*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_ '''🎐G•W•A🎐''' *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* *SADAUKARWA GA:-* *GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 1📑* *__________📖* Wayar tace ke rura, tana son ta tashi ta ɗauka amma ta kasa, saboda irin yadda ya manne ta a jikinsa. Sosai wayar ke rura aƙalla anfi yin miss call goma amma tana ji ta kasa tashi ta ɗauka. Ba dan komai ta kasa tashi ba sai dan kada ta ɗan mutsa ta ta da shi,abinda bata so ita kuma. Wayar ce taƙi dai na ƙara,kuma gashi bata son ƙarar data ke, dan bata son ƙarar ta dame shi yana baccin sa,dan haka ta fara tafiyar da hannuta slow-slow har ya kai kan wayar. Ɗauko wayar tayi lokacin kuma wayar ta sanya wata ƙara. Da sauri ta sanya ta silent, duba miss call ɗin tayi taga wake kiran ta. Fara dubawa tayi aikuwa gaban ta ne ya yi munmunar faɗuwa da taga wanda ya kira ta. Tana cikin wannan fargabar sai ya fara mutsi alamun zai tashi,jikinsa ya ƙara jawuta kana ya ɓuɗe idonsa waɗan da bacci basu gama sakin shi ba. Ahankali ya fara mata magana akunne yace, "My Sweet nah, ki tashi ki haɗemun abunda zan karya saboda yanzu na ke son tafita office dan jirana akeyi". Ba musu tace, "yanzu kuwa Hayateena". Kumatunta ya shafa haɗe da kai ma kiss kana yace, "shiyasa nake ƙara sonki". Murmushi tayi mai ɗan sauti kana ta tashi taje kitchen ta haɗa masa abunda yake buk'ata. Har takusa kammalawa wayar ta tasake ƙara,da sauri ta ɗauku waya tana mai duba sunan dake yawo saman screen ɗin wayar. Gabanta ne yaba da dummm hannuta na karkarwa ta kara akunninta. Kafin tayi wata magana har anfara magana cikin faɗa-faɗa. "Hafsa ina kikaje?ina kika kwana?miyasa kikeso kijamin abun magana da mahaifinki, ehh!". Muryar ta narawa tace, "Mama wallahi karutune yayimin yawa kuma kinsan munkusa Fara exams kuma wannan karun mai zafice zamuyi shiyasa nayi bacci na a hostel,amma ki bashi hak'uri anjima kaɗan zan dawo". Sai Mama tace, "to naji amma kirinƙa faɗamin idan zaki kwana saboda nasamu natsowa kinji ɗiya ta". Tace, "tau Mama sai nazu anjima". Bayan sunyi sallama da Mamar ta,tashi tayi ta haɗe masa komai na breakfast,bayan ta kammala taje toilet ta haɗa masa ruwan wanka,bayan ta gama haɗe masa taje ta faɗa masa yazo yayi wanka. Bayan yayi wanka ya fito,da kanta ta shirya sa ta fesheshi da turare mai ƙamshi kana ta kaishi dining Yayi bearkfast. Bayan ya kammala ya tashi zai fita office,jikin sa ya jawota kana ya kai mata kiss a baki,ido cikin ido ta dubeshi ciki da shagwaɓa tace,"Hayatee nah, anjima zanje gida dan Mama takirani tana faɗa dan ma nace mata ina hostel ne ta ƙyaleni". Tunda ta fara Magana ya heɗi fuska har ta kai karshe. Yace,"bawani Mama ta kiraki kina dai son kitafi dan yanzu naga alamun kin daina sona". Kamar tayi kuka tace, "kadaina faɗin haka wallahi inasonka sosai,amma tunda bakaso naji na fasa zan san me nace mata. Aikuwa tana faɗin haka wani murmushi ya bayyana afuskar sa,lokaci ɗaya ya fara kiss ɗinta. Abun ne yaga zaifi ƙarfinshi kuma anajiran sa a office dan haka yasake ta ya ɗau jikar sa ya fice batari da ya saki waiwayo wa ya dube taba...... _*Idan kunji daɗi mucigaba idan ko bakujiba na aje na huta*😁_ *#Vote* *Comment* *Shere* *UMARNIN SAURAYI°* *1441H/2020M.* *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* *SADAUKARWA GA:-* *GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.* ~_Wattpad~@ ~GaskiyawritesAsso_~ *SHAFI NA 2📑* *__________📖* Saman kujerar parlour ta faɗi tana maida numfashin ta ,dan sosai ya taso mata da sha'awar ta, dan ita bata masu yafita ba, taso ya tsaya ya cikaga ba da abunda sukeyi ko ba komai zata samu natsuwa. Ta jima kwance saman kujera kafin ta tashi, ko shi lokaci taga ya tafi kuma bata son ya dawo bata gama aiki ba dan haka ta tashi ta fara aiki, cikin ƙan-kanin lokaci ta gama gyaran gida da abunda zai ci idan ya dawo. Bayan ta kammala komai tayi wanka ta shirya cikin shigar da tasan yana so, dressing ɗin english wears kenan . Jikin ta ta feshe da turarukka masu masifar ƙamashi bayan tagama shafe jikin ta da humra ta ƴan sokoto wanda akayi ma haɗi na musamman. Tayi kyau sosai dan idan ka ganta bazaka ce ita ba haushiya ce ba. Bayan ta kammala gyara jikin ta,zama tayi saman kujera haɗi da ɗauko wayar ta ta kunna kana ta kira Mamar ta dan tagaya mata yau ma ba zata samu damar zuwaba sai gobe. Ringing ďaya Mama tayi picking call ďin ďiyar ta. Kafin tayi magana sai Mama tace, "kina kan hanya ne?". Hafsa tace,"a'a Mama yau ma bazan dawo ba sai gobe dan munada Lectura da safe kuma Babane damu kin san tsohon ba dai fitina ba,amma da mungama zan dawo". "Tau ba komai amma naso ki dawo gida,amma gobe da kun gama ki dawo". Tace, "tau Mama ki gaida Abbana". Sallama sukayi ta aje wayar,sai jin tayi ana mata knocking,tashi tayi taje ta buɗe masa ƙofa. Tunda ta buɗe ƙofa ya kifeta da ido dan ba karamin kyau ta masa ba,lokaci ɗaya ya jawota jikin sa,haɗi da kai mata kiss a goshe. Kallon dressing ɗin da ta masa ya shigayi dan tunda yake da ita bata taɓa yimasa irin wannan shagar ba kuma sosai yake son irin wannan shigar. English wears ɗin data ke sanye da su ya bi da kallo,jan riga ce da wani matsatsin wando wanda ya kamata sosai, ahankali ya kai hannusa ya fara shafar jikin ta yana shaƙar ƙamshin dake fita ajikin ta. Tunda ya fara shafar jikin ta tafara jin yarrrr......sosai ta ƙara manne jikin ta da nashi. Tsayuwar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta ya ƙarasa bedroom ďinsa da ita. Sosai yayi romances ďinta kafin ya ƙyaleta. Itako haka tabiye masa ya yi duk yadda ya keso da ita duk da bawani son abun take ba amma bazata iya nuna masa bata so ba saboda bata son ransa ya ɓaci. Bayan ya gama abunda ya ke so kana ya dube ta yace,"kije ki haɗe man ruwan wanka dan fita nake son yi". Ba musu taje tayi yadda yace,bayan ya yi wanka ya ci abinci kana ta dubeshi cikin kwantar da murya tace,"Hayatee nah". Idonsa ya ɗago ya kalleta kana yace, "ya dai sweet nah". Sai da ta kwantar da kanta ajikinsa kana tace, "dama-dama amma kayi haƙuri ba dan na ɓatama zanje ba please Hayatee ka fahince ni"...tana faɗa kamar zatayi kuka. Kallon ta yayi kana yace, "inajiki ki faɗa zan fahince ki. Murmushi tayi haɗe da kai masa kiss agoshi kana tace, "ina son naje gida na faɗama Iyayena zan kuma hostel da zama kaga sai na dawo nacigaba da zamana anan hankali kwance,amma fah acan zanyi weekend,amma sai ina ka yarda"...tafaɗa haka kamar da tsoro aciki. Sai da akayi ƴan seconds kana yace, "banyarda har kiyi weekind ba sai dai kije da safe da yamma ki dawo amma ban amince kije har kiyi kwana biyu acan ba". Haƙuri ta fara bashi haɗe da masa alƙawar idan zaije Plateau zata rakashi ,dan kwannan zaiyi tafiyar dan awajan akin da aka turashi can dan yayi wani bin cike,ko dama yace zai je da ita amma bata amuntaba saboda alokacin ne zasu fara exmas amma yanzu ta amince masa.....to kuma ban san wani za'ayiba tsakanin exmas da tafiya. Da safe da zai fita aiki ya ajeta kan hanyar gidan su,itako ta ƙarasa da ƙafa dan banisa da wurin da ya aje ta. Da sallama ta shiga aikuwa ƙanninta najin muryar ta suka fara mata oyoyo,sosai suka ji daɗin gani Yayar tasu. Bayan sun gama gaisawa da ƙannenta kana ta ƙarasa wajan iyayinta wanɗanda tunda ta shigo gidan fara'arsu ta bayyana musamman Abbanta. Gaishesu ta farayi suka amsa ciki da kulawa da son ƴar tasu ƙwaya ɗaya mace. Bayan sun gama gaisawa suka shiga firar yaushe gamu haɗi da basu labarin karatunta. Sai da fira tayi daɗi take gaya musu zata koma hostel da zama saboda yanzu karatunsu ya ɗau zafi kuma tana buƙatar tana tsu tayi karatu. Sosai iyayinta suka gamsu da abunda tace kuma suka amince mata da haka. Dan haka tace musu zatayi weekind anan sai Monday ta tafi ,amma data tafi sai bayan exmas zata dawo. Ba abunda suka ce da ita sai fatan alhairi. Bayan sungama fira da ita tashi tayi taje ɗakin da ya ke mallakin tane dan tana son ta ɗan huta dan jiya bawani barci yabar ta tayi ba,dan iya wuya yabata. Tana shiga tayi kwanciyar ta dan ɗakin ko da yaushe Mama sai ta gyarashi sosai,dan haka bashi da wani datti. Bata jima da kwanciya ba, bacci yayi awun gaba da ita. Tajima tana bacci dan ko sallah bawace tayi tsaka nin azahar da la'asar dan ita Mama ta ɗauka ɗiyar ta ta na fashin sallah shiyasa bata tashe taba. Aikuwa ba ita ta farkaba sai biyar saura,lokaci taga yatafi dan haka da sauri ta tashi taje tayi sallah. Da dare har ta kwanta dan tana son tayi bacci da wurin dan ta tashi da wuri,sai ga wayar ta tafara ƙara,ɗan tsaƙi ta ja kana ta ɗauko wayar daniyar ta kashe,sunan da taga yana yawo saman screen ɗin wayar ne yasa da sauri tayi picking ďin call ďin haɗi da faɗin, "Hayateenah". Ba abunda yace da ita sai ki fito gani aƙofar gidan ku. Lokaci ɗaya jikin ta ya ɗau karkarwa muryar ta na rawa tace,"kayi haƙuri yanzu Abbana yana gida kuma bazai barni ba". Tsawa ya daka mata yace, "minti biyu nabaki kifito dan bana son yawan magana". Haƙuri ta fara bashi kafin ma ta ida faɗa har ya kashe waya sa. Jikinta na karkarwa ta ɗau hijab tasaka kana tayi ɗakin Mamar ta. Da sallama ta shiga tace Mama zanje gidan su Safiya na karɓo wani book ɗina ina son karatun shi a daren nan". Mama tace, "a'a ba zaki jeba kibari nasa ƙaninki yaje ya karɓo, amma bake ba". Mama tana ce baza taje ba ita ko Hafsa tana ce sai taje dan har kuka sai da tawa Mama. Itako Mama tace taje amma da ƙaninta zasuje,ban dan taso ba haka ta aminta tace tayar da suka fita ita da ƙaninta Marwan. Har zasu fita tace, "Marwan kaje ɗakin ku ka kwanta dan naga bacci kakeji". da yake ɗakin nasu asoron gida yake. Yace, "eh Aunty bacci nakeji". Sai da tabari ya shiga ɗakin su kana ta fito ta sameshi amota. Ahankali ta buɗe marfin motar ta shiga,haƙura ta bashi na jimawar da tayi bata fito ba. Komai bai ce mata ba yaja wota jikinsa ya fara kissing ɗinta haɗe da sanya hannusa cikin rigar ta yana shafar dukiyar fulanin ta,sosai yayi romance ɗinta acikin motar kan ya ƙyaleta. Wayar sa ya ɗauko ya shiga gallery ya kamu wani videos yayi playing ďin ɗaya yaba ta yace ta kalla yadda sukeyi haka zata mishi yanzu. Jikinta na karkarwa ta karɓa ta fara kallo,dan har tasu tayi masa magana taga ba fuskar yin haka ɗin. Bayan ta gama kallon abunda ya bata itama tamishi yadda taga sunayi,sosai yake jin daɗin abunda take masa dan sun kusan kai sha biyu bai tafiba. Kuka ta fara yi masa kana ya yarda ya ƙyaleta amma bandan ya gajiba. Abunda yasu mata ya bata yace kafin ta kwanta tashi zata ji daɗin bacci. Amsa tayi jiki na rawa tayi masa sallama ta shige gida. Koda tashiga gidan Mama batayi bacci ba tana nan tana safa da marwa atsa kar gida. Kallonta Mama tayi da kyau kana tace, "me ya tsaidaki?ina kuma Marwan yake?". Alamun rashin gaskiya suka bayyana afuskarta amma sai ta wayen ce tace,"Marwan ya shige ɗakin su yanzu,dan bacci ya fara shiyasa na kaishi ɗakin su. Mama tace, "tau ina book ɗin da kika karɓo?". Jikin tane ya fara karkarwa sai kuma ta nuna mata ledar da ya bata tace, "gashi". Har Mama zata karɓa sai sukaji mutsin Abban Hafsa dan haka da sauri Mama tace ta wuce ɗaki dan bai masan ta fitaba. Koda ta shiga ɗaki zama tayi tana mai dafe gaban ta saboda ta tsallake rijiya da baya. Ledar da ya bata ta buɗe,kaza ce da wasu ƙwayoyi,kazar kawa tace ta aje ƙwayoyin dan tunda yake ba tasu bata taɓa shaba sai indai tana gabansa take sha,koshi dan bata son gani ɓacin ransa. Da safe wajan ƙarfe goma bayan ta tashi daga bacci tayi wanka tana zaune tana shafe jikin ta da Vaselin,sai jin tayi ana mata sallama abakin ƙofar ɗakin ta. Kanta ta ɗago dan taga wake mata sallama. Aikuwa suna haɗa ido tace, "shin wai kece bangane muryar kiba?waya cemiki nazo hala ?". Tace, "amma kya bari ko gaisuwa muyi kafin ki fara jerumin wannan tambaya. Kallon ta safiya tayi tace,"yaushe kika dawo gida ai na ɗauka kin tare ne gabaki ɗaya a gidansa". Sai da Hafsa tama ta kallon sama da ƙasa kana tace, "zan dai tare dan ko yanzu weekind ne nazu nayi natafi sai wanda yagani bari ya yaɓamin magana. Safiya tace, "har yanzu bazan gaji da baki shawara ba,kice inda gaske yake yana sonki ya fito kuyi aure abunda yafi kenan dan wallahi ni ke nake tausayi nan gaba. Aikuw rigama sukayi sosai dan duk lokacin da zasu haɗu da Safiya haka ne dan ita Safiya ba abunda ta tsana kamar yadda ƙawar ta kebin *UMARNIN SAURAYI*..... *#Vote* *Comment* *Shere* *© SUMY NA'IGE.* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ```Ga masu buƙatar complete ɗin wannan book za iya nemanshi a wattpad👇``` ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 3📑* *__________📖* Wacece Hafsat?. Alhaji Usuman haifaffin ɗan garin sokoto ne shi ne mahaifin Hafsat, matar shi ɗaya Hajiya Fatima mutane ne musu haƙuri da jama'a dan tunda suke ba'ataɓa jin su ba,bare da maƙutan su, kowa lafiya suke dashi sai wanda ba'arasa ba. Suna da yara shidda maza biyar mace ɗaya. Hafsat itace ƴarsu ta fari kuma ita kadai ce mace,ta taso cikin gata da tarbiya mai kyau, yarinya ce mai natsuwa da kamun kai,sosai ta keba mutane girman su, bata damu da kowa ba dan ko tarin ƙawaye batayi, sosai mutane ke ganin girman ta,tana da ilimin addini dana zamani dai-dai gwar-gwado. Tun tashin ta ƙwarta ɗaya ce ita ce Safiyya, koshi abunda ya ƙara ƙarfafa ƙawan cin su saboda school ďin su ďaya da Safiyya. Sunyi primary school da secondary school duk atare kuma class ďaya islamiya ma haka,dan shi suka shaƙu sosai dan idan ka gansu za kace ƴan gida ɗaya ne,ko kayan sawa iri ɗaya ake musu sosai suke son junansu. Lokacin da suka gama secondary school gidan su safiyya ba'abarin yaro ya ƙara gaba sai yayi aure amma saboda Hafsat zata ciki gaba Baban Safiyya yace ya barta itama sutafi tare. Ba'a ɗau wani lokaci ba aka samar musu admission a Usumanu ɗan Fodiyo Unversity sokoto. Inda kowa ce burinta ta zama doctor ta mata, dan ta taimakama ƴan wunta mata, kowa ce shine burin ta. Haka suka ci gaba da karatu cikin kwanciyar hankali ko wace na karatu dai-dai gwargwado. Ba wata matsala akaratun su har suka kai UG 3 going to 4 Hasfat ta haɗu da Anwar ,sosai ya nuna so gareta amma taƙi kulashi,ya sha wahala kafin ta kulashi dan yana nuna mata so bana wasa ba har ita Safiyya takan mata faɗa akan ta daina masa haka ta kulashi ko kaɗan ne. haka dai aka samu ta fara sake masa fuska har soyayya ta kullu tsakanin su mai tsanani. Abun har mamaki ya dawo ba Safiyya dan yanzu yadda Hafsat ke nuna ma Jawad so abun yana bata tsoro. ana cikin haka ya kwanta ciyo sosai yake jin jiki dan haka Hafsat tagaya ma Safiyya tace ta raka ta su dubashi gidan sa. Da ƙyar Safiyya ta yarda zata je duba sa. Bayan Safiyya ta amince Hafsat takira shi tace za su zo duba shi. Address ɗin gidan ya basu yace sai sun zo. Bayan sun zo school sun gama lecture safe suka kama hanyar gidan sa dake arƙirla. Basu sha wuya ba wajan gane gidan,dan maƙocin sa sanan ne ne agarin sokoto. Tun kafin su ƙarasu ya faɗama maigida zai yi baƙi dan haka suna ƙarasuwa maigida ya kaisu har part ɗinsa. Godiya sukayi ma maigadi kana suka ƙarasa ciki. Kwance suka same shi anɗaura masa drip a hannun sa. Da sauri Hafsa ta ƙarasa gareshi,irin yadda ta ganshi ai bata san lokacin da tafara hawaye ba. Alama yayi mata da hannu ta daina kuka ,amma sai ƙara kukan takeyi. Safiyya ce tayi mata magana tace ita kam sauri takeyi dan haka ta daina kuka su gaisa su wuce gida. Dakyar ta daina tayi masa ya jiki ,Safiya ma ta masa kana suka ɗan zauna kaɗan har drip ɗin da aka sama sa ya ƙare,Hafsa da kanta ta cire masa kana sukayi masa sallama suka wuce gida ba dan ran Hafsa ya soba. Bayan kwana biyu da zuwan su takira sa tayi masa ya jiki yace jiki da sauki amma har yanzu bai daina shan drip ba. Sosai ta tausaya masa har tace zata zo ko da yamma ne idan sun gama lecture. Haka kuwa akayi tace Safiyya ta rakata tace itakam bazata koma dubin saba tunda taje. Komai Hatsat bata ce da itaba dan ranta ya ɓaci akan abunda Safiyya ta mata dan haka tace ita sai taje amma idan taje gida ta faɗa musu sai yamma zata dawo dan tana da lecture ƙarfe huɗu. Komai Safiyya bata ce da ita ba kowa ya kama gabansa. Ita Safiyya tayi gida ita ko Hafsa tayi gidan saurayin tah. Koda taje doctor na duba shi har yana bashi shawara yarinƙa cin abinci kuma ya rinƙa shan magani. Bayan doctor ya fita Hafsat ta ƙarasa gareshi kamar zatayi kuka tace, "yanzu Hayat baka cin abinci,to ya kake so nayi, ko so kakeyi na kwanta?".....tana faɗa tana fitar da ƙwallah Ahankali ya taso daga kwanciyar da yake kana ya ƙaraso gareta, handkerchief ya bata dan ta goge hawayen ta. Bayan ta gama kana yadube ta da kyau yace, "My sweet heart,bawai bana son cin abunci bane, a'a abinci sayarwa ne bana so ko da na hotel ne, shiyasa ban cika cin abinci ba". Kallon sa tayi da kyau kana tace, "yanzu meza kaci?". Yace, "zan sha lemo sai nasha magani dan bazan iya dafa wani abinci ba bare nadafa". Tambatar sa tayi inada kitchen yake ya nuna mata bata ce dashi komai ba, ta tashi tashiga kitchen ɗin ta kunna gas ta ɗura masa jallof ďin taliya wadda taji kayan haɗi. Tana cikin aikin ya shigo,bata masan ya shigo ba dan baka jin mutsin ma tafiyar sa har yazo kitchen ɗin. Tunda ya ƙarasu ya ƙife bayan ta da kallo yana ayyana wani abu aransa. Kamar ana kallonta taji dan haka da sauri ta juyo dan taga wake kallonta. Ido biyu sukayi dashi da sauri ta ɗauko mayafinta dan tasaka amma yayi sauri ya rikeshi kana yace, "miye afanin rufewa tunda watarana yazama mallaki na". yana faɗa yana kashe mata ido ɗaya. Komai bata samu damar cemasa ba ya umarce ta data cigaba da akinta. Yana zaune yana kallonta har ta kammala ta zuba masa yaci, amma yace sai tare za suci tace sauri takeyi ta koma gida yace duk batare za su cibashi bazai ciba. Da kyar ta yarda ta zauna sukaci. Bayan sun kammala ta ɗauko maganin sa tabuɗe ta bashi yasha kana tayi masa sallama tace zata wuce. Har takai ƙofa ya ce gobe tazo har tace ba zata zoba ya yi kamar ya yi kuka, da taga haka tace masa zata dawo. Haka Hafsat taci gaba da zuwa wajansa har ya samu sauki. Ranar koda taje ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya yi kyau sosai, gashi abu ga mai kyau jinin fulani gashi kuma nira ta zauna masa. Tunda ta shigo suka kife junan su da wani kallo mai wuyar fassarawa haɗi da sakarma ko wane murmushi mai ciki da so da ƙauna. Alamu yayi mata data ƙaraso. Ba musu taje gareshi,tasowa yayi daga wajan dayake zaune yazu daf da ita. Kallonsa tayi haɗe da gaidashi ya amsa jikin sa duk akasalan ce. Tashi ya yi ya ɗauko mata ruwa haɗi da wani lemo mai haɗe da wata ƙwaya wadda shi ka dai yasan ko tame ce ce. Zuba mata ya yi tasha aikuwa tunda tasha ta farajin wani sauyin yanayi a jikin ta, lokaci ɗaya wata muguwar sha'awa ta taso mata. Shi kuwa tunda tasha lemun yake binta da kallo har yaga maganin da yasa ya fara aiki ajikin ta lokaci ɗaya. Akuwa lokaci ɗaya ya fara shafar jikin ta haɗi da yima ta kalamai masu kashi jiki,yana yadda yaso da ita haka yaci gaba da romance ɗinta har ya samu ya rabata da mutun cinta. Koda maganin ya sake ta tayi kuka har tagaji kuma ta jefeshi da miyagun kalamai sosai ya ji zafin kalaman ta. Amma ya dake yaci gaba da bata haƙuri,amma ko kallo bai isheta ba. Haka tasanya kayanta tayi tafiyar tagida. Aikuwa tun daga ranar duk wata hanyar da zai ganta ta rufeta,shiko duk inda yasan zai ganta yaje amma bai gantaba haka har ya haƙura,ranar yana kwance yara sa miya ke masa daɗi agarin sokoto dan har ya yi niyar ya bar garin ya koma garinsu ,sai wata dabara ta faɗu masa lokaci ɗaya yamike yaje wajan wata abokiyar karatun Hafsat ya gaya mata abunda ake ciki kuma ya bata kuɗi masu yawan gaske yace idan ma tashirya su abunda zai bata sai tayi mamaki. Sosai Hajara ta ruɗe dan haka ta ɗau alƙawarin ko ta halin ƙa-ƙane sai ta kawo masa Hafsat. Aikuwa tun daga lokacin Hajara ta liƙema Hafsa duk inda Hafsat take Hajara na can,dan shi Safiyya ta jama Hafsat baya dan Hajara kowa yasan ta ba yarinyar kirki ceba. Watara na suna fira da Hajara sai ta ɗauko mata labarin Anwar da rashin lafiyar da ya yi yanzu haka yana kwance ba shida lafiya sosai. Duk da abunda tafaɗa ya dake zuciyar Hafsat amma tadake bata cema Hajara komai ba. Sai ma magana tama ta akan ta daina yi mata maganar sa dan har da faɗa sai da sukayi kafin su rabu. Dare nayi Hafsat ta kasa kwanciya ba abunda take tunani sai shi,sosai ta matsu safiya ta waye taje gidan sa tagano ko ya ya tashi. Tun shidda da rabi ta fito daga gida ta kama hanyar gidan sa. Koda taje sai da ta musu knocking a ƙofar gidan maigida ya buɗe ƙofa ya fito. Gasheshi tayi kana ta tambaye shi ko Anwar nanan. Yace baya gari dan ya kwana biyu baya nan,sosai taji zafin rashin samun sa dan yanzu wani son shi ne takeji wanda ji take idan bata ganshi ba zata iya mutuwa. Godiya tama Baba maigida kana ta kama hanyar makaran ta. Har akatashi shoocl bata ga Hajara ba kuma duk inda tasan zata ganta taje amma bata same taba. Ba ƙaramin tashin hankali ta shigaba lokacin da takira wayar Hajira akace kashe take. Alokacin duk wanda ya ganta yasan bata cikin natsuwar ta. Danhar Mamar ta ta tambaye ta amma sai tace wata exmas ce za suyi mai zafi shiyasa take jin tsoro. Addu'ar samun nasara Mamar ta tama ta haɗi da bata shawara. Dadare tana kwance ta kuma gwada kiran Hajara tace ko zata samu,aikuwa cikin sa'a tana kira tafara ringing. Ringing da bai wuce uku ba Hajara ta ɗauka tace, "Ya aki ciki ne Hafsat?". Sai da Hafsat ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "kina ina yanzu?". Kai tsaye tace, ina layin bugi". Sai Hafsat tace, "Subuhanallah, miyakai ki layin bugi kuma?". Sai Hajara tace, "tambayana kikayi nabaki amsa,dan haka bana sun dugon surutu". Sai Hafsat tace, "kodama numbar Jawad nake son ki bani idan kina da ita ko kimin misalin wajan da zan samun sa". Aikuwa Hajara najin me tace ta bushe da dariya haɗi da cewa,"komai kikeso nabaki ki sameni wajan da nafaɗa miki yanzu nabaki abunda kike so". Duk da dariyar da tasa mata tayi mata zafi amma sai ta dake tace, "dan Allah Hajara ki bani wallahi bazan iya zuwa layin bugi ba,bare yanzu da dare". Sai Hajara tace, "tunda abunda kike nema bai dameki ba sai anjima". Har zata katse waya sai Hafsat tace,"zanzo ki gayamin dai-dai ina zan sameki. Tace, "dakin zo kikirani zan fito". Tace kada ki kashe waya gani zuwa. "Aa bazan kasheba". Aikuwa suna gama waya jikinta har rawa yake ta shiyar taje ɗakin Mama tace zataje gidan su Safiyya ta karɓo jikarta dake hannuta dan karatu zatayi. Mama tace to taje amma kar tajima. Tana fita taje bakin ti-ti ta tare mai adai-daita ta faɗa masa sunan inda zai kaita. Bayan ƴar tafiyar da sukayi ya kaita wajan, tun abakin wajan zaka fara ganin mata da maza suna kai kawo kuma dukkan su ba mai shigar kirki. Gabanta ne ya fara faɗuwa har taso ta juya kuma ta fasa. Waya ta ɗauko takira Hajara tace gata nan ƙarasu. Bata jima da kiran Hajara ba ta ƙarasu cikin wata shiga kace ita ba ƴar muslmiba...... *#Vote* *Comment* *Shere* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMMY M NA'IGGE✍🏼•* ```Don neman cikon labarin👇``` ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *NA 4📑* *__________📖* Shigar da Hajara tayi Hafsat tabi da kallo har ta buɗe baki zata yi magana sai Hajara tace, "zo muƙarasa daga ciki kina tawani kallona sai kace yau kika fara ganina". Sai Hafsat tace, "ni kawai kibani abunda nice dan bazan iya shaga wannan wajanba". Wani kallo Hajara tabita dashi kana tace, "abunda ki ke nemane bai dame kiba dan haka kin ga tafiya ta" . tana faɗar haka takama hanyar zuwa inda tafito. Da sauri Hafsat tabita tana kiran sunan ta amma sai tayi kamar bata san da ita. Ɗakin da taga Hajara tashiga nan ta fara ƙuƙarin shiga,warin wiwi da sigari ne suka bige hancin ta,aikuwa lokaci ɗaya taje da baya,dan bazata iya shaga ɗakin ba. Wayar ta ta ɗauko ta sake kiran Hajara tace, "Hajara gani ƙofar ɗakin da kika shiga, dan Allah kifito ki ba ni". Wata tsawa Hajara ta daka mata kana tace, "Idan bazaki shigo ba kina iya tafiyarki". Wani maƙaƙi ya rufe mata zuciya har taso ta tafi sai kuma wani abu ya taso mata wanda ita kanta bata san ko na meye ba. Sai da ta ɗauke sheɗar ta kana ta buɗe labulen ɗakin ta shiga. Abunda tagani ne yayi matuƙar bata tsoro da mamaki. Dan gabaki ɗaya ɗakin maza da mata ne,kuma ba mai shigar kirki a cikin su. Sosai abun yaba Hafsat tsoro dan kowane namiji rungume yake da mace. Dan ko Hajara kwance take ajikin wani sugar boy daga ita sai wata vest mai haɗe da brazier wadda ta bayanar da surar jikin ta sosai. Wani kallo tabi Hafsat dashi kana tace, "kin tsaya ma mutane akai, in bazaki shigo ba saiki tafi". Hafsat tace, "Hajara dan Allah kibani wallahi sauri na keyi". Batari da ta kalle taba tace "gashinan zuwa yace ki jirashi". aikuwa tana cewa haka sai wannan sugar boy ya yi sauri yace wa ashe itama ƴar hannuce to abamu muɗana". yana faɗa yana kallon Hafsat wadda ta haɗe fuska sai kace akwai wanda ya tilasttamata zuwa wurin Hajara hara zata buɗe baki tayi magana sai wayar ta tafara rura. Ɗauka tayi haɗe da faɗin "ka ƙarasu?". banji me akace ba a ɗayan ɓangarin iya dai tace gatanan zuwa. Kallon Hafsat tayi dake durƙushe a ƙasa tace, "kizo muje". daga haka bata sake magana ba ta fice warta. Itama Hafsat da sauri tabi bayan ta. Wajan wata mota tanufa itama Hafsat tabi bayan ta. Aikuwa suna ƙarasuwa wajan motar sai sukayi ido biyu da Anwar, lokaci ɗaya wani sanyi ya ziyar ci zuciyar ta ai bata san sanda ta faɗa jikin saba tana sauke wata sassanyar ajiyar zuciya. Jikin sa ya matse ta yana jin wani abu a zuciyar sa. Gaba ɗaya ya manta da wata Hajara dake tsaye sai da tayi gyaran murya kana ya ɗago da idanun sa waɗan da suka fara sauyawa zuwa launin ja. Tace, "kizo muyi magana dan sauri nakeyi jirana ake". Raba jikin sa da Hafsat yayi kana ya dube ta yace, "tabari na zo". Nesa kaɗan da ita suka yi kana Hajara ta dube shi tace, "Nagama aikina dan haka kabani abunda kace". Tun bata rufe baki ba ya ɗauko wasu kuɗi masu yawan gaske ya bata,aikuwa tana gani yawan kuɗin da yabata bakin ta ya kasa rufuwa sai godiya take zuba masa dan har jikin sa tasu tafaɗa ya ɗaga mata hannu alamar ka da ta soma,sosai tayi masa godiya kana ta buɗa baki tace, " duk akan Hafsat zaka bani wannan kuɗe,sai yanzu na tabbar da son da ka ke yi mata mai yawan gaske ne,amma bari gaji yadda nayi nasamu kanta". Karasuwa tayi gab da kunnin sa kana ta faɗa masa wata magana. aikuwa tana gama faɗa masa ya bita da wani kallon mamaki kana yace, "Amma gaskiya banji daɗin haka da kika yimin ba" har ya buɗa baki zai sake wata magana sai ga Hafsat ta ƙaraso wajan da suke jikin ta na karkarwa tace musu gida zata koma dan Mamar ta har takirata a waya. Sallama yayi da Hajara kan sai yakira ta,kana ya dau Hafsat ya kaita gida. To tun daga wannan lokacin duk abunda yace da Hafsat bazatayi masa musuba,sai wani son shi da kaunar sa da suka addabe ta wanda yasa takejin zata iya rabuwa da kowa akan sa. Wanda a halin yanzu ta koma kamar matar sa, dan sai yadda yace da ita.... *Cigaban labari* Bayan Safiyya ta fita taci gaba da shirin ta bayan ta kammala tafito domin ta gaida iyayanta. Bayan ta gaishe su kana tayi beark bayan ta kammala Mama ta dube ta tace, "Hafsat anjima zan aikeki gidan Hajiya tah ki ƙarɓomin saƙo daga can ki gaya mata zaki koma makaranta sai kun gama jarabawa". Tace, "tau Mama Allah ya kaimu ajima lafiya"nan suka cigaba da firar su. Suna cikin fira wayar ta tafara rura,sunan da taga ya baiyana saman screen ɗin yasa da sauri ta saka wayar slient,sai da ta tsinke kana tayi sauri ta mike taje ɗakin ta haɗe da cema Mama tabari tazo Safiyya ce zata gayama sunan wani book wanda zata nemu mata shine za ta je ɗakin ta dubu dan yana cikin jikar ta kuma ta manta sunan shi. Komai Mama bata ce da itaba har ta fice. Tana shiga ɗakin ta ya koma kira,da sauri ta ɗauka haɗe da faɗin "Hayateey kayi haƙuri wallahi muna tare da Mama ne shiyasa ban ɗauka ba" . yadda ta ke maganar kamar tana gaban sa. Yace, "naji amma anjima zaki dawo ko?". Cikin muryar rarrashi tace, "kayi haƙura zuwa Monday na dawo, dan anjima Mama tace zata aikeni shine ma nake sun na kiraka na faɗama kayar da naje?". Ataƙai ce yace, "ban aminta ba kuma anjima nake son ki dawo dan ina buƙatar ki" yana kai ƙarshin zancin ya datse kiran bata ri da yaji me zata ceba. Wayar dake hannuta ta fara kallo dan ita bata ma san me zata cewa Mama ba. Dabara ce ta faɗu mata dan haka ta hau gado tayi kwanciyar ta har lokacin da za'a aikin ta ya yi. Kiran ta Mama ta farayi amma tanaji taki ta karɓa har Mama tagaji ta shigo ɗaki. Tasheta Mama ta farayi dan a tunanin ta bacci take bata san ko idon ta biyu ba,tayi hakan ne dan kada taje aikin da za'ayi mata. Kanta ta ɗago kamar mai bacci gaske Mama tace,"Hafsat ki tashi kije rana tafito sosai kinji". Magana tayi mata cikin muryar marasa lafiya tace, "Mama kiyi hakuri ki aike su Marwan wallahi kaina ke ciyo" ta faɗa haka kamar tayi kuka. Sannu Mama ta fara jeramata haɗi da kawu mata magani dan tasha. Aken da bata zoba kenan sai da Mama takira Abban su Hafsat tace masa yayi mata izine taje wurin Hajiyar ta karɓu saƙo. Aikuwa Mama nafita Hafsat tamiƙe kamar ba itace ke sheiɗa ɗaya-ɗaya ba. Koda Mama ta dawo Hafsat tace taji sauki dan kan ya daina ciyo. Dare nayi ta fara tunanin yadda zata cewa Mama zata tafi makaranta. Dan ya da meta da kira kuma ta rasa yazata cewa Mama. Wanka tayi ta shirya ta kama hanyar ɗakin Mama dan ta gaya mata zata koma makaranta..... *#Vote* *Comment* *Shere* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 5📑* *__________📖* Labulen ƙofar ta ya ye kana ta shiga ɗakin. Saman sallaya ta same Mama dan haka ta ƙaraso a hankali ta samu waje ta zauna tana jiran Mama ta shafa. Bayan Mama ta shafa itama Hafsat ta shafa haɗi da gaishe da Mamar ta. Bayan Mana ta amsa sai Hafsat ta ɗagi da kanta ta ce, " Mama yanzu abokiyar karatuna ta kirani tace Malamin mu ya bada wani Asignmen tun Jumu'a bayan fitowarmu kuma yace Monday za'ayi summitng kuma ni ban masani ba sai yanzu kuma yace a makin teat ɗin mu ne, kuma rashin yin sa gareni babbar matsala ce. Sai da ta kai ƙarshin zancin mama ta ɗago ta dubeta kana tace, "Kina nufin yanzu na barki kije?". Kai ta ɗaga ma mama alamar " eh". Sai mama tace, " Tare da Safiya zaku je?". Sai Hafsat tace, " a'a Mama kinsan ba department ɗin mu ɗaya da ita ba". Sai Mama tace, " to gaskiya Hafsat abar wannan tafiya har da safe" har zata koma wata magana sai ga Abban Hafsat ya dawo daga masalaci. Bayan ya shigo ya zauna san gama gaisheshi kana Mama tayi masa bayanin da Hafast tama ta, kuma tafi ɗa masa yadda tace da Hafast . Bayan ta gama yace, " a'a baza mu hanamata zuwaba, kuma kinsan wannan karatun da takeyi yana buƙatar kula sosai dan haka tashi ga kuɗi kije kinji ƴar Abba ". yana faɗa yana dubanta. Sai Mama tace, " Kafison ta tafi?". Yace, "eh haka yafi abunda na ke so shine muyi mata fatan alhairi". Bayan Abba ya bata kuɗi ta ɗau kayan ta tayi musu sallama tafice. Bayan tafiyarta Mma ta dube Abba kamar tayi kuka tace, " yanzu karatun Hafsat bana son shi dan gabana yana yawan faɗuwa akan karatun Hafsat shiyasa yanzu bani da wata natsuwa akanta". Sosai Abba ya yi mata magana akan ta aje wannan maganar gyafe kawai suyi mata fatan alhairi. Tana fita takirashi tace ina yake gata ta tafito. Faɗa mata wurin ya yi , ba ɓata lokaci taje ta sameahi. Tana shiga mitar shiko ya yaja suka tafi. Ti-ti taga ya miƙe yana ta tafiya dan ba hanyar gidansa ce taga ya bi ba, dan haka ta dubeahi tace, Hayati naga sai miƙi ti-ti kake hala ina zamu je?". Batare da ya ɗago ya dubeta ba yace, " Zamfara". " Yanzu da dare nan hayet?". Yace, " eh yanzu nake da ra'ayin zuwa, in bazaki je ba na saukeki". Tace, "a'a kayi haƙuri idan na ɓata ma". Ta faɗi haka ciki da ƙanƙan da kai da tsoro. Bai sake cewa da ita komai ba har suka isa Zamfara. Hotel suka sauka ɗaki ɗaya ya kama musu , bayan sunyi wanka sunci abinci kana ya bata wasu ƙananun kayan bacci ya umarceta da sa su, jiki ta narawa ta saka su waɗanda da su da babu duk ɗaya suke a jikinta. Jikinshi ya jawota ya rungumeta haɗi da shaƙar ƙamshin jikin ta, lokaci ɗaya ya fara romance ɗinta. Hannunsa yasa ya fara shafar duk wani ilahirin sassan jikinta. Sosai take jin daɗin abinda yake mata dan haka ta ba da kai sai yadda ya yayi da ita, sosai ya bata wuya a daren ranar, dan sune basu kwanta ba sai biyar saura na asuba. Kuma asuba nayi ta farka tayi sallah kana tazo tana kwanta. Shima yana gama sallah ya kwanta haɗi da jawo ta jikin sa , romance ɗinta ya fara duk da yanzu bata so amma saboda jiya ba ƙaramar wahala ya bata ba, amma bazata iya ce masa bata so dan kar ransa ya ɓace. Sai bakwai da wani ya barta, kushi ba dan ya gaji ba sai dan meeting ɗin da yake dashi 7:30. Wanka ya yi kana ya yi beark yayi mata sallama ya tafi yace sai ya dawo. A dawo lafiya tayi masa haɗi da addu'a sai kace mijinta😏. Yana fita tayi wanka ta shirya tabi lafiyar gado dan bacci ne a idon ta sosai. Haka suka cigaba da zama garin Zamfara har tsawon kwana biyar. Zaune suke saman kujera ita dashi sai wayarta ta fara kaɗawa, har taso ta ƙi ɗauka kuma sai ta ɗauka, tana karawa kan kunninta ba abinda aka fara ce da ita sai, " kina ina?". Sai Hafsat tace, ina ruwanki da inda nake". Sai Safiyya tace, " to wallahi bari kiji yau zuwa gobe na baki , duk inda kike ki dawo , kuma inba haka ba zanje gida na faɗamusu abunda ake ciki, dan na gaji da ganinki cikin wannan muguwar rayuwa". tana faɗar haka ta datse kiran saboda wani kukan baƙin ciki da yazo mata. Tana kuka tana faɗin, " me Hafsat ta nemi ta nema ta rasa da da zata riƙa bibiyarshi kamar mijinta". Kuka tashiga rairawa kamar ta cire zuciyar ta jefar saboda baƙin ciki kuma ba abinda yafi ƙona mata rai gashi yanzu saura sati ɗaya a fara exmas amma ita Hafsat ba itace gaban taba. Tunda suka gama wayar da safiyya jikinta tane ya yi sanyi sosai kan ta ɗago ta dubeshi dan shima ita yake kallo kana ta buɗe baki tace, Safiyya ce takirani har tana yiminbarazanar zata gayawa su Mama bana schocl, kuma nasan tunda tace zatq faɗa to sai ta faɗa, dan Allah kayi haƙuri mu koma dan nasan halin Abba ko kasheni zai iya yi". Ta faɗi haka hawaye na fita a idonta. Haɗi fuska ya yi haɗi da goge mata hawaye dake fita a idonta yace, " Dan takiraki ta gaya miki haka shine harda wani tada hankali, aikinsan duk bazata faɗa ba saboda tana faɗa za'a dakatar da karatun ku , kuma ai zata fiki jin haushi tunda tafiki son karatun". haka yaci gaba da yi mata faɗa da daɗin baki ƙarshe ma ya umarce ta data kashe wayar ta dan ko an koa kiranta baza'a same taba. Dan yace bazaiyi komai ba sai yagama aikin da ya kawoshi. Tun daga lokacin Safiyya ko ta kira wayar Hafsat kashe take, sosai hankalinta ya ƙara tashi dan har gadin sa taje amma mai gida yace ya yi tafiya , tunda taji haka gaba ɗaya ta rasa natsuwar ta har dai lokacin da Mamar Hafsat ta kirata tace takira wayar Hafsat kashe ko lafiya?. Tace eh mama karatu ne yayi mata yawa dan har saƙo tabank na faɗa muku to nima ban dawo ba saboda hostel nake kwana. Aikuwa Mama Hafsat na jin tare da Safiyya suke ta samu natsuwa kana tayi musu fatan alhairi..... *SUMMY M NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 6📑* *__________📖* Bayan ya kammala abunda zai kaishi suka dawo gida da sati ɗaya taneme ya barta dan taje school dan Monday za su fara exams. Yace ta shirya ya kai ta amma kafin ya dawo gida ta tabbatar da tadawo dan baya son yadawo babu abunda zaici. School ɗin ya aje ta kana ya ƙarasa wurin aikin sa. Class ɗin su taje bata jima da zuwa ba aka fara lectura. 2 dai-dai suka gama lectures ďinsu,kuma suna fitowa bata tsaya komai ba ta kama hanyar fita. Har zata fita daga cikin makarantar sai Safiyya ta ganta tana ta sauri,da saura Safiyya tayi ƙarasa gare ta. Mayafin ta ta riƙo,lokacin da take daf da fita school ɗin. Safiyya tace, "ina zakije dakike ta wannan sauri haka?". Kallon sama da ƙasa tayi mata kana tace, "wurin da kika aikeni zan je" tana faɗa tana hararar ta. Sai Safiyya tace, "koma dai me yau ba inda zaki dan Mama na can hankalin ta tashe tana sun ganin ki dan haka yau gida zamuje ta gannki ko tasamu natsuwa". Hafsat tace, "Safiyya har sau uku taki ra sunan ta, bana son kina shiga rayuwa ta Safiyya kirabu dani nayi rayuwata,ki barni rayuwar ki ko tawa? kuma bazan je gidan ba inki haihu da uwarki kije kifaɗa ɗin ina gidan saurayi na". Tana faɗar haka ta kama hanyar fita ta bar Safiyya sake da baki tana kallon ikon Allah. Har zata fice sai ta dawo,gaban Safiyya ta ƙarasu kana tace, "daga yau kada ki kara shiga rayuwa ta dan ni tunda jimawa nafitar dake rayuwa ta dan haka kema ki barni bana son sa idon". Mai adai-daita ta tara kana ta faɗa masa unguwar da zai kaita. ita ko Safiyya gaba ki ɗaya mamaki da tsoro sun da baibaye zuciyar ta,dan gani take kamar ba kai sake Hafsat ke gaya mata wannan maganar ba,amma a ko da yaushe tana wa Hafsat fatar shiriya itada kullihin musulmi. Bayan ta dawo daga school wanka tayi kana ta gabatar da sallah sannan tazo ta fara gyaran gida,tana kammalawa ta ɗura sanwa. Saura ƙiris ta kammala sai gashi yadawo,aikuwa tunda taji horn ɗin motar sa gaban ta ya bada dummmm,saboda bata kammala girgin taba kuma tasan halin sa sarai baya sun jira. Tana cikin wannan tunani tafara jin knocking ɗinsa. Da sauri taje ta buɗe masa ƙofa dan kar ta ƙara ma kanta wani laifi. Ƙarɓar jakar dake hannun sa tayi haɗi dayi masa sannu da zuwa. Karɓawa yayi haɗi da ƙarasuwa daga ciki. Ruwan wanka ta haɗa masa,bayan yayi wanka ya fito, ta tayashi shiri,bayan ya kammala shirinsa parlour ya fito dan yaci abinci dan ya kwasu yunwa yau. Komai bai gani ba a dinning, dan haka ya ƙwala mata kira,ita ko tana can tana sauri taga komai ya kammala amma ina dan tana cikin haka taji yana kiran ta. Da hanzari tazo gareshi,aikuwa tunda ta ƙarasu ya jefeta da wani kallo wanda yasa cikin ta juyawa lokaci ɗaya. Tambayar ta ya farayi yace, "ina abinci na?". Jikin tane ya fara karkarwa tace, "kayi haƙuri nakusa kammalawa". Sai da yajefe ta dawani kallo kana yace, "sai yanzu kika dawo kenan?". Kai ta fara girgiza masa tace, "a'a muna gama lectures na dawo wallahi ko ina banje ba". Tsawa ya da kamata haɗe da cewa karya kikeyi kin dai tsaya iskancin kine shiya sa baki dawo ba" nan ya dinga cin zarafin ta har da kukan ta tana bashi haƙuri amma yaƙi ko saurarin ta,daga ƙarshe ma key ɗin motar sa ya ɗauka yafi ce a gidan. Har ya fita ya dawo ya ƙwala mata kira, da sauri tafito daga kiching haɗi da durƙusawa gaban sa. Tun bata kai da durƙusawa ba yace ta haɗa kayan ta tabar masa gidan sa. Aikuwa yana faɗar haka da sauri ta faɗa jikinsa tana bashi haƙura,amma ina baya ko saurarin ta dan da ƙarfi yajaye ta jikin sa ya kifeta da wani azaftaccin mari har guda biyu kana yace, "kuma wallahi kafin na dawo kinbar gidan nan tunda ba na ubanki neba" yana faɗar haka ya ficewar sa yana huci". Kuka takeyi kamar ranta zaifita dan ita ba komai yafi ƙona mata raiba irin yadda yace tabar masa gida, to ina zata je?. Wani tunani ya faɗu mata arai aikuwa da sauri ta miƙe daga durkushin da take ta koma kiching taci gaba da aikin ta. Bayan ta kammala girki, sosai ta fara gyaran gida,bayan ta kammala tasaka turare mai ƙamshin gaske wanda lokaci ɗaya yasa gida yabada wani ƙamshi mai sanyaya zuciya. Toilet taje tayi wanka,bayan ta fito ta shafe jikin ta da ma yukka masu ƙamshi haɗi da hummara ta musamman,dressing ɗin english wears tayi masa wanda tasan yafi so sosai. Tana gamawa ta ɗauko wasu turarukka ta feshe jikin ta dasu. Tarigi ya ta ɗauru alwala,sallah magarb da isha'i ta gabatar kana ta fito parlour ta zauna zaman dawowar sa. Batayi minti biyar da zama ba sai ga horn ɗin motar sa. Aikuwa da sauri ta ƙara feshi jikin ta da turare haɗi da dauko lollipop tasaka a baki, ta fara tsutsu sai kace wata ƴar yarinya. Bai ma tsaya wani knocking ba yasa key ya buɗe ƙofar. Tsaye ya ganta tana masa murmushi haɗi dayi masa wani kallo mai ciki da so da ƙauna. Jikin sa tafaɗa haɗi da faɗin "My Hubby nah, sannu da zuwa". Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi sauri ta haɗa bakin sa da nata tana shayar da shi lolopop ɗin da ke bakin sa. Aikuwa tuni jikinsa ya karɓi saƙon da take bashi haɗi da shaƙar ƙamshin da ke fita a jikin ta. Bare abu ga ma abuci son ƙamshi,sosai ta mantar dashi fushin da yakeyi da ita,tsayowar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta zowa bedroom ɗinshi. Sai da komai ya lafa kana ya jawuta jikin sa sosai kana yafara magana ahankali yace, "My love jibi ne ta fiyar dan haka ki kasan ce cikin shiri dan tafiyar safe zamuyi". Gabanta ne ya faɗi dan ita har ta manta da wata tafi ashe tafiyar na nan kuma gashi Monday za su fara exmas. Jikin ta asanyaye tace, "Allah ya kaimu jibi lafiya". "Ameen" yace da ita haɗi da kai bakin shi da nata ya fara kissing ɗin ta. Duk abunda yake mata bata wani jin daɗin sa saboda tunda yayi maganar tafiyar jikin ta yayi sanyi dan tunani take anya zata bishi tabar exmas ɗinta?kum gashi aski yazo gaban goshi dan daf take da ta kammala degree ta afannin gaenacology kuma da bata ci wannan exmas ba zasu iya withdraw ďinta kuma gashi tana da carryover har guda biyu. Suna cikin haka tace, "a'a gaskiya bazan jeba". Ahankali yace, "mikika ce?". Tace, "aa ba da kai naki ba". ************* Yau takama Monday kuma yau zasuyi tafi kuma yau zasuyi exmas..... Wani zatayi tafiya ko exmas...... *__________📖* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 7📑* *__________📖* Yana gama shiri yafito dumin su tafi dan baya sun suyi rana. Kiran ta ya farayi,ita ko tana can tana tunani ta tafi ko karta tafi,rasa me zatayi tayi,gashi tana tsoro rashin yin exmas ɗinta, kuma tana tsoron ɓacin ransa. Kiran da taji yana mata yasa gabanta dukan uku-uku,alamun zai shigo ɗaki data ke ciki taji dan haka da sauri ta fara haɗa kayan ta cikin jikar da zata tafi da ita. Koda ya shigo har tasa tufafin ta tana yafa mayafin ta,amma fuskar ta a ɗaure kamar tayi kuka. Magana yayi mata yace, "kefa nake jira". Tace,"nashirya mutafi" tafaɗa haka kamar tayi kuka. Fitowa tayi ɗauke da jika a hannunta,jikin ta a sanyaye ta rasa ya zatayi,tana cikin haka taji yace, "muje zan kulle ƙofa". Fita tayi ya kulle ƙofa kana ya shiga mota ya tada. Gabanta ne ya tsanan ta faɗuwa sosai, lokaci ɗaya wasu hawaye suka fara fita a idon ta. Magana yayi mata yace ta shigo sutafi. Kamar bata ji shiba tayi sai da yayi magana cikin faɗa-faɗa kana tabuɗe motar tashiga tana mai saka kuka kamar wani yayi mata dole sai taje😏. Aikuwa yana tada mota kukan da takeyi ya tsanan ta. Dubanta yayi kana yace, "mi akayi miki da zaki saka min kuka,ko tafiyar ce bazakiyi ba ne?". Kanta ta fara girgiza masa kana tace, "a'a kayi haƙuri na daina". Yace, "to ki shafe hawayin ki dan bana son jin kuka kinji ko". Hawayen ta tashafe haɗi da cemasa "to". Tunda suka kama hanyar tafiya gaba kiɗaya hankalin ta atashe yake, dan tunda take dashi bata taɓa jin irin wannan tashi hankali ba kamar na yau,amma kuma bazata iya ce masa baza ta jeba,har suka fara fita daga cikin gari ba wanda ya cema ɗan uwansa komai. Saura minti biyar afara exmas sai Safiyya tazo bakin class ɗinsu taga ko Hafsat tazo,aikuwa tana ƙarasuwa taga class ďin kowa yazo amma sit ɗin Hafsat wayam,gaban Safiyya ne ya bada dummm da sauri tashigo class ɗin. Wata abukiyar karatun Hafsat, Naja'atu ta tambaya tace, ina Hafsat?". Sai Naja'atu tace, "ai Hafsat ta daina zowa school dan tun dawo wa hutu sau biyu ta shigo class,kinga ma exam card ɗinta yanzu haka ita nake jira". Safiyya tace, "bata da lafiya,amma nasan yanzu zata zo,bani card ɗin nabata dan sauran kayan ta ma na hannuna". Ba musu Naja'atu ta bata. Aikuwa tana ƙarɓa da sauri ta fito ta kama hanyar hostel,tana zowa tasumu arun niƙaf tasa afuskar ta ta dake ma ran,ta tashiga class ɗin haɗe da addu'oi Allah kasa kada agane ba Hafsat ce ba. gaban ta na duka uku-uku haka taje ta zauna saman sit ɗin Hafsat batari da tawa kowa magana ba. Ko minti biyu batayi da zama ba aka fara raba Question paper. Ana kawo wa gaban ta,gabanta ya bada dummmm,addu'a takeyi Allah kasa kada ace sai ta ciri niƙaf ɗin da ta sanya..... *To fah Safiyya kin iya ganganci*🤔 *# Vote* *Comment* *Shere* *©SUMY NAIGE.* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 8📑* *__________📖* Cikin ikon Allah ya aje mata Question paper ya wucewarsa batare da yayi mata magana ba. Aikuwa yana wuce ta ta fara yiwa Allah kirari a zuciyar ta haɗi da godiya a gare shi. Tunda ga lokacin taci gaba da rubuta mata exams har suka kammala ba tare da ta samu wata matsala ba, sai dai gaba ki ɗaya ta dawo hostel da zama dan bata da lokacin komai sai na karatu, kuma tunda ta fara rubuta ma Hafsat jarabawa ba wanda ya gane ba Hafsat bace in ba ƙawar karatun Hafsat ba Naja'atu. Sosai taba Safiyya gudunmuwa wajan ganin tayi ma Hafsat jarabawa, duk da ba department ɗaya suke da Safiyya ba amma tayi ƙoƙari sosai dan gabaki ɗaya ta hana ma kan ta barci ko da yaushe tana library wajan karatu, tayi nata tayi na Hafsat, har Allah ya nuna mata ta gama lafiya sosai tayi rama saboda rashin natsuwa da rashin isashen bacci. Tunani ta farayi lokacin da suka gama exams yadda zata koma gida ba tare da Hafsat ba, dan haka ta yanke shawarar taje gidan sauranyin nata ta gani ko zata ganta,har zata je kuma ta fasa saboda ba ƙaramin baƙin cikin ganin sa takeyi ba dan haka ta yanke shawarar takira ta a waya. Miss call kusan biyar tayi mata amma bata ɗauka ba sai ga na shidda kana ta ɗauka batare da tace komai ba. Safiyya ba tadamu da rashin maganar taba dan haka tace, "kidawo dan ni zan koma gida kuma kin san da naje zasu tambaye ki dan haka gobe zan koma ko ki dawo ko kada ki dawo na dai faɗa miki". Bata ma bari taji me zataceba ta tsinke wayar. Ita ko Hafsat tunda suka sauka ya kama musu hotal bata sake koda leƙo ƙofa ba dan baya barin ta. Kuma yanzu ko lafiya bata isheta ba dan yanzu bata da wani kuzari, ga wata rama da takeyi duk tabi ta bushe kuma tana cin abinci amma kamar bata ci, sosai abun ke bata tsoro dan ita gabaki ɗaya tunda sukayi tafiyar nan bata cikin kwanciyar hankali, abu kaɗan ya isheta kuka. Yau ma kamar kullum suna kwance yana romance ɗin ta son ran shi, sosai yake jin daɗin abunda yake mata, ƙoƙarin shigar ta ya fara amma tana ɗan kaucewa, saboda yanzu ko kaɗan bata son abun da yake mata dan yanzu da ya gama abunda yakeyi da ita sai wani azaftaccin ciwon mara ya taso mata wanda kesa jikin ta kar-karwa lokaci ďaya. Sosai take wahala kuma duk wannan uban ciwon marar dake taso mata ta gagara faɗa masa ya dena amfani da ita ko suje hospital a'a ita baza ta iya faɗa masa ba dan kar ransa ya ɓaci. Duk da tana ƙoƙarin hanashi amma shi bai masan tanayi ba. Ba ɓata lokaci ya afka cikin ta ya fara abunda yake so da ita son ranshi. Aikuwa yana gamawa ya ɗan kwanta dan ya huta yaci gaba da abunda yake yi. Ita ko yana sauka daga kanta, lokaci ɗaya wani abu ya taso mata ƙasan marar ta, tun tana dauriya kar ya gane har abu yazo yafi ƙarfin ta, lokaci ɗaya ta fara fita hayyacin ta, duban sa ya kai gare ta aikuwa lokaci ɗaya ya zabura ya mike zaune haɗi da tambayar ta, "lafiya mike damun ki"?. Ita ko batama san yana yi ba saboda a lokacin bata masan inda kanta yake ba. Abun yaga yafi ƙarfin sa dan haka da sauri ya saka jallabiya ya ɗauke ta domin suje hospital. Cak ya ɗauke ta ya kai mota, rasa asibitin da zai kai ta yayi, dan dare yayi gashi kuma bawani sanin garin yayi ba. Masu gadin hotel ɗin ya tambaya yace su nuna masa hospital mafi kusa? dan matar shi ce ba lafiya haɗi da nuna musu ita a cikin motar. Wani private hospital dake kusa da hotel ɗin suka nuna mai godiya yayi musu kana yaja motar da gudu bai tsaya ko ina ba sai cikin hospital ɗin. Cikin gaggawa Likitoci suka karɓe ta, lokaci ďaya suka fara bata taimako . Sun jima kanta kafin su shawo kan lamarin. Bayan komai ya ɗan lafa kuma ta samu barci dan haka suka fito daga ɗakin da take. Yana ganin sun fito ya fara tambayar su ya jikin nata?. Komai basu ce dashi ba sai babban doctor daga cikin su yace dashi "ka biyo mu office". Komai bai ce dasu ba ya bi bayan su. Bayan sun isa office dukan su suka zauna, kana suka nuna masa kujera domin ya zauna. Bayan ya zauna sai babba daga cikin Likitocin yayi gyaran murya kana yace, "da farko dai munyi nasarar ceto matar ka dan yanzu haka ta samu bacci kuma insha Allahu ina har takiyaye ƙa'idojin da zamu ɗaura ta akai to babu shakka zata samu lafiya sosai da sosai. Sai abu na biyu muna tayaka murnar matar ka na ɗauke da juna biyu har na tsawon wata huɗu....." aikuwa tun Doctor bai kai da ƙarasa maganar ba yace, "what haɗi da faɗin ciki!. Gabaki ɗaya Likitocin kallon shi suka farayi cike da mamaki. Dubin doctor yayi kana yace, "Doctor kun duba da kyau kuwa? dan ni matata bata da ciki gaskiya". Results ďin scanning ďinta dake gaban sa ya bashi yace, "duba kagani". Karɓa yayi ya fara dubawa, abunda yagani ne yayi matuƙar bashi mamaki da tsoro. Yana gama dubawa sai ya ɗago da kansa yana kallan Doctor kana yace, "Doctor na gani kuma na yarda tana da ciki amma ina son a zubar da shi dan ba yanzu zamu haihu ba, ko nawane zan biya kawai a zubar da shi". Tunda ya fara magana gaba ki ɗaya Likitocin suka zuba mishi ido suna kallon shi har ya kai ƙarshen zancen shi. Sai da ya gama kana babba daga cikin Ƙikitocin yace, "kafin na gaya maka komai ina son kasan wani abu ɗaya, lokacin da kake ba matar ka ƙwayoyin hana ɗaukar ciki to kasani sosai sukayi mata illah a mahaifar ta, dan ikon Allah ne yasa wannan cikin ya shiga cikin mahaifar ta har ya zauna ya kai wannan lokacin ba tare da ya zube ba,sosai mukayi mamaki lokacin da muka ga yadda mahaifar ta take dan sanadiyar wannan magani da kake bata mahaifar ta tafara lalacewa sosai, dan ko da wannan cikin ya kai matakin haihuwa to na tabbata bazata iya haihuwa da kanta ba sai ammata aiki, dan haka yanzu idan kace a zubar da cikin to za'ayi ɗayan biyu, dan sanadiyar haka mahaifar ta zata iya lalacewa bazata ƙara ɗaukar ciki ba ko kuma wajan cireshi ta rasa ran ta, kaga ko baza kayi fatar ko ɗaya a cikin waɗan nan su samu matar kaba". Sai da Anwar ya nisa kana ya dube Doctor yace, "Doctor kada kaji komai nasan haka bazata faru ba, kawai a cire shi dan bana son cikin". Gabaki ɗaya Likitoci da ke office ɗin kallon sa sukeyi dan abunda ya faɗane ya basu mamaki. Sai Doctor yace, "banƙi ta taka ba amma sai nayi magana da matar taka idan ta aminta acire to ba komai zamu cire amma idan bata aminta ba to gaskiya ba zamu cire ba saboda aikine mai wuyar gaske?". Sai Anwar yace, "kada ka damu da matata dan nasan zata aminta dan haka kuyi aikin kawai". Sai doctor yace, "a'a sai naji ta bakin ta". Sai Anwar yace, "ba damuwa idan ta farka zaka iyayi mata bayani". Doctor yace, "ba damuwa". Bayan gari ya waye kusan ƙarfe goma Hafsat ta farka, kuma Alhamdlillah dan ta samu sauƙi sosai. Bayan tayi wanka tayi break tasha magani Doctor yazo ya duba ta kuma yaga jikin da sauki dan ba wata matsala yanzu dan haka yace bari yakira sauran Likitocin. Aikuwa yana fita Anwar ya ƙarasu gareta wani kallo ya jefa mata haɗi da yimata ya jiki. Bayan ta ƙarɓa yace, "ni zaki munafur ta, ashe kin san kina da ciki amma kika ƙi sanar dani, to bani kika cuta ba kanki dan ni bazan aureki da ciki ba dan haka tun wuri kisan abunyi". Da sauri ta ɗago da kanta ta kalleshi bakin ta na kar-karwa tace, "wani ciki, wallahi ni banda ciki kuma da'ace inada ciki da kai kanka zaka sani". Wani kallo ya watsa mata haɗi da jefa mata wasu takardu yace, "duba kigani". Jikinta na kar-karwa ta ɗauka ta fara dubawa aikuwa tana gama dubawa ta zabura haɗi da sanya hannu akai tace,"ciki gareni fah!. Wasu hawaye suka fara bin kuncin ta haɗi da durkusawa ƙasa ta fara kuka mai tsoma zuciya. Tsawa ya daka mata haɗi da faɗin tayi shuru zaiyi magana da ita. Hannun ta ta ɗaura kan bakin ta kana tace, "na daina". Yace, "abunda nake so dake idan Likitoci suka tambaye ki kin yarda azubar da cikin kice eh kin yarda, dan idan baki yarda ba to wallahi bazan aureki ba kuma sai dai kije kisamar masa uba amma ba niba". Jikin ta na kar-karwa tace' "na yarda ko ma basu tambayeni ba na yarda kuma kayi hak'uri kada ka fasa aurena please". Har zai sake magana sai ga Likitoci sun shigo ɗakin. Ƙarasawa sukayi gaban gadon da take kwance, bayan sun gaisa sukayi mata ya jiki kana sukayi mata bayanin da sukayi ma Anwar har wanda yayi musu na azubar da ciki. Bayan sun gama yimata bayani sai ɗaya daga cikin su ya dube ta yace, "kin amince azubar da cikin?". Duƙar da kanta ƙasa tayi wasu hawaye masu zafi nabin kunci ta, tunani ta fara idan aka cire shikenan baza ta sake haihuwa ba kenan?ko ta rasa ranta, kuma yace bazai aureni da ciki ba to ya zanyi?. Shurun da sukaji tayi ne yasa suka yi mata magana kallon su tayi da idon ta dasu ka sauya zuwa ja, sosai ta basu tausai dan haka suka ce da ita kin amince?". Sai da ta rufe idon ta kana tace, "a'a ban amince ba". Tun bata kai da rufe bakinta ba Anwar ya daka mata tsawar da tasa ƴan cikin ta kaɗawa. Bai ma damu da Likitocin dake wajan ba yace, "me kika ce? baki amince ba?". Jikinta na kar-karwa tace, "Hayat kayi haƙuri dan Allah ka taimaki rayuwata". Har zaiyi magana sai ɗaya daga cikin Likitocin yace, "Malam bari kaji koda a ce ta aminta azubar da cikin tomu ba zamu zubar ba, dan mu ba aikin mu bane, idan kaga zaku iya zama har ta samu sauƙi to bazamu hanaka ba amma idan kaga baza ku iyaba to zaku iya ƙarawa gaba amma mudai bazamu zubar mata da ciki ba bare ciki har na wata huɗu". . Yace, "ko minti biyar baza muyi anan ba bare har na sa kuɗina taci gaba da kwanciya anan". Kallon ta yayi yace, "ki tashi muje sai kije can ki haifar musu shi dan wallahi kar ma ki soma cewa nawa ne" yana faɗar haka ya kama hanyar fita batare da yaji mi zasu ce dashi ba. Suma Likitocin fita sukayi har sun fita sai ɗaya daga cikin su ya dawo ya sameta sai kuka takeyi kamar ranta zai fita yace, "Shawara zan baki duk yadda yaso kada ki yarda a zubar miki da ciki dan ke zai cutar, shi a kowane lokaci yake son haihuwa zai iya wani aure ya haihu amma ke shikenan baza ki saki haihuwa ba har abada, dan haka ki tashi kije yana jiranki " yana faɗar haka shima yafice daga ɗakin. Sai da tayi kusan minti biyar kana ta tashi ta fara bin bango ta fita a ɗakin har ta kai wurin da motar sa take. Tun bata ƙarasu wajan saba ya fara afka mata wata muguwar harara. Motar ta buɗe ta shiga aikuwa tana shiga yaja motar da ƙarfi kamar zai tashi sama ya fice. Suna isa hotel ɗin ko kallo bata ishe saba ya buɗe motar ya barta ba tare daya kalleta ba. Haka tafito tana tafiya a hakali har ta isa ɗakin da suke. Koda ta shigo yana toilet yana wanka wuri tasamu ta zauna, bata jima da zama ba ya fito yayi kamar bai san da zaman mutum a wurin ba. Har ya gama shirin sa zai fita kana ya dube ta yace, "ki tattara naki da naki dan gobe zamu koma gida kuma wallahi ba zaki sauka gidana ba sai dai kije gidan ubanki" yana faɗin haka yafice warsa batari da ya tsaya yaji mi zata ceba. Yana fita ta fara kuka mai ban tausai, tana cikin kukan ne Safiyya takira ta kuma abunda yasa tak'i magana dan kar taji tana kuka. Haka ya barta har dare batare da ya sake wai-wayar taba. Kuma babbar matsala duk baifi rashin ƙarfin jikin da bata dashi ba kuma ga yunwa ta dame ta dan tun safe rabun ta da abinci gashi yanzu dare yayi kuma har yanzu bai dawo ba. Har barci ya fara ɗaukar ta sai gashi ya dawo, da sauri ta tashi dan a tunanin ta ko zata samu wani abun da zataci koda tea ne tasha. Koda ya shigo sarai ya gan ta amma sai yayi kamar bai ganta ba har yaje toitel yayi wanka yazo ya kwanta, sai ta ƙaraso da sauri gareshi tace, "Hayat dan Allah ka taimakamin da ko ruwan tea ne wallahi yunwa nakeji?" tana faɗa kamar tayi kuka. Kallo ma bata isheshi ba bare tasa ran zai ƙarɓa mata magana. Data ga alamun bazata samuba dan haka ta zo ta kwanta. Bata jima da kwanciya ba ya fara jawota jikin sa yana wasa da ita son rashi, ita ko tunda taga abunda yake son yi da ita ta fara masa kuka tana faɗin, "dan Allah kayi haƙuri ka barni wallahi banda lafiya kuma yunwa nakeji". Yi yayi kamar bai jita ba haka yayi yadda yake so da ita kafin ya barta. Sosai tayi kuka a wannan daren dan iya wahala ta wahala dan har ƙaramin suma sai da tayi, kuma tundaga lokacin bata koma barci ba har gari ya waye....... *#Vote* *Comment* *Shere* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad ~Summy M Na'ige~ *SHAFI NA 9📑* *__________📖* Bayan ta idar da sallah asuba tajima kafin ta ta shi sabida ko da ta tashi faɗuwa zatayi dan bata da wani kuzari a jikin ta. Tana kan sallaya ya tashi ya je ya yi wanka kana ya yi sallah, bearkfast yaje ya karɓo musu,yana dawo ya kai duban shi gareta kaifin ya yi mata magana ita tafara gaisheshi ciki da ladabi. bai ma karɓa ba yace, "kizo kiyi bearkfast dan yanzu na keson mu kama hanya kuma idan ki ka tsaya wasa sai na barka". yana faɗa yana antaya mata harara. Ahankali ta tashi kayan da yanuna mata na beark su ta ɗauka ta haɗa tea ta farashi,sosai taci kayan da ya kawo mata,sai da taji ta ƙoshi kana ta tashi taje toilte tayi wanka. tana cikin shiri sai gashi ya fito cikin shirinsa na tafiya,ko kallon ta baiyi ba ya kama hanyar fita. Ɗakin da taga yana ƙoƙarin rufewa yasa da sauri ta ɗauko kayan ta tafito waje ta karasa ya fa mayafin ta. Key ya kai ma masu hotel ɗin kana yazo ya ɓuɗe mota ya shiga itama tashi kana suka kama hanyar garin sokoto. Tafiya sukeyi amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai har sukayi nisa sosai. Wayar Hafsat ce tafara ruri dan haka ta ɗauko ta duba wake kiran ta. Safiyya taga ya bayyana dan haka taja tsaki kana ta ɗauka. Safiyya tace, "Hafsat kina ina wallahi yau zan koma gida kuma kin sa za su dame ni da tambayar ki dan Allah kidawo mutafi tare". Sai da ta kai ƙarshen zancin Hafsta tace, "wai Safiyya ke waci iri ce,nace kirabu dani kinƙi to bazanje gidan ba kije ki faɗa kinji kuma bari kiji kada ki saki kira na sabida ba ajiya ki ka bani ba ehe". tana gayamata haka ta tsinki kiran. Duk abunda takeyi yana kallon ta amma ya yi kamar bai san ta nayi ba. Haka suka cigaba da tafiya har suka shiga garin sokoto. Suna kawowa Flyover ya yi packing ďin motor sa yace, "ki sauka dan ni zan wuce". "Haba Hayat kayi haƙuri muje gidan ka idan na ɗan huta zuwa ajima sai naje gida". Wata tsawa ya daka mata wandda tasa tafice daga motar bata shiyar ba. Har zai tada motar tace,"Hayat bani da kuɗin da zan ƙarasa gida kuma bazan iya ƙarasawa da ƙafa ba gashi kuma dare ya yi". Ko kallon ta bayi ba yaja motar sa ya bar ta tsaye a hanya. Hawayen da kifita a idonta ta goge kana ta ɗau jikar ta tafara tafiya kan ti-ti. Mai napep ta tsayar dashi, ta faɗa masa sunan unguwar da zai kaita. Bai tsaya da ita ko ina ba sai ƙofar gidan su. Fita tayi tace dashi zata shiga ta karɓo masa kuɗi yace to. Sallam tayi ta shigo cikin gidan,aikuwa ƙannin ta najin muryar ta suka fara yimata oyoyo kamar za su kayar da ita gashi ba wani ƙarfin jiki ne da itaba. Da ƙyar tasamu suka sake ta,ita ko Mama tunda taji suna oyoyo ta san ƴar ɗiyar tace ta dawo dan haka da sauri tafito waje sabida ta ganta. Gaban tane ya yi muguwar faɗuwa lokacin da taga Hafsat,dan gabaki daya ta rame tayi fari sosai. Har zata tambaye su Mama sai suka haɗa ido da ita,murmushi Hafsat ta ƙaƙalo tace, "Mama ya nasameku?". Bata karɓa ba dan kallon ta takeyi sosai dan kamar tana son ta karantu wani abu,sai Hafsat ta katsa mata tunani tace, "Mama nafa tsayar da mai napep ban bashi kuɗi ba". Sai Mama tace, "dole na kifeki da ido wannan ubar ramar da fari da kikayi Hafsat, lafiya kike kuwa?". Tace, "Mama bari na sallame mai napep nazo". Tambayar ta kuɗin sa tayi ta faɗa mata sai Mama tabaiwa ƙaninta Ammar ya kai masa. Sai Mama tace, "kinyi tsaye ki ƙaraso daga ciki". Parlour Mama ta shiga ta zauna Mama tace,"Hafsat mike damunki ki ka yi wannan ramar haka?". Sai da ta ƙaƙalo murmushi tace, "Mama wahalar exams ce ta ramar dani" tana faɗa tana yin ƙasa da kanta. Sai Mama tace, "a'a Hafsat da alamu akwai ramar zazzaɓi aciki". Tace, "eh Mama dan jiya ma naje hospital suka rubutumin magani kin gama tagarda maganin" tana faɗan haka tana buɗe zip ɗin jikar ta ta ɗauko mata tagardar maganin da aka rubuta mata a can hospital ɗin da ya kaita dan cewa ya yi tunda bata yarda azubar da cikiba to ko magani ba zai saya ba. Ɗaukowa tayi taba Mama itako Mama takira Marwan tace yaje pharmacy ɗin Baban shi ya karɓo magani. Karɓa yayi yaje itako Mama tace Hafsat ta koma ɗakin ta tayi wanka tayi sallah t azo taci abinci ta sha magani. Tashi tayi taje ɗakin ta, tana shga kafin tayi komai wayar ta ta dauko ta fara kiran Anwar. Kusan missed call biyar tamasa amma bai ɗaga ba daga ƙarshe ma kashe wayar sa yayi gabaki ɗaya. Sai da taji ya kashi wayar kana ta tashi taje tayi wanka tayi sallah magarib da isha'i. Tana idar da sallah Marwan ya shigo ya kawo mata magani da abinci. Bayan ta ci abinci tasha magani ta koma ɗauko waya ta ƙara kira ko ya ɓuɗi?. Amma har yanzu kashe take,tunani tafarayi ko taje gidan sa dan gabaki ɗaya bata da natsuwa dan ita kanta tasan ko tana samun natsuwa sai ta ganshi,kuma tasan Mama baza ta barta tafita ba. Tana cikin wannan tunani barci ya fara ɗaukarta saboda maganin da tasha har da na barci akwai. Ko da babanta ya dawo daga masallaci har barci yayi awongaba da ita dan ko da Mama ta aiki Marwan ya kirata ta yi bacci sai Babanta yace ka da a tasheta abarta sai da safe sai su gaisa. Ko da gari ya waye Mama taje ɗakin ta dan ta kira ta, amma sai ta tarar har yanzu bacci takeyi bata tashi ba, abin ya ba Mama mamaki da taga har rana ta kusa fitowa Hafsat bata tashi ba sabod tasan ba halin taba ne baccin asubah. Tayar da ita ta farayi tana kiran Hafsat tashi kiyi sallah rana tayi, miƙa ta farayi alamun zata tashi Sai ta fara magana cikin muryar bacci tace, " Mama rana ta fara fitowa?". "Eh Ki tashi ga Abbanki can yana jiranki ku gaisa saboda yanzu fita zai yi,Tashi tayi ta nufi toilat Cikin hanzari tayi wanka sannan ta daura Arwala. Ita ko Mama tana ganin ta tashi ta shiga toilat sai ta fice daga dakin Koda tafito bata tarar da Mama ba dan haka ta gabatar da sallah kana ta shirya tafito taje ta gaishe da Abbanta. Da sallama ta shiga parlour,bayan sun ƙarɓa mata ta ƙaraso gaban Abban nata wanda tun shigowar ta yake kallon ta ciki da so da ƙaunar ƴar tasa. Bayan ta gaisheshi ya karɓa kana yace, "Hafsat ashe har ciyo kikayi?Allah ya ƙara sauki kuma kiri ƙa shan magani muga kwana biyu abunda Allah zaiyi". Ya ƙara da faɗin "ya exmas da fatar kun kammala lafiya?". Tace, "eh Abba mungama sai dai muna baran addu'ar samun nasara". Sosai ya yi musu addu'ar samun nasara ita da Safiyya kana ya yi musu sallama yafita wajan aiki. ********* Bayan kwana biyu da dawowar ta tasamu sauƙi sosai dan har cikowa ta farayi ba kamar lokacin da tadawo ba. Kuma tundaga ranar da ya sauke ta bai saki nemanta ba kuma bai saki ɗaukar wayar taba dan ko takira ba zai ɗauka ba shiyasa gabiki ɗaya bata cikin natsuwa dan yanzu burin ta taganta tari dashi dan haka taje tagayawa Mama zataje gidan ƙawar ta ta dubata sabida batada lafiya,da kyar tasamu Mama tabarta amma tace kada tajima. Wanka tayi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗikin rika da sikt ne sosai suka karɓe ta tayi kyau abunta har ta ɗauko turare tasa jikinta sai ta tuna Mama bazata barta tafitaba idan tasa shi ba, dan haka ta saka shi ajika ta har sai tazo gidan sa haɗi da wani mitsi-tsin gyale. Babban hijab tasaka ajikin ta kana ta fito tanufe ɗakin Mama. Da Sallama tashiga tace, "Mama zan tafi". Kuɗi napep Mama tabata haɗi da ƙara faɗamta karta jima. Karɓa tayi haɗi da faɗi, "bazan jimaba". kana taficewar ta. Tana fita ti-ti ta tsayar da napep,sunan unguwar da zai kata tagaya masa, shiga tayi yaja suka tafi. Basu tsaya ko inaba sai bakin gidan sa. Bayan ta sallame mai napep ta ƙaraso bakin gate ɗin gidan ta fara knocking,bata jima tana knocking ba maigadi ya leƙo yaga wanene?aikuwa yana ganin ta ya yi sauri ya buɗe mata ƙofa haɗi da gaisheta. bayan ta ƙarɓa take tambayar sa ko Anwar nanan?. Yace "eh yana ciki". Part ɗinsa ta ƙarasa , kafin ta isa ga part ɗinsa ta buɗe jikarta ta ɗauko turare tafeshi jikinta dashi kana taciri hijab ta sanya wannan mitsi-tsin gyale wanda dashi da babu duk ɗaya. Ƙofar da zata sadata da falon shi tashiga kai tsaya. Ahankali take tafi har takawo gab dashi yana zaune yana kallon labaru bai masan ta shigo ba. Ƙamshin turarin da ya bige hancin sane yasa ya dago kansa, aikuwa suna haɗa ido dashi ta fara sakar masa murmushi mai ciki da nuna tsan-tsar so da ƙauna. Har yaso ya ƙoreta amma yadda yaga ta ƙara kyau kuma ga ko ina nata ya ciko musammam abunda ya keso wato dukiyar fulani. Irin kallon da yake matane yasa tafara tafiya ɗaya-ɗaya har ta ƙaraso gareshi. Ahankali tazo ta zauna saman cinyarsa haɗi da kai masa kiss abaki tare da faďin,"I miss you so much My Hayat nah". Aikuwa yana jin bakinta cikin nashi lokaci ďaya yaji wata Sha'awa tabi jirumasa bai san lokaci da yafara kissing ďinta ba cikin zafin nama. Hannunsa yasa cikin rikar ta yafara shafar duk wani ilahirin jikin ta,musammam abu son shi sosai yake matsar su itako sai ƙara narke masa takeyi ajiki tana wani nishi ɗaya-ɗaya. Cak ya ɗauke ta ya yi bedroom ɗinshi da ita,kayan jikin ta yacire mata kana yacire nasa romance ɗin ta yafara cikin zafin nama kana yashiga aiki, sosai ya bata wuya dan har wani abu taji ya tsaya mata amara amma bazata iya cewa ya daina ba. Sai da yagaji dan kansa kana ya sauka daga gareta ciki da samun gamsuwa dan shi yake masifar sonta,sosai yake samun natsuwa gareta. Itako yana gamawa ta gagara tashi dan gabiki ɗaya marar ta ta ƙulle, gawani ciyon da takeji a ƙasan ta. Shi bai masan tanayi ba, jan yota jikinsa yayi yafara baccin hutu itako ta jima kafin taji dama-dama,daga baya bacci yayi awun gaba da ita. Sai kusan ƙarfe shidda yabar ta ta koma gida koshi sai da taga neman halakata yake ta sanya masa kuka da kyar ya barta ta tafi gida. Shiko duk abunda yake mata da gayyane yakeyi sabida burinshi yaga cikin ya zube. Tun ahanyar zuwa gida taji mararta na ciyo kuma gawani zazzaɓi da ya taso mata lokaci ɗaya. Batafi minti biyar da shiga gida ba cikin ta yafara juyawa kamar abunda ke cikinta ya fito. Kuma gashi ita kadai a ɗakin, tajima kwance tana birgima a ɗakin sai can Mama ta shiga ɗakin ta dan tayi mata faɗan jimawar da tayi bata dawo ba sabida ƙarfe huɗu tayi da ita ta dawo. Aikuwa ko da Mama tashaga ɗakinta halin da ta sameta ne ya yi matuƙar razanata. Rasa me zatayi tayi sabida gabaki ɗaya tafita hayyacinta ga kuma wani jini dake fita ta ƙasanta. Da gudu Mama tashiga ɗakin su Marwan tace "yakira mai napep Hafsat ba lafiya za su kaita hospatal". Dayake ba suda nisa da ti-ti yana fita ya tsayar dashi suka ƙaraso gida. Shida Ammar da Mama suka ɗaukota suka sa a napep suka wuce hospatal ko mayafi babu ajikin Mama sabuda firgita😢....... *#Vote* *Comment* *Shere* *©SUMY NA'IGE•* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad ~Summy m Na'ige~ *SHAFI NA 10📑* *__________📖* koda suka isa hospital emregency room suka kaita,ba ɓata lokaci aka fara bata taimako cikin gaugawa. Tunda suka shiga da ita Mama sai safa da marwa takeyi a harabar hospital. Marwan Mama tasa yakira Abban su yafaɗa masa abunda ake ciki,kana yaje gida ya ɗauko mata hijab ɗinta. Tare suka shigo da Abba hijab ɗinta Marwan ya bata tasaka Abba yace, "ina suka kwantar da ita?". Jikin Mama sai rawa yake tace, "Abban su har yanzu basu fito ba"....tun bata kai da ƙarasa maganar ba sai ga doctor yafito daga cikin ɗakin. Da sauri Abba da Mama suka zo wajan sa. Tambayar su ya yi ko su suka kawo Hafsat? sai Abba yace, "eh". Magana doctor ya yi musu yace su biyushi office. Bayan ya shiga office ya zauna suma suka shigo kallon su ya yi yace, "wanene mijin ta ?". Kallon-kallon suka fara tsakanin Mama da Abba. Sai Abba ya buɗe baki yace, "bata da miji mune dai iyayen ta". Doctor kallon Abba ya yi sosai kana ya nuna masa kujera yace ya zauna. Bayan ya zauna sai doctor ya kai duban sa ga Mama yace, "kefa miye matsayinki a wajanta?"...... tin kan Mama tayi magana sai Abba yace, "mahaifiyar tace". kujere doctor ya nuna mata yace ta zauna. Bayan ta zauna sai doctor yace, "ba abinda zan ɓoye muku gaskiya,muyi nasarar tsayar da jinin da yafara fita jikin ta,amma cikin da ke jikin ta nanan bai fita ba.....tun kan ya kai ƙarshen zanci sai Mama tace, "a'a ba ƴata baca ka duba danni ƴata bata da ciki ka da kayi mata sharri" magana Mama keyi amma gabiki ɗaya bata cikin natsuwar ta. Abba yace, "ka da kisa ke magana ki bari muji me doctor zai ce". Abba kallon doctor ya yi yace "inajinka". Doctor yace, "iya bin ciken da mukayi mata, munganu tana ɗauke da ciki har na tsawon wata huɗu, kuma cikin na gab da zubewa saboda irin yadda ....bai ƙarasa zancin ba saboda da nauyi maganar da zai faɗa, ya faɗa musu ko yanzu saduwar da ya yi da ita ne yajamata wannan ciyo sai yaƙi faɗa yace, amma yanzu tasamu sauki dan har barci ta samu sai zuwa ku san awa huɗu zata farka saboda mun mata allura bacci. Yana kai ƙarshin zancin Abba ya sauke wata ajiyar zuciya haɗi da goge ƙwallar da ta zubo masa yace , "to doctor muna godiya". Sai Mama tace, "yanzu Abbansu har ka yarda Hafsat na ɗauke da ciki?wallahi nikam ban yarda ba dan nasan ba halin ƴata bane" magana takeyi amma kamar zata faɗi. Doctor ya dube ta bayan yaba Abba ta kardar maganin da za'a sayo mata yace da Mama "zaki iya gane ƴar taki idan kin ganta?". Tace "sosai kuwa". Sai yace, "zo muje kiga ko ita ce" yana faɗin haka ya tashi ya kaisu ɗakin da aka kai ta. Suna shiga gadon da take kwance ya nuna mata yace, "gata ko ba ita bace?". Kallon Hafsat Mama keyi wadda ke kwance tana barci bata masan abunda akeyi ba. Gaban gadon Mama ta ƙaraso tace, "Hafsat! Hafsat! mi ki ka rasa wanda bamuyi miki ba,ci ki ka rasa ko sha? ! ki gayamin miyasa zaki sakamin da haka Hafsat!, kinsan aure kikeso meyasa bazaki gayamin ba" . tana magana tana wani kuka mai ban tausai. Alamun zata faɗine Abba yagani dan haka da saure ya tare ta ta faɗu jikin sa sume.... ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba lokaci ɗaya jikin sa ya yi sanyi yama rasa me zaiyi. Doctor ne yakira wasu nurse suka ɗauke ta aka ɗura ta kan godon yafara dubata. Cikin lokaci kaɗan ta farfaɗo. Sunan Abba ta fara kira,doctor yasa aka kirashi,yana zuwa yafita dan yaga ba komai ne ke damun taba sai ruɗuwar da tashiga. Jikin Abba tafaɗa tana kuka tace, "ka ga abunda Hafsat tayi muna yau mu zata saka ma da ciki kuma ko ciki na shege! ". ajiyar zuciya Abba ya sauke kana yace, "ta dai yi ma kanta, dan haka ki rage sa damu wa aranki,kuma ki tashi mu koma gida idan tafarka gasu Marwan nan su dawo tare". Sai Mama tace, "da ka barni idan ta farka mu dawo tare sai kuje kai da su Marwan......tun bata kai ƙarshen zancin ba ya daga mata wata irin tsawar da yasa ta sauka daga gadon bata shirya ba. komai bai ce da itaba ya kama hanyar fita ya barta. Itama tana ganin yafita ta bi bayan sa. Waje suka tarar da Ammar da Marwan suka ce sujira idan Aunty su ta farka su dawo gida tare. Haka kuwa akayi tana cika awa huɗu ta farka. Dubi- dubi tafarayi Marwan da Ammar tagani sunyi tagumin kamar sun san mike faruwa. Ammar ne ya kula da farka warta dan haka da sauri ya ƙaraso gare ta yace, "Aunty ya jikin naki?". Da sauki tace dashi kana tace, "Ammar ina Mama?". Yace, "ta koma gida ita da Abba". Yana faɗa mata haka wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncin ta sabida tasan yanzu kowa yasan tana da ciki. Lokaci ɗaya tafara rera kuka mai ƙunar zuciya tana faɗin, "Ammar kada kugujeni wallahi nima ƙaddara ce ta afka kaina ni kaɗai nasan me nakeji gami dashi,duk duniya banajin abunda nakeji da shi ga kowa sai gareshi dan Allah ƴan uwana kutayani da addua, dan wallahi ina cikin wani hali". Sosai ta baso tausayi duk da su kansu basu san me ake ciki ba. Duk da Abba yace kada su kwana komai dare su dawo amma basu gaya mata ba sukayi kwanciyar su har safiya ta waye. kuma basu fito ba sai da doctor ya dubata ya rabuta mata magani Marwan yaje ya sayo haɗi da kayan beark bayan tayi beark tasha magani suka kamu hanyar zuwa gida. Abba da Mama ba wanda ya samu bacci a ckin su kowa nin su tunani abunda ƴarsu wadda suka fi so a duniya ta aikata ya keyi Tun cin dare yake zuba ido amma basu dawo ba,dan haka ko da akayi kiran sallah asuba yaje masallaci ana gama sallah ya dawo . Bai jima da dawo ba sai gasu sun dawo. Sallama sukayi bayan Abba ya ƙarɓa suka wuce suka zauna. Komai Abba bai ce dasu ba kuma suma basuyi masa magana ba saboda ba suga wurin yi masa magana ba, dan fuskar sa haɗe take. Kallon sa ya maida ga Ammar kana yace, "je ka kiramin Safiyya". Tashi Ammar ya yi yafice yaje kiran Safiyya. Mama na fitowa ɗaki bata ce da kowa kamai ba ta fara dukan Hafsat tana faɗin kin ci amana ta Hafsat mikika rasa tana faɗa tana dukanta iya ƙarfin ta. Tashi takeso tayi dan ta gudu amma takasa saboda bata da wani ƙarfin jiki. Abba na kallo amma ya yi kamar bai san abbun da ke faruwa ba. Wani ice Mama ta raramo dan ta bugama Hafsat aikuwa da sauri Marwan ya riƙe yana kuka yana faɗin, "dan Allah Mama kirabu da ita me ta muku ki ka dukan ta, ki dakeni mada-din ta ko lafiya fa bata da komai tayi kuyi mata uzuri mana". Tun bai kai ƙarshen zan cin ba Mama ta ki feshi da mari har sau biyu. Abba ne ya yi magana yace "ta ƙyalesu kada ta koma magana ta barshi da su. Anacikin haka sai ga Ammar da Safiyya sun zo tare....... Nagaji🤦‍♀ *#Vote Comment Shere* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad Summy M Na'ige~ *SHAFI NA 11📑* *__________📖* Bayan ta ƙaraso ta gaishe da Abba da Mama amma kowa bai samu damar karɓa mata ba sai ma tambayar da suka jefa mata. Abba yace, "Safiyya ashe kin san halin da ƴar uwarki ta ke ciki amma ki ka kasa faɗa mana?". Tace, "wani hali Abba....! Ai bata kai ga k'arasawa ba ya da ka mata tsawa haɗi da faɗin. "Ki bani amsar tambayar dana miki?". Jikin ta na karkarwa tace, "Abba kayi haƙuri amma ni ban san wane hali take ciki ba". Mama ce tace mata, "baki san tana ɗauke da ciki ba ne". Aikuwa Mama na rufe bakin ta, Safiyya ta fashe da kuka mai tab'a zuciya kana tace. "Wallah Mama ban sani ba". ta na faɗa tana kuka. Abba ne yace, "Ba komai Safiyya kuma ina fatan baki biyema halin taba?kuma daga yau nara baki da ita ka da ta koya miki mugun halin ta, kuma ki sani wallahi bazaki zauna min a gida da wannan ciki ba, dan haka ki tattara kayanki ki koma wurin wanda ya yi miki ciki na bar masa ke har abada, dan wallahi daga yau na cireki daga cikin zuri'a ta, kuma bari kiji minti biyar na baki ki tashi ki barmin gidana ko na illataki" . yana faɗin haka ya shigewar sa ɗakin sa. Kuka mai tsanani Hafsat keyi kamar ranta zai fita,rasa bakin magana tayi dan gabaki ɗaya kalaman sa sunyi mata tsauri. Ko Mama abunda Abba yace yayi mata zafi kuma tasan tunda ya furta to ba abinda zai canja,dan haka taja bakin ta ta kulle amma zuciyar ta na mata zafi. Safiyya najin abinda Abban Hafsat yace dan haka da gudu taje gida su ta zo da Baban ta. Tace masa ga Abban Hafsat can ya kore Hafsat. Safiyya na fita sai ga Abban Hafsat ya fito a ɗakin sa,kallon Hafsat yayi haɗi da antaya mata harara kana yace, "bazaki tashi ki barmin gidana ba?". Kafin tayi magana Marwan da Ammar suka fara bashi haƙuri,magana yafara musu cikin faɗa yace, "bari ma kuji wallahi duk a cikin ku duk wanda ya taimaka mata ko da bayan idona ne to banyafe ba". sai Mama tace, "a'a ka dai ce ta bar maka gidanka amma ba ruwanka tsakanin ta da ƴan wuna ta, kuma tabar maka gida taje ina Abbansu?, komai zakayi yana da kyau ka dubi gaba dan komu muna da namu laifi....kafin ta rufe bakin ta ya daka mata tsawar da tasa tayi shuru bata shirya ba. Duban sa ya kai ga Hafsat yace,"ki tashi kibarmin gidana kafin nasa afitar dake". Ahankali ta tashi ta fara tafiya har ta kai ɗakin ta,kayan ta ta haɗa gabaki ɗaya ta fito tana kuka mai cin zuciya,kallon ta Mama tayi tace, "kinga abinda kika jama kanki kika kuma jamin dan haka......Abba ne yafito yace Mama tayi masa shuru kana ya dube Hafsat yace, "fita ki barmin gidana" yana faɗa yana nuna mata ƙofar fita. Kuka take kamar ranta zai fita, ta kama hanyar fita Mama ta dube Abba tace, "yanzu barin ta zamyi ta tafi? to ina zata je?". Sai Abba yace, "tafiki sanin inda zata je" yana kawai nan ya koma cikin ɗakin sa. Gabaki ɗaya kannen ta kuka suke lokacin da zata fita,har ta kawo bakin ƙofa sai ga Safiyya da Baba ta sun ƙaraso da sauri Safiyya ta ƙarasa wajanta tana faɗin, "ina zakije haka da kaya?". Tace, "Abba ya koreni yace na bar masa gidan sa,...Baban Safiyya ne ya katse musu magana yace Safiyya taje ta kiramasa Baban Hafsat. Shiga tayi tafaɗa masa ba jimawa ya fito fuskarsa haɗe ba alamar fara'a. Bayan sun gaisa da Abban Safiyya sai Baban safiyya ya faɗa masa abunda Safiyya tafaɗa masa tace ya kore Hafsat shin ko gaskiya ne?. Bayanin da Safiyya tayi masa to shi Abban Hafsat yayi masa kana yace, "wallah bazata zauna gidana da cikiba,Alhaji Abbakar minene banyi ma Hafsat da har zata saka min da cikin, wallah bari gaji yanzu ko ganin ta bana sonyi, gabaki ɗaya Abban Hafsat ya rikice duk yadda Baban Safiyya yaso yayi haƙuri Abban Hafsat yaƙi,kunsan abu ga mai haƙuri idan ya tashi bai iya ba. Da Baban Safiyya yaga Abban Hafsat yaƙi haƙuri sai yace, "tunda kace bazata zauna gidan kaba to ni zan ɗau Hafsat ta zauna gidana har nayi mata aure.....tun bai kai da rufe bakin shiba sai Abban Hafsat yace, "kada kasoma kace zaka haɗeta da ɗiyan ka dan zata lalata musu tarbiya". Sai Baban Safiyya yace, "naji kuma na ɗauka Allah ya shirya min su gabaki ɗaya" rigima sukayi sosai da Baban Safiyya kafin su rabu. Baban Safiyya nafitowa falon Abba dube su Hafsat yayi yace,"ko zo muje gida" yana faɗin haka ya kama hanyar gida sa ranshi a ɓace. Suna isa gidan su Safiyya sai Baban Safiya ya kira Ummar Safiyya ya faɗa mata abunda ake ciki kuma ya shaida mata cewa Hafsat nan gidan zata ci gaba da zama har Allah ya sauke ta lafiya kuma ya kawo mata mijin aure. Aikuwa Ummar Safiyya najin ace Hafsat zata dawo gidan da zama ta fara kumfar baki tana faɗi, "itakam gaskiya baza'a kawo mata Hafsat a gida ba salon tazo ta lalata mata tarbiyar yara,wallah bazata yarda ba" sai da ta kai ƙarshin zanci sai Baban Safiyya yace, "wallahi ba wanda ya isa ya hana Hafsat zama ana gidan, nan ya dinga ci mata mutunci har yace idan tasake cewa Hafsat bazata zauna gidan ba bakin auren ta,ba shiri ta kama bakin ta,Safiyya yace da ita suje ɗakin ta su cigaba da zama ita da Hafsat,ba musu suka je ɗakin. Bayan kwana biyu da faruwar haka gabaki ɗaya Hafsat bata da natsuwa, gashi ko fita batayi kuma ko takira shi a waya baya ɗauka. Kuma yanzu ko barci take mafarkinsa take, ko me taki tunanin sa take, gabaki ɗaya ta koma wata iri gashi Ummar Safiyya da ƙannen ta har ma da yayun ta duk sun tsane ta abu ka ɗan sai Ummar Safiyya ta dinga yimata faɗa, sosai abun ke ɓata mata rai amma sai ta dake ma zuciyar ta saboda irin yadda Safiyya da Baban ta ke nuna mata amma daba dan suba da tuni ta bar gidan . Yau ma kamar haka suna kwance da dare dan har bacci ya ɗauke su tana cikin bacci taji kamar antsaƙure ta,da sauri ta zabura ta tashi,komai bata gani ba, lokaci ɗaya taji tana son taji koda muryar sa ce dan haka ta ɗau waya ta kira koda Allah zai sa ta samu. Missed call biyar tamasa amma bai ɗauka ba,har taso ta aje wayar ta kwanta sai tace bari ta koma kira,aikuwa tana kira ringing da bai wuce uku ba ya ɗaga tare da faɗi, "wake magana?". Toilet ɗin dake ɗakin ta shige kana tace, "Hayat nice fa,baka ganeni ba?". Yace, "oh nagane shin kece?lafiya dai ko?". Tace, "eh kodama nakirane naji ko lafiya kake?". Yace, "eh ƙalau nake"...har zai katse kiran tace Hayat kayi haƙuri nasan ko dan mi kake fushi dani amma in har nasamu fita zan zo dan nayi missing ɗinka sosai, kuma kayi haƙuri ka yafemin idan na ɓatama"......tana faɗi tana fitar da ƙwalla. Gajiya yayi da surutun ta dan haka ya datse kiran batari da yaji sauran zancin ba,daga baya ta lura da ya kashe wayar dan haka taci gaba da kuka dan gani take kamar ta aikata babban laifi fushin da ya keyi da ita. Washi gari baya sungama aikin su na gida ita da Safiyya sai Mamar Safiyya ta shirya tafita unguwa ta barta daga ita sai Safiyya tace sai ta dawo. Fitar ta ba da jimawa ba Safiyya ta kwanta barcin rana,aikuwa Hafsat naganin haka taje tayi wanka ta shirya cikin hanzari ta bar gidan, tana fita ta tsayar da mai napep ,basu tsaya ko ina ba sai gidan sa, kuɗi da suka rage mata taba mai napep kana ta shiga gidan. Parlour tasame shi yana waya, da sauri ta ƙarasa jikin sa tana faɗi, "Missing you Hayatee nah". Yana jinta jikinsa ya ɗago ya kalle ta haɗe da katsi wayar da yakeyi, dan jinta kawai yayi dan har taso ta bashi tsoro,har ya buɗe baki yayi magana ta haɗe bakin ta danashi tana kissing ďinshi kamar tasamu lolipop,lokaci ɗaya ya fara karɓar saƙon da take aika masa, martani yafara mai dama ta sannan yafara ƙoƙarin rage mata kayan jikin ta, bayan ya cire mata ya fara romance ɗinta son ranshi,daukar ta yayi ya kai bedroom ďinsa daga can yafara sarrafata yadda yake so,dan kowane buƙace yake da wani. Sosai hankalin Safiyya ya tashi, lokacin da ta farka bataga Hafsat ba dan ta ɗauka ko guduwa ne tayi sabida abinda mamar take mata,sai da taga kayan ta hankalin ta ya ɗan kwanta. Tunani tafarayi to ina Hafsat ta tafi ne tasan ba gidan su tajeba . Shiko ya samu jaka sai yadda yaso yakeyi da ita,tagaji iya gajiya amma takasa buɗe baki tace ta gaji,sai da ya gaji dan kansa sannan ya barta. Sai da suka ɗan huta ta ƙara shigewa jikin sa,a hankali ta buɗa baki ta fara faɗa mishi abinda ya faru da ita,sannan ta ƙara da cewa, "Hayat ko na ɗauko kayana na dawo nan da zama zan fi samun natsuwa bisa ga inda nake". Sai da ya kalle ta kana yace, "a'a kada ki dawo dan nima ko wata bazanyi garin nan ba zan koma garin mu dan nagama aikin dana zo yi". Kuka ta fara masa wai zata bishi garin su,bai kulata ba yaci gaba da abinda yake so da ita. Roƙon sa tayi ya barta taje gida amma yayi kamar bai jita ba,sai can yace taje ɗin kuma gobe ta dawo. Wanka kawa tayi ta sanya kayan ta tafito,roƙon sa tayi ya bata ƙuɗi ta hau napep,sai da yagama jamata aji kana ya ɗauko dubu ɗaya ya bata yace taje Taci sa'a koda ta dawo mamar Safiyya bata dawo ba Safiyya kadai ta isake a tsakar gida tana safa da marwa. Kallon ta Safiyya tayi tace, "daga ina kika fito?". Bata karɓa mata ba ta shige ɗaki ta barta tsaye,ɗikin Safiyya tabi ta tace, "dake nake magana kinyi min shuru" sai Hafsat tace, "mi zance miki to, fita nayi ko so kike na faɗamiki inda naje,to ba aikina kikayi ba bare na faɗa miki" tana magana tana antaya mata harara Komai Safiyya bata sake cewa da itaba dan tasan ba ida taje sai gidan shegen saurayin ta kuma ta ɗau alwashin sai ta ci mutunci sa duk ranar da ta ganshi. Ko da dare yaya ba wanda yayi ma ɗan wunsa magana har suka zo kwanciya ,Hafsat a tunanin ta Safiyya bacci take dan haka ta ɗau waya ta kirashi,bayan ya ɗauka ta gasheshi to fa nan suka cigaba da fira amma mafi yawan firarsu ta batsa ce,hirar ce ta dame Safiyya wai a ce ƴar uwar ta ke wannan firar dan haka ta farar kuka har da shisheka, kukan Safiyya da Hafsat taji ne yasa tayi sauri ta katse wayar kana tace, "Safiyya lafiya kike kuka?". Kyaleta Safiyya tayi dan abin nan na Hafsat yanzu tsoro yake bata, a ce har mutum yayi sanadiyar barin ka gidan iyayenka amma ka kasa barishi wannan wani irin so ne,tana kuka tana tunani cikin zuciyar. Jin da tayi Stuna in bata amsa mata ba yasa ta ƙaraso wajan ta hawayen da suka Zuni matane ta goge tace, "My Safiyya kiyi haƙuri nasan dan kinji wayar danakeyi ne kike kuka,wallahi Safiyya koni zuciya ta na ƙuna abinda nakeyi dashi amma ya zanyi dan wallahi bani da natsuwa duk banji shiba ko bantare dashi ba, nidai abinda nake so dake kiyi min addu'a kada na mutum ina cikin wannan hali kinji ƴar wuta". Jikin ta Hafsat ta faɗa gabaki ɗayan su kuka suke mai ciki da kunar rai. Haka Hafsat taci gaba da zama gidan su Safiyya har aka kuma hutun makarantar su amma duk ranar da tasamu damar fita sai taje wajansa,itako yanzu Safiyya da dare yayi take tashi kuma ta tashe da Hafsat suyi alwala sufara nafil-fili suna kai kukan su ga Allah. Kuma cikin ikon Allah yanzu Hafsat tarege jin soshi a zuciyar ta sosai. Bayan sun koma makaran ta da kwana biyu ranar Safiyya na zaune class ɗinsu sai ga wata ƙawar ta tazo wajan ta kuma ƙawa ga Hajara dan abinda yasa Safiyya ta barta saboda taga ko ina Hajara take itama tana can danshi ta bar ta... *#VOTE COMMENT SHARE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~Wattpad Summy M Na'ige~ *SHAFI NA 12📑* *__________📖* Bayan sun gaisa sai ƙawar ta Ummi tace,"ina Hafsat kwana biyu na daina ganin ta?". Sai Safiyya tace, "tana nan lafiya". Sai Ummi tace, "ki ce dai da dama,wace lafiya ne da ita tana ɗauke da ciki". Sai Safiyya ta haɗe fuska kana tace, "wani ciki?" tana faɗa ta na hararar ta. Sai Ummi tace, "Safiyya bari kiji wallahi ba abinda zaki ɓoye min gami da Hafsat wanda ban sani ba, tun farkon haɗuwar ta da Anwar har cikin da ya yi mata ba wanda ban sani ba,ni dai shawara zan baki dan na ga irin cin zarafin da yakema Hafsat ya yi yawa, shiyasa na yanke shawar na zo na faɗa miki abinda ake ciki dan ki nema mata mafita,amma idan zaki saurare ni, dan nasan haliki na rashin kulani shiyasa tun wancan lokacin ban faɗa miki ba amma mikika ce zaki saurareni ko ya ya?". Murmushi Safiyya tayi mai ciyo kana tace, "ina jinki ki faɗa min". Sai Ummi tace, "komai na faɗa miki kiyi haƙuri dan na san zakiji zafi sosai". "Kifaɗa ina jinki"....tafaɗa haka ataƙaice. Sai da Ummi ta numfasa kana tace, "zaki iya tuna lokacin da Hafsat ta samu saɓani da Anwar? har ta ji ko ganin sa bata sonyi,to ba komai bane ya kawo haka sai rabata da mutuncinta na ƴa mace da ya yi, ta hanyar samata maganin da zai gusar da hankalin ta,ita ko tundaga lokacin ta daina kulashi,ince ma har wajanki ya zo amma ki ka kasa shawo masa kan Hafsat,to da yaga yaki samun nasara gareku sai yaje gun Hajara ya faɗa mata abinda ya ke so tayi masa,ita ko Hajara da son kuɗi tace zatayi masa,to fa tundaga lokacin Hajara tafara bibiyar Hafsat har tasamu ta fara kulata har tayi nasarar rabaki da ita, to fa lokaci ne Hajara ta fara yimata magiya kan ta yarda su shirya da Anwar amma Hafsat taƙi,to da Hajara taga Hafsat ta faye kafiya sai kawai ta kaita wajan wani malami ta faɗa masa abinda ta ke so ya yi mata,bayan ya yi mata aikin da zai sa ta yarda da Anwar, kuma duk abunda yasa ta bazatayi masa musu ba,anyi kuma aiki yaci dan komai sai Anwar yace Hafsat keyi takeyi , koda kowa uwar ta ce tace tayi in har Anwar bai yadda ba bazatayi ba,ya maida ta kamar matar sa, sai yadda yaso yakeyi da ita kuma ba wai dan baya son ta bane a'a yana son ta sosai sai dai yanzu yace bazai iya auren taba saboda taki yarda azubar da ciki,dan haka nake son kije ki nemar mata makarin abinda sukayi mata ko zata samu sauƙin abunda ke damunta". Hawaye masu zafi ke fita daga idon Safiyya,kallon Ummi tayi tace, "yanzu Ummi kin san komai amma ki ka kasa sanar dani,ashe ba son Allah kikemin ba, dan da son Allah kikemin da kin faɗamin abinda kika sani gami da ƴar uwata". Ummi tace, "kiyi hak'uri Safiyya wallahi koni ban sani ba sai daga baya,saboda yanzu ita Hajara ta kamu da son Anwar kamar ta mutu shiko yace ko zaman bariki ba zai iyayi da ita ba, bare har ta kai ga aure,to lokacin ne Hajara ke bani labarin yadda ta yi sanadiyar soyayyar su da Hafsat". Kuma wallah na san yanzu ko kashe Hafsat Hajara na iyayi akan Anwar,dan haka ku ɗau mataki" ...tana faɗa tana tashi tace, 'Kinga tafiya ta dama nazo ne na faɗamiki saboda har gobe kina matsayin masoyiya ta, dan haka sai anjima".....tana faɗa tana tafiya. Magana Safiya take so tayi mata amma saboda biƙin ciki kasa buɗe baki tayi sai kukan da takeyi kamar ranta zai fita. Ko lecture basu gama ba Safiyya taje wajan Hafsat tace tazo suje gida. Hafsat tambayar Safiyya lafiya za su je gida kuma gashi ko locture basu gama ba,Safiyya nuna mata tayi suje gida dan ita ko natsuwa ba ta da , ita ko Hafsat ta kafe bazata jeba,kuka Safiyya ta sanya ma Hafsat tana faɗin sai sunje,kukan da Safiyya ke yi ne ya sa Hafsat jikin ta ya yi sanyi ta yarda zata bita suje gida amma ba dan ranta yaso ba, dan taso Safiyya ta tafi ta barta dan ta naso idan tagama lecture taje gidan Anwar. Bayan sun fita school ďin suka tsayar da mai napep Safiyya tagaya masa sunan unguwar da zai kaisu,kallon ta Hafsat tayi kana tace, "ina zamuje ne?". Safiyya batayi mata magana ba har suka kai inda zasuje. Bayan sun sallame mai napep kana suka shiga wani gida da sallamar su,bayan an karɓa musu,suka gaida wata tshowa, bayan ta karɓa sai Safiyya tace, "lnna ina Malam?Allah dai kasa baiyi nisaba?". Sai wadda ake kira da lnna tace, "a'a yana ɗakinsa,mikika kawo masa dakike neman sa". Bata bata amsaba ta wuce ɗakin malam. Bayan sun gaisa da Malam tayi masa bayani abinda ya kawo ta gami da Hafsat,tana masa bayani tana kuka,sai Malam yace, "ki daina kuka Safiyya,insha Allah komai yazo ƙarshe". Magani ya haɗa mata dana hayaƙi dana sha harda na wanka ya bata zaitun da habba yace ta rinka shafawa duk lokacin da tayi wanka. Godiya tayi masa sosai sannan ya tambayeta Mamar ta tace lafiya ƙalau suke. Har za su fito daga gidan Malam ya ɗauko husunul musulim ya basu ita da Hafsat yace ko wace safiya surinƙa karatunsa,kana yayi musu faɗan da suriƙa addu'o i nema kariya ako wace rana. Sallama sukayi masa kana suka wuce gida. Tundaga lokacin suka cika gaba da yimata magani ba dare ba rana, kuma duk abin nan da ake Mamar Safiyya bata san mike faruwa ba,duk da iyayenta ne ke ba Hafsat magani amma bai sa tasani ba. Kuma cikin ikon Allah yanzu abin yayi ma Hafsat sauƙi sosai, dan yanzu har kiran ta yake amma ba ko da yaushe take ɗauka ba kuma yanzu so ya ke tazo suyi bankwana dan satin nan zai koma gida..... *#Vote* *comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 1📑* *__________📖* *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* *SADAUKARWA GA:-* *GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 13📑* *__________📖* Ko yau suna zaune a ɗakin su ita da Safiyya suna fira sai wayar ta tafara ringing,duba saman secreen ɗin wayar tayi,Hayateenah taga ya bayyana,da sauri ta datse kiran kana ta kashe wayar gabaki ɗaya. Kallon ta Safiyya tayi tace,"hala waya kira ki ka datse kiran?". Sai da taya tsane fuska kana tace, "Anwar ne yake dumuna da kira,amma na san maganin sa gobe ko yakira ba zai samu ba". Har Safiyya ta buɗe baki tayi magana sai suka ji Mamar Safiyya na ƙwala musu kira. Da sauri Hafsat tace "ga Mama can na kiran mu ki tashi muje".......tana faɗa tana tashi tsaye. Suna ƙarasowa sai da Mama tayi ma Hafsat wani kallo kana tace, "ga wankin yara can ki ɗauka kiyi har da na Yayan su dan shima ya ce ki wanke masa kayan sa,kuma saura kada ki wanke ya fita". Tace' "tau Mama zanyi da kyau". Duban ta ta maida ga Safiyya kana tace,"ke ko je ki shirya zan aikeki gidan su lnna"....mahaifiyar Mamar Safiyya kenan. Tace, "tau Mama bari mu ɗan rage wankin nan sai natafi". Ai tun Safiyya bata kai da rufe bakin taba Mama ta daka mata tsawa wadda bashiri ta rufe bakin ta. Hafsat tafiya tayi wajan tulin wankin da ke zobe a ƙasa ta ɗauko ta kai bakin fanfo ta ɗauko kujera dan ta zauna dan yanzu bata iya wani dogon duƙe,aikuwa tun ba takai da zama ba Mama ta daka mata tsawa tari da faɗin, "kada ki zauna kiyi shi a haka,salon ki zauna kiyi min wankin da bai fita ba?". Sai da Hafsat ta goge hawayen da suka zuba a idon ta kana tace, "wallahi Mama bana iya duƙi sai naji marata ta kulle, dan Allah ki bari na zauna zan fi jin daɗi....ai tun bata rufe bakin ta ba sai ga Abbas Yayan Safiyya ya fito daga ɗakin sa yana faɗin, "Oh Mama ce zata faɗa kina faɗa?dan baki da kirki baki da tarbiya,ashe rashin tarbiyarki ba wajan bin maza ta tsaya ba harda ciwa manya mutun ci?". Safiyya na ɗakin su taji duk abinda ke faruwa har lokaci da yayan ta kema Hafsat faɗa,abinda taji ya faɗane yayi mugun ƙona mata rai dan haka bata san lokacin da ta fito ba. Cikin hanzari tafito d'akin su tana faɗin, "wallahi Yaya kaima baka wuce k'addar da tasame Hafsat ba, da har zaka buɗa baki kayi mata faɗe....... ba ta kai da rufe bakin ta ba taji saukar mari har guda biyu wannda ya gi-gita ta lokaci ɗaya.. Ba ta kai da dawowa hayyacin taba tafara jin saukar duka ta kowane fanni na jikin ta. Dukan ta yake yana faɗin, "ni zan faɗa kina faɗa ehh?". Ilata ta taga zayi dan haka da gudu ta yi hanyar d'akin su. Tana shiga ta kulle ɗaki kana taci gaba da kuka tana mai tausayawa Hafsat. Koda yaje d'akin yaga ta kulle dan haka ya dawo wajan Hafsat,ita ko tunda taga abinda yayiwa Safiyya ta duk'a haka nan ta fara wanki tana jin ba daɗi ajikin ta. kallon ta yayi yace, "wallahi minti kad'an nabaki ki kammala Kuma duk basu fita ba hmmmmm Allah kad'ai zai karb'arki a gidan nan"......yana fad'a yana ficewa a gidan gabaki d'aya. Haka nan Hafsat taci gaba da wanki tanayi tana share hawaye,sosai ta wahala kafin ta kammala,kuma tana kammalawa Mama ta hadata da wanki-wanke da shara da aikin abin ci,aikuwa tana kammalawa sai zazzab'i ya rufeta,sai da Safiyya ta lallab'a taje wani pharmacy ta karb'o mata magani. Haka dai ta kwana a wannan ranar wahalce. ****** Yau Monday rana school ce kuma babbar rana ce ga y'an makaranta kowa ne ɗan makaranta burinshi yaga ya isa cikin school d'insu cikin lokaci. Safiyya ce tafito daga d'akin su ta same Hafsat kichen tace, "Hafsat wai mekikeyi a kichen kuma kinsan muna da lecture k'arfe ta kwas kuma yanzu 8:30 gashi ko shiri bakiyi ba,to har yaushe zamu kai school d'in?". Tace, "kiyi hak'uri Safiyya wallahi Mama ce tasani d'aurama yaran can ruwan wanka kuma gashi wutar ma tak'i ru-ruwa". Sai Safiyya tace, "kitashi kije ki shirya sai na k'arasa kafin ki fito sunyi zafi". Tace, "tau Safiyya"..... tana faɗa tana tashi. Har zata shiga ban d'aki ta watsa ruwa sai ga Mama ta fito daga d'akin ta. Magana ta fara mata cikin faɗa-fad'a "me zakiyi a ban d'aki? ba aiki nasaki ba ne?". Har zatayi magana sai ga Baban Safiyya ya shigo gidan. Kallon Mama yayi da Hafsat dake tsaye yace, "lafiya na ganko haka cirko-cirko?". Sai Mama tace, "aki nasakata shine taki tayi min". Sai Baba yace, "amma kin san yanzu lokacin makaranta ne kuma zaki sata aki salon su makara,to bawani aikin da zatayi sai tadawo makaranta"......yana fad'in haka yace Hafsata tayi sauri ta shirya su wuce makaranta. A gurguje ta shirya dan ko beark bata yiba suka Kama hanyar school d'insu. Takwas saura minti biyar suka isa makaranta,kai tsaye kowa class ɗin su ya wuce, aikuwa bata jima da shiga ba sai ga malamin su yashigo dumin su fara karatu. Basu jima da fara karatu ba sai ga sak'o yazo daga office d'in sugaban makaranta, bayan d'an sak'on yayiwa Malamin bayanin abinda aka aikoshi na kiran d'aliban da aka umarce shi,malamin ya bada izinin a kira su,nan kowa ya fara kiran su,kuma daga cikin su Harda Hafsat a ka kira. Bayan ankira sunan su aka umarce su da suje office d'in sugaban makaranta acan ake neman su. Aikuwa ana faɗin haka gaban Hafsat yayi mummunar fad'uwa, lokaci d'aya wasu hawaye suka fara zoba a idon ta,tunani tafarayi ko korar ta za'ayi sabida batayi jarabawa ba ko sunji labarin tayi cikin shege ne?aikuwa tana kawowa nan a tunanin ta fashe da kuka mai k'unar zuciya, kuma gashi ba mace a cikin wad'an da aka kira dukan su maza ne bare ta samu sauk'in abinda take ji. Haka taci gaba da biyar su har suka kai office d'in sugaban makaranta. Gaban tane ya ba da dummmm lokacin da za su shiga offece ɗin,amma ta dake ma ranta had'i da addu'a kana ta shiga. Office d'in cike yake da malamai har ma da waɗan da ba malaman makarantar ba,sukuwa d'alibai wanɗa da aka kira suna gyefe d'aya suna jiran a fad'a musu abinda yasa ake kiran su,ma fi yawan su maza ne,dan mata ba su wuce uku ba,wajan da mata suke ita ma nan tazo ta tsaya. Bayan zowan su da mintuna ƙalilan sai shugaban makaranta ya fara jawa bi. Bayan ya kammala abinda zai ce kana ya mai da duban sa ga d'aliban da suke tsaye yace, "ba komai yasa muka taraku anan ba,sai dan wani abin farin ciki da ya samemu Kuma ya same ku,amma ga wanda yaji yana so ko iyayen shi za subar shi,Wannan abin farin cikin shine gwamnati ce ta ba da scholarship ga ɗalibbai mafi hazaƙa kuma waɗan suka ci jarabawa, suje k'asa she daban-daban suyo karatun master,amma bamu ce dole sai kaje ba, a'a in kana da ra'ayi kuma iyayen ka za su barka to muna maka barka da zowa,Inma baka da ra'ayi ba komai sai kafad'a asa musu son zowa". "Dan ko wane department zamu d'au mutum biyar mafi ƙwazo a cikin su, kuma waɗan da suka ci wannan jarabawar da ta gudana, amma idan kin san,ko kasan, baza kaje ba ko ba'aza a barka ba to ku faɗamuna,dan haka mun baku kwana uku kuje koyi shawara da iyayen ku sai kozo ku gaya muna dan bama son lokaci ya kule,dan gabaki daya wannan ta fiyar ba zata wuce sati uku ba insha Allah". Hafsat najin wannan maganar ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya,saboda jin daɗi har da 'yar kwalla ta fitar. Har suka fara fita bata sani ba saboda ta tafi duniyar tunani. Wadda ke kusa da ita ta dan ta ɓata sannan ta san me ake ciki. Da fitowar su cikin office ɗin,cikin zomud'i taje class ɗin su Safiyya dan ta faɗa mata abinda a ke ciki. Da zowan ta bata tsaya komai ba ta fad'a jikin Safiyya dan ita har ta manta abinda take d'auke dashi sai da Safiyya tayi mata magana a tsorace tace, "Hafsat! baki gudun kijima kanki ciyo ne?". Ba sarwa tayi kana tace, "My Sufy tashi kiji wani abin farin ciki da ya sameni,yanzu aka aiko kiran mu a office d'in sugaban makaranta, wallahi na d'auka korana za'ayi dan kin san banyi exmas ba,kinga yadda gabana ke famar dukan uku-uku wallahi har k'walla sai da ta zobo min kafin muje,ashe ba kurana za'ayi ba...... nan ta faɗa mata abinda ya wakana,sosai Safiyya tayi murna dajin har da masoyiyar ta cikin wand'an da zasuje waje suyi karatun master,murna da farin ciki wajan Safiyya ba'ace wa komai dan kamar ma tafi Hafsat jin dad'in abin. Suna gama lecture basu tsaya b'ata lokaci ba suka wuce gida dan su faɗi abin farin ciki da yasa mesu. Koda sukaje Mamar Safiya tafita unguwa dan haka suka cigaba da aikin su inyaso da tadawo su faɗa mata. Sai bayan isha'i tadawo kuma ko da tashigo suna sallah,dan haka kai tsaye ta wuce ɗakin ta. Bajimawa da shigar ta sai suka ji sallamar Baban Safiyya,dan haka da sauri Safiyya taje ta shin fiɗa masa ta barma haɗi da kawo masa abinci da ruwa. Dan koda ya shigo Hafsat bata ida sallah ba. Bayan yaci abinci ya koshi kana Hafsat tazo ta gaisheshi haɗi da ɗauke kwanokan da yaci abinci. Mama ce ta fito daga ɗakin ta tazo ta zauna saman tabarmar da yake zaune. Gasheshi tayi kana suka fara taɓa fira. Safiyya ce tace, "Hafsat tashi muje mugaya ma Baba da Mama abin farin cikin da ya samemu". Sai Hafsat tace, "a'a kije kigaya musu dan gabana sai dukan uku-uku yake dan ji nake kamar baza'abar ni naje ba........ *#Vote* *Comment* *Shere* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 14📑* *__________📖* Safiyya tace, "a'a ki tashi muje insha Allah za su barki". Ba musu ko ta tashi su kaje wajan da Baba da Mama ke zaune,zama sukayi haɗi da gaishe da Mama. Ba su jima da zama ba sai ga Yayan Safiyya ya shigo shima inda ya gansu nan yazo ya zauna. Sai da sukayi ƴan second Safiyya ta buɗe baki tayiwa Baban ta bayanin abinda ke faruwa. Aikuwa tun bata kai ƙarshin zancin ba sai Mama tace, "tunda muna mahaukwata sai mu barta taje har wata ƙasa karatu ko?ko wannan karatun da takeyi anan gida me tasa ka ma iyayen ta dashi bare yanzu taje wata ƙasa, gaban idon mu ma tayi bare bayan idon mu,dan haka ni ban baka shawara ka barta taje wata ƙasa karatu ba,amma in ka yarda da shawara ta".....tana faɗa tana kallon Baban Safiyya. Tana rufe bakin ta sai Yayan Safiyya yace, "wallahi ba ina da zata je kawai da ta haihu ka haɗata da liman ɗin unguwar nan dan kaga har yanzu bai sake aure ba tunda matar sa ta rasu kaga sai yayi maneji da ita dan inba shi ba ba mai iya auren ta". Sai da suka gama faɗar abin da zasu faɗa kana Baban Safiyya ya ɗago da kansa ya dube su ɗay bayan d'aya kana yace,"wannan surutun naku bashi zai sa nace baza ta jeba a'a idan nayi ra'ayi na barta taje ba wanda ya isa yahana taje dan haka kuriƙe shawarar ku har nace zan nemi kubani shawara". Kallon sa ya maida ga Hafsat kana yace, "naji abinda kuka faɗa amma zanyi shawara zowa safe duk abin da na yanke zan gaya miki" yana faɗar haka ya tashi ya bar wajan batari da ya sake magana ba. Suma suna ganin ya tashi suka tashi dan sukoma ɗakin su. Bakin ciki da ta kaici duk ya cika Mama dan shi ko magana ta kasa. Suna shiga ɗaki ba wanda yayi magana a cikin su har sukayi shirin kwanciya haɗi da addu'a suka kwanta. Ba jimawa da kwanciyar su wayar ta ta fara ringing amma tanaji ta share sai da akayi mata miss call uku kana ta ɗauko wayar ta duba taga wake damun ta da kira yanzu da dare,ba ƙuwar number tagani har taso taƙi ɗauka sai kuma ta ɗauka haɗi da kara wayar a kunnin ta. Ba'ayi magana ba dan haka itama batayi magana ba, sai can taji ance "Hafsat".....gabanta ne ya faɗi sabida ko a cikin mafarki taji wannan muryar zata shaida ta. Ƙo ƙarin katsa wayar ta fara sabida gudan kada ya haifar mata da wata matsala. Kamar yasan abinda take da niyar aikatawa dan haka ya fara magana kamar zayi kuka yace, "Hafsat nasan ni mai lafine amma dan Allah kada ki barni wallahi nasan kin fikowa sanin irin son da nake miki Hafsat,ki taimakeni kada ki barni,kuma wallahi yanzu ashiryi nake da na aureki Hafsat please kada ki barni dan yanzu haka tunda kika barni akwance nake nakasa cin komai I love you My Sweet baby inasonki over"....haka dai yayi ta cika ta daɗan baki har ta fara jin wani abu ya ɗarsu a zuciyar ta. Hankali ta ɓuɗa baki tace, "kana wata magana kamar da gaske, amma kabari gobe mayi magana"..tana faɗin haka ta katse kiran dan ko magana ƙasa-ƙasa takeyi masa sabida bata so Safiyya ta gane dawa take waya. Irin yadda yaji tayi magana ya gane cewa zayi nasara dan haka tana katse kiran yayi wani tsalle haɗi da yin wata shewa mai ciki da jin daɗin samun nasara. Abukin sa dake kusa dashi yace, "hala anyi nasara da zaka buga wannan uwar shewa?". Sai da Anwar ya murmusa kana yace, "sosai,dan gobe nasa zata zo nayi yadda nake so da ita inyaso da yamma na bar garin kaga ko baza ta saki gani na ba kuma nima bazan saki tunata ba daga ƙarshe ma na manta da ita". Sai wannan abukin sa Lawal yace, "shegin kaya kaki fa Anwar,kana yadda kaso da Hafsat wallahi,amma tunda kai ka gama da ita ni mi zai hana ka haɗani da ita ko naji wannan daɗin da kake kwasa a wurin ta". Kallon baka isaba ya wurga masa kana yace, "dan kaji nace zan manta da ita, to bari kaji koda ace na koma gada wallahi duk lokacin dana so na kusan ce ta sai ta yarda kai bari kaji in har ban aure ta ba to bawani ɗa namijin da zai aure ta dan banji zanyi iya yarda wani ya kusan ce taba in bani ba". Sai da ya kai ƙarshin maganar sa Lawal yace, "ai gani nayi kana da Hajara.....aikuwa tun bai kai ƙashin zanci ba ya katse shi da faɗi idan kana so muci gaba da mutun ci kada kasa kiyimin zancin wata Hajara"....yana faɗin haka ya tashi ya shige bedroom ɗin sa dan ba ƙaramin bacin rai yake ba idan aka taso masa zancin Hajara. ****** Koda gari ya waye bayan sun karya Baban Safiyya ya aiko kiran Hafsat a ɗakin sa. Da Sallama ta shiga ɗakin sa haɗi da gaisheshi, bayan ya amsa ya dube ta kana yace, "Hafsat jiya nace kibari nayi shawara,to gaskiya nayi tunani akai kuma nayi shawara, dan haka kiyi haƙuri da abinda zan faɗa miki gaskiya bazan iya bari kije ba a matsayena na mahaifin ki kuma mariƙin ki,ba dan komai yasa nace haka ba sai dubin abinda ya faru ne tsakaninki da iyayenki ,kuma babban abinda ya hana na barki shine cikin da kike ɗauke da shi,dan haka kiyi haƙuri idan Allah yace kije nan gaba sai kije idan kuma bai kaddara ba sai kiyi haƙuri,dan ni yanzu burina ki sauka lafiya kuma kusamu miji nayi muku aure ke da Safiyya,dan gaskiya naso na ƙi barinku ku ƙarasa wannan karatun sai kuma naga koda na ƙi barinku to ba aure zakuyi ba dan haka nace da zaran kin haihu zan muku aure keda Safiyya insha Allah". Tunda taji Baban Safiyya yace ba zata jeba gabanta ya bada dummmmm to tunda ga wannan maganar bata saki jin miyake faɗa ba, dan gabaki ɗaya hankalinta baya jinkin,sosai maganar sa tasa ta damuwa,amma bata nuna masa ba,sai ma cewa datayi "bakomai Baba Allah ya tabbar muna da alhairi".....tana faɗin haka ta koma ɗakin su. Inda tabar Safiyya nan tazo ta same ta,Safiyya naganin tashigo ɗaki jikin ta a sanyaye sai tayi saurin cewa, "Hafsat me Baba yace ne naganki a haka?". wayin cewa tayi kana tayi mata bayanin yadda yace mata,tana mata bayani amma sai ta nuna bata damu ba,amma a zuciyar ta ita kadai tasan mi take kiyastawa aciki. Sosai Safiyya taji zafin haka dan da badan tasan halin mahaifin ta da magana ɗaya ba da tasake tunkarar sa. Haƙuri tacigaba daba Hafsat har ta nuna mata ita ko ajikin ta,kuma Allah ne bai nufi tajeba,amma a zuciyar ta ita kaɗai tasan me take shiryawa. Haka suka cigaba da fira har sukayi aiki suka kammala. Biyu dai-dai ta shirya zowa school dan biyu darabi Hafsat ke da luctura,ita ko Safiyya yau bata da luctura kuma batajin daɗin jikin ta bare ta raka Hafsat makaran ta,dan tunda taji baza a bar Hafsat taje ba taji jikin ta duk ba daɗi, dan har ƴar ƙwalla sai da tayi. Tana sauri tashiga makaranta, ita kuma Hajara zata fito,gabaki ɗayan bata lura da ita ba sai da taji sunyi karu dawani mutum,dan haka da sauri Hafsat ta ɗaga kanta,aikuwa tana ɗaga kanta dan taga dawa tayi karu,waza tagani inba Hajara ba. Gaban tane yayi masifar faɗuwa lokacin da tayi ido biyu da Hajara,Addu'ar neman tsari ta farayi a zuciyar ta,har dai tasamu ta buɗe baki tace , "kiyi haƙuri dan Allah wallahi ban lura dake ba".....tana faɗin haka ta ƙarasa daga cikin makaran ta batari da taji me Hajara zata ce da ita ba. Ita ko Hajara ranta inayayi dubu ya ɓaci dan haka tayi kwafa haɗi da antaya ma bayan Hafsat wani kallo kana ta wuce. Saura kaɗan tayi late dan tana shiga malamin ya shiga. Ƙarfe 6:00,dai-dai suka gama lecture,da sauri tafito dan tasamu bus tashiga takoma gida cikin lokaci dan tasan halin Mama ko takoma kan lokaci sai tayi mata faɗa bare ma bata koma ba,amma ina dan tana ƙarasuwa bus ɗin natashi da mutane cike. Aikuwa tana ganin sun ɗaga tabuga wata ubar ƙara haɗi da faɗin "ya Allah!. Gashi mafiyawan mutane sun watsa,amma ya ta iya dole tajira zowan wata bus. Tana cikin tsayin jira bus sai ga wata ƴar budurwa tazo wajan ta wadda bazata wuce sa'arta ba tace, "Hafsat mikikeyi anan har yanzu baki je gida ba". Sai da Hafsat ta kalle ta haɗi da tunanin ina tasan ta kana tace, "ina jiran bus ne". Sai wannan budurwar tace, in badamuwa kizo musaukeki dan bus kam ba yanzu ba". Irin kallon da Hafsat tayi mata ne yasa tace, "nasan haliki baki da yadda,amma tunda bazaki jeba ni zan tafiya ta tunda ke ko ƴan class ɗinku bazaki gane ba". Sai Hafsat tace, "a'a wallahi,ina tunani idan nasanki ne,amma kiyi haƙuri muje ai nagode ko bakin hanya ne ki sauke ni sai na ƙasa". Sai wannan buduwar tace "har gida sai munkai ki". murmushi Hafsat tayi haɗi da godiya kana suka tafi bakin wata baƙar motar da akayi picking wadda ko glass ɗinta baki ne. Suna karasowa wajan motar ta ɓuɗe mata murfin motar tace, "Hafsat shiga". Gaban tane ya faɗi amma sai tayi bismillah ta shiga. Tana shiga sai aka rufe marfin da sauri suka tada mota suka wuce batari da wannan budurwar ta shiga ba. Suna tafiya sai wannan buduwar tayi murmushi kana tace, "Hafsat kenan inkinsan wata baki san wata ba"....tana faɗan haka itama tashiga wata motar ta bar wajan..... ```Comment dinku nayin kad'an fa``` *#Vote* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 15📑* *__________📖* Mamar Safiyya ce ke kwalama Safiyya kira,da sauri safiyya dake ɗaki tafito haɗi da faɗin, "gani Mama". Kallon ta tayi haɗi faɗin, "har yanzu Hafsata bata dawo ba?tana can ta tsaya wajan shiri-ritar da ta saba kenan". Sai Safiyya tace, "a'a mama kila bus ce bata samu kan lokaci ba,amma bari nakirita naji ko sun taso"....tana faɗa tana shiga ɗakin ta dan ta ɗauko wayar ta. Koda takira wayar akace mata wayar kashe take,amma duk da haka bata haƙura ba sai famar kira take tana faɗin, "tasan duk wayar ta ba kashe take ba network ne ,dan haka tace bari ta aja zowa ajima idan bata dawo ba tasake kira duk da tasan tana kan hanya"...tayi maganar ne ita Kaɗai. Sunanan suna jira har akayi magarb har a kazo da isha'i,kuma gashi duk aka kira wayar ta sai ace kashe take,sosai hankalin Safiyya ya fara tashi dajin Hafsat shuru bata dawo ba. Ita ko Mama sai zoba masifa take wai Hafsat ta tsaya wajan shiriritar da tasaba,sosai faɗan kema Safiyya ciyo dan abin yazo ya haɗe mata waje ɗaya, ga rashin jin Hafsat ko a waya ga masifar Mama. Mama nacikin wannan masifar sai ga Baba ya dawo gida,nan Mama tashiga yimasa bayani wai Hafsat tun safe da taje makaranta har yanzu bata dawo ba,sosai hankalin Baba ya tashi,aiko yace bai ga zama ba,bari yaje makarantar yagani ko wani abu ya tsaida ta?. Har zai fita sai Yayan safiyya Saminu yace, "Baba kada kaje ka wahal da kanka, dan nasan ba inda taje sai gidan saurayin ta".....ai tun bai kai da rufe bakin sa ba, Baba yayi cikin sa yana masa faɗa,sai da Baba yayi masa faɗa sosai kana ya bar gidan da sunan yaje ya nemu Hafsat. Har zai fita ya kwalama Safiyya kira yace tazo sutafi tare dan ita tasan kan makarantar,ba musu ta ɗauko mayafin ta tafito suka tafi. ****** Hafsat na shiga cikin motar, wani mutum wanda bata san ko waye shi ba ya rufe mata baki haɗe da ɗaure mata fuska,dan duk ihu da take ba mai jinta har suka tada mota suka bar makaranta,Basu tsaya da ita ko ina ba sai wani gidan. Tunda sukayi packing ɗin motar gaban ta ke famar dukan uku-uku,ina ba ambatun Allah ba ba abinda takeyi a ranta,tanaji suka ɓuɗe marfin motar suka fitar da ita,sai da suka isa da ita parlour gida kana suka kwance mata fuska haɗe da buɗe mata baki. Aikuwa tana ɗago idonta wazata gani inba Anwar ba,wani uban zabura da tayi kamar bata ɗauke da komai ajikin ta. Nunisa da ɗan yatsa ta farayi har tasamu ta ɓuɗa baki tace, "Anwar dama kaine kasa a ɗaukoni?minayi ma Anwar? mikake nema dani?dan Allah kabarni hakanan na huta,wallahi ina cikin gararin rayuwa,wadda sabida kai na faɗa acikin ta,duk abinda kayimin baiyi isheka ba sai ka kasheni ne!to gani kashini,macuci azalumin,kayimin ciki kuma karabarni,sanidiyar ka nabar iyayena"....ai tun bata kai da rufe baki ba ya wanke ta da mari har guda biyu,wanda lokaci ɗaya ta rasa inda kanta yake. Nunin ta ya farayi da ɗan yatsa kana yace, "waye sa'arki da zaki riƙa buɗe baki kina faɗi masa magana sun ranki ehh?Narabaki da iyayenki kuma yanzu zan rabaki da wadda kika fiso dan haka wallahi sai kinyi dana sanin faɗamin maganar daki kayi" ..yana faɗa yana nuninta da ɗan yatsa. Waɗanda suka kamuta ya duba kana yace,"koje ko nemunin Safiyya duk inda take,kuma nabaku zowa nan da gobe"....ai tun bai kai da rufe baki ba,cikin hanzari da kaɗuwa da maganar sa tafaɗa jikin sa tana faɗin,"Anwar dan Allah kada kayi min haka wallahi na yarda duk abin da kakeso zamakashi amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,dan Allah na ruƙeka"....tana faɗa tana wani kuka mai kunar zuciya. Har yaran nasa zasu tafi dan cika umarinin da ya basu sai kuma ya tsaida su yace suji rashi falo zasuyi magana da Hafsat. Bayan sunfita ne ya dubeta kana yace, "idan har baki son nataɓa lafiyar Safiyya to sai kin yarda da abinda zance,amma idan baki yarda ba wallahi ba makawa sai nasa anɗauko min ita gobe,amma idan kinyar da to ba damuwa". Kallon sa tayi kana tace, "inaji kafaɗa idan zaniya ɗan". Yace, "dole ma ki iya,kuma daga yau zaki zauna gidan nan har tsawun sati ɗaya,kuma duk abinda kikasan kina min wancan lokaci zakiyi min shi a yanzu, dan haka idan har kin yarda to amma idan baki yarda ba sai nasa su ɗaukomin ita gobe". Idontane ya cigaba da fitar da hawaye kana tace, "dan Allah kayi haƙuri Anwar kabarni na koma gida, na yarda sai na riƙa zowa har sati ya cika"....tun bata rufe bakin taba ya kwalama yaransa kira yace gobe su ɗauko mishi Safiyya. Cikin hanzari ta faɗa jikin haɗi da faɗin, "na yarda Anwar duk abinda kakeso zan maka amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,amma kasani yanzu bani da wata isassar lafiyar da zan riƙa abinda nake maka a da,dan kasan cikin dake jikina baya bani lafiya"....tana faɗa tana share hayen ta. Wani kallo yake jifa ta dashi kana yace, "yanzu kina nufi har yanzu biki zobar da wannan cikin ba? to bari kiji daki zobar da karki zobar duk ɗaya suke a wajena dan sai kinyi abinda nace kiyi"...yana faɗin haka ya kama hanyar bedroom ɗinsa batare da yasake magana. Itako faɗuwa tayi saman kujerar parlour ta fara rera kuka kamar ranta zai fita,tana kuka tana ruƙun Allah ya kawo mata mafita. Koda suka kawo bakin gate ɗin makaranta tsit yake sai ɗai-ɗaikun mutane dake wucewa amma ba alamar wata bus. Cikin makaranta sukayi packing ɗin motar su,cikin hanzari Safiyya ta fito ta nufe class ɗinsu,koda ta ƙarasa ba kowa aciki dan haka da sauri ta wuce hostel wajan abukan karatunta,abukiyar karatun ta Maryam ta fara cin karu da ita, Safiyya tace, "yauwa Maryam, nace Hafsat tashigo makaran ta yau kowa?". Sai Maryam tace, "eh ta shigo dan kusa dini ma ta zauna har aka gama luctura". Safiyya tace, "wallahi ita nake nema dan har yanzu bata koma gida ba". "Aikuwa ana gama lecture tace bari tayi saura tashiga bus dan bata son magirb tayi mata kan hanya"...cewar Maryam. Har Safiyya zata wuce sai ga Saratu ko ita abukiyar karatun suce, har zata wuce taji suna zanci Hafsat dan haka ta ƙarasu garesu tace, "Safiyya Hafsat kam tajima da tafiya dan gaban idona ma tashiga wata mota baƙa ita da wata yarinya,amma ban san yariyar ba, ina dai yawan gani yarinyar tare da Hajara". Gaban Safiyya ne ya bada dummmmm,lokaci guda jikin Safiyya yayi sanyi,dan da ƙyar tasamu ta ɓuɗa baki tace musu, "nagode bari na koma gida wata ƙila ta isa"....tana faɗar haka ta kama hanyar da zata kaita wajan da tabar Baban ta. Tana isa wajan sa ta ɓuɗe mota tashiga tana mai faɗin, "Baba muje ƙila ta isa gida,dan antabbartarmin da tashiga mota". Tana faɗin haka bai tsaya wani jiraba ya tada mota suka bar makarantar. Koda suka isa gida akace bata dawo ba,sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi,irin tashin hankalin da Safiyya taga yashiga ne dan haka taje wajan da yake tsaye tace, Baba ka daina tada hankalinka akan ɓatan Hafsat,Hafsat bata ɓace ba, ta dai je gidan saurayin ta wanda yayi mata ciki,abinda yasa nace haka sabida ko jiya da dare bayan mun kwanta, dan ita atunanin ta bacci nake, inajin abinda tace dashi,naso nayi mata magana tunjiya amma na fasa nace sai naga tasake wayar dashi....sai da ta numfasa tace, zan yarda wancan lokacin asiri yayi mata amma yanzu nasan bawani asiri atare da ita.....nan dai tagaya musu asirin da Anwar yayi mata a wancan lokaci. Baban Safiyya ya kalle Safiyya jikin sa asanyaye yace, "zaki iya gane gidan nasa kikai ni gobe?". Shuru tayi bata bashi amsaba,kafin ta buɗa baki tayi magan Yace, "dole gobe ki kaini gidan, dan bazan iya barin ta awajansa ba,amana na ɗauko ta fa,dan haka ko ina Hafsat take sai na nemuta,dan ban sani ba ko yanzu asiri ne yayi mata"....yana faɗin haka ya fice daga gidan gabaki ɗaya. Kukan datayi ne har ya saukar mata da zazzaɓi mai tsanani dan koda yafito daga bedroom ɗinsa kwance yasame ta saman kujera jikin ta sai famar karkarwa yake saboda zazzaɓi. Hankali ya ƙarasu gareta,hannunsa ya kai jikinta lokaci ɗaya ya ɗauke yana mai faɗin, meke damun ki hala naji jikin ki da zafi?". Komai bata ce dashi ba sabida ko bakinta ta ga-gare ɓuɗewa bare tayi magana. Dayaga alamun bazatayi magana ba yace, "wallahi ba ruwana da wani zazzaɓi, duk baki tashi kika fara aikin ki ba wallahi gobe sai anzomin da Safiyya"....aikuwa tana jin furicin sa,da sauri ta zabura ta miƙi zaune haɗi da faɗin, "nashirya mi zanyi maka yanzu"....abinda tayi ne ya bashi dariya dan haka ba san lokacin da yayi dariya ba... *#Vote* *Comment* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 16📑* *__________*📖 Nuni ya yi mata da ta zauna saman cinyar sa, ba musu ko ta tashi ta zauna,tana zama ya sanya wata sassanyar ajiyar zuciya,ɓsabida jin fatar shi da ta ta sun haɗu waje ɗaya, shi kansa ya san yana son Hafsat so ba nawasa ba amma a zahirin gaskiya ba za'iya auren ta ba duk son daya kemata,kuma ba dan komai ba sabida yariga da yasanta ƴa mace,kuma da ta yarda zata zubar da cikin wata ƙila ya yarda ya aure ta. Jikinsa ya ƙara sanya ta, kana ya fara shaƙar ƙamshin dake fita jikinta, hannun sa ya kai saman sassan jikin ta ya fara shafar ta, lokaci ɗaya yaji wani sanye ya mamaye zuciyar sa,sosai yake son taraiya da Hafsat ba dan komai ba sai dan yadda ya ke samun natsuwa da ita sose. Ita kowa tunda taji ta saman jikin sa wasu hawaye masu zafi suka fara fita a idon ta,uwa uba lokacin da ya ɗora hannusa saman jikin ta,jikin ta ne ya fara karkarwa sabida baƙin cikin ɗaura hannusa da ya yi kuma ga ciyo da ke ɗawai niya da ita. Bukinsa ya fara ƙoƙarin ɗaurawa saman nata, lokaci ɗaya ta fara ka-karin amai haɗi da sauka saman jikinsa, Wani baƙin ciki ne ya rufe shi bai san lokacin da ya kifeta da mari ba kana yace, "Wallahi Hafsat muddin ki na buƙatar kanki da lafiya ki bi abinda nake so, dan wallahi ko aman jini ki kai sai nayi yarda nake so dake ko nayi miki abinda har ki mutu bazaki mantani ba,dan haka maza kije ki gyara jikin ki ki sameni bedroom yanzu nan". Yana faɗa yana kama hanyar da zata sada shi bedroom. Sanin halinsa da tayi dan haka ta tashi taje ta gyara jikin ta kana ta sameshi a bedroom ɗin sa. Koda ta shiga ɗakin yana waya yana faɗin, "My love kin san na kusa dawowa kuwa?,dan haka ki fara shirin, dan kin san dana dawo ba jimawa za'ayi aure na dake". Daya ke hands-free yasa dan haka tana jin dun abinda suke fada. tace, "hmm My dear har kasa naji ƙunya". Murmushi ya yi kana yace, "kada ki damu ba jimawa zan cire wannan kunyar take dan ni tana cutar dani". Mumushi tayi mai ɗan sauti kana tace, "yaushe zaka dawo ina son na kasance cikin shiri?". Yace,"a'a bazan faɗa ba akoda yaushe dai ki kasance cikin shiri kinji tawa". Tace "to tace dashi". Haka dai suka cigaba da waya cikin so da ƙaunar junan su. Bayan sun kammala wayar ne ya kai duban sa ga Hafsat dake tsaye kamar wadda aka da sa kana yace, "kinyi min tsaye akai, ki ƙaraso mana". Jikin ta a sanyaye ta ƙaraso gareshi, Tana ƙarasowa ya jawuta jikinsa haɗi da sanya bakin sa cikin nata,to fah daga nan labari ya sauya. Washe gari tunda safe Baban Safiyya yace suje ta gwada masa gidan Anwar, hijab ɗinta ta saka batare da tayi ko beark ba suka kama hanyar gidan Anwar. Sun sha wuya kafin ta gano gidan dan har za su juyo su dawo gida sai tagane gida,amma kuma ganin gidan da sukayi baiyi affani ba dan gidan kulle yake kuma ko da suka tambaya akace mai gidan ya jima da barin garin. Sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi na rashin ganin Hafsat, dan koda suka dawo gida ba inda ba suneme ta ba amma basu ganta ba,dan haka Baban Safiyya ya yanke shawarar yaje ya sanar da Baban Hafsat abinda ake ciki duk da yasan bai rasa jin ɓatan Hafsat a unguwa amma gwanda yaje ya ƙara sanar dashi koda ya sani. Da yamma bayan ya dawo daga kasuwa ya shirya yaje wajan Baban Hafsat. Koda yaje wajan Baban Hafsat,bayan sun gaisa kana Baban Safiyya ya faɗa masa abinda ke faruwa gami da ɓatan Hafsat. Sai da Baban Hafsat ya numfasa kana yace, "Alhaji Aliyu to miyasa zaka tare ni da wannan magana bayan tun wancan lokaci na shaida maka na fitar da Hafsat daga cikin ƴaƴana,amma kuma yanzu kazomin da wannan zanci,dan haka bana son wannan zanci dan Allah daga yau kada ka ƙara haɗani da ita". Har Baban Safiyya zaiyi magana sai Baban Hafsat yace, "a'a kada kasoma, kai kaji zaka iya riƙunta kuma yanzu tace bata so duniya take so tabi dan haka ka kyale ta ga duniyar nan ta ishe ta riga da wando". Yana faɗar haka ya shigewar sa gida ransa a ɓace. Haka baban Safiyya ya dawo gida jikinsa a sanyaye kamar ba lakka ajikinsa. Haka dai suka canye kwana biyu suna neman ta amma basu ganta ba,daga baya sukayi haƙuri suka cigaba da addu'a Allah ya bayya nata. Tunda sallah asuba da ta farka tayi wanka haɗi da ɗuru alwala tayi raka atanin fajar kana tayi sallah asuba,tajima zaune tana istigifari da hailala da addu'a nema tsari daga sharin mutum da aljan. Bakwai saura ya farka haɗi da wata irin miki,gyafin da take ya kalla kana ya buɗa baki yace, "waya baki umarnin ki tashi daga nan ehh?". Ko kanta bata ɗago daga ƙasa ba tace, "lokaci sallah ne ya bani umarnin tashi". Aikuwa cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya ƙaraso gaban ta yana nunin ta da ɗan yatsa kana yace,"saki faɗin abinda kika ce?". Irin yadda yake mata maganar ko ita ta tsora ta sosai dan haka bata ce komai ba taci gaba da lazumin ta amma gaban ta sai dukan uku-uku yake. Magana yayi mata cikin tsawa yace taje ta haɗa masa beark,aikuwa ba musu ta tashi taje kitchen ta fara haɗa masa abinda yake so. Tana tashi yabita da kallo haɗi dayi mata kwafa kana yace,"zanyi maganin ki,nan ba da jimawa ba". Yana faɗin haka ya kama hanyar da zata sadashi da toilet. Ita ko badan komai ta tashi tashiga kitchen ba sai dan kar ya hanata zowa makaranta. Agurguje yayi wanka ya fito dan so yake yaje gun Hajara ta rakashi wajan malamin da yayi masa aiki akan Hafsat a wancan lokaci dan ko yanzu so yake ayi masa aki a kanta,dan yaga yanzu sai wata gardama take mishi idan yace tayi masa abu saɓanin da. Koda ya zo parlour tana kitchen bata ƙarasa aiki ba dan haka ya sameta kitchen ɗin yace, "ya fita yadawo yanzu". Bai jira cewar taba yafita yana ta sauri kamar wanda akayi ma kyata zata tsere masa. Key yayi ma motar sa, kana ya kama hanyar da zata sada shi da layin buge,dai-dai kan kwanar gidan yayi packing ɗin motar sa. Yana fitowa a mota ba abinda ya fara cin karo dashi ina ba condoms ba, tsaki yayi kana yace, "shiya bana sun zuwa wannan unguwar sabida haka". Kwanar ya shiga,aikuwa yana shiga sai ga ƴan mata da samari sai fitowa suke cikin ɗakunan da suka kwana,wasu da alamu ma matan aure ne dan ga sunan har da goyon su,abin dai sai wanda yagani,yana ƙara tafiya sai yaga wata yarinya ita da wani saurayi za su shiga wani ɗaki, kuma daka ganta ita ƴar makaran tace dan ga kayan makaranta nan ajikin ta na secondary school, ɗaki suka buɗe suka shiga kana suka rufe ƙofa. Gab da zai shiga ɗakin Hajara yaga wasu samari su biyu sai tunkuɗar wata yarinya suke suna faɗin, "wallahi yau sai kin bari muna ɗaki tunda ba ubanki ne ya bamu kuɗin da zamu biya ba". Ita ko sai turjiya take wai ba inda zata je. Da suka ga zata ɓata musu lokaci suka tisa ƙyayar ta gaba suna faɗin,"shigiya jarababba wallahi mungaji dake dan haka yau sai kin bar muna ɗakin mu". Yarinya ta sosai dan idan ka ganta bazaka ce tasan wani abu ɗa namiji ba,tsaki yayi haɗi da ƙarasawa ɗakin Hajara. Yana zuwa ba Knocking ba komai yatura ƙofar ɗakin ya shiga. Cikin sa'a koda ya shiga ba kowa aciki dan ko ita tana toilet tana wanka,koshi dan yaji motsin ruwa ne ya tabbatar da haka. Zama yayi sama katifar dake ya she a ɗakin yana jiran ta. Bai jima da zaman ba sai gata tafito daga ita sai wani ƙaramin towel da bai rufe cinyar taba. Bata ma lura dashi ba sai da yayi gyaran murya kana ta san da zaman sa. Aikuwa suna haɗa ido dashi wani sanyi daɗi ne ya ziyarci zuciyar ta lokaci ɗaya,dan haka bata san lokacin da ta faɗa jikin sa ba. Ƙoƙarin raba ta da jikinsa ya fara amma sai ya tuna da akin da zatayi masa dan haka ya kyale ta,jikin sa ta fara shafa duk da baya so amma abinda ya keson tayi masa ya hana ya dakatar da ita. Ita ko da taga bai da katar da itaba yasa ta kai bakin ta zuwa nasa ta fara kissing ɗinsa,ba yadda ya iya haka yabiye mata har suka samu biyan buƙata kana ya jawo ta jikin sa haɗi da kai mata kiss a baki kana yace, "My dear na,ina so ki kaini wajan malamin da ya taɓa yimin akin akan Hafsat".....ai tun bai rufe baki ba ta ɗago kanta da sauri ta dube isa kana tace, " nifa bana sun kana min maganar ta dan a rayuwa ba ƴar da na tsana kamar ta". Da ƙyar dai yasha kanta ta yarda zata kai shi amma sai laraba da ƙarfe uku na dare yazo su tafi dan lokaci ne ake zowa wajan malamin. Yace, "to sai yazo". Yana faɗa yatashi ya shiga toilet yayi wanka,jikin sa ta goge masa haɗi da tayashi sanya kayan sa. Har mota tarakashi gab da zai shiga mota ya juyo ya kalle ta kana yace, "Hajara yanzu shikenan kin bar hostel kin dawo nan dazama ko". murmushi tayi haɗi da faɗin,"sai mun haɗu ko". tana faɗar haka ta wuce ta barsa batare da taji mi zai ce ba. Key yayiwa motar sa kana ya dawo gida, koda ya shigo zaune ya same ta tashirya tana zaman jiran dawowar sa. Kallon ta yayi yace, "ina beark yunwa nakeji". "yana dining". Tafaɗa haka ataƙaice. Sai da tabari yagama beark tazo tace mishi makarnta take sun zuwa sabida lecture ne da ita ƙarfe goma. Wani kallo yabita dashi kana yace, "bawani makaranta so dai kike ki tsere,amma kisani bana gudun ki gudu dan na san da kanki zaki dawo gareni, kana yace zaki iya tafiya". Yana faɗin haka takama hanyar fati,har zata ɓuɗe ƙofa ya dakatar da ita yace ta bari yazo ya kaita da kansa kuma zai jiri da tagama abinda take ta dawo in kuma ba haka tasan sauran. Ba musu ta tsaya har ya kammala abinda yake yazo ya kaita makaranta. Da shigar ta school bata tsaya ko ina ba sai office ɗin shugaban makaran ta. shugaban makartar ya bata wata takarda wadda akayi ma signing yace taje ta kaima iyayen ta su sa hannu,idan sun sa sai ta kawo dan wani sati za suwu ce abuja daga can kuma kowace a bata ƙasar da zata je karatu. Bayan ta fito ɗakin shugaban makaran ta tashi ga class ɗinsu,bayan sun gama lecture tana sauri ta fito ne sai ta haɗu da ƙawar ta Maryam. Hafsat bata ma ganta ba sai Maryam tace, "Hafsat ran jumu'a yaushe kika koma gida dan naga Safiyya sai nemanki take?". Murmushi Hafsat ta ƙaƙalo kana tace,"tana fita niko na koma". Sai Maryam tace, "gaskiya Hafsat Safiyya na son ki da yawa kinga yarda tabi tarikice kuwa". Mumushi Hafsat tayi haɗi da cewa, "bari na wuce sai gobe idan na shigo". Tana faɗar haka tafice batare da ta tsaya jin me zata ce ba. Da sauri take tafi har tafita daga makarantar, bakin gate ta ganshi yana jiran ta dan haka bata tsaya komai ba tashiga motar sa suka wuce. Tana wucewa Safiyya na fitowa daga class ɗinsu,Maryam tagani zata wuce hostel dan haka da sauri taje gare ta tayi mata magana. Juyuwa Maryam tayi haɗi da yimata murmushi kana tace, "Safiyya Hafsat kike nema ne hala". Sai tace,"eh wallahi har yanzu bamu ganta ba". Tace, "yanzu fah naga Hafsat kuma tare muke har aka gama lecture". Safiyya tace, "yanzu!". Ta faɗa haɗi da zari ido. Suna cikin wannan maganar sai ga ƙawar su Saratu tazo tace, "nima naga Hafsat yanzu bakin gate tashiga wata mota". Wani baƙin ciki ne ya turnuƙata,tace kena Hafsat su ta rainama hankali tana gidan saurayin ta. Tayi wannan maganar a zuciyar ta. Kallon su tayi tace, "oky nagode sai anjima". Tana faɗar haka takama hanyar fita makaranta,sosai ran ta ya ɓace wato Hafsat suta mayar ƴan isaka wanɗanda basu da aikin yi, to daga yau ba mai koma shiga harkar ta inta iya ta tabbata tare dashi. Gida ta koma dan ko lecture da zatayi bata tsayayi ba sabida ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba. Cikin sa'a koda ta isa gida Baban ta bai fita ba,bayan ta zauna sai Mamar ta ce, "har kin dawo ne?". Sai tace, "eh Mama". Sai ta kalle Baban ta da idon ta da sukayi ja-jir tace, "Baba Hafsat fa bata ɓata ba"......nan dai ta faɗa musu abinda tasani. Ko Baban Safiyya ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba amma bai ce komai ba sai Allah kashirya. Mama ko inda take fita ba nan take sauka ba kuma tace wallahi ko Hafsat tadawo baza ta zauna gidan ba. Ko Yayan Safiyya shima yayi faɗa kamar ya shaƙo Safiyya tunda itace mafarin zuwan ta gidan. Tunda Hafsat tashiga makaranta duk abinda take akan idon sa har maganar da sukayi da Maryam,abin da kwai bai sani ba shine shigar ta office ɗin shugaban makaranta. haka ya dawo da ita gidan sa ba abinda take masa sai aikin bauta amma yana kai ta makaran ta tayi abin da zatayi ya mai data har akazo darin da za su je wajan malamin su shi da Hajara. Tun shabiyun dare ya fara jin cikin sa na murɗawa har akazo lokacin da sukayi yazo sutafi,kuma lokacin ne ma cikin nasa ya fara yimasa wata murɗa wada yasa yafita haiya cinsa lokaci ɗaya. Ita ko bata masan abinda ake ciki ba sai gab da asuba tana tashi ta ganshi cikin wannan halin sosai hankalin ta ya tashi dan haka cikin hanzari ta ɗauko wayar sa,kuma sai tara waza ta kira tunda bata san kowa nasa ba. Har aka gama sallah asuba tarasa ya zatayi sai can ta tuna da akwai mai gadi gida,dan haka da gudu taje ta sanar da mai gadi abin da ke faru,aikuwa mai gadi na shiga cikin gidan ita ko ta lallaɓa ta ɗau kayan ta na makaran ta ta gudu. Cikin sa'a tana fita tasamu dan acaɓa ta faɗa masa suna unguwar su suka kama hanya..... *#Vote* *Comment* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 17📑* *__________*📃 Bakin ƙofar gidan tace ya sauke ta, kuɗi tabashi haɗi dayi masa godiya,dan ƙuɗin da ta bashi sunfi hakanan amma ya amsa baice da ita komai ba, gidan ta kaman hanyar shiga har ta shigar da ƙafar ta ɗaya sai Yayan Safiyya Abbas yazo da sauri ya tare ƙofa haɗi da antayamata wani kallo kana yace,"wallahi ba inda zaki shiga dan ba gidan ubanki bane, sai da kika gama lalacin ki zaki ɗauko wasu shegun ƙafafunki kice kizo gidan ubanki ko?, To barikiji tun wuri ki kama gabanki tun ban illatakiba". Haƙuri ta fara bashi tace, "wallahi Yaya ba inda naje sune suka saceni"....tun bata rufe baki ba ya wanke ta da wani mari wanda yasa ƙiris kaɗan ta kai ƙasa. Suna cikin haka sai ga Mama ta fito taga wake musu hayaniya bakin ƙofar gida. Hafsat tagani tana ƙoƙarin tashigo shiko Abbas ya hanata shigowa,aikuwa da sauri Mama ta ƙarasa wurin tana kunfar baki tace, "wallahi baki isa kishigo gidannan ba,tunda ba ubanki ne ya gina munashi ba". Roƙun Mama Hafsat tafariyi amma Mama taƙi koda saurarin ta,daga ƙarshe ma Mama komawa tayi gida ta ɗauko mata kayan ta ta jefomata su waja. Mazan dake zaune bakin ƙofar gidane suka taso suna ba Mama haƙuri amma ko kallo basu ishetaba,kuma gashi Baban Safiyya bayanan yayi tafiya tun jiya,kuma Safiyya ma batanan jiya gidan gwaggon ta ta kwana. Mutanin dake wajan da suka ga Mama taki haƙura ita da yaranta sai ɗaya daga cikinsu ya dube Hafsat kana yace,"kinga tunda sunce baziki shigar musu gidaba to kije ki koma gidan iyayenki zaifimiki".....tun bai rufe bakiba sai ga Ammar ƙanin ta yazo wajan,da sauri ya ƙarasa gareta yana faɗin,"Aunty daina kuka zo muje gida kinji,ai kema kinada gidan uba dan ba shegiya ceke ba". Kai ta fara girgiza masa kana tace, "a'a Ammar kaji ne bazanje ba"....jikar kayanta ya ɗauka haɗi da jan hannunta yace dole sai sun tafi,ba yadda ta iya haka suka tafi gidansu. Suna isa gidan har zasu shiga sai ga Baban ta ya fito domin ya tafi wajan aiki sai yayi arba da su,wani kallo yayiwa Ammar shida yake riƙi da hannuta da jikar ta kana yace, "wazan gani a gidana?, wallahi muddin kana son kankai da lafiya kabata kayan ta ta ɓacemin da gani".....tun bai rufe bakinsa ba ta durƙusa gabansa tana kuka tace, "Baba dan Allah kayimin haƙuri wallahi ba lafina bane dan Allah Abba ka koma bani wata dama".....wata uwar tsawa ya daka mata wadda yasa ta haɗe sauran maganar da zata faɗa bata shirya ba. Tswar da yayi ne yasa Ummar Hafsat fitowa bata shirya ba. Hafsat tagani durƙushe da ƙasa ita da Ammar suna ba Baba haƙuri,da sauri ta ƙaraso garesu kana tace, "Hafsat lafiya waya taɓamin ke"....tsawa Abban Hafsat yayi mata haɗi da yimata nuni da ta koma cikin gida. Gabansa tafaɗi tana kuka tana faɗi, "dan Allah Abban Hafsat ki barmin ƴata "......kallon da yayi mata ne haɗi da wata tswa wadda tasa ta komawa cikin gida bata shirya ba. Yana ganin Ummar Hafsat ta koma gida yayi ma Ammar nuni da yashiga gida,ba musu ko yashiga ita ko Hafsat ya nuna mata hanya kana yace, "tunda duniya kike so to gaki gata".. ...yana faɗar haka ya maida ƙofar gida ya rufe yabar Hafsat durkushe da ƙasa tana kuka. Tana ganin ya maida ƙofa ya rufe ta tashi ta haɗa kayan ta zata fara tafiya kenan sai taji zuciyar ta tafara ciyo,lokaci ɗaya mararta ta fara murɗawa amma duk da haka sauri take ta bar unguwar tasu. tayi nisa kaɗan da unguwar ciyon mara yataso mata wannada bata taɓa jin irinsa ba kuma lokaci ɗaya ta gagara tafiya,wani waje ta samu domin ta zauna amma kafin ta ƙarasa ta faɗi,lokaci ɗaya jini ya fara bin ƙafafun ta kuma gashi hanyar mutane basu cika bintaba sai ɗai-ɗai ku. Tanacikin wannan uwar wuyar sai ga wani mai napep ya fito cikin unguwar,tun bai ƙaraso wajan ba yaga mutum yashe aƙasa sai birgima yakeyi,har yasu yayi tafiyar sa sai kuma ya tsaya,jinin da yaga yana fita jikinta ne yasa ya ɗauke ta da sauri yasa cikin napep yashiga ya wuce hospital da ita. Emergency room aka kaita,taimakon gaugawa suka bata kuma cikin ikon Allah sai gashi ta dawo cikin hayyacinta,kana sukayi mata allurar bacci. Doctor ne yafito riƙi da ta kardar magani yaba wannan mai napep yace yaje ya sayo yanzu nan,ba musu ko yaje yasayo magani da ƴan kuɗin da yasamu yanzu da safe har ma da ragoyar najiya,aikuwa yana kai ma Doctor magani bai tsaya komai ba ya kama ga bansa. Bayan doctor yasa mata ruwa da magani yafito dumin suyi magana da wannan mai napep amma bai ganshi ba,haka yayi tajira har yamma kuma bai dawo ba,kuma gashi anasun akaru wasu maganukkan da babu. Har akayi magarb bai dawo ba,kuma lokacin ta farka da ƙarfin jiki sose,Nurses ɗin dake kula da sune taje tasanar da doctor farkawar ta,dan haka da sauri sai gashi yazo,kallon ta yayi kana yace, Mike miki ciyo yanzu?". Tace, "ba komai". Yace, kin tabba ta". "Tace eh". Wanda ya kawoki bai dawo ba har yanzu dan naso nayi masa bayani amma tunda bai dawo ba bari nayi miki bayani dan naga jikin naki da alamun sauki". Mamaki ta farayi to waya kawo ta, gani kamar zata ɓata masa lokaci ne tace, "to inaji". Yace, "da farko dai kiyi haƙuri dan cikin dake jikinki ya zobe.....ai tun bai rufe baki ba wasu hawaye suka fara bin kuncinta haɗi da jero ma Allah godiya cikin ranta. Haƙuri ya ƙara bata ganin hawayen dake zuba a idonta sannan yace,"kuma kina yawan sa damuwa aranki,dan haka ki daina dan kina gab da kamuwa da ciyon zuciya". A hankali ta ɓuɗe bakin ta kana tace, "insha Allahu zan daina". Tambayar ta yayi tana jin unwa tace eh,Nurses yayiwa magana yace taje ta kawo mata tea da magani. Bayan Doctor yafita ta kai dubanta ga kayanta dake kusa da ita,tashi tayi taje gun kayan ta duba kana taga komai akwai dan haka hamdala tayi kana taje toilet tayi wanka,tana fitowa sai ga Nurses tazo da tea da magani aikuwa tanasha ta ƙara jin ƙarfin jikinta sosai ba jimawa sai bacci yayi awun gaba da ita. Ba ta farkaba sai da gari yawaye kuma koda Doctor ya dubata ba wata matsa dan haka ya rubata mata magani haɗi da bata kardar sallama. Yana sallamar ta tashi tayi ta haɗa kayan ta tafice,mai napep ta tare ya kaita makaranta,bayan ta sallameshi ta ɗau kaya tawuce hostel,ɗakin ƙawar ta Naja'atu tashiga kuma koda taje bata sameta ba dan suna cikin makaranta,kayanta ta aje kana taje ta kwanta,bata jimaba da kwanciya ba bacci yayi aun gaba da ita. Koda su Naja'atu suka dawo daga lecture bata farka ba sai kwasar bacci ta take. Dubanta Naja'atu tayi sosai taga Hafsat ce kwance a gado,dan haka da sauri tashiga tashe ta,a hankali ta fara ɓuɗe idon ta ta sauke su kan Naja'atu da sauri Naja'atu tace, "Hafsat dama kinshigo makaranta amma bakije office ɗin shugaban makaranta ba har anyi summiting ɗin takardun da akace iyaye suyi signing dan gobe ne za suje abuja,dan haka kitashi kiyi sauri ki kai kafin yafice daga makarantar". A hankali Hafsat tace, "Naja'atu wallahi bazan iya zowa ba dan ban da lafiya,amma kiɓuɗa jikata ki ɗauka ki kaimasa". Naja tace,"a'a bazaiyi nakai ba dan kinsan sai kinyi signing dan haka tashi narakaki muje". Ba yadda ta iya haka ta tashi suka tafi office ɗin shugaban makaranta,cikin ikon Allah suka sameshi akayi duk abinda ake kana suka dawo hostel. Bayan kwana biyu da faruwar haka jikinta ya warware sosai dan yanzu ba abinda bazata iyayi da kanta ba,kuma ba abinda ake sai shirye-shiryen tafiyar su. Yadda Baba maigida ya same Anwar sosai hankalinsa yatashi dan haka yafito da gudunsa yaje wani gida maƙotansu ya kira wani maigadi ya kamamasa suka kaishi hospital... *#Vote* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 18📑* *__________📖* SHAFI Yasha wuya kafin a samu ciyon cikin ya lafa,sai da a kace musu ya samu bacci sannan Baba mai gida hankalinsa ya ɗan kwanta lokacin kuma ya tuna da yarinyar da tazo ta sanar dashi amma yanzu ba gantaba to ina take?. Tunda Baba Safiyya ya shigo garin, kan hanyar sa ta zuwa gida wani maƙofcin sa ya taresa ya faɗa masa abinda matar sa da ɗiyansa suka wa Hafsat,sose ya nuna bacin ransa a kan haka dan haka bai tsaya wata-wata ba ya ƙarasa gida da sauri ransa a matuƙar ɓace. Tun a suron gida yafara ƙwalama Mamar Safiyya kira yana faɗin, "Suwaiba! Suwaiba! Suwaiba!. Gabanta ne yayi mutuƙar faɗuwa dan abu mai wuyane kesa Baban Safiyya yakira sunan ta,amsawa tayi jikinta a sanyaye. Kallon da yayi matane yasa ta ƙarashiga tashin hankali kana ya buɗe baki yace, "an cemin Hafsat ta dawo amma kin koreta keda ɗiyanki, to bari kiji wallahi duk inda Hafsat take sai kin nemumin ita,muddin kina son kici gaba da zama gidan nan".....yana faɗin haka ya ficewar sa gidan ko takan maganar da take masa bai tsaya bi ba. Sosai Hankalin Maman Safiyya ya tashi kuma lokaci ɗaya ta fara dana sanin abinda tayiwa Hafsat. Ɗakin Safiyya tashiga ta faɗamata abinda a ke ciki kana tace, "Safiyya wai ina kika san Hafsat na zuwa?". A hankali Safiyya ta buɗe baki tace, "wallahi Mama ban saniba , aikune kuka koreta da kunbari Baba yazo duk hukunci da yayanke ba shikenan ba amma kuce sai kun koreta,kuma ni ko makaranta na daina ganinta bare nasa ran zan ganta". Sai da Mamar Safiyya ta shafe hawayen da suka zobu mata kana tace, "idan Allah ya kaimu gobe kiƙara dubumin makarantar ku, ko Allah nasa tana can". Safiyya tace, "tau Mama Allah yasa a dace". Tace "Ameen Safiyya". Haka suka kwana Baban Safiyya na zuba musu masifa Ita ko Ummar Hafsat tunda Abban Hafsat ya umarceta da ta koma gida aikuwa tana shiga gida ta fara kuka mai cin rai,lokaci ɗaya ta fara tunanin ƴan uwanta da iyayenta, dan da tana tare da iyayen ta da bazaiyi mata haka ba, gashi yanzu ya rabata da iyayenta kuma yanzu ya rabata da ƴarta kwaya ɗaya tak, lokaci ɗaya ciyon zuciyar ta yatashi, cikin ƙanƙanin lokaci tafara fita hayyacin ta,aikuwa Abban Hafsat naganin haka ya hankalinsa yayi ƙololowar tashi,da sauri ya ɗauke ta yakai mota suka wuce hospital dan a lokacin sheɗarta tayi sama kamar zata fita. Bayan kwana biyu da dawowar shugabanin makarantar su abuja aka aika kiran ɗaliban da za suyi wannan tafiyar,bayan kowa yazo aka bashi duk wani abinda zaya buƙata acan kana aka faɗama kowa ƙasar da zaije karatu,haɗi dayi musu nasiha mai ratsa zuciya, Hafsat ita da wasu maza huɗu su za suje India karatu haka dai akaraba kowane department namiji huɗu mace ɗaya, kowane da ƙasar da aka turashi. Bayan angama rabamusu kayansu da wani abin affanin su kana akace kowa yaje yayi bankwana da iyayensa da ƴan uwansa da kwana uku ne suka ragemusu da su tafi, kuma ga rana ta uku za suwuce abuja dan daga canne za suyi tafiyar. Bayan angama yi musu bayani kowa ya kama gabansa, wasu ma suna fitowa suka wuce gidan iyayensu, murna fil a zuciyar su. Saɓanin Hafsat , dan inkowa na murna ita kuka take haɗi da fargaba, dan itakam ba wanda tasan zata je tayiwa ban kwana dan ba mai sonta dan ko iyayenta sun koreta bare ma wasu, haka ta koma hostel ciki da baƙin ciki da dana sanin bin *UMARNIN SAURAYI* da kuma biyema Hajara. Tana isa hostel ta faɗi kan gado tafara kuka kamar ranta zai fita, Naja'atu ba irin magiyar da batayi ba ta faɗa mata damuwar ta amma taƙi, daga baya data ga bata son faɗamata ta dawo rarrashin ta tana faɗin, "haba Hafsat keda yaka mata ki kasance cikin farin ciki amma gashi sai kuka kikeyi, ai Allah ya kamata kiyima godiya bakiyi ta kuka ba, ai duk gamu muna so amma Allah ke ya zaɓa dakije dan haka dan Allah kitashi ki daina kuka please".....haka dai tayi ta bata magana har tasamu ta daina kuka kuma daga baya sai ga zazzaɓi yarufe. Bayan sun isa hospital likitoci suka dubata kana suka bata gado, sai da ta kwana sannan Ummar Hafsat ta farfaɗu, bayan likitoci sun ƙara dubata suka tabbatar da ciyon ya lafa kana suka ba Abban Hafsat izinin shiga ya ganta. Koda ya shiga tana kwance kanta na kallon cilin alamu kamar tunani take, a hankali ya ƙaraso gab da gadon da take wance, ƙujerar dake wajan ya jawu ya zauna kana ya ɗura hannansa saman nata, sai a lokacin tasan da yashigo, dubansa tayi haɗi da fitar da kwalla kana tace, "Abban Hafsat, inason nayi maka wata magana wadda ban taɓa yimaka irin taba, dan haka bari kaji, da farko dai inason naje ga iyayena, na biyu kuma ina har kanaso nacigaba da zama da kai amatsayi mata to ba shakka sai ka nemumin ƴata wallahi ban zan iya jure rashin taba a halin da nake ciki, muddin kana so nacigaba da rayuwa sai kanemun ƴata......kukane ya kufuce mata lokaci ɗaya ta furta ashe haka iyaye keji idan ƴa-ƴansu sukayi nesa da su?".....tarine yaci ƙarfinta kuma gashi tana tari sai jini ya biyu baya, sosai hankalinsa ya tashi dan haka da gudun sa yaje ya ƙira doctor, koda Doctor yazo halin da yasame Ummar Hafsat baƙarimin tayar masa da hankali yayi ba, sauran ƴan uwansa likitoci ya kira suka zo dumin a ceto rayuwar ta. Wannan karun Abba da yaransa gabaki ɗaya hankalinsu ya tashi aka rasa ma me rarrashi wani, su yaran sai kuka suke aka rasa wazai ba wani haƙuri a cikin su, lokaci ɗaya shima ya fara tuni ƴan uwansa. Baban Safiyya ne ya hana kowa zama yace wallahi sai sun nemumi shi Hafsat kan su samu kwanciyar hankali, aikuwa haka suka je neman ta amma duk inda suke tunanin zata je bata jeba, sosai hankalin mamar Safiyya ya tashi da ita da yayan Safiyya dan Baban Safiyya yafi ganin laifinsu akan nakuwa. Mamar Safiyya tace ma Safiyya taje makarantar su taga ko tana can, sai Safiyya tace bata can da yanzu weekend ne amma wata ƙila Monday tashiga. Haka dai suka cigaba da nemanta cikin kwana biyu hankalin su tashe. Anwar yanzu yasamu sauƙi dan har abinci ya kanci saɓanin lokacin da aka kawoshi, bayan ya dawo hankalinsa yake tambayar mai gida Hafsat, sai mai gida yace shi bai saki ganin taba tun lokacin da tafaɗimin baka da lafiya. Hankalinsa ne ya tashi sose amma yayi alwashin da ya fita daga hospital duk inda take sai ya nemuta. Tunda dare duk wani abin buƙata Hafsat ta haɗashi cikin ikon Allah da taimakon ƙawar ta Naja'atu dan yanzu Naja tasan waye Hafsat itama tasan waye Naja. Tun ƙarfe huɗun dare ta tashi tayi wanka haɗi da shiryawa dan ita bata son ajirata kuma gashi antabbatar musu ƙarfe shidda na safe za su tashi zowa abuje dan ƙarfe goma jirginsu zai ɗaga. Bayan tashirya suna zaune suna fira Naja'atu ta ɗako wasu kuɗi ta bata tace, "Hafsat, ga wannan canjin kiriƙi a hannuki kafin su baku kuɗi yana da kyau kirƙi koda kinga wani abu ko ace kasaya da kanka". Kai Hafsat tafara girgiza mata kana tace, "dan Allah Naja kibarsu wallahi ko yanzu nagode da karmcin da ki kayimin dan Allah kibar kuɗinki dan nasan duk wani ɗan makaranta yana buƙatar kuɗi".....tun bata rufe bakin taba sai Naja tace, "Nasan da haka amma duk baki karɓa ba bazan ji daɗi ba". Ba yadda ta iya haka ta karɓi kuɗin haɗi dayimata godiya sose. Suna zaune a ka kira sallah asuba dan haka suka tashi sukayi alwala suka gabatar da sallah. Hospital koda Umma ta farka ba abinda take kira sai sunan Hafsat, Abba na cikin bacci yaji ta farka kuma da sunan Hafsat a bakin ta, doctor yaje ya faɗa masa farkawar ta. Bayan doctor yazo ya ƙara dubata kana ya koma yimata allurar bacci kana ya dube Abba yace, "gaskiya yana da kyau kaje kanemu mai wannan sunan dan wallahi da gani tana buƙatar taga mai wannan sunan, kuma kodan matsalar ta ya kamata kanemuta dan mu kan mu zamuji daɗin haka ". Yana faɗan haka yafice daga ɗakin ya bar Abba da tunani. Tunanin yaga bashine mafita ba dan haka yakira ɗansa Marwan yace yayi sauri yazo dan fita yake sunyi. Ba ɓata lokaci sai ga Marwan yazo yana zuwa yayi masa sallama ya fice daga hospital hankali ta she. Sai da ya fito ya fara tunanin ina zaije neman Hafsat, a nanne hankalinsa ya tashi saura kiris ya faɗi ƙasa a wannan lokacin. Gidansu Safiyya ne ya faɗomi shi a rai, dan haka da sauri yayiwa mota kye ya tafin gidan nasu. Yana isa gidan dai-dai Safiyya tafito domin taje makaranta neman Hsfsat,da jiya ba wanda ya runtsa a cikin su dan Baban ta yaki bari kowa ya runtsa sai masifa yake musu. Tana ganin Abban Safiyya da sauri tazo gareshi ta fara gaidashi, bai ma karɓa ba ya jefumata tambaya yace, "Safiyya ina Hafsat?". Kasa karɓa masa tayi sai da yasake mai-mai tamata kana ta ɓuɗa baki idonta na fitar da kwalla kana tace, "muma itace muke nema yanzu ma haka school ɗinmu ce zanje na ƙara dubawa ko zan sameta".....tun bata rufe bakinta ba Abban Hafsat yace, "Shigo mota mutafe ko Allah nasa mudace". Tace, tom". Haɗi da buɗe mota tashiga. Har zasu tafi sai ga yayan Safiyya yafito, ganisu dayayi ne yasa da gudunsa ya zo garesu, bai ma tsaya tambayar ina za su je ba ya buɗe mota yashiga kana suka kama hanya.. Tun shidda saura motocin da za su kaisu abuja suka ƙaraso, kuma ba ɓata lokaci duk waɗanda za su yi tafiyar suka zo kowa yashiga motarsu, kuma kowace mota namiji huɗu macce ɗaya. Kowa ƴan uwansa suka rakoshi saɓanin Hafsat da ƙawarta ta rakota, lokacin da zata shiga motar jikin Naja ta laƙe sai rusar kuka take ba ƙau-ƙautawa, da ƙyar Naja ta rabata da jikinta tana bata haƙuri kana ta buɗe mata mota tashiga dan tafiya za suyi. Har motoci za su fara tashi sai Hafsat ta buɗe jikarta ta dauko wata takarda taba Naja tace dan Allah kibawa Safiyya". tana bata motoci suka fara tafiya..... *Dan Allah kuyi haƙuri da wannan* *#Vote* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 19📑* *__________*📖 Hawayen da suka zoba a idonta ne ta shafe haɗi da ɗaga musu hannu har suka fita daga makarantar, sose ta tausaya ma Hafsat wannan halin da takeci, ita dai fatar ta Allah yasa Hafsat suyi nasara a karatun da suka je. Bayan kamar minti goma da tafiyar su, sai ga motar Abban Hafsat ta shigo hara bar makarantar cikin hanzari, suna shigowa Safiyya ta hango Naja zaune tayi tagumi kamar mai tunanin wani abu, tun Abban Hafsat baiyi packing ɗin mota ba tace, "Abba bari naje ga ƙawarta can nasan wata ƙila tasan gun da take"....tun bata rufe baki ba yace, "je kisame ta Safiyya". Da sauri ta ɓuɗe marfin mota tafito ta ƙarasa wajan da Naja'atu ke zaune tana tunanin Hafsat. Sallama tayi mata haɗi da gaishe ta, Naja ta amsa mata haɗi da murmushi a fuskar ta kana tace, "Safiyya ke kuwa nake nema kuma gashi har sun wuce baku haɗu ba, amma tabani saƙo nabaki".....cikin hanzari Safiyya tace, "wace?" Tana faɗa tana zare ido. Jikin Naja a sanyaye tace, "Hafsat". Jikin Safiyya na karkarwa tace, "ina taje Naja". Ahankali ta ɓuɗi baki tace, "kin san ai tasamu scholarship na zuwa india karatu, to shine suka je yanzu ". Ido ta zare kana tace, "Hafsat ta tafi kenan? ina zanganta Naja, dan Allah ki gayamin ina zan sameta, wallahi muna matuƙar buƙatar ta".....kuka ne ya kufuce mata sose wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar da zatayi. Wajan da Abba yake shida Yaya Abbas suna hangota, dan haka da sauri suka ƙaraso gare ta suji mitake ma kuka. Ko da suka ƙaraso tafaɗa jikin Naja sai rusar kuka take kamar ranta zai fita tana faɗin, "Naja dan Allah ki gayamin inda zangan ta".....Abban Safiyya ne da ya ƙaraso yace, "Safiyya lafiya kike kuka? kodai ta ɓata ne?". Baki ta buɗe tana son magana amma ta kasa sabida kukan da yaci ƙarfinta. Naja ce tamasa bayanin abinda ake cike. Ai tun bata kai da rufe bakinta ba, Abban Safiyya yayi magana cikin rawar murya yace, "wani airport za su shiga jirgi?". "Na abuja". Tafaɗi haka ataƙaice. Hankalinshi ne yayi ƙolo-lowar tashi, aikuwa ba shiri yakai zaune haɗi da dafe kansa, dana sani da baƙinci suka haɗe masa waje ɗaya, tunani ya fara to ina zai ganta? da sauri ya miƙe tsaye kamar wani zararre , duban sa ya kai ga Safiyya yace, "ta tashi mutafi" ba musu ta tashi sai famar rusa kuka takeyi. Irin yadda Naja taga halin da Abban Hafsat ya shiga a wannan halin ne yasa hawayen da suka maƙale a idonta tun tashi su Hafsat suka zobo bata shirya ba. Yana ƙarasawa wajan mota ya buɗi mota ya shiga, suma suka shiga dan shi Yayan Safiyya kasa magana yayi sabida bai san mi zai ceba. Gida ya sauke su kana ya koma hospital, koda ya shiga ɗakin da Mama take lokacin ta farka, kuma sai sunan Hafsat take faɗa, gashi jininta ya hau kuma duk wani taimako da likitoci za su bata sun bata amma jinin yaƙi sauka dan ko bacci takasa samu sai sunan Hafsat da take kira. Abinda ya gani ne lokacin da ya shiga ɗakin yayi matuƙar bashi tsoro, dan ƙirs kaɗan ya kai ƙasa, ɗayan likitan da yaga shigowar sa ne yayi masa magana yace, Kazo da Hafsat ɗin ko?". Abban Hafsat rasa bakin magana yayi,sai can da yaga likita ya tsare shi da ido kana ya buɗa baki yace, "gatanan zuwa, amma bari² na kirata"..... Yana faɗin haka ya fice bai ma tsaya jin mi likita zai ce ba. Yana fita daga ɗakin yaga Ammar zaune yayi ta gumi yana tunani, sunan sa ya kira kana yace, "Ammar ba tunani ya dace kayi ba, addu'a ita tafi dacewa da ita, dan haka ga kuɗi ka riƙe ko za su buƙaci wani abu kasayu, dan ni yanzu wanuri zanje na dawo, amma kar kaga najima ban dawo ba dan zanje wani wuri mai ɗan nisa". Yace, "tau Abba Allah ya dawo da kai lafiya". Yace, Ameen".....kana ya fice daga hospital ɗin cikin sauri. Mai napep ya tsayar ya faɗa masa wurin da zai kaish, ba ɓata lokaci ya isa ta shar mota, kuma koda yaje motar abuja saura mutum biyu ta ciki, dan haka yace sutafi shi zai biya kuɗin ɗayan, ba ɓata lokaci suka ɗau hanyar abuji ciki yake da fargabar Allah kasa ya ganta. ***** Hajara ce tafito cikin shiryan ta cikin wasu ƙananun kaya musu bayyanar da surar jikin mutum sose, iya kyau tayi, sai da kashiii, idan ka ganta bazaka ɗauka ƴar musulmi bace, tafiya takeyi kan titi sai can ta tsayar da mai napep ta faɗa masa wurin da zai kaita kana tashiga, basu tsaya da ita ko ina ba sai hospital ɗin da aka kwantar da Anwar. Bayan ta sallame shi taƙarasa cikin ɗakin da aka kwantar da shi, tana wata tafiya kamar bata son taka ƙasa. Ahankali ta tura ƙufar ɗakin da yake kwance tashiga, kwanci ta tarar dashi yana baccin sa cikin kwanciyar hankali, dan idan ka ganshi zaka zata lifiyar sa ƙalau. Kamar anshigo ɗakin yaji, dan haka da sauri ya buɗi idonsa, Hajara yagani, itako tana ganin ya farka da sauri ta ƙaraso gareshi tana faɗin, "Gaskiya kaji sauƙi sose "....tana faɗa tana sakar masa da murmushi haɗi da kai hannuta saman nasa. Sai da yagama yimata wani kallo kana yace, "eh naji sauƙi, dan yau ma nake son su sallameni naje gida dan so nake muje kikaini wajan Malamin da kikace". Tace, "to kama daina wahalal da kanka da wadda kake danta ta bar ƙasar gabaki ɗaya". Tun bata rufe baki ba ya ɗago kansa da sauri yace,"wace kenan!. Yafaɗi haka cikin razana. "Hafsat". tace dashi ataƙai ce. Ido ya zare haɗi da cakomuta kana yace, "ina kika kamin ita?". Dariya ta sanya masa kana tace, "scholarship tasamu, yanzun nan ba jimawa motocin makaranta suka ɗauke su zuwa airport ɗin abuja dan acan ne za su tashi. Ai tun bata rufe bakin ta ba ya ɗauko waya yakira wata number, ana ɗauka yace, "Salim zai samu jirgin da zai kaini abuja yanzu?". Bansan mi akace dashi aɗayan ɓangarin ba yace, "oky ganin zuwa yanzu". Ko kallon ta baiyi ba ya ɗau kayansa ya bar hospital ɗin, batari da an sallame shiba. Har zai fita tayi sauri taci gabansa tace, "ina zakaje ne?". Ko kallon ta baiyi ba ya ture ta gyafe ɗaya ya fice warsa. Bayan shi ta biyu tana kiran sunanshi, yana jinta amma yayi kamar bai jiba. Haka har yazo kan ti-ti ya tsayar da mai napep ya shiga tana kallo amma batayi gi-gin magana ba dan taga yau ba sauƙi, filn jirgi ya kashi, kuma yana sauka ba ɓata lokaci jiringin nasu ya ɗaga. Tunda suka shiga motar ta haɗe kanta da ƙafafunta sai famar rusar kuka takeyi kamar wadda za'a raba da ranta. Ko waɗan da suke tare a motar ba wanda bai mata magana ba, har dai suka gaji suka kyaleta, tana kuka haka dai har bacci ya ɗauke ta. Cikin ikon Allah tara da rabi suka isa airport ďin Abuja, kuma koda suka ƙaraso ba ɓata lokaci suka shiga jirigi suka wuce India. Minti talatin da ta fiyarsu sai ga Anwar ya dira garin abuja kuma aka tabbatar masa da basu jima da tashi ba. Wata ƙara yasaka sabida wani bakin cikin da ya rufeshi, rasama abinyi yayi, sai can ya ciji yatsa kana yace, "wallahi ko ƙarshin duniya kika kai Hafsat sai na nemuki, bari makarantar india". Awa ɗaya da tafiyar su Hafsat sai ga Abbanta ya shigo garin abuja, ba ɓata lokaci yasa aka kawoshi airport ɗin garin, tambaya yayi ko jirigin india ya ɗaga aikuwa aka tabbatar masa da ya ɗaga nan da awa ɗaya da suka wuce. Aikuwa ba shiri sai ga hawayen baƙin ciki sun fara zoba a idonsa, lokaci ɗaya ya fara rawar sanyi, kuma lokaci ɗaya ya hango halin da matar sa take ciki, ba shiri ya samu waje ya zauna haɗi da dafe kansa..... *#VOte* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 20📑* *__________*📖 Ya kai kusan minti talatin a wajan yarasa mi zaiyi, zaman da ya keyi yaga bashine mafita ba dan haka ya tashi jikinsa a sanyaye ya tafi. Tashar mota ya koma, kuma cikin ikon Allah koda yaje mutan ɗaya ake jira motar ta tashi, haka yashiga bawani ƙarfin gwuwa atari dashi. Safiyya da Yayanta suna shiga gida Baban ta yafara tambayar su ina Hafsat?. Gaba ɗayansu kasa magana sukayi,dan kowane bakinshi yayi masa nauyi sose, tambyar su ya ƙarayi cikin faɗa², Safiyya har ta buɗi baki tayi magana sai kuma ta rushe da kuka tana faɗin, "Baba dan Allah kayi haƙuri".... tsawa ya daka mata kana yace "baza ku faɗamin wurin da kuka kaimin ƴar ba?". Abbas ne yayi ƙarfin halin buɗa baki yayi masa bayani, ai Mamar Safiyya najin haka ta faɗi ƙasa tana ba Baban Safiyya haƙuri, shi Baban Safiyya sabida baƙin ciki kasa magana yayi, bai ce komai ba ya saka takalman sa ya fice gidan, sabida yasan da ya buɗa baki ba zai faɗi abu mai kyau ba. Sai bayan isha'i Abba ya sauka, masallaci yaje yayi sallah, yajima zaune yana addu'a samun mafita kana ya tashi yaje hospital jikinsa a sanyaye dan duk yinin yau ba abinda yasama cikin sa sabida tsananin tashin hankali. A hankali ya shiga ɗakin da aka kwantar da ita, Ammar ya fara cin karu dashi yana zaune saman kujera yana kallon Mamar sa, buɗa ƙofar da akayi ne yasa ya kai dubansa ga ƙofa, Abban sa yagani, aikuwa da sauri yazo yatare shi haɗi da faɗin, "Abba barka da zuwa". Sai da ya zauna kan kujera kana yace, "Ammar ya jikin Ummar taka?". "Da sauki yace". Dubansa yayi da kyau kana yace, "tun yaushe take bacci hala". Yace "bayan fitar ka ba jimawa". Tea ya haɗa yasha kana yace bari yaje gida yayi wanka idan ya dawo sai Ammar yaje. Tunda taga Anwar yashiga ke-ke napep yabar ta tsaye takasa koda ɗaga ƙafa ta tafi bare ta mutsa, sose abin da Anwar yayi mata ya bata tsoro, to me Hafsat take dashi wanda ita bata da?, tunanin ne taga bashine mafita ba tayi kyafa kana ta tsayar da mai napep, sunan wata ungwa tafaɗa mishi tashiga ya kaita. Abba na fita Umma ta farka haɗi da ƙiran sunan Allah, da sauri Ammar da ke kusa da ita ya ƙaraso gareta yana faɗin, "Umma ya jikin, mike miki ciyo?". Buɗar baki tayi ahankali tace, "Ammar ba abinda kemin ciyo yanzu" sai da ta ɗan huta tace, "ina Abbanka yake ko har yanzu bai zomin da Hafsat ba?". Ammar kasa magana yayi sai can yace, "kiyi haƙuri Umma nasan zai zo da ita". Komai bata saki faɗa ba, amma tayi alwashin in har dai ta fita daga wannan hospital to ba shakka sai taje gida ganin iyayenta, dan tasan ko hakkinsu na kanta, amma ya ta iya tunda ba laifinta bane. Bayan kwana biyu da faruwar haka jikin Umma yayi sauƙi sose dan har abinci tana iya ci da kanta, sai dai wasar ɓoyar da ake tsakanin Abba da Umma, dan yanzu baya son shigowa sai tayi bacci, dan baya son ta tambaye shi Hafsat. Itako da ta lura da haka data ji alamun zai shigo sai tayi kamar bacci take har sai yafita kan ta buɗe idonta. Yau Monday, Doctor nashigowa ya tambaye ta yatakeji gami da lafiyar ta, sai tace batajin komai, magani yarubuta mata haɗi da takardar sallama kana ya ƙara jamata kunne akan ta daina sa damuwa aranta. Bayan Doctor yafita Ammar ya ƙira Abban sa ya sheida masa ansallamesu, ba jimawa kuwa sai ga Abba yazo sutafi, kayansu suka saka a mota kana suka shiga suka tafi gida, amma duk wannan abin Abba yakasa haɗa ido da Umma har suka ƙaraso gida. Yana sauke su ya wuce wajan aikin sa, da yamma bayan ya dawo daga aiki har zai shiga gida sai suka haɗu da Baban Safiyya, bayan sun gaisa sai Baban Safiyya yace, "Kunɓatar min da ɗiya hankalinku ya kwanta ko?". Murmushi Abban Hafsat yayi kana yace, "ayi haƙuri Alhaji,fushin zuciya ne da sharin sheiɗan, amma dan Allah ayimana haƙuri wallahi yanzu haka ni kaɗai nasan halin da nake ciki, amma dan Allah kar ayi fushi damu a cigaba da sanyamu a addu'a". Sai da Abban Safiyya yayi murmushi kana yace, "ba komai, kuma inaji ajikina ƴata tana hannun nagari, kuma insha Allahu lafiya zata dawo".....daga nan suka cigaba da firar su, daga baya sukayi ma juna sallama suka wuce. Ƙarfi tara da rabi na dare, jirgin su Hafsat ya sauka a airplane ďin India, aikuwa tunda jirigin ya sauka taji gabanta ya fara dukan uku-uku, lokaci ɗaya wasu hawaye masu zafi suka fara antayu mata, abukin tafiyar sune Sulaiman yace, "Hafsat ki shafe hawayinki ki taso mu fita".....yana faɗa yana tashi domin su fita. Bayan sa ta bi har suka zo matakalal jirgi, yana gaba tana biye dashi suma sauran na biye da su, aikuwa tana taka matakalar farko, sai wani iska mai haɗi da sanyin daɗi ya ziyarce ta, bashiri ta buɗa baki haɗi da ɗago harshin ta tafara yiwa Allah kirari..... *#VOte* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 21📑* *__________*📖 A hankali taci gaba da ta kawa saman mattakalar jirgin har ta sauko, suna sauka gaba ki ɗaya, ba jimawa sai gashi anturu motar da zata kaisu makarantar. Bayan angama duba jukkunan su kana suka shiga mota suka kama hanyar da zata sa dasu da makaranta, basu tsaya ko inaba sai bakin gate ɗin makarantar, kafin su shiga da ga ciki sai Hafsat ta dago da kanta, dan tun lokacin da suka shiga motar kanta na kasa taƙi ta ɗago bare taga jajayin fata . Aikuwa tana ɗago kanta sai da tayi suman zaune, dan ganin wannan katafariyar makaranta da tayi sai da tayi tasbihi ga Allah, makarantar tabi da kallo, wadda aka rubuta sunanta da manya haruffa, wato (GALGOTIAS UNIVERSITY). Bata ƙarasa kallon ba direban motar ya shiga cikin makarantar, bai tsaya dasu ko ina ba sai gyefin saukar baƙi da ke cikin makarantar, bayan sun shiga sun zauna aka kawo musu abin motsa baki, bayan sun kammala kowanin su yayi wanka ya ɗan huta kafin safe sai su fara shiga makarantar. Sulaiman ne ya kalle abukain tafiyar sa kana yace, "wai ina Hafsat?, ayya taci wani abu kuwa?, dan nasan ƙila bataci komai ba tana can tana sana'ar ta ta kuka". Sai ɗayan wanda akekira da Safuwan yace, "wata ƙila bata ciba, amma bari nayi mata knocking idan ta fito zamu gani ko taci". Yana faɗa yana tashi dan ya ƙarasa ɗakin da akayi mata ma sauki. Knocking da bai wuce uku ba ta ɓuɗe, wannda tagani bakin ƙofar ɗakin yasa ta ƙaƙalo murmushi haɗi da yin ƙasa da kanta, kafin ta ɓuɗa baki tayi magana yace, "Idan kin kammala muna son magana dake". Tace "tom gani zuwa". Yana barin wajan itama ta koma ɗakin ta shirya jikinta tasaka hijba kana ta fito wajan su. Sallama tayi musu, suka amsa haɗi da bata izini sannan ta shigo. Bayan ta shigo ta gaishe su haɗi da musu ban gajiya kana ta zauna. Dukan su suka amsa kana suka tambaye ta ko taci wani abu ba kuka taje tanayi ba?. Sai da tayi murmushi kana tace, "wallahi naci kuma na koshi". Suka ce to hakan yafi sannan suka ɗan taɓa fira gami da yadda karatun su zai kasance a wannan ƙasar, bayan sun ɗanyi shuru sai Sulaiman ya dube su kana yace, " Gami da zaman Hafsat hostel ne, duk da hostel ɗin ƙasar yana da kyau amma ina ga kamar zaifi in kin yarda ko kun amice sai na kaita gidan Yaya ta dan itama karatu takeyi anan kuma tanada miji da yaro ɗaya, amma shi mai gidan nata sai wani lokaci ya kan shigo kuma ba zai wuce kwana biyu ba ya koma, dan wancan lokacin da nazo acan na zauna kuma naga zaki fi jin daɗin zama acan gaskiya, amma inkunga hakan yayi muku kuma yayi miki". Gaba ki ɗayan su sukayi na'am da maganar sa kana ya dube Hafsat da tayi shuru ba tace komai ba yace, "Hafsat mikika ce akan maganata". Ahankali ta ɓuɗa baki tace, "ba abinda zance tunda ni ban san kan ƙasar ba, amma tunda kai kasan kan ƙasar duk yadda kayi ba komai, sai dai kar mutakura ta". Yace, "a'a kar ki damu dan Aunty Shemah ta wuce haka". Sai da suka gama tattaunawa kana tafito ta koma ɗakin ta kafin safiya ta waye aba kowane class sai kuma ta wuce gidan da zata zauna. ******* Wata unguwace mai napep ya sauke ta, bayan ta sallameshi tashiga wani longo tana shiga tafiya kaɗan sai tazo ƙofar wani ɗaki, da yake ɗakunane jere a unguwar kuma da gani ɗakunan hayane, na tsaka daga cikin su ta tura ƙofa tashiga. Ƴan mata biyu ne aciki ɗayan na kwance ɗayan na shirin kayan sawar su, aikuwa suna ganin ta gabaki ɗaya suka buga shewa haɗi da faɗin, " Matar Anwar ce tazo wurin mu?". Sun faɗi haka ciki da tsokana. Tsaki ta musu kana tace, "kubarni da ɗan iska, wai yau ni zaima walaƙanci akan wata banzar yarinya, wallahi naga har yanzu kansa bai daina rawa ba, amma dani yake zanci". Tafaɗa haka ranta amatuƙar ɓace. Ɗayan wadda ke kwance mai suna Zahara ita tace, "me ya haɗaki da Anwar ɗin naki hala?". Kafin tayi magana sai ɗayan mai shirin kaya wato Hafiza tace, "ta tsoniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ni dai wallahi Hajara da zaki bi tawa da kinbar Anwar da Hafsat, dan wallahi ko da zaki je wurin bokayin duniyar nan ba zai iya rabuwa da Hafsat ba, dan ni nasan son da yake ma Hafsat cikin jininsa yake, amma dan baki da imani kikabi kowace hanya kika lalata musu zama to gashi gaki ya aure ki .....aitun bata kai da rufe baki ba Hajara ta miƙi tsaye zata cikumo ta sai Zahara tayi saurin tashi tariƙi Hajara tana faɗin, "dan Allah Hajara ki kyaleta idan har ta isa tasa Anwar ya aure Hafsat, kuma bari kiji, wallahi Anwar koda mi yake taƙama sai ya aureki barin ni dashi, ai inyasan wata bai san wata ba". Hafiza tace, "kanku akeji" tana faɗin haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice batare da tasaki magana ba. Tana fita sai Zahara ta dube Hajara da tacika tayi fam, abu kaɗan take jira ta fashe, Zahara irin yanayi da taga Hajara tashiga yasa ta ƙarasowa jikin ta sose, haƙuri ta fara bata kan ta ɗura hannunta saman dukiyar fulaninta, haɗi da kai bakinta kan na Hajara,kissing ɗinta cikin sigar rarrashi. Sai da suka gama fanɗarewar su kana Zahara ta ƙara matse Hajara jikita tana faɗi, "ke daina sama ranki damuwa, indai Anwar ne kina zaune zaki gansa dan haka ki bar komai a hannu na nasan yadda zanyi da shi". Dubanta Hajara tayi, taga da gaske take dan haka tace, "nagode masoyiya ta, haka dai suka cigaba da firar su daga baya kuma Hajara tayi mata sallama ta koma unguwar su. Tunda Umma ta dawo daga hospital ta daina sakin jikinta da Abba dan yanzu ma haduwa wuya take musu, yau ma da dare bayan ya dawo daga masallaci ta kai masa abinci yaci har yayi shirin kwanciya sai gata ta turu ƙofar ɗakinsa haɗi da sallama. Bayan ya amsa mata ya ɗago da kansa ya kalleta ciki da son matar tasa yaci, "ƙaraso daga ciki Fatima". Ba muso ta ƙaraso ta samu waje ta zauna nesa kaɗan dashi. Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi saurin cewa, "Abban Hafsat, dama maganar da zan faɗa itace, ina son zanje gidan iyayena dan ina son naje na gansu, ko banza najima banje ba,kuma idan naje bazan dawo ba har sai ka nemumin ƴata". Tana faɗar haka ta miƙi dan ta fita. Da sauri ya ƙaraso gareta yana faɗin, "haba Fatima miyayi zafi haka, dan Allah karki barni wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki, kuma zanci zuwa gida ki bari idan nasamu huta muje tare, dan koni ina son naje naga gashesu"......ai tun bai kai ƙarshin zanciba ta fice daga ɗakinsa yana kiranta amma tayi kamar batajiba ta shige ɗakinta haɗi da rufe ƙofa. Tanda ta rufe ƙofa ta fara kuka mai cin zuciya da baƙin cikin rashin inda ƴar ta take, amma a gaskiya baza iya cigaba da zama ba Hafsat ba, inhar yana son taci gaba da zama dashi sai ya nemu mata ƴar ta, dan gobe tunda safe zata ta kama hayar garinsu ko da kuwa ba zata gane gidan ba, dan ita gani take bazata gane gida ba, dan rabunta da gida kusan shekara ashirin, aikuwa tana tuna haka ta fara kuka maicin zuciya. Ko da yazo ga ƙofar yaga har ta rufe, ai basan sanda ya dafe kansa ba haɗi da faɗin "ya salam".....kansa ne yaji ya fara sarawa, dan haka ya koma ɗakinsa ya zauna haɗi da ɗauko magani yasha kana ya kwanta. Koda gari ya waye bayan sun gamala komai sun shirya sunyi beark aka turu azo dasu cikin school ɗin. Bayan sunje aka ba kowa nasa abinda za'a bashi kana akayi musu jagora zuwa class ɗinsu. Bayan sun gama lecture ne sai Saulaiman shida abakan tafiyar su suka kai Hafsat gidan Aunty Shemah, kuma gidan ba nisa da school ɗin, shiyasa batayi wuyar ganewa ba. Bayan sun shiga gida Aunty Shemah ta karɓe su hannu biyu² haɗi da kawu musu kayam mutsa baki, bayan su ɗan ci abinda ta kawo musu nan Sulauman ya ƙara yimata bayani akan Hafsat itama Hafsat ya ƙara yimata bayani akan Aunty Shemah. Aunty Shemah sose tayi murna da samun abukir zama, dan zaman kaɗaice bayayi mata daɗi, dan mijinta bayar da taje ko inaba daga makaranta sai makaranta,wani ɗaki ta nunama Hafsat tace tazo ga ɗakin da zata zauna ,tashi tayi tabi bayan ta tanuna mata ɗakin, sose ɗakin yayi mata kyau, dan ɗakine mai haɗe toilet da ƙaramin gado da wadiruf, bayan komai ya kammala sai Sulaiman yayi musu sallama yayi tafiyar sa. *Wanene Anwar* *#Veto* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 22📑* *__________📖* Anwar hafafin ɗan garin kaduna ne, sunan mahaifin sa Alhaji Umar, fittacin ɗan kasuwa ne kuma babban ma'akacin gwamnati, yayi suna a cikin gari kaduna sose, dan kowa yasan Alhaji Umar dallah-dallah ,mahafiyar sa Hajiya Ruƙayya, suna da yara huɗu, Zainab, Hafsat, Sajida, sai autansu Anwar, iyayen su suna nuna musu so da ƙauna sosai, musamman Anwar da ya kasance auta, dukan su sunyi karatu mai zurfi sannan sukayi aure, yanzu Anwar ne ya yarage baiyi ba, kuma koshi iyayen sa na son yayi amma sai wani ƙaƙale² yake musu shi sai yayi karatu mai zurfi, bayan ya kammala karatun sa ne ya ƙaƙalo zuwa sokoto dan ya dubama mahaifin sa wani ƙamfanin shi, to acan ne ya haɗu da Hafsat har ya fara soyayya da ita, sosai yake son Hafsat kuma har cikin ransa aurin ta zaiyi sai daga baya sheiɗan ya shiga tsakanin. *Cigaban labari* Anwar dake airport sai kai da komowa ya keyi yarasa abinyi, ji yake kamar yayi tson-tso ya ganshi Indian, rasa abinyi yayi dan haka ya tsayar da ɗan aceɓa yace ya kaishi wata unguwa. Dai-dai wani katafarin gida ya ajeshi, kud'i ya bashi bai ma tsaya karb'ar canjiba ya wuce cikin gidan, mai gadi na masa magana amma ga baki d'aya hankalin sa bai tare da shi shiya sa bai karb'a masa ba ya wuce cikin gidan. Bai tsaya ko ina ba sai wani ƙayataccin falo wanda aka ƙawatashi da kayan ado na more rayuwa,iya haɗuwa wannan falon ya haɗu, ɗayan kujerun ya zauna haɗe da dafe kansa lokaci ɗaya yaji kansa ya fara sarawa, carpet ɗin dake shinfiɗe atsakar parlour ya kwata, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awun gaba dashi. Aunty Zainab ko da ta fito kwance ta ganshi a tsakiyar parlor, ba tama ganeshi ba sai data kara masa kallon kana tagane Anwar ne, da sauri ta ƙaraso gareshi tafara ta dashi tana faɗin, "Anwar lafiya katashi mike damunka?"....tafaɗi haka ciki da firgici. A hankali ya fara ɓuɗa idonsa da sukayi masa jawur yace, "Aunty"..... girgizashi ta farayi ciki da tashin hankali tana faɗin, "mike damunka haka duk ka rame kayi baƙi, kafaɗamin dan Allah?". Irin yadda yaga ta rikice duk tawani tada hankalinta yasa ya buɗa baki yace, "ba komai Aunty, lafiya ce ba nida kwana biyu amma yanzu nasamu sauƙi". Bata yarda da abinda yace ba amma sai ta kyaleshi tace, "tau Allah ya ƙara lafiya, amma katashi kaci wani abu". "A'a Aunty yanzu zan koma sokoto dan gobe nake son na koma gida dan har yanzu ban koma ba"......kafin ya rufe baki tace, "mi kazoyi abuja yanzu?". Yace, "wani aiki ya kawuni nida abokina kuma koda nazo har ya wuce Indian "..... tace, "to duk da haka sai kaci wani abu kafin katafi. Ba musu ya tashi ya ɗanci kaɗan kana yayi mata sallama ya wuce warsa. filin jirgi ya isa, ciki ikon Allah ya samu jirgi ya shiga ya dawo da shi sokoto, gidansa ya isa koda yaje ga baki ɗaya garin yaji yayi masa zafi dan haka lokaci ɗaya ya fara haɗa kayansa kamar wani ma haukwaci, dan gaskiya bazai iya bacci a cikin garin ba, gara yabar garin ko yaji sauki abinda yake ji aransa. Tunda aka nemi Hafsat ba a ganta ba Baban Safiyya ya daina kula kowa a gidansa, ba yadda Mamar Safiyya batayi ya haƙura ba amma yaƙi, sose suka shiga damuwa na rashin kulasu da Baban Safiyya ya daina. Shiko Abbas Yayan Safiyya wani tashin hankali ya shiga wanda lokaci ɗaya har kwanci yayi kuma duk ba komai ya jawu haka ba sai rashi ganin Hafsat, dan yanzu shi kaɗai yasan ya yakeji na rashin Hafsat, dan ko ba afaɗa masa ba yasan ya kamu da son ta, kuma so bana wasa ba, dan ji yake a ransa duk inda take sai ya nemuta,dan a halin yanzu ji yake bazai iya rayuwa ba inba ita. Safiyya ma duk tabi ta ƙare dan yanzu ko abinci da ƙyar take samun ci, ga school duk bata jin daɗin zuwa kuma gashi sun kusa fara jarabawa amma komai ta daina ganewa saboda rashi ƴar uwata.l Tunda safe Umma ta fara shirin tafiya garinsu, ta haɗa duk wani abin buƙatar ta, tana cikin shirin tafiya sai ga Abban Hafsat ya shigo ɗakin ciki da tashin hankali, da sauri ya ƙaraso gareta yana faɗi, "haba Fatima miyayi zafi haka, dan Allah ki tausayamin wallahi ina cikin tashin hankali, kuma dan Allah ina son ki tsaya ki saurareni kona minti ɗaya ne Fatima".....yana faɗa amma kamar ya durƙusa mata sabida kaɗuwa. Ba abinda tace dashi, kuma bata fasa haɗa kayanta ba dan ta tafi. Daya ga ba alamun wasa acikin lamarin ta dan haka ya ƙarɓe jikar da take koƙarin fita da ita yana faɗin, "Fatima bari kiji duk son da kikewa Hafsat nafiki sonta nesa ba kusa, kuma bazan hanaki zuwa gida ba, amma kibari gobe insha Allah zan kai ki da kaina, kuma kisani fa Hafsat ba ko ina tajeba sai wajan karatu"....nan dai ya faɗa mata duk abinda ya sani game da Hafsat. Sose Mama tayi kukan rashin ƴarta, amma duk da haka tace sai taje ganin iyayenta, ba yadda ya iya haka ya kaita tashir mota tashiga mota ta tafi garin su tabar Abba cike da kewarsu. Awa ɗaya ta kaita tashar garin dange, napep ta hawa ya kaita cikin garin, tunda tashiga garin gabanta sai famar dukan uku-uku yake, bakin wata ƙofar gida mai napep ya ajeta, tunda ya ajita gabanta ya ƙara tsananta faɗuwa, sallamar mai napep tayi kana ta ɗau kayan ta dan ta ƙarasa cikin gidan, gab da zata shiga gida taga wani ɗan tsoho kwance da alamu ma bashi da lafiya, har zata wuce shi sai kuma ta ƙara kallonsa, gabanta ne ya bada dummmm ai basan lokacin da tasake kayanta ba ta ƙarasa gareshi tana faɗin Baba! Baba! lafiya kuwa na ganka haka?".....tafaɗi haka tana mai sanya kuka. Kafin ya buɗa baki yayi magana sai ga wata mata ta kurnu kai dan taga wake kuka. Ita kuma Umma mutsin da taje ne yasa ta ɗago kanta, ɗagowar da zatayi aikuwa sai ganin wata mata tayi tsaye tana kallon ta, suna haɗa ido ta zabura da ƙarfi ta tashi tana sun tayi magana amma takasa, bawani ɓata lokaci sai gashi ta faɗi ƙasa sume. ****** Sose Hafsat ke jin daɗin zama da Aunty Shemah, kuma tana jin daɗin karatu ba kamar da tana najeria ba, dan yanzu idan kaga Hafsat kamar ba ita ba, sose kyauta ya ƙara fita kamar wata balara ba. Yau ma kamar kullum tana ɗaki kwance tana duba wusu books ɗinta sai jin wayar ta tayi tana ƙara, kamar baza ɗauka ba kuma sai ta ɗauka, suna Sulaiman taga ya bayyana, ba ɓata lokaci ta danna picking ,kafin ta ɓuɗa baki tayi magana yace, "ki samemu muna parlour muna jiranki". Kafin tayi magana har ya datse kiran. Cikin tsanaki ta tashi ta gyara jikinta kana ta sanya hijab ɗinta tafito falon gidan. Ahankali take tafiya cikin natsuwa har ta kawo cikin parlour haɗi da sallama abakinta, izini sukayi mata da tashigo, tana buɗe labulen ɗaki sukayi ido huɗu da Sulaiman, murmushi yayi mata, itama ta mayar masa da martani haɗi gashe da su, amsawa sukayi da nuna faricikin ganinta afuskar su. Bayan sun gaisa Sulaiman yace, "Aunty wai me kike ba ƙanwar taki ta koma kalar indian"......ya faɗa haka yana kallon Hafsat yana murmushi. Sai Aunty Shemah tace, "kodai ka ƙyasa". kafin yayi magana abukin tafiyar su Lukuman yace, "Hafsat shikenan kin bar mu tunda kin samu Aunty gashi ko a school baki neman mu". Murmushi tayi tace, "a'a wallahi ba haka ba, lokaci ne babu amma naso na kai muku ziyara wannan satin". Sai Sulaiman yace, "bawani nan ke dai kin samu Aunty kin manta damu"....haka dai suka sha firarsu, daga bisani kuma sukayi musu sallama suka tafiyar su, amma ako da yaushe Sulaiman na kirata yana tambayar ta koda tana buƙatar wani abu, watarana ko bata buƙata yakan yumata aiki, sose take jin daɗi yadda yake kula da ita, amma awani gyafe tsoro takeji. Yau Monday tunda sassafe tashirya dumin taje makaranta, parlour ta fita ta same Aunty zaune tana jiran fitowar ta, Aunty Shemah na ganin ta fito murmushi ya bayyana afuskar ta kana tace, "Hafsat ki ƙaraso muyi breakfast muwuce school dan ƙarfe 8:00 zan shiga lecture kuma saura ƙan ɗan lokaci ya cika". A gurguje sukayi beark suka fito suka wuce makaranta, koda suka isa saura kaɗan Aunty Shemah ta makara, dan haka suna shiga tayi parking ta fito batare ma da ta kashe mota ba ta bar ma Hafsat kye ta wuce warta. Mota ta kashe haɗi da zare kye ɗin motar ta fito ta rufe, juyuwar da zatayi sai tayi arba da ƙawar ta Zeenatu, wadda suka haɗu da ita a nan kuma class ɗinsu ɗaya, kuma itama ƴar najeria ce, murmushi suka sakar ma junasu suka gaisa kana suka kama hanyar class ɗinsu, suna cikin tafiya sai jikin Hafsat ya bata kamar ana kallonta, juyuwar da zata yi sukayi ido huɗu da Sulaiman, murmushi tayi masa kana ta gaisheshi, magana yayi mata yace idan tagama lecture yana neman ta, tace tom sai ta fito. Gaba ki ɗaya Anwar ya kasa zama ya kasa tsaye ba shiri ya kama hanyar kaduna cikin dare dan shi kam bazai iya zama garin sokoto ba Hafsat ba. ƙarfe biyun dare ya isa garin kaduna, koda ya isa gida ko part ɗin iyayensa ba shigaba ya wuce part ɗinsa, ciki da damuwa ..... *Bani da bakin magana gareku, ku ƙara haƙuri pls, abubuwane sukayi min yawa, dan Allah ina baran addu'a gareku pls*🙏 *#Vote* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 23📑* *__________*📖 da hanzari matar da ke ƙofar gidan tayi saurin ƙarasowa gareta tana faɗin, "Fati kitashi kinji"....tana faɗa ta ɗauku ruwa ta shafa mata a fuska. Ba ɓata lokaci sai numfashin ta ya fara dawowa dai-dai, cikin hanzari Ummar Hafsat ta tashi tana riƙi Mama tana kuka mai cin zuciya tana faɗin, "Mama dan Allah kuyafemin". Kafin tayi maga Baban ta dake kwance yana jin ance Fati ya tashi daga kwanciyar da yake, bakin sa na karkarwa yace, "wa na keji kamar muryar Fatina, koda gizo ne takemin ko mafarkin da na saba ne?". Mama ta ɓuɗa baki cikin sanyi jiki tace, "eh Malam Fati itace"..tun bata rufe baki ba ya fara wa Allah hamdala kana yace, "Fati ƙaraso gareni kinji". Ba musu ta ƙaraso gareshi tana faɗin, "dan Allah Baba kuyafemin nasan niyi kuskura amma dan Allah ina neman afuwarku". Yace, "ba komai Fati, na yafemiki har a wajan Allah, kuma naji daɗin ganinki ina yaraye bam mutuba, sai dai dan Allah abinda nakeso dake shine Fati kuriƙa zumunci ko bayan raina kada kiyar da ki katse zumuncinki da ƴan uwanki,amma yanzu idan an kwana biyu ki shirya kije duk inda ɗan uwanki yake ki sada zumunci"....nasiha yayi mata sose akan tariƙa zumunci, daga baya suka tashi suka ƙarasa cikin gida. Bayan kwana biyu da zuwan Ummar Hafsat gidan iyayenta ta kwashe duk abinda ke damun ta na ɓatan Hafsat har cikin da Hafsat tayi ta gaya musu, sose hankalin su ya tashi da suka ji wannan labarin, Malam da Mama faɗa sukayi mata sose kana suka nuna mata ba abinda yaje mata haka face katse zumuncin da tayi, bayan komai ya lafa suka bata magana mai sanyi kuma sukayi mata alƙawarin za su taya ta addu'a Allah ya bayyana ta duk inda take. Mamar ta tace, 'ke Fati ke da mijinki bansa wanda yafi wani laifi ba, ace ka kwashe shekaru kana cikin garin sokoto amma kakasa leƙa ƴan uwanka, dan mi Allah bazai jarabe ku ba, ke kin kama waje kin zauna baki damu da kowa ba shima haka, wallahi kuntafka kuskure babba, amma muna ƙara godiya ga Allah da har ya nuna muku dai-dai". Kuka Ummar Hafsat keyi kamar ranta zaifita. Kwanta uku cin garin sai ga Abban Hafsat ya zo, aikuwa shima kansa yasha faɗa a wajan iyayenshi daga baya suka haƙura suka karɓeshi, bayan komai ya lafa shima ya faɗama ƴan uwansa abinda ke faruwa, sose mahaifinshi yayi masa faɗa kana yace ba komai ya ja masa haka ba sai katse zumunci da sukayi. Da yake garin su ɗaya da Umma, bayan komai ya ɗan dai-dai ta tsakanin shi da iyayenshi kana yaje can wajan iyayen Ummar Hafsat suma suka ɗura daga wajan da iyayenshi suka tsaya. Bayan kwana biyu da zuwan sa sun ɗan huta shida Ummar Hafsat duk ida wani ɗan uwa yake sai da sukaje, haka da yayi ne Ummar Hafsat ta ɗan ji sanyi har ta fara saki jikin ta dashi, satin su uku garin dange sannan suka dawo cikin garin sokoto. Gari na waye wa Anwar ya shirya ya isa part ɗin iyayensa, koda yaje suna parlour zaune suna fira, sallamar Anwar da sukaji ne ta katse musu fira, da sauri iyayen nasa suka ɗago kai suka kallesa haɗi da mamaki a fuskukin su. Kafin suyi magana ya ƙaraso garesu yana faɗin, "Daddy , Mumy barka da safiya".....yana faɗa yana kwanciya saman cinyar mahaifiyar sa. Daddy ne ya buɗe baki yace, "Son saukar yaushe? haka akazo ko ka faɗa mana sai kayimana bazata?". Sosa ƙyar kansa ya fara kana yace, "afuwan Daddy , garin ne naji ya isheni yasa nazo tun cikin dare". Da sauri Mumy tace, "au kace tun cikin dare ka dawo". Yace, "eh Mumy, amma kuyi haƙuri gajiya nayi da garin shiyasa na dawo"....kafin ya rufe bakinsa sai Daddy yace, "Ai na ɗauka danaga ka jima acan ka samo muna sirika". Murmushi Anwar yayi amma bai ce dasu komai ba, sai can yace, "Mumy yaunwa nakeji haďamin breakfast". Tace, "tau autana taso muje dining kayi beark ɗin". Daddy yace, "tashi muje har ni muyi beark ɗin....haka sukaje dining Mumy ce tayi serving ɗin su suka fara ci. Kowa naci abinda ke gabansa amma ban da Anwar da ke jujjuya spoon ɗin dake hannusa. Mumy ce ta kula da haka dan haka tace, "auta na, mike dumunka naga komai baka ciba sai juya spoon ke yi". murmushi ya ƙaƙalo kana ya buɗa baki yace, "ba komai Mumy"....kafin ya rufe baki Daddy yace, "Son bana son karya kafaɗa muna abinda ke damunka dan tunda ka shigo na fahince akwai abinda ke damunka". Ƙyyar kansa ya fara sosa kana ya sadda kansa ƙasa yace, "Daddy ba komai, kwai wani abuki nane da bashi da lafiya kuma nake son naje dubinsa amma ina gudun kuce yawon yayi yawa bazan jeba". Kallon sa Daddy yayi yace, "hmm kai dai auta faɗi gaskiya, ai bazan ce haka ba, zaka iya zuwa dubinsa aduk lokacin da ka gadama". Murmushi yayi haɗi da godiya ga mahaifin nasa kana yace, "Daddy ba fa nan yake ba india yake". Sai Daddy yace, "a'a ba komai "dubiyace Allah dai ya baka ladar zuwa, amma dai ba jimawa zakayi ba autan Hajiya". Da ameen ya amsa kana yace, "au Daddy ba da kai ba kenan"....ya faɗa haka ashagwaɓan ce, kana ya ƙara da cewa "next week insha Allah zanje".....fatar ahairi sukayi masa haɗi da sama ɗan nasu albarka. Suna fitowa lecture ita da ƙawar ta Zeenatu, bayan sunyi ma juna sallama ita takama hanyar da za su haɗu da Aunty Shemah ita ko Zeenatu ta kama hanyar hostel. Wajan da sukayi parking ɗin mota ta nufa dan ita gabaki ɗaya ta manta da maganar da sukayi da Sulaiman da yace idan ta fito lecture yana nemanta. Tunda ta fito yake kallon ta tana tafiya cikin natsowa, a hankali take taka ƙafar ta har takowa gab dashi, bata ma lura da mutum ba har tazo zata wuceshi, da yaga alamun bata ganshi ba dan haka ya ɗauku waya ya danna kiran ta, tana tafiya taji wayar ta tafara ƙara, wayar dake hannuta ta duba taga wake kiranta, dan ita atunanin ta ko Aunty Shema ce? dubawar da zatayi sai taga sunan Sulaiman na yawo saman screen ɗin wayar ta, tunawa tayi da abinda yace mata, ɗagowar da zatayi sai sukayi ido huɗu dashi, zaune yake sai aikamata da wani ƙayataccin murmushi yake, wanda ke ƙarama fuskar sa kyau da annuri. Akalar tafiyar ta ta juya zuwa wajan da yake, shiko sai famar kallon ta yake kamar yau ya saba ganin ta, kallon da yake mata ne bata so, shiyasa sai famar tura baki takeyi waje, shiko hakan da take ba ƙaramin kyau yake ganin tayi ba, haka dai taci gaba da tafiya har ta ƙarasa wajan da yake. Kujera dake kusa dashi ya nuna mata yace ta zauna, kamar ba zata zauna ba sai kuma ta zauna, littafin dake hannta ya ƙarɓa ya fara dubawa har ya kammala kana ya ɗago kansa ya kalleta yace, "ba ko gaisuwa". Murmushi tayi haɗi da buɗa baki tace, "ina wuni Yaya Sulaiman".....bata kai da rufe baki ba yace, "waye yayanki hala? mama kiriƙe gaisuwar ki bana so tunda sai da na ruƙa". Murmushi tayi haɗi da faɗi, "kai mana". Yace, "a'a nikam kije kinemu Yayanki ba dai niba". Alamun kuka tayi tace, "tau shikenan bari natafi tunda kai ɗin ba yayana kaki ba". Ido ya zuba mata yana kallonta, dan yadda take magana yana masifar burgeshi, lokaci ɗaya yaji wata gogowar sonta ta ƙara laulayi zuciyar sa. Mayafinta ya riƙe yana faɗin, "sorry My kanwa, kallonta yayi yace haka yayi miki ko?". Bakinta ta cinnu gaba alamun yayi mata. har ya buɗa baki zaiyi magana sai ga Aunty Shemah ta ƙarso tana faɗin, "au nan kake tsayar min da ita kana hana ta shiga lecture ko?". Kafin yayi magana tace, "Hafsat tashi muje, idan kana son ganinta kazo gida amma adaina tsayar min da ƙanwa makaranta". Murmushi yayi haɗi da haɗi hannayi sa waje ɗaya yace, "tuba nake Aunty, insha Allah bazan koma ba, amma akowane lokaci zanzo gidan naku". Tace, "naji tana" faɗar haka suka fara tafiya. Har suka shiga mota suka tafi gida Aunty Shemah ba tace da Hafsat komai ba, bayan tayi wanka ta shirya ta fito parlour dan tayi ma Aunty magana idan akwai abinda tayi mata ya ɓata mata rai ta yafe mata, dan taga kamar fushi take da ita. Tun bata ƙarasa parlour ba sai ga Affan ɗan Aunty Shemah ya zo da gudun sa yana faɗin, "oyoyo Aunty". Hannayita ta ware shiko ya shige yana murnar ganinta. Ɗaukar sa tayi suka ƙarasa falo, zaune suka sameta tana duba wasu books ɗinta, a hankali ta zo ta zauna kusa da ita, bayan ta zauna ta gaisheta, bayan ta amsa suka ɗan jama kaɗan amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai, Hafsat ce ta katse shuru da faɗin, "Aunty ". Kanta ta ɗago ta kalle Hafsat tayi mata kallon ya dai. Sai da ta sadda kanta ƙasa kana tace, "Aunty dan Allah in akwai abinda nayi miki kiya femin, naga kamar fushi kikeyi dani". Sai da Aunty Shemah ta haɗi fuska kana tace, "abinda naga kinayi ɗazo shine bamin daɗi ba, ace tun yanzu har kin fara rashin shiga class, to bari kiji muddin kina son tamu tazo ɗaya sai kin aje komai ki kama karatu, bana son kiriƙa tsaye da wani makaranta da sunan wani zance, ban yadda da wanna ba koda ace Sulaiman ne ƙanena, kuma aganina karatu kika zo ba wata shiririta ba, dan haka nake haɗaki da Allah ki dana tsayi kina zance makaranta, in ma mutum yace yana sonki zaki iya bashi dama yazo nan ya sameki amma ni a makarnta bana so gaskiya, dan ko iyayenki ne baza su barki ba, kuma ni har ga Allah tunda na ganke jin kin shiga raina". Sai da ta kai ƙarshe zanci Hafsat ta ɗago da kanta tace, "kiyi haƙuri Aunty, kuma insha Allah bazan koma ba, duk da sai dana fito class ne, amma bazan sake ba koda ma can ba ra'ayi na ba ne". Nan dai suka cigaba da firar su shiko Affan sai gwalamniya yake musu kamar yana jin miso ke faɗa. Bayan kwana uku da dawowar Anwar ya fara shiri-shirin zuwa india. Tunani ya fara to idan yaje india wace makaranta Hafsat take, da yaga abin zai bashi walaha ya fara tunanin kiran Hajara dan yasan ita ce zata samu masa address ɗin duk inda take. Kwance take tana tunani Anwar da koma yadda zai shigo hannuta lokaci ɗaya, sai ji tayi wayar ta na ƙara, wayar ta ɗauka ta duba screen ɗin wayar , sunan da tagani ne yasa tayi picking bata shirya ba. A kunne ta kara wayar amma bata yi magana ba sai da ta tsaya fitar da numfashi a hankali, dan ita kanta tasan tana son Anwar so bana wasa ba. Da yaji batayi magana ba yasa ya buɗe baki yace, Hajara kin min shuru kamar baki san waya kira ba". Tambaya ta jefamasa tace, "yanzu kana ina ne". "Kaduna". haka yace da ita ata ƙaice..... kana yace da ita wani aiki nake son nasaki shine nace bari naji ko zaki iya?". Tace, "inaji faɗa idan zan iya zan faɗa idan ma bazan iya ba zan faɗa". Yace, "zaki iya, yace, address ɗin makarantar da Hafsat take nake so asamun na andia". Wata dabara ce ta faɗu mata tace, zanyi maka amma da sharaɗin".....yace, "faɗi sharaɗin naji". Tace, "a'a sa idan kazo zakaji sharaɗin". Yace, "ba damuwa idan kinsamu sai ki faɗa nazo inyaso sai ki faɗamin sharaɗin kafin ki bani address ɗin". "Naji zanje na samu, amma idan har ba ka yarda da sharaɗin ba to koda nasamu bazakaji komai daga waje na ba". Yace, "kar kidamu". haka dai suka cigaba da waya daga baya kuma sukayi sallama. Tunda lokacin Hajara ta bazama neman address ɗin Hafsat na andia.... *#Vote* *Comment* *Share* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 25📑* *__________📖* gidan iyayen sa ya sauka ya gaishesu kana ya wuce gidansa, part ɗinsa ya wuce kai tsaye bai ma bi taka matar tashi da Baby da aka haifar masa ba ,tana parlour zaune ita da ƙanwar ta da wasu ƙawayen ta, alamun shigowarsa taji dan haka ta dube ƙawayen ta tace dasu dan Allah kujira ni ina zuwa, tana faɗar haka ta ɗau Baby ta kama hanyar part ɗinsa, duk da bata da cikakin sanin da zata ce shine amma jikinta har wani karkarwa yeke burinta ita dai ta ganshi gata gashi. Yana isa part ɗinsa, ko kayan jikinsa ba tsaya yarage ba ya ɗau waya yakira Aunty Shemah, bayan ta ɗauka sun gaisa yake tambayar ta Hafsat, sai da ta wani haɗe rai kana tace, "ai kana da number ta". Yace, "na ɗauka kuna tare ne amma kiyi hakuri naji kamar ranki ya ɓaci". Tace, "a'a ba haka bane kawai naga ko iyayena baka bari na ji lafiyar su sai ka ɗauku min wani zance". "kiyi haƙuri Aunty na". Tace, "ba komai, ka kirata kaji dan naga yau kamar bata jin daɗi"..... ai tun bata kai ƙarshin zancin ba ya datse kiran nata. Number ta ya kamu ya saka kira, kwanci take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, tunanin mafarkin datayi jiyane takeyi, wayar tace da ta shiga rura ta mai data daga duniyar tunani, wayar ta ɗauku haɗi da danna picking ta kara a kunni ta. Sallama tayi masa ya amsa, bayan ta gasheshi haɗi da masa ban gajiya kana yace, "naji muryarki kamar mara lafiya?". Murmushi tayi kana tace, "lafiya ta ƙalau ya Baby tah". karki tambayeni dan sai da nace kizo ki ganta kikace a'a, kin ga ko ba dole na faɗamiki ya Baby take ba". Tace, "kayi haƙuri Babban Yayana". har zayi magana sai aka turu ƙofar ɗaki, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yaci gaba da firarsa. Jikita a sanyaye ta fara takawa har ta kawo wajan da yake kwance, Baby ta aje kusa dashi kana ta zauna zaman jiran ya gama waya, baya ya gama kana ta ƙaraso kusa da shi tana faɗan, "Baban Baby barka da zuwa". Sai da ya ɗau Baby kana ya amsa mata haɗi da tambayar ta lafiyar ta. Baby ya zubama ido wadda tunda ya ɗauke ta yaji sonta na shiga zuciyar sa, huɗuba yayi mata yana gamawa sai Maryam ta dubeshi tace, "wani suna zaka saka mata?". Batari da wani tunani ba yace, Hafsat". Dubansa tayi da kyau tace, "kenan ka canja suna dan na zata sunan Mumy zaka sa". Yace, "a'a sai wani lokaci nasa insha Allah". Haka dai ya daure yana fira da ita kana ya tashi yaje yayi wanka ta kawu masa abinci yaci, amma duk abinda yake ɗiyar na hannusa, wanka ne kawa da zaiyi ya ijeta. Yana cikin haka sai akaturu ƙofa, abukin sa Jabir yagani tsaye yana masa wani kallo, a hankali ya buɗe baki yace minayi zaka yimin wannan kallon haka". Kafin ya bashi amsa Maryam ta gashe da Jabir kana ta ɗau Baby ta fice. Bai ce dashi komai ba sai da ya shigo cikin parlour yace, "wai yaushe zaka gama course ɗin da kajeyi ne?". Sai Sulaiman yace, "sai ta gama ". Jabir yace, "wallahi ni nasan bawani course da kaje, kajene dan kayi tsaron ta, to bari kaji wallahi baka isa ka tsareta ba, dan yanzu kazo nan amma bakasan meke faruwa acan ba, ni dai shawara ta gareka ka dawo kacigaba da aikin ka kuma kariƙe matar ka duk yafiye maka bin sauran wani".....tun bai kai ƙarshe ba ya ɗaga masa hannu yace, "Jabir daka ta!". Idonsa ya ɗago ya kalleshi waɗan da saka sauya lokaci ɗaya yace, "bari kaji Jabir wallahi ko ɗa ɗay-ɗaya har ashirin Hafsat ta haifa tare da Anwar ba ta hanyar aure ba wallahi sai na aure ta muddin tace ta amice da haka". Jabir yace, "har yanzu baka san waye Anwar ba, kuma waye Hafsat ba, kuma nasa ko yanzu Anwar yaje ga Hafsat zata yarda dashi dan tana masa son bana wasa ba". Irin yadda yada yaga bacin rai afusakar Sulaiman dan haka ya tashi ya kama hanyar fita, sai da ya kawo gab da ƙofa kana yace, "nasan baka san me nasani ba gami da Anwar ba, to bari kaji yanzu haka Anwar yahe india". yana faɗar haka ya rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi kana ya bar gidan ciki da ƙunar zuciya. Aikuwa Sulaiman najin haka basan lokacin da ya tashi zaune ba, "yana faɗin wallahi ƙarya ne". Ba tsaya wata-wata ba ya ɗau kye ɗin motar ya bar gidan, School ɗin su Hafsat yaje neman Safiyya da ƙawar ta Naja'atu. Shiko Jabir ba abunda ya tsana kamar yaji abukin sa yace zai aure Hafsat, dan shi aganinshi bata dace da Sulaiman ba, dan shi abinda yafi tsana hulɗa da talaka. Koda ya isa school ɗin ba kowa ya samu ba, sai ɗai-ɗaiku, sabida ana weekend dan haka ya samu wata cikin ƴan makarantar taje hostel take ki rumasa Naja, amma koda taje Naja batanan taje gida weekend. Koda ta zo ta gaya masa hauka ne kawai baiyi ba, kuma gashi bai san gida ko ɗaya daga cikin su ba, dan haka ya shigo mota ya dawo gida, Allah ne ya kaishi gida lafiya dan yadda yake gudu kamar ya gaji da ransa. Yana zuwa gida ya kasa zama ya kasa tsaye, dan haka ya shiga mota ya kama hanyar gidan iyayen sa. Parlour ya tarar da Mumy sa da Abbansa, tunda ya shigo suka zuba masa ido suna kallon sa, Abban sane ya fara magana yace, "Yaro na mike damun ka na ganka haka kamar kana cikin tashin hankali?". Sai da ya sauke ajiyar zuciya yace, "eh to Abba dan akwai wani abinda ya taso gami da karatun da naje can india shine nake son gobe na koma"......tun bai rufe baki ba Mumy sa tace, "kar kasoma dan idan ka ga ka bar ƙasar nan to anyi suna, na gaji da wannan ƙaƙale-ƙaƙale naka fa, tunda akayi auren nan baka zauna ba bare ku fahinci juna kai da Maryam, dan haka ba inda zaka je". Sai da ta gama Abban sa ya dube shi kana yace, "my Son kaje kashirya idan Allah ya kaimu gobe sai kaje ɗin". Har Mumy zatayi magana Abba ya ɗaga mata hannu haɗi da faɗin "fatar alhairi kawai nakeson kiyi masa". Ba dan ranta yaso ba tayi masa fatan alhairi haɗi jadda da masa yaje ya tambaye Maryam duk abinda bata da tagaya masa. Yace tom haɗi da tashi dan yaje ya fara shirin komawa, har zai fita Abbansa yace, "son wani suna kake so asawa yarinyar nan". Sai da ya sosa ƙyya kana yace, "Hafsat". Yana faɗa ya fice bai jira cewar su ba. Wani sanye daɗi ne ya mamaye Mumy ita da Abba, sai Abba yace "mun gode da wannan kyautar". Ita Mumy kasa magana tayi sabida daɗi, dan sunan mahaifiyar ta ne, kuma tunda ɗiya ta taso asa mata amma ƴan uwan Abba suka hana sai yanzu da Allah ya yarda asa ga jikar ta. Kafin ya koma gida sai da ya tabbatar da ya samu bisa da duk wani abun da yake buƙata. Lokacin da ya faɗawa Maryam tafiyar sa, har kuka sai da tayi amma dayake mai sanye ce daga baya tayi masa addu'ar tafi lafiya da dawo lafiya. Tun shida na safe jirginsu ya ɗaga zuwa india, sune basu sauka ba sai cikin dare. Koda ya isa masaukin sa sose yagaji dan haka ya watsa ruwa ya kwanta. ***** Tunda tayi sallah asuba bata sake kwanciya ba, gyaran gida tayi kana ta hada musu beark, bayan ta kammala taje tayi wanka tashiriya, cikin sauri tayi beark sannan tazo ɗakin Aunty Shemah tace zata tafi sabida lectura ne da ita da safen nan, key ɗin mota Aunty Shemah ta bata haɗi da iyimata adawo lafiya sabida ita yau bazata je ba. Karɓa tayi da sauri ta ƙarasa wajan aje mota, tana shiga tayi mata key ta fice da sauri sabida gab take da ta makara. Anwar tunda yayi sallah asuba ya tashi ya shirya dan tun yau yake son ya fara ne manta, sabida bashi da lokaci, dudu sati ɗaya ne zaiyi ƙasar, abukin sa na shiryawa suka fita zuwa cikin makarantar. Sulaiman sabida ya gaji bai farka da wuri ba, dan ko sallah yau sai da ya makara baiyi ba, kuma yana gama sallah sai da ya kwanta, aikuwa koda ya farka rana ta fara fitowa, cikin hanzari ya shirya ko beark bai tsaya yayi ba ya kama hanyar gidan Aunty Shemah. Koda yaje parlor ya tarar da ita tana beark, sallama yayi kana ya shigo, ido da baki ta zuba masa sai kallon sa take kamar yau ta fara ganin sa. Ƙarasowa yayi ya zauna kana ya gaisheta, ba ta karɓa ba sai jefa masa tambayar da tayi "miya dawo da kai yanzu?". Sai da ya ɗau kofin tea kana yace, "akwa abinda ya mai dani, Aunty ina Hafsat?". "Hafsat ta mai daka ko". A'a Aunty, su Mumy na gaisheki kuma sunci kin daina kiransu". Shareshi tayi dan sose ya bata haushe ace ya dawo jiya. Sai da ya ta kurata da tambaya tace, "taje makaranta". Ƙofin dake hannunsa ya aje yace bari nazo. Mamaki ya cika ta, dan haka takasa baki sai kallon sa takeyi, dan ta lura yadda yadamu da Hafsat ita bata damu da shi ba, sai ma gani take kamar batasan yana son ta ba. Tanayin parking ta fito haɗi da kulle motar, tana cikin haka sai ga ƙawar ta Zeenatu ta ƙaraso tace, "kizo muyi sauri mutafi dan munkusa mu makara, "tace to muje" . Tafiya suke suna fira har suka kusa kai class. Anwar da abukinsa sai sauri suke su isa wajan da suke tunanin zasu ganta, tafiya suke ita da Zeenatu, shiko Anwar yana bayan su shida abukinsa, dan har yasu ya ijesu ya wuce sabida basa sauri sai wata tafiya suke kamar basa son taka ƙasa, kuma ga hanyar da zata sada su class ɗinsu akwai cinko so da yawa, abukinsa ne ya riƙeshi yace mubi komai cikin natsowa insha Allahu zaka ganta". Badan yaso ba suka biyewa tafiyar su har suka kawo hanyar da zata sada su class kana suka raba hanya. ******** Kamar wadda aka koro sai gata tashigo ɗakin tana faɗin, "Zahara! Zahara!. Da sauri ta fito daga toilet tana faɗin, "Hajara lafiya kuwa kikazo min haka?". Tace, "ina lafiya tunda Anwar ya asirceni duk abinda yace namasa shi zan masa, amma ni duk abinda na nuna masa ina so wallahi bayayimin, gashi yanzu nabashi address ɗin shegiyar yarinyar nan, dan haka nake son ƙarfe ukun dare ki rakani muje wajam Malam kinga sai na kwanan anan iyaso lokaci nayi muje". Sai Zahara tace, "to mi kike son iya gami dashi Anwar da Hafast ". Hajara tace, "ni so nake iya masa abinda baya ganin kowa sani, sannan ita ko akorota daga karatun da take a india, dan na tsane jin tana can , kinga idan ta dawo tana gani tana ji muyi Aure da Anwar inya so tazo tanamuna wanki da wanke-wanke". Tafawa sukayi haɗi da sanya dariya mai ciki da ma'anuni da yawa. Tun biyu da rabi na dare suka tashi suka shirya kana suka ɗau hanyar gidan Malamin su.... *#Vote* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 24📑* *__________📖* Bayan kwana biyu suna zaune da Aunty Shemah parlour suna fira sai suka jiyo sallama bakin ƙofar parlour, tun kan su ƙarɓa sai affan ya zo da gudu yana faɗin, uncle, uncle". Sulaman hannayensa ya ware Affan ya shiga jikin sa yana faɗin, "my son lafiya kake?". Sai da suka ƙaraso cikin parlour kana Affan yace, "eh uncle". surutu ya fara mishi amma Sulaiman bai kulashi ba ya kai dubansa ga Aunty yace, "My Aunty ya kuke ya gida?". Kafin ta amsa masa ya kai dubansa ga wajan da Hafsat ke zaune duk ta ta kura, dan ba wani kayan kirki ne ajikinta ba kuma gashi yayi musu bazata, tana so ta gaisheshi amma ta kasa sabida yadda ya kifeta da ido, shiko yaƙi ya janye idon sa, sai jira yake ta gaisheshi, ita ko ta kasa buɗa baki ta gaisheshi, muryar Aunty Shemah ce da yaji ta amsa masa haɗi da tambayar sa yaushe zai je gida, sannan ya mai da duban sa ga Aunty Shemah yace, "wata ƙila gobe na wuce". Tace, "bawani wata ƙila dole gobe kaje, sabida zuwanka dole ne dan inba kaje ba sai aɗauka dan baka sonta ne zaka ƙin zuwa". Suna cikin firar sai Hafsat ta sulale tayi ɗakin ta. Duban Aunty yayi da kyau kana yace, "kada ki damu Aunty insha Allahu gobe zanje". haka suka cigaba da fira har wani lokaci. Duban wajan da Hafsat take zaune yayi, amma sai yaga bata wajan, dubar parlour ya fara amma bai ganta ba, lura da haka da Aunty Shemah da tayi sai tace, "wai Sulaiman me ke son afkuwa ne gareka gami da Hafsat?". murmushi yayi haɗi da sose ƙyyar kansa, bata jira cewar saba tace, "bari na turumaka ita". tana faɗar haka ta tashi taje ɗakin Hafsat. Bata jima da tafiya ba sai ga Hafsat tazo parlour sanye da wata atamfa wadda akayi ma ɗikin riga da sikit, sose kayan suka karɓe ta duk da ba wata kwaliya tayi ba. Zama tayi kan kujera da ke nasa dashi kaɗan kana tace, "ina wuni Yaya Sulaiman". Bai amsa ba sai ido da ya zuba mata yana kallonta kamar yau ya fara ganin ta. Har zata sake maga yace, "ƴan matan Aunty ya karatu". Murmushi tayi haɗi da sadda kanta ƙasa kana tace, "alhamdullah". Shuru ya biyu baya sai can tace, "ashe Yaya munsamu ƙaruwa, Allah ya raya akan sunnanh". da yake matar shi ta haihu shine Aunty Shemah ta gaya mata kuma dan haka ma zai koma najeria yayi weekend ya dawo dan iyayen sa sun da meshi akan sai yaje, kuma in bai jeba za suga kamar dan bai son matar ne yaƙi zuwa, ba dan ranshi yaso ba ya amnci zai je. Kallon ta yayi yace, "ko zaki je gobe muje tare in zan dawo sai mudawa tare?".... kafin ya kai k'arshin maganar tace, "a'a ni ba inda zanje sai na kammala karatuna gaba ki ɗaya". kallon baki isaba yayi mata kana yace, "idan ƙarshin shekara tayi naga mai barikin anan". Murmushi tayi tace, "Yaya Sulaman ai nasan ko kai bazaka bari na koma najeria ba sai na kammala". Yace, "hmmm nasan ko yanzu aikwai abinda ya hana ki zuwa, da ko dan kiga sahibinki zaki zo muje". yafaɗi haka zuciyar sa na ƙuna dan ba abinda yafi tsana kamar ya tuna Anwar. Duban sa tayi ido cikin ido tace, "wake nan?". Sai da ya aikai mata kallo mai kama da harara yace, "kin fi kowa sani". Tsaf ta gano wajan da ya nufa amma sai ta sauya magana tace, "gobe da ƙarfe nawa zaka je". Ƙyaleta yayi kamar bai jiba har ta koma mai-mai ta masa amma bai ce mata komai ba, kuma tasan sarai yaji ta amma ya ƙyaleta. Tashi yayi ya kama hanyar fita batari da yace mata komai ba, tana ganin haka da sauri tazo gareshi tana faɗi, "haba Yaya Sulaiman me na maka yanzu nan". tana faɗa kamar zatayi kuka. Hankan da tayi magana ne yasa ya dubeta, lokaci ɗaya yaji son ta na ƙara fizgarshi, ji yake kamar ya jawota jikin sa, a hankali ya fara taka ƙafar sa har yazo gab da ita, kallon ta yayi ido cikin ido da yace, "ba abinda kikayi min sai dai ina son ki kulamin da kanki kafin na dawo, duk da nasa Aunty na iya ƙoƙarin ta amma dan Allah ki ƙara kula". Kwarjini yayi mata dan haka ta kwada idon ta kyafe ɗaya tana faɗin,"kar kadamu Yayana insha Allah zan kiyaye". irin yadda suke magana da junan su gwanin ban sha'awa. Har zai tafi tace, "bakayi sallama da Aunty ba?". Yace, "zan dawo gobe kafin na wuce". bai bari yaji mi zata ce ba ya fice warsa. ******* Duk wata hanya da zata samu masa address ɗin ta bi kuma cikin ikon Allah ta samu masa sunan makarantar da take, amma abu ɗaya ne bata samar masa ba, wanda ita kanta bata sani ba gidan data ke zaune. Bayan ta kammala komai ta kirashi ta faɗa masa, yace ta turu masa, sam ta manta da alƙawarin da suka yi tsakanin su, bawani ɓata lokaci ta tura masa da address ɗin, sai da ta tura masa kana ta tuna, sose hankalinta ta ya tashi, dan haka ta ɗau mayafinta ta fice taje wajan ƙawar ta zahara . Shiko Anwar tana tura masa bai tsaya ɓata lokaci ba ya fara bincikin makaranta, bayan kwana biyu da fara bincike ya gano duk wani abinda yake buƙata, dan haka ya fara shirin tafiya. Ana gobe zai tafi yaje ya same iyayen shi ya faɗa musu cewa gobe idan Allah ya kai mu zai tafi india, addu'a suka mishi haɗi da fatar tafiya lafiya da dawo lafiya. Safiya na waye wa ƙarfe bakwai jirginsa ya ɗaga zuwa india. Shiko Sulaiman tunda sassafe yazo yayi musu bankwana ya wace filin jirgi yashiga jirigi ya wace najeria. Mama ko tunda suka dawo daga garinsu ta ɗan ji sanyi har ta ɗan dawo dai-dai amma ba kamar daba, dan burinta a kullum ta ga ƴar ta ta tadawo hannunta. Haka shima Abba, dan ako da yaushe ba abinda yake sai addu'a da sadaka, Safiyya ko ako da yaushe tana wajan su tana ɗan rage musu kyawar Hafsat, Yayan Safiyya shima ba'a barshi abaya ba, dan yanzu ko kasuwa yaje duk abinda ya sayo ma iyayenshi shi yakan sayo ma iyayen Hafsat, dan yanzu sose yake kula da iyayen Hafsat da ƙannin ta. Ƙarfe goman dare jirgin su Anwar ya sauka ƙasar india, Sulaman ma haka ya sauka najeria. Anwar na fitowa cikin jirgin sai yaga har abukinsa ya zo ɗaukar sa, sose sukayi murna da ganin junan su, ba ɓata lokaci ya ɗauke shi zuwa masaukin sa dake cikin makarantar, da yake koshi abukin nasa karatu yake amma shi wannan sheƙar zai kammala. Ɗaki ɗaya ne mai ɗauke da gado da wadirif, iya haɗuwa ɗakin ya haɗu da idan ka ganshi sai kace ba school ba, ba wani ɓata lokaci ya shiga toilet yayi wanka ya ci abinci kana ya kwanta bacci. Shima abunkin nasa yana ganin ya samu bacci shima ya kwanta. Koda gari ya waye bayan sunyi breakfast Anwar ya sanar da abukin sa abinda ke tafi dashi. Sai da ya kai ƙarshe sai Abukinsa Nura ya dubesa da kyau yace, "ko dama nasan wannan zuwa ba danni kazo ba, amma ba komai zan tayaka neman abinda kazo nema har sai kasameta, da yake tunda ƴan najeria suka zo ban wani haɗu da suba, amma kabar Monday duk wani ɗan makarntar zai fito kuma insha Allah za'a dace". Murmushi Anwar yayi kana yace, "shiyasa nake sonka, dan tunda nayi bincike na gano makartar kuce nace abu yazo gidan sauki". Yana faɗar haka suka tafa haɗi da dariyar samun nasara. Tunda Sulaiman ya tafi jikin sa duk ba daɗi sai ji yake kamar wani abu zai same sa, amma haka yaci gaba da addu'a har a kazo ɗaukar sa. Tana cikin bacci ƙarfe ukun dare sai ta farka cikin razana sabida wanin mummunar mafarkin da tayi, wanda ya bata tsoro matuƙa, ba wani ɓata lokaci ta tashi taje toilet ta ɗauru alwala tazo ta tada sallah..... *#Vote* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 26📑* *__________📖* Basu jima da fitaba saka samu ɗan acaɓa wanda zai kaisu wannan ƙauye, koshi da ƙyar yayar da zai kaisu, tafiya suke amma tafiyar taƙi ƙarawa dan ɗan acaɓa yaga haka yasamu waje yayi parking kana yace, "ku sauka". Sauka sukayi sun ɗauka ko wani abu zai gyara. Dabansu yayi yace, "wai nawa ne zaku bani da har zaku kawuni cikin wannan jeji?". Hajara tace, "nawa kake so mu baka?". Yace, dubu biyu zaku bani". Kuɗi Hajara ta zaro ajikarta ta miƙa masa, karɓa yayi haɗi da tada babur ɗinsa, Zahara na ƙoƙari ta hau shiko yaje babur da guda ya bar ti-tin, kururuwar kirasa suka fara amma ko alamar ya tsaya babu. Hannu Hajara ta ɗaura akai tana faɗin, "yau munshiga uku".... kafin ta rufe baki sai ganin motar ƴan sanda tayi a gabansu, tashin hankali wanda ba'asa masa rana, kafin su ankara ƴan sanda biyu sun fito cikin motar suna faɗan, "ƴan isaka, duk kune ke ƙara lalatamuna ƙasa". Suna faɗa suna saka su cikin mota, kuka Hajara da Zahara suka fara suna faɗin "wallahi mu ba isakanci ne yafitar da muba".... kafin ta kai ƙarshin zancin ɗaya daga cikin ƴan sanda ya buga mata kulki abaki, bashiri sai ga jini ya fara tsiyaya abakin Hajara, Zahara naganin haka taja baki ta rufe kukan ma da take haɗiye shi tayi batare da ta shirya ba. Ƴan sanda suna sasu suka ja mota sai police station ɗin dake cikin ƙauyi garin. ********* Koda Sulaiman ya isa school bai ma bi takan lectura ɗinshi ba, ya fara neman Hafsat, sai da yaje class ɗinsu ya ganta zaune suna karɓar karatu sannan hankalinshi ya ɗan kwanta, tunani yayi yace gwara yaje yaga ko suna da lectura yashiga, yana gama wannan tunani ya kama hanyar da zata sadashi class ɗinsu. Gab da zai bar block ɗin su Hafsat, aikuwa sai ya hango Anwar zaune gab da class ɗin su Hafsat. Gabansa ne yayi mummunar faɗuwa, lokaci ɗaya yanemi natsowar sa ya rasa, maganar abukinsa Jabir ne ya tuna, kuma lokaci ɗaya ya fara girgiza kai yana faɗin, "kenan da gaske ne,waye yaba Anwar address ɗin Hafsat, sai wata zuciya tace itace ta bashi da bata bashi ba taya yasan makarantar da take har yasan class ɗin da take. Jiri ya fara ɗaukar sa lokaci ɗaya, dole yasamu waje ya zauna haɗi da laluba wayar sa aljihu, Aunty Shemah ya kira, tana ɗauka ko Sallamar datayi bai tsaya karɓa ba yace, "Aunty, bayan tafiya ta wani yazo wajan Hafsat?". Yayi magana ciki da ɓacin rai. Sai da ta sauke numfashi kana tace, "Sulaiman, wai mikake son zamane akan Hafsa?, yariyar da bata damu da kaiba wadda bata masan kana son taba, haba Sulaiman ka sassautawa rayuwarka gami da Hafsat ko kasamu natsuwa". Ba abunda yace da ita sai ƙara mai-mai tamata tambayarsa. Abun taga bana wasa bane tace, "a'a ba wanda yazo kuma ba inda taje sai yau da tafita makaranta". Tana faɗar haka lokaci ɗaya ya sauke ajiyar zuciya kana ya datse kiran. Warin da yake zaune nan yaci gaba da zama har ta fito daga lectura, yana ganin sun fara fitowa da sauri ya tashi ya ƙarasa bakin class ɗin nasu. Fitowar ta keda wuya ita da Zeenatu yaja hannunta haɗi da karɓar hand out ɗin dake hannunta, ita abin tsoro ma ya bata, tabayan class ɗinsu yabi da ita har sukaje wajan datayi parking ɗin motar ta, magana taso tayi mishi, amma irin yadda taga fuskarsa haɗe yasa taje bakinta tayi shuru, magana yayi mata fuskarshi haɗe, yace ta bashi key ɗin mota, ba musu ta ɗauko ta bashi, buɗewa yayi tashiga kana yashiga yaje motar bai tsaya ko ina ba sai gidan Aunty Shemah. Yana yin parking tabuɗe marfin mota tafito, shima ya buɗe ya fito, koda ya fito har tafara takawa zuwa cikin gidan, cikiin zafin nama ya zawuta ta faɗu jikinsa, kallon-kallon suka farayi tsakanin su, rabata da jikin sa yayi kana ya fara magana cike da ƙunar zuciya yace, "waye Anwa?!. Gabantane ya bada dumm, lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi haɗi zubda hawaye masu zafi saboda tunawa da wannan sunan da tayi, tana cikin haka taji yasake tambayar ta. Rasa miza tace masa tayi, dan bata san ya akayi ya san Anwar ba, kuka ta fara mai cin zuciya tace karda ace wani abu zai samuna, tafaɗi haka duk acikin zuciyar ta. Magana ya fara cikin faɗa-faɗa yace, "ashe har yanzu kina tare da Anwar Hafsat, gayamin me Anwar keda wanda bani da, nasan ke kika bashi address ɗinki dan ya kawo miki ziyara, to bariki ji wallahi duk son dana kemiki zan iya ajeshi muddi kikace zaki cigaba da hulɗa da Anwar"....har ya buɗe baki yayi magana amma takasa fita sai ƙoƙarin riƙe zuciyar sa yake wadda ke masa zafi kamar tafasa ƙirjinsa ta fito. Tunda ya fara magana Hafsat ke kallonsa dan ita gabaki ɗaya tarasa wajan da yasan Anwar, faɗuwar dataga yana ƙoƙarinyi kuma gashi riƙi da ƙirjinsa alamun zuciyarsa na ciyo, ai bata san lokacin da tazo garisa tana kuka tana ƙoƙarin tareƙo shi kar yafaɗi amma ina, dan koda ta isa gareshi ya kai ƙasa, rasa mizatayi tayi kuma takasa ƙarasawa cikin gida kuma takasa ƙarasawa garishi komawa tayi kamar wata zararriya kuka ma yaƙi zo mata bakin tane tasamu ya buɗe lokacin tasamu ta fara anbatun Allah, aikuwa tana fara anbatun Allah sai gashi tayi hanyar part ɗin Aunty Shemah ciki da tashin hankali. Parlour tasamu Aunty Shema tana duba wani book dake hannuta, cike da tashin hankali tace, "Aunty kizo karya mutu!". Da sauri Aunty Shemah ta ɗago kanta arazane tace, "waye zai mutu?". Kasa magana tayi, hannun Aunty Shemah taje suka tafi batari datayi magana ba. Tun kan su isa Aunty Shemah tagan shi kwanci rai ga hannun Allah, ai da hanzari taje gareshi, kasa magana tayi lokaci ɗaya taje wajan maigida takirasa yazo suka sashi mota taje suka wuce hospital. Taimakon gaugawa likitoci suka bashi, cikin ikon Allah sai gashi ya farfaɗo, alurar bacci sukayi mishi kana suka fito. Suna fitowa Aunty Shemah ta taresu da yajikin nasa, tabbar mata da sukayi jiki yayi sauƙi dan nan da awa ɗaya zai farka da ikon Allah. Sai a lokacin ita da Hafsat suka saukar da ajiyar zuciya mai sanyi. Cikin ikon Allah yana cika awa ɗaya ya farfaɗo, kuma alhmadullah dan yasamu sauƙi sose, likitocin naganin haka suka basu Aunty Shema damar ganin sa. Aunty Shemah ta fara shiga ɗakin, aikuwa tunkan ta ƙaraso gareshi yace, "Aunty ina Hafsat?". Mamaki abin ya bata amma ta basar tace, "Sulaman miyasameka haka har ya tadamaka da ciyon zuciya?". Kafin yayi magana sai ga Hafsat tashigo ɗakin, ƙarasowa tayi wajansa kana tamasa yaji, bai karɓa ba sai jefumata tambayar da yayi. Yace, "da gaske wajanki yazo, kuma har yanzu kuna tare?". Sai da tashefe hawayen da suka zuba a idonta kana tace, "Yaya Sulaiman kabar wannan zanci har sai munfita daga nan, bakaga bakada lafiya"..... Tun bata rufe baki ba yace, "Idan har kina son nasamu sauki to ki gayamin gaskiya". Ita dai Aunty Shemah sai kallon su take saboda mamaki da tsoron Allah duk yacika ta. Ahankali ta buɗa baki tace, "wallahi duk abinda kake magana akai bansan dashi ba, to waya ga yamaka nayi alaƙa da Anwar, kuma waya gaya maka har yanzu munatare, wallahi ni tunda na bar Anwar bansaki ganin saba har ila yanzu, kuma dan Allah kadaina yimin zancishi in har kana son ganin farin ciki na". Tafaɗi haka tana mai haɗa hannayen ta waje ɗaya. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke kana yace, "duk zan baki amsoshin tambayoyinki amma ba yanzu ba, kuma daga yau na ba zaki sake fita school ba har sai ya bar ƙasar nan". "badawa". Haka tace dashi ataƙaice. Ita dai Aunty Shemah ba abinda take sai kallon ikon Allah, dan sose abun nasu ya bata mamaki, kena duk ciyon sone yatada mishi da ciyon zuciya . Bata ida mamaki ba sai da taga Sulaiman ya tashi tsaye kamar bashine suka kawo rai ahannun Allah ba. Duban su tayi bata ce dasu kumai ba, tace, "to tunda kungama muje gida". Tana faɗin haka ta kama hanyar fita batare da tajira mi zasu ce ba. Bayan ta suka bi har suka kawo wajan mota, buɗewa sukayi suka shiga kana taje motar, basu tsaya ko ina ba sai gida.... Tundaga lokaci Hafsat bata sake fita makaranta ba, shiko Anwar, ba inda bai je nemataba a school ɗin amma bai ganta ba, har hostel yasa adubu masa amma bata can, kuma gashi lokaci ya tafi amma baiyi komai ba, sose hankalinsa ya tashi na rashin ganinta, har yake tunanin kodai Hajara bata bashi address ɗin dai-dai ba, yace ko idan ya bincika bata bashi dai-dai ba, to sai ya wahalar da ita, dan sose ranshi ya ɓaci na rashin ganin Hafsat da baiyi ba. Da yaga alamun bata cikin makarantar ya fara shirin dawowa gida n9.... *#Vote* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 27📑* *__________📖* Anwar yana gama shirin tafiya lokaci kawai yake jira, amma ransa bai yi daɗi ba sose, dan yaji zafi rashin ganinta, yana cikin haka sai ga iyayensa sun kirashi bayan ya ɗauka haɗi da gashesu, Abban sa yace, "Anwar nace kaje gidan Yayan ka Aminu kuwa? duk dana san baya ƙasar amma kafin ka dawo kaje ka kaima iyalinsa ziyara". Shi sam ya manta dawani Yayanshi sai yanzu da Abbansa ya kirasa. Anwar yace, "to Abba zanje zuwa anjima dan yau ma nasun na taso amma tunda zanje gidan Yaya Aminu to sai gobe dan nasan idan naje Aunty Shema nacewa sai na kwana kafin nadawo, har ma idan taji nayi sati garin nan". Abba yace, "ba damuwa amma daga kwana ɗaya ban aminci ka kuma kwana ba, kadawo gida sabida akwai aiki da yawa a office". Yace, "tau Abba insha Allahu zan dawo, ka gaishemin da Mumy tah". Abba yace, "naƙi kai kakirata". Murmushi Anwar yayi kana yace, "yanzu kuwa Abba". Yana faɗar haka ya datse kiran. Mumy sa yakira suka sha fira kuma ya tabbar mata zaije gidan Yayanshi Aminu daya ƙara kwana ɗaya sai ya dawo gida. Tunda ya hanata zuwa makaranta bata sake zuwa ba, kuma shima tunda suka dawo hospital bai ƙara dawo gidan ba. Tunani maganar sa ta farayi inda yace wai in har tana tare da Anwar zai barta, tana kawowa nan tayi ƙwafa kana tace, "yau da a ce duk abinda ke duniyar nan na Anwar ne, kuma zai malkamata shi to bazata ƙarɓaba bare ta dawo masa sabida ƙinsa da take. Tana cikin wannan tunani taji marata tafara ciyo kaɗa-kaɗan magani ta ta tashi ta ɗaku tasha amma kamar ma anci ta ƙara dan wata ƙirsa ce tamata aikuwa bashiri tafara birgima a cikin ɗakin, sose take wahala indan zatayi period kuma idan ciyo yazo har ƙafafu take riƙe mata shiyasa yanzu da take kwance ta kasa tashi ta ɗauku magani bare ta ƙara sha taji ko zata samu sauki. Anwar kiran Yayanshi Aminu yayi ya bashi address ɗin gida, aikuwa da bashi bai tsaya wani ɓata lokaci ba yabi address ɗin gida sai gashi har ƙofar gida. Knocking yayi musu ba jimawa akazo aka buɗe masa yashiga, parlour yashiga da sallamar sa, Aunty Shemah ce dake zaune ta ƙarɓa masa haɗi da ɗago kanta ta dubeshi sose. Aikuwa tana gininsa ta faɗaɗa murmushi haɗi da faɗin, "wazan gani a gidannan". Murmushi yayi haɗi ƙarasowa ya zauna kusa da kujerar da take zaune. Gasheta ya fara kana yace, "ina Affan?". Tun kan tabashi amsa sai gashi yafito da gudu yana faɗin, "Aunty zansha Ice cream". Yafaɗa haka kamar zayi kuka. Tace, "baka ga Uncle ɗinka bane naji baka gasheshi ba". Sai alokacin ya lura da mutum zaune, aikiwa da saurin shi yashiga jikinsa yana murna yana faɗi" "Uncle ɗina yaushe kazo, kazo kabani lce cream". Aunty Shema tace, "shi bai san komai ba sai abashi lce cream". rigama taga zaiyi musu kuma bazai bari su gaisa ba dan haka ta tashi taje ta ɗauko masa ta bashi, yana murna ya karɓa yana faɗin, "naje wajan Aunty Hafsat". Aikuwa yana faɗin Hafsat sai da gaban Anwar ya bada dumm. Kallon Aunty Shema yayi yace, "baƙine daku a gidan ?". Tace, "eh ƙanwata ce tazo". Yace, "oky". Tace, "saukar yaushe Anwar kuma ya kabar su Mumy da Daddy?". Wallahi nayi sati ɗaya ƙasar nan, gabaki ɗaya na manta da kuna ƙasar nan ai da nan zan sauka, amma kuyi haƙuri dan ƙila yau ma zan kuma dan naso nayi muku kwana ɗaya amma gaskiya bazan iyaba sabida ƙasar duk naji bata yi min daɗi". Yakai ƙarshin zancin damu baiyane afuskarsa. Aunty Shemah tace, "bawani kai dai dan Yayanka bashi ƙasar ne shiyasa baza zauna ba, kuma na gode". Yace, "a'a Aunty zan dowo nan bada jimawa ba insha Allah". Gabaki ɗaya jikinsa duk yayi sanyi kuma kamar kar yaji Affan ya faɗi sunan Hafsat. Aunty Shema tace, "amma sai zuwa anjima zaka tafi ko?". Yace, eh". Suna cikin haka sai ga Affan ya fito ɗakin Hafsat da gudunsa yana faɗin, "Mumy zo Aunty batada lafiya". Gaban Anwar ne ya ƙara faɗuwa yarasa dalilin haka. Aunty Shema tace, "mike damunta?". Komai baice da itaba sai ma hannuta da yaje, ba musu ta tashi ta bishi zuwa ɗakinta. Kwance ta sameta sai birgima take atsakiyar ɗaki, da sauri Aunty Shemah tazo gareta tana faɗi, "subuhanallah, Hafsat meke damunki, irin yadda taga tana riƙi ciki ya tabbatar mata cewa marata ce ke ciyo, dan haka ta ɗauko magani ta bata tashi. Bata jima da bata maganin ba ciyo ya fara lafawa, bawani ɓata lokaci bacci yayi awon gaba da ita. Aunty Shemah na shiga ɗakin Hafsat, sai ga Sulaima ya shigo parlour ɗauke da sallama abakinsa, Anwar dake zaune yana kallon labaru ya amsamasa tare da miƙa masa hannu suyi musabaha, hannun ya bashi sukayi musabaha Kafin ya bashi hannu sai da ya kalleshi sose ya tabbatar da Anwar ne, ranshi ne ya ƙara ɓaci, kenan shi tamaida marar hankali ita da Aunty Shema, to yaji ba ita ta bashi address ďinta ba to yanzu waya bashi na gidannan, yana cikin wannan tunanin sai Aunty Shemah tafito daga ɗakin Hafsat. Tana fitowa taga Sulaiman ya sadda kansa ƙasa, ƙarasowa tayi tana faɗin, "waye nake shirin gani yau a gidannan". Ɗago kansa yayi haɗi da sanya wani murmushin sannan ya gaishe ta. Sai da ta zauna ta amsa kana tace, "yanzu nake shirin nakiraka nace maka Hafsat ba lafiya, amma yanzu tasamu sauki dan tana shan magani bacci yayi awun gaba da ita, sai idan ta farka sai ka ɗan dubata tunda ita naga alamun ba duba kanta take sonyi ba". Dubanta yayi yace, "tana inane?". "Tana ɗaki". Haka tace dashi. Tashi yayi yashiga ɗakinta, kwance ya ganta kuma da ganin baccin datake bana daɗine ba, dan lokaci-lokaci sai ta yatsane fuska. Karasowa yayi wajanta hannusa ya ɗura kan nata yaji ko da zafi, ba zafi sose amma da alamu tana jin jikin. Anwar zaune yake amma duk lokacin da suka anbace Hafsat, sai yaji gabansa ya faɗi, sose yaso yaga wannan Hafsat sabida shidai yana jin wani baƙun al'amari atare dashi gami da ita, amma sai ya basar dan yasan wannan ba ita bace. Bayan ya gama dubata ya fito kafin ta tashe yayi mata wasu tambayoyi. Falo yasame su Aunty da Anwar zaune suna fira, har yaso yafita kuma sai yadawo ya zauna, bai jima da zamaba Anwar ya miƙi yana faɗi, "Aunty ni zan tafi dan so nake na sauka cikin lokaci dan Daddy yace min aiki yayi yawa office". Alamun rashin jin daɗin ne ya bayyana fuskar ta tace, "bawani ba kadai yi niya ba, kuma na gode ka gada su Mumy". Haƙuri ya bata tare da tabbatar mata bajimawa zai dawo kuma wajanta zai sauka. Addu'ar sauka lafiya ta masa sannan yayi ma Sulaiman sallama ya fice. Yana fita Sulaiman ya dube Aunty Shemah da idonsa da sukayi ja yace, "Aunty waye wannan?". "Anwar ƙanin Baban Affan ne, da Babanshi da Babanshi uwa ɗaya Uba ɗaya". Yace, "tun yaushe yazo nan?". "Iya karsa awa ɗaya" tace dashi. Har ya buɗe baki yayi magana sai ga Hafsat ta fito riƙi da ciki tana faɗin, "Aunty ki kaini hospital zan mutu". Tana faɗa tana tangaɗi alamun zata faɗi, saura ƙiris ta faɗi Saulaiman dake zaune yayi sauri ya tare ta tafaɗa jikinsa. Bawani ɓata lokaci suka wuce da ita hospital. Wata hospital ce ta mata wadda yataɓa aiki a can suka wuce da ita, suna isa da ita likitoci suka karɓeta suka wuce da ita ciki ɗakin bincike, sai da suka kammala komai sannan suka fito sukace yasamesu office. Suna isa office ɗin nasu bayan sun gaisa da yake sun sanshi sose, sabida wancan lokacin yayi aiki a hospital ɗin kuma sose suka ji daɗin zama dashi dan ba yadda basuyi ya zauna yaci gaba da aiki dasu ba yace a'a shima zaije ya taimakawa ƙasarshi. Duban doctor yayi yace, "ya mai jikin ina fatar tasamu sauki". Sai da doctor ya gyara zaman sa yace, "eh ta samu sauƙi sose kuma idan takiyaye dukukin da zamu bata kuma ta kiyaye shan magani to zata sauma sauƙi dan haka sai ankula sose". Aunty ta dube doctor tace, "mike damunt?". Sulaiman yace, "a'a Aunty ai ba sai munji ba kawai mu barsu suyi aikinsu". Aunty tace, "a'a gwara muji inyaso akiyaye gaba". Tace, "Doctor inajinka". Doctor yace, "dama bawani abu babba bane lokacin dai datayi miscarriage ba awani bata kula sose ba, kuma gashi tana buƙatar haka dan yanzu idan ba kulaba aka aji wannan abun da ya tushe mata mahaifa yakan iya zama sanadiyar haka bazata sake ɗaukar ciki ba". Wata ajiyar zuciya Aunty ta sauke mai ƙarfi kana tace, "ayi mata duk abinda yakama doctor". Tana faɗar haka bata tsaya komai ba ta fito daga office ɗin ranta aɓace. Irin yadda Sulaiman yaga ta fito jikinsa duk sai yayi sanyi dan shi bai so doctor yayi bayani akan matsalar Hafsat ba, da yasan zatace ayi mata bayani wallahi da bai bari ta shigo office ɗin ba, tunanin yaga bazai ƙareba, dan haka ya tashi yabita yaji mi zata ce. Tunda Anwar ya bar gidan gabansa ke famar faɗuwa har inda yazo masaukin sa ya haɗa duk wani abun buƙatar shi yayi sallama da abukinsa sannan yarakashi filin jirigi. Shidda na yamma Anwar yabar ƙasar india zuwa ƙasar sa ta haihuwa wato nigeria. Koda yaje har tashiga mota shi kadai take jira, dan da ace makulin motar na hannuta da tuni tajima da bari hospital ɗin. Yana ƙarasowa yashiga motar yaja suka tafi gida, har suka isa ba wanda yayiwa ɗan uwansa magana. Yana yin parking ta buɗe mota tafito zuciyar ta na ƙuna sabida wani baƙinciki da ya rufe ta. Bayan ya kashe motar ya bi bayan ta, parlour yasame ta sai safa da marwa take cikin parlour. Ɗayan kujera ya zauna kana ya dube ta yace, "Aunty"......kafin ya kai ƙarshe tace, "dakata Sulamain! bana son jin komai daga bakin ka, wato ni kamai da wawuya marar hankali shiyasa har za ka ɗauku budurwar dakake tare da ita ka kawomin gida matsayin ƴar makaranta wai ita mai kamun kai ko! kuma har kana iƙirarin auren ta, to kasani daga yau ba kai ba ita dan haka kar ka kuskura kadowo da ita gidannan kuma yanzu zan kira su Abba na gaya musu abinda ake ciki, ni kodama nayi mamakin abin da ya maidaka ƙasar nan da sunan karatu ashe kai kadai kasan karatun da zakayi". Haka taci faɗanta har ta gama bai ce da ita komai ba, sai da aka ɗau lokaci yana zaune kana ya buɗe baki yace, "Haba Aunty wallahi bansanki da haka ba, ni nasan Aunty na mai tausayi ce da kuma haƙuri kuma nasan Aunty na bata zartar da hukunci har sai tayi bincike akai, dan haka nake ruƙunki dan Allah ki tsaya ki saurareni plees". Dubanta yayi yaji miza tace amma sai yaji bata ce komai ba, irin yadda yaga tabada natsuwar ta yasan zata saurareshi. "kamar yadda kika sani ina son Hafsat so bana wasa ba dan tun lokacin da na fara haɗuwa da ita makaranta nakamu da sonta, amma itako alokacin ba soyayya ce gabanta ba kartu shine gabanta shiyasa ko saurarena bata tsayayi ba, ban jima da haɗuwa da itaba ne nazo ƙasaranan dan na yi phd, sai dai duk wani mutsi nata idan tayi sai nasani koda kuwa bani tare da ita, kuma dakika ce Hafsat yarinya tace wallahi ko ɗaya, ni banta sanin Hafsat ƴa mace ba, ke ba itaba duk wata mace babu ta inba Maryam matata ba, Aunty, Hafsat daki ka gani wata ƙaddara ce ta afka akanta, wadda duk wani musulmi mai imani ya tausaya mata, data na nigeria Allah ya haɗata da wani sheɗanin saurayi wanda ya illata mata rayuwa kuma duk da haka bai bar ta ta huta ba yaƙi ya rabu da ita, nikuma lokacin dana samu labarin haka shine nayi shige da fice har tasamu scholarship na tafiya waje karatu ko zai rabu da ita, to nayi nasar rabasu amma yanzu haka yananan yana neman ta ruwa ajallo, danshi na hanata fita makaranta kwana biyu wannda ke da ita baku san dalilil haka ba". Dubanta yayi yace, "Aunty labarin Hsfsat nada tsayi amma kiyi haƙuri sabida duk lokacin dana tuna sai nayi ƙwalla, amma wani lokaci zan baki insha Allah". Kallonsa tayi da kyau kana ta buɗa baki tace, "yanzu har kasan yadda take amma kake ƙoƙarin kajefa kanka aciki, to bari kaji koda zan yarda taci gaba da zama gidannan to bazan yarda ka aureta ba, dan da alamu ba ajinka bace, dan haka nake baka shawara tun wuri kaciri wannan so dakake mata dan gaskiya bazamu barka ka aure yarinyar da bata da kamunka ba". Yace, "Aunty kuyi haƙuri dan inaji ajikina rasa Hafsat dai-dai yake da rasa raina, Aunty bansaki da haka ba, kuma ki gayamin gaskiya, zaman da Hafsat tayi agidannan akwai abinda tayi wannda zai nuna rashin kamun kanta?". Kai ta girgiza masa alamar a'a. "Kingani dan haka Aunty kirufamin asiri karki bari kowa yaji wannan maganar kuma kitaya ni da addu'a". Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kana tace, "na fahince ka, kuma insha Allah ba maijin wannan zance". Yace, "yauwa Aunty na, na gode sose". Murmushi tayi kana tace, "yaushe zaka zo muje muga yadda jikin nata yake?". "Sai gobe, sabida ina tunanin idan muka tafi tare da ita zamu dawo inyaso taciga da shan maganinta". Tace, "to haka yayi". Sallama yayi mata yatafi da sunan gobe zai dawo. ******* Safiyya ce kwanci ɗakinta ita kadai, ba abinda take sai aikin tunanin ƴar uwata Hafsat, tayi kuka har tagaji na rashinta, gashi har yanzu ko waya basu taɓayi ba, kuma ga Babanta har yau fushi yake dasu, duk abu yazo ya haɗe mata waje ɗaya, dan yanzu maganar da ake Baban ta yace wata biyu ya bata ta kawo masa miji dan aure zaiyi mata, kuma ita duk cikin masu sonta bataji wanda ya kwanta mata araiba, tana ciki haka taji Yayan ta Abbas na kiranta, da sauri ta tashi ta fita. Zaune ta samesu shida Mama zaune, ƙarasowa tayi ta zauna kusa da Mama tana faɗin, "gani Yaya". Wata leda dake gabansa yace, "gashi kije ki kawa Umma, kice ina gaisheta anjima zanzo". Karɓa tayi tace tau bari nasa hijab ɗina". Tana sawa ta ɗauka tafice Mama tace tana gaisheta.... *#VOTE COMMENT SHARE* *SHAFI NA 28📑* *__________📖* Koda taje gidan su Hafsat, sose Umma taji daɗin ganin ta tace, "Umma gashi inji Yaya yace na kawo miki yana gasheki kuma anjima zai zo". Sai da Umma ta karɓa tace, "to mungode, ai yanzu bashi ba ko ke kin daina zuwa, yanzu nida Mamarku kaɗai ke zumunci, amma kema dan ƴar uwarki bata nanne, nasan da kinzo". Sai da Safiyya ta sadda kanta ƙasa kana tace, "a'a Umma yanzu ba ko ina nake zuwa ba sabida bana jin daɗin fitar". Ta kai ƙarshin zanci kamar tayi kuka. Dubanta Umma tayi da alamun tausayawa tace, "wai Safiyya har yanzu baki samu ko number wayar taba? wallahi yanzu haka sabida baƙincikin rashin ta har na kamu da matsalar ido, dan yanzu ba komai nake gani sose ba, Safiyya dan Allah ki ƙara bincika muna koda mai number ta yabamu, dan kwannan ina yawan mafarkinta tana kuka". Magana take amma hawaye na zuba a idonta. Safiyya ma da taga Umma na kuka itama bata san lokacin da yazo mata ba, cikin kuka tace, "Umma insha Allah gobe zanje makaranta na ƙara bincike koda Allah zai sa musamu number ta". Godiya Umma tayi mata haɗi da sanya mata albarka. Safiyya tashi tayi ta taya Umma sauran aikace-aikacin gida daga baya tayi tafiyar ta. ******* Saida su Hajara sukayi kwana biyu police station sannan akafito dasu dumin atambaye su daga ina suke?. Wani ɗan ƙaramin ɗakine mai kama da akurkin kaji wannda ko mutum ɗaya yace ya zauna sai ya wahala bare mutum biyu, shi aka buɗe suka fito daga ciki kamar wasu ƴa yunwa, sabida kwana biyun da sukayi har sun fara zanja kala. Gaban DpO aka tisasu, sai da yagama yimusu kallon tsaf kana yace, "watu kune ke fitowa dan kulalata muna ƙasa ko?". A wahalce, "Hajara ta buɗa baki tace, "wallahi a'a asali mu ƴan makarantane". DpO yace, "wace alama zangani wadda zata tabbatar min ku ƴan makaran tane". Jiki na karkarwa ta buɗe jika ta ɗauku l. D card ɗinta na makaranta ta nuna masa. Karɓa yaya kana ya duba yace, "to mi yafitar duku cikin dare?". Rasa mizata ce tayi sai can tace, "Kakatace kuma ita kaɗai ta ragemin aka bugu min waya akaci ta rasu shine na ce sai naje ita kuma ƙwata tace nabiri da safe muje nace a'a to shine tace zata rakani, muna fitowa muka samu ɗan acaɓa to yana shigowa damu cikin garin sai yatusamu wajan da kuka ganmu". Takai karshin maganar tana kuka sose. Bayan dpo yagama ƴan rubuce² sa ya sallamesu tare da jamusu kunne sose, kana suka kama hanyar fita. Bayan sun fito kallon-kallon suka farayi tsakanin su sai Zahara ta buɗa baki tace, "to yanzu ina zamuje?". Sai Hajara tace, "muƙarasa wajan gidan Malam, dan wallahi wannan uwar wahalar da muka sha bazata tashi abanza ba sai munɗau fansa akan Anwar da Hafsat". Sai zahara tace, "da muntafi gida zai fi". Hajara tace, a'a gaskiya ni ba inda zanje, sai inke zaki tafi na tarar miki napep kije". Tace, "a'a tare muka zo kuma tare zamu koma, haka suka ƙarasa cikin garin da Malamin yake, wani gida suka yadda zango kuma suka ruƙesu nan zasu zauna har lokaci da zasu je wajan Malam yacika, bamusu ko suka yardar musu har lakaci ya cika. Ƙarfe ukun dare nayi suka fito suka tafi wajan Malamin can saman wani dutsi, kuma koda suka je wajan cike yake da mutane duk wannda ke wajan burisa ya ƙarasa wajan bokan nasu. Sai wajan ƙarfe huɗu su Hajara suka samu shiga, bayan sun shiga basu wani jama ba suka fito ɗauke da murmushi afusakar su, waje suka samu suka zauna har inda gari yayi haske sannan suka kamu hanyar gida ciki da farin ciki a zukatansu. Hafsat tana hospital kwance tana bacci, kanata take gargizawa tana so ta tashi amma takasa, sai can ta samu ta buɗa baki ta ambace sunan Allah, aikuwa tana faɗin haka ta farka cikin razana sai haki take kamar wanda tayi tsarar gudu. Ba ɓata lokaci ta tashi tashga toilet ɗin dake cikin ɗakin, alwala ta ɗuru tazo ta tada sallar nafila. Haka ce ta faru wajan Ummar Hafsat itama wani mugun mafarki tayi kuma akan Hafsat, ba ɓata lokaci taje ta ɗuru alwala ta tada sallah tana kai kukanta wajan Allah. Hafsat tana gama sallah ta ɗauku wayar ta ƙur'ani dake kan wayar ta ta buɗe ta fara karatu, sai datayi karatu sose tafara koro addu'oi tana kuka tana faɗin, _Lailahailla anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin._ _Hasbiyal lahu lailaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul arshil azeem._ Haka take ta mai-mai tawa tana kuka sose, dan baƙaramin tashin hankali tashigaba gami da wannan mafarki, tana kan sallaya har akayi kiran sallah ta gabatar da sallah tana cikin tasbihi bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Gyafin Umma ma haka ta kasance. Kusan ƙarfe goma sai ga sulaiman yazo wajan Aunty Shemah dan su yake suje suga ya jikin nata. Bai jima da tahuwa ba sukaje wannan karum har da Affan. Koda suka isa wajanta sai bacci take, mutsin da tajine shi ya farkar da ita daga baccin da take, ahankali ta buɗe idonta, wayar dake kusa da ita ne ta ɗauku ta duba lokaci, sose tayi mamakin wannan baccin da tayi, kuma yanzu wasai take jin jikinta kamar bata taɓa ciyo ba,juyawar da zatayi sai ganin Aunty da Sulaiman tayi suna mata murmushi, martanin murmushin ta mayar musu kana tace, "Aunty ku ƙaraso". Affan ne ya antayo da gudu ya faɗa jikinta yana faɗi, "missing you Aunty na". Murmushi tayi kana tace, "missing too Affan". Tana faɗa tana jan kuma tunsa. Har zai sake magana Aunty tace, "kada kacika mu da surutu nan ba gida mukeba hospital muke". Murmushi Hafsat tayi haɗi da gaishesu. Amsawa sukayi sannan sukayi mata yajiki?. Tace, "gaskiya ni yanzu ba abinda ke damuna, ni kwai mu koma gida". Sulaiman yace, "bari naje naji mi zasu ce idan suntabbatar da kin ji sauƙi sai muwuce gida. Bai jima da fitar sa sai gashi ya dawo tare da faɗin, "Aunty sunce zamu iya tafiya dan duk wani bincike sun mata kuma sunce yanzu bawani matsala sai dai takiyaye shan magani". Aunty tace, "insha Allahu zata kiyaye". Daga haka suka juyo zuwa gidan Aunty Shemah. ***** Tunda ya tashi bacci yaji sabon al'amari ajikinsa, dan jiyake kamar bashi ba, ya kasa tsaye ya kasa zaune, shidai burinsa yaganshi a sokoto yanzu. Wayar sa ya ɗauka ya dan yakirata kuzai samu natsuwar abinda yakeji.... *#VOTE COMMENT SHERA* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 28📑* *__________📖* Koda taje gidan su Hafsat, sosai Umma taji daɗin ganin ta tace, "Umma gashi inji Yaya yace na kawo miki yana gasheki kuma anjima zai zo". Sai da Umma ta karɓa tace, "to mungode, ai yanzu bashi ba ko ke kin daina zuwa, yanzu ni da Mamarku kaɗai ke zumunci, amma kema dan ƴar uwarki bata nan ne, nasan da kin zo". Sai da Safiyya ta sadda kanta ƙasa kana tace, "a'a Umma yanzu ba ko ina nake zuwa ba sabida bana jin daɗin fitar". Ta kai ƙarshin zanci kamar tayi kuka. Dubanta Umma tayi da alamun tausayawa tace, "wai Safiyya har yanzu baki samu ko number wayar taba? wallahi yanzu haka sabida baƙin cikin rashin ta har na kamu da matsalar ido, dan yanzu ba komai nake gani sosai ba, Safiyya dan Allah ki ƙara bin cika muna koda mai number ta yabamu, dan kwannan ina yawan mafarkinta tana kuka". Magana ta ke amma hawaye na zuba a idonta. Safiyya ma da ta ga Umma na kuka itama bata san lokacin da yazo mata ba, cikin kuka tace, "Umma insha Allah gobe zanje makaranta na ƙara bin cike koda Allah zai sa musamu number ta". Godiya Umma tayi mata haɗi da sanya mata albarka. Safiyya tashi tayi ta taya Umma sauran aikace-aikacin gida daga baya tayi tafiyar ta. ******* Saida su Hajara sukayi kwana biyu police station sannan akafito dasu dumin atambaye su daga ina suke?. Wani ɗan ƙaramin ɗakine mai kama da akurkin kaji wannda ko mutum ɗaya yace ya zauna sai ya wahala bare mutum biyu, shi aka buɗe suka fito daga ciki kamar wasu ƴa yunwa, sabida kwana biyun da sukayi har sun fara zanja kala. Gaban DpO aka tisasu, sai da yagama yimusu kallon tsaf kana yace, "watu kune ke fitowa dan kulalata muna ƙasa ko?". A wahalce, "Hajara ta buɗa baki tace, "wallahi a'a asali mu ƴan makarantane". DpO yace, "wace alama zangani wadda zata tabbatar min ku ƴan makaran tane". Jiki na karkarwa ta buɗe jika ta ɗauku l. D card ɗinta na makaranta ta nuna masa. Karɓa yaya kana ya duba yace, "to mi yafitar duku cikin dare?". Rasa mizata ce tayi sai can tace, "Kakatace kuma ita kaɗai ta ragemin aka bugu min waya akaci ta rasu shine na ce sai naje ita kuma ƙwata tace nabiri da safe muje nace a'a to shine tace zata rakani, muna fitowa muka samu ɗan acaɓa to yana shigowa damu cikin garin sai yatusamu wajan da kuka ganmu". Takai karshin maganar tana kuka sose. Bayan dpo yagama ƴan rubuce² sa ya sallamesu tare da jamusu kunne sose, kana suka kama hanyar fita. Bayan sun fito kallon-kallon suka farayi tsakanin su sai Zahara ta buɗa baki tace, "to yanzu ina zamuje?". Sai Hajara tace, "muƙarasa wajan gidan Malam, dan wallahi wannan uwar wahalar da muka sha bazata tashi abanza ba sai munɗau fansa akan Anwar da Hafsat". Sai zahara tace, "da muntafi gida zai fi". Hajara tace, a'a gaskiya ni ba inda zanje, sai inke zaki tafi na tarar miki napep kije". Tace, "a'a tare muka zo kuma tare zamu koma, haka suka ƙarasa cikin garin da Malamin yake, wani gida suka yadda zango kuma suka ruƙesu nan zasu zauna har lokaci da zasu je wajan Malam yacika, bamusu ko suka yardar musu har lakaci ya cika. Ƙarfe ukun dare nayi suka fito suka tafi wajan Malamin can saman wani dutsi, kuma koda suka je wajan cike yake da mutane duk wannda ke wajan burisa ya ƙarasa wajan bokan nasu. Sai wajan ƙarfe huɗu su Hajara suka samu shiga, bayan sun shiga basu wani jama ba suka fito ɗauke da murmushi afusakar su, waje suka samu suka zauna har inda gari yayi haske sannan suka kamu hanyar gida ciki da farin ciki a zukatansu. Hafsat tana hospital kwance tana bacci, kanata take gargizawa tana so ta tashi amma takasa, sai can ta samu ta buɗa baki ta ambace sunan Allah, aikuwa tana faɗin haka ta farka cikin razana sai haki take kamar wanda tayi tsarar gudu. Ba ɓata lokaci ta tashi tashga toilet ɗin dake cikin ɗakin, alwala ta ɗuru tazo ta tada sallar nafila. Haka ce ta faru wajan Ummar Hafsat itama wani mugun mafarki tayi kuma akan Hafsat, ba ɓata lokaci taje ta ɗuru alwala ta tada sallah tana kai kukanta wajan Allah. Hafsat tana gama sallah ta ɗauku wayar ta ƙur'ani dake kan wayar ta ta buɗe ta fara karatu, sai datayi karatu sose tafara koro addu'oi tana kuka tana faɗin, _Lailahailla anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin._ _Hasbiyal lahu lailaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul arshil azeem._ Haka take ta mai-mai tawa tana kuka sose, dan baƙaramin tashin hankali tashigaba gami da wannan mafarki, tana kan sallaya har akayi kiran sallah ta gabatar da sallah tana cikin tasbihi bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Gyafin Umma ma haka ta kasance. Kusan ƙarfe goma sai ga sulaiman yazo wajan Aunty Shemah dan su yake suje suga ya jikin nata. Bai jima da tahuwa ba sukaje wannan karum har da Affan. Koda suka isa wajanta sai bacci take, mutsin da tajine shi ya farkar da ita daga baccin da take, ahankali ta buɗe idonta, wayar dake kusa da ita ne ta ɗauku ta duba lokaci, sose tayi mamakin wannan baccin da tayi, kuma yanzu wasai take jin jikinta kamar bata taɓa ciyo ba,juyawar da zatayi sai ganin Aunty da Sulaiman tayi suna mata murmushi, martanin murmushin ta mayar musu kana tace, "Aunty ku ƙaraso". Affan ne ya antayo da gudu ya faɗa jikinta yana faɗi, "missing you Aunty na". Murmushi tayi kana tace, "missing too Affan". Tana faɗa tana jan kuma tunsa. Har zai sake magana Aunty tace, "kada kacika mu da surutu nan ba gida mukeba hospital muke". Murmushi Hafsat tayi haɗi da gaishesu. Amsawa sukayi sannan sukayi mata yajiki?. Tace, "gaskiya ni yanzu ba abinda ke damuna, ni kwai mu koma gida". Sulaiman yace, "bari naje naji mi zasu ce idan suntabbatar da kin ji sauƙi sai muwuce gida. Bai jima da fitar sa sai gashi ya dawo tare da faɗin, "Aunty sunce zamu iya tafiya dan duk wani bincike sun mata kuma sunce yanzu bawani matsala sai dai takiyaye shan magani". Aunty tace, "insha Allahu zata kiyaye". Daga haka suka juyo zuwa gidan Aunty Shemah. ***** Tunda ya tashi bacci yaji sabon al'amari ajikinsa, dan jiyake kamar bashi ba, ya kasa tsaye ya kasa zaune, shidai burinsa yaganshi a sokoto yanzu. Wayar sa ya ɗauka ya dan yakirata kuzai samu natsuwar abinda yakeji.... *#VOTE COMMENT SHERA* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 29📑* *__________📖* Tana kwance ɗakin su Zahara, dan tunda suka dawo bata koma ɗakinta ba, bari tayi har ta ɗan dawo dai-dai, dan ta san da taje can ɗakinsu zasu cikita da tambaya miya faru da ita, tana cikin wannan tunanin taji wayar ta na ƙara, tsaki taja sannan ta ɗauka daniyar tayi piking, aikuwa sunan da taga ya bai yana kan screen ɗin wayar ai bata san lokaci da ta tashi zaune ba haɗi da faɗi, "Zahara zo kigani". Tafaɗi haka ciki da farin ciki. Zahara da ke toilet da sauri ta fito, kafin tayi magana Hajara ta nuna mata wayar ta da ke rura, sunan da taganine yasa tayi guɗa haɗi da ta ka rawa, sannan tace, "kada ki ɗauka barshi har sai ya kawo kanshi". Hajara tace, "ko dama bani daniyar ɗauka, aikuwa haka tayi ta ƙarar har yagaji da kira ya aje wayar zuwa ajima ya koma kira ko zai ta ɗauka. Anashi ɓangare ba ƙaramin haushi yaji na rashin ɗaukar wayar da batayi ba, lokaci ɗaya yaji gwara yaje da iran yadda yakeji shi baya iya zama bai gantaba, part ɗin iyayensa ya nufa cikin sa'a koda yaje lokacin suka fito dan yin beark, ƙarasowa yayi wajansu kujrar dinning yajewo ya zauna sannan ya gaishesu, bayan sun amsa sai Mumy ta dube Anwar da kyau, kana tace , "Autana, wai mike dumunka naganka yau duk kawani ya mutse kamar ba kaiba". Sai Daddy sa yace, wallahi tunda yaje sokoto ya dawo nake ganinsa haka, kafaɗamuna idan akwai abinda ke damunka muji idan zamu iya baka taimako sai mu baka, amma katsaya kana tawani ɓoye muna abu, gaskiya bamasan haka". Yakai ƙarshin maganar yana dubin Anwar ranshi kamar a ɗan ɓace. Jikinsa a sannyaye yace, "a'a Daddy ba abunda ke damuna gaskiya, kuma da kukace duk na yamutse, ai kwanan ina fama da zazzɓi ne shiya kawo min haka amma yanzu alhmadulillah". Ba dan sun yarda ba suka ce to Allah ya ƙara lafiya. Daddy yasake magana haɗi da duban Anwar yace, "kuma kashin sati nasama za'aje neman aurenka da Saudat, ƴar gidan Alhaji Sambo". Da dauri Anwar ya ɗago kansa yace, "mikace Abba!. "Abinda kunnenka yaji shi nace". Yace, "gaskiya Daddy ni ba ita nake so ba". Ai Daddy da Mumy lokaci ɗaya suka ɗau salati kana suka ce atare, "baka sonta!!. "Eh" yace dasu, ai tun bai rufe baki ba Daddy yace, "wallahi Anwar karya kasha kuma baka isaba dan bazaka maidani ƙaramin mutum ba, farko kace kana so yanzu kuma kace baka so, to bari kaji wallahi ba gudu baja da baya in har kaga ba iyiba to ɗayan mune bashi da rai". Yana faɗar haka suka tashi domin su bar wajan ransu amatuƙar ɓace, wato su Anwar zai rainawa da hankali ya maidasu ƙananan mutane. Shima ɗin ranshi amatuƙar ɓace ya tashi ya je ɗakinsa, key ɗin motar sa ya ɗauka, ai fusace yazo ya fige motar ya kama hanyar garin sokoto. Gudu yake kamar ya fira sama cikin awa huɗu sai gashi yazo garin sokoto, hanyar da zata sadashi da unguwar da Hajara take zaune ya ɗauka, gudu yake ko kallon gabansa bayayi, kwatsam gaji abu yaba da gab gab, har yaso yaƙi tsayawa, amma irin yadda yaga mutane sun taso masa yasa ya tsaya amma ba dan ransa yaso ba. Kuda yafito cikin motar yazo wajan dan yaga waya bige, wani mutum shi ba tsofo ba kuma shi ba yaro ba, yagani kwance da alamu ko numfashi bayayi, aikuwa Anwar na ganin haka hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin hanzari yasa wasu daga cikin mutanin aka ɗaukeshi a kasa mota kana suka wuce hospital. ******* Kwance take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, dan gabaki ɗaya hankalinta baya jikinta, wayar tace ta fara rura, ɗauka tayi batare da ta buɗe ido ba bare ta duba wake kiranta, muryarsa ce dataji yasa ta shaidashi . Sallama yayi mata kana ta karɓa sannan ta gaisheshi, shuru ne ya biyu baya sai can yayi magana cikin kasalaliyar murya yace, "Hafsat". Da taji haka sai da taji wani abu ajikinta kana ta buɗe baki can ƙasan maƙoshi tace, "na'am Yaya". Sai da ya sauke ajiyar zuciya kana yace, "yajiƙin naki, ina fatar kinsamu sauƙi". Tace, "sosai kuwa dan yanzu wasai nake jina kamar banyi ciyo ba". murmushi yayi kana yace, "kodama nace bari na gayamin ko zakije gida kiyi hutun ƙarshin shekara a can? inyaso idan hutu ya ƙare sai nabiya miki kuɗin jirgi ki dawo". Tun bai kai ƙarshin zancen ba tace, "Aunty Shema zata je ne". Yace, "a'a ita sai ta kammala zata koma dan kwanannan mai gidanta zai zo". To nima gaskiya bazanje ba, dan koni bazan sake komawa gida ba sai na gama karatu gabaki ɗaya, amma inaso idan kaje kayi min abu ɗaya, ka karɓumin number Safiyya da Naja'atu please". Rasa mi zaice da ita yayi, dan haka yace, "tom naji, ƙoƙari datse kiran ya fara, sai tayi saurin faɗin, "in ba damuwa inaso na koma hostel da zama tunda mijin Aunty zai zo ka ga kar na takurasu". Kasa magana yayi sai can yace duk yadda kikayi dai-dai ne". Yafaɗi haka ransa a ɓace yana faɗa ya datse kiran batare da ya ji mizata sake faɗa ba. Tanajin yadda yayi maganar tasan baiji daɗin abinda tace ba, amma ita gaskiya ji take idan yazo yatar da ita gidan kamar ta takurashi dan haka ma yasa tayi wannan tunanin. Ummar Hafsat ce zaune tayi tagumi abin duniya duk yabi ya dameta ga Baban Hafsat tun safe yafita har yanzu bai dawo gida ba, kuma takira wayarsa amma ance kashe take, kuma gashi su Marwan har yanzu basu dawo ba bare tace su nemumatashi wata ƙila yaje wurin aikin sane, dan yanzu gabaki ɗaya duniya tayi musu zafi dan tun wancan watan aka sallame Abban Hafsat daga aiki, sabida wata sata da a kayiwa , company kuma a kace sai sun biya, haka Abban Hafsat ya tattara duk wata ƙadara tashi ya sayar yabiya su kuma suka sallameshi daga aiki, a cewarsu har dashi cikin masu yimusu sata, abubuwa duk sun tsaya dan ko karatun su Marwa ya tsaya sabida ba abinda za ayi afani dashi wajan cigaban karatunsu, abun dai sai wanda ya gani danshi yanzu sai sun fita kasuwa sunyi dako sannan zasu samun abinda suka ci, ko Baban Safiya yayi musu aike ko Abbas Yayan Safiya. Yau ma kamar kullum akatashi ba komai a gidan, dan ko abin da zasu karya babu kuma gashi Abban Hafsat ko kwabo baya da, dan haka yace a bari yazo, fita yayi yaje wajan wani abokinsa ko da zai samu rance, to yana kan hanyar tafiyane ya kawo dan ya tsallake ti-ti bai san da wani abin hawa ba, dan haka yazo dan ya tsallaka, aikuwa yana dab da tsallakewa yaji wani abu yabashi gab-gab...... *#VOTE COMMENT SHERA* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~VOTE & FOLLOW 4~ ~Wattpad Summy M Na'ige~ *SHAFI NA 30📑* *__________📖* Tun lokacin bai saike sanin inda kansa yake ba sai a gadon hospital, lokacin da ya farko, da ƙyar ya buɗe bakin sa ba abinda yake ambatowa sai sunayin Allah, yana cikin haka sai ga Anwar ya shigo, da sauri ya karasa gareshi yana faɗin, "Abba sannu ka farka? ya kakeji yanzu?". Bai ce dashi komai ba, sai da ya kuma wata magana yace, "Abba ko kana da waya a kira iyalinka a shaida musu halin da ake ciki?". Sai da Abban Hafsat yaji an ambace iyalinsa sannan ya ɗago da kansa ya buɗe baki da ƙayar yace, " ina tunanin banzo da waya ba, amma idan kana da ita sai nasaka number yarona ko mai ɗakina ka kira". Yayi wannan maganar kamar sheɗar sa tafita daga jikinsa. Sosai Anwar ya tausayawa halin da yake ciki dan har ga Allah bai da niyar ya tsaya, amma da yaga halin da wannan bawan Allah yake ciki yaji zai tsaya har yasamu ɗan sauki. Wayar sa ya ɗauku ya miƙa masa yace, "Abba gashi kasanya number". Ba musu ko ya karɓa, da ƙyara yake danna wayar har yasanya ya bashi yace yakira ya faɗa musu halin da a ke ciki. Ringing da bai wuce uku ba aka dauka, Maryar namiji yaji dan haka yayi masa sallama, bayan sun gaisa yake faɗa masa Abbanka yace, "a sanar da ku yasa mu haɗari dan yanzu haka an kwantar dashi asibiti, amma da sauƙi dan har ya farfaɗo kuma shi ya bada number ka a kiraka"....tun bai kai ƙarshin zancin ba sai Marwan yafara magana cike da tashin hankali yace, "dan Allah wanne asibiti?". Wata hospital ɗin kuɗe ce ya faɗa masa, yace gasu nan zuwa yanzu. Aikuwa Marwan na gama waya da Anwar ya ƙarasa gida ciki da tashin hankali ya faɗawa Ummar su halin da ake ciki, hannun ta ɗura saman kai tafara kuka kamar ranta zai fita, da ƙyar Marwan ya rarrashe ta tayi shuru kana suka shiriya sukaje hospital ɗin. Dayake hospital ɗin da ya kaishi sannan na ce aciki garin sokoto, dan haka basusha wahala wajan gane wajan da yake ba. Suna shiga ɗakin da Abba yake suka tarar da Anwar zaune kusa dashi shiko Abba yana bacci, da sauri Umma ta ƙaraso garesa tana kuka tana faɗan, "dan Allah kar katafi ka barmu Abban Hafsat". Yana cikin bacci yaji kukanta, dan haka ya buɗe idonsa, hannu ya ɗura saman kanta, ɗagowa tayi da kanta, alamun yayi mata da tayi shuru , ba musu ko ta ɗan rage kukan da takeyi. Anwar dake zaune yanajin sun ambace Hafsat sai da gabanshi ya faɗi, shi bai san mike faruwa dashi ba, duk lokacin da yaji sunan Hafsat sai yaji faɗuwar gaba. Tashi yayi yayi musu sallama yace zuwa ajima zai dawo. Da fitarsa bai tsaya ko inaba sai wajan da a kace masa zai ga Hajara, yana isa kuma a kace yanzu suka bar wajan, yinin ranar duk inda yake tunanin zai ganta yaje amma bai ganta ba, sosai yaji zafin wannan lamar yayi danasanin zuwan sa garinnan yanzu, dan da yasan haka zata faru dashi da bai zo ba, kiran sallah da yaji anayi ne yasa yayi parking ɗin motar sa yashiga masallace, bayan an idar da sallah sai limamin wajan yayi karatu tare da karanta wasu ayoyi na alƙur'ani kuma ya fassarasu har inda ya kawo cewa duk wani bala'i ko musiba idan sun afku gareka to ka yawaita sadaka, kuma duk wani abu dakake san samu to yawaita sadaka, nan dai limamin yaci gaba da wa'azi da nuna mahin mancin sadaka, sosai Anwar ya natsu yana saurarin abinda ake magana akai, dan rabanshi da yaje wurin wa'azi ko ya saurareshi har ya manta, bayan limamin ya kammala kana a kayi sallah isha'i sannan Anwar yafito daga cikin masallacin, aikuwa bai bar unguwar da yake ba sai da yafitar da kuɗi masu yawan gaske ya fara sadaka, da yake unguwar da ya tsaya marasa ƙarfi sunfi yawa, aikuwa sai ganin mutane kake suna fitowa maza da mata yara da manya wajan karɓar sadaka. Duk kuɗin dake hannunsa sai da yara bar da su, kuma suna ƙarewa sai ga wata tshowa tazo wajansa tana faɗin, "dan Allah Alhaji ka taimaka min wallahi ƴata ce bata da lafiya kuma likitoci sunce sai ammata aiki kuma wallahi bamu dasu dan yariyar marainiya ce". Tafaɗi haka hawaye na zuba a idonta. Rasa mai zaiyi yayi dan kuɗin dake hannunsa sun ƙare dan haka yaje mota ya ɗauko cheque, rabin million ya rubuta mata yace gasu ayi haƙuri, sosai ƴar tsohor nan taji daɗi lokaci ɗaya ta fara suburbuɗu masa da addu'oi tana faɗin, yadda kayaye min wannan baƙinciki kaima Allah yaya ye makashi haka ta cigaba da kwararo masa addu'a har yabar wajan. Masalacin da yayi sallah ya koma, limamin masallacin ya je sukayi magana dashi a kan zai gyara masallacin, dan masallacin yana son gyara sosai, dan haka ba ɓata lokaci ya rubuta cheque ɗin million ɗaya ya bayar yace a gyara masallaci, sosai sukayi masa addu'a daga baya ya shigo mota ya dawo hospital dan yaga ya mai jiki. Tuƙi yake amma sai jinsa yake kamar anɗauke masa wani abu aka. Koda yaje asibiti jikin Abba Alhmdulillah dan sosai yasamu sauki dan shi abin har mamaki ya bashi, gaishesu yayi kana ya aje musu abinda ya sayo musu sannan yayi musu sallama kan sai da safe idan ya dawo, sosai suka yi masa godiya irin yadda yatsa ya jajirce akan ciyon Abba, dan yanzu sau tari mutum ya bige mutum amma ba zai tsaya ba bare ya bashi kulawa, wani ko ya tsaya da zaran ya kai shi asibiti zai gudu, amma shi ya tsaya har yana faɗin gobe zai dawo, tunanin da Ummar Hafsat keyi kenan. Yana fita daga ɗakin sai ga Safiyya tazo ita da iyayenta da Yayan ta, Allah ne kawai bai haɗasu ba, dan saura kaɗan suyi karo da Yayan Safiyya akan hanya. Yana fitowa a hospital bai tsaya ko ina ba sai ma saukin sa, yana shiga bayan yayi parking ɗin motar yafito bai tsaya ko ina ba sai falon gidan, zama yayi saman kujera three seated ya ɗan huta, dan yanzu ji yake kamar an ɗauke masa wani abu kai, wanka yaje yayi sannan ya kwanta, wayar sa ya ɗauku ya kira iyayensa ya shaida musu wani uzuri ya kamashi na gaugawa yanzu haka yana sokoto, basuce dashi komai ba sai fatan alhairi. ___________________ Suna gama waya da Anwar wata ƙawarta takirata tace, "wai hala Hajara baza kizo birthday ɗina ba, kuma kinsa za'ayi casu". Aikuwa Hajara najin haka tace, "kar ki samu damuwa yanzu zaki ganni". Tana gama faɗar haka ta tashi tashiga toilet tayi wanka, sosai ta ɗan ɗasa kwaliya kamar wani abu bai same taba. Kallon Zahara tayi dake zaune tace, "Zahara zaki rakani shukura hotel wajan birthday ɗin ƙawata?". "A'a bazanje ba dan kinsan ba wajan zuwa nane ba". Cewar Zahara. Tace, "ba damuwa ni zanje sabida nasan akwai harka". Tana faɗar haka ta kama hanyar fita daga ɗakin. Zahara tace, "ki tsaya mufita tare inyaso kowa yaje wurin da zashi. Haka kuwa sukayi dan suna kawowa bakin ti-ti ko wace ta tsayar da mai napep ta faɗa masa wajan da zai kai ta. Dai-dai shukura hotel aka aje Hajara, kuɗinsa ta bashi kana ta ƙarasa daga ciki, tun bata ƙarasa ba ta fara jin kiɗa natashi kamar zai tsaga ƙasa, koda ta ƙarasu wajan da aka kiɗan yacika sosai, maza da mata kuwa sai rawa yake kuma cikinsu ba mai shigar kirki, kace su duk ɗiyan arnane. Tana cikin tafiya taji an rungumuta ta baya, juyuwar da zatayi dan taga kowaye, bashiri taji bakinta cikin nasa, a hankali yake tafiya da ita har ya ƙarasa gaban musu kiɗa, a hankali ya cire ta daga jikinsa, da sauri ta ɗago ido ta kalloshi dan taga kowaye, murmushi ya sakar mata itama ta mai dar masa da martani, dan ta gane kowaye, lokaci ɗaya a ka cigaba da kiɗa suna rawa ciki da shauƙi. Bayan angama kiɗa da raye-raye kuwa yazo ya zauna a ka kawo abin mutsa baki, suna cikin haka ita dashi sai ga wasu ƙawayen su sun zo suka ci tazo minti biyu, ba musu ko ta tashe taje, wani ɗaki suka shiga da ita, zama sukayi saman kujerun dake jere a cikin ɗakin, basu jima da zama ba sai ga wata ƙawar su tafito tana tafe tana rangwaɗa kamar wata arniya, gaban Hajara tazo wani ƙofi ta miƙo mata tace, "karfi ki shanye dan ke kaɗai zan ba, kinsan kayan harka ba kuwa a ke baiwa ba". Tafaɗa haka murmushi ɗauke a fuskarta. Ba ɓata lokaci Hajara ta ƙarɓa ta kafa kai tanasha. tunda ta fara sha suka fara wani murmushi mai ɗauke da ma'anuni da dama. Bata ɗauke kai ba sai da ta shanye. Ƙofin ta miƙo mata tana murmushin jin daɗi. Fira suka tsayayi daga baya suka fito dan kowa yaje wajan da zashi. Koda suka fito mafi yawan cin mutane duk sun watse dan suna can suna fira mutane har sun fara tafiya. Koda Hajara ta zo wajan da suke zaune har wannan mutum yayi tafiyar sa. Wajan ƙawayen ta taje suka cigaba da fira daga baya kowa ya kama gabansa. Sabida dare yayi Hajara bata tsaya komai ba tadawo ɗakinsu sabida bata jin daɗin jikinta. Tana zuwa ko ta kan Zahara bata biba tayi kwanciyar ta. Tana cikin bacci taji kamar wani abu yana murɗarta, lokaci ɗaya ta sanya wata ƙara wadda yasa duk wanda ke layin sai da ya farka, Zahara dake ɗaki ɗaya da ita ciki matsanancin tsoro ta faraka haɗi da ƙarasawa wajan ta, ido tazara tare da ɗaura hannu a kai tana faɗin, "nashiga uku Hajara mi yasa meki haka?". ******* Sulaman tun daga lokacin bai sake kiran Hafsat ba, amma sai famar nemar mata aiki yake sabida baya son ya bar ƙasa batare da ta fara aiki ba, dan idan tana aiki albashinta zai isheta har tariƙe kanta batare da ta nemi taimakon kowa ba, kuma cikin ikon Allah ya samar mata aiki a wata asibiti, sosai taji daɗin haka dan haka tace zata cigaba da zama gidan Aunty shemah batare da ta koma hostel ba. Sai da yaga komai ya dai-data wajan aikin ta sannan ya tattaru nashi da nashi ya dawo ƙasar shi ta haihuwa ciki da kyawar ta. Ita ma haka ta kasance gareta da har kuka sa da tayi lokacin tafiyarsa. Haka dai tacigaba da karatu kuma tana zuwa wajan aikin ta, batada wata matsala ko damuwa, matsalar ta itace yanzu Ummar ta take yauwan mafarki a ko da yaushe, dan tunda tazo bata taɓa kewar gida ba sai wannan lokaci, kuma bataji zata iya tafiya ba har sai ta ida phd, dan yanzu shekara ɗaya ce ta rage mata ..... *#VOTE COMMENT SHERE* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 31📑* *__________📖* Soyayya mai ƙarfin gaske tashi tsakanin Hafsat da Sulamai, wanda a yanzu ji suke in ba ɗaya guda bazai iya rayuwa ba, kuma duk wani ɗan uwa Sulaiman yasa Hafsat, dan har waya sukeyi da iyayenshi, sosai suke sonta itama haka, kuma yanzu kowani burinsa yaga ya mallaki ɗan uwansa, ita kanta Aunty Shemah har mamaki take a kan wannan soyayya tasu, jira suke Hafsat ta ida karatunta sannan aje ayi maganar aure gidan su. ****** Bayan kwana biyu Abba yaji sauƙi sosai dan har an salame shi yadawo gida, kuma duk da haka Anwar yana kula da su sosai, dan tunda yazo gidan yaga halin da suke ciki suka bashi tausayi dan haka duk bayan kwana biyu ya kanzo yaga yaya suke, kuma sosai yake taimaka musu, dan yanzu har makaranta ya maida su Marwa, Abba ko ya samar masa aiki a company siminti, kuma yanzu alhmdullih komai na Abba ya fara dawo ahankali, kuma ko Yayan Safiyya ba'abarshi a baya ba dan shima sosai yake kula da su Umma. *A gurguje* Zahar ciki da fargaba ta ƙaraso wajan da Hajara ke kwanace wadda ta naɗe waje ɗaya kamar ranta zaifi, lokaci ɗaya kamanunta suka canja, ba abinda ke fita bakin ta sai wasu yawu masu yauƙi, knocking ɗin ƙofar Zahara da akeyi ne ya fargar da ita, cikin tsoro da fargaba ta ƙaraso wajan ƙofar ɗakin tana faɗi, "waye?". Muryar ƴan layinsu taji dan haka da sauri ta ƙarasa jikin ƙofara taɓuɗe musu. Ko magana basuyi mata ba suka shigo ɗaki dan suga mike faruwa? Hajara da suka gani kwance sai birgima take kamar ranta zai fita. Ɗayan wanda suka shigo ɗakin ya dube Zahara yace, "Zahara mike faruwa da ƙawarki?". Jiki na ƙarƙarawa tace, "wallahi bansani ba koni haka na ganta". Sai ɗayar mace tace, "to wallahi tun bata mutuba ki samu mai napep ya kaita can layi buge ya aje dan wallahi ta mutu ɗakin nan sai ƴan sanda sun tambaye ki". Sosai Zahara tashiga ruɗuwa, jiki na karkawa tace, "to yanzu ina zan samu mai napep cikin wannan dare?". Sai ɗayar mace tace, "kizo muje ɗakin Yawale idan zai yadda sai ya ɗauko motarsa ya kaiki inyaso da kun aje ta kujuyu". Haka ko ta kasance, dan da ƙyara Yawale ya yarda suka je, koda suka je mutane basu fara fitowa ba, dan haka suka ajeta dai-dai bakin ƙofar wani ɗaki suka tahowar su. Koda mutane suka fito sukaganta yasha da ƙasa, waɗan da suka santa su sukaje school ɗinsu aka nemu ƴan garinsu aka haɗata dasu, su sukayi duk yadda za suyi aka kata gidansu, sosai iyayenta suka shiga tashin hankali lokacin da aka kawo musu ita, ita ba matattaba, ita ba mai rai ba, dan sose take jin jiki. Koda labari yariske saurayinta, sosai hankalinsa ya tashi kuma duk wani bincike yayi amma bai ganu kamai gami da lamarin ba, dan ko ƙawayen ta antambaya amma bawani abu da akasamu wanda zai nuna ambata. ******** Suna tashi daga wajan aiki yashigo mota, bai tsaya ko ina ba sai bakin ƙofar gidansu Hafsat, yana fitowa ƙanninta suka fara yimasa oyoyo sabida yanzu jinshi suke kamar wani ɗan uwansu, bai ma tsaya wani neman izini ba ya shiga cikin gida bakinsa ɗauke da sallama. Ummu dake tsakar gida tana girki ta karɓa masa murmushi ɗauke a fuskar ta, kujera da ya gani ce ya zauna kana ya gashe da Umma. Bayan ta amsa ya tambaye ta Abba, tun kam ta buɗe baki tayi magana suka jiyo sallamar Abba. Amsa suka yi haɗi da gaisheshi. Anwar da ya ganine ya faɗaɗa murmushin sa, hannu ya miƙo masa sukayi musabaha kana suka cigaba da firarsu. Suna cikin haka har Umma ta kammala abinci ta kawo musu shida Abba suka ci, bayan sunci sun ƙoshi suka koma ɗura wata fira, suna cikin haka sai ga Safiyya ta shigo gidan ɗauke da sallama a bakin ta, gaishe da Umma tayi kana ta ƙasara wajan Abba dan ta gaisheshi, har ta buɗe baki tace, "Abba ina wuni"....bata kai da ƙarasawa ba sabida ganin Anwar da tayi zaune gaban Abba, cikin tashin hankali ta buɗe baki tace, mugu mika zoyi muna agida? ina ka kaimin ƴar uwata!". Tana faɗar haka tazo gareshi haɗi da cungumo masa rifa tana faɗi, "wallahi sai ka nemun ƴar uwa". Irin yadda yayi mata shuru bai ce komai ba, yasa ta raramu wani icci dan ta buga masa, da sauri Abba dake zaune wanda mamaki yaci kasa ya tashi ya karɓe iccin dake hannuta, amma duk da haka sai da ya shafe wani sashe na jikinsa. Komawa tayi kamar wata zararriya, koma ɗauko wani tayi dan ta buga masa da ƙyar Umma da Abba suka shawu kanta ta ɗan natsu, lokaci ɗaya ta fara kuka tana faɗin, "mi kazoyi gidan nan? Ko ka ɗauka ta nan ka karasamin ita?". Gabaki ɗaya kan Anwar ya ɗauri, ga mamaki wanda ya a ddabe shi a zuciya, ahankali ya ɗago idonsa waɗan da sukayi jajar yace, "Safiyya dan Allah kiyi haƙuri ki nunamin wajan da take wallahi da gaske ina sonta, kuma ashirye nake dan na aure ta". Wata harara ta antayo masa sannan ta fara kici niya ta ƙwace daga riƙon da Abba da Umma sukayi mata, suna cikin haka sai ga Yayan ta Abbas yashigo gidan, aikuwa kamar kar yashigo ta ƙwace daga riƙon da su Umma suka yimata ta faɗa jikinsa sannan tace, "Yaya Abbas ga wanda ya lalatamin Hafsat, shi ne sanadin rushi duk wani jin daɗinta, kuma shine yayi mata ciki kuma daga baya ya guje ta.... aitun bata kai ƙarshin zanci ba sai ga Abbas gaban Anwar zai kai masa naushe, da sauri Abba yace, "Abbas kada kasuma wallahi zan ɓata maka rai!!". Faɗa Abba ya fara yi masu sosai sannan suka natsu, bayan komai ya lafa nan Safiyya ta faɗa musu komai wanda tasani tsakanin Anwar da Hafsat, sosai su Abba da Umma ransu ya baci, dan ita Umma sabida baƙin ciƙi kasa magana tayi ba abinda take sai kuka baƙin ciki. Abbane ya dube Anwar da kansa ke ƙasa ba abinda yake sai dana sani da zubar da hawaye yace, "ashe dama haka rayuwar ka take? to ina maka nasiha da kaji tsoron Allah, kasani duk abinda kake Allah na kallon ka, kuma ba abinda zance da kai sai dai nace kaje na barka da Allah". Tun Abba bai kai da rufe baki ba Anwar ya durƙusa gaban Abba yana kuka kamar ransa zai fita yana faɗin, "wallahi Abba na tuba kodama sharin shaiɗan ne amma wallahi son gaskiya nake mata"....tun bai ka da rufe baki ba Abba da Umma suka shige ɗakinsu suka kulle ransu amatuƙar ɓace. Abbas nagani haka ya tasa ƙeyar Anwar gaba yace ya bar musu gidansu kuma yaja masa kunne akan kar ya kuskura ya kuma dawo gidan. Ciki da rashi abinyi Anwar yaja motar sa ya bar unguwar. Allah ne ya kawoshi ma saukin sa, dan yadda yake jan motar ko gani bai yi, yana yin parking ɗin motar yayi haka ya buɗe marfi motar ya fito wani abu yaji ya dakar masa zuciya, lokaci ɗaya ya dafe ƙijinsa, cikin ƙarfin hali ya fito daga cikin motar dan ya ƙarsa falon gidan, ta ko ɗaya zuwa biyu ya faɗi a farfajiyar wajan lokaci ɗaya numfashinsa ya ɗauke. Mai gida da ya gama rufe gate yazo ya shiga ɗakinsa yaga Anwar yashe a ƙasa kamar bashi da rai, da gudunsa yazo gareshi, rasa mi zaiyi yayi dan haka da gudun sa yaje wajan wani maƙocinsa ya faɗa masa halin da ake ciki, daya ke koshi abukin Anwar ne dan haka da sauri yazo suka ɗauke shi suka kaishi hospital. Abbas yana ganin Anwar ya tafi shima ya kama hanyar gida, Safiyya ko ta zauna taci gaba da kuka, Umma ko sai da ciyon ta yatashi sosai tasha wahala kafin ya lafa. Iyayen Anwar da suka ji Anwar shuru dan haka suka kira wayar sa amma bata shiga dan haka hankalin iyayensa ya tashi sosai, dan haka ba ɓata lokaci suka kama hanyar sokoto dan suje suga ko lafiya ɗan su yake. Koda suka isa garin sokoto suka samu labarin abinda ya same ɗan su, dan haka basu tsaya ɓata lokaci ba su tafi hospital ɗin da yake, da ƙyar suka samu aka bari suka ganshi sabida har yau bai farfaɗo ba, sosai hankalinsu ya tashi ganin halin da ɗansu ke ciki kuma autan su. Koda suka tambaye doctor da ke kala dashi dan suji mike damun ɗan nasu, sai doctor ya shaida musu cewa ya kamu da ciyon zuciya saka makon wani abun da yake so ya samu amma bai samu ba, kuma likitan ya shaida musu suyi ƙoƙari su bashi abinda yake so inhar suna son yaci gaba da shaƙar numfashi a durun ƙasa. Hankalinsu ya tashi sosai, haka dan mahaifiyarshi taji har kuka sai da tayi. Kwanan su uku sannan Anwar ya farfaɗo daga dogon suman da yayi, bayan ya farfaɗo suka sake yi masa allurar bacci, sai da ya kwana huɗu sannan iyayenshi suka samu ganawa dashi. Aikuwa yana ganinsu ya fashe da kuka yana faɗin, "Daddy zan mutu, ku taimaka min kuce su bani ita wallahi inasota sharin shaiɗan ne yashiga tsakanin mu amma wallahi har cikin zuciyata ina sonta....tari ya farayi mai haɗi da jini aciki, ruɗewa iyayensa sukayi dan haka da sauri suka kira likita suka shaida masa halin da ake ciki, da sauri suka zo suka fara bashi taimakon gaugawa. Mahaifayar Anwar kuka take ba ƙau-ƙautawa, sabida halin da taga ɗanta keci, ƴa-ƴanta mata tayi ma waya tace su zo suga Anwar dan yayi nisa. Sosai hankalinsu ya tashi dan haka su huɗu suka shigo jirgi zuwa sokoto. koda suka zo suka ga halin da Anwar yake ciki hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, dan haka su yanke shawara zasu fita dashi waje a duba musu lafiyar sa, musamman halin da suka ga iyayayesu sun shiga, dan haka ba ɓata lokaci akayi masa base zuwa ƙasar india. Yayan su Aminu ɗan Yayan Daddy suka kira suka faɗi masa halin da ake ciki dan haka yace to su haɗu acan india dan yanzu haka baya nigeria. Cikin kwana ɗaya akayi musu base suka wuce ƙasar india, kuma cikin ikon Allah sai gashi ankawoshi hospital ɗin da take aiki. Dayaki yanzu suna shiri-shirin kammala karatunsu, dan abu mai wuya ne kesa tayi wata ɗaya ƙasa, dan ita inbanda Sulaiman da gaskiya sai ta ƙara wasu watanni, amma tasan bazai bar ta taƙara koda kwana ɗaya ba bare wata ɗaya dan shi burishi a yanzu duk bai wuce ace ya mallake ta ba amatsayin matar sa. Zaune take laptop na gabanta tana wani bincike gami da karatun, wayar tace tayi ƙara, kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauku, sunan da taga yana yawo kan screen ɗin wayar ne yasa ta sanya wani murmushi wanda ya ƙarama fuskarta kyau da annuri, ɗauka tayi haɗi da karawa akunnin ta, sallama tayi masa amsawa yayi tare da faɗin amarya ta, i miss you". Yafaɗi haka tare da rufe idonsa. Sai da ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "miss you too angona". Shuru ne yabiyu baya, sai can yace, satin nan ne za'ayi bikinku ko?". "A'a sai wani sati". Haka tace dashi ata ƙaice. Gaskiya bazan iya jirin har wani sati ban ganki ba, dan haka ki shiya tarbona daga gobe zuwa jibi". "Da gaske?". "Ki zuba ido zaki sha mamaki, wani sanyin daɗine ya mamaye mata zuciya sannan ta buɗe baki cikin marai-rai cewa tace, "My ango nah". Amsawa yayi yana mai jin wani sanyi azuciyar sa. Tace, "idan ban saka aiki ba ina so dan Allah".... kuma sai tayi shuru ta ƙasa ƙarasawa . Yace, "ƙarasa mana ina ji". Yafaɗa haka da sigar rarrashi. Tace, "koda-kodama ina so in ba damuwa zan turu maka address ɗin gidansu Safiyya ka dubumin ita da iyayen ta dan Allah ba danni ba". Ta karasa maganar kamar zatayi kuka. "Dan wannan ne kike so kimin asarar hawayenki to karki suma, yanzu ki turumin anjima zanje insha Allah". Wani murmushi jin daɗi ta sanye har shi kansa sai da yaji sautin murmushi, kana tace, yanzu zan turum ma". Tana faɗa ta da tseki. Kominti uku ba'ayi ba ta tura masa. Aikuwa zuwa yamma ya shirya yabi address ɗin da ta bashi har ya kawo gidan su Safiyya. Yaro aika yace yakira masa Safiyya, Ko da yaro yaje Safiyya na zaune sai aikin tunani take musamman yanzu da Babban ta ya matsa mata sai ta fitar da miji dan aure yake son yayi mata. Tana cikin haka taji ance ana sallama da Safiyya, gabanta ne ya bada dummm, dan ita batayi dakowa yazo wajan taba. Mamar tace ace gata zuwa, kallon Safiyya dake zaune Mama tayi tace. "to maza ki tashi kije kin bar mutum waje yana jiranki". Dan kar ma tayi mata magana yasa tana faɗar haka ta haɗi fuska. Safiyya da taga alamu haka ba musu ta sanya hijab ɗinta ta kama hanyar waja. Tsaye ta ganshi nesa da gidan su kaɗan, dan haka ta ƙarasa gareshi bakin ta ɗauke da sallama. Amsawa yayi sannan tace, "bangane ka ba". Sai da yayi murmushi yace ko gaisuwa babu? ina fatar kece Safiyya". Yafaɗi haka ajere. Kai ta girgiza masa alamar eh". Sai da ya numfasa sannan yashiga yimata bayani dallah-dallah har sai da ya kammala. Kuka ta sanya masa sannan ta durƙusa gabansa tace, "dan Allah ka taimaka min ka kaini wajan ta dan girman Allah". Magana take hawaye sai famar zuba yake akan kuncin ta. Magana yayi mata yace in har iyayen ki zasu yarda to zai kai ki har wajan Hafsat, sosai taji daɗin abinda yace da ita dan haka tace yazo suje ta kaishi wajan iyayen Hafsat yayi musu bayani ko za su samu natsuwa atare dasu. Ba musu ko yayarda yaje yayi musu bayanin inda Hafsat take kuma da wajan da take zaune, godiya sukayiwa Allah kana sukayi masa godiya sannan suka ce in akwai yadda za'ayi suna son suje suga ƴar su, yace kar su damu su shirya zuwa jibe sai suwace. Haba murna tsakanin Umma da Abba ba'a magana dan kamar anyi musu albishir da shiga aljannanh. Koda Baban Safiyya ya dawo Abban Hafsat ya gaya masa, sosai yayi farin ciki yace shima yana son yaje yaga ƴarsa. Cikin kwana uku aka yimusu base suka wuce india..... to asauka lafiya. *Wai nagaji🤦‍♀️* *SAURA KUKI COMMEN AIKO NIK'I ƘARASASHI* *#VOTE COMMENT SHARE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 34 & 35🔚📑* *__________📖* Ƙanwar Ummar ta dake zaune ita ta karaɓa musu sannan suka ƙaraso cikin falo, ɗaya daga cikisu tace, "yau zanga matar Yayan Anwar wada akanta ya tashi rasa ransa". Gabam Hafsat ne ya faɗi tace to miya haɗata da Anwa?. Ta faɗi haka duk cikin zuciyar ta. Tana cikin wannan tunanin taji anyaye mata mayafi da ta rufe fuskar ta, kanta ta kara saddawa ƙasa Yayar sa Zainab ce tace, "Hafsat buɗe idonki ga iyayensa". Gabanta ne ya sake faɗuwa karu na biyu, ana cikin haka sai ga Yayar shi ta riƙo hannusa tashigo dashi ɗakin, zaunar dashi tayi wajan da Hafsat ke zaune sannan suka riƙa ɗaukar su hoto, hanunsa Mamar sa ta riƙo ta haɗa dana Hafsat, lokaci ɗaya suka ji wani yarrrr, addu'ar samun zaman lafiya tayi musu sannan ta fice suma sauran ƴan uwasa haka sukayi sannan suka fita suka bar Aunty Zainab tare dasu. Sai da tabari duk sun fita sannan Aunty Zainab tace, " Hafsa, to zan gaya miki abinda baki sani ba, tunda sunce sai kinzo na faɗa miki, zan fara baki haƙuri sabida anyi wannan auren bata re da saninki ko amin cewariki ba, dan haka nake mai baki haƙuri bisa ga wannan abin da muka aikata kuma Allah yariga da ya tsara abinsa duk yadda muke so to idan Allah ya kaddara sai muyi haƙuri, ba abinda zance sai dai nace miki yau ke da Anwar kunzan miji da mata....tun bata kai da rufe baki ba Hafsat tace, what!!!. Tafaɗi haka tari da miƙiwa tsaya tace, "wallahi bazai taɓa yuwa ba, ina Sulaiman?". Ƙanwar Abbanta ce da tashigo ɗakin dai-dai lokaci da take magana tace, "gashi ko ya yuwu, Sulaiman kuma baruwanki dashi dan yanzu ba muharra miki bane". Tafaɗi haka ciki da masifa dan ita gwaggo Saratu koda ma masifafface. Hannu ta ɗura aka tace, "yau nashiga uku dan Allah ina kuka kaimin Sulaiman". Ƙanwar Mamar tace tace, "kiyi haƙuri ƴa ta, Sulaiman shima yana can da amaryar sa". Idon Hafsat ta zaro sannan tace, "wani Sulaiman?". Wannda kika sani mana". Haka gwaggo Saratu tace da ita. Jikin ƙanwar Mamar ta Masa'uda ta faɗa tace, "Mumy ya haka ta kasance?". A hankali ta ƙara janyota jikinta tace, "sai kin daina kuka zan gaya miki". Ahankali ko ta share hayen ta tadaina kuka. Waya suka ɗauka suka kira Abban ta sukace ya faɗa mata da bakin sa. Kiransa sukayi haɗi dasa hands-free ya fara faɗin, "Hafsat bari na tuna miki kafin na gaya miki yadda haka ta kasance, kinsan kimin alƙawari duk inada aka kaiki zaki zauna, kuma kituna hukunci musu alƙawari idan sun saɓa, sannan ya ƙara da cewa, lokacin da iyayen Anwar suka zo suka nemeki da ki aure ɗansu Anwar, to dakiƙa ƙi basu amsa ashe duk abin da ake Sulaiman yana tsaye yana jin komai, irin yadda yaga iyayen sun shiga wani hali danshi yace dasu sabida shi ne zakiƙi auren Anwar amma yasan har ga Allah kina son shi, bayan kwana biyu sai Sulaiman ya kaiku dan ku dube shi aiku nan kuwa ya ƙara tabbatar da tabbas kina sonshi, to bayan kun dawo ne ya yanke shawar zai barwa Anwar ya aureki ko dan a ceto rayuwar sa daga halin da yake ciki, kuma nan yanemi da mu amince masa ya aure Safiyya, haka kuwa a kayi dan ke da Safiyya bawan da muka gayawa sai ankai ku gidajin ku, kuma dan Allah ina roƙonki da kici alƙawarin da kika ɗauka ki tsaya kiwa mijinki biyya da iyayensh". Yana faɗin haka ya datse kiran. Tana jin ya katsa wayar ta shige jikin Mumy ta Masa'uda sai kuka take kamar ranta ya fita. Anwar ko tunda Auntyn shi ta fara magana ya suɗaɗa ya bar ɗakin. Sai da tayi kuka mai isarta sannan tayi shuru sanadin ciyon kan da ya tasoma mata. Magani suka bata tasha, ba bata lokaci bacci ɗauke ta. Itace bata barka ba sai da asuba. Tashi tayi tayi sallah, bayan ta idar da sallah tajima kan sallaye tana azkar da addu'a Allah yayi mata sauki abinda take kiji kuma Allah ya yaye mata son Sulaiman a cikin zuciyar ta kuma ya bata ikon biyya ga iyayin ta da mijin ta, tana haka bacci ɗauke ta. Sai kusan ƙarfe goma ta farka, wanka taje tayi sannan ta shirya, beark aka kawo musu amma ita ƙin ci tayi da ƙyar aka samu tasha ruwan tea, bayan sun kammala akace su zo sukai amarya part ɗinta, daya ke gida ɗaya suke da iyayenshi dan sunce basa son yayi musu nisa dan haka suka zauna gida ɗaya. Part ɗinta suka kaita wannda iya haɗuwa ya haɗu, dan tsayawa faɗar haduwar sa ɓata lokaci ne. Bayan sun gama shiga ko ina na part ɗin sannan suka zo suka fara shiri tafiya, haba aikuwa Hafsat naganin haka tafara shirin kuka, da ƙyar suka rarrashita ta haƙura. Amma lokacin da zasu shiga mota saida tayi kuka sosai, haka suka tafi ciki da jin daɗin karamcin da iyayen Anwar dashi kansa yayi musu. Bayan sun tafi da awa ɗaya sai su Aunty Zainab suka shigo, kuka suka tar da tanayi dan haka suka rarrasheta sannan sukayi mata sallama sannan suka tafi suka barta ciki da kewa. Anwar ko tun jiya da ya suɗaɗa ya gudu bata sake gininshi ba har yanzu. Gab da sallar magariba ta tashi taje tayi wanka ta shirya, tana idar da sallah sai gashi ɗakin, a hankali yake taka ƙafar sa kamar wani ɓarawo. Zama yayi kan kujerar dake kusa da ita, haka yajira har ta gama azkar, saukuwa yayi daga kan kujer da yake zaune ya dawo saman sallayar da take zaune. Kanta ta ƙara yin ƙasa dashi, lokaci ɗaya wani baƙin ciki ya fara rufe ta amma sai ta dake, sunayen Allah take ta kira a zuciyar ta har tasamu sauƙi abinda take ji. Shiko rasa abinda zaice mata yayi sabida yana tsoron tace bazata zauna dashi ba. Sun jima a haka kafin ya buɗe baki yace, "kizo muci abinci dan Allah ba danni ba". Ya faɗi haka kamar yayi kuka. Yada take bata ko ɗago ba bare yasa ran zatayi masa magana. Ruƙonta ya farayi amma sai tayi banza dashi, da taga zai dameta sai ta tashi tabar wajan. Haka dai taci gaba da kasancewa tsakanin su har tsawo sati biyu ba abinda ke haɗasu, Yau ma kamar kullum yana parlour zaune yana kallo labaru sai wayar ta shiga rura, number da yagani ne yasa ya faɗaɗa murmushin sa, ɗaukar wayar yayi tare da karawa kunninsa yana faɗin, "ango kasha ƙamshi". Sai da yayi dariya mai sauti sannan yace, "sosai kuwa, ina fatar kaima kasha?". Anwar bai bashi amsa ba sai yace, "ina amaryar taka?". Sulaiman yace, "gata kusa dani". Wayar ya bata yace, "gata ku gaisa". amsa tayi suka gaisa da Anwar sannan tace, "ina Hafsat?". Rasa mizai cemata yayi sai da Sulaiman yace, "ina amaryar taka su gaisa tace". Kamar da ɗan tsoro yace, "bari na kai mata". Sulaiman yace, "wato baku ma tare kenan, ko har yanzu baka sha mansha nu ba?". Yana faɗin haka shiko dai-dai lokaci da ya shigo ɗakin da take dan haka baiyi magana ba, ƙarasowa yayi wajan da take zaune a hankali yace, "ga Safiyya zakuyi magana". Tunda aka buɗe ƙofar tasan shine yashigo amma ko mutsi batayi ba bare yayi tunanin cewa zatayi masa magana. Jin da tayi ya ambace Safiyya yasa ta ɗago kai amma batare da ta kalleshi ba, wayar da ke hannunsa ta karɓa haɗi da karawa a kunninta, sallama tayi Safiyya ta karɓa, bayan sun gaisa, sai Hafsat tace, "Safiyya haka su Abba sukayi muna ko?". Safiyya tace, "kenan sunyi miki bayani?". Bata bata amsa ba sai Hafsat tace, "kenan kin san za'ayi haka?". Safiyya tace, "wallah bansani ba sai da aka kawuni suke min bayani". Ta kai ƙarshin zanci kamar zatayi kuka. Hafsat tace, "ni karkimin kuka, wa Yaya Abbas ya aure?". Naja'atu ƙawarki". "Wace Najaatu? Kardai kice min Naja'atu Nasir?". ''Ita fah". Cewar Safiyya. Ina suka haɗu?". Sulaiman dake zaune tare da Safiyya yana jinsu sai yace, "kin fah cika mu da tambaya² kibari idan kinzo zakiji". Marairaicewa tayi tace, "Yaya Sulaiman dan Allah kayi haƙuri". Bai ce da ita komai ba sai Safiyya tace, "lokacin da mukaje india ne tazo nemana to koda tazo bama nan tunda ga nan yaji yana sonta amma bai gaya mata yace sai mun dawo idan kin amince zaki aure shi to shikenan idan ko baki amince ba sai ya gayama ta, to koda muka dawo yaji haka shine ya gaya mata ba ɓata lokaci akayi komai a kagama". Sai da Hafsat taje dugon numfashi sannan tace, "kunji daɗin ku". Safiyya tace, "ba wani jin daɗi biyyace kawai zamuyi ma iyaye, dan haka kema dan Allah duk abinda kike ji ki ajeshi ki tsaya ki kula da mijinki". Nan dai tayi-tayi mata nasiha, daga ƙarshi kuma suka dawo kuka kafin suyi sallama. Yana ganin ta fara kuka ya karɓe wayar dake hannun ta, a hankali ya jawo ta jikinsa ya fara rarrashin ta, amma kamar ance ta ƙara, sai datayi mai isar ta sannan tayi shuru. Haka dai taci gaba da kasancewa tsakanin su bawata jituwa har akayi wata biyu, dan idan ga tayi masa magana to suna gaban Daddy da Mama. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya. Yau Monday kuma yau ce ranar da zata fara fita aiki, bayan ta shieya taje ta gaishe da su Daddy da Mama sannan suka tafi ita da Anwar, bayan sun isa asibitin da zatayi aiki, kai tsaye a kayi mata jagora zuwa offce ɗinta, bayan ta zauna tayi ƴan rubuce² sannan ta tashi dan taza gaya wajan marasa lafiya, suna cikin jagayawa ita da wasu likitoce da waɗanda ke nuna mata yadda wajan yake, suna cikin haka sai sukaji kamar ana kiran Anwar, gaba ɗayansu shida ita suka juya dan suga wake kiransa. Wata mata suka gani kwance saman gadon hospital, sai ɗaga musu hannu takeyi. Ƙarasowa wajanta sukayi dan suga wacece ita?. Koda suka zo wajanta amma basu gane taba, da taga alamu basu gane taba tace, "baku ganeni ba ko?". Atare suka ce "eh". Kallon Anwar tayi tace, "Anwar kar dai a ce labarin danaji ance ka aure Hafsat da gaske ne?". Sai da suka kalle juna sannan yace, "eh da gaske ne". "Allahu akbar, Allah ya nunamin ikonsa, duk yadda nashiga na fita dan kar kuyi aure yau gashi kunyi aure". Ta kai ƙarshi zanci da kuka mai ƙunar rai. Tace, "tun lokaci da kace kana son Hafsat abin baiyi min daɗi ba, sabida sai naga baka dace da ita ba dani kadace, dan haka tundaga lokaci na fara shiga da fita dan kar Hafsat ta amince maka amma ina ƙaddara tariga fata, dan sai da ta amince kuka fara soyayya, hakan ba ƙaramin baƙinciki naji ba, duk da haka banyi ƙasa a guwa ba, sai da naji wajan wani boka yayi maka akin da zai sa kalalata mata rayuwa haka kuwa a kayi to bayan komai ya afku kuma sai Hafsat ta guje ka, to ana cikin haka sai kazo wajena dan nan shirya ku da Hafsat, to a lokacin ne nasamu galabarku har nashiga tsakanin ku na rabaku, to duk da haka ban kyaleku ba, nan dai tagaya musu har ƙarshin zuwan datayi wajan malami da kuma yadda tace yayi mata akan Anwar, to anacikin haka wannan ciyon yasameni ta, a ka mai dani gida naci gaba da jinya, to ina cikin haka aka kawomin hotonan auren ku, to tunda ga nan bansake sanin inda kaina yake ba sai a wannan asibitin. Tana kai ƙarshin zanci tayi haka tasake magana amma ina, sabida sheɗar ta sai sama da ƙasa takeyi. Cikin hanzari likitoci suka fara bata taimakon gaugawa. Tunda Hafsat tagano ko wacece take kuka har inada Hajara ta kawo ƙarshin zance. Anwar kuwa yana ganin yadda take kuka yaja hannunta yace suje gida sai wani sati zata fara aiki. Haka suka dawo gida ciki da Mamaki Hajara. Har dare yayi Hafsat bata dawo dai-dai ba. Bayan yayi wanka yayi shirin bacci yaje wanta ya rarrashi ta har yasamu taci abinci daga haka dai yayi ta bata magana har yasamu abinda yake so a wannnan dare, sosai ya bata wahala danji yake sai yanzu yasan ta ƴa mace dan da safe har da zazzaɓi sai da tatashi da shi. Haka dai suka cigaba da rayuwa, sosai yanzu Hafsat ta sake jiki dashi, shiko sai nuna so yake gareta. Bayan sati ɗaya Hafsat taje asibiti ta bincike Hajara a kace ai tun ranar Allah yayi mata cikawa, sosai Hafsat taji zafi da faruwar haka. Koda ta dawo gida ta sanar da Anwar amma bai wani nuna da muwa ba, sai dai Addu'ar da yayi mata. Haka rayuwa tacigaba da kasancewa, dan yanzu soyayya mai ƙarfi ta kullu tsakanin Safiyya da Sulaiman hakama Hafsat da Anwar dan Abin har namaki ya bani. Koda taje ganin gida tasha mamaki, dan gababki ɗaya Anwar yasa anrushe wannan gidan anyi musu sabo, gaba ki ɗaya koma na gidan ya dawo sabo haka tazo tayi kwana biyu gida koshi da kyar ya barta, koda suka haɗu da Safiyya har cikin Safiyya ya fito haka ma Naja'atu, Hafsat ce ka ɗai keda shigar ciki, dan sai wani kwaɗayi take suko suna tsargowar ta. Haka dai rayuwar ma'aratan ta kasanci cikin so da ƙauna, bayan shekara ɗaya Safiyya ta haifi ɗanta namiji mai kama da maihaifinsa itama Na'atu ta haifi ƴar ta mace, ita ko Hafsat ta haife ɗanta sak Anwar, murna wajan dangin Anwar da iyayensa ba'a magana kowa faɗi yake Anwar yasamu magaji, bayan angama shagalin biki tace zata kuma gida wankan jego amma Anwar yace shi sam bai san haka ba, da ƙyar iyayenshi suka rarrashe shi ya yarda tatafi....... *ALLHAMDULILLAH* To nima Hafsat na tafiya nikuma na aje alƙalamina🤩 fatan alhari gareku masoyan wannan littafi, inama kowa fatan alhairi. Kuma duk wannada na ɓata ma dan Allah kuyafemin🙏🙏 _Sai bayan sallah idan Allah mai kowa mai komai yasaki haɗamu acin sabon littafe na mai suna *AUREN RASHIN DACE ko kuma SANADIN BARIKI(narasa raina).*_ *Ko huta lafiya🤗* *#VOTE COMMENT SHARE* *©SUMY NA'IGE* *Share*