KOWA YA ƊEBO DA ZAFI... NA MEENAT A 'YANDOMA DA ZARAH ROYAL STAR WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSHI FREE PAGE 1&2 Ƙarar saukar ruwan sama me haɗe da iska yayi sanadin farkarwarta, a firgice tana me maƙurewa can ƙarshen gado tare da sakin a jiyar zuciya. Mummunan mafarkin da tayi ne ya dawo mata sabo fil, tamkar yadda mirror ke maido ma mutum ainahin suffar shi. Tuntsurewa tayi da dariya sakamakon tunawa da tayi da ƙudirinsu, sai dai saurin haɗiye dariyarta tayi sakamakon turo ƙofar ɗakinta da ta ji anyi. "Ninaah! Dariyar me kike yi haka? Ke tsaya ma! Me ya hanaki rufe ƙofa duk da ruwan nan da ake tsalawa?" "Umma bacci ne ya sace ni ina gama sallah, amma yanzu zan rufe" kallon tuhuma Mahaifiyar ta ke mata sakamakon hango rashin gaskiya ƙarara a fuskarta. Ganin Mahaifiyarta zata karbo jirgin ta ya sakata saurin kawar da zancen "Umma Abba ya dawo?" "A'a bai dawo ba ke ya ke jira" Umma ta ƙarasa maganar tare da ficewa daga ɗakin. Murmushi ta sake saki a karo na barkatai tare da ɗaukar wayarta tana tafiya cikin sanɗa. Jin mahaifiyarta ta shige ɗaki hakan ya bata damar shiga ɗakin da mahaifinta ke ajiye kudi ta kwashi adadin da zai isheta. Ƙarar shigowar sako a wayarta yasa ta firgita tare da saurin kallon screen "Lokaci ya na tafiya, ki tabbatar kin kasance cikin shiri" dariya ta saki tare da daka tsalle ta rungume wayarta, cikin sanda ta koma daki tare da fara haɗa kayanta bakin ta ɗauke da wakar Umar m Sharif mai taken gamu nan dai... Cikin nutsuwa ta sauke wayar daga kunnenta ta na kallon tagar dakin ta da iska ya bude da ƙarfi. Walkiyar da aka yi ce ta saka ta saurin duƙewa tare da ambaton Sunan mahaifiyar ta. Ta share daƙiƙu kafin ta ɗago cikin tashin hankali don in akwai abinda take tsoro to bayan ruwan sama yake. Kiran Ninaah ne ya shigo wayar ta cikin hanzarin ta dauka. "Yanzu haka cikin shiri nake, ruwan nan ne ya tsayar dani, kin san dai ba zamu fita ba sai su Hajiya sunyi bacci" "Ban gane sai munyi bacci ba" Mahaifiyar ta da shigowar ta kenan ɗakin ta karasa maganar tare da kafe Zainabu kamar yadda take kiranta da ido. Dabur-burcewa Zuzuuh tayi kamar yadda kawayena ke kiranta. "Hajiya dama yanzu nake shirin zuwa in duba in ga shin kinyi bacci?" " Ke kada ki mayar da ni shasha mana, ina za ki je kike fadar sai munyi bacci?" Hajiya ta ƙarasa maganar cikin haɗe fuska. "Dama... Dama, gobe ne zamu je wani bikin kawarmu shine na ce a bari da safe zan fada miki yanzu ina zanje tunda kinyi bacci"ƙure ta da ido Hajiya tayi tare da jefa mata kallon tuhuma don ko alama bata gamsu da wannan zancen ba, girgiza kai tayi tare da ficewa daga ɗakin. "Haba Hajiya! Sai ma gari ya waye kin nemeni kin rasa lokacin zaki gane karya na miki" Zuzuuh ta ƙarasa maganar tare da bude akwatin da ta zuba kayanta. Kudi ne barbaje da tayi nasarar kwasowa a dakin mahaifiyarta. Alamar shigowar sakon da taji ne ya saka ta daukar wayar "Ki fito yanzu, muna jira" kallon ƙofa tayi taga ruwan ya fara lafawa don haka daukar akwati ta tayi cikin sanda ta bar gidan ba tare da kowa ya sani ba... Shurun da taji ita ta tabbatar mata da yan gidansu sunyi barci, don haka cikin natsuwa ta janyo katon akwatinta tana niyyar barin gidan. "Laaa! IBINA ina za ki je cikin daren nan ga ruwa anayi." Gabanta ne ya yi mummunar faduwa ganin asirinta na shirin tonuwa. A fusa ce ta kalli ƙaramin ƙaninta "zan kai kayana dakin Momy ne uban yan sa ido, me ya fiddoka cikin daren nan?" "Motsinki na ji na fito" cikin dabara ta mayar da akwatinta daki tare da jan hannun ƙaninta taje ta kwantar da shi sai da ta tabbatar yayi bacci sannan ta fito tare da ja masu dakin kasancewar ita ce babba duk dare sai kannena sunyi barci take yi. "Shukurah bakiyi bacci ba har yanzu ?" "E Momy yanzu dai zan kwanta" ta karasa maganar da sauri ta shige dakinta. Jin tsit! Da tayi hakan ya tabbatar mata kowa yayi barci don haka cikin sauri ta bar gidan. "Ke kadai muke jira" shine sakon da ta gani kwance a screen din wayar ta. Murmushi tayi tare da bin wata hanya, don tana da tabbacin suna can suna jiranta... Meenat A 'Yandoma 0813356279 KOWA YA ƊEBO DA ZAFI... NA MEENAT A 'YANDOMA DA ZARAH ROYAL STAR ƘIRƘIRARREN LABARI NE Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji. WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSA PAGE 3&4 Sauri take gudun kada wani ya ganta, duk da duhun daren da ake amma haka ta rika zabga sauri tamkar zata tashi sama. Tsak! Ta tsaya cike da tashin hankali ganin kamar mutum ya gifta ta gabanta cikin babaken kaya. Ja da baya ta fara yi gabanta na tsananta faduwa. Hasken motar da ta fara hangowa ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya tare da kara saurin barin wurin, domin bata yadda da inda take ba. Bude gidan baya tashi ta shige inda Ninaah da Zuzuuh suke sai ita cikon ta uku. A gaba kuma Fu'ad ne ke tuki sai Ammar da Haris a kujerar mai zaman banza. "Beb kin so fa ki bata mana lokaci, domin mun jima a wurin nan." Ta tsinkayo Muryar Fu'ad na fada. "Ba zaka gane bane, baro cikin gida a irin wannan lokacin ba ƙaramin tashin hankali bane." Fadar Ibina "Bari ke dai Ibina! Da kyar na baro gida, kadan ta hana asirina ya tonu." Cewar Zuzuuh. "Haba Guy’s! Mu je mana ni fa na kagara mubar garin nan kafin asirin mu ya tonu, don kunsan ko wane lokaci ana iya kama mu, ga jirginmu karfe bakwai na safe zai tashi." Ihu suka ɗauka a tare ganin suna daf da cimma burinsu. Gudu suke tsalawa cikin duhun daren ga ruwan sama da bai karasa daukewa ba. Karfe dayan dare suka sauka garin Abuja, kai tsaye Hotel suka nufa domin anyi masu booking din komai, gajiyar da suka kwaso ita ta saka suka kwantawa da wuri zuciyoyinsu fal da farin cikin ƙudurinsu. Karfe bakwai suka farka a gigice domin a tunaninsu sun maka sai Haris ke fada masu sai fa takwas jirginsu zai tashi. Shirye suke cikin kaya na alfarma, wanda kallo daya zakai masu ka fahimci gayu da kuma wayewa ta bi jikinsu. Abinda Ninaah bata taɓa ji ba shi ne ta fara jinsa, wato tuhumar kanta anya ta yima iyayenta adalci? Sai kuma wata zuciyar ta fara fada mata kada kuyi wasa da cikar burin ki, domin kuwa ranar huce takaici kai ya cire. Sanarwa aka fara don haka a tare suka shiga jirgin da yake niyyar tafiya kasar Umbull Ammar ne ya fara magana "Ni fa a matse nake mu isa kasar nan kodan mu bazama ganin abubuwan mamaki" Haris ne ya karbe zancen "Ni dai damuwata daya ce, kada muje mutanen nan basu zo tarbar mu ba" "haba dai! Ai in kaga ana rashin daukar Costomers da muhimmanci to a naija ne, amma can mu gama magana da Company nin sune da zasu bamu wurin zama da komai hatta duk wuraren da zamu ziyartan su zasu kai mu" Fu'ad ya karasa maganar. " Yau fa ba zanyi bacci ba, haba dai gani a kasar da nafi kauna" cewar Ninaah. Tuntsurewa suka yi da dariya a tare. Nan suka cigaba da labari har jirgi ya sauko. Babu bata lokaci aka zo aka dauke su. Kamar yadda aka nuna masu wurin a online kafin zuwan su, a haka suka samu masaukin nasu. Katon daki mai dauke da gadaje shidda sai kujeru da sauran abubuwan bukata babu abinda babu. Tsalle Ibina tayi ta faɗa saman gadon tare da furta. "Rayuwar 'yanci Assalamu alaikum!" Tuntsurewa da dariya suka yi suna mata shegantaka cike da kaunar juna. "Kunga! Kada ku takurama masoyiya ta" cewar Fu'ad. "Fadama wanda bai da masoyi a kusa, Ammar ka fa ji abinda yake fada ko" Zuzuuh ta karasa maganar tare da kashe mai ido. "Beb zo ki kwanta ki huta, kada su dawo kan mu." Haris ya fada tare da kallon Ninaah. "Jama'a a fidda batun wasa ni fa yunwa nake ji." Cewar Ninaah "Kura ci da gashi, daga saukar mu ko wanka ba muyi ba sai ki hau ciye-ciye." Cewar Ammar, Haris ne ya cabe zance. "Kada fa ku sako min masoyiya a gaba, kinga rabin rai je ki ci abinci kiyi nat! " Shigowar ma'aikatan wurin dauke da abinci mabanbanta ne ya saka su yin shuru tare da hadiye yawu. "Wow! Wannan rashana duk mu kadai" Fu'ad ya karasa maganar yana kokarin daukar abincin. Saukin rike ma shi hannu Ammar yayi "kaga Malam mu je kowa yayi wanka, muyi sallar azahar sannan a Ci. "Ci ya na gaba da sallah fa" "mu je kawai" Ninaah ta faɗa. Ɗaya bayan ɗaya suka yo wankan tare da gabatar da sallah domin lokacin azahar ya shiga. Nan fa suka fara shirin cin abinci "Drink din nan ban yadda da shi ba, kamar giya." Ibina ta faɗa tana jujjuya lemun. Amsar shi Haris yayi yana kare ma shi kallo "Da gaskiyar ki fa, to amma sun rubuta non alcohol." "Ku miko shi nan ku gani, tunda har suka rubuta ba giya a ciki tabbas sai na sha" Ammar ya karasa maganar tare da bude kwalbar ya kafa mata kai. "Zuzuuh nake don haka masoyi gama sha nima sai nasha, in mutuwa ce mu mutu tare, bare ma nasan bamu mutuwa sai munyi aure" Dariya suka kwashe da ita a tare ganin da gaske Zuzuuh take don har ta karasa shanye lemun. Ma'aikacin wurin dake laɓe yana kallon duk abinda ke faruwa murmushin mugunta ya saki ganin sun sha lemun. Tafiya ya yi domin ya sanar ma Shugabansu ce wa an samu waɗan da suka sha. Kamar yadda aka tsara karfe hudu na yamma cikin shigar kananun kaya suka fito motar Hotel din ta dauke su. Ba ƙaramin yawo suka yi ba domin basu dawo gida ba sai dare. A gajiye suka yi wanka suna labarin abubuwan da suka gani a fitar su. Zuzuuh ce tari ya sarke, sannu suke jero mata cike da tausaya wa. Duk Ammar ya rude, bayan ya lafa ta sha ruwa tana mayar da numfashi. Daki yayi tsit domin sun tsorata matuka, babu fa abinda ta ci amma ta hau tari ga idanunta lokaci daya sunyi jajur. Miƙewa tayi da nufin ta shiga Toilet, jirin da taji yana dibarta ne ya sakata dafe bango. Tamkar wadda aka fizgo haka suka ga ta baro bangon tare da yanke jiki ta zube ƙasa tana shure-shure. ƙasusuwanta suna wata irin lankwashewa. Cikin hanzari Ammar ya nufi inda take, sai dai kafin ya ƙarasa sai gani suka yi shi ma ya yanke jiki ya fadi. Cike da tashin hankali suka rasa wa zasu taba domin su biyun sai shure-shure suke. Cikin karfin hali Fu'ad ya kira daya daga cikin ma'aikatan wurin suka nufi su Ammar. Shure-shuren ya tsaya sai dai jini ne ke fita ta hanci da kuma bakinsu. Wata mace ce ta shigo dakin dauke da ɗan karamin akwati, na bada taimakon gaggawa. Nurse din saitin fuskar Zuzuuh ta kanga kanta don taji shin tana raye, sai dai kafin ta dago kanta ji tayi Zuzuuh ta cafke wuyanta tare da kafa mata hakoranta da suka yi tsini tamkar wuka. Ihu Nurse din keyi tana neman taimako, su Haris ja da baya suka fara yi cikin zallar rudewa. Ba zato ba tsammani sai gani suka yi Ammar ya daka tsalle tamkar an harbo shi a kibiya. Nan fa suka fara gudun ceton rai, kafar Ibina Ammar ya fizgo da karfin tsinya tare da jefa ta da daki bango. Ƙarar data saki ita tayi sanadin dakatawar guje-gujensu. Ibina ce a gefe kwance cikin jini kanta ya fashe jini na tsartuwa.... Meenat A 'Yandoma 08133562798 KOWA YA ƊEBO DA ZAFI... NA MEENAT A 'YANDOMA DA ZARAH ROYAL STAR WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSHI ƘIRƘIRARREN LABARI NE Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji. PAGE 5-6 Ibina dake kwance a sume da mugun sauri Fu'ad ya nufi inda take kwance, wani sauran ruwa ya rarumo ya fesa mata a fuska. Wata irin zabura sukai su duka ganin Nurse d'in da Zuzuuh ta cafke ma wuya itama ta fara wata irin mik'a k'asosuwan jikinta na bada wani sauti, k'as-k'as. Ninaah ce ta matsa kusa dasu Fu'ad dake bakin k'ofa, tana k'ank'ame Fu'ad dake tsaye rik'e da Ibina, zazzare ido sukai ganin Ammar da Zuzuuh da Nurse sun mik'e suna wata irin jijjiga bakinsu da hak'uransu sunyi wani mugun tsini, kwayar idonsu ta zama fari fat ta koma irin na horror, jikinsu da fatar jikin nasu tayi wata irin kala kamar yalo, kamar an shafa masu tuka. Banko k'ofar d'akin da akai ne yasa suka zabura sukayi waje a da mugun gudu. Shugaban hotel d'in ne ya zo, kai tsaye d'akin ya kutsakansa a ciki, wadda yaje ya sanar dashi jikinsa na kyarma da harshan turanci ya ce "ranka ya dad'e karfa ka shiga d'akin nan, wallahi gwajin nan an samu matsala,kamar wata annoba ce ke shirin tunkaro mu in..... "Ka rufe ma mutane baki na ce ko" da sauri ma'aikacin hotel d'in ya tushe bakinsa da tafin hannunsa yana zare ido. Kai tsaye shugaban hotel d'in ya Banga k'ofar d'akin dasu Ammar ke ciki. Ai da mugun sauri ya fara ja baya, ganin yadda suka nufo k'ofar gadan-gadan suna faman mik'a hannunsu gaba, suna son kamoshi. Da gudu ya juyo zaiyo waje, sai dai akwatin maganin da Nurse d'in nan ta shigo dashi ya tade shi ya zube a k'asa. Ammar ne yayi kukun kura ya fad'a kansa yana neman kaima wuyan sa cizo. Kokowa suka shiga yi yana ihun taimako, gasu Zuzuuh dake gaf rufe sa suna wani gurnani da shinshine-shinshine. Motar asibiti ce ta k'araso tare da doctors wadda ma'aikacin hotel d'in ya kira su cikin sauri. Wani mugun k'arfi ne ya zo mai ya jawo akwatin maganin yana kwad'ama Ammar shi a saman kai, ai ko danda nan ya zube a sume. Sai dai yana k'ok'arin tashi su Zuzuuh suka turmushe shi, wata irin kokowa suka kamayi dashi, Zuzuuh ce ta samu sa'ar sa y'an yatsunta masu d'auke da farce mai mugun tsini ta karci wuyansa, danda nan jini ya kama zuba ta wuyan nasa. Ma'aikacin hotel d'in ne yayi hanzarin d'aukar wani k'arfe ya daddage iya k'arfin sa ya kwad'ama Zuzuuh a kai, ai ko Nurse d'in nan data rage ganin ta nufo shi yasa baiyi wata-wata ba itama ya kwad'ama shi itama ta zube a sume. Wata irin zabura shugaban hotel d'in yayi yana rungume ma'aikacin hotel d'in, rik'e wuyansa yayi yana sauke ajiyar zuciya, da sauri ya kalli doctors d'in dake tsaye ya ce "ku kwashe su mu tafi asibiti, ayi bincike mike damunsu, tunda nake ban tab'a ganin masifa irin wannan ba" Da sauri Doctors suka sasu akan gadon aka daure su tare da yin asibiti dasu. Fu'ad dasu Ibina suka rungume ya janye su daga jikinsa yaja hannunsu da nufin subi su asibitin, sai dai Haris dake tsaye ya dakatar dashi yana cewa "mun shiga uku, wannan wacce irin masifa ce?, ina kuma zaku je naga kana niyar binsu?" "Zamu bisu asibitin ne ai, domin hankalin mu bazai tab'a kwanciya ba, har sai an duba mike dumunsu" Da sauri Haris yaja baya yana cewa "kutumelesi inbisu su cinye ni, kana ganin yadda suke cafke mutane suna neman cizon mutum, gaskiya ni tsoro nake ji" Da sauri Ibina ta dafa shi tana cewa "haba! Haris tare fa mukazo dasu bai kamata dan wani abu ya sami y'an uwanmu mu kuma mu juya masu baya ba, sorry muje kawai" Jikinsa ne yayi sanyi, ganin Fu'ad yayi gaba, yasa suka rufa masa baya Motor hospital su duka suka shiga harda shugaban hotel, dake rik'e da wuyansa yana yamitse baki, saboda wani irin zafi da yake jin wajan na mai, gani yayi wajan jini ya daina zuba, sai wani irin jini kalar ruwan ganye dake zuba, wani iri ya fara ji cikin jikinsa, ya fara wani irin gurnani da tari yana tushe bakinsa, ji yayi ba abunda yake bala'in so irin yaci nama, ko wanne iri ne, bai dai idasa kamuwa da cutar ba, sai yayi saurin gyara wuyan rigar tasa dankar wani ma yaga wajan yadda ya koma. Har suka isa asibiti ba wadda yayi magana kowa d abunda yake sak'awa a ransa. Babban asibiti ne mai girman gaske, mai cike da marassa lafiya, kota ina da y'an uwan marassa lafiyar cike da hospital d'in. Kai tsaye da motar asibitin ta tsaya, wasu doctos ne da Nurses suka nufo wajan da gadon d'aukar marar lafiya guda hud'u, saboda shugaban hotel d'in, su duka sakkowa sukai akasa su Ammar dake a sume har yanzu basu farka ba. Kai tsaye cikin ainahin asibitin aka wuce dasu, wani d'aki mai girma da tsari da kyau aka kwantar dasu. Wani doctor ne ya shigo ya fara zuwa wajan shugaban hotel d'in yana kallon sa ya ce "George, kai ne a nan, mi yake faruwa ne?" Dan ya mutse fuska George yayi yana k'ara dafe wuyansa da yake jinsa yanzu kamar ana tsikara masa allura, bai amsa ba saima damk'e hannun doctor da yayi da mugun k'arfi. Ba shiri doctor ya sake juyowa yana duban George, ganin yadda yake wata jijjiga akan gadon, gadon na girgiza kamar zai rabe gida biyu, k'asusuwan jikinsa ne suka fara wata irin k'ara kamar ana kakkaryarsu, idonsa a rufe, can aka ji ya daina wannan jijjiga, da sauri Fu'ad ya ce "anya George shima ba komawa irin su Ammar zaiyi ba, izuwa yanzu na gane duk wadda suka ciza ko suka karceshi zai iya komawa irinsu" Danda nan Haris ya k'ara ja da baya, wani irin tsoro ya k'ara rufe sa, yana gaf fita k'ofa Ibina ta cafke hannunsa, wata irin zabura yayi yana kiran "na shiga uku na, shikenan tawa ta k'are" Jijjigasa Ibina tayi tana cewa "kai Haris nifa ce, ina kake niyayar zuwa naga kana niyar fita" Tana rufe baki suka ji ihun doctor, su duka da mugun sauri suka kai dubansu a inda suke, ganin yadda George ya koma shiga ya cafke hannun doctor ya kai mai wani mugun cizo, jini sai zuba yake a hannun nasa, ba shiri Fu'ad ya tuna idan ka buga masu wani abu a kai suna suma, kuma suna dad'ewa basu farka ba, yasa ya d'au wani k'arfe yana nufar inda suke, yana zuwa ya shammaci George ya kwad'a mai shi a kai. Suma yayi, inda doctor ganin ya sakar mai hannu yasa ya fara yamutse fuska yana rik'e hannunsa dake zubar jini, kallonsa Fu'ad yayi da tausayi, yana sharce gumi. Haris dake tsaye Ibina rik'e da hannunsa, ya fisge yana cewa "cika ni na ce, na rantse bazan zauna a nan ba, haka kawai idan zaku iya zama ku zauna kunga tafiya ta" Yana shirin b'ude k'ofar ya fice yaji muryar doctor na magana cikin wata irin murya me kama da saukar aradun... ZAHRA ROYAL STAR KOWA YA ƊEBO DA ZAFI... NA MEENAT A 'YANDOMA DA ZARAH ROYAL STAR WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSHI ƘIRƘIRARREN LABARI NE Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji. FREE PAGE 7&8 "Ku kira min doctor Anna, da sauri ta taho da allurar nan mai sa dogon bacci". Cewar doctor dake dafe da kansa yadda ya fara jin ya fara sara mai. Da sauri wata Nurse ta fice domin aiwatar da abunda doctor ya ce. Haris zare ido yayi ganin yadda doctor yake jujjuya kansa ya runtse ido. Da sauri yayi wajan Fu'ad yana cewa "dan girman Allah kuzo mubar asibitin nan". Wani kallo Fu'ad ya jefama Haris yana cewa "wai mi yasa Haris kake hakane?, y'an uwanmu ne fa ke cikin wani hali na rayuwa da mutuwa in... Maganar ce ta mak'ale ganin doctor ya nufo wajansu. Wata irin zabura Haris yayi yana komawa bayan Fu'ad "na shiga uku shima ya koma dodon hala?" Haris ya fad'a yana b'oye fuskarsa a bayan Fu'ad. Fu'ad ya jawo shi yana cewa "banza lafiyarsa lau bai koma ba tukunna, gaskiya ka cika tsoro da yawa, ka natsu mana". Doctor dake kallonsu ya saki wani k'aramin tsaki yana cewa "ya kamata ku bamu had'in kai, ya akai wannan abu ya fara, tun fari ku natsu kuyi mana baya ni". Da sauri Haris ya ce "mu natsu fa ka ce ana cikin wannan hali ina wata maganar natsuwa, nikam iyanzu nayi dana sanin zuwa wannan k'asar duk abunda ya same mu dasa hannun George a ciki duk yasan komai shida wani ma'aikacin hotel d'insa". Wani tsaki Fu'ad yaja ya fara magana yana ba doctor bayanin duk abunda ya faru, daga k'arshe ya ce "kawai abun sha ne fa suka sha suka koma haka, sai dai idan wani abu akasa mana a cikin abun shan nan" "Tabbas akwai abunda akasa haka nan mutum bazai koma kamar dabba ba". Cewar doctor yana girgiza kai alamar tabbatarwa. Daurewa kawai yake cikin jikinsa ji yake kamar ana yankan naman jikinsa, Fu'ad dake kusa dashi bai lura ba da yadda yake shinshinarsa kamar yana son kai mai cizo. Da sauri Haris ya ce "nifa ban yarda da wannan doctor d'in ba, na rantse muyi nesa dashi ya kusa komawa shima", "Wai Haris mi yasa ka zama haka ne wai?" Ibina ta idasa maganar tana kallon Haris. "Kinga laifi na ne?, gaskiya fa nake fad'a, idan mukai wasa gaba d'aya sai mun koma irinsu wallahi". Doctor jin shigowar Doctor Anna, yasa ya juya inda take cike da kulawa ta kama hannunsa ganin jinin ya daina zuba sai fatar wajan data fara komawa bulu, cike da d'an mamaki ta ce "doctor Daniel mi yake faruwa ne?. D'an bayani ya fara mata sana ya ce "yanzu karki damu dani, ki fara masu allurar please dan suna gaf farkawa, and idan suka farka bana jin zamu iya dasu, domin wani shegen k'arfi gare su, domin da George ya kama min hannu na rantse ji nayi kamar ba'a duniya nake ba" Dariya ce ta kama Haris jin yadda doctor ke bayani, saida ya dara da sauri kuma ya maze ganin kallon dasu Ninaah suke mai. Allurar ta fara masu sana ta dawo wajan doctor Daniel. Ganin yadda yayi shuru kamar baya cikin hayyacinsa kansa yayi k'asa, ta nufi inda yake takun tafiyarta na buguwa da zuciyar Haris duk taku d'aya sai zuciyarsa ta buga. Domin shi ya tabbata doctor Daniel ya kamu da irin cutar dasu Zuzuuh suka kamu da ita. Runtse idonsa yayi yana faman cewa "Fu'ad mubar d'akin nan na rantse maka doctor d'in can shima ya koma". Sai lokacin ma su Ninaah suka tuna an cizi doctor shima, da mugun gudu Ninaah da Ibina su kayi bakin k'ofa, sai dai kamin ma su isa bakin k'ofar Haris ya rigasu isa, da mugun sauri ya bangajesu yana niyar tura k'ofar jikinsa na kyarma. Fu'ad ne kawai yayi azamar nufar inda doctor Anna dake niyar isa inda doctor Daniel yake. Sai dai kamin ya isa doctor Daniel ya d'ago idonsa ne ya koma fari fat hak'oransa sunyi masifar yin tsini, ya wage baki yana faman yin wani irin gunji kamar mage ta samu nama. Wata irin zabura doctor Anna tayi duk da haka tana gaf dashi tana faman yi mai magana, wai yana lafiya kuwa? Miye yake yi haka?. Daga can wajan bakin k'ofa Haris dake hango su ya bud'e baki ya ce "zaki ci uwarki ne kika tsaya tabbayar wadda zai hallakaki wai yana lafiya tabbas zai nuna miki yana lafiya ai". Duk da halin da suke ciki bai hana sauran doctors d'in yin dariya ba, domin da harshan turanci yayi maganar. Fu'ad yana gaf isa inda take kawai suka ji ihun doctor Anna, doctor Daniel yayi kukan kura, wani mugun tsalle yayi yana kada doctor Anna k'asa ya turmushe ta, kokowa suka farayi tana sun kwatar kanta, shi kuma yana neman inda zai kafa mata cizo........ Nigeria.... Kwance yake kan makeken gadonsa, sai faman juye-juye yake. Can kuma ya zabura yana faman kiran sunan Ammar. Da sauri Haj Maria dake kusa dashi a kwance ta tashi tana kunna fitilar dake kusa da ita. Kallonsa tayi ganin duk yadda zufa ta wanke masa fuska, cike da kulawa Haj Maria ta ce "Alh lafiya kuwa?". Sauke ajiyar zuciya yayi ganin cewa mafarki yayi ya ce "wani irin mafarki nayi da Ammar". Kallonsa tayi da d'an mamaki ta ce "Alh Ammar ai yanzu na tabbata yana d'akinsa a kwance". Da sauri Alh Lado ya sakko daga kan gado yana nufar k'ofar fita yana cewa "hankali ya kasa kwanciyar wallahi wani fa mugun mafarki nayi dashi yana cikin wani hali, dama tun jiya naga alamunsa kamar suna shirya wani abu shida abokansa kinsan Ammar baya jin magana". Da sauri itama tabi bayansa. Suna shiga d'akin nasa suka ja turus suka tsaya, ganin wutar d'akin a kunne dubunsu suka kai akan gadon nasa babu komai akai ga waduruf a bud'e, hatta durowar da yake aje kud'i a bud'e take an yashe komai na ciki. Wata irin zufa ce ta yanko ma Haj Maria zuciyarta na bugawa da mugun sauri. Alh Lado kuwa wani irin jiri ne yaji yana neman kayar dashi, ba shiri ya nemi waje ya zauna yana dafe kansa. Kallon Haj Maria yayi idonsa yayi jawur gabanta ne ya fad'i ganin irin kallon da yake mata da sauri ta ce "na rantse Alh bada sa hannuna a ciki banma san baya gidan nan ba". Tashi yayi a hargitse yana nunata ya d'an yatsansa yana cewa "waye ya basa makullin duruwar kud'in nan to?, bana amsheta a hannunsa ba? , kuma kinsan yaron nan baya jin magana ko kad'an mi yasa baki sa mai ido yadda ya kamata ne?, yanzu wannan yaro ina zaize cikin uban ruwan nan cikin dare haka?". Haj Maria tama kasa magana sai hawaye dake zuba ta cikin idonta, domin bama fad'an Alh ne yake damunta ba, tunda suka shigo d'akin jikinta ya bata akwai wani abu mummuna dake faruwa da yaronta. Da sauri ta juya tabar d'akin tana nufar d'akinta. Wayarta ta d'akko tana danna ma wata number kira. Tana jin an d'au wayar bata tsaya jiran jin mi za'a ce ba ta fara magana tana cewa "Haj Aliya, ko Ammar yana gidanku yanzo wajan Haris ne?" Daga cikin wayar Haj Aliya itama cike da tashin hankali ta ce "nima abunda nake shirin kiranki naji shin Haris yazo wajan Ammar ne?". "Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un" kawai Haj Maria ta take anbata ta sake cewa "tabbas duk inda suke suna tare da juna, amma bari na kira Haj Bilki ko suna tare da Fu'ad". Da sauri Haj Aliya ta tari hanzarinta tana cewa "ai yanzu na gama waya da ita suma suna cikin tashin hankali dan shima Fu'ad d'in baya gida". Haj Maria bata san sadda wayar ta fad'i kasa ba ta tarwatse. Dafe kanta tayi tana tunanin ina yaran nan zasuje haka, tana tabbacin baza su zauna a k'asar nan ba, domin taga irin mak'udan kud'in da Ammar ya d'iba. Haj Salma dake zaune kusa da Alh Mande ta ce "yau ka dad'e baka dawo gida da wuri ba, domin d'azo Zainab (Zuzuuh), ke tabbayar baka dawo ba". Kallonta yayi yana kai lumar abinci a bakinsa yana cewa "yauwa kira min itama ina son ganinta", "amma yanzu baka ganin tayi bacci". "Ki taso min ita". Shuru Haj Salma tayi tana nufar d'akin Zuzuuh, koda ta shiga sai da ta kwanna wutar d'akin, ta kai dubanta akan gadon Zuzuuh, murmushi ta saki ganin kamar mutum ne ke kwance akan gadon duk daukarta Zuzuuh ce kwance kai. Sai dai tana yaye abun rufar, ta zaro ido tana kallon yadda aka jera fulillika a tsaye sai yayi kamar mutum ne akan gadon yana kwance. Da mugun sauri ta fice daga d'akin tana nufar darning inda Alh Mande ke zaune, ganinta a hargitse yasa ya ajiye cin abincin yana cewa "lafiya dai na ganki kin fito haka?" "Alh ba lafiya ba wallahi, na duba ko ina na d'akin Zuzuuh ban ganta ba, dama tun d'azo na lura kamar bata da gaskiya kamar tana shirya wani abu" Tashi Alh Mande yayi ba shiri yana cewa "gidan ubanwa zata je cikin wannan daren da ake tsula uban ruwan nan, maza ki kira k'awayenta su biyu ko suna tare........ ZAHRA ROYAL STAR KOWA YA ƊEBO DA ZAFI... NA MEENAT A 'YANDOMA DA ZARAH ROYAL STAR WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSHI ƘIRƘIRARREN LABARI NE Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji. PAGE 9&10 ...Hannunta Denial ya cafke tare da kafa mata haƙora. Ihu take tamkar ranta zai fita sakomakon azababben zafin da yayi mata dirar mikiya. Fu'ad ne ya lura da allurar da suka jefar can gefe, shammatar Denial yayi tare da daka masa ita a kai, nan take ya sulale a kasa sumamme. Numfashi Doctor Anna fita ya rika yi da kyar cikin radadin ciwo take fadar a miko mata karamin akwatin ta. Kafin ta rufe baki sauran likitoci sun shigo dakin a gigice. Nan suka hau ba Doctor Anna taimakon gaggawa. Babban abinda ke tayar masu da hankali shi ne wannan wace irin cuta ce da zaka riƙa cin naman jikin dan uwansa. Daga taimako ga shi suna shirin rasa manya-manyan likitoci su guda biyu. Allurar bacci suka yima Anna nan take nannauyan bacci yayi awon gaba da ita. Ninaah da Haris ne suka shigo dakin tamkar ka ce masu tak su tsere. Tsattsaye suka yi ganin ana dibar jinin wadanda suke fama da cutar, "mutum biyu su biyo mu don akwai binciken da muke sonyi" daya daga cikin likitocin ya fada. "Babu inda zanje, ta ya zan fita in bar yan uwana cikin wannan halin?" Fu'ad ya fada ranshi a matukar bace. "Kaga Haris da Ninaah su je mu sai mu tsaya nan" Bayan fitar su Haris Fu'ad ne ya matsa kusa da gadon Ammar. Kafe shi da ido yayi cike da tausayin halin da suka tsinci kansu, kamar ba sune cike da farin ciki a jiya ba. Tabbas rayuwar nan akwai ban tsoro, Ammar ne kwance bai son wanda ke a kanshi ba, shin me zasu fadama iyayensu in suka koma gida, ina bazai yiwuba dole ku warke. Maganar da Ibina tayi ma shi ce ta dawo da shi cikin hayyacina shi. "Fu'ad dubi jikin Zuzuuh ka gani duk tayi fari ga inda aka cije ta yana fitar da wani irin ruwa mai yauki." "Jikinsu duk haka yake tunda lamarin nan ya faru, anya ba zamu nemi transper ba mu tafi wata kasar da su?" Turo kafor da aka yi ce ta saka su yin shuru, Haris ne da Ibina jiki a sanyaye. Duk faman tambayar da suke masu amsa ta kasa samuwa sai faman binsu da ido suke. A hasale Fu'ad ke magana "kada ku mayar da mu sakarkari mana, ya zamu yi maku magana amma ku kasa bamu amsa" ya karasa maganar tare da nufar inda Haris yake gadan-gadan. Da sauri Ibina ta sha gaban shi don tasan shi da zafin zuciya ba tun yau ba. "Fu'ad mun mutu, ku dauka mun mutu kawai" Haris ya fada hawaye banin fuskar shi tamkar mace haka yake cizgar kuka. "Bangare mun mutu ba?" Ibina ta faɗa cikin tashin hankali "Lemun da su Zuzuuh suka sha, hade yake da wani acid mai matukar hatsari ga lafiyar dan adam." Ninaah ta karasa maganar tare da share hawayen fuskarta. "Wa ya sanar da ku?" "Likitocin" Haris ya bada amsa. Yaraf! Ibina ta koma ta zauna cike da tashin hankali tare da dafe kanta da take jin yana barazanar tarwatsewa. Tsit dakin yayi kowa da abinda yake sakawa. "Duk wancan la'anannen ne Goarge ya haddasa mana wannan masifar, don haka banga amfanin rayuwarsa ba." Fu'ad ya karasa maganar a fusce tare da nufar inda Goarge yake kwance." Saurin shan gabansa Haris ya yi. "Mi zaka yi ma shi, wannan ba lokacin fada bane mafita ya kamata mu nema tun kafin lokaci ya kure mana" "mafita fa ka ce? Wace irin mafita bayan ya salwantar mana da rayukan abokan tafiya biyu, bayan raunin da ya ji ma Ibina. Ka matsa ka bani wuri tun kafin raina ya ba ci." Ya karasa maganar a fusce. "Fu'ad ka dawo cikin hayyacinka, mafita zamu nema ba fada ba" tatss! Kake ji Fu'ad ya dauke Haris da lafiyayyen mari. "Naga alamar bakinku daya da George, ko dai siyar da mu kayi ka fada Mani." Fu'ad shaƙe da wuyan Haris ke maganar cikin ƙaraji. Ibina da Ninaah ne suke kokarin ɓanɓare Haris amma sun kasa don ba rikon wasa yayi ma shi ba. Kuka suke suna rokon su daina fadan amma ina bugun juna suke tare da farfasa duk wasu glass dake wurin. Ganin zasu yi kisan kai ya saka Ninaah fita a guje ta Kira ma'aikata, da kyar aka raba su, nan take aka koro su daga cikin dakin. Ibina Kuka take tamkar ranta zai fita "Yau suke ke fada bama cacar baki ba, abinda tunda suke basu taba yi ba tun daga kuruciyarsu, anya basu debi ruwan dafa kansu ba, domin hausawa sunce kowa ya ɗebo da zafi bakin shi." "Haris Fu'ad! muna cikin wannan halin kuke fada, abinda tunda muke ko a kuruciyar mu bamu taba fuskanta ba. Na roke ku mu aje komi a gefe yanzu ne lokacin da zamu rungumi juna ba lokacin fada ba, muyi wa kanmu adalci na rokeku." Ninaah ta karasa maganar tare da sake fashewa da kuka. Samun kansu suka yi jikinsu yayi sanyi, domin tabbas gaskiya ta faɗa, dama Fu'ad akwai saurin zuciya. LAB Tun bayan shigowar su abu daya suke yi, wato gwaje-gwaje akan jinin da suka deba. Duk iya binciken da suka yi abu daya suke gani wato cuta mai haddasama kwalwa cin naman ko wane iri ne. Babban tashin hankalin su ga George cikin mugun hali bare ya sanar da su inda ya sami wannan kwayar cuta domin sanin inda zasu samu maganinta, basu baro lab ba sai da dare ya raba amma duk da haka sun kira babban likita ya sanar masu yana zuwa da safe. Su Fu'ad kuwa juyin duniya anyi da su akan su shiga inda aka tanada domin kwanan masu jinya amma fur sunki tafiya sai ma suka kwanta saman kujeru dake daf da ɗakin da su Ammar suke. Dare ya tsala asibitin tayi tsit baka jin karar komi sai ta karnuka alamun kowa ya yi bacci. Su George tare da su Ammar dake kwance a gadajensu lokaci daya idanunsu suka bude. Dirowa suka fara yi daga saman gadajensu suna jan kafa kansu ya karkace kafa a murgude tare da nufar kofar fita. Cikin baccin Ibina ta ji kamar mutum tsaye a kanta, bude idanunta yayi daidai da sakin gigitacciyar karar da ta saka su Fu'ad farkawa, bude idon da zasu yi su Ammar suka gane sun zagaye da su sun saka su tsakiya idanunsu fari fat bakunansu na dalalar da jini.... Meenat yandoma