Ummu Amjad MAƘABARTA NE Daga Alƙalamin Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba) JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Yadda na fara lafiya Ubangiji kasa na gama lafiya. Gaisuwa a gareka dukkan masoya🤗 0️⃣1️⃣ Misalin ƙarfe 3:am na dare gudu take yi a kan titi sai waigen banyata take, wayar dake hannunta ta yi ringing, a hanzarce ta danna za ta yi magana ta ji an yi sama da ita shuu. Ihu take kurmawa ta na faɗin. "Waiyo Umma ku taimakeni za a saceni." Wani irin ɓakin duhu ne ya mamaye idanunta abin da ya ƙara kaɗa hantar cikinta, idanunta tamkar za su fito waje saboda firgici da tsananin tsoron da take ji. Idanunta ta runtse bakinta na rawa zuwa wannan lokacin ta kasa furta koda kalma ɗaya, ji ta yi an dire ta a kan wani abu mai ɗan tudu ta yi saurin buɗe idanunta, ƙara ta ƙwalla ta na ƙanƙame jikinta sakamakon ganin wani zabgegen abu wanda ta kasa ganin tsayinsa, baƙi ne sosai ba ta iya ganin wani kalar abu ne, shi dai gashi nan kamar mutum kamar doguwar bishiyar giginya.. "Hahaha! Ta ji wata dariya mai sa zuciya firgici ta ziyarci dodon kunnenta. Sake ɗago kai ta yi ta juya gefenta ai da sauri ta zaro idanu ta na ja da baya sai ji ta yi ta bugi wani abu, jiki na rawa ta juyo cike da zullimin mai idanunta za su gane mata ta yi arba da ƴar ƙaramar yarinya wacce ba za ya wuce shekaru 7 ba. Bakin yarinyar jini ne ke fita haka zalika kanta yana ɗauke da ƙahuna guda uku, hannayenta har jan ƙasa suke masu dauke da baƙaƙen faracuna masu tsayi da kaifi, kannuwanta tamkar na tunkiya jajaye sai juyawa suke kamar yadda dabbobi ke yi da nasu, ƙafarta sak irin ta biri. Baki na rawa ta ce. "Baiwar Allah ku su waye wai?" Wata mahaukaciyar dariya yarinyar ta yi cikin muryarta irin na ƙananun yara ta soma magana. "Karki sake tambayata mu su waye, idan ba haka ba "Ta ƙarashe maganar ta na zaro mata manya-manyan idanunta baƙaƙe tamkar gawayi ne a kwayar idanun." Muƙut! Ta haɗiye yawu ba shiri, dafata ta ji an yi ta baya ta zabura ta juyo, arba ta yi da wannan dogon ɓakin abin. Saboda tsananin tsoro futsari ta saki cikinta ya murda ta saki zawo ganin wannan shirgegiyar halitta. Runtse idanu ta yi ta ƙasa furta komai in banda futsari babu abin da take saki. "Hahaha! Hahaha! Hahaha!" Sautin dariyarsu suka shiga gigita ta, zuwa can ta ji tsit hakan yasa ta buɗe idanunta. "Waiyo na shiga uku! Ta faɗa ta na kallon ƙasan inda take. Tsalle ta yi ta koma gefe ta na kallon wajan a firgice ta soma magana. "Waiyo ni! A MAƘABARTA NE nake kuma a kan kabari?" "Kwarai kuwa a MAƘABARTA NE kike." Ta ji an ba ta amsa daga gefenta. Juyowa ta yi cike da tsoro ta sake arba da yarinyar nan, baki na rawa ta kuma cewa. "Wai me kuke nufi da ni ne? Me na muku kuke bibiyar rayuwata? Z.. Tsawa aka daka mata ta kasa ƙarasa maganar. "Mu ba'a tambayar mu." Shuru ta yi sai kallon ƙaburburan dake kusa da ita take. Tim! Ta ji ƙaran faɗuwar wani abu, da sauri ta kalli inda abun ya faɗo, baki ta buɗe ta na son yi magana ta ji an manne mata bakin kawai ta zazzaro idanu ta na kallon mutumin da yake ɗan nesa da ita. Kamar kiftawa da bismillah ta ga an fille kan wannan mutumin, zubewa ta yi a ƙasa ta na son yin magana ba hali ta rarrafa ta nufi gangar jikin mutumin idanunta waje. Jini kawai ke ta malala a jikinsa ta ɗaura hannu a ka ta kurma ihu ta ce. "Uncleeeee!" Firgigit ta farka daga baccin da take jikinta ya yi sharkaf kamar an zuba mata ruwa, numfashi take fitarwa ta na jinjina kai sai kuma ta fashe da kuka wiwi ta soma surutai. "Allah ka tseratar da ni daga wannan mugayen mafarkan da nake, wannan abun biyu su waye su da kodayaushe suke kaini maƙabarta?" Zabura ta yi jin ana shafa bayanta ta juyo, ihu ta sa ta na sauka daga kan gadon ganin jarirai guda biyu kwance a kan gadon, kallon fuskarsu ma abin firgita ne. Kafin ta yi ƙwaƙƙwaran motsi sai ganin ɗaya daga cikin jariran ta yi ta tashi tsaye ta na tafiya ta doso ta, ai a zabure ta nufi ƙofar fita ta na kiran sunan duk wanda ya zo bakinta, sai dai ta na zuwa bakin ƙofar ta kasa buɗewa ga wannan jaririyar na doso ta ta na zaro mata ido. Fuskar jaririyar ƙofa-kofa ce wani ɓakin ruwa mai yauki yana fitowa haɗi da wasu irin tsutsoyi suna fitowa suna shiga cikin idanunta. "Waiyo Allah Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Umma! Ku taimakeni aljana za ta kamani Umma, Abba! Abba! Ku ceceni kar ta ƙaraso gurina." Haka take faɗa ta na buga ƙofar da ƙarfi kamar za ta ɓalla ƙofar, juyowa ta yi taga jaririyar ta kusa isowa inda take ta taƙarkare ta kurma ihun da ya fito da dukkan 'yan gidan suka yo ɗakinta. "Suhaima! Suhaima! Buɗe ƙofar mana. Ta jiyo muryar mahaifiyarta na kiran sunanta, sai yanzu ta tuna ƙofar a kulle take, cikin rawar jiki ta murda makullin ƙofar ta buɗe. Ƙoƙarin tareta suke ganin ta na neman gudu, mahaifinta ya kamo hannunta ya ce. "Suhaima wai anya lafiya kike." Kasa magana ta yi sai cikin ɗakin da take nuna musu ta na ƙara ƙanƙame mamanta, mamaki ne ya kamasu suka kalli ɗakin ba su ga wani abu ba.. A tsorace ta ce. "Abba aljannu ne a ɗakin nan ni dai ba zan sake kwana a ɗakin nan ba, yanzu fa ja.. Ba ta ƙarasa maganar ba sakamakon arba da ta yi da wannan jaririyar ta na girgiza mata kai fushi ya baiyana a kan fuskarta. Sororo duk suka tsaya suna kallon Suhaima da zazzaro idanu ta na musu nuni da ɗakin, ƙanenta ya shiga ɗakin ya duba bai ga komai ba ya fito. Tsaki ya ja ya ce. "Dalla can Wallahi Anty kin soma samun ciwon hauka tsakanin jiya da yau" Ya faɗa yana wucewa.". Fama aka dunga yi da Suhaima ta shiga ɗakin amma ta ce ita fa ba za ta kwanta a ɗakin nan ba, Umma ta jata ta kaita ɗakin yayarta ta kwanta. Ganin ita ɗaya ce za ta kwanta ta ce. "Umma don Allah ki zo mu kwanta Wallahi sake ganinsu zan yi ki taimakeni." Ta faɗa ta na zare idanu tare da ƙanƙame hannun Umma. Ganin da gaske tsoro take ji Umma ta ja ta suka kwanta ta maƙale a jikin Umma ta na runtse idanunta. Sosai mamaki ya kama Umma jin yadda zuciyarta ke bugawa, addu'a ta dinga tofa mata ta na shafa kanta har bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.. Washe gari bayan an fito daga Sallah Abba ya dawo gida, a palo ya yada zango ganin Suhaima a palon sai ƙifƙifta idanu take kamar barawon da dubunsa ta cika. Ganin Abba yasa ta dan sunkuyar da kai ta ce. "Go..good morning Abba." Tsuru ya mata da ido yana amsa gaisuwar da ta masa, wayarsa ce ta soma ruri ya fito da ita daga aljihu, ganin mai kiran sai abin ya bashi mamaki har sai da fuskarsa ta nuna. Yana ɗaga kiran da sallama cike da mamaki ya ce. "Sani ina shi Abdullah yake naji wayarsa a hannunka da safiyar nan?" Kuka ya ji Sani yasa ya soma koro masa jawabi. "Uncle Daddy ya mutu." What! Ban gane me kake nufi ba da gaske ya mutu?" Amsa ya basa da. "E muma sai da muka tashi muka gansa an masa yankan rago." "Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Sai ya yi baya rajaf ya zube a kan kujera ya saki wayar ta faɗi ƙasa. Umma da ta fito daga kitchen jin maganar Abba ta ce. "Lafiya dai? Me ya faru naji kana sallallami?" Suhaima kuwa kwalalo idanu waje ta yi ta na jiran taji mai Abba zai faɗa, dafe kai Abba ya yi da ƙyar ya iya cewa. "Abdullah ya wasu." Zabura Suhaima ta yi za ta fankaya da gudu Umma ta yi saurin kamo hannunta , a ruɗe ta kalli Abba ta ce. "Abba Wallahi sune suka kashe Uncle na gansu a gaban idona suka cire masa kai, Abba Wallahi n.. Ba ta ƙarasa ba ta zube a ƙasan carpet a sume..... # comments #share #noting _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [2/25 23:18] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU. *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO( Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣2️⃣ Hankalin Abba da Umma a tashe suka ɗago da Suhaima, da sauri Umma ta nufi kitchen ta ɗauko ruwa har ta na haɗawa da gudu ta miƙawa Abba, ya amsa ya shafa mata a fuskar amma shuru. Umma ta durƙusa ta ɗauki ruwan ta kurɓa ta fesa mata a fuska, numfashi ta ja kamar wadda aka tsikara ta miƙe zunbur ta na zare ido, ganin su Abba a zaune yasa ta matso kusa da Abba ta ce. "Wallahi Abba na gani sun fille masa kai." Kallan kallo Umma da Abba suka dinga yi a tsakaninsu, tunani suke ko dai Suhaima ta samu taɓin hankali ne basu sani ba. Dafata Umma ta yi cikin tashin murya ta ce. "Suhaima wai me ke damunki ne? Shi Baban Sanin ne kika gani an fille masa kai? To in haka ne a ina kika ga an masa hakan?" Fashewa ta yi da kuka ta na riƙe hannayensu ta ce. "Jiya na yi mafarki naga an fille wa Uncle kai a gaban idona, sai gashi yanzu kuma an ce an kashe sa. Ina jin fa abin da shi Yaya Sanin ya faɗa ya ce yankan rago aka yi wa Uncle." Ta ƙarashe maganar ta na kallonsu, sosai take jin wani baƙon al'amari na ziyarar zuciyarta. Ta runtse idanu hawaye suka gangaro Umma ta goge mata ta na ba ta baki har ta yi shuru... "To waye ya kashe shi Suhaima?" Abba da Umma suka tambayeta a tare, dan ba ƙaramin al'ajabi suka shiga ba. "Nima ban ga wanda ya kashe shi ba, amma dai ina gani aka fille masa kai jiya a cikin baccina." Ta faɗa ta na sake fashewa da kuka. Abba ya ce. "Yo wa ya ce miki mafarki gaskiya ne? Kar ma na ji kin faɗawa wani wannan maganar shashancin." Sai da ya gargadi Suhaima sannan ya wuce ya nufi gidan Alhaji Abdallah. Hankalin Suhaima har yanzu ya kasa kwanciya ta kasa tsaye ta kasa zaune, ƙaguwa ta yi da jiran Umma data shiga ɗaki zata shirya su tafi jana'izar Abdullah. Miƙewa ta yi ta shige ɗakin data kwana, a hankali ta shiga tamkar ɓarauniya sai lalleƙa ko'ina take, ganin ba komai ta ja gwauron numfashi ta zauna a kan gado ta na dafe ƙirji. Ko minti ɗaya cikakke ba ta yi a ɗakin ba wani ɓakin duhu ya mamaye ɗakin, hankalinta ne ya tashi ta ƙanƙame jikinta ta na rufe ido. Wata irin zirgiza ɗakin ya ɗauka tamkar zai kifa cikin ƙasa, Suhaima ta ƙarawa kukanta sauti ta na kiran Umma. "Suhaima! Suhaima! Ta ji ana kiran sunanta daga samar ɗakin, hakan yasa ta ɗago kai bakinta na rawa ta kalli samar. Saurin sadda kai ta yi ƙasa ganin yarinyar da ta gani a cikin mafarkinta ita da wannan jariran ta ruƙo su a hannu ɗaya ta na miƙo mata su. Saukowa yarinyar ta yi tare da yaran ta iso gaban Suhaima wutar ɗakin ta ɗan haska kaɗan ta yadda za kaga wanda yake kusa da kai, dariya Yarinya ta yi ta haɗe fuska ta ce. "Suhaima shin kin taɓa ganin inda aka raba hanta da jini?" Girgiza kai Suhaima ta yi ta ƙi yarda su haɗa ido da yarinyar, tsawa ta daka mata cikin fushi ta kuma faɗin. "Ke! Idan kika kuskura na sake yin magana kika girgiza mini kai sai na mayar dake Mage ko Ɓera." Da sauri Suhaima ta ce. "A'a don Allah ki taimakeni ki rufa mini asiri karki mayar dani Mage, ni hasali ma tsoron Mage da Ɓera nake z.. Kafin ma ta ƙarasa maganar su duka ukun suka zama Maguna manya-manyan da su, ɗaya fara, ɗaya baƙa, ɗaya blue duk suka zubo mata idanu tare da yin kukan maguna. Tsalle Suhaima ta yi ta koma ƙuryar gado ta na ƙanƙame jikinta, ganin haka yasa suka kwashe da dariya suka dawo yadda suke . "Za mu tafi amma ki sani muna nan dawowa gareki dan dole ne ku girbi abin da kuka shuka, yanzu wasan zai fara." Waro idanu Suhaima ta yi cike da rashin sanin inda maganarta ta dosa ta ce. "Baiwar Allah to ni mai na muku da har kike cewa zan girbi abin da na shuga? Ni fa ko zagin babba ban taɓa yi ba ballantana kuma yaro kamar ke. Ga kuma wasu jarirai sai firgitani kuke don Allah ku yi haƙuri ku rabu da rayuwata." Wani mugun kallo jariran suka mata wanda yasa ta ji cikin ya bada sautin ƙululuu! "Zan iya taimakon ki amma sai na gama aiwatar da aikina akan sauran bil'adama da nake son gama shi nan da wani lokaci, wannan jariran kuma bani da hurumin faɗa miki su waye su da kansu za su fada miki komai. Rakosu na yi sun ce suna son ganinki shi ya sa na rakosu, amma in ba haka ba ba za ki ganni ba sai a mafarkin ki mu haɗu a maƙabarta, inaso zan yi ramuwar gaiya wadda tafi ta gaiya ciwo." Baki buɗe Suhaima ke kallon Yarinyar har ta dasa aya a maganarta ba ta san ta gama ba, haushi ne ya kama Yarinyar nan ta zabga mata mari a fusace ta ce. "Idan ina magana ba'a tafiya duniyar tunani." Wani irin raɗaɗi da zafi ne suka ziyarci kuncin Suhaima, sosai taji marin har cikin ƙwaƙwalwarta ta dafe kuncin ta ce. "Y..Yi haƙuri Anty." "In kika sake ce mini Anty sai na mayar dake duniyar aljannu." Ta faɗa ta na sauka a gadon, yaran ta rungume kafin Suhaima ta yi magana ta kuma juyowa ta na zaro mata idanu ta ce. "Idan na sake ji kin faɗi wani abu game da mafarki kin san gabar." Ta faɗa ta na ɓacewa daga ɗakin, Suhaima na ganin ta tafi ta miƙe jiki ba ƙwari ta faɗa toilet da sauri, kafin ta tsugunna tuni ta saki futsari a jikin dole tasa ta cire kayan ta nufi bahon wanka.. Ta na murda famfo idanunta na rufewa ta miƙa hannu ta taro ta kai fuskarta, ƙarni ta ji ruwan na yi ta yi saurin buɗe idanunta ta kalli hannunta, zabura ta yi ta na zubar da na hannunsa sakamakon ganin ruwan ya zama jini.. Ta na gefe tsaye sai ta ga famfon ya kunna kansa ta zuba ido ta na kallon ikon Allah, ganin babu jinin ta matsa a tsorace ta tari ruwan zuciyarta na bugawa, a hannunta ta zuba ta ga bai canja ba hakan yasa ta yi sauri ta wanke hannu da ƙafa da kuma fuska gudu-gudu ta fito daga toilet ɗin.. Babu abin da ta yi data fito riga doguwa kawai ta zura ta janyo hijabinta ta sa, da yake a ruɗe take ƙasar kan hijabin shi ne a sama, samar kuma a ƙasa haka ta fito ta na buga sauri kamar za ta tashi sama.. Galala Umma ta saki baki ta na kallon Suhaima ganin yadda ta saka hijabin, sai da ta iso Na'im ya dube ta yana riƙe baki ya ce. "Anty Suhaima da alama sai mun kaiki Kano Dawanau, dan naga alama kin soma abu irin na masu lalurar ƙwaƙwalwa." Harara ta watsa masa tare da jan tsaki ta ce. "To fitsararre maza ka zageni kaji daɗi, ni ban san me ya sa ka raina ni ba. Kodayake ai ban soma kai maka hannu ba ne shi ya sa, wuce dalla can malam ka kaimu lokaci na tafiya." Ta faɗa ta na kuma jan wani tsakin tare da amsar makullin motar dake hannun Umma ta cilla masa ya cafe. Umma ta ce. "To sai ki gyara hijabin ko." Ta ji muryar Umma ta daki dodon kunnenta, hannu ta kai ta laluma hijabin ta ji ba daidai yake ba sai ta juya ya dawo nomal sannan suka wuce a gidan... Kasancewar gidan Alhaji Abdullah ba shi da nisa da nasu gidan basu ɗauki lokaci ba suka iso bakin get ɗin gidan, hon Na'im ya yi Maigadi ya buɗe masa ya shigo ciki. A harabar gidan Abba ne tsaye tare da jami'an tsaro da wasu mutane biyar suna magana a kan kisan, Suhaima ta miƙo kafarta waje ta ɗago ɗayar za ta fito da ita wata irin iska ta bigi inda take ta wuntsila za ta faɗo Umma ta yi saurin tareta. "Ke ki bi a hankali mana saurin mai kike yi?" Ta faɗa ta na sakin ta, dafe ƙirji ta yi jin gabanta na faɗuwa a haka dai ta lallaɓa ta fito. Daret ciki suka wuce Umma da Suhaima, tun daga ƙofar shiga palon suke jin sautin kukan matar Alhaji Abdallah. Cike suka tarar da palon suka nufi inda matarsa take suka zauna Umma na ba ta haƙuri. "Haba Umman Suhaima ku barni na yi kuka, taya za mu kwanta da mijina lafiya lau amma a samu wani ya shigo har ɗakinsa ya masa yankan rago kuma ku ce kar na yi kuka? Shi kenan an mayar da yarana marayu ni kuma na tashi daga matar aure na koma bazawara? Wallahi ko wane ne ya kashe mini miji ba zan taɓa yafe masa ba ko ƙabarinsa yana cin wuta." Matar Alhaji Abdallah ta faɗa ta na kallon 'yan falon idanunta sun yi jajur fuskarta ta kumbura saboda kukan da take. Su Suhaima masu ruwan ido a kusa tuni ta dinga zubar da hawaye, tsoro da firgici sun ƙara samun mazauni a cikin zuciyarta da ma gangar jikinta. Tagumi ta rafka ta na magana murya ƙasa-ƙasa ta ce. "Waiyo Allah ni Suhaima! Me Uncle ya yi suka kashe shi?" Ta tambayi kanta tambayar da tasan babu mai ba ta amsa sai wannan aljanar yarinyar, goge hawaye ta yi ta rausayar da kai gefe ta kalli maman Sani a sanyaye ta kuma cewa. "Allah sarki Mommy ai kuwa za ku shekara dubu ba ku gano komai ba game da kisan Uncle ɗina, duk wahalar banza ce kuke. To amma me yasa suka kashe shi?" Ta kuma tambayar kanta a karo na biyu duk da tasan ba mai ba ta amsa.. Cikin ƙanƙanin lokaci su Abba suka wanki gawar Alhaji Abdullah shi da wasu malamai, ana gamawa aka suturta gawar suka sakata a makara motar malam. Matarsa aka kira ta zo ta amsa addu'a ta na kuka da ƙyar Sani ya janye ta daga kan gawar, bayan ta fita 'yan'uwansa suka shigo kowa ya masa addu'a sannan suka fito da shi daga ɗakin zuwa waje inda za a masa Sallah. Firgita Suhaima ta yi ganin gawar Uncle ɗin nata ana fita da ita, ba ta san lokacin data ɗaura hannu biyu a ka ba ta fashe da kuka ta na kiran Uncle. Mutanen palon suka dinga rarrashin ta da ƙyar ta kyale.. Bayan an dawo daga jana'izar Alhaji Abdullah da Yamma su Suhaima suka koma gida. Shaf-shaf suka shiga kitchen suka ɗaura abincin dare, Suhaima ta yi lamo da ta soma wani abu sai kawai ta yi shuru ta na kallon gefe, idan Umma na mata magana sai ta maimaita iusan sau 5 kafin ta fahimci mai take faɗa. Ita kuwa Umma a tunaninta jimamin mutuwar Uncle ɗinta ne yasa duk ta koma haka, shi ya sa ba ta matsa da tambayarta a kan tunanin mai take.. Suna ɗaura abincin ana kiran sallar Magariba, fitowa suka yi Suhaima ta bi bayan Umma har sun kusa shiga sai kuma ta yo ribas ta nufi ɗakinta. Aro jarumta ta yi ta yafa ta yi bismillah ta sa kai ɗakin ta na muzurai, ba komai a ɗakin kamar yadda ta barsa jiya da dare haka yake, hamdala ya yi ta nufi toilet ta ɗauro alwala. Bayan ta fito ta riƙe baki fuskarta na bayyana mamakin dake cikin zuciyarta ta ce. "To wai ya ma aka yi na manta da ambaton sunan Allah ne lokacin da na yi mafarki? " Ta tambayi kanta ta na sa yatsu biyu ta ɗaura a gefen kan ta murza tare da faɗin. "Da alama fa Na'im maganarsa gaskiya ce ƙila na fara zarewa ne." Sauke hannun ta yi ta gabatar da sallar cikin sauri wacce Hausawa ke cewa shaf-shaf, minti uku ma ba ta yi ba ta gama Sallar. Koda ta salamce miƙewa ta yi ba salatin Annabi(s.a.w) ba addu'ar komai ta fice a ɗakin... Bayan sallar Isha'i Abba ya shigo suka ci abinci aka taɓa hira zuwa ƙarfe goma suka soma sallama kasancewar gobe Monday . Suhaima ta yi tsuru ta tsaya a bakin ƙofar ɗakinta, ganin dai ba sarki sai Allah ta wakkala ta faɗa ɗakin, kan gado ta faɗa ko minti ɗaya ba ta kara ba bacci ya shureta... "Barka da zuwa Suhaima." Muryar wani garjejan ƙato ta ziyarta majiyarta, a zabure ta ɗago ta ganta a tsakiyar ƙungurmin daji, gefe ta kalla ta ganta a gaf da wani ƙaton ƙabari. Kukan da take juyowa ne ya ƙara firgitar da ita, tun da take ba ta taɓa jin sautin kuka mai tsorararwa da saka firgici ba irin wanda take ji ya karaɗe dajin gabaɗaya. Shuu! Ta ji ƙaran wucewar wani abu daga samar kanta, kafin ta yi ƙwaƙƙwaran motsi wannan abin dake samar kanta mai kama da tsuntsuwa ya shureta sama ya illata cikin maƙabartar...... #share #commets _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [2/27 22:36] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣3️⃣ Tim! Aka watsar da ita a kan wani ƙabari babba, daskarewa ta yi a gurin tamkar gunki numfashinta na barazanar rabuwa da gangar jikinta. "Suhaima! Suhaima! Suhaima! Ta ji sautukan muryoyi daban-daban suna kiran sunanta a haɗe, ƙara ta ƙwalla ta na rufe kunnuwanta jin yadda sautukan muryoyin ke ratsa mata kunne har cikin ƙwaƙwalwarta. "Buɗe idanunki na ce!" Aka faɗa cikin tsawa, babu shiri Suhaima ta buɗe idanunta ta sauke su akan yarinyar nan ta fashe da kuka ta na ja da baya yarinyar na biyota. Juyi aka yi da ita sai gata a gaban wani halitta mai sanye da kaya jajaye, baki ya buɗe mata yana dariya. "Hahaha! Hahaha! Hahaha barka da zuwa Suhaima." Zuwa wannan lokacin idanun Suhaima sun ƙafe babu alamar hawaye sai zaro su da take, a firgice ta kalli halittar nan jin an daka mata tsawa jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari ba ta san lokacin da ta dinga taune lips ɗinta na ƙasa ba.. "Wai ni me na muku ne? Ta faɗa bakinta na zubar da jini sakamakon taune lip ɗinta da ta yi." "Har kin manta abin da kika kika mana ne? Aka ba ta amsa daga gefenta; juyowa ta yi ta dubi yarinyar dan yanzu ta na son jin lefin data aikata musu har suke kawo ta maƙabarta, da sauri ta ce. "Wani abu na muku ki faɗa mini sai na baku haƙuri, ku rabu dani na zauna lafiya cikin salama ." Ta yi magana jikinta na rawa, hannu ta kuma haɗewa ta dubi yarinyar ta ce. "Baiwar Allah ki sanar dani lefina a gareku na miki alƙawarin zan gyara halaiyata na nemi yafiyarku. Ni dai a iya sanina ban yi komai ba." Ta faɗa ta na sauke hannayenta. Wani firgitaccen kallo ta aiko mata, nan da nan tsoro ya ƙara shiga jikin Suhaima, ta sadda kanta ƙasa, a fusace ta ce. "Au har ma kin manta abin da kuka aikata mana? Tambayata ma kike na faɗa miki lefinki a garemu? To yanzu kuwa za ki sani sai kin gwammace ba ki tambayeni ba. Yarinyar ta faɗa ta na damƙar gashin kan Suhaima ta mayar da ita cikin maƙabartar ta jefar." Kuka Suhaima ta shiga yi ta na haɗa hannaye ta na roƙon yarinyar amma ta juya mata baya ta yi kamar ba ta san mai take yi ba, wata irin guguwa ce ta mamaye cikin maƙabartar mai tsanani duhu haɗi da ciyayi Suhaima ta ƙanƙame jikinta jin yadda ƙasa ke shiga hancinta da idanunta. Sake damƙar gashinta ta yi ta janyota ƙiii sai gasu a bakin wani ƙaton rami mai zufi, macizai ne a cikin ramin suna ɗaga baki kowanne yana neman abin da zai sara. Kwalalo idanu Suhaima ta yi ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri karki sakani a cikin bala'in wannan, zan yi duk abin da kuke so ki taimaki rayuwata kinji." Ta ƙarashe maganar hankalinta a matuƙar tashe ganin masifar da take tunkaro ta; Tashi sama yarinyar ta yi tamkar tsuntsuwa ta tsaya a samar ramin ta na kallon Suhaima da jikinta yake rawa ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa yi saboda firgici ta tashin hankalin da take ciki. Dariya ta yi cikin hargowa ta soma magana. "Karki sake haɗani da Allah ki cuceni, ina so na yi ramuwar gaiya dan ba zan taɓa yafe abin da kuka yi wa rayuwata ba Suhaima. Idan kuma ki na so na rabu da ke to sai kin sadaukar mini da wani abu wanda kika fi so fiye da komai a rayuwar duniya, idan kuma ba za ki iya ba to zan ɗaura daga inda na tsaya sai kin zaɓi mutuwa fiye da rayuwarki. Ni sunana Janu idan na sake ji kin kirani da wannan sunan sai na yanke miki harshe." Ta ƙarashe maganar ta na dawowa gaf da Suhaima; shuru Suhaima ta yi ta na tunanin wannan sunan da yarinyar ta ambata ta ce sunanta kenan, sosai ta lula duniyar tunani ta na son sanin inda ta san mai sunan amma ta kasa tuno komai.. "Shin za ki yi sadaukarwar ne ko yaya? "Ta kuma faɗa ta na ɗaga Suhaima sama ta kawo ta samar ramin, kwalalo idanu ta yi ganin wata ƙatuwar macijiya na ƙoƙarin kawo mata hari, baki na rawa ta ce. "Zan yi Janu ko mai kake so na sadaukar miki zan miki matsawar za ki rabu da rayuwata. Amma nima ina da tambaya idan kin bani dama, sannan ki taimaka ki mayar dani ƙasa amma ba cikin maƙabarta ba waje sai mu yi maganar." Ta faɗa ta na fatan kar taƙi amincewa; Wani irin gurnani Janu ta yi sai ga fuskarta ta juyo ta bayanta ai kuwa Suhaima ta runtse idanu tare da rufe bakinta dan kar ta yi abin da zai sa ta fusata ta afka ta cikin wannan ramin. Dariya ta kuma yi ta daɓi kan Suhaima, kanta ne ya shiga juya mata jin zafin ya kawo wa ƙwaƙwalwarta ziyara ta ɗaure ba ta ce uffan ba . A dajin da ta fara ganin kanta ta gansu sun dawo cikinsa, shuru ta yi ta na sauraron Janu ta ji me take so, hannu Janu ta daga sama sai ga wani haske ya bayyana a gaban Suhaima.. Cikin tsoro ta kalli hasken kamar jira ake ta kalla sai ga wasu mace da namiji sun bayyana fuskokinsu na ɗauke da damuwa, idanunsu na zubar da hawaye hannayensu sarƙe da na juna suka ƙurawa Suhaima idanu. Zunbur Suhaima ta miƙe tsaye ta na nuna su da hannu ta soma ƙoƙarin yi musu magana amma hakan ya cittura sai bakinta da take buɗewa ta na nuna su da hannu, durƙushewa ta yi ta fashe da kuka marar sauti dan muryarta ta kasa fitowa; Janu kuwa na gefe ta na dariyar ƙeta tare da ƙara matso mata da wannan mutanen su kuma suna zubar da hawaye a tare suka ce. "Shin kin tuna mu ne." Da sauri Suhaima ta ɗago kai bakinta na rawa ta yi ƙoƙarin yin magana amma sautin muryar yaƙi fitowa, ganin hakan yasa Janu ta kuma fashewa da dariya dajin na amsa kowar muryarta, su kuma sun ƙura mata idanu suna jiran ta basu amsa amma shuru. Janu ta dubesu ta ce. "Wannan ta na ƙarƙashin ikona ne ba za ta taɓa iya muku magana ba sai na ba ta izinin yin hakan, na kira ku ne don ku sheda sadaukarwar da za ta yi ta fanshi rayuwarta, idan maye ya manta mai ɗa ba za ta taɓa mantawa ba ina fatan kun gane ko?" Ta ƙarashe maganar ta na kuma yin wata dariya ta ɗago Suhaima kamar wata jaririya sai kawai ta yi sama da ita ta sako ta ƙasa tim! Da sauri suka kalli Janu matar ta ce. "Kar mu yi haka dake Janu ki faɗi sharaɗin ki." Ta ƙarashe maganar ta na haɗe rai ganin yadda Janu ke yi ko a jikinta . Ita kuwa Suhaima ta na yashe a ƙasa sai numfashi take saukewa, a galabaice ta ce. "Ki faɗi me kike so na miki." Ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya Janu ta yi ta ce. "Ina so ki sadaukar mini da jinin iyayenki da na 'yan'uwanki, idan ki ka yi haka zan rabu da ke na yi sabgar gabana." Kwalalo idanu waje Suhaima ta yi jin wannan ƙatoton tashin hankali da Janu ke son sakata ciki, to idan ta sadaukar da jinin Abba da Umma da Na'im da Suhaila ita meye amfanin zaman ta a duniya? Shin me na aikata a gareki Janu da kike bibiyar rayuwata har kike neman rabani da ahalina gabaɗaya? Ta faɗa a cikin zuciyarta ba ta san maganar ta fito fili ba sai da ta tsinkawo muryar Janu cikin fushi na cewa. "A MAƘABARTA NE lamarin ya fara, ke kika taɓo abin dan haka ke za ki rufe shi in ba haka ba masifa da bala'i sun yi ta bibiyar rayuwarki kenan. Ina ba ki lokaci ne shi ya sa ma ban kasheki ba kamar yadda na kashe wannan mugun Uncle ɗin naki, amma dai ki ci gaba da yi mini gardama ke ba fille kai ba ma zan miki farke ki zan yi na feɗe neman jikinki na gasa na cinye na shanye jinin. Ba ki san wace ce Janu ba zan nuna miki asalin kalata." Ta ƙarashe maganar ta na miƙa hannunta sai ga takobi fara sol mai baki biyu ta bayyana a hannunta, cikin zafin nawa irin nasu na aljannu ta kai wa Suhaima suka a ciki, wani mahaukacin ihu Suhaima ta kurma wanda har sai da su Umma suka fito a guje suna banka ƙofar ɗakinta jin ihun da ta yi.. A matuƙar firgice take kallon jikinta ta na laluma cikinta, kalle-kalle ta soma nan idanunta ya kai kan su Umma dake tsaye sun zuba mata idanu. "Wai yarinyar nan anya kuwa ciwon hauka bai kama ki ba?" Umma ta faɗa ranta a matuƙar ɓace ta na kallonta; Zufa ta jiƙa inda take zaune ta miƙe a hankali ta sauko daga kan gadon ta iso garesu, da kallon tsoro take binsu ta soma magana. "Umma ba dai abin da ya sameku ko? Anty Suhaila ta na lafiya kuwa? Abba wai me yake son faruwa dani ne? Kullum fa sai na ganta ta yi ta kaini Maƙabarta ta na firgitani yau kuma ta ce wai A MAƘABARTA NE lamarin ya fara ni na buɗe dan haka ni zan rufe da kaina. Abba Shin wai me ya faru A MAƘABARTAR da kullum nake ganin kaina a ciki? Ku bani amsa don Allah me kuke ɓoye mini wanda na kasa sani? A kan idona fa aka fille wa Uncle kai kuma ina tashi ya rasu, yau kuma ni aka soka da wuƙa Abba yanzu kenan mutuwa zan yi?" Ta faɗa ta na ƙarawa kukanta sauti, sannan ta ci gaba da cewa. "Don Allah ku fitar dani daga cikin duhu A MAƘABARTA NE wani al'amari ya faru wanda ku kun sani amma ni ban san komai ba, gashi ana ta firgitani shin me ya faru A MAƘABARTAR Abba? "Ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka tare da riƙe ƙafar Umma ta kuma faɗin. "Umma ke ki faɗa mini me kuka sani game da mafarkina A MAƘABARTA da nake yi? Ku faɗa mini kar Janu ta kashe ku." Ta faɗa cikin ƙaraji; Abba ya kamo hannunta fuskarsa ɗauke da tashin hankali har jikinsa ya ɗauki rawa ya soma magana a firgice. "Suhaima.. _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/1 22:03] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba) _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO(Malam)* 0️⃣4️⃣ "Suhaima babu abin da ya faru A MAƘABARTA kawai dai mugayen mafarkan da kike ne kike gani kamar da gaske A MAƘABARTA NE wani abu ya faru; ki kwantar da hankalinki zan samu Liman na masa bayanin irin mafarkan da kike sai a taimaka miki da addu'a. Kar naji kin faɗi maganar nan a wani guri, saboda za a miki kallon mahaukaciya sabon kamu." Ya ƙarasa maganar yana addu'ar kar ta kuma jefo masa tambayar da bashi sa amsar ta; ita kuwa Suhaima ƙurawa Abba idanu ta yi ta na son gaskata maganarsa amma sam zuciyarta taƙi yarda da maganar ta Abba, dawo da kallonta ta yi kan Umma sai kawai ta miƙe tsaye ta goge hawayen dake zarya kan kuncinta cikin raunatacciyar murya ta soma yi wa Umma magana. "Umma idan na gano wani abu wanda bai mini ba to tabbas zan bar gidan nan na shiga duniya." Ta faɗa kai tsaye ta na hura hanci; Kwalalo idanu Umma da Abba suka yi cike da mamakin kalamanta, dukkansu nanata kalmar shiga duniya suke kamar ɗalibin da aka daurawa sabuwa aya yana bitar ta. Komawa ta yi bakin gado ta zauna ta haɗa kai da guiwa ta dinga rera kuka mai tsuma zuciya, ita kan taga ta kanta ba dama ta kwanta sai ta haɗu da wannan muguwar aljanar wai ita Janu kamar wani danƙo, waye zai faɗa mata gaskiyar da aka ɓoye mata? Shin mene ne ya faru A MAƘABARTA da har ake ƙoƙarin ɗaukar rayuwarta? Ajiyar zuciya ta sauke tare da tsagaita kukan nata, cike da mamaki take kallon su Umma dan ita a tunaninta tun tuni sun bar mata ɗakin sai ta gani suna nan sun yi jugum-jugum suna kallon ta, kanta ta kuma mayarwa ta ci gaba da kuka yadda zuciyarta ke ba ta shawara ta aiwatar da abin da take so, amma wani sashe na zuciyarta na gargaɗar ta sai ta kuma ƙarawa kukanta sauti ta yi baya ta zube a kan gadon.. Zuwa yanzu ta ji ba ta jin tsoro dayawa ba kamar da ba, sai da ta gaji da kukan dan kanta ta bari Umma ta iso gareta ta zauna tare da ɗago da ita suka yi facing ɗin juna. "Suhaima ki daina saka wa kanki damuwa game da mafarkin da kike, kin san dai mafarki ba gaskiya ba ne duk ƙarya ce ko?, Sheɗanu ne ke son rikita miki lissafi ki dawo haiyacinki." Tsayar da kuka ta yi ta ce. "Umma tabbas akwai abin da kuka ɓoye mini, kuma da mafarkin da nake ƙarya ne to da zai kasance ba kullum zan ke yi ba, amma ko gyangyaɗi na yi sai na ganta ta na azabtar da ni ya zan yi Umma?" Ta faɗa hawaye na zirya kan kuncinta zarr³; Shuru Umma ta yi dan ta rasa ma da wata kalma za ta yi amfani dan ta gusar da tunanin mafarkin nata, zuwa can ta ruƙo duka hannayenta cikin kulawa tare da tausayin ganin halin da take ciki ta fara magana. "Ƴata ki kwantar da hankalinki babu abin da zai same ki sai alkhairi." Ba dan Suhaima ta yarda da maganar Umman nata ba ta gyaɗa mata kai tare da goge hawayen da ke kan kuncinta wanda har sun gaji da zirya , a sanyaye ta ce. "To Umma." Murmushin yaƙe Umma ta sakar mata, ita kanta lamarin ya tsaya mata a rai, tsoro da tashin hankali sun mamaye zuciyarta har sai da suka bayyana a kan fuskarta, jiki ba ƙwari ta miƙe tsaye a lokacin Abba ya bar ɗakin sai Na'im da yake tsaye yana kallon yayar tasa cike da tausayawa. Fita suka yi tare da rufo mata ƙofar, Suhaima ta yi shuru surar mata da mijin data gani sun tsaya mata a rai sai tambayar kanta take. "To su kuma wannan su wane ne? Sannan me ya sa suke tambayata na gane su?" Ajiyar zuciya ta sauke ta na shaƙar numfashi ta lumshe idanunta zuciyata ta cunkushe komai ya tsaya mata cak, nemen mafita kawai take ta na son ta gano maƙasudin haɗin ta da maƙabartar da take gani, da kuma aljana Janu me ta aika mata duk ta hana ta sukoni a rayuwarta.. Juyi ta yi da koma gefe sai ta ji ta rungumi wani abu , da sauri ta buɗe idanunta ta yi arba da jariran nan kwance gabanta sun ƙura mata idanu wannan karon suffarsu da dama-dama irin ta mutane ce.. Da hanzari ta janye jikinta ta na tashi zaune ta zuro ƙafafunta za ta sauka ta ga ɗayar gaf da ƙafarta ta na shafa mata ƙafar, Wani irin sautin murdawa cikinta ya bada ƙuuuuu! Ji ta yi kamar ta yi zawo a jikinta da sauri ta janye ƙafar ta haɗe ta da ƴar'uwarta ta na haki.. "Kada ki ji komai yau ba za mu ba ki wahala ba, mun zo ne mu tayaki hira ya ke Mama. " Jaririyar ta faɗa ta na dawowa kan gadon ta ɗane kan cinyar Suhaima ta kwanta luf kamar wacce za a shaya nono; ganin haka shi ma ɗayan ya kwanta a ɗayar cinyarta suka dinga kallon ta suna murmishi.. Suhaima ko motsi kasa yi ta yi ganin sun haye mata cinya ta sume daga zaunen da take, macen ta dubi ɗan'uwan nata ta ce. macen ta dubi ɗan'uwan nata ta ce. "Kai Mama fa ta suma." "To tashe ta mu yi sauri mu koma. Ya ba ta amsa yana zama; Gefe ta kalla sai ga ruwa daga samar kan Suhaima yana zuba kan fuskarta, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta buɗe idanunta ta ga sun yi mata cirko-cirko duk sun yi fuskar tausayi suna kallon ta. "Ku wai su waye? Ta tambayesu jiki na ɓari tsoro ya cika mata ciki ganin jarirai na magana . Macen ta matso ta kwanta a jikinta ta lumshe ido Suhaima ta kwalalo idanu waje kafin ta motsa shi ma ɗayan ya kwanta a jikinta, macen ta ɗago daidai fuskar Suhaima ta ce. "Mama Baba na gaisheki." Baki da hanci Suhaima ta saki ta na nanata sunan Mama a zuciyarta, wai kuma Baba na gaisheta ta yi ta maza ta ce. "Waye kuma Baba? "Ta faɗa cikin nuna mamaki da al'ajabin wannan jarirai. "A MAƘABARTA yake shi ma ya ce mu zo mu gaisheki. "Cewar namijin yana kallon ƴar'uwarsa; sake kashe ta suka yi da mamaki ta yi kim ta na tunanin to waye shi Baban da suke cewa ya ce su gaishe ta? Sannan ma meye haɗin ta da su da suke zuwar mata bayan wannan muguwar aljanar? "Mama ki daina tunani dayawa za mu taimakeki, muna son mu rabaki da Janu kar ta kashe mana ke, amma dole sai mun shiga mun karanci tunaninki da komai naki sai mu faɗi daga inda matsalar take. "Namiji ya faɗa yana gyara kwanciyar shi a kan ƙirjinta... Jin abin da ya faɗa ba tunanin komai ta ce. "Na yarda ku bincike tarihin rayuwata in dai hakan zai sa wannan muguwar ta rabu da ni na zauna lafiya, sannan ku ba ku faɗa mini su waye ku?" Murmishi suka yi a tare suka ce. "Ba buƙata yanzu ki ji su waye mu har sai mun yi miki abin da ya kawo mu daga baya za mu faɗa miki, Baba ne yasa mu taimake ki ya ce ya bamu dama mu yi komai dan mu rabaki da Janu." Jinjina musu kai ta yi ji ta yi ba ta jin tsoron yaran ta sakar musu murmishi, ganin haka yasa macen ta ce. "Rufe idanunki Mama." Ba muso ta rufe idanun su kuma a tare suka sa 'yan yatsunsu ɗai-ɗaya a gefen kanta suka danna, shuru Suhaima ta yi jin wani abu ya ɗan soke ta kamar haki. Basu fi sakan ashirin ba suka ce ta buɗe idonta, buɗewa ta yi ta na kallonsu za ta yi magana suka rigata cewa. "Mun tafi lokacin mu ya ƙare kar Janu ta gane muna bibiyar ta." Kai kawai ta ɗaga musu a gaban idanunta suka ɓace ta ɗan ji tsoro sai dai ba sosai ba, lumshe idanu ta yi sai yanzu ta tuna da addu'a ta shiga karanto Ayatul kursuyu har bacci ya ɗauke ta... Washe gari Suhaima ta tashi da zazzaɓi amma hakan ta daure suka tafi gidan Uncle ɗin ta. Koda suka je kasa yi wa kowa magana ta yi ba e ba a'a, duk abin da take Umma na ankare da ita har aka yi sallar Azuhar ba ta saki jikinta ba; jin zazzaɓin na ƙara ƙarfi yasa Suhaima ta kalli Mommy ta ce. "Mommy zan kwanta." A sanyaye Mommy ta ce. "Shiga ɗakin part ɗin Sani akwai ɗaki ɗaya sai ki kwanta a can nan mutane ne." Jinjina kai ta yi ta miƙe da ƙyar ta nufi hanyar da za ta sada ta da part ɗin Sani; a hankali take tafiyar kanta na sara mata ta kai hannu ta dafe goshinta ta shige part ɗin. Ɗakin ta shiga ta kwanta a kan gadon ta lumshe idanu. Ta na rufe idanu ta bacci ya ɗauke ta; kamar jira ake ta rufe idanun sai ga ta a kan hanya ta na ta buga sauri . Da gudu ta miƙe wata hanya ta yanka cikin dajin ta ci gaba da gudu ta na waiwayen bayanta, turus ta ja ta tsaya ganin ta a gaban get ɗin maƙabartar da take yi wa gudu a baya. Jiki na rawa ta kuma falfalawa da gudu tamkar motar da ta sha mai, sai da ta yi nisa sosai ta ji ba ta jin hucin abin da yake binta ta sunkuya ta na haki a wahalce; dan ba ƙaramin gudu ta ci ba. Ɗago kai ta yi da nufi ta ci gaba da gudu ta kuma yin arba da maƙabartar a gabanta get ɗin ma a buɗe wayam, kwalalo ido waje ta yi ta na yin baya ganin yadda ƙaburburan suke motsi kamar wani abu zai fito daga ciki; tamkar wadda aka dasa a wajan ta kasa motsa ƙafarta sai kallon cikin maƙabartar take cike da firgici. Wani kalar ɓakin hayaƙi ne ya dinga fitowa daga cikin ƙaburburan yana haɗuwa waje ɗaya, Suhaima ta kasa guduwa ta na son ta motsa amma gam an riƙe ƙafar tayi-tayi ta kasa ɗaga ƙafar; hayaƙin na taruwa ya nufo ta gadan-gadan ta ƙwalla ƙara ta na jiran zuwan wannan annoba ta iso gareta dan ta saddakar yau dai kashe ta za su yi. Kamar daga sama ta ji ana faɗin. "Suhaima! Ki matsa sauri." Da sauri ta yi ƙoƙarin daga ƙafar tata ai kuwa ta ji ta ɗago, a 380 ta fankaya da gudu wannan hayaƙin na bin ta, ji ta yi an ɗauke ta an cilla ta gefe ta faɗi timm Kamar ba ta ji ciwo ba ta miƙe tsaye sai ta ga wani farin haske na tunkaro ta. Baya ta soma ja ta ji an yi magana da ƙarfi. "Ki tsaya!" Aka faɗa ta ja birki ta tsaya numfashinta na sama da kasa, kamar an ce ta kalli gefen ta ga wannan ramin mai macizai a bayanta; da sauri ta yo baya hasken ya ƙaraso gareta ta na kallonsa , jariran suka bayyana ta musu kallon mamaki ta ce. "Kuma kenan kuna son ku kasheni?" "A a Mama za mu ceceki dai sannan mun gano miki maƙasudin matsalar dake tsakanin ki da Aljana Janu "Suka faɗa a tare." Baki na rawa ta ce. "Ku taimaka ku faɗa mini kun ji." Macen ta ɗaga baki za ta yi magana Suhaima ta ji ana bubbuga pilon da ta kwanta a kai; A zabure ta tashi ta na zare idanu kanta ya yi mata mugun nauyi Kamar an daura mata ƙaton dutse a cikin kan haka take ji, da ƙyar ɗago ta kalli wanda ya katse mata bacci da maganar da take son ji wadda za ta kawo mata mafita; ganin Na'im ne haushi ya kama ta ta ja tsaki ta ce. "Dalla can malam ka wani tasheni ina bacci." Shi ma Na'im harara ya aiko mata ya ce. "Ƴar rainin hankali yo dan na taimakeki ma shi ne kike ja mini tsaki Kamar wata tsaka, to ki tashi har an yi la'asar kina baccin asara kasa kawai, ke bakya gajiya da bacci ne." "Tsuwww! To matsa ka bani guri ko in bangaje ka na wuce futsararre kawai ina yayarka amma kake ce mini Ƴar ranin hankali dan ka ɗaukeni kamar wata ƴarka ko? Wallahi sai na haɗa ka da Abba ya mana tsakani ɗan'iska kawai." Banza ya mata ya juya ya wuce bai ce mata komai ba... Toilet ta shiga ta ɗauro alwala ta nufi gurin su Umma ta gabatar da Sallah. Tun kafin ta ƙarasa yin salatin Annabi (s.a.w) jikinta ya ɗauki rawa ta maƙure a jikin bango ta na kallon 'yan ɗakin, Umma data shigo yanzu ta kai kallon ta kan Suhaima ta ga idanun na lumshewa da buɗewa; da sauri ta ƙaraso gareta ta ɗago da ita ta na kiran sunan ta. "Suhaima me ya sameki? Zazzaɓi kike ji?" Umma ta faɗa a rikice ganin ɓakin idanunta suna sama sai farin kawai. 'Yan ɗakin hankalinsu ya yo kan su wata mata ta ce . "To ku kaita Asibiti mana dan da alama ta na jin jiki sosai." To Umma ta ce ta soma ƙoƙarin tayar da ita amma ta kasa saboda ta saki jiki, wasu daga cikin matan suka taimaka mata suka ɗauke ta aka firo da ita sharaf-sharaf kamar gawa. Waya Umma ta buga wa Abba sai ta ji Na'im ya ɗauka, kafin ya yi magana murya na rawa ta ce. "Ka turo Na'im ya kaimu Asibiti Suhaima ba ta da lafiya." Da sauri Na'im ya miƙe tsaye ya amsa mata da to ai shi ne ma ba Abban ba sannan ya kashe kiran ya yo inda suke; suna fitowa yana isowa ya buɗe motar suka saka ta zuwa lokacin jikin Suhaima ya yi tsanani sosai zufa sai tsatstsafo mata take a goshinta,. Suna shiga aka buɗe musu ƙofar suka bar gidan.... _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/2 21:43] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣5️⃣ Cikin ikon Allah suka isa Asibitin Murtala, Na'im da kansa ya ɗauketa da sauri ya nufi ciki yana kwaɗawa Nurse kira, yana isowa ciki suka amshe ta suka nufi emergency room da ita. Umma ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake wajan ta na goge hawayen tausayin Suhaima; Safa da marwa Na'im ya dinga yi ganin abin ba na tsayuwa ba ne ya iso kusa da Umma ya durƙusa a gabanta ya ce. "Haba Umma ba fa mutuwa ta yi ba." Ɗago kai Umma ta yi a sanyaye ta ce. "Ina jin tsoron Suhaima ta gano abin da muka ɓoye mata bana son rabuwa da ita Na'im. Ka na ji abin da take cewa wai za ta shiga duniya indai ta gano mun ɓoye mata wani abu." Cike da rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa yake kallon ta, wato kenan akwai abin da suke ɓoye mata to mene ne shi abin da suka ɓoye mata? In ko haka ne shi ma zai so na ji wannan ɓoyayyen sirrin da suke rufewa. Tashi ya yi ya dawo kan kujera ya fuskanci Umma ya ce. "Umma kenan mafarkin Suhaima take ba ƙarya ba ne? Me ya sa kuka ƙi faɗa mata abin da kuke ɓoye wa? Ko shi sirrin naku ba me daɗin ji ba ne?" Ya jero mata tambayoyin da yasa Umma ɗago wa da sauri; sai yanzu ta tuna da saɓutar bakin da ta yi, share fuskarta ta yi ta ce. "No ba wani sirri ba ne wanda zai gagara faɗi, kasan dai Suhaima da saka damuwa a rai musamman ma mafarkan nan da take yi. Tsoron da nake ji idan ta gano aljannun da take gani a mafarki gaske ne za ta fi haka shiga tashin hankali, abin da ba na fata ya faru shi zai faru shi ya sa na damu." Shuru Na'im ya yi yana nazarin kalamanta, ita kuwa Umma kawar da kanta gefe ta yi dan kar ya kuma jefo mata wata tambayar.. A can ciki kuwa gwaji suka shiga mata nan take suka ga ba ta da jini ya zo matakin ƙarshe, ruwan jikinta ma ya ƙare, ruwan suka ɗaura mata suka mata allurorin da za su taimaka mata kafin asa mata jinin. Ɗaya daga cikin Nurse ɗin ce ta juya ta bar ɗakin da sauri Doctor na mata bayani ta ɗauki wata takarda ta wuce; a tsaye ta gansu ganin ta yasa suka yo wajanta suna tambayar ya mai jik? Kallonsu ta yi sannan ta soma musu bayani. "Hajiya muna buƙatar jini da gaggawa ba ta da jini kwata-kwata, ku samo wanda za a ɗiba a jikinsa ko kuma ku saya in aka wuce minti 20 ba'a sa mata to gaskiya komai zai iya faruwa." "Doctor muje a gwada nawa idan ya zo daidai da nata sai a sa mata, idan kuma bai zo ba za mu saya kawai." Cewar Na'im yana matso wa kusa da Nurse ɗin; nuna masa inda zai shiga a gwada ta yi ta na jadadda masa ya hanzarta ya amsa da to sannan ya wuce, Umma kuwa komawa ta yi gwajab ta zauna ta rafka tagumi ta na ƙara jin tausayin Suhaima... Cikin ikon Allah aka gwada jinin Na'im ya zo daidai da na Suhaima, ba ɓata lokaci suka ɗibi leda biyu; wata Nurse aka miƙa wa ta amsa ta wuce da sauri.. Sai da Na'im ya jima a zaune sannan ya tashi ya nufo inda ya bar Umma; da sauri tare sa ta na faɗin. "Ya ya Na'im an dace kuwa?" Jinjina mata kai ya yi hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna; shi ma zaman ya yi sai ga Suhaila ta shigo mayafi a hannu ta na rusar kuka ta zauna a ƙasa hannunta a bisa kanta ta soma magana. "Kin gani ko Umma? Dama sai da na ce kar ku faɗi maganar da za ta tarwatsa mata zuciya amma shi ne kuka sanar da ita? Yanzu a wani hali take ciki Umma?" Na'im ya yi shuru gabaɗaya duk sun kulle masa kai, yana tambaya a cikin zuciyarsa; wai wani abu ne wanda ake tsoron faɗa wa Suhaima wanda shi ma a iya tunaninsa bai sani ba? Girgiza kai ya yi ya dubi Suhaila wacce har yanzu ba ta daina kuka ba ya ce. "Malama ki mana shuru kin shigo mayafi a hannu kamar rainon 'yanmata, kuma meye ba ku so ku faɗa wa Anty Suhaima? Ni fa kun ɗaure mini kai da yawa ki fahimtar dani Umma." Mayafin ta ɗauka ta yafa ta lulluɓe jikinta sannan ta kalli Umma da ta ƙura mata idanu ta ce. "Umma ki yi wa wannan ɗan rainin hankalin magana ni ta ƴar'uwata nake yanzu bani da lokacin yin faɗa da shi, in ban da ma ka rainani ni yayarta ce ta biyu amma so kake ƙarfi da yaji kai ka koma babba dan ka ga ka girma ka fimu tsayi ko? To ka fita idona karka sake tambayata." Ta ƙarashe ta na tsuke bakinta dan kar ma ya sake faɗa mata magana.. Kwafa ya ja dan ya lura basa son shi da Suhaima su san abin da suke ɓoye musu, ita kuwa Umma lokacin da Suhaila na magana kaɗan ya rage ta rufe mata baki jin ta na neman kira musu ruwa; itama kanta Suhaila gane za ta yi katobara ya sa ta rufe Na'im da faɗa ta ci sa'a kuma bai ce komai ba... Sai gaf da Magariba likitocin suka fito daga pɗakin su uku biyu mata ɗaya namiji suna biye da shi a baya, suna ganinsu namijin ya tsaya a gurin su Umma ya ce. "Ku biyoni Office." Na'im ya bi bayansa su kuma suka zauna zaman jiransa; bayan sun zauna Doctor ya shiga masa bayani dalla-dalla.. "Babu wata matsala mai yawa kawai dai ta firgita ne ko na ce ta ga abin da ya firgitar da ita, hakan ya haddasa mata bugawar zuciya da zazzaɓi mai zafi sosai har ruwa da jinin jikinta suka ƙare. Amma Alhamdu Lillah abun ya zo da sauƙi zan rubuta maka magunguna sai take sha in sha Allah za ta warware, amma fa kuke kulawa da ita sosai kar ta kuma firgita da taimakon Allah numfashinta ya daidaita." "To in sha Allahu Doctor hakan ba za ta sake faruwa ba, na gode sosai." Cewar Na'im yana miƙa hannu suka sallama sannan ya kuma cewa. "Za mu iya ganinta?" "E amma sai gobe in sha Allah za mu sallame ku.. Miƙe wa ya yi ya fita zuciyarsa na wasi-wasin lamarin gidan nasu. Bayan ya dawo ya faɗa musu yadda suka yi da Doctor suka mata fatan samun lafiya, Abba ya kira suka ce bacci take sannan suka shiga ciki. Kwance suka ganta kamar gawa hannu ɗaya an sa mata ruwa ɗaya an sa mata jini, fuskarta ta yi wani irin haske ta koɗe kamar ta kwashi watanni ta na cutar; bakinta ya bushe ƙayau kamar ta kwana ba ta sha ruwa ba.. Zama suka yi suka sa ta a gaba suna kallon ta cikin tausaya wa halin da take ciki. Washegari wuraren ƙarfe goma na safe aka basu sallama, zuwa lokacin Suhaima taji sauƙi sosai sai dai rashin ƙwarin jiki haka suka dawo gida. Suhaila ta haɗa mata ruwan wanka ta dawo ta taimaka mata ta shiga sannan ita ta dawo; shuru ta yi ta na tunanin jariran nan so take ta sake ganinsu su faɗa mata abin da zai fitar da ita daga wannan masifar da take ciki. Lumshe idanu ta yi kamannin yaran na mata zigo a idanun zuciya, ganin dai zaman ba zai fishe ta ba ta daure ta watsa ruwan ta ɗauro alwala ta fito. A zaune ta samu Suhaila ta miƙa mata hijabi ta amsa ta na binta da kallo. "Ya dai malama ko kin ga na canja ne kike mini kallon ƙurulla?" Murmishi Suhaima ta yi ta juya ta tayar da sallar da ake binta daga ta jiya har ta yau duk sai da ta rama sannan ta zauna; shayi mai kauri ta miƙa mata, ba muso ta amsa ta soma sha. Bayan ta shanye ta miƙe a hankali ta isa bakin gadon ta zauna ta kalli Suhaila ta na ƙaƙalo murmushin yaƙe ta ce. "Anty Suhaila wai tun yaushe kike tare damu?" Harara ta aika mata sai kuma ta mayar mata da murmishin ta ce. "Ai tun jiya nake nan ke kina bacci shi ya sa ba ki san lokacin da na zo ba; yanzu ya jikin naki? Don Allah Suhaima ki daina saka damuwa a ranki kin ji kar ki ja wa kanki ciwo kuma, waye ya firgita ki wai jiyar?" Kukan da take ƙoƙarin danne wa ne ya fito ta faɗa jikin Suhaila ta fashe da kuka wi-wi tamkar ana yankan naman jikinta; jikin Suhaila ya yi sanyi sosai ganin yadda Ƙanwar tata ke kuka bil'haƙƙi. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta ɗago da ita ta ce. "Ƙanwata ki faɗa mini me ke damunki? Ko Abba ne ya takura a kan maganar fito da miji?" Girgiza kai ta yi ta tsayar da kukan da take ta ce. "Anty ya zan yi da rayuwata ne? Da na kwanta bacci ita nake gani ta na son kasheni." Waro idanu Suhaila ta yi cike da al'ajabi ta ce. "Wace ce ke son kasheki?" "Ni ma ban san ta ba, haka kawai nake ganinta a mafarki na faɗa wa su Abba amma sun ce mafarki ba gaskiya ba ne, Anty ki taimakeni Wallahi tsoron ta nake ji." Ta ƙarashe maganar ta na sakin wani sabon kukan ta shiga ba ta labarin aljana Janu da take gani a mafarkin ta, amma ba ta faɗa mata jariran nan ba.. Ajiyar zuciya Suhaila ta sauke ta ce. "Ki kwantar da hankalinki in sha Allah da kin samu sauƙi zan ɗauke ki mu tafi Kaduna akwai wani babban Malamin addini zan kaiki wajansa mu gani ko zai gano abin da yake haɗa ki da ita wannan aljanar, yanzu kwanta ki huta Umma ta ce gobe Inna Laure za ta zo gurin sadakar uku na Uncle. Wai ashe basu ji mutuwar ba sai yau kin ji irin ɗibar albarkar da ta yi wa Abba kamar za ta fito daga waya ta dake shi, Inna Laure ba dai masifa ba Allah ya kawo ta." Wani sanyi Suhaimata ji ya ratsa ta ko ba komai ƴar'uwarta ta fuskanci damuwarta, bugo da ƙari kuma ga Inna Laure za ta zo wadda ko kallon banza ba ta so a yiwa Suhaima lelenta take kamar Auta.. "Allah sarki Innata Allah ya kawo mini ita lafiya har na ƙagara ma na ji muryarta. " Dariya Suhaila ta yi ta ce. "To ai shi kenan bari na ba ki guri ki huta nima baccin nake ji sai an jima." Jinjina mata kai ta yi ita kuma ta fita daga ɗakin ta rufo mata ƙofa... Gyara kwanciyarta ta yi so take ta yi bacci ko ta haɗu da yaran su ci gaba da mata bayani, amma kuma wani ɓangaren na zuciyarta tsoro ya cika shi ba ta son ta sake ganin Janu. Ajiyar zuciya ta sauke ta rufe jikinta da bargo ta dinga karanta Ayatul kursuyu ta na addu'ar ko bacci ya shure ta kar ta haɗu da Janu da duniyar mafarkinta... Zaune suke a tsakiyar ƙungurmin daji ita da wani tsoho da mata da mijin nan an ɗaure su da sarka; Janu ce ta bayyana a gabansu cikin mummunar suffa hannayenta riƙe da dalleliyar takofi mai kaifi da tsini sai walkiya take.. Idanu waje Suhaima ke kallon Janu ganin ta nufo gareta, wata irin dariya ta yi mai haɗe da kuka ta tashi sama ta tsaye a kan mata da mijin nan ta ce. "Kina tunanin za ki iya kuɓuta daga tarkona ne? Kin yi kuskure da kike son sanin wani abu da ya shafeni, ke ɗin mallakina ce an mallaka mini ke tun ma kafin ki san ke wace ce. Zan maimaita abin da na yi shekarun baya idan har ba ki bani jininki na sha ba ko kuma ki bani na wasu ki ceci kanki." Ƙirjin Suhaima ya shiga bugawa ta juyo da nufin da yi wa tsohon nan magana sai ta ga babu kowa daga ita sai Janu a tsakiyar dajin, jefen Janu ta juyo baki na rawa ta ce. "Janu to ni taya aka yi na zama mallakinki. Sannan waye ya mallaka miki kaina da kike son kaini lahira?" Wata gigitacciyar tsawa ta daka mata ta dawo gabanta ta ce. "Ba zan faɗa miki ba indai har ba ki sani ba, to ki zauna a haka kasheki dai sai na yi na shanye jinin jikinki yanzu a nan ba'a ko'ina ba." Takobin ta sa ta yanki hannun Suhaima sai ga jini yana ta zuba, ƙara Suhaima ta ƙwalla jin wata irin azaba ta karaɗe mata jiki, kafin ta motsa ta ga jinin jikinta na ƙara kwarara. Ita kuwa Janu hannunta mai kama da na biri ta miƙa ta ba tarar jinin ta na shanye wa, ganin zubar jinin ya ragu ta kuma ɗaga takobin ta yanki ciyar Suhaima. "Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Ta faɗa cikin tsananin azaba, ita kuma Aljana Janu ta dinga lashe jinin dake zuba ta na yin wata mahaukaciyar dariya. Tashi ta yi ta soka takofin a ƙasa sai gasu a cikin maƙabarta, ta miƙa hannunta gefe sai ga sabon ginan ƙabari ya bayyana ta kwashe da dariya ta ce. "Yau zan cika burina a kanki Suhaima, yanzu zan ci gaba da shan jinin ki idan na shanye tass sai na faɗeki ta cinye naman jikinki, idan na gama kuma na binne kasusuwanki a cikin ƙabarin nan." Ta na gama faɗin haka ta kuma nufo Suhaima da numfashinta ya kai wa da komo wa, takobin ta ɗaga za ta soka mata sai ga haske ya bayyana ya musu tsakani.. A fusace Janu ta dubi hasken ta kai masa sara ya kauce sai ya bayyana a suffar mutane, namiji ne dogo sosai ya lulluɓe ko'ina na jikinsa idanunsa kawai ake iya hango wa; Suhaima ta ɗago ta na kallon yadda suke fafatawa tsakanin shi da Aljana Janu, matso wa ya yi kafin Janu ta ankara ya shuri Suhaima suka ɓace.. A ɓakin ƙofar gidansu ya sauke ta ya juyo ya hura mata iska, ji ta yi jikinta baya ciwon komai ya juya zai wuce ta ce. "Bawan Allah!" Juyo wa ya yi bai yarda sun haɗa idanu da ita ba kuma bai masa ba ya dai tsaya. "Kai wane ne? Sannan ya sunanka don Allah? Ina so na ga fuskarka." Kyakyawan hannunsa ya kai kan fuskarsa ya soma ƙoƙarin yaye lulluɓin da ya yi.... Allahu Akbar! Allahu Akbar! Sautin muryar Ladanin Masallacin Unguwarsu ne ya farkar da ita daga baccin da take; hawaye sharr suka zubo mata a fili ta furta. "Me ya sa ban ga fuskarka ba? Kai ɗin kuma waye?" Rai ba daɗi ta miƙe ta yo alwala ta tayar da iƙama. Wunin ranar haka Suhaima ta wuni ta na tunanin wannan wanda ya ceci rayuwarta, haka dai ta kwanta har dare ta na fatan in ta yi bacci ta gansa ya buɗe masa fuskarsa ta gani.... Washegari Inna Laure ta iso Kano, ta na dira daga mota ta dinga sababi tun daga harabar gidan har ta shiga cikin palon; bakinta har kunfa yake saboda masifa ta tsaya a tsaye.. Da gudu Suhaima ta fito suka rungumi juna cikin nuna farincikin ganin juna. Da ƙyar aka shayo kan Inna Laure ta daina faɗa sai dai ta ce baza ta ci abincin gidan ba Suhaima ta je ta sayo mata masa da miya a nan bayan layinsu, hijabi ta sa ta fita cikin sauri... Tafiya take ta na sauri, ta iso jikin wata bishiya dake bakin hanya tsaya ta na gyara hijabint. "Yarinya!" Da sauri ta ɗago kai; idanu ta zaro baki na rawa ta ce. *To fa masu karatu ga dai Suhaima a inuwar bishiya ko mai zai faru?* _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce )*_ [3/5 16:23] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣6️⃣ Baki na rawa ta ce. "Baba." Kallon ta tsohon ya yi fuskarsa na dauke da damuwa bai ce da ita komai ba; ganin haka yasa Suhaima ƙaraso wa inda yake zaune ta durƙusa cikin tashin hankali ta ce. "Baba ka yi magana mana. Ba kai ba ne na gani jiya cikin mafarkina? Ko kaima so take ta kashe ka kamar yadda take son ta kasheni ban mata komai ba? Baba shin ka na da alaƙa da ita ne? Ko turo ka ta yi ka kai mata ni?" Ta jero masa tambayoyi a jere kamar wata ƴar jarida tsoro da firgici sun mamaye zuciyarta. Shi kuwa tsoho ya yi shuru sai ma soke sandarsa ya yi ya riƙe ta yana daga zaune ya sunkuyar da kai har ta gama maganar bai ɗago ba, Suhaima ta kuma faɗin. "Baba ba ka ce komai ba." Ta yi maganar a sanyaye zuciyarta na ce mata ta gudu shi ma cutar da ita zai yi, wani ɓangaren na zuciyarta na hana ta guduwar.. Ɗago kai ya yi ya dube ta kamar ba zai ce komai ba zuwa lokacin jikin Suhaima rawa yake ganin yadda idanunsa suke wani irin haske, har ta yanke shawarar tafiya ta tsinkayo muryarsa kamar daga sama yana magana.. "Ni ba cutar da ke zan yi ba, halisa ma na zo ne na ba ki haƙuri a kan abin da na aika miki tun kafin ki zo duniya." Baki sake Suhaima ke kallon tsohon to dama ya san ni wace ce kenan? To in ko haka ne bari na masa tambaya ko zan samu mafita daga wajansa. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama shawara da zuciyarta ta ce. "Baba to ni kuwa mai ka aikata a gareni da har kake neman yafiya ta? Da alama dai ka san wannan muguwar ko?" "Kwarai kuwa na san ta sosai ma, mun yi zamani da ita lokaci mai tsayi da ya shuɗe. Da ban yi mu'amala da ita ba yanzu da ki na cikin kwanciyar hankali, amma sai dai na kasa wannan tunanin gashi yanzu ke da kika rage ta na son ɗauke ki ta sha jininki.. Baki Suhaima ta bude ta na jin wani hargitsatsen labari mai cike da ɗaure kai da rashin sanin bakin zaren; jin ta ƙage da durƙushen ta gyara ta zauna ta ce. "To in kuwa haka ne Baba bani labari ka na da wata alaƙa da ni ne?" Murmushi tsoho ya yi ya ce. "Kwarai kuwa yarinya ni kuwa nake da alaƙa da ke, ki bari ba yanzu ba zan ba ki labarin rayuwarki. Zan warware miki zare da abawa idan na sake dawowa, idan kuma ban dawo ba zan turo wani a madadina." Yana gama faɗin haka ya miƙe tsaye da ƙyar, su Suhaima har da miƙe wa ta riƙe masa sandar ya tsaya da kyau sannan ta ce. "Baba to amma me ya sa ba za ka faɗa mini yanzu ba? Wallahi ina cikin damuwa da tashin hankali, Abba da Umma sun ƙi faɗa mini abin da suke ɓoye wa." "Za mu yi magana wani lokacin. Kafin ta ɗago ta ga ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa a wajan ba; rushewa ta yi da kuka ta sunkuya ta ɗauki zoben da ya yada ta na kallo, zoben fara ce sol sai sheki take.. Kamar wadda ake yi wa magana a kunne ta yi shuru, zuwa can kuma ta yi saurin saka zoben a yatsarta ta hagu sannan ta miki jiki ba ƙwari; goge hawaye ta yi ta juya ta fice zuwa inda take son zuwa... Ta na isa wajan mai masar ta miƙa dubu ɗaya ta ce. "Maman Yusuf ki bani Masa ta ɗari uku, ko kuwa ma bani ta dubun kawai." . Baki a washe Maman Yusuf ta amsa ta zuba mata a cikin leda, sai da ta miƙa mata suka haɗa idanu Maman Yusuf ta waro idanu cikin zallar mamaki ta ce. "Suhaima kece kuwa? Me ya faru dake haka na ga kin rame sosai?" Murmushin yaƙe ta yi ta ce. "Bani da lafiya ne shi ya sa." Fatan samun lafiya ta mata ita kuma ta wuce gida. Koda ta iso bakin get ɗin gidansu tsayawa ta yi ta saisaita nutsuwarta sannan ta buɗe ta shiga; Inna Laure na zaune ta kafe ɗaurin ɗan kwali a gaban goshi ta na kaɗa kai sai ga Suhaima ta Shigo. "Yawwa ƴar albarka ɗiyar Innarta maza kawo mini masar nan rabona da abinci tun jiya, kwana na yi ina kukan takaicin rashin faɗa mini mutuwar Abdallah. Yanzu in ban da rashin mutumci irin ubanku taya za ayi mutuwa amma sam ya kasa sanar dani, wannan ai rashin sanin darajar 'yan'uwantaka ne." Ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka har da sauke ɗankwalin daga kanta ta rufe fuska da shi; Shuru duk suka yi Suhaima ta iso gabanta a sanyaye ta ce. "Innata ki yi haƙuri Abba ya kira wayarki ba ta shiga ƙarshe ma a kashe ake ce masa, shi ya sa ba kiji a kan lokaci." "Allah sarki Audu kwanaki ya kirani ashe hirar ƙarshe ce muka yi da shi, ba komai Suhaima na yafe wa Mukhtar ba dan halinsa ba. Yanzu bari na tafi gidan na marigayi akwai masu zuwa gaisuwa za su zo daga garinmu.. Murmushin yaƙe ta yi ta shiga kitchen ta ɗauko mata kwano ta zuba mata; sauko wa ta yi daga kan kujera ta zauna ta yi bismillah ta soma cin abincin, ganin Suhaima ta yi tagumi yasa ta yatsar da cin abincin ta zuba mata idanu ta ce. "Ƴata lafiyarki kuwa?" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Innata da sauƙi dai zazzaɓi na yi na kwana ɗaya shi ya sa." "Subhanallah! Bari muje mu dawo mu zauna za mu yi magana Allah ya ba ki lafiya.. Amin ta ce ta koma kan kujera ta kwanta tare da lumshe idanu; tunanin mafita ta shiga yi amma sam ta kasa gano inda lamarin nan zai tsaya mata cikin daɗin rai, jariran nan suka faɗo mata a rai ta buɗe idanunta ta sauke su a kan Inna Laure dake cin wainar ta na goge hawaye. Dariya abin yaso ya ba ta ganin ta na cin abinci ta na kuka, sake rufe ido ta yi ta na jiran Innar tata ta gama su tafi dama su kaɗai suka rage su Suhaila sun wuce tun ɗazu... Bayan Inna Laure ta gama suka wuce zuwa gidan Abdallah, koda suka shiga Inna Laure guri ta samu ta zauna ta na goge hawaye mutanen da suka santa suna mata gaisuwa ta na amsa musu tare da musu godiya.... Yau aka yi sadakar bakwai, kuma har yau Inna Laure ba ta samu sun zauna da Suhaima ta faɗa mata damuwarta ba. Misalin ƙarfe goma da dare, zaune take ta rafka tagumi kwanciya take son yi amma tsoro da fargaba sun hana ta kwanciya. Wutar dakin ce ta ɗauke, shuru ta yi ta ƙasa motsawa daga kan gadon sai ji ta yi an tsikara mata wani abu kamar allura a gefen cikinta; da sauri ta dafe gurin ta juyo, babu abin da ta gani ta shafa wajan ta jan bargo ta rufa jikinta na rawa. Garam! Ta ji an banko ƙofar ɗakin da ƙarfi, kin buɗe ido ta yi sai ma ƙara ƙanƙame jikinta da ta yi; surutai ta dinga ji cikin kunnuwanta ba shiri ta miƙe zaune ta na zaro idanu. "Mama! Mama! Ta ji muryarsu ta kawo wa kunnenta ziyara; saurin juyo wa ta yi gefen da taji muryar tasu ai kuwa ta gansa a samar ɗakin suna mata murmushi, itama murmushin ta musu suka yo ƙasa-ƙasa zuwa kan gadon ta miƙa hannu ta taro su sai taji nauyi sosai. Waro idanu ta yi ganinsu a siffar yara 'yan shekara shida, kasa daure wa ta yi ta ce. "Ya aka yi naga kun koma masu girma?" Macen da take haƙarƙarinta ta ce. "To ai mun girma ne, kuma za mu iya zuwa miki a duk yadda muke so mu zo; sai dai Baba ya ce muke zuwa a suffar mutane dan kar ki tsorata da yawa." Jinjina kai ta yi ita dai mamakin yaran nan take da suke kiranta da Mama , ga shi har maganar Baba suke mata wanda ba ta san shi ko wani kala ba ne; ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Ranar da kuka zo kun ce za ku faɗa mini matsalata , to yanzu ina jiranku ku bani amsa me kuka gano game da mafarkin da nake da wannan muguwar kun ga jiya ma har yankar jikina da dinga yi ta na shan jinina, ta na gaf da kasheni sai ga wani ya zo ya ceceni amma ban san shi ko waye ba dan yaƙi yin magana ballantana na ga fuskarsa." "Mama kamar yadda Janu ta faɗa an mallaka mata ke ta sha jininki ta yi yadda take so da ke; idan ta so za ta iya sarrafa zuciyarki take amfani dake ta na cutar da mutane dan dama halinta kenan. Yanzu haka ta na nan ta na son taga bayanki abin da yasa ma ba ta samu damar yin hakan ba muna lalata wasu abubuwan da take yi ne a kanki, amma ba dan haka ba da tun shekarun baya za ta yi abin da takeso da ke.." Kallon rashin fahimta Suhaima ke yi wa yaran, tsoro, mamaki, al'ajabi, tashin hankali, duk sun tattaru sun kawo mata ziyara a lokaci ɗaya ta numfasa ta ce. "To waye ya mallaka mata ni?" Kallon kallo yaran suka dinga yi wa juna ganin haka yasa idanun Suhaima kawo ruwa ta soma magana. "Kun yi shuru ba ku ce dani komai ba, waye ya mallaka mata ni kuma meye haɗina da wanda ya mallaka mata ni?" "Mama indai har kina so ki san hakan to ki fara tambayar su Abba su faɗa miki abin da suke ɓoye miki, idan sun faɗa miki mu kuma zamu ƙara binciko miki komai. A halin yanzu dai muma ba mu san waye wanda ya sadaukar da jininki ga aljana Janu ba; Baba ya sani amma yaƙi faɗa mana." Namijin ya faɗa yana kallon Suhaima da jikinta ya yi sanyi; Tsayar da hawayen ta yi ta ce. "To ya zan yi ? Umma da Abba sun kasa faɗa mini abin da suka ɓoye taya zan gano bakin zaren matsala ta ne?" Ta faɗa ta na kallon su; Hayewa jikinta suka yi suna goge mata hawayen ita kam Suhaima ba shiri ta kallesu jin yaran sun yi nauyi, hannu ta kai ta rungume su ta soma magana. "Har yanzu ba ku faɗa mini sunanku ba, idan har da gaske ni mamanku ce to ki faɗa mini sunayenku." "Sunanmu Ayan da Iman Mama kuma ke mamanmu ce. Macen ta faɗa ta na kallon Suhaima; murmishi ta yi ta daga baki za ta yi magana taji ana buga ƙofar, zaro idanu ta yi ta ce. "Kun ga ana buga ƙofa ku tafi sai mun sake haɗuwa." Ayan ya ce. "Ba sai mun tafi ba Baba ya ce mu jima ya bamu lokaci mai yawa." Ita dai Suhaima shuru ta yi ta na kallon ƙofar, buɗe ƙofar ta yi ta shiga da sallama ta na cewa. "Ke ƴar nan yanzu kina jina ina buga ƙofa amma kin kasa tashi ki buɗe mini?" Kallon su Ayan dake lafe a jikinta ta yi, ta ce. "Inna na gaji ne kasa tashi na yi amma dai a nan za ki kwana ko?" "Kwarai ma kuwa ina so mu tattauna ne naga duk kin rame sosai, wani lokacin ma sai ki yi tagumi me ke damunki ne?" Ba ta ɓoye mata komai ba ta faɗa mata duk abin da yake faruwa da ita, sai dai itama ba ta ce mata ta yi mafarkin an kashe Uncle ɗinta ba. Riƙe baki Inna Laure ta yi ta na gyaɗa kai ta ce. "Ikon Allah yo ke kuwa Suhaima me ya haɗaki da mafarkin aljannu?" "Mama ki tambayeta abin da Abba suka ɓoye. Taji muryar Ayan na magana; jinjina kai ta yi ta ce. "Inna wai kin san wani sirri ne da su Abba suka ɓoye mini?" Da mamaki Inna Laure ta dube ta ce. "Wani irin sirri kuma Suhaima? Dama akwai abin da suka ɓoye miki wanda kike son sani ne?" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "E Inna akwai dai abin da basa so na sani." To ki yi haƙuri gobe ni zan tasa shi Mukhtar ɗin gaba sai ya faɗa miki abin da kike son sani, ni ba na son ganinki a cikin damuwa kwanta ki huta gobe za ki sani." Baya ta yi ta kwanta su Ayan na manne a ƙirjinta suna jin su. Sai da suka ga ta soma jin bacci suka ɓace daga jikinta... Aljana Janu ce zaune a maƙabarta ta tasa Suhaima a gaba fuskarsa har fitar da wani hasken wuta take saboda ɓacin rai, a fusace ta miƙe tayo kan ta sai dai ta na zuwa gef da ita aka yi sama da ita aka watso ta gefe. Cike da mamaki take kallon Suhaima taga ba kowa a tare da ita, idanunta ne ya sauka a kan zoben dake yatsar Subaima sai haske take, manya-manyan idanunta baƙaƙe ta zaro ta ce. "Ke! Wa ya ba ki wannan zoben?" Ita kuwa tuni ta firgice sakamakon arba da idanun aljana Janu da ta yi, zata sake yi mata magana wata ƙatuwar macijiya ta ɗauketa ta yi sama da ita... Futsarin da ya matse ta ne ya farkar da ita, da sauri ta kalli zoben dake tsayarta ta na mamaki yadda zoben ya ba ta kariya; miƙe wa ta yi ta shige toilet jin ana kiran salla... Takwas duk Inna Laure ta kira su Abba ɗakin Suhaima shi da Umma suka shigo tare da Na'im da Suhaila. Kallon Abba ta yi ta ce. "Mukhtar ka saurareni da kyau." Sunkuyar da kai Abba ya yi ya ce. "To Yaya Laure ina jin ki." "Ina so ku faɗa wa yarinyar nan abin da kuka ɓoye mata wanda ni kaina ban san da wannan sirrin ba.." Dam! Ƙirji Umma da Abba da Suhaila ya buga,, ya kalli Inna Laure ya ga ba wasa nan ya ƙara tabbatarwa kansa yau dai abin da ya ɗauki shekaru yana ɓoye wa sai ya faɗa, sirrin da ya ɗauki shekaru yana ɓoye wa saboda farin cikin Suhaima amma yau gashi ta haɗa shi da wadda ba zai iya mata wayo ta bar maganar ba. Gyara zama ya yi ya ce. "Ki gafarceni Yaya Laure da ban sanar da ke wannan maganar ba." "Ina jinka maza ka faɗa mini. "Yaya Laure Suhaima ba mu bane asalin iyayenta, m.. bai ƙarasa ba Suhaima ta ƙwalla ƙara sai gata a gaban Abba ta damƙi ƙafarsa cikin tsananin tashin hankali ta ce.. _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/7 14:32] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣7️⃣ Cikin tsananin tashin hankali ta ce. "Ab..Abb.. Abba don Allah ka ce dani mafarki nake kamar yadda nake yi kodayaushe." Tamkar wata zautacciya ta juyo ga Inna Laure data saki baki ta na kallon Abba da ya sadda kai ƙasa, faɗa wa jikinta ta yi sai yanzu taji wani irin kuka ya zo mata ta soma yi wa Inna Laure magana. "Innata kin gani dan na ce sai na san abin da suka hana na sani, shi ne Abba ya faɗi wannan mummunar kalmar wadda ko a mafarki naji ta ba zan sake komawa bacci ba. Innata don Allah ki ce masa na haƙura da jin maganar ba zan sake tambayar su ba har numfashi ya ƙare , Inna ki yi magana mana." Ta ƙarashe maganar da ƙyar ta jan numfashi. Kafin Inna Laure ta ɗaga hannu tuni ta saki jiki a jikinta alamar suma ta yi; hankali a tashe Inna Laure ta soma jijjiga Suhaima amma shuru kake ji babu alamar motsi, ɗago da idanunta ta yi wanda ya yi jajur saboda tashin hankali ta dubi su Umma da ko ƙwaƙƙwaran motsi sun kasa yi, baki na rawa ta ce. "Na..Na'imu kawo ruwa don Allah kar su kashe mini 'yata." Jiki ba ƙwari ya miƙe ya nufi freezer ɗin ɗakin ya buɗe ya fito da ruwan ya kawo mata har ya fara ƙanƙara; shi kansa ya shiga ruɗu, tashin hankalin da yake ciki ji yake kamar shi ne aka ce ba ɗan Abba ba ne, tunanuka sun masa dirar mikiya masu cike da tambayoyi kala-kala. Indai har ba Abba ba ne mahaifin Suhaimar sa to waye ya haife ta? Sannan me ya sa suka yada ta? Anya kuwa Abba gaskiya yake faɗa musu?" Na'im ya faɗa a cikin ransa bai san maganar ta fito fili ba sai jin muryar Inna Laure ya yi ta na amshe zancen nasa. "To ka dai tambayar mana shi Na'imu wannan ai masifa ce mai rawani, kai yanzu Mukhtar so kake ƴar taka ta mutu ko? To Wallahi sai na yi ƙaran ka Hisba sai sun bi mata haƙƙinta na sumar da ita da ka yi, wannan ai makasar ta kake nema. Ka faɗi abin da yarinya take son sani wanda ya danganci mafarkinta ba wai ka tsoratar da yarinya ba da wannan ɓakar kalmar, bani da mutumci Mukhtar ka sani Wallahi zan ci kwalarka na zazzabga maka mari, shin za ka yi magana ne ko sai na yi maka dakan tsakwara ne?" Ta faɗa tana fashewa da kuka, ita kanta hankalinta a mugun tashe yake da maganar ta Abba, taya ma zai ce wai basu bane asalin iyayen ƴarta Suhaima wadda duk yaransa tafi son ta fiye da su Na'im.. A sanyaye Abba ya ɗago ya kalli Inna Laure da take kuka wiwi ta na shafa fuskar Suhaima wadda sai a lokacin ne numfashi ya dawo, amma sam ta kasa buɗe idanu. "Yaya Laure babu abin da muke ɓoye wa Suhaima illa wannan sirrin, tabbas Suhaima ba mu muka haife ta ba hasalima ba a ƙasar nan muka tsinci Suhaima ba." Zabura Suhaima ta yi jin kalmar Abba take tamkar ana zuba mata ruwan wuta a ko wata kafa ta jikinta, kallon Abba ta yi zuciyarta na mugun bugawa ta ce. "Abba!" Ta faɗa da wata iriyar murya wadda duk wanda yaji yasan mai maganar ya kai ƙarshe a tashin hankali; Suhaila ta dubi Umma ta ce. "Umma wai da gaske ne maganar da Abba yake magana a kaina? Don Allah ku fitar damu cikin duhu kar zuciyata a buga, taya za ku ce wai ba ku bane iyayen Suhaima dani aka je asibiti lokacin da za a haife ta kuma aka fito da ita ni na fara rungume Suhaima a lokacin, amma yanzu ku fito da wannan maganar wani lefi ta aika a gareku kuke son hawan jini ya kama ta lokaci guda?" Umma ta goge hawaye ta dubi Inna Laure ganin Abba ba zai iya magana ba ta ce. "Suhaima ki tashi ki ji sirrin da muke ɓoye miki wanda bama son ko a mafarki kiji, an ce ranar wanka ba'a ɓoyan cibi dan haka yau ni zan sanar dake komai." Saurin tashi Suhaima ta yi jiki na rawa ta tabbata dai ba su suka haife ta ba kenan? "Waiyo Allah rayuwata to su waye iyayena Umma?" Ta faɗa jikinta na rawa har sai da Inna Laure ta riƙe ta ganin ta na neman faɗuwa. Gyara zama Umma ta yi ta soma magana hawaye na sauko wa daga cikin idanunta. . Shekaru ashirin da bakwai da suka wuce, ni da mijina mun yi auren soyayya; asalin mu 'yan garin Kaduna ne iyayenmu suna Hayin rigasa. Mijina su uku ne a wajan iyayensu Inna Laure sai Abbanku sai Abdallah. Suna da haɗin kai sosai ita Inna Laure kasancewar dangin babanta suka riƙe ta ba a Kaduna ta zauna ba a can Katsina take a wani ƙauye, a nan aka mata aure shi ya sa ba sosai take zuwa Kaduna ba dan ba ta saba da iyayenta ba; ba ta taɓa haihuwa ba amma ba ta damu ba ko kaɗan ni kuma ina jin tausayinta sosai a lokacin ina amarya. Wata na goma da aure na samu ciki ranar an sha murna a dangin mijina da ma nawa dangin, cikina na isa haihuwa na haifi mace kyakyawa mai kama da mahaifinta. Ranar suna yarinya ta ci sunan surukata wato Saudat muke kiranta da Suhaila; haka muka ci gaba da kulawa da ita a lokacin Abbanku ya gama karatu yana koyar da yan jami'a dan aikin da yake so bai samu ba sai ya amshi koyarwa. Ya karanci ɓangaren computer ne, to da bai samu aikin ba sai ya nemi na koyarwar; sai da Suhaila ta yi shekara da haihuwa sannan ya samu aiki a nan Kano. Tun da muka zo Kano ban san kowa ba ni kaɗai nake zama sai sannu a hankali na sama da maƙotana; ana haka Abbanku aka tura shi ƙaro karatu a ƙasar Ghana. Ranar na yi murna ganin yadda hanyar samu take zuwan mana a lokacin kuma na yaye Suhaila Inna Laure ta zo ta ɗauke ta suka tafi ƙauye sai bayan wata ta dawo da ita. Muna ta shirin tafiya Ghana Abdallah ya kira Abbanku ya ce matarsa ta haifi ɗa namji, ai kuwa mun sha murna sosai kasancewar saura kwana goma mu tafi sai muka shirya ana saura kwana biyu suna muka tafi wajan suna. Washegarin suna na tafi gidanmu na musu sallama, sun so na bar musu Suhaila amma na ce babanta ba zai bari ba suka haƙura muka dawo; da Yamma lis muka shirya 'yan'uwa suka mana fatan alkhairi sannan muka dawo cikin kewar dangi. Lokaci na cika muka shirya tsaf zuwa muka wuce Ghana cikin farinciki musamman ma ni nafi Abbanku murnar zuwa gari; muna sauka aka zo aka ɗauke mu aka kaimu wani gida, wanda ya kaimu yake sanar da mu anan za mu zauna muka masa godiya ya tafi.. Washegari Abbanku ya fita zuwa wajan aiki, ranar sai dare ya dawo da har na tashi hankalina ganin ƙarfe takwas ta yi bai zo ba hankali a tashe nake tambayar sa. "Abban Suhaila lafiya dai tun safe sai yanzu ka dawo?" Sai ya ce dani. "Aiyuka ne suka min yawa sosai shi ya sa, yanzun ma ba dan na gama na dawo sai gobe." Jin abin da faɗa sai hankalina ya kwanta.. Haka muka ci gaba da rayuwarmu a Ghana Suhaila ta yi wayo sosai wani lokacin yaran maƙotan mu suke zuwa su tafi da ita, sai zuwa Yamma suke dawo da ita; anan garin Abbanku ya sakani Islamiyar Unguwar da ake zuwa bayan La'asar... Haka muke rayuwa a ƙasar; har muka kai shekara biyu a ƙasar Ghana, Suhaila a lokacin ta na da shekaru huɗu amma har lokacin ban sake samun ciki ba.. Haka na takurawa kaina akan rashin sake haihuwa na matsa muka tafi Asibiti; ko da muka je aka mana gwaji aka tabbatar mana da lafiyarmu ƙalau kawai dai haihuwar ce ba ta zo ba.. Addu'a na dinga yi ina roƙon Allah ya bani haihuwa dan kullum Suhaila sai ta dinga cewa. "Umma ki haifa min sister ni ma irin na su Aruf, a gidansu su uku ne ni ma so nake mu zama uku." Idan ta faɗi haka sai dai na ce mata to kawai na rabu da ita.. Sai da na ƙara wata shekarar biyu sannan na samu ciki; ranar na sha murna sosai daga ni har Abbanku, ko Maman Aruf ban ɓoye mata samun cikin ba; ita ma ta tayamu murna, a lokacin ita ce Ƙawata kuma maƙociyata ta na da kirki sosai kullum Suhaila na gidanta. Haka muka ci gaba da rainon cikin har ya kai watan haihuwa. Wata ranar Lahadi cikin dare ƙarfe 4:30pm ciwo Gadan-gadan ya zo gashi ranar bai kwana gida ba; ƙoƙarin ɗaukan wayata na yi dan na kira shi amma na kasa motsa wa . Ƙarfe biyar daidai na yi na haihu ni kaɗai a cikin ɗaki a kan carpet; ko da jaririyar ta faɗo ba ta yi kuka ko kaɗan ba abin da yasa hankalina mugun tashi. Rarrafa wa na yi na janyo wayata jikina na rawa dan babu kuzari a jikina; na danna wa Maman Aruf kira sai da ta kusa tsinke wa ta ɗauka cikin mamagin bacci ta ce. "Hello Maman Suhaila lafiya dai?" A wahalce na ce mata. "Na haihu please ki zo." Ba shiri ta miƙe ta ce gata nan zuwa ta kashe kiran; ta na shigo wa ɗakin sai ga Abbanku ya dawo, a rikice ya kwashe ni da jaririyar Maman Aruf ta ce za ta gyara gurin in ta gama za ta biyo mu a baya.. Muna cikin tafiya mun kusa isa Asibiti motar ta tsaya, hankali tashe ya fito dan ya ga meye matsalar; sai ya ga faci ne tayar gaba duka biyun suka yi, ɗayar tayar ma ta tsage ta na ƙoƙarin fashe wa. Kamar daga sama naji kukan jaririya ya daki dodon kunnuwana, saurin kallon tawa jaririyar na yi naga ba ita ba ce sai na sauke glass ɗin motar ina waige; can jikin bishiyar bakin hanya na hango jaririyar a cikin zani sai ɗaɗɗaga ƙafafu take. Sake waro idanuna na yi naga dai mutum ne ba idanuna ba ne, juyo wa na yi na dubi Abbanku na ce. "Abban Suhaila ka ga jariri a jikin bishiyar can yana kuka." Da sauri ya kalli inda na kalla ya ga abin da nake faɗa masa, wajan ya nufa bakinsa ɗauke da addu'a ya ɗauko jaririyar jinin da aka haife ta a jikinta ko bushewa bai yi ba an dai yanke cibiyar; ya bani ita na ɗaura ta a ɗayar cinyata ya shiga muka wuce Asibitin.. Muna isa aka shiga duba lafiyarmu Doctor na cewa me ya sa na bari na haihu a gida, sai na ce mata. "Maigidan ne baya nan shi ya sa." Allura aka mini har da ƙarin ruwa, suma yaran aka zo duba su nan ake sheda mana cewar ɗaya daga cikin jariran sun rasu, a ruɗe na kalli doctor na ce. _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/8 16:15] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣8️⃣ A ruɗe na kalli doctor na ce. "Ta rasu?" Na faɗa muryata na rawa dan ni a tunanina jaririyar da muka tsinta ce ta rasu. "E hajiya ta rasu sài haƙuri ga dai ɗayar jaririyar. "Ta faɗa tare miƙo mini ita; ganin tawa ce ta rasu na fashe da kuka saboda na ƙwallafa rai akan abin da yake cikina tun kafin ya zo duniya, haƙuri ta dinga bani ta ɗauke jaririyar na ce ta miƙa wa mijina yana waje. Sosai naji mutuwar jaririyata amma kuma da na tuna akwai wata sai naji damuwata ta ragu sosai nan bacci ya ɗauke ni.. Doctor na fita da jaririyar a lokacin Maman Aruf ta zo tare da Suhaila da Aruf; ta na isowa Suhaila ta dage ita za a bai wa jaririyar, ganin haka yasa Abbanku ya ce ta zauna a mata. Jiki na rawa ta zauna sai washe baki take aka runguma mata jaririyar; bayan ta bata ne nan take sanar da su cewa ɗayar jaririyar ta rasu nan fa Maman Aruf ta kalli Doctor cike da rashin fahimta ta ce. "Kamar ya ya ɗayar ta rasu? Dama biyu ta haifa ne?" Ta faɗa fuskarta ɗauke da mamaki ƙarara; Abbanku ne ya ce Allah ya jiƙan ta su je a bashi ita a mata sutura, jagora ta masa zuwa inda ake aje gawawwaki.. Bayan na farka ne aka bar su Maman Aruf suka shigo ɗakin, zuwa lokacin ina zaune suka sameni, da sauri Suhaila ta iso inda nake bakinta yaƙi rufuwa ta soma rattaɓo mini bayani. "Umma sister na mai kyau ce sosai; Umma a goya min ita zan ke zuwa wasa da ita tare da su Aruf." Murmushi kawai na mata ban iya ce mata komai ba, kallon Maman Aruf na yi ganin yadda take kallona sai na gane ƙarin bayani take son na mata; a sanyaye ta ce da ni. "Maman Suhaila dama 'yan biyu kika haifa ne?" Kallon Abbanku na yi sai ya mini alama da kar na ce mata a'a, kallon ta na yi ina murmishi na ce. "E biyu ne ai bayan na zo aka haifi ɗayar, ita wadda na haifa a gida ta rasu sai wannan ɗin." Jinjina kai ta yi sai kuma ta saki murmushi ta na faɗin. "Ai dama na sha faɗa miki wannan cikin naki yara biyu a ciki, amma kika kasa yarda yanzu dai gashi maganata ta tabbata kin haifo biyun." Murmushi na yi muna haka sai ga Doctor ta iso ta bamu sallama shi kuma Abbanku ya tafi ya biya kuɗin magani ya dawo muka tarkata muka dawo gida... Ko da muka zo gida na ɗage sai mun koma Nigeria amma ya ce sam ba za mu tafi ba; ranar har kuka na yi amma ya yi burus dani sai kira ya yi ya sanar da su haihuwar, su kansu sun so ya dawo dani gida amma ya ce gaskiya a barni zai kula dani ba sai an ɗauke ni ba daga gurinsa. Inna Laure na jin labarin ta kira ta zazzagi Abbanku ta ce ya dawo da ni amma ya ce Sam ba zai zo ba sai dai su su zo suna zai biya kuɗin jirgi; kasancewar yanzu Allah ya buɗa masa har da shagon atamfofi garesa. Bayan kwana biyu muka ya kira iyayensa da nawa iyayen muka musu bayanin komai da ya faru, ni kan tsoro naji kar su ƙi amincewa; amma abin mamaki a cikinsu ba wanda ya ce wani abu sai ma sa mana albarka suka yi sannan suka ce wannan ya zama sirri tsakanin mu shida ɗin nan. Naji daɗi sosai ganin sun fahimce mu muka musu godiya... Tun da muka tsinci Suhaima nake ta ganin abubuwan mamaki, yarinyar ba ta yin rigima ko yunwa take ji ba ta kuka. Ranar kwananta huɗu da haihuwa ina toilet na ji kukan ta na fito da sauri, turus na tsaya ganin Suhaila ta na kiciniyar ɗaukan ta, ganin fa da gaske ɗaukan nata za ta yi na ƙaraso na hana ta ta ɗauke ta. Sai da na rungume ta na zauna ina shayar da ita kawai naga hannunta na hagu an ɗaura mata wani ɓakin zare mai kyau, sosai abin ya bani mamaki na kama hannun ina juya zaren, sai kuma na ga ya mini kyau sosai na bar mata shi... Washegari sai ga Inna Laure da Maman Sani da Ƙanwata da mamana har yan'uwan mamana, sai Abdallah da ƙanena Salim; na sha murna sosai kamar zan goya su, Inna Laure na zama ta ɗauke Suhaima ta rungume ta na kallon jaririyar har idanunta suka kai kan ɓakin zaren nan, cikin murmishi ta ce. "A su Bintu ba a manta da gargajiya ba kin ga ta sa wa jaririyar nan ɓakin zare." Murmushi kawai na yi ina kallon su suma suna ta cewa ai kuwa ya yi wa jaririyar kyau, haka muka wuni Maman Aruf ta musu girki mai rai da lafiya sai sa mata albarka suke... Ranar suna jaririya ta ci sunan Inna Laure sai na ce ake kiran ta da Suhaima; ranar Inna Laure ta sha kukan farinciki ganin Abbanku ya mata takwara ni kaina Abbanku ya birgeni da ya sa mata sunan Inna Laure... Sai bayan suna da kwana biyu suka tafi da ƙyar aka rabani da jikin mamana ina kuka sai na bisu, sai da na ga shigarsu mota na koma ciki na ɗauki Suhaima na zauna.. Su Suhaila abin na ya samu ko school ta je sai ta ce da 'yan ajinsu. "Ni ma ina da sister." Aruf ya tayata faɗa kaf 'yan ajin ba wanda bai san sunan Suhaima a bakin Suhaila ba, kodayaushe maganar Suhaima ɗin ta take an kusa saka ta makaranta za suke tafiya tare.. Haka muka ci gaba da rainon yaranmu Suhaima na daɗa wayo, sosai nake mamakin yarinyar idan na tafi Islamiya na kaita gidan su Maman Aruf har na dawo ba ta kuka, wani ƙarin abin mamakin ma idan dare ya yi haka kawai zan ga fuskar Suhaima na haske ta na ta wasa cikin tsakiyar dare; sosai nake ganin abubuwan al'ajabi a gurin yarinyar.. Haka dai take girma abin ta har ta yi shekaru biyar sannan aka sa ta a makaranta; ranar zuwan ta na farko ana tashi aka neme ta aka rasa a makarantar.. Suhaila ta dawo gida ta na kuka ta ce mini wai an rasa Suhaima, hankalina ya yi mugun tashi na kira Abbanku na sanar da shi wai Suhaima ta ɓata; nan da nan muka tafi makarantar tasu. Ko da muka isa nan suke sheda mana cewa suma neman ta suke kaf makarantar an zagaye basu ganta ba; hankalina ya kuma tashi na dinga kuka Abbanku na rarrashina muka tafi police station muka bada pictures ɗin ta, ranar dai haka muka dinga bayar da cigiyar ta a gidajen radio.. Yamma ta yi lis muna hanyar dawowa daidai get ɗin wata maƙabarta na hangi wani abu kamar mutum zaune; na yi saurin ƙara kallon gurin ai kuwa na ga Suhaima zaune ta na ta wasa a gurin, bakina na rawa na ce. "Abban Suhaila ka ga Suhaima can a get MAƘABARTA." Da sauri ya kalli inda nake nuna masa ya ganta muka paka na fito har ina haɗa wa da gudu na isa bakin get ɗin maƙabartar, ina isa na kamo ta ban tsaya yin komai ba na rungume ta na miƙe da sauri na isa motar muka wuce. A hanya nake kalle ta na ce. "Suhaima me ya sa kika fito daga makaranta? Kuma wa ya kawo ki bakin maƙabarta kika zauna kina wasa?" Dariya ta yi ta kalle ni ta ce. "Umma wata Anty ce ta ɗauko ni daga School ɗin ai, shi ne ta kawoni nan ta ce na zauna za ku zo ku ɗauke ni. Kuma har da abinci ta saya mini mai ɗaki ta kaini wajan wasa sannan ta kawo ni nan ta shiga cikin gidanta ta barni a waje.." Kwalalo ido na yi ina kallon Suhaima shi kansa Abbanku a lokacin saboda al'ajabi har so ya yi ya bigi wata mota garin kallon Suhaima, a kiɗime na ce. "Gidanta kuma Suhaima? To nan ai ba gidanta ba ne MAƘABARTA ce inda ake binne mutum idan ya mutu, ita Antyn naki ce ta ce miki nan ne gidanta?" Gyara kwanciyar ta ta yi a jikina ta ce. "E haka ta ce har ma da mijinta Umma, ta ce nan ne gidanta ni ma na shiga ciki." Tsananin al'ajabi yasa na ce. "Ke! A MAƘABARTAR NE kika zauna?" "E." Kawai ta faɗa ta koma ta kwanta ta na lumshe idanunta sai sauke ajiyar zuciya take... Ko da muka zo gida sai juya kalaman Suhaima nake, hankalina ya kasa kwanciya da maganarta, Abbanku ya watsar da magana ya ce kawai magana ce irin ta yara ba komai ba; amma kuma ni hankalina ya kasa kwanciya, ganin bani da mafita sai kawai na dinga mata addu'a ƙarshe ma na hana ta zuwa School ɗin... Tun da na hana Suhaima zuwa School ni ma na daina zuwa Islamiya a satin; haka kawai naji hankalina ya kasa kwanciya da lamarin yarinyar. Ashe dai ba'a rabu da bukar ba an haifi habu, sai na bar Suhaima a ɗaki amma da an jima sai dai naji ta buɗe ƙofar palo ta shigo, idan na tambaye ta ya aka yi ta fito sai kawai ta ce wasa suke da ƙawayen ta. Washegarin ranar data fara fita cikin dare muka nemi Suhaima muka rasa; babu inda ba mu duba ba a cikin gidan amma sam bamu ganta ba hakan ya ƙara sa zuciyata bugawa, waje Abbanku ya fita ya tambayi Maigadi ko ya ga Suhaima; sai ya ce bai ganta ba gaskiya.. Ganin ba ita ba dalilin ta sai muka fita bakin get muna ta duba wa amma sam bamu ganta ba, gefen layin gidanmu muka dinga bi da mota muna nemen ta ko Allah zai sa mu ganta. Abin mamaki sai ga Suhaima a get ɗin maƙabartar da muka tsinto ta ta yi zaune ta na surutu, da sauri muka tsaya Abbanku ya fita ya iso gareta yana mata magana. "Suhaima me ya sa kika zo nan cikin daren nan?" Buɗar bakinta sai cewa ta yi. "Abba wasa muke ni da ƙawayena, kuma dama na ce musu zan tafi gida yanzu ina jin bacci." Cike da tsoron lamarin yarinyar ya dinga duba wa ko zai ga wani ɗan'adam a gurin amma ba kowa, hannunta ya kama ya ce. "To tashi mu tafi gida." Da ƙyar ta yarda suka tafo daga get ɗin maƙabartar, ko da ta zo shiga sai cewa take. "Sai gobe zan sake dawowa mu yi wani wasan, zan kawo muku kayan wasa." Ni kan tuni jikina ya ɗauki rawa saboda tsoro gani nake kamar ba Suhaima ɗina ba ce an canja mini ita; ta na shigo wa motar ta faɗa kaina ta na dariya da yi shuru ban ce mata komai ba dan tsoro ma take bani . Muna zuwa gida na mata wanka na tofe ta da addu'a sosai ranar a tsakiya muka saka ta muka yi bacci da ita. Washegari Suhaila ta dage sai sun koma makaranta ba dan na so ba na shirya su muka je na kaisu; Maigadin makarantar na yi wa magana kamar zan yi kuka saboda fargaba. "Don Allah Baba kar ka bari Suhaima ta fita daga School ɗin nan, idan ba ni na zo ɗaukan ta ba kar ka bari ta fito ka taimakeni Baba." Jinjina kai ya yi ya ce. "Babu matsala yarinya zan kula da ita in sha Allah." Godiya na masa na wuce gida ina ta zullimi. Tun kafin lokacin tashi ya yi aka kira Abbanku daga School ɗin ku, nan suke sanar masa ya yi maza ya zo Suhaima ba lafiya har suma take; hankali a tashe ya kira ni ya faɗa mini ya zo muka wuce. Muna isowa muka samu an kewaye ta ita da Suhaila da Aruf suna ta kuka; ni kaina da na ga halin da Suhaima take ciki sai da hankalina ya tashi matuƙa har ban san lokacin da na ture mutane ba na iso gaban su Suhaila. Wasu irin ƙuraje ne suka feso mata a jiki kamar ƙurajen da in ana zafi yake fito wa mutane, sai dai jikinta ya yi mugun zafi kanta kuma sanyi kamar an saka shi a freezer. Haka muka nufi Asibiti da ita ta na mimmiƙe wa a jikina; taimakon gaggawa suka ba ta ta samu ta yi bacci sannan doctor ya kira mu ciki.. ce mana ya yi kawai wasu ƙuraje ne suka feso mata masu saka zafin zazzaɓi har ma su shanye ruwan jikin mutum, ƙarshe ma har da jini; magani ya rubuta mana muka saya kwanan mu uku ta samu sauƙi.. Bayan sati ɗaya ya kuma dawo mata muka koma Asibiti aka kuma bamu gado, mun fi sati biyu muna Asibiti kafin ta samu sauƙi muka dawo gida; muna dawowa na takura wa Abbanku na ce sai mun dawo gida gara ayi mata maganin gargajiya, bai musa ba ya nemi a masa transfer zuwa Nigeria ga halin da ƴarsa take ciki. Da ƙyar da sidin goshi suka yarda dan sun ce su gaskiya aikinsa mai kyau ne in ma kuɗi yake buƙata zasu linka masa akan wanda suke biyan sa, shi kuma ya ce musu a'a kawai dai zai koma Kasar su ne sannan suka masa transfer. Yana faɗa mini na miƙe na haɗa kaf kayanmu a cikin akwatuna na shiga na yi wa Maman Aruf sallama, har da kuka na rabuwa da juna dan mun shaƙu ba kaɗan ba. Haka na tubure na ce ranar za mu tafi a lokacin an yi la'asar, ticket ya nema mana na jirgin dare sai ma muka ci sa'a akwai na ƙarfe shida ba ɓata lokaci muka wuce zuwa airport... A Kano muka sauka daret muka wuce gidanmu, sai bayan mun huta ne na kira Maman Sani na sanar da ita mun dawo gida; sai gata sun zo ita da yaranta uku Sani da Maryam da Ma'ida... Bayan kwana biyu muka tafi Kaduna muka zaga dangi kowa sai murna yake idan yaji an ce an yi wa Abbanku transfer ya dawo Kano da aiki; sati muka yi sannan muka tafi ƙauyen su Inna Laure. Kamar ta goya mu ,Suhaima kuwa dama ba ta yardar kowa ya taɓa ta ta na lafe a jikina, amma abin mamaki muna zuwa ta bar jikina ta koma gurin Inna Laure ta goye ta duk da ta girma amma haka ta goya ta.. Ranar Abbanku ya koma ni kuma sai da muka yi kwana uku sannan muka soma shirin dawowa, ai kuwa Suhaima ta ce ba ta san maganar a raba ta da Innarta ba ; kasancewar magani muke nema sai na keɓe da Inna Laure na faɗa mata ga abin da yake faruwa da Suhaima, amma zan barta a nan a nema mata maganin gargajiya ko Allah zai sa a dace.. Inna Laure har kuka ta yi na barta muka dawo gida ni da Suhaila. Ranar Monday aka mayar da Suhaila School amma kullum mita take yaushe Suhaima za ta dawo, sai na ce mata sai zuwa sati za a kawo ta... Alhamdu Lillah da taimakon Allah da taimakon surukin Inna Laure Malam Habu; Suhaima ta samu lafiya watan ta uku a can ana mata rubutu ta na sha ana shafa mata rass Allah da ikonsa ya ba ta lafiya.. Haka aka dawo da ita naji farin ciki ganin yadda ta yi sharr abin ta, Suhaila kam jan ta ta yi aka kaisu gidan Abdallah sai murna take. Tun da aka kawo Suhaima ba ta taɓa fita ba ko ta yi wani abu makamancin wanda ta dinga yi a Ghana; amma duk da haka Inna Laure sai ta bada magani an kawo mata har da rubutu, sosai suka shaƙu da an musu hutu ita ta ce ƙauye za ta tafi, ita kuma Suhaila sai ta ce ba ta zuwa ƙauye ta wuce Kaduna gidan Ƙanwata.. Wata rana muna hira ni da Abbanku na ce da shi. "Yanzu dai Alhamdu Lillah Abban Suhaila komai yana tafiya lafiya, amma ba ka tunanin wannan abin da yake faruwa da Suhaima ko yana da gami da alhalin ta? Ni fa ina jin tsoron kar wata rana asirin mu ya tonu gashi ba wanda muka sanar wa da maganar nan sai iyayenmu kawai suka sani." Kallona ya yi shi ma ya cè. "Gaskiya da dai abin na bani tsoro, ballantana ita a cikin jinin haihuwar ta dan rashin imani irin na mutane aka jefar da ita, ko mai ta yi wa wanda ya mata haka? Kawai ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru sai alkhairi tun da an yi wa tufkar hanci." Na gamsu na bayanin sa na na ce. "Haka ne ni fa ina tunanin aljannu ne ta kwaso A MAƘABARTAR nan, amma dai tun da Allah ya raba ta da su Alhamdu Lillah za mu ce." "Umma waye ba shi da lafiyar?" Da sauri muka juyo jin muryar Suhaila a bakin ƙofa; sosai na tsorata na dube ta na ce. "Me kika ji muna cewa?" Fuska a dame ta ce. "Umma na ji kun ce wai Suhaima ta na ciwo to ba ku so ta sani ne?" Ajiyar zuciya na sauke jin ba ta fahimci komai ba sai kawai na ce mata ta iso ciki, zaunar da ita na yi na soma tsara mata magana ta yadda za ta yarda da maganar. "Suhaila 'yar'uwarki wani ciwo ne take mu kuma ba ma son ta sani?" "Wani ciwo kenan? "Ta faɗa ta na zaro idanu. "Yawwa kin san ciwon zuciya ko?" Gyaɗa mini kai ta yi na ci gaba da magana. "To shi ne take ɗauke da shi tun kuna ƙanana, to shi ne bama so ta sani dan kar ta saka kanta cikin damuwa; idan har ta sani ba za ta yi farinciki ba kuma ƙarshe ma zuciyarta ta buga ta mutu." Dafe ƙirji Suhaila ta yi ta ce. "A'a Umma kar a faɗa mata ku ɓoye ya zama sirri daga ni sai ku kar wanda ya ji." Wani sanyi naji jin ta yarda da maganar na ce. "Yawwa ķe ma ko kaɗan karki faɗa mata sannan zan miki albishir mai daɗi. " Da sauri ta dubeni ta ce. "Umma kamar wanne?" "Zan sake haifo muku wani ɗan'uwan ko mace." Da sauri ta rungume ni ta na dariya ta ce. "Da gaske Umma za ki sake haihuwa." Jinjina mata kai na yi alamar tabbatar wa sai ta mike ta wuce ta na kiran Suhaima dan ta mata albishir zan musu sabon baby.. Abbanku ya ji daɗin wayon da na yi wa Suhaila duk da lokacin ta na shekara 12 ne ita kuma Suhaima shekara 8 ba ta cika ba ma... Bayan wasu watanni na haifi baby boy, murna sosai muka yi sai ɗaukan sa Suhaila take in ta gaji ta miƙa wa Suhaima shi ; washegari sai ga Inna Laure ta iso.. Ranar suna yaro ya ci sunan Na'im naji daɗi dan ni na zaɓa da kaina aka sa masa sunan; haka aka yi suna aka watse ni kuma Abbanku ya ce ba inda zan je na yi zamana, ba dan na so ba na zauna.. Haka rayuwarmu ta ci gaba da tafiya har duk kuka girma Suhaila ta na gama JSS3 ɗan yayata wadda da mamanta da mamana uwa ɗaya uba ɗaya suke, ya ce shi fa son ta yake a musu aure sai ta ci gaba da karatu. Da farko Abbanku ya ce a'a dan lokacin shekaru ta 18 ne, amma su Baba suka ce ai ba komai a mata kawai. Ba'a wani daɗe ba aka musu aure ta cigaba da karatun ta a can Kaduna... "Wannan shi ne asalin abin da ya faru; ko da kika fara mugayen mafarkai a tunaninmu ciwon ki ne zai dawo wanda tun kina ƙarama kika yi sa, to shi ne yasa hankalinmu ya tashi matuƙa dan kar a goma gidan jiya..." Idanun Suhaima ya yi jajur saboda kukan da take, tashin hankalin da take ciki ya wuce gaban kwatance ta yi kalli Umma ta ce. "Umma ko da ace iyayena suna raye ba zan taɓa son su ba kamar yadda nake son ku, kune komai nawa ban san kowa ba sai ku dan haka kune iyayena tun da ke kika shayar dani kika reneni , dan haka kece mahaifiyata Umma." Ta faɗa ta na faɗawa jikin Umma; rungume ta Umma ta yi ta dinga bubbuga bayanta ta ce. " Suhaima ke Ƴata ce ki daina kukan kin ji." Ta faɗa ta na shafa bayanta idanun ta suka kai kan zoben dake yatsar ta, da sauri ta ce. "Wannan zoben fa?" Ɗago wa ta yi ta ce. "Wannan zoben wani tsoho ya bar ta nan dai ta faɗi yadda suka yi da tsohon, ta ƙara da cewa. "Umma ina so ku kaini Ghana tabbas maganar Aryan haka take A MAƘABARTA NE lamarin ya fara. Dan haka ina so naje wannan maƙabartar dan na gano komai da ya shafi iyayena." Inna Laure ta ɗaura hannu biyu a kai ta ce. "Na shiga uku Suhaima su waye kuma Aryan?" Kai tsaye ta ce mata. "Inna 'ya'yana ne su, kuma zan so mu sake haɗu wa kafin ku kaini Ghana." Kwalalo idanu waje suka yi Na'im ya ce. " 'ya'yanki kuma to kamar ya ya?" _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/9 21:48] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣9️⃣ " 'Ya'yanki kuma to kamar ya ya? "Ya faɗa cike da al'ajabin Suhaima. Ajiyar zuciya ta sauke ba ta kuma ce musu komai ba ta yi shuru kanta a ƙasa; wani irin zafi zuciyarta ke mata ga tunanuka barkatai, wanda suke neman tarwatsa mata ƙaramar ƙwaƙwalwarta.. Inna Laure ta matso kusa da ita, ɗago da fuskarta ta yi cike da alhinin ganin ƴar tata a cikin wannan halin; a sanyaye ta ce. " Ƴar Innarta!" Kuka ne ya ci ƙarfin ta sai ta faɗa jikin Inna Laure ta fashe da sabon kuka; jikinta ya ɗauki ɓari tamkar mazari, Inna Laure ta dinga bubbuga bayanta cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Suhaima kada ki ce mini kukan rashi iyaye ne kike? Mu ne iyayenki har gaban abada ki daina kukan kin ji. Ko da a ce waɗanda suka haifeki sun fito ba za mu bari su raba mu da ke ba; ki yi haƙuri don Allah ki daina maganar zuwa Ghana nan hankalina tashi yake, tashi ki daina kukan kar ki sake tunanin komai tun da ki na da Allah ki na da mu. "Ta faɗa cike da damuwa; ita kanta hankalinta a mugun tashe yake ba ta taɓa tunanin Suhaima ba ɗiyar ƙanenta ba ce, ko da a mafarki ne ta ga haka ba za taɓa ba wa mafarkin muhimmanci ba, amma gashi dai yau sirrin ɓoye ya fito fili.. Tsagaita kukan ta yi ta soma magana cikin raunatacciyar murya. "Innata ya zan yi? Yanzu su Umma ba su suka haifeni ba kenan? Su iyayen nawa a ina suke? Kuma me ya sa suka jefar dani a lokacin da na zo duniya? Me na musu Innata? Wallahi ko da na gansu ba zan taɓa yafe musu wulaƙanta ni da suka yi ba; indai da son ransu suka jefar dani to ba na son ganinsu ko a mafarkina su yi zaman su a inda suke, ni ma zan zauna da waɗanda suke so na da ƙauna ta.. Na tabbata wannan tsohon ya san inda iyayena suke; gashi kuma ban san ta ina za mu sake haɗu wa ba, Inna ina jin zuciyata na tafasa, ji nake kamar ana zuba mata zuwan zafi tafasashe." Kuka sosai take ta na sunbatu Inna Laure na rarrashin ta; su Umma kuwa kasa magana suka yi kowa tausayin halin da take ciki yake yi, ganin sun kasa shayo kanta Na'im ya miƙe daga inda yake ya iso gaban Inna Laure cikin kwantar da murya ya soma mata magana. "Anty Suhaima ki yi haƙuri mana; ko wani bawa fa da kalar tashi ƙaddarar ke taki a haka ta zo, ki gode wa Allah da ba a mugun hannu kika tashi ba; sannan ki ƙara gode wa Allah da ya sa kika faɗo a hannun musulmai ba kiristoci ba. Tashi kinji in sha Allah komai zai wuce. "Ya faɗa yana miƙa mata hannunsa." Tsayar da kukan ta yi Inna Laure ta tashe ta daga jikinta; kallon Na'im ta yi ya mata alama da ta zo garishi, hannunta ta sa a cikin nashi ya kama ta ta tashi ya miƙar da ita. Su ko su Umma suna kallon su, da ƙyar ta tsaya a kan ƙafafuwanta jikinta na rawa, ganin haka yasa Na'im haɗa ta da jikinsa ta kwanta kanta a kafaɗarsa. Kasancewar ya fita jiki da tsayi sai ta koma kamar ita ce Ƙanwar shi ne yayan; ɗakinsa suka nufa su Inna Laure suka raka su da idanu har suka wuce.... Inna Laure ta jinjina kai cikin damuwa ta dubi Abba. "Wallahi Mukhtar ba ka kyauta min ba, ai na ɗauka sirrinka sirrina ne amma sai ka ɓoye mini wannan." Ƙara sunkuyar da kansa Abba ya yi ya ce. "Yi haƙuri Yaya Laure Baba ya ce kar na sanar muku ke da Abdallah; shi ya sa ma ban sanar da ke komai ba game da Suhaima." "Ba komai ya wuce ni yanzu Suhaima nake tausaya wa, yanzu hankalinta kacokan ya karkata zuwa ga asalin iyayenta, ba mu san taya aka jefar da ita ba, ko kuma sato ta aka yi Allah amsanin gaibu." Ta ƙarashe maganar ta na sa haɓar zaninta ta goge hawaye; ta ci gaba da magana. "Yanzu dai mu samu a hana ta zuwa Ghana nan, ba kowa ta sani ba kuma ƙila ma iyayen nata ba a nan suke ba; mu samu a shayo kanta a mantar da ita damuwar da take ciki ina son ta sosai yarinyar nan, akwai hankali ga nutsuwa." Suhaila ta miƙe jiki ba ƙwari ta wuce ɗakinta suka bita da kallo, tattauna wa suka yi sosai a kan lamarin sannan su Umma suka fita a dakin aka bar Inna Laure zaune ta rafka tagumi. Ko da suka shiga ɗakin zuwa lokacin jikin Suhaima ya ɗauki zafi; a dame ya ja ta suka zauna a bakin gado ya ce. "Anty Suhaima don Allah ki yi haƙuri komai zai wuce; bana son ganin ki cikin damuwa duk bana jin daɗi." Ɗago wa ta yi ta dube shi hawaye na bin kuncinta ta ce. "To Na'im me zan yi? Da ina tunanin mafarkan da nake ne damuwata; ashe ma ni tsintacciya ce iyayena suka jefar da ni, yanzu a ina zan gansu?" Kuka take sosai har da shiɗe wa take, ganin haka ya gyara zama ya janyota ya shigar da ita jikinsa; da sauri ta maƙale shi ta ci gaba da kukan ta na sunbatu.. "Na'im rayuwata ba ta amfani in dai ni ba jinin gidan nan ba ce, wa ya sani iyayena ko a wata duniyar suke; ko ma na gansu na tsane su tsana mai tsanani tun da suma suka tsaneni sai n... Ba ta ƙarasa ba ya yi saurin rufe mata baki da hannunsa jin ta na neman yin saɓo; "Ki daina magana Anty kin ji jikinki har zazzaɓi ya rufe ki, kar ki kuma cewa kin tsani iyayenki ko ba ki son ganinsu; yanzu ba ki da tabbacin ta ya ya suka rabu da ke, dan haka karki yanke hukunci a kansu. "Ya faɗa yana ɗago da ita.." Ba ta yarda sun haɗa idanu ba ta kuma koma wa ta kwanta; shi kuwa Na'im wani irin tausayin yayar tasa yake ji na ratsa masa ko'ina na jikinsa, shi kansa yana son sanin iyayenta da dalilin rabuwa da ita a lokacin da take buƙatar su.. Matsa wa ya yi kan gadon ganin ta na rawar sanyi ya lulluɓa mata bargo shi kuma ya jingina da jikin gadon; ƙoƙarin raba ta da jikinsa ya yi amma sam taƙi yarda sai kawai ya haƙura ya zuba mata idanu cike da tausayin ta; addu'a ya dinga tofa mata a ta na lumshe idanunta, daga ƙarshe wani wahalallan bacci ya yi awon gaba da ita. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya lallaɓa ya raba ta da jikinsa ya maye mata gurbinsa da pilo, da sauri ta rungume pilon ya ƙara rufa mata bargon har kanta sannan ya fita a ɗakin... Kafin Yamma ta yi tuni jikin Suhaima ya yi tsanani; ko idanunta ba ta iya buɗe wa lokaci ɗaya ƙafafuwanta suka lauye ta kasa tafiya da su. Hankalin su Umma ya tashi suka dinga yi mata addu'a ta na ƙyarma ta na fisge-fisge, zuwa can ta daina yi duk suka zuba mata idanu; wasa-wasa har bayan Isha'i Suhaima ba ta farka ba, Inna Laure ta ɗauko wani magani a cikin leda ta dubi Umma ta ce. "Bintu kawo garwashi a mata turaren iska kar abin ya ƙara gaba." Umma dai ba ta iya cewa komai ba ta je ta hura gawashi ya kunnu ta sako a kaskon turaren wuta ta kawo; amsa ta yi ta buɗe ledar ta dauko garin maganin ta afka a ciki... Cikin minti ɗaya hayaƙin ya gauraye ɗakin ta kuma fito da 'ya'yan habbatussauda shi ma ta afka a kan garwashin ta na cewa. "In sha Allah za ta samu sauƙi wannan 'ya'yan habbatussauda ɗin zai ba ta kariya in sha Allah." Tari Suhaima ta dinga yi ta na juya kanta jikinta na rawa, a firgice ta tashi zaune idanunta a lumshe za ta sauko daga kan gadon; Na'im dake kusa da ita ya ruƙo ta da sauri ganin ta na ƙoƙarin kwace jikinta. "Ku sakeni na tafi. Suka tsinkayo muryar Suhaima; da sauri ya kuma matse ta ta na fisge wa ya shiga karanto mata Ayatul kursuyu a cikin kunne, hakan yasa ta dinga mimmiƙe wa ta na wani irin kururuwa. Sai da ta yi lakwas sannan dukkansu suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala ganin ta samu bacci; mayar da ita ya yi ya kwantar ya ƙara tofa mata addu'o'i sannan ya rufe mata jikinta. Inna Laure ta zauna ta na ta na faɗin" Allah ya ba ki lafiya." Sai wuraren ƙarfe 11: am na dare suka bar ɗakin aka bar ta tare da Inna Laure; shi kuma Na'im ya shiga ɗakinta ya kwanta a kan kujera. Bacci take amma yatsina fuska take ta na juya kai; Inna Laure ta tsaya a kanta ta na mata addu'a har ta daina juye-juyen sannan ita ma ta kwanta a ƙasa... "Mama! Mama! Buɗe idanunta ta yi a hankali ta na kallon ɗakin; can ta hango su a ƙofar ɗaki suna kallon ta. Kamar an cire mata ƙaya haka ta ji ta miƙe ta isa bakin ƙofar ta tsaya ta na kallon su idanunta cike da hawaye ta ce. "Ayan sun ce ba su ba ne asalin iyayena; ko kuna da masaniya a kan asalin iyayena? "Ta faɗa ta na rufe bakinta da hannu gudun kar kukan ta ya tashi Inna Laure." Iman ta matso kusa da fuskarta ta kai hannu ta share mata hawayen ta ce. "Mama ki daina kuka Baba ya ce yana sonki; yanzu mun zo mu tafi dake ne dan ki ga Baba, ya ce yana son yin magana dake." Baki buɗe Suhaima ke kallon Iman za ta yi magana Ayan ya ce da ita. "Mama ki zo mu tafi wajan Baba." Murya ƙasa-ƙasa ta ce. "To idan Inna ta tashi ba ta ganni ba damuwa za ta shiga; ba za mu daɗe ba ko?" "Za mu daɗe Mama; wannan kuma ba matsala ba ne. "Ayan ya kuma faɗa tare da buɗa hannunsa wani haske ya fito ya nufi gadon; yana isa sai ga mace sak Suhaima kwance da irin kayan da yake jikinta... Kwalalo idanu Suhaima ta yi tsananin al'ajabi yasa za ta kurma ihu Iman dake daf da fuskarta ta rufe mata baki; da kansu suka buɗe ƙofar ta yadda Inna Laure ba za taji ba suka yi wa Suhaima nuni da ta fita a ɗakin.. Kallon wadda aka aje a kan gado take a matsayin ita; ganin ta na ɓata musu lokaci suka ɗauke ta suka ɓace daga ɗakin... A bakin ƙofar gida suka bayyana; waro idanu Suhaima ta yi ganin ta a waje ta ce. "To ina za mu je wai?" Ayan ne ya ba ta amsa "Wajan Baba za mu je mana." Ya faɗa kai tsaye yana yin gaba; kama hannunta Iman ta yi suka wuce. Tafiya suka dinga yi har suka bar unguwar; ita dai da idanu take kallon ikon Allah amma ta kasa magana tamkar raƙumi da akala haka take bin su. Hannunta suka kama su duka suka ɓace; kawai ganinsu ta yi a cikin daji fili ne tantawarai bishiyoyi 'yan tsuraru ne, tsoro ya kama ta ta na ƙyarma ta ji sun zaunar da ita... Ayan ne ya matso daf da ita ya soma magana. "Mama kin san su waye ahalinki?" Da sauri Suhaima ta girgiza kai cikin zaƙuwa da son sanin iyayenta; murmishi Ayan ya yi sannan ya soma magana. "Mama ba kin taɓa haɗu wa da wani tsoho ba?" Nan ma gyaɗa kai ta yi kamar wata ƙadangaruwa; shi kuma ya ci gaba da magana. "To wannan shi ne Kakan ki; kin taɓa ganin wasu mata da miji?" A tsorace ta ce. "E Ayan na gansu amma ƙila wannan muguwar ta kashe su." Girgiza mata kai ya yi ya ce. "To ai dama sun da mutu tun da daɗe wa." Zaro idanu ta yi ta na kallon Ayan baki na rawa ta ce. "Sun mutu fa ka ce? To amma me ya sa nake ganinsu?" "Saboda su ɗin suna son ki ne; kuma Janu ce ta shanye jininsu ta kashe su su duka ukun "Iman ta faɗa ta na dafa kafaɗar Suhaima. Cikin rashin fahimta ta ce. "To amma su me suka mata ta kashe su?" "Sun sadaukar da rayuwarsu a kanki, sun fanshi ranki da tasu rayuwar. Wannan mata da mijin sune iyayenki na asali "Ayan ya faɗa yana riƙe hannayenta." Miƙe wa ta yi a kiɗime suka mayar da ita ta zauna, cikin tashin hankali ta ce. "Kenan su ne iyayena?" "Kwarai kuwa su ne iyayenki, kuma ni na kashe su yau kema zan kashe ki tare da wannan hatsabiban yaran. Muryar Aljana Janu ta ɗakin dodon kunnensu; a zabure Suhaima ta kalli su Iman da suka miƙe tsaye suna fuskantar Aljana Janu. Wata mahaukaciyar dariya Janu ta yi hannunta riƙe da sarƙa, wurga wa Suhaima ta yi Ayan ya tare sarƙar ta sauka a kansa; wani irin ƙara Ayan ya yi Iman ta kurma ihu mai tada hankali wanda dajin gabaɗaya ya amsa. "A a Ayan!" Ta faɗa da ƙarfi hakan yasa hankalin Suhaima mugun tashi ganin Ayan ya koma haske kala biyu; Gefe ɗaya fari ɗaya baƙi, ita kam Aljana Janu dariya ta dinga yi ta miƙa dogon hannunta ta ɗamko Iman. Wani irin zafi ya ziyarci ta ba shiri ta sake ta ta faɗo kan Ayan; hankalin Iman a mugun tashe ta murza zoben hannun ta hasken na isa kan Ayan ganin bakin hasken na ƙoƙarin mamaye farin hasken. "Dama ai na faɗa muku karo da Janu ba abu ba ne mai sauƙi; ku har kun isa ku ja da sarauniya wadda ta kashe aljanu bila adadin ballantana wannan ƴar'adam ɗin? To kun shiga komar Janu ni bana jin tausayin kowa ba ni da imani, duk wanda ya karya mini alƙawari to gabaɗaya sai na ga bayansa daga shi har ahalinsa. Matsa ki bani guri na ɗauki mallakina." Ta ƙarashe maganar ta na zaro idanunta marassa ƙyan gani.. Kuka Suhaima take ganin bala'i ido da ido a gabanta; yau ga ta a tsakiyar aljannu ana artabo a tsakaninsu, Iman kuwa tuni ta fusata ta taƙarkare ta kurma ihu idanunta suka koma yellow ta dubi Aljana Janu ta ce. "Kin yi ƙarya ki ce za ki taɓa mana mahaifiyarmu ki kwana lafiya; ke kin sani mu ba kanwar lasa ba ne tun da kin kara damu a kan Mama kin kasa cin galaba, shi ne yanzu kika samu ta yadda kika cutar min da ɗan'uwa? To kin taɓa mutuwar ki da kanki." Ta na gama faɗin haka ta rufe idanu cikin wata kalar murya ta soma faɗin mai haɗe da kuka-kuka ta taƙarkare ta soma magana. "Baba! Baba! Baba!" Dajin ne ya ɗauki girgiza tamkar zai kifa cikin ƙasa; ita kuwa aljana Janu na tsaye kan wata bishiya ta na dariya, so take ta ga wanda zai zo... Wata irin iska ce ta mamaye dajin mai ƙarfi; babu wanda yake jin ƙarfin iskar sai Suhaima data cure a guri ɗaya ta na karanto duk addu'ar da ta zo bakinta, har da su addu'a shiga banɗaki, da addu'ar gama cin abinci take karanto wa cikin fitar haiyaci... Sai da iskar ta lafa Suhaima ta ji dirar wani abu a gabansu; ta ɗago da sauri idanun a waje tamkar za su faɗo ƙasa. Tsaye ta gansa rufe da fuskarsa sanye da fararen tufafi takobinsa mai harshe biyu riƙe a hannunsa.. A razane take kallon sa; Iman na ganinsa soma magana cikin tsananin ɓaci rai da kaiwa maƙura a kan abin da Janu ta musu... _*MAMAN NUSAIBA CE*_ [3/11 22:35] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 1️⃣0️⃣ "Baba ina so yau ka yi maganin wannan azzalumar; ta hana Mama ta zauna cikin salama duk ta addabe ta, ka kashe ta kamar yadda take kashe bil'adama da aljanu. Baba kaga Mama ta na zubar da jini ka yi wani abu kar Janu ta zuƙe mata jini yanzu." Cikin ɓacin rai take magana har muryarta na canja wa; shi kansa Baban nasu kallon ta kawai yake. "Hahaha! Hahaha! Wa ya isa ya ja da ƙarfin ikona? Ku har kun isa ku fara arangama da Janu; na bar ku ne dan ba ku isheni kallo ba amma tun da kuka za ku iya zan kashe ku gabaɗaya har Maman taku. Kai Sayyid kake ko Sayi ma? To daga kai har 'ya'yan naka duk kun kawo kanku inda za a kashe ku. "Janu ce ke maganar ta na daga kan bishiya sarƙar hannunta na wani irin hasken wuta ja; Suhaima tuni ta yi sumar tsaye sai da Iman ta dafe ta sannan ta zabura, a firgice ta nuna Baban su Iman ta ce. "Yaya Sayyid!" Kallon kasa kallon ta ya yi kansa a ƙasa; wani irin hayaƙi ne ke fita a fuskarsa shi kuma baya so Suhaima ta gansa a asalin suffarsa, dan haka ya daure ya rikide ya dawo suffar mutane yadda ta san shi sannan ya ɗago. Fashe wa da kuka ta yi ta soma ƙoƙarin motsa ƙafarta amma ba ta kuzari iya sarrafa gangar jikinta; kallon shi ta yi a rauna ce ta kuma faɗin. "Sayyid ɗina! Ta faɗa cikin wata kalar murya ta na masa wani irin kallo; kallo ne irin na kewar masoyi wanda haka ya haifar mata da rashin kuzari a jikin ga kuma tashin hankalin da take gani, ita har ma ta manta da Janu da kuma Ayan da ya koma haske. Murmushin gefe baki ya mata ya gyara tsayuwar sa tare da miƙa hannu ya janyo ta ta dawo kusa da shi; kallon Ayan ya yi wanda yake tsakanin mutuwa da rayuwa; ya miƙa hannu ya ɗago gasken yana kallon Janu kamar yadda itama take kallon su da jajan idanunta. "Ummu! Ya faɗa a hankali yana matso da hasken kusa da su; kamar ƙiftawar ido sai ga Ayan ya dawo yadda yake, amma idanunsa a lumshe suke. Ita dai Aljana Janu na gefe ta na dariya sai juya sarƙarta take. Ayan na buɗe idanu ya yi ido huɗu da babansa; da sauri ya ce. "Baba ina Mama?" Nuna masa ita ya yi da hannu ya matso kusa da ita ganin yadda take kallon baban nasu ya kuma faɗin. "Mama ki kwantar da hankalinki komai ya zo ƙarshen tun da har Baba ya zo; ki daina kuka Mama." Haɗiye kukan ta yi tasa hannu ta goge hawayen ya tayata goge wa, kallon Ayan ta yi fuskarta fauke da alamar tambaya; shi kuma ya yi murmishi ya ce. "Mama nasan mai kike tunani; ki bari duk Baba zai miki bayani." Ba dan ta so ba ta yi shuru ta na ƙara koma wa bayansa , so take ta sake kallon fuskarsa dan ta tabbatar da shi ɗin ne, amma kuma tsoro ya hana ta yi hakan... "Idan kun gama ku miƙo mini ita nan; na faɗa muku ba na son raina ya ɓaci fa. "Janu ke faɗa ta na sauko wa daga kan bishiyar ta ja ta tsaya. Ayan da Iman suka shiga gaba suka tsaya, Iman na aiko mata wani irin kallo ta ɗaga hannu ta nuna ta da ta soma magana. "Ke har kin isa muna gani ke kashe mana Mamanmu? Wace ce ke? Dama Baba ke hanani aika ɗanyan aiki a kanki nake haƙura, amma yau kin kai haƙuri ƙarshe mu da ke za a ga wanda zai kashe wani." Wata kalar figitacciyar dariya Janu ta yi; wanda hakan yasa Suhaima maƙale wa a bayan Sayyid ta na faɗin. "Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Sayyid ka taimakeni kar ta kasheni Wallahi muguwa ce ajin farko." Sunbatu ta dinga yi jin yadda sautin dariyar Janu ke hautsina mata hantar ciki; gashi kuma shi Sayyid ɗin ko motsi bai yi ba ta maƙale a bayansa. "Mama ki nutsu mana. "Iman ta faɗa a sanyaye fuskarta na nuna ɓacin ran dake cikin zuciyarta. Hannu Sayyid ya buɗe ya saka yatsunsa biyu a kan gishinta ya ce. "Ummu yi shuru." Ɗif ta tsayar da kukan kamar ba ta wajan ma; Iman ta juyo ga Janu ta ce. "Idan har kin cika ke mai ƙarfi ce ki zo mu kara." "To! Yarinyar nan naga alama kina son na aika ki inda ba'a dawowa. Ke ko wanda ya haifeki yasan ko ni wace ce ballantana ke ƴar ƙarama dake ki ce za ki ja da ƙarfin ikona.. A harzuƙe Ayan ya ce. "Karfin ikon banza da wofi; muguwa azzaluma." Wannan kalma ba ƙaramar ɓata wa Janu rai ta yi dan haka ta yi girgiza ta na kwarara ihu; sai gata ta dawo wani darkekiyar Damisa ta nufo kansu a sukwane.. Ganin haka yasa Ayan da Iman suka koma Giwaye manya-manya; bakinsu na feshin wuta suka tsaya ƙyam suna jiran zuwan ta. Kafin ta iso suka kuma rikide wa zuwa wata kalar halittar ta da ban, suna haɗe wa aka dinga kaiwa juna sara da suka ta ko'ina. Yaƙi suke ba kakkauta wa , har zuwa lokacin ba wanda ya yi nasarar kai ɗan'uwansa ƙasa sai fafatawa ake ba ji ba gani.. Janu ta shammaci Iman ta shaƙo ta da ɓakar sarƙar dake hannunta; ita ko Iman rintse idanu ta yi duk da azabar ciwon da yake shiga cikin rubuta amma saŕa take kaiwa iya bakin ƙoƙarin ta. Sayyid na tsaye yana kallon su ko motsaw bai yi ba; ganin Janu na neman shaƙo Ayan ya yi wani irin huci da babbar murya ya ce. "Ayan! Maza ka kashe ta kar ku raga mata, riƙe nan "Ya ƙarshe maganar yana cilla ɗaga takobinsa sama." Saurin buɗe hannunsa Ayan ya yi sai ga takobin ta bayyana a hannunsa; Janu na ganin wannan takobin ta dakka tsalle irin nasu na aljannu ta daki hannun Ayan takobin ta faɗi. "Hahaha! Hahaha! Riba uku kenan ga takobin da na ɗauki shekaru ina neman ta, ga kuma jinin da zan sha na ƙara ƙarfi da ƙarfin dake jikinku idan na kashe ku" Ta faɗa ta na nufar takobin da wani irin sauri." Murmushi Sayyid ya yi ya juyo ya kalli Suhaima wadda ya mayar da ita kamar gunki a tsak cak take, kan Janu ya yi yana jiran ta isa ga takobin. Hannu ta kai za ta ɗauka aka yi sama da ita aka sako ta tim! Ta faɗo;cikin mamaki ta kalli takobin ta kuma murza hannunta ta miƙa za ta ɗauka. Wannan karon tsananin haske ne ya fito a jikin takobin ya nufi jikin Janu; ihu ta kurma ta na faɗuwa ƙasa, wani irin azaba ce take huta mata ruhi ba'a iya ganin komai na jikinta duk hasken ya mamaye ta hakan yasa ta ɓace ɓat a gurin.. Ayan ya duƙa ya ɗauki takobin yana murmishi ya ce. "Baba ka bari na bi bayanta na kashe muguwa ko an huta da zalincin ta." Ita kuwa Iman sai ɗaure fuska take dan ba ta so Janu ta gudu ba a karo na barkatai; kallon Sayyid ta yi cikin fushi ta ce. "Baba ka bari mu bita mana." "A a kada ku bita za ta dawo ai; dama takobin nan take nema da jimawa amma ba ta san a ina take ba, to yau ta ganta kunga kuwa ai za ta kuma dawowa." "Mama! Iman ta faɗa a firgice ganin Janu ta soka mata wata ƴar wuƙa a gefen cikinta; Wani kalar tsalle Ayan ya daka sai gashi a gaban su, bai tsaya yin komai ba ya farmaki Janu cikin sa'a ya yanke ta a fuska... Wasu irin kalamai ta dinga yi kamar ƙiftawa da bismillah sai ga dajin ya cika da wasu irin halittu masu firgitar wa; wuta na fito wa daga bakinsu, bayansu wuta ce ke ci ta kewaye dajin. Wata mahaukaciyar dariya Janu ta dinga yi ganin sun kewaye su; ta kalli Sayyid ta ce. "Ka bani takobin nan ko kuwa yanzu waɗannan dakarun nawa su lamushe ku." Sai yanzu Sayyid ya juyo suka haɗa idanu da Janu; babu shiri taja da baya sai kuma ta tsaya cak ta na ɗaure fuskar, shi ko gyara tsayuwarsa ya yi hankali kwance ya ce. "Idan na ce ba zan bayar ba fa?" "Sai na amsa da ƙarfin ikona. "To ki kwata mu gani azzaluma; yau duk inda kika gudu sai na kamo ki na miki kisan gilla a dajin nan, ko kina tunanin wannan ƙudajen da kika zo da su za su bamu tsoro ne? To kin yi ƙarya." Ya faɗa yana zaro wata takobin daga bayansa ya kamo Suhaima ya miƙa ta gurin Iman wadda ta canja halitta zuwa wata ƙatuwar mata. Ganin haka Janu ta dubi wannan tawagar tata ta ce da su. "Ku kashe mini shi; sannan ku kwace duk wani ƙarfi da yake da shi, yau zan kawo ƙarshen ka dama ka hanani sukoni." A haukace suka dinga sa kibiyoyi a jikin kwari da baka mai ɗauke da wuta suka dinga yi wa Sayyid ruwan ta; Ayan ya murza zoben hannunsa kafin kibiyoyi su iso hasken ya musu rufa, suna isowa sai kawai suak tsaya cak ba su iso kansu ba... Janu ta cika da ɓakin ciki ta ɗaga hannu saba sai ha takobi ta bayyana a hannunta; nuna Sayyid ta yi ta ce. "Idan ka isa ka fito mu gwabza ni da kai ba tare da yaranka ba ko wasu tawaga." Murmushi ya mata ya juya takobin hannunsa ya ce. "Dama ke kika ɓata wa kanki lokaci; ni nafi ƙarfi wannan ƙananun yaran naki " Wani irin kallo ta masa ya fito fili itama ta fita ; a tare suak yo kan juna kowa da haushin ɗan'uwansa suka haɗe a guri ɗaya. Yaƙi suke ba ji ba gani kafin wani lokaci tuni Sayyid ya soma jikatar da Janu da ƙyar take kare kanta; Iman ba huci ganin Baban nasu yaƙi kashe Janu ta rufe idanunta, wani irin ɓakin hayaƙi ne ya bayyana a cikin idanunta ta na buɗe wa suka fita zuwa kan janu. Yana isa ya shige jikinta ta yi wata irin kururuwa ta zube a ƙasa, Iyan ya fito ya iso inda suke ya ɗaga takobin ya sara mata ta kuma kurma ihu azaba, a fusa ce ya ce. "Shin za ki rabu da Mamana ko sai na aika ki can ne?" Duk da raɗaɗin azabar da take ji hakan bai hana ta mayar wa da Ayan martani ba. "Yaro koma baya da ubanka nake yi ba kai ba." Sake kai mata suka ya yi ta kuma yin kururuwa dajin na amsa-koyawar muryarta, ta na wani irin huci ta ce. "Kar ka kasheni Ayan ita ɗin fa an sadaukar mini da jininta, dan haka ka rabu dani ku yi rayuwarku ni ku bani ita na rabu daku; ina son shan jininta dan yana da garɗi sosai. Idan za ka bar mini ita zan kirkiro maka wata sabuwar uwar mai kama da ita sak sai ka bani ita z.. Ba ta ƙarasa maganar ba Iman ta daka tsalle ta fille mata dogon hannunta; cikin azaba da zafi ta juyo ta kalli Iman ta na numfashi da ƙyar ta ce. "Karki kasheni zan baki ƙarfin tsafina ki ƙara ƙarfi, wannan uwar taki an bani ita." Wani irin juyi Iman ta yi ta watsa hannun ta a kan Janu sai ga sarƙar dake hannun Janu ta daure Janu gam-gam... "Na haƙura da ita ku rabu da ni zan tafi na barta har abada ba zan, zan baku komai nawa ni duka yankin ma zan bar muku na koma yankin da ba kowa na zauna. "Janu ta faɗa a gakabaice ta na roƙon Iman dake murza zoben hannunta ta na ƙara matse Janu, duk inda sarƙar ta kwance sai ta zuba mata wata irin azaba mai raɗaɗi." "Kin yi ƙarya wallahi ki tafi ba tare da kin warware sihirin da kika yi wa Mama ba; kuma shi wanda ya sadaukar miki da itan ba kin kashe shi ba? Saboda zalinci irin naki iyayenta sun sadaukar da kansu dan ki bar musu ɗiyarsu ta rayu; sai kika yarda amma daga baya kika dinga bin ta kina shan jinin jikinta ke muguwa, to yau ƙarshen ki ya zo Ayan ka fille mata hannun ɗaya "Ta ƙarashe maganar ta na mai bai wa Ayan umarni da ya aiwatar da abin ta saka shi ya yi." Kafin ta juyo ga Ayan buɗe bakinsa wani irin hayaƙi Green ya fito daga bakinsa ya sauka a kan hannun sai ga shi a ƙasa... "Waiyo! Waiyo! Ku rabu dani ba zan sake ba kar ki kasheni ku taimaka. Haka take faɗa jin yadda ake yankar ko'ina na jikinta. Sake kai mata suka ya yi ta kurma wata irin kururuwa; birgima ta dinga yi ta na kiran wani suna tak ai ta na ƙoƙarin tashi. Cikin mugun sauri Ayan ya caka mata takobi; ta dinga juyi ta na wuliliya zuwa can dajin ya ɗauki girgiza, wuta ce ta kama dajin gabaɗaya har da jikin Janu wutar na ci amma ana jin sautin muryar ta ta na roƙon su Ayan... Sai da suka ji ta daina maganar sannan Sayyid ya janyo Suhaima ya sa hannu ya zare mata wuƙar da Janu ya caka mata; kama su ya yi gabaɗaya suka ɓace a dajin.. Basu bayyana a ko'ina fa sai a cikin wani daji mai cike da furanni ga kukan tsintsaye; kan wani gado mai mugun kyau ya kwantar da ita. Ayan ya matso kusa da ita ganin yadda jini ke zuba ya dafe gurin yaan rufe idanunsa, can ya buɗe ya jikin ya raga zuba amma bai tsaya duka ba.. Tattaba jikinta ya yi yaji a sake ya rufe idanu ya ɗaura hannunsa akan saitin zuciyarta yaji ba ta bugawa, a tsorace ya buɗe idanunsa wanda suka koma ja ya dubi Sayyid ya ce. "Baba ta kashe Mama." Saurin ɗauko ta Sayyid ya yi yana tattaba amma sam ba ta motsi.. Wani irin ƙara Ayan ya yi ya kwanta a kan Suhaima cikin tashin hankali ya ce. "Mama kada ki mutu ki barmu muna sonki, Mama! Ya faɗa cikin tashin hankali... *mai ke faruwa da Suhaimar Sayyid?😢* _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/14 22:54] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 1️⃣1️⃣ Lumshe idanu Sayyid ya yi tare da kai hannunsa saitin zuciyarta; danna ƙirjinta ya yi da ƙarfi amma shuru, Iman da ta yi lamo kamar marayan da bai ci komai ta dubi Sayyid ta soma magana.. "Baba ka tashi Mama mana." Kafin ya yi magana ta ja dogon numfashi sai tari ya biyo baya; saurin canja suffarsu suka su duka suka dawo suffar mutane kamar yadda ta san su, gabaɗaya kan ta suka yo Ayan ya yi saurin kiran sunanta. "Mama ki tashi kasa ki tafi ki bar mu." Buɗe idanunta ta soma yi a hankali har ta buɗe tarr; ta juyo jin hannunta a cikin wani lallausan hannu ta kalli hannun sai ta ga nashi ne, yunƙurin tashi ya soma yi Sayyid ya ɗago da ita ya zaunar duk sai jera mata sannu suke. Hannu ta kai kan gefen cikinta wanda zuwa yanzu jinin ya daina zuba, da sauri ta kalle su ta ce. "Dama ba ciwo naji ba yanzu?" Ta faɗi maganar ta na kallon su kamar ta samu TV; gyara mata zaman ya yi sannan ya ce. "Kin warke ne yanzu nasan bakya jin ciwon komai ko? "Cewar Sayyid yana shafa summar kanta; ita kuwa shuru ta yi jin wani sanyi na ratsa mata sassa jikinta, tunano abin da ya faru ta yi ba shiri ya zabura za ta tashi ya kalle ta. "Ya dai?" "Wannan muguwar tana raye kuwa?" Iman ta yi murmishi sannan ta cè. "Mama ai yau mun shafe tarihin rayuwarta, daga yau kin daina jin tsoron yin bacci ko fita wani guri." Sororo take kallon Iman har za ta yi magana sai kuma ta fasa mata ta juyo kan Sayyid. "Sayyid wai dama kaine baban su Ayan shi ya sa suke ce mini Mama?" Gyaɗa mata kai ya yi yana murmishi; ita kuwa ta ƙura masa idanu tuna matsayin su Iman yasa ta kuma faɗin. "To dama ka yi aure ne? Kuma ina mahaifiyar su Ayan take ne?" Kallon ta ya yi da kyau sannan ya ce. "To ai 'ya'yanmu ne ni da ke." A zabure ta kalleshi jin amsar da ya ba ta, cike da mamaki ta ce. "Ni kuma? E to tun da naka ne ai ni ma sun zama nawa?" "Ba irin haka nake nufi ba Ummu; ina nufin ke matata ce. "Ya faɗa cike da tabbatar mata maganar tasa. Tamkar wata zautacciya haka take kallon Sayyid; murmishi ta yi ta ce. "Sayyid yaushe kuma muka fara wasa da kai? Ni fa rabona da na ganka an fi shekara goma lokacin fa tun muna yara ni da kai, amma sai ka ce wai ni matarka ce a wa ya ɗaura mana auren ne?" Jinjina kai ya yi yasan dama za a rina; kamu hannayenta ya yi cikin nuna so da ƙaunar da yake mata ya ce. "Kwarai kuwa ni mijinki ne Kakan ki ya bani ke tun ranar da kika zo duniya." Wani irin sarawa kan ta ya yi ta yi saurin runtse ido; wannan wacce irin kalma ce haka? Ita ɗin ce aka aurar tun tana jaririya anya ma da gaske Sayyid ɗinta yake? To in ko haka ne kenan yasan inda za ta ga ahalinta. Saurin buɗe ido ta yi ta ce. "To ka sanar dani a ina ahalin iyayena suke? Sannan taya ka aureni ban sani ba ina buƙatar jin haka Sayyid ka daure ka fitar dani daga cikin duhun da nake ciki." Sai da ya kamo hannunta ya murza a hankali sannan ya ce da ita. "Ni ba bil'adama bane kamar ke." Ƙuuuuu! Cikin Suhaima ya bada ta zaro idanu bakinta na rawa ta ce. "B..Ban gane ba? Kai ɗin ne ba mutum ba?" "Sosai ma ni ba bil'adama ba ne; kuma nasan kin san yaran nan suma ba bil'adama ba ne kamar ke, dukkanmu aljanu ne ba mutane ba kuma nine mijinki uban 'ya'yanki gasu nan Iman da Ayan." Luuu! Ta yi baya za ta faɗi ya taro ta ta dawo ta zauna; a ruɗe take kallon su nan da nan ta tuna su Umma, yanzu shi kenan dama dan su kawo ta yankin aljanu ne suka ɗauke ta? Shi kenan ba za ta sake ganin su Umma ba? Saurin dafe kai ta yi ta ce. "To amma taya ka zauna da kakana har ya ɗaura ma aure dani?" Gyara zama ya yi ya ce. "Kada ki tsorata dani Ummu; ki kwantar da hankalinki ba wanda zai sake cutar min da ke. Zan mayar dake gida bayan na ba ki labarin rayuwarki da kuma yadda aka yi aka mallaka wa Janu ke, ina so ki nutsu da kyau kiji wannan labarin." Cikin zaƙuwa ta ce. "To." "A can baya wasu shekaru da suka shuɗe; akwai wani gagarumin Boka mai suna Kata wanda yake a ƙasar Ghana a yankin Yamma. Boka Kata ya kasance yana aiki kamar yankan wuƙa, hakan yasa mutane bila'adadin suke ziyartar shi a kodayaushe, yana da alaƙa da aljannu kala-kala akwai mugaye, akwai masu saukin kai, akwai baƙaƙen aljannu. Akwai sheɗanun aljannu, akwai masu haɗa soyayya tsakanin mace da namiji. Ni na kasance ɗaya daga cikin wanda yake haɗa so koda kuwa namijin baya so sai na sa ya so budurwar, ko in macen ce ba ta so sai na cusa mata son saurayin nata dole ta so shi kamar ta cinyeshi.. Janu tana ɗaya daga cikin sheɗanun aljanu, duk wani aiki na kisa ita ce nakasa mutum, makanta, gurgunta,kurumta,hauka, sa mutum ya shiga duniya, sa mutum ya zama ɗan iska, mayar da mutanen kirki abin tausayi, waɗannan kaɗan daga cikin aikin Janu kenan.. Muna nan tare da Boka Kata sai kawai naga wata mace a cikin jeji ta na gudu; a wannan lokacin na sauko na tambayeta lafiya take gudu? Sai ta ce dani. "Abin bauta ya taimake ka ana so a kasheni ne zan shiga duniya." Jin haka sai ce da ita. "To zan taimake ki idan za ki bini inda nake." Ba ta musa min ba sai ta bini muka tashi gidan Boka Kata; koda muka je lokacin ya tashi daga aikin ganin ɓaki na gabatar masa da ita, ganin nine na kawo ta bai musa ba ya bata masauki... Haka yake kyautata mata ni kuma ganin Boka Kata ya samu abokiyar rayuwa sai na yi amfani da tsafina na haddasa a tsakaninsu; gari na waye wa yaje ya faɗa mata yana sonta amma shi dai Boka ne zata iya aurensa? A lokacin murmishi ta yi ta ce masa ita ma ai suna bauta wa wani gunki ne dake cikin wani teku, a dokar garin nasu idan har baku haihu da saurayinka ba kafin aure; to ba sai ace ba ka haihuwa daga ranar an sadaukar wa da sarkin garin kai, shi zai yi yadda yake so da kai, ko ya dinga amfani da kai har ƙarshen wayuwarka, Ko kuma ya mayar da kai baiwa. Ita kuma a garin nasu ta samu wannan matsalar; sun kai shekara suna tare da saurayinta amma ba ta samu ciki ba, dan haka aka miƙa wa sarki ita ya ce sai dai ta zama baiwarsa. Ita kuma taga ba za iya ba sai ta sulale cikin dare ta wata hanya dake cikin dakin da aka kaita ta gudu, har zuwa safiya ta na tafiya sai suka dinga binta ƙarshe dai ta samu ta tsira ta yo nan.. Ko da Boka Kata yaji labarin rayuwar wannan yarinya sai ya cika da mamaki; amma kuma sai ya aje gefe ya tambayi sunanta, ta ce da shi sunan ta Dudu.. A ranar mu muka ɗaura aurensu aka yi shagali da dare muma muka tafi yankin mu.. Haka suka ci gaba da rayuwa har ta samu ciki, Boka Kata ya cika da murna ganin shi ma zai samu wanda zai gaje shi; Suna ta rainon cikin, lokacin da ta kusa haihuwa sai ya kirani ya ce na duba mu gani me za a haifa masa.. Tsafi na aiwatar nan na gano Namiji ne a cikin matar tasa, ya kamu da murna jin abin da yake so ne. Wata rana sai ta haifi ɗanta namiji mai kama da ita; aka sha shagali ranar Janu ta yi wata tafiyar ba ta nan aka yi haihuwar amma na sanar mata komai . Boka ya sa wa ɗansa suna Damisa; wannan suna nima ya birgeni sosai har ita uwar yaron.. Haka ya dinga girma har ya zama cikakken saurayi; tun daga shi ba su sake haihuwa ba, yana fita farauta sai dare yake dawo ba. Da taimakon mu ya zama mai ƙarfin gaske amma sai dai shi baya son yin aikin Bokanci, idan Boka Kata na nuna masa yadda ake aikin Bokanci da kiran aljannu sai ya nuna baya so sài ya shiga jeji ya yi farauta.. Ana haka wata rana ina zaune cikin jejin da yake farauta sai na gansa da wata yarinya dauke da kwano a hannunta suna hira, sun jima suna hira inda take faɗa masa su a yankin Ethiopia suke garinsu yana da nisa ba mutane sosai a can inda suke, shi ya sa ma suka yo nan dajin na wajan Ghana suka zauna suna ci gaba da kiwon dabbobinsu, ina jinsu suka gama hira shima ya bata labarin shi sannan ya raka ta har kusa inda suak yada zango sannan ya dawo gida.. Wasa-wasa suka kalla soyayya nima na ƙara musu da ƙarfin son juna; a kwana a tashi Damisa ya ce ai shi fa ya ga wata yarinya yana so a aura masa ita... Sosai Boka Kata da Dudu suka cika murna jin ya yi maganar aure; bayan ya tafi ya kiramu ya faɗa yaronsa ya ga wata yana so a bincika daga ina ta zo.. Ni na faɗa masa labarin da ta ba wa Damisa, Boka Kata ya ce sai Janu ta dawo sai aje anemo masa auren ta. Haka kuwa aka yi sai da Janu ta dawo Boka ya sanar da ita, da farko ta so kar ayi auren sai Boka Kata ya tambaye ko da matsala ta ce babu. Amma dai yarinyar in ta gano uban mijin da za ta aura Boka ne za ta sa su gudu ita da Damisa; a lokacin da take bayanin na gane ƙarya take sai kawai na ce ta barsa ya yi auren, ba dan ta so ba ta bari Boka Kata da shi da Dudu da Damisa da ni da Janu da sauran tawaga muka tafi inda suka yada zango.. Muna zuwa muka nemi auren yarinya, sai Mahaifiyar yarinyar taƙi amincewa har sai da muka sa ta da ƙarfin tsafi ta amince da auren, nan ne aka faɗa mana sunanta Zaira, bamu dawo ba sai da aka daura auren aka bamu ita muka dawo gida... Tare suke zuwa farauta Zaira da Damisa, muna zamansu lafiya shi da ita.. Lokacin da ta gane uban mijinta Bokanci yake sai ta ce gaskiya mijinta ba zai yi Bokanci ba, Janu taji haushi sosai jin kalaman Zaira amma ta rabu da ita; haka ta dinga cusa wa Damisa kin yin Bokanci wato gadan babansa. Cikin ƙanƙanin lokaci Zaira ta samu ciki suna ta murna... Cikin nata girma kuma ba daina fita farauta a tare ba. Aikin Boka Kata ya soma ja baya babu mai zuwa neman a masa wani abu, a lokacin ne kuma na yi wata tafiya zuwa gurin dangina dake can wata nahiya; ya kira su Janu ya ce musu ya aka yi hakan take faruwa ne yanzu ba masu zuwa. Janu ta dube shi ta ce. "Matsawar ka na son aikin ka ya dawo yadda yake; to sai an zubar da jinin bil'adama." Jin haka sai Boka ya kamu da farin ciki ya ce da ita. "Ai samo bil'adama ba wahala zai yi ba ko yau zan kawo miki ku sha jini ku ci gaba da aiki." Janu ta ce. "Jinin wani naka muke so ba na kowa ba; ka sadaukar min da jinin ɗanka ko matarka ko cikin dake jikin matar ɗan ka, in yaso da mun sha jinin sai ta samu wani cikin." Jin haka sai Boka ya shiga tashin hankali dan yana mugun son abin da yake cikin Zaira ; dukkansu baya son daya daga cikinsu asha jininsa, ita kuwa Janu dariyar mugunta ta yi ta yi tafiyar ta ta na jadadda masa indai bai yi sadaukarwar nan ba to tabbas zai rasa komai.. Kullum haka za ta zo ta yi ta masa maganar sadaukarwar, shi kuwa Boka ya kasa sanar da ahalinsa wannan al'amarin.. Ganin yana ɓata mata lokaci Janu ta haɗa kai da wasu aljanu suka kwashe duk dukiyar Boka, riga basu bar masa ba duk suka kwashe, Boka na zuwa ya ga an kwashe komai cikin mamaki ya kira Janu ya tambaye ta me yake faruwa da shi ne. Buɗar bakinta sai ta ce ai masu buƙatar shan jini ne suka kwashe kayan ita kuma ba yanda za ta yi da su, hankalin Boka ya kuma tashi sosai.. A takaice dai Boka ya koma bashi da komai, shi kansa Damisa da Zaira idan suka fita basa kawo komai hakan yasa Boka ya nemi da Janu ya ce ya sadaukar da cikin jikin Zaira a dawo masa da jin daɗinsa, dama abin da take nema kenan ta ji daɗi sai ta ce suje indai zai yo alƙawarin sadaukarwar, sannan a kawo mata wasu mutane kamar uku ta sha jininsu, inyaso Zaira ta haihu sai a bata jariri ta sha jinin ,idan ya yi haka zai fi da yin suna a faɗin duniya duk wani ɗan iska da masu mulki za su san da shi kuma suke zuwa suna neman taimako gurinsa. Jin jawabin Janu sai Boka ya cika da murna, ya tura Aljannu da yake aika in haka ta taso su kamo mutane biyu; daret ya kaisa wata maƙabarta a nan tasa ya yi alƙawarin bayar da jinin abin da yake cikin Zaira, suka ɗaura wani ɓakin ƙyanle a jikin wani dutse suka rufe sannan suka dai. Aljannun da ya tura ba muso suka shiga duniya suka samu mutane biyu matafiya suka kawo su. Ita kaɗai ta shanye jinin mutane ukun kafin wani lokaci tuni ta dinga karkato da hankalin mutane kan Boka; nan da nan jin daɗin sa ya dawo.... Shi Boka abin da bai sani ba; Janu ta haɗa kai da wani ɓakin aljani wanda yawanci A MAƘABARTA yake zama, ta na zuwa tana karo sirrikan cutar da mutane da aljannu. Ana tsaka da wannan halin na dawo daga tafiyar da nayi, nan Boka yake faɗa min abin da suka yi da Janu. Sam na kasa yarda da wannan tsarin na Janu na ce masa kada ya kuskura ko da Zaira ta haihu a sadaukar da abin da ta haifa, to dama shima ba dan ya so ba ya bada sai ya ce taya zai kare abin da yake cikin Zaira ya tsira ko zai bata wani mutum ɗin a madadin abin da yake cikin Zaira? E na ce masa na ce zan same ta mu yi magana duk da ba wani shiri miki da ita ba saboda zalincin da take yi; nan yake sanar dani indai aka haifi mace ya yi alƙawarin zai aura min ita saboda yadda bake kyautata masa, naji matuƙar daɗi dan tuni na gano mace za a haifa sai ya miƙo min ɓakin zare; ya ce daga an haifi mace in sa mata wannan aure ni da ita an gama. Muna gama magana naje na same ta na sanar da ita komai.. Cikin ɓacin rai ta ce ba za ta taɓa yarda a canza mata ba dole jaririn da aka haifa za a bata , in kuma ba haka ba to za ta kunno masifa kala-kala wanda ni kaina ba zan iya dakatar da ita ba, faɗa muka yi sosai ta ita a kan jaririn cikin Zaira wanda su basu san me ake ciki ba.. Tun daga ranar Janu take gadin Zaira ta kuma sa ana bin ta duk inda za su je da Damisa, ni ma ina ta bibiyarsu dan sosai naji ina son abun da yake cikin nata.. .. Ranar Zaira ta tashi da nakuda, Janu na samun labari ta yi wa Boka kiran gaggawa ya zo. Bayan ya iso ta ce da shi ga Zaira ce za ta haihu dan haka ya zo suje inda za ta ƙaro masa ƙarfin tsafinsa, sanin ina biye da Zaira yasa Boka ya bi Janu suka wuce cikin Maƙabartar da suka yi alƙawari.. Cikin mamaki yake kallon ta ganin ta kawo sa maƙabarta; dariya ta dinga masa ta na nuna sa sai ga ɓakin aljani ya fito suka haɗu tare suna ta yi wa Boka dariya abin da ya firgita shi kenan, ganin abin nasu ba na ƙare wa bane ya ce da ita. "Me za mu yi a nan da kika kawoni? Ko nan ɗin ne inda za a ƙara mini ƙarfin tsafin nawa?" Tsayar da dariyar ta yi ta soma bashi amsa. "Boka kenan wai daka ɗauka da gaske tsafin ka za a ƙara wa ƙarfi? To ka yi kuskure dan yau karshen ka ya zo, ɓakin aljani ya faɗa min indai ina son burina ya cika to lalle sai na kashe ka zan samu cikar burina; kuma gashi na kawo ka nan.. "A MAƘABARTA NE ka min alƙawarin jinin jaririn ciki Zaira; sannan kuma A MAƘABARTA NE zan kashe ka na sha jininka na cinye naman jikinka, A MAƘABARTA NE lamarin ya fara dan haka dole A MAƘABARTA NE zan karɓi wannan mulki da nake nema shekaru ɗaruruwa. Ka ɗauka da wai ina tare da kai zan na yi ta ma aiki? To ba ka isa ba ina so ne dama ka cika lokacin da zan kawo ka nan shi ya sa nake tare da kai." Tun da ta soma magana Boka ya tsora ta sai yanzu ya yi da-na-sanin biyo ta da ya yi, kafin ma ya yi magana ta tsira masa takobi nan take ya mutu suka shanye jininsa ita da ɓakin aljani.. Bayan sun gama ta nufo gidan Boka dan ta kashe su... Ina tare da Zaira da Damisa da kuma Dudu matar Boka labari ya sameni. Sai dai kash kafin na yi wani yunƙuri sai ga Janu ta baiyana a nan, a lokacin kuma Zaira ta haifi ƴar mace wato ke kenan. Zabura Suhaima ta yi jikin na mugun rawa ta ce." "Sa..Sayyid!" Janyota ya yi jikinsa ya rungume ta tsam yana bubbuga bayanta, a nutse ya ce. "Ki nutsu na ƙarasa miki labarin." Tsayar da kukan ta yi; hakan yasa ya ci gaba da magana. "Faɗa sosai muka yi akan sai ta dauke ki ni kuma na hana ta, hakan yasa muka dinga yaƙi a tsakanin tawaga ta da tata tawagar. Hankalin Damisa ya tashi jin yadda ɗakin yake girgiza, hakan yasa suka fito da sauri Zaira na rungume da Jaririyarta suka bar gidan; tafiya suka dinga yi har suka iso wani gari suka tsaya a bakin gari.. Bayan na ci nasarar jikata Janu na bi bayan su Damisa na same su, nan na sanar da su komai suka tada hankalinsu na nuna musu zan kare ku. Mun shiga cikin Ghana da su Janu ta cin mana ta zo da baƙaƙen aljanu masu yawa. In taƙaice miki dai a nan suka kashe Iyayenki ni ma sun so su kasheni na samu nasarar dauke ki muka ɓace. Sai da na tsire musu na iso jikin wata bishiya na aje ki da jinin haihuwar ki a jikin ki, ganin wasu mata da miji suna tafiya sai na sa motarsu ta tsaya na saki kuka, nan suka ɗauke ki kafin su tafi na sa ɗiga miki wani farin abu wanda zai kare Janu ba za ta gano inda kike ba, ɓakin zaren nan na sa miki daga lokacin kika zama matata, sai da naga tafiyarsu sannan na tafi... Ita ko Janu can maƙabarta ta kai su Damisa suka yi ta cin naman su, sannan duka binne ƙasusuwansu A MAƘABARTAR. Amma duk da haka ta taso ruhinsu har kakanki ta soma amfani da su tana cutar da mutane... Ni kuma jinyar kaina na yi har na tsayin shekaru biyar, kuma har zuwa lokacin Janu ba ta gano inda kike ba, idan ina son ganinki sai na bari zuwa dare na ɗauke ki na kawo ki inda nake mu yi ta wasa, wani lokacin na zama yara mata kamar ke wani lokacin kuma na zama namiji.. Ana haka Janu ta gano kina a raye zuwan ki na farko Makaranta na haɗu dake muka ƙulla soyayya duk da kina yarinya ne ba ki san mai ake nufi da so ba; haka na tafi zuwa yankinmu sai kawai naga Janu ta jaki zuwa Maƙabarta na yi sautin tarwatsa hanyar na ɗauke ki, na koma mace na kaiki gida na baki abinci na kaiki wajan wasa, ganin iyayen naki na neman ki sai na aje ki a bakin maƙabartar hanyar da suke wuce wa suka ganki.. Tun daga ranar nake baki kariya, kina jaririya na ɗaura miki wannan ɓakin zare wanda da shi nake iya sarrafa tunaninki,sai na ɗauke ki mu bar yankin kar Janu ta kashe ki.. Kwalalo idanu Suhaima ta yi jin yadda yake bata wannan rikitaccan ahali nata masu zama da aljannu; kuka ta sa masa ta na ƙoƙarin kwace ruƙon da ya mata amma ta kasa, a ruɗe take faɗin .. "To amma me ya sa na daina ganin ka na tsayin shekaru tun ina da shekaru 14 na fasa haɗu wa da kai, zuwa yanzu kuwa ina da shekara 24 ko ma fi?" Ɗago da ita ya yi ya ce. "Janu ce ta yi nasara a kaina shi ya sa na kwanta jinya, nahiyar ma gabaɗaya na bari, lokacin da kike shekaru 12 to a lokacin har mun haifi Ayan da Iman su 'yan biyu ne na ɗauke su muka bar yankin. Sai bayan kin ƙara girma na fara basu izinin su zo su ganki saboda sun takura suna son ganin ki, ranar farko tsorats ki suka yi hakan yasa na musu faɗa sosai na ce musu suke zuwa a suffar mutane ba irin tamu suffar ba. Bayan na gama dawowa nan yankin duk na ga abin ya dinga faruwa dake, da kaina na taso ruhin iyayenki na haɗa ku a mafarki." Da sauri ta ce. "E ai na gansu sau uku ne, sai kuma shi Kakana na gansa sau biyu." "Wannan dai shi ne asalin ki kuma dama can Boka iyayensa sun jima da mutuwa sai shi kaɗai, dangin mahafiyarki kuwa sun tashi sun koma Kasar su Ethiopia can inda suke. Sai wannan lokutan ina yawo na gano inda suke kuma har yau suna son ganin ƴarsu." Shuru Suhaima ta yi sai kuma ta kalli Sayyid ta ce. "Kana nufin ka ce ni na haifi yaran nan? Kuma har yanzu ba ka musulunta ba?" Gyaɗa mata kai ya yi ya miƙe tsaye ya juya mata baya; cikin nuna tabbatar da maganar tasa ya ce. "E ban musulunta ba, kuma ina matuƙar ƙaunar ki fiye da tunanin kowa. Shi ya sa ma na kawo ki nan dan mu ci gaba da rayuwarmu mai daɗi kamar yadda muka saba a shekarun baya." Jiki na rawa ta kuma cewa. "To amma me ya sa ka sawa kanka sunan musulmai har da yaranka?" "Saboda ina son sunayen ne, ki saki jikin ki mu yi zaman mu a nan ki ci gaba da haifa mana yara mu tara su, sannan zan kaiki ki ga dangi mahaifiyarki." Jin abin da yake faɗa ta fashe da matsanancin kuka; sai kawai ji ta yi ya rungume ta yana shafa bayanta nan da nan jikinta ya yi sanyi amma ba ta daina kukan ba.. "Ni fa ban ga wani abin kuka ba a nan, nine dai mijinki kuma zan iya komai a kanki wadda take addabar rayuwarki na kawar da ita ni da yaranki, dan haka ki daina damuwa. Kuma na miki alƙawarin ba zan taɓa futo miki a suffar aljannu ba sai ta mutane, idan kina so ma zan je na nemi auren ki a inda aka riƙe ki a mana aure sai na saya miki gida a cikin gari mu zauna mu da yaranmu." Saboda tsabar tashin hankali ba ta ma san hular dake kanta ta faɗi ba sai da taji ya mayar mata yana lallaɓa ta, kalamai yake mata kunne yana saukar mata da hucin bakinsa. Ita kan taga ta kanta miji aljani yara aljannu, sai ka ce a garin gaɓa-gaba, taya ma tana mutum za ta auri aljani wannan ai haramun ne ko ita ba musulma ba ce ba za ta iya auren aljani ba; wani sabon kukan ta saki ta ce. "Sayyid ni dai ka rabu dani ka mayar dani gida, mu a addinin mu rahamun ne ka auri jinsin aljannu kana mutum; kai ko ba musulma ba ce ba za ta auri aljani ba ta na matsayin mutum.. Ka yi haƙuri ka rabu da rayuwata na zauna a cikin mutane ba zan iya rayuwa a nan ba." Ta faɗa cikin wani mugun tashin hankalin da yafi na baya, taya ma za ta Kubota daga hannun Sayyid da yake ikirarin ita matarsa ce wai har ma da yara? "Ba zan taɓa rabuwa dake ba, ke tawa ce ba mai rabamu muna tare. Ta tsinkayo muryarsa ta ziyarci dodon kunnenta; ta yi hanzarin tashi ya hana ta, duka take kai masa a ƙoƙarin ta na ya rabu da ita sai taji ya ce. "Wannan ai dukan soyayya ne kike min, hakan ya ƙara tabbatar mun kina matuƙar so na." Wani sabon kukan ta saki sai ya haɗa hannayensa ya tashi ta zauna; murmishi ya yi ya hura mata cikar bakinsa a fuska. Kallon shi ta yi ta na kuka suna haɗa idanu ta ji masifar son shi ta mamaye ta ,ji take kamar ta tsaga jikinsa ta shiga saboda yadda take ji, hannu ya buɗe mata ai kafin ya gama buɗe wa ma ta faɗa kansa ya mayar ya rufe yana wani kalar murmishi.. Murmishi Ayan ya yi duk da bai ji daɗin kalaman maman nasu ba da ta ce za ta barsu; amma ya ji daɗin yadda Baban nasa ya yi wa maman nasu, kallon su ya yi ya ce. "Baba ka rabu da Mama ta koma inda take so mana; za mu ke kai mata ziyara ai; tun da ta ce ba za ta iya zama a nan ba." Ɗaure fuska Sayyid ya yi ya kalli Ayan ya ce. Am so sorry my fans kwana biyu van yi post ba duk na yi busy ne, yau dai na fanshe muku two fage na muku a ɗaya. Ina matuƙar godiya da ƙaunar ku a gareni masoya Allah ya bar zumunci💞💞😘 _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/16 23:22] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 1️⃣2️⃣ "Babu inda zan sake bari ta tafi ba tare dani ba; in har kaga Ummu ta bar nan to ni da ita da ku be muka tafi wata nahiyar dan ci gaba da gudanar da rayuwarmu. Ba zan kuma yin sake Ummu ta ƙara tafiya ta barni ba, dama ba son zaman inda take nake yi ba duk da babu abin da suke mata na ɓacin rai." Tun da ya fara magana Ayan yake kallon shi cike da mamaki; ganin ran Baban nasu ya ɓaci a kan kalamansa sai ya sunkuyar da kai tare da ita gabansa ya soma basa haƙuri. "Ka yi haƙuri Baba kada ranka ya ɓaci a kan wannan ƴar maganar; naga Mama ta ce ba ta son zama a nan sai mu barta ta zaɓi inda take son zama indai muna so mu faranta mata rai Baba. Nasan kuma ta na sonka Baba ka yi haƙuri ka bar Mama ta koma inda aka riƙe ta." Jinjina kai ya yi bai ce komai ba; ganin haka yasa Iman matsowa ta tashi Ayan ta na murmishi ta ce. "Kaga ka rabu da su tun da dai Mama ta dawo garemu ai bamu da wata damuwa kuma; kawai dai mu yi ƙoƙarin faranta mata rai." Kallon ta Sayyid ya yi yana jinjina kai dan ba ƙaramin faranta masa rai ta yi ba da kalaman ta. "Iman ku tafi ku tono wannan kwalbar A MAƘABARTA wadda Janu ta binne ita da ɓakin aljani; in ba'a tone ba ko da Janu ta mutu to fa ku sani ruhinta ba zai taba barin mu , maza yanzu ku yi abin da na umarce ku." Ya yi magana yana nuna musu hanya; da sauri suka kalli juna Iman ta kama hannun Ayan suka ɓace a gurin. Dawo da kallon shi ya yi kanta ta yi luf a jikinsa idanunta a lumshe ka.ar mai bacci. "Ummuu...! Ya kira sunanta cikin wata kalar murya wadda ta sa Suhaima buɗe idanu ta kalle shi; murmishi ya sakar mata itama ta mayar masa da martani, magana ta fara cikin kasalalliyar murya. "Sayyid ɗina..! Ta ja sunan ta na yi masa wani irin kallon; ji take kamar ta shiga cikin jikina saboda wata zazzafar ƙaunar sa da ta mamaye kowacce kusurwa ta jikinta. Ajiyar ta sauke sannan ta ce. "Zan ci abinci." Fuskarta ya kamo cikin hannayensa masu matukar laushi; ya sumbaci kumatunta tare da mayar da ita jikinsa sannan ya ce. "Wani kala kike so?" Murya can ƙasa ta ce. "Tuwon shinkafa da miya nake so." Hannu ya ɗaga sama ya haɗe yatsunsa guda biyu ya ɓala su sai ga abinci ya bayyana a kan trey; tashin ta ya yi ya ce. "To gashi ki ci ki ƙoshi." Da sauri ta gyara zama ta sa hannu ta ɗauko loma ba bismillah ta soma cin abinci da sauri-sauri; shi kuwa sai wani kalar murmishi yake yana kallon yadda ɗan ƙaramin bakin bakinta yake motsawa wajan tauna abincin.. Tana gama wa ya nuna mata waya kyakyawar roba a gefen kular abinci ta kalle shi; gira ɗaya ya ɗage mata yana mata nuni da ta sa hannu. Ba muso ta sa hannun da kansa ya wanke mata hannu da baki duk ta na kallon shi ta na lumshe idanunta kamar wata ƴar ƙwaya; ganin bai ci ba ta ce. "Sayyid kai ba ka ci ba." "A'a ni na ƙoshi ai muje ki kwanta ki huta. Ya yi maganar yana miƙar da ita tsaye; kafin ta yi wani yunƙuri ya kai hannu ya rufe mata idanu. Ita dai ji kawai ta yi an ɗauke ta an rungume can kuma ta tsinkawo muryarsa yana magana. "Ummu to kwanta a nan." Ya yi maganar yana nuna mata wani makeken gado mai mugun kyau; tarr ta buɗe idanunta ta kalli gadon baki buɗe saboda mamaki ta ce. "Sayyid nan ɗin ina ne ka kawoni kuma? Ni fa ka mayar dani wajan su Umma inaso na zauna a can, ka taimaka ka mayar dani idan kuna son ganina sai ku zo ku ganni a kodayaushe ka ji." Ta yi maganar wasu zafafan hawaye zarya kan kuncinta ; ta ci gaba da magana. "Indai har da gaske sona ka barni na tafi gida; yanzu haka hankalin su Umma a tashe yake duk da an aje mai kama dani a ɗakin." Tun da ta fara magana yake kallon ta, ganin yadda take kuka da gaske sai ya ji zauna yana kallon ta fuskarsa cike da damuwa, hannunta ya kamo ta yi saurin buge nashi ta ƙudundune nata ta na faɗin. "Ni ka mayar dani wajan su Umma ba na son zama a nan; idan kuna so ku ganni ai ba sài kun kawoni nan ba." Murmishi ya yi ya shafa hannunsa duk da ba wani zafin dukan yaji ba ya ce. "Haba Ummu me ya sa kike gudun mu wai?" "Saboda babu aure a tsakanin mutum da aljan, sannan Addinin Musulunci ya haramta yin mu'amala ta aure tsakanin mutum da aljani, ina mai baka haƙuri da ka rabu da rayuwata ka samu wata a jinsin ku na aljanu ka aura, na san za ka samu wadda ma ta fini komai. Ni ma ka barni na zauna a cikin jinsi na, yaran kuma da muka haifa ni dai ban dauki cikìn kowa ba, amma na yarda ana haihuwa da jinsin ku. Kuna aurar jinsin bil'adama ku sadu da shi ta hanyar mafarki, wani lokacin ma zai ji kamar da gaske ne yana mu'amalar aurataiya da wani; amma da ya buɗe idanu sai yaga ba kowa kaima kuma nasan ta haka ka zo min har na samu ciki na haifa ma yaran nan. Ka daure ka sadaukar da soyayyar da kake mini Sayyid ka mayar dani cikin yan'uwana mutane na zauna, kuma ina fatan ko ba yanzu ba ka musulunta kafin mutuwar ka ta zo gareka.." Wani irin ƙyarma jikin Sayyid ya ɗauka, idan ta furta kalmar ya rabu da ita sai ya ji tamkar ana zare masa zuciyarsa ne, lumshe idanu ya yi jin yadda jikinsa yake ƙoƙarin canza wa zuwa asalinsa na aljani; ya yi saurin saita nutsuwar shi ya kalle ta cikin tsananin tashin hankalin rabuwar da take cewa ya yi da ita.. "Ummu!.. Yanzu in na rabu da ke wa zan samu wadda zan so ta kamar yadda nake matuƙar son ki?" Da sauri ta ce. "Za ka samu kai dai ka yi haƙuri ka rabu da rayuwata, idan su Ayan sun so ganina sai su zo. Ni kan rahamun ne a gareni na zauna da kai,naso ace ka fito a jinsin matane amma kuma ba yadda na iya dole mu rabu... Mamaki sosai ya kama Sayyid ganin fa da gaske Suhaima ta dawo cikin haiyacinta, ya rasa ma taya aka yi abin da ya mata ya sake ta cikin ƙanƙanin lokaci haka? Girgiza kai ya yi yana tunanin in har yana so ta yi farinciki to gara ya barta kawai ta koma inda ta taso.. "Ummu naji zan rabu da ke amma ba dan na so hakan ba, ina sonki fiye da komai na duniya." Da sauri ta kalle shi baki na rawa ta ce. "D.. Da gaske Sayyid ka haƙura za ka barni na yi rayuwata ba tare da ka takura mini ba?" Jinjina mata kai ya yi alamar tabbatarwa ya ce da ita. "E na barki ki yi rayuwarki a cikin jinsin ki saboda son da nake miki zan sadaukar da ke miƙo min hannunki na cire miki wannan zaren da na ɗaura miki." Ya yi maganar yana miƙa mata nasa hannun; ba ta musa ba ta miƙa masa ranta fes. Tsintsiyar hannunta ya dan danna sai ga zaren ya bayyana, sosai Suhaima ta cika da al'ajabin wannan zare, tana cewa ashe dama tun tana jaririya zaren nan na cikin jikinta ba ta sani? Tab lalle aljannu lamarin ku na daban ne. Ta na wannan tunanin ya cire zaren yana kallon cikin idanunta ya ce. "Ga su Ayan nan za su mayar dake su dawo min da mai hidima na." Jinjina masa kai ta yi ransa ya yi sanyi haka ma jikinta, ta na jinjina irin son da Sayyid ɗin yake mata sai yanzu ta tabbatar da gasken-gaske yake son ta ba dan ya cutar da ita ba, inda wani ne da har abada ita da ta ga jinsin mutane har ƙarshen rayuwarta zai aje ta a nan ya tsafe ta, ƙila ma ƙarshe ya mayar da ita rabi mutum rabi aljana, amma gashi shi yaji tausayin ta ya ce zai mayar da ita gida.. A sanyaye ta ce. "Sayyid ka yi haƙuri na so ace a mutum ka zo da babu abin da zai hana na aure ka, in kaga ba mu yi aure ba to wani ikon Allah ne ya hana mu zama ma'aurata." "Babu komai ai na fahimce ki, sannan da kin shirya zan kaiki ki ga dangin mahaifiyarki. Ga wannan da kin shirya ki murza ta za ki ga Ayan da Iman sun zo gareki." Ya yi maganar tare da miƙa mata zobe ruwan gwal; amsa ta yi ta sa ta na murmishi ta masa godiya sannan ta ce. "Ina ƙara jadadda maka in har kaji kana son shiga addinin musulunci kai da yaran nan to zan fi kowa jin daɗin hakan." "Ummu zan yi tunaniin gani ko zan shiga. Ya ba ta amsa a sanyaye kamar wani mutum. Murmishi ta yi ta na kallon zoben ta ce. "Sayyid shi addinin Musulunci ba a shigarsa ba tare da an ji ana son za a shiga ba, ka shiga addinin Musulunci bisa raɗin kanka ba wai dan na maka maganar sa ba. Ka ji a ranka cewa ka yi imani da Allah ka kuma ji ƙaunar Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam sai ka amshi kalmar shahada, amma in ba ka wannan shauƙin guda biyu to kada ka shiga; ka bari har sai lokacin da ka ji zuciyarka ta aminta da su imani ya shige ka sannan ka amshi kalmar shahada." "To Ummu yanzu dai ba na jin hakan; amma Ayan ya soma jin hakan dan yana son ya ga musulmai suna ibada ya yi ta kallon su suna birgeshi; musamman idan suna karanta littafin nan." Ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi ta ce. "Shi ma ya bari ya yarda da wannan abubuwan sai ya amshi kalmar shahada, yanzu su zo su mayar dani gida." Bayyana Ayan da Iman suka yi yana riƙe da ita; kallon su Sayyid ya yi ya ce. "Ya ya dai? Ko kun samu matsala a hanya ne?" Rai a matuƙar ɓace Ayan ya ce. "Mun je za mu tone sai kawai tawagar Janu suka zo, shi ne muka yi ta faɗa karshe muka kashe su muka tone muka ƙona. Shi ne Iman ta jikata ɓakin aljani ya tare ta." A zafafe Sayyid ya ce. "Ina fatan dai kun kashe shi?" "Tun tuni ni na kashe mugu Baba yanzu itama za ta warke." Ya yi maganar yana ciro zoben hannunta ya ɗago da ita Suhaima ta yi saurin kamo ta ta riƙe ya ɗaura zoben a kan gurin sarar ya kawo haske. Nan da nan ya ɓace ciwon suka kira sunanta ta buɗe idanunta a kan Suhaima, kafin ma ta yi magana Sayyid ya musu bayanin komai ya basu umarni da su mayar da ita gida. Ba dan Iman ta so ba suka ɓace a gurin... Wani irin huci Sayyid ya dinga yi yana zagaya ɗakin, sosai yake jin ciwon rabuwa da Ummun sa amma ba yadda zai yi tun da farin cikinta yake so... A ɗakin Suhaima suka bayyana; wadda suka kawo a matsayin Suhaima suka tasa ta miƙe daga zaman da ta yi. Kanta a ƙasa ta ce. "Shugaba ai nasha ba za ku zo yanzu ba." Ayan ya ɗaure fuska ya ce. "Ina fatan dai ba ki bada ƙofar da aka gane ba Mama ba?" "E ban bada ba; yanzu ma na ce zan yi wanka ne na shigo dan haka ita sai ta shiga wankan mu mu wuce." Murmishi Suhaima ta yi ganin mai tsananin kama da ita sak ba wata maraba, miƙa mata towel ɗin ta yi ta kalle su ta ce. "Yaran Mama sai wata rana in na shirya za mu tafi ku kaini garin su Mamana." Iman ji take kamar ta zauna a wajan Suhaima amma ba haki, rungume su ta yi suka ɗauki lokaci sannan suka rabu, jin muryar Inna Laure suka yi saurin mata sallama suka ɓace... Shigo wa Inna Laure ta yi ta na riƙe da kwanon abinci ta harari Suhaima ta ce. "Kenan dama dan kar ki ci abincin nan shi ya sa kika ce wanka za ki yi? Kwana biyun nan duk bakya cin abinci ko wani abin kuma yake damun ki?" Murmishi Suhaima ta yi ta ce. "Kai Innata babu wani abu da yake damuna kawai dai na ƙoshi ne, yanzu na shige wanka in na fito zan ƙara ci." "Oho dai ke kika sani, idan na dawo ban ga kin ci abincin nan ba za ki sani ne." Ta na gama faɗin haka ta aje abincin ta wuce... Bayan ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa wadda ta amshi jikinta; tururuwa masu ƙamshi ta feshe jikinta da shi sannan ta fito zuwa palo.. A palon ta same su su duka har ma da Sani ya zo gidan, suna haɗa idanu ya ce. "To ci ba kama kenan, ya jikin naki?" Harara ta masa ta amsa masa ta na turo baki gaba. "Kai fa ka cika takura Yaya Sani, shi ya sa bana son ka zo gidan nan Wallahi." Dariya ya yi ta zauna aka ci gaba da hira, sosai suka ga fara'a kan fuskarta saɓanin kwana biyu zuwa uku da ta dinga daure fuska ta na kunshe kai a ɗaki... Tun da Suhaima ta dawo ta kasa nutsuwa, sam ba ta son ta sanar da su Umma wannan labarin amma kuma ya ta iya? Dole ta faɗa musu dan su san ta tafiyar tata ko za a samu wanda zai mata rakiya.. Yau suna hira ta gyara zama ta basu labarin duk abin da yake faru da ita, da tarihin asalin ta da na mahaifiyarta babu abin da ta ɓoye musu har auren ta da Sayyid da rabuwar da ya yi da ita da yaran suka haifa kaf ta haɗa ta musu bayanin komai... Inna Laure ta kwalalo idanu waje ta na kallon Suhaima ai kuwa Suhaila ta kwashe da dariya... "Ƴar Innarta aradun Allah kin yiƙoƙari da ba ki mutu ba; Haba inda ni ce tuni zawo zan dinga yi har mala'ika ya iso gareni." Inna Laure ke maganar ta na zare idanu ta kara da cewa. "Alkur'anin Allah yau ba zan kwana a ɗakinki ba, na je ina bacci sai dai na ji ni a sama ina yawo." Dariya suka yi Suhaila har da riƙe ciki haka dai suka gama hirar . Sai da za'a tashi Abba ya ce mata duka gabaɗaya za su tafi amma a jirgi ta faɗa wa Sayyid ko su Ayan ya bisu a jirgi, to ta faɗa ta na fatan su amince da wannan buƙatar.. Ta na kwanciya Inna Laure ta zo ta kwashe kayan baccin ta da gudu ta bar ɗakin, Suhaima ta dinga dariya.. Ba ta jima ba sai ga Ayan ya zo ya sheda mata ya ji maganar da suke ɗazu kuma Babansu ya amince su tafi a jirgin.. Cikin kwana biyu Abba ya samo musu ticket ɗin jirgin da zai je Ethiopia.. Washegari suna zaune sai ga Iyan da Iman da Sayyid cikin shigar ta alfarma, basu canja kama ba a yadda Suhaima ta sansu a halittun mutane a haka suka zo dan su faranta mata rai, ai ko Suhaima ta ji daɗi sosai.. Suna isa airport jirginsu na isowa ɓata lokaci suka shiga ya ɗaga zuwa Ethiopia..... Sai wuraren ƙarfe 2 suka sauka a Ethiopia, daga nan Sayyid ya yi gaba ya ce su biyo shi ba muso suka bisa baya.. Su Inna Laure an yi tsit ko tari ta ji riƙe kayanta take ba wanda ta yarda ya kalle tsakanin Ayan da Iman har Sayyid ɗin ma, wani mugun tsoro take ji wai yau ita ce tare da aljanu suke tafiya? Kuma gasu nan kamar mutane sak, sai yau ta ƙara tabbatarwa da maganar da ake cewa aljani babu irin suffar da ba zai fito ba in yaga dama... Suna yin nisa Sayyid ya ce kowa ya rufe idanunsa; cikin Inna Laure ya bada ƙuuuuu! Ta yi saurin dafe cikin ta damƙi hannun Abba ta maƙale a bayansa, wai in ko tashi sama za su yi to fa ita tana jikin ɗan'uwanta.. A wani gari suka bayyana bakin wata ƙofar gida, izini Sayyid ya basu ya ce su buɗe idanunsu, ba muso suka buɗe. Suhaima ta ƙagara ta ga dangin mahafiyarta sai kuka take ƙasa-ƙasa. Wani mutum ya fito daga gidan mai tsananin kama da Suhaima yana ganin Sayyid ya yi murmishi ya iso tare da cewa. "A'a Malam kaine? Sannun ku da zuwa." Inna Laure tana rakube a bayan Abba a hankali ta ce. "Tab da kaina waye da ba ka bashi hannu ba." Sarai Sayyid ya jita ya miƙa wa mutumin hannu ya ce. "Dama na faɗa muku zan dawo to gani dai na kawo muku ƴar Zaira har gida." Ya yi maganar yana nuna Suhaima dake tsaye tana goge hawaye. Waro idanu mutumin ya yi yana faɗin. "Ikon Allah sak Zaira ɗin mu,zo nan yarinya kuma ku biyoni muje ciki." Ya yi maganar cikin tsananin farin ciki; Suhaima ta iso gabansa ya rungume ta yana faɗin kamr an tsaga kara da Zaira, hannunta ya kama suka sa kai cikin gidan yaan kwaɗawa 'yan gidan kira.." _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [3/18 20:14] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 1️⃣3️⃣ Gabaɗaya mutanen gidan duk suka fito jin yadda yake kiran kowa da sunansa; wata tsohuwa ta iso ta na gyara mayafin kanta ta ce. "Kai ko Sulaiman ya kake kwarara mana k... Maganar tata ce ta maƙale sakamakon arbar da ta yi da Suhaima dake tsaye ta na kallon masu kamanni da ita sak, jiki na rawa ta nuna Suhaima da hannu har ta iso gaban Suhaima sai ta fashe da kuka. "Zaira ashe zan sake ganin ki a rayuwata? Allah sarki! Ina kika shiga duk tsayin shekarun nan Zaira?" Sosai Suhaima ke kuka jin yadda ake kiran sunan Mahafiyarta; abu ɗaya yake matuƙar saka ta damuwa a wannan gaɓar ,idan ta tuna iyayenta sun mutu ba tare da sun musulunta ba, shi ya sa take yi wa Sayyid da yaransu fatan Ubangiji yasa musu imani a zuciyarsu su ƙarbi kalmar shahada kafin mutuwa ta riske su.. Kamo hannun tsohuwar Suahaima ta yi ta ce. "Kaka ba ita ba ce ƴarta ce ni." Tsayar kukan nata ta yi ta ƙura wa Suhaima idanu ta na nazarin maganarta; sai da ta gama ƙare mata kallo ta gane wannan fuskar shekarunta ba su kai na Zaira ɗin ta ba, Jinjina kai ta yi ta ce. "Ku zo mu shiga ciki ." Ta yi maganar ta na jan Suhaima; sauran 'yan gidan kowa baki buɗe yake kallon Suhaima, ita kuwa jinta take kamar an cire mata wani nauyi da ya danne mata zuciya, duk da Su Umma sun zame mata bango majingina amma taji sanyin daɗi da taga masu kama da ita. Sau tari takan yi shuru ta dinga hasaso kamannin familyn gidansu; amma duk sai taga basa kama da juna ita kaɗai ta fita zakka a cikinsu, wani lokacin har Umma take tambaya shin ita me yasa ba ta kama da kowa a kaf familynsu. Idan ta faɗi haka Umma wayo take mata ta kawar da maganar ta kawo wata sai ta manta, amma yau dai gashi ta ga masu kama da ita sak wasu suna mugun kama wasu kuma kamar daidai misali, wasu kuma ta yanayin halitta ne suke kama da juna.. Cikin palon tsohuwar suka shiga dukkansu har 'yan gidan; Suna zama wanda ya shigo da su ya yi wa wata kyakyawar budurwa wadda take mugun kama da Suhaima magana da yarensu ta miƙe ta nufi wata hanya da saurin ta, ita kuwa Suhaima ƙurawa dangin nata idanu ta yi hawaye na bin kuncinta farinciki sosai take ta na aiyana a ranta ina ma ace mamanta na raye ta kwanta a jikinta ta ji ɗumin jikinta kamar yadda kowacce 'ya take ji . Ji ta yi ana goge mata hawayen dake kwaranya akan kyakyawar fuskarta; ta juyo sai ta ga Ayan ne yana girgiza mata kai, murmishi ta yi ta tsayar da kukan sai ga wannan budurwar tare da yara biyu sun shigo musu da nau'ikan abinci kala-kala sun dire musu a gabansu.. Sayyid ya miƙe tsaye yana kallon su ya ce. "Bari za mu fita waje ni da yaran nan idan kun gama za mu dawo." Da mamaki suka kalle shi tsohuwa ta ce. "Haba dai ɗan nan ai ka zauna ku ci abinci; ya za ka ɗauke yara ku fita waje bayan kun zo a gajiye?" Murmishi ya yi kawai, wani irin azabbaben son ummunsa ke masa yawo a cikin zuciyarsa har baya so ya daina kallon ta, amma kuma ba yadda ya iya dan ya riga da ya sadaukar da komai dan farin cikinta. Ranar da yasa su Ayan suka dawo da ita gida da ƙyar ya iya saita nutsuwarsa , yana jin in dai babu Ummu a kusa da shi to fa ya zama ba shi da amfani. Fita kawai ya yi su Iman suka bi bayansa da sauri,Suhaima na ganin haka ta tashi ta bi bayansu duk yan falon suka bisu da kallon mamaki.. Tsohuwa ta kasa daure wa ta ce. "Sulaiman wannan ko shi ne mijin na jikar tawa?" Ta yi maganar ta na miƙe ƙafafuwanta dan ta ji daɗin zama. "A'a Ummi wannan ba mijin jikar ki bane; ya taɓa zuwa gidan nan muka haɗu da shi nan yake sanar dani Zaira na da ɗiya zai kawo mana ita mu ganta, amma dai ban sani ba ko soyayya suke a tsakaninsu saboda yadda yake kallon ita ƴar tamu." Inna Laure ta gyaɗa cikin raɗa-raɗa ta ce. "Hmm ku dai a bar kaza cikin gashinta kar a fige ta labarin ya canja salo, da kun san waye wannan zankaɗeɗan mutumin da wannan yaran; da tuni kun suma aljannu ƙarara gasu nan kamar mutane mu dai Allah ya kaimu gida lafiya." Na'im na jinta ya girgiza kai yana murmishi; tsohuwa ta ce. "Allah sarki amma ko Allah ya masa albarka. " Ko da ta fita ba ta gansu ba a harabar gidan hakan ya tabbatar mata ƙila sun koma gida ne. "Ummu!.. Taji ya kira sunanta daga bayanta; juyo wa ta yi fuskarta a dame suka haɗa idanu sai ya bata tausayi, sosai ta hango soyayyar ta a cikin idanunsa a sanyaye ta ce. "Sayyid me ya sa ka fito wai? Kuma ina yaran suke ne?" Murmishi ya sakar mata sannan ya ce. "Kin san dai mu bama cin abincin ku ko? Shi yasa muka fito kar ace sai mun ci." Jinjina kai ta yi ta juya ta hango wata bishiyar Mangwaro dake harabar gidan ta kuma dawo da kallon ta kansa ta ce. "Ni ma na ƙoshi muje can mu zauna kafin su gama cin abincin." "A'a ba za ayi haka ba Ummu ki koma ki ci abinci da kun gama zan shigo har su Ayan ɗin. Kamar za ta masa kuka ta narke fuska, ji take ina ma ace Sayyid ɗin nata a matsayin jinsin ta ya fito da tafi kowa dacen miji kamilalle. Sai dai kash shi ɗin ba jinsin ta ba ne dole kuma ta rabu da shi, inda take ƙara jin tausayin shi in ta tuna yadda ya sha gwagwarmaya duk dan saboda son da yake mata ya bata kariya, ta na jin ƙaunar sa sai dai kuma shi ɗin ba mutum ba ne ballantana in bai ce yana sonta ba ita ta tunkare shi ta ce ina sonka wane, kukan zuci take ta na addu'ar Allah ya ba ta managarcin miji ko da kuwa wanda bai kai Sayyid ɗinta ba ya zama yana da nutsuwar Sayyid. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Kar fa ka tafi!" Ta yi maganar ta na goge hawayen da ba ta san dalilin zuwansu ba, ji kawai take babu lalle ta samu wanda zai mata zallar madarar so da ƙauna kamar Sayyid, in kuwa ta same shi to tabbas ita ɗin mai sa'a ce a duniya, ballantana ma da wahala ta samu mai son ta kamar shi ɗin, shi ya fara sonta fiye da komai nasa, duk da shi ba mutum ba ne amma ya iya nuna mata zallar so.. "Yi haƙuri Ummu kin ji! za ki samu wanda ya fini komai ma, za ki samu Ummana. Jinjina masa kai ta yi sannan ta juya ta koma ciki ya bita da kallo , sai da yaga shigewar ta ciki sannan ya isa inuwa ya samu kan wata kujera ya zauna... Ta na shiga ta same su duk sun yi shuru suna sauraron Tsohuwa da take musu godiya cikin kukan ta; a kusa da tsohuwar ta zauna ta na murmishi ta ce. "Kaka kukan me kike bayan Allah ya haɗa fuskokinmu kafin mutuwa?" "Kaiya ƴar nan ba dole na yi kuka ba; wannan mutanen arzikin masu zuciyar salihai nake yi wa addu'a da suka riƙe ki amana tamkar su suka haifeki, ina ƙara muku godiya Allah ya faranta muku duniya da lahira." Amin Suhaima ta ce ta na kallon su Umma da fuskokinsu yake ɗauke da murmishi, wani sanyi ta ji ya ratsa sassan jikinta yau dai gata ga masu kama da ita, ba iya mutum ɗaya ba duk kusan mutanen gidan suna kamanni da juna, murmishi ta yi ta tashi zaune ta dubi wadda suke tsananin kama ta ce. "Ya sunan ki?" Kallon ta yarinyar ta yi alamun ba ta san mai take cewa ba; Sulaiman ne ya yi ƴar dariya ya ce. "Suhaima Aminatu ba ta san Hausa ba, mu ne dai da yake muna fita zuwa Nigeria mun koyi Hausa sosai ba kamar su ba da ko gaisuwa basu sani ba da Hausa." Dariya Suhaima ta yi tsohuwa ta miƙe ta soma magana da yarensu,, gani kawai suka yi duk mutanen palon sun bar gurin itama ta juya za ta fice Suhaima ta kamo hannunta ta ce. "Kaka ina za ki je to?" "So nake ku ci abinci tukun sai mu dawo." Ok Suhaima ta ce sannan ta sake mata hannu ta wuce. "Anty yau dai kin ga masu kama dake ko?" Na'im ya faɗa yana murmishi. "Wallahi kuwa kaga wacce tafi kama dani amma dai ba ta jin Hausa, ko Uncle zai bamu ita sai mu tafi da ita ta koyi Hausa?" "To ni ina na sani ki bari in sun dawo ki tambaye. Shi kawai." Abincin suka ci sai yaba girkin suke; ita kuwa Suhaima farinciki ya hana ta ci abincin yadda ya kamata, da an jima sai ta ce. "Iko sai Allah! Ga dai masu kama dani." Dariya suke mata in ta faɗa har suka gama sannan 'yan gidan suka dawo aka ci gaba da hira, cikin hirar da suke ne Suhaima da take yin tambaya ta matso kusan Sulaiman ta ce. "Uncle a baya mamana ce a wajan su Kaka, ku lokacin kuna ina? Sannan a da su Kaka ba musulmai ba ne ina son sanin bayan kun bar mamana a wannan yankin me ya faru daku har lokacin da kuka musulunta?" Tsohuwa ta goge ƙwallar da ta zubo mata ta ɗaga kai ta kalli suma. "Lokacin da za mu tashi daga wannan yankin mun nemi gidan Zaira mun rasa, ƙarshe muka tafo ni da mijina muka bar ta a can. Dama tun farko akwai su Sulaiman lokacin da aka yi wani faɗa ne aka tayar da bom muka rabu da su, sai bayan mun dawo yankin namu muka samu an samu canji sosai wani mai kuɗi ya gyara mana garin nan a gidansa muka samu Sulaiman da Abubakar. Mun sha murna da ganin juna sannan mun basu labarin Ƙanwar su an mata aure amma mun rasa gidansu, sun sha kuka nan dai aka gyara mana gidanmu muka koma su kuma suka ci gaba da karatu. Kullum kukan rashin ƴarmu nake, wata rana dai muka yi ɓaki a gidan nan ashe su musulmai ne, a hankali suke nuna mana kyakyawar alaƙa irin ta musulmai har muka ji imanin shiga wannan addini mai ni'ima da nutsuwar zuciya; ba ɓata lokaci muka karɓi kalmar shahada. Wannan shi ne abin da ya faru, yanzu kuma alhamdu Lillahi komai ya wuce sai tarihi." Umma ta ce. "Allah sarki dama rayuwa haka take wata rana sai labari." Haka dai suka ci gaba da hira inda Umma ta ce gobe za su koma, Tsohuwa ta ce to abar musu Suhaima ta yi musu ko wata biyu ne su kara sanin juna. Ba dan Umma ta so ba ta ce to sannan suka tashi.. Sayyid dake zaune yana jiran su gama hirar sai jin muryar Suhaima ya yi ta na cewa, ita fa ba za ta iya wata tare da su Umma a kusa da ita ba kawai dai za ta yi sati ɗaya. Murmishi ya yi sai ya iso cikin palon ya ce shi zai koma gobe zai dawo su tafi da su Umma, Sulaiman ya ce a'a ya yi haƙuri kawai zuwa goben sai su tafi tare ya daure. Ba dan ya so ba ya amsa da to... Washegari su Umma suka bar Suhaima a cikin danginta cike da kewarta, ita kuwa har da kuka ta janyo su Iman ta rungume su a hankali ta ce da su. "Yaran Mama fatan za kuke ziyartata ba za kuke barina da kewa ba?" Gyaɗa mata kai suka yi Iman ta ce. "Mama za muke zuwa kullum muna hira dake, ki sani kodayaushe muna a tare dake da kin ji ki na son ganinmu to za ki ganmu. " Murmishi ta yi ta ce. "To shi kenan ku gaishe da babanku sai kun zo." Ta yi maganar ta na sakin su suka wuce suna ɗaga mata hannu. Tun da suka fara magana Sayyid na jinsu, jin ta ce su gaishe shi sai ya yi murmishi ya tsaya su kuma suka wuce dan yana son mata sallama.. Kallon shi ta yi ta na murmishi ta ce. "Sayyid to sai wani lokacin ina godiya da kulawar ka a gareni ina ma fatan samun mace mai hali irin naka." Ta yi maganar muryarta na rawa; jin ta na shirin masa kuka ya ce. " A'a Ummu kada ki yi kuka; kin san abin da nafi shiga damuwa to shi ne naji kina kuka ki shiga ciki da zarar ki na son ganina za ki ganni ina tare dake Ummu." Goge hawayen da ya zubo mata ta yi ta na murmishi ta ce. "Wai kai ma kana da zuciya kamar bil'adama." Dariya maganar ta ba shi sai ya yi murmishi ya ce. "Ummu kenan! Kamar yadda kuke jin zafi da raɗaɗi idan kun rabu da abin da kuke so; to haka muma muke ji fiye ma daku, muna da zuciya kamar yadda mutane suke da ita, muna jin sha'awar abubuwan da duk wani bil'adama yake ji, kawai mu mun fiku ƙarfi ne sannan halittarmu ba ɗaya ba ce da ku, amma muna jin duk abin da kuke ji ko ma in ce fiye da ku mutane. Ina jin ba daɗi da baki kasance jinsi na ba, amma kuma ba komai hakan ba zan iya goge ƙaunar da nake miki ba, ina sonki sosai Ummu musamman lokacin da kika haifa min su Ayan. A lokacin naji kin gama yi mini komai a rayuwa; kin bani yaran da nake ta son samu duk da ke a zahiri ba ganinsu kike ba sannan ba ki ɗauki cikinsu a fili ba." Murmishi kawai Suhaima ta yi in taji ya ce wai ta haifa masa su Ayan jin abin take ban-bara-kwai wai ita ce ta haifi yara biyu tun ba yau ba. "To sai wani lokacin. Taji sautin muryarsa yana mata sallama; hannu kawai ta ɗaga masa dan a wannan gaɓar ba za ta iya ce masa komai ba, duk da shi ba mutum ba ne amma ya iya magana mai daɗi komai nasa irin na mutane yake mata kamar shi ba wata halittar ba ce.. Ciki ta koma cike da tunanin maganganun Sayyid har bacci ya ɗauke ta... Sai dà Suhaima ta yi wata ɗaya sannan ta birkice ta ce kawai ita su Umma take son gani su mayar da ita.. Washegari sai kawai ganin Sayyid ta yi ya bayyana a ɗakinta ya ce ta haɗa kayanta ta fita ƙofar gida yana jiran ta ya mayar da ita gida; sake da baki take kallon sa duk da ba tsoro ya ba ta ba amma ya zo mata zuwan bazata, sai da ya ɓace ta janyo akwatinta ta fito ta na gyara zaman hijabinta ta ce Sayyid na waje yana jiran ta. Da mamaki Sulaiman ya dube ta ya ce. "Kai yarinyar nan! Yanzu yana waje ba ki sanar damu ba ya shigo ciki ko da ruwa ne ya sha sai ki barsa a waje." Murmushi Suhaima ta yi a ranta ta na cewa da kun san waye Sayyid ɗina da ba sai kun wahalar da kanku ba. Tsaraba ba kaɗan ba suka haɗa mata a nan ta dage sai an ba ta Aminatu sun tafi da ita; ita ko Aminatu sai murna take da aka ce mata za ta je Nigeria da Suhaima, da gudu ta ɗauko kayanta ko wanka ba ta yi ba ta ce su tafi. Dariya duk suka mata tsohuwa ta ce su tafi dan ta ga inda Suhaima take zama, haka dai suka fito har gurin Sayyid ya gaisa da yan gidan sannan suka wuce zuwa bakin hanya... Mota ya tara suka shiga zuwa cikin birni daret airport suka nufa, ita dai Aminatu sai kalle-kalle take yau dai gata a birni. Jirgin su ya sauka suka shiga ciki. Sayyid ya so kawai ya kai Suhaima gida cikin daƙiƙu kaɗan, amma ganin Aminatu sai ya haƙura suka zauna a jirgin.. Jirgin su na sauka suka samu Na'im ya zo ɗaukan su ya yi tsaye yana jiran zuwansu. Bai gansu ba su kuma sun gansa Suhaima ta saki Jakar hannunta ta nufi Na'im cikin jin dadin ganinsa.. Bai ankara ba sai taji an faɗo kansa ya juyo da sauri sai ya ga Suhaima ce, dariya ya yi ya ce. " Anty sannu da zuwa ku zo muje." Sayyid ya musu sallama ya fice suma suka nufi gida.. Suna zuwa aka dinga murnar zuwansu sosai Umma ta ji daɗin ganin Suhaima, da har ta shiga damuwa ganin sun ce ta zauna da su ta ɗauka amshe abarsu za su yi, sai gashi ta dawo har da ƙari ma suka mata na Aminatu... Cikin sauri ta shirya saboda ta yi latti; da sauri ta fito ta ɗauki tea a tsaye ta dinga sha ta na cusa bredi hannu baka hannu gwarya ta dinga yi har ta cinye ta wuce da sauri. Na'im ta samu a mota tare da Aminatu ta ce. "To fa! Yau kuma Aminatu za ka ɗauka ku shiga gari ko?" Dariya ya yi ya ce. "Kai Anty to ai so nake ta zama ƴar gari makarantar koyon Hausa zan saka ta." Murmishi kawai Suhaima ta yi suka wuce zuwa school... Bayan an tashi ta fito ta na tafiya a hankali saboda muguwar gajiyar da ta yi, dan yau sun sha darasi sosai. "Am Suhaima!. Ta ji an kira sunan ta cikin wata kalar murya mai daɗin sauraro; ta yi saurin juyo wa suka haɗa idanu ta ja da baya ta na zare idanu.. TAKU HAR KULLUM MAMAN NUSAIBA. [3/21 00:33] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ SADAUKARWA GA MUTANE BIYU: *AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)* *JIBRIL ADAMU RANO (Malam)* بسم الله الرحمن الرحيم 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 1️⃣4️⃣ Da mamaki yake kallon ta ganin yadda ta tsora daga yin arba da shi; riƙe baki ya yi ya soma magana cike da mamaki. "Suhaima! Ya kira sunan ta cikin wani irin yanayi; yadda ta zaro masa fararen idanunta ba ƙaramin tafiya da imaninsa ta yi ba. Baki na rawa ta ce. "Sa...Sayyiddd! Taja sunan cikin rikicewa haɗin da zallar tsoro bisa kan fuskarta, jikinta duk ya ɗauki rawa sai ta ƙura masa idanu ta na binsa da kallon ƙurulla. Shi kam harde hannayensa a ƙirji ya yi yana mamakin jin ta kirasa da Sayyid, to waye ma wani Sayyid da take haɗa sa da shi? Ya tambayi kansa yana ciza lips ɗinsa na ƙasa. "Waye kuma Sayyid Suhaima? Ya yi maganar yana waro nasa idanun. Jin abin da ya faɗa sai taji ta ɗan samu nutsuwa, sosai ta dinga mamaki ganin mai kama da suffar da Sayyid ke bayyana a gareta, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma ba shi haƙuri. "Yi haƙuri Malam; ka yi min kama da wani ne da na sani shi ya sa kaji na kira ka da haka." Ƙayataccan murmishi ya sakar mata sannan ya gyara tsayuwarsa cikin nutsuwa ya ce. "Am dama ina son mu yi wata magana ne; tun wancan satin nake ta neman inda zan ganki amma kuma Allah bai nufa ba, idan ba damuwa ban takura miki ba muje na kaiki gida." Sunkuyar kanta ta yi ta na wasa da gefen hijabinta, ji ta yi jikinta ya mutu murus har bakinta hakan yasa ta kasa ce masa komai. Ganin haka yasa shi ƙara yin magana. "Please Madam." Ya yi maganar yana yin gaba; ita kuwa ji kawai ta yi ta na binsa a baya har gurin motar. Suna zuwa ya buɗe mata gaba; a sanyaye ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, haka kawai taga ya cika mata idanu ya mugun yi mata kwarjini. Ba ta san lokacin da ya tayar da motar ba sai da taji suna tafiya; nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ya kalle ta tare da yin murmishi ya soma koro mata jawabi. "Am Suhaima tun ranar da na fara zuwa School ɗin nan na dinga jin matata na cikin wannan school ɗin; sai kuma gashi a hankali Allah ya haɗa mu can kwanaki muka bigi juna ni da ke, har kika fasa min waya kina ta bani haƙuri." Ya kalle ta fuskarsa cike da farin ciki ya kuma faɗar. "Ina zamu bi ne Gimbiya?" Tun da ya fara maganar ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta, yau dai gashi ta samu mai kama da Sayyid kuma ya furta mata kalmar so, lumshe udanu ta yi ta na tunano yadda Sayyid ke faɗa mataza ta samu wanda ma ya fishi komai; sai dai ta na da wahala a samu wanda yake mata son so kamar Sayyid ba ta gansa ba, kuma ba ma za ayi sa ba a cikin maza. Ajiyar zuciya ta sauke har yanzu zuciyarta ta ƙasa goge soyayyar Sayyid duk da shi ba mutum bane amma har ƙasan ranta take jinsa, saboda ya taimaka mata tun kafin ta zo duniya yake ɗawainiya da ita har ta zo ta zama mutum bai gajiya ba, kuskure ɗaya ya aikata a gareta; shi ne auren ta da ya yi har ta haifa masa jinsinsa wanda haramun ne aljani ya auri mutum. Wannan lefin ta kuma yafe masa shi saboda alkhairansa ya yi yawa a cikin rayuwarta, dan haka ba ta ganinsa a matsayin mugu dan ya aure ta wanda kakanta ne ya bada auren nata dan ta rayu a doron ƙasa ya yi haka. Ɗago kai ta yi ta dube sa a kunyace ta masa kwatancan gidansu, daga haka kasa cewa komai ta yi har suka iso. Hannu ta kai za ta buɗe ƙofar ya yi saurin kulle wa ta kalle shi da sauri, tamkar wani ya yaro ƙarami ya shagwaɓe fuska ya ce. "Please give me phone number sai mu ƙarasa maganar a waya, naga alama kunyata kike ji." Rufe fuska ta yi ta na murmishi ta miƙa masa hannu ya bata wayarsa ta sa masa sannan ta masa godiya ta fita a motar. Sai da ya ga ta shige cikin gida sannan ya juya kan motarsa ya koma inda ya fito... Ta na isa gida wanka ta fara yi ta ci abinci har zuwa lokacin Na'im da Aminatu basu dawo ba, ta na gama yin komai ta haye kan gado ta janyo waya ta shiga WhatsApp. Wata baƙuwar number ta ci karo da ita wadda bata Nigeria ba ce, da mamaki ta shiga cikin number ta tarar da voice yafi goma ta soma ɗaga wa, muryar Uncle Sulaiman taji yana ce mata sun yi kewarta ga Tsohuwa za ta mata magana... Wani farinciki ne ya mamaye zuciyarta ta dinga ɗaga saƙon ɗaya bayan ɗaya ta na mayar musu da amsa, bayan ta gama ta fita a number ta yi saving sai ta kuma ganin wata number an mata magana; da mamakin ta ta shiga ta ga an rubuta saƙo kamar haka. "Ummuna Uncle ɗin ki ya amshi number ki za ki ga ya yo miki magana, sannan ka su Iman nan za su kawo miki ziyara." Sake da baki Suhaima take ƙara karanta saƙon, tunani ta dinga yi to dama aljannu suna yin social media ne? Kenan yanzu sai ka iya yin friend da aljani ba ka sani ba a social media? Murna ta yi ganin ya kuma turo mata da wani saƙon. "Ummu kenan! Wai kina mamaki ne dan na miki magana a WhatsApp? To ki daina mamakin hakan dan duk abin da mutane suke muna shiga cikinsu mu yi mu'amala da su basu san me me mutane bane; muma muna yin social media ɗin nan za ki iya ɗaura abota da aljani ba ki sani ba Ummu, da haka wasu ke shiga jikin bil'adama in macuta ne su dinga cutar da mutum ayi ta zuwa Asibiti amma a ƙasa warke wa... Dariya Suhaima ta yi bayan ta gama karanta saƙon, wani abu ta tuna ta yi saurin danne voice ta soma masa magana. "Tab Wallahi Sayyid abin ya bani al'ajabi, a da in aka ce aljannu na yin social media sai nake ɗaukar abin a wasa; sai gashi na ga zahiri a wajan ka. Yawwa wai ni ko dama ina so na maka wata tambaya akan Uncle ɗina; shi wai me ya yi wa Janu ne ta kashe shi?" Ta na ƙarasa faɗar haka ta saki, tana cikin number taga ya ɗaga sai dai bai dawo mata amsa ba, sai can ya ce da ita ga su Iman nan za su zo mata da amsar. .Da murna ta amsa da to sannan ta sauka sai ga kira ya shigo, kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta yi shuru ba ta ce uffan ba. "Assalam alaikum Girmbiyata ina fatan kin shiga gida lafiya dai ko?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce masa. "Alhamdu Lillah fatan kaima haka ka isa lafiya." Murmishi mai sauti ya yi sannan ya ci gaba da magana. "Ni sanana Hamid dan cikin garin nan ne ni, har iyayena maganar gaskiya Suhaima ni ba da wasa na zo ba, ina so ki bani dama na gabatar da kaina a wajan su Baba sannan na turo da iyayena. Sunan Mahafina Alhaji Hamza na san ma za ki sanshi a garin nan ba ɓoyayye bane a kaf garin nan.." Waro idanu ta yi ta ce. "Minister kake nufi fa! "Kwarai shi dai. Ya ba ta amsa yana murmishi; jinjina kai ta yi kamar yana ganin ta ya yi ta roƙo ta bashi dama ya zo ta ce ba damuwa ya zo kawai. Sun jima suna hira sannan hira daga bisani suka yi sallama... Washegari bayan sallar Isha'i Suhaima na zaune ta ba duba takardu ta ji saukar wani abu, da sauri ta juyo sai ta yi arba da su Iman. Da sauri suka zo a tare suka rungume ta suna murnar ganin ta, ɗago da su ta yi ta ce. " A'a haka kuka koma?To ina Babanku yake?" Da sauri Iman ta ce. "Mama Baba ya ce yana gaishe da ke, sannan ya ce mu faɗa miki amsar tambayar ki." Gyara zama ta yi ta ce. "Ina ji Iman faɗa mini." "Abin da yasa Janu ta kashe Uncle Abdallah shi ne; wata rana ta zo ɗaukan ki sai ta samu ke da shi kuna zaune a palo, ta so shiga jikin ki shi kuma a lokacin ya kunna karatun littafin ku à TV ya ƙure volume, hakan yasa jikin Janu ya soma ƙone wa da ƙyar ta gudu ta bar gurin. To shi ne bayan ta yi jinyar kanta ta yi alƙawarin sai ta kashe shi har ke ɗin ba, to bayan ta kashe shi aka soma bincike a kan kisan ,ko kwana biyu ba'a yi ba ta sa duk kowa ya manta maganar kess ɗin aka manta da taya ma ya mutu. Wannan shi ne abin da yasa ta kashe shi." Goge hawaye ta yi ta ce. "Allah sarki Uncle; ta sanadina ya rasa ransa Allah ya maka rahama. Ta yi maganar ta na kallon Ayan da ya yi kikam kamar wani gunki, da mamaki ta ce. "Yarona lafiya yau duk naga ba ka yin fara'a?" Murmishi ya yi ya ce. "Mama ina Inna Laure take ne? So nake na ɗan tsorata ta." Itama dariyar ta yi ta ce. "A'a Ayan kar ka tsora min Innata kasa ta sheka kwananta bai ƙare ba." Murmishi ya yi suka ci gaba da hira anan yake faɗa musu haɗuwar ta da Hamid sak Babansu a suffarsa ta mutane, dukkansu suka ce ta amince kawai tun da yana sonta, bata musa ba ta amsa da to sannan suka tafi... Cikin kwanaki kaɗan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Suhaima da Hamid, hakan yasa ya faɗa wa mahaifinsa su zo nema masa auren ta, ko da suke zo Abba sai da ya kira Uncle Sulaiman dan dama tuni ya faɗa masa zuwan nasu, ta waya aka yi magana da shi ya ce ai ko mai Abba ya zartar aksn Suhaima to ba za su ce komai ba, dan haka komai yana garesa. Sosai Abba ya ji daɗi matuƙa da wannan karar da ahalin Suhaima suka masa ya ce ya bai wa Hamid auren Suhaima, hakan ya yi wa mai girma Minister daɗi aka sa biki wata ɗaya suka dawo gida da labari mai daɗi... Ranar Hamid da Suhaima kusan kwana suka yi suna hira farinciki ya hana su yin bacci a wannan ranar.. Lokaci yana ta tafiya biki na matsowa, aba saura sati ɗaya ɓakin sai ga su Uncle Sulaiman da dukkanin familynsu gabaɗaya babba da yaro ba wanda aka bari kowa ya zo, waɗanda ba su taɓa zuwa Nigeria ba suka matsa Aminatu sai ta kaisu sun ga gari, Na'im ya ɗauke su ya dinga jigila da su idan suka fita sai kusan Magariba suke dawowa gida, sosai suka ji daɗin Ƙasar.. Amarya ta sha lalle ɓaki da ja ta sha gyara sosai duk inda ta nufa sai ta baza ƙamshin ta take wuce wa. Misalin ƙarfe 2:pm aka ɗaura auren Suhaima Mukhtar da Hamid Minister Hamza akan sadaki naira dubu ɗari, layin gidan taf ya cika da mutane sosai daga abokan Mahaifin Hamid da na Abba da nasa shi kansa angon, Sani da Na'im ma sun gaiyato abokansu haka zalika su Uncle Sulaiman ma ba'a barsu a baya ba duk wasu abokan kasuwancinsu sai da suka gaiyato su ɗaurin aure, Inna Laure ma ba'a barta a baya ba itama duk yan ƙauyensu sai da ta gaiyato su har da 'yan matan gidansu duk ta haɗo kansu aka kawo su a mota... Kasancewar Suhaima ba ta da Ƙawaye daga ita sai Aminatu da Suhaila sai kuma friends na school da suka zo mata kowa sanye da anko, tana zaune ya kira ya ce an ɗaura aure ai kuwa ta fashe da kuka, shi kenan za ta bar su Umma ta koma wani guri... Bayan La'asar aka tafi gurin dinner party; sosai Hal ɗin ya cika sai ga amarya da anko sun shigo, haka aka rakosu har mazaunin su suka zauna aka soma gabatar da abin da ya tara su. Shuru Suhaima ta yi ta na kallon gefe da gefe can ta hango Sayyid da su Iman zaune a kan kujera suna ɗago mata hannu, wani sanyi ya ratsa ta ta musu alamar da su zo sai suka kalli Sayyid ya jinjina musu kai suka tashi.. Suna isowa ta rungume su suna tayata murna, Hamid ya dubi Suhaima ya ce. "Sweetheart waɗannan beautiful baby's ɗin fa? Ban taɓa ganinsu ba." Murmishi ta yi ta nuna masa inda Sayyid yake ta ce. "Kaga mahaifinsu can sun zo tayamu murna ne." Kallon inda Sayyid yake Hamid ya yi; saurin juyo wa ya yi ya kalli Suhaima ya ce. "To ai kama yake dani baban yaran." Ƴar dariya ta yi ta ce. "Ranar da muka fara haɗuwa shiyasa na firgita na ɗauka shine." "Ikon Allah! Ai kuwa zan so ki haɗani da shi mu gaisa. To Suhaima ta ce su Iman na gefenta a zaune; haka aka dinga shagali sai gaf da magriba aka tashi.. Washegari aka yi walima bayan sallar Isha'i aka kai amarya gidan iyayen ango dake J R.A. Bayan an yi mata nasiha, da murna dangin Hamid suka amshi Suhaima suka mata nasiha suma sannan aka kaita gidanta dake bayan gidan... Bayan an gama sayan baki ango ya raka amarya ya dawo ya kulle ko'ina sannan ya shigo ɗakin da take lulluɓe da mayafi sai zuba ƙamshi take, wani irin sanyin daɗi ya ziyarci zuciyarsa sakamakon yin arba da hannuwanta wanda suka sha lalle gwanin birgewa. Lumshe idanu ya yi jin shi yake yafi kowa sa'a da Allah ya mallaka masa Suhaima a matsayin mata, ƙarasowa ya yi kan gadon ya buɗe fuskar tata ya furta. "Tsaki ya tabbata ga Allah da ya yi wannan halittar." Murmishi ta yi; ya kamo fuskarta ya yi kissing ɗin ta a kumatu, wani irin yanayi suka ji a tare kowa ya lumshe idanu. Zuwa can ya umarce ta ta yo alwala, ba ta musa ba ta shige toilet shi ma ya nufi nasa ɗakin. Wanka ta ta yi ta canja kaya zuwa wasu riga da wando na bacci masu mugun kyau ta ɗaura hijabi ta zauna tana jiran zuwansa, ba ta jima ba sai gashi ya iso ya yi gaba ya tayar da iƙama suka gabatar da nafila su.. Bayan sun gama ya gabatar mata da gasasshiyar kaza, da kansa ya ciyar da ita ta ci ta ƙoshi ta na kan ciyarsa ya goge mata baki sannan shi ma ya ci, bayan ya gama ya ɗauke ta ya kaita toilet suka yo brush suka fito, kwantar da ita ya yi shi ma ya kwanta tare da janyo ta jikinsa ya mata masauki a kan ƙirjinsa. Tsuru Suhaima ta yi jikinta ya ɗauki rawa, hannu yasa yana shafa kanta a hankali yana rada mata magana a kunne har ya samu ta nutsu, blanket yaja musu ganin yadda take ja baya ya matse a jikinta ta sa masa kuka, kamar bai san ta na yi dan ya manta a ina yake... Washegari da kansa yake mata wanka da ruwan dumi ta na masa mita shi kuma yana lallaɓa ta, da ƙyar ta bari ya shirya ta ya kwantar da ita ya fita. Tea ya haɗo mata mai kauri ya shiga ɗakinsa ya fito da magani a hannunsa ya dawo. "Sweetheart tashi ki sha tea da magani." Ya yi maganar yana ɗago da ita, kuka tasa masa ta ce. "Ni ka sakeni mugu kawai." Danne dariyarsa ya yi ya lallaɓa ta tashi ya bata tea ɗin tasha ya bata magani, bayan ta shanye ya kwantar ya ita shima ya kwanta ya lallaɓa ta tana mita har bacci ya yi gaba da ita... Haka suka ci gaba da amarcinsu, Suhaima na ta yi wa Hamid taɓara shi kuma yana biye mata, ji yake kamar ya mayar da ita ciki saboda so da ƙauna. Tuni yan biki sun koma gida Aminatu ta ce ita fa taga gari ba inda za ta je haka suka barta; Inna Laure ma ta koma ƙauye haka ma yan Kaduna har Suhaila duk sun koma gida... Rayuwar Suhaima da Hamid ba'a cewa komai soyayya suke zuba wa madarar, wata irin kakkarfar soyayya ce ke ta guda a tsakaninsu ko wajan aiki ya tafi suna maƙale a waya har ya dawo... BAYAN WATA UKU Yau ta tashi ba lafiya cikin damuwa Hamid ya kira Family Doctor ɗinsu ya zo ya duba ta nan ya gano ciki a jikinta na wata biyu, murna a wajan wannan masoyan ba'a magana. Bayan sun gama murna Hamid ya tafi raka Doctor waje sai ga su Ayan sun iso. "Assalam alaikum Mama!. Suka faɗa a tare; Suhaima ta kalledu da sauri ta miƙe ta rungume su ta ce. "Kai gaskiya wannan rana ta yau ta musamman ce a gareni;tun da naji kun yi sallama jikina ya bani kun musulunta." "Kwarai ma kuwa Mama mum musulunta shi ne Baba ya ce mu zo mu miki albishi. Ayan ya faɗa yana murmishi, itama faɗa musu tayi tana da ciki suka tayata murna suan tsaka da hira sai ga Hamid ya shigo gidan. Da mamaki yake kallon su Ayan ya ce. "Beautiful yaushe kuka zo ban ga shigowar ku ba?" Iman ta matso kusa da shi ta gaishe shi ya amsa yana ɗago da ita ya zaunar. Suhaima ta gyara zama ta faɗa amsa cewa su Iman fa ba mutane bane, ta bashi labarin duk abin da ya faru da ita saboda yanzu Hamid ya zama komai nata ba za ta iya ɓoye masa komai nata ba.. Shuru ya yi yana jin gabansa na faɗu wa, wai tare suke da aljannu kuma wanda Suhaimarsa ta haifa. Jin bai ce komai ba idanun Suhaima ya cika da ƙwalla dama wannan ranar take tsoro,ba ta son faɗa masa wannan sirrin da in yaji ƙila ma ya ce zai rabu da ita. Kallon shi ta yi ta ce. "Ba ka ce komai ba Sweetheart." Kallon ta ya yi bai ce da ita komai ba, hakan yasa ta fashe da kuka ta rungume su Ayan ta ce. "Nasan dama in kaji wannan sirrin ba lalle ka yarda ka zauna dani ba, shi ya sa ma naƙi sanar da kai sai yanzu da suke zuwa yasa naga ya dace na faɗa ma a matsayinka na mijina uban abin da zan haifa nan gaba." Da sauri Hamid ya dawo inda take yasa hannu ya goge mata hawayen ya ce. "Haba Sweetheart kina tunanin dan wata jarabawa ta faru dake in kika faɗa min zan gujeki ne? Ai ko a gaske kika haifesu ba zan taɓa gudunki ba har abada, ina sonki saboda Allah ba dan wani abu ba su kuma ina murna da musuluntar da suka yi da babansu, za muso suke ziyartarmu in so samu ne ma kullum." Haɗa su ya yi ya rungume Suhaima ta dinga masa godiya, su kansu su Iman sun ji daɗi matuƙa. Ranar a nan suka wuni sai dare suka yi wa su Suhaima sallama suka wuce... Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin Suhaima na ƙara girma sosai take samun kulawa ta ko'ina... Yau Suhaima ta tashi da nakuda hankalin Hamid a tashe ya kaita Asibiti, sai kusan Azuhar ta haifi ɗanta namiji kyakyawa mai kama da ita, sosai aka sha murna zuwa dare aka sallame su suka nufi gida.. Kula ta musamman ake bai wa Suhaima da Babynta Hamid kuwa duk wani abokinsa sai da ya faɗa masa an masa haihuwa. Ranar suna yaro ya ci sunan Sayyid wannan abu ba ƙaramin faranta ran Suhaima ya yi ba, su Iman kuwa suna manne da Baby Sayyid cike da farinciki an yi wa babansu takwara. Haka aka yi suna aka watse Suhaima da babynta ta tafi zaman wanka. Sosai Sayyid ke girma yana ƙara wayo; watan ta biyu a gidansu sannan aka mayar da ita gidanta ranar taga soyayya kala-kala.. Sayyid na da wata biyar Suhaila ta haifi ƴar ta mace daɗi ya mamaye Suhaima. Tun ranar kwana biyar ta haɗa kayanta ta tasa Hamid gaba ta dinga masa kuka sai ya kaita Kaduna, ba dan ya so ba ya tarkata su ya kaita ya dawo cike da kewar matarsa sa yaronsa... Bayan an gama hidimar suna Na'im ya ce shi fa Aminatu yake so, wannan abu ya yi wa su Umma daɗi Abba da abokansa suka je nema masa aurenta, ba ɓata lokaci suka basu auren Aminatu. Sai bayan sun dawo Sani ya ce shi ma fa yaga wata a cikin dangin Suhaima mai suna Karimatu yana so. Abba dan murna har sai da ya yi sujjada bayan kwana biyu suka kuma komawa suka nema masa auren Karimatu aka basu, gabaɗaya wata biyu aka sa bikin.. Suhaima ta ji daɗi ganin dangin har biyu za su zo kusa da ita, tun ana saura sati ta haɗa kaya ta goya Sayyid suka tafi Ethiopia wajan biki... Sai da aka ģama biki da bayan kwana biyu kana Hamid yaje ya dawo da ita shi ma sai da ya mata zuwan bazata ta gansa.. Haka dai rayuwa ke ta tafiya wataran daɗi wataran akasin hakan.. BAYAN SHEKARA GOMA. A gajiye ta shigo palon ta yada zango akan kujera, yara hudu suka biyu uku maza ɗaya mace suna faɗin. "Oyoyo Mommy. Murmushi ta yi duk suka haye kanta ta ce. "Ku tashi mana Mimi ina yayanku yake ne har Daddyn naku ban ji motsin sa ba.. Kafin Mimi ta bayar da amsa sai busa taji an fito daga bayan labule aka soma faɗin. "Happy birthday to you! Happy birthday to you. Hamid ya iso ta rungume shi tana dariya, ta ce. "Thank you so much my love." Murmushi ya yi suka rabu aka kawo cake suak yanka ta fara ba wa Hamid kana Sayyid sai sauran yaran. Bayan an gama Hamid ya miƙa mata gift ta amsa tana dariya, tana buɗe wa taga wata ce sabuwa dal cikin farinciki ta rungume shi tana amsa godiya... Bayan an gama komai yaran suka wuce dakinsu, juyo wa ta yi ta kalle shi ta ce. "Ni fa na manta yau ne birthday na." Zai yi magana suka ji ana kwankwasa ƙofa, suak bada izini. Ayan ne da Iman suka shiga ciki shigar da kamala hannuwansu riƙe da ledodi, da murna suka tare su bayan sun gaisa suka miƙa wa Suhaima ledar Ayan ya ce. "Murnar ƙarin shekara Mama Allah ya ƙara lafiya da kwanciyar hankali." Amsa ta yi tana murmishi ta ga sarka ce mai kyau, ɗayar ledar kuma takalmi da jaka ne har da hijabai guda uku da material shi ma biyu. Cikin tsananin farin ciki ta rungume su tana musu godiya. Nan suke sanar mata babansu zai yi aure, sosai ta yi murna ta ce su gaishe shi shi ma Hamid ya ce su gaishe sa Sayyid suak amsa da to sannan suka fice.. Ɗaukan ta ya yi cak ta waro idanu ta ce. "Kai ba ka tunanin yaran nan su fito su ganmu a haka?" "Ni ba ruwana da su muje na miki wanka ki huta sai mu bi lafiyar gado. Dariya ta yi ta maƙale shi suka shige ɗaki.... TAMMAT BI HAMDULILLAH ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN NA *(A MAƘABARTA NE)* Allah ya yafe min kuskuren dana rubuta ya bani ladan abin da yake daidai.. Mu haɗu da ku a littafin FA'IMA bayan salla in sha Allah ni ce taku har kullum da koyaushe *Maman Nusaiba.*