni ban yarda ba. “Shalele don Allah mu koma Kamaru,wallahi tsoro nake ji duk a takure nake ji nake ana kallona ” Ryam ta faɗa ta na kuka. Na ce “to ba gani a kusa ba? Wa ke kallon ki kuma? Za mu tashi” “A'a ba za ka fahimta ba,irin kallon da nake ji a jikina tamkar ana son cinye nama na” “Ya isa haka yi shiru bari kukan,za mu je hotel daga nan sai mu wuce filin jirgi” na faɗa cikin rarrashi kafin na haɗa kayan da muka zo da su na kai mota,sai da na yi wa ma'aikatan da na ɗauko alheri kafin mu bar gidan.Wannan karon direba ne ke jan mu,muna daga baya zaune sai aikin rarrashi nake har muka isa wata haɗaɗiyar hotel. Ko kayanmu ban cire ba daga bot Ryam ta fara girgiza kai “ban son wannan hotel ɗin ,mu tafi Shalele” sai ta riƙe ni gam ta na cusa kanta a ƙirjina kamar mai gudawa daga wani abin tsoron,na kuma fi tunanin hakan. “Ya Rabb ! Mi kuma kike gani yanzu?” “Tsohuwar hotel ce fa,dubi yadda gininta duk ya tsage ya tsufa” ta bani amsa ba tare da ta ɗago ba. Cike da kulawa na riƙe kanta na soma yi mata karatu,a sannu ta fara sauke ajiyar zuciya har ta tsagaita kukan da take. “Ryam kin ga kaf ƙasar nan babu hotel ɗin da ta fi wannan haɗuwa,kawai tunanin ki ne ke baki tsohuwar hotel ce amma dubi fa komai nata sabo ne” “Ni dai kawai mu je can filin jirgi ɗin mu jira” ta furta ta na mai ƙoƙarin komawa mota,na dafe kai amma babu yadda na iya haka muka shiga direba ya kai mu can. Inda aka tanadi kujerun zama na ja ta muka zauna,muna nan ne aka yi kiran sallar azahar na miƙe ina mai ce mata “zan je na yi sallah kar ki gusa daga nan” ta jinjina kai,na tafi can Toilet na yi ɗahara sannan na yi alwala na shiga masjid. Maryam na zaune wata tsohuwa ta zo ta zauna a kujerar da Ja'afar ya tashi ,ba ta ganin fuskarta sai dai hannuwanta uwanda suke fari sol kamar na zabaya.“Sannu ƴata” ta faɗa cikin muryar tsofi,Ryam ta yi mamaki don yadda ta ganta jawur ɗin nan sam ba ta yi tunanin ta iya Hausa ba “yawwa babah ina wuni?” “Lafiya lau!” ta amsa ta na fiddo wasu awarwaro da zabba masu bala'in kyawu da ƙyalli, duk na ƴan yara ne.Yadda walwalinsu suka shiga idon Maryam har ba ta san lokacin da ta kai hannunta gare su ba ta ce “babah na sayarwa ne?” “Eh ƴata ga su nan ki zaɓa na yara ne” har wannan lokacin ba ta buɗe fuskarta ba,Maryam ta ruɗe ta rasa wane za ta ɗauka ma can ta zaɓi masu duwatsu jajaye haɗi da wani zobe na farar dalma. Tsohuwar ta karɓi sauran, Maryam ta ce “nawa ne kuɗin?” “Duk abin da kika bayar ƴata” Maryam ta soma laluben jakar Ja'afar da ya bari can ta ciro 10mill ,ta ce “ungo!” ta karɓa ta na juya takardar kuɗin ta ce “nawa zan cire?” Cike da jin daɗi take kallon awarwaron ta na juya shi ta ce “Ki ɗauka duka na gode sosai” “Da wa kike magana ne haka?” na furta daidai lokacin da na dawo daga sallah na tarar da Ryam na magana ita ɗaya.Ta ɗago da sauri ta fara waige-waige,kafin ta dube ni ta ce “yanzu na sayi wannan ga wata mata fa nan take zaune ” sai kuma ta ci gaba da dubawa ko za ta ganta ai kuwa ta hange ta can nesa,sosai ta yi mamakin yadda aka yi har ta kai can ɗin cikin daƙiƙun da ba su wuce goma ba. “Mu je ki yi sallah kar lokaci ya shige” na karɓi awarwaron da niyyar saka shi a jaka ta amma abun mamaki sai na ji wani irin contact kamar ina da alaƙa da shi amma sai na yi watsi daga wani tunani na ja Ryam har toilet na yi mata rakiya muka kuma fito tare ta yi alwala.Ta na nan zaune kan tapis muka fara jin sanarwa jirgin da zai tafi Kamaru zai tashi nan ba da jimawa ba. Cike da kulawa nake riƙe da hannunta muka zo na ja trollyn kayanmu muka isa can inda za a shiga jirgin.Babu jimawa kuwa duk muka shiga ciki,da kaina na ɗaura mata belt ina mai yi mata raɗa a kunne “ki nutsu don Allah” ta saki murmushi kawai,bayan komai ya kammala jirginmu ya cira a sararin samaniya. Yadda na ji ta wani damƙo hannuna yasa na yi saurin kallonta,“ya dai?” “Dubi yadda samaniya take kam...kamar ana bin bayanmu” “Da zarar kin ji wani abu ki ce Hasbunallahu wani'imal wakil! ” Ba tare da tace komai ba ta jingina da kafaɗata ,ni kuma na riƙe mata hannu . Lokacin da muka isa sai da na tashe ta daga bacci,muna fitowa ƴan jarida ne suka yo mana caaa kowa da kalar tambayarsa.Ban amsa ko ɗaya ba na ja matata muka wuce mota a can inda direba ke jiranmu,“a kai ni gidanmu please ” Ryam ta faɗa ta na kallona cikin ido.Na girgiza mata kai na ce “a'a kin san ba zan juri rashin ki kusa da ni ba” Ta ce “umarnin Mama ne fa! Ba za mu jima ba akwai maganin da zan yi wanka da shi” “Hum!” kawai na iya cewa don ba tun yau na fahimci mahaifiyar Ryam na son harakar malamai ba. Babu yadda na iya haka muka je gidan nasu,sai da masu tsaron gidan suka bincika motar tawa sannan muka shiga duk da kuwa sun yi min farin sani. Tarba mai kyau muka samu daga Mamar,sai da muka yi sallar la'asar da ba mu samu mun yi ba ajirgi sannan muka ci abincin da aka gabar mana.Kafin kuma Mama ta janye Ryam domin gudanar da wankan,ina nan zaune har aka yi sallar magrib na je na yi na dawo muka haɗu da mahaifinta wanda shi ne minista. Hira sosai muke da shi ya na ƙara jajanta min game da haihuwar da aka yi min irin ta ko da yaushe kafin ya soma yi min tallar malamansa da kuma bani shawarar doli sai da malamai in ka taka wani matsayin. “In sha Allah zan duba na gani yalaɓai ” na furta ina karanta saƙon Dr Hannah da ta yi min na barka da zuwa,ban yi mata reply ba don ban son irin rawar kan da take nuna wa a kaina. Lokacin da Maryam ta fito ƙarfe goma na dare ta gota don har sai da na gaji da jira,har mota Mama ta yi mana rakiya bayan ta bata wata ƙatuwar leda. “Baby sai wani irin ƙamshi kike irin na aljanu” na faɗa bayan mun ɗauki hanyar zuwa gidanmu.Ta yi ƴar dariya ta ce “ka san halin Mama game da bin ƙa'idar magani ni kaina sai da na gaji wanka da turare-turaren nan kuma fa wai a haka zan kwanta bacci ” Na yi sauri na ce “da wannan ƙamshin kamar ƴar bori?” Wata dariyar ta ƙara yi kafin ta ce “ai kuwa dai gwara ka so ƙamshin nan don haka zan dinga yin wanka da maganin har sai na haihu Mama ta ce ƙalau zan haifi babyna kuma rayayye ” Na girgiza kai kawai amma ni sam ban yarda da zancen nan ba,muna isa gida Ryam ta fiddo wani magani ta shiga yayafa wa ko ina na gidan tun daga bakin ƙofa ta ce “sheɗanu ba sa son wannan ƙamshi” sai kuma ta kira ma'aikata ta sa su idasa aikin da ta soma. Kan salon muka zube,Dr Hannah ta zo ta fara duba lafiyarta ta tabbatar min komai normal.Har zan tafi can bedroom ta ce “bani awarwaro da zoben nan Shalele ” Na buɗe jaka na bata sannan na haye can sama. Haka kawai Maryam ta zauna ta na juya awarwaron shi kuma ya na fitar da wani sauti da haske sosai abin ke yi mata daɗi,da ace ta aje hankalinta to tabbas da ta lura wani jan haske mai kamar an saita fitilar hannu haka yake dalle saitin cikinta yayin da kuma hoton dunƙulen tsokar wacce ta kasance fœtus ne tsaf za a iya ganinsa ta jikin dutsen da ya fita daban a cikin duwatsun.... [18/06 à 18:38] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔 *INUWATA DA TA GABATA*🕸️ 🦔🦔🦔 ```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)``` MRS SADAUKI💫✍️ FCWA ☀️ Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa) _____________________________________________________________________________________________ *Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina* 4 Cike da tsantsar so muke rainon cikin jikin Maryam,dukkan wata kulawa da miji ke bai wa matarsa ni tawa har ta kusan yin yawa.Kusan kullum ina tare da ita don yadda take barbaɗe gidanmu da magani duk safiyar Allah abin sai ya dinga bani tsoro sai na ji kamar in na yi nisa da ita gaske za a cutar da ita.Duk wasu ƙawayenta na datse alaƙarsu sai bayan ta haihu kuma,ɓangaren mahaifiyarta ta zage dantse wurin bin malamai da bokaye duk don bai wa ƴarta da abin da ke cikinta kariya ashe ƙara ƙaimi ne take wurin rogaza rayuwarmu ba tare da dukkanmu mun sani ba. Aikin hajji ya matso kamar kowacce shekara ina ware kujeru sama da 50 na wanda nake biya ma su je su yi Hajj kyauta .Takarda na bai wa Maryam na ce “ki rubuta sunayen dangin ki uwanda kike son bai wa damar zuwa aikin hajj” Da murna ta karɓa sunan mahaifiyarta ne farko da kuma na aminiyarta,kafin ta rubuta sunayen wasu goma can da ban san su ba .Bayan ta gama rubuta su sannan na karɓa na saka sunan Dr Hannah da sunan masu gadin gidana uwanda ban taɓa kai wa ba da aka zo ɓangren masu yin hidimar cikin gida kuwa ƴan aiki dukkansu na kira na ce “ a cikin ku zan biya kujerar Makka 5 kenan sai ku yi shawara su wane za su tafi a wannan shekarar su kuma za su yi haƙuri har wata shekarar?” Kallon-kallon suka shiga yi kowacce da alamu ta na so,ganin haka yasa na guntsira takardu masu yawa na yi rubutu na dunƙule na zuba a ƙasa“kowacce ta ɗauki ɗaya wadda ta ɗauko 0 to za ta zauna in kuma lamba ɗaya kika ɗauko to za ki je Hajj ” Bayan sun gama zaɓa na fitar da uwanda za su je ɗin,a ranar duk wanda sunansa ke kan liste muka sanar masa sannan suka fara shiri.Tun daga gyaran takardu har abincin da mutum zai ci in ya je can ni na ɗauki nauyin komai,irin addu'o'in da nake sha kuwa Allah kaɗai ya san iyakarsu. Duk da na so tafiya aikin Hajj kamar kowacce shekara amma haka na zauna domin kula da abincin ruhina.Duk wata sangarta Ryam ta iya ta da salon jan hankali,sosai muke more rayuwar aurenmu kasancewar sam cikin nata ba mai laulayi ba ne.Har aka yi aikin Hajj aka gama kullum sai sun yi waya da mahaifiyarta video call,abu guda ke ban mamaki yadda Mama ke da mugun son duniya sam ba ta yi duba da ƙasa mai tsarki ce za ta je kitson gashin doki aka yi mata. Ina daga gefe ina aiki kan system ɗina na saka casque 🎧a kunnena,yayin da gefe na kuma Ryam ce ke aikin abin da ta saba wato video call.Kamar an ce na tsayar da abin da nake saurare sai ji na yi ta na cewa “Mama kin fi kowa sanin Ja'afar na sona babu buƙatar sai na yi wani abun don mallakarsa ” “Duk da haka dai ba ki ji ƴan magana na cewa ko ka na da kyawu to ka haɗa da wanka ba? Duk wannan rawar ƙafar da yake yi a kan ki da zarar kin haihu dukkan soyayya zai ɗauke ya ɗora wa babyn” shi ne abin da Mamar ta faɗa. Ina gani ta ƙasan ido lokacin da Ryam ta saci kallona kafin ta bai wa mahaifiyarta ta amsa da “ Mama in ma aikin ne bai wuce a yi min yadda Ja'afar zai bar ni na tuƙa mota da kaina ba,sam ban son direba kuma ina son zuwa na yi aiki ba wai don kuɗi ba a'a kawai ina ra'ayi” Na lumshe ido jin abin da take faɗa zuciyata na dakan uku-uku,‘wato Ryam ke a tunanin ki na hana ki tuƙa mota ne don wata manufa ba ki san duk cikin kulawa ba ce da tsantsar kishin ki. Maganar aiki kuwa ba zan iya ba ” ban san ƙarshen maganar a fili na yi ta ba sai da na ji ta yi magana a ɗan tsorace “wayyo Allah dama ka na ji na? ” na dube ta muka haɗa ido ta yi saurin katse kiran ta soma yi min kuka ta na rantse-rantse duk ta bi ta rikice ta fita hayyacinta. “Yi shiru mana!” na furta tare da jawo ta jikina, na ci gaba da cewa “ni na yi imanin ki na sona kuma ba za ki iya cutar da ni ba,Ryam na san da ba tun yanzu Mama ke son baki maganin da za ki zuba min a abinci amma kika ƙiya.Ki sani ina mugun son ki ke ce farin cikin da kika rage min a duniyar nan” ina gama faɗa haka na tallabo haɓarta na soma yi mata sumba mai tsaya wa a rai. Sai jan ajiyar zuciya take,motsin da cikinta ke yi yasa na yi saurin tsayawa na ɗage rigarta ina kallo sai motsin yake har yanzu.Wani mugun daɗi ya ƙara luluɓe ni na soma shafarsa,“Daddy na son ka babyna..” Ryam ta yi saurin katse ni “a'a mace ce wannan karon don wallahi har mafarkinta na yi” Na dube ta cike da so na ce “to Ammyn Abrar ” Ryam ta saki murmushi mai sauti ta na shafar gefe da gefen fuskata inda ke da saje “ina sonka Shalele” ƙuri na yi mata da ido ta hura min iska na lumshe ido da sauri. “Shalele na ce ba in na mutu wurin haihuwa ya za ka yi?” furucinta ya yi mugun bala'in dakar min zuciya ban san lokacin da na zabura ba.“Ni za ki tonawa asiri Ryam? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” na furta tare da miƙewa tsaye dukkan jikina na rawa,kaina na bala'in sarawa yayin da zuciyata ke barazanar faso allon ƙirjina ta fito. Ina jin lokacin da ta dafa bayana “Shalele...” cikin tsawa na ce “babu abin da za ki faɗa min Ryam! ” sai kuma na juyo muna facing juna kamar wani zararre na kamo dukkan tafukan hannunta na ce “faɗa min duk rintsi ba za ki tafi ki bar ni ba” Idonta tab ƙwalla ta ce “na yi maka alƙawari za mu rayu tare kuma za mu mutu tare” na jawo ta na rungume ina furzar da huci duk da cewa na san mutuwa ba ta barin wani don wani amma haka kawai yadda furucinta ya tsorata ni na ji ina son jin tabbacin ba za ta tafi ta bar ni ba. A wannan ranar ban san mi ya shigi Ryam ba sai ta bani kulawa fiye da ta kullum,feshin kalaman soyayya kam ba a magana. A washegari ne kuma jirgin su Mama ya sauka a Kamaru,tun a cikin daren na kai Ryam gidansu a can ma ta kwana.Tun da safe bayan na je can ofis sai na wuce gidansu wuraren ƙarfe goma,na samu tarba mai kyau kamar yadda aka saba yi min.Ina cin abinci amma fuskar Ryam sam babu walwala,ina ankare kuma da Mama yadda take jifarta da muguwar harara.Gabana ya faɗi ‘kar dai ace muguwar uwar can magani ta zuba min cikin abinci?’ na tambayi kaina a zuci amma don son tabbatar wa kawai sai na ce “Ryam zo mana” jikinta na ɗan rawa ta taso ta zo gare ni,ba tare da jin kunyar komai ba na jawo ta na ɗora ta kan cinyata “kin wani tsare ni da ido halan ba ki ci komai ba?” na faɗa ina mai kai cokalin abinci bakinta,ta girgiza kai ta ce “na ƙoshi” na ɓata rai na ce “wallahi sai kin ci ko kuma mu ɓata” Ta ɗaga ido ta kalli Mama ta buɗe baki da niyyar magana na saka mata abinci a doli ta ci ta na wani zaro ido. Na yi murmushi na ce “abincin yayi daɗi fa har da wani ɗanɗano na musamman kamar yaji kamar citta” Ryam ba ta ce komai ba ta dai sunne kanta,kafin kuma in ga ta dafe ciki “mine ne?” ba ta bani amsa ba sai ƙara da ta saki,hankalina ya tashi musamman da ta fara cewa “wayyo zan mutu ana halbi na” Mama ma ta soma tambayarta amma ta ƙi bamu amsa,hannuna na rawa na kira Goggo Dije tare da sanar da ita su yi sauri su zo ita da masu kula da lafiyar Ryam. Cikin mintinan da ba su wuce goma ba Ryam ta haɗa uban gumi sai zufa ke mata tsiyaya duk da kuwa akwai sanyin AC.Ina daga gefe na ƙurawa cikinta ido da nake ganin shatin yatsun ƙafa jariri kuma sai motsi yake kamar zai fasa cikin ya ɓullo.Ko da likitocin da goggo Dije suka iso suka fara duba ta “naƙuda ce ta soma ya kamata a mayar da ita keɓaɓen wuri” haka ina ji ina kallo aka shiga da Ryam cikin ɗaki,tsawon lokaci kafin na ji muryoyinsu ana cewa “ma sha Allah yarinyar tubarkallah kamar ba ƴar wata bakwai ba” Ban ji kukan jaririyar ba kamar yadda duk in baby ya zo duniya yake yi ba,kawai sai na ɗauka ita ma ɗin a mace ta zo.Amma ga mamakina sai ganin Goggo Dije na yi ta fito fuskarta cike da annuri ta na cewa “ angon jego barka ” sai a lokacin Mama ta miƙe ta na tambayar mi aka samu. Goggo Dije ta ce “a kawo zane an samu ƴa mace” ita ma murnar ta hau yi,ni kuwa har izuwa yanzu ina cikin tsaka tsaki ina nan har tsaye har sai da aka fito da babyn cikin zane fara sol da ita kamar baturiya. Na karɓe ta ,haka kawai na ji gabana ya faɗi lokacin da idona ya sauka kan kyakkyawar fuskarta mai bala'in kyawu.Dukkanmu daga ni har Ryam baƙaƙe ne amma kuma ga baturiya mun haifa,kamar Goggo Dije ta shiga zuciyata sai ji na yi ta ce “babyn nan dai ina tsoron farin Gambo ta biyo” ta na nufin mahaifiyata wacce ta kasance albino ce an haifeta ne bayan ƴan biyu maza shi yasa ta ci sunan Gambo. Na ja ajiyar zuciya ina jin son babyn na ratsa min zuciya,na kai baki na sumbaci goshinta sai na ji gau kamar wuta da sauri na janye ina mai ci gaba da kallon ta daidai nan ta buɗe idonta taram cikin nawa kai kace wata mai wayo har wani taɓe baki take yi amma sam ban kawo komai a raina ba na miƙa wa Mama ita sannan na wuce ɗakin da Ryam take. Ina ganinta na san ta galabaita,na je na sambace ta na ce “sannu jarumata ” ta ce “ina Abrar ɗin?” “Ta na wurin Mama” ban rufe bakina ba sai ga su kuwa sun shigo,Mama ta miƙa wa Ryam babyn ta karɓa ta na kasa ɓoye tsantsar farin cikinta ba tare da ta san farkon uƙubar rahuwarta ne zai soma...... [19/06 à 14:02] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔 *INUWATA DA TA GABATA*🕸️ 🦔🦔🦔 ```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)``` MRS SADAUKI💫✍️ FCWA ☀️ Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa) _____________________________________________________________________________________________ *Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina* 5 Cikin ƙanƙanen lokaci ƙaruwar da muka samu ta Abrar ta karaɗe garin Kamaru,tuni kuma muka koma can gidanmu da babynmu.Cikin zumuɗi Ryam ta ɗauko awarwaron da ta saya ta saka wa Abrar shi,a gaban idona babyn ta wani zabura ta na juya hannunta kafin ta fashe da kuka. “Ryam ina ga awarwaron nan ya matse ta kawai a cire” na furta ina ƙoƙarin cire shi ɗin ,Ryam ta hana ni ta fara ririga Abrar “shuuut! Yi shiru mana yarinyata,ado ne na yi miki ba ki ga hannun ki har yayi kyau ” duk yadda take ririga babyn amma ta ƙi yin shiru,, Goggo Dije ta shigo ta na cewa “ oh yarinyar nan tun da aka haife ta yanzu kawai na ji kukanta har mitsikarta nurse ta yi amma ta ƙi kokawa ,ina cewa kishiyar tawa soja ce ashe ragguwa ce miƙo min ita na yi mata wanka ga ruwan zafin nan sun tafasa ” Ryam ta miƙa ta babyn ta na cewa “ ai kuwa dai duk kukan nan saboda awarwaro take yinsa kamar wacce ake cire wa rai” Goggo Dije ta zauna ta na son cire awarwaron amma abun mamaki ya ƙi fita ga Abrar sai kuka take kamar ranta zai fita, wannan kukan da take yi ni kuwa sosai yake taɓa min zuciya na ce “ƙila kuma yunwa ce take ji” “To bari na yi sauri na yi mata wanka sai a bata ta sha” cewar Goggo Dije ta na mai tsoma ta cikin ruwa,tsit Abrar ta yi ta bar kukan sai ajiyar zuciya.Ni ma sai na ji raina yayi sanyi,ina kallo har aka yi mata wanka aka naɗe ta a towel aka miƙa wa Ryam ita ta soma bata bata nono.Ta na gama sha ta yi bacci sai wani jan numfashi take,a doli na fita saboda yadda ƴan Barka suka fara shigowa. A farfajiyar gida na zauna na soma kiran abokaina ina shaida musu Madam ta sauka lafiya.Ina nan zaune sai ga Alhaji Hamza babban abokina wanda muke raba ɗan fara guda,da murna muka rungume juna ya na cewa “barka! Barka Alhaji Ja'afar lokaci yayi mai haƙuri mawadaci” Bakina kamar gonar auduga na amsa “barka kade abokina,dama haka Allah ke al'amarin shi.Ya gida ya yara?” “Duk lafiyarsu lau,in sha Allah zuwa gobe Madam za ta zo yanzu ma su na can gidan ƙanwarta su na shagalin suna” “Bai komai Allah nuna mana,ya kasuwanci?” Ya ce “komai na tafiya daidai,ya maganar Nera an ce ta faɗi warwas ” Na ce masa “ai ni na fita sha'aninta kawai na maida hankali wurin saffarar kayan ƙasashen ƙetare ina son ƙara buɗe wani kamfanin zuwa Hajj da umara ” Alhaji Hamza yayi ƴar dariya ya ce “abokina ka san mi na tuna ?” Na ce masa “a'a sai ka faɗa” Ya ce “lokacin da muna yawon ƙwadigo duk kayanmu a koɗe wasu ma sun cire yanzu kuwa dubi gizner da muke sakawa,ka ga gidan ka kamar filin idi tsabar girma ga motoci jibga-jibga ,lamarin Allah kenan ” Shiru na yi ina tuna tsohuwar rayuwar tamu,wacce ta na ɗaya daga cikin abin da yasa sam ba na ƙyama ko gudun talaka na san zafin talauci.Shi yasa nake girmama masu aiki ƙasa da ni ban taɓa jin wannan girman kan irin na masu kuɗi ba,ci gaban maganar shi ne ya yanke min shirun da na yi. “Ita rayuwa sadaukarwa ce muddin ka na son canji,abokina talauci bai yi ba .Arziki shi ke kankaro wa mutum rigar mutumci,dubi goggon ka Dije sai ka ce ba ita ce wacce take koro mu ba in mun je gidanta yanzu ga shi ta ɓararaje ta na cin arziki” Murmushi kawai na yi,Alhaji Hamza ya ci gaba da cewa “ya kamata fa mu je can Asungula” Murmushin da ke kan fuskata ne ya ɗauke ɗif raina yayi bala'in ɓacewa in akwai abin da na fi tsana shine dajin Asungula da duk wani abu da ya shafi can. “Yi haƙuri mana dama wasa nake,zan tafi sai goben” Alhaji Hamza ya faɗa ƙila ya lura da yanayin da na shiga. Har bakin motarsa na yi masa rakiya sannan na koma can ciki,direct ɗakina na shiga na kwanta kan bed ina tunanin *INUWATA DA TA GABATA* sam ban son tuna abubuwan da suka shuɗe,hasali ma a doli na mantar da kaina su amma yanzu Alhaji Hamza ya faman min ciwon da ya daɗe ya na murƙusa ruhina.Na lumshe ido ina yi wa Ubangiji hailala,da wannan tunanin bacci ya ɗauke ni na kuma tsunduma duniyar mafarki. A tsaye take da fararen kayanta kamar yadda ta taɓa zuwar min lokacin da muna Dubai .Idonta fari ƙal da su babu ɗogon baƙi sai shatun busashen jini a kumatunta. A hankali na fara takawa inda take har na iso dab da ita na kamo hannunta “Ummaaa!” na furta daidai nan kuma ta ɓace ɓat ta bar ni da awarwaron hannunta wanda yake ta ƙyalli cikin tafin hannuna.Ruwan sama suka fara sauka ,a sannu a hankali dattin da ke jikin awarwaron ya fara fita kyawawan duwatsun suka fara bayyana a gare ni. Kukan Abrar ne ya tashe ni daga baccin,na zabura na tashi zaune na dafe zuciyata da ke bala'in bugawa videon mafarkina na dawo min a kai sai dai duk da haka ban mayar da hankali kan awarwaron da na gani a hannun Umma sak irinsa ne wanda Ryam ta saya. Da sauri na fita zuwa falo ina tambayar “lafiya kukan mi take yi?” Ryam na hawaye tace “Shalele zo ka ga zabura take kamar wacce aljanu suka taso wa” “To mine ne na kukan kuma?” na faɗa tare da karɓar babyn ai kuwa ta yi shiru ta na jan numfashi . “Sai kin dinga bi a hankali wurin ɗaukarta don jikinta bai da wani ƙwari sosai” na faɗa ina kallon Ryam wacce ke shafar ƙwalla ƙila ta ji tsoro ne kar ita ma ace wannan ɗin mutuwa za ta yi kamar sauran. Sai da baby ta koma bacci sannan na aje ta na je na shiga toilet domin yin wanka sai dai abun mamaki ruwan sun ƙi zuwa.Har zan mayar da kayana sai kuma suka fara sauka a hankali,na ɗaga kai sama na kalli shower idan ba gizau idona ke yi ba kamar fata maciji nake gani daga cikin hudodin.Kamar wanda aka shuka haka na yi tsaye ina kallon ikon Allah har na soma jin “surururuuu!” alamun ana tafiya daga can cikin ƙarfen pampon sai kuma ruwa shaaaa.Da sauri na rufe ido,hancina ne ya shaƙo min wani ƙarni marar daɗi a nan take ya haifar min da amai na shiga kwarara shi kamar raina zai fita sam ban yi lura da irin halittun da ke fitowa bakina ba wasu ƙananun tsutsotsi ne. Ko da aman ya tsaya sai na ji kamar na fitar da wata guba na ji sakau babu nauyi.Dakyar na yi wanka na fito na shirya cikin jallabiya na fita zuwa masjid saboda kiran sallar magrib da ake,ba ni na dawo ba sai kusan ƙarfe goman dare.A falo na tarar da su ana ta hira,inda Abrar ke kwance na nufa na je na ɗauke ta na ce “bacci ma take” Ryam ta ce “tun fa na ɗazu ne lokacin da ka ɗauke ta har wankan da aka yi mata ba ta farka ba” “Shi ne kuma ba ki tashe ta ba kika bata abincinta?” na faɗa a hassale cikin ɗaga murya tsit falon yayi yayin da Ryam ke ƙyafƙyaf da ido. Na tamke fuska na ce “kin ga in kin san ba za ki iya kula min da ita ba na nemo mai raino ko madara ce sai a dinga bata,sama awa biyar yarinya na bacci ba za ki tashe ta ba in fa yunwa ta kama ta?” Goggo Dije ta ce “haba Ja'afar ya za ka dinga yi mata magana haka ? Ita fa ta haife ta akwai wanda zai fita son ta ne? Dama can jarirai lokacin baccinsu ya fi yawa kan wanda suke ido biyu” Na ce “duk da haka dai Goggo ai sai a tashe ta ,na san da Dr Hannah ta dawo duk hakan ba zai faru ba ita ma sai ta yi faɗa” “To sai ka kai wa Dr Hannah ɗin ta shayar da ita” Ryam ta faɗa tare da direwa daga kan salon ta wuce ƙuuu ta shige ɗaki,na bi bayanta da kallo kafin na take mata baya ina rungume da Abrar. “Ke mine ne haka wai? Daga na faɗa miki gaskiya shikenan sai fushi?” na faɗa cikin sigar rarrashi amma sam Ryam ba ta saurare ni ba ta ci gaba da danna wayar hannunta can na ji muryar mahaifiyarta na “Lafiya kike kira na cikin dare?” kuka ta fashe da shi kafin ta soma yi mata bayani a ƙarshe ta ce “wallahi Mama ashe kin yi gaskiya Ja'afar ya bar sona Abrar yake so a kanta fa yake ɗaga min murya abin da bai taɓa yi ba” wayar a hand free take hakan yasa ina jin duk abin da suke cewa. “Jarrrr ubaaa! To ya kai wa uwar Dr Hannah ɗin ta shayar da ita ai na ga alamu wani tashen rashin mutumci yake ji haka fa ɗazu a gaban idona ya ɗora ki kan cinya shi ga ɗan iska don ya nuna min abin da kuke yi ko a gidan,to ai ba sai yayi hakan ba iya cikin jikin ki ma ya isa ya sanar da ni amma bar shi da ni yake zancen gani nan zuwa” ƙittt ta kashe kiran. In raina yayi dubu to ya ɓace ,sam ban san Mama wacce irin uwa ba ce mai ɓata tarbiyyar ƴaƴanta.Har zan yi magana baby Abrar ta fashe da kuka sai inyaaa ! Inyaaa take,na ja wata ajiyar zuciya na ce “ki yi haƙuri Ryam na tuba ba zan sake ba ungo bata ta sha ƙila yunwar ce ta tashe ta” Wani mugun kallo ta yi min ta na cewa “ai kai ma ka na da shi sai ka bata,ko kuma ka kira a kawo Dr Hannah ɗin a yau ai ka na da iko” Ban kula ta ba na je na ɗora Baby kan cinyarta ,da ƙarfin tsiya na yaga rigar jikinta sannan na fara taimakawa Abrar ta soma shan abincinta baiwar Allah yunwar kuwa take ji.Tun Ryam na motsi har ta bari,a ƙarshe kuma ta tallabe ƴarta ta ci gaba da shayar da ita. Na saki murmushi na ce “ai dama uwa da ɗa sai Allah,ga shi har kin haƙura” Ryam ta yi saurin janye Abrar ta ce “na fasa shayar da ita ɗin kuma wanda na bata sai ka biya ni kiɗinsa”sai kawai ta fashe da kuka haka ma babyn kukan ta canyara,duk yadda na so ta ci gaba da shayar da ita ɗin abu ya faskara har Goggo Dije ta shigo ta yi lallaɓar amma ta ƙi a ƙarshe ta fita da ita ta soma bata ruwan ZamZam ta na sha. Waya na yi akan a sayo madara da biberon babu jimawa kuwa aka kawo, Goggo Dije ta haɗa ta baiwa babyn ta sha ta ƙoshi sai bacci. A yadda Mama ta shigo falon sam babu alamar rahama kan fuskarta sai da na ji tsoro,“Maryam? Maryam fito mu tafi” shi ne abin da ta faɗa cikin ɗaga murya kafin ta ɗauki Baby Abrar,ita kuwa Maryam tuni ta fito daga ni har Goggo Dije babu wanda ya ce musu kanzil har suka fice. MARYAM Duk abin nan da ya faru ta biye wa Mama ne don Ja'afar ya ji tsoro ya shiga hankalinsa amma sosai soyayyar ɗiyarta ke danƙare a zuciyarta.Bayan sun fito ita da Mama ta karɓi Abrar suka shiga mota,har suka isa gida Mama na ta faman yin masifa ita dai Maryam kawai saurarenta ne take amma ba ta niyyar cutar da Ja'afar ta hanyar yi masa asiri. Sabon zanen gado Mama ta shimfiɗa sannan Maryam ta hau ta zauna ta na shafar gashin Abarar. “Ki yi kwancin ki nan ba za ki koma ba sai ya zo ya baki haƙuri” Cewar Mama ta na aje kaskon turaren wuta. Maryam ta ce “Mama tun gida fa sai da ya ban haƙuri” “Ke ni dai kwanta sai da safe ” “Mama ki kwanta nan tun da Abba bai gida” “A'a akwai aikin da zan yi cikin daren nan,na ga alamun shegen mijin nan naki sai mun tashi tsaye a kansa” da ace Mama ta kalli Abrar to da ƙila ta ga irin mugun kallon da jaririyar ke yi mata mai cike da tsana sai dai har ta fice ba ta waigo ba. Maryam ta ce “oh babyna kin tashi” sai kuma ta yi shiru ganin yadda Abrar ɗin ke juya ido wasa ta yi ta yi mata kafin bacci ya ɗauke ta.Ko minti biyu Maryam ba ta yi ba da fara yin bacci Abrar ta tashi zaune ta na raraba ido ko ina,kafin ta hango window.Kallo ɗaya ta yi wa ƙwan lantarki nan take ya fashe da shi da sauran duk ƙwayaƙwayin da ke gidan.Hayaƙin turaren wutar da ke tashi sama ta yi tsalle ta haye kansa kafin ta ja reshensa ta ja shi yayi tsayi ba ta sauka ko ina ba sai a ɗakin Mama. Za ku iya fara yin payment ɗin ku tun yanzu,don a page 7 zan tsaya da free page.My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [20/06 à 18:18] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔 *INUWATA DA TA GABATA*🕸️ 🦔🦔🦔 ```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)``` MRS SADAUKI💫✍️ FCWA ☀️ Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa) _____________________________________________________________________________________________ *Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina* 6 Idon Abrar a birkice baƙi ƙirin ta yi saukar ungulu a ɗakin Mama wacce ta baje kayan da malamai da bokaye suka haɗa mata. Sam idonta ba sa ganin Abrar sai hayaƙin turaren wuta wanda har yanzu da ƙamshinsa,cike da mamaki Mama ke kallon hayaƙin wanda duhun ɗakin sam bai ɓoye shi ba. Motsi ta soma ji kamar ana wasar guje-guje,shuuu! Ta ji an bi ta gabanta da gudu haka ma ta bayanta.Da sauri ta juya kafin kuma ta fara laluban wayarta,hannunta ta tsinta tsamo-tsamo cikin jini jikinta na rawa take kallon yadda jinin ke ɗiga da ƙasa har wani ɗil! Yake yi . “Mike faruwa da ni ne? Ya ban ganin komai sai hayaƙi da jinin?” ta tambayi kanta ta na mai kai hannunta kusan fuskarta don sake tantance wa sai kuma ta ji ƙuuu! Rudududuuu! An wuce da mugun ƙarfi a can saman rufin ɗaki kamar za a faɗo ciki. Hankalin Mama bai ida tashi ba sai da ta soma jin ƙurmus! Ƙurmus ! Kamar ana cin ƙulli a ƙarƙashin gadonta.Da gudu ta nufi hanyar da za ta fitar da ita daga ɗakin,ta ci burki ta ja ta tsaya ganin handle ƙofar ya soma rikiɗa ya na fitar da wani kalolin haske ko kafin Mama ta ida tantance mine ne a gabanta ta ji wani irin cizo gefen wuyanta.Ta ƙwala uban ihu kafin ta zube nan ƙasa warwas,Abrar ta haye bindin macijiyar ita kuma ta mayar da ita can ɗaki kusa da Ryam wacce ke ta sharar bacci. Washegari sai ga Mama da kumburaren wuya kamar wacce ta kwana ta na busa wuta.Har aka yi wa Maryam da ƴarta ruwan ɗumi suka yi wanka Mama ba ta leƙo su ba,Goggo Dije wacce tun asubar farin ta dira gidan ita ce ma ta yi ƙarfin halin tambayar Mamar mafarin ta fito kenan. “Mine ne ya same ki Mama?” Ryam ta tambaya cike da tsoro. Dakyar ta iya buɗe baki ta basu labarin irin uƙubar da ta gani daren jiya,nan fa tsoron Ryam ya ƙara hauhawa ita da take cewa sam ba za ta bi Goggo Dije ba har sai in Ja'afar ne ya zo da kansa . “Ki na nufin fatalwa kika gani Mama?” “A'a ya za ki ce haka? Ai sam shirme ne babu fatalwa a duniya ƙila ruɗewar da ta yi ne sakamakon cizon yasa idonta ba su gane mata daidai ba.Mu ga wuyan?” cewar Goggo Dije, Mama ta ɗan rage tsayi ta yadda za a ga wurin da kyau. “Kin ga Maryam zo ki ga yadda sawun haƙora suka fito ras” “Wannan ai haƙoran mutum ne ba maciji ba Goggo ” Ryam ɗin ta faɗa. “Ya kamata dai a kai ta asibiti can su za su san abin da ya kamace ta” “Yanzu nake cewa zan kiran exellency sai na shaida masa” Mama ta faɗa ta na matsar ƙwalla. “Yanzu dai zan wuce da Maryam ta koma ɗakinta, wannan ba girman mu ba ne ace hakan ta faru” Goggo Dije ta faɗa. Mama ta haɗe rai sai yanzu ma ne ta tuna sam ba ta ga kayan tsafinta ba duk an kwashe komai,sai dai kafin ta kai ga yin magana Ryam ɗin ta ce “eh Mama gaskiya Goggo Dije ta faɗa ya kamata na koma tun da ga Marfu'a nan sai ta kula da ke” “To ” Mama ta faɗa. Goggo Dije ta ɗauki baby Abrar wacce ke sharar bacci suka fice ita da Ryam direba ya kai su gida. JA'AFAR Sosai na ji baƙin cikin abin da Ryam da mahaifiyarta suka yi min.Ban taɓa jin takaicin zama da mace ɗaya ba sai yau,da wannan baƙin cikin na kwana kuma na tashi.Da na dawo daga sallar asubah kamar wani marar lafiya haka na zube kan salon ina tunanin mafita,a gaban idona Goggo Dije ta fita ko ba ta faɗa min ba na san biko za ta je kuma har ƙasan zuciyata addu'a nake yi Allah sa Ryam ta haƙura ta dawo.Don ba ƙaramin abin kunya ba ne abokaina su zo ganin baby na ce musu Madam na gidansu.Ganin kewar za ta yi min yawa yasa na ɗauki waya na fara shating,status ɗin Dr Hannah na gani ta ɗora video ta na sanye da farin hijabi a saman kanta kuma ta ɗora jan hirami na maza ta na yin magana cikin harshen larabci kai kace Yarenta ne tun asali.Ban yi wani dogon karatun Addini ba amma na ɗan tsinci wasu kalmomi da na fahimta,wato godiya take yi wa Allah da suka gama Hajji lafiya sannan ta sanar da cewa a yau za su dawo.Tamkar wani gara haka nake ta maido videon baya ina sake kallo,laɓanta irin baƙaƙen nan ne duk da fuskarta na fara .Ta saka hauren maka har guda biyu sosai suka ƙara mata kyau,dakyar na iya barin videon na ci gaba da kallon sauran hotunan da suka yi ita da ma'aikatan gidana. WhatsApp ɗina ba GB ba ne ballantana na ɗauki video ɗin,sai kuma na ji nauyin in ce mata ta turo min ita.Na shafi gefen wuyana ina murmushi wanda ban san ko na mine ne ba,na shagala sosai wurin kalle status Dr Hannah su Goggo Dije suka shigo.Kukan Abrar ne ya fargar da ni,na ɗago kai na dubi Ryam wacce ta yi tsaye ƙiƙam kamar wata baƙuwa . “Zauna ki shayar da ita,kin ga tun da na yi mata wanka take baccin nan” cewar Goggo Dije . Ina kallon Ryam ta zauna a sanyayye kafin ta ɗora wa Abrar maman amma ta ƙi karɓa sai kukan take ci gaba da yi. Na kawar da kai gefe ganin ta na kallona,karon farko da ban ji wannan shauƙin son nata ba . “Goggo zo ki ga ta ƙi karɓa wanda nake ɗan matsa mata ma ga shi nan ta na maido shi” Ryam ta faɗa cikin rawar murya. Duk yadda aka so Abrar ta sha maman ƙiya wa ta yi,a ƙarshe Goggo Dije ta kaɗa madara ta soma bata abin mamaki sai ta yi shiru ta na sha har wani tsutsutsu kake ji ta na kame kan biberon ɗin. “Daga yau a dinga bata madarar Goggo ” na furta ina mai tashi na shige can ɗaki,jallabiyata na cire na shiga toilet.Na lumshe ido ruwa na dukan fuskata babu abin da nake gani sai murmushin Dr Hannah da kyawawan haƙoranta da suka sha adon hauren Makka . Ƙiiii! Na ji ƙarar buɗewar ƙofa,ko motsi ban yi ba ballantana na juya har lokacin da ta yi hugging ɗina ta baya ban juyo ba. “Ka yi haƙuri don Allah Shalele ” ta furta cikin shashekar kuka,sai a lokacin na juyo muna facing juna ni da ita.Ina mugun son Ryam amma abin da suka min ita da mahaifiyarta ina jin kaso biyar ya fita,ban ce mata komai ba sai na soma cire kayan jikinta.A tare muka yi wankan ta bani nutsuwa sosai wacce ta sa zuciyata ta ɗan wanke,da kanta ta shirya ni cikin manyan kaya har da ɗora min hulla.Na sumbaci goshinta kafin na fito falo,Abrar na ɗauka na tsura mata ido ita ma ɗin ni take kallo na saki murmushi na ce “love You babyna ” Goggo Dije ta ce “Allah sa ta amsa ma,a to yaran yanzu ba ku da ta ido a gabana kake irin wannan zancen” Na yi murmushi mai sauti na ce “haba dai Goggo in ba kula da Abrar ba na bata dukkan soyayyata wa zan bai wa? Ita kawai gare ni fa” sai kawai na miƙa mata ita.Ina kallon ta taɓe baki kawai amma ba ta ce komai ba,a harabar gidana na fita direba na ganina ya rugo da gudu ya na tambayar inda zan je. Na ce “no yau da kaina zan yi tuƙi” “To yalaɓai wacce motar za ka hau?” “Fara” “Wace daga ciki?” “Kunna duk wacce ka ga za ta fi min kyau” ina faɗar haka na wuce cikin lambu,kira na yi aka tabbatar min lokacin da jirgin zai sauka.Na ɗan jima zaune kafin na je na ɗauki motar na wuce filin jirgi,na ɗauki kamar minti talatin sannan jirgin ya sauka sai a lokacin kuma na fara tambayar kaina ‘to wai mi ma na zo yi? Tarben ta? Mi zan ce mata?’ da ire-iren tunanin nan har mutanen ciki suka fara sauka. “Assalamu aleykum !” Dr Hannah ta faɗa lokacin da ta iso wurina,na amsa mata cikin kula wa kafin na ce “Hajj Mabroor!” “Na gode sosai” “Ke ɗaya ce cikinsu?” “Eh su jirgin su bai taso ba” “Okay” na furta tare da yin shiru,ita kuma ina lura da ita sai satar kallona take. “Zan tafi” ta faɗa ta na sunne kai. “Ki jira mu tafi tare mana” na faɗa ina danna waya. Ta ce “ina son fara zuwa gida ne kafin na je can” Na ɗago na tsure ta da ido aka yi sa'a ta ɗago kai idonmu ya shiga cikin na juna,duk sai na ga ta ruɗe. Na ɗan kawar da kai na ce “can ina?” “Gidan ka mana Alhaji !” Na saki murmushi ina mai miƙe wa tsaye,sai da muka je ta nuna ƴan kayan da ta zo da su ma'aikatan wurin suka kai mana su har mota cike da girmamawa. Na buɗe mata mota ta shiga ta zauna,ni kuma na shiga daga can ciki na yi wasu ƴan dube-dube dangane da alhazzai uwanda suka tafi ta kamfanina. “Na tsayar da ke ko?” na furta bayan na shiga na zauna, murmushi kawai ta yi.Sai da muka fita sannan na ce “ina za mu je?” Unguwar da ta faɗa min ta talakawa ce,sosai na yi mamaki jin wai can ne take.Da taimakonta muka shigo layin mai cike da ruwa ko ta ina amma ko kaɗan ban nuna ƙyanƙyami ba,har muka isa ƙofar gidansu. “Ka na nufin ba za ka shiga ciki ba?” ta tambaye ni a lokacin da na yi mata fatan a huta lafiya. “Na ce zan zo karɓar tsaraba ta ai in an jima” Ta washe baki ta ce “to sai ka zo,ina fa jiran ka” na jinjina kai.Sai da ta fitar da kayanta kafin na ja motata na wuce ina ta mamakin kaina shin mike faruwa da ni??????? My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,DM +22795045822 [22/06 à 10:36] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔 *INUWATA DA TA GABATA*🕸️ 🦔🦔🦔 ```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)``` MRS SADAUKI💫✍️ FCWA ☀️ Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa) _____________________________________________________________________________________________ *Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina* 7 Ina tuƙi ina tunanin Dr Hannah,ya aka yi duk uban kuɗin da take samu amma a ce a nan unguwar suke rayuwa? Sosai nake mamakin haka don iya albashin da nake biyanta da shi ya isa ta ɗauki gidan haya mai kyau kuma su ci abinci har na tsawon wata,banda ma asibitocin kuɗi da take aiki don ta na da ilimi sosai za a iya cewa ma kusan duk Kamaru ita ce lamba ɗaya a mata in dai fannin aikinta ne.A haka na nufi can kasuwa inda nake da manyan shaguna da ake kula min da su,lokaci zuwa lokaci kawai nake zuwa can don duba yadda komai ke tafiya. DR HANNAH Faɗin farin cikin da ta yi da Ja'afar ya ce ta shiga motarsa Allah kawai ya san wannan,har suka iso ta na mamaki gani take ma kamar mafarki ne take wai yau ita ce a motar shi ya na tuƙa ta domin faranta ma ba don saboda ta je duba lafiyar matarsa ba. Ta na shiga gida aka hau murna tare da ƴan gaishe-gaishe,maƙobta ma duk sun shigo yi mata sannu da zuwa Umma ce ke raba musu dabino da kuma bagaruwar Makka .Haka suka yi ta shigowa har suka ɗan tsananta,wanda hakan ya baiwa uwa da ɗiya zantawa. “Hannatu ya hanya fatan kin yi aikin Hajj lafiya? Allah sa karɓaɓiya ce” Umma ta tambaya. “Lafiya lau Umma alhamdullah,Amen ya Rabb ” Dr Hannah ta amsa murmushi na kan fuskarta wanda shine ke ƙarawa ummar kwanciyar hankali. “Umma Alhaji fa ya kawo ni ” ta ƙara faɗa ta na wasa da yatsunta. Umma ta murmusa ta ce “ ki yi ta addu'a Hannatu in sha Allah za a dace ai Allah da kansa yayi alƙawarin cewa in ka roƙe shi zai baka” “Umma tun da na dira a Makka babu wata addu'a da zan yi ba tare da na ce Allah ya mallaka min Alhaji ba,har kuka na yi fa na kusa da ni dai su na kallona.Umma kuma fa kamar Allah ya karɓi addu'a ta inda kin ga yadda yake kallona” ta yi furicin cikin tsantsar farin ciki,Umma ta karɓe zancen “ in ba abun ki ba Hannatu ka yi addu'a nan ya karɓa ballantana a ƙasa mai tsarki? Ke dai kawai ki ci gaba da riƙe Allah don in kin kama shi kin gama komai tashi ki yi wanka ki zo ki ci abinci” Dr Hannah ta miƙe ta ce “to amma dai ban jin yunwa” sai da ta rage kayan jikinta sannan ta cika bokiti ta je ta yi wanka.Bayan ta fito ne ta shirya cikin baƙar abaya ta yane kanta da kallabi,ƴar ƙaramar jakar nan ta mahajjata ta ɗauko ta fiddo tsarabar da ta yi wa Umma ta bata turare ne mai shegen ƙamshi umma sai godiya take,“sai sauran kayan sun zo ma ki ga abubuwan da na sayo miki ” “Ko wannan ma yayi na gode,ina na Alhajin?” Umma ta tambaya cikin zolaya,Dr Hannah ta shiga yin dariya ta na rufe fuska kafin ta ce “ wannan dai nake son kai wa matarsa tun da ta na jego kin san sai da turare” “Eh kin kyauta kuwa” nan dai suka ci gaba da yin hirarsu. ★ Ana gama sallar magrib na koma gida na ƙara ɗaukar wanka sannan na nufi gidansu Dr Hannah.Tun a hanya na sanar da ita,ina isa na kira ta a waya ta na ɗauka ta ce min “ ka shigo daga ciki mana Alhaji” Na ce “ki fito ki min iso dai” da “to ” ta amsa ni kuma ina zaune ina ta mamakin kaina don har yanzu ganin abin nake kamar wasar kwaikwayo. Ina ganin ta fito na yi saurin buɗe mota,ta yi tsaye ta na gaishe ni ban amsa ba sai ƙare mata kallo nake cikin abayar da na ga ta mayar da ita kamar balarabiya. “Mu je ko” ta sake faɗa,sai a lokacin na dawo hayyacina na ce “ok to” sai na fito ta na gaba ni kuma ina take mata baya muka shiga farfajiyar gidan wacce ke ɗauke da ƙaton icce ,ko ina fes da shi babu ƙazanta haka komai na wurin da ya dace. Da na shiga falon kuwa ƙamshin turaren wuta ne ke tashi,tun daga kujerun ɗakin har labulayen dukkansu fes da su babu ƙazanta. “Ka zauna ga wuri nan” cewar Dr Hannah lokacin da muke gaisawa da Ummarta.Na ɗan harare ta kafin na ce “nan fa ba asibiti ba ce ballantana ki ce ke ce shugaba ” Umma ta yi dariya ta ce “in dai Hannatu ce akwai matsuwa,in banda lafiya haka take matsa min wurin shan magani” Na ce “ai kuwa dai kuma ƙila ita ba ta son shan maganin” “Ina sha allura dai a ban so” sai a lokacin ta yi magana kafin ta kawo min ruwa masu sanyi na sha,Umma ta miƙe ta koma can ƙurya ɗaki sai ya zamana daga ni sai ita a wurin. A yadda na ga ta na wani sunne kai sai abin ya bani mamaki,ita da kullum cikin yi min kallon bege take yau kuma da na kawo kaina shine ta wani sunne kai. Na yi gyaran murya na ce “ don Allah Dr Hannah nake nema ba Hannatu ba” Da sauri ta ɗago kai muka haɗa ido,wani irin daram na ji yadda idonta suka sha baƙin kwalli suka ƙara haske sai na ji ya tafi da imanina ban sani ba ko don Ryam ba ma'abociyar saka shi ne ba? Ita kanta Dr Hannah ɗin na yau ya sha banban da na kullum. “Ni dai don kar ka sake ce min Hannatu ” ta faɗa cikin wata yanga,na kuwa shagala da yadda take maganar kafin na yi dariya na ce “ au! Dama kwaskwarima ne kika yi wa sunan naki? To ni ma Hannatun zan dinga cewa” “Ni kuma na ce Alhaji Jafaru ” Yadda ta kira sunan sam kasa riƙe dariyata na yi sai da na dara,na ce “Allah sarki sai kika tuna min da Momah ” “Wace ce haka?” “Mamana mana wacce ta rasu” “Wai dama ba Goggo Dije ce mahaifiyar ka ba?” Na kalle ta cike da mamaki na ce “sai yau kika sani? Momah ta rasu fa shekaru wajen biyar yanzu” “Allah ya jiƙanta yayi mata rahama” Na ce “Amen!” sai kuma na ɗauki wayata na shiga gallery na nemo hoton Momah na ce “ kin ga hoton ta” ta taso daga inda take ta karɓi wayar ta tsure hoton da ido,kafin ta ce “ni kuwa kamar na san matar nan hoton bai fita da kyau ba sosai” Na ce “ eh shi ma dakyar na same shi” ta bani wayata na dube ta na ce “ba za ki je ki ga Baby ba?” Ta langaɓe kai ta ce “wai da sai gobe na je” Na haɗe fuska na ce “ Dr Hannah ki ji tsoron Allah ke ce fa mai kula da ita haihuwar nan in ba don ta zo cikin wani yanayi ba ke ce za ki karɓe ta” Ta turo baki ta ce “bari na tambayi Umma in za ta bar ni ” sai kuma ta wuce can ƙurya ɗaki ta ɗan jima kafin ta fito ta ce “ tashi mu je” Umma ta fito muka yi ban kwana sannan muka fito,ina tsaka da tuƙi ta miƙo min wani ɗan ƙaramin akwati ta ce “ ga tsarabar ka” na karɓa ina murmushi na ce “na gode mine ne a ciki” “In ka buɗe za ka gani” ta ban amsa daga nan ba mu sake magana ba har muka isa gidana. A waje na tsaya ita kuma ta wuce ciki,Dr Hannah ta shiga da sallama duk aka amsa mata. Fuskarta fal annuri ta soma yi wa Maryam Barka tare da tambayarta jikinta,sanin ita ɗin likitarta ce yasa take bata amsa daki-daki. “Nurse Jamila miƙo min kayan aiki na duba ta” cewar Dr Hannah ta na gwale idon Ryam,nurse Jamila wacce ta na ɗaya daga cikin uwanda suke taya Dr Hannah aiki ta yi sauri ta je ta ɗauko kayan a ɗakin da Ja'afar ya ware matsayin ɗakin kula da Ryam. Awon tension ta soma yi mata sannan duba bugun zuciyarta,“mike damun ki haka ne? Ki na cin abinci kuwa? Shayi fa bai yi miki a yanzu doli ki dinga ci ki na ƙoshi yadda baby za ta samu nono” “Ruwan nonon ma sun tsaya sun bar zuba fa” Ryam ta bata amsa cikin wani yanayi. Dr Hannah ta ce “ kamar ya sun bar zuba? Ku haɗo mata tea a saka garin hulba a ciki ta sha.A kawo babyn mu ga ta ɗora ta” Goggo Dije ce ta ɗauko Abrar wacce ta lumshe ido kamar mai bacci ta ɗora kan ƙafafun Maryam,Dr Hannah kuwa maman Ryam take matsawa don tabbatar abin da aka ce ɗin sai kuwa ta ga ko ɗigo ɗaya bai zuba ba. “Ɗorata a kai mu ga ƙila ta zuƙo...” ta faɗa ta na mai kallon fuskar Abrar,gaban Dr Hannah yayi mummunan faɗuwa har sai da ta ɗan ja baya kafin kuma ta ƙara gwale idonta sosai kan fuskar Abrar zuciyarta na ci gaba da buga wa yayin da kuma take addu'a Allah sa abin da take gani ba gaskiya ne ba. Ta kai hannu da niyyar taɓa kumatunta,wuluk Abrar ta buɗe idonta suka sauka cikin na Dr Hannah.Muƙut ta haɗiye yawu kafin murya na rawa ta ce “Mar....y.am zan je na dawo kaina na min ciwo” ba ta jira abin da za ta ce ba ta nufi ƙofar fita. Ina tsaye ina waya da abokina da ya kira ni na ga Dr Hannah ta fito kamar a firgice,gabana ya faɗi ina addu'ar Allah sa dai ba Ryam ta yi mata wani abun ba. Har inda nake ta iso,ido cikin ido take kallona kafin ta jefo min wata tambayar rainin hankali “ wane ne kai?” “Ke kin san abin da kike cewa kuwa?” na tambaye ta “Wane ne kai tambayar ka nake kawai ka bani amsa ?” ta min magana cikin ɗaga murya kafin kuma ta fashe da kuka,ta na shirin tafiya na cabko hannunta na ja ta izuwa can baya na tsure ta da ido na ce “mine ne ke damun ki Hannah ?” “Ka bani amsa ta wane ne kai? ” “Ja'afar ne ko ba ki gane ni ba?” Ta girgiza kai ta ce “ bari nuna kamar ba ka san mi nake nufi ba,duk wanda yake cikin ɓoyayyar duniya in aka masa tambayar nan zai amsa kai tsaye ne” Na yi wata irin dariya na ce “ Dr Hannah wai lafiyar ki kuwa? Bayan wannan duniyar har akwai wata ɓoyayya wacce ni ban sani ba?” Cak ta tsaya da kukan da take ta na wani kallona tsakiyar ido kafin ta faɗa min abin da har ƙasa ta naɗe ba zan taɓa manta abin ba,kuma tsanarsa ba za ta fita zuciyana ba. “Za ka iya tuna rayuwar ka ta baya wacce kuka je ƙauyen Asungula ?” Ban san lokacin da na saki hannunta ba ,na soma yi mata wani kallo ba tare da na ce komai ba. Dr Hannah ta ci gaba da cewa “ *INUWAR DA NA GABATA* ce ta soma biyayata,na yi tunanin komai ya ida tun da har na dawo gidanmu amma yanzu abin da na gani a tattare da Abrar....” sai kuma ta tsaya cak kamar wata zararriya ta ce “ Alhaji mu ga hoton nan da ka nuna min na Momah ” Ƙarfin hali kawai na yi na nemo mata shi,“ eh tabbas ita ce! Eh yanzu na tuna! Na tuna Ja'afar kai ne ta ban saƙo wurin ka shekaru biyu da suka wuce don Allah ka faɗa min ka bani labarin ka Momah na cikin matsala ta na neman taimakon mu” Na riƙe kaina da dukkan hannuwana na cikin ƙaraji na ce “ Dr Hannah ya isa ! Mi kike so da ni ? Haukata ni kike son yi? Duk wannan banzan shirmen naki ban gane komai ki fito kai tsaye ki yi min magana ta yadda zan gane” Sai da ta wani zo dab da ni ta min raɗa a kunne ta ce “ Kuɗin ka haramtattu ne,kuɗin ka same su ne ta hanyar sadaukar da jinin Momah ba tare da kai kanka ka sani ba za ka iya tuna ƙauyen Asungula?” Ƙafafuwana ne suka soma yin rawa sam hankalina ba zai iya ɗaukar wannan al'amari ba jiri ya soma ɗiba ta ina shirin zubewa Dr Hannah ta riƙe ni gam.Amma duk da haka numfashina barazanar tsaya wa yake,dakyar ta zaunar da ni ta yi saurin fita daga wurin sai ga ta sun dawo da maza ma'aikatan gidana. “Ku taimaka ku kai shi mota za mu wuce asibiti” Haka suka kama ni aka sani mota aka kai ni babban asibitin da take aiki,ita ce da kanta ta shiga bani taimako.A sannu na fara jin zuciyata na ɗan samu rangwame Dr Hannah ta yi tsaye kai gare ni ta ce “ don Allah ka nutsu kar kasa zuciyar ka ta buga duk abin da ya faru Momah ta faɗa min ta ce ba da sanin ka ba ne ka bayar da ita” Idona suka fara zubar da hawaye na ce “ kalaman ki Dr Hannah su ke ƙara tarwatsa ni Momah ta rasu kusan shekara biyar ki na kuma zancen kin ganta ba a fi shekara biyu ba” Ta ce “ ƙwarai kuwa don ba ka san wace ce ni ba shi yasa ka yi mamaki,amma kafin nan ina so ka ban labarin ka mine ne dalilin da yasa ka sadaukar da Momah?” Tsabar haushi da takaicin da suka rufe ni har bn san lokacin da na zabura na wanka mata mari ba,na ce “ ki tsarkake halshen ki,a duk duniya babu abin da na fi so sama da Momana ita ce komai nawa ta yaya kike tunanin zan bayar da jinin ta?” Dr Hannah ta ce “ za ka iya tuna lokacin da za ka yanka baƙar agwagwar da bokan na ya ce ka yanka ka ji muryar mutum?” tambayar nan da ta jefo min tasa komai nawa da ya wuce ya dawo min a kai,da sauri na toshe kunnuwana saboda sautin abin da ya wuce da ya soma dawo min “ kar ka yanka niiii! Saboda kuɗi za ka kashe niii” ihu na ƙurma wanda yayi sanadiyar faɗuwar duk wani abu da ke wurin ƙwan lantarki ya fashe taratseeee,labulen da ke sarkaye ga window ya soma tashi sama ya na wuwilniya ɗakin ya ɗauki wani irin duhu mai tsanani wanda yayi bala'in bani tsoro.Ba a mafarki ba ido biyu na ga wani haske ya huɗo daga can ƙasa ya dalle idona wanda har ta kai da na sa hannu na kare fuskata. Dr Hannah ta riƙo hannuna ta na cewa “ Ja'afar dubi ga Momah nan ta fito ta na roƙon ka” a hankali na soma ware idon nawa sai dai ban ganin komai sai wani dogon halshe da ke jan ƙasa kamar wani ƙaramin yaro na laɓe bayan Dr Hannah ina ce mata “ aljani! Aljani ne” amma abun mamaki sai na ji murya Momah raɗau a kunnena ta na cewa “Jafaru ka yi abin da ta ce ma” Kamar ƙyabtawar ido kuma sai komai na ɗakin ya dawo normal,na dubi Dr Hannah kallo irin wai duk abin da ya faru gaske ne? Ta jinjina min kai ta ƙara jefo min tambayar nan “wane ne kai?” Ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai tura 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f ,na bar detail ki tura kawai ki turo evidence in kin san ba ki shirya biyan kuɗin karatun ki ba don Allah kar ki min magana na gode.