Compiled By Umar Dalha Funtua. 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA 0⃣1⃣ Ma dai daichin gida ne wanda ya tsaru iya tsaruwa, masu hidimar gidan sai kaiwa da komowa suke. Gabaki dayansu suna zaune a dinning table suna breakfast ba wanda ke cewa komai har suka kammala Ammii ce ta kwashe kwanukan takai kitchen tahau wanke wa. 30mints later Daddy ne ya fito cikin shirin sa na zuwa daurin auren dan kaninsa wanda xa ayi a garin Karaye "To Ammii zan wuce to daddy Allah ya kiyaye hanya " " Ameen ameen sai na dawo. Tafe yake akan hanyar sa ta zuwa Karaye gudu yake ta tsulawa kamar dan shi akayi titin kasan cewar titin ba cunkoson abin hawa. Sai da yaxo dai dai inda ze shiga garin gwarzo ya taka kusa aiko tayar sa ta fashe. INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJU UN shine abinda daddy yake maimai tawa, waye zai tai makeshi da sanyin safiyar nn gashi bashida spare tier balle ya canja. Daddy yana tsaye jikin motarsa yana neman mafita tunani yake kodai ya bar motar ne yatafi gurin daurin auren? To in ya tafi wa zai bar wa motar sa, yasan komai zai iya faruwa idan ya tafi. "To ynx ya zanyi yace afili. Sauri yake tayi kasan cewar yau daurin auren amininsa ya zama dole ya halarchi wnn daurin auren. Tundaga nesa ya hango shi kuma tabbas yaga alamar yana cikin yanayi na neman taimako kasa ya farayi da motarsa yayi parking dan gaba da daddy sannan ya fito. Sannu Alhaji Yawwa sannu yaro "wani abu yasami motar ne? " Ehhh taya ce ta fashe gashi banida spare. "subahanallahi" Aikuwa inada spare a bayan motata nn ya xagaya ya dauko masa tayar. Bari naje nn gaba kadan akwai masu gyara sai suzo su saka maka To madallah inji daddy yana mai fadada fara 'arsa. Daga nn safeer yy gaba shikuma daddy ya tsaya. Befi 20mints sai gashi da Mutum biyu sun dawo nn suka shiga daura taya suka gama. Nagode sosai yaro "Bakomai wlh ae yiwa kaine " Ina kanufa daddy ya tambaya. Karaye zani daurin auren abokina, Ae nima nn na nufa Daga nn kowannen su ya shiga motarsa suka kama hanya wanda cikin lokaci kadan suka isa kuma aka daura auren dasu. Sai bayan da aka daura auren ne Alh. Al 'ameen sarakee Ya samu kebewa da safeer inda ya bashi complementary card dinsa "Ga wnn card dina ne don Allah gobe ka sameni a office" To nagode kuma insha Allah xaka ganni.... ASSALAMU ALAIKUM wa alaikumussalam sannu da zuwa Alhaji "yawwa Ammii ya gidan? " " lafiya kalau Ammii tace tana binka bayan Alhaji zuwa daki. 3 hours later Shukra kixo inji daddyn ki yana son magana dake To Ammii shukra tace tana mikewa daga kwancen da take Da sallama ta shigo cikin dakin cike da biyayya ta gaida mahaifinta ya answer da fara 'arsa. Zuwa chan daddy yayi gyaran murya ya fara magana kamar hk "shukra inaso ki bude kunnenki ki saurare da kyau kuma ki dauka cewa maganar da xan fada miki umarnine ba shawara ba. Gaban shukra ne yashiga bugawa da sauri sauri to me daddy xe gaya mata ne wae " Kina jina ya katse mata tunanin da take " " Ehhh Kawai ta iya cewa tana sauraronshi Nayi miki miji kuma nn ba da dade waba sai zo ku fahimci juna " miji kuma shukra tace tana xaro idonta Alhaji miji fa kace "Ehhh miji mana menene "? Ae naji ka fadi abinda baxe yiwu bane Ae kuwa dae sai ya yiwu kuma ki zuwa ido ki gani yana gama fadar hk yafice daga gidan ma gaba daya. KO WANENE MIJIN DA ALH SARAKEE YA XABA WA YARSA? SHIN XASU AMINCE DA AUREN KO KUWA A A? SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [3/22, 9:24 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA 0⃣2⃣ Knocking yake a kofar office din Alh sarakee " yes come in inji sarakee, Kai tsaye safeer ya shiga cikin office din har kasa ya durkusa yana gaida Alh sarakee Abun ba karamin dadi yama sarakee ya answer fuskarsa a sake " Have a sit "Thank you sir Safeer nasan xakayi mamakin abinda yasa na nemeka kuma ni anawa ganin ba abun mamaki bane, Alfarma nake so kayimin dan Allah " Alh wace Alfarma kakeso nayi maka Inaso dan Allah duk abinda nace kayi min kayi "indai be sabawa addiniba me zai hana nayi maka " be saba bama cewar Alh sarakee cikin sauri " gyara xama yayi yafara dacewa A gaskiya na yaba da hnklin ka shine nakeso na hada ka da yata dan Allah ka aure ta Maganar ta xowa safeer a BAZATA baxe iya cewa a a ba amma shi har ga Allah bashida burin Aure a wnn lokacin " Dan Allah karka ce a a inaso kasani yata batada wani aibu ba kuma dan tarasa mijin aure ne na bakaba a a kawai dai dan na yaba da hankalin kane nakuma ji dadi da ka temaka min a lokacin da nake tsananin bukatar temako " To Alhj madallah nagode " nine da godiya safeer ynx sai ka bani number wayar ka kuma in kuma in ka samu lokaci sai kazo ku sasanta kanku ko To insha Allah xanxo. Yawwa baka gayamin suwaye iyayenka ba da kuma karatunka da inda kake aiki "sunana safeer muhammad mai lafiya babana shahararren dan kasuwane, nayi makarantar primary da secondry a garin Abj kasancewar kasuwanchi yakai mahaifina can garin Abj bayan na kammala secondry ne muka dawo garin kano inda na samu Admission a B U K na karanci "Architectural technology" ynx hk ina aikin gwamnati sannan kuma ina aiki on my own nakanje gari gari indai ai nemeni ina zuwa nayi Aiki. To masha Allah, Allah ya taimaka " Ameen ameen Alhj nagode " Nine da godiya sai najika Daga hk sukayi sallama. WASHE GARI shukra wai me yake damunki ne ace tunda aka miki maganar auren nn shikenan bakida wani aiki sai kuka "Ammii ya xanyi da raina wae ni xa ayi wa auren dole To shukra ya xakiyi ae sai hkr kawai " yanzu Ammii ba abinda xakiyi akai? To me xanyi shukra ae a gabanki yace na zuba ido ko? sbd haka rungumar kaddara ne kawae ya dace dake a halin ynx "Bazan iya ba wlh Ammii banason koma wane ne kawai a kyaleni To ae sai ki bari inya dawo kije ki gaya masa (zuwa wannan lokacin Ran Ammii ya soma baci da kalaman shukra) tana kaiwa nn tafice mata a dakin. Wayar shukra ce ta fara ringing kamar BAZATA dauka Ba sai kuma da dauka "Aneesa ce class mate dinta tun a secondry har zuwa ynx da suke karantar" Optometry " a B U K. " Hello Aneesa Y kk "lfy shukra are you coming today? "i don't think so Buh why? Am not feeling better "wishing u quick recovery shukra luv Thanks Aneesa dan Allah inkin gama lectures ki biyo gida kafin ki tafi "to insha Allah zaki ganni Da sallama Aneesa tashigo cikin gidan Ammii ta samu a falo suka gaisa ann ne ta tambayeka shukra.. Tana ciki tana aikin kuka. " kuka kuma Ammii bari nashiga ciki na sameta to..... SHUKRA YARA GATAN MIEMIE BIE 💞 [3/24, 3:58 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA 0⃣3⃣ Shukra wae me yake damunki ne Ammiii tace min kina kuka Hmmmm Aneesa ba dole inyi kuka ba wae ni xa ayi wa auren dole.. What...come again shukra i didn't get u aure fa kika ce "Ehhh aure wae daddy xemin da wani banza wnd ban sanshi ba To ynx shukra zuba ido xakiyi ayi auren bawani mataki da zaki dauka. Hmmmm banida wani zabi Aneesa abinda dae na sani shine" Wallahi tallahi daga ranar da aka daura auren nn daga ranar koma wane mijin yayi sallama da kwanciyar hankali da xaman lafiya.... Tunda dae ya zabi aure na tokwa ya xabar wa kansa masifa ne wae ni shukra zai Aura.... Hmmmm!!! Hmmmm to nidai ba abinda xance sai dai Ince Allah ya kyauta "Ameen inji shukra" Nidai Kinga tafiya ta cewar Aneesa tana mikewa "ki gaida mamah" Zataji insha Allah tafada tana ficewa daga dakin. @Safeer's house Dukansu na gani zaune a palourn mamah suka kallo Safeer ne ya ke ta satar kallon Abba, Abban ne ya lurada shi "Safeer ya akayi ne " Abba wata magana nake so nayi daku sai dai ban san yanda zaku dauki maganar ba, Juyowa Dukansu sukayi suna fuskantar shi suna jiran suji me zai ce "muna jinka Safeer fadi me kake so kace kaji Nan Safeer ya gyara zama ya fara basu labarin tun haduwar sa da Alhj sarakee har zuwa bashi yar shi da yayi " Alhamdulillahi "shine abinda daddy yace yana me kara fadada murmushin kan fuskar sa " ynx yaushe ne bikin to inji Mamah ta fada da murnar ta. Yace baxe dau lokaci ba To Allah ya nuna mana Ameen Dukansu suka hada baki gurin fada Yeyyyyyy!! Miemie ce tasa ihu ynx xan fara kiran kawaye in fada musu bikin yaya na yazo Kae ranar akwai buduri wlh xamusha rawa da one leg yeeeeyyyyy ta cigaba da ihu.... Dukansu dariya suke banda Safeer daya hade ransa dama shi ba shiga harkarsu yake ba shi baya son rainin hnkl "zan koya miki hnkl wlh meye hk mtwsssssss ya fada yana ficewa daga palourn. Allah ya shirye ki miemie inji Aysher (yayar miemie ita take bin Safeer). Alh sarakee ya yanke auren Safeer da shukra nn da sati biyu xa a daura aure inyaso ta tare koma yaushe ne. Yau ta kama ranar da Safeer xexo Ammiii ce ke shirye shiryen ta banda shukra dake kwance a daki kamar kullum tana aikin kuka.............. Safeer ne ke saukowa daga upstairs cikin shirin sa na zuwa gidan su shukra sanye yake da shadda light brown gezna hannunsa sanye da agogo kirar rolex kansa da hula Kai tsaye falon Mamah ya nufa ya shiga ya durkusa kusa da Abba ya shiga gaida iyayensa cike da ladabi Da fara arsu suke answer wa "za a tafi neman auren ne miemie ta fada tana buya a bayan mama Ai kuwa a xuciye ya taso kamar wanda xe doke ta "yi hkr inji mamah kaifa babba ne " Mamah yarinyar nn ta raina ni wlh inaji fa dana gaisheku sai da answer Dariya daddy yayi yace ayi hkr kaji "tashi ka tafi kar ka makara To kawae yace ya fice ransa a bace..... DEDICATED TO MIEMIE BIE SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [3/26, 2:28 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘. 0⃣4⃣ "kai tsaye safeer gidansu shukra ya nufa wanda cikin lokaci kadan ya karasa, parking yayi a inda aka tanada domin parking motochi sannan ya fito "kai tsaye cikin gidan yanufa xuciyarsa tana harbawa da sauri da sauri ai kuwa sai yaci karo da kaninta "yana ganinsa ya taso da fara arsa " Good afternoon uncle "Afternoon! How are you "Not bad " good " Shukra fa? Ya tambaya " tana ciki tana kuka "toooooo to ynx xaka iya karamin ita "Ehhh ammii tace in kazo ka shigo daga hk yayi gaba shikuma yabishi har guest room ya zauna shi kuma ya fita Ammii! Ammii! Ammii " Na am meye ne kake ta kirana ta fada tana fitowa daga kitchen "Ammii mijin Aunty shukra ne yazo " ohhh har yazo ince dai ka kaishi guest room ko "Ehhh Ammii yana chan yace in kirata " to jeka abinka zan turo ta "To kawae yace ya koma gurin safeer inda suka cigaba da hirar su kamar dama chan sunsan junansu ne. "sanda Afeer ya fita Ammii kai tsaye dakin shukra ta shiga 'shukra tashi ki shirya ga safeer chan yaxo yana jiranki' tana gama fadar hk tafice ba tare da ta jira me Zata ceba" Koda Ammii ta fita shukra xamanta tayi batada niyyar tashi har sai da takai 40mints a zaune "Ammii ce ta leko 'ynx shukra har ynx kina nn a zaune kinbar yaro yanata jiranki shima fa yana da abinyi amma ya vari yatawo gurinki amma kika barshi a zaune ko? " A a Ammii ynx xan tafi fa. "karma ki tafin mana ynx in kira Daddy in fada masa " Dan Allah kiyi hkr Ammii wlh ynx xani ta fada tana mikewa Ammii ce ta fara fita sannan itama ta fita "kai tsaye guest room ta shiga Amma koda ta shiga sai tayi tsaye abinta ta kuma sunkuyar da kanta dan ko kallo ma be isheta ba" "Tsahon lokacin suka dauka ba wanda yace da dan uwansa komai " safeer ne ya katse shirun ta hanyar mikewa yana cewa toni xan wuce "sai na dawo ko " komai bata ce ba illa matsa masa da tayi ya huce Yana fita ita ma ta fice kai kai tsaye dakinta ta shige ta rufe. "koda safeer ya koma gida be nuna wa iyayensa hk ne ya faru ba kuma koda Alhj sarakee ya kirashi cemasa yayi to karbe shi hannu biyu - biyu. " To biki fa ya gaba to kamar yadda Alhj sarakee yace xa a daura aure inyaso ta tare daga baya hk kuwa akayi " Yau ta kama saturday wanda yaune za a daura AUREN iyayen sai farin ciki suke banda yayan da suke a cikin tsananin bakin ciki musamman shukra da ba son auren take ba 'Har gwara na safeer wanda shi daman tunda yaga shukra yaji sonta ya shige shi sai dai yayi wa kansa ALKAWARIN baze taba nuna mataba har sai ya koya mata sonshi (🤔🤔 uhmm su safeer manya) "To abokan safeer duk sun hallara a gurin daurin auren don taya shi murna". Sanye yake da farar shadda tasha aiki wanda aka yimusu shida Abbansa iri daya, bakin takalmi da bakar hula yasa sai kuma farin agogo da yasa sai kyalli yake yana ta fara a wadda shi kansa besan na menene ba kawae dai ya tsinchi kansa cikin farinciki ne a yau din ( Niko nace luv ne). To Daurin auren ya samu halartar manya manyan mutane daga ko ina a fadin Nigeria wanda yawanchinsu abokan Abba da daddy ne "An daura AUREN akan sadaki naira dubu dari. Haka dai daurin aure ya watse kowa na farin ciki ana kuma ta sa albarka. To kamar yadda daddy yace shukra BAZATA tare ba hk kuwa akayi bata tare dinba tunda ynx ma final exam dinta xata fara ta kammala university. To shukra fa sun fara exams gadan gadan wanda ynx ma sun kusa gamawa shikuma safeer ya cigaba da zuwa Aikin sa kamar da. Shukra ta kammala exams dinta kuma ansa ranar tare war ta nanda sati uku. "Duka banga rorin biyu shirye shiryen su suke tunda xa ayi mothers night kafin akai amarya dakinta. " yau ta kama saturday wanda yaune xa ayi mothers night shukra taci kwalliya kamar ba gobe "Fancy Makeover" itace ta mata kwalliya kuma tayi shirinta cikin wani material me tsadar gaske kalar peach tasa head orange (hmmmm abin dai ba a cewa komai readers zanso kuga shukra yau din nn ba karya) takalmi da jaka duka orange tasaka..... "Daga nn dai aka dunguma zuwa" Shukra event centre "inda ann ne za ayi mothers night din. To anchi ansha Alhamdulillahi guri ya kayatu daga nn ne aka kwashi shoki sannan aka rufe taro da addu a aka dauki amarya aka wuce da ita gidan ta dake nn Nassarawa G R A................................. SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [3/27, 9:52 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Beauty, intelligent, respecting peoples are what makes you swthrt #MIEMIE BIE i Dedicated this page to you. 0⃣5⃣ ASALIN SU Alhj AL 'ameen sarakee haifaffen garin adamawa yola ne yayi karatun primary & secondry dinsa a garin Adamawa wanda daga nn yayi exam jinsa wato Jamb ya kuma samu point me kyau Ya nemi admission a usman danfodio university sokoto wanda cikin yardar Allah ya samu ya fara karanta 'Geology'. To bayan ya kammala karatun sa ne be dade ba yasamu Aiki a wani company a garin kano inda ya tattaro gaba daya ya dawo kano da xama "Alhj sarakee ya hadu da matar sa fateema ne (Mahaifiyar shukra) a saudiyya inda yaje aikin hajji " itama fateema gabaki daya yan gidan su suka je Aikin hajjin kasancewar mahaifinta me Arzikin gaske shine senator na kano central a wnn lokacin "To kasan cewar A lokacin Aikin hajji suka hadu yasa basu wani fahimci junansu ba sundai yi exchanging numbers na niyyar in sun dawo gida sarakee zaije ya sameta. " to bayanda suka dawo gida ne Alhj sarakee yaje gidansu fateema kuma ta hada shi da iyayenta.. Baban fateema ya yaba da hnklin sarakee kwarai shiyasa ma bayan dayayi bincike a kanshi sosai ya nemeshi ya kuma shaida masa ya turo iyayensa. " Iyayen Alhj sarakee sun zo sun kuma yi duk abinda ya kamata akasa ranar biki wanda ba a wani dau lokaci ba aka daura auren aka kuma kai fateema gidanta dake unguwar 'Farm center'. To zaman fateema da sarakee xama ne abin sha awa domin akwai girmamawa da mutunta juna. 'Haka zaman su ya cigaba har na tsawon shekara biyar wanda a wnn shekara biyar din fateema ko bari bata taba yiba balle haihuwa abinda yayi matukar daga mata hnkl kenan "A bangaren sarakee kuwa sam abin be dameshi ba shine ma kullum yake kwantar mata da hankali yana cewa haihuwa ta Allah ce Kuma lokaci ne beyiba in yayi xa ta haihu " To da wannan kalami na sarakee fateema tayi amfani wajen kwantar da hankalin ta. Ana cikin haka ne fateema ta sami ciki, zo kaga murna wajen sarakee da fateema kai har ma da iyayansu wanda daman suma rashin haihuwar ya damesu shiru dai kawae sukayi. "Ciki dai yana samun kulawa yadda ya kamata Haka suka cigaba da kulawa da cikunsu har watan haihuwa yayi wanda Alhj sarakee takanas ya tafi 'Egypt' danyin siyayyar kayan baby " To ana gobe fateema xata haihu sarakee ya dawo wanda washe gari da asuba fateema ta tashi da ciwon mara da ciwon baya wanda sarakee be bata lokaci ba ya dauki fateema sai asibiti. " Cikin lokacin da be wuce awa daya ba fateema ta haifo kyakykyawar yarta me kama da Alhj sarakee sak daga nn akayi discharging dinsu kasan cewar fateema da babyn lafiya kalau suke. " Ranar suna yarinya tachi suna 'ZAINAB' wato mahaifiyar Alhj sarakee hakan nema yasa suke kiranta da suna 'SHUKRA' " Sai da shukra ta kai shekara 7 sannan fateema ta kara samun wani cikin. To wnn cikin ma anyi farin ciki da samun shi kasancewar sun cire rai ma da kara samun wani cikin. ," Haka dai take ta rainoncikin har lokacin haihuwar yaxo inda ta haifi yaron ta namiji. "shikuma sunan mahaifin fateema yaci wato Mukhtar suke kiransa da 'AREEF. " Tundaga kuma wannan lokacin har zuwa ynx fateema bata kara haihuwa ba. "Haka yaran suka taso cikin soyayya da kuma kulawar iyaye sosai yaran suke da tarbiyya ga girma ma manya ga kuma kunya da tsoron Allah. CIGABAN LABARI " TO koda safeer ya taso daga office gidan mahaifin shi ya wuce kai tsaye inda iyayen nashi suka hadu suna mai nasiha kan ya kula da matar sa domin amana ce a gurin. " Godiya safeer yayi musu sannan kuma ya kama hanyar gidansa xuciyar sa cike da sake sake tunani kawae yake wace irin tarba shukra xatayi masa? " zata karbi kaddara ne ta zauna dashi a hk ko kuma BAZATA karba ba? "To da wnn tunanin ne safeer ya karasa gurin wani suya spot ya siyi kaji da kuma fresh milk xe kaiwa amaryar sa........... " Bayan yagama da suya spot kai tsaye gidansa dake nassarawa G R A ya nufa koda ya isa yayi worn a gate, gate man ne Y taso da fara arsa ya bude mishi yana gaida shi da fara arsa. " To safeer dinma da fara arsa yake answer wa kafin ya wuce gurin da aka tanada don parking yayi parking motarsa sannan ya nufi cikin gidan kai tsaye.......................... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [3/29, 4:33 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA I don't care weather people will like it or not, ☹if they like it "cool ' if not it left for them (Hmmmm such is lyp). I only know that i luv u #MIEMIE BIE Dedicated to you 👆🏻 0⃣6⃣ Ko da SAFEER ya shiga cikin gidan kai tsaye dinning area ya huce ya ajiye kayanda ya shigo dasu sannan ya shige dakinsa. "kayan jikin sa ya rage ya fada bathroom don yin wanka. " A bangaren shukra kuwa yan kawo amarya na fita ta mike ta rufe kofar ta sannan ta koma tayi wanka tasa sleeping dress nata ta kwanta. "Bayan kamar 30 mints da shigar SAFEER toilet ya fito daure da towel a waist nasa da kuma wani a hannun sa yana goge kansa dashi. " kai tsaye gaban dressing mirror sa ya wuce ya shafe jikinsa da lotion sannan yasa turare ya wuce kan gabon sa dan sa kaya wanda already dama ya fito dasu. Bayan da ya gama shirya ne ya fito ya nufi dinning area ya dauko ledar da yashigo da ita sannan ya wuce dakin shukra. "Yana karasawa ya murda handle din kofar amma ga mamakinsa sai yaji kofar a rufe gam. Cikin bacci shukra taji ana taba handle tsaki kawae taja tana hararar kofar kamar yana kallonta. " A zuciyar ta take cewa munafiki da ajinka xan bar kofar a bude ne" mtwsssssss ta dada jan tsaki sannan ta juya baya ta cigaba da baccin ta. "Shiko SAFEER juyawa yayi ya nufi dakinsa jin kofar shukra a rufe. " Washe gari misalin karfe 12:00 na Rana ko wannen su na dakin sa. "knocking din da ake a kofar falo ne yasa SAFEER fitowa ya karasa ya bude kofar. "kokarin tureshi take yi xata shiga ciki da basket a hannunta " ke bakida hankali ne wae kike ture mutane ya fada a tsawace yana binta da mugun kallo...... Wallahi ki kiyaye miemie inba hk ba hmmmm ya fada yana wuce wa cikin falo. "Dan nazo gidan ka shine kake min hk ta fada tana tura baki gaba kamar xatayi kuka. " Ammiki din ya fada yana hararar ta (shi sam be so wannan yarinyar tazo ba don surutun ta yafi aikinta yawa). "Wae ke me kika zo mn gida da sassafe. " Baki ta saka tana kallon shi da mamaki 'ynx ne safiya ya SAFEER?... "To ynx ma ba wannan ba ina Aunty na. Tana ciki ya fada a takaice. "Au ita bata rashi ba 🤔 ikon Allah koda yake ae da gajiya gwara ta huta. " Gajiyar me ya fada yana mikewa wane zai daketa. "Tana ganin haka ta mike gajiyar biki fa nake nufi. God save you ya fada yana koma kan kujera. " To ynx yaya haka xan tafi ban ganta ba. "Ehhh yace yana nuna mata kofa 'fita Dalla kinzo kin Sani a gaba da surutu Fita tayi tana waigensa tana zuwa bakin kofa ta labe shikuma ganin ta fita yasashi komawa daki tunda bashi da abinda xeyi. " Aiko miemie na ganin ya shige daki tashigo cikin gidan da saurinta tana waige- waige. Kai tsaye dakin shukra ta huce aiko sai ta ganta tsaye jikin dressing mirror tana makeup. " Aunty shukra ta fada tana yi mata murmushi. "Murmushi itama shukra take mata haka kawai taji tana son yarinyar. " ya sunanki ta fada tana kamo hannunta. Sunana miemie. "Miemie ya gida ya mamah? " lafiya kalau muke. Aunty wae me yasa yaya ya hanani inzo gurinki ta tambaye ta tana karewa dakin kallo. "Bakomai miemie inaji saboda sanda ya fita ina bacci shiyasa yayi tunanin ban tashiba (Tayi mata karya). Ok na dauka sbd yaga kin gajine bayaso in tashe ki. " Gajiyar me miemie? Ni ban gaji ba ae. Uhmm kawae tace tana hayewa gadon. " Dariya shukra tayi ta koma ta cigaba da makeup dinta. "A takaice dai miemie a gidan ta yini sunata hira da shukra kamar dama sun saba da juna. " Sanda miemie xata tafi sai da shukra ta cika katuwar leda da kayan makeup ta bata. Godiya sosai tayi mata sannan SAFEER ya dauketa suka tafi. " Yau ma da safeer ya dawo dakin shukra ya wuce amma yasame shi a rufe juyawa kawai yayi ya koma dakinsa kasan cewar a gajiye ya dawo (shi dama ba wani abu xe mata ba kawai dai zai duba lafiyar tane kamar yadda mahaifinsa yace amana ce a gurin sa). " Yau sati biyu da bikin safeer & shukra amma cikin sati biyun nn safeer be taba sa shukra a idonsa ba. Dawowar sa daga masallaci knn amma ga mamakinsa sai yaga kofar shukra a bude ae kuwa sai Y xarce dakin. " Shigarsa yy dai dai da fitowar shukra daga toilet daure da towel dinda be karasa rufe mata cinya ba.. Kallon kallo suka shiga yi kafin shukra ta bude baki ta fara zaggaga mishi masifa. SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [3/29, 5:00 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie ❣ 0⃣7⃣ Wnn wani irin hauka ne xaka shigo dakin Mutum ba excuse ta fada tana hararar sa.. Hauka ya nanata kalmar a zuciyar sa "Allah ya baki hakuri ya fada yana juyawa zai fita. " Yana zuwa bakin kofar ya rufe da key sannan ya xare key din ya sa a aljihun wandonsa. "Takowa yayi gabanta fuskar sa a daure ba alamar dariya. " Iya tsorata shukra ta tsorata nn ta shiga yin baya - baya shi kuma yana binta. "Hannu yasa ya jawota yana kokarin kunce towel din jikin ta" Bari ba miki cikin mahaukachi yanda ko waje kika fita kika ga mahaukachi vazakiyi masa goriba tunda kina dashi. "Kuka tashiga yi tana turashi yayinda take rike towel dinta da dayan hannun, Amma dake karfin ba daya ba sai da ya kunce towel din sannan ya turata zuwa gadon shima ya hau. " Ganin batada wata mafita yasata fara rokonsa 'Dan Allah ya safeer ka bari wlh tsoro nakeji, na tuba bazan sake ba. " Gani kawai shukra tayi safeer ya mike ya nufi kofar fita sannan yasa key ya bude ya fece. (shi dama beyi niyar mata komai ba kawae dae barazana ya mata). " Tun daga wannan rana shukra take masifar tsoron safeer bakuma ta sakachin kin rufe kofar ta. " Yau ta kama monday kuma yau safeer zai koma aiki sbd hk ya tashi da wuri ya gama shirin sa na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa. Ko dinning be kalla ba tunda yasan shukra ba zatayi masa girki ba. " Yasa kai xe fice kawae tasha gabansa hade rai yayi yana kallon ta shi sam be ma kula da ita a palour'n ba, ," ya safeer dan Allah xan bika ka kaini gida To jeki dauko hijabi mu tafi.. Ihu murna tasa ta shige daki da gudu SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [3/31, 2:28 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Wishes to congratulates you as you finished your novel that always makes people happy, because it composed a lots of lessons. May God bless your entire life #MIEMIE BIE Dedicated to you 👆🏻 0⃣8⃣ "koda shukra tashiga cikin dakin bata wani dade ba kasan cewar dama a shirye take mayafi kawae ta dauko ta fito ta samu safeer zaune cikin motarsa yana jiranta. "Bude motar tayi ta shiga bata cemasa ba shima bece mata ba haka suka kama hanyar gidan su shukra kowa na sake sakensa cikin ranka. "cikin lokacin da be wuce 40 mints ba suka karasa gidan su shukra, kasancewar safeer nada aiki sosai a office yasa ko da shukra ta fita be bita cikin gidan ba. " Ango kasha kamshi abokinsa yace masa yana dariya irinta tsokana. "Koma bece ba yakaro yana mika masa hannu suka gaisa sama - sama kasan cewar sun kusan makara. " sanda shukra tashigo cikin gidan bata samu kowa a palour ba hakan nema yasa ta shigewa dakin Ammii kai tsaye. "zaune ta samesu ita da Areef suna kallon wani serious. " Da mamaki suke kallon ta kafin Ammii tayi karfin halin mata magana "ke kuma lafiya kika xomana gida da sassafe, ina safeer din yake ta fada taba kallon kofa kamar me neman shi. " Ya wuce office in ya tashi zai shigo ae ta fada tana wucewa kan gadon Ammii. "Aunty shukra yaushe ya safeer xe dawo inji Areef. " Ban Saniba ta fada tana juya masa baya. "To Aunty ki kirasa ki tambaye sa mn. " Karka dameni Dalla malam. " Bekara cewa komai ba illa ma fitan da yayi daga dakin. " Duk abinda suke Ammii na jinsu sai da Areef ya fita ne ta juyo tana kallon shukra "shukra anya ko kuna zaman lafiya da yaron nn " Ammii wace irin magana kikeyi ne wae, waya gaya miki bama zaman lafiya. "Halinka nasani ae shukra. " To Ammii ki kirasa mn ki tambayesa. "Bazan kirasa ba sai dai in bari shawara kan kiji tsoron Allah kada ki tauye wa yaron nn hakkin sa karki ganshi shiru - shiru ki zaluncesa, idan mu bama ganinki Allah na ganin ki. " Kai Ammii dan Allah wae waya fada miki bama zaman lafiya me ma ya kawo maganar xalunta da wani tauye hakki. " kedai kika Sani inji Ammii tana ficewa daga dakin. "shiru shukra tayi tana tunanin mgnr da Ammii ta gaya mata, tanason daukar maganar Ammii amma shedan yana mata huduba. 4:00 pm " Daddy ne ya shigo cikin gidan daga office shukra yasamu a palour, da mamaki yake binta da kallo. "Daddy sannu da zuwa ta fada kafin Ta durkusa har kasa ta gaida shi. " Ba yabo ba fallasa ya answer sannan ya shige dakinsa, Ammii ma ta fito daga kitchen tabi bayan daddy. 4:40 daddy ya fito palour yace Ammii ta kira masa shukra. "Bayan Ammii sun fito tare da shukra dukansu suka zauna a kasa suna jiran me xance. "shukra lafiya na ganki a gida kuma. Ita abinma mamaki ya bata exactly tambayan da Ammii tamata irinta daddy ya mata. " Lafiya kalau daddy kasan yau ya koma office shine yace bari ya kawoni gida inya dawo xexo mu tafi. "Ajiyar zuciya daddy ya sauke yace to madallah Allah ya dawo dashi lafiya. Ameen sukace dukkansu kafin kuma shiru ya ratsa palour ' n. " Shukra ce ta katse shirun ta hanyar cewa daddy daman inason magana da kai. "Dawo da kallon sa yayi kanta sannan yace ina jinki. " Daddy so nake asamomin Aiki in dinga zuwa da xaman gida, kaga duk kawayena damuka gama service aiki suka samu. "sbd kawayenki na aiki shine kema xakiyi Ammii ta tamabeyata. " A a Ammii gani nayi da zaman gidan ai gwara na dinga zuwa aiki ko. "To shukra ae alhakin aikinki ba a hannu na yake ba mijin ki keda ikon samo miki aiki baniba. " To daddy kamishi magana dan Allah ta fada kamar zatayi kuka. "In banda abinki shukra ae kin fini kusa da safeer ke yakamata ki tamvayeshi, kuma bama wannan ba yana iya yiwuwa in tamabyeshi kuma bayaso amma ya amince sbd ni na tamvaya baxe iya cewa a a ba kuma Kinga ae na shiga hakkin sa ko, Amma idan ke kika tamabyeshi tunda ba tsoronki yake ba xe gaya miki gaskiya in yana so ko baya so. "To tace tana goge kwallar data cika mata idonta. Shiko daddy yana gama maganar sa ya tashi ya shige dakinsa. Ammii ce ma ta tsaya tana bata baki kantayi hkr ta tambayi mijinta inya bari to, in be bari bq kuma sai ta hkr. 6:00 pm safeer ya tashi daga aiki yana cikin tattara files din dake gabansa abokinsa ya shigo. "Gaisawa suka shiga yi kafin Abokinsa ya zauna, " safeer wae ya naganka haka ne so silent inji haiydar. "Bakomai safeer yace yana dauke kansa daga kallon haiydar. " Da komai safeer sai dai in baxaka fadamin ba, amma a gani na be kamata ka boye min komai a yadda muke da kai Amma bakomai in bakason fadamin bazan matsa mk ba. "ka gane haiydar wallahi kwata kwata banida kwanciyar hankali tunda akayi auren nn, na dauka bayan auren komai xe dai - daita ashe tashin hnkl ma yana gaba. " Haba safeer ynx akan wnn ka tayar da hankalin, maxa fa gwagwarmaya aka sansu dashi, ae kai da kanka xaka jata a jikin ka ka mantar da ita cewa AUREN BAZATA aka yimata ka koya mata sonka bawae ka tsaya zuba ido ba. " Ta yaya haiydar? Taya zan koya mata sona, bayan tunda akayi bikin yau sati biyu knn ban taba sata a ido na ba sai yau, beside ma she is arrogant as a dethroned chief, she is feeling herself because she comes from a very influensive family. Thats why she's doing what she want to me, Amma bakomai idan munada rabon farinta ran juna watarana sai mu faranta idan kuma bamuda shi sai Allah ya kawo mana mafita. To Allah ya kyauta haiydar ya fada yana mikewa. Mikewa shima yayi yana cewa Ameen suka a tare inda safeer ya nufi gidansu shukra kai tsaye bayan ya tsaya a well care ya musu shopping..... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/1, 1:00 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA 0⃣9⃣ 7:30 pm safeer ya isa gidan shukra bayan yayi parking motar sa ya fito ya nufi cikin gidan rike da shopping din daya yi musu. "Dukkansu a palour ya samesu, durkusawa yy har kasa suka gaisa da daddy sannan Ammii. "Bayan kamar 10mints suka fito gabaki daya don musu rakiya, har gaban motar su suka rakasu Ammii na dada yiwa shukra nasiha kan tabi mijinta. " uncle zan biku " " A a Areef gobe akwai skul ka bari ran friday zanzo sai mu tafi" To kadai yace ya koma cikin gidan ransa a bace don ba hk yaso ba. Minti talatin ne yakai su shukra gida bayan safeer yayi parking ne duka suka fito kowa ya nufi dakinsa. "To washe gari safeer gidansu yakai shukra daze tafi office. " Da murnar Mamah ta tare ta, bayan ta gabatar mata da abun motsa baki ta kira mata Aysher ta fice ta basu guri "Hira sosai sukeyi da Aysher anan ta gane Aysher nada kirki aranta tace dukansu suna da kirki da son mutane sosai. " Aysher wae ina miemie ne " " miemie taje skul amma ynx xaki ganta ta dawo sbd suna exams ne" "To Allah ya dawo da Ita lafiya" "Ameen Aysher tace" sannan suka cigaba da hirar su. "Ko da lokacin girki yayi ma tare sukayi da shukra kasancewar shukra ta iya girki sosai. " 12:14miemie ta shigo cikin gidan da gudun ta kamar an jefo ta aiko tana ganin shukra tayi gurin da gudu ta fada kanta tana murnar ganin ta. "Itama da murnar ta take tamvayar ta" ya exams " " Exams Alhamdulillahi Aunty, ina ya safeer? "Yaje office miemie" "to kawae tace sannan tashiga cikin don yin wanka. 08:40 safeer yazo ya dauki shukra inda Mamah ta cika shukra da tsaraba suka rakasu har gurin mota. "Aunty shukra xan biki miemie ta fada a hnkl yadda bazasuji ba " To jeki debo kayanki mu tafi " " Aunty Mamah bazata bari ba sbd skul " " To kiyi hkr ran friday zansa ya safeer yazo ya tafi dake kimin week end a chan ko. "Ihu murna tasa ta shige cikin gida da gudu. " Yau ta kama friday kamar yadda safeer yayi Areef alkawari yaje ya dauko shi bayan sun sha Fama da Ammii wae baza shiba ze takura musu. Ko da suka shiga cikin gidan shukra da miemie da Aysher suka samu a palour suna hira abinsu. Dakinsa ya xarce bayan sun gaisa dasu Aysher don watsa ruwa. " mamaki ne ya cika Aysher ganin shukra ko kallon Safeer batayi ba ballan tana ma ta gaida shi. " Wai dama har ynx basa zaman lafiya ne? Ta tambaya kanta. "Ataikace dai su miemie yini sukayi agidan da daddare safeer ya maida su gida. 11:00pm shukra, safeer, Areef na zaune a palour suna kallo, safeer ne ya mike yayi wa Areef sai da safe sannan ya wuce da kinsa. " Uncle ni a gurinka zan kwana inji Areef ya fada yana bin bayan safeer " To Areef je Aunty tama wanka kazo mu kwanta. "To ya ce sannan ya wuce dakin shukra. " karfe uku dai - dai shukra ta farka sbd wNi axababben ciwan mara, dama tayi yi ko wani month, kuka take tayi tana juyi tun tanayi ita kadai a daki har ta saki ihu wanda ya sa safeer farkawa a gigi ce. " Da sauri ya karaso dakin shukra inda ya sameta tanata juyi a kasa. " jikin sa har wani rawa yake yana kokari dakata sai jero mata sannu yakeyi. Haka dai ya daga ta ya kaita motar sa sannan ya dawo dakinsa daukan key. "Duk wannan abun da akeyi Areef be saniba baccin sa kawai yake hakan ne ma yasa safeer be taba shiba ya dauki key dinsa ya fice da sauri. Kai tsaye asibitin Aminu kano ya wuce da ita inda cikin sa a a ka karbeta akayi emergency da ita. "kaiwa da komowa kawae yake a bakin emergency gumi duk ya jika shi, sai tunani yake azuciyar sa 'wnn wani irin ciwo ne yarinya sai suma takeyi (Don sau uku tana suma a hanya kafin suxo). " yana cikin wannan tunanin ne wata nurse ta fito take gayamasa an bawa shukra gado takuma bashi list na maganin da ake bukata. " sai asuba bayan safeer ya dawo daga mosque ne yasamu ganin shukra. "koda yashiga cikin dakin idonta biyu tana ganishi ta dauke kai tare D rufe ido kamar me bacci. " ya jikin ki ya tambaya yana xaman abakin gadon. "Kamar baza tayi magana ba sai kuma chan tace 'Da sauki'. " ALLAH ya kara sauki to" "shiru ne ya ratsa dakin kafin safeer ya dauko wa yarsa yayi dialing number'n Aysher. " Bayan sun gaisa ne yake fadama ta shukra ba lafiya ynx hk ma suna Asibiti. "Dakin Mamah ta shiga ta gaya mata sannan ta wuce kitchen don hada musu breakfast. " Kallon sa take tanason masa mgn amma takasa. "shine ya fahimci hkn a nn ya tamvayeta. " wani abu kike so " " Ammii nakeso ka kira min" "komai bece B yashiga dialing number'n Ammii inda yana shiga yamika mata tare da ficewa a dakin. " kusan tare Ammii D mamah suka iso. "Bayan sun gaisa ne Mamah ta yiwa shukra ya jiki. " Da ladabi ta answer sannan ta gaidasu duka. "shukra wae meke damunki ne inji Ammii. " kamar baxata answer ba chan tace 'ciwon mara' Baki sake Ammii take kallon ta da mamaki wae ciwon mara. "ita dai tasan in mace na ciwon mara da zaran tayi aure take denawa, likitochi da kansu suke bada shawarar auradda mace mai ciwon mara. " to meyasa har yanzu shukra take ciwon mara, kardai har ynx ba abinda ya shiga tsakanin yaran nan? Inko hk ne shukra zata gane kurenta..... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/2, 12:45 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 💋❣ 1⃣0⃣ SAFEER ne ya shigo cikin dakin hannunsa rike da kaya, a bakin kofa ya ajiye kayan sannan ya karaso ciki ya durkusa kusa da Mamah suna gaisawa da Ammii cike da ladabi. "ya me jiki Mamah ta tambaya" "Da sauki Mamah" "Allah ya kara sauki " " Ameen suka hada baki dukansu wajen fada. "Ammii ina Areef" "Areef yaje skul " To Allah ya dawo dashi lafiya. Ameen. " Safeer bazaka je office bane Ammii ta tambaya? "Ehhh Ammii zan zauna Ann! " A a baza ayi hk ba tashi xakayi ka tafi inyaso anjima kazo kaji jikin nata inji Mamah. AE tama ji sauki inji Ammii Tafada tana hararar shukra, don ita jira take su kebe da shukra ta fada mata dalilin dayasa taki bawa safeer kanta" "Tashi kaje gida kayi wanka ka tafi office kaji dan Albarka cewar Ammii." "To Ammii Allah ya bata sauki ya fada yana ficewa daga dakin" 2:40dai - dai safeer suka shigo shida haiydar hakan ne ma yasa bayan sun gaisa da su mamah suka fita suka basu guri" "Gaisawa haiydar sukayi da shukra cike da girmama juna, sannan haiydar ya ajiye mata bandir na 100 ya mata sallama suka fito tare da safeer. " se bayan magrib sannan safeer ya tafi kai maamah da Aysher gida, sai a nn ne Ammii ta samu damar kebewa da shukra. " shukra " " Na'am Ammii ta fada ba tare da ta dago ta kalle taba. "HAde rai Ammii tayi sannan tace' dake nake shukra dago idonki ki kalle ni" "A sanyaye shukra ta dago tana kallon Ammii zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri wane zata fito don tsoro da fargabar. " ki fadamin dalilin dayasa kika kika hana safeer kanki shukra " " Tambayar tazo mata a BAZATA dan bata taba tunanin Ammii zata gane ba (Yaro yarone). "uhmm uhmm Ammii.... Ke ki kiyaye, ki kiyaye ni shukra ni ba sa'ar bace wallahi. " kafura ce ke shukra da zaki dinga tauyewa miji hakki? "Ashe dama baki daukemu da daraja ba shukra? " Mu bamu isa dakeba ashe shukra? " Wallahi shukra ki bani kunya ban taba tunanin xakiyi haka ba da hankalin ki dakomai, Ace mahaifinki ya isa da safeer Amma be isa dake ba ko" karki manta bafa mu muka haifi safeer ba Amma yamana biyayya amma ke kikasa yimana biyayya shukra. "A wnn lokacin shukra kuka take wane dashi aka aikota" "To ki Sani wallahi idan mijinki yabi mata alhakin harda ke xa a raba" "zakiso ace mijin ki na neman mata shukra? " Da sauri shukra ta girgiza kanta alamar bata so " To wallahi shukra kiyiwa kanki gata tun baki kaishi bango ba ya sake ki ko ya karo miki aure a banzaba. " AUREN BAZATA hauka ne shukra? " A a Ammii dan Allah ki yafe min wlh bazan sake ba dan Allah karki gayawa daddy, nayi miki Alkawarin "ZAN GYARA KUSKURE NA". "" Karma ki gyara kinji shukra " " Ammii dan Allah kar kiyi fushi dani wlh na dena hali na, insha Allah bazan kara halina ba. "Daga nn Ammii bata kara cewa komai ba, shukra ko kukanta ta cigaba dayi tana me dana sanin" KUSKUREN DATA TAFKA A RAYUWAR TA " " kwanan su shukra uku akayi discharging dinta kuma alhamdulillahi ta samu sauki hakan nema yasa Ammii tace a wuce da ita gidanta. "Ammii da kanta tace safeer ya dinga kula da shan maganin shukra sbd shukra batason mgn, kuma yayi mata Alkawarin hakan" "To kullum safeer shike bawa shukra maganin sbd tunda ta dawo din nn bata rufe kofa kuma har gaida shi take yi. " jiya shukra ta gama shan maganin ta hakan nema yasa safeer beje dakinta ba kamar yadda ya saba duk dare. "shukra ganin har yanzu safeer bezo ba yasa taji BAZATA iya hkr ba sai taje ta duba shi saboda yanzu ba lefi ta dan fara sabawa dashi kasancewar har hira yana dan yimata inyaje bata magani. " Dakinsa ta nufa kai tsaye gabanta na faduwa dan bata san ya zai dauki xuwan nata ba....... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/3, 11:17 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 1⃣1⃣ "Jiki asanyaye shukra ta tura kofar dakin safeer da sallama a bakin ta. "zaune yake a bakin gado da laptop dinsa a gabanshi da alama aiki yake, da fara arsa yake answer mata sallamar yayin da take karasawa cikin dakin. " zama tayi a kasa daga gefen gadon dai - dai kafarshi, ai kuwa da sauri yace "A a dan Allah karki zauna a kasa in gadon ne bazaki hauba saboda ni vari na sauka na barmiki ya fada yana sauke laptop dinsa kasa. " A a wlh kayi zamanka nanma yayi" ta fada cikeda da ladabi. "komai be ce ba sai zaman dayayi a gefenta yana me cigaba da abinda yakeyi. " shiru ne ya biyo baya yayin da shukra ta shiga karewa dakin kallo cike da sha 'awa, dakin yayi mata kyau komai na dakin coffee & milk ne, iya tsaruwa ya tsaru kamar dakin wata amaryar sai dai dakin a hargitse yake sosai kamar ba a taba gyara waba(Abinka da dakin namiji). "Yi hakuri ban kawo miki komai ba ko" "Lah bakomai wlh" "Naga ae kina ta karewa dakin kallo kin ganshi a hargitse ko, abinka da dakin gwauro sai hakuri " " Wata kunya ce da takaichi suka hadu suka rufe shukra 'ae ita ya kamata ace tana gyara dakin tun asalin, Amma batayiba har wani cewa yake wae dakin gwauro sai hakuri " " karfin hali tayi sannan tace, bawani dakin gwauro insha Allah gobe xan gyara dakin in ka tafi office " " komai bace ba sai tunani yake gaskiya shukra ta gyaru, Allah ya kara shirya ta ya fada a ransa " " Dama naga bakazo bane shine nace bari nazo naji ko lafiya, ta fada tana kallon sa" "Lafiya kalau wlh aiki ne ya rike ni" "Aikin me?" ta tambaya tana leka system din " " Wallahi wani kwangilan construction na' fly over ' muka samu shine naketa fama " " To Allah ya taimaka, Amma fa ta zanu " " uhmm wannan dai zolaya ne ni ina na iya wani zane! "Bawani zolaya ka iya ne shiyasa na fada" "Ae shknn" "Haka dai suka cigaba da hirar su sama - sama, 10:00pm shukra ta mishi sallama, tayi tunanin zece ta kwana a nn amma ga mamakin ta sai bece ba " " washe gari 70:30am safeer ya gama shirinsa na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa. "sam be kula da shukra dake zaune ba sai da kai bakin kofa yaji tana masa magana. " Ya safeer breakfast fa " " Hannunka ya daga yana kallon wrist watch dinsa kafin yace 'shukra yanzu in nace zan tsaya gaskiya makara zanyi ki ajiye min inna dawo zanci " " Kamar zatayi kuka tace dan Allah ka tsaya kachi ko kadan ne karka tafi da yunwa. "karki damu innaje chan zanci. " Dan Allah ya safeer ka tsaya kaci bazaka dade ba. "yana son chi amma bayason ya sake da ita don ba wani yarda da tuban ta yayi ba har ynx" "Bata rai yayi sannan ya dauki hanyar dinning" "Da sauri ta karaso wane xata fadi ta jamasa kujera ya zauna sannan tayi serving nashi. " Abincin yayi masa dadi sosai yanaso ya yaba amma ya danne xuciyar sa har wani yamutsa fuska yake,ya manta when last yaci abinci me dadin wannan. "Ture plate din yayi bayan ya gama sannan ya mike. " Shukra ma mikewa tayi ta dauki briefcase dinsa ta rakasa har bakin motar sa, sai da taga fitar motar sannan ta dawo ta cigaba da gyare - gyarenta. "coconut rice da eng sauce tayi ta saka a flask sannan tayi fruit salad tasa a friend. " Toilet ta shige tayi wanka sannan ta fito ta zauna ta tsara kwalliya (irin wadda ta koya a gurin fancy Makeover). 6:20pm shukra ta kara gyara makeup dinta sannan ta fito palour ta zauna jiran safeer. " sai 07:12 safeer ya shigo cikin gidan shukra ko najin horn dinsa ta nemi nutsuwar ta ta rasa fargaba kawai take karya wulakanta ta tunda tasan ita ta siya wa kanta. " baki sake yake kallon ta da mamaki tayi kyau sosai kamar ya dauke ta " " sannu da zuwa ya safeer ta fada yayin da take karasowa gurinsa ta karbi briefcase dinsa " " Yawwa shukra ya gidan? "Alhamdulillahi" "Daga nan ya shige dakinsa itama tabi bayansa, kan gado ta ajiye masa jakarsa kamar ta tsaya ta hada masa ruwan wanka amma tana tunanin kar yace ta fiye shishshigi " " To inma kin masa shishshigin meye? Ba mijin kibane wata zuciyar tace mata. "Juyawa tayi hanyar toilet din ashe wae har ya shige bata saniba tana tunani. " karasawa tayi ta ciro masa kaya ta ajiye a kan bed tana addu'ar Allah yasa ya saka kayan data dauko masa. "Kitchen ta koma ta debo flask din abinci ta zo ta jere su a dinning, sannan ta dawo palour ta zauna tana jiran fitowar sa. " Daddadan kamshin turaren da taji ne yasata dago wa tana kallon shi, da mamakin sai taga kayan data fitomai yasa. "zama yayi hade D daukan remote yana canja changes. " Ya safeer taso muchi abinci " " Alhamdulillahi shukra naci abinci a gidan Mamah kafin in shigo. "Kukan da batasan dalilin saba ta saki ' a yau ta kara data sanin halayyar ta ada. " Arude take tambayar ta menene. " " ko nafadi wani abu dabe miki dadi bane? " " yi hakuri ki dena kukan to, ko saboda naje gidan Mamah ne kike kuka? "Da sauri ta girgiza kanta alamar A a" "To menene ya sake tambayar ta? " ya safeer dan Allah kayi hakuri ka yafemin abinda nayi maka a baya kachi abincin nan" "shiru yayi kamar me tunani kafin yace to naji zanci abincin shikenan. " Eh tace da murnar ta ta tashi a debe flasks din takawo palour ta shiga serving dinsa. "kingani kin bata makeup din ki garin kuka ko, dazu kinfi kyau wallahi 'ya fada ba tare da ya saniba" "fuskarta dauke da murmushin jin dadi tace' Ae na dena kukan ynx. " komai bece ba saboda wani haushin kansa yakeji na yaba kwalliyar ta da yayi " SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/4, 8:45 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie ❣ 1⃣2⃣ "Kwashe plates din shukra tayi ta kai kitchen bayan sun kammala cin abincin, tare da wankesu ta maida komai mazaunin sa sannan ta fito ta sami safeer a palour kamar yadda ta barshi. "sannu da zama ya safeer" "Yawwa shukra sannu da kokari kema" "Yawwa" "Ya safeer yaushe zaka kawo min miemie ne? "Ke yarinyarnan batada kirki surutun ta yafi aikin ta yawa" "Tana dariya tace ai dama ni ba aiki zata tayani ba, kawai dai bana jin dadin zaman gidan ne ni kadai in baka nn. "To shikenan zan kawota amma sai sun gama exams" "To Allah ya kaimu lkc tace sannan suka cigaba da kallon su" "10:15pm safeer yayi wa shukra sallama bayan ya kashe TV" "Yau ma tayi tunanin xece tazo su kwana a dakinsa amma shiru, ita abin ya soma damunta gashi har lokacin mensis dinta ya kusa zagayowa ita tsoron ta daya Ammii tasan cewa zatayi ita taki alhalin ba haka bane" "Wasu zafafan hawaye ne suke shigo zubowa shukra tana kara data sanin rashin rungumar kaddarar da batayi ba a baya, a haka dae ta gama duk abinda ya dace ta kwanta. WASHE GARI " Tun bayan asuba shukra bata koma bacci ba gyaran gidan ta shiga yi sai da tagama sannan ta shiga kitchen " " kunu tayi sannan ta soya sweet potato, tayi sauce tazo ta jerasu a dinning ta shige toilet don yin wanka " " kusan tare suka fito daga dakunan su suna hada ido suka sakarwa junansu murmushin da basu san sunyi ba" "Good morning ya safeer" "morning, how was your night" "Awesome" "Good "ya fada yana yin hanyar kofa " saurin shan gabansa tayi, ya safeer breakfast fa" "Zanyi a office shukra" "Haba ya safeer dan Allah kayi a nan da auren xaka dinga yin breakfast a office" "Shi mamaki ma ta basa sai yanzu tasan yana da auren? Ko da batasan a office din yake ba" "ki bari kawai ai daman a chan nake, so karki damu kinji ya fada yana wuceta" "kara shan gabansa tayi ta durkusa tana rokonsa yaci abinci a gida" "Tashi to naji zanci shknn" "Eh tace tana goge hawayen fuskarta, nan ta karasa dinning din taja masa kujera ya zauna sannan tayi serving dinsa" "sosai yaji dadin kunun dama shi yana so kawai dai dan Mamah batayi ne" "thank you very much shukra Allah ya miki Albarka" ya fada yana mikewa bayan ya gama " " Ameen nagode ya safeer Allah ya kiyaye hanya " " Ameen " " Yauma kamar jiya har gaban motar sa ta raka sa tajira ya fita sannan ta dawo cikin gida. "Abokina yane yau na ganka cikin nisha di kodai yau ka angonce" inji haiydar "Kai dan iska ne wallahi bawani angon cewa kawai dai ina jin dadin yadda shukra ta canja halinta yanzu" "To Alhamdulillahi ae haka akeso" " Kaga ni tafiya ma zanyi " " Gurin shukra inji haiydar yana dariya kasa - kasa " " Ban Sani ba " " Allah ya baka hakuri " " kai ni gidan Mamah zani mu gaisa kwana biyu banje ba " " ok bari muje tare nima na kwana biyu banje ba wallahi " " To shknn " " Daga haka suka fito suka kamo hanyar gidan Mamah " Shigowarsu yayi dai _ dai da shigowar miemie cikin gidan da gudun ta har tana ture haiydar kiris ya rage be fadi ba" "Safeer ne yayi saurin janyota yaja kunnenta da karfi wane ze cire shi" "Aiko sai ta fasa kara tana kiran Mamah" "zakiyi shiru ko sai na fasa bakin kukan, bakida hankali ko, bakisan kin girma ba kin wani shigo a guje kamar karamar yarinya, kuma kin ture Mutum bakisan ki bashi hakuri bako" "Allah ya baka hakuri to tafada tana hararar sa kasa - kasa. " Bani zaki bawa hakuri ba shi xaki bawa ya fada yana nuna mata haiydar " " Kusada haiydar taje tana hararar sa harda murguda baki Allah ya baka hakuri " " ji yayi ta masifan burgeshi "ya wani saki baki yana kallon ta, bemasan cewa safeer baya wajen ba sai da yaji su shida Mamah suna sauko wa daga stairs suna hira" "saurin saita kansa yayi sannan ya sauko daga kujera ya gaida Mamah cikeda ladabi" "5:20 suka bar gidan, haiydar yaso ta kara ganin miemie amma hakan be yiwu ba" "sai da suka shigo unguwan su haiydar sannan haiydar din yafara magana " Safeer wai yarinyar dana gani kanwar kace? "Ba tare da ya kallo shi ba yace Ehh ya akayi? " number ta nakeso ya fada yana dauke kansa " " Baki sake yake kallon sa da mamaki 'me zakayi da number ta kai kuma kar dai kace da Abdallah zaka hada su (kanin haiydar) "wani irin Abdallah kuma, da kaina dai" "Bangane ba" "sonta nake" "wani wawan birki safeer ya taka wanda har saida yabige get din gidan su haiydar sannan ya juyo ya kalleshi" "kace me safeer ya tambaya da mamaki" "nace sonta nake haiydar ya fada in an i don't care tone. " kaji kunya wallahi toni banida number ta kaje inda ka ganta ka karba " " kaga malam karka raina min hankali kan nace kabani number zanje har gidan na karba " yana gama fadar hk yafice mai a mota tare da buga masa murfin motarsa. " juyawa safeer yayi ya kama hanyar gidansa yana tunanin wae duk haduwar haiydar ya rasa wa ze so sai miemie" "Yau ma kamar jiya shukra ta shirya tsaf kuma ta yiwa safeer kyakykyawar tarba da abincin ta me dadi" "Da daddare safeer da shukra na zaune a palour wayarsa ce ta fara ringing, ganin miemie ce me kiran ya sashi kin picking" "wayar Mamah ta dauka ta kara kiranshi" "shiko ganin mama ce me kiran ya sashi picking da sauri" "ya safeer abokin nan naka daga gani sona yake, kaga yadda ya saki baki yana kallo na kuwa," "ke yaushe na fara wasa dake ne wae, ni kike fadawa wannan maganar ko miemie? zanyi maganin ki wallahi........... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/4, 1:32 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 1⃣3⃣ Washe gari " Ya safeer zan bika ka sauke ni a gidan Mamah na dade ban ganta ba" "To je dauko mayafin ki mu tafi sauri nake" "sai da safeer ya sauke shukra a gidan Mamah sannan ya wuce office" "Haiydar fa" Safeer ya tambayi Massinger'n sa "Be karaso ba" "ok nagode ya fada yana shigewa office dinsa. "sai 5:00 sannan safeer ya tashi a office, kai tsaye office din haiydar ya wuce dan yasan yana fushi dashi ne shiyasa ma yau bezo gurin saba" "Da sallama ya karasa ciki kafin ya zauna a kujeran dake facing dinsa" "Ciki ciki ya answer sallamar ba tare da ya dago ya kalle saba" "Haba haiydar me yayi zafi wae hk" "Ban Sani ba" "kaga in dai akan number ne kayi hakuri ni gsky bazan iya baka number yarinyarnan ba dan bana son rainin hnkl, ba a wasa da itama ya aka cika balle ana wasa da ita" "kaga malam karka samin ciwon kai ka gane, kace bazaka bada number ba nace zanje da kaina na karba ba shknn ba" "Shknn kam kaga yanzu gidan zanje sai kazo mu tafi ko" "Ba zani ba ai nima ina da motar ka tafi kawai in na gama zani da kaina" "Allah ya baka hakuri haiydar naga ka dauki abin da zafi" bari na wuce zanje na maida shukra gida ne, sai ka tawo. "Mtwsssssss haiydar yaja tsaki kamar wani mace ya cigaba da abinda yake" "Safeer be kara cewa komai ba sai fitar da yayi ya shiga motar sa ya nufi gidansu" "Kan cinyar shukra ya taradda miemie tanata zuba mata zance suna ta kyalkyala dariya abunsu" "zama yayi yana kallon su 'ke zo nan ya nuna miemie yana hararar ta" "kankame shukra tayi tana cewa Aunty kin ganshi ko ze dakeni dan Allah karki barsa kinji" " ME kikayi masa shukra ta tamvaye ta tana dago kanta" "Raba ido miemie ta shiga yi dan tasan batada gaskiya' nidai Aunty kawai ki bashi hakuri " " To tace sannan ta juya tana kallon safeer kafin ta ce "Ya safeer dan Allah kayi hakuri BAZATA sake ba" "Da kin barni na fasa bakin rashin kunya ae" "Daga haka sukayi shiru har ann miemie na jikin shukra kamar wata munafika sai leken safeer takeyi" "Mamah ce ke saukowa daga upstairs tana kiran miemie" "kasa ya sauko daga kujerar da yake ya durkusa yana gaida Mamah mama cike da ladabi" "Ashe ka shigo bakayi magana ba" "Yanzu na shigo ae, zuwa nayi na zane autar ki" "ME tayi kuma? " Rashin kunya tamin, daga nn ya kwashe yadda sukayi a waya jiya ya gaya mata " " Dariyar shirmen miemie sukeyi dukansu, banda safeer daya hade rai don shi bega abin dariya a ciki ba " " Se bayan sallar isha sannan su safeer suka koma gidansu. " " To haka dai rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin girmama juna amma babu abinda ya taba shiga tsakanin su" "Yau ta kama friday tun safe shukra kejin ciwon mara tana cijewa sai fargaba take kar ciwon yayi worst" 7:12pm safeer ya gaji da zaman falon da yake shi kadai, don duk yau bega shukra ba se yakejin ba dadi don ko ba komai sun saba " " Dakin ya tura ga mamakinsa sai ya ganta kwance tana juyi da hanzari ya karasa bakin gadon yana jero mata sannu " " Ya safeer dan Allah karka gayawa Ammii banida lafiya xata min fada wallahi " " Bazan fada mata ba shukra bari mu tafi asibiti " " A a bazan iya ba ka siyo min magani kawae mutuwa zanyi wallahi " " subahannalli "Bazaki mutu ba shukra bari na kira doctor ya duba ki " "wayarsa ya dauko ya kira, DR waheeda yasanta tun a secondry skul" "Hello waheeda" "Na am safeer ya gida " " lafiya kalau doctor " " Dan Allah idan bazaki damuba gidana nakeso kixo madam ba lafiya " " subahanallahi "yimin sending address di gidan gani nn zuwa" "Ba afi 40mints ba sai ga waheeda ta zo, kai tsaye bedroom din shukra ya kaita ya fito ya basu guri" " waheeda tabawa shukra magungunan da suka dace amma tana mamakin yadda matar aure take irin wannan ciwon " " Kasa hakura tayi sai da ta fita ta kira safeer ta hada su ta tambaye su "shin wani abu be taba hada su bane ko me? " kunya ce ta rufe su dukansu " " Itako waheeda masifa tai tayi musu kafin ta dawo nasiha "Haba shukra ya zaki hana mijin ki kanki bayan kinsan hukuncin yin hakan (haramun ne miji ya kiraki shimfidar shi kiki, mala'ikun Allah zasuyita tsine miki ne har ixuwa wayewar gari) ko kinason Allah yayi fushi dake ne? Ko kuma kinason mijin ki ya fara bin matan waje " " Da sauri shukra ta girgiza kanta alamar A a kafin ta fara magana a kunyace "To aini be taba cewa nazo dakinsa mu kwana ba" "Tana gama fadar hk tafice daga dakin da saurinta" "Hakane safeer" waheeda ta tambayeshi tana hararar sa " " Nan safeer ya kwashe duk yadda akayi akai auren da kuma zaman da sukeyi a gidan har i zuwa ynx " " sosai waheeda tayi mamaki takuma bashi shawara, kafin ya rakota har falour, nn suka sami shukra a zaune waheeda tayi mata sallama hade da karban number ta da niyyar bata shawarwari "Har bakin mota suka rakata sai da motar ta ta fita daga cikin gidan sannan suka dawo cikin gidan cike da kunyar juna........... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/5, 5:17 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Jealousy can die we are together insha Allah #endless luv Dedicated to miemie bie 😘 1⃣4⃣ "koda safeer ya kwanta tunani yayi tayi a ransa me shukra take nufi da tace "Ae shine be taba cewa muje dakinsa mu kwana ba" "ke nn hakan na nufin shukra ta shirya ne ko me? "indai haka ne to Alhamdulillahi" "Da tunanin nn bacci barawo ya kwashe shi. Washe gari bayan safeer ya tafi office, shukra tayi duk ayyukan gida tayi wanka sannan ta dawo palour ta kanta ta dau wayarta ta hau WhatsApp. " bakuwar number ta gani tamata sallama sai bata answer, bayan kamar 1mint akayi kara mata sallama sai ann ne ta answer. "Wa alaikisalam " " DR waheeda ce" "Eyya doctor yi hakuri banida number ki ban ganeki wlh " " Bakomai shukra ya jikin " " jiki Alhamdulillahi " " Bayan sun gama gaisawa ne waheeda tashiga yi wa shukra nasiha kamar yadda ta daukar wa kana alkawari " " sosai nasihar ta shiga shukra dan sai godiya takewa waheeda ". " Waheeda ta kuma yi adding shukra a wani Grp na matan aure domin tasan zata karu sosai " " Bayan da sukayi sallama shukra kwanciya tayi tana tunanin yadda zata bullowa al amarin daga hk bacci ya kwashe ta "Knocking din da ake a kofar palour ne ya tadata daga baccin da take,". "A nutse ta karasa bakin kofar ta bude, matashiya ce bazata wuce taba ko a shekaru take mata sallama da fara 'arta. " Answer mata sallama tai sannan suka shiga palour suka, shukra ce ta mike ta kawo mata drinks da snacks kala - kala sannan ta dawo ta zauna" "Sunana ibtisam, nice makociyar ki" "Wow nice to meet you ibtee" "nice to meet you too" "Ina fatan za a min afuwa ni ya kamata ace nazo ba keba" "Bakomai wallahi komai nufin Allah ne ae" "ni kuma sunana shukra" " Nice name" "Thanks shukra ta fada tana daukar yarinyar ibtee, kasancewar shukra tana son yara sosai " " Hira suka shiga yi dan da alama jinin su ya hadu sosai " " Ibtee ce ta mike ta dauki yarinyar ta " " To shukra ni na tafi sai kuma kinzo ko" "To ibtee nagode sosai insha Allah gobe zaki ganni ta fada lokacin da suka fito waje" "Har bakin gate shukra ta raka ibteesam sannan ta dawo gidan donyin girki" "Haiydar ne ya shigo gidan su safeer da sallamar ma ya taradda Aysher a palour suna karatu itada miemie, har kasa Aysher ta gaida haiydar amma miemie ko a jikin ta cigaba ma da abinda take tayi" "Kusada miemie yaje ya zauna yana tambayar ta ya exams" "Sai a nn ta dago ta kalle shi, " Lah Aunty aysher Kinga wanda zan aura wanda na baki labarin sa rannan, sai ta dawo kan cinyarsa tana mishi surutu shi kuma sai biye mata yake suna kyalkyala dariya " " Itadai Aysher bata ce komai ba sai kallon su take yi dae " " Sosai yaji miemie na kara shiga ransa kasan cewar miemie me farin jini duk wanda ya ganta sai ya sota kawayenta harda manya masu yaya ma kai har kawayen mamah ma kawayenta ne, takanas suke zuwa gurinta " " Sallamar safeer ne ya katsewa miemie surutun ta " " Da mamaki safeer kebin haiydar da kallo shiko haiydar ko ajikinsa juyawa ma yayi suka cigaba da hirar su da miemie " " Haiydar wae dama nan zaka zo safeer ya tamvaya" "Eh ya answer shi a takaice" "Amma ae baka fada min ba" "To ae yanzu gashi nan mun hadu ko" "Buh atleast ae ya kamata ka fadamin ko" "Kaga malam karka samin ciwan kai dama haka akace duk inda zani sai na nemi ixinin ka kikuwa" "Ko dan nazo gidanku shine ka wani tsare ni da tambayo yi hk" "Nidai bance ba, Allah ya baka Hakuri amma" "Ameen" "Aysher ina mama me safeer ya tambaye ta " " Mamah taje unguwa amma bazata dade ba " " Nikam gaskiya sauri nake kya fada mata nazo " " Tom insha Allah tace mishi yayinda yake fita " " sannu da zuwa ya safeer inji shukra da tun dazu take zaune tana jiran shigowar sa, ta miki hannu ta karbi brief case dinsa ta wuce dakinsa shima ybi bayan ta" "Yau shukra da kanta ta hadawa safeer ruwan wanka ta kuma fito masa da kaya ta feshe su da perfume sannan ta dawo palour ta zauna" "Bayan safeer ya fito ne shukra ta kawo musu abincin nan palour ta shiga serving dinsa" "Kai shukra ae da baki wahalar da kanki ba keda baki lafiya" "Bakomai ae hakki nane(niko nace 🤔😏da bakisan cewa hakkin ki bane sai yau). " Haka dae suka kammala cin abinci kowa ya shige dakinsa " " Haka dai rayuwa taciga da tafiya har ranar da shukra ta gama mensis" "Da daddare suna zaune a palour su biyun bayan sun kammala cin abinci, wayar safeer ce tayi kara aiko da hanzarin sa ya daga" "Hello babyna ya kike? "Gaban shukra ne yayi mummunar faduwa jikanta ya hau rawa" "Ok kina son gani na? To ganinan zuwa ynx" "ME zan tawo miki da? " To ganinan daga nn ya kashe wayar ya mike ba tare da ya kalli shukra ba ya dau car key dinsa ya fice da sauri" "Ae safeer na fita shukra ta fasa ihu, kuka take baji ba gani a nn bacci ya kwashe ta batare da taga dawowar sa ba................. SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/6, 9:29 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 1⃣5⃣ 10:40pm safeer ya shigo cikin gidan, shukra ya gani kwance a palour kamar zai tasheta sai kuma ya fasa ya mata addu 'a ya tofe mata jikinta sannan ya wuce dakinsa " ASUBA " Karar bude kofar da Safeer yayi ne ya tashi shukra daga baccin da take, suna hada ido ta wani dauke kai ta shige dakinta, shima tabe baki yayi yayi gaba abinsa kasancewar an fara kiran sallar asuba " " 6:50am shukra ta gama shirinta tsaf ta dauki car key dinta ta fito palour janye da trolley dinta " " Fitowar shukra yayi dai - dai da fitowar Safeer daga dakinsa, ko kallo be isheta ba ta wuce abinta ta fita daga palour 'n" "SHUKRA ce ta shigo cikin gidansu a kitchen ta tayadda Ammii tana hada breakfast Kawai sai ta sa mata kuka sosai " " A rikice Ammii take tambayar ta wani abun aka mata ne? Ko wani abu ya samu Safeer, Amma ko kulata batayi ba saima cigaba da kukan ta da tayi" "Ammii ma bata ce komai ba ta cigaba da aikin ta, zuwa can kukan shukra ya fara cimata rai, batamasan sanda ta daka mata tsawa ba, "Dalla malama kin cikamin kunne da kuka kinajina, in kukan kike sha'awa ki fita ki bani guri kije kiyita yi tunda bakida abunyi, tun dazu sai tambayar ki nake me akai miki kinmin shiru " " Ammii Aure fa zai yi " " Waye zeyi AUREN wae Ammii ta tambaye ta? "Ammii ya safeer ne zeyi Aure, jiya a gabana tayi mishi waya wae tana son ganin shi shine ya tafi ya barni, tana kaiwa nn ta sake fashe wa kuka sosai " " To sai me aini wallahi ya burgeni, haushin ma daya bani baze wuce rashin sakin ki da beyi ba, Ae naso ma sakin ki yayi ya huta tunda ke bakida kirki bakya jin mgn kin raina mu ko " " Ammii wallahi shine...... "sai kuma tayi shiru ta cigaba da kukan ta " Shine me Ammii ta tambayeta a fusace" "Komai bata ce ba sai ma kara sautin kukan ta da tayi " " Tashi ki fita ki bani guri kafin na kwada miki mari wallahi " " Tashi tayi ta fita tana cigaba da kukanta, kusan chin karo sukayi da Daddy. "Ke lafiyar kuwa? " " Daddy ya Safeer ne zai kara Aure " " To shine me "? Daddy ya tambaya irin ko ajikinsan nn" "Ae Wallahi kadan kika gani, badai ke kince ban isaba, Har Safeer yamin biyayya ke ki kasa min ko? Ae duk abinda kike ina sane dake zuba miki ido kawai nai naga iya gudun ruwanki gashi tun ba 'aje ko inaba kin fara kuka da idanunki" "Shigowar Safeer ne ya katsewa Daddy maganar da yake, ya durkusa har kasa suka gaisa da Daddy Sannan Ammii " " Yawwa Safeer yanzu nake shirin kiranki ae sai gashi kazo "Inji Daddy " Eh Daddy naga shukra ta tawo gida ne kuma ni ba wani abu ne ya hada muba, lafiya kalau muka rabu jiya amma yau naga ta dauko Trolley ta tawo " " Eh wae zuwa tayi dan shashanci tana kuka wae zakayi Aure "Ammii tace tana hararar shukra. " Wace yarinyar ce zaka aura? Daddy ya tambayi Safeer " " Sunkuyar da kansa yayi yace a office dinmu take " " Masha Allah "Ni da kaina zan nema maka aurenta kaji dan Albarka, tashi ka tafi office karka makara kaji" "To kawae yace sannan Y mike yana satar kallon shukra ita ko sai zabga masa harara take wane idonta zai fado kasa " " Kuma ki tashi ki dauki kayanki ki koma gidan mijin ki kafin in bata miki rai wallahi, Daddy ya fada a fusace" Ko motsi shukra batayiba sai kukanta take baji ba gani " " Zaki tashi ko sai na kwada miki mari " " Jiki ba kwari ta mike taja trolley ta fice daga palour 'n " " Kamar kullum yau ma tayi girkin ta bayan ta gama ne tayi wanka ta tsara kwalliya tanaso taje gidan Ibtee amma kuma bata tambayi Safeer ba gashi batada number shi balle ta kirashi ta tambaye shi" "Tana nn zaune Safeer ya shigo gidan da sallamar shi " " Kamar bazata Answer ba sai kuma ta Answer, ta mike da kyar ta karbi briefcase dinsa da ledar daya shigo dashi ta kai komai mu hallinsa, ta dawo ta zauna abinta" "Yau shukra sai wani share Safeer take yana bata labarin office, shiko sai nunawa yake kamar bema san tanayi ba ya cigaba da bata labarin har zuwa lokacin bacci a nn ne kowa ya tashi ya shige dakinsa" "Yau kwana 3 kenan Safeer na fita zance, abin na matukar damun shukra, Amma idan ta tuna cewa itace ta bata rawarta da tsalle ta kanyi kuka, in ta zauna ma sai dai tayita istigfari tana rokon Allah ya yafe mata " " Yau ta kama friday Safeer ne ya fito cikin shirinsa na zuwa office shukra ya tarar a palour idonta duk ya kumbura dan kukan da tayi " " Ya safeer An tashi lafiya? "Lafiya kalau shukra " " Wani abun ya farune naga kina kuka? Ko kin gaji da zama danine? "Girgiza kai tashiga yi tana goge hawayen da ke gangarowa daga idonta tana kuma kokarin hadiye kukan dake son subuce mata" "Ko gida kike so ne? "Eh ka kaini gida gurin Ammii ta fada tana fashewa da kuka " " To naji zan kaiki amma ki bari sai na dawo daga office " " Tom " Amma ina so in shiga makota gurin Ibteesam wadda na gaya maka tazo rannan" "Tom shknn ki gaishe ta "sai na dawo " Adawo lpy " " Allah yasa daga nan ya fice daga cikin gidan "Sallamar shukra ne yasa Ibteesam fitowa daga bedroom ae tana ganin shukra ta fara murna tana mata sannu da zuwa " " Bayan Ibteesam ta cika shukra da drinks suka fara hira, sosai yarinyar Ibtee ta shiga ran shukra kamar ta kwace ta ta tafi da ita, sai addu 'a take itama Allah ya kawo mata masu Albarka " " Sai gurin 03:00pm sannan sukayi sallama shukra takoma gidanta " " Sosai taji dadin zuwanta gidan Ibtee kasancewar ta gaji da zaman gidan ita kadai, shiyasa ta matsu ayiwa su miemie hutu tazo mata" "To Safeer ya kai shukra gida Amma Ammii bata wani sakar mata fuska ba, sama sama take kulata, sai dare sannan Safeer yazo ya dauketa suka tafi " " Abin duniya fa ya ishi shukra ganin cewar bikin Safeer ya matso sosai sai wani sabga yake yana wani rawar kai, wani karin abin takaichi ma shine Safeer daya karbo kayanda zai sa ran DAURIN AUREN dakinta ya kawo ya ajiye " " Yau saura sati biyu bikin Safeer saboda hk ya kawo wa shukra invitation cards ko zata gayyaci kawayenta............... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/7, 2:03 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 1⃣6⃣ " Gajiya Safeer yayi da mikawa shukra invitation cards din ya ajiye mata a bedside drower ya fice daga dakin" "Kuka kawai ta saki sannan ta private tashi ta dauki envelop din daya kawo mata ta wulla ta bayan gado ta kwanta ta cigaba da kukanta " " Kukan da shukra tayi ne yasa ta ciwon kai sosai, Safeer ganin duk yau bega Shukra ba yasashi zuwa dakinta duba ta " " Kwance take a kan bed tana kallon sama yayinda hawaye ke gangarowa daga idanunta " " Bakin gadon yaje ya zauna tausayin shukra fal zuciyar sa amma ya dake ya fara tambayar ta ko wani abu ne yasameta " " Kaina kemin ciwo "Tace a takaice " Sannu Allah ya kara sauki, ko zamuje hospital " " Ko kallo ma be isheta ba ta juya mai baya saboda wani mugun haushin sa takeji yanzu " " Gajiya yayi da zama ya mike ya fice, be dade ba kuma ya dawo dauke da leda a hannunsa ya ajiye a bedside drower sannan ya fice ya dauko bottle water da glass cup ya dawo ya zauna a kusa da ita, ita dai bata ko kallo shiba " " Ruwan ya zuba mata a cup sannan ya balla maganin ya mika mata " " karbi kisha kinji " " To tace sannan ta karba ta kora ta koma ta kwanta " " Shima ficewa yayi a dakin ya wuce dakinsa don yin wanka " " Kwana uku ne kawai ya rage ayi bikin safeer, Shukra ta rasa yanda zatayi jitake kamar ta kai kanta gurin Safeer amma tasan ko zuwa tayi ma baze kulata ba tunda Aure zeyi " " Safeer ne ya shigo dakin shukra dauke da trolley, tsaye take tana ninke abin sallah kasan cewar idar da sallahr ta kenan ya shigo " " Shukra kayan fitar biki na kawo miki " " Harara ta watsa masa sannan tace banaso ka hadawa Amarya " " Dariya yayi sannan yace ae Amarya an dade da kai mata nata " " Kai ya shafa kuma wannan sannan ta juya ta shige bathroom ta barshi nan tsaye " " A na gobe daurin aure safeer ko shigo gidan beyiba tun fitar da yayi da safe, Shukra kuwa sai kuka take tana data Sani, ko bacci ta kasa sai jira take ya shigo " " Haka ta hakura da jiransa ta kwanta tana istigfari har bacci barawo ya kwashe ta " WASHE GARI " Tun asuba Shukra ke jiran Fitowar Safeer tana zaune a palour ta daura kafa daya kan daya tana wani cika tana batsewa " " Daga shi sai singlet da short nikker ya fito har ya wuce ta ya dawo yana mata wani shu'umin murmushi " " Shukra cute sannu da zama, naga kin tashi da wuri ko naki taron zakiyi ne bazakije na Mamah ba" "Harara ta watsa masa kafin tace Bansaniba " " Allah ya baki hakuri shukra cute yace yana dariya kasa - kasa " " Mtwsssssss taja tsaki kafin tace munafiki kawae " " Tana nn zaune ya fito daga kitchen hannunsa rike da cup ya zauna a kusa da ita yana shan tea hankali kwance " "SHUKRA yi sauri ki debo min kaya na dana ajiye a dakin ki sauri nake wallahi kinsan da safe za a daura AUREN" "To ina ruwa na " " Babu Amma dae debo min kayana wanka kawai zanyi mu tafi, ya fada yana mikewa yayi hanyar dakinsa " " Dani na ajiye maka kayan, yarda ka ajiye haka zaka zo ka dauka wlh taja tsaki sannan itama ta shige dakinta " " Fitowar Safeer daga wanka kenan yaga Shukra bata debo mai kayansa ba, ae kuwa kai tsaye dakinta ya nufa " " Direct wardrobe dinta ya nufa ya shiga cire kayansa, A nn gurin ya shiga sa kayan sannan ya dauki perfume dinta ya feshe jikansa dashi " " Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubowa shukra ganin cewa da gaske ne fa bikin Safeer yau " " Shiko bema kula da ita ba ya fice daga dakin cikin sauri " " Fitowar Safeer yayi dai - dai da fitowar Shukra tana ganin sa ya fito yana gyara hularsa ta fasa masa kuka " " Zaro idanu yayi ya karaso gurinta donjin me akayi mata " " Aiko yana karasowa gabanta ta fada jikinsa ta rungume shi gam - gam kamar wata zata kwace mata shi " " Cikin kuka sosai ta fara Magana "Ya Safeer dan Allah kayi hakuri karka kara Aure na tuba bazan kara ba nayi maka Alkawari yima ladabi da biyayya, Dan Allah ka tausaya min wallahi bazan iya zama da kishiya ba tana kaiwa nan ta kuma fashe wa da kuka ta kara kankameshi a jikanta" "Hakuri zakiyi Shukra kishiya dai sai anyita kuma maganar yafiya ni na dade da yafe miki, so kiyi hakuri yanzu ki barni na tafi it's Already time Kinga sunata kirana ya fada yana janyeta daga jikinsa" "Kara fadawa jikinsa tayi tana kuka me tsuma zuciya, shi kansa Safeer sai da ta bashi Tausayi dakewa kawai yayi ya tureta sannan yace "Bari naje inna dawo zamuyi magana kinji " " Gani kawai yayi shukra tayi baya jikake tim ta fada kan kujera " " Cikin hanzari Safeer yayi kan shukra jiki na rawa ya daga ta sai motar sa " " Gudu kawae yake hankali a tashe sai emergency na" Aminu kano ", cikin hanzari yashiga da ita likitoci suka rufar mata shikuma yayi waje" "Wayarsa ce ta shiga ringing kamar baze dauka ba sai kuma ya dauka hade dayin sallama " " Daga daya bangaren akace kana ina ne wae? Kai kadai fa ake jira " " Kana jina haiydar yanzu haka ina hospital shukra ba lafiya so kuje kawai in daura sai ka fadamin " " Tom shknn " " Yawwa Haiydar Nagode saina jika " " Daga haka ya kashe Wayarsa ya cigaba da kaiwa da komowar dayake a gurin" "Wata nurse ce ta fito aiko da sauri ya nufeta "Ya jikin Shukra? "Meya sameta? "Ta farko? Ya jero mata wadannan tambayoyin a tare" "Calm down ok" Yanzu dai mun bawa Shukra Bed so ya kamata ka kira azo daga gida" "To Aini baki fadamin abinda ya sameta ba" "Ka fara kiran gida tukun Doctor ze maka bayani, tana gama fadar hk ta wuceshi" "Mamah ya fara kira sannan Ammii ya musu bayanin inda suke sannan ya nufi office din Doctor " Sallama ya masa ya Answer sannan ya nuna masa sit ya zauna" "Doctor ne yafara masa bayani kamar hk "Wato jinin matarka ne yau sosai sakamokon firgita da tayi Amma insha Allah komai ze daidaita bari na rubuta maka magunguna kaje ka siya kafin ta tashi " " Da kyar ya iya cewa nagode Doctor sannan ya karbi card din ya fice da sauri " " Mamah da Miemie ne suka fara zuwa sannan Ammii da Areef, Alokacin ance za a iya ganin Shukra " " A tare dukansu suka shiga banda Safeer daya tafi gida debowa Shukra kaya ".............. SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/8, 6:24 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 1⃣7⃣ "Shukra ba ganin su Ammii sun shigo ta fara kokari tashi, Mamah ce ta riketa tana mata sannu " " Ammii dan Allah ku taimaka min ku bawa ya Safeer hkr karya kara Aure wallahi na chanja hali na, kuma bazan kara rufe masa kofa ba" "Mamah ce tayi saurin rufe mata baki tana jero mata sannu " " Yi hakuri kinji Shukra Kinga Doctor yace ki dena damuwa ki kwanta ki huta kinji " " Kuka kawai shukra tasa don ita tayi tunanin Mamah zata ce an fasa AUREN amma sai taji shiru " " Da sallama Safeer ya shigo cikin dakin hannunsa rike da trolley wanda ya debo kayan shukra a ciki, bayan sun gaisa da su Ammii ne ya nemi guri ya zauna " " Kokarin tashi shukra keyi Amma Ammii ta hana hakan, kuka take tayi tana kallon Safeer shima kallon ta yake cike da tausayi " " Ya Safeer dan Allah ka rufa min Asiri kamar yadda Allah ya rufa maka karka kara AUREN nn wallahi bazan iya zama da kishiya ba bana sonta bana kaunar ta" "Ammii ce tayi saurin doke bakinta tana hararta" "Karki so kishiyar to kinsan bakya son kishiyar kike abinda kike " " Ammii wallahi na dena kuma ki tambaye shi ta fada tana kara fasa wani kukan " " A a Ammii ba hk ake ba gsky ki dena mata fada Kinga batada lafiya, hawan jini ae ba wasa bane "inji Mamah " zuwa wannan lokacin kukan shukra ya fara ciwa Safeer rai don Shukra tsakani da Allah take kukan hakan ne yasa Shi saurin tashi ya fita daga dakin " " Mamah ce ta dawo kusa sa Shukra tana ta lallabata taci Abincin da Aysher ta kawo dazu" "Mamah bazan iya ci ba mutuwa zanyi wallahi, dan Allah ki bawa Ammii, Daddy da ya Safeer hakuri kinji ta fada tana kara rusa kuka wane shi aka aiko ta" "Da daddare Mamah cewa tai ita zata Zauna da miemie, Ammii ta tafi gida tana ganin kirki irin na Maman Safeer " " Washe gari da safe Aysher ta kawo abinci sannan ta wuce School " 9:00am Safeer da Haiydar suka shigo duba Shukra, Gaisawa sukayi da Haiydar sannan ya fita dama Mamah da Miemie sun tafi gida don yin wanka saboda haka dakin ya rage daga Safeer sai Shukra" "Shiru ne ya ratsa dakin ba wanda ya cewa dan uwansa ci kanka, gajiya Shukra tayi da kallon da Safeer ke mata ta mike ta shige toilet abinta " " Shima Safeer mikewa yayi yaje ya samu Haiydar a waje suka fice daga Asibitin ma gaba daya " " Ammii ta riga Mamah zuwa saboda haka ta samu damar yiwa Shukra tatas " " Sosai Shukra take kuka tanajin inama zata iya cewa Ammii "Ni na shirya basa kaina shine be nemeni ba" Amma bazata iya ba, Hakan ya sata ci gaba da kukanta kamar an aiko ta tanajin inama mutuwa tazo ta dauketa a wannan lokacin ta huta da bakin cikin da take ciki a yanzu " " Wasa - wasa sai da Shukra tayi one week a Asibiti sannan akayi discharging dinta, Mamah ce ta dage sai ta tafi da Shukra gidanta saboda tana kallon yadda Ammii takewa shukra kamar ba ita ta haifeta ba " " Haka dai suka tattara suka koma gidan Mamah, sosai Shukra take samun kulawa gurin Mamah da Aysher, Miemie ma ba a barta a baya ba don Sosai take damun Shukra da surutun ta kuma itama Shukran tana jin dadin zama dasu, mutanen kirki yadda suke mata ko safeer basayiwa haka " " Sosai mutanen Mamah da Ammii suke zuwa duba Shukra, Abokin Safeer ma sunzo, Haiydar ko dama kullum sai yazo kodan yaga sahibarsa (Miemie) " " Kawayen Miemie duk sunzo dan gida - gida tarinka zuwa tana fada musu azo a duba Auntyn ta batada lafiya, in ba kazo ba kuwa zuwa take ta tawo da kai " " Sati biyu Shukra tayi a gidan Mamah sannan ta koma gidan Ammii kasancewar next week zata koma gidan Safeer " " Sosai Safeer ya gyara gidansa har furniture's din Shukra sai da ya changer mata, gida dai ya hadu iya haduwa dan da mukaje nida Miemie cewa nayi bazan tawo ba(lols) "Ammii ta dage sosai take gyara yarta dan ta fahimci ba abinda ya taba shiga tsakanin su da safeer " " Yau saura kwana 3 Shukra ta koma ji take gaba daya batasan komawa tunanin taya zata soma zama da kishiya " " Yau ta kama wednesday kuma tun 7:00pm Safeer yazo tafiya da Shukra kasancewar yau zata koma, Kuka take baji ba gani ko a mota bata kalleshi ba sai kukanta ta take har suka karasa gidan............ SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/8, 10:52 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Just to fulfilled a promise as you win the game, Am so grateful that you are following my novel 😘 Dedicated to miss softie 1⃣8⃣ "Cike da fargaba Shukra ta fito daga motar Safeer, Bakinta dauke da addu 'a ta nufi cikin gidan " " Baki ta saki tana kallon yadda gidan ya changer yayi mata kyau wlh sai taji zuciyarta tayi sanyi kamar bawani abu dake damunta, Amma data tuna wae su biyu ne cikin gidan sai taji wani bakin ciki ya mamaye zuciyarta " " Dakin ta tashige nanma sai da tasha mamaki don ya hadu iya haduwa, sai takejin inama ita kadai ce a gidan da tayi amfani da damarta ta faranta ran mijin ta yadda ya faranta mata " " Wanka shukra tayi tayi sallah'r isha ta kwanta zuciyar ta cikeda tunane - "tunane tana so ta fito palour tayi kallo dan sam batajin bacci amma kuma tana fargaban haduwa fa Amarya haka dai bacci barawo ya kwashe ta a gurin" "Asubar fari Shukra ta farka, mikewa tayi bayan tayi Addu 'ar tashi daga bacci ta nufi toilet tayi alwala tazo tayi nafila ta Zauna tana addu' a kasancewar ba a tada sallah a masallaci ba " " Koda ta idar da sallah zama tayi tana lazimi tanaso ta fita ta gyara gidan ta daura breakfast amma tana tsoron ganin wata a cikin gidan ta " " 10:14am tayi shahada ta fito daga dakin ta fitowar ta yayi dai dai da fitowar safeer daga dakinsa, har kasa ta durkusa tana gaidashi tana kuma kokarin mayarda kukan dake son subuce mata " " Kin tashi lafiya Shukra " " Lafiya kalau " " Ya karfin jikin " Alhamdulillahi na samu sauki ae" "To masha Allah " " Har ta wuce sai kuma ta dawo Ya Safeer ina Amaryar? "Za tazo ku gaisa ae karki damu " " Durkushewa tayi a gurin tana kuka mai tsuma zuciya " " Ganin hk safeer yayi saurin zuwa ya daga ta ya rungume ta tsam a jikansa, "Yi hakuri Shukra nasan ni Mai lefi ne a gurinki, A sanadiyya ta kika kamu da ciwon hawan jini " " Kiyi hakuri nayi hakan ne dan na gwadaki naga ko kina sona ko bakya sona, Ashe dai kina sona " " Amma ba maganar Aure " " Batasan sanda ta saki ihu ba ta kara kankameshi a jikin ta " " Ya Safeer dan Allah ka kara gayamin bakayi aure ba, kacemin wasa kake min " " Shukra wasa nake miki banyi wani Aure ba wallahi " " Sakinsa tayi taja hannunsa suka zauna akan kujera " " Ya Safeer bikin wa akayi to " " Bikin Abokinmu ne Tareeq, a office dinmu yake" "To invitation cards din fa da kaka kawo min zuwa kayi akayi maka su? "A a na Tareeq dinne fa na kawo miki, baki ganiba " " Sai a nan ta tuno hakan ta ta fara dariya kafin tace, Ae kana ajiye wa ka fita na tashi na jefa bayan gado " " Dariya safeer yake hadda rike ciki yace "Har na tuno Shukra a gadon Asibiti tana cewa "Ya safeer dan Allah ka rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa maka karka min kishiya " " Dukan wasa ta fara kai masa yana dariya yana karewa, Ae ko ta sakar masa kukan shagwaba 'ni wlh ka dena bana so' " " Janyota yayi zuwa jikansa yana lallashinta " " Yi hakuri Shukra cute, dena kuka kinji yan mata na, Safeer naki ne ke kadai Shukra " " Na miki Alkawari baki kulawa, Namiki Alkawari bazan miki kishiya ba, A gurina mazaunin mace "HUDU" kike "Kara lafewa tayi ajikinsa kafin tafara magana " " Lokacin da akayi auren nn bada son raina akayi shiba, shiyasa na dinga horaka ta hanyar rufe maka kofa " " A hankali na gane AUREN BAZATA ALHERI NE" "Ina kara rokonka da ka yafemin lefina a gareka " " Baki min lefi ba shukra we only mis understood each other and now we burry da hatchet " " Haka dai sukayita ga yawa juna su sirrin zukatan su (☹yan duniya ashe suna son junansu gulma ta hana su bayyanawa) " " Haka suka yini a gidan basuje ko ina ba suna ta hira kamar dama can suna shiri " " Safeer sai wani farin ciki yake yau fa shi ango ne " " Da daddare safeer ya je ya siyo musu kajin amarchi, ya dawo ya samu shukra tana jiran shi " " Bude mata hannayensa yayi bayan ya ajiye ledar daya shigo da ita, Aiko da saurinta taje ta fada jikinsa suka rungume junansu suna masu jin kaunar junansu" "AS YOU START YOUR NEW LIFE TODAY I WISH YOU ALLAH 'S BLESSING, MAY GOD BLESS YOU WITH BEAUTIFUL CHILDS, MAY GOD PROTECT YOU FROM EVERY EVIL DEED" SHUKRA & SAFEER 👌🏻 SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/9, 5:54 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 1⃣9⃣ "Jan Shukra Safeer yayi Ya zaunar da ita a tsakiyar palour sannan ya wuce kitchen ya dauko plate, fork, and knife ya dawo ya ajiye a gaban ta, sannan ya dauko ledar daya shigo da ita ya juye musu kajin" "Knife yasa ya yanka sannan ya dauka da fork ya kai bakin shukra" "Cike da jin kunya ta kawar da kanta gefe guda, sannan tasa wani fork din ta dauka ta fara ci " " Karki ce min kunya na kike ji Shukra " " Komai bata ce ba sai ma sunkuyar da kanta da tayi, dan duk batajin dadin yadda ya kafe ta da ido" "Shiru sukayi suka ci gaba da cin abincin su zuciyoyin su cike da nishadi, duk daga idon da shukra zatayi sai sun hada 👀hakan yasata mikewa kawae" "Karki ce min kin koshi " " Eh na koshi ta fada tana turo baki gaba " " Tab ai biki isaba kefa Amarya ce" "Amarya ko Uwargida 3 month wasa ne " " Koma dai menene dawo ki kara "Ya fada yana kokarin kawar da waccan maganar" "Seriously am satisfied ta fada tana bin hanyar dakin ta " " Shima mikewa yayi ya kai plate din kitchen sannan ya shige dakinsa donyin wanka " " Fito wa shukra tayi daga wanka ta karasa jikin wardrobe dinta ta fito da sabon sleeping dress ta saka, sannan ta dawo jikin dressing mirror ta shafe jikin ta da lotion ta fesa turare sannan ta hau gado donyin bacci " " Shima da ya fito jallabiya yasa coffee colour ya shafa cream sannan ya feshe jikansa da turare " " Zama yayi a gefen bed ya dauko system dinsa ya daura kan bedside drower ya fara aikin sa, construction na company yakeyi, wani balarabe ne ya basa kwangilar company 'n kuma nn bada dadewa ba ze tafi don ayi komai akan idonsa " " Sai 12:00pm safeer ya kammala construction din nan, kashe system din yayi ya mai data cikin jaka sannan ya mike ya kashe globe din dakinsa ya fice" "Dakin Shukra ya nufa da sallama ya shiga sai dai ba answer kasancewar Shukran baccinta yayi nisa " " Globe din dakin daya kunnan ne ya farkar da Shukra tamike tana salati " " Karasowa yayi ya hau kan bed din sannan ta jawo ta jikin sa " " Nokewa ta shiga yi dan ita tsoro take ji, fahimtar hakan ne yasashi fara mata magana " " A a Shukra cute kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki kawai dai bazan iya kwana ni daya a dakina bane shine nazo tayaki kwana " " Jitayi kamar ta daura hannu aka tasa ihu, tana son Safeer tana kuma so ta faranta masa, tanajin zata iya jure duk wani radadi indai hakan ze se sashi farin ciki " " ME yasa Bazai karbi hakkinsa ba a wuce gurin kawai? Sai taji tana data sanin nokewar da tayi, ita kuma anata ganin ae jan ajine tunda mace dai da jan aji aka santa " " Ji take inama zata iya cewa ya safeer a shirye nake "Amma BAZATA iyaba" "Haka dai suka kwanta rungume da juna zuciyar ta na mata zafi, Amma tasan komai lokaci ne in lokacin yazo ko bataso sai anyi " " Da Asuba Safeer ne ya fara bude ido kasancewar dama sama - sama yayi bacci yau, A hankali ya zare Shukra a jikinsa ya kwantar da ita sannan ya shige toilet don yin alwala " " Ko da ya fito bata farka ba saboda haka ya karasa kan bed domin tashin ta " " Hannunta na dama ya kama yasa a bakin sa yana tsotsa a hankali, sun kai kusan 2 mints a haka kafin Shukra ta fara bude idonta a kansa " " Yana ganin ta bude ido ya mikar da ita zaune yana karanto mata addu 'ar tashi daga baccin " " Bin addu' ar tashiga yi har suka kammala sannan ta mike ta yi hanyar toilet din " " Yi sauri Shukra kiyo alwalar kizo muyi jam 'i "To tace sannan ta shige toilet zuciyarta cike da farin cikin kulawar da Safeer ya soma bata " " Koda ta fito tarar wa tayi ya fito mata da hijab ya kuma shimfida musu abin sallah " " Karasawa tayi ta dauki hijab din ta hau abin sallah shi kuma ya soma ikama " " Koda Su kazo Sujjadar karshe Safeer ya dade yana musu addu 'ar samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a sabuwar rayuwar su" "Bayan sunyi addu' a ne Shukra ta mike zata fita " " Kamo Hannunta yayi ya jawota ta fada jikinsa ya rungume ta hade da dora kansa akan nata " " Ina zaki kuma? Ya tamvaye ta murya can ciki " " Duk sai taji ya kashe mata jiki da kyar ta iya cewa ' breakfast zan hada mana " " No ki bari sai zuwa 10:00am in mun tashi a bacci kyayi kinji ya fada yana shafa smooth cheek nata " " Office dinfa ta tambaye shi a kasalance " " Bazani ba kin manta ni Ango ne " " Nan ta fara kokarin tashi daga jikinsa, yasake mai data ya kwantar " " Ina zakije ne wai? Ko toilet zaki "ya rada mata a kunne" "ji tayi wani abu na yawo a jikanta jin hucin bakinsa a kunnenta " " Bacci zanyi ta bashi Answer da kyar " " To kiyi kwanciyarki zansa kiyi bacci kinji " " Komai bata ceba sai kara lafewa datayi a jikinsa hade da lumshe ido " " Bayan ta ya shiga bubbugawa a hankali kamar yana son yasa baby bacci, A hankali baccin ya kwasheta " " Saukar numfashinta daya fara ji a hankali ne ya tabbatar masa tayi bacci, Don haka ya je ya kwantar da ita a tsakiyar bed din shima ya kwanta ya rungume ta sai bacci " " sai gurin 11:00 suka farka Shukra tayi hanyar kitchen shi kuma ya nufi dakinsa " " Breakfast me rai da lafiya ta hada musu sannan tayi wanka, Tayi shirin ta cikin wasu English wears riga pink, skirt blue tayi parking gashinta da pink ribbon dama shukra bata son kitso a rayuwar ta " " Pink din hijab tasa karami tasa blue slippers ta fito palour a gurguje, Suna hada ido ya sakar mata murmushi, murmushin itama ta sakar mai sannan ta wuce dinning ta kwaso breakfast din ta kawo palour........... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/10, 5:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 💞 2⃣0⃣ "Cikin plate daya ta zuba musu abincin, haka ma tea a cup daya ta hada musu, Haka sukaci Abincin Safeer ba bawa Shukra Labarin Haiydar da Miemie sai dariya take kyalkyalawa abinta, shiru yayi yana kallon yadda take dariyar bilhakki Sai yaga ta masa kyau, ita ko jin shirun yayi yawa yasa ta dena dariyar tana kallon shi " " Meye kake kallo na "Ta fada tana murguda masa baki" "Shi abinma dariya ya basa kamar wata karamar yarinya har da murguda baki " " Shiru sukayi dukansu har suka kammala cin Abincin, sannan Shukra ta kwashe kayan ta kaisu Kitchen ta fara wanke wa " " Jin shirun da Safeer yayi ne yasashi bin Shukra kitchen, Tana jikin sink tana wanke wanke abinta, Ya karaso yana tattare hannun rigarsa " " Kawo in taya ki " " Jiyowa tayi tana kallonsa "ka tayani me? " Wanke wanke ya bata answer yana kokarin karban sponge din hannunta " " A a kabarshi wallahi " " Bakya so namiki jika -jika ko shiyasa bazaki bani bako " " A a ba haka bane hutar da kai nayi wanke wanke ae sai mata " " To ae ni ko a gida ran duty'n Aysher nike mata wanke wanke da shara tayi girki " " Ah lallai Miemie fa baka tayata " " Mtwsssssss ni sa 'an tane to "? " Ni kawai ki bani na tayaki kinji " " Haka ta bashi yana wanke tana daurayewa sai ta samu kanta cikin nishadi bata san cewa Safeer yanada sauki har haka ba " " Bayan sun gama gyara kitchen dinne suka fito palour donyin kallo, Shukra ta zauna a One sitter amma Safeer ya dage wae anan yake son zama " " Mikewa tayi ya zauna, Gashi nan na barma gurin shknn ko " " A a ya fada yana janta zuwa jikinsa " " Ae Kema Anan zaki zauna " " To ae ya mana kadan ka bari na zauna a can ta fada tana nuna masa two sitter dake opposite dinsu " " A a kiyi zaman ki a nan ya fada yana kwantar da ita a jikin sa " " Bata kara masa musu saima lafe da tayi ajikinsa kamar wata marar lafiya (sub-conscious mind) " Yinin ranar Safeer beje ko ina ba sai da yamma ne yace da Shukra ze tafi gidan Mamah" "Ko da tace zata bisa kin yarda yayi wae Amarya bata fita ae" "To shknn zanje gurin Ibteesam kaji " " To kije amma karki dade " " Yawwa tnx" "Har bakin motar sa ta raka sa saida taga fitar sa sannan ta dawo tayi shirin zuwa gidan ibtee " " Bata wani dade a gidan ibtee ba ta koma gida don ta naso tayi girkin dare da wuri " " plantain rings tayi sannan tayi fruit salad tayi ginger drink tasa a fridge, sannan ta shiga wanka " " Wani coffee and milk material nata ta saka dinkin riga da skirt kayan sunyi dai dai da jikinta ta saka milk din Ear ring tayi parking kanta da Ribbon milk colour, Bata wani yi makeup da yawa ba tadai shafa powder da lipstick sannan ta feshe jikinta da turare ta fito palour " " Wayarta ta dauka ta hau online tana karanta wani novel na MIEMIE BIE mai suna #Yar gata ce, sai murmushi take ita kadai abinta tana son writern nn tanajin dadin novels dinta" "Fusge wayar ta da akayine yasata waiwayowa da sauri " " Kai ya Safeer ni kabani wayana YAR GATA CE fa nake karantawa ta fada a shagwabe " " Yanzu saboda Allah Shukra bakiji sallamar da DAN GATAN Ki yaketa bugawa ba kin kafawa waya👀kinata murmushi " " Sannu da ya Safeer wallahi banji ka dawo ba novel din ne ya tafi da Imami na " " Zan baka amma sai kayi wanka ta fada tana jansa zuwa dakinsa " " Da kanta ta hada masa ruwan wanka ta kuma rakasa har kofar toilet, sannan ta dawo ta fito masa da kaya ta turare su ta zauna a gefen bed tana jiran fitowar sa " 40minutes ya dauka a toilet din sannan ya fito, straight gaban dressing mirror yaje ya dauko cream dinsa ya dawo kusa da Shukrah ya zauna" "Shukra cute tayani shafa cream din nan hannuna ciwo yake ya fada wane zeyi kuka " " Dariya take yi kasa kasa sannan ta karbi cream din tana shafa masa " " Baki shafamin a baya na ba " " Cream a baya kuma ya Safeer ta fada tana mika masa kayansa " " Turo baki yayi gaba kamar wani karamin yaro 'Ni bazansa kayan bama wasu zan dauko tunda bazaki shafamin a baya ba " " Yi hakuri dan Allah ya Safeer zo in shafa maka to " " To yace sannan ya juya mata baya ta hau shafa masa, bayan an gama ne ya shirya taja Hannunsa sai dinning " " Tun da yaji kamshin plantain rings din nan ya kasa sukuni burinsa kawai yaji shi a bakinsa " " Ae yana fara ci yahau mata santi ita ko sai dariya take masa harda yi masa waigi da serving spoon " " Bayan sun gama ne Shukra ta kai komai kitchen ta dawo ta sameshi a palour " " Yana ganin ta fito ya mike ya karaso gurinta hade da rike hannunta " " Shukrah cute zo muje mu kwanta ni bacci nakeji " " To kawai tace shikuma ya ja hannunta sai dakinsa" "A bakin bed ya zaunar da ita sannan ya fita yaje dakin ta ya debo mata wasu sleeping dress iya gwuiwa, sannan ya dauko mata brush dinta ya fito ya sameta kwance akan bed " " Tashi kiyi wanka kinji shukra ya fada yana mika mata towel dinsa, batayi musu ta karba har sleeping dress da brush nata ta shige toilet " " Cike da kunya take kallon kanta a mirror, anya zata iya fita a haka kuwa? "Mutuwar tsaye tayi lokacin da taji safeer na turo kofar hade da kiran sunanta " " Shukra kiyi sauri ki fito mana nima fa wankan xanyi ya fada sanda ya shigo toilet din" "Baki sake yake kallon ta tayi masa kyau, Besan sanda ya daga ta sama yana guyi da ita ba kamar wata baby " " Kinyi kyau ya fada mata cikin kunnenta " " Nagode tace tana sauka daga jikansa " " Be wani dade B ya fito yasaka farar jallabiyarsa ya hawo gadon inda shukra take " " Jikinta ya shige yasa hannunsa cikin gashi kanta yana shafawa a hankali " " Shukra najinsa ta mishi shiru, shi duk tunanin sa bacci take, saboda da haka ya dunga bin ko ina na jikinta yana shafawa" "Shukra fa taji kanta cikin wani ya nayi saboda haka ta kara kankame Safeer wane zata shige cikinsa " " Bakiyi bacci ba Shukrah ya fada yana dago kanta da hannunsa " " Dakyar ta iya tattaro nitsuwar tace EH " " Ok tashi muyi Nafilah to ya fada yana mikarda ita zaune " " A tare suka shiga toilet suka daura alwala suka fito danyin Nafilar Ma'aurata............... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/12, 5:41 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 2⃣1⃣ "Sun dade sosai sunayin sallar, sunawa kansu addu 'ar samun zaman lafiya, Bayan sun idar ne Safeer ya fuskanci Shukra ya fara mata Tambayoyi akan Addinin ta kuma Alhamdulillahi yaji Abinda yake sonji, kasan cewar Shukra Ma' abociyar Addini ce " " Tashi ki kwanta kinji Shukra " " To tace sannan ta cire Hijab dinta ta hau gadon ta kwanta " " Sai da Safeer ya karayin Sallah raka 'a Biyu ya kara rokon Allah kan ya basu zaman lafiya sannan ya musu Addu' ar samun zuri'a dayyiba" "Daf da Shukra ya kwanta har tana iya jin numfashin sa akan fuskarta, Hakan ne yasa ta Runtse idonta sosai " " Shafa kan Shukra yake A hankali har zuwa jikinta, Sannan yasa bakinsa akan nata yana tsotsa a hankali " " Wani nishadi Shukra taji tanaji bata masan cewar ta iya kiss ba sai yau Kawai jitayi ta fara mayar masa da martani " " Ganin da nayi Safeer na kokarin zame rigar jikin Shukra ne yasa na jawo musu kofar na dawo palour na zauna " " 4:00Am inata gyangyadi nafara jin kukan Shukra nace barin leka ko za a nemi taimako na " " A zaune Safeer yake yayinda Shukra ke rungume a jikansa yana aikin lallashi " " Sannan Shukra kinji kwanta bari na hada miki ruwan wanka "Ya fada yana kwantar da ita" "Toilet ya nufa ya hadawa Shukra ruwa me zafin Gaske yasa Dettol a ciki sannan ta fito" "Cak ya daga Shukra be direta ko inaba sai cikin ruwan zafin, Ae Shukra najin ta A ruwan zafi ta Kankame Safeer sosai hade da Sakar masa kuka sosai " " Hankali tashe shima ya kara Kankame ta yana mata sannu " " Kiyi hakuri kinji Shukra in kika shiga ruwan zafin nn zaki dena jin zafin kinji " " A hankali ta gyada masa kai hade da runtse idonta " " Sai da Safeer ya gama Gasa Shukra sannan ya hada mata ruwa ta tsarkake kana, ya dauke ya maidata kan gado wanda dama ya changer bed shirt din tun tana wanka" "Toilet din ya koma shima yayi wanka sannan ya fito ya kwanta a kan gado ya jawo Shukra jikinsa yana lallashinta yana kuma gaya mata How sweeter she is " " A haka dai bacci ya kwashe su dukansu, Sai Asuba sannan suka farka " " Daga ta yayi Cak kamar dazu ya kaita toilet ya zaunar sannan ya zuba mata ruwa tayi Alwala " " Jiransa tai yayi Alwalar shima sannan suka fito tare, Shine ya shimfida musu abin Sallah ya daukowa Shukra Hijab tasaka sannan ya tada Ikama " " Sai da su kayi Nafila raka 'a 2 sannan sukayi Sallar Asuba, kafin suka koma gado suka kwanta rungume da juna " Shukra ce ta fara yin bacci ta barshi yanata tunanin Daren jiya, Yayi matukar farin ciki da ya samu shukra virgin, Dama yasan Shukra kamila ce ya kuma sa ran samun budurcinta" Sai gurin 11:15Am suka farka Shukra ce ta mike tana takawa a hankali kamar wata me koyan tafiya tayi hanyar kofa " " Riko hannunta yayi yana tambayar ta inda zata " " Zanje kitchen ne ta fada masa kanta a kasa don wani kunyarsa taji tanaji, Batajinma zata iya hada 👀dashi " " No kibarshi kawai ki koma ki kwanta zansa Aysher tayi mana breakfast din ko Miemie sai ta kawo mana" "A a ba sai ka basu wahala ba zanyi da kaina" "Sai yaji ta burgeshi sosai ya kuma kara mata matsayi a zuciyarsa " " Haba Shukra kinfa gaji taya zakiyi wani girki, Tunda nace zansa Aysher tayi ki hakura kawai " " Gani tayi bazata iya cigaba da musu dashi ba saboda wani zazzabi daya ke neman rufe ta sai kawae ta cire hannunta a nasa ta koma kan gadon ta kwanta " " Parlour ya fito ya zauna sannan ya kira Aysher ya fada mata tayi musu breakfast ta aiko miemie dashi Shukra batajin dadi" "Bayan kamar minti Arba'in Shukra ta fito daga wanka kenan sukaji ana knocking a kofar parlour " " Safeer ne ya mike daga kwancen da yake ya fita ya bude kofar, Miemie ya gani tsaya a bakin kofa rike da basket " " Karban Basket din yayi sannan yace 'ki gaida Mamah yana kokarin rufe kofar " " Shammatar sa tayi a shige parlour' n tana masa dariya, Ae da sauri yayi kanta yana cewa'Zo ki fita malama " " Da gudunta ta kara sa dakin Shukra ta sameta kwance a kan bed ta lumshe idonta kamar me bacci " " Aunty wai bakida? Ko dai haihuwa zakiyi ne ta fada tana shafa cikin Shukra tana neman baby" "Mikewa Shukra tayi zaune ta cire hannun Miemie dake kan cikinta " " Miemie ina Mamah? "Tana Gida tace na gaisheki " " Ina Answer wa " " Miemie Harda kara matsowa kusada Shukra tana tambayarta 'Aunty wae inji Anty Aysher wae bakida lafiya? 'Aunty ciki ne da k..... " "Shigowar Safeer ne ya katse wa Miemie surutun ta" "Har gaban Miemie yazo yaja kunnenta har sai da tayi kara yace "Wae me yasa bakya jin magana ne, Ba ce miki nayi ki tafi gida ba shine harda fakar ido na ki shigo da gudu kina min dariya ko" "Yi hakuri yaya dan Allah Sakar min kunne da zafi fa ta fada tana goge kwallar data zubo mata, Dan sosai take jin zafin rikon da yayi mata " " Bazan sake ki ba sai kin fada min me kike cewa kika ganni kikayi shiru" "Shukra ce ta janyo miemie tana goge mata hawayen fuskarta" "Kai ya Safeer yanzu kan tazo muna hirar mu shine zaka sa ta kuka fisabilillahi Shukra ta fada kanta a kasa hk kuma murya can ciki don sosai take jin zazzabi da ciwon kai " " Ni Gulman tane banaso shiyasa ya fada yana fita daga dakin" "Tare sukayi breakfast din harda Miemie dan dama batayi ba ta tawo " " Zazzabin daya rufe Safeer ne yasa shi yin bacci, sai bayan la 'asar sannan ya farka yayi sallah ya koma bacci" Ganin duk suna bacci ne yasa miemie tayi musu Tuwon semovita miyan agushi tasha busashshen kifi da ganda😋, A flask tasa tajera a dinning sannan ta koma dakin Shukra ta samu bata tashi a bacci ba " " Kayan jikinta ta cire tashiga toilet tayi wanka, Ta fito ta shirya sannan ta koma parlour ta zauna tana jiran Safeer ya tashi ya maidata gida" "Sai bayan magrib dukansu suka farka inda Safeer ya jasu sallah dan bayajin ze iya zuwa masallaci " " Sai da sukayi Dinner ne Safeer yace Miemie ta taso ya maidata gida dan yasan inya barta zata iya cewa zata kwana" "Dukansu suka fito harabar gidan, Inda Shukra ta shiga gaba Miemie kuma baya suka kama hanyar gidan Mamah............. SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/14, 12:42 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 😘 2⃣2⃣ "Cikin lokacin da be wuce minti Arba 'in ba suka karasa gidan Mamah " " A tare suka shiga cikin gidan dukansu inda suka tararda da Aysher kadai a parlour tana karatun wani hand out " " Mikewa tayi da fara' ar ta ta riko hannun shukra suka zauna sannan ta shiga gaida ta cike da ladabi " " Sama taje ta kira Mamah sannan ta dawo suka cigaba da hirar su, Bayan kamar minti 3 sai ga Mamah Da Abbah sun sauko a tare " " Shukra ce ta sauko daga kujerar da take suka shiga gaisawa da surikanta Kanta na akasa, Sannan Safeer ma ya gaisa da iyayen sa " " Shukra ya jikin "Mamah ta tambaya " Jiki Alhamdulillahi ae naji sauki " " To Allah ya kara lafiya " " Ameen suka ce dukansu kafin Aysher ta tashi ta kawo wa Shukra ruwa da lemo " " Da kinbarshi ma Aysher muda zamu tafi yanzu ta fada kasa _ kasa kuma a kunyace" "Lah bakomai Wallahi Aunty " " Bayan kamar minti goma Safeer ya mike. Yana duba agogon hannun sa "Tashi mu tafi Shukra dare nayi fa" " a a kabarta Anan mana tadan kwana biyu tunda bata jin dadi "Inji Mamah" "Jiyayi zuciyarsa tabada wani Dum, Aiko ya hade rai A a Mamah dan Allah ki bari mu tafi ae taji Sauki ya fada yana Riko hannun Shukra " " To marar ta 👀 cewa akayi ra 'a rike tane wae kake wani cin Magani " " Ba hk bane Mamah nima fa banida lpy ina bukatar kulawar ta nima dan Allah kiyi hakuri " " Miemie! Miemie dauko min key din dadin Safeer kizo ki bude masa " " Mamah tace sannan ta juya tana kallonsa "kai ma sai ka zauna a nn din a kula daku gaba daya tunda bakada lafiya" "Komawa yayi ya zauna hade da dafe kansa yana magana da zuciyarsa "Mamah BAZATA gane irin son danakewa yarinyarnan bane tayama zan iya barinta ae inma yazama dole ta zauna nima ko zama zanyi" "Abbah ne ya kalleshi sannan ya dawo da kallon sa gun Mamah. "Mamah ki barsu su tafi mana tunda ta samu sauki ko, Kuma shima yace bayajin dadi yana bukatar kulawar tafa " " Aiko ko zasu tafi sai dai suje da Miemie ko shara da wanke wanke ta dinga tayasu tunda basuda lafiya "Inji Mamah" "Safeer ne yayi saurin dawowa kusa da Mamah 'Dan Allah Mamah ki barta baseta jeba, (Shi harga Allah bayason zuwan yarinyarnan gidan sa) "Sai fa taje, In ko BAZATA jeba sai dai kabar Shukra anan, Dan ba ta yarda za a bar me yaron ciki tana wahalar da kanta " " A zuciyarsa yace kowa yace mata Shukra cikin da ita, A fili kuma yace To naji Mamah amma dan Allah ki bamu Aysher wannan yarinyar ba abinda zatayi mana wallahi " " Bawani nn kaidai kawae baka so najene amma naga yau ni nayi muku dinner akaci ana santi Miemie tace tana hararansa " " Pillown kujera ya jefa mata sannan yafara magana yana huci (wai shi ransa ya baci) " " Yaushe nafara wasa dake wae miemie, wallahi zan gyara miki zama, mayyata kawae nace bazaki kin dage sai kinje " " Kome zakace sai dai kace amma saita je Mamah tace sanda tamike tayi hanyar room din su Aysher dan hadawa Miemie kayan tafiya " " Yi hakuri kaji Safeer addu 'a zakayi mata Allah ya shirye ta inji Abbah " " Yanzu saboda Allah Abbah yarinyar nan abinda take ya dace shekara goma sha biyu ae ba wasa bane, Ita Aysher sanda tana shekarun Miemie haka tayi wallahi sai na gyara mata zama in tazo gida na " " Hakuri zakayi Kaji Safeer kidinga yimata fada da nasiha amma banda duka " " Fitowar Mamah rike da trolley ne miemie na biye da ita yasasu yin shiru, Miemie sai dariya takewa Safeer shi kuma yana watsa mata uwar harara, Aysher da shukra ma dariya suke " " Mikewa sukayi dukansu suka fito dan yimusu rakiya, sai da motarsu ta fita daga get din gidan sannan su Mamah suka koma " 8:20pm suka karasa gida Safeer ne yafara shiga gidan sannan shukra janye da trolley 'n miemie a bayanta kuma miemie ce sai muxurai take tasan haduwarta da Safeer ba sauki" "Sai da Shukra takai Miemie dakinta ta sata tayi wanka ta fito ta shirya ta kwanta ta yi mata add' a, ta kashe mata switch din dakin sannan tayi dakin Safeer " " Sanda ta shiga ta tarar har yayi wanka yayi bacci, Wankan itama tashiga inda bata wani dau lokaci ba ta fito tayi joining Safeer a bed " " Karfe 3:00dai dai zazzabi ya damu Safeer ya tashi yana ruwan sanyi, Bayan son ya tashi Shukra shiyasa ma ya sauka akan bed din " " Kamar ance Shukra bude idonki ta farka ga mamakinta bataga safeer akan bed ba sai tayi tunanin ko toilet ya shiga " " Bayan kamar minti biyar ta mike da niyar zuwa toilet din ta duba shi, can ta hangoshi kwance akan center carpet " " Da sauri ta karasa gurin shi ta da goshi ae batasan sanda ta sake shi ba saboda wani xafi da taji jikinsa yayi (tsaf za a gasa masara tsabar zafin da jikinsa yayi lols) " " Sai sannun take jera masa duk tabi ta ruda kanta " " Shukra ki kwantar da hankalin ki zazzabi nefa kawai " " Ya Safeer zazzabi ne kawae fa kace "Ta fada tana mikewa ta shige toilet" "Hannunta rike da wani dan karamin farin towel da kuma wani bowl cikeda ruwa ta fito takaraso wajensa" "Dago kansa tayi ta dora akan cinyarta sannan ta cire singlet din jikansa ta sa towel din a ruwan ta matse sannan ta fara goge mai jikinsa " " Haka ta dinga yi masa har sai da taji jikinsa yayi sanyi sannan ta maida bowl da towel din toilet " " Ko kafin ta fito har Safeer yayi bacci a gurin, Ganin bazata iya maida shi kan bed din ba ne yasata kwanciya a kusa dashi da daura kansa a Hannunta (Yadda akewa yaro in xeyi bacci) Ai bata wani dade ba baccin ya dauketa itama " " Da asuba safeer ne yafara tashi shi kwanciyar tasu ma dariya ta basa kamar wani danta" "Sai da yayo alwala sannan ya dawo gurin Shukra, Daga ta yayi a hankali yadda bazata firgitaba " " A hnkl take bude idonta akan Safeer, Murmushi yake mata itama haka, Addu 'ar tashi daga bacci yashiga karanto mata, Binsa tashiga yi har suka gama sannan ya rakata har bakin toilet din ya dawo yana jiran Fitowar ta " " Sai da je tashi Miemie tasata yin Alwala sannan suka dawo dakin safeer yasasu Sallar " " Duk su ukun a gurin suka kwanta sai gurin 9:15 shukra ta tashiga tashiga toilet don yin breakfast " " Ruwan zafi ta dafa tasa cikin tea flask ta debo kayan tea ta jera su a dinning sannan ta dawo kitchen tafara musu Gireba, wadda zasu hada da tea" "Bayan ta gama ne taje ta tashi miemie ta hada mata ruwan zafi tasata wanka, Sannan itama tashiga wanka a dakin Safeer " " Bata fito ba sai da shima ta hada masa ruwan wankan sannan ta fito ta tarar ya tashi a bacci ma " " Ya safeer ka tashi lafiya " " lafiya kalau " " Ya karfin jiki kuma " " Alhamdulillahi " " Masha Allah, ka shiga na hada maka ruwan wanka " " To nagode Shukra Allah yayi miki Albarka "Ya fada yana shiga toilet" "Wata Ash colour jallabiyya tasa ta daura bakin dankwali tashafa powder da maroon lipstick ta fito parlour tasamu Miemie suka fara hira abinsu " " Dukansu nagani a kan dinning suna breakfast Miemie nayiwa Shukra labarin Haiydar sunata dariya abinsu " " wayar Shukra ce ta fara ringing, Duk suka juyo suna kallon wayar sai da Shukra ta fasa ihu sannan ta dauki wayar " " Hello Neesa luv " " Bawani Neesa luv munafika kinyi Aure kin manta mutane ko" "Haba dae Aneesa ni na isa na manta ki ne, kiyi hakuri dan Allah tafada kamar zatayi kuka" "Ke kika Sani, Dama fada miki zanyi anjima zamuzo sai kimin sending address naki" "Yanzu ma kuwa shukra tafada cikeda murna, Baki fadamin kedawa zaki zo ba" "Ni da DR. Sumayya wannan wadda ta tafi sudan din " " Na ganewa, Dawa kuma? "Da soofy galadanchi, Da Aysher bichi, da Aunty Ameena kaura, Da Eeshatullah da fancy da Ma sultan da Aunty sis da meela adeel " " Ihu ta saki ashe yau inada manyan baki a gidan, ME kuke so na girka muku " " Bamuda zabi mudai inji Neesa " " Yawwa Neesa naji kamar kince da meela adeel za a zo " " Eh meye" "Dan Allah ki rufa min asiri kar tazo tamin snatching Irin yadda taso tayi wa Ruky mama " " Hhhh ni ban iya rashin mutunci ba bazan iya cewa bazamu zo da ita ba, Kema da kinsan irin rokon da ta dinga min azo da ita da baki ce hk ba " " jiki a sanya ye SHUKRA tace to Neesa luv sai kunxo, Ta kashe wayar tana bawa Safeer labarin yau sunada Manyan baki a gidan " " Tare suka shiga Kitchen ita da Miemie, steamed cous - cous da Egg sauce suka farayi sannan sukayi fried rice sukayi Banana, coconut and pineapple Drink suka sa a fridge sannan Shukra tashiga wanka don sun mata waya sun tawo, Tabar Miemie tanayin liver sauce........... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/14, 5:36 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to miemie bie 😘 2⃣3⃣ "Bayan kamar minti goma Miemie ta gama liver sauce din ta shige toilet don yin wanka ita ma " " Shukra da Miemie ne kadai a parlourn suna kallo kuma suna jiran zuwan Manyan bakin su " " Knocking din dasuka ji a kofa ne yasasu mikewa dukansu suna rige rigen bude kofar, Shukra ce tayi nasarar bude kofar ae ko sa Aunty sis ta fara cin karo, Rungumeta tayi tana murnar ganinta don she really missed her " " Basu guri tayi suka shigo parlourn suka zauna, Meela se karewa palour kallo ake, Miemie ce ta durkusa har kasa tana gaida su daya bayan daya " " Shukra ce ta shiga kawo musu drinks da bottle water, Bayan sun gaisa da shukra kuma sai suka tsinke da hirar yaushe gamo" "Shukra a ina kk aiki ne "Soofy ta tambaya" "Ke ni bana wani Aiki, Aikin gidan miji na nake " " Shukra knn meyasa bazaki sa ya nema miki aiki ba ko a nn Maryam clinic ne da kuke kusa " " Ke nifa Aikin ya fita a raina, Amma dae zan gwada " " Sai bayan zuhr prayer sannan Miemie ta Fara kawo musu Abinci, Neesa ce tayi service nasu suka fara ci suna santi (Kunsan ni na koya ma Shukra girki dole suji dadin sa) " " Shigowa Safeer yayi da Sallama a Bakinsa ya durkusa har kasa yana Gaida Aunty sis, Bayan sun gama gaisawa ne kuma su soofy Galadanchi, Neesa luv, DR. Sumayya suka fara gaida shi cike da ladabi, Sosai ya yaba da Hankalin kawayen Shukra " " Meela dai batasan sanda glass cup din hannunta ya fadi kasa ba gurin kallon Safeer (Snatcher anga HANDSOME guy 🤣) " " Juyowa sukayi dukansu suna kallon meela da mamaki, Shukra ko hade rai tayi tana kallon Meela kafin ta juya taja Hannun Safeer ta shige Bedroom dinsa dashi " " Meela wae har ynx kina nn da halinka saboda Allah, ki sa Mutum a gaba da kallo har da fasa cup inji Aneesa Rai a bace " " Nan dai suka sa Meela a gaba suna ta mata fada, Aunty sis tace suyi shiru duk sukayi kuwa " " Nasiha tashiga yiwa Meela me ratsa jiki,(Uwar Arziki) Har kuka sai da Meela tayi tana bawa Aunty sis Hakuri tana kuma tabbatar nata ta dena Halinta " " Hade rai tayi tana watsa wa Safeer harara 'Ya safeer ba seda nace karka dawo gidan ba sai sun tafi, Amma shine ka dawo ko? "Haba Shukra me yayi zafi wae haka nifa zuwa nai mu gaisa da Aunty sis " " Bata kara cewa komai ba ta juya ta fice tana huci" " Shukra ce ta fito tana huci taja Hannun Meela ta turata waje sannan ta nuna ta da dan yatsa 👉🏻kada ki kuskura koda wasa ki kara zuwa gidan Daga hk ta rufe kofar ta ta dawo suka cigaba da hirar su da kawayenta " " Sai da sukayi sallar La 'asar sannan suka tafi inda Shukra ta cikasu da tsaraba, Suka tafi suna murna, Suna fita Soofy Galadanchi ta dawo tana tanbayar Shukra ta koya mata yadda ake Garnished cous - cous " " Karki damu Soofy anjima mu hadu online zan koya miki " " Godiya tayi mata sannan tafice inda ta samu suna jiranta, daga nn suka wuce gida " " Tunda Shukra ta shiga daki bata fito ba sallar Magrib ma a daki tayi ta har ynx bata gama hucewa ba kan abinda Safeer yayi mata, Tace kar ya dawo saboda tana kishinsa bataso wata mace ta kalleshi, Office ma da dahali da ta hanasa zuwa, Amma sai da ya dawo " " Da sallamar sa ya shiga dakin Shukra ya hango ta can karshen gado ta kifa kanta jikin pillow da alama kuka take " " Da sauri ya karasa kan bed din ya dagota ya Rungume tsam a jikinsa yana bubbuga bayanta " " Batayi wani yunkurin kwa cewa ba sai ma kara kankame shi da tayi don dama hakan take bukata a halin yanzu, So kawai take ya lallasheta ya bata hakuri ko taji sanyi a ranta " " Yi hakuri kinji Shukra cute, Kidena zubar da hawayenki a banza bayan nace miki Mazaunin mace HUDU kike a gurina, Ba wadda ta isa na kalleta bayan inada ke, Cry no more swthrt kinji " " Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki batasan sanda murmushi ya kubuce mata ba, Ta wani kara narke masa " " Nagode Ya safeer " " Murmushi shima ya sakar mata ya shafa fuskar ta yace 'Ashe kina sona har haka Shukra, irin wannan kishi Haka " " Harara ta watsa masa irin ta wasan nn sannan tace' waye yace maka ina sonka " " Kishin da kika nuna da kuma kukan da kike kan wata ta kalleni yasa nagane kina sona " " Hannayenta Biyu tasa ta rufe idonta cike da kunyar sa, tana dariya kasa kasa " " Dagata yayi suka sauko daga bed din suka fito parlour hannunsa rike dana Shukra " " Sai zuwa 10:00pm suka tashi Miemie tayi dakin Shukra sukuma sukayi dakin Safeer don yin Bacci " " Washe gari Wajen 12:00am bayan sun gama breakfast Shukra tace zata Gidan Ibteesam, Tare suka tafi da Miemie suka bar Safeer kadai a gida yana cigaba da Aikin Construction na company da yasamu " " Wayarsa dake kan center table ne tashiga ringing, Karasawa yayi ya dauka da Sauri ganin Haiydar ne me kiran " " Assalamu alaika Haiydar ya kk ya Hajiya " " Lafiya kalau muke Safeer me kirki cikin kwanta goman da kayi kana hutu baka taba kirana a waya ba koda wasa, Amarya ta mantar da kai mutane ko" "Eh ta mantar din in kayi zuciya kaima kayi AUREN " " Karka damu nanda Shekara uku zanyi Aure Miemie nayin Graduation (Candy), " " Ka wahala wallahi Haiydar lokacin ina nn da dan yaro ma " " Kai ka Sani nidai AUREN SOYAYYA zanyi ba AUREN BAZATA Haiydar ya fada yana dariya " " To sai me ae AUREN BAZATA Alheri ne, duk wanda beyi Auren bazata ba ae be ji dadin Aure ba wallahi " " Hhhhhhhhh a hakan " " Nidai yanzu ba wnn ba jiya mutumin daya baka Aikin Company a san Francisco yaxo munata kiranka bakayi picking ba, So yace next week yakeso a fara Aikin so saika zama cikin shiri ko" "Eyya kuyi hakuri kunsan in ana tare da Amarya ba a iya komai amma insha Allah zan kirasa muyi magana " " Kai ka Sani jibi dai zaka dawo Aikin ae inji Haiydar wanda yana gama fadar hk ya kashe Wayarsa " " A nn Safeer ya kira mutumin suka gama mgn kan Next week ze tawo san Francisco " " Sanda su Shukra suka dawo Safeer ya basu labarin komai, Zo kuga tsalle gurin Miemie za aje inda ba 'a taba zuwaba ko a mafarki " " Ke kuma Ihun me kike hk, To ba inda zani dake Anan kinzo kin shiga rayuwar mu shine kike so ki bimu can a cigaba da samana eyes ko "inji Safeer yana hararan Miemie" " Fasa masa ihu Miemie tayi ni wallahi sai kunje dani "Shukra dai batace komai ba sai kallonsu take " Baki sake Safeer yake kallonta, Wani sabon salon iskanci ne wnn kuma Miemie? To wlh zakiyi kuka me dalili kinji ya fada yana murde mata bakinta " " Shukrah ce ta janye ta tana lallashinta " " Kai ya Safeer dan Allah kawai kasata kuka ana zaune kalau, In bazaka jeda itaba kace bazani da keba ba saika sata kuka ba " " komai beceba sai daukan car key dinsa da yayi ya fice daga gidan ya tafi gidan Mamah ya fada mata, Sosai suka tayashi murna tare da yimasa fatan alkhairi " " Bayan yabar gidan Mamah gidan Ammii ya wuce wanda cikin sa 'a ya tarar da Daddy, Nan suma yayi musu bayanin tafiyar sa sukayi masa Addu' a sannan ya dawo gidansa ........ SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/16, 6:56 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 😘 2⃣4⃣ "Yau ta kama Monday kuma yau Safeer ze koma Aiki saboda hk Shukra tunda tayi sallar Asuba bata koma ba tashiga Kitchen don hada musu breakfast " " Sweet potato ta soya tayi egg sauce sannan dafa ruwan zafi tasa a tea flask ta jera a dinning sannan ta shiga dakinta donyin wanka " 6:50am Safeer ya turo dakin Shukra cikin shirin sa na fita office, Ita kuma lokacin ta fito a wanka knn tana shafa cream a jikinta" "Wae har ka shirya ya Safeer ta fada cike da Mamaki " " Eh mn zokiyi serving dina breakfast na wuce sauri nake yau Ahmad zezo " " Waye Ahmad kuma " " Wanda zanyiwa Aikin company a san Francisco mana " " ok, To jirani insa kaya sai inxo " " To, miemie bata tashi bane ita " " Eh itada ba fita xatayi meye nata na tashi da wuri haka, " To kiyi sauri dae kizo ya fada yana fita daga dakin" "Bayan Safeer ya gama breakfast sai da Shukra ta rakasa har mota ta jira ya fita a gidan sannan ta dawo ta fara gyaran gidan " " 12:00pm Ahmad yazo Office din Safeer kuma sun gama mgn kan cewa ran friday zasu tawo san Francisco, Sosai yaji dadi yadda Safeer ya karbi Aikinsa ya kuma yi masa alkawarin zuwa akan lokaci " " Yau saura kwana 2 tafiyar su Safeer saboda haka yace Shukra ta shirya kayan Miemie su Maidata Gida da daddare " " Bata rai Miemie tayi wane zatayi kuka, Sai hararar Safeer take kasa kasa, karaf suka hada ido " " Zo nan Miemie ya fada rai a hade " " Kukan shagwaba ta saki taje ta makale a jikin Shukra kamar karamar yarinya "Aunty Shukra Kinga yaya ze dakeni ko " ME kika yi masa Shukra ta tambaya tana kallon Safeer da Fuskar tausayi (Irin kar ya daki Miemie) " " Harara na tayi ya bata Answer yana dauke kai " " Shukra ta dawo da kallonta kan Miemie wadda take ta zare ido kamar tayiwa sarki karya, Miemie bakya jin Magana ko kina abun kamar karamar yarinya, Ya Safeer din sa 'ankine da kike hararar sa? " A a Aunty Shukra yi hakuri bazan kara ba " " Kima kara, Shukra ta fada tana jan hannun Miemie zuwa daki " " Koda suka shiga dakin kayan Miemie suka hau hadawa, Sosai Shukra ta yiwa Miemie nasiha kan halayenta, Da alama nasihar ta shige ta don har kuka sai da tayi tana bawa Shukra hakuri " " Tun 7:00 pm suka tafi gidan Mamah maida Miemie, Mamah tayi mamakin nitsuwar Miemie don yan kwana kin da tayi a gidan Safeer sosai ya ke mata fada, Shukra kuma tayi nasiha " " Sun dade gidan don se wajen 11:00 su Aysher suka rakasu mota suka tafi gidansu" "Washe gari Da Safeer zai tafi Office sai da ya sauke Shukra a gidan Ammii sannan ya wuce " " 4:30pm Safeer ya shiga Office din Haiydar da sallama a bakin sa, Ya samu guri ya zauna yana fuskantar Haiydar " " Malam wae yaushe zaka fito da mata ne kayi Aure, ko baka gaji da zaman gidan Hajiya ba? "sai nan da shekara uku meye matsalar ka? "Kaga Malam in zaka dawo hayyacinka ka dawo Miemie fa tayi maka kankanta kabarwa Abdallah kawae ka nemi wata " " Bazan bar masaba yaje shima ya nema mana inji Haiydar ya fada rai a bace " " To na fahimce ka bakada Budurwa ne shiyasa, Ko kanason Aysher na baka ita " " Banason ta ni Miemie nake so kuma ko kaine babanta baka isa ka hanani AUREN taba" Haiydar ya fada sanda ya mike yana tattara kan table dinsa " " ni na isa na hanaka auren Miemie? Allah ya baka Hakuri zo muje gidan Ammii zan dauko Shukra sai ku gaisa ma " " To kawai yace sannan suka fito a tare kowa ya shiga motar sa suka kama hanyar gidan Ammiii " " Sanda suka je gidan Ammii ana kiran sallar Magrib saboda haka basu shigaba sai da sukayi sallah a wani masallaci kusada gidan " " Sai bayan sallar isha sannan suka baro gidan Ammii, Areef harda kukansa (Kukan rabuwa) " " Washe gari Safeer beje Aiki ba fita yayi yayo musu siyar yar duk wani abu dayasan zasu bukata kuma bazasu samuba acan " " Da yamma wajen karfe biyar Safeer da Shukra kwance akan gado rungume da junansu suna hirar su ta masoya akayi Knocking a kofar parlour " " Safeer ne ya mike yasa rigarsa sannan ya fice don duba waye " " Yana bude kofar yaga wata yarinya kamar Shukra take da yarinya a hannunta, Yarinyar na ganinsa ta fara mika masa hannun alamar ya dauketa tana kiransa da Daddy" "Hannu yasa ya karbeta sannan suka gaisa da Mamanta, Guri ya bata ta shigo parlourn sannan ya wuce bed room din Shukrah don kiranta " " Da fara 'a dauke a Fuskar ta ta karaso parlourn "Sannu da zuwa Ibtee, ya Gida ya Amal? " Lafiya kalau muke, ae Amal fushi take dake tunda kin dena zuwa gurinta " " Eyya Amal tayi hkr tana raina wlh, Naga ta makale wa ya Safeer kamar ta sanshi " " Ae da alama mijin kin nn yana son Yara da yawa, Yaushe za haihu ne Ibtee ta fada tana neman daga rigar Shukra " " Rike Hannun Ibtee Shukrah tayi tana dariya, Ke ni banida ciki fa " " Zama ki fadi gsky ne " " Daga nn Shukrah ta mike ta kawo wa Ibtee lemo da ruwa " " Sai da aka kira sallar magrib sannan Safeer ya kawowa Ibtee Amal yawuce Mosque, itama gidanta ta tafi" "Zuwan Ibtee ne ya hana Shukrah hada musu kayan su sbd hk bayan sun gama cin abinci sunyi sallar isha shukra ta shiga daki don hada musu kayan " " A tare suka hada kayan da Safeer sannan sukayi shirin bacci don jirgin karfe bakwai zasu bi " "Safeer ne ya musu addu ' a ya tofe musu jikinsu sannan suka kwanta rungume da juna" "Yimin labari me dadi Shukrah, Safeer ya fada mata a kunnenta " "Ya Safeer ni ban iya lbr ba sai dai kai ka yimin, Shukra ta fada kasa kasa" "To zan miki wani iri kike so " " Kowanne ma " " Nan Safeer ya fara mata labarin cikin kunnenta " " Sai dariya Shukrah take kyalkyalawa tana kara shigewa jikinsa, a takaice dai sai da Suka raya daren ranar, " " Tun kafin Asuba Suka farka sukayi wanka sukayi nafila suka jira sallar Asuba, Tea kawae suka sha suka sa kayan su a booth suka tafi gidan Mamah " " Aysher da Miemie suka dauko sannan suka wuce Airport " " Jiran minti goma sukayi sannan aka kirasu, Suka wuce suna daga musu hannu, Zo kuga kuka gun Miemie harda birgima a kasa wae kar Shukrah ta tafi ta barta " " Aysher ce taja motar ta maidasu gida har amotar Miemie kuka take, suna zuwa gida ta kwanta a parlour sai bacci....... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/18, 6:59 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 😘 2⃣5⃣ "Cikin jirgi Shukra sai bacci takeyi daga Zaunen da take, Safeer ne ya kwanto da ita jikinsa dan tafi jin dadin baccin" "Ko da aka kawo musu abinci ma be karba ba don yasan Shukra bazata ciba, kuma dama shi bayajin yunwa, Cigaba da Aikinsa yayi har suka isa San Francisco " " Jirginsu na landing Shukra ta farka tana raba ido, Mikarda ita safeer yayi suka sauko a tare " " Wayarsa ya dauko ya shiga dialing number Ahmad, Wanda tana fara ringing ya dauka don dama sunyi waya da safeer ya fada masa sun kusa sauka " " Mota Ahmad ya dauko yazo ya samesu a zaune kan resting chairs na airport din, safeer na ganinsa ya mike da fara 'arsa sukayi musabaha kafin suka gaida da Shukra " " Nan ya kwashi trolley dinsu yasa a mota suma suka shiga suka kama hanyar gidan sa " " sun samu tarba ta musamman gurin matarsa Azeeza, Yar Nigeria ce itama, bayan sun ci abinci ne kuma Safeer da Ahmad suka fita dan ganin inda za a gina Company 'n sukabar Azeeza da Shukra suna hira kamar dama can sun san juna " " Har dare basu dawo ba, Abinda ya daga hankalin shukra kenan sosai take son ganin mijinta, wayarta ta dauka da niyyar kiransa sai kuma ta tuna batada number sa, Dan karamin tsaki taja kamar zatayi kuka wae batada number mijinta (Abin takaici) " " Azeeza ganin dare yayi sosai kuma dawowar Ahmad ba yanzu ba yasa ta nunawa SHUKRA dakin da zata kwanta, Ita kuma ta shige nata, Zaman kusan awa biyu Shukra tayi amma shiru Safeer be dawo ba sbd hk ta shige daki kawai ta kwanta " " Shiru tayi bayan ta kwanta zuciyar ta cike da tunanin Safeer, Batajin zata iya bacci ba a jikin Safeer ba juyi kawai take a kan gadon sam bacci ya ki zuwa, Ahaka dae bacci barawo ya kwashe ta " " Cikin bacci taji ana shafa ta tai saurin bude ido don dama baccin beyi wani nisa ba " " Cikeda shagwaba take kallon sa idonta taf da hawaye "Ya Safeer shine kaje kayi zaman ko, Ka barni inata jiranka" Tafada tana fashewa da kuka "Jawota yayi jikinsa yana bubbuga bayanta a hankali "Yi hakuri Shukra cute kinki insha Allah gobe bazan dade ba yau dinma dan farko ne bakiga guraren da mukajeba, Amma wallahi kina raina sai tunanin ki nake" "Murmushin jin dadi tayi ta kara shigewa jikinsa 'kaci abinci ya Safeer? "Naci dazu Shukra yanzu wanka zanyi " " A tare suka mike suka shiga toilet din ya tsaya a gefe ita kuma ta hada masa ruwan wanka "Bitayi jefensa zata wuce yayi saurin rike hannunta" "Ina zakije kuma ya tambayeta kasa kasa yana kashe mata ido daya " " Zanje in fito ma da kayane fa ta bashi Answer tana kokarin kwace hannunta " " Kara damke hannun yayi 'ki bari muyi wankan mana " " A a ya Safeer nifa nayi tun dazu " " Ban yarda ba sai kin sake " " Kasa cigaba da jayayya dashi tayi dan haka kawae sai ta rufo musu kofar toilet din ta dawo ciki " " Safeer ne ya shiga ciremata kaya, ita ko kunya duk ta hana ta sukuni sai sunkuyar da kanta take, haka dae ya gama cire mata kayanta tsaf shima ya cire nasa ya hau jikata da ruwa " " Itama jikashi ta fara yi suna dariya abinsu, A hk dae suka soma wanke junansu wanda tun Shukra na nokewa har sai da ta saki jiki " " Safeer na gani ya fito daga toilet dauke da Shukra a hannunsa kamar wata baby ya nannade ta da towel, Karasawa yayi ya kwantar da ita a tsakiyar gadonsu sannan yaje inda trolley 'nsu ya dauko cream ya dawo kan gadon " " Kunce towel din jikinta ya shiga yi inda Shukra ta runtse idonta, Shiko ko a jikinsa sai da ya cire mata towel din gaba daya sannan ya soma shafa mata cream din cikin wani salo me wuyar fassaruwa yake shafa mata, Shukra dai jinta tayi kamar ba a duniya wani irin abu ne taji yana yawo a jikinta, batasan lokacin data janyo hannun Safeer ba ya fada jikinta " " Nan suka shiga kissing junansu cike da kaina wane zasu cinye kansu, Romancing kansu sukayi tayi kamar ba gobe, Niko ganin haka yasa na fito na barsu susha love " " Washe gari tun 7:00am Safeer da Ahmad suka bar gidan har dare Shukra nata baza ido ba labarin Safeer, Hawaye ne ya cika idonta tanason ganin Safeer tana tsananin bukarsa, Gashi ta manta bata karbi number sa ba " " Ganin kuka na neman cin karfinta yasata mikewa da sauri tashige daki, Kwantawa tayi kan gado ta rungume pillow tana kuka mara sauti " " Karar wayarta ne ya katse mata kukanta, kamar bazata dauka dan saida yazama missed call ma sannan ta dago wayar ganin Aneesa ce me kira yasata saurin dialing " " Ringing biyu Neesa tayi picking "Hello Neesa luv ta fada can ciki" "Shukra Y kk, Ya jikin kuma? "Jikin me kuma Neesa nace miki banda lafiya ne? "Muryanki ya fada min bakeba " " Keni lafiya na kalau " " uhmm, Yaushe zaki haihu ne Neesa ta tambaya tana dariya kasa kasa " " Wani irin Haihuwa ana zaune kalau ae ni sainaci amarchi na kamar shekara 2or 3 kafin na fara haihuwa " " Koba shekara biyu ko uku ba Neesa ta tambaya tana dariya sosai " " Dariyar me kuma haka Shukra tace wane zatayi kuka " " Jinayi kince shekara uku Shukra wa yasani ma ko yanzu kinanan da katon cikin ki, Zama da kyar tashi dakyar Aneesa ta bata answer " " Dogon tsaki kafin ta kashe wayar ta ta kifa kanta jikin pillow ta cigaba da tunanin other half nata " " Tanaji Neesa nata kiranta amma batabi takai ba ta cigaba da tunaninta tana addu a Allah yasa kar yau ya dade kamar jiya " " To yau kam Su Safeer sun dawo da wuri dan agida sukayi sallar isha, Bayan sun idar sukaci abinci sannan kowannensu ya shige dakinsa " " Shukra bako kunya ta tashi tabi bayan Safeer inda ta tarar harya shige toilet, Azeeza ma ganin Shukrah ta mike yasata itama mikewa tabi bayan Ahmad " " Sai da Safeer ya kira Haiydar sukayi hira sosai, Sanda sukayi sallama ne Haiydar ya fara tambayar Safeer Shukra " " Safeer ya dawo da kallon shi kan Shukrah dake kwance akasa ta nannade kafafunta da nashi kamar mejin sanyi,Gashin kanta ya rufe mata fuskarta, Hannu yasa ya ture Gashin gefe ya dago kanta, sai anan ya gane ashe ma bacci take, Nan dae ya fada ma Haiydar Shukrah tayi bacci sukayi sallama, sannan yayi wa Shukrah addu a shima yayi " " Sai da Safeer da Ahmad sukayi kwana 5 basa zaman gida Shukrah har ta fara ramewa " " Shukrah ce zaune kan abin sallah bayan ta idar da sallah azahar tana yiwa Safeer addu 'ar kariya, Jin datayi a turo kofar dakinsu yasata saurin dagowa " " Ware ido tayi tana kallon sa da mamaki, Tunda sukazo san Francisco basu taba haduwa da rana ba " " Fuskarta dauke da Murmushi ta karaso ta rungumeshi " " Ya Safeer sannu da zuwa Shukrah tace tana riko hannunsa, Ta zaunar da shi a bakin gado ta haye cinyarsa bakinta yaki rufuwa dan dadi " " Yawwa Shukra na sameki lafiya? "Lafiya kalau, Ya Aikin? "Alhamdulillahi, Aiki ma ankusa kammalawa " " Masha Allah shiyasa yau kadawo da wuri knn" "Eh mana, Gobe ma bazan fitaba zan kaiki yawo " " Ihun murna Shukrah ta sa kafin ta mike taje ta hadawa Safeer ruwan wanka, Bayan ya shiga toilet ne ta fito masa da farar t-shirt da three quarter ta fesa musu perfume ta zauna tana jiran fitowarsa " " Shukrah ce kwance kan jikin Safeer da alama bacci zasuyi " " Kinsan irin son da nake miki kuwa Shukrah " " Saurin sa tafin Hannunta na dama tayi ta toshe bakinsa 'Yi shiru Ya Safeer kayi bacci kaji "Shukrah ta fada tana harar sa " Harshen sa yasa yana tsotsar tafin hannun nata, Bata janyeba haka bata hana saba, sai ma kwantar da kanta datayi a kirjinsa hade da lumshe ido, A haka dae bacci me dadi ya kwashe su............ SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/21, 9:01 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 😘 2⃣6⃣ "Kamar yadda Safeer yayi wa Shukra Alkawari kan cewa ya yau baze fita ba haka kuwa akayi be fitan ba," "Bayan Sallar Azahar ne Safeer ke Sanar da Ahmad yana so ya fita da Shukra, Ahmad din kuma ya Amince ze zagaya dasu suga garin kamar yadda Safeer din ya bukata" "Dukansu na gani a harabar Gidan cikin Shirin su na fita, Ahmad ya zauna a driver sit inda Safeer ya zauna a gaba Shukra da Azeeza kuma Suka zauna a baya " " Mesium ya fara kaisu, Sannu a hankali yake musu bayan duk abinda suka gani,Bayan sun gama da Mesium ya daukesu ya kaisu San Francisco state University sosai suka zagaya a cikin University kafin suka fito suka tafi wani hadadden Restaurant nan Suka ci abinci suna ta hira abinsu, " " Bayan sun fito ne Shukra taga wani dan Asibiti karami a gefe tace tanason shiga, Ae kuwa sai da suka shiga aka zagaya dasu, tayi kuma magana da wata likitan ido inda Shukra ke fada mata Optometry ta karanta, Sosai Doctor taji dadin Haduwa Da Shukra har tayi mata tayin Aiki cikin Asibitin, Shukra ta mata bayani kan cewa ita bakuwa ce a San Fancisco Aiki ne ya kawo mijinta, Sun dan taba hira kadan Sukayi Exchanging phone number daga nn sukayi Sallama Suka bar Asibitin " " Koda Suka bar Asibitin ba gida Suka wuce ba Saida suka ce Bitch suka yi kalle kallensu sannan suka dawo gida da niyyar gobe zasuje San Fancisco state zoological garden " " Koda Suka dawo Gidan Sallar isha kawae sukayi kasan cewar sunyi Magrib nan cikin Asibiti, Kwanciya Shukra tayi bacci me dadi ya dauketa, Shi kuma Safeer sai da Suka dade da Ahmad a Parlour suna magana kan Company kafin sukayi sallama kowa ya shige dakinsu " " Bayan Safeer yayi shirin bacci ne ya kwanta kusa da Shukra yana ta binta da kallo kamar me Shirin gano wani abu a tare da ita, Kawai gani yayi ta kara haske tayi wani kyau, Idan har idonsa be masa karya ba ze iya cewa Shukra tayi kiba, To ko weather garin ta karbeta ne " " Matsawa yayi sosai ya Rungumeta a jikinsa yana shafa ta sai yaji jikinta yayi santsi kamar jikin jariri, Ransa yana basa wani abu sai kawai ya share, Yana addu 'ar Allah yasa hasashensa ya zama gaskiya A haka dae bacci ya kwashe shi " " Washe gari gurin sha daya bayan sun gama breakfast ne suka shirya sai Zoological Garden, Sosai gurin yayi wa Shukra kyau dan ko kusa bazaka hadasu da na Kano ba don iya shi ta taba zuwa " " Riko Hannun Safeer Shukra tayi lokacin da Zuwa zo Gurin lion, Yana ganin su ya fara ihu yana tsalle kamar yana son fito, Shukra ta kankame Safeer a jikinta ta fasa masa kuka jikinta har wani rawa yake ta tsorata iya tsorata har bata iya jin abinda Safeer din ke ce mata " " Sun dau Tsawon lokaci a haka Safeer sai shafa bayanta yake yana bata hakuri a Ransa kuma yana tunanin wannan irin tsoro na Shukra " " Shukrah ce ta fara dagowa daga jikin Safeer ta kalle shi tana goge hawayen fuskarta "Ya Safeer mu tafi gida Zazzabi nakeji" "Sannu Shukra bari su Ahmad su Dawo sun dan za gaya can ne ya fada yana jan hannunta suka zauna " " Riko shi tayi sosai don har yanzu a tsorace take Shima ganin hakan yasa shi Kwantar da ita kan kirjinsa yana buga bayanta a hankali, A haka su Ahmad suka dawo suka samesu inda Safeer yayi musu bayanin komai, Nan dae suka koma gida" "Shukrah ce ta fara shiga gidan ta kwanta nan palour ta rufe idonta, A tare suka shigo dukkansu, Ahmad da Azeeza suka shige dakinsu Safeer kuma ya dauki Shukra cak ya kai daki ya kwantar " " Sai wajen 3:20pm Shukra ta farka duk jikinta ba dadi ga Zazzabi ta rasa inda zatasa kanta taji dadi kawae sai tasaka kuka, Safeer yana toilet yajiyo kukan Shukra ya fito da Saurin sa ya hawo kan gadon inda take " " Shukrah tayi Saurin fadawa jikinsa ya kankameshi kamar zata shiga cikin sa, Nan yaji jikinta yayi zafi sosai abin ya bashi tsoro, Yayi Saurin kwantar da ita ya fice daga dakin " " Azeeza kadai ya samu a Parlour yayi mata bayanin komai, Nan ta mike da sauri takira Ahmad suka je inda Shukra, Azeeza jin yadda jikin Shukra yayi zafi yasa ta fashe da kuka, abinda ya daga hankalin Safeer " " Da Hanzari Ahmad ya dauko car key dinsa Safeer ya dauko Shukra bayan Azeeza ta sa mata Hijab Suka wuce Asibiti " " Suna zuwa Aka karbe ta, Bayan test test da akayi Doctor tayi musu babban Albishir cewa Shukra nada ciki har na wata Biyu " " Zo kuga murna gun Safeer kai bama shi kadai ba harda Azeeza da Ahmad tunda su basu taba haihuwa kuma sun dau Safeer da Shukrah tamkar yan uwansu wannan ne yasasu jin kamar su za ayi wa haihuwar " " Sai ba adi salatul Magrib sannan suka baro hospital kuma Alhamdulillahi jikin Shukra yayi sauki sai dai rashin kwarin jiki kawai " " Sosai Shukra ke samu gata gun Ahmad, Safeer da Azeeza, Don Azeeza ta hana tayin komai cikin gidan har ruwan wanka ita ke hada mata da kanta " " Kayan baby kuwa abin ba a cewa komai don kullum Ahmad ya fita sai ya siyo su hakama Safeer don ya zama dan gari " " Safeer ne ya kira Aysher ya gaya mata Ankoyi sa a ranar Ammii da Areef sun zowa Mamah ziyara, Nan Aysher ta fada musu maganar cikin Shukra, zo kuga murna gun Ammii da Mamah bakin su yaki rufuwa su a dole murnar samun babban jika suke a take Ammii takira Daddy ta fada masa kusan ma Daddy duk ya fisu don cewa yayi inyagama abinda yake a Dubai zai wuce san Fancisco ya gansu " " Mamah ta kira Shukra tayi mata murna tayi mata addu 'ar samun lafiya, Ita dai Shukrah kunya kamar ta nutse, sai bayan sunyi sallama da Mamah ta juyo kan safeer tana dukansa da hannu biyu tana mai kukan shagwaba " " Shine kaje ka fada wa su Mamah inada ciki ko? Yanzu da wani ido kake so na kallesu " " Rike hannayenta yayi ya janyota Jikinsa ya Matse ta har sai da ta saki yar kara sannan ya sassauta rikon " " Shukrah Ai ko ban fadawa mutane ba zasu gani ae in mun koma " " Ni bazan koma ba sai na haihu, Ta fada cike da shagwaba " " Ae baki isa ba nanda 2 weeks zamu tafi don next week za a gama Aikin company kuma office suna nema na " " Ni bazan tafi ba sai dae kaje ka barni a nan " " Bazan barki ba Shukrah " " Nan dae Shukrah ta cigaba da kukanta na shagwaba wae ita bazata je aga cikin taba sai dae a ganta da baby " " Shiko Safeer shiru yayi yana jinta don yasan inya biye mata rigima zatayi tayi masa don ita cikin nata da tabara, Rigima da shagwaba yazo mata, Ahaka dae bacci ya dauketa ya sauke ta daga jikinsa ya mata addu a shima yayi ya Rungumeta sai bacci........... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/22, 9:13 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 😘 2⃣7⃣ "Misalin karfe daya da rabi Shukra ce da Azeeza a kitchen da Alama Lunch suke hadawa, Azeeza na daga gefe tana dafa white spaghetti Shukra kuma tanayin Beef Goulash " " Wayan Shukra ne ya shiga ringing ta ajiye spoon din Hannunta ta nufi wayar, Ibteesam ce me kiran shiyasa Shukra tayi saurin picking tana mata sallama "Shukra Fadamin da bakin ki dan Allah inji Ibteesam da murnar ta" "ME zan fada miki Shukra ta tambaya " " Ki fada min SIRRIN BOYE (sabon Novel dina bayan AUREN BAZATA insha Allah) inji Ibtee tana dariya " " Dariyar itama Shukra tayi don ta gane me take nufi " " Wata nawa ne? "Wata Biyu ne " " kice Amal ta kusa samun kanwa inji Ibtee " " Ta kusa kam " " Daga nn dae suka cigaba da Hirar su ta kawaye har sai da Shukra taji Beef Goulash dinta na neman kamawa sannan tayiwa Ibtee sallama ta koma kan girkin ta " " kamar yadda Daddy yayi Alkawarin zuwa San Francisco ganin Shukrah Haka kuwa akayi ranar wata friday ya kira safeer ya fada Masa gobe ze biyo jirgi yazo ya gansu, Shukrah kamar ta zuba ruwa a kasa tasha don Farin ciki " " Ranar da Daddy zezo Abinci kala kala Shukrah da Azeeza sukayi, Karfe Uku saura jirgin su Daddy yayi landing a San Francisco, Inda ya kira Safeer a waya Sukaje Shida Ahmad suka tawo Da Daddy " " Rungume Daddy Shukrah tayi don Murna kafin taja Hannunsa ta Zaunar da shi kan One sitter ita kuma ta zauna a gaban sa tana masa labari sai dariya suke " " Azeeza ce ta kawo wa Daddy Abinci da Drinks sannan Suka gaisa Nan Safeer da Ahmad ma Suka zo suka kara Gaisawa da Daddy kafin suka tafi suka barshi yaci Abinci " " Koda Ahmad da Safeer suka fita Hotel room suka kamawa Daddy sannan suka je sukayi masa Siyayya me yawa suka kai Room din sannan suka dawo gida " " Sanda Suka tafi Mosque ne suka yiwa Daddy bayanin Komai kuma yaji Dadi, Da suka idar Suka kai Daddy Hotel din Sannan suka dawo gida " " Safeer da Shukra zaune a dakin su Ga abinci a gaban su "Shukrah yanzu bazaki ci abinci ba, kin taba ganin inda akayi haka? Bafa ke kadai bace ba " " Ni bazan ci wannan abin ba ta fada tana nuna masa plate din gabansu kamar zatayi kuka " " To naji me zaki ci " " Dan wake ta fada tana kwanta wa a jikinsa " " 😳Dan wake kuma Shukra? Haba da Allah yanzu a ina zan samu dan wake a nn, Kuma naga da ae bakya cin Dan waken " " Toni yanzu shi nake so ta fada tana fashe da kuka kamar an mata wani abun " " Rungume ta yayi tsam yana lallashi amma taki jinsa sai kara volume din kukan ma tayi " " Yi hakuri Shukra dan Allah ki fada min wani abun amma banda wanda bazan samu a nn ba " " To naji na canja Dan - Malele zanci " " Safeer kamar zeyi kuka yake ji, Tabarar Shukrah ta soma damunshi, "ynx fisabilillahi Shukrah a ina zan samu wani Dan -Malele a nn" "Toni shi zanci " " Shiru yayi mata be kara cewa komai ba ya janyo plate din ya fara cin abincin sa " " Shukrah ganin ya kyaleta ya sata fasa masa kuka sosai har tana bubbuga kirjinsa, Rike hannayenta yayi da nasa guda daya yana cigaba da cin abincin sa har anan bece mata komai " " Shiru tayi ta kara lafewa a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya har bacci ya dauketa " " Sai da ta gama cin abincin sannan ya kwantar da Shukrah a kan gado sannan ya dauki plate din yakai kitchen ya dawo ya kwanta a kusa da Shukrah bayan ya musu addu 'a, Da tunanin rigimar Shukra bacci ya dauke shi " " Cikin dare yunwa ta damu Shukrah ta mike ta fara bubbuga Pillow' n safeer, Bude idonsa yayi ya sauke su kan Shukrah da tayi kalar tausayi tana kallonsa " " Ya akayi? Ya tambayeta da muryan bacci " " yunwa nakeji ta fada tana jan hannunsa " " Mikewa yayi ya fita, kitchen ya je ya hada mata Tea sannan ya dawo ya samu ta shiga Toilet " " Tana fitowa ta nufi inda yake da sauri ta karfi cup din hannunsa bata damu da zafin da tea din yake da ba ta kafa kai ta fara sha, Bata ajiye ba sai da ta shanye tsat, Ta zauna bakin gado ta rufe idonta tana maida numfashi, Wani tausayin ta yaji yana shigarsa sosai " " wani zafi Shukrah taji tana ji sai gumi take, Ganin da yayi tana gumi ne yasashi shiga toilet ya hada mata ruwan wanka, Ya dawo ya daga ta ya cire mata rigar jikanta ya dauketa cak sai toilet, Da kansa yayi mata wanka sannan ya dauko ta ya dawo da Ita ya kwantar kan gado shima ya kwanta sai bacci " " Sai da Daddy yayi 1week a San Francisco, sosai yayi wa baby siyayya shima sannan Y soma shirin komawa Nigeria, Shukrah yar Rigima wae sai ta bishi,jin safeer be ce mata komai ba yasata yin shiru da maganar " " Ranar da Daddy ze koma dukansu ne suka rakashi Airport sai da su kaga tashin su sannan suka koma gida suma " " Yau ake taro bude Company 'n Ahmad, Sosai manyan mutane suka halarci taron kasan cewar Ahmad shahararre kuma fitacce a San Francisco state, Bayan gaishe gaishe, ciye ciye Ahmad ya gabatar da Safeer a matsayin Manager' nsa, sosai abun ya bawa Safeer mamaki don be taba tunani ba kuma koda wasa Ahmad be fada masa ba, " " Se bayan da aka kammala taron ne Safeer ya samu kebewa da Ahmad inda yayi masa godiyar wannan alherin da yayi masa " " Nan Ahmad ya nuna masa ba komai ae duk daya ne, Saf [4/22, 11:55 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 😘 2⃣8⃣ "Safeer ya kira Mamah ya fada mata irin Alherin da Ahmad ya masa, Nan Mamah ta bukaci Safeer ya hada ta da Ahmad din, Ya bashi wayar kuwa inda Mamah tayi masa godiya sosai sannan tayi masa Addu 'a, Sosai Ahmad din yaji dadin yadda Mamah tayi masa " " Yau saura kwana Biyar su Shukrah su koma Nigeria, Sosai Ahmad da Azeeza suke musu tsaraba wanda yawanci kayan Babe ne, Azeeza ce ma tayi wa Aysher da Miemie tsaraba, inda Ahmad yayi wa Mamah da Ammii tsaraba shi kuma " " Ana gobe zasu koma cikin gidan ba wanda yayi bacci suna tunanin rabuwa (sabo turken wawa), Jirgin bakwai da rabi zasu bi hakan yasa koda su safeer suka dawo daga mosque wanka ya shiga bayan ya fito ne itama Shukrah tayi " " 6:40am dukansu suka fito suka shiga mota Sai Airport, Cikin mota Shukra da Azeeza sai kuka suke sun rungume junansu, Suma su Safeer kawae dauriya suke irinta mazaje amma suna jin ba dadi a ransu wannan ne dalilin da yasa basu hana su kukan ba ma " " 7:30 aka fara kiran sunansu, safeer da kyar ya janye Shukra a jikin Azeeza bayan ya mata alkawari zasu sake dawo wa kafin ta haihu tunda shine manager 'n company' n Ahmad so akwai bukatar zuwansa San Francisco akai akai " " Sai da Su kaga tashin su sannan Ahmad yaja Azeeza mota wadda har anan kukan take (Sabo da dadi rabuwa ba dadi) " " A Nigeria Miemie da Aysher ne a kitchen suna ta girki kala kala, Dama Mamah ta nemi alfarmar Ammii kan tazo gidanta su tari su Shukrah gaba daya " " Ammii bata watsa kasa a idon Mamah don tun 9:00am sukazo ita da Areef " " To cikin jirgi Shukra sai kukanta take Safeer na Aikin lallashi, Da kyar ya samu tayi bacci sannan hankalinsa ya kwanta " " 2:00pm Jirgin su yayi landing a Airport na Malam Aminu kano, Suna fita Safeer ya kira Haiydar ya fada masa sun karaso sannan suka koma gefe suna jiran zuwan Haiydar din " " Bayan kamar minti ashirin sai ga Haiydar ya zo ya fito ya tayasu zuba kayan su a booth ya jasu sai Farm Centre " " Miemie najin tsayawar mota ta fito da gudu dai dai sanda Shukrah ke fito da ga motar Haiydar, Miemie tayi tsalle ta Rungume shukra cike da murnar Ganinta, ita ma Shukra da murnar ta ta rungume miemie suka shige gidan gaba daya " " Shukrah na ganin Ammii ta fada kanta ta rungume hade da sakar mata kukan shagwaba " " Baki Ammii ta saki tana kallon Shukrah da mamaki "Kukan na meye to Shukrah" "Na dadi ne Mamah ta bawa Ammii Answer " " Sai Anan Safeer da Haiydar Suka shigo gidan Nan fa aka shiga gaishe gaishe kowa fuskar sa dauke da fara 'a, Bayan an gama ne Aysher ta shiga kawo musu drinks " " Ruwa kawai Safeer yasha suka tafi Mosque shida Haiydar, To itama Shukrah Sallah tayi sannan tazo tace Miemie ta bata abinci taci don ita cikin nn harda wani mugun ci yasa mata " " Coconut rice da Egg sauce Miemie ta zuba mata sai mixed fruit ta ajiye mata a gaban ta, " " Ae Shukrah na kai Spoon din baki taji zuciyar ta ba tashi ta yarda Spoon din da sauri tana kokarin mikewa, Amma kafin ta mike tuni ta fara Amai a inda take " " A tare dukansu suka nufeta Aysher ta rike ta tana mata sannu jikinta sai rawa yake "Aysher ki dauke wannan abincin banason ganinsa Shukra ta fada a wahale" "Sai da Aysher ta dauke abincin takai kitchen sannan ta dawo ta fara gyara gurin " " Mamah ko rike Shukrah tayi suka shiga daki ta taimaka mata ta dauraye bakinta ta hada mata ruwan wanka ta shiga sannan ta dawo palour inda Ammii " " Sanda Safeer ya dawo gidan sai dube dube yake yanason ganin Shukrah Amma bai ganta, Kiran Miemie yayi da hannu ta dawo kusa dashi ta zauna " " Shukrah fa? Ya tambaye ta kasa kasa " " Nan miemie ta masa bayanin komai, aiko yayi saurin ture plate din gabansa ya shige dadin Mamah " " Tana kwance a kasa da alama fitowarta a wanka knn idonta a rufe kamar me bacci ya kara sa kusa da ita ya zauna, Shafa fuskarta da yayi ne yasa ta bude idonta da sukayi ja alamar tana jin jiki sosai " " Mikewa tayi ta shige jikinsa don ba abinda take bukata a halin yanzu sai shi, Tana so taji dumin jikinsa " " Kara rungume ta yayi tsam kamar za a kwace masa ita yana shafa gashi kanta har zuwa bayanta, yana mata rada a kunnenta " " Kara shigewa jikinsa tayi tana lumshe ido, ita kadai tasan abinda takeji a jikinta (Nace wannan ko sun manta a gidan Mamah suke) " " kokarin kunce towel din jikinta yake aka bude kofa ya juyo da sauri yana kallon kofa, miemi ya gani a tsaye ya watsa mata harara " " ME ya shigo dake cikin dakin nn? Ya tambayeta rai a bace " " Ammii ce tace in kira kaci abinci " " Dalla fita k bani guri ya fada yana nuna mata kofa " " Fita tayi da sauri dan tana tsoron bacin ransa " " Wayarsa ya ciro yana snapping fuskan Shukra, Kafin kuma ya shiga kiran Aysher " " Da Sallama tashigo cikin dakin Amma ganin a yanda suke yasata saurin juyawa " " Dariya yayi sannan ya ce ta daukowa Shukra kaya tasa " " Fita tayi bata wani dade ba ta dawo kanta a kasa ta mika masa kayan ta fice da sauri" "Da kansa ya saka wa Shukra kayan kafin ya soma lallabata kan tazo suci abinci amma tace bata san cin komai, da kyar ta yadda zata sha Tea " " 4:15 pm Ammii tace itafa gida zata tafi, Safeer ne ya maidata gidan sannan ya dawo " " Sai bayan Magrib Abbah ya dawo suka gaisa da Safeer ya kara masa murnar zama manager a San Francisco " " Shukra ma tazo suka gaisa da Abbah inda yayi ta samata albarka yana addu ar Allah ya sauke ta lafiya ya bada nagari " " Sai da sukayi Sallar isha sannan suka musu rakiya har mota suka tafi gidansu, Gidan tsaf yake don Aysher da Miemie sun zo jiya sun gyara" "Shukrah ce ta fara wanka tana fitowa ta kwanta sai baccin gajiya, Safeer ma da ya fito daga wankan kwanciya kawae yayi ya musu addu a sai bacci............ SAFIYA TA GARI SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞💞 [4/22, 7:37 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 💞 Wishes to show my appreciation to you Bilkisu galadanchi $Safiyya galadanchi for your luv, care and advice giving to me, I wish you Success where ever you may go more power to your elbows ❣ 2⃣9⃣ "Washe gari Safeer beje ko ina ba a gida ya yini, Sai bayan la 'asar ne Haiydar yazo, Sosai suka yi hira, Shukrah ta fito daga daki da gani a bacci ta tashi, Tana ganin Haiydar ta saki ranta suka shiga gaisawa cikeda girma ma juna, Kallon Safeer tayi taga ita yake kallo " " Ta bata rai tana harararsa' Zani gidan Ibtee tace tana turo baki " " Maida kallon sa yayi kan wayarsa yace 'Bazaki ba' " " Tafi minti biyu tsaye tana kallonsa kafin tasa kukan shagwaba harda bubbuga kafa a kasa kamar karamar yarinya " " Ganin ko kallonta yaki yi yasa ta zuwa gabansa ta Fisge wayar hannunsa "Ni wallahi sai ka kula ni" "Dariya Dukansu kusa sa ba kamar Safeer da yakeyi tsakani da Allah harda Sakkowa daga kujera " " Abin ya kara bata haushi dama yanzu abin haushi ba wuya yake mata ba, Ta kara fashe wa da kuka tana kallon Haiydar wanda yake kokarin tsayar da dariyar sa " " Harda kai ko? Nagode " " yi hakuri Shukra, Ki rabu dashi kinji, yi tafiyar ki gidan Ibtee ki tawo min da Amal in zaki dawo, Safeer ya fada kamar bashi ya gama mata dariya ba yanzu " " Bazani ba ta fada tana hullar da wayarsa a kasa sannan ta wuce dakinta ta rufe kofa harda key ta fada kan gado tana cigaba da kukanta " " A parlour Haiydar ya kalli Safeer "wae kae meye hk ne zaka sa yarinya a gaba kana mata dariya" "Dariyar ya kuma yi kafin yace ae mu biyu mukayi mata dariyar naga "inji Safeer " Amma ae taka tafi bata mata rai, wae meye ma abin dariya " " Ni mamaki ta bani Duk fa yau bata kulani ba in nayi mata magana sai tamin Shiru ko kallo ban isheta ba, shine ta bani dariya yanzu ae tazo tana wani bata rai wae zata gidan Ibtee " " Murmushi me kyau Haiydar yayi sannan yace me kayi mata taki kula ka? "wallahi ban mata komai ba rigima ce kawai irin tata " " To Allah ya kyauta Haiydar ya ce tana kallon wayarsa da ta shiga vibrating, Sanda Haiydar ya daga wayar shi kuma Safeer mikewa yayi ya shige Dakin Shukrah " " Tana zaune tana charting a bakin gado ya karasa kusa da ita ya zauna sannan ya karbe wayar Hannunta " " ME zaki ci, Ya tambaye ta yana kallonta " " Murya can ciki tace bakomai " " kamo hannayenta yai duka biyun yana kallon cikinta daya dan turo kadan dan ita shukra dama cikinta a shafe yake, "Haba Mana Shukrah Cute ya zaki ce ba zaki ci komai ba, ki daure ko tea kisha" "Ni bazan sha ba ta fada wane zatayi kuka " " Ni Gidan Ibtee zani tayi min Tuwo " " To Alhamdulillahi tunda zaki ci tuwon tashi na rakaki gidan Ibtee, Ya fada yana nikam da ita, Hijab ya dauka a kan gado ya sa mata ya rike Hannunta suka fito parlour inda tayiwa Haiydar sallama don ba da wuri zata dawo ba " " Har bakin gate din su Ibtee yakai Shukra yace ze jira ta ta kawo masa Amal, Tana shiga parlour taga Amal tana wasa ta dauketa takai masa sannan ta koma cikin gidan " " sanda ta shiga gidan taga Ibtee tana leka bayan kujera, Shukra ta hade rai don batason yin dariya " " Lafiya Ibtee, Meye a gurin shukra tace tana lekawa itama " " Ke banga Amal ba kuma fa wallahi yanzu na shiga daki na dawo kuma ban ganta ba Ibtee tace hankali tashe " " Shukrah ta gimtse dariyar ta ba tare da Ibtee ta gane ba tace to waye ya shigo gidan ya dauketa? dama baki rufe parlour ba? " " Inafa na rufe, keni zo mu fita Dalla ta fada sanda tasa Hijab dinta " " Ai kuwa bamuga ta zama ba Shukrah tace sannan tana hannun Ibtee suka fito " " Fitowarsu tayi dai dai da fitowar Haiydar da Safeer, Amal na hannun safeer ya bata wayarsa tana wasa da ita " " wata Nannauyar ajiyar zuciya Ibtee ta saki ta kalli Shukra, Shukrah ta tuntsire da Dariya harda rike ciki " " Ibtee takai mata duka 'bakida kirki Shukrah dama kinsan tana gidanki baki fadamin ba kikasa na tashi hankalina" "Har anan Shukrah dariya take taja hannun Ibtee ni zo muje kimin Tuwo shi nake so wallahi, " Kin jawa kanki ae bazan yiba" "Haba Ibtee Swthrt, matar abu turab, uwar gida sarautar mata daga ke ba kari, Maman Amal Beauty, dan Allah kimin tuwon kinji Shukrah ta fada sanda suka shigo parlourn " " To naji zanyi shknn Ibtee tace tana karasawa kitchen, ita kuma Shukrah tayi zaman ta a parlour dan in ta shiga kitchen taji kamshin miyar baxata iya ciba " " Sai ba adi salamu magrib sannan Shukrah ta koma cikin gidanta inda ta dauko Amal ta dawo wa da ibtee ita ta koma ta samu Safeer zaune a palour yana Aiki a system dinsa " " Ya Safeer zo muci tuwo ta fada tana ajiye flask din hannunta a kusa dashi, Ta wuce kitchen dauko plate da spoons ta zuba musu, Ta mike ta bude fridge ta dauko musu lacasera ta ajiye tana kallon Safeer " " Sai da ya kammala abinda yake sannan ya switching off system din sannan ya sauko suka soma cin abincin " " Washe gari gurin 11:00 Safeer yace Shukra ta shirya yakai ta gidan Ammii daga nan su biya su gaida Hajiyar Haiydar, Shukra harda dan tsalle ta shige toilet don yin wanka " " Safeer ya juya ze fita kenan ya hango wayar Shukra dan dressing mirror, Da sauri ya karasa ya dauka Kai tsaye contact dinta ya fara dubawa cikin sa 'a kuwa yaci karo da wata Number anyi saving as MY NUMBER, Da sauri ya dauko wayarsa ya dau Number yasa yayi dialing, Tana fara ringing yayi saurin Rejecting yayi mata Saving number sa as "HUSBY" "Sannan yayi saving tata number as "WIFEY" "Koda Shukrah ta fito da sauri ta shirya ta samu Ya Safeer a parlour suka kama hanyar gidan Ammii" "sanda suka isa Safeer ne ya dauko wa Shukrah tsarabar su Ammii suka shiga a tare cikin sa a kuwa suka tarar da Daddy na gida " " Safeer ya dade sosai yana hira da Daddy sannan Y musu sallama ya tafi " " Misalin karfe hudu da rabi wayar Shukrah dake hannun Areef ta soma ringing, mika mata yayi da sauri "Baki sake take kallon number ita dai tasan ba ita tayi saving number nn ba, Tana ta mamaki har kiran ya katse wani ya shigo, Sai anan ta dauka da Sallamar ta" "Jin muryan Safeer yana Answer mata sallama yasata sauke ajiyar zuciya" "ki fito mu tafi gidansu Haiydar" "To kawai tace sannan ta shiga dakin Mamah tayi mata sallama ta fito ta samu Safeer a motar sa suka tafi Gidansu Haiydar " " Sosai Shukrah ta samu karba ta musamman a gurin Hajiyar su Haiydar, Don Hajiyar Haiydar mace ce mai kirki da son mutane duk da kasan ce watar ta mai kudin gaske amma kudinta be sa mata girman kai ba " " Sai da sukayi sallar isha sannan suka koma gidansu inda Hajiya ta cika Shukrah da tsaraba, sosai Shukrah ta shiga ran Hajiyar don har tana tambayar ta sanda zata sake zuwar Mata......... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [4/27, 1:53 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 😘 3⃣0⃣ Three Months later "Shukra zaune a dakinta ta sa akwatuna a gaba tana duba wa zallar kayan Babe ne aciki, a zuciyarta tana mamakin irin wannan soyayya da iyayen ta, iyayen Safeer kai harma da Hajiyar Haiydar suke nuna wa babynta, takai one hour tana aikin kayan kafin ta ture kayan ta jingina a jikin gado tana shafa cikin ta dan wata shida wanda ya yayi girma sosai sai kace dan wata tara, Mamaki da tsoron girman cikin ya hana mata nutsuwa a yan kwanakin nan ga nauyi kamar me " " Tana cikin haka Safeer ya shigo cikin dakin yana Waya da alama da friend dinsa suke wayar, Sai da ya gama ya juyo yana karawa Shukrah kallo wadda gaba daya ma hankakinta baya wajensa, janyota yayi jikinsa yana shafa kanta " " Shukrah meye matsalar?? "Tsoro nakeji ya Safeer ta bashi Answer kamar zatayi kuka " " Dago kanta yayi yana mata kallon mamaki kafin yace tsoron me? "Wannan cikin mana yayi girma da yawa kamar wadda zata haifi guda goma " " To Shukrah ae lafiya ce, kuma ma ko guda goma kika haifa ai ba matsala bane indai Allah ya baki lafiya ko " " Kuka kawae tasaka masa wae ita BAZATA haifi guda goma ba " " Safeer dae yana mamakin Shukrah yanzu ba dama ayi magana sai tasa kuka, ayi mata wasa ta dauka da zafi, lallashinta yashiga yi yana cewa insha Allah daya zata haifa mai kama dashi tunda batason goma " " o o ni me kama dani zan haifa tace tana turo baki " " To naji Allah ya sauke ki lafiya shike nan " " A a " " Sai me kuma " " Sai da ta dauke kai kafin tace ni gidan Ammii zaka kaini " " Kema dae kya ji kunya Shukrah jiya fa har 10:00pm kina gidan Ammii kuma yau ma wae sa rai kike na kaiki " " Kukan ta ta cigaba wannan karon har tana hadawa da kaimai duka " " Ganin Abin Shukrah ba me kare bane yasa Safeer saurin ture ta a jikinsa ya mike ya fice, ita ko Kukan ta take tsakani da Allah a haka dae bacci ya kwashe ta a gurin " " Sai bayan sallah magrib sannan Safeer ya dawo gidan Shukra na zaune a parlour tana cin gireba, suna hada ido ta daure rai ta maida kallon ta jikin TV" "Yammata na, yanzu kina kallona na shigo cikin gidanki amma ba sannu da zuwa ba komai " " Ban iya ba tace ba tare da ta kalleshi ba " " Baki iya gaisuwa ba Shukrah ya fada sanda ya karaso kusa da ita yana binta da kallon mamaki " " To kaima baka iya dubiya ba ta fada tana murguda masa baki " " iye Shukrah ya Safeer din kike yiwa haka? Yayi maganar irin abin ya bashi mamakin nan " " komai ba tace ba sai ma juya masa baya datayi tana cin gireba hankali kwance " " Ya dade a tsaye yana mata kallon mamaki kafin ya girgiza kansa ya wuce dakinsa a ransa yana cewa "Shukrah dae ta zama a lallaba" "Shukrah na nan zaune har 9:00tayi, wayarta ce tayi ringing tayi saurin dauka kamar me jira DR WAHEEDA ta gani jikin screen din sai da tayi murmushi kafin tayi picking, tayi mata Sallama ta answer " " Bayan yan gaishe gaishe ne, waheeda tace Shukrah bakida kirki wallahi ace kin samu cikin har 6 Months amma baki fada min ba " " Shukrah wadda kunya ta rufe tayi murmushi batada abinda za tace shiyasa tayi shiru " " Kinyi Shiru Shukrah ko bakya jina ne? Waheeda ta tambaya " " Da kyar Shukrah ta ce mata kiyi hakuri ae nayi tunanin ya fada miki " " Inafa ya fada min, Ae zan gamu dashi ne kedai Allah ya sauke ki lafiya, Badai wata matsalar ko? "Ba matsala wlh " " Daga haka dae Shukrah yi sallama Shukrah dae har anan bata dena jin kunya ba, Don sosai take jin nauyin DR Waheeda hakan nema ya hanata sanar mata tun farko " " To kamar yadda Safeer Yayi wa Shukrah alkawarin zasu sake zuwa San Francisco haka kuwa akayi don yau Safeer Bayan ya tashi daga office Golden season travelling agency ya nufa kai tsaye yayi musu visa shida Shukrah da Miemie " " Sanda ya shigo gida tarar wa yayi Shukrah tayi baki wasu yan uwansu sune na katsina suka zo, Tsayawa yayi suka gaisa sannan ya wuce, Shukrah kamar bazata tashi ba tayi zamanta ta cigaba da hirar ta sai da wata Auntyn ta Aunty Nabeehart ta harare ta " Kin tashi kin bi mijin ki ko sai na kwada miki mari tukun na" "Turo baki Shukrah tayi ta tashi tana cewa Aunty fa banida lpy sannan ta shige dakin Safeer " " Sanda ta shiga ta samu har ya shige wanka saboda haka sai kawae ta fito mai da kaya tayi kwanciyar ta kana game a wayar sa " " Sanda ya fito gaban dressing mirror ya nufa ya dauko cream ya dawo kusada Shukrah ya zauna, Tana ganin haka tayi saurin minimizing game din ta ajiye wayar ta mike, sai da ta karbi cream din hannunsa sannan ta kalleshi ta fara magana kasa kasa "Ya Safeer ka dawo lafiya ya office? " Alhamdulillahi, Yau na zo miki da albishir " " Cikeda zumudi tace ya Safeer menene dan Allah "? " Inna fada miki me zaki bani as a gift " " Duk me kake so zan baka wallahi " " Are you sure! Yace in between laughter dan shi kadae yasan tanadin da yayi mata " " Absolutely sure inji Shukra don bata me yayi ba, "To shknn zan fada miki koma menene amma ba ynx ba sai dare " " me yasa sai dare Shukrah ta tambaya cikeda rashin fahimta "banason tambaya tayi yawa tunda nace sai dare ae saiki hakura ko" "Shukra bata sake cewa komai ba har dae ta gama shafa masa cream din ta koma wajen bak'in ta " " Da daddare bayan Safeer ya fito daga masallaci be wuce ko inava sai gidan Mamah inda yayi mata bayanin tafiyar tasu, ya kuma fada mata tare da Miemie zasu tafi " " Miemie da tunda ya shigo cikin gidan ta rufe idonta kamar me bacci wae don karta gaishesa ta fasa ihu hade da duro wa daga kan kujera " " Ya Safeer dan Allah dani zaka tafi San Francisco wayyo dadi, Wayaga Miemie a cikin turawa wai! A gaskiya ka gama min komai wallahi God bless your unborn Babe ta karasa harda yar rawar ta " " Baki sake Safeer ke kallon ta haka kuma rai a hade, azuciyarsa yana daya sanin yi mata visa, Wai dama ba bacci take ba tsabar iskanci ne ya hanata gaida shi "" "Wata uwar tsawa ya mata wadda ba Miemie ba har Mamah da Aysher da Abbah dake kokarin shigowa parlourn sai da suka tsorata "Bakida hankali ko, to wallahi ki kama kanki kinsan me yake miki ciwo, in kuma kinki wallahi zan baki mamaki useless kawai" "Abbah ne ya karaso cikin parlourn ya dafa kan Safeer sannan yace''kayi hakuri babban yaya sai hakuri addu a zaka tayata da ita kaji " " To kawai yace sannan ya mike yana kallon Mamah yace''ta shirya wednesday zanzo na tafi da ita tunda friday zamu tafi, yana kaiwa nan ya fice daga gidan " " Tafiyar 40mints ne ya kaishi gidansa, a parlour ya tarar da Shukrah a kwance kamar me bacci, ya kara so kusada ita ya dauke ta cak sai a kan bed bayan ya sauketa ya shige toilet sai anan Shukrah ta bude idonta don kwanciyar bata mata dadi ba " " Minti goma ya yayi yana shiryawa bayan ya fito a wanka, kan bed yahau ya zauna kusa da Shukrah ya riko hannunta ya akayi ne Shukrah cute? "Abinda zaka fada min dazu kace na bari sai dare zaka fadamin " " Me kike ci na baka na zuba ae ynx zan fada miki, kedai ba kince duk me nakeso zaki baniba " " Saurin daga masa kai tayi don ta matsu taji me zai ce " " Good gal dama fada miki zanyi Friday zamu tafi San Francisco " " Ae Shukrah batasan sanda ta fada jikin Safeer ta kankame shiba " " Shima kankame ta yayi hade da zame rigar jikinta ya zura harshen sa cikin bakinta yana tsotsa as if ya samu sweet ne.............. SASSANYAR ASUBA TA GARI 👌🏻 [4/28, 7:08 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie ❣ 3⃣1⃣ "Yau tuesday Safeer na zaune a office dinsa da yamma misalin karfe 3:20pm Haiydar ya shigo da sallama a bakinsa, Sai da Safeer ya answer masa kafin ya kariso ya zauna yana facing Dinsa " " Ajiye Files din hannun sa yayi sannan ya ce "Haiydar ya Aikin? " Alhamdulillahi " " Dan Allah ka tayani yiwa Hajiya Godiya tana ta hidima wallahi Allah dae ya kara girma " " Sai da Haiydar yayi murmushi kafin yace ae bakomai Safeer yiwa kaine " " Duk da haka dae kae mata godiyar " " To insha Allah zan mata, Daga nan dae suka cigaba da Hirar su wanda mafi akasarin hirar dae akan Miemie ake yinta, Har sai da ran su ya baci dukansu sannan Haiydar ya mike yana bin Safeer da Mugun kallo " " Ae dama na dade da sanin baka sona da kanwar ka shiyasa kake ta wani kakkaucewa to wallahi duk a binka sai na Auri miemie insha Allah, kuma gobe xanje na samu Abban na masa magana da kaina Haiydar ya fada yana nuna safeer 👉🏻" "Murmushi Safeer yayi yana mikewa da niyyar fita sannan yace Haiydar kanada Matsala wallahi kullum anyi ta maimata magana daya ne wae, Haba da Allah be a man mana me xakayi da wata miemie yarinya ko gama mallakar hankali batayi ba " " Naji koma me zakace sai dae kace amma dae sai naje na samu Abbah inyaso kafin naje ka rigani zuwa ka zuga kaji ko " " Ni na isa na zuga shi Haiydar Allah ya bada sa a kaje wallahi, Kuma Allah ya huci zuciyarka " Daga nn dukansu suka fito kowa ya shige motar sa ba tare da sunyi sallama ba" "Sanda Safeer ya isa Gida Shukrah na kitchen tana toasting bread, ta fito da sauri tazo ta kama hannun sa tana masa sannu da zuwa " " ME ake mana ne Shukrah cute naji gidan kamshi Safeer yace yana rungumo Shukrah jikin sa " " Bread nake toasting wallahi yau shi nake Sha 'awa shukra tace sanda suka karasa dakin, Shigewa toilet tayi don hada masa ruwan wanka shikuma ya cire kayan jikinsa ya daura towel ya bi bayanta " " A bakin kofa suka hadu, ta raba zata wuce ta gefensa yay saurin janyota, "Ina zaki kuma? " Kitchen zan koma ta bashi answer tana kokarin janye jikin ta a nasa " " Ya kwantar da murya kamar me shirin yin kuka 'Da wanka zaki min Wallahi na gaji yau tunda na zauna ban tashi ba " " Dariya tayi sannan ta kwace jikinta ta fita da sauri tana masa gwalo, shima dariyar yayi sannan ya fara wankan sa " " sanda ya fito ya samu shukra a parlour tana cin toasted bread nata nan yayi joining dinta suna ci suna hirar su abin sha, awa, sanda suka kammala Shukrah ta kai bowl din kitchen ta dawo ta sameshi suka cigaba da hirar su har zuwa lokacin sallar magrib sannan Safeer ya fita mosque ita kuma tashiga daki don yin sallah " " Washe gari Safeer beje office ba a gida ya zauna ya taya Shukrah hada musu trolley sai bayan sallah la 'asar sannan ya tafi gidan Mamah dauko Miemie kamar yadda ya mata alkawari , Sanda ya shiga gidan Miemie ce kadai a parlourn Aysher na kitchen, Mamah kuma na sama, Miemie tasa trolley a gaba ta buga tagumi harda dan hawayenta don ta gama fitar da ran zuwan Safeer, Ae tana ganin ta fasa ihun murna ta nufo shi da gudun ta, Saurin dakatar da ita yayi ta hanyar mata wata gigitcciyar tsawa "Kina kara sowa nan sai na kwada miki mari wallahi, shashasha kawai" "Kuka ta fasa tana kwalawa Mamah kira kamar Safeer yamata wani abun , A tare Mamah da Aysher suka iso parlour'n suna tambayar ta lafiya " " Ba yaya Safeer din nan bane bezo da wuri ba kuma yanzu yazo wae ze mare ni, Miemie ta fada cikeda da shawgwaba tana kara fashe wa da kuka " " Ba Safeer hatta Mamah da Aysher da Abbah da ya shigo yanzu sakin baki sukayi suna mamakin Karfin hali irin na Miemie " " Kinsa Allah in baki rufe min bakin ki a gurin ba zan fasa shi inyaso kiyi me dalili Safeer yace rai a bace " " Ganin da gaske yake yasa Miemie sa hannunta ta rufe bakinta tana sauke ajiyar zuciya, zuwa can ta dawo kusa dashi ta durkusa har kasa sannan tace "Ya Safeer Dan Allah kayi hakuri kaje dani wallahi na dena rashin ji" "Komai beceba sai juyawa da yayi gurin Abbah suka gaisa sannan yayi wa Aysher da Mamah Sallama, ya juyo yana hararar Miemie wadda har ynx take a durku she a gaban sa "Kin dau trolley mun tafi ko sai na bigeki tukun, Da sauri Miemie ta dau Trolley tayi gaba abinta ko sallama bata yiwa su Mamah" "Cikin Mota Ko kallo Miemie bata ishi Safeer ba, ita kuwa sai satar kallon sa take, kula da hakan da yayi ne yasa shi kallon ta tayi Saurin sunkuyar da kai kasa, sai yaji ta basa tausayi, Har ga Allah yana son Miemie fiye da Aysher ma amma halinta ne ke hada su fada, " " Meye kike kallona ya fada yana maida kallon sa ga titi " " Bakomai tace tana kallon gefe, shiru ne kuma ya biyo baya har suka karisa gidansa " " Shukrah najin horn tayi Saurin leko wa, ae MIEMIE na ganinta ta saki trolley hannunta taje da gudu zata rungumeta, Ae Safeer ma sai ya sa gudu ya riga miemie zuwa ya shiga tsakanin su yana wa Miemie wani mugun kallo, "Nawa ake biyana a gidanku da zaki barmin trolley a wajen nufinki na dauko. Miki ko, kuma da kika tawo da gudu da me zakiyi" "jiki a sanya ye Miemie ta koma ta dauko trolley ta zo tashiga gidan " " Yau ta kama friday kuma yau zasu tafi San Francisco, kasancewar jirgin 8:00am zasu bi yasa suka gama shirin su tun 7:00 suka fito suka tafi daukan Aysher a gidan Mamah don ita zata dawo da motar gida, 7:40 a Airport ta musu, Nan aka zauna hira har sai da aka kira su, sukayi sallama da Aysher suka Shige jirgi" "Cikin jirgi Shukrah da Miemie duk bacci sukayi tayi har sai da jirgin su yayi landing a San Francisco sannan suka farka, Shukrah ce ta fara fita sannan Safeer, miemie na ziro kai ta shaki iska me sanyi, ae bata san sanda ta saki ihu ba ta ware hannayenta duka biyun ta rufe idonta tace""Wayyo Allah wayaga Miemie a sabuwar duniya, Ni anya ma kuwa zan koma gida " " Ae Safeer besan sanda ya finciko ta ya matse bakinta cikeda da Bacin rai ba don iya kunyata wa ta kunyata sa............. SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [5/1, 6:22 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie bie 💞 3⃣2⃣ "Ahmad Safeer ya kira ya shaida masa sun iso sannan suka koma gefe suka zauna miemie tacika tayi fam kamar zatayi kuka don taji zafin matse mata bakin da safeer yayi, Sai hararan sa takeyi kasa kasa shiko bema san tanayi ba don duk hankalinsa nakan Shukrah da take masa hira sai dariya suke abinsu " " Zaman kamar minti talatin sukayi wayar Safeer ta fara ringing, yai Saurin cirota a pocket dinsa sunan Ahmad da ya gani ne yasa shi Saurin picking don ya gaji da zaman gurin " " Mun iso fa kuna wajen ina "Ahmad ne ke masa wannan tambayar? " Mikewa yayi sai ya hango Ahmad da Azeeza, Gani ina hango kuma bari mu karaso Safeer yace yana yiwa Shukrah da Miemie alamar su taso, Kafin sukayi sallama da Ahmad " " Sanda suka karasa inda suke Shukrah tayi tsalle ta rungume Azeeza ta ma manta da cikin dake jikin ta "Kibi A hankali Shukrah karkije ki bige mana Babyn mu inji Ahmad, sai a nn Shukrah ta tuno da cikin tai Saurin dafe wa sakamakon wani juyawa da taji yana yi ta runtse idonta sosai, Sannu kawae suke mata bama kamar Safeer daya bi ya rude, Azeeza ko ji tayi dama a jikin ta ciwon yake don tana jin Shukrah a ranta ta dauke ta kamar lil sis din ta Zafeera " " A haka dae suka shiga motar Ahmad yaja su, ko cikin motar Shukrah na dafe da cikinta ta kwanto a jikin Safeer sai Sannu yake mata, Tafiyar kusan minti goma sukayi sannan suka isa gidan Azeeza ta fara fita ta bude kofar parlour sannan Miemie da Ahmad suka fito, Safeer ne karshen shiga gidan rike da Shukrah tanata kukan shagwaba wae ciwo, Niko nace wannan yarinyar ta fiye dangwa lolo 🤣" "Azeeza taja hannun Miemie ta kaita wani karamin Room tace tayi wanka sannan taje ta dauko mata trolley dinta, Sanda ta dawo har miemie ta shige toilet hakan ne yasa ta fita ta wuce kitchen tana kwaso flask tana kae wa dinning sai da ta gama shirya dinning din sannan ta wuce dakin ta " " 30 minutes later " " Dukansu na zaune a dinning suna cin abinci, Miemie na kusa da Azeeza suna hira, Miemie tace Aunty can you do me a favour pls " " why not! What do you want? "I want you to take me out just to see your state " " ok i promise to take you difference places like Zoological garden, Cinema and shopping mall " " Cike da murna Miemie tace When? "Next tomorrow insha Allah inji Azeeza " " Ae MIEMIE bata san sanda ta mike ta fara rawa ba 💃🏻💃🏻, Ahmad da Azeeza sai dariya suke mata don ta shiga ransu sosai a dan zuwan nn nata, Takaichi ya cika Safeer gashi ba kusa dashi take ba balle ya kwada mata mari ko ya huce takaichi, Yayi ta jifanta da harara amma ta share as if to say ba da ita yake ba, " " Azeeza tace Miemie you are very good in dancing when are you going to teach me? "Till you take me out, Then i will teach you different types of dance " " Am so grateful that you are here you are such a durlin Miemie inji Azeeza tana fara a jitake dama za a bar mata miemie don ba karamin son yarinyar take ba, cus she's very clever " " Safeer dae da haushi ya ishe sa sai kawae ya mike ya shige dakinsu suko basu kawo komai a ransu ba suka cigaba da cin abincin su suna hirar su " " Da daddare bayan kowa ya shige dakinsa Safeer ya shigo dakin Miemie lokacin tana tsaye tana shirin kwanciya ya hade rai yana kallon ta "Bakida hankali ko Miemie, Ke bazaki nitsu ba a rayuwar ki ko kin fi son kiyita hauka ana miki dariya ko, kin dauka birgewa ce wannan? Shekara goma sha uku amma bakida nitsuwa ko kadan, You have to maintain your dignity or else you will regret your life coming to this world, stupid gal kawae yana gama fadar haka ya fice rai bace " " Miemie dae ta dade a tsaye tana tunanin rayuwar ta Tanaji a ranta ya kamata ta kama kanta ta dena abinda take ko zasu shirya da Brother 'n ta, haka dae ta kwanta ranta ba dadi har bacci ya kwashe ta " " Washe gari tare Safeer suka fita da Ahmad, Safeer ya tarar da aiyuka birjik a office saboda haka ne ma koda lokacin tashin Ahmad yayi safeer cewa yayi baze bishi ba sai ya gama aikinsa ya tawo daga baya, hakan kuwa akayi Ahmad yaje yahau commercial car ya bawa Safeer car key dinsa yace ya tawo a ciki " " Sanda Shukrah ta jiyo Sallamar Ahmad ta yunkura ta mike dakyar don cikinta ba karamin girma yayi ba ta fito parlour taga Azeeza na welcoming Ahmad, sai tayi turus ganin Ahmad kamar shi kadae ya dawo, to shi Safeer din a ina ya tsaya? Kamar Ahmad yasan me Shukrah take tunani yace safeer ko? Na baro shi a office yace in kin ganshi a gidan nn yau to ki tabbatar ya gama ayyukan sa ne "Shukrah dae kamar zatayi kuka ta ce to Allah ya dawo da shi lafiya sannan taja kafarta da kyar ta koma daki tayi kwanciyar ta kan centre carpet bata wani dade ba kuma bacci me nauyi ya kwashe ta" "Sai ba adi salatul Magrib Safeer ya shigo gidan a gajiye, Azeeza da Miemie ya samu a parlour don Ahmad be dawo mosque ba, Miemie tayi masa sannu da zuwa sannan ta karbi brief case din hannunsa ta kai masa daki, sai da ya gaisa da Azeeza sannan ya wuce dakinsu nan yaga Shukrah a kwance tanata bacci abinta sai yaji ta bashi tausayi tuno war da yayi jiya be barta ta samu baccin kirki ba, nan dae ya cire kayan jikinsa ya daura towel sannan ya shige toilet don yin wanka, " " Sanda ya fito Strait gurin Shukrah ya wuce ya zauna a gefenta ya dago ta ya rungumeta tsam a jikinsa sannan ya sa hannunsa cikin lallausan gashin kanta yana shafawa a hankali sai a nn Shukrah ta bude idonta ae suna hada ido ta fashe da kuka tana kokarin sauka a jikinsa, kara rike ta yayi sosai sannan cikeda lallashi yace Me kuma nayi ake min kuka, yi hakuri kinji Shukrah cute " " Lafewa tayi a jikinsa tana sauke ajiyan zuciya sannan tace 'Bakai bane ka tafi kayi zaman ka a office ba " " Eyya yi hakuri kinji bazan kara ba " " To kawae tace tana murmushi daga nn kuma suka cigaba da hirar su, Tuni Shukrah ta manta da fushin da take ta ware sai zuba hira suke suna dariya abinsu " " Washe gari Kamar yadda Azeeza tayi promising Miemie zasu fita hk kuwa akayi 3:20 suka fita su biyu dan Shukrah cewa tayi baxata bisu ba, Azeeza ce tayi driving basu zame ko inaba sai zoological garden, Sosai gurin ya burge Miemie, sundan dade a gurin kafin kuma suka wuce Cinema suka yi kallo daga nn kuma suka wuce wani shopping mall Azeeza tace Miemie tadau duk me take so, Miemie dae bata dau komai ba sai wani Makeup kit data dauka (Dama Miemie mayyar makeup ce) "Daga nn dae suka dawo a gajiye, wanka kawae sukayi suka ci abinci suka kwanta sai bacci......... SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [5/4, 4:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Dedicated to Miemie Bie 💞 3⃣3⃣ "Yau ta kama wednesday kuma yau ce ranar da Miemie bazata taba mantawa ba a rayuwar ta, 12:23pm Miemie na kwance a dakinta taji cikin ta ta juya ta mike ta shiga toilet, Tsugunar da zatayi taga jini ya zuba me zatayi in ba ihu, Don ta tsorata iya tsorata though an fada musu a islamiyya amma abun yazo mata unexpectedly, Mikewa tayi a tsorace taba kuka kamar dan shi aka aikota tana bubbude kafa kamar me koyon tafiya a hk ta fito palour, Bataga kowa a parlour ba saboda hk sai ta wuce dakinsu Shukrah " " Sanda ta shiga dakin Shukrah na toilet Safeer ne kwance yana duba wayar sa, Motsin da yaji ne yasa shi Saurin dago wa, Miemie ya gani ta wani ware kafar ta tana kuka sosai " " Ke zonan, Me ya sami kafar safeer yace sanda ya ajiye wayar sa akan bed side drawer " " Karasa wa tayi still tana kuka, Tana kokarin daga skirt dinta, Safeer ya rike hannunta, meya same kine wae? "Ba jinayi inajin fitsari ba nashiga toilet ina tsuguna wa naga jini yana fita a nn ba, Ta karashe maganar tana fashe wa da kuka, haka kuma tana nuna masa gurin " " Dan murmushi Safeer yayi don ya gane gaskiyar abinda ya daga hankalin Miemie, " " To naji na fahimta Ae ba wani abu Bane dena kukan kizo nan, safeer yace a kokarin sa na kwantar wa da Miemie hankali, "Karasowa tayi ta tsaya a gefen sa, tana goge hawayenta " " Ae a islamiyya an fada muku cewa duk jinin daya fito a jikin mace yar shekara tara zuwa sama, jinin haila ne ko? Inji Safeer, Daga masa kai kawae miemie tayi alamar Eh, Good, Shekaranki nawa? 13,"ta Bashi answer " To Kinga wannan jinin na Haila ne bana ciwo ba so ki kwantar da hankalin ki, An koya muku wankan tsarki? " Eh an koya mana miemie ta basa answer kasa kasa don wata kunyar sa ne taji ta rufe ta " " Yawwa to yimin bayanin yadda aka koya miki inji, Fitowar Shukrah a toilet yasa duk suka mayar da hankalin su kanta, ta rike hannun Miemie tajata zuwa Toilet, " " Cikin kayanki akwai sabon pant Shukrah ta tambayi Miemie? "Ehhh akwai, Miemie ta bata answer, To ina zuwa yanzu ki cire kayanki kiyi wanka kinji inji Shukrah inda tana gama maganar ta ta fito hade da rufe wa Miemie kofar toilet din" "Kai tsaye Shukrah dakin Miemie ta wuce ta bude trolley dinta ta dakko sabon pant ta dawo dakin su ta Shirya dan dama a wanka ta fito, Sanda Shukrah ta gama shiryawa toilet taje tana bugawa don ta fuskanci Miemie ta gama wankan kunya ta hanata fito wa" "Bude min kofa kinji Miemie " " Kamar bazata bude ba sai kuma ta bude, idonta a kasa don wani nauyin su takeji dukan su, Shukrah tace Miemie dago kiga, Miemie ta dago a hankali, nan Shukrah ta shiga nunawa Miemie yadda ake sa Pad a jikin pant sannan ta mika mata ta fice " " Bayan kamar minti goma Miemie ta fito don taga tsaiwar bazata kaimata ba, Kanta a kasa tayi hanyar kofa, Safeer yace zonan Miemie, jiki a sanyaye Ta dawo ta zauna a kasa kusa da Shukrah, safeer yace baki min bayanin yadda ake wankan ba " " Kunya ta kama Miemie tayi kasa da kai tana wasa da danyatsanta, ehen ina jinki Miemie, shi Safeer ma mamaki Miemie take basa yadda take wani kasa dakai" "Shukrah tace Miemie ko ya Safeer ya fita ni kimin bayani? Daga mata kai Miemie tayi, hakan yasa Safeer kara mikewa akan gado, ke nake sauraro Miemie karki bata min lokaci don bacci zanyi, Miemie ganin ba sarki sai Allah yasa ta bude baki da kyar ta fara masa bayani kamar hk : "Da farko zan samu ruwa mai kyau wanda dandanon sa ko kamshin sa ko colourn sa bai changer ba, Idan a budadden abu yake kamar bucket sai na karkata nazuba ruwan na wanke hannuna sau uku, in kuma a rufaffen a bune kamar kettle basai na wanke hannunba tunda ba taba ruwan zanyi ba, tana kaiwa nn ta dago ta kallo shi idonsa a kanta, ya daga mata kai alamar ta cigaba, tayi murmushi ta dora : "sai nayi alwala dai dai, wasu sunce bazan wanke kafa ba sai an zo karshan wankan wasu malaman kuma sunce za a wanke, Sai na hade hannayena duka biyun na cika su da ruwa na zuba a kaina na tabbatar ko ina ya samu zanyi hakan sau uku, daga nn kuma sai na raba jikina biyu a tsaye na fara wanke side din dama na sannan na hagu........ "Masha Allah Allah ya albarkachi rayuwar ki kinji inji Safeer, Shukrah ta kalli miemie tace kinyi kokari sosai, Maganar Safeer tasasu juyowa dukansu suna kallo sa, To Miemie sai ki nutsu yanzu kisan me ya dace dake banda wasa da Maza, su rike hannun namiji ko hawa cinyarsa, in ba hk ba wallahi zaki samu ciki, kuma kinsan ba kyau ae ko " " Miemie fa cikinta ya duri ruwa ta gama tsorata sai raba ido take kamar tayi wa sarki karya, haka dae Safeer da Shukrah sukayi tayi wa Miemie nasiha, Miemie harda kukanta bayan sun gama Miemie ta mike jiki ba kwari ta shige dakinta ta kwanta sai bacci... "Haka rayuwa ta cigaba bayan kwana uku Miemie ta tsarkake kanta ta cigaba da rayuwar ta, " " Yau watan su daya a San Francisco kuma next week Miemie zata koma school hakan yasa da daddare Mamah, aysher da Abbah suna zaune a parlour suna hira har suka gangaro maganar Safeer, Mamah tace Au bari ma nakira shi ya kawo min yarinyata tunda shi zaman can be ishe shiba, Mamah ta janyo wayarta takira Safeer Ringing biyu yayi picking da sallamar sa, Suka gaisa da Mamah " " Tunda zaman San Francisco bae ishe kuba kana iya kawo min yarinya ta next week zata koma school " " Insha Allah Mamah jibi zaki ganta gobe da safe zan mata visa, Amma ni bazan samu zuwa ba wallahi aiki yamin yawa anan " " Kai dae kasani nidai kawae naga yarinyata ehe inji Mamah " " Yar dariya Safeer yayi yace insha Allah zaki ganta, my regards to Aysher daga hk sukayi sallama " " washe gari sanda Safeer zashi office ya tsaya yaywa Miemie visa sannan ya wuce " " sanda ya tashi a office ma beje gidan ba sai da ya tsaya a market yayi wa Miemie siyayya sosai sannan ya wuce gidan " " Washe gari Miemie jirgin 12:00 zatabi, 11:30 dukansu suka shiga mota Ahmad yaja su sai Airport, Azeeza ta siyawa miemie wani Makeup kit, Miemie sai godiya take mata suna haka har 12:00 tayi aka kira Miemie sanda zata wuce Ahmad ya bata wata lada, taja trolley ta wuce tana masa godiya " " Da daddare Safeer ya kira Mamah ya tabbatar Miemie ta sauka lafiya suka taba hira da Aysher kafin sukayi sallama, Nan ya kira Abbah suka gaisa sannan ya kira Daddy 'n Shukrah suka gaisa......... 💞 [5/7, 6:12 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻 WRITTEN BY *ZAINAB YAKASAI* *SHUKRAH* Dedicated to *MIEMIEBEE* 3⃣4⃣ *Nigeria* "Aysher kwance a kan gado tana duba wani handout yayin da Miemie take gefen ta zaune tana duba kayan da ta dawo dasu Daga San Francisco, poly thene din da Ahmad ya bata ta dago da sauri dan taji kamar kwali ne a ciki, budewa tayi me zata gani inba waya ba IPhone 6s+ ta bude idon ta sosai tanaso ta gasgata abin da idon nata ke fada mata, iPhone din dae ta gani, ta fasa ihun murna, Aysher ta juyo da Sauri tana binta da harara don ita har ga Allah tayi tunanin wani abu ya same ta Amma ta ganta a zaune kuma har a lokacin ihun take " " Meye hk Dalla malama ina bacci zaki dinga min ihu, inji Aysher ta fadi ranta a bace " " Aunty Aysher ki tashi Uncle Ahmad abokin ya Safeer ne ya sai mun IPhone 6s+, Miemie tace tana janyo Hannun Aysher zata tayar da ita " " Da sauri Aysher ta tashi tana zare ido ganin da gaske IPhone din ce a gaban ta, kin nuna wa Mamah ne,? Aysher ta tambayi miemie " " Nima fa ban saniba kawae dae ya bani polythene ne Dazan tawo so ban bude ba sai ynx nake gani Miemie ta bata Answer sanda take saukowa akan bed ta fice ta shiga dakin Mamah, Abbah zaune a gefen bed yana duba wasu papers yayinda Mamah take kwance akan bed din da Alama ta fara bacci" "Ihun Miemie ne ya sa suka dago dukansu da sauri suna kallon ta, ta karaso cikin dakin da gudun ta tana mikawa Abbah Wayar hannunta " " Abbah kagani Uncle Ahmad ne ya bani ita " " Murmushi Abban yayi sanda ya karbi wayar yana kallonta kafin ya dago yace "Miemie ae wannan wayar ta miki girma kinsan ma fa ni banason rike waya da wuri saboda batawa yaro brain yake, haka kuma yana bata tarbiyya" "Wallahi kam, ae kawae karike mata wannan sai tayi graduation (Candy) sai ka bata, in wayar take so sai ka siya mata baby nokia ta dinga communicating da friends nata, Mamah dake kwance har a lokacin ta fada ba tare da ta dago kanta ta kalli Miemie ba " " Miemie ta bata rai kamar zatayi kuka tana kallon Abbah daya maida kansa jikin papers dinsa yana cigaba da dubawa, Abbah Please karka ji Mamah ka bani wayana kaji " " Ae kinji me na fada miki bazan bayar ba, zan siya miki karama wannan sai kin gama skul zan baki Abbah yace sanda ya mike ya shige toilet " " Kuka kawae Miemie tasa ta juya ta shiga dakinsu inda ta tarar Har Aysher tayi bacci, nan ta kwanta tana kuka a hk har bacci ya dauke ta " " To Rayuwa ta cigaba da tafiya, ynx Aysher ta kai level three (3)a B. U. K inda take karantar nursing, so ynx haka madai anyi posting su Aysher hospitals daban daban don yin practicals inda Aka kai aysher Malam Aminu kano teaching hospital, so Aysher bata wani shan wahala kasancewar ta mai kokarin gaske, sosai Doctors din keji da ita kasan dae itace over roller, " " Aysher da kawayenta Maryam da Nuriyya tsaye a var render 'n S. O P. D da wani handout a hannunsu suna duba wa, gabaki daya hankalin su nakan abinda suke, Sallamar da sukaji anyi musu ne yasasu Saurin juyo wa suna kallonsa " " Black jeans ne ajikinsa da white t~shirt yayinda ya dora white lab ~coat akai yayi un buttoning lab coat din, kafarsa sanye da wani black shoe hannunsa daure da white watch, Answer sallamar sukayi cikeda ladabi don shine doctor'n da aka hada su da yanada sakin fuska sosai shiyasa suka saba dashi sosai " " Cikeda fara a ya answer gaisuwan su sannan ya kalli Aysher wadda gaba daya hankalin ta nakan handout, Aysher in kin gama ki sameni a office yace kafin ya juya ya koma office dinsa " " Mikawa Nuriyya handout din tayi sannan tabi bayansa, Be dade da zuwa office dinba ta shiga itama, kara gaisawa sukayi kafin kuma sukayi shiru tsawon minti goma, zuwa can yace "Aysher wata magana zamuyi dake to amma kuma naga kamar Karatu kike so kibani number ki inyaso sai muyi magana a waya ko zuwa anjima ne" "Badan Aysher taso ba sai dan kawae ganin girman sa da take ne yasa ta karbi wayansa da yake miko mata ta sa masa number ta ta mika masa, Hannu ya miko mata alamar ta basa wayarta aiko ba musu ta miko masa nan dae yayi mata saving number sa as Mahmoud sannan ya bata, ta masa sallama ta fice " " Bayan kamar kwana 2 da faruwar Hakan Mahmoud ya kira Aysher suka gaisa, Aysher batayi wani mamakin jin cewa Mahmoud yana sonta ba don dama ta dade da ganin alama, Mahmoud dae be kyale Aysher ba har sai da ya tabbatar ya samu shiga " *San Francisco* " Shukrah da Azeeza zaune a parlour suna hirar haihuwar Shukrah don yanzu cikin nata nada wata takwas kenan, inda Azeeza ke cewa ita tafi son a haifi Namiji ita kuma Shukrah wae tafi son Mace suna cikin wannan musun ne Ahmad da Safeer suka shigo da kaya masu uban yawa daga gani dae daga kasuwa suke, Azeeza ta mike ta karbi kayan ta shige dasu wani dan karamin daki inda anan ne suka ware don tara kayan Baby, Shukrah dae daga zaunen da take ta musu welcome don baxata iya tashiba saboda swelling da legs nata sukayi, Safeer ne ya karaso inda take ya durkusa gaban ta ya fara massaging mata legs din har sai da ya tabbatar swelling din ya ragu sosai sannan ya taimaka mata ta mike suka shige dakinsu, a tare sukayi wanka bayan sun shirya suka dawo parlour inda Safeer da Ahmad suka fice Azeeza kuma ta shige kitchen " " White spaghetti ta musu bayan ta gama ta daura soup kan gas, bata wani dau lokaci ba ta gama ta dauko flask set din ta jera a dining sannan ta dawo parlour tayi joining Shukrah suka cigaba da hirar su har lokacin magrib yayi suka tashi sukayi " " Ba *Ahmad* da *Safeer* suka dawo ba sai ba'adi salatul Isha, abinci sukaci a tare suka danyi kallo sannan sukayi wa junansu sallama Suka shige dakinsu, *Shukrah* ce kawae ta sake wanka don cikin nn yana sa mata jin zafi sosai,Sanda ta fito har Safeer yayi bacci saboda haka itama ta kwanta gefen shi sai bacci " " To rayuwa tanata tafiya don ynx cikin *Shukrah* ya shiga watan haihuwa saboda haka *safeer* da *Ahmad* sukayi handling company 'n su gurin wani yaron Ahmad *Ammar* don Ammar yanada Amana da hankali sosai, zaman gida kawae su *Safeer* suke, Da zarar *Shukrah* tayi wani motsi na nuna alamar jin ciwo zasuyo kanta suna jero mata sannu " " To ana cikin haka har E D D' n Shukrah ya cika, tun safe Azeeza ta shirya musu trolley, Shukrah dae ta dage bazata hospital ba wae ita batajin ciwo saboda hk a gida zata haihu " " Haka suka yini lafiya cikin gidan, sai zuwa yamma sannan Mara da bayan Shukrah suka fara mata ciwo nan fa hankalin kowa ya tashi ba kamar Safeer da hankalin ya gama tashi, wani karfi yaji yazo mishi bemasan sanda ya daga Shukrah ba sai mota, nan Ahmad ya biyo shi, nan Azeeza ma ta fito da trolley sai hospital......... SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE 💕 [5/8, 1:47 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA* 👮🏻 WRITTEN BY *ZAINAB* *YAKASAI* *SHUKRAH* DEDICATED TO *MIEMIEBEE* 3⃣5⃣ "Sun isa asibitin cikin sa a aka karbi *Shukrah* aka wuce labour room da ita, Shukrah tafi karfin awa daya acikin labour room amma ta kasa haihuwa hakan ne ya bawa likitocin damar bata inducing drug tasha amma ta kasa haihuwar, Anan kuma suka fara tunanin yimata C. S ". " *Safeer* ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kewaye yake ya rasa inda zaisa kansa, duk da Air condition din dake gurin amma gumi sai zuba yake a jikinsa kafafunsa sai rawa suke jiyake kamar ya cire ciwon ya dawo kansa, *Azeeza* da *Ahmad* sai kokarin bashi baki suke amma sam yaki jinsu, ya zauna ma yaki zama *Shukrah* kam sai ihun ta take tana kiran *Ammii, Mamah, Aysher, Miemie kai har meela ma sai da Shukrah ta kira, yana cikin wannan halin daya daga cikin Doctors din da suka karbi *Shukrah* ya fito Sukayi Saurin mikewa suka nufeshi, *Safeer* bakinsa sai rawa yake ya kasa ma yimasa magana, doctor ne ya dafa kafadar *Safeer* yana bashi baki kafin ya miki masa wani paper wa yayi signing ayiwa *Shukrah* C. S " " Duk jarumta irin ta *Safeer* besan sanda ya fashe da kuka ba, da kyar ya karbi pen a hannun Doctor din ya dora kan paper, maganar da Wata Nurse ta fito tana yiwa doctor be kan yazo *Shukrah* ta haihu ta samu baby Boy ne yasa *Safeer* wulli da pen & paper hannunsa ya bi bayan Doctor cikin dakin, nan *Azeeza* da *Ahmad* ma suka rufa musu baya sai dakin, Sanda suka shiga dakin har Nurse ta dauki Babyn ta fice dashi" " *safeer* ya kara da gudu da niyyar rungume *Shukrah* Amma sai yayi Saurin dakatar da kansa don ganin tayi wani mugun nushin sai ga baby Girl ta fito, Zaro ido sukayi cike da mamaki da kuma farin ciki, *Safeer* ya rungume *Shukrah* tsam a jikinsa yasa kukan farinciki, besan da bakin da zeyiwa *Shukrah* godiya ba don ta bashi farin cikin sa Twins, *Shukrah* tayi karfin hali tasa hannunta tana goge wa *safeer* hawayen idonsa, Don tafi kowa sanin irin son da *safeer* yakewa yara, Doctor ne yayi gyaran murya *Safeer* yayi Saurin daga *Shukrah* yana goge hawayen daya gangaro masa " " Nan dae Nurses su 2 suka shigo da babies *Safeer* yayi Saurin karasawa ya karbi Baby girl din shikuma *Ahmad* ya karbi boy din, anan kuma Nurse ta shiga da *Shukrah* toilet don ta gyara jikinta " " Nan safeer ya shiga snapping babies yayi marking duk contact nasa na WhatsApp yayi musu sending, nan fa aka fara kiransa ana masa murna, Aysher ma ta kirasa sanda yace takai wa *Mamah* wayar kin karba tayi, tadai ce Allah ya raya *Twins* " " washe gari akayi discharging nasu, Abokan aikin su *Ahmad* sai zuwa suke, kayan Babies kuwa kamar zasuyi magana don yawa, sai zuwa dare sannan *safeer* ya samu damar kebewa da *Shukrah* ya zuba mata ido tana rike da Baby girl dinta, tsawon minti Arba 'in suna hk, Har sai da *Shukrah* ta gaji da da kallon nasa tayi magana" "Your look is so intense, it makes me nervous, what do you want? *Shukrah* ta tambayi *Safeer* sanda ta dauke kanta " " *safeer* ma dauke kansa yayi sannan yace ALL what i want is your love, can you do me a favour and give me that much? I promise to live with you for ever, Indeed you are a blessing, kinbani farin ciki a rayuwa ta, i have never expected dis, being a Daddy of twins at this very tym" "Why not? I will give you my luv for the joy you brought into my life, for understanding my needs, for allowing me to be part of you at the same time for turning back to the face of all my mistakes *Shukrah* tace harda dan hawayenta " " Rungume *Shukrah* , *safeer* yayi itada Babies dinsu ya musu selfie....... SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE 💞 [5/11, 9:17 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA* 👮🏻 *WRITTEN* *BY* *ZAINAB* *YAKASAI* *SHUKRAH* Dedicated to *MIEMIEBEE* 3⃣6⃣ " *SAFEER* ya kurawa twins dinsa ido fuskarsa dauke da murmushi, yanaji a ransa yanzu bashida wata matsala tunda Allah ya masa babbar kyauta wadda ba kowa yake waba, a fili yace 'Alhamdulillahi' " *SHUKRAH* ta juyo ta kalleshi ya mata murmushi yace 'Baki tambayeni wani suna nayi wa yara khudubah (Huduba) dashi ba' " tayi murmushi sannan tace abinda nake taso in tambaya kenan wallahi, wani suna aka sa musu? "Murmushi Ya fadada sannan ya dauki Baby boy dinsa ya rungume yace 'Saboda karamci, da mutunci, da Alfarma da kuma babbar kyauta da *ALHAJI* *SARAKEE* Yamin yasa nayiwa dana huduba da suna *AMEENULLAH* Alkunyar sa kuma shine *LABEEB* Inaso a ringa kiransa haka don suna ne me kyau sosai, Ya ajiye shi gefe sannan ya dauki Baby girl din, itadai *SHUKRAH* sakin baki tayi bawae batayi sammanin haka ba, a a kawae dae abin yazo mata a *BAZATA* ne, Ta zame daga kan bed din ta durkusa akan kafafunta zatayi magana *SAFEER* Shima ya zame yayi Saurin sa hannunsa daya ya rufe mata baki sannan yace, ita kuma nasa mata sunan Mamana wato Khadeeja za a dinga kiranta da suna *LABEEBA* " " Hawayen farin ciki ne yazubo mata tayi Saurin goge wa tana murmushi tana kara jin son *SAFEER* Na ratsa jinin jikinta don ya mata komai a rayuwa yayi wa *DADDY* ' *NTA*Takwara, tasa hannu ta zame nasa hannun sannan tace ' Hakika banida bakin yimaka godiya don kayiwa mahaifi na abinda ba a taba yimasa, yayi Saurin dakatar da ita ta hanyar cewa 'Nima Yamin abinda ba a taba min ba a rayuwa ta inajinsa kamar *ABBANA* , banajin a kawae abinda zan masa nabiya sa abinda yamin saboda hk karki ce zaki min godiya kinji " " Wayarsa ce ta fara ringing yayi Saurin mikewa ya dauko akan bed *MAMAH* Yagani ajikin screen din yayi Saurin dagawa yamata sallama " " Idan kai bazaka dawo ba to ka kawo min *SHUKRAH* kaji ko bakaji ba tace rai a bace " " Dakyar ya iya bude baki yace *MAMAH* naji kuma insha Allah cikin satin nan zamu dawo " " Gobe nake so ku dawo na fada maka... Tana gama fadar haka ta kashe wayarta " " *SAFEER* YA juyo ya kalleta yace *MAMAH* Tace gobe take so mukoma so ynx zan fita nayi mana Booking flight, Da sauri *SHUKRAH* tace to don itama zaman garin ya isheta musamman ma ynx data haihu tana bukatar ganinta kusada *AMMI*' *NTA* , tare suka fito *AZEEZA* Kadai ce a a parlour don *AHMAD* Bayanan, *SHUKRAH* ta mika mata babyn hannunta sannan ta karbi na hannun *SAFEER* , " " shiko yana fita ya nemi commercial car yace driver ya kaishi ' *AL* *HARAMAIN* *TRAVEL* *AND* *TOURS* *LIMITED* , be dauki wani lokaciba ya gama komai, sai da ya shiga wani shopping complex yayi shopping sosai sannan ya wuce gidan, Sanda ya isa ana kiraye~kirayen sallar magrib nan yayi alwalla suka fice mosque tare da *AHMAD*, sai da su kayi sallah isha sannan suka kamo hanyar gida, a hanyar dawowar sune *SAFEER* Yakewa *AHMAD* Bayanin tafiyar su gobe, sosai *AHMAD* Yanuna rashin jin dadin tafiyar su koba komai sun saba, kuma yana jin tausayin *Azeeza* sosai don tasa *LABEEB*& *LABEEBA* Sosai azuciyarta, besan yadda zasuyi goben ba, Saurin goge Hawayen dasuka taru a idon sa yayi dai dai sanda suke shigowa parlourn gidan, a tare *Ahmad* & *Safeer* sukaci abinci don tuni su *SHUKRAH* sukaci nasu " " Sanda suka gama cin abincin sukayi sallama, lokacin da *Safeer* yashiga dakin tararwa yayi *SHUKRAH* na hada musu trolley yakarasa kan bed ya dauko *LABEEBA* Yamata kiss a kanta yace Babyna ki tashi ga *PAPA* YA dawo, Baby kice you are welcome *Papa*" " *SHUKRAH*tasa dariya tace kai *ya* *safeer* karfa son baby yamaka illa, yarinyar da kwanan ta 3 kawae a duniya kake expecting tayi welcoming naka " " Hade rai *safeer* yayi yana hararar ta toke ina ruwan ki, Ni banason irin hk ehe, Dariyar ta cigaba da yi har sai da ta k'ularda Safeer yaja tsaki sannan ya kwantarda *Labeeba* ya musu addu a sannan ya kwanta" "Sanda *SHUKRAH* ta gama hada trolley toilet ta shige tayi wanka, koda ta fito kitchen ta wuce tahada tea tasha sannan ta dawo dakin tasaka wata doguwar sleeping dress ta kwanta a bayan *Safeer* " " Ya Safeer kayi hakuri dani naga kamar kayi fushi, Shiru yayi mata alhalin yana jinta, nan ta cigaba da masa magiya amma yaki kulawa, zuwa can dabara ta fado mata tasa harshen ta a fuskarsa tafara yawo dashi, nan *safeer* ya juyo ya rungume ta.... *washe* *gari* "Dukansu a airport, *Azeeza* rungume da *labeeba* tanata kuka kamar shi aka aikota, ita tunaninta daya yadda zatayi rayuwa bau tare da Shukrah ba gakuma twins da tasa su a zuciyarta,j *Ahmad* ganin kukan *Azeeza* bame karewabane yasashi mata alkawarin kaita Nigeria before or after naming ceremony, saida sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida ~~~~~~~~~~~~~~~ *HAIYDAR* zaune gaban Hajiyarsa da alama fada take masa "Haiydar wai kai yaushe zaka nutsu kayi Aure ne, akan idonka Safeer yayi Aure gashi har matar ta haihu amma kai kaki kafitarda matar ko" "Ba hk bane Hajiya yarinyar da nakeso yanzu tayi junior waec dinta, so jira nake tayi grads sai a fara maganar auren " " Kana hauka ne Haiydar, nace hauka kake Haiydar, ajinka zan cigaba da zama da kai har nanda shekara 3 to inma bacci kake ka farka, Nabaka two weeks kakawo min mata ko in zabo maka da kaina hajiya ta fada rai bace daga hk tafice ta barshi yana tunanin wae shi za a samowa mata yarasa me zai kira wannan auren da Hajiya take shirin yimasa (Niko nace *AUREN* *BAZATA* Xatayi maka), Ringing din dawayarsa yake ne yasa shi daukan car key dinsa ya fice daga gidan, tafiyar minti talatin ce ta kai shi Airport, nan ya kwashe su sai gidan Mamah, A hanya ne yake fadawa Safeer Hajiya zatamai AUREN BAZATA, me Safeer zeyi inba dariya ba. . . Dakyar ya tsayar da dariyar sa yace karka damu Haiydar *AUREN* *BAZATA* *ALHERI* *NE*. . . *SHUKRAH* *YAR* *GATAN* *MIEMIEBEE*💞 [5/12, 1:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA*👮🏻 WRITTEN BY *ZAINAB* *YAKASAI* *SHUKRAH* Dedicated to *MIEMIEBEE* 3⃣7⃣ "Sanda suka karasa gidan Mamah cike suka shame shi da mutane as if to say ranar sunan ne, *MIEMIE* Tazo da gudu ta rungume *SHUKRAH* tana murna da ganinta nan dae aka fara gaishe gaishe, daga nan *Safeer* ya fadawa *Mamah* ze tafi gidan su *Haiydar*don nan akwai hayaniya sosai, To kawae yace sannan suka fice " " Saida *SHUKRAH*tayi wanka taci abinci Sannan ta kira *Amminta*, *Ammii* naganin kiran amma taki picking don ita dama me alkunya ce, Text *SHUKRAH* ta mata tace sun sauka lafiya, Bayan kusan awa daya ta mata reply tace sannun ku to" *MIEMIE* sai nan nan takeda twins taki yarda kowa ya dauke su, wae 'ya' yanta ne Washe gari *Ibteesam* tazo ta kawo wa babies kaya masu yawa, Hajiyar Haiydar ma tazo nan take yiwa Mamah bayani cewa tabawa Haiydar two weeks ya kawo mata kuma taga kamar be dau maganar T serious ba amma dae ta shirya bashi mamaki, don dama akwai wata yar yayarta *Zafeera* zatayi wa yayar tata magana sai a hadasu don zafeera yarinya ce mai hankali da nutsuwa sosai, dama tun farko tayi wa Haiydar sha awarta amma da taga kamar zafeera bata gabansa yasa takyale amma tunda dae yanzu yaki kawo matar toko zata hadasu, sosai Mamah ta goyawa Hajiya baya acewarta ae Haiydar ya girma, kuma ma ae shirme me zai sashi cewa wae sai ya jira Miemie, nan dae suka gama magana Hajiya tayiwa Mamah alkawarin duk me ake ciki zata fada mata, Sanda zata tafi ta ajiye wa twins Rapper na 100 sannan ta fice, Mamah ta bita tana mata godiya " " Duk wannan shirin da hajiya takeyi Haiydar be Sani ba don shi tunda tamishi magana bata kuma yimasa ba, saboda hk yace ko dama wasa take masa shiyasa ma yasake ya cigaba da harkokinsa" "Gobe ne suna amma har yau *Ammii* taki zuwa taga su *labeeb* ,, *Mamah* ta kirata yafi a Kirga amma kullum cewa take gata nan da taga abin bame karewa bane yasa takashe wayarta, Gidan *Ammii* ya cika da yan uwa da abokan arziki amma ba *SHUKRAH* koda sukayi wa *Ammii* maganar sunason akawo ta gidan ayi sunan anan cewa tayi ita ba ruwanta haka sukayi ta surutansu suka gaji" "Da yamma Alh Sarakee ya duro Nigeria don dama ya dade a Senegal bayanan ma akayi haihuwar amma *SHUKRAH* ta mishi albishir din *Safeer* ya mishi takwara, Sanda ya iso ana kiran sallar la asar saboda haka saida ya tsaya yayi sallah sannan ya karaso gida, *Ammii* ta mishi girki kala kala amma saboda zumudin ganin *Labeeb*& *labeeba* Yasa koda yayi wanka be tsaya cin abinci ba ya dauki babbar trolley daya shigo da ita ya fice, Sanda yake tada mota *Ammii* ta same shi "Yanzu Daddy fisabilillah gidan mutane xakaje ba kara ba alkunya, koni fa har yau banje ba" "Daddy dariya yayi sannan yace to Ammii ni na hanaki zuwa ne? Akwai bukatar naga grand child's dina shiyasa kikaga ma nadawo don bayau zan dawo ba ka ida sai next week zan dawo amma na tattara komai na ajiye nazo sannan kice zaki hanamin zuwa ganin su, yana kaiwa nan yayi reversed ya fice daga gidan, jiki ba kwari Ammii ta koma cikin gidan azuciyarta tana mamakin Daddy don gaba daya yariga ya saba da turawa komai nasa irin nasu yake " " Cikin Sa a Daddy ya samu Safeer da abbah a guest room da alama suna tattatuna abu me mahimmanci ne, Da fara 'a Abbah ya tare shi yayi da Safeer ya durkusa har kasa ya gaida shi cikeda ladabi " " Ashe kuma an samu karuwa? *DADDY* Yace yana maida kallon sa gun *ABBAH* "wallahi kam an samu Alh. *sarakee* D Hajiya *Khadija* Abban yace fuskarsa dauke da murna, Allah dae ya raya mana su bisa tafarkin addinin musulunci " " Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen "gyaran murya Daddy yayi sannan yace Madallah Nagode da Girmamawa ko kuma ince da bani wani matsayi da kayi safeer, hakika kai abin alfahari ne kuma ka can can chi yabo Allah ya maka albarka, Sakamon alkhairin dakamin ka sama yaronka sunana nayi alkawarin daukan nauyin duk wani abu da za'a ci ko sha na kuma dau nauyin gurin da za'a zauna kai hatta ragunan sunanma na hutar da kai insha Allah daga nan zuwa dare za a kawo " " Abbah yayi Saurin kallon shi yace haba Alhaji ae baza ' ayi haka ba, hidimar tayi yawa ae yau fa ka dawo kasar ma gaba daya, ka barshi wallahi zamuyi komai insha Allah " " Murrmushin manya Daddy yayi yace bafa ku kuka Sani ba haka kuma badan bazaku iyaba yasa zanyi A a kawae dae tukwucin Alheri ne, so karku damu kudai kawai kuyi fatan ayi taro lafiya a tashi lafiya " Godiya dukansu suka mai kafin safeer yace bari yaje yasa akawo Twins, to Daddy yace sannan suka cigaba da hirar su da Abbah" "Sanda safeer ya shiga cikin gidan A parlour ya tararda *AYSHER*, *SHUKRAH* & *MIEMIE*, Shukrah na Rike da Labeeba yayinda miemie ta rike labeeb, hararar miemie yayi sannan yace waye ya baki ixinin daukar min yaro salon kiyar dashi ko, ke daman ba nutsuwa gareki ba, Hade rai Miemie tayi ta ajiye labeeb da karfi kan kujera har sai da yaron ya fasa kuka, Safeer ya zo da gudu zai rike ta tayi dakin Mamah da gudu ya bita, Aysher ce tayi Saurin daga labeeb tana jijjiga shi " " Jikin Hajiyar Haiydar ta fada, Hajiya Kinga ya Safeer yanamin gori akan 'ya' yansa ko, kuma don na ajiye masa shine zai dakeni, tana kaiwa nan ta fashe da kuka kamar wadda ya daka, Shi safeer ma mamaki ne ya hana masa cewa komai shi a duniya be taba ganin yarinya irin miemie ba, Mamah tace ae sai ka fita tunda burinka ya cika kasata kuka kaji dadi, Miemie ta fakin idon Mamah tamasa gwalo tace cikeda shagwaba Mamah yaushe zaki haifar mana twins muma adena min gori " " dariya sukayi dukansu sannan safeer ya fice yasa Aysher Da Shukrah su kaiwa Daddy twins" WASHE GARI Tun asuba mutane suka fara cika gidan duk da cewa a tourist camp za ayi taron sunan amma kafin7:00 gida ba matsaka tsinke, ba ayi girki a gida ba kasancewar an riga anyi order a can tourist camp din snacks kuma anyi order a me. Biggs, Drink ko Wata Aminiyar Mamah ce Hajiya Maryam Anas ce tadau nauyi " °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° 12:00pm na isa tourist camp gurin ya cika sosai da yan uwa da abokan arziki, Bayan bude taro da Addu ' a da wata babbar Malama *safiyya* *yakasai* da tayi ne kuma aka vukaci D. J Yasa sauti nan fa yan *SHUKRAH NOVELS suka zage sai rawa suke ba kamar Safiyya* *Galadanchi* da *Zee* *zee*, sai da komai ya lafa sannan aka fara rabon Mutane sai karba suke, can nagano wasu mutane sun koma gefe sunata dura abinci da lemo a jaka kara matsawa nayi don ganin ko suwaye, wazan gani inba, *MEELA* *SOFTIE* *EESHATULLAH* *MAMAH* *SKY* *FEUXER* *MARYAM*& *NURIYYA* ba, suna ganina suka fara raba ido, Haka dae taro ya watse mutane sae sawa twins albarka suke " " Sai wajen 11:00pm safeer ya samu kubewa da Shukrah, fitowarta a wanka knn tana shiryawa yakarasa ya rungume ta taba ya a tare suka sauke ajiyar zuciya, yace mata a cikin kunnen ta "Bazan taba gajiya da yimiki godiya ba Shukrah kinmin komai a rayuwa ta, Allah ya miki Albarka kinji, yanzu ki fadamin duk me kike so insha Allah zan miki " " Shukrah tai Saurin juyowa tana kallon shi sannan tace da gaske ya Safeer " " Yace Da gaske " Tace Aiki nake so na fara, yace wannan shine yafi komai sauki, akwai wata kawar Mamah tare sukayi Uni Maid insha Allah zan mata magana itace me *MARYAM* *CLINIC* Din can... . [5/15, 7:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻 *WRITTEN BY* *ZAINAB YAKASAI* *SHUKRAH* Dedicated to *MIEMIEBEE* 3⃣8⃣ " *SHUKRAH* tace karka cemin *AUNTY MARYAM ANAS*, *Safeer* ya kalleta cikeda mamaki sannan yace karki ce kinsan ta? " *SHUKRAH* ta mishi hararar wasa sannan tace lallai yaza ayi ace bansan taba tare fa sukayi secondry skul da *Ammii* fa kuma tana zuwa gida sosai, *Safeer* yayi murmushi mai kyau sannan yace Masha Allah ynx inna fita zanyi wa *Mamah* magana insha Allah komai zaizo da sauki don *Mamah* tana bani labarin saukin kan *Mummy Maryam Anas* tun suna uni maid haka take duk da kasancewar ta over roller amma bata da girma kai, *SHUKRAH* ma murmushi tayi sannan tace Allah sarki Allah dae ya shige mata gaba, kuma nagode sosai da Amincewar dakayi *PAPA'N TWINS*, matsowa *Safeer*yayi ya rungume ta sosai sannan yace kinfi karfin komai a gurina wallahi *SHUKRAH* Allah dae yayi miki Albarka ya kuma kara miki lafiya ya kare ki daga sharrin masu sharri, sosai *SHUKRAH*taji dadin addu 'ar tasa saboda haka ta manna bakinta akan nashi ta soma kissing dinsa sundau lokaci sosai a hk kafin *LABEEB*ya fasa kuka sukayi Saurin janye wa haka kuma suka nufeshi da sauri,, *SHUKRAH* C tayi nasarar daukan sa Tasan yunwa yakeji don duk basu zo hannunta ba, shiyasa tayi Saurin yaye rigarta tasoma feeding nashi" "sanda *Safeer* ya fita a dakin gurin *Mamah* yaje yamata bayani yadda sukayi da *SHUKRAH* kuma hakan ya mata dadi at last dae zata taimaki mutane da yawa kuma ta mishi alkawarin zatayi, *Mummy Maryam Anas* maganar a yau ba sai gobe ba, nan *Safeer* yashiga godiya sannan sukayi sallama da *Mamah* da kanshi ya kai Hajiyar *Haiydar* gida sannan sukaje ya samu *Haiydar a gida saboda hk suka zauna sunata hira Safeer* sai Tsokanar *Haiydar* yake wae za ayi masa *AUREN BAZATA* Sai da *Haiydar* ya bata ransa sannan *Safeer* ya kyaleshi sanda ya masa sallama ma ko answer wa ma beyi ba haka *Safeer* ya tafi ya nayiwa *Haiydar* dariyar mugunta" °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *Hajiyar Haiydar* T samu yayar ta *Hajiya Safiya* kan tana son hada *Haiydar* & *Zafeera* Aure kuma Alhamdulillahi maganar ta tasamu karbuwa a wajen *Hajiya safiya Da Alhaji mai kano* mahaifin *Zafeera* kenan Don Alhajin cewa yayi nanda wata biyu za ayi bikin acewarsa ae su suka haifi yaran kuma sunada hakki akan su haka kuma suna da ikon zaba musu abinda yayi dai~dai da rayuwar su, saboda hk ba bukatar tambayar *Zafeera* ko bata sonsa" " *ZAFEERA* Itace 'ya mace guda daya tilo a gurin *Hajiya Safiya* shiyasa ta dauki son duniya ta dora mata" "hajiya kawae dauriya take don sam bata son abinda zai taba *gudaliyar ta*,kuma tana tunanin yadda zasu kwashe da *Zafeera* DUK da dae tanada saukin kai kuma tasan bazata ce A a ba, Amma tana ganin dae kamar an shiga hakkin ta, da kyar ta iya bude baki tace Allah dae ya sa komai yazo da sauki " " Ameen Hajiyar Haiydar tace " " Shiko *Alhaji Mai kano* cewa su kashe kansu in anyi AUREN, daga nan dae ya mike ya fice, To itama Hajiyar Haiydar sallama tayi wa Hajiyar Zafeera ta fice " " Da daddare har Zafeera ta kwanta Hajiya ta shigo ta kwashe duk yadda sukayi da Hajiyar Haiydar ta fada mata sannan tace "kuma Baffanki yasa bikin Nan da wata biyu," "Zuciyar Zafeera ta bada wani *Dum Dum Dum* tanason Hajiyar ta, kuma bata jin zata iya watsa kasa a idanun soyayyar da Hajiyar take mata uwa uba kuma tarbiyyar da Hajiyar tamata, Saboda hk tace *TO* Asanyaye " " Sosai Hajiya taji tausayin 'yar tata amma saboda batason maganar tayi nisa har tasa *Zafeera* kuka yasata mikewa tace kiyi Addu' a *Angel* sai da safe " " nanma *To*kawai tace mata sannan ta kwanta" "Duk wannan Abun da ake Haiydar be Sani ba don Hajiyar bata kuma yimasa maganar ba, cikin sati biyu magana ta kankama don har ta isa katsina dangin su Haiydar din kenan, Hajiyar Haiydar da Hajiyar zafeera sun shirya staf zasuje Dubai don hado lefen *Zafeera*, koda *Haiydar* ya tamvayeta inda zata cewa tayi ina ruwansa " " Sati daya kawae su Hajiya sukayi suka hado kaya masu yawan gaske uwa uba kuma ga kyau da tsada, Sai bayan da suka dawo ne Hajiyar tace wae yazo yaga lefen shi, ko kallon kayan beyiba yayi fice war sa don wani mugun takaichi ne ya durar mishi" °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° "yau kwanan su *LABEEB DA LABEEBA* 40 A duniya amma *Ammii* bata taba sasu a idanun ta ba sai dae ko a picture shidin ma sau biyu ne, Ranar da *AREEF* Yaje ganin su yayi snapping dinsu ya nuna mata sanda ya dawo sai kuma sanda *SHUKRAH* tayi mata sending a WhatsApp " " Wannan dalilin ne yasa *Mamah Shukrah Aysher da Miemie* suka shirya mata ziyarar *BAZATA*.. . . *SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💞 [5/16, 1:15 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻 ( *An unexpected marriage*) *WRITTEN BY* *ZAINAB YAKASAI* *SHUKRAH* *DEDICATED TO MIEMIE BIE*💞 3⃣9⃣ " *AMMII* Na daga cikin daki ta jiyo sallamar su, ta fito da sauri ta tare shu da fara 'arta "Sannunku da zuwa, wannan irin zuwa na bazata haka, da kun Sani kun kira ni kun cemin zakuzo ae" " *Mamah* ta dan harare ta sannan tace to in an kira picking kike, ae ina sane na shirya wannan zuwan bazatan sai da na kira *AREEF* Ma na tambaye shi ko kina nn ya tabbatar min kina nn din sannan muka tawo " " Murmushi kawae *AMMII* Tayi ta wuce fridge ta kawo musu drinks, *Aysher* ta durkusa kusa da *Mamah* tana gaida *AMMII*, da fara a ta Answer sannan *MIEMIE* MA ta durkusa ta gaida ta, *SHUKRAH*ma ta gaida ta, ta Answer ba tare da ta kalle taba " *MAMAH* Ta dawo da kallon ta gun *AMMII* Sannan tace, ae kawo muki twins mukayi tunda kinki zuwa ki gansu, Murmushi *AMMII*Tayi sannan tace ba haka bane ba, abubuwa ne sukayi min yawa, *Mamah* tace to aini gashi nan nazo da kai na" " *SHUKRAH* ta dan kallo *AMMII* Aiko suka hada ido, Ammii tayi saurin dauke idonta, Shukrah tayi Murmushi sannan ta mike ta do rawa Mata *LABEEB* Kan cinyarta, *AMMII* Tayi saurin sa hannu ta ture shi saura kadan ya fadi Shukrah ta tare shi tana Murmushi, Mamah tace yanzu dan Allah wae sai ki ture shi haba *Ammii* gaskiya ki rage wannan kawaichin naki yayi yawa wlh ynx zamani ya canja fa, Dariya *Ammii* tayi tace to ae shi kunya, kara da kawaichi a jinin fulani yake, Amma kamar yadda kika ce na rage zan danyi kokari na rage din, yawwa ae haka akeso *Mamah* tace tana do rawa *Ammii* *Labeeba* akan cinyarta, cikeda kunya *Ammii'n* ta daga ta tana Murmushi sannan tace Allah ya raya su yasa masu jin k'ai ne" "Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen" "Yinin ranar duk sunyi shine a gidan *Ammii* amma *Mamah* ta kula bawata magana data shiga tsakaninsu da *SHUKRAH* a zuciyarta tana mamakin hali irin na *Ammii* kusan wata biyar fa bataga Shukrah 'n ba tun tafiyar su San Francisco gashi ynx tazo amma sai share ta take, Tana wannan tunanin ne taga *Ammii* ta mike ta shige Bed room, *Mamah*ta Dawo da kallon ta gun *SHUKRAH* tace *SHUKRAH* tashi kibi *Ammii' nki* kuyi magana kinji " Kamar dama jira take tayi saurin mikewa ta shige dakin da sauri, juyawa Mamah tayi azuciyarta tana dada mamakin *Ammii*, Sanda *Shukrah* ta shiga dakin lokacin ita kuma Ammi zata fito, Shukrah tayi saurin rike hannunta tace *AMMA NA* ynx kin dena sona ko? Ta fadi haka ne sanda hawaye ke fitowa a idanunta " " *Ammii* cikeda tausayin 'yar tata tace ban dena sonki ba *SHUKRAH* ya jikin ki? "jiki Alhamdulillahi, twins suna fushi dake tunda kinki zuwa ganin su, Dariya kawae *Ammii* tayi sannan tace ae ynx gashi nan kun kawo su ko? Eh mun kawo su kam, sun danyi hirar yaushe gamo sannan suka fito, sai bayan sallah 'r magrib sannan suka tafi bayan *Ammii* ta cika su da tsaraba " " washe gari da sassafe *Safeer* ya shigo cikin gidan *Mamah* ya tarar a parlour tana Karanta *Hisnul muslim* ya durkusa kusa da ita yana gaida ta, Bayan sun gama gaisawa kuma shiru ne ya biyo baya don *Mamah* cigaba tayi da karatun ta shi kuma *safeer* zama yayi yana dan Satar kallon ta, lura da hakan da *Mamah* tayi ne yasa ta ajiye littafin hannunta ta ta dawo da kallon ta gurinsa " " Ya akayi ne *Safeer*? "kara kasa da kansa yayi kafin yace' *Mamah* dama zuwa nayi mu tafi da *SHUKRAH* & *TWINS* Tunda sunyi Arba ' in dinko? "Mamah ta rike ha'ba tana masa kallon mamaki sannan tace to fitsararre mara kunya ni ae nafika sanin sunyi Arba,in din, to barin fada maka baxata koma ba sai nan da two weeks don bamu gama gyaran da muke ba" *Safeer*ya bata rai kamar zeyi kuka yace wae wannan wane irin gyara ne dan Allah, nidae kawae a barshi haka wannan ma wanda akayi mata ya isa " " Dalla can rufe min baki mara kunya kawae sai kace bakai ake yiwa gyaran ba, ta nuna masa kofa tashi ka fita ka bani guri, haka *Safeer*din ya fita yana mita "Wannan wace irin rayuwa ce, dan anga Mutum me hakurine sai a dinga masa yadda ake so, an cemin 40 days zasuyi na hakura amma ynx an canja magana wae sai nn da two weeks, yaja tsaki sanda ya shige motar sa ya bar gidan" *SHUKRAH* *SHUKRAH* *SHUKRAH*, Na am *Mamah* Shukrah ta Answer sanda take fitowa daga daki, wuce kije kitchen ki dauko babbar tukunya a dora ruwan wanka, to kawae Shukrah tace sannan ta dauko ta ajiye a gaban Mamah" "Sassaken bagaruwa Mamah ta zuba sannan ta matse lemon tsami akai tace Aysher tashi kije ki ta fasa, in yayi saiki jiya ki kira Shukrah ta shiga ciki" "Sanda Shukrah ta fito a wanka Mamah tasa Aysher ta dauko kaskon turaren wuta da bucket na karfe, Mamah tasa Kaskon cikin bucket din tazuba angurya(wanda ake samu a jikin audiga) tazuba bawon (kwanson) citta Shukrah ta zauna akai, Bayan an gama wannan Mamah ta kara zuba wani turare da wata kawar ta ta kawo mata daga Senegal " " T haka dae rayuwa ta cigaba da tafiya kuma yau Shukrah tayi sati biyun da Mamah ta kara mata, Mamah tasan halin Safeer sarai shiyasa ma bata kirasa ta tuna masa ba, Amma ga mamakin ta har bayan magrib Bai shigoba, abin ya damu Shukrah sosai shiyasa ta faki idon Mamah ta shige dakin ta fara kiran wayarsa, bugu biyu tayi yayi picking " " Hello *Papan Twins* "Yap *Mamin Twins* ya kuke? "Lafiya kalau muke, kai muketa jira dae" "Murmushi Safeer yayi wanda har Shukrah na iya jiyo sautinsa yace ke bakin biyewa Mamah ba kin share ni, nifa da har na fara tunanin dama akwai wata yarinya teemerh luv tana masifar sona to da har nayi niyyar zuwa gurin Dad nata in nemi AUREN ta nanda two weeks in za ayi bikin Haiydar a hada namu kawai " " Shukrah ta saki kukan shagwaba tana bubbuga kafa Ni wallahi bazan yarda ba, Ni wallahi kawai kazo mu tafi ko in tawo da kai na " " Kukan da Shukrah take ne yasa Mamah ta shigo dakin, jin abinda Shukran ke cewa yasa Mamah ta fahimci da wanda suke wayar, saboda haka ta ta koma ta ta samu Miemie aparlour "Miemie je ki kiramin Aysher tazo ku kai Shukrah gidanta, to Miemie tace sannan taje ta kira ta, Mamah da kanta tayi wa Shukrah bayanin Su Aysher zasu rakata, Bayan kamar minti goma sha biyar Shukrah ta shirya tsaf haka ta shirya twins, Aysher da Miemie suka tayata sa kaya a booth, Mamah dae tana tsaye sai da taga fitar su ta koma ciki... . . *SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💞 [5/17, 4:49 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻 ( *An unexpected marriage*) *WRITTEN BY* *ZAINAB YAKASAI* *SHUKRAH* *DEDICATED TO MIEMIE BIE*😘 4⃣0⃣ "Cikin Mota *SHUKRAH* tayi wa *SAFEER* Text tace masa tana hanya, zo kuga murna gun sa don beyi tunanin *Mamah* zata yarda ta barta ta tawo ba, saboda tsabar zumudi zaman cikin gidan gagarar sa yayi saboda haka ya sa jallabiyya ya fito ya zauna gurin gate man, jefi jefi suke hira, Zaman kamar minti goma sha biyar yayi yajiyo horn a, ko ba a fada ba yasan su *SHUKRAH* ne shiyasa ma yayi Saurin mikewa yaje get din da sauri da nufin bude musu, get man yayi Saurin karaso wa " " Ranka ya dade, kabari za a bude yace yana kara sawa jikin get din" "Yi sauri ka bude dae, ba surutu nace kayi min ba *Safeer* yace cikeda kaguwa" "Nan get man ya bude musu, Aysher ta shigo da motar, yayi Saurin ban bayan motar, Tun kafin Aysher ta gama Parking *SHUKRAH* ta bude ta ziro kafarta, kadan ya rage *labeeba* ta fadi a hannunta, Da sauri *Safeer* ya karaso ya hada ta da *labeeba* ya rungume su cikeda so da kaina, sam ya manta ma dasu *Miemie*(Baki abun magana) suna tsaye " " Aysher tayi Saurin dauke kanta, *Miemie* ta tabo Aysher, Aunty Kinga ya *safeer* din nn ko kunyar mu ma beji ba, lallai ", Aysher ta buge mata baki tace kin cika surutu wallahi, bazaki iya dauke idonki ba" "Duk wannan maganar a kunnen *SHUKRAH*sukeyinta shiyasa tayi Saurin ture *Safeer* din tace su *miemie* na kallon muda, dariya kawae yayi sannan ya daga kafada irin ko a jikin sa din nn, *SHUKRAH* ta kallo *Aysher*, *Aysher* tayi Saurin dauke kai, ita Shukrah dariya ma aysher ta bata tace Bazaku shiga bane kuka tsaya wae, Aysher tayi Saurin kallon ta ta girgiza kai tace baxamu shiga ba Aunty dare ya fara yi kuma ban iya driving din dare ba" "To Kawai *SHUKRAH* Tace sannan *MIEMIE* ta mikawa *Safeer* *Labeeb* dake hannun ta, *SAFEER* Tsabar mugunta sanda ya karbe shi sai da ya murde hannun *MIEMIE* yace fitsararriya kawai, Allah ya sa dae kina karatu don naga har ynx kanki yana rawa " " Yar kara *Miemie*ta saki sannan ta kallo shi da fuskar tausayi tace Eyya ya *Safeer* akwai zafi fa, cika mata hannun yayi yace wuce ki bani guri ni, harda dan gudun ta ta wuce ta shiga mota *Aysher* tayi musu sai da safe sannan ta shiga motar tayi reversed T fice a gidan" 10:15 *Safeer* ya samu *SHUKRAH* a dakinta tana shirin kwanciya, ya karaso ya rungume ta ta baya yace mata a kunnen ta kinsan fa yau ke amarya ce, hope you are ready " *SHUKRAH*ta danyi murmushi tace twins dae suna jinka ni ba ruwa na, Dariya shima yayi ya juya ya kallon su, bacci suke hankali kwance, ya dawo da kallo shi gurinta yace Bawani nn wayo kike son min, ae sun riga sunyi bacci, Dan ture sa *SHUKRAH* tayi sannan ta ja hannunsa suka kwanta suna fuskantar junansu " " *safeer* ya kara matsowa jikinta yace mata *i luv u Babe beyond your expectation* "Murmushi *SHUKRAH* tayi tace kayi shiru bacci zamuyi, Matseta *Safeer* ya kuma yi sannan yace tunda nake da ke ban taba jin kince min i luv u ba, kodai har ynx bakya sona ne" " *SHUKRAH* tayi Saurin matse hannunsa dake cikin nata haka kuma ta runtse idonta don tana masifar jin nauyin kalmar nan, dakyar ta iya bude baki tace *My feelings for you are so strong and deep that i cant convey them in words, because i found no word strong enough to tell you how much i luv u, You are more than amazing, my heart is all yours*~i luv u~" "tana kaiwa nn ta kifa kanta jikin pillow tana dariya kasa kasa, *Safeer* fa be taba tunanin jin wannan maganar a bakin taba though he's quit sure tana sonsa, tunda dae alamu sun nuna hkn, Saurin dago kanta yayi ya zira harshen sa cikin bakinta ya fara tsotsa cikeda so da kauna da kuma kewarta, kara shigewa jikinsa tayi don tayi missing dinsa sosai 54 days basa tare fa, haka dae suka raya wannan daren" ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ "yau saura kwana biyar bikin *Haiydar* amma bemasan me ake ciki ba, don *hajiya* kobi ta kansa batayi ba, duk wani abu da yakamata da *Safeer*take hatta kayan da zesa suna gidan *safeer* haka ma invitation cards suna gurin sa " 03:25 pm *safeer* ya shigo office din *Haiydar* da sallamarsa ya ajiye envelop kan desk sannan ya zauna yana fuskantar sa, ko kallo *Safeer* be ishi *haiydar*don yana kula da take~takensa, kuma sam zuciyar sa bata aminta da yawan zuwan da *safeer* din yake gidan su " " *Haiydar* ga wannan invitation cards din ka ne ko zaka bawa abokanka na gida, don na office na gama basu *Safeer*yace yana nuna masa envelop din daya kawo " " Murmushin takaichi *haiydar*yayi yana bin *Safeer*da mugun kallo tsawon lokaci sannan ya dauki envelop din ya mika masa yace cikeda takaichi karbi ka fitar min a office kafin ranka ya baci, kuma wallahi ka cire hannunka a maganar nan don gudun bacin rai" "Dariya Safeer yayi sannan ya mike yace ni bazan karba ba don bana bukatar su, kuma ni bana gudun bacin rai indae akan wannan maganar ne " " Fita Dalla malam kafin rai na ya gama baci don wallahi komai yana iya faruwa " *Haiydar* yace yana nuna masa kofa, Dariya *Safeer* Yayi sannan ya fice yana cewa ba lefin ka bane wallahi nanda wani dan lokaci zaka dawo dai dai ae *Auren Bazata Alheri ne* " Kwanaki sunja kuma gobe za a daura Auren *haydar*amma *Miemie* bata samu labari sai yau din da taji Aysher da Mamah suna maganar, ta zaro ido sannan tazo da sauri ta durkusa kusa da Mamah tace ki kace wae bikin ya Haiydar za ayi da wata banida ta fashe da kuka tace wallahi ina sonsa ina kaunar sa Mamah ku rufa min asiri zan mutu wallahi" "Aysher ta harare ta tace Dalla can rufe mana baki wae, ina sonsa ina kaunar sa, ke har kinsan wani so " " Mamah ta janyo miemee jikinta tace yi hakuri kinji Kinga ynx makaranta kike kuma wadda zai aura yar uwar sa ce, kema inkin gama school zai aure ki ae" "Miemie ta turo baki tace ni wallahi bana son kishiya sai dae ya sake ta ya aure ni, Mamah tace yawwa hk za ayi ke dai ki kwantar da hnkl 'nki kawae, ynx kitashi kije daki ki dauki ankon ki kan bed ki gwada" "Mikewa tayi ta nufi dakin tana bubbuga kafa' ni wallahi bazan je bikin kishiya ba... . *SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💞💞 [5/23, 11:43 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻 ( *An unexpected marriage*) *WRITTEN BY* *ZAINAB YAKASAI* *SHUKRAH* *DEDICATED TO MIEMIEBEE* 4⃣1⃣ "Friday 26 october 2015 da karfe hudu na rana daukacin al'ummar musulmai suka shaida daurin auren *ALIYU KABEER DAN KASA* ( *HAYDAR*) Da amaryar sa *KHADEEJA ABDALLAH MAI KANO*( *ZAFEERA*) Kan sadaki naira dubu dari da hamsin, daurin auren da ya samu halartar manya manyan mutane daga fadin Nigeria kai harma da mak'otan Nigeria, " Da daddare akayi kayatacciyar dinner ta gani ta fada, abokan haiydar duk sun halarchi dinner din haka ma kawayen zafeera guri ya cika har ba masaka tsinke kasan cewar harda yan gayyar sodi ma sun je, haka akaci aka sha aka tashi mutane sai sawa auren albarka suke " " Washe gari akayi yini da daddare kuma Aka kai amarya dakinta, misalin karfe goma sha daya na dare haiydar yana mike a dakinsa na gidan Hajiya bama shida niyyar fita, a bangaren amarya Zafeera kuwa har ta gaji da jiran ango ta kwanta ta fara bacci kuma generator ya mutu saboda zafi ya dameta, mikewa tayi ta leko palour amma duhu ya gauraye gurin da kyar ta lallaba ta leka dakin dake kusa da nata, wanda take kyautata zaton na Haiydar ne amma ga mamakin sai taga baya ciki, parlour ta dawo ta zauna amma tsoro ya hana mata sukuni sai take ganin kamar Mutum ne ke giftawa ta gefen ta hakan yasa ta mike jikinta na rawa ta shige bedroom dinta ta dau wayar ta, number Safeer ta nemo tayi dialing, Allah ya taimaka mata kuwa ringing biyu tayi yayi picking "Hello Safeer "Zafeera tace murya na rawa, ba tare da ta jira yace wani abu ba ta cigaba " Safeer dan Allah kazo ka kunna min generator wallahi tsoro nakeji " " Shi Haiydar din yana ina? Safeer ya tamvayeta cike da mamaki" "Nina wallahi ban Sani ba, dan Allah kazo, Zafeera ta Bashi answer tana fashewa da kuka, dan har ga Allah tsoro takeji tunda a gidansu bata saba zama cikin duhu ba " " To shknn gani nan zuwa ki dena kuka, tare ma zamu tawo da haiydar din kinji safeer yace sanda ya mike ya dau car key dinsa, dakin Shukrah ya wuce ya mata bayanin komai, ta mishi Allah ya kiyaye hanya sannan ya fice da sauri " " Gidan Hajiyar Haiydar ya wuce direct don ya tabbatar Haiydar yana can, Sanda ya karaso gidan dakin Haiydar ya tura, ae ko ya ganshi kwance yana ta bacci abinshi, Safeer yaja tsaki sannan ya karasa ya fara buga mishi pillow 'nda yake kai da karfi, don iya haushi yau haiydar ya bashi " " Bude ido Haiydar yayi waze gani in ba Safeer, ya hade rai yace lafiya zaka tashe ni ina bacci " " Ba lafiya ba Haiydar kai kazo nan hankalinka a kwance kana bacci kabar yarinyar mutane a cikin duhu ko, to wallahi ko ka taso mu tafi ko kuma inje in kira hajiya Safeer yace yana hararar Haiydar " " Haiydar wanda yasan in aka kiramai hajiya tasa ta kare yayi Saurin mikewa yana hararar safeer sannan yace muje cike da kulewa, tabe baki Safeer yayi sannan yayi gaba, shima Haiydar din takalmi kawae Yasa ya bi bayansa, " " Cikin mota ba wanda yace da dan uwansa ci kanka kowa sai cika yake yana batsewa, Sanda suka karaso gidan ne Safeer ya kalli Haiydar yace "Haiydar Zafeera amana ce a gurinka duk wani nauyi nata da hakkin ta a wuyanka ya rataya, kada ka manta zamu mutu zamu koma ga Allah kuma za a tuhume mu kan duk wani aiki namu, kuma kasan Allah baya yafe hakkin wani akan wani, iya abinda kai masa ne kawae in ka rokeshi gafara zai gafarta maka, Wallahi indae k zalunci yarinyar nan sai Allah ya kamaka karka manta yanzu tun a duniya dan adam yake girbar abinda ya shuka, kuma a hakanma sai Allah yasoka da rahma, kaje kayi tunani Haiydar, kada ka yarda ranka ya baci hankalinka ya gushe, nasan anmaka wannan auren ne ba a son ranka ba wannan aurene na baxata, Amma inaso kayi tunani sosai nanda dan wani lokaci zakaji dadi, yana kaiwa nan ya fice ya koma motar sa ba tare da ya jira answer ba, don ya nada tavbacin nasihar sa ta samu shiga tunda yaga jikin Haiydar din yayi sanyi sosai " " Generator Haiydar ya kunna sannan Y shiga cikin gidan, Sanda ya shiga ya ganta a takure idon ta harya kumbura don kukan da tashi, take yaji wani tausayin ta ya shige shi nasihar safeer ta dawo mishi ya tuna Zafeera fa yar uwarsa ce Kuma yana daya daga cikin wanda zasuji bakin ciki in wani ne ya aure ta ya wulakanta ta, sannan ya tuna *RAYUWAR SAFEER DA SHUKRAH* Ta da data yanzu, yasan hakuri da juriya shine jigon farin cikin su yaji a ransa yana son dan dana rayuwar kwanciyar hankali da zaman lafiya, shiyasa ma yaji duk tsanarta ta goge a cikin zuciyarsa haka wani sonta da tausayin ta suka mamaye zuciyarsa, saboda haka ya karasa gaban ta ya durkusa gab D ita ya riko hannaye ta duka biyun yana mata wani kallo, tsawon wani lokaci kafin ya bude bakinsa dakyar yace "Zafeera ki dago ki kalleni, Haiydar ne a gaban ki yake magana, nasan zakiji zafin wannan auren haka kuma zakiyi bakin cikin auren wanda bakya so kuma baya sonki, Ni dan uwanki ne bazan ki kiba, matukar dae zaki cire kowa a ranki ki rungumi kaddara, to insha Allah bazaki samu matsala daga bangarena ba" "Daga mishi kai kawae tayi alamar gamsuwa daga nan dae yaja hannunta suka shiga daki, sunyi alwala a tare suka gabatarda sallar godiya ga ubangiji haka suka kwanta kowa yana sake saken sa, kai a takaice dae a wannan Daren Haiydar ya zama cikakken namiji don ya dan dani zumar da bai taba dan danar taba ya kuma jinjinawa kanwar sa haka kuma ya samata Albarkar rike mutunci ta da tayi" "kwanaki sun ja sosai Haiydar ya shiga sabuwar rayuwa ya yarda zagin iyaye yafi zabinka ya tabbatar wa kansa wannan itace Kyakykayawar kaddara haka kuma yayi amman na da cewar safeer a kullum wato( *AUREN BAZATA ALKHAIRI NE*) " ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Yau watan twins shida a duniya sun girma sunyi wayo sosai haka kuma kyansu ya dada fito kamar ka sace su, kuma yau Shukrah zata fara aiki a *MARYAM CLINIC* Hakan ne yasata tunda ta tashi tayi sallar a suba bata koma B tanata kiciniyar hada breakfast ga twins sai rigima suke ta rasa inda zata sa kanta ta dauki wannan ta goya wannan sukayi shiru abinsu zuwa can ta ajiye su ae tana juyawa suka kuma fasa kuka, zuciya ta cita ta kwada wa *Labeeba* duka a bayanta ae ko akan idon safeer wannan abun ya faru ya kara so ransa a hade kamar be taba dariya ba ita kanta Shukrah ta tsorata, ya daga *labeeba* yana jijjagata saida tayi shiru sannan ya juya yana kallon Shukrah da fuskarshi datayi ja saboda bacin rai ya nuna da yatsa yace "wannan ya zama na farko kuma na karshe dazaki sake dukarmin yara in bakya sonsu ni ina son su, wannan ma ae mugunta ne zaki kama yarinya kina duka me ta Sani? Kuma ki hada min kayan su zan kaisu gidan Mamah kafin in auro wadda zata kularmin dasu, yana kaiwa nn yayi ficewarsa ya barta, ae Shukrah bata san sanda ta zube ba a gurin tana kuka kamar ranta zai fita, tayi data sanin dukan labeeba datayi sau ba a dadi, ganin datayi lokaci yana kure mata yasata mikewa taje tayi wanka a gurguje ta shirya tadau labeeb ta fice a gidan, Gidan Ammii ta kaisa sannan ta fice, Sanda ta karasa asibiti office din *DR. MARYAM ANAS* Ta wuce kai tsaye" "Shukrah bata wani yi mamakin ganin karamci da mutunci da kuma girmamawar da *Maryam Anas* tayi mata ba don tasan labarinta gurin Ammii, Mamah da Safeer ta babbatar zatayi abinda yafi haka" " *DR. MARYAM* Da kanta takai *SHUKRAH* office dinta, kuma a gaban ta tafara attending patients, sosai ta ya bawa Shukrah kuma bata boye a cikin ta ba saida ta fito ta fadamata" "Shukrah nayi mamaki sosai yadda kika iya aiki haka " " Dariya Shukrah tayi sannan tace ai ban manta ba saboda nasa abun a raina kuma ina karanta littattafai sosai dasuka shafi bangaren ido" "ae haka ake so Shukrah Allah yayi miki Albarka kinji DR. MARYAM Tace sannan ta fice" 1:35pm *SHUKRAH* ta gama komai saboda hk sai da ta jira 2:00tayi sannan taje tayi wa Dr Maryam sallama, gidan Ammii ta fara zuwa tayi sallah taci abinci sannan ta dauki labeeb suka wuce gidan Mamah, basu wani dade ba tadau labeeba suka wuce gidansu" "4:35 pm safeer ya shigo gidansa yana wani cin magani wae shi a dole fushi yake da Shukrah, Shukrah wadda take cikin kitchen da gudun ta ta rungume shi tana mishi oyoyo, ya tabbatar baze iya yin fushi da Shukrah ba don ta zame mishi jigo a rayuwar sa, matseta yayi sosai a jikin sa yana kissing wuyanka, zuwa can yadago yana kallon ta, Shukrah ya office da Aunty Maryam hope every thing is moving fine " " Lafiya kalau Shukrah ta bashi answer sannan taja hannunsa zuwa dakinsa, da kanta ta mishi wanka ta tayashi shirya wa sannan suka dawo parlour tadau labeeb ya dauki labeeba, sunacin abinci suna basu haka kuma suna dan taba hirar su, cikin hirar ne Safeer yake fadawa Shukrah iyayen DR. MAHMOUD Sun kawo kudin auren Aysher kuma ansa ranar biki nanda wata goma " " To Allah ya sanya alheri ya kuma sa ayi damu Shukrah tace fuskarta dauke da murmushin jin dadi " " Ameen ameen likitan ido me bawa mutane glasses, nima idona namin ciwo har bana iya gani sosai yaushe zaki min glass Safeer Yace yana dariya sosai" "Dariya itama Shukrah tayi tace duk sanda ka shirya ka sameni a office zanmaka daga hk tadau plate din da suka ci abinci tawuce kitchen don wankewa........ *SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💘 [5/24, 10:20 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻 ( *An unexpected marriage*) *Written by* *Zainab Yakasai* *Shukrah* *Dedicated to Miemie bie* 4⃣2⃣ "sosai shukrah take jin dadin aikin ta don batada wata matsala da mijinta tunda yana so, HK batada matsala da *Maryam Anas* don ba laifi shukrah ta iya aikin ta kuma batada kyashi" "kasan cewar mutane masu matsalar ido basuda yawa yasa SHUKRA kullum take tashi a office da wuri hakan yayiwa kowa dadi musamman ma Safeer a cewar sa gwara Shukrah tayi tarbiyyar yaranta da kanta, bawae don bae yarda da da tarbiyyar su Mamah bane a a shudae kawae yafi ganewa hakan ne" °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *Bayan wata takwas* Abubuwa da yawa sun faru a rayuwar ma'auratan nn guda biyu,twins sun girma sunyi wayo sosai don yanzu har suna iya tafiya,magana ma suna tilastawa Kansu suna dan gwadawa" "Yau ta kama Saturday kuma kamar yadda suka saba basa fita week ends saboda haka yau duk suna gida, Safeer na kan one sitter ya daura Labeeba kan jikinshi yana mata wasa yayinda labeeb ke wasan sa daga kasa kusada Shukrah ,ita kuwa Shukrah tana zaune ta maida hankalinta kan wani littafi da take karantawa" "Safeer ya kalli Shukrah sannan ya kalli labeeb yace 'Sweetheart ' kirawo min Shukrah" "Labeeb ya dago Kansa ya kalli Daddy'nsa sannan ya kalli Shukrah wadda batama San me sukeyi ba ya Kara kallon Safeer,Safeer ya daga Masa kai,sannan ya Mike yana tafiyarsa irin ta 'yan koyo yazo gaban SHUKRA ya riko hannunta yana Mata murmushi yace" "Chuklah Jo Daddy". Yana nuna mata Safeer Wanda ya dage sai Dariya yake mata, ta turo baki gava ta bata fuska wane zatayi kuka ta kalleshi" " Ynx sabida Allah other half Shukrah zaka koya was yaran nn fada ko,? Dariyar ya tsagaita sannan yace yi hkr yan matana ni bance yacemiki Shukrah ba shi ya fada" "Murmushi kawae Shukrah tayi ta mayar da hankalinta kan book din hannunta don tasan in ta biye masa haushi da takaici zaita tura mata" "shirye shiryen bikin Aysher ya kankama tunda next month za ayi bikin hakan nema yasa Mamah da Hajiyar Haidar suka shirya tsab suka tafi Cairo donyin siyayyar bikin ,sati biyu kawae sukayi a can suka dawo inda aka shiga cikin bikin gadan gadan" "Mutanen Mamah duk sun halarchi bikin kuma sunyi bajinta ba kadan ba, ciki kuwa harda *Aunty Maryam Ana's* ,sosai Mamah keji da ita don a duniya batada kamarta duk da kasan cewarta kawace a gurinta amma tamata abinda yan uwanta da yawa basuyi mata ba,hakan ne yasa ta Kara mata matsayi sosai kuma take alfahari da ita" Sunday 23 December 2016 aka daura AUREN *Mahmoud Mustapha da Aysher Muhammad mai lafiya* Kan sadaki naira dubu hamsin, musalin sha biyu na rana, sosai Auren ya samu albarkar manya manyan mutanen da suka halarta" "Karfe takwas da rabi na dare aka kai amarya dakin ta" "Rayuwar Safeer da Shukrah rayuwa CE da aka gina ta cikeda so da kauna,yarda ,amana, karamci dakuma mutunta juna, sosai suke son junansu sika kuma yarda da Kansu" "Shukrah a kitchen tana wanke wanke yayinda labeeb da labeeba suke tayata da barna, Safeer ne ya shigo cikin kitchen din yana Yar wakar sa da alama dae yana cikin nishadi,karasowa yayi kusada Shukrah ya nannade hannun rigarsa ya sunkuya yana tayata daurayewa" "Other half yaushe za ayiwa twins kani ne sunyi girma fa yace yana kallon ta cikin ido" "Dau ke idonta tayi daga kallonsa tana murmushi kasa kasa sannan tace 'ynx idan nacema inada ciki ae saika rufeni da duka yara wata goma sha biyu amma ace za a musu k'ani" "Ware idanunsa yayi sosai a kansa don ta bashi mamaki sosai be taba tunanin zatace HK ba shi a ganin sa Shukrah tanada hankalin da ko ciki ta samu bayan ta haihu da wata biyar bazata yi korafi ba, amma sai yaji Sabanin hk, shiyasa ma yace' Haba Shukrah da girman ki da hankalinki zakice HK," "Dariya tayi don taga kamar abinda tace ya bata ransa tace' yi hkr Ya Safeer ni ko ynx ma a shirye nake kazo kamin ciki shknn" "Haka kikace Shukrah? "Haka nace, meye to ae mu munci dubu sai ceto ya safeer Shukrah tace tana dariya sosai,daga nn ta kwashe plates din da cups duk ta jerasu a muhallin su sannan ta dawo ta wanke sink din" "Shammatar ta Safeer yayi ya dagata cak ya nufi bedroom da ita yana cewa bakince kinci dubu sai ceto ba,kuma a shirye kike nayi miki ciki ko,ae ko ynx zan baki triplets Ma, kan gado ya ajiyeta, itadae Shukrah batada bakin magana tunda ita ta janyo wa kanta,shafa ta ya fara yi tunda kanta har zuwa kirjinta duk ya wani susuce dan dan kwana biyun da beyi ba, haka dae yayita romancing dinta har ya cimma burinsa ae nan ya Kara susucewa donji yayi Shukrah ta zamar masa sabuwa fill don Shukrah bata wasa da gyara sam nan ya fara Mata surutai ,Shukrah na baki gidana na zoo road, na baki duk wani dukiya Dana mallaka na baki kaina Shukrah na baki raina gaba daya gani kiyi yanda kikeso dani Shukrah ki juya ni yadda kike so kinji...... "Da yamma bayan sunyi wanka suna zaune suna hira Shukrah ta kalleshi ta kyalkyale da dariya ,ya hade rai yana hararar ta don yasan mugunta ta shirya masa, a kufule yace' meya faru kuma' "Dariya Shukrah ta cigaba dayi harda rike ciki tana kallonsa HK kuma tana nunasa da daya hannunta ,haushine ya cika shi ya mike yazo kusa da ita, Kafin tace zata tashi ta gudu harya riketa ya matseta sosai har saida tayi Yar Kara ,yace fadamin me yasaki dariya kafin in bata miki rai" "Sai da takara darawa sannan tace""Shukrah na baki dukiya ta ,nabaki gidana na baki kaina kiyi yadda kikeso dani ta karashe tana sake yin dariyar sosai" "Sake matseta yayi ya hade rai don ya gano abinda take nufi yace to waye ya fadi hakan? "Dariya ta kuma yi sannan tace waye to inba Ya Safeer ba" ."Murmushi ya kuma yi sannan yace nidae sharri kika min amma zan hkunta ki da daddare," Bayan kamar sati uku Shukrah ta Fara ganin canji a jikin ta don ynx wata kasala CE ke addabar ta ga yawan zazzabi da ciwon kai ga kuma wani saurin bacci da take data dan jingina sai bacci wani lokacin ma ko girki take data dan zauna sai bacci," "Shukrah CE a kitchen tana dafawa twins indomie don basa son cin abinci sosai, da zarar sun faracin wani abun da sunci sau uku zuwa hudu zasu dena ci, ga kuma rigima dasuke damunta dashi Sam basa barinta ta huta in bacci ma take haka zasuje su hau kanta suna tsalle suna'chuklah ci taci cijo Daddy ,wani lokacin sai ta hada da duka suke nutsuwa su kyaleta shiyasa ma ta yanke shawarar yaye su tunda sunyi wayo sosai" "Tana zuba indomie din ta dawo ta kwanta a kasa Dan danan kuwa bacci ya kwashe ta zuwa can indomie ta fara kamawa ,Safeer dake bacci a parlour yaji kauri na Neman halaka shi ga twins sai tari suke suna kuka, da sauri ya karaso kitchen din kai tsaye gurin gas ya nufa ya kashe sannan ya dawo gun twins ya daga su yana jijjiga su,duk wannan abinda ake Shukrah bata sani ba, Haushi ne yasa Safeer fara bubbuga Shukrah yace meye HK wae yake damunki Shukrah ko ina kika samu sai bacci kin barmin girki yana konewa yarana sai tari sukeyi amma ke sai baccin ki kike hankali kwance ,kije kiga doctor mana in cuta kike ya baki magani" "Taikaici ne ya rufe Shukrah don tasan ko a mafarki bazata iya mayar masa da magana ba shiyasa ma ta mike ta dau wayarta ta koma parlour tayi kwanciyar ta sai bacci, sanda Safeer ya futo yaga har ta koma bacci tsaki kawae yaja ya rike hannun yaransa suka bar Gidan........... *SHUKRAH YAR GATAN MIEMIEBIE*💞 [5/26, 1:14 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻 ( *An unexpected Marriage*) *Written By* *Zainab Yakasai* *SHUKRA* *Dedicated to MIEMIEBEE* 4⃣3⃣ "misalin sha biyu da rabi *Shukrah* ta gama attending patients NATA,tana zaune shiru kasan cewar bazata tafi gidaba sai 2:00pm bacci ta fara ji tun tana kokarin hana kanta yi har ta saduda ta kifa kanta a jikin desk dan danan ko ta fara baccin" *Aunty Maryam Ana's* taji shukrah shuru don ta saba in dae ta gama attending patients gurin ta take zuwa suyi hira,hakan ne yasata mikewa da niyyar dubo Shukrah, sai da ta fara duba Dr.Nuriyya taga tana nn sannan ta wuce office din Shukrah" "Da sallamar ta ta karasa office din amma ga mamakin ta sai taji shiru, tura kofar tayi ta shiga taga Shukrah kwance tanata bacci abinta, ta karasa jikin desk din tana bugawa, kamar daga sama shukrah taji bugun ta dago da sauri don ta tsorata sosai,Ganin Aunty *Maryam Ana's* yasata turo dan bakinta tana shirin yin kuka" "Sleeping on duty ko? Good ki sameni a office, zaki answer query Aunty Maryam Ana's tace tana dariya sannan tayi gaba, Dariyar itama Shukrah tayi sannan ta dau handkerchief ta goge fuskar ta ta fita ta rufe office din ta wuce office din Doctor Maryam, a zaune ta sameta tana duba wani file ta karaso ta zauna a side chair din office din tana kallonta" "Lazy Doctor daga duba patients basufi 30 ba amma har kin fara bacci ko,meye matsalar kine wae kwana biyun nn ?Inji Dr.Maryam Ana's" "Murnushi Shukrah tayi ta kauda kai don tana gudun abinda zai je ya dawo, kamar bazatayi magana ba sai can tace' Nima Aunty bansan meke damuna ba gaba daya banajin dadi, yawan bacci, jiri wani lokacin ma har da zazzabi nake ta fama dasu a yan kwanakin nn"ta fada cikeda damuwa "Kin harbo jirgi Shukrah, Allah ya raba lafiya da kaina zan miki test don INA son sanin watansa nawa Dr.Maryam tace sanda ta taso ta dawo kusa da Shukrah" " Result na Test din da akayiwa Shukrah ya nuna tanada ciki har na tsawon wata biyu da kwana uku, Dr.Maryam Ana's ta kalli Shukrah da fara'Arta tace sannu Shukrah Allah yasa twins ne ko nasamu amin takwara, Shukrah ta bata fuska kamar zatayi kuka'Aunty nifa banason cikin nn watan twins fa Tara, yazanyi dasu fisabilillahi" "Murmushi Dr Maryam tayi tana kallon Shukrah, tace koda wasa karna kara jin kince bakyason k'aruwa Shukrah,ko kinsan wani son haihuwa yake kamar zaiyi hauka amma Allah bai bashi ba,ita haihuwa babbar kyauta ce bakowa Allah ke bawa ba amma ke kinsamu kice bakya so Shukrah, Allah da kansa yace yanajin kunyar idon duk Wanda bai azurta da haihuwa ba, haba Shukrah ina hankalinki ya tafi? Yaranki sunyi girman da ko yanzu zaki iya yaye su, me kike tunani Shukrah" "Hakikanin gaskiya maganar Aunty Maryam ta shiga Shukrah, kuma itama ta sani amma ta share tayi rau -rau da ido kamar zatayi kuka tace insha Allah koda wasa bazan kuma fadar hakan ba kuma Alhamdulillahi Allah yana sona shiyasa ya bani haihuwa Allah ka bani ikon tarbiyyantar dasu kan hanya madai~daiciya" "Ameen Yar gata na cewar Dr.Maryam sanda take hada kayanta, atare suka fito da Shukrah Inda take rokon Shukrah tazo da twins gidanta ran Saturday, Shukrah kuma ta tabbatar mata zasuzo harda Safeer ma ,nan sukayi sallama kowa ta shiga motar ta suka fice *MARYAM CLINIC*" " yau ta kama saturday kuma Kamar yadda Shukrah tayiwa Dr.Maryam Alkawarin kawo mata ziyara ran Saturday haka suka shirya tsaf gurin 12:00 bayan Shukrah ta gama duk ayyukan ta suka kama hanyar Gidan Doctor Maryam Ana's, cikin mota Labeeb ya tabo Shukrah yace 'Chuklah jidan Aunty mayyam jamu ae ko' ,Shukrah ta doke bakinsa tace wace'''Shukrah'''? ,ae kamar jira yake ya fasa ihu harda fadowa daga kan sit ya buga kansa kuwa a jikin driver sit ya dinga birgima wane Shukrah Zane mishi jikinsa tayi,Safeer yayi saurin gangarawa gefen titi yayi parking ya juyo yanawa Shukrah mugun kallo sannan yace'Wae Shukrah sau nawa zan hanaki dukarmin yara,ko saboda ban isaba ne yasa bazaki jiba, meyayi miki ma da har ya cancanci duka daga gareki, sai kace bake kika haife suba komai duka, me zakiji ajikin yaron nn in kin dakeshi" "Labeeb ko tunda Daddy'nsa ya Fara magana yayi shuru kamar yasan me yake cewa sai ya kalli Shukrah ya juyo ya kalli Safeer,...Shukrah bata iya mayarwa da safeer magana koda kuwa rashin mayar da maganar zai zamo mata matsala, amma tanajin tausayin Safeer bataso son da yake yiwa yaransa yasa shi rufe idanunsa ya kuma toshe kunnensa haka kuma ya juyawa gaskiya baya shiyasa ma yau ta daure tace "Haba ya Safeer Dan Allah me yasa wae kai kullum in yaran nn sukayi laifi saika rufe idonka ka nuna kai bakason ayi musu hukunci,bayan ice tun yana danye ake tan kwara shi.. Kuma naga ae ba wani Abu nayi masa bige masa baki kawae nayi sabida ya kirani da sunana ko saboda Ina son su sai ya barsu suyi yadda suke so ?karka manta fa yaranmu amana ce Allah ya bamu kuma zai tambayemu, me zamu ceda Allah in ya kasance mun koma gareshi ba tare da mun sasu akan hanya madai daiciya ba,nasan kafini sani kuma ba fada maka nayiba dan baka sani a a na tuna tarda mune, Amma dan Allah in na bata maka rai ka yafe min ban Dada da niyyar bata ran kaba kaji.. Tana kaiwa nan ta Kifa kanta jikin window wasu zafafan hawaye suka fito Mata a kokaci days kuma tana da tasanin saukin bakin da tayi ita a rayuwar ta batason wani ma ya bata ran safeer bare ma ita da kanta ta bata" "Shiru Safeer yayi yana nazarain maganar ta ya tabbatar da cewa gaskiya ta fada, take yaji ya kara mata matsayi ya kuma Dada tabbatar wa yayi dacen mace ta gari kuma yaransa sun yi dacen nahaifiya ta gari.. Sonta yaji yana ratsa duk wata gaba ta jikin sa,ya juyo yana kallon ta har a lokacin bata dago ba yace cikin zuciyar sa'Ya Allah ga salihar baiwarka nan kayi mata gafara ka buda mata ka kuma kareta daga sharrin duk wani mai sharri, Karasowar da sukayi Gidan Doctor Mariam Ana's yasa Shukrah dagowa suka hada ido da Safeer suka sakarwa juna murmushi ,Safeer ya fito ya bude mata kofar motar ta fito bayan ta dauko labeeb daga kasa nan inda ya gama rigimarsa yayi bacci" "Safeer ya rike Mata hannunta yace Other half bacci? "Murmushi tayi tace wallahi nima bansan inayiba saida motar nn ta tsaya sannan na farka, Murmushin shima yai sannan suka shigo parlour" "Da murnar ta tafito ta taresu tana musu ya hanya bayan sun zauna ne kuma ta tashi ta fara kawo musu drinks, hira sosai sukeyi Dr.Maryam sai yaba halayen SHUKRA take Safeer yana tayata, yinin ranar a Gidan sukayi harda Safeer Wanda sallah ce kadai ke fitar dashi a Gidan, don dama can shi jinin su yafi a haduwa Dana Dr.Maryam duk cikin kawayen Mamah tanaji dashi kamar danta" "Sai bayan sallar isha suka bar Gidan,Labeeb Dan rigima wae anan zai kwana suna tafiya ko barin layin basuyiba ya dasa kuka wae Sai ta kaishi Chuklah,ae kuwa ba shiri ta Kira su suka juyo sukadau Dan rigimar su suka wuce gida" *Bayan wata takwas* "Cikin *SHUKRAH*ya girma sosai kusan ma yafi na twins girma abinda ya tashi hankalin Shukrah Knn musamman ma in ta tuna kalar wahalar da tasha da haihuwar twins har kuka take duk ta Hana kanta sukuni gani take kamar zata mutu sai ta zauna tayi shiru tana tunani don yanzu ta dena zuwa aiki tunda cikin ta yakai wata takwas" "Yau ta kama Saturday amma Shukrah ce kadai a gida sai Labeeba dake kwance jikin Shukrah shi Safeer yaje Gidan Haiydar shida Labeeb sun tafi kai Zafeera asibita zata haihu, Kasan cewar Zafeera mai juriya yasa ba a wani sha fama da ita ba ta haihu cikin kankanin lokaci, ta haifi da namiji murnaa a gurin Haydar da Safeer kamar me dan danan suka kira Hajiya a waya suka sanar da ita ,nan itama ta Fara kiran yan uwa a waya cikin kankanin lokaci asibiti ya cika da jama'a ,a ranar da yamma kuma aka yi discharging dinta tunda lafiyarsu kalau " "Washe gari a can Shukrah ta yini yan uwa sai zuwa Duke,ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Zafeera wato Abdullahi za a dinga kiransa da little " Bayan wata biyu ranar wata Friday Shukrah ta tashi da matsanan cin ciwon Mara har bata iya motsi ko kuka ta kasayi sai hawayene kawae yake zuba a idanunta ,ga wayarta tana gani takasa dauka ta Kira Safeer kasancewar bayanan yanacan wajen Gina company dinsa tun safe *Shukrah Yar gatan Miemie bie💞 [5/26, 7:37 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻 ( *An unexpected marriage*) *Written by* *Zainab Yakasai* *Shukrah* *DEDICATED TO MIEMIEBIE* 4⃣4⃣ DaKyar cikin sa'a Shukrah ta mika hannu ta dauko wayarta number Safeer tayi dialing, Safeer dake tsaye yaji vibration cikin aljihun sa yayi saurin dauko wayar yayi picking da sauri ganin Shukrah CE me kiran, "Hello other half kazo zan mutu kawae Shukrah ta iya cewa tayi wulli da wayar sakamakon marar ta data juya mata ,rike cikin tayi tanata juyi a kasa, A bangaren Safeer ma jin shirun da Shukrah tayi yayi mugun daga masa hankali ko sallama beyiwa haiydar ba yayi ficewar sa da sauri" "Sanda ya karasa Gidan Shukrah gaba daya ta fita a hayyacin ta, duk karfin hali irin na Safeer sai da ya goge kwalla ganin irin halin da shukrah ta shiga ga jini sai zuba yake, ya rasa yadda zaiyi, dakyar ya tattaro nutsuwar sa ya daga Shukrah cak ba tare da ya damu da jinin dake zuba a jikin taba, yanasata a mota ya zagaya ya shiga yayi reverse ya fita da gudun gaske" "Kai tsaye ya wuce Standard (Asibitin Dr.Mariya galadanci) cikin sa a ya samu Dr.Zainab zata fita, Zainab ganin halin da Shukrah take ciki yasata karbar ta tawuce da ita labour room" "Ba karamin tashin hankali Safeer ya shiga ba ganin awan shukrah uku cur a labour room amma ta kasa haihuwa ko kuka ta kasa sai innalillahi wa innailayyi raji'un take fadi ,nan danan ya kira Mamah ya fada mata sannan ya kira Ammii ma ya sanar da ita, bayan kamar minti goma wata nurse mai suna Salmah tazo tace masa dole fa sai Shukrah tasha inducing drug saboda HK yaje ya nemo,ba tare da yasan Inda zai samu ba ya fito duk Air condition din dake cikin dan karamin hospital din nn amma Safeer ya jike da gumi,kicibus sukayi da Haiydar Wanda Mamah ta kira ta sanar dashi zancen haihuwar,Haiydar ya dafa Safeer cikeda tausayawa yace haba Safeer be a man mana duk ka wani rude ka gigice, cuta ae ba mutuwa bace" "Dafe kai kawae Safeer yayi don bayason magana ma gaba daya zuwa can yace inducer zaka samo min Haiydar ,Shukrah tana cikin wani hali.. Pls help me I can't afford loosing her, I just love her "Da sauri haydar ya wuce be Dade ba sai gashi da inducer yaje ya mikawa wani Nurse yace ya kai musu sannan ya dawo gurin Safeer yana bashi baki," "Cikin ikon Allah Shukrah nashan inducer ta nemi ciwo ta rasa ji tayi kamar zatayi amai, ta kira nurse tace mata "Amai zanyi kamani inje toilet" "Yi aman ki Anan kinji tace mata, kakarin Aman Shukrah tashiga yi nan danan sai ga baby ta fado ta sa kuka kuwa Shukrah ta koma ta lafe sai bacci,cikin bacci Shukrah taji bayanta ya wani amsa,ta bude ido a firgice ta fara kuka jitake kamar zata mutu ga baby tana gani nurse tana gyarawa, sake sakin ihu tayi sakamakon mararta da bayanta da suka kuma kullewa tace wayyo Allah ka taimakeni, duk likitocin suka yo kanta, Dr Zainab ta matsa cikin ta tace Salma zo akwae wani acikin nn da alama, Salma ta karaso da sauri tarike Shukrah tace yi nishi kinji Shukrah yanzu babyn zai fito, Shukrah ta marai raice tace vazan iya ba wallahi ni mutuwa zanyi ki kiramin other half muyi sallama" "Cikeda tausayi Dr.zainab shiga shafa kan Shukrah,tace cutafa ba mutuwa bace Shukrah kiyi hkr kiyi nishi ko guda days ne please" "shukrah bata San sanda ta kankame Dr Zainab ba tayi wani nishi ae ko sai ga baby nan placenta ta fito, an an aka shiga gyara babyn cikin kokaci kadan aka jerewa Shukrah twins dinta duk mata, sai anan aka bar Safeer da haiyar su shigo,Shi Safeer bamaya yin ta Twins shi ta Shukran sa yakeyi ya karasa da sauri ya rungume ta yana mata sannu, shiko haiydar Twins yaje ya hade ya rungume yana kissing dinsu nan da nan suka shiga ransa, yashiga snapping face nasu yana turawa mutane, kafin kice kwabo asibiti ya cika da yan uwa da abokan arziki, zuwa dare aka yi discharging nasu suka tafi gida " " Washe gari tun safe mutane suka cika gidan ba masaka tsinke Safeer ko wanka be samu yayi ba sai gidan Haiydar ya tafi yayi acan, haka dae gida ya cigaba da cika har ana gobe suna, da sassafe Aunty Maryam Anas ta aiko da trolleys uku cikeda kayan babies dana maman babies, da kuma raguna guda biyu, " " Ranar suna da asuba safeer ya fadi sunayen da yayi yaransa huduba da, ta farkon yasamata *Fateema*za a dinga kiranta da ( *Afaf*) sunan Ammii 'n Shukrah ta biyun kuma *Maryam*( *Anan*) taci sunan Aunty Maryam Anas, haka aka sha shagalin suna kowa sai murna yake, don har yan uwan su Shukrah na kd, dana maid, dana Damaturu sai da suka zo, haka yan Adamawa duk sunzo, Washe gari da yawa suka tafi wasu kuwa sunce sai next week " " Safeer baya samun ganin Shukrah kwata kwata amma be damu ba kasan cewar shikansa bashida lokacin kansa don aikin company yayi nisa sosai kuma akwai bukatar lallai yaje gurin saboda hk kullum inya fita da safe baya dawowa sai dare " " Yau sati biyu da haihuwar Shukrah kuma yau aka kammala ginin company 'n Safeer, Yan uwa duk sun koma sai Shukrah kadae da twins don labeeba da labeeb an tafi dasu gidan Ammii acewar ta wae basaji zasu iya buge mata yaranta, wanka tayi ta shirya cikin wani material blue tasa ear ring pink da bangles pink colour ta shafa powder kawae da lip stick ta daura pink din karamin veil a kanta ta dauki *AFAF* Tana feeding dinta, safeer ne ya shigo cikin dakin hannunsa rike da shopping ya ajiye yana mata murmushi , karasowa kan gadon yayi ya zauna ya kura musu ido yana jin son su sosai aransa, dauko *ANAN* Yayi ya daura kan cinyarsa yana shafa gashin daya rufe mata goshin ta, yace Other half wannan yarinyar tana kama dake duk nafi sonta cikin yaran nn 4 " " Dariya Shukrah tayi tana kallon *AFAF*Tace Nikuma nafison wannan saboda da kai take kama wallahi, murnushi yayi yace mummuna da ita kuwa sannan ya dauko wayarsa yayi snapping Shukrah a yadda take tana feeding *AFAF* bata rai tayi wane zata yi kuka tace wallahi banaso me yasa zakimin hoto a hk, sai wasu sun gani ko, ta zare *AFAF*daga jikinta sannan ta gyara rigarta ta ajiye ta ta mike da niyyar fita, yayi Saurin ajiye *ANAN* Yazo ya rungume ta tabaya yace meye nayin fushi kuma, ungo wayar kiyi deleting da hannunki kinji tawan" "Karbar wayar tayi tayi deleting pictures din sannan ta juyo ta rungume shi tayi masa kiss a forehead, Saurin rike fuskarta yayi yashiga kissing din ko ina na fuskar kafin ya gangaro bakinta yafara tsotsa kamar wani mayunwaci " " Yau akayi bikin bude company'n safeer, bikin daya samu halartar manya manyan mutane yawanci abokan Abbah ne sai ko abokan aikin Safeer din, *Ahmad da Azeeza* ma sun zo, zokuga murna gun Shukrah jitake kamar ta goya *Azeeza* ta rasa inda zatasa kanta sai hidima take da ita, haka aka bude company mai suna *MAI LAFIYA GROUP OF COMPANY*, haka taro ya watse washe gari kuma aka yi saukar Alqur'ani mai girma akayi addu ' ar kariya sannan aka tashi" "Bayan kwana arba' in Shukrah ta koma aikin ta don miemie ta dawo gidanta da zama ynx tana ss3 sun gama waec suna jiran Neco saboda hk bata zuwa ko ina sai zaman rainon twins" "Bayan shekara uku " An samu nasorori masu yawa a company'n Safeer haka ma Shukrah tasamu nata nasororin don ynx tayi suna sosai kan kwarewarta a fannin ido, Mutane da dama Shukrah ta dauki nauyin musu aiki haka ma glasses kyauta takewa mutane (Nima ita tayi min nawa kyauta), sosai take samun albarka gurin mutane, haka ma Daddy ya naji da ita yana kuma alfahari da ita" Yau Aysher ta haihu, sai dai dan bezo da rai ba, haka aka sha kuka aka barwa Allah, " " Yau graduation din su miemee, zo kuga rawar kai sai da Shukrah Ta mata dinki kala biyar na get together da zasuyi, haka Mamah ma set uku ta dinka mata" "6:20pm Miemie ta gama shirin tafiya Get together, riga tasa body hug pink da jeans blue tayi rolling da pink din veil tasa pink flat shoe tadau wata pink purse tasha makeup kamar wata makeup artist maryam tafida ce tayi mata, parlour ta fito ta kalli Mamah, Mamah yanzu zamu wuce ina car key dinki zanbiya in dauki Amatullah mu wuce" "To Allah ya kiyaye hanya, Mamah tace tana mikawa Miemie car key dinta, kaci bus sukayi da safeer yana kokarin shigo wa karemata kallo yayi sannan yace 'gidan ubanwa zaki a hk'?, tura baki tayi sannan tace get together zani, kwada mata lafiyayyen mari yayi yace ke mahaukaciyar inace? A hk zaki fita ko to wallahi ba inda zaki, har gaban Mamah ya kaita yayi mata fada yayi mata nasiha sosai har sai da tayi kuka sannan ya wuce ya bar gidan" "Labeeb da labeeba ne suka shigo cikin gida da gudu daga school Shukrah da safeer suna zaune suna hira a parlour suka fado kansu" "Labeeb cikeda ihu yace mamy kinsan yau me akayi mana a skul, Shukrah ta girgiza kai alamar a a, yace wild animal 1.LION 2.TIGER 3.LIZARD Labeeba tayi Saurin katseshi tace mamy karya yake lizard reptilian ne, Labeeb da bayason raini ya buge bakinta yace waye makaryachi, ta bare baki zatayi kuka Safeer yayi Saurin cewa selfie🤳🏻 da sauri duk suka dawo bayansa ya kashe musu selfie kuwa" " *ALHAMDULILLAHI* *ANA NAKAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN DUK WANI KUSKURE DANAYI, READERS IDAN NAMUKU BA DAE DAE BA KUYAFE MIN, ALLAH YA YAFE MANA GABA DAYA* *I DEDICATE THE WHOLE BOOK TO THE CHARMING, PIOUS, FAMOUS, GENTLE, TALENTED AND SUPER AMAZING SOUL MIEMIE BIE, MAY ALMIGHTY GOD DOUBLE FOLD YOUR UNDERSTANDING AND LEARNING, MAY GOD MAKES THE BEST OUT OF EVERY THING FOR YOU SWEETHEART, ILYSM BEYOND YOURS AND EVERY BODY EXPECTATIONS* *CANT FORGET WITH YOU GUYS* *ZEE ZEE (JEWEL)* *SOFTIE* *H. JIDDAH* *SAFIYYA GALADANCHI* *BILKISU GALADANCHI* *EESHATULLAHI GONI* *AUNTY SIS* *LUBNAH SUFYAN* *MEELA, MURJA TIJJANI DA*.. *AND THE REST DABAN FADOKUBA KNOW THAT YOU ARE ALWAYS IN MY HEART* *YAN TASKAR NOVELS DA SHUKRAH NOVELS GROUP DA MIEMIEBEE NOVELS DA SHUKRAS KITCHEN DA EESHATULLAHI NOVELS DA KHALEESAT HAYDAR NOVELS KUNA RAINA* *SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE CE KE MUKU FATAN ALKHAIRI*