SHIMFIDA. A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! Me zai faru a lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai? A lokacin da ka shiga shiga cikin wata duniya da zaka ji baka son barinta? ka bi ahalin cikinta kuna nutsewa cikin ramin da baku san dashi ba? ka shagala da kallon FARAR WUTAR da ta juye tunaninsu, ta wanke kwakwalwar su har kowa a duniyarsu ya manta cewar wuta, WUTA ce! Duk kuwa irin FARINTA. #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA ƊAYA. ~~~~~ Wajen karfe goma sha biyu na rana, matar dake cikin kitchen ɗin da aka zagaye da langa-langa daga ɗan madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani ɗaurin itace dake gefe ta ƙara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ƙiyasi. Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa. Sai da ta tabbatar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ƴarta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da komai. Ƴar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai ɗaukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an ɗiga wani abu a cikinsu. "Yi sauri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a ɗora don yanzu zaki ji su sun dawo." Amina ta buɗa labule ɗakin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace. "Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi." "Garin ne ba zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki." Da murmushi tace. "Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta." Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen ruwa da ita tana fadin. "Ki cigaba da addu'a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah." Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi kyau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ƙulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba. Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta daɗe da soke Jami'a a lissafinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa wajen kula dasu da ɗan abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ƴaƴan sa zasu huta da duk wani gata na duniya. Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ƙarama inda zata dan koyi aikin lafiya... Don mahaifiyarta tasha faɗa mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye da ace ta zauna bata yin komai. Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ƙarshe yake a can wata jami'ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kuma hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ƙanwarsa. Mu'amalarsu daban take da yadda take ganin tsakanin ƙawarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko ɗaga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu'amalarsu aure zata kai. "Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa." Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin. "Ta nawa?" Ta tambaya. "Ta naira Ashirin." Sai ta ajiye farantin waken ta miƙe ta karbi kudin, watanni hudu kenan da fara sana'arta ta saida alawar madara, gullisuwa da kuma albishir, kuma ciniki take yi sosai don a kwana uku kawai take sake yin kowannensu na dubu biyu. Wannan shine babban abinda ke ɗebe mata kewa da kuma faranta ranta ganin yadda take iya yin wasu bukatunta da kanta har ma ta taimakawa ƙannenta da ɗan kuɗin kashewa, saɓanin a watannin baya da bata komai. Lokaci shine rayuwarka ta duniya da kuma lahira, babu amfani ka barshi yana tafiya haka sakaka... Kalaman Ammansu kenan a kullum idan tana bayanin abubuwan da suka dace da rayuwar mutum. Ta ɗebowa yaron gullisuwar hade da canjinsa, ta fito daga falon nasu da babu komai sai shimfidadden carpet daidai lokacin da Fatima tayi sallama ta shigo. "Amma ina wuni." Ta gaishe da Ammar dake wanke bayan tukunyar data dauka. "Lafiya kalau Fatima, Hajiyan ta fita ko tana nan?" Hajiya mahaifiyar Fatiman ce, kuma tana zuwa jinyar kakar Fatiman ne da aka kwantar a asibiti kullum. "A'a bata fita ba, girki take yi tukunna." "To bari in gani nima idan na gama nawa ko zan iya bin ta, tun jiya nake waƙar ya kamata in koma wallahi." "Ai jikin nata ma da sauki." Cewar Fatiman tana nufar hanyar ɗakin su Amina rike da ledar hannunta, ganin hakan yasa Amina ta dauko farantin waken da ta gama gyarawa, ta nufi wajen rijiya ta zago ruwa ta wanke shi sannan taje ta zuba a tukunyar dake gab da tafasa. "Kaya Ahmad ya kawo min jiya da yazo." Tana bude labulen ɗakin Fatiman ta fada, da fara'arta kuwa ta goge ruwan hannunta a jikin doguwar rigar da ta saka sannan ta ƙarasa gefen katifarta inda Fatiman ke fito da kayan, atamfa ce har guda biyu da kuma farin mayafi ɗaya sai kayan kwalliya. "Gaskiya ne Fati, wallahi ki gode Allah, Ahmad na ji dake." Fatima ta juya idanunta alamun dadi tana murmushi. Fara ce ita sosai, farin da take alfahari dashi a kodayaushe, tana ganinshine silar samuwar abubuwa da yawa a rayuwarta, don iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne sosai. "Ni kaina wallahi na sani Amina, shi yasa nake gode masa kullum." "Allah kuwa yana da kyauta, Allah ya saka masa da alkhairi... Kai wannan tafi kyau wallahi." Ta fada tana daga wata. "Kamar kin san nima nafi ganin kyanta, har cewa nayi ko in barta sai Sallah kawai muyi ankonta ni dake." Amina ta bude kwalin wata hoda sannan tace. "Sallah fa da nisa, ki ɗinka abarki kawai. Ma yi wani ankon idan lokacin yazo." "To shikenan." Fatima ta gyara zama tana kallon yadda take kallon kayan, sai kawai tace. "Wai yaushe rabon Abdallah da ya miki kyauta ne Amina?" Amina bata bar kallon kayan kwalliyan ba tace. "Shi da yake dan makaranta ta yaya zai iya wata dawainiya yanzu, in dai sallah tazo ai yana min kaya kin sani." Fatima ta tabe baki. "Wannan fa daban, kyauta kuma daban. Ni wallahi Amina na sha gaya miki ki ƙyale Abdallah nan, da tuni kin fara ganin wadanda suka fishi, don naga alama yanzu idanunki basa ganin kowa." Sai a lokacin Amina ta kalle ta. "Fatee, ke fa kin san ni duk wannan abin ma ba a gabana yake ba, shi yasa nake son mu'amala ta da Abdallah saboda shima yanzu karatunsa yake son gamawa, baya takura min nima kuma bana takura masa." "Wai har yanzu kina ganin zaki cigaba da karatun ne?" Ta daga kanta. "Wallahi ban fidda rai ba Fatee, duk da na san Baba ba zai iya ba, kuma babu wanda zai yi min bayan shi din.' "Shi yasa nake gaya miki ki hakura kawai, ba komai mutum yake samu a rayuwa ba, a yanzu auren kawai ya kamata kiyi, ki ragewa su Baba nauyi sannan kema ki sami wajen da zaki iya ɗaukar ɗawainiyar wasu ma." Kallonta kawai Amina take tana murmushi don ta riga ta sani cewa ba zata taba fahimtar abinda take ji a zuciyarta bane, sai da ta kai ƙarshe sannan ta shiga haɗa kayan tanafaɗin. "To shikenan, ki bari sai bayan maulidi, idan mun fara kai ki, sai in fara wannan lissafin. Jin haka yasa ba shiri itama tayi murmushi tana kara juya idanunta, don kamar yadda aka tsayar da rana, bayan maulidin ne bikinta ita da Ahmad din. "Baki san wani abu ba ma, wata mata na samu mai sayar da magunguna a can layin..." Da haka ta shiga bawa Amina labarin da yasa ta bar hada kayan ta zare idanu tana kallonta kafin ta shiga ɗaka mata duka alamun bata son zancen, ita kuma tana kyalkyala dariya. Mahaifin Amina mai suna Alhaji Sulaiman dattijon mutum ne mai sana'ar harkar aikin katako, ya samu wadata a da, don gidan da yake zaune da iyalansa na kansa ne, amma a yanzu abubuwa sun tsaya masa ta yadda ya ɗauki hakan ya sanya a ransa har ya zama shine damuwarsa a kodayaushe. Ƴaƴan sa biyar tare da matarsa Halimatus- Sadiya bafulatanar Niger da iyayenta suka dawo Nigeria da zama. Amina ce ta farko, sai Aminu, Maryam, Adam da kuma autarsu Hafsa. Maryam, Aminu, da Adam suna matakin secondary ne a karatu yayin da Hafsa kadai take Primary, amma da yake makarantar da suke zuwa wata community school ce dake waje ɗaya, tare suke tafiya dukkaninsu tare suke dawowa. Babban damuwar Alhaji Sulaiman a yanzu shine ganin ƴaƴan sa na ƙara tasawa kuma harkar samun sa na ƙara yin baya, karayar arziƙin da ya samu ta taimaka ƙwarai wajen karya zuciyarsa akan komai, kullum cikin lissafi yake da kuma damuwar da ƙarara kowa ke gane ta duk da irin nuni da kuma nasihar da matarsa ke yi masa a kullum. *** Ƙarfe Biyu da rabi. "Yaya dan girman Allah zaki bani naira dari? Ƙunshi zanyi." Maryam ta fada lokacin da take ƙoƙarin cire uniform ɗin ta bayan sun dawo daga makaranta. Amina na zaune tana ninke kayan wankinta tace. "Ƙunshin me zaki yi?" "Bikin yayarsu Na'imah fa, kin manta jiya nazo da katin." Jin tayi shiru yasa ta sake tambaya. "Zan baki Maryam, Allah ya kaimu gobe." "Me za'a bayar? Idan ana ƙaunar Allah nima a taimaka mun." Aminu ya fada yana shigowa cikin ɗakin. "Kaima ƙunshin zaka yi?" "Me kyau ma kuwa, don kin san sai yafi fitowa a hannu na ma akan bakar fatarta." Ya fadi hakan sanin cewar shi fari ne, don ƴan mazan biyu su suka yiwo mahaifinsu sak a kammani da kuma hasken fatan, matan kuma Suka yo mahaifiyarsu, har gwara Maryam ma ana cewa idonta irin na babansu ne, amma Amina da Hafsa babu abinda suka bari a kammanin Amman. "Wallahi ni ba baƙa bace kaima ka sani, irin wannan kalar fatar sai ka zagaye garin nan kaf baka samu irinta ba." "To idan ma an samu me za'ayi da ita? Da dai irin ta Amina kika ce sai in yarda, amma ke duk gidan nan ma akwai mummuna kamar ki." Maryam ta kara haɗe ranta tana saka hijabin data ɗauko. Amina ta jefo masa wata riga dake hannunta tana murmushi. "Haɗa mu kayi kawai kake zagi Aminu, dani da ita ɗin me ya banbanta damu, ka takurawa Maryam wallahi." "Haba ya zaki hada kalar ki data wannan fingilar? itama ta hakura ta karɓi kanta yadda take ne taƙi, sai faman iyayi fal ciki." Da ƙunƙuni Maryam ta faɗi wani abun kafin ta tayar da sallarta. Hakan yasa shi dariya don shi kansa ya sani girman dake tsakaninsu ne kawai yasa take raga masa a azababbiyar magana da kuma rashin kunyar dake cikinta. "Sai yaushe zaka fita yau?" Amina ta tambaya sanin cewar da ya dawo baya dadewa a gidan yake tafiya can inda yake koyon gyaran mota a can hanyar gidan zoo, har ma ya fara kwarewa don kusan shekara biyu kenan da Baba ya kai shi wajen. "Sai na ƙarbowa Baba, kayansa daga wajen guga..." Ya shafo kansa. "... Tun dazu ma fa ya kamata in je, sun ce sun gama." Kafin Amina tayi magana, Hafsa ƙaramar ƙanwarsu ta shigo gidan hannunta riƙe da ƙullin farar ledar atturuhun data siyo na girkin dare da kuma takardar yashin madina tana zubawa a ɗaya hannunta tana lashewa. Amina ta ɗaga murya ta kirata ganin bata da alamun shigowa. "Ki shigo ki cire kayan nan ki saka na islamiyya, ga uku nan har ta kusa, Adam har ya tafi kina nan." Tana jin hakan Idanunta irin na Amina suka kaɗa a take sannan muryarta ta koma ta kuka, ta shigo ɗakin da sauri tana faɗin. "Dan Allah kice Ya Maryam ta raka ni, wallahi zane ni za'ayi..." Kafin Aminan ta amsa, Aminu yace. "Saka kayan muje in raja ki daga nan sai in wuce. Ai kuwa da murnarta ta ruga da gudu zuwa dakin Amma inda kayanta suke, ta sani ba wanda ya isa ya dake ta makarantar tunda Aminu ne zai raka ta. Aminu ya ciro Naira dari biyu daga aljihunsa ya cilla kan sallayar da Maryam ke sallah yana faɗin. "Gashi nan kije a zana miki abinda ba ganinsa za'ayi ba." Amina tayi murmushi tana godewa Allah a zuciyarta, tana son yadda suke tallafar junansu akan irin ƙananun buƙatun nan. Hafsa bata dawo ba suka tsinci sallamar mahaifinsu, dukkaninsu suka kalli juna a lokaci guda sanin cewa lokacin ba lokacin dawowarsa bane, ƙa'ida ne sai bayan sallar magriba kullum yake dawowa don har Aminu yana yawan riga shi isowa ma. "Allah yasa kar ya tambayi kayan nan..." Aminu ya faɗa yana dafa kansa. Ta tsakanin raga-raga labulen Amina ta hango yadda mahaifin nasu ya dafa kan Hafsa da ta taho ta rungume shi, sannan kai tsaye ya nufi hanyar ɗakinsa. Taga Amma ta fito daga falo sanye da hijabi alamun salla tayi ta bin bayansa tana fadin sannu da dawowa. "Ke maza ki dauko takalminki mu fita." Cewar Aminun, sannan ya juyo ya kalli Amina. "Kice masa tun dazu na tafi karɓi kayan." Ai kuwa yana sanya kafarsa waje suka ji Baban yace. "Fita ce ta kama ni Halima, ina kayan da nace a karbo min?" Basu ji amsar da Amman ta bayar ba sai muryarsa da ta sake dagawo wajen kiran Aminu. "Aminu! Yana gidan nan?" "Na shiga uku.." Cewar Aminun, kuma Amina na kallon sanda Maryam ta murmusa a sallarta don daɗi. "Baba sannu da zuwa, wani abu ne ya faru ka dawo yanzu?" Ta tsinci muryarsa da yayi sauri ya tsugunna yana shafa kai ganin ya fito. "Ni da gidana don na dawo sai ka tambaye ni me nazo yi? Ina kayan da nace ka karbo min?" "To, to, bari aje a karbo." Ya fada kamar sai a lokacin yace 'je ka karbo din,' kuma bai jira ya sake cewa komai ba ya kama hannun Hafsa da ta gama shiryawa suka yi waje. Alhaji Sulaiman ya girgiza kansa kawai saboda takaici sannan ya kalli Amma dake tsaye a gefensa. "Hajiya Kilishi ce yanzun nan ta kira ni tace tana son ganina." Daga cikin ɗakin Amina zata rantse daga ita har Amman a lokaci guda suka yi murmushi. Hajiya Kilishi ƴaruwar Baba ce, mace ce mai kirki da son kyautatawa, ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu ta kowanne fanni, tun kafin Mahaifinsu ya rasa arziƙinsa har bayan komai ya cakuɗe musu, don hatta kuɗin rubuta jarabawarta ta fita daga secondary ita ta tallafa aka biya, babban taimakon da tayi musu na kwanan nan shine lokacin da Maryam ta kamu da rashin lafiyar ciwon ciki, wanda daga ita har su kowa ya wahala kafin a gano cewar wani ƙari ne ke fito mata a gefen cikin kuma yayi girman da har sai an cire shi. A wannan lokacin komai nasu ya riga ya ƙare wajen jinya, don hatta abinci sai daga gidan wan Baban ake kawo musu kullum ko tukunya basa dorawa, ɗan abinda Baba ya samu da kuma na wajen Amman daga ƴan sana'o'in da take yi duk a asibitin suke karewa. Don haka a dole Baban ya shiga neman bashi ƙofa-ƙofa, ƴanuwansa suka hada masa iya abinda zasu iya amma ko kwata ba'a shafe na lissafin ba, Hajiya Kilishi ita taji labari a danginsu, ta kira Baban har gida ta bashi tallafin naira dubu ɗari uku, kuɗin aikin har da ɗoriya akai, tun daga wannan lokacin zuciyoyinsu suka kara girman darajarta a wajensu. Mijin ta wani babban mai kuɗi ne kuma sanannen mutum ne, itace matarsa ta biyu kuma ƴaƴan ta biyar dukkaninsu mata, amma ance saboda zaman amanar da suke yi da uwargidanta babban ɗanta ma a wajen Hajiya Kilishin ya tashi tun yana yaro ta yadda ba kowa ne ya san cewa ba itace ta haife shi ba, Baba yasha gaya musu cewar ko gidan yaje baya iya banbance ƴaƴan ta dana uwargidan. "Shinkafa da wake kuka yi? A zubo min dan Allah kafin yaron nan ya dawo." Muryan Baban ta katse tunanin Amina daidai lokacin da Maryam a gefenta ta idar daga sallah, ta sake kallonsa ta cikin labulen sanda da yake cewa. "Allah yasa Amina ta daka yajin nan nata mai daɗi." A lokaci guda murmushi ya suɓuce a fuskarta, sai kawai ta mike tana faɗin. "Akwai Baba, Bari in kawo maka." *** Royal Brompton Hospital. Sydney St, London SW3 6NP, United Kingdom. ...So I took your hand, back through lamp-lit streets, I knew, Everything led back to you So can you see the stars over Amsterdam? You're the song my heart is beating to... Waƙar a hankali take fitowa daga cikin labtop ɗin dake ajiye a wani ɗan ƙaramin tebur da kujerarsa dake can jikin dogon windon ɗakin, ɗakin asibiti ne da banda gadon mara lafiyar da kuma tarin computers ɗin gefe dake auna lafiyar wanda ke kwance, babu komai sai wata drawer daga can gefe wadda aka yi mata ado har da wasu ƴan fulawoyi, ɗakin a gyare yake tas yana kuma ƙamshi mai daɗi, ga room heater dake fitar da wani ɗumi mai daɗi sakamokon sanyin ƙanƙarar snow ɗin dake zuba daga waje. A hankali idanun mara lafiyar dake kwance akan gadon suka buɗe, kuma duk da lumshewar su girman su ya fito a lokaci guda, matashi ne mai siririyar fuska, yana da yalwar gashin kai da kuma na gira kamar yadda na idanunsa suke dogwaye ta yadda idan ka kalle shi zaka ga kamar baya iya buɗe idanun nasa ne sosai. Ya ɗago da hannunsa dake maƙale da allurar ruwan drip ɗin gefe, ya kalli hannun tsawon wasu sakanni kafin yasa ɗaya hannun nasa ya murza goshinsa alamun takaici, sannan a lokaci guda ya fizge drip ɗin daga jikinsa ya mike zaune, jini ya shiga fitowa daga inda allurar ta fita amma bai ko bi ta kai ba ya kalli rigar dake jikinsa, rigar asibitin ce wadda ake bawa kowanne mara lafiya. Ya shiga ƙarewa ɗakin kallo a hankali har zuwa kan drawer dake can gefe, a lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa da jakar da Ishaq ya ajiye a ciki jiya don haka ya mike tsaye, jiri ya so ɗaukarsa amma ya dage ya tsaya akan ƙafafunsa sannan ya isa ga drawer. Ya buɗe ciki ya fito da wata baƙar jaka ya shiga fito da kayan ciki, ƙamshin turarensa na 'Dior Sauvage' shi ya tabbatar masa da cewar kayansa ne tun kafin ma ya gane su, kala biyu ne sai kuma wata ƙatuwar rigar sanyi wadda ke zuwa har gwiwa, bai yi tunanin komai ba ya shiga canjawa zuwa kayan, sai da yazo ɓalle maɓallan rigar saman sannan ya kula da jinin dake fita daga hannunsa. Don haka ya saka rigar asibitin da ya cire ya goge sannan ya ɗora daya rigar, ya kuma jawo rigar sanyin ya dora akai, bai ko ɗauke rigar asibitin dake kasa ba ya saita facing Cap ɗin da ya ɗauko a ciki daidai fuskarsa sannan ya nufi hanyar kofar ɗakin, ya san duka wayoyinsa basa nan kuma Ishaq bai bar tasa a gefen labtop ɗin ba don haka ya nufi ƙofar ya buɗe, dogon korido ne a wajen mai dauke da kofofin ɗakuna da kuma mutane dake ta wucewa ta cikinsa, ya tabbata babu ma'aikatan da suka san shi a cikin waɗanda ke wucewa don haka kansa tsaye ya bi ta cikin mutanen dake tafiya ya saje, yana mai nufar hanyar waje. Iskar dake kaɗawa a wajen mai tsananin sanyi ta ratsa fuskarsa sanda ya fito daga asibitin gabaɗaya, dare ne lokacin, ga fitulu a koina, na kan titi dana motoci, ga mutane birjik musamman na ƙafa sai faman wucewa suke. Haka ƙofar asibitin take a kullum, tun daga shekarun da ya fara zuwansa har yau. Sanyi ya shiga ratsa kunnuwan sa dake buɗe sannan a lokaci guda yaji wata irin yunwa ta mamaye shi, sai kawai ya saka tafin hannayensa duka biyu ya gefen fuskarsa lokacin da idonsa ya sauka akan sunan wani kanti daga can tsallake, kantin da yake yawan yin siyayya duk lokacin da yazo kasar. "24 dollors." (Dubu goma.) Baturen dake kan kantar ya faɗa a lokacin da ya gama lissafa abubuwan daya ɗebo. Ya kai hannunsa bayan aljihu kamar zai fito da wallet sai kuma ya dawo dashi, ya matso daidai jikin kantar yana kallon mutumin yace. "You know me right?" (Ka san ni ko?) Kallon da mutumin yake masa yasa ya cigaba da cewa. "I used to come around, from that hospital...(Ina yawan zuwa, daga wancan asibitin..)" Ya juya ya nuna asibitin sannan ya dawo ga fuskar mutumin da bata canja ba, sai kawai ya daga hannayen sa sama alamun sallamawa sannan yace. "What I mean is my brother is coming to pick me from here... So do you mind If I just wait for him while I eat these? Because honestly I dont have anything with me right now but I assure you he's going to pay when he arrive...." (Abinda nake nufi shine ɗan uwana zai zo yanzu ya dauke ni anan... so ba zaka damu ba idan naci wadannan kafin yazo, don bani da komai a jiki na yanzu amma ina tabbatar maka shi zai biya ka idan yazo...) Mutumin ya saka hannunsa ya danne kayan da yake shirin ɗiba, sannan da sautin muryarsa da yafi kauri a yanzu ya sake maimaita masa adadin kudin. "24 dollors." (Dubu goma.) Har ya haƙura ya ɗauke hannunsa yana shirin juyawa sai kawai mutumin dake tsaye a bayansa yace. "You're holding up the line, man! If you can't pay just leave." (Malam kana riƙe mana layi, idan baza ka iya biya ba ba ka bar wajen mana.) A sakannin da mutumin ya rufe bakinsa, a sakannin wani irin naushi ya ziyarci fuskarsa, naushin da ya kusan kaishi har kasa, ya ɗago jini na fara zuba ta hancinsa lokacin da wata mata a gefensu ta ƙwalla ƙara shi kuma ya furta kalmar zagi yana share jinin, kuma baiyi wata-wata ba ya nufo kansa da nasa naushin shima dsya haddasa fada a tsakaninsu ba shiri, kuma kowannensu yaji lokacin da mai kantin ya kwalla ƙara yana faɗin. "Someone should call the police!" (Wani ya kira ƴan sanda!) **** British Transport Police Station No. 2 Melton St, London NW1 2BW, United Kingdom. "Kun tabbata dukkan waɗannan bayanan file ɗin gaskiya ne?" Ɗan sandan ya tambaya daga tsallaken teburin da Ishaq ke zaune tare da wani ma'aikacin asibiti a gefensa. "Da gaske muke ranka ya dade, mara lafiya ne ya fito ba tare da an sallame shi ba, kuma a yanzu haka ma ba'a hayyacinsa yake ba." Ɗan sandan ya kalli ma'akacin asibitin da yayi magana, ya kara kallon ID Card ɗinsa da ya mika masa sannan ya gyada kansa yana sake kallon cikin file ɗin. "Naga dukkan wasu bayanai na cewar yana da matsalar kwakwalwa, amma banga wani bayani ko sau daya na abinda ciwon ke saka shi ba..." "Ai da yake yallabai, mu a asibiti cutar kawai muke bayani ba abinda zata haifar ba." Jin haka yasa Ɗan sandan ya dawo da hankalinsa ga Ishaq dake zaune yana kallon can gefe inda aka ƙulle tarin mutane a cikin wani budadden cell da aka zagaye da karafa kawai. "Kai ɗanuwansa ne ko? Zaka iya gaya mana abubuwan da yake yi, don mu san cewa ba da gangan yayi abinda muka kama shi yanzu ba?" Ishaq ya gyara zamansa bayan ya dawo da hankalinsa nan, sannan cikin harshen turanci shima yace. "Yayi abubuwa da yawa yallaɓai, waɗanda suka fi wannan ma, ba tun yanzu ba..." "Misali..." Ɗan sandan ya katse shi. "Misali zaka bani ba wani bayani ba." Jin haka yasa Ishaq haɗiye yawu ba shiri, ya juya ya sake kallon idanun da suke kallonsa daga cikin cell ɗin sannan ya gyara zamansa kaɗan, muryarsa can kasa yace. "Yallabai, a karo na ƙarshe da ciwonsa ya tashi saura kaɗan yayi kisan kai." Idanun ɗan sandan basu canja ba, ya cigaba da kallonsa na wasu sakanni kawai kafin ya gyaɗa kai, sannan ya nuna file din dake hannunsa. "Zan baku belinsa ne yanzu saboda wannan kawai, amma ku tabbatar bai sake barin asibitin nan ba sai da cikakkiyar lafiyarsa. Idan ba haka ba idan muka sake kama shi, mu zamu riƙe shi har sai ya warke." Dukkaninsu suka gyada kai alamun sun fahimta kafin ya juya ya kira wani ɗan sanda dake ƙoƙarin wucewa. "Stone! bring the Black one out." (Stone! Fito da baƙin cikinsu.) Stone ɗin baya bukatar wani karin bayani don wanda aka nuna masa shi kaɗai ne baƙi a cikin tarin turawan cell din, don haka ya zaro muƙullai daga jikinsa ya nufi wajen. Ɗan sandan ya sake kallon file ɗin hannunsa a karo na ƙarshe, idanunsa suka sauka akan sunan dake rubuce a jiki. Ma'aruf Mansour Bakori! #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA BIYU. ~~~~ "Kowanne ɗan adam yana da tarin ƙalubale a rayuwarsa, amma ga wanda suke da cutar 'Bipola disoder' nasu ƙalubalen daban ne. Bipola disoder cutar ƙwaƙwalwa ce dake canja yanayin mutum a lokaci guda, ta canja ƙarfinsa, yanayin tunaninsa har da ɗabi'arsa. Cuta ce dake iya taba rayuwar mutum ta bangaren aikinsa, karatu, zamantakewa har ma ta iya dakushewa mutum hanyar cigaba a rayuwarsa, don tana yawan tashi ne akai-akai. Cutar tana farawa ne daga lokacin ƙuruciya, kuma duk da cewar babu takamaimai maganinta ana samun saukinta ko kuma ƙaruwarta idan har ba'a bin ƙaidojin magani daidai. Tana da matakai huɗu kuma na ƙarshen da ake kira da "Mania" shi yafi kowanne hatsari. A matakin 'Mania' mara lafiya yana jin tsananin ƙarfi da jin cewa zai iya komai, da kuma tsananin fushi da yawan tunanin abubuwa barkatai, wanda ke jawo mutum ya harzuƙa ta yadda babu mai iyawa dashi, mara lafiyar yana samun ƙarancin bacci da kuma rashin nutsuwa sannan wasu ƙwaƙwalwar su tana buɗewa ta yadda za su yi abinda idan a lafiyarsu ne baza su iya ba. Matakin dake bi wa wannan kuma shine 'HypoMania'...." Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga wata Tv dake kafe a saman harabar wajen, ƙaton wajen jira ne na asibiti inda tarin ma'aikata ke wucewa wajen wasu gadaje daga can baya da aka kwantar da marasa lafiya, labulayen da aka sassaka a tsakanin kowanne gado sune kadai abinda ya raba gadajen. Bayanin dake fitowa daga Tvn, na irin rashin lafiyar ƙwaƙwalwar da ake dubawa a wannan ɓangaren asibitin ne, masu jiran kuma na zaune suna saurarar bayanan da ake yi mai dauke da hotuna don sauƙin fahimta ga marasa lafiyar da kuma masu jinyar, Ishaq yana ɗaya daga cikin masu jiran, yana zaune daga karshen kujerar kamar mai jiran ƙiris! Ya mike, kafarsa ta bangaren dama yake faman bubbugawa yayin da gefen bakinsa yake a cije. A bayyane yake ga duk wanda ya kalle shi cewa jira kawai yake likitocin dake tsaye a wajen gadon ɗan'uwansa su fito daga bayan labulen da aka zagaye gadon dashi. Sun taru kusan su bakwai a ciki har da Nurses don hankalinsu ya tashi jin cewar daga police station aka taho dashi bayan an neme shi an rasa. Ya sani cewar dukkaninsu tsoro suke yi game da ciwonsa, don Ma'aruf ya riga ya kai mataki na karshe a ciwon ƙwaƙwalwar tasa, ya riga ya kƙure komai a Bipolar Disoder, don idan har akwai wani mutum a duniya da baya taimakon kansa to Ma'aruf ne. A shekaru goma da cutar nan ta same shi babu irin fadi tashin da ba'ayi ba daga kowanne ɓangare na iyaye da kuma ƴanuwansa amma rashin tasa tallafawar ya haɓɓaka ciwon har sai da ya ƙaraso matakin ƙarshe, 'Mania Stage'. A baya bai fi ƴan awanni ko kwana ɗaya zuwa biyu ba yake yi idan ciwon ya taso masa, amma a yanzu sati guda cur, har suka zo ƙasar nan Ma'aruf ba'a hankali sa yake ba, hakan yasa dole aka kwantar dashi a asibitin da alluran bacci wanda suka taimaka, ya farka cikin hayyacinsa yanzu. Don duk da cewar a police station suka je suka same shi, idanunsa kawai ya kalla ya san cewar ya dawo hayyacinsa tun kafin likitocin ma su gane, shi yasa ya matsu da fitowarsu a yanzu don yaje ya same shi, ya sauke maganganun dake zuciyarsa tun daga ranar da Mami ta kira shi muryar ta na rawa taje ya taho gida Ma'aruf ya shigo musu da gawar wani. Likitocin duka fito a daidai wannan lokacin, kuma bai tsaya jiran komai ba ya zagaya ta ɗaya hanyar da wandanda ba ma'aikata ba ke wucewa ya nufi wajen gadon. "Minti biyar! minti biyar kawai na fita Ma'aruf amma kayi tsalle daga asibitin nan zuwa police station!" Ya faɗi hakan da harshen hausa daidai sanda ya bankaɗa labulen da aka zagaye gadon. Dama abinda Ma'aruf ɗin yake jira kenan, ya riga ya sani cewar ya daɗe a waje yana kaɗa ƙafa yana jira likitocin su fita ya shigo da tarin ƙorafinsa, don haka hankalinsa a kwance ya ɗago da idanunsa ya kalle shi. "Kaima sani bana iya rike yunwa, na tafi in samu abinda zanci ne and you left me with nothing, ba dole su kaini police station ba." Ishaq ya girgiza kansa. "Ma'aruf ba a Nigeria muke ba, ko baka gane bane da ka farka? me kake tunani idan suka kama ka a ƙasar nan?" Maimakon ya bashi amsa kai tsaye, sai ya koma da baya a jikin gadon, ya zura hannayensa duka biyu cikin gashin kansa sannan yace. "Na sha gaya maka kana damuwa da yawa Ishaq, kana damuwa akan abubuwan da suke faruwa dama wanda basu zo ba." "Kuma matsalar kenan, kai da baka damuwar, baka damuwa da kanka balle kuma na kusa da kai, shi yasa har muka zo wannan matakin Ma'aruf! Mania!" Ya faɗi sunan mataki na karshe a cutar da Ma'aruf ɗin ke fuskanta, kuma ga mamakinsa, a lokaci guda Ma'aruf ɗin ya juyo ya kalle shi, sannan a cikin sakan biyu idanunsa suka haska da wani abu da Ishaq ɗin zai rantse da ubangijin dake busa musu numfashi cewar bai taba gani a idanunsa ba. Tsoro da kuma fargaba! Sai kawai ya girgiza kansa sannan ya cigaba da faɗin. "Shekara biyu da suka wuce a asibitin nan ko HypoMania test ɗinka basu kai ba, baka da lafiya amma babu wanda ya sani babu mai ganewa, muna ɓoye komai daki-daki don rayuwarka ta tafi daidai. Amma yanzu ka gaya min me kayi kafin mu taho nan Ma'aruf? Daniel ka yiwa dukan da har ya suma akan baiyi maka submitting takardu a office ba, ka dake shi har ya suma Ma'aruf sannan ka sako shi a mota ka kaishi gida, ka shiga dashi har falon Baffa kana gaya masa wai ka kawo shi ya kore shi daga aiki!" (Mahaifinsa.) Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da ɗaukacin jama'ar da suka sanka, waye bai san kana fama da ciwon ƙwaƙwalwa ba Ma'aruf? Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da duk ɗaukacin kewayen da mutane suka sanka, waye a yanzu bai san cewa kana fama da matsala a ƙwaƙwalwa ba? Waye bai san cewa kana da wannan nakasar ba Ma'aruf?" Muryar Ishaq ɗagawa take a lokacin da yake fadar hakan, sautin ta na fitowa cike da wani irin daci da takaicin duk abubuwan da yake faɗa din, kuma har a lokacin yana ganin adadin kifta idanun da Ma'aruf ke yi alamun cewa kowacce kalma tana bada ma'anar da yake son ya gane a ƙwaƙwalwar sa. Bai ce komai ba ya cigaba. "Ka san me ya fitar dani ɗazu? Ka san abinda yasa na bar ɗakin har kaje ka aikata abinda kayi?..." Ya tambaya kamar yana jiran ya bashi amsa. "... Office din likitan ka naje, shi ya kira ni personally Ma'aruf! Yayi min dukkan bayanin halin da kake ciki, kuma albishirin ka abinda kake so zai faru, idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma'aruf! Kana gab da rasa komai gabaɗaya..." "And so what idan na rasa?!" Yadda Ma'aruf ɗin ya katse shi a lokaci guda da tasa sautin muryar ya bashi mamakin da har sai da ya haska a idanunsa. Kallonsa yake har a lokacin da nasa idanun da suka canja, yanayinsu na kara lumshewa kamar kodayaushe idan yana cikin ɓacin rai. "Nace sai me idan na rasa komai? Idan dai har ragowar lokacin da nake dashi zai bani dama na iya cimma abinda ke gabana sai me idan na rasa hankalina?" Sai ya girgiza kansa kawai yana cigaba da kallonsa. "Nasha gaya maka Ma'aruf ya mutu shekaru goma da suka wuce Ishaq, kaƙi ka yarda dani ne, amma Ma'aruf ya riga mutu, babu shi anan." Ya ƙarasa yana nuna ƙirjinsa, daidai lokacin da labulen dakin ya buɗe, wani bature ya leƙo fuskarsa a murtuƙe yace. "What the in the world are you two talking abou..." Bai karasa ba sakamakon kallon da su duka biyun suka juyo suna yi masa kowanne ransa a ɓace, sai kawai yayi sauri ya maida labulen ya juya, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya alokaci guda. Shiru ya ratsa wucewar sakan ɗaya, biyu, uku... kafin Ishaq ya ƙaraso a hankali ya zauna a gefen sa. "Kwana na nawa a asibitin nan?" Ma'aruf ya katse shirun da sautin muryarsa da ya koma daidai, mai zurfi dake fitowa can kasa. "Huɗu, you were unconscious for three days a Nigeria kafin mu taho." A hankali ya haɗiye yawu cikin maƙogwaronsa sannan ya ƙara tambaya. "Me Baffa yace?" "Ransa ya ɓaci sosai, ransa ya ɓaci fiye da duk yadda kake tunani, kullum sai ya kira waya ya tambaya idan ka farka, kuma yace da zarar ka dawo hayyacinka mu koma gida." Yaji lokacin da ya zuƙi numfashi ya fitar sannan ya koma da baya ya jingina da gadon bai ce komai ba, don haka shi ya cigaba da cewa. "Mami kusan duk bayan awa guda take kira Ma'aruf, suna can ne amma hankalinsu anan yake, kowa ya damu, Hajiya tace hatta Abdurrahim jiya gidanka ya tafi ya kwana, dan Allah Ma'aruf, dan Allah ka taimaka ko don waɗannan mutanen ka tallafi rayuwarka, dan Allah." Kai tsaye maganganun suka shiga har wani waje dake can ƙasan zuciyar Ma'aruf, kuma yana jin yadda tasirin su ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinsa yana tafiya tare da gudun jinin cikinsu, sai kawai ya sake cusa yatsunsa cikin gashin kansa sannan ya runtse idanunsa. Ishaq yana kallonsa, yana jin yadda tausayinsa ke bin zuciyarsa kamar kullum, ba sauki bane rayuwa da irin wannan cutar ya sani, ba sauki bane daurewa irin abinda ke zuciyar Ma'aruf din, ba sauki bane yadda yake iya daurewa abubuwa tsawon shekarun nan, ba sauki bane ba zama Ma'aruf din da yake gabaɗaya ya sani... Shi yasa fatansa a kodayaushe bai wuce Allah ya tallafi rayuwarsa ta wata hanya daban da take sabuwa ba, domin Allahn ya sani cewa su sun gwada duk wata hanyar da take a tunaninsu amma babu wani sauki. Ya haɗiye yawu a hankali cikin maƙogwaron sa yana cigaba da kallonsa yace. "Nayi mana booking flight, gobe zamu koma." Kuma ba don kallonsa yake ba ya tabbata ba zai ji sanda ya amsa da 'Allah ya kaimu' ba. Saboda haka kai tsaye sai ya sake tambaya. "Yaya kake ji?" Ma'aruf yasa yatsu biyu ya shafo saman hancinsa har a lokacin bai buɗe idonsa ba yace. "Ina ji ne kamar zan mutu saboda yunwa, nace ka taimaka min da abinci amma kana ta masifa, Idan na sake fita daga nan kar barni kawai kar kaje beli na." Ba shiri wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskar Ishaq ɗin na tabbas ɗin da yake dashi cewar ya dawo daidai, don har abada irin Ma'aruf guda daya ya sani a duk tsayin rayuwarsa. Ma'aruf yaji lokacin da ya fita amma duk da haka bai bude idanunsa ba, hoto ɗaya ne ke yawo a cikin kansa, hoton ɗakin bincikensa, yana hasko tarin takardu da kuma hotunan da suke cikin ɗakin nan, sannan yana hasko yadda hanya ta ƙarshe da yake tunanin zata kai shi ga nasara bayan shekaru huɗu ta rushe har garinta, wanda takaicin haka shine sanadiyar tashin ciwon nasa da abinda yayi har suka taho nan. Wata jijiya daga gefen kansa ta bullutso cike da wani sabon takaicin da ya sake ratsa shi, sabon takaici... Don wannan ɗauke yake da wani layi na fargaba da kuma tsoro, tsoron da bai taba ji a ransa game da ciwon nasa ba tsawon shekaru goma da suka wuce, maganganun Ishaq suka sake haskawa a cikin kansa. ...idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya, kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma'aruf! *** Alhaji Muhammad Mansour Bakori, sanannen mutum ne wanda yake da babban Kamfanin yin robobi a garin Kano tare da ƙaninsa Alhaji Usman, wanda su biyu ne kacal a wajen iyayensu, mahaifinsu ya rasu shekaru da daɗewa amma mahaifiyar su tana raye. Alhaji Mansour Bakori yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha ɗaya, yayin da Alhaji Usman bai taba haihuwa ba tsawon shekaru talatin da aurensa, wanda hakan ya faru ne sakamakon wani hatsari da yayi tun kafin tun yana saurayi har ya zame masa sanadin hakan, shi yasa kowa a danginsu yake girmama matarsa Hajiya Madina da kuma jinjina mata na zaman da take dashi a duk shekarun nan alhali ita lafiyarta ƙalau. Matan Alhaji Mansour biyu, Uwargidan itace Hajiya Maimuna, wata mata mai kirki da kuma alkunya, ɗanta na farko Jamal ya rasu shekaru goma da suka wuce, daga shi sai Ma'aruf wanda shi a wajen kishiyarta ya girma, sai Shukra, Munaya, Abdurrahim wanda shi tun yana shekaru biyu a duniya ya kamu da matsalar rashin magana amma yana ji kamar kowa, sai kuma autarsu Zahra. Hajiya Kilishi itace mata ta biyu a gidan, wata mace ce mai tsananin kirki da kyautatawa, don faɗa ko da na rana guda bai taɓa haɗa su da Hajiya Maimuna ba tun zuwanta gidan, wani irin zaman lafiya da mutunta juna ne a tsakaninsu tun farkon zuwanta gidan, hakan yasa basu kaɗai ba ko wanda yake nesa ba zai taba cewar su ɗin kishiyoyin juna bane idan ya gansu tare. Ita ta raini Ma'aruf tun daga watannin da aka yaye shi har zuwa girmansa na yanzu. Hajiya Maimuna, mace ce mai hali irin na mutanen da, tsananin kawaici akan abinda suke ganin shine daidai, don haka tun daga ranar da Hajiya Kilishi ta karɓe sshi bata ƙara nuna cewa shi nata bane, a suna kawai Ma'aruf ya santa a matsayin mahaifiyarsa, amma a wajen Hajiya Kilishin da suke kira da Mami ya samu dukkanin wata kulawar da ɗa ke samu daga mahaifiyarsa. Ita ta raine shi da ƙarfin jikinta da kuma na zuciyarta, har zuwa girmansa kuwa ya zama tsakaninsa da Hajiya Maimuna gaisuwa ce kawai amma Mami ce komai nasa, duk da ƴadda wasu daga cikin ƴanuwan Hajiya Maimunan suke nuna rashin jin daɗin su akan hakan a yanzu da ya zama shine kaɗai namiji babba a gidan. Ƴaƴan Hajiya Kilishi biyar ne, dukkaninsu mata kuma dukkanninsu harafin sunansu ya fara ne da harafin S, Safiyya, Salma, Surayya, Samira da kuma Sahla kamar yadda take so, don a wajen Daddy babu ruwansa da raɗin suna, duk wanda iyayensu mata suka zaba shi zai saka ba ruwansa. Zahra ce ma kawai taci sunan Inna Danejo 'Fatima' kamar yadda Hajiya Maimunan ta nuna tana so a saka. Hajiya Maimuna ta sami matsalar shanyewar ƙafafu bayan ta haifi ƴarta ta ƙarshe Zahra, kuma babu irin maganin da ba'ayi ba a ƙasashe daban- daban amma ba nasara, don haka a dole yanzu sai akan Wheelchair take yawo. Gidan Alhaji Mansour dake unguwar NNDC quarters a garin Kano, ƙaton gida ne mai ɗauke da bangare-bangare, akwai ɓangaren iyalansa guda biyu wanda kowanne iri daya ne, ƙaton falo da ɗakuna hudu kowanne da banɗakinsa a ciki da kuma sauran wajaje irin Kitchen, store, courtyard da dai sauransu, sai bangarensa inda shine waje na farko a gidan mai ɗauke da ɗakuna biyu da falo da kuma wajen meeting ɗinsa inda yake ganin baƙi a gida. Akwai bangaren boys quarters inda masu a gidan suke zaune sai kuma wajen Inna Danejo kakar gidan, wato mahaifiyarsu Alhaji Mansour inda itama take da ƙaton falo, ɗaki ɗaya da kuma toilet, sai ɓangaren ƴan aiki, sai kuma bangare na karshe daga gefen hagu na harabar gidan, wato bangaren Alhaji Usman da suke kira da Alhaji Baba, wanda shima da a gidan yake tare da matarsa daga baya sai ya siyi wani gida gaba dasu kaɗan ya koma, don haka wajen a ƙulle yake babu kowa. Ishaq abokin Ma'aruf ne kuma ɗan'uwansa, don da Mahaifiyar Ishaq ɗin da Hajiya Maimuna iyayensu ɗaya, asalin mahaifinsa ɗan Kaduna ne kuma shi kaɗai iyayensa suka haifa, mahaifinsa ya daɗe da rasuwa amna mahaifiyarsa sai da yazo matakin shiga Jami'a ne sannan Allah ya ɗauki ranta, don haka da shawarar Mami, Hajiya Maimuna ta tambayi Alhaji Mansour da kowa ke kira da Baffa, Ishaq ya dawo gidansu da zama daidai lokacin da Ma'aruf ke kokarin shiga Jami'a. Mamin tayi haka ne don ganin ta samowa Ma'aruf sauki akan halin alhinin ɗanuwansa da har a lokacin bai gama warkewa daga ransa ba, don haka tare da Ishaq ɗin Baffa ya ɗauki nauyin karatunsu a wata Private University dake London har suka kammala, kuma hakan ya sanya shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da cewar ɓangare daban-daban suka karanta. Ma'aruf ya karanci harkar Kasuwanci ne yayin da Ishaq ya karanci ɓangaren aikin lawyer kamar yadda yake da buri tun yana yaro. *** Washegari... No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Qauters. .07:30 Pm. Tun daga ƙofar gidan zaka gane cewar anyi wani taro ne a gidan an watse, don hatta gate din a bude yake gabaɗaya sannan ga motoci daga ciki suna kokarin fitowa. Idan ka biyo ta cikin mutanen, zaka wuce ko'ina hanya ta kai ka har ɓangaren Hajiya Maimuna inda taron mutanen yafi yawa musamman a ƙaton falon ɓangaren da zaka tarar wanda yake cike da tarin mutane gabaɗayansu mata, kowa na zaune da abokin hirarsa yayin da ƙamshin turarukansu ya haɗe da ƙamshin daddaɗan abincin da aka gama ci a falon, don ga tarin plates nan wasu ma har da ragowar abincin sannan kuma a can gaban Tv stand na ɗakin akwai wasu manya-manyan flasks cike da snacks kala-kala ga duk wanda yake so ya diba. Sai dai duk wannan ba shine abin kallo a dakin ba, tarin akwatunan dake zube a makeken carpet din tsakiyar falon ne, an buɗe kowannensu dake cike da kaya fal. Lefen Babbar ƴar Hajiya Maimunan mace da suke kira da Shukra ne, amma ba zaka banbance adadin yawan ƴanuwan Hajiya Maimunan ko kuma na Hajiya Kilishi a falon ba, sun riga sun zama ɗaya dukkanninsu don ko a sati biyu da aka karbi lefe biyu na ƴaƴan Hajiya Kilishin Safiyya da Salma, duk sune dai a wajen, shi yasa a yanzu ma rabi hirarsu ta shirye-shiryen bikin da aka saka nan da wata guda mai zuwa ce. Hajiya Kilishi ta ratso ta cikin mutanen, sanye take da wata doguwar rigar lace daya sha adon stones sai wulgawar kyalli yake a cikin hasken fitulun dakin, ta karaso inda Hajiya Maimuna ke zaune akan kujerar Wheelchair dinta tana hira da wata ƴaruwarta, ta sunkuyo daidai saitin fuskarta sannan tace. "Hajiya su Ma'aruf sun iso, yanzu na tura Malam Sani (direba) ya ɗauko su daga airpot, mukullin store dinki zan karba na ajiyemusu abinci ɗazu, Hajiya Madina ce tace zata tafi nace idan direban nata ya sauke ta sai ya karasa ya kai musu abinci don na san baxa su shigo yau ba." "Toh Alhamdlilah, Muƙullin yana hannun Sameera ita ta karba dazu wai sun ajiyewa ƙawayenta abinci su ma." Hajiya Maimunan ta amsa a hankali itama. Dukkaninsu sun sani cewa a duk tarin jama'ar gidan babu wanda bai san abinda Ma'aruf ɗin yayi ba da kuma cewar baya ƙasar don labari baya taba ɓuya, amma duk da haka gwara ace basu fallasa zancen ba duk kuwa da cewar duk ƴanuwa ne a gidan, amma hakan ba zai hana cece-kuce ba. Daga nan ɓangarenta ta nufa, inda babu mutane sosai, kuma ƴanmatan gidan da wasu kawayensu suka tare suna ta hayaniyar da jiran a ragu don suma suje su buɗe nasu babin kallon kayan. A falo ta tarar da Zahra da Sahla ƴan autan gidan kuma sa'annin juna sun baje litattafansu suna ta aiki kamar basu san da bidirin da ake yi a gidan ba, dama yayyensu sun riga sun manna musu sunan Allazi boko 1 da kuma Allazi boko 2, don mayun karatu ne kamar ba gobe, yanzu suka shiga SS1 amma abinda suka sani ko Abdurrahim da yake SS3 bai sani ba, kwanaki har Surayya dake level three suka koyawa wani abu a Biology. Har Hajiya Kilishin zata yi musu maganar abinci sai ta kula da plate din snacks dake tsakiyar litattafansu, ta sana aikin Mama Rabi ne hakan, wata dattijuwa ma'aikaciyar gidan da har yanzu bata daina kula dasu ba kasancewar ita ta yaye su tun suna ƙanana. Don haka ta amsa sannu da shigowar da suka yi mata kawai ta wuce. Ta nufi kofar dakinsu Salma inda ƴanmatan suke, hayaniyarsu tun daga falon zaka ji ta, cike da raha da kuma nishadi kamar an fara bikin, kuma duka hirar da suke ta tsare-tsaren bikin ce da suka daɗe suna yi tunda wannan shine karo na farko da za'a aurar da mata a gidan, kuma har guda uku a lokaci guda. "A'a ranar kunshi ne fa za'ayi style iri daya, ranar Kamu kamar kowa zaiyi style dinsa ne ko?" Muryar Munaya ta tambaya cikin hayaniyar. "Ranar kunshi fa shi babu anko Munaya kin manta ne kowa kayansa zai saka, da Kamu ne za'ayi har style ɗaya." Wata kawar Salma, mai suna Aysha ta bata amsa. Hajiya Kilishi ta buɗe kofar dakin daidai lokacin da Munayan ke gyara glass din idonta tana kallon wayar Sameera dake hannunta inda take ƙoƙarin banbace tarin atamfofi da kuma lesukan da zasu yi ankon dasu. A ƙaton gadon ɗakin gabaɗayansu suke a baje dasu da tarin plate din snacks din da suke ci, sai wadanda basu sami waje bane suka zauna daga kan bedside drawers. "Ni fa wallahi gani nake kamar wata ɗaya ba zai isa duk wannan shirye-shiryen ba." Shukra ta faɗa tana danna tata wayar. "What?!" Salma ta mike daga kwance tana kallonta. "... Ai Ya Shukra kar ma ki fara wannan zancen don wallahi Imran ba zai taɓa yarda a ƙara mana ko sati ɗaya ba." Salma ta faɗa wanda hakan yasa dukkaninsu yin shewa a lokaci guda, don duk cikin amaren tafi kowa ɗokin bikin, yayarta Safiyya ba ruwanta don ita dama ba mai magana bace tun farko, kuma wanda zata aura mai mata ne da ƴaƴan sa biyu duk da cewar ba wani manyan ta yayi ba. Shukra kuma dake kan matakin masters dinta a bayyane yake cewa hankalinta yafi tafiya ga Project work din da take kan gaɓar yi fiye da bikin, duk kuwa da irin rawar kafar da Suraj ɗin da zata aura ke yi shi, wanda dan wani abokin aikin Baffa ne. Har Salma zata sake cewa wani abu Sameera dake gefenta ta daka mata duka, wani duka da idan zata yi ɓaram-ɓaramarta Mamin tazo wucewa suke yi mata shi, don haka a lokaci guda ta juyo ta kalli kofa inda Hajiya Kilishin ke tsaye tana kallonsu da murmushi. "Mami ina wuni..." Duka kawayensu na ɗakin suka hada baki wajen gaishe ta don tun zuwansu basu ma ganta ba. Da murmushin ta amsa musu sannan ta kira Sameera. "Ina muƙullin store dinsu Munaya? Yayanku sun dawo yanzu, kizo ki tayani mu debo abincinsu a saka a motarsu Hajiya Madina." Da wani irin murmushi mai faɗi Sameeran ta amsa, don Allah ya sani duk da kowanensu yayi waya dashi tun a jiya, da kuma hayaniyar gidan ta yau, suna cike da tunanin halin da Ma'aruf ɗin ke ciki, don abinda yayi wani abu ne da basu taɓa gani ba tsawon rayuwarsu duk da sun san cewa kuwa yana da wannan cutar. *** Mallam Aminu Kano International Airport 08:30 PM. "Wata nawa aka saka bikin yaran nan ne Malam Sani?" Ishaq ya tambaya a lokacin da yake kokarin saka jakar kayansu cikin boot ɗin motar da Malam Sanin ya buɗe. "Wata ɗaya aka saka wallahi, ai gidan ma har yanzu yana nan a ɗinke, shi yasa Hajiya tace ba sai kunzo ba, kawai in wuce daku gida." Ishaq ya gyaɗa kansa yana rufe boot ɗin. "Ai dama bamu da plan din zuwagidan nan yau, amma Lallai su Baffa sun shirya, har su uku ne fa a wata ɗaya kawai." "To ai rufin asirin Allah ake ciki kullum kuma shi ke rufawar." Cewar Malam Sanin yana dariya. Duk maganar da suke yi, Ma'aruf na zaune a cikin motar daga baya, wayarsa na riƙe a hannunsa haskenta na haska siririyar fuskarsa da a cikin ƴan kwanakin ta ƙara ramewa, message ne kawai ke tururuwar shigowa da kuma tarin emails tunda ya kunna wayar har zuwa yanzu, ya lumshe idanunsa kawai sai kallonsu yake a lokaci guda kuma yana jin hirar su Ishaq ɗin daga waje. Allah ya sani gabaɗaya ya manta cewa shirye-shiryen bikin akeyi sai a jiya da Mamin ke tuna masa cewa yau ne za'a karbi lefen Shukra, kuma jin cewa gidan a cike yake yasa shima baiyi tunanin ya kamata su je ɗin ba, amma kuma ya kamata yaga Baffa a yau, idan yana gidan kuma fa? Sai yasa yatsan sa ɗaya ya share dukkan messages ɗin sannan ya lulubo nambar mahaifin nasa amma sau biyu ya buga bata shiga ba, don haka ya nemo ta Mami. Bugu ɗaya kuwa muryarta ta shiga kunnensa. "Mai gaskiya na, kun taho?" Ta kira shi da sunan data laƙaba masa tun yarintarsa. Sai ya sake lumshe idonsa ya koma da baya jikin kujerar lokacin da Ishaq da Baba Sani suka buɗe ƙofofin motar suka shigo. "Eh Mami, Baffa yana gida kuwa?" "A'a yana office shima har yanzu. Na bayar direban Hajiya Madina zai kawo muku abinci yanzu, wataƙila ma kuyi daidai dashi." Wani abu ya motsa a kirjinsa, don yayi kewar irin wannan kulawar tata a ƴan kwanakin nan, sai dai kafin ya saurari abinda ta cigaba da cewa hankalinsa ya kai ga abinda Ishaq ke cewa cikin wayar sa da aka kira ya amsa. "To shikenan gamu nan insha Allahu..." "... Akwai maganar da zamu yi Ma'aruf, nima nafi son ka samu hutu sosai zuwa goben." Sauran maganar Mamin ta shiga kunnensa bayan Ishaq ya kashe wayar da yake yi." "Ma'aruf, kana jina kuwa? Da kaci abinci ka sha magungunan da aka baka " Yaji ta sake faɗa lokacin da Ishaq ke cewa Malam Sani... "Sakataren Baffa ne yakira, wai Baffan yana son ganinmu a office ɗinsa kafin muje gida, ka juya ta wanna U-turn ɗin sai mu koma." Ba shiri Ma'aruf yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaronsa, don tun bayan farkawar sa sau ɗaya kawai yayi waya da Baffan, a jiya daya kira ta wayar Ishaq, ya tabbatar masa da cewar lafiya yake jin kansa shikenan bai kara nemansu ba, amma ko Baba Usman ya sake kira a safiyar yau kafin su taho. Yana jin yadda Mamin ke cigaba jero masa tarin tambayoyi ta cikin wayar amma hankalinsa sam baya kanta har Malam Sani yasha kan U-turn din da Ishaq ya nuna wanda zai komar dasu baya zuwa hanyar Office ɗin Baffan, wani ƙaton branch na kamfanin su inda iya ma'aikata ne kawai a wajen. "Muhammad..." Muryar Baffan ta kira shi kuma a lokaci guda amonta ya ratsa har cikin kansa bayan sun isa Office ɗin, bayan sun shiga ciki kuma Baffan ya sallami wasu mutum biyu da yake tare dasu a lokacin, sannan bayan Ishaq ya dauki wata wayar ƙarya ya fita don dukkaninsu sun fahimci cewa dashi kadai yake son magana. Don haka ba shiri Ma'aruf yaji maƙogwaronsa ya bushe a lokaci guda, saboda Baffa baya taɓa kiransa da wannan sunan sai idan har wani zance mai muhimmanci zasu yi, kuma rana ta karshe da zai iya tuna ya kira shi da hakan shine ranar da aka daura auren sa. Ya gyara zama a hankali yana jin yadda Baffan ya cika masa office din ta koina saboda kwarjini. "Sun turo min da takarda wadda take bayanin ciwon naka." Ya san takardar shima, sun tura ta email ɗinsa sannan sunyi printing ɗinta a cikin tarin takardun da aka sallamo shi dasu. "Sun ce a cikin shekaru biyu kawai ciwon ka ya kara haɓɓaka har ya kai matakin karshe, shi yasa abinda kayi ya faru..." Baffan ya faɗi haka sannan kuma yayi shiru, wannan dai al'adar ta manya. Ƙarar sautin shigowar saƙo daga wayar dake aljihun Ma'aruf ya cika shirun dakin kafin ya cigaba. "Ko zaka iya gaya min a shekaru biyun baya kana ina Ma'aruf?" Sai ya gyara zamansa a hankali, yana tuno ranar da Baffan ya naɗa shi a matsayin manajan kamfanin 'Bakori Enterprises' ranar da burinsa na farko ya fara cika a duniya. "Baffa... Shekaru biyu baya shine lokacin da ka bani matsayin manaja a kamfanin nan." Bai kalle shi ba, amma yaji sanda ya girgiza kansa. "Ba wannan ba, rayuwarka personally Ma'aruf, kana ina?" A yanzu ya rikice, yana jin kamar ma bai warke ba gabaɗaya, kamar ya sake bin jirgi ya koma asibitin nan ya kwanta. "Ka manta?" Ya tambaya amma bai bari ya amsa ba ya cigaba. "... Bari ni na tuna maka, shekaru biyu baya kana tare da iyalinka Ma'aruf, shekaru biyu baya kana tare da matar da naje na karba maka aurenta har ma da yarinya, a shekaru biyu baya kai cikakken mutun ne mai kamala da mutunci a idon mutane, kuma a tsawon shekarun da kayi cikin wannan mutuncin, hankalinmu da naka bai taba tashi kamar yadda yayi a yanzu ba." Wani abu ya zarce a maƙogwaron Ma'aruf, yaji wani ɓangare na ƙwaƙwalwar sa na gaya masa cewa wannan ce damarsa, yau shine lokacin da zai gayawa Baffa abinda shi da ishaq suka dade suna ɓoyewa, yau ya kamata ya gayawa Baffa cewa ba haka bane, abinda ya faru a zamansa da Ruƙayya har zuwa rabuwarsu ba yadda suke tunani bane sam. "Na san da wannan tunin da nayi maka ka fahimci abinda ni dama duk sauran al'umma suka fahimta Muhammad, don haka kaje ka fara shirye-shirye, nan da wata guda zan karɓa maka wani auren tare da na ƙannenka." Sai da aka shafe sakanni kafin maganar ta shiga cikin ƙwaƙwalwar Ma'aruf, da wani irin ƙarfin da sai da yayi da gaske kafin ya iya jawo iska ta shiga ƙirjinsa, sannan a karo na farko tun bayan fitar Ishaq ya ɗago idanu ya kalli mahaifin nasa. Sai dai me? Maimakon fuskar Baffan, sai hoton wajen ya canja a idonsa da wani lokaci da ya faru a shekaru biyu da suka wuce... Lokacin daya shaƙe wuyan Rukayya da duka hannyensu biyu, yaji ƙarar sautin karkarin da take fitarwa a lokacin da kuma yadda hawaye ke zuba daga idanunta yayin da take kallon ƴarsu da bata fi watanni shida a sannan ba... Babyn da ya karɓe daga hannunta ya wancakalar da ita a cikin falon, kanta ya bugu da kujerar gefe ta shiga ƙwallara kukan daya karaɗe gidan gabaɗaya, wannan sautin kukan da a kowanne daren duniya, dashi yake kwana a kunnuwan sa! *** Me ya faru shekaru goma da suka wuce? Wane bincike Ma'aruf ke yi da har ya kai ga tashin ciwonsa? Wacece Rukayya? Me ya faru da ita da kuma ƴar ta? Sannan wacece amarya ta huɗu a bikin iyalan gidan Alhaji Mansour Bakori? #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA UKU. **** A wannan daren... NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano. . A cikin ƙawataccen ɗakin, wata yarinya ta buɗe ƙofar ta shigo, ba zata fi shekaru uku da kaɗan ba, tana sanye da irin kayan yara kamarta, wani ɗan gajeran skirt kalar lemon greeen, (lemon tsami) sai farar rigar da itama akayi mata da ado da irin kalar, gashinta da ba wani yawa ne dashi haka zalika tsawo ba an tufke shi cikin kalba guda biyu da ribbon masu kalar kayan. Ta karaso cikin ɗakin daya gauraye da sanyin A.cn da aka kai maƙurarta, akwai wani tebur irin na ado dake gaban hadadden gadon dakin, ta kansa ta taka ta isa kan gadon, ta hau tana bi ta kan ƙafafun wadda ke kwance har ta isa daidai fuskarta da ta rufe da bargon data lulliba gaba ɗaya. "Mammy Mammy Mammy...." Ta kira ta na bubbuga daidai kanta da ƴan hannayen nata, a lokaci guda mahaifiyar tata ta yaye bargon daga fuskarta ta buɗe idanunta da kyar tana kallonta. "Menene Hameeda? Me ya kawo ki?" Ta tambaya ranta a ɓace. "Mammy I'm hungry. (Yunwa nake ji.)" Taja tsaki a hankali. "Ina Nannynki?" Sai kawai ta miko mata takardar hannunta, kamar ba zata karba ba sai kuma ta yatsunta biyu ta sakala ta cikinsu sannan ta buɗe ta. 'Ajiya I'm sorry Oo, dey don call me now say my mother dey hospital. I'll return tomorrow by God grace.' Ta sake jan wani tsakin mai tsayi, bata san sau nawa take gayawa Mary cewar ta daina yi mata pidgin a gida ba, amma don rashin mutunci shine har rubuto mata take yi a takarda. Ta juya ta sake kallon yarinyar data tsura mata idanu, dogwayen gashin idanunta sun kusa haɗewa da juna, yadda take lumshe su ya tuna mata da fuskarsa a lokaci guda. ...idanunka kake gani ko Ma'aruf? Irin naka ne sak! Muryar Mami ta haska a cikin kanta ranar farko na zuwan Hameedan duniya, ta tuno fuskarsa, yadda ya kalmashe ta cikin hannunsa, lumsassun idanunsa na haskawa da tarin ƙaunar da kamar wani abu ba zai taɓa giftawa a cikinta ba. Ruƙayya ta sake yin wani tsakin da ya riga ya shiga cikin dabi'arta kafin ta ture bargon gadon ta miƙe, wata lallausar doguwar rigar bacci ce a jikinta da idan ka kalle ta zaka ga kamar tana zamewa ne tsabar santsi da kuma kyallin da take yi. Ta kalli agogo wajen karfe bakwai na dare. "Baki ci abinci bane da rana?" Ta tambaya tana daure gashin kanta da za'a kwana a yini ana musu da wani akan cewar nata ne, don human hair ne (gashin mutum) da aka dinka mata shi cikin nata ya saje tsaf! "Mami tun da na sha tea, Mary bata bani komai ba. Waya take ta yi." Gwarancin yarinyar mai daɗi ya fito tana kallonta. Wani tsakin ta sake ja kafin ta dauki wayarta sannan tace. "Oya, taho muje to." Da sauri yarinyar kuwa ta sauko tabi bayanta, suka fita daga ɗakin zuwa wani dogon korido daya hada fuskokin ɗakuna, suka isa wani rantsatstsen falon da komai na cikinsa kalar ruwan gwal ne da kuma makuba, a gefensa akwai matattakalar bene, suka sauka har kasa zuwani falon da yafi wannan girma, ta jikin dining area suka shiga wata kofar da take ta kitchen ce, wani katon kitchen da yake a gyare tas. Babu ko tukunya guda daya akan gas don haka ta san babu wanda ya dawo a cikin kannen nata uku maza, suma can yawonsu waye ma zai gansu yanzu da magaribar nan? Dama Ashraf mai bi mata ne idan ya dawo daga aiki sau da yawa zai shigo ya dafa abincinsa tun bayan da suka rasa Josh (mai yi musu girki) yanzu kuma yayi aure sati uku da suka wuce don haka babu mai shigowa kitchen din. Hameeda ta ɗane kan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye worktable din kitchen din sannan ta zuba mata idanun tana jiran taga me zata yi, Allah ya sani ita bata son wani girki yanzu, da safen nan fa dawowarta kenan Nigeria daga ƙasar Paris inda suka tafi ita da mahaifiyarta, shi yasa ta kwanta take ta sharɓar baccin ta kuma yanzu ta tashi ta kama girki?... sai kawai ta dago da wayarta ta shiga nemo nambar Mariya, babbar ma'aikaciyar gidan. "Hajiya barkanmu da safiya. Ina kwana." Muryar dattijuwar ta cika kunnenta, bata ko amsa ba tace. "Mariya, abinci zaki kawowa Hameeda yanzu, a dafa mata duk abinda zata iya ci kawai." Daga cikin wayar Mariyan tace. "Hajiya ai bana gidan, yau kwana na uku a madobi, mahaifina ne ya rasu wallahi, amma su Jamila da Aisha suna nan." Ta ɓata rai a lokaci guda don ta manta lokacin da suna can taji mahaifiyarta ta na fada, sai kawai tace. "Allah ya jiƙansa." sannan ta kashe wayar. Ba zata yarda ƴarta taci abincin waɗannan kazaman yaran ba su tsaya a iya gyaran gidan da suke yi kawai, don ko Mama Mariyan ma da suka saba da ita tun yarintarsu ba kowanne girkinta suke ci ba, tunda Josh ya mutu shikenan kowa ya ta'allaƙa akan siyan abinci a waje tunda dama gidan ƴan maza ne ita kadai ce mace. "Hameeda me zaki ci?" "Mammy banda indomie." Ta fadi hakan alamun da gaske ta gaji da cin indomien, haka yasa ta gane cewar Indomie kawai Maryn ke ɗura mata da basa nan don haka ta gyaɗa kai kawai. Ta ajiye wayar akan table din sannan ta juya ta shiga store, ta fito da kwai guda uku a hannunta, ta kunna ruwa a kettle sannan ta fasa kwan ta soya shi cikin ƴan mintuna, ta haɗa mata tea da ruwan zafin da yayi sannan ta ɗauko biredi a fridge ta saka mata kwan a tsakiyar, ta zauna a kusa da ita tana kallon murnar dake kan fuskarta sanda ta fara cin ƙwan, har yanzu bata kai shekara hudu ba amma tsaf ta iya cin abinci da kanta, sai kawai tayi murmushi sannan ta janyo wayarta. Ta shiga whatapp tana fara ganin yadda messages ke tururuwa har da sababbin nambobi, sai da suka gama tsaf sannan ta danna kan sako guda ɗaya mai sunan Jawad da mintuna biyu kawai akayi da turo shi. "Baby kin dawo ko? I'm badly missing u here... Zanzo anjima kinji." (Ina mutukar kewar ki anan.) "Mammy nayi missing dinki." Muryar Hameeda ta katse ta daga amsar da take shirin rubutawa. Ta juyo ta kalle ta, tana ta cin biredin da sauri alamar da gaske yunwa take ji. Itama tayi kewarta da gaske shi yasa ma ta kasa jiran Maamah ta taho. Bayan bikin Ashraf ne suka tafi Paris ɗin ita da mahaifiyarta don medical check-up kasancewar hidimar bikin ta wajiga su da yawa, kuma satinsu ɗaya acan ta gaji ta taho don ranar da suka tafi ma Hameedan na bacci a hannun Mary ko sallama basu yi ba. Allah ya sani ta fara gajiya da wannan rayuwar, ba haka take hango ta ba sam, ba haka ta dinga hango abubuwa ba lokacin da mahaifiyarta dama kawayenta suka bata goyon bayan kashe aurenta ba, Maamah cewa tayi... "Idan baki fito daga gidan nan ba kin kusa kashe kanki ki tsufa a banza Ruƙayya, ta yaya zaki zauna babu wani isasshen hutu sannan kuma ki fara tara ƴaƴa bi da bi? Yanzu kika fara rayuwar ki fa, kina da dama mai yawa a gabanki Rukayya." Haka take gaya mata kullum, shi yasa ta rufe idanunta a wancan lokacin ta danne zuciyarta tayi abinda ya fito da ita ɗin, kuma har bayan aurenta da Alhaji Ahmad, tafiya take akan wadannan kalaman na mahaifiyar tata, takunsu take bi har ya kai ga mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad ɗin shima, kuma ko a yanzu ma bata fasa gaya mata cewar komai kaddara ce ta cigaba da cin ganiyarta ba, amma ita ta sani cewar bayan wannan ƙaddarar har da ƙaddarar zuciyarta akansa shi ma. Ta san duk irin halayen da zuciyarta ta shiga a gidan Alhaji Ahmad, ta san duk irin wahalhalun data fuskanta a kowanne lokaci na zamanta a gidan yadda ta dinga kwatanta abubuwa a gidanta na farko da kuma nasa tana ganin bambanci su a baiyane har suka kai ga matakin ƙarshe na mutuwar auren, don Maamah bata taɓa sani bane, amma MA'ARUF shine sanadiyar mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad. Kuma ko a yanzu da kowa ke kwaɗaita mata auren Jawad, ita ta sani cewar abinda ya faru shi zai sake faruwa, babu wanda zai taɓa iya cike gurbin Ma'aruf a ranta, ta so shi tun bata ma san kanta a duniya ba balle ta san menene son, ta so shi da dukkan kowanne bangare na ruhinta, don rayuwarta ma gabadaya tare dashi ta gina ta. Iyayensu maza abokan juna ne tun da dadewa, saboda haka ba zata taba iya cewa ga ranar data san Ma'aruf ba, tayi wayo ne kawai a duniya tana iya lissafo shi a cikin abubuwan da ta sani na rayuwa, don haka kowa ya sani cewar tsananin kulawar da take yi masa shi ya janyo hankalinsa akanta shima har ya kai ga soyayyar su. Sai dai a lokacin da ta aure shi, ta auri wani Ma'aruf din ne daban saɓanin wanda ta sani, ta san hakan don yasha gaya mata cewa Ma'aruf din data sani ya mutu babu ko da digonsa a cikin zuciyarsa, amma ta rufe idonta daga komai tace taji ta gani har aurensu ya tabbata. Auren da tun a darenta na farko a gidan abubuwa suka yi juyin waina daga yadda take hasko su. Ta rufe idanunta a hankali tana tuna dukkan abubuwan da suka faru a waɗannan shekarun, irin wahala da barazanar da rayuwarta ta fuskanta, sai dai ashe bata san gwara su sau dubu akan abinda zata je ta tarar a gaba ba, don a yanzu ta gane abinda taso ta manta a baya, cewar duk duniya Ma'aruf ne kadai namijin daya tattara duk wasu halayen da take so a wajen namiji. Shi yasa bata son sake maimaita kuskure na uku a yanzu, bayan guda biyun da tayi a baya na fitowa daga gidansa har kuma da auren Alhaji Ahmad. Ta riga yankewa kanta shawarar cewa ba zata sake biyewa kowa ba, ra'ayin zuciyarta kawai zata bi, zata samo yadda zata koma cikin rayuwar Ma'aruf kotawacce hanya kuwa, kuma bata ma tunanin cewa hakan zaiyi mata wuya tunda tana da abinda daga shi har iyayensa zai kassara su. Hameeda... Tayi murmushi tana sake kallon yarinyar, lokaci yayi da a yanzu zata san waye mahaifinta! *** A wannan daren.... Na baki amanar rai na, daiman Yau zaki ceton raina, abadan Kin ƙulle mini kwaɗon raina, da'iman Ki taho, raina yana sururi numfashina kece abadan dai'man! "Maryam dan Allah ki kashe waƙar nan, dan Allah." Amina ta faɗa tana hararar rediyon da Maryam din ta kunna, ta jingina ta da langa-langar langar kitchen ɗinsu yayin da ita take ciki tana girki. "Haba mana Yaya, kin san yadda nake son irin waƙoƙin nan fa, kuma yanzu zasu cire ma don wani shirin zasu fara." Maryam ɗin ta faɗa daga cikin kitchen ɗin, kuma jin tayi shiru yasa ta kara da... "Idan ana yi wallahi ji nake kamar in tashi sama don dadi, da wayarki android ce ai da har sai kin gaji da jin su ma." Amina ta girgiza kanta daga kan tabarmar da take zaune Hafsa a kwance akan cinyar ta tana tsefe mata kalbar da ta baɗe ta tsaf da wani sabon yashi da aka zube a layin nasu inda yara kamarta ke tururuwar wasa. "Ni basu dame ni ba sam, kawai a yanzu ne ban ga amfanin jin waƙar ba tunda kin san abinda yake faruwa." Jin haka yasa Maryam ɗin tayi shiru tana cigaba da yanka cabbage ɗin dake hannunta, kuma a daidai lokacin ma suka cire waƙar, muryar wani ma'aikaci daga gidan rediyon ta fara gabatar da shiri na gaba a jerin shirye-shiryen su, amma tuno abinda ke faruwar kamar yadda Amina tace, yasa Maryam ta ajiye wuƙar hannunta ta taso ta kashe rediyon gabaɗaya. A jiya da Baba ya fita zuwa kiran Hajiya Kilishin da yace, bai dawo ba sai wajen sha ɗaya saura na dare har su Hafsa da Adam sunyi bacci a sannan, wanda hakan wani abu ne sabo a wajensu, wani abu daban, saboda ba don sun kira shi a waya har ya ɗauka ba ma, Amina ta san tsaf Amma zata iya saka hijabinta a daren ita da Aminu su fara tafiya nemansa. Shi ba mutum ne mai dadewa a waje ba musamman idan dare yayi, abubuwa da yawa komai muhimmancin su in har dare ya raba to zai ajiye su ne sai zuwa gobe, ko hirar maza irin ta daren nan Baba baya taɓa zaman yinta, tun suna yara sun taso da sanin cewa lokacinsa da daddare nasu ne, a cikin iyalansa zai zauna ayi wasa da dariyar da a cikinta zai fahimci dukkan matsalolinsu. Don haka a jiyan da ya kai goma sha ɗayan dare dole zuciyoyinsu suka kasa nutsuwa sai lokacin da suka ji ƙarar shigowarsa da kuma rufe kofar gidan da yayi, babu wuta a lokacin, sannan Aminu ya fara tararwa jingine da bango yana danna wayarsa. Kuma ta cikin ɗan hasken fitilar tsakar gidan da batiranta suka gama yin sanyi, Amina ta hangi fuskarsa tattare da dukkan wani nau'i na damuwar dake fitowa har a cikin sautin muryarsa sanda yake amsa gaisuwarsu, gaisuwar da daga ita bai sake cewa komai ba, ya nufi hanyar ɗakin sa kawai ya shige. Amma ta ɗebi kwanukan abincinsa ta bishi dasu yayin da suma kowa ya kama hanyar makwancinsa, Aminu yayi hanyar soro inda ƙofar ɗakinsu shi da Adam take, su kuma suka dauki Hafsa suka shige nasu dakin, kuma ba sai ta tambaya ba, Amina ta sani daga ita har Maryam da Aminun babu wanda yayi baccin kirki a ranar. Kuma babban abinda ya ƙara tsurar dasu shine na yadda har a yau basu ji komai ba, ko daga bakin Amman kuwa. Baban bai ko je aiki ba a yau, tun safe ya fita zuwa gidan wansa da suke kira da Kawu mallam kuma bai dawo ba har yanzu, Amman ma kusan a daki ta yini tun bayan fitarsa, ita kadai tayi ta kai kawo a gidan bayan sun tafi makaranta, tace mata wai gyaran durowarta take yi, amma tsaf Amina ta sani cewa kayan nata data barbaza akan katifar ɗakinta ba don ninki ta fito da su ba saboda yanayin dake fuskarta kusan iri daya ne da wanda ke kan fuskar Baba tun a jiya da daddare, kuma wajen la'asar sai ga kiran Baba a wayar Aminan cewa Amman taje ta same shi a gidan Kawu mallam ɗin, wanda hakan shine abinda ya ƙara ɗaga hankalinta, da ƙyar Aminu ya shawo kanta bayan sun dawo daga makaranta kafin ya tafi wajen aikinsa shima. Sai dai kafin ta bawa Maryam amsa, Adam yayi sallama yana shigowa. "Salamu alaikum, wallahi Yaya yarinyar nan ƙarya take, babu wanda ya ture ta, wasan banzan su kawai suke yi, ga sauran ƙawayen nata can ma har yanzu a kusa da yashin." Ya zayyano dukkan wannan bayanin daga tsaye kasancewar shi yaje ya zaƙulo ta tsakiyar masu wasan yashin. Da jin haka kuwa Hafsa tayi narai-narai da muryarta ta shiga rantsuwa tana faɗin da gaske ture ta akayi ta faɗa kan yashin, wanda kowa ya san ƙarya ne wasanta tayi daga yadda baƙin gashin kan nata ya burɗine tsaf da ƙasa. "Ko baki ɓata kanki ba meye amfanin zuwa wajen yashi da magriba Hafsa?" Amina ta faɗa a hankali tana kama wata jelar, don ita ko kaɗan ba ta fadan nasu take yi ba, jikinta ne kawai zaune a gidan amma hankalinta ruhinta zarya kawai suke a hanyar gidan Kawu mallam kamar tururuwa, shi yasa ko girkin daren ma tace Maryam tayi. Allah ya sani abu na ƙarshe da zata so a yanzu shine wata matsala ta sake gifta musu, rayuwarsu ta haska da kaloli mabanbanta a shekarun baya, sun fuskanci abubuwan da ko a labari basa son tunawa, kuma har yanzu ƙoƙarin tashi suke, ƙoƙari Baba yake don ganin rayuwarsu ta daidaita ko da ba kamar a baya ba, don haka ta yaya zasu taɓa son ace sai sun sako daga farko idan wani abu ya sake gifta musu ya a yanzu... Har sai da ta gama wankewa Hafsa gashin nata da karkashi sannan Amma ta dawo, Baba kuma bai shigo ba sai bayan sallar isha, wanda kafin ayi hakan har Aminu ya riga su dawowa, a tsakar gidan ya tarar dasu tana sake yiwa Hafsa wata kalbar bayan ta wanke matta kan, yayi wanka yazo ya zauna a cikinsu shima yana ta mita da tsokana akan girkin da Maryam ɗin tayi, jollof din shinkafa da taliya ce da ko a ido tayi kyau, amma tunda ya zauna yake sukar abincin yana kuma kai loma. "Wallahi akayi miki aure kika je kina irin wannan abincin sati daya zaki yi ya koro ki, ace jollof amma ba mai sa faman kora ruwa nake kamar dambu nake ci." An kawo wuta a lokacin don haka tsakar gidan yayi tar da wasu sababbin ƙwan fitilar da ya haɗa da kansa ya saka musu. Maryam da a lokacin take wanke uniform dinta daga can bakin famfo tace. "A haka babu man kake ƙoƙarin tayar da plate din ai." "To idan ina jin yunwa ya zanyi? rufa miki asiri kawai nake ma wallahi, don yanzu ina tafiya wajen Isah (mai shayin layinsu) kowa sai ya gane cewar a gidanmu ba'a iya girki ba kenan, kinga masu kokarin zuwa nan gaba ma sai su fasa. Kuma Amina ita ta riga ta samu kece a ruwa." Maryam ta juya bayanta amma yana ganin adadin yadda gefen fuskarta ke juyawa wajen murguɗa baki tana faɗar wasu abubuwa da ba jin su yake ba. Yayi murmushi yana sake faɗin. "Hotonki zan nemo a wayata in maida shi fari da baki in rubuta ga matar da akan girkinta aka ƙirƙiri sunan abincin 'Ci kar ka mutu, 1987.'" Bai saurari abinda take cewa ba ya juya ya kalli Amina da bata sanya baki a hirarsu har yanzu ba, ganin damuwar dake kan fuskarta har a lokacin ya dawo da hankalinsa kanta sosai. "Wai har yanzu damuwa kike? Nace miki fa ki kwantar da hankalinki tun dazu. Ni alamar ma da na gani kamar wasu maƙudan kuɗi Baba ya samo shine aka tafi gidan Kawu mallam ɗin ake ta faman lissafi." Ba shiri dole Amina tayi murmushi tana kallonsa. "Aminu Allah ya shirye ka, komai sai ka maida shi wasa wallahi." "To me yasa zaki yi ta damun kanki akan abinda bai ƙaraso ba tukunna." Ya faɗi hakan sanda ya juyo, idonsa ya kai kan hannun Maryam dake ta cuɗa kayan wankinta. "Ke, idan kinyi ƙunshin nan ma haka zaki cigaba da irin wannan wankin? Kwana biyu ya goge? Kuɗina zaki taso ki dauko min Allah indai haka ne." "Kudin ka ai sun riga sun shigo kenan wallahi baza su dawo ba, sai dai idan nayi ƙunshin ka kankare shi." Amina ta kalli yadda yake murmushi yana kallon Maryam din, ta san shima ya damu, watakila damuwar ma har tafi tata, amma haka Aminu yake a kodayaushe, shi mutum ne da zai sa kaji kamar baka da wata matsala koda kuwa kana nutsewa a cikinta ne tsamo-tsamo. Lokacin da Baba ya shiga tashin hankalin karayar arziƙinsa, Amma tace Aminu shi ya ɗauki kaso mai yawa bayan addu'a wajen dawo dashi daidai. A daidai lokacin Amman tayi sallama ta shigo, kuma kallonta kawai Amina tayi taji gabanta ya faɗi duk duk da cewar yanayin damuwar fuskar tata ya ragu akan da safe. "Haba Amma kun barmu sai kace marayu a gidan nan, ko shirin yaƙin duniya kuka tafi yi yaci ace kun gama." Duk da yanayin Amman sai da tayi wani guntun murmushi tana girgiza kai sanda suka shiga yi mata sannu da zuwa, don ta saba a irin lokutan wasansa, Aminu ya riga ya mayar da ita kamar kakarsa. A lokaci guda sai komai ya dawo daidai a gidan, da duk yawansu ji suke kamar a cikin wani fanko suke, Adam ya dawo daga siyan wainar fulawar da Maryam ta aika shi, Aminu ya kafa ya tsare cewar sai yaci rabi don wai ya san da kudinsa ta siyo, duk dauriyar Maryam sai da ta rufe idaninta ta fito da duk masifar dake cikinta wanda dama abinda yake jira kenan don haka shi da Adam suka dinga kyalkyala mata dariya. Sannan a ƙarshe bayan sun shiga falo, wani film din indiyan da ake yi a tashar Bollywood ya ɗan daukewa Amina hankali daga wannan damuwar ganin cewar Amman ma har ta sake tana kokarin sakawa Hafsa maballi a wuyan rigar makarantar ta, tana yi tana mitar yadda Hafsan ke yawan yar da maɓallan rigar. Falon ya ɗauka da sautin wakar film ɗin da ake yi lokacin da take ke kallon fuskar kowa tana murmushi, yadda Hafsa ta zuba manyan idanunta tana saurarar kashedin da Ammar keyi mata akan maballin, da yadda Aminu da Adam ke cigaba da dariya tsokanar Maryam da bata ganewa ta daina biye musu, har ma da idanun Maryam ɗin da suka cika da haushi fal! Haka take so... Haka take so rayuwa ta kasance musu a kodayaushe. Sai dai rayuwar bata taɓa biyewa muradan zuciya, ita da zuciyar ma sunyi hannun riga, ƙaddara take kallo a kodayaushe tana bin takunta, don a lokacin da Baba ya dawo bayan sallar isha a lokacin komai ya ruguje, zuciyar Amina ta sake ruftawa cikin ramin da yafi wanda ta fito daga cikinsa zurfi. Su Hafsa suna makarantar dare a lokacin, Aminu kuma ya fita wajen abokansa sannan Maryam da wata ƙawarta sun tafi bakin titi wajen mai yin zayyanar allo kasancewar suna dab da yin sauka a islamiyya, gidan ya rage sai ita kaɗai, kamar dama ƙaddarar ta zaɓi wannan lokacin ne don ita kadai ɗin. Amma ta kira ta zuwa ɗakin Baba lokacin da take kokarin haɗa kan kitchen ɗinsu, kiran daya tabbatar mata da cewar abinda take jira ne zai kasance kuma a hanyar zuwan tunanin ta ya ɗan ɗaure don a zaton ta ita da Aminu ya kamata su zayyane wa komai. Ta shiga ciki lokacin da Baba ya rufe flask din nasa abincin da ya gama ci, ta zauna a daidai saitin Amma da har a lokacin ta kasa tantance yanayin fuskarta. "Amina jiya da naje gidan Hajiya Kilishi aurenki na bayar ga ɗansu." Maganar ta fito daga bakin Baban kai tsaye ba wane shamaki balle kewaye kewaye, kuma ta tafi kai tsayen har zuwa cikin ƙwaƙwalwar ta, sai dai bata nutse ba, zagaye kawai ta dinga yi a zaman kan nata kamar mai jiran a buɗe mata ƙofar shiga. Shiru ya ratsa ɗaukacin dakin, shirun da a cikinsa Amina ta kasa ko zuƙar numfashi, kuma bata damu da tsayinsa ba don har a lokacin bata gane maganar da Baban ya faɗa ba, shiru kawai tayi kamar bata ji shi da farko ba a yanzu take jira yace wani abu, sai da shi da kansa yaga bata da alamar magana sannan ya sake kiran sunanta. "Amina.." Ta kuwa ɗago ta kalle shi, da idanunta dake haskawa a cikin hasken fitilar ɗakin, sai ya cigaba shima kamar bai fadi maganar farko ba. "Jiya da naje gidan Hajiya Kilishi da mijinta nayi magana ba da ita ba, kiran nasa ne ba nata ba, don da na isa gidan mota kawai tasa aka ɗauke ni aka kaini har ofishin mijin nata. Acan na tarar dashi tare da ƙaninsa, mutane ne manya-manya Amina masu mutunci da kuma kwarjini, kuma kai tsaye suka shaida min cewar aurenki suke nemawa ɗansu, yace min Hajiya Kilishin ita da kanta ta roƙe shi alfarmar hakan saboda yarda da hankali da kuma tarbiyar da muka baki. Al'amarin ya girgiza ni kamar yadda kika ji shi a yanzu kema, amma wallahi a wannan lokacin ba zan iya kallon idanun wadannan mutanen ince musu 'A'a' ba don bani da wata hujja ko dalilin da zai sa in faɗi hakan..." Ba fahimtar abinda yake faɗa Amina take ba har a lokacin, kallonsa kawai take tana jin yadda muryarsa ke karyewa da kowacce kalma daya fada, mahaifinta mutum ne da ta sani jajirtacce, ko a lokacin da yake cikin tashin hankalin karayar arziƙinsa, baya taba fasa binsu da alkawuran cewa zai inganta rayuwarsu don kar su karaya da komai. Amma a yau kiri-ƙiri take jin duk wata amon karaya a muryar tasa, amon da take ji yana bin jijiyoyin ta yana tayar da tsigar jikinta bi da bi ta kowanne ɓangare. "Na san karatu ne a ranki Amina, kuma na san ba sau daya ba sau biyu ba na sha yi miki alƙawarin cika miki wannan burin amma a kullum abinda muke tsarawa daban, wadda ƙaddara ta tanadar mana daban, kuma na san ba sai nayi miki bayanin wannan ba don a ƙananun shekarunki kin gan kalolin ƙaddarar mabanbanta, shi yasa nake son ki kalli wannan ɓangaren ƙaddarar ma, ki kalle ta idanun rahma Amina, Allah ya sani a zuciyata na yarda cewa ban miƙa ki inda zaki wahala ba, don komai halin da zan shiga a duniya ba zan yarda da duk abinda zai cutar daku ya matso kusa ba balle har in kai ku da hannu na. Kin san Hajiya Kilishi kin san kirkinta, kin san yanayin gidanta, ina ga kinje kusan sau biyu ke da mahaifiyarki, saboda haka Amina wallahi zuciyata bata bani cewa zaki wahala a wannan wajen, damuwata kawai shine yunƙurin rushe miki burin ki da nayi da kuma cewar na yanke hukunci a lokaci guda." Yayi shiru a lokacin, Amina ta haɗiye wani abu a makogwaron ta da bata san sunansa ba, maganganun Baba a gefe suke daga cikin kanta, har a yanzu damuwar dake cikin muryarsa itace a gabanta, ita take lissafawa tana son kirga adadinta. A hankali ta juyar da idanunta kan Amman dake zaune a saitinta, kuma a hankalin idanunta suka fahimci abinda ta kasa ganewa a fuskar tata ɗazu, damuwa ce fal ke yawo a cikin nata idanun! Wani abu da ya ƙara rikita tunaninta a lokaci guda... Don bata taba tunanin cewa irin wannan maganar ce zata saka Amma cikin damuwa itama ba, idan har zata iya tunawa tun farko dama ita tafi son zancen aurenta akan karatun da take naci, kawai ganin cewar daga ita har Baban akan son karatun suka tsaya yasa ta sallama itama, amma duk da haka tasha gaya mata cewar ba ba lallai sai ta gama karatun zata yi aure ba, to me yasa wannan maganar zata dame ta? Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa sannan ta gyara zamanta a hankali, tana jin nauyin idanun iyayen nata biyu dake kallonta, so take tace musu in har wannan ne abinda ya tashi hankulansu a gidan tun jiya to su kwantar dashi, don a cikin aure da zancen rashin karatun tana jin ba wanda na zata iya daurewa ba don farin cikinsu. "Baka ƙarasa zancen naka ba ai Mallam, baka gaya mata abinda yafi komai muhimmanci ba." Kamar saukar ruwan sama a lokaci guda muryar Amman ta faɗa, kuma a lokaci gudan Amina taji gabanta ya faɗi, abu muhimmanci tace, kenan wani abu ne daban, wani abu da yafi girman abinda ya faɗa, wani abu da wataƙila shine dalilin damuwar dake kan fuskar Amman da ma zuwansu gidan Kawu mallam a yau. Taji Baba ya sake gyara zamansa sannan ya kira sunanta. "Amina..." Ya kira kamar tayi nesa dashi, kuma ta san me hakan ke nufi saboda haka da sauri ta ɗago idanunta daga kan ƴan yatsunta ta kalle shi, ƙaguwar ya furta abinda zai faɗa na haskawa tar a cikin idanunta. "Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!" A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin! *** A wannan daren.... Wajen ƙarfe tara saura a lokacin da wata mota ƙirar kamfanin 'Elantra' ta shigo cikin layin, ƴan yara maza dake wasa akan hanya suka dinga darewa da gudu cikin wasansu suna bawa motar hanya kasancewar faɗin layin ba zai yiwu ta wuce kuma suna wajen ba. Ko'ina yayi tar da wutar nepar da aka kawo don gaka ƙyallin sabubtar motar haskawa kawai yake yi a idanun mutane kamar an shafe ta da maiƙo. A cikin motar saurayin dake zaune a kujerar gefe mai suna Jamilu ya nuna ƙofar wani guda inda hasken jan kwai ke ci a samansa. "Wancan ne gidan yallaɓai, in dai gidan Alhaji Sulaiman ɗin daka kwatanta min ne to shine gidan." Ma'aruf dake rike da sitiyarin motar a gefen sa ya gyada kai a hankali yana kallon ƙofar gidan shima. "Nagode sosai kaji." Saurayin ya washe baki. "Ah haba yallabai ai ba wani abu wallahi. A sauka lafiya." Ya faɗi hakan da tsantsar murna yana ƙara rike sababbin kudin da Ma'aruf ɗin ya danka masa tun lokacin da ya shigo motar, a can farkon layin ya dauko shi, cikin dandazon wasu samari a inda ake sayar da rake. Kuma duk yadda ya kai ga kwatanta musu gidan Alhaji Sulaiman ɗin da yake nema, saurayin ne kaɗai ya gane don haka ya roƙe shi yazo ya ƙarasa dashi. Saurayin ya rufe ƙofar motar daidai lokacin da kira ya sake shigowa a wayarsa, tun dauko shi dama ake kiran wayar kuma daga nambobi biyu kawai Ishaq da Mami, yana kallon yadda saurayin ma ke ta kallon wayar tun da ya shigo idanunsa na haskawa da mamakin cewa me yasa ba zai ɗauki kiran ba. Ya ƙyale wayar yayi gaba a hankali zuwa daidai kofar gidan da yake kallo ya tsayar da motar daga gefe sannan ya janyo ta. "Ma'aruf kana ina? Ina ka tafi?" Muryar ishaq ta fito a lokaci guda da ya amsa, sai ya koma da baya ya jingina kansa da kujerar motar sannan yayi murmushi. "Kana magana kamar kana neman wani yaro ɗan karami, sau dubu nawa a rayuwata na ɗauki mota na fita da daddare Ishaq?" Yaji yadda Ishaq din ya fitar da numfashi cike da takaici. "Wai ka haukace ne gabadaya Ma'aruf? Yanzun nan fa muka dawo ƙasar nan, minti biyar kawai kayi a gida kayi wanka ka fito! Yanzu ƙarfe nawa? Tara fa ta wuce, ta yaya zaka ɗauki mota ka fita a halin da kake ciki?" Ya sanya ɗaya hannunsa ya cusa yatsuntsa cikin gashinsa yana tuno abinda ya faru bayan barinsu Office ɗin Daddyn, tsaf ya zayyanewa Ishaq abinda Daddyn ya shaida masa tun a hanya kafin su ƙarasa gida, kuma zai iya rantsewa kamar yadda maganar ta tsorata shi haka ta daki Ishaq ɗin shima, amma duk da haka ya boye ta hanyar gaya masa cewa ya kwantar da hankalinsa kawai insha Allah zasu daidaita komai a hankali, wasu maganganu da jinsu kawai yayi a lokacin da yake furtawar. Don suna shiga gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wasu riga da wando duka kalar baki sannan ya dauki wata rigar mai hula (hood) da dogon hannu ita kalar ruwan toka ya dora akai, ya rufe kansa da hular amma duk da haka ana ganin sumar kansa data taru itama baƙa wuluk da ita kamar kayan. Lokacin da ya fito falo Ishaq ya shiga wanka shima, don haka wayarsa kawai ya dauka da muƙullin motar Ishaq ɗin yayi waje, don shi tasa motar tana can gida ba'a dawo da ita ba tun ranar da al'amarin ya faru (lokacin da ya ɗauko mutumin da yayi wa duka daga Office ya kaishi wajen Daddyn.) Ya tabbata Ishaq yaji lokacin da maigadi ya buɗe masa gate ya fita, don bai ko bar kan layinsu ba kiransa na farko ya shigo, amma bai dauka ba, sai da ya katse sannan ya lalubo nambar Sameera a cikin wayarsa ya kira. Sameera itace kusan komai na gidan nasu don itake kula da kusan harkar komai a gidan, shi yasa duk wanda zaiyi wani abu sai ya neme ta, saboda haka ya sani duk wani information in dai ya taɓa ratsawa da gidan ba lallai ne taƙi samunsa ba. Daddy ya gaya masa cewa mahaifin yarinyar da suke zancen zata shigo rayuwarsa ɗan'uwan Mami ne kuma sunansa Alhaji Sulaiman. Don haka kai tsaye bayan Sameeran ta gama murnar dawowarsa da kuma shaida masa cewar ai direban Hajiya Madinan da yayi clear dashi kafin ya fito titi zai kawo musu abinci yanzu, sai ya tambaye ta. "Waye Alhaji Sulaiman a ƴanuwan Mami?" Shirunta ya nuna alamun tambayar ta bata mamaki amma duk da haka mamakin nata baiyi tsawo ba tace. "Ko wanda yazo jiya? Ɗan'uwansu Hajiyar Mami ne, yana ɗan zuwa dai ba sosai ba." Ya cije gefen lebbensa kafin ya sake tambayarta. "Da yazo jiyan me yayi?" "Bai wani daɗe ba Yaya, Mallam Sani ma aka saka ya tafi dashi office ɗin Daddy wai zasu yi magana." Da jin haka ya tabbata shine wanda yake nema don haka kai tsaye ya sake tambayarta. "Kin san gidansa?" "A'a, amma Mami tace a Gadon ƙaya yake wai wajen layin transformer." Ya gyada kansa. "Kin san sunan ƴaƴan sa?" "Eh, Babbar dai kawai na sani sunanta Amina." Ya riga ya gama samun abinda yake so don haka ya gyada kansa kawai yana gode mata sannan ya kashe wayar, kwatancen daya kawo shi har kofar gidan kenan a yanzu. "Ina Gadon ƙaya." Ya bawa Ishaq amsa ta cikin wayar. "Gadon ƙaya? Wajen wa? Me zaka yi?" "Ni da kai mun sani cewa abinda Daddy ke shirin ba ƙaramin hadari bane Ishaq, don haka zuwa nayi na warware komai tun kafin lokaci yaja da abinda ba zai taba faruwa ba." "What?" Ƙarara mamaki da kuma fargaba suka fito daga muryar Ishaq ɗin, kuma Ma'aruf zai rantse ya shiga girgiza kansa lokacin da yake faɗin. "Kar kayi haka Ma'aruf dan Allah, ka juyo ka dawo. Zuwa wajen mutumin nan ba shine zai kwance komai ba..." "Ba wajensa nazo ba don dashi da Daddy duk abu ɗaya ne. Ita nazo gani Ishaq, saboda a yanzu maganar ta koma ni da ita kawai." "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un... Ma'aruf me zaka yi?" Salatin ya saka shi sake yin murmushi yana cije lebbensa. "Nuna mata zanyi irin ramin da ake shirin jefa ta, nuna mata zanyi da gaske bani da hankali." "B, tsaya kaji..." Dib. Ya katse kiran ya ma kashe wayar gabaɗaya. Idonsa ya sake kallon ƙofar gidan yayin da zuciyarsa ke zana masa dukkan hotunan abinda zai faru kafin ya kashe motar ya fito. Ya sake janyo hular rigar yana ƙara rufe fuskarsa daidai lokacin da wasu yara biyu mace da namiji suka zo shiga gidan idanunsu akan shi da kuma motarsa. Da sauri ya yafito namijin alamun yazo. Ya kuwa taho yayin da macen ta tsaya tana kallon su hannunta rike da wani abu da take ta lasa. "Bigboy ya sunanka?" Amon muryarsa mai zurfi da taushi ya tambaya sanda yaron ya ƙaraso. "Adam." Ya gyada kansa yana murmushi lokacin da ya zaro wata sabuwar ɗari biyar daga aljihunsa yana miƙo nasa. "Idan ka shiga gidan nan Adam kace wai Amina tazo." "Toh." Ya amsa da nasa murmushin shima sannan ya juya, idanunsa ko kaɗan bama su ga kuɗin da yake bashi ba. Da murmushin da bai san dalilinsa ba Ma'aruf ya maida kudinsa cikin aljihu yana kallon tafiyarsu zuwa ciki, ƴar yarinyar har sai da sake juyowa ta kalle shi lokacin da Adam ɗin yaja hannunta zuwa ciki. A hankali ya dawo da fuskarsa kan katangar gidan, idanunsa na hasko masa dukkan abinda zai faru nan da mintunan dake shirin tahowa! *** Me zai faru?? Me zai faru?? . . . Me Ma'aruf zaiyi?? #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA HUDU. ~~~~~ "Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!" A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin! Kuma bayan walƙiyar ta ɗauke a idanun Amina, Baba ya cigaba da maganarsa. "Wannan maganar ita ta sanya a safiyar yau dana shaidawa Kawu mallam dukkan abinda ya faru ya tara meeting din da ya sanya yinin mu a gidan, don har su Kawu Ibrahim da Kawu Hamza sun zo a yau..." Ba shiri tasirin sunayen ya sanya Amina ta sake ɗago da idanunta ta kalli mahaifin nata, yayyen Baba hudu ne kuma shine ƙaraminsu, Daga Kawu mallam sai Kawu Abubakar da suke kira da 'Baban kurna' sai kuma Kawu Ibrahim da Kawu Hamzan da dukkansu biyun suke zaune a garin Abuja tare da iyalansu, don haka bata san adadin mamakin da zata iya kiyastawa ba na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda Babn ke kallonta yana son fassara yanayinta yasa ta maida idanunta ƙasa a hankali yayin da hannunta na dama ya kamo karshen skirt dinta da ƙarfi. "Amina a jiya babu irin boren da mahaifiyarki bata yi min ba akan maganar nan, dukkan ku shaida ne cewa Halima mace ce mai biyayya gare ni, don tun daga ƙuruciyarku har yanzu babu ranar da ɗayanku zai ce kunji kanmu ni da ita game da wani al'amari a gidan nan, duk abinda na fada ko nayi daidai ne a wajenta, amma a karo na farko jiya mahaifiyarki ta bijire min akan wannan hukuncin, tace bata yarda ba, tace ba ni kadai na haife ki ba itama tana da nata haƙƙin akanki don haka ba zan siyar dake ga wasu mutane ba kamar yadda ta fassara al'amarin. Kuma bayan zuwan su Kawu Ibrahim a yau sai suma duk suka goyi bayanta, da ni da Kawu mallam da Baban kurna Amina mune kadai muka hango wannan al'amarin ta fuskar alkhairi da kuma cigaban ki wanda su basa gani. Don haka na san a shekarunki da kuma hankalin yabzu zaki iya banbance daidai da akasinta, don haka muka yanke cewar matsayar tana gare ki yanzu, duk ɓangaren da kika zaɓa shi zai fi rinjaye kuma maganar ta zauna kenan har abada, kar ki ga cewar na amsa musu acan, ki faɗi ra'ayinki Amina babu wanda zai taɓa ganin laifinki don rayuwar ki ce, mu duk ƴan kallo ne kawai. Don haka kije kiyi tunani daga yau zuwa gobe, saboda idan har ɓangaren mahaifiyarki kika ɗauka, ina so ne muje mu sami mutanen tare da su Kawu Ibrahim kafin su koma kuma kafin wani abu ma daga ɓangarensu yayi nisa. Kije kiyi tunani Amina." Shikenan! Shikenan sai duk bayanin ya ƙare da wannan jimlar, lokaci kuma ya fara bugawa da adadin awannin da zasu tadda goben, goben da Baba ta furta kamar tsawonta na shekara guda ne. Taji lokacin da ya miƙe ya zo ya wuce ta, taji shi ya zura takalmansa daga waje sannan taji ƙarar takunsa na nufar hanyar soro, sai kawai ta rufe idanunta gabaɗaya tana hadiye wani abu da bata sanshi ba a maƙogwaron ta. "Duk abinda mahaifinki ya fada haka ne ya faru Amina, kuma ba komai yasa nayi hakan ba sai don nemar miki ƴancinki..." Da wani sassanyan amo muryar Amma ta maye gurbin ta Baban tun kafin ta bude idanunta "... Ƴancinki nake nemar miki Amina, don ni na hango abinda mahaifinki ya kasa ganowa, mutanen nan masu kudi ne da gaske, kuma duk tsananin kirkin mai kuɗi a zaune yake cewar baya taba son mu'amalar rayuwarsa da talaka kamar mu, zasu taimaka, zasu yi zumunci kamar yadda ita wannan Hajiya Kilishin ke yi amma aure Amina, aure babban abu ne da shine linzamin rayuwarka ta duniya har zuwa lahira, don haka kowa ya sani cewa hakan ba ƙaramin abu bane ga rayuwar mutum da zai haɗa shi da kowa. Da ke muka je auren wani ɗansu a shekarun baya da suka wuce, kinga matar daya aura ai, kinga irin tarin dukiyar ubanta da danginsu, don ba a banza bahaushe ke cewa 'ƙwarya tabu ƙwarya ba... Kowa daidai dashi yake nema. Saboda haka Amina ko makaho yaji wannan zancen ya sani cewa mu ba daidai da mutanen nan muke ba, sun nemi aurenki ne kawai don son zuciyarsu..." Sai tayi shiru kamar tana kokarin haɗewa wani abu da ya taso mata ƙirji yayi sanadiyar canjawar muryarta. "Amina, ciwon yaron nan na 'Hauka' ne na tabbata suka yi masa ado da matsalar ƙwaƙwalwa kawai, kuma kin san wannan ba ƙaramar magana bace, kowa ya sani, su ma sun sani shi yasa basu tunkari kowa da wannan zancen ba sai mu, mu talakawa da aka mayar kamar ba mutane ba, mahaifinki dasu Kawu mallam suna ta danganta al'amari da ƙaddara, alhalin basu ƙara binciken komai akan yaron nan ba, amma ni nace idan har ƙaddarar ce me yasa basu kai ta ga irin ƴaƴan masu kudin da ɗaya ɗan nasu ya aura ba? me yasa sai a yanzu ne irinmu zasu yi musu amfani... Na sha gaya miki masu kuɗi basa kallon kowa sai kansu, suna ganin talaka kamar shi ya zaɓawa kansa rayuwar sa, kamar dama Allah ya halitto shi ne kawai don ya kawar musu da matsalolinsu. Rayuwarki zaki sadaukar musu idan har kika zaɓi tafiya Amina, don aure ba karamar gwagwarmaya bace ko da mutum mai hankali kuma wanda kake so balle babu duk biyun a naki, rayuwarki zaki sadaukar musu a banza, dukkan wani mafarki da burinki sai ya mutu wajen yi musu bautar da baza su san kina yi ba, don wannan sigar auren a wajensu, bata da banbanci da cewar siyen ki suka yi..." Ta sake yin shiru sakamakon yadda Aminar ta runtse ido da tasirin maganar, amma duk da haka sai ta cigaba. "...Annabi yayi gaskiya da yace kudi sune masifar ƙarshen duniya, a karo na ba adadi wallahi na sake yarda da hakan, don ban taɓa tunanin cewa mutum kamar mahaifinki zai iya faɗawa cikin tarkonsu ba..." Wannan karon kalaman suka daki zuciyar Amina da tasirin da yasa a lokaci guda ta ɗago ta kalle mahaifiyar tata tana girgiza kai. Ta sani dukkan abinda ta faɗa gaskiya ne, amma ba ta yarda da wannan hasashen nata na ƙarshe ba, ba zata taɓa yarda cewa kuɗi zasu rufewa Baba ido har ya mika ta ga inda zata cutu ba, haba mana! ta manta ne? Ta manta duk wannan tarin ƙaunar tasu dake tare dashi? Ta mata tarin sadaukarwar da yayi a rayuwarsa saboda su kawai? Sai dai kallon da Amman ke mata yasa ta sake sunkuyar da kanta a hakali tana rufe idanunta da ƙwalla ta taru a cikinsu, dukkan maganganun da Amma ta fada gaskiya ne ta sani amma har a lokacin ta kasa gasgata zancenta na karshe don ta sani cewa ko da numfashinta na ƙarshe a duniya ne zata yarda cewa ba zai taɓa mika ɗayansu ga inda zasu cutu ba... A kullum shi mai son gyara rayuwarsu ne. Ta kai hannu tana share idanunta lokacin da Amman itama tace. "Kije kiyi tunani zuwa goben Amina, ki auna kowanne ɓangare ki ga wanda yafi rinjaye, ni dai a matsayina na mahaifiyarki kuma mace kamar ki na gaya miki abinda nake ganin shine daidai" Ta rufe bakinta daidai lokacin sallamar su Adam daga makarantar dare ta kwararo a tsakar gidan. Shi da Hafsa ne suka karaso har cikin dakin bayan sun duba falon da babu kowa, da sauri Amina ta saka bayan hannunta ta share hawayenta kafin su ƙaraso da hayaniyarsu. "Amma kaina ciwo yake yi." Muryar Hafsan ta ambata tun kafin ta shigo ɗakin da kalar ƙorafinta na kullum yayin da Adam shima ya shiga ƙaryata ta. "Amma wallahi makaranta ce bata son zuwa gobe ƙarya take yi, yanzun nan fa har kusan faɗa fa suka yi ita da wasu a wajen ƴar tsohuwa, ba don nazo da wuri ba da ko kafi-kazan data siya ma baza ta samu ba." Babu wanda ya lura da yanayin dakin a cikinsu sai bayan da suka ga Amman bata basu amsa ba, tayi shiru kawai tana kallonsu, wanda hakan yasa Adam yasha jinin jikinsa, ya sake kallon fuskar Amman da kuma ta Amina ya tabbatarwa kansa cewa basu yi daidai da lokacin da ya kamata ba, don haka ya nufi kofa, sai dai har yasa ƙafarsa ɗaya a waje ya tuna da saƙon da aka bashi. "Au na manta wallahi, Yaya in kin fito ana kiranki a waje." Da haka ya juya yayi hanyar Kitchen ayana fadin zai sake zuwa yaci abinci. Amina ta ƙara share hawayen idanunta, Abdallah ne ta sani, don dama tun jiya take tsammanin zuwansa dama don ta sani lokacin komawarsa makaranta yayi, sai dai yazo a lokacin da take jin bata son ganin fuskar kowa, maganganun Baba da Amma sun riga sun cike duniyarta ta yadda bata tunanin a cikin zuciyarta ma akwai wani waje komai kankantarsa da zai sake ɗaukan wani abu a daren yau. "Ki tashi kije, ganinsa zai sa ki sake yankewa kanki hukuncin da ya dace Amina, daga daren yau zuwa gobe kawai kike dashi..." Muryar Amman ta sake faɗa, taji kamar tayi ihu lokacin data ɗago ta kalle ta, Hafsa na tsaye har yanzu sai kallonsu take alamun rashin fahimta akan fuskarta, kuma daga yanayin Amman ta san ko ihun tayi ba zata canja maganarta ba don haka ta sake goge hawayen da bayan hannunta sannan ta miƙe a hankali tana jin yadda kowa ce kalma da iyayen nata duka furta tayi mata tsaye a zuciya bayan nauyinsu da take ji a kafaɗunta. Akan igiyar tsakar gida ta tarar da hijabin da Maryam ta goge ɗazu don gobe za'ayi musu hotunan photo album ɗin sauka a islamiyyar su, na sallar idinsu ne, dogo har ƙasa kalar ruwan ƙasa, ta jawo shi kamar zata saka amma sai ta fasa, ta nufi ƙofar soron ta tsaya, ziciyarta na ƙoƙarin ƙulla ta yadda zata yiwa Abdallahn bayanin komai, komai ɗin da itama bata gama sani ba, taji ɓangare da yawa a cikin ƙwaƙwalwar ta na gaya mata cewa fitar ta a wannan lokacin ba alkhairi bace, don haka sai kawai ta dawo ta kira Adam dake karo da kwanuka a kitchen. "Adam zo." Ya juyo riƙe da plate yana kallonta kafin ya ajiye shi ya biyo bayanta, suka koma har hanyar soron. "Adam dan Allah kaje kace masa bani da lafiya sosai, ya dawo gobe ba zan iya fitowa yanzu ba." Kamar ya tambaye ta dama ta sanshi ne tunda bai taba ganinsa a gidan nasu ba, sai kuma kawai ya fasa ganin yadda idanunta suka yi ja ya san ba lallai taso tambaya a lokacin ba, ya juya ya fita, ita kuma ta tsugunna a wajen tana ƙara share hawayenta ba tare da ta fahimci kuskuskuren da tayi ba. Lokacin da Adam ya fita, Ma'aruf na tsaye har a lokacin kuma ganin tahowarsa yasa ya ɗago da hannayensa duka biyu a hankali yayi baya da hular (hood) dake kansa, fuskarsa ta fito cikin hasken ƙwan fitilar barandar gidan, "Yaya tace wai dan Allah kayi haƙuri bata da lafiya ba zata iya fitowa ba ka dawo gobe." Ba shiri wani murmushin ya subuce a fuskar Ma'aruf, For real? Shine ma zai dawo goben? Bata san me ta tsallake bane, sai kawai ya gyada kansa tare da faɗin. "Okay." Har Adam zai juya yayi saurin tsayar dashi. "Kana ji ko, ɗan tsaya ka bata wannan." Adam ɗin kuwa ya tsaya, shi kuma ya buɗe ƙofar motar ya buɗe aljihun dake jikin dashboard ya zaro wata jotter da biro daya san Ishaq baya taba rabo dasu motarsa a matsayinsa na lawyer, ya yago takarda guda ɗaya ya ɗora daga saman yayi wani rubutu layi biyu da rabi kawai sannan ya rubuta sunansa daga ƙasa. Ya kalli abinda ya rubuta din yayi wani guntun murmushi kafin ya juyo ya mikowa Adam ɗin "Nagode sosai kaji." Ya faɗa yana sake yi masa wani murmushin, da fara'a shima Adam ɗin ya amsa yana masa a sauka lafiya kafin ya juya, shi kuma ya jefa kansa baya jikin motar yana cusa hannunsa na hagu cikin gashin kansa. Ba haka yaso ba, amma hakan ma yayi... Ya riga ya gama da yarinyar nan ya sani, don abinda su Baffa ke tunani ba zai taɓa yiwuwa ba. Aka ɗauke wuta a daidai lokacin, unguwar tayi wani irin duhu dinɗim kamar yadda yake jin zuciyarsa! Don haka ba shiri ya kunna motarsa ya shiga ya bar wajen. "Gashi yace in baki." Adam ya faɗa a cikin duhun soron bayan ya koma, Amina tayi saurin sake goge hawayenta kafin ta karbi takardar ba tare da tunanin komai ba don ta san ba wani abu bane Abdallahn ya iya rubuto mata fatan samun sauƙi dama, ta damƙe ta a hannunta sannan ta miƙe ta bi bayansa. A kitchen suka tadda Amma na kokarin kunna kyandir guda biyu Hafsa kuma na sake zuba abinci itama, kuma bayan ta amsa sallamarsu sai ta miƙowa Amina guda ɗayan yayin da Adam ya shiga fadan cewar Hafsan ta dauki farantinsa. Ta wuce ɗakinsu kai tsaye, ta ajiyewa Maryam Hijabin akan katifarta sannan ta manna kyandir din akan wata kwalbar magani, a gabansa ta tsugunna hannunta rike da takardar, daga jikinta har zuciyarta daban take jinsu, wucewar awa guda kawai ta tafi da Aminar da take a baya, a yau da safe ma... tana jin zata rubuta dukkan abinda ya faru a daren yau a wajaje da yawa ta yadda ba labarinsa ba zai taɓa gogewa ba. Ta sake goge wani hawayen sannan ta buɗe takardar a hankali, zuciyarta cike da fatan ta karanta wani abu mai rangwame daga Abdallan ko yaya ne wataƙila ya iya zaftare wani ɓangare na damuwarta, sai dai kuma rubutun da idanunta suka gani a jiki shine abu mafi tashin hankali fiye da duk maganganun da rayuwarta taci karo dasu a wannan daren. Kar ki yarda da auren nan, da gaske ne abinda suka faɗa miki, I'm a psycho, zan kashe ki idan har kika shigo rayuwata. Ma'aruf B. ***** 11:15Am. "Mai gaskiya kaci abincin kasha magunguna naka?" Muryar Hajiya Kilishi ta tambaya cikin wayar dake kare a kunnenta, kuma a cikin wayar aka bata amsar data sa ta gyaɗa kanta kafin ta sake cewa. "Zan kira Ishaq, zamu yi maganar komai dashi, idan zaka shigo kawai ka taho da magungunan duka." Har tayi shiru sai kuma tace. "Dan Allah Ma'aruf kafin ka shigo kaje ka aske gashin nan dan Allah, ko ɗazu da na shiga wajen Inna Danejo abinda ta fara tambayata kenan." Amsar da Ma'aruf ɗin ya bayar mai tsawo ce, don ta dade tana saurarensa kafin tace, "Shikenan idan ka shigo kayi mata wannan bayanin da kanka, akwai faten dankali a ɗaya daga cikin kwanukan abincin nan ka ganshi?" Ya fadi abinda ya saka ta yin dariya kafin ta sake cewa. "To aci lafiya, sannan idan ka wuce 1 baka shigo ba, zaka ganmu gabadaya gidan mun taho." Ya fadi wani abun da ya kara saka ta dariyar da tafi ta farko tana fadin. "Ai da ƴanmata zamu zo sai suyi muku sharar." Da haka suka yi sallama, tana sauke wayar daga kunnenta. "Wallahi na dade ina gaya miki Hajiya, da irin mahaukatan secret agent din nan na turawa ya kamata ki samu aiki, ko banza dukkanku zaku amfana da juna, ke da kudinsu su kuma da kissa irin taki." Cewar Hajiya Salamatu, wata hamshaƙiyar ƴar gayu dake zaune daga gefen Hajiya kilishin. Wajen ƙarfe goma sha ɗaya ne na safe a lokacin, kuma kasancewar ranar ta asabar ce kowa yana nan, gidan cike yake da hayaniya da kuma hada-hadar masu aiki da suka gama abincin safe suke kokarin ɗora na rana. A cikin ɗakin da suke zaune an ɗage labulayen tagogin dakin guda biyu iska da hasken rana na shigowa yayin da a lokaci guda kuma filutulun ɗakin suke a kunne haɗe da fankar da aka ware har ƙarshenta. Hajiya Kilishi dake zaune itama cikin nata adon daidai misali ta ajiye wayarta a gefe sannan ta kai hannu ga robar ketchup ɗin dake kan katon farantin da aka zubo musu kayan breakfast akai, ta sake zubawa a farantin dankalin turawan dake hannunta ta sannan tace. "Idan har zaki samo min me zai sa in ƙi sanya hannu Hajiya, kin san ai waje in dai da raɓa da kuma sirri ba na ƙinsa." Hajiya Salamatu ta sake kai kofin shayinta baki tana girgiza kai. "Ai kullum ina gaya miki al'amarinki abun mamaki ne Kilishi, wallahi duk yawona a doron duniya ban taɓa ganin mace irinki ba, yadda ba boka ba malam, kike juya komai da ɗan yatsa guda kuma hankalinki a kwance." Hajiya Kilishin tayi wata guntuwar dariya alamun ta saba da jin hakan daga bakin ƙawar tata. "Mu bar wannan zancen yanzu Salamatu, mu tafi ga abinda yasa na kira ki." Sai da Hajiya Salamatun gyara zamanta a hankali tana ajiye kofin daga durowar gefen gadon, idanunta kaɗai zaka kalla ka san cewar da gasken ta tattara dukkan hakalinta ga abinda Hajiya Kilishin ke ƙoƙarin ɗorawa akan tsohon shirin da suka saba. "Auwalu yana riƙe da ma'aikata har yanzu, sannan wannan auren kamar ya tabbata ne mu ajiye shi a gefe, me kika cigaba da shiryawa daga ƙarshen ƙullin da muka yi wa zaren, me kika tsara?" "Tsari na da yawa Salamatu, farko dole ne in fara sakin manufata tun yanzu akan ita yarinyar, dole ne ta ɓoyayyiyar hanya in ƙara bincike akan zuciyarta ta yadda zan fara ƙawata tunaninta da miƙakkiyar hanyar da zata ƙulle ta a gaba. Na biyu, dole ne a yanzu inyi taku mai nisa daga mahaifin yarinyar da kuma maigidana, zan ƙara zame hannuwa daga al'amarin na in zama ƴar kallo ta yadda ko ƙura ba zata hau kan farina ba, balle wani ɗigo na baƙi, amma zan kusanci mahaifiyar yarinyar dole, don haka ne ingantacciyar hanyar da kowa zai kalla a yanzu. Sannan na san Ishaq zai shaida min dukkan sabon tsarin magungunan Ma'aruf, don haka wannan ma babu matsala, komai zai cigaba ne daga inda ya tsaya. Game da auren su Salma kuma wannan komai tsaftatacce ne don kin san bana taɓa haɗa ƙasa da gari waje guda. Daga Auwalu kuma, mun sake bude wani sabon account zai loda kudaden wancan watan..." Ta faɗi hakan sannan tayi shiru a hankali, ramin bakinta na wasa da wani murmushi mai armashi. "A yadda lissafin komai yake Salamatu, shekara guda tayi yawa kafin komai ya ɓare!" Hajiya Salamatun tayi nata murmushin itama yayin da take kallon fuskarta. "Na fahimta Kilishi nima na lissafa wannan adadin tun a wancan karon. Sai dai kin san a kullum nice mai hasko miki ƙalubalen da ke bakya ƙirgawa dasu. Ƙalubalen da duk zare ɗaya ne ya ƙulle su suke reto a jikinsa, ƙalubalen kuma da shine raunin ki Kilishi, shi kadai ne raunin da na san ubangijin ya halitta a ƙirjinki, Ma'aruf!" Murmushin da kullum ke sauka a fuskarta duk sanda Hajiya Salamatun ta furta mata magana makamanciyar wannan shi tayi a yanzun ma, tayi shi tana ajiye farantin hannunta, ta jawo tissue a gefe ta goge maiƙon hannunta sannan ta miƙe, ta isa ga makekiyar wardrobe ɗin dake ɗakin ta buɗe waje na biyu, a ciki kayan Ma'aruf ne wanda ya cire daga jikinsa ranar da aka tafi dashi tafi London ba'a hayyacinsa ba. A gaban kayan akwai dukkan tarkacen dake cikin aljihunsa a wannan ranar, muƙullin mota, chewing gum, chapet, biruka da kuma wallet ɗinsa, wallet ɗin ta dauko sannan ta rufe wardrobe ɗin ta dawo gaban Hajiya Salamatu ta miƙo mata ita. Sanin halinta sarai yasa Hajiya Salamatun ta karɓa ba tare da ta tambaya ba, ta ware cikinta, kuma bayan tudun kuɗin da taji a ciki da kuma jerin credit cards, wani hoto da aka maƙala a jiki shi ya ɗauki hankalinta, samari biyu ne a jikin hoton wanda kallo ɗaya kawai zai shaida maka cewar wa da ƙani ne, don bayan girman da ɗaya yafi ɗaya, akwai kammani sosai a fuskarsu. Suna dariya mai cike da nishaɗi yayin da babban ke miƙo hannunsa kamar zai naushi ƙaramin. Ƙaramin Ma'aruf ne Hajiya Salamatu ta sani, babban kuma... "Jamal..." Sassanyar muryar Hajiya Kilishi ta furta tare da tunanin Hajiya Salamatun. "Jamal shine ƙalubale na kuma shine rauni na Salamatu, shi yasa na rufe idanuna nayi abinda ya kamata akansa, don haka kamar kullum zan gaya miki cewa ki yarda bani da wata matsala a duniyar nan yanzu idan ba kuma ƙaddarar ubangiji ba. " Ta fadi hakan yayin da take tsaye akanta, Hajiya Salamatun ta ɗago ta kalle ta, wannan murmushin na baya ya tafi, idanunta sun canja ta yadda ko ɗigon raha babu a cikinsu. "Kar ki ƙara lissafa Ma'aruf a cikin ƙalubale na Salamatu, don kinfi kowa sanin matsayinsa a waje na." Kuma a cikin idanuwan nata, Hajiya Salamatun ta shiga hango abubuwan da suka faru wasu tarin shekaru da suka wuce! ****** 11:20 Am "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wai baka da imani ne Ishaq? Tun da na tashi kake ta masifa a gidan nan kana mita, nace maka wallahi ko ganin yarinyar banyi ba balle inyi mata wani abu, do I have to bury myself before you believe?" (haƙa kabari zanyi in shiga kafin ka yarda dani?) Ma'aruf ya fada a lokacin da yake zaune kan dining table din falon gidansu, inda ya samu ya ture wasu litattafai da kuma kayan wankin Ishaq ya dora plate ɗin abincin da yake ci. Ishaq na tsaye daga cikin falon shima rike da nasa kofin shayin da kuma remote ɗin da yake kokarin chanja channel daga ta labaran da Ma'aruf ya kai. "Ka gayawa wani ba ni ba, na san halinka sarai B, hankalinka ba zai taba kwanciya haka ba idan har ba kayi abinda kake so ba. I'm just advising you (shawara nake baka) komai zai iya faruwa idan har maganar nan ta lalace kuma Baffa ya san da saka hannunka." Ma'aruf yayi murmushi a hankali sanda yake jin zafin faten dankalin dake sauka cikin maƙogwaronsa wanda motsawar Adam's apple ɗinsa kadai zai shaida maka hakan. "Wai ina zaka je ne ma? Yau asabar fa?" Ya canja akalar zancen nasu ba tare da ya kalle Ishaq ɗin ba, don tun da farko kayan jikinsa sun riga sun nuna masa cewa Office zai je. Babu adadi na lokutan da zuciyar Ma'aruf ke motsawa a duk lokacin da yaga Ishaq na yin wani abu da ya danganci aikinsa, aikin da yake so kuma abinda shine mafarkinsa ya fito dashi zahiri kuma yake yi ɗin. Shi nasa burin da kuma mafarkin sun dade da kaɗewa shekaru goma da suka wuce. Abinda yake yi a yanzu, ba rayuwarsa bace ko kaɗan, wata rayuwa ce da ta zama dole ya ƙarasawa mai ita. "Thanks to you, nayi missing tarin ayyukan da dole inje in san halin da ake ciki kafin Monday, Idan ciwon ka ya sake tashi Ma'aruf wallahi ka nemi mai raka ka asibiti." Murmushi Ma'aruf keyi har a lokacin yana cigaba da cin abincinsa yayin da ƙamshin curry da kuma naman dake cikin abincin ke gauraye ɗakin, ya kai hannu yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa, wani abu da ya riga ya zama ɗabi'arsa kafin yace. "Ka san me Mami take ce min yanzu? Wai inyi aski kafin in shiga gida, don Inna Danejo na tashi da safen nan abinda ta tambaye ta kenan." Ba shiri Ishaq shima yayi nasa murmushin kafin ya gyaɗa kai don har ya hango irin rigimar da za'ayi da Ma'aruf din da ba zaiyi askin ba da kuma Inna Danejon da ba zata haƙura, don kafin tafiyarsu London ta kawo dalilai sun fi ashirin na cewar rashin lafiyar Ma'aruf tana maƙale da gashin kansa ne, Baffa ne kawai bai bada goyon baya ba da tuni sai dai Ma'aruf ɗin ya tashi yaga kansa ɗal! "Hular sanyi kawai zaka dauka, in zaka shiga wajenta ka saka kace anyi askin ba'a bude kan ne." Ya faɗi hakan lokacin da ya gama neman abinda yake so a jikin Tvn don haka ya ajiye remote din ya juyo ya kalle shi. "Za'a kawo maka motar ka ne?" "Eh, na kira direban Office tun dazu nace yaje ya ɗauka ya kaita Carwash, I'm sure kafin 12 zai dawo da ita." Ishaq ya gyaɗa kansa. "Shikenan mu haɗu a gidan, nima can na nufa idan na tashi insha Allah." Ya faɗi hakan yana juyawa hanyar ƙofa, idanun Ma'aruf suka bishi da kallo yana tunanin wani abu, kuma sai da ya isa ƙofar da zata fitar dashi waje har ya buɗe ta sannan yayi saurin kiran sunansa. Ya kuwa juyo a take kamar shima dama jiran kiran yake yi. Ma'aruf ya girgiza kansa yana kallonsa. "Wallahi ban ga yarinyar ba Ishaq, kawai dai na bata wani saƙo ne da na san dole ba zata taba yarda ba." **** 11:30Am. "Na yarda!" Kalaman guda biyu suka fito daga bakin Amina lokacin da take tsugunne a gaban iyayenta guda biyu da dukkan fuskokinsu ke haskawa da tsananin mamaki. Tata fuskar fayau take, ba abinda zaka iya tsinta a jiki. Ta gyara zamanta sannan ta sake maimaitawa kamar wani ya sata. "Na yarda zan aure shi Baba." Maimaitawar ta fiyo tare da faɗowar flask ɗin ruwan zafin da Amma ta ɗauko don juyewa Baba ruwan wanka, ya subuce a hannunta ya faɗi har ƙasa, kwalbar ciki ta tarwatse yayin da ruwan zafin ya fallatsa akan dukkaninsu. * Me kuke tunani yasa Amina ta yarda da auren Ma'aruf? Wacece ainihin Hajiya Kilishi? Me ya faru da Jamaal? Shekarun cikin labarin sun wuce da wasu abubuwa da zamu fara kwance su daga Babi na gaba insha Allah...☺️ #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA BIYAR. ~~~~~ Ana gobe sallah ne ranar, ita da Maryam sun je kasuwa siyayar mayafai da takalmi, tun kusan sha biyu suka fita har mutane suka fara alwalar sallar la'asar basu gama siyayyar ba. Maryam dake riƙe da ledar kayan da suka siyo kalli tsinken kwakwar da suka auno tsawon kafar Hafsa dashi tace. "Ai wallahi dama na san takalmin yarinyar nan shi zai bamu wuya, kafa kamar ba ta mutane ba ƴar firit da ita." Amina ta share gumi a gefen fuskarta tace. Har tunani nake ko ba daidai na auno ba wallahi gashi mun kusa gama siyen komai..." Bata karasa ba ta tuno da sakon garin da Amma tace su siyo zata yi teba dashi da daddare. "Kin san na manta da garin Amma... zo muje wancan layin na san zamu samu." Maryam ta girgiza kanta. "Mu raba tafiyar kawai lokaci ƙara wucewa yake, ga wani kantin takalma can, bari naje na duba idan ma ban samu ba zan jira ki sai kizo ki same ni anan." Da haka suka raba tafiyar, Maryam ta tsallaka ta cikin cunkoson mutanen ta nufi kantin ita kuma tabi layin gefensu inda nan ɗin ma turuwar mutanen ce wadda dama sun riga sun shirya mata, don tun ana saura sati ɗaya sallar suka so zuwa kasuwar amma rashin haɗuwar kudin yasa dole sai yau suka samu suka fito. Ga rana, ga azumi amma yadda mutane suka hargitse baza kace kowa a gajiye yake ba. Da kyar ta samu ta ɓulla layin da masu garin suke, kuma akan ragin naira hamsin ɗin da zasu yi kuɗin mota dashi, sai da ta kusan shanye layin tana tambaya da ƙyar ta samu wani acan ƙarshe yace zai rage mata. Tana tsaye yana ƙoƙarin auna mata, wani yaron shagon nasa ya shigo, irin samarin nan ne masu magana, yana shigowa ya haye kan ɗaya daga kantocin shagon yana fadin. "Allah na tuba a yadda ake wannan ranar ga azumi ai wallahi komai talauci na ba zanyi aikin sauke gari ba, don mugunta kaga yadda suke jefo musu buhun nan daga sama, wani har sai ya kai ƙasa wallahi kafin ya ɗago." Maganar ta ɗauki hankalinta, tana hango yadda nauyin buhun gari yake ace mutum ya dauka a wannan ranar. "Yau ma mota ta sauka ne?" Mai shagon ya tambaya yana miko mata ledar garin. "Gata can yanzu ta tsaya, ka san shi Auwalu ko da goma yaga sunyi ƙasa sai yayi aike." Ta miƙa masa kuɗin tana faɗin ta gode, amma kafin ya karba saurayin yayi saurin miƙo hannu ya karba sannan ya miƙo mata yana mata murmushi, irin halin ƴan kasuwa. A kofar shagon kuwa tana fita taga motar ana ta sauke garin, tausayin masu yin dakon ya tafi har cikin ranta ganin yadda ko a ido buhun ke da nauyi, tana tafe tana ganin fuskokinsu lokacin da idonta ya kai kan fuskar da ta sa ba shiri hannunta ya saki ledar garin nan... Mahaifinta ta gani dauke da wani katon buhu yana ƙoƙarin kaiwa inda sauran ke saukewa, mahaifinta dai Baba, Baban daya shirya tsaf a yau ya fita suna yi masa a dawo lafiya. A wannan lokacin yana gaɓar farfaɗo wa daga karayar arzikinsa ne, don duk da kokarinsa wajen yi musu kayan sallah, har saida aka haɗa da kuɗin Aminu kafin komai ya isa, bata san lokacin da hawaye ya fara biyo kuncinta ba, taga ya sauke ya koma sake ɗauko wani... Baba mutum ne mai tsananin son dogaro da kansa kowa ya sani, yayyensa duka sunyi kokarinsu wajen tallafa musu tunda al'amarin ya faru, amma babu wanda ya isa ya ɗauke maka cin yau da gobe sai Allah, don haka ta san nauyin ya cigaba da tambayarsu ne yasa har ya kawo kansa yin wannan aikin don kula dasu. Hawayen ya cigaba da bin fuskarta yayin da zuciyarta ke rawa a kirjinta, tunanin ta ɗaya ne a lokacin, idan har mahaifinta zai iya sadaukar da girmansa yayi wannan aikin don kawai ya fita kunyarsu meye su baza suyi don fita tasa kunyar a duniya da kuma lahira ba? Ta share hawayenta lokacin da wani mai wulbaro ke miko mata ledar garin da Allah yaso bata fashe ba. Kuma bata fadawa Maryam abinda ta gani ba, bata fadawa Amma ba, bata fadawa kowa ba, don ta san hakan wani abu ne da Baban ba zai taɓa so waninsu ya sani ba. Kuma a wannan daren sai gashi ya dawo da ledar kaza har guda biyu ta miyar sallah, su Hafsa suka yi ta tsallen murna yana binsu da nasa murmushin shima. Wajen karfe biyun dare bayan kowa ya kwanta, ta hango shi ta ƙofar ɗakinsu a wajen banɗaki yana miƙe bayansa, kukan da tayi a cikin filonta a wannan daren Allah kaɗai ya san yawansa, abu ɗaya kawai ta sani shine tayi wa kanta alƙawari a wannan ranar cewa ko abinda yafi rayuwarta ne zata sadaukar a duniya don farantawa mahaifinta. * "Wallahi gani nake yi kamar zaki ƙyalƙyale da dariya ki gaya min wasa kike yi." Fatima ta faɗa tana kallon Amina data idar da sallah a gabanta. "Ke ma kin san ai ban taɓa miki irin wannan wasan ba, da gaske nake Fatee, don yanzu haka ma Baba ya tafi gidan Kawu Mallam ya faɗa masa." "Ya fada masa cewa kin yarda zaki auri wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa Amina...? inalillahi wa'inna ilaihir raji'un Amina kin san Allah ko da nake cewa ki rabu da Abdallah ki samu wanda yafi shi ba irin haka nake nufi ba, ya za'ayi kiyi irin auren da ake bada labarin ire-iren sa a sigogi mara sa daɗi?" Fatiman ta ƙarashe muryarta na karyewa. Amina ta cire hijabin sallar tana kallonta, "Ban gane me kike nufi ba?" Ta tambaya tana kallonta. Fatima ta girgiza kai kafin ta gyara zamanta. "Amina duk wanda yaji batun auren wallahi shaidar da zaiyi miki daban, kowa cewa zaiyi auren kuɗi zaki yi, musamman ƴan unguwar nan da kin san daman ƙiris suke jira akanki." Amina ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, abinda Fatiman ta faɗa gaskiya ne ta sani, kuma maganar iri ɗaya ce da maganganun Amma na jiya, duka su biyun ƴancinta suke nemar mata, amma a wajenta darajar mahaifinta itace a gaba da ita kanta don haka ta riga ta gama yankewa kanta hukunci, ta gayawa zuciyarta cewa zata tsaya tare da mahaifinta koda zata mutu sau biyu idan ana yi. "Fatee na tabbata ba fa ba wai matsala ce sosai ba, kawai sun faɗa ne saboda kinga a aure ba'a ɓoye komai, kuma ma Baba yace baza'a bari maganar ta fita ba, kema kin san ba zan iya ɓoye miki bane." Ta faɗi hakan yayin da idanunta ke hango takardar data cusa cikin kayanta a jiya, babu wanda ya san da ita, babu wanda ta gayawa hatta Amma kuwa duk yadda kowanne abu mai hankali a cikin kanta ya tsorata da maganar dake rubuce, amma ta sani cewar in har iyayenta suka ji hakan dole zai iya sake zama wani ƙalubale musamman ma a wajen Amma don haka ta yanke hukuncin ɓoyewa tunda ba zata taba fatan abinda zai hadassa mahaifinta yaji kunya ta dalilinta ba. Kuma kafin Fatiman ta sake cewa wani abu suka tsinci sallamar Ummi daga tsakar gida, ƴar Kawu mallam wadda suke kusan sa'anni da Aminan. "Ina amaryar take?" Muryarta ta fito da fara'a bayan ta gaisa da Amma da kuma Maryam wadanda suke kitchen, ta karaso ya ɗage labulen ɗakin tana kallon Amina bakinta a washe. "Yarinyar nan da tsinannen wayo, sai dai muji kawai wai zaki yi aure?" Sai dai Amina tayi wani guntun murmushi kafin tayi mata sannu da zuwa. "Ni ba zan amsa ba wallahi, tunda sai da muka ga meeting ɗin su Kawu yayi tsawo sannan da kyar muka san me ake ciki, da ake ɓoye mana naga wanda zai raka ki siyayyar kayan bikin ai." A cikin maganar ta Amina ta tsinci wani abu, cewa da gaske Baba yake a ɗazu daya shaida mata cewar kowa zai ji maganar auren ne ta fuskar alkhairi, babu wanda zai san me ake ciki, gashi kuwa ko iyalan Kawu Mallam ɗin da ake taruwa a gidansa basu san komai ba, zurfin maganar ya tsaya a iyakar Baba da yayyensa ne sai kuma Amma, Fatima, Maryam da Aminu da suka sani a yau. Ance zancen duniya baya ɓuya, amma har cikin ranta tana fatan zancen ya tsaya a iya wadannan mutanen kawai. "Ai ni ban yi zaton har ɗan bokon naki ya gama makaranta ya shirya ba, shi yasa wallahi abun ya bamu mamaki sosai, har su Umma ma cewa suka yi koda wasa Amma bata yi musu zancen a kurkusa ba." Amina ta girgiza kanta. "Ai ba shi bane Ummi, wani ne daban." Sai da Ummin tayi shewa kafin tace. "Gaskiya ne yarinyar nan, kice da karfinki kika taso, Fatima bani labari don na san zanfi ji a wajenki, wane ne sabon kamun?" Fatima tana take tace. "Wallahi kin san al'amarin Allah ai, kawai komai a lokaci guda yazo." "Eh, amma dai da maiƙon sa ko? Yadda komai ya taso a lokaci gudan ai na san a shirye yazo ko?" Kawu malam mutum ne malami mai sauƙin sha'ani, amman sai Allah ya bashi matansu duka ukun masu azabar son kuɗi, kuma suka taso da ƴaƴansu ma gabaɗaya akan hakan, gashi mata sunfi yawa a ciki don haka a zaune yake cewa basa auren kowa sai mai abin hannunsa ire-iren ƴan kasuwa, gasu da surutu da kuma kauɗi, hakan yasa duk kusancinsu dasu Amina basu fiye shiga cikinsu sosai ba don halayensu sun banbanta duk kuwa da cewa suna da mutukar kirki. "Ai kuwa dai yana da kuɗi gidansu ma haka." Fatima ta bawa Ummin amsa har a lokacin tana murmushin yaƙe. "Kice dole ne mu raƙashe a bikin nan, wallahi azo a saka mana rana ma nan kusa Momi tazo mu fara shirye-shirye, zaki yi anko?" Amina taji wani abu ya tokare mata a maƙoshi, don ita har ta yanke hukunci bai taɓa zuwa kanta cewar ma biki za'ayi ba, gani take kamar jana'iza kawai za'ayi akaita, kuma sai Allah ya taimake ta kiran Amma yazo a daidai lokacin don bata san amsar da zata bawa Ummin ba. Amma ta kalle ta bayan ta isa kitchen din, fuskarta fayau tace. "Kizo ki zuba muku abinci gashi nan an sauke." Ta haɗiye yawu a hankali tana ƙarasawa ciki, lokacin da flask ɗin ruwan zafin nan ya faɗi daga hannun Amma, sai ya zama kar ya fashe da dukkan irin hukuncin da take tunanin Amman zata dauka akan ƙin bin maganarta da tayi, don a lokacin bata ce komai ba, juyawa tayi kawai ta bar wajen yayin da Baba ke saka mata albarka, kuma bayan taje ta same ta a ɗaki, abu daya kawai tace. "Rayuwarki ce dama Amina, na nuna miki kuskuren dake ciki ne kamar yadda yake alhaki na a matsayin uwa, kuma tunda har kinga zaki iya dauka, ga fili ga maidoki nan, zuciyata ba zata riƙe ki da komai ba, Allah ya baki sa'a." Daga haka bata ƙara cewa komai ba, kuma bata yi fushin da Amina tayi zato ba, harkokinta ta cigaba da yi a gidan kamar dama maganar bata taso ba, kamar dai shekaranjiya da Baba bai ko ziyarci gidan Hajiya Kilishi ba, balle su san da komai. Ta zuba abincin ta kai musu, suna ci Ummi na daɗa bada bayanin yadda abubuwa zasu kasance wanda daga ita har Fatiman yaƙe kawai suke suna amsa mata, wajen la'asar ta tafi, lokacin ma Fatima ta daɗe da tafiya asibiti inda tace yau za'a sallamo kakarta. Wajen ƙarfe biyar, Aminu ya shigo gidan riƙe da wani flask lokacin da take wanke-wanke ita kaɗai a gidan, don Amma ma ta shirya ta tafi gidan wata ƴaruwarta a Goron dutse ta shaida mata al'amarin. "Ina yarinyar nan take?" Ta san Maryam yake nema don haka tace. "Ta tafi makaranta tun ɗazu." Sai ya ajiye flask ɗin a ƙofar kitchen sannan ya ƙaraso ya tsugunna a kusa da ita, muryarsa ɗauke da nutsuwar da zaka shafe rabin rayuwarka kafin kaji ta a wajen Aminu yace. "Hukuncin da kika yanke yayi daidai Amina, ba don Amma ba daidai ta faɗa ba, sai don kare mutuncin Baba da kika yi, kuma na tabbata Allah zai duba hakan ya kyautata rayuwarki." Kwalla ta taru a idonta lokaci guda, don haka ta gyada kai kawai ba tare da tace komai ba. Wucewar wasu ƴan sakanni shima yana tsugunee kamar yana sake biya abinda ya fada a zuciyarsa, sai kuma yayi gyaran murya sannan ya koma Aminun da yake. "Kin gayawa Malam ne?" Ta san Abdallah yake nufi don dama haka yake kiransa, saboda haka ya girgiza kanta tace. "Na san dai zai zo anjima." "Kice yau Malam zai danɗani baƙin cikin latecomer kenan." Bata san lokacin da ta watso masa ruwan wanke-wanken ba tana jin wani abu a zuciyarta na fadawa, ya kauce shima yana dariya sannan yayi hanyar fita yana faɗin. "Idan wannan ƙwalamammiyar ta dawo kice mata ga wainar masar da take ƙalata nan na samo mata." Bayan ta gama wake-wanken ta koma ɗakinsu har a lokacin ƴan islamiyar basu dawo ba balle kuma Amma, a ƙasan kayanta ta sake ɗauko wannan takardar tana karantawa, idanta suka tsaya akan sunan yayin da a yanzu bayan tsoron ma'anar rubutu wani sabon tsoro daban ke shigarta. Ma'aruf B. Ta karanta sunan tana jin yadda tsoron harafan kadai ke zanuwa a zuciyarta, ba wai don ta sanshi ta gane waye ba sai don zuciyarta bata cika manta fuskokin mutane ba koda kuwa sau ɗaya ta taba arba dasu, kamar dai shi rana guda ta taɓa ganinsa a rayuwarta kuma bata ƙara ba daga sannan. Ranar ɗaurin aurensa, ranar da Baba yasa suka tafi tunda sassafe ita da Amma don wai suyi yinin bikin da gaske kamar yadda aka rubuta, a lokacin da ya shigo gidan shi da abokansa da ƴanuwansa bayan ɗaurin auren, ita da Amman suna rakuɓe daga can jikin wata kujerar a falon Hajiya Kilishin, kuma duk da tarin ƴan bikin mata da suka yanyame shi da tsokanar 'ango kasha ƙamshi...' sai da idanunta suka iya hango mata shi yasha farar shaddar dake ƙyalli kamar murmushinsa, yana tsaye daga tsakiyar mutane yayin da masu hoto ke ta yi musu kala-kala. A wannan lokacin gani take kamar bambancin su ita da Amma da mutanen gidan ya zarta na mutum-mutum, don bayan Hajiya Kilishin da ta amsa gaisuwar su cike da fara'a ta kuma sa aka kawo musu abinci babu wanda ya ƙara lura dasu a gidan, sai wata mace guda ɗaya da tace Amma ta ara mata hijabinta lokacin sallar azahar, itama da alama irinsu ce don ta ɗebo tarin ƴaƴan da ta cika musu faranti taf da abinci suna ta ci. Daga baya ma dole suka bar cikin falon suka zagaya baya can wajen ɗakunan masu aiki, inda anan ne suka ɗan sake har Amma ma taga wata ƴar ajinsu ta sakandire a ƴaƴan dattijan da sune manya-manyan masu aikin gidan. Don haka kwatanta tsoron cewar a wannan karon ita zata maye gurbin wannan kyakkyawar amaryar da aka shigo da ita gidan wajen yamma abu ne da ta tabbata babu wanda zai iya kwatanta shi a duniyar nan. Tsaya ma tukunna... Ina matar tasa take?? ***** "Baffa ya gaya maka komai ko?" Hajiya Kilishi ta tambaya tana kallon Ma'aruf ɗin dake zaune a gabanta, a cikin falon ɓangarenta suke su biyu sai Surayya dake can wajen dining tana danne-danne a wayarta, yana zaune a kujerar dake kallon Tv yana kokarin canja channel daga ta india zuwa wata channel da ya san a lokacin ana wani Tv show na likitoci mai suna 'Code Black'. Sai da ya kai tashar ya karo volume sannan hankalinsa a kwance ba kamar yadda ta zata ba ya juyo ya kalle ta. "Ya gaya min, and I was surprised har dake Mami." Tayi murmushi tana kallonsa daɗi na cika kowanne lungu da saƙo na zuciyarta na ganinsa a gabanta, zata rantse da alƙur'ani ko ya'yan da suka fito daga cikinta basa ƙarasawa inda Ma'aruf ke kaiwa a zuciyarta, matsalar ɗaya ce kawai... duk wani ado da zai ƙawata kusancinsu dole ana kaiwa gabar da za'a yaye cewar shi ba mallakinta bane, kuma tana jin cewa da zata iya samun mai gyara mata hakan babu makawa zata bada komai na duniyarta don kawai a wayi gari duniya ta shaida cewa shi nata ne. "Baffa ya riga ya gama yanke hukuncinsa shi da Alhaji Baba, daga ƙarshe kawai suka tuntubeni Mai gaskiya kuma ka san ba zan iya cewa Baffa A'a ba, shi yasa sai na bada tawa gudunmawar ta hanyar zaɓo maka yarinyar da na san zata dace da yanayinka. Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata." Wani murmushi yayi kaɗan sannan yace. "Na dade ina gaya miki kulawarki kaɗai ta ishe ni in rayu Mami, tunda har Rukayya ta kasa bana tunanin akwai wadda zata iya jurewa mess ɗina a duniyar nan kuma." Maganganun suka taɓo wani abu a can ƙasan zuciyar Hajiya Kilishi, wani abu da sai da ta ji shi har a ƙarƙashin tafin ƙafarta musamman yadda muryarsa ta fito da wannan amon mai zurfi da kuma sanyi. Kuma sai da ta maida wata ƙaramar ƙwalla a idanunta sannan tace. "Yanzu dai ka san baza'a fasa ba ko? Don haka zamu fara shirye-shirye, za'a kai musu lefe dole sannan idan kana so ma zaka iya zuwa ka ganta." Maimakon ya bata amsa, sai kawai ya juyo ya kalle ta, lumsassun idanunsa suka tsaya a nata. "Wai zaman me Ishaq yake yi ne ma? Me yasa Baffa baice a haɗa dashi ba?" "Sai gida ya koshi ake kallon na waje Ma'aruf, kaine damuwar mu a yanzu ba shi ba." Kamar bai ji dadin maganar ba, don juyawa yayi yana cigaba da kallonsa ba tare da yace komai ba. Hakan yasa tayi saurin gyara zancen ta. "Kar ka damu amma, da an gama zancen nan ni da kaina zan saka shi a gaba sai ya motsa." Murmushin da ya sake yi ya sata jin wani ɗaci a zuciyarta, ba sau daya ba sau biyu ba tasha tunanin kawar da Ishaq daga hanyarta kamar yadda ta kawar da abubuwa da yawa a rayuwar Ma'aruf, don duk wani abu da zai jawo ya raba zuciyarsa da kowa bayan ita, bata ƙaunarsa sam! Amma matsalar shine Ishaq ba ƙaramin amfani yake mata ba, amfanin da shi ta lissafa har ta bada shawarar dawo dashi wajensu bayan ya rasa iyayensa ba don kyautatawar da duniya ke kallonta dashi ba. "Akwati nawa kake so a haɗawa yarinyar?" Kamar bai damu ba, hankalinsa kwance yace. "Duk yadda kika yi Mami daidai ne, ni yanzu abinda ke gabana daban harkar Office ce da zanje in gyara, Baffa yace anyi asara da yawa a wannan watan." Ba shiri maganar ta doka wata tsawa a cikin kan Hajiya Kilishi tana janyo ta daga ramin da zuciyarta ke shirin kai ta, taji kamar ta miƙe tsaye tana karkaɗe raunin daya baibayeta tun bayan data ɗora idanunta akan Ma'aruf ɗin. "Shikenan, Allah ya taimaka. Ka taho min da magungunan naka?" Wata ƴar ƙaramar jakar daya shigo da ita a gefensa ya ɗauko ya miƙa mata ba tare da ya janye idonsa daga Tvn ba, kuma da Ma'aruf ya saurara da kyau, zai ji lokacin da ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta buɗe jakar tana nazarin kayan ciki. A lokacin Samirah ta shigo ɗauke da lemo mai sanyi da kuma cake a faranti, yarinya ce ita mai tsananin kula da son kyautatawa kowa, shi yasa kusan komai na gidan yanzu sai da izininta ake yi, hatta abincin Baffa ta daɗe da karɓar ragamarsa sai dai ko in tana makaranta sai wani a cikin yayyenta yayi, don su Hajiya Kilishi basa girki a gidan. Kuma ko a ɓangaren Hajiya Maimuna akayi baƙi Sameerah ita zata fara tarbarsu da waje da kuma kayan cima kafin kowa, ƙarya ne wani ya shiga gidan nan yace ya fito da yunwa in har tana nan. "Dan Allah Yaya ka bani kwangilar sati ɗaya in cicciko maka da waɗannan kasusuwan, wallahi baka ga yadda ka rame ba." Ta faɗa tana ajiye masa farantin a gabansa. Ma'aruf ya ɗago ya kalle ta yana murmushi lokacin da Hajiya Kilishi ta mike riƙe da jakar magungunan tayi hanyar ɗaki. Kusa dashi ya nuna mata a kujerar yace. "Zo ki zauna muyi ciniki Please, how much do you need? ( Nawa kike so) coz ƙarfi nake nema nima yanzu." Ta kuwa ƙyalƙyale da dariya daidai lokacin da Shukra (ƙanwarsa dake bi masa a wajen Hajiya Maimuna) ta shigo daga hanyar wajensu, kuma ganin Ma'aruf ɗin yasa tayi murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau tana fadin 'Alhmdlilah" sannan ta juya da sauri don ɗebo takardun research ɗin da ta tara zai duba mata. Don haka Ma'aruf bai samu shiga wajen Hajiya Maimuna ba sai da yamma tayi sosai. Kuma a falo ya same ta itama, tana zaune daga kan Wheelchair ɗinta tana karatun azkar ɗin yamma, yayin da Zahra da kuma Sahla ke zaune suna kallon video ɗin wani tutorial daga labtop ɗin Munaya da suka aro. Ya durƙusa har kasa a gabanta ya gaishe ta cike da girmamawa, girmamawar da bayan ita baya taɓa kallonta da wani abu. "Yaya jikin naka?" Muryarta mai taushi ta tambaye shi bayan sun gama gaisuwa. "Lafiya ƙalau Hajiya, naji sauki ai." "Allah ya ƙara sauki. Kaje wajen Inna ne?" Ya girgiza kansa. "Yanzu zan shiga idan na fita." Tayi shiru yayin da idanunta ke nazarinsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa sanye da dogwayen kaya na farin yadin da ko a ido mai laushi ne don ya kwanta a jikinsa sosai ta yadda ya fito da ƙirar jikinsa mai tsari, wani abu dake ɗaya daga cikin abinda ke ƙara masa kwarjini a idon mutane. A lokacin ne kuna maganar ƴar uwarta a kwanakin baya ta haska a cikin kanta. 'Ban ce ki tada hankalin gidan ki ba Maimuna, amma abin yayi yawa, kin rasa Jamal kuma Ma'aruf shine Babba a gidan yanzu, ko yaya ne ya kamata ya dinga tunawa cewa ke kika haife shi ba ita ba...' Tayi saurin kawar da wannan tunanin tana haɗiye wani abu da batasan sunan sa ba, a lokainda ƙwaƙwalwar ta ke tuno mata damagaar da Baffa ya yanke taauresa jiya da daddare, sai dai har ta buɗe baki zata yi masa magana kawai taga ya miƙe tsaye yana yi mata sallama, sai ta mayar da maganarta a hankali sannan ta amsa, kuma murmushin da yayi wa su Zahra a matsayin amsa tasu sallamar ya sake ɗago wani abu a zuciyarta da ta daɗe tana danne shi tsawon shekaru. Idanunta suka bishi da kallon da har ya rufo mata ƙofar falon hankalinta bai koma kan karatun da take yi ba. A falon Inna Danejo Ma'aruf ya tarad da ita tana sallah daga kan sallayar ta da anan take kwana ta yini in har ba tashi ne ya kamata ba, don haka ƙafafunsa suka tako cikin falon a hankali, yana jin kamar zai nutse a sabon carpet din da aka shimfide mata falon dashi, (wall to wall). Ya karaso ya sami waje daga gefenta ya jingina da wasu ƙullin kayanta da ya san na wanki ne sannan ya zaro wayoyinsa daga aljihu. Tarin messages ɗin da har yanzu bai duba ba suka shiga tururuwa akan screen ɗinsa, sai ya zura hannunsa ɗaya cikin gashin kansa kawai sannan ya cillar da ita a gefe ya dauko ɗayar. A ciki ya lalubo nambar Faruk, aboki ɗayan da yake dashi bayan Ishaq kuma mataimakinsa a wajen aiki. "Ka gaya min ba maganar aiki bace dan Allah B, don wallahi as we are talking now ina Coldstone ni da yara, kowa yana son hutu a rayuwarsa Ma'aruf." Faruk din ya faɗi hakan tun kafin yace komai, don shi kansa ya sani ba zai iya kirga adadin wayar da suka yi akan zancen Office ɗin ba tun bayan dawowarsa. Sai dai kalmar yaran da ya furta ta daki zuiyarsa da wani irin tasirin da baya taɓa sabawa dashi don haka ba shiri ya tafi kai tsaye ga abinda yake son tambayarsa. "Account number Daniel zaka turo min." "Me zaka yi da ita? Na gaya maka gayen yana can har yanzu da kumburarriyar fuska wallahi." Ya cije leɓɓensa a hankali yana hango fuskar Daniel ɗin a idanunsa, sanda ya cakumo wuyansa yana kai masa naushin da baya ƙarewa, kuma duk da zafin dukan nan Daniel baya kare ba ko sau ɗaya, kallonsa kawai yake da idanunsa dake nuna tsantsar mamaki da kuma ruɗani har ya fita daga hayyacinsa. Ya sake tuno yadda ya jawo shi ya fito dashi har waje ɗimbin jama'ar Office ɗin na kallonsa, da lokacin da ya saka shi a boot din motarsa ya rufe sannan yaja motar zuwa gida, yaje gidan kuma ya fito dashi dashi daga boot ɗin motar ya ja shi har falon Baffa a lokacin ma ya riga ya suma... Sai kawai ya sake mai da kansa baya, yana motsa ytsunsa cikin gashin kansa a hankali, idonsa ya cigaba da hango masa yadda a lokacin duk da baya cikin hayyacinsa amma nauyin idanun Baffa suka sa ya durƙushe akan gwiwoyinsa sanda ya kai Daniel ɗin har gabansa, amma kuma duk da hakan bai fasa gayawa Baffan cewar wai ya kawo shi ne ne don ya kore shi daga aiki ba... "Just send it Umar..." (Kawai ka turo min...) Ya faɗa yana katse tunaninsa kuma bai ƙarasa abinda zai ce ba hayaniyar yaran nan ta shiga kunnensa daga cikin wayar, don haka ba shiri ya katse kiran yana ƙoƙarin ture abinda ke ƙoƙarin tasowa daga ƙasan zuciyarsa. Ya cillar da ita gefen ɗayar itama sannan ya rufe idanunsa yana cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin nasa daidai lokacin da Inna Danejo ta idar daga sallarta. "Wai rana kika koma bautawa ko me? Wannan wace irin sallah ce bayan la'asar?" Inna Danejo ta kalle shi zuciyarta fara ƙal! da farin cikin ganinsa lafiya ƙalau, don a cikin addu'inta na tsukin kwanakin bata jin ko kanta ta ambata a cikin addointa banda fatan nema masa sauki, don haka da guntun murmushi a fuskarta ta kai laziminta na sallamar sallah sannan tace. "Idan ranar na koma bautawa Muhammadu, iyayenku ai su zasu fara biyo ni kafin ku." Murmushi yayi a hankali sannan ya buɗe idanunsa ya juyo ya kalle ta dasu a lumshe. "Allah yasa da kika dama furar kin rage min, tun da na shigo nake jin ƙamshinta." Maimakon ta bashi amsa sai tace. "Yanzu Allah baza ka ji magana ta ka aske gashin nan ba ko? Ko iska ba ka so kaji tana ratsa ka Muhammadu?" Ba shiri murmushinsa ya karu. "Saboda me zan so iska ta ratsa ni? Wadda ke shiga hancina ma ta ishe ni Inna... Ki tashi ki ɗauko min furar dan Allah." Ai kuwa kamar ya ziga ta ne akan irin mitar da tayi a duk lokutan da baya nan a gidan, ta faro ta tunda daga farko daki-daki har tana faɗin idan ma ba zaiyi askin ba wai ya tsaya ta wanke masa da sabulun salo ta tabbata ranar sai yayi bacci mai daɗi, murmushinsa kawai yake yi yana jinta tunda dama ya riga ya shiryawa hakan. A haka har Ishaq ya shigo ya same su, shima aka zuba masa furar sannan ta tasa su a gaba su duka biyun kuma da zancen aure. A lokacin Ishaq ke gaya mata hukuncin da Baffa ya yanke game da Ma'aruf, don haka bayan ta gama hamdala da mitar cewa Baffan bai zo ya same ta ya gaya mata ba, sai faɗan kuma ya koma kan Ishaq shi kaɗai, tana yi tana zayyano masa jikokin ƴanuwanta na ƙauye, kowacce ta faɗo Ishaq sai ya gyada kai yace "Kuma da alamun tana da hankali." Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, tunani da yawa ke yawo a cikin kansa game da abubuwan dake gabansa, sai dai ko kaɗan babu batun auren nan a cikinsu, don tunaninsa ya gaya masa cewa ko iyayen yarinyar nan mahaukata ne idan ta nuna musu wannan takardar dole ne auren ba zai yiwu ba. A hankali ya sake rufe idanunsa yana tuno dukkan irin matakan dake rubuce a jikin takardun asibitinsa, Allah ya sani a baya baya taba damuwa da ciwonsa, yana ajiye shi ne a can ƙarshen lissafinsa, amma a yanzu... yanzu bai san me yake ji ba, tsoro ko kuma taraddadin cewa abubuwa zasu iya ƙwace masa kafin ya kai ga cimma manufarsa? A cikin duhun idanun nasa ya hango a inda yake manufar tasa, abinda shi kaɗai ne abu guda a duniyar nan da baya taɓa haɗawa da kowa, ɗakin bincikensa yake hangowa, tunda ya dawo bai buɗe shi ba don haka a yadda ya tafi ya barshi yake hango shi... Yadda yayi kaca-kaca da takardu cikin takaicin da shine linzamin dukan da yayi wa Daniel. "... Kaga Rabi ma ƴar wajen Baɗɗejo, yarinya ce mai hankali, ga kyau..." Muryar Inna ta shiga kansa da wani irin tasirin da ya doka a ƙirjinsa, tasirin da yasa ba shiri ya buɗe idanunsa yana kallon Innar da kuma Ishaq din dake cigaba da gyada kai yana shan furarsa, sai dai ba saurarar abinda suka cigaba da cewa yake ba, muryar Inna ta shekaru goma da suka wuce ce ta shiga haskawa a cikinsa, shekaru goma cikin wannan ɗakin. Kuma bayan muryar sai hoton ma ya canja a idanunsa, yaga yadda tsufan Inna ke raguwa da shekaru goma da yadda komai na ɗakin ke canjawa da abubuwan da suke a mazauninsu a shekaru goman da suka wuce, sannan a lokaci guda Ishaq ɗin ma ya bace, siffar Jamal ta maye gurbinsa yayin da yake zaune a gaban Innar yana dariya. "Ga Halima ma ƴar gidan Baffayo, yarinya ce mai hankali, ga kyau, ga kyau..." Ya ga yadda Jamal ke girgiza kansa yana dariya kafin yace. "Akwai abubuwa da yawa a gabana yanzu Inna, ki ajiye maganar yaran nan... Akwai abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan kafin ma in fuskanci aikina..." Kuma a lokaci guda ƙwaƙwalwar Ma'aruf ta tsinto kalamai biyu a cikin zancen... Abubuwan da nake son daidaitawa a cikin gidan nan... Abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan... Tabbas! Ya akayi bai taɓa tunawa da wannan lokacin ba? Me yasa ƙwaƙwalwarsa bata taɓa hasaso masa wannan ranar ba? Babu shiri idanunsa suka shiga hasko masa tarin abubuwan dake ɓullewa ga wannan maganar, yaji su suna sauka a cikin kansa kamar zubar ruwan da aka tunkuɗo da ƙarfi. "B, Yaushe zaka fita?" Muryar Ishaq ta janyo shi daga tunaninsa, sai kawai ya lalubo wayoyinsa a gefe da mukullin motarsa ya mike tsaye. "Yanzu." Ya bashi amsa idanunsa na muna tsantsar nazarin abubuwan da shi kaɗai yake hangowa. Kuma da haka bai jira komai ba yayi waje, yana ji Inna Danejo na ƙokarin tsaida dashi amma bai tsaya ɗin ba, ya fita yana jin tasirin idanun Ishaq da ya biyo da kallo. A harabar gidan ya gano Munaya tsaye tana waya, duk ta rikice kamar yadda take kullum sai faman gyara glasses ɗinta take alamun bayani ake mata ta cikin wayar, don haka bata ma ganshi ba har ya buɗe motarsa ya jata ya bar cikin gidan, kuma zai iya rantsewa zuciyarsa na lissafa kowanne wucewar lokaci kafin ya isa gida. A ƙofar gidan ya ajiye motar don ƙwaƙwalwar sa ta gaya masa cewa ba zai iya jira har maigadi ya buɗe masa gate ɗin ba. Ya shiga har ciki zuwa ɗakinsa, ya buɗe ƙofar da ko waye ya shigo ɗakin zai ce wardrobe ce. A ciki komai yana nan kamar yadda yake hango shi kafin tafiyarsa. Tebura ne da duruwoyi masu cike da files ɗin takardu da kuma hotuna, ga tarin printers da photocopier a gefe, sannan bayan kayan rubutu akwai allo har kala uku ɗaya na rubutu biyun kuma ya manne su da takardu da kuma hotuna. Ɗaki ne da ko makaho ya shafa zai danganta shi da kalmar binceke balle kuma ga mai ganin da kallo ɗaya da zai yi masa zai bashi amsar da ba sai ya tambaya ba. A jikin allon nan bayanai ne da kuma hotunan mutanen da Jamal yayi mu'amala dasu tun daga lokacin da ya dawo daga karatu har zuwa ranar mutuwarsa, kuma a jikin kowacce takarda da hoto Ma'aruf ya zana tambarin × da jar marker alamun abinda yake nema bai ɓulle ga wannan hanyar ba, kusan hakan ne ma a jikin kowacce takarda dake barbaje a ɗakin har kuwa da waɗanda aka yayyaga. A wata durowa daga can ƙarshen ɗakin ya shiga fito da duk takardun cikinta har hannunsa ya kai kan wani file daga can ƙasa. A cikin file ɗin tarin takardun Jamal ne wanda suka haɗa da duk certificate dinsa na gama makaranta da kuma takardun ɗaukarsa aiki a matsayin sabon ma'aikaci a kamfanin Baffa, takardun ɗaukar aikin ya shiga buɗawa ɗaya bayan ɗaya idanunsa na nazarin komai sai dai har yaje ƙarshensu bai ga komai ɗin da yake nema ba, ya zauna daga tsugunnen da yake, ya sake bin komai dalla-dalla, amma har a lokacin babu komai ɗin. Hannayensa duka biyu ya cusa cikin gashinsa yana fitar da iska ta hancinsa... Tunani da yawa ke tsere a cikin kansa, yana ji yadda yanayinsa ke ƙoƙarin canjawa, ciwo na harbawa a cikin kansa yana gaya masa cewa zai koma halin da baidade da fitowa ba. A lokacin ne kuma idanunsa suka hango masa wata ƴar mitsitsiyar takarda da alamun ta faɗo daga cikin file ɗin ne ba tare da ya kula ba, ya miƙa hannu da sauri ya ɗauko ta... Rubutun Jamal ne, hanwriting ɗin sa... Mamaki ya kama shi tun kafin yafahimci me aka rubuta, don yasha buɗe file ɗin nan ya zazzage shi amma bai taba ganin takardar ba. Kuma mamakinsa bai karu ba sai da hankalinsa ya gane masa me Jamal ɗin ya rubuta a jiki. Amina Sulaiman. Gadon ƙaya. *** Me kuke tunani ya haɗa marigayi Jamal da Amina? Me Hajiya Kilishi ke yi da magungunan Ma'aruf? Me yasa Ma'aruf baya son hayaniyar yara? Me Ma'aruf yake son cimma ne game da bincikensa? Waye ya saka kansa a takalmin Amina?😅 #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA SHIDA. ~~~~~~ Wani mai adaidaita sahu ya shigo layin har zuwa ƙofar wani gida mai baranda, kuma da tsayuwarsa Aminu ya fito daga ciki yana dariya alamun sun daɗe suna hira da saurayin dake jan adaidaita sahun wanda shima ya fito bayan ya kashe mashin ɗin, kuma a tare suka kamo wani buhun shinkafa ƙato guda suka shiga kiciniyar shiga dashi cikin gidan, inda tin daga soro ƴar hayaniyar mutanen ciki zata shaida maka cewar an samu baki fiye da mutanen gidan. A tsakar gidan Amma ce tare da ƴanuwanta su uku da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ta kiciniyar hada wasu kayayyaki a cikin kwalaye. Yayarta mai suna Zahra'u da suke kira da Tanti wadda ke zaune a goron dutse ta kalli Amman da ta fito daga kitchen riƙe da ƙaton tire ɗin data yanko kankana tace. "Ni kuwa Halima wai yarinyar nan kaya kala nawa ta ɗinka a cikin lefen?" Amma ta ajiye farantin hannunta a tsakiyarsu kafin tace. "Ina ga kusan rabi ne, ai tun zuwan su Momi ƴar gidan Kawu Mallam wancan satin suka ɗiba suka kai mata wajen mai ɗinkinsu, har da na fitar bikin." Tanti ta gyada kanta tana faɗin. "Ko da naji, don na lura ita bata da wannan niyyar, a baki kawai Amina ta karɓi zancen auren nan amma banda a al'amuranta wallahi." "Kinga ko jiya..." Ɗaya ƙanwar Amman mai suna Ma'u ta shigo zancen. "... Abinda nake gaya mata kenan, nace tunda dai har ta amsa, ya kamata ta saki ranta tayi komai kamar kowacce amarya a haka ne zancen zai cigaba da rufuwa, komai ya tafi daidai." Ɗayar da take ƴar autarsu Safiya tace. "Ai ce miki zata yi hankalinta a kwance yake, ba irin faɗan da banyi mata ba wancan satin amma ƙiri-ƙiri ce min tayi ita ba abinda ke damunta." "Allah ya kyauta, yaya kuka sake yi da ita Hajiya Kilishin? Yaushe za'a fara kai kayan ne? Ya kamata ma aje a ga wajen." Aunty Zahra'u ta tambaya tana rufe ƙaton kwalin da ta gama tara ƴan ƙananun kayan kitchen a ciki. Kuma tambayar ta dawowa da Amma tarin abubuwan da suka faru a cikin wucewar sati uku, yadda ka ranar da taje gidan Tantin a goron dutse, ta hau ta da fada bayan ta shaida mata komai, tace Uba yana da ikon zaɓawa ƴarsa mijin aure don haka ita bata ga aibu a cikin zancen ba, tunda a yadda ta san Baba ta ba zai aurawa ƴarsa mara hankali ba kamar yadda Amman ta kira lamarin. Don haka babu yadda ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru, kuma kamar wasa al'amarin auren ya cigaba gudana bi da bi, a yanzu saura sati guda bikin, an karɓi kuɗin aure hade da lefen da bai wani girgiza su ba kamar yadda take zato a gidan Kawu mallam, sannan har sau biyu Hajiya Kilishi ta kira ta a waya tana shaida mata yadda wasu daga cikin al'amarin bikin zasu kasance a wajensu da kuma cewar gidan da za'a kai Aminan a cikin gidan da suke ne. Sannan a jiya ta aiko da ɗan aike ya kawo tulin wasu katinan ɗan aure da ba su ko san yadda zasu yi dasu ba, don haka a dole ta karɓi al'amarin itama suka fara shiri sosai, Baba yana ta fafutukar kayan katako da ƴan kudin hannunsa da kuma wanda yayyensa suka haɗa masa, yayin da ita da ƴanuwanta mata ke iya nasu ƙoƙarin na kayan kitchen da kuma sauran na amfanin gida, wanda su Aunty Safiyan ke ta sintirin zuwa kasuwa tun wancan satin. Sai da al'amarin ya kai duk da irin halin da zuciyoyinsu ke ciki, shirye-shirye a yanzu sun kama kamar dama sunyi tanadin lokacin. Don haka kafin ta bawa Tantin amsa su Aminu suka yi sallama a lokacin suna shigowa da buhun shinkafar nan. "Yawwa master, nagode sosai..." Cewar Aminun bayan sun jingine buhun shi da wani saurayi daya kamo masa, saurayin yayi waje yana fadin babu komai yayin d shi kuma ya juyo ya kalli su Amma dake kallonsa suna jiran ba'asin abinda zai ce. "Haba Amma ke ma fa kin san bana sata, Baba ne ya kira ni yanzu naje na karɓo a wajensa." Ya faɗa cikin raha yana kallon Amman. Aunty Ma'u tace. "Na ga ranar da zaka yi al'amarin ka kai tsaye Aminu, in ma satar kake ai kowa ya san ba zaka kawo gida ba." "Ameen wallahi..." Cewar Aunty Safiya. "Amma da ƙyar ne canjawar Aminu, ai hali ZANEN DUTSE ne." Ya ƙaraso ciki da dariyarsa yana shirin buɗe babin shafin tsokanar Aunty Safiyan da yafi rainawa, amma tun kafin ya zauna Amma ta katse shi. "Zaka koma ne?" Ta tambaya. "Eh yace in ɗebi kati in kai masa." Kai tsaye ya bada amsar da a lokaci guda ta shiga kunnen Amina wadda ta fito daga ɗakinsu a lokacin riƙe da tsintsiyar laushin da abin kwashe sharar data ɗebi abinci fal a ciki kasancewar Aunty Safiya da Aunty Ma'un duk sun zo da ƙananun ƴaƴansu, suna ta dabdala a ɗakin. Riga ce ƴar kanti a jikinta kalar ruwan toka da wani tsohon zanin atamfa da babu mitar da Amma bata yi ba amma ta kasa rabuwa dashi saboda daɗin ɗaurawarsa, sai ta bayar da sabuwar atamfa ma amma shi yana nan, Gashinta mai laushi yana ta fitowa ta saman ɗankwalinta dake zamewa. Tayi wajen sharar ta zubar lokacin da su Amma suka cigaba da zancensu, Aminu kuma ya dage wai sai sun yi cinikin sabuwar motar Aunty Safiyan da mijinta ya siya mata kwanakin baya kasancewar sa mai hali. Sai ta juya ta koma ɗakin a lokacin da wata ƴar Aunty Ma'u mai suna Yusra ke janyo kaya daga cikin drawer ta. "Me kike nema anan Yusrah?" Yarinyar ta juyo ta kalle ta. "Hijabi Aunty Amina, Sallah zanyi." "To ya zaki yi da hijabina, duka sun fiki tsawo... Kije ɗakin Amma ki ɗauko na Hafsa, me yasa ma baki bi su Hafsa aiken ba?" Ta faɗa sanin cewar Hafsan da ƴar gidan Tanti da kuma ɗaya yayar Yusran basu daɗe da fita siyan kayan miya ba. Adam ma tunda ya samu sa'ansa ɗan gidan Tanti mai suna Mubarak suka fita filin ball shikenan sai an gansu kuma. Ta tsugunna tana ƙoƙarin kwashe kayanta bayan fitar Yusran, yayin da hayaniyar ƴan ƙananan yaran da suka ɗane katifar Hafsa suna doki ke shiga kunnenta, tunda satin nan ya kama komai ƙara gaya mata yake yi cewar sauran wasu ƙaiyadaddun kwanaki rayuwarta ta fara daga gaɓar da zata ƙare. Musamman wannan haɗuwar ta ƴanuwan Amman a gidansu, wani abu ne daban da basu saba ba don Tanti itace babba a cikin su Amman, don haka mafi yawanci a gidanta ake yawan haɗuwa, ko da Sallah kowa can yake tafiya su haɗu har su, shi yasa ganin yadda gidan nasu ya zama wajen haɗuwa yanzu yana ƙara tabbatar mata cewa da gaske komai ke shirin faruwa, gashi Baba ma har ya fara aiko da tanadin abincin biki duk da Amma ta daɗe da kafa layin cewa ba wani taro za'ayi mai yawa ba, ko ƴanuwansu a can Niger tace duk a waya za'a shaida musu kawai, sai dai idan maza zasu zo ɗaurin aure don ya zama shaida a wajensu. Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta lokacin da idonta ya kai kan tulin katinan ɗaurin auren nan, sunayen mutane takwas ne a jiki banda sauran bayanai, amma idan ta kalle shi ba abinda idonta ke gani sai nata sunan dake ƙasan rubutun Ma'aruf Mansur Bakori, sunan da ko sau nawa zata maimaita shi sai ta ji bugawar zuciyarta a cikin allon ƙirjinta. Ta rufe idanunta ta buɗe tana jin yadda har yanzu zuciyarta ta kasa yarda cewa tana shirin buɗe shafin kaddarata ne da hannayenta. Ba lallai ne ya kashe ta kamar yadda ya rubuto a takardar nan ba ta sani, ya rubuta ne kawai don ya tsoratar da ita, amma hakan ba zai hana ta ɗanɗani gwargwadon azabar da ya tsara mata ba, tunda ta tankwabe gargaɗin da yayi mata. Ta tuno shekaranjiya lokacin da Tanti ke tambayar Amma 'yaron kuwa yazo?' sai da ta ƙware da yawunta tsabar yadda tsoron hakan ya shige ta, ita har yanzu bata hango cewar in dai wannan Ma'aruf ɗin da ta sani ne zata ganshi a kusa da ita ma balle ƙaddara ta haɗa su. Gani take yi kamar za'ayi auren ne kawai a kaita wajen Hajiya Kilishin da sunanta ne kaɗai ke yawo a gidansu game da auren. Shi yasa bata fatan kowa ma ya ambace shi, tafi son ayi dukkan abinda za'ayi a kaita ɗin kawai, acan zata tsara matakan da watakila zasu iya siyar mata lokaci kafin dukkan abinda zai faru ya faru har Amma tazo tace. 'Dama na gaya miki Amina' Fatima ma tace. 'Me yasa kika yi tunanin zaki iya Amina?' Maryam zata dinga da binta da kallo kawai, Aminu kuma zai iya cewa. 'Ko ba komai kin ƙoƙorta Amina.' Baba ne kadai zai saka mata albarka ta sani, yayi mata addu'o'in da wataƙila zasu iya gyara rayuwarta a gaba, don ya san tayi komai ne don shi, don tallafar mutuncinsa. Ta kai ƙarshen tunaninta lokacin da sallamar su Ummi da Momi ta cika tsakar gidansu, taji su suna gaisawa dasu Amma har da muryoyin wasu daban don haka ta rufe wardrobe ɗin ta juyo tana korar yaran zuwa waje. A lokacin Ummi ta ɗage labulen ɗakin ta shigo. "To amaryar ƙulle, kina nan mu munje mun samawa kanmu mafita.." Suka shigo suna ajiye ledojin hannayensu yayin da Momy ke cewa. "Amina ruwa dan Allah, wallahi mun ɗebo rana." Da murmushi ta fita zuwa kitchen ta ɗauko jug ɗinsu na roba haɗe da kofinansa ta ɗebo musu ruwa sannan ta dawo. "Wai daga ina kuke?" Muryarta a hankali ta tambaya tana ajiye musu ruwan. Ummi ta miƙo mata ledar kusa da ita tace. "Buɗa ki ga." Ta karɓa kuwa ta shiga zaro wasu atamfofi masu kyau kalar ruwan hoda, (pink). Wani abu ya zarce ta maƙogwaronta, tun lokacin da aka kawo kayan lefen nan su Ummi suka san zancen auren, tunda suma sun san Hajiya Kilishin a matsayin ƴar uwarsu kawai dai tafi shiri da Baba ne duk a cikin si Kawu Mallam ɗin, don haka sai rawar ƙafarsu ta ƙaru kamar me sanin cewar bikin irin wanda suke so ne. "Kowacce dubu ɗaya kenan da ɗari biyar, jikinsu mai kyau ne baza ki taɓa cewa roba bace." "Wai na meye?" Momi tace. "Har tambaya kike? To anko ne muka fito dashi tunda ke baki da niyya, kin san mu ƴan ayi sha'ani ne babu ta yadda za'ayi muyi biki lami ko amaryar bata so." Amina bata ce komai ba, Momi ta sake cewa. "Ina Fatima? Ga guda ɗaya nan ta Maryam mun siyo sai ta nunawa ƙawayenku ita, wanda yake da hali yayi tunda dai saura ƴan kwanaki, waɗannan kuma ƙawayen mu ne su ma gashi sun siyo tasu." Sai a lokacin ta ɗago ta kalli ƙawayen nasu da murmushi a fuskarta tace. "Allah ya saka da alkhairi, nagode." Ummi ta kalle ta tace. "Su da kuɗinsu kike musu godiya? Zo muje ni kiga wani abu." Da haka ta ja ta suka fita daga ɗakin, a tsakar gida su Amma duk sun shige can ɗakinta suna cigaba da haɗa kayan dake ciki, sai Aminu kawai dake ta ɗaga yaran nan sama suna dariya. A ƙofar ɗakin Baffa suka tsaya Ummin tace. "Amina duk shiru-shirunki na san ba haka halaiyarki take ba, akwai wani abu game da auren nan da kike ɓoye mana, kin sani ni da Momi ƴanuwanki ne kuma sa'aninki da zamu iya jin irin ciwonki, idan akwai matsala ki gaya mana, wallahi in zamu iya zamu taimake ki." Amina ta haɗiye wani abu, duk kauɗin su Ummi ta sani cewa suna da zuciya mai kyau a can ƙasa, kuma ta sani cewa suna sonta fiye da yawanci daga cikin ƴan uwansu don haka zasu iya taimaka matan da komai, sai dai bata yi tunanin cewa Ummin zata iya ganin damuwarta sama da ɗokin bikin da suke yi ba. Amma duk da haka ta san babu amfani sanin nasu kamar yadda Baba ya shar'anta tun farko, musamman su biyun nan da ta san idan suka ji kamar ta saka lasifika ne a tsakar gidan Kawu mallam ta faɗawa kowa. Don haka sai kawai ta girgiza kanta. "Wallahi ba wani abu bane Ummi, kin san ban taɓa kawowa kaina aure a yanzu ba ne kawai, kuma sai komai yazo a lokaci guda shi yasa kawai nake jin wani iri." Kamar Ummin bata yarda ba, amma bayan ta kalle ta na wasu sakanni sai ta gyaɗa kanta tace. "To ai shikenan, idan wannan ne da an kai ki sati ɗaya na san zai tafi, don duk da haɗa ku akayi ke bata wasa bace Amina, kuma duk yadda yake jin kansa na san zaki iya dashi....Wai yaushe zamu ganshi ne ma? Ya bamu kuɗin walima..." Wai me yasa kowa yake son ganin sa? Me yasa kowa yake son jawo shi da baki? Basu san a lisafin tashin hankalinta wannan shi ne a sama ba? Jin bata ce komai ba yasa ta sake cewa. "Ko da yake da alama kema ba wani ganinsa kike ba, masu kudin nan sai a hankali, amma dai na san zaku haɗu kafin wani satin sai ki karɓo a madadinmu, idan ba haka ba kuma ni zan karɓi lambar wayarsa na tambaya da kaina." Jin haka yasa tayi saurin girgiza kanta tace. "Kar ki damu baza'a kai hakan ba ma." Ina zata kai kanta idan har Ummi ta kira shi da wannan zancen? Ai ko a mummunan mafarki ta san wannan rashin sa'a ce babba a rayuwarta. Ummin ta kalle ta sosai. "Amina auren masu kuɗin nan fa dama ce da kuma rabo, ki saki jikinki ki ci kuɗin gayen nan son ranki, don baki san irinsa ba, ba lallai ne in kin shiga ma ya buɗa miki ba." A yanzu ta dawo Ummin data santa, ƙanwar ƴanmatan Kawu mallam me cike da buri, don haka sai kawai ta faɗaɗa murmushin ta tana fadin. "Toh shikenan." Da haka suka koma wajen su Momi, inda suka dasa hira su da ƙawayensu, hirar da taso tafiya da yawan tunanin zuciyarta, don hira suke har da dariyar da har ƙasa suke kaiwa wajen ƙyaƙyata ta, daga baya ta zubo musu abinci a ƙaton faranti suka zagaye shi su bakwai suka cinye tas, a lokacin su Tanti duk sun tafi kuma har Amma ta yaba da atamfar da suka siyo bayan an nuna mata. Maryam ma ta dawo ita da ƙawayenta da suka tafi gidan wata mata tambayar Beads ɗin da zasu yi amfani dasu a bikin, kuma ganin atamfar murnarta ta ƙaru don tace tayi kalar beads ɗin da ta bayar ayi mata na atamfar da Baba yayi musu na fitar bikin. Kallonta kawai Amina take don ta lura ita mantawa ma take da zancen cewar ba auren da suke so za'ayi ba, don gabadaya ma ta manta da zancen saukarsu da suke ta shiri, yanzu bikin ne a gabanta don ko jiya tana jinta tana takurawa Aminu cewa ya ƙara mata kuɗi zata siyo kayan da zata yiwa ƙawayenta 'takeaway'. "Tun safe Fatee, tun ɗazu nake ta kallon hanya, baku dawo da wuri bane?" Ta faɗa lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin ƴaruwarsu. Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta zata sai kawai tace. "Go slow ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu." Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin ɗiɓan ruwa a buta suka yi soro. "Amina dama wanda zaki aura da kika ce min ɗanuwanku ne shine wani Ma'aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?" Sai da gaban Amina ya faɗi duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soron. "Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?" "Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ƙanwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ƴan gidan kuma da gaske bashi da hankali." Sai ta girgiza kanta. "Su Baba fa sun gama duk bincikensu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gabaɗaya." Fatima ta girgiza kanta. "Amina baki san me tace min bane..." Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta shiga girgiza shi itama tana faɗin. "Mutane sun iya yaɗa irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha'anin aure..." "Yana da wa sunansa Jamal?" Fatiman ta katse ta, ba shiri ta ɗago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma'aruf ƙani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya. 'A'a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa ɗaya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma da suka wuce...' "Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?" Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta. "Me ta faɗa miki?" Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ƙasusuwanta ne suka shiga rawa ba tare da kwakwaran dalili ba. "Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal ɗin shekaru goma da suka wuce!" **** "Kar ki ɓata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ƙwaƙwalwar da ake cewa ko shaiɗan na tsoron kaidin da zaki iya fitarwa ta cikinta?" Muryar Hajiya Kilishi ta faɗa cikin shirun ɗakin yayin da wayarta ke kare a kunne. Ƙawarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace. "Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma kuɗin da na zuba na neman tafiya a banza." Wani murmushi ya suɓuce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani ɓari na sirrin mafi yawan nasarorinta. "Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata ɗorewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai ɗore ba, har wani ƙato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta? Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shekarata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana ɗaya da na taba takaws wajen wani malami da sunan taimako. Da yatsa ɗaya nake juya kowa a gidan nan yadda nake so kuma kin san ko ƴanuwana da muke ciki ɗaya su ma basu san wata fuskata bayan wadda Iyalan gidan nan suka sani ba. Shi yasa nake son ki gaya min meye amfanin buɗe miki cikina da nake yi ke da Salamatu? Ba don mu taru akan bigire guda bane? To don me a yanzu zuciya zata ja ki ki kauce?" Tambaya ce, amma Hajiya Saratun bata amsa ba, don ta san halin Kilishin sarai, ranta ne ya ɓaci amma har a cikin ɓacin nata halayyar ta kan yi rinjaye a zuciyarta. Don haka tana jinta tayi ajiyar zuciya a cikin shirun sannan tace. "Yanzu a ina kuka tsaya?" "Yace ita zai mayar can Egypt ɗin Kilishi, ni uwar garke in zauna in kular masa da ƴaƴa." Ta furta hakan tana furzar da wani irin huci da Hajiya Kilishin zata rantse tana jin zafinsa tun daga nan. "Bi shi a hakan, kar ki sake ki nuna ranki ya ɓaci, kiyi kwalliya ki tausasa muryarki, ki gaya masa zaɓin da yayi daidai ne, ya duba ɗawainiyar yaranki ya taimake ki. Sannan ki faɗaɗa murmushin ki a gabanta itama, ki gaya mata ko da ke ya zaɓa ba zaki bishi ba dama. Bayan haka kiyi mata ɗawainiya a lokacin da zai gani, misali, samu yaji da irin su busashshen tattasai kice tunanin amfaninsu kika yi musu, don kwana biyu ne abincin can zai gundure su. Idan kin aikata hakan, ki kira ni sai mu ɗora." "Kina ganin zan iya Kilishi? Ba kowa Allah ya halittawa irin zuciyarki ba fa?" Muryar Saratun ta tambaya ɗauke da rauni da kuma wani irin tuƙuƙin dake cin ranta. Sai ta sake wani guntun murmushin tana miƙewa tsaye kafin tace. "Zuciyar da Allah ya halitta min nazo duniyar nan daban take da wadda nake da ita yanzu Saratu, ni da kaina na sami wannan zuciyar don haka kema ki tashi ki samarwa kanki abinda zai ɗore. Ki kira ni idan kin gama abinda na gada miki." Da haka ta katse wayar tana mai taya kawar tata jin ɗacin dake faruwa a rayuwarta, da ace tana da ikon juya zuciyar Saratu yadda taga dama, tayi rantsuwa a ciki wata daya kacal zata gyara mata komai, ta samar mata fiye da ƴancin da take dashi a wajen mijin nata tun kafin sake aurensa. Amma zuciya ce kowa da irin tasa duk yadda ka kai ga iyawa, wani a baki kawai zaka bashi labarin dukkan nasararka amma tasa zuciyarsa ba zata taba iya ɗauka ba. Ƙawayenta biyu kenan a duniya Saratu da Salamatu, kuma bayan abotar tasu, tana zana su ne a cikin wasu mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarta, suka yi mata amfanin da zata rantse ko uwar data kawo ta duniya bata yi mata ba a wajenta, don haka su biyun ne kawai duk duniya kawai take iya buɗewa cikinta su ga ainihin kalolin da take ɗauke dashi bayan farar fatar ta. Matsalar guda ɗaya ce a wajen kowannensu, zuciyar Saratu bata iya jajircewa abubuwa har tayi yaƙi da iyawarta kamar yadda ita kanta ta furta a yanzu, Salamatu kuma sun sha banban da abinda kowannensu ke wa kallon nasara, don ita yanzu ko aure bata dashi, tafi ganewa yawon kasuwanci ga manyan mutanen da zasu dinga bata kuɗin da suka fi ƙarfin kayan nata. Ta ja tsaki a hankali tana nufar ƙofar wardrobe ɗin ta, yau ita ke da turakar Baffa, ta gama shiryawa tuntuni wayar Saratun ce ma ta tsaida ita, a cikin wardrobe din ta dauko wata baƙar ledar magani da kuma muƙullin ɓangaren sannan ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe, ta buɗe ta sanda hayaniya ta cika kunnenta, hayaniyar da a yanzu kullum cikinta suke saboda ƙaratowar bikin. Mutane ne kawai ke zuwa musu Allah sanya alkhairi tun yanzu, musamman daga ɓangaren ƴanuwan su Baffan na can ƙauye, masu kwana ma babu adadinsu don wasu tun wancan satin suka taho ma da zugarsu wai sun zo taya aiki, aikin da kullum sai anyi musu bayanin babu shi. Don daga harkar jere har harkar abincin da za'aci lokacin bikin da duk wata hidima, kuɗi suka biya a dunƙule wa mutane daban-daban da zasu ɗauki nauyin hakan. Kamfanika biyu na interior decoration suka biya don su yi jeran gidajen amaren, kawai ƴanuwanta dana Hajiya Maimuna ne ke zuwa su sa ido akan aikin don a hada har da tunanin mata komai ya tafi daidai, don haka su ɗin da suka zo, ba abinda suke ma illa ƙara aikin, don in banda ci su da ƴaƴansu ba abinda suke yini suna yi, dadinta ɗaya kawai basu barwa ma'aikatan gidan komai ba dasu ake girkin da duk wani aikin da ya taso, shi yasa ba wanda ya kai Inna Danejo murna a gidan yanzu ganin duk inda ta juya kawai ƴanuwanta take gani. Surayya ta fara gani a falon tana danne-danne a wayarta kafin dandazon matan da ke ta fitar da kaya daga kitchen suna yin waje. Ta wuce Surayyan da bata ko dago ba zuwa tsakiyar falon inda suka fara ganinta. "Hajiya sannu da fitowa." Wajen mutum biyar dake rike da wasu manyan fanteku tun na aurenta suka fada. "Yawwa, waɗannan kayan fa? Ina za'a kai su?" "Sameera ce tace a fita dasu waje Hajiya, na aikin cincin ɗin da za'a fara ne." "Cincin kuma? Ina ita Samiran take?" Tana tambayar kuwa ta fito ita da wata sa'arta mai suna Khadija da take ƴar ƙanwar Hajiya Kilishin, suka fito suna jan ragowar wani buhun sukari da ya kusan kai kwata. "Cincin ɗin me ake yi shirin yi a gidan nan Samirah?" Ta tambaya tana katse dariyar da suke yi ta kasa ɗaukar buhun. "Mama yara ne ke jin yunwa kafin a sauke abinci musamman da safe, shine nace bari ayi cincin sai ya dinga rage musu hanya." Girgiza kanta kawai tayi tana kallonta, kowa da irin ƙaddararsa a rayuwa, ita tata ta abinci ce, don duk da science take yi a makaranta, amma course ɗin da take son yi a University shima ɓangaren girki ne, (Nutrition and dietetics.) "Allah ya baku sa'a, kafin ku fara ki kawowa Baffa abincinsa yanzu, can zan je." Ta faɗa sanda ta juya, a cikin zuciyarta tana lissafin layin da zata saka Samiran daya danganci ra'ayinta nan da shekara guda idan ƙwarya ta fashe! Sahla ta fito daga ɗakinta a lokacin riƙe da labtop ɗin Munaya tana sake gyara gilasan idonta. "Mami dan Allah ki bani 1000 muyi subscription, datar da muke streaming ta ƙare kuma Aunty Munaya tace mu kai mata labtop ɗin wallahi ba zata sake siya mana ba." "Kije ɗaki, na ajiye wasu canji akan mirror ku ɗauka." Ta san ita da Zahra ne don kullum suna manne da juna, shi yasa bata san me zai faru dasu ba nan da shekara ɗayan nan. Ta fita daga ɓangaren zuwa harabar gidan kamar wata sarauniya, don duk ɗaukacin mutane kowa tsugunnawa yake yana mata sannu da fitowa yayin take binsu da murmushin da zuciyarta ta wanke shi tsaf, ta tace shi kafin fitowarsa. Kuma ɓangaren Inna Danejo ta fara biyawa ta kai mata maganin cikin ledar nan, na ciwon ƙafa ne wanda Innan tace tana jin daɗinsa saboda haka take sawa ana kawo mata duk wata. Kuma bayan sun yi ƴar hira da sauran tsofaffin dake wajen da kuma tarin albarkar da Innar ke sanya mata, ta fito zuwa ɓangaren Baffa, kafin ta shiga ta hango Munaya daga gefen ɓangaren tana waya, sai gyara glasses ɗinta take alamun tana sauraren wani abu, kuma fuskarta kaɗai ta kalla ta san a rikice take tunda dama ita ko doguwar magana akayi yanzu zata rikice tace bata gane ba, duk kuwa irin mahaukacin ƙoƙarin da take dashi a ɓangaren karatu, don tun suna yara Jamal ke cewa Ma'aruf da Munaya sune Geniuses (masu kokarin) ɗin gidan. Zuciyarta ta cunkushe a lokaci guda da ambatar sunan, shekaru goma kenan da shafewarsa a doron ƙasa, amma har yanzu yaƙi barin zukata su huta, don ƙaryane a gidan nan ance an shafe sati guda na kowanne wata ba'a samu wani ya ambace shi ba, hatta ita kuwa tunaninsa na yawan wulga mata a zuciya, ta tabbata da ace Jamal na raye har yanzu to da itace a bayan ƙasa, don ta daɗe da lissafa cewa shi da ita mutane ne da baza su taba rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba. Ta zira muƙullin hannunta ta buɗe bangaren ta shiga. Komai yana nan kamar yadda ta sanshi, don dama ɓangaren a suna yake na Baffan amma ita ke da iko da komai na cikinsa, me ta gayawa Saratu ne ɗazu? Babu abinda ƙwaƙwalwar mace baza ta iya ba idan har ta saka kanta, ta tuno shekarun da ranta ke ɓaci idan ta ɗaga labulen ɗakinta ta hango kyakkyawar surar Hajiya Maimuna na shiga ɓangaren Baffan, idan taci kwalliyar nan tata za'a shafe tsawon dare ana musu da wani cewa bata ajiye kamar Ma'aruf balle ma wanda yafi shi a duniya ba, kuma da tayi tunanin cewa bata don ganinta a wajen lokaci yayi da zata bar mata bangaren ita kaɗai, me ya faru yanzu? Tayi wani guntun murmushi lokacin da take kunna turaren wuta a jikin burner, a lokacin kuma Samirah ta shigo riƙe da katon tray ɗin dake shaƙe da kayan abincin da ita kadai ta san me ta dafa. Ta ajiye su daga kasa kujerar da ta san nan ne wajen zaman Baffan sannan ta juya. "Bana jin zan fito sai gobe kuma, kar ki daɗe a waje." "To Mami." Cewar Samiran tana saurin fita, sai dai tana isa bakin kofar Hajiya Kilishin ta sake kiranta. "Da gaske nake miki magana, kar ki wuce goma a wajen mutanen nan." Kuma duk da ta amsa ɗin sai da taga yadda ranta ya ɗan ɓaci kafin ta fita. Dole ne ma ta ƙara dagewa wajen kokarin fara ɓanbare tarin abubuwa daga jikinsu, don komai ya kusa ƙarewa, wannan rayuwar ba dahir ɗinsu bace. Fitar ta ke da wuya kuwa taji muryoyi daga wajen suna bin layin gaishe da Baffan da ta hango hasken fitilar motarsa da direba ya sauke shi ta labulen falon. Sai ta taho wajen kofar don ta bude, so take ya fara yin tozali da ita da kuma kwalliyarta kafin wani abu ma na ɗakin. Sai dai kafin ta ƙarasa ɗin wayar hannunta tayi ƙara, ya kalli lambar dake kiran ke shigowa kafin ta dauka, Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗi kasa ta tarwatse! *** Hasken safiyar ya shigo ta tsakanin fararen labulen ɗakin yana ratsowa har ciki zuwa kan gadon da shima komai a jikinsa fari ne, Rukayya ta motsa a cikin baccinta tana ƙara binne kanta a cikin filon amma tasirin wasu dogwayen yatsu dake shiga cikin gashinta suka hana baccin nata cigaba. "J dan Allah mana.." Muryarta ta fito a can kasan numfashinta. Jawad ɗin dake tsugunne a gaban gadon sanye da singlet fara ƙal da kuma wandon gogaggiyar shaddar daya sanya bayan ya fito daga wanka ya sake motsa yatsun nasa cikin gashinta yana matso da fuskarsa kusa da ita. "Na gaya miki ina da meeting by 10 a Abuja, ko so kike in tafi in barki anan?" Bata bude idanunta ba tace. "And what time is it now? (Kuma yanzu karfe nawa?) "Eight tana dab da ƙarasawa, kamar yadda zuciyata take dab da shirin fashewa akanki." Bata san lokacin da tayi dariya ba sannan ta bude idonta akansa. "Sai yaushe zaka dawo?" "Sai nayi kwanakin da kika yi Paris." Ta juya idanunta tana jin yadda yatsun nasa ke ƙara shiga cikin gashinta. "Ka san bani da matsala ko zaka ninka kwanakin ne." Ya gyada kansa a hankali. "Na sani Barbie, na san ni zan haukace..." Sai kuma yayi shiru yana kallon kyawawan idanunta yayin da itama tayi shirun tana sauraren yadda sautin numfashinsa ke fitowa akan fuskarta. "You never know what I went through da bakya nan Rukayya, zan iya tsayawa a gaban ko waye in faɗa miki ke daban ce." Ta lumshe idanuwan nata tana murmushi, tana da tarin hujjojin da zata yarda cewar dukkan maganganun Jawad akanta gaskiya ne, yana ƙaunarta ne da gaske, sai dai maganganun basa taba ƙarasawa har cikin zuciyarta don bata so ya tsallake huruminsa, tafi so ya tsaya a iya matsayin da tsananin kulawarsa gare ta da kuma matsayinsa na ɗan gidan minister da mahaifiyarta ke kwaɗayi yasa ta bashi kawai. Amma akwai wajajen da duk yadda ta kai ga jin sa a zuciyarsa bai isa ya tsallaka ba, Ma'aruf ne kadai mai wannan ikon akanta. Ta tuna da text ɗin da ta tura masa a jiya ta nambar da aka tabbatar mata tasa ce, wani text layi guda kawai da ta tattara dukkan fatanta a cikinsa tana fatan ya zama silar niyya da kuma ƙudirin da ta gama tsarawa a cikin kanta har ma tayi masa ado da ƙarin wasu kyawawan abubuwan da zuciyar tata ke so. 'M'aruf, Hameeda ta tambaye ka...' Kuma sai bayan da ta tura ne sannan bangaren ƙwaƙwalwar tata mai hankali ya shiga jero mata kuskure tare da wautar ta, yana gaya mata kamar ba haka ne daidai ba, yana hasko mata tarin yarjejeniyar data yarda da ita a cikin doguwar takardar nan, lokacin da ta yarda tasa hannu akan komai yayin da zuciyarta ke cike da ɗokin rayuwa mai kyau a gaba kamar yadda mahaifiyarta tace, yana gaya mata cewa saboda ta sami saɓanin tunaninta hakan baya nufin cewa ta shirya fuskantar duk waɗannan sharaɗan? "Jibi zan dawo, ki gaya min zan ƙara samunki dan Allah." Muryar Jawad ta jawo ta daga tunanin yayin da yake ƙoƙarin ƙara matsowa. Sai kawai tayi murmushi sannan a lokaci guda ta shammace shi, ta ture shi ta miƙe tsaye tana dariya, yayi ƙoƙarin kamo ta amma ta kauce saboda haka shi ya faɗa kan gadon inda ta taso. "Zo." Ya faɗa daga kwancen yana kallonta, ta matse kafaɗarta ɗaya. "Zanje in shirya ne kar kayi missing flight dinka." "Wani abu zan gaya miki." Ta ƙara matse kafaɗarta. "Ka barshi sai na fito." Da haka ta shige banɗakin tana murmushi yayin da Jawad ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu yana jin wani abu kamar taraddadi akan abinda ke shirin faruwa. Allah ya sani da gaske yana sonta, irin son da bai san adadinsa ba kuma bai san lokacin da ya shige shi ba, abinda ya sani kawai shine a matan da yayi mu'amala dasu a rayuwarsa Rukayya daban ce, komai nata daban ne ta yadda tun daga lokacin da ya santa, sanda suka haɗu a airport zuciyarsa ke bin ta kamar raƙumi da akala. Shi yasa a yanzu da iyayensa ke damunsa da maganar aure ya ture duk wani kokwanton zuciyarsa ya tsayar da abu guda, don ya tabbata idan yayi saɓanin hakan zai zama kamar an bar baya ba zani ne. Saboda haka a lokacin da ta fito take tsaye a gaban mudubi tana shiryawa, sai ya ture komai ya jawo ƙwarin gwiwarsa ya isa kusa da ita ya tsaya daga bayanta. Ta ƙifta masa idonta ɗaya tana murmushi ta cikin mudubin kafin ya kira sunanta. "Ruƙayya.." Sai ta juyo ta kalle shi amma yasa hannayensa ya komar da ita gabaɗaya, tana kallonsa ta cikin mudubin shima yana kallonta lokacin da da ya buɗe baki yace. "Ina so zan aure ki." Ga mamakinsa sai kawai ta kalle shi na wasu sakanni ta cikin mudubin sannan ta ƙyalƙyale da dariya. "Me kace?" Ya haɗiye wani abu mai zurfi a maƙogwaronsa kafin ya saka hannayensa ya sake juyo da ita yana kallon fuskarsa. "Wallahi da gaske nake, ina so zan aure ki Rukayya, ki bani dama ko a weekend ɗin nan zan turo iyayena, saboda na fahimci cewa I can't live without you. (Ba zan iya rayuwa ba sai da ke)" A lokaci guda ta shiga girgiza kanta yayin da duk wannan rahar ke barin fuskarta, kamar tana karkade ta ne tare da girgizawar kan nata. "Ba muyi wannan alkawarin ba Jawad, saboda haka don me yasa zaka yi tunaninsa, ofcourse kana burge ni saboda wasu abubuwa a gefe, amma bana sonka, na daɗe ina gaya maka hakan, zuciyata ba taka bace." Tana kallon yadda dukkan wani ƙwarin gwiwar da ya tashi dashi a safiyar ke zagwanyewa daga cikin idanunsa, tana kallon yadda yanayin dake cikin idanun nasa ke juyewa zuwa wani abu da ba zata iya fassara shi ba. "Saboda me?" Yayi tambayar kamar iyakarta zata sa ta canja ra'ayinta. "I'm sorry J, amma saboda gidan tsohon mijina zan koma kuma na riga na tsayar da zuciyata akan hakan, idan har ba zaka iya rayuwa ba sai da ni, to ni wataƙila munyi tarayya akan hakan, don nima ba zan iya rayuwa babu Ma'aruf ba Jawad." Bata san me yake tunani ba, bata san me yake lissafawa ba, kawai kallonta yake ɗauke da wannan yanayin da, da ace lokacin da ta buɗe ido daga bacci ne ta ganshi a hakan, zata rantse cewar ba shi bane. Saboda haka tayi baya a hankali ta fita daga cikin hannayensa, kuma sai ƙarar wayarta tazo a daidai wannan lokacin don haka ta isa wajen jakarta dake yashe daga can gefen gadon ta ɗauko wayar, bata ko tsaya tantance lambar dake kiran ba, ta ɗauka ta kara a kunnenta. Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗo kasa ta tarwatse! *** Ina Ma'aruf yake? Kuna tunanin saƙon cikin wayar nan ya dangance shi? Meye gaskiyar labarin Fatima? #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. Please go and read RAI DA ƘADDARA by LUBNA SUFYAN... that story is touching me.😍 BABI NA BAKWAI ~~~~~~~ "Mark my words, idan har wani abu ya same ta, babu wanda zan saurara Ishaq, babu wanda zan saurara." Muryar Ma'aruf, ta faɗa a cikin ɗakin asibitin da misalin ƙarfe takwas na wannan daren, yana zaune daga gefen gadon ɗakin da waya kare a kunnensa yayin da daga tsakiyar gadon, wata ƙaramar yarinya ce kwance tana bacci. Da hannunsa ɗaya ya shafo kansa sannan ya sake cewa. "Saboda me? Shekaru biyu ta hana ni ganinta amma yau sai na tsince ta a tsakiyar wannan gidan arnan? Idan kana yiwa Allah ka gaya min cewa zan iya maka ta a kotu a hukunta ta." Daga cikin wayar Ishaq ya sake cewa. "Ka taimaka ka fara kwantar da hankalinka yanzu B, ba dai yarinyar tana hannunka ba? ai anci rabin matsalar abinda zai biyo ba mai yawa bane. Sannan na tabbata shi kansa Baffan yanzu idan yaji komai, ba zai sake goyon bayanta ba, mu godewa Allah ma da ba'a dauki shekarun da suka fi haka ba." Baice komai ba ya cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin kansa kawai yana sauraren duk bayanin da yake yi kafin wayar tasu ta kai ƙarshe, suka yi sallama bayan Ishaq ɗin ya gaya masa cewa sai jibi zai dawo don aiki ya kaishi wani gari a can hanyar Abuja. Ma'aruf ya sauke wayar a lokacin da idanunsa suka sake komawa kan yarinyar, Hamida ce... ƴarsa, har yanzu tunaninsa ya kasa gasgatawa, ya kasa yarda cewa ita ɗin ya gani bayan tsawon shekaru rabonsa da ita kuma a wani waje da bai taɓa zato ba. Tsawon sati uku kenan da ya sadaukar da duk lokacinsa da komai wajen ƙoƙarin daidaita al'amarin da yake faruwa a kamfanin nasu. Wata irin asara suka yi da bata da tushe, bata da reshe kuma babu wani abu da yaja zuwanta. Dawowarsa kawai aka wayi gari da report din ɓatan maƙudan kuɗaɗen da babu ma wanda ya kula dasu sai a lokacin da aka zo fitar da wani kaso na harajin ƙarshen shekara da ake cirewa a duk ƙarshen kowanne wata. Anyi duk wani bincike amma babu abinda aka tarar daga ƙarshe, don haka Baffa yace a rufe zancen kawai su karɓi hakan a matsayin ƙaddara,. kasuwancinsu ya cigaba da gudana, amma haka kurum sai zuciyarsa taƙi bashi cewa hakan daidai ne, wannan aiki ne da ya riga ya saka ransa akai... Ba yana yinsa don yana sonsa bane yana yinsa ne don ya zame masa dole, dolen da a cikinta ba zai taɓa bari a lissafa da wata tangarɗa ba, don haka ya bi maganar Baffan ya cigaba da gudanar da aikinsa a gefe guda kuma shi da Faruk suna cigaba da bincike akan lamarin. A cikin binciken nasu Faruk ya samo wani mutum ne a cikin ƙananun ma'aikatan wajen da yace yana yana da wani bayani da zai iya basu, amma bayan Faruk ɗin yaje ya same shi har gida, sai ya ƙi bashi haɗin kai game da hakan duk kuwa yadda yayi dashi. Sun fahimci tsoro ne ya kama shi don haka shi yace zai je ya same shi duk kuwa da magiyar da Faruk ɗin yayi masa akan cewar kar yaje, magiyar da ya riga ya san ta mecece don dukkansu du niyun sun san cewar idan lamarin ya ɓaci babu wanda zai iya kallon Baffan a cikinsu da wani bayani. Amma shi kansa Faruk ɗin ya san cewa tunda har ya saka ransa babu abinda zai tsaida shi don ba tun yau ya sani cewar idan har ya furta abu zai yi to tabbas zai yi ɗin, bai taɓa ganin ya sa kansa yin abu ya fasa ba. Don haka kai tsaye bayan ya tashi daga aikin ya nufi unguwar sabongari da address ɗin da Faruk din ya turo masa don ba yadda zai yi. Ya isa da kyar bayan ya haɗa da tambaya sannan kwatancen ya tsayar dashi a daidai kofar gidan mutumin da yake nema. Sunansa Okafor, wani dattijo ne arne daya dade yana aikin shara a kamfanin, ya san shi tun lokacin da idan sun dawo hutu daga makaranta yake zuwa kamfanin, kuma har sai bayan ya fara aiki ne sannan aka ƙara masa matsayi zuwa aikin hada takardu saboda tsufan da ya kama shi, ya kalli takurarren gidan dake gabansa, mutane ne ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, a ransa ya ayyana cewa idan har Okafor yana da sa'a watakila zaman gidan ya kusa kare masa shi da iyalansa. Wani saurayi da ba ko riga a jikinsa sai gajeren wando da kuma sarƙa ya samu ya raka shi zuwa cikin gidan, kuma duk inda suka wuce juyowa ke an kallonsu da mamaki saboda manyan kayan dake jikinsa, nasa mamkin ya fara ne daga lokacin da suka shiga ciki inda yaga ashe gidan wani irin ƙato ne mai kuma tsawo, ga tarin ƙofofi birjiki daga kowanne gefe sannn da ɗimbin mutanen da ya san zasu iya tashin unguwa guda, ƙaton tsakar gidan ya cika taf da kaya da kuma igiyoyin shanya kota'ina, ga kwata layi-layi dake tashin wari kamar bola aka buɗe, sannan hayaniya kamar zata fasa kunne. Ba shiri ya haɗiye yawu yana sake damƙe mukullin motar dake hannunsa lokacin da idonsa ya fara arba da tiƙa-tiƙan mata sanye da ƙananan kaya suna ta harkokinsu tare da maza da kuma tulin yaran dake yawo koina, daga can gaba ya hango wasu suna faɗa, mata biyu ne sai ihu-ihu da zage-zage suke cikin yarensu, yaga masu raba su basu da yawa kowa harkarsa kawai yake a wajen. "Abeg no vex eh, this is Mr. Okafor's room." (Kar ka damu dasu kawai, ga ɗakin Mr. Okfor ɗin nan.) Saurayin nan ya katse shi lokacin da suka tsaya a kofar wani ɗaki mai ɗauke da ragwajajjen ƙofar net. Sai kawai ya gyada kansa sannan cikin nasa kwantaccen turancin yace da saurayin ya fara shiga ya sanar musu zuwansa tukunna, kuma minti guda bayan tshin hayaniyar da ya jiyo a ciki sai saurayin ya fito yace zai iya shiga. Hannunsa ya zaro dubu guda a cikin aljihunsa ya miƙa masa, ai kuwa ya washe baki yana godiya gami da sake buɗa masa ƙofor ɗakin. Da takalmansa ya shiga amma har a jikinsa yana jin dattin da yake takawa akan baƙin carpet ɗin ɗakin, kuma rashin iska da wari ko ƙansnin wani abinci ya hau kansa a take, amma yayi kokarin dannewa ta hanyar murmushi wa tarin al'ummar ciki dake ta ɗebe kaya don sama masa waje ana faɗin. "Welcome sir." Shi kansa Mr. Okaforn jikinsa rawa yake yi na ganinsa balle kuma tarin ƴaƴan sa da kowannensu ya riga ya zube a ƙasa, kuma cikin gurbataccen turncinsa Mr. okaforn ya shiga faɗin. "Ban san da kanka zaka zo ba yallabai, ai na cewa yallaɓai Faruk ne ya bari sai na dawo aiki tukunna, matata ce ba lafiya muna ta faman jinyarta." Ya fada yana nuna wata tsohuwa dake kwance cikin tarkacen kaya, daga nesa ƙaryane ka banbance ta ma da tarin kayan dake wajen. Ya amsa masa bayanin yayin da ya dawo da kallonsa daga kan matar zuwa tarin ƴaƴan da suka zube a gabansa, kusan su tara wanda da kammaninsu kaɗai ya san duka ƴaƴan Mr. Okaforn ne, yaji a ransa yana ƙudirta cewa ya riga ya gama samun bayanin da yake nema don romon da yake shirin kwaɗaitawa Mr.Okaforn wani abu ne da ko mahaukaci ba zai ƙi tayin ba. Sai dai ɗan adam baya taɓa hango tazarar faruwar wasu al'amuran, don a lokacin da ya buɗe baki zai yi magana ne, a lokacin babbar ƴar Mr. Okaforn ta fito daga wani ɗaki ɗaya tal dake manne da falon, hannunta ɗauke da Hamidan da ta saba a kafadarta a lokaci guda kuma tana ƙoƙarin cusa wasu kaya cikin jakar data ratayo tace. "Papa, make I run go drop their pikin that woman go eat me alive if she returned." ( Baba zanje na kai musu ƴarsu, wannan matar zata iya cinye ji idan ta dawo.) "Mary!" Mr. Okforn ya daka mata tsawar da lokaci guda ta dago da idanunta kuma lokacin gudan itama ta durƙushe kamar ƴanuwanta tana faɗin. "Welcome sir." Ya tuna yadda ta dinga rantsuwa jikinta na rawa tana gaya masa cewa kula da yarinyar take a wajen aikinta ce ta taho da ita saboda an kira ta cewar jikin mahaifiyar tasu ya tashi, idanunsa a rufe ya cigaba da hango ta sanda ta biyo shi har bakin motarsa tana fadin yayi mata rai ya bata yarinyar, kuma ya san cewa sanin da tayi cewa shi shugaban mahaifinta ne, shine kadai abinda yasa bata yi masa ihu ba. A hankali ya taso, ya dawo daga gefen Hamidan dake baccinta har yanzu, tun a gidan ya fahimci cewa baccin da take yi yayi nauyi, don har yazo ya sanya ta a mota, sau ɗaya ta buɗe idanunta ta koma bata sake farkawa ba, jikinsa ya bashi cewar tabbas hakan da matsala don haka kai tsaye ya wuce da ita wani asibiti mai zaman kansa inda aka karɓeta da gaggawa kafin likitoci su tabbatar cewar maganin bacci aka bata wanda da alamu ma ta daɗe tana yinsa don jikinta babu kwari sam, a take aka bata gado aka shiga ɗura mata drip mai haɗe da ruwan magani. Kuma sai bayan da ya sami kansa ne sannan ya iya kiran Mami ya gaya mata dukkan abinda ya faru, bai san me ya faru lokacin da suna waya ba, amma sai a wayar Samira ta kira shi daga baya ta shaida masa cewa gata nan zuwa ta cikin hayaniyar da yake jiyowa a gidan. Ya sake gyara zamansa a hankali yana kallon fuskar yarinyar, wani irin abu yake ji yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daɗe da binne ta, yawan ƙaunar yana sashi ganin irin ƙoƙarin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi alaƙanta abinda yake ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A hankali ya lumshe idanunsa yana tuno kalaman Rukayya wanda su suka yi sanadin raba shi da ita. "...bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zabi dawowarka." Kuma ya yarda da maganarta ne a wancan lokacin ba don komai ba sai don nauyin laifin da ya san nasa ne. Don ranar da ya shaƙe Ruƙayya bayan ya karɓe yarinyar daga hannunta yayi wulli da ita, a wannan ranar ne kanta ya bugu da kujera, har buguwar ta haddasa wani ciwo a ƙwaƙwalwar ta wanda da duk da karancin shekarunta aka fahimci cewa bata iya gane mutane a lokacin, kuma sai likitoci suka bada shawarar cewar a ƙaiyade iya adadin mutanen da zata iya sani a ƙwaƙwalwar tata har sai ta fara wayo tukunna, don haka sanin cewar gidansu cike yake da mutane yasa Baffa ya bada umarnin cewa ko bayan an yaye ta baza su karɓe ta daga hannun Ruƙayyan ba sai tayi wayon da za'a tabbatar ciwon yayi sauƙi tukunna. Kuma bayan hakan sai Ruƙayyan ta sanya shi cikin wannan lissafin shima, tace. "Ka taimaka kayi nesa damu Ma'aruf, wannan rayuwar ba itace mafarkina ba, ko kaɗan ba haka nake hango abubuwa ba a lokacin kake gaya min, kuma Allah ya sani na yin dukkan ƙoƙarina wajen gyara maka rayuwar amma ka ƙi barina don ban kasa ba, don haka ina so mu ka barmu mu gyara tamu, Hameeda baƙuwa ce a duniyar nan bata san komai ba, dan Allah kar son zuciyarka ya hana ka bari ta gina tata rayuwar. Allah ya sani ina tsoron kasancewar ta kusa da kai, bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zaɓi dawowarka." Kuma bayan wannan ranar bai sake ganin Hamidan ba, abinda ya sani kawai shine a cikin shekaru biyun ya tura mata isassun kuɗin da ya san sunyi yawa ma wajen kula da yarinyar, kuma a watanni shida da suka wuce sanda aka ce Ruƙayyan zata yi aure ya san cewa sun kai ta wani asibiti a makkah, ba zai iya zuwa ba a lokacin don haka Baffa ya tura Hajiya Kilishi da Shukra da kuma wata ƙanwar Hajiya Maimuna suka je can suka duba ta suka dawo. Yaji kansa yana ɗaurewa da tsananin mamakin da ya kasa lissafawa, tsawon lokaci... tsawon shekaru an hana shi da yake mahaifinta da kuma ƴanuwansa raɓarta akan dalilin da har iyayensa suka tsaya akansa, don tun su Samirah na naci da ƙorafi akan suna zuwa gidansu Rukayyan ana hana su ganinta har sai da suka daina suka cire ta a ransu, sai gashi yau ya tsince ta a irin wannan gidan, tsakiyar sabon gari zagaye da tarin arnan da bai san adadinsu ba. A lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe, wata Nurse ta shigo da takardar jerin magungunan da za'a siya kafin farkawarta kamar yadda likitan ta shar'anta, da yatsa daya kawai yayi mata nuni da ta ajiye akan drawer dake gefe, kuma budewar kofarta wajen fita yazo daidai da shigowar Hajiya Kilishi da kuma Samira dake bayanta riƙe da kwandon abinci, duk da halin da yake ciki sai da yaji zuciyarsa tayi fatan yarinyar nan tana tuna Allah kamar yadda take tuna abinci. "Innalillahi wainna ilaihir raji'un, me ya faru mai gaskiya? A ina ka samo ta?" Muryar Mamin ta faɗa, sai da ya taso ya miƙe sosai sannan ya shiga gaishe ta, ta amsa tana ƙoƙarin riƙe hannun Hamidan da ya saki. Kuma sautin muryarsa a hankali ya shiga yi mata duk bayanin da zai iya a wannan lokacin yayin da take kallonsa da wannan tsananin kulawa da kuma damuwar da kullum ke ɗamfare a fuskarta game dashi. "Kar damu, komai zai daidaita insha Allah Ma'aruf, daɗin abin komai bai ja da nisa ba, ka kwantar da hankalinka dan Allah mu bi komai a sannu kar ka damu kanka da wani tunani, Baffa ya dawo na shaida masa, shima yayi mamaki sosai amma yace a bari ta fara farfaɗowa tukunna kafin komai ya biyo baya, don haka mu tsaya anan, mu tsaya a iya nan dan Allah mai gaskiya." Roƙon da take ya san har da wani bari na muryar Baffa a ciki, don dukkaninsu sun san irin abinda zai iya, don haka bai ce komai ba kawai yayi shiru yana sauraren ta, sauraren da a cikinsa ta fahimci cewa ko ta cigaba da maganar ba fahimtar ta zaiyi a lokacin ba don haka sai tayi shiru kawai ta juya tana kallon fuskar Hamidan. A lokacin Samirah ta zubo abinci a plate ta miƙo masa, kuma ganin ƙoƙarin ta ne kawai ya gaya masa cewa ya kamata yaci abincin ba wai don ya so ba, don haka ya karɓa a lokacin da itama ta koma gefe tana kallon fuskar yarinyar. A cikin tunaninsa yaji Samiran na waya dasu Munaya da kuma amaren da wai dawowarsu kenan daga wajen gyaran jiki suna tambayar sunan asibitin zasu zo, amma Mami ta karɓi wayar tace duk suyi zamansu don in suka ce zasu taho ɗin a yanzu ba'a san adadin wanda zasu biyo su ba kasancewar suna dab da fitowa yanzu ma wasu ƴanuwan Hajiya Maimuna ma suka sauka daga jigawa. Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, wayarsa kawai yake kallo idanunsa na wasa da adadin messages ɗin dake shigowa bi da bi suna nunawa akan screen ɗin, amma a cikin zuciyarsa tunawa yake da zagayen halin da yake ciki bayan wannan, cewar wannan shirye-shiryen bikin da ake shirin farawa har dashi a lissafin. Don tun daga lokacin da ya samu wannan takardar mai dauke da sunan Amina, kuma ya tabbatar cewa zancen auren bai lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha'afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwar auren ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal. Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi wasu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za'ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa sharaɗin cewa gidan zai dawo ɓangaren da Baba Alhaji ya taɓa zama, yaje kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukkan bincikensa akan yarinyar. Ya cije leɓɓensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya faɗa masa kwanakin baya. "Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle ince kana sonta ne, beleive me akwai tarin ƴaƴan masu kuɗin da har layi zasu yi idan kace zaka zaɓa." Ya faɗi hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin ɗaurin auren ga kowa a Office ɗin kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk ɗin yayi wannan ƙorafin ne bayan ya shaida masa yadda al'amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arziƙi bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin waɗannan gidajen, misali aurensa da Ruƙayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci ɗaurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne. Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, kuma kuɗin mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma taɓa ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya kamata a kira wannan al'amarin auren gaske bane wannan. "Ina kika baro masu yin cin-cin ɗin ne da kika biyo ni?" Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita ɗin ta bata amsa ba ya miƙe tsaye, muryarsa da zurfi yace. "Zanje in dawo." Sai ta girgiza kanta.. "A'a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta ɗebo min ƴan kayan kayan da zamu buƙata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min." Ya cije leɓɓensa kaɗan yana bin maganganun nata kafin ya gyaɗa kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da ɗaukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe. Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na riƙe da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damuwa da kuma kulawar da ba mai iya ƙiyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ƙiyasta yadda zuciyarta ke iya ɗaukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a wajenta. Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ƙaunar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata. A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin ɗakin asibitin bayan fitarsu, zuciyarta na ƙara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ƙaiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar Ma'aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa? Ta ƙara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da kuma yadda ɗan ƙaramin ƙirjinta ke ɗagawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a ɗaya gefen ƙwaƙwalwar ta tana hango idanun Ma'aruf da suka tafi ɗauke da tsananin damuwa da kuma ƙaunar yarinyar dake nunawa ƙarara. Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali, ai alƙawari ne cewar ba zata taɓa iya raba zuciyar Ma'aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita kaɗai? Ba har da tsoron wannan yasa ta haɗa aurensa da yarinyar data san ba zata taɓa tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ƙara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam. Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana so ta kai karshen lissafinta... Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta suɓuce daga hannayenta a lokacin da Ma'aruf ɗin ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan gaɓar da kwakwalwarta tayi tanadinsa tun a gida... Gaɓar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta taɓa ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin ɗakinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya suɓuce a fuskarta cike da fatan ruhinsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ƙaryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai buɗe don yaga sabon saƙon da zata aika masa a daren yau wanda zai ƙara ƙaryata kalamansa fiye da cikin masaki. Ta miƙe a hankali ta nufi wajen da ta ajiye jakarta, kan teburin da Ma'aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don ɗakin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya taɓa farinta. Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sannan hannunta ya jawo jakar da niyyar buɗe ta.... *** A cikin ɗakin, da misalin ƙarfe goma na safe, Ruƙƙaya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ƙulli-ƙulli, ta girgiza kanta tana share hawaye. "Wallahi Maamah Hanan ƙawata ce ta haɗa ni da ita, tace ta taɓa yin aiki da wata ƴaruwarta suna da ƙoƙari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na ɗauke ta a lokacin, kuma itama ta taɓa fada min inda take amma na manta." Kukanta ya ƙaru lokacin da ta sake cewa. "Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma'aruf zai sake kallona idan har babu ita?" Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ruƙayya na zaune a cikin ƙaton falon gidan na ƙasa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta daure da ƙaramin mayafin rigar yayi da wayarta ke riƙe a hannu. Idanunta na kallon Ruƙayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na ɓatan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo samanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ƙasar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ruƙayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana biyu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba. Saboda haka kai tsaye ta kira Ruƙayyan ta shaida mata cewar ba'a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ƙaraso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address ɗin gidansu ta karɓo yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba. Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ruƙayya ne, don babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa haɗin kan ƴar tata, ita kaɗai ce mace kuma babba a cikin maza huɗu amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu'amalarta da mazan akan ita. Ta sani cewa tun daga lokacin da Ruƙayya ta fara hankali a duniya ta rasa ta, don daga lokacin da ta ɗauki zuciyarta ta danƙa a hannun Ma'aruf shikenan take zaune da ƙirjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira na hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata baƙin ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ƙwaƙwalwar ta tsaf ya goge wannan Ruƙayyan da take a baya, ƴar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ƴaƴan manya ake samun masu kwaikwayon ta. Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure, ɗaya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ƙwararrun chefs(masu girki) mata bama maza ba don sanin halin Ma'aruf ɗin, amma wucewar sati guda Ruƙayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ƙin Rukayyan da girki haka ta ajiye ra'ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don kawai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don Ma'aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa. Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ƴar tata, a lokacin ta miƙe tsaye tayi wani yunƙuri da bai bawa Rukayyan zaɓin komai ba illa bin umarninta, kuma sa'arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciyarta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma'aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito. Ƴarta Hamida bata taɓa damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai karɓe ta koma wajensa, don haka bata ko waiwayarta a al'amuranta ta Ruƙayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ƙawarta akan alaƙarta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ƴan kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sake komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin. Har ta buɗe baki zata yi magana, Ahmad, ƙanin Ruƙayyan dake bin Ashraf (wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga. "Wai Maamah ki dawo ƙasar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo." Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka. "Me ya faru?" Yayi tambayar ga dukkansu biyu. Hajiya Nafisa ta nisa sannan ta bashi amsa. "Hamida ce ba'a gani ba, ita da mai kula da ita." "What? Ta yaya? Tun yaushe?" "Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna." Ransa a ɓace yace. "Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ƙedara wai ita zata dinga kula da ƴarta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?" Hajiya Nafisa ta girgiza kanta. "Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za'ayi?" Kafin ya bada amsa, Ibrahim ya shigo riƙe da wayarsa a hannu yana faɗin. "Is it true yarinyar nan ta ɓata? Umar just called me now wai ya ganki a waje ɗazu kuna tambayar Hamida." Hajiya Nafisa ta gyaɗa kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar. "Ƴansanda ɗin dake gadi a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba." "Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?" Tambayar tasa Ruƙayya sake fashewa da kuka. Ahmad yace. "Akwai wani abokin Ashraf da ya taɓa zuwa nan yace min ya san ita mai aikin, ban ɗauko wayata daga ɗaki ba, Ibrahim kira shi." Ya kalle shi. "Wa zan kira?" "Ashraf ɗin zaka kira kace ya baka number B-man." Wayar Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don lokacin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta ɗauki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da ƴan sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn. Kuma bayan ta sauke wayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir ɗan autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri. Gayawa zuciyarta take yi cewa ba zata sake kuskuren rasa ƴarta ba a karo na biyu, bata son Ma'ruf amma idan har yanzu shine zaɓin Ruƙayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta karɓi wannan ƙaddarar, zata dawo mata da Ma'aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya. *** "Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Allah yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a ranar alƙiyama, Allah ya sanya albarka a zuri'ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi..." Duk wannan addu'ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ƴaruwar Amma mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da ɗimbin jama'ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ƙa'idar zuri'arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin ɗaurin aure, al'amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka samu baƙoncin ƴanuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu. "Bikin ƴarki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan ɗaurin aure amma ace wai iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ƴarki ta sunna bace kina tunanin zamu ƙi halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne? Amina tana tuna yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al'amarin auren yazo, kuma fahimtar al'amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, waɗanda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada ƴarsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba. Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta faɗi hakan a lokacin da take kallon idanun Amma dake ɗauke da sauran labarin da bata ƙarasa musu ba, sauran labarin da ko ƴanuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar ba, bata ce komai ba. Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya ɗorar da saɓanin cewa faɗa ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba'ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tarin wasu gidajen auren, kawai babu ƙofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninta da mijinta. "Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika buɗe kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa gaɓar da wani ne zai iya magance miki damuwarki..." Zata lissafa Ammanta cikin manya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take taƙama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne. Sai dai duk yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu'ar tana zuba ruwan ɗumi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wataƙila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji. Tana sanye da wani farin saƙi dasu Gwaggon suka taho dashi, anyi mata ɗaurin ƙirji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa, tana zaune akan wani sabon turmi dasu Aunty Safiya suka siyo a cikin kayanta, yayin da sauran jama'ar bikin ke tsaitsaye zagaye da, gidan ya cika danƙam don har ƴan unguwa sun shishigo. Taga lokacin da Tanti ta shigo cikin masu zuba ruwan ta ɗebo nata itama tana kwara mata tare da nata addu'oin dake ƙara karya zuciyarta suna saka kukanta ƙaruwa. A lokacin ne kuma fuskar Ma'aruf ta haska Idanunta, ranar da ta fara ganinsa, ranar da ta taɓa ganinsa, yana dariya a tsakanin mutanen dake taya shi murnar aurensa, babu shiri wani kukan mai ƙarfi ya sake suɓucewa a bakinta. A haka sai da duk wani babba na danginsu da kuma dangin Baba suka zo suka yi sannan aka rufa mata wani farin saƙin, aka lulluɓeta dashi har ƙasa sannan kuma sauran ƴanuwan Amman da basu kai irinsu Gwaggo Balkisa ba suka shiga fesa mata turare ana guɗa. Al'ada ce sabuwa ga duk wanda ya halarci wajen, irin dangin Baba da kuma sauran ƴan unguwa don haka abin ya birge kuma ya ƙayatar ga duk wanda ya gani, kuma duk da cewar ba wani abinci aka raba ba, amma kowa ya tafi yana yaba abinda akayi. "Na gaya miki su Nusaiba duk cewa suka yi baza su zo ba wai tunda ba ke kika fada musu ba, ba'a gaiyace su ba kenan." Fatima ta faɗa da daddare bayan an gama komai mutanen duk sun tafi, wadanda suka rage iya na cikin gidan ne kawai. "To ba shikenan ba, su sha zamansu. Dasu da masu karyatawa suna cewa karyane duk su ƙarata can, ranar da suka zo nemanki akace musu kina gidanki sai su san cewar da gaske ne." Ummi ta faɗa tana kallon Aminar wadda a yanzu ta canja zuwa wata doguwar riga daga cikin ɗinkin kayan sallarta, har yanzu bata fara amfani da kayan lefen nan ba duk kuwa da an karbo daga dinki, gani take kawai kamar basu gama tabbata nata ba har yanzu. Dukkaninsu suna zaune ne a cikin dakinsu tare da ƙawayen su Ummin da kuma ƙawayen Amina da basu fi biyar ba, don kamar yadda Ummin ta faɗa ne da yawansu da Fatima ta gaya musu cewa suka yi ƙarya ne basu yarda ba. Amina bata ce komai ba saurarensu kawai take yayin da take riƙe da ƙaramar ƴar Aunty Safiyya da tayi bacci a cinyarta, daga tsakar gida hayaniya ce kawai ke tashi cikin hausa da kuma zabarmanci daga ƴanuwan Amma, ƴaƴan Baban kurn dana Kawu Malam da kuma yayyensu Ummi duk suna nan, tabarmarsu daban ana ta hirar yaushe gamo, don ma ƴaƴan su Kawu Ibrahim dana Kawu Hamza basu ƙaraso daga Abuja bane, wanda su dama ba sa'anninsu bane, su hudu ne duk sunyi aure a can Abujan ɗaya ce kawai a Kaduna, don haka ko zasu zo tabbas sai ana i gobe ɗaurin auren ne tare da iyayensu, Kawu Hamza ne kawai yake da ƴa sa'ar su Aminar amma tana Ghana ta samu scholarship tana karatu. Amina ta sani cewar ƴanuwan mahaifinta suna da arziƙin da tun lokacin da ta gama karatu zasu iya daukar nauyin cigabanta, amma basu yi ɗin ba, don duk yadda zumuncinsu yake da karfi akwai raunin taimako a tsakaninsu, kowa yafi maida hankali kan iyalansa kawai, kuma Baba mutum ne mai son dogaro da kansa a komai shi yasa shima bai cika tambayarsu abu ba idan har ba wanda hannunsu ya miƙo masa ba. Ta lumshe idanunta tana sauraren hirar dasu Fatima ke yi a gefenta, Baba bai ƙara yi mata maganar auren ba har yau tun daga ranar da ta shaida masa amincewarta, amma a kodayaushe ta kalli fuskarsa sai taji ƙarfin gwiwarta na ƙaruwa, taji zata iya yin abinda yafi wannan ma idan har zai umarce ta. A hankali maganganun da ta gayawa Fatima ranar da tazo mata da labarin Ma'aruf suka shiga dawowa kunnenta. "Fatima, Baba yasha wahala akanmu a rayuwarsa, yaga tashin hankalin da ba zan iya lissafa miki ba duk saboda mu. Lokacin da nake shekara hudu, Amma tayi fama da wata irin rashin lafiya bayan haihuwar Aminu, Baba shi yayi ɗawainiyar konai damu har tsawon shekara guda kafin ta warware. Lokacin da ina aji ɗaya a sakandire nayi wata rashin lafiyar ciwon ƙafafu har bana iya tafiya, wani abokinsa ya kwantanta masa wajen wani mai magani a garin Benue, ni dashi kawai muka tafi, daren farko a hanya mota ta lalace mana gashi motocin dake wucewa basa tsayawa saboda gudun ƴan fashi, a bayansa ya goya ni Fatima, muka dinga bi ta daji tare da sauran mutanen motar har washegari kafin Allah ya taimaka mu isa wani ƙauye. Lokacin da zanyi jarabawar shiga sakandire, Baba ya sadaukar da lokacinsa da komai wajen koya min karatu ba dare ba rana, idan ya dawo daga kasuwa yana gyangyadi yana hamma zamu yi karatun nan, ranar da sakamakon jarabawar ya fito kuma naci, ranar na fara ganin hawaye a idanun Baffa, hawayen farin ciki. Sanda Maryam bata da lafiya kuma karayar arziƙi ta same shi, kin sani Fatima, kin san yadda Baba ya koma kamar mai roƙo yana bi kusufa-kusafa don tara adadin kudin da ake buƙata. Kullum so yake mu girma, mu zama wasu mutane da al'umma zasu amfana suyi alfahari dasu, don haka ba lallai ne mu hango fa'idar wannan hukuncin nasa a yanzu ba, amma na tabbatar miki Baba ba zai yarda da zancen auren ne haka kawai ba, yace ya amsa musu ne saboda nauyin idanunsu da yaji, amma ni na sani cewar akwai wani abu daban da yasa ya amsa wanda ba lallai ne dukkanmu mu fahimce shi yanzu ba. Kema na yarda da maganarki kamar yadda na yarda da ta Amma, sai dai bana jin zuciyata zata dauki taku sama da tasa, don ban san wane irin butulci zanyi ba idan har na kunyata mahaifina a idon duniya, gwara ko meye ya same ni da inyi sanadin hakan." Kuma tun daga lokacin, shikenan ta kashe bakin Fatiman, bata kara cewa komai ba, bata ƙara ƙalubalantar ta da komai ba, ta fauwalawa ubangiji al'amarin kamar yadda itama tayi, har ta saki jikinta cikin su Ummi itama ta siya atamfar nan ta kai ɗinki. "Gobe zanje in karbo ɗinkina, kuma zamu je ni da Maryam wajen masu sarƙar nan mu ƙara yi musu tuni." Fatiman ta faɗa tana katse tunaninta. Sai ta gyada kai kawai sannan tace. "Ɗazu Maryam take gaya min, wai ta samo me zuwa ta mana ƙunshi ma." "Ƙunshi a ina? Me zuwa gidan ce zata miki? Ai kar ma ku fara wannan zancen, kuɗi zaki karɓo zoo road zamu tafi jibi-jibin nan, idan aka gyara miki gashin nan naki da hannayenki, ba wanda za'a sake yiwa bayanin cewa ke amarya ce." Ummi ta faɗa, kuma tana ƙarashewa wata ƙawarsu ma ta ɗauka da faɗin. "Ni wallahi naga ta kara haske ma akan ranar da muka zo daga kasuwa." "To kina raba amare da gyare-gyaren jiki ne? Kawai ki tambaye ta sirrin tunda kema kin kusa fara naki." Momi ta faɗa suna ƙyalƙyalewa da dariya, Amina kuwa ta haɗiye yawu, don ita bata san wani abu gyaran jiki ba, vasiline ɗin da take shafawa kullum shine dai, robar ko ƙarewa bata yi ba balle ta canja ko kuma ta waiwayi mayukan cikin lefen nan, abinda ta sani kawai shine idan har da gaske tayi fari to kuwa tabbas na tsora ne. Don Allah ya sani idanunsa kaɗai idan ta tuno zuciyarta na bugawa da sautin dake barazanar saka ta kuka duk da ƙwarin gwiwar da take ji, tsoron daban ne don bata san me shi da kuma zuciyarsa suka tanadar mata ba... Ta rufe nata idanun a hankali tana jiyo hayaniyar su Aunty da Aminu daga waje akan motar da zata fara ɗaukan kaya, don gobe Tanti tace ya kamata a fara jere. Tsoro take ji da gaske, Tana ji kamar tana faɗowa ne daga wata sama mai nisa, kamar tana tafiya cikin idanun nasa inda ruwan cikinsu zai nutsar da ita da kuma numfashinta. Abinda bata sani ba shine har yanzu a gaɓa take, bata shiga koina ba ma balle ta fara nutsewar! *** Wasa farin girki! #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. Bari nayi sauri na wuce, a yafe min.🙏🙏🙏 BABI NA TAKWAS. ~~~~~ Ɗimbin jama'ar dake yin tururuwa suna ƙara cika kowanne ɓangare na cikin masallacin su suka shaida auren mutum takwas ɗin da aka ɗaura kowanne kan sadaki mabanbanci, motoci kawai kake gani daga koina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa suna daɗa adadinsu. Jama'a kuwa babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin daya tara su gurin, dattijai da samari har ma da yara masu tasowa, gasu nan kala-kala kowanne ango da ƙungiyarsa da sai faman gaisawa ake ana ɗaukar hoto. Daga can gefe, Kawu Ibrahim ya ƙaraso inda tasu tawagar ƴanuwan take, ya tsaya a kusa da Kawu Hamza yana girgiza kansa. "Ka san yaron nan har yanzu bai iso ba." "Ai ba zuwa zaiyi ba, gwara mu ma mu hanzarta mu bar wajen nan don ni jirgi na na ƙarfe uku ne ma, kuma akwai abubuwan da zanyi kafin nan." Kawu Ibrahim ya juya ya hango su Kawu Mallam dake tsakiyar mutanen yana gaisawa da sauran ƴanuwansu fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, sai kawai ya juyo da kansa yace. "Har yanzu na kasa gano dabararsu akan auren nan, babu wani abu dake nuna min cewa ba don saboda kudin mutanen nan komai ya faru ba." "Koma meye dalilin nasu, a yanzu komai ya riga ya faru, kuma duk matsalar data faru daga yanzu kuma na tabbata shi ɗin yana da hannun ɗaukarta." Kawu Ibrahim ya girgiza kansa. "Muyi fatan alkhairi kawai, don har cikin zuciyata ina tausayin yarinyar nan, Amina tana da hankali wallahi." "Hankalin da bai kamata ace an ƙuntata rayuwarta tun daga yanzu ba. Ai wallahi da nine da ikon Kawu mallam, auren nan ba zai taɓa faruwa ba." Kafin Hamzan ya sake magana wayarsa tayi kara don haka ya dauka yayi gefe yana ƙoƙarin amsawa. Kuma sai a lokacin idanun Ibrahim suka iya hango masa Baba (mahaifin Amina) yana daga tsakiyar mutanensa sai faman gaisawa yake dasu fuskarsa ɗauke da ɗimbin fara'ar da ya kasa auna nauyinta dana kuɗin sadakin auren dake cikin aljihunsa, dubu ɗari cif! A cikin ƙwaƙwalwar sa lissafi yake cewar ko da kudin zasu iya ninka adadinsu sau goma baya jin zai taɓa iya bada ƴarsa aure ga mutumin da akace yana da matsalar ƙwaƙwalwa, tunda gashi tun a yanzu sun fara gani, in ba haka ba wane ango ne yake ƙin halartar wajen ɗaurin aurensa? *** Motar ta shigo kamfanin da saurin da ya saka maigadin da ya buɗe gate ɗin juyowa yana kallonta, kuma duk saurin nata sai da ta isa ga layin da ake ajiyar motoci ta tsaya sannan ƙofar mazaunin direba ta buɗe. Ishaq ya fito sanye da wasu kaya kalar sararin sama, wayoyinsa rike a hannu ya rufe ƙofar sannan ya tunkari cikin ginin dake kallo shi, wani gini mai hawa uku da yasha adon gilasai tun daga samansa har ƙasa. Security ɗin daya bude masa ƙofa har sunkuyawa yayi bayan ya gane shi yana fadin. "Yallaɓai sannu da zuwa." Kuma maimakon ya amsa sai kawai ya tambaye shi. "Ma'aruf yana ciki ko?" "Eh tabbas, ai tun safe ya iso yallabai" Jin haka yasa Ishaq ɗin yin gaba zuwa hanyar matattakalar da zata kaishi sama, wata receiptionist (mai karbar baki) a wajen mai suna Rafi'at ta shiga gaishe shi tana murmushin da ke manne cikin tsarin ayyukanta, kuma da mamakin yadda akayi bata manta fuskarsa ba duk da karancin zuwansa wajen ya ɗaga mata hannu yana zarcewa zuwa saman. A hawa na farko can ƙarashe ofishin Ma'aruf ɗin yake, don yana tuna lokacin da yake gaya masa cewa ya canja office, ya isa ƙofar daidai lokacin da sakatariyar Ma'aruf ɗin mai suna Martha ke fitowa riƙe da wasu files a hannunsa. "Sannu da zuwa yallabai, yana tare da wasu baki ne a ciki, ko zaka jira su kammala." Martha ta fada da murmushin dake nuna masa da gaske take, kuma ya san lallai baƙin masu muhimmanci ne don babu ta yadda za'ayi ta tsaida shi idan ha haka ba. Gyada kansa kawai yayi alamar ya fahimta sannan ya ƙarasa kofar ya buɗe ta, idonsa ya gane masa wasu inyamurai biyu da kuma wani ɗan china, dukkansu suna zaune a kujerun dake tsallaken teburin Ma'aruf ɗin, kuma budewar kofar tasa dukkaninsu suka juyo suka kalle shi, Ma'aruf na sanye da wani bakin yadi mai sealed ɗinkin da ya fito da tsarin jikinsa, hular kansa ma baka ce data dace da shigar da ita kadai ya kamata ta tabbatarwa da Ishaq cewar abinda yake tunani tabbas haka ne, dama baiyi niyyar zuwa wajen daurin auren ba. "Bismillah, ka shigo mana." Ma'aruf ɗin ya faɗa yana kallonsa, sannan a lokaci guda ya maida kansa kan takardar dake gabansa yana ƙarasa rubutun da yake yi, ya kuwa karaso cikin daidai lokacin da ya rufe takardun ya miƙowa mutanen tare da murumushin daya dace da fuskarsa. Ɗaya daga cikin inyamuran ne ya karba tare da yin godiya kafin dukkanninsu suka mike a lokaci guda, Ma'aruf ɗin ma ya mike yana miƙa musu hannu, ɗaya bayan ɗaya suka gaisa kowanne da murmushi yayin da yake sake yi musu alkawarin cewar kar suji komai, suyi aikin da zasu yi kawai babu abinda zai gifta a tsarinsu. Kuma watakila yanayin fuskar Ishaq ɗin suka kalla don babu wanda yayi masa magana a cikinsu suka yi hanyar kofar suka fita. "Wanne za'a kawo? Tea ko Coffee" Muryar Ma'aruf ɗin tasa hankalinsa dawowa daga rakiyar da yayiwa mutanen nan, ya juyo ya kalle shi. "Kaima ka san ba abinda ya kawo ni ba kenan." "Na sani..." Ma'aruf ya faɗa yana komawa kan kujerarsa. "Shi yasa na tambaye ka hakan ai, don idan ka fara muryarka zata fi fitowa idan da abu mai zafi a kusa." Sai kawai ya girgiza kansa, yace. "Wane irin rashin mutunci ne wannan B? Ya za'ayi ranar da za'a ɗaura maka aure guda ka taho Office? Ka san tarin mutanen da suka neme ka a wajen nan?" "Really? Ai da ka sani kawai su biyo bayanka ku same ni anan sai su ganni." Wani irin abu ya sake tasowa Ishaq, sai kawai ya karaso gaban teburin nasa ya zube wayoyinsa sannan ya kalle shi sosai yace. "Abinda kake yi ba daidai bane Ma'aruf, me yasa ko sau ɗaya a rayuwarka ba zaka yi abu irin na mutane ba? Ka nuna baka son auren nan da farko, daga baya kazo ka nuna ka yarda saboda Baffa, to idan haka ne me yasa zaka kunyata shi a yau? Me yasa baka je wajen ba alhali ka san rashin zuwan naka zai iya haifar da wani abu?" "Me zai haifar?" Ya tambaya alamun hankalinsa a kwance, kafin ya cigaba. "Zai haifar da rashin faruwar auren ne? Kana tunanin akwai abinda zai saka Baffa ya canja maganarsa? Na gaya maka na yarda da auren ne saboda naga ba zan iya karewa ba, naga babu abinda zanyi wanda zai canja ra'ayinsa, yanzu ka gaya min da ban je ba ya fasa ɗaurawa?" Ishaq yayi shiru kawai yana kallonsa, sautin numfashinsa na fita da yawan da ya zarce daidai, don akan fuskar Ma'aruf din yake gane cewa abinda ya fada ba haka bane, dole akwai wani dalili daban da yake dashi game da auren nan, saboda abinda ya faɗa da farko gaskiya ne. Su biyun sun sani cewar wannan auren ba ƙaramin haɗari bane, abu ne da bai kamata ya faru ba, don haka ba saboda Baffa ya ture hakan ba ya sani, shi yasa babban tsoronsa shine abinda zai iya yi, don shi shaida ne akan tarin abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da basa furtawa har yanzu balle na ukunsu ya sani, abubuwan da ba wai sunyi shawarar ɓoyewa bane kawai akwai su ne amma kamar babu su ɗin. Ya haɗiye wani abu a ƙirjinsa yana jin yadda shakka da kuma tsoron abinda Ma'aruf din zai iya ke bin koina a jikinsa, bai san yarinyar nan ba, bai taɓa ganinta ba amma yana tausayinta tun yanzu, don ya san wani rauninta a rayuwa aka kalla aka haɗa wannan auren, tunda a bayyane yake ga kowa cewar ba kowanne uba ne zai iya ɗaukan ƴarsa ya bawa mutum irin Ma'aruf ba, kamar babu banbanci ne da ka tura ƴar taka cikin dokar dajin da babu ranar fitowa. Sai kawai ya zaro wallet ɗinsa daga aljihu, kuma har a lokacin Ma'aruf ɗin na kallonsa da nasa idanun dake danne tarin abubuwan da yake dannewa, a cikin wallet din Ishaq ya zaro ID Card ɗinsa ya nuno masa shi, kuma da ganin haka Ma'aruf ya san me yake nufi, ya san cewa da gaske ransa ya ɓaci, don rana ta ƙarshe da ya fito da ID card ɗinsa yana tuna masa cewa shi lawyer ne zai iya ɗora aikinsa sama da alaƙarsu shine ranar da aka kai Baffa asibiti saboda ciwon zuciyarsa da ya tashi ta dalilinsa. "Ban san me kake shiryawa ba Ma'aruf, amma na yarda cewa ba ka yarda da auren nan saboda Baffa ba, akwai wani abu da kake ɓoye min..." "Jamal ya san yarinyar." A lokaci guda muryar Ma'aruf ɗin ta katse shi yana kallonsa. "Me kace?" Ya tambaya idanunsa na shaida rashin ganewar. Ma'aruf ya gyara zamansa, ya ƙifta idanunsa yana kallon Ishaq ɗin sannan ya sake maimaitawa. "Jamal ya san yarinyar Ishaq, so nake na san yadda akayi Jamal ya san yarinyar, wataƙila hakan zai iya bani damar da zan iya gano mutanen da suka sa na kashe shi!" Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Faruk ya shigo Office ɗin yasha adon wasu fararen kaya har da babar rigar, bakinsa a buɗe yace. "Wai da gaske baka je ɗaurin auren ba?" **** Kayan jikin Amina wani farin Lace ne wanda aka ɗinka daga cikin kayan lefen, ta yafa farin mayafin da shima a cikin kayan yake, hannayenta sun sha ƙunshin da suka je har zoo road tare dasu Ummi suka yini ana yi, ɗaurin ɗankwalin da Momi tayi mata yayi baya da yawa ta yadda hakan ya fito da gashinta ta gaba, akwai fararen awarwaro a hannyenta har da wani zobe mai kyalli ma. Babu ko kwalli a idanunta amma ita kanta ta sani cewa kamanninta ba ɗaya suke da sauran ranaku ba, watakila suna da kuma matsayin aure yana zuwa ne da tasirin dake banbanta kowacce amarya da sauran fuskoki, don ita kanta ta sani cewar fuskarta tayi wani irin fresh da kuma kyan da kowa ke gani tare da fararen idanunta, fatar fuskarta har maiƙo take saboda yadda take tas babu ko ɗigon ƙananun ƙurajen da ta saba fama dasu. "Fatee, ina gurasar? Jiranki fa muke yi!" Wata Shukra ɗaya daga cikin kawayenta a islamiyya ta kwallawa Fatiman dake can cikin hayaniyar tsakar gida kira, a cikin ɗakin nasu ƴanmata me fal da suka haɗa da kusan duka ƙawayen su na islamiyya da kuma na makarantar boko wanda duk a ƙoƙarin Fatima ne ta tattaro su, sannan ga su Ummi ma da tasu tawagar ƙawayen, don haka ɗakin ya cika taf sai faman hayaniya suke wadda ke sajewa cikin tarin ta gidan gaba ɗaya. Don ko'ina a cike yake taf da mutane sai faman rabon abinci kawai ake, babu wanda yayi tunanin za'ayi wannan taron, Amma bata taba lissafa cewa yawan waɗannan mutanen zasu taru ba, amma ance wai biki dama ba'a masa gayya da kansa yake fallasa kansa, musamman ga su ɗin da kusan duk wanda suka mu'amalanta yana jin daɗin zama dasu. A lokacin Maryam ta shigo ɗakin riƙe da wani faranti da aka cika da ƙullin zobo. Ummi da tasha kwalliya cikin ankon atamfar nan tace. "Yawwa Mary, matso ta nan, tun dazu dama Aunty Safiyya ke cewa mu jira a kawo." "Taɓ! Wallahi na wannan ƙawaye na ne suna can a dakin Aminu, plate nazo nema idan kun gama zan zuba gurasa." "Au ba zaki bamu ba?" "Waashi can fa ana ta ɗiba a ɗakin Amma, kuje ku ɗebo naku kafin ya ƙare don wallahi har yaje rabi." Ummi ta miƙe da sauri tace. "Mu nawa ne a dakin?" "Ai kawai je ki ɗebo ashirin, in ma da saura ma kara." Cewar wata a cikin ƙawayen Aminan suna ƙyalƙyalewa da dariya gabaɗayansu. Ummi ta fita daidai lokacin da Fatima ta shigo rike da plate guda biyu na banɗashen gurasar, Maryam kuma ta juya ganin ba zata samu abinda tazo nema ba. "Wallahi kowa ya ɗauke hannunsa kafin in ajiye." Cewar Fatiman ganin yadda kowannensu yayi shiri da hannunsa. "Dalla malama ki ajiye kawai meye haka wai?" Cewar Shukra. "Wallahi sai kowa ya ɗauke hannunsa, salon ina ajiyewa in rasa." Ta faɗa tana dariya, yayin da hayaniyarsu ta ƙaru kowa na fadin ta ajiye, ai kuwa tana dire farantin kafin ta mika nata hannun ta nemi gurasar ta rasa, sun wawushe ta tsaf suna ƙyalƙyala dariya, kuma yanayin fuskar Fatiman yasa Amina dake daga gefensu yin dariyar itama, lebbenta yayi talewar da har haƙoranta suka fito, don abu ne da ba yau suka saba ba, tun a makaranta sun saba irin wannan abin da an kawo abinci kawai wanda ya samu ya samu. Kuma dariyar taji tana tafiya har ciki ƙirjinta, tana taɓo wani abu da ya kamata dama ace yana nan, wannan farin cikin da mace ke ji a lokacin aurenta. A cikin hayaniyar da ɗakin ya ƙara ruɗewa dashi Aunty Ma'u tazo ta kira ta, tana fita taga Aminu ne yazo da mai hoto, aka shiga ɗaukar hoton kowa da ƙungiyarsa, Aminu na tsaye shine mai bada umarnin dake sa kowa yin dariya, don haka kusan duk a hotunan an ɗauka ne Amina na dariya, tayi kyau a cikin kayan da suka zauna a jikinta sosai ga kuma skirt ɗin kayan daya buɗe ta ƙasa, ita kanta ta yarda cewa telan nasu Ummi ya iya ɗinki ba'a banza suke ta yabonsa ba, kuma a kowanne hoto ita idonka zai fara gani saboda shigar kayan nata farare tas da kuma baƙin gashinta daya fito ya haɗu da baƙin ƙunshin hannaye ta yana ƙara haska farin. Hatta Amma tayi kyau cikin shigar wani lace da ya dace da maman Amarya, itama tana ta dariyar da har ta mantar da ita haushin da zuciyarta ke ciki game da kayan jere da suka kai aka ƙi karba. Ranar da su Tanti suka tafi za'a fara jeren nan, ranar zuciyarta ta sake yin baƙi game da al'amarin auren, don a waya Hajiya Kilishi ta kira tana gaya mata cewar ai su basu ce su kawo kaya ba, wai mahaifin yaron daya bada kudi ayi gyaran gida ya bayar har dana komai don haka su sun riga sun gama jeran su amarya kawai suke jira. Sai da ƙyar bayan Tanti ta dage cewar baza su kawo ƴarsu haka ba sai da abinda zata kalla itama ta san cewar iyayenta ne suka yi mata kamar kowacce ƴa, sannan Hajiya Kilishin tasa aka fitar da kayan gado guda daga wani ɗaki suka jera nasu, kayan Kitchen kuwa suka zube mata gabaɗaya don shi dama abubuwan da aka ajiye basu da yawa, sai a sannan ne zuciyar Amman ta ɗanyi sanyi, amma har a wayewar garin yau bata dawo dai-dai ba sai a yanzu da Aminu ya saka ta yin dariyar dole. Kuma duk yadda bikin ya kai ga zuwa a gaɓar da kowa ke ganin ba'a shirya ba, yayi mutuƙar yin daɗin da wataƙila ko da sun shekara ne suna tanadi haka komai zai kasance, banbancin kawai na farin cikin da za'a samu a zuciyoyinsu ne. Wajen yamma, Adam ya kawowa Amina saƙon wata sallaya mai kyau da kuma alƙur'ani daga Abdallah, a hannayenta Amina ta rungume ledar ba tare da tace komai ba, idanunsa kawai take hangowa a ranar da ta gaya masa aure zata yi, yana kallonta da yanayin da bata iya fassara shi ba. "Dama na gaya miki, ba wani son ki yake yi har cikin zuciyarsa ba." Haka Fatima tace lokacin da ta gaya mata yadda suka yi, amma sai ta girgiza kanta ta bata amsa. "Cewa yayi dama ya sani ba lallai ya iya aurena bane Fati, yace ya san ba lallai ni ko iyayena mu iya jurewa tazarar dake tsakani na dashi ba." Da yamma Fatima dasu Ummi suka sa ta canja zuwa wani material kalar ruwan madara, a lokacin kuma kusan duka ƙawayen nasu na nesa sun tafi sai mutum uku kawai da kuma wasu daga cikin ƙawayen su Ummi, kalar kayan ta ƙara fito da hasken fararen idanunta, suka saje sosai cikin wani ɗauri mai kyau da Momi ta sake yi mata. "Kece amarya ta farko a wannan lokacin da naga anyi bikinta bata yi make-up ba Amina, Allah ya shirya miki halinki." Cewar Momin sanda take ɗaura mata ɗankwalin, sai kawai tayi wani murmushi tana kallon ƙunshin hannunta yayin da wata ƙawarsu ta ke cewa. "Amma kuma tayi kyan da wasu amaren ma da yawa basu yi ba, kin san natural look ƙarshe ne." Da haka sai hirar ɗakin ta koma kan kwalliya, kowa na faɗin ko a kwalliya simple make-up tafi kyau, wasu kuma na lissafo masu kwalliyar da ko heavy make-up ɗin suka yi tana yin kyau. Ta sani itama da aurenta bai zo a karkace ba zata yi kwalliyar, amma babu kalar tanadin data shiryawa wannan, ƙunshin ma don su Momi sun takura ne kuma ta san shine abinda kowa zai fara lura dashi akanta. "Dama da kika haɗa kayanki baki ɗebi waɗancan litattafan ba?" Fatima ta tambaya daga gefenta sanda idonta ya kai kan wani kwali a can saman durowarsu na litattafan makarantar ta, litattafan da ta san ba zata taba rabo dasu ba, don kullum cikin bitarsu take yi. "Maryam ce ma ta haɗa kayan ai, ni ban san me da me ta haɗaba, kawai dai tace min ta hada su ne tare da sauran kayan akwatunan." "Allah yasa dai bata haɗa miki da kayan sawa da yawa ba, don yawa zasu yi miki idan aka hada da sababbin, gwara ita a ta ɗan ƙara akan nata. Ina ledar su sallayar da aka kawo, bari na haɗa na kaisu kusa da akwatunan, kar a manta." Fatiman ta faɗa tana ƙokarin miƙewa, sai dai kafin ta kai ga miƙewar Amina ta jawo hannunta da sauri, ta juyo ta kalle ta, idanunta sun kaɗa daga farinsu ta girgiza mata kai. "Ki zauna kawai Fatee, ki bari ko anjima sai ki ɗauko su." Muryarta da kaɗan tafi kuka, kukan dake kwance a ƙirjinta tun bayan ɗaurin auren da su Kawu Mallam suka kirata soro bayan dawowarsu, Kawu mallam ɗin ya danƙa mata sadakinta dubu ɗari a hannunta, da kuma bayan tafiyarsu da ƴanuwansu na Niger suka ƙaraso suna faɗin angon bai je ba... Kalaman da suka sata tambayar me yasa take yaudarar kanta ne? da kansa yazo har nan ya gargaɗe ta tun kafin komai yayi nisa don haka don ya fara nuna mata bala'in da ta kawo kanta cikinsa hakan ba komai bane. Har bayan sallar magariba gidan nasu a cike yake, koina yayi kaca-kaca da ruwa da kuma abincin da aka zuzzubar, sannan ga tarin wanke-wanke fal a gefe, don haka ana idar da sallar magaribar ƴanuwansu na Niger suka fara aiki kotaina, Allah ya taimaka da wutar Nepa don haka akwai haske koina. A lokacin ne kuma motocin ɗaukar amarya suka hallara! *** A cikin motar dake tafiya kan titin Lamido cresent, ɗan karamin mayafin da Ruƙayya ta yafa akan doguwar rigarta ya zame ya sauka kan kafaɗunta, gashin kanta baƙi sidik da ya haɗu dana ƙarin data nannaɗe cikin bun ya fito ta cikin hasken street lights da kuma na fitilar motar ƴan sandan dake jiniya a bayansu, amma bata damu ba, hannayenta na rawa ne yayin da take kokarin sake kiran layin mahaifiyarta daya katse saboda rashin service yanzu da suke magana. Ta samu kiran ya shiga a lokacin da muryar Ashraf dake tuƙa motar da kuma ta abokinsa Bilal da suke kira da B-man ta shiga kunnenta. Ashraf ɗin ne ke tambayar abokin nasa idan har lambar wayar da suke jira an turo masa, amma a gajarce kawai ya bashi amsa yana girgiza kai. "Ina jin ki Ruƙayya kuna ina?" Muryar mahaifiyar tata ta shiga kunnenta daga cikin wayar. Sai a lokacin ta jawo mayafin ta sake rufe kanta sannan tace. "Maamah muna hanya, mun ɗauko Bilal ɗin yanzu zamu tafi can sabon garin, su Ibrahim ma sun je sun taho da police ɗin suna bin mu a baya, muna jira ne yanzu a turo masa da number wanda ya sani a gidan don a tabbatar idan tana nan." Daga cikin wayar Hajiya Nafisa tace. "Ko bata nan ku ƙarasa ku sami iyayenta ko kuma duk wani wanda zai iya baku bayani akanta, duk abinda ake ciki da kun isa you let me know, yanzu zan kira Daddy in gaya masa." Ta gyaɗa kanta kafin kiran ya katse, idanunta na tafiya kan abokin Ashraf ɗin dake danna wayarsa hankali a kwance, tsawon kwanaki kenan suna nemansa amma ba'a same shi ko a waya ba sai a yau da da wanin abokin Ashraf ɗin ya kira cewar gashi nan ya dawo daga Ondo, don haka ba shiri suka taho har wajen da aka kwatanta musu yana nan, kuma cikin sa'a suka same shi. Amma don rashin mutunci irin nasa bai fito ya same su ba sai da suka yi kusan awa guda suna jiransa, har su Ibrahim da Ahmad da suka je suka taho da police ɗin da aka kai report wajensu, sannan ne ya fito da uzurin cewar wasu abubuwan yake kammalawa da baza su iya jira ba. Kuma duk da irin tashin hankalin da yaji suna ciki da kuma ma babban labari na ɓatan ɗan mutum guda, bai nuna ko a jikinsa ba bayan Allah ya sawwake guda din da ya furta. Ta sani cewa shi kansa Ashraf ɗin yaji haushi amma bai nuna bane saboda abu suke nema daga wajensa dole sune a ƙasa, amma duk da haka ta fahimci cewa akwai wani abu ne da ya faru da babu wannan kalmar ta abota a yanzu tsakaninsu. Sai dai ba wannan ne a gabanta ba yanzu, a cikin kwanakin da suka gabata, zuciyarta ta mutu ta miƙe fiye da ƙirgan mai ƙirga, ƙarya ne ta iya kwatanta tashin hankalin da take ciki, tashi hankalin da sai da ya shafi kowa a gidan nasu gabaɗaya, ya zamana ba abinda ake yi banda fafutukar neman Mary ko ta wacce hanya amma basu same tan ba, hatta mahaifinta dake can ƙasar Romania yana aikinsa kullum sai yayi waya tsakaninsa dasu da kuma ƴansanda akan abinda ake ciki. Idanunta kaɗai idan ka kalla sune shaidar rashin baccin da kuma na abincin da take ciki. Ta rantse a ranta fiye da sau shurin masaki cewar Mary zata gwammace bata zo duniya ba idan har suka kama ta, tunaninta baya iya lissafa abinda ya kamata tasa ayi mata. Sun isa cikin unguwar ta sabon gari a lokacin da duhu ya riga yayi sosai, a lokacin kuma gabanta ya shiga faɗuwa cike da tsananin tsoro ganin irin cakuɗaɗɗun layikan da suke wucewa da kuma mutanen cikinsu, zata yi rantsuwa ba adadi cewa Mary ba zata taɓa rabarsu ba inda ta san daga waje irin wannan take fitowa, amma a haka ta zauna tana kula da ƴarta tsawon watanni bakwai. Kwatancen Bilal ya kai su har wai takurarren gidan da mutane ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, bata san lokacin da ta dunƙule ƙarshen mayafinta akan bakinta ba yayin da kwalla ta shiga fitowa daga idanunta da suka riga suka kaɗa, zuciyarta bata iya kwatanta mata cewa Hamida tana wannan wurin ko kaɗan. Ibrahim da Ahmad da suka fito daga motarsu bayan sun tsaya suka bada shawarar cewa ta tsaya su suka shiga ciki, amma jikinta na rawa ta girgiza musu kai, ruhinta zai bisu ciki ne ko da ta tsaya ɗin. Ashraf da Ahmad ne suka fara shigewa gaba sai Bilal da kuma Ahmad, ita tana daga bayansu sai kuma ƴansanda biyar dake rufa musu baya, warin iskar gidan ta fara shaƙa kafin ta fahimci girman da yake dashi daga ciki, ga tarin ƙofofi birjik daga kowanne gefe inda hayaniya ke fitowa kamar zata fasa kunne. Kuma ganin ƴan sandan yasa hayaniyar gidan ta ƙaru har da masu ihu suna shigewa ɗakunansu, a tsakar gidan su Ashraf da kuma ƴansandan suka shiga tambayar cewa Mary suke nema, kuma wasu ƙattin inyamurai da su kaɗai suka tsaya suka shaida musu cewar Maryn dake gidan sun fi mutum ashirin. Koina a jikin Rukayya kawai rawa yake yayin da take kallon ƙofofin ɗakunan da dukkan fatanta na duniya, da ƙyar da kwatance aka samu wani a cikinsu ya gane wadda suke nema, kuma kai tsaye suka shaida musu cewa kwana biyu da suka wuce Maryn tare da iyayenta suka kwashe kayansu tsaf! suka tafi garin su. Sai da ƙyar ƴan sandan nan suka samu mutanen nan suka fito musu da wani tsoho da akace ɗanuwansu ne. Kuma shima ganin ƴan sandan ya ruɗa shi, ya dinga rantsuwa bai san komai ba sai da yaga da gaske ana shirin tafiya dashi sannan yayi bayani cewar ya san yarinyar da ake neman, kuma har da ita a dalilin barin su Mary garin bayan ciwon mahaifiyarsu. Ruƙayya gabansa taje ta tsugunna a lokacin yayin da yake bayani da gurɓataciyar hausarsa. "Wani mutum ne anan yazo ya dauki yarinyar ya tafi dashi, kuma Mary yace ya bawa yarinya maganin bacci mutumin zai kamata, kuma the madam she's serving zai ce ta ɓatar da yarinya, ita bata san yadda zata yi ba, don haka sun kwashe kaya nasu sun tafi." "Shi mutumin da yazo ya tafi da yarinyar waye shi?" Wani daga cikin ɗansandan ya tambaya tsaye akansa. "Mary yace shine oga na inda babanshi Mr. Okafor yake aiki." "Ka san wajen aikin nasa?" Ya ɗago cike da tsoro yana kallon ɗan sandan. "Ka san wajen da baban nata yake aiki?" Wannan karon Ruƙayya ce ta tambaya, muryarta na rawa da dukkan fatan na cewar amsar da zai bayar ta kasance abinda take son ji, kuma cikin abinda zata iya kira da sa'a, sai ya daga kansa yace. "Eh ya sani, wajen inda ana..." Bai karasa ba ɗan sandan ya bashi umarnin tashi su tafi, jikinsa na rawa ya miƙe tsaye ya shige gaba, aka sanya shi a motar ƴan sandan bayan sun fita, suka fara yin gaba sannan su kuma suka shiga nasu motocin suka bi su. Wannan karon Ibrahim ya shigo motarsu ya zauna a wajen Bilal da shi ya koma motar Ahmad, tana ji kowannensu na waya, Ashraf da matarsa yana gaya mata inda suke, Ibrahim ɗin kuma da Daddy yana yi masa bayanin abinda ya faru. Fuskarta ta juya waje idanunta na bin fitulun kan titi ke haskawa akan gilashin da kuma fuskarta, hawaye take sharewa da gefen mayafinta yayin da hannyenta ke rawa kamar zuciyarta, bata iya hango yadda zata kasance idan har bata sami Hamida a wajen nan ba. Sun iso daidai gaban wani dogon gini mai ɗauke da gilasaivda kuma fitulu kamar rana, akwai manya-manyan rubutu a sama wanda bata iya karantawa ba saboda halin da take ciki da kuma ƙwallar da ta taru a idanunta. Ashraf da ya tsayar da motar ya juyo ya kalle ta, kuma ganin yadda take share hawaye yasa ya girgiza kansa yace. "Stay inside, bari muje mu gani." Da haka ya buɗe ƙofar motar ya fita, Ibrahim na bin bayansa. Sai kawai ta kifa kanta akan cinyoyinta ta shiga rera kukan da take kasancewa a cikinsa duk dare, gani take idan har ta rasa Hamida rayuwarta ta gama rushewa gaba ɗaya, ba lallai ne ta samu fatan da dashi take ganin zai sake gina rayuwarta ba. Don samun Ma'aruf shine ƙarshen fatanta yanzu a duniya, bata hango komai a gabanta sama dashi, wani gefe na zuciyarta na jin cewa zata iya hakura da Hamidar ma idan har rayuwa zata iya dawo mata da Ma'aruf ta wata hanyar, amma ta san daga shi har iyayenta babu mai sake kallonta idan babu yarinyar, don haka ba zata taɓa rasa ta ba. Wayarta tayi ƙara a lokacin daga gefenta, ta kalli screen ɗin tana karanta sunan Jawad da ya fito tar! akai, tun da ta barshi a hotel ɗin nan bata ƙara bi ta kansa ba, ya kira wayarta sau da yawa bata ɗaga ba, a jiya da yamma har gidansu yazo amma ta aika masa da saƙon ba zata iya fitowa ba, tana kallonsa ta tagar ɗakinta ya juya da motarsa ya fita. "Babe I'm really sorry, ki manta maganar da na gaya miki dan Allah, just talk to me!" Sakƙon message ɗinsa bayan katsewar kiran ya nuna akan wayar, sai kawai ta ɗauke kanta tana kallon waje, bata lissafa Jawad a cikin matsalolinta na rayuwa ko kaɗan. Ta kalli wajen daidai lokacin da idonta ya kai kan su Ashraf da ƴan sandan nan, magana suke da wasu mutane a ƙofar wajen basu shiga ciki ba, kuma ta cikin hasken fitulun wajen taga Ibrahim ya dafo kansa ta baya tare da riƙe ƙugunsa alamun wani abu ake gaya musu da ya sa shi mamaki don ta hango mutanen na magana. Ta hango Ashraf daga gefen tsohon da ya rako su yana sauraren mutumin kafin ya dunƙule hannunsa ɗaya akan bakinsa alamun nasa mamakin shima. Ba shiri ta buɗe handle ɗin motar ta fita, hasken fitulun wajen na shigar mata ido amma bata damu ba ta ratsa ta tsakanin sauran ƴan sandan da kuma Bilal ta isa gabansu, ta isa gabansu lokacin mutumin ke cigaba da cewa. "... Ai na gane wanda yake bayani, shine dai Ma'aruf ɗin manajan kamfanin nan, sai dai idan kuna da hanyar da zaku same shi a gida, amma bana jin ko ranar litinin zai shigo, don yau aka ɗaura aurensa na gaya maka!" Ya rufe bakinsa lokacin da ta cikin hasken fitulun wajen ƙwaƙwalwar Rukayya ta karanto mats manyan rubutun dake saman ginin... 'Bakori Enterprises' Kuma wayar hannunta da ta fara faɗuwa, ita ta juyo da hankalin kowa a wajen kafin su ankara da tata faɗuwarta har ƙasa! *** Daga Babi na gaba labarin FARAR WUTA zai fara insha Allah! #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA TARA ~~~~~ Let's go back to when we had not learn our names, when we introduced our souls, while our heart gasped for breaths. -Aliyu Jalal. * A cikin sabon gidan mutane sun fara raguwa sosai, ba kamar a ɗazu da koina yake a cike da mutane ba, Aunty Safiyya ta taho daga hanyar falo ta biyo wani ɗan dogon korido mai ɗauke da ɗakuna ta shigo ƙofar ɗakin dake gefe, a cikin ɗakin duk ƴan uwa ne na kurkusa sai kuma amaryar dake tsakiya kanta a sunkuye tana faman kukan da babu sauti sai hawaye kawai da take sharewa. Aunty Safiyan da ta shigo tace. "Na rasa yadda akayi aka manta da tsitsiyoyin nan wallahi, yanzu da ba sai a share gidan ba kafin mu tafi." "Aunty ai na zata sharar dare babu kyau." Ummi dake kokarin dora akwatuna can saman wardrobe din dakin tare dasu Momi ta fada tana juyowa. "Wannan ai kamawa tayi..." Cewar Aunty Ma'u. "Baki ga falon nan ba duk kasa ce wallahi, don bana ji akwai wanda ya shigo babu takalmi." "Ni maigidan ma nake ji, haka zai shigo yaga waje duk ƙura?" Ɗaya daga cikin matan Baban Kurna tace. "Da za'a iya tunda akwai kofa ta baya sai a shiga gidan a tambayo su wallahi. Mahaifiyarsu Ummi da itace zaune a gefen Amina rike da hannayenta ta girgiza kai tace. "A hakura kawai, gobe da safe insha Allah sai su Maryam su zo su kawo mata kawai, su taya ta sharar ma." Ta fada tana kallon Maryam din dake tsugunne a gaban Amina ta riko ɗaya hannunta. "Ɗan kunnayen nan naki suna cikin wata ƴar ƙaramar jaka pink, ina jin a cikin wata Ghana must go aka saka." Cewar Maryam din tana kallon idanun Aminan da duk yadda suka yi ja saboda kuka wannan kyallin na cikinsu na nan. Ta san ba zata amsa ba saboda haka ta cigaba da cewa. "Hijaban sallarki ma suna cikin wannan karamin akwatin na undies, Amma ce tace in sa miki anan." Sai ta gyada mata kai kawai tana ƙara share hawayenta lokacin da Aunty Safiyya ke tambayar su Ummi idan sun kwashe kayan cikin akwatunan kafin su dora su. "Duk mun zuba su a cikin wadrobe ɗin, na kayan kwalliyar nan ne da kuma wannan Ghana must go ɗin zamu bari a ƙasa. "Eh, ku barsu ta gyara ta kanta, sai ku zo mu tafi kuma don goma ta wuce." Jin haka yasa Fatima ta taho daga wajen su Ummin tana ƙarasowa gaban Amina, lokacin da Maryam ke cewa. "Idan zamu zo goben zamu zan taho da Hafsa insha Allah." Fatiman ta sunkuyo tace. "Amina litattafan nan naki ba'a ɗebo ba, sai dai daga baya ko Aminu ya kawo miki." Sai a lokacin ta ɗago da idanunta ta kalle su, me yasa ne suke ta yi mata zancen kaya bayan ba abinda ke gabanta kenan ba? Mantawa suka yi cewa tafiya zasu yi su barta? Su barta a wannan wajen da bata san makamar abinda zata fuskanta ba, ko Abdallah ta aura ai dai sun san cewa wannan lokacin mai ciwo ne a wajenta, balle kuma mutumin da bata san ya yake ba balle takamaimai halinsa. Aunty Ma'u ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta tace. "Sai hakuri Amina, kin ji dai duk nasihar da akayi miki daga can gida, sannan su ma iyayen mijin naki kinga yadda suka karɓe ki, sunce ƴa suka karba ba suruka ba tunda dama duk ɗaya ne, kuma kowa ya san halinki Amina, duk wanda ya sanki yabonki yake yi... Mutanen nan sune basu sanki ba, kuma yanzu ne mafarin zamanku, dan Allah ki ɗorar da halinki a wajensu Amina... Don wannan gaɓar itace mafi alkhairin rayuwarki, ki sa su zasu zo suna bamu labarin kyautatawarki..." Ba shiri Amina ta sake fashewa da wani sabon kukan da ya nemi mazauninsa a zuciyar duk wanda ke ɗakin, taji zuciyarta na sake karyewa da tausayin kanta, kalaman suna tuna mata da na Gwaggo Balkisa a dazu kafin tahowarsu, ɗakin Amma da suka cika aka kaita don ayi mata wannan fadan na al'ada, kuma sai da kowa ya gama nasa sannan ita Gwaggon ta kamo hannayenta duka biyu tace. "Amina kin sani cewa daga yau sabuwar rayuwa zaki fara wadda babu iyayenki bale kuma sauran ƴanuwanki a kusa, zaki zama ɓarin wani mutum daban da zai bukaci tsananin kulawarki, Kiyi amfani da hankalinki da kowa yake yabo ki zame masa mata kuma Uwa, ki kokarin zame masa komai a rayuwa ta duk wata hanyar da zaki iya. Ba abu ne mai wuya ba Amina, don maza banbancin su kadan ne dana yaro ƙanƙani, kulawarki kawai yake buƙata sai ki ganshi a tafin hannunki. Kar ki dauki kulafucin barin gida ki sa a ranki fiye da ƙima, shima nasa iyayen zai bari yazo ya zauna dake, banbancin kawai shi namiji ne da zai daure ke kuma mace ce, ki saki ranki ki saba da sabuwar rayuwar da zaki fuskanta don itace rayuwarki ta yanzu dama ta gaba. A kowanne aure akwai sirri Amina, ki riƙe sirrin gidanki ki riƙe sirrin sa, ki zauna lafiya kamar mahaifiyarki, kina ganinta dai shekaru fiye da ashirin kenan da muka kai ta daki amma daidai da rana guda bamu taba jin bakinta ba. Kiyi wa mijinki biyayya, ki girmama shi, idan kika yi haka kema kin girmama kanki. Mace mai wayo ita ke gina gidanta Amina, sakarya kuma da hannunta take rusa shi." Don haka a yanzu ma da Aunty Ma'u ta fara sai taji kukan da ta sha ɗazu ya sake dawo mata sabo. Fatima ta taho ta rungume ta daga tsaye tana gaya mata abinda kowa ke faɗa, cewa tayi haƙuri, kuma sai su Ummi ma suka karaso suna tayaa ta, tanajin yadda kukan bata ke jijijiga jikinsu kafin Aunty Safiyya tasa su suyi gaba. "Wannan shine dakin da muka kawo miki kaya, watakila zaki ga sauran biyun dake gefe sun fi shi kyau, amma kiyi zamanki a cikinsa Amina, don shine mutuncinki." Aunty Safiyya ta raɗa mata a kunne lokacin da kowa ke mata sallama, kuma tana ji tana gani dukkaninsu suka tafi, tayi niyyar tasowa suje ko wajen kofa ne amma mamansu Ummi ta hana, tace tayi zamanta kawai. Ta dade a zaune tana kallon hannyenta bayan tafiyar tasu, ji take yi kamar an saka ta a wani jikin ne da ba nata ba, an ce komai nisan jifa kasa zai faɗo, ta yarda da auren nan kamar wasa, zuciyarta na hango mata shi a can nesa sai gashi tun ba'a je koina ba har anyi an gama, kowa ya taka rawarsa ya matsa, an bar mata filin da tace zata iya yakin a cikinsa. Kamar wani yana kallonta da kyar ta ɗago idanunta tana karewa dakin kallo, kayan cikinsa dama ta riga ta sansu, har gadon a waya Aminu ta nuna mata don tare suka je shi da Baban wajen masu kayan katakon, labulen kuma duk a tsakar gidansu akayi ta dagawa ranar da su Aunty Safiyya suka siyo daga kasuwa, carpet din da aka shimfida a kasan gadon ma, a ɗakinsu aka jingine shi. Don haka ginin gidan da shine baƙo a wajenta take kallo, ɗakin kato ne yasha fenti da kuma tsarin fitulun da ba sai an gaya mata ba ta san masu tsada ne. Ta tuno yadda taji su Ummi nata yabon sauran bangaren gidan, ba shiri taji wani abu ya wuce ta makogwaronta, kowa ya sani cewar akwai dalilan da suka kawo ta wannan gidan, ba'a banza kamar ita zata sami irin wannan wajen ba, kowa ya sani cewa akwai wani abu daban a tare da auren nan, kawai kowa yayi shirun ne yana jiran ganin abinda zai biyo baya. Tafi minti goma tana tunane-tunanen abinda zai iya faruwa da kuma mafita kala-kala, amma duk abinda ta kamo sai ya suɓuce idan ta tuna cewar a yau zata yi ido biyu da mutumin da aka daura mata aure dashi, mutumin da ya riga yayi mata gargadin cewa kar ta yarda ta aure shi, zuciyarta ta sake matsewa kamar zata fashe zuwa wasu dubunnan ƙananan atoms. Da kyar ta cillar da komai a cikin kanta ta miƙe ta nufi toilet din dake manne a dakin, kuma sai da numfashinta ya tsaya sanda idonta ya kalli ciki, toilet ne da yasha adon wasu baƙaƙen marbles masu kyalli da santsi, anyi wasu hadaddun drawers a ciki da wani bakin katako da ya dace da kalar marbles din, ta ja numfashi a hankali sannan tayi addu'a ta taka kafarta ciki a hankali tana jin sanyinsa na ratsa ta. A gaban katon mudubin ciki ta tsaya tana kallon yadda idanunta suka yi ja dama yadda fuskarta ta dan kumbura, sai kawai ta bude fanfon kasan sa tayi alwalarta, ta haɗa da wanke wuyanta dama rabin bayanta, kuma dadin ruwan yasa wata zuciyar tace mata taje ta ɗauko sabulu a akwatin cosmetics ɗin nan tayi wanka gabaɗaya amma ta girgiza kanta. Ba yau ba, ba yanzu ba. A akwatin undies ɗin nan da Maryam tace ta dauko hijabinta guda daya, ta dawo kan carpet din dakin tayi sallah raka'a biyu, bayan ta idar ta dago da hannayenta da niyyar addu'a amma sai ta rasa ma me zata roƙa, saboda haka sai kawai ta dunƙule jikinta waje ɗaya ta ɗora kanta daga gefen gadon tayi shiru. Shirun da a cikinsa taji lokacin da aka buɗe kofar dakin. ** Karfe sha ɗaya daidai ta iso da Ma'aruf ƙofar gidan, ginin ya tsaya a gabansa kamar wani tsauni, babu wanda zai ce ma a cikin gidansu aka fitar dashi, don gate dinsa yayi gefe da yawa ta daya bangaren. Ya lashe lebbensa na kasa daya bushe yana gayawa zuciyarsa cewa sun zo matakin da suke jira, sakon ya isa kuma maimakon ya dawo cike da kwarin gwiwa sai ya dawo da wani raunin da kalaman da Ishaq ya gaya masa a dazu suka yi sanadiyarsa. "Ka sani cewa wannan ba labari bane Ma'aruf, ba labari ne da zaka rubuta a yadda kake so kuma har ka kai ƙarshe da son zuciyarka ba. Na fahimci dukkan abinda ka faɗa da kuma dalilin da yasa ka dawo ka yarda da auren, amma hakan baya yana nufin cewa ka tsallakewa abinda zai iya faruwa ne. Kar ka manta a baya ciwonka ko matakin HypoMania bai kai ba abubuwan da suka faru suka faru, yanzu kana stage na karshe Ma'aruf, kai da kanka kana tsoron wannan matakin, ba sai ka gaya min ba, a idanunka kawai nake gane cewar kaima kana tsoron faruwar wani abu kamar yadda kayi tunani a farko, tunda ni da kai mun sani cewa ba lallai ne mu iya binne komai ba a wannan karon..." Ya sake lashe leɓɓensa yana jin yadda har a yanzu tasirin kalaman ke yawo a cikin kansa, gargadi Ishaq ɗin yake yi masa ya sani, gargadin da shima ya riga yayi wa kansa duk da cewa bai tsara komai game da auren ba bayan cewar yana son samun bayanansa daga yarinyar, zai tafi da abinda lokaci ya bashi ne kawai yana kuma ƙoƙarin kiyayewa dukkan abinda gaban zata haifar, haka ya gayawa Ishaq, ya kara gaya masa cewar shi yanzu abubuwan dake gavansa ma Allah yayi yawa dasu, sai yaga komai ya lafa masa tukunna ma zai maida hankali kan yarinyar. Ta cikin glass ɗin motar ya hango ƙofar gate ɗin shiga wajen su Mami dake can gefe, babu kowa a wajen alamun da gaske dare yayi don ya sani cewar an sha hidimar mutane tunda yau ne rana ta karshe a bikin. Wayarsa ya jawo ya kira Mamin, bugu daya biyu, kuwa ta dauka tunda dama jiran isowar tasa take, har a hanya ta kira shi taji idan ya taho. "Ma'aruf..." Muryarta dake shaida dimbin gajiya ta kira shi da sunansa. "Mami na iso amma ba zan shigo ciki ba." Sai da ta ɗanyi shiru kafin muryarta tace. "Kai da mutane ne?" Ya girgiza kansa. "Ko Ishaq ma nace yayi zaman sa kawai. I'm alone." "Tohm shikenan da safe na ganka, dama bana son kayi dare sosai baka iso bane, don tun wajen Isha'i suka ƙawo ta, anyi muku addu'o'i masu tarin yawa, hatta ƴan uwan Hajiya Maimuna da basu so abin da farko ba sun yaba sosai da ita da kuma ƴanuwanta Ma'aruf, Ina fatan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa a zaman da zaku yi, Allah ya baka ikon sauke sabon nauyin da ya hau kanka." Bai san lokacin da ya haɗiye wani abu a makogwaron sa ba kafin ya amsa a hankali, don ji yayi kamar itama tana tuna masa da abinda Ishaq ya faɗa ne. "Insha Allah Mami. Nagode." Yaji kamar ta gyada kanta kafin ta sake cewa. "Na san da wuya idan kaci wani abun, ga abinci nan ma nasa Samira ta tanadar maka tun dazu, a miƙo maka ne?" Ya girgiza kansa tun kafin ma ta ƙarasa, don baya tunanin a yanzu ko ruwa zai iya sha, tarin abubuwan da ƙwaƙwalwar sa da kuma zuciyarsa ke rabawa basu da adadin da har zai sami nutsuwa ta cikinsu. Saboda haka sai kawai ya canja zancen da cewar. "Na zata ma kowa yayi bacci Mami." "Baccin mai gaskiya? Yanzun nan fa suka dawo daga kai sauran amaren, ai gidan nan yana nan kamar rana don baka shigo daga ciki bane, kuma naku ɓangaren ai yasha dab-dalarsa, sai da kayi haƙuri da abinda zaka gani." Wani guntun murmushi da bai san dalilin sa baya suɓuce a gefen fuskarsa, don shi a yanzu baya son ganin yarinyar baya jin akwai abinda ya dame shi na harkar auren, sai kawai ya zaro hannunsa daga cikin gashin nasa yana bude kofar motar dashi sannan yace. "Shikenan Allah ya bamu alkhairi, Allah ya huta gajiya, ta amsa kafin ya kashe wayar. Ya tsaya daga wajen yana kallon ginin gidan kafin ya sake komawa kan wayarsa ya danna wata number, bugu ɗaya biyu matar dake ɗaya layin ta dauka, kuma bayan sun gaisa ta tabbatar masa da cewar Hamida tayi bacci sannan ya katse wayar. Inda ya kira ɗin, wani Creche ne kamar asibiti inda ake bawa yara kulawa ta musamman, na wasu ƴan Turkey ne musulmai, amma akwai hausawa a cikin ma'aikatan nasu, asibitin da aka kwantar da Hamidan ne da farko suka bashi shawarar ya kawo ta wajen, kuma sai hakan yazo daidai da cewar bai shirya kaita gida a lokacin da ake hidimar bikin nan ba. Ranar farko da suka je, tayi rigimar cewa ba zata zauna, amma cikin ƙwarewar aikinsu da kuma tarin abubuwan wajen dake kama zuciyar yaro, sai rigimar tata bata je ko'ina ba. A iya kwanakin nan yana zuwa kullum ya ganta wanda hakan yasa yayi sabo da ita sosai don har ta fara sakewa dashi tana amsa duk ƴan ƙananan tambayoyin da yake mata, da farko ne duk maganar da zai yi mata sai dai ta kalle shi kawai, sai bayan barinsu asibitin ne da ya kawo ta nan sannan ta fara yi masa magana, kuma ya fahimci tana da maganar sosai, kawai bata gama sabawa dashi bane har yanzu, amma ya san aƙalla suna making progress din da za'a zo gabar da zata fahimci cewa shi mahaifinta ne. Ya sake kallon gidan, babu maigadi don haka shi ya shiga da motar, sannan ya sake rufe gate din ya dawo, ƙafafunsa suka taka kan barandar gidan sannan ya tura ƙofar falon ya shiga a hankali. Hasken fitulun ɗakin ya shiga idanunsa tare da hotunan kayan da suke ciki, daga kujeru labulaye dama carpet ɗin cikin komai kalar Army green ne da kuma brown, babu wajen dining don haka kofofin korido biyu ne kawai da ya san ɗaya ta kitchen ce ɗaya kuma ta hanyar ɗakuna, sai kawai ya juya a hankali ya rufe kofar falon. Iskar da akeyi a waje mai zafi ce, yaji ta bayan ya fito daga Acn motarsa, amma a yanzu da ya shigo gidan yaga yadda labulayen falon ke dagawa sai yaji kamar ba irinsu ɗaya da ta wajen ba. A hankali ya zame takalmansa daga kafarsa sannan yayi gaba, ya kuwa ji ƙurar da Mamin ke fada amma bai damu ba, ya shiga hanyar koridon a lokacin da yake jin wani abu kamar bugun zuciyarsa na ƙoƙarin canjawa. Ƙofofi uku ne a ciki, kuma bai buɗa kowacce ba don guda ɗayan dake gefe da kuma ta can karshe ta kasan kofofinsu ya kula duk fitulunsu a kashe suke, ta farko daga gefen daman sa ce kawai hasken cikinta ya saje da na cikin koridon. Don haka kai tsaye ya ƙarasa gare ta ya ɗora hannunsa akan mariƙinta, sannan ya buɗe ta a hankali ba tare da tayi wata ƙara ba, kuma babu wani hijabi idanunsa suka sauka akan matar da kowa ke kira da tasa, ɗan karamin frame ɗin jikinta na naɗe a gefen gadon ɗakin, ta jingina kanta da gefen gadon idanunta a rufe, rabin fuskarta na shigewa cikin gadon yayin da hasken fitilar ɓangaren ɗakin ya haske ɗaya gefen fuskar tata. Hijabin dake jikinta ne ya shaida masa cewa sallah tayi, kuma kafin ya iya sake wani tunanin ta buɗe idanuwanta duka biyun ta kalle shi. Bai san me ya zata ba, bai san yadda yayi tunanin zai zo ya ganta ba, bai taɓa ma hasko ta a cikin kansa ba balle ya kintaci yanayinta, amma a lokaci guda yaji wani abu ya balle daga cikin zuciyarsa ganin ƙanƙantar ta, don duk a lissafinsa irin Ruƙayya zai gani, amma wannan ƙarama ce sosai, idanunta are so young haka ma jikinta ƙarami ne, yawun da ya sake haɗiyewa yana kallonta yasa wannan karon Adam's Apple dinsa motsawa sama da ƙasa. Kuma a lokaci guda kallon dake cikin idanunta ya canja zuwa wani abu kamar tsoro, yaga ta mike tsaye da sauri rike da hijabinta sannan ƙafafunta suka yi taku biyu baya, a yanzu ya tabbatar tsoratar tayi. * Lokacin da ta mike tsaye tana kallonsa, zuciyarta ta shiga tseran kilomitoci a ƙirjinta, yayin da take jin ƙafafunta na rawa kamar ma zasu iya daukanta ba, don haka ba shiri zuciyar tata ta shiga ambaton kalaman Innalillahi har zuwa ƙarshe yayin da take cigaba kallonsa. Bata yi tunanin kawai bude ido zata yi ta ganshi tsaye a gabanta ba, bata ma yi tunanin haka yake ba, yadda take hango shi a tunaninta ya zarta hakan, dogo ne sosai ɗan siriri amma kuma mai cikar halitta, ba fari bane ko kadan haka nan ba baki bane, idanunsa na kallonta da wani yanayi da suke lumshewa, fuskarsa fayau yana tsaye yana kallonta daga bakin ƙofar, kayan jikinsa kalar ruwan toka ne mai irin sealed dinkin nan, babu ko hula akansa sai gashin kansa mai yawa da ya taru. Zuciyarta ta cigaba da fat, fat, tana kallonsa, so take yi ta tantance idan har shi ɗin ne ma ko kuwa aljani, tunda bata ko ji sallamarsa ba, sai kuma wata zuciyar tace mata ta yaya mutumin dake shirin fara nuna mata wutar da ta kawo kanta zai fara da yi mata sallama? Taji kamar ta tafi ta shige toilet din dakin kawai ta kulle kanta, amma wani bangaren zuciyarta ya ture hakan, yana gaya mata cewa ya kamata ta jajirce ta fara ganin abinda zai yi tukunna, don ta gayawa zuciyarta zata iya yafi cikin carbi, kuma dukkan kalaman da ta faɗawa mahaifinta dama kowa suna nan a cikin kanta, don haka bai kamata ta fara karaya tun yanzu ba. Kuma ga mamakinta sai abinda take jira din ya faru. "Assalamu alaikum." Muryarsa mai zurfi ce da a lokaci guda ta daɗa hargitsa tunaninta, tasa numfashinta katsewa a maƙogwaronta. Ma'aruf ya sake lura cewa a tsorace take, don bayan yanayin fuskarta yana iya ganin yadda ta damke hijabin jikinta da duka hannayenta biyu tana cigaba da kallonsa, bata amsa sallamar ba, kamar ma bata ji yayi ba, kamar jira kawai take yi yayi wani abu ta ɓace daga dakin. Ya fitar da numfashin daga ƙofofin hancinsa, me ya zata dama ga yarinyar da yayi wa wannan barazanar, don haka ya sani cewar yanzu a farko dole ne yayi kokarin kore wannan tsoron nata game dashi, yasa ta fahimci cewa a yanzu ba abinda ke gabansa game da ita kenan ba. "Ki kwantar da hankalinki, na shigo ne don kawai mu gaisa ki san cewar ba ke kaɗai ce a gidan ba, idan akwai wani abu da kike bukata kuma zaki iya gaya min..." Kalaman suka daki zuciyar Amina ta yadda numfashinta ya tsaya cak! Wani abu a cikin kanta ya gaya mata cewar hatta lokaci sai da yayi shawara sau biyu kafin ya motsa. Kallonsa kawai take yi da tsananin mamakin da ta kasa auna shi a mizanin hankalinta. Ya fahimci ba zata yi magana ba don haka ta ga ya sake riƙe hannun kofar sannan ya furta mata. "Sai da safe." Ya rufe ƙofar daidai lokacin da kafafunta suka kasa ɗaukarta gabaɗaya. ** Hasken safiyar dake shigowa ta liner labulen ne ya tada ita, ta kifta idanunta tana kallon yadda wajen yayi mata kyau a ido, yadda hasken ya haɗe da kalar labulen dama liner yana ratsowa ta cikinsu, amma duk da kyan nasa sai taji kewar gida ta kamata, taji tana kewar ɗakinsu har ma da katifarta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe da taje wani wajen ta kwana ba tun bayan data gama makarantar Boarding fin da tayi. Ta rufe idanunta ta buɗe tana sake kallon windon wanda tsawon yadda take ganinsa yasa ta tuna cewa a ƙasa take, akan carpet din nan, don anan bacci ya dauke ta bayan zuciyarta ta cika da sake-saken al'amarin da ta kasa ganewa. Ba irin tunanin da bata yi ba da abinda bai zo kanta ba a jiyan nan, amma daga ƙarshe da ta tattara duk lissafinta da kuma abubuwan da aka gaya mata dama abinda ta shirya, sai taga cewar bata da wani zaɓi illa ta fara fahimtar manufarsa akanta kafin ta yanke hukuncin da zata iya kare kanta dashi. Ta miƙe zaune a hankali tana son daidaita ganinta, a sannan ne ƙwaƙwalwarta ta tuna mata cewar bata yi sallar asuba har gari ya waye haka, ƴar wayarta dake gefe ta jawo tana tunanin yadda akayi alarm ɗinta bai tashe ta ba amma sai ta tarar ta mutu saboda ba caji, don haka ta mike da sauri ta nufi bandakin a lokacin da idanunta suka sake kallon ƙofar dakin ta tabbatar muƙullin data kulle ta dashi yana jiki har yanzu kafin ta shiga ciki. Bayan ta idar da sallar ta daɗe tana addu'ar neman gafara da kuma ƙwarin gwiwar tunkarar duk abinda ke gabanta kafin ta mike, a cikin akwatin kayan kwalliyar nan ta samo sabulu, ta shiga tayi wanka, kuma duk da cewar komai sabo ne a wajenta bata sha wahalar gane kan fanfunan dake ciki ba tayi wankan ta fito. Ta dawo cikin ɗakin dake ƙara tuna mata cewar rayuwarta ta canja da gaske, don har yanzu yanayin da take ciki ba zata iya fassarashi ba, aayƙin da take ji daya ne kawai na cewar ƴan gidansu zasu zo, don haka da ƙyar ta ture duk wani tunani dake ranta ta shirya cikin wata doguwar rigar da hannunta ya fara kaiwa a cikin kayan dasu Ummi suka jera mata jiya, bata ɗaura ɗankwalin ba sai kawai ta yafa shi akanta. Ta kalli kanta a mudubin ɗakin tana ganin yadda idanunta suka fara washewa da kukan da tasha a jiya kafin tasa duka hannayenta tana gyara zaman ɗankwalin akanta, siraran awarwarayen da har yanzu ke hannunta suka shiga rawa suna tuna mata da zamansu, don haka tayi saurin cire su gabaɗaya ta ajiye akan mudubin sannan ta juya ta kalli kofar dakin. Kai tsaye ta ture komai a ranta ta nufi kofar ta buɗe ta, korido ne mai dan tsawo dake dauke da ƙofofin ɗakuna guda uku, ta sani cewa dole a daya daga cikin dakunan ya kwana tunda yace mata yana nan, don haka bata ko yi gigin bude kowacce ba kafafunta suka taka suka fita zuwa falo, anan ne, zuciyarta ta narke da kowanne abu na cikinsa dake shaida haɗuwarsu tun daga nesan da take, komai yana haɗewa cikin kalar ɗanuwansa cikin wani simple ado daya dace da wurin. Ta jinjina kai a hankali kafin ƙafarta ta tafi zuwa daya korido ɗin anan, tana jin yadda fatarta ke sulalewa akan santsin wajen duk da ƙurar data lura akwai, kofar wani katon kitchen anan da komai na cikinsa ash ne da kuma fari, akwai store mai ɗan girma data buɗa ta tarar da kayanta fal a ciki, wasu ma duk a cikin buhu suke ba'a buɗe ba. Ta dade tsaye tana kallon kayan da kuma tsarin drawers din kitchen din kafin ta hango wats kofa a can gefen fridge, taje ta bude ta, hanya ce mai dan fadi dake zagayawa kowanne bangare na gidan, inda daga can jikin katangar kuma ta hango wata kofa data tabbatar ta nan ne ake shiga cikin gidansu. Ta rufe kofar ta dawo tana sake komawa store din nan don ganin kayanta, tsji wani abu kamar magana amma bata tabbatar ba ta cigaba da duba kayan. A lokacin ne kuma ta jiyo muryarsa, kamar irin ruwan saman dake sauka a lokaci guda tana ƙarasowa hanyar kitchen ɗin, ba shiri hannayenta suka nemi hannun kifar store ɗin amma kafin ta iya rufe ta gabadaya, ya karaso don hannun nata ya tsaya cak tare da numfashinta, idanunta suka hango mata shi ta zirin ƙofar da bai gama rufuwa ba, kuma a lokaci guda taji zuciyarta tayi kuli-kulin kubra ta faɗo daga wata sama mai nisa. Ashe jiya bata lura da tsawonsa sosai ba, a yanzu daya canja cikin wani yadi kalar sararin samaniya da irin ɗinkin rigar da bai kai gwiwa ba, bata jin a cikin abokan Aminu gabadaya data sani akwai wanda zata iya kwatanta shi tare dashi. Ta hadiye yawu tana kallon yadda idanunsa ke lumshewa da sauraren abinda ake gaya masa ta cikin wayar kafin yayi magana. "Me kace?" Muryarsa a hankali ta fito, da wani irin amon da yasa jikinta girgizawa, numfashinta yana katsewa ba gaira ba dalili. Me yazo yi ne ma a kitchen din? Ta ga ya girgiza kansa sannan ya zura hannayensa cikin gashin kansa yana motsa su, a lokacin ne kuma iska ta buso mata da ƙamshin turarensa, wani abu kamar ƙamshin musk ko mint, ko kuma meye hancin nata ya jiyo mata, sai kawai ta juyar da kanta gefe yayin da muryarsa ta sake fitowa. "That issue aside Faruk, ba yanzu zamu neme shi ba, let's give him atleast two weeks to settle down, (mu bashi kamar sati biyu da zai huta) babu wuya zamu kama shi a sannan. Yanzu let's just focus akan waɗannan mutanen, I have somewhere to be now amma zan kira Martha ta min sending duk wani back-up da muke dashi akansu, zuwa yamma we decide where to meet sai ka kawo naka mu ga me zamu fitar." Murza ƴan yatsunta kawai Amina ke yi tana fatan ya juya ya fita, amma ga mamakinta sai kawai taji wata muryar mace ta taho tana faɗin. "Yaya baka ganta bane?" Kuma kafin ƙwaƙwalwar ta ta gama lissafawa, wata budurwa ta shigo cikin kitchen ɗin hannunta dauke da wani katon food flask, doguwar riga ce a jikinta shade din albasa (onion color) da wani dan karamin mayafi data yafa a sama maroon colour. "Bata nan kitchen ɗin?" Ta sake tambaya tana ƙarasowa ciki fuskarta ɗauke da murmushi, a lokaci guda taji wani abu ya ratsa ta har tafin kafa, don babu wata kwana-kwana ta gane ƙannensa ne suka zo, kuma shigowar sa kitchen ɗin ita yake nema. Taga yadda hannayensa ke motsawa a cikin gashin nasa alamar bai san me zai ce ba lokacin da yarinyar ta tafi tana ajiye food flask ɗin can kusa da gas cooker. Sai kawai tayi karfin halin ɗauko wani jug a gefe sannan ta buɗe ƙofar store ɗin ta fito, zuciyarta na gaya mata ai tunda a yanzu ƙirgen ya tashi daga su biyu ta tsira. "Sannu da zuwa." Muryarta tasa duka su biyun juyowa suna kallonta, yarinyar ta washe baki cikin fara'a sannan ta taho da sauri ta rungume ta. "Ashe kina ciki, Barka da safiya." Sai da zuciyarta ta buga a kirjinta saboda mamaki, mamakin da ta daure cikin nata murmushin itama tana rungume ta. "Sunana Samira, tare muke da Surayya da Munaya suna falo, fatan kin tashi lafiya?" Ta faɗa bayan ta janye daga jikinta, sai ta ɗaga kai da nata murmushin mai fadi ta amsa da. "Lafiya kalau, nagode sosai." A lokacin ne kuma idonta ya kai kansa, ta san kallonta yake tun da ta fito don tana jin tasirin yadda idanun nasa ke shiga jikinta, gabanta ya faɗi sakamakon haɗa idanun da suka yi, kallon da yake mata mai cike da nazari ne, kamar yana saka scanner cikin idonsa yana son tantance ta. Kuma a lokacin ne babban al'amarin safiyar ya faru, bakinsa ya motsa da wani guntun murmushi yana rufe idanunsa ya buɗe su akanta, kamar ma ƙifta mata idanun yayi, abinda kafin ta gama tantacewa ya juya ya bar kitchen ɗin. A kusa da kafafunta taji cikinta ya faɗi gabaɗayansa har ƙasa tsabar tsurewa da kuma mamaki, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kafin muryar Samirah ta cigaba da magana cikin tunaninta, sai ta hango kanta ta tsugunna tana ƙoƙarin tattara jikinta waje ɗaya kafin ta iya fahimtar me take cewa. "Abinci muka kawo muku kafin mu fara zagayen gidan sauran amaren, gamu nan da kaya fal cikin mota kowacce tayi mantuwarta... Na san kema kinyi taki ko?" Bata gama daidaita tunaninta ba, don haka bata san sanda ta ɗaga mata kai ba tace. "Ina tashi nima naga na manta chager wayata." "Ai sai a hankali ma zaki yi ta neman wasu abubuwan, Ya Shukra har da system ɗinta gabadaya ta manta kuma project ɗin masters take yi..." Ta gyada kai tana ƙoƙarin murmushi sanda wata ta ƙaraso cikin kitchen ɗin itama, watakila itace zasu yi sa'anni ɗaya ko kuma ace ta fita da kadan, tana da glasses wanda kana gani ka san medicated ne, ita kuma bakar abaya ce a jikinta wadda ta fito da ɗan hasken fatarta don ita ba fara ce sosai kamar Samiran ba, zata iya jera su layi ɗaya da yayan nasu. "Ashe kina nan matar Yaya..." Ta fada da nata murmushin itama tana karasowa kuma ga mamakin Amina itama sai kawai ta rungume ta tana fadin. "Oyoyo, we welcome you into the Family dear, jiya mutane basu bar mu mun ganki ba." A yanzu ƙwaƙwalwar Amina kwancewa tayi gabadaya, don ita ko a gyangyadi bata taba kawowa haka abubuwa zasu kasance ba, ko jiya sai da su Aunty Ma'u suka gaya mata cewa tayi taka-tsan tsan da ƴanuwansa. "Ƴan gayu ne na karshe Amina, kija jikin ki ki tsira da mutuncinki..." Haka Aunty Ma'un ta raɗa mata a kunne. To me yasa ne komai yake faruwa saɓanin tunaninta ne? Ko dai akwai wani abu da ba daidai yake tafiya bane? "Sunana Munaya.." Ta kara faɗa tana miko mata hannu, sai tayi karfin halin mika nata tana murmushi itama. "Yanzu zaki ganta kamar normal mutum amma idan kika tabo wajen karatu zaki fara tunanin aljana ce." Samirah ta faɗa tana kallonta. Sai kawai ta girgiza kanta. "Yarinyar nan ta raina ni da yawa, kar ki yarda da ita." "Wallahi da gaske nake Aunty Amina idan kina da ƴanuwa a Buk ki tambaye su kowa zai ce miki ya san GB (Genius Brain) haka suke ce mata, irin ƙwaƙwalwar su ɗaya da Yaya." Munaya ta girgiza kanta tana murmushi. "Astagfirullah, Allah ka tsare ni daga sharrin yarinyar nan, zo muje ku gaisa da Surayya, tana can tana ta aikin pressing waya." Da haka Munayan taja hannunta suka yi hanyar fita, Samurah ta biyo bayan su. A falon wadda suka kira da Surayya na zaune kan kujera mai zaman mutum ɗaya tana ta faman danna wayar hannunta, daga ƙasa kuma wasu ƴan mata biyu ne su ma da kallo daya zaka yi musu ka san ƴan aiki ne, gabansau dauke da wasu trays din dake dauke da food flask har hudu da kuma jug na lemo shima kala biyu, alamu su suka shigo dashi daga motar da Samirah tace suke. Kuma da shigowarsu Surayyan da zata ce sun yi sa'anni da Munaya ta dago da nata murmushin itama sannan ta ajiye wayar ta taho ta rungume ta, a yanzu Amina taji kamar ta saba ne ma da yanayin gaisuwar tasu. "Na san ma wannan mai bakin ta gaya miki sunana koh?" Ta tambaya tana kallon Samirah da tayi wajen ƴan aikin nan tana gaya musu akwai wata baƙar keda da badu shigo da ita ba. "Nima tun kafin in shiga ta gabatar dani ai." Cewar Munaya tana neman waje kan daya daga cikin kujerun. Amina ta daga kai tana murmushi. "Ta fada min, naji dadin ganin ki kuma." "Haba dai godiyar tamu ce ai, na san na samu wajen zuwa idan Mami ta matsa min da zancen waya, da fatan dai ba zaki damu ba idan kina ganina a compound din gidan nan." "You dey mad? Kike fada a gaban yarinyar nan? Kema kin san kamar Mamin taji ne ai." Cewar Munaya tana dariya, Surayya ta kalli Samiran dake tsaye tana jinsu. "Ta gaya mata mana, itama ai tana da nata secret din a wajena." "Ba dai zancen wannan cake pack din Ya Salma bane, wlhy sai inyi confessing in fada, tunda idan nayi cake din ai har da Mamin ake ci ace yayi dadi." "What? Kayan Salman kika dauka? Amma bata sani ba har yanzu ko?" Cewar Munaya. Surayya ta koma kan kujera tana sake ɗaukar wayarta. "Ki bari kawai, kuma wallahi guda daya ne a cikin kayanta, ranar da ta nema ta rasa, inaga Yaya Ishaq za'a kira yayi aikinsa a gidan nan." Suka kyalkyale da dariya gabadayansu yayin da Amina ke tsaye har yanzu da jug din nan data dauko a hannunta tana taya su da murmushi. A lokacin ɗaya yarinyar nan ta dawo daga waje. Samirah ta karbi kedar tana miko mata tace. "Gashi Aunty Amina, cupcakes ne na san zaki iya yin baƙi a cikin satin nan, wadannan kuma abinci ne breakfast da Dinner, naga yayan ma ya fita, flask din da na kai Kitchen kuma miya ce a ciki, murfin suka balla yanzun nan da safe shi yasa na riƙo shi kar ta zube." Wannan karon Amina ta tabbata mamakin da take ciki ta kai ta har wuya tana shirin nutsewa. "Kar ki wani damu idan yarinyar nan ce ina jin sai kin dinga korarta daga gidan nan akan abinci..." Kafin Munayan ta karasa fada wayarta tayi kara. Sai ta miƙe tana cewa... "Ya Shukra ce, kuzo mu tafi kafin ta fara mitar nan tata." Surayya ta mike kuma ga mamakin Amina sai suka zo suka sake rungume ta daya bayan daya suna gaya mata cewa in suka dawo zasu shigo sai suje cikin tare ta gaida su Mami. Itama ta rako su har kofa tana fadin su gaishe su. Bayan sun fita, ta tsaya daga barandar falon tana kallon compound din gudan da yasha wasu interlocks masu ƙyalli, da kuma shukokin wasu kananan bishiyu a jikin katangar da basu fara girma sosai ba. Ji tayi zuciyarta ta washe da wani abu da baza ta iya fassara shi ba, mamaki na yawo akanta har yanzu na yadda abubuwa ke canjawa daga zaton ta, kirkinsu yasa taji sun burge ta sosai yadda basu ɗauki kansu wani abu ba, taji zuciyarta na dokin ta saba dasu fiye da haka, kafin ta juyo ta dawo tana rufe kofar ɗakin, idonta ya kai kan tarin flasks din nan tana tunanin yadda zata yi da abincin, ko da yake ba ita kaɗai suka kawowa ba har dashi ta sani. Zuciyarta ta buga da ta tuno cewar zai sake dawowa gidan ya same ta, ta tuno kallon da yayi mata har da murmushi da yadda taji a lokacin tana kasa tantance tsoro ne ko akasin sa... Ashe dukkan abubuwan da take hangowa da sauki sun sha banban da tunaninta... Kwankwasa kofar da akayi ya katse tunaninta, ta tafi da sauri ta bude tana fatan su Maryam din da take jira ne, su din kuwa... Har da Hafsa dasu Mimi da Fatima da wasu daga cikin ƴaƴan Baban kurna, su takwas, sun riko wasu sauran tarkacenta da tsintsiyoyin nan... Ranta ya karasa yin fari ƙal ta hau rungume su daya bayan daya tana murna, rungume sun da bata san tayi ba sai da taji Fatima na cewa. "A ina kika koyo wannan sabuwar gaisuwar kuma?" Ita kaɗai ta cije lebbenta tana murmushi. ** A cikin ɗakin Hajiya Kilishi, ta kalli kawarta Salamatu tana girgiza kai. "Banbanci na dake kenan, bana faɗuwa na hakura, a sannu nake bin abu ina gutsira har in kai ga ci, kuma nasha gaya miki hakurin da kika kasa a tare da Shamsu (mijinta) kenan. Shi yasa har rayuwa ta kawo ki wannan gaɓar." Hajiya Salamatun ta girgiza kanta itama. "Gaɓar da nake cin duniya ta da tsinke ba, kar ki kawo wannan zancen kuma bayan mun gama na Saratu, mu tattauna abinda ya kawo ni, Ya zaki yi da al'amarin ƴar tasa?" Hajiya kilishi ta kalle ta sosai tace. "Na gaya miki ai, saboda ban samu nasara akanta a asibitin nan ba hakan baya nufin na hakura, ai na rantse sai naga bayanta don ko wajen uw*rta ba zan bari ta koma ba tunda har zata fara zame min ƙalubale tun daga yanzu. Babu wanda ya isa ya shiga zuciyar Ma'aruf da tasirin da yafi nawa Salamatu kema kin sani. Saboda haka matsalolin nawa zan hade guri guda, bayan tsinannun asibitin nan da suka hana ni kwana a wajenta sun sallame ta, wani Creche wai ya kaita a hanyar Bompai saboda kin san muna cikin sha'anin bikin nan. Saboda haka a yanzu da komai ya lafa zan saka ne ya dawo da yarinyar wajen ita Aminar, ta yadda zan aiwatar da manufata hankali a kwance. Kin san dai dalilin da yasa na shiga na fita ya auri yarinyar nan, saboda daga ita har iyayenta zan iya juya su sannan an tabbatar min tana da sanyi halin da al'ummar gidan nan kaf zasu karbe ta cikin ƙankanin lokaci, na gaya miki tana da irin fuskata Salamatu, fuskar da zata daɗe tana yin abun da ba mai iya ɗora zarginsa akanta." Hajiya Salamatu ta kalle ta tsawon wasu sakanni tana nazarin maganganunta kafin ta girgiza kanta tace. "Kin san nice mai gano miki da matsalar dake ba kya taba hangenta Kilishi, jiya da suka kawo yarinyar nan banga fuskarta ba, amma daga yanayin jikinta kawai na san ƙarama ce, kuma idan har halinta ne zai sa jama'ar gidan nan su sota, ba kya tunanin zuciyar yaron ma zata iya ta karkata kanta?" Hajiya Kilishi ta gyaɗa kai tana murmushi. "Daɗina dake ragon azanci Salamatu, ai dama haka nake so, in ba haka ba don me nake ta koɗa ta da ƴanuwanta a wajensa, so nake ta siye min zuciyar kowa har shi ɗin kamar yadda nima nayi, ta yadda a nutse zan sa ta dinga kai min saƙona kowacce kusurwa babu mai zarginta." Hajiya Salamatu ta sake girgiza kanta. "Baki gane ba Kilishi, abinda nake nufi shine idan har ta siye zuciyar Ma'aruf da darajar da zata fi taki nauyi fa? Idan har yayi nisa a duniyarta ta yadda ba zai iya jiyo ko da muryarki ba fa?" Wannan karon dariyar da Kilishi tayi sai da ta ratsa kowanne bango a dakin ta kuma fita ta windon ɗakin da yake a rufe, tabi iska zuwa nisan da ƙarfin amonta zai iya kaiwa, hatta jikinta sai da ya girgiza saboda nauyin dariyar, kafin ta kalle ta sosai tace. "Ita kanta yarinyar ai na shirya mata Salamatu, sau nawa zan gaya miki ne Ma'aruf nawa ne ni kadai?!" *** Tafiyar ta fara! Insha Allah. #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA GOMA. Ina mai baku hakuri, an samu jinkirin wannan babin ne saboda rasuwa da aka yi min ba a gari ba don haka har tafiya sai da ta kama ni zuwa can... Ina rokon ku taya ni addu'ar Allah ya jikanta ya gafarta mata. Sannan duk a cikin kwanakin nan mun rasa Abdallah ma, ɗan gidan Sanah S. Matazu editar Fikra, ina rokon Allah ubangiji ya bata hakurin rashinbsa yasa mataryin can ne, sannan ina yiwa duk wanda ya rasa wani nasa ma addu'a, mutuwa na taɓa mu a bangarorin da bamu san muna dasu ba, Allah yaji ƙan wadanda muka rasa mu kuma ya kyautata namu zuwan. Ameen ya Allah. ~~~~~~~ We should talk. - Unknown ** "Maamah don me yasa zai kira shi? Nace ya kira shi ne? Me yasa zai yi deciding abinda bai shafe shi ba kai tsaye?" Muryar Ruƙayya ta fito da ƙarfi a lokacin da take kallon ƙaninta Ahmad dake tsaye a gaban gadon da take kwance. A cikin asibitin da aka kwantar da ita ne, tun bayan lokacin data faɗi take asibitin ba'a sallame ta ba sakamakon hawan da jininta ke tayi babu sauka, don hatta fuskarta da kafafunta dukkansu a kumbure suke suntum. "To hell with you and him! Shi waye da baza'a kira shi a gaya masa yayi ba daidai ba? Me yasa akan Ma'aruf ƙwaƙwalwar ki ba zata taba hankali bane Rukayya? Meye a duniyar nan ki gani a jikinsa da sauran maza badu dashi? I swear to God idan kika kara daga min murya a yanzu zan sake kiranshi na zage shi a gaban idanunki." "Maamah kina jinsa ko? Kina jin abinda yake faɗa?!" Ta faɗa tana juyawa wajen mahaifiyarsu Hajiya Nafisa dake zaune daga gefe tana haɗa mata tea, idan da sabo ta saba da wannan fada a tsakaninsu, don ko Ashraf da yake sakon Rukayyan basa faɗa tare kamar yadda suke yi da Ahmad ɗin, shi mutum ne kaifi ɗaya mai tsatsatsauran ra'ayi, Rukayya kuma ba'a taka ta tayi shiru, don haka inuwarsu bata taɓa zama ɗaya. A yanzu ma dalilin ɗaga jijiyoyin wuyan nasu, Ahmad ɗin ne ya zo ne yana shaida musu cewa shi ya sake kiran Ma'aruf akan zancen Hamida, tunda sunyi magana da Ashraf yace zai tuntube su kuma bai sake cewa dasu komai ba, don haka shi ya kira shi da ɓacin ran hakan wanda a ƙarshe wayar tasu bata ƙare da daɗi ba, don Ma'aruf ɗin har gargadi ya masa da cewar labarin zai canja idan har ya sake kiransa. Ita kanta bata ga aibu a abinda Ahmad ɗin yayi ba, don Allah ya sani idan da Ruƙayya zata bata dama a lokaci guda ne zasu juya dukkan tanadin da suke mata akan Ma'aruf ita da kawarta zuwa sharri, zata fi jin karfin gwiwar cutar dashi akan abinda suke yi a yanzu, don haka ta cigaba da haɗa mata shayin kawai tana jinsu, tana ji kamar Ahmad na furta rabin kalaman dake cikin ranta ne da ba zata iya faɗawa Rukayyan ita da kanta ba. Kuma sai da taji kalaman nasa na shirin yin tsauri da yawa sannan ta kalle shi tace. "Ahmad, fita daga wajen nan." System ɗinsa da ya ajiye akan Fridge din ɗakin bayan shigowarsa ya ɗauka cike da fushi sannan ya nuna Rukayyan da ɗan yatsa tace, "Daga yau kar ki sake kirana a matsayin danuwanki duk sanda wani abu ya haɗa da mutumin nan, idan ba haka ba daga ke har shi I'm gonna rip your as* off! (Zaku gane kuranku!)" Da haka ya fice tana bugo ƙafar ɗakin asibitin, Rukkaya ta koma da baya ta rufe fuskarta da duka tafukan hannayenta biyu lokacin da Hajiya Nafisan ke miƙo mata kofin shayin. "Kin san halinsa ai sarai, amma kika biye masa kuke ɗaga murya a cikin asibiti, na sha gaya miki da kin ga ransa ya ɓaci kawai ki rabu dashi, wannan shine girman." Ta girgiza kanta a hankali sannan ta buɗe fuskar tana karbar kofin. "Maamah ba zan iya shiru akan abinda yake fada ba, kina ji fa yace har gargadi Ma'aruf yayi masa, to waye ya san iyakar abinda ya gaya masa ma? me yasa zai sake ɓata min al'amura ya sake ɓallo wani abu kuma?" Ta ƙarasa tana karɓar shayin, kuma garɗin abubuwan da aka cika masa da kuma ɗuminsa ya sauka har cikin ƙirjinta, ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali kafin ta buɗe su sosai akan kofin, da ɗaya hannun nata shiga murza bakinsa a hankali ba tare da ta kalli Mahaifiyar tata ba tace. "Maamah kince kawai aura masa yarinyar akayi ko?" Taji sanda Hajiya Nafisan tayi ajiyar zuciya kafin tace. "Tabbatar min akayi cewa a cikin sati uku akayi komai, ance bai taba ganinta ba ma har aka daura auren, sannan yarinyar bata da wani daraja, mahaifinta ance irin sana'ar ƙananun aikin katakon nan yake yi, don haka na tabbatar miki akwai wata manufa ta daban dangane da auren nan da bamu sani ba, amma ba wai aure yayi irin wanda kika sani ba." Wannan karon Ruƙayya rufe idanuwanta tayi duka, tana jin yadda wani tiririn zafi na daban da yafi karfin shayin dake hannunta yana cigaba da zurara a cikin ƙirjinta yana kona duk inda ya bi. "Nima na sani ba auren gaske bane Mami, don wallahi na san babu ta yadda za'ayi yarinyar nan ta shigo cikin tsarinsa, a yanayin arzikinsa dana gidansu ko haukacewa yayi akwai ƴanmatan sa suka fita daraja da yawa da zasu so shi a haka." Shi yasa bana son inyi wasa da kowacce irin dama Mami, a yanzu ban damu da duk hanyar da zamu bi mu lalata komai ba, don ban damu da manufar kowa ba, burina kawai kada yarinyar nan ta daɗe a rayuwar Ma'aruf, don ta haka ne kawai zan iya cimma burina Maamah, idan akwai ta, na sani ba zan taɓa iya samun abinda nake so ba." Kafin Hajiya Nafisan dake kallonta tace wani abu, ƙarar ringtone ɗin wayarta ya cika ɗakin, don haka ta dauko wayar tata dake gefen bedside drawer ta miko mata, Ruƙayya ta karba tana kallon sunan da ya fito akan screen ɗin, Jawad... Taji ranta ya ƙara dugunzuma ya ɓaci a take, bata san wane irin mutum ne shi marar zuciya haka ba? Me yasa zai cigaba da damunta alhali da kowanne yare da zai iya fahimta ta gaya masa cewa ya rabu da ita? Sai kawai ta danne buttton ɗin wayar gabaɗaya ta kashe ta sannan ta ajiye ta a gefe. Takaicin dake cike fal da tausayin ƴar tata ya nuna akan fuskar Hajiya Nafisa kafin ta girgiza kanta a hankali. "Na gaya miki ki kwantar da hankalinki ki samu sauƙi mu koma ki gida, don Hajiya Saude ta gaya min sai da haɗin kanki tukunna sannan komai zai daidaita, nayi miki alƙawarin Ma'aruf da ƙafarsa zai tako har inda kike ya neme ki." Wani abu kamar murnushi ya fito kan lebben Ruƙayyan yayin da ta sake jingina kanta baya da jikin gadon kafin a hankali kuma ta ɗago da kofin shayin nan ta kai bakinta. Daga can jihar Abuja, a cikin gidan rawar da Jawad yake a can sama, inda yaken wani lungu yana zaune akan luntsememiyar kujerar wajen shi kadai, a gabansa wani haddadden kwandon shisha ne da yake zuƙa yana hurawa lokaci zuwa lokaci, a ɗaya hannun nasa kuma wayarsa ce da hasken screen ɗinta ke haska fuskarsa yayin da yake danna number guda cikin contact list ɗinsa ana kuma maimaita masa abu guda daga daya bangaren wayar. "The number you're trying to call is currently switched off, Please try again later." (Lambar da ake kira a kashe take, a sake gwadawa bayan wani lokaci.) Hannunsa ya sake danna number yayin da aka sake maimaita masa maganar. "Jawad?? For real? Kai kadai anan sama? Na zata wasa su Sa'id suke da suka ce kana nan ai." Wani abokinsa da suke kira da Haro ya ƙaraso daidai wajen yana zama daga gefen kujerar, bai ce dashi komai ba don haka ya sake kallonsa yace. "Naji rumours din, it was bad man, amma bai kamata hakan ya dame ka ba, kar ka jawowa kanka depression." Sai a yanzu Jawad ya juyo ya kalle shi, ya san abinda yake magana, jita-jitar dake yawo cewa za'a cire mahaifinsa daga kujerar Minister, har a tunaninsa abinda zai dame shi kenan? To me zai same su idan an cire shin tunda ko a yanzu sun tara dukiyar da ya san har su mutu ba zata kare ba, ya zuki hayakin ya fesar sannan yace. "Kar Allah yasa a fasa cire shin, al'amarin wannan tsohon ya isa ya dame ni ne Haro? abinda yake gabana daban." Kan shishar Haro ya karɓa yana dariya sannan yace. "Pray tell." Sai kawai ya jefo masa wayar hannunsa shima sannan ya jingina da kujerar. Haro ya cafe wayar sannan ya kalli screen ɗinta, kuma sunan da ya karanta na farko akan call log din ya sashi jan tsakin da bai shirya ba. "Ban san ranar da asirin da yarinyar nan ta naka zai karye ba Jawad, har sau nawa zan gaya maka ka rabu da wannan tsilar abar, ub*n me zata tsinana maka da baka samu ba a duniyar nan? You're young, kana da kudi, kana da status mai kyau, kana kan lokacinka Man, sannan babu yarinyar da zaka kalla duk kasar nan ka kasa samunta. Me yasa ba zaka yi hankali ka fahimci cewa wannan yarinyar sharri ce ma a rayuwarka ba?" Jawad ya lumshe idanunsa ya bude yana saurarensa ta cikin sautin kidan dake tashi daga can kasa kuma sai da ya kai har karshe sannan ya girgiza kansa, idanunsa na kallon fitilar dake samansu mai kala-kala a cikin duhun wajen yace. "Ba zaka gane ba Haro, ba zaka gane abinda nake ji bane, na rantse da Allah idan Ruƙayya bata aure ni ba, ba zata sake auren kowa ba a duniyar nan!" *** "What do you find? Me ka samo?" Faruk ya tambaya riƙe da Tab ɗin hannunsa yana kallon Ma'aruf dake kokarin fitar da lissafin da suka kwashe fiye da awa guda suna yi akan kamfanin wasu abokan kasuwancinsu da suka gano cewar suna da nasu kamashon cikin wannan mummunar asarar da har yanzu suke bincike akanta. Suna zaune ne daga cikin office din Ma'aruf ɗin, bayan kusan jiran awa uku da Faruk din yayi yana jiran dawowar Ma'aruf da ya bar office din tun kusan sha ɗaya na safe. Kuma sai da ya dawo sannan ya buɗe email dinsa ya karanta bayanan da Martha sakatariyar tasa ta turo masa sannan suka fara haɗa komai suna tarawa da ƙaiyadewa. "So shi wannan Mr. Ishmael Grahm ɗin shine ya karbi aikin accountant ɗinsu a farkon shekarar nan kenan kuma sunansu ɗaya da wanda ya tafi har surnane ɗin." Ma'aruf ɗin ya faɗa, idanunsa manne da tab ɗin gabansa yayin da muryar tasa ta fito kamar ta ƙwace ne daga cikin tunaninsa. "What a ina ka ga hakan? Dama sun canja accountant ne? When?" Faruk yayi tambayoyin yana komawa cikin kan tasa wayar. "A cikin wanda ka min sending zaka duba, anyi naming dinsa 13th March na wannan shekarar." Kuma sai da Faruk din ya kusan zuwa can ƙasa wajen nemowa kafin ya isa inda yake gaya masan, idanunsa suka ƙanƙance yayin da yake karanta bayanin dake wurin. "Bala'i! B ya akayi hankalinka yaje wajen nan, I was goung through it fa tun safe amma wallahi ban gani ba." "Shi yasa na gaya maka na kusa korarka daga aikin nan, ban san me yake ɓata maka tunaninka ba kwana biyu." Dariya Faruk ɗin yayi yana cigaba da karantawa kafin yace. "Aikin Shahida ne wallahi, tunda ta yaye Aarif nake ji kamar watannin farkon auren mu muka koma." A lokaci guda Ma'aruf ya tsaya da karanta abinda yake yi ya juyo ya kalle shi, sai kuma ya girgiza kansa sannan yace. "Baka da hankali Faruk, na daɗe ina gaya maka." Faruk ɗin ya sake yin dariya yana daukar tambulan ɗin lemon da Martha ta kawo musu kafin yace. "Inji wanda yake amsa sunan sabon ango, you didn't even tell me ya yarinyar take." Yaya yarinyar take. Maganar ta sake tuno masa da fuskarta a yau da safe kafin ya fito, sati guda kenan da yin auren, kuma a cikin sati gudan nan baya jin magana ta haɗa su wadda tafi kirgen cikin yatsu, wani lokacin dai su kan haɗu da asuba idan jamlock ɗin kofar falo ya rufe bayan ya fita masallaci, zata zo ta buɗe masa idan yayi knocking sanye da dogoon hijabinta har kasa, ranar farko bata ce dashi komai ba, amma a rana ta biyu ne ta fara gaishe shi. Sannan kuma sau da yawa idan ya koma da daddare zai ganta, har ya fahimci wani lokaci ma tana fitowar ne kawai don ta gaishe shi. Bayan hakan maganganun da suka haɗa su baya jin sun wuce biyar, ya san ranar juma'a da zai fita masallaci ya tambaye ta dardumar sallah ta dauko wata sabuwa kuwa fil mai laushi ta kawo masa, sai kuma ita da ta tambaye shi Panadol ya fita da kansa ya siyo mata, amma bayan hakan baya tunanin wata maganar ta kara hada su don baya son ya takura ta ko kadan, so yake hankalinta ya kwanta ta fahimci cewa da gaske ba abinda zai mata, don a o farkon nan ya lura cewa da gaske a tsorace take dashi. Ya rasa irin tasiri kalamansa suka yi a zuciyarta, ya kasa gane ma me yasa ta yarda da auren idan har tana tsoronsa haka, wataƙila laifin tun na wannan ranar ne, da ta fito ya ganta, da tun a lokacin zai san tayi ƙanƙanta yayi mata wannan barazanar, don haka yake son da kanta ta karkade duk wani tunani da take yi game dashi da kuma damuwar kalaman nan. A shekaranjiya da yaji tana waya da wata tana yi mata bayanin cewa har yanzu bata fara girki ba, a cikin muryar tata yaji da wani abu kamar damuwa, wani abu da ya tsaya masa a rai yasa yasa ba shiri a lokacin da ya shiga cikin gida yaji Mami na yiwa Malam Sani lissafin cefenan wata, ya bishi a baya ya ƙara masa wasu kuɗin yace duk abinda ya siya na cikin gidan ya sake siyan rabin sa ya kai mata. Komai na wannan auren daban yake da lokacinsa da Rukayya ya sani, babu abu ko guda daya da zai danganta shi da farkon wancan ɗin, kamar komai ɗin yana zuwa ne a kishiyar ɗayan, sai dai abu daya kawai zai iya dorarawa shine a yanzu yana jinsa mutum mai ƴanci tunda babu ruwanta dashi sabanin a wancan da kwanakin farko suka sa shi yaji kamar an tsare shi a wani waje ne da lissafin abubuwan da ya kamata yayi. "Kaji ai matsalata da kai kenan, da an taɓo wani zancen ba na aiki ba you lack interest, na tabbata da nayi ta jiranka ma anan wani aikin ka tafi yi." Faruk ya faɗa yana jawo shi daga cikin tunaninsa, kuma ba tare da ya juyo ya kalle shi ba yace. "Saboda ni ba mutum bane kenan bani da wasu personal problems, to ka leƙa motata ka gani wanki naje na karɓo sannan na karbo ɗinki, har B&L naje samo maigadi, sannan na tsaya a zoo road nayi aski." Faruq ɗin yana nazarin sumar kansa da banbancin ta kaɗan ne da yadda ya ganta jiya, yace. "A haka wannan gashin naka an aske shi?" Ya girgiza kansa har yanzu bai kalle shi ba yace. "A'a fixing nayi." Sai kawai Faruq ɗin yayi dariya sannan ya juya kan tasa tab din dake blinking alamun shigowar wani sabon saƙon, suka cigaba da tattauna duk abinda ke gabansu har magariba ta tadda su anan, wanda kafin magaribar suka yi sa'ar ganowa cewa tabbas wannan kamfanin sun karbi kaya na maƙudan kuɗaɗen a hannunsu kuma dukkan receipt din kudin an saka adadin kudin daidai, har ma da alert din shigar kudin cikin bankin kamfanin, amma takardar da Faruk ɗin ya gano cewa an duba balance a wancan lokacin kuma kudin bai kai ba, ita ta daure musu tunani. Don basu san yadda za'ayi alert ya shigo da wani adadin kuɗi ba alhali ba hakan aka turo ba. Anan suka tsaya kasancewar magriba ta taho kusan kowa a Office din ya tashi tunda dama a ƙa'ida ƙarfe biyar ne lokacin tafiyar kowa. A wajen Hamida ya daɗe bayan yayi sallar magaribar, kuma wannan karon har nuna alamun cewa zata biyo shi tayi, ransa ya cika da farin ciki kafin ta ƙarasa da cewar zata bishi ne ya kaita wajen Maminta, kuma Allah kadai ya san sau nawa ya zura hannunsa cikin gashinsa ya fito dashi kafin ya iso gida, don game da al'amarinta bashi da wata mafita ko kaɗan, abu ɗaya ya sani shine ba zai taɓa iya sake rabuwa da ita ba ko da me Ruƙayya da iyayenta zasu tunkare shi. Ya tuno wayar da suka yi da Ahmad kanin Ruƙayyan a jiya, yaron bashi da hankali ya daɗe da sanin hakan, tunda har sunyi magana da Ashraf ya gaya masa cewa zai neme su bai ga dalilin da zai sa shi ya sake kiransa ba, kuma yadda yake masa magana ma ji yayi idan akwai wani mataki da yafi na haukan, zai iya saka shi a wannan layin, don haka ƙarara yayi masa gargaɗin cewa zai iya sawa a kama shi idan har ya sake kiransa da wannan batun. Ya riga ya sani cewa duk cikinsu babu wanda zai iya ja dashi don yana da da hujjar da zai kaisu ƙasa ko a gaban waye za'a tsaya, bama wannan ba ya sani cewa babu inda Ruƙayyan zata je ta samo karfin halin da zata iya fuskantarsa a yanzu, tana yawo ne da nauyin waɗannan kalaman ɓoyayyiyar yarjejeniyar da suka yi kamar yadda koda da rana guda shima bai taɓa manta su ba. Ya isa gida bayan ya tsaya a wani masallaci yayi sallar isha'i, ya shiga da motarsa ciki sannan ya fito ya rufe gate din yana takaicin yadda sai wani satin zai samu maigadi kamar yadda kamfanin suka shaida masa. Kuma bayan ya ɗauko wayoyinsa biyu daga cikin motar ya dade tsaye a wajen yana waya da Ishaq, a yanzu haɗuwarsu ta ɗanyi wuya, yana ta yawon zuwa Abuja ne akan wani workshop da suka fara a kotun tasu, don haka a cikin satin ma sau daya kawai suka haɗu. Magana suke tayi akan gininsu, wasu filaye da suka siya a Lamiɗo Cresent ana musu gini iri ɗaya, bayani yake yiwa Ishaq ɗin cewa zasu canja masu gini don na yanzun an basu kudin kaya mai kyau amma sun siyo wani siminti da bashi da kyau har wani waje a cikin ginin Ishaq din ya rufta. Daga karshe suka tsaya akan Idan ya dawo zasu fara neman wasu ma'aikatan kafin suyi sallama da kalaman da Ishaq din ke gaya masa a mafi yawancin ƙarshen maganarsu. "Dan Allah ka kula B." Ya cije leɓɓensa yana kallon wayar, har yanzu Ishaq bai yarda dashi ba ya sani, gani yake a kowanne lokaci wani abu zai iya faruwa saboda yanayin ciwon nasa, amma shi baya jin hakan, akwai abubuwan da yawa a gabansa amma baya jin sunyi yawan da a cikinsu zai iya samun abinda zai canja yanayinsa, don haka yana amsa masa ne kawai don ko yayi bayanin ba zai yarda dashi ba. Ya kashe wayar sannan ya debo kayansa na cikin motar ya shiga ciki da ƴar karamar sallamarsa, babu kowa a falon amma ƙamshin turaren wutar daya kula kwana biyu ana yinsa a gidan ya shiga hancinsa. Yayi sallamar da babu mai amsa masa sannan ya cire takalmansa daga gefe ya taka zuwa ciki, zuwa hanyar korodon nan, fitilar dakinta a kunne take kamar kowanne lokaci irin haka idan ya dawo, ya jiyo motsinta daga ciki har da ƙara ma kamar wani abu ya fadi kafin ya zarce zuwa dakinsa. Wanka zaiyi ya fito ya shiga cikin gida, a can wajen Mami yake cin abincinsa kullum, kafin ya fita dai ya san watakila zai ganta su gaisa, amma zuwa lokacin da zai dawo ma ta riga ta kashe fitilar dakinta ta kwanta, ta kasan kofarta yake ganin hakan idan zai wuce. Ya isa ɗakin nasa lokacin da yake tuno maganganun Baffa sanda yake masa fadan rashin halartarsa wajen daurin auren nan, Baba Usman yana daga gefensa yake cewa. "... Idan kana tunanin zaka wulakanta yarinyar nan saboda iyayenta ba masu arziki bane Muhammad, ina so ka kalli iyayenka biyu da suke cikin gidan nan, daga ita Kilishin har Maimunan da ta haife ka, ka gaya min waye ya fito daga gidan mai kuɗi, ko kuma ni kaina da nake mahaifinka, ka gaya min gidan iyayena na gado da yake Bakori yaya yake, Mahaifina har ya mutu ɗakin kwanansa na ƙasa ne bai ko kai girman ɗakin nan ba ka sani. Saboda haka na daura aurenka da yarinyar nan ne saboda shaidar halayen kirki da aka yi mata ita da iyayenta, ba don abin duniya ba babu ruwana da abinda mutane ke faɗa wai kwarya tabi kwarya, zaman aure nutsuwa da kwanciyar hankali ake nema a cikinsa ba suna ba, game da aurenka na farko kaima shaida ne akan hakan, don haka ina rokonka kar ka bani kunya a karo na biyu Ma'aruf." Ya rufe idanunsa lokacin da ya saki ruwan shower akansa, indai Baffa zai kira shi da sunansa na asali ya sani cewa babban al'amari ne. *** Doguwar riga ce a jikin Amina ta atamfa kalar milk da sea green, ta daura dankwalin sannan ta yafa wani karamin mayafi shima kalar sea green ɗin da ya tsaya iya kafadunta, ba kwalliya tayi ba don babu ko hoda a fuskarta amma fatar ta da'a kwana biyu ta kara washewa sakamakon canjin ruwa tana haskawa tare da fararen idanunta, kuma kawai ta yafa mayafin ne don bata son fita haka, taji lokacin da Ma'aruf ya shigo, har wucewarsa ta gani ta kasan ƙofar dakin daidai lokacin da robar vaseline ɗin dake hannunta ta subuce ta fadi. Sati guda kenan da fara rayuwarta tare dashi amma har a yanzu duk sanda ya fita ya dawo sai taga kamar shine ganinta dashi na farko, taji zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda duk da cewar wannan taraddain da take ji a farko ya fara tafiya, don bata san me yasa ba komai yazo ne sabanin tunsninta kuma lokaci yana saukaka mata abubuwa fiye da zatonta. Ko kaɗan bata ga wani yunƙurin cutar da ita a tare dashi ba, hasalima harkokin gabansa yake, da sun gaisa shikenan ba zai kara bi ta kanta ba. Ita kanta ta fara sabawa da gidan a yanzu, ranar da su Fatima suka zo sun taya ta sake kimtsa komai nata, sauran kayan kwalliyar nan da jakunkuna da takalman dake cikin Ghana must go ɗin nan duk an samar musu wajen daya dace dasu, ta basu kayan kwalliyar ma da yawa da kuma wasu daga cikin undies din. Sannan a kitchen ma sun jera komai a muhallinsa, store din ya zama babu komai sai iya abubuwan da ba lallai amfaninsu yazo a kusa ba, bata san adadin mamakin da tayi ba na yawan ganin kayan, don bayan wanda aka siya mata kusan duk wanda zai kawo wata gudunmawa kayan kitchen ɗin ne, don haka har wasu abubuwa ta ware a cikin ranta cewar zata ajiyewa Maryam idan lokacin nata auren yazo. Sauran ɗakunan nan biyu ashe ɗaya carpet ne kawai da labulaye da kuma su tintin a jere, sai ɗayan ne aka tsara shi da wani irin nau'in furnitures masu tsananin kyau da ɗaukar ido, komai kalar grey, milk da kuma ash ne, wani silk bedsheet din da aka shimfide gadon dashi yana ta daukar ido a cikin hasken fitulum ɗakin, Aunty Safiyya bata sani bane da take cewa tayi zamanta a dakinta, dama ba'a tsara wannan don ita ba, shi suka yiwa abinsu, don har wasu fitulu aka saka a tsakiyar ceiling ɗin dogwaye masu haske, ga kalar fentin shima grey ne, labulayen kuma milk gabaɗayansu. Kasa rufe bakinta tayi a lokacin da su Ummi ke cigaba da santin ɗakin daga inda suka tsaya a bakin kuma ƙaton akwatin dake ajiye akan gadon, shi ya hana kowannensu shiga don ba sai ta gaya musu ba sun riga sun gama sanin dakin na waye. Ta fita ɗakin ta rufe kofar a hankali kamar mai tsoron kar a jita sannan ta nufi hanyar kitchen, daga tsakiya akan work table ɗin nan tray din dake dauke da flask din abincin da ta gama ne, a yau zata danne zuciyartaa tayi abinda ta kasa jiya, shekaranjiya ya aiko aka kawo kayan abinci kamar ya san dana ta matsu ta fara girki da kanta, don haka kai tsaye ta gayawa Samirah cewa ta huta tunda dama ita ke kawo mata abinci kullum, abincin da ita kadai take ci don ko yana sanin an kawo ɗin ma bai taɓa tambaya ba, ta fahimci idan ya dawo yayi wanka wajen Mami yake tafiya yaci abincinsa sannan ya dawo. Don haka ko jiya da tayi girkin, har dashi tayi amma tana ɗaki tana biya abinda zata ce masa taji ya buɗe kofar falon ya fita, haka ta debi abincinta ta rufe a fridge, amma yau ta gama shirya cewar ba zata bari ya fita ba, ba don komai ba sai don tarin nasihohin nan da aka yi mata suna ta yawo a cikin kanta, gani take kamar laifi take idan zata yi girkin babu shi, don akwai nasa hakkokin akanta kamar yadda shi ya sauke nasa wajen kawo abincin. Bayan haka ma, ta karanci kalolin kayautata zamantakewa fiye da adadi a wajen Ammarta, abinda ke cikin zuciyarta kenan fal kuma dashi tayi tunanin zata iya cin galabar komai dama, har yanzu bai nuna wata alama ta cutar da ita ba don haka don me yasa ita zata fara da abinda bai dace ba? A cikin addu'o'in da Gwaggo Balkisa tayi mata tace '... Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa..' To idan bata kyautata masa ba ta yaya zai ji tausayin nata, Me ƴan uwansa ma zasu yi tunani idan hakan ta cigaba? Idanunta suka hasko mata Hajiya Kilishin da yake zuwa wajenta yaci abincin, bata san me yasa ba ita har yanzu zuciyarta bata kwanta da ita ba, ranar da su Samirah suka fara kaita wajenta, hannayenta duka biyu ta kamo tace. "Barkanki da zuwa cikinmu Amina, zuciyata cike take da murna idan na tuna cewa ƴa ta na kawo gidan nan ba kowa ba, ki saki jikinki ki saba da kowa, don a gidan nan bama taba banbanta kanmu, kowa ɗaya ne kuma kowa yana samun tallafawar ɗan uwansa saboda ƙaunar dake cikin zuciyoyin mu, kuma kema kin shigo kenan cikin wannan lissafin namu, rayuwarki zata canja da dukkan alkhairin da dake tare damu, kuma ina fatan kema zaki bamu damar amfana da irin naki alkhairin." Haka kurum a lokacin sai taji maganganun basu tafi har cikin zuciyarta ba, sai taji kamar sun tsaru da yawa ace kai tsaye take faɗarsu daga zuciyarta a wannan lokacin, amma ko da ta daga ido ta kalli fuskarta, sai zuciyarta ta ture wannan kokwanton a gefe, tana tuna mata cewa itace wannan Hajiya Kilishin da ta tallafi rayuwarsu ta ɓangarori da yawa. Hajiya Kilishin da kullum Baba yake ambato da kyawawan kalamai sannan kuma kamar yadda ta gani ta itace jagorar wannan gidan, don a yinin yau kawai ta fahimci abubuwa da yawa sai da izininta ake yi, don haka saboda tana ganin itace umul'abasin faruwar wannan auren bai kamata zuciyarta tayi wannan tunanin ba. Amma Allah ya sani da suka shiga wajen Hajiya Maimunan wadda aka gaya mata itace asalin mahaifiyar Ma'aruf, zuciyarta kusan narkewa tayi tun kafin ta kai ga zama, mace ce har mace, irin manyan matan nan masu tsananin kamala da nutsuwa, fukarta fuska ce da za'a iya amfani da ita a koina a fadin duniya ta wakilci kalmar 'Uwa a rayuwar bahaushe' sai dai babu ƙafafu, tana zaune kan Wheelchair ɗinta da Hisnul Muslim a hannunta. Kuma abinda ya bata mamaki shine itama da fara'arta da komai itama ta karɓeta, tana ta zuba tarin addu'oin fatan alkhairi da kuma fatan zaman lafiya a tsakaninta da Ma'aruf, wani abu data lissafa cewa yayi ƙaranci a kalaman Hajiya Kilishi. Sai kawai ta ture wannan tunanin ta dauki tray din ta taho falon, sai da ta tsaya tana ta tunani inda zata ajiye kafin ta tsugunna a hankali daga gaban Three-sitter dake gabanta, kuma tsugunnawar tata tayi daidai da fitowar Ma'aruf daga falon, ta dago da kanta lokacin da kafafunsa suka tsaya cak yana kallonta daga hanyar kofar da ya nufa. Yayi wankan, ya canja yansa zuwa wani bakin wando da dark navy blue riga data dace da kalar daren, kallonta yake yi da mamakin dake nunawa karara a fuskarsa, sai kawai tayi saurin ƙarasa ajiye tray din sannan ta mike tsaye itama. Kanta a sunkuye hannayenta cakude da juna tace. "Barka da dare." A cikin shirun dakin muryarta ta fito kamar wani fukafikin dake tahowa kasa a hankali, Ma'aruf ya gyada kansa yana kallonta har yanzu da mamakin a fuskarsa kafin ya amsa da. "Kin yini lafiya?" Haka yake tambayarta kullum, don haka ta gyada kanta ba tare da ta dago ko ta daina cakuɗa yatsunta cikin juna ba, kuma sai tayi shiru bata ƙara cewa komai ba. Amina ta san ya kamata tace wani abun game da abincin da yake kallo a gabanta amma bata san me zata fara cewa ba, kuma ga mamakinta sai kawai taji yace. "Wannan abincin..." "Naka ne..." Ta ƙarasa da sauri tana ɗago da kanta, idanunsu suka haɗu waje guda sai tayi saurin sake maida kanta kasa ta cigaba da murza yatsunta, amma zata iya karanta mamakin daya karu cikin muryarsa sanda yace. "Masha Allah, kamar kin sani dama yunwa nake ji." Wani abu a cikin zuciyarta yayi tsalle da jin hakan, yayi kokarin subucewa daga zuciyarta zuwa kan fuskarta amma ta tare shi da karfi tana cigaba da motsa hannunta, ƙarar takunsa taji yana tahowa don haka tayi saurin tsugunnawa ta ɗauki plate din tana bude murfin flask ɗin farko. Ƙamshin abincin ya shiga hancin Ma'aruf sanda ya karaso kan carpet din, idanunsa na kallonta tana zubawa yayin da ƙaramin mayafin data yafa kalar kayanta ya zame yana reto a gefen fuskarsta, wani abu yake ji na daban yana shiga zuciyarsa bayan mamaki, sai kawai ya zube wayoyin hannunsa akan kujerar sannan ya ƙarasa kan kapet ɗin gaban abincin ya zauna, ƙamshint turarenta mai sanyi ya shiga hancinsa tare da na abincin don a yadda ya zauna tray ɗin shi kaɗai ya raba tsakaninsu. Kuma bai ce mata komai ba, yana kallonta ta zuba iya adadin da take so na komai sannan ta ture tray din gefe a hankali ya tafi cikin laushin carpet din kafin ta ajiye plate din a gabansa. Shinkafa ce fara da vegetables a ciki sai kuma miyar dake tashin ƙamshin daya baɗe falon a lokaci guda, akwai wani abu a dan bowl data zuba na cabbage da kuma Irish potato mai hade da nama duk da wanda yake cikin miyar. Wani abu ya motsa a cikin zuciyarsa cike da yabawa kokarinta dama abincin tun kafin ya kai bakinsa, yana tuna masa da wani al'amari daya shuɗe a labarin aurensa na farko, ba kai tsaye ya samu irin wannan gatan ba. "Thank you so much." Muryarsa ta furta a hankali da wani sauti da yasa numfashin Amina katsewa a kirjinta, ba shiri ta gyada kanta sannan ta mike da sauri. "Ina zaki je?" Shima yayi tambayar kamar kai tsaye bai shirya mata ba. "Zanje in kawo ruwa ne." Muryarta ta fito tana fallasa bugun da zuciyarta ke yi, kuma kafafunta basu motsa ba sai da ya ɗaga mata kansa. Ta isa kitchen din ta ɗauko robar ruwa guda ɗaya da ba'a fridge ba, don ta kula duk sanda zata ganshi da ruwa a hannunsa to ba mai sanyi bane, shi yasa lemon data haɗa ma ta kaishi can kasan fridge din baiyi sanyi sosai ba, Samirah ce ta koya mata hada lemon, kuma ta tabbatar tayi komai daidai, sai dai bata san dadinsa ko akasin sa ba tunda bata taba sha a wani waje ba. Ta isa falon lokacin da idonta ya sauka akansa ta baya ya kai lomar da bata san ta nawa bace cikin bakinsa, zuciyarta ta kara nutsewa cikin kirjinta da tsarin nata ya tafi daidai, a hankali kafafunta suka ƙarasa kan carpet din, tana jin yadda kafar tata ke shigewa cikinsa saboda laushin sabunta. Wannan karon nesa kaɗan dashi ta zauna sannan ta fara ƙoƙarin zuba lemon a kofi. Ma'aruf ya dago ya kalle ta, har yanzu mamakinta bai bar kan fuskarsa ba, kuma a lokaci guda yaji kalaman da Mamin ta taɓa gaya masa suna dawowa cikin kansa. ... Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata. Abinda Mamin bata sani bane, ita kanta Rukayyan tayi iya kokarinta a zamansu, don ta canja abubuwa da yawa a rayuwarta zuwa bukatarsa, matsalar kawai shine don son zuciyarta tayi komai, babu abinda tayi saboda shi ko don ta kyautata masa, don haka itama zai iya yiwuwa ta fara hakan ne don an saka ta, don bin umarnin da ya tabbatar shi tayi har auren nasu ya kasance, yaji zuciyarsa ta matse da wannan tunanin amma kuma sai ya samu sauƙi da hasashen cewa haka ba zai iya zama gaskiya ba. Ta gama zuba lemon a wannan lokacin, ƙarar awarwaron dake hannunta ya janyo hankalinsa sanda take ajiyewa a gabansa daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga kan kujerar nan, don haka tayi amfani da damar don miƙewa ta bashi waje amma sai muryarta ta tsaida ta. "Ki zauna." Fuskarsa fayau yana kallonta kafin ya juya ya dauki wayar. Ta haɗiye wani abu a makogwaronta a hankali sannan ta dawo da baya ta zauna ɗin, nesa kaɗan dashi kamar ɗazu. Ya ɗauki wayar yana magana ta ciki, ta fahimci da wani yake magana kuma akan harkar aikinsu ne bayan hakan bata gane komai ba, amma kuma yanayin yadda yake maganar ya saka taji zuciyarta na sakewa da amon muryar tasa. Ya gama wayar ya ajiye ta a gefensa sannan ga mamakinta taji yace. "Faruq ne, abokina ne a wajen aiki." Sai ta daga kanta lokacin da ya sake kai wata lomar bakinsa sannan yace. "Abincin nan yayi daɗi sosai Amina. Kinyi kokari." Wani abu ya matse a zuciyarta daga yadda muryarsa ta ambaci sunanta, kamar zata yi magana amma kuma sai ta sake gyada kanta kawai tana wasa da karshen mayafinta. Kuma Yanayinta yasa Ma'aruf yaji a lokaci guda yana son suyi hira, aƙalla yau maganar tasu ta tsallake babin gaisuwa saboda haka yana kallonta yace. "Munaya ta gaya min kina son karatu, tace ta samu wasu novels a wajenki. kina da litattafai da yawa." Sai da sakanni biyu suka wuce sannan Amina ta yarda da maganar da ya furta saboda ɗan mamakin da ya kamata, ranar da take kokarin samawa litattafanta waje ne Munayan ta shigo ta ganta, a ciki har da wasu English novels dama na Hausa wanda take tarawa tun tana makaranta, shikenan sai suka shafe kusan rabin yinin suna hirar labarai kala-kala har ta ara mata wasu ma ta tafi dasu, don haka ta tabbata a yanzun ma ganinta yayi tana karatun ɗaya daga cikin wanda ta ɗauka. "Wanne da wanne kika karanta?" Muryarsa tana fitowa ne kamar yadda take jinta a kullum idan yana waya ko kuma da wani, amma a yanzu da ta san cewa ita yake wa magana sai take ji ta daban, tana saka ta ƴar rikicewar da bata shirya ba. A hankali ta daurewa hakan muryarta ta shiga jero masa sunayen littattafan da ta san sunyi suna amma da yawansu yace bai san su ba saboda yawanci akan Romance ne shi kuma yace ma yafi karanta Non-fiction, yana yi yana cin abincin cike da wani abu da zata iya kira da nishadi. "Akwai wani 'The Life we had' na san zaki san shi.'" Ta ɗaga kanta da sauri don ji tayi kamar hakan na kaɗe tasirin da muryarsa ke yi a zuciyarta, kuma a lokaci guda bakinta ya ɓalle da wani murmushin da bata shirya masa ba tana tuno yadda akayi ta karanta littafin a wani shagon bakin titin unguwarsu inda ake sayar da shi, zuwanta shagon nan bakwai kafin ta kai karshen littafin saboda yayi mata tsadar da ba zata iya siya ba, kuma wata ƙawarta da suka yi makaranta ɗaya da yawanci litattafan wajenta ma ita ta bata, itace ta dame ta zancensa, bayan sun bar makaranta ne a lokacin ita tana can Bauchi babu ta yadda zasu iya haɗuwa sai dai ta kira ta a waya tayi bata labarinsa. Tana tuna ranar da ta kai ƙarshen labarin da wani a cikin masu tsaron shagon ya gane ya tada ballin sai ta biya, da taimakon Aminu aka rufe case ɗin. Bata sani ba ko shima murmushi yayi don kanta yana sunkuye amma taji muryarsa ta ɗan canja lokacin da yace. "Ke ma kamar su Munaya ce ashe, ban san me marubucin littafin yayi da ya siye zuciyarku da yawa ba, babu wani abu da yake gaskiya a labarin nan." Amina bata san sanda ta ɗago ta kalle shi ba tana girgiza kai, tace. "Ai dama Fiction ya gaji ƙirƙire-ƙirƙire da yawa, shi yasa ya kirkiro komai ɗin don ya fito da ma'anar labarin sosai." Ya girgiza kansa shima. "Saboda kawai ya karya zuciyar mutane ne, shi yasa ma ya kashe su daga karshe, daga lokacin da na fahimci itama yarinyar mutuwa zata yi, na tsayar dashi ban ƙarasa kallo ba." Sai ta sake ɗagowa ta kalle shi. "Na zata novel ne." Ta fada kamar tana tsoron labarin nasu zai banbanta, amma sai yayi saurin daga mata kai. "Novel ne, amma lokacin da Munaya ta takura min da zancen labarin bani da time ɗin karatu, so sai kawai na siyo film din na kalla instead." Ta gyada kanta sau daya sannan ta sake maida shi ƙasa ba tare da tace komai, yaji wani abu na shiga zuciyarsa yadda ta fara sakewa dashi a yanzu, don haka kai tsaye ya sake tambayarta. "Baki kalli film din ba?" ya tambaya yana nazarin abinda bata faɗa ba akan furkar ta, kuma sai ta bashi amsar da ya riga ya sani ɗin ta hanyar daga kanta. "Insha Allah zan kawo miki ki gani." Sai ta ɗago ta kalle shi, yayin da hannunta ya tsaya da wasa da mayafin nata. "Allah ya yarda." Ta furta a hankali tana kallonsa, kuma a cikin idanun nata Ma'aruf yaga daren ya tsaya cak kafin ta sake sunkuyar da kanta a hankali, yaji wani abu yaji kamar tausayinta na bi ta kan zuciyarsa. Tana da rayuwarta ya sani, watakila har ma da mafarkai na abubuwan da take son cimma, amma yanayin yadda auren yazo ya sani cewa yabi ta kan abubuwa da yawa a rayuwar tata, wanda da shine baya taɓa jin zai jurewa hakan, amma ita gata a zaune har tana kokarin yi masa hidima, yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaron sa a lokaci guda, a baya yana jin zai iya bin kowacce hanya don sanin meye haɗinta da Jamal amma tun a yanzu ya fara jin cewa ba zai iya yin abinda zata yi dana sanin haɗuwa dashi a rayuwarta ba. *** Washegari da safe Hajiya Kilishi ta buɗe kofar ɓangarenta, fuskarta ta faɗaɗa da wannan murmushin nata mai armashi a duk lokacin da ta ganshi duk kuwa da cewar a jiya tayi ta kallon agogo cikin lissafin zuwansa amma bata ganshi din ba, dalilin da yasa a yau ta tashi da sassafe kenan don ta san yana da karbar magani a yau, don haka ta buɗe kofar zuciyarta na fatan ya kasance Ma'aruf ɗin ne, kuma fatan nata ya karɓu don yana tsaye a gabanta yana murmushin da take jinsa kamar ashanar dake ƙyasta zuciyarta wajen kamawa da wuta. "Tun jiya muke kallon hanya Ma'aruf..." Ta fada tana kallon idanunsa da kullum suke gaya mata shi daban ne a lissafinta ba sai ta rantse ba, zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da ta ganshi a gabanta irin haka. "Mami I'm sorry, jiya aiki ne yayi min yawa kuma a gida naci abinci shi yasa baki ganni ba." Maganar ta taho kamar wani gingimeman dutsen da ya faɗo daga kolulowar sama ya dira a tsakiyar kanta, a lokaci guda murmushin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka tsaya akansa cak a sanda ya kara wayar hannunsa a kunne ya shiga yiwa wani Benjamin magana cewa yayi wa Legal Department ɗinsu bayani su ƙarasa shiryawa kafin ya ƙaraso. Ya katse wayar ya juyo ya kalle ta a lokaci guda da yanayin nata ya baje, fuskarta ta cakuɗe da murmushin da yasa shi gyaɗa mata kai kafin ya wuce zuwa ciki, Abinda bai sani ba shine wannan karon murmushin ba nasa bane, na halittar da take hangowa a cikin idanunta ce... Amina! A yau an ƙaraso gaɓar da take jira, a yau tsarinta zai fara ba sai gobe ba, bata wasa da lokaci balle har tayi sake da koda ƴar mitsitsiyar dama ce... A yau Amina zata shigo cikin ukunta! A yau duk wani mahalukin da yake da kusanci da Amina zai shigo cikin lissafinta! ** #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA DAYA. ~~~~~~~ I've never fallen from quite this high Fallin' into your ocean eyes Those ocean eyes. -Billie Ellish A wannan ranar Amina na kwance daga kan gadon ɗakin tana sauraren wani shiri mai taken 'Allah ɗaya gari banban' da baya taɓa wuce ta daga cikin rediyon wayarta. Idanunta kusan a rufe suke yayin da take sauraren maganganun mutanen dake gabatar da shirin, yau hira ake akan daya daga cikin garuruwan da take son zuwa a rayuwarta, Paris... Don haka sosai take jin daɗin duk wani bayani da baƙin da aka gaiyato suke yi na yadda garin yake da kuma tsare-tsaren su. Sai dai duk yadda hankalinta ke kan shirin zuciyarta kuma nata zarya a can falon gidan inda ta kammala komai na abincin Ma'aruf ta ajiye masa kaar jiya, a yau ta riga ta tsarawa kanta cewa ba zata fita ba don Allah ya sani bata so yaga kamar tana kokarin shige masa ne ko kaɗan, ƙundubalar da tayi wajen yi masa abincin ta wadatar tunda har yanzu bata san manufarsa akanta ba. Ko a jiya umarnin da ya bata ne kawai yasa ta zauna ba wani abu ba, yadda muryarsa ta furta 'Ki zauna' da kuma yadda ya kalle ta da idanunsa bai bata damar zabi ba ko kadan. Duk da cewa kuwa taji dadin hirar, tsaya... Ba hirar tasu ce ta mata daɗi ba, zancen cewa wannan labarin yana da film ne, don Allah ya sani zata so ganin yadda dukkan tunaninta game da komai na labarin zai fito zahiri. "... Wato ina gaya maka samun gida a garin nan shine babban abu mai wahala, gidaje ba karamin tsada ne dasu acan ba..." Hirar rediyon ta cigaba da fitowa yayin da zuciyarta ta fara lissafin kamar yau ya daɗe da yawa, don ko da safe bata ganshi ba kuma yau ita kadai ta yini a gidan, su Sahla da Zahran da suka yi mata alkawarin zasu sake shigo mata yau sun manta da zuwansu makarantar Haddar da suke zuwa shi yasa bata gansu ba. Tun da tazo gidan basu shigo mata ba sai jiyan, kuma sai a jiyan ta gane ashe su ma suna da magana kamar su Samirah, a cikin gidan idan ta gansu da littafinsu kawai gaishe ta suke yi su cigaba da harkokinsu, amma jiyan da suka shigo tasha labarai kala-kala wanda mafi yawanci ba komai ta gane ba. Don a baiyane yake yanayin rayuwarsu da tata ba iri ɗaya bane, abubuwan da suka taso suka sansu ita har yanzu saninta bai ƙaraso nan ba, yanayin makarantar su dama ƴaƴan masu kuɗin da suke mu'amala dasu ba iri daya bane da abinda ita ta taso ta sani. Ta tuno wata magana da Aminu ya taɓa gayawa Maryam ranar da yake tsokanarta bayan ta gama kurin cewa ai ita babu inda zata je a raina ta. "... Nan bayan layin nan idan aka ƙarasa ba sai anje da nisa ba za'ayi iya ɗebo sa'anninki biyar da in suna hira ba zaki taba iya magana ba wallahi sai dai kiyi ta binsu da kallo kina wage baki." Itama dai kuwan ta wage jiya, don murmushi kawai tayi ta binsu dashi kamar yadda take yi a wajensu Samirah, don har gwara su Zahran ma, su idan suka fadi wani abu sai ta biya shi sau biyu akanta kafin ta fahimta musamman Surayya da ta fahimci tafi su iyayi gabaɗaya. Suna da daɗin mu'amala sosai, da gaske suke sun karbe ta a cikinsu ba tare da tunanin komai ba, Ta tuna sanda Samirah ke mata bayanin dalilin da yasa basu je gidansu da biki ba. "Mu fa bamu san da bikin ku da Yaya ba sai ana saura two weeks da aka haɗa lefe sannan Mami ke gaya mana, kuma ko ranar dinner ma munso mu kai muku cards din. Yaya Shukra ce ma ta bani ranar luncheon na saka a jakar Khadija (wata kawarta) ita kuma sai tazo da wata jakar kuma ta manta bata ɗebo ba. A ranar ni kuma I was so busy kamar me, shikenan ban samu time munje mu ɗauko ba. Da na kira Yaya kuma na gaya masa cewa yayi kar mu damu kawai." Amma duk da yadda ta fara sakewa a cikin nasu, tana kewar gida kamar ba gobe, abubuwa da yawa akwai su anan na duk wata buƙatar rayuwa, ga komai sabo koina ƙal-ƙal, gashi babu wanda ya taɓa ko haɗe mata rai har yanzu, idan ta shiga cikin gidan kowa haba-haba yake da ita, hatta su Salma amaren da akayi bikinsu tare dukksnsu sun gaisa a wayar Samirah, da Salman ma ba sau biyu suna gaisawa. Ga Hajiya Kilishi da take nan-nan da ita kullum fuskarta dauke da fara'a tana fadin ita ƴarta ce, Ranar da taje ta gaishe da Baffa ranar ta fahimci dalilin da yasa Baba ya bada aurenta a gabansa ba tare da wani tunani ba, dattijo ne kamili mai nutsuwar da a fuska kadai kowa zaiyi masa shaidar hali na gari, don haka babu wata matsala da ta guskanta a gurinsa shima. Sannan shi kansa uban gaiyar har yau ko haɗe rai bai taba yi mata ba, amma duk da haka, tafi son rayuwar cikin ƴanuwanta akan wannan, tunda har yanzu zuciyarta bata gama kwantawa da komai ba, tunaninta iri ɗaya ne da Amma dama kuma Fatima, dukkaninsu sun yarda cewa akwai wani abu dake tahowa wanda bai karaso ba, don ba'a ɗora turbar auren da cewar komai ya tafi daidai ba, sun sani cewa ba sun kawo ta cikinsu ne don su nuna mata kirkinsu ba dashi da ƴan gidan nasu, dole akwai wani abu da yake a ɓoye wanda har yanzu basu kai ga saninsa ba. Su Aminu da Baba ne kawai hankalinsu a kwance don duk sanda suka yi waya da Baban, zai yi ta zubo mata tarin addu'o'in da suke karya zuciyarta, shi har yanzu zuciyarsa guda ɗaya ce game da auren, ya riga ya aminta da Baffa da ma Hajiya Kilishi ta yadda baya taɓa iya hango komai. Ta lumshe idanunta a hankali tana jin yadda bacci ke shirin ɗaukarta a lokacin, ta shiga ƙokarin kore shi don aƙalla tana son jin lokacin da Ma'aruf zai dawo amma baccin mai nauyi ya ƙara karfinsa, don haka wata zuciyar ta gaya mata cewa zata iya ɗan runtsawa tunda tayi sallar isha kuma bata wani samu baccin safe ba sosai, da wannan lasisin da zuciyarta ta bata taji maganganun cikin rediyon nan suka zuƙe daga kanta a hankali, taji su suna yin nisa da kunnenta kafin a lokaci guda taga Aminu a tsaye daga bayan idonta. "Me yasa kika kasa Amina?" Kai tsaye ya tambaye ta yayin da idanunsa ke kallonta, kuma kalaman suka isa kanta amma suka kasa bada ma'ana saboda dukkan tunaninta ya tsaya cak tana kallonsa da dimbin mamaki, Yaushe yazo? Yaushe yazo ko kuma ita yaushe ta bar cikin gidan, don daga nesa tana hango duhuwar wasu dogwayen bishiyu, hakan yasa gabanta fadi da dukkan tsoron da zuciyarta zata iya dauka. Tayi ƙokarin ta kalli kanta amma sai ta fahimci bata iya ganin jikinta kwata-kwata, kamar idanunta ne kawai a wajen suke ganin komai amma babu gangar jikinta, ta ɗago ta sake kallon Aminun da har yanzu ke tsaye a gabanta. A lokacin ta kula cewa idanunsa sun canja, kalolinsu ba iri ɗaya ne daga yadda ta sansu ba, sun koma baƙiƙ-ƙirin dauke da kyallin kwalla yayin da fuskarsa ke nuna dukkan wasu kalolin tashin hankalin da bata taɓa gani a fuskar Aminun ba, Aminun mai raha da fara'a, Aminun data sani mai ɓoye damuwarsa a kodayaushe. "Me yasa kika kasa Amina?" Muryarsa ta sake tambaya da amon da ya kara hargitsa ta, kuma bata san lokacin da ya matso gabanta ba sai kawai taji ya riƙo hannunta na dama. Ta kalli inda hannun nata ya kamata ya kasance, babu komai sai yadda yatsunsa suka riƙe ta, lokacin da ta ɗago da idonta sai taga ashe ya jawo ta ne har sun iso wajen duhuwar bishiyun nan, tashin hankalin ta ya ƙaru don tana jin yadda ƙafafunta da basa nan suke tafiya, da kuma yadda hannayenta ke rawa a cikin nasa. Hankalinta ya kasu wajen nazarin bishiyun sanda suka tsaya a wani waje, ta juyo tana kallon yadda yanayinsa ke haskawa da dukkan raunin da bata taɓa hange ba, taji ta ƙara rikicewa, taji abubuwa da yawa suna tasowa cikin kanta, tambayoyi fal suna ihu da kokawar fitowa daga bakinta da ta san babu shi balle har ta iya furta su, kowanne lungu da saƙo na tunaninta ya cika da hanƙoro, kamar tana jiran wani abun da bata san meye ba. Kuma kwatsam sai ta nemi bishiyun nan dake kewaye dasu duka ta rasa, warin ƙonewarsu ya cika hancinta amma babu su ɗin balle kuma alamun wutar, kuma babu wani ɓata lokaci kunnenta ya fara jiyo mata muryoyinsu, Maryam ta fara ji, tana ihu mai haɗe da salati, sai ta jiyo ta Hafsa da Adam ma, kowanne yana kuka mai nuna tsananin azaba, bata san ya akayi ta iya tsinto muryoyin su Fatima, Ummi har ma da ta wasu daga cikin ƴaƴan kawu Malam ba. Kuma kafin wani abu ya sake giftawa a cikin kanta ta jiyo muryar Baba yana faman kiran sunayen su Maryam ɗin har ma da sauran mutanen da bata iya tantance muryoyinsu ba, hankalinta ya kara tashi duniyarta ta rikice, ihu da hargowar suka cika kanta kota'ina, kuma a lokacin da ta juya zata kalli Aminun sai taga babu shi, a yanzu Amma ce tsaye tana kallonta, fuskarta ɗauke da wani irin murmushi mai ciwo yayin da take kallonta da dukkan wani fata na duniya. "Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina?" Tayi tambayar a lokaci guda da itama ta neme ta ta rasa, wajen ya koma babu komai sai tashin ihun ƴanuwanta da kuma hargowarsu yayin da warin ƙonewar nan ya cigaba da cika wajen. Ta kasa gane komai ko kuma abinda yake shirin faruwa, abinda kawai zata ita tunawa kafin ta farka shine daga cikin muryoyin dake ihu, ta jiyo wata murya da ta kasa gane wacece ko kuma inda ta santa, muryar tana ƙyalƙyala wata irin dariyar da bata taɓa jin irinta ba! Dariyar ta shiga amsa kuwwa a kowanne ɓangsre na wajen yayin da ihun mutanen dake amsa sunan rayuwarta ke cigaba da tashi.... A lokacin ne kuma ta farka a firgice, kafafunta suka mike tsaye akan gadon bakinta na biyo kalaman Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, a cikin ɗakinta take har yanzu, akan gadon da bacci ya ɗauke ta, amma tun yaushe? Don rediyon wayarta da ta bari a kunne yanzu ƙarar shuuuu kawai take fitarwa. Tasa hannu ta jawo ta da sauri, ta kashe rediyon tana neman lokaci, karfe ɗaya da rabi na dare, wani salatin ya sake suɓucewa a bakinta cike da mamakin yadda akayi tayi bacci mai nisan haka, sai kawai ta wullar da ita gefe ta janyo dankwalinta daya zame akan filon data kwanta tayi saurin ɗaure kanta, koina a jikinta rawa yake har yanzu yayin da mafarkin ke ƙara dawowa cikin kanta, bata fahimci komai a cikinsa ba amma Allah ya sani ta tsorata sosai da yadda abubuwa suka faru don bata iya tunawa idan ta taɓa irin wannan mafarkin a rayuwarta. Taji maƙogwaronta ya bushe yayin da amon muryar nan dake dariya a cikin mafarkinta ke dawo mata, bata san me hakan ke nufi ba, bata san waye zaiyi dariya alhali tashin hankali irin wannan yana faruwa ba, kuma har a yanzu tana jin cewa kamar ta san muryar amma ta kasa tabbatar da inda ta santa. Makogwaronta ya ƙara bushewa yayin da take kokarin saita zuciyarta da har yanzu ke bugawa, ta sauko daga kan gadon, wata doguwar riga ce a jikinta ta bacci da bata kai ƙasa ba ta gaba, don haka kusan tun daga saman gwiwoyinta a waje suke, kuma ba tare da tunanin komai ba tayi hanyar fita daga ɗakin. Kitchen zata je ta ɗauko ruwa, wataƙila zai iya wanke bugawar da zuciyarta ke yi bayan ƙishirwar, idan ta dawo tayi sallah raka'a biyu kuma, watakila tunaninta zai iya komawa daidai. Jikinta na rawa har a lokacin da ta isa kitchen ɗin, ta buɗe ƙofar a lokaci guda da hasken fitilar da aka kunna ya shiga idonta kafin shi, yana zaune daga kan worktable ɗin tsakiya na kitchen din, fitilar dake saman wajen ita ce a kunne da labtop a gabansa yana danne-danne, a gefe kuma foodflask ɗin abincin data dafa ne. Kuma duk da rikicewar da take ciki, ta gane cewar babu riga a jikinsa, wata bakar singlet ce kawai da ta fito da faɗin kafaɗunsa ta kowanne gefe, shima ya dago daga kan labtop din yana kallonta daidai lokacin da ta bude ƙofar. "Me ya faru? Me ya same ki?" Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, kuma ba shiri wani abu ya zarce maƙogwaronta jin yadda muryarsa ta fito a cikin shirun daren tana gaya mata kamar har yanzu a cikin mafarkin take, sai ta ɗaga girgiza kanta kawai da sauri sannan ta sake haɗiye abinda ke bakinta kafin tace. "Ba komai, ruwa zan ɗauka." Da haka ta saki hannun kofar ta nufi wajen fridge, Ma'aruf ya bita da kallo zuwa wajen fridge ɗin, yanayin fuskarta a firgice yake sosai duk da kokarin da tayi wajen ɓoye hakan, kuma ko daga yadda muryarta ta fito ya san akwai wani abun, da wuri tayi bacci ya sani don bayan ya dawo yaga alamun hakan duk da yau cikin gida kawai ya wuce wajen Mami, acan yaci abincin darensa ma bayan sun tattauna maganganun da yasa ta kira shi, zancen Hamida. Kuma bayan ya shigo ya tarad da nata abincin jere a falo, haka kurum sai yaji wani iri, sai yaji kamar bai kyauta ba, ya sani ba zata ji dadi ba idan har ta farka ta ganshi a yadda ta ajiye tunda jiya ta bashi kuma yaci. Bai tsara komai tare da ita ba, abinda ya sani kawai shine aurensu zai zame masa garkuwa ne har lokacin da zai gama da case ɗin dake gabansa na kamfanin nan kafin ya fara binciken da zai shafe ta. Amma tun jiya da yaci abincin nata, sai yaji wani gefe a zuciyarsa ya kara nutsuwa da ita, har yana gaya masa gwara nata ma akan na Mami, tunda aƙalla ya san ita tayi da kanta, na Mamin kuma idan Samirah bata nan masu aikinta ne kawai. Don haka dole a yanzu da ya ɗebo aikin daya shirya zai kwana akansa, ya ɗauko abincin daga falo ya taho kitchen tunda babu Dining area a gidan, kuma ba yunwar yake ji ba amma da ya zuba ya fara ci sai yaji kamar dama bai ci komai ba, yaji hankalinsa ya sake nutsuwa sannan aikin da yake yi na tafiya akai-akai yayin da dukkan maganganun da suka yi da Mamin akan Hamida ke dawowa kansa kafin ta shigo a yanzu da yanayinta a hargitse. Sai kawai ya tura kujerar da yake kai baya ya mike tsaye. "Wani abu ne ya same ki?" Ya sake tambaya yana tahowa inda take shirin buɗe fridge ɗin, kayan jikinta yake kallo a yanzu, kamar na bacci ne... wata riga mai tsawo daga baya amma daga gaba kamar an guntule ta har wajen gwiwarta, don haka kafafunta na tsaye a waje, kuma bai san me yasa ba sai yaji wani abu a zuciyarsa na yabawa da yadda ɗankwalin kanta yayi kala ɗaya da rigar, Pink. Kallonsa take yi itama, idanunta farare na nuna dukkan wani alamun tsoron da ba sai ta furta ba, don haka kai tsaye cikin hasashensa ya sake tambaya. "Mafarki kika yi?" Amina bata san lokacin da ta ɗaga kanta ba don kayan jikinsa a yanzu sun karawa rikicewarta tasiri, bayan baƙar singlet din nan, three-quarter din wando ne kuma a jikinsa wanda da kadan ya wuce gwiwa, sannan ga muryarsa mai zurfi da taji tana tayar da wasu abubuwa akan fatar ta bayan rawar da jikinta ke yi. Kuma bata yi aune ba sai jin hannunsa kawai tayi ya riƙo nata ɗaya, ya jawo ta zuwa wajen kujerar daya taso ya zaunar da ita a ta gefen inda yake zaune kafin shima ya zauna. "Kinyi addu'a?" Tambayar ta tuna mata da abu na farko da ta kamata a e tayi, amma tsabar rikicewar da tayi, zuciyarta bata kawo mata wannsn lissafin ba, sai ta girgiza ksnta a hankali don ko tayi ƙokarin yin ƙaryar ma bata san me zata ce ba, ba zata iya wani tunani mai kyau ba slhali har yanzu yana riƙe da hannunta sannan ga kafafuwanta tun daga kan gwiwarta a waje daga ƙasan rigar nan, bama za'a lissafa da kayan jikinsa ba... "Suratul Ikhlas sau uku, Suratul Falak sau uku, Suratul Nas sau uku..." Muryarsa mai zurfi ta sake faɗa yana kallonta, bata da wani zabi sai ta rufe idanunta, ta haɗiye yawu a maƙogwaronta kafin a hankali bakinta ya shiga karanto su, bata jin sautin muryarta yana fitowa amma tana kaiwa karshe, ya sake cewa. "Ayatul Kursiyu..." Ta kai ƙarshe lokacin da taji kamar almara, ƴar rikicewar tata na bin iska, kuma shirun da yayi riƙe da hannunta bai saki ba wani abu ne daya saita numfashinta daga hawa da saukar da yake faman yi, taji kamar hannayen nasa sunyi wa nata wata rumfa ne ko kuma sun zama wani bango da ba abinda ya isa ya ratsa ta cikinsu ya cutar da ita, don haka a hankali nutsuwarta ta fara dawowa jikinta. "Mafarki ba gaskiya bane, daga shaidan yake zuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru insha Allah." Sai kawai ta gyada kanta a hankali yayin da take ture dukkan wani tunani daga cikin kanta tana yarda da kalaman nasa don ta samu zuciyarta ta dawo daidai, Mafarki ba gaskiya bane, ta shiga biyawa zuciyar tata layi bayan layi. Abinda bata sani ba a wannan lokacin shine, wani lokacin mafarki na juyewa tamkar mudubi, ya nuna abinda zahirin ke iya haifarwa! *** Ƙarfe bakwai na safe. Idan akwai wani abu daya rage a rayuwar Ma'ruf ta baya, shine ƙaunarsa da football (ƙwallon kafa) shi kaɗai ne abu guda ɗaya bayan sunansa da kuma kamanninsa da zai ce basu canja daga Ma'aruf ɗin da yake a baya ba, Ma'aruf ɗin da yake kafin rasuwar Jamal, amma duk wani abu bayan hakan komai da yake yi ba rayuwarsa bace. Son football ɗin ne kawai yayi yawa a zuciyarsa da ba zai iya barinsa ba, shi yasa yawanci duk weekend da safe yana stadium ɗin Sani Abacha, team ne dasu guda da suke da ranakun yin wasa da kuma ranakun training, sannan yana ɗaya daga cikin members ɗin dake kula da wajen ma, duk wani taimakon harkar kudi da ake yi a wajen su suke badawa, idan ya gama ya fito haka zaka ga samarin nan ma'aikatan wajen sun biyo bayansa har wajen mota don ya sallame su, don haka babu wanda bai sanshi ba a wajen. Yau asabar can yayi niyyar zuwa don tun da ya dawo daga sallar asuba ya shirya, amma yayi-yayi da motarsa taƙi tashi, jiya lafiya lau ya ajiye ta kuma a saninsa bata da wata matsala amma sharrin karfe ance ba abinda ba zai iya ba, haka ya hakura ya rabu da ita, sai kawai ya fito da ball ɗin sa daga booth ɗin motar ya shiga training ɗin da ya saba a compound ɗin gidan. Kusan ƙarfe bakwai da rabi lokacin da wayarsa tayi ƙara daga can saman motar inda ya ajiye ta, kuma sai da ya kai ball din sama sau biyu sannan yazo ya ɗauka, Martha ce. "Barka da safiya sir, RTL sun bugo waya cewa yau zasu sauka a Kano, don haka meeting din zai zama karfe huɗu na yamma." Ta zayyano dukkan bayanin da harshen turanci, hannunsa ya zura cikin kansa don kwata-kwata ya manta da zancen cewa zasu iya yin meeting din a yau, yayi niyyar babu inda zai fita zai zauna ya huta ne don Allah ya sani ya aikatau a cikin satin nan gashi jiya ma bai wani samu bacci mai yawa ba. A hankali ya cije leɓɓensa yayin da ta cigaba da yi masa bayanin cewar sunyi waya da Faruq da sauran board members ɗin nasu ta shaida musu komai, shi gabadaya ya manta ma da nasa takardun da ya kamata ya karanta kafin a shiga meeting din jiya a Office. "Sannan kuma Sir ka manta papers na background Information din a Office, dole zaka buƙace su kafin a shiga meeting ɗin." Ya sake motsa hannunsa a cikin gashin kansa. "Na sani Martha, yanzu kuma ban san ya za'ayi ba gashi motata taƙi tashi, amma bari na kira Ishaq sai a ɗauko min tasa." "Okay sir." Ta amsa muryarta a ƙasa. Da haka suka gama wayar sannan ya shiga laluben nambar Ishaq ɗin da har yanzu bai dawo ba, bugu ɗaya biyu kuwa ya ɗaga. "A ina ka ajiye muƙullin motarka?" "Me za'ayi?" Ishaq ɗin ya amsa daga cikin wayar. "Motata ta samu matsala ne kuma ina da meeting anjima." "Ka kira Jamilun?" (Makanikensu.) "Ban kira shi ba, tunani nake sai anjima tukunna saboda gabaɗaya na manta da meeting ɗin ne." Dariya Ishaq ɗin yayi daga ciki yace. "Wallahi tayar motar nan a sace na tafi na barta, I don't know ma ya take take yanzu." Ya girgiza kansa kafin yace. "Baka da amfani." Da haka ya kashe wayarsa, ya kira Malam Sani. "Yallaɓai Barka da safiya." "Barka dai Malam Sani, nace dan Allah akwai mota a cikin gida ne?" "Ai kuwa Babu ranka ya daɗe, don su Baffa sun tafi gona a tasa shi da Baba Usman, ta Hajiya kuma a tsaye take tun wancan watan don haka na baro za'a kaita asibiti da ta Mami, school bus din kuma ka ganni da ita a ƴankaba." Sai kawai ya gyaɗa kansa alamun ya fahimta kafin suyi sallama ya kashe wayar, Martha ya sake kira yace ta kira direban kamfanin nasu kawai ya kawo ta kawo masa takardun. Da haka ya mayar da ball ɗin cikin booth ɗin motar sannan yayi hanyar cikin gidan, ya shiga cikin falon ya shiga cikin a lokaci guda da ƙamshin wani air freshener mai sanyi ya shiga hancinsa, yana tabbatar masa da cewar matar gidan ta tashi kenan, ya nufi hanyar dakinsa don yayi wanka ya shirya yayin da yanayin fuskarta a jiya da daddare ke haskawa a idonsa da kuma waɗannan siraran ƙafafun nata. *** Ƙarar kwankwasa kofar gidan ta shiga kunnen Amina a lokacin da take kammala aikinta na karshe a kitchen, ta san ba Ma'aruf bane, don a yanzu ƙwaƙwalwarta ta haddace yanayin nasa bugun kofar duk da ba kullum yake manta mukullinsa ba. Ta kashe gas ɗin da sauri sannan ta goge hannunta kafin ta fito, har yanzu wani iri take jin jikinta, mafarkin jiyan nan dana abinda ya faru bai gama barin tunaninta ba sam, don bayan ta koma ɗaki a jiyan bata iya komawa bacci ba, sallah tayi sannan ta zauna tunane-tunane har lokacin asuba, kuma sai bayan asubar sannan bacci ya ɗauke ta, baccin da baiyi nisa ba ƙarar wani abu ta tashe ta. Kuma ba'a dade ba wata yunwa ta dame ta, don haka a gurguje ta karasa karatun Azkar ɗinta sannan tayi wanka kafin ta fito zuwa kitchen, inda anan ta hango Ma'aruf ta cikin sliding windows ɗin dake wajen sink yana ball, ta fahimci ƙarar data tashe ta kenan. Yana sanye da wata loose-fitted riga fara kal, da bakin wando irin na sports, (track pants) da kuma takalmin ball, rigar ta fito da ƙirar jikinsa sosai, sannan yadda yake juya ball din a kafafunsa cikin kwarewa ya tabbatar mata cewar da a cikin filin ball yake tabbas zai iya yin kokarin ture kowa ya ci. Ta daɗe tsaye tana kallonsa cike da mamaki, don bata taɓa tunanin mutum so committed kamar shi zai samu irin wannan lokacin ba, ta fahimci a kullum ƙara sanin wasu halayensa dake bata mamaki take kuma har yanzu ba'a zo kan wani abu guda da tayi hasashensa game dashi a baya ya zama gaskiya ba. Komai zuwa yake saɓanin tunaninta, ita har yanzu bata ga wata alama ta ciwon nan nasa da ta riga ta gama tsorota dashi ba, shi yasa zuciyarta ke ta tantama ma akan idan shi ya rubuto mata wannan saƙon, har Fatima ta gayawa cewa in dai ba warkewa yayi ba, to ba koyaushe ciwon ke tashi ba. Shi yasa tare suka yarda da tsarinta na kyautata zamansu, da tunanin idan ya san bata da niyyar cutar dashi, ba lallai yayi mata wani abun ba duk lokacin da ciwon nasa ya tashi. Sai dai ita bata tsara da yadda zuciyarta ke jin dadi tun lokacin da ya fara cin abincin nata ba, jiya duk da rikicewar mafarkin nan da take ciki sai da zuciyarta ta faɗa ganin kwanukan abincinta a gefensa... Tunanin hakan ya tuna mata da yadda ya riƙe hannunta a lokacin, har yanzu tana jin kamar shatin yatsun sa akan fatar ta, tana jin kamar akwai wani abu dake ƙonewa a jikinta saboda tasirin yadda yatsun nasa suka zagaye duka hannun nata gabaɗaya. Da wannan tunanin ta kammala haɗa abincin breakfast ɗin lokacin da ta tsinci bugun ƙofar nan. Kayan jikinta riga da skirt ne na wata atamfa ash da tun ganinta da ita da farko tayi mata kyau wa ido, kuma sai akayi sa'a mai dinkin ya zabi wani ɗinki mai kyau da ya dace da ita don haka suka karbeta sosai, kuma yau bata saka mayafin data saba ba sai ta yiwa ɗankwalin V kawai ta yafa shi a haka. Ta buɗe ƙofar lokacin da hoton wata budurwa ya shiga idonta, doguwa ce, fara, kamaninta na yare ne amma kuma kyakkyawa ce, ta bazo gashin data ɗora a saman kanta mai kyau sannan matsatstsiyar rigar data saka ma mai kyau ce, don ta fito da kowanne lungu da saƙo na jikinta yayin da hannunta ke rike da wata ƙatuwar jaka irin ta aiki. "Good Morning my name is Martha, I'm..." ( Barka da safiya, sunana Martha, nice...) "She's my sectary." (Sakatariyata ce.) A lokaci guda muryar Ma'aruf ta faɗa daga bayanta, kuma ba tare da jiran komai ba taji hanayensa masu dumi dun sauka a bayanta, daidai wajen da zip din rigarta ya fara, sannan ƙamshin turarensa ya cika hancinta. Bata san lokacin da ta juyo da kanta ta kalle shi ba, idanunta na nuna mamakin da dukkan wani abu mai hankali a jikinta ke yi na yadda ya tsaya kusa da ita amma shi ba ita yake kallo ba, wadda ta kira kanta da Martha din yake kallo da wani dan guntun murmushi a leɓɓensa. Kuma bata sake shiryawa ba sanda taji ya jawo ta baya kaɗan yana haɗa ta da jikinsa, kanta ya tsaya daidai kafaɗunsa. "You're welcome Martha, meet my wife Amina Sulaiman." Sai da numfashin Amina ya katse a ƙirjinta jin yadda ya ambaci cikakken sunanta amma hakan baiyi nisa ba saboda Martha da ta miƙo mata hannu tana jiran su gaisa, sai tayi saurin mika mata nata itama tana murmushin da bata san a yaya ya fito ba. "You came with everything right?" (Kinzo da komai ko?) Taji muryarsa daga saman kanta tana sake tambayar Martha ɗin wadda ta ɗaga kai. "Yes sir, everything is intact, I just need to explain some things to you about Document A." (Eh yallaɓai, komai ya cika bayanin wasu abubuwan kawai zan yi maka.) Har yanzu da murmushi a fuskarta ta amsa, kuma sai kawai yasa hannunsa ya sake matso da Amina gefensa, suka bawa Marthan hanyar shiga ciki, ta wuce su kuwa tana ƙoƙarin fito da takardu da kuma labtop daga jakar hannunta. "Kin tashi lafiya?" Muryarsa ta tambaye ta tun kafin ta dawo da hankalinta kansa, sai tayi baya da ƙafafunta da sauri wanda hakan yasa ya saki hannun nata, kuma maimakon ta amsa sai tace. "Barka da safiya." Ya shafo gashinsa ta baya. "Barkanmu dai, hope kin dawo daidai?" Ta san me yake nufi don haka ta ɗaga kanta sau biyu idanunta akan yatsunta, ya cigaba da cewa. "Wannan sakatariyata ce sunanta Martha zamu yi meeting anjima ne and I left my things a office shine tazo ta kawo min." Bata san me yasa yake mata bayanin mutanen dake rayuwarsa ba, Farko da Faruk ya fara, sannan wani Ishaq da har yanzu bata gabshi ba bands yawan wayar da take jin suna yi, sai kawai ta ɗaga kanta a hankali alamun ta fahimta. "Zamu ɗan yi briefing a ciki, ba zaki damu ba?" Da sauri ta sake girgiza kanta, a wane dalilin zata damu, gidanta ne? ya gyada kansa shima sannan ya juya ya shiga ciki, hannayensa duka biyu sanye a cikin aljihunsa duka biyu, don rigar shaddar dake jikinsa bata kai gwiwa ba, kayan kamar ma sababbi ne, light brown, suna ta kyalli a cikin hasken safiyar. Wajen da ya dora hannunsa a bayanta ya sake ɗauka da irin abinda take ji a hannunta, sai kawai ta shaƙi wani numfashi mai nauyi a ƙirjinta sannan ta rufe ƙofar falon a hankali. *** "Me? Me kika ce Amina? Ya kawo wata arniya cikin gidan da sassafen nan?" Muryar Fatima ta faɗa cikin wayar dake kare a kunnen Amina, a hankali ta rufe idanunta sannan ta kai kofin shayin dake hannunta baki ta kurɓa. "Ba yadda kike tunanin bane Fatee, yace min sakatariyarsa ce, kuma zancen aiki ma suke tayi wai meeting suke dashi anjima." "Duk da haka ni dai banga wannan ya dace ba, ko ba komai gidan aurenki ne ya kamata a mutunta ki a cikinsa ko ba komai." Saura kaɗan murmushin da take yi ya suɓuce a cikin wayar saboda yadda Fatiman ke yawan fadar 'Gidan aurenta' ita kanta da take ciki bata ganin hakan kamar gaske tunda har yanzu babu wanda ya san abinda gobe zata haifar. "Ni sai naji muryarki ma kamar akwai wata damuwar daban bayan wannan, me ya same ki?" Fatiman ta sake tambaya, sai tayi ajiyar zuciya kawai, Fatima ta santa ciki da bai kwatankwacin yadda Amma ta santa, don sau da yawa ma abubuwan da zata iya ɓoyewa Amma da Fatiman zata yi shawara su haƙa su binne, ko Maryam da take ƴaruwarta ba komai nata ta sani kamar yadda Fatin ta sani ba, Don haka a yanzu ma dalilin kiran da tayi mata kenan, sai gashi ta gane tun kafin ta kai ga gaya mata. "Wani mafarki nayi da ya tashi hankalina jiya, ban taba irinsa ba Fatee, wallahi na tsorata sosai don har na farka ina jin kamar gaske ne." "Ya salam! Allah ya kyauta, kinyi addu'a dai ko?" Tambayar ta dawo mata da muryarsa sanda ya tambaya jiya 'Kinyi addu'a?' "Nayi, har asuba ma ina ta nafila, amma da na sake tunowa hankalina yake kara tashi, gashi na kasa fahimtar komai a cikinsa." "Babu abinda yake nufi insha Allah, ki cigaba da addu'a kawai kina kokarin yin taka-tsan tsan da komai insha Allah ba abinda zai faru Amina. Zanje wajen Malam mai almajirai anjima insha Allah in saka ayi miki rubutu, wataƙila wani satin zamu zo da Maryam sai in taho miki dashi." "Ba watakila ba, ku zo dan Allah Fatee..." "Kin san Amma ce tace sai an kwana biyu tukunna." Ta katse ta, sai ta girgiza kanta kamar tana kallonta. "Wallahi ko kullum zaku zo na gaya miki mutanen nan basu da matsala Fatee, yanzu kwana biyu ma kusan kullum ni kadai nake yini saboda duk sun koma makaranta, babu mai shigo min." Fatima ta girgiza kanta itama. "A abinda muka sani yanzun kenan Amina, gwara mu jira mu ga abinda lokaci zai haifar kafin komai ya daidaita, kar a sake ɓallo wani abu daban." Ta haɗiye wani abu a makogwaronta kafin ta amsa. "Toh shikenan. Ki gaishe min dasu Mamah da Ahmad idan yazo." Sai Fatiman tayi dariya tace. "Na gaya masa waccar gaisuwar taki ma sai cewa yayi wai kina matar auren yanzu kike cewa a gaishe shi? Wai in gaya miki kiyi azumi guda uku." Suka yi dariya a tare kuma da haka suka yi sallama fuskar Amina ɗauke da murmushin dake cike fal da kewar gida kamar kodayaushe. Ta ajiye wayar a gefenta tana kallon lokacin daya nuna akan ɗan screen ɗinta kafin hasken ya ɗauke. *** "Eh, yanzu zan fito... I will be there in 10 minutes insha Allah. " Ma'aruf ya faɗa cikin wayar da yake yi a lokacin da ya fito daga ɗakinsa. "Idan kana yiwa Allah Faruq kar ka tsaya a wani wajen, Let's not make them wait." (Kar mu barsu su jira.) Abinda aka faɗa a cikin wayar yasa shi kallon lokacin a agogon hannunsa kafin ya kashe wayar, a yanzu ya shirya cikin wasu kayan daban ba na safe ba, ƙarfe uku daidai, Martha ta daɗe da tafiya kuma shima bai daɗe da tashi daga kan system ɗinsa ba. Don bayan tafiyar Marthan anan Amina ta same shi da kayan breakfast ɗinta, ta durƙusa har ƙasa ta ajiye a gabansa, ya tuna yadda skirt din kayanta ya baje a kan carpet ɗin lokacin da ta durƙusa, a lokacin yaji yana don ganin yadda ƴan siraran ƙafafun nan nata suka lanƙwashe da durkusawar, kuma bata ce komai ba ta shiga zuba masa kawai, idonta a kasa, dogwayen gashin idon na sama ya haɗe dana kasa kamar ta rufe su ne gabaɗaya amma kuma tana cigaba da abinda take yi. Bai san me yasa duk abinda tayi yake jin kamar wannan ne karon farko da yake fuskantar rayuwar aure ba, shekarar sa uku tare da Ruƙayya a matsayin matarsa, amma har yanzu ba'a zo wajen da yaga wani abu nata yayi kamanceceniya da irin rayuwar da yayi da Ruƙayya ba, gani yake kamar komai sabo yake faruwa. Yaso sunyi magana a lokacin nan, amma yawan aikin dake gabansa bai barshi ba, ya raina meeting din daga farko sai a yanzu da yaga yawan abinda za'a tattauna ya san cewa da gaske mutanen suke kuma idan har suka yi nasara ba karamin alkhairi zasu samu tare dasu ba, saboda haka dole ya ture komai gefe ya maida hankalinsa kan nazarin bayanan nasu, kuma watakila itama ta lura da hakan don tunda ta shiga ɗaki bayan yaci abincin tazo ta kwashe kayan bata sake fitowa ba. Jamilu yazo tun dazu yayi tabe-tabensa a motar komai ya dawo dai, dama ya sani gyaran ba lallai ya zama mai yawa ba tunda motar bata cika bashi matsala ba tunda ya siye ta, don haka bayan ya gama saka links din ya nufi hanyar kofa rike da wayoyinsa kawai, ya riga ya kai duk abinda yake bukatar tafiya dashi motar tun ɗazu, din ya kusan haddace komai, zuciyarsa dama idanunsa kawai biyo dukkan abinda ya san zaiyi magana akai suke. Ya ɗora hannunsa akan ƙofar falon har ya buɗe lokacin da yaji muryarta. "A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a." Idanunsa suka juyo da sauri zuwa inda take tsaye, daga hanyar koridon nan ne alamun daga daki ta fito, hannunta na hagu na riƙe da wani baƙin bokiti data ciko jikakkun kaya dasu, yabi hannun nata da kallo da kuma gaban rigarta daya jiƙe yana tabbatar masa wanki tayi, ɗankwalin da take yafe dashi tun safe ta ɗaura shi a yanzu, yayi baya ma kamar zai zame gashinta na fitowa ta gaba, mai laushi ne da alama don duk ya tashi sama. Bai san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskarsa ba kafin ya ɗaga mata kai. "Ameen ya Allah, nagode sosai." Kuma ga mamakinsa sai itama tayi nata guntun murmushin sannan muryarta ta ƙara fitowa. "Insha Allah meeting ɗin zai tafi daidai." Tana faɗin haka ta shige hanyar Kitchen ɗin dake gefenta bokitin na bin bayanta. *** Dab da magariba ne lokacin, Aminu ya kammala komai na aikinsa na ranar a garejinsu, kuma har yayi sallama da kowa ya fito bakin titi lokacin da wayarsa tayi kara, yana tsaye da gefen titin ya dauko ta ya duba, Baba ne, don haka ya dauka da sauri ya kara a kunnensa yana gaishe shi. "Lafiya kalau Aminu, kun tashi ne?" "Eh Baba, yanzu ma na fito zan taho gida." "To ka biyo ta nan, akwai kayan da zaka dauka sai mu tafi tare." "Insha Allah Baba gani nan." Da haka ya kashe wayar, ya sauke ta ɗaga kunnensa daidai lokacin da mai mashin ɗin ya taho da wani irin saurin da ba Aminun kaɗai ba hatta mutanen dake baya dashi basu ga wucewarsa ba sai dai ƙarar injin mashin ɗin da kuma sanda yabi ta kan Aminun dake tsaye a bakin titin ya take shi tun daga kan ƙafafuwan sa. Salatin mutane har da ihun wasu ya gauraye iska a lokacin da mai mashin ɗin ya murde kan mashin ɗin ya miƙe titi ba tare da ta tsaya ba, kansa na dauke da hular kwano baka don haka babu wanda ya iya ganin fuskar sa. Wasu daga cikin mutanen suka bishi da jifa amma babu wanda ya same shi, gudu kawai yake yi har lokacin da ya fita daga unguwar baki ɗaya, ta lunguna ya dinga gujewa danja ba tare da ya tsaya a koina ba har ya zuwa unguwar Sardauna Cresent ƙofar gate ɗin gidan da ya fito, inda tun kafin ya karasa mai gadin dake zaune a waje yana jira yayi saurin buɗe masa gate ɗin ya shige. A gaban wata ƙatuwar bishiya dake harabar gidan ya tsayar da mashin ɗin sannan ta cire hular kwanon dake kansa, daidai lokacin da wayarsa ta shiga fitar da karar vibration daga aljihunsa. Ya ɗago ta ya danna wajen amsawar ba tare da ya damu ya duba sunan mai kiran ba. "Awa ta biyu a waje kafin yaron ya fito." Ya faɗa yana ƙoƙarin balle maɓallin rigarsa na gaba. Daga ɗaya ɓangaren wayar, Hajiya Kilishi tayi murmushinta mai armashi kafin tace. "Kace min an gama kawai Awwalu." "An gama Hajiya, kema kin san komai daidai yake tafiya." Ta gyaɗa kanta a hankali, tabbas haka ne, komai daidai yake tafiya, me yasa ma zata damu da tambaya? Awwalu ya taɓa kasawa umarninta ne?ko kuwa ta manta sanda yayi babban aikin da yafi wannan a wajen hatsari ne ma? Aikin da shine ginshiƙi samun ƴancin da take kirgawa dashi a kowacce nasarar da take samu. Bakinta ya sake tafiya da wani murmushin, abinda ya faru yanzu tsaraba ce ga Amina, don ba'a banza zata buɗe mata fuskarta ba, ba'a banza zata san wace ce ainihin Kilishi ba, dole ne ta tunkare ta da kakkarfar hujjar da kokwanton ikonta ba zai taɓa samun waje a zuciyarta ba.... Aminu shine farko a yanzu, kuma idan komai ya tafi daidai zai zama na karshe, amma da an samu wani akasi ƙofar ta buɗe kenan, duk wanda ya jiɓanci Amina ya shigo cikin lissafinta. Zata ɗaure Amina ne da jijiyoyin jikinta, bata isa ta tsallakewa dukkan sharrinta ba a yanzu, ta riga ta shigo cikin jerin mutanen da take juyawa da yatsan hannunta. "Ya batun Ma'aruf ɗin Hajiya? Na gaya miki yayi nisa a binciken da yake yi, idan har ya riga mu nemo inda Mr. Okafor yake wallahi abubuwa zasu canja daga kalar da muka san su, ya kamata ki tsayar dashi har sai mun riga shi nemo mutumin nan mun tura shi lahira tukunna." Muryar Awwalun ta katse ta daga tunaninta, kuma a lokaci guda sai murmushin dake kan fuskarta ya ɗauke, yanayin fuskarta ya koma wani iri da babu abinda zaka tsinta a ciki, ta haɗiye wani abu a cikin maƙogwaronta tana kallon tarin magungunan Ma'aruf ɗin da ta baje daga kan gadonta, a hankali ta girgiza kanta sannan tace. "Kar ka damu Awwalu, ina sane dashi so nake ya kammala da mutanen RTL ɗin nan tukunna, idan sun gama daidaitawa kuma kuɗaɗen sun shigo zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne, kafin ya dawo hayyacinsa munyi gaba da kuɗin kuma munyi gaba da shi Mr. Okafor ɗin... Kamar koyaushe sai bayan ya tashi zai fara lalube cikin duhu!" *** #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA BIYU. Life is what happen to us when we are busy making other plans. -Unknown. ** Ranar lahadi ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma, Amina na tare da Samirah da kuma Munaya a kitchen suna aiki tare da hirarsu wanda mafi yawanci Samiran ce ke tsokanar Munaya akan zuwan da tayi, tunda tun farko Samiran ce ta fara zuwa kafin ita kuma ta shigo m daga baya. "Wallahi sai ayi baƙi kashi-kashi su zo gidan nan su tafi baki ganta ta fito ba, amma kiga wai itace yanzu tazo taya aiki babu gaira ba dalili." Cewar Samiran a lokacin da take daka tafarnuwa ƴar kadan da zata saka a miyar dake kan wuta daga bayanta. Munaya tana yanka carrots ta ɗago ta kalle ta tace. "Ki kara faɗar abu guda ɗaya ki gani idan ban jefe ki da grater nan ba." Amina tana murmushi daga inda take blinding abarba tace. "Ki ƙyale ta haka mana Samirah, shikenan don tazo sai da dalili? Da nan da cikin gidan ai duk ɗaya ne." Samiran ta girgiza kanta. "Ba zaki gane bane Aunty Amina, saura fa sati biyu ta fara exams, da su Zahra suna nan zasu gaya miki a irin wannan lokacin ba'a ganinta wallahi, idan ta shiga ɗaki sai ta yini akan littafi sallah ce kawai ke tada ita, ko Hajiya sai dai tayi ta faɗan taci abinci, Allah karatun da take yi har na gama rayuwata a duniyar nan ba zanyi rabinsa ba..." Bata karasa ba kuwa lokacin da Munaya ta saita daidai bakinta da wani katon karas din dake gefenta ta jefe ta dashi, amma duk haka Samiran bata yi shiru ba, ta cigaba da bayanin ta tana faɗin ita bata yarda da zuwan nan nata ba sam, wanda ke saka su dariya. Amina ta tsiyaye ruwan abarbar a hankali cikin wani katon bowl tana kokari kar ya taɓa ciwon hannunta da bata daɗe da jinsa ba wajen yanka albasa, tana jinsu har yanzu Munaya na rokonta akan ta kyale ta amma Samiran taki yin shiru. Munaya tana da saukin kai sosai, don tazarar shekarun dake tsakaninsu da Samiran da ɗan yawa, amma idan suna hira irin haka ba zaka ce ba, ta juya tana kallonsu, ita kanta dai ta ɗanyi mamaki zuwan Munayan tunda tun bayan ranar da suka zo gabaɗaya suka gaisa sau ɗaya ra kara shigowa ranar da suka yi zancen littafin nan. Samirah ce dama kusan kullym zata leko ɗan bsyami ko saƙonta, a dazu ma tazo kawo mata wata darduma ne mai kyau daga Hajiya Maimuna taga tana aikin shine ta tsaya don ta taya ta, bata daɗe ba kuma sai ga Munayan itama ta shigo, ganin suna aikin yasa itama ta tsaya taya su. "Ki cigaba Kar ki fasa, I have my ways of torturing you kin sani wallahi." Munayan ta faɗa yayin da suke dariya dukkaninsu, Amina ta ɗauko bowl din da ta juye ruwan abarbar ta taho don ta saka shi fridge ya ɗanyi sanyi kafin ta ƙarasa abinda zata yi tazo haɗa lemon. Fridge ɗin yana daga gefen kofar shigowa kasancewar shine na karshe a yadda drawer kitchen ɗin take a jere, don haka ta taho wajen daidai lokacin da Ƙofar kitchen din ta buɗe Ma'aruf ya shigo ciki, yana sanye da wata loose riga fara mai dogon hannu, gashin kansa a barbaje kota'ina kamar yadda yake tun safe kasancewar bai fita ba yau, amma babu banbanci da cewar yana nan din, don tun safen yana ɗakinsa yana faman wani aikin a computer, banbancin jiya da yau shine a yanzu fuskarsa fayau take, babu gajiya irin ta jiya ko kadan, ya riga ya manta duk wannan tunanin meeting din nan, don bayan dawowarsa a jiyan ya bata labarin cewa komai ya tafi daidai tsakaninsu da mutanen da suka yi meeting ɗin. "Kinyi addu'a mai kyau kuma Allah ya amsa." Kalaman da ya gaya mata kenan a jiyan wanda ta kwana suna yawo acikin kanta. Shi yasa a yau ma da safe breakfast mai daɗi suka yi yana kara gaya mata irin nasarar da suka yi suka shawo kan mutanen nan ɗaya kamfanin suka kulla alakar kasuwancin a tsakaninsu, hirar dake ƙara sawa tana fahimtar abubuwansa da yawa, tana jin zuciyarta na canjawa game da tunaninta akansa, wasu abubuwa da yawa a cikin kanta na gaya mata cewa ba shine wannan Ma'aruf ɗin da ya bata wannan saƙon ba... Ba shine kuma wanda Iyayenta suka gaya mata yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba. Shi yasa ko da ya gaya mata cewa Ishaq ɗin da suke waya kullum ya dawo daga tafiyar da yayi zai zo a yau, zuciyarta tayi tunanin aƙalla ta tarbe shi da irin tarbar da ya kamata, ba don komai ba sai don ta san hakan ne ya dace kuma ko zata yiwa kanta ƙarya ta sani cewa tana son yadda zamansu ke tafiya duk kuwa da yadda koina a tunaninta ke gaya mata cewa akwai abinda ke shirin faruwa. Ƙafarta ta ƙarasa wajen Fridge ɗin ne daidai lokacin da ya shigo, taga idonsa ya haska da mamaki yana kallon su Munayan da kuma aikin da suke yi. "Me yake faruwa anan?" Muryarsa tasa dukkaninsu juyowa a lokaci guda, kuma a taken fuskar kowannensu ta faɗaɗa da murmushi yayin sa Munaya ta kira shi cikin wani abu mai kama da waƙa. "Yayaaaaa B...." A ƴan kwanakin nan Amina ta fahimci kusan duk sanda suka ganshi haka ne, haka gaisuwarsu ke farawa kamar sun daɗe rabonsu dashi, hakan ya tabbatar mata cewar ba ganinsa suke yi sosai a baya ba, a yanzu ne lokaci ya kawo musu shi kusa dasu wataƙila kamar yadda suka saba a ganinsa a baya. Kuma kafin tace wani abu, dukkansu suka ajiye mata aikinta sunyi wajensa, wani abu ya faɗa a zuciyarta ganin yadda kowannensu fuskarsa ke ɗauke da fara'a sun baibaye shi da maganganun da kallon fuskokinsu kawai yake yi, ba irin Samirah da ta shiga bashi labarin da ta gama bata a ɗazu na wani competition ɗin kamfanin Maggi da aka zaɓe ta zasu je suyi a Abuja, Munaya kuma tana ta maimatawa wai ta gaya masa labtop ɗinsa take so ko kuma ya siyo mata wata sabuwa irinta... Me yasa ne wai take tunanin akwai wani rami a rayuwar waɗannan mutanen? Tana jiyo muryoyinsu har lokacin da ta shiga store don neman wani abu ba tare da ita taxe komai ba, kuma ba'a daɗe ba taji an ƙwankwasa kofar store ɗin dake buɗe a hankali sau biyu kafin muryarsa tayi magana a bayanta. "Akwai ruwa anan?" Ta juyo ta kalle shi, yana tsaye daga ƙofar store ɗin, ta manta cewa ruwan dake ajiye a kitchen ya ƙare tun dazu kuma bata fito da wani ba, don haka da sauri ta juya bayanta inda katan din ruwan yake a jere ta buɗe na saman ta ɗauko ɗaya, yana tsaye yana kallonta har ta ƙaraso ta miƙo masa, kuma ga mamakinta tana ƙarasowa sai kawai ya hado robar ruwan da hannunta gaba ɗaya ya jawo ta zuwa gabansa, ƙafafunta suka taho dab dashi yayin da ya dago da hannun nata yana kallo, ba shiri numfashinta ya katse a ƙirjinta lokacin da yasa ɗan yatsansa ɗaya ya taɓa daidai wajen data yanke ɗazu. "Me ya faru?" Muryarsa ta fito a yana kallon ciwon. Sai da ta haɗiye yawu tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin tace. "Da wuƙa na yanke." "Me kika saka a wajen toh?" Muryarsa ta sake tambaya a hankali ta yadda har tana jin ƙarar wukar da Munaya ke amfani da ita daga can kitchen ɗin, da kuma nuryar Samirah da ta fita waje tana waya. Ta sake haɗiye wani yawun a makogwaronta. "Ba komai na wanke ne kawai." Sai ya kawo daya hannunsa yasa su duka biyu ya rike natan, sannan ya buɗa ciwon sosai don yaga zurfinsa, zafin ya tafi har cikin kanta ta runtse idanunta da sauri tana cije lebbenta, sai yayi saurin sakin wajen sannan ya rufe yatsan nata da duka hannayensa biyu kafin yace. "I'm sorry na duba ne na ga yadda yayi and it was deep." (kuma yayi zurfi.) Ta buɗe idanunta a hankali sannan ta ɗaga kai ba tare da tace komai ba, kuma bai saki hannunta nata ba sai ya cigaba da rike shi yana kallonta, hakan yasa ta ɗago da idonta kalle shi da ɗan ƙaramin mamaki. "Aikin me kuke yi haka?" Ya tambaya tun kafin tayi wani tunanin, sai ta girgiza kanta. "Abinci ne kawai." "Kala-kala haka?" Muryarsa ta sake fitowa da wani abu da ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta yana kassara ƙarfinta, taji kamar wani yana zazzaga mata wani magani mai karfi ne da aka haƙiƙance zaiyi tasiri akanta, kuma a yadda tata muryar ta fito tana rawa, kamar dama anyi mata baki ne cewar hakan ne zai faru. "Kace abokin ka zai zo." "Ishaq?" Ya tambaya kai tsaye sai kuma ya sake cewa. "Ya salam duka saboda shi kuke yin wannan aikin?" Shi ko kadan unaninsa bai kawo masa cewa don Ishaq ɗin zai zo ya kamata ayi wani abu ba, duk da a baya ma idan zaiyi baƙi Ruƙayya kan shirya musu wani abun amma a yanzu ya riga ya manta da hakan kwata-kwata, saboda haka a lokaci guda zuciyarsa taji dadin hakan, sai kawsi ya gyada kansa yana kallonta sannan yace. "Thank you." Ta ɗaga kanta da sauri itama tana fatan hakan ne karshen zancen nasa, don bata san me zata zama ba idan har ya cigaba da magana rike da hannunta a hakan. Kuma kamar yaji fatanta, sai ya zare hannunsa nasa a hankali, taji ɗuminsu yana barin fatarta. "Zan nemo abu in rufe miki ciwon anjima insha Allah." Da haka ya juya ya fita rike da robar ruwan a hannunsa. A lokaci guda Amina taji kamar numfashinta yayi wata tafiya mai nisa ne sai a yanzu take iya zuƙo shi, ssi kawai ta juya itama ta ɗauko wata robar ruwan ta balle hancinta ta shiga sha yayin da bayanta ya jingina da drawers din store ɗin. Sai da ta kusa shanyewa sannan ta tsaya, tasa bayan hannunta tana goge wanda ya zuba a gefen bakinta. Bata san me yake shirin fara damunta ba amma koma meye, so take ta tunawa kanta cewa duk abinda ke faruwa wannan gaske ne ba labari ba da komai zai tafi daidai, abubuwa ba zasu tafi kamar a mafarki tare da mutumin da daga shi har ita basu san juna ba sai bayan aurensu kuma har yanzu bsta san manufarsa akanta ba. Ma'aruf ba zai taɓa sauko da kansa haka akan ita ɗin da ba kowa ba, don ta sani cewa bayan matar daya aura Allah kadai ya san matan daya sani a a rayuwarsa ko ma wanda yake tare dasu a yanzu, to don me yasa hankalinsa zai tsaya akan ita din da ba kowa ba, ita ɗin da sa baiyane yake cewar ba sa'ar rayuwarsa bace. Ta girgiza kanta tana kokarin rufe robar ruwan, wannan lokacin kamar zubar ruwa ne kawai kafin zuwan tsawa, kamar iska ce mai daɗi kafin guguwa, sannan kamar kaɗawar ruwan teku ne a hankali kafin ambaliyar sa, akwai wani abu dake jiran ta bayan wannan, kawai dai dan adam baya taba sanin lokacin da ƙaddara ko kuma wata masifar rayuwar ke zuwar masa ne. Muryar Amma ta cikin mafarkin nan ta gifta a cikin kanta lokacin da take cewa "Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina..." A hankali tayi ajiyar zuciya tana fatan Allah yasa koma meye ke shirin faruwa ta iya tunkararsa da ƙafafunta a tsaye, daidai lokacin da a zahiri ta jiyo muryar Samirah ta shigo tana kiranta. "A ina kika ajiye sugar?" Sai kawai tayi sauri ta ƙarasa goge bakinta sannan ta ajiye robar ruwan ta fita. **** Karfe Bakwai daidai Ishaq ya iso, kuma Amina bata san me ya faru ba, don minti biyar bayan zuwansa sai ga sallamar ɗaya abokin Ma'aruf da shima ta riga ta haddace shi a waya mai suna Faruk. Su uku kaɗai suka cika falon da surutu kamar su biyar, kuma duk yadda take ganin Ma'aruf na da magana sai a lokacin taji nasa mai sauki ne, don kafin taji muryarsa taji tasu da yawa musamman Faruk ɗin, don shi yafi Ishaq yi mata magana sosai ma, har matarsa da ƴaƴansa yayi alkawarin kawo mata tunda yace yanzun a sama kawai Ma'aruf ya kira shi yace masa yazo. Kuma har lokacin da suka zo ɗin su Munaya basu tafi ba, Samirah dai taso tafiya amma sai Munayan tayi ta roƙonta akan su ƙara tsayawa tukunna, wani abu da ya ƙara bawa Amina mamaki don ita kanta ta san babu wani dalili Munayan ba zata yi ta cewa su tsaya ba. Ilai kuwa a lokacin da suka je kai musu abincin nan, a lokacin ta samu amsarta, saboda idon Ishaq na kan Munaya tunda suka shiga har ta juya Kitchen don ta ɗauko wani abun, kuma zata rantse ma taga sanda suka yiwa junansu murmushi lokacin da take zuba masa lemo, Allah ya sani yau ta fara ganin Ishaq ɗin amma sai taji zuciyarta na jiyewa Munaya daɗi idan har hasashenta akansu gaskiya ne, don duk inda nutsatsen namiji yake za'a saka Adam a wannan layin, kuma itama Munaya babu ruwanta da wani hargitsi sam. Sun ji daɗin tarbar da suka samu kwarai, don ba'a kalamansu kaɗai ta fahimci hakan ba, har a fuskar Ma'aruf da kuma yanayin kallon da yake mata tun lokacin da taje ta sako wani dogon hijabi bayan shigowar su, wani abu da ita kanta taji ta kyauta da tayi hakan. Bayan sallar isha'i ne sannan suka yi musu sallama suka fita, kuma sun daɗe a waje suna magana don har bayan tafiyar Faruk ɗin shi da Ishaq suna nan, har su Munaya suka tafi ta ƙarasa wanke iya kwanukan da aka ɓata kasancewar basu tara wanke-wanken ko ɗaya ba dama a ɗazu. Kuma tana sallah lokacin da ta jiyo ƙarar fitar motar Ishaq ɗin, sai dai har ta idar ta gama addu'o'in ta da komai bata ji lokacin da Ma'aruf ya shigo ba ko kuma don haka ta ƙudirta a ranta cewa cikin gida ya shiga. Da wannan tunanin ta ninke sallayar tare da hijabin ta ajiye su a gefe, ta ɗauko wayarta don kiran su Amma, sai dai daga layin nata har na Aminu bai shiga ba, kuma bata son kiran Baba a wannan daren, don haka ta bari zuwa gobe, ta nufi wardrobe ɗinta don ta ɗauko kayan bacci, wata sabuwar doguwar riga ta dauko sannan ta dawo gaban gadon don ta canja. Ɗankwalinta ta fara cirewa ta ajiye shi a kan gadon sannan ta shiga kokawa da zip ɗin rigarta, amma ga mamakinta saiya riƙe ɓam yaki ko motsi, gashi ciwon hannunta ba zai bari ta rike shi da kyau ba, na dama kuma yaki ƙarasawa can saman, dama tunda tazo saka kayan ta kula yana da matsala amma bata yi tunanin ta kai haka ba. Har sai da hannunta ya ƙage ta tsaya ta tattaro dukkan ƙarfinta sannan ta cigaba da jansa, kafin a lokaci guda kamshin turaren Ma'aruf ya shiga hancinta. *** A waje bayan Faruk ya tafi, sun dade a tsaye shi da Ishaq suna hirar tarin wasu abubuwan da suka shafe su wanda yawanci duk akan matsalolin dake baibaye da rayuwar Ma'aruf ne, sai kuma zancen Abdurrahim, ƙanin Ma'aruf ɗin dake can New York wata makaranta ta Bebaye irinsa, (Rochester Institute of Technology.) Don Baffa ya gaya musu cewa saura watanni biyu kawai ya kammala ya dawo gida. Bayan wannan sun tattauna zancen Hamida ma inda Ishaq yayi-yayi da Ma'aruf akan ya ɗauko yarinyar daga inda ya kaita ya dawo ta ita cikinsu, amma ya ɓata bakinsa a banza don ya riga ya rantse cewar Ruƙayya ba zata taɓa sanin inda Hamida take ba sai ya kammala da al'amarinta gaba ɗaya, ko shekaranjiya da Mami taso yi masa zancen itama kai tsaye ya dakatar da ita ta hanyar gaya mata cewa lokacin da zai ɗauko ta bai yi ba, don haka itama taja bakinta tayi shiru, don dukkaninsu sun sani cewar idan har ya furta abu, Baffa ne kawai zai iya sauke shi daga kansa, amma ko da suka yi magana da Baffan shima cewa yayi... "Wannan zancen naku ne kai da mahaifiyar yarinyar Muhammad, duk abinda kuka yanke idan har ba kuskure bane mu namu addu'a ne tunda kune kuke da iko akanta fiye damu. Kuma kowannen ku yana da ikon da zai riƙe ta, duk da dai a matsayinta na mace an fi so ta zauna a gaban mahaifiyarta, amma idan har za'a samu matsala wajen tarbiyarta ko lafiyarta kamar yadda aka fara yanzu, to zamanta a wajen naka zai fi." Wannan zancen na Baffa shi ya bashi ƙwarin gwiwar cigaba da shirin da yake da niyya wanda yake jiran lokacin kawai. Daga ƙarshe kuma suka ƙare da zancen ginin su wanda Ishaq ɗin ya gaya masa cewar ya samo wasu sababbin masu ginin da zasu fara aikin tunda Ma'aruf ya sallami waɗancan. Kuma baiyi mamaki ba da Ishaq ɗin baiyi masa zancen Amina ba, don ya riga ya fahimci cewa ba sai yayi ɗin bane, akwai wasu abubuwa da ba lallai sai sun furta su a tsakaninsu ba, wasu abubuwa ne da ƙarara kowannensu ke ganewa idan ɗayan yana ciki, don haka a yanzu ma Ishaq ya riga ya sani cewar ya riga ya yanke koma wane irin hukunci ne game da zamansu ba sai sun ɓata lokaci wajen biya shi ba. Da haka suka yi sallama, sabon maigadin da ya samo ya sake budewa Ishaq gate ɗin gidan, shi kuma ya koma ciki. *** Yayi sakanni biyu tsaye daga bakin kofar yana kallon yadda take kokawa da zip ɗin rigarta kafin ta ankara dashi, watakila jikinta ne kawai ya bata cewar yana daga bakin kofar, don a lokaci guda ta juyo da sauri tana kallonsa, fararen idanunta suka zare akansa yayin da a lokaci guda ta saki hannayenta duka biyun suka sauka a gefenta. "I'm sorry banyi sallama ba ko?" Sai ta girgiza kanta. "Babu komai ban ji lokacin da ka shigo bane." Ya cije lebbensa tsaye a jingine kofar kafin yace. "I'm sorry bana so in ɗauki lokaci ne kiyi bacci." Idanunsa na kallon fuskarta da yaga kamar tana ƙoƙarin kore wani abu wani abu mai kama da mamaki kafin ta tambaya. "Wani abu kake so?" Lokaci ne ya tsaya cak a cikin kansa da wannan tambayar yayin da fatar bakinsa ta bude kamar zai ce wani abu yana kallonta, tsakaninta da Allah ta fadi hakan ba tare da ta san tarin ma'anonin da za'a iya fitarwa daga kalaman nata ba, ganin tana cigaba da kallonsa yasa ya sake cije leɓɓensa na ƙasa sannan ya girgiza mata kai. "I want to treat your hand." (Hannunki zan duba.) Ya faɗa yana kallon yadda fuskarta ke nuna tarin yanayi kala-kala, ƙafafunsa suka tako cikin ɗakin a hankali zuwa inda take tsaye, kuma kamar a wani shiri sai iska ta buso daga windon da yake fuskantar su daidai lokacin da ya tsaya a gabanta, kuma bai ɓata lokaci ba yasa hannunsa ɗaya ya ɗauko nata mai ciwon nan. Gabaɗaya tsawonta iya kafadarsa ne, gashin kanta da babu dankwali ya taso sama yana shaida laushinsa, da zai iya a wannan lokacin zai zare ribbon din data ɗaure shi ne don ya sauko kafadunta yaga iya tsawonsa, amma sai ya daurewa wannan tunanin ta hanyar kallon yatsun hannunta da yake riƙe dasu. Ya san cewa shi mutum ne da yake ƙarbar respect daga ɗimbin mutane, kuma a iya kokarinsa yana kokarin ganin ya kyautatawa duk wanda ya shigo hanyarsa, da kuma kaffa-kaffa musamman a yanzu don ganin bai yi wani abu da zai iya cutar dasu ba, amma Allah ya sani bai taɓa haɗuwa da wanda a lokaci guda yaji zuciyarsa na tsoron ciwonsa akanta ba irin yarinyar nan, yarinyar da a baya bai damu da yadda zaiyi kokarin samun bayanin da yake so daga gare ta ba, Wani bandeji ne mai haɗe da audugarsa a jiki, don haka magani kawai ya ɗiga a jiki daga cikin wata ƴar kwalba sannan ya rufe ciwon nata dashi, ai kuwa ta runtse idanunta a lokaci guda tana jin zafin na tafiya har tafin ƙafarta. "Zuwa safe zaki iya cirewa sai a saka wani, insha Allah a kwana biyu zai warke." Ya faɗa yana sakin hannun nata, kuma duk da zafin da take ji haka ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta. Ya rufe maganin sannan ya wuce ta zuwa wajen da mudubin ɗakin yake, ya ajiye roll ɗin plaster da kuma kwalbar maganin akai sannan ya juyo ya dawo inda take tsaye tana cigaba da danne ciwon. Kuma bata yi wani tunani ba lokacin da ya tsaya a bayanta, dab da ita sosai, don haka da sauri ta juyo gabadaya ta kalle shi amma sai ya saka hannayensa duka biyu akan kafaɗunta ya juyar da ita. "Zan taimaka miki da zip ɗin ne..." Ya faɗa muryarsa na fitowa dab da kunnenta sosai, kuma kafin tayi ƙokarin kamo tunaninta muryar tasa ta cigaba da cewa. "Akwai abubuwa da yawa game dani a zuciyarki na sani, amma ina so a saman komai kisa a ranki cewar ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah." Ya furta hakan yayin da hannunsa ya kai kan zip ɗin, sauran yatsunsa na ɗaya hannun suna taba fatar bayanta, sai kawai ta rufe idanun gabadaya tana ƙoƙarin saita numfashinta, kuma da ja ɗaya kawai hannunsa yayi ya sauke zip ɗin sai dai bai kai shi har ƙasa ba, daga daidai tsakiya ya barshi, taji sanda yatsunsa suka dauke daga saman fatar ta, da kuma sanda yake matsawa, sai ta buɗe idonta lokacin da ya zagayo daidai saitin ta. "Nagode." Ba zata ba taɓa iya tantance yanayin yadda muryar tata ta fito ba, ya gyaɗa kansa. "You are welcome, sai da safe." Da haka ya juya ya nufi kofar ɗakin yana rufo mata ita. Sakan ɗaya, biyu, uku, suka wuce Amina tana ƙoƙarin saita numfashinta kafin a hankali ta ɗauko rigar baccin nan ta karasa abinda zata yi, wanda har ta gama komai ta kashe fitilar ɗakin kalamansa na yawo a cikin kanta. ...ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah. Sai kawai ta rufe idanunta sannan ta dunkule jikinta akan gadon, kuma bata bawa zuciyarta wani damar tunani ba don bata san buhu nawa zata kwance na tambayoyin da bata da amsar su a zahiri dama cikin kanta ba. Ya rabbi lakaal hamdu kam yanbaghi li jalaali wajhika wa adheemu sulɗaanik. Bakinta ya furta addu'ar hankali yayin da take jin ma'anar ta na tafiya har ƙasan zuciyarta. *** Washegari... Ƙarfe goma na safiyar Litinin, a irin wannan lokacin Amina ta saba da wani irin shiru don ko'ina tsit yake, duk wani mai fitar safe ya daɗe da yin gaba, ƴan makaranta da masu aiki da mafi yawanci sun fi yawa a kowanne gida. Tana daga kitchen a lokacin tana ƙoƙarin fara aikinta ta tsinkayi ƙarar ƙwanƙwasa kofar, mamaki ya ɗan kamata don ta san babu wanda zata yi tunanin zuwansa a wannan lokacin, ta gyara zaman ɗankwalinta yadda ta yafa shi sannan ta fito daga kitchen ɗin ta iso ƙofar falon kuma ba tare da tunanin komai ba ta buɗe ta,a lokaci guda siffar Hajiya Kilishi dake tsaye ta shiga idonta tun kafin sakon saninta ya ƙarasa ƙwaƙwalwar ta. Tana sanye da wata haɗaddiyar lafaya ruwan makuba (maroon) da ta nannaɗe ta tsaf a jikinta, fuskarta kamar kullum ɗauke da wannan murmushin nata, murmushin dake haska annurin fuskarta a kodayaushe yana ƙawata kammaninta. Babu dalili Amina taji gabanta ya faɗi amma tayi saurin kore hakan wajen yin nata murmushin itama. "Sannu da zuwa Mami, barka da zuwa." "Barkanmu dai Amarya. Yau dai na ajiye kyuiyata a gefe nazo ganin ɗakin amarya." Wani murmushin mai haɗe da kunya Amina ta sake yi kafin tayi baya don bata hanya tana kara fadin 'Barka da zuwa', kuma kai tsaye kuwa ta shigo haɗe da sallama yayin da ƙamshin daddaɗan turarenta ke rufo mata baya. "Wa'alaikum salam." Ta amsa sallamar tana rufe ƙofar har a lokacin da murmushi a fuskarta, murmushin da a lokaci guda ya ɗauke sakamakon juyowar da Hajiya Kilishi tayi tun kafin ta kai tsakiyar falon tace. "Idan akwai muƙulli rufe ƙofar dashi Amina, akwai maganar da zamu yi ne." Zuciyarta ce ta fara bugawa a kirjinta kafin ta juyo ta kalle ta, amma ganin murmushin dake kan fuskarta har yanzu, yasa itama ta dawo da wani dan guntu kan leɓɓenta sannan tace. "Toh Mami." Da haka ta rufe kofar tana ƙoƙarin gayawa zuciyarta cewa gabanta ba faɗuwa yake ba sannan ta juyo ta ƙaraso ciki. A lokacin ta zauna daga tsakiyar kujera mai cin mutum uku a falon don haka ita tameni waje daga ɗaya karshen ƙaton carpet ɗin ta zauna tana fuskantar ta. "Barka da Asuba Mami, fatan kun tashi lafiya?" Ba kallonta take ba amma daga yanayin yadda muryarta ta fito wajen amsawa ta fahimci har yanzu murmushin take yi. "Mun tashi lafiya, Ya bakunta kuma? Ko da yake ai naga su Samirah sun saka kin saba tuni." Bata ce komai ba illa wasa da karshen skirt dinta da take yi tana cigaba da murmushin da zata kira na dole, don bata san me yasa zuciyarta ta kasa zama waje ɗaya ba. Hajiya Kilishi ta kalli ƙaton screen din Tvn dake tsakiyar falon dama sauran kayan kallon da aka jera akan hadadden stand ɗin Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace. "Gidan shiru ke kaɗai baki ko kunna Tv ba?" Da wani murmushin a fuskarta tace. "Ai ba'a hada Tvn ba har yanzu Mami." Muryarta ta fito ƴar ƙarama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ƙanƙanta da kuma rauninta. "Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha'anin Tv ba. Sai ta sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin. "Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza'a makara ba ai." Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita. "Ina ziki je kuma?" "Mami, kayan breakfast zan kawo miki." Ta faɗa taka kallonta, sai ta girgiza kanta. "Barsu nagode, dawo ki zauna." Umarnin dake cikin muryar ya kaɗa hantar ta, taji wani abu yana ƙoƙarin ɓallewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna ɗin, hannunta na taɓa hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta. Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet ɗin nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun ɗakin da cewar. "Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?" Sai da ta haɗiye wani dunƙulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai. "A'a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba." "Ina wayarki?" Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa. Kan Tv's stand ɗin nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta saka ta a caji. "To matso ki kira su." Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa ta lalubo nambar Amma. Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa'a, bugu ɗaya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ƙirjinta tun kafin ta fahimci abinda take faɗa. "Amina yi haƙuri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa..." "Asibiti? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!... Me ya faru Amma? Me ya faru?" A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa yake, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta. Daga cikin wayar Amma tayi ƙokarin gyara muryarta kaɗan sannan tace. "Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun ce jikin nasa da sauƙi kar ki ɗaga hankalinki, yanzu mu ma zamu shiga mu ganshi..." Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta riƙe da wayar tasa hannu ta ɓare bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da ɓata wani lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama. Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sautin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ƙawata mata tarin hanyoyin da kullum suke ɓullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum huɗu ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar ɗin, cikon da take fatan zai zama mataki na ƙarshe da take da yaƙinin zai kai ga nasararta. "Barka da shigowa cikinmu Amina." Kalamai biyar ɗin data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman da take shirin ɓare mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta. *** Wane shiri Ma'aruf ke yi akan ƴarsa Hameeda da kuma Ruƙayya? Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq ya fahimta? Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya? Munaya and Ishaq, me kuke tunani? Hajiya Kilishi... Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata buɗe muku abubuwa da yawa game da ita... Babi na gaba zai nuna muku me ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta... Ba boka ba malam! #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA UKU. ~~~~~~~ There's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets. - Unknown. ** Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi. "Taɓa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta." Tayi shiru bayan ta faɗi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta. "Ya akayi Awwalu?" Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake ɗagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaɗai abinda zai sa ka san cewa idan ka taɓa ta ba zata tafi ta faɗi ba. Wataƙila magana guda ɗaya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda "Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce. Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..." Ta gyara zamanta kaɗan sannan ta cigaba... "... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika ɗauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taɓa samunsa ba ko zaki mutu sau ɗari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba. Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaɓi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke kaɗai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf ɗin da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na ɗora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole." A yanzu Amina tayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba'a saka masa rana. Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa. "Bari in ɗauko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na. Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata ɓulle ga matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa. Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ƴanuwana, don mahaifinmu matansa uku ne kuma ƙaramar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ƴaƴa tara, sauran biyun akwai mai goma sha ɗaya da kuma sha uku. Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take riƙewa, don haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani hatta mahaifiyata kuwa da hankalinta yafi karkata kan yayyena da suka fi girma a lokacin, don haka da lokacin shigata babbar sakandire yayi sai na samu mahaifina nace ya maidani makarantar kwana don zata fi mun daɗi, al'amarin kamar ba zai yiwu ba da ƙyar da rabo dai na samu na tafi. A can na hadu da ƙawayena biyu kuma ƴanuwan da zan iya kira da na jini wato Salamatu da Saratu, wadannan mutane biyun Amina sunyi min duk wani gata a lokacin zama na a makaranta da ya kamata ace iyayena ne suka yi min, hatta kuɗin jarabawar karatuna tsaf su suka biya min har muka kammala, don ban daɗe da shiga makarantar ba mahaifina ya rasu abubuwa suka sake harigitsewa a gidanmu. Kowacce mace taƙi fita tare da ƴaƴanta kuma aka ƙi a raba gado kowa ya koma yana zaman kansa ne da kuma zaman gasa a tsakani don kowacce mace tana so ne ace ƴaƴanta sune suka fi samun arziƙi, musamman Innata da take ganin itace ƙarama an riga an rainata ita da ƴaƴanta don haka bata damu da duk wata hanyar da yayyena ke bi su samo kuɗi ba indai za'a samun, burin kowacce kawai ace ita da ƴaƴan ta su ke ƙyallin maiƙo a gidan. Abinda nazo na tarar kenan bayan na kammala makaranta na dawo, wani abu da tun bana saka shi a raina har ya zamo kwanci tashi nima tunanina ya karkata ga hakan, sai dai ni tawa ƙwaƙwalwar ta raina irin hanyoyin da suke bi, na kasa yarda cewa mutum ba zai iya magance matsalolin kansa a rayuwa ba sai ya tsugunna neman taimakon wani daban, don haka na shiga amfani da ƙwaƙwalwata wajen cimma manufata. Almajirin da kakata ta riƙe Awwalu yana aikin masinja a wani kamfani, da taimakon sa da kuma dabara ta na samu aiki a kamfanin a matsayin mai gyara da kuma harhaɗa takardu... In taƙaice miki zance Amina, wata na biyu a wajen nan na fara karbar kuɗi sama da albashi na ba tare da kowa ya sani ba, kafin a shekara kuwa, ni da Awwalu muna samun daidai da abinda ma'aikatan wajen nan ke samu, ban taɓa bawa wani jikina ba sannan ban taɓa bin wani malami ko boka ba, da wayo da dabarata nake komai ta yadda babu mai zargina kuma dukkan wani bincike ba zai taɓa biyowa ta kaina ba. Kuɗin da nake samu a kowanne wata sai da ya zama hatta a cikin gidanmu babu wanda ake kallo sai ni, mahaifiyata da ƴanuwana duk suka dawo suka raja'a a kaina, aka shiga bani wani irin girma da ban san yana wanzuwa a duniyar nan ba, ya zama zan iya taka kowa a gidanmu in zauna lafiya, nasa aka rushe ɓangaren ɗakunan mu aka gina mana danƙarere da ya tsone idon sauran ƴanuwana kafin daga baya suma su dawo su kwantar da kansu." Muryarta tayi shiru a daidai wannan lokacin alamun ta tuna wani abu da ya saka ta murmushi, wani murmushi da har sautin sa sai da ya fito kafin tace. "A wannan lokacin ne kuma na nemowa kaina mijin aure Amina, munyi ƙoƙarin canja kamfanin aiki ne ni da Awwalu don na yarda da karin maganar da hausawa ke cewa zama wuri ɗaya tsautsayi, don haka muka je kamfanin Bakori a wata ranar laraba, inda kafin mu shiga na hango Alhaji Mansoor ya fito daga ciki ya shiga motarsa, tun da na ganshi a wannan lokacin na sawa zuciyata cewa shine mijin aure na, don haka bamu nemi aikin ba nace da Awwalu mu juya, kuma kafin sati ya zagayo na bi hanyar da sani na ya manne a zuciyar Alhaji Mansoor. Na kashe kuɗi sosai a wannan lokacin duk da ba sai na gaya miki yadda na aiwatar da komai ba zan gaya miki cewa sati guda na shafe ina siyan shafi guda a jaridar da Alhaji Masoor ke karantawa, ana wallafa hotona cikin irin ayyukan da na san dole suka ja hankalinsa. Har da masinjan ofis ɗinsa da ma direbansa na haɗa baki dasu suna bashi labaraina, kuma bayan ya yarda da auren nawa, sai da na toshe bakin mutane da yawa wajen fallasa wani abu mummuna akaina. Lokacin da na shigo gidan nan kuwa Amina da naga Maimuna, a lokaci guda na raina kaina na kuma ƙara yarda cewa sa'ata ce kawai ta shigo dani cikin rayuwar Baffa, don wanda yake da mata irin Maimuna babu abinda zai kaishi auren irina. Amma ban damu sosai ba, tunda na san na shigo daular arziƙi ne kuma na ciri tuta a cikin ƴanuwana da a lokacin suka maida ni kamar mahaifinmu saboda biyayya. Ban daɗe ba lokacin da Maimuna ta sami cikin Shukra ƴarta ta uku, don haka sai nayi amfani da hali irin nawa na ja ɗanta na biyu wato Ma'aruf a jikina, na so haɗawa har da Jamal ma amma shi da yake yafi wayo a lokacin sai ya mannewa uwarsa. Ni na yaye Ma'aruf da hannuna Amina, ni na raine shi tun daga wannan shekarun har zuwa girmansa, don ko bayan haihuwar Maimuna bai bar wajena ba itama kuma bata yi magana ba saboda nauyi na da take ji a sannan, don a lokaci guda na zage na karɓi gidan, ni nake yin komai musamman da bata da lafiya, bayan tayi haihu kuma ni nayi ɗawainiyar da ƴanuwanta ma basu yi ba, hakan yasa a lokaci guda na samu soyayyar kowannensu, hatta Baffa kuwa, don sanda ya aure ni ba zan tantance irin son da yake min ba, amma a cikin shekara guda sai da na tabbata ni da Maimuna munyi kunnen doki a zuciyarsa. Soyayyar kowa na siya tsakani da Allah don bana yarda da gaibu Amina, kamar yadda baba yarda da aikin wani boka ko malam da baya zuwa ko'ina, ni ina yin shiri na shekara da shekaru ne ba na wani ɗan lokaci kaɗan ba. A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana har ta kai na fara haihuwa nima, a wanann lokacin tsananin kirki da kyautatawata yasa na kere Maimuna a zuciyar Baffa ta yadda ita kanta bata damu ba, don tana ganin cewar na cancanci hakan." Tayi shiru wucewar wasu sakanni tana kallon Aminan kafin ta cigaba. "Bari na gaya miki wani daga cikin babban sirrina don ki ƙara tabbatarwa cewa da gaske nake al'amarina... Nice na gurguntar da Maimuna..." Babu shiri Amina ta ɗago ta kalle ta, idanunta na haskawa da tsananin mamakin da yake ƙaruwa akan wanda take ciki. Sai kawai tayi murmushi mai zurfi tana kallonta itama. "Ƙwarai Amina, ni na saka Maimuna ta rasa ƙafafunta, kin san dalili?" Ba ta bata damar amsawa ba ta cigaba. "Na gaya miki Maimuna tana kyau, to labulen ɗaki na kawai nake ɗagawa in hango ta ranar girkinta ta nufi ɓangaren Baffa, idan tayi kwalliyar nan bana iya daurewa kishina dake tasowa Amina, rana daya na yanke cewar ba zan iya jurar cigaba da ganin zuwanta ba don haka takanas na tafi asibiti na samu wani ma'aikaci a ɓangaren ƙashi, na bashi maƙuden kuɗaɗen da a lokaci guda ya bani wani magani mai kama da poison wanda ke lalata har ƙashin mutum. Kuma sai da na jira har bayan watanni huɗu da rashin lafiyar zazzaɓi ya kamata sannan na haɗa baki da wani yaro daga Nijar yazo har gida yayi mata allurar maganin nan a matsayin likita, kuma babu wanda ya san ni na dauko shi don nambarsa na sanya a wayar Baffa da sunan likitan gidan Dr. Ashiru, nace idan yazo yace Dr. Ashirun ne ya turo shi. Kuma bayan yayi mata allurar ƙafafun nata sun lalace gabaɗaya na bashi kuɗi ya koma ƙasar sa Nijar, shi kuma Dr. Ashiru yazo yace bai san yaron ba, da aka duba lambar aka ga ma ba tasa bace dole aka haƙura don ko ƴan sanda basu iya samo komai ba. Kuma bayan haka ni na zauna nayi jinyarta Amina, tun kafin a yanke ƙafafun har muka je India aka cire su gabaɗaya, shekara guda da rabi na ɗauka ina jinyarta, na hana kowa wannan ɗawainiyar hatta ƴaƴanta da ƴanuwanta tunda na san na samu abinda nake so, na san tsawo na da nata ba zai taɓa daidai a idanun Baffa ba, kuma hakan ya ƙara min ƙima a idanun kowa a gidan nan ta yadda nake cin kare na babu babbaka, kowa yana girmama ni da bani darajar dana siya a wajensu, hatta ƴaƴan Maimuna a idon kowa kamar nawa suke don babu adadi su Munaya zasu zo su faɗa min abinda mahaifiyar tasu ma baza su iya faɗa mata ba ko kuma su nemi shawarata akan abinda ita bata ma sani ba. Don haka yanzu na san kin fahimci cewa saboda ni kika samu soyayyar kowa gidan nan, da kuma abinda nake nufi cewa duknwanda kika furtawa wannan zancen kamar kin bude masa kofar lahirarsa ne." Muryarta tayi shiru a wannan lokacin, wucewar wasu sakanni sai kuma ta taso a hankali ta dawo kujerar kusa da inda Aminan ke zaune, kuma bata damu da rashin kallonta da har yanzu bata yi ba ta cigaba. "Mu dawo kan abinda ya kawo ni, dalilin da yasa na aura miki Ma'aruf Amina, kamar yadda na faɗa ba don ki zo kiyi rayuwar zaman aure bane kamar yadda naga kin fara kokarin yi a yanzu, na kawo ki gidan nan ne saboda ki taya ni mu ƙarasa babban burin da nake dashi a duniya. A farkonsa ban tsara dake ba, amma daga ranar da Baffa ya yanke shawarar cewa dole Ma'aruf ya ƙara aure, daga ranar kika shigo cikin lissafina Amina, don Ma'aruf ginshiƙi ne guda a cikin burin da nake son cimmawa a yanzu, ina ɗora shi ne akan matakan da zasu kaini ga yin nasara ɗaya bayan ɗaya, don haka idan har aka samu matar da zata raɓe shi wadda ba zan iya juyawa ba Amina abubuwa zasu lalace min ba kaɗan ba, shi yasa tun kafin kowa yayi wani yunƙuri musamman mahaifiyarsa dana san a tarin ƴanmatan dake danginsu zata iya haɗa shi da wata, na duba bayana na zaɓo ki." Sai da ta sake gyara zamanta tana fuskantar Aminan dake zaune a gabanta ta sunkuyar da kanta sannan tace. "Ɗago nan ki kalle ni Amina..." Ta kuwa ɗago da kan nata amma bata kalle ta ba, gashin idanunta sun hade suna shaida jiƙewar hawaye alamun kuka take yi, wani murmushin yaso giftawa a leɓɓen Hajiya Kilishin amma ta tare shi, don da kukan Aminan da kuma shi ɗin, duka bata ga muhallinsu a yanzu ba. "Sati guda zan baki kiyi tunani, idan har kika yarda dani, zan ƙawata rayuwarki da dukkan ƙawar da baki taba tunani ba Amina, zan miki liƙin alheri har sai hannayenki sun kasa tarewa, zan ɗaga ki ki zama tauraruwa a idon kowa musamman cikin danginki, zan kyautata rayuwarki da ta dukkan makusantanki idan har kika miƙo min hannunki na kama kamar yadda na tsara komai..." Ta sake yin shiru tana kallon haɗewar gashin idon nata, sai kawai ta haɗiye yawun dake bakinta sannan ta ƙarasa furta abinda ke tahowa tun daga ƙasan zuciyarta, abinda take jin ko da duniya zata taru akanta ba zai canja ra'ayinta ba. "... Idan kuma har kika zabi yin katoɓarar fallasa ni don ki tsira, na rantse miki da ubangijin da ya halicce mu rayuwarki zata dulmiya ne a baƙin ruwan da zaki yi ta yin ihun da babu wanda zai taɓa jiyo muryarki!" *** Tun da ya shigo gidan jikinsa ya bashi akwai wani abu da ya faru, don fitilar falo ma a kashe take, iya hasken ta korido ne kawai yake a kunne, a falon ya ajiye wayoyinsa da su kaɗai ne a hannunsa sannan kai tsaye ya nufi hanyar koridon, ɗakinsa yayi niyyar wucewa ya watsa ruwa don Allah ya sani a gajiye yake, amma a lokaci guda idanunsa suka kai kasan ƙofar dakinta da nan ma fitilar a kashe take. Har ya wuce ya dawo ya tsaya ya kwankwasa, kusan sau uku amma shiru bata amsa ba, sai yayi tunanin sallah take don a lokacin masaltai ke kiran isha'i, don haka sai kawai ya juyo ya dawo ɗakinsa. Ya kunna fitulun ciki da suka gauraye da haske a ɗakin komai yana fitowa tar cikin kammalen da yake. Ma'aruf yana da tsaftar da duk wanda ya zauna dashi zai gane, don indai abu nasa ne to ba zaka taɓa zuwa kaga komai ba'a muhallinsa ba, sannan kuma yana da haƙurin da zai zauna da wanda bai damu da hakan ba, shi yasa ya iya zama da Ishaq dake wular da komai inda yaga dama. Minti goma kawai ya ɗauke shi gama shiryawa cikin wasu kayan bayan yayi wanka, ya dawo falon daidai lokacin da wayarsa ke ƙara a inda ya ajiye ta, lambar mutumin da yasa ya nemo masa bayani akan Mr. Okafor ne, ya tsaya kawai yana kallon kiran ba tare da ya dauka ba har ya katse sannan ya tura masa dan guntun saƙo cewar suyi magana zuwa gobe. A yanzu ya sani cewar tarawa kansa abubuwa yana ɗaya daga cikin abinda ke saka shi damuwa har ciwonsa ya tashi don Allah ya sani a yanzu yana tsoron ciwonsa fiye da kowa, ya sani cewa idan abubuwa suka lalace masa a yanzu bai san me ya cimma a rayuwarsa ba. Shi yasa bai ɗauki kiran mutumin ba, don a yau kaɗai abubuwan da ya fuskanta suna da yawa. Takardar sammacin da ya samu ɗazu a Office ta girgiza shi ba kaɗan ba, ya kasa hango inda Rukayya da iyayenta suka samu karfin gwiwar kaishi kotu akan zancen Hamida, kalaman Baffa su suka bashi damar ƙin saurararsu amma bai taba tunanin hakan daga garesu ba. Ya kira Ishaq sunyi maganar amma duk tsawon tattaunawar su ya gaya masa cewa chance din da suke dashi kaɗan ne don a matsayin Hamida na mace dole ne a wajen mahaifiyarta ya kamata ta zauna har girmanta kuma ƴan bayanan da suke dashi game da dalilin su na dawowarta wajensa basu da karfi sosai. Sannan bayan yayi haka ya san yayi aiki a Office din amma ya tabbata idan ya koma gobe zai samu kura-kurai da yawa, don a cikin aikin ya gama yanke dukkan abinda ya riga ya tsara game da zancen kotun da kuma Hamida. Kuma baya buƙatar yin zancen da kowa shi yasa ko cikin gida bai shiga ba tunda Baffa baya nan yayi tafiya Abuja, yaga kiran Mami amma shima bai bi bayansa ba kuma itama bata sake kiran ba har yanzu. Ƙafafunsa suka sake komawa kitchen ɗin bayan ya kunna fitila yana nazarin komai, akan table ɗin kitchen ɗin, jerin kayan abincinsa ne kamar yadda take tsara su kullum, yaji wani abu ya zarce cikin makogwaronsa, a cikin ƴan kwanakin nan ya sani cewar yarinyar nan ta taimakawa ƙwaƙwalwar sa wajen samun hutu ta wani ɓangaren, don akwai nutsuwa sosai ace idan aiki ya zuƙe shi da rana akwai inda zai iya zuwa ya huta ba wannan hargitsatsen gidan nasu shi da Ishaq ba. Kamar ya zauna yaci abincin sai kuma kawai yaji ba zai iya hakan ba alhallin bai ganta ba. Sai kawai ya zaro wayarsa ya kira lambar Samirah, bugu ɗaya biyu kuwa ta dauko, muryarta a ciki ta fara cewa 'To Mami.' kafin tayi sallama. "Yaya barka da dare." "Kun yini lafiya?" "Lafiya ƙalau." Ta amsa sannan tayi shiru tana jiran abinda zai faɗa a gaba, kuma hakan kaɗai ya bashi amsar da yake nema cewa Aminan bata ciki don haka kai tsaye yace. "Sai da safe." Ya kashe wayar ya zura ta a aljihunsa sannan ya koma cikin gidan, ɗakinta da bai shiga ba a yanzu shi ya nufa kuma bai jira komai ba ya buɗe shi, fitilar a kashe take kamar yadda ya gani sai dai babu duhu a ciki don hasken fitilar waje na shigowa ta windon ciki, kuma a lokaci guda idonsa ya hango masa ita, tana zaune daga gefen gadon ɗakin ta ɗora kanta akan gadon yayin da jikinta yake a dunƙule, kamar dai ranar daya fara ganinta, ranar da ya fara ganinta a matsayin matarsa. Wannan shine karonsa na biyu shigowa ɗakin kuma ya sake tarad da ita a irin wannan yanayin da ya san cewa tabbas akwai abinda ya faru. Hannyensa duka biyun suna cikin aljihu, sai ya fito da ɗaya daga aljihunsa ya sosa kan hancinsa yana kallon idanunta da suke a rufe. "Assalamu alaikum." Muryarsa ta ratsa ɗakin cikin amonta. Kamar wancan karon ta dago kanta da sauri ta kalle shi amma bata mike ba, kallonsa take yi cikin hasken ɗakin wucewar sakanni biyu kafin bakinta ya amsa sallamar tana ƙoƙarin dagowa daga kishingiden da take. Sai kawai ya juya ya koma ya kunna fitilar dakin, haske ya gauraye koina, yana nuna masa kumburarrun idanunta da tabbas kuka tasha dasu. "Me ya faru? Me ya same ki?" Tambayar ta fito sak kamar ranar da ya ganta cikin daren nan, amma wannan karon sai yaji abinda yake son tambayar yafi hakan, zai iya jero kusan guda goma don ya samu gamsashshiyar amsa. "Babu komai." Ta fada tana ƙoƙarin juya kanta gefe don naɗe sallayar da take kai, yana iya ganin dogon hancinta wanda da alama ta murza shi fiye da kima. "Kayi hakuri, ban ji lokacin da ka shigo ba, barka da dawowa..." Muryarta ta faɗa sanda ta gama ninke sallayar ta miƙe tsaye tazo zata wuce shi, amma sai kawai ya riko hannunta na hagu ta baya ya tsayar da ƙafafunta. Ba shiri Amina ta cije lebbenta tana kallon tiles ɗin dake ƙasan dakin, gayawa zuciyarta take yi cewa ta daurewa wani kukan dake shirin tasowa a ƙirjinta amma sakon baya tafiya sam, don lokacin da ya jawo ta baya ta dawo gabansa ƙwalla ta sake cika idanunta taf. A yau ɗaya rayuwarta ta canja, ta shiga tashin hankalin da bata san da me zata kwatanta shi ba, a cire mamakin halayen Hajiya Kilishi daya nade zuciyarta a gefe, tsoro da taraddadin hatsarin da ta kawo kanta cikinsa ya hargitsa kowanne abu mai kyau na tunaninta, tana tuna kalamanta, tana tuna ranar da ta yanke hukuncin karɓar auren nan, da wani zai gaya mata da wani abu ko da makamancin haka ne... da tabbas labarin zai canja daga yadda yake yanzu. Ita bata san ma me take ji ba, bata san yadda zata fassara halin da take ciki ba, kawai dai ta sa zuciyarta ta karye da kowanne abinda kalaman Hajiya Kilishin ke nufi, kuma shi kansa Ma'aruf ɗin ma a yanzu bata yarda dashi ba, don bata san me Hajiya Kilishi ke nufi da 'matakan da take ɗora shi akai don tsarinta ya tafi daidai ba.' Zuciyarta tayi rauni da yawa ta yadda fuskar Aminu ce kawai ke yawo a kanta da tunanin halin da yake ciki, shi yasa a karo na farko tun bayan ranar da aka kawota gidan, hawaye ya kasa tsayawa a idanunta, don a wannan lokacin tana jin cewa kukan shine kawai sauƙin abinda take ji a kirjinta. "Ki gaya min abinda ya faru da kuma dalili da yasa kike kuka." Ma'aruf dake riƙe da hannunta ya fada da muryarsa cike da ikon dake nuna mata cewa da gaske yake yi, sai tayi ƙokarin maida kukanta ta hanyar share idanunta da ɗaya bayan hannunta sannan ta shiga gyara tsayuwarta don ji take kamar zata fadi. "Me ya same ki Amina?" Bai gaji ba ya sake tambaya a lokacin da take jin kamar ƙamshin turarenta na kassara kasusuwanta ne, bata da wani zaɓi da ya wuce ta lalubo wani sauti daga can ƙasa maƙoshinta idanunta har yanzu suna ƙasa tace. "Aminu ne ya gamu da hatsari, yana asibiti tun jiya." "Ya salam, Ya salam, wane asibiti ne?" Bai san waye Aminun ba, amma ya fahimci ɗanuwanta ne. Ta girgiza kanta wani kukan na shirin ƙwace mata. "Ban sani ba, muna waya da Amma sai... Sai wayar ta ɗauke." Zancen ya fito daga can ƙasan maƙoshinta ba tare da ta tsara shi ba. Sai kawai yasa ɗaya hannunsa da baya rike da ita ya zaro wayarsa daga aljihu, santsinta ya biyo hannyensa yayin da ya kunna password ɗin da yatsansa sannan ya shiga wajen dial log kafin ya miƙo mata. "Ki kira ta sai muji wane asibiti ne?" Sai a yanzu ta ɗago ta kalle shi kuma kafin tayi saurin sake maida idanunta ƙasa, ya gani cewa har yanzu kwalla ce taf a cikinsu, a hankali nata hannun suka karbi wayar don babban abinda take bukata a lokacin kenan, kuma ga mamakinsa bata matsa ba ta shiga danna nambar wayar Amman. "Assalamu alaikum." Sautin muryar mahaifiyarta da ya fito ta ciki yasa a yanzu ƙwallar idanunta ta gangaro... Karo na farko a duniya taji so take ta ganta a gabanta wannan lokacin ta rungume ta, so take ta cusa kanta a jikinta ta rera kukan da har yanzu take jin nauyi ta a ƙirjinsa, ta gaya mata cewa tayi nadamar ƙin gasgata maganganunta, don abinda ya shigo cikin rayuwar tasu yanzu wani abu ne da duk ƙarfin hangensu basu gano ko rabinsa ba, wani tashin hankali ne da ya tsallake dukkan tunaninsu. A yau ta ƙara yarda da zancen Amma na cewar babu wani auren gaske tsakanin mai kuɗi da talaka a wannan zamanin, indai ya faru to tabbas akwai wani boyayyen abu dake ƙasa, Amma tace rayuwarki zaki sadaukar musu Amina, ashe su duka basu sani ba cewar bayan tata rayuwar suma tasu ta shigo ciki wataƙila har da sunan duk wani da ya rabe su ma. "Amma, Amina ce." Muryarta ta fito tana kakkarwa kamar yadda hannunta keyi acikin nasa. "Amina... Amina." yadda muryar Amman ta kira ta a jere da wani irin sautin ajiyar zuciya yasa lebbenta talewa cikin kokarin wani kukan. "Me ya faru ɗazu wayar ta dauke? Mun gwada yafi sau hamsin kuma bata shiga ba. Har Hajiya Kilishi na kira ita kuma ba'a dauka ba?" Sai da ta hadiye wani abu a ƙirjinta jin sunan Hajiya Kilishin sannan ta iya cewa. "Amma wayar mutuwa tayi kawai, kuna ina yanzu? Ya jikin Aminun?" "Gamu nan mun dawo gida don Baba yace bai yarda yayi zaman asibitin ba, yanzu dai sunyi masa abinda zasu yi masa mun dawo gida, gobe kuma zamu tafi jigawa gidan wannan ɗanuwansu Fatiman mai gyaran karaya, saboda duka ƙafafun nasa biyu sun karye Amina." Sautin kukan da ya fito daga bakinta shi yasa Amman cewa. "Ba kuka zaki yi masa ba Amina, addu'a zamu yi Insha Allahu zai samu sauƙi don ance shi mutumin ya iya aikinsa, ba za'a haɗa dana asibiti ba." Muryar Amman dake lallashinta itama a karye take kawai, ta sani suna da kuma matsayinta na Uwa shine abinda ke rike ta daga nata kukan. "Ku duka zaku tafi Amma?" Tayi ƙokarin tambaya ta cikin kukan muryarta a rarrabe. "A'a, dani da Baba da kuma Fatiman da zata kaimu gidan zamu tafi, su Maryam suna nan saboda makaranta, ita kuma Hajiyan Fatiman saboda jinyar Inna (kakar Fatiman) ne ba zata samu zuwa ba." Sai da tayi wata ajiyar zuciya mai nauyi sannan tace. "Ina Aminun?" "Bacci yake Amina, tun jiya sai yanzu bayan magaribar nan sannan ya samu baccin, idan ya tashi na kira ki, wannan nambar waye?" Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, kuma shirunta ya bawa Amma amsarta don haka sai tace. "Addu'a zaki yi tayi masa Amina, kowanne ɗan adam baya wuce ƙaddararsa, komai zai zo da sauki insha Allah." Kalaman kaɗai sun isa su kara tsoratar da Amina, don ta san idan har Amma zata faɗi haka to al'amarin ba ƙaramin abu bane, don komai tsananin rashin lafiyar mutum Amma bata zuzuta shi haka, balle ma akan Aminu da yake namiji, don haka bata san lokacin da bakinta ya ƙara talewa da ƙoƙarin yin kukan da har yanzu take dannewa ba. "Zan saka Maryam ta kira ki da safen kafin mu tafi, su can gidan Kawu Malam zasu koma kafin mu dawo." Ɗaga kai kawai take kamar Amman na kallonta yayin da sautin kukan ke shaƙewa a ƙirjinta yana fitowa a kakkatse, Allah ya sani rabonta da irin wannan kukan tun Maryam bata da lafiya, lokacin da aka nemi kuɗin maganinta aka rasa, tana kallonta a kullum tana tunanin mutuwa zata yi. Ma'aruf yasa hannu ya karɓi wayar daga wajenta bayan sunyi sallama, ya maida ita aljihunsa, bata kalle shi ba har yanzu tasa bayan ɗaya hannunta tana ƙoƙarin share hawayenta, da hannun da ya mayar da wayar ya sake riko ɗaya hannun nata ya tsayar da ita daga goge hawayen, sannan a lokaci guda ba tare da ta ankara ya jawo ta jikinsa, karo na farko ya rungume ta, hannunsa ɗaya ya zagayo wajen ƙugunta yayin da kanta ya samu mazauninsa a kusa da wuyanta. "Kar ki maida shi zai cutar dake... Just let it out." Muryarsa ta faɗa a cikin kunnenta da wani sauti daya shiga dagargaza dukkan wata jijiya ta dauriya a jikinta. Kuma a karo na farko Amina ta manta komai akan Ma'aruf ta sunkuyar da kanta a jikinsa don babban abinda take buƙata kenan, kukan da sautinsa kaɗan ne ya suɓuce daga bakinta yayin da jikinta ke girgizawa a cikin hannunsa. *** Bayan kwana biyu. "Kin shirya?" Ma'aruf ya tambaya yana kallon Amina data fito riƙe da wata ƴar ƙaramar jaka a hannunta da kuma wani madaidaicin basket, doguwar riga ce a jikinta ta baƙar abaya, ta yafa baƙin mayafin kawai akanta ba tare da ta saka ɗankwali ba, tana tsaye daga hanyar koridon dakunan tana cakuɗa yatsunta cikin junansu, har yanzu ta kasa yarda da abinda yazo dadaddare ya gaya mata jiya cewa ta shirya zasu je jigawa a yau. Jiya da safe a wayar tasa suka yi waya da Amma ta shaida mata lokacin tafiyarsu wanda bayan hakan tayi ta binsa da kallo tana so taji yace wani abu amma bai faɗa ɗin ba har ya fita, ya barta a zagayen halin da take ciki, kuma Allah kaɗai ya san yawan abubuwan data saka ta kwance a cikin kanta a jiyan wanda duk iya tunanin nata yana ƙarewa ne a gaɓar da bata san yadda zata yi ba. Haka ta yini har a jiyan tana share hawaye duk lokacin da ta tuno cewa duk irin halin ciwon da Aminu ke ciki saboda ita ne, saboda itan da bata san yadda zata budi baki ta gayawa wani ba, ko da Ma'aruf ɗin ne kuwa tunda shi kansa babu alamun yana da wata masaniya irin wadda ita ta sani yanzu akan Mamin, duk da cewa bata gama sanin ainihin abinda take nufi game dashi ba ko kuma shi nasa ra'ayin akanta. Sai da daddare bayan ya dawo ne kawai yace ta sako mayafinta zasu shiga cikin gida, wajen Mami suka fara zuwa kamar yadda suka zata, kuma gaishe ta kawai suka yi kafin ya furta abinda yasa kowannensu mamski daga ita har Hajiya Kilishin. "Gobe zamu wuce Jigawa Mami, na san kin samu labari, brothern ta ne ya gamu da hatsari zan kaita ta dubo shi." Har yanzu tana jin nauyin yadda idanun Hajiya kilishi suka dinga kallon fuskarta, tana jin tafiyarsu a ko'ina na fuskar tata, yadda ta dinga kallonta da wani irin yanayi da yake nuna mata cewa itama a lokacin taji zancen, da kuma yadda tata zuciyar ta dinga bugawa har sai da taji kamar ta tsugunna ƙasa ta ɗauko ta lokacin da suka miƙe tsaye, don tsabar tsoro ƙirjinta fayau ta dinga jinsa kamar yadda jikinta ya zama kamar fallen takarda har lokacin da suka tafi ɓangaren Hajiya Maimuna, idan acan ma suka sha addu'ar Allah ya kiyaye hanya kamar yadda Mamin tayi tata. Jiya haka ta kwana tana juyi akan gado, da asuba kuma tunda tayi sallah bata koma ba, don yace mata ƙarfe takwas zasu tafi a yau ɗin zasu je su dawo kamar yadda ya tsara. Abincin breakfast ɗin da tayi ma bai ci ba don yace mata azumi yake yi kasancewar ranar Alhamis ce. A yanzu ya shigo daga wajen maigadi ne da ya gama wanke masa motarsa, yana tsaye daga bakin ƙofar falon yayin da karar yadda maigadin ke share ruwan wankin motar daga waje ya cika falon. "Kin shirya a haka?" Ya ƙara tambaya yana kallonta, sai ta sunkuya ta kalli kayan jikinta sannan ta dago ta kalle shi tace. "Eh na shirya." Shi nasa kayan dogwaye ne kalar sararin samaniya, ya saka hula wadda ta dace dasu, da ace zuciyarta a nutse take ta sani tsaf zata tsaya yabawa yadda kayan suka karɓe shi amma a yanzu ba abinda ke gabanta kenan ba, tashin hankalin dake kwance a ƙasan zuciyarta ya isa ya binne ta da ranta. Sai kawai ya taho gabanta riƙe da mukullin motarsa a hannu, kuma bata matsa ba, don watakila a yanzu ta saba dashi a kusa da ita, kar a lissafa da shekaranjiya lokacin da ya rungume ta, wannan don ba'a cikin hayyacinta take ba kowannensu ya sani. Hannunsa taji ya sauka akan gashinta da ya fito ta gaba kafin yace. "Shi wannan ba'a rufe shi?" Zuciyarta ta buga yayin da wani abu ya tsarga tun daga saman kan nata har zuwa tafin ƙafafunta amma ta haɗiye shi, sai ya matsa baya kadan sannan yaba cigaba da kallonta yace. "Bana son wani yaga gashinki." Bata ɗago ta kalle shi ba amma kalaman sun daki zuciyarta ta yadda duk tarin hargitsin dake ciki sai da suka girgiza. girgizawar da bata yi tunanin zuciyar tata zata yi ba a yanzu tare da abinda ya faru game da ita. A hankali ta juya ta koma ɗaki, wani pink dankwali ta ɗauko ta daura, ai kuwa ya hau sosai da kayan ya ƙara haska fuskarta, wanda bata ko gani ba ta sake ɗaukan ƴar ƙaramar jakarta da kuma wannan basket din ta fito, sai da ta tabbata ta kashe fitulu da switches ɗin ko'ina, na fridge kawai ta bari sannan ta fito. Yana tsaye daga bakin barandar falon yana jiranta, wani guntun murmushi da yayi mata yasa gumi fitowa a tsakanin yatsunta kafin ta bashi waje ya kulle ƙofar gidan, kuma juyowar da yayi yasa shi tsayawa dab da ita, wanda kafin tayi tunanin yin gaba idonta ya hango mata wasu manyan ledoji akan booth ɗin motarsa. "Mami ce ta aiko a kawo miki, yanzu muka yi waya tace ki kai musu." Muryarsa ta faɗa dab da bayanta. Zuciyarta ta buga a ƙirjinta, hannayenta suka fara rawa riƙe da kayan nan, ta sani bana tasirin muryarsa ne kaɗai bane har da na sunan Hajiyan Kilishin daya furta. Numfashinta ya shiga kakkatsewa a kirjinta ta yadda tayi tunanin zai iya jinta amma sai taji lokacin da yayi baya ya ɗauki waya yana cewa. "Zuwa 10 zasu iso Faruk, idan kana ƙaunar Allah ka tabbata kana nan..." Sai kawai tayi ƙarfin halin motsa kafafunta ta tafi wajen motar, ta isa wajen daidai lokacin da idonta ya nuna mata sauran kayan daga gefen motar, buhun shinkafa guda biyu da jarkokin mai suma guda biyu. Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta kafin ta ajiye kayan hannunta, ta buɗe ledar farko inda kayan tea manya-manya gwangwanayen su Madara ya shiga idonta, a ɗaya ledar kuna wani ƙaton food flask ne shi kadai mai faɗi, taji har a lokacin hannunta na girgizawa a hankali sanda ta buɗe shi, kuma tun kafin ta gani ƙamshin wani farfesun naman kaza ya cika hancinta, shine fal ya kusan cika flask din har baki. Ba shiri ta rufe idanunta tana jin koina a jikinta na girgizawa. Fata take da dukkan imaninta cewa Allah ya kawo mata mafita akan matar nan. "Ya ubangiji kaine tanadin kowanne bawa idan ya fada masifa, Ya Allah na miƙo maka hannaye na ka taimake ni akan wannan al'amarin da yafi ƙarfina, ba zan iya ba ya rabbi! Bani da wata mafita da wata dabara wadda ta wuce taka ya Allah." Wani lokacin bawa yana yin addu'a ne akan gaɓa, wani lokacin ubangiji yana amsa addu'a ne a take! Kuma komai yana da tushe yana da asali, kamar yadda tafiyarsu Jigawa ke shirin zama tushen faruwar abubuwa masu yawa. Kuma rashin sani yana ɗaya daga cikin raunin ɗan Adam! *** Waye yake cikin wannan rashin sanin ne? A cikin dukkan wannan hargitsin, me yake jiran mu a jigawa ne?😉 Wace mafita Amina zata samu game da Hajiya Kilishi kafin zagayowar sati guda? A yau kun fara jin tarihin Hajiya Kilishi!😰 Ku shiryawa abinda ke faruwa daga ɓangaren Ruƙayya. Har da Jawad ma.😅 #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA HUDU. ~~~~~~ I fall in love with your kindness, because it adds peace to my wounded but striving soul. - Unknown. *** Ruƙayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar nazarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta. " ... Da mun tura wanda za'a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci..." Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan ɗin kafin kai tsaye ta katse ta. "Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?" "Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tunanin me kike yi bayan wannan?" Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan ɗin wani shu'umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace. "Ƙyale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf." Ta fada ba tare da ta ɗauke idonta daga kan Rukayyan da itama ke kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ƙaraso ta zauna a gefenta. Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta... Allah ya sani bata son matar sam, don ta daɗe tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da ita daga gidan Ma'aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan ɗin ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ƙarasa ta zauna ba tare da kallonta ba. Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta. "Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari'a ba kamar yadda nayi miki bayani, a iya gaban alkali za'a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki faɗa da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za'a baki ƴarki ki taho gida da ita. Kwana ɗaya kawai a tsakani, zaki haɗa kayanta wanda a ciki zamu san yadda za'a dinke ƙullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku haɗu ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta koma hannunsa kamar yadda kuka shar'anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta. Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za'a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokacin za'a sami dabarar da zata kwance ƙullin nan, wanda da anyi hakan Ruƙayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya." Ta ƙarashe zancen da wani faffaɗan murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yasa ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta. "Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakarƙarin mu ya huta haka kije can ki ƙarata." "Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan kinga an samu saɓani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai." Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ruƙayya ta juya ga wayarta da ta shiga ƙara daga can inda ta baro ta a jikin windon data tsaya. Ta mike a hankali riƙe da kofinta ta koma wajen, sunan Jawad daya nuna akan screen din wayar yasa ta kurɓar shayin kafin ta ɗauki wayar ta kara ta a kunnenta. "Barbie yau kika ce, 5pm." Me yasa zai tuna mata? Ta sani, ta sani cewa shekaranjiya ta gaji da nacinsa da ba zai kare ba tace masa zasu hadu a yau, kuma da zata iya a yanzun ma zata kara masa lokaci ne, amma ta san ko ta kara ba zai barta ba don haka dole ne ta daurewa kanta a yau ta fuskance shi. A hankali ta ajiye kofin hannunta akan windon, sannan tace. "Ban manta ba J." Taji ajiyar zuciyarsa daga ciki kafin yace. "Then where did you decide?" (Ina kika zaba?) Ta sake cije lebbenta na ƙasa "Where we first met." (Wajen da muka fara haɗuwa.) Kalaman suka daki zuciyar Jawad da tasirin da ita bata san shi ba, don a nata ɓangaren ta zabi fadar haka ne don zuciyarta ta tsara mata cewar a wajen da suka fara haɗuwar anan ya kamata ta kawo ƙarshen alaƙarsu gabaɗaya, ko yaƙi, ko ya so. Kuma ƙarfe biyar da ƴan mintunan tayi mata a kofar Joint ɗin 'Harish', ta fito daga motar ta bayan ta jera ta a layin sauran dake wajen sannan ta gyara zaman dan mitsitsin mayafin data dora akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, wadda akayi mata wani ɗinkin mai kyau daga kasa kuma tayi buɗewar umbrella, takalmin kafarta ba mai tsini bane wannan karon don ta sani rashin nutsuwar zuciyarta ba zai barta ta iya tafiya a cikin mai tsinin ba, ta shiga ciki babu mutane sosai, ƴan kaɗan ne kawai ke zaune akan kujerun wajen yayin da iskar yamma da kuma ƙamshin shuke-shuken wajen ke shiga hancinta. Daga can karshe ta hango Jawad, zaune akan table din da a wajensa suka fara haɗuwa, ba zata tantance idan tebur din ne ko an canja shi ba amma dai wajen ne, yana sanye da wasu dogwayen kaya Kaftan, yasa hula dark brown wadda ta fito da hasken fatarsa tar a cikin yammar, Jawad mai kyau ne ba sai kowa ya tuna mata hakan ba. Kuma da alamu ya jima a wajen don tuni an sauke shi da shishar da yake bula hayakinta a iska. Kafafunta suka ƙarasa wajen a hankali sanda shima ya hango ta, kuma a lokaci daya murmushi ya sauka akan lebbensa yana ƙara tuna mata da kammaninsa. "Kina da cika alƙawari Babe, yana daya daga cikin abubuwan da suke kara haukatani akanki." Bata yi murmushin da ta saba kamar kodayaushe ba sai kawai ta jawo kujerar dake fuskantarsa ta zauna. "Wane flavour za'a kawo miki?" Ya tambaya yana tasowa daga kishingiɗen da yake. Ta ajiye wayarta akan table din tare da earpiece ɗin hannunta sannan ta kalle shi sosai. "Ka san ba abinda ya kawo kenan ba Jawad, idan zaka kyauta ma just put yours aside muyi magana." Ya gyada kansa yana kallonta. "Zanyi duk abinda kika ce Barbie." Da haka ya ajiye tasan gefe yana cigaba da kallonta, idanunsa na lumshewa akan fuskarta. Bata damu da yadda yake kallon nata ba kai tsaye ta fara magana. "Jawad abubuwa sun cakuɗe a rayuwata yanzu, I've got alot going on table da ba sai nayi maka bayaninsu ba amma hakan ne yasa na yanke alaƙa ta da kai, don bani da wannan lokacin Jawad, abinda nasa a gabana ya karato don haka dole ne na ajiye ka a gefe. Kuma nayi ƙoƙarin nuna maka hakan ta duk hanyar da zan iya amma ka kasa ganewa, shi yasa na yarda muyi wannan haduwar don in shaida maka komai baki da baki." Tunda ta fara maganar bai ko kifta idanunsa ba, kallonta kawai yake da dukkan irin emotion din da zata iya tsinta a cikin idanunsa, wanda basu dame ta ba ta cigaba. "Idan baka manta ba Jawad, tun farkon alakarmu na gaya maka cewa babu aure a tsakaninmu na san baka dauki maganar da muhimmanci ba a lokacin amma ni da gaske nake tun a sannan. Bari na fito fili na gaya maka gaskiya Jawad, a lokacin da na haɗu da kai ina cikin damuwar da ni kaina ban san mecece ita ba that is bayan mutuwar aurena na biyu, so na kula ka ne kawai don ka taimaka min in manta damuwa ta, and you really did help 'cox we wasted away ta hanyar ta hanyar da har sai da kasa na kusa manta cewa ina da abinda nake so bayan kai. Yadda kayi treating ɗina Jawad da tsananin kulawa da komai shi yasa zuciyata ta yi laushi akanka har kayi tunanin duk abinda nake yi maka zai iya sawa na canja ra'ayina akanka, but honestly ban ɗauke ka komai ba more than a toy (abin wasa), baka taɓa zama wani abu mai daraja har da zan kalla da sunan aure ba Jawad. Zuciyata ta mutum ɗaya ce a duniyar nan kuma ina jin cewa ko za'a tsaida tashin duniya akaina ba zan taba iya canja hakan ba. So ka taimaka min mu karkare komai a yanzu, Let's just end everything here don ni tuni na fara gudanar da da sabuwar rayuwar da a cikinta zan cimma burina, ka taimaki kanka ka manta dani kaima Jawad. Erase all those memories kayi pretending babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu wanda na san a cikin kankanin lokaci zaka ji ka manta dani gabaɗaya. Ka kalli kanka, kana da komai the looks, status, kuɗi, age, time... You have it all J. (Kana da komai) zaka samu ƴanmata guda dubu da kallo ɗaya zaka yi musu and in no time they will be throwing themselves over you. Ka fahimta dan Allah Jawad cewa ni ba komai bace a rayuwarka." Ta ƙarashe da dukkan fatan ya fahimce ta a cikin idanunta, kuma har a lokacin kallonta yake shima, sai da ta kai ƙarshe ɗin sannan ya ƙifta idanunsa a hankali, yana komawa da baya, ya jingina sosai da kujerar da yake kamar kwanciya zai yi sannan muryarsa ta fito. "Anything more Barbie?" (Akwai wani abu kuma Barbie?) Ta haɗiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta. "Nothing more Jawad, shikenan idan har ka fahimce ni." Sai ya gyada kansa haɗe da rufe idanunsa ya buɗe kafin yace. "Thank you." ( Nagode.) Ta kalle shi tsawon wasu sakanni zuciyarta na son nazarin yanayin dake kan fuskarsa wanda bata gane ba kuma ta kasa gano komai ɗin, hakan yasa kawai ta dauki wayarta data ajiye sannan ta mike tsaye. "Nagode nima, sai wani lokacin." Ya sake gyada mata kansa ba tare da yace komai ba, kuma da haka ta juya ta tafi, idanunsa suka bi bayanta da kallo, zuciyarsa na tsagewa da yadda jikinta ke kaɗawa da tafiyar da take yi yayin da ƙwaƙwalwar sa ke dawo masa da kalaman abokinsa Haro. "Ka sake gwada ta for the last time Man, idan har tana nan akan bakan ta cewar ba zata saurare ka ba, nayi maka alƙawari ni zan taya ka yarinyar nan tayi biyu babu a rayuwar ta, dama na tsane ta J, kaima ka san na tsane ta!" Ya cije bakinsa da ya bushe yayin da wani guntun murmushi ya sauka akan leɓɓen nasa lokacin da Ruƙayya tayi kwana ta fita daga wajen tana ɓacewa ganinsa. Wayarsa ya zaro a cikin aljihunsa ya shiga neman nambar Haron, bugu kaɗan kuwa ya ɗaga lokacin da ya jawo kan shisharsa, kuma sai da ya zuƙo hayaƙinta ya busa a iska sannan yace. "Tayi biyu babu Haro, let the plan start!" *** Jigawa, 11:05 Am. "Gwara ki fito fili kawai ku fadi gaskiya, yanzu ke baza ki so in fara tafiya in gano me akeyi ba? Idan yaso ko ta email sai na rubuto muku abubuwan da zaku tanada?" Aminu ya fada yana kallon Amina da ta gama gaya masa irin tashin hakalin da ta shiga jiya, tana zaune a gabansa tana ƙoƙarin zuba sukari a kofin tea ɗin data take hada masa. Abinda ya faɗa yasa ta yin murmushin da bata shirya masa ba tana kallonsa, kafin tace. "Allah ya shirye ka Aminu, ai wallahi ina jin mutuwar ce kaɗai ma zata iya kashe bakin ka." "Daga fadar gaskiya, yanzu ke tsakani da Allah baza ku so ku sami wata ƴar expo ba? Wannan harkar fa harka ce ta dindin idan an tafi an tafi kenan." Tissue din dake gefenta Amina ta dauko ta jefe shi dashi a fuska. "Aminu wannan fa ba zancen wasa bane." Ya ɗaga duka hannayensa sama. "To shikenan, ai ke yanzu naga alama dama baki shirya mata ba, gashi nan har kin canja sai washewa kike yi wai ke amarya, dan Allah Amma bata yi haske ba?" Ya tambaya yana kallon Amman da ta idar da sallar walha a lokacin, bata amsa ba sai jawai ta juyar da kanta gefe kawai ta cigaba da laziminta. Kuma sai akayi sa'a kafin shima ya kara cew komai wayarsa a gefe tayi kara, ya ɗauka ya shiga sake amsa gaisuwar tarin mutanen da duk bayan ƴan mintuna ake kiransa. Amina ta sake kallon Amma data juyar da kanta tana lazimi, kafin itama ta sunkuyar da nata ƙasa a hankali ta shiga wasa da wani zobe a yatsanta, wani abu take ji yana tokarewa a cikin zuciyarta duk sanda ta kalli Amman. Kusan awar su guda kenan da sauka, awa guda da zuciyarta ta narke lokacin da Ma'aruf ya tsugunna a gaban su Baba harma dasu Baban Kurna da suka yi sa'ar ganinsu don a safiyar ranar suma suka zo, yadda ya tsugunna a gabansu kansa a ƙasa suna amsa gaisuwarsa wani abu ne da girmansa yasa har yanzu ta rasa inda zata ajiye shi a cikin ranta, don har ciki ya shigo ya gaishe da Amma da kuma Aminun, sannan har yanzu idanunta suna hango mata damin kudin daya ajiye a gefen shimfiɗar Aminun lokacin da zai fita. "Guess what?" (Kin san me?) Ta tuna yadda muryarsa ta furta hakan daga bayanta lokacin da ta sake binsa wajen mota tare da wasu yara don su ɗauko kayan nan ita kuma ta dauko jakarta da lokacin da suka tsabar zumuɗi tsaya bata ko tuna da ita ba ta buɗe kofar motar ta fita. Yadda ya tsaya a kusa da ita bayan ta juyo yasa ta kallon gefe ta hango yaran suna tafiya cikin gidan kafin girgiza kanta a hankali idanunta a kasa tana kallon jakar data dauko. "Naga yadda zaki koma idan kin ƙara girma." Hakan yasa tayi saurin ɗagowa ta kalle shi, ya harde hannayensa duka biyi a kirji riƙe da wayoyinsa, kuma a take sai ya bata amsar tambayar da idanun nata ne suka yi masa. "Kamar ki ɗaya da Mamanki, na daɗe ban ga masu kama haka irinku ba." Ruɗani idon nata ne ya tafi lokacin da ta sake sunkuyar da kanta kafin ta iya lalubo muryarta. "Haka kowa yake cewa." Ta faɗa a hankali. "Haka kowa yake gani that's why." Bata ce komai ya sake cewa. "Naji dadin ganinsu sosai Amina, yanzu naga inda kika samo wannan kirkin naki." Bata san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a lebbenta ba duk da halin da take ciki. Ta sake ɗagowa ta kalle shi, har a lokacin kallonta yake da yanayin da bata iya fassara shi, yanayin da yake ƙara tuna mata cewa har yanzu bata san inda zata ajiye shi a zuciyarta ba. "Nagode sosai." Sai a lokacin tayi masa godiyar da tunda suka taho a hanya take fama da ita a bakinta tana tunanin yadda zata fade ta, kuma murmushin da yayi a wannan lokacin sai da ya kusan tsinka zuciyarta ba don kalaman Hajiya kilishi dake daure da zuciyar tata tamau ba. A wannan lokacin Ma'aruf na kallonta ne tunanin mai yawa a zuciyarsa, Allah ya sani wani abu ya motsa a zuciyarsa game da ita tun daga ranar da ya fara ganinta. Ya cewa zuciyarsa tausayinta ne da kuma mamakin ganin ƙankantar ta, don a lokacin da Mami tayi masa zancenta da kuma lokacin da ya tsinci sunanta a kayan Jamal, zuciyarsa bata kawo masa ko kadan cewar zai ganta karama irin haka ba. Kuma duk sanda ya sanda yake tare da ita a yanzu yana mantawa da dalilin da yasa ya yarda da aurenta ko kuma yadda na auren nasu ya kasance, yana ji ne kawai kamar zamansu wani abu ne da ya daɗe daga cikin tsarinsa, don abubuwa da yawa ya banbanta da irin zaman da yayi da Rukayya. Tare da Ruƙayya gani yake kamar duk abinda yake yi dole ne, don ita tana da tarin expectation ɗinta akansa, ta daɗe tsara wata irin rayuwa tare dashi a cikin kanta da a wancan lokacin shi ba abinda ke gabansa kenan ba, shi yasa abubuwa da yawa kai tsaye zata gaya masa tace yayi kaza ko ya kamata yayi kaza wanda duk da ba saurarata yake yi ba, hakan baya masa daɗi, amma ko fuskar Amina ya kalla, innocent kammaninta kaɗai yana sashi jin wani cikakken iko irin wanda kowanne namiji ke ji akan iyalinsa. Don haka yadda take kallonsa a wannan lokacin, yasa shi ture abubuwa da yawa a cikin kansa ya tako ya karaso gabanta, ya tsaya dab da ita sosai lokacin da kallon cikin idanun nata ya koma kalar mamaki da kuma ruɗani, irin ruɗanin da ya kula dashi tun ranar da ya dawo ya same ta tana kuka, zuciyarsa ta gaya masa cewa so yake ya rungume ta har sai kayanta sun koma ƙamshin turarensa gabaɗaya, amma yayi kokarin ture zuciyar dake gaya masa hakan yace. "Kin manta baki ɗauko basket ɗinki ba." Ta kuwa juya ta kalli basket din dake ajiye akan kujera kamar bata san dashi ba sannan ta dawo da fuskarta wanda hakan yasa ta ƙara matsowa dab da jikinsa amma sai tayi saurin yin taku baya kaɗan kafin tace. "Abinci ne a ciki, ban sani ba ko zamu yi magariba a hanya, kace kana azumi." Bayan ta faɗi hakan, bata san me yake tunani ba don sai da wasu sakanni suka wuce kafin yayi magana. "Ban san ta yaya zance miki nagode ba, amma I'm really grateful, Allah ya saka miki da alkhairi dear." Dear, dear, dear.... Sunan da ya kasa barin zuciyarta kenan har yanzu, yake rikita zuciyarta duk sanda ta tuno duk kuwa da irin zagayen tashin hankalin da take ciki ba cewar shi kansa a yanzu bai kamata ta yarda dashi ba duk kuwa da yadda komai nasa ke nuna mata akasin haka. "Amina..." Muryar Amma ta dawo da ita zahiri, ta ɗago da sauri ta kalle ta, har Aminu ya gama wayar yana shan tea din data hada masa. "Ko zaki karɓo mana maganin da za'a saka masa yau a cikin gidan, kina shiga ɗaki na farko ne wajen Malam Ibrahim ɗin." Malam Ibrahim Mijinyawa shine ɗanuwansu Fatima mai dorin, kuma gidan nasa ba'a cikin garin Jigawan yake ba, a wani ƙauye ne dake gaba kadan mai suna Kuɗai, gida ne kato da iyalansa, amma kusan rabin dakunan gidan yana saukar marasa lafiya ne wanda ciwonsu yayi tsamari ya zama sai anyi kwanaki ukun da yake bayarwa kafin a bar wajensa, don haka inda suke ɗin dakuna ne a jere kamar asibiti, sai dai bayan su ɗin wani ɗaki ne kawai daga can gefe inda aka sauki wani yaro da nasa iyayen suma da suka zo daga Kaduna. A jiya su biyar Amma tace mata sun zo, bayan ita da Aminun da kuma Baba, sai kuma Fatiman da ta kawo su gidan da kuma wani ɗanuwanta Yusuf da a jiyan su suka koma, dama an taho dashi ne don yayi mata rakiya tunda ita ba kwana zata yi ba. Sai ta mike a hankali ta shiga neman inda ta ajiye mayafinta a dakin lokacin da Aminu yace. "Anjima su Baban Kurnan zasu tafi Amma?" "Eh, Babanku yace da sun dawo daga masallaci zasu kama hanya, su zasu tafi da waɗannan kayan da Amina ta kawo ma don mu sami sauƙi jibin." Kalmar 'waɗannan kayan' ita ta tsaida kafafun Amina cak a inda taje, don ta san waɗanne kaya take nufi, kayan abincin da suka fito daga hannun Hajiya Kilishi. "Wallahi matar nan tana ƙoƙari Amma, Allah dai ya saka mata da alkhairi." Taji Aminun ya sake faɗa kuma ga mamakinta sai taji Amman tayi shiru bata ce komai ba, zuciyarta ta buga a kirjinta, ta juya da sauri a lokaci guda ta kalle ta, kanta na kasa a yanzu tana ninke wasu kayan Aminun, fata take ta fadi wani abanin tunanin sauran mutanen ko ta sami kofar da zata iya tunkararta da zancen da bata san ita ina fara ba, amma ga mamakinta sai tayi ajiyar zuciya sannan tace. "Amin ta kyauta kam, haka Babanku ma yayi ta fada." Sai kawai tayi saurin sunkuyawa ta damƙo mayafinta dake ƙasa sannan ta haɗiye abinda ke bakinta da karfin da zata iya kafin ta muryarta ta fito wani iri. "Bari naje Amma." Da haka ta tura ƙofar net ɗin ɗakin ta fita, tana jin kamar tana ɗauke da nauyin duniya ne bakiɗaya a kafaɗunta, Amma ce kadai fatanta amma ko ita bata san ta yadda zata fara gaya mata komai ɗin ba. Abinda bata sani ba shine, idan ubangiji ya amsa addu'ar bawa, sai komai yazo masa a bazata, don wajen karfe ɗaya Aminu ya samu bacci, Baba kuma tun bayan tafiyarsu Baban kurna ya fita zuwa cikin gari. A lokacin ne Amma ta kira ta zuwa waje, kasan wata katuwar bishiya daga cikin gidan suka zauna inda aka shimfiɗa wata tsohuwar tabarma, kuma kalamanta na farko suka gutsirtsira duk wani saurin ƙarfin gwiwa da take jin cewa tana dashi na iya fuskantar wannan tashin hankalin. "Amina a wannan zamanin mafarki baya tabbata, kin sani ba zan taɓa yarda cewa lafiya kike zaune a gidan nan ba ko?" Lokacin da ta faɗi hakan kallonta take da ƙwallar data cika idanunta taf, amma sai ta girgiza mata kai ta cigaba da cewa. "Ni uwa ce ina kallon abinda ya shige wannan zahirin, dukkan kalamanki da kuma abinda ke faruwa basu isa su sa in kasa hango damuwarki ba... Watakila a kwanakin baya muryarki a waya taso ta ɓoye min wani abu tunda ba ganinki nake yi ba, amma a yau kallonki kawai na yi Amina, na zaƙulo tarin abubuwan da ban sanki dasu ba fal." Sautin muryar Amman ya fito da ɗimbin abubuwa masu yawa, masu yawan da a cikinsu babu wanda bai sake karya zuciyar Amina ba, yana tuna mata da rayuwarta ta baya data shuɗe cikin wani kankanin lokaci, lokacin da Hajiya Kilishi bata yiwa Baba wannan kiran ba balle har a fara ƙulla zaren ƙaddarar ta, lokacin da bata kirga damuwa a cikin lissafinta tana kwana tana tashi ne kawai da mafarkin abinda gobe zata haifar. "Me suke yi miki Amina? Ki faɗa min abinda yake ƙasan wannan kyautatawar..." Ba shiri leɓɓenta ya tale cikin kokarin yin kuka yayin da take cakuɗa yatsunta cikin juna, kuma kaf a cikin bayanin da bakinta ya fara, layi biyu ne kawai ya sa fuskar Amma haskawa da tsananin mamakin da ko na nesa zai ganshi karara, amma bayan wannan layi biyun, saurarar bayanin ƴarta tata take yi da dukkan wata nutsuwar da take da ita a duniya... Nutsuwar da take da ita ta Halimatus- Sadiyar ta, sannan nutsuwar da a cikinta ta shafe shekaru ashirin da ɗoriya a gidan aurenta ba tare da wani mahaluki a duniyar nan ya taɓa jin kanta game da mijinta ba. Nutsuwar da a cikinta ne idan za'a taro duk mutanen da suka santa a rayuwa, ƙaryane a samu mutum guda da zai tabbatar da wani aibinta baiyananne... Nutsuwar da a cikinta wasu tarin abubuwa suka faru da idan da za'a buɗewa Hajiya Kilishi su, zata yi dana sani sau dubu na inda ta kawo kanta, zata raina duk wani tunaninta dama wayonta, zata san cewa tayi kuskure wajen amfani da ƙwaƙwalwarta wajen cimma munafunci, mugunta, yaudara har ma da zalunci. Zata gane cewa ba an halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta fitar da da kaidi kamar yadda take taƙama ba, zata san cewa Allah ya halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta samarwa kanta duniya da kuma lahirarta a tafin hannunta kamar yadda ita tayi. Kuma a karo na farko tun bayan tsawo lokaci wani murmushi ya suɓuce a fuskar Amman, ita ta sani ba'a banza jikinta ya bata cewar bata son kai ƴarta cikin wannan gidan ba, ashe wata halittar ce mai ɗauke da irin ƙwaƙwalwar ta a wajen, banbancin kawai shine ita waccan ƙwaƙwalwar cike take da duhu tata kuma fara ce kal! Idan kissa da dabara Kilishi ke taƙama dashi, tazo wajen da yake daidai ita, hausawa sunce karen bana maganin zomon bana! wasan nasu ne yanzu, kowa zai yi nasa cizon da sunan ceto! Kuma Amina da Ma'aruf ɗin data zaɓa dasu za'ayi wasan! Wasan da a karshensa Sarki ɗaya zai tsaya a wani matsayi da ita ta riga ta saba dashi. Don mutane ukun da ta ga ƙarshen makircinsu a rayuwarta, bata jin Kilishi ta ko kamo yatsan ƙafarsu, kuma kamar yadda ta nuna musu, haka zata tabbatarwa da Kilishi itama yadda cikakkiyar macen data amsa suna da matsayinta ke amfani da ƙwaƙwalwarta a bigiren da ubangiji ya halitta mata ba bigiren shaidan ba, zata nuna mata irin yadda tayi asarar nata tunanin a duniyar nan! A hankali ta gyara zamanta sannan ta furta. "Daga yau kar na ƙara ganin hawaye a fuskarki kamar yadda baki taɓa ganinsa a tawa ba...!" Waɗannan kalaman su suka zama na farko da ta shiga sauke ƴarta daga raunin da ta hau kai zuwa dakakkiyar Aminarta da ta san ta baro hannunta da ƙwarin gwiwar cewa zata iya tunkarar yaƙin dake gabanta saboda mahaifinta. Banbancin shine wannan karon zata sa ta fuskanci yaƙin ne saboda kyautatawar rayuwarta... a tafin hannunta zata ɗora mata rayuwar gidanta sannan a ɗaya tafin, zata ɗora mata Kilishi bayan sun sa ta biyo ta kan matattakalar... 'Ɗan hakin da ka raina...! *** Haseenah Guest Inn, Jigawa. 04:30pm "Gidan da ka dauko Hamidan zaka koma Ma'aruf, a cikin mutanen gidan na san baza a rasa wanda zai tsaya maka a matsayin shaida ba, na gaya maka kuɗi kawai zaka basu har sai kayi limiting iya wadanda kake so, don wannan ita kadai ce hanyar da nake ganin zamu bi." Muryar Ishaq ta faɗa a cikin wayar dake kare a kunnen Ma'aruf wanda ke tsaya a barandar wani ƙayataccen Guest inn dake cikin garin na Jigawa. Hannunsa ɗaya ya zura a cikin gashin kansa kasancewar ya cire hular kansa ya baro ta a cikin mota. "Na gaya maka babu shaidar da zan gabatar Ishaq, ka barsu suyi dukkan abinda zasu yi, I have my ways akanta ita Ruƙayyan ita ta sani." "Ka shirya faɗuwa kenan tunda ka san kotu ita da shaidu take dogaro ko?" Ya cije leɓɓensa kaɗan. "Ko hakan ne zai faru let them Ishaq, na san abinda zanyi. Kar ka tanadi komai kawai ka cigaba da harkokin ka, Allah ya kaimu ranar." Da haka suka yi sallama a wayar da wataƙila itace ta huɗu tsakaninsu a yau kaɗai, ya kashe wayar daidai lokacin da wani ma'aikacin Guest inn ɗin ya ƙaraso inda yake. "Yawwa yallaɓai, gashi an kammala komai." Cewar matashin yana miƙo masa wani muƙulli. "Nagode sosai." Ya faɗa da murmushi yana karbar muƙullin ya zura a aljihunsa, kuma a cikin wayar tasa ya sake nemo nambar Hajiya Kilishi. A wanna lokacin Hajiya Kilishi na ɗakin Baffa wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi zuwa Kaduna, shayinsa take ƙoƙarin hada masa yayin dashi kuma yake daga can kan kujera yana shafa man robb akan kafarsa don fitowarsa daga wanka kenan a lokacin. Fuskarta ɗauke da faffaɗan murmushi ta ɗaga wayar tana fadin. "Mai gaskiya na, kun taho ne?" Ma'aruf ya girgiza kansa lokacin da yake tafiya wajen motarsa. "A'ah Mami, yamma tayi sosai, so zamu kwana ne sai gobe, yanzu ma zanje in dauko ta daga can." A lokaci guda irin wannan shirun dake biyo bayan walƙiya bayan haskawarta kuma kafin zuwan tsawa ya ratsa ƙwaƙwalwar Hajiya Kilishi da ta tsaya daga kokarin ɗebo madarar da take yi tana jinsa. Biyu kenan! Sau biyu kenan a jere Ma'aruf ya yanke irin wannan hukuncin ba tare da tuntubarta ba, na farko tafiyar tasu zuwa Jigawan da kai tsaye yazo yake gaya mata tare da kowa, a yanzu kuma kwanansu a garin? Me yake shirin faruwa ne? Ta girgiza kanta a fili lokacin da shi yake cigaba da gaya mata wani sabon labari na cewar baya son tuƙin dare ne, ba sai wani satin ba kamar yadda ta tsarawa Awwalu, a gobe ko jibin nan Ma'aruf zai sake komawa cikin ciwonsa. Ba ta yin saken da abubuwa ke cakuɗe mata, dole ne ta kwantar dashi don ta fahimci duk abubuwan data gano cewa suna ɗagewa daga cikin tsarinta. Wani abu da bata sani ba shine, abubuwa ma basu fara ɗagewa ba ko kaɗan! *** Kun fahimci cewa kowa ya shirya a wannan Babin??😅😅 To su waye zasu yi nasara? su waye zasu fara su kasa? Su waye kuma zasu faɗi kasa wanwar?? Me kuke tunani game da Amma da kuma ƙudirinta?😀 Kar ku manta kuma, zamu yi kwanan Jigawa....😍😆😆 #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA BIYAR. ~~~~~~~ This could be the start of something new. -High School Musical "Ina zamu je?" Aminah ta tambaya lokacin da Ma'aruf yayi wata kwana data dauke su daga titin da ta kula cewa tun da suka shigo cikin garin Jifaywan a dazu shi suka yi ta miƙewa, muryarta a hankali ta fito yayin da take kallon hanyar. "Wani waje." Amsar tasa ta fito a gajarce ba tare da ya kalle ta ba. Sai ta juyo a hankali ga barin kallon titin da suke kai ta kalle shi ita, idanunta na shaida rashin fahimtar zancen, a can ciki kuma ruɗanin da take ciki, kamar ba zata ce komai ba amma sai muryarta ta sake fitowa. "Nayi zaton gida zamu tafi." Kalaman suka fito tare da nauyin yadda a yau bakinta ya furta wani waje daban da sunan Gida, saɓanin wajen da ta taso da rayuwarta a ciki. Ya girgiza kansa sannan ya juyo ya kalle ta, nauyin idanunsa suka sa taji kamar ta sunkuyar da kanta amma ta daure. "Dare yayi kuna bana son tuƙin dare a babbar hanya, so anan garin zamu kwana sai gobe tukunna." Yadda sautin muryarsa ya fito a cikin motar da kuma yadda yake kallonta yasa ta haɗiye wani abu a makogwaronta da bata san meye ba kafin ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan kuma ta sunkuyar dashi ƙasa ta shiga wasa da karshen mayafinta, tattaunawarsu da Amma bata kare ba sam zuwansa ne ya katse su, wanda ta san haka ne, da tun a can ta roƙe shi fa ya barta ta kwana tare dasu idan yazo da safen sai ya koma ya ɗauke ta, wani abun ya sake zarcewa makogwaronta tuna cewa a yanzu bata san ina zai kaita su kwana ba ma. Amma duk da haka sai taji wani ɓangare a cikin zuciyarta na washewa, zuciyarta na rage nauyin da take ɗauke dashi a ɗazu mai cike da taraddadin rashin sanin abinda zata yarda dashi a al'amarin Hajiya Kilishi, ko ba komai yanzu ta san tana da babbar hanyar da take da yakinin zata samawa kanta mafita kamar yadda Amma ta fara gaya mata, Har a yanzu tana jin tasirin kalamanta da ya cika kanta taf! Yana ƙara buɗe wasu sababbin shafuka da a iya zagayen tunaninta gabaɗaya ita bata hango su ba. Tana jin yadda amon kalaman nata ke zagaye cikin kanta, ma'anarsu na bi ta cikin jijiyoyinta suna taso da ƙarfin gwiwar da ta nemi ta rasa, kuma duk da taraddadin da take ji, koina a cikin kanta dama jikinta yana gaya mata cewar yanzu ne komai zai fara, don kamar yadda Amma ta fada ne babban kuskuren da Hajiya Kilishi tayi, ya riga ya bude musu ƙofar nasarar su. "Mafitar ta riga tazo hannunki Amina, buɗe idonki kawai zaki yi ki kalle ta, kina da rabin maganin wannan matsalar yanzu a hannunki, wanda babban abun shine sanin halinta da kikayi, ita kanta bata sani bane amma tayi babban kuskure wajen bayyana miki sirrinta duk kuwa da na san cewa iya abinda take so ki sani kawai ta faɗa akwai sauran ƙurar da dole na san ta lulluɓe. Amma tun ana na fara raina lissafinta Amina, don da ace tayi bunƙasar da zan sara mata, da zata sami tarin hanyoyin da kema zata juya ki ba tare da kin san sirrinta ba..." Wasu daga cikin kalaman Amman kenan da suka ƙara saka ta yarda cewa mahaifiyarta na cikin irin daidaikun matan da ake misali dasu a duniya, masu halayen da dimbin jama'a zasu gani tamkar a mafarki, da kowacce kalma da ta gaya mata a yau, zuciyarta ta ƙara yarda cewa mahaifiyarta itace babban makamin da zata iya tunkarar komai dashi a duniyar nan bayan addu'a. Sai dai akwai wani abu guda daya a cikin kalaman nata dake fassara abinda zuciyarta bata taɓa lissafawa ba, abinda har yanzu da ta tuno yake rikita lissafinta yana sa hannayenta rawa, har yanzu bata gama sanin tunanin Ma'aruf game da ita ba, don haka ba zata taɓa iya ɗorar da komai ba a wannan fannin. Ta rufe idanunta tsawon wasu sakanni kafin ta sake buɗe su tana ƙoƙarin saita kanta. Amma ta gaya mata cewa lokacin wani rauninta ya kare, kar ta yarda wani abu ya gaya mata cewa an fi ƙarfinta ba zata iya ba, tace mata itama macece, duk wani abu da take taƙama dashi itama tana dashi, kawai ita tana amfani da nata wayon ne ta mummunar hanya, don haka idan ita zata ɓullarwa gaskiya, a lokaci kadan ne zata kawo karshenta don gaskiya itace sama da komai a duniyar nan. "Kilishi bata fi kowacce mace ba a duniyar nan Amina, yadda take takama da wayo da kuma dabararta, haka Allah ya halittawa ƙwaƙwalwar dukkan mata don ita mace uwa ce, an halicci mutane da yawa da zasu rayu a ƙarƙashinta wanda kowanne da irin ƙalubalen rayuwarsa, shi yasa Allah ya buɗe ƙwaƙwalwarta ta yadda zata iya samar da mafita kala-kala a fannin rayuwa. Wasu matan basa gane hakan ne har suyi yunƙurin sanin abinda zasu iya, matan kuwa da kika ga suna zaune lafiya tare da mazajensu ƴaƴansu harma da duk wanda zai raɓe su, sune wanda suka iya buɗe wannan baiwar tasu, Mata irin Kilishi kuma sune wanda suke amfani da wannan baiwar ta hanya mai munin da har suke ganin cewa sun fi kowa. Yanzu girma yazo kanki da gaske Amina, kin fara ganin hakan tun daga ranar da kika bar karƙashinmu, kuma hausawa sun ce aure yakin mata, yaki ne da kowacce mace akwai kalar nata, don haka kema dole ne ki bude ƙwaƙwalwar ki, ki karɓi wannan girman sannan ki fuskanci naki yaƙin Amina..." A daidai wannan lokacin suka shigo harabar wani haddadden gini mai tarin fitulun dake ta haske suna maraba da daren da bai kai ga ƙarasowa ba. Ma'aruf ya tsayar da motar a jerin motocin dake tsaye a wajen daidai lokacin da idonta ya zare akan sunan wajen. Haseenah Guest Inn. *** "Mene ne total charges for Adjustment and Uncollectables?" Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar da yake yi daga cikin dakin, yana zaune ne akan wani dan karamin dining table dake can karshen dakin yayin da hannunsa ke rubutu a cikin notepad din dake kan teburin. Kayan jikinsa wata loose T-shirt ce da ya siyo da kuma wani gajeran wando kalar grey. "Next..." Ya sake faɗa bayan mai maganar na ciki ya gaya masa wani adadi da ya rubuta a cikin wayar. "Ka gaya min Net Patient Revenue din?" "Na gaya maka yallabai, shine na biyu bayan total charges na Patient Care gabaɗaya." Mai maganar daga cikin wayar ya fada, sai ya gyada kansa yana bude shafin baya, ya karanta abinda ya rubuta sannan ya sake dawowa inda yake yace. "Operating Expenses din fa?" Mutumin na ciki ya sake faɗo masa wani adadi da ya shifa rubutawa. "Sannan sir akwai Bad debts ɗin wancan..." "Sai kuma Natural Expense ɗin?" Ya katse shi ba tare da ya saurari abinda yake cewa ba, mutumin ya ɗanyi shiru kafin ya faɗo wani adadi na makudan kudin da saida Ma'aruf ya jinkirta kadan yana saurarar sa kafin ya rubuta. "Yallaɓai ka saurare ni akan zancen bashin nan, bamu da wata hanya ne dole..." "Just tell me the total Sadiq." (Kawai ka gaya min jimlar komai gabadaya Sadiq.) Muryarsa ta fito a hankalin da take tun bayan sallar magariba da yayi buda baki. "Wallahi yallabai zai fi kyau ka duba Report ɗin gaba ɗaya tukunna gabadaya 42 pages ne, idan ka karanta komai you will realize that..." "Ka gaya min total din kawai Sadiq." Yadda sautin muryar tasa ta fito wannan karon ita tasa Sadiq din sarewa daga dukkan ƙokarin da yake fanin zai iya shawo kansa, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya fadi wasu makudan kudade da shi kansa Ma'aruf ɗin ya sani idan za'a bincike account dinsa na bankuna tsaf a tattaro komai baza 'a taba samun wannan adadin ba, don haka bai ma rubuta ba, wani guntun murmushi ne ya suɓuce a lebbensa yayin da yayi baya ya jingina da kujerar da yake kai yana kallon gabansa tamkar Sadiq ɗin ne a wajen. "Wallahi yallabai..." "Sadiq" Ya katse shi, sautin muryarsa can ƙasa amma kuma a kausashe. "A rufe asibitin, a tsayar da komai, kwana kaɗan na baku, I'm coming in few days, ku san yadda zaku gyara wannan abin in a reasonable way kafin zuwa na. Idan ba haka ba, na rantse da Allah wasu ne zasu ci muku abinda kuka ɗiba ba ku ba, and just dare me and see.!" Yana faɗin haka ya kashe wayar, ya cilla ta kan teburin da karfi har sai da screenguard ɗin dake kanta yayi wata katuwar tsaga guda daya, sannan ya cusa hannayensa duka biyu a cikin gashinsa yana ƙoƙarin saita numfashinsa, ransa ne yake shirin baci ya sani, amma yana kokati da dukkan iyawarsa ya danne hakan kamar yadda ya saba yanzu a kwanakin nan. Bakinsa ya shiga karanto hasbunallahu wa ni'imal walkil daidai lokacin da kofar toilet din dakin daga can gefe ta buɗe bayan abinda zai iya kira aƙalla minti talatin. Ya sauke hannayensa daga fuskarsa kafin ya juyo ya kalle ta, tana tsaye daga kofar kamar zata koma ciki ne ta sake rufewa, babu shiri yaji dukkan abinda ke cikin kansa na sulalewa yana bin iska, rigar da ya siyo ita ta saka, kusan iri daya ce da wadda ya taɓa gani ta saka a gida ranar da tashi cikin daren nan, me tsawo daga baya amma ta gaba kuma iya gwiwa take kawai, kuma yadda idanunsa suka riƙe hoton siraran kafafunta a wancan lokacin shi yasa kai tsaye yace a mayar da wanda ya ɗauko a ciro masa ita. Daga yanayinta kawai ya san ta saka ne don bata da wani zaɓi, tunda wani mai wanki da guga na Hotel ɗin yasa yazo ya karɓi kayansu don ya wanke zuwa gobe, idanunsa kallonta kawai suke tun daga nan, ta yafa bakin mayafinta da bata bayar dashi ba akanta amma duk da haka gashinta na fitowa kamar ɗazu da safe. Daga inda Amina take tsaye, cakuɗa yatsunta kawai take yi cikin junansu saboda rawar da hannayenta ke yi musamman a yanzu da take ƙara ganin wautarta na fitowa a haka, amma ya zata yi, har tawul a cikin toilet din ta ɗauko ta ɗaura taga abin bai dace ba ta cire shi. A ajiye ma zancen ƙafafunta dake waje a gefe, tunda take bata taɓa lissafawa cewa zata yi kwanan hotel a rayuwarta ba idan har ba wai Makkah ko wata kasar taje ba, wanda shima ba'a irin wannan yanayin take hango shi ba, shi yasa tun da suka shigo zuciyarta ke rabewa gida biyu tana sake haɗewar da har a yanzu ta kasa samun sauƙi duk kuwa da ƙarfin halin da ta tattaro a ranta. Ganin yadda yake kallonta yasa ta juya da sauri ta ƙarasa jawo ƙofar toilet ɗin ta rufe sannan ta shiga tahowa cikin ɗakin. Wani abu ya zarce maƙogwaron Ma'aruf da yake kallonta tana tahowa sai mutstsika yatsunta take yi cikin junansu yayin da siraran ƙafafun nata ke tafiya. Tare da Ruƙayya yasha tambayar kansa meye babban interest dinsa game da mace, sai dai a lokacin ya kasa tsaida zuciyarsa akan komai banda kyawunta don ita ɗin kyakkyawa ce, amma a yanzu ya samu wannan amsar da ya daɗe yana nema, don yadda zuciyarsa ke sake ɗaukan hoton ƙafafun Amina tana masa kyakkyawar ajiya, a wani yanayi ne da wataƙila ko bayan ransa ba zai manta ba. Ta ƙaraso kamar mara gaskiya ta wuce shi ta nufi wajen wani ɗan ƙaramin table da ma'aikatan wajen suka kawo musu abinci kamar yadda ya basu umarni. Kuma sai a sannan tayi magana, tun bayan da suka idar da sallar isha da ya bata wayarsa ta sake kiran mahaifiyarta ta shaida mata cewa basu bar garin ba sai gobe tukunna. "Wanne abincin zan zubo maka?" Yaji ta tambaya daga bayansa inda taje ta tsaya, sai kawai ya ture komai a ransa ya taso ya taho inda take, ta juya bayan nata kamar yadda ya zata tana ƙoƙarin buɗe plates ɗin masu wasu irin manyan-manyan murafe kamar na abincin sarakai, a hankali ƙafafunsa suka tako ta kan carpet ɗin dake shimfide a wajen ya ƙaraso ya tsaya dab da bayan nata idanunsa na nazarin ɗan karamin jikinta dama siraran hannunta, bayan haka tsawonta ma gabadaya iya kafaɗarsa ne, ya san yana da tsawo don shi da Jamal ana cewa duk tsawon Hajiya Maimuna suka yi, amma bai taɓa tsayawa yayi nazarin yadda yafi wani tsawo irin haka ba sai akanta, don ko Ruƙayya ya sani ne cewa da kaɗan yafi ta. Kuma wataƙila shirun da yayi ne yasa ta juyowa a hankali hannunta rike da murfin da ta ɗauko guda ɗaya, idonsa ya sake kaiwa kan kafafunta a yanzu data juyo, sai yanzu ya lura cewa akan farcen kafafun nata akwai kalar baki alamun lallen da bai gama fita ba, kuma yadda farcen ya rabu kala biyu fari da baki yasa shi kasa daina kallonsu. Amina ta sunkuya kalli ƙafafunta da yake kallo tana son ta nemo abinda ke wajen amma bata ga komai ba, yadda yake tsaye dab da ita kaɗai ya isa yasa zuciyarta rabewa gida biyu, amma tunda bata rabe tun a lokacin data fahimci cewa yau zata kwana daya daki daya dashi ba, bata jin a yanzun ma zata yi. Ta sake haɗiye wani abu karo na ba adadi a maƙogwaronta tana son kore ɗimbin tunanin dake kanta kafin ta sake yin magana. "Zaka ci abincin?" Muryarta ta fito ne kamar tana son tuna masa cewa ba'a kafarta fuskarta take ba, kuma hakan yayi aiki don a lokaci guda ya ɗago da idonsa ya kalle ta. "Naci abincinki, kin manta?" Ta yaya zata manta, da wannan busashshiyar doya da ƙwan data soya tun safe yayi buɗa baki, tea ɗin wajen kawai yasha ya cinye doyar gabaɗaya, a lokacin tana waya dasu Amma, tana daga karshen ɗakin kallon yadda yake buɗe-bude a cikin labtop ɗinsa yana cin doyar, wani abu da ya kara nutsar da zuciyarta a cikin kirjinta tana jin dama abinda tayi yafi doyar kaɗai, sannan kuma wani abu da ya fara buɗewa kalaman Amma dake sa hannunta rawa kofa a zuciyarta. Sai ta girgiza kanta a yanzu tana ƙoƙarin cigaba da kallonsa. "Ai wannan ba zai isa ba, idan mutum yayi azumi gwara yaci abinci da yawa." Ya gyaɗa kansa shima yana kallonta. "Na sani, amma raina ne ya fara ɓaci yanzu, bana jin zan iya cin abincin." Kawai sai ta samu kanta da tambayar. "Me ya faru?" Kuma fitowar tambayar yasa taji kamar ta fara yin nisa da taraddadin dake zuciyarta. Hannunsa ɗaya taga ya zura cikin gashin kansa kamar abinda zai faɗa zai yi masa wahala kafin wucewar sakan biyu yace. "Ina da abubuwa da yawa a gabana, so mutane na using wannan opportunity ɗin suna cuta ta, Annual report din MMB- 6 aka aiko min yanzu, kuɗin da suka ce sun kashe a shekarar nan Amina ko ni bani dasu yanzu." Ba maganganun ne suka daki zuciyar Amina ba, sautin muryarsa ne yadda ya fito cike da wani rauni da idan za'ayi musu da ɗimbin mutane zasu kwana suna rantsewa cewa ba daga muryar Ma'aruf wannan raunin yake ba, ba shiri taji ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace. "Meye MMB-6?" Wataƙila idan ta fara sani meye shi din zata fahimci abinda maganar tasa take nufi. "Asibiti na ne da yake Abuja." Sai ta sake gyaɗa kanta tana jin kamar maganar tafi karfinta, amma kuma kai tsaye sai tace. "Ance idan hankali ya ɓata hankali ake sawa ya nemo shi, yanzu ko ranka ya ɓaci babu abinda zai canja, kamata yayi ka samu nutsuwa mai kyau, sai kayi amfani da hakan ka gano koma wane irin akasi ne aka samu." Maganganun suka tafi har ƙarshen zuciyar Ma'aruf, suna fito da irin kwanciyar hankalin da yake ji a duk lokacin da ya gayawa Mami damuwarsa kuma ta bashi ɗaya daga cikin shawarwarin ta, Amina bata sani bane amma itace mutum ta farko daya dangance shi bayan Ishaq da suka san da zancen asibitin nan. Abu ne da ko Mamin bata sani ba, kuma shi yasa dama yake damuwa duk sanda aka samu matsala akansa don ya san babu wanda zai iya bashi shawara mai kyau akan hakan tunda ko Ishaq baya yiwa zancensa. Kuma haka kurum ya zaɓi boyewa kowa sanin da zaman asibitin don so yake yi da gaske ya binne duk wata halayyarsa ta baya tare dasu kamar yadda yayi wa kansa alƙawari. Zama likita yana daya daga cikin burinsa na farko a duniya, don haka nacin da zuciyarsa ke masa shi yasa shi tsallakewa zuwa garin Abuja ya gina ƙaton asibitin guda inda ya danka amanarsa a hannun wani likita mai suna Sadiq, shi yake jagorantar komai na asinitin don hatta tarin likitocin dake musu aiki shi yake biyansu, shekaru biyar kenan da kafa asibitin, kuma tun bayan shekaru biyun farko aka fara samun matsala a annual report din da suke bashi duk ƙarshen shekara, ya zama kudin da suke cewa duna amfani dashi duk shekara ya fara fin karfin tunaninsa. Sai gashi yanzu minti ɗaya kawai gaban Amina duk dauriyarsa ya kasa riƙe wannan sirrin ya fallasa mata komai, amma kuma da ta bashi sai tasa bai ji yayi nadamar sanar da itan ba, hasalima zuciyarsa gode masa ta dinga yi don aƙalla abinda ta faɗa ɗin ya sama mata wani sauƙin. Sai kawai ya gyaɗa kansa yace. "Thank you." Sannan ya zagayo ta gefen table ɗin yace. "Me zaki zuba mana?" Tambayar tasa ta juyowa itama tana jin nauyin abinda ya faɗa, plates din ya shiga budewa gabadaya yana tara murafansu a hannusa ɗaya. "Wanne kafi so a ciki?" Ta samu kanta da tambaya babu wani dalili. Ya girgiza kansa shima. "Ni zan ci ko meye kika zuba, favourite abinda nake so baya cikin wadannan." Ya fada yana kokarin ajiye murafan a gefe, sannan kai tsaye ya shiga gaya mata irin abincin da yake so wanda kusan duka na gargajiya ne, sanda yace mata har da ɗanwake sai da ta tsaya tana kallonsa, don ita a tunaninta mutane kamarsa basa ɗaukar abincin gargajiya da muhimmanci. Ya tambaye ta abinda take so itama kuma sai ta samu kanta da ture komai a ranta ta shiga gaya masa, kuma da kowacce kalma data faɗa tana ji kamar tana karkaɗe ragowar taraddadin dake ranta ne. "Ina son chocolate, sannan zan sha lemon zoɓo a koina kuma a kodayaushe." Ta fada lokacin da yake tambayarta abinda take so na kayan kwaɗayi. Ya gyada kansa. "Naga alama, cox naga zoɓo da yawa a fridge dinki." Ta gyada kanta a hankali itama. "Ina ga ba zan taɓa iya dadewa babu shi ba a koina." "Wow, I like the enthusiasm."(ina son kwarin gwiwar nan.) Muryarsa ta gito da slamun cewa shima ya fara jin dadin sakewarta. Sai tayi wani guntun murmushi da bata san daga ina ya fito ba tana kallon abinda take zubawa. "Wane kalar chocolate kika fi so?" Da alama so yake hirar ta cigaba da yin nisa. "Kowanne." Wannan karon muryarta ta sake fitowa kamar silin gashin dake faɗowa ƙasa a hankali ba tare da ta dago ba. "Chocolate bai dame ni ba amma I always enjoy Ferraro Rocher." (Ina jin dadin Ferraro Rocher.) Bata taɓa jin ko sunan ba, kuma sai Allah ya taimake ta kafin tayi tunanin abinda zata faɗa, wayarsa dake can kan table ɗin daya baro ta ta shiga ƙara, don haka ya karbi plate din da gama zubawa ya tafi wajen, ya ajiye plate shi akan table din sannan ya kara wayar a kunnensa ya shiga magana da wani cikin Pidgin english, irin tsantsar Pidgin din da ita bata taba ji ba ma, amma kuma sai yayi mata dadi, yadda sautin muryarsa yake haɗewa cikin accent ɗin da kana ji ka san ya fito ne daga Jinsin Hausa/Fulani. 'Matar ƴan gayu.' Haka Aminu yayi ta tsokanarta ɗazu, kuma ita kanta duk da hargitsin yanayin da take ciki ta sani cewa kamar yadda Hajiya Kilishi ta faɗa ne, idan banda kaddara ko zata mutu sau ɗari ta dawo Ma'aruf yafi karfinta, don a yanzu da kowacce wucewar rana tana ƙara gane cewa yafi ƙarfin hangen da take masa a lokacin da ta yarda da auren nan. Shi yasa ko a yanzu kawai ƙwaƙwalwarta ta kasa auna mata adadin kuɗin da ya kashe wajen kama ɗakin nan don kwana ɗaya kawai. Ta ɗebo farfesun kifi na ƙarshe a cikin wani ɗan bowl sannan ta juyo tana hango shi daga can inda ya zauna a jikin table din yana magana, kuma kayan jikinsa na T-shirt da gajeran wandon nan suka sake tuna mata da wanda ke jikinta itama, ba shiri ta hadiye wani yawu a maƙogwaronta tana jinjinawa kaddara, don in ba ƙaddarar ba ba zata taba hango kanta a irin wannan yanayin tare da wani namiji kuma dadin daɗawa a Hotel ba. Ƙafafunta duka karasa a hankali har gabansa, ta tsaya daga gefensa sanda ya dago daga rubuta wani abu da yayi a jikin wata ƴar jotter yana kallonta, ya taimaka ya ture mata kayansa dake kan table din kafin ta ajiye plate din a hankali kusa da dayan sannan ta juya niyyar dauko ruwa wanda tun dazu ta ganshi a fridge din dake can gefe, amma sai kawai taji ya riƙo hannunta na hagu, dogwayen yatsunsa suka ratsa cikin nata yana riko ta, a lokaci guda numfashinta ya katse a ƙirjinta yayin da yatsunta suka yi sanyi kalau! Ya sake riƙo hannun nata sosai sannan ya jawo ta baya ta dawo gabansa, shi yana zaune ita kuma tana tsaye a gabansa da kafafunta duk a waje, ba shiri ta dunƙule tafin kafarta akan sassanyan marbles din ɗakin, sannan ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yake motsa yatsunsa a cikin nata. Ta buɗe su daidai sanda ya gama wayar, idonsa yana kan kafafunta ne da har yanzu ta rasa me yake gani a jikinsu, kuma kafin ta gama tunanin hakan taji ya jawo ta zuwa kasa a hankali, ya durƙusar da ita a gabansa, dab dashi sosai wanda hakan yasa ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana cije gefen lebbenta. "Wata magana nake son muyi Please..." Yadda muuryarsa a fito a hankali da kuma zurfi ya haddasa faduwa da saukar numfashinta. "Zamu iya yi yanzu?" Ya ƙara tambaya a lokacin da take kokarin tsayar da iska a kirjinta, da kyar ta daure ta daga kanta sau biyu babu kari. Shina ya gyada nasa kan a hankali yana cigaba da kallon fuskarta. "Na sani a yadda komai ya fara a tsakaninmu akwai tarin irin tunanin da kike yi akaina, na san an gaya miki tarin abubuwan da ba lallai ne na iya ƙaryata miki su ba, kinji wanene ni ta bangare da yawa na sani Amina, kuma har nima na bada gudunmawa wajen saka miki wani tunanin akaina tun a wancan lokacin, wani abu da nayi shi ne ba don komai ba sai don in hana faruwar auren a tsakanin mu." Yayi shiru ya cigaba da kallon fuskarta, kuma ganin yanayinta bai canja ba yasa shi cigaba. "I'm a mess Amina, akwai tarin abubuwan dake gabana kuma a tsakiyarsu ne na tsinci zancen aurenmu wanda ni tun bayan lokacin dana rabu da Ruƙayya ban kara tunanin cewa zan sake aure ba, abubuwa sunyi min yawan da bana son nauyin komai ya sake ƙaruwa akaina, saboda haka wannan wasiƙar da na baki nayi ne don in tsorata ki ta hanyar da zai sa ki ƙi yarda sabida su Baffa baza su saurare ni ba a lokacin, abinda na manta a wannan lokacin shine ban isa in canja ƙaddarar da Allah ya hukunta ba tunda hakan babu abinda ya canja." A wannan lokacin numfashin dake ƙirjin Amina ya kasa tsayawa waje guda, sai kokari take dashi kamar kifin da ya fito daga rywa yana wutsil-wutsil, hasken fitukub dakin ya karu a idanunta yayin da wata iska ta shiga busuwa daga maka-makan windunan dskin kasancewar a sama suke. "Daga ranar da na fara ganinki Amina, nayi nadamar abinda nayi, na san cewa ban kyauta ba da har na saka wannan tsoron da na gani a cikin idanunki, wanda duk da hakan kuma bai hana ki kyautata min ba, bai hana ki nuna min kirkin ki da kuma halayenki na gari ba, kuma yanzu wannan kirkin naki nake kwaɗayin cigaba da samu Amina, ina son nutsuwar da nake samu a wajenki don itace babban abinda nake bukata wajen tafiyar da rayuwata a yanzu, shi yasa nake rokonki da ki manta duk wani hasashe da kike yi kaina Please, ki bani damar da zamu yi normal life kamar yadda kowa yake yi, wallahi nayi alkawarin ba zan taɓa cutar dake ba insha Allah." "....Kamar yadda na faɗa miki mafitar ta riga tazo hannunki Amina, Kilishi ta bude miki kofar samun nasarar da ita kanta bata sani ba, so nake ki dauki dukkan maganganunta kiyi wa taki zuciyar ado dasu Amina, don takunta zaki bi, dukkan abinda ta fada kema shi zaki yi, banbancin da za'a samu tsakanin ke da ita shine, ke ita zaki yiwa Amina, ita zaki lulluɓe da rigar amincinki ba kowa ba, ita zaki zamewa farar wutar da ba zata taɓa sanin cewa ƙonata kike yi ba. Kuma hanyar farko da hakan zata kasance shine idan kika sami soyayyar mijinki..." Kalaman da Amma na ɗazu su suka biyo bayan dukkanin bayanin Ma'aruf a cikin kan Amina, ta tuna yadda take kallon Amman cike da ƙarin bayanin da bata furta ba Amman ta cigaba. "Kilishi ta gaya miki cewa soyayyar mijinta ta fara samu a saman ta kowa, shi ya fara yarda da ita kafin ta buɗe zuciyar kowa ta fara aiwatar da manufarta, idan baki sani ba yau ki sani Amina cewar taƙamar kowacce mace a duniyar zuciyar mijinta ce, idan taci riba anan to wallahi duk girman wata matsala koda kuwa ta mahaifiyarsa ce ta tsallake ta. Yaron nan ya riga ya zama mijinki a yanzu ko munso ko bamu so ba, don haka kije ki ƙara dagewa, ki dage wajen kyautata masa har zuciyarsa ta ƙara yarda dake akan yanzu, sannan da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..." Waɗannan sune kalaman dake saka sa hannyenta rawa a ɗazu, sune kalaman Amman dake rikita lissafinta suna gaya mata cewar ba zata iya dorar da wani abu akan Ma'aruf ba tunda bata gama sanin tunaninsa akanta ba... Sai gashi tun ba'aje koina ba hanyar farko tazo mata da sauki. Allah ya amsa addu'ar ta, Ma'aruf ya cire dukkan wani kokwanton dake zuciyarta da waɗannan iya kalaman nasa, a yanzu ta yarda cewa shi da gaske zuciyarsa wankakkiya ce akansa, abinda take ta taraddadi daga bangaren Hajiya Kilishi yake dama. Taji yadda mamaki ke cinye zuciyarta tun daga ƙasa, ashe komai ba mai wuya bane kamar yadda Amman tace, kowacce mace tana da irin nata ikon a hannu, kawai burga da barazana ce ke saka wasu yin ƙasa su yarda cewa an fisu su baza su iya ba, gashi tun basu ko bar garin nan ba ta fara samun yardar Ma'aruf a hannunta, idan haka ne kuwa ta yarda da maganar Amma na cewar da gaske Kilishi ta kiyaye su, don ko ita a yanzu tana jin ƙarfin gwiwar cewa zata iya. Kuma cikin wata irin sa'a, sai ya ƙyale ta bai nemi amsarta ba har suka kammala cin abincin da komai. Wajen ƙarfe goma sha ɗaya saura Amina ta dunkunkune a karshe gadon ɗakin har a lokacin tana ta faman sake-sake a ranar, don ko ka kaɗan ba bacci take ji ba, abubuwan da ta fuskanta a yau suna da yawan da har yanzu basu gama narkewa a cikin ranta ba. Ta juya bayanta ne tana kallon ɗaya gefen ɗakin yayin da hannunta ke wasa da ƙarshen bakin mayafin nan data yafa a akanta. A yanzu fitulun ɗakin duka a kashe suke, Ma'aruf ya kashe su kafin ya shiga toilet don ta riga shi kwanciya, sai da ya gama aikinsa tana kwance tana sake-sakenta sannan ya tashi ya kashe fitulun duka ya shiga toilet din. A yanzu babu wani haske sai na waje da yake shigowa cikin ɗakin, kuma wucewar minti biyar kawai sai kofar toilet din ta buɗe, hasken fitilar ciki ya ratsa duhun ɗakin kuma duk da ta juya bayanta sai da hasken ya shiga idonta kafin taji ya rufe ƙofar duhun na sake dawowa. Taji gadon ya motsa yana shaida mata hawowarsa zuwa daya gefen da sanda yaje jan sauran bargon da ta rufe ƙafafunta dashi zuwa nasa jikin. Sakan ɗaya, biyu, suka wuce tana cigaba da wasa da mayafinta kafin taji muryarsa, can ƙasa a hankali kamar duhun daren. "Amina..." Ya kira sunanta kamar wannan ne karo na farko daya fara faɗa, yadda tunaninta ya tsaya cak haka ma daren ya tsaya, kamar shima yana jiran amsar da zata bayar ne. Tayi kokarin haɗiye wata busashshiyar iska a makogwaronta sannan tayi dauriyar amsawa a hankali. "Can I hold you.. ?" (Zan iya riƙe ki?) Bata san me take tunanin a wannan lokacin ba, bata san ma me taje yi va ko kuma abinda yake faruwa a cikin kanta, ta san dai kawai zuciyarta ta ƙirga wucewar wasu sakanni ne data san cewa jiranta yake yi kafin duk wata dauriyarta ta rinjaye ta wajen ɗaga kanta a hankali. Kuma bata san ya akayi yaji ta ba, don a lokaci guda yasa hannunsa daya ya janyo ta zuwa jikinsa, ya juyo ta tana fuskantar sa yayin da hannunsa ɗaya ya zagaye waist ɗinta, sannan ɗan kaɗan ya ratsa ƙafafunsa a tsakanin nata. Ya hade ta da jikinsa har tana jin kara bugawar zuciyarsa kamar kaɗawar igiyar ruwa a bakin teku wanda sautinsa ya haɗe da amon tata zuciyar, ya zama idanunta basa ganin duhun daren sai wanda ke tsakaninsu kawai, numfashinsu ya hade waje guda yayin da ƙamshin turare da kuma sabuntar kayansu ya cika hancinta. Kuma bai isa Ma'aruf ya gama rikita zuciyarta ba sai da ya sunkuyo da fuskarsa daidai cikin wuyanta ba shiri kuwa jikinta ya shiga girgizawa gabaɗaya a cikin nasa, kuma ga mamakinta sai taji yayi wani abu kamar murmushi sannan a cikin kunnenta ya furta maganar data rikito da duniyarta bakiɗaya ta rugurguje. "Kar ki damu, not now, not here." (Ba yanzu ba, ba anan ba.) Shikenan! Ma'aruf ya gama da rayuwarta! *** Kano. 09:30Am No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Quaters. "Wai har kun dawo?" Surayya ta faɗa a lokacin da ta fito dafa daki tana kallon Amina daje zaune a tsakiyar falon nasu tare da Sameerah wadda ta cika gabanta da kayan breakfast. "Tun wajen ƙarfe takwas fa suka dawo. Yayan har ya tafi aiki ma." Sameerah ta bata amsa lokacin da take hada nata tea din. "Auren ma'aikacin kamfani na da wuya ko?" Surayyan ta fada tana kallon Amina lokacin da tazo ta zauna a kusa da ita tana ɗaukan pillow ɗin kujerar zuwa cinyarta. Da murmushi a fuskar Amina tace. "Gashi nan dai, ni ban saba ba har yanzu." "Gaya min zaki yi idan da wuya tun wuri in kori Tahir." Kafin ta amsa Sameerah tace. "Ki kore shi ma, don Wallahi Baffa yace ba wanda zai sake yiwa aure a gidan nan sai man da shekara biyar. Su Salma sun karya tattalin arzikinsa." Dariya kawai Amina tayi tana kallonsu lokacin da musun da suka saba a kullum ya kaure tsakaninsu, don ma wai Munaya na can ɓangarensu ne. Sai dai duk yadda dariyar tata ta kai akan lebbenta kawai take, don daga can kasan zuciyarta taraddadi ne fal da kuma tunanin abinda ke shirin faruwa. Don kamar yadda Samirah ta fadawa Surayya ne, tun wajen karfe takwas da ƴan mintuna na safe suka iso garin Kano, don Ma'aruf ya gaya mata cewar yana da tarin aikin dake jiransa a office, kuma ya sauke ta a gida ne ya tafi bayan ya rungume ta yayi kissing saman kanta lokacin da suka shigo ciki ya buɗe mata gidan da muƙullin dake jikin na motarsa, sannan ya juya ya barta tana kokarin hada zuciyarta waje guda ya koma wajen motar tasa da ya bari a waje. Kuma shigarta gidan ya sake tsayar da zuciyarta waje guda, yana tuna mata da kalaman Amma. "...da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..." Zuciyarta ta gaya mata cewa wannan lokacin shine zaiyi daidai da zuwanta wajen Hajiya Kilishin, don a yanzu ne zata yarda cewa da gaske zuciyarta ta wanku wajen yarda da ita. Shi yasa ta tattaro dukkan dauriyarta ta taho cikin gidan inda Sameerah ta shaida mata cewa Mamin tana wanka. "Kin gama? Mamin tace tana jiranki a ciki." Muryar Sameerah ta dawo da ita zahiri, ta ɗago tana kallonta daga can jikin hanyar koridon dakin Mamin, ta san lokacin da Surayya ta tashi ta shiga ciki amma ita bata san lokacin da ita ta tashi ba, taji zuciyarta ta buga a cikin ƙirjinta amma kuma sai fuskar Amma ta gifta a idanunta ta kore hakan, ta gyara yafen mayafinta sannan ta mike a hankali tana zagaye table din da Sameerah ta cika da kayan breakfast din, kafafunta suka taja cikin korido din lokacin da Sameerah ke gaya mata cewa ta tafi ta shiga wanka, kanta kawai ta gyada mata kafin ta rike handle din kofar dakin. Da dukkan addu'o'in da zata iya karantowa a zuciyarta ta tura kofar dakin, kuma kamshin turaren wutar da taji tunda ta shigo dakin shi ya fara shiga hancinta, ta hango shi kuwa yana ci daga can kan bedside drawer dakin daga cikin wata haɗaddiyar burner irin wadda Sameerah ta taba kai mata. Sai taji ta shaki wata busashshiyar iska a makogwaronta lokacin da ta hango Mamin, tayi wankan kamar yadda aka fada ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa da aka baza mata stones tana ta kyalli, kamar ƙyallin dake son nunawa duniya cewa ita kadai ce Kilishi irinta. Ƙafafunta suka karaso ciki da sallama, sallamar da Mamin ta amsa da murmushi a fuskarta, murmushin nan nata mai nauyin da sai a yanzu Amina ke jinsa a saman kafadunta. "Ashe ƴan jigawan har sun dawo, yaya kuka tarar dashi Amina?" Takaicin da ya taho ya taru a kirjinta wani abu ne da ba zata iya misalta shi ba, amma haka ta daurewa masa ta amsa. "Jikinsa da sauki Mami." Kuma sai da ta jira ta nemi bakin gadonta ta zauna sannan kai tsaye muryarta ta sake fitowa. "Mami na yarda da dukkan zancenki, na yarda zanyi dukkan abinda zaki sani ba tare da wani ya san komai ba, dan Allah kar ki sa a sake taɓa kowa a cikin ƴanuwana, raunin dake jikin Aminu yayi yawa, dukkan kafafunsa biyu sun karye... Zanyi dukkan abinda kika ce da yanzu Mami don ni kaina ina son rayuwata ta inganta, na miƙo miki hannayena kamar yadda kika umarta don ba zan taɓa yin katoɓarar yin ganganci da rayuwar iyayena da ƴanuwana ba, darajarsu tafi komai a wajena." Muryarta tayi shiru na wani lokaci sannan ta sake ratsa shirun ɗakin amonta na rawa. "Na rantse da ubangijin daya halicce ni Mami, zan yi miki biyayya kamar yadda kika umarta, baza ki taɓa dana sanin bayyana miki sirrina ba insha Allah." A cikin ɗakin wani irin shiru ya sake giftawa, irin shirun nan mai tsantsar zurfi, zurfin da a cikinsa zukata ke saƙa abubuwa da yawa, kamar yadda zuciyar Kilishi ke saka mata dubunnan abubuwa a wannan lokacin yayin kallon Amina take da dukkan irin nazarin da ƙwaƙwalwarta ke iyawa, tana jin yadda a bayan kanta wasu kofofi ke buɗewa kuma tunaninta na nutsewa cikinsu na son gano wani abu daban saɓanin abinda bakinta ke furtawa. Sai dai duk iya kokarinta, ta kasa gano abinda yake saman fuskar Aminan, a wannan lokacin, don tsoro da kuma rudanin da take gani karara suna fitowa tare da kalamanta, kuma takaicin yadda ubangiji ya biye sirrin kowacce zuciya ya kamata, don baza ta taɓa yarda kai tsaye cewa yarinyar nan ta karbi tayin ta kai tsaye haka ba, amma da yake ita Kilishi ce, sai tayi gyaran murya a hankali sannan ta faɗaɗa murmushin dake kan fuskarta, a kusa zata gane komai ba sai anje da nisa ba ta yiwa kanta wannan alƙawarin. "Shi yasa na barku kuyi tafiyar nan dama Amina, don so nake kije ki ga ɗanuwanki ki san cewa babu wasa a al'amarina kamar yadda na jaddada miki komai, kuma Alhamdlilah naji dadi sosai da idonki ya buɗe kika fahimci gaskiya tun a yanzu, tun kafin mu shigo da wasu cikin lissafin." Muryarta ta fito ne da wani irin sanyi kamar ƙanƙarar dake narkewa a cikin ruwa, Kuma da faɗin hakan bata jira komai ba sai ta taso, ta wuce ta ta nufi wardrobe ɗin dake dakin. Wajen da ta bude na farko ya nuna mata ajiyar da tayi na wata bakar jaka, ta dauko ta sannan ta sake buɗe wani wajen inda jakunkunan ta suke a jere, kuma a cikin aljihun guda ɗaya ta ɗauko Sachet mai yawa na wani magani sannan ta rufe komai ta juyo, da takunta a hankali ta sake dawowa wajen da Aminan ke zaune akan carpet, inda daga gabanta akwai wani stool da aka bari a wajen, ta ajiye wannan jakar da kuma magungunan a gaban Amina sannan ta nemi kan stool din ta zauna kafin muryarta ta sake ratsa dakin. "Komai mai sauƙi ne Amina, umarni na kawai zaki dinga bi shikenan sai duniyarki ta koma kamar aljanna, don zan cika miki dukkan wadannan alkawuran dana dsukar miki har ma da karin wasu da bamu lissafa ba, Kin fahimce ni ko?" Kuma kamar yadda ta zata, sai ta ɗago ta kalle ta idanunta na shaida sauran tsoron da a lokacin dama ya kamata ace yana barin fuskar tata, ta gyaɗa kanta sau biyu sannan ta sake maida shi kasa, kuma abinda Hajiya Kilishi ta gani a idanun nata ya shiga barazanar goge kokwanton da take yi akanta, amna tayi wulli dashi a lokaci guda. "Yayi kyau, yanzu ki saurareni sosai kiji abinda nake so dake." Amina ta sake gyaɗa kanta tana ƙara gyara zamanta lokacin da Muryar Hajiya Kilishin ta cigaba da shiga kunnenta. "Akwai abinda zanyi a kamfanin su Ma'aruf cikin satin nan, kuma zan yi shi ne ba tare da yana nan ba, don haka yanzu za ki taya ni abinda ya kamata ace ni zanyi don dama lokaci yayi da hakan zai koma hannunki. Abinda ke cikin jakar nan magunguna ne, na san an gaya miki cewa Ma'aruf yana da wata rashin lafiya ta ƙwaƙwalwa, sunanta 'Bipolar Disorder' ya same ta ne a shekarun baya lokacin da rayuwarsa ta canja bayan rasuwar ɗanuwansa, cuta ce dake canja tunaninsa a duk lokacin da ta tashi, abubuwa suna cakuɗewa a cikin kansa har baya sanin abinda yake yi. A London ake yi masa magani tun daga wancan lokacin kuma suna ɗora shi akan ingantattun magunguna tun daga sannan, amma da farko Ma'aruf bai karbi ciwonsa hannu biyu ba balle har ya dinga kula da kansa, baya taba shan magungunan sa akan kari wanda hakan ke ƙara bawa ciwonsa bigiren yaɗuwa, tun kafin yayi aure nake yi miki wannan zancen Amina kuma tun a sannan na karɓi magungunansa na ajiye a wajena. Ma'aruf kamar ɗan dana haifa na dauke shi, kin sani tun a wancan labarin dana baki, don haka a baya na tsaya da ƙafata sosai wajen takura masa a duk lokacin da ya kamata yasha maganin, kafin daga bisani na fahimci cewa hanyar nasarata tana tattare da ikon da nake dashi ne akan magungunan sa. Ina son Ma'aruf Amina, amma son da nake yiwa cikar burina yafi karfin nasa, shi yasa nake rufe idona a duk lokacin da buƙatar in kwantar dashi ta taso min ina yin hakan." Tayi shiru na tsawon wasu sakanni tana kallon yadda tasirin maganganun ke aiki a fuskar Amina kamar yadda ta zata kafin ta cigaba. "Magungunan dake cikin jakar nan har America naje na nemo su Amina, magunguna ne dake birkita ƙwaƙwalwar mutum a lokaci guda ya fita daga hayyacinsa, kuma dama ciwon Ma'aruf abinda yake bukata kenan ya tashi, don haka duk sanda nake shirin yin wani abu da na san zai iya zame min ƙalubale, sai in kwantar dashi in gama duk abinda zan yi kafin ya dawo hayyacinsa." Ta kai karshen maganar kamar bata karasa ba, don dukkansu shiru suka yi yayin da nauyin kalaman ke zagaye iskar dakin, ba irin ga Amina da taji hannayenta har rawa suke yi ɗauke da sabuwar rikicewar da maganganun suka sata, don yau ne karo na farko da ta ji ciwon Ma'aruf daga makusantansa, ko shi bai gaya mata ba, cewa kawai yayi 'I'm a mess Amina...' Zuciyarta ta ajiye komai a gefe ta shiga gaya mata cewa har ta gama rayuwarta a duniya ba zata taba iya haɗuwa da wata muguwar halittar irin Hajiya Kilishi ba. "Na san idan Ma'aruf yayi aure dole ne zargi zai shiga zuciyar wasu idan har na cigaba da rike magungunan sa, don haka wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa na kawo ki gidan nan, daga yau magungunan nan sun koma hannunki. Ki ɗauka ki tafi dasu, guda uku ne a ciki, ki ɓalli kowanne guda ɗaya ki bashi a gobe, don jibi zan fara aiwatar da abinda ke gabana kuma a sannan bana buƙatar ganinsa a kamfanin. Wannan shine aikin ki na farko Amina, kuma idan komai ya tafi daidai, zaki fara ganin daidai bari nayi miki alkawarin farko tun a yanzu, idan na samu abinda nake so Amina zan sa a fitar da ɗanuwanki Aminu ƙasar waje a gyara masa kafafunsa su kamar yadda duke a da." Shirun da ya sake ratsa ɗakin mai tsawo ne da babu abinda zaka tsinta a ciki kafin Hajiya Kilishi ta kai ƙarshen zancenta da magana ta karshe kuma mafi girman da daki zuciyar Amina babu zato, maganar da daga ita har Amma basu taba hango ta ba balle tasa ta a jerin tunanin Hajiya Kilishin, kuma duk da dauriyar da take da ita a lokacin sai da kalaman suka tasa allon kirjinta girgizawa da karfin da ta san har Mamin ta lura. "Maganin dake gefe kuma naki ne Amina, ki dauka ki dinga shansa kullum, na san ba zan iya hana Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kadan a cikin lissafina!" *** Yaya kuka ga sharaɗan farko na Kilishi?? Ta yaya kuke ganin Amina zata bullo musu??😅😅 Ta yaya zata sa komai ya faru ba tare da Hajiya Kilishi ta ɗorar da zargin da take mata ba?? Mu dai jira hukuncin Amma ko?? And the Uban gaiyar is over there going crazy akan ƙafafun Amina ba tare da ya san me ke shirin tunkaro shi ba!😅 Wani ya gaya masa cewa su Rukayya ma na can nayi masa nasu shirin suma... Jawad ma kuma yana nasa! A tsakiyar komai kuma dai, zamu samawa Ma'aruf wannan nutsuwar da yake nema insha Allah.😍😍 #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. SANARWA. ~~~~~~ Assalamu alaikum. Fatan alkhairi ga tarin Masoyan FARAR WUTA da ma duk wani littafi da ya kasance nawa. A lokaci irin wannan nakan nemi kalamai in rasa, nagode da dukkan support ɗin ku tun daga shafin farko na farar wuta zuwa in da na tsaya. Ina kuma ganin tarin saƙonni da ƙorafin ku akan rashin samun update akan lokaci, ina jin kalmar HAKURI kamar tayi kaɗan, amman ita kaɗai nake da ita. Na fara littafin nan ne ba tare da na hango tarin uzururrukan da suka dinga taso mun ba, suka kuma zama dalilin rashin samun update ɗin da ba kwayi. Na sani... Na kuma fahimta tun kafin ku furta. Kuyi HAƘURI, don saboda dalilai da yawa littafi na biyu (Farar Wuta 2) zai koma Paid Story cikin tsarin da nake fatan dukan mu zamu ji daɗin shi. Wanda na ɓatawa a farkon tafiyar nan zuwa yanzun, banda kalamai masu yawa sai neman afuwa da kuma bada hakuri. Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma bamu aron lokacin sake haduwa dan karasa tafiyar FARAR WUTA. Kar ku manta yanzu tafiyar ta fara... Zan baku labarin yadda nasara ke samuwa babu boka ba Malam! Zan baku labarin soyayyar Ma'aruf da wataƙila zata narkar da zuciyarku kamar ruwa. Zan kuma baku labarin yadda mata ke samawa kansu mafita ta hanyar wayo da dabarar da Allah ubangiji ya halitta a ƙwaƙwalwar kowacce mace. Ku tuntube ni ta wannan lambar. 08067794315. Nagode muku fiye da yadda baki zai iya furtawa. #AyshaShafi'ee #fikrawriters #FararWuta.