[8/30/2020, 3:59 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 1* Ahankali yasanya hannu a handle ɗin ƙofan yamurɗa yashige, tana tsaye a gaban tanƙamemen gadonshi me tsananin kyau da burgewa, ganinsa ba ƙaramin tsorata ta yayi ba har batasan sanda tazaro ido waje ba tana kallon shi, shima ɗin ita yake kallo cike da mamakinta ganin yanda tafirgita lokaci ɗaya da ganin shigowar sa, hakan yasaka yatsaya yana kallonta na tsawon mintuna uku kafin yaɗauke kansa yaci gaba da takowa ciki cike da tafiyansa na ƙasaita, kai tsaye wajen gadon nasa yanufa ya'aje briefcase ɗin sa da rigan aikinsa asaman gadon, kana yataka yashige cikin toilet, tana ganin shigewan sa tasaki wani wawan ajiyan zuciya me ƙarfi har da sanya hannu tana dafe ƙirjinta, dasauri tanufi hanyan fita tafice, kai tsaye inda ɗakinta yake tanufa jikinta har yana rawa, sosai tatsorata da ganin da yayi mata, fatan ta ɗaya kar yaɗaura ayan tambaya a kanta, kuma ta gode Allah da be ganta tana wani abun ba da yau kashinta ya bushe. Kusan 20mint yaɗauka acikin toilet ɗin kafin yafito ɗaure da tawul a ƙugunsa, ɗaya kuma ya ɗaure sa saman kansa, jikinsa duk ruwa ke ɗiga, haka yaƙarisa tanƙamemen Mirror ɗin sa wanda aka cika gaban da kayan shafa kala da iri, zama yayi bayan da yawarware towul ɗin kansa yafara goge suman gashinsa da yake baƙinƙirin me yawan gaske, sai da yagama goyewa tas yabusar dashi kafin yasoma shafa wasu Expensive Lotions akan Black skin ɗin sa me kyan gaske, sai da yagama tas yagyara gashinsa yashafe shi da mayuka masu saka gashi ƙyalli da taushi, bayan ya gama tashi yayi yanufi wajen sip ɗin kayan sa yabuɗe yaciro wata farar riga me gajeren hannu da wuyan V, sai farar Three qweater me manyan aljihu, sai da yashirya tsaf yakoma gaban mirror yafesa tsadadden Parfumer's ɗin sa me daɗin ƙamshi, yaƙara kallon kansa ba ƙarya ya haɗu sosai duk da shi ɗin me kyau ne, wayoyinsa yaɗauka yafito palow yana tafiya yana dannawa har yaƙariso saman luntsuma-luntsuman kujerun yazauna, ya ɗan jima yana latsa wayan kafin ya'aje yaɗau remote yafara sanja channels, akan CCTV NEWS yatsayar yasoma kallon labaran da ake yi, shi ba kasafai yake kallon fina-finai ba, yafison kallon labarai ko wrestling, Ringing tone ɗin wayan sa ne yasaka shi ɗauke idanuwan sa akan plasma ɗin yamaida kan wayan, kallo ɗaya yayi ma wayan yaɗauke kansa yaci gaba da kallon shi, sai da akayi mishi 2missed call be ɗaga ba, ana 3 ɗin ne yasa hannu yaɗau wayan ganin dai ba fasa kira za'ayi ba, kuma sosai kiran yake damun sa, hakan yasaka yayanke shawaran yaɗauka "Ya dai?" Yafaɗa hakan cikin cool voice ɗin sa yana me jingina bayan sa da jikin kujeran, jin muryanta ya doki kunnunsa yasaka shi lumshe idanu yana buɗewa "My Ib da fatan ka isa gida lafiya?" Ataƙaice yace "lafiya". Shiru ne yagibta a tsakanin su, hakan yasaka shi sake lumshe idanu yana jiran tasake magana, itama daga ɓangaren ta so take yayi mata wata maganar ko da irin tambayar da tayi mishi ne, cikin sanyin murya tace "Dama na kiraka naji ko ka isa gida lafiya ne, sai anjima.." Be bari ta aje numfashi ba ma yakashe wayan yana ajewa yaci gaba da kallon sa, sai kuma yaƙara ɗauka yalatsa yanemo wata Number yakira "Kizo". Daga haka yakashe yasake ajewa, 3mint sai gata ta buɗo wani ƙofa ta shigo, ahankali tanufo sa taduƙa agaban sa tace "Gani Sir". Idanun sa akan t.v yace "Kihaɗa min tea kikawo min". "Tom". Tace dashi tana miƙewa dasauri tanufi hanyar kichen, har ta kama ƙofar zata buɗe taji muryan sa ya ratsa cikin kunnuwanta "Lubna". "Na'am Sir". Tace hakan lokacin da tajuyo tana kallon sa "Kibar shi kawai". Yana faɗan haka yamiƙe tare da wayoyinsa yanufi ɗakin sa, sai da taga shigewar sa tasaki ajiyan zuciya, shiru tayi tana tunani kana cike da sanyin jiki takoma inda tafito Be jima ba yafito riƙe da keeys ɗin mota, ya sauya shigan sa cikin wata Farar t.shirt me dogon hannu da zanen cat 🐈 agaban rigan, sai dogon wando pencil blue colour, ƙafansa da Combat kalan wandon da ratsin fari, yana saka wrist watch a hannun sa yabuɗe ƙofan yafice, directly compound ɗin gidan yanufa yanufi wajen da yake aje cars ɗin sa, acikin wata kyakkyawar farar Mota yashiga yaja slowsly yanufi bakin Gate, gateman na ganin shi yataso yabuɗe masa yafice, ahankali yake tafiyar hakan yasaka ya ɗau tsawon 30mint kafin yadangana ga wata tanƙamemen Gate, abuɗe yatarda Gate ɗin hakan yasaka yatura hancin motansa ciki, kai tsaye inda ake ajiye Motocin gidan yanufa yatsaya daidai setting wata Black cars, atare suka fito yayinda suka kalli juna suka sakar ma junan nasu murmushi, bayan ya rufe motan yataka yanufi wajen shi, tafawa suka yi suka cafke hannayen su "Ya Bro". "Manya-manya iyayen mu, sai yau zan ganka?". Cewar Sameer yana kallon sa da murmushi a face ɗin sa Ɗan shafa kansa yayi yace "Uhmm Bro kenan Bara ka gane bane, aiki ne yayi min yawa fa". "Na sani ai ba sai ka faɗa ba, ku da kuke manyan mu". Smile kawai Khalil yayi be ce komi ba "Ok muje ciki nima yanzu isowa ta kenan". Tare suka jera suka nufi hanyar da zai sada su da main Palow, Kai da ganin su kasan jini ɗaya ne su sabida tsananin kamannin su, sosai komi nasu yakasance ɗaya har ta da skin ɗin su, tsawo ne kaɗai Khalil yafi Sameer dashi, yayinda shi Sameer ɗin matsakaici ne kuma yana da ɗan ƙiba sosai. Suna shiga da sallama matar dake zaune saman sofa ta'amsa musu, kallo ɗaya zakayi mata katabbatar da ita ce mahaifiyarsu bcoz tsananin kamannin da suke da juna, sai dai ita fara ce sosai saɓanin su da suka biyo Mahaifinsu "Mom". Suka faɗa atare suna nufar inda take, Sameer har da ƙarawa da sauri yaje yayi Hugging ɗin ta yana sakar mata kiss a goshi, sannan yasami wuri gefenta yazauna yana ɗaukan Apple ɗin dake gaban ta cikin plate, sai da yagutsira yace "Mom Afternoon". Lokacin da shima Khalil yaƙaraso yazauna ɗaya side ɗinta suka saka ta atsakiya, atare tashafo kansu tana murmushi tace "Welcome My twinsies, nayi kewarku kwana biyu, musamman ma kai Autana". Taƙarisa maganar ta tana kallon Khalil da shima yakarkace kai yana kallonta, ƙara shafo kanshi tayi tana faɗin "Ya aiki?" "Alhmadulillah Mom". Sameer yace "Mom ni fa?" Kallon shi tayi, da ido tatambaye shi mene? "Naga kina kallon sa ne kina tambayansa banda Ni". "Oh to ai sai kajira nagama dashi ko? Ko kai ba Babba bane?". Ɓata fuska yayi yace "kullum haka kike cewa ai, dole sai kin nuna banbanci a tsakanin mu". "Kaima ai ban hanaka zuwa inda akafi sonka ba, sai kabari dai nagama tambayan Autana kafin nazo kanka". Murmushi yayi yace "Mom kenan, wanda kika damu dashi ɗin ma ba take yake yi ba, ina nan zaune ai zan ganku a rana". "Ee dai nasan haushi kake ji don nafi nuna masa kulawa".Cewar Mom tana dariya Lokacin ne Khalil yaɗago kansa daga latsa wayan da yafara yi, yakalli Sameer yaharare shi yana ɗauke kai, waro ido Sameer ɗin yayi yace "Mom harara na yake yi fa". Mom tace "to ai kaine kamatsa mishi Ni banga laifin shi ba ai". "Mom ni yunwa fa nake ji". Cewar Khalil yana langaɓe kai "Oh sorry My Son, bari insa akawo maka, me kake so?" "Mom koma menene kukayi zanci, bazan iya jiran adafa min wani ba". "Okey". Mom tace hakan tana ƙwala kiran ƴar aiki Sai da tazo tafaɗa mata tahaɗo ma Khalil abinci takawo masa nan, sannan takalli Sameer tace "Kai fa?" "No Mom.. ni sai da aka cika min ciki kafin nafito, kidai ji da wannan sanƙamemen da yaƙi aure yatsaya ɗaura ma mutane ɗawainiya". Mom tace "me kake ci na baka na zuba.. kuma wlh kadena takura masa ko yanzu nakora ka inda kafito". Dariya yayi yace "oh Mom wasa nake wlh, shi da ma yake da zuƙeƙiyar budurwa sai ma kin ganta Mom". Khalil da yake ɗan tsakuran abincin da aka kawo masa ɗago kanshi yayi yana kallon Sameer yace "Mom karki yarda da maganar sa wlh". "A'a bar Ni yafaɗa min, Ni da nakeson inga kayi aure? Kaji bani nasha inajin ka, aina take ne yarinyan?" "Uhmm awajen aikin su mana Mom, sai kin ganta ma Mom ta bala'in dacewa da ɗan naki, yanda tahaɗu haka tadace da sunan ta, Bilkisu me gadon zinare". Washe baki Mom tayi tace "masha Allah.. kace na kusa samun suruka kenan? To Allah yanuna min nidai wannan ranan". "Ameen Mom ai nima na ƙosa ranan tazo". "Son yaushe zaka kawo min ita naganta?" Ɓata fuska Khalil yayi yace "Mom nima ba wani sonta nake ba itace take sona". "To ai kaima a sannu zaka so ta karka damu kaji". Mom tafaɗi hakan tana shafa kanshi Dariya Sameer yayi yace "hmm Mom ke kin yarda dashi ko? Ni da nakama su suna zance, kullum kikaje fa office ɗin sa sai kin gansu tare". Buga abincin Khalil yayi saman table yamiƙe tsaye zai tafi, dasauri Mom tariƙe sa tana faɗin "Sorry son karka tafi, bari shi in kore sa". Juyawa tayi tana kallon Sameer har da ɗan ɗaure fuska tace "Kama hanya katafi". Dariya yayi yace "to Mom amma baki bani abinda yakawo ni ba". "Ok yanzu ne kasan da tambayana? Kaje sai anjima zan haɗa sai kazo ka amsar mata, tunda dama kaƙi kadawo da ita nan kai wahala yasama". Sameer yace "Mom to me zatazo tayi miki anan? Tunda acan ɗin ma ina kula da ita". "To kema Mom kibar masa matar sa mana, inace shi ɗin likita ne kuma yafiki sanin yanda zai kula da ita". Khalil yafaɗi hakan yana kai spoon bakin sa, sai kace bashi ne yayi maganar ba". Mom tace "rufe min baki, tun kafin a haife ku gaba ɗayan ku nake kula da masu ciki, koda shi likita ne bazai fini sanin yanda zai kula da ita ba, ku kanku babu wanda yataimake Ni lokacin da nake da cikin ku har sanda nahaife ku kuwa". "To fa Mom ke da ɗan gaban goshin naki kuma har kun soma ɓatawa?" Sameer yace hakan yana gumtse dariyan sa Atare suka banko mishi harara yayi saurin tashi yana sakin dariya, yayinda yaɗaga hannayen sa sama yana faɗin "Babu ruwana nayi nan". Yafice da sauri, duk kansu sai da suka murmusa kana sukaci gaba da ɗan taɓa hira a tsakanin su, duk da Khalil baya wani amsa mata wayansa kawai yake latsawa, be wani jima ba shima yayi mata sallama yatafi. [8/30/2020, 9:09 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 2* Ahankali yatura kan motan sa cikin gidan nashi, yaƙarisa parcking space yatsaya, yaɗau 3mint kafin yabuɗe motan yafito, tun sanda yatunkari Compound ɗin gidan yahango bayan ta tana zaune ƙarshen farandan, ga duk kan alamu bata ma san da shigowan sa ba, har zai wuce sai kuma yatsaya yana kallon ta duk da baya ganin face ɗin ta sai bayanta but yasan da akwai abinda ke damunta, shi mutum ne da yake saurin gane damuwar mutum, sau tari aɗan kwanakin nan yana ganin ta cikin wannan hali, sai dai yasan ba hurumin shi bane shiga abun da babu ruwansa, yanzun ma har yafara takawa zuwa wajenta sai kuma yaja yatsaya kana kuma yajuya yashige cikin Palon sa, dai-dai lokacin da ita kuma tasanya hannunta tagoge hawayen da suka zubo kan fuskarta, sosai in kakalle ta zaka hango tsantsan damuwa a tattare da ita, ahankali tamiƙe tanufi cikin gidan, direct kichen tanufa tafara aikin ta, ta ɗau tsawon minti 30 kafin tagama girkin tazuba cikin coolar taje tajera su kan dainning table dake cikin ƙayataccen palon, bayan ta gama tsayawa tayi awajen tayi shiru tana kallon ƙofan ɗakin sa, ta daɗe ahaka sai da taji idanunta sun cicciko da hawaye kafin taɗauke idanunta dasauri tanufi hanyan ɗakinta, akan gadon ta tafaɗa tasaki kuka me tsuma ran me sauraro, ita kaɗai tasan me ke damunta, kuma tasan babu wanda zai iya cire ta daga cikin matsalan da take ciki sai rabbi, domin ita kanta batasan ta ina zata fara aikin da aka sanya ta ba, sai da tayi kukan ta ma'ishi kafin tamiƙe tashige toilet dan ɗauro alwala. Tunda yashiga ɗakin sa yacire kayan jikinsa direct yashige toilet, ya ɗau tsawon lokaci kafin yafito, yasoma shirya wa cikin sauri, ƙananan kaya yasanya riga sky blue me gajeren hannu wanda tamatse masa Arms ɗin sa, kana yasaka Black trouser, sosai yayi kyau cikin shigan nasa, flate cover shoes yasaka baƙi yafito yanufi masallaci, da tazara sosai da inda gidan sa yake zuwa masallacin, bayan yayi sallan direct gida yanufa yashige ɗakin sa, wani ƙofa yabuɗe yashige, cikin ɗakin kamar Labrary yake, anan yake karatun sa yake duk wani bincike abinda yashafi aikinsa, akan Hill chair yazauna yajawo lapton ɗin sa dake saman table ɗin yabuɗe yasoma aikin sa. Wajen ƙarfe 06:00pm tafito daga ɗakin ta tanufi kan dainnig table ɗin, gani tayi babu abinda aka taɓa awajen, aran ta tunani take yi ko be dawo bane? Bata da masaniya, dan haka tayanke shawaran fita taduba motan da yafita da ita, koda tafita ta hangi motan yana nan a inda yake, ga kuma sauran nan da alama dai yana gidan, komawa tayi jiki a sanyaye tashige ɗakin ta, dama tafito da ninyan tagirka mishi abincin dare ne. Sai da yaji an kira sallan magriba kafin yatashi yafito, direct toilet yanufa yaɗauro alwala yafita masallaci, be dawo ba sai da akayi sallan isha'i, koda yashigo gidan kan dainning yanufa yazauna, yahaɗa ma kan sa Black tea yasha, bayan ya gama yaɗan ci abincin kaɗan yatashi yashige ɗaki, sai da yayi wanka yasanya sleeping dress yafeshe jikinsa da farpume's ɗin sa sannan yazauna gefen gado, briefcase ɗin sa dake ajiye asaman gadon yajawo yaciro wata Black Computer, buɗe wa yayi yasoma aiki, sai da ƙarfe 11:00pm yayi kafin yarufe yakwanta lokacin tuni dama barci yasoma cin ƙarfin sa, yana shafa addu'ar da yayi ko minti 5 be ƙara ba barci yatafi dashi. ......... ............ ......... Washe gari ƙarfe 07:00am Brr. Khalil yagama Shirin sa, yayi shigansa cikin suit black colour, ta cikin kuma white ne, ya sanya socks and black cover shoes, ya gyara gashin kansa sai ƙyalli yake yi gunun sha'awa, gaba ɗaya in banda ƙamshi babu abinda yake tashi ajikin sa, briafcase ɗin sa yaɗauka yafita da sauri ko kallon dainning ɗin da Lubna tagama jera masa break fast be yi ba yafice, ɗaya daga cikin motocin sa kalan sky blue yashiga yaja yafice bayan da Gateman yawangale masa Gate. Yana fita Lubna tafito daga cikin Toilet ɗaure da showel ajikin ta, kai tsaye inda kayanta yake a sif tanufa taciro wata baƙar doguwar riga me ƙyalƙyalin kwalliya tasaka, tana cikin shafa lotions bayan da tazauna gefen gadon ta taji wayanta yasoma Ringing, dasauri takalli wayan sai da gabanta yafaɗi ganin wanda ke kiran, jikinta na rawa taɗau wayan takara a kunne, bata kai ga cewa komai ba taji muryan sa yana faɗin "Da fatan kin aikata abinda muka saki?" Cikin rawan murya tace "Ban samu dama ba har yanzu". "Kina so kice min har yanzu babu wani ci gaba?" "Ee, har yanzu be bani.." Katse ta yayi cikin kakkausan murya yace "Kin san abinda zai biyo baya, karki manta Mahaifiyarki da ƙannin ki.." Sai kuma yakece da dariya "Uhmm kinsan sauran, kuma kinsan bazan tsaya jiranki har lokacin da time zai ƙure mana ba, dake na dogara.." Daga haka yadatse kiran batare da yabari tasake magana ba, ahankali ta'aje wayan cike da sanyin jiki, kasa ci gaba tayi da shafa man sai ma tashi da tayi tafara zagaye ɗakin tana me cike da tunani, so take tasamu mafita amma har yau zuciyarta tagaza barin ta, tsananin tausayin sa take ji aranta duk da ita zata cutu, wani ɓangare na zuciyanta tace "Haba Lubna kifarka daga mafarkin da kike yi, karki manta fa babu abunda yahaɗa ki dashi, kuma kimanta da wata alaƙan dake tsakanin zuciyarki dashi, ki ceto Mahaifiyarki da ƙannin ki daga halaka, idan har kinyi hakan babu cutarwa a wajen shi, kuma hakan shine dai-dai". Wannan tunanin yasaka tayi saurin fita tadoshi ɗakin sa cike da tunani kala-kala. [8/30/2020, 9:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 3* Har ta kama handle ɗin ƙofan zata murɗa sai kuma tayi saurin saki tajuya dasauri tasauke idanunta kan tanƙamemen agogon dake manne can saman bango, ƙarfe 07:25am hakan yasaka tasauke ajiyan zuciya don tasan babu shi yariga ya fita, ahankali tamurɗa tashige tasoma dube-duben drowers da sif ɗin sa, ta daɗe tana dube-dube cikin ɗakin bata ga komi ba, ƙarisawa tayi jikin ƙofan da yake shiga yayi aikin sa tare da aje duk wasu muhimman abubuwan sa, tana taɓa ƙofan kamar ko yaushe a kulle yake hakan yasaka tajuya jiki a sanyaye tasoma gyaran cikin bedroom ɗin, bayan ta gama tawanke toilet sannan tafito palow, nan ma sai da tagyara ko ina kafin tanufi ɗakin ta. .... .... ..... .... .... .... Nocking ƙofan da akayi ne yasaka shi ɗan tsakaitawa daga aikin da yake cikin Computer "Yas come in". Yabada umarni yana ci gaba da aikin sa Ahankali taturo ƙofan tashigo, sai da tajingina da ƙofan tana ƙare mishi kallo na 30soconds kafin daga bisani tasoma takowa cikin office ɗin tanemi kujera tazauna inda aka tanada don baƙi, shiru tayi taci gaba da kallon sa batare da tayi magana ba, sam bata gajiya da kallon shi sabida sosai take mutuwar ƙaunar shi, komi nashi me kyau ne ba inda yake da makusa, ya haɗu ne tako ina duk da kasancewar shi baya da farar fata but skin ɗin sa irin golden colour ɗin nan ne me shaining, yana da kyawun fuska wanda yake zagaye da ɗan siririn saje baƙi siɗik gunun sha'awa, idanuwansa farare ne ƙal kamar zaiba, yana da dogon hanci har zuwa ɗan madaidaicin bakin sa me ban sha'awa da ƙananun lips, shi ma'abocin barin suma ne me tarin yawa, don haka koda yaushe sai dai kaganshi yayi gyaran fuska ba dai yayi aski ba, yana da tsayi sosai da faɗin chest kuma yana da ɗan jiki don baza'a kira sa siriri ba. "Wai lafiya kika tasani gaba kike kallona?" Muryan shi takatse mata tunanin ta da take yi a kansa Ɗan firgigit tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin tasaki yalwataccen murmushin da yaƙara ma face ɗin ta kyau, cikin sanyin murya tace "Koda yaushe bana gajiya da kallon ka ne My Ib, Burina ako yaushe kakasance mallakina ni Ni kaɗai, ina Son ka da yawa My Ib, har yaushe ne zan ta jiranka kayarda dani a matsayin wacce zata zama abokiyar rayuwanka? Yaushe ne nima zaka nuna min ƙauna kamar yanda nake tsananin ƙaunarka da begen ka? Yaushe zaka tausaya min kaji ƙaina kagane babu wacce tafini ƙaunarka a faɗin duniyar nan?". Duk maganar da take yin nan idanuwanta na kansa batare da ko kaɗan ta ƙifta su ba, hakan yasaka har ƙwalla suka taru cikin idanun suna shirin zubowa Sai lokacin yaɗago kanshi yasauke idanunshi cikin nata, dai-dai da lokacin da wasu siraran hawaye suka ɗigo saman kuncin ta, tsira mata idanun sa masu matuƙar kaifi da kyawu yayi na ɗan wani lokaci kafin yaɗauke kai yaci gaba da aikin sa, cikin sweet voice ɗin sa yace "Bilkisu wai yaushe ne zaki fahimce ni nima? Kigane nifa bazan iya ɓata time ɗina kan wani soyayya ba". Ɗan tsakaitawa da maganan yayi kafin yace "Please ki dena ɓata lokacin ki akan wanann batun, yanzu ki koma kije kiyi aikin ki, ina Son yau ki kamalla komi ki kawo min". Lumshe idanuwanta tayi tabuɗe su akan shi, duk maganganun da yafaɗa bakin sa kawai take kallo, sosai take jin daɗi idan yakira sunan ta don ji take yi kamar yafi kowa iya faɗan sunan Nocking door ɗin akayi yabada umarnin shigowa, abokin sa Brr. Tahir ne yashigo, ita kuma Bilkisu tatashi tafice batare da tasake cewa komi ba, inda tatashi yazauna yana sakin murmushi yace "Guy ya naga ta fita kuma? Kar dai ace laifina ne na katse muku jindaɗin ku?" Brr. Khalil ɗago kan sa yayi yasauke mishi wani kallo kafin yace "Wai meyasa kai in bakayi tsegumi kamar mace bane baka jindaɗi?" Barr. Tahir dariya yayi yace "To menene na tsegumi kuma? Akan kai da Billy ne zan yi tsegumi? Uhmm gaskiya ce fa kai na kula baka son ta ko kaɗan, Ni wlh na rasa meyasaka yarinyan nan tanace akan dole sai tasame ka, meye amfanin tsayawa wajen da ake wulaƙanta ta, ga waɗanda suka dace da ita suke son ta tsakani da Allah but taƙi su tana tusa kanta inda bazata taɓa karɓuwa ba". "Ok na gane, kafito fili kawai kace min kai kana ciki ba wai katsaya kana faɗamin baƙa ba". Brr. Khalil yafaɗi hakan yana yatsina fuska "Ohh sorry abokina wasa fa nake maka, Ni dama nasan kana son yarinyan nan, kawai halinka ne yasaka bazaka iya nuna mata ba, but ni dai shawaran da zan baka Please and please Ib kadena wahal da yarinyan nan katausaya mata, Tsaki Brr. Khalil yayi yana kau da kansa yaci gaba da aikin sa, shi kuma Brr. Tahir murmusawa yayi yace "Uhmm kai dai gaskiya ne baka so abokina amma ni banga makusa kan Billy da har zaka ƙi ta ba, yakamata kadawo tunanin ka kasan masoyin ka Ib". "Please kafita kabani waje kana damuwana da banzan surutunka". Brr. Khalil yafaɗi hakan yana ɗago kan sa fuskarshi a ɗaure Dariya Brr. Tahir yayi yace "Babu inda zan fita wlh, idan har kaga na fita to lokacin tashin ka ne yayi". Harara yabanka mishi yaja ɗan siririn tsaki still yaci gaba da aikin sa "Wai ya maganar Alhaji Mubarak ne? Me ake ciki yanzu? Yakamata fa musan abin yi tun kafin lokaci yaƙure mana". Cewar Brr. Tahir kenan yana ɗan gyara zaman sa Kamar bazai ce komi ba, sai can kuma yabuɗi baki ahankali yace "Muna da enough time ai insha Allahu komi zai zo da sauƙi, zuwa nan da nest week ma zan je Eygpt ɗin". Jinjina kai Brr. Tahir yayi yace "Gaskiya Shari'a da irin su Alhaji Mubarak hatsari ne dashi, yakamata kakula Ib kasaka idanu da kyau, kafin lokacin zasu iya yin komi don kawai su hanaka samun nasara, but naga alaman kana ɗaukan abun kamar da wasa ne". "Hmm babu abunda zasu iya yi, kai dai kazuba idanu kagani duk wani take-taken su ina sane dashi, kuma bazasu taɓa samun nasara ba, da yardan Allah sai nayi nasara sai na ƙwato mata haƙƙin ta, insha Allahu ta sanadiyar Nazeefa sai na kawo ƙarshen Alhaji Mubarak da duk kan mabiya bayan sa". Brr. Khalil yafaɗi hakan yana kallon Brr. Tahir ɗin "Gaskiya ne, Allah dai yabaka sa'a, yanzu ya take? Ina fatan tana samun lafiya?" Ɗan jingina kan sa yayi saman kujeran da yake yana lumshe idanun sa kafin yagyaɗa masa kai sai kuma yace "Ina son namaida ita asibiti ne domin ina son aƙara duba ta da kyau, zamanta gida babu amfani". "Hakan yafi dacewa ai, amma baka ganin kakaita asibitin da Sameer yake? Inaga shima zai fi kula da ita". "Nima nayi tunanin haka, sai dai kasan Dr. Hashim yace "abarta agidan hakan zai fi sirri, sannan kasan Big bro ba aikin sa bane, tun farko shi yace dani in nemi Dr. Hashim zai fi bata kulawa, kuma sosai take samun lafiya ba kamar da ba". Gyaɗa kan sa Brr. Tahir yayi cike da gamsuwa, daga nan hira suka ɗan taɓa zuwa lokacin tashi aikin nasu kafin suka fito ko wanne yahau motan sa yatafi. Kamar ko yaushe ahankali yake jan motan sa, yanzun ma hakan yake yi kamar baya son tafiya, ta cikin mirror ɗinsa yahango wata baƙar mota tana binshi, da farko be wani damu ba don a tunanin sa ko bashi take bi ba, sai yatsaya yana kallonta ta cikin mirror itama motan packing tayi can nesa dashi, tsawon minti 5 be tada motan ba itama haka motan tana nan yanda take, ahankali yataka yaci gaba da tafiya batare da yaƙara speed ɗin motan ba, yana yi yana kallon motan da taci gaba da bin sa, sai da yayi nisa sai kuma yasake tsayawa itama motan taja tasaya. [8/31/2020, 8:20 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 4* Gani yayi kuma Motan tayi revers tajuya da gudu ta tafi, ahankali yasauke ajiyan zuciya yatada nashi motan yaci gaba da tafiya, agaban wani ɗan madaidaicin gida yatsaya, har ya buɗe ƙofan zai fita wayan sa tafara Ringing, dakatawa yayi yakalli wayan dake ajiye a gefe, ganin sunan BILKISU ya fito asaman screan ɗin yasanya shi jan gajeren tsaki yafice tare da rufo ƙofan, direct gidan yanufa yashiga da sallama a bakin sa, matar dake zaune bakin ƙofanta ta'amsa mishi cike da fara'a tana faɗin "Maraba lale Ibrahima sannu da zuwa". Tana maganan ne tana janyo tabarma dake kusa da ita "Zauna mana anan". Cire black Combat ɗin dake ƙafan sa yayi yasamu waje yazauna yana faɗin "Ina yini Baaba?" "Lafiya lau Ibarahima, yagida ya aiki? Da fatan kowa dai yana lafiya ko?" "Alhamdulillah Baaba". "Ai jiya naji ka shiru bakazo ba, ince dai lafiya?" Ɗan gajeren murmushi yasaki yace "Lafiya lau Baaba, ban samu daman zuwa bane shiyasa, da fatan babu wata matsala baku nemi wani abu ba?" "A'a wlh Alhamdulillah, Nazeefa ce dai ma tafarka ajiyan take neman ka, kuma daga baya sai barci yaɗauke ta, koda tafarka kuma yau bata tambaye ka ba ko magana ma batayi ba". Ajiyan zuciya yaɗan saki kana yace "Ina ga yau zan tafi da ita, Nagode sosai da taimakon ki Allah yasaka, ga wanna babu yawa". "Ikon Allah bawan Allah baka gajiya? To Nagode Allah yasaka, ai babu komi yiwa kai ne, ita kuma Allah yabata lafiya". "Ameen". Ya'amsa ataƙaice yana miƙewa Itama tashi tayi tana faɗin "Shiga tana ciki ai". Be ce komi ba yashiga, yarinya ce da bazata gaza 16yrs ba a kwance akan katifa, fara ce sol sai dai shatin kwarmin idanunta yaɗan yi baƙi-baƙi kaɗan, barci take yi hankalinta kwance, ahankali yamatsa kusa da ita yasanya hannayen sa yaɗauke ta cak ajikinsa yafito, har waje Baaba Talatu tarako shi tana ta saka mishi albarka tare da godiya ga ɗawainiyan da yayi mata A back sit yakwantar da ita kana yashiga yaja motan ahankali kamar yanda yasaba, shiru yayi yana nazarin abinda yakamata yayi, ta cikin mirror yake kallon ta duk da baya hango ta sosai, but jefi-jefi yakan kai idanun sa kanta. A bakin Gate yadakata yayi hon, ba daɗewa aka wangale mishi gate ɗin yatura hancin motan ciki, a packing space yatsai da motan, sai da yaɗan yi minti 3 kafin yabuɗe motan yafito da ƙafan sa, wayoyin sa yaɗauka yashigar dashi cikin aljihu kana yafito yabuɗe bayan mota yana ƙoƙarin fito da ita, ahankali tabuɗe idanuwanta tasauke kan kyakkyawan face ɗin sa, hakan yasaka taɗan saki murmushi ahankali tace "Yayana". Shima murmushin yasakar mata yaɗan ja jikin sa daga ɗaukan ta da yayi ninya yace "Nazeefa.. kin tashi?". Gyaɗa masa kai tayi still tana murmushi "Ok fito ahankali muje ciki, yau na dawo dake gida na, anan zamu ci gaba da zama kinji?" Nan ma gyaɗa masa kai tayi kafin tayunƙuro tatashi tafito daga cikin motan, ahankali take kallon cikin gidan kafin tamai da idanuwanta kan sa, murmushi yasakar mata kana yariƙo hannun ta suka taka ahankali suka nufi cikin gidan, a main palow suka tsaya yanuna mata kujera yace "Zauna anan". Ba musu tasami waje tazauna tana ci gaba da kallon Palon don ba ƙaramin burge ta yayi ba, sosai yatafi da imanin ta, tsarin Palon da kayan cikin kan shi abun burgewa ne da sha'awa, fridge yanufa yaɗauko faro water yadawo yazauna gefen ta, miƙa mata yayi ta'amsa tana sakar masa murmushi, shi kuma wayan sa yazaro cikin aljihu yaɗan latsa yakara a kunne "Ina kike?" "Ok kizo palow Ina jiran ki". 3minute tafito cikin ɗakin ta, har gaban sa taƙarisa taduƙa tace "gani Sir". "Kikai ta ɗakin ki daga yau zakici gaba da kula da ita, zuwa anjima kiyi ma drever magana yakai ki super makert duk wani abun da take buƙata kisiyo mata". Ita sai lokacin ne ma takalli wajen da Nazeefa take zaune, a ranta tana tunanin "to wacece ita awajen shi?" Batakai ga ƙarisa zancen zucin nata ba taji muryan sa yana ma Nazeefa magana "Tashi kibi ta ciki". Babu musu tatashi, itama Lubna miƙewa tayi takama hanyan ɗakin ta Nazeefa na biye da ita abaya, da ido yabi su da kallo har suka shige kafin yasauke ajiyan zuciya, tashi yayi yanufi cikin ɗakin sa, wanka yayi yasauya kaya cikin ƙaraman t.shirt fara da yellow ɗin Three qweater, yafito palow yanufi saman dainnig yasami waje yazauna, tea cup yahaɗa yafara sipping yana latsa wayan sa, tsawon mintuna ashirin yaɗauka awajen kafin yamiƙe yanufi cikin ɗakinsa, be fito ba sai da aka kira sallan magriba kafin yaɗauro alwala yasanya jallabiya fara sol yafito yanufi masjid, sai da aka yi isha'i kafin yadawo, yana shigowa yatarda Nazeefa zaune saman kujera ta ƙudundune jikinta tana kallo, shigowan sa yasaka taɗago kai tana kallon shi, kujeran dake gefen ta yasamu yazauna yana kallon ta "Sannu da zuwa yaya". Tace dashi tana gyara zaman ta dakyau "Yauwa.. kinci abinci?" "Eh Yaya". "Ok." Shiru yagibta a tsakanin su na ɗan wani lokaci kafin yaɗago da kansa daga duba wayan sa yana kallon ta yace "Kije kikwanta dare yayi, ki kira min Lubna". tace "to". Tamiƙe tawuce ciki, Lubna ce tafito taƙariso kusa dashi "Kihaɗa min Coffee". Amsa mishi tayi kawai tawuce cikin kichen, shima tashi yayi yanufi ɗakin sa, ko 2mint be yi ba yafito riƙe da briafcase ɗin sa, yana zama itama tafito tamiƙa mishi takoma ciki, ahankali yasoma aikin sa cikin Computer yana yi yana sipping ɗin Coffee ɗin, har wajen ƙarfe 11:00pm yana nan zaune cikin Palon be gama abinda yake ba, can yaji ihu cikin ɗakin su Lubna, ɗan tsakaitawa yayi daga latsa Computern da yake yi yana kasa kunne. [8/31/2020, 8:26 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` _wannan shafin naku ne masoya Littafina, ina jin daɗin yanda kuke nuna ma Book ɗina ƙauna, thank you._ ❤️ . *CHAPTER 5* Tashi yayi yanufi ɗakin yabuɗe yashiga, duhu ne ako ina hakan yasaka yalaluba makunnin wutan ɗakin yakunna ko ina yagame da haske, akan ta yasauke idanun sa tana zaune saman gadon babu inda jikinta baya rawa, gefen ta yakalla yaga Nazeefa na kwance sai sharan barcin ta take yi ko motsi batayi ba, maida kyawawan idanun sa yayi akanta da itama tazuba nata cikin nashi sai ɓari take yi, ahankali kamar baya son magana yace "Menene kike ihu cikin dare? Lafiyan ki ƙalau kuwa?" Cikin rawan murya tace "Mafarki nayi". Tsare ta da idanu yayi yana nazarin ta, gaba ɗaya tsoro da firgici ne yabayyana a fuskarta, ɗan numfashi yaja sannan yace "Wani irin mafarki ne haka da yabaki tsoro?". Sharto gumin fuskanta tayi still cikin rawan baki tace "Am uhm Mafarki nayi ak..akan Mamana". "Kina son kije gida kenan?" Yaje ho mata tambayan tare da ci gaba da faɗin "Sai in saka drever yakai ki yanzu in kinaso". Dasauri tagirgiza mishi kai tana faɗin "A'a". "Ok koma kikwanta, kitabbatar kinyi addu'a tukun". Daga haka yajuya yafita bayan yakashe wutan ɗakin, ahankali tasulale takoma takwanta tana jin hawaye na sulalo mata a fuska, cikin raunin murya tace "Dan Allah karku kashe min su, zan yi duk abinda kukeso". Sai kuma tasaka hannu tashare hawayen fuskanta tana tuno fuskar sa a yanzu da yashigo, take wasu hawayen suka shiga sintiri saman fuskanta ahankali tafurta "Ina matuƙar ƙaunar ka". ....... ....... ......... ...... Shi kuwa koda yakoma cikin Palon aikin sa yaci gaba da yi, be fi 20minutes ba yatashi yashige ɗakin sa, sai da yayi wanka yashirya cikin kayan barci farare sol yafeshe jikinsa da turare sai zuba ƙamshi yake yi kamar wanda yayi wanka dashi, kwanciya yayi yayinda fuskar sa ke kallon cilling ɗin ɗakin, yaɗaura kan sa saman dantsen hannun sa yayi matashi tare da lumshe idanun sa, ahankali yabuɗe idanunsa yana ƙure cilling ɗin ɗakin da ido, tunani yake yi cikin ransa, ya daɗe ahaka batare da yaji barci yazo mishi ba, ganin haka yasaka shi tashi yanufi Toilet yaɗauro alwala yazo yatada sallah yafara jero nafiloli, sai da yadaɗe yana Sallah kafin yasoma jin barci yatashi yahau gado yayi addu'a yarufe idanunsa, ba jimawa kuwa barci yasure sa. . ****** ****** ****** Tsaye take a bakin titi tana jiran keke napep, tana sanye da uniform ɗin makaranta, riga da wando farare, sai ɗan ƙaramin Hijab kalan ruwan goro, sosai kayan suka yi mata kyau kuma suka ƙara fito da zallan yarintan ta da kyawun surar ta, school bag ɗin ta dake rataye a kafaɗan ta tazamo shi cike da gajiyawa, sosai ranan wajen yake dukan ta, tun ɗazu tana tsaye amma har yanzu bata sami abin hawa ba, gashi har abokan tafiyanta sun watse ita tana nan tsaye ba yau ba gobe, yatsina fuskarta tayi taɗan ɗaga face ɗin ta tana kallon ƙwallelen ranan da yasake fantsamo wa, bata kai ga sauke kanta ba taji hon ɗin mota a gefen ta, dasauri tasauke kanta taɗaura idanunta saman motan dake tsaye ɗan nesa da ita, cikin socond ɗin da be wuce 3 ba takalli motan taɗauke kanta, wanda ke cikin motan ne yafito ɗan kyakkyawan sauri ne yatunkaro inda take "Assalamu alaikum". Yayi mata sallama yana kallon fuskarta da yake a yatsine Bata kalle sa ba taɗan yamutsa fuska tana motsa ƙaramin bakin ta, hakan yasaka yaɗan saki murmushi yace "Baiwar Allah da fatan dai ba laifi nayi ba da ban samu an amsa min sallama ba? Duk da nasan be dace natare ki anan ba, amma kuma babu yanda na iya ne tunda bazan iya bari kisuɓuce min ba". Kallon sa tayi fuskanta a yatsine ga duk kan alamu hakan ya zame mata jiki ne, batace komi ba sai gyara zaman jakan ta da tayi tana kallon hanya "Baiwar Allah ko dai ke kurma ce?" Yasake tambayan ta still yana kallon ta Ahankali tagyaɗa masa kai tana ɗan kwaɓe fuska kamar zata yi kuka "Ayya sorry rashin sani akace yafi dare duhu, kiyi haƙuri but ina son insan sunan ki gashi kuma ina son narage miki hanya, to ya za'ayi yanzu?" Cikin sanyi da muryanta me daɗi tace "Ce maka akayi ina buƙata?" Sai kuma tayi saurin kallon sa tana ɗaura hannu abaki tare da zaro idanu waje tace "Na manta". Don ko kaɗan tamanta da yanzu tayi masa ƙaryan ita kurma ce, shi kuwa da yasaki baki yana kallon ta be san sanda yatuntsire da dariya ba yace "Kai Allah Nagode maka, kinga lokaci ɗaya Allah ya kamaki, sai yasaka ki kika manta kika yi magana, Uhm babu rabon ki wahalar dani kenan, kuma banda abinki ai ƙarya be kamace ki ba, ko kadan bakiyi zubi da masu faɗan magana wanda ba dai-dai ba shiyasa na'amince dake nan take". Murmushi kawai tayi tana jin kunya na kama ta, ba haka taso ba, taso in yagane ita kurma ce yatafi yabata waje amma kuma sai gashi asirinta ya tonu "To yanzu dan Allah kitaimaka kifaɗamin sunan ki, kuma dan Allah karki ƙi tayina muje nasauke ki gida kinga akwai rana kar yayi miki illa, kamar ki kyakkyawa be kamata kina tsaye rana na gasa ki ba, ko ba haka ba?" Ɗan taɓe baki tayi tace "Ni fa bansan meyasaka kake faɗamin waɗannan kalaman ba, kuma bansan meyasaka kakeson taimako na ba, meyasa zaka damu idan rana tagasa ni? Baka tunanin nafison hakan ne shiyasaka nazaɓi tsayuwa anan ɗin?" Murmusawa yayi yace "Ai banga aibu ba idan har nataimake ki, kuma kinsan da cewa duk namiji idan har yaga mace ahanya yanemi yataimake ta to akwai abinda yake so wajenta ne, kuma kema kinsan da haka sai dai in bazaki faɗa ba". "Zai fi kyau dai kasanar dani da bakinka, tunda nasan da cewa Maza kala da iri ne kuma ko wannen su da abinda ke kawo su wajen yarinya, to kai kuma bansan menene yakawo ka ba". Ɗan numfashi yaja yana kallon ta cike da burgewa yace "Tunda kinfi son sai nafaɗa miki dalla-dalla to shikenan, Ni sunana Yazeed tunda Ni kinyi min ruwan sunan ki, kuma abinda yatsai dani wajen ki so da ƙauna ne, tun sanda naƙyalla idanu na naganki naji zuciyata ta kamu da matsananciyan ƙaunarki, kuma wlh ba da wasa nake miki ba, ina son kibani dama Dan Allah na nuna miki irin yanda kika shiga zuciyata kika mamaye min ita acikin mintuna ƙalilan kinji dan Allah". Ɗan gajeren murmushi tayi kana tace "Ayya Malam Yazeed Nagode da ƙaunarka gare ni, sai dai ina tunanin ka makaro domin Ni ɗin nan da kake gani tuni na zama mallakin wanin ka, ina faɗa maka wannan maganan ne don kar nawahal da kai". Murmushi yasaki cike da rashin yarda yace "To shikenan amma dai kizo muje nasauke ki mana, dan Allah karkice a'a plz ƴar kyakykyawa". Batasan sanda tasaki murmushi ba takalle sa tace "Uhm kana son kayi min daɗin baki ko?". "Ai gaskiya nafaɗa ƴan mata, ko makaho yashafa yasan akwai kyau anan". Taɓe bakinta tayi tace "to muje". Gaba yayi yabuɗe mata gaban motan tashige, shima yazaga yashiga yaja motan, sai da yadaidaita motar tasa asaman kwalta ɗin kafin yace "Har yanzu dai anƙi sanar dani sunan Gimbiyan, sai faman rowa ake min" . Murmushi kawai tayi ataƙaice tace "HALWA". "Wow nice name, Gaskiya sunan yadace dake sosai, Masha Allah suna me daɗi". "Ko?" Yace "eh mana, ko bakisan da haka bane?" Batayi magana ba sai murmushi da tasaki me sauti, daga haka yayi ta jan ta da surutu ita kuma tana amsa mishi wasu kuma iyakan tayi murmushi kawai, har bakin layin gidan su yakaita tace "ya aje ta nan". Bayan yayi packing ɗin motan yajuyo yana kallonta yace "To bakiso nakai ki har ƙofar gida ne?" Ɗan kallon sa tayi tagyaɗa masa kai "Meyasa to?" "Babu komi". Ta'amsa mishi ataƙaice "Uhmmm ko dai bakiso nahaɗu da saurayin ki ne?" Turo bakin ta gaba tayi sai kuma tataɓe shi tace "Ba laifi bane hakan ai tunda na sanar da kai dama". Murmushi yayi yace "Gaskiya ne, to yanzu bani Numbanki mana tunda kinga ban sauke ki har gida ba, kar kuma yanzu in kin tafi shikenan na rasa ki". "Hmm tunda har kakawo ni nan ai kamar kakawo Ni gida ne, babu wanda zaka tambaya anan wajen be kai ka gidan mu ba idan har kafaɗa masa suna na, kuma gidan mu ai ba ɓoyayye bane, kana cewa gidan Malam Ayuba za'a kawo ka". Yazeed yace "to NUMBAN kuma fa bazan samu ba kenan? Please". Yaƙarike maganar yana ɗan marairaice fuska Cike da ƙosawa tace "bani da waya, sai anjima nagode sosai". Tabuɗe motan tafito, shi kuma yana ɗaga mata hannu tare da faɗin "Sai kin ganni kenan ko?" Kawai gyaɗa masa kai tayi tawuce abin ta, shi kuma yaja motan sa yatafi fuskarsa cike da nishaɗi. Da sallama tashiga gidan, matar dake zaune tana tatan koko ta'amsa mata tana faɗin "ƴan makaranta an dawo?" Cike da gajiyawa taƙarisa kusa da ita tazauna saman turmi tace "Eh wlh Umma, kin ganni sai yanzu". Umma tace "gaskiya ne kinsha hanya, ga uban rana da ake ƙwalla wa ai yau ko da gani kin gaji". "Uhmmm Umma bari ke dai, wlh yau nasha wahala ga wuyan abun hawa da ban samu da wuri ba". Cewar Halwan tana tashi ta'aje jakan ta saman turmin tanufi wajen randan ruwa tabuɗe tana ninyan ɗiba Umma tace "karki sha wannan ruwan, je ɗakina kiɗauko fure water yanzu na'aiki yara suka siyo min". "To Umma". Ɗakin tashige sai gata tafito riƙe da fure water'n ahannu tana faɗin "Umma ya jikin Zainab ɗin?" "Alhamdulillah dasauƙi sosai, zazzaɓin ya saukar mata ai, tana nan kwance cikin ɗaki inaga ko barci take yi ne?" "Ok bari in shiga in ganta". Ɗaukan jakan ta tayi tashige ɗakin Zainab ɗin, kamar yanda Umma tace kuwa tana kwance tana sharɓan barci duk tayi ɗai-ɗai saman katifan ta sai baza hanci take" bakin gadon tasamu waje tazauna tatsiyaya ruwan ahannun ta tazuba mata a fuska, jin sanyi ya ratsa mata fuska atake tabuɗe idanunta da suka ƙanƙance suka yi ja tana maida su tana rufewa "To kasa tashi haka barcin ya isa, don nasan ba tun yanzu kike yi ba". Ɗan yamutsa fuska Zainab tayi taƙara ware idanunta tana kallon HALWA kana tatashi zaune tana sakin hamma, cike da kasala tace "Har kin dawo?" Halwa tace "eh na dawo, ya jikin naki? Umma tace "kin samu sauƙi ko?" "Eh dasauƙi sosai, dama wlh don kaina ya matsa min ne da babu abinda zai sa naƙi zuwa makaranta". Zainab ɗin tafaɗi hakan tana zamewa takoma takwanta "Gaskiya gwara da kika zauna ɗin don yau babu abunda akayi, Monday ma za'a fara test, amma fa ina faɗamiki show ya wuce ki". "Dan Allah fa? Ke da mutumin naki?" Harara Halwa tasakar mata tana yatsina tace "Banson iskanci fa Zainab, wlh yanzu sai mu ɓata idan kika sake kiran min ɗan iskan nan, mtwww". Taja tsaki tana ɗaure fuska tare da huro hanci Ita kam Zainab dariya tayi tace "Sorry ƙawalliya roman jaɓa wasa nake miki fa, kinsan ni dake bamu haka, bani labari to me yafaru?" "Ai kuma baki isa ba wlh tunda kika taɓo ni nafasa baki labarin, kinga Ni tafiya ma zanyi dama na biyo ne don naduba jikin naki, tunda yanzu na ganki garas to kinga tafiyata". Tashi tayi tasaɓa jakan ta a kafaɗa tafice, Zainab na kiran ta amma ko waige batayi ba, tana fita taga Umma har yanzu bata gama tatan ba tace "Umma na tafi". "To har zaki tafi? Ina jiran in sauke Dambu nasawo muku kuma?" Umma tace hakan tana kallon Halwa "A'a Umma kibar sa kawai yau banjin tsayawa ne". "To shikenan kigaida gida, kigaishe min da Maman naku". "To zataji". Daga haka tafice [8/31/2020, 8:29 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 6* Shiga tayi cikin gidan nasu da sallama a bakin ta, Mama da fitowar ta kenan daga ɗaki riƙe da kwano ahannu ta'amsa mata tana kallon ta, ƙarisowa Halwa tayi tana kallon Maman nata da tasami waje saman tabarma tazauna tace "Mamana sannu da gida". "Yauwa ƴata takaina, kin dawo?". "Washh.. nagaji wlh Mama". Halwa tafaɗa tana zama gefen Maman "Ai daga ganin yanayin ki nasan da haka, da fatan dai ba wahalan mota ce tatsai dake ba?" "Shine wlh Mama, kuma sai nabiya gidan su Zainab na je duba jikinta". Mama kallonta tayi tace "To ya ya jikin nata? Ta samu sauƙi dai ko?" "Alhamdulillah Mama jikin nata ya warware ai sosai, Umma ma na gaishe ki". "Tom Ina amsawa, naso ma in shiga in gaishe ta Allah be yiba, sai ki tashi kije kiɗau abincin ki yana ɗakin ki, don nasan tunda kika langaɓe anan sai kizauna kiyi ta zuba bazaki ci ba, kuma nasan da yunwa atattare dake". Dariya Halwa tayi tace "Wlh Mamana shiyasa nake ƙara son ki sabida ƙaunar da kike nuna min, uhm ai yau bazan iya wasa da abinci ba sabida yanda naji hanjin cikina suna kaɗawa, bari dai inje in ɗauko". Tamiƙe tsaye tana kwaɓe hijabinta, Mama kuma taɓe baki tayi tace "Da dai bansan halinki bane, yanzu sai ki jagula kibar shi nan". Halwa shigewa ɗaki tayi tana ɗaga murya tace "Mama banda yanzu dai, kibari kigani har ƙari ma sai kinyi min". "To bansan surutu kimaza kiɗauko kizo nan kizauna kici". Fitowa tayi riƙe da coolar ahannun ta da wayanta, zama tayi tana tanƙwashe ƙafafunta tasoma danna wayan tana faɗin "Mama har yanzu Yaya be dawo ba?" "Ni ban ganshi ba, sai ki neme sa ta waya kiji inda yatsaya". Cewar Mama tana ci gaba da ɓare maggi Wayan takara akunni tasoma buɗe coolar'n, hannu tasaka tasoma kai loman abincin dai-dai lokacin da aka ɗaga wayan nata tace "Wai yaya ina kaje ne har yanzu shiru baka dawo ba?" "Sorry my Dear, Ina nan kusa naje wajen abokina ne, amma yanzu zaki ganni". Ɗan shagwaɓe murya tayi tace "To kayi sauri kaji?" "Ok karki damu my dear, Yayanki yakusa dawowa". Daga haka sukayi sallama ta'aje wayan gefe, taci gaba da cin abincin tana yi tana zuba ma Mama surutu, ita kam sai Umm take ce mata, Mama da tagama ɓare maggin miƙewa tayi tashige kichen, lokacin ne Nura yayi sallama yashigo, ɗago kanta tayi dai-dai lokacin da ta'afa shinkafan cikin baki tana kuma amsa mishi sallaman "A'a yi ahankali mana karki ƙware, wannan loma haka sai kace abincin zai gudu". Nura yafaɗa hakan yana dariya bayan da yaƙaraso kusa da ita yasami wuri yazauna, ɗan yatsina fuska tayi sai kuma tasakar masa harara tana faɗin "To aina kaga na zuba loma yaya? Ko bakaga yanda naɗibo bane?" Ɗan sakin murmushi yayi yana ƙare mata kallo yace "Na gani mana, ba gashi kin ciko hannu ba kamar wanda take gudun shigowan wasu don halin rowa, nasan fa halin ki Sarkin rowa ce". Ture abincin tayi tana ɓata fuska, cikin shagwaɓa tace "Mama kin gansa ko?" Daga kichen ɗin Mama ta'amsa mata da faɗin "Ni kin ganni babu ruwana kunfi kusa, karki sako ni cikin zancen ku". Nura dariya yasaki yana mata gwalo, ai ko kawai tasakar masa kuka "Kai wai me tayi maka ne Nura daga zuwanka zaka sa ta kuka? Bansan haka fa tam". Cewar Mama kenan tana leƙo kai waje "Wlh Mama Ni ban mata komai ba kinsan halinta ai bata raina abun kuka, to kiyi shiru mana beuaty daga wasa? kinga nakama kunni na ma". Dena kukan tayi tana turo baki gaba tace "Ai kuma mun ɓata tunda Ni kace ma me rowa". Haba ƴar ƙanwata abar ƙauna ta, kiyi haƙuri kiyafe ma yayanki, ban sakewa wlh kinji? Matso da kunnin ki ma kiji wata magana?" "Me zaka faɗamin?" Tafaɗa tana kallon sa Murmushi yayi mata yana kashe mata ido ɗaya yace "Kalaman da kikafi so mana" ko in aje kayana baƙya buƙata?" "Ina so mana yaya". Tafaɗi hakan dasauri tana matso da kunnen ta kusa dashi Magana yaraɗa mata tasaki dariya tana janye kunnen ta, ɗage mata giran sa yayi yace "To muje mana". "To bari in sauya kaya, kaje kajira ni a zaure sai ka'aiko yaro ko?". "Eh haka zamuyi". Nura yafaɗi hakan yana miƙewa dasauri Itama tashi tayi tashige ɗaki, Mama da tafito daga kichen tabi Halwa da tashige ɗaki da kallo, kana tamaida idanunta kan Nura da yasaka takalmin shi yana shirin ficewa waje tace "To yanzu kuma me kuka shirya ne na ji kuna ƙus-ƙus?" Dariya Nura yayi yace "Zance zamuyi mana Mama, amma yau a zaure zamuyi, zan aiko yaro yakira min ƴar taki, dan Allah karki hanata fita". Kama haɓa Mama tayi tabi shi da kallo don takasa cewa komai, shi kuma fita yayi yana faɗin "Sweety kiyi sauri fa, karki shanya Ni kuma don nasan shegen nawan ki". Babu jimawa kuwa Halwa tafito riƙe da ɗankwali da Hijab ahannu, tsayawa tayi tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin Mama tace "eh haƙiƙa yaran nan dagaske kuke yi, yau kuma gaba ɗayan ku kenan haukan taku tamotsa?" Halwa dake shirin magana sai ganin yaro tayi ya shigo yana faɗin "Wai Halwa tazo inji Nura". Ƙarisa saka Hijabin ta tayi tana faɗin "Kai kace gata nan zuwa". Sai takalli Mama tace "To Mama Ni nafita". Bata jira jin ta bakin Maman ba tafice dasauri, girgiza kanta kawai Mama tayi tana murmushi tace "Allah yashirya ku, yaran zamani baku da kunya wlh, ai bari Baban naku yadawo sai ya ji komi". . ****** ****** ***** Shigowan ta kenan ɗakin taji wayan ta na ringing dasauri taƙarisa taɗauka tana karawa a kunni "LUBNA kenan". Cewar Mutumin da yakira ta yana sakin dariya Shiru tayi tana sauraron shi, sai dai babu inda jikinta baya rawa, har zuciyanta na wani irin tsalle kamar zai faso ƙirjinta "Har yanzu dai kin ƙi aikata abinda muka sakaki ko? Da alamun kina son kirasa kowa naki ne". Kallon inda Nazeefa take akwance tayi wanda sai sharɓan barcin ta take yi ta ƙudundine jikinta cikin bargo, cikin ƙasa da murya tace "Dan Allah kuyi haƙuri har yanzu Ban samu nasara bane, wlh kullum sai nashiga nayi muku bincike amma baya barin komi". "Kina dai wasa da rayuwan Mahaifiyarki da ta ƙannin ki, domin muddin bakiyi abinda mukasa ki ba zaki rasa su, tun yaushe muka baki aikin nan amma kullum magana ɗaya kike faɗa? To ki saurare ni da kyau, akwai wata yarinya da yakawo ta gidan nan kitabbatar da kin fito da ita cikin gidan nan, zan aiko yarana su ɗauke ta". Cikin rawan murya Lubna tace "Meee? Nazeefa?" "Yess ita, ita nake so naɗauka, kijira umarni na". Ƙitt yakashe wayan, yayinda ita kuma taciro wayan daga kunnen ta tana kallon Nazeefa "Menene alaƙan su da wannan yarinyan? Me tayi musu? Me suke so da ita?" Dasauri tamatsa bakin gadon tazauna tana ƙare mata kallo, sai kuma taji kawai hawaye na zubo mata, kifa kanta tayi saman gadon tasoma rera kuka mara sauti "Meyasaka waɗannan mutanen suka shigo rayuwanta? Me tayi musu ne? Meyasaka sai ita ne zasu zaɓa? Meyasa basuyi tunanin bazata iya aikata duk wannan aikin ba musamman ma akan shi? Tabbas tana da rauni bazata taɓa iyawa ba". "Waye zai fitar dani cikin wannan ƙangin?" Tafaɗi hakan lokacin da taɗago kanta idanuwanta sharkab da hawaye "Allah gani gare ka kataimake ni". Kallon Nazeefa tasake yi kafin tamiƙe ahankali tashige toilet. . . _shin su waye waɗannan mutanen ne?_ _Meyasaka suke takura ma Lubna?_ _meye alaƙan su da Nazeefa?_ 🤷🏻‍♀️ 💃💃💃💃💃💃 [8/31/2020, 8:31 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖️ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 7* Ahankali yake taka motan kamar koda yaushe, wayan sa dake ajiye ne tasoma ringing, hannu ɗaya yamiƙa yaɗau wayan bayan da yaduba yaga me kira, picking call ɗin yayi tare da saka ta a speaker 🔊 yamaida ya'ajiye "Hello Bro". Daga can Sameer yace "Kana ina da Allah?" "Yanzu gani na taso wajen aiki zan koma gida". Sameer yace "yauwa kazo kaɗauke ni Please, motata ce tasami matsala an tafi da ita, ina office Ina jiran ka". "Ok ganinan". Juya kambun motan yayi yasauya hanya, minti 15 yakawo shi babban asibitin da Sameer yake aiki, bayan yayi packing fitowa yayi yashiga cikin asibitin, direct office ɗin Sameer yazarce, yana shiga yaganshi zaune yana cike wasu takardu, hannu yabasa suka gaisa sannan yasami waje yazauna Sameer yace "just give me 10 mint don Allah yanzu zan ƙarisa sai mutafi". "Babu Matsala". Khalil ɗin yafaɗa yana gyara zaman shi kan kujeran yalumshe idanun sa "Ka gaji ko?" Ɗan yamutsa face ɗin sa yayi ba tare da ya buɗe idanun sa ba yace "Sosai ma, barci kawai nake ji wlh yanzu". Ɗan kallon sa Sameer yayi yace "Wai ya maganar tafiyan ka ne? Har yanzu banji kace komi ba?" Idanuwan sa yabuɗe yana kallon Sameer ɗin yace "Zuwa Friday zan tafi". Jinjina kai yayi yace "But Yakamata kayi taka tsantsan kasan Alhaji Mubarak ba ƙaramin mutum bane, don bani da shakka duk abun da kake shirya wa ana sanar masa, Ni yanzu maganar ma da nake so nayi maka kan Nazeefa ce, Yakamata kaciro ta daga wannan gidan kakaita wajen Mom hakan zai fi". Khalil yace "ai jiyan nan naɗauko ta namaida ita gida na, inaga can zata zauna". "Kana ganin babu Matsala?" Cewar Sameer Gyaɗa masa kai kawai yayi "Ok amma dai Yakamata kaƙara masu gadi, don nafi tunanin in har tana gidan ka zasu fi sanin haka, sannan kuma kaga kai tafiya zakayi Yakamata kaduba shawarata". Shiru Khalil yayi naɗan wasu sokonni kafin yace "Ok Bro". Daga haka hira suka soma duk dai akan case ɗin Alhaji Mubarak, kafin Sameer yagama suka tashi suka fice, har gidan sa yasauke sa Sameer ɗin yace "Baza ka shiga ba?" Girgiza kan sa kawai yayi yace "No kagaishe min dai da auntyna, sai wani lokacin zan shigo". Ɗan taɓe bakin sa kawai Sameer yayi yace "Kunfi kusa ai". Kafin yabuɗe motan yafice, shi kuma yaja ahankali yatafi, a bakin Gate yadakata yadanna hon aka buɗe masa yashige, bayan yayi parcking motan yabuɗe yafito riƙe da briefcase ɗin sa a hannu, yafara tafiya cikin ƙasaita yanufi cikin gidan, hannun sa yasaka yabuɗe ƙofan yana ɗan motsa bakin sa yashige, tana tsaye wajen dainning table tana jera abinci taɗago kanta takalle shi, saurin sauke kanta tayi ganin sun haɗa idanu, cike da sanyin murya tace "Sannu da zuwa". Gyaɗa mata kai kawai yayi yana ci gaba da kallon ta, ahankali yasoma takowa cikin Palon kafin yace "Ina Nazeefa?" "Tana ciki tana barci". "Tasha maganin ta?" Yasake jeho mata tambayan still yana kallon ta Lokacin itama taɗago kai taɗan saci kallon sa dasauri taɗauke kanta tace "Tasha". "Ok ki tashe ta taci abinci". "To Sir". Wucewa ɗakin sa yayi, ita kuma tabi sa da kallo tana jin tsananin ƙaunar sa na ƙara shigan ta, ɗauke kanta tayi bayan da yashige tana sauke ajiyan zuciya, tasan da cewa babu yanda za'ayi tasame shi, yafi ƙarfin ta tako ina koda a mafarki ne, haƙiƙa zuciyanta tayi ganganci da takamu da ƙaunar wanda be san ma tana yi ba, tasan da cewa zuciyarta ba ƙaramin yaudaranta take yi ba da har taso uban gidan ta a matsayinta na ƴar aiki. Ci gaba da jera dainning ɗin tayi kafin tagama tashige ɗaki Shi kuwa yana shiga ɗakin sa kayan jikin sa yasoma ragewa kafin yashige toilet, be daɗe ba yafito yasaka farar singlate da Black Three qweater yafaɗa saman gado, sosai yake jin barci kuma gashi yana jin yunwa, sai dai bazai iya tashi yaje yaci abinci ba sabida tsananin barcin da yake ji cikin idanun sa, ai kuwa yana kwanciya babu daɗewa barci yaɗauke shi Ba shi yatashi ba sai 05:04pm, yana buɗe kyawawan idanun sa yaɗaura kan agogon dake manne jikin bango, dasauri yamiƙe yana salati, direct toilet yawuce agurguje yayi wanka yaɗauro alwala yafito, jallabiya kaɗai yazira ajikin sa yashimfiɗa dadduma yagabatar da sallan asar, lokacin da ya'idar ne yaji wani yunwa na ƙwaƙwulan cikin sa, ɗan shafa cikin nasa yayi yana lumshe idanu kafin yabuɗe su yamiƙe tsaye, gaban sif ɗin sa yanufa yaciro kayan da zai sa, kafin yakoma gaban mirror yasoma shafa Lotions, sai da yagama sannan yasaka kayan sa, riga da wando ne, rigan kalan maroon ne me hoton kan sarki, daga saman ta an rubuta THE KING da black colour, haka ma wandon sa Black jeans ne, sai yazira room slippars yafeshe jikinsa da turare sai tashin ƙamshi yake yi, wayoyin sa yaɗauka yanufi palow, babu kowa ciki yanemi kujera a ɗaya daga cikin kujerun dainning yazauna, buɗe coolar'n gaban shi yayi yaga farar shinkafa ne zalla da yankakken hanta a sama, be da sha'awan buɗe sauran, plate kawai yaɗauka yaɗibi abincin yarufe, sannan yabuɗe coolar'n dake kusa da wancan ɗin yaga miya ce na jajjage wanda yaji kifi sai tashin ƙamshi yake yi, zubawa yayi yasoma ci ahankali yana yi yana latsa wayan sa Nazeefa ce tafito daga cikin ɗaki sanye da doguwan riga ja me kwalliyan furanni, ta yafa gyalen kayan tana tafiya ahankali kamar wacce ƙwai yafashe mata a ciki, saman kujerun Palon tanemi wuri tazauna tana kallon shi, cikin sanyin murya tace "Yaya ina wuni". Sai lokacin yaɗan ɗago kai yakalle ta naɗan wani lokaci kafin yamaida idanun sa kan wayan sa yaci gaba da abin da yake yi, can kuma ya'amsa mata da "Lafiya". Shiru ne yabiyo baya, sai kuma tagyara zamanta tana kallon shi, gaba ɗaya hankalinta da tunanin ta yana gare shi, komi nasa yana matuƙar burgeta, to meyasa? Take tatuno sanda suka fara haɗuwa yataimake ta duk da bata cikin hayyacin ta, wani kyakykyawan murmushi tasaki tana jin zuciyarta na mata sanyi da daɗi, memakon tariƙa kukan maraici sai dai ko kaɗan yanzu ji take yi tamkar bata rasa komi nata ba, duk sanda tatuna fuskar sa tana ji ne kamar tafi kowa Sa'a a duniya "Wannan wani irin yanayi nake ji haka? Meyasaka nake jin sa daban da sauran maza?" Zuciyarta tayi mata wannan tambayan, batakai ga lalubo amsan ta ba taji muryan sa me tsananin daɗi a cikin kunnen ta yana faɗin "Kidena yawo da yawa saboda aikin dake cikin ki, kiriƙa tambayan Lubna duk abinda kikeso bana son yawan fitowa nan in ba da ƙwaƙwƙwaran dalili ba". Nazeefa gyaɗa masa kai tayi, sai kuma ta'amsa mishi ganin baya kallon ta yayi maganan "To Yaya". Tafaɗa cike da sanyin murya kafin tatashi tasoma tafiya don komawa ɗaki, ahankali take takawa har tashige, tana shiga Lubna takallo ta sai kuma taɗauke idanun ta taci gaba da tunanin ta, itama Nazeefa samun waje tayi gefen gadon tazauna tana tunanin Brr. Khalil, daga ƙarshe tazame takwanta tana rufe idanuwanta, tashi Lubna tayi tafice zuwa kichen don ɗaura abincin dare, koda tafito idanuwanta akan shi suka sauka, sosai yau yayi mata kyau duk da ko yaushe shi ɗin me kyau ne, amma yau sai takasa ɗauke idanunta akan sa har sai da tagama ƙare masa kallo kafin tashige kichen Ahankali yamiƙe yanufi ƙofan fita, a Compound ɗin gidan yatsaya yajingina bayan sa da bango yana lumshe idanuwan sa tare da sanya hannun sa ɗaya cikin aljihun wandon sa, shiru yayi yana sauraron bugun zuciyan sa yana tunani, ya jima awajen har sai da yaji kiran sallah kafin yanufi inda me gadi yake yayi alwala anan, tare suka jera da me gadin da sauran ma'aikatan biyu suka nufi masallaci, shi dama ba ma'abocin girman kai bane ga masu aikin sa, wani lokacin ma in yasami time wajen su yake zuwa suyi ta mishi hira shi kuma yana kallon su, duk da baya magana amma sosai yake fahimtar su, wani lokacin har yaɗan dara in suna bashi labari me daɗi, acan suka baro shi sai da yayi sallan isha'i kafin yadawo gida, Direct saman dainnig yanufa yahaɗa tea yasha, ko minti 10 be yi ba yatashi yakoma ɗakin sa, acikin ɗakin da yake aikin sa yashige, kujera yasamu yazauna yajanyo lapton ɗin sa yasoma aiki ciki, minti 5 da soma aikin nasa yamiƙe yafita, briefcase ɗin sa yaɗauko yadawo yazauna, Computer yaciro da wasu ducuments yaci gaba da aikin sa, sai da ƙarfe 12:017pm yayi kafin yadakata yarufe lapton ɗin da Computer, tashi yayi yana miƙa cike da gajiyawa yafice yanufi Toilet, alwala kaɗai yayi yafito yasauya kaya zuwa kayan barci yakwanta tare da kashe fitila. . _to nima bari in dakata anan, karku manta da_ *Like* *Comments* *Vote* *Share* _ina yin ku masoyana_ 💃💃💃💃💃 [9/1/2020, 10:12 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 8* Tafiya suke yi suna sanye da uniform, fitowan su kenan akan hanyan su tazuwa school, Halwa take bata labarin haɗuwan su da Yazeed jiya, ita kuma Zainab zai ɓaɓɓaka dariya take yi har da riƙe ciki "Ke kiyi fa ahankali karki jawo mana mutane nan". Cewar Halwa kenan tana kallon Zainab "Ƙyale ni in dara, wlh kin bani dariya, hhhhh wai ke adole ga kurma, kai wlh banji daɗi ba da bana nan akai wannan draman, kawai lokaci ɗaya Allah yatoni asirin ki". Sai takuma kwashewa da dariya, Halwa bige mata kafaɗa tayi tana faɗin "Ke fa tsiyata dake ba'a zancen arziƙi dake, yanzu sai kihau ma mutane wannan haukan naki, mtswww". Taja gajeren tsaki tana ɗaure fuska, sai lokacin Zainab taɗan sassauta dariyan da take yi tace "Wooo kurma ta Yazeed yi haƙuri ban sakewa". Wani irin kallo tayi mata tace "Gyara kalaman ki, kidena danganta ni dashi, kinsan dacewa ni ɗin mallakin Yaya Nura ne shi kaɗai, to dan Allah kidena bana so". Taɓe baki Zainab tayi tace "Nafi kowa sanin haka ai, amma babu yanda Allah baya lamarin sa, yanzu sai kiga an sauya d.." Saurin bige mata baki Halwa tayi tana faɗin "Kull.. karki soma, wlh in kika ƙarisa sai an ji mu dani dake, Allah ni nakula ma kamar baƙin ciki kike min, to ta Allah ba ta ki ba, insha Allahu sai na zama mallakin Yaya Nura na sai dai kimutu". Zainab dariya tayi tace "Hmmm yi haƙuri ƙawalli na dena, in kinso ma gobe aɗaura miki aure dake dashi, ni wlh bata shafen ba". Halwa tace "to ai ko bakice ba, ni inda za'abi ta shawarata wlh kafin muƙarisa wannan makarantan kawai aɗaura mana aure, domin ni a tsarina bana son nagama secondary batare da nashiga daga ciki ba". Baki Zainab tariƙe tana kallon ta "Lallai Halwa kin ƙosa da yawa, amma bansan haka ba sai yanzu, to gaskiya Yakamata su Mama suyi saurin miƙa ki tun kafin aji sautin kiɗan ya sauya". "Ni da ma zaki taimaka min da yafi, kije kisanar mata tunda su har yanzu sun kasa sanin haka, wlh Zainab ina faɗamiki auren wuri daɗi ne dashi, kema dai ki aje wannan aƙidan naki kawai mu jone ayi mana tare ko ma huta, ko ba haka ba?" Cewar Halwa tana kallon Zainab tare da ɗage mata gira Girgiza kai Zainab tayi tace "A'a ke dai da kikaga zaki iya sai kiyi tayi, wai ma duka-duka nawa muke da har zamuyi aure, just 18years fa kenan, kinga ke kin riga da kin lume a soyayyan Yayan ki bazaki gane ba, amma ni bar ni sai na zaɓa Wanda naga ya dace dani, kuma wanda yafi kwantawa da ra'ayina". Halwa tace "ni fa nasan halin ki, be wuce kice me kyau kike nema ba, to me zai hana nahaɗa ki da Yazeed wlh zaku dace sosai, domin ya haɗu tako ina kamar dai yanda kikeso". "Haba dan Allah?" "Wlh kuwa sai ma kin ganshi, nima ba ƙaramin burge ni yayi ba, sai dai kinsan tuni zuciyata ta riga ta makance ga wanin shi, babu wanda nake gani da zaifi min Yaya Nura na". Zainab taɓe baki tayi tace "Na kula fa kamar ma kinfi son sa akan shi, ke dai baki da zance sai ta wani Yaya Nura, uhmmm Allah dai yanuna mana ranan, amma ni gaskiya ba yanzu zanyi aure ba, sai na yi nisa a karatuna". Daidai lokacin da wata keke napep tazo wucewa Halwa tatare tana faɗin "Ameen inda gaske kike, kuma ko me zakice sai dai kice". Zainab batace komi ba in banda dariya da tayi, napep ɗin suka shige yaja suka tafi, a cikin motan ma hiran suke tayi har yakawo su, bayan sun sauka Halwa ce talaluba cikin jakan ta taciro gudan ɗari tamiƙa masa, har sun soma tafiya sai wata mota tasha gaban su, atare suka tsaya suna kallon motan, wani ingarman saurayi ne yafito, yana sanye da ɓakin singlate da farar wando Three qweater, jikin sa duk zanen tatue ne kai da gani kasan irin ƴan iskan nan ne waɗanda suke tsula tsiyan su cikin gari, wani shegen aski ne akan sa oho ni na manta sunan sa ma, wuyan sa duk sarƙoƙi ne har guda biyar, tun sanda yafito yazuba ma Halwa idanu yana wani irin murmushi tare da ɗage mata gira, ita kuma sai taɗauke kanta takama hannun Zainab zasu kewaya su wuce, wuf yashige gaban su yana ci gaba da bin ta da wani mayataccen kallo yace "Babyna babu magana?" Ko ɗago kai bata yi ba illa sake riƙo hannun Zainab da tayi tana son sauya hanya, yasake shan gaban ta yana cewa "Wai Baby bakiyi missing ɗina bane? Meyasaka kike min haka ne? kinsan da cewa ina matuƙar ƙaunarki da sha'awanki why bazaki bani dama ba?" Yaƙarike maganar sa yana matso da fuskar sa kusa da nata still yana murmushi me ma'anoni da yawa Ɗan ja da baya tayi tana yamutsa fuska kana tabi shi da banzan kallo, batace komai ba dai tajuya da ninyan barin wajen gaba ɗaya sai ji tayi ya janyo mata Hijab, kiiiii sai gata tadawo gaban sa, yasanya hannu yariƙo hannun ta yana faɗin "Common Baby sai yaushe zaki waye ne.." Marin da tasauke mishi a fuska ne yakatse mishi maganar shi, sakin ta yayi yadafe kuncin sa da hannayen sa biyu yana kallonta cike da tsantsan mamaki, ba shi ba har Zainab sai da tatsora ta da marin da Halwa tayi mishi Muryan Halwan ne yakatse musu mamakinsu su duk ka biyun "Wlh koda wasa kasake ɗaukan banzan hannunka me datti kaɗaura shi akaina sai nayi maka mafiyin wannan, banza ɗan iska". Tajuya zata tafi yayi saurin sake tare ta, cikin tsananin ƙunan rai kamar wanda zai kai mata duka wanda har sai da taɗan tsorata da ganin yanayin sa yace "Ni kika mara Halwa? Ni Ko?" Ɗan girgiza kan shi yayi yana sakin murmushin gefen baki yaci gaba "Zan nuna miki waye Haris, wlh sai kinyi nadaman zuwanki duniya, sai nayi miki abinda har kimutu bazaki taɓa manta ni a rayuwanki ba tunda har kika iya cire hannu kikayi min abinda ba'a taɓa min ba, kijira kika me zai biyo baya". Yana faɗin haka yajuya dasauri yabuɗe motan sa yashige, har motan shi yayi nisa bata ɗauke idanunta kan shi ba, sosai tatsora ta da ganin yanayin sa, ita tasan waye Haris, ba ƙaramin tantirin ɗan iska bane batasan me zai biyo baya ba kamar yanda yace "tajira zata gani" amma kuma ko kaɗan batayi nadaman marin da tayi masa ba, inda tana da ƙarfin da zatayi mishi mafiyin haka to wlh sai tayi masa Zainab ce takatse mata tunanin ta da faɗin "Mun shiga uku Halwa me kikayi haka? Haris fa kika mara? kuma kinsan ko shi waye a garin nan, wlh sai yaɗaure kaf dangin mu babu wanda ya'isa yafiddo mu, meyasa dan Allah kikayi wannan ɗanyen aikin? Kinsan fa ba yau yasaba miki irin haka ba". Kallon ta Halwa tayi cike da jin haushin maganan ta tace "Kenan kinaso kice min in barshi ya taɓa min jiki a banza? Kinsan halin sa ɗan iska ne idan har ban taka mishi birki ba gobe ma sakewa zai yi, yaje yayi duk abinda zai yi ta Allah ba tashi ba, mtswww ke kike jin tsoron sa". Tana faɗin hakan tawuce tabar ta nan, biyo bayan ta itama tayi tana kiran sunan ta, ita ko bata kula ta ba tabuɗe Gate ɗin tashige, babu wasu mutane cikin school ɗin sai ƴan tsiraru, Direct class ɗin su da yakasance s.s3 suka wuce. . _To fa me zai faru?_🤔 *Comments & share plz* [9/1/2020, 4:35 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 9* "Mom wai yaushe Dad zai dawo?" Shafo suman kanshi tayi tace "Inaga sai gobe zai dawo, amma kaneme shi ta waya mana". "Ok". Mom tace "ɗazu Sameer yake sanar dani jibi tafiyan ka ko?" Gyaɗa mata kai kawai yayi yana gyara zaman shi "Ok Allah yakaika lafiya, kadai ta addu'a banaso kana wasa da addu'a, kasan aikin nan naka akwai maƙiya sosai dole sai kariƙa neman kariya wajen Allah, nima ina nan ina tayaka, Allah yamaka albarka yasa kafi haka Autana". Murmushi Khalil yayi yace "Ameen Mom, dama Ina so ince miki zan dawo da Nazeefa wurinki sai tazauna anan". "Ok ai babu damuwa kadawo da ita, dama nan ɗin yafi dacewa kakawo ta, yanzu katashi muje kaci abinci tunda an gama". Be musa mata ba yamiƙe yanufi wajen dainning ɗin, itama biyo shi tayi suka zauna a jere sannan tayi saving ɗin sa, yasoma cin abincin ita kuma tana masa hira, shi kuma sai dai yasaurare ta da kunni kawai wani lokacin kuma yana gyaɗa mata kai. ****** Shigowan ta sau biyu cikin ɗakin tana ganin ta kwance, sai dai ta kasa aiwatar da abinda tazo yi ɗin, yanzun ma har zata koma sai kuma tayanke shawaran kawai zuwa, ahankali tatako tazo bakin gadon tasami waje tazauna, shiru tayi don ta rasa ta ina zata fara, ba kasafai suke magana ba tun kwana biyu da zuwanta cikin gidan, daurewa tayi dai ahankali takira sunan ta Nazeefa da idanuwanta ke kulle sai dai ba barci take yi ba, hakan yasaka tabuɗe idanunta tabi Lubnan da kallo, sai tasakar mata murmushi tace "Na ganki shiru ne tun ɗazu, shiyasaka nace ko zakizo kiraka ni zanje gidan mu kar in fita in barki ke kaɗai". Itama murmushi tayi mata sannan tatashi zaune tace "Ai babu damuwa anty, muje in rakaki, dama zaman ya ishe ni haka". Murmushin samun nasara Lubna tayi tatashi tana faɗin "To muje ko". Miƙewa Nazeefa tayi taɗau hijabinta dake ajiye saman gadon tasaka, tabi bayan Lubna da har tasoma tafiya zata fice a ɗakin, ahankali take takawa sai dai tafiyan ta ba normal take yin sa ba sabida aikin dake cikin, hakan yasaka take ɗan duƙawa kaɗan, fitowa sukayi daga cikin gidan suka tunkari bakin Gate, har suka ƙarisa babu kowa, shima me gadi ya zagaya baya, don haka kai tsaye suka tunkari ƙofan Lubna tabuɗe suka fice Daga can nesa wata baƙar mota ce aka faka, ba'a ganin cikinta ko kaɗan, tunda suka fito Lubna tahango motan don haka Direct wajen suka nufa, ita dai Nazeefa sai bin bayanta take yi tana yi tana kalle-kallen tsarin wajen, gaba ɗaya layin gidajen masu kuɗi ne kamar g.r.a haka layin yake. . _shin me zai faru?🤔 Ina Lubna zatakai Nazeefa?_ _ku bini asannu don jin me zai faru._ *More comments more post* 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ [9/2/2020, 1:47 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 10* Har sunyi rabin wajen motan sun kusa isowa sai ga motan Khalil ta shanyo kwana, ahankali ya'iso wajen su yatsai da motan yana zuge glass ɗin motan, tsananin ruɗewa Lubna tayi har batasan sanda tazaro idanu waje ba tana kallon shi kamar yanda shima ɗin yake bin su da kallo, sai da yagama ƙare musu kallo kafin yasauke idanunshi kan Lubna wacce tagama tsurewa yace "Me yafito daku nan?" Gaba ɗaya ta rasa ma me zatace sai duƙar da kanta da tayi tana jin ƙirjinta na bugawa kamar zai faso waje "Kushiga mota". Yace dasu yana ɗauke kan shi daga kallon su Nazeefa ce tafara buɗe gaban motan tashige, ita kuma Lubna jikinta na rawa tabuɗe baya tashige, jan motan yayi slowsly yanufi gida, sai da yayi hon har sau biyu kafin Gateman yabuɗe masa, kutsa hancin motan yayi ciki ya'isa har packing space, bayan ya tsai da motan gaba ɗayan su suka fita sukayi cikin gidan, yayinda shi kuma yatsaya cire wayan sa dake chagi yafito, Direct wajen me gadi yanufa, tun sanda me gadi yahango shi yanufo shi dasauri yana faɗin "Ranka yadaɗe Barka da zuwa, sannu da dawowa". Fuskar shi aɗaure yace dashi "Meyasaka kabar Nazeefa tafice cikin gidan nan?" Me gadi da mamaki yacika shi yace "Nazeefa kuma ranka yadaɗe? Ai banga tafita ba, wlh bansani ba ranka yadaɗe". "Kenan wasa kake yi da aikinka ko? Ina kaje har tafita cikin gidan nan baka sani ba?" "Wlh ranka yadaɗe wlh bansan tafita ba, kuma wlh babu inda naje in banda zagayawa da nayi". Khalil soka hannun sa yayi cikin aljihu yana kallon sa yace "Kakula da aikinka bana son wasa, idan har kana min irin haka tabbas zamu sami matsala ni da kai". "To ranka yadaɗe insha Allah, ayi haƙuri bazan sake ba". Be sake cewa komai ba yajuya yatafi, yana shiga cikin Palon babu kowa Direct ɗakin su yanufa, yabuɗe yashiga yana bin su da kallo har yanzu fuskar shi a ɗaure, yayinda su ma kallon shi suke yi suna zaune tsamo-tsamo saman gado musamman ma Lubna da tagama tsorata da yanayin shi "Meyasaka kuka fita cikin gidan nan? Ina zakuje?" Yayi tambayan yana kallon Lubna da idanuwansa masu kaifi da burgewa Cikin rawan murya tabuɗi baki tace "Uhm dama.. dama zamuje gidan mu ne". Wani kallo yayi mata me cike da ma'anoni sannan yace "Kar in ƙara ganin kun fita cikin gidan nan, idan har gida kikeso kije kifaɗamin zan saka drever yakai ki, kuma ke kaɗai zaki fita karki soma janta kufita tare, kina jina?" Yaƙarike maganar da kakkausan murya Atare suka gyaɗa mishi kai, har Nazeefa da itama tagama tsorata dashi domin bata taɓa ganin shi ahaka ba, shi mutum ne me sauƙin kai ba kasafai yake nuna fushin shi ba Juyawa yayi yafice yanufi ɗakinsa, akan gado yazauna yasoma cire Combat ɗin ƙafan sa da socks ɗin sa, sai da yagama yacire farar suit ɗin dake saman farar rigan ciki ya'ajiye, ahankali yazuge necktie ɗin wuyan sa yacire gaba ɗaya ya'ajiye, agogon hannun sa yacire itama ya'ajiye sannan yakwanta yana lumshe idanun sa, yayinda ƙafafunsa ke ajiye a ƙasa gangan jikin sa kaɗai ke saman gadon, tunani kawai yake yi cikin ran sa har be san sanda time yaƙure masa ba, miƙewa yayi ahankali yanufi cikin Toilet, wanka yasoma yi kafin yaɗauro alwala yafito, Direct gaban mirror yanufa yazauna, sai da yawarware shawul ɗin dake kan sa sannan yasoma goge kan, bayan ya gama yabusar da kan da handrayer sannan yasoma shafa Expensive lotions ɗin sa, har gashin kan sa sai da yashafe su da mayuka masu tsananin ƙamshi da ƙara taushin suma, yaɗau kumb yataje gashin yagyara shi yayi matuƙar kyau, kana yamiƙe yanufi sif ɗin sa, wata farar riga me gajeren hannu yaciro sai blue jeans yasaka, da alamu dai shi ma'abocin son fararen kaya ne, wrest watch ɗin sa da Combat ɗin ƙafan sa duk farare ne yasaka, sai da yagama gyara jikin sa yafeshe ko ina na jikin sa da farpume's ɗin sa masu ƙamshin daɗi kana yaɗau wayan sa da car keey yafito, fita yayi yanufi wajen motan shi yashige yaja yana danna ma me gadi hon, ba ɓata lokaci yabuɗe masa yafice, sai da yatsaya bakin masallaci yafita yayi sallan asar kafin yakoma yaja yatafi A bakin gidan Brr. Tahir yatsaya yaɗau wayan sa yakira sa, babu jimawa shima yafito yashiga cikin motan yaja suka tafi, a wani madaidaicin gida suka tsaya wani mutum yafito daga gidan yayi musu jagora suka shige ciki, tattaunawa sukai tayi akan aikin su har wajen magrib suna tare, sai da sukayi sallan magriba da isha'i kafin suka rabu, har gida Brr. Khalil yasauke Brr. Tahir kafin shima yakamo hanya zuwa gidan shi. Koda ya'isa kai tsaye ɗakin shi yawuce, yacire kayan jikin shi yabar wandon da singlate yafito palow, a saman sofa yazauna yana ɗaukan remote yakunna t.v, sai kuma yatashi yanufi kan dainning yahaɗa tea me zafi yadawo yazauna, yana sipping tea ɗin idanunsa na kan t.v, ahaka har yashanye sannan yatashi yamaida cup ɗin saman dainnig, kashe kallon yayi yakashe komi na na'ura dake cikin palon yanufi ɗakin sa, wanka yayi yasauya kayan barci, yazauna bakin gado yasoma aiki cikin computer ɗin shi, wajen ƙarfe 11:56pm yagama sannan yakwanta. ........ ........ .......... *WASHE GARI* Ƙarfe 03:10pm yatashi daga aiki, ya fito cikin office ɗin sa yana rufewa itama Bilkisu tafito daga office ɗin ta, har tagama rufe nata office ɗin shi be gama ba, sai tatsaya tana kallon shi har sanda yagama yajuyo sukai ido huɗu, dasauri yaɗauke kan sa yasoma takawa yana barin wajen, itama biyo bayan shi tayi har zuwa inda ya'ajiye motan sa, yana ninyan buɗe motan yatsinkayi muryan ta abayan shi "Dan Allah kasauke ni agida mana, yau banzo da tawa motan bane, kuma gashi ana jirana Uncles ɗina sun zo daga garin mu". Juyo da kansa yayi yakalle ta sai kuma yataɓe baki yabuɗe motan sa yashige, hakan yasaka itama tazagaya dasauri tabuɗe gaban tashiga, be ce mata komi ba yakunna motan yaja suka fice, shiru cikin motan babu wanda yayi magana, sai dai ita tana yi tana satan kallon shi, sosai yayi mata kyau yau ɗin cikin shigan sa da yasaba yi koda yaushe, suit ne kalan ash da ƴar cikinta milk colour, haka komi da yasanya sun kasance milk ne har ta da Expensive wrest watch ɗin da yaɗaura a hannun sa A bakin Gate ɗin gidan su yatsai da motan, ita kanta batasan an kawo ba sai da taji tsayuwar motan, kallon gidan su tayi sai kuma takalle shi don bata zata zai iya gane gidan nasu ba duk da zuwan sa sau ɗaya ne, tun farkon fara aikin su tare lokacin tanemi yarage mata hanya, cikin sanyin muryan ta me daɗi tace "Nagode.." Sai kuma tayi shiru tana wasa da hannun jakan ta, ɗan ɗago kanta tayi takalle sa idanuwanta na cikowa da hawaye tace "Har yanzu dai bazan daina nuna maka ƙaunar da nake maka ba, ina ƙaunarka Ib, ina ƙaunar ka sosai, ni kaina bazan iya juran yanayin da natsince kaina aciki ba shiyasa nakasa ɓoye ƙaunar da nake maka, don Allah koda sau ɗaya ne tak a rayuwa kafurta min kana sona ko zuciyata zata sami sukuni, Allah ne yaɗaura min ciwon son ka kuma kai kaɗai ne zaka iya min maganin ta, har yanzu har gobe bazan gaji ba Ib, ina matuƙar matuƙar ƙaunarka". Tana kawo nan azancen ta tayi shiru tana jan numfashi, sai kuma tabuɗe ƙofan tafice, idanuwan shi yaɗago yabi ta da kallo, tafiya take yi tana share hawayenta da gefen gyalen ta har tashige cikin gidan nasu, kafin shi kuma yaɗauke idanun shi yana sauke ajiyan zuciya, ya sani duk acikin ƴan matan da suke nuna masa ƙauna ba wacce takai Bilkisu, yasan da cewa ita ɗin ta daban ce cikin mata, tana da hankali da nutsuwa, gata kyakkyawa babu abunda tarasa, sai dai ko kaɗan shi soyayya bata burge shi, tunda yake be taɓa son wata ɗiya mace ba, be san ma ya ake soyayya ba, shi dai kawai yasan da cewa mata suna matuƙar bashi tausayi, sosai yake jin ta cikin ran shi sai dai bazai iya yin abinda take so ba ahankali yaja motan sa yaci gaba da tafiya, zuciyan sa cike fal da tunanin ta. . *Comments* *Vote* *Share* [9/3/2020, 2:24 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 11* A Compound ɗin gidan sa yayi packing ɗin motan, tsawon mintuna 5 yaɗauka kafin yabuɗe murfin motan yafito, ahankali yake tafiyan nasa cike da salon burgewa har yakai bakin ƙofan main Palon yabuɗe yashiga yana motsa bakin sa, babu kowa ciki sai ƙaran T.v plasma da yacika cikin Palon sai aiki yake yi shi kaɗai, Direct ɗakin sa yanufa yashige yarufo ƙofan, asaman gado ya'ajiye briefcase ɗin sa, yazaro wayoyin sa dake aljihun wando yazube su akan gadon, sannan yacire links ɗin rigan sa yakuma cire agogon hannun sa yabuɗe drower yasaka, zama yayi saman gadon yaɗau wayan sa yalatsa yakara a kunni "Kihaɗa ma Nazeefa kayanta kice tajira ni a palow". Abinda yafaɗa kenan yatsinke kiran ya'ajiye wayan, tashi yayi yanufi Toilet yasillo wanka yafito ɗaure da towul ajikin sa, duk jikin sa ruwa ne ke ɗiga haka yanufi gaban mirror yazauna a stool, shiru yayi yana kallon kan shi a madubi, kyakykyawan surar jikin sa yake bi da kallo na tsawon lokaci kafin yaɗauke idanun sa, sai kuma yamayar da idanun nasa yana ƙare ma beauty face ɗin sa kallo, ya daɗe ahaka shi kan sa be san meyasaka yake kallon halittan nasa ba, amma dai yasan da cewa shi kan sa yana tsananin burge kan sa, komi nasa me kyau ne musamman ma ƴan manyan idanuwan sa masu ɗaukan hankali farare ƙal dasu, da yawa ƴan mata suna nuna masa matuƙar ƙauna kamar su cinye sa, tun yana ƙarami haka yataso me farin jinin jama'a kowa son sa yake yi ba mazan ba ba kuma matan ba, shi ba mutum bane me yawan shiga abun da babu ruwan sa kuma ba me yawan magana bane shiyasaka wasu suke ce mishi me girman kai, kuma ba haka bane sai dai in baka zauna dashi ba, anan ne zaka fahimci halin sa sosai yake da kirki da sauƙin kai. Ajiyan zuciya yasaki yasoma shafa Lotions ajikin sa, bayan ya gama sai yaɗau kumb yataje suman kan sa yakwanta luf sai shaining yake yi, kai da gani kasan sosai kan yake shan kuɗi wajen gyara, miƙewa yayi yanufi sif ɗin sa yaciro kayan sa, sanya wa yayi yana gyara wuyan rigan tare da ɓame bottles ɗin, yadi ne fari ƙal tamkar tissue har singlate ɗin da yasaka ciki ana gani, sun bala'in ɗaukan golden skin sa, sosai sukai mishi kyau, sai da yafeshe jikin sa da farpume's ɗin sa sannan yasaka Black cover shoes a ƙafafun sa, yanufi gaban gadon sa yaɗau wayoyin sa da mukullin mota yatako yabuɗe kofa yafita Dasauri taɗago kanta takai duban ta gare sa, haɗa idanun da sukayi yasaka hawayen dake maƙale a kurmin idanun ta daman zubowa, saurin ɗauke kanta tayi taduƙar dashi ƙasa, sosai tashiga damuwa tun sanda Lubna tasanar mata da abinda yace, duk da batasan ina zai kai ta ba but ko kaɗan bata son rabuwa dashi, bata son tayi nesa dashi, a ɗan zaman da tayi na kwana uku rak cikin gidan sa yafiye mata sauran tsawon shekarun da tayi a duniya, zaman ta gidan sa tamkar wani haske ne cikin zuciyarta Muryan sa da yadoki kunnin ta shi yadawo da ita duniyar da taburma "Tashi muje". Abinda yafaɗa kenan yayi gaba, itama kuma ahankali tamiƙe tajanyo trollyn kayan ta tabi bayan sa, lokacin da ta'isa jikin motan har ya shige ya bar mata Boot abuɗe, ɗaya daga cikin ɗan aikin gidan shi ya'amsa trolly ɗin yasaka a Boot ita kuma tabuɗe gaban motan tashiga, keey yayi ma motan yaja ahankali yafice daga gidan, cikin motan ma babu wanda ke magana cikin su, Nazeefa kaɗan-kaɗan take ɗago kanta takalle shi tana sharan hawaye, tuƙin sa yake amma duk yana lura da ita, kuma akan idanun sa ɗazu hawayen ta yazuba, ahankali cikin cool voice ɗin sa yace "Lafiya kike kuka?" Tambayan ba kaɗai yashige ta ba don batayi zaton yasan tana yi ba, ɗago kai tayi takalle shi, sosai yayi mata kwarjini da cika idanu, sauke kanta ƙasa tayi tana ɗan saka yatsa tashare sauran hawayen nata, bata iya buɗe baki ba bare tabashi amsa, hakan yasaka tayi shiru don batasan me zatace ba, shima ɗin be sake tambayan ta ba, sai can kuma da sukayi nisa yace "Ko dai ciwon ki ne ke miki zafi?" Yafaɗa maganan kamar me raɗa yana kallon ta Sai da taɗago kai takalle sa sannan yakau da kanshi, cike da sanyin murya tace "A'a, bana son rabuwa da kai ne yaya". Jin maganan yayi ta ɗan duke shi, hakan yasaka yasake kallon ta sai kuma yaɗauke kai yamaida ga titi "Kidena damuwa Nazeefa ba wani waje zan kai ki ba, wajen Mahaifiyata zan mayar dake zaki fi samun kulawa, ke yarinya ce yakamata ace akwai wacce zata riƙa kula dake, zaman ki gidana akwai takura da yawa, ki kwantar da hankalinki nasan kina tunanin ko mun rabu kenan". Ahankali tagyaɗa masa kai tana ƙara share sauran hawayen nata da suka zubo mata, sosai taji zuciyar ta tayi sanyi, sai dai tafi ƙaunar zama agidan sa fiye da wani waje A bakin Gate ɗin gidan yatsaya yayi hon kafin aka buɗe masa yashiga, bayan yayi parcking fitowa sukayi, sai da yabuɗe Boot yaciro mata trolly ɗin ta kafin suka nufi cikin gidan, Mom na zaune a palow suka shigo da sallama, amsa musu tayi tana kallon su, sai kuma tasaki murmushi tana faɗin "Bari in cinka baƙuwa ta, ƴata Nazeefa sannu da zuwa". Ita Nazeefa kallon Mom kawai take yi cike da burgewa, sosai taga kamannin Khalil a fuskarta duk da skin ɗin su ba ɗaya bane, take kuma taji sauran farin cikinta ya dawo mata da ganin matar, muryan Khalil ne yakatse mata tunanin ta "Mom ai dama kinsan da zuwan ta, ba wani cinka da kika". Ya faɗa maganar ne lokacin da ya'isa gare ta yazauna agefen ta, ƙara sakin murmushi Mom tayi tace "To ai bansan ta a fuska ba dai, tunda rowanta kake ta min sai yanzu da kaga daman kawo ta, kinji ƴata ƙariso taho kizauna anan". Kanta aƙasa tataho ahankali cike da kunyar matar tazauna agefen ƙafarta "Ah kin zauna a ƙasa kuma? Taso kizauna anan mana, tashi maza". Babu musu kuwa tatashi tazauna agefen ta, yayinda suka saka Mom ɗin a tsakiya, cikin sanyin murya tace "Ina wuni Mama". "Lafiya lau Nazeefa, ya jiki da fatan yanzu kinji sauƙi sosai ko?" Gyaɗa kanta tayi sai kuma tace "Alhmadulillah dasauƙi". "Allah yasawaƙe, kinga yanzu kin dawo gidan mu, ina fata zakiji daɗin zama dani? Kizauna anan tamkar ƴata daga yau kin zama ƴar gidan nan kema". Murmushi kawai Nazeefa tayi tana wasa da yatsunta "Bari in saka anuna miki inda zaki zauna ko? Kisaki jikin ki kinji daga yanzu na zama mahaifiya gare ki". Gyaɗa kanta tayi tana jindaɗi aranta, sosai matar tayi mata, gata mace me fara'a ko kaɗan ba ƙyama a ranta, nan Mom tayi kiran me aikinta, tana zuwa tace "tatafi da Nazeefa takai ta ɗakin da tasanya ta gyarawa, bayan sun tafi ne takalli Khalil da tun soma maganar nasu yaciro wayansa yana latsawa tace "Kai masha Allah, yarinyan gata kyakykyawa, daga gani tana da hankali da nutsuwa, da alama dai zanji daɗin zama da ita, har naji tashiga raina sosai wlh tamkar ƴata ta cikina". Ɗan ɗago kan sa yayi yakalle ta, sai kuma yamaida idanun sa kan wayan yaɗan latsa ta kaɗan yasaka cikin aljihun gaban rigan sa yace "Ni zan tafi Mom, ba zama zanyi ba ina da wani aiki kinsan gobe ne tafiyana, ina son inje wani waje ne". Yaƙarike maganar yana miƙewa tsaye Mom tace "to shikenan, amma dai zaka dawo ko zuwa anjima ne don muyi hira, bana son katafi bamu sake haɗuwa ba kaji ko?" Murmushi yasaki me kyau da burgewa, yaduƙo gaban ta yasakar mata kiss agoshi yaɗago yana kallon ta yace "Mom ai dole ne nadawo muyi sallama, idan ma ban sami dawowa yau ba da safe zan dawo kinji". Itama murmushi tayi tace Ok Autana, kasan yanzu ma drever yatafi ɗauko Dad ɗin ku a airport". Ɗan waro idanu yayi yace "Dagaske Mom?" Hararan sa tayi tana jan kumatun sa tace "Da ƙarya". Dariya yayi yace "Sorry Mom, bari in zauna to in jira sa". "A'a tashi katafi, kai da baka da lokaci, katafi zuwa anjiman in kadawo sai kazo ko kuma goben kamar yanda kace". "Ok Mom ni na tafi, ki miƙa masa gaisuwa ta kafin nadawo, kice masa kuma ya'ajiye min tsarabata da kyau zanzo in amsa da kaina, kar yasoma yaba Bro". Dariya sukayi gaba ɗayan su, sai da yasake mata kiss a goshi kafin yafice yana faɗin "Mom byeee". . ******* ******* **** Ƙarfe 05:11pm. Halwa ce zaune bakin ƙofa tana yankan ƙunba wani yaro yashigo gidan yace "Wai ance Halwa tazo?" Ɗago kai tayi takalli yaron sai tamayar da idanunta kan yankan ƙunban da take yi tace "In ji wane?" "Wani ne a mota". Shiru tayi taci gaba da abinda take yi, yaron kuma yatsaya yana kallon ta, daga cikin ɗaki Mama tace "Wai inace dake akeyi Halwa?" "Mama ƙyale shi yatafi, kai kaje kace bata nan". Tafaɗi hakan lokacin da tasake ɗago kanta takalli yaron Har ya juya zai tafi Mama tace "Kai yaron nan yimaza kaje kace gata nan zuwa". "To". Yaron yafaɗa yana rugawa waje da gudu "Kitashi kiwuce kitafi da Allah bansan wulaƙanci". Zumɓuro baki tayi kamar Maman tana ganin ta tamiƙe tashige ɗaki sai magana take yi ƙasa-ƙasa, Mama kamar taji me take cewa tace "Ke kenan kullum koran samari, inace dai dole sai an ɗaura miki aure da Nuran shine kin zama mallakin shi? Kaji min shashashan yarinya haka ake yi". Halwa da tafito daga ɗaki riƙe da gyale a hannu tace "To Mama meye amfanin fitan nawa tunda inada wanda nake so?" "Kinci gidan ku, ai babu yanda Allah baya sanja ƙuduran sa, kuma fitan ki ai ba zai hana kisami wanda kikeso ba, Ni wulaƙanci ne bana so wlh, in kin fita sai kice mishi kar yasake dawowa ba shikenan ba?". Yafa gyalen tayi kan doguwar rigan ta na atamfa me ruwan toka da akai mishi sirki da ja da milk, slippers tasanya tafice batare da tabi takan Mama dake ta surutu ba. [9/3/2020, 7:51 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 12* Tana fitowa suka haɗa idanu da Yazeed da yake jingine jikin motan sa, tun sanda tafito yasoma murmushi har ta ƙari so wajen sa da sallama a bakin ta, amsa mata yayi still yana murmushi yace "Barka da fitowa gimbiyar Mata kyakykyawar yarinya". Murmushi tayi tace "fatan kazo lafiya?" Yace "tun sanda dai muka haɗu dake ban sake jin lafiya ajikina ba, har kuwa fitowar da nayi daga gida nazo gare ki, but yanzu da nagan ki agabana sai naji kamar an kwaso duk lafiyan mutanen duniya ne an ɗaura min ni kaɗai, kinga kuwa yanzu zan iya ce miki lafiya ƙalau kenan". Murmusawa tayi tana kallon shi tace "Na kula dai kai ɗin nan kana da son wasa da yawa". Shima murmushin yayi yace "Gaskiya ne ƴan mata, to fatan kina lafiya kema? Ya su Mama da kowa da kowa? Kinga ban zo ba sai yau ko? Wlh kwana biyun nan aiki ne yayi min yawa, amma baki ji yanda na azabtu ba da rashin ki, ji nake kamar na shekara ɗari tare dake, sosai nashiga damuwa Burina kawai nazo nasake tozali da kyakykyawar fuskar nan taki". Ita dai batace komi ba sai murmushi da take yi "Ƴan mata da fatan dai za'a bani matsuguni acikin zuciyar ki, wlh sosai nakamu da ƙaunar ki, ina fata dai babu wanda yariga ni?" Halwa tace "ai tun farko kamar in ban manta ba sai da nafaɗa maka ni ɗin mallakin wani ne, sai dai in baka haƙuri Malam Yazeed domin ma fitowan nan da nayi nazo ne nasanar maka an riga da anyi min miji". Cikin fuskar damuwa yace "Dan Allah wai dagaske kike yi?" "Wlh dagske nake maka, ina da mijin aure kuma nan ba da daɗewa ba za'a sanya mana ranan aure ni dashi". Cike da rashin jin daɗi Yazeed yace "Yanzu shikenan wani ya rigani? Shikenan kina nufin zan rasa ki? Wlh Halwa sosai na kamu da ƙaunar ki a lokaci guda, yanzu kuma bansan ya zanyi in cire son ki cikin zuciyata ba". Cike da tausayin sa saboda sosai tayarda dashi kuma ta ga tsantsan gaskiyar sa a fuskar sa tace "Kayi haƙuri a sannu zaka manta dani ai, dama baka daɗe da sani na ba, don haka insha Allahu nan ba da jimawa ba zaka neme ni karasa ko tuna ni bazaka sake yi ba". Ɗan murmushin gefen baki yasaki yace "Kayya a naki fahimtar kenan Halwa, wlh bakisan yanda nake jin ki cikin zuciyata bane zai yi wuya nacire ki sabida ƙaunar da nake miki ya wuce tunanin ki, ni kinga ban iya saka abu cikin rai ba, kuma zan faɗamiki gaskiya ta kece macen da nafara so nafara kulawa a matsayin wacce nake ƙauna, taya kike tunanin lokaci ɗaya kuma zan inya manta ki?" Girgiza kan shi yayi sannan yace "Nagode sosai da faɗamin gaskiya da kikayi, Nagode da baki bar ni nasha wahala ba kinji?" Gyaɗa masa kai kawai tayi "To yanzu sai yaushe kuma? Ko bazamu sake haɗuwa ba? Yakamata muyi zumunci don Allah kibani numbanki". Bata musa ba tace "ok babu damuwa". Takaranto mishi numaban kafin tace "Ni zan shiga gida, sai wani lokacin kuma". Yace "to Nagode sai kin ji ni a wayan kenan, kigaida su Mama". Kanta kawai tagyaɗa masa tajuya zata tafi, kawai tayi tuntuɓe da dutse hakan yasaka tayi taga-taga zata faɗi shi kuma yayi saurin taro ta, dai-dai lokacin da Nura yashanyo kwana yagansu ahaka Yazeed ya riƙo ta, kuma sun ƙame ahaka suna kallon juna, wani irin baƙin ciki ne yatokari zuciyar shi, take yaji kishi ya kama shi, tsayawa kawai yayi yana kallon su har sanda yasake ta suka yi magana ita kuma tashige ciki, take yaji zuciyar shi tana faɗin "Daman yaudaran ka take yi abinda take aikatawa kenan, yau Allah ya toni asirin ta". Take kuma yatuna da abinda yafaru jiya, nan yaharhaɗa abubuwan nan da nan yaji zuciyar shi na tafarfasa, aransa yace "Tabbas dole nayi tunani akan maganar ka, wannan dama ce tasame ni". Daga haka yasoma takowa yanufi gidan nasu, yana shiga suka haɗa idanu da Halwa dake tsaye bakin ƙofa tana magana da Mama da har yanzu take cikin ɗaki, murmushi tasakar mishi tace "Yaya har ka dawo?" Ɗan dai-dai ta fuskar sa yayi shima yasakar mata murmushin yanufo ta yana faɗin "Kinga na dawo da wuri ko?" "A'a Yaya, amma dai Allah yasa an dace?" Mama da tafito daga ɗaki itama tace "Da fatan dai an sami abinda akaje nema?" Shiru yayi na ɗan wani lokaci, yayinda duk kan su suka zuba mishi idanu suna jiran amsan shi, sai kuma yasaki murmushi yace "Yau dai an dace, na sami aiki insha Allah komi ya wuce". "Alhamdulillah". Atare suka faɗa hakan, Mama har da shafa hannu saman fuskarta, yayinda Halwa tasaki fara'a tana me cike da farin ciki da jindaɗi Sallaman Baba yakatse Mama dake faɗin "Masha Allah. Allah Ubangiji yasanya alkhairi". Amsa mishi sallaman suka yi, yaƙariso yana kallon su yace "Ya naga kunyi cirko-cirko daku, wani abun ya faru ne?" "Malam ɗan ka yau yasamu aikin dai da yadaɗe yana shan wahala, yau an dace". Fara'a Baba yasaki yace "Ah masha Allah, da kyau Allah yatabbatar da alkhairi". "Ameen duk kan su suka amsa, kafin Mama tace "Bari in kawo maka tabarma Malam". Ɗaki tashige taɗauko tashimfiɗa masa yazauna, itama tazauna gefen shi yayinda Halwa tazauna kan dokin ƙofa tana cire gyalen jikinta tajefa ɗaki, Yaya Nura ma zama yayi a saman kujera ƴar zuƙune dake wurin Baba yace "ina tayaka murna, yau dai gashi ranan da muke jira tazo, to Allah yataimaka yasa kafara a Sa'a". Gaba ɗaya suka amsa da "ameen" Baba yaci gaba da cewa "To yanzu fa an sami abinda ake nema sai kuma aure kenan?". Duƙar da kai Nura yayi, ita kuma Halwa wani farin ciki ne yasake kama ta jin maganar Baban Mama murmusawa tayi tace "gaskiya ne Malam tunda babu abinda za'a jira". Baba yace "to insha Allahu nan ba da daɗewa ba za'a tsai da ranan auren, kuma ba wani daɗewa za'ayi ba tunda dama kana aikin ka, mun dai fi so ne kakama na gwamnatin hakan zai fi, tunda gashi an samu shikenan magana ta ƙare zuwa gobe insha Allahu ko jibi za'a tsai da ranan". Sosa kai Nura yayi yamiƙe yana faɗin "Bari inje wajen abokina". Dariya Mama tayi tace" ko dai kunya ne zai kora ka?" Dariya shima yayi yace "A'a Mama akwai dai abinda zanyi can ne, ni na tafi". Yafaɗi hakan yana ficewa dasauri "Ɗan nema za ma kadawo ne, ke kuma me kike jira, ko ke kunyan bata kore ki bane?" Mama tafaɗi hakan tana mayar da idanunta kan Halwa Itama tashi tayi da gudu tashige ɗaki tana dariya Baba yace "ahh ya haka kibar ta mana tazauna, kunyan wa zataji bayan mu ne iyayen ta?" Dariya Mama tayi tace "bari dai in kawo maka ruwa kashare waɗannan yaran duk gulma ne irin nasu". Koda takawo mishi ruwan hira sukaci gaba da yi duk akan maganar samun aikin Nura, da kuma saka ranan su. . . _shin wani abu ne yafaru jiya da har Nura yatuna?_ _Wanene yafaɗa masa maganar da har yace zai yi tunani akai?_ _wani ma magana ce?_ _JIKAR LAWALI CE_ 😉 [9/3/2020, 10:48 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 13* *WASHE GARI* ƙarfe 02:45pm. Drever'n Brr. Ibrahim Khalil yatafi kai shi airport, suna isa ba ɓata lokaci jirgin su yaɗaga dasu zuwa ƙasan Egypt. _Sai muce Allah yaba da sa'a BARRISTER_🤒 ....... ....... ........ ..... Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, tun sanda yafice gidan tazauna anan palow take ta rizgan kuka, sosai take cikin damuwa abubuwan duk sun haɗe mata, har yau takasa samun mafita, ta kasa samun nasara akan abinda aka saka ta, gashi yanzu mutanen nan sun sako ta gaba, sosai suke mata barazana, gefe ɗaya kuma zuciyarta ta azalzale ta da ƙaunar mutumin da besan tana yi ba, haka kawai take jin baƙin cikin tafiyan nan nasa, shikenan bazata sake ganin sa ba sai sanda yadawo? kuma batasan ranan dawowarsa ba, sai kuma tasake fashewa da kuka tuno mahaifiyar ta da tayi, yanzu da waɗannan mugayen basu ɗauke taba da tuni takoma gida, acan zata zauna har yadawo, "take tatuna sanda yakira ta yana zaune a palow tazo tazuƙuna gaban sa, sai da yagama latsa wayan sa kafin yaɗago kai yakalle ta yace "Gobe zan yi tafiya, zaki iya komawa gida har sanda zan dawo, kiriƙe wannan ko zaki buƙaci wani abun". Yamiƙo mata wasu maƙudan kuɗi, ahankali tasaka hannu ta'amsa tana jin zuciyarta babu daɗi, godiya tayi masa, sannan yabata umarnin "tafiya" Shiru tayi tana ajiyan zuciya, rufe idanuwanta tayi tana sauraron bugun zuciyarta "Meyasaka ban faɗamasa halin da nake ciki ba da yatambaye ni zuwa gida? Wataƙil yataimake ni, ya zanyi da waɗannan mutanen". Take tasake tuno wayan da sukayi yanzu fitan shi, mutumin da yake kiran ta, shine dai yasake kiran ta yana tambayan ta, "ance zai yi tafiya, ko tasan ina zashi?" Runtse idanunta tayi wasu hawaye na sulmiyo mata tuna amsan da tabashi "A'a bansani ba, bansan ma zai yi tafiya ba". Mutumin be ce mata komi ba sai yakashe wayan, da alamun kamar wani abun ne yataso shiyasaka yakatse kiran batare da sun gama magana ba, sake runtse idanun ta tayi zuciyarta na ci gaba da bugawa, tasani dole zai sake kira, amma batasan me zai biyo baya ba idan har sukasan ya tafi? "Wataƙil ma su zo da kansu suyi binciken abinda suke nema". Tafaɗi hakan afili tana buɗe idanuwanta, ɗaura kan ta saman kujera tayi tarufe idanunta tana ci gaba da tunani kamar yanda yazame mata jiki yanzu. . ****** ****** ***** "My dear tashi muje kiraka ni". "Ina yaya?" Tatambaye shi tana kallon shi "Ke dai kitashi kiraka ni, zan amso sabon ɗinki na ne, kuma daga nan sai mu yawata kinsan mun daɗe bamu fita ba". Washe baki tayi tace "hakane Yaya, bari to in sauya kayan jikina". "Ok" yace da ita yana zaro wayan sa a aljihu yasoma dannawa Ita kuma tashige ɗakinta dasauri, tasoma sauya kayan jikinta, wata black and peach colour material me taushi taɗauko daga cikin kayan ta, riga da sket ne sunyi kyau sosai tasaka ajikinta, hakan yasaka kyawun kayan suka sake fitowa sosai sabida yanda yahaɗe da kyan ta, sai da tashafa powder tazizara lipstick a baki sannan tasaka hijabin ta sky maroon da iya kacin sa gwiwa, babu ɗankwali akan ta sai gashinta da tatufke a can ƙasan ƙeyan ta, kasancewar hijabin me hula ne don haka ba'a ganin gashin kanta, flate shoes tasaka kalan baƙi da kwalliyan tuntu asaman me ruwan zamba, fitowa tayi tana faɗin "Yaya na fito, muje to". Ɗago kan sa yayi yana ƙare mata kallo, sai yasaki murmushi yace "Baby kinyi kyau, kinga yanda yarintan ki yasake fitowa?" Fari tayi da idanun ta tace "Dagske yayana?" "Dagaske mana Dear". "Ina kuma zakuje haka?" Cewar Mama da tafito daga ɗaki tana kallon su "Mama raka ni zatayi, zan amso ɗinkina". "To kar dai kudaɗe, nima fita zanyi zuwa sunan Asabe, saura kuma kuje kuzauna inta jiran ki baki dawo ba". Nura yace "Mama bazamu daɗe ba ai, sai mun dawo" Gaba yayi itama Halwa tabi bayan shi tana faɗin "Mama sai mun dawo". "Adawo lafiya". Tafiya suke yi a ƙasa suna yi suna hiran su cike da nishaɗi, kallon ta Nura yayi yace "Ko dai mutaka a ƙasan ne? Naga kamar tafiyan na miki daɗi?" Ɗan waro idanunta masu kyau tayi tace "A'a Yaya tare mana dai napep, akwai rana fa a gari". "Ok my dear, dama bana son Kisha wahala, gwara dai mutari napep duk da nan kusa ne". Lokacin sun iso bakin titi wani me keke napep dake fake ɗan nesa dasu, yatuƙo yaƙariso wajen su yana faɗin "Tafiya ne?" Nura ɗan kallon sa yayi suka haɗa ido yace "Eh bakin kasuwa zaka kai mu?" "Ok kushiga kuɗin ku saba'in ne". "Ai mun sani". Cewar Halwa tana turo baki gaba Murmushi Nura yayi yace "Ke dai da neman magana kike, menene laifin sa anan don yafaɗa miki kuɗin sa?" "Ai Yaya babu wanda be san kuɗin haka bane, tunda ba yau suka saba kai mu ba, wannan fa doka ce da suka saka kuma kowa yasan da hakan ba sai sun sake maimaita mana ba". Ta faɗi maganar ne tana shigewa cikin napep ɗin Me napep ɗin yace "Baiwar Allah kiyi haƙuri ni baƙo ne ai, nayi tunanin ko baku sani bane". Taɓe baki tayi takalli Nura da shima yashigo yazauna a gefen ta tace "Yaya daga nan mubiya cikin kasuwan mana zan siya kayan kwalliya, nawa sun ƙare". "An gama ranki yadaɗe, komi ma kikeso sai kisiya tunda Allah ya kawo mu ko?" Murmushi tasaki cikin jindaɗi tace "Eh Yayana, Nagode sosai, ina jindaɗin yanda kake kula dani". "Babu komi ai, ke ɗin ƙanwata ce kuma Matata insha Allahu". Dariya tayi tana jin farin ciki a zuciyarta, daga nan hira suka soma yi, yayinda me napep tuni yasoma tafiya dama, gab da zasu kawo wajen da za'a sauke su napep ɗin tatsaya "Oh shitt.. dan Allah kuyi haƙuri bari in duba naga me yafaru". Nura yace "ai babu komi, bari musauka anan kawai tunda babu nis..". Be gama faɗin abinda yakeson faɗa ba yaji ya shaƙi wani abu cikin hancin sa, ko sceonds biyar basu sake ba gaba ɗaya suka ɓingire cikin motan daga shi har Halwa har suna gwara kai, murmushi me napep ɗin yasaki yajuya yagyara zaman sa yatada keke napep ɗin yaci gaba da tafiya. . _Tofa 🤔 me kuke tunanin zai faru?_ _da Allah ku ƙara yawan comments yana min kaɗan, kunsan comment ɗin ku shi ke ƙara min ƙwarin gwiwa har in ji ina suburbuɗo muku ba ƙaƙƙautawa, don haka sai ku bada himma, yawan comments yawan post._ 😉🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ [9/4/2020, 7:56 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 14* Ahankali tasoma buɗe idanuwan ta tana rufewa har sanda tabuɗe gaba ɗaya idanun tana kallon rufin ɗakin, ta ɗan jima ahaka tana son tuno abinda ke faruwa kafin komi yadawo ƙwaƙwalwan ta, dasauri tazabura daga kwancen da take tatashi zaune tana kallon tsararren Palon da yagaji da haɗuwa, idanuwanta akan Nura yasauka da shima yake yashe ƙasa da alamun dai shi be dawo hayyacin sa ba, a gefe da gefen sa kuwa wasu mutane ne manya dasu su biyu sun tsaya a kansa, sai kuma tadawo da ganin ta gefen ta dasauri, nan ma wasu mutane biyun ne kusa da ita, da alama gadin su suke yi "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. ina ne nan?". Ta faɗi hakan ne a fili tana jin zuciyarta na tsinkewa, don tasadakar gidan cin kai ne aka kawo su "Gidana ne". Taji maganar ya doki kunnin ta, dasauri tajuyo tana wurwurga idanu, nan kuwa idanun ta yasauka akan sa, yana zaune saman kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sakin murmushi, daga shi sai farar singlate da gajeren wando me ruwan ƙwai da iyakacin sa gwiwa, gefen sa kuma da akwai mutum ɗaya dake tsaye yana gadinsa, wani irin bugawa zuciyarta tayi kamar zatayi tsalle tafaso cikin ƙirjinta, take wani irin tsoro yashige ta har batasan sanda tawaro idanun ta waje ba tana kallon shi, still yana murmushi yace "Barka da zuwa turaka ta Amarya ta, yau dai gaki cikin gidana abinda nadaɗe ina fata da buri kenan". Ahankali yatashi yanufo ta har zuwa gaban ta kafin yadakata yana ƙare mata kallo, sai kuma yasoma zagayeta yana tafa hannun sa, wanda duk taku ɗaya da yake yi tana ji ne kamar yana tafiya da bugun numfashin ta, sai da yagama zagaye ta sannan yazuƙuna agaban ta yana kallon cikin idanun ta da tatsayar akan sa ko motsin kirki takasa yi, sosai ganin shi yayi tsananin firgita ta har tana jin komi na jikinta ya dena aiki, murmushi yasaki yana faɗin "Yau dai na baki mamaki ko? Baki zatan zaki iya zuwa hannun Haris cikin sauƙi ba?" Sai kuma yasaki dariya yaci gaba "Dama nace miki zan kafa tarihi cikin rayuwan ki, zanyi miki abinda har kimutu bazaki taɓa mantawa dani ba, to ga ranan tazo, yau duk zan huce wahalan da kika bani, kin bani wahala sosai Babyna". Yaƙarike maganar yana kai hannun sa saman fuskarta yashafo gefen face ɗinta, kafin yacire hannun dasauri yana zuba murmushi "Ohh kince in dena taɓa ki ko?" Uhmmm saboda na taɓaki kika cire hannu kika wanka min mari ko? To yau kuma bari inga wani hukunci zaki min, kin san me?" Yatambaye ta yana matso da fuskar sa kusa da nata, sai lokacin tasami daman motsa jikin ta, dasauri taja baya tana girgiza mishi kai, nan da nan hawaye suka cika idanun ta suka soma zubowa, cikin rawan murya tace "Don Allah.. don Allah na roƙe ƙa kayafe min, wlh bazan sake ba dan Allah kayi haƙuri". Dariya yakece dashi yana zama dirshan a ƙasa yace "Da wuri haka? Taya kike tunanin mayunwacin zakin da yadaɗe yana farautan abincin da zai ci, yau ya samu sai kuma yasaki abincin yatafi?" Sam wannan ba me yiwuwa bane, yau sai nacika Burina akan ki Halwa, yau zan yi maganin ishin ruwan da nadaɗe ina fama dashi cikin raina, yau zan cire duk wata sha'awan ki dake damuna". Riƙo hannun ta yayi yana son jawo ta jikinsa, tayi saurin ja baya tayunƙura tatashi aguje tanufi wajen Nura da har yanzu yana nan kwance, girgiza shi tasoma yi cikin kuka tana faɗin "Yaya Nura dan Allah katashi, katashi kataimake ni dan Allah Yaya". Dariya Haris yakwashe dashi, dai-dai lokacin da Nura yabuɗe idanu yana jin kukan Halwa yayi saurin zabura yana kallon ta, saurin shigewa jikinsa tayi tana faɗin "Dan Allah yaya kataimake ni zai raba ni da mutuncina, dan Allah yaya karka bari yacin ma burin sa kataimake ni". Tasake fashewa da kuka har da su majina, gaba ɗaya duk tagama tsorata, shima sake riƙo ta yayi yace "Kiyi shiru Halwa babu abinda zasuyi miki kinji, idan har ina raye babu abinda zai same ki kidena kuka". Muryan Haris ne yacika wurin "Kai kuriƙe min shi da Allah". Ai kuwa nan da nan mutanen nan gaba ɗaya sukayo kan su suka damƙo Nura suka rirriƙe shi, shi kuma Haris yafinciko Halwa dake ta faman rusa kuka kamar ranta zai fita, sai roƙon sa take yi tana faɗin "Don Allah don girman Allah kaji tausayina karka raba ni da mutuncina, wayyo Allah don Allah kayi haƙuri kataimaki rayuwata wlh ni marainiya ce". Dariya yake yi yana jan ta yanufi wani ɗaki da ita, Nura kuwa sai son ƙwacewa yake yi yana faɗin "A'a dan Allah karkayi kaƙyale ta, dan Allah kasake ta". Garam haka yaji ƙaran kulle ƙofa da Haris yayi, runtse idanuwan sa yayi yana jin wasu hawaye na kwaranya a idanun sa, tsananin tausayin ƙanwar sa ce yakama shi "Meyasa?" Yafaɗi hakan a fili yana sake runtse idanun sa da ƙarfi jin ihun ta dake shiga kunnin sa ...... ...... ....... ........ .... Tana zaune saman gado ta ƙudundune jikinta cikin hijabin ta, ta haɗa kai da gwiwa tana wani irin kuka na fitan hankali, kuka take yi sosai tana sake matse kanta da ƙafafunta waje ɗaya, ji take yi ina ma Allah yaɗauki ran ta a yau ɗin, ko kaɗan bata fatan tasake minti ɗaya cikin duniyar nan Buɗe ƙofan ɗakin akayi, Nura ne yashigo idanuwan sa ƙyarr akan ta, ahankali yasoma takowa zuwa wajen ta yana jin kukan ta na shiga masa har cikin ƙwaƙwalwa, sosai kukan nata ke taɓa masa zuciya, koda ya isa hannu yasaka yadafa kafaɗan ta, sai taɗago dasauri tana kallon sa da idanuwanta da suka gama rinewa sukayi jawur sai tsiyayan hawaye suke yi, dasauri tasaka hannu biyu tariƙo ƙafafunsa tatusa kanta ajikin sa tana sake fashewa da wani irin kuka me tsuma ran me sauraro, ahankali yaɗaura hannun sa saman kan ta zuciyarsa cike fal da tausayin ta, so yake yi yararrashe ta amma ko kaɗan yakasa buɗe baki, be san da wani kalma zai fara ba, ita kuwa sake tusa kanta take yi cikin kuka da ba'a jin muryan ta sosai tace "Yaya.. Yaya ya cuce Ni, ya cuce ni Yaya ya gama da rayuwata, ya raba ni da martaba na na ɗiya mace, yaya ya gama dani wlh ya gama dani, wayyo Allana nashiga uku na lalace". Kuka tasake kecewa dashi tana buga kanta saman ƙafafunsa, dasauri yariƙe ta yana tallabo fuskarta yace "Ki dena kuka Halwa, kidena kuka dan Allah, kukan ki na taɓa min zuciyata, dan Allah kiyi shiru kitashi mutafi kinji". Girgiza kan ta tasoma yi cikin kuka tace "Yaya ina zani? Ina zani da wannan abun kunyan? Ina kake so naje yaya? Dan Allah yaya katafi kabar ni anan, katafi kabar ni zan kashe kaina ne, bani da sauran wani farin ciki cikin rayuwan nan, wlh Yaya mutuwa zanyi, zuciyata zata buga, dan Allah yaya kakashe ni nahuta.." Saurin ɗaura hannun sa saman bakin ta yayi yana kallon ta yace "Ki nutsu Halwa dan Allah, kinsan me kike faɗa kuwa? Ni Yayan ki ne kuma zan rufa miki asiri, babu wanda zai sani wlh har Mama, nayi miki alƙawari kuma zan aure ki, nasan abinda kike tunani kenan, Halwa babu wanda zai ji kitashi mutafi gida dan Allah". Daƙyar yalallaɓa ta tamiƙe, yana riƙe da ita suka fito palow da babu kowa ciki, ɗaukan mata takalmanta yayi yace "tasanya" babu musu tasaka har lokacin hawaye take zubar wa, fitowa suka yi cikin gidan, wajajen babu wasu gidaje da yawa, don haka sai da sukayi tafiya sosai sannan suka kawo bakin titi, Halwa bata iya tafiya sai da taimakon Nura, gaba ɗaya ajikin sa take ya rungume ta ahaka suke tafiya, basu jima da tsayuwa ba suka sami napep suka hau, a ƙofar gida yasauke su suka fito suka shiga gidan, a cikin zaure Nura yadakata yana kallon ta yace "Dan Allah kidena kukan nan karki sa Mama tafahimci wani abu daga gare ki, bansan me zance mata ba". Gyaɗa kanta tayi tana saka hannu tasoma share hawayen ta, still kuma wasu na tsiyayowa, Nura yasoma shiga yaleƙa yaji shiru, sai yadawo yariƙo ta suka nufi ɗakinta, a saman katifan ta yazaunar da ita sannan yafita, sai da yataɓa ɗakin Mama yaji shi a kulle, ashe be kula bane labule tasaki takulle ɗakin, koda yatura yaga ƙofan ya buɗe, sai da yaleƙa ko ina yatabbatar babu ita sannan yadawo cikin ɗakin Halwa, tana nan kwance sai kuka take yi, ƙarisowa yayi kusa da ita yakira sunan ta, shiru tayi bata amsa ba "Kitashi kigyara jikin ki Mama bata nan, Halwa karki sake Mama tafahimci akwai wata matsala atare dake kinji ni ko?" Kuka tasake fashewa dashi tana ɗaura hannun ta saman fuskarta "Wai don Allah kukan na menene? Inace duk dan ni kike yi kuma nace zan rufa miki asiri zan aure ki". Buɗe idanunta tayi tana kallon shi, sai kuma tarufe idanun taci gaba da kukan ta, sam bazai gane me take ji cikin zuciyarta ba, amma tasan da cewa komi nata ya ƙare, Haris ya gama cutar ta har abada, bazata taɓa yafe mishi ba". Miƙewa yayi yana kallon ta yace "Ni zan fita, kidena kukan nan haka dan Allah, ki saka ma zuciyar ki salama Allah zai saka miki, kinsan baza mu iya faɗa dashi ba ya riga da yafi ƙarfin mu, kibar sa da Allah kinji My Halwa?" Zuciyarta ne tayi mata sanyi, shiru tayi tana sake lafewa saman katifan sai ajiyan zuciya take yi "Yauwa my dear dan Allah karki bari Mama tafahimci kinyi kuka bare tasan wani abu na damunki, yanzu bari in fita yanzu zan dawo kinji?" Gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma yafice, ahankali taci gaba da kukan ta, tasan da cewa sosai tayi dacen Yaya, wanene zai iya auren ta da wannan tabon cikin rayuwanta? Amma gashi Yayan ta mafi soyuwa cikin ran ta ya amince zai aure ta bayan yasan abun da yasame ta, tabbas yayan ta ya cika masoyin gaskiya, da ko wani namiji zai fahimci cewa ko wace Yarinya da hakan yasame ta ƙaddara ce Allah yarubuto mata, su gane cewa auren ta babban jihadi ne kuma sadaukarwa ne, da mata da yawa da suke kukan baƙin ciki sun dena. Ji tayi ƙaunar yayan nata na sake ninkuwa cikin ranta "Allah Sarki Yayana, tabbas kai me ƙaunata ne da bansan ya zanyi ba, wani miji zan aura da zai iya zama dani ahaka? Nagode Yayana ina matuƙar ƙaunar ka, Nagode Nagode sosai da karufa min asiri". Tafaɗa maganar afili tana sakin murmushi kamar yayan nata na ganin ta, sai kuma can tafashe da kuka tana cewa "Allah ya isana mugu azzalumi, bazan taɓa yafe maka ba, insha Allah sai anyi ma yaranka kaima abun da kayi min, mugu azzalumi kawai". "Ke da wanene haka kike ta ja mishi Allah ya isa?" . _Toooo 🤔 me zai faru?_ _kuna ganin asirin ta zai rufu kuwa?._ [9/6/2020, 7:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *⚜{{F.W.A📚}}* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 15* "Ke da wanene haka kike ta ja mishi Allah ya isa?" Cewar Mama tana bankaɗo labulen Dasauri taɗaura hannu a saman fuskarta, cikin ruɗewa tace "Ahm Ma.. Babu kowa". "Ya zakice min babu kowa bayan naji da kunnina kina mishi Allah ya'isa, tukunna ma me yayi miki da za'ayi ma yaran shi?" "Mama wani ne fa yakusa yabige ni, shine sai ƙunduma min zagi yake yi, shine fa abun yanzu yake damuna". Guntun tsaki Mama taja tana sakin labulen tace "Shine ke kuma tunda baki da haƙuri zakizo kina taja mishi Allah ya isa? Allah yashirya ki Halwa, nima da naji ku shiru ne nafice abuna". Ɗaki Maman tashige tana ci gaba da surutun ta, yayinda Halwa kuma gyara kwanciyan ta tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da fargaba, rufe idanuwanta tayi tana jin wani kukan na sake zuwan mata tuna abun da yafaru da ita yau, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne suka tokare mata wuya, take tafashe da kuka tana toshe bakin ta "Shikenan yau an raba ta da abu mafi daraja ajikinta, wai yau ita ce wannan ƙaddara yasame ta, abinda ko a mafarki bata taɓa tunanin wannan ɓakin ranan zai zo mata ba, ya zatayi da rayuwan ta? Ji take yi kamar takashe kanta duk sanda tatuna yau wani namiji yasanta a ɗiya mace batare da aure ba "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Abinda take ta maimaita wa kenan har tasoma jin zuciyarta na mata sanyi. . **** **** **** **** *WASHE GARI* *EGYPT* Zaune yake saman Three sitter ya harɗe ƙafafunsa yana danna Lapton ɗin sa, takardu ne birjik agaban sa sai faman aiki yake yi, yana sanye cikin fararen kaya masu taushi sosai, wandon Three qweater ne sai Rigan me kamar singlate Tun jiya da yasauka a ƙasan yake faman aiki babu ƙauƙautawa, bincike sosai yake akan mutumin da yazo don shi amma har yanzu yagaza samun koda bayani ɗaya akan sa, sosai yake cikin damuwa ko lokacin kansa baya dashi, yanzun ma aikin yake yi but tunanin sa na wani wajen daban, wayan sa da tasoma ringing yayi saurin ɗauka domin dama abinda yake jira kenan "Hellow Poker.." "Ok.. ok turo min da address ɗin wajen". Cire wayan yayi a kunne yariƙe a hannu yana kallon screan ɗin wayan, 1mint sai yaji Message ya shigo, dasauri yabuɗe yaduba sannan yatashi, cikin sauri yasauya kayan sa cikin farar riga me gajeren hannu da blue jeans, sai yaɗaura jaket saman rigan baƙi ne me belt a wajen cikin sa, jaket ɗin me hula ne sai dai be sanya hulan ba iyakan yasaka Combat a ƙafan sa Black, yaɗau wayoyin sa yazuba a aljihu yafito yarufe ɗakin, kasancewar a Hotel ne ɗakin sa yana hawa na uku ne, cikin sauri_sauri yake taka step ɗin har yasauko ƙasa, yana fita yatari taksi yashige suka tafi, a wani haɗaɗɗen club aka sauke sa yafito yabiya me taksi ɗin kuɗin sa kana yamatsa gefe kaɗan yana ƙare ma wajen kallo, tsawon mintuna 5 yaɗauka awajen kafin yajanyo hulan Jaket ɗin ya'aza akan shi yasoma takawa yashige wurin, sosai ciki yake da duhu, mutane ne birjik ciki kowa na sha'anin gaban sa, ba abinda ke tashi aciki sai daddaɗan cool music da aka sanya wasu sai cashewa suke yi, yana shigowa kallon wajen kawai yake yi har ya'isa wani hill chair yazauna yana kallon mutane, tsawon mintoci yana zaune a wajen yana nazarin inda zai ga mutumin da yazo nema, sai kawai yayanke shawaran nufan wasu matasa maza da mata dake zaune gefe can saman wasu haɗaɗɗun kujeru sai kurɓa alcohol suke yi, wata matashiyar budurwa ce taƙariso kusa dashi hannun ta riƙe da cup, kallo ɗaya zaka yi mata kagane irin waɗannan gogaggun karuwan nan ne, skin ɗin ta baƙi ne but ko kaɗan batayi yanayi da ƴan Nigeria ba coz yanayin shiganta da wayewan ta "Hi". Tace dashi lokacin da ta'isa gaban shi Kallon ta yayi sai yaɗauke kan sa dasauri batare da ya amsa mata ba, murmushi tayi tace "Kana son wani abu ne? Naga tun ɗazu kazo kazauna anan kamar kana neman wani ko?" Gyaɗa mata kai kawai yayi batare da yasake kallon ta ba "Ok ko zan iya taimaka maka?" Tafaɗi maganar tana kurɓan Juice ɗin dake hannun ta Shiru yayi kamar bazai ce komi ba sai kuma yace "Ina son ganin Mr. Jay pitter ne, me wajen nan, ance min in nazo nan zan same shi". Murmushi tayi tana gyara gashinta takalle shi dakyau, sai kuma tagirgiza kan ta tana jawo kujera tazauna taci gaba da shan Juice ɗin ta, shiru ne yagibta a tsakanin su har Khalil yana shirin tashi sai yaji muryan ta ya doki kunnin sa "Meyasaka kake neman sa?" Ɗan kallon ta yayi sai yakau da kai be ce komi ba, ƙure shi da ido tayi tana wani irin murmushi tace "Daga Nigeria kake ko? Nima acan nake ai". Taƙarike maganar tana kau da kan ta taci gaba da sipping juice ɗin ta kamar ba itace tayi maganar ba, shi kam kallon ta yake kamar me neman wani abu jikinta, mamaki ne kwance acikin ran sa domin ko kaɗan batayi kama da zubin ƴan Nigeria ba, musamman ma da yaga tana mishi turancin kamar tana wani yare, sam ba wani fahimta yake ba, murmushi tasake yi wannan karon da Hausa tayi maganar tace "Kana mamaki ko? Uhmmm kadena mamaki sabida ni da kake ganina cikakkiyar Bahaushiya ce ƴar Nigeria, Nigrian ma a Kano, sunana Fadila kuma musulma ce ni, but anan ana kira na da baby Dil". Ɗago kai yayi sosai yana kallon ta da tsantsan mamaki a face ɗin sa wannan karon, but yaƙi furta komi "Kafaɗa min meyasaka kakeson ganin Mr. Jay pitter?" "Meyasa kikeson nafaɗamiki?" Yayi maganar yana kau da kai kanta "Sabida zan taimaka maka, bazaka taɓa samun shi anan ba, koda zaka kwana kana sintiri ne, wahala kawai zakayi, but Ni kuma zan iya taimaka maka in kaika inda yake". Khalil yace "Please kitaimaka min ina son ganin shine sabida wani bincike da nakeson yi". Dariya tasaki tana kallon shi cike da sha'awa tace "Sau da yawa ina ganin irinka suna zuwa nan don neman sa, kuma tun sanda naganka nagane kai ɗan Nigeria ne kuma nasan abinda yakawo ka har kake neman sa". Da mamaki Khalil yakalle ta yace "Taya kika sani". Sai da tashanye sauran Juice ɗin ta'ajiye cup ɗin sannan takalle shi tace "Idan har kana son taimakona to mubar nan wajen, Ni kuma zan faɗamaka duk abinda kakeso kasani, har da wanda ma bakaso". Shiru yayi yana nazari kafin yace "Ok muje to". Tashi tayi takalle sa tana kashe mishi idanu, tamatso kusa dashi kaɗan ahankali tace "Kabari in nafita sai kabiyo bayana". Hakan ko akayi, sai da tafice kafin yabiyo bayan ta, daga can nesa yahango ta tsaye tana ware hannayen ta tana yarfe su, wajen ta yanufa yana kallon ta, bata bari yayi magana ba tace "Kasamar mana taksi mubar nan". Sai kuma tasakar masa murmushi tace "Ko muje musaukin ka". Wani irin kallo yayi mata, sai tawaro idanu still tana murmusawa tace "nan zai fi sirri, coz za'a iya samun matsala ne". Jimm yayi kana yace "Ok" Daga nan yatare musu taksi suka shiga suka tafi. [9/10/2020, 11:42 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📚* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 16* Lokacin da suka isa cikin ɗakin sa na Hotel ɗin Baby Dil akan sofa tayi wa kan ta matsuguni, taɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tajingina bayan ta da kujeran tana kallon shi, shi kuma Direct cikin Toilet yashige, be jima ba yafito yanemi wuri kan kujera yazauna kana yace da ita "Ina jinki, Please ina son nasan komi ga mutumin nan". Ɗan sakin murmushi tayi still tana kallon shi tace "Ni kuma zan sanar da kai komi insha Allahu, katambaye ni duk abinda kakeso". Gyaɗa mata kai yayi kafin yagyara zaman sa yace "Akwai wani Alhaji Mubarak da muke Shari'a dashi acan Nigeria, kuma tabbas an tabbatar min da Mr. Jay pitter abokin harƙallan shi ne, don haka nazo bincike kuma ina son nahaɗu dashi". Baby Dil tace "tabbas da ka isa wajen shi babu abinda zaka samu, domin Alhaji Mubarak na hannun daman sa ne, kaga kuwa babu abinda zaka samu a wurin sa illa ma kasake jagula abin, kamar yanda nace maka xan sanar da kai komi sabida nasan sirrin su ne, a baya mutane irinka sun zo kamar kai don bincike, wasu ƴan sanda ne wasu kuma lauyoyi ne, but kai bansan menene aikin ka ba?" "BARRISTER". Yafaɗa ataƙaice "Ok Amma tun sanda naganka naji zuciyata ta kwanta da kai sosai shiyasa nazo wajen ka bcoz nima ina buƙatar taimakon ka". Shiru tayi tana sauke numfashi, sai kuma tasauke ƙafan ta tahaɗe hannayen ta waje ɗaya tana kallon shi, sannan taci gaba da faɗin "Zan soma da baka tarihina duk da baka tambaye ni ba but nasan duk abinda kake nema yana da alaƙa da abinda akai min, shekaru 7 kenan da zuwata wannan ƙasan, ko ince aka sai dani a wannan ƙasan, zaka yi mamaki idan nace maka ta sanadiyan maƙocin mu nazo wannan ƙasa, mun kasance mu talakawa ne don haka maƙocin mu yake taimaka mana kasancewar sa me kuɗi, haka kawai watarana yace inxo zai sama mana aiki awani gida, dama abinda muke nema kenan musami aikin da zamu dogara dashi ni da iyayena, kwana biyu da soma zuwana, uban gidan mu yakai ni wani gida, ni dai ban fahimci ko ina ne ba amma akawai ƴan mata irina da yawa don mun kai mu sha biyu, muna ji muna gani akai mana allura wanda bamu fahimci na menene ba, tun daga lokacin hankalin mu yagushe, ashe makocin mu ne yasiyar dani ga mutumin da yasamar min aiki gidan sa, shima kuma yasiyar dani ga wani uban gidan sa". Shiru tayi tatsira ma waje ɗaya idanu taci gaba da faɗin "Wannan alluran da akai mana yagusar mana da hankali, anyi haka ne don su cin ma manifan su akan mu, suna harƙallan sai da coken that's why suke samun ƴan mata sufarka cikin su azuba musu coken ɗin nan aciki, alluran da ake yi yana da ƙa'ida, yana ɗaukan iya awannin da zai kai mu ƙasan da za'a kai mu ne, don haka lokacin da akai mana hankalin mu gushewa yayi bamu sake sanin inda muke ba sai a wannan ƙasar, sun kawo mu nan an kuma mana aiki an cire mana coken ɗin, sai dai basu bar mu haka ba suka sai damu ga Mr. Jay pitter, mutum ne shi da yake safaran ƴan mata ƙasa-ƙasa wasu kuma yamai dasu karuwan sa don samun kuɗi dasu, acikin waɗanda muka taho tare gaba ɗaya yasiyar dasu a wasu ƙasashe sai ni da wata yabar mu a matsayin karuwan sa, tun sanda natsinci kaina a wannan ƙasa nake kuka ina roƙon su da sumai dani ƙasata, sai dai aikin gama yariga da yagama su mutane ne da basu tsoron Allah, daga farko da sukaga ina musu taurin kai har nayi yunƙurin guduwa haka sukai ta gana min azaba, but duk da haka ban sa ran wataran zan ƙi guduwa ba, sai dai duk wani hanya da yakasance zan bar ƙasar nan sun toshe ta, ataƙaice dai zan faɗa maka babu yanda za'a yi nabar ƙasan nan batare da sanin su ba, haka nahaƙura naci gaba da zama dasu nima har lokacin da nasaba, nima nadawo nagoge azahiri namanta da komawa ta gida, sai dai abaɗini abin na nan araina, aduk sanda natuna da iyayena sai nayi kukan baƙin ciki, ina tunanin awani hali suke na rashina, shiyasaka har yanzu ban fid da raina zan koma ba". Muryan ta da yasoma rawa ne yasaka ta yin shiru, sai da tashare hawayen fuskarta kafin taci gaba "Shi kuma Alhaji Mubarak tare suke harƙalla da Mr. Jay Pitter, yana kawo masa ƴan mata sosai, duk wani aikin da Mr. Jay yake yi tare suke yi dashi, nasan shi sosai domin yana yawan zuwa nan ɗin, kuma insha Allahu duk wani sirrin su zan iya nemo maka inhar kayi alƙawarin zaka mayar dani ƙasata, ina son nakoma gun iyayena, kataimake ni don Allah, sosai naji zuciyata ta aminta da kai". Taƙarike maganar tana fashewa da kuka Brr. Khalil kallon ta kawai yake yi cike da tausayin ta, sosai tabashi tausayi kuma yana ji aran sa insha Allahu sai ya taimaka mata, dama wannan daman yake nema wanda zai kawo ƙarshen masu safaran mata, koda iyakan Alhaji Mubarak da mutanen sa yakawar tabbas yasan ba ƙaramin Jihadi yayi ba, ko ba komi za'a rage yawaitan mugaye irin su, ajiyan zuciya yasauke yana tuno Nazeefa "Yanzu shikenan da itama nan za'a kawo ta? Yarinya ƙarama, kai amma waɗannan mutanen basu da imani, Allah kaɗai yasan iya adadin yaran da suka kawo waɗanda ma basu kai ta ba". Numfashi yaɗan ja yana kallon ta yace "Kiyi shiru Fadila, insha Allahu zan taimaka miki kibar wannan ƙasan, zaki koma ga iyayen ki in Allah ya yarda nayi miki alƙawari". Kallon shi tayi da idanuwanta da sukai jazur tayi masa murmushi tace "Nagode sosai". "Babu godiya tsakani na dake, ke dai ki aiwatar da duk abinda zan saka ki". Daga nan yasoma bata bayanai akan abinda yakamata tayi masa, sun daɗe suna tattaunawa kafin tatafi, shi kuma tashi yayi yashige toilet yayo wanka tare da ɗauro alwala yafito, shirya wa yayi cikin farar jallabiya da dogon wandon jeans yashimfiɗa sallaya yayi sallah, sannan yamiƙe yaɗau tellphone ɗin dake ɗakin yakira Receptionist yayi odan abinci, yana zama babu jimawa akayi nocking door ɗin yaje yabuɗe ya'amso yadawo yazauna yasoma ci, abincin yake ci sai dai hankalin sa baya wajen yana nazari, wayan sa dake saman gado tasoma ringing hakan yasaka yaɗan kalli wajen kafin yasauke ajiyan zuciya, yamiƙe yanufi inda wayan take yaɗauka, ganin Bro ɗin sa ne babu ɓata lokaci yayi peacking call ɗin yana zama "Hello My Bro". "Hi ɗan ƙanina ya kake?" Ɓata fuska Khalil yayi yana shafa goshin sa yace "Bro bana so". Dariya Sameer yayi yace "Sabida me um ɗan ƙanina?" Shiru yayi yaƙi magana Still dariya Sameer yasake yi yace "I'm sorry dama tsokanan ka nake, ai yanzu kai big boy ne tunda kafara aje yara, kasan fa Hakima ta haihu". "Dagaske Bro? Yaushe? Me tahaifa?" Yayi masa tambayoyin ajere yana miƙewa yakoma wajen abincin sa "Yanzu babu daɗewa, ai nayi tunanin Mom tariga ni sanar maka, namiji tahaifa". "A'a tun safe da mukai waya bamu sake ba, Allah yaraya shi Yaya, ina fata ni za'a yi wa takwara ko?" Sameer yace "tabb kai awa?" "Ni a Dadyn sa, Please Bro kasan munyi alƙawari dani da kai, duk wanda yahaihu cikin mu zamuyi ma junan mu takwara". "A'a to ai bance maka na fari ba, ni Dad zan ma takwara sai dai kabari tasake haihuwa lokacin ma kayi naka auren, kaga sai su tashi tare ko?" Ajiyan zuciya Khalil yayi yace "Dama haka zakace ai, kafison Dad dani, shikenan sai kayi ta sakawa". Dariya Sameer yasaki jin yanda Khalil ɗin yayi maganan cike da shagwaɓa, cikin dariyan yace "Haba autan Mom Kar kayi fushi tunda nace zan saka, kuma kasan da cewa ni dama na wurin Dad ne, dole na fifita shi akan ka, amma fa ina son ka sosai fa, daga shi sai kai a zuciyata". Murmushi Khalil yayi yace "Uhmm naƙi daɗin bakin, ai dama Mom ta sanar dani kuma yanzu na yarda, yanzu ni dai kagaishe min da me jegon da kyau da kyau tare da My Son". "Ok zasu ji, ya aikin naka? Dafatan komi yana tafiya normal?" "Alhamdulillah Yaya, Ina samun duk abinda naje nema". "To Allah yataimaka yabaka Sa'a". "Ameen Bro, katura min photon Baby ta WhatsApp in ganshi". Sameer yace "ok yanzu kuwa". Daga nan sallama suka yi, yaci gaba da cin abincin sa yana latsa wayan sa. [9/12/2020, 1:32 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 17* *WASHE GARI* *NIGERIA* Da sallaman ta tashigo gidan, Mama dake zaune tana gyaran lagwani ta'amsa mata tare da faɗin "A'a maraba da Zainaba" "Mama ina wuni?" "Lafiya lau, ya Umman taki?" "Tana lafiya, tace in gaishe ki". "Ina amsawa, ya wajen su Zaituna, ina fata kina leƙata?". Murmushi Zainab tayi tace "Eh Mama ina zuwa sosai". "To madallah haka akeso, kishiga ƙawar taki na ciki ai, bata jindaɗi ne". "Eyya Allah yasawaƙe, ai bani da labari". Mama tace "ameen, ai zazzaɓi ne kuma jiya da dare ne ma jikin yamatsanta mata". Cike da tausayin ƙawartan tasake cewa "Mama Allah yasawaƙe bari in shiga wajen ta". "Ameen Zainab". Zainab na shiga taga Halwa saman gado ta kwanta tajuya ma ƙofa baya, ƙarisawa tayi kusa da ita tazauna a gefen katifan tana faɗin "Halwa ya jikin naki?" Halwa da tarufe idanunta batare da tamotsa ba tace "Dasauƙi". "Allah yabaki lafiya, shine kuma baki kiran awaya kin sanar dani ba? Yanzu da ba don naji Umma tana maganan saka ranan ki jiya ba shikenan bazaki faɗa min ba? Abin yaban mamaki ai ince kina cikin wannan farin ciki nasan da tuni kin garzayo kin fesa min". Duk wannan surutun da Zainab take yi Halwa taƙi cewa komi illa jinta da take yi, hannu Zainab ɗin tasaka tataɓa wuyan Halwan tana cewa "Wai jikin yayi tsanani ne haka da bazaki tashi muyi magana ba?" Ahankali Halwa tabuɗe idanunta tatashi zaune tana kallon Zainab ɗin, cikin kasala tace "Wani magana zamuyi?" Zainab kallon yanda duk tayi wani yaushi idanuwanta sukayi luhu-luhu suka yi ja tayi tace "Ƙawata me ke damunki ne? Kinga yanda kika koma? Ke da ciwo baya hana ki walwalan ki amma yanzu duk kin wani iri kamar kin daɗe kina ciwo?" Ɗan dafa kan ta Halwa tayi tace "Zazzaɓi ne kawai". "To Allah yasawaƙe". "Amin" Halwa tafaɗa tana komawa takwanta "Banji daɗi ba ƙawata da baki da lafiya, sai da lokacin farin cikin ki yazo sai kuma gashi ciwo na son hanaki walwalan ki". "Inji wa yace miki bana farin ciki?" Cewar Halwan tana ƙirkiro murmushi "Hmm kowa yagan ki yasan da cewa sosai kina jin jiki Halwa, ciwon kwana ɗaya ya maidake haka, nasan da cewa da bakya jin jiki tabbas bazaki kwanta haka ba, ƙafan ki babu inda bazai zagaya wajen sanar da cewa an sanya miki ranan aure ba". Halwa hararanta tayi tace "Tunda an ce miki bani da kunya ko?" Dariya Zainab tayi tace "Anan kam ai nasan baki da kunya, zakiyi abinda yafi hakan ma". "Ke dai kika sani". Halwa tace hakan tana ɗaura hannu asaman goshinta "Yauwa ya maganar Assignment ɗin nan na Malam Isma'il? Kinsan yace "shine Test ɗin mu, kuma wlh na duba nawa bangani ba, ara min naki in kwafe Questions ɗin" "Kiduba jaka na kiɗauka nima banyi ba, kije dashi kiyimin don Allah". Miƙewa Zainab tayi tana faɗin "Ok ba damuwa". Inda take rataye School bag ɗin tanufa taciro, taduba littafin taɗauko tadawo tazauna tace "Ni zan tafi gida Umma na can tana jirana zataje anguwa, amma goben zakije school ɗin? Don naga jikinki ya matsanta miki" "Zani". "Tom sai muhaɗe acan kenan, ina Yaya Nura? gashi zan tafi ban mishi Allah yasanya alkhairi ba". Halwa tace "ki neme sa a waya mana, ko kin ban ajiyar sa?". "To ai naga kece Gimbiyar tasa wataƙil kinsan inda yake, kinga ni ba jan magana zan yi ba na tafi". Fita Zainab tayi tayima Mama sallama tatafi. ***** ***** ****** Kwance take saman gadonta ta ɗaura hannayen ta saman fuskarta, babu abinda take tunani sai Khalil, tun sanda yakawo ta gidan nan har tafiyan shi takasa samun sukuni, kullum dashi take kwana kuma dashi take tashi, tarasa meyasaka tunanin sa yake damunta kullum, kuma ta kasa gane takamaiman abinda take ji acikin ranta game dashi, tsananin kewar sa ne yake damunta ako da yaushe, burin ta kawai yanzu tasanya shi a idanunta ko ta sami sauƙin zuciyarta, ahankali tamiƙe zaune tana ƙura ma waje ɗaya idanu, can tasaki ajiyan zuciya tatashi tsaye tasanya room slippers tanufi ƙofa, tafiya take yi ahankali tana saukowa daga upstairs, tun sanda takusa saukowa tahango Mom zaune a parlour tana waya, har takusa isa kuma sai tajuya da ninyan komawa Mom takira ta "Ina zakije kuma Nazeefa? Zo ga yayan ki kugaisa". Jiki a sanyaye tajuyo tazo wajen Mom tana jin zuciyarta cike da farin ciki, amsan wayan tayi bayan da tazauna takara a kunne tana faɗin "Hello Yaya". "Nazeefa". Yakira sunan ahankali cike da salo Hakan yasaka Nazeefa lumshe idanuwanta cikin jindaɗin muryan sa da yaratsa mata har cikin kwanya tace "Ina wuni Yaya". "Lafiya lau, ya jikin ki? Dafatan kina shan maganin ki akan ƙa'ida?". Gyaɗa masa kai tayi kamar yana kallon ta, sai kuma tace "Eh ina sha". "Ok kici gaba da kulawa". Shiru ne yagibta, hakan yasaka Nazeefa taɗan saci kallon Mom taga hankalinta na kan t.v, sai tace "Yaya yaushe zaka dawo?" Shi da har yai tunanin ko ta ba Mom ne still yaji muryan ta tana tambayan shi "Kina so in dawo ne? Yatambaye ta cike da kulawa "Eh Yaya nayi kewarka ne sosai". Tafaɗi maganar ahankali, don ita kanta batasan sanda tafaɗa ba, umarnin zuciyarta kawai tabi Shi kam Khalil jin maganar yayi wani iri a zuciyar sa, sai kuma yashare tunanin da yakawo mishi rai yace "Very soon zaki ganni, miƙa ma Mom wayan". Ba musu tacire wayan a kunni tamiƙa ma Mom, waya suka ci gaba da yi ita kuma Nazeefa tana zaune tana sauraron su, duk da bata jin muryan Khalil ɗin but sai sakin murmushi take yi kamar an mata bushara, tunanin ta kawai yatafi wajen tuno kyakykyawar fuskar sa ne, tana jin wani iri sosai a game dashi musamman ma duk sanda zasu haɗa idanu sai taji gaban ta ya faɗi, ko kuma da zaran ta gan shi hakan ke faruwa da ita, sai dai ita batasan menene ba bare tace ga matsayin abinda take ji, sai dai tasan shi ɗin wani haske ne a rayuwanta, me haskaka mata duk wani baƙin duhun dake cikin rayuwanta, kuma Mai Taimakon rayuwanta. _Shin zaku iya faɗamata abinda ke damunta Fan's? Don nasan kun sani ai._ ~Khalil-Billy~ ~Khalil-Lubna~ ~Khalil-Nazeefa~ _Muje zuwa Fan's_ _karku manta ku suburɓuro comments fa._ [9/15/2020, 11:32 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` ~Khalil-Billy~ ~Khalil-Lubna~ ~Khalil-Nazeefa~ . *CHAPTER 18* *TOMORROW* *MONDAY MORNING* Halwa ce tsaye cikin ɗakin ta tana riƙe da Hijab ahannu, kayan makaranta ne ajikin ta da tagama sakawa, tanufi wajen jakan ta dake rataye taciro tasaƙala shi a kafaɗa sannan tasanya Hijab ɗin tafito waje, leƙa ɗakin Mama tayi dake zaune tana cin tuwo tace "Mama ni na tafi sai na dawo". "To uban wa kika bar ma abin karyawan naki?" Yamutsa fuska tayi da yazame mata jiki tace "Mama ni nayi latti banda lokacin cin abinci". Harara Mama tawurgo mata tace "Tunda an faɗi maƙiyin ki ai dole kice kinyi latti, kizo kizauna kici tun kafin in saɓa miki, ayi mutum sam baya son cin abinci? Rayuwan zata yiwun miki ahaka ne? Nura dai zai yi aiki wlh". Buga ƙafa Halwa tayi cike da shagwaɓa tace "Ni wlh Mama bazan iya cin tuwon nan ba, ki ƙyale ni kawai natafi". "Wlh kuwa in bakizo kinci ba sai dai kifasa zuwa makarantan nan, shegiyar yarinya me taurin kai". Fuska a kumbure Halwa tashiga cikin ɗakin tawafci kwanon tuwon dake ajiye agefe zata fita "Dan ubanki dawo nan, zauna kici anan don nasan in dai kika fita sai dai kizubar". Babu musu takoma tazauna, sai dai gaba ɗaya in kakalli fuskarta zaka gane ranta aɓace yake, haka tatsulma hannu tasoma kai abincin baki tana yamutsa fuska kamar tana cin kashi, Mama kam bata ƙara bi takanta ba taci gaba da cin tuwon ta duk tana ankare da ita, ganin tana yunƙurin yin mata amai a ɗaki ne tace "Wlh Halwa idan har kikai min amai a ɗaki sai na mugun saɓa miki". Gyaran murya Baba dake bakin ƙofa yayi yace "Wai menene haka kika tasa yarinya gaba kina ta mata faɗa?" "Kaima kasan halinta tunda an haɗa ta da abokin gaban ta, makaranta zata tafi bataci komi ba". Murmushi Baba yayi yace "Kiriƙa lallaɓa ta mana Hauwa, kinji tashi kije ɗakina akwai raguwan ƙosai da narage kiɗauka kitafi dashi". Miƙewa tayi kamar zatayi kuka ta cika bakinta da tuwo amma takasa haɗiye wa "Ungo nan riƙe wannan kiƙara ki sayi wani abun kici". Amsan kuɗin tayi tafice dasauri, ɗakin Baban tashiga taɗauko ƙosan tafito, sai da tazubar da tuwon dake bakin ta tukunna takuskure bakin tafice dasauri, akan hanya suka haɗu da Zainab "Ai da naji shiru baki biyo min ba nace bari in zo in duba Madam ɗin nan lafiya?" Cewar Zainab kenan Yamutsa fuska Halwa tayi tace "Ƙalau, Mama tatare ni dole sai na karya sannan zan fita". Dariya Zainab tayi tace "Ke dai har yanzu bazaki dena wannan halin naki ba sai kace ƙaramar yarinya, kullum sai kin saka Mama ta ɗaga murya akan cin abinci, Allah yakyauta miki, Yaya Nura dai zai yi aiki wlh". "Uhm itama haka tagama cewa, ko wani aiki zai yi oho?" Zainab tace "ai da gaskiyar Mama, kullum wajen cin abinci zai yi fama dake". Taɓe baki kawai Halwa tayi bata sake cewa komi ba, ita kuma Zainab sai mata hira take har suka kai bakin titi suka tari abin hawa Bayan sun kai suka sauka Halwa taciro Hamsin tamiƙa, ita kuma Zainab tajuya da ninyan tafiya Halwa tariƙo ta tana faɗin "To uwar son banza ai ban bada da naki ba, sai ki biya sa". Kuɗin taciro cikin jaka tamiƙa mishi suka juya suka tafi Zainab tace "wlh ke ƴar wulaƙanci ne Halwa, nima zan rama". Dariya Halwa tayi tana waro idanu tace "me nayi miki kuma? Don kawai nace kibada kuɗi?". "Oho ke kika sani". Cewar Zainab Still dariya Halwa tayi tace "Kiyi haƙuri to, wlh banda kuɗi ne yau, nasan kuɗin da nake dashi bazai ishe ni har nabiya miki ba, coz akwai abinda nake so nasiya dashi". Zainab tace "uhmm naji, but kinsan da muka zo nan sai natuna da Haris? Wlh sai naji gabana na faɗi sabida abinda kikai mishi ranan Wednesday kullum mukazo nan sai na tuna, I know zai zo yarama". Jin sunan Haris da Halwa tayi ba ƙaramin bugawa zuciyar ta tayi ba, tsoro da fargaba suka zo suka dirar mata alokaci ɗaya, nan da nan annurin fuskarta yaɓace ɓat, ɗan sauran kuzarin da take ji shima yaɓace ɓat, take tasoma jin kamar wani sabon zazzaɓi ne zai rufe ta, Zainab sai magana take mata but ko kaɗan takasa furta komi har suka shige makarantan, koda suka shiga cikin class ɗin su tunda Halwa tazauna bata sake magana ba, Zainab da tatambaye ta ce mata tayi "kanta ke mata ciwo, da alamu zazzaɓin ne ke son dawo mata", don haka Zainab ɗin bata wani matsa mata ba taƙyale ta, a ranan haka ta wuni duk bata da walwala, sai gab da za'a tashi ne wani Malami yayi musu Test sannan aka tashe su. Lokacin da suka dawo gida, suna zuwa ƙofar gidan su Zainab, Zainab ɗin tace mata "To ƙawata sai gobe kenan". Gyaɗa mata kai kawai Halwa tayi tawuce gida, akan dakalin ƙofar gidan su tahangi Nura zaune shi kaɗai, ƙarisawa tayi tasami waje kusa dashi tazauna tana kallon shi tace "Yaya har kadawo aikin yau?" Ɗago kan sa yayi dasauri don da alamun be san da zuwan ta wajen ba sai maganarta da yaji, yace "Uhm kin dawo? ai banji zuwan ki ba". Murmushi tayi masa tace "Tunanin me kake yi to?" Ɗage kafaɗa yayi yace "Tunanin wajen aiki mana". Still murmushi tayi tace "Menene abin tunani to? Ada da baka samu ba kana tunani, yanzu kuma kasamun ma baza kabar zuciyarka tahuta ba?" Murmusawa yayi yace "Bazaki gane bane Dear, amma dai yanzu share wannan batun, kinga kin dawo kinsha hanya kishiga gida". "To kai kuma fa?" Tatambaye sa tana ƙure sa da ido Ɗan kawar da kan sa yayi yabata amsa "Ba yanzu ba, ni yanzu ma wajen Ali zani". "Ok.. sai kadawo". Tafaɗa tana wuce wa tashige gida batare da tajira amsan shi ba Shi kuma kallon bayan ta yayi har tashige kana yakau da kan sa yana sakin ɓoyayyen ajiyan zuciya, hannayen sa yasaka yatallabo cheeks ɗin sa yana ci gaba da tunanin sa. **** **** **** ***** Da gudu tashigo cikin parlour'n tana kiran sunan Mami, matashiyar budurwa ce da shekarunta bazai gaza 24yrs ba, bayan ta kuma matashin saurayi ne me kimanin 20yrs, da alamun ƙanin ta ne don sosai suke kama da juna, Mami da fitowar ta kenan cikin ɗakin ta taji muryan ɗiyar nata tana kwaɗa mata kira, sai tawashe baki tana faɗin "Oyoyo daughter". Da gudu tazo tayi Hugging ɗin ta tana me cike da farin ciki "Mamina I'm back". Tafaɗa tana sakin Mamin Murmushi Mamin tayi tace "Welcome My daughter, fatan kin dawo lafiya?" Tana murmusawa tace "Lafiya ƙalau Mamina" ina Dady?" "Ai yanzu yafita". Mami tabata amsa Ɓata fuska tayi kana tace "Shine yafita bayan yasan da zan dawo?" Mami tace "Ayya Daughter be yi ninyan fita ba, kiran sa akayi daga office yayi baƙi shine yafita but bazai daɗe ba zaki ganshi ai". Matashin saurayin me suna Ahmad yace "Aunty ga jakan ki nan tunda kin manta dani". Juyowa tayi tana kallon shi, dariya tayi tace "Sorry my bro, murnan ganin Mami ne". Hugging ɗin sa tayi tasakar masa peck a cheeks ɗin sa Mami tace "kashigar mata da kayan mana, muje ke kuma kizauna kihuta sai kici abinci ko?" Langwaɓar da kanta tayi tace "O'o Mami bari dai in soma wanka, na gaji wlh da yawa". "Ok tom je kidawo" cewar Mami sannan tajuya taƙarisa cikin parlour'n, su kuma suka wuce suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunan da suke parlour'n, Ahmad yana aje mata trolly ɗin ta yafito yadawo wajen Mami dake zaune cikin parlour'n suka soma hira Ita kuma bayan tayi wanka tasauya kaya cikin wata ƙaramar riga ja me kwalliyan heart 💓 agaban, tasanya blue pencil jeans sannan taɗaura hula akan ta tafito parlour'n, a kusa da Mami tazauna tana faɗin "Washhh Mamina". Mami tace "har yanzu gajiyar ne?" "Wlh kuwa Mami, kinsan zaman jirgi". "To ya Maleysian? Yau dai kin dawo gida komi ya ƙare". "Wlh kuwa Mami, kullum fatana naganni na gama karatun nan na dawo gare ku". Mami tace "alhmadulillah gashi ai komi ya ƙare, yanzu kije kici abinci kar kuma kin dawo da yunwa". Kallon Ahmad tayi tace "Bro ɗauko min inci anan, bana jin zan iya tashi". Dariya Ahmad yayi yace "Aunty Kausar uwar son jiki, kin dawo kenan". Itama dariya tayi tace "Kai dai bari Baro, but yanzu fa na sauya kar kayi tunanin ko da ne". Dawowa yayi riƙe da coolar a hannu haɗe da plate yace "Ai bazan yarda ba sai naga kin soma aiki". Shafa fuskarta tayi kana tace "Wa ke maganar aiki yanzu?" Tabb ai sai na huta". "You see? Dama na faɗa ai, kina jinta ai Mami". Mami tace "ai kibar ma wannan maganan, don tuni Dadynku ya samo miki aiki a gidan t.v dake nan garin". Waro idanu tayi tana tsayar da hannun ta daga zuba abincin da tasoma tace "Mami da wuri haka? Ya Dady zai min haka bayan ni ba haka mukayi dashi ba?". "Ai sai kibari in yazo kitambaye sa kun fi kusa". Kaɗa kai kawai Kausar tayi taci gaba da zuba abincin, yayinda Ahmad yasaki dariya yamiƙo mata spoon yana cewa "Aunty to meye amfanin zaman naki? Tunda kin riga kin gama karatun ki ai aiki yadace dake, ko kuma kin fi so kiyi aure ne?" Harara tawurgo masa tana kai abincin bakin ta, sai da tagama taunawa kana takalli Mami tace "Mami naga anguwar tamu duk tacika da sabbin gini, duk yanzu mun sami maƙota". Mami tace "ai kam, ai gine-ginen ma sun jima, don waɗanda ma suke maƙotaka damu sunyi shekaru kusan biyu da tarewa". Girgiza kai kawai Kausar tayi, daga nan sukaci gaba da ɗan taɓa hira tana cin abincin ta. [9/15/2020, 11:32 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 19* *4DAYS* Ƙarfe 10:00pm. Na dare jirgin da yakwaso su Brr. Ibrahim Khalil daga Egypt yasauke su a airport ɗin Katsina, driver'n shi yaje yaɗauko shi, lokacin da suka isa gidan kowa yana barci don ba kowa yasan da dawowan sa ba illa me gadi, bayan sun shiga yafito daga motan yanufi cikin gidan jaye da trolly ɗin sa, ƙofan parlon a kulle yake don haka sai yasaka keey yabuɗe yashiga, duhu ne dumɗun cikin parlour'n, Direct ɗakin sa yanufa yabuɗe yashige tare da rufowa, akan gadon sa yayi ma kan sa mazauni, sai da yaɗau 10mins yana hutawa kafin yamiƙe yasoma rage kayan dake jikin sa yashige toilet, wanka yayi yaɗauro alwala yafito, baƙar jallabiya me hula yasanya sannan yatayar da Sallah, magrib da isha'i yayi, bayan ya idar yayi shafa'i da wutri kafin yamiƙe yahaye saman gado cike da gajiya, babu daɗewa kuwa barci me nauyi yaɗauke sa, wanda be tashi farkawa ba sai da gari yayi haske sosai wajajen ƙarfe 11:03am. Hasken ranan da yashigo ta cikin windon sa ne yabugi fuskar sa, ahankali yasoma buɗe idanun yana rufewa har yaware su gaba ɗaya, take hasken yaƙyalle masa idanu don haka yayi saurin juyawa yaba ma windon baya, 5mins yaɗauka ahaka kafin yamiƙe zaune yana miƙa tare da hamma, ahankali yasanyo ƙafafunsa saman shimfiɗaɗɗen carfet ɗin dake malale cikin ɗakin, bedroom slippers yasaka a ƙafan nasa yamiƙe yanufi toilet, a bakin Toilet ɗin yacire slippers ɗin yashiga bayan yasanya Toilet slippers. Koda yafito yana ɗaure da towel ajikin sa, ya riƙe ɗaya yana goge suman kan sa, Direct wajen mirror yanufa yasoma shafa Expensive Lotions ɗin sa, bayan ya gama kintsawa yanufi sif ɗin sa yaciro kayan sa, brown t.shirt ne me gajeren hannu sai blue jeans yasaka, feshe jikin sa yayi da Parfumer's ɗin sa masu ƙamshin daɗi sannan yafito parlour hannun sa zube cikin aljihu, dainning yakalla yaga babu komi sai yajuya da ninyan komawa ɗakinsa ɗauko waya, har yariƙe handle ɗin kuma sai yaja siririn tsaki yana juyawa yanufi ɗakin Lubna, ahankali yatura ƙofan yana motsa bakin sa, shashsheƙan kukan ta ne yasoma shiga kunnin sa kafin yasauke idanun sa akan ta, tana zaune a ƙasa ta manne a jikin gado sai takifa kan ta saman gadon, shiru yayi yana kallon ta na tsawon daƙiƙu kafin yakira sunan ta in a cool voice Dasauri taɗago da kanta face ɗin ta jage-jage da hawaye tasauke idanunta kan shi, sosai tayi mamakin ganin shi don batasan ya dawo ba, shi kam takowa yayi yashigo ciki sosai yana kallon ta yace "Meke damun ki?" Ahankali tasunkuyar da kanta ƙasa cikin sanyin muryan ta da be fita sosai tace "Babu komi". "Ke banson ƙarya ki faɗa min abinda ke damun ki nace?" Yafaɗa da ɗan ƙarfi murya a kausashe Jikin ta har rawa yake yi tace "Dama wasu ne suka sace min Mamana da ƙannina". "Whatt.." yafaɗa da ɗan ƙarfi yana tsare ta da idanu "Meyasa to?" Yasake jeho mata tambayan Cikin rawan murya tace "Dama.. dama sabida sun saka ni aiki ne ban musu ba shine suka kama su". Wani kallo yasakar mata kana yace "Wani aiki kenan?" "Uhmm hm sun ce ne naɗauko musu duk wani abu da nagani cikin ɗakin ka kamar takardu ko Lapton ɗin ka.." Sai kuma tayi shiru tana zub da hawaye, Khalil ajiyan zuciya yasauke har yanzu idanun sa akan ta, dama yadaɗe da zargin ta, tun sanda yashigo ɗakin sa yaga ta tsorata hakan yasaka yaɗaura ayar tambaya akan ta, daga lokacin ne yasaka Camera 📷 cikin ɗakin sa yana ɗaukan masa duk abinda take yi, wannan dalilin ne yasaka ko kaɗan baya barin ɗakin da yake aje muhimman abubuwan sa aciki abuɗe, but besan da cewa mutanen da suka saka ta aikin sun yi garkuwa da mahaifiyar ta da ƙannin ta bane, sai yaji tsananin tausayin ta ya kama shi, ahankali cikin sanyin murya yace "Ki dena kuka Lubna, insha Allahu Mahaifiyarki da ƙannin ki zasu dawo gare ki karki damu, ki kwantar da hankalin ki kinji?" Ɗago kanta tayi tana kallon sa kafin tagyaɗa masa kai tana jin zuciyarta na mata sanyi sosai, bata yi tunanin zai ɗau abin da sauƙi haka ba idan har yagane cin amanar sa take yi, take tasake jin ƙaunar sa na sake shiga cikin zuciyarta "Bani wayan ki". Yace hakan yana ciro hannun sa cikin aljihu Dasauri tamiƙe taɗauko mishi tabashi, amsa yayi kawai yafice, ita kuma tabi bayan sa da kallo tana sauke ajiyan zuciya, zamewa nan ƙasa tayi tazauna tana share hawayen fuskarta Shi kuma Direct waje yafita yanufi motan sa yashige yafita gidan, kamar ko yaushe yana jan motan ne ahankali yana riƙe da wayan sa ahannu yana neman layin Brr. Tahir, dai-dai zai karya kwana yafita titi yaɗago kan sa don duba hanya, nan yaga wata farar Mota itama ta shanyo kwana kamar zasu yi karo da juna, dasauri yaja burki yana son kaucewa but duk da haka sai da suka gwarawa juna, aje wayan nasa yayi kafin yabuɗe motan yafito dai-dai itama tafito cikin motan ta suka kalli juna, atare kuma suka faɗi "I'm sorry". Hakan yasaka sukayi murmushi kafin ita tace "Kayi haƙuri bansan da zuwan ka ba ne". "No laifina ne ai, nima ban kula ba, but kiyi haƙuri ko". Murmushi tayi masa tagyaɗa kan ta "Babu damuwa". Tace dashi kana tajuya tashiga motan ta "Shima ɗin motan nasa yashiga, sai da taja nata motan yawuce kafin itama tawuce, Direct police station yawuce yayi reports ɗin ɓatan mahaifiyar Lubna da ƙannin ta biyu sannan yawuce gidan su. [9/16/2020, 8:26 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 20* Tana kwance saman katifan ta daga ita sai farar doguwar riga irin me taushin nan da zanen flowers ajikin rigan, kanta babu ɗankwali sai gashinta da yawargaje yazubo mata har kafaɗunta, littafi ne a hannunta tana karanta wa tajiyo sallaman ƙawarta daga waje, amsa mata tayi sannan tashigo takalle ta tana faɗin "Ƙawata hutawa kike yi ne?" Tashi zaune Halwa tayi tana yatsina fuska tace "Uhm hutu kuma? Karatu dai nake yi". "Yayi makaranciya, kinga ni wlh ban ma bi ta karatun ba don bani da lokaci yanzu, ina Mama naji kamar ke kaɗai ce gidan?" "Eh Yaya Nura ya kai ta kasuwa". "Kai ƙawata wlh baki ga yanda kika sauya ba, wai meye sirrin ne ni naga kamar kina ƙara wani haske ne da kyawu kamar bakijin dawan garin? Ko dai yaya Nura ne?" Zainab tafaɗi hakan tana ƙare mata kallo tare da dariya Murmushi Halwa tayi, sosai itama take ganin sauyi daga gare ta, tayi wani haske fayau duk da ita ɗin ba fara bace, gashi kuma ko ina nata yaciko gunun sha'awa "Hmm ke dai ban son tsegumi me kikeson cewa akan Yaya Nura?" Dariya Zainab tayi tace "A'a babu komi, kawai dai ina tunanin ko har yafara sauya kulawan sa ne daga gare ki tunda yaga kin kusa zama mallakin sa, kin gane dai irin uhm uhmmm.." Dukan ta Halwa tayi a cinya tana cewa "Banson sharri shegiya ke babu abinda kika iya sai saka idanu, yanzu me kikazo yi ne don nasan ba banza takawo ki ba?". Waro ido Zainab tayi tace "To me kike nufi? Ko nace miki wani abu nazo amsa wajen ki? Kinga ni tare da Safna muke zamuje gidan aunty Zaituna, shine nace bari in shigo ko zamuje tare sai gashi Mama ma bata nan". Halwa tace "wato da Safna ma kuke taƙi shigowa? Lallai kam zataci uban ta wlh dani take zancen". Zainab tace "ni fa bana faɗa miki bane kije kuyi halin naku". "Ai kibar ni da ita zamu haɗu ne wlh, kuma kisanar da ita hakan". "Baki da ƙafa ne? Kifito kije kisame ta mana". Zainab tafaɗi hakan tana nufan ƙofa zata fice Gyara zaman ta Halwa tayi taɗau littafinta tana faɗin "Banda lokacin ku yanzu, sai mun haɗe a school". Zainab tace "Allah yakai mu to" sannan tafice da gudun ta Kifa littafin Halwa tayi saman katifan tabi kai takwanta tana sakin numfashi, shiru tayi tana tunani aran ta, abun da yafaru da ita kwanaki 8 da suka wuce ne yadawo mata cikin ranta, take hawaye masu zafi suka soma sulmiyo mata a fuska "Har yaushe ne zata dena tuna wannan abinda yafaru da ita? Yaushe ne zata manta da wannan baƙin ranan acikin sauran ranakun da tayi a doron ƙasa? Har yaushe ne zuciyarta zata dena shiga cikin wannan ƙunci da baƙin cikin?" "Ya Allah gani gare ka, ya Allah kabi min haƙƙina akan wannan azzalumin, haƙiƙa yazalunce ni yasaka min tabon da bazan taɓa iya cire wa ba, Allah ya isa tsakanina dashi bazan taɓa yafe masa ba har duniya tanaɗe". Tafaɗi hakan afili tana saka bayan hannunta tashare hawayen fuskarta. ***** ***** ******** *AFTER THREE DAYS* Fitowa yayi daga ɗakin sa hannun sa riƙe da waya, yasami waje saman kujera yazauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayan sa yasoma latsawa yana yi yana ɗan ɗago kan sa yana kallon t.v, Lubna ce tafito daga kichen riƙe da coololi a hannun ta, dainning tanufa tajera kana tasake komawa taɗauko wasu su ma tajera su, bayan ta gama tanufi inda yake zaune ahankali tace mishi "Na gama girkin, ko akwai wani abu?". Girgiza mata kai kawai yayi idanun sa a kan wayan sa, juyawa tayi tanufi ɗakin ta, shi kam sai da yafi 10mins kafin yamiƙe yanufi dainning ɗin yazauna, aje wayan nasa yayi yasoma buɗe coololin abincin yana taɓe baki, gaba ɗaya babu abinda yayi masa aciki don baya tunanin zai iya sanya wani abu me nauyi acikin sa, rufewa yayi yatashi yanufi kichen, babu daɗewa yadawo hannun sa riƙe da glass cup ya haɗa Black tea, direct dainning table ɗin yakoma yaɗau wayan sa yadawo cikin parlour'n yazauna yasoma sipping tea ɗin yana kallon t.v, ahaka har yagama kafin ya'ajiye cup ɗin saman Centre table yaɗau remote yasoma sanja Channels, har yasaka wani tasha me suna *ƳAN CI T.V* yana shirin sauyawa aka nuno fuskar ta, hakan yasa yatsayar da tashan yana ƙure ta da idanu, duk da ba sosai yakalli yarinyan ba but zai iya shaida itace wacce sukayi karo a kwanakin baya, tana sanye ne cikin wata baƙar abaya me ɗan karen kyau da tsada, ta yane kan ta da Black veil, kasancewar ita fara ce sosai tayi kyau cikin kayan, tana gabatar da shirin ta kamar haka: "Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa acikin sabon shirin mu na *RAYUWAR DUNIYA,* wacce ni Kausar Ali Aliyu zan riƙa kawo muku aduk ranan Litinin da Alhamis, shiri ne dake kawo muku abubuwan dake faruwa acikin duniyar mu, tare da bankaɗo muku duk wani abinda ke ɓoye don kusani..." Ahankali yalumshe idanuwan sa yana jingina kan sa saman kujeran, yana jin muryan ta na ratsa cikin kunnen sa, sai kuma yabuɗe idanun sa yasake saukewa akan fuskarta, sosai yarinyan yaji ta burge shi, rana ta farko kenan da yaji mace tabashi sha'awa har be san sanda yadunga murmusawa ba, yanda take gabatar da shirin ta da komi nata a natse ne Wayan sa da yasoma ringing ne yasaka shi ɗan ɗago kai yana kallon wayan, ganin sunan DPO na yawo a screan ɗin wayan, hakan yasaka shi miƙa hannu yaɗau wayan tare da rage volume ɗin t.v'n yana karawa a kunne, basu fi 5min suna wayan ba yacire Phone ɗin a kunnin sa yamiƙe yanufi ɗakin sa, Direct sif ɗin sa yawuce yasauya kaya zuwa milk colour ɗin riga me dogon hannu, rigan kamar Jaket ne da coller a wuyan, but sai dai bata da nauyi ƴar shugula ce, wandon sa pencil ne kalan blue Black, sai yasaka Combat shi ma kalan wandon da igiyar shi milk, sosai yayi kyau cikin shigan yafeshe jikin sa da Expensive Parfumer's ɗin sa me shegen ƙamshi, yaɗau wayoyin sa da car keey's yafice, yana fita Compound ɗin gidan yashiga cikin motan sa ash colouer yabar gidan. ...... ....... ......... Yana zaune a office ɗin DPO yana mishi bayani kamar haka: "Ah BARRISTER a binciken da mukayi na daga ɓatan Matar da kakawo mana, ahm lokacin da kabamu report mun je wajen gidan ka don gudanar da binkice anan muka haɗu da wani mutum yana leƙa gidan ka, dama numban da kabamu mun riga da mun duba sai dai akashe yake kuma an datse hanyar sadarwan shi, to wannan dai mutumin mun kamashi don bamu yarda dashi ba, don haka koda muka kawo shi nan muka saka shi yayi bayani sai yayi mana taurin kai, sai da muka bashi wahala tukun yafaɗa mana abinda yasani, yace "shine wanda yake gadin Matar da ƴaƴan ta, sannan yazo gidan ka ne saboda aiko shi da akayi wajen ƴarinyan Matar da take gidan ka, munyi-munyi yayi mana bayani akan mutanen da suka saka shi aikin but yace "shi be san su ba, shi dai kawai an saka shi yatsare su ne", kaji abinda yafaru, but duk da haka dai muna tsare dashi ko zamu sami wani inpermation akan su". Gyara zaman sa da kyau Khalil yayi yana kallon DPO ɗin yace "Yanzu ina suke?" "Suna nan mun aje su a wani ɗaki, zaka iya tafiya dasu yanzu haka but ko wani lokaci zamu iya neman su". "Ok babu matsala ai". Miƙa mishi hannu yayi sukayi musabaha kafin suka miƙe atare suka fice. Bayan kamar minti goma Khalil yafito cikin station ɗin, bayan sa wata dattijuwar mata ce da matasan yara maza su biyu, buɗe musu mota yayi suka shiga sannan yakulle shima yashiga yaja yatafi, Direct gidan sa ya'isa, bayan yayi parcking yasake buɗe musu suka fito yace "su biyo bayan shi" babu musu suka bi shi a baya har cikin parlour'n, zama yayi bayan da yace "Umma kuzauna mana". "Toh". Cewar matar sannan suka zauna Wayan sa yasaka yakira Lubna sai gata tafito, ai tana cin karo dasu tasheƙo da gudu tana kiran "Ummana", rungume Umman tayi tasaki kuka, su ma ƙannin ta suka rungume ta duk suka fashe da kuka, Khalil kallon su kawai yake yi yana murmushi cike da tausayin su, sai da suka gama rungume-rungumen junan da koke-koken kafin Lubna taɗago kanta fuska a jiƙe takalle shi tace "Nagode Sir, ban san da bakin da zan maka godiya ba, na gode sos.." "Shiiiiihh ya isa haka, kibasu abinci suci su huta sai ki kira ni bayan sun gama ok?" Gyaɗa masa kai tayi tana share hawayen ta, shi kuma tashi yayi yashige ɗaki yarufo ƙofan, ahankali ya'isa gaban gadon sa yazauna tare da jinginar da kan sa a jikin gadon, rufe idanuwan sa yayi yana jan iska da ƙarfi yana fesar wa, tunanin abinda yakamata yayi kawai yake yi, tsawon lokaci kafin yaji wayan sa tana ringing, Koda yaduba yaga Lubna ce sai yamiƙe kawai yafice Kallon Umman yayi bayan da yazauna yace "Umma kuna da wasu ƴan uwa ne a wani wajen, ko dama anan kuke zaune?" Umma tace "a'a muna dasu a ƙauye, dama mu ma can muke zaune sanadiyan aiki ne muka dawo nan muka kama haya". Gyaɗa kan sa yayi kana yace "To Yakamata ki ɗauki ƴaƴan ki gaba ɗaya kubar nan, ko ki koma ƙauyen ko kuma ku sauya wani waje me nisa, sabida mutanen da sukayi garkuwa daku ko wani lokaci zasu iya dawowa gare ku". Sannan yamayar da idanun sa kan Lubna wacce itama kallon shi take yi yace "Kije kihaɗa kayan ki". Daga haka yamiƙe yakoma ɗakin sa, ita kam Lubna kasa riƙe kukan da yazo mata tayi tasake shi ahankali, Umman nata tace "Ai hakan yadace muyi Lubna, wlh ko be ce mubar nan ba baza mu sake kwana ba, ai Allah mun gode maka da yataimake mu da bamusan me mutanen nan zasu yi mana ba, kitashi kije kihaɗa kayan ki mutafi". Babu musu tamiƙe tashiga ɗaki, lokacin da tafito riƙe da trolly ɗin kayan ta shima Khalil yafito yana kallon ta, sauke kanta ƙasa tayi hawaye na zubo mata, bazai iya juran ganin hawayen ta ba don haka yaɗauke kan sa yanufi wajen Umma yace "Ga wannan Umma, da fatan zai ishe ku ko da sana'a ne sai ku kama". Jiki na rawa Umma tasaka hannu ta'amshi maƙudan kuɗin da yamiƙo mata "Har da ɗawaniya ɗan nan? To mun gode Allah yasaka da alheri, Ubangiji yabiya maka duk kan buƙatun ka, mun gode ƙwarai da gaske". Murmushi kawai Khalil yayi yana motsa laɓɓan sa, yana nan tsaye har suka fice kana yasami waje saman kujeran yazauna, lumshe idanuwan sa yayi yana tuna ranan da Mom ɗin shi takawo mishi Lubna a matsayin ƴar aiki, wacce zata riƙa taimakon shi da gyaran gida Asali ita Umman Lubnan itace ƴar aikin Mom, daga baya ne tayi wani ciwo da yakwantar da ita tsawon lokaci har ta'ajiye aiki Mom kuma tasamo wata, lokacin bayan Umma ta sami sauƙi sai tazo wajen Mom tane mi alfarma ta samar ma Lubna aiki, shine ita kuma Mom tace "Khalil yaɗauke ta yatafi da ita, tunda dole yana buƙatar wacce zata riƙa dafa mishi abinci da sauran abubuwa na gyaran gida" babu musu Khalil yatafi da ita, wannan shine dalilin da yasaka LUBNA take aiki a gidan sa, kuma a gidan nasa take kwana but wani lokacin kuma tana komawa gidan su, musamman kamar ranan Weekends haka. Ajiyan zuciya yasauke yana buɗe idanun sa, gyarawa yayi yakwanta a kan kujeran yasake lumshe idanun sa. [9/16/2020, 8:26 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 21* Kiran sallan magriba ne yasanya shi buɗe idanun sa da suka yi ja sakamakon barcin da yaɗauke shi, ahankali yamiƙe yanufi ɗakin sa, alwala yaɗauro yafito yanufi masjid, as usual sai da akayi sallan isha'i yadawo gida, Direct ɗakin sa yawuce yacire rigan sa yabar singlate ɗin dake jikin sa, drower yabuɗe yaɗauko keeys sannan yarufe, yaɗau briefcase ɗin sa yafito parlour, akan 2sitter yazauna yana ajiye briafcase ɗin saman Centre table, wayan sa yaɗauka sai da yalatsa kafin yakara a kunne, yana jin an ɗauka yace "Kazo ina neman ka". Daga haka yacire wayan ya'ajiye, buɗe jakan yayi yaciro Computern sa yasoma aiki Da sallama wani matashin saurayi yashigo ciki, amsa masa sallaman yayi batare da yaɗago daga abinda yake yi ba "Gani Sir". Cewar saurayin bayan da yaduƙa gaban sa Ɗago kai yayi yana kallon sa yace "Sale daga yau aikin ka zasu ƙaru agidan nan, zaka riƙa zuwa kana gyara min cikin gidan nan, don haka zan ƙara maka albashi in babu matsala". Washe baki Sale yayi yace "Ai babu komi Sir duk zan iya, har da ma abun da bakace ba". "Ok.. ga keeys ɗin gidan sai kariƙe a hannun ka ko". Hannu biyu yasa ya'amsa Yace "katashi kaje". Miƙewa Sale yayi yana godiya kafin yatafi, shi kuma yaci gaba da aikin sa, wajen ƙarfe 09:00pm. Yadakata kasancewar yunwan da yaji yana ƙwaƙulan cikin sa, miƙewa yayi yanufi kichen, tsayawa yayi yana nazarin abinda zai ci domin sosai yaji cikin sa na kukan yunwa, don haka kawai yayanke shawaran dafa indome, cikin abinda be gaza minti 12 ba yagama, indome ne haɗe da ƙwai yasoya yaɗauka yafito, zama yayi yasoma ci ahankali yana tunani har yagama, yatashi yamayar da plate ɗin da spoon cikin kichen sannan yadawo yaci gaba da aikin sa, sai wajen ƙarfe 12:04pm. Sannan yanufi ɗakin sa, sai da yaɗauro alwala yagabatar da sallan nafila tukunna yasauya kayan sa zuwa kayan barci yakwanta. Washe gari ƙarfe 06:45am. Tuni yagama shirin sa na zuwa office, suit yasanya sky blue da ƴar cikin milik colour, sosai yayi kyau babu abinda yake yi sai tashin ƙamshi, yaɗau briafcase ɗin sa yafice, a farar motan sa yashiga yabar gidan. Ƙarfe 02:30pm. Yadawo gida, yana shiga cikin ɗakin sa ya'ajiye briafcase ɗin sa sannan yazauna yasoma zare Combat ɗin ƙafan sa da socks, bayan ya gama yacire suit ɗin tare da necktie ɗin wuyan sa duk yazube saman gado, miƙewa yayi yashiga Toilet, be daɗe ba yafito yanufi parlour, kichen yawuce yahaɗa tea me kauri yazauna nan yasoma sha, bayan ya gama yafito yakoma ɗaki yacire kayan sa yashiga wanka Lokacin da yafito yashirya cikin wani ɗanyen Boyel maroon colour, ba ƙaramin kyau suka yi masa ba kamar wani sabon ango, yafeshe jikin sa da farpume's yakwashi wayoyin sa da keeys ɗin mota yafice, mota yashiga yabar gidan, Direct super makert yawuce yayi shopping masu yawan gaske, yahau motan sa yanufi gidan ɗan uwan sa Lokacin da ya'isa yana yin hon aka buɗe masa motan yakutsa ciki yayi parcking, yanayin gidan da komi irin nasa ne, sai dai ɗan abinda ba'a rasa ba, yana fitowa me gadi yanufo sa da gudu yana kai gaisuwa tare da taimaka masa yashigar da kayan, a parlour ya ajiye masa, shi kuma yaciro kuɗi yabashi yana ta godiya sannan yafita, zama yayi saman sofa yana sauke idanun sa akan plasma dake aiki shi kaɗai babu kowa, yafi minti 5 da shigowan sa be ji wani zai fito ba, hakan yasaka yaɗau wayan sa yasoma latsawa yana neman layin Sameer, sai ga Abida tafito, ƙanwa ce ga matar Sameer ɗin, tana hango shi tanufo wajen shi cike da fara'a tana faɗin "Laa Ya Khalil yaushe kashigo?" Ɗago kan sa yayi yakalle ta kana yace "Yanzu". "Sannu da zuwa to". "Yauwa, ina masu gidan?" Yatambaye ta yana mayar da idanun sa kan wayan sa Murmushi tayi tana zama akan hannun kujeran da yake kai, kana tace "Suna ciki, ko in Kira su?" Gajeren tsaki yaja batare da yace mata komi ba, yana ganin rainin hankali ne, har sai yace ma takira su zata kira mishi su? wayan sa yakara a kunne yana faɗin "Bro gani a gidan ka fa". Abinda yafaɗa kenan yakatse kiran, ita kam Abida kallon sa kawai take yi tana murmushi, sosai take ƙaunar Khalil sai dai ko kaɗan shi baya sakar mata fuska, ko tayi yunƙurin shiga jikin sa to baya bata dama Sameer ne da Hakima suka fito daga ɗakin su, sun ci ado cikin wani farar kamfala iri ɗaya har aikin "Uhmm ai wlh nayi fushi ba kaɗan ba, wai ace tun yaushe kadawo ƙasan nan har akayi suna bakazo ba sai yanzu?" Cewar Hakima tana zama a ɗaya daga cikin kujerun parlour'n, yayinda shima Sameer yasami gefen ta yazauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kyakykyawar murmushin sa yayi kana yace "Afwan Matar Bro, I know nayi laifi, amma sai da nace ma Bro yafaɗa miki uzurina, ko ba haka muka yi ba Bro?". "O'o niii? Kar kahaɗa ni da matata, a yaushe mukayi haka da kai?" Cewar Sameer ɗin yana ɗaga hannaye sama tare da fito da idanuwan sa "You see ka gani ko? Ai nasan Mijina bazai maka ƙarya ba, kai dai kawai bakayi ninyan zuwa ba sai sanda kaga dama". Hakima tafaɗi hakan tana murmusawa "To yanzu dai first kifara ɗauko min My son nagan shi sai aci gaba daga baya". "Hmm ai yayi fushi shima bazai gan ka ba". "Haba Matar Bro Ni ne fa ko kin manta ni? Bro kasaka baki mana". Khalil yafaɗi hakan yana langwaɓar da kan sa kamar ƙaramin yaro "To sweetheart ki yafe masa tunda naga kamar yayi nadama, but nest in yasake ki hukunta shi". Gaba ɗaya sukayi dariya, yayinda shi Khalil ɗin murmushi kawai yayi yana shafa kan sa Hakima tace "Abida ɗauko mishi Aamir". "Tom Aunty". Miƙewa tayi tawuce ciki, ita ma Hakima tashi tsaye tayi tana faɗin "Bari nakawo maka abin motsa baki Mijin". Khalil yace "No kibar sa kawai na hutar she ki". Sameer yace "waɗannan ledojin fa? Menene aciki kakawo mana?". "Shopping ɗin My Son ne". Hakima tace "to mun gode". Lokacin Abida tafito riƙe da Aamir a hannu takawo mishi, hannu yasaka ya amsa wanda har hannun su yana gogan juna, shi be ma lura ba yaron kawai ya'amsa, yayinda ita kuma Abida taji wani iri ajikin ta hakan yasaka tasaki murmushi tana jin farin ciki, yau rana ta farko jikin mafi soyuwa a cikin zuciyarta ya haɗu da nata Bayan yagama ganin yaron ma sai tamiƙo hannu don yaba ta, but sai yamiƙe yaje yamiƙa ma Hakima yana faɗin "To ni tafiya zan yi, sai kuma na sake kewayo wa". "Da wuri haka?" Cewar Hakima bayan ta amsa yaron Amsa mata kawai yayi ataƙaice, daga nan suka yi sallama suka fito tare da Sameer, sun kai wajen mintuna 30 atsaye wajen motan Khalil suna tattaunawa kana yashiga motan sa yatafi. Yana tafiya a cikin motan sa ya kawo anguwan su, zai sauka kan titi yaji Motan tayi faci sakamakon taka ƙusa da tayi, tsaki yaja yana ɗan murza hannun sa a sitiyarin motan, yajingina kan sa jikin kujeran yana kallon saman motan, tsawon mintuna yana nan ahaka kafin yaji hon a bayan sa, hakan yasaka yaɗago kan sa yana kallon motan dake bayan sa ta mirror, siririn tsaki yaja yana mayar da kan sa yalumshe ido, motan ce tazo dai-dai setting shi kana tazuge glass ɗin motan tana kallon shi "Kana neman taimako ne?" Tafaɗi hakan cike da sanyin murya Ɗago kan sa yayi yakalle ta, ita ce dai budurwan da sukayi karo kwanaki kuma yaganta cikin t.v, sai yagyaɗa mata kai a hankali still yana kallon ta, murmushi tayi masa don ita tariga da tagane sa hakan yasaka tatsaya "Ok why not kazo narage maka hanya in babu damuwa fa". Murmushi yayi mata kana yafito daga motan yarufe, sai da yaciro wayan sa yayi ɗan gajeren text yatura kafin yanufi motan nata yashiga, taja suka tafi. _Ku ƙara yawan Comments plzzzzzzz_ 🥰🥰🥰 [9/17/2020, 11:04 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` _Wannan shafin naku ne duk wani masoya littafin Brr. Ibarhim Khalil, ku ji daɗin ku_🥰🥰💃💃💃💃 . *CHAPTER 22* "Anan zaki sauke ni". Yafaɗi hakan yana nuna mata setting gidan sa "Laa kace kusa da juna muke ma". Tace hakan lokacin da tatsayar da motan Kallon ta yayi yace "Really?" Murmushi tayi itama tana kallon shi tagyaɗa masa kai "But ban taɓa ganin ki ba ai? Kuma ina yawan ganin wani matashin saurayi yana fitowa gidan". "Eh ai ni bana ƙasan ne, ina can Maleysia ina karatu, sai kwanan nan nadawo". Gyaɗa kan sa yayi kana yace "Ok thanks for your help me". "Babu damuwa, yiwa kai ne ai". Sai kuma tamiƙo mishi hannu still da murmushi a face ɗin ta tace "Zamu iya zama friends?" Kallon hannun nata yayi sai kuma yakalle ta, sannan yagyaɗa mata kai batare da yamiƙa mata hannun ba, janye hannun nata tayi tana yarfe shi tace "Oh sorry" nayi tunanin ko maleysia muke". Tafaɗi maganar tana waro idanu Hakan yasaka shi murmushi batare da yace komi ba, yabuɗe motan zai fita "Aff baka sanar dani sunan ka ba?" But ni sunana Kausar Ali Aliyu, and You?" Tafaɗi maganar tana ƙure shi da idanu "BRR. IBRAHIM KHALIL". Yayi maganar ataƙaice shima yana kallon ta "Wowwww! Nice Name, zan ji daɗin abota da kai kenan coz ni ƴar Jarida ce". Cike da ƙosawa da surutun ta yasaka ƙafarsa awaje zai fice still tasake faɗin "Am baka ji ba?" Yajuyo yana kallon ta fuska a haɗe tare da nuna gajiyawar sa, ita kuma sai tayi murmushi tace "Sorry na takura ka, dama zance ne kagaishe min da Madam kafin nashigo". "Wa yace miki ina da mata?" Yafaɗi maganar yana ficewa gaba ɗaya yataka yatafi batare da yajira amsar ta ba, ita kam babu abinda take yi sai murmushi, sosai Guy ɗin yaburge ta, ko kaɗan bashi da rawan kai irin samarin zamanin nan, sai da taga shigewan sa sannan ta tada motan tanufi bakin Gate ɗin gidan su tadanna hon da ƙarfi. Shi kuma daga shigan sa gidan yamiƙa ma Gate Man keeys ɗin motan sa in Drever yazo yabashi, sannan yashige cikin gida, bayan yayi wanka ya kintsa cikin ƙananan kaya yasake fitowa yanufi masallaci, sallan asar yayi yadawo yazauna nan parlour yana danne-dannen waya, tsawon 1 hour yana wajen kafin yamiƙe yanufi kichen, Coffee yahaɗa yafito yazauna yakunna t.v yasanja channel zuwa MBC Action, abinda yake so kuwa ake yi wato wrestling, haka yakafa idanun sa akan kallon yana yi yana spping Coffee ɗin, sai da aka gama yamiƙe yanufi kichen ya ajiye cup ɗin yashiga ɗaki, ahankali yabuɗe ɗakin da yake aikin sa yazauna kan kujera, yajanyo Lapton ɗin sa yasoma aiki. ......... ........ ........ ..... Asalin Alhaji Abdurra'uf Abdullahi da Hajiya Hajara fulani ne kuma mazauna garin Katsina, Alhaji Abdurra'uf wato Dad shi irin baƙaƙen Fulanin nan ne na daji masu yawo wannan garin zuwa wancan garin, yayinda Hajiya Hajara wato Mom ita kuma irin fararen nan ne waɗanda kallo ɗaya kayi musu zaka gane su ɗin Fulani ne, Babban Family ne dasu, lokacin da su Dad suka zo Garin Katsina dashi da iyayen shi Mahaifin Mom ne yabasu mazauni a nan gidan su, zuwan sa gidan ne kuma yasoma karatu har matakin degree, da sannu da sannu suka saba da ƴan gidan har suka zama tamkar Family ɗaya, kuma alokacin ne Soyayya me ƙarfin gaske yashiga tsakanin Dad da Mom har suka yi aure, Allah ya albarkace su da yara biyu duk ka Maza Sameer da Ibrahim Khalil, kuma daga kan su basu sake haihuwa ba. Rayuwan Sameer da Ibrahim Khalil sun yi shi ne cikin gata da ƙaunar iyayen su har zuwa matakin da suka girma, kuma sun yi karatun su ne a ƙasan Gamerny har zuwa sanda suka gama suka dawo, shi Sameer ya karanci Doctoring ne fannin ƙashi, shi kuma Ibrahim Khalil ya karanci BARRISTER A tare Sameer da Khalil suka ƙera gidan su, sai dai ba anguwa ɗaya bane, Lokacin da Sameer ɗin yayi aure shima Khalil yace "bazai zauna a gidan su ba" shine yakoma sabon gidan shi, shekaru kusan biyu kenan da faruwan hakan. Wannan shine taƙaitaccen tarihin su. ***** ****** ****** *TWO WEEKS AGO* Da dare wajen ƙarfe 09:00pm. Khalil ne zaune a cikin Garden ɗin gidan sa, gaba ɗaya wajen haske ne yamamaye wajen tamkar rana don baza kace dare ne ba, yana sanye cikin wasu kaya riga da wando three qweater tamkar na sanyi, red colour ne irin dack ɗin nan, sun bala'in yin masa kyau sosai, kan sa babu hula sai gashin sa da iska ke ta kaɗawa, gaban sa kuma ɗan ƙaramin table ne ya ɗaura Lapton ɗin sa akai, gefe ɗaya kuma glass cup ne da Fruits a cikin plate, aiki yake yi time to time kuma yana ɗan kurɓan Black tea ɗin, wayan sa dake ajiye ne tasoma ringing yaɗan tsayar da aikin yakalli wayan, ganin sunan Dad ya fito raɗo-raɗo a screan ɗin yasanya shi saurin ɗauka yana peacking call ɗin tare da karawa a kunne "Hello Dad.. au assalamu alaikum". Murmushin Dad ɗin ne yabayyana cikin wayan kafin yace "Kai dai baza ka dena halin nan naka ba ko?" "Sorry Dad na manta ne, but ai na gyara ko?" Yayi maganar a shagwaɓe Still Dad murmusawa yayi yace "Auta kenan, Mom ɗin ka tariga ta gama ɓata ka, kana yin abu sai kace ƙaramin yaro". Murmushi Khalil yayi yana shafa kan sa yace "Dad ai ku kaɗai nake ma wa, coz a wajen ku ni har yanzu yaro ne". Dad yace "to gobe da safe kafin kawuce office kabiyo gida ina neman ka". "Dad lafiya kuwa?" "Lafiya lau My Son, sai dai in ka zo zaka ji, kar kuma kace min ka manta kashanya ni jiran ka". "Tom Dad, insha Allahu zan zo". Khalil ɗin yafaɗa cike da girmama wa Daga nan sallama suka yi Khalil ya'ajiye wayan sa yaci gaba da aikin sa. [9/17/2020, 7:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 23* *TOMORROW MORNING* Khalil ne zaune a parlour'n mahaifin nashi yana sauraron abinda yake faɗa mishi "Ibrahim har yanzu dai bakasan zurun ba ko? Tun yaushe nayi maka maganar aure but har yanzu shiru babu wani motsi da kake yi". Ɗago kan sa yayi yana kallon Mahaifin nashi, be yi tunanin wannan maganar ce tasaka yakira shi ba, kuma ko kaɗan be shirya ma hakan ba "Ina jin ka tunda ka bari sai na tambaye ka, yanzu kasanar dani wacce yarinya ce kake so don mugaggauta nema maka auren ta?" Shiru Khalil yayi yana sad da kai ƙasa "Kayi shiru kuma?" Dad yatambaye sa yana kallon sa "Uhm Dad ni har yanzu ban sami wacce nake ƙauna ba". "Ohho nagane me kake nufi Ibrahim". Cewar Dad yana kaɗa kan sa, sannan yaci gaba da cewa "But nasan maganin ka tunda naga kamar har yanzu baka yi hankali ba, tun yaushe muke wannan maganar da kai amma dayake baka ɗau maganar ta wa da wata muhimmanci ba shine ka shashantar dashi, yanzu gashi har Sameer yana da yaro kai kazauna kana son kazama tuzuru, to na baka nan da lokacin da zaku gama wannan shari'an, katabbatar ka sami matar aure idan ba haka ba ni da kai ne, kana ji na?" Dad ɗin yaƙarike maganar yana riƙe kunnen sa tare da kallon sa Ɗan turo baki gaba yayi kana yagyaɗa masa kai "To tashi katafi, Allah yamaka albarka". Ciki-ciki ya'amsa yamiƙe yafita daga parlour'n, girgiza kan sa Dad yayi yana ɗaukan Jaridan da yake karantawa yace "Wannan yaron in ba haka nayi maka ba, to naga alaman ba auren ne a gaban ka ba, in ba ma rashin wayau ba ya zauna har War haka be yi aure ba". Shi kam Khalil daga fitan shi ɗakin Mom yashige, tana zaune a gefen gado tana gyara drowan ta data hargitsa tana neman sarƙan da zata saka, yashigo fuska a turɓune hannun sa cikin aljihu, ɗago kai tayi tana kallon sa, sai da takaranci yanayin sa kafin tace "Yah ya Me yafaru ne? Me Dad ɗin naka yafaɗamaka naga fuskar ka ta sauya?" Ahankali yatako yazo kusa da ita yazauna kafin yasoma magana ciki-ciki "Wai Dad ya bani nan da bayan gama Shari'a na da Alhaji Mubarak in fito da mata, sai kace neman matan sauƙi ne dashi". Murmushi Mom tayi tana riƙo hannun sa ɗaya da yaciro su daga aljihu yaɗaura saman cinyoyin sa yadunƙule su "Haba My Son ya zaka ga laifin Dad ɗin ku? Ai ni inaga ya baka lokaci sosai tunda ba yau yasaba maka maganar ba?" Kallon ta yayi yace "Mom kwanaki ne fa suka rage? Meyasa bazai ƙara min zuwa nest year ba?" Hannu taɗaura a saman kan shi tana shafa baƙin gashin sa da yasha gyara yakwanta luf gunun sha'awa tace "Wai to menene na tada hankalin ka ne Son? inace Kai ɗin me farin jinin ƴan mata ne, duk wacce kazaɓo acikin matan da suke son ka da gudu zata aure ka, ko acikin Family ne sai kazaɓa ɗaya kaga hakan ma sai yaƙara mana ƙarfin Zumunci, don ban faɗa maka bane kwanaki ma Hajja Mero tazo har nan, takawo min maganar ƴar ta Shukra, me zai hana a haɗa auren ku tare, kaga in ka amince kawai sai in Kira ta in sanar da ita, cikin lokaci ƙanƙani sai ayi komi a gama ko ba haka ba?" Kwaɓe fuska Khalil yayi yace "Wai menene haka Mom, ya na kawo miki magana don ki rarrashi Dad yaƙara min time kuma kike mayar da hannun agogo baya? Ni in rasa ma waɗanda zan aura sai yaran nan da basu da kunya, kullum idanun su a tsatstsaye kamar zasu cinye mutum, ina Allah yakyau wlh". Yaƙarike maganar kamar yaga abin ƙyama Dariya Mom tayi tace "Ban da abin Auta to menene laifin su? Kuma menene laifin wanda ke son ka, in ma kana tunanin sun yi maka yara ne ai naga hakan kuka fi so yaran zamani, kuma sun fi daɗin zama ai, zaka ji daɗin zama dasu wlh". "To ni Mom bance miki Ina son yara ko manya ba, Ni kawai har yanzu ban ga wacce nake ƙauna bane, and Mom kuma ki dena maganar yaran nan ma kar suji su ce zasu raina ni". Mom tace "to shikenan na daina Autana, yanzu dai katabbatar ka samo matar da zaka iya zama da ita tun kafin Dad yazaɓo maka". Marairaice fuska yayi yana faɗin "Yanzu Mom baza ki roƙe sa ba?" "Kasan halin Dad ɗin ka, in yariga yaba ma mutum dama kasan bazai saurare shi ba, don haka kawai kayi abinda yace maka, but insha Allahu dai zan yi masa magana yaƙara maka lokacin yanda zaka samo min suruka me kyau da hankali kamar kai, wanda take ƙaunar ɗana kuma takula min dashi sosai". Murmushi Khalil yayi yace "Mom kenan, to amma dai bari ince ameen". mom dariya tayi tana jan kumatun sa tace "Ja'iri kawai, kana so kana kai wa kasuwa ko?". Shima dariya yayi kawai yana sosa kan shi "To tashi kaje kar kayi late da yawa, kaga har 08:00am. Ta kusa". "Ok Mom". Sai da yayi mata peck a cheeks ɗin ta kafin yamiƙe yayi mata sallama yafice, har yakusa isa ƙofar da zai fita daga Parlour Nazeefa tafito daga kichen riƙe da plate a hannun ta, tana hango shi takira sunan shi "Yaya". Har yariƙe handle ɗin ƙofan yajuyo yana kallon ta, saurin ɗauke kan ta tayi daga kan shi ganin kallon da yake mata, ita kan ta batasan me zatace mishi ba takira shi, sai dai kuma bataso yatafi batare da ya ganta ba, ko da magana ce yahaɗa su "Ina kwana Yaya". Tace dashi tana ɗago kan ta takalle shi "Lafiya, ya jiki?" "Alhamdulillah Yaya". Fita kawai yayi batare da yasake furta ko kalma ɗaya ba, ita kam murmushi tasaki tana jin daɗi a ranta, juyawa tayi tanufi ɗakin ta. Lokacin da ya'isa yayi parcking yafito, ahankali yake tafiya har ya'isa office ɗin sa, har yakama handle ɗin ƙofan zai murɗa sai yakalli setting office ɗin Billy dake rufe, taɓe bakin shi yayi kawai yashige office ɗin sa yamayar da ƙofa yarufe, ahankali ya'isa jikin window yana saka hannu ya yaye cooten ɗin, gyara tsayuwan sa yayi yasanya hannayen sa cikin aljihu yana ƙure waje da idanu, a zahiri titi yake kallo but a baɗini tunanin mafita yake yi, tsawon mintuna yana wajen kafin yataka yanufi kujera yazauna, buɗe computer'n sa yayi, sai kuma yadunƙule hannun sa biyu yaɗaura a haɓar sa yaci gaba da tunanin sa Nocking Brr. Tahir yayi yashigo, har yazauna Brr. Khalil be san ya zauna ba, sai da yakaɗa masa hannun sa a setting face ɗin sa tukun yaƙyafta idanu yana kallon shi "Wai tunanin me kake yi ne har nashigo baka sani ba?" Ajiyan zuciya Brr. Khalil yayi yana gyara zaman sa yace "Wlh Dad ne yake son tada min da hankali". "Me yafaru?" Brr. Tahir yatambaye sa "Wai cewa yayi nan da lokacin da zamu ƙarƙare Shari'a nafito da matar da zan aura, ko wa yace mishi na damu da auren yanzu, kawai zai jagula min lissafi wlh". Dariya Brr. Tahir yayi kana yace "Wlh kana bani mamaki Ib, wani lokacin har tunani nake yi ko dai ba lafiyanka ƙalau ba, ni a ganina kai kakeso katakura kan ka but ban ga aibun Dad anan ba". "To me kake nufi kenan?" Khalil ɗin yatambaye sa yana ɗaure fuska "No babu komi, but ni dai shawaran da zan baka kafitar da wata cikin matan da suke ƙaunar ka, ko da kai ba ka ƙaunar ta". Khalil yace "kana nufin kenan in yi auren rashin ƙauna?" "Eh mana tunda har yanzu baka sami wacce tayi maka ba duk acikin matan da suke son ka, ba mamaki kai irin mazan nan ne da basu gane meye so sai lokacin da suka auri matar, sannan alokacin zasu gane sun faɗa tafkin ƙauna". Shiru Khalil yayi yana tunani Brr. Tahir yace "kar ka matsa ma kanka Ib, me zai hana ka amince wa Billy, tunda ita kaɗai naga alaman zatafi dacewa da kai, kuma kai kan ka sheda ne yanda take matuƙar ƙaunar ka, zata iya yin komi sabida kai, don haka kawai kaba ma zuciyar ka dama takoyi son ta kafin zuwan lokacin, idan har kaji zuciyar ka bata kwanta da ita ba zaka iya sauya wa". Still dai shiru Khalil yayi yana nazarin maganganun Brr. Tahir ɗin, kuma daga baya sai yace "Shikenan zan yi tunani akai". "Ok". Daga nan tattauna wa sukaci gaba da yi kafin Brr. Tahir yatafi yabar shi, shi kuma yaci gaba da aiki har zuwa lokacin tashin shi, ahankali yamiƙe cike da gajiya yatattara kayan sa yafice, a hanya suka haɗu da Brr. Tahir har suka ƙarisa wajen motan su Brr. Tahir yace "yau baka tambayi mutumiyar ka ba? Kuma kana gani yau ɗin baka ganta ba". Ɗan taɓe fuska kawai Khalil yayi yabuɗe motan sa yana shirin shiga, riƙo murfin motan Brr. Tahir yayi yace "Kenan baza ka tambaya ba ko?" "To tunda kayi ninyan faɗa min menene kuma sai na tambaya?" Khalil ɗin yafaɗa yana tsare shi da idanu Murmushi Brr. Tahir ɗin yayi yace "Gaskiya baka da dama Abokina, in ba ni ba babu wanda zai iya da halinka". Harara Khalil yayi masa kamar wani mace yace "Tunda gani me baƙin hali ko? Dole kace babu wanda zai iya dani". Dariya yayi yana rufe bakin sa yace "Rufa min asiri don Allah wasa nake maka, but seriously Billy ɗin ka bata da lafiya fa, yanzu nima nake ji wajen Brr. Kuma". Wani irin kallo Khalil yayi masa, be ce komi ba yajanye murfin motan sa yarufe, leƙo da kai Brr. Tahir yayi yace "Bakace komi ba zaka tafi?" "Me kake so nace maka Umhm?" Khalil ɗin yafaɗa yana ma Motan keey "Muje mu gaishe ta mana, kaga daga nan sai kashigar da kanka ka gane ai". Brr. Tahir yace hakan yana dariya ƙasa-ƙasa Gajeran tsaki yayi tare da jan motan sa yayi gaba, shima dai Brr. Tahir ɗin motan sa yanufa yashiga yana ci gaba da dariya tare da girgiza kan sa. [9/18/2020, 9:47 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 24* Lokacin da ya'isa gida yayi parcking motan sa, sai da yayi kusan mintuna 5 kafin yabuɗe motan yafito, ahankali yake takawa har yashiga cikin gidan, akan sofa yazube yana kwantar da kan sa cike da gajiya, dafe goshin sa dake ɗan sara masa yayi yana lumshe kyawawan idanun sa, few minutes ago yacire hannun yana tashi tsaye yanufi ɗaki, koda yashiga wanka yasoma yi sabida yaji ƙarfin jikin sa, don sosai yake jin sa kamar an mishi dukan tsiya, bayan ya shirya cikin brown ɗin jallabiya da Three qweater sai yafito parlour yanufi kichen kai tsaye, shiru yayi yana tunanin abinda zai dafa, don sosai yagaji da cin indome, kuma so yake yaci abu me ɗan nauyi coz yunwan dake ƙwaƙulan sa, tea yafara haɗawa yazauna nan kichen ɗin yashanye cikin ƙanƙanin lokaci, kana yasoma girka makaroni, shi ba wani ma'abocin iya girki bane don be taɓa yi ba in banda indome da yake dafa wa, but haka dai yayi karanbanin sa yasoma ƙoƙarin girka wa, sai da yaɗaura tukunya a wuta sannan yakurma ruwa rabin tukunyan, yana soma zafi yaɗauko makoroni biyu yasake, don yana son yagirka ne har dare yahuta da ɗame-ɗame, bayan ya sake ne sai yaɗauko Maggi yazuba sannan yaɗauko kayan miya, blanda yaɗauko yasoma yunƙurin blanding ɗin sa, lokacin duk zufa ya ishe shi hakan yasaka yatashi yafice, rigan jikin sa yacire yajefa saman sofa, yadawo daga shi sai singlate ajikin sa yasoma blanding kayan miyan, bayan ya gama duk yasake cikin tukunyan, yazauna nan yana jiran yanuna, gaba ɗaya ya manta da cewa ko mai be zuba ba, sai da yabuɗe yaga yana ta zaɓarɓaka yatuna ai be zuba mai ba, ɗauko wa yayi yadiddila yamayar yaci gaba da zama, sai da yabashi good 30min kafin yabuɗe, lokacin tuni ya nuna sai dai ruwa da yayi yawa hakan yasaka yacaɓe, but be damu ba yaɗauko plate yaɗiba yarufe sauran, ɗauka yayi yafito yanufi saman dainnig ya'ajiye, sai yaje yaɗauko Faro water da kwalin Juice yadawo yazauna, spoon yaɗauka yana kallon abincin, kamar baya son ci sai kuma yasaka spoon ɗin yaɗiba yakai bakin sa, taunan farko yadakata yana taɓe baki, ahankali kuma yaci gaba da taunawa har yahaɗiye, kana yasoma tsakalan abincin kaɗan-kaɗan yana ci, ko kaɗan babu daɗi but yakasa dena ci sabida yunwan da yake ji, yayi dana sanin dafa wa, da tun farko yayi indome'n sa da tuni yacinye lafiya lau duk da ba wani iyawa yayi ba, but yafi wannan jagwalgwalon, sai da yaji cikin sa yasoma murɗa masa yana mishi ciwo kafin yamiƙe yaɗau plate ɗin yakai kichen tare da sake sauran cikin tukunya Parlour yadawo yazauna yana ɗaukan wayan sa dake ajiye yasoma latsawa, ahankali yatsai da abinda yake yi yana nazarin abinda yake son aikata wa, tsawon minti 3 kafin yaci gaba da latsawa sannan yakara a kunne "Assalamu alaikum". Jin muryan ta a cikin kunnen sa yasaka shi lumshe idanun sa yana gyara zaman sa tare da ɗaura kan sa saman kujeran "Wa'asalaikis Salam". Ya'amsa mata cikin cool voice ɗin sa me daɗin sauraro Shiru ne yabiyo bayan amsa sallaman nasa, domin ita a fannin ta mamaki ne yakusa kashe ta, abinda bata taɓa gani ba ko da a mafarki ne wai Brr. Khalil zai kira ta.. katse mata tunanin ta yayi da faɗin "Baki iya gaisuwa ba?" Bilkisu da rawan baki tace "Ina yini?" "Lafiya, ke fa yakike?" Tace "lafiya lau". "Ke da akace min baki da lafiya kuma shine kike Son yin min ƙarya?" Batasan sanda tasaki murmushi ba cike da tsananin farin cikin da yakusa kashe ta tace "Ai naji sauƙi, dama zazzaɓi ne". Taɓe baki yayi sai kuma yagyaɗa kan sa, still kuma yace "Ai naga alama tunda gashi kina min dariya". Kamar yana ganin ta tayi saurin rufe bakin ta tana faɗin "Wlh ba da kai nake yi ba". "To da wa kike?" Yatambaye ta yana wani rage murya Bilkisu ta kasa magana fa, sai kace ba abinda take nema bane yasamu amma kun ji tayi gumm kamar munafuka "Kin yi shiru kuma? Ko bazaki faɗa min ba?" "Uhm babu kowa". "Ok dama nakira naji jikin ki ne, tunda kin sami sauƙi naji daɗi, bye". Be jira cewar ta ba yakatse wayan. Ita kam Bilkisu tana jin yakashe kiran sai tawani kurma ihu tana burgima saman gadon ta, Allah yasa ita kaɗai ce a gidan da har waje sai an ji "Wayyo Allana yau daɗi zai kashe Ni, wai Ib ne yakira ni? Wayyo ko dai mafarki nake yi?" Sai tamiƙe daga kwancen da take tana rarumar wayar ta taduba, washe baki tayi ganin dai ba mafarki bane, kwanciya takuma yi tana rarumo pilow tamatse tana cewa "Wayyo daɗi kashe ni, wayyo ni Billy yau duniyar ta kai min inda nake so, gaskiya yau na kasance me Sa'a, wayyo Allana Wayyo Allana wa zai taya ni farin ciki?" _(Ni kam nace *NAFEESA GROUP FAN'S* su taya ki, ko kuma *BRR. IBRAHIM KHALIL FAN'S* don Ni dai ban da lokacin ki lol😅 💃💃)_ Shi kuma da gama wayan miƙe wa yayi yaɗau rigan sa yasaka kafin yashige ɗaki, alwala yaɗauro yafito yanufi masjid, bayan ya idar da sallah yafito yakamo hanya, gab da yakusa isa gidan sa yahango Kausar tafito daga gida, tana sanye ne cikin wata Farar riga me dogon hannu zuwa cinyan ta, sai wani burgujejen wando Three qweater me manyan aljihu kalan Orange 🍊, sai tasanya hula facing cap shima kalan wandon, kitson da tayi guda biyu jelan tazubo shi gefe da gefen kafaɗan ta, tunda itama tahango shi tanufo shi da murmushi a fuskar ta, tana iso wa wajen sa tace "Yanzu nake tunanin ka a raina sai ga ka". Yanda tayi maganar ne yasaka shi ɗan murmusawa yace "Zaki bani wani abu ne?" Sai ta langaɓar da kan ta tace "Eh in dai kana so". "Why not?" Yafaɗa yana waro idanun sa Sai tayi murmushi kana tace "Dama ina so muhaɗu ne kawai, coz akwai tambayan da zan maka". Be ce mata komi ba sai dai ƙure ta da idanu da yayi, yana jiran abinda zatace "An bani labarin kuna Shari'a da wani Alhaji Mubarak mai kuɗi, and nan da five days zaku koma Court, shine zan iya zuwa muyi hira akai, ina nufin ina son nasan komai". Taƙarike maganar tana ɗan kwantar da murya tare da ƙifƙifta idanu Shiru yayi still har yanzu idanun sa akan ta, sai tasake cewa "Please kaji?" "Ok". Yafaɗa ataƙaice yana ɗage kafaɗa "Tom gidan ka zamu je yanzu ko?" tayi maganar cike da zumuɗi "No kibari zuwa gobe sai kizo". Daga haka yayi gaba, ita kuma tatsaya nan tana kallon shi har yashige, sai tasaki murmushi tanufi wajen gidan su tatsaya, dama abinda yafito da ita kenan shan iska, a cewar ta gidan yayi mata zafi, tana nan tsaye tana kallon tsare-tsaren gidajen mutane tana tunane-tunanen ta, wayan ta yasoma ringing, cirowa tayi cikin aljuhu takalli fuskar wayan, sunan HONEY ne yafito ɓaro-ɓaro hakan yasaka tasaki murmushi tana amsa call ɗin, tajuya tashige gida. ........ ........... .......... Washe gari wajen ƙarfe 03:30pm. Kausar tashigo gidan Khalil, yau tana sanye cikin wata doguwar riga ce mare nauyi red colour, sai ɗankwalin shi da tayafa akan ta kawai, tansaya Hill shoes a ƙafafun ta, tana riƙe da wayan ta iPad fara, nocking tasoma yi amma shiru, hakan yasaka taci gaba da yi babu ƙauƙautawa, tafi minti goma a wajen tana nocking, sosai tagaji but kuma taƙi tafiya A ciki kuwa tun da yadawo aiki yakwanta barci, sama-sama yake jiyo nocking ɗin daga ɗakin sa, ahankali yabuɗe idanun sa yana sake jiyo nocking ɗin, tsaki yaja yatashi zaune yana miƙa, sai da yafi 3min a zaune kafin yamiƙe yafito daga shi sai baƙar singlate ajikin sa, da gajeren wando yellow, ƙofan yabuɗe suka haɗa ido da ita, dasauri tasad da kai ƙasa tana jin matsananciyar kunya, cikin sanyin murya tace "Sorry ban san kana barci bane, bari in koma zan dawo". "Kishigo". Abinda yafaɗa kenan yajuya yashige ɗakin sa Sai da taji ƙaran rufe ƙofa tukun taɗago kan ta, leƙawa tasoma yi kafin tashiga, saɗaf-sadaf haka take tafiya kamar wata munafuka, har ta'isa kan kujera tazauna tana kallon parlour'n, sosai tsarin gidan yayi mata kyau, har yaso yafi nasu duk da su ma nasu yana da kyau, but wannan komi kakalla kasan ba ƙaramin abu me tsada bane, sosai aka kashe kuɗi cikin parlour'n duk da ba wani kaya ne a ciki ba, tana nan tana kalle-kallen ta kamar wacce bata taɓa ganin irin sa ba, yafito sanye da riga me ruwan zuma da zane-zanen fari ajiki, sai wando Three qweater fari, ƙariso wa yayi yazauna a kujeran dake facing ɗin ta yana kallon ta, ɗago kai tayi itama tana kallon shi tace "Ina yini?" "Lafiya". Ya'amsa ataƙaice yana jingina bayan sa da kujera yalumshe idanu Ita kuma sai tatsaya tana kallon shi cike da burgewa, komi nasa me kyau ne, yana da matuƙar kyau da kwarjini, babu macen da zata gan shi batayi fatan samun shi ba, buɗe idanun sa yayi yasauke a kan ta, sai tawayan ce takau da kai Yace "me zaki sha?" Sai tamaida idanun ta kan sa, kamar bashi yayi maganan ba "I'm ok". Tace dashi tana mayar da idanun ta kan wayan ta da taɗaura saman jikinta, tasoma latsawa kana tace "Ko zamu iya farawa?" "Ok". Daga nan yasoma bata bayani akan komi, har zuwa sanda suka gama yamiƙe yanufi hanyan kichen, wata iriyan yunwa yake ji, komi be saka a cikin sa ba tun tea ɗin safe, kuma da yadawo barci sosai yarufe masa idanu sakamakon jiya be yi ishashshe ba Yana tsaye cikin kichen ɗin yana ƙoƙarin ɗaura tukunya, yaji muryan ta a bayan sa "Me zaka dafa?" Juyowa yayi yana kallon ta, don be tsammaci zuwan ta ba, murmushi tayi masa tatako ta'iso wajen sa tana faɗin "Kaje sai in yi maka girkin". Tayi maganar tana ɗaura hannun ta saman tukunyan tana gyara mishi zama Babu musu kuwa yajuya yatafi, be san meyasaka yarinyan take son shige masa ba, but ko kaɗan ba ta bashi haushi sai burge shi da take yi, yana nan zaune a Parlour yana kallo har tagama tazubo mishi, a gaban shi ta ajiye saman Centre table tace "Bismillah ko". Tayi maganar tana kallon sa da murmushi a face ɗin ta Shima kallon ta yayi sai yakalli abincin, taliya ne me manygaɗa da yaji cUrry da yankakken ƙwai a sama, murmushi yasaki yace "Thank you, kema ki zubo naki kici". Yarfe hannun ta tayi tace "No ni na ƙoshi, ina sauri akwai inda zan je". Gyaɗa mata kai kawai yayi, sai tajuya tatafi shi kuma yabi ta da kallo, sai da takai bakin ƙofa tajuyo tana kallon sa taɗaga masa hannu sannan tafice. [9/23/2020, 7:28 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 25* *FEW DAYS* "My dear kiyi sauri Kar kiyi late kuma?" Halwa dake cikin ɗaki cikin sanyin murya tace "to Yaya ga ninan". Fitowa tayi riƙe da Bairo a hannun ta tana kallon yayan nata, shima kallon ta yake yi cike da tausayin ta, gaba ɗaya duk ta rame sabida zazzaɓin da yasako ta agaba kwana biyu, tayi haske kallo ɗaya zakayi mata kagane sosai take cikin ciwo, itama Mama dake zaune kallon ta tayi tace "Ni kuwa idan ba yazama dole bane Halwa a fasa zuwa makarantan nan mana, kinga yanda kika yi kuwa? Ba fa sauƙi kika ji ba?" Kallon Maman tayi kawai tana marairaice fuska kamar zatayi kuka Nura yace "Mama wannan jarabawan fa tana da muhimmanci tunda na fita ne, haka nan zata lallaɓa tayi har su kammala, kinga jiya ma taje tayi tadawo lafiya, zaki ga sauran ma kamar yanzu ne har an gama". "Um um Nura, yau kaduba kagani sosai take jin jiki ko abinci ta kasa ci, ga wahalan da zataje tasha, me zai hana abari wani shekarar sai tarubuta". Nura yace "kai Mama har shekara sai tayi ta zama agida? Kema kinsan halinta ba yarda zatayi ba". Halwa tace "Mama ki dena maganar nan ma, kuma Ni haka nan zan je in zana jarabawa ta, sai dai in ciwon ya kwantar dani ne amma banga abinda zai hana ni zuwa ba". Murmushi Nura yace "to kin ji dai". Kaɗa kai Mama kawai tayi tace "ai shikenan Ni dama tausayin ki nake ji, yanzu ku hanzarta kutafi kar lokaci yaƙure". Fita suka yi, A mashine ɗin Abokin Nuran yakai ta har cikin makaranta, yasauke ta a bakin ajin su. Bayan kamar mintuna 20 aka zo raba musu pepper, lokacin ne kuma sosai jikin Halwa yayi tsanani, jikin ta sai kakkarwa yake yi zazzafan zazzaɓi yarufe ta, kasancewar mutum ɗaya-ɗaya ake zama a sit shiyasaka babu wanda ya lura da ita, tana can kusa da baya ajikin bango ta takure waje ɗaya, sai takifa kan ta a table tana hawaye, ita kan ta takasa jure yanayin da take ji, sai da Wani Malami yazo miƙa mata Pepper yakira sunan ta "Halwa lafiyan ki lau kuwa? Za'a yi jarabawa kina kwance". Ahankali taɗago kan ta tana ƙanƙame jikinta, face ɗin ta duk hawaye, kuma sai rawan ɗari take yi "Subhanallah.. baki da lafiya ne?" Malam ɗin yafaɗa yana kallon ta Gyaɗa masa kai tayi don takasa magana ma "To yanzu ya za'a yi kenan? Zaki iya yin jarabawan?" Shiru tayi bata iya cewa komai ba, su kuma ƴan ajin yawancin su hankalin su na wajen, har da Zainab aciki, duk tausayin Ƙawartan ya kamata, ɗaya daga cikin Malaman dake tsaron su yace "Ku me kuke kallo ne baza kuyi abinda ke gaban ku ba?" Sai kowa yamayar da kan sa ƙasa suka soma duba peppern, Malam Isma'il dake can bakin ƙofan yace "Ai kabar su Malam Kamal, time na cika amsa zamuyi mu wuce". Malam Jamilu dake tsaye har yanzu kan Halwa still yace da ita "Halwa ko dai bazaki iya bane? In ciwon yayi tsanani kije ki amso magani kisha kinji?". Cike da ƙarfin hali tace "zan iya Malam". "Ok to gashi". Aje mata yayi a gaban ta, yaja gefe nan yana kallon ta tare da kula da waɗanda suke wajen, ita kam ahankali tajanyo pepern ta'aza Bairo akai, tayi shiru ta kasa rubuta komi, sai da tayi kusan mintuna 5 kafin tasoma rubuta sunan ta daƙyar, bayan ta gama tasoma amsa Questions ɗin, Number One taɗauka tafara dashi, ahankali tatsayar da hannun ta daga rubutun da take yi tana runtse idanu, wannan karon jikinta sosai yake rawa har da hannun ta, Malam Jamilu dake tsaye yana kallon ta yace "Gaskiya bazaki iya wannan jarabawan ba, tashi kije kisha magani, inyaso sai asamo wani yarubuta miki". "Halwa". Malam Isma'il da yaƙaraso wajen yakira sunan ta Zuwa lokacin kuka take yi kan ta a ƙasa ta kasa amsawa Yace "wai meke damunki ne? Ciwon me kike yi sai a amso miki maganin?" Still shiru babu amsa sai kukan ta dake daɗa ƙaruwa Malam Jamilu yace "Zainab taso kije da ita tasha magani". Dasauri Zainab tataso tataho wajen tariƙo Halwa dake langaɓe wa, ta rufe fuskarta still tana kuka, suna fita tasoma sheƙa amai kamar zata amayo hanjin cikin ta, sabida babu komi a aman kasancewar bataci abinci ba, nan da nan hankalin Malaman yatashi suka fito waje suna mata sannu Malam Kamal yace "gaskiya wannan ciwon be kamata abarta anan ba, yakamata amaida ita gida". Malam Isma'il yace "Eh haka za'a yi kuwa, tunda nasan gidan su bari inje in kai ta". Daga haka yajuya dasauri yanufi inda suke parcking yaburgo mashine ɗin sa yataho wajen, da taimakon Zainab aka ɗaura Halwa akan mashine ɗin, zuwa lokacin duk ta galabaita bata ma iya tsayuwa Malam Jamilu yace "Zainab kihau bayan ta kuje tare, sai ku dawo tare da Malam Isma'il". "To Malam". Cewar Zainab kenan, kana tahau bayan mashine ɗin Sai da sukaga tafiyar su kafin Malaman suka koma ciki. Koda suka isa gida bayan sun sauka, Zainab tariƙo ta suka shiga cikin gidan, Mama na ɗaki tana kwance tajiyo sallaman Zainab, amsa mata tayi tana tashi zaune, ahankali suke tafiya har suka isa bakin ƙofar Maman, Zainab taɗaga musu labule suka shige "Subhanallah.. lafiya Zainab me yafaru da ita?" Mama tafaɗa tana tashi tsaye cike da ruɗewa "Mama wlh jikin ta ne yayi tsanani, shine Malaman sukace adawo da ita gida". Mama tariƙo ta tana zaunar da ita saman gadon ta, kana tace "Dama tunda naga jikin nata da tsanani na san bazata iya taɓuwa komi ba, sai dai taurin kanta ya saka taƙi haƙura, gashi an dawo dake ai". Zainab tace "Mama bari inje, Allah yaƙara lafiya". "Ameen ameen Zainab, mungode kinji?" Zainab na fita, Mama tazauna gefen gadon tana kallon Halwa da har yanzu take rawan sanyi tana kuka tace "Yanzu kuma da ina da ina yake miki ciwo inje nasiyo miki magani? Kamar ma amai kika yi ko? Don gashi duk kin ɓata Hijabin ki". Tana sauke maganar ta Halwan tasoma kwarara wani aman daga kwance, dasauri Mama tariƙe ta ganin zata faɗo daga kan gadon, sai da tagama aman kafin tasake ta tana faɗin "Oh Ni Hauwa, gaskiya ban ga tazama ba dole muje asibiti, tashi tashi muje kiwanke jikin ki mutafi asibiti, Allah dai yabaki lafiya ƴar nan, wannan ciwo haka". Da taimakon Maman suka fito waje, taje taɗibo ruwa a botiki ta'ajiye a gaban ta, ita da kan ta Maman taɗauraye mata jikin takaita har ɗaki, kana tazaɓo mata wasu riga da wando na Pakistan, rigan Light and Dack Orange 🍊 colour ne, sai wandon kuma dack orange ne da ɗankwalin "Gashinan ki saka, bari inzo". Mama tafaɗa tana ficewa Ahankali Halwan tatashi tasaka kayan, sannan tasanya ƙaramin Hijab Baƙi tafito, itama Mama lokacin ta sanyo Hijabin ta suka fice. Lokacin da suka isa asibiti minti goma suka ɗauka kafin sukaga likita, bayan sun shiga office ɗin sun zauna ne Doctor ɗin yasoma mata tambayoyi tana amsa mishi, har sanda yagama sannan yakira Wata Nurse yace "taje da ita tayi mata gwaje-gwaje". Bayan kamar mintuna 20 sai gashi sun dawo tare da Nurse ɗin, sakamakon Nurse tabashi sannan tafice, bayan ya amsa ya gani yayi rubuce-rubuce sannan yaɗago yana kallon su "Am Mama.. a binciken da mukayi mata, sakamakon ya ba mu tana ɗauke da ciki har na wata ɗaya da sati, kuma sannan.." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ci..Cikiii?". Mama tafaɗa da ƙarfi tana kallon Likitan da shima yadakata yana zuba mata nashi idanun "Haba dai Likita kasake dubawa kagani sam ban yarda ba, ciki fa kace? Ciki Halwa take dashi? Ina sam ƙarya ne wlh". Halwa kuwa tun sanda kalman cikin yadaki kunnen ta, atare zuciyarta da ƙwaƙwalwan ta suka amsa, tsananin tsoro da firgici yabayyana a fuskarta har sai da komi dake motsi a jikin ta yadena aiki na tsawon wasu sakonni kafin tadawo dai-dai, sai kuma tazamo saman kujeran da take kai tazube ƙasa jikinta na wani irin kyarma tana shatatar da hawaye. . _To ya kukaji FAN'S?_ _Ya za'a kaya?._ _Me zai faru?._ _Hmm yanzu aka fara muje zuwa._ _Taku Jikar LAWALI CE✍️ kubiyo ni don jin Me zai faru next.. karku manta ku suburbuɗo Comments da yawa da yawa don samun post me yawa._💃💃💃💃💃💃💃 [9/23/2020, 7:28 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 26* Tunda suka fito daga asibitin suka shiga cikin keke napep Halwa take faman kuka, duk ta takure waje ɗaya ta rufe fuskarta da Hijab, Mama kuwa itama tunda tazauna taɗauke kai gefe, maganganun Doctor kawai suke dawo mata cikin kunnen ta, zuciyar ta sai wani irin tafarfasa take yi ƙiris take jira, suna kai wa tasauka tabashi kuɗin shi tashige gida dasauri, Halwa kuwa ahankali tasauko tanufi gidan nasu, sai dai takasa shiga ciki sai tatsaya a zaure tana ta kuka, tana nan tsaye a wajen sai ga Baba da Nura sun shigo atare, suna ganin ta sukasan babu lafiya, domin Mama takira su a waya tace su dawo yanzu, kuma bata faɗa musu abinda ke faruwa ba, Baba ne yasoma cewa "Halwa me kike yi anan? Me yafaru ne?" Bata ɗago kai ba sai ma ƙara volume ɗin kukan ta da tayi, nan da nan jikinta yasoma rawa kamar an sakata a shocking, Nura zuwa yayi yariƙo ta yana faɗin "Lafiya Halwa? Menene haka wa yabige ki?" Still shima shiru tayi masa Baba yace "Nura taho da ita mushiga gidan sai muji ba'asi wajen Maman taku". Riƙo ta kuwa Nura yayi, babu musu tabi shi suka shiga ciki, ɗakin Mama suka nufa gaba ɗayan su, Mama na zaune tana faman hawaye suka shigo, abinda yaƙara ɗaure musu kai kenan suka hau tambayan ta "lafiya?" Hankalin su duk atashe, but Mama taƙi tayi magana sai Hawayen ta take yi, zama Baba yayi gefen ta yayinda Nura ma yasamu waje yazauna yajanyo hannun Halwa itama tazauna kusa dashi Baba yace "wai Hauwa lafiya muka ganku a wannan yanayin? Meke faruwa ne kiyi mana bayani?" Ɗago kan ta tayi cikin baƙin ciki tace "Wani bayani kakeso kaji Baban Nura? Ace wai yau Halwa ce tayo mana ciki agida, cikin shege fa Halwa tayi a gidan nan". Sai tasake fashewa da kuka Atare Baba da Nura suka maimaita cikin Shegen, Nura har da ja da baya yana matsawa kusa da ita, cikin kaɗuwa Baba yakalli Halwa da har yanzu takasa buɗe idanun ta yace "Dagaske ne cikin Shege kikayo min agida?" Shiru Halwa tayi "To ya za'a yi tafaɗa maka? yanzu muka dawo daga asibiti likita yatabbatar mana tana ɗauke da cikin Shege acikin ta, to wlh tallahi ba dai nan gidan ba, bazai taɓa saɓuwa ki haifa mana ɗan Shege agidan nan ba, duk gatan da mukayi miki Halwa kikasa saka mana da abun kirki sai abun tsiya? ashe duk zaman da muke yi dake amanar mu kike ci mu duk bamu sani ba? To baza mu ga wannan abun kunyan ba dole ki koma can dangin mahaifin ki tunda bakisan halacci ba, na rabo ki da can ne don naga kina shan wahala amma kin nuna mana ke ba mutumiyar arziƙi bace". Baba ya'amshe zancen cikin sauri yace "Ni Malam Ayuba za'a zubar min da mutunci agida? da ƙima ta da daraja ta yau za'a haifa min shegen ciki?" Halwa kuwa in banda kuka babu abunda take yi, sosai zuciyarta takaɗu da kalaman Maman nata, "wanna wace irin baƙar rana ce tazo mata?" Meyasa duniya take son juya mata baya?" Baba yaci gaba da faɗin "Kin bani mamaki Halwa kinci amanar yardan da mukayi miki, kina son ki zubar mana da mutunci duk yanda ake ganin mu a gari sai gashi ace za'a haifi ɗan Shege a gidana, to ba dai nan gidan ba dole kibar min gida, iya zaman da kikayi agidan ma ya isa haka, kitashi kiwuce kije kihaɗo kayan ki tun kafin wasu suji, in kin shirya kizo ki amshi kuɗin mota". Ɗago kanta Halwa tayi da idanuwanta suka kaɗa sukayi jazur sukayi luhu-luhu, cikin tsananin kuka tace Don girman Allah Mama kuyarda dani wlh Fyaɗe akayi min, Yaya Nura ma ya sani wlh ban taɓa sanin wani namiji ba.." Dasauri Nura yace "keeee Halwa sharrin kuma kaina zai koma? Aina nasan anyi miki Fyaɗe? Ke dai kawai kina zuwa makaranta kina yawon banzan ki kin kwaso ciki zakice na sani, kinci amana ta Halwa, kinci amanar soyayya da yardan da nayi miki, Allah ya isa tsakani na dake". A firgice takalle shi sai dai takasa furta komi sabida zallan mamaki da kuma rawan da bakin ta yake yi, shi kuma Baba cikin ɓacin rai yace "Halwa wato so kike yi kidangana akan ɗana? Cikin ma sai ki iya cewa shine yayi miki ko?". Girgiza kan ta kawai take yi tana hawaye, ita har yanzu takasa yarda da cewa Yayan ta Masoyinta shine yajuya mata baya yake faɗan kalman ɓatanci akan ta, takasa yarda Mama da Baba zasu ƙi yarda da ƙaddaran da yasaukar mata "Ya Allah.. meke shirin faruwa da ni ne? Wayyo Allana ko dai mafarki nake yi?". "Abinda kika aikata ne yake bibiyanki Halwa, kitashi kiwuce kibar mana gida, wlh nayi imani da Allah da Lubabatu tana raye kika kwaso wannan abun kunyan wlh da sai ta kashe ki". Mama tafaɗi hakan tana sake fashewa da kuka, cikin kukan take faɗin "Allah mun gode maka da ɗana be auri mazinaciya ba, da yanzu anyi auren shikenan kin cuce shi". Tsawa Baba yasake daka mata babu shiri tamiƙe tana dafe da kanta dake faman sara mata kamar zai rabe gida biyu tafice, bata iya tsayawa ko ina ba Direct waje tanufa, sabida gaba ɗaya hankalin ta da tunanin ta sun gushe, maganganun Nura kawai suke dawo mata cikin kunne _"Ke dai kawai kina zuwa makaranta kina yawon banzan ki kin kwaso ciki zakice na sani, kinci amana ta Halwa, kinci amanar Soyayya da yardan da nayi miki, Allah ya isa tsakani na dake"_ Hannu biyu tasanya tatoshe kunnuwan ta tana wani irin kuka me tsuma ran me sauraro, kuka take yi sosai da har yasa bata iya ganin gaban ta, sabida yanda hawayen suke ambaliya kamar an kunna famfo, har yanzu takasa yarda da cewa abinda ke faruwa da ita a yau ɗin gaske ne, so take yi kawai tafarka daga wannan mummunan mafarkin, tasan dacewa Mama, Baba, Nura bazasu taɓa juya mata baya haka ba Wani lungu tasamu tazauna nan tana ta rizgan kuka har muryan ta yadena fita, sai hawaye da suka ƙi ƙafewa a idanun ta, ta jima a wajen tana son ko wani ne yazo yatashe ta yace mata "Mafarki ne Halwa". Sai dai babu wanda yagibta tun zaman ta, haka tatashi takoma wajen gidan nasu tatsaya tana kallon gidan, idanun ta fal da hawaye, zuciyarta na wani irin bugawa kamar zai faso yafito _"Kin bani mamaki Halwa kinci amanar yardan da mukayi miki, kina son ki zubar mana da mutunci, duk yanda ake ganin mu a gari sai gashi ace za'a haifi ɗan Shege a gidana, to ba dai nan gidan ba, iya zaman da kikayi agidan ma ya isa haka, kitashi kiwuce kije kihaɗo kayan ki tun kafin wasu suji"_ _Wlh nayi imani da Allah da Lubabatu tana raye kika kwaso wannan abun kunyan wlh da sai ta kashe kiiiiiii"_ _"Wato so kike yi ki dangana akan ɗana? Cikin ma sai ki iya cewa shine yayi miki ko?_ _Ki tashi kiwuce kibar mana gida, ki tashi ki wuce kibar mana gida, ki tashi ki wuce kibar mana gida"_ Maganganun su ne suke ta kai kawo cikin ƙwaƙwalwan ta, Wani abu ne yazo yatokare mata wuya batasan sanda taƙwallara ƙara ba tazube nan tana fashewa da sabon kuka, bata taɓa tunanin ita ɗin marainiya bace sai yau "Wayyo Allana na shiga uku na lalace, meyasaka zakuyi min haka? Bakusan cewa wannan shine ƙaddara ta ba? Ya zan yi in kauce masa?" Meyasa? Meyasaka Yaya zaka juya min baya bayan kasan komi? Meyasaka ka aikata min haka duk da kasan abun da yafaru agaban ka akayi komi? Shin ko ka manta soyayyar dake tsakanin mu ne? Ka manta ni ce Halwa Halwan ka kuma ƙanwar ka? Dan Allah kafito kaban amsa Yaya, kazo kafaɗa min dalili". Wasa-wasa Halwa tazama tamkar mahaukaciya a wajen, gaba ɗaya tagama fita hayyacin ta, kuka kawai take yi, kukan da babu hawaye a yanzu bare kuma murya, ta jima anan wajen kuma ikon Allah babu wanda yafito suna can suna jajanta abun da yafaru Kamar an tsikare ta kuma tatashi dasauri tana saka bayan hannun ta tana share hawaye, nufan hanya tayi tana tafiya tana tangaɗi kamar wacce tasha wu, dai-dai lokacin da ta'iso ƙofar gidan su Zainab tanufi gidan, tana saka ƙafa a zauren sai taja tatsaya, maganganun Baba ne suka dawo mata cikin kunnin ta _"Kina son ki zubar mana da mutunci duk yanda ake ganin mu a gari, sai gashi ace za'a haifi ɗan Shege a gidana_" _"Ki tashi kije ki haɗo kayan ki tun kafin wasu suji"_ "Kenan sun gunmaci ni nabar su akan ƙimar su da mutuncin su yazube? Shin bakusan ƙaddara bace? Ashe dama zaku iya korata akan laifin da na aikata bada son raina ba?" Meyasa zakuyi haka?" Tafaɗa afili cikin dashashshiyar muryan ta tana runtse idanu wasu sabbin zafafan hawaye suna gangaro mata Still hannu tasaka tashare hawayen, tajuya da sauri tatafi, tafiya take yi ahankali har ta'isa bakin titi, tadoshi hanya tasoma tafiya a gefen titin batare da tasan takamaiman inda zataje ba, don ko alokacin ba cikin hayyacinta take ba tafiyan kawai take yi, tana juya baya tawuce sai ga Zainab ta ɗaya side ɗin an wuce da ita a cikin keke Napep. _Shin ina kuke tunanin Halwa zata je?_ _wani irin hali zata faɗa?_ _mene yasaka Nura yayi mata wannan abun?_ _Shin ko ya manta da ita wacece a gare shi yayi mata hakan?_ _amsan ku na wajena kubi ni asannu don jin Me zai faru hmmmm._ [9/23/2020, 10:00 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 27* Tayi tafiyan da yakai kusan awanni biyu batare da ta gajiya ba, kuma bata da alaman tsayawa tafiyan kawai take yi but batasan inda take tsulmiya ƙafafuwan ta ba, har sai da taji ƙafafun nata sun soma nauyi suna takawa daƙyar kafin tasamu gefen wani shago tazauna tana sakin nishi, kallo ɗaya kayi mata zaka gane tana cikin wani mawuyacin hali da baza ka iya fassara shi ba, idanunta gaba ɗaya sun wani jeme sun yi luhu-luhu, har alokacin kuma basu gama washe wa daga canza kalan da suka yi ba, hannun ta tasanya tariƙe goshin ta tana runtse idanu, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta da yanzu yaƙara hauhawa kamar zai faso ƙirjin ta sabida wani irin bugawa da yake yi Takun takalmi taji da gudu-gudu, hakan yasaka tabuɗe idanun ta tasauke akan sa, shima ɗin itan yake kallo har ya'iso wajen ta, sai yashiga wani lungu da shaguna biyu suka rufe wajen, bata sauke idanun ta a wajen ba kuma bata motsa ba har sai da tajiyo takun wasu mutanen, hakan yasaka tajuya tana kallon su, mutane uku ne da baƙaƙen kaya sun sha Suit, hannun su na cikin rigan su da alamun dai akwai abinda suka ɓoye, har sun gibta ta sai ɗaya yadawo da baya yana kallon ta da fuskar shi a ɗaure yace "Keee ƴan mata bakiga wani yawuce tanan ba? Ina kikaga yabi?" Ɗauke idanun ta tayi akan sa tamayar inda taga mutumin nan ya ɓoye, sai taga yaleƙo kan sa suka sake haɗa idanu, kallon ta kawai yake yi da idanun sa masu bala'in kyawu ko ƙyaftawa baya yi batare da ko yayi mata alaman kar tatona shi ba "Ke magana muke miki fa? Baki ga wani yawuce tanan ba?" Gyaɗa kan ta kawai tayi tana sauke idanun ta ƙasa, wucewa sukayi batare da sun sake magana ba, sai da sukayi nisa da tafiya kafin yafito, ita kuma taɗago idanu tana kallon sa still shima kallon ta yake yi, sai da sukayi 2min suna kallon juna kafin yajuya dasauri yawuce, kau da kai tayi tana tunanin abinda yasaka mutanen suke neman sa? Sai kuma taruntse idanuwan ta tana jin damuwan ta na dawo mata, hawaye ne suka soma zuba cikin idanun suna gangarowa saman kuncin ta "Ya zan yi?" Tafaɗa a fili tana wurwurga idanu a hanya "Wayyo Allah Ni Halwa, Allah na roƙe ka Allah kakawo min agaji, Allah na roƙe ka ya Allah kataimake ni, kataimaki rayuwata, Allah ina buƙatan taimako". Sai tafashe da kuka me ban tausayi Ɗaura kanta akan ƙafafunta tayi tasoma rerawa, kai daga jin kukan kasan na ƙunci da baƙin ciki ne, ta jima a wannan yanayin kafin tamiƙe tasoma tafiya, alokacin hankalin ta baya jikin ta tana can tana tunanin kalaman Nura tana yi tana sharan hawaye, sosai tadamu ƙwaƙwalwan ta da son sanin meyasaka ya'aikata mata hakan? sai jinta tayi a ƙasa batare da tasan abinda yasame ta ba "Subhanallah.. don Allah baiwar Allah kiyi haƙuri, wlh bansan kin taho ba nabige ki da motata". Sai alokacin Halwa taɗago kanta tasauke shanyayyun idanunta kan matashiyar budurwan da aƙalla zata bata shekara ɗaya zuwa da rabi "Don Allah kiyi haƙuri, muje chemis ayi miki dress ɗin ƙafan kinji don Allah?". Hakan yasaka halwa tamayar da idanunta kan ƙafanta dake zubo da jini sakamakon ƙurjewan da tayi, but ko kaɗan bataji zafi ba bare tasan taji ciwon, bcoz zafin da take ji cikin zuciyarta da jikinta ya hana taji zafin ciwon, yarinyan taɗago ta suka nufi Motan ta, tabuɗe mata gaba tashiga sannan itama tazagaya tashiga taja motan, Chemis ɗin takaita akayi mata dressing ƙafan sannan suka fito, kallonta yarinyan tayi tace "Ina ne gidan ku sai in Kai ki ko?" Shiru Halwa tayi batare da takalli yarinyan ba, kuma bata da alaman bata amsa, ita kuma yarinyan sai kallon ta take yi da alamun tagane tana cikin wata damuwa sakamakon yanda fuskarta yanuna, ga kuma yanayinta, dafa kafaɗanta tayi tace "Ƴar uwa don Allah kifaɗa min ko wani abu na damunki ne zan iya taimaka miki? Haƙiƙa duk wanda yakalle ki yasan da cewa akwai wani babban al'amari dake damunki, don Allah kisanar dani kamar yanda natambaye ki?" Sai alokacin Halwa tasake ɗago kai takalle ta a karo na biyu tun haɗuwan su, still dai batace komi ba tasake sad da kanta ƙasa tana jin hawaye na son zubo mata "Ko baki yarda dani bane?" Yarinyan tafaɗa tana ɗago haɓan ta, dai-dai da lokacin da hawayen da suka taru a cikin kwarmin idanun nata suka gangaro izuwa saman kuncin ta "Subhanallah.. kuka kuma? Me yayi zafi ƴar uwa? Don Allah kifaɗa min damuwar ki?" Tafaɗi maganar itama tana son yin kukan Hakan da Halwa tagani ne yasanya ta motsa baki kaɗan, sai dai yarinyan batasan me tafaɗa ba, don haka tariƙo hannun ta taja ta suka shiga mota, kana tayi wa motan keey tasoma tafiya, shiru babu wanda yayi magana ciki, ita kuma atunanin yarinyan Halwa zata faɗa mata inda zata kaita, saɓanin haka sai taji shiru, hakan yasaka kawai tayanke shawaran tafiya gidan su da ita, don sosai Halwa ɗin taba ta tausayi, haka kawai kuma taji ta kwanta mata arai, kuma nan take tagane tabbas akwai abinda yakorota daga gidan su, ba kuma ƙarami bane babban abu ne A wani gida me ɗankaren kyau da yalwa yarinyan tatsaya tare da yin hon, babu jimawa aka buɗe mata Gate ɗin takutsa motan ciki, bayan tayi parcking ne tajuyo tana kallon Halwa da itama tabaza idanu tana kallon gidan, ita tun sanda tasaka ta cikin motan tarasa tunanin da zatayi, kawai tatsaya ne taga ikon Allah ina zata kaita, kuma ko kaɗan babu tsoro a fuskarta, domin ita yanzu duk abinda zai same ta idan har wanda zai rabata da duniyar ta ne to tana maraba dashi "Muje ko?" Yarinyan tafaɗa tana buɗe motan tafita Babu musu Halwa itama tabuɗe tafito, tabi yarinyan abaya kamar yanda taga ta doshi cikin gidan, bayan sun shiga parlour'n ne yarinyan takalle ta da murmushi a fuskarta tace "Kizauna bari in Kira Ummina". Daga haka tajuya tanufi wani ƙofa tana kwaɗa ma Ummin nata kira Halwa kuwa ƙyam tayi anan tsaye bata da alamun zama, kuma kanta a ƙasa yake batare da taɗago shi ba, babu jimawa yarinyan suka fito tare da wata babban mata me kama da ita sak, sai kuma wani babban mutum da shima suke yanayi da yarinyan, don hasken shi ma tabiyo, atare suka iso cikin parlour'n suna kallon Halwa da itama taɗago idanunta tasauke akan su "Baki zauna ba? Kizauna don Allah?" Yarinyan tace hakan lokacin da ta'iso wajen Halwa takama hannun ta suka zauna kan 2sitter, su ma iyayen nata zama sukayi duk fuskar su cike da mamaki duk da sun san halin ƴar tasu, Mahaifin nata ne yasoma magana da cewa "Saleema ina kika samo wannan yarinyan kuma?" "Abba wlh a hanya ne nabige ta da zan dawo daga school, shine nakaita akayi mata dress". Sai tamarairaice fuska taci gaba da faɗin "Kuma Abba naganta cikin damuwa ne shiyasa nace bari in taimaka mata". Ummee tace "kuma banda abinki Saleema, kinganta cikin damuwa kina son taimaka mata ai gidan su zaki kaita ba nan ba". Abba murmushi yayi yace "Ina ruwan ƴar Baba, kinsan halinta da son taimako". Saleema tace "to Abba ai na tambaye ta inane gidan su bata sanar min ba, shine nakawo ta nan". Jinjina kansu gaba ɗayan su sukayi suna kallon Halwa da kanta ke ƙasa tana sauraron su "To ke kuwa Baiwar Allah Aina kike? Ina ne gidan ku?" Cewar Ummi kenan Shiru Halwa tayi tana wasa da hannun ta don batasan me zatace ba, Abba shima kallon ta yayi yace "Yarinya ki sanar damu mana, zan saka amayar dake har gida insha Allahu". Cikin dashashshiyar muryan ta da ba'a ji sosai tace "Iyayena sun kore ni". "Saleema me tace ne? Mu bamu ji ba". Ummi tafaɗi hakan "Wai iyayen ta sun kore ta". Saleeman tafaɗa cike da tausayi "Subhanallah.. kora kuma?" Abba da Ummi suka faɗa atare "To me kikayi musu?" Ummi tasake tambayar ta Sheshsheƙan kuka Halwa tasoma yi tare da rufe fuskarta da Hijab, cike da tausayin ta Ummi tace "Baiwar Allah kisanar damu abinda ke damun ki, inda hali kibamu tarihin ki, muna Son musan meysaka iyayen ki suka kore ki sabida musan ta inda zamu taimaka miki kinji? Kidena kuka kifaɗa mana damuwar ki". Riƙo ta Saleema tayi tasoma rarrashinta kamar zatayi kuka, duk fuskarta ya nuna tsananin damuwa, sai da tayi shiru tukun tasoma basu labari kamar haka, tanayi tana kuka. Ni sunana Halwa, kuma Ni marainiya ce, tun ina ƙarama Mamana da Babana suka rasu, shine dangin Babana da suke garin Gombe suka ɗauke Ni, na taso a hannun su cikin baƙar azaba har izuwa sanda nasoma girma, shine lokacin da ƙanwar Mahaifiyata tazo ganina taga wahalan da nake sha a hannun su taɗauke ni tadawo dani hannun ta, daga nan naci gaba da zama a wajen ta har suka saka ni makaranta, sun ɗauke ni ita da mijinta tamkar ƴar su, sun bani gatan da ko iyayena ne iyakacin abinda zasu bani kenan". Fashewa tayi da kuka me tsananin gaske, daga nan taci gaba da basu labarin zamanta a gidan da rayuwan da tayi har soyayyarta da Yaya Nura, zuwa iftila'in da yafaɗa mata da abinda yafaru da ita a yau ɗin. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." atare Ummi da Abba suka faɗa cike da tsananin mamaki da al'ajabi "Dama har yanzu akwai irin waɗannan iyayen da zasu kore yaran su akan ƙaddara ta faɗa musu? Ashe har yanzu akwai marasa imani irin su? Basu tunanin abinda zai faru da ita yarinyan idan har sun kore ta? Meyasa wasu iyayen jahilai ne? Me zai saka su kori yarinyan su don kawai wani iftila'i ta afka mata? Basu tunanin kuma taje tafaɗa hannun ɓata gari? Ko kuma abinda suke gudu na zubewar mutunci taje taci gaba da aikata wa? Sannan kuma daga ƙarshe tadawo musu da abun kunyan da suke gudu? Gaskiya su Mamanki sunyi ganganci sun yi wauta, sun maye ladan su da babban zunubi, Allah bazai bar su ba wlh sai sun yi dana sanin abinda suka aikata miki". Ummi ce take faɗan hakan cike da ɓacin rai Saleema kuwa me saurin kuka tuni tasoma hawaye sabida tsananin tausayin Halwa Abba dake ta faman girgiza kai sabida al'ajabi yace "Tabbas sun yi ganganci sun aikata babban kuskure, amma Allah ai ba azzalumin bawan sa bane kuma shi ke kare duk wanda yaso, sun kore ki don kawai mutuncin su kar yazube, sun gunmaci ke ki wulaƙanta don kawai taki ƙaddaran kenan, amma insha Allahu bazamu taɓa bari ki wulaƙanta ba, mu zamu maye miki gurbin iyayen ki, zamu zame miki haske cikin rayuwan ki, a kuma shirye muke muɗau duk wani ƙaddaran da Allah yaɗaura miki, zamu tayaki yaƙi don kici jarabawan ki, haƙiƙa Allah shi yasan yanda yayi yahaɗa ki da ƴar mu don mutaimake ki, idan har muka bari kika bar gidan nan to tabbas sai Allah ya tambaye mu, ƴata zaki zauna tare damu zamuci gaba da kula dake kamar yanda muke ma ɗiyar mu, kuma insha Allahu duk abinda kike nema bazaki rasa shi agidan nan ba, kiɗauke mu tamkar iyayen ki waɗanda suka zuƙuna suka yahaife ki, mu nan munyi alƙawari zamu share miki hawayen ki". Ahankali Halwa dake ta faman rusa kuka tazamo ƙasa, cikin kukan take faɗin "Haƙiƙa kun cika iyaye na gari waɗanda basusan suga na wasu sun wulaƙanta, Nagode Allah da yahaɗa ni daku, wlh koda iya haka kuka bar ni da kalaman ku bazan taɓa manta ku cikin rayuwata ba, Nagode Allah yasaka da mafificin Alkhairin sa, Nagode Nagode.." Kukan da yaci ƙarfin ta ne yasaka ta yin shiru, dasauri Saleema tasauko tarungume ta tana nata hawayen tana rarrashinta Abba yace "Saleema kamata kuje ɗaki sai ki rarrashe ta acan". "To Abba". Miƙe wa tayi taruƙo ta suka nufi ɗakin ta, yayinda su kuma suka bi bayan su da kallo har suka shige, atare suka sauke ajiyan zuciya sannan suka dawo da fuskokin su izuwa junan su. . _Yanzu Labarin yasoma muje zuwa FAN'S._🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ [9/24/2020, 4:49 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 28* Ringing tune ɗin wayan sa ne yadawo dashi cikin nutsuwar sa, ahankali yasaka hannun sa yaɗau wayan yana duba wanda ke kiran sa, sai kuma yayi peacking call ɗin yana karawa a kunne, shiru yayi don haka Brr. Tahir yace "Ya man meke faruwa ne wai? Nafita nazo na tarar da missed calls ɗin ka, I'm so surprised da naga kiran ka har 5missed call, ina fata lafiya dai?" Numfashi Khalil yasauke a hankali kana yace "Brr. Tahir yau fa daƙyar nasha hannun wasu mutane". "Subhanallah.. wasu mutane kenan? Me kayi musu?" Brr. Tahir ɗin yafaɗa cike da firgici "Hmm wasu mutane kasani in banda mutanen da muke Shari'a dasu, kasan da cewa kwanaki nafaɗa maka suna bibiyana but duk da haka ban yi tunanin abun ya kai hakan ba, nafita zuwa wajen Mr. Abdullah, lokacin nafito daga gidan sa sai natsaya nan Resturent inci abinci, bayan nafito nagan su sun biyo ni, wlh naji tsoro sosai coz suna ɗauke da bindiga, daƙyar nasha ina faɗa maka, ƙarshe dai can nabaro motan sai dai na'aika drever yaɗauko min". Brr. Tahir yace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Ib ina tsoron fa mutanen nan su cutar da kai, why not mu sanar da Police👮? sannan yakamata kabar gidan nan zuwa lokacin da za'a gama, hankalina be kwanta ba maybe su biyo ka har gida". Shiru Khalil yayi naɗan wasu sakonni kafin yace "Nima hakan ne araina, but nariga da nayi ma DPO magana, yace "zai turo yaran sa suyi gadina". Ajiyan zuciya me ƙarfi Brr. Tahir yasauke kana yace "But duk da haka dai hankalina be kwanta ba wlh". Murmushi Khalil yayi yace "babu abinda zai faru sai alkhairi, insha Allahu gobe komi zai wuce". "Hakane.. Allah yakaimu to". "Ameen" Khalil ya'amsa masa Daga nan sai da suka daɗe suna tattaunawa akan aikin nasu kafin suyi sallama, ya'ajiye wayan yana sakin ajiyan zuciya, kana yaɗan kwantar da kan sa saman pilow yana rufe idanun sa, fuskar ta ne yabayyana acikin ƙwayan idanun nasa, dasauri yabuɗe yana jin zuciyar sa na bugawa "Meyasaka yarinyan taƙi ɓace masa?" Yatambayi kan sa yana dafe kan sa dake sara masa a hankali Tun da yadawo gida yake tunanin ta, da zaran yarufe idanun sa kuma fuskar ta yake hangowa, kuma sosai yake ganin tsananin damuwa a fuskar nata, afili yafurta "Wacece ita? Meyasaka tataimake ni? Meke damun ta?" Sai yatallabo kumatun sa yana tsira wa waje ɗaya ido, ya jima ahaka yana tunanin da besan na menene ba kafin yamiƙe yashige toilet, alwala yayi yafito yashinfiɗa sallaya yagabatar da sallan magriba, yau be jin zai iya zuwa ko ina, don haka tun da yashigo ma yasanar da ma'aikatan sa kar wanda yafita, sannan yabada umarnin a kulle masa gida, yana nan zaune har aka kira isha'i yagabatar sannan yamiƙe yafita, kichen yawuce yahaɗa Coffee yazauna nan yashanye kana yakoma ɗaki, wanka yasoma yi yasauya kaya izuwa na barci, yakashe wuta yahaye gado, addu'a yayi yashafa tare da rufe idanun sa, ya jima kafin barci yaɗauke sa Can cikin dare yatashi afirgice yana salati, gaba ɗaya yahaɗa gumi sakamakon mafarkin da yayi da ita, runtse idanun sa yayi yana tuna kukan da take masa cikin mafarkin kuma tana neman taimako a wajen sa, shiru yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, sai yadafe kan sa da duk ka hannayen sa yana sake runtse idanun, ya jima ahaka kafin ahankali yazuro ƙafafun sa ƙasa yasauka saman gadon, sai da yayi kusan mintuna biyar a tsaye yana tunani kafin yataka yashige toilet, alwala yaɗauro yafito yasauya kayan sa zuwa jallabiya yasoma gabatar da nafila. _*****_ Alhaji Mubarak mai Kuɗi wani babban attajiri ne da yayi ƙaurin suna a faɗin garin Katsina da kewaye, matar sa ɗaya da ƴaƴan sa biyu, Hassana ita ce Babba tana aure a ƙasan England, sai A'isha da take zaune a wajen ta tana karatun ta acan ɗin. Mutum ne shi me taimako wajen mutanen gari, kuma kowa ya shaida hakan domin sosai ake girmama sa sabida ana ganin sa me ƙaunar talakawa, sai dai abinda basu sani ba na daga halin sa, shi mutum ne da ko kaɗan baya da imani baya da tausayi abaɗini, sana'ar sa shine kasuwan ci, sai dai babu wanda yasan da cewa yana safaran ƴan mata zuwa wani ƙasa, sannan yana harƙallan sai da Coken, yana kuma gudanar da sana'ar tasa ne batare da kowa ya sani ba. Dr. Sabit shine wanda yake taimaka masa, kuma tare suke harƙallan tasu, babban Likita ne shi da yayi fice sosai kuma wanda ake ji dashi cikin garin Katsina, Shine Doctorn da yake ma duk wasu yara da suka samu operation yazuba musu Coken ɗin sabida afita dashi waje batare da an gano su ba. Akwai wani Doctor Salis abokin aikin Doctor Sabit ne, shi yafara gano abinda suke aikatawa, har yayi yunƙurin kai su ƙara don yatona musu asiri, but daga ƙarshe sai dai aka nemi Doctor Salis aka rasa ya ɓace ɓat, kuma ba'a san me yafaru dashi ba. Alhaji Mubarak ba iya mutanen gari kaɗai yake ma kirki ba, har ta da ƴan aikin gidan sa, don haka sosai suka saki jiki agidan, sai dai abinda basu sani ba yana amfani da hakan ne don cin ma burin sa, coz sau da dama yawancin masu aikin suna da yara, sannan kuma akwai ƴan mata acikin su, babu wanda yasan meyasaka masu aikin gidan sa mata basu daɗewa, sai dai lokaci kaɗan za'a neme su a rasa. Hajjo tana ɗaya daga cikin masu aikin gidan, kuma tana ɗaya daga cikin waɗanda suka daɗe sosai suna aiki a gidan, asalin ta bafulatana ce mazauna ƙauye, sun zo tare da mijinta da yarinyan su ɗaya Nazeefa cikin birni, wata mata ce tayi ma Hajjo hanya har tasami aiki agidan, sosai take jin daɗin aiki a gidan Alhj. Mubarak me kuɗi kuma suna samun duk abinda suke so Bayan wasu shekaru ne mijinta yarasu don haka taɗauki Nazeefa suka taho gidan Alhj. M. Me kuɗi don tanemi alfarma wajen sa don yaba su waje agidan nasa su zauna tunda ya saba yin haka, lokacin da tagabatar masa da alfarman ta gare sa babu musu ya amince, Hajjo tayi murna sosai sai dai batasan cewa Alhj. M. Me kuɗi ya amince ne don ganin Nazeefa da yayi, yasan da cewa idan suka zauna agidan sa hakan zai basa daman cikan burin sa akan ita Nazeefan. Rayuwa taci gaba da gudana, lokaci ɗaya Allah yajarabbi Hajjo da ciwo, ashe ciwon ajali ne, don batayi sati ɗaya ba tarasu, Nazeefa tayi kuka sosai sabida tasan bata da wasu ƴan uwa kuma da suka rage mata, sannan batasan ma ina ne ƙauyen su ba bare takoma, ana haka Alhj. Mubarak yakira ta har parlourn sa bayan yayi mata ta'aziya yace "Nazeefa sunan ki ko?" Kanta a ƙasa ta'amsa mishi "Ok zakici gaba da zama anan idan kinaso, sai ki maye gurbin Mahaifiyarki, sannan duk abinda kike nema ki sanar dani ko ki sanar da Hajiya, daga yau karki ɗauki kan ki marainiya tunda har kina damu". Sosai Nazeefa tayi murna da jin maganar sa, don haka tayi masa godiya tafice, shi kuwa murmushi yayi yaɗau Jaridan sa yasoma karantawa, yasan da cewa nan da ɗan lokaci kaɗan zai cika burin sa akanta Ana nan wata rana Hajiya ta aiki Nazeefa gidan ƙawar ta ta'amaso mata saƙo, kasancewar babu nisa da gidan su a ƙasa tatafi, bayan taje ta dawo ne a hanyan ta na dawowa gida sai ga Motan Alhj. Mubarak ya tsaya tare da zuge glass ɗin motan yana kallon ta da murmushi a face ɗin sa, ita kuwa tayi mamaki sosai ganin sa shi kaɗai babu drever, umarni yabata tashigo motan babu musu kuwa tashiga, don shi mutum ne me tsananin kwarjini da babu yanda za'ayi kayi masa musu a matsayin sa na babba, lokacin da suka iso gidan sai taga sun wuce but bata iya ce mishi komi ba, sai dai sosai tayi mamaki kuma tana son tatambaye shi sai dai babu dama, har suka isa wani babban gida yace da ita tajira sa bari yazo, fita yayi yashiga gidan, ita kuma gaban ta sai faɗuwa yake yi, tasan da cewa shi ɗin mutum ne me sauƙin kai, amma babu abinda yahaɗa ta dashi a matsayin ta na ƴar aikin gidan sa bare yaɗauko ta cikin motan sa, that's why gaba ɗaya hankalinta yaƙi kwanciya, duk tsoro ya cika ta, tana nan zaune wani mutum yazo yace mata tashigo inji shi, babu musu tafito tabiyo bayan mutumin suka shiga gidan, lokacin da suka shiga babu kowa, a lokacin ne taji kamar ana buga mata guduma a ƙirjinta, tsinkayan muryan mutumin tayi yana faɗin "tabiyo shi" wani ƙofa taga yabuɗe yashiga sai tabi bayan sa, suna shiga tatsaya tana kallon tsarin ɗakin da babu komi sai gado da sif taji ƙaran rufe ƙofa, kallon ƙofar tayi sannan kuma tawur-wurga ido cikin ɗakin taga babu mutumin da suke tare, a sukwane tanufi ƙofan da yake a kulle tasoma taɓawa tana son buɗewa, sai dai da alamun an rufeta ta baya ne, wani irin bugawa zuciyarta tayi batasan sanda tasoma jijjiga ƙofan ba tana ɓarkewa da kuka, cikin kukan take faɗin "Don Allah kabuɗe, ina ne nan ina kakawo Ni? Na shiga uku Ni Nazeefa, wayyo Allana Wayyo Mamana". Kuka take yi sosai tana jijjiga ƙofan da ko motsi baya yi, daga ƙarshe zubewa nan ƙasa tayi tasoma rusa kuka tana shushshura ƙafafu, ta jima ahaka tana kukan wanda har muryan ta yadena fita sai hawaye dake ta zirara. [9/25/2020, 11:26 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 29* Wasa wasa sai da Nazeefa tayi kwanaki bakwai a wannan gidan batare da tasan takamaiman inda take ba, tayi kukan duniya tayi ihun duniya babu wanda yazo wajen ta, sai dai da zaran tayi barci ta farka zata tashi taga an ajiye mata abinci, tun bata taɓawa da taga alamun kanta take cuta sai tasoma ci, sau da dama tayi yunƙurin kwana ido biyu don tasami nasaran guduwa idan akazo kawo mata abinci, but bata taba samun sa'a ba, abinda bata sani ba akwai Camera cikin ɗakin, idan har sukaga batayi barci ba to bazasu kawo mata abinci ba, haka zata ƙariki zamanta babu su babu alamun su, daga ƙarshe har tacire rai da samun daman fita, jira kawai take yi ranan da zasu kawo ƙarshen rayuwanta, domin a tunanin ta gidan cin kai take. Wata rana tana zaune taga wannan mutumin da yashigo da ita yabuɗe ƙofan yashigo, zabura tayi tayi kansa da gudu tana ƙoƙarin guduwa yayi saurin cafko ta da hannu ɗaya, abinku da wacce bata da ƙarfi ko na sisin kwabo nan tadawo baya tafaɗa jikin sa, kuka tafashe dashi tana faɗin "Don girman Allah kataimake ni kabar ni in tafi, wayyo Allana me kuke so dani ne..?" Bata rufe baki ba Doctor Sabit da Alhj. Mubarak suka shigo, duk kan su face ɗin su a ɗaure ne babu alaman wasa, doctor Sabit ne yanufo ta riƙe da wani allura a hannun sa, ita bata kula da alluran ba sai kallon Alhj. Mubarak take yi tana kuka don takasa magana, so take yi taroƙe shi yafitar da ita amma ina, kafin ma tagama tunanin zucin ta har taji an sanƙama mata allura, batasan sanda takurma ihu ba tana riƙe hannun doctor ɗin, kallon shi take yi idanun ta cike da hawaye tana motsa baki, sai kuma tatafi luuuuuu tafaɗi nan ƙasa. Alokacin da tafarka alluran be gama sakin jikin ta ba, ga wani zafi da yaziyarci ƙwaƙwalwanta, nan take taɗaura hannun ta saman maranta tana sakin kuka mara sauti, tayi tsawon mintuna 5 ahaka kafin tayi yunƙurin miƙewa, daƙyar talallaɓa tatashi zaune tana jin kanta na sara mata, ga wani irin jiri dake ɗiban ta tana ganin abubuwa bibbiyu, ɗakin take bi da kallo sai dai ba wanda aka ajiye ta bane, wannan cike yake da mata Sa'annin ta da waɗanda suka girme ta, su ma da alamun dai abinda akayi mata shi akayi musu, sai dai su basu farka ba saɓanin ita, Allura ne da akayi musu na tsawon awanni but abun mamaki ita be yi tasiri ajikin ta ba, mintuna 20 kenan da yin mata sannan tafarka, kuma anyi musu ne har sai an fita dasu zuwa ƙasashen da za'a kai su sannan su farka Miƙewa tayi cikin yanayin rashin hankali tasoma tafiya aduƙe tana tangal-tangal kamar wacce zata kife ƙasa, tariƙe cikin ta dake mata bala'in zafi, ƙofa tabuɗe tafice sai gata cikin parlour, babu kowa ciki suna can suna shirin yanda zasu fitar da ƴan matan bayan sun dawo cikin hankalin su na mintuna ƙalilan, domin alokacin da suke zuwa Airport dasu a farke suke kai su har sanda zasu shiga jirgi, sai dai hankalin su da tunanin su sun riga sun gushe, duk yanda akayi dasu haka zasuyi Direct wani ƙofa tanufa tabuɗe tafice, Allah yabata Sa'a ashe waje ne, haka tafita gidan batare da taga kowa ba, tafiya take tayi batasan inda take saka ƙafarta ba, tayi tafiyan da ita kanta batasan awanni nawa yaɗauke ta ba, sai faɗi tayi ƙasa a sume batare da tasan inda kanta yake ba. Lokacin da tafarka garin yayi duhu sosai kuma babu wanda yaganta, kasancewar anguwan na masu kuɗi ne zai yi wuya kaga mutum a waje, zuwa lokacin tsananin azaba take ji a cikin ta, a lokacin kuma ta dawo hayyacin ta gaba ɗaya, sai tariƙe cikin ta tana ta kuka tana burgima awajen, tsawon lokaci kafin tayunƙura daƙyar tamiƙe taci gaba da tafiya tana kuka, a wannan lokacin ne Brr. Ibrahim Khalil yazo wucewa yabige ta batare da yasani ba, yana fitowa yaganta yashe a ƙasa da alamun ta sume ne, ɗaukan ta yayi yasaka ta a mota yanufi da ita asibiti, lokacin Dr. Sameer be riga ya tafi ba, shi ya'amshe ta yakira abokin sa Dr. Hashim, babu jimawa kuwa yazo yasoma dubata, duk Brr. Khalil yadamu yakasa zama waje ɗaya sai zagaye yake yi, sai da Dr. Sameer yabashi ƙwarin gwiwa tukun hankalin sa yakwanta Sai da akayi 2 hours ana duba ta kafin Likitocin dake kan ta su fito, Dr. Hashim ne yayi musu bayanin da yaɗaga musu hankali, sosai suka shiga damuwa jin cewa Coken ne acikin ta, kuma ya kai tsawon lokacin da Yakamata acire mata but ba'a cire ba, don haka har yasoma narkewa yataɓa mata hanji dole sai anyi mata aiki an cire, sannan kuma sai anyi mata dashen hanji, Khalil ne yasaka hannu aka shiga da ita Theater, tsawon awa biyu kafin aka fito da ita, sai alokacin suka tafi gida bayan da suka tabbatar komi normal. Watan ta biyu kafin tafarfaɗo, kuma duk alokacin tana ƙarƙashin kulawan Khalil ne tare da Doctor Hashim da Doc. Sameer, sosai take jin jiki duk da an samu nasaran aikin, ko magana bata iyayi bare tashi, komi sai dai ayi mata Khalil sosai yadamu da halin da take ciki haka kawai yake jinta tamkar ƙanwar sa, kuma yayi imani cewa yarinyan zaluntar ta akayi, don haka alokacin ne yasoma bincike akan ta, kuma ya yi ƙudirin sai ya ƙwato mata haƙƙinta, tsawon wata yana bincike sannan yagano inda take zaune, wato gidan Alh. Mubarak, a ranan da yashirya yaje yayi hira da me gadi har yagano labarin ta a wajen sa, bayan ya dawo ne a ranan wasu suka zo kashe ta cikin asibitin, abinda be sani ba Khalil yana tafiya me gadin yasanar da Alh. Mubarak, tunda dama neman ta ake yi ana tunanin ɓata tayi, Dr. Sameer ne yashigo cikin ɗakin lokacin da mutumin da zai kashe ta yaso kashetan, shine yagudu batare da yayi abinda yazo yi ba, wannan dalilin ne yasaka suka yanke shawaran afitar da ita daga asibitin, don sun gano kasheta ake da ninyan yi, Shine Khalil yakaita gidan Baaba Talatu, anan akaci gaba da kula da ita sannan shi kuma yaci gaba da bincike kan lamarin, har sanda yagano komi akan Alhj. Mubarak tare da Doc. Sabit, babu ɓata lokaci yashigar dasu ƙara zuwa kotu A lokacin hankalin su Ahj. Mubarak be wani tashi ba, domin acewar su babu yanda za'a yi akama su da laifi, sannan kuma su ɗin masu hannu da shuni ne waɗanda sukayi fice kuma kowa yasan halin su, babu yanda za'a yi yayi nasara, but zaman farko a kotu sai ido yaraina fata, yanda Brr. Khalil yayi takawo shaidu hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba, anan Alƙali yabada hutun wata ɗaya da sati biyu bayan da kowa yagama kawo shedun sa, kuma ya bada umarnin ranan da za'a dawo yakasance Nazeefa ta hallara, sakamakon hujjojin da Brr. Khalil yaba da ne aka tsare Ahj. Mubarak tunda an gano yana da laifi Wannan shari'ar ya ja cece kuce sosai a wajen jama'a, sosai mutane suka ƙosa suga ranan da za'a dawo don yanke hukuncin, kuma duk alokacin mutane basu yarda cewa Alh. Mubarak yana da laifi ba, sai dai mujira ranan dawowan kamar yanda yakasance gobe da ƙarfe 02:00pm. _Hmmm masu karatu ku ma sai kushirya don jin Me zai wakana a Court._ 😅 _ina gayyatar Masoya Brr. Ibrahim Khalil da Nazeefa, kuzo kugani da idanun ku._💃💃💃💃 [9/29/2020, 12:44 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What'sapp Number 07065334256~ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 30* Washe gari ƙarfe 07:15am. Saleema tagama shirin ta na zuwa school, tana shirin ɗaukan jakan ta taji cikin ta yasoma murɗa mata, dasauri tariƙe tana runtse idanun ta, lokacin ne Halwa tafito daga Toilet tana kallon ta, ganin tana riƙe da ciki taƙi jirgawa yasa tamatso kusa da ita cikin sanyin murya take tambayan ta "ko wani abun na damun ta?" Murmushi Saleema taƙaƙalo tare da girgiza mata kai, sai dai har alokacin tana riƙe da cikin nata ne, hannu tasanya taɗau jakan kafin takalle ta tace "Ni natafi school sai na daw.." Bata ƙarisa maganar ba tadurƙushe nan ƙasa tana faɗin "Wayyo cikina wayyo Allana". A ruɗe Halwa tabi ta ƙasan tana kiran sunan ta tare da tambayan ta abinda ke damunta, ganin tasoma kuka sosai tana sake riƙe cikin ta yasaka tamiƙe dasauri tafita, ɗakin Ummi tashiga dasauri, tana tsaye kuwa itama tagama shirin ta nazuwa Hospital kasancewar ita ɗin Nurse ce, taburmo ɗakin tana kiran sunan ta, Ummi kallon ta tayi tace "Lafiya Halwa meke faruwa?" Cikin rawan murya kamar zatayi kuka tace "Saleema ce babu lafiya". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ummi tafaɗa cikin tashin hankali kafin tanufo wajen ta tana faɗin "Tana ina? Ina take?" "Tana ɗaki". Atare suka isa ɗakin lokacin gaba ɗaya Saleema tafita hayyacin ta sai kuka take yi, ga duk kan alamu tana jin jiki sosai, riƙo ta Ummi tayi tana kiran sunan ta tare da tambayan ta "Ina ke mata ciwo?" Duk hankalin Ummi atashe yake tarasa ma me zatayi Halwa tace "Ummi ko za'a kira Abba akaita asibiti?". Sai alokacin tunanin hakan ma yazo ma Ummi, tayi saurin cicciɓan ta Halwa tatayata suka fito da ita, suna fita waje Drever yazo da gudu yabuɗe musu mota suka saka ta, Ummi tashiga baya kusa da Saleema, ita kuma Halwa tashiga gaba tare da drever suka tafi, sai acikin motan Ummi ta'ari wayan drevern takira Abba tasanar masa. Lokacin da suka isa asibitin tuni an amshe ta kasancewar ba yau suka saba zuwa ba, kuma dama tana da Doctorn da yake duba ta na musamman acikin asibitin, ana shiga da ita Abba shima ya'iso duk hankalin sa atashe, Halwa yanda taga su Ummi sun tashi hankalin su sosai itama sai taji duk ta damu, haka tazauna waje ɗaya tatakure tana tuna ɗan zaman da sukayi daga jiya zuwa yau, sosai tafahimci ita ɗin yarinya ce me tausayi da son mutane, sannan kuma ta fahimci akwai ƙauna sosai a tsakanin ta da iyayenta, take taji hawaye ya zubo mata tayi saurin saka hannu tana sharewa. Koda aka fito da ita Abba ne yanufi wajen doctor, Ummi da Halwa kuma suka shiga ɗakin da aka kwantar da Saleema, tana kwance ne asaman gado, abun tausayi kamar ba itace lafiyan ta lau yanzu ba, amma Allah da ikon sa numfashi ma bata iya yi sai da taimakon Oxygen, Ummi hawaye tasoma zubarwa da ganin tilon ƴarta a irin wannan yanayin, takawa tayi taƙarisa wajen gadon, itama Halwa ahankali ta'isa jikin gadon tana ƙure Saleeman da idanu, zama Ummi tayi tariƙo hannun ta ɗaya wanda ba'a saka mata drip ba tana ƙare mata kallo, cikin zub da hawaye tace "Allah Sarki Saleema, Allah yabaki lafiya, haƙiƙa kinga jarabawa a rayuwan ki, ko yaushe ne zakiji daɗi kamar kowa?" Cikin tsananin tausayi da jin kalaman Ummin Halwa tazame nan gefen gadon tazauna, share hawayen ta Ummi tayi taɗago kanta tana kallon Halwa tace "Tun tana ƙarama Allah yajarabce ta da ciwon zuciya, dashi tataso har girman ta, duk iya maganin da muka nema akan ta Allah be sa an dace ba, tasha baƙar wahala kamar bazata rayu ba, acikin shekaru biyu da suka wuce akayi mata aiki a ƙasan OXFORD, Allah yasa an dace, duk da haka muna gudun ɓacin ranta domin da zaran ranta ya ɓaci ciwon ta yana ƙoƙarin tashi ne, sai dai ba'a rufa watanni biyu ba tasoma ciwon ciki me tsanani, koda muka kaita asibiti aka gano tana ɗauke da ciwon hanta ne". Cikin sheshsheƙan kuka Ummi taci gaba da faɗin "Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta Ni da mahaifin ta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine musaka ta farin ciki, duk abinda take so shi muke yi, sai dai fargaban mu wanene zai ci gaba da kula mana da ita idan har takoma ƙarƙashin sa, wani namiji ne zai iya zama da ƴar mu yasaka ta farin ciki kamar yanda Likitoci suka sanar mana? yah Allah gamu gare ka, ya Allah kasauƙaƙa ma wannan baiwa taka, Allah yabaki lafiya Saleema". Halwa batasan tana zirarar da hawaye ba sai da taji danshin su akan hannun ta, cikin rawan murya ta'amsa ma Ummi da "Ameen". Tana saka hannu tashare hawayen, Abba ne yashigo cikin ɗakin, dasauri Ummi tamiƙe tana kallon sa tace "Abban Saleema me likitan yace? Da fatan babu abinda yasami ƴar mu? Ya Allah..". Sai tafashe da kuka tana saka hannu tarufe idanun ta Ahankali yasaka hannun sa yana bubbuga kafaɗan ta, cikin ƙarfin hali yace "Kiyi shiru don Allah, babu abinda zai sami ƴar mu insha Allahu, Doctor yace ciwon ta ne kawai yatashi but zata sami sauƙi very soon". Ummi tace "Ina jin tsoro sosai Abban Saleema, ina jin tsoro kar mu rasa ta". "Baza mu rasa ta ba Asma'u, ki dena faɗan haka kinji?" Rarrashinta yayi sosai, sai da yaga tayi shiru ta kwantar da hankalin ta kafin yamayar da kan sa zuwa ga Halwa da har yanzu take zuban hawaye, gaba ɗaya ta takure waje ɗaya ta duƙar da kanta ƙasa, kiran sunan ta Abba yayi kana yace "Kema ya dace kiga likita coz ɗazu kafin nafita Saleema tafaɗa min da zazzafan zazzaɓi kika kwana, kuma dama Yakamata aduba lafiyan ki da abinda ke cikin ki, be kamata abarki haka da ciwo ba, bari nafita nayi ma Doctor ɗin magana". Daga haka Abba fita yayi ita kuma Ummi takoma tazauna tare da riƙo hannun Saleema tana kallon ta. ***** ****** ****** Ƙarfe 01:10pm. Brr. Khalil yagama Shirin sa, ya saka riga da wando white colour, sannan yaɗau rigan aikin sa tare da hulan yariƙo briafcase ɗin sa yafito, Direct wajen farar motan sa yanufa yabuɗe yashiga yazauna, ya kai wajen five minutes kafin yatada motan yanufi bakin Gate, hon yadanna Gate man yazo yabuɗe masa yaja motan ahankali yafice, sai da yadaidaita motan saman kwalta kafin yaɗau wayan sa yakira Sameer "Hello Bro". Daga can Sameer ya'amsa mishi da faɗin "Kana gida ne ko ka tafi?" "No gani a hanya, zan wuce gidan Mom". "Ok shikenan, dama tambayan ka zanyi don mu mun riga mun isa". Sameer ɗin yafaɗi hakan "Ok nima bazan daɗe ba, yanzu insha Allahu zan ƙariso". Daga haka sallama sukayi ya'ajiye wayan, sannan yamayar da hankalin sa ga tuƙin sa, be ɗau lokaci ba ya'isa gidan su Kasancewar yau ɗin ya ɗan taka motan da gudu, yana yin parcking yafito yanufi cikin gidan, a Parlour yatarar da Mom tana zaune tana shan Fuirt, ƙarisawa yayi yazauna gefen ta yana riƙo hannunta yayi mata peck a bayan hannu kana yace "Sannu da hutawa Mom". Murmushi tasakar masa tace "Yauwa My Son, har ka iso?" Gyaɗa mata kai yayi yana ɗaukan Apple yasoma gutsira yana taunawa a hankali "Masha Allah.. yanzu itama Nazeefan tashiga ɗaki taje shiryawa, nima wannan karon dani za'a je, bari inje in shirya". "Yakamata kam, but ina Dad yake?" "Oh Dad ɗin ka yafita tun safe akwai meating ɗin da yake dashi, but yace "idan sun gama da wuri zai same mu acan". Nazeefa ce tafito cikin shirin ta na riga da wando farare, sai taɗaura Coffee ɗin Hijab, sosai tayi kyau kasancewarta fara, tana hango Khalil shima da fararen kayan sai wani irin farin ciki Yakamata, ko ba komi sun yi anko yau, kuma hakan yayi mata daɗi "Ƙariso mana kin tsaya, me kike tunani?" Muryan Mom yadawo da ita hayyacin ta Sai alokacin Khalil yakalli inda take tahowa, idanun sa kawai yaƙura mata har ta'iso wajen kanta a ƙasa tagaishe sa, amsa mata yayi yana tauna Apple ɗin dake bakin sa har yanzu kuma yaƙi kau da idanun nasa kanta Mom tace "bari inje in shirya". Tashi tayi tawuce ɗakinta, shima kuma Khalil dake kallon Nazeefa yayi mata alama da ido alaman tazauna gefen sa, babu musu tazauna cike da kunya, sauran tufan dake hannun sa yamiƙa mata, hakan yasaka taɗago kanta tana kallon sa don bata fahimci abinda yake nufi ba "Ki ci". Yabata umarni yana kawar da kansa Ahankali tasanya hannu ta'amsa takai bakin ta idanun ta akan sa, gutsira tayi tana lumshe idanuwanta cike da wani irin daɗi da yaziyarci zuciyarta, shi kuma hakan yabashi daman sake maida idanun sa kanta yana ƙare mata kallo, har sanda tabuɗe idanun ta tasauke acikin nasa, sai tayi saurin Sad da kai ƙasa tana murmusawa kiran sunan ta yayi, bata amsa ba sai ɗago kai da tayi tana kallon sa "Kina jina ina son in sanar dake, kikasance me juriya ga duk tambayoyin da za'a yi miki a Court, bana son ki nuna tsoro ko firgita a wajen, ina son ki amsa duk wasu tambayoyi da za'a miki batare da fargaba ko tsoro ba, Nazeefa kina dani a wajen don haka kiɗaura wa kanki ƙwarin gwiwa kinji?" Yayi maganar cikin tausasa murya still yana kallon ta Gyaɗa masa kai tayi, kana tace "insha Allahu Yaya zan amsa duk wata tambaya batare da na nuna tsorona a fili ba". Murmusawa yayi kawai yana kau da kan sa, lokacin ne kuma Mom ta'iso wajen tana cewa "Kutashi Muje to na shirya" Gaba ɗaya suka tashi suka fice, motan Khalil ɗin suka shiga yaja yafice a gidan. [9/29/2020, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 31* Lokacin da suka isa, gaba ɗaya haraban court ɗin cike yake da mutane, Khalil ce musu yayi "su shiga ciki". Don haka suka fice suka bar sa cikin motan yaɗau wayan sa yana neman layin Brr. Tahir. *20 minutes* Shigowan Alƙali yasaka kowa yayi shiru, duk kan su tashi sukayi har sai da Alƙali yazauna kafin kowa ma yazauna, daga nan Maga-takarda yamiƙe yasoma bayani kamar haka: "Ayau 26 September 2020 zamu ci gaba da gabatar da shari'ar Alhaji Mubarak Mai kuɗi da Nazeefa Shehu". Sannan yamiƙa takardun ga Alƙali, shi kuma ya'amsa yana gyara glass ɗin sa yasoma dubawa, sannan yaɗago kansa yana cewa "Lauyoyi zaku iya farawa". Khalil ne yatashi yasoma gabatar da kan sa "Ni sunana ```BARRISTER IBRAHIM KHALIL ABDURRA'UF.``` lauya me kare wacce takawo ƙara, tare dani kuma akwai abokan aikina..". "Brr. Tahir .A. Tahir". Cewar Brr. Tahir kenan da shima yatashi yagabatar da sunan shi "Tare dani Brr. Bilkisu Ahmad Sofana". Zama sukayi gaba ɗayan su. "Ni kuma ni ne Brr. Mahmud Sudais, lauya me kare wanda ake ƙara, tare dani akwai..". "Brr. Shamsudden Munir". Su ma zama sukayi, Alƙali duƙar da kansa yayi yaɗan yi rubutu tukun yaɗago kai yana kallon su, hakan yasaka Brr. Khalil yamiƙe yasoma magana "Ya me girma me Shari'a, ina son agabatar min da Nazeefa Shehu don in mata tambayoyi". "Kotu ta baka dama". Alƙali yafaɗi hakan yana aje Bairo ɗin hannun sa Maga-takarda yamiƙe yace "idan akwai Nazeefa Shehu anan tafito". Nazeefa da jikin ta yayi mugun sanyi, gaba ɗaya sai taji cikin ta yasoma rugugu ƙafanta kuma sai faman rawa suke yi don bata taɓa tsayawa cikin taron mutane ba, Mom dake kusa da ita tace "Tashi kije mana, ki cire tsoro aran ki kinji". Gyaɗa kai kawai tayi taɗago tana kallon mutane nan idanun ta yafaɗa akan na Khalil, kafe ta da idanu yayi ko ƙiftawa baya yi hakan yasaka tamiƙe tafara nufo shi, tana isowa wani ɗan sanda yace tashiga nan". Babu musu kuwa tashiga tatsaya kanta a ƙasa, takowa Khalil yayi ya'iso gaban ta "Kotu zataso taji cikakken sunan ki". Bata ɗago kai ba tace "sunana Nazeefa Shehu". "To Nazeefa Shehu zan so in san menene alaƙan ki da wanda kika kawo ƙara, ina nufin Alh. Mubarak me kuɗi". Sai alokacin taɗago kanta tana kallon Khalil, yayi mata alama da ido, hakan yasaka tamayar da idanun ta kan jama'a sai kuma tasauke kanta tasoma bayani "Muna aiki ne a ƙarƙashin sa". "Kenan kina nufin ke ƴar aikin gidan sa ne?" Gyaɗa kanta tayi sai kuma tace "Eh". "Ok zan so ki bama kotu taƙaitaccen labarin ki, da yanda har kuka zauna a gidan Alh. Mubarak". "Ni bansan sanda muka soma aiki a gidan sa ba, sabida alokacin bani da wayau sosai, sai dai a sanda mahaifina yarasu nasan sanda muka koma gidan sa da zama". Daga nan tasoma bada labari tiryan-tiryan abun da yafaru da ita a gidan, har sanda yaɗauke ta yakaita wani gida, zuwa taimakon da Khalil yayi mata har kawo iyanzu, tanayi tana kuka, sai da tagama bada labarin surutun mutane yasoma tashi, sai da Alƙali yabuga guduma kafin sukayi shiru "Ya me girma me Shari'a iya tambayoyin da zan iya mata kenan" Khalil yafaɗi hakan kana yaje yazauna Brr. Mahmoud ne yatashi "Ya me girma me Shari'a ina so nayi ma Nazeefa Shehu tambayoyi". "Kotu ta baka dama". Ƙarisawa wajen ta yayi yana ƙare mata kallo, ita kam har yanzu kanta a ƙasa yake tana share hawaye, don haka batasan ma yanayi ba "Malama Nazeefa zaki iya faɗa min iya adadin mutanen da suke aiki a ƙarƙashin Alh. Mubarak?" Ɗago kanta tayi takalle sa sai tace "Eh zan iya, zamu kai mu Goma ne". Jinjina kansa yayi kana yace "A sanda Alhj. Mubarak yafita cikin motan yabaki umarnin kijira sa, meyasaka kika fito?" "Wani ne yace min in zo yana kira na". "Kina nufin wani ne yajagoran ce ki zuwa ciki? Meysaka to kika bishi? Alamu sun nuna kenan ta yiwu wasu ne suka aikata miki hakan?" "Ya me Shari'a Brr. Mahmoud yana ƙoƙarin canza mata tunani sannan yatilasta ta tafaɗa abinda bashi ne ba". Alƙali yace "kagyara tambayoyinka Barrister Mahmoud". "Ok ya Me Sharia". Sannan yamayar da kallon sa gare ta yaci gaba "Ina jinki, kin tabbatar kinga Alh. Mubarak a wannan gidan koda kika shiga?" "Eh na gansa alokacin da suka shigo shi da wani mutum har sukayi min allura". Jinjina kansa yayi kafin yajuyo yana kallon Alƙali yace "Iya abinda zan iya tambayan ta kenan". Sannan yaje yazauna Miƙewa Khalil yayi yace "zan so a gabatar min da Alh. Mubarak Me kuɗi don amsa tambayoyina". "Kotu ta baka dama". Fito da Alh. Mubarak akayi, wasu ƴan sanda suka tsaya bayan sa "Alh. Mubarak shin kasan wancan yarinyan?". Kallon Nazeefa yayi sannan yace "Eh na santa". "Menene alaƙan ka da ita?". "Babu wata alaƙa da nake da ita, illa ita ɗin ƴar aikin gidana ne". Jinjina kan sa Khalil yayi kana yace "To yanzu ka yarda da abinda tafaɗa ko har yanzu kana tantama?" "Ni ban yarda da abinda tafaɗa ba, coz ni ba mutumin banza bane da har zan yi wannan mummunan harƙallan". Murmushi Khalil yayi yace "kenan duk kanaso kace mana abinda ake zargin ka ba Gaskiya bane?" "Eh ba Gaskiya bane, don Ni taimakon ta kawai nayi shine take so ta saka min da sharri". "Kamar ya taimakon ta kayi?" "Eh lokacin da naganta a hanya shine naɗauke ta nakaita gida, shikenan iya abinda yahaɗa ni da ita". Khalil yace "a matsayin ka na babban mutum ka taho ka ganta a hanya, sannan kuma babu nisa da gidan ka da inda take, meysaka kayi sha'awan kaɗauke ta a mota ka ƙariso da ita gidan ka?" "Kasan taimako ajinina yake don haka don na ɗauke ta na kawo ta gida wannan bazai saka a zarge Ni ba, sannan kuma ina tausayin ta ne saboda Mahaifiyar ta a gidana ta rasu". "Ya me girma me Shari'a iya tambayoyin da zan masa kenan,, sannan zan so abani dama nasake yin ma Nazeefa tambayoyi". Khalil yafaɗa hakan sannan yakoma wajen zaman sa Alƙali da yagama rubutu yaɗago kansa yace "ko lauyan da yake kare wanda ake zargi yana da abin cewa?" Miƙe wa Brr. Mahmud yayi yace "A'a ya me Shari'a, sannan yakoma yazauna "Kotu ta baka dama". Tashi Khalil yayi ya'isa gaban Nazeefa yace "zan so ki sanar dani tun sanda kika taso da wayon ki kika ganki agidan Alh. Mubarak masu aiki nawa ne aka sanja agidan? Ko waɗanda kika sani iya su ne agidan har tafiyan ki?" Cikin sanyin murya Nazeefa tace "gaskiya tun zuwana gidan har sanda natafi masu aikin gidan waɗanda aka sauya bazan iya ƙirgawa ba, amma suna da yawa sosai". "Kenan kina nufin a gidan Alh. Mubarak ansha sauya masu aiki batare da wasu dalili ba?.." Miƙe wa Brr. Mahmoud yayi yace "Of jection my Lord Brr. Ibrahim Khalil yana neman yaɗaura wacce yake karewa akan hanya". "Kakula Brr. Ibrahim". Cewar Alƙali "Nagode ya me Shari'a, ok ina jin ki, ko zaki faɗa min akwai wani laifi da kikasan suna yi ake sauya su?" "A'a Ni bansani ba, haka kawai muke neman su mu rasa sai akawo sabbi". "Ok zaki iya komawa kizauna". Sannan yajuya ga alƙali yace "ya me Shari'a ina son nayi ma Malam Umaru tambayoyi". "Kotu ta baka dama". Maga-takarda yatashi yayi kiran sa sannan yafito "Malam Umaru abaya na tambaye ka wasu tambayoyi, sannan nace idan da buƙatar nasake kiran ka zan sake". Gyaɗa kansa Malam Umaru yayi "Yauwa a lokacin da Nazeefa tafita gidan Alh. Mubarak a matsayin ka na me gadi kana ina?" "Ina bakin Gate ɗin tazo tafita". Kaɗa kansa Khalil yayi kana yaƙure sa da idanu yace "to kaga dawowan su kamar yanda Alh. Mubarak yafaɗa shine yadawo da ita?" Hannu Malam Umaru yasanya yagoge zufan da yake tsatstsafo mishi kana yace "Eh na gani". "Kana nufin sun dawo tare ɗin?" "Eh tare suka dawo a motar sa bayan mituna ƙadan da fitan ta". Murmushi Khalil yayi yana sake tsare sa da idanu yace "Ok to idan har kaga dawowar ta cikin gidan, to da yaushe kenan takuma fita?" Malam Umaru yace "gaskiya ban sani ba". "A matsayin ka na me gadi ya akayi har mutum yafita cikin gidan baka sani ba?". "Eh.. uhm naje zagayawa ne ai, don haka bansan ta fita ba". "To a yaushe kafara jin ana cigiyar ta?". "Bayan sa'o'i uku da dawowar ta, sai Hajiya tazo tasame Ni take tambayana "har yanzu Nazeefa bata shigo bane?" Shine nace mata ai tun ɗazu Tawuce". Daga nan Brr. Kahlil zama yayi, sai Brr. Mahmoud yatashi shima yayi masa tambayoyi, Kana Brr. Kahlil yasake tashi yace "Ina son inyi wa Hajiya Asiya Tambayoyi". "Idan akwai Hajiya Asiya tafito". "Zan so insan alaƙan ki da Alh. Mubarak". "Mijina ne". "Kun kai shekaru nawa dashi?" "Mun kai shekaru 32yrs dashi". "Ok kin taɓa fuskantar wata matsala dashi? Kamar kina zargin sa da yana aikata wani abu a ɓoye batare da sanin ki ba?" Kallon inda Alh. Mubarak yake tayi, sai tayuyo da kanta tare da sad da kan ƙasa tace "Ni ban taɓa zargin sa ba, kuma Mijina baya ɓoye min komi". "Ok lokacin da kika ji shiru Nazeefa bata dawo miki aike ba, me kikayi akai?". "Nazo na tambayi me gadi sai yace min "tariga da tawuce ai". "Sannan kuma da kika koma nemanta kika yi ko me?" Khalil yafaɗa yana tsare ta da idanu Yawu tahaɗiye kana tace "eh naje na neme ta ciki amma ban ganta ba". Murmushi Khalil yayi yajuya yana kallon Alƙali yace "Ya me girma me Shari'a ko da wannan jawaban da Malam Umaru da Hajiya Asiya sukayi zai tabbatar da ƙarya suke yi, coz inda Nazeefa ta dawo gida kamar yanda sukace ya akayi aka rasa ta lokaci guda? Taya har zata fice gidan batare da wani ya ganta ba idan akayi duba da gidan na mutane ne, sannan idan akayi la'akari da Labarin da Nazeefa ta bayar za'a gane gaskiya take faɗa, sannan kuma ansha neman masu aikin gidan Alh. Mubarak ana rasa su lokaci ɗaya batare da wasu dalili na laifi da suka aikata ba, sai dai aga an kawo sabbi, ko anan ya me Shari'a yakamata asan cewa Alh. Mubarak yana amfani da wannan daman ne wajen ɗaukan yaran mutane yana safaran su zuwa wani ƙasa, Nagode ya me Shari'a". Komawa yayi yazauna, sai da Alƙali yayi rubutu kana yace "Brr. Mahmoud ko kana da tambayan da zakayi?" "A'a ya me Shari'a". Rubutu yasake yi sannan yaɗago yana kallon Brr. Khalil yace "Zaka iya ci gaba da bada shaidun ka". Miƙewa Khalil yayi yana sakin wani kyakykyawar murmushi kana yace "Ya me Shari'a abani dama Brr. Tahir zai je yazo da shedata ta gaba". "An baka dama". Miƙewa Brr. Tahir yayi yafita, bayan kamar mituna 3 sai gasu sun shigo da wani mutum, dasauri Alh. Mubarak dake tsaye tsakankanin ƴan sanda yaɗago idanun sa kamar wanda zasu fito waje yana kallon mutumin. _To fa wanene wannan mutumin?_ [9/29/2020, 1:10 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 32* Alh. Mubarak murmushi yasaki, coz yasan da cewa babu abinda Brr. Khalil zai samu a wajen mutumin, sabida sun riga da sun biya sa zunzurutun kuɗi kuma yayi musu alƙawarin bazai taɓa tona musu asiri ba Ƙarisawa gaban sa Brr. Khalil yayi yace "kotu zata so tasan ainihin sunan ka da sana'ar ka?" "Sunana Aliyu Gusau, amma amfi sanina da Gadanga, kuma sana'a ta shine gadi". "Madalla.. to zan so kafaɗa min wa kake ma gadi?" "Ina yiwa Alh. Mubarak da Dr. Sabit gadi ne". "Ma'ana kana nufin kana aiki a gidan Alh. Mubarak sannan kuma kana aiki gidan Dr. Sabit?" Girgiza kan sa yayi kana yace "ina musu gadi ne a wani gidan su dake Sabon layi G.R.A". Brr. Khalil yace "to zan so kasanar da kotu abinda kasani a waɗannan mutanen biyu da ka lissafo". "Da farko dai Ni me gadin gidan ne, kuma shekaruna 20 ina tare da waɗannan mutanen, abinda nasani shine suna kawo mata gidan suna ajiye su, kuma Ni ne jagoran da nake taimaka musu wajen tsare musu Matan da suke kawo wa, sannan Ni ke basu abinci a ko yaushe". Murmushi Brr. Khalil yayi yace "ina jin ka, daga nan kuma ya ake yi dasu?" "Dr. Sabit shi ke musu allura sannan yasaka musu Coken acikin su, bayan kamar mintuna 20-30 za'a zo da motoci a tafi dasu, suna safaran su zuwa wasu ƙasashe ne, Ni iyakan abinda nasani kenan". Still Murmushi Brr. Khalil yayi kana yace "ita kuma Nazeefa ya akayi tabar gidan batare da sanin ku ba?" "A lokacin Dr. Sabit ya aike Ni zuwa gidan sa don naɗauko wasu yara, to ina tunanin a lokacin ne tafita don basuyi zaton zata iya farkawa a time ɗin ba". Gaba ɗaya kotun ne yahargitse da surutu sai hayaniya ake yi, shi kuwa Alh. Mubarak tun sanda yaji Gadanga yana zayyano bayani yarufe idanun sa yana jin wani baƙin ciki a ransa, saɓanin Dr. Sabit dake zaune cikin mutane, be taɓa tunanin asirin sa zai tonu ba da be zo wajen ba, sosai yashiga firgici don yasan yau kashin su ya bushe tasu ta ƙare Brr. Khalil yace "ina son kotu tabani dama zan kira Dr sabit don amsa tambayoyi". "Dr. Sabit zaka iya fitowa gaban kotu". Jiki a sanyaye yafito yana gyara glass ɗin idanun sa duk zufa ya jiƙa masa fuska, matsowa kusa dashi Khalil yayi yace "Dr. Sabit shin me zaka iya cewa game da bayanin Gadanga?" Shiru yayi yana sad da kai ƙasa, gaba ɗaya hannayen sa rawa suke yi don be san kuma abinda zai iya cewa ba, "shin yaƙaryata abinda aka faɗa akansa ne ko ya?" "Dr. Sabit kai muke sauraro, kana da abin cewa ko kuwa ka yarda da zargin da ake muku?" "Eh.. eh na amince mun aikata duk abinda ake zargin mu dashi.." "Ƙarya ne wlh ƙarya yake min ni dai, Ni ban amince da abinda yafaɗa ba". Cewar Alh. Mubarak gaba ɗaya yazama tamkar zararre, sai ƙara maimaita abinda yafaɗa yake yi Buga guduma Alƙali yayi yace "ya isa Alh. Mubarak, nan kotu ne Yakamata kanutsu kasan me kake yi". Sai alokacin yayi shiru yana share zufan dake keto masa, mutane kuwa sai faɗin albarkacin bakin su suke yi, sai da Alƙali yasake buga guduma sannan suka nutsu, takowa Brr. Khalil yayi zuwa tsakiyan kotun yana cewa "Ya me girma me Shari'a sai kuma Shaidata ta ƙarshe, abani dama in gabatar da Fadila Muhammad". "Idan da Fadila Muhammad tafito". Baby Dil dake zaune can baya tamiƙe tataho, sai da idanun kowa yakoma kanta coz yanda take tafiya cike da yanga, wanda kallo ɗaya zakayi mata kagane ita ɗin ba ƙaramar gogaggiyar ƴar duniya bace, duk a yanzu ɗin tayi shigan mutunci, but hakan be hana bayyanuwan Tatue ɗin dake zane a jikin ta ba, ƙarisawa tayi tasaya kamar yanda kowa ke yi, sannan shi kuma yatako kusa da ita yana faɗin "Fadila zan so kisanar da Kotu sunan ki da inda kike?" Murmushi tasakar masa kana takalli dandazon mutanen wajen tace "Sunana Fadila kuma Ni ɗin ƴar garin Kano ce, but ina zaune a EGYPT yanzu, kuma daga can nadawo nan". "Ok shin ko kinsan Alh. Mubarak me kuɗi?" "Ƙwarai kuwa nasan shi tun shekaru 7 da suka wuce, yana yawan zuwa EGYPT wajen uban gidan mu". "Shin menene alaƙan shi da uban gidan naku? Kuma kinsan me yake zuwa yi?" "Eh na sani, yana siyar wa da Mr. Jay pitter ƴan mata, shi kuma sai yazamar dasu karuwai". Murmushi Brr. Khalil yayi yace "mun gode Fadila, zaki iya komawa kizauna". Sannan yajuya ga wajen zaman sa, kallon Brr. Bilkisu yayi yai mata alama da ido, sai tamiƙo masa wasu Files, amsa yayi yadawo tsakiyar kotun yana cewa "Waɗannan Files ɗi su ne duk wani shaidu da ke kan Alh. Mubarak me kuɗi na zuwan sa EGYPT da safaran ƴan mata da yake yi duk suna cikin nan". Sannan yamiƙa ma Maga-takarda yaci gaba da faɗin "Da wannan nake roƙon kotu da tayanke wa Alh. Mubarak da Dr. Sabit da duk wasu waɗanda suke da hannu aciki hukunci dai-dai da abinda suke aikatawa, Nagode ya Me Shari'a". Zama yayi, Alƙali yakalli Brr. Mahmoud yace "Kana da abin cewa Brr. Mahmoud?" Miƙe wa yayi yace "a'a ya me Shari'a, sannan yakoma yazauna Rubutu yasoma yi Alƙalin kafin yaɗago kansa yana kallon mutanen wajen yace "Abisa zargin da ake ma Alh. Mubarak me kuɗi tare da abokan aikin sa bisa ga tarin hujjoji da aka gabatar, kotu ta gamsu kuma ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga Alh. Mubarak me kuɗi tare da Dr. Sabit, sakamon kama su da yin babban laifi na safaran mata tare da raba su da iyayen su amaishe su karuwai, sannan tare da laifin siyar da Coken, zasu ƙare rayuwan su cikin Jail tare da horo me tsanani, sannan kuma zasu biya taran Miliyan biyar ko wannen su, sannan kotu ta yanke ma Aliyu Gadanga ɗaurin gidan kaso na shekara 10 sakamakon da hannun sa cikin aikata laifin, wannan shine sakamakon hukuncin da suka aikata". Daga nan Alƙali yabuga guduman sa yamiƙe tsaye, gaba ɗaya mutanen wajen suka miƙe suna me faɗin "Kooooooootuuuuuuu". Hayaniya wajen yakaure dashi yayinda mutane ke ta turuwan ficewa, alokacin ne kuma ƴan sanda suka taso ƙeyan su Alh. Mubarak zasu tafi dasu, iyalan su in banda kuka babu abinda suke yi Brr. Khalil kuwa tun aciki yasoma gaisawa da mutane ana masa murna sai zuba murmushi yake yi, koda suka fito waje nan ƴan jarida sukayi masa caaa, dasauri Kausar tature mutane tamatso kusa dashi tana cewa "Brr. Zamu so kasanar mana wani irin farin ciki kake ji yayinda kayi nasara a wannan gagarumar shari'ar?" Murmushi yasakar mata kana yace "Farin ciki mara misaltuwa, ko ba komi yau na kawo ƙarshen wasu daga cikin mugayen ƙasar mu, kuma ina roƙon Allah yatona asirin duk waɗanda suke da hannu a ɗaukan ƴaƴan mutane suna fita dasu wasu ƙasan don karuwanci". "To wani jan hankali kake dashi a gare su?" "Su tuna cewa su ma suna da ƴaƴa, idan hakan tafaru dasu bazasu ji daɗi ba, idan har basu tuba sun dena wannan banzan harƙallan ba to da sannu zasu girbe abinda suka yi sannan ƙarshen su bazai taɓa kyau ba". Wasu tambayoyin suka soma mishi amma yayi gaba abin sa batare da ya amsa musu ba "BARRISTER". Yaji an kira sunan sa daga bayan sa, juyowa yayi yana kallon ta sai yasakar mata murmushi, ƙarisowa tayi wajen itama tana murmusawa tace "Congratulations, na gode sosai da taimakon ka gare Ni, haƙiƙa bazan taɓa mantawa da kai ba, thank you so much BARRISTER". Still yana murmusawa yace "Babu komi Fadila, yanzu yaushe zaki koma gida?" Ɗan fari tayi da idanu tace "yanzu". "Ok sai kin kawo mana ziyara kenan?". Murmushi tayi tace "insha Allahu". Daga nan sallama sukayi kafin yanufi wajen motan sa inda su Sameer da su Mom tare da su Brr. Tahir suke jiran sa, yana isowa Sameer yaja kumatun sa yace "Ɗan ƙanina na tayaka murna". Dariya gaba ɗayan su sukayi kafin sukayi sallama duk suka shiga motocin su ganin Ƴan Jarida na damun su, suka bar wajen. [9/30/2020, 10:43 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ ~Wattspp Number 07065334256~ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 33* Halwa ce zaune saman gado kusa da na Saleema dake barci har yanzu bata farka ba, but yanzu babu Oxgyen da aka saka mata sabida Numfashin ta ya dai-daita itama Halwan an sanya mata drip a hannun ta, Ummi dake zaune saman kujera tana yanka Lemo cikin plate, bayan ta gama sai taɓare ayaba shima duk tajera akan plate ɗin tamiƙa ma Halwa tace "Riƙe kisha wannan nasan zai fi miki, bazaki zauna haka tun safe baki ci komi ba". Babu musu Halwa ta'amsa tasoma ɗauka tana sha, Nurse ce tashigo da sallaman ta taƙariso wajen su tana cewa "Ya jikin naki? Da fatan yanzu kina jin ƙarfi sosai ajikin ko?" Gyaɗa kai Halwa tayi tana kallon ta "Ok gashi wannan maganin ki ne zaki riƙa sha a rana sau biyu, Allah yasauwaƙe". Ummi ne ta'amshi maganin tana cewa "Ameen mungode". Matsowa tayi tagyara mata ruwan kafin tafito da allura cikin aljihun ta tasoma haɗawa tana faɗin "Har yanzu ita bata farka bane?". "Eh". Ummi ta'amsa mata tana kallon Saleema". "Ok idan ta farka Sister Asma'u sai ki sanar da Doctor ɗin". Ummi tace "ok ba matsala". Alluran tatsira cikin Drip ɗin Halwa kana tayi musu sallama tafice, ruwa Ummi tamiƙo mata tare da ɓallo maganin shima tamiƙa mata tace "Gashi kisha, amma kiyi sauri kishanye Fruits ɗin kinsan babu komi acikin ki". Gyaɗa kanta tayi ta'amsa maganin tazuba a baki tana runtse idanu kafin takora da ruwa, daƙyar ta iya haɗiyewa tana sakin nishi, murmushi Ummi tayi tace "Da alamu bakison magani ko?" Itama Halwa murmushin tayi tana sauke kanta ƙasa "To yi sauri kishanye mana". Ci gaba tayi da shan Fuirts ɗin har tashanye, Ummi ta'amsa plate ɗin ta'ajiye, gyara zaman ta tayi tana kwanciya tare da rufe idanun ta, barci take ji sosai kasancewar Alluran da akayi mata cikin Drip ɗin na barci ne coz ana son tasamu hutu sosai, babu jimawa kuwa barci yayi awon gaba da ita, koda Ummi tayi magana taji shiru hakan yatabbatar mata da barci ya ɗauke ta, tashi tayi takoma saman kujerun dake ɗakin taɗau remote tana sauya tasha, a *ƳAN CI T.V* tabari tasoma kallon Labaran da ake nunawa na hukuncin da aka yanke akan su Alh. Mubarak, in banda girgiza kai babu abinda Ummi take yi. Tsawon awa ɗaya kafin ruwan da aka saka ma Halwa yaƙare, har wannan lokacin kuma acikin su babu wacce tafarka, tashi Ummi tayi tacire mata Drip ɗin kana tashiga Toilet tayi alwala tafito, fita tayi babu jimawa tadawo riƙe da dadduma, sallan la'asar tayi, bayan ta idar tana zaune tana lazimi Abba yashigo, ƙarisowa yayi yazauna yana kallon ta, itama ɗago kanta tayi tai masa sannu da zuwa, amsawa yayi yace "Yakamata ki koma gida sai in zauna dasu, tunda yau ba aiki zakiyi ba". Ummi tace "a'a Abban Saleema babu abinda zan yi ko na koma gida, nasan tunda akwai Larai zata kula da komi, kuma zata kawo mana abinci nan tunda tasan muna nan ɗin". Gyaɗa kansa yayi yace "ok shikenan, bari ni inje yanzu zan dawo insha Allah, idan ƴar Baba tatashi ki kira ni awaya idan ban dawo ba". "Toh". Daga nan tashi yayi yafice ita kuma taci gaba da lazimin ta. ***** ******* *********** Shigowan sa kenan cikin gidan nasa, tun gama shari'an gaba ɗaya suka wuce gidan su sai yanzu yadawo, ahankali yabuɗe ɗakin nasa yashiga, aje komi yayi tare da cire kayan jikin sa yawuce cikin Toilet wanka yayi sannan yafito, ko mai be shafa ba yaɗauko kayan sa ƙaramar riga fara da dogon wando robber shima fari yasaka, fitowa Parlour yayi yazauna saman 3sitter, wayoyin sa da suke kashe duk ka biyun yaɗauka yakunna, saƙonni ne suka soma shigowa, sai da suka gama gaba ɗaya sannan yasoma buɗe wa yana gani, duk yawanci Abokan sa ne da waɗanda yasani suke tayasa murna, be fi guda goma yabuɗe ba yamayar da wayan ya'ajiye tare da kwanciya yana ɗaura hannun sa ɗaya saman fuskar sa yalumshe idanun sa, ya ɗau tsawon awanni yana ahaka, babu abinda yake yi sai tunani, sai da yaji kiraye-kirayen sallan Magriba kafin yamiƙe a kasalance yashiga Toilet ɗin dake parlour'n yaɗaura alwala yatafi masjid. *** ***** **** **** *BAYAN KWANA BIYU* A kwana biyun nan sosai jikin Saleema yayi sauƙi, don haka aka sallame su suka koma gida, gaba ɗaya Ummi tahaɗa su tana basu kulawa kasancewar har alokacin itama Halwa sosai take fama da jikin ta, laulayi ya sako ta gaba ko abinci sai anyi dagaske take ci, gaba ɗaya ta rame sai haske da tayi, komawar su gida ma sai da Ummi tasake saka mata Drip sabida yawan aman da take yi. Yanzun ma kwance take saman gado, duk ta ƙudundune jikinta cikin bargo tana ta rawan ɗari, Saleema kuma na zaune gefen ta tabuga uwar tagumi tana kallon ta, fuskarta ya nuna damuwa sosai kamar tayi mata kuka, cikin tsananin tausayawa tace "Wai meyasaka baza'a cire cikin bane? Kina shan wahala da yawa.." Ummi da shigowar ta ɗakin kenan taji maganar da Saleeman take yi tayi saurin katse ta "Kull.. kar in sake jin kin bata wannan shawaran, bakisan haramun bane zub da ciki? Bana son in sake jin kin faɗa mata hakan kinji ni?" Gyaɗa kanta Saleema tayi tace "Toh Ummi". Zama Ummin tayi tana ajiye Coolarn da tashigo dashi tare da plate tace "Tashi kici abinci Halwa, Faten wake ne nasanya akayi miki nasan zakiji daɗin sa kinji? Tashi maza kici". Saleema tace "to Ummi kawo in zuba mata". "Ai har dake zakici, in kun gama sai kusha maganin ku ni zan tafi asibiti, sannan nasaka Larai tayi muku Farfesun kayan ciki, shima sai kuhaɗa dashi kuci, ni natafi ku kula da kanku sosai kunji?". Gyaɗa mata kai sukayi, daga nan ficewa tayi bayan Saleema tayi mata "adawo lafiya". Tana fita Saleema tabuɗe Coolar'n tazuba musu Faten waken da yaji nama sai tashin ƙamshi yake yi, kallon Halwa da har yanzu take kwance tayi tace "Tashi muci". Sai kuma ta'ajiye abincin a ƙasa tana matsowa kusa da ita tataimaka mata tasauko, zama sukayi a ƙasa suka soma ci, Halwa bata wani ci sosai ba tamatsa gefe tana ɗan sakin nishi, Saleema kallon ta tayi tana shirin yin mata magana sai taga tasoma kwarara amai, dasauri tamatsar da abincin tamiƙe tana riƙo ta ganin tana shirin faɗuwa, sai faman sannu take mata kamar zatayi mata kuka, sai da ta amayar da duk wani abinda ke cikin ta sannan tatsakaita tana numfarfashi cike da galabaita, taimaka mata Saleeman tayi suka shiga Toilet tawanke jikin ta kafin suka fito, zaunar da ita saman gadon tayi takoma Toilet ɗin taɗauko kayan Moping tawanke wajen tare da sharewa, sai tadawo tazauna tana kallon Halwan da itama tazuba mata idanu tana jingine jikin gadon, murmushi tasakar mata cikin sanyin murya tace "Na.. go..de". Waro idanu Saleema tayi tana mata alama da hannu "na mene?" "Bansan da me zan saka miki ba, kin taimaki rayuwata sosai, kin zame min ƴar uwa alokacin da narasa kowa nawa, sannan kin kawo ni gidan ku kin maishe da ahalin ki ahalina, wlh bansan da bakin da zan miki godiya ba, haƙiƙa bazan taɓa manta ki cikin rayuwata ba, daga yau kece komi nawa kuma insha Allahu zan ɗauke ki ƴar uwa kuma wacce zata maye min gurbin ƙawata Zainab". Runtse idanun ta tayi jin hawaye na son zubo mata, Sai kuma tabuɗe tana murmushi tace "Daga yau bazan sake kewarta ba tunda har nasami madadin ta". Riƙo hannun ta Saleema tayi itama tana murmusawa tace "Ki dena faɗan haka, Ni nayi ne duk sabida Allah, sannan naji daɗi da kika ɗauke Ni ƴar uwa ƙawa, dama na daɗe ina jiran ranan da zan sami tawa ƴar uwan, sai gashi Allah yabani ita har gida". Sai kuma tasaki dariya har haƙoran ta suna bayyana, tamiƙe tsaye tana faɗin "Bari in amso mana ferfesun sai ki ƙara ci tunda kin amayar da wannan da kikaci, ina zuwa". Daga haka fita tayi dasauri, bata jima ba tadawo ta'ajiye musu a saman gadon, sai taɗauko maganin Halwan dake ajiye a kan drower tadawo tazauna, nata tabuɗe taɓalla tasha tare da korawa da ruwa, sai takalli Halwa tana sakar mata murmushi tace "To kema kici sai kisha maganin ko?" Gyaɗa kanta tayi tana saka hannu tashare hawayen da suka sulmiyo kan kuncin ta batare da Saleeman tagani ba, bayan ta ɗan ci kaɗan sai tasha maganin sannan taci gaba taci, Saleema kuwa cire hannun ta tayi tana yin gyatsa tare da faɗin "Alhmadulillah Ni dai na cika cikina, saura ke". Kallon juna sukayi sai suka saki dariya gaba ɗayan su "Kinsan me?" Cewar Saleema tana shafa cikin ta Girgiza mata kai kawai tayi tana kallon ta Cikin sakarci irin na yaran masu kuɗi tace "Idan kin haihu ko Ni zaki bama Baby, Ina son shi ni zan kular miki dashi, zamu riƙa wasa tare in koya masa karatu da komi da komi, kinji zaki bani ko?" Saurin sauke kanta ƙasa Halwa tayi tana jin hawaye na zubowa daga idanun ta, sai tayi saurin tare hannun ta tasharce shi, hannu itama Saleeman takai tana sharo mata hawayen cikin sanyin murya tace "Kuka kike yi? Ni ce ko? Kiyi haƙuri Don Allah". Ɗago kanta tayi tana kallon ta tare da girgiza mata kai, still tana hawayen tace "A'a ba don ke nake yin kukan ba, kawai na tuna da gida ne, ina matuƙar kewar su Mama, ina matuƙar kewar su sosai.." Sai tafashe da kuka, nan da nan jikin Saleema yasoma yin rawa sai itama tafashe da kukan _"Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta ni da mahaifinta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine mu saka ta farin ciki.."_ Tunawa da maganganun Ummi ne yasaka Halwa saurin katse kukan ta tana kallon Saleeman da ita har yanzu bata dena nata kukan ba, dafa kafaɗunta tayi cikin murmushi tace "Menene na kuka ke kuma? Kinsan da cewa baki da lafiya don Allah ki dena kar wani abu yasame ki". "Taya kike tunanin zan dena bayan na ganki cikin ƙunci? Ina matuƙar tausaya miki idan natuna labarin ki, bana jin daɗi ko kaɗan idan naganki cikin damuwa". Dariya Halwa tayi tace "to na daina ai, kuma Ni ina kuka ne sabida farin ciki, farin cikin na sami ƴar uwa me ƙaunata, wacce take ƙaunar abinda zan haifa tun kafin yazo duniya, insha Allahu idan har nahaife shi na baki shi kyauta, daga lokacin kece mahaifiyar duk abinda zan haifa". Itama dariya Saleema tayi tace "wayyo naji daɗi sosai, bari su Ummi su dawo zan sanar musu, amma kuma kinsan me Yakamata in saka masa a suna?" Girgiza kanta Halwa tayi tana dariyan shirmen Saleema, wani lokacin in tana abu tamkar ƙaramar yarinya, kuma duk sangarta ne da yayi mata yawa, sai da ta ɗan yi tunani kana tawashe baki tace "Idan mace ne zan saka mata sunan Ummi, idan kuma na miji ne sai in saka masa Abbana". Murmushi Halwa tayi tace "hakan yayi". Matsowa sosai Saleema tayi kusa da ita kana tace "yauwa yanzu ya jikin naki dasauƙi ko?" Gyaɗa mata kai tayi, duk da tana jin ciwo amma bazata iya nuna mata ba coz yanda taga tana nuna damuwarta sosai "Ok bari in baki labari, zan baki labarin school ɗin mu tare da ƙawaye na". Labarin tasoma bata suna ta dariya kamar basu ba, kuma duk kan su idan kakalle su zaka gane ba ishashshen lafiya ne dasu ba, sai dai ƙarfin hali kawai da suka ara suka yafa, daga ƙarshe ma barci ne yaɗauke su sakamakon maganin da suka sha akwai na barci aciki. _Allah Sarki wannan shi ake cewa gamon jini, Allah yahaɗa mu da masu son mu fisabilillahi._❤️🙏🏼 [10/1/2020, 1:46 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 34* Kwance take saman gadon ta daga ita sai ƴar shimi fara ƙal, sai jan wando robber da yamatse ta sosai wanda da kaɗan yawuce gwiwarta, wayan ta dake ajiye saman gadon ne tasoma ringing sai tajawo tana kallon screan ɗin wayan, ganin sunan HONEY yafito ɓaro-ɓaro yasaka tayi peacking call ɗin tana kangawa a kunne, shiru tayi tana sauraron sa sai kuma ta'ajiye wayan tamiƙe tsaye tana ɗaukan Red colour Jaket ɗin dake ajiye saman gadon tasaka, Jaket ɗin irin me buɗaɗɗen gaba ne sai Belt da aka saka a iya tsakiya wajen cikin ta, iyakan cinyan ta yatsaya mata, sai taɗau Facing cap shima Red tasaka tafito, Ahmad ne kaɗai yake zaune Parlourn yana kallo takalle shi tace "Idan Mami tafito kasanar mata nafita wajen Sharif". Ahmad yace "ok". Fita tayi tanufi inda yake tsaye jikin motan sa, tun fitowan ta yake kallon ta yana murmushi har ta'iso wajen "My beautiful girl". Yace hakan yana sake faɗaɗa fara'ar sa Ɗan cije laɓɓanta tayi tana kallon sa itama cikin murmushi tace "ya kake?" "Lafiya, kefa?" "Lafiya lau". Tayi maganar tana jingina da motar itama kamar yanda yayi, sai dai facing juna suke yi "Kinsan me?". Girgiza kanta tayi still tana kallon sa "Kullum sai in riƙa jin ƙaunar ki na ƙara zauta Ni, har yanzu nakasa sabawa da yanayin da nake ji a kanki". Sai ya ɗan yi murmushi yana shafa kwantaccen ƙasumban sa yaƙure ta da ido yace "Na ƙosa Kausar kikasance mallakina, ina ji ajikina kamar in ban yi dagaske ba zan iya rasa ki". Kallon da take masa ne yasauya zuwa mamaki, amma sai batace komi ba taɗauke kai tana jin zuciyar ta na bugawa, kiran sunan ta Sharif ɗin yayi, sai taɗago kai kawai tana kallon sa Yace "har yanzu baki bani amsa ba akan maganar da mukayi dake". "Wace magana kenan?" Tatambaye sa cike da rashin fahimta Murmushi yayi yace "har kin manta maganar da mukayi lokacin da zamu dawo Nigeria? Haba Dear yakamata ki bama zance na muhimmanci, Ni nayi miki alƙawari wlh zan bar ki kici gaba da aikin ki koda munyi aure, be kamata mu zauna muna ɓata lokaci ba bayan kinsan da cewa mun fahimci juna, kuma iyayen mu sun san komi, to me muke jira?" Shiru kawai tayi tana sauraron sa har sanda yadasa aya, sai kawai tasaukar da kanta ƙasa tana tunani, gaba ɗaya murmushin dake fuskarta ya ɓace, sai damuwa da yamaye gurbin "Kausar". Saurin ɗago kai tayi takalle sa "Wai me ke damun ki ne? Na kula gaba ɗaya kin sauya yau meke faruwa?" "Ban jin daɗi ne Honey". "Eyya shine baki sanar min ba? Kinsan bana Son abun da zai dame ki, yanzu meke miki ciwo?" Yaƙe tayi tana kallon sa tace "kar ka damu kawai gajiya ne yahaddasa min ciwon kai". "Eyya sorry, kije gida to sai muyi maganar awaya, Allah yasawaƙe kinji?" "Ameen". Sake sallama sukayi sannan tajuya tatafi, shi kuma yabi bayan ta da kallo har sanda tashige, ajiyan zuciya yasauke yana buɗe motan sa yashiga yabar gidan Ita kuma tana shiga parlour tawuce ɗakin ta dasauri, akan gadon ta tafaɗa tana sauke numfashi, shiru tayi na ɗan wani lokaci kafin tajawo wayan ta tana latsawa, Numban Khalil talalubo sai tatsaya kawai tana kallo, daga ƙarshe sai tadanna masa kira, har yatsinke be ɗauka ba, akaro na biyu ma da takira be ɗaga ba sai tayi jifa da wayan tana kifa kanta tare da rufe idanu, kamar an tsikare ta kuma sai tamiƙe tafito parlour, har yanzu Ahmad ne kaɗai zaune, ficewa kawai tayi shi kuma yabi ta da ido. Tana fitowa gidan su ta'isa bakin Gate ɗin gidan Khalil tasoma nocking, Me gadi ne yaleƙo da kansa yana ganin ta yabuɗe mata, murmushi tayi masa tace "Yana nan ko?" "Eh yana nan, yanzun nan yadawo". Shiga tayi tanufi cikin gidan, tana isa tasoma nocking sai dai shiru babu amsa, ta ɗan jima a wajen tana tunani sannan kuma sai tasaka hannun ta tamurɗa handle ɗin ƙofan yabuɗe, shiga tayi tana kallon parlour'n, babu kowa sai plasma dake aiki shi ƙadai, kan kujera tasamu tazauna sannan tasoma sallama Khalil dake cikin ɗakin sa, fitowan sa kenan daga wanka yajiyo sallaman ta, ya gane ko wacece don haka kawai yaci gaba da shiryawan sa, bayan ya gama ne yafito parlour'n yasami wuri yazauna yana kallon ta, murmushi tayi masa tace "Ashe kana lafiya? Na kira wayan ka naji shiru baka ɗauka ba shine nashigo in duba ka". Shima murmushin yayi mata yace "sorry ban jiba ne, to ya aikin naki?" Still tana murmusawa tace "alhmadulillah, kai fa?" Sai ya ɗan kwaɓe fuska sannan yace "ba daɗi". Dariya tayi sosai tana kallon sa yayinda shima ɗin ita yake kallo yana sakin murmushi, sosai take jinta cikin farin ciki ganin ta tare dashi "Yunwa nake ji ko zaki dafa min abinci irin na ran nan?" Tsayar da dariyan nata tayi tana kallon sa da murmushi a face ɗinta tace "Me zai hana, ko me kake so zan yi maka ai". Sai tatashi kuma tana faɗin "kabani mintuna 20 yanzu zan gama maka". "Ok to muje nima in tayaki ko na koya nima". Kausar taji daɗi sosai ganin yanda Khalil yasaki jiki da ita a yau ɗin, atare suka gama abincin suka zubo kuma sukaci tare, duk kan su in kakalle su zaka gane suna matuƙar farin cikin kasancewar su tare, duk abun da ɗaya yayi sosai yake burge ɗayan, Kausar ba ita tabar gidan ba sai bayan la'asar. ***** ***** ***** **** "Zainab wai yaushe zaki dena wannan kukan ne? Tun sanda Halwa tatafi kullum cikin kuka kike yi, ko kukan naki ne zai dawo da ita?" Shiru Zainab tayi sai dai har yanzu hawaye basu dena zuba cikin idanun ta ba Umma tace "ki tashi kije ki ɗiba ruwa kiyi wanka tunda yanzu kin zama ƙazamiya wankan ma kin dena". "Umma Ni har yanzu na kasa yarda da abinda Mama da Nura suka faɗa mana, ta ya Halwa zata tafi tabar su lokaci ɗaya? Ya za'a yi Halwa tatafi batare da ta sanar min ba? Tunda muke da ita ban taɓa jin Halwa tayi maganar dangin mahaifin ta ba, ta ya zasu ce don sun zo ganin ta zata bi su tabar su?" Sai kuma tafashe da kuka, cikin kukan take cewa "Wlh Umma ƙarya ne, ƙarya suke yi suce Halwa tazaɓi dangin Mahaifin ta akan su, zuciyata takasa yarda da abinda suka faɗa, suna nufin kenan fa tatafi bazata sake dawowa ba? Ni na tabbata sai dai in wani abu ne yafaru amma Halwa baza ta taɓa tafiya ba". "To don ubanki tunda baki yarda dasu ba sai kiyi tayi, ko kuma kibi ta inda kikasan tatafi". Umma tafaɗi hakan a zafafe domin Zainab ɗin tasoma kai ta maƙura akan zancen Halwan Tashi Zainab ɗin tayi tashige ɗakin ta batare da tasake furta komi ba. October 2020. [10/19/2020, 7:48 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 35* Dad da Mom da Nazeefa ne zaune saman dainnig table suna yin luncing, baka jin ƙaran komi sai Spoons, ita Nazeefa kanta na ƙasa daƙyar take cakalan abincin, don har yau bata saba dasu ba, gwara-gwara Mom in suna tare su biyu. Sameer ne yashigo cikin parlour'n yanufo su yana faɗin "wow nazo a sa'a domin yunwan nima nake ji". Mom da taɗago kai tana kallon sa tace "ba daga gida kake bane?" "Eh naje wajen Friend ɗina ne, kuma daga nan muka wuce Hospital shine nabiyo ta nan". Gyaɗa kai kawai Mom tayi tamayar da hankalin ta ga abincin ta "My Dad barka da rana". Sameer ɗin yafaɗa yana dafa glass table ɗin da hannayen sa Dad kaɗa masa kansa kawai yayi sakamakon ya sanya abinci a baki sai lokacin Nazeefa taɗago kanta tace "sannu da zuwa Yaya". Sameer ɗaura hannun sa yayi akanta yana kallon ta yace "Yauwa ƙanwa ta, abinci kike ci ne haka babu tayi?" Murmushi Nazeefa tayi tana Sad da kai ƙasa, zama yayi gefen ta kana yace "To nima yi saving ɗina in tayaku". Plate tajawo tasoma saving ɗin shi Dad yace "Sameer yau wai ya naji wayan Ibrahim be shiga lafiya dai? Kuma ban gansa ba kwana biyu". Ɗago kai yayi Sameer yana kallon sa yace "Dad wlh ban sani ba, nima dai tun yesterday rabona dashi kuma bamuyi waya ba". "Ok ƙara try Numban sa kaji yanzu". "Ok Dad". Wayan sa yaɗauka yasoma kiran Khalil, ringing ɗaya tashiga but babu answer, sai da yayi two missed calls kafin Dad yace masa "yaƙyale sa haka". Abincin su sukaci gaba da ci, kamar 5mint kuma sai ga wayan tana ringing, Khalil ɗin ne yakira, ɗauka Sameer yayi zai miƙa ma Dad sai yace masa "Ɗauka kawai kace masa ina kiran sa yanzu yazo yasame Ni". "Ok Dad". Peaking call ɗin yayi yace "Hello ɗan ƙanina". Khalil dake zaune bakin gado daga shi sai gajeren wando yaɓata fuska yana cewa "Bro bana so fa nace maka". Ɗan dariya Sameer yayi kana yace "ok na daina, kazo Dad na Kiran ka". Ɗan jimm Khalil ɗin yayi kana yace "ok ga ninan". Daga nan kashe wayan sukayi ya'ajiye tare da miƙewa tsaye yanufi wajen sif ɗin kayan sa yafito da wanda zai saka, bayan ya shirya as usual cikin ƙananan kaya farar riga da blue jeans, yasanya brown cover shoes yanufi gaban looking glass yabuɗe locker yafiddo car key yafice, a cikin ɗaya daga cikin motocin sa kalan ruwan zuma yashiga, be cika hawa motan ba sai yaga dama, yanzun ma yau yafiddo ta yasaka aka wanke masa, yana isa bakin Gate yadanna hon aka buɗe masa Gate ɗin yafice, ahankali yake tuƙin nasa har yakai gidan nasu yafito yashige cikin gidan, a lokacin su Mom sun dawo saman kujerun parlour'n suna zaune suna hira, in kaɗauke Nazeefa da bata wajen ta shiga ɗakinta Lokacin da ya'isa cikin parlour'n bayan ya gaishe da iyayen nashi zama yayi kusa da Sameer dake zaune kan Two sitter Dad yace "yauwa ina maganar mu da muka yi, shin ka samo matar da zaka aura?" Shiru Khalil yayi yana kallon Dad ɗin batare da yace komi ba, haka zalika su ma kallon sa suke yi suna son suji me zai faɗa, ganin shirun nasa yayi yawa Mom tace "Auta kayi shiru, ko har yanzu baka samu matar bane?" "Ai kuwa idan be samu ba Ni sai in nema masa tunda naga abun nasa yana ɗaukan sa da wasa ne". Cewar Dad kenan Khalil kuwa shafo gashin kansa yayi yajuya kai yana kallon Sameer Wanda shima ya kafe shi da nashi idanun yana kallon sa, alama yayi masa da ido sai yakau da kansa yana kallon Dad ɗin yace "Dad na samu". "Masha Allah haka ake so, yanzu yarinyan aina take kuma ƴar wacece?" "Suna zaune a Jan Bulow, mahaifinta sunan sa Alh. Ahmad Sofana". "To Alhmadulillah insha Allahu zamu je zuwa gobe ko jibi don gwara ayi a huta". Mom washe baki tayi tace "My Son na tayaka murna, Allah yatabbatar da alkhairi". Murmushi kawai yayi yana faman sosa kai, Sameer kuwa ɗan bugun kafaɗan sa yayi yace "Congratulation My Lil Bro Allah yasanya alkhairi Allah yasa ayi damu, Burina dama kenan naga auren ka gashi komi yakusa zuwa". Mom itama cikin farin ciki ta karɓe zancen da cewa "wlh kuwa ai nima nafi kowa son ganin wannan ranan, amma Auta mene sunan surukar tawa? ya kamata kasanar min tun yanzu in sani sannan kakawo min ita in ganta don in tabbatar da cewa ka dace da yarinyan ko kuwa". Dariya Dad yayi yace "kai uwar yara wannan zumuɗi haka? Ai sai ki bari komi yakankama tukuna ko?" Itama dariya tayi tace "Uhm baza ka gane bane amma Ni kaɗai nasan irin farin cikin da nake ji, Ni kaɗai nasan me na tanada a auren Autana". ...... ........ ........ ....... Da gudu ta'isa kan gadon ta tafaɗa tana sakin kuka me ƙarfi, sosai take kuka sai kazata yanka ta ake yi, kukan baƙin ciki na jin hiran nasu, bata taɓa tunanin ƙaunar Khalil take yi ba sai a ɗan kwanakin nan tagane, hakan yasaka wani baƙin kishi yaturnuƙe ta jin ya sami wacce zai aura "shikenan yanzu ita ta rasa shi?" Tambayan da tayi ma kanta kenan tana sake kecewa da kuka, duk da tasan yafi ƙarfin ta amma sosai take matuƙar ƙaunar sa fiye da tunanin me karatu, batasan wani hali zata shiga ba idan har tarasa shi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba Jin motsi kamar za'a shigo tayi saurin tsayar da kukan nata cak tana juyawa takalli ƙofan shigowa, dasauri takuma saka hannun ta tashare hawayen fuskarta dai-dai lokacin da Mom tabuɗo ƙofa tashigo, kallon ta tayi yayinda ita kuma tasad da kanta ƙasa tana murɗe yatsun hannunta "Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa naga kamar kin yi kuka? Meke damun ki?" Mom tatambaye ta cike da kulawa Shiru Nazeefa tayi sai kuma tabuɗe baki ahankali cike da rawan murya tace "ba..bu ko..mi Momy, wani abu ne yafaɗa min a idanu". "Subhanallah sannu, yanzun ya fita ko kuwa?" Still Mom ɗin tasake tambayar ta cike da nuna kulawan ta tana saka hannayen ta taɗago kan Nazeefan tana kallon idanun da suka sauya kala "Eh ya fita". Mom tace "ok sannu ko? Allah yakyauta gaba". "Ameen". "To tashi yanzu kije Yayan ki na kiran ki zakuyi maganar School ɗin ki da zai saka ki". Nazeefa ta'amsa mata da "Toh". Kana tatashi tanufi ƙofa, itama Mom bayan ta tabi suka fice atare. ****** ****** ******* A cikin satin ne Alhaji Abdurra'uf tare da abokin sa Alh. Mustapha sai kuma Yayar Mom Alh. Maddibo suka je nema ma Khalil auren Bilkisu, koda suka isa gidan kyakykyawar tarba suka samu wajen ƙanin Mahaifin ta kasancewar a wajen sa take zaune, bayan da su Dad suka gabatar da abinda suka zo nema, Alh. Umar wato ƙanin Mahaifin nata nan yasoma magana cikin dattako "Alhmadulillah gaskiya naji daɗi sosai da akace kamar ku kun zo neman auren ƴata hakan ya faranta min rai matuƙa, sai dai matsalan da akwai wanda nayi mamaki matuƙa cewa ita yarinyan bata sanar muku ba sannan kuma nayi mamaki kan cewa ta turo wani don yanemi auren ta". Ɗan jan numfashi yayi yana kallon su yaci gaba da faɗin "Zan baku haƙuri da cewa mun riga da munyi wa ƴar mu Miji tun tana ƙarama, wanda hakan shine abinda muka saba tun farkon dangin mu wato haɗa auren zumuncin, ina fata zaku fahimce Ni kuma hakan bazai ɓata muku rai ba?" Alh. Maddibo ne yace "a'a wlh babu komi, ai kayi mana bayanin da zamu fahimta hakan ya gamsar damu, shikenan dama Allah yayi nufin ba matar sa bane Muna godiya sosai". Alh. Umar yace "ai Ni ne da godiya bisa abinda ƴar mu tayi, tunda da tasanar dashi duk hakan bazai faru ba". Daga nan dai tashi su Dad sukayi tare da yi masa sallama suka tafi, a hanya Alh. Maddibo yayi musu sallama suka rabu yayinda Dad da Alh. Mustapha suka wuce wajen aikin su. Bilkisu asalin su Nufawa ne ƴan garin Minna, tana zaune wajen ƙanin Mahaifinta ne anan Katsina, babban Family ne dasu kuma sun saba yin auren zumunci ne, ita kanta Bilkisu akwai wanda aka haɗa ta dashi tun tana ƙarama, sai dai shi ɗin baya ƙasar ne yana zaune can Sudan yana aiki, daga zuwa karatu yazauna har yanzu yaƙi yadawo, Allah ne yasaka mata ƙaunar Khalil har takasa haƙuri dashi duk da tasan zai yi wuya ta aure shi, amma soyayya ya rufe mata idanu kwata-kwata ta manta da cewa akwai wanda iyayen ta zasu bata, kuma nan bada jimawa ba ake tunanin sanya ranan auren nasu. [10/21/2020, 4:12 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` _wannan shafin naki ne ZEENAT, ina godiya da yanda kike ƙaunar Littafina, Allah yabar ƙauna_❤️ . *CHAPTER 36* Dad na zaune a parlour'n sa Khalil yashigo yazauna kan kujeran da ke Facing Dad ɗin, Dad ce masa yayi "Ina fata kaji abinda ke faruwa ko?" Gyaɗa kansa Khalil yayi Dad yace "yanzu kana da wata ko kuwa?" "Dad ni Banda wata, ni abar ma maganar sai zuwa nan gaba don ban shirya aure yanzu ba dama". Kallon sa Dad ɗin yake yi be ce komi ba, sai kuma can yabuɗi baki yace "Ibrahim ba maganar wasa muke yi da kai ba, aure nake so kayi kuma a wannan lokacin na gaji da ganin ka haka, idan har maganar neman mata kake yi to Ni na samo maka, akwai yarinyan Abokina da zaka je kanema domin yanzu mun riga da mun gama maganar da Alh. Mustapha". Ɓata fuska Khalil yayi yace "Dad meyasaka kake son kabani wacce bana so?" Murmushi Dad ɗin yayi yace "har yanzu kai yaro ne Ibrahim, ba wai zan maka dole bane amma tunda naga matar ce kakasa nemowa shine Ni nayi maka gwanin ta nanemo maka, kaje wajen ta idan har kun dai-daita kanku shikenan". Khalil yace "Dad don Allah meyasaka baza'a janye maganar ba? infact ma Ni yanzu bani da lokacin aure sabida zan tafi England yin wani course, kuma One year zanyi acan". Dad yace "ok kana nufin Adena maganar auren ka har sai kaje kadawo?" Gyaɗa kansa yayi yana kallon Dad ɗin tare da turo baki, daƙuwa Dad ɗin yayi masa yace "Kaga naka Ibrahim babu inda zakaje sai kayi aure koda kuwa gobe ne zaka tafi". Cikin shagwaɓa Khalil ɗin yace " Haba Dad please Mana kabari sai nadawo inyaso sai in auri ita yarinyan da kakeso". Shiru Dad ɗin yayi yana kallon sa kana yace "ok shikenan, dama itama yarinyan tana karatu kuma dama Mahaifin ta yace min zuwa nan da shekara ɗaya da rabi zata kammala, kaga idan kadawo sai asaka ranan auren hakan yayi?" Jinjina kansa yayi yace "eh Dad". "Ok tashi kaje Allah yataimaka, yaushe ne zaka tafi?" Khalil da yamiƙe tsaye yabashi amsa da cewa "nan da Three weeks". Dad yace "kana da lokaci ai Yakamata kaje wajen yarinyan kaganta, kuma bana son inji cewa bakaje ba". Gyaɗa masa kai yayi kafin yayi masa sallama yafice. Koda yafito babu kowa a palrour, kawai ficewa yayi batare da yashiga wajen Mom ba, motan sa yashiga yabar gidan, wayan sa yaɗauka yakira Brr. Tahir ringing biyu yaɗauka yace "Ango ango". Ɓata fuska Khalil yayi yace "wanene Angon?" Dariya Brr. Tahir ɗin yayi yace "ai naji komi wajen Dr. Sameer, yace "min anje nema maka auren Billy". Tsaki Khalil yaja cike da haushi da zaka gane cikin muryan sa yace "kabari dai kawai Tahir, yarinyan nan ashe yaudarana tayi". Brr. Tahir yace "bangane ba kamar ya yaudaran ka tayi?" Daga nan Khalil yasanar masa da abinda yafaru da su Dad da sukaje kana yaƙara da cewa "Dama abinda nake gudu kenan Tahir tun farko shiyasaka bana son yin soyayya bcoz yawancin matan mayaudara ne, and duk da bana wani son ta but naji haushi sosai ɓata min lokacina da tayi, gashi yanzu taja min Dad ya samo min wata". "To fa haka akayi? Gaskiya banji daɗi ba kuma Bilkisu bata kyauta ba, amma kayi mata uzuri mana don Ni banga laifin ta anan ba matsalan daga iyayen ta ne, meyasaka baza su bata wanda take so ba?" Gajeren tsaki Khalil yayi yace "har kana da bakin kare ta anan? Ni Abokin wasan ta ne?" Brr. Tahir yace "kayi haƙuri kabi abin a sannu, kuma don Allah karka ce zakayi mata wata magana da be dace ba". Shiru Khalil ɗin yayi don shi yariga da ya rufe shafin ta "Yanzu to aina yarinyan da Dad ɗin yasamo maka take?" Brr. Tahir ɗin yatambaye sa Taɓe baki Khalil yayi yace "wai ƴar Abokin sa ne, sai kace suna neman kai dani". Brr. Tahir dariya yayi yace "kai masha Allah Allah yasanya alkhairi, gaskiya naji daɗin wannan haɗin domin kuwa idan Dad yabiye taka baza kayi auren yanzu ba". Yamutsa fuskar sa yayi yace "kaga ni zan aje waya ina tuƙi ne sai anjima". Still dariya Brr. Tahir yayi yace "ok zuwa a anjiman zan kira ka bye". Daga nan ajiye wayan yayi yaci gaba da tuƙin sa. **** ***** ****** ******* Ummi ce zaune kan Three sitter Saleema tayi matashi akan cinyan ta, gefe ɗaya kuma Abba ne zaune kan Two sitter suna hira Abba ne yace "ƴar Baba tashi akwai maganar da zamuyi dake me muhimmanci". Amsa mishi Saleema tayi tana tashi zaune "Shin kin tuna Abokina Alh. Abdurra'uf?". Kallon Abban tayi kana tace "eh Abba nasan shi, ko ba wanda ada kake yawan kai ni gidan ba?" Murmushi Abba yayi yace "yauwa shi ƴar Baba, kinsan yaran sa ko?" Gyaɗa kai tayi tace "nasan su Abba". "To ki saurare ni da kyau ƴar Baba, kinsan Burin mu shine mu aurar dake ga mutumin da zai kula dake kamar yanda muke kula dake, muna Son farin cikin ki Daughter wannan dalilin ne yasaka muka yanke shawara Ni da Mahaifiyar ki mu samo miki Miji wanda zai baki duk wani kulawa, ɗan gidan mutunci wanda zai iya riƙe mana ke bisa amana, akwai ɗan sa Ibrahim Khalil shine mahaifin sa yake nema masa auren ki, Ni kuma ganin haka yasa na'amince but duk da haka sai na tambayi ra'ayin ki, idan har kin amince zai zo wajen ki don ku dai-daita, kiyi tunani da kyau My Daughter don baza mu taɓa baki abinda baki so ba, zaɓin ki shine namu". Saleema kallon Abban nata kawai take yi har yadire maganar kafin cikin zaƙuwa tace "Abba wai kana Nufin Yaya Barrister?" "Eh Shi ƴar Baba". Rufe bakin ta tayi tana waro idanu cike da wani irin farin ciki tace "Kaiiiii.." Ummi tace "lafiya Daughter me yafaru?" Dariya tasaki tana yarfe hannayen ta sai kuma tasake rufe bakin ta tana kallon iyayen cike da tsananin farin ciki, su kuwa kallon ta kawai suke yi suna tunanin "meyasaka ta farin ciki haka lokaci ɗaya?" Muryan ta suka tsinkaya tana cewa "Anya Abba Yaya Barrister shine Wanda mahaifin sa ke nema masa aure na? Ina mamaki Abba taya?" Murmushi Abban yayi yace "Ƴar Baba kenan ki dena mamaki ai komi ba yanda Allah baya nuna ikon sa, yanzu menene ra'ayin ki akai? shin kin amince ne?" Saurin gyaɗa kanta tayi tana me tsananin farin ciki, riƙo hannun ta Ummi tayi tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace "Wai farin cikin na menene da alamun dai kina son sa kenan?" Saleema har ta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi saurin rufewa don baza ta iya yin musu bayanin abinda ke ranta ba, illa tashi da tayi da gudu tanufi hanyan ɗakin su tana ci gaba da dariya, bin bayan ta sukayi da idanu cike da tsananin mamakin ta kana Abba yace "Ikon Allah wai lafiyan ƴar Baba ƙalau?" Ummi cike da farin ciki tace "ai inaga Abban Saleema da alamun ƴar mu ta daɗe tana ƙaunar sa ne, domin Ni sheda ne abaya sanda kake yawan ɗaukan ta kuje gidan kullum idan tadawo bata da magana sai na Yaya Barrister, Kai har dai na gaji daji don idan tazauna labarin kenan, to tun sanda tayi ciwon nan sosai aka kwantar da ita asibiti kadena kaita to ban sake jin tayi maganar ba, amma Ni ina da tabbaci son sa take yi kuma ina ganin tana cikin mamakin abun ne". "Kai amma idan ko hakane zamuyi farin ciki sosai ai dama fatar mu kenan, burin mu shine tasami miji na gari kuma ina da yaƙini ta samu, domin Khalil be da wani matsala yaro ne me tsananin kirki da biyayya na tabbata bazai taɓa wulaƙanta mana ƴa ba, wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin haɗa wannan auren". Ummi jinjina kanta tayi cike da gamsuwar bayanin mijin ta kana tace "to Allah yatabbatar da alkhairi Allah yasa ayi damu". "Ameen ameen". Cewar Abba still yana me nuna farin cikin sa "Amma ina tunanin ba yanzu za'a yi auren ba sabida yaron zai yi tafiya, kin ga har sai ta gama school ma anan, sai kiyi mata bayani yanda zata fahimta". "To babu matsala ai hakan yayi ma". Cewar Ummi kenan Daga nan hira sukaci gaba dayi suna tattaunawa akan maganar. [10/30/2020, 8:51 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 37* Tana shiga ɗakin tafaɗa kan Halwa dake barci, hakan yasaka Halwan tafarka tana kallon ta da idanuwanta da sukayi ja, cike da tsananin farin ciki Saleema tace "Wayyo Allana yau ina farin ciki sosai kitashi ki tayani murna". Ahankali Halwan tatashi zaune tana ci gaba da kallon ta tace "me yafaru ne Sister?" Murmushin da yabayyana haƙoran ta tayi tace "kinsan me Abba yazo da maganar aure na Ni da ɗan Abokin sa". Waro idanu Halwa tayi tana kallon ta, sai kuma tayi dariya tace "shine yasaka ki farin ciki?" Gyaɗa kanta tayi tana sake washe bakin ta tace "eh mana abin ne ya matuƙar bani mamaki, ban taɓa tunanin wannan ranan ba, ban taɓa tunanin Ni Saleema ina da matsayin da zai sa ace yau zan zama matar Barrister ba, Mutumin da ko magana ban taɓa samu ya haɗani dashi ba, ada nayi burin ace Barrister ya zama nawa but ko kaɗan babu hanyan da naga yiwuwar hakan, amma yanzu kiji abin mamaki sai gashi lokaci ɗaya Allah ke ikon sa wai ni ce yau ake son haɗa ni dashi, abun sai kace amafarki wlh". Yanda taƙarike maganar nata ne yaba Halwa dariya, sai da tadara kafin tace "to menene aciki? Ni a ganina banga Namijin da yafi ƙarfin ki ba, kar ki manta kema fa kina da kyau da haɗuwar da ko wani namiji zai yi fatar samun ki, ki dena zuzuta shi da yawa don nasan bazai fi ki da komi ba". Saleema tace "uhmmm baza ki gane bane Sister, ko wace mace idan har tagan shi zata so yazama shine Mijin ta, ba wai don haɗuwan sa ko kyawun sa ba amma yana da nagartan da idan har kin ganshi kema wlh sai kin so shi, domin bakiga yanda mata suke rushing akan shi bane". Taɓe baki Halwa tayi tana kallon ta tace "da alamu dai kina son sa da yawa, amma to kina ganin shima yana ciki?" Zaro idanu Saleema tayi tace "hmm mutumin da ban taɓa magana dashi ba taya kike tunanin yana sona? I Think ko sanina be yi ba". Shiru kawai Halwa tayi tare da tunanin Nura aran ta "Burina a rayuwa shine in Sami Miji tamkar Barrister sai gashi shi ɗin na samu, nasan ko baya so na watarana zai ƙaunace ni domin kuwa zan yi duk abinda yake so". Saleema taƙarike maganar tana rufe fuskarta cike da farin ciki Buɗe fuskar tayi tana kallon Halwa da tafaɗa tunani, sai tataɓo ta tana cewa "Sister lafiya tunanin me kike yi?" Ajiyan zuciya Halwa tasauke kana tace "Babu". Murmushi tayi tace "to faɗa min kema, menene burin ki a rayuwa?" Shiru Halwa tayi tana kallon ta batare da tace komi ba "Sister kisanar min mana kinji?" Duƙar da kanta tayi tana murza ƴan yatsun hannayen ta masu tsawo da burgewa kana taɗago kanta tana kallon Saleema da murmushi a fuskarta tace "ada bani da wani buri a rayuwa sama da inyi aure in ganni gidan Yaya Nura amma.." Shiru tayi tana kawar da kanta kana taci gaba da cewa "amma a yanzu Burina inyi karatu me zurfi in zama lauya ko dan naɗau fansar abinda Haris yayi min". Ɗaura hannun ta Saleema tayi akan na Halwan tana cewa "meyasaka kike Son ɗaukan fansa? Meyasaka baza ki barshi da Allah ki manta dashi cikin rayuwan ki ba? Idan har kikace zaki ɗau fansa hakan na nufin kenan zaki riƙa tuna sa har zuwa wani lokaci?" Halwa tace " Ni kaina nayi tunanin barin shi da Allah kamar yanda tun farko nabar shi, amma yanzu wani tunani yazo min arai saboda shigan ciki a gare ni, idan har nahaifi abinda ke cikina dole ne watarana yatambaye Ni "ina Mahaifin sa?" kina tunanin wani amsa zan bashi?" Taƙarike maganar hawaye na cikowa cikin idanun ta, kana taci gaba da cewa "Wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin na zama lauya don nan gaba na kaisu ƙara kotu domin hakan ne kaɗai zai saka gidan su Haris su amshi abinda nahaifa, baza su taɓa amsan abinda zan haifa ta daɗin rai ba dole sai ta wannan hanyan". Numfashi taja me ƙarfi still taci gaba da faɗin "Burina na biyu shine in San meyasaka Yaya Nura yajuya min baya? Ina son in San dalili ina son insan meyasa?.." Sai kuma tasaki kuka me ƙarfi, cikin rawan murya tace "na.. na kasa yarda cewa Ya..ya Nura zai juya min ba..ya, zuciyata takasa amince wa da hakan.." Kasa ci gaba tayi da magana dole yasaka tayi shiru, rungume ta Saleema tayi cike da tsananin tausayin ta tace "Kiyi shiru don Allah Sister ki dena kuka kinji? Ni nan zan taimake ki wajen cika burin ki, in Allah ya yarda zaki cika burin ki, zanyi wa Abbana magana zai saka ki aduk makarantar da kike so a faɗin duniya domin cikar burin ki, please ki dena kuka". Shiru Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya, ɗago kanta Saleema tayi tasaka hannu tasoma share mata hawaye. ***** *TWO WEEKS* Khalil ne zaune ƙasar Roll ɗin parlour'n sa, daga shi sai gajeren wando fari da baƙin t.shirt, gaban sa takardu ne masu yawan gaske yake dubawa, gefe kuma Kausar ne kan kujeran da yajingina bayan sa tana ɓare maggi dake cikin Vowel A ɗan wannan lokacin sosai suka shaƙu da juna kullum Kausar tana gidan, ita take mishi girki da gyaran gidan, su zauna suyi ta hira kamar wanda suka daɗe da sanin juna, yanzun ma hiran suke yi aciki yasako mata maganar auren sa da zai yi Ɗan kallon ta yayi yana smile yace "kin kusa hutawa dai duk ranan da akace nayi aure, babu ke babu ɗawainiya dani". Tsayar da abinda take yi tayi tana ɗago kanta takalle shi, kana cikin rashin fahimta tace "ban gane ba?" Ɗan taɓe bakin sa yayi yana kawar da kai yace "nan ba da jimawa ba zanyi aure.." Ɗif Kausar tayi gaba ɗaya tadena jin abinda yake cewa, maggin kawai take ɓarewa amma batasan ma takamaiman a halin da take ciki ba, sai da yagama maganar sa kana yajuyo yana kallon ta, ganin kamar tayi nisa a tunani sai yakau da kansa yaci gaba da abinda yake yi Ita kuwa sosai tashiga ruɗu da jin abinda yafaɗa, ba don komi ba sai don ƙaunar da tatsinci kanta dumu-dumu aciki tana yi masa Nocking ɗin da akeyi ne yadawo da ita hankalin ta Khalil yace "Yes Come in". Brr. Tahir ne yashigo ciki da sallama, sauke idanun sa yayi akan su yana bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo cike da tsananin mamaki da al'ajabi, Kausar itama shi take kallo sai dai kawai kallon nasa take yi but tunanin ta yana wani wajen daban, maganar Khalil ne kawai ke mata yawo a tsakar kai "Lafiya katsaya nan? Kashigo mana". Cewar Khalil kenan yana kallon sa Ahankali Brr. Tahir yasoma takowa yana shigowa, sai da ya'iso wajen yazauna saman sofa kana Kausar tamiƙe tsaye da hanzari tana ajiye Vowel ɗin hannun ta asaman Centre table, kallon Khalil tayi fuskarta babu walwala tace "Zan je gida". Shima ɗin kallon ta yake yi cike da mamaki, sai kuma bai iya cewa komi ba in banda gyaɗa mata kai da yayi, ita kuma tajuya tayi hanyan ƙofa dasauri yayinda Brr. Tahir yaraka ta da idanu, sai da tafice kana yamayar da kallon sa ga Khalil yace "Kai Man ina kasamo wannan Babe ɗin? Shin anya ba idanuna bane ke min gizau?" "Kamar ya?" Khalil ɗin yatambaye sa yana ɗago kansa yakalle sa _plz Share🙏🏼_ [11/1/2020, 9:10 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 38* Brr. Tahir yace "abin ne da mamaki mace nake gani agidan ka? Taya hakan zai faru? Meye alaƙan ka da ita?" Gajeran tsaki Khalil yasaki yana kawar da kansa, domin shi a tunanin sa ko wani abun yagani don har ya tsorata shi "Kayi min bayani mana meye alaƙan ka da ita? Kar dai ace.." Wani kallo da Khalil yasakar masa ne yakasa ƙarisa abinda yayi ninya, sai yatsaya kawai yana kallon sa batare da ya ɗauke idanun sa akan sa ba, Khalil kuma juyar da kai yayi yaci gaba da abinda yake yi kana yace "Ba abinda kake tunani bane, maƙociya ta ce". "Maƙociyar ka?" Brr. Tahir yamaimaita maganar kamar be fahimta ba, sai kuma yasaki murmushin gefen baki yana cewa "Kayi min bayani yanda zan gane har yanzu ban fahimce ka ba?" Tsaki Khalil yaja yana hararan sa, nan dai yabashi labari yanda suka haɗu da alaƙan sa da ita dariya Brr. Tahir yakece dashi yana cewa "Cab ɗi.. wai dama ka iya sakewa da mata har haka?" Kallon banza Khalil yayi masa yace "me kaɗauke ni to?" Ɗage hannu Brr. Tahir yayi yace "No babu". "Kafaɗa karta kashe ka, ai nasan duk abinda kake tunani". Shi dai Brr. Tahir dariya kawai yake yi, sai da yagama dariyan sa son ransa Khalil be sake kula sa ba, sannan daga baya yace "Kasan me? na samo maka shawara, me zai hana kawai kakai ma Dad ita a matsayin wacce kake so tunda naga taku tazo ɗaya". Idanun Khalil kamar zai faɗo ƙasa sabida kallon da yake yi masa, Brr. Tahir da yabuɗe baki zai ci gaba da magana Khalil yayi saurin katse sa da cewa "Banso don Allah kadena wannan maganar, ce maka akayi ina son ta? ko ce maka akayi ita tana so na? Babu wani abu da zai haɗa mace da namiji ne sai soyayya? Ni kawai burge Ni take yi ba wani abu ba". "To ai hakan shi ke kawo ƙauna, don me zata burge ka idan har babu ƙauna aciki?" Ɗaure fuska Khalil yayi yakawar da kai don bazai iya biye masa ba, kuma yasan halin Brr. Tahir idan yakama abu to baya jin bari "Uhm Ni kawai shawara nake baka, idan kuma kafison wacce Dad zai baka ai shikenan , ta yiwu ma kaje kaganta batayi maka ba". Shiru dai Khalil yayi be ce komi ba, amma tunanin maganar Brr. Tahir ɗin yake yi da yayi a ƙarshe Brr. Tahir yakatse masa tunanin sa da cewa "katashi kashirya mana mutafi, in kuma ka fasa ne sai nayi tafiyana don ina da abin yi". Miƙe wa Khalil yayi still be ce masa komi ba yanufi ɗakin sa, sai da yayi wanka yashirya cikin wani farin Gezna da yayi masa kyau ainun, yasaka baƙar hula me ƙube tare da baƙin Sandal shoes, babu abinda ke tashi ajikin sa sai sassanyan ƙamshi, car key yaɗauka tare da wayoyin sa yafito parlour, Brr. Tahir kallon sa kawai yake yi ganin yanda yayi masa mugun kyau "Kai Abokina kaga yanda kayi kyau? Ni namiji kenan ina ga mace ta ganka? wannan wanka gaskiya Amarya dole tabiya mu". Tsaki Khalil kawai yaja yanufi ƙofa batare da ya tanka sa ba, shi kuwa Brr. Tahir biyo sa yayi yana ta tsokanar sa yana faman dariya A cikin motan Khalil ɗin suka fita, mintuna ashirin yakaisu gidan Alh. Mustapha, suna yin hon aka buɗe musu Gate don dama gateman ɗin yasan da zuwan su, lokacin da sukayi parcking duk kan su suka fito alokaci ɗaya, Brr. Tahir sai gyara wuyan rigan sa yake yi yana faman doka murmushi sai kace shine aka rako, Khalil kuwa in banda harara da yake aika masa babu abinda yake yi, ahaka akayi musu iso har zuwa Parlour'n Alh. Mustapha inda anan ne aka sauke su, me aiki aka saka takawo musu abin motsa baki, babu abinda suka taɓa sai hira da Brr. Tahir yake jan Khalil dashi, shi kuwa sai latsa wayan sa yake yi ko kula sa be yi ba A ciki kuwa Saleema ce taci uban kwalliya cikin wani tsadadden less me ruwan toka, ɗinkin riga da sket ne da yayi mata kyau matuƙa, tayi ma fuskarta Light makeup Wanda yaƙara fito da tsantsan kyau ɗin ta, dama Saleema ba baya ba wajen kyawu, Halwa na zaune tana kallon ta har tagama shiryawa tayafa gyale fari ƙal me kwalliyan stone, haka ma flat shoes ɗin da tasaka a ƙafafun ta fari ne, murmushi kawai Halwa take zubawa kafin tace "Gaskiya kinyi kyau My sister, anya baza ki zautar da Angon nan naki ba yakasa manta ki?" Washe baki kawai Saleema take yi cike da farin ciki, kana tace "dagaske nayi kyau Sis?" Halwa tace "wlh sosai kinyi kyau Sister, kuma ina da yaƙini dole ki shiga ran sa alokaci guda, don babu wanda zai ganki be yi fatan ki zamo matar sa ba". Dariya Saleema tayi tace "Thank you My Sister, bari inje kar suji Ni shiru tunda nace kizo muje kinƙi". Girgiza kanta Halwa tayi tana murmushi tace "O'o Ni bazan iya zuwa ba, ke dai kawai kije ke kaɗai, idan yasake dawowa watarana sai mu gaisa". "To na tafi, sai na dawo Sis". Daga nan fita tayi ita kuma Halwa kwanciya tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da tunani a ranta, Saleema tana shiga Parlour'n da sallama Brr. Tahir da yatsare ƙofan da idanu ya'amsa mata yana sakin murmushi, a ransa kawai "masha Allah yake faɗa". Don ba ƙarya Abokin nasa ya dace da zaɓi, Saleema kanta a ƙasa ta'iso tazauna kan sofa me facing nasu, sai tagaishe su alokaci ɗaya tana ɗago kai tana kallon su, dai-dai da shima Khalil ya ɗago kai yasauke idanu kanta suka haɗa idanu, sauke kanta ƙasa tayi cike da tsananin kunya tare da zallan farin ciki, shi kuwa taɓe baki kawai yake yi amma yakasa ɗauke idanun sa akanta, Brr. Tahir kuwa cikin murmushi ya'amsa mata tare da tambayan ta "ya take da ƴan gidan?" Amsa mishi tayi, sai Brr. Tahir ɗin yakalli Khalil dake faman ƙare mata kallo, hakan yabashi dariya yayi saurin ƙumshe bakin sa yana cewa "To Abokina ga fa Amarya ta iso, Ni bari in fice in baku space don kutattauna ko?" Sai lokacin Khalil yaɗauke kansa yamayar ga Brr. Tahir, be ce masa komi ba hakan yasaka Brr. Tahir yatashi yafice Shiru ne yabiyo bayan fitan Brr. Tahir, ita Saleema tunani kawai take yi yanda Khalil ɗin yasauya mata sosai fiye da yanda tasan shi, wani irin kyau da kwarjini yasake yi tare da wani irin gogewa yasake ƙiba, kai da gani kasan hutu da kwanciyan hankali tare da kuɗi sun zauna masa, so take yi tasake ɗago kai takalle sa amma ta kasa domin yanda take jin idanun sa masu matuƙar kaifi suna yawo ajikin ta, shi kuwa a nashi fannin zuba mata idanuwa yayi yana ta kallon ta, a haƙiƙanin gaskiya dogon tunani yafaɗa har be san iya adadin mintocin da suka wuce ba, Saleema dai har ta gaji taɗago kanta tana kallon kyakykyawar fuskar sa da yatsare ta da kallo, cikin sanyin murya tace "Ko in Kira Abokin ka ku fara cin abincin ne?" Sai alokacin yaɗan ƙifta idanun sa da alamun yadawo tunanin sa, kallon ta yayi yana ɗan jije leɓe, ba ƙarya ayanda yafahimta yarinyan zatayi sauƙin kai, duk da ba wai tayi masa yanda yake so bane kuma ba wai yaji ta a ransa bane, but ta kwanta masa arai kuma zai iya zama da ita a matsayin matar sa, ajiyan zuciya yasauke kafin yace "Kina lafiya?" Saleema da har tagaji da shirun nasa tasad da kai ƙasa tana wasa da yatsun ta, jin sassanyan muryan sa me daɗi yasaka ta ɗago kai tana kallon sa kana ta'amsa mishi cikin biyayya da son burge shi "Nasan kinsan me yakawo ni nan ɗin don nasan an riga da an miki bayani? Any way ni sunana Brr. Ibrahim Khalil Abdurra'uf, ina fata.." Shiru yayi don be san me zai faɗa ba, ita kuwa kallon sa kawai take yi tana jin yanda muryan sa me tsananin daɗi yake shiga kunnuwan ta, kamar an matse bakin sa sai yace mata "Me kike karanta a School?" Cike da farin ciki ta'amsa masa da "Pharmacy". Gyaɗa kansa yayi sai kuma sai kuma yayi shiru yana ajiyan zuciya, wayan sa yaɗauka kana yaɗago kai yana kallon ta yace "kiyi haƙuri ni ba gwanin iya soyayya bane Thats why ban iya hiran ba". Murmusawa tayi kawai tana sunkuyar da kai, sosai yaburge ta hakan na nufin kenan be taɓa budurwa ba kamar yanda itama bata taɓa yi ba? Duk kallon da take masa bata taɓa tunanin yana da sauƙin kai irin haka ba Brr. Tahir yakira yace masa "yashigo". Babu jimawa kuwa yashigo yana kallon su yana murmushi yace "Har an gama hiran?" Khalil be basa amsa ba sai miƙewa da yayi yana saka wayan sa a aljihu hakan yasa Brr. Tahir cewa "To Amarya mu zamu tafi, sai kuma gani na gaba". "To bakuci komi ba". "No karki damu next time idan muka zo zamuci yanzu muna sauri ne". Gyaɗa kanta tayi tana tashi tsaye, daga nan raka su tayi har wajen motan su kafin suka sake sallama tataho gida. . _More Comments More post._🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ [11/1/2020, 9:23 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 39* *AFTER SEVEN MONTH* A wannan watannin da suka shuɗe abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da haihuwar da Halwa tayi, ta haifi yarinyan ta kyakykyawa me ban sha'awa, sosai yarinyan take kama da ita, sai dai kuma ta ɗakko abubuwa da dama na mahaifin ta wanda idan kakalle ta tabbas zakasan ƴar sa ce, sunan Ummi aka saka mata kamar yanda Saleema tabuƙaci asaka, wato Asma'u suna kiran ta da Husna, duk wani hidima kama daga kan kayan Baby zuwa na uwar Babyn babu abinda Abba be siya musu ba, komi ya wadata su dashi tamkar tana gaban iyayen ta, tun sanda tahaihu kuma Ummi tace "baza ta shayar da yarinyan ba". Don haka da madaran kanti ake shayar da ita, Halwa sosai taji daɗin hakan ko ba komi an ɗauke mata wani nauyi kuma an taimake ta, duk wani hidiman yarinyan Saleema ce me yi, kullum yarinyan tana hannun ta ita take kula da ita, ita take mata komi sai dai wanka da Larai ƴar aikin su take mata, ita kuwa Halwa sai dai taci tasha takwanta hakan yasaka gaba ɗaya tasauya tasake ƙiba tayi kyau gunun sha'awa, dama gashi tana tsaka da jego ne kuma ga hutu da yayi mata yawa Yanzun ma zaune take agaban madubi tana shafa lipstick a ƙananun laɓɓan ta, fuskarta babu wani kwalliya illa powder da tashafa sannan tazizara kwalli cikin idanuwanta, miƙe wa tayi tana gyara zaman rigan ta, doguwar riga ce na atamfa tasaka Milk and Coffee colour, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau duk da kasancewar ta bata da hasken skin, Halwa irin Chocolate Colour ɗin nan ce me ɗan haske, tana da kyau na ban sha'awa da burgewa, idan har zaka ganta to dole sai ka sake kallon ta coz yanayin ta da komi nata yana da kyan kallo, bata da wani tsayi amma tana da ɗan kauri kaɗan tare da sura me kyau da ɗaukan hankalin me kallon ta, duk da kuwa ita ɗin ba ma'abociyar son cin abinci bane, kallo ɗaya idan kayi mata zaka fassara ta da me sanyi don ko a maganarta ne cikin sanyi sosai zakaji muryan ta, sai dai kuma akwai ta da tsiwa sannan tana da surutu matuƙa sai dai idan bata sami wajen yi ba Tana cikin ɗaura ɗankwali Saleema tashigo ɗakin, itama ɗin doguwar riga tasaka iri ɗaya da na Halwa har ɗinkin da komi, Ummi taba da aka ɗinka musu wajen kala bakwai lokacin da Halwan tahaihu, itama ɗin sosai yayi mata kyau kasancewar ta fara ce, murmushi tasakar wa Halwa kana tace "Kinyi kyau Sister". Murmushi Halwa tayi tana kallon ta tace "Thanks". "Ok Ina kayan Husna? Larai ta gama mata wankan za'a shirya ta". "Ban ciro mata ba". Halwa tabata amsa tana saka Room Slippers a ƙafafuwan ta da suka sha lalli ja da baƙi Saleema wajen kayan Husna tanufa tana cewa "but sai da nace miki ki ciro kafin in dawo fa" Ƙarisawa kusa da ita Halwa tayi tana taya ta cirowa tace "I'm sorry Sis, ban gama shiryawa bane shiyasa". "Ok". Fita sukayi gaba ɗayan su bayan sun gama ɗaukan abinda zasu ɗauka, suna fita parlour Halwa zama tayi akan sofa ita kuma Saleema tawuce da kayan ɗakin Larai, can kuma sai gata tafito ɗauke da Husnan a hannu, an shirya ta tsaf-tsaf cikin kayan ta masu kyau, zuwa tayi tazauna gefen Halwa tana cewa "Kinga Babyna yau tayi kyau sosai, har carbing mukayi mata". Halwa kallon yarinyan tayi sai kuma taɗauke kai tana yamutsa fuska kamar yanda tasaba Kallonta Saleema tayi tace "Yauwa Sis idan nayi aure kema zaki dawo gidana ko? Sai mu zauna tare". Murmushi Halwa tayi tace "to sai mu bar Ummi da wane? Kinga ke kin tafi dole zasuyi kewarki". Gyaɗa kai Saleema tayi kana kuma tace "but duk da haka dai zaki riƙa zuwa kina min sati ko fiye da hakan, kinga kuma Ni ban ma iya girki ba idan naje wanene zai min?". Halwa tace "zaki sami House girl ne sai tayi miki". Kwaɓe fuska Saleema tayi tace "no bana son ƴar aiki sai dai muje muriƙa yi tare dake". "To ai nima ban iyaba wlh". Halwa tafaɗa tana dariya Dariya itama Saleema tayi tace "haba dai? Kice duk jirgi ɗaya taɗauko mu?" "Eh mana, ko Mama tasaka Ni bana yi har ma ta saba ta dena cewa inyi, sabida Ni dai gani nake yi tunda bana cin abincin to bazan koya ba". Still dariya Saleema tayi tace "tabb ai kuwa dole mu saka Larai gaba takoya mana". Ummi ce tayi sallama tashigo "Oyoyo Ummi". Cewar Saleema tana miƙe wa ta'isa wajen ta Ummi kuma amsan Husna tayi tana dariya tace "iyeee ga takwarata ga takwara ta". Sannu da zuwa sukayi mata sannan tazauna tana cewa "Abban ku be dawo ba?" Saleema tace "ya dawo ya fita ne". "Ok". Yarinyan tamiƙa wa Saleema sannan taɗau jakan ta, ita kuma Halwa lokacin tadawo ɗauko ma Ummi ruwa tace "Ummi ga ruwa kisha". Murmushi Ummi tayi tace "Yauwa na gode". Har ta juya Ummi tasake cewa "zo riƙe wannan ledan". Halwa amsan ledan tayi tana kallo "Magani ne idan Larai zatayi miki wanka sai ki riƙa Using dashi". Gyaɗa kai Halwa tayi tana komawa tazauna, ita kuma Ummi miƙe wa tayi tanufi ɗakin ta, sai da tashige sannan Saleema tace "Menene acikin ledan?" Kallon ta tayi taɗage kafaɗa alamun bata sani ba, sai kuma tace "ki tambayi Ummi". Ɗan waro idanu Saleema tayi sai kuma tasaki dariya tace "ai bazan iya bane wlh". Harara Halwa tayi mata tace "ashe kin sani kenan kike tambaya?" . **** ***** ***** ****** Wani irin kallo take masa har sanda yadasa aya a maganar sa sannan tabuɗi baƙi cike da baƙin ciki tace "Wlh Nura kabani mamaki domin ban taɓa tunanin haka halinka yake ba, har Ni zaka dubi idanuwana kace kana so na? Idan har baka bar mana ƙofar gida ba wlh zan maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba..' Bata rufe baki ba Nura yace "haba Zainab wai meye laifina anan? me namiki da baza ki so ni ba? Kar ki manta fa wacce kike tunani akanta bata nan don me baza ki bani dama in maye gurbin ta dake ba, wlh ina ƙaunar ki tsakani da Allah.." Cikin wani irin tsawa Zainab takatse shi "Dalla kayi mana shiru, duk wani mutunci da nake gani naka wlh ka ɓarar dashi, bari kaji wlh koda maza sun ƙare a duniya Nura bazan taɓa son ka ba bazan taɓa auren ka ba, har yanzu kallon ka nake yi a matsayin saurayin ƙawata kuma Ni bana cikin maciya amana, and nasan da cewa Halwa baza ta taɓa barin ka ba coz nasan irin ƙaunar da take maka, duk inda take a faɗin duniya tana nan tare da kai aranta, idan ma har wani abu kuka ƙulla domin tabar gidan nan to wlh kun ci amanarta". Wani irin kallo tabuga masa kafin taci gaba da cewa "kasani duk inda Halwa tatafi zata dawo wannan alƙawari ne, anan ne zan tabbatar maka da cewa ita ɗin me ƙaunar ka tsakani da Allah ne ba irin ka ba". Daga haka tajuya tashige gida batare da tabari yasake furta komi ba, shiru Nura yayi yana kallon hanyan da tabi, ya jima anan tsaye kafin yabuɗe kyakykyawar motar sa yashiga yabar wajen, gidan da yasiya wa iyayen sa yanufa, yana zuwa yadanna hon aka buɗe masa Gate yakutsa motan ciki, bayan yayi parcking yafito yashiga cikin gidan, Mama na zaune a parlour tana faman kallon da tasaba, don tunda suka dawo gidan da zama yazame mata jiki kallon, zama yayi akan kujeran da yake Facing ɗin nata, ita kuma kallon sa take yi ganin yanda duk yasauya face ɗin sa kamar wani abu na damun sa, hakan yasaka tatambaye shi da cewa "Lafiya Nura meke damunka ka fita cikin walwala kadawo fuska a turɓune?" Sai alokacin yakalle ta yace "Mama Zainab ce". Numfashi Mama taja don tariga tasan da zancen, sai da taɗan ɗau lokaci tana ci gaba da kallon sa kafin tace "wai ni Nura meyasaka baza ka nemi wata bace sai ita? Taya zaka zauna yarinya tana wulaƙanta ka amma kaƙi kasauya ta? Ni fa dama hankalina be kwanta da ita ba tunda ita ɗin ƙawar Halwa ce ƙut da ƙut, kuma dama abokin ɓarawo ai ɓarawo ne ban ɗauke tsammanin itama halin su ɗaya ba". Cike da rashin jin daɗin kalaman Maman nashi yace "Mama don Allah ki dena aibanta ta, Ni nasan Halin Zainab baza ta taɓa aikata abinda Halwa tayi ba duk da kuwa suna ƙawaye, kuma Ni ita kaɗai nake jin zan iya aura sabida ina matuƙar ƙaunar ta tun ba yanzu ba, kawai ki taya ni da addu'a shine nafi buƙata a wajen ki". Yana ƙarisa maganar nasa yamiƙe yayi hanyan fita, ita kuma Mama tabi shi da kallo har yafice, sai kuma takaɗa kai cike da tausayin ɗan nata a ranta tana masa fatan alkhairi ...... ...... ...... ...... . .. Tun tafiyan Halwa babu daɗewa Nura yazo ma iyayen sa da zancen zai tafi Legos wani kasuwanci acewar sa bazai dogara da aikin gwamnati ba, dama can yana siye da sayarwa ne na kayan gona, yanda yayi musu bayani akan kuɗin da zai iya samowa hakan yasaka basu wani ja maganar ba suka barsa yatafi, to be rufa watanni uku ba yadawo da zunzurutun kuɗi acewar sa sana'ar da yayi ne Allah ya albarkace sa, iyayen sa sunyi murna matuƙa da samuwan ɗan nasu, acikin lokaci ƙanƙani Nura yayi kuɗi ya buɗe shaguna da yawa ya saka masu kula dasu, kuma ya siyan ma iyayen sa gida me kyan gaske suka koma, sannan shima ɗin yasoma ginin sa inda zai yi aure Tun dawowar sa yasoma neman Zainab a matsayin wacce zai aura, amma har yanzu ita Zainab taƙi amincewa dashi, shi kuma yaƙi haƙura da ita sabida mugun son da yake mata. . _To ya za'a kaya?_ _Plz Kar ku manta kuyi_ *Shere* *Vote* *Comments.* [11/1/2020, 9:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` _*NANA FARUK* wannan shafin naki ne ke kaɗai, Allah yabar ƙauna🥰_ . *CHAPTER 40* Turo ƙofan Mom tayi tashigo cikin ɗakin, Nazeefa dake zaune tsakiyan gado ta tanƙwashe ƙafafun ta tana faman tunani taɗago kai tana kallon Mom ɗin, ita kuma ƙarisowa tayi tazauna gefen gadon tana kallon ta tace "Meke damunki Nazeefa?" Nazeefa kallon Mom tayi tace "babu komi Momy". "Ban yarda ba ki faɗa min gaskiya idan da akwai abinda ke damun ki, gaba ɗaya na lura dake tun da daɗewa kina cikin damuwa, kullum cikin tunani kike kuma kinƙi kifaɗa min abinda ke damun ki, bana son in ganki cikin damuwa hakan na damuna coz Ina jinki tamkar ƴata ta cikina ne". Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana jin hawaye na son zubo mata, idan da tana da daman faɗa mata abunda ke damun ta da tuni tadaɗe da sanar mata, sai dai kashhh baza ta taɓa iya faɗa mata gaskiyan abinda ke cin zuciyarta ba Dafa bayanta Mom ɗin tayi tace "ki sanar dani kinji Nazeefa zan miki duk abinda kike buƙata idan har ina da halin yi, bazan taɓa barin hawayen ki yazuba ba zan kasance me share miki hawayen ki". Wani irin sanyi Nazeefa taji acikin ranta tare da wani irin ƙaunar Mom na sake shiga zuciyarta, sai dai baza ta taɓa iya faɗa mata ciwon son ɗanta ne yakamata ba, "to taya?" Hawayen da taji suna son zubo mata ne tayi saurin mayarwa tana ɗago kai takalli Mom cikin sanyin murya tace "Momy babu abinda ke damuna, idan har akwai kece ta farko da zan faɗa miki sabida na ɗauke ki tamkar ke kika zuƙuna kika haife ni, ki yarda dani Momy babu abinda ke damuna". Shiru Mom tayi tana kallon ta, sai dai ko kaɗan bata yarda babu abinda ke damun ta ba bcoz ko wanene yaga halin da take ciki dole yatabbatar wa kansa tana cikin tsananin damuwa, sosai take mamakin abinda ke damunta har takasa bayyana mata, amma kuma tayi wa kanta alƙawari sai ta gano ko me ke damun ta kuma sai ta share mata hawaye da iznin Allah, ajiyan zuciya tasauke kafin tace "To shikenan na yarda dake, amma duk abinda ke damun ki kiyi gaggawar sanar dani ki dena ɓoyewa kinji?" Gyaɗa kanta Nazeefa tayi sai kuma tace "insha Allahu Momy". "Ok tashi ki cire kayan makarantan akwai inda zaki raka Ni". Amsa mata tayi tana tashi tare da saukowa daga kan gadon, itama Mom tashi tayi tafice a ɗakin, sauya kayan ta tayi tasanya doguwar rigan abaya Blue Black, sannan sai tayi Rolling da ɗankwalin abayan, komai bata shafa a fuskarta ba illa flat shoes da tasanya a ƙafafuwan ta, sosai tayi kyau white skin ɗin ta sai sheƙi yake yi kasancewar ta samu hutu har wani ƙiba tayi tare da ƙara girma, fita tayi ta'iske Mom a parlour suka fice, motar Mom ɗin suka hau drever yatuƙa su suka bar gidan. A wani ɗan madaidaicin gida Drever yasauke su suka fito suka shiga, matar gidan tana zaune a parlour tatarbe su cikin fara'a tare da kawo musu Drinks, sai da suka ɗan yi hira kafin Mom tace "Yauwa Hajja Turai maganar da muka fara dake a waya ne akan kayayyakin da zaki ɗauko min a London, don haka shiyasa nataho muyi maganar sosai sai ki faɗa min da yaushe zaki tafi?" Cikin fara'a Hajja Turai tace "ai ina da kaya a ƙasa gaskiya ba yanzu zan koma ba, inaga sai nan da One Month, yanzu abinda yakamata dai sai kiyi min list ɗin komi kibani hakan zai fi, bari in ɗauko miki Littafi". Miƙe wa tayi tashige ɗaki babu jimawa tadawo riƙe da Littafin tamiƙa mata, Mom amsa tayi tana cewa "Yauwa sannan kuma zan baki saƙon ƴata ga tanan, itama ɗin kizaɓo mata kayan fitan biki masu matuƙar kyau, acikin gwala-gwalan da zaki siyo min sai ki ɗaukar mata ɗaya, Ni dai ina son ki gwangwaje ta sosai komi yakasance Expensive ne nata". Dariya Hajja Turai tayi tana kallon Nazeefa tace "ai babu matsala Hajiya Hajara duk abinda kikeso hakan za'a yi, amma ko itace Amaryan don naga kina ji da ita?" Mom tace "a'a ƙanwar sa ce ai". "Allah Sarki". Cewar Hajja Turai still tana kallon Nazeefa Mom tace "don Allah Hajja kaya masu kyau nake so sabida kinsan bikin Autana ne that's why nazo wajen ki, and sai kuma Furnitures ɗina don Ina son nasauya komi na ɗakina". "Baki da matsala insha Allahu duk abinda kikeso zan yi ƙoƙarin naga na samo miki dai-dai da zaɓinki". Ita kuwa Nazeefa da tun sanda tazauna tasad da kai ƙasa tana sauraron su, wani irin ƙunci take ji a maƙogaron ta, ji take yi tamkar tabuɗe baki tayi ta zunduma ihu sabida tsaban baƙin ciki, har hawaye sai da tai ta sharewa batare da sun kula da ita ba suna ta tattaunawa, bayan Mom ta gama yin mata list ɗin gaba ɗaya sannan sukayi sallama suka fito, har wajen mota Hajja Turai tarako su sai da taga fitarsu kafin takoma cikin gida Suna cikin motan Khalil yakira Mom, bayan tayi peacking call ɗin suka gaisa take cewa "Ɗazu ka kira bana ji ne matsalan network ne, yanzu kuma muna kan hanya ne naje gidan Hajiya Turai". Khalil da be san ma wacece Hajiya Turan ba sai tambayan ta da yayi "me taje yi?" Nan take faɗa masa sannan taƙara da cewa "wai kuwa kana kiran surukar tawa don nasan Halin ka?" Shiru yayi don be san amsan da zai bata ba, shi idan har basu suke masa maganar bikin ba sam mantawa yake yi zai yi aure, kuma ita yarinyan tun sanda yabar ƙasar yamanta irin ta, ko za'a tsare sa da bindiga yafaɗa yanda take bazai iya ba, abinda yasani kawai fara ce ita but kamannin ta ya daɗe da gushe masa, sunan ta ma kanshi be riƙe ba duk da su Mom wani lokacin suna faɗar sunan idan suna waya "Kayi shiru ko dai dagaske ba ka kiran ta?' "Ina kiran ta mana Mom". Yafaɗa cike da sanyin murya don shi sai yanzu yasan be kyauta ba tunda ko Phone numbern ta be amsa ba Daga nan sallama suka yi Mom ta'ajiye wayan cikin jaka, kallon Nazeefa da tatakure a jikin motan tayi idanuwanta a rufe ruf, numfashi kawai Mom taja tana ɗauke kai. . *** *** *** *** *** *** Da hannu biyu tazuba tagumi tana tunani har batasan sanda Mami tashigo tatsaya a kanta ba, sai da tagama ƙare mata kallo kafin takira sunan ta Firgigit Kausar tayi tana ɗago kai takalli Mamin nata "Wai ke lafiyan ki lau kike yawan tunani meke damun ki ne?" Shafo fuskarta da hannun ta tayi cikin sanyin murya tace "babu komi". "Baza ki faɗa min ba kenan?". "Mami babu komi fa tunanin aiki ne kawai". Gyaɗa kai kawai Mami tayi kafin tace "to ki tashi kije Sharif na parlour yana jiran ki". Kausar kallon Mamin tayi fuska babu walwala tace "Mami kice masa bana nan Ni bazan iya fita ba". "Wai ke kanki ɗaya kuwa? Wai meyasaka yanzu bakison fita ne idan yazo? Ko faɗa kukayi ne?" Kausar tace "a'a kema Mami kinsan Da da yanzu ba ɗaya bane, bana son takura ne kawai". Baki Mami tabuɗe tana kallon Kausar, ita kanta da take Mahaifiyar ta tasan Kausar ta sauya, gaba ɗaya ta dena walwala agidan, sai tashige ɗaki ita kaɗai tazauna su rasa me take yi cikin ɗakin, kuma duk uzurin da zata kawo be da wani kan gado, ajiyan zuciya tasauke kafin tace "Ki fito ki same sa yana parlour yana jiran ki". Daga haka tajuya tafice batare da tajira ta bakinta ba Ita kuwa Kausar ba'a son ranta ba tamiƙe tafito, yana zaune a parlour'n shi kaɗai, gaban sa duk an cika masa da kayan motsa baki amma be taɓa komi ba, shi kansa idan kakalle sa baya cikin hayyacin sa duk ya rame yasaka damuwa a ransa sakamakon sauyawan da Kausar tayi masa, kuma hakan sosai ke barazanan tarwatsa rayuwan sa sabida ba ƙaramin so yake mata ba, kullum ji yake yi ƙaunar ta na sake hauhawa acikin ransa memakon raguwa, ya rigada ya saka ta acan cikin zuciyarsa wanda rabuwa da ita zai mishi matuƙar wahala kuma zai taɓa masa rayuwan sa Tunda tafito yake kallon ta har taƙariso tazauna akan kujeran dake Facing nasa, cikin sanyin murya batare da ta kalle sa ba tace "Barka da zuwa". Murmushi yasaki yace "yauwa gimbiyata kina lafiya?" "Lafiya lau". "Kwana biyu ina ta kiran wayan ki akashe na kasa haƙura dole nayi tunanin zuwa yau, shin meke faruwa ne Baby?". Sai alokacin taɗan kalle sa kana taɗauke kai tace "kashe wa nayi". Shiru kawai yayi yana kallon ta, sai kuma daga baya yace "wai Kausar ko dai kin samu wani ne kikeson min wulaƙanci?" Sosai taɗago kanta a wannan karon tana kallon sa, shima ɗin ita yake kallo cike da tuhuma, sun jima suna kallon juna batare da ta sami amsar da zata bashi ba kafin taɗauke kai tare da haɗiyan yamu "Kinyi shiru ina son insan abun da yasaka kikeson juya min baya Kausar, don Allah ki sanar dani idan wani laifi nayi miki wlh nayi alƙawari zan nemi yafiyar ki". Sai kuma yayi shiru yana saukowa kan kujeran yayi Neeldown agaban ta yana ci gaba da cewa "Idan ma kina so in duƙa a gaban ki ne to gani na duƙa don Allah ki yafe min, wlh Kausar ina matuƙar ƙaunar ki bazan iya rabuwa dake ba, dan Allah ki taimaki rayuwata ki faɗa min laifin da nayi miki in nemi gafarar ki". Yaƙarike maganar nasa da rawan murya Kausar kallon sa kawai take yi don batasan sanda yazuƙuna ba, take taji hawaye sun cika mata idanu sabida tausayin sa, tasan da cewa tana ƙaunar Sharif matuƙa amma yanzu shigowar Khalil rayuwan ta tarasa soyayyan sa a zuciyarta, tayi iya ƙoƙarin ta don taga tayi yaƙi da abinda ke damun ta amma ina ta kasa, ta kasa dawo da ƙaunar da take masa aranta, burin ta yanzu kawai tazama mallakin Khalil, amma tarasa ta wani hanya ne hakan zai faru, tasan da cewa yanzu Khalil yayi mata nisa nisan da baza ta iya samun sa ba tunda yana shirin aure Wani irin kuka yataho mata batasan sanda tasake sa ba, jikin Sharif har yana rawa wajen matsowa kusa da ita yana tambayan abinda ke faruwa da ita, gaba ɗaya ya shiga damuwa ya rasa yanda zai yi, ita kuwa kukan take yi tana toshe bakinta da hannayen ta, sosai take tausayin kanta don batasan halin da zata shiga ba nan gaba "Dan girman Allah kiyi shiru Kausar, kiyi shiru ki faɗa min abinda ke damun ki, wlh idan har Ni ne baki ƙauna yanzu zan barki, zanyi nesa da rauyuwan ki idan har hakan zai saka ki farin ciki, bana son kukan ki". Still kallon sa take yi da idanuwanta da sukayi jazur tana ci gaba da kukan ta, daƙyar ta'iya buɗe baki tace "Bakayi min komi ba Sharif kuma babu abinda ke damuna, idan har ka shirya aurena to katuro". Tana faɗan haka tatashi da gudu tayi ɗakin ta, tana zuwa tafaɗa kan gado tana sakin wani kukan da ƙarfi Ta san da cewa hakan shine kaɗai mafita agare ta, ta hakan ne kaɗai zata sami salama tamanta shi cikin rayuwanta, hakan zai sa tayi nesa dashi gaba ɗaya. _ ****_ A cikin kwana biyu Sharif har ya turo magabatar sa, kuma komi ya kammala har an saka rana nan da wata biyar masu zuwa, SAI MUCE ALLAH YAKAIMU LAFIYA MUSHA BIKI😅 . _Plz karku manta da comments da Vote_ [11/7/2020, 2:21 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 41* *FIVE MONTHS AGO* Yau ake saka ran dawowar Brr. Ibarahim Khalil, don haka Mom tashirya tarban Autan nata, Sameer da matar sa tare da ƙanwar ta Abida duk sun zo gidan su ma tarban sa, su suka taya Mom girki tare da gyare-gyaren gida, anyi soye-soye anyi duk abinda yadace sannan ne lokacin driver yatafi ɗauko sa a airport don ƙarfe 02:00pm. Jirgin su zai sauka, drever na tafiya shima Brr. Tahir yazo da nashi iyalin matar sa Suhaila da ɗan su ɗaya Adam. Bakin Nazeefa har kunne sabida tsaban farin ciki zataga Yayan nata kuma mafi soyuwa a ranta, da ita ake aikin komi don ko kaɗan babu wanda yakula da yanda tasaki jiki take ta fara'a kamar bakin ta zai tsake becouse su ma ɗin cikin su kowa tashi murnan ya ishe sa. Lokacin da jirgin yai landing *BRR. IBRAHIM KHALIL* yana ɗaya daga cikin waɗanda suke sauko wa ta matattaƙalan jirgin, Ni dai gaskiya bangane sa ba sai dai bansani ba Fans ɗinsa ko ku zaku gane sa, don dagaske ya sauya sosai fiye da yanda nasan shi, gold skin ɗin sa yayi wani irin haske sosai sai ɗaukan ido yake yi, hutu da kwanciyar hankali kawai nake hangowa a tattare dashi da alamun dai ƙasar tayi mugun amsar sa don ba ƙarya ya sauya ɗin, sai zuba murmushi yake yi abinda ba kasafai kake gani a face ɗin sa ba Har sanda ya'amso trolly ɗin sa yafito haraban airport ɗin sannan ne drever yahange shi yataho dasauri yazo wajen sa yana miƙo masa gaisuwa, amsa masa yayi cike da fara'a sannan suka shiga mota sukayo gida, bazan iya fasalta muku yanda Familyn suka nuna farin cikin su ba, bayan an gaigaisa ya huta sosai sannan aka wuce dainning, anan kowa yaci abinda yakeso tukun suka dawo parlour, hira aka dasa ana ta dariya, wlh idan kukaga Khalil baza kuce shine ba domin har dashi ake ta wasa da dariya, kai sai ince har da ɗabi'u aka sauyo masa acan ɗin, Nazeefa da Abida kuwa babu abinda suke yi sai kallon sa ko wacce zuciyarta na mafarkin yakasance nata na har abada, don har alokacin Abida taƙi tacire sa aran ta duk da kuwa Hakima sai da tagargaɗe ta tamanta dashi baza ta taɓa samun sa ba coz yanzu aure zai yi, kuma itama taso ƴar uwan nata ta aure shi har mitan maganar tarinƙa ma Sameer but basu samu nasara ba. Su Brr. Tahir suka soma tafiya sannan Khalil shima yayi musu sallama drever yanufi gida dashi, lokacin da suka isa layin su motoci yai ta gani duk sun cika layin, sai da suka matso gab gidan sa sannan ne yafahimci agidan su Kausar ake taron, ga jama'a nan burjik awaje maza da mata kowa na sha'anin gaban sa da alamu dai biki ake yi, mamaki sosai ne a fuskarsa sai dai be iya furta komi ba har Drever yayi hon agidan sa aka buɗe musu Gate motan tashige, bayan drever yayi parcking Khalil yafito lokacin duk ma'aikatan gidan sa sunyo wajen suna miƙa masa gaisuwa, haka yai ta amsa musu cikin sakin fuska sannan ne yanufi cikin gida Sale na biye dashi da trolly ɗin sa Cikin gidan an gyara masa ko ina kuma yasan duk aikin Sale ne hakan ya faranta masa rai sosai, anan parlour yaba ma Sale umarnin ya'ajiye Jakan sannan yafice, shi kuma yaja trolly ɗin yanufi ɗakin sa, yana shiga yasaki hannun trolly ɗin yazauna gefen gadon sa, ya ɗan yi wajen mintuna 5 kafin yatashi yacire kayan sa yashiga wanka, yayi kusan mintuna talatin kafin yafito yashirya cikin farar t.shit da gajeren wando fari da ɗige-ɗigen ja, zuwa yayi yazauna kan kujera yasoma latsa wayan sa, kusan mintuna goma yaɗauka sannan yasoma laluban numban Kausar yadanna mata kira Lokacin Kausar na zaune a ɗakin ta tare da ƙawayen ta an gama mata kwalliya, kasancewar yamma tayi har motocin ɗaukan amarya sun zo, becouse acan garin Daura zasu zauna tunda anan ne Sharif ɗin yake aikin sa, duk da dama nan ne tushen sa amma iyayen sa anan Katsina suke zaune Tsananin firgita Kausar tayi da ganin wanda yake kiran ta har batasan sanda takusa sulmiyar da wayan ƙasa ba, sai wata ƙawarta dake kusa da ita ne tayi saurin taro wayan tana cewa "Kee Kausar Ina hankalin ki yaje zaki saki waya ƙasa?" Kausar da tayi mutuwar zaune sabida mamaki, ƙyafta idanun ta tayi da suka cicciko da hawaye tana bin wayan da kallo, ƙawarta me suna Rumaisa tamiƙo mata wayan da aka sake kira akaro na biyu tace "Riƙe gashi an sake kira". Ahankali tasaka hannu ta'amsa wayan sai dai takasa anwer call ɗin, ko kaɗan bata taɓa tunanin ganin kiran sa a wannan lokacin ba duk da tasan cewa lokacin dawowan sa yayi, tun sanda yatafi basu taɓa waya dashi ba wannan dalilin ne yasaka tashiga ruɗu da bugawar zuciya Shi kuma a fannin Khalil tunda yatafi ya nemi layin ta sama da biyar duk sanda zai kira ta wayanta sweech off, daga ƙarshe shine yadena kiran ta gaba ɗaya don a tunanin sa ko akwai matsala ne, ita kuma kullum da tunanin kiran nasa take kwana dashi kuma take tashi, koda yaushe tana jiran taga kiran sa amma har tsawon wannan lokacin babu shi babu labarin sa kuma gashi ita bata da numaban sa na can Batasan tana zub da hawaye ba sai da Rumaisa tadafa ta tana cewa "Wai lafiyan ki ƙalau kuwa? Kuka fa kike yi Kausar?" Sai alokacin tadawo hankalin ta tana kallon Rumaisa da tabi ta da kallo cike da tsananin mamakin ta, lokacin gaba ɗaya hankalin ƴan matan har ya dawo kan su, dasauri Kausar tatashi batare da ta furta komi ba tashige Toilet tana rufo ƙofa, hakan yasaka duk suka bi ƙofan da kallo suna tunanin abinda ke faruwa da ita Tana shiga kiran yasake katsewa, sai ga wani kiran don shi Khalil ya kasa haƙura da kiran nata, sai da tajingina da bango kafin ta'amsa kiran tana sakawa a kunne, cikin ƙasa da murya tace "Hello". Daga can ɓangaren Khalil kuwa shima jingina bayansa yayi da kujera cikin cool voice ɗin sa me daɗi yace "Hello Friend". Kausar danne duk abinda ke cikin ranta tayi cikin ƙarfin hali tace "dama ashe zaka iya mantawa dani?" Ɗan shafo sajen sa yayi yace "Kausar kiyi haƙuri nasan ban kyauta miki ba, amma kuma nayi ta neman Phone Numban ki bana samun ki". Hannun ta taɗago tana kallon fingers ɗin ta da suka sha jan lalli, cikin son maida kukan da yataho mata tare da ɗaura jarumta a muryan ta tace "Na gane Barrister, ya hanya to?" "Alhmadulillah.. da fatan kema kina lafiya?" Murmushi taƙirƙiro dai-dai lokacin da hawaye suka sauka kan kuncin ta tace "sai alheri friend". Khalil shima cikin murmushin yace da ita "Allah ko?" "Ƙwarai". Tataɗa tana dariya ahankali "To bani nasha". Sai da taja numfashi kafin tace "Allah yayi an ɗaura aurena yau". Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Khalil yace "haba dai serious fa?" Kausar tace "I'm serious.." Sai kuma taɗan saki murmushi me sauti tace "kaga na rigaka ko?" "Sosai don ban yi tunanin hakan ba, sau da dama kina bani labari kuma ban taɓa jin kinyi min maganar samarin ki ba, ashe ashe.." Sai kuma yai dariya yana cewa "to Allah yatabbatar da alheri gaskiya naji daɗin wannan maganan". Shiru kawai Kausar tayi bata amsa ba, hakan ya tabbatar mata da cewa tabbas bata cikin zuciyarsa, ita kaɗai take kiɗan ta kuma take rawan ta Murmusawa shi kuma yayi yace "Amarya kenan bari in barki haka ko? don nasan yanzu kina busy". Share hawayen ta tayi cikin rawan murya tace "to". Daga haka bata iya furta komi ba don idan tasake faɗan kalma ɗaya zata iya fashewa da kuka Nocking ƙofan da akayi yasaka tayi saurin juyowa tana kallon ƙofan, sai kuma tamaida idanunta kan wayan lokacin ne Khalil yadatse kiran, lumshe idanuwan ta tayi tana jin wani ƙunci da baƙin ciki na mamaye ilahirin zuciyarta "Kausar wai me kike yi aciki? ki buɗe mana". Maganar Rumaisa yadawo da ita cikin hayyacin ta, dasauri tasanya hannu tashare sauran hawayen ta tanufi ƙofan tabuɗe, duk bin ta suka yi da kallo har da ƙanwar Mamanta da tashigo yanzu, ita kuma sai tasad da kai ƙasa don bata son su fahimci wani abun Ƙanwar Maman nata ne tace "wai me kuke jira ne, ku fito motoci sun rigada sun iso". Juyawa tayi tafita tana cewa "su hanzarta". Kausar sai da tasha nasiha wajen ƴan uwa kafin aka fito da ita, a lokacin sai kuka take yi, Ni dai bansan ko na menene ba ni dai naga an saka ta a mota sun fice, to sai muce Allah yasanya alkhairi *KAUSAR.* ....... ....... . .. .... Khalil kuwa tunda suka gama wayan ya'ajiye yalumshe idanun sa yana tunani, yaji babu daɗi yanda suka rabu sabida shaƙuwan da sukayi, be taɓa tunanin baza su sake haɗuwa ba idan yadawo, ya so ba yau bane auren ta ko shima yahalacci auren nata, amma gashi har anyi an gama batare da yaje mata ba, hakan yaƙara saka shi rashin jindaɗi Allah Sarki haka shaƙuwa yake dama, a ranan kuwa haka yawuni shiru duk bashi da walwala, har yayi sallan magriba da isha'i yadawo gida komi be ci ba yakwanta, ya daɗe yana tunani kafin barci ɓarawo yaɗauke shi. . **** **** ***** ***** A cikin kwana biyu da dawowar Khalil sai gashi ya samu kira agidan gwamnati, koda yaje meeting akayi dashi, sun tattauna na wajen awanni kafin su gama, daga ƙarshe dai an ɗauke shi aiki a matsayin Lauyan gidan Gwamnati, ga albashi me tsoka da zai riƙa samu, duk da dama can sosai Khalil yake samun kuɗi don zan iya cewa ko mahaifin sa be fi sa kuɗi ba, sai dai shi Lauya ne me zaman kansa haƙƙin talakawa kaɗai yake ƙwatowa, Duk wani mara galihu idan har yaje gare sa shi kuma zai share masa kuka, asannu-asannu sunan sa yayi shura sosai talakawa sun soma sanin sa, gaba ɗaya gidajen talabijin da rediyo, jaridu duk maganar sa yanzu ake yi, acikin lokaci ƙalilan Allah ya ɗaukaka shi fiye da Da, kuma duk saboda ƙarin girman da yasamu ne yanzu da kuma ɗaukan sa aiki da akayi agidan gwamnati, sanin da talakawa sukai mishi yanzu har sun soma kawo masa Cases kala-kala, shi kuma don yashare musu kuka haka yake faɗi-tashi wajen taimaka musu da ƙarfinsa da kuɗin sa. _dama akace dare ɗaya Allah kan ɗaukaki bawa fiye da tunanin me tunani, yanzu sunan Brr. Khalil ya zagaye duk faɗin garin Katsina da kewaye sabida ƙwazon sa, sosai ake ji dashi. October 2020. [11/7/2020, 2:40 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 42* An tsai da ranan auren Brr. Kahlil da Saleema nan da Four Month, zuwa lokacin tarigada ta rubuta Final Exams ɗin ta, asannu-asannu rayuwa taci gaba da tafiya cikin nasarori da akasin sa, wasu tazo musu da daɗi wasu kuma tazo musu a yanayin da babu daɗi, ga dai shi Saleema a wannan lokacin sosai ciwon ta yatashi kullum cikin nema mata magani ake yi, wani lokacin adace wani lokacin kuma rashin sa, ga kai ya ɗau zafi karatun su ya zo ƙarshe haka take lallaɓawa take zuwa School sai dai ba kullum ba, duk ta rame sosai take jin jiki. A fannin Khalil kuwa yanzu yana da Numban ta kuma yana kiran ta akai-akai yatambayi jikin ta tunda yasan bata da lafiya, kusan sau biyu yana zuwa gidan, shima yanzu aiyuka sun yi masa yawa baya zama sosai kullum cikin aiki yake, ahaka Allah yasa biki yaƙarato ko wani fanni tuni sun soma shiri ana hidima kala da iri, amma ta fannin Amarya babu lafiya har yanzu sai dai ba kamar da ba don yanzu jikin da sauƙi Ummi tare tahaɗa su da Halwa ake musu gyaran jiki, itama yanzu Halwa ta soma shirye-shiryen zana WAEC da zatayi. Yau ta kasance saura sati ɗaya biki kuma a yau ne Halwa zata soma zana jarabawan ta, haka tatsallake tatafi bada son ranta ba don ko kaɗan bataji daɗin yanda za'ayi bikin Saleema ita kuma tana Exams ba, sai idan taje tadawo ne ake Hidiman biki da ita. Fannin su Mom yanda suka ɗau bikin nan da girma zai baka mamaki, komi cikin wadata da nuna su ɗin masu kuɗi ne don tun ana saura sati biyu ake shagulgula agidan, idan kashiga cikin gidan ko matsuguni baza ka samu ba tun kafin ma bikin yazo kenan, ƴan uwa da abokan arziƙi duk sun cika gidan. Nazeefa kuwa damuwan da tasaka aranta har bacci bata iya yi ishashshe hakan yahaifar mata da ciwon kai me tsanani tare da zazzaɓi, duk shagulgulan da ake yi tana ɗaki taƙule taƙi fita ayi da ita, sosai take jin jiki har sai da Sameer yakaita asibiti aka dubata, koda suka dawo Mom tayi ta kula da ita tana bata drugs duk ta tashi hankalin ta, gaba ɗaya ko lokacin kanta bata dashi ga jinyan Nazeefa ga hidiman mutane, wannan yasaka taba Nazeefa tausayi sosai hakan yasa tadaure taɓoye duk abinda ke damunta tayi kamar ta samu sauƙi tana fitowa ana biki da ita, hakan yasa Mom taji daɗi har hankalin ta yakwanta. Fannin Ango kuwa baya zama yanzu sabida Case ɗin da yake gudanarwa a Court, shiyasa duk wani shagulgula bashi ciki, sai idan ya sami kansa ko zuwa dare ne yake zuwa gidan su. ..... ...... ...... ...... .... Gidan su Amarya su ma ba laifi ana ta shagulgula duk da babu wani armashi Amarya tana kwance babu lafiya, wannan dalilin ne ma yasa basu shirya komi ba in banda taron bikin kawai da za'a gudanar Duk abunda ake ma Amarya anyi wa Saleema, an mata lalli an mata gyaran jiki komi an mata, sosai tayi kyau tafito a Amaryan ta duk da kuwa zallan raman da tayi Sai ana gobe biki ita Halwa akayi mata nata Lallin sabida ranan bata da Exams, kuma a ranan akayi musu gyaran kai ita da Saleema, komi har gida ake zuwa ayi musu basu zuwa ko ina. *** **** **** **** **** Washe gari ya kasance Saturday aka shaida ɗaurin auren *BARRISTER IBRAHIM KHALIL ABDURRA'UF* tare da Amaryan sa *SALEEMA MUSTAPHA* Ana gama ɗaurin auren ango da abokanan sa suka tafi Hotel inda zasuyi ƙwarya-ƙwaryan liyafan da suka shirya. *GIDAN SU AMARYA* Amarya tasha kyau cikin shigan ta na Material Less me ruwan Hoda da ratsin ash colour, ɗinkin riga da sket da suka ɗauki jikinta sosai, ba'ayi mata kwalliya ba don taƙi yarda shiyasa ba'a matsa mata ba tana zaune akan gado ta ɗaura Husna ajikin ta da take ta faman wasa da kayan Saleeman, sosai yarinyan tasake girma ga wayau sosai, idan kaganta baza kace watanni tara da haihuwar ta ba Cikin ɗakin akwai friends ɗin ta na school su wajen biyar, sai hira suke yi suna shewa, wasu kuma suna mata tsiya "gwara tawarke don dole akaita yau ɗin" Ita kuwa ɓata fuska tayi sai sake marairaice face ɗin ta take yi, kallo ɗaya idan kayi mata zakasan ta faɗa ainun hakan yasa tasake haske sosai, bata kula su ba sai dai bin su da ido da take yi Ana haka Halwa taturo ƙofa tashigo, dawowarta kenan daga Exams da taje tarubuta, fuskarta yalwace da murmushi take kallon Saleema da itama tasanya mata idanu tana ƙara ƙwaɓe fuska kamar zatayi kuka, takowa tayi tashigo ciki tana gaisawa da ƙawayen Saleeman sannan tanemi wuri tazauna gefen Saleema tana sake yalwata fuskarta da murmushi, sosai take farin ciki a yau ɗin tana taya ƴar uwan nata murna Hannu tasaka tadafa kafaɗun Saleema bakin ta yaƙi rufuwa, sai kuma tamaida hannun kan kumatun ta taja tana cewa "Haba ƴar uwa ya haka kin ɓata fuska? Don Allah ki saki ranki kiyi farin ciki yau ranan ki ne, ko so kike Angon yayi tunanin bakya son sa ne? Kinga hakan zai jawo masa matsala akasa gane kansa". Hakan yasa Saleema tasaki dariya babu shiri saboda maganar Halwa ɗin, ita kuwa Halwa kallon ta take yi tana murmusawa cike da jindaɗi, sai kuma tamaida kallon ta kan Husna tana haɗe rai tace "Waye kuma yakawo wannan yarinyan nan?" Itama Saleema kallon Husnan tayi da tatsare su da idanu ta saka hannu ɗaya cikin baki tana ɓashe bakin kamar tana jin su "Kawo ta in kaita wajen Larai, yau fa ranan ki ne be kamata kizauna kina raino ba, banda abinki ma ke da baki da lafiya?" Ture hannun ta Saleema tayi tana hararan ta tace "to Ni nace akawo ta ina ruwan ki?" "Haba Sister don Allah yau rana ɗaya kibarta wajen Larai". Cewar Halwa tana sake kai hannu zata ɗauke ta Sake ture hannun Halwan tayi tarungume ta da kyau tana cewa "Ni fa nace akawo min ita, wlh babu inda zata don tana nan wajena har mu tafi". Waro idanu Halwa tayi tana cewa "wai da ita kike nufin zaki tafi?" "Eh mana.. da dake zan tafi?" Sai ƴan ɗakin dake kallon su suka kwashe dariya Zaliha tace "kai wani lokacin Saleema bata da hankali al'ƙur'an tana jinta kamar sokuwa ne". Sai suka sake ɓarke wa da dariya, ita kuma tabi su da harara tana cewa "Ni ce bani da hankali ko?" "Ai da gaskiyar Zaliha idan ba sokuwa bace ke taya ma zaki tafi da yarinyan nan? Ai mijin ma sai yakoro ki". Cewar Dija Babbar ƙawarta tana sake kecewa da dariya Halwa murmushi tayi tace "Sister wlh kuwa maganar su gaskiya ne, kema kinsan Ummi baza ta barki ki tafi da ita ba gwara ki sauya shawara". Shiru kawai Saleema tayi bata sake cewa komi ba Cikin lallami Halwa tasake cewa "kinga koda nan da sati ɗaya ne sai in kawo miki ita idan ma wai tafiyar da ita zakiyi". Saleema tace "sati ɗaya ai yayi yawa, sai dai idan zakiyi min alƙawari gobe". Gyaɗa mata kai kawai Halwa tayi don ba wai ta yarda zata kai mata ɗin ba, daga nan hira sukaci gaba dayi, sai da Saleema tace ma Halwa taje tashirya sannan tamiƙe tashiga wanka. ***** Da ƙarfe 08:00pm. Akazo ɗaukan Amarya, tasha kuka sosai haka taƙanƙame Ummi taƙi tafiya, daƙyar aka samu aka shiga da ita mota Halwa tazauna kusa da ita tana rarrashin ta A gidan sa aka kaita, sosai gidan yaɗau hankalin duk wanda yashigo, kamar ba gidan da akayi amfani dashi ba komi an sauya sai ƙamshin sabunta yake yi Ɗakin ta kusa dana Khalil aka shigar da ita, haka mutane sukai ta zagayawa suna ganin abun arziƙi har da Halwa a zuwa gani, anan sukayi sallan isha'i suna ta hayaniya kamar zasu tsaga gidan Wajen ƙarfe 10:00pm. Abokan ango suka zo tafiya dasu, lokacin ne itama Halwa takira Drever'n gidan su A wayan da Abba yasiya mata don yazo yaɗauke ta, ko kaɗan bata son bin abokan Angon sabida yanda wani yamaƙale mata ɗazu da suka zo daga ta buge sa bata sani ba, ita ta ma rasa uban wa yace musu ita ɗin Sister ɗin Amarya ce, yanzu da suka shigo parlour'n sai faman kiran ta suke yi, komi akayi sai suce "ina Sister ɗin Amarya tazo tayi musu sheda" daga ƙarshe ma tashi tayi tashiga ciki tazauna kusa da Saleema dake zaune saman gado Har Drever yazo basu tafi ba, sannan ne ma suka soma haraman tafiya, anan ne fa Saleema tariƙe Halwa tana kuka wai baza ta tafi ba, in banda dariya babu abinda su Dija suke mata sai faman tsokanarta suke yi, daƙyar dai tasaki Halwa suka tafi suka barta ita kaɗai kamar Mayya. . _Nace ko ina Mijin Oho?_🤔😅 [11/7/2020, 3:02 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 43* Ƙarfe 10:30pm. Su Khalil da Brr. Tahir tare da Sameer suka shigo gidan, daƙyar ma Khalil yayarda suka biyo shi don da yace "baya son rakiyan". Shi da kan sa yashiga har ɗakin ta yace "tafito parlour" daga haka yajuya yafita, ita kuma tamiƙe jiki a sanyaye tagyara mayafinta tafito, ahankali taƙarisa tazauna aƙasa tana gaishe su, cike da fara'a suka amsa sannan ne Sameer yasoma musu wa'azi cikin raha, daga ƙarshe suka yi musu fatan alkhairi tare da sanya alkhairi a auren nasu Har bakin Gate Khalil yaraka su da zasu tafi, yadawo yatarda Saleema tana nan zaune inda take, be ce komi ba yanufi ɗakin sa, yana shiga yasoma cire babban rigan dake jikin sa bayan ya cire Hulan kansa, agogon hannun sa yacire tare da cire links ɗin rigan sa yazube su yanufi parlour Har yanzu tana nan zaune inda take, zama yayi kan kujera yana kallon ta, sai kuma yaɗauke kai yana kallon ledan da suka shigo dashi, miƙewa yayi yanufi kichen sai gashi ya dawo da plate a hannu tare da wuƙa, zama yayi a ƙasa kamar yanda itama take zaune a ƙasan, yajawo ledan yabuɗe yaciro Kazan ciki yasoma yanka wa cikin plate ɗin don yayi daɗin ci, bayan ya gama duk yajera mata a gabanta da su Holandia sannan yakalle ta yace "buɗe fuskar ki kici". Ahankali tayaye gyalen daga kanta taɗago tana kallon sa sai kuma takalli abinda ke gabanta, cike da tsananin kunya tanoƙe ko motsi ta kasa yi, ganin haka yaja baya yana ɗaukan wayan sa yasoma latsawa yana cewa "Ki ɗauka kici nace". Wannan karon batayi musu ba ganin ya matsa can baya kuma hankalin sa baya kanta, hakan yasa tasoma ɗauka tana ci duk da dama tana jin yunwa amma baza ta iya buɗe ciki taci ba, kaɗan taci tacire hannun ta cikin sanyin murya tace "Na gama". Ɗago kai yayi yakalli plate ɗin sannan yasake maida kansa kan waya yace "ki ƙara". Hannu tasaka taci gaba taci, bata daɗe ba tasake tsame hannun ta, wannan karon da yaɗago kai miƙewa yayi yaɗau komi yanufi kichen dashi, yana dawowa yace tataso su je ɗaki, miƙewa tayi tabi bayan sa, suna shiga yanuna mata Toilet tashiga tawanke hannu da bakinta tafito, yasake nuna mata kan gadon.. ta ko haye can lungu taƙudundune da gyalen ta Shi kuwa Toilet yashiga yayi wanka yafito yashirya cikin kaya sannan yahayo kan gadon yakwanta, shiru sukayi ko wanne yana jin numfashin juna, can kamar amafarki tatsinkayi muryan sa "Ya jikin naki?" Cike da jindaɗi ta'amsa masa ganin yanda yadamu da ita sosai, daga haka basu sake yin magana ba har sanda Khalil yaji numfashin ta na fita da ƙarfi hakan yagane tayi barci, juyowa yayi setting ta duk da baya kallon fuskarta hakan be hana yaƙure ta da idanuwansa ba, shiru yayi yana tunani yana bin ta da kallo, abinda be taɓa faruwa dashi ba yau sai gashi zai kwana da mace Ya daɗe ahaka yana ta saƙe-saƙe kafin yasauke ajiyan zuciya yamiƙe yakashe fitila yadawo yakwanta, addu'a yayi yarufe idanun sa, lokaci ƙanƙani barci yaɗauke sa kasancewar baya samun hutu. Washe gari shi yasoma tashi bayan da suka koma barcin asuba, wanka yayi yashirya yasaka Milk colour ɗin Gezna da yayi masa kyau matuƙa gaya, duk da bashi da aiki ya ɗauki hutu amma Shari'an da yake yi be rigada ya ƙarƙare ba, akwai sauran aiyukan da yake yi a Court, yana cikin saka Wrest watch yaji Nocking ƙofa, fita yayi yaje yaduba yaga drever'n gidan su ne Mom ta aiko sa da breakfast, amsa yayi kawai yaje ya'ajiye a dainning table yakoma ciki, sai da yayi rubutu a ɗan Pepper ya'ajiye mata saitin kanta sannan yaɗau abubuwan da zai ɗauka yafita. Babu jimawa da fitan sa tafarka, ahankali tabuɗe idanuwan ta yayinda ƙamshin turaren sa suka cika ƙofofin hancin ta, sake lumshe idanun tayi tana murmushi cike da jin daɗi, sai da tajima ahaka bataji motsin sa ba sannan ne tayaye gyalen fuskarta, da takardan da ya'ajiye mata tasoma cin karo, take gaban ta yafaɗi babu shiri tayi saurin kai hannu taɗauka tana jujjuya shi, sai kuma tamiƙe zaune idanun ta har yanzu akan takardan, buɗewa tayi sai taci karo da . _"Aslm alaikum Ni na fita zuwa wani waje bazan jima ba zan dawo, and akwai breakfast a dainning Mom ta kawo..."_ _Mijin ki✍️_ Batasan sanda murmushi yasuɓuce mata ba, kalman Mijinki shi ke ta mata yawo a ƙwaƙwalwa, gaskiya Brr. Daban ne da sauran Mazaje, duk da kuwa ta tabbatar ba son ta yake yi ba amma kuma kulawan sa agare ta da tausayin ta ya wuce tunanin me tunani, yana da halin ƙwarai sosai, memakon yanuna mata tsangwama a'a sai yana sauke haƙƙinta akansa, wannan shi ake kira adalin namiji, tayi imani koda baya son ta zata zauna dashi ahaka domin tasan shine ɗorewar farin cikin ta na har abada "Allah yabarmu tare". Tafaɗa a maƙoshi tana sake faɗaɗa fara'an ta Miƙewa tayi tasauko kan gadon tanufi ɗakin ta, Toilet tashige tawanke bakin ta tafito parlour tanufi dainning, tana jin yunwa sosai don haka baza ta iya jira har sai tagama abinda take yi ba gudun lafiyan ta, zama tayi tahaɗa tea me kauri tasha tare da ƙwai da Arish, bayan ta gama tatashi tashige ɗaki taɗauko Maganin ta cikin kayan ta taɗiba tafito tasami ruwa tasha dashi, sai kuma takoma ɗakin Khalil ɗin tasoma gyarawa musamman kan gadon da sukayi amfani dashi, duk da ita ba ma'abociya aiki bane komi yin musu ake yi, ba'a barin ta tayi komi amma aɗan kwanakin da zatayi aure sai da duk takoya abinda zai bata wahala, don bata son me aiki cikin gidan ta tana da kishi sosai Bayan ta gama takoma ɗakin ta tayi wanka tashirya cikin farar shadda wanda tare akayi musu da Khalil ɗin, shi kuma yarigada ya saka nashi jiya, ta fito ɗas Amaryan ta sai zabga ƙamshi take yi, kallo ɗaya idan kayi mata zakaga ƙyallin amarci atattare da ita (aure ba wasa ba🤫) Parlour takoma tazauna a lumsassun kujerun ta masu tsantsan kyau da burgewa, wayanta dake hannun ta talatsa takira Ummi, ringing biyu taɗauka "Ummina I miss You so much". Tafaɗa cike da zumuɗi Daga can Ummi murmushi tayi na jindaɗi tace "me too My dear, har kin tashi?" "Eh Ummi kuna lafiya? Ya Daddy da Halwa?" Cikin dariya Ummi ta'amsa mata tana cewa "ai ga Halwan ma anan". "To Ummi bata mu gaisa". Miƙa mata wayan tayi suka gaisa cike da kewan juna sannan tamaida ma Ummi nan ma sukaci gaba da hira, daga baya kuma tabuƙaci akawo mata Husna, Ummi tayi ta rarrashinta akan tabari zuwa nan da sati biyu amma sam Saleema taƙi yarda ita lallai sai an kawo mata Husna yau "Haba ɗiyata ki kwantar da hankalin ki, ki bari zuwa gobe insha Allahu zan sa akawo miki ita, kinga yau su Gwaggon ki zasu zo zasu kai ki gidan iyayen mijin naki to wa zaki bar ma wa? Ki bari gobe sai akawo miki ita kinji". "To Ummi amma kar yawuce gobe". Tafaɗa a shagwaɓe". Daga nan sallama sukayi, tana nan zaune tana tunanin mijin nata sai murmushi take yi, sai da tagaji don kanta ga barci da tasoma ji hakan yasaka takwanta a 3sitter tana rufe idanun ta, babu jimawa barci yaɗauke ta Can tasoma jin hayaniyan baƙinta tare da bugun ƙofa, babu shiri tatashi tana riƙe kanta dake faman sara mata, daƙyar take tafiya sabida yanda take jin wani zazzaɓi-zazzaɓi na son kawo mata cafka, tana buɗe ƙofan suka shigo nan tatare su da fara'a, duk ƴan uwan Abbanta ne dana Ummin ta su wajen biyar Su suka sakata tashirya cikin wata Farar atamfa anyi mata Flower da kalan ja da baƙi, sosai atamfan tayi mata mugun kyau kasancewar ta fara, ga ɗinkin da yaɗauki jikin ta sosai na riga da zani, Hijab tasaka fari da takalmi ,sannan suka fito sukayo waje, a motoci biyu suka bar gidan. ***** Tarba me kyau Mom tayi musu cike da farin ciki sai nan nan take da Saleema, hakan sosai yafaranta ran Ƴan uwanta har basuyi fargaban danƙa mata amanar ƴar su ba, ita kuma Mom ta'amshe ta hannu bibbiyu Basu jima ba sukace zasu tafi duk da Mom tayi musu tayin abinci amma sukaƙi ci illa ruwa da suka sha, haka suka tafi suka bar Saleema anan, sauran dangin Mom da basu rigada sun tafi ba sai shigowa ɗakin Mom suke yi suna ganin amarya, bayan sun tafi yarage daga Mom sai Saleeman, duk da Saleema tasaba da Mom abaya hakan be sa taƙi nuna kunyan ta ba, Mom kuwa sai janta da hira take yi cike da ƙaunar ta, daga ƙarshe dai da taga taƙi sakin jiki da ita sai tatashi tana cewa "Tunda kinƙi sakin jiki dani bari in Kira miki Nazeefa tataya ki hira tunda Ni fita zanyi". Saleema dai batace komi ba har Mom ɗin tafice. Nazeefa tana kwance akan gadon ta duk abin duniya yabi ya ishe ta, tun sanda aka soma hayaniyan zuwan Amarya tana jin su amma takasa fita, sosai take jin baƙin ciki da kishi aranta sai dai tadage tana ta ƙoƙarin hana kanta kuka, shigowar Mom cikin ɗakin yasa tatashi tana ma Mom ɗin sannu "Yauwa Nazeefa bakije kinga Amarya ba ga ta can an kawo ta?". Murmushi Nazeefa tayi tasauke kai ƙasa tace "Mom banji bane barci ya soma ɗauka na". "To tashi kije wajen ta tana nan aɗaki sai ki tayata zama ko". Batayi musu ba tatashi sai dai bada son ranta ba tafito tanufi ɗakin Mom ɗin, ita kuma Mom tanufi wajen Dangin ta Sallama tayi tatura ƙofan tashiga, Saleema dake zaune saman gado ta'amsa mata tana ɗan jan Hijabin ta baya da tarufe idanun ta dashi, kallon kallo sukai ma juna ko wacce da tunanin dake ranta Ita Nazeefa tana kallon Amaryan Yayan nata ne cike da jin haushi duk da kuwa ta burge ta don kyakkyawa ce sosai wacce kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa ba ƙaramar ƴar jindaɗi da hutu bane, coz ko kaɗan ma batayi yanayi da ƴar talakawa ba Ita kuma Saleema tana mata kallon rashin sani ne don tasan dai ba ƴar gidan bace, sai dai ko ƴar uwan shi ne duk da babu wani kama da sukayi Zama tayi akan kujeran dake ɗakin tana ci gaba da kallon Saleeman sannan taƙaƙalo murmushi tace "sannu Amaryan mu, kinzo lafiya?" Murmushi itama Saleema tayi ta'amsa mata cike da sakin fuska kasancewar ta me yawan fara'a ga kowa Daga haka shiru ne yabiyo baya dan Nazeefa batasan me zatace mata ba saboda ita ba me yawan surutu bane, itama kuma Saleeman bata sake furta komi ba tayi shiru tana sad da kanta ƙasa, ahaka har Mom tashigo da wasu baƙi tatarar dasu haka, baƙin sun zo ganin Amarya ne, haka Saleema tagaishe su cike da kunya su kuma suna ta yaba mata suna sanya alkhairi, hakan ba ƙaramin sake ƙular da Nazeefa yayi ba har takasa jurewa tatashi tasulale ɗaki batare da sanin Mom ba koda Mom suka tashi fita bata kula ba haka suka fita ɗakin aka bar Saleema ita kaɗai tana ta zaune, daga ƙarshe kwanciya tayi sabida yanda take jin zazzaɓin jikin ta yana ƙara yawa, lokaci ƙanƙani ciwo yarufe ta ga sanyi da take ji sosai, haka ta ƙudundune jikinta sai faman maƙyarƙyata take yi Ahaka Mom tashigo taganta, hankalin ta idan yayi dubu ya tashi nan tasoma neman wayan ta, sai tatuna tabar wayan a palrour, fita tayi dasauri babu jimawa sai gata ta dawo tare da wasu mata su biyu, su ma duk hankalin su ya tashi ganin yanda jikin Saleeman yai zafi zauuu Mom Kiran Khalil tayi tabashi umarnin yai maza-maza yazo matar sa tana gidan ta babu lafiya. [11/7/2020, 3:33 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 44* Lokacin da Khalil yazo har su Mom sun fito da ita parlour, babu ɓata lokaci yariƙe ta suka fito waje inda motan sa yake, Mom tace mishi "yakai ta asibiti" amma ita Saleeman tace "tana da maganin ta a agida" don haka gida kawai yanufa Suna zuwa yayi parcking yafito yabuɗe mata motan yariƙo ta tafito, duk da a halin ciwo take amma sosai taji daɗin kusancin sa gare ta, har wani sanyi take ji aranta tana jin kamar ciwon na son tafiya Tana jingine da jikin sa har suka isa parlour yataimaka mata tazauna sannan yakalle ta cike da tausayi yace "Ina kika ajiye maganin in ɗauko miki?" Cikin muryan marasa lafiya tace "yana cikin trolly na Wanda nazo dashi daga gida". Gyaɗa kai kawai yayi yanufi ɗakin nata, yana shiga yasoma wurwurga idanu, can yahangi akwatunan da yayi mata guda shida, sai yamaida idanun sa kan wani babba kalan sa daban, yana da tabbacin shine wanda take nufi Wajen yanufa yabuɗe, duk abubuwan amfanin ta ne da tazo dashi daga gida, yana soma bincika wa yaga ledan maganin, ɗauka yayi yanufi parlour'n Zama yayi gefen ta yabuɗe tare da nuna mata alamun tayi masa bayani, nuna masa waɗanda zata sha ɗin tayi yaciro yamiƙa mata sannan yatashi yaje yaɗauko ruwa a Fridge yabata Har tagama sha yana ta kallon ta kamar wanda zai haɗiye ta, hakan yasa taji kunya tana sad da kanta ƙasa, be san sanda yasaki guntun murmushi ba yamiƙe tsaye yanufi kichen ita kuma tabi bayan sa da kallo cike da tsananin ƙaunarsa a ranta Be wani jima ba yadawo riƙe da Cup a hannun sa, miƙa mata yayi yana tsaye a kanta, ita kuma tasaka hannu ta'amsa tana kallon abinda ke ciki, Tea ne yahaɗo mata, be ce mata komi ba sai dai kallon ta da yake yi har tashanye tatashi da ninyan kai Cup ɗin "No kawo cup ɗin, je ki kwanta idan an kira sallah zan tashe ki". Babu musu tanufi ɗakin ta tashige, shi kuma bayan ya kai Cup ɗin kichen yadawo yanufi ɗakin sa, ɗakin karatun sa yashige (Library) yasoma binciken abinda yakawo sa, har aka kira sallan azahar yatashi yagabatar yakoma yaci gaba da aikin sa, yana tune da Saleema sai dai yaƙi tashin ta ne saboda bata daɗe ba aka kira sallan, don haka yabari zuwa sallan Asar yatashe ta Sai da aka kira sallah yafito yashiga Toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yana warware hannun rigan sa da yanannaɗe wajen yin alwalan, yafito daga ɗakin nasa yashiga ɗakin Saleema, yana shiga ya'isa bakin gadon yatsaya yana kallon ta, barcin ta take yi cikin kwanciyan hankali, sai dai yanda take fitar da numfashi da ƙarfi hakan zai sa kagane ba lafiya ba Ya daɗe atsaye a wajen yana kallon ta cike da tsananin tausayin ta, yasan da cewa tana fama da ciwo tunda lokacin gab da za'ayi auren su Abbanta yakira sa musamman don su tattauna matsalan Saleeman, anan yake faɗa masa komi kuma yaɗaura da roƙon sa akan don Allah yariƙe masa ƴa bisa amana Ajiyan zuciya yasauke kana yasaka zara-zaran hannun sa me yalwataccen gashi a kwance yasoma tadata, pilon yake ɗan ja ahankali yanda zata iya tashi, kasancewar bata da nauyin barci hakan yasa yana soma taɓa wa tabuɗe idanunta da sukayi ja alamun barcin yayi nisa sosai, suna haɗa idanu tayi saurin yunƙurin tashi amma yanda jikinta be da ƙarfi dole takoma takwanta tana sake rufe idanunta "Ya jikin naki?" Yafaɗa ahankali cike da kulawa kuma har alokacin idanun sa na yawo a jikinta Bata buɗe idanun ta ba tace "da sauƙi". Gyaɗa kansa yayi kafin yace "ki tashi kiyi sallah". Daga haka yajuya yafita batare da yajira me zatace ba Sai da tatabbatar ya fita kafin tabuɗe idanun nata cike da kasala tatashi zaune tana riƙe kanta, babu ƙarfi ko kaɗan ajikin ta ga kuma kanta dake faman ciwo baya ga haka babu komi yanzu dake damun ta, waigawa tayi taɗauki wayan ta dake kan drowan Gadon taduba lokaci, zaro ido tayi tana kallon wayan cike da mamaki, batayi tunanin har tayi barci me nisa haka ba tunda har gashi ƙarfe 04:07pm. Ajiye wayan tayi tazuro ƙafafuwan ta ƙasa tasauko, Toilet tanufa taɗauro alwala tafito tasanya Hijab ta tada sallah, azahar da la'asar tayi sannan tacire Hijabin ta'ajiye, wanka tashiga tayi don tasami ƙarfin jikin ta, tana fitowa tashirya cikin jan atamfa me ratsin baƙi da fari, ɗinkin riga da skert ne wanda yayi mata kyau sosai sai zuba ƙamshi take yi, ɗankwali kawai taɗaura tafito Parlour Yana zaune saman kujera yana latsa wayan sa, ƙamshin turaren ta yasa shi ɗago kai yana kallon ta, sosai yake bin ta da idanu sabida tayi masa kyau ainun Ita kuwa bata kula dashi ba sai faman gyara zaman ɗankwalin ta take yi da be gama zama da kyau ba, sai da ta'iso cikin parlour'n kafin taɗago kanta su haɗa idanu, yanda yake kallon ta ne yasa ta jin kamar tajuya takoma amma babu hali dole ta'iso tazauna can kujeran da ke gefen sa, hakan yasa babu yanda za'ayi yaganta dole sai idan ya juya kansa Ɗan lumshe idanun sa yayi yabuɗe yaci gaba da latsa wayan sa, amma yanda turaren ta ke shiga masa ƙofofin hanci hakan yasa duk yarasa tunanin sa, sosai turaren yayi masa daɗi, sai lumshe idanu yake yi yana buɗewa, daga ƙarshe yaɗago kai yana kallonta yace "Kin sha maganin ki?" Ita da taɗan buga tagumi tana tunani nan taji saukar muryan sa a kunnen ta, tayi saurin ɗagowa tana kallon sa kafin tace "a'a sai anjima ne lokacin sha". Be ce komi ba yakau da kansa yaci gaba da latsa wayan, dama chatting yake yi da Brr. Tahir, ganin dai turaren duk ya ishe sa da ƙamshi hakan yasa yatashi yanufi ƙofa yafice Tabi bayan sa da kallo tana tunanin inda zai je Yana fita Garden ɗin gidan yanufa yazauna kan fararen kujerun dake wajen, lumshe kyawawan idanun sa yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, hannu yasaka yana dafe setting zuciyar sa tare da faɗa wa duniyar tunani Har yau ya gaza gane meke damun sa, meyasa yake shiga damuwa akan abinda baya tunanin zai sake gani, kullum zuciyar sa ƙulafucin ranan da yakasa mantawa yake yi tare da fatan sake ganin makamancin ta Numfashi yaja tare da fesarwa yana ci gaba da latsa wayan sa, be tashi a wajen ba sai da yaji kiran sallah, miƙe wa yayi yasaka wayan sa a aljihu yanufi wajen Me gadi, anan yayi alwala yafita masjid, sai da akayi isha'i kafin yadawo gida Tana nan zaune a parlour'n, sallah kawai taje tayi tadawo tasake zama, sai dai yanzu kallo take yi, yana shigowa ta'amsa masa sallaman sa tare da yin masa "sannu da zuwa" Amsa mata yayi yana kallon ta kafin yanufi ɗakin sa yaɗauko car keey yafito yafice Mintuna goma da fitan sa yadawo riƙe da Ledoji, miƙa mata yayi yace "tasake abincin dake cikin Take-away ɗin a plate" ta'amsa tayi yanda yace sannan tadawo takawo masa, umartan ta yayi tazauna su ci, babu musu tazauna suka ci abincin suka gama sannan tatashi takwashe komi takai kichen, dawowa tayi tazauna taci gaba da kallon ta yayinda shi kuma yana ƙasa har yanzu yana danna waya, babu jimawa kuma yamiƙe yashiga ɗakin sa yaɗauko computer'n sa yadawo yazauna kan kujera yasoma aiki aciki Har barci yakwashe Saleema a wajen yana nan yana aikin sa, sai wajen ƙarfe 11:00pm. Sannan yadakata yana kallon ta, hakan yasaka yamiƙe ba don ya gama aikin ba yatattara kayan sa yamayar ɗaki yadawo yatashe ta yace "su je su kwanta". Bayan shi tabi suka shige ɗakin sa yarufo ƙofa. . ***** ****** ****** **** Yau a makare suka tashi sai ƙarfe 11:30am. Sannan Khalil yasoma farkawa, wanka yayi yafito yana tsane jikinsa, alokacin ne Saleema tafarka itama sai dai taƙi tashi bare tanuna alamun ta farka, har yagama shiryawa yafita parlour yazauna, Kallo yakunna yasaka tashan CCT.V NEWS yana kallon labarai, jefi-jefi kuma yana latsa wayan sa Ƙaramar wayan sa dake ajiye ne tayi ƙara yaɗauka yana karawa a kunne tare da yin sallama Brr. Tahir amsa mishi sallaman yayi yana faɗin "Ango Ango kasha ƙamshi". Murmushi Khalil yayi yana shafo kwantaccen gashin kansa yace "zaka fara ko?" Dariya Brr. Tahir yaƙyalƙyale dashi yana cewa "iyeee Ango uhmm Ango Mijin Amarya.." Katse shi Khalil yayi yana ɗaure fuska "Wai kai meye haka ne kanka ɗaya kuwa?" "Uhmm ai baza ka gane kaina ɗaya ba sai idan nazo ganin Amarya". Cewar Brr. Tahir Yana sake sakin dariya me sauti Shiru Khalil yayi be sake ce masa komi ba sai yamayar da hankalin sa kan kallon sa "Hello kana jina kuwa?" Guntun tsaki Khalil yaja yana faɗin "ina jinka mana idan ka gama zan kashe wayana". Brr. Tahir murmushi yayi yace "sorry Man akwai magana fa, kasan narigada naga gidan da mutumin nan yake zaune sai dai be bani dama har yanzu mun tattauna ba". Khalil ɗan tattaro naman goshin sa yayi cike da takaici yace "yana son Raina mana wayau ne fa, but bari dai in taho sai mu tattauna don nima na samu ƙwaƙwƙwaran hujjan da dole sai ya saurare mu". "Ok sai ka zo". Daga haka sukayi sallama yaciro wayan daga kunnen sa yana miƙe wa tsaye yakoma ɗakin sa, abubuwan da zai buƙata yaɗauka sannan yanufi wajen gadon sa yana kallon Saleema da har yanzu tana nannaɗe acikin bargo taƙi tashi, yasan da cewa tun ɗazu ba barci take yi ba don haka yamatso gab da ita yaraɗa mata "Ni na fita bazan daɗe ba zan dawo, ki kula da kanki uhmm?" Tun sanda yasoma mata magana tabuɗe idanu tana kallon sa, sai tasaki murmushin da yakufce mata batare da ta shirya yin sa ba tayi saurin gyaɗa masa kai Shima murmushin yayi bece komi ba yajuya yafice tabi bayan sa da kallo. [11/7/2020, 4:01 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuƊahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.``` . *CHAPTER 45* Minti goma da fitan shi kafin tamiƙe tasauko daga gadon, Toilet ɗin sa tashiga tayi wanka tasaka towel ɗin sa tafito tanufi ɗakinta, akan stool tazauna gaban dressing mirror tasoma shafa Lotions a tattausar farar skin ɗinta, shafa Lotions ɗin take yi but hankalin ta baya wajen, sai faman zuba murmushi take yi cike da tsananin nishaɗi da kallo ɗaya kayi mata zaka fahimta, har tagama batasan a wani duniyar take ba, hakan yasa tashafe fiye da awa ɗaya tana abu ɗaya, daga ƙarshe tamiƙe tanufi wajen kayan ta tazaɓo wanda zata saka Jan Material Less me stone ajikin sa, ɗinkin doguwar riga pitted, yayi mata kyau sosai ya kamata cif-cif cike da sha'awa, tayi wannan ɗaurin na ture gaka tsiya sai ƙamshin amarci take zabgawa Fitowa tayi takoma ɗakinsa tagyara tasaka air freshener, har toilet sai da tawanke kafin tafito tazauna aparlour takunna t.v Zaman ta babu daɗewa tajiyo Nocking, miƙewa tayi tanufi ƙofan don tasan ba Khalil bane, tana buɗe ƙofan idanuwan ta suka faɗa cikin na Halwa dake tsaye tana zabga mata murmushi, tana riƙe da Husna da hannu ɗaya rungume ajikinta, ɗayan hannun kuma tana riƙe da ɗan ƙaramin trolly Cike da tsananin murna Saleema tatarbe ta tana rungume ta daga ita har Husnan dake barci Daga ƙarshe shigowa sukayi suka yada zango a parlour'n bayan Saleema ta amshi Husna ta shimfiɗe ta akan kujera "Sister kinga yanda kika sauya kuwa? Sai ƙyallin amarci kike yi sai dai fa kin rame". Cewar Halwa da tazuba mata idanu tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta Itama Saleema dake faman zabga murmushin tace "Hmm Ni dai bana son sharri, duka yaushe nayi auren da zakice ina ƙyallin amarci". "Allah kuwa dagaske my Sister kin sauya sosai, gani nake kamar na shekara ban ganki ba saboda tsaban kyau da kikai min, gaskiya aure rahma ce". Dariya Saleema tayi wannan karon tace "Allah ko ƴar uwa?" Ɗage gira ɗaya Halwa tayi tace "dagaske My Sister". "To kice kema kin kusa motsawa musha biki?" Ɓata fuska Halwa tayi tana sauya zancen da faɗin "ƴar uwa nifa ba zama zanyi ba don tare da drever nake zai kai ni School, ƙarfe 02:30pm nake da Exams, Ina Mijin naki mu gaisa kafin in tafi?" Saleema tace "ya fita yanzu". Murmushi Halwa tayi tana kama haɓa tace "har ya gama cin amarcin ne ya soma fita?" Hararan ta kaɗai Saleema tayi tana wani irin murmushi da bakinta yaƙi rufuwa "To sister zan tafi kinga lokaci ya ja da yawa, akwai saƙon Ummi cikin jakan nan tabani in kawo miki, tace tana gaishe ki tare da Abba ma". Saleema kamar zatayi kuka tace "Allah Sarki ina amsawa nayi kewar su sosai". Dariya Halwa tayi tamiƙe tana faɗin "ko dai zakiyi kuka ne?" Hararan ta tayi itama tatashi tana cewa "Sister ko ruwa baki sha ba fa? Bari in ɗauko miki". Taƙarike maganar tana nufan wajen Fridge batare da tajira cewar Halwan ba, ɗauko ruwan tayi tadawo tana cewa "Sai yaushe kuma sister?" Wulla idanuwan ta tayi alamun tunani tace "uhmm sai dai idan nagama Exams ɗin nan sai in zo inyi miki wuni ko?" Turo baki Saleema tayi kamar zatayi kuka tace "kai sister kenan har sai na jira kin gama Exams zaki sake zuwa?" Murmusawa Halwa tayi tace "ke dai karki damu zuwa gidan ki ai sai kin gaji da ganina, yaushe ma akayi auren ne? Ki kwantar da hankalin ki". Dariya Saleema tayi tace "to shikenan muje in raka ki". Har wajen mota Saleema taraka ta, anan suka gaisa da Drever, Halwan tashiga mota yaja suka bar gidan Sai ɗaga musu hannu take yi har Me gadi yarufe Gate ɗin kafin tasauke hannun ta tajuya cikin gidan cike da kewar ƴar uwan nata Tana shiga parlour'n ta'iske Husna ta farka sai wutsil-wutsil take yi tana son sauko wa, dasauri taƙarisa wajen ta taɗauke ta tana dariya cike da ƙaunar ta tasoma yin mata rawa tana mata wasa "Iyeee Mamana kin tashi? Yau kin dawo wajena ko? Oh i miss You so much". Tamanna mata peck a baki, ita kuma sai faman ɓangale mata bakin take yi tana yarfe hannayen ta tare da tsalle jikin ta Dariya Saleema tayi tana sake riƙe ta dakyau ganin yanda take ta zillewa wai adole tana wasa "My dear ki dena karki suɓuce min kinsan girma ne dake". Ita kuma kamar tana jinta taci gaba da zillewa tana tsallen murna sai ɓangale baki take yi, Allah ya zuba mata wayau gata kuma bata da ƙyuya ko kaɗan, duk wanda yaɗauke ta haka zatai ta ɓangale masa baki kamar tasan shi Tana nan zaune tana ta jijjiga yarinyan tana mata wasa kamar ta sami sa'ar ta sai faman yin mata hira take yi da surutu Khalil yaturo ƙofan yashigo da sallama a bakin sa Ɗago kai tayi tana kallon sa kamar yanda shima ɗin yaƙure su da nashi idanun me tsananin kyawu da kaifi Gaban Saleema ne yafaɗi, sai Lokacin tatuna bata sanar masa da maganar dawowar Husnan ba, daƙyar takawar da fargaban nata tana amsa mishi sallaman Takowa yayi yashigo ciki still idanun sa na kansu, yarinyan kawai yake kallo cike da sha'awa, shi me son yara ne sosai suna matuƙar burge sa Matsowa kusa da ita yayi yana faɗin "wannan yarinyan wacece?" Yaƙarike maganar yana duƙowa gaban ta ya'amshi yarinyan yana sake ƙure ta da idanu, sosai yarinyan tayi masa kama da wacce yasani, lokaci ɗaya kuma yaji ta shiga ran sa har be san sanda yasakar mata kyakkyawar murmushin sa yana wasa da hannun ta ba, itama ɗin sai ɓangale masa baki take yi kamar yanda tasaba tana kallon sa Mai da idanun sa kan Saleema da taduƙar da kanta ƙasa yayi Har alokacin bata iya basa amsar tambayan da yayi mata ba cikin murmushin sa yace "Ya sunan ta?" Cike da sanyin murya tace "Husna". Kallon yarinyan yasake yi sai kuma yamiƙe tsaye yana zama kan kujera ya'ajiye ta a cinyan sa yaci gaba da mata wasa Ita dai Saleema na zaune tana jin su tare da satan kallon su, sosai taji daɗin yanda yanuna son yarinyan duk da kuwa be san ita wacece ba "Ina Maman ta ne?" Yajeho mata tambayar yana kallon ta Cike da fargaba Saleema tace "tana gida". Ɗan waro idanun sa yayi cike da mamaki yace "kenan kawo miki ita akayi?" "Eh zata zauna a wajena ne". Kallon ta kawai yake yi cike da tsantsan mamaki, be kai ga magana ba yahangi ɗan kyakykyawar Trolly ɗin dake ajiye gefe "Kayi haƙuri don Allah nasa an kawo min ita ban tambaye ka ba, wlh na manta ne". Tayi maganar cikin ladabi da sanyin murya Still kallon ta yasake yi sai kuma yamaida idanun sa kan yarinyan Shiru kamar bazai yi magana ba sai kuma yace "yanzu har kin warke da zaki iya raino?" Murmusawa tayi bata iya cewa komi ba sai ɗauke ganin ta da tayi daga kansa Ajiyan zuciya kawai yasauke be sake cewa komi ba kuma be bata yarinyan ba, aransa kuma tunani yake yi yanda ita Saleeman take son yara har da zata ɗauko yaran mutane da sunan riƙe wa, sai kuma tsananin mamakin uwar yarinyan da ta'iya rabuwa da ƙaramar yarinya kamar wannan, yana son yayi mata tambayan ya zatayi idan zata shayar da ita amma kunya ya hana sa tambayan ta, baya ga haka akwai tarin tambayoyi da yake son yin mata Saleema ganin shirun dai yayi yawa sai tamiƙe taja Trolly ɗin tanufi ɗakin ta. . ***** ***** ******* **** *BAYAN SATI BIYU* A cikin wannan kwanakin shaƙuwa ne sosai yashiga tsakanin Khalil da Saleema, sun yi kwanakin ne cikin nuna kulawan junan su tare da girmama juna Duk wani kulawa Khalil yana nuna mata tare da tausayin ta me tsanani da yake yi cikin ransa, baza ka taɓa tunanin su ɗin ba masoya bane domin yanda suke gudanar da zamantakewar su ko masoyan asali albarka A yanzu soyayyar Khalil sosai yaginu a zuciyar Saleema, tasan da cewa tayi dace ga miji na gari don Khalil ɗan halak ne kuma ya haifu Shi kuma har alokacin ya kasa jin soyayyar ta cikin ransa, sai dai yasan yayi dace da mata na gari kuma yana ji aransa zai iya zama da ita har ƙarshen rayuwan sa batare da yayi dana sani ba Zan iya cewa tare suke rainon Husna sabida yanda Khalil ke nuna kulawan sa agare ta, idan har yana gida ko baya aikin komi yarinyan ko yaushe tana hannun sa, sosai yarinyan tashiga cikin ransa. Jikin Saleema alhmadulillah yanzu ta warke sumul babu abinda ke damunta, tattalin mijinta kawai tasaka agaba sai kuma rainon Husna. ******* Yau ce ranan da Halwa tace zata zo don haka da sassafe Saleema tatashi cikin ɗoki tasoma aiyukan ta, babu laifi yanzu ta saba da duk wani hidiman gidan duk da ba wani aiki me yawa take yi ba Shi kansa Khalil yasan da zuwan Maman Husna don tun jiya da sukai ta waya da Halwa yaga tana ɗoki yatambaye ta take faɗa masa Mamar Husna ce zatazo Shirin Office yayi cikin Ash colour ɗin Suit da yayi masa kyau matuƙa yawuce wajen aiki bayan yayi musu solfie su ukun cike da nishaɗi. Har tagama abinci da duk abinda yakamata kafin Halwa ta'iso. _Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen BOOK ONE sai ku tara a BOOK TWO don jin me zai faru._ . _ya zaman Khalil da Saleema sai kaya, kuna ganin tausayin da yake mata zai iya juye wa yazama ƙauna?_ _Shin kuna ganin Halwa zata cika burin ta?_ _me zai faru idan ta mayar da Husna ga Mahaifin ta?_ _ya Maganar Haris da be san yana da ƴa ba?_ _kuna ganin Zainab zata amince da soyayyar Nura?_ _Ya maganar Nazeefa da takamu da soyayyan wanda be san ma tana yi ba?_ _kuna ganin idan har Mom tagane zata aura mata shi kamar yanda tayi alƙawarin gano meke damunta kuma tashare mata hawaye?_ _Shin kuna ganin Halwa zata koma ga Iyayen ta?_ _Shin ya za su karɓe ta?_ _duk a Two ne zaku samu amsar tambayan ku da dalilin da Nura yajuya wa Halwa baya?._ _sai ku biyo NI don ji amsoshin ku_ _Nafisat Jikar Lawal ce_✍️ Ba_byeee 👋👋👋👋👋👋👋👋😉🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ [11/9/2020, 9:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 _WhatsApp Number 07065334256_ *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ ````Allah ya dawo dani mu tsunduma cikin labarin Na gode masoyana.``` *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER One* ________🎓Suna zaune su Biyu akan dainning table suna cin abinci Halwa kai abincin bakin ta tayi tana lumshe idanun ta cike da jindaɗi, sai kuma tabuɗe idanun taɗaura akan Saleema da itama tamayar da hankali wajen cin abincin ta, murmushi me sauti Halwa tasaki still tana kallon ta tace "Sister gaskiya abincin nan kamar zai tsinke min kunnuwa, kina gani fa har rawa suke yi sabida tsaban daɗin abincin nan". Dariya Saleema tasaki tana kallon Halwa da taƙara ɗibo wani abincin takai bakin ta tana faman lumshe idanu "Bari dai in tashi in ɗauko pilow in tare ki dashi, idan ba haka ba babu me iya tare ki nan gaba in kikaci gaba da wannan santin". "Allah Sister ba santi bane, kinji yanda abincin yake da matuƙar daɗi ne sai kace wacce tadaɗe da ƙwarewa, wlh ko Ni bazan iya rin wannan ba". Murmushi Saleema tayi cike da jindaɗi sai dai bata iya cewa komi ba "Ƙara min miyan". Halwa tace hakan tana miƙo mata plate ɗin shinkafan Zuba mata miyan tayi tana faɗin "Kinsan jiya da Zazzaɓi Husna ta kwana, wlh duk na ruɗe sabida yanda naga tana yi, da ba don Yaya Barrister ba bansan yanda zan yi ba, shi yatashi yayi ta rarrashin ta har yana cewa in koma in kwanta". Taƙarishe maganar nata tana wani irin murmushi me ma'anoni da yawa wanda Ni kaina bangane mata ba Shiru Halwa tayi bata ce komi ba illa kai abinci bakin ta da take yi Ɗago kanta Saleema tayi takalli Halwan sai kuma tamayar da kanta kan abincin tana sake yin murmushi Tasan da cewa baza ta taɓa tankawa ba, halin ko in kula shi Halwa ke nuna wa Husna, tunda tahaife ta ko ɗaukan ta idan ba ya zama dole bane to ko kallo bata ishe ta ba, baza ka taɓa tunanin itace uwarta ba Basu sake magana ba har sanda suka gama cin abincin suka koma parlour, Hira suka ɓarke dashi cike da nishaɗi, sai da aka kira sallah kafin Saleema tashige ɗaki don yin Sallah, ita kuma Halwa tadasa Kallo kasancewar bata sallah Khalil ne yaturo ƙofan da sallama a bakin sa hakan yasa Halwa ɗago idanuwan ta tasauke acikin nashi idanun wanda yayi dai-dai da yankewar gaban su a lokaci ɗaya Kallon kallo suke ma juna cike da wani irin yanayi me wuyan fassara Khalil sandarewa yayi a tsaye a wajen kakkaifan idanun sa akanta, ganin abun yake yi tamkar a mafarki yau yarinyan da tahana zuciyarsa sukuni tsawon lokaci itace agaban sa a kuma cikin gidan sa, kullum cikin tunanin ta a barci kuma mafarkin ta Janye idanunta Halwa tayi daga kallon sa, ko kaɗan kuma bata gane sa ba sai dai idanun sa sun mata kama da wanda tataɓa gani Be jirga daga wajen da yake ba illa zuba mata idanuwa kawai yayi kuma ya kasa ɗauke wa Fitowar Saleema daga ɗakin ta tahange sa tsaye ya kafe Halwa da kanta ke ƙasa da kallo, irin kallon da yake mata shi yasaka gabanta yayanke yafaɗi, take taji wani abu ya soke ta a ƙahon zuciya da yasaka tayi saurin ɗaura hannunta a ƙirjin ta tana runtse idanu Halwa da har yanzu take jin idanuwan sa masu tsananin kaifi suna yawo ajikin ta, dai-dai tana ɗago kanta tahangi Saleema tsaye dafe da ƙirji, dasauri tamiƙe tana faɗin "Sis lafiya kuwa?" Buɗe idanuwan ta tayi tana kallon ta sai kuma tamaida ga Khalil da maganar Halwan shima yadawo dashi hayyacin sa, haɗa idanuwan da sukayi yasaka shi sakar mata kyakkyawar murmushin sa yana takowa cikin parlour'n Wannan murmushin da yayi mata shi yasaka taji sanyi aranta, takalli Halwa dake nufo ta a yanzu ɗin taƙirƙiro murmushi tace "Babu komi". "Anya kuwa? Ko dai wani abun ke damun ki?" Halwa tasake tambayar ta cikin damuwa don bata yarda babu komi ɗin ba Still Saleema tana murmushi tariƙo hannun Halwan suka nufi kan kujera tana faɗin "Yaya sannu da zuwa". Idanun sa akan su ya'amsa mata cike da kulawa Zuciyar Halwa har alokacin bugawa yake yi kuma ta rasa dalili, har a time ɗin kuma bata iya ɗago kai ta sake kallon sa ba, zama kawai tayi tana sake mayar da idanun ta kan t.v Cike da son kawar da abinda ke cikin zuciyarsa yayi hanyan ɗakin sa cikin takunsa me burgewa da cikan mazan taka "Yaya baku gaisa da Maman Husna ba". Saleema tafaɗi hakan tana kallon bayan sa Cakk yatsaya zuciyar sa na wani irin bugawa dasauri-dasauri "Ina yini". Cewar Halwa itama da taɗago kanta tana kallon bayan nasa Runtse idanun sa yayi da ƙarfi yana sake danne abun da yake ji, cikin wani irin murya da dole kagane akwai wata matsala ya'amsa mata da "lafiya". Sannan yawuce ciki da sassarfa Basu kawo komi akai ba illa mayar da hankalin su ga juna da sukayi Cikin murmushi Halwa tace "baza ki bi bayan sa bane?" Hararan wasa Saleema tasakar mata tana murmushi da son kawar da abinda take ji cikin zuciyarta, domin kallon da Khalil yayi wa Halwa sosai yatsaya mata arai har tana son dasa zargi cikin zuciyarta, bata iya cewa komi ba sai murmushin da take faman yi Matsowa Halwa tayi taraɗa mata magana a kunne, dariya suka fashe dashi suna tafawa. ____________________ Cike da sanyin jiki yaƙarisa kan gadon sa yazube yana ɗaura kansa akan pilow, sosai zuciyarsa yake faman bugawa kamar zai faso ƙirjin sa ba don komi ba sai maganar da Saleema tafaɗa masa Halwa itace Mamar Husna, numfashi yasoma fesarwa yana son dai-dai ta nutsuwar sa dake son gushe wa, hannun sa yaɗaura akansa yariƙe yana lumshe idanuwan sa sabida jin yana faman sara masa, baya son ko kaɗan zargin sa yazama gaskiya "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Abinda yake ta faman maimaita wa kenan har yasoma jin nutsuwarsa na dawo masa tare da sassaucin bugun zuciyar sa Dantsen hannun sa yaɗaura akan kyakykyawar face ɗin sa yayi shiru kamar ruwa ya cinye sa Har Saleema tashigo be motsa ba Maganar abinci tayi masa amma sai yagirgiza mata kai alaman bazai ci ba Shiru tayi kamar zata yi masa magana sai kuma takasa tajuya tafita Parlour takoma sukaci gaba da hiran su da Halwa, har sanda tajiyo kukan Husna dake barci a ɗakin ta, zuwa tayi taɗauko ta tadawo parlour'n tahaɗa mata abincin ta tasoma bata Khalil har akayi sallan la'asar be tashi daga inda yake shingiɗe ba, abun duniya duk yayi masa yawa, sai daga baya daƙyar yamiƙe yasoma cire kayan jikin sa, zuwa yanzu kuma kansa sosai yake mishi ciwo kamar zai fashe Toilet yashiga yayi wanka yaɗauro alwala yafito, jallabiya yazura yafito parlour'n fuskarsa duk babu walwala, kallo ɗaya yayi musu yaɗauke kansa saboda haɗa idanun da sukayi da Halwa Itama dai sauke kanta ƙasa tayi tana me mamakin kanta da wannan mutumin, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta wanda haɗa idanun da sukayi yahaddasa mata hakan Miƙewa Saleeema tayi da Husna a hannun ta tace "bari inyi sallah sister". "Ok muje nima in shirya tafiya zanyi". Halwan tafaɗa tana tashi tsaye Hararan ta Saleema tayi tace "tun yanzu? Ai ba haka mukayi dake ba". Dariya kawai Halwa tayi tazo tawuce ta tayi gaba Itama tabi bayan ta tana ƙorafi Suna shiga ɗakin Saleema tashimfiɗe Husna da takoma barcin ta, ita tasoma shiga Toilet ɗin taɗauro alwala kafin tafito Halwa tashiga Bata jima ba tafito tazauna akan drowan Gadon taɗau wayan ta tana neman layin Drever, sai dai wayan tasa akashe ne, tsaki taja tamiƙe tanufi kan stool dake gaban mirror tazauna tasoma shafa Powder tana gyara fuskarta Tana nan zaune har Saleema ta'idar da sallan ta tajuyo tana kallon ta tace "Wai don Allah dagaske yanzu zaki tafi? Please ki bari sai dare mana". Murmushi Halwa tayi tana kallonta ta cikin mirror tace "kina son gobe in ƙi zuwa miki kenan?" Girgiza kanta Saleema tayi itama idanun ta akanta, sai kuma tace "amma dagaske zaki zo ɗin gobe?" Cike da son riƙe dariyan ta dake son kufce wa tace "sosai ma sister gobe zan dawo shiyasa zan tafi yau da wuri". Gyaɗa kanta tayi sannan tamiƙe tana cire Hijabin ta tace "to shikenan na yarda ki tafi amma goben ki zo da wuri". Halwa bata iya bata amsa ba saboda dariya da yacika cikin ta sosai ƙiris yarage tasaki dariyan, ɗaga mata kai tayi tana sauke kanta ƙasa tasoma dariyan ta yanda baza ta ganta ba Saleema kuwa kan gado tanufa batare da ta kula da ita ba, sai zayyano mata saƙon gaisuwa da zata kai ma su Ummi da Abba take yi Ɗago da kanta Halwa tayi tajuyo gaba ɗaya tana kallon Saleema cike da murmushin da yabayyana haƙoran ta tace "amma fa na kira drever wayan sa be shiga ba kuma gashi ban fito da kuɗi ba". Saleema tace "to nima ai bani da kuɗi gaskiya, amma bari in duba ko Yaya Barrister ya dawo sai ince yayi ma Drever magana yakai ki". Gyaɗa kanta kawai Halwa tayi Ita kuma tatashi tafita tashiga ɗakin Khalil Yana tsaye ne agaban mirror ya sauya kayan jikin sa zuwa ƙananan kaya, yana fece suman sa da Cumb tashigo Takowa tayi tazo inda yake tana kallon sa cike da ƙauna, sosai yayi mata mugun kyau har ta manta abinda yashigo da ita ta shagala wajen kallon sa Ajiye cumb ɗin yayi yajuyo yana kallon ta, tayi saurin duƙar da kanta cike da kunyan kamata da yayi tana kallon sa Be ce komi ba yamatsa gaban gadon sa yaɗau Wrest watch ɗin sa yana ɗaurawa a tsintsiyan hannun sa "Uhm dama Halwa ce zata tafi gida shine nace ko zakayi ma drever magana yakai ta?". Tayi maganar a hankali tana kallon sa Tsayar da abinda yake yi yayi yana juyowa yakalle ta, ganin sun haɗa idanu sai yagyaɗa mata kansa tare da ci gaba da ɗaure Wrest watch ɗin Murmushi tayi tajuya zata fice, har ta kai bakin ƙofa tajiyo muryan sa "Tafito sai in sauke ta". Kallon sa tayi shi kuma yaɗauke kai yana takawa yanufi wajen takalman sa Cikin sanyin murya ta'amsa mishi sannan tafice. [11/11/2020, 7:49 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Two* ________🎓Da murmushi a face ɗin ta tashigo cikin ɗakin, tana kallon Halwa wacce itama tazuba mata nata idanun tace "Sis ki shirya Yaya Barrister zai kai ki". Halwa wani kallo tayi mata sai dai batace komi ba tamiƙe taɗauki Veil ɗin ta tayi Rolling ɗin sa akanta, sai taɗau HangBag ɗinta tarataya, wayan ta a hannun ta suka fito tare da Saleeman, waje suka fice a tunanin su zasu ganshi sai dai babu shi be fito ba, a compound ɗin gidan suka tsaya suna taɓa hira har sanda sassanyan turaren sa yakawo ma hancin su cafka Saleema kallon kyakykyawar Mijin nata tayi cike da tsananin ƙaunar sa Ita kuwa Halwa tunda tayi masa kallo ɗaya taɗauke kanta Zuwa yayi yawuce su yanufi wajen Farar motan sa yabuɗe yashiga Su ma takowa sukayi har wajen motan, Saleema tabuɗe mata ƙofan tashiga tarufe mata Tana nan tsaye har suka fice a gidan kafin taja numfashi ahankali takoma cikin gidan Shiru cikin motan babu me motsin kirki ahaka sukai ta tafiya Halwa ma duƙar da kanta tayi ƙasa tana faman juya wayan ta Yayinda Khalil yake tuƙi amma hankalin sa gaba ɗaya yana kanta, so yake yi yacire duk wani abu dake cikin ransa a game da ita tunda yasan ita ɗin mallakin wani ne Tafiya suke yi sosai babu me magana cikin su "Ina ne gidan naki?" Tatsinkayi sassanyan muryan sa me tsananin daɗi a kunnen me sauraro, ɗago kai tayi takalle sa kamar me tunani sai kuma taɗauke kanta tana faman maimaita maganar nasa aranta har sanda tafahimta sannan tabashi amsa "Sabon layi". Kallon ta yayi kamar zai yi magana sai kuma yafasa, ya san cewa Sabon Layi ne gidan su Saleema, to amma taya ita zatace masa anan take? Sai kuma yayi tunanin maybe itama a anguwan take aure Be sake magana ba har sanda yashigo cikin anguwan, yana jiran yaji ta nuna masa hanya ko wani gidan but shiru hakan yasaka yaci gaba da tafiya batare da ya sake tambayan ta ba Sai da aka kawo dai-dai gidan su Saleema taga yana shirin wuce wa, takalle sa tace "Nan ne fa". Tsai da motan yayi kafin yayi Rivers yakoma baya yadanna horn me gadi yaleƙo sannan yabuɗe musu, tura hancin motan yayi cikin gidan sannan yayi parcking Tana ganin ya tsaya tabuɗe motan sannan taɗan juyo takalle sa suka haɗa idanu tayi saurin janye nata cike da tsananin faɗuwar gaba "Na gode". Tafaɗa ahankali kafin tafice dasauri tarufe masa ƙofan tatafi Har tashige yana kallon ta cike da mamaki aransa, yana da tarin tambayayo aran sa sai dai be san wanene zai amsa masa ba Yasan da cewa Saleema ita kaɗai iyayen ta suka haifa bare yayi tunanin ƴar uwanta ce, sannan ma basu kama ko kaɗan, sai dai yana tunanin ko dangin ta ne Motan sa yaja yabar gidan yanufi inda zai je. *____________________* Sallama tayi tashigo gidan agajiye Umma ta'amsa mata tana kallon ta Zuwa tayi tazauna akan tabarman da Umman take zaune "Kin dawo?" Gyaɗa mata kanta tayi tana me zame jakan ta kafin tace "sannu da gida Umma". "Yauwa Zainab da alamun dai yau kinsha wahala tunda naga kina langaɓewar nan?" Zainab tace "uhm umma ai ba'a magana, wahala kam akwai ta, ko abinci yau ban iya ci ba tun safen nan wlh lectures yayi zafi". Sake kallon ta dakyau Umma tayi tace "sai kika zauna haka babu abinda kika ci? To ai dama Dole kisha wahala, ki tashi kije ɗakina ki ɗauko abincin ki". Miƙewa Zainab tayi don dama sosai cikin nata yake ƙwaƙulan ta, shiga ɗakin tayi taɗauko abincin tafito tazauna inda tatashi Tana ci suna hira kuma duk na hiran makarantan ne "Ni wlh dama zaki haƙura da karatun nan haka nan abu yaƙi ci yaƙi cinye wa, memakon ki samu miji kiyi aure sai ƙara karatun ma kike yi shi kuma ba me ƙare wa ba". Kumburo fuska Zainab tayi tace "Umma kema kinsan karatu nake so a yanzu, ban tashi yin aure ba shiyasa ma bana kula kowa a yanzu ɗin". "To wa yace miki karatu na hana aure ne? Tunda gashi kin soma ai abu me sauƙi ne Mijin naki yabar ki kici gaba, shiyasa wlh nake miki sha'awar auren Nura tunda shi yayi karatun kuma bana da haufi akan zai barki kiyi karatun ki". Tashi Zainab tayi tsam bayan da Umman nata tagama zayyano maganan, batace komi ba tashige ɗakin ta tafaɗa kan gado Umma kuwa da tabi ta da kallo baki sake tayi ƙwafa tana faɗin "wawiya kawai wacce batasan me yake mata ciwo ba". Lumshe idanun ta Zainab tayi wasu hawaye masu zafi suka sauko mata a kunci Ta rasa meyasaka Umman ta take magana akan Nura, meyasa Ummanta take son auren ta da Nura, taƙi tagane cewa ita baza ta iya auren sa ba, baza ta taɓa auren saurayin da Halwa take mutuwar son sa ba koda kuwa ita tana son shi". Hannu tasaka tana share hawayen ta tare da yin matashi da duk ka hannayen ta Tana jin sanda Abban ta yashigo Umma take ta rattabo masa bayani, har da faɗin "wlh Malam tun wuri ayi wa tufkan hanci idan har ba so kake yi Zainab ta tsofe agida babu mashinshini ba, ga yaro son kowa ya fito yana son ta amma ita ƙiri-ƙiri ta shafe wa idanun ta toka taƙi shi akan dalilin ta na banza dana hofi, to Ni gaskiya bazan iya zuba idanu har sai sanda tagama wannan ƙaddararren makarantan ba, kawai kace ma Nura yaturo idan yaso sai taƙarisa can agidan sa yafi". Murmushi Abba yayi yace "Jummai Ni wannan cece kucen da kike yi banga amfanin sa ba, tunda yarinyan nan ta nuna bata son yaron nan menene na son sai ta aure shi? Duk a ƴaƴana babu wacce nayi mata auren dole bare kuma kan Autana, kibari idan har sun dai-dai ta kansu falillahil hamdu amma Ni bazan mata auren dole ba". Shiru Umma tayi tana gyaɗa kanta cike da takaici, ba wai don tarasa abun faɗa bane sai dai don haushin Abban da yake goya wa Zainab baya, idan da ya amince ita ana ta da tuni anyi an gama, in taje can sai su daidai ta. Miƙe wa Abba yayi be sake cewa komi ba yaɗau buta yashiga bayi don taɗauro alwalan magariba da har an soma kira Ita kuwa Zainab sanyi taji cikin ranta ko banza tasan Abba bazai bari ayi mata aure ba sai da yardan ta, kuma idan har itace zata amince da Nura kafin ayi musu aure to baza ta taɓa amincewa ba har abada.. *______________________* Turo ƙofan tayi tashigo da sallama a bakin ta Khalil dake zaune gefen gadon sa yana faman aiki acikin Lapton yaɗago yayi mata kallo ɗaya sannan yamayar da kansa yana amsa mata sallaman Takowa tayi zuwa wajen gadon tashimfiɗa Husna akai sannan itama tazauna tana kallon sa Shima alokacin yasake ɗago kansa yakalle ta sannan yamaida idanun sa kan Husna, tsawon sokonni biyar yana faman kallon ta kafin yace "Wai ina Mahaifin yarinyan nan?". Yaƙarike maganar yana aza idanun sa kan Saleema Shiru tayi tana sad da kanta ƙasa, ba ta jin zata iya sanar masa haƙiƙanin gaskiya kuma bata san me zata ce masa ba a yanzu Ci gaba da danna Lapton ɗin sa yayi be sake ce mata komi ba, sai can kamar mintuna biyar yasake jeho mata tambayan "Ina Mahaifin yarinyan nan nace?" Yanda yayi maganar ne a kausashe yasa hantan cikin ta ya yamutse, batasan sanda bakin ta yafurta "sun rabu ba". Cakk yatsaya da abinda yake yi yajuyo yana kallon ta Itama ɗin shi take kallo cike da tunanin meyasaka yake son sanin Mahaifin Husnan bayan ada be taɓa tambayan ta ba? Kau da kansa yayi yaci gaba da aikin sa Ita kuma ajiyan zuciya tasauke sannan tagyara takwanta tana tunani aranta "Shin meyasa nake son kawo zargi ne acikin auren mu? Meyasa zuciyata take son kawo min abinda zai hargitsa min rayuwa? Shin menene abun zargi anan?" Kwanciyar ta tagyara tana kallon sa, ahankali kuma tafurta "Allah na tuba Allah ka cire min zargi araina". Aikin yake yi amma maganar Saleema ke kai kawo cikin ransa, duk da yaji sanyi ta wani gefe nasa amma kuma yasan cewa mafarkin sa bazai taɓa zama gaske ba A haƙiƙanin gaskiya zuciyar sa ta kamu da ƙaunar Halwa tun ranan farko da yaganta, amma taya zai iya mallakan ta bayan ita ɗin ƴar uwa ce ga matar sa? Har Saleema tayi barci yana nan zaune yana latsa Lapton ɗin sa duk da kuwa tunani ne cinkushe aran sa wanda yahana sa jindaɗin aikin Daga ƙarshe ma tashi yayi yashige toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yazauna a bakin gadon yana kallon Saleema dake maƙale da Husna, sosai yake mamakin yanda take ƙaunar yarinyan Ya jima a zaune awajen yana kallon su, amma azahiri tunani ne aransa wanda har yasoma haddasa masa ciwon kai Kwanciya yayi yaci gaba da tunanin, yafi mintuna 20 kafin yamiƙe yatashi yasoma jero nafilfilu ganin hakan shine kaɗai mafita a gare shi, domin ko kaɗan ayau ɗin baya jin barci zai iya ɗaukar sa. . *Plz Share and Vote* _More Comments more typing._ [11/13/2020, 11:10 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Three* ________🎓Washe gari ƙarfe 07:30am. *BRR. IBRAHIM KHALIL* yagama Shirin sa na zuwa office Yau yayi shiga na Red colour suit, sai na cikin kuma whiter ne, necktie ɗin sa da Belt ɗin wandon sa baƙi ne, yayi kyau sosai sai tashin ƙamshi yake yi, sosai kwarjinin sa da cikan halittansa suka sake fitowa ainun Be tsaya yayi breakfast ba duk da kuwa Saleema tuni tatashi tayi masa, haka yafice sabida yana sauri Aiki sosai yake dashi a office, gashi kuma zasu je wani waje shi da Brr. Tahir Sai wajen 12:00pm. Yagama sannan suka tafi. Ƙarfe :2:30pm. Suka gama yanufi gidan su Yana yin horn me gadi yazo yabuɗe masa, shiga yayi da motar ciki yayi parcking yafito yarufe murfin motan yashiga gidan Mom na zaune a parlour tana cin Fruits tana kallon tashan African t.v ana wa'azi tajiyo sallaman sa Fara'a tasaki tana amsa masa sallaman kafin taɗau Remote tarage t.v n Ahankali yatako cike da gajiya yazauna gefen ta sannan yagaishe ta Murmushi tayi tana shafa kansa ta'amsa masa tana tambayan Saleema Sai da yayi releasing akan kujeran kafin yabata amsa da "lafiyan ta ƙalau Mom". "Masha Allah haka ake so". Sai da tagutsira 🍌 Bananan hannun ta kafin takalle sa tace "ko asawo maka abinci?". Gyaɗa kansa kawai yayi yana jan numfashi Mom har ta buɗe baki da ninyan kiran ƴar aikin ta sai ga Nazeefa ta fito daga ɗakin ta riƙe da plate a hannun ta "Yauwa Nazeefa sawo ma Yayan ki abinci". Nazeefa da idanun ta ke kan Khalil ta'amsa mata da "Toh". Sannan tagaishe da Khalil ɗin Idanun sa shima akanta ya'amsa mata Kichen ɗin tanufa zuciyarta cike da ƙaunar sa, sosai yau ɗin yasake mata kyau fiye da ko yaushe, domin ta ɗan jima rabon da tagan shi, ko da yazo gidan ita tana makaranta a lokacin Fitowa tayi riƙe da plate da spoon aciki, taƙariso ta'ajiye masa kan Centre table bayan ta ɗan matso masa dashi, zuwa tayi tazauna can kujeran dake Facing nashi taduƙar da kanta tana satar kallon sa Shi kuwa abincin sa yaɗauka yana ci yana sauraron hiran Mom da take yi masa akan Yayan nasa Sameer Ko kaɗan bata gajiya da kallon sa, da ace zata kwana tana kallon sa to baza ta taɓa gajiya ba, a kullum ƙaunar sa sake wanzuwa yake yi a zuciyar ta, ta rasa yanda zatayi tacire sa aranta, bata da damuwa a ko yaushe sai nasa, burin ta kullum tasami hanyar da zata mallake sa duk da tana ganin abu ne me wahala ta same sa, amma baza ta cire rai ba da ikon Allah sai Allah ya mallaka mata shi, koda kuwa zata kasance matar sa ta huɗu ne to zata zauna dashi in dai zai aure ta.. "Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa tunanin me kike yi?" Maganar Mom yadawo da ita hayyacin ta, dasauri taɗago kanta tana kallon su Mom ce kaɗai idanun ta ke kanta, yayinda shi kuma yake cin abincin sa hankalin sa kwance Cikin daburce wa tace "Mom ban ji bane". "Yayan ki ne ke magana". Nazeefa sauke idanun ta kansa tayi tace "Yaya me kace?" Sai alokacin yaɗago fararen idanun sa yana kallon ta, hararan ta yayi yace "ban sani ba". Bata san sanda tayi murmushi ba sabida yanda yayi maganar har hararan sai kace wani mace Mom ma sai da tamurmusa don itama taga sanda yayi hararan, cikin murmushin tace "ayi mata afuwa mana Auta wannan harara haka?". Ajiye abincin yayi yana kallon Nazeefan da tasauke nata idanun ƙasa yace "meyasa baki taɓa zuwa gidana ba?" Hannun ta tamatse waje ɗaya cike da fargaba taɗago kanta tana kallon sa tace "Yaya makaranta ne yahana Ni zuwa". Hararan yasake aika mata dashi cikin ɗaure fuska yace "makarantan ne zai hana ki zuwa gidana?" Mom tace "ai nima nayi godo da ita taje amma taƙi zuwa wlh, Ni bansan meke damun Nazeefa ba yanzu, ko ranan Saturday ɗin nan sai da nasake yin mata magana". Nazeefa sad da kanta ƙasa tayi kamar zatayi kuka, ko kaɗan bata son zuwa gidan Yayan nata ba don komi ba sai don kishi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba idan har ba ita ba "Je ki shirya kizo mu tafi, ki haɗo da kayan makarantan ki don kwana zakiyi, idan kin wuce makaranta kya dawo nan". Tashi tayi batare da tace uffan ba tanufi ɗakin ta, tana shiga tacire riga da skert ɗin jikin ta tasaka dogowar riga baƙi da yasha stone masu ƙyalƙyali, sosai take son dogoyen riguna shiyasa ma Mom Ko da ɗinki zata bada ayi mata, dogayen riguna take saka wa ayi mata, tunda ko anyi mata sauran ɗinkunan bata saka wa sai taga dama Ɗan ƙaramin jaka taɗauka tasaka kayan makarantan ta sannan taɗau school bag ɗin ta tafito Ko kaɗan bata murna da zuwa gidan Yayan nata, sai dai sauƙin ta ɗaya zata riƙa ganin sa yanzu Tana fitowa Khalil miƙe wa yayi sukai sallama da Mom sannan yayi gaba Nazeefa tabiyo bayan sa bayan itama tayi ma Mom ɗin sallaman. *_____________________* A mota babu me magana cikin su, tun sanda yatambaye ta karatun ta be sake magana ba, hankalin sa na ga titi har suka iso gidan Bayan yayi horn me gadi yabuɗe masa yasaka motan ciki, yana parcking suka fito atare, yana gaba tana bin sa a baya sai bin gidan take yi da kallo, komi an sauya ba kamar sanda tataɓa zuwa ba Suna shiga babu kowa sai Husna dake wasa a ƙasa Wajen ta Khalil yawuce yaɗauke ta yana saɓa ta sama yana mata wasa Sai Nazeefa tasaki baki kawai tana kallon su Sai shine da yajuyo yaganta har yanzu a tsaye yace "tsayuwar me kike yi kuma?" Sai alokacin tadawo duniyar tunanin ta tasamu wuri tazauna Shi kuma yawuce ɗakin Saleema da Husna a saɓe a wuyan sa Yana tura ƙofan da sallama yahange ta zaune kan stool tana shafa Lipstick a bakin ta, tayi shiga cikin riga da skert na ɗan kanti, farar riga me gajeren hannu sai jan skert me ɗan faɗi tare da tsagi ta baya, kayan sun yi mata kyau gashi kuma sun ɗauki white skin ɗin ta, kanta da ɗan siririn ɗan kwali da taɗaura be gama rufe mata tsakiyar kai ba Amsa sallaman tayi tana juyowa takalle su Sosai tayi masa kyau yatako wajen yana kallon ta batare da yace komi ba Sannu da zuwa tayi masa tana murmusawa Ya'amsa mata still yana kallon ta kafin yace "kin yi kyau matata". Rufe fuskarta da tafin hannayen ta tayi tana ɗan sakin dariya me sauti kafin tace "Nagode Mijina". Shima sai yayi dariyan yana sauko Husna yariƙe ta sosai a hannun sa sannan yace "ga ƙanwata nan nazo da ita zata kwana gobe zata tafi". Miƙe wa tayi ta'amsa mishi da "Toh". Tanufi ƙofa, shima yabi bayan ta Suna fitowa idanun ta yahaɗe dana Nazeefa, har yanzu dai bata san wacece ita agare su ba duk da kuwa tasan ba ƙanwar Khalil ɗin bane, amma ta danganta hakan da ƙila ƴar uwansa ce Zuwa tayi da fara'an ta tazauna Ita kuma Nazeefa ganin Khalil shima yazo ya zauna ne tasaki fuskarta itama sannan tagaishe ta Saleema ta'amsa mata tana murmusawa sannan tatambaye ta Mom? Ita kuma tabata amsa "tana nan lafiya tace agaishe ki". "Yaya ko in kawo maka abincin nan ne?" Saleema tayi maganar tana kallon Khalil da yatasa Husna gaba yana faman mata wasa Girgiza mata kai yayi batare da ya kalle ta ba yace "no sai nayi wanka zuwa anjima zanci". Sannan yamiƙe tare da Husnan yanufi ɗakin sa "Ƙanwata taso muje kici abinci". Saleema tafaɗa tana kallon Nazeefa da tabi bayan Khalil da kallo Murmushi taƙirƙiro tana kallon Saleeman tace "a'a Aunty Alhmadulillah sai da naci abinci kafin na taho". "Haba dai ko ɗan ruwa ne ai kya sha, bari in kawo miki". Tashi tayi tanufi wajen Fridge Nazeefa taraka ta da kallo, sosai take mamakin yarinyan da tagani don bata da masaniyar zaman ta agidan, har Mom ma itama sai daga baya tasani, sai kuma tataɓe baki aranta tace "to Ni ina ruwana". Saleeman tadawo riƙe da Drinks da taɗauro saman plate ta'ajiye Mata a gaban ta kan Centre table sannan takoma tazauna tana faɗin "bismillah". Babu musu Nazeefa taɗauka Robbern Fanta tabuɗe tazuba cikin glass cup ɗin da tahaɗo mata dashi, tana sha suna kallo batare da ɗayan su ya sake magana ba tunda babu sabo ko kaɗan a tsakanin su Suna nan zaune har Khalil yafito, da alamun yayi wanka ne don ya sauya kayan sa cikin shiga na ƙananan kaya wanda sukai ma jikin sa kyau sosai Duk kansu kallon sa suke yi cike da tsantsan ƙauna Shima dai kallon su yayi sai ya'aza idanun sa kan Saleema yaɗan ɗage mata gira ɗaya yace "My dear na wuce masallaci, ga ƴar ki can tana barci". Murmushi Saleema tayi tace "to adawo lafiya". Gyaɗa kansa yayi yanufi ƙofa yafice "Ƙanwata muje in Kai ki ɗaki". Maganar Saleema yakatse mata tunani, cikin son kawar da abunda yatokare mata maƙoshi tamiƙe da jakanta tabi bayan ta Ɗakin ta takai ta sannan tafito tanufi ɗakin Khalil, anan ita tayi sallan ta kafin tadawo parlour Alokacin shima Khalil ya dawo har ya zauna saman dainnig yana latsa wayan sa Wajen tanufa tasoma saving ɗin sa sannan tajuya zata tafi "Ke kinci abincin ne?" Juyowa tayi tana kallon sa sannan tagyaɗa masa kanta tana murmusawa Be ce komi ba yaɗau spoon ɗin yasoma cin abincin sa Nazeefa tunda tagama Sallah tazauna nan kan sallayan taƙi tashi, sai ma zuba tagumi da tayi ta'af ka tunani Bata sake fitowa ba har dare Koda Saleema tashigo tayi mata maganar tafito Parlour ko zata fi jindaɗi, sai tace "a'a nan yayi mata". Juyawa tayi kawai tabarta takoma parlour taci gaba da kallon ta don shi tuni Khalil ya shige ɗakin sa yana faman aiki a Library ɗin sa Daga karshe da tagaji da zaman sai tanufi kichen tayi musu girki me sauƙi, taliya tadafa da raguwar miyan ta na jiya Sai da tagama komi taje tajera a dainning table, lokacin har an kira sallan magriba Ɗakin Khalil ɗin tanufa tashiga ciki, alokacin ya fito daga Toilet bayan ya ɗauro alwala, kallon ta kawai yayi yafice dasauri Ita kuma tanufi kan gadon inda Husna ke kwance tarigada ta farka tana ƙananun kukan ta, ɗaukan ta tayi tanufi ɗakin ta da ita Shiga tayi da sallama a bakin ta, kallon Nazeefa dake sallah tayi tawuce cikin Toilet Kayan Husna tacire tawanke mata kashin da tayi sannan tayi mata wanka tafito taɗaura ta kan gado, sai takoma taɗauro alwala tadawo tagabatar da Sallah Nazeefa na zaune akan kujera tana faman kallon Husna dake ta mutsil-mutsil cikin towel da aka nannaɗe ta dashi tana son cire wa tasauko Har Saleema ta'idar da sallan ta tamiƙe tasoma shirya Husnan, ta kula Nazeefa ba me son yin magana bane shiyasa itama taƙyale ta batare da ta kula ta ba, amma abinda yadace tana tambayan ta Har tagama abinda zatayi tafito Parlour tazauna tana ma Husna wasa tana kallo Sai bayan isha'i sannan Khalil yadawo gidan Suna zaune kan dainning shi ya ɗaura Husna ajikin sa yana cin abinci yakalli Saleema da itama take saving nata yace "Ina Nazeefa ne?" "Tana ɗaki tana sallah nayi mata magana yanzu zata fito.." Bata rufe baki ba nazeefan tafito taƙariso wajen tana gaishe da Yayan nata Amsa wa kawai yayi yaci gaba da cin abincin sa Itama zama tayi tayi saving kanta tasoma ci, can kuma taɗago kanta tana kallon sa yanda duk yabada hankalin sa kan Husna ko abincin ma baya ci sosai "Yaya wai wannan yarinyan wacece?" Tayi tambayar tana ci gaba da kallon sa Daga shi har Saleema suka ɗago kansu suna kallon ta Sai da yakau da kansa gare ta kafin yace "Ƴata ce". Bata sake cewa komi ba taci gaba da cin abincin ta sai dai zuciyarta haushin amsar da yabata take ji Ita kuwa Saleema murmushi kawai tayi tana kallon Khalil ɗin cike da ƙaunar sa, sannan taci gaba da cin abincin ta Shi yasoma tashi yanufi ɗaki Kamar ana tsikarar Nazeefa tana ganin ya shige itama tamiƙe tanufi parlour Saleema dai bata ce mata komai ba illa kallo ɗaya da tayi mata taɗauke kanta, sai da tagama tattara komi takai kichen sannan tanufi ɗakin ta Wanka tayi tasanya kayan barci sannan taɗau abubuwan da zata buƙata tare dana Husna tafito tana kallon Nazeefa dake zaune tana kallo "Ƙanwata koda akwai abinda kike buƙata ne?" Sai alokacin Nazeefa taganta ma, kallon ta kawai take yi cike da tsananin kishi, tasan tunda tagan ta da shiri ɗakin Khalil zata tafi "Kenan ko hiran daren ma basuyi sai su shige ɗaki?" Tatambayi kanta tana ci gaba da kallon Saleeman cike da tsantsan haushin ta Ita kuma Saleema ganin tayi shiru sai tabuɗe ɗakin Khalil kawai tashige abunta aranta tana jinjina wulaƙacin yarinyan, ko ba komi ai ita Matar YaYanta ne bare ma ta girme mata sosai don aƙalla zata bata shekaru uku ƙwarara Tana ganin ta shige itama tatashi tanufi ɗakin Saleeman zuciyarta kamar zata tarwatse, har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙoshin ta. Sai Khalil ne daga baya yafito yakashe t.v n yakulle ƙofan Parlourn yakoma ɗaki. Washe gari ƙarfe 07:20am. Ya riga ya gama shirin sa har breakfast yayi sannan yafita Lokacin itama Nazeefa tafito da shirin ta na makaranta tana rataye da school Bag ɗin ta tare da jakan da tasaka kayan da tacire, fuskarta duk babu walwala idanunta sunyi luhu-luhu kamar wacce bata samu ishashshen barci ba Saleema dake kakkaɓe parlour'n taɗago tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace "Ƙanwata har kin fito?" Itama Nazeefan murmushin tayafa ma fuskarta sannan tace "eh Aunty Ina kwana?" "Lafiya lau kin tashi lafiya? Ya baƙunta?" Saleema tasake yin maganar da fara'a "Alhmadulillah". "Ok ga breakfast ɗin ki kizo kici". Nazeefa tace "a'a bazan iya cin komi ba, zan tafi Aunty sai kuma wataran in na sake dawowa ki gaida yaya". Saleema kallon ta kawai take yi cike da mamakin ta, sai kuma dai batace komi ba ta'amsa mata sannan tabata saƙon gaisuwa wajen Mom Tana kallo Nazeefan har tafice sannan taci gaba da aikin ta Drever yaɗauki Nazeefa yanufi da ita school ɗin su. [11/16/2020, 6:56 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Four* ________🎓 *TWO MONTHS AGO* A cikin wannan watannin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da soma zuwan Halwa makaranta, tayi farin ciki matuƙa Da farko Saleema ce ma Abba tayi yakaita Abroad tayi karatun, har Abba ya amince amma Halwa ita tace sam bata son tayi nesa dasu dole aka barta anan Katsinan Tunda tasoma zuwa school ɗin babu ruwan ta da kowa harkan gaban ta kawai take yi, kuma sosai take gane karatun tunda shi tasaka a gaba Duk da kuwa mutane da dama suna sonn ƙulla alaƙa da ita amma taƙi yarda musamman ma maza da yawancin su suke nuna suna son ta, wannan dalilin ne ma yasa take saka niƙap, da zaran drever ya kawo ta zata ɗau niƙap ɗin ta tasaka, idan kuma yazo ɗaukar ta sai ta shiga motan sai tacire Har yanzu ta kasa manta tabon ɗa namiji cikin rayuwan ta, ta kasa manta abinda Haris yayi mata, sannan takasa manta abinda Nura yayi mata duk da kuwa har yanzu zuciyarta na mishi uzuri Ko kaɗan ta tsani namiji yanuna yana son ta sabida tarigada ta cire soyayya cikin ranta Zuwan ta gidan Saleema sau biyu shima daƙyar taje don aranta ko kaɗan bata son sake haɗuwa da Mijin nata da yatsaya mata arai yaƙi gushe wa, sau tari tana tunanin sa sai taji gabanta ya faɗi kuma tarasa me yasa, sai dai tana ƙoƙarin yakice sa aranta musamman ganin ta dena tuna sa gaba ɗaya, sosai take mamakin haɗuwa da cikan halitta irin Mijin Saleema, sai yanzu tagane abinda Saleeman tahango atare dashi har tamutu a ƙaunar sa haka, domin samun irin sa sai wanda yake da babban daraja wanda kuma yakai Zuwan da tayi gidan duk sun haɗu amma gaisuwa kaɗai ke haɗa su, shima daga nan ko kallo baya sake yin mata har kuwa tatafi Don shima a nashi fannin sosai yake son cire ta aran sa musamman yanzu da yasan matsayin ta a wurin shi, yana auren ƴar uwan ta, ko kaɗai baya son abunda zai kawo saɓani a tsakanin zaman sa da matar sa tunda yana jindaɗin zama da ita ainun Amma abinda akace zuciya na so babu me iya raba ta da shi, bare shi da ya jima a ƙaunarta tun lokacin da be san ita ɗin wacece ba, a kuma kallo ɗaya da yayi mata, sau da dama yana mamakin irin Wannan soyayyan, har zama yake yi yayi ta tambayan kansa "wai dama ana soyayya irin haka daga kallon farko da akayi wa mutum koda kuwa baka san ko shi waye ba? Koda kuwa bakasan zaku sake haɗuwa ba?" A yanda take zuwa masa a mafarkin sa ne yake basa mamaki, kullum idan har be yi mafarkin ta ba to zai yi tunanin ta, idan har zata zo mishi kuma a mafarkin tana me kuka ne tana neman taimakon sa, ya kasa gane irin wannan mafarkin musamman yanzu da yaganta cikin gatan ta. *______________________* A fannin Nazeefa ma tana nan tana ta fama da son maso wani, ta ari damuwa duk ta yafa ma kanta, yanzu abun har yakai ko karatun ta bata maida hankali a kanshi Mom tayi mitan sauyawan ta har ta gaji amma taƙi faɗa mata abinda yake damun ta Wannan halin da take ciki kullum idan taje makaranta bata kula kowa ko ajin ma sai taga daman shiga, da zaran taje zata wuce bayan makarantan inda ɗalibai ƴan Pramary suke wasa taɓoye anan tazauna tayi ta tunanin ta Ƙawarta Haneefa ita take damun ta kullum tafaɗa mata damuwarta, ta kai ta kawo ma har faɗa sukayi akan ƙin faɗa mata da tayi, daga ƙarshe dai Haneefa da taga fushin bazai kai ta ko ina ba sai tadawo tana rarrashin ta don tasanar mata damuwarta, daƙyar dai Nazeefa tabuɗe baki aranan tasanar mata tana yi tana kuka kamar ana yankan naman jikin ta, har wani rawa jikin nata yake yi sabida tsaban yau komi ya kai mata maƙura Haneefa na zaune gefen ta tana bin ta da idanu cike da tsananin mamakin ta, bata hana ta yin kukan ba har sanda tayi ma'ishi tafitar da duk ƙuncin dake cikin ranta, sannan ne tadafa kafaɗan ta da hannu ɗaya tace "Ban taɓa tunanin akan ɗa namiji bane kika shiga duk wannan damuwar Nazeefa, sabida ɗa namiji kika dena shiga aji kika dena mayar da hankalin ki kan karatun ki duk a sabida ɗa namiji? nayi mamaki wlh ƙawata duk kyawun ki kizauna kina ma ɗa namiji kuka". Shiru Haneefa tayi tana jan numfashi tare da tsare Nazeefan da idanu Ita kuma Nazeefa alokacin ne taɗago kanta tana kallon ta da rinannun idanuwan ta tace "baza ki gane a halin da nake ciki bane Haneefa, zuciyata tariga da ta mutu a ƙaunar sa, nayi duk iya abinda zanyi don in cire sa araina amma na kasa, wlh ji nake yi kamar in mutu saboda yanda nake ji a kansa, bana jin zan iya auren wanin sa idan bashi ba, bazan taɓa zama da kowa ba sai shi, tun bansan meye so ba zuciya ta takamu da mahaukacin ƙaunar sa har sanda nagane, gashi yanzu yayi min ratan da samun sa babban wani aiki ne agare Ni". Dariya ma abun yaba ma Haneefa, sai tasaki baki tana yi Hararan ta kawai Nazeefa tayi tana ɗauke kai cike da haushi Tsai da dariyan Haneefa tayi tace "ƙawata kenan kin faɗa da yawa, Ni kuwa zan so ganin wannan Jarumin me babban matsayi a wurin ki, amma fa idan har kina son samun sa to ba wani babban aiki bane a wurin ki ƙawata sai dai idan kece baza ki bi hanyan da yadace ba, Allah na tuba don yana da mata sai kice yayi miki nisa?" Kallon ta kawai Nazeefa take yi kamar idanun ta zasu faɗo ƙasa har sanda tadire aya kafin taɗaura da nata "Wace hanya ce tadace da zanbi don samun sa? Kina ganin har akwai sauran hanyan da zanbi Ya Khalil yakalle Ni a matsayin Masoyiya?" "Ƙwarai kuwa, me zai hana ki faɗa ma Mahaifiyarsa tunda ita tabuƙaci haka, na tabbata wlh zata share miki hawayen ki tunda tana ƙaunar ki". Shiru kawai Nazeefa tayi don tasan baza ta taɓa iya faɗa mata ba, to taya shi Khalil ɗin zai kalli maganar? Abinda take tunawa kenan, ba wai faɗan bane.. matsalan ta na ga Uban gayyar". Maganar Haneefan ne takatse mata tunanin ta, taɗago tana kallon ta cike da wani irin kallo me wuyan fassara, bakin ta har rawa yake yi wajen cewa "Baki da hankali ne wannan wani irin shawaran banza ce? No bazan taɓa iya aikata hakan ba, idan kuwa nayi masa haka tabbas na zama butulu, tabbas idan na aikata hakan mutane zasu zage Ni sannan zasu la'ance ni tunda ban riƙe maraicina ba.." Sai kuma tagirgiza kanta cikin kuka tace "bazan taɓa iya aikata masa haka ba, wlh gwara in mutu da in je wajen boka in cutar da wanda yataimaka min". Haneefa cikin son nuna mata abunda take nufi tace "ƙawata ki gane mana hakan shine kaɗai mafita kuma hanyan da zaki samu zuciyar sa..." Ɗaga mata hannu Nazeefa tayi tace "ya isa bana son ji, Kar ki sake min irin wannan maganan". Tana faɗan haka tamiƙe tawuce tabar Haneefa nan zaune baki sake tana bin bayan ta da kallo. Tun daga ranan kuma sai Nazeefa tadena sake ma Haneefa fuska, ko tazo school ɗin babu ruwan ta da ita, ita a ganin ta Haneefa ba ƙawar kirki bace da har zata bata wannan shawaran, duka-duka ma nawa suke da har zata bata shawaran zuwa wajen Boka? Ita ma dai Haneefan tasha jinin jikin ta, tun daga ranan itama taja baya da ita, idan ba gaisuwa ba babu abinda ke haɗa su, a ganin ta taimakon Nazeefa zata yi, amma tunda ta nuna bata so to itama ta bar maganan, duk ranan da komi yarincaɓe mata tazo taneme ta ita kuma anan ne zata taimaka mata. . *Facebook: Muh'd Lawal Nafisat* *Wattpad: UmmuDahirah* *WhatsApp number:07065334256* _plz karku manta da share, Vote, Comments. Nagode._ [11/22/2020, 1:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Five* ________🎓Rayuwan Khalil da Saleema rayuwa ce da suke yin ta cikin jindaɗin juna da nuna ƙauna da kulawa, zuwa yanzu komi yana tafiyan musu dai-dai Gefe ɗaya kuma ciwon Saleema na zuwa mata jefi-jefi, duk da tana shan magani amma wataran haka zata tashi da tsananin ciwo har asibiti Khalil yake kai ta, sai kuma daga baya ciwon nata yalafa Yanzun ma kwana biyu kenan bata jindaɗi sai dai ba sosai ba tana yin duk aiyukan ta tare da taimakon Khalil, idan yana gida shi yake taimaka mata da rainon Husna, girki kuma hanata yayi sai dai yayi musu Take-away, idan tatashi kuma da ƙwarin jiki sai tayi musu girkin ........ ........ ....... ........ Yau tun safe da Khalil yatafi aiki bayan ta gama gyaran gidan tayi ma Husna wanka itama tayi, sun shirya cikin farar atamfa me zanen ja da ruwan goro, ɗinkin riga da skert akayi mata sai akayi ma Husna doguwar riga dai-dai ita, duk kwalliyan da akayi iri ɗaya akai musu a rigan Fitowa Parlour tayi da Husna a hannun ta ta'ajiye ta saman carpet, ita kuma tahaye kan 3sitter takwanta, yau sosai jikin ta yamatsa mata ga sanyi da take ji sosai duk da kuwa ta kashe AC da Fan ɗin parlour'n A hankali ciwon yaci gaba da cin ta, hakan yasa tamiƙe takoma ɗaki tahaye kan gado taƙudundune da bargo, nan da nan tasoma rawan ɗari. Wajen awanni biyu da shigan ta Khalil yadawo gidan, da sallama yashigo cikin parlour'n, da Husna yasoma cin karo tayi wasan ta har ta gaji tasoma ƙananun kukan ta daga ƙarshe barci yaɗauke ta a dungure a wajen ta kofa kanta kamar wacce take sujjada Dasauri yaƙariso yana ajiye briafcase ɗin sa yasaka zara-zaran hannayen sa yaɗauke ta, sannan ne yaga ashe barci take yi, murmushi yayi yana kallon fuskarta da tataɓe baki duk hawaye ya gama bushe mata a fuskar Gaban sa ne yafaɗi sakamakon ganin yanda kamannin ta da Halwa yasake fitowa ainun, basu da maraba a yanzu ɗin Shiru yayi yana ƙure ta da kyawawan idanun sa, ya ɗau tsawon mintuna 3 kafin yamiƙe yanufi ɗakin Saleema da ita a hannun sa, yana shiga yahangi Saleeman kan gado nannaɗe cikin bargo Dasauri yanufi bakin gadon dan yasan babu lafiya, ajiye Husna yayi can ƙarshen gadon kafin yamatso kusa da Saleeman yana zama ya yaye bargon yana kiran sunan ta Zafin da yabuge sa ne yayi saurin sake yaye bargon yana tallabo kanta, nan yaga fuskarta sharkaf da hawaye idanun ta kuma sun kaɗa sunyi jawur gunun tausayi, gaba ɗaya jikin ta rawa yake yi ga shegen zafi kamar tafashashshen ruwa, shi kanshi dauriya yayi wajen riƙe ta Cikin tsananin firgici yace "subhanallah.. Saleema meke damun ki? Tun yaushe kika fara ciwon?" Bakin ta rawa yake yi ta ma kasa magana in banda hawaye da ke zuba kan kuncin ta yana gangara ta gefe yasauka hannun sa Dasauri yakwantar da ita yana miƙe wa cikin sauri, wayan sa yaɗauka yakira doctorn ta, sai dai baya shiga hakan yasaka ya'ajiye wayan yafita da sauri Sai kuma yasake dawowa yaɗauki Husna yakaima drever akan yakaita gida sannan yadawo yatallabi Saleema yasaka mata Hijab suka fito A back seat yakwantar da ita yashiga yaja motan yafice cikin gidan da mugun gudu. *___________________________* Drever na zuwa gidan su Saleema Gateman yamiƙa ma Husna sannan yatafi Nocking gate man yayi a bakin Parlour Halwa na tsaye gaban Fridge tana shan ruwa, dawowar ta kenan dama daga makaranta tasoma nufan Fridge ɗin, ajiye ruwan tayi tanufi ƙofan tabuɗe, kallon Gate man tayi tare da Husna dake hannun sa "Dama drever ne yakawo ta inji Mijin Hajiya Saleema". Cewar Gate man ɗin yana kallon Halwa Mamaki ne Yakamata amma sai batace komi ba ta'amshe ta tarufe ƙofan takoma cikin parlour'n, ajiye ta anan ƙasan carpet tayi tanufi kan kujera inda jakar ta yake tazaro wayan ta tasoma kiran numban Saleema, sosai hankalin ta yaba ta babu lafiya ne don tasan babu ta yanda za'a yi Saleema tayarda adawo da Husna, ƙirjin ta sai fat fat fat yake yi gashi Ummi tana Hospital kuma tace mata zata biya anguwa, so dawowarta ma ba yanzu ba Ringing wayan take yi but not answer, zuwa lokacin Halwa ta kasa zama sai Safa da marwa take yi tana sake danƙara mata kira, tsaki taja tana ɗaukan jakan ta tanufi ɗakin Saleema wanda yazama nata a yanzu Ta dawo makarantan yau agajiye Allah-Allah take yi tadawo tayi wanka ko zata rage gajiyan, ga mugun yunwa dake addabar ta, amma a yanzu bata jin zata iya cin wani abu idan har batasan halin da take ciki ba, kayanta tacire tashiga wanka. Larai ce tafito daga ɗakin ta tahangi Husna tana kuka, dasauri taƙarisa wajen ta taɗauke ta tasoma jijjiga ta tana tambayan ta "ina Mamarta? Wa yakawo ta?" Sai kace tana jin ta Ɗakin Halwan tanufa tunda a tunanin ta Saleeman ce tazo gidan, amma koda tashiga babu kowa sai ƙarar ruwa da taji, hakan yasa tafita takoma ɗakin ta da Husnan. *________________________________* Lokacin da Khalil yakai Saleema asibiti Ummi tabar asibitin Emargancy ward aka nufa da ita, hankalin Khalil duk ya tashi haka yake ta Safa da marwa, gashi be zo da wayan sa ba bare yakira gidan su yasanar musu Wajen 1hour aka ɗauka ana duba ta kafin likitan yafito yabuƙaci ganin Khalil, kan dai matsalan ciwon ta ne sai kuma shigan ciki na sati Uku, gashi kuma sun gano da matsala sosai a mahaifar ta zai yi wuya ta'iya ɗaukan ciki har yagirma a jikin ta, sai dai sun ɗaura ta akan magani don aga yanda hali zai yi Hankalin Khalil sosai yasake tashi da jin bayanin doctor, sai dai komi ya fawwala ma Allah hakan shine cikan imani Motar sa yashiga yanufo gida tunda dama a kulawan likitoci take, yanke shawara yayi yasoma wucewa gidan su Saleeman yafaɗa ma iyayen ta don haka yakarya kan mota yanufi gidan. _...... ........ ....... ....... ......_ Fitowar Halwa a wanka doguwar riga kawai tazira taɗaura ɗankwalin rigan tafito parlour Tana zama Larai tafito cikin ɗakin ta goye da Husna abaya zataje kichen "Au Ashe kin fito? Na shigo ɗakin ai duba ko Saleema ce tazo amma bangan ta ba". Halwa kallon ta tayi da yanayin damuwa a face ɗin ta tace "eh na fito amma ba Saleeman bace tazo drever ne yakawo ta". "Allah yasa dai lafiya ko?" Larai tafaɗa itama a yanayin wasi-wasi Domin sun san babu yanda za'a yi akawo ta gidan idan har ba Saleeman bace tazo "Wlh nima bansani ba, na kira dai wayan ta amma shiru ba'a ɗaga ba hankalina duk ya tashi, nayi tunanin kiran Ummi kuma kar yazo fahimtar mu ce hakan". Larai tace "eh gwara kam kar ki kirata saboda bamu da tabbacin ko matsala ne, amma dai kici gaba da gwada kiran wataƙil adace". Gyaɗa kanta kawai Halwa tayi taci gaba da kiran wayan kamar yanda Larai ɗin tace Ita kuma Larai kichen tanufa don ɗaura girkin dare Tashi Halwa tayi tanufi kan dainning tazauna, sosai take jin yunwa kamar hanjin ta zai tsinke, yau bata ci komi a school ba haka taje tadawo Zama tayi tazuba abincin da yakasance Macoroni ne me manja, tana cin abincin tana sake kiran layin Saleema, ko kaɗan ta gaza haƙura, zuwa yanzu hankalin ta yayi ƙololuwar tashi, tabbas tasan akwai matsala Abincin ma sai yakoma baya mata daɗi, turewa tayi dai-dai da lokacin da taji ana buɗe Gate ɗin gidan Dasauri tamiƙe tanufi hanyan fita don tasan bazai wuce Ummi bane ko Abba, hankalin ta ne ya gaza kwanciya shiyasa tanufi wajen don tarban su duk da kuwa bata san me zatace musu ba Tana fita tahangi motan da bana gidan ba, bata san cewa Khalil bane aciki tunda bata ganin shi, kuma ba wai tasan motan gidan shi bane bata tsayawa kallo bare ta tantance, tasan dai yana da motoci aƙalla sun kai biyar agidan Shi kuwa tun sanda tafito idanun sa yasauka akan ta, har yayi parcking yafito yarufe motan Zuciyar ta ne tabuga sakamakon ganin sa, duk da dama idan har zata ganshi hakan ke faruwa da ita amma kuma da fargaban ko wani abu ne yasamu Saleema, tana nan tsaye tana kallon sa yayinda zuciyarta ke ci gaba da dukan uku-uku, gaba ɗaya ta dunƙule hannun ta waje ɗaya saboda rawan da suke yi, daƙyar ta'aro jarumta da ya'iso wajen tagaishe sa Amsa mata yayi yana ci gaba da kallon ta kamar zai cinye ta, tsananin ƙaunar ta ne ke ɗawainiya dashi, ya jima rabon da yaganta sai yaji wani sanyi aransa tare da wucewar wani abu da yatsaya masa a maƙoshi kwana da kwanaki Matsa masa a hanya tayi batace komi ba Shi kuma sai yashiga kafin tabiyo bayan sa A kan ɗaya daga cikin kujerun yasamu wuri yazauna Ita kuma taje taɗauko masa ruwa duk da kuwa batasan ko yana buƙata ba Ajiyewa tayi a gaban sa saman Centre table tajuya da ninyan wuce wa duk da kuwa tana son tambayar sa Saleema, gashi kuma yanda idanun sa yake faman yawo ajikin ta yayi bala'in takura ta Har ta soma tafiya taji sassanyan muryan sa yayi mata magana "Ina Ummi?" Juyowa tayi sai dai wannan karon baza ta iya kallon sa ba tasad da kanta ƙasa tace "bata dawo ba". Shiru yayi kamar bazai yi magana ba Ita kuma hankalin ta yagaza kwanciya, bata san sanda tajeho masa tambayan "Meke damun ƴar uwata?" Tayi maganar idanun ta na kansa Kai tsaye Khalil yasanar mata inda take Hankalin Halwa atashe kamar zatayi kuka tace "don Allah zan bika mu tafi". Gyaɗa mata kai kawai yayi yamiƙe yanufi hanyan fita Dasauri taɗau wayan ta tacire ɗankwalin ta tayafa tabi bayan sa, lokacin har ya shige motan ya tayar yana jiran ta Cikin sassarfa taƙarisa tabuɗe gaban tashiga yaja motan yafice bayan da me gadi yabuɗe masa Gate ɗin Duk da Khalil yana son zuwa gida amma bazai ƙi biya mata buƙatar ta ba, wannan dalilin ne yasaka yayi tunanin kai ta kafin yakoma gidan Koda yakaita be daɗe ba yace mata zai tafi Bata tanka shi ba har yafice, sannan ne tasoma kiran layin Ummi, bugu biyu taɗauka anan Halwa tasoma sanar mata Saleema ce babu lafiya tana Hospital Hankalin Ummi ya tashi nan da nan takaryo motan ta don har takusa isa gida, tana zuwa tatarar da Saleeman barci take yi Halwa ta tasa ta gaba sai kallon ta take yi Fita tayi tanufi Office ɗin Doctor ɗin ta, anan take jin bayanin matsalan Saleeman, idan hankalin Ummi yayi dubu to ya gama tashi, sosai taruɗe da jin abinda ke faruwa Koda tafito lungu tasamu tafashe da kuka na tsananin tausayin ƴar nata, babu abinda bakin ta ke furtawa sai salati, tabbas Saleema tana cikin jarabawa Da fari ciwon zuciya sannan kuma ciwon hanta, yanzu kuma ga ciwo a mahaifar ta wanda ke barazanar da zata rasa haihuwa har abada Tasha kuka sosai kafin tashare hawaye tagyara fuskarta, sannan taciro wayan ta a jaka takira Abba tasanar masa Shima babu jimawa yataho Gaba ɗaya sun yi zugun a ɗakin sun saka ta gaba sai kallon ta suke yi Sai gab da magriba tafarka lokacin shima Khalil ya dawo, sosai take jin jiki don ko magana bata yi A lokacin ne Abba ya lallaɓa Ummi suka tafi gida da Halwa tunda an sake mata alluran barci ta koma Babu jimawa itama Mom tazo tare da Nazeefa, sun jima har wajen ƙarfe 11:00pm kafin suka tafi Khalil shi yace zai kwana da ita don haka babu musu Abba yataho yabarta. [11/24/2020, 2:36 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Six* ________🎓 Wasa-wasa sai da Saleema tayi kwana biyar cur kafin tasoma samun sauƙi, sai kuma daga baya ciwo yazo mata rigigim, blending take tayi nan likitoci suka rufu akan ta Halwa kuka Ummi kuka sun rigada sun cire rai ma Saleema zata iya rayuwa Khalil shi kansa ya rasa inda zai saka kansa, tsananin tausayin matar sa gaba ɗaya ya cika sa, sosai yadamu da halin da take ciki A ranan duk wani me tausayi dole yatausaya mata, ashe wai duk ɓari zatayi shine yaja mata hakan, sai da aka ƙara mata jini leda biyu sabida yanda tazubar da jinin ta wajen ɓari Kwanan ta biyu kafin tafarfaɗo, sosai Saleema tayi jinya gaba ɗaya ta rame tayi baƙi sabida jinin da ake ƙara mata, kullum zuwa gaishe ta ake yi Ita Halwa ma gaba ɗaya dena zuwa school tayi sai da tasoma samun sauƙi sannan ne Ummi tatakura mata tafara zuwa Idan kuma tadawo nan take fara wuto wa sai dare takoma gida Haka shima Khalil yake yi, duk da aiki yayi masa yawa amma kullum yana kan zuwa Satin ta ɗaya aka sallame ta duk da ba wani warkewa tayi ba amma haka takoma gida tana jinya, Khalil shi ke kula da ita ko kaɗan baya gajiya, tausayin ta tsantsa ne a ransa Haka rayuwa taci gaba da shuɗewa gashi yanzu har an shafe watanni uku da ciwon da Saleema tayi, yanzu komi ya koma normal sai dai ciwon da ba'a rasa ba wanda take fama dashi koda yaushe. *________________________________* Ƙarfe 03:20pm. Su Zainab da friends ɗin ta suka fito lectures Tafiya suke yi suna hira ɗaya daga cikin su tana basu labarin gwaraman da akayi a anguwan su, sai dariya suke yi sabida yanda me basu labarin ta dage tana nuna yanda matar take ɗaukan mijin ta tana tiƙa sa da ƙasa Daga bayan su can ɗan nesa kaɗan Halwa ce ke tafiya tana latsa wayan ta, tun daga inda take tana jiyo dariyan su sai dai hankalin ta baya kansu sai faman neman layin Drever take yi Yau yayi late be zo ya ɗauke ta ba shiyasa take sake kiran sa taji inda yake, yana ɗagawa yace mata "gashi nan yanzu zai shigo school ɗin" Tsayawa tayi a wajen har sanda tahango shi ya shigo cikin makarantan, sai tanufi wajen shi tana ɗaga masa hannu, shima ɗin ya ganta don haka yatsaya tahau yaja yayi reverse suka nufi bakin Gate Lokacin su Zainab har sun kusa fita motan tazo tawuce su, har alokacin sai faman dariya suke yi, ahaka suka fita cikin school ɗin cike da nishaɗi Suna fita sauran friends ɗin ta duk suka dare biyu daga ciki sukai musu sallama suka ci gaba da tafiya sabida babu nisa da gidajen su, ɗaya ce tahau keke napep tatafi aka bar Zainab ita kaɗai tunda ba hanya ɗaya zasu bi ba Tana nan tsaye wajen sai ga wata dalleliyan mota ta faka a gaban ta, tunda takalli motan sau ɗaya takau da kanta tana kicin-kicin da fuska Fitowa yayi daga cikin motan yana kallon fuskarta, ɗan taku uku yayi ya'iso gaban ta, murmushi yasaki yace "Plz Zainab don Allah kihau in Kai ki gida, yau rana ɗaya dai kiyi min wannan alfarman". Tsaki Zainab taja batare da ta kalle sa ba, ji take yi idan har tatanka masa zuciyarta zata iya bugawa sabida tsaban jin haushin sa, don haka batace komi ba tajuya taci gaba da tafiyan ta Nura kallon ta kawai yake yi har sanda taɗan yi nisa sannan yanufi motan sa yashiga yabi bayan ta Kullum ranan duniya sai yazo domin ta amma bata taɓa masa kallon arziƙi ba, kuma shi be taɓa gajiya ba sabida yanda yake jin ta cikin ransa, duk wulaƙancin da zata yi mishi zai iya jurewa idan har zai same ta, yana matuƙar ƙaunar ta fiye da tunanin mutum Yana biye da ita abaya har sukai nisa, gashi ta kasa samun keke napep duk rana sai faman gasa ta yake yi Shi kuwa gab da ita yazo suka jera yana mata magiya ta cikin motan amma firr Zainab taƙi kallon sa bare tatanka masa Gajiya tayi kawai tasamu acaɓa tahaye tunda babu napep ɗin Nura yana kallon ta har tahau suka tafi yabi bayan su, duk inda me machine ɗin yabi nan shima yake bi har suka kawo ƙofar gidan su Zainab ɗin tasauka tamiƙa ma me machine ɗin kuɗin sa tajuya tashige gida batare da ta amshi canjin ta ba, don baƙin cikin ganin Nura ƙofar gidan su ya hana ta ma tsayawa Ajiyan zuciya Nura yasauke yana bin ƙofar gidan da kallo, ya jima acikin motan.. shi be tafi ba shi kuma be fito ba, sai da yashafe mintuna 20 zaune anan kafin yafito yana rufe motan Kalle-kalle yai tayi sai daga baya yahangi yaro yakira sa yace masa yashiga ciki yakira masa Zainab Da gudu yaron yashige gidan ...... ....... ....... ..... Zainab tun shigan ta da tayi sallama taji babu umma sai tashiga ɗaki kawai ta'ajiye jakar ta tare da gyalen ta tafito tashiga kichen taɗauko abincin ta Zama tayi anan farandan ɗakin su taci abincin tagama, miƙe wa tayi takai coolarn wajen wanke-wanke taɗibi ruwa a buta tashiga Toilet. Tana cikin Toilet ɗin tajiyo sallaman yaro, bata amsa ba har sanda tafito tabi yaron da kallo, bata raba ɗayan biyu Nura ne ya'aiko shi Ai kuwa bata gama tunanin zucin ta ba yaron yace "Wai ana kiran Zainab a waje". Ajiye Butan hannun ta tayi tazauna kan dutse a bakin Toilet ɗin, sannan takalli yaron tace "Je kace masa baza ta zo ba". Babu musu kuwa yaron yajuya yatafi don isar da saƙon ta Sosai baƙin ciki ke ɗawainiya da Zainab, ta rasa wani irin maye ne wannan mutumin, ko kaɗan ita bata ƙaunar sa a ranta bata jin kuma zata iya son sa ko anan gaba, sa'ar ta ɗaya Umma bata nan amma da dole sai ta saka ta fita Shiyasa take roƙon Allah aranta Allah yasa yatafi kafin Umma tadawo Ta soma alwala kenan yaron yasake dawowa yace "Wai yace don Allah tazo zai bata saƙo ne". "Dan ubanka wuce anan gidan". Zainab tafaɗa cikin tsawa tana zazzare ma yaron idanu Da gudu kuwa yasheƙa yafice har da waigen ta Baƙin ciki da ƙunci ne suka taru mata iya wuya, ta rasa me za tayi ma Nura don huce takaici Ƙyalla idon ta tayi tahangi taɓarya, dasauri tatashi tanufi wajen taɓaryan taɗauka tayi hanyan fita a fusace Yau dole ne sai ta kawo ƙarshen zuwa wajen ta da yake yi. . _hahaha Fans kar ku damu ba daku zata rotsa ma kai ba, Nura kawai tanufa banda ku._ _Kuyi haƙuri da wannan babu yawa, aiyuka sun yi min yawa shiyasa nayi muku ɗan kaɗan._ _kar ku manta da Comments ɗin ku shi ke ƙara min ƙwarin gwiwa._ _Ina jiran Comments ɗin ku shin ayi maganin Nura ko ya? Nasan da yawa haushin sa kuke ji bayan kuma be muku komi ba bawan Allah._😅 [11/24/2020, 2:50 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Seven* ________🎓Tana shiga zaure sukaci karo da Umma dole taja tatsaya tana ƙifƙifta ido Umma da tafiddo ido waje tana kallon Zainab ɗin da taɓaryan dake hannun ta tace "na shiga uku ni Jummai me zan gani haka Zainab? Ashe dama baki da mutunci dan ubanki? Yanzu abun naki har ya kai kifita da taɓarya kije wajen Nura? To me kike shirin aikatawa kenan?" Turo baki Zainab tayi tana sosa kai, sai kuma tajuya dasauri tayi ciki tana jefar da taɓaryan "To dan ƙwal uwar ki zo ki wuce kije wajen shi". Cewar Umma tana bin bayan ta itama tashiga cikin gidan "Wlh Umma babu inda zani, nifa nace miki bana ƙaunar sa bana son sa bana son sa, Ni bazan iya son sa ba wlh". Umma kama haɓa tayi tana kallon Zainab ɗin dake masifa kamar batasan da wa take yi ba "Zainab Ni Sa'an wasan ki ne ina faɗa kina faɗa? Wlh sai kin fita ko in saɓa miki kamanni, shashashan yarinya mara hankali.." Kuka Zainab tafashe dashi Sai umma kawai takama haɓa tana kallon ta Cikin kukan take cewa "wlh Umma bana ƙaunar sa, koda kuwa be so Halwa ba Ni bana son sa, har cikin raina nake faɗa miki bazan iya auren sa ba wlh". Sai taja majina tanufi wajen butan ta tazuƙuna tasoma alwala "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yanzu Zainab har kin isa in saka ki abu kice baza kiyi ba? Baza ki tashi ki wuce ba yana jiran ki?" Cikin tsananin ɓacin rai Zainab tace "Umma zan yi sallah ne lokaci na ƙurewa, kuma kinsan illan rashin yin sallan Asar da wuri, yana ɗaya daga cikin sallolin da ake so mutum yakula..." "Dalla rufe min baki, kiyi sauri ki idar kizo ki wuce". Zainab bata sake cewa komi ba taci gaba da alwalan ta, sosai take mamakin Mahaifiyar ta akan yanda tasauya lokaci ɗaya akan Nura, duk da tasan Nura yana banka mata kuɗi da kaya amma kuma bata taɓa tunanin zata sauya har haka ba Tana idar wa tashiga ɗaki tasaka Hijab tasoma sallah, ta ɗau lokaci tana yin Sallah taƙi tasallame sai da Umma tazo tasake mata magana sai faman masifa take mata Dole Zainab ba don taso ba tamiƙe tafito tafice Tana fita kuwa taganshi tsaye gaban motar sa, ta rasa wani irin mayen mutum ne wannan Nura tunda tafito kallon ta kawai yake yi yana murmushi, ko kaɗan be ji haushin daɗewan da yayi a wajen ba tunda Umma tace mishi yajira zata fito, kuma yasan dole zata fito ɗin Wani mugun kallo Zainab tabuga masa tana jan tsaki taɗau hanya taci gaba da tafiyan ta batare da taƙarisa inda yake ba Yana kallon ta har taƙule ma ganin shi Ita kuwa tana shan kwana tasheƙa aguje bata tsaya ko ina ba sai gidan Yayarta Zaituna Suna zaune ita da kishiyarta suna ƙullin Gishiri sai ganin ta sukayi ta faɗo gidan "Subhanallah..lafiya Zainab?" Atare suka tambaye ta yayinda Zaituna taƙara da faɗin "Wa yabiyo ki ne kika shigo haka kamar an jeho ki?" Zainab da tariƙe gwiwowin ta tayi ruku'u tana numfarfashi ta ma kasa magana Kishiyar me suna Murjana tace "ikon Allah wai lafiya ko dai gudun fanfalaƙi kika yi ne?" Bata ce komi ba tanufi wajen randan ruwan su tana sake jan numfashi, ɗiban ruwan tayi tasha kafin tadawo taja kujera ɗan tsuƙuno tazauna agaban su, duk sun tsare ta da idanu suna ganin ikon Allah kuma suna jiran suji abinda yakoro ta gidan da gudu Sai da taƙara gyara zaman ta tana kallon su tace "wlh daga gida nake.." Tsaki Zaituna taja tana hararan ta tace "amma kinji kunya wlh, ƙatuwa dake shine kika sheƙo hanya da gudu ga mutane ko kunya ko?" "To Aunty ki tsaya mana kiji me yakoro Ni, wlh Umma ce tatakura min akan maganar Nuran nan shiyasa na'ari na kare nayo nan". Dariya Murjana tayi tace "kai wlh Zainab baki da dama, to Ni wai meye laifin Nuran nan kullum kina wahalar dashi? Magana dai taƙi ci taƙi cinye wa". Taɓe baki Zaituna tayi tace "kema dai kya faɗa, bata da hankali Zainab ko kaɗan, wai inace duk kina wannan abun ne don Halwa?" "Aunty baza ki gane ba wlh, nifa gaba ɗaya tun sanda yasoma nema na natsane shi, wlh koda ba batun Halwa aciki Ni bazan iya auren sa ba, kullum idan yazo min da nacin nan nasa kullum sake jin tsanar sa nake yi araina". Zainab tayi maganar cike da baƙin ciki "Aiki ya ganki". Zaituna tafaɗa tana ci gaba da ƙullin ta Murjana tace "kiyi ma kanki faɗa don Allah, ko wace mace tana burin tasamu masoyi me ƙaunarta amma ke kin samu kina wasa da damar ki, wlh Nura yana son ki tunda kikaga yana jure wulaƙancin nan naki, Zainab babu batun yaudara anan ki karɓe shi hannu bibbiyu tun kafin lokaci yaƙure miki, dama ce tazo miki har gida, idan kuma kikace zaki tsaya tunanin wata to zaki rasa wannan damar taki, ki duba magana ta". Numfashi Zainab taja, baza su taɓa gane abinda take nufi ba, ita tayi alƙawarin wlh sai dai gawan ta za'a kai gidan Nura amma baza ta taɓa auren sa ba, koda kuwa Halwa ce tazo da kanta tace ta'aure shi, amma a yanzu tarigada ta ƙudurta ma kanta dole ne tasamu saurayi tayi aure ko Allah zai sa yabarta, ada dai bata da burin aure yanzu amma tunda taga abun yazo da haka tasan komi zai iya faruwa Yanzu ma baza ta koma gidan ba sai dare, sai dai idan ta koma Umma tahaɗiye ta Hannu tasaka tasoma tayasu ƙulla gishirin batare da tasake cewa komi ba Su kuma tuni sun sauya zancen ma sun ci gaba da hiran su da suke yi. . *__________________________* *BAYAN WASU WATANNI* A halin yanzu Saleema tasake samun ciki a karo na biyu, kamar dai wancan haka tasha baƙar wahala watan shi ɗaya yafice bayan da tazubar da jini sosai kamar baza ta rayu ba A wannan lokacin ne kuma tasan matsalan ta, tayi kuka kamar baza ta dena ba, har sai da iyayen nata sukai dana sanin faɗa mata sabida gudun tashin ciwon zuciyarta Ita kanta Halwa ta taya ta kukan kuma ta tausaya mata sosai Sai da tayi jinya na tsawon sati biyu a asibiti kafin a sallame ta Tun daga ranan kuma Khalil yasoma bata maganin hana ɗaukan ciki batare da sanin ta ba, ita a ganin ta duk cikin drugs ɗin da aka bata ne a asibiti tunda wani lokacin shi ke bata magungunan, kuma bata taɓa saka wa aranta zai iya cutar da ita ba bare tayi tunanin wani abu, sosai yake matuƙar tausaya mata baya son tasake shan wahala kamar yanda tasha a baya, duk da yana son yara amma hakan shine mafitan da zai iya taimaka mata idan har yana tausayin ta A sannu a sannu rayuwa taci gaba da tafiya, tun Saleema na damuwa da matsalan da take fama dashi tunda itama tana ƙaunar yara har dai tacire komi a ran ta, ta buƙaci a dawo mata da Husna taci gaba da riƙe ta amma firr Ummi taƙi tunda har yanzu jiya iyau take, yau lafiya gobe ciwo, kuma Ummi tayi tayi takawo mata ƴar aiki but Saleema ta baɗe ma idanun ta toka akan baza'a kawo mata ƴar aiki ba, ita ta saka a ranta duk ƴar aiki tana ƙwace Mijin matar gida ne, shiyasa take jin tsoron a kawo mata ƴar aiki watarana taƙwace mata miji, anan Ummi tace "to tunda baza ta yarda akawo mata me taimaka mata ba dole tahaƙura da rainon Husna har sai taji sauƙi", ba da son ranta ba haka tahaƙura Khalil na iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya taimaka mata ainun, a haka zaman su yaci gaba har zuwa wani lokaci, kuma har a lokacin soyayyar Halwa na nan cikin zuciyar sa sai dai ya binne abun aransa tunda babu yanda zai yi Ita kanta Halwan abun da take ji akan sa ne har yanzu takasa sakin jiki dashi bare su saba, ko magana zata iya ƙirga iya adadin da yataɓa shiga tsakanin su, sau tari idan tayi tunanin komawa gidan Saleema don ta tayata zama sai ta fasa, bata son ko kaɗan abinda zai sa su haɗa hanya, duk da har yanzu batasan menene musabbabin abinda yasa take jin haka daga gare shi ba, amma ita a ganin ta nesa dashi shine kwanciyar hankalin ta Har yanzu kuma bata taɓa tunanin yin saurayi ba duk da kuwa ansha biyo ta, amma a ranan farko take taka ma mutum burki Ummi kanta sai da tazaunar da ita akan tadena koran samari auren nata shine abunda yadace da ita, amma ita Halwa abinda take hangowa tabon da ɗa namiji yayi mata a rayuwa, ta tabbata ko wanene zai so ta idan har yasan da Husna wacce tahaife ta bata hanyar aure ba to zai tafi yabarta, bata son taba ma namiji yardan ta a karo na biyu, tunda wanda yafi kowa sanin ta a duniya kuma yafi kowa sanin me zata iya aikata wa ya juya mata baya akan hakan, tayi imani ko waye ma hakan zai mata, shiyasa maganin kar ayi kar a fara, ta yarda zata ci gaba da rayuwan ta ahaka har ƙarshen numfashin ta, idan har ba Nura bane yadawo gare ta to bata jin zata iya auruwa A yanzu haka ta shiga aji na biyu, babu abinda tasaka a gaba sai karatu, ko ƙawaye taƙi yarda tayi har yanzu, sai dai mutunci kawai da take yi da wasu daga cikin ƴan ajin su Har yanzu har gobe tana tunawa da ƙawarta Zainab, sau tari tana tunanin zuwa koda gidan su ne, amma kuma hakan na nufin kamar ta tona ma kanta asiri ne duk ranan da takoma wajen waɗanda suka santa, kuma hakan na nufin zubar da mutuncin su Baba kamar yanda suka guda tun farko, wannan dalilin yake saka wa tafasa zuwa. . *____________________________* Baku tambaye Ni labarin Haris ba? Tunda baku tambaya ba nima bari in ƙyale KU, byeeee👋👋👋 sai ajiman ku ko in CE sai gobe.😅🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ _kar ku manta don Allah 🙏🏼ku danna Vote sannan kuyi comments don jin ra'ayoyin ku, na gode._ [11/24/2020, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Eight* ________🎓Haris ɗan wani babban attajiri ne ɗan siyasa, yanzu haka yana riƙe da kujeran Minister, shi ɗaya ne ɗa wajen iyayen sa duk da iyayen Familyn su ɗaya ne kuma babban Family ne dasu Ya taso cikin gata sosai, babu abinda yarasa a rayuwan sa, wannan dalilin ne yasa yake taka duk wanda yaso yakuma hukunta duk wanda yake ƙi, sabida yana da ɗaurin gindin mahaifin sa don ko kaɗan baya ganin laifin sa Haris yana da son mata da yawa sannan kuma yana da farin jinin ƴan matan, su da kansu ƴan matan suke kawo kansu wajen sa don yayi amfani dasu yabiya su kuɗi, duk da sau da dama suna kawo kukan su akan ya taimaka ya aure su amma shi a ganin sa babu macen da ta'isa yaso ta, shi dai kawai ya san mata a wajen sa su biya masa buƙata ne yajefar dasu don basu da wani Amfani Ana cikin haka kwatsam yazo giftawa ta hanyar makarantar su Halwa yakusa bige ta, tun a lokacin da yaganta yakamu da tsananin kaunar ta har yana jin koda zai yi aure to babu shakka ita zai aura, duk da alokacin mafi rinjaye na zuciyarsa sha'awar ta ce, amma kuma ita kaɗai ce yake iya mata kallon wacce zata iya kasancewa matar sa anan gaba Sai dai abinda be sani ba Halwa ta mutu a ƙaunar Nura a lokacin, duk da alokacin yaso yanuna mata kuɗi da gadara, amma da yaga yarinyan tana da taurin kai babu yanda zai yi yasame ta sai yakoma yana bin ta talalama Sai kuma tsautsayi yagifta a ranan da Halwa tamare shi, wannan dalilin ne yaɗau alwashin sai yayi mata abinda baza ta taɓa mantawa dashi ba, domin kuwa tunda yake babu wanda yataɓa taɓa masa lafiyan jiki A lokacin babu abinda be sani akanta ba, har soyayyar da suke yi da Nura ya san komi sabida yana da yaran da suke bibiyan masa ita Abu na farko da yasoma yi shine neman Nura, har gida aka kawo masa Nura kuma yafaɗa masa buƙatarsa, a lokacin Nura be amince ba sai da yaji kuɗi Miliyan uku da yayi masa alkawarin zai basa in dai zai sadaukar masa da budurcin Halwa, shi a ganin sa idan har yakawar da sha'awar Halwa aransa to tabbas duk wani soyayya da yake mata zai gushe, wannan dalilin ne yasaka yanemi aikata mata fyaɗe bayan ya nemi taimako wajen Nura Shi kuma Nura babu musu ya amince, a ganin sa idan har yasadaukar da budurcin Halwa akan wannan zunzurutun kuɗin be faɗi ba, kuma hakan yana ganin dama ce tazo mishi da zai yi kuɗi batare da yasha wahala ba, sannan yarigada ya saka ma ransa shi zai auri Halwa ɗin yarufa mata asiri tunda SHINE SILA, kuma shine zai ɗau alhakin duk abinda zai same ta don yarage girman laifin sa Take nan ya amince sannan suka shirya yanda za'a yi har Halwa tazo hannun Haris, kamar yanda kuka gani abaya Duk wannan abinda yafaru da Halwa da haɗin bakin Nura, sannan kuma lokacin da yaji maganar ciki hankalin sa yayi mugun tashi duk da alokacin yana tunanin bazai iya auren macen da yasan ba ta tare da mutuncin ta ba, anan ne dabara yazo masa har yanuna shi be san da maganar Fyaɗen da akayi mata ba don kawai ya yakice ta ajikin sa Haris kuma tun sanda yayi mummunan aika-aikan nan yakoma Abuja kasancewar acan yake aiki, yana kula ma mahaifin sa da ƙaramar Companin sa da yabuɗe na Shinkafa, amma me tunda yakoma sai yazamana bashi da sukunin zuciya, ƙaunar Halwa tayi masa bakeke a rai ta hana sa saƙat, be taɓa tunanin sonta ya kai haka ba sai da yayi nisa da ita, ya so yadanne yajure ko zai manta da ita amma hakan ba me yiwuwa bane Dole yadawo gida don ganin ta ko yaji sanyi a ransa, lokacin watan sa biyu acan kuma a lokacin tuni Halwa tayi wajen two weeks da barin gida Dawowar sa da jin abinda yafaru wajen Nura hankalin sa yayi ƙololuwar tashi, yayi baƙin cikin koran ta da sukayi da cikin sa ajikin ta, ya sake shiga damuwa matuƙa, haka ya bazama neman ta ko Allah zai sa adace, domin ya rigada ya ɗau alwashin muddin yaganta zai aure ta kuma su raine abunda zata haifa, yana matuƙar son ta bazai iya rabuwa da ita ba, har Gombe can dangin mahaifin ta sai da yaje amma akace bata zo ba, su ma alokacin suka ji abinda yafaru, sai dai basu wani damu ba tunda Mama ta faɗa musu cikin Shege tayi suka koro ta nan ashe bata zo ba, su aganin su hakan ma da tayi yadace tunda ko tazo su ma ɗin korata zasu yi don baza su iya riƙe ta da abun kunya ba Rayuwa ta sauya ma Haris matuƙa ya shiga damuwa sosai akan rasa Halwa wanda har sai da yakwanta ciwo, kullum bashi da buri idan ba yahaɗu da ita ba, a haka iyayen sa suka tilasta masa auren ɗaya daga cikin dangin su, domin su a ganin su idan har yasamu mata hakan zai dawo masa da nutsuwar sa, duk da dai basu san musabbabin abinda yafaru ba amma sun san cewa akan mace yashiga wannan halin, tunda be da abin faɗa sai sunan ta Be musa musu da auren ba tunda shima hankalin sa baya jikin sa, ahaka akayi auren Amarya Zubaida tatare a gidan auren ta, da daɗi babu daɗi haka tazauna dashi tunda dama ita tana matuƙar ƙaunar sa, haka rayuwa taci gaba da tafiya har komi yalafa ma Haris duk da har yanzu ƙaunar Halwa na ransa sai dai yanzu ya cire duk wani damuwa aran sa ya dawo daidai yaci gaba da aikin sa, sai dai yaƙi komawa Abuja acewar sa anan Katsina Yakamata yazauna yayi aikin sa koda Allah zai haɗa sa da Halwa, baya son ko kaɗan yayi nisa da garin duk da be san cewa tana nan ko bata nan ba Haka shekara ɗaya da watanni yashuɗe Zubaida bata taɓa koda ɓari ba, gashi burin iyayen sa su samu jikoki masu yawa tunda shi kaɗai Allah yabasu, hakan sosai yaɗaga musu hankali har shi Haris ɗin don shima yana son ganin yaran sa, don haka suka soma ziyartan asibiti amma sakamako ya nuna lafiyan su ƙalau lokaci ne be yi ba Ana cikin haka Mahaifiyar Haris tasake ce masa yayi aure domin ita bata yarda matsalan ba daga wajen Zubaida yake ba, shi kuma Haris ko kaɗan baya ƙaunar tara mata da yawa don haka yabijire mata duk da kuwa ba wai yana son Zubaida bane amma suna zaune lafiya sosai sabida kyautata masa da take yi An kai ruwa rana kafin Haris yayarda aka yi masa aure, don iyayen nasa duk sun goyi bayan ƙara auren nasa tunda suna son suga jikokin su nan kusa, duk da kuwa shekara biyu kenan da auren Haris ya rigada ya sa aransa duk sanda yahaɗu da Halwa idan har zata aure sa to tabbas sai ya rabu da duk matan nasa tunda shi a tsarin sa mace daya yake so, sosai yaji daɗin cikin da tatafi dashi, kuma hakan yasa ya gane cewa shi ɗin yana haihuwa Allah ne be kawo ba, bashi da buri a yanzu illa yaga abinda tahaifa masa, ƙaunar ɗan nasa da be taɓa gani ba tuni ya shiga ransa sosai Da maganar ƙara auren nasa da auren be fi wata biyu ba akayi komi aka gama, Amaryan sa Fahima ta tare a sabon gidan da mahaifin shi yagina masa tare da Uwar gida Zubaida Itama dai tunda tazo ɗin bata taɓa koda ɓatan wata bane, har sanda itama tashafe shekara ɗaya curr kafin Allah yabata Ciki, zo kuga murna wajen Familyn baki ɗaya don kowa ya ƙosa yaga yaran Haris, iyayen sa babu wanda yakai su murna, haka akai ta tattalin Fahima da ɗan tayin cikin ta Sai dai tunda tasamu cikin babu lafiya, yau suna asibiti gobe suna gida, yana watanni uku tayi ɓarin sa wanda har sai da aka dangana ga asibiti saboda yanda take zuban jini ta fita hayyacin ta gaba ɗaya, haka aka ɗauke ta ranga-ranga aka nufa Hospital da ita duk hankalin su a tashe. ______________________ A wannan lokacin itama Saleema ashe ciki ya shiga jikin ta, duk yanda kaso da dabara Allah idan yariga yaƙaddara abunsa to babu yanda zakayi, duk maganin hana ɗaukan cikin da Khalil yay ta bata amma a banza gashi ta samu shigan ciki har na wata ɗaya kamar yanda idan yakai hakan take ɓarin sa wannan ma karon hakan tayi, sai dai na wannan karon yafi na kowanne baƙin wahala Tunda aka kai ta asibiti suke sintiri su ji me zai biyo baya amma babu likitoci babu alamun su, sai da akayi kamar mintuna 30 kafin suka fito suka nemi jini, tana buƙatar jini leda huɗu saboda ta bala'in zub da jinin ta Haka aka ɗibi na Khalil dana Abba, sai aka siya ɗaya duk aka saka mata, su kansu Likitocin basa tunanin ma ko zata iya rayuwa a yanda take, ko numfashi bata yi sai da taimakon Oxgyen Likitan ta yarigada yayi ma su Abba bayani dole sai an juya mata mahaifa sabida idan taci gaba da samun ciki to ƙarshe rasa ta zasu yi har abada, yanzu ma basu da tabbacin ko zata iya rayuwa. Can ɗakin da aka kwantar da Saleema, su Ummi ne suka shiga tare da Halwa, gaba ɗayan su hawaye suke yi, yanda suka ganta tamkar matacciya hankalin su ya daɗa tashi ainun, Halwa kasa jurewa tayi tarufe bakin ta tafita dasauri cikin ɗakin, wani lungu tasamu tasoma gurzan kuka kamar zata shiɗe, kuka sosai take yi na tausayin Saleema Haris lokacin yashigo asibitin kawo ma Matar sa abubuwan buƙata tare da abinda zasu ci, tunda a ranan kwanan ta biyu a asibitin kuma har tasamu sauƙi ana saka ran sallaman su yau ko gobe Tunda yashigo idanun sa yasauka kan Halwa da tahaɗa kai da gwiwa tana ta sharɓan kuka, sosai yaji babu daɗi aran sa, haka kawai kuma yaji yana son ganin ko wacece yasan damuwar ta, sai kallon ta yake yi kamar yaje sai kuma yashige cikin asibitin yanufi ɗakin da aka kwantar da matar sa Ƙanwar Maman Fahiman ce take jinyan ta, su biyu ne a ɗakin Yana shiga suka gaisa ya'ajiye kayan da yazo dashi, tunda yazauna yarinyan da yawuce tana kuka ita ce tahana zuciyarsa sukuni, daga ƙarshe sai yamiƙe yafito don zuwa wajen ta yatambayi abinda ke damunta. [11/24/2020, 9:03 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ _Wannan shafin naku ne masoyana na cikin group ɗin Khaleesat Haydar, na gode da nuna soyayyar ku gare Ni, Allah yabiya._❤️ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Nine* ________🎓Yana zuwa wajen sai dai babu ita, ya dudduba amma be ganta ba don haka yakoma cikin ɗakin da aka kwantar da Fahima, dama kawai don ta tsaya masa a rai ne but tunda yaduba be ganta ba sai be sake tuna ta ba har yabar asibitin. ____________________ Halwa tana tashi a wajen komawa ɗakin tayi, sai dai tana zuwa bakin ƙofa kunnuwan ta suka jiye mata maganganun Abba dake faɗa ma Ummi matsalan Saleema ɗin, sai kawai tazame nan ƙasa tasaki kuka me sauti, daga inda take zaune tana jin kukan Ummi itama don takasa jurewa, sai da Abba yayi ta rarrashin ta yanuna mata zata iya damun Saleema idan bata dena kukan ba tunda an ce kar suyi hayaniya da zai dame ta, hakan yasa Ummi tarage kukan ta takoma kukan zuci da hawaye Abba ne yafito yatarda Halwan anan ƙasa tana nata sharɓan kukan, gaba ɗaya idanunta sun rine sun kumbura suntum wanda kallo ɗaya zaka yi mata katabbatar ta jima tana kuka yanda har fuskarta sai da yakumbura "Subhanallah.. Daughter me kike yi anan? Kukan me kike yi?" Yatambaye ta yana saka hannu yaɗago ta Halwa bata iya bashi amsa ba sai ƙara sautin kukan ta da take yi, duk da kuwa ta toshe bakin ta da Hijabin ta hakan be hana an ji fitan sautin kukan ta ba Dafa kanta Abba yayi cike da ƙarfin halin sa yace "kiyi shiru kinji? insha Allahu ƴar uwanki zata samu sauƙi ki dena kuka haka nan". Ya daɗe yana rarrashinta kafin yabuɗe mata ƙofar ɗakin yabata umarnin tashiga, shi kuma yajuya yatafi. Tana shiga taƙarisa gaban gadon inda Ummi ke zaune ta tasa Saleema agaba tana zirarar da hawaye Gefen gadon taɗan ɗofana mazaunan ta tana kallon Saleeman itama, wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta sabida tausayin ta, lumshe idanuwan ta tayi tabuɗe su akan Ummi da har yanzu ko ƙifta idanu bata yi, cikin rawan murya tace "Yanzu shikenan Ummi.. baza ta haihu ba? Meyasa za'a juya mata mahaifa? Meyasa baza'a nema mata magani ba? Don Allah.. kar ayi.. gaggawan wannan..aikin". Taƙarike maganar nata cikin tsananin rawan baki da jan numfashi Itama Ummi numfashin taja cike da sanyin murya da idan kaji zaka san tana cikin matuƙar damuwa tace "Ni kaina bansan wani irin ciwo ne wannan dake damun ta ba, sai dai sun tabbatar mana akwai wasu tsirrai a cikin mahaifan ta da baza su taɓa bari ta raini ciki ba, sannan kuma mahaifan ta babu ƙarfi ko anyi mata aiki ba lallai ne asamu nasara ba". Halwa tace "Ummi idan har za'a iya dashen cikin ajikina Ni zan iya rainon mata, zan haifa mata idan har zata ga ɗan ta a duniya, a shirye nake in sadaukar da komi nawa don samun farin cikin ta". Ummi kallon Halwa take yi kamar bata gane me take nufi ba Sai Halwan tasake cewa "Ummi ki duba magana ta, idan har Saleema tasan da cewa an juya mata mahaifa hakan na nufin baza ta ƙara haihuwa ba to zata shiga matsanancin damuwa, kuma kinsan tana da ciwon zuciya idan hakan yayi tasiri zamu iya rasa ta, tunda ina da hanyan taimakon ta zan rainan mata cikin in haifa mata sai in bata yaron ta". "Halwa idan har na amince za'a yi hakan Mahaifin ta da Mijin ta ba lallai su yarda ba, bansan me zan faɗa musu ba". Daga maganar Ummin sai suka yi shiru gaba ɗayan su suna tunani A lokacin ne Mom suka zo ita dasu Dad har da Khalil dasu Sameer, gaigaisa wa akayi tare da tambayan me jiki? itama Halwa tagaishe su suka amsa cikin farin ciki, daga haka bata ƙara cewa komi ba tana jin su suna maganan su, daga baya su Dad suka fita ɗakin yarage daga Mom sai Ummi sai ita Halwan, har sai da likita yazo kafin suka fito waje Sai dare ita Mom tatafi gida lokacin Khalil ya dawo sai yatafi da ita Ita kuma Halwa sai da Larai takawo musu abinci sannan suka koma tare A ranan Ummi ta kwana ne da maganganun Halwa a ranta, sosai tahau tunanin neman mafita, daga ƙarshe kuma tayanke shawaran zata soma tuntuɓan mijin Saleema da maganar idan ya amince tasan sauran babu matsala Da sassafe Khalil ɗin shi yasoma zuwa, Ummi batayi ƙauron baki ba tafaɗa masa komi da kuma taimakon da Halwa tace zata yi ma ƴar su Khalil shiru yayi kawai yana sauraron Ummi har sanda tagama maganar ta, lokacin hawaye kawai take yi Sai tausayin ta duk yakama sa, shi kansa zai so hakan sabida tsananin tausayin Saleema dake ransa, yasan da cewa idan har taji komi zata shiga wani hali sosai, ba abu ne me sauƙi ba ace baza ka taɓa haihuwa ba bare kuma fa waɗanda suke son ƴaƴan, yana matuƙar tausayinta ta yanda Allah yajarabce ta da cututtuka kala-kala, gwara shi namiji ne yana da damar da zai iya ƙara aure yahaihu da wata matar, idan har hakan shine maslaha to ya yarda zai taimaka mata, idan tasamu ɗanta ko guda ɗaya ne hakan zai sanyaya mata ranta, sannan ma ba wai wata daban ce zata rainan masa cikin ba Masoyiyarsa wacce yake matuƙar ƙauna aransa ne zata raini cikin, ko babu komi zai yi farin ciki da hakan Don haka koda yanuna ma Ummi ya amince tayi farin ciki sosai, su biyun suka nufi office ɗin Doctor sai suka bar Halwa don alokacin tarigada tazo Sun jima suna tattaunawa, duk da shi doctor ɗin ya nuna musu kuskuren yin hakan tunda musulunci Bata yarda da hakan ba, amma kuma duk kansu sun rigada da sun san hakan mafita kawai suke nema, ba don komi ba sai dan taimakon Saleema, sun manta da cewa haka ƙaddaran ta yake, sai dai sun san idan da lafiyan ta lau ba ta ɗauke da ciwon zuciya tabbas haka nan zata ɗau ƙaddaran ta Kasancewar akwai kayan aikin a asibitin don haka anan suka shirya yin aikin Doctor shi da kansa yayi ma Abba bayani kamar yanda suka shirya, kuma Ummi bata son Abba yasan da zancen, don haka Doctor yayi masa bayani akan baza su juyar mata da mahaifa ba zasu soma ɗaura ta a magani da suke sa ran za'a iya dacewa A zahiri kuma sun shirya za'a juya ma Saleeman mahaifa batare da kowa ya sani ba sai su kaɗai ɗin, ko da nan gaba Halwa ta haifa mata yaron kowa zai ɗauka Saleeman ce tahaifa tunda sun san dama ba'a juya mata mahaifa ba, ita kuma Halwa zata koma gidan Khalil da zama ta raini cikin a sirri har tahaifa. ___________________________ Kwanan Saleema biyar kafin tafarfaɗo, tunda tafarka take kuka Ummi tayi rarrashin duniya taƙi yin shiru, duk hankalin Ummi ɗin ya tashi kar yazo wani abun yafaru da ita A lokacin Ummi ita kaɗai ce a ɗakin Sai doctor da yashigo yanzu yaganta tana kuka, yasoma tambayan Ummi abinda yafaru Cikin tsananin tashin hankali Ummu tace "wlh doctor bansan meke faruwa da ita ba, yanzu tatashi kuma tunda tatashi take kuka, nayi-nayi tayi shiru taƙi yi, yanzu nake shirin kiran ka sai ga ka ka iso". Kallon Saleema dake kwance tana sharɓan kuka yayi, cikin tausayawa yace "Saleema meke faruwa ne me yasaka ki kuka? Ko wani wajen na miki ciwo ne?" Girgiza kanta tayi tana kallon su da rinannun idanuwan ta wanda suka faɗa suka yi baƙi, ita kanta gaba ɗaya ta zurma ta faɗa sosai gunun tausayi "To menene faɗa min?" Likitan yasake tambayar ta Cikin kukan take cewa "Doctor.. cikinaa.." Sai tasoma numfarfashi kamar ranta zai fita "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Ummi tafaɗa cikin ruɗewa tana ruƙo ta tare da fashewa da kuka Shima Doctor ɗin ya ruɗe Nan da nan yamatso da zumman taimaka mata Sai tasake cewa "doctor.. cikina.. ya zube ko?" Duk kan su shiru suka yi don basu san amsar da zasu bata ba, ita Ummi kuka ya hana ta magana Sai Doctor ne yayi ƙarfin halin kwantar mata da hankali "Don Allah Saleema ki kwantar da hankalin ki, yanzu insha Allahu mun samo matsalar ki komi zai wuce kinji? Kiyi haƙuri kar ki saka ma ranki damuwa tunda yanzu lafiyan ki muke so, Ummin ki zata yi miki bayani kinji kiyi shiru". Ummi ma cikin son ƙara kwantar mata da hankali tace "my Dear ki dena kukan yanzu komi yazo ƙarshe kinji?". Sai tasaka hannu tana share mata hawayen Doctor yace "Sister yanzu abata ko ruwan tea ne tunda jikin ta babu ƙarfi, idan nadawo zan yi mata allura sai in saka mata Drip, ki kula da ita sosai Please". Gyaɗa kanta Ummi tayi sannan tace "to doctor". Sai da yasake duba ta tare da yin mata tambayoyi kafin yafice. Ummi taimaka mata tayi tatashi zaune, tagyara mata pilow abayan ta yanda zata ji daɗi sannan takoma tazauna tana kallon ta, cikin tausayin ta tace "Daughter don Allah ki dena kukan haka nan, kinsan bazan ji daɗi ba idan naga hankalin ki ba'a kwance ba". Share hawayen ta Saleema tayi wasu na sake fitowa, cikin muryan mara lafiya sosai tace "Ummi shikenan idan nasami ciki zai dinga zube wa bazan haihu ba? Kullum haka zan riƙa shan wahala idan na samu ciki?" Hannun ta Ummi taruƙo cikin lallami tace "kar ki damu komi ya wuce zaki haifi yaron ki kema?.." "Taya Ummi bayan ina da matsala?" Takatse Ummin da faɗin hakan idanun ta na zirarar da hawaye Ummi har ta buɗe baki zata yi magana Halwa taturo ƙofan tashigo, daga school tabiyo ta nan tunda dama haka take yi Ganin Saleema zaune ya matuƙar faranta ranta, nan da nan tawashe bakin ta tanufo bakin gadon tana faɗin "Sister kin tashi?" Sai kuma tasauya fuska tana kallon Ummi tace "Ummi me yafaru ne meyasaka take yin kuka?" Numfashi Ummi taja kafin tace "tunda tatashi take yin kuka sabida cikin ta ya zube". Kallon ta Halwa tayi kafin tariƙe ɗaya hannun ta da Ummi bata riƙe ba tace "Sister meyasa zaki riƙa saka ma kanki damuwa bayan kinsan kina fama da ciwo? Don Allah ki dena in ba so kike mu ma mushiga wani hali ba". Cikin rawan baki Saleeman tabuɗe baki zata yi magana sai kuma takasa sabida kukan da yataho mata, saurin duƙar da kanta tayi tana sakin kukan ahankali Itama Halwa sai tasoma kuka tana sake riƙe hannun ta sosai Ummi tace "kiyi shiru don Allah Saleema Allah ne yabaki cikin nan kuma shine ya'amsa ko baki yarda da ƙaddara bane?" Shiru Saleeman tayi sai dai bata yi magana ba tana sauraron Ummi ɗin da taci gaba da maganar ta, cakk tahaɗiye sauran kukan nata tana ɗago kanta tana kallon Ummin, sai kuma takalli Halwa da tasakar mata murmushi tana gyaɗa mata kai alaman tabbaci da abinda Ummi ke faɗi Shafa fuskar ta Ummi tayi tana murmushi tace "Halwa ta amince zata rainan miki cikin ki har tahaifa miki, sai dai ban sanar ma Abban ki ba don kar yahana, amma kuma da yardan Khalil muka yanke hukunci, yanzu kar ki bari Abban ki yaji ko kuma wani kinji? Mun yanke hukunci Halwa zata yi rainon cikin a sirri ne". Saleema kallon Halwa kawai take yi cike da farin ciki, tabbas bata san da bakin da zata yi ma Halwa godiya ba, kawai sai tafashe da kukan farin ciki tana faɗin "Wlh bansan da bakin da zan miki godiya ba ƴar uwata, amma na san cewa..." "Shiiiiiiii... Yi shiru my Sister". Halwa tafaɗa tana rufe mata baki, sannan taci gaba da faɗin "Duk abinda zan miki Sister babu godiya a tsakanin mu, ke ce kika taimaki rayuwata a lokacin da narasa tudun dafawa, inda baki shigo rayuwata ba a yanzu bansan wani hali zan shiga ba, duk abinda zan yi wlh sister bazan taɓa biyan ki ba don haka kar ki soma kiyi min godiya kinji?" Taƙarike maganar tana cire hannun ta kan bakin Saleeman, idanun ta cike da hawaye Murmushi Saleema tasaki hawaye na zirara a kuncin ta Hannu tasaka tashare mata lokacin itama nata sun zubo Ummi kuwa kallon su take yi cike da farin ciki, ta gode Allah da yahaɗa su da Halwa, idan ba ita ba babu wanda zai iya taimaka ma ƴar su, tabbas ta cancanci Godiya me yawa Murmushi tayi tace "yanzu to bari in haɗa miki tea ɗin kisha kar doctor yadawo tunda hankalin ki ya kwanta". Kallon Ummin suka yi gaba ɗaya suna murmushi Vowel tasoma ɗauko wa tare da ruwa tace "ki wanke bakin ki don kiji daɗin bakin, bari in taimaka miki". Amsar Vowel ɗin Halwa tayi tace "kawo Ummi bari in taimaka mata". Da taimakon Halwa Saleema tawanke bakin ta don ko kaɗan bata da ƙarfi ajikin ta, bayan ta gama tasha tea ɗin kaɗan Doctor da yadawo yaɗaura mata Drip sannan yabata magani, babu jimawa tasoma barci tunda har da maganin barci aka bata don samun hutun ta Sanda su Abba suka zo suka ji ta farka jikin kuma alhmadulillah sun ji daɗi sosai, tunda basu yi zaton hakan ba, amma Alhmadulillah kowa yake faɗi. [11/26/2020, 6:00 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Ten* ________🎓 Satin Saleema biyu acikin asibitin kafin abata sallama tunda ta samu sauƙi sosai A ranan da aka sallame ta Ummi tasamu Abba da maganar komawar Halwa gidan Saleema ɗin a matsayin zata zauna da ita Abba be kawo komi akai ba ya'amince tunda shi da kansa Khalil ɗin yabuƙaci hakan kamar yanda Ummi tafaɗa masa A ranan Halwa tahaɗa kayan ta da komi drever yakai ta gidan, ɗakin da Lubna tazauna ada nan aka gyara mata komi sai da Khalil yasauya mata na ciki Wannan ranan kuma tazo ma Khalil cikin wani irin farin ciki, sosai yatsinci kansa a matuƙar murna kasancewar sa gida ɗaya da abar kaunar sa. Tun daga ranan Halwa take musu komi girki, gyaran gida da duk abinda yadace, har alokacin kuma gaisuwa kaɗai ke haɗa su Ahaka har kwanaki suka shuɗe inda Saleema tasake samun sauƙi sosai, a lokacin ne kuma suka shirya gaba ɗaya suka tafi asibiti inda za'a yi aikin saka ma Halwa ƙwayoyin haihuwar su don tahaifa musu ɗa, Ma'ana Invibrosfertilization a turance A can suka haɗu da Ummi tana jiran su, babu ɓata lokaci Likita yahaɗa duk abinda Yakamata sannan aka shigar dasu ɗakin Theater aka yi, a lokacin ne kuma aka juyar ma Saleema da mahaifa batare da ta sani ba, tunda ita a tunanin ta duk aikin da za'a yi ne wajen saka ma Halwa ƙwan haihuwar ta Har yanzu basu faɗa mata za'a juyar mata da mahaifa ba sai zuwa nan gaba idan hankalin ta ya kwanta sanda Halwa tahaifa mata yaron ta, hakan zai sa baza ta wani tada hankalin ta ba. ****** ****** ******* ***** ******* *TWO MONTHS AGO* A cikin wannan watannin sai ga Halwa ta soma Laulayin ciki, koda suka je asibiti an tabbatar musu tana ɗauke da cikin dagaske har na tsawon watanni biyu Zo kuga murna wajen Saleema da Khalil, sosai suke tsananin murna, ita dai Halwa sai dai tataya su da murmushi Tun daga ranan kuma sai yazamana babu abinda Halwa take yi sai zaman hutu idan taje makaranta ta dawo, Khalil da kanshi wani lokacin yake kai ta school idan tana da lectures ɗin safe, sai drever kuma yaɗauko ta Sun saba sosai dashi tunda yanzu suna zaune gida ɗaya, har hira suna yi tare Saleema bata barin ta tayi komi duk ita take yi yanzu duk da Halwan tana taimaka mata tunda cikin ba me laulayi sosai bane kamar yanda tayi na Husna me wahala Ummi ita da kanta tasanar da Abba Saleema na da ciki, sosai yayi farin ciki musamman jin cikin ya wuce wata ɗaya hakan na nufin an samu nasara kenan. ***** Yau ma tana da lectures ƙarfe 11:00am. Bayan ta shirya cikin blue and white colour ɗin atamfa ɗinkin riga da skert, tayi Rolling Farin gyale akanta, sai tasaka flet shoes shima fari da kalan baƙi a ƙasan, ta ɗau jakar ta kenan tana ƙoƙarin ratayawa Saleema tashigo ɗakin riƙe da Plate a hannun ta, tana sanye cikin atamfa ja da kalan ruwan Powder ajiki, ɗinkin riga da zani sai taɗaura zanin ta gefe, ɗankwalin kuma taɗaura sa normal Zuwa tayi kusa da ita tajanye jakan tana faɗin "ina zaki je baki ci abinci ba?" Murmushi Halwa tayi tana kallon ta tace "wlh sister bana jin yunwa ne". Hannun ta tajanyo suka zauna gefen gado tace "ai baki isa ba babu inda zaki je sai kinci wannan, shiyasa ma nashiga na dafa miki taliyan nan me ɗan romo-romo sabida yayi miki daɗi, kin gani ma har da yaji nazuba miki da yawa zai miki daɗi ai". Sai kawai Halwa tasoma dariya Itama kuma Saleeman dariyan tasoma duk da batasan me take ma dariyan ba, kafin taɗibo taliyan a cokali takai bakin ta tana faɗin "Haaa bakin ki". Hakan yaƙara saka Halwa tsananin dariya har tana tuntsura wa kan gadon Wannan karon baki Saleema tasaki tana kallon ta Kusan shuɗewar one minute kafin tace "wai menene kike ma dariya haka?" Tashi zaune Halwa tayi tana ci gaba da dariyan nata kafin tace "Allah dariya kike bani Sister kin maishe Ni tamkar yarinya". Murmusawa Saleema tayi tace "to ba dole ba kina ɗauke da cikin babynmu, nifa wlh ma kewar Husna nake yi dole zan saka Yaya Barrister yaje yaroƙi Ummi tabani ita". "Me kike ci na baka na zuba tunda ga sabon baby zai fito? kibar wancan me ƙwallon kan". Hararan ta Saleema tayi tace "Ummina ce me ƙwallon kai ko?" Sai Halwa tayi saurin girgiza kanta tana fiddo ido waje tace "wlh suɓutar baki ne". Sai da Saleema ta dara sabida yanda tayi maganar a tsorace "To shikenan naji amma kar ki sake, yanzu kici abincin kar kiyi latti". Amsan Plate ɗin tayi tana faɗin "wlh bana jin yunwa my sister don ke kawai zan ci". "To na gode yi maza kici sai kisha ruwa". Saleeman tafaɗa tana tsare ta da idanu Murmushi Halwa tayi lokacin da takai spoon ɗin bakin ta, ahankali tay taci ba don ranta na so ba don dai kawai ta faranta ran Saleeman, suna yi suna hira har tagama sannan Saleema taɗauko mata ruwa taba ta tasha suka fito Har wajen mota sai da taraka ta taga fitan su kafin tadawo cikin gidan. ****** ****** ****** ***** Ƙarfe 01:45pm. Khalil yabar office yanufi gidan su, yau a waje yayi parcking ɗin motan nasa tunda baya son yadaɗe, kwana biyu rabon sa da zuwa gidan shiyasa yau yayanke shawaran zuwa daga nan kuma yasanar ma Mom ƙaruwar da suka samu Saleema na da juna biyu Koda yayi sallama cikin parlour'n Mom ɗin ce kaɗai zaune, ta ɗan kishingiɗa kanta saman kujera tana ta faman kallo Sallaman sa shi yatada ita tana amsa mishi kafin tace "my son idanun ka kenan ko?" Shafa kansa yayi yana nufo ta Shi kansa yasan be kyauta ba, musamman yanzu da ba samun lokaci yake yi ba ko waya ba suyi a kwanakin Zama yayi yana kallon ta da tsadadden murmushin sa yace "I'm very sorry Mom kinsan aiki yayi min yawa shiyasa bana samun zuwa wlh, ina yini?" "Lafiya lau my son ya matar taka?" Mom ɗin ta'amsa masa cikin fara'a "Lafiya lau Mom tana gaishe ki ma". "Ina amsa wa, yanzu Sameer yafita baku haɗu ba?" Girgiza kansa yayi yana kallon ta, kafin yace "Mom babu lafiya ne?" "To lafiyan dai za'a ce, Aamir ne yake fama da zazzaɓi, duk da dai Baban nasa ma yace min ya samu sauƙi". Cike da damuwa Khalil yace "ayya bansani ba insha Allahu zan je gaishe shi yau ɗin nan". "To Allah yabaka iko". Sallaman Nazeefa yasaka suka kalli ƙofan suna amsa mata "Nazeefa an dawo?" Cewar Mom tana kallon ta da murmushi Itama Nazeefan murmushin take yi cike da farin cikin ganin Khalil tana tahowa ta'amsa mata da "Eh Mom Barka da gida". Sannan takalli Khalil ɗin da a yanzu yafito da waya cikin aljihu tace "Yaya ina wuni". Sai da yaɗago yakalle ta kafin yace "lafiya ya school?" "Alhmadulillah Yaya". Je ki cire kayan makarantan sai ki zo ki zuba ma Yayan naki abinci, yau babu Atine agidan". Kafin takai ga amsawa Khalil yayi saurin faɗin "a'a Mom bana jin zan iya cin komi yanzu". Mom ɗin bata tsawaita bincike ba tace "to shikenan". Ita kuma Nazeefa sai tayi hanyan ɗakin ta Mom tabi ta da kallo, kafin tajuyo ga Khalil dake latsa waya tace "Wai ni kam Auta dama akwai maganar da nake so muyi da kai". Be amsa mata ba illa ɗago kai da yayi yana bata attention ɗin sa Nazeefa da har ta shiga ɗaki tana ƙoƙarin rufe ƙofa tajiyo muryan Mom tana faɗin sunan ta, hakan yasa tadakata don jin me zata ce "Ni kuwa ina maka sha'awar Nazeefa". Kallon rashin fahimta Khalil ɗin yayi mata, kafin kuma yace "Mom sha'awa kuma? Kamar ya?" Murmusawa tayi tace "Ni naga tunda matar ka bata da lafiya kuma kaima kana buƙatan ƴaƴa, ba'a son ranan dacewa ba bare ta haifa maka, me zai hana kaƙara aure? Ga ƙanwar ka Nazeefa tunda ba wani matsala ce da ita ba sai ka aure ta, in yaso sai wani hidindimun dake kan Saleeman su ragu, kaima zaka fi samun nutsuwa ko?" Tunda tafara maganar yake yamutsa fuska, maganar tazo masa a bazata sosai, cikin rashin jindadin abinda tafaɗa yace "Momyyy why zaki yi irin wannan tunanin? Ni fa na ɗauki Nazeefa tamkar ƙanwata ce wacce muka fito ciki ɗaya da ita, ban taɓa kallon ta a matsayin da kike magana ba, don Allah ki dena wannan maganar ma kar wani yaji". Mom dariya tayi tace "sai kace wani abun kunya? Tunda baka so shikenan, dama sai da nayi ma Daddyn ku magana yace "shima babu ruwan sa idan ka amince to" tunda yanzu ka nuna baka so ai shikenan babu dole a zancen". "Kuma Mom komi yanzu ya zama normal tunda yanzu tana ɗauke da ciki har na tsawon Two month". Yayi maganar yana turo baki Da fara'an ta tace "haba dai? An dace kenan?" "Insha Allahu Mom haka muke saka rai tun da gashi ya wuce wata ɗaya". "Masha Allah, Allah Sarki wlh yarinyan nan tana bani tausayi matuƙa Allah yaraba lafiya, yanzu tana gidan su ne ko kuwa don kasan dai baza ta zauna ita kaɗai ba?" Khalil yace "A'a bata koma gida ba, sai dai Halwa tana zaune da ita". "To masha Allah haka ake so, har yanzu ita babu labarin komawar ta gidan mijinta ne?" Khalil ɗan waro ido yayi don be fahimci maganar da take yi ba Hakan yasa Mom ɗin tasake cewa "ina nufin ita Halwan tunda naji ance sun rabu da mijin ne". Ɓata fuska Khalil yayi yana shafa sajen sa yace "Ni bansani ba". Yanda yayi maganar ne sai da Mom tasake duban sa, sosai taga ɓacin rai a fuskarsa har a maganan da yayi sai da yanuna "Mom zan tafi". Yafaɗa yana miƙewa tsaye Itama miƙewar tayi tana faɗin "yauwa bari in baka saƙo sai kabata, ina zuwa". Wuce wa ɗaki tayi taɗauko tabashi sannan suka sake sallama yafice. **** Kuka Nazeefa tafashe dashi tana zame wa ƙasa, da rarrafe tanufi cikin ɗakin har zuwa bakin gado tahaɗa kai da gwiwa tasoma rera kuka ahankali, kukan rashin madafa a wannan halin da take ciki, shikenan tasan babu ita babu auren KHALIL tunda be taɓa mata kallon yanda take masa ba, infact ma ya ɗauke ta tamkar wacce suka fito ciki ɗaya ne, hakan yasa tasake fashe wa da kuka tuna abinda yace, sai dai yanzu tasan dole tararrashi zuciyarta tunda baza ta taɓa samun sa ba. [12/2/2020, 3:00 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Eleven* ________🎓 A parking lot yayi parking ɗin motan sa sannan yafito saƙale da briafcase ɗin sa a kafaɗa yanufi cikin gidan Yana shiga parlour'n da sallama a bakin sa Saleema tafito cikin ɗakin ta riƙe da waya, amsa masa tayi tana kallon sa cike da fara'a a face ɗinta sannan tanufe sa, jakan hannun sa ta'amsa tana mishi sannu da zuwa Amsa mata yayi yana ɗan guntun murmushi Har ta juya yariƙo hannun ta suka jera tare cikin ɗakin A gaban gadon suka tsaya ta'ajiye masa jakan tana shirin janye hannun ta yasake riƙe wa yana kallon ta, don haka bata yi yunƙurin sake janye wa ba tatsaya tana kallon sa cike da so Murmushi yasakar mata yana zama kan gadon kafin yajanyo ta ya'aza ta kan jinyan sa yana faɗin "yau Halwa taje school kenan tabar min matata ita kaɗai da kewa ko?" Murmushi Saleema tayi tana ɗan gyaɗa masa kai cike da kunyan sa Numfashi yaja yana lumshe idanun sa kafin yabuɗe akan ta, yanda yake mata wani irin kallon ƙurilla hakan yasa tayi saurin cewa "Uhmm abincin ka.. in kawo maka nan?". Shiru yayi kamar bazai ce komi ba har alokacin idanun sa na yawo ajikin ta, ahankali yaɗan matso da kansa kusa da fuskarta yaraɗa mata "Saiiiii nayiii wanka zan ciiiiii..." Yanda yayi maganar cikin jan kalmomin hakan yasa tsigan jikin ta miƙe wa, tayi saurin ɗaga kanta hakan yasa kansu yahaɗe waje ɗaya Dasauri yaɗan ja baya da nasa yana yarfe hannu cikin shagwaɓe fuska tare da runtse idanu yace "zaki fasa min kai ne?" Yanda yayi maganar yasa ta yin dariya itama tana sosa goshin ta tace "ya haƙuri ban kula ba". Taɓe baki yayi kafin yace "sai na rama". Kafin ma tayi magana ya ɗaura hannun sa akanta yazame ɗankwalin dake kan ta, sannan yamayar da hannayen nasa bayan ta yasoma jan zip ɗin rigan yana faɗin "bari muyi wanka tare ko?" Murmushi Saleema tayi tana Sad da kanta ƙasa Sai da yagama zage mata zip ɗin kafin yasake faɗin "zamu je gidan Bro.. Aamir yana fama da zazzaɓi, zuwa yaushe Halwa zata dawo?" "Zuwa 04:00pm. Tafaɗa min zasu gama lectures". Tayi maganar ahankali Shiru yayi kawai yaci gaba da zame mata hannun rigan, sai da yagama yaja sa ƙasa zuwa cikin ta, sannan yaɗaga ta shima yamiƙe, cakk yaɗauke ta suka nufi cikin Toilet ɗin batare da ya cire kayan ba. *30minutes* Khalil zaune kan dainning yana cin abinci, yana shirye cikin farar shadda ɗinkin jamfa wanda yayi matuƙar masa kyau sosai, hulan ƙube yasaka wanda aka saƙa shi da farin zare sai aka sirka da blue colour, don haka yasaka cover shoes ɗin sa da Wrest watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyan hannun sa kalan blue ɗin Fitowar Saleema cikin ɗaki yasaka sa ɗaga kai yana kallon ta, ƙare mata kallo kawai yake yi yana taunan abincin dake bakin sa Itama tana sanye da baƙin Material ne da ratsin fari, ɗinkin riga da skert ne wanda yazauna mata daidai, sai tayi ɗaurin ture kaga tsiya, sannan tayafa farin gyale har zuwa kanta wanda yarufe mata tulin gashin ta da yafito ta ƙasan ɗan kwalin, takalmin ƙafan ta Black Colour me ɗan tudu sannan sai jakan ta shima baƙi me matuƙar kyau da tsada, kallo ɗaya idan kayi mata zaka hango tsantsan raman da yake a fuskarta wanda yasa fuskarta yayi fayau sai dogon hancin ta da yaƙara fitowa sosai Har taƙariso wajen yana bin ta da kallo, sai da tazauna sannan yace mata "kin yi kyau Matata". Murmusawa tayi tana kallon sa itama, don ba ƙaramin tafiya da imanin ta yayi ba "Kayi kyau kaima". Murmushi kawai yayi yana ci gaba da cin abincin sa Itama kuma wayan ta taɗauka tana ƙoƙarin sake kiran Halwa sai ga kiran ta ya shigo, peacking tayi tana karawa a kunne cikin fara'a tace "My dear Ina kika shiga na kira baki ɗauka ba?" Daga can Halwa tayi magana cikin sanyin muryanta da koda yaushe a haka yake tace "wlh Sister muna lecture ne sai yanzu nafito afwan". "Babu komi ai, dama Yayana ne yace in faɗa miki zamu biyo mu ɗauke ki idan mun dawo gaishe da Aamir". Halwa tace "be da lafiya ne?" "Eh yana fama da zazzaɓi". "Eyya Allah Sarki Allah yaba sa lafiya". "Amin". Saleema ta'amsa mata Ɗan guntun dariya Halwa tayi tace "Sister kar ki manta fa ki riƙa yin practical kinsan yanzu kina da shigan ciki fa". Saleema kallon Khalil tayi Shima ɗin idanun sa na kanta tun sanda tasoma wayan, sai dai baya jin abinda Halwan ke ce wa Kau da kanta tayi tana murmushi tace "sis ai na gane, nariga na ɗau komi tun sanda kike da cikin Husna, so abu me sauƙi ne a wajena nima in yi na masu cikin". Sai kuma tasaki dariya tana faɗin "ok sai munzo ɗin ki kula min da Baby". Ciro wayan tayi a kunnen ta tana sakawa cikin jaka Shi dai Khalil kallon ta kawai yake yi batare da yace uffan ba, sai kuma ya ajiye spoon ɗin hannun sa yana miƙe wa yace "Tashi muje". Miƙe wa tayi tabi bayan sa suka fita, sai da yarufe ƙofan kafin suka nufi wajen motan yabuɗe mata gaban tashiga, sannan shima yazagaya yashiga yaja yanufi Gate yana horn Me gadi na buɗe masa yacilla motan waje Ko acikin motan hira suke ɗan taɓa wa, Saleema sai tambayan sa abubuwa take yi idan tagani ahanya, shi kuma yana bata amsa Suna isa yayi horn a bakin Gate ɗin, sai da me gadi yaleƙo yaduba wanene sannan yakoma yabuɗe masa, shigar da motan yayi yay parcking kafin suka fito, atare suka jera har cikin gidan Wannan zuwan shine zuwan Saleema na uku kenan Suna shiga da sallama Hakima dake zaune Aamir na kan cinyan ta ta'amsa musu, sai kuma tafaɗaɗa fara'an ta tana faɗin "Iyeee maraba da manyan baƙi, sannun ku da zuwa". Saleema zama tayi kan kujera tana murmushi Khalil kuma sai yanufi Hakiman yasaka hannu ya'amshi Aamir yana faɗin "a'a my Daddy Kai da zan zo in ganka akan gado ya naganka anan?" Yaron na washe haƙora cike da murna cikin tsamin maganar sa yace "Ankul ai na waice". "Haba dai?". Sai yagyaɗa masa kai yana tsalle a jikin sa kafin yace "wayyayi". Dariya gaba ɗayan su suka yi Zama Khalil yayi yaɗaura sa a jikin sa A lokacin ne Saleema suka gaisa da Hakima tana tambayan ta jikin Aamir ɗin "Ai gashi nan yaji sauƙi sai rigima". Khalil yace "wai haka Daddy kana rigima?" Cinno baki yayi gaba yana maƙe kafaɗa yace "kayya ne Ankul". Yanzu kam dariya sosai yaba su, har Khalil sai da yadara duk da be cika son yin dariya ba Hakima tace "iyeee Ni nake maka kayyan?" Sai yawaigo yana kallon ta yana ƙyafta idanu, kafin kuma yagirgiza mata kai alamun "a'a". Murmushi Saleema tayi tace "My son Ni baka ganni bane?" Sai yamayar da idanun sa kan ta, dasauri kuma yazamo a jikin Khalil ɗin yanufo gaban ta yana faɗin "Auncy.." "Na'am ɗan Aunty". Tafaɗa tana ɗaukan sa cike da fara'a Hakima miƙe wa tayi tana cewa "kunga na barku haka ban kawo muku komi ba kuma". Khalil yace "ina Bro ne ban ji motsin sa ba?" "Wlh ya koma Hospital yana da Patient". Hakima taba sa amsa tana ciro drinks cikin Fridge Sai kuma tajuya tana nufan wani ɗan ƙaramin table da aka jera plates da Spoons tare da Cups akai anyi danki dashi "Caa nake kunyi waya ai?" Tatambaye sa tana zaro plate ɗaya "No ban Kira sa ba". Zubo drinks ɗin tayi saman plate ɗin takawo musu, sannan takoma tazauna "Saleema tace "Aunty Ina Abida yau ban ji ta ba?" "Ai kam tana school bata dawo ba". "My Daddy zo muje mu yawata". Khalil yafaɗa yana miƙe wa tsaye Hakima kallon sa tayi tace "ya haka kuma zaka tafi baka ci komi ba?" Ɗaukan Aamir yayi yana bata amsa da "A ƙoshe nake ai, bari mu fita waje". Tunda yafice kuma sai sukai ta hira da Saleema. ***** Lokacin da suka dawo tare da Sameer suka shigo gidan Khalil nan yace "Saleema tatashi su tafi". Hakima sai tsiya take mishi wai yanzu suka zo har zasu tafi baza su kai musu dare ba Shi kuwa be ce komi ba Saleeman ce take ta dariya tana faɗin "zasu biya ɗauko Halwa ne". Sannan ne fa Hakima tayi shiru da bakin ta Har waje suka rako su suka hau mota suka bar gidan A lokacin ne Khalil yaƙyalla idanu yaga saƙon da Mom tabashi yaba Saleeman, shaf ya manta shiyasa yabar shi cikin motan, don haka ya ɗauka yamiƙa mata yana faɗin "Gashi in ji Mom ɗazu na manta ban Baki ba". Amsa tayi tana kallon ledan, sai kuma tabuɗe jaka tasaka tana cewa "Allah Sarki Mom ɗina, Allah yasaka da alheri, zan kira ta in mata godiya". Shi dai be ce komi ba illa murza sitiyarin da yake yi, ahaka har suka shiga cikin makarantan Saleema takira ta awaya tasanar da ita inda sukai parcking motan Don haka babu ɓata lokaci Halwa tafito cikin holl ɗin da suka gama karatu ta tunkari inda zata same su, tana sanye da niƙab da tasaka yanzu da zata fito har ta'isa wajen motan tayi Nocking Da farko da suka kalle ta basu gane ta ba, sai kuma Saleema tasaka dariya tana zuge glass ɗin tace "Kaii sis Wai dama kina saka niƙab ne idan zaki zo?" Murmushi Halwa tayi wanda basu san ma tana yi ba, idanun ta tasauke akan Khalil da shima yazuba mata nashi, tayi saurin lumshe wa tana buɗe su sannan tabuɗe bayan tashiga tana faɗin "Saboda ƴan saka idanu ne shiyasa nake saka wa, sannu Yaya". Taƙarishe maganar tana rufo ƙofan Jan motan yayi yana amsa mata da "yauwa, ya makarantan?" "Alhmadulillah". Tace ataƙaice Saleema tace "gaskiya ne Sister kuma yayi miki kyau fa wlh". Cire niƙab ɗin Halwa tayi tana saka wa ajaka tace "ko Ƴar uwa?" "Eh mana ki tambayi Yaya Khalil". Kallon gefen sa Halwa tayi sai suka haɗa idanu ta mirror, tayi saurin ɗauke kanta batare da tace uffan ba Shi kam be ɗauke idanun sa akan ta ba, kallon fuskarta kawai yake yi, a ransa kuma sosai yaji daɗin ganin ta da niƙab ɗin Saleema ce kaɗai take ta faman surutun ta Halwa na bata amsa a taƙaice Har yanzu bata iya sakin jiki a gaban sa, sabida yanda take ji a game dashi duk da kuwa sun ɗan saba ba kamar da ba. [12/2/2020, 3:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twelve* ________🎓 Koda suka isa gida Halwa wanka tasoma yi tasauya kaya zuwa riga da skert na kanti me ruwan bula, sannan tafito tasami Saleema a kichen tana ɗaura musu abincin dare Fita tayi tanufi kan dainning taɗibo abinci tasake dawowa cikin kichen ɗin tazauna akan Kujeran Robber dake ajiye gaban Freezer, Saleema na girki tana taya ta hira. Khalil kuwa ɗakin sa yawuce kai tsaye, cire kayan jikin sa yayi yasauya da farar jallabiya da gajeren wando sannan yafito parlour, Kallo yakunna yaɗau Remote yana sauya Channels, ya saka wannan yasaka wancan har sanda Halwa tagama cin abincin tafito don taƙara wani Tana fitowa suka haɗa ido dashi, ɗauke kai tayi tanufi kan dainning, tana cikin zuba abincin tatsinkayi muryan sa yana cewa "Maman Husna kawo min ruwa". Lumshe idanun ta tayi tana sauraron bugun zuciyarta dake fita dasauri-sauri, ware idanun tayi kansa wanda shima yazuba mata nashi idanun, dasauri taɗauke kanta tana nufan Fridge tabuɗe taciro masa sannan tahaɗo da cup tanufo sa, akan Centre table ta'ajiye masa tajuya da ninyan tafiya, batayi aune ba sabida yanda duk natsuwar ta yabar jikin ta sai ji tayi tay karo da Centre table ɗin ta tafi yarab ta faɗa kansa, sai gata ɗare-ɗare a jikin sa Kunya tsoro duk su suka taru mata lokaci ɗaya wanda hakan yasaka takasa tashi bare taɗago kai takalle sa, in banda gudun da zuciyarta ya ƙara kamar yafaso ƙirjin ta Shi kuwa abin ma dariya yaba sa, haka kawai yatsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, sai kawai yazuba mata idanu yana murmushi me sauti Lokacin ne kuma tasamu ƙwarin jikin da har ta'iya yunƙurin tashi, har a time ɗin bata iya kallon sa ba illa miƙe wa da tayi tana shirin barin wajen "Maman Husna halan baki gani ne kike son ki karya Ni?" Yafaɗa still yana murmushi Ɗago kai tayi takalle shi, sai kuma taɗauke kai tana murmushi bata iya cewa komi ba tanufi hanyan kichen dasauri Tana shiga Saleema ta ɗan kallo ta kafin tamaida kanta taci gaba da aikin ta Zama Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya har da dafe ƙirjin ta tare da lumshe idanu "Me yafaru ne Sister wannan murmushi haka?" Tatsinkayi muryan Saleema tana faɗin hakan Dasauri tabuɗe idanun ta suka haɗa ido da Saleema wacce tajuyo gaba ɗaya a yanzu tana kallon ta "Babu komi". Halwa taba ta amsa cike da sanyin muryan ta Sai kuma tamiƙe tana nufo ta "Da me zan taya ki?" Saleema tace "ai na gama, sai dai ki kwashe min zuwa dainning". "Ok". Tare suka fito kichen ɗin har a lokacin kuma Khalil na zaune a Parlour yana kallon sa Kallo ɗaya Halwa tayi masa taɗauke kai ganin sun haɗa idanu Kan dainning ɗin suka kai suka jera, sannan Saleema tanufi parlour'n tazauna gefen sa Halwa kuma sai tayi ɗakin ta dasauri "Sis Ina Zaki kuma?". Halwa da har ta buɗe ƙofan zata shiga tatsinkayi muryan Saleeman, sai tajuyo tana kallon ta tace "kawai zan ɗan kwanta ne kafin a kira sallah". "Kwanciya kuma yanzu? Ki dawo ki zauna anan zuwa anjima kya shiga ki kwanta". Gaba ɗaya kallon sa suka yi wanda kamar ba shine yayi maganan ba, don hankalin sa na kan t.v yana sake sauya Channel Takowa tayi tadawo tazauna can gefen su Su biyu kaɗai suke hiran su yayinda Halwa tamaida hankalin ta kan t.v amma tana sauraron su, idan Saleema tasako ta kuma tana bata amsa, har sanda aka kira sallah Khalil yatashi yashige ɗakin sa Su ma tashin suka yi don gabatar da farali. ****** ******** ******* Tunda Zainab tayanke shawaran fid da miji ko ta samu sauƙin nacin Nura hakan kuwa tayi, akwai wani saurayi Aliyu da suke makaranta tare, anguwan su ɗaya dashi sai dai ba layin su ɗaya ba, to shi yana degree ɗin sa ne a school ɗin, suna yawan haɗuwa a makarantan shiyasaka suke ɗan gaisawa har idan Zainab tana da assignment ko wani abinda bata gane ba kai tsaye wajen sa take zuwa, tunda dama sun san juna sosai a anguwan su magana ce kaɗai be haɗa su Wannan dalilin ne yasaka shaƙuwa yasoma shiga tsakanin su, har dai Aliyu yazurma son ta lokaci ɗaya, ahankali-ahankali dai bayan shaƙuwar su ta sake nisa sai yasanar mata da sirrin zuciyar sa Zainab bata wani ja aji ba ta amince don dama itama tana son sa aranta, komi nasa yayi mata, bare kuma dama neman saurayi take yi tayi aure ta huta. Aliyu na zuwa wajen ta, a school kuma koda yaushe suna tare hakan yaƙara ƙarfafa soyayyar su da shaƙuwar su, kuma a gidan su babu wanda be san Aliyu ba Umma ko kaɗan hakan be mata daɗi ba tunda Aliyu ko ƙwaƙƙwaran sana'a bashi dashi, iyakan dai karatun sa yasaka agaba sai kuma ɗan jiran shago da yake yi, sosai ran Umma yasake ɓaci musamman da tasan ko shi wanene don haka tasoma rura ma Zainab wuta dole tarabu dashi takoma ma Nura tunda shi yana da sana'ar sa Zainab ita kuma ta nuna mata sam ita Aliyu take ƙauna, hakan yajawo har sai da Umma tayi mata tsinannen duka Ba ƙaramin ɓaci ran Abba yayi ba, a ranan shima sai da yayi kamar zai duke Umma akan abinda tayi, wannan dalilin ne yasaka yanemi Aliyu yabashi damar yaturo idan har zai iya auren Zainab Duk da Aliyu be da wani abun yi sosai wanda ke kawo masa kuɗi, sai dai yana da ƴan uwa waɗanda ciki ɗaya suka fito su ne kuma suke taimaka masa a fannin karatun sa sabida suna da hali sosai, jiran shagon da yake yi yana yi ne kawai don rage zaman banza Koda Abba yayi masa zancen yaturo hakan ya faranta masa, kai tsaye sai yanufi gidan Babban Yayan su yasanar masa, dayike su ma suna son yayi aure sai Yayan nasa yace "yatafi zai neme sa idan suka yi shawara da Umman su". A cikin sati ɗaya har an nema wa Aliyu auren Zainab kuma Abba ya basu ita, sai aka saka ranan nan da wata uku bayan ta gama final exams ɗin ta da sati biyu, dama ƴan uwan sa zasu yi masa komi na bikin don haka basu wani damu ba koda aka saka ranan babu yawa. Fannin Nura kuwa yayi baƙin cikin hakan sosai, ya tabbata ya rasa Zainab bazai taɓa samun ta ba tunda yasan bata son sa, amma kuma har yanzu yaƙi ba ma zuciyar sa haƙuri be dena zuwa wajen ta ba. Sai mu ce Allah yakyauta maka. . _kuyi haƙuri da wannan babu yawa._ _sai kun ji Ni a next page._ _kar ku manta plz Vote and share 🙏_ [12/2/2020, 3:31 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Thirteen* ________🎓 *AFTER THREE MONTHS* "Wai jikin ne Sister?" Halwa tafaɗa lokacin da take zama gefen gadon Numfashi Saleema taja tana sake jan bargon da tarufe jikin ta dashi a lokaci ɗaya tana bata amsa "Wlh kuwa sis, gaba ɗaya bana jin daɗi yau, dama tunda naga a kwana biyun nan jikina ya soma kumbura na san akwai matsala". Cike da tausayin ta Halwa tace "eyya ko dai in Kira Ya Khalil mu je asibiti, don bana son wlh ciwon ki yatashi da tsananin nan". Ɗan guntun murmushi Saleema tasaki tana kallon ta cike da nuna jarumta tace "kar ki damu babu abinda zai faru, bari dai insha magani na sai in kwanta in ɗan samu barci insha Allahu zan ji daɗi domin barcin nake buƙata a yanzu". "Tom bari in ɗauko miki Maganin". Dasauri tamiƙe tazagaya side ɗin gadon tabuɗe drower taɗauko mata, tanufi Fridge tahaɗo mata da ruwa sannan tadawo tazauna "Tashi kisha". Tayi maganar tana ajiye goran ruwan da maganin ajikin ta Sai da tataimaka mata tatashi zaune kafin tabuɗe mata maganin taba ta tasha ta'ajiye ruwan a ƙasa "Ki ɗan tsaya yanarke tukun sai ki kwanta". Murmushi Saleema tayi tace "to Nagode sis, Ina jin daɗin kula dani da kike yi Allah yabiya ki da mafifin cin alkhairin sa.." "Ya isa don Allah duk abinda zan miki be kai kwatankwacin taimakon da kikai min ba, kar ki damu sister insha Allahu Allah zai yaye miki duk wani damuwar ki, Allah maji roƙon bawan sa ne kuma yana jin mu". Cikin jindaɗin maganar ta Saleema tace "Sister to ki je ki ƙarisa assignment ɗin naki mana ko kin gama ne?" Gajeren tsaki Halwa taja tana shafa gefen fuskarta tace "wlh na kasa ƴar uwa, duk wani searching da zan yi ban samu abinda nake so ba, na dai ƙoƙarta nayi biyu a cikin biyar ɗin, kuma gashi Lecturer ɗin nan yace mana shine Test ɗin mu na rasa ya zan yi". Saleema tace "to ki kai ma Yaya Barrister mana zai taimaka miki, tun farko ma na manta wlh da shi kika kai ma wa". Halwa dai batace komi ba illa jinjina zancen da take yi aranta, ba wai kai mishin bane bata so kusancin su ne ko kaɗan bata so.. "Kin yi shiru Sister?" Saleema takatse mata tunanin ta "To". Kaɗai ta'amsa mata dashi kafin tamiƙe tanufi kan kujera taɗau Hijabin ta tana ƙoƙarin saka wa "Wlh Sister ban taɓa ganin wanda ciki yake masa kyau ba kamar ke, Ni har na fi ganin kyan wannan cikin akan wancan, kinga yanda kika yi kuwa?" Cewar Saleema tana dariya ahankali Itama Halwan dariyan tayi tana ƙarisa saka Hijabin sannan taɗau Peppers ɗin ta tana kallon Saleeman "Ke dai Sister kin fiye saka idanu, ina wani kyau anan kina ganin yanda yaƙara min muni ya mayar dani sai kace wata uwa". Dariya suka yi gaba ɗaya kafin Halwa tafice Ita kuma Saleema tagyara kwanciyar ta. Tana fita tatarda Khalil ɗin zaune saman sofa yana latsa wayan sa Ƙarisawa tayi ahankali tayi masa sallama Hakan yasa yaɗago kai yana kallon ta at the same time yana amsa mata sallaman tare da ɗaura murmushi a fuskar sa "Maman Husna". Yafaɗa idanun sa akan ta Murmushi tayi tana Sad da kanta ƙasa don bata son ko kaɗan suna haɗa idanu, sai taji kamar wasu abubuwa suna fita ta cikin nasa idanun su shiga cikin nata "Dama yaya Khalil nazo ne kayi min wannan assignment ɗin". Gyara zaman sa yayi yana ajiye wayan yace "mu gani". Miƙa masa tayi Ya'amsa yana duba wa, ya ɗau tsawon mintuna biyu yana duba wa kafin yaɗago kansa yana kallon ta yace "ina Bairo ɗin?". Miƙa masa tayi dasauri Ya'amsa yaci gaba da dubawa kafin yasoma rubutun Ita kuma tana tsaye tana kallon sa "Baki gaji ba? ki zauna mana". Tatsinkayi muryan sa yana faɗin hakan batare da ya ɗago ya kalle ta ba Babu musu tazauna kan hannun kujeran Tsawon mintuna goma yaɗauka yana mata kafin yagama yakalle ta yana cewa "matso in yi miki bayani yanda zaki fahimta koda nan gaba". Hakan kuwa yayi mata daɗi don babu ita akai karatun shiyasa duk bata wani fahimta ba Zama tayi kan kujeran sosai, shima kuma yamatso ta yanda zata iya ganin rubutun sannan yasoma mata bayani Sosai tatsayar da hankalin ta waje ɗaya tafahimce sa duk da kuwa yanda take ji sabida kusancin su da yayi yawa Sai da yagama sannan yaɗago kai yana kallon ta da murmushi yace "yauwa to na gama saura biya ko?" Itama kallon sa tayi tana fid do idanu waje tace "ba kyauta kayi min ba?" "Laa ba kyauta nayi miki ba, ki duba ai nayi ƙoƙari Yakamata ace kin biya Ni" yayi maganar yana shafa suman kanshi yana dariya ƙasa-ƙasa "To nawa ne sai in biya ka?". "Duk yanda kika ba da babu matsala, amma meyasaka kike son karantan Low?" Kanta tasauke ƙasa, batasan me zata ce masa ba illa jujjuya Bairo ɗin hannun ta da take yi "Kinyi shiru". Yace mata a hankali idanun sa ƙyam akanta Ɗago kai tayi takalle sa, ganin sun haɗa ido tayi saurin maida kanta ƙasa tana jin gabanta na sake matsanancin bugawa "Ina so ne kawai". Tafaɗa a matuƙar sanyin murya Shiru yayi be yi magana ba, illa kallon ta kawai da yake yi cike da ƙauna, wannan kusancin nasu ya saka sa matuƙar nishaɗi da wani irin farin ciki ainun Miƙe wa tayi ta ɗan saci kallon sa kafin tace "na gode yaya Khalil, Allah yasaka". Murmusawa kaɗai yayi be ce komi ba Har ta juya kuma sai yace "ina Saleema?" "Bata jindaɗin jikin ta shine takwanta". "Subhanallah.." yafaɗa yana miƙe wa "Muje in duba ta". Ɗakin suka nufa Suna shiga sukai wajen gadon, zama Khalil yayi yana kallon fuskarta Har ta samu barci, gaba ɗaya jikin ta a rufe yake ruf sai fuskarta dake waje, a yanda take fitar da numfashi da ƙarfi zaka san jikin ta be mata daɗi, gashi fuskarta ya jiƙe sharkaf da zuba, gaban goshin ta sai tsatstsafo da gumi yake yi Hannun sa yaɗaura a saman gashinta kasancewar ɗankwalin ta ya zame, shafa gashin kawai yake yi yana kallon ta cike da tausayi Haka zalika Halwa dake tsaye itama kallon Saleeman take yi cikin tsananin tausayin ta Babu wanda ke magana cikin su kowa da tunanin dake ransa, tsawon wasu mintuna kafin Khalil yamiƙe yafice a ɗakin Yana fita Halwa takoma inda yatashi tazauna, tasaka hannun ta itama kamar yanda yayi tana shafa mata gashin Bata tashi a wajen ba sai da taji kiran sallan Asar, kafin tashiga Toilet taɗauro alwala tafito, sallah tayi tacire Hijabin tana zama kan sofa, sai tabuga tagumi kawai tana kallon Saleema, sai dai abaɗini tunani kawai take yi Daga ƙarshe tashi tayi tafito parlour, sai tayi hanyan kichen tana tafiya a hankali, tana shiga sai tatsaya tana tunanin abinda zata yi Ta ɗan jima a tsaye kafin ta'isa wajen kanta tasoma kiciniyar ɗaura musu girkin dare, duk da dama girkin ranan Khalil ne yayi musu Take-away, ita taje yin test a makaranta, Saleema kuma rashin jindaɗin jikin ta yasaka bata girka ba, da Khalil ɗin yadawo sai be ma tambayi ba'asi ba yakoma yasiyo musu Motsin da taji a bayan ta ne yasaka tajuya dasauri Khalil ne tsaye ya harɗe hannayen sa akan ƙirjin sa ya zuba mata kyawawan idanun sa masu tsananin kaifi da burge wa, fuskarsa kuma yalwace da murmushi Duƙar da kanta tayi tana jin matsanancin kunya ya kamata kasancewar ta bata da Hijab a jikinta, duk da riga da sani ne na atamfa a jikin ta, amma kuma duk da haka cikin ta yafito sosai ga kuma ƙiba da yasaka ta tayi "Me zaki yi?" Yatambaye ta yana kallon ta yana ji kamar yahaɗiye ta sabida tsananin ƙaunar ta da yake ji a ransa Halwa taba shi amsa batare da ta ɗago kai ta kalle sa ba "Dama zan yi mana girki ne". Khalil yace "a'a ki bar shi kawai, idan na fita anjima zan siyo kar ki wahal da kanki uhmm?". Kaɗa masa kai tayi kamar ƙadangaruwa, bata sake ɗago kai ba sai da taji tafiyar sa kafin taɗaga kanta a lokaci ɗaya kuma tana sauke ajiyan zuciya me ƙarfi har da dafe ƙirji Bata san meyasa take zama wata daban ba a gaban sa, sai takoma kamar ba ita Halwan da tasani ba Murmushi tayi a fili tace "wlh na sauya sosai kamar ba Ni ba". Sai kuma tasaki dariya tana juyawa tanufi wajen Freezer bayan ta ɗau ɗanyen naman da taɗauko tamayar cikin Freezern, sai kuma tatsaya tana tunanin abinda zata girka taci, sosai take jin kwaɗayi tana son ta ɗan saka wani abun da zai mata text a baki "Ko dai inyi ɗan wake ne?" Tafaɗa tana juya ido alamun tunani Sai kuma tagirgiza kanta "A'a bari in yi dai kalallaɓa, yeessss shi zan yi". Taƙarike maganar da dariyan farin ciki a fuskarta Kasancewar suna da komi sabida haka cikin ƙanƙanin lokaci tayi tagama sannan taɗauki Plate ɗin da tazuba tanufi hanyar fita, har ta kai bakin ƙofa sai tadawo taɗau Robbern yaji tafice A Parlour tazauna taɗaura plate ɗin saman cinyan ta, tana ci tana kallon ta cike da nishaɗi da jindaɗin kalallaɓan Bata san sanda Khalil yazo wajen ba sai tsinkayan muryan sa tayi "Ashe dai hanci na be jiyo min ƙarya ba". Dasauri taɗago kanta a tsorace tana kallon sa Hakan yasa yayi dariya yana zama yace "sorry na tsorata ki ko? Menene wannan kuma?" Yaƙarike maganar yana kallon cikin Plate ɗin Tana murmushi taba shi amsa da "kalallaɓa ne, bismillan mu". Taɗago Plate ɗin tana ajiye wa a tsakiyar su "Ai kuwa zan ci, wannan abun tun daga ɗakin karatuna na jiyo ƙamshin sa". Yayi maganar yana dariya Sai kuma yasaka hannu yagutsira yakai bakin sa Duk tana kallon sa tana murmusawa Taunawa yasoma yi a hankali yana ɗan yamutsa fuska, sai kuma yasoma gyaɗa kansa yana wani lumshe idanu "Waiii wannan abun daɗi yake dashi, me kika ce ma sunan sa?" Dariya tayi tace "kalallaɓa". "Uhmm kalallaɓa yayi daɗi fa, Ni ban taɓa cin abun da yakai wannan daɗi ba, so texting". Murmushi tayi me fid da haƙora tace "ko dai santi kake yi?" Saurin girgiza mata kai yayi yana taunan wanda yasaka a baki, a kuma time ɗin yake bata amsa da "a'a dagaske nake miki". Halwa dariya kawai take mishi, shi kuma sai zuba santi yake yi cike da barkwanci Be cire hannun sa ba sai da suka cinye gaba ɗaya Halwa ƙoƙarin miƙe wa tayi zata maida Plate ɗin kichen Yayi saurin cewa "no koma ki zauna bari in Kai". Ya'amshi plate ɗin yakai kichen tare da wanke hannun sa yafito "Gaskiya yayi daɗi, kinga daɗin sa ya saka na cinye miki ban rage miki ba, Allah yasa dai ya ishe ki?" Yayi maganar bayan ya dawo wajen ya zauna Murmushi Halwa tayi tace "sai yanzu kenan zaka tuna bayan ka gama cinye min? To ya zan yi haka nan zan haƙura ai tunda ba wani". Shafo kansa yayi yana dariya yace "sorry na manta ne wlh". "Babu komi ai". Tafaɗa cike da nishaɗi "Wai yaushe ne zaku soma Exams ɗin nan ne, naga time na ƙure wa?" Halwa tace "jibi ne insha Allahu". Zai sake magana wayan sa yasoma ƙara, ciro wa yayi cikin aljihun wandon sa yana kallon screan ɗin wayan, be ɗaga ba sai yamaida kallon sa gare ta yana faɗin "Bari inje Tahir na jira na, idan Saleema tatashi jikin babu daɗi Please ki kira ni kinji? Bazan daɗe ba ma zan dawo". "To sai ka dawo Allah yatsare". "Ameen na gode". Yafaɗa alokacin da yake miƙe wa yayi hanyan fita yana ɗaura wayan a kunne sa bayan yayi peacking call ɗin Bin bayan sa tayi da kallo har yafice "Yana da matuƙar kirki". Tayi maganar a fili tana murmusawa tare da kwanciya kan kujeran, lumshe idanun ta tayi cike da tsantsan farin ciki tare da tunanin Khalil ɗin Yau dai baza ta iya hana kanta tunanin sa ba, don haka tabaje zuciyarta tana tariyo duk wani abu da yataɓa shiga tsakanin su, har da ma wanda be faru ba sai da zuciyar nata takawo mata tunanin tare da ƙawata mata abun ta yanda zai saka ta nishaɗi. _kun san dai zuciya 🤣🤣🤣🤣__ [12/3/2020, 5:34 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Fourteen* ________🎓Sai da akayi kiran sallan magriba sannan tamiƙe tanufi ɗakin Saleema Har a lokacin barci take yi bata farka ba, don haka tawuce kai tsaye cikin Toilet taɗauro alwala, hijab tasaka tayi sallah Lokacin da tasallame Saleema tatashi Jin motsin ta yasa Halwa juyawa tana kallon ta, sai kuma tamiƙe dasauri tanufe ta tare da faɗin "Sannu Sister ya jikin?" Ahankali ta'amsa mata da "alhmadulillah" tana yunƙurin tashi Taimaka mata tayi tatashi zaune kafin tasake tambayan ta "yanzu ina ke miki ciwo?" Murmusawa tayi tana kallon ta tace "babu, sai dai kawai ƙarfin jiki ne bana ji". "Sannu gashi jikin ki duk zafi". Halwa tafaɗa cike da tausayin ta bayan ta ɗaura hannun ta saman wuyan ta tana tattaɓa wa Saleema tace "taimaka min in tashi zan yi sallah". Taimaka mata Halwan tayi tamiƙe sannan tariƙe ta takai ta har Toilet ɗin tafito, sai da tadaidaici ta gama abinda zata yi takuma komawa tariƙo ta suka fito, akan dadduma ta'ajiye ta taɗauko mata Hijabin ta Sai da tafara sallan kafin tazauna gefen gado tana kallon ta A zaune tayi sallan har ta idar A Lokacin ne Khalil yashigo ɗakin da sallama Halwa ce ta'amsa masa yayinda Saleema tabi shi da idanu Takowa yayi zuwa wajen Saleeman yaduƙa agaban ta yace "Ya jikin naki?" "Da sauƙi". Hannun sa yasaka yana taɓa jikin ta yaji zafi sosai, sai yamaida idanun sa kanta yace "but ga jikin ki da zafi anya baza muje asibiti ba?" Duƙar da kanta kaɗai tayi batare da ta bashi amsa ba, domin ko kaɗan bata son yin magana sabida kanta sara mata yake yi Hannun sa yamaida kan haɓan ta yaɗago kanta yana ƙura mata idanu, yayinda itama tazuba nata idanun cikin nashi tana kallon sa cike da rauni Halwa dake zaune tana faman kallon su, sai tamiƙe dasauri tayi hanyan Toilet, sai kuma tadawo tayi wuri-wuri tarasa ina zata bi kawai sai tafice a ɗakin Shi Khalil be ma lura da fitan ta ba illa ɗago Saleema da yayi tamiƙe tsaye, yajanyo ta jikin sa suka nufi kan gado suka zauna, hannun ta ɗaya yariƙe yana murza wa yayinda ita kuma takwantar da kanta saman kafaɗan sa ta saƙalo ɗaya hannun zuwa bayan sa tana lumshe idanun ta Sun jima a haka babu me magana, sai kuma yasaki hannun nata yana ɗago kanta yace "Bari in ɗauko ruwa da towel in rage miki wannan zafin jikin ko zaki ji daɗi". Bata yi magana ba har yamiƙe yashige toilet, ita kuma sai takwanta tana sake rufe idanun ta. Fitan Halwa ɗakin ta tashige takwanta saman gado tana tarufe idanun ta tare da sauraron bugun zuciyar ta, sai kuma tasoma juye-juye ta kasa zama waje ɗaya don dai kawai tahana kanta tunani da kuma abinda take ji cikin zuciyarta Tsaki taja tana miƙe wa zaune, sai kuma tamiƙe tafito parlour, anan tatarda ledojin da Khalil yashigo dasu, ɗauka tayi taduba sai taga abinci ne ciki hakan yasa ta kwashe tanufi dasu kan dainning Kichen tanufa taɗauko coolars tasake abincin, sannan tasake farfesun kayan ciki shima a cikin coolar tarufe su yanda bazai yi sanyi ba, sai da tagyara wajen tayi setting komi abinda zasu buƙata kafin takoma ɗakin ta, sallan isha'i tayi tazauna nan tana lazimi batare da ta fita ba, sai da taji motsin su a Parlour kafin tatashi tafito itama Saleema ce kaɗai zaune, ta sauya kaya zuwa kayan barci me taushi riga da wando farare Wajen ta tanufa tazauna tana cewa "sannu Sister ya jiki?" Murmushi Saleema tayi tace "alhmadulillah, dama ke nake shirin kira muci abinci kuma kin ƙule ɗaki". Dariya kaɗai Halwa tayi batace komi ba tamiƙe Itama Saleeman miƙewa tayi suka nufi dainning, bayan sun zauna Halwa take cewa "Ina yaya Khalil ɗin ko ya fita ne?" "A'a yana ɗakin sa, yace be jin yunwa yana da aiki ya shiga yi". Gyaɗa kanta tayi tana zuba musu abincin A haka sukai ta ci suna ɗan taɓa hira har lokaci yaja suna nan zaune a wajen Daga ƙarshe Halwa tamiƙe ta tattara kayan takai kichen tafito tana kallon Saleema da har yanzu tana nan zaune bata motsa ba "Sister Ni zan shiga ɗaki ina son Nima in Yi bitan karatu". Miƙe wa Saleema tayi tanufo ta tana faɗin "to muje nima in taya ki karatun". Halwa dariya tayi tace "kai sis ke dai ki wuce wajen mijin ki kar yaji ki shiru, ko baki san dare yayi bane?" Itama dariyan tayi tace "na fiki sani ai, Ni dai muje in tayaki bana jin barci wlh, yanzu idan naje shima ya ƙufe akan aiki sai in ta zama Ni kaɗai". Shiga ɗakin suka yi suka zauna, Halwa ta jawo handout ɗin ta tana karatun Saleema na kwance tana jinta, kaɗan-kaɗan kuma suna taɓa hira Sai wajen 10:00pm. Kafin Saleema tamiƙe tayi mata sallama tafice Itama tashi tayi tarufe ƙofan sannan tasauya kayan ta zuwa na barci takwanta, bata ɗau lokaci ba barcin ya ɗauke ta tunda shine cike fal a idanun ta. **** ***** ***** ****** ***** *WASHE GARI* Washe gari ta kasance Sunday ranan da ake ɗaura auren Zainab Babu laifi gidan an cika maƙil don dama suna da ƴan uwa da yawa, yayyin Zainab su uku duk ka mata ko wacce ta zo da iyalan ta, Haka zalika shima babban Yayan su dake zaune a Yola da nashi iyalan shima ya zo Umma dai babu yanda zata yi ne amma kowa yaganta ya san akwai abinda ke damun ta, don ko gayyan mutane sai Zaituna ne ta'aika ma mutane, kuma ita taraba ma mutanen anguwa Chwingum duk dai don Umma taƙi yi. Ƙarfe 11:30am. Aka shaida ɗaurin auren Zainab da Aliyu A ranan kuma ƴan uwanta suka je ganin ɗakin ta suka ga abinda Yakamata su saka sannan suka wuce kasuwa, labulayen ɗaki da ƙarafen da za'a buga duk suka siyo, da sauran abubuwan buƙata, sannan suka koma gidan suka kafa Lokacin ne kuma aka ɗauko kayan ɗakin ta da Abba yayi mata, don haka suka tsaya suka shirya mata komi inda yadace, ɗakin Amarya yafito fes gunun sha'awa Sabon gini ne da yayyin Aliyu suka haɗa kuɗi sukai masa tunda dama yana da filin sa a cikin gidan su, daga Umman sa sai shi sai kuma autar su agidan. Sasan sa daban akayi masa, sai da aka kewaye da gini, ɗakuna ne ciki biyu sai ƙaramin parlour a tsakiya, sannan ko wani ɗakin akwai Toilet a ciki, idan kafito a bakin ƙofan ɗakin shine kichen ɗin ta yake, har da kantan kichen sai da akayi mata inda zata riƙa ajiye-ajiye Sai kuma babban Bayi dake sasan Umma Komi yayi dai-dai gunun sha'awa Amarya kawai yake jira ɗakin Da dare aka kawo ta gidan ta inda kowa yatafi yabar ta ita da Angon ta, sai muce Allah yasanya alkhairi *ZAINAB* ya nuna mana na ƴan baya lafiya. _sai mun zo cin dubulan da cin-cin, kar agaji damu_🤣 [12/4/2020, 5:52 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ _Wannan shafin naki ne *NANA ALIYU* ki more kiji daɗin ki ke kaɗai bance wani yataya ki ba, na gode da ƙaunar ki gare ni._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Fifteen* ________🎓 *TWO DAYS* Yau agajiye yadawo aiki, bayan yayi parcking motan sa yafito riƙe da briafcase ɗin sa da Suit ɗin sa da yacire, rufe motan yayi yanufi cikin gidan cikin tafiyan sa me burge wa, duk da kuwa a yanzu ɗin salon tafiyan ya sauya yana yi ne kamar me tsoron taka ƙasa, nan kuwa duk cikin gajiya ne Tura ƙofan yayi kafin yayi sallama wanda a dai-dai laɓɓan sa yatsaya Babu kowa cikin parlour'n don haka kai tsaye ɗakin sa yanufa, sai da ya'ajiye komi na hannun sa sannan yazauna yasoma zare Combat ɗin ƙafafun sa da Socks, bayan ya gama sai yaɓalle bottles ɗin rigan sa gaba ɗaya singlate ɗin jikin sa ya bayyana, be cire rigan ba sai yagishingiɗa akan pilow yana lumshe idanun sa Tsawon mintuna biyar yaɗauka kafin yamiƙe yanufi parlour riƙe da wayan sa a hannu yana latsa wa Har alokacin babu kowa a parlour'n don haka kansa tsaye yanufi kan dainning, har ya zauna kuma sai yamiƙe yanufi ɗakin Saleema Ƙofar a buɗe yake ba'a rufe duka ba, har ya saka hannu zai sake tura wa yashige sai yaji maganar Halwa wanda yasaka dole ya ɗan dakata yana sauraron su "Ki dena ma maganar Haris a yanzu, yanzu na rigada na cire wannan burin a raina, Ni ce Mahaifiyar Husna kuma na baki ita har abada wlh, kin san kuma be da iko da ita tunda dai ba aure aka ɗaura mana dashi ba, musulunci ya yarda idan an haifi yarinya ba da aure ba uwa ke da alhakin riƙe ta". Rungume ta Saleema tayi cike da farin ciki tace "gaskiya na gode ƴar uwata, kin bar burin ki akaina duk sabida ki faranta min bansan da me zan saka miki ba, Allah yabiya ki.." Katse ta Halwa tayi da faɗin "Ni fa nace miki bana son godiya, idan na baki Husna ba ke ne zaki gode min ba, Ni ce zan gode miki, don haka ki dena min godiya don Allah". Sakin ta Saleema tayi tana murmushi tace "ai bazan dena miki godiya ba wlh, kin bani Husna sannan kina shirin haifa min wani ɗan, idan ban miki godiya ba me zan miki?" Halwa tashi tsaye tayi tana yamutsa fuskarta tace "kinga Ni bani da lokacin wannan yanzu, bari inje inyi wanka in shirya in tai school, tunda yau Pepper ɗaya zan yi insha Allahu zan biya gida nagaishe da Ummi". Zaro ido Saleema tayi tace "me zaki je yi bayan kin san tace kar ki so ma ki je? Babu ruwana wlh". Dariya Halwa tayi tace "to na fasa". "Da dai yafi miki, banda ma kinibibi muna haɗuwa fa a Hospital salon dai ki ja mana tonon silili". Ƙofa Halwa tanufa tana ci gaba da dariyan ta "Dama tonon ki nake yi in ji me Zaki CE". Ahankali yaɗaga ƙafafun sa da sukai mishi nauyi yamatsa bakin ƙofan sa yabuɗe yashige Dai-dai da Halwa ta fito taji ƙarar rufe ƙofan nasa, kallon ƙofan tayi na ɗan seconni kafin taɗauke kan ta tana jan numfashi tare da shaƙan daddaɗan turaren sa da ya mamaye ilahirin wajen Ɗakin ta tanufa tabuɗe tashige, tana shiga wanka tafaɗa. *** A hankali ya ƙarisa gaban gadon sa jiki a matuƙar sanyaye, zama yayi yana dafe kansa dake barazanar tarwatse wa sakamakon abinda yaji, be ma san a wani yanayi zai fassara kalaman ta ba "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." yafaɗa a wani rikitaccen murya da dole kasan cewa yana cikin wani yanayi A duk abinda yafahimta tana nufin kenan ita ɗin karuwa ce, ta haifi Husna ba ta hanyar aure ba, "Why zuciyar sa zatay masa irin wannan gangancin? Meyasaka zata so wacce bata kama ce sa?" Hannu yaɗaura setting zuciyar sa yana ji tamkar yaƙwaƙulo zuciyar yawanke yagoge duk wani son ta da yataɓa wanzuwa a cikin ta Sake runtse idanun sa yayi sai ga wasu siraran hawaye sun soma fitowa suna sauka kan dandamalin kumatun sa, wani irin ƙunci me haɗe da raɗaɗi ne yatsaya masa iya maƙogwaron sa, wanda ji yake yi tamkar yahaɗiye zuciya ya mutu sabida tsaban baƙin kishi da yake ji Tsakiyar gadon yafaɗa yana ɗaura duk ka hannayen sa saman fuskar sa batare da ya buɗe idanun sa ba, shiru kawai yayi yana sauraron bugun zuciyar sa dake fita a wani irin yanayi me haɗe da firgitar wa ga duk wanda yasaurara Tsawon lokaci yana a wannan yanayin mara daɗi wanda har sai da hawayen fuskar sa suka bushe batare da ya sake ƙwaƙƙwaran motsi ba Saleema ce taturo ƙofan tashigo kasancewar Halwa da zata fita taje ta sanar mata Khalil ɗin ya dawo, hakan yasa tafito daga ɗaki tazo gare sa Har taƙariso bakin gadon be motsa ba be kuma buɗe idanun sa ba, yana nan ayanda yake tamkar be san da wanzuwar ta ba, gadon itama tahau tana ɗaura rabin jikin ta kan nashi tace "Mijina don Allah kayi haƙuri ashe ka dawo bansani ba, na Barka kai kaɗai". Idanuwan sa yabuɗe waɗanda suka sauya kala ainun, yazuba mata su batare da yace komi ba, kuma babu ko alamun walwala a face ɗin sa Kallon sa itama take yi cike da tsoro don bata taɓa ganin sa a haka ba, cikin rawan baki tasoma jero masa tambayan "Lafiya me yafaru da kai? Meke damun ka?" Rufe idanun sa yayi yana haɗiye abinda yatsaya masa a maƙoshi tun ɗazu, daƙyar yaɗaga hannun sa ɗaya yajanye ta a jikin sa yamiƙe da hanzari yana shige wa cikin Toilet Sai kawai tasaki baki tana bin sa da kallo cike da wani irin baƙon yanayi, tunda take ko kaɗan bata taɓa ganin fushin Khalil ba, ko kaɗan baya da saurin fushi, babu abinda zaka taɓa gani a tare dashi da zaka san ransa a ɓace yake, amma yau kallo ɗaya idan kayi masa zaka san tabbas yana cikin wani hali me wuyan fassara Tana nan zaune duk ranta a jagule, ƙiris take jira tasaka kuka, gaba ɗaya hankalin ta yayi mugun tashi fiye da tunanin me karatu, gaban ta sai bugawa yake yi tamkar zai faso ƙirjin yafito Har mintuna 20 suka shuɗe be fito ba, sai kawai tasaki kuka jikin ta na wani irin rawa kamar mazari Ahankali kukan nata yasoma isa kunnen sa, lumshe idanun sa yayi yana buɗe su a lokaci ɗaya, idanu yatsira ma kansa ta cikin mirror batare da ya sake motsa wa ba, sai da yaji kukan nata na fita da ƙarfi sannan yawanke fuskar sa yanufi ƙofa yabuɗe yafito Dasauri kamar an tsikare ta ta'isa gaban sa, cikin kukan take cewa "don Allah mene yafaru ka ɗaga min hankali, ban taɓa ganin ka a haka ba me yasame ka?" Idanu kawai yatsira mata cike da ƙaunar ta aransa, sosai taba shi tausayi yanda tanuna damuwar ta akan shi, hannun sa kawai yasaka yajanyo ta jikin sa yarungume ta sosai kamar zai maida ta ciki, gaba ɗaya ya zagayo da hannayen sa ta bayan ta yana faman shafa mata bayan, cikin sanyin murya a hankali yasoma rarrashin ta "Shiiiiiiii.. Ya isa menene kuma na kuka? Ke abun kuka baya miki kaɗan ne ko kin manta halin da kike ciki ne..?" Numfashi yaja kafin yaci gaba "Babu abinda ke damuna kawai na tuna wani abu ne, amma duk kin bi kin ɗaga min hankalin ki". Yaƙarike maganar yana ɗago ta daga jikin sa tare da sakar mata lallausan murmushi Izuwa yanzu ta tsai da kukan nata sai dai kallon sa kawai da take yi tamkar t.v, sosai take hango matsanancin damuwa a fuskar sa da muryan sa wanda shi kansa ya kasa ɓoye hakan Hancin ta yaja yana faɗin "ki dena saka damuwa haka kinji, bari in Yi wanka ina zuwa". Sai yajuya batare da ya jira me zata ce ba yashige toilet ɗin Tana nan tsaye bata jirga ba har sanda yafito Shi kansa yayi mamakin ganin ta a wajen sabida daɗewan da yayi cikin Toilet ɗin Matsowa kusa da ita yayi yana kallon ta "Kina nan tsaye har na dawo?" Kanta tasauke ƙasa batare da tace uffan ba Hannun ta yariƙe yajanyo ta jikin sa yasake cewa "wai menene lafiyan ki ƙalau kuwa?" Murmusawa tayi kafin tagyaɗa masa kai batare da ta furta komi ba, sai kuma tajanye jikin ta tana shirin juyawa tatafi yasake riƙe hannun ta yamaido ta jikin sa "Ki faɗa min meke damun ki? ko dai.." Sai yayi shiru be ƙarisa ba illa zuba mata idanu da yayi Idanun ta tasanya a cikin nasa sai dai baza ta iya juran kallon cikin idanun ba, sai takawar da kai tana cewa "mu je in taimaka maka". Matse baki yayi kafin yanufi gaban mirror yazauna, tasoma tsane masa jikin sa da towel ɗin da yaɗaura a kafaɗa Shiru yayi kawai yana kallon ta ta cikin mirror, har tagama masa komi sannan tadube sa tace "Wani kaya zan ɗauko maka?" "Ko wanne". Yaba ta amsa a taƙaice Juyawa tayi tanufi gaban sip ɗin sa tabuɗe tazaɓo masa riga da wando Three qweater, takawo masa har gaban sa sannan tajuya tafice. Bayan ya gama shiryawa yafito yatarda ita zaune tana kallo Tana ganin shi tamiƙe tanufo sa tana murmushi "Kayi kyau". "Thank you Matata". Yayi maganar yana maida mata martanin murmushin Dainning suka nufa tayi saving ɗin sa, yasoma ci tana zaune gefen sa, tana so tayi masa hira sai dai yanda fuskar sa har yanzu babu walwala kamar yanda tasaba gani shiyasa tayi shiru abunta Har yagama sannan suka koma Parlour Tunda yazauna yaɗau wayan sa yana ta latse-latse wanda a zahiri ba wai komi yake yi ba, ya Bama kansa damar yin tunani ne batare da Saleema ta gane hakan ba, daga ƙarshe ma sai yatashi yashige ɗakin sa bayan ya sanar mata zai je yaduba wani aiki ne Ita kuma sai tagyara takwanta saman Three sitter da suke zaune taci gaba da kallon ta Har barci ya soma ɗiban ta Khalil yafito yatashe ta akan taje tayi sallah an kira, shi kuma yafice masallaci. Lokacin da yafito masjid ɗin yahangi drever na ƙoƙarin shigar da mota cikin gidan, yana isowa yashiga gidan dai-dai itama Halwa ta fito cikin mota, ganin sa sai tatsaya jiran sa Shi kuwa sai yaɗauke kai tamkar be ganta ba tare da ɗaure fuska tamau, ta gaban ta yazo yawuce be kalle ta ba, sai tayi saurin cewa "Barka Yaya Khalil". Tafiyan sa yaci gaba da yi batare da ya amsa ba, yanufi Garden ɗin gidan Halwa jiki a sanyaye tabi bayan sa da kallo yayinda tanufi cikin gidan, bata bar kallon sa ba har sai da takusa cin ƙasa sabida tuntuɓen da tayi, sannan ne tadawo da nutsuwar ta jikin ta tabuɗe ƙofa tashige. . _plz kuyi comments da share sannan ku danna Vote._ [12/5/2020, 3:34 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Sixteen* ________🎓 Ɗakin Saleema tashiga nan taganta tana nannaɗe dadduma alamun ta idar da Sallah "Oyoyo Maman Baby". Saleeman tafaɗa tana kallon ta fuskar ta cike da fara'a Murmushi Halwa tayi taƙariso tazauna kan sofa tana faɗin "washh na gaji da yawa". Ajiye dadduman tayi tazo tazauna kusa da ita "Lallai kam ki ce zan yi tausa yau kar Baby yayi fushi damu". Dariya Halwa tayi "To ya jarabawan yayi sauƙi dai ko?" Halwa tace " alhmadulillah komi normal ƴar uwa". Saleema tace "masha Allah haka nake son ji, ya Baby be dai takura miki ba ko?". Miƙe wa Halwa tayi tana bata amsa "to ga dai shi nan duk yabi ya ishe ni ya hana Ni saƙat yau". Saleema marairaice fuska tayi tace "eyya sister Baki bashi abinci bane, i know kin bar shi da yunwa, muje yanzu ki bashi kar yasoma kuka". "Ai kya bari nayi sallah ko?" Halwa tace tana dariya Kafin tanufi hanyan ƙofa Saleema ma miƙe wa tayi tabi bayan ta, suka fito tare Saleema tana faɗin "Kiyi sauri sister Plz". Halwa bata ce mata komi ba illa dariya da take mata tashige ɗakin ta, ajiye jakan ta tayi tacire Hijabin ta tashiga Toilet, alwala taɗauro tafito tashimfiɗa sallaya tamaida Hijabin ta tayi sallah, tana idar wa tazare Hijab ɗin tafita parlour Lokacin Khalil ya shigo suna zaune shi da Saleema kan Two sitter, yayinda shi kuma yake latsa wayan sa Ƙariso wa wajen tayi tana shirin zama Saleema tayi saurin cewa "Sister je ki ɗibo abincin mana". Yamutsa fuska Halwa tayi tazauna sannan tace "wlh bana jin yunwa fa, kuma ban ce miki kukan yunwa yake min ba". Saleema kallon Khalil tayi tace "kana ji ko Ya Barrister, wlh sis sai ta haifa mana yaro ramamme ko kaɗan bata son bashi abinci". Khalil be ɗaga kai ba bare yayi magana ba Hakan yasa Saleema tasake kallon Halwa dake kallon Khalil tana jiran jin me zai ce, don dama sun saba irin hakan kuma yana saka musu baki, amma yau saɓanin tunanin su be tanka ba "Sister don Allah kije ki ɗibo abinci, baki ji me Ummi tace miki bane?" Miƙe wa Halwa tayi tana nufan dainning tace "to bari dai in ɗibo shikenan ko?" Dariya Saleema tayi tana faɗin "shikenan wlh, sai kuma inga kin cinye". Ɗago kai yayi yazuba mata idanu na tsawon soconni kafin yalumshe su yana jin wani baƙin ciki na ƙara shigan sa Ji yake yi tamkar yaɗauke ta yakaita a cire cikin, kwata-kwata yanzu baya ƙaunar cikin kamar yanda yake jin son sa a baya, tunda a yanzu ɗin zai fito ne ta ƙazantar zina, "shikenan shi kuma yana ji yana gani za'a haifa masa yaro da dattin zina?" Halwa na dawowa wajen yamiƙe yanufi ɗakin sa batare da yace komi ba Saleema tabi bayan sa da kallo har yashige ɗakin sa, kafin tasauke ajiyan zuciya tana maida idanun ta kan Halwa wacce a yanzu ta lula duniyar tunani Sosai taga damuwa akan fuskar sa wanda kuma yahaddasa mata rashin jindaɗi sam, sun rigada sun saba a ɗan kwanakin nan ko batay masa magana ba sai yayi mata, kuma kullum sai ya tambayi lafiyan Babyn sa, shiyasa da taganshi be tanka ta ba hakan be mata daɗi ba "Sister yau kamar wani abun na damun Barrister ko baki lura da hakan ba?" Saleema takatse mata tunanin ta da faɗar hakan Idanun ta tamurza tana kallon Saleeman tare da ƙirƙirar murmushi tace "Haka ne sister nima naga sauyi a tare dashi, but ki bashi lokaci zai koma normal tunda kinsan ba halin sa bane, kar ki ce zaki saka damuwa a ranki kinji?" Murmusawa Saleema tayi tana gyaɗa kanta, sai kuma tace "yauwa Sister na gode har naji daɗi wlh, Allah ya yaye masa damuwar sa". "Amin". Halwa ta'amsa mata tana saka abinci a bakin ta Daga nan hira suka ci gaba da yi cike da nishaɗi. **** Tun daga ranan kuma sai yazamana Khalil ya dena kula Halwa, ita kanta tuni ta fahimci hakan, idan har ya amsa gaisuwar ta daga hakan babu maganar dake sake shiga tsakanin su Wannan dalilin ne yasaka itama ta dena shige masa kamar da, duk da abun na matuƙar damun ta aranta amma kuma ta danganta hakan da sabawar da sukayi ne a kwanakin baya, yanzu kuma ya zo ya dena mata magana. Fannin Khalil shi kuma duk yayi hakan ne sabida son cire ta aran sa, amma kuma tamkar ƙara masa wutar ƙaunar ta ake yi, ya rasa ya zai yi duk da ko kaɗan baya ƙaunar wani alaƙa yashiga tsakanin su, koda yaushe babu abinda yake tuna wa a ransa illa kalaman ta, hakan na ɓata masa rai matuƙa A yanzu kuwa tuni ya sake rungume matar sa wanda yasan ita kaɗai ce kawai zai iya zama da ita, tunda wacce zuciyar sa ke so bata kama ce sa ba, soyayya tsantsa yake nuna ma Saleema wanda a yanzu ita kanta tasan da banbanci dana Da, yanzu sosai yake ƙaunar ta ko kaɗan baya son abunda zai ɓata mata rai Ita dai Halwa ta zama ƴar kallo ne domin ko a gaban ta haka zai zaƙe yanuna mata soyayya ko a jikin sa, don haka wani lokacin in dai akwai shi a wajen ta gummaci tashiga ɗaki tazauna ita kaɗai, da tazauna tana ganin abinda ke ɗaga mata hankali yana saka ta tunani tare da hana ta ishashshen barci Har yanzu ba wai ta yarda da cewa zuciyar ta na begen sa bane, wanda bata san cewa tuntuni ta afka kogin ƙaunar sa ba, kuma ko kaɗan bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tunda babu ta yanda za'a yi ta auri Mijin Saleema wacce ta taimaki rayuwan ta, tabbas idan hakan yafaru da ita ta gummaci ta mutu da ƙaunar sa amma baza ta taɓa ba ma zuciyarta damar wannan tunanin mara amfani ba. Haka kwanaki suka shuɗe wanda har Halwa ta gama jarabawan ta an yi musu hutu Kwanaki sun ci gaba da tafiya haka satikai yayinda aka tasar ma watanni, gashi yanzu har sun koma hutu sun shiga aji na uku Ta ci gaba da rainon cikin ta yayinda yake ƙara girma, sosai cikin yake da girman mamaki wanda duk wanda yagani sai ya tausaya mata sabida tsaban girman sa, gashi ya saka ta ta kumbura ainun, kuma tun sanda yashiga wata na tara ta dena lafiya, yau ciwo gobe lafiya, tuni ta jingine karatun ta a gefe har sai sanda Allah yasauke ta lafiya Shi kansa Khalil yanzu ba ƙaramin tausayi take bashi ba, duk da har a yanzu ba wai magana na shiga tsakanin su bane, idan ko kaji magana me tsawo ya haɗa su sai dai akan cikin ne Tun farko shi ke kai ta awon cikin har yau kuma be fasa ba, wani lokacin su je da Saleema wani lokacin kuma su biyu suke zuwa. Yau ma ɗin gaba ɗaya tare suka shirya zasu je asibitin, kasancewar yau ɗin Halwa tatashi jikin babu daɗi sosai, duk da a gobe ne Yakamata su koma Hospital a duba ta amma kuma Khalil ɗin yace su shirya su je yau Saleema ke riƙe da ita har zuwa wajen motan, tabuɗe mata tashiga daƙyar sannan itama tashiga Khalil na zaune cikin motan yana kallon su ta cikin mirror, sai da Saleema tarufe motan sannan yasaki ajiyan zuciya yana tada motan yanufi bakin Gate Me gadi ya wangale masa Gate ɗin yafice da hanzari Waya Saleema taɗauka takira Ummi "Ummi ga munan zuwa asibitin". "Subhanallah.. me yafaru ne ko haihuwar ne?" Girgiza kanta Saleema tayi kamar tana kallon ta tace "a'a Ummi jikin ne dai babu daɗi shine zamu je". Ummi tace "to gashi kuma yau ban samu zuwa ba naje duba jikin Sultan baya jindaɗi, amma idan kun ƙarisa sai ki nemi Sister A'isha ta duba ku". "To Ummi ki gaishe da Aunty, Allah yabashi lafiya". Daga haka sallama suka yi tasaka wayan a jaka, sannan takalli Halwa dake jingine da kanta jikin kujera ta rufe ido ruf "Sannu Sister". Saleema tafaɗa kamar zatay kuka Buɗe idanun ta tayi tasakar mata murmushi tana gyaɗa mata kai don baza ta iya magana ba sabida yanda take ji. Koda suka isa cikin asibitin Saleema ce tariƙo ta sukai ciki, yayinda Khalil yabiyo su a baya yazauna a reception yana waya da Brr. Tahir Sister A'isha tayi musu jagora zuwa wajen Likita, an duba ta babu wani matsala kuma ba haihuwa bane, don akwai sauran kwanaki a yanda suka ce musu, illa magani kawai da suka bata, sai ta ɗan kwanta na tsawon mintuna goma sannan suka sallame ta Sun fito suka haɗu da Khalil ɗin, shi ya'amshi takardan maganin da suka rubuta mata yabar su nan yaje yasiyo sannan yadawo suka fito Dai-dai sun kawo haraban Hospital ɗin, wani baƙar Mota dake fake a gaban Gate aka zuge glass ɗin, sai jin harbi suka yi wanda yasauka a kafaɗan Khalil dake gaban su yana tafiya, be tabbatar da abinda ke faruwa dashi ba yasake jin wani a setting inda aka sakar masa wancan, idanuwan sa ne suka juye lokaci ɗaya yasulale ƙasa riƙe da wajen, cikin second ɗaya ya dena motsi gaba ɗayan sa Wanda faɗin nasa yayi dai-dai da kurma ihun da Saleema da Halwa suka yi suka bi shi da idanu da suka firfito dasu waje Wani irin bugawa zuciyar Saleema tayi tay saurin riƙe ƙirjin ta tana kallon sa, bakin ta na rawa takira sunan sa da ƙarfi wanda yayi dai-dai da zubowar jinin bakin ta, sai kuma tasulale ƙasa tafaɗi babu alamun numfashi Kuka Halwa tafashe dashi, tayunƙura tabi Saleeman ƙasa tana girgiza ta, lokaci ɗaya itama numfashin ta yaɗauke tafaɗi warwas sabida tsananin firgita da tayi "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Gaba ɗaya jama'ar wajen sun hargitse sai salati suke saka wa, masu kuka nayi masu guduwa nayi, ƙalilan mutane ne sukayo kan su Khalil dake yashe a ƙasa babu rai a jikin su. Baƙar Motar nan wanda a cikin ta aka yo harbin tuni sun arce a tsiyace. [12/6/2020, 9:59 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Seventeen* ________🎓 *2 Hours Ago* Suna zaune gaba ɗayan su a reception sun yi cirko-cirko hankalin su duk a matuƙar tashe, babu abinda suke tsimaye yanzu sai fitowar doctors su san wani hali suke ciki Ummi da Mom sai faman share hawaye suke yi domin labarin abinda yafaru da yariske su ba ƙaramin girgiza su yayi ba Fitowar Babban doctorn da ya jagoranci duba Su Khalil yasaka suka nufe sa gaba ɗayan su suna jera masa tambayoyi ko wannen su yana tare da fargaban amsar da doctor ɗin zai bayar Likitan be ce komi ba illa ce musu da yayi su bi sa Office A tare Dad da Abba tare da Sameer suka bi bayan sa yayinda su Mom suka kasa haƙura suka take musu baya Bayan sun shiga sun zazzauna likitan yacire Glasses ɗin sa yana saka Handkerchief yashare zufan goshin sa sannan yadube su ɗaya bayan ɗaya yasoma da faɗin "To alhmadulillah zamu ce tunda komi ya zo da sauƙi ba kamar yanda muka yi zato ba, duk kan su suna da rai, kuma munyi nasaran cire masa harsashin dake jikin sa insha Allahu nan da kwana biyu zai iya farfaɗo wa, sannan..." Sai yasaki numfashi yana ci gaba da faɗin "Ita kuma Saleema gaskiya matsalan ta babba ne, domin sanadiyar hakan zuciyar ta tayi wani irin razana wanda yahaddasa mata matsala ainun, kuma hakan ya saka Zuciyar ta tana barazanar bugawa wanda Allah ne kaɗai yatsare be kai ga bugawan ba, but.. yanzu ta shiga Coma farfaɗowar ta sai ikon Allah.." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ummi tafaɗa tana fashe wa da kuka, a tsaye take sai taja da baya tajingina da bango tana kuka kashirɓan jin halin da ɗiyarta mafi soyuwa a gare ta take ciki Su kansu su Dad hankalin su yayi matuƙar tashi musamman Abba da yacire hulan sa cikin tashin hankali, babu abinda yake yi sai salati, sosai zuciyar sa ta taɓu da halin da yaji ƴar sa a ciki, sai dai ƙarfin hali da ya ara ya yafa ma kansa yayi juriyar hana kansa kuka Shiru ne yaratsa a tsakanin su gaba ɗaya babu wanda ya'iya buɗe baki a cikin su Girgiza kansa Doctor yayi cike da tausayin su yace "haƙuri zaku yi haka Allah yaƙaddaro, am.. ita kuma ɗayar Allah ya sauke ta lafiya duk da dai itama sakamakon gigitan da tayi jinin ta ya matuƙar hawa, sai dai muyi fatan samun lafiyan ta". Kallon likitan suke yi don basu fahimci me yake nufi ba "Yanzu ana duba lafiyan Babyn ne kasancewar be yi kuka ba, amma da zaran sun fito zaku ji bayani". "Doctor Wai me kake nufi?" Cewar Sameer yana kallon sa da mamaki Shima dai Doctor ɗin kallon sa yayi a rashin fahimta yace "me kenan kake magana akai Docta?" "Likita maganar Halwa muke maka kuma mun ji kana maganar haihuwa?" Cewar Abba da yatari numfashin Sameer dake shirin magana Cikin Ummi ne yayi ƙululu tuna abinda ke shirin faruwa, sam ta manta da cikin Halwa ɗin sai yanzu da ake maganar, gashi ba wancan likitan bane da yayi musu aikin bare yarufa musu asiri "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Rufe baki tayi kukan nata yatsaya cakk tana sauraron abinda doctor ɗin ke faɗi cike da nunkuwan tashin hankalin da take ciki Hannun sa yahaɗe waje ɗaya yana kallon su yace "too Ni dai ina muku magana ne akan ita ɗayar yarinyan wacce suka zube tare da ɗiyar ku, tana da juna biyu kuma ta haihu ɗa namiji, wannan shine maganar da nake muku". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Gaba ɗaya suka faɗa a lokaci ɗaya, yayinda Abba yaƙara da faɗin "To taya? Ta ina zata haifu bayan bata da juna biyu wannan wani irin abu ne?" Yayi maganar yana kallon Ummi da a yanzu hawayen fuskarta suka ci gaba da kwaranya Ita kanta bata san me zata iya faɗa a yanzu ɗin ba amma kuma ta san dole ne kowa yasan abinda ke faruwa "Kun ga yanzu ba wannan maganar zamu tsaya yi ba, mu je mu duba ta mu ganin ma idanun mu wataƙil ba ita ce ba". Dad yafaɗa yana tashi tsaye Gaba ɗaya miƙe wa suka yi suka fito, da jagorancin doctor ɗin suka isa ɗakin da aka kwantar da Halwa wanda har a lokacin bata farfaɗo ba sabida alluran barcin da aka yi mata, sai dai kuma a lokacin an dawo da jaririn nata an ajiye sa kusa da gadon ta yana kwance sai wutsil-wutsil da ƙafafu yake yi yana ƙwalala idanuwa, baya kuka sai dai hannu ɗaya da yasaka a bakin sa yana ta gwagwiya Shigowar su sai gaba ɗaya idanun su yasauka akan yaron wanda a lokaci ɗaya suka nufi gaban gadon, Mom CE tasaka hannu taɗago shi tana kallon sa cike da zallan mamaki wanda duk kan su haka fuskar su yanuna Yaron bashi da maraba da Khalil sak kamannin sa har skin ɗin sa, duk da kuwa Halwa itama baƙa ce amma skin ɗin iri ɗaya ne dana Khalil komi nashi yaɗauko Salati da tasbihi suka saki suna sake kallon yaron cike da tsananin zargin da yaɗar su lokaci ɗaya a zuciyoyin su, wanda kuwa gaba ɗaya sun ɗaura zargin ne akan ɗan Khalil ne wannan, babu ta yanda za'a yi ta raini ciki a gidan sa be san da cikin ba har kuwa ya isa haihuwa, hakan yasake tabbatar musu da zargin su gaskiya ne Kuka Mom tafashe dashi tana kallon Dad tace "Alhaji kana ganin abinda nake gani kuwa? Khalil.." Sai kuma tayi shiru takasa ƙarisawa sabida kukan da yaci ƙarfin ta Al'amarin da yaƙara ta azzara zuciyar Dad da Sameer kenan, domin su ma tunanin da suke yi kenan a ran su na cewar wannan yaron Khalil ne Gaba ɗayan su shiru suka yi kamar an yi ruwa an ɗauke, in banda kukan Mom da ƙaran fanka babu abinda ke tashi a ɗakin, har ta da Doctor tsayawa yayi shima yana kallon su batare da yasan me zai yi ba Motsin Halwa shi yafargar dasu daga tunanin da ko wannen su yake yi a ransa Ummi ce tayi saurin matsawa kusa da ita tana ɗaura hannu saman nata tare da kiran sunan ta Ahankali Halwan tabuɗe idanu tana bin mutanen dake cikin ɗakin da kallo, kana daga bisani kuma tasauke idanun ta kan Ummi da har yanzu take zirarar da hawaye, lumshe idanun ta tayi sai tabuɗe su cike fal da hawaye, cikin wani irin karyewan murya tare da sanyi sosai tace "Ummi... Ina Saleema? Bata mutu ba ko? Don Allah kar kice min wani abun ne yasame ta?" Sai kuma tajujjuya kanta tana kallon ƴan ɗakin kafin tace "Yaya Khalil.." Shiru tayi tana zirarar da hawaye sosai kamar an kunna famfo Likitan ne yamatso kusa da ita yana faɗin "ki kwantar da hankalin ki kinji kinga kina cikin wani yanayin da ba'a son jinin ki yasake hawa, duk kan su lafiyan su lau babu abinda yasame su kinji ko?" Kallon Ummi tayi, sai Ummin tagyaɗa mata kai "To yakamata ku bata wuri ta huta ba'a son tana hayaniya, sannan sai ku nema mata abinci taci za'a bata magani". Likitan yafaɗa kafin yayi musu sallama yafice Fitowa suka yi gaba ɗayan su suka bar Ummi a ɗakin, daga nan inda aka kwantar da Khalil suka wuce suka ganshi Yana kwance babu riga an naɗe masa kafaɗa da bandage, tamkar matacce haka yake ko motsi baya yi, numfashi ma sai da taimakon Oxgyen kuka sosai Mom tafashe dashi har sai da Dad yariƙo ta suka fito shima yana share hawayen sa, duk sun shiga tashin hankali matuƙa baka ma iya bambance wanda yafi shiga wani hali Saleema kam ma basu samu damar ganin ta ba, domin an hana su ganin ta tunda har a lokacin akwai likitoci akan ta Basu sake tayar da zancen yaron Halwa ba tunda kowa hankalin sa baya jikin sa duk da kuwa abun na ransu, itama kanta Halwan an sake yin mata alluran barci ta koma sabida har yanzu jinin ta be sauka ba, kuma suna son tasamu hutu sosai tayanda komi zai zama normal Mutane sun soma tururuwan zuwa inda akai ta zuwa gaishe su, duk wanda yaji halin da suke ciki dole ya tausaya musu, Brr. Tahir ma yazo da matar sa, haka ma su Hakima da Abida drever ya kawo su, Nazeefa ma tazo sai kuka take yi tunda tashiga ganin Khalil, shiyasa Dad yasaka Sameer maida su gida gaba ɗaya, sai aka bar Mom da Ummi tare dasu Dad ɗin a asibiti Kasancewar dare yayi bayan su Dad ɗin sun gama yin abinda yadace sai suka tafi, aka bar Mom wajen Khalil, ita kuma Ummi da Larai suka zauna wajen Halwa tunda Ita Saleema sun ce basu buƙatar kowa wajen ta, kafin su tafi da daren sai da aka bar su suka ga Saleema ta cikin Glasses, hakan ya ƙara ɗaga ma iyayen ta hankali sosai Abba kuwa da tashin hankali yakoma gida, a ranan mutane da dama basu runtsa ba yanda suka ga dare haka suka ga rana Halwa sai tsakar dare ta farka, tunda ta tashi Larai ta haɗa mata tea me kauri tasha, sannnan tace taba ma yaron Nono tunda sai tsala kuka yake yi domin shine ma yatashe ta, amma ina Halwa ko kallon ta bata yi ba bare ta tanka mata Lokacin Ummi na sallah tana kai kukan ta wajen rabbi domin yaji ƙan ɗiyarta yaba ta lafiya A karo na ba adadi Larai tace "Halwa ki shayar da yaron nan mana in dai ba so kike yi ya mutu ba, kinsan kuwa tun yaushe ake godo dashi yayi kuka be yi ba sai yanzu? Amma kuma kin ƙi kula sa bayan kuma kin san yunwa ke cin sa". Kallon Yaron Halwa tayi wanda yake lulluɓe da kayan sanyi hannun Larai ta ƙanƙame shi, numfashi taja kafin ta kawar da kanta tace "Bazan iya shayar dashi ba, sai dai ki kai ma Saleema shi domin yaron ta ne". "Ban gane ba me kike nufi?" Larai tafaɗa a matuƙar ɗaurewar kai, dama tunda tazo take neman wanda zai amsa mata tambayoyin ta da suke cin ta arai bata samu ba, sosai tayi mamaki da aka ce Halwa ta haihu, bare kuma da taga yaron sak irin Khalil, kawai sai taɗaura wa zuciyar ta zargin cewa wannan yaron tabbas na Khalil ne, amma yanzu kuma zancen na son Shan banban.. Bata kai ga sake magana ba taji muryan Ummi tana faɗin "Larai ki bashi ruwa don Allah ki lallaɓa sa yakoma barci". "To Hajiya". Larai ta'amsa mata cike da ƙullewar kai, sai dai babu yanda zata yi tasake wani tambayan tunda ba'a bata dama ba Ruwan taba ma yaron sannan taci gaba da lallaɓa sa yana ta ƙananun kukan sa Halwa kuwa juya bayan ta tayi tarufe idanun ta kamar me barci, amma ina tunani ne fal a ranta na abinda yafaru a yau ɗin, hawaye tasoma zirarar wa tuna yanda taga Khalil ya faɗi ƙasa baya numfashi, take zuciyarta ta wani irin bugawa lokaci ɗaya ta zabura tana ɓarke wa da kuka. [12/13/2020, 1:09 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Eighteen* ________🎓 Lokacin Ummi taci gaba da sallan ta, sai Larai ne tayi mata magana "Halwa wai lafiya kukan me kike yi?" Shiru Halwa tayi taci gaba da zubar da hawaye tare da haɗiye kukan nata Larai ajiye yaron tayi lokacin yayi barci sai takoma shimfiɗar ta takwanta, babu jimawa kuwa barci yaɗauke ta, to bata san dai ya aka ƙare ba sai washe gari da suka tashi da safe Lokacin yaron sai ɓaɓɓaka kuka yake yi amma Ummi na gani bata ce Halwa taba shi Nono ba, sai ma ɗaukar sa da tayi tana rarrashin sa, sannan takalli Larai da tasaki baki tana kallon su "Yauwa Larai ke nake ta jira, don Allah kije yanzu ki amso min madaran sa wajen Sister A'ishah, naji ta shiru bata kawo min ba gashi kuma yana ta kuka". Larai tace "to". Sannan tanufi ƙofa tafice "Itama kuma a lokacin Halwa ta gama cire kayan ta ta ɗaura zani tanufi Toilet don yin wanka "Halwa kiyi wankan nan da kyau don Allah, yanzu zan zo idan Larai ta dawo sai in taimaka miki". Gyaɗa kanta tayi tabuɗe Toilet tashige batare da ta furta komi ba. Lokacin dasu Abba suka shigo asibitin a time ɗin ne kuma ƴan sanda suka zo, don haka basu shigo ɗakin ba sai da suka gama da Police ɗin, sun zo yin bincike akan harbin Khalil da aka yi Bayan duk sun yi abinda yadace sai Dad dasu Brr. Tahir suka bi su can Station ɗin kamar yanda suka buƙata Abba ne kaɗai yashigo ɗakin Halwa na zaune saman gado tana shan tea, sai Ummi dake zaune kan kujera riƙe da jaririn tana sake bashi madara Sallaman Abba ne yasaka duk suka ɗago kai suna kallon sa sannan suka amsa Shigowa yayi ciki yana kallon Ummi fuskar sa da tsananin mamaki "Ina kwana Abba". Halwa tafaɗa kanta a ƙasa "Lafiya lau ƴa ta ya jikin naki?" "Alhmadulillah". "Masha Allah haka ake so Allah yaƙara lafiya". A laɓɓa ta amsa masa da "ameen". Ummi ma gaishe sa tayi tana goge ma Yaron baki wanda duk ya ɓaci da madara Abba kallon Yaron yasake yi sannan kuma yamaida idanun sa kan Ummi yace "ya naga kina bashi wannan abun bayan ga mahaifiyar sa? Meyasaka baza'a shayar dashi ba?" Shiru Ummi tayi bata bashi amsa ba Yayinda itama Halwa tasake duƙar da kanta ƙasa tana sauraron Abban "Ɗiya ta me yafaru da baki shayar dashi ba ake basa madara?" Ummi ce tayi magana "Abban Saleema akwai abinda nake son faɗa maka dama, amma kuma na bari ne sai mun samu nutsuwa, Halwa baza ta shayar da yaron ba sabida ta ba ma Saleema ne, kuma gashi ita bata da lafiya bare ta shayar dashi". Idanuwa Abba yafid do waje yace "ban gane ba me kike nufi?" Shiru Ummi tayi ta rasa ma me zata ce Abba kallon ta kawai yake yi na wani lokacin kafin yajuya yafice Ajiyan zuciya Ummi tasaki Lokacin ne kuma su Mom suka yi sallama ita da Nazeefa suka shigo Amsa musu Ummi tayi tana kallon su "Sannu da zuwa Hajiya". Murmushi Mom tayi tana aza idanun ta kan Halwa kafin ta'amsa, sannan suka gaisa a mutunce kafin tatambayi lafiyan me jiki Ummi tace "alhmadulillah ga ta nan jiki ya wartsake". "Allah yaƙara lafiya". "Ameen ameen, ya shima Khalil ɗin?" Ummi tatambaya Numfashi Mom taja kafin ta'amshi Yaron tana cewa "to dasauƙi dai za'a ce, Allah yarufa asiri gaba ɗaya yakuma basu lafiya gaba ɗaya". "Ina kwana Momy". Halwa tafaɗa tana ajiye cup ɗin hannun ta Da fara'a Mom ta'amsa mata tana ƙara wa da "Ya jikin naki?" "Da sauƙi". Mom tace "to Allah yasawaƙe yaƙara muku lafiya". Nazeefa ma sai a lokacin ta gaishe da Ummi Itama ta'amsa cikin fara'a tana tambayan ta School ɗin ta Daga nan shiru ne yagibta a tsakanin su Nazeefa ita dai idanu kaɗai tazuba ma Halwa tana faman kallon ta, jiya da ita takwana a ranta, musamman yanda aka ce ita ce Maman yaron nan me kama da Khalil, duk da dai bata taɓa ganin ta ba amma a fahimtan ta tasan cewa itace ƴar uwan Saleema wacce take zaune da ita, har yanzu mamaki yaƙi barin ranta yanda aka yi yaron ta yake kama da Khalil, sannan kuma ita ba aure ne da ita ba, kuma har yanzu taƙi yarda da zuciyar ta akan cewa Khalil zai iya aikata mummunan wannan zunubin da ranta ke kitsa mata Itama Mom yaron kawai tazuba ma idanu tana kallo, ta rigada ta yarda a ranta tabbas yaron Khalil ne wannan, sai dai bata so tayi maganar ne yanzu sai idan hankalin kowa ya kwanta duk da kuwa zuciyar ta a matse take da son sanin gaskiya Tabbas ba'a shedan ɗan yau, bata taɓa tunanin Khalil zai iya aikata mummunan aiki irin wannan ba, a jiya tayi kuka sosai akan wannan al'amarin, har abun ma yafi tada mata hankali a bisa ciwon Khalil ɗin, yanzu tana ji tana gani an haifa mata jika shege "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tafaɗa a ranta tana ɗauke idanun ta kan yaron zuciyar ta cike da ƙunci Numfashi taja kafin tamiƙa ma Ummi yaron tana faɗin "Bari muje, dama zan koma gida ne sai anjima in dawo". Amsar yaron Ummi tayi sannan tace "to Hajiya sai kin dawo". Sallama suka yi daga nan suka fice ita da Nazeefa. ***** Da yamma aka sallami Halwa kasancewar yanzu babu wata matsala dake damun ta, lokacin da zasu tafi Abba ya zo don haka shine yace su haɗo kayan su yakaisu Halwa ta so taje duba jikin Khalil da Saleema amma babu hali, gashi har a lokacin ba'a basu damar sake ganin Saleeman ba Lokacin da suka isa gida Halwa tawuce ɗakin ta kai tsaye, tana shiga ta'ajiye Yaron saman gado sannan tazauna tana riƙe kanta dake faman sara mata sakamakon kukan da tasha daga jiya zuwa yau Husna ce tashigo ɗakin kasancewar ƙofan a buɗe yake, gaba ɗaya jikin ta da kayan ta ta ɓata shi da garin Flower, har ta a fuskarta zuwa gashin kanta dake ɗaure da Ribom duk Flower ne Tunda tashigo Halwa take bin ta da kallo batare da ta motsa daga inda take ba Ita kuma Direct wajen Halwan tanufo tana yarfe hannayen ta tana faɗin "Mammaaa.." Tana washe baki da ƙananun haƙoran ta guda shida da tamallaka Gaban Halwan ta'isa tana miƙa mata hannu alamun ta ɗauke ta Ita kuma ta zuba mata idanu wanda a baɗini tunani take yi don hankalin ta baya wajen Husnan Ganin dai ba ɗaukan ta zata yi ba sai tajuya tafice tana sake kiran "Mammaaa.." Fitowar ta yayi dai-dai da fitowar Larai daga ɗaki tana kallon ta tazaro idanu tare da nufo ta tana cewa "Ke.. ke.. ke haka kikai ma jikin ki wannan ɓarnan? Kai Husna ba kya ji yanzu ji be yanda kika ɓata jikin ki, da alamu dai kin zubar min da flowern nan?" Ɓangale baki Husna tayi tana ƙyalƙyale mata da dariya Ɗaukan ta Larai tayi tace "mu je in sauya miki kayan tunda kin ɓata". Ɗan ƙaramin hannun nata taɗaura saman fuskar Larai ta damalmala mata da flowern da yaɓata mata hannu Ita kuma Larai sai tacafko hannun tasaka a baki tana dariya Still Husna ƙyalƙyace wa tayi da dariya tana janye hannayen ta "Ƙaniyar ki, yarinya sai rashin jin tsiya, ke ko muje in sauya miki kayan inga kuma kin sake ɓata wa". Daga haka tashige cikin ɗakin ta da Husnan a hannu tana mangare mata ƙeya. Halwa na zaune a inda take har yanzu tasoma jiyo hayaniyan Abba da Ummi, abinda bata taɓa ji ba tun zuwan ta gidan, hakan yasa sosai tayi mamaki tayi shiru tana kasa kunne don jin abinda ke faruwa Izuwa yanzu muryan Abba ake jiyo wa sosai yana ɗaga murya, duk da kuwa ba ta fahimtan abinda yake cewa amma tasan faɗa yake ma Ummi Bata motsa a wajen ba sai da taji hayaniyan ya lafa sannan tamiƙe tafito, lokacin tahangi Abba har ya buɗe ƙofa ya fice Ɗakin Ummin tanufa don jin abinda ke faruwa, duk da kuwa wani sashi na zuciyarta na kawo mata musabbabin faɗan, be wuce sanin gaskiyan samuwar jaririn nan ba. [12/13/2020, 3:37 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ _wannan shafin naku ne wattapad fans kusha sha'anin ku, Nagode da soyayyar ku gare ni❤️_ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Nineteen* ________🎓 Nocking tayi tare da sallama, bata shiga ba sai da Ummi taba ta izni bayan ta amsa sallaman nata Tura ƙofan tayi tashige tana kallon Ummin dake zaune gefen gado, kallo ɗaya tayi mata tahango tarin damuwa a fuskarta, wanda kowa yakalle ta ya san tayi kuka "Lafiya Halwa?" Ummi tayi maganar tana sakar mata murmushi Kanta tasauke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace "dama naji kamar hayaniya ne shine nazo duba ko lafiya". Still Murmushi Ummi tasaki tace "lafiya lau Halwa babu damuwa, yanzu ina yaron yake ne?" "Yana ɗaki yana barci". "To kema Yakamata kije ki kwanta ki huta sabida kin san abinda likita yafaɗa kenan". Murmushi Halwa tayi kafin tagyaɗa mata kai tajuya tafice, ɗakin takoma tayi kamar yanda Ummin tace don dama barci sosai take ji, ga jikin ta duk babu daɗi. ***** Fitan Abba babu inda yazarce sai asibiti, kasancewar sun yi waya da Dad ya tambaye sa inda yake zai zo su tattauna wani matsala Dad ɗin sai da yace masa shi yabari yazo yasame shi har gida, but Abban yaƙi hakan Lokacin da ya'isa waya yaɗauka yakira Dad yafito suka shiga mota suka zauna, sun daɗe sosai suna tattaunawa kafin Dad yafito ranshi duk a ɓace, duk da kuwa cewa sai da suka tsayar da mafita akan zancen kafin yafito, amma ɓacin ran da yake ji akan maganar ya gaza gushewa Cikin Hospital ɗin yakoma Shi kuma Abba yaja motar sa yatafi. Yana shiga ɗakin Mom da Sameer dake zaune suna taɓa hira suka kallo sa, ganin yanda fuskar sa yake a matuƙar ɗaure sai abun yabasu mamaki "Lafiya dai Alhaji meke faruwa?" Mom tatambaye sa har alokacin tana kallon sa Numfashi yaja kafin yasauke idanun sa kan Khalil, kamar yana jin sa cikin ɓacin rai yace "zaka tashi dan ƙaniyar ka zaka gaya min abinda yasaka ka aikata ma ƴar mutane hakan". Ƙirjin Mom ne yabuga da ƙarfi, cikin ruɗu tace "Alhaji kana nufin shine yay ma Halwa ciki?" Girgiza kan sa yayi cikin takaici yazauna yana faɗin "yo ai ban ga banbancin abunda suka yi mata ba da cikin, wai ƙwanyin haihuwar su shi da matar sa aka saka mata don ta haifa musu ɗa". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Cewar Mom cike da tsananin al'ajabi Sameer kam kasa magana yayi sai mayar da idanun sa kan Khalil ɗin da yayi yana kallon sa, be san cewa ɗan uwan nasa har yanzu be da wayau ba sai yau "Menene hakan kenan?" Wai yanzu kana nufin ɗan su ne Halwa ta rainan musu?" Dad yace "wlh raina yayi mugun ɓaci da Alh. Mustapha yafaɗa min, amma dole zan ɗau mataki bari yafarka zai gane be da wayau". Daga haka yamiƙe yafice yabar su nan shiru suna mamakin wannan abinda Khalil ya aikata, abun ma yay musu girma da yawa don haka basu sake yin magana ba har sanda Atine me aikin Mom tazo, sai Sameer yatashi yay ma Mom sallama yatafi akan sai gobe zai dawo sabida yau yana da dutyn dare. ****** Washe gari da yamma Khalil yafarka Mom CE lokacin ita kaɗai a wajen sa, doctor takira yaduba sa sai da yatabbatar babu matsala sannan yatafi Tea tahaɗa masa me kauri kamar yanda doctor ɗin yabuƙaci aba shi wani abun yaci, sai da tagama haɗa wa kafin tamiƙo masa Cup ɗin tace "Ga shi ka daure kasha ko zaka ji daɗin jikin ka". Numfashi yaja kafin yasoma yunƙurin dai-dai ta zaman sa, yana yi yana cije baki Hakan yasa Mom ɗin ajiye Cup ɗin hannun ta, tamiƙe tataimaka masa yazauna tare da jingina da pilow A hankali cikin sanyin murya na maras lafiya yace "zan wanke baki". Vowel ta ɗauko sannan taɗauko ruwan gora ta buɗe ta kafa masa a baki Yakurɓa yakuskure bakin sa yazuba cikin Vowel ɗin Sannan ta'ajiye tamiƙo masa Cup ɗin ya'amsa yafara sha Yana sha yana rufe idanun sa har ya ɗan sha rabi tukun yamiƙa mata Cup ɗin, a karo na biyu tun tashin sa yasake magana "Mom Ina Saleema?" Ita kawai tafaɗo masa a rai saboda yasan dole zata shiga wani hali da abinda yafaru dashi Amsar da taba shi shiyasaka shi ɗaura idanun sa akan ta, be iya yin magana ba illa kallon ta kawai da yake yi Har maganar haihuwar Halwa sai da tayi masa duk da kuwa bata nuna masa tasan ainihin zancen ba Ɗan waro idanu yayi still yana kallon ta zuciyar sa na bugawa da tsananin ƙarfi Ganin kallon da yake mata ba ƙaƙƙauta wa tace "lafiya ko akwai wani abu ne?" Lumshe idanun sa yayi yana kwantar da kansa, be sake yin magana ba duk da kuwa Mom ɗin tana ta yin masa hira Har sanda su Hakima da Nazeefa da suka zo a tare be sa ya buɗe idanun sa ba, iyakan gaisuwar su ya'amsa yasake juya bayan sa tare da ci gaba da tunanin sa Hakima na ta tsokanar sa but be ma san tana yi ba. Har dare suna nan zaune, sai da Sameer yazo sannan suka tarkata har da Mom drever yakai su gida, Sameer ne zai kwana dashi a yanda suka tsara tunda ya tashi Tun fitan su Sameer ɗin yake tsaye bakin ƙofa yana yin waya, sai da yagama kafin yazo yazauna yana kallon Khalil da idanun sa suke rufe kamar yanda yake tun ɗazu "Khalil wai su wanene kake zargi akan wannan abun da akai maka?" Sai a lokacin yabuɗe idanun sa yana kallon Sameer ɗin, sai kuma ya yamutsa face ɗin sa sabida zugin da yake ji a ciwon sa, kamar bazai yi magana ba har Sameer ya buɗe baki da ninyan sake yin masa magana sai kuma yace "Bana zargin kowa". Jinjina kai Sameer yayi yace "su ma har yanzu ƴan sanda sun kasa samun wani ƙwaƙƙwaran shaida wanda zai sa agane me hannu ciki, wannan aikin naka yana da maƙiya da yawa matuƙa hakan yasa baza mu iya gane wanda yake da hannu ba, sai dai Allah yaƙara tsare wa, but insha Allahu ko ma wanene sai asirin sa ya tonu". Khalil dai yana jin sa be tanka ba, har sanda yasauya maganar da faɗin "Ni ban taɓa tunanin baka da hankali ba sai yanzu Khalil, wani wauta ne zai saka kayi wannan gangancin, kana tunanin wannan shine maslaha da zaku cutar da ƴar mutane? Haramun ne hakan a musulunci but har da kai aka haɗa baki wajen aikata wa, ka bani mamaki wlh". A yanzu Khalil ya maida idanun sa kan Sameer ɗin yana kallon sa, sai dai be iya yin magana ba "Yanzu kowa yasan cewa Halwa ta haifa mana ɗa?" Yatambayi kansa batare da yasan afili yayi maganar ba Hannu Sameer yasaka yadungure masa kai yace "baza ka san kowa ya sani ba sai ka haɗu da Dad, wlh zaka sha mamakin sa domin yayi fushi sosai, meyasaka zaka biye ma yarinya don kawai bata haihuwa ku cutar da Halwa.." "Ni fa ba Ni ne na bada shawaran hakan ba, itama ɗin ai har da yardan ta tunda ba mu mukai mata tilas ba". Khalil yakatse sa da faɗin hakan yana turo baki "To tunda har da yardan ta kai kuma babban banza ko sai ka amince?" Marairaice fuska Khalil yayi kamar zai yi kuka yace "Bro wlh tausayin Saleema yasaka na amince da wannan shawaran da Ummi takawo, kuma wlh ban tashi dana sani ba sai daga baya, Ni kaina na so azubar da cikin sai dai kuma hakan ba me yiwuwa bane tunda Matata ta ƙwallafa ran ta akai". Sameer yace "kana nufin kenan da Ummi cikin zancen?" "Eh". Yaba shi amsa yana sake langaɓe kai Taɓe baki Sameer yayi yace "zaka sani ne babu ruwana Ni dai". Ɓata fuska Khalil yayi be sake yin magana ba, sai kuma yasaki ajiyan zuciya jin Sameer ɗin shima be ce komi ba yakalle sa yace "Brother taimaka min zan yi sallah". Tashi Sameer ɗin yayi yazare masa ƙarin ruwan da aka saka masa sannan yataimaka masa yamiƙe tsaye "Kayi a hankali kar ka zuba ma wajen ruwa". Sameer yafaɗa yana koma wa yazauna Be ce komi ba yataka a hankali yashige toilet ɗin, be wani jima ba yafito A lokacin Sameer ɗin yamiƙe yashimfiɗa masa sallaya yasoma gabatar da sallan da ake bin sa bayan ya tambaye sa kwanakin da yayi a kwance Sai da yagama sannan yakoma kan gadon yakwanta bayan Sameer ya mayar masa da ruwan, rufe idanun sa yayi yana sauke tagwayen ajiyan zuciya, be sake motsawa ba har sanda barci yaɗauke sa cikin ƙanƙanin lokaci. **** ***** ***** ***** *BAYAN KWANA BIYU* Alhmadulillah jikin Khalil yana ta samun sauƙi, har a lokacin ana ta binciken waɗanda sukay mishi hakan but ba'a samo su ba Gwamna da kansa yasaka ayi bincike sosai don gano su, duk da kuwa har yanzu an kasa samo shaida ko guda ɗaya, Asibitin babu CCTV 📷 cameras Wanda zai sa ayi saurin gano su, amma duk da haka an zuba jami'an tsaro a Hospital ɗin don tsaron Khalil ɗin, suna da tabbaci waɗanda sukai yunkurin wannan aikin suna da ninyan kashe sa ne zasu iya dawowa at any time. Fannin Saleema dai babu abinda yaci gaba tana nan a yanda take, su Ummi sai dai su zo ganin ta tunda har yanzu ba'a barin kowa yashiga inda take kwance, ta Glasses kamar yanda suka saba suke ganin ta sannan su koma gida, idan nace muku hankalin iyayen ta yana kwance nayi ƙarya, sosai suke cikin damuwa da halin da ɗiyar su take ciki, ita ba matacciya ba ita kuma ba rayayyiya ba. Kamar yanda Dad yabuƙaci ganin su a yau saboda tattauna matsalan su Khalil ɗin gaba ɗaya, yau ne suka taru a gidan Dad ɗin, har da Halwa aka zo da ita sai aka bar yaron wajen Larai Bayan sun hallara gaba ɗaya, Ummi Abba Halwa Dad da Mom sannan sai Sameer aka buɗe taro da addu'a Dad ne yasoma magana da faɗin "Asma'u abinda kuka aikata hakan be mana daɗi ba, ko kaɗan bamu ji daɗin hakan ba domin wannan ba koyarwa ne ta addinin musulunci ba, shiyasa muka zauna don samun mafita kamar yanda muka yanke hukunci Ni da Alh. Mustapha, wannan yarinya dai an cuce ta matuƙa saboda da agaban iyayen ta take hakan zai jawo mana matsala, sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba tunda wannan yarigada ya faru". Sai ya ɗan ja numfashi kafin yaci gaba "Sai dai ku gafarce Ni sabida hukuncin dana yanke daga baya, na cewar Ibrahim ɗin zai auri ita Halwan sai su zauna gaba ɗaya domin hakan shine yafi dace wa". Gyaɗa kai kawai Abba yake yi kafin yace "wannan shine daidai domin nima da tunanin hakan a raina, ai ko ba'a haɗa su aure ba babu yanda za'a yi Khalil yazauna da Saleema ita kaɗai dole zai ƙara aure, tunda ba zai zauna haka nan babu yara ba". Ummi kanta bata ji haushin wannan abun ba, sabida tasan dole ne Khalil yasake aure nan gaba, to abun farin cikin su ne tunda Halwa ce zata zama kishiyar ƴar su, ta tabbata baza ta taɓa cuta mata ba Itama Mom ta nuna goyon bayan ta tare da farin cikin ta sosai duk da har a yanzu bata san ainihin wacece Halwa ba, but shi Dad ya sani tunda sai da Abba yafaɗa masa komi da wannan maganar tafito Halwa kuwa tunda aka soma maganar kanta na ƙasa, ta shiga matsananciyar faɗuwar gaba jin cewa za'a haɗa ta aure da Khalil, sai dai bata iya nuna musu wani hali take ciki ba duk da kuwa cewa taji sanyi aranta ganin Iyayen Saleema basu nuna rashin amincewar su ba, har aka gama tattaunawan bata ɗago kai ba kuma su ma basu tambaye ta jin ra'ayin ta ba, shiyasa itama bata furta komi ba Da zasu tafi Ummi ce tayi mata maganar tatashi, don haka tamiƙe suka fito sukai gida. . _To pa Kuna ganin hakan babu matsala?_ [12/13/2020, 6:17 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty* ________🎓 An tsai da ranan auren nan da kwana huɗu masu zuwa ranan juma'a kenan Kuma duk wannan abun da ake yi babu sanin Khalil, Dad ne yace kar a faɗa masa a bari sai ranan ɗaurin aure Don haka Sameer da Brr. Tahir ne suke ta shirye-shiryen bikin, wanda yadace su gayyata sun gayyace shi duk da ba wai taron biki za'a yi sosai ba, kuma duk wani gyara na gidan sa su ne kan gaba akai Abba ya haɗa mata duk wani kayan ɗaki da Yakamata ayi mata, shiyasa da aka kai kayan gidan sai su Sameer suka kwashe kayan Khalil ɗin dake ɗakin sa suka zuba nata, sai suka bar masa abubuwan da zai iya buƙata, amma gadon sa dasu sip ɗin sa duk an sauya dana Halwa Ummi bata yi ƙyashin gyara Halwa ba duk da kuwa lokaci yazo a ƙure kuma gashi tana cikin jego, but duk wani abinda yakamata tayi mata Halwa dai bata iya mata musu duk abinda tasaka ta tana yi, ko kaɗan bata damuwa da kanta wai ko tana son sa ko bata son sa, ita kawai Saleema ce a ranta, me zai faru idan har tasan cewa ta aurar mata miji? Hakan na ɗaga mata hankali matuƙa har tashiga ɗaki tayi ta kuka, tana jin cewa bata kyauta ba kuma sannan ita butulu ce, ta ɗau alwashi da dama aranta wanda babu wanda yasan hakan sai ita kanta. Fannin su Mom sun haɗo akwati guda biyar maƙare da kaya, komi sai son barka, duk da a ƙurarren lokaci aka yi komi amma kasancewar da kuɗi komi ya tafi yanda suke so. Ranan Friday Dad da kansa yakai ma Khalil kayan da zai saka, sun matsa sai da aka sallame shi a ranan saboda jikin da sauƙi sosai domin har riga yake iya saka wa Khalil yayi mamaki sosai yanda aka bashi sabbin kaya yasaka, sannan kuma har yau yana fargaban Dad da be mishi maganar jaririn sa ba kamar yadda Sameer yafaɗa masa zasu haɗu ne, saka kayan yayi su Sameer ɗin sai tsokanar sa suke yi Su ma a lokacin suna cikin ɗakin sun sha sabbin kaya iri ɗaya har Dad, sai dai shi nashi har da malin-malin, abun ya ɗaure ma Khalil kai amma be yi magana ba bare yatambaye su Haka suka fito suka kwashe komi nasu suka hau mota sukai gida A ƙofar gidan mutane ne sosai ƴan ɗaurin aure duk da ba wani gayya sukai ba, su ma su Dad basu shiga ciki ba sai suka fito suka nufi masallacin ƙofar gidan Khalil na biye dasu yana ta mamaki, musamman da yaga wasu daga cikin abokan aikin sa, sai kuma yanda ake bashi hannu ana gaisawa dashi suna kiran sa Ango, sai abun yasake ɗaure masa kai, kallon Brr. Tahir dake kusa dashi yayi yace "Wai meke faruwa ne?" Dariya Brr. Tahir yayi yace "su Daddy aure zasu yi maka shine abinda ke faruwa". "Auree". Khalil yafaɗa da tsananin mamaki wanda lokaci ɗaya gaban sa yay mugun faɗuwa Aure kuma? Shi ɗin ne za'a yi ma aure? Mamaki al'ajabi da suka cika sa shine yakasa sake yin magana bare kuma yasake tambayan wani abun Suna shiga Masallaci bayan sun zazzauna yana ji yana gani aka ɗaura masa aure tunda abun yafi ƙarfin tunanin sa, har fa alokacin mamaki yake yi wanda ya kasa yarda cewa maganar Brr. Tahir gaskiya ne Amma jin sunan wacce tazame masa mata a yau ɗin sai lokaci ɗaya yayarda da cewa tabbas shine akayi ma aure, shirun da Dad yayi masa yana nufin zai aura masa Halwa ne Baza ka taɓa sanin wani hali Khalil yashiga ba domin gaba ɗaya jin sa da ganin sa tare da tunanin sa sun tsaya cakk, be san ya aka ƙare a wajen ba, shi dai yasan Brr. Tahir ya riƙo sa sun fito taron jama'a sannan sun shiga cikin gida, ɗakin su dake gidan a nan yanufa dashi, tunda ya'ajiye sa saman gado yazame yakwanta yarufe idanun sa be sake motsawa ba Shi kansa Brr. Tahir ya shiga damuwa ganin yanda Khalil ɗin yakoma, gashi mutane suna ta shigowa suna masa magana amma tamkar gunki haka yakoma musu, baya magana baya kuma jin su. ***** Fannin Amarya ma hakan take, baza ka taɓa gane wani irin hali take ciki ba, ko kaɗan bata murna da wannan ranan, ita dai kawai tana yin duk abinda aka saka ta ne, har dare ba ta iya cewa uffan sai dai tabi mutane da idanu Kuma duk a yau ɗin ne akayi sunan jaririn da yaci suna Ahmad, zai ci gaba da zama wajen Ummi ne har sanda Saleema zata samu lafiya. Brr. Tahir ne aka wakilta wanda zai ɗauko Halwa yakai ta gida ita kaɗai, don haka lokacin da yazo har an saka ta sake yin wanka ta shirya cikin Swiss less milk colour, duk da kasancewar ta baƙa kayan yayi mata kyau sosai, bare kuma yanzu da tasake haske sosai skin ɗin ta yasake fresh Ummi ita da kanta taraka ta har mota tabuɗe mata tashiga Halwa bata yi kuka ba iyakan dai tunda taɓoye kanta a gyalen ta bata sake motsa wa ba Brr. Tahir yana ta tsokanar ta yana jan ta da hira amma shiru tayi masa tana sauraron sa, har sanda suka kai yaraka ta har ciki sannan yanuna mata ɗakin Khalil a matsayin nan ne ɗakin ta, shiga tayi shi kuma yafice a gidan gaba ɗaya Ɗakin tabuɗe tashiga a hankali, daddaɗan ƙamshin turaren sa ne yay mata maraba cikin hanci, sai taja gauran numfashi tana sake buɗe ƙofofin hancin nata don sake shaƙa, sosai take jindaɗin ƙamshin shiyasa koda yaushe burin ta kawai tashaƙa a hanicin ta, sauke gyalen daga kanta tayi tana ƙare ma ɗakin kallo, bata taɓa shigowa ba sai a yau ɗin Sai da tadaɗe a tsaye anan tana kallon ɗakin kafin tataka tanufi gaban gadon tahaye takwanta Allah babu yanda baya tsara lamarin sa, Wai yau ita ce aka kawo gidan nan a matsayin matar gidan, tabbas yau tana cikin wani yanayin da babu me gane wa sai ita kaɗai ***** Khalil kuwa yana can gida su Dad sun saka sa gaba suna mishi nasiha, duk da basu san menene a ransa ba amma sun gane baya cikin nutsuwan sa ko kaɗan, sosai yake tattare da damuwa, kuma sun san cewa dole ne zai shiga wani yanayi tunda tamkar auren dole sukai mishi a ganin su Bayan sun gama mishi nasiha yafito Drever yatuƙo sa zuwa gida batare da yayi tunanin wai yasiyo abubuwan da ake tarban Amarya ba. Halwa na kwance taji ƙarar buɗe gate da rufe wa, bayan wajen minti 5 kuma taji an buɗo ƙofan ɗakin an shigo, a yanzu tarigada ta ƙudundune kanta cikin gyalen sai dai tana kallon inuwar sa har sanda yasoma takowa yanufo wajen gadon Tun sanda yashigo idanun sa suka faɗa kanta, don haka yanufi wajen gadon yatsaya ƙerere yana faman kallon ta, ya saka hannun sa ɗaya cikin aljihun wandon sa Gaban Halwa sosai yake faɗuwa jin sa a bakin gadon, rufe idanuwan ta ruf tayi tana sauraron bugun zuciyar ta da kuma abinda zai biyo baya Leɓen bakin sa na ƙasa yacije da ƙarfi yana sakin huci, sai yajuya yanufi Toilet, wanka yayi yafito har lokacin Halwa bata motsa ba duk da kuwa tasan baya wajen Wajen Sip yanufa yabuɗe, yamutsa fuskar sa yayi ganin babu komi a wajen, sai yanzu ma yasake ƙare ma ɗakin kallo yatabbatar an sauya masa kayan ɗaki Be ce komi ba yasake buɗe ɗaya side ɗin anan ne yaga kayan nasa, jallabiya yazaƙulo tare da gajeren wando yakoma cikin Toilet yasaka, sai da yagama yafito yanufi ƙofa yafice, ɗakin Saleema yashiga yakwanta saman gadon ta Rufe idanuwan sa yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, bazai ce baya farin ciki ba a yau, sai dai abinda yasani a game da ita shine ya jagula masa duk wani buri na ransa, taya zai iya zama da mazinaciya a matsayin matar sa? Har yau yana matuƙar ƙaunar ta aransa domin kuwa ji yake yi tamkar ana ƙara masa wutan ƙaunar ta, sai dai duk sanda yatuna Halwa tayi rayuwan ƙasƙanci har da rabon ɗiya hakan na mugun ɓata masa rai, kuma ba komi yajanyo hakan ba sai tsananin kishin ta da yake yi, duk sanda yaganta sai zuciyar sa tariƙa raya masa rayuwan da tayi da ƙattin banza, shi a ganin sa tunda har ta iya haifar yarinya tabbas ita ɗin ba ƙaramar tantiriyar karuwa bace, maybe yanzu ta tuba ne shine tadawo gidan su Saleema tazauna Baya jin zai iya rayuwan aure da ita, sai dai tayi ta zama ahaka har sanda zai huce watarana ƙila yaɗauke ta a matsayin matar sa, wannan shine shawaran da yayanke a ransa, a cewar sa yana da mata ita kaɗai ta ishe sa Numfashi yaja yaci gaba da tunanin sa zuciyar sa duk babu daɗi sabida yanda tunani masu yawa suka zo sukai mishi rututu. Itama Halwa tunda yafita tasaki numfashi tana fito da kanta cikin gyalen, daman tasan hakan zai iya faruwa, ita kanta tariga ta sanya ma ranta zaman gidan kawai zata yi ba a matsayin matar sa ba, baza ta taɓa amince wa da auren nan ba sai idan Saleema ta yarda zata iya zama da ita a matsayin kishiyar ta, idan har bata amince ba ba za ta taɓa zama ba dole ne tabar gidan, wannan alƙawari ta ɗaukar wa kanta duk ranan da Saleema tanuna rashin jindaɗin ta to tabbas zata bar rayuwan su gaba ɗaya. . _to fa masu sauraro kuna jin yanda Khalil da Halwa suka sha alwashin zaman nasu yanda zasu aiwatar dashi._ _me zai faru?_ 🤔 [12/16/2020, 10:36 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty One* ________🎓Washe gari babu wanda yatashi da wuri duk kan su, barci suka sha sosai har wajen ƙarfe 11:30am. Sannan ne Khalil yasoma tashi, wanka yashiga yayi a Toilet ɗin Saleema, sai da yafito yatuna kayan sa na ɗakin sa, dayike be taɓa kwana anan ɗin ba don haka babu kayan sa ko ɗaya a ciki, jallabiyan jikin sa yamayar yanufi ɗakin sa Yana tura ƙofan yashiga yahange ta kwance saman gado sai sharan barci take yi, wajen gadon yaƙarisa yana kafe ta da idanuwan sa Tana kwance ta ɗaura kanta saman pilow tare da matse shi sosai a tsakankanin hannayen ta, gyalen da ɗankwalin ta gaba ɗaya sun yi hanyan su, sai ta nannaɗe ƙafafuwan ta waje ɗaya tacure kamar wata me jin sanyi Idanu kawai yazuba ma face ɗin ta yana kallon yanda tabuɗe baki tana sharan barci, be san sanda yasaki murmushi yana jin tsananin son ta a ransa Ya ɓata lokaci sosai yana ƙare mata kallo ko ta ina, sai da yagaji don kansa kafin yanufi sip ɗin sa yazaro ƙananan kaya yasaka, sannan yanufi gaban mirror yayi shafe-shafen sa tare da gyara yalwataccen gashin kansa yafeshe jikin sa da turaren sa masu shegen ƙamshi sannan yafice. Ƙamshin turaren sa shine yatashe ta, lokaci ɗaya tabuɗe idanunta batare da ta motsa ba, sai da tadaɗe ahaka tana ta shaƙar daddaɗan ƙamshin sa kafin tamiƙe zaune, ɗankwalin ta taɗauka taɗaura tasauka tanufi Toilet, bata fito ba sai da tayi wanka kafin tariƙo kayan ta a hannu tana ɗaure da towel tafito, ajiye kayan tayi tanufi gaban mirror tashafa Lotions sannan tanufi wajen Trolly ɗinta tazaɓo kayan da zata saka Doguwar riga ne na atamfa iya ƙasan gwiwan ta, sai skert pencil me tsagi ta baya, kayan sun yi mata kyau da tasaka kasancewar atamfan ja ce da ratsin blue, ɗan kwalin kawai taɗaura tafito sabida yanda take jin yunwa sosai a cikin ta Babu kowa parlour'n sai tanufi kichen kanta tsaye, dashi tasoma cin karo yana zaune a bakin ƙofa saman kujera, hannun sa riƙe da tea Cup yana latsa wayan sa Shigowan ta yasa yaɗago kai yana kallon ta, wanda idanuwan su suka haɗe cikin na juna, sai tayi saurin cire nata idanun tana gaishe sa "Ina kwana?" Be ɗauke kansa akan ta ba sabida tayi masa kyau sosai duk da kuwa babu kwalliya a fuskar ta, kuma kasancewar tana jego sai skin ɗin ta yaƙara fresh duk da kuwa ta rame a fuska, amsa mata yayi a taƙaice Sai taƙara ce masa "Ya jiki?" Wannan karon sai da yaja lokaci kafin ya'amsa mata wanda har ita tayi tunanin ba zai amsa ɗin ba, kuma tana tsaye a wajen taƙi jirga wa, ji kawai tayi gaba ɗaya kamar an zare mata kuzarin ta sabida yanda take jin idanuwan sa akanta, wanda ta tabbatar kallon ta yake yi shiyasa takasa gaba takasa baya Miƙe wa yayi yanufi cikin kichen ɗin ya'ajiye Cup ɗin hannun sa sannan yafice Fitan sa yayi daidai da sauke numfashin da tayi, dafe ƙirjin ta tayi tana jin yanda yake luguden bugawa, ta jima a tsaye bata san me zata yi ba kafin kuma taja ƙafafun ta taƙarisa ciki cike da rashin jindaɗin yanda Khalil yasauya mata tun kafin haihuwar ta, ta rasa mene tayi masa yasauya lokaci ɗaya, ada abun baya damun ta amma a yanzu sosai take jin haushi da rashin yin mata magana da baya yi Tura baki gaba tayi tasoma neman abinda zata yi breakfast, ruwan tea ta dafa sannan tasake a Cup ɗin da yasha, sai tasoya ƙwai guda uku, sai da tagama tahaɗa Tea ɗin sannan tazauna a inda yatashi tasoma karya wa, ba ta son tafita Parlour ta tarar dashi don haka tayi zaman ta nan Sai da tagama sannan tafito, babu shi cikin parlour'n sai tanufi ɗakin sa wanda yazama nata a yanzu, tana tura ƙofan tahange sa bakin gado, dasauri tajuya takoma parlour tazauna Kallo takunna tayi zaman ta anan tana ta saƙe-saƙe a ranta. Khalil be fito ba sai da yaji kiran sallan azahar, da keey ɗin mota a hannun sa yafice agidan. Itama tashi tayi tashiga ɗaki tagyara kwanciyar ta takwanta saman gado bayan ta ɗau wayan ta da tabari akan drower, kasancewar tana jego hakan yasa bata da tsarki, wayan ta tay ta dannawa har zuwa wani lokaci, gaba ɗaya ta gaji da zaman ta haka nan har Ummi ta kira sun yi waya, daga ƙarshe sai tajawo jakan makarantan ta tasoma duba handout ɗin ta, a ranta tana tunanin dole ne gobe takoma school tunda baza tay ta zama haka nan ba koda yaushe bata da abokin hira Da wannan shawaran tatashi tasoma gyara gidan, duk da kuwa ko ina fesfes yake jin sa, amma haka tagyara ko ina tasaka turaren ƙamshi gidan yabaɗe da ƙamshi sosai, ganin Khalil be dawo gidan ba sai tasake sakin jikin ta tana ta harkokin gaban ta, a Parlour tabaje tana ta kallo gefe ɗaya kuma ga handouts ɗin ta ta baje su tayi karatun har ta gaji Sai da yamma tayi sosai sannan tatashi tashiga kichen tagirka musu shinkafa da miyan jajjage sannan tayi musu zoɓo tahaɗa salat, takai dainning duk ta jera tanufi ɗaki tasake yin wanka tasauya kaya. Sai dare Khalil yadawo, lokacin tana Parlour zaune yashigo, sannu da zuwa tayi mishi ya'amsa yawuce ɗakin ta, wanka yayi yasauya kayan sa yafito Parlour Kasancewar da yunwa yadawo yana fito wa yakalli dainning, nan yaga coololi an jera su don haka can yanufa yazauna yazuba abincin yaci Halwa tun fitowar sa tashige ɗaki, dama zaman jiran sa take yi taga dawowar sa sabida zuciyarta haka kawai tamatsa mata da rashin jindaɗin dawowar nasa, sauya kayan ta tayi zuwa na barci riga da wando sannan tahaye gado takwanta, babu jima wa barci yay gaba da ita Khalil be dawo ɗakin ba sai da yagama kallon sa sannan yashigo yaɗau kayan barcin sa yasaka yafice yakoma ɗakin Saleema. Washe gari da safe Halwa tana tashi tagyara gidan tayi musu breakfast sannan taci nata takoma ɗaki tashiga wanka, tana fito wa tashirya cikin riga da skert na atamfa ruwan madara sai ratsin brown da baƙi, ɗinkin yayi mata kyau sosai ya sake haska ta matuƙa, Hijab tasaka brown Colour wanda yatsaya mata dai-dai gwiwar ta, sai taɗau HangBag ɗin ta tafito Lokacin Khalil ya fito daga ɗaki yana shirin shiga nata don saka kaya suka ci karo Dasauri tamatsa masa tare da gaishe sa Kallo yabi ta dashi kafin ya'amsa mata batare da ya tashi a hanyan da yatsare mata ba, mamaki yake yi ganin ta da shiri "to ina zata je?" Yatambayi kansa gaban sa na faɗuwa jin wani sashi na zuciyar sa ta kawo masa tunanin ƙila gida zata koma Halwa kamar tasan me yake tunani tace "Uhmm dama zan je school ne". Be ce komi ba yamatsa mata tawuce shi kuma yashige ciki Tana fita tahaɗu da drever, tayi masa maganar makaranta zai kai ta zuwa yayi yaɗauko motan tahau suka fice cikin gidan. Khalil dake tsaye bakin window yana kallon su, sai da suka fice sannan yasauke ajiyan zuciya yaƙarisa yasaka kayan sa yafito Parlour yay zaman sa, dayike ba wai ya gama samun sauƙi bane shiyasa bazai iya koma wa bakin aiki ba, har yanzu ciwon na damun sa don baya iya yin tuƙi, jiya da yafita har ya shiga mota ya zauna ya kunna yana shirin tuƙa wa yaga bazai iya ba, shine yakira drever suka fita tare. ***** Drever na sauke Halwa tanufi department ɗin su, yau bata saka Niƙap ba don bata da sha'awar saka wa kamar ko yaushe A hanyan ta taci karo da wata Course mate ɗin ta Nafeesa, suna mutunci sosai da ita don haka tayi saurin kiran ta Hakan yasa Nafeesa tajuyo don taga me kiran nata, ganin Halwa sai tafaɗaɗa fara'an ta tace "A'a yau Halwa ce a school ɗin?". Murmusawa Halwa tayi lokacin ta ƙariso wajen ta sai taba ta hannu sukai musabaha sannan tace "Wlh kam ya kike?" "Lafiya lau ya gida kwana da yawa?" Nafeesa ta faɗa tana murmushin itama "Alhmadulillah". Nafeesa tace "to masha Allahu mu ƙarisa mana yanzu zamu yi Lecture". Halwa bata ce komi ba har suka ƙarisa class ɗin da zasu yi Lecture ɗin Sai da suka zauna Nafeesa tace "ya ban ga Babyn namu ba? Tunda abun ma babu gayyata ba'a ɗauke mu a bakin komi ba shiyasa zumuncin ma ba'a son yi damu". Halwa kallon ta tayi sai dai ta kasa cewa komi, bata yi tunanin zuwan da take yi ada zasu fahimci tana da ciki ba, sabida tun lokacin da yasoma girma take zumbula Hijab har ƙasa sannan kuma tana kaffa-kaffa dashi don kar agane, kuma tana saka niƙap a fuskar ta bare su ce zasu fahimta Abunda bata sani ba da yawa waɗanda take gaisa wa dasu sun san tana da ciki, har gulman ta suke yi ashe tana da aure ne bata faɗa musu ba, daga ƙarshe ma sai suka dena ganin ta gaba ɗaya duk da kuwa suna tunanin cewa ƙila saboda cikin ne tadena zuwa Murmushi Nafeesa tayi tace "wai kina tunanin bamu sani ba ko? Ai kallon ki kawai muke yi tunda kin ƙi faɗa mana, kinga da mun zo suna ai". Itama Halwan murmushin taƙaƙalo tace "eyya kiyi haƙuri Nafeesa". "Babu komi ai". Nafeesa tafaɗa tana dariya Sai kuma tace "Me muka samu ne?" Tana murmushi tace "Ahmad". "Allah Sarki ki ce sunan Saurayina ne? To Allah ya raya sa ta hanyan gaskiya". Ita dai Halwa murmushi kaɗai tayi tana amsa wa aranta Nafeesa tace "to gashi kuma abubuwa da dama sun wuce ki, an sha karatu wlh ga kuma tests da akai ta yin mana". Cikin damuwa Halwa tace "eyya ban ji daɗi ba, yanzu ya zan yi kenan?" "Kar ki damu zan raka ki wajen malaman sai kije ki nemi alfarma ko zasu yi miki tunda kinga an kusa fara Exams, kinga sai ki siya handouts ɗin da yawuce ki kije kiyi ta karanta wa". "Ai kuwa Na gode". Halwa tafaɗa cike da jindaɗi "Babu komi ai muna tare". Daga nan sun ɗan taɓa hira akan karatun su wanda Nafeesan take ta ƙara mata bayani akai, sai da Malam yashigo sannan suka nutsu suka maida hankalin su ga karatun. Kamar yanda Nafeesa tace mata zata raka ta wajen malaman, suna samun free suka tafi, taci Sa'a don wasu daga cikin malaman sun ce gobe tazo zasu yi mata, sai kuma waɗanda suka bata assignment, mutum ɗaya ne yayi mata text ɗin sa nan take, ai kuwa daƙyar ta amsa uku cikin biyar tunda babu wanda aka yi da ita, su ma ɗin wanɗanda ta'amsa turancin ta ne tagwamitsa yanda tafahimta sannan tamiƙa tafito. Tunda tadawo gida babu abinda tatasa agaba sai karatun, sai wajen ƙarfe biyar tatashi tayi musu abincin dare sannan taƙara koma wa tadasa daga inda tatsaya tunda babu abinda zata yi. [1/5, 9:31 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty Two* ________🎓Zaman Khalil da Halwa zama ne tamkar ba mata da miji ba, babu abinda ke haɗa su sai gaisuwa, idan yatafi aiki itama sai tatafi school ɗin ta Zata gyara gidan tayi musu girki kullum bata gajiya amma magana wannan baya haɗa su in ba ya zama dole ba A ɗan zaman nan da suka yi a matsayin ta na matar sa tuni ta gane ta afka ƙaunar sa, bata da aiki yanzu sai tunanin sa da kuma zaman da suka yi abaya lokacin yana mata magana sosai, karatun da yasaka ta a gaba da kuma soyayyar Khalil wanda bata san sanda tafaɗa ba sun haɗe mata sun yi mata yawa, don haka gaba ɗaya yanzu ta rame ko kaɗan bata da sukunin zuciyarta, ga karatu ga tunanin da yazamar mata jaraba, da farko ta so duk yanda za'a yi ta yakice sa a ranta amma ina hakan ya gagara, wani lokacin har zuwa take yi tazauna kusa dashi tana masa magana ko wai zai riƙa kulata tasamu sukunin zuciya sabida yanda ƙaunar sa ke azalzalan ta, amma yanda tazauna haka zata tashi babu abinda ke haɗa su, hakan na ƙara saka ta shiga mawuyacin hali, har tashiga ɗaki tayi ta kuka tana tirr da zuciyar ta akan rashin adalcin da tayi mata, duk a maza ta rasa wanda zata so sai mijin ƴar uwanta da take ganin ƙimar ta sosai, wanda idan ba ƙaddara da ya haɗa su ba ba ta tunanin zata iya auren sa, a yanda tafahimta Khalil bazai taɓa son ta ba Saleema kaɗai yake so, ita kawai zata yi zaman haƙuri ne har sanda Saleeman zata samu lafiya tasan makomar ta, tunda tarigada ta saka a ranta idan Saleema bata son auren to guduwa zata yi, wannan shine kaɗai hanyan da taga zata iya guje wa auren nan. ***** Ahmad na wajen Ummi har yanzu ita take kula dashi, idan tatafi aiki sai kuma Larai tahaɗa su ita da Husna taci gaba da kula dasu, idan kuma ta dawo sai tarage mata aiki wajen amsar Ahmad ɗin, tunda aiyukan sun yi ma Larai yawa, ga aikin gida ga kuma raino. Har yanzu dai Saleema babu labarin ci gaba, kullum iyayen ta addu'a suke yin mata Allah yatashi kafaɗun ta, idan Ummi taje aiki wuni take yi a wajen ta tunda yanzu ana barin ta tana shiga Itama Halwa wani lokacin tana zuwa duba ta, takan yi kuka duk sanda taje taga Saleema cikin wannan halin da ba ta sanin a duniyar da take ciki. Rayuwa taci gaba da tafiya yanzu gashi har Saleema ta shafe wata biyu curr kafin tafarfaɗo, zo ku ga murna wajen ahalin ta duk da kuwa ba wai ta dawo hayyacin ta gaba ɗaya bane tana cikin ciwo sosai, amma dai ahaka kowa ke murna da samun lafiyan ta An ci gaba da treating ɗin ta har zuwa ɗan wani satikai inda tasamu lafiya sosai alhmadulillah sai abinda ba'a rasa ba, ciwon zuciyarta yanzu shine matsalan ta, but duk da haka an ɗaura ta akan magani Duk idan Khalil yatashi daga aiki can yake wuce wa, wani lokacin ma idan zai tafi da safe sai ya soma leƙa ta kafin yawuce aikin sa Haka itama Halwa daga school can take wuce wa tayi zaman ta sai dare idan Khalil yazo sai su taho tare Hakan na faranta ran Saleema sosai, musamman idan taga ƴan uwanta tare da ita, babu jima wa aka sallame ta gaba ɗaya suka dawo gida Tunda suka dawo sai kuma Halwa takoma kula da ita, ita take yin mata komi bata barin ta taɗauki ko tsinke, idan har ba wani muhimmin abu suke a school ba bata zuwa, tunda a yanzu ba an cika yin musu lectures bane sabida kusantowar Exams ɗin su, idan kuma suna da Lecture irin guda ɗayan nan ƙin zuwa take yi Shima Khalil yana bata kulawan sa sosai, yana faranta mata da iyawan sa, sosai yake ƙara jin son Halwa aransa musamman yanda yaga tana ɗawainiya da Saleema ko kaɗan bata gajiya, wani lokacin sai yazauna yay ta tambayan kansa meyasaka yake mata haka? Halwa tana da kyawawan hali da shiga rai ga duk wanda yazauna da ita dole sai ta burge sa, to shi meyasaka bazai yafe mata ba? A yanzu dai ba laifin take aikata wa ba tunda ta tuba, yakamata yabata dama yacire haushin ta a ransa ya amshe ta hannu bibbiyu a matsayin matar sa tunda abinda yafaru ya rigada ya wuce, ko Allah ana masa laifi ya yafe bare kuma shi bashi ne tay ma laifin ba, kawai yayi amfani da hakan ne yana cuta ma kansa bayan kuma yana ƙaunar ta sosai a ransa, shiyasa yanzu yasassauto yake shiga harkan ta Hakan ba ƙaramin faranta ranta yayi ba, sosai a yanzu take matuƙar farin ciki saɓanin abaya da koda yaushe take cikin damuwa Saleema duk bata fahimci komi akan auren Khalil da Halwa ba tunda ba wai faɗa mata akayi ba, kuma Khalil ba kwana ɗakin Halwan yake yi ba, babu abinda ke haɗa su wanda zata iya zargin su, saboda tunda tadawo Halwa takoma ɗakin ta na da tadena kwana a cikin ɗakin Khalil ɗin, kuma tayi hakane duk wai saboda Saleema kar ta zargi wani abun tunda ba'a so tasani sai idan ta samu lafiya Shima Khalil ɗin ganin haka sai yadena kwana aciki yana bin Saleema ɗakin ta, tunda dai babu daɗi ace yana kwanar mata a ɗaki shi da wata matar Hakan yasa Halwa ta ƙara ganin ƙimar Khalil a idanun ta, tabbas Khalil mutum ne na daban, tsananin kyawun halin sa tare da kirkin sa ya wuce yanda ake zato, ɗaya ne tamkar da dubu, dole ko kana so ko baka so ka ƙaunace sa, idan har kuwa zaka yi mu'amala dashi dole ne yashiga ranka. Ahaka har su Halwa suka soma Exams ɗin su na First semester wanda daga shi ne sai Finally, sai kuma School of Low da zata shiga. **** ***** ***** Yau aka yi ma su Halwa hutun school don haka da wuri tadawo yau ɗin tunda Pepper ɗaya suka yi Saleema na kwance kan two sitter ta ɗage ƙafafunta ta ɗaura saman jikin kujeran tajiyo sallaman Halwan lokacin da taturo ƙofan tashigo, tashi tayi dasauri tana mata oyoyo, suka yi Hugging juna suna dariya cike da nishaɗi sai suka zube saman kujeran "Ai gwara da Allah yadawo dake da wuri, dama yanzu nake tunanin kiran ki in sanar miki zan je gida don yau da kewar su Abba na tashi, na tambayi Barrister ya bar Ni". Saleema tayi maganar idanun ta kan Halwa tana dariya Yamutsa fuskar ta Halwan tayi kamar yanda yazame mata jiki tace "kai sis yanzu sai ki tafi ki bar ni kenan?" "A'a wlh nayi tunanin ba yanzu zaki dawo ba, Ni har nayi tunanin bari sai gobe ne kuma sai ga ki kin dawo, sai mu tafi tare yanzu". Kaɗa kanta Halwa tayi kafin tace "anya zan je kuwa wlh agajiye nike, barci kawai nake so in Yi". Saleema tace "to ki kwanta ki huta mana, ina tunanin ma idan naje zan taho dasu Husna ne". "Aa Iyeee wlh baza ki kawo mana aiki ba, akan me zaki ɗauko su?" Wani kallo me kama da harara Saleema tasakar mata "Me kike nufi?" Halwa dariya tayi tace "wlh babu komi, amma don Allah ki bar Husnan ki ɗauko Ahmad ne". Miƙe wa Saleema tayi tay hanyan ɗakin ta tana faɗin "kar ki damu sister Ni ban ce ki tayani rainon su ba wlh Ni kaɗai zan iya tunda Ni ce uwar su dama ai". Bata tsaya jin amsar Halwan ba tashige ɗaki abun ta Itama Halwa tashi tayi tabi bayan ta don taga fushi tayi da ita "Haba Sister daga wasa?" Turo baki Saleema tayi tana hararan ta batare da tace mata komi ba tasoma cire kayan jikin ta Ganin dai ba tanka ta zata yi ba, sai tace "to nima zan je bari in shirya, tare zamu je taho wa dasu". Baki Saleeman tawashe tace "dagaske sis?" Gyaɗa mata kai Halwa tayi tace "bari ma kigani". Tayi hanyan ƙofa tana faɗin "nima bari in je in shirya". **** Bayan sun gama shirin su drever yakai su gidan su Saleeman Ummi tayi murnan ganin su barin ma da taga Saleeman ta sake samun sauƙi sosai har wani ƙiba tayi na kwanciyar hankali "Ummi ina Abba ne don Allah". Saleeman tafaɗa tana kwaɓe fuska tana kallon Ummi ɗin Ummi murmushi tayi cike da ƙaunar diyar ta tace "ai yau Abban ki yayi nisan zango, amma ina tunanin zai iya dawowa kafin ku tafi". Gyaɗa kanta tayi tamiƙe tana faɗin "wai ina Husna ne ban ganta ba?". "Tana wajen Larai wlh, shima Ahmad ɗin don yayi barci ne takawo shi amma da duk suna wajen ta". Ɗakin Larai tanufa da ɗan gudun ta tana cewa "bari inje inga Ummina". Tun bata kai ba take kiran sunan Husnan har tashige Ummi dawo da kallon ta wajen Halwa tayi tana dariya wanda itama Halwan dariyan take yi tace "Ummi wlh Saleema son yaran ta yayi yawa ko kunyan ki bata ji". "To ina kuwa zata ji kunya na? Ai Saleema sai ikon Allah, ita da tazauna tana mana kukan cikin ta ya zube wani kunya zata ji anan". Dariya sosai Halwa take yi itama Ummin na taya ta Ummin tace "Allah yay muku albarka yarana, yaba ku waɗanda zasu ji ƙan ku". Halwa na murmushi ta'amsa da "ameen Ummi". Lokacin Saleema tafito daga ɗakin Larai tana faɗin "itama tayi barcin". Dariya Halwa tayi tace "ai da kin taso ta tunda zumuɗin ganin su kike yi". Hararan ta Saleema tayi tana zama gefen Ummi tace "bazan tashe sun ba". Halwa dariya kawai take mata tana tsokanar ta, ita kuma tana rama wa cike da wasa da dariya Ummi dai tana jin su bata saka musu baki ba, yau dai tayi ninyan faɗa ma ɗiyar nata auren dake tsakanin Halwa da Khalil, sabida a ganin ta be kamata ayi ta ɓoye mata ba kuma ana cutan Halwan, idan kuma hakan yaci gaba da tafiya tasan sun so kansu da yawa tunda sun gummaci su faranta ran ƴar su sannan su cuta ƴar mutane, yanda tagan su ahaka da tsananin shaƙuwar su bata jin Saleema zata wani damu, don haka ajiyan zuciya tasauke tana aza idanun ta kan Saleeman takira sunan ta "Na'am Ummi". Saleema ta'amsa mata tana kallon ta Ummi tace "nasan kinsan ƙaddara Saleema kuma kinsan duk wanda yacika musulmi dole ne ya yarda da duk wani ƙaddara da tasame sa me kyau ko mara kyau.." Gaba ɗaya shiru suka yi har Halwa suna sauraron ta, yayinda itama kuma tasoma zayyano ma Saleema duk abinda ke faruwa har da juya mata mahaifa yau sai da tafaɗa mata, kuma tayi hakan ne wai don Saleema tasake ganin girman Halwa, tasan cewa bata cancanci ɗaukan wani mataki akanta ba tunda ta taimake ta ta fanni da dama, tayi mata abunda babu wanda ya'isa yay mata shine kyautar yara har biyu, Halwa ba wacce zatayi kishi da ita bane domin ita ɗin me son farin cikin ta ne Sai da Ummi takai aya a zancen ta kafin Saleema tamiƙe tsam daga wurin tawuce ɗakin su Hakan yasa suka bi bayan ta da kallo cike da fargaba aran su Matse baki Halwa tayi hawaye na cika cikin idanuwanta Kallon ta Ummi tayi suka haɗa idanu sai Halwan tasauya fuskarta da ƙirƙirar murmushi batare da tasan cewa hawayen cikin idanun ta sun sauka saman kuncin ta ba "Menene na kuka kuma? Bana son shirme kinji ko?" Ummi tafaɗa tana ɗaure fuskarta Dasauri Halwan tasaka hannu tana share hawayen jin danshin su sosai saman kuncin ta wanda har ɗiga akan hannun ta suka yi, tana so tayi magana amma kalma ɗaya takasa furta wa, tana so tamiƙe tabi bayan Saleema amma ta kasa tashi Ummi ce tatashi tanufi ɗakin, inda tasami Saleema kwance saman gadon ta danne fuskarta saman pilow, zama tayi akan gadon tasoma yin mata nasiha me ratsa zuciya tare da kwantar mata da hankali, sannan tana nuna mata koda ba Halwa bace dole ne Khalil yaƙara mata kishiya. Halwa na zaune a inda take ta haɗe hannayen ta waje ɗaya jikin ta nata tsuma, so kawai take yi tasami damar da zata yi kuka sai dai baza ta iya nuna raunin ta anan ba, bashi da amfani ko kaɗan Tana nan zaune su Ummi suka fito, idanu kawai taɗaura ma Saleema tana son karantan yanayin da take ciki Ita kuma Saleema sai taɗauke kanta gefe batare da ta bari sun haɗa idanu ba Larai ce tafito daga kichen tanufi dainning tana jera musu abinci Cike da farin ciki Ummi tace "to ku tashi muje kuci abinci tunda an gama". Babu musu gaba ɗayan su suka bi umarnin ta, kan dainning suka zauna Ummi na ta jan su da Surutu duk dan wai su saki jikin su ganin yanda gaba ɗayan su suka yi shiru, babu wanda ke saka mata baki sai murmushi kaɗai da suke saki, sai kuma gajerun amsa da ke fitowa a bakunan su Bayan sun gama suka dawo Parlour Saleema bata zauna ba ta wayance tashige ɗakin Larai akan zata wurin Husna. Har suka gama wunin su Saleema bata sake bari magana ta haɗa su da Halwa ba, yamma na yi Saleeman tace zasu tafi ganin Ummi ma zata wuce wajen aiki, haka suka yi sallama suka fito tare da Ahmad da Larai tahaɗo masa kayan sa tunda Ummi tace baza ta tafi da Husna ba, kuma dama yanzu Husnan ta soma zuwa school ɗin ta ba ma wuni take yi a gidan ba A cikin mota ma tsit suka yi babu me magana, Halwa ta kasa yin mata magana ne sabida fargaba, ta rasa wani kalma ne zata iya amfani dashi wajen furta ma Saleeman, musamman yanda taga ita kanta bata son kula ta bare kallon ta, sai hakan yasake saka ta damuwa da tsoro cikin zuciyarta Suna shiga gidan suka fito cikin motan atare, Saleema na rungume da Ahmad tana ƙoƙarin jan Trolly ɗin sa da drever yaciro mata a Boot Sai Halwa tayi saurin miƙa hannun ta dake faman rawa tace "sister bari in taimaka miki". Saleema bata ce komi ba tabar mata tajuya dasauri tawuce Bin bayan ta da kallo Halwa tayi har sai da tashige cikin gidan, ahankali taja ƙafafun ta a matuƙar sanyaye tanufi ciki itama cike da rashin ƙwarin jiki, tana shiga da sallama idanun ta suka sauka kan su ita da Khalil ɗin dake zaune riƙe da Ahmad ajikin sa yana masa wasa, kallo ɗaya kayi masa zaka ga farin ciki tsantsa a fuskar sa wanda ganin tilon ɗan nasa ne yasaka sa wannan tsantsan murnan Tunda tashigo shima yaɗago kansa yana kallon ta, wani irin kallo yake aika mata dashi me cike da zallan soyayya da nuna shauƙi ga duk wanda yagani Hakan yaƙara saukar ma da Halwa kasala da mutuwar jiki, idanuwan ta tajanye daga kansa wanda suka kawo ruwa lokaci ɗaya tana ɗaura wa akan Saleema dake wasa da hannun Ahmad Daƙyar tasoma jan ƙafafun ta bayan tacire idanun ta daga kallon ta tashigo cikin parlour'n, bata ce komi ba tayi hanyan ɗakin Saleeman tashige don ajiye mata Trollyn Hakan yasa Khalil yabi ta da kallo cike da wani irin yanayi ganin yanda tasauya lokaci ɗaya duk da kuwa be ga hawayen idanun ta ba, amma ya tabbata akwai abinda ke damun ta "Me yasami Maman Husna naganta ahaka?" Yayi maganar lokacin da yamaida idanun sa kan Saleema Murmushi Saleeman tayi tace "babu komi wlh me kagani?" Numfashi kawai yaja batare da yace komi ba yamaida idanun sa kan t.v Lokacin Halwa tafito tanufi ɗakin ta tashige har da rufe ƙofan da keey, ahankali tazame ƙasa a jikin ƙofan tahaɗa kanta da gwiwa tasoma rere kuka, kuka take yi sosai wanda tatoshe bakin ta da gyalen ta ta yanda babu me jin ta, ita kanta bata san kukan na menene ba, sai dai tasan yana da alaƙa da yanda Saleema tanuna mata, wannan dalilin yasaka zuciyarta take mata wani irin zugi wanda ta san cewa dole ne rabuwar ta da wanda zuciyarta take bege a halin yanzu, alƙawari ne taɗauka kuma dole ta cika shi baza ta taɓa yin sanadin da Saleema zata sake shiga ƙunci a rayuwan ta ba, wanda ta tabbatar da cewa muddun tazauna batare da son ta ba bata jin zata yi farin ciki Bata tashi a wajen ba sai da aka yi kiran sallan magriba, tamiƙe ahankali jiri na ɗiban ta sabida tsananin kukan da tasha, har gaban ta bata iya gani haka talallaɓa tashige Toilet taɗauro alwala Sallah tayi tazauna nan bata tashi ba, sai da aka kira sallan isha'i sannan tatashi ta gabatar. Lokacin da Khalil yadawo daga sallah shi kaɗai yazauna a Parlour, shiru-shiru yana jiran yaga sun fito amma babu wanda yafito cikin su, tashi yayi yashiga ɗakin Saleema nan yaganta zaune tana aikin gyaran kayan Sip da tawargazo gaba ɗaya tana maida wa "Wai baza ku fito mu ci abinci bane?" Yace da ita lokacin da yaƙarisa gaban ta yana saka hannun sa ɗaya yadogare da Sip ɗin Kallon sa tayi tace "zan zo amma yanzu Ni dai bana jin yunwa ne sai anjima". "Ok bari inje ɗaki nima ina da aiki". Abinda yafaɗa kenan yajuya yafice Yana fita yatsaya yana kallon ɗakin Halwa, shiru yayi yana tunanin yaje ko kar yaje, haka kawai yaji gaban sa na faɗuwa, gashi kuma yana jin babu daɗi ganin yanda tashigo a ɗazu kuma ya san bata sake fito wa ba har yanzu tunda tashiga Numfashi yaja yanufi ɗakin sa yashige. ***** Ƙarfe 11:30pm. Lokacin gidan yayi tsit baka jin ƙaran komi Ahankali Halwa dake zaune a ƙasa jikin gado tamiƙe tasaka Slippers ɗin ta taja Trollyn dake gaban ta shaƙare da kayan ta, cikin sanɗa tafito tana tafiya ahankali har ta'isa bakin ƙofan parlour tasaka hannu tamurɗa keey ɗin tabuɗe tafice A haraban gidan babu kowa sai hasken lantarki da ya haskaka gaba ɗaya wajen, inda akwai duhu nan take raɓa wa tana bi duk da kuwa zuciyarta cike take da tsananin tsoro, amma abinda take hango wa shine kawai tabar gidan, bata son ko kaɗan tasake kwana a gidan nan Tana isa bakin ƙofa taci Sa'a babu me gadi, sai dai ya rufe ƙofan ya shige ɗaki ya ɗan kwanta zuwa anjima sai yatashi yaci gaba da aikin sa Ahankali tasaka hannu tazare saƙatan ƙofan taja Trollyn ta dasauri tafice batare da ta rufo ƙofan ba. . _uhmm wlh yau na gaji nasha typing da yawa, nayi muku har gobe ne ku karanta rabi yau sai ku bar rabin gobe😆, Asha karatu lafiya Fans, Ina matuƙar ƙaunar ku._ [1/5, 12:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ _Wannan shafin naku ne *Mommyn Teema* tare da *Mmn Adnan/Yusra* ku more da wannan ɗin 👇 ina godiya da ƙaunar ku gare ni._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty Three* ________🎓 Washe gari da safe Khalil ne yasoma tashi yay Shirin sa na zuwa Office, dayake yau ɗin yana da aiki sosai don haka da wuri ya shirya be tashi Saleema ba yafito Parlour, yasan cewa Halwa ce ke yin musu girki a yanzu shiyasa yanufi dainning ɗin kanshi tsaye, amma me? abun mamaki babu breakfast ɗin Tsayawa yayi yana kallon wajen cike da tsantsan mamaki, yasan bata taɓa late ɗin yin musu abin kari ba, musamman da tasan yanzu yana yawan fitan safe sosai Ganin dai tsayuwar sa babu amfani sai yajuya yashige ɗaki yaɗau briafcase ɗin sa yafito, kasancewar sauri yake yi duk da kuwa yana son shiga yadubo ta ko lafiya sai dai kuma be yi hakan ba yanufi ƙofa zai buɗe yafita, abun mamaki ƙofan abuɗe yagani babu keey, sosai yayi mamaki a ransa yatsaya yana tunani ko dai jiya basu rufe ƙofan bane? shiru yayi yana son tuno wa, tabbas jiya ba shi yarufe ƙofan ba maybe su Saleema sun manta ne, da wannan tunanin yabuɗe ƙofan yafice Motar sa yashiga yaja yay bakin Gate yana danna horn Me gadi dake zaune bakin ƙofan a saman benci yayi saurin tashi yawangale masa Gate ɗin yafice Sai a lokacin Gate man ɗin yasaki wata wawan ajiyan zuciya, tunda yatashi da asuba yaga ƙofan abuɗe yake a cikin ruɗu, yasan dai Khalil baya fita sallan asuba sai idan ta ɗauro, kuma ajiyan yariga kowa tashi agidan bare yay tunanin wani ne yazo yabuɗe, saboda ma yatabbatar da zargin sa sai da yatambayi ma'aikatan gidan duk suka ce masa basu bane, to yanzu jira yake yi yaji ko Oga Khalil zai yi masa maganar wani abun ya faru a daren jiya but ganin ya fita batare da ya tunkare sa da wata magana ba shine yaji dama-dama aransa, domin dai yana da tabbacin ya rufe ƙofan, kuma be sake dawowa wajen ba sabida barcin da yasha jiyan. Saleema bata tashi ba sai wajen ƙarfe 10:00am. Wanka tasoma yi sannan tashirya cikin doguwar riga na yadi me ruwan kuka, ɗinkin fitted gown ne sannan sai aka yi kwalliya da red stone a gaban rigan, ɗaura ɗankwalin simple tayi sannan tanufi kan gadon taɗauki Ahmad tazauna tasoma cire masa kaya A lokacin yafarka yana saka mata kuka Rarrashin sa tasoma yi tana ci gaba da kwaɓe masa kayan, bayan ta gama ajiye shi tayi tashiga Toilet tahaɗa masa ruwa a bawo tafito taɗauke sa, wanka tayi masa tadawo tashirya sa, sai da tahaɗa masa abincin sa taba shi sannan takwantar dashi tafito Parlour Direct kan dainning tanufa sai dai ganin babu komi a wajen sai taja ta tsaya, shiru tayi na ɗan daƙiƙa kafin tasaki murmushi Daman tasan za'a rina, Halwa zata shiga wani hali a sabida yanda tanuna mata a jiyan, ita har a zuciyar ta ba wai haushin Halwa take ji ba, tabbas dai taji kishin ta da Ummi tafaɗa mata yanzu tana matsayin kishiyar ta ne, amma kuma abinda yaƙara saka ta damuwa ce mata da akayi an juya mata mahaifa, sosai tashiga wani irin ruɗu da yahaddasa mata jin haushin Halwan a lokacin tare da tsananin kishin ta har takasa haɗa idanu da ita bare tayi mata magana, sai dai kuma ba wai tayi ne don muzguna mata ba tayi hakan ne kawai don samun damar yin tunani da zuciyar ta batare da tafito da damuwar ta fili sosai don su gani ba A jiya kwana tayi tana sallah sabida gode ma Allah da yakawo mata Halwa cikin rayuwanta, sannan ta kwana tana roƙon Allah yaba su zaman lafiya a zaman da zasu yi, ta sani cewa zuciya bata da ƙashi duk ƙaunar da suke yi wa junan su tunda har kishi yahaɗa su tabbas sai sun ɓata, don itama jiya ba ƙaramin ƙarfin hali tayi ba da danne zuciyarta har zuwa yau ɗin da tatashi sakayau babu abinda ke damun ta, burin ta a yau ɗin tafaɗa ma Khalil yaraba musu kwana su zamto matan sa su duka. Numfashi taja tana saka hannunta ta sosa goshin ta kafin tanufi ɗakin Halwa, tura ƙofan tayi tashiga da sallama tana wurwurga idanu cikin ɗakin ganin babu ita, bakin gadon tanufa tazauna a tunanin ta ko tana cikin Toilet, sai dai har tsawon shafewan wasu mintoci babu Halwa babu dalilin ta Miƙe wa tayi tanufi Toilet ɗin tasaka hannu tayi Nocking, jin shiru sai tatura ƙofan tashiga taduba babu kowa, fito wa tayi tana sake bin ɗakin da kallo, a ranta kuma tana tunanin inda Halwa taje, tuna ko tana kichen ne yasaka ta fita tadoshi kichen ɗin, sai dai nan ɗin ma babu ita "Haa'a to ina taje ne wannan matar?" Tafaɗa a fili lokacin da tafito Parlour tana sake kewaye parlour'n da kallo Numfashi taja kafin tafice dasauri, Garden ɗin gidan tanufa tasoma dube-dube sai dai duk inda tasan zata iya ganin Halwa agidan ta duba babu ita, hankalin Saleema ya soma tashi sosai, cikin ruɗu tanufi bakin Gate Me gadi tunda yahange ta yatashi yana muzurai Tana isowa tambayan da tasoma yin masa sai da hantan cikin sa yakaɗa, amma cikin ƙarfin hali yabata amsa da cewa "wlh Hajiya Ni dai yau ban ga gilmawan ta ba, rabon da na ganta tun jiya da kuka dawo cikin gidan nan". Goshin ta ta dafe cike da tashin hankali, sai kuma tasake kallon sa tace "to ko ka ga sun fita da Barrister ne?" "O'o O'o shi kaɗai yashiga motar sa yatai abin sa". Juyawa tayi dasauri har tana cin tuntuɓe, yanda zuciyarta lokaci ɗaya takawo mata banzan tunanin cewa ta gudu ne hakan yasaka hankalin ta yay mummunan tashi, har tana tuntuɓe tana faɗi wajen isa ɗakin Halwan da mugun saurin ta, Direct gaban Sip ɗin kayan ta tanufa tabuɗe tasoma duba wa babu komi aciki Dayake ta dawo da kayan ta ɗakin, akwatunan auren ta kuma Khalil ya ɓoye mata a Library ɗin sa. Wani irin mugun bugawa ƙirjin ta yayi, tana shirin zube wa ƙasa tahangi farar takarda dake kan gadon an danne rabin sa da pilow wanda tun shigowar ta ɗazu bata kula dashi ba, dasauri ta'isa wajen taɗau takardan tana buɗe wa gaban ta na faman faɗuwa, rubutun tabi da kallo kafin tasoma karanta wa _Aslm alaikum ƴar uwata, nasan zaki ga wannan saƙon ne a lokacin da nayi nisa da rayuwan ku, kar ki damu bare ki ɗaga hankalin ki, Ni naga dacewar barin ku sabida wasu dalilai na, i know zama daku a yanzu be da wani amfani sabida naga kamar ina son shiga rayuwan ki ke da mijin ki, wlh sister bani da ninyan ƙuntata ma rayuwan ki, babu wanda ya tambayi ra'ayina akan aure na da Yaya Khalil, shiyasa yanzu na gummaci barin ku akan nazauna da auren sa batare da son ki ba._ _Abu ɗaya nake roƙon ki kiyi min alƙawarin zaki kula min da kanki, kar ki taɓa saka damuwa a ranki duk inda nake zan rayu ne cikin farin ciki tare da kewar ki a raina, sannan ki roƙa min Mijin ki yasake ni sabida bana son in zauna da auren sa a kaina._ _Allah yaba ku zaman lafiya da ɗorewan lafiyan ki ƴar uwat..."_ Yanda hawayen idanun ta ke sintiri saman fuskarta yasa takasa ganin sauran rubutun, gaba ɗaya ta jiƙe takardan da hawayen ta, kuka tafashe dashi tana zame wa ƙasa tafaɗi, kuka sosai take yi wanda yahaɗe mata da tari sai yi take yi babu ƙaƙƙauta wa, magana take son Yi amma Ina da zaran ta soma buɗe bakin sai takasa furta wa sabida tari da kukan da take faman yi, babu abinda harshen ta ke iya ambata sai sunan Halwan tana wani irin kuka me cike da tsantsan firgici tare da fita hayyaci Zabura tayi dasauri tatashi tanufi ɗakin ta da gudu riƙe da takardan a tafin hannun ta, wanda tamatse sa gamm ta kasa saki, wayan ta taɗauka tafito Parlour tasoma neman layin Khalil, ringing ɗaya yaɗauka Kuka tasake fashe wa dashi da ƙarfi tana tattaro numfashin ta wajen har haɗa kalmomin da zata faɗa masa "Hal..wa.. ta tafi ta gudu.. ta bar ni, ta tafi.. Halwa...". Kasa ƙarisa maganar tayi sabida wani irin tari me haɗe da gudan jini da yataho mata Khalil dake zaune kan kujeran Office ɗin sa, tun sanda yasaka wayan a kunne yasoma jiyo kukan Saleeman hankalin sa yay ƙololuwar tashi, tambayan ta yake yi ko lafiya duk da yaji tana magana but ya kasa jiyo me take cewa sai sunan Halwa da take faɗi, dasauri yaharhaɗa kwarmatsan sa yasaka wayan a aljihu batare da ya kashe ba, keey ɗin motan sa ya ɗauka yafito da mugun sauri duk hankalin sa a tashe, sosai yashiga ruɗu da faɗuwar gaba don yasan babu lafiya Cikin mintunan da basu gaza 10 ba ya'iso gidan. Saleema na nan zaune a inda take, izuwa lokacin tayi kiran Numban Halwa ya kai sau ashirin but amsan ɗaya ne a kashe yake Numban Shigowar Khalil yayi dai-dai da sakin wayan da tayi tana sake fashe wa da kuka Gaban sa ne yafaɗi time ɗin da ya sauke idanun sa akanta yaga jini a bakin ta, ga kuma wanda yaɗiga a ƙasa, cikin kiɗima yatunkare ta dasauri yana duƙawa gaban ta yariƙo ta tare da tambayan ta abinda ke faruwa Amma ina ta kasa magana illa ƙara Volume ɗin kukan ta da tayi, daƙyar taɗago hannun ta tamiƙa masa takardan dake ciki Dasauri yasaka hannu ya'amsa yana warware wa sabida yanda tacukuikuye shi duk ya yage, wani irin rawa jikin sa yasoma yi ganin abinda ke ƙunshe a takardan, idanun sa yakai kan Saleema da tuni numfashin ta ya rabu da gangan jikin ta, lokaci ɗaya sai ga hawaye sun cika masa idanu yana zama dirshan a ƙasa tare da dafe kansa da yasoma mugun sara masa, cikin wani irin sarƙewan murya yace "Why Halwa? Why kike azabtar da rayuwana? Me na miki?" A dai-dai lokacin da hawayen suka sauka kan kyakykyawar fuskar sa. . _kai gaskiya *SALEEMA* kina ganin rayuwa._ _anya baza mu bar Halwa taƙara gaba abinta ba abar Barrister da Saleeman mu? Tunda naga kamar kun fi sonta dashi._ _ko kuma daga nan Saleema tatafi tabar mana Halwan mu da Barrister._ _don haka yanzu ina son jin ra'ayoyin ku, ku zuba min ƙuri'a duk wacce tafi Fans tsakanin *SALEEMA* da *HALWA* to ita ce zamu bar ta da *BARRISTER* sai na ji ku._ 💃💃💃💃💃 [1/5, 12:23 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ ```Wannan shafin naku ne masoyana Fhadeela, Fateeymuhammad, Auta Safna, Nana Faruk, Nafisa Ibrahim, Mum Afnan $ Yumna.. kuji daɗin ku da wannan page ɗin domin naku ne kyauta, na gode da ƙaunar ku gare ni.``` *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty Four* ________🎓 Jiki na rawa Khalil yamiƙe yanufi Fridge ya ɗauko ruwa yazo ya yayyafa mata a fuska, bata motsa ba sai da yasake zuba mata sosai kafin takawo numfashi alamun ta dawo hayyacin ta, bata buɗe idanun ta ba sai dai hawaye dake fitowa ta cikin idanun suna gangarowa gefen kunnen ta Kiran sunan ta yasoma yi but taƙi ta amsa masa duk da kuwa tana jin sa, hankalin sa ne yasake tashi yana shirin ɗaukar ta sai wayan ta tasoma ringing, ɗauka yayi ganin Ummi ne me kiran sai yayi peacking Daga can Ummi ce tasoma magana da faɗin "Hello My dear". "Aslm alaikum Ummi ba ita ce ba". "Ok Khalil Kai ne ashe, to lafiya dai ko?" Ummi tafaɗa gaban ta na faɗuwa "Ummi babu lafiya, Halwa ce tabar gida ita kuma Saleema gata nan akwance har suma tayi sabida tafiyan nata". Yayi maganar ahankali cikin dauriyan murya da dannewar tashin hankalin sa Cike da tsananin tashin hankali Ummi tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ta tafi kuma me yafaru ne?" Bata jira kuma amsar sa ba sai tace "gani nan zuwa gidan yanzu insha Allahu". Wayan takatse tana ɗaukan gyalen ta tayafa tare da jakar ta tafito Parlour Daidai lokacin da shima Abba ya fito daga nashi ɗakin yana saɓa malin-malin, hannun sa riƙe da takardu, su yamanta shine yadawo ɗauka Kallon sa tayi yayinda shima yake kallon nata "Lafiya na ganki ahaka meke faruwa?" Ummi kamar zata yi kuka saboda tashin hankalin da take ciki tace "Abban Saleema wlh babu lafiya, wai Halwa ce tabar gidan ga kuma Saleema can hankalin ta atashe har suma sai da tayi". "Subhanallah.. mu je muje gidan". Abba yafaɗa yana yin gaba dasauri Ummi na take masa baya ***** Shashsheƙan kukan Saleema ne kaɗai ke tashi cikin parlour'n, tana jingine jikin Ummi, Abba kuma na zaune gefen Saleeman sun saka ta tsakiya, yayinda Khalil ke zaune a kujeran dake Facing nasu Tunda suka zo suke faman rarrashin ta but taƙi yin shiru sai ma ƙara tayar musu da hankali da take yi, musamman yanda suka ga in tayi tari jini ke fita, kuma taƙi tashi akaita asibiti illa nuna musu cewa babu abinda ke damun ta ita Halwa kawai take son tadawo, baza ta taɓa iya rayuwa babu Halwa ba, taɓara dai irin na ƴaƴan gata shi tazauna tana ta musu, yayinda su kuma suke ta faman lallaɓa ta Ummi har da ƙwallan ta, kai da gani kasan ba'a hankalin ta Saleeman take ba Shi kanshi Khalil tsananin tausayin ta ne ya cika sa, shima yayi rarrashin but taƙi kula sa sai kuka take yi tana surutai Abban ne yace su koma gida in yaso sai akira Doctor yaduba ta, daga nan sai anemi Halwan ko za'a ganta, don haka suka tattara gaba ɗaya har Khalil da yaɗauko Ahmad yamiƙa wa Ummi suka bar gidan, su sun wuce gida shi kuma Khalil yabi cikin anguwa ko Allah zai sa yahaɗu da Halwa Idan kukaga Khalil a yanzu zai matuƙar baku tausayi, sosai yashiga damuwa akan tafiyar Halwan, gaba ɗaya zuciyarsa ta kasa sukuni tun sanda ya karanta takardan nan, yana ji ajikin sa ta tafi kenan, wannan dalilin ne yasaka yashiga matsanancin tashin hankali, sai dai juriya da ƙarfin hali da yake dashi hakan yake saka wa baza ka gane a halin da yake ciki ba Yayi yawo sosai babu inda be je ba wai ko zai ganta, duk da Halwa bata da wajen zuwa but inda be yi tunanin zata je ɗin ba duk ya duba, haka yaƙarishe yawon sa yawuce gidan su, inda anan ne yafaɗa musu halin da ake ciki Su ma Dad da Mom sun tashi hankalin su matuƙa, anan ne ma Dad ɗin yake faɗa musu labarin Halwan da alaƙan su dasu Saleema Lokacin da Dad ɗin yagama faɗa musu komi sai kawai hawaye suka ciko idanun Khalil, miƙe wa tsam yayi yafice daga parlour'n yadoshi part ɗin su inda ɗakin su yake na Da Akan gado yakwanta yana lumshe kyawawan idanun sa, haushi da takaicin kansa kawai yake yi Meyasaka ya ɗau laifi ya ɗaura wa baiwar Allah batare da yasan musabbabin rayuwan ta ba? Shin meyasaka yamanta cewa ƙaddara irin wannan zai iya samun ta batare da laifin ta ba? Shin meyasa mutane suke ɗaura laifi ga macen da suka ganta tana rayuwan ƙasƙanci? Shin sun tambaye ta dalilin da yasa har tafito gida take wannan rayuwan? ko kuma sun manta cewa wasu sanadin fyade ne yajawo musu rabuwa da gida akan tsangwama da kyara da ake musu, menene laifin su don ƙaddara ta faɗa musu ake koran su? Shin mun manta da cewa idan suka tafi zasu ci gaba da wannan rayuwan ne ko kuwa su faɗa hannun ɓata gari wani abu yasame su ta sanadiyar mu ne.. Allah dai yatsare mana imanin mu yasa mufi ƙarfin zuciyar mu, ya Allah ka kare mana zuri'armu daga faɗa wa mummunan rayuwa.. Ajiyan zuciya kawai yake sauke wa, ya jima a haka kafin daga bisani yamiƙe yaɗauro alwala jin ana kiran sallah yafice. Wasa-wasa har dare babu Halwa bare labarin ta Izuwa lokacin har ƙarin ruwa sai da aka yi ma Saleema, sai da akayi mata alluran barci sannan suka samu sukuni domin yanda tashiga wani hali hakan ya ɗaga wa iyayen ta hankali, babu daman tayi tari sai jini ya fito, gashi Doctor yayi musu bayanin cewa idan har taci gaba da kasancewa ahaka to tabbas akwai matsala domin zuciyarta ta gama kumbura sosai Abba yaso akai ta asibiti but likitan yace abar ta zuwa safiya idan jikin ya sake tsanani. Bata farka ba sai washe gari, Ummi ita ta taimaka mata tayi wanka tashafa mata mai tare da saka mata kaya, sabida ko kaɗan bata da ƙarfin jiki bata iya yin komi da kanta, sosai suke ta lallaɓa ta suna faɗa mata kalamai masu daɗi yanda zata kwantar da hankalin ta Abinci ma abaki Ummi taba ta sannan taba ta maganin ta tasha. **** **** **** **** ***** Tunda Halwa tafito daga gidan sai tasaka kuka, tafiya take yi batare da tasan inda zata nufa ba, ahankali take jan Trolly ɗin duk da kuwa zuciyarta cike take da tsoro matuƙa ganin yanda garin yaƙara duhu gashi babu kowa sai haushin karnuka, but bata jin zata iya tsaya wa hakan yasaka taci gaba da tafiyan ta tare da danne tsoron ta cikin rai, tafiya ɗaya sai ta waiga ahaka har tafito titi inda anan ne take ɗan ganin motoci suna wulƙa wa Hannun ta tasaka tasharɓe hawayen fuskarta kafin tanufi titin don ta tsallaka, babu zato tahangi mota tayo kanta duk da kuwa bata san da zuwan motan ba sai ganin ta tayi kusa da ita, ƙwalla ƙara tayi amma ina tuni motan ta bige ta Dasauri matar dake cikin motan tafito ita da ƴaƴan ta biyu suka yo Kan Halwa "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Matar take faɗa Yayinda ƴan matan tuni sun saka kuka sabida halin ruɗe wa "Ku taimaka min.. ku taimaka min na ɗauke ta". Matar tasake faɗa cike da rawan baki Daƙyar suka ɗaga Halwa suka nufi motan da ita suka saka ta daga ita har Trolly ɗin ta, matar taja motan suka bar wurin Direct asibiti suka nufa, dayake sananniya ce wajen Likitan sai yasaka Nurse suka amshi Halwa batare da bincike ba akayi Emargency Ward da ita A reception suka zauna zaman jiran fitowar likitan Mintuna kamar 20 yafito yanemi Matar tabiyo sa, bayan sun zauna a Office ɗin sa yasoma mata bayanin abinda ke faruwa "Ba wani abu bane yasame ta sai buguwa da tayi akanta wanda hakan yaja mata dogon suma, amma da yardan Allah zuwa gobe zata iya farka wa". Wannan bayanin na likita shi yakwantar wa matar da hankali, daga nan suka tattauna sannan tafito tasami ƴan matan ta suna jiran ta Tambayan ta suka hau yi har yanzu suna zub da hawaye don ba ƙaramin tashi hankalin su yayi ba Kallon su tayi cikin kwantar musu da hankali tace "ya isa haka babu abinda yasame ta illa buguwa da tayi akanta". Atare suka sauke ajiyan zuciya suna faɗin "alhmadulillah". Murmushi tayi kafin tace "to yanzu yakamata ku koma gida inyaso Ni sai in zauna da ita don baza mu tare anan ba, kuma ban ce ko waccen ku takira Daddynku tafaɗa masa ba don kar hankalin sa yatashi kuna jina?". Matar Taƙarike maganar da jan kunnen ta Gyaɗa mata kai suka yi atare suna cewa "to Mami". "But Mami ki bari Ni zan kwana da ita mana tunda ba wani abu me wahala bane". Cewar Safina tana kallon Mami ɗin cike da son amincewar ta "Ok to bari mutafi gida Ni da Nafisa, but ki kula bana son rawan Kan nan naki kinji Ni? Idan da akwai matsala kiyi kiran Doctor". Safina tace "to Mami insha Allahu". Daga haka babu abinda suka sake faɗa illa wuce wa ɗakin da aka kwantar da Halwa da suka yi, basu fi mintuna goma ba Mami da Nafisa suka fito suka bar Safina a wajen ta. _sai muce Allah yabaki lafiya Halwa._ [1/5, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ _Fateema Zahra, Hauwa Ali, Wanka Yakubu Isa, Munir Y Abdullah, M. Bintu Thank You for the loving My Book._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty Five* ________🎓Washe gari da sassafe Mami tadawo Asibitin da breakfast, Safina na gaishe ta ta'amsa tace mata "Yauwa to tashi kije yi maza Drever na jiranki ki koma gida ki shirya kar kuyi late, ki tabbatar kinyi breakfast kafin ki tafi ko kuma ki ɗiba ki tafi dashi kina jina?" Murmushi Safina tayi lokacin da tamiƙe tana ɗaukan gyalen ta "Mami sai kace wata yarinya haka kawai sai inje da Breakfast school?" Hararan ta Mami tayi tace "Ni dai na faɗa miki kuma na bada sallahu idan ma baki je dashi ba Nafisa zata faɗa min, ai na faɗa miki daga yanzu na dena baku kuɗi, wuce ki tafi kar in saɓa miki uwar shiririta". Turo baki gaba tayi tafice batare da tasake cewa komi ba Ita kuma Mami zama tayi idanun ta akan Halwa wacce ko motsi ba ta yi tun jiya tana nan ayanda take, an naɗe mata kai da bandage sabida ba ƙaramin rauni taji ba Ajiyan zuciya kawai Mami take sauke wa cike da tsananin tausayin Halwa, kawai aranta tunanin yanda aka yi matashiyar yarinya kamar wannan tafito gidan iyayen ta da tsakar dare take yi. Tana nan zaune wajen ƙarfe 09:00am na safe sannan ne Halwa tafarka, don haka tamiƙe da hanzari takira Doctor coz tunda tafarka ɗin tabuɗe idanun ta bata sake motsawa ba, duk sannun da tajero mata taƙi ta amsa ta Doctor da yazo yadudduba ta yatabbatar bata da wani matsala sannan yace aba ta abinci taci sai tasha magani Sai da yafita kafin Mami tasoma haɗa mata abin kari, bayan ta gama takalle ta kamar yanda Halwan tazuba ma matar idanu tamkar me neman wani abu ajikin ta Murmushi tayi mata tace "tashi kisha kinji?" Halwa batace komi ba tayunƙura tagyara zaman ta, duk da babu abinda ke damun ta amma sosai kanta ke mata ciwo daƙyar take iya motsa shi, amsar Cup ɗin tayi tariƙe da hannu biyu ta kasa sha Sai da matar takula da ita kafin tace "af na manta baki wanke baki ba ko zaki fi jindaɗin sha". Amsar Cup ɗin tayi tamiƙo mata ruwa, sai da tawanke bakin kafin tamiƙa mata Tea Cup ɗin, sannan alokacin tasake ciko mata Plate da Arish da soyayyan ƙwai ta'ajiye mata akan gadon, sai tatashi tafice don tabar ta tasake Tana fita Halwa talumshe idanunta, aranta kewar gida kawai take yi tare da tunanin makomar ta a yanzu, bata dena tunanin ba take ta tsoma bakin ta tana shan tea ɗin zuciyarta duk babu daɗi Ta jima ahaka batare da tasan awani hali take ciki ba, har Mami tadawo tatarda ita ahaka ko rabin Cup ɗin bata yi ba, babu ma abinda tataɓa acikin Plate ɗin Mami kallon ta tayi tana nazartan ta, kafin kuma tatamke fuska cikin serious face tace "har yanzu baki ci komi ba ashe? Bana son shashanci Yi maza ki cinye ki bani Plate ɗin da kofin". Kallo ɗaya Halwa tayi mata ta tabbatar matar ba ta ɗaukan raini, nan da nan taji tsoron ta ya kamata ta batare da tayi mata musu ba tayi yanda tace mata tamiƙa mata Plate ɗin kamar yanda tabuƙata "Good kinyi kyan kai". Mami tafaɗa bayan ta amsa ta ajiye sannan tafice Da kallo Halwa tabi ta tana tunanin ita kuma wannan matar daga ina? Menene haɗin ta da ita? Ita dai tasan an bige ta to ko dai ita ce tabige ta ɗin?". Tana cikin wannan tunanin ne suka dawo da doctor, magani yaba ta bayan ya tambaye ta "ko akwai abinda ke damun ta?" Dayake Halwa jin ta take yi tamkar a ƙaya musamman yanda matar nan tanuna mata sai taji ta ƙosa su raba hanya, don haka tace masa babu abinda ke damun ta Hakan yasa Doctor ɗin ce ma Mami zuwa anjima za'a sallame ta. Ƙarfe 02:35pm. Safina da Nafisa suka kawo abincin rana, ganin Halwa ta farka ga jikin ta dasauƙi hakan ya faranta musu rai sosai musamman ma Safina, kasancewar ita akwai ta da son mutane ga fara'a ba kamar Nafisa ba, hakan yasa lokaci ɗaya tashige ma Halwa tana ta janta da Surutu Itama Halwa sosai tasaki jikin ta zuwan su ba kamar ɗazu ba duk da kuwa ba magana take yi ba iyakan ta murmushi da bin Safinan da kallo me zuba mata surutu. Da yamma aka sallame su suka taho gida, babban gida ne dasu me kyau sosai, kai da gani kasan ba ƙaramin kuɗi ne da me gidan ba Suna isa Safina taruƙo mata hannu suka yi ciki, ɗakin su takai ta tahaɗa mata ruwan wanka tashiga Itama Nafisa sai gata ta shigo da Trolly ɗin Halwa ta'ajiye mata tafice Safina na zaune bakin gado tana jiran Halwa har tafito, murmushi tayi mata tace "Aunty ga kayan naki nan sai ki shirya ina zuwa". Taƙarike maganar tana miƙe wa cike da zumuɗi Gyaɗa mata kai Halwa tayi tare da mata murmushi, har tafice tana kallon ta kafin tazauna gefen gadon tana zuba tagumi, ta ɗau lokaci ahaka har Nafisa tashigo ɗakin batare da ta sani ba, sai da tataɓa ta kafin taɗago kai dasauri tana kallon Nafisan, ko kaɗan ba wai ta gane ko wacece acikin su ba duk da kuwa taji sunayen su tun a Hospital, but tsananin kaman da suke da juna baka banbance wacece Nafisa wacece Safina, iyakan dai a fuska idan kakalli Nafisa zaka iya shaida ta sabida bata da fara'a ko kaɗan, miskila ce na ƙarshe saɓanin Safina ko yaushe haƙoran ta awaje suke Murmushi Nafisa tasakar mata ganin yanda tatsare ta da idanu tana son tantance Nafisa CE ko Safinan "Ki taso Mami na kiran ki". Tafaɗa ahankali tana juyawa tayi hanyan ƙofa Ɗan numfashi Halwa taja batare da ta ɗauke kanta daga kallon Nafisa ba har tafice, yanda tanuna mata ɗin tuni ta gane ba Safina bace Miƙe wa tayi tabuɗe kayan ta taciro riga da skert na atamfa kalan Baby pink sai ratsin Milk da aka yi amfani dashi wajen zanen Flower jefi-jefi, bayan ta gama saka wa taɗau siririn gyale baƙi tayafa akanta sabida bata saka ɗan kwalin kayan ba sannan tanufi ƙofa tafice Suna zaune gaba ɗayan su a falo, Halwa da tafito ƙasa tasamu tazauna cikin sanyin muryanta tayi wa Mami sannu Amsawa tayi idanun ta akanta kafin takalli su Nafisa tace "ku tashi ku bamu wuri". Babu musu suka tashi, sai ma suka yi ƙofar fita suka fice gaba ɗaya Juyo da idanun ta kan Halwa tayi tace "yauwa so nake yanzu ki faɗa min abunda yasa kika baro gida, ayanda nafahimta da nazarin da nayi miki hasashe na ya bani kin baro gida ne sabida wani dalili naki hakane?" Halwa da kanta ke ƙasa ta kasa ɗago kai bare ta'amsa mata, sosai matar take bata mamaki da kuma yanda halin ta yake, kai da gani kasan ba ƙaramin jarumar mace akayi a wajen ba, dakakkiyar mata me tsananin kwarjini da baiwa.. "Kinyi shiru ina magana? bana son ina maimaita ma mutum magana biyu kinji Ni?" Dasauri Halwa tagyaɗa mata kai cikin tsananin shakkar matar da yakamata tun ganin ta da tayi "Ki buɗe baki kiyi min magana ba gyaɗa kai nace kiyi ba". Cikin rawan baki Halwa tabuɗe baki tasoma sanar mata da abinda take buƙatar ji a wajenta, iyakan abinda tasanar mata tafito gida ne sabida anyi mata aure da mijin ƴar uwanta, ganin tanuna kamar bata ji daɗi ba shine ita kuma tabi wannan hanyan don guje ma auren". Jinjina kai Mami tayi idanun ta kafe kan Halwa ɗin, cikin kausashshiyar murya tace "wato kin zaɓi guduwa ne don kawai ƴar uwanki bata ji daɗin wannan haɗin ba? Kin nemi ki baro iyayen ki sabida ki faranta mata ko?" Cikin zub da hawaye Halwa tasake duƙar da kanta, cike da raunin murya tace "nayi hakan ne kawai saboda farin cikin ta, Ni bazan so in shiga rayuwanta ita da mijin ta ba, sannan zan so takasance cikin farin ciki ko dan ciwon da take fama dashi". Shiru ne yabiyo bayan maganar ta illa shashsheƙan kukan ta dake tashi Wajen shuɗewar mintuna biyar kafin Mami tace "shin ke kina son Sa ko kuwa bakya son sa?" Baki na rawa tace "Ina son sa". Murmushi Mami tasaki tana kaɗa ƙafafuwan ta, sai da taja lokaci kafin tace "shikenan yanzu abinda Yakamata zuwa gobe zan maida ki gida saboda babu ta yanda za'a yi in barki kibi duniya akan wannan banzan dalilin naki, idan yaso in namayar dake sai in faɗa musu su raba auren tunda baki son zama dashi, kinga babu ke babu guduwa kenan, tashi ki wuce na sallame ki". Jiki a sanyaye Halwa tamiƙe takoma ɗakin su Nafisa, tana shiga tazauna kan gadon tana ci gaba da tsiyayar da hawaye kamar an kunna famfo Ba wai maganar mayar da itan bane yaɗaga mata hankali, jin cewa zata faɗa a raba auren ta da Khalil, ita ji take yi a yanzu ta gummaci tatafi da auren sa tayi ta yawo da araba auren, hakan zai saka zuciyarta tayi sanyi daga zugin da take mata na tsananin ƙaunar sa da take yi, auren Khalil akanta shi zai sa duk inda taje takasance cikin farin ciki, ko babu komi zata mutu da auren wanda tafi ƙauna fiye da ranta a yanzu ɗin atare da ita. Ita kuma Mami murmushi tayi lokacin da Halwan tashige ɗaki, sosai aranta ta tausaya mata domin tunda take bata taɓa ganin irin wannan sadaukarwan da Halwa tayi ba, kina son mutum amma sabida farin cikin ƴar uwanki ki zaɓi rugujewar rayuwan ki gaba ɗaya akanta, gaskiya samun me hali irin Halwa da wahala, tana da kyakykyawar zuciya matuƙa, tana iya sadaukar da komi nata akan masoyi (Hmm nace Mami don ma bakisan sauran sadaukarwan da tayi mata bane) Mami tana zaune da ƴaƴan ta biyu Nafisa da Safina masu shekaru 16 a duniya, twins ne su kuma daga kansu bata sake haihuwa ba, mijinta babban soja ne sosai yana aiki a Kaduna Baza ku gasgata maganar nan da ake cewa matar Soja itama Soja bane sai kun haɗu da Mami, Kai in taƙaice muku tsaurin idanun Mami da dakakkiyar zuciyar ta ta ninka na mijinta da shine ma Sojan, bata da tsoro ko kaɗan gata macece me tsayawa akan komi da yashafe ta da tsananin jarumta, bata nuna gazawar ta a komi, tana da fara'a sosai sai dai ba ta yin sa sai a inda yadace, shiyasa Nafisa a halayya ita taɗauko, sai dai ita Mami ba wai miskilanci ne da ita ba dakakkiyar macece da bata ɗaukar raini koda yaushe, wannan dalilin ne zaka ga tamkar bata cika wasa ba Yanzu haka ita ma'aikaciyar gwamnati ne me amsar zunzurutun albashi don babba ce sosai a wajen aikin su. *WASHE GARI* Wajen ƙarfe 10:00am. Mami tasaka Halwa tashirya Dama tuni su Nafisa sun tafi school, Safina har da kukan ta jin cewa a yau ɗin Halwa zata tafi, domin sosai jinin ta yahaɗu da Halwa ɗin a kwana ɗayan nan da tayi agidan, ta ɗauke ta tamkar babban Yayarta wacce suka fito ciki ɗaya shiyasaka tasaki jiki sosai da ita, taso Mami tabar su yau dai rana ɗaya kar suje school atafi dasu kai Halwa gida, amma ina Mami taƙi yarda, daga ƙarshe ma sai da tayi kamar zata mangare Safinan kafin tatafi school da kuka Ita kanta Halwa sosai taji ƙaunar Safinan aranta, sai bata ji daɗin yanda Mami tayi ɗin ba, sai dai bata da bakin magana iyakan nata idanu ne domin wargi ma wuri yaka samu Bayan Halwa tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na Baƙin yadi da zanen Flower da aka yi da dack orange Colour, fitet ne rigan sai tayi Rolling da gyale me ruwan madara irin me taushin nan sosai ya rufe mata har bandage ɗin kanta Janyo jakan tayi tafito Parlour inda Mami ke zaune tana jiran ta, kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kai tana ci gaba da latsa wayan nata Ita dai Halwa tana nan tsaye a waje ɗaya ko ƙwaƙƙwaran motsi bata iya yi Kamar shuɗewar mintuna goma kafin Mami tatashi tayi wa Halwa nuni da hannu alamun su je Gaba Halwa tayi dasauri tana jan Trolly ɗin ta, koda tafita sai da tajira Mami ɗin takullo ƙofa tazo tasame ta kafin su ƙarisa wajen motan A lokacin har me gadi ya ƙariso wajen yana kai gaisuwa wajen Mami Amsa masa kawai tayi tana buɗe Boot Dasauri yanufi wajen Halwa yana ƙoƙarin amsar jakan nata don yasaka mata a Boot ɗin, but Mami tatsai dashi da faɗin "Ƙyale ta tasaka da kanta Ali, je kabuɗe min Gate". "To Hajiya". Yafaɗa dasauri yana nufan Gate ɗin Ita kuma Halwa saka Trollyn tayi sannan Mami tarufe suka shiga motan, sai da taja motan zuwa bakin Gate ɗin kafin tatsaya tazuge glass ɗin tana kallon me gadin tace "Ali idan su Nafisa sun dawo kace musu su duba keey ɗin a inda nasaba ajiye musu, sannan kafaɗa musu su tabbatar sun tafi islamiyya yau bazan dawo ba sai zuwa dare". "To Hajiya insha Allahu zan faɗa musu, Allah yadawo dake lafiya". "Ameen ya Allah". Tayi maganar tana maida Glasses ɗin tarufe sannan taja motan taƙarisa fice wa. . _To ga fa Halwa za'a koma gida Fans, ko me zai faru?_ [1/5, 2:40 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty Six* ________🎓Kamar yanda Halwa tafaɗa mata address ɗin gidan su Saleema can tanufa, a cikin motan babu me magana, ita dai Halwa kallon hanya kawai take yi tana kitsa abubuwa aranta da tunanin abinda zai faru idan takoma.. Ƙaran horn ɗin da Mami ta danna ne yadawo da ita hayyacin ta, takai duban ta ga Gate ɗin lokacin har me gadi ya leƙo don ganin wanene, be buɗe musu ba sai da yazo har wajen motan yayinda Mami tasauke Glasses Motan Har ya buɗe baki da ninyan yin magana sai yahangi Halwa, cike da tsagwaron murna da al'ajabin ganin ta don zuwa yanzu har ma'aikatan gidan sun san abunda yafaru duba da yanda iyayen gidan nasu hankalin su yake a matuƙar tashe da halin da Saleeman ke ciki Washe baki yayi yace "Hajiya Halwa ke ce?" Murmushi tayi masa cikin sanyin murya tace "eh Yusha'u". "Masha Allah bari in buɗe muku ƙofan to". Yayi maganar yana nufan Gate ɗin dasauri har da haɗa wa da gudu Yana shiga yabuɗe musu Mami taja motan zuwa ciki Har wajen motan me gadin yabi su bayan da yamayar da Gate ɗin yarufe, anan ne suka gaisa da Mami itama Halwa tagaishe sa sannan sukai ciki Halwa ce agaba don haka ita tabuɗe ƙofan tashiga da sallama a bakin ta Ummi dake zaune saman kujera ta riƙe waya a hannu tana latsawa, kallo ɗaya kayi mata zaka hango tsantsan damuwar da take ciki Sallaman Halwan shine yasa taɗago kai sabida jin muryan da bata taɓa zaton ji ɗin ba a halin yanzu, dasauri tamiƙe ganin dai itan ce zuciyarta cike da zallan mamaki tare da wani irin murna "Halwa.." takira sunan ta idanun ta akanta don tama kasa motsawa Murmushi Halwa tayi takalli Mami dake bayan ta, sai kuma tasad da kanta ƙasa Mami gaba tayi zuwa cikin parlour'n hakan yasa itama Halwa tabi bayan ta, sai da suka zauna kafin Ummi tasake samun bakin magana "Halwa ina kika shiga ne? Ina kika shiga kika bar mu cikin neman ki?" Tayi maganar tana dawo wa kusa da Halwan tare da riƙe mata hannu Hawaye Halwa tasoma yi, cikin rawan baki tace "don Allah ku gafarce Ni Ummi nabi son Raina na tafi na barku amma bazan sake ba". Washe baki Ummi tayi tana rungume ta cike da tsantsan murna, bakin ta sai faɗin "baki yi mana komi ba Halwa, baki yi mana komi ba wlh.." Mami dai tana kallon su batare da ta furta komi ba Tsawon mintuna biyu kafin suka nutsu har Halwan dake yin kuka "Ummi tace tunda kika tafi Saleema taƙi lafiya, kullum cikin neman ki muke yi, yanzu ma haka tana nan ɗakina ta kwanta tana barci". Zumbur Halwan tamiƙe tana shirin nufan ɗakin Ummi sai taji saukar muryan Mami tana faɗin "Oh baza ki gabatar dani bane zaki tafi ki bar ni? Tunda anga uwa dole ki manta dani". Ta yi maganar ne fuskarta yalwace da murmushi Juyowa Halwa tayi sai dai bata kai ga magana ba Ummi tariga ta da cewa "Don Allah kiyi haƙuri wlh murnan ganin ta ne yaɗauke min hankali sam gashi ko gaisawa bamu yi ba". Murmushi Mami tayi tace "babu komi ai". Sannan suka gaisa kafin Mami ɗin tace "ina son ganin mahaifin ta idan babu damuwa sabida maganar da nazo dashi". "To babu komi bari in Kira sa". Cewar Ummi tana ɗaukan wayan ta. Halwa ita tuni ta shige ɗakin Ummi ganin sun manta da ita, koda tashiga Saleeman na barci kamar yanda Ummi ɗin tafaɗa, tunda tasauke idanun ta akan Saleeman hawayen ta suka sake gudu wajen fitowa, toshe bakin ta tayi ahankali tasoma takawa zuwa gadon, sai da tazauna sannan tasaka hannun ta tana shafa mata saman goshin ta cike da tsananin tausayin ta, wuni biyu kacal yasa ta wani irin mugun ramewa kai da ganin ta kasan tana jin jiki Kasa riƙe kukan ta tayi tasoma shashsheƙan kuka duk da kuwa tana dannewa kar yafito fili Sai dai hakan be tasiri ba don tuni kukan nata ne yatashi Saleema, ahankali tabuɗe idanun ta akayi Sa'a sai tasauke su kan Halwa da hawaye suka cika idanun ta har bata iya gani sosai sai ta rage su da hannu Kallon ta kawai Saleema take yi batare da ta motsa ba Sai Halwan tasakar mata murmushi cikin rawan baki tace "ƴar uwa.." Lumshe idanuwan ta tayi tasake buɗe su akanta amma kuma bata da alaman motsawa, tsira mata idanu kawai tayi tana tunanin ko dai mafarkin da take yi ne a yanzu bata farka ba? Sake kiran sunan ta tayi cikin sanyin murya tana cewa "Ya jikin naki?" Sai da tasake ɗan ƙif-ƙifta idanun nata ta yanda zata tabbatar ba mafarki take yi ba, ganin dai har yanzu tana ganin Halwan sai tayi saurin tashi zaune idanun ta akanta takai hannun ta tana taɓa ta Hakan sai yaba ma Halwa dariya don ta gane me take nufi tana kokwanton ita ce ko ba ita ba Murmushi tayi taruƙo hannun nata da take shafa mata jiki tace "ƴar uwa Ni ce fa, na dawo gare ki ne". Sai kawai Saleeman tafashe da kuka tana rungume ta, cikin kukan take faɗin "Don meyasa zaki tafi ki bar ni? Kina tunanin zan iya ci gaba da rayuwan farin ciki ne bayan kin tafi? Ƙaunar da nake miki shine zai hana Ni samun farin ciki a rayuwata, wlh da baki dawo ba bazan taɓa yafe miki ba". Itama Halwan kuka take yi sosai zuciyarta cike da tsananin rauni, tabbas tayi nadaman tafiya, da yanzu Mami Bata dawo da ita ba shikenan haka zata tafi tabar ƴar uwan ta cikin damuwa na rashin ta, abun da taguda ashe shine zai faru, tayi nesa dasu don farin cikin Saleeman amma kuma tafiyan nata yazama barazana ga rayuwan ta, ko kaɗan bata taɓa tunanin hakan ba, tabbas ƙaunar da Saleema take mata ya wuce tunanin ta Sun jima ahaka kowa yaƙi sakin ɗan uwan sa, kuma basu fasa yin kukan ba sannan babu wani kalma da tasake shiga tsakanin su Ummi ce tashigo ɗakin, ganin su ahaka sai tasaki murmushi tare da saka hannu tana share ƙwallan da yacika mata idanu, ahankali tataka wajen su cikin farin ciki tace "To ya isa kukan haka kunji? Tunda komi ya wuce Allah yasa kin dawo sai mu gode waa Allah". Sakin junan su suka yi yayinda Saleema takasa dena kukan "Please sis ki dena kukan mana kar ki saka inji na tsani kaina mana, domin idan wani abu yafaru dake bazan taɓa yafe wa kaina ba". Murmushi Saleeman tayi duk da hawayen basu dena zuba a idanun nata ba Ummi tashafa kanta cikin jindaɗi da ganin ƴartan ahalin lafiya, sai takalli Halwa tace "muje kiyi sallama da Baƙuwar tamu zata tafi". "To Ummi". Halwa ta'amsa mata tana tashi tsaye Dasauri itama Saleeman tamiƙe tana jeho ma Halwan tambaya akan wacece? Don tuni Ummi tayi gaba ta fice Ataƙaice Halwa taba ta amsa da faɗin "wacce tadawo dani ne". Abba da Dad ne zaune a parlour'n suna sake sallama da Mami, kafin kuma su ɗunguma gaba ɗaya da Ummi dasu Saleeman suka je raka ta zuwa wajen motan ta, anan suka sake sallama yayinda Ummi take sake mata godiya tare da faɗa mata insha Allahu zasu har gida su sake mata godiya Itama Halwa godiyar tasake mata tare da bata saƙon gaisuwa zuwa wajen su Safina Har sai da tabar gidan sannan suka yo cikin gidan, Ummi tasoma yin gaba tabar su nan Har zasu shige su ma suka jiyo ƙaran buɗe Gate, a tunanin su ko Mami ɗin ne sai duk suka waiga, saɓanin haka sai suka ga motan Khalil na shigowa ciki Ahankali Halwa tajanye idanun ta daga kallon motan tabuɗe ƙofan tashige Saleema da bata san da shigewar ta ba tajuyo da murna zata yi mata magana sai kuma taga wayan babu ita, murmushi tayi tagyara tsayuwar ta tana jiran isowar sa. A ciki kuwa Halwa na shiga tanemi ƙasa tazauna tana gaishe dasu Abba duk kunya ya cika ta, su kuwa kamar babu wani matsala suka amsa mata cike da fara'a Har ta tashi zata tafi Ummi tace mata takoma tazauna Babu musu tabi umarnin ta A lokacin ne su ma su Khalil suka shigo Kusa da ita Saleema tazauna tana riƙo hannun ta gam, duk yanda ka kalli fuskarta zaka san tana cikin tsantsan farin ciki wanda hakan ba ƙaramin faranta ran iyayen nata suka yi ba, dawowar Halwa ɗin ya yaye mata duk wani ciwo da take fama dashi, tamkar ba ita ce take a mawuyacin hali ba ɗazu, har sai da aka yi mata alluran barci hankalin su yakwanta Shima Khalil a ƙasa yazauna sabida girmama iyayen nasu, idanun sa ƙyam akan Halwa wacce kanta ke ƙasa ta kasa ɗagowa, sosai zuciyarsa tayi masa sanyi da jin labarin dawowarta wajen Dad.. Maganar Abba shi yadawo dashi hankalin sa har yaɗauke kansa daga kallon ta yana sauke ajiyan zuciya, a kwana biyun nan da babu ita har ya faɗa sosai sabida zullumi da tunanin rasa ta har abada, sai gashi kuma ta dawo wanda be taɓa tunanin hakan ba.. Faɗa sosai Abba yayi mata akan abinda tayi, daga ƙarshe kuma yayi mata nasiha me ratsa zuciya inda shima Dad yaɗaura da nasa, sannan yaƙare da faɗin "Ina ga kamar yanda Hajiya tabamu shawara hakan yakamata muyi, Ibrahim ya sauwaƙe mata kar a sake samun matsala irin hakan, in yaso sai mu haɗa su ita da Sameer". A razane Khalil yaɗago kansa yana ware idanun sa kan Dad zuciyarsa na matsanancin bugawa.. [1/5, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER twenty Seven* ________🎓Kuka Saleema tasaka tana roƙon Dad akan kar araba auren Murmushi Dad yayi yana girgiza kai cike da mamakin irin wannan soyayyar nasu "Don girman Allah kar araba auren nan Dady, wlh idan aka raba nima bazan zauna dashi ba dole sai ya sake Ni". Babu wanda maganar Saleema be basa dariya ba har Khalil kuwa dake a cikin matsanancin ruɗu, a yanda tayi maganar cikin taɓara da sangarta wanda kuma ita iya gaskiyar ta take faɗa tana ci gaba da kukan ta "Ya isa to ƴata baza'a raba ba, nima wasa nake yi wlh". Cewar Dad yana zuba murmushi Cak kuwa taɗauke kukan nata jin abinda Dad ɗin yace Yayinda Khalil yasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya yana sauke kansa ƙasa zuciyarsa cike da tsananin ƙaunar Saleema, lumshe idanun sa yayi batare da ya sake jiyo zantukan da ake yi ba, domin tuni ya faɗa duniyar tunani, sai da Dad yaɗan zungure sa da ƙafa kafin yadawo hayyacin sa yana ɗago idanun sa masu tsananin haske da kyawu yazuba masa "Tunanin me kake yi ana ta magana kana jin mutane?" Ɗan wur-wurga idanu yayi ganin Dad ɗin ne da Abba kaɗai a cikin parlour'n, sauke kansa ƙasa yayi yana sosa ƙeya be ce komi ba Murmushi Abba yayi yace "To Khalil sai kayi haƙuri da duk abinda zaka gani na zamantakewar ku, dama zaman tare zo mu zauna ne zo mu saɓa ne, bare in an haɗa da sha'anin mata, duk abinda zaka ganin kayi ta haƙuri kamar yanda kasaba, Allah yayi muku albarka gaba ɗaya". "Amin Abba". Khalil yafaɗa idanun sa a ƙasa Tashi Dad yayi yana faɗin "to Ni dai bari in soma gaba ko?" "ai jira Ni sai mu koma tare nima ba zama zanyi ba". Cewar Abba shima yana miƙewa Lokacin su ma su Saleema suka fito sai sukai waje gaba ɗayan su, inda Ummi tayi musu rakiya har waje Dad da Abba sun hau motar su daban-daban suka bar gidan, kafin shima Khalil yahau nasa yana jiran ƙarisowar su Saleema dake gefe suna magana da Ummi, Saleeman ce tatsaya tana ma Ummi magiya akan gobe a haɗo mata kan ƴaƴan ta adawo mata dasu, yayinda Halwa ke tsaye tana sauraron su tana murmushi Abun da yasa ma yanzu batace zata tafi dasu ba saboda ita Husna tana school tunda ta fara zuwa, shi kuma Ahmad yana wajen Larai ta tafi dashi gidan su Sai da Ummi tayarda zata kawo su gobe kafin tasamu sukuni wajen Saleeman, motan suka ƙarisa suka shiga yaja yay bakin Gate yafice bayan an buɗe masa Gate ɗin Yana dai-dai ta motan nasa akan titi yasauke idanun sa kan mirror yana kallon Halwa dake baya zaune Itama dai-dai lokacin ta ɗago kai tana amsa wa Saleema maganar da tayi mata suka haɗa ido Yanda yakafe ta da ido ne yasa tajanye nata tana lumshe su tare da kau da kai gefe, bata sake gigin ɗago kai ba har suka kai gida. ***** Kusan ƙarfe 05:30pm. Saleema tafito haraban gidan, Sale takira taba shi aike sannan takoma ciki, dayake lokacin Khalil ya fita sabida wani waje da zai je yau ɗin, dama yaso yawuce ne lokacin da yatashi Office sai kuma Dad yakira sa akan dawowar Halwa, hakan ne yasa be je ba sai yanzu da yamma Ita kuwa Halwa tunda suka dawo sallah kaɗai tayi ko abinci bata nema ba takwanta barci, har yanzu kuwa barcin take yi batare da ta tashi ba Saleema tayi mitan tashin ta don taci Indomien da ta girka musu amma ina tamkar wacce mayen ƙarfe ke ja sabida barci ko motsi taƙi yi Yanzu ma da tashigo ɗakin nata kai tsaye gaban Sip ɗin kayan ta tanufa tabuɗe tasoma ciro mata kayan ta, sai da taciro su tsab sannnan tazuba cikin Trolly taja zuwa ɗakin Khalil, buɗe sip tayi tasoma jera mata har tagama sannan tasake fice wa Nocking door ɗin da akayi yasaka tazarce kai tsaye bakin ƙofan, tana buɗe wa Sale ne tsaye da Ledoji guda biyu da ta'aike sa saƙo Amsa tayi tayi masa godiya tare da rufe ƙofan tajuya ciki, ɗakin ta takai ta'ajiye inda baza'a gani ba sannan tafito takoma ɗakin Halwa Halwan na zaune abakin gado tashin ta kenan tana maida ɗankwali kanta da yakwance time ɗin tana barci "Kasa kin ta shi?" Cewar Saleema tana murmushi Fuskarta taya mutsa tamkar dai yanda tasaba sai kuma tasaki murmushi tana gyaɗa mata kai kasancewar hamma ya taho mata, hannu tasaka takare bakin ta tana sake waro idanu kan Saleeman dake gaban mirror tana kwashe kayan kwalliyan ta tana zuba wa cikin wani farin kwando "Sis me zaki yi dasu ne?" Halwan tatambaye ta da mamaki Bata ɗago kai ba illa amsa da taba ta "Zan mayar miki ɗakin ki ne, daga yanzu komi naki zai koma ɗakin Barrister ne tunda can ne ɗakin ki ba nan ba, yanzu ke matar gida ce bare ki zauna a ƙaramin ɗaki". Shiru Halwa tayi bata sake cewa komi ba amma zuciyarta na jujjuya maganar nata, sai kuma tamiƙe ahankali tashige Toilet, wanka tasoma yi duk da lokaci ya ƙure mata sannan sai taɗauro alwala tafito Gaban Sip tatsaya tana ɗan murza idanun ta da sabulu yashiga wajen wanka, guntun tsaki taja kafin tabuɗe Sip ɗin tana kallon ciki da mamaki ganin babu komi, sai kuma tajuyo tana kallon Saleema wanda a yanzu har ta gama kwashe kayan gaban mirror ɗin tana tattara takalman Halwa a cikin wani kwandon "Sister yanzu har kaya na kika kwashe?" "Eh mana baki ji me nace miki bane? Ai daga yau kema zaki fara amsa matar *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* na haƙiƙa, domin yau Amarya ce ke". Duk maganar nan da Saleema tayi tana ci gaba da aikin ta ne batare da ta ɗago ta kalli inda Halwan ke tsaye ta saki baki tana kallon ta ba Shiru tayi tatsira mata idanu na tsawon lokaci batare da tayi abinda zai fishshe ta ba, sai da tagaji don kanta kafin tanufi ƙofa tafice tayi ɗakin Khalil, tana shiga tasauke ajiyan zuciya ganin babu shi ciki, da sauri ta'isa bakin sip ɗin tabuɗe tazaro doguwar rigan atamfa da tagani asama tare da ɗankwalin shi, Hijab tasake ciro wa tare da under wear tarufe, memakon tasaka a ɗakin sai takuma koma wa can ɗakin inda tabar Saleema har yanzu tana faman aiki, saka kayan tayi tahau kan sallaya tasoma gabatar da sallan Asar da bata yi ba Lokacin da ta idar tuni Saleema ta gama kwashe mata komi, shigowar ta ɗakin ne Halwa dake zaune kan dadduma har yanzu tabi ta da idanu Murmushi Saleema tayi tana dafe ƙugun ta da hannu biyu, taƙariso bakin gado tazube tana faɗin "washhh Allahna wlh nasha aiki, kin jini ne tamkar zan rabe gida biyu". Babu shiri Halwa tasaka dariya tana sake juyowa yanda zata ganta "To dama wa yasaki? Aikin da babu lada kawai kin saka kanki". Hararan ta Saleema tayi tana tashi zaune tace "ai in ke baki gode min ba Mijin ki zai gode min, kuma ai taimakon ku nayi ko?" Dariyan dai Halwa tayi bata ce komi ba, murza hannun ta tayi tana tunanin yanda za'a yi tafurta abinda ke bakin ta, sai kuma tasake kallon Saleeman da a yanzu take ta faman jan hannayen ta tana naushin iska tamkar zata yi kuka, hakan sai yasake ba ma Halwa dariya, ai kuwa tasaka mata dariya Yayinda ita kuma Saleema tasake kwaɓe fuska tana cewa "wlh sister ki dena min dariya dagaske nake yi baki ji yanda jikina ke min ciwo ba". Rage dariyan nata tayi tana kallon ta tace "to Sister ai gaskiya nafaɗa miki dama, meyasa zaki yi wannan aikin baki jira Ni na tashi in taya ki ba? Kin san Baki da lafiya amma don Allah kin ɗaura wa kanki abinda yafi ƙarfin ki". Saleema tace "to ai ke Amarya ce taya zan bar ki kiyi aiki? Bari ma kiji sai kinyi sati ɗaya curr Sannan zaki soma aiki agidan nan don na rigada na amshe komi". Taƙarishe maganar cike da fara'a wanda kana kallon ta zaka san maganar da tayin ya saka ta nishaɗi ne sosai Halwa har ta buɗe baki da ninyan yin magana Saleeman takatse ta da cewa "Yauwa yanzu kinga saura abinci zan je in dafa mana shi kaɗai yarage min". Dasauri Halwa tamiƙe tana faɗin "ki barshi Ni zan yi". Hararan ta Saleema tayi tana yin gaba tafice batare da ta tanka mata ba Itama bin bayan ta tayi har zuwa kichen ɗin, duk magiyan da Halwa tayi ma Saleema akan tabar shi ita zata yi but samm taƙi sauraron ta, dole ta haƙura tahau taya ta tana mita Abinci me rai da lafiya suka shirya cikin awannin da basu gaza biyu ba, sai da suka gama suka kai dainnig suka jera sannan suka zube saman kujera suna taɓa hira, har sannan Khalil be dawo gidan ba. Sai gab da magriba yashigo, alwala kawai yaɗaura yasake ficewa zuwa masjid, be dawo ba sai da akayi sallan isha'i kamar yanda yasaba akoda yaushe Suna zaune a parlour'n yashigo da sallama, atare suka amsa masa tare da mishi sannu Amsawa yayi idanun sa na kan waya, zama yayi yana ci gaba da latsa wayan sa kamar yanda yashigo yana yi Saleema ce tatashi takawo masa ruwa ta'ajiye masa, ganin hankalin sa baya kansu sai suka ci gaba da hiran su, yayinda shi kuma yake ta latse-latsen wayan sa, ga duk kan alamu abu me muhimmanci yake yi, daga ƙarshe ma tashi yayi yashige ɗakin sa, be fi mintuna goma ba yafito Saleema da tayi masa maganar abinci sai be amsa mata ba kasancewar a yanzu ɗin ya saka waya a kunne yana amsa Call, da hannu yayi musu nuni su je su ci, sai suka miƙe suka nufi dainning ɗin suka zauna Kamar mintuna biyar da zaman nasu shima yaƙariso yana jan kujera gefen Saleema yazauna, yayinda suka saka ta tsakiya kasancewar Halwa na zaune ɗaya side ɗin nata Khalil ɗin be wani ci abincin sosai ba saboda hankalin sa kacokan yana kan waya, Call yake ta amsa wa, daga ƙarshe sai yamiƙe yana jan kujeran baya yawuce abin sa yakoma ɗaki Ajiyan zuciya Halwa tayi aranta tana mamakin yau kuma lafiyan sa ƙalau? To waya babu ƙaƙƙautawa sai kace wani ɗan Film Miƙewa itama Saleema tayi tawuce ɗaki bayan tayi mata bayanin zata je tayi wanka tayi shirin barci sabida yau da wuri zata kwanta, duk gaba ɗaya ta gama tara gajiya a jikin ta, kasancewar bata jin ƙarfin jiki hakan yasa aikin yayi tasiri duk yasaukar mata da gajiya Gyara zama Halwa tayi kan kujeran dainning ɗin, aranta itama tana son taje tayi wankan tayi shirin kwanciya amma tunawa da cewa kayan ta na ɗakin Khalil sai bata yi gigin zuwa ba, Allah yaso ta da wayan ta a hannu sai tayi zaman ta abunta tasaka Game tana yi. Shi kuwa Khalil tunda yashige zama yayi bakin gado, ya daɗe yana wayan kafin yasauke idanun sa kan agogo, lokacin ƙarfe 10:30pm. Sai yamiƙe yashige toilet yayi wanka yafito, Direct sip ɗin kayan sa yanufa, yana buɗe wa idanun sa suka sauka kan kayan Halwa, mamaki ne yakamasa Shiru yayi yana tsirawa kayan idanu, ya jima ahaka kafin yarufe yana buɗe ɗaya side ɗin yaciro jallabiya fara da gajeren wando, sai da yafeshe da turaren sa me ƙamshi kafin yasaka yafito zuwa ɗakin Saleema, ko kaɗan be lura da Halwa dake zaune kan dainning ba, tunda yakalli cikin parlour'n yatabbatar babu su sai yashige ɗakin Saleeman a tunanin sa ko suna ciki. Halwa dake zaune tana kallon fitowar sa da shigewar sa ɗakin Saleeman, hakan yasa tasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya don tasan maybe bazai fito ba ya shiga kenan, Bata san meyasa ba tunda Saleema tayi mata maganar ɗazu sai jikin ta yayi sanyi, komi tana yin sa ne tare da fargaban me zai biyo baya tunda har yanzu bata san makomar ta wajen Khalil ba, "shin zai amshe ta a matsayin matar nasa ne ko kuwa zasu ci gaba da zaman da suka yi ne na baya?" Wannan amsar ne bata sani ba don haka tatashi tanufi ɗakin nashi. ***** Ƙariso wa Saleema tayi tazauna kusa dashi tana faɗin "Mijina yau fa ƴar uwata ke da kai bani ba?" Murmushi Khalil yayi, duk da abinda ke ransa kenan amma be san yanda zai ce mata ba Cuz baya son tayi tunanin ko ya ƙosa ne, that's why yabari ko zuwa gobe sai yazauna yaraba musu kwana, sai ma gashi kamar ta fahimce sa take faɗan hakan Girgiza hannun sa tayi ganin yayi shiru ya tsira mata idanu "Ko baka ji me nace bane?" Tayi maganar tana faɗaɗa fara'an ta Basarwa yayi yana taɓe baki yace "naji ki mana Matata, But Ni ba yau nayi ninyan zuwa ba, sai ki bari zuwa jibi inyaso sai in koma ɗakin ta tunda kece babba ai". Yaƙarishe maganar yana kashe mata idanu tare da janyo ta jikin sa Bata san meyasa ba sai taji farin ciki aranta da maganar nasa, lumshe idanu kawai tayi tana ƙara lafewa a jikin sa, sai dai kuma bata jin zata iya barin hakan domin yau ta tanadar musu ranan nasa ne da Halwa, a ganin ta yau ɗin ɗakin ta yakamata yaje ba nata ba, don haka taɗago tana gyara zaman ta da kyau tace "A'a Ni dai na yafe wlh, Ni fa na rigada na bar muku ka soma cin angoncin ka kamar yadda ko wani Ango yake yi na tsawon sati ɗaya, haka Shari'a ta yarje mana sannan sai mu raba kwana, bari ma kagani don Ni nayi muku tanadi". Taƙarishe maganar tana miƙe wa tanufi lungun gadon ta ta ɗaya side ɗin taɗauko ledojin da ta'aiki Sale yasiyo mata kaji da kayan maƙulashe Khalil dake kallon ta yana ganin ikon Allah har ta'iso ta'ajiye masa a gaban sa tana sake zama sannan takalle sa da murmushi tace "gashi nan na tarban Amarya ne". Kallon ledan yayi, sai kuma yasaka hannu yaɗago yana duba wa, ɗago ido yayi yana kallon ta Sai taware masa idanu still tana murmusawa Be san me zai ce mata ba don haka sai yarungumo ta jikin sa yaɗago ta zuwa cinyan sa tare da haɗe bakin su waje ɗaya Tabbas yau ya sake tabbatar wa Saleema na daban ce, da ita da Halwa bai san wacce tafi kyakykyawar zuciya ba, duk da Saleema tafi Halwa komi don bazai ce kyawu ne yaruɗe sa ba amma kuma zuciyarsa Halwa take tsananin ƙauna, be san meyasaka hakan ba, a ranan farko da yaganta be san komi nata ba but a kallon da sukai ma juna kaɗai zuciyar sa taharbu da tsananin ƙaunar ta, baya ga haka baya tunanin akwai abinda yaja ra'ayin sa ajikin ta da har yaji yana son ta tunda be san komi nata ba a lokacin, abun dai da zai iya cewa ƙaunar ta kawai daga Allah ne, shine yadasa masa ƙaunar ta a zuciya wanda yake jin sa yana gudana da jinin jikin sa tare da bugun numfashin sa, kullum ƙara jinta aransa yake yi memakon raguwa.. Tunda yahaɗe bakin su Saleema lumshe idanun ta tayi tana sauraron saƙon da yake aika mata dashi, ko kaɗan bata yi tunanin taya sa ba sabida bata son hakan yaɗau lokaci Ganin dai yana wuce gona da iri sai tajanye jikin ta tana ƙara marairaice fuska ganin yana shirin sake haɗe bakin su, roƙon sa tasoma yi tana faɗa masa lokaci yaja be kamata yazauna anan ba Daƙyar dai tasamu yabar mata ɗakin don sai da yaƙara ɓata lokaci wajen ta Yana fita tagyara rigan ta tana faɗawa kan gadon tare da lumshe idanun ta hawaye masu ɗumi suka soma sulmiyo mata, wani irin tsananin ƙaunar mijin ta da kishin sa ne yake nuƙurƙusan ta, amma kuma tasan cewa yanzu ya tashi a nata kaɗai dole sai tayi sharing ɗin sa da wata, ko kaɗan bata jin haushin Halwa a yanzu, idan ma taƙi Halwan da mijinta ai dole sai ya auro wata tunda bazai zauna babu haihuwa ba Danne zuciyarta kawai tayi taci gaba da rarrashin kanta, sai dai ta daɗe ahaka barci be ɗauke ta ba, sai kawai tatashi taɗauro alwala tasoma raya daren tare da roƙon Allah yaba su zaman lafiya kuma yakaɗe musu sheɗan a zamantakewar su, tare da roƙon Allah ya ƙara mata juriya da haƙuri, domin tabbas ba kaɗan ba zuciyarta tsananin zugi take mata kasancewar ta me fama da ciwo a zuciyan, shiyasa ta kasa jure zafin da take mata har tasaka kuka cikin sallan nata don dai kawai tasamu salama a zuciyar [1/5, 3:37 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty Eight* ________🎓Yana tura ƙofan Halwa tabuɗe idanun ta, dama tun ɗazu bata yi barci ba tunani ya cika mata zuciya Jin ya nufo wajen gadon sai tasake Rufe idanun ta tana sauraron bugun zuciyar ta dake sake hauhawa Ajiyan zuciya yasauke lokacin da ya'iso bakin gadon yasami waje yazauna, fuskarta yake kallo kasancewar Facing ɗin sa take yi kuma da hasken lantarki da yakunna shigowar sa, yasan ba barci take yi ba don haka yace "Tashi zaune muyi magana". Runtse idanuwan ta tasake yi, sai kuma ahankali taware su kan bayan sa da yajuya mata, tashi tayi tazauna tana sake jawo bargon jikin ta duk da ba wai ta saka kayan barcin me nuna tsiraici bane, sai dai kasancewar yanda yalafe a jikin ta ana ganin komi, gashi kuma rigan iyakan ƙasan gwiwan ta yatsaya Shima gyara zaman sa yayi sosai yana fuskantan ta Kanta a ƙasa tana jiran abinda zai biyo baya, sai dai shiru yaƙi yin magana, ita kuma ta kasa ɗago kai bare ta kalle sa sabida tasan idanun sa na kanta Zuba mata idanu kawai yayi yana kallon ta, jujjuya maganar da yake son furta mata yake yi a zuciyar sa, sai da ya ɗan ja lokaci kafin yafesar da numfashi yabuɗe baki yasoma magana "Halwa". Yakira sunan ta a hankali "Na'am". Ta'amsa masa batare da ta ɗago kanta ba Hannayen sa yahaɗe waje ɗaya kafin yace "Da farko dai ina so in baki haƙuri agame da zamantakewar da mukayi abaya, sabida yanda na nuna miki halin ko in kula a matsayin ki na Matata, duk da ba wai nayi hakan a son Raina bane, har a cikin zuciyata ina jin zafin abubuwan da nayi miki, don Allah idan na ɓata miki ki yafe min yanzu ina so mu gyara zaman auren mu ne shiyasa nake so mu soma fahimtar juna a yanzu ɗin". Lumshe idanuwan ta tayi hawayen da suka soma sintiri a fuskarta tun soma maganar sa suka ci gaba da tsiyaya, wani irin sanyi ne yake ratsa ta har cikin zuciyarta, har a yanzu ɗin ma bata ɗago kanta ba tace dashi "Yaya Khalil wlh baka yi min komi ba, idan ma har kayi min to na yafe maka domin ban taɓa kallon ka matsayin me cuta min ba". Tattausan hannayen ta yariƙo cikin nasa wanda sai da yasaka suka ji tsigan jikin su ya tashi, domin hakan ba wai ya taɓa faruwa bane dasu, fatar jikin junan su be taɓa haɗuwa waje ɗaya ba Sauke ajiyan zuciya yayi yana ƙara damƙe hannayen nata, idanun sa kafe akanta duk da ba wai kallon sa take yi ba, sannan yasoma magana "Duk da bansan cewa kina sona ko baki sona ba but ina me neman alfarma ki bani dama a cikin zuciyar ki, Ni kuma zan koya miki ƙaunata sannan nayi miki alƙwari zan faranta miki da iyawa ta, sannan duk abinda ke faruwa naji komi wajen Dad". Shiru yayi yana jan numfashi sabida jin wani kishi ya turniƙe shi tunawa da wani banza shi yasoma ɓata wa Halwan sa rayuwa, ɗan daidaita muryan sa yayi yace "Ina so in ƙwato miki haƙƙin ki wajen tsinannen mutumin da yaruguza miki rayuwa". Yanda yayi maganar cikin wani irin murya da dole ne kagane tsananin kishin sa, duk da kuwa ya daure sosai wajen dai-dai ta muryan nasa, hakan yasa taɗago kai akaro na farko tazuba masa idanu, bata yi tunanin wai ko wannan maganar yake son faɗa ba koda yace mata yaji komi wajen Dad, cikin sanyin murya tace "A'a Yaya Khalil abinda yawuce ya rigada ya wuce, duk da ada Ina da burin ɗaukan fansa amma yanzu tuni na cire hakan a raina, Husna yanzu ta zama mallakin Saleema na bata ita har abada.." Katse ta yayi da faɗin "duk da haka dole ne na ƙwato miki haƙƙin ki, Ni lauya ne ke kuma Matata ce, taya kike tunanin zan iya barin wanda yataɓa yin ma Matata Fyaɗe batare da na ɗau mataki ba? Ba wai mayar masa da Husna za'a yi ba but dole ne Kotu ta yanke masa hukuncin abinda yayi, na rigada na gama bincike a kansa zuwa kwana biyu da yardan Allah zan miƙa Case ɗin kotu". Wani irin farin ciki me haɗe da kuka ne suka taho mata, ko kaɗan ta kasa ɗauke idanun ta akansa, sai dai ta matse bakin ta gamm ta hana kukan nata fitowa illa hawayen dake ƙara sintiri saman fuskarta tare da murmushin farin ciki dake gudana Kazalika shima kallon nata yake yi, yayinda yasauya riƙon da yayi wa hannayen ta yana murza mata su a hankali yana jin ƙaunarta na ƙara shiga zuciyar sa tare da ƙara girma sosai, yana son yafaɗa mata sirrin dake ransa sai dai kuma baya son yasanar da ita da baki illa a aikace, don haka yabata umarnin tamiƙe tasauko su gabatar da Sallah kamar yanda ko wanne ma'aurata suke yi Hakan kuwa yafaru, ita tasoma yin alwalan tafito tasanya Hijab tazauna zaman jiran sa Shi kuma sai da yayi wanka sannan yafito da alwalan sa, doguwar riga kawai yazira suka ta da Sallah, har suka idar yayi musu dogon addu'a inda daga nan kuma yafice zuwa kichen yaɗauko Plates da Spoon yasake kazan da Saleema taba shi, sai da yagama dai-dai ta komi sannan yayi wa Halwa magana akan tasauko su ci, don ita tuni ta haye kan gado tana lissafi cikin zuciyarta, tayi mamaki da ganin abinda ke gaban sa wanda hakan yatabbatar mata ya shirya ma daren, duk da ko kaɗan bata ji ƙamshin ba sa'ilin da yake sake wa illa motsin leda da take ta faman ji kuma bata yi tunanin dashi yazo ba Babu musu tasauko duk da bata jin yunwa, amma kuma zuciyarta bata ba ta shawaran musa masa ba ko dan faranta masa da take son Yi, domin kuwa ta ɗau alƙawari faranta masa sosai a daren nan ta yanda zata nuna masa godiyar ta a duk kan komi da yayi mata kuma yana shirin sake mata wajen ƙwato mata haƙkin ta Bata wani ci ba, shima haka ɗin, ita ta tattare komi zata kai kichen yadakatar da ita yakwasa yamayar Kafin yadawo har ta shiga ta wanke bakin ta, yana shigowa tana fitowa sai tanufi kan gado tahaye Shima ɗin Toilet ɗin yashiga, babu jimawa yafito yanufi gaban mirror, anan yagama shafe-shafen sa tamkar wani mace, sai da yabi ko ina nasa da turaruka kafin yakashe wutan yanufi kan gado ya haye... A wannan dare Khalil da Halwa sun raya sa ne cike da farin ciki da annashuwa, tare da soyayya me tsayawa a rai ga duk kanin su, wanda tuni ko wannen su ya sanar da ɗan uwansa sirrin dake cikin ransa batare da sun an kare ba, har gabanin asuba kafin suka yi barci manne da juna tamkar zasu maida junan su ciki. 🤦🏻‍♀️🙄 ***** Washe gari a makare suka tashi dukan su, don lokacin ƙarfe 07:38am. Ne, Sallah suka gabatar a gurguje, suna idarwa Halwa tasake nannaɗe wa akan gadon don barci ne sosai a idanun ta tunda basu samu sun yi ishashshe jiya ba Khalil kuwa shirin Office yayi a gaugauce Cuz lokaci ya ƙure masa, gashi babu daman zama agida tunda yana tsaka da soma wani Shari'a ne aiki yayi masa yawa sosai Koda yagama shiryawa wajen gadon yanufa yasakar wa Halwa kiss a kumatu sannan yaƙara mata a goshin ta, yashafa kanta yana murmushi ganin yanda take yamutsa fuska tana gyara kwanciyarta, Sosai idan tana yamutsa fuska take masa kyau ainun, ya kula hakan ya zame mata ɗabi'a ko da yaushe sai tayi Gyara mata Bargon yayi yasake rufe ta yafice dasauri riƙe da briafcase ɗin sa, ɗakin Saleema yashiga sai dai babu ita ciki, har Toilet ya leƙa be ganta ba don haka yafito Direct yanufi kichen Tana ciki kuwa tana haɗa musu Breakfast, daga ita sai doguwar riga iya cinya da gajeren wando baƙaƙe, sai hula me raga-raga shima baƙi tasaka a kanta, kasancewarta fara sai kayan sukai mata kyau suka sake haskata sosai Ƙamshin turaren sa shi yasanar da ita zuwan sa, juyowa tayi dai-dai lokacin da ya'iso gaban ta idanuwan su suka haɗe waje ɗaya yayinda suka sakar wa juna murmushi Ita tasoma gaishe sa, ya'amsa mata cikin fara'a yana janyo ta jikin sa, sannan yatambayi lafiyan ta da yanda tatashi Murmushi tayi cike da tsananin ƙaunar sa aranta ta'amsa masa da "alhmadulillah Mijina, da fatan ƴar uwata tana ƙoshin lafiya?" Sai da ya ɗan ja numfashi idanun sa na kanta yace "Lafiya ƙalau tatashi, but yanzu ta koma barci ne". Narke fuska tayi tace "amma kuma baka yi Breakfast ba zaka tafi?" "No sauri nake yi ina da aiki a Office in naje zan yi a can, ki kula min da kanki, Allah yamiki albarka". Yamatso da bakin sa yasakar mata kiss a libs ɗin ta, har ya janye bakin sa sai kuma yamaida yahaɗe bakin su yayi socking na tsawon sokonni biyar kafin yajanye bakin sa, idanun sa yazuba mata yana kallon ta yayinda talumshe nata idon cike da tsananin shauƙi "I Love You so much". Yafaɗa ahankali still yana kallon ta Buɗe idanun ta tayi suka shige cikin nasa, yau ne ranan farko da ta iya juran kallon cikin idanun sa har na tsawon wasu mintuna batare da ta janye ba, tsantsan farin ciki ne yacika ta har takasa motsawa bare tasauke idanun nata har tafurta wani kalma Murmushin sa me kyau yasaki yana saka hannu yaja hancin ta domin sosai yagane bata cikin tunanin ta a lokacin Ɗan ƙifƙifta idanuwan ta tayi kafin tace "I Love You too My husband". Sai kuma takau da kai tana murmusawa Hannun sa yaɗago yakalli agogo kafin yasake kallon ta yasakar mata Peck a goshi yace "na tafi Byeee ki kula kinji". Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace "Allah yatsare yadawo da kai lafiya". "Ameen". Ya'amsa ta yana juyawa yafice dasauri Ta daɗe tsaye a wajen tun fitan sa batare da tayi yunƙurin yin wani abu ba, in banda murmushi babu abinda take sakar wa, sai da tagaji don kanta kafin tajuya ga Ruwan zafin da take tafasawa, lokacin tuni ya tausa har ya gaji, dasauri tazuba citta da kanumfari a ciki, sai tasaka Lipton taƙara ruwa don ya gama ƙonewa, rufewa tayi taci gaba da sauran aiyukan ta Cikin mintuna ƙalilan tagama komi sannan takwashe takai kan dainning, daga nan ɗaki tawuce tasillo wanka tashirya cikin jan atamfa me ratsin ruwan hanta, ɗinkin doguwar riga me hannun fanka, sosai rigan tabuɗe daga ƙasa kuma tayi mata kyau ainun, sai taɗaura ɗankwalin normal tayi Light makeup da yaƙara fito da ita sosai Parlour tanufa da waya a kunne suna gaisawa da Ummi da takira ta. Bata daɗe da zama ba itama Halwa tafito, har tayi wanka ta shirya cikin ƙananun kaya 🍑Baby Peach colourn riga da Skert, rigan me santsi ne da dogon hannu da aka saka bottles, tana da coller sannan kuma shara-shara ne domin har farar Vest ɗin da tasaka a ciki ana gani, skert ɗin kuma me Robber ne me ƙaramin tsagu ta baya dack peach colour, sai tasaka baƙin ɗankwali taɗaure kanta tare da zagaye gashin ta da ta taufke a tsakiyar kai Masha Allah tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, sai dai ta saka Powder da kazal a idanun ta, fuskarta sai fitar da annuri yake yi tana ƙyallin amarci, kallo ɗaya kayi mata zaka san tana cikin farin ciki da walwalan da yakasa ɓoyuwa a face ɗin ta. Lokacin da ta'iso Saleema ta gama wayan takalle ta tana murmushi tace "Ƴar uwa kinyi kyau sosai wlh, wannan ƙamshi da kike yi haka kowa yaganki ya ga Amarya?" Dariya Halwa tayi lokacin da tasami wuri kusa da ita tazauna tana faɗin "kai Sister ban da sharri". "Wlh dagaske nake yi, baki ga sai shaining kike yi ba, halan baki kalli madubi bane?" Saleema tasake faɗa tana tsatstsare ta da idanu ta sigan tsokana Hararan ta Halwa tayi tace "Uhm to Ni dai ban gani ba gaskiya". Saleema tace "to ina ga idanun ki ne, amma dai bari Barrister yadawo sai ya bambance mana gaskiya, yanzu tashi muje mu yi Breakfast dama yanzu nake Shirin kiran ki". Tashi suka yi suka nufi wajen dainning ɗin inda Halwa tuni ta sauya hiran nasu. Da rana da Khalil yadawo be jima ba yasake fita, sabida yace musu akwai abinda zai je yayi ba zai dawo ba sai dare, don haka su kaɗai suka zauna suka buɗe shafta suna ta hira Da yamma sai ga Larai ta kawo Husna da Ahmad, Murna wajen Saleema kamar me, tsaban murna har rawa ta dinga yi tana shilla Ahmad tana cafewa shi kuma yana wangale mata wawulan bakin sa Ai itama Husna sai tasaka mata kuka akan ba'a ɗaga ta ba Me su Halwa zasu yi ita da Larai in ba dariya ba, sai suka koma tonon Saleema ɗin ganin yanda take ta nishi daƙyar taɗaga Husna dake mata kukan taɓara tana cewa "ita be ishe ta ba a ƙara ɗaga ta" yarinyan sai uban wayau kamar me Shi dai Ahmad tunda aka kwantar dashi kan kujera wasan shi yaci gaba da yi don be san ma me suke yi ba Basu bar Larai ta tafi ba sai da takai musu har magriba sannan tawuce gida. [1/19, 6:29 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twenty Nine* ________🎓 *ONE WEEK AGO* Suna zazzaune akan dainning table suna yin breakfast wayan Haris tayi ƙara, sai da yakai Cofin shayin sa baki yakurɓa kafin yakalli wayan, ganin sunan Dady yafito ɓaro-ɓaro sai yayi saurin ajiye Cup ɗin yana kai hannu yaɗauki wayan tare da yin peacking yana karawa a kunne "Aslm alaikum Dady.." "Eh Dady ban fita ba but yanzu zan fita". "Ok to". Cire wayan yayi daga kunnen sa yaɗau tissue yana share bakin sa, be ce komi ba sai da yamiƙe yajanye kujeran da yatashi sannan ya dube su yace "Ni zan wuce but bazan dawo ba yau sai zuwa dare insha Allahu sabida akwai inda zan je". Miƙe wa Zubaida tayi don ta rakasa, yayinda Fahima tayi masa adawo lafiya tana ci gaba da breakfast ɗin ta Har bakin ƙofan Parlour takai sa kafin tamiƙa masa briafcase ɗin sa suka yi sallama yafice Mota yahau sai Family House ɗin su domin amsa kiran Dady da yayi masa. Bayan ya shiga da motan sa tanƙamemen gidan nasu wanda yakasance me tsananin kyau da burge wa, duk da iyayen sa kaɗai ne agidan ada, but a yanzu Daddyn nasa ya dawo da ƙannin sa biyu da iyalan su suna zaune agidan, kasancewar su kaɗai Allah yaba ma iyayen su that's why mahaifin Haris ke ji dasu sosai, shiyasa da yadena siyasa a yanzu sai yagina wannan tanƙamemen gidan kuma yayi musu umarnin dawowa kowanne da nasa Part ɗin. Fitowa yayi a motan yanufi cikin gidan, koda yashiga parlour'n; Daddyn sa ne da Mamyn sa zaune cikin damuwa, shi kansa Haris da yashigo ya tabbatar ba lafiya ba ganin yanda sukai tsamo-tsamo fuska duk babu walwala, gaishe su yayi suka amsa masa Dady ne yadube sa fuskan sa da damuwa yace, "Haris". "Na'am Dady". Ya'amsa masa ahankali yana kallon sa Numfashi yaja kafin yace, "wacece Halwa?" Wani irin bugawa gaban Haris yayi jin sunan Halwan, still sake tsatstsare Dadyn da idanu yayi ya kasa furta komi "Kayi shiru ina magana?" "Alhaji na fa faɗa maka kamar yarinyan nan ce da yayi haukan son ta har yakwanta a Hospital". Cewar Mamy idanun ta na kan Dadyn Jinjina kansa Daddy yayi kafin yaɗauki Envelope ɗin dake kusa dashi yamiƙa wa Haris batare da yace uffan ba Hannu na rawa Haris yasaka hannu kamar zai amsa sai kuma yatsai da hannun nasa yana cewa "Dady menene?" "Abun da ka shuka ne yake son bibiyan ka Harisu, ashe dama Ciki kayi wa ƴar mutane har da rabon ɗiya atsakanin ku? To ka amsa gashi nan sun maka ka a kotu domin ƙwato mata haƙƙin ta". Amsar Envelope ɗin yayi yaciro yasoma warware wa, sai da yagama karanta abinda ke ciki kafin yakalli Dad idanun sa cike fal da hawaye, ba komi yasaka shi shiga wannan yanayin ba sai famo masa gyambon da akayi, hakan na nufin cewa da rabon yasake ganin Halwa a rayuwarsa? Murmushi yasaki me haɗe da hawaye, gaba ɗaya tsaban farin ciki ya kasa yin magana Sai da Mamy tace, "Haris kayi magana mana kayi shiru, shin cikin ka ne ko kuwa?" Cikin zumuɗi yakalli iyayen nashi yace "Wlh nawa ne, yarinyan da nake ta nema shekara da shekaru yau sai gata zan same ta cikin sauƙi, don Allah Dady kafaɗa min aina take yanzu inje inga ɗiyata, ina son ganin ta Dady har yanzu ina ƙaunar Halwa araina, Please Dady kashige min gaba wajen nema min auren ta, na yarda Wlh zan aure ta in dai sabida hakan ne zasu kai Ni kotu". Baki sake suke bin Haris da kallo ganin yanda yakoma kamar zautacce "To kai ban da abun ka ina zan ga yarinyan tunda ba ita ce tazo takawo takardan ba? daga kotu aka aiko don haka sai mu jira zuwa nan da Monday ɗin kamar yanda aka rubuto, yanzu abinda zaka yi kaje wajen Brr. Musbahu kuyi magana Idan nadawo zuwa gobe sai mu san abun yi". Marairaice fuska Haris yayi yace, "Dady please asan yanda za'a yi anemo gidan da suke wlh bazan iya zama har zuwa Monday kafin in gansu ba". Mamy tace, "To ya kake so ayi ne Haris? Kabari mana zuwa goben kamar yanda Daddyn ka yafaɗa, Ni kaina tun kafin naga yarinyan naji ƙaunar ta araina, wlh Ni farin ciki nayi gwara da suka miƙa case ɗin Court adawo mana da Jikar mu kusa damu tunda cikin naka ne". Washe baki Haris yayi yace, "Ai Mamy nasan da cikin tun sanda iyayen ta suka kore ta, kuma na neme ta but ban same ta ba SHINE SILAN ciwo na". Girgiza kansa Dady yayi yace "na ga alamu ko kunyan mu baka ji Haris, don baka ji nace zan hukunta ka ba ko?" Sunkuyar da kansa yayi yana sosa ƙeya fuskar sa cike da murmushi Mamy ma na taya sa "To je ka wajen aiki lokaci na ƙure wa, amma kasamu ku haɗu da Brr. Musbahu kaji ko?" "To Dady". Haris ya'amsa masa yana miƙe wa tsaye Sallama yayi musu yafice dasauri yana duba agogon hannun sa. Maida idanun sa ga Mamy yayi yana cewa "kin gani ko? Abinda muka ja wa kan mu kenan silan sangarta yaron nan, da yanzu ban dena siyasa ba shikenan haka za'a ɓata min suna". "To ya zamu yi Alhaji? yaro ne ka haife sa yanzu baka haifi halin sa ba, Ni ina ga ko da bamu sangarta sa ba dama zanen ƙaddaran sa ne haka, gashi abinda muka rasa muna fatan samu ashe da rabon zamu samu, wlh Ni har na ɗebe tsammani akan zan ga yaran Haris". Murmushi Dady yayi yace "ban da abun ki duka-duka nawa Haris ɗin yake don be samu haihuwa ba har yanzu zaki cire tsammani? Ni ina ga saboda saka ran da muka yi ne shiyasa muke ƙosa wa, tunda dama matar sa ta taɓa ɓari bare muyi tunanin shine me matsalan, yanzu tunda yace "har yanzu yana ƙaunar yarinyan" kinga sai mu aura masa ita tazauna da ƴar ta, kin ga haɗo min kayana in tafi kar inyi late". "To shikenan Alhaji Allah yasa mu dace dai". Tayi maganar tana miƙe wa don bin umarnin sa. **** **** **** ***** ***** Abun zai baku sha'awa zaman Halwa da Saleema, sun ɗau kansu tamkar ba Kishiyoyin juna ba, kamar yanda kuka san suna zaune a baya haka yanzu ɗin ma suka ci gaba da zama da junan su, su kansu suna manta cewa Miji ɗaya suke aure bare har suyi kishin juna, ƙaunar da suke wa juna ƙauna ce ta tsakani da Allah Shi kansa Khalil yana matuƙar alfahari dasu da jindaɗin kasancewar su mata a gare shi ganin yanda suka haɗa kansu fiye da Da, komi tare suke yi basu banbanta komi a tsakanin su, baza ka taɓa gane wanene me girki ba sai idan dare yayi wajen kwana, shine Khalil zai shiga ɗakin wacce take dashi, gyaran gida, girki, komi da komi tare suke yi, zaman su sai son BARKA, sai dai muyi musu fatan ɗaurewa ahaka. 😅 Yau ma Halwa ce tatambayi Khalil ɗin zuwa gidan su, domin tayi ƙudurin zuwa musamman don ganin Mama da kuma Zainab ƙawar ta, akoda yaushe suna ranta shiyasa yau tatambaye shi Khalil be yi mata musu ba ya amince, duk da yaso yabi su sai dai aiki sunyi masa yawa, ga cases da yake dasu ciki kuwa har da nata, yanzu be da lokacin zama agidan ma Saleema cewa tayi zata bi ta don haka suka yi shiri tare, kaya iri ɗaya suka saka, Jan Material Less ɗinkin riga da Skert, har da Gyalen da suka saka White colour da takalmin ƙafafun su iri ɗaya ne Tubarakallah Masha ALLAH sun yi kyau matuƙa, kallo ɗaya kayi musu zaka san hankalin su akwance yake, in banda ƙyalli da ɗaukan ido babu abinda suke yi Kasancewar yau Saturday Husna bata je school ba don haka har dasu aka shirya cikin kayan su masu tsananin tsada wanda yayi musu kyau ainun, duk wanda yaga yaran sai sun bashi sha'awa Saleema da kanta tayi musu dreving, Halwa tazauna gefen su tana riƙe da Ahmad, yayinda Husna take zaune a baya. Tunda suka shiga anguwan nasu Halwa take baza idanu tana kallon lungu da tsaƙo na cikin anguwan cike da tunano rayuwan ta na baya, har sanda suka kai ƙofar gidan su, gidan da tayi rayuwa aciki tare da sauyawan ƙaddaran ta Numfashi tasauke lokacin da Saleema tatsai da motan dai-dai ƙofar gidan, fitowa suka yi gaba ɗaya yayinda Saleeman taɗauki Husna dake ta faman tsalle-tsalle Gidan suka nufa suka shiga ciki da sallama Wata matashiyar yarinya ne zaune tana haɗa lagwani a risho ta'amsa musu sa'ilin da taɗago kanta tana kallon su Su ma dai kallon ta suke yi, yayinda Halwa taɗauke kanta daga gare ta tana bin gidan da kallo, gaba ɗaya an sauya gidan da sabbin abubuwa, musamman face_face da akayi wa gidan da kuma penti da akayi wa ko ina na gidan wanda ada babu shi.. Maganar budurwan ce tadawo da Halwa cikin tunanin ta tamaida idanun ta kanta, but aranta kuma tana mamakin wacece yarinyan don ita tasan ba cikin dangin su take ba bare kuma na Baba "Ko dai matar Yaya Nura ne?" Tatambayi kanta aranta "Ku shigo mana kun tsaya anan". Budurwan tayi maganar lokacin da tamiƙe tana share hannayen ta ajikin zanin ta Shigowa suka yi suka nufo ɗakin da tanuna musu wanda ada ya kasance na Baba ne, shiga suka yi da sallama budurwan na biye dasu, sai da suka zauna tukun tasake fita tashiga ɗaya ɗakin, babu jimawa sai gata da ƙaton Jug cike da ruwa aciki, ajiye musu tayi tana faɗin "Bismillan ku". Babu wanda yayi ƙoƙarin ɗauka yasha a cikin su illa haɗa baki da suka yi wajen cewa "alhmadulillah mun gode". Yayinda Halwa taƙara da faɗin "don Allah baiwar Allah wajen Mama muka zo". "Mama kuma? Ai babu Mama gidan nan gaskiya, ko dai Aunty Zulaiha?" Yarinyan tafaɗa idanun ta akan Halwa Girgiza mata kai tayi tace, "ina nufin masu gidan nan na asali, but kin san yaya Nura amma?" Shiru yarinyan tayi tana tunani, sai kuma tagirgiza kanta tace, "a'a gaskiya sai dai kunyi ɓatan kai ne, nan daga Ni sai Auntyna da Mijin ta muke zaune anan ɗin, kuma shi sunan sa Aƙilu ne ba Nura ba, babu wasu kuma dake gidan nan, amma dai abinda nasani Mijin Aunty Zulaiha siyan gidan yayi, to ban sani ba ko waɗanda kike neman su ne suka tashi kenan?". Murmushin yaƙe Halwa tayi bata iya cewa komi ba Ganin haka yasa Saleema tace, "to don Allah ko kinsan inda suka koma?" "Wlh ban sani ba". "To shikenan bari mu tafi mun gode". Cewar Saleema tana miƙe wa tsaye Itama Halwa tashi tayi suka fito waje, takalman su suka saka suka yo wajen gidan "To yanzu ina zamu je?" Saleema tayi tambayar time ɗin da suka iso jikin motan su Kallon ta Halwa tayi fuskarta da alamun damuwa tace, "wlh ban sani ba, Allah yasa ba wani abun bane yafaru dasu wlh hankali na ya matuƙar tashi, Nasan babu yanda za'a yi su siyar da gidan su in dai ba wani abu bane ke faruwa". "A'a ki dena faɗar haka, babu komi insha Allahu ki cire komi aranki kinji ko?" Murmushi Halwa kawai tayi tana sake rungume Ahmad dake hannun ta Saleema tace, "To ko dai zamu tambayi maƙota ne?" "A'a muje gidan su Zainab Nasan zamu ji komi acan idan ma wani abu ya faru ne". Motan suka shiga suka nufi gidan su Zainab da babu nisa da nan ɗin, Saleema nayin parcking suka fito suka shiga gidan suna doka sallama tun daga zauren gidan Umma na cikin ɗaki ta'amsa musu sallaman tana fitowa, duk da ta kalle su but bata gane Halwa ciki ba illa maraba da tayi musu tace musu "su shigo daga ciki". Sai da suka zauna taba su ruwa sannan suka gaishe ta Ta'amsa cikin fara'a tana sake duban su "Sai dai ban gane ku ba wlh, ko dai wajen Zainab kuka zo?" Murmushi Halwa tayi tace, "laa umma Halwa ce fa, baki gane Ni ba?" Sake kallon ta da kyau Umma tayi sai kuma tace, "oh ikon Allah Halwa kece? Wlh ban gane ki ba ko kaɗan gaba ɗaya kin sauya min, Allah Sarki ashe da rabon zamu ganki?". Still Murmushi Halwa take yi, tasake gaishe da Umman Ta'amsa mata cike da fara'a tana bin ta da idanu "ALLAH Sarki tamkar ba ke ba abin ki, waɗannan yaran naki ne?" Umma tayi maganar tana kallon Husna da talafe a jikin Halwan, yayinda Ahmad ke kan cinyan ta shima kwance "A'a Umma ga mahaifiyar su nan". Halwa tayi maganar tana nuna Saleema Jinjina kanta Umma tayi tace "Masha Allah to Allah ya raya su ta farkin Gaskiya". "Ameen Umma, Ina Zainab ko bata nan ne?" "Ai Zainab tayi aure kusan watanni bakwai kenan". Halwa cikin tsantsan farin ciki tace, "Umma yanzu Zainab tayi aure ashe? Allah Sarki ashe bazan ga auren ƙawata ba?" Umma na murmusawa tace, "ai kam Zainab tayi aure, ai dayake babu nisa da nan ɗin da gidan ta, sai in saka yara ma sukai ki idan zaki je". "To umma amma naje gida ban ga su Mama ba, ko wani abun ya faru ne?" Umma tace, "ai su Mama sun tashi tuni, ai ba anan anguwan ma suke zaune ba, Nura ya sai musu sabon gida, ashe baki sani ba?" Murmushi Halwa tayi tana gyaɗa mata kai, kafin kuma tace, "eh umma ban sani ba wlh". "To kin tafi can Gombe kin ɓoye ba dole ba, ina ga kema har auren kinyi bamu da labari ko?" Umma tafaɗa cike da fara'a Still Murmushi Halwa tayi bata ba ta amsa ba Sai Saleema ce taba ta amsa da "Eh umma itama tayi aure ai". "Allah Sarki to Allah ya sanya alkhairi, bari inje maƙota in Kira yaro sai yakai ku gidan Zainab ɗin". Umma taƙarishe maganar tana tashi tafice. [1/20, 4:52 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Thirty* ________🎓 A ƙofar gidan da Zainab take aure Saleema tafaka motar ta ta kamar yanda yaron da Umma tahaɗo su dashi yace musu, fitowa suka yi tare da sallaman yaron suka shiga cikin gidan, sallama suka yi duk kan su wanda yajawo fitowar Mahaifiyar Aliyu daga ɗaki Amsa musu tayi cikin fara'a tare da musu maraba Halwa ce tayi mata bayanin wajen Zainab suka zo "Allah Sarki, to ku shiga tana nan ai, ku bi tanan ne ga hanyan sasan ta nan, sannun ku da zuwa". Still tayi maganar cike da fara'a tana sake musu sannu Inda tanuna musu nan suka shiga, a bakin ƙofar ɗakin suka yi sallama Zainab dake zaune a tsakar ɗakin ta, ta baje ƙafafuwa da ɗan ƙaramin cikin ta da be wuce watanni huɗu ba, yanzu ne ma yake shirin shiga na biyar ɗin, dayake ta taɓa yin ɓari, yanzun ma salat take yanka wa tana so tayi kwaɗon shi taci Jin sallaman su yasanya tatsai da yankan tana ɗago kai ta'amsa musu tare da basu iznin shigowa Shigowar kuwa suka yi Halwa ce a gaba Hakan yasa Zainab tasauke idanun ta kan Halwa ɗin duk da bata gama gane ta ba, sai tawaro idanu tana son gasgata gizau ɗin da idanun ta ke mata Lokacin tuni sun gama shigowa, yayinda Halwa kuwa kallon ta kawai take yi tana zuba murmushi, a take anan wani irin farin ciki yamamaye ta sakamakon ganin Aminiyarta wacce suka fi kowa shaƙuwa tun ƙuruciya, babu abinda ke raba su akoda yaushe har tasowar su, sai gashi rana tsaka sun rabu wanda basu sake ganin juna ba tsawon shekaru kusan biyar "Halwa". Zainab tafaɗa da rawan baki still itama tana bin ta da idanu batare da ta motsa daga inda take zaune ba "Zainab ɗina". Halwa itama tafaɗa ahankali idanun ta na kawo ruwan hawaye Ai tuni Zainab ta yunƙura tamiƙe cikin tsananin murna ta nufo ta tarungume tana sake kiran sunan ta batare da ta furta wani kalman ba, kuka suka fashe dashi na tsananin kewar juna da farin ciki. Saleema da tuni ta nemi waje ta zauna, Ahmad na hannun ta dayake tun shigowar su ta'amshe shi, kallon su kawai take yi cike da tsantsan tausayin su, kasancewar ta me rauni itama tuni ta soma hawaye batare da ta san tana yi ba Sun daɗe rungume da juna suna ta sambatu da nuna kewar da sukai wa junan su, kafin kuma suka saki juna suka sami waje suka zauna, bakin su gaba ɗaya yaƙi rufuwa Cuz farin cikin da suke ji a yau ɗin "Wlh bansan da bakin da zan iya nuna murnan da nake ciki ba da ganin ki Halwa, nayi kewar ki nayi kewar ki fiye da yanda kike tunani, tun ina saka ran dawowar ki har sai da kika saka nacire rai da ganin ki, nayi kewar ki wlh". Zainab taƙarike maganar nata tana me share ƙwallan da yacika mata idanu Murmushi Halwa tayi tace "kiyi haƙuri Ƙawata, kina raina bazan taɓa manta wa dake ba, naso zuwa a lokuta da dama sai dai Allah be nufa haɗuwar mu ba sai yanzu". Hannu Zainab tasake saka wa tashare hawayen ta, sai kuma takalli Saleema dake kallon su har yanzu ta kasa cewa uffan Hakan yasa Halwa tace "Sunan ta Saleema, ƴar uwata da tamaye mini gurbin ki, da ba don ita ba ban san ya rayuwata zata koma ba, ita ce tamaye min farin cikina dana rasa abaya.." "Haba ke kuwa kiyi shiru mana mu gaisa". Cewar Saleema tana katse mata maganar ta Baki a washe Zainab tagaishe ta duk da kuwa Saleeman ba wai ta basu tserayan shekaru bane, da shekara ɗaya ta girme musu Cikin fara'a Saleeman ta'amsa cike da ƙaunar Zainab ɗin aranta Sai da suka gama gaishe-gaishen nasu har Zainab ɗin tatashi takawo musu drinks, Ahmed ta'amsa daga hannun Saleema takoma tazauna tana faɗin "Kema ƴar lukuta zo nan wajena". Husna dake maƙale jikin kujera tana jan igiyoyin kwalliyan da akayi, tataho dasauri ganin Saleema ita take kallo, dayake yarinya ce me shegen wayau ga son mutane Ɗaukan ta Zainab tayi taɗaura saman kujeran tana cewa "Yauwa ƴan mata na, ya sunan ki?" "Husna". Tafaɗa tana jujjuya jikin ta cikin wasa Kallon Husnan tayi da kyau, sai taɗago tana duban Halwa tana murmusawa tace "wlh sak irin ku ɗaya, daga gani yarinyan nan taki ce, ashe kema kinyi aure?" Dariya kawai Halwa tayi batare da tace komi ba Saleema ce taba ta amsa da "Eh". "Allah Sarki rayuwa kenan, ashe babu rabon muga auren juna, amma mun gode Allah tunda Allah ya haɗa mu da ran mu da lafiya". Sai kuma takalli Ahmad tace "kai kuma ya sunan ka ɗan kyakykyawa?" Husna ce taba ta amsa da faɗin "cunan sa Ahmad, amma kincan mene Aunty Mamy take ce mici?" ( Tana nufin Halwa) "A'a sai kin faɗa?" Zainab tafaɗa tana shafa mata kai "Tana ce mici Amadidi". Dariya suka yi ban da Halwa da tayi murmushi kaɗai kana tace "To Sarkin surutu faɗi ba'a tambaye ki ba". "A'a ki ƙyale ta tayi surutun ta, ai duk surutun ta baza ta kai ki ba na sani". Cewar Zainab tana dariya Yayinda Saleema ke taya ta, ɗan barkwanci suka taɓa na tuna baya kafin Zainab ɗin tace "Wlh na shiga damuwa lokacin da su Mama suka faɗa min kin bi Dangin mahaifin ki Gombe, ban san meyasa naka sa yarda cewa wani abun ne yafaru dake ba, domin Ni dai har ga Allah nasan baza ki taɓa tafiya batare da kin sanar min ba". Murmushin takaici Halwa tasaki tuno da abinda yafaru da ita a shekarun baya, sai dai ko kaɗan baza ta taɓa iya ɓoyewa Zainab sirrin ta ba, ita ɗin Aminiyarta ta ce wacce suka shaƙu matuƙa, kuma ta san ko babu komi zata taya ta jimamin abinda yafaru da ita, don haka tagyara zaman ta tasoma bata labarin komi da komi tun tafiyan ta har zuwa yanzu, abinda ta ɓoye mata kaɗai shine haihuwar Ahmad, don ko kaɗan bata kawo shi a zancen ta ba Sai da Zainab ta dinga share hawaye sabida tausayin ƙawarta "Ashe abun da yafaru dake kenan? Meyasaka su Mama suka aikata miki hakan? Dama akwai ranan da zata zo su guje ki? Waɗannan wasu irin mutane ne masu baƙin hali marasa yarda da ƙaddaran Allah, tirrrr da su wlh, tun farko shiyasaka zuciyata takasa amince wa da abinda suka faɗa mana". Numfashi Halwa taja kana tace "Ni har yanzu ban ga laifin su ba Zainab, abinda nasani kawai shine Yaya Nura da yaƙi faɗa musu gaskiya, na tabbata wlh da ya sanar musu dole zasu yarda, har yanzu na kasa manta kalaman da Yaya Nura ya faɗa min aranan, bayan komi a gaban sa yafaru, shin meyasa ya aikata min hakan? shine abinda nake so in sani". "Ya kuwa zaki sani tunda maci amana ne shi, idan be faɗa musu gaskiya ba su basu san ƙaddara bane? Ko kuwa basu fi kowa sanin halin ki bane? Dama sun yi ne da gayya don su kore ki sai gashi Allah yasa baza ki taɓa muzanta ba, wlh sun bani mamaki ko a mafarki bazan taɓa yarda zasu iya juya miki baya ba". Haka Zainab ta dinga faɗa kamar zata ari baki, sai zagin su take yi musamman ma Nura da tafi tsanar sa a yanzu, bata dena ba sai da tayi ta gaji don kanta Anan ne Halwa take faɗa mata tana son zuwa inda suka koma tagan su, gashi sun fito Umma bata faɗa musu ba bare su san gidan Zainab ce mata tayi "ai Ni wlh ko na sani bazan faɗa miki ba balle ma ban sani ba, me zaki je kiyi musu tunda su suka kore ki? Wlh kar ki soma ki je tunda sun kore ki; ki bar su har abada". Sai anan Saleema tasaka musu baki "A'a hakan be kamata ba, su ɗin dolen ta ne kuma makusantan ta, kar ki manta Ƙanwar mahaifiyar ta ce, ko babu komi taci darajan ta, insha Allahu zamu je ko ba yau ba, kuma duk abinda suka yi su da Allah ne ba mu da hurumin ɗaukan mataki". Ita dai Zainab taɓe baki tayi bata sake tanka zancen ba, sai ma sauya wa da tayi nan da nan suka ɓarke da hira, daga ƙarshe Zainab ɗin tatashi don yin musu girki, amma basu bar ta ba don tare suka shiga kichen ɗin gaba ɗayan su suka yi girkin, koda zasu ci ma a Plate ɗaya suka ci cike da nishaɗi. Sai yamma sakaliya sannan suka baro gidan Zainab, yayinda itama tayi musu alƙawarin zuwa nan ba da jima wa ba, duk da dama Halwa ta faɗa mata zasu shiga Kotu jibi, kuma tayi mata alƙawarin zata saka Aliyu ya kawo ta Court ɗin, domin baza ayi babu ita ba. ***** ***** ****** ****** *MONDAY* Tun ƙarfe 07:00am. Brr. Khalil yafice a gidan. Su kuma su Halwa sai wajen ƙarfe 09:00am. Suka gama shiryawa, dayake sai ƙarfe Goma ne za'a shiga court ɗin Husna tuni an shirya ta drever ya tafi da ita school, shi kuma Ahmad tare dashi zasu tafi yana hannun Saleema, sai da suka shiga mota ne sannan Halwa ta'amshe shi tunda Saleema ce zata tuƙa su Direct gidan su Khalil suka wuce, saboda zasu taho tare da su Mom ne Lokacin da suka je ba wani zama suka yi ba Mom tafito suka tafi, tunda dama ita kaɗai zata bi su, yau Monday Nazeefa na school, shima Dad yana da aiki don haka bazai samu zuwa ba Kafin goma sun isa court ɗin, acan suka haɗu da Ummi har da Zainab da tayi musu alƙawarin zuwa Abun mamaki kuma har da Mama da Baba da Nura a wajen, duk da Halwa bata gan su ba, su ma ɗin basu gan ta ba, amma su sun zo ne kasancewar Nura yace musu za shi ana Shari'a da uban gidan shi, shi ne Baba yace "be kamata su zauna agida ba dole su je, ko don martaba uban gidan sa tunda yayi musu halarci, a sanadiyar sa ɗan su ya sami kuɗi sosai, sannan basu da masaniyar komi akan Halwa ce wacce za'a yi Shari'an da ita Nan kuwa basu sani ba, Haris ne yasaka shi tilas yazo, kuma yace "idan be zo ba zai iya tona masa asiri, don haka gwara yazo yaga me zai faru, be san cewa Haris wayau yayi masa ba don ya rigada ya shirya amsa duk wani tuhuma da ake musu sabida samun ƴarsa, sannan kuma ko hakan zai sa Halwa ta yafe masa har ta aure sa. Lokacin da suka isa Halwa aka bari a baya, tana rungume da Ahmad tana shirin fitowa sai ganin Haris tayi a gaban ta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tafaɗa a fili sa'ilin da tayi tozali dashi Gaban ta ne yayi matsanancin faɗuwa, sai dai bata nuna firgitan ta a fili ba, ta kai duban ta gare shi fuskarta a ɗaure tamkar bata taɓa sanin sa ba, tana shirin sake yunƙura wa tafito taji muryan sa ya daki dodon kunnen ta "Halwa ashe zamu sake haɗuwa? Nasan bani da bakin da zan roƙe ki; ki yafe min, but duk da haka ina neman afuwar ki, wlh nayi nadaman abunda..." "Kai da Allah dakata min". Takatse sa da faɗin hakan tana me banka masa harara tamkar zata maƙure sa dan baƙin cikin ganin sa da jin muryan sa "Ka ɓace min agaba ko in maka wulaƙacin da sai kayi nadaman zuwan ka duniya". Shi kansa Haris yayi mamakin furucin nata da yanda tafaɗa cikin tsananin fushi tamkar ba Halwan da ya sani ba abaya, duk da dama ta sauya masa sosai amma hakan be sa ya kasa gane ta ba, kuma yasan irin hakan take masa magana domin dai bata sauya ba a yanda ya santa Yana shirin sake magana taja ƙofar da ƙarfi ta rufe kanta aciki, domin dai babu yanda za'a yi tabar wajen dole sai ya matsa, ita kuma baza ta iya juran sake jin maganar sa ba, ta matuƙar tsanar sa fiye da kowa a duniya Hannun sa ya kai zai ƙwanƙwasa Glasses Motan, sai jin murya daga bayan sa yayi, wanda ya dakatar dashi daga abinda yayi ninya "Malam don Allah kayi haƙuri ka bar nan wajen, Halwa yanzu matar wani ne baka da hurumin da zaka iya mata magana kaji ko?". Cewar Saleema dake tsaye gefe tana kallon duk abinda suke yi tun ɗazu Shima dai kallon ta yayi tamkar sakarai, babu abinda ke kai kawo a zuciyar sa sai ce masa da tayi "Halwa matar wani ne". "Kenan tayi aure?" Ya tambayi kansa batare da zai iya samun amsar ba Be sake motsawa ba, tamkar gunki ya zama sabida ba ƙaramin taɓa sa maganar yayi ba, har be san ma a wani yanayi yake ciki ba "Excuse me zan wuce". Tayi maganar tana kallon sa ganin be da ninyan jirga wa Ɗan ja baya yayi kaɗan ya matsa mata kamar wanda be da jini a jiki Buɗe ƙofan tayi ta'amshi Ahmad daga hannun Halwa, sannan tayi mata maganar tafito Ko kallo be ishe ta ba sanda tafito, gaba kawai tayi tabar Saleema na rufe ƙofan kafin tabiyo bayan ta Idanu kawai ya kafa ma bayan ta hawaye na sintiri a face ɗin sa. [1/20, 5:15 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Thirty One* ________🎓 Kafin Shari'an su Halwa akwai Shari'an da Khalil ya soma yi Na wani yaro ne da yayi wa ƴar aikin gidan su fyaɗe, tun wajen watanni uku da soma Shari'ar sai yau ne ake shirin ƙarƙare shi Kasancewar uban yaron me kuɗin gaske ne, tun a zaman farko da yaga Khalil na shirin yin nasara akan su, shi ne sanadin da ya samo ƴan daba suka je suka harbe shi, sun so su kashe sa ne gaba ɗaya sai Allah be basu Sa'a ba Lokacin da Alh. Sheƙau (kar ku ce da Sheƙau ɗin sambisa nake yi fa lolx 🤪) ya basu aikin; to ya bar ƙasan ma gaba ɗaya shi da ɗan sa tunda ya samu beli, ƴan daban kuma da suka yi aikin sun tabbatar masa Khalil ya mutu duk da kuwa su ma daga baya suke jin yana da rai, sun so su sake komawa asibitin su kashe sa but a time ɗin akwai jami'an tsaro, to sai suka yi wa Alh. Sheƙau bayanin cewa sun wulla Khalil barzahu, don haka ya biya su kuɗin su sukai gaba a bin su Sai kwanaki biyun nan suka dawo ƙasan sabida a yau ɗin za'a koma kotu a yanke hukuncin ƙarshe, sun saki jiki babu abinda zai faru tunda an kashe musu Khalil, duk da a time ɗin har da Brr. Tahir ya taya shi shari'ar, amma sun fi so su ga bayan Khalil tunda shine yadage sai ya amsar wa yarinyan haƙkin ta. Yau kuma da aka shiga kotu sai hankalin su yayi mummunan tashi ganin Khalil a raye be mutu ba Shi kuwa Khalil murmushi kawai yayi yana bin su da kallo, don shi tuni ya gane Alh. Sheƙau ne ya saka a kashe shi, be faɗa ma kowa bane don baya son maganar tayi tsawo, duk da kuwa yana da hanyan da zai sa a hukunta Alh. Sheƙau komin girman sa a ƙasan kuwa, tunda yana da gwamnati a hannu, but be yi hakan ba ya ƙyale su tunda dama zargi yake yi, amma yau da ya gansu sai ya tabbatar da zargin sa Be damu kansa ba kawai Shari'an ya gabatar, kuma cikin ikon Allah ya ƙwato wa yarinyan haƙƙin ta, inda aka yanke wa Yaron Alh. Sheƙau hukuncin zaman gidan yari na shekara 8 sakamakon kama sa da yin wa yarinya fyaɗe, kuma babu Beli, sannan kuma dole zai bada kuɗi dubu ɗari cif don nema mata magani. Hakan ya faranta ran mutane matuƙa, ya saka wasu kuka da hawayen su sabida tsaban farin ciki, da yawan su kuma hakan ya taɓa faruwa da yaran su, sai dai rashin samun wanda zai taimake su ba sa iya ƙwato wa ƴar su haƙƙin ta, amma kuma wannan hukuncin da aka yanke wa mutum ɗaya ya sa zuciyoyin su fari da wanke duk wani tabo da ƙuncin dake cin su Kowa sai sanya wa Khalil albarka yake yi, tare da addu'ar gamawa da duniya lafiya, gaskiya yayi na mijin ƙoƙari, kuma samun irin su a duniyar mu masu jajircewa wajen tsayawa tsayin daka don hukunta masu laifin fyaɗe, hakan zai saka a rage yawaitan su a duniyar mu, idan suka ga ana musu hukunci to dole zasu dena abinda suke yi Sai dai kuma matsalan al'umman mu suna jin tsoron su fito da irin wannan maganar su bayyana wa mutane don ƙwato wa ƴar su haƙƙin ta, suna ganin tamkar sun tona wa kansu asiri ne, kuma hakan zai ja musu tsangwama a wajen mutane, wannan dalilin yasaka suke ɓoye wa har a kasa hukunta masu laifin fyaɗe, su kuma hakan ke saka wa suna ci gaba da aikata laifin tunda babu abinda ake iya musu. Don Allah mata duk wanda hakan ya faru da ita, ya jajirce wajen ƙwato wa kansa haƙƙi, iyaye su ma su dage su tabbatar an hukunta wanda ya aikata ɗin, hakan na taimaka wa sosai wajen rage yawaitan laifukan, Allah ya ƙara tsare mu da zuri'armu baki ɗaya Ameen. Daga wanann Shari'an ne aka shiga na su Halwa, alokacin ne Halwa da su Mama suka ga juna, sai dai babu halin magana tunda Alƙali na ciki Shima Nura ya ganta, sai dai ita bata ganshi ba, mamaki sosai ya cika sa ganin yanda ta sauya gaba ɗaya tamkar ba ita ba, tsananin kyan da tayi masa ma ya kasa ɗauke idanu akanta, yanayin canjin rayuwan da ta samu duk da su ma suna da rufin asiri sosai, amma kuma yanzu tana cikin daula ne dole kaga sauyawan Halwa, ga ta dama tun farko tana da kyan ta da dirin jiki, but yanzu komi nata ya sake canja wa tayi kyau matuƙa, skin ɗin ta tuni ya sake haske tare da wani irin fresh, Kai da gani kasan babu wahala a rayuwan ta, jin daɗi da kwanciyar hankali ya zauna mata, bare uwa uba tana tsaka da cin amarcin ta ne, ƙyallin amarci da Albarkan aure ya sake fito da ita.🥶😫 Koda Khalil ya tashi ya gabatar da kansa a matsayin Lauyan dake kare wacce ta kawo ƙara, komawa yayi ya zauna Sai dai su Haris basu da lauya, domin tuni Haris yace "be buƙatar lauya a halin yanzu, ya yarda zai amsa laifin sa sannan a bashi ƴar sa". Don haka ya ga babu amfanin ya samu Lauyan ma Dadyn sa da Mamy basu ji daɗi ba, amma babu yanda zasu iya tunda yace "zai amsa laifin sa". Brr. Khalil ne ya miƙe yafito gaban kotun bayan ya nemi iznin magana da Halwa Fitowa tayi tatsaya a inda aka tanada don tsayawar masu amsa tambayoyi Khalil ya tambaye ta sunan ta da sunan mahaifin ta, sannan kuma ya buƙaci ta ba ma kotu Labarin asalin abinda yafaru a ranan da mummunan ƙaddaran yafaru da ita Tiryan-tiryan tasoma faɗa wa kotu abinda yafaru Tsit kotun tayi ana sauraron ta, tuni masu saurin kuka da tausayi sun soma zub da hawaye, sabida sosai abinda yafaru da Halwan ya matuƙar basu tausayi Ita kanta tana ba da labarin ne tana kuka, sabida yanda take jin ƙunci da baƙin ciki a zuciyar ta tamkar lokacin da ake keta mata haddi ne Zina tabo ne babba ga duk wanda ya tsinci kansa a halin; dole ne ya koka, musamman waɗanda akayi musu ta ƙarfi, su kansu masu aikata wa da za su gane illa da girman laifin da suke yi, wlh wlh da har su mutu baza su dena kuka ba saboda tsoron haɗuwar su da ALLAH😭, ya Allah ka kare mu da kariyan ka, bamu da wayau ko dabara ya Allah ka kare mana zuri'armu daga faɗa wa mummunan makoma. 🙏🏼 Har sanda ta dasa Aya tana shashsheƙan kuka Khalil kallon ta kawai yake yi cike da tsantsan tausayi tare da tarin ƙaunar ta a ransa, ji yake yi tamkar yajawo kayan sa yarungume ta ya rarrashi abin sa, amma kuma babu hali 🤠, don haka yaja numfashi yana lashe bushashshen laɓɓan sa, cike da sanyin murya yace mata "taje ta zauna". Sannan ya juya ya fuskanci Alƙali ya nemi iznin ganin Haris Fitowa yayi ya tsaya inda Halwa ta tashi Khalil kallon sa yake yi tamkar ya kama sa ya maƙure shege😃, sai dai babu hali, don haka ya murtuke fuska yasoma masa tambayoyi Babu abinda Haris ya musa a tuhuman da ake masa, sai ma ƙara wa da yayi da abinda basu sani ba, ya faɗa musu komi da yanda ya nemi taimako wajen Nura. Tirƙashi! nan ake yin ta fa, ai nan da nan kotu ta hargitse saboda jin bayanan Haris, waɗanda suka san Nura kuwa kamar su: Mama, Baba Zainab Halwa, da su Saleema, daskare wa suka yi sabida tsantsan mamaki da Al'ajabi Halwa bata iya ko motsi ba, don ba ta tunanin kunnen ta ya jiye mata dai-dai, shiyasa tabi Nuran da kallo wanda tuni Khalil ya buƙaci ganin sa, zuba masa ido kawai tayi tana sauraron abinda zai fito daga bakin sa Lumshe idanuwan ta tayi da suka cika da hawaye, ko kaɗan baza ta iya juran abinda yake faɗa ɗin ba, don haka tasaka hannun ta biyu ta toshe kunnuwan ta tana fashe wa da kuka me tsananin sauti Duk mutanen wajen sai da suka kallo ta, sosai ta basu tausayi wasu har da zubar mata da hawaye Ita kanta Saleema dake kusa da ita hawayen take zubar wa, tasaka hannu tariƙo mata nata hannayen, cikin rawan murya tasoma rarrashin ta Halwa bata dena kukan ba, sai ma ɗaura kanta da tayi saman cinyoyin ta tasoma rerawa kamar zata shiɗe, babu abinda zuciyarta ke maimaita mata sai sunan Nura, taya hakan ma zai faru? Taya ɗan uwanta masoyin ta, wanda tafi yarda da shi a baya fiye da kowa, shine zai yi sanadin shigar ta wannan halin, meyasa? Me tayi masa? Guduma Alƙali yabuga don hayaniyar kotun tayi yawa, tsit kake ji an yi duk da kuwa har yanzu Halwa bata dena kukan ba, amma kuma ba'a ji acikin kotun sai can wajen su Khalil bayani ya sake yiwa kotu kafin yakoma wajen zaman sa ya zauna Sai da Alƙali yayi rubuce-rubucen sa kafin ya ɗago yasoma yanke hukunci, hukuncin ɗaya ne aka yanke musu daga shi Nuran har Haris, domin dai basu da maraba tunda duk laifi ɗaya suka aikata, don haka an yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na shekara 8 batare da beli ba, sannan kuma dole Haris zai biya kuɗin rainon masa ɗiya da akayi, kuma bashi da damar amsar ɗiyar sa sai idan mahaifiyar sa ta amince. Sosai iyayen Nura suke kuka sabida abinda suka ji, tabbas yau suna nadaman abunda suka yiwa Halwa, shin da wani ido zasu kalle ta? Sun kore ta sabida gudun zubewar mutuncin su, ashe ɗan su shine SILAR KOMAI, Mama tafi kowa shiga tashin hankali, tana ganin tafi Nura ma laifi, domin abinda ta aikata wa ɗiyar ƴar uwanta yafi na Nura muni, shin ina hankalin ta yaje ne a lokacin da har ta manta wacece Halwa a wajen ta? Suna ji suna gani aka tasa su Nura, amma ko kallon inda yake ba suyi ba, suna ji da ƙuncin dake ransu. Halwa kuwa sabida shiga ruɗu da kukan da take yi, tuni numfashin ta ya rabu da gangan jikin ta, ta kasa jure abinda taji, ta rasa taya ma zata ɗaura abun akan mizani, shin dama akwai ɗan uwa irin haka da zai iya cutar da ƙanwar sa sabida kuɗi? Hankalin Khalil da su Ummi ya tashi sosai, musamman ma Saleema, ai nan da nan Khalil ya ɗauke ta ya fice da ita suka take masa baya, mutane sai kallon su suke yi kowa da tunanin da yake yi aransa Asibiti Direct aka wuce da ita, domin a cikin su babu wanda yayi tunanin zuba mata ruwa ko zata iya farfaɗowa. 𝗕𝗔𝗬𝗔𝗡 𝗦𝗛𝗨𝗗𝗘𝗪𝗔𝗥 𝗔𝗪𝗔𝗡𝗡𝗜 *2* Tuni su Halwa sun koma gida, sai dai har alokacin sun kasa gane kanta, abinda Nura yayi mata ya matuƙar saka ta a Shock, kuka kawai take yi ta kasa yin shiru Khalil da Saleema in banda zaman rarrashi babu abinda suka zauna yi Sukuku ta koma, gaba ɗaya ta dena walwala, to idan ɗan uwanka yayi maka haka, wanene ma bazai maka ba? Nura ya cuce ta, duk tsanar da take yi wa Haris, sai taji gaba ɗaya ma ya gushe ya koma kan Nura, tsantsan tsanar sa ne ya ɗarsu a ranta, ji take yi ta tsane sa fiye da mutuwar ta, kuma ba ta tunanin zata iya yafe masa har ta koma ga mahaliccin ta. Bayan kwana biyu sai ga su Mama da Baba sun zo har gida neman gafarar Halwa, kuka suke yi suna roƙon ta, yayinda itama take nata kukan tare da rungume Mama, tabbas tayi kewar iyayen nata fiye da zaton me karatu, taya zata ƙi yafe musu bayan su ne iyayen da tabuɗe idanu tagan ta tare da su? Bata taɓa kallon wasu a iyayen ta ba sai su, su ne tatashi tasani; su ne kuma suka raine ta, ko waɗanda suka haife ta bata jin su kamar su Shiyasa tanuna farin cikin ta da ganin su, ko babu komi iyayen ta sun dawo gare ta, shekaru kusan biyar basa tare, gaskiya tayi kewar su matuƙa, kuma ko kaɗan bata kalle su da abinda ɗan su yayi mata ba. Mama kuwa kunya da dana-sanin abinda suka aikata mata yasa ta kasa kallon Halwan, gashi sabida son zuciyar su sun aikata babban kuskure, sai dai Allah ya yafe musu. . 𝑇𝑜 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑟𝑎𝑏𝑎 𝑚𝑢 𝑑𝑎 𝑚𝑎𝑠𝑢 ℎ𝑎𝑙𝑖 𝑖𝑟𝑖𝑛 𝑛𝑎 𝑠𝑢 𝑀𝑎𝑚𝑎, 𝑠𝑎𝑏𝑖𝑑𝑎 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎 𝑦𝑎 𝑓𝑎𝑑𝑎 𝑤𝑎 '𝑦𝑎𝑟 𝑠𝑢 𝑠𝑎𝑖 𝑠𝑢ka 𝑚𝑎𝑛𝑡𝑎 𝑑𝑎 ℎ𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑠ℎ𝑖𝑛𝑒 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎𝑛 𝑡𝑎, 𝑠𝑎𝑖 𝑠𝑢ka 𝑘𝑜𝑟𝑒 𝑡𝑎, 𝑘𝑜𝑑𝑎 𝑚𝑎 𝑑𝑎 𝑔𝑎𝑛𝑔𝑎𝑟 𝑡𝑎 𝑎𝑖𝑘𝑎𝑡𝑎 ℎ𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑏𝑒 𝑘𝑎𝑚𝑎𝑡𝑎 𝑠𝑢 𝑘𝑜𝑟𝑎 𝑡𝑎 𝑏𝑎, 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 ℎ𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑏𝑎𝑏𝑏𝑎𝑛 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑒 𝑛𝑒, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑘𝑦𝑎𝑢𝑡𝑎. [1/20, 5:29 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ 𝐁𝐀𝐑𝐑𝐈𝐒𝐓𝐄𝐑 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐊𝐇𝐀𝐋𝐈𝐋 ♠️ 𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔:✍️ 𝐵𝑦 𝐍𝐚𝐟𝐢𝐬𝐚𝐭 𝐈𝐬𝐦𝐚'𝐢𝐥 (𝐹𝑒𝑒𝑛𝑎ℎ 𝐽𝑖𝑘𝑎𝑟 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎) *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ 𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖 ®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓ 𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️ 𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈 \𝗙.𝗪.𝗔📚/ 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!!! 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑛𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑒 𝑚𝑎𝑘𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑑𝑎𝑚𝑎𝑟 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖𝑛 𝐵𝑟𝑟. 𝐼𝑏𝑟𝑎ℎ𝑖𝑚 𝐾ℎ𝑎𝑙𝑖𝑙, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑖𝑘𝑜𝑛 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑎𝑏𝑖𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑖 𝑎𝑚𝑓𝑎𝑛𝑖 𝐴𝑙'𝑢𝑚𝑚𝑎𝑛 𝑚𝑢, 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑒𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑛 𝑦𝑖 𝑎𝑐𝑖𝑘𝑖 𝑘𝑢𝑚𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑦𝑎𝑓𝑒 𝑚𝑖𝑛 𝐴𝑚𝑖𝑛 🤲 𝑦𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ. 𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔 𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 ƴ𝑎𝑛 𝑢𝑤𝑎𝑛𝑎 𝑚𝑢𝑠𝑢𝑙𝑚𝑎𝑖 𝑏𝑎𝑘𝑖 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗕𝗢𝗢𝗞 𝗧𝗪𝗢 . _______________________________ 𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 𝗧𝗵𝗶𝗿𝘁𝘆 𝗧𝘄𝗼 ________🎓 Bayan sati Uku da faruwan abun Hutun su Halwa ya ƙare, ta koma school yanzu bata cika zaman gida ba, tunda yanzu sauran su ɗan watanni ne su ƙarashe, karatu suke yi sosai. Sai ga Zainab wani ranan asabar ta kawo musu ziyara, ai kuwa sun yi farin ciki matuƙa, ranan wuni suka yi hira har yamma kafin Aliyu yazo ya ɗauke ta, sun rabu cike da kewar juna Washe gari kuma sai ga iyayen Haris sun zo wai ganin Husna, tare da matan Haris ɗin da wasu makusanta cikin Familyn su, duk da kuwa da yawan su ganin ƙwaƙwaf suka zo yi Tarba me kyau Halwa da Saleema suka yi musu Tunda suka zo Mamy da Daddy suka naniƙe Husna ko sakin ta sun ƙi yi, dayake har ciki Daddy yashiga, ƙaunar yarinyan sosai yashige su, yanzu basu da abunda suke tunawa sai ita, tunda yanzu ɗan su yana magarƙama, har hawaye Mamy take share wa idan ta kalli Husnan, tana jin soyayyar yarinyan sosai aranta duk da kasancewar ta shegiya, amma su suna son ta a matsayin jikar su Sun roƙi Halwa taba su ita su tafi da ita, amma firr Halwan taƙi, sai ma faɗa musu tayi ta kyautar da ita yanzu, don haka su yi haƙuri Babu yanda zasu yi haka suka haƙura, sai dai sun sake neman alfarman zasu riƙa ɗaukan ta tana musu hutu. Da zasu tafi Daddy ya ajiye masu kuɗi me yawan gaske, duk da Halwa taƙi amsa, sai Khalil ne yace "ta'amsa" tukun ta amsa. Bayan kwana biyu kuma sai ga Mamy ta sake dawowa da kaya niƙi-niƙi, wai ta kawo ma Husna ne, har da Ahmad sai da takawo mishi nashi Ranan ma Halwa tana school daga ita har Husnan, sai Saleema da Khalil ne da shima dawowan sa kenan, sun amshi kayan tare da yin mata Godiya Ƙin tafiya tayi, har sanda aka dawo da Husna ta ganta kafin tatafi. Rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi babu daɗi, gashi har su Halwa sun rubuta Exams ɗin su ta ƙarshe, yanzu kuma sai jiran result. **** ***** ***** **** Itama Nazeefa a wannan shekaran ne tagama Secondary School ɗin ta, koda result ɗin ta yafito sai Dad yatambaye ta Aure ko karatu? Ita kuma tace masa karatu take so taci gaba, tunda har yanzu soyayyar Khalil ne aranta bata taɓa tsayawa da kowa ba, ko da tace auren take so ba ta da wanda zata iya fitar wa, kuma ba ta jin ma zata iya aure yanzu idan har ba ta cire soyayyan Khalil bane aranta, duk da tayi iyakan ƙoƙarin ta amma ta kasa manta sa, don haka ta samu Dad tafaɗa masa tana son tayi school ɗin nata ne ba'a state ɗin nan ba, ko ba komi tasan idan tayi nesa dashi zata manta shi Dad be yi musu ba kuwa, yace mata ta zaɓa inda take so A.B.U Zaria ta zaɓa don nan ne yafi mata, duk da kuwa bata san school ɗin ba, amma yanda take jin labarin sa tasan ba ƙaramin makaranta bane tunda yayi fice a ƙasar Nigeria. Dad sai da yatara Sameer da Khalil ya faɗa musu komi don jin shawaran su, nan Khalil yaba da shawaran akai ta Abroad tayi acan, cikin su babu wanda yanemi ja da maganar nasa tunda suna ganin shine yakawo ta gidan, don haka shi yafi iko da ita fiye da kowa, Mom CE ma tanemi ta hana, amma kuma ganin Nazeefan tana murna sai tasaka albarka kawai ta ɓame bakin ta Ƙasan Sudan Nazeefa ta zaɓa, domin tafi son fannin Islamic shi za ta karanta, su ma su Dad sai hakan yayi musu daɗi. Cikin ikon Allah aka fara mata shirye-shiryen tafiyan ta, Sameer ne akan komi har sai da komi ɗin ya kammala, sai kuma tafiyan ta nan da ɗan watanni kaɗan. *** **** **** ******* **** Yau su Halwa sun tashi da farin cikin haihuwar Hakima ne, wajen ƙarfe 10:00am. Suka shirya suka tafi gidan Sameer ɗin A lokacin ma tuni ƴan uwan Hakiman sun soma zuwa, kasancewar agida ta haihu, kuma lafiyan ta lau da ita da Babyn ta, wannan karon ma namiji ta haifa "Masha Allah". Abin da su Saleema suke ta faɗa kenan da suka ga yaron, sak Sameer basu da maraba, dayake shima Aamir ɗin Dadyn nasa yabiyo, sai yaron ya koma tamkar Aamir sanda yake ƙarami ( na kula jinin su shi da Khalil ƙarfi ne dashi lolx🥴) A can suka wuni suna ta hira, Abida ma ta shige cikin su ana tayi da ita, dayake yanzu ta ajiye batun soyyayyar Khalil agefe bare tayi kishi dasu, yanzu ma haka har ta fitar da mijin aure acikin waɗanda suke zuwa wajen ta, tunda tasan wanda take so ɗin ba samun sa zata yi ba, shiyasa tayi wa kanta faɗa, wata biyu masu zuwa zasu sha biki Har yanzu tana zaune agidan Hakiman ne, tunda iyayen su sun rasu, shine Hakima ta ɗauke ta, kuma Sameer cewa yayi shine zai mata auren. Sai dare Khalil yazo ya wuce dasu. To rayuwa dai haka taci gaba da tafiya, zaman su Halwa sai son BARKA, babu ruwan su da faɗa ko kishin juna, sun zama tamkar ƴan uwan juna ba kishi ne ya haɗa su ba, komi tare suke yi, shi kansa Khalil yana alfahari da samun su matsayin matan sa, babu abinda zai ce wa Allah sai godiya, farin ciki kullum sake wanzuwa yake yi agidan sa, ko wacce cikin su yana matuƙar ƙaunar ta kuma yana jin ta arai da magudanan jinin sa, babu ma wanda zai iya tantance wacce yafi so, sai dai shi Khalil ɗin yana ji aran sa yafi ƙaunar Halwa, a ganin sa fa. 🤣 An yi suna lafiya an gama lafiya, yaron yaci sunan mahaifin Hakima, Abdulrahman, zasu ringa ce masa Haneef. 𝐀𝐅𝐓𝐄𝐑 𝐎𝐍𝐄 𝐘𝐄𝐀𝐑 𝐀𝐆𝐎. A wannan shekaran abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da zamowar Halwa cikakkiyar Lauya, yau ta amshi certificate ɗin ta Ko wani masoyin ta yau yana taya ta farin ciki Don haka Khalil shi da kansa ya shirya mata gagaruman walima don faranta mata Kasancewar yanzu yayi sabon gini, zasu tashi a anguwan da suke zaune, ya tsara musu babban gida wanda ya ninka wanda suke ciki a yanzu, ko wacce da nata Part ɗin, sai dai kuma haɗe yake da babban Parlourn na su gaba ɗaya Saura kwana biyu su tare don haka ake ta faman shirye-shirye babu kama hannun yaro, tunda abun ya haɗe musu biyu ne, ga Waliman taya Halwa zama Barrister, ga kuma Waliman koma wa sabon gida. Babu abinda zasu ɗauka na tsohon gidan su, komi sabo aka sanya agidan Mom ita ta ɗaukar musu me gyaran jiki, don tana so su fito sosai, har gida ake bin su ana musu komi, an zana musu lalli me tsananin kyau, sai aka yarfa musu kitso wanda ya sake fito dasu ainun, idan ka gansu sai ka ɗauka sabbin amare ne, sabida duk abinda ake ma Amare ƴan gata an yi musu. A ranan tarewan suka koma can sabon gidan nasu, tare da ƴan uwa na kusa Zuwa ƙarfe 04:00 gidan ya cika maƙil da jama'a, su Mama da Baba ma duk sun hallara gidan, iyayen Haris ma sun zo, Zainab da ƙanwar Mijin ta har da mahaifiyar sa da Umman ta ma duk sun zo, su Zaituna ma sai da suka zo mata kara Ana fara taron su Halwa suka fito, duk kansu sun sha kyau cikin Milk ɗin Material me tsananin tsada, doguwar riga aka yi musu fitet gown, sai akayi kwalliya da ston masu ƙyalli, an yi musu Light makeup da ya ƙawata fuskar su, takalmin su da gyalen da suka yi Rolling duka kalan baƙi ne, sun yi kyau Masha Allah, ba ma zaka iya tantance wacce tafi ba a cikin su Ƙaramin cikin Halwa ya fito ɗass yayi mata kyau matuƙa, ga haske da tasake yi sosai sabida cikin Haka Husna da Ahmad su ma an shirya su, tubarakallah Masha Allah kowa ya gansu sai sun burge sa Mamy tunda ta hangi Husna ta ɗauke ta tana ta nan-nan da ita. An gudanar da taro lafiya an gama lafiya, kowa ya tafi da tarin ɗumbin kyaututtukan da aka raba Sai dai aka bar ma su aiki da gyara gidan Su ma su Saleema ciki suka shige, suka ɗaura alwala saboda kiran sallan magriba da aka yi, sallah suka yi suka cire kayan jikin su suka sauya da wani atamfa me ruwan kuka da ratsin ja da baƙi, ɗinkin riga da skert ne iri ɗaya komi da komi, parlour suka fito suka zauna suna hiran Waliman cike da nishaɗi Husna da Ahmad tuni barci ya ɗauke su, Dattijuwar matar da suka ɗauka me aikin su, ita tayi musu wanka ta shirya su a kayan barcin su ta kai su ɗakin su. Sai da aka kira sallan isha'i kafin suka tashi suka je suka gabatar suka sake dawowa. Shima Khalil ɗin be dawo cikin gidan ba sai da yayi sallan isha'i sannan ya shigo. . 𝚙𝚕𝚣 𝚜𝚑𝚊𝚛𝚎 𝚊𝚗𝚍 𝚟𝚘𝚝𝚒𝚗𝚐 [1/21, 1:38 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ 𝐁𝐀𝐑𝐑𝐈𝐒𝐓𝐄𝐑 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐊𝐇𝐀𝐋𝐈𝐋 ♠️ 𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔:✍️ 𝐵𝑦 𝐍𝐚𝐟𝐢𝐬𝐚𝐭 𝐈𝐬𝐦𝐚'𝐢𝐥 (𝐹𝑒𝑒𝑛𝑎ℎ 𝐽𝑖𝑘𝑎𝑟 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎) *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ 𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖 ®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓ 𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️ 𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈 \𝗙.𝗪.𝗔📚/ 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!!! 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑛𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑒 𝑚𝑎𝑘𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑑𝑎𝑚𝑎𝑟 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖𝑛 𝐵𝑟𝑟. 𝐼𝑏𝑟𝑎ℎ𝑖𝑚 𝐾ℎ𝑎𝑙𝑖𝑙, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑖𝑘𝑜𝑛 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑎𝑏𝑖𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑖 𝑎𝑚𝑓𝑎𝑛𝑖 𝐴𝑙'𝑢𝑚𝑚𝑎𝑛 𝑚𝑢, 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑒𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑛 𝑦𝑖 𝑎𝑐𝑖𝑘𝑖 𝑘𝑢𝑚𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑦𝑎𝑓𝑒 𝑚𝑖𝑛 𝐴𝑚𝑖𝑛 🤲 𝑦𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ. 𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔 𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 ƴ𝑎𝑛 𝑢𝑤𝑎𝑛𝑎 𝑚𝑢𝑠𝑢𝑙𝑚𝑎𝑖 𝑏𝑎𝑘𝑖 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗕𝗢𝗢𝗞 𝗧𝗪𝗢 . _______________________________ 𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 𝗧𝗵𝗶𝗿𝘁𝘆 𝗧𝗵𝗿𝗲𝗲 ________🎓 Kallon su yayi duk kan su kafin ya lumshe idanun sa ya buɗe yana zuba murmushi, hannun sa ya saka acikin aljihun sa ya ciro Keeys kana ya kalle su, batare da yace uffan ba, yaja hannayen su ko wacce ya saka mata keey ɗin, be bari sun yi magana ba yace da su "Keey ɗin mota ce, kyauta na a gare ku". Duk kan su ɗago keey ɗin suka yi suna murmushi cike da farin ciki, kafin kuma su rungume sa cikin tsagwaron murna suka soma masa godiya, Halwa har da hawayen ta Hannu yasaka kawai yana shafa kansu kana yace, "to ku tashi muje ku ga motan ko". Babu musu suka tashi suka fice, ai kuwa motocin sun bala'in burge su, ga su masu tsada ne daga gani, na Saleema green CE, ita kuma na Halwa fara, sai da duk kan su suka shiga ciki suka dudduba sai santi suke yi, duk da Saleema ba yau ta saba yin mota ba, but kyautar mijin nata sosai ya faranta mata, kuma ji take yi kamar ma bata taɓa yin mota ba sai akan wannan Shi Khalil ma dariya sukai ta bashi, ganin abun nasu yaƙi ci yaƙi cinye wa sai murnan santi suke masa, sai da ya ja hannun su suka yo ciki sannan suka haƙura. Dayake ranan a ɗakin Halwa yake, ai kuwa ranan yaga gata, sosai ta zage ta faranta masa rai Shi kansa yasan yau ya samu tukuici. Washe gari ma haka masu zuwa taya su murna sukai ta shigowa, musamman waɗanda suke cikin anguwan, da yamma kuma suka je nuna wa su Ummi motan nasu, Saleema ita ta tuƙa nata, shi kuma Khalil ya tuƙo na Halwa, tana zaune a gefen sa, sun jima agidan har magriba kafin su wuce gidan su Khalil ɗin, can kuwa sai wajen sha ɗayan dare suka baro gidan. Tun daga ranan kuma sai Khalil yake fita da Halwa koya mata motan, idan be samu time ba tare suke fita da Saleema tana koya mata, ahaka har aka shafe tsawon watanni biyu lokacin ta ƙware sosai, gashi ta soma aiki, duk da wajen aikin su ɗaya da Khalil, wani lokacin tare suke zuwa, bare ma yanzu da cikin ta yashiga watanni shida, so be barin ta tana tuƙi sosai, tare suke tafiya. Itama Saleema ya buɗe mata Chamis, a shagunan dake bakin layin anguwan su anan ya kama mata hayan ɗaya, duk idan zata tafi tare da Ahmad take tafiya, duk da yanzu yayi wayo sosai babu inda ba ya yawata wa da ƙafan sa, har magana ya soma, amma ba ta barin sa agida, sosai take ƙaunar yaron koda yaushe yana liƙe da ita, shiyasa ma har ƙyuya yake dashi, don be cika yarda da kowa ba sai ita. Yau ɗin kasancewar Asabar ne gaba ɗaya a cikin su babu wanda ya fita, suna zaune a Parlour duk kan su Khalil da Halwa suna zaune a ƙasa sun yi baja-baja da takardu, shi ke aikin ita kuma tana taya sa, yayinda Saleema ke kwance saman dogon kujera, ta ɗaura Ahmad a jikin ta dake barci, idanun ta a lumshe suke, jefi-jefi suke ɗan taɓa hira, Husna na can gefen dainning table da kayan wasan ta, ta baza su sai yi take yi tana surutun ta. Sosa kanta Halwa tayi da hannun da take riƙe da Bairo, sai kuma ta ɗan juya kai ta kalli Saleema tace mata "sis Wai yau naji ki so slowly ne, ko wani abun na damun ki?" Ɗan buɗe idanun ta tayi kaɗan kafin ta saki murmushi tace, "a'a babu abinda ke damuna, yau dai kasala nake ji wlh". Khalil dake faman aiki a Lapton yana jin su be saka musu baki ba, ahaka suka ci gaba da zaman, sai dai zuwa lokacin Saleema ta dena saka musu baki gaba ɗaya, numfashi kawai take sauke wa a hankali tana sake ƙanƙame Ahmad dake jikin ta, kwana biyu kenan da zuciyarta take mata zugi duk ta hana ta sukuni, sai dai bata ba da ƙofan da za'a gane wani abun na damun ta ba, don ba ta son ta tayar musu da hankali, sai ta mayar da hankalin ta kan shan maganin ta, sai dai yau gaba ɗaya jikin ta ya matsa mata tunda bata sha ba, har soma kumbura tayi wanda in ba kayi mata kallon ƙurilla ba; ba lallai kagane hakan ba Ci je leɓen ta tayi ahankali, kafin ta buɗe idanuwan ta da zuwa yanzu sun sauya kala, sun koma kore-kore, miƙe wa take ƙoƙarin yi jikin ta na rawa tana son zame Ahmad dake kanta Ɗago kai Halwa tayi ta kalle ta, sai kuma tayi saurin faɗin "sis meke damun ki ne wai? Lafiyan ki ƙalau kuwa?" Sai alokacin shima Khalil yaɗago kai jin tambayan da Halwa take mata, da alamun ruɗu a muryan ta, shima dai saurin tambayar Saleeman yasoma yi ganin yanda duk ta sauya lokaci ɗaya, gashi jikin ta sai rawa yake yi tana faman cije baki, miƙe wa yayi ya koma kan kujeran yana tallabo ta yasake cewa "lafiya kuwa meke damun ki? Ko wani waje na miki ciwo ne?" Murmushi tayi tana lumshe idanun ta kafin tace, "ban sha magani na bane yau, shine zan tashi in ɗauk.." Be bari ta dasa Aya ba yakatse ta da faɗin "ya salam! Meyasa to? Wannan ganganci ne ai". Sai yaja tsaki yana faɗin "nima bansan me ya hau kaina ba yau ɗin ban tambaye ki ba, tun safe ma baki sha ba ko?" Gyaɗa masa kai tayi kawai Kallon Halwa yayi ransa duk babu daɗi yace, "je ki ɗauko min maganin". Dasauri tatashi tana zare hannun ta da tariƙe na Saleeman, ɗakin ta tawuce ta ɗauko magani ta kawo masa, sai ta koma ta ɗauko ruwa cikin Fridge tasake dawowa ta miƙa masa Shi da kansa ya bata, sannan yace ta kwanta ta huta, idan anjima jikin babu daɗi sai su nufi asibiti Halwan ɗaukan Ahmad tayi tamayar dashi ɗaki, don Saleeman ta samu sake wa akan kujeran. Gaba ɗaya sauran wunin ranan sai suka yi a rashin walwala, musamman ma Halwa da duk motsin ta yana kan Saleeman, gwara-gwara Khalil ya fita gab da magriba, kuma be dawo gidan ba sai da akayi isha'i. Ita kuma Halwa taliya ta girka musu me sauƙi bayan ta idar da sallan magriba, zuwa lokacin ne Saleema ta tashi, duk hankalin Halwa kacokan yana kan ta sai tambayar ta take yi ko akwai inda yake mata ciwo? Komi ita take mata To dayake dama jikin dasauƙi, ita dai Saleema sai dai tabi ta da murmushi duk da har yanzu zuciyar ta be dena zugi da radaɗin da yake mata ba, har sanda Khalil ɗin yashigo gidan shima ya hau tambayan ta, sai dai yaji daɗin ganin ta wasai da lafiyan ta, don har hira suka koma suna yi, nan ne hankalin su ya ɗan kwanta. Washe gari Sunday har yamma Saleema lafiyan ta ƙalau, domin a ranan ma tafi samun lafiya fiye da jiya, sai dai da dare jiki yaƙi daɗi dole suka dangana ga asibiti. Duk wani makusantan su tun a daren tuni yaji labarin rashin lafiyan ta, su Ummi duk sun hallara asibitin hankalin su duk a tashe, musamman yanda suka ga likitocin sai kai komo suke yi a ɗakin da aka kwantar da Saleeman, kuma sun ƙi ce musu uffan bare su san meke wakana. Zuwa goman dare, lokacin wajen awanni uku da shigar da saleema sannan likitan ta ya nemi ganin su, gaba ɗaya suka ɗunguma wajen su, doctor ɗin be musu wata ƙwaƙƙwaran bayani ba, illa kwantar musu da hankali da yayi, sannan ya faɗa musu baza su samu ganin ta ba har sai gobe. Zuwa lokacin Halwa tasha kuka kamar zata ƙarar da hawayen ta, da zasu tafi gida cewa tayi babu inda zata je, daƙyar su Ummi suka lallaɓa ta suka koma gida har Khalil ɗin aka bar Ummi ita kaɗai, tunda su ma su Abba duk sun dawo, kowa ya tafi da fargaba a halin da Saleema take ciki. Zuwa washe gari tuni duk sun hallara, har lokacin dai babu wani labari daga wajen doctors, sai daga baya tukun Doctorn ya nemi gana wa dasu, dalla-dalla yayi musu bayani Zuciyarta ta rigada ta gama kumbura har ta kai matakin da dole sai dai ko ayi mata Theater da gaggawa a cire mata a sauya mata, ko kuma tarasa ranta domin ya daina aiki gaba ɗaya Babu wanda be girgiza ba da jin wannan zance, amma ya suka iya da ikon Allah? Tuni anyi cuku-cukun yanda za'a samu ayi mata aikin a cikin kwana biyu, Abroad za a fitar da ita Sai dai kuma Allah shi yafi su ƙaunar ta, a kwana na uku ranan da ake saka ran tafiya da ita, a ranan Allah ya amshi abun sa, Saleema ta amsa kiran Allah batare da ta sake shaƙan numfashin duniya ba, tunda tun lokacin da aka kawo ta komi na jikin ta ya dena aiki sai da na'ura. Musalta muku yanda Familyn nan suka shiga ɓata lokaci ne, domin dai alƙalami na bazai iya muku bayanin tashin hankali da ruɗun da suka kasance ba, tun a asibitin ma Halwa da Ummi suka zube ƙasa a sume, shi kansa Khalil sai da jiri ya ɗibe sa aka kwantar dashi, ga dai shi idanun sa biyu sai dai komi nasa ya dena motsi har sai da yayi kusan awanni biyu ahaka, (ma'ana yayi suman Ido buɗe ne) sosai mutuwar ta shige sa, tabbas kuka rahma ne ga bawan da yashiga ruɗin rayuwa, sai dai Khalil ya kasa samun hawayen da zai zubar don yaji daɗi da salama a zuciyar sa, wannan dalili ne yasaka zuciyar sa tayi masa nauyi fiye da tunanin mutum, be iya ma buɗe baki yayi magana kawai ya zama tamkar status ne Itama Ummi an yi Sa'a ta farka tun a time ɗin, shi kam Abba dauriya kawai ya ara ya yafa wa kansa, but duk da haka sai da yayi ta sharan hawaye sabida ya kasa jurewa. Halwa dai bata farka ba har aka kai Saleema gidan ta na gaskiya, mugun hawa jinin ta yayi, kasancewar tana da hawan jini tun lokacin cikin Ahmad da aka harbi Khalil, bata farka ba sai a washe gari, sai dai duk wanda yake ɗakin a lokacin dole ne ya zubar da hawaye sabida tausayin ta, sai da Nurse suka yi mata alluran barci kafin suka samu sukuni, Dattijuwa me aikin su ita aka bari a wajen ta, tunda duk sun tafi gida karɓan gaisuwa Sai a daren ranan ne Khalil yasha kukan sa ma'ishi, tare da raya daren don nema wa Saleema gafara wajen Allah Sarki, a zaune ya kwana a ranan, kuma koda safe be samu yayi barci ba ya tafi asibiti ganin lafiyan Halwa, bata farka ba alokacin, sai ya nufi gidan su Saleema inda anan ne ake karɓan gaisuwa. Sai da yamma ne aka faɗa musu ta farka, dole suka ɗunguma zuwa wajen ta A kwana biyu kawai ta fita hayyacin ta, ga ciki da take fama dashi, gashi kuma ba'a son masu irin laluran ta da tashin hankali, amma ya aka iya, sai dai kwantar mata da hankali kawai da suke tayi tare da mata nasiha me ratsa zuciya, da kuma nuna mata yin tawakkali ga duk wani ƙaddara da yasame mu, Mom CE me ƙarfin halin mata wannan maganan, don ita Ummi ma tana gida ba da ita aka zo ba Sai dai Halwa ta kasa barin kukan, domin ko tayi yunƙurin dena wa, da zaran ta tuna Saleema ce ta rasu sai kukan ta yadawo sabo, an yi rarrashin duniya taƙi yin shiru, dole suka zuba wa sarautar Allah ido, duk idan kukan nata ya dawo yi take yi kawai babu me tsayar da ita, sai idan ta gaji don kanta sai tayi shiru anjima ta sake dasa wa, gaba ɗaya duk ta ya mutse ta saka wa kanta ciwo na ƙarfi da yaji, domin dai sai da tayi wajen sati ɗaya a asibitin kafin a sallame ta, ga hawan jinin ta da yaƙi sauka, likitoci sun yi mata maganar hakan zai iya shafan lafiyan ta da abinda ke cikin ta amma taƙi sauraron su. Tunda suka koma gida ma babu lafiya, haka rayuwan taci gaba da Gara mata yau ciwo gobe lafiya, Khalil haka yake fama da ita ko kaɗan ba ya gajiya da mata hidima, duk wani farin ciki dake gidan nan nasu yanzu babu, rasa Saleema cikin rayuwan su ba ƙaramin giɓi yay musu ba, idan kashiga gidan sai dai kaji shiru ko motsin kirki ba sa yi Su Husna sai dai me aikin su ke kula dasu, ita take musu komi. Daga baya ma Mom zuwa tayi ta tafi da Halwan gidan ta, tunda sosai take jin jiki, kullum cikin ciwo take Shima Khalil can yake wuni idan ya je aiki ya dawo, aikin ma ba kullum yake zuwa ba, saboda shima har yanzu ya kasa dawo da kuzarin sa, ya kasa manta Saleema a ransa, baya iya taɓuka komi. Ahaka rayuwan taci gaba da tafiya har sanda cikin Halwa ya shiga watan haihuwa, lokacin ma tuni tana asibiti saboda yanda takoma sai kun tausaya mata, gaba ɗaya ta kumbure tayi suntum kamar ba ita ba, cikin yayi girma sosai har ba ta iya ma tafiya Lokacin da tasoma naƙuda an ma fid da ran zata iya rayuwa, domin kwanan ta biyu tana a halin ciwon naƙuda, gashi hawan jinin ta yayi mugun hawa Likitoci sun yi iya yin su amma ta kasa haihuwa da kanta, tunda jinin ta ya kai matakin da baza ta iya haihuwan ba, kuma komi zai iya faruwa da ita Ganin idan taci gaba da zama ahaka zata iya rasa ranta dole aka shirya yin mata CS, ahaka aka shigar da ita ɗakin Theater bata ma san a inda kanta yake ba. Khalil yasha kuka sabida tausayin matar sa, daƙyar ma ya iya saka hannu da za'a yi mata CS ɗin, dole Sameer da Brr. Tahir sukai ta tausan sa suna ba sa baki, su ma duk hankalin su a tashe, kowa yayi jugun ana jiran abinda hali zai yi. Alhmadulillah an samu nasaran ciro wa Halwa yara biyu duk ka maza, kuma duk ka yaran suna a cikin ƙoshin lafiya, sai dai Mahaifiyar su ne da akayi zaton ta mutu ma, sai da likitocin suka yi iya yin su kafin suka gane tana da rai, Oxgyen suka saka mata sannan suka fito da yaran suka yi musu albishir da samun ƙaruwar twins Sun yi murna sosai duk da suna cikin damuwa da halin da aka sanar musu Halwa na ciki, Khalil kawai aka bari ma yashiga wajen ta Tunda ya shiga idanun sa na kanta, hawaye ne kawai suke kwaranya a saman kuncin sa, yana saka hannu yana share wa cike da raunin zuciya, ganin yanda Halwan nasa ta koma tamkar ba ita ba, har wani baƙi tayi sabida tsaban rame wa, tamkar ba ita ce wacce ta kumbura tayi himm ba, amma yanzu lokaci ɗaya ta zabge tamkar ba ita ba A hankali ya taka ya isa gaban gadon, a ƙasa ya ajiye gwiwowin sa yana tura hannun sa cikin tafin hannun ta da aka saka mata Drip, damƙe hannun yayi sosai kafin ya ɗaura kansa saman cikin ta yana ci gaba da hawaye, hawayen tausayin ta, gaba ɗaya zuciyar sa ta gama rauni, bazai iya juran itama ya rasa ta ba, taya zai iya rayuwa idan ta tafi? Ɗago kansa yayi yana kallon fuskarta, cikin sanyin murya yace, "Ina ƙaunar ki Halwa, don Allah.. kar ki tafi kema ki bar Ni, wlh idan na rasa ku duka zuciyata bugawa zata yi, don Allah kiyi haƙuri ki tashi, ki tashi mu raini ƴaƴan mu da Allah yayi mana kyautan su, kinji ki tashi don ALLAH.." Dole yayi shiru sabida kukan da yataho masa, sai ya sake ɗaura kansa saman jikin ta yana ci gaba da tsiyayar da hawaye, sosai yake ji a jikin sa itama zata tafi ne Yanda hawayen sa ke zuba ajikin ta hakan yasa take jin sanyin har cikin fatar ta, wannan dalilin ne yasa tafarka a time ɗin, idanuwan ta kaɗai ta buɗe tana bin ɗakin da kallo, tsawon sokonni kafin tagane akwai mutum kusa da ita, sai kuma daga baya ta fahimci Khalil ne, hakan yasa taɗago ɗayan hannun ta ahankali ta aza a kansa Cakk ya tsai da kukan nasa yana ɗago kai dasaurin sa, nan idanun sa suka faɗa cikin nata da suka ƙanƙance suke a lumshe, daƙyar ma take iya buɗe su sabida halin ciwo Be san sanda ya washe baki ba yana ta faɗin Alhamadulillah... 𝗧𝗢 𝗯𝗲 𝗰𝗼𝗻𝘁𝗶𝗻𝘂𝗲..✍️ _Nima ALHMADULILLAH anan na kawo karshen book ɗin 𝐁𝐑𝐑. 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐊𝐇𝐀𝐋𝐈𝐋, abun da na rubuta daidai Allah ya amfanar damu, kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min._ 𝑎𝑚𝑖𝑛 𝐼𝑛𝑎 𝑚𝑎 𝑚𝑎𝑠𝑜𝑦𝑎𝑛𝑎 𝑓𝑎𝑡𝑎𝑛 𝑎𝑙𝑘ℎ𝑎𝑖𝑟𝑖, 𝑠𝑎𝑘𝑜𝑛 𝑘𝑢 𝑚𝑎𝑠𝑜𝑦𝑎 𝑦𝑎 𝑖𝑠𝑜 𝑔𝑎𝑟𝑒 𝑛𝑖 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑏𝑎𝑟 𝑧𝑢𝑚𝑢𝑛𝑐𝑖 𝑛𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑒 𝑘𝑤𝑎𝑟𝑎𝑖 𝐽𝑖𝑛𝑗𝑖𝑛𝑎 𝑎𝑔𝑎𝑟𝑒 𝑘𝑖 𝐒𝐇𝐔𝐆𝐀𝐁𝐀 𝐒𝐀𝐅𝐍𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔 𝐉𝐀𝐖𝐀𝐁𝐈, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑘𝑎𝑟𝑎 𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑘𝑎 𝑘𝑖, 𝑦𝑎 𝑘𝑎𝑟𝑒 𝑘𝑖 𝑎 𝑑𝑢𝑘 𝑖𝑛𝑑𝑎 𝑘𝑖𝑘𝑒, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎𝑠𝑎 𝑘𝑖 𝑓𝑖 ℎ𝑎𝑘𝑎, 𝑓𝑎𝑡𝑎𝑛 𝑎𝑙𝑘ℎ𝑎𝑖𝑟𝑖 𝑘𝑎𝑤𝑎𝑖 𝑧𝑎𝑚𝑢 𝑟𝑖𝑘𝑎 𝑚𝑖𝑘𝑖 ℎ𝑎𝑟 𝑚𝑢 𝑘𝑜𝑚𝑎 𝑔𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑏𝑎 𝑘𝑢𝐧𝑔𝑖𝑦𝑎𝑟 𝑘𝑖 𝑛𝑎 𝐏𝐞𝐫𝐟𝐞𝐜𝐭 𝐖𝐫𝐢𝐭𝐞𝐫'𝐬 𝑛𝑎𝑠𝑎𝑟𝑎, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑠𝑎𝑘𝑒 𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑘𝑎 𝑠𝑎 𝑓𝑖𝑦𝑒 𝑑𝑎 𝑛𝑎 𝑦𝑎𝑛𝑧𝑢 𝑎𝑚𝑖𝑛. 𝑩𝒊𝒔𝒔𝒂𝒍𝒂𝒎 𝒎𝒂𝒔𝒐𝒚𝒂🤝, 𝒌𝒖 𝒕𝒔𝒖𝒎𝒂𝒚𝒆 𝒏𝒊 𝒂 𝒔𝒂𝒃𝒐𝒏 𝒃𝒐𝒐𝒌 𝒅𝒊𝒏𝒂 𝐑𝐀𝐔𝐃𝐇𝐀 𝒏𝒂𝒏 𝒃𝒂 𝒅𝒂 𝒋𝒊𝒎𝒂 𝒘𝒂 𝒃𝒂. 🥰😍👌 𝐉𝐢𝐤𝐚𝐫 𝐋𝐚𝐰𝐚𝐥𝐢 𝐜𝐞 𝐭𝐚𝐤𝐮 𝐦𝐞 𝐤𝐚𝐮𝐧𝐚𝐫 𝐤𝐮...❤️ 𝕃𝕠𝕧𝕖 𝕪𝕠𝕦 𝕗𝕒𝕟𝕤.