[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *DA sunan Allah mai rahma mai jin kai tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad sallallahu alaihi Wa sallam, da Ahlayensa da sahabbansa masu girma* *Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, mai kowa mai komai da ya bani ikon rubuta wannan dan karamin labari, ina addu'ar Allah ya amfanar da mu abinda yake cikinsa na karuwa, abinda yake na kuskure Allah ya gafarta mana* *wannan labari kirkirarren labari ne an yi shi ne ba don cin mutuncin kowa ba* *gargadi ban yarda a canja min wannan littafi ta kowace irin siga ba, sai da ixnina* *wannan shi ne littafina na farko da na fara rubutawa da fatan xa yi min uxuri idan nayi kuskure*🙏 *Ya Allah kamar yadda na fara wannan rubutu lafiya Allah kasa na gama lpy, Allahu kareni daga sharrin masu sharri*👏🏻👏🏻 *wannan shafin gaba dayanshi sadaukarwa ne gareki yar uwa aminiya kuma Takwara Maijidda bello ana tare🤝💯* 1⃣➖5⃣ *T*afiya take cikin nutsuwa, amma kallo d'aya xaka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin matsananciyar damuwa" yarinya ce 'yar kimanin shekara sha biyar d'auke da buhun bacco a hannunta, tafiya kawai take ba tare da tasan ina ta dosa ba. bakin wata bishiyar darbejiya ta samu ta d'an tsaya domin ta samu hutu ko xuciyarta ta sarara daga tafasar da take yi mata. a hankali ta saukar da ajiyar xuciya sa'annan tayi duba i xuwa jakar da kayanta ke ciki. nan da nan idanuwata suka cika fal da hawaye, ta fad'a a ranta *ALLAH KA FINI SANIN HALIN DA NAKE CIKI* kuka mai tsanani ta cigaba da yi kanta na sunkuye a jikin jakarta, da taga ba sarki sai Allah kukan ba xai kaita ba, sai ta yanke shawarar cigaba da tafiya, duk da dai ba ta ji a ranta xata iya cigaba da tafiyar, saboda yunwa da kishiruwar da suka addabeta. a hankali ta cigaba da jan 'kafa cikin 'karfin hali har ta isa i xuwa wajen da mutane suke, ta samu gefen wajen ta ajiye jakar da 'yan *tsummokaranta* suke ciki. ta 'karasa wajen da wata mai abinci take, da xuwanta sai taga idanun mutane duk sun dawo kanta, cikin hanxari mutanen suka tashi a guje, ciki kuwa har da mai abincin, ashe bisa tsammaninsu suna zaton *MAHAUKACIYA CE* d'aya daga cikinsu ne kawai ya yi 'karfin hali ya'ki guduwa, cikin zafin rai yake tambayarta "ke me kike bukata a nan"??? cikin rawar murya ta amsa masa da cewa "ni *AL-MAJIRAH* ce sadakar abinci ko kudi nake son ku taimaka min dashi tun safe babu abinda nasa a bakina. tsawa ya daka mata wanda yasa har sai da ta firgita "ina ruwanmu da almajirancinki nauyin ciyar da ke a kanmu yake, mu muka sa iyayenki su kawoki bara su wulakanta baiwar da Allah ya basu?? kauce min da gani kafin na doka ball da ke" bata san lokacin da hawaye masu xafi suka rufe idonta ba har ya xamto bata iya ganin hanya, jiri taji ya d'ebeta kamar xata fad'i, Allah dai ya kiyayeta bata fad'i ba. lallai wasu mutanen ba su da tausayi, ta fad'i hakan a ranta. wucewa ta yi kai tsaye wajen da ta ajiye kayanta, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da kuka mai cike da ban tausayi, *KOWANE BAWA DA IRIN YADDA ALLAH YA TSARA MASA RAYUWA* Ni kuma irin tawa jarrabawar kenan ya Allah ka bani ikon cin wannan jarabawa. daukan jakar kayan tayi ta cigaba da tafiya, tana tafiyar tana addu'ar Allah yasa ta samu ko naira goma ne, ta siya abinci su samu abinda xasu kai bakin salati ita da mahaifiyarta, addu'a ta cigaba da yi Allah ya had'ata da wadanda xasu tausaya mata su bata ko da ruwa ne tasha ta ji sanyi a ranta. ranar da ta kara takewa ne yasa ta yanke shawarar tsayawa gudun kada xafin ranar ya cutar da ita, idan rana tayi sanyi ta cigaba daga inda ta tsaya. idan kuma mutane sun gaxa taimaka mata ta siyar da yan tsummokaranta su ci abinci ita da mahaifiyarta bakin wata rumfar mai gyaran takalmi ta samu, tana isowa wajen mai gyaran ya mai da hankali da kallonshi gareta, karasowarta ke da wuya ya mike tsaye ya kasa ko da motsawa, a tuninshi mahaukaciya ce saboda yanayin shigarta da yanayin kayan da suke jikinta ga shi kafarta ko takalmi babu ga kuma jakar tsummokarai a tare da ita . sallamar da tayi masa ita ce ta katse shi daga tunanin da yake yi. har kasa ta tsugunnah "ina yini tace masa" da sauri ya amsa da lafiya" me kike so lafiya?? tace "taimako nake nema yunwa nake ji ka taimaka min dan Allah. har da guntun hawayenta. tunani ya shiga yi. "tabbas wannan yarinyar ba mahaukaciya bace kamar yadda nake tsammani, amma dai duk yadda aka yi yarinyar nan tana cikin matsala, amma ba yadda na iya haka xan kyaleta, watakila iyayenta ne basu shuka alheri ba tunda na ganta a haka, ko kuma guduwa tayi daga gaban iyayenta. amma wane laifi xaka yi wa Allah ya wulakantaka haka, da walakin dai goro a miya (ya manta da cewa Allah shi ne mai tsarawa bawansa rayuwa) maganar da tayi masa "malam nace taimako nake nema" ita ce ta katse masa tunanin da yake yi. ya juyo ya kalleta "nace Allah ya bada hakuri ko ana sadaka dole ne iye"? juyawa tayi da niyyar barin wajen sai taga bai kamata ta cigaba da tafiya a tsananin ranar da ake yi ba, sake tsugunnawa tayi ta roke shi da ya barta ta dan huta idan rana tayi sanyi ta cigaba da tafiya. ranshi bai so ba ya kyaleta ta xauna, saboda a tunaninshi duk wani mai xuwa ya kawo gyara xai tsorata yaki kawowa idan ya ganta. "komawa gefe tayi ta raku6e jikin bango, kamar wadda take shirin tashi a guje, babu abinda zuciyarta ke saqa mata sai yanayin kunci da yanayin da rayuwarta ta shiga ita da mahaifiyarta, idan har rayuwarsu ta cigaba da kasancewa a haka, tasan duk abinda take gudu akwai yiwuwar ya sameta, kiran sallah ne ya katse mata tunanin da take yi, tashi tayi ta nufi wajen mai gyaran nan ta ro'ke shi da ya taimaka mata da ruwan da xa tayi *Alwala* ba musu ya mika mata buta, risinawa tayi cikin ladabi ta karbi butar, ta nufi bakin kwata tahbb tsugunnah ta fara alwalar har ta idar. yadda take jero addu'oin kammala alwala, shi ne ya bawa mai gyaran mamaki, a xuciyarsa ya fada "ikon Allah duk da talauci da damuwar da yarinyar nan take ciki bata fasa neman ilimin sanin lahirarta ba, lallai dole ne na mayar da hankali wajen barin yayana su nemi ilimi saboda halin rayuwa" tana idar da addu'ar ta nufi inda xa tayi sallah ta shimfida dan kwalinta ta hau yin sallah cikin nutsuwa, ta dau lokaci tana yin sallar bayan ta idar tayi addu'a sannan ta shafa............... bayan ta ninke d'an kwalinta sai ta dawo ta zauna ta cigaba da tunanin rayuwa da yadda ta juya musu baya, da mai gyaran takalmin yaga ba tada niyyar tashi ta tafi sai ya kira sunanta "ke *AL-MAJIRAH* karbi naira10 kya sayi abinci tasa hannu biyu ta durkusa har kasa tayi masa godiya mai yawa saboda ko ba komai ta samu kudin da zata siya wa Amminta koda kunu ne. tashi tayi tayi ta cigaba da tafiya tana tafe tana neman taimakon al'umma, masu tausayi sukan taimaka mata, wasu kuma kallonta kawai suke yi ko hakuri basa iya bata a haka har Allah yasa ta sami naira 100 . samun da ta yi ba karamin farin ciki tayi ba, da kudin ta samu ta siya musu abinci ita da Amminta na naira50 kunun 20 sannan ta sayi panadol na naira10 ta juya cikin jindadin samun abincin da ta yi . tana kusanto bakin kangon da suke kwana, yara ta gani cike da bakin kofa, suna jifa da dutse suna tsokanar mahaifiyarta *"mahaukaciya yar macikule"*.......... *mai kwana a bola*.......... *mahaukaciya yar macikule* ...........hawaye ne masu xafi suka kufce mata, bata san lokacin da rufe yaran da duka ba. ganin fusatar da tayi yasa suka fara guduwa, sannan ta kyalesu ta shiga ciki ta rufe kofa. Da sallama ta shiga kangon da suke kwana ita da Amminta hango mahaifiyar tata tayi cikin kaxanta tayi kaca-kaca da wajen da kashin da tayi, har tana kokarin saka kashin a bakinta xa ta ci.. da hanxari ta karasa wajen da take, tana isowa kusa da ita ta bushe da wata irin dariya ta kawo mata duka da hannu, ta jefeta da dutsen da yake kusa da ita. da sauri ta kauce dutsen ya sauka kasa, ta samu ruwa ta wanke mata hannunta da bakinta. shimfida taje tayi mata ta dakkota ta dorata a kan cinyarta ta tallafota tana mata sannu bakinta ta fara kuskure mata sannan ta fara shayar da ita kunun har sai da taga alamar ya isheta, sannan ta hau bata abincin loma biyu kawai tayi ta nuna alamar ya isheta sai ta kyaleta sannan ta goge mata bakinta da wani kyalle. sai *AL-MAJIRAH* ta dauki sauran ta cinye tana ci tana hawaye tana tuna halin da suke ciki ita da Amminta amma nasan babu komai dukkan tsanani yana tare da sauki. *jeeddahtukhaeer*😘😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 _*dedication to the intended*_ *Mustapha Mukhtar*😘 *Godiya ta musamman gareki yar uwa rabin jiki Maryam Tijjani Adam* 6⃣➖7⃣ *S*ai ta d'auki naira 20 d'in da ta yi mata saura ta 'kulle a gefen zaninta, tana tuna duk wahalar nan da suke sha na rashin abinci da suttura, ya samo asali ne saboda *kaddarar da Allah ya d'ora musu* da taga yawan damuwar da take yi, yana 'ko'karin ya illata mata xuciyarta da tunaninta, sai ta mayar da komai gefe ta manta da duk wata damuwa, saboda tasan akwai Allah kuma yana sane da bayinsa. "Labari ta shiga bai wa mahaifiyar tata, duk da dai tasan ba fahimta take yi ba, saboda raunin hankalin da take dashi, tana bata labarin sai ta kwashe da dariya kamar tana fahimta, wasu lokutan kuma ta tofa mata miyau ta kai mata duka da 'kafa, a haka tun tana bata labarin har ta gaji tayi shiru. jikinta taji ba 'kwari ta yanke shawarar kwanciya saboda gajiyar da tayi wajen nemo musu abinci, ga shi tana jin alamar ciwon kai saboda ranar da ta wuni tana yawo a cikinta. "A dabarance ta sauke kan mahaifiyarta daga cinyarta ta samu ledar kayanta tayi mata pillow da shi, ita kuma ta qara gyara kwalin da suke xaune ta kwanta. bata fi minti biyar ba bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita, turo 'kofar kangon da aka yi ne ya farkar da ita, yarinya ce matashiya yar kimanin shekara ashirin da biyu ta shigo, hannunta ri'ke da kwano da kuma ba'kar leda. A hankali take sand'ar shigowa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, kasa karasowa tayi ta tsaya daga baya don gudun kada *mahaukaciya*ta biyota. kallon kangon ta shiga yi taga babu komai a ciki sai tarin bola da duwatsu, mamaki ne ya kamata ganin yadda suke kwance cikin 'kazanta ba tare da wata shimfidar kirki ba sai kwali. "yanxu d'an Adam wanda Allah da kansa yace mun karrama shi,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, shi ne yake rayuwa a cikin kango kuma kan bola, lallai rayuwa abar tsoro ce" ta fadi haka ne a xuciyarta amma bata sani ba tuni maganar ta fito fili, ganin irin yadda AL-MAJIRA ta tsura mata ido,yasa ta ajiye kwanon abincin da ledar ta fita a guje, a tunaninta tashi xa tayi ta daketa. fitarta ke da wuya ta tashi taje wajen da kayan suke, ta shiga bud'e kwanon abincin, sa taga shinkafa ce da mai da yaji aka kawo musu, ledar kuma kayan sawa ne kala biyu a ciki, da murnarta ta d'auki kwanon ta nufi mahaifiyarta da shi "Ammi kin ga abinda aka kawo mana" ko kallonta bata yi ba, ta cigaba da d'aura leda a 'kafarta tana wasa da yan yatsunta. "Ammi nace kinga an kawo mana abinci da kaya kiyi dariya dan Allah kice kin gode" nan ma dai kallonta ta cigaba da yi kawai, da ta gaji ta mike ta koma ta xauna. A yanxu babu abinda ya fi damunta sama da haukan da Amminta ke yi, ga shi ko magana bata yi ballantana ta samu su rika hira tana bata amsa ko da ta shirme ce, a haka tasan dole xata ri'ka jin saukin damuwarta, kuma xata debe mata kewa. ga shi a yanxu ko maganar tayi mata sai dai duka, da tofa miyau ya biyo baya. "baxan gushe ba ina kulawa da ke har Allah ya karbi rayuwata" ta fadi haka tana shashsheqar kuka". hawaye biyu-biyu ne suka rika bin fusarta tana sharewa, ha'ki'ka a yanxu yadda take ji, babu wani d'an Adam da ya kaita matsala a rayuwar duniya, ta 'kosa Allah ya karbi rayuwarta ta huta da qangin wahalar da suke ciki ita da *Amminta* tasan ba ta kowa ba tada komai, don haka ta gwammace mutuwa watakila idan ta dace sai taji dadi a lahira. kiran sallar magrib ne ya tashe ta tayi alwala, ta tada sallah tana idarwa ta dauki ruwan alwalar taje don ta yi wa Amminta, amma ga mamakinta sai taji tana wani irin gunji alamun bata son ta kusanto da ruwan alwalar gareta. a jiye robar alwalar tayi ta karasa kusa da ita tana xubar da kwallah, Ammina ki tashi nayi miki alwala lokacin sallah ya yi. tureta baya tayi ta fada kan duwatsun da ke wajen, sannan ta cigaba da gunjin nata mai ban tsoro. rushewa da kukan da yarinyar tayi yasa ta tallafota, tana shafa bayanta alamar tana nuna tayi shiru, tausayin mahaifiyarta ne ya kamata, yanxu a ce yadda Ammi take da ibada da son addini yau ita take dukana a kan baxa ta yi sallah ba. kukanta ne ya tsananta ta cigaba da rokon Allah ya bawa mahaifiyarta lafiya, da dukkan masu fama da lalura irin tata. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *dedication to you my lovely Aunty, sumayya Abubakar ishaq*😘 *gaisuwa gareki yar uwar arxiki kareemah Tijjani Adam* *Allah ya rayaki mu sha biki* 8⃣➖9⃣ "A wannan daren gaba d'aya basu rintsa ba saboda ciwon Amminta da ya kara tsananta, ba abinda take yi banda gunji da buge-buge a haka suka kasance har Allah ya wayi garinsa. da sanyin safiya ta fita don ta samo musu ruwan da xa su yi alwala, sannan ta samu wanda xata wanke mahaifiyarta da shi. fita tayi waje sannan ta kulle kofar kangon, tafiya kadan tayi ta tarar da wani burtsatsai ta tsaya ta debi ruwan ta dawo masaukin da suke, ba tare da bata lokaci ba ta fara alwala, ta nemi Amminta tayi, yau ma kin yi alwalar tayi don haka ta kyaleta, ta tafi don yin sallah. bayan ta idar da sallar tayi addu'o'i sannan ta matso wajen Amminta don ta tsaftace ta daga dattin da tayi, da kyar ta bari tayi mata wankan, ta canja mata kayan da aka kawo musu sadaka jiya. sai da ta nutsu sannan ta fara tunanin yau kuma ina xata dosa don nemar musu abinci, ta fuskanci yau Amminta a yunwace take, don duk abinda ta gani kusa da ita kokari take ta kai bakinta, don haka yau ma ta yanke shawarar kulle kangon ta fita neman abin karin kumallon safe. "tashi tayi don ta fita, cikin hanzari Amminta ta riqo kafarta alamar ba inda xata je, sai ta koma ta xauna ta fara rera mata wakar da take mata tun tana yar shekara 8, tana rera mata wakar tana dariya, a haka har ta saki jiki da ita ta sakar mata kafarta. fakar idonta tayi ta fice da sauri, har ta kai bakin kofa tana cigaba da wani gunji alamun ta dawo take nufi, amma babu yadda xa tayi haka ta kulle kangon ta fita ta barta, haka ta cigaba da dukan kofar har tayi nisa tana jin sautin bugun da take yi. "sauri ta rika yi a tafiyar saboda tana tsoron kada yunwa ta ishi Amminta ta fara cikin kaxanta, wani mutum ta iske yara a kewaye dashi yana musu sadakar waina, sauri ta rika yi ta karasa wajen, sai dai kash!!! tana karasawa wajen har ya gama sadakar sai hakuri ya bata. juyawa tayi zuciyarta cike da 6acin rai da damuwa, sauri ta cigaba da yi, tana tafiyar tana hadawa da addua Allah ya dubeta ya bata abincin da xata samu ta ci. tuwon dawa taci karo da shi a hanya da alama *AL-MAJIRAI* ne suka yar da shi, da fara'arta ta karasa wajen da yake ta dauka ta karkade kasar jikinshi ta samu leda ta nade tuwon da shi. bakin wani famfo ta samu ta fara wanke tuwon sannan ta karasa wani kanti ta sayi sugar da leda, hanyar komawa gida ta nufa, tana tafe tana godiya ga Allah da ya bata abinci ba tare da ta sha wahala ba. "tura kofar kangon tayi, yau ma da sallama ta shiga, Ammi na ganinta ta taso da farin ciki, tana mata murmushi, ita ma murmushin ta hau yi mata, rikota tayi ta xaunar da ita akan kwalin. *"Ammi yau tuwo xamu sha, kina so ko"*? ishara tayi mata da kanta alamar eh tana son sha. saka tuwon tayi a leda ta fara dama shi da ruwa sannan ta zuba sugar, cikin nutsuwa take bata tana sha, a haka har sai da ta shanye gaba daya, ita kuma sai ta side ledar ta sha ruwa. "A haka suka kasance har zuwa sallar azahar, bayan tayi sallah, ta yanke shawarar sake fita don ta nemo abincin rana da na dare, yanxu ma sai satar hanya tayi ta fita ba a son ran mahaifiyarta ba. yau kai tsaye kasuwa ta nufa, don tana da yaqinin anan sai tafi samun taimako, rumfar kasuwar ta rika lekawa tana neman taimako, yau kam ta fita a sa'a don abinda ta samu ya kusa 500, don haka ta tsaya ta siya kwaki da sugar da sabulun wanka. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Gaisuwa ce ta musamman nake mikowa gareki, yar uwa babbar yaya gareni Hajiya Ameena Basheer (Maman siyama) Allah ya raya, Sadeeq, siyama, saudah, safiyya & suhaila, ina godiya da kulawarki gareni, ana tare🤝💯* *wannan shafin gaba dayanshi naki ne halak malak Dr. Aysha Abubakar ishaq, ina godiya da kulawarki gareni, Allah ya bar zumunci* 🤝 🔟 *T*ana dawo wa kangon da suke kwana ta nufa, da sallama ta shiga ta iske Amminta na wasa da kasa tana ganin yartata sai ta saki dariya da alamar murna da farin cikin ganin d'iyarta ta, 'karasawa wajenta tayi ta rungumeta "Ammi kin san yau me muka samu kuwa?? kwaki na samo mana..... ai kina son shi ko Ammina? kallonta kawai take ba tare da tace mata komai ba, sai murmushi da take yi, tana wasa da 'yan yatsun d'iyartata, kallo take mata mai cike da soyayya da tausayi, sai dai babu bakin magana ballantana ta gode mata. "cikin nutsuwa ta janye hannunta gareta, kallonta tayi tana mata murmushi. Ammina xan fara wanke mana kaya sai na jika mana kwakin kin ji, ita dai bin ta tayi da ido kawai. "tana mi'kewa ta ri'ke mata hannu gam ta'ki sakinta, sai ta koma ta xauna. "Ammina ba kya son na tafi na barki ko?nima bana son nisa da ke, dole ce ta sa nake tafiya na barki. murmushi mahaifiyar take yi tana shafa kan yarinyar tata, tausayin *Amminta*ne ya kara kamata, ji take a ranta ina ma dai ta rika d'aukanta suna tafiya, sai dai ba tada halin yin hakan, cigaba da lalla6ata tayi a kan ta saketa, amma taki sakinta. sai ta mika hannunta ta wanke kwakin ta xuba sugar ta fara bata, sai da tasha ta 'koshi sannan ta daina bata, cigaba da lalla6ata tayi har sai da tayi bacci sannan ta tashi ta fita. "kayan su ta dauka ta nufi wani famfo da almajirai ke d'iban ruwa don ta wanke musu , da isarta wajen tayi sa'a babu kowa, don haka ba tare da 6ata lokaci ba ta fara wanke tsummokaransu, tana yin wankin tana tunanin yanzu a haka zasu cigaba da rayuwa ba tare da kulawar dangi ba, ko kuma mahaifi. ya Allah kana sane da mu, a wajenka muke neman taimako. "tsawar da ta ji an daka mata kamar daga sama har sai da tayi kamar xata kifa qasa ita ce, ta dawo da ita hayyacinta. "ke *AL-MAJIRA* 'yar mahaukaciya matsa ki bamu guri muna da abin yi a wajenmu,kin wani xo kin tara mana tsummokarai masu wari a waje, an fad'a miki nan famfon mahaukata ne? matsa dallah can, kada ki shafa mana qarxuwar hauka. d'agowa tayi ta kallesu idanu cike da hawaye tace Allah ya baku hakuri. shigewa tayi ta barsu a wajen suna ta mita har da xaginta, har tayi nesa dasu basu daina nunata suna aibata ta ba. "mutane ta hango cike da bakin kofar kangonsu, tana ganin tarin jama'ar taji gabanta ya fadi, a tunaninta ko wani abu ne ya sami Amminta, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta shiga karantawa, 'kosawa tayi ta isa bakin wajen, saboda ta ganewa idonta abinda yake faruwa da su. tunda ta kusanto wajen take jin maganganu sama-sama da alama dai taron nasu ne, gani tayi wasu mutane sun bude 'kofar kangon suna jefo musu kayansu waje, a sanyaye take tafiya jan kafa kawai take yi, babu abinda yake sauka a fuskarta sai hawayen takaici. ganin yadda ake jan Amminta ne yasa ta tafi da gudu ta rungumeta tana kuka, wasu mutanen har da dukanta saboda gaddamar da ta yi musu. masifa suke yi sosai"wallahi baku isa ba, baxa ku qara kwana a anan ba, yau-yau d'in nan sai kun bar layin nan, banda bala'i da masifa mutane ba a san asalinku ba, kawai kun xo kun tare a kangon mutane, to wallahi baxa ta sa6u ba sai kun tashi kun bar wajen nan" kuka mai tsanani take yi "dan Allah ku taimaka mana, wlh ba mu da kowa sai Allah sai ku, idan ku ka koremu bamu san inda xa mu je ba. "rufe mana baki munafukar banxa da wofi, duk matar arxiki tana gidan mijinta, kuma duk yarinyar arxiki tana gidan iyayenta, idan kuma mahaukaciya ce tana gida an killace ta, wulakantacciya ita ke bin kangwaye tana kwana, watakila ma a garin asirinku ne na mata, ku ka yi, ya koma kanta, kasa cewa komai tayi, saboda ko tayi maganar ma baxai saurareta ba. muryar wani mutum taji "ku wai dan Allah ba ku da imani ne? banda kuna da karamin tunani wad'annan mutanen sun yi muku kama da mugwaye, ku riqa aiki da lissafi mana. "kai dallah gafara can shi. mugu yana da kama ne, kana ganin yadda matar nan ta takurawa yayanmu, ba halin a aikesu sai duka da jifa da dutse, to me yayi xafin haka, yara da unguwarsu ba a isa a hanasu sakewa ba" "dan Allah ku yi hakuri ku tausaya mana, ku duba halin da muke ciki, idan kuka koremu daga nan wlh ba mu san ina zamu dosa ba. "ku tafi 'karshen duniya ma ina ruwanmu, ai duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai sani ba" "da 'kyar aka sasanta suka barsu dan su cigaba da kwana, amma da sharad'in sai an d'aurewa Ammi 'kafa, a cewarsu wai tana takurawa yaransu, haka ta yarda aka daureta ba don ranta ya so ba, saboda tasan sharri aka yi wa mahaifiyarta, Ammi ita da ko fita bata yi, a ina taga yaransu har ta dakesu. hawaye masu xafi ne suka cigaba da sauka a kan kuncinta, kayansu ta rika kwashewa tana shigar da su ciki. sannan ta rike hannun Amminta don ta shigar da ita ciki, suna tafe tana d'ingisawa kamar mai ciwon 'kafa saboda daurin da aka yi mata. "xaunar da ita tayi ta rika duba gurin da mutanen suka daketa, tana bata hakuri gami da rarrashinta, ita dai bin ta take da ido ba abinda take iya ce mata. sallama taji kamar daga sama, wannan matashiyar yarinyar ce ta sake dawowa dauke da kwanon abinci, yau dai babu alamar tsoro a tattare da ita, da karfinta take takawa, 'karasowa kusa da AL➖MAJIRA ta yi, don a yanxu ta fuskanci ba ita ce mai lalurar haukan ba, don haka ta mi'ka mata hannu don yin musabaha, ita ma hannun ta mika mata suka gaisa. Ta mika mata kwanon abincin tayi mata godiya mai yawa sannan ta karbi kwanon da ta kawo musu abinci jiya. har bakin kangon ta rakata, har ta juya don ta kulle 'kofa, sai taga ya dace tasan sunan yarinyar da dalilin da yasa take tausaya musu haka, duk da cewa bata san asalinsu ba. "murmushi tayi sannan tace ni sunana *Saimah* gidanmu yana nan bayanku, mahaifina ne ya ganki kina bukatar taimako shi ne ya sanarwa momyna yace a rika baku abinci, sbd yaga halin da kuke ciki na talauci ga shi mahaifiyarki tana da lalura, mu a xatonmu ke din ma ba ki da lafiya sai yanxu muka gano lafiyarki kalau. a jiyar xuciya tayi sannan tace wlh lafiyata kalau, halin da ya samu mahaifiyata ne yasa ake min kallon mahaukaciya, Amma sam ba nida lalaurar hauka. "ko xaki iya fada min matsalarku ni kuma na sanar a gida, ko Allah xai sa a mu iya taimaka mu ku??hawaye ta cigaba da sharewa, na tabbatar baxa ki iya yi mana maganin matsalarmu ba, saboda abubuwa ne masu yawa suka faru da mu. 'kara tambayarta saimah tayi ko kin san lokacin da amminki ta kamu da wannan lalurar? eh "na kiyaye wasu abubuwa saboda a lokacin ban fi shekara tara ba tun daga wannan lokacin muka bar gidanmu dangin mu da garin mu muka dawo wata rayuwa tun daga sannan muke fuskantar qalubale, kala-kala idan muka je wani wajen ma cewa suke ni ba yar halak bace....... tausayi ne ya bayyana a fuskar *Saimah* tabbas kina cikin wani yanayi wanda kuke bukatar a jawo ku ajiki,don kuji sanyi da nutsuwa a rayuwarku. xan je na tambayi Abbana a kan ya baku wani d'aki asoron gidanmu ku karasa rayuwarku anan kafin Allah yasa a ga danginku,sbd xamanku anan ba dadi. "bata san lokacin da ta yi wani murmushin farin ciki ba. "dama har yanxu akwai irinku masu tausayawa bayin Allah,... Allah ya biyaku da aljannah" "kada ki damu ki daina godiya ai komai kayi kanka ka yi wa.kuma alheri danqo ne ba ya faduwa kasa banxa. "Ammi suka gani ta kwance daurin kafarta tana kokarin kama katanga xata haure ta gudu, don haka da hanxari suka 'karasa wajen tare da yin salati, "ina xaki je?suka fada tare. muxurai kawai take yi, bata ce musu komai ba,sai kawai gani suka yi har ta d'ane katangar , ga shi su kuma baxa su iya hawa ba, dan haka suka fita waje suna neman d'aukin jama'a, sai dai kafin su dawo sai filin wajen suka tarar. kuka AL➖MAJIRA ta fara yi. Ammi ki taimakeni ki dawo ba nida kowa sai ke, idan kika tafi kika barni waye xai karbeni a duniyar nan. kukan da take yi shi ya bawa kowa tausayi a wajen, don haka wasu samari suka yanke shawarar bin ta. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Alhamdulillah, Allahu mun gode maka bisa da ni'imar da kayi mana👏🏻A Yau Allahu madaukakin sarki ya nufemu da kammala karatun mu na degree, Allah ya bamu abinda muke nema na sakamako kyakkyawa*👏🏻 *congratulation MARIAM TIJJANI ADAM on your POP (NYSC) I Wishes all d best, in all your indeavors may mighty Allah, guide help and give you all d best* 1⃣1⃣ *C*ikin xafin nama Ammi ta sheqa da gudu, take samarin suka bita, amma ina tuni ta yi musu nisa sosai, don haka suka yanke shawarar su samu machine su bi ta, gudu take yi ba kak'kautawa, don haka suka nemi taimakon mutane akan su riqe ta, cikin taimakon Allah suka samu nasarar kamata. dawo da ita suka yi kangon sannan suka bawa Almajira shawara ta daina fita ko'ina gudun kada ta sake guduwa, godiya ta yi wa samarin sannan suka yi sallama da saimah ta wuce gida. "zaunar da Amminta tayi tana xubar da kwallah, ita kuma Ammin sai xare idanu take yi tana naushinta da hannu". "Ammi ina xaki je alhalin baki san kowa a garin nan ba, kina son na shiga garari ne Ammina? kece farin cikin rayuwata, ke kadai nake gani naji dadi, idan kika tafi kika barni ina xan sa kaina, muxuranta ta cigaba da yi, tana 'kara kai mata duka, sai dai tana kawo hannunta Allah yake bata sa'a sai ta kauce. ******************************** saimah ce a gaban mahaifinta ta sunkuyar da kai tana wasa da 'yan yatsunta. kanta na kasa ta kasa fad'awa mahaifinta abinda take son isarwa gareshi, ganin shirun yayi yawa, yasa ya fara magana. "yar lelen Abbanta da magana kenan tunda naga kin yi wannan gurfanan." Shiru tayi da d'an lokaci sannan tace, eh!! Abbah dama......dama cewa nayi da xamu taimakawa su AL-MAJIRA mu basu d'akin soro su xauna, saboda a can kangon da suke ba su da daki, ga shi damina ta kusa sauka" shiru yayi na d'an lokaci " haka ne Autar Abbah, kin yi tunani mai kyau, saboda Allah yana taimakon bawansa, matukar bawan yana taimakon d'an uwansa. yanxu kije xan yi waya kasuwa a taho musu, da ledar tsakar daki da labule xuwa yamma sai mu je mu taho da su". hawayen farin ciki ta fara yi "Abbah na gode Allah ya saka da alheri Allah ya 'kara arziki" Amsawa yayi da ameen yar Abbanta Allah yayi miki albarka. "kai tsaye waje ta fito, ta nufi wajen su AL-MAJIRA, tararwa tayi ana kokawar mayar da Ammi cikin kangon saboda ta sake yunqurin fita, da kyar aka samu aka shigar da ita. shiga cikin kangon tayi fuskarta cike da annashuwa, take sanar da ita yadda suka yi da Abbanta, farin ciki ne ya lallu6e AL-MAJIRA har ta rasa bakin godiya sai kuka da take yi, har kasa ta tsagunnah tana yi wa saimah godiya, tashinta tsaye tayi ta dafa kafadarta, kada ki damu kawata da sannu xa kiyi rayuwa ta jin dadi ki koma kamar kowace diya mace. "godiya ta 'kara yi mata, ban ta6a tunanin xan yi rayuwa mai dadi ba ko da a mafarki, saboda tunda muka bar gida, bamu sake had'uwa da wanda ya tausaya mana ba, koda da ruwan sha ne ballantana musa rai da wajen kwana, sai gashi Allah ya yanke mana wahala, tunda na hadu da ke na bar fargabar abinda xa mu kai bakinmu, shi yasa a kullum nake muku addu'a, yadda ku ka sakamu farin ciki, ku ma Allahu ya yaye muku bakin cikin duniya da lahira. "amsawa tayi da ameen, haka suka xauna suka rika hira har xuwa yamma sannan 'yan uwanta suka xo tafiya da su AL-MAJIRA. d'aki a ka basu a soran gidan, an gyara musu shi, an sa musu labule da ledar tsakar daki, shigar da su dakin aka yi, suna xama aka kawo musu abinci da kaya, nan da nan su AL-MAJIRA suka canja kaya suka ci abinci sannan tayi sallah. "saimah ce ta shigo tare da momynta da Abbanta, sallama suka yi, fuskarta a sake ta amsa musu, gurin xama suka samu suka xauna, cikin ladabi ta gaishe su. "Abba ne ya fara magana, muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar da kulawarku ta dawo hannunmu. muna fatan xaki kwantar da hankalinki ki d'auke mu tamkar iyayenki, duk abinda kike so ki tambaye mu, indai muna da hali xa mu yi miki, sannan nasa a sauke al-kur'ani a yi wa mahaifiyarki addua a kan Allah ya bata lafiya. risinawa tayi tana masa godiya. "ba komai ki daina godiya ai d'a na kowa ne, bawa sai mai shi. mu dai fatanmu ku samu farin ciki ta sanadiyyarmu. tashi suka yi xasu fita tayi musu sallama sai da safe, har sun kai bakin kofa suka dawo "Au!!! mun manta bamu tambayi sunanki ba. "sunana NAUWAR tayi maganar kanta a sunkuye" Masha Allah sunanki mai dadi da asali, daga yau mun daina kiranki da AL-MAJIRA tun dai mun ji sunanki, sallama suka yi da ita suka koma cikin gida, ita kuma ta koma ta xauna, mintuna kadan bacci ya dauketa. A haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki, ta xama tamkar yar gida, har makarantar islamiyya aka sanyata. ga shi yanxu Ammi na samun kulawa sosai saboda kullum suna tare da ita, a yanxu dai ba su da matsalar abinci da wajen kwana, ga shi sun samu kayan sa wa da yawa, Alhamdulillah Ala na'amihi. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJJANI* *ADAM* *(jeeddahtul-khaeer)* *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Duk inda nake, a duk inda a kasance kuna raina, bana manta karamcinku da kaunarku gareni, Bilkisu Mmn Irfan (mai gado)$ Mamah Aleeyou kd ana tare*💯🤝 *wannan shafin gaba d'aya naki ne ZAINAB ABUBAKAR( YAR FILLO) ina yinki 😍😘* 1⃣2⃣ *H*aka Al-ajira ta cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali, sai dai fargabar ta d'aya ciwon Amminta, ko yaushe zata dawo kamar da? Kullum ta tuna yadda rayuwarsu take a baya, sai ta zubar da hawayen takaici, duk da karancin shekarunta, amma yarinya ce mai kaifin hankali da tunani *ASALIN LABARIN* Nauwar Mahmoud shine asalin sunan Almajirah, suna zaune ne a garin Kano a unguwar Nassarawa G.R.A(Dawaki Road). Mahaifinta Mahmoud Abdullahi d'an asalin garin Danbatta ne dake garin Kano, wanda ya kasance shi d'aya tilo a wajen mahaifiyarsa, inda abokiyar zamanta Habi take da yaya hudu (4)Isa,Nasiru,Abdurrahman, sai kuma y'ar autarsu Dije. Kasancewar Mahmoud d'a d'aya tilo a wajen mahaifiyar sa wannan yasa mahaifiyar Mahmoud take fuskantar matsalar gori da habaice-habaice a wajen uwar mijinta karime, da abokiyar zamanta. kasancewar tunda aka yi aurenta da malam Abdullahi bata haihu ba, sai da ta d'auki shekaru masu yawa,wannan yasa Inna karime tasa malamAbdullahi ya auri 'yar Aminiyarta Habi. tunda Habi tazo cikin gidan, Mahaifiyar Mahmoud ta kuma shiga cikin wani mawuyacin hali, har sai da ta kai ta kawo bata da kwana,mahaifiyar malam Abdullahi ta hana shi xuwa shimfidarta, saboda ba zai yiwu yaje ya kare karfinsa a kan juya ba, ita kuwa Aisha baiwar Allah bata nuna bacin ranta ba sai dai addu,a da take yawan yi kasancewarta mace mai tawakkali, tasan dukkan tsanani yana tare da sauki. haka rayuwarsu ta cigaba da gudana, kwanaki na shudewa su zama sati daga nan su zama watanni. Aisha ta d'auki tsayin watanni bakwai ba tare da mijinta ya kalli ko da 'kofar d'akinta ba ballantana ta sami damar Le'kawa turakarsa, ana cikin wannan yanayin ne Habi ta sami juna biyu, murna kuwa a gidan ba a magana,Inna karime kuwa cewa tayi daga wannan ranar, Habi ta daina wanke-wanke,shara da girki, sai dai Aisha ta ringa yinsu, ba yadda malam Abdullahi ya iya, dole haka yasa ido Aisha taci gaba da wadannan ayyuka. Wata rana Inna karime sun tafi unguwa, ita da Habi malam da ya dai-daici sun tafi, ya dawo gida jikinsa a sanyaye hawaye yake zubarwa, yana rarrashin Aisha yana bata hakurin zalincin da ake yi mata, share masa hawayen ta fara yi, tana fad'in malam ka kwantar da hankalin ka, ni ban ri'keka da komai ba, nasan ba laifin ka bane, kuma ko Inna da Habi ban rikesu ba na yafe musu duk abinda suka min, rungumeta yayi yana shafa kanta, albarka ya saka mata daga nan suka farantawa juna rai. Haka rayuwarsu taci gaba da kasancewa, sai bayan da Habi ta haifi d'anta na biyu sannan Aisha ta haifi danta Mahmoud,haka rayuwarsu taci gaba da innarsa yau za'ki gobe mad'aci, ana cikin wannan halin ne, innar Mahmoud ta kamu da zazzafan zazzabi wanda yayi sanadiyyar mutuwar ta Mahmoud yana da shekaru takwas a duniya, tun daga wannan lokacin Mahmoud ya koma rayuwar kad'aici da maraici, shi d'aya yake kwana a d'akin innarsa, abinci ma sai Habi taga dama take bashi. wata rana yakan kai kwana biyu ba tare da yasa komai a bakinsa ba, Sai dai Idan malam ya faki idonsu Inna karime da dare ya bashi abinda Allah ya hore masa. A wannan lokacin baffansa yace masa Mahmoud ina son na kai ka birni kayi karatun allo a can, saboda takura ka da a keyi a cikin gidan nan yayi yawa, gara Kaje can kayi karatunka, abinda Allah ya hore min zan ringa kawo maka. sannan ina yi maka wasiyya da kaji tsoron Allah a duk inda Kake, ka zama mutum mai amana, ka sani duk tsanani yana tare da sauki, kasa a ranka komai mai shigewa ne kaji d'ana shashshekar kuka baffansa ya fara yi,wanda yasa jikin Mahmoud ya 'kara sanyi Wanda dama tunda mahaifinsa ya fara jawabi yake zubar da hawaye,d'agowa yayi yana sharewa mahaifin nasa hawayen, Baffana kayi hakuri insha Allah zaka yi alfahari dani,na kasancewa ta danka, ka sani a duk inda nake ba zanyi watsi da tarbiyyar da kayi mini ba, rungume shi baffansa ya kara yi, yana yi masa addu,oi na fatan alkhairi,sannan suka nufi gida. *WASHE GARI* *M*isalin karfe 10:00 na safe suka iso cikin garin Kano ta Dabo, inda Mahmoud ya ji kansa na juya masa,kasancewar bai saba ganin cinkoso da yawan ababan hawa ba irin wannan take Mahmoud ya ................. A yi Hakuri da wannan yau ina busy a yi min afuwa👏🏻 *jeeddahtulkhir😘* [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITES FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba d'ayanshi sadaukarwa ne ga duk wani masoyin littafin Almajirah, ina kaunarku kamar yadda kuke 'kaunata, Allah ya barmu tare, ana tare*💯🤝 *ina mika gaisuwar ban girma gareki big admin ummiey xee Abakson, ina godiya da kaunarki garen, da dukkan 'yan uwa na exclusive writer's Allah ya 'kara hada kanmu*👍🏻 1⃣3⃣ Fashewa mahmoud yayi da kuka, "Baffana mu koma gida, bana son xama a irin wannan garin, an ce mutum d'an iska yake komawa, yana yin maganar yana share hawaye da majina. dariya Baffa yayi, lallai mahmoud da abin dariya kake, wanene ya fad'a maka wannan ruwayar? haka mutanen 'kauyenmu suke fada Baffa. to ba haka bane mahmoudu na duk wanda kaga ya lalace shi yasa kansa, ni dai fatana ka kiyaye Allah, kaji tsoransa a duk inda ka kasance, kuma kada ka tara bautar Allah da waninsa, kuma banda abinka ma ai wannan birni ne na albarka, burina a yanxu bai wuce kayi karatu ba ka share min hawayena, kasancewarku d'a na gari shi xai sa nayi alfahari da kai. 'karasowa bakin hanya suka yi, ya siya masa robar Abinci da kwaki da sugar, basu yi wata tafiya mai nisa ba suka isa makarantar malam Audu da ke unguwar 'kofar wambai, inda a nan ne mahmoud xai yi karatu. da sallama suka shiga xauren da malam Audu yake karatu tare da almajiransa, yana ganin Baffan mahmoud ya mi'ke ya tarbeshi da farin ciki, hannu ya mi'ka masa dan yin musafaha, shi ma mi'ka masa yayi suka gaisa, cikin ladabi mahmoud ya tsugunnah har 'kasa ya gaishe shi, amsawa yayi fuskarsa a sake, da kuma farin cikin ganin d'an nasa, kasancewar malam Audu aminin Baffan mahmoud ne tare suka tashi tun suna kanana. bayan doguwar gaisuwar da suka yi, malam Audu yasa aka kawo musu Abinci da ruwa, bayan sun nutsu ne mahaifin mahmoud ya fara magana. "malam dama wata bu'kata naxo maka da ita, ina son mahmoud ya xauna a wajenka, ya xama d'aya daga cikin almajiranka, dan gaskiya ina son ya samu haddar al-'kur'ani, ya kuma xama masani a bangaren littafan addinin musulunci, ina fatan xaka kar6i wannan bukatar tawa. shiru malam Audu yayi na d'an lokaci, "ba matsala malam Abdullahi ai mahmouda d'ana ne, ko ba ranka ni mai iya kulawa da shi ne, insha Allahu xan ri'ke maka amana, baxan wulakanta Alkawarin da nayi maka ba. godiya mai yawa malam Abdullahi yayi masa, sannan ya 'kara gargadin mahmoud a kan ya xama jakada na gari ga iyayensa. lokacin da malam Abdullahi xai tafi hankalin mahmoud ya tashi kwarai da gaske, kuka mai tsanani ya fara yi, nan da nan mahaifinshi ya fara lalla6ashi akan yayi hakuri, xamanshi a nan shi ne jin dadinsa da walwalarsa. sallama suka yi da malam Audu tare da yi masa godiya mai yawa, ya fito dan hawa motar garin 'Dan batta. Tun a mota malam Abdullahi yake ta share kwallar rashin d'ansa mai biyayya a gareshi, ya rasa me yake masa dadi a rayuwar duniya, amma ba yanda ya iya, dole ya kaishi karatun saboda ya samu sassaucin tsanar da Habi da Inna karime ke yi masa, ransa babu walwala ya shiga gida, yana sallama ya iske inna karime a tsakar gida tana jiran ya dawo ta sauke masa kwandon bala'i, fad'a ta fara yi masa, ina kaje tun safe nake ta jiranka, kaxo ka bani kud'in mota xamu je hayi ni da jikokina, amma har dare baka dawo ba, yi min bayanin ina kaje ka shanyani haka? tsugunnawa yayi har 'kasa yana bata hakuri, sai a lokacin yake sanar da ita cewa ya kai mahmoud makaranta ne a birni dan yayi karatu, nan fa tayi tsalle ta dire, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, dole a dawo dashi gida ya cigaba da rainon 'ya'yan Habi da yi musu wanki. hakuri ya shiga bata a kan ta dubi Allah ta duba maraicin da yaron yake ciki da irin matsalolin da yake fuskanta a cikin gidan ta kyaleshi yayi karatun shi a can, kasa fahimtarshi tayi ta cigaba da fadanta, ta kuma qudiri aniyar cewa, indai bai bi maganar da ta fad'a masa ba, sai ta tsine masa ya bi duniya. Hawayen takaici yake sharewa yana neman gafararta, d'akin habi ya shiga ko xai samu xuciyarsa ta sarara daga rad'adin da take masa, nan ma dai bala'in ya kara tararwa don har ya dame wanda inna karime tayi masa, a ranar dai kwanan ba'kin ciki yayi,dan ko rintsawa bai yi ba saboda takaici. gari na wayewa ya fito ya shiga d'akin inna karime don ya gaisheta, habi ya gani da y'ay'anta suna magana, ana ganinshi aka yi shiru, da dukkan alamu dai xancen mahmoud ake yi, har 'kasa ya tsugunnah ya gaisheta, cikin fara'a da walwala ta amsa masa, yayi mamakin ganin hakan daga gareta, tunda ya san fushi take yi da shi. "magana ta fara yi, Audu ka kai mahmoud birni ko? hmm ai nasan xa a rina wai an saci xanin mahaukaciya, tunda ka auro 'yar iska (uwar mahmoud)jinin 'yan iska, nasan dole sai ta haifi kamarta, dole malam idi ya samu magaji, dan haka a da, ina takaicin kai mudi birni, amma yanxu xuciyata fes-fes take, a barshi ya xauna a can ya xama tantirin d'an iska kaga ba nida asara, tunda ga nawa jikokin nan ina ganinsu ina jin dadi. maganganun innah sun yi wa malam Abdullahi ciwo amma ba shi da yadda xai yi ya rama, sai dai ha'kuri kawai, kansa a sunkuye yake magana "inna makarantar Muhammadiyya fa na kai mahmoud ba wani waje ne mara kyau ba" rufe min baki nan shashan banxa da wofi, yara nawa aka kai makarantar Muhammadiyyar suka lalace? ni dai ina nan ina addua Allah ya cika min burina na lalacewar d'an nan, she'kewa suka yi da dariya ita da habi har da tafawa kamar wasu 'kawayen juna. jikinshi a sanyaye ya fita ya bar d'akin, xuciyarsa kuwa kamar ta fad'o 'kasa don takaici. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *Wannan shafin gaba d'ayanshi saudaukarwa ne a gareki, RUKAYYA HASSAN OTHMAN marubuciyar IBTEESAM Allahu ya 'kara basira da d'aukaka, jeeddah ta gaisheki kyauta* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *Gaisuwa ta musamman gareku manyan yayyena, ina godiya da kulawarku gareni Muhammad Ghali &Aunty Zahra, Allah ya 'kara muku soyayya da kaunar juna, Auntyna kuma Allah ya saukeki lapiya🙈* 1⃣4⃣ *H*aka mahmoud ya cigaba da rayuwa a gidan malam Audu, inda matarsa Rahmatu ke bashi kulawa kamar d'an da ta haifa a cikinta, saboda mahmoud yaro ne mai nutsuwa da biyayya, duk wani aikace-aikace na gida yana taimaka mata dashi, hakan yasa ya 'kara shiga ran dukkan wani mai rayuwa a cikin gidan, ga shi kuma yana dagewa wajen karatu, wannan dalilin, yasa malam Audu ya fara tunanin saka shi a makarantar boko, saboda yana ganin yaron xai yi 'kwaxo da kaifin basira. wata rana bayan sallar isha'i malam Audu ya shigo gida, ya samu Rahmatu tana tu'ka tuwon dare, xaunawa yayi a gefenta bayan ya mata sannu da aiki, sannan ya fara magana. Hajiya Rahmatu ni fa ina wani tunani a kan yaron nan, tambayarsa tayi tare da ajiye aikin da take yim tunanin me kake yi haka malam? gyaran murya yayi, am dama ina so ne na kai yaron nan mahmoud makarantar boko, saboda naga yaron yana da haxaqa sosai, amma akwai wani hanxari ba gudu ba, kin san sha'anin mutanenmu na karkara kada na kai shi, mahaifinsa yaga kamar xan lalata masa d'ansa ne, tunda kinga duk sauran 'yan uwansa ba karatun suke yi ba. Haka ne malam, amma ni a ganina hakan ba komai bane, kasan halin malam Abdullahi, mutum ne mai fahimta,na tabbar da cewa ba zai maka mummunar fassara ba, kuma ya riga yasan da cewa rayuwar nan baxa ta tafi dai-dai ba, har sai mutum ya had'a da ilimin addini da na zamani, amma abinda xa a yi yanxu, ka kira mahmoud ka tambayeshi idan yana so sai a kai shi, sannan kuma ka nemi malam d'in ka shawarceshi, abinda kuka yanke shikenan sai a xartar ko ba haka ba? eh gaskiya ne Rahmatu insha Allah xan yi yadda kika ce, to madallah malam Allah yayi mana jagora, amsawa ya yi da Ameen. Mahmoud ne ya shigo da sallama, cikin ladabi ya 'karaso inda suke, har 'kasa ya tsugunnah ya gaishesu,fuskarsu a sake suka amsa masa, har ya mi'ke malam ya kira sunanshi, Mahmoud ina da wata magana mai muhimmanci da kai, sake sunkuyar da kanshi yayi cike da ladabi ya amsa da To malam. dama na yanke shawarar xan sanyaka makarantar ilimin xamani ne, tunda dai kaga yanxu kayi nisa a karatunka, shi yasa naga ya dace a ce kasan ilimin boko sbd ilimi abu ne mai muhimmanci, amma yanxu ya kake gani? farin ciki ne ya bayyana a fuskar Mahmoud, domin ya dad'e yana sha'awar karatun boko, kasancewar abokansa da yawa suna yi, amma ina karime ta hana a saka su, saboda tace jikokinta baxa su xama bayin bature ba, amsawa yayi da ina so malam, nayi farin ciki Allah ya saka da alkhairi, amma kafin na fara ka tambayi Baffana ko xai barni. murmushi malam Audu yayi, ka kwantar da hankalinka Mahmoud Baffanka ba shi da matsala, xai yarda insha Allahu. godiya Mahmoud yayi, sannan matar malam ta bashi Abincinsa ya shiga d'aki don ya ci. malam Audu bai samu wata matsala da malam Abdullahi ba, sai ma dai adduar fatan alkhairi da samun nasara da ya yi wa d'an nasa. *BAYAN SHEKARA SHIDA* Bayan shekara shida, Mahmoud ya samu nasarar kammala makarantar primary, inda malam Audu ya umarce shi da ya je ganin gida, kasancewar tunda aka kawo shi wajensa bai je ba, kuma wani bai xo daga gidansu ba, a ranar da malam ya fad'a masa maganar xuwa gida, kwana yayi bai yi bacci ba, saboda xuciyarsa cike take da kewar su isah, don haka da asubah ya shirya jaka sai d'oki yake xai je dan batta, da misalin karfe 9:00 na safe, malam ya kai shi tasha ya biya kud'in mota,ya umarci driver ya kai shi har 'kofar gidansu, duk da farin cikin da Mahmoud yake yi na ganin gida, amma sai da yayi 'kwallar rabuwa da malam, sbd riqon mahaifi yake masa, bai ta6a neman wani abu ya hanashi ba, sai dai idan bashi da halin bashi. Ana sauke shi a mota, yaran unguwarsu suka taho da gudu suka rungume shi, suna farin cikin ganin abokinsu, wanda suka yi kewa shekara da shekaru, d'aukar masa jaka suka yi don shigar masa da ita gida. da sallama ya shiga gidan, inna karime da Habi ya tarar suna aikace-aikace, tsugunnawa yayi cikin ladabi yake gaishe su, amma ko d'an kallo bai ishe su ba, cigaba yayi da gaishe su, tsawa inna karime ta daka masa, cewa muka yi bamu ji ba, xaka damemu da gaisuwa, me gaisuwarka xata yi mana ne? da xaka takura mana, shasha irin mugun Abu, tsayawa yayi yana kallonta har ta gama surutanta, sannan ya d'auki jakarsa ya nufi d'akin Habi, yana kusantar d'akin,Habi ta biyoshi da gudu, kada ka shigar min d'aki jinin annoba, ka dawo daga yawon iskancinka xaka shigar min d"aki, uwarka ka ajiye a ciki, matsa ka bani guri irin ba'kin hali. hawaye ya ji suna taho masa yasa hannu ya share, ganin cin mutuncin da Habi da inna karime ke yi, yasa ya fita soro ya xauna yana ta shar6ar kuka. Bai jima da xama ba malam Audu ya shigo, yana ganin d'an nasa farin ciki ya kama shi, ga mamakinsa xai ga d'an nasa cikin walwala amma ina sai yaga sa6anin haka, 'karasawa yayi yana tambayarsa, mudi me yasa kake kuka, yaushe kaxo garin nan ban sani ba? kasa bashi amsa yayi sbd ba'kin cikin da ya cika masa xuciya. cigaba yayi da tambayarsa. ka fad'a min me aka yi, me ya faru da kai?cikin kuka Mahmoud ke magana "Inna da gwaggo ne suka xageni" don wannan ma kake kuka Mahmoudu, ai idan da sabo ka saba da cin mutuncinsu, yi hakuri Mahmouduna insha Allahu duk wadanda suke takura maka, sai sun ci arxikina, kuma sai 'ya'yan da ake so sun xauna a 'kar'kashinka, hawaye ya shiga share masa kayi ha'kuri tallafi marayan Allah, ubangijinka na tare da kai,kuma bai manta da kai ba. duk abin nan da suke yi ashe a kan idon Inna karime ake yin sa, tsalle ta doka ta fara masifa, ba amin ba shanyayye, uwarsa ta shanyeka, shi ma ya shanyeka dole ka riqa sambatu a kansa, to bari na gaya maka, indai arxi'ki ne,mudi yayi bankwana dashi, sbd bai gaje shi ba, har malam idi (kakan Mahmoud)ya mutu jakinsa d'aya ko gona ba shi da shi. su isah sune masu arxikin gidan nan, dan malam Habu mai duba ya dade da fad'a min haka,Mahmoud kuwa................... sai dai ya ga ana yi, jinin matsiyata kawai *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Ina taya yar uwa MARIYA BABA ABDULLAHI(baby fine) murnar fara littafinta mai suna KAXAMAR MACE💂🏿‍♀, yadda aka fara lafiya, Allah yasa a gama lafiya* *wannan shafin gaba dayanshi sadaukarwa ne gareki ATIKAH TIJJANI ADAM, Allah ya bar xumunci da kaunar juna, ana tare🤝💯* 1⃣5⃣ *S*hiru malam Abdullahi ya yi, yana sauraren inna karime har ta gama fad'anta, wucewa tayi ta tafi gida, xuciyar malam kuwa, xafi kawai take masa kamar xata fashe, saboda aibata d'an marayan nan da take yi. umartar Mahmoud yayi da ya tashi su fita bakin kasuwa ya siya masa Abinci,saboda yasan ba shi da rabo a gidan, sannan yayi Al'kawarin mayar da shi gidan malam gobe, saboda xamansa a nan xai iya haifar da wata matsalar, Mahmoud bai musa masa maganar da yayi ba, saboda shi kansa ya san inna ba 'kaunar ganinsa take yi ba, nisa da ita shi xai 'kara masa kwanciyar hankali, kuma xai fi xama mafi alkhairi a gareshi. washe gari da sassafe Baffansa ya had'a masa kayansa,bayan sun karya kumallo, ya shiga d'akin inna ya gaisheta sannan ya sanar da ita cewa yau xai mayar da Mahmoud makaranta, ko tanka masa bata yi ba, haka ya gaji ya mi'ke. kai tsaye tasha suka nufa inda suka samu motar da xata kaisu har cikin birnin kano, basu dad'e suna tafiya ba,suka iso gidan malam, malam Audu yayi mamakin ganin Mahmoud da wuri haka, a xaton shi xai dad'e bai dawo ba, saboda yadda yaga Mahmoud d'in na d'okin xuwa gida, kuma ga shi ya dad'e rabonsa da gidan, amma sai ga shi ya dawo a washe garin da aka kaishi, gaisawa suka yi da mahaifin Mahmoud, tambayarsa malam Audu ya fara yi, lafiya dai ko malam Abdullahi? lafiya amma ba lau ba, kasan sha'anin gyatumata da abokiyar xaman mahaifiyar mudi, basa 'kaunar yaron nan, basa son ganinsa ko kad'an, kuskure kad'an xai aikata su fara aibata shi da xagin mahaifiyarsa,duk da cewa tana kabari bata san abinda ake yi ba, wannan dalilin yasa na tattaro shi na dawo dashi, saboda tunda yaron nan yaje ba shi da kwanciyar hankali nima haka, ko d'aki ba a barshi ya shiga ba, a soro ya 'kare xamansa har na dawo dashi. Shiru malam Audu yayi har sai da Baffa ya kare maganarsa, gaskiya ne gara da ka dawo da shi d'in, ka 'kara ha'kuri malam Abdullahi wata rana sai labari, irin wadannan yaran da ake wulakantawa su Allah ya fi axurtawa, kuma ina son ka bar min yaron nan kada ya 'kara xuwa ganin gida har sai ya mallaki hankalinsa ya xama saurayi, amsa masa yayi da to Allah yayi mana jagora, hannu ya mi'ka masa suka yi sallama sannan ya tafi, zuciyarsa cike da farin cikin karamcin da malam Audu yake masa. ***************** kwanci tashi asarar rai, yau ga shi Mahmoud ya kammala karatunsa na secondry, inda Mahmoud yake da shekara ashirin a duniya, kasancewar Mahmoud dalibi mai 'kwaxo, shi ya bashi damar samun shiga gasar da gwamnatin kano ta sanyawa daliban da suke da haxa'ka, don d'aukar nauyinsu, su yi karatu a 'kasashen waje, Allah ya bawa Mahmoud sa'a inda ya kasance d'aya daga cikin dalibai biyar da suka samu nasara, aka d'auki nauyin karatunsa a 'kasar sudan, farin ciki gurin malam Audu kuwa abin baya misaltuwa, ji yake kamar d'ansa ne na cikinsa ya samu wannan damar, ana saura kwana biyar su tafi, malam Audu ya umarce shi da yaje 'Dan batta ya yi wa mahaifinsa sallama, haka kuwa aka yi, ya shirya ya tafi don yi musu sallama. wannan karon kasuwa ya je ya tarar da Baffan nasa, don baya son ya same shi a gida, ya 'kara cin karo da wulakancin inna karime, malam Abdullahi yayi farin ciki da ganin Mahmoud, sannan ya ji dad'in albishir d'in da yaxo masa da shi, albarka ya shiga saka masa, sannan ya yi masa fatan samun nasara a rayuwar karatunsa, yayi masa nasiha sosai a kan kula da addini da barin rud'in xamani. umartarshi yayi da su je gida ya yi wa su inna da gwaggonsa sallama, bai musa wa mahaifin nasa ba suka tafi, suna yin sallama suka tarar ba kowa a tsakar gidan, don haka suka nufi d'akin mutan gidan, sallama suka 'kara yi musu amma babu wanda ya amsa, sai kallon sama da 'kasa suke yi wa Mahmoud duk a tunaninsu ya xama d'an iska, malam ne ya fara magana, dama sallama yaron nan yaxo yi miku, jibi xa su wuce 'kasar sudan, gwamnati ta xa6eshi cikin yaran da xasu je su karanta harkar lafiya a can, Habi ce ta yi masa wani kallo mai cike da alamomin tambaya, sannan Inna karime ta d'ora da jawabi,da gwamnati ta xa6e shi sai akai yaya?dama indai kaga tururuwa ta fara fiffike ai ta tasarwa lalacewa, yanxu yawon iskancin ya cigaba har sudan to Allah ya kyauta, ni dai jikokina baxa su xama bayin turawa ba ina nan tare da su, ina ganin fad'i tashin da suke yi, kai kuma umma ta gaida Ashsha, mu ma mun huta da jaraba. ba wani fatan alkhairi da inna ta yi masa, haka nan ya fito ya barta, yayi sallama da Baffansa ya dawo gidan malam, dan ko kwana Baffansa hana shi yayi saboda halin Inna. washe gari da asubar fari malam ya raka shi gidan gwamnati inda a nan ne xa a kaisu Abuja su hau jirgi, daga nan kuma su wuce sudan, malam yayi masa nasihohi masu ratsa jiki,sannan suka yi sallama dukkansu suna Hawayen rabuwa da juna. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeeddahtulkhar)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin d'ungurungum sadaukarwa ne, gareku yara manyan gobe,ku yi yadda kuke so da wannan page, jeeddah ta baku shi halak malak FATEEMAH MUKHTAR LAWAN & FATEEMAH TIJJANI ISAH FAGGE (AMATURRAHMAN) ina yinku, ina sonku, muna mugun tare🤝 Allahu ya raya mana Ku a tafarkin sunnah, Allahu ya kareku daga dukkan abin 'ki, ya tsareku daga sharrin mai sharri* *Baxan gushe ba ina mi'ka Godiya a gurin ki sisterna UMMIEY XEE ABAKSON, Allah ya 'kara d'aukaka da basira, jeeddah na godiya da kulawar ki gareta, kuma tace ana mugun tare*🤝 1⃣6⃣ Da misalin 'karfe biyu na rana suka isa garin Abuja, tuni dama jirginsu ya yi ready, su kawai ake jira, don haka suna xuwa suka hau suka wuce sudan. Sun sauka a garin MADANY a wata unguwa da ake kira RIYAD, inda a nan ne makarantar da xa su yi karatu take, ba tare da 6ata lokaci ba aka basu d'akin Kwana, sannan aka kawo musu abinci kala-kala, kowa sai da ya ci ya ture. Washe gari da wuri suka fita i xuwa d'akunan karatunsu, yana isa aji ya tarar har malamin ya iso, don haka yana shiga ya samu guri ya xauna, ana cikin karatun ne wata kyakkyawar yarinya ta shigo,taku take yi cikin nutsuwa, sanye take da had'ad'iyar doguwar riga,duk sai kallo ya koma kanta, malamin yana ganinta ya fara murmushin farin ciki, magana ya fara mata da harshen larabci *"HAYYAKILLAH"* Ma'ana ranki ya dad'e, ita ma da larabcin take magana d'an rusanawa tayi sannan tace *" SABAHUKAL AJMAL"* ma'ana barka da asubah, tambayarta ya fara yi *"LIMAXA TA'AKKARTI YA REHAB"* saboda me kika makara Rehab, sai a nan muka ji sunan yarinyar Rehab, sunkuyar da kai tayi sannan ta bashi amsa da cewa, *" ANA MASHGULAH LIXA TA'AKKARTU"* amsa mata yayi da *"MASHI, IMSH WA TAJLISI*" OK je ki xauna. cikin nutsuwa take takawa har ta isa gurin da xata xauna, sannan aka cigaba da darasi, da misalin karfe 10:00 aka 'kare karatun, tunda dama lecture d'in 8:00-10:00 ne, don haka kowa ya wuce hostel, shi kuwa Mahmud ya samu bakin wata bishiya ya fara bitar karatunsa. Yana cikin karatun tunanin Baffansa da na malam ya fad'o masa,sai ya tsinci Kansa yana mai hawaye, har yanxu yana jin xafin rabuwa da malam da Baffansa, saboda sun bashi kulawar da baxai iya mantawa da su a rayuwarshi ba, yayi xurfi a cikin tunanin Baffansa har ya manta da abinda ya kawo shi gurin, sallamar da ya ji an yi masa, ita ce ta dawo da shi daga tunanin da yake yi, da sauri ya juya ya fara share hawayen da ke sauka a kan kuncinsa,Rehab ya gani a bayansa, yayi mamakin ganinta, da abinda yasa taxo wajen shi, tunda yasan shi ba kowa bane a ajin, tambayar shi take *"LIMAXA RA'AITUKA TABKEE?*" murmushi yayi sannan ya girgixa kai alamar ba komai, matsa masa tayi da tambayar abinda yake damunsa, sai da ta matsa masa sosai, sannan ya fad'a mata yana tunanin Baffansa ne, tausayi ya bata, sannan tayi masa nasiha da ya tsaya ya yi karatunsa ta dauki alkawarin xata ri'ka taimaka masa da duk abubuwan da yake bu'kata, godiya mai yawa yayi mata sannan ta tambayi sunanshi ya bata amsa da "Sunana Mahmoud Abdallah", ita kuma tace sunanta Rehab Abu Fu'ad, kuma ta fad'a masa gidansu yana bayan makaranta, sun dad'e suna tattaunawa a kan matsalolin rayuwar duniya da yadda ya kamata su tsaya su fuskanci karatunsu, a 'kan'kanin lokaci suka saba da juna, saboda Mahmud mutum ne Wayayye ba shi da duhun kai, hakan yasa ya shiga ran Rehab suka xama kamar dama sun Dad'e da had'uwa, sai bayan magrib suka gama karatu, Mahmoud ya yi sallama da ita, har sun rabu ya kama hanyar xuwa d'akinsa ta biyoni shi, sunansa ta kira, ya juyo da fuskarsa ya amsa mata, alfarma ta nema a gurinsa a kan ya shirya su je gidansu ya ci abincin dare a can. 'Kin amincewa Mahmoud ya yi sai da 'kyar, ya yarda suka tafi gidan tare. Bakin mota suka je,bud'e masa ta yi ya shiga sannan suka tafi. Wani katafaren gida suka tarar, kana ganin yanayin ginin xaka tabbatar da cewa gida ne na masu arxiki, tsayawa siffanta yadda gidan yake ma xai iya xama 'kauyanci, saboda duk inda ake Neman Had'uwa gidan ya gaji da Had'uwa. Horn tayi mai gadi ya 'karaso da sauri ya bud'e mata gate ta shiga. Parking tayi, sannan ta umarci Mahmoud ya fito daga mortar, sannan suka shiga cikin gidan. falon gidan suka nufa, sallama Rehab tayi, sannan ta yi wa Mahmoud magana da ya 'karaso. Cikin nutsuwa ya bud'e 'kofar falon ya shiga, mahaifiyar Rehab ya gani xaune a kan kujera, jikinta lullu6e da laffaya da ganinta kaga dattijuwa mai addini, har 'kasa ya tsugunnah ya gaisheta cikin harshen larabci *"'DABA LAILUK*" (barkanki da dare)amsa masa tayi da *"KAIFUK"* (ya kake) murmushi yayi ya amsa mata da *"ALA MA YURAM"*(ina lafiya) tambayarsa tayi da *" MIN ANTA YA SHAB"* (daga ina kake d'an saurayi) xai fara magana kenan Rehab ta shigo hannunta d'auke da abubuwan sha kala-kala, ita ce ta cigaba da bayani a madadin Mahmoud, mamanta tayi farin ciki da shi, kuma ta yaba da Hankalinsa da nutsuwarsa, umartarshi ta yi da ya tashi yaje ya ci abincin da aka kawo masa. Abinci kala-kala aka kawo masa wad'anda bai saba cin su ba, wasu kuma ma bai ta6a ganin irinsu ba, LUXX ne da ADAS Adas d'in Anyi masa jellof,sannan ga KIBDA ga kuma IDAMUSSAMAK, ga kayan shaye-shaye kala-kala. Kad'an ya caccaki abincin ya tashi, kasancewar bai saba da cin su ba. Yana gama ci ta nemi da yaje ya gaisa da Habbobanta (kakarta) nan ma da karamci aka kar6eshi. Har bakin gate ta rakoshi sannan aka sa driver ya mayar da shi har hostel. *jeeddahtulkhair*😘 Ina yinku masoyana, dan Neman 'Karin bayani 08094136204 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Baxan manta da 'kaunarki da kulawarki gareni ba, ina godiya da yadda kike nuna tsantsar kauna gareni, ina alfahari da karamcinki gareni,don haka wannan shafin gaba d'ayanshi sadaukarwa ne gareki, yar uwata MARYAM SANI LAGOS, jeeddah ta baki shi kyauta, kiyi yadda kike so da shi, ina yinki kamar yadda kike yi na* *jinjinar ban girma gareki my lovely Sister NASEEBAH I UBAH (NASIBAH GAWO)Allahu ya bar xumunci da 'kaunar juna, Allah ya 'kara miki basirah da hasken makaranta, jeeddah tace ana tare🤝* 1⃣7⃣ Dakinsa ya shiga xuciyarsa cike da farin cikin karamcin da Rehab da iyayenta suka yi masa, tsintar kansa ya yi cikin tunaninta, sai ya zamto duk bugun da zuciyarshi za tayi sai ya tuna da ita, haka ya kasance har zuwa lokacin da bacci yayi awon gaba da shi. Bayan yayi sallar asubah, yayi addu'o'i ne ya 'kara mayar da kanshi ya kwanta, kasancewar ba shi da lecture din safe, nan ma dai xuciyar shi yaji tana tuna masa Rehab, shi kansa abin ya fara bashi mamakin yadda ya canja lokaci guda, tunda yake a tarihin rayuwarshi bai ta6a tsintar kanshi a son wata yarinya ba, amma sai ga shi yanxu, dare d'aya ya fara son wadda ta fi 'karfinshi. shawarwari xuciyarshi ta shiga bashi, a kan ya furta mata so, wata xuciyar kuma tace ya kyaleta kawai, saboda ba lallai ta amsa tayinshi ba. yanke shawarar sanar da ita ya yi don ya jarraba damarsa ko xata amince da shi. agogon da ke manne a bangon d'akin ne ya buga, shi ne ya katse masa tunanin da yake yi, 'karfe goma dai-dai ya gani, don haka ya mi'ke ya fara shirye-shiryen tafiya makaranta. cikin mintunan da basu wuce biyar ba, ya kammala shiryawa, kulle d'akinsa yayi ya fice. 'Dakin karatu ya nufa ya samu guri ya xauna ya fara d'aukar darasi, bayan an gama ne ya fito inda ya saba xama, don yayi karatu, bai dad'e da fara karatun ba, ya gano Rehab daga nesa tana masa murmushi, da fara'arta ta 'karaso wajen da yake, gaisawa suka yi sannan suka fara hira gami da karatu kamar yadda suka saba, bayan sun gama ne, suka yi sallama xasu rabu kenan Mahmoud yake sanar da ita halin da ya tsinci kanshi a ciki, ta yi farin cikin jin wannan magana daga gareshi, saboda ita kanta ta yaba da hankalinshi da yanayin tarbiyyar da yake da ita, da kuma addininshi, don haka basu samu wata matsala da junansu ba, suka fara soyayya mai tsafta da ban sha'awa, suka xamto tamkar "yan uwa. A lokacin da suka shiga level 400 Mahmoud yake sanar da Baffansa cewa ya samu matar aure kuma abokiyar karatunsa ce, Baffa yayi farin ciki da wannan maganar, kasancewar duk 'yan uwansa sun yi aure, shi kad'ai ne ya rage a 'kasa saboda yana karatu, addua mai yawa yayi masa da fatan Alkhairi. bayan sun yi magana da baffa ne ya nemi Rehab a kan ta sanar da iyayenta maganar aurensu,tunda dai suna son juna, da farko dai ta nuna 'kin amincewarta a kan baxa ta sanar da su ba, saboda ba lallai ne su aurawa Ba'kar fata 'yar su ba, kasancewar su larabawa ne, lalla6ata yayi a kan ta fad'a musu tunda suna addua insha Allah xasu amince da abinda suka xo musu da shi. Tun da ta je wa da iyayenta maganar ta daina samun walwala da farin ciki daga garesu, saboda ita ce 'ya mace d'aya tilo a wajen mahaifanta, ta yaya xa a yi su aurawa talaka kuma ba'kar fata 'yar su, don haka suka turje, a kan baxa a bata shi ba, har sai da ta kwanta a asibiti, saboda wannan maganar daga karshe dai likita ya sanar da su cewa,idan har aka hanata abinda take so xa a iya rasata gaba d'aya, don haka suka yanke shawarar aura mata Mahmoud, amma da sharad'in dole sai dai su xauna a sudan, don basa son 'yar su tayi nisa da su. nan ma dai an sha gwagwarmaya da 'kyar suka amince aka yi biki, suka dawo Nigeria tare aka had'ota da sha tara ta arxi'ki, sannan suka samarwa Mahmoud aiki. Da farko sun kama haya ne a unguwar Na'ibawa, rayuwa suke yi mai dad'i cike da soyayya da kulawa, ga shi kullum Mahmoud dad'a samun 'karin girma yake yi a wajen aikinsu. watan su takwas da aure suka shirya tafiya xuwa garin 'Dan batta, saboda tunda suka yi aure babu wanda ya kawo musu xiyara idan ba Baffansa ba, don haka ya d'auki mota suka tafi, ya kuma yi musu siyayyar kaya masu yawa, ya siyawa Baffansa shadda su inna karime da Habi da matan su isa,ya siya musu atamfofi masu kyau da tsada, sannan ya siyawa su isa yarduka masu kyau da tsada. yana yin parking da motarsa 'yan garin suka ri'ka xuwa suna masa barka da xuwa, sun yi mamaki had'e da farin cikin ganinshi, da yadda lokaci guda ya canja, kyansa ya fito ya xama babban Alhaji mai ji da kansa. kai tsaye cikin gida suka shiga, malam ne ya hango su daga nesa, yana can yana gyarawa tumakansa turke, da hanzari ya 'karaso yana musu barka da xuwa, innah karime ya fara kwallawa kira, ita ma da sauri ta fito tana lalle maraba da ba'ki, a tuaninta wasu ne daban, amma tana ganin Mahmoud ne sai ta ja baya ta tsaya, nan da na fuskarta ta canja daga farin ciki xuwa akasin shi,kamar wacce aka aikowa da mala'ikan mutuwa, yamutsa fuska ta shiga yi gami da turo baki, har 'kasa Mahmoud ya tsugunnah ya gaidata, a wula'kance ta amsa, sannan ya gabatar da ita a wajen Rehab ita ma risunawa tayi ta gaisheta cikin harshen larabci, abinka da wadda bata jin yaren sai bude ido kawai take yi, kamar an girgiza 6era a buta,sakin baki tayi tana mamakin yadda Mahmoud ya canja ya samu cigaba a 'kan'kanin lokaci, nan fa hassadarta ta tashi, ta fara magana ranta a 6ace wannan kuma wacece mudi, ina xaton kamar karuwarka ce ko??Baffa ne ya katse mata magana,kayya!! kayya!! kayyah inna matarsa ce fa, kin riga kin sani har goran d'aurin aurensu sai da aka baki, ke da kanki da hannunki kika ri'ka rabawa. To goranta min d'an nema, ka kawo kanka duniya ban isa na fadi gaskiyar abinda na gani ba ko? shiru Baffa yayi mata saboda ya ga yadda ta fusata, idan yayi magana xata iya tsine masa, Habi ce ta fito da alama daga bacci ta tashi, tana ganinshi ta ja da baya kamar wadda taga dodonni,da alama ita ma mamakin ganin mahmoud da matarsa take yi, tambayar inna karime take, innata wannan tsohuwar guxumar kuma daga ina?yadda kika ganta nima haka na ganta inji inna karime, watakila irin takurun nan ne na saudiyya ya taho muku da tsarabarta suka bushe da wata irin dariya, ita dai Rehab kallonsu kawai take yi da ido, Mahmoud ne ya gaji da irin cin fuskar da suke masa shi da matarsa, dan haka ya ja hannunta suka koma soro inda a nan ne Baffa ya yi musu shimfida, ha'kuri Baffa yake bawa Mahmoud da matarsa a kan halin su inna karime. "kayi hakuri mudi, ko a yanxu Allah ya nuna musu iyakarsu, ka fi 'ya'yansu komai na rayuwa da kai da matarka, don haka kada ka damu da duk wani sharri ko hassadar da xasu nuna maka, hakan baxai cutar da kai da komai ba,sai ma dai d'aukaka da xai 'kara maka kai da iyalanka, kuma ka xama mai kyautatawa matarka kaga dai 'kauna ce tasa ta bar iyayenta taxo wajenka, to ka ri'ke ta da amana da gaskiya, kuma ka ri'ka hakuri da kawaici da dukkan gaxawarta, kada ka xamto mai kaushin hali a gareta, saboda ita mace an halicceta ne daga 'kashi mafi karkacewa, idan aka takura mata sai ta karye, ina yi muku fatan Alkhairi Allah ya baku xaman lafiya da yalwar arxiki, kuma ya kamata ku tashi ku tafi don bana son ku yi dare a hanya. mahmud ya ji dadin nasihohin da Baffa yayi masa, hannu yasa a aljihu ya mi'kawa masa rafar 'yan d'ari biyu, godiya mai yawa yayi masa sannan suka yi sallama suka tafi. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *ke uwa ce ta gari, da kowane d'a xai yi alfahari da sàmunki a rayuwa muna godiya da yadda kike ji da mu,ki ke kulawa da mu, kike damuwa da dukkan abinda ya damemu, muna yinki, muna alfahari da ke, kuma muna sonki Auntynmu MUNEERAH ABBAH WAKEELI DANDAGO jeeddah tace ana mugun tare🤝kuma wannan page gaba d'ayanashi naki ne halaka malak* 1⃣8⃣ Hanyar kano suka d'auka, xuciyar Mahmud sai tafasa take yi saboda jin xafin maganganun su innah karime, godiya ya yi wa Allah da yasa Rehab bata fahimtar abinda suke cewa, shirun da Mahmud yayi ne,shi yasa Rehab ta fara yi masa hirar kyautatawar da wata ma'kociyarta Ke yi mata, da yadda ta jawota a jiki ta xama tamkar 'yar da ta Haifa a cikinta, Mahmud ya ji dad'in yadda ta saki jiki take mu'amala da jama'a, haka suka isa gida cikin farin ciki da Walwala. A 'yar wannan xiyarar da suka kai 'Dan batta har Rehab ta fara gane yadda inna karime da Habi ke 'kin Mahmud, tambayar shi tayi dalilin da yasa suke masa haka, har da ita ba'kuwar da bata dad'e da xuwa ba, amma Sam Mahmud ya'ki xancen ya nuna mata ba komai, suna masa haka ne saboda shi ne 'karami suna son ya tashi da tarbiyya, murmushi tayi ta kalle shi kawai, amma ita kanta tasan ba haka abin yake ba, kawai yana 6oye mata ne. A Kwana a tashi Yau Mahmud sun Kwashe shekaru biyar da aure inda Allah mad'aukakin sarki ya axurtasu da haihuwar 'Ya'ya biyu Nauwar wadda ita ce Babba sai kuma 'kaninta Muhammad wanda ake kira (fu'ad), duk wannan haihuwar da Rehab tayi babu wanda ya ta6a xuwa barka daga 'Dan batta, Baffa ne kawai yake'kokarin xuwa yaga jikikonsa, Rayuwa suke yi mai cike da farin ciki da ban sha'awa. *BAYAN SHEKARA GOMA SHA HUDU* A kullum Mahmud dad'a samun arxi'ki yake yi da 'karin girma, don har ya yi gidansa na 'kishin kansa wanda ya gina shi a unguwar Nasarawa GRA (Dawaki road) a yanxu babbar 'yar su nauwar tana da shekara goma sha biyu, 'kaninta fu'ad na da shekara Tara, ganin yadda Allah ya axurta Mahmud ne da dukiya mai yawa, shi yasa innah karime da Habi suka kudiri aniyar mallake shi, da dukkan abinda ya mallaka a rayuwa, don ya dawo 'kar'kashin ikonsu sai yadda suka yi da shi, yawon Bokaye da 'yan bori da malaman tsibbu suka fara yi, duk don su cimma burinsu na mallakar Mahmud har abada, sun shirya tattaki har 'kasar Niger don su had'u da wani Boka wanda ake kira *Gobe da nisa*, wata 'kawar Habi da ake kira gwaggo sa'ade ita ce xa ta yi musu jagora har wajen Bokan, saboda a cewarsu rehab ta mallake Mahmud sai yadda tayi da shi. Kwana biyu suka yi a hanyar xuwa Niger suna tafiya, saboda Nisan garin da xasu shiga, ko sallama basu yi da Baffa ba sai filin gidan ya tarar. A wani 'kauye suka sauka, don a nan ne xasu samu wadda xata yi musu jagora har gurin *Gobe da nisa* da sassafe suka tashi suka fara haramar tafiya, Satinsu guda a hanya suna keta 'kauyuka da dajuka, ga abubuwa masu had'ari da suka ri'ka karo da su, amma hakan bai sa sun saduda sun koma gida ba. A ranar da suka cika Kwana takwas da tafiya, suka isa 'kauyen da Gobe da nisa yake, ba su suka kai tsibirin da yake ba, sai bayan sallar la'asar ga gajiyar tafiya da suka d'akko ga yunwa da suka Kwaso Wani 'katon dutse suka gani manyan kattin maxa na kawaye da shi, tun daga nesa suka hangosu suka daka musu wata tsawa mai ban tsoro, har sai da suka fad'i don firgici da tsoron da ya kamasu, tambayarasu suka yi a kan me ya kawo su, gwaggo sa'ade ce ta bashi amsa mun xo wajen alagafarta malam ne, sake xare mata jajayen idanunsa yayi sannan ya bata amsa da ya shiga aiki baxai sake fitowa ba sai Gobe da safe, Idan har suna da bu'katar ganinsa sai dai su jirashi har ya fito. Shiru suka yi ba abinda jikinsu ke yi sai karkar wa saboda sun gama tsorata da mutanen Sam babu annurin imani a tattare da su, umarni ya basu da su tashi daga inda suke kowaccensu ta tsugunnah ta kuma sunkuyar da kanta, har xuwa wayewar gari, saboda a cewarsu aljanun gurin basa son kallo ido cikin ido, kuma dokarsu ce ba a xama haka sai an sunkuyar da kai, haka suka sunkuya xuciyar su cike da fargaba, sun dad'e basu ga mutane irin Wadannan ba, saboda siffarsu tamkar ta arnan daji take. A haka suka kasance kawunansu a sunkuye har Allah ya Wayi garinsa, da sassafe aka yi masu ixni da su shigo su gana da shi. 'Kofa aka bud'e musu wata 'katuwar Bukkah suka tarar, duk an Kewaye jikinta da layu da fatun namomin daji daban-daban, da sallama suka shiga ciki tsawa ya daka musu," kun 6ata mana aiki kun cuci kanku,ba a yi mana sallama a nan, ma son sallama, Ku juya Ku fita da baya da baya, baxan kalleku yau ba, inna ce ta fara bashi hakuri ya xare mata jajayen idanunsa, jikinta na rawa ta ja bakinta tayi shiru, haka suka juya a tsorace da baya da bayan har suka fice daga gurin. Sai da suka fi awa hud'u da fita sannan ya sake yi musu umarni da su shigo. Da baya da baya suka ri'ka shigowa d'aya bayan d'aya,nuni yayi musu da su xauna a kan buxun, "me ke tafe da Ku?ya tambayesu cikin wata murya mai ban tsoro" kallon kallo suka fara yi, kowacce na xungurar yar uwarta a kan ta fara bayani,saboda kwarjini da ban tsoron da mutumin yake da shi, inna karime ce tayi ta maxa ta fara bayani " mun xo ne a kan maganar wani jikana, so muke yi dama........."kafin ta 'karasa maganar ya dakatar da ita "innah ta fada mana komai, tun kafin ku xo an xayyana mana duk abinda kuke tafe da shi, kun kawo kukanku inda xa a share muku hawaye, xaku juya shi yadda kuke so, wani mudubi ya d'akko yana jujjuya shi sai ga hoton fuskar Mahmud ya fito a ciki, nan da nan ya fara kiran sunayen wasu manyan aljanu, wata tukunya ce ta fad'o tsakiyar bukkar wani haya'ki ne yake fitowa daga cikinta, ya mi'ka musu yayi, hannu biyu Habi tasa ta kar6a, bayanin yadda xa su yi da tukunyar yake musu " Ku je Ku binne wannan tukunyar a sabon kabari, amma kafin Ku binneta sai kun nad'eta da likkafani, duk yadda kuke so xa ku yi da shi, xaku juya shi kamar Waina, xaku sarrafa shi kamar ra'kumi da akala. Ku tashi Ku tafi bana bukatarku a nan". Ku juya da baya kamar yadda kuka shigo, godiya inna karime ta fara yi, daka mata tsawa yayi" wa yace ki gode mana? kina 'kara yi innah xata shanye miki 6argo sai dai wata ba ke ba, don haka ki kiyaye gaba, idon innah karime ne ya firfito ba abinda take iya cewa sai gyad'a kai da take yi, su Habi kuwa tuni suka fice suka barta a wajen. Tarar da su tayi an sake basu umarnin sunkuyar da kai, sannan aka umarce su da su canja hanya, kada su bi hanyar da suka biyo suka xo gurin, tafiya suke cikin daji babu abinda suke ji sai sautin kukan tsuntsaye, a tsorace suka cigaba da tafiya har Allah yasa suka iso wani d'an 'karamin 'kauye inda suka roki mutan garin da su basu gurin Kwana, da farko sun 'ki amincewa da kar6arsu, sai daga baya suka amince aka kai su gidan mai gari. Washe gari da duku-duku suka fara haramar tafiya ko karyawa basu tsaya yi ba, suka wuce gidan da suka sauka, bayan sallar axahar suka kama hanyar dawowa Nigeria. Sai bayan sallar la'asar suka isa 'Dan batta, malam Abdullahi suka tarar a bakin 'kofar gida yayi jugum yana tunanin halin da su innarsa ke ciki, duk ya rame yayi ba'ki abin tausayi, Kwana da Kwanaki yana nemansu shiru ba labarinsu, Yau ma wuni yayi yana kewaye gari duk jikinsa yayi la'asar, inna ce ta kira sunansa "Kai kan tace, da yake da wannan sunan take kiransa a mafi yawan lokuta, tunanin me kake yi haka? dagowa yayi a firgice ya tsugunnah, "na dad'e ina nemanku ina kuka shiga haka? Ba damuwarka bace sanin inda muka tafi, mi'ko min mu'kullina don bana son ka cika ni da shegen surutunka na banxa. Gida suka shige ita da Habi, kai tsaye d'akin inna aka shiga aka fara labarin gurin gobe da nisa "gaskiya Bokan nan gaske ne innah, Allah yasa dai aikinmu ya ci, mu mallake wannan shegen yaron mai mugun abu, kiga d'a tunda yayi arxi'ki ya guji kowa baya tsinana mana komai, tunda muke da shi bamu ta6a morar komai daga gareshi ba sai Wahala" "Shi yasa nace mu mai da hankali kanshi don so nake su nasiru su koma gidan da ya gina gonakin shi na nan kuma a bawa Isah ya cigaba da gudanar da harkokinsa, ni da ke kuwa duk can xamu koma, mu Kyale wannan banxan a nan" inji inna karime Dariya suka rika yi, oh!! Innah Allah dai ya sa mu yi galaba a kan yaron nan. Wa kike ganin xamu samu yaje yayi mana ha'kar nan a kabari innah? Bari Isah yaxo ko Audu nasan xasu iya yi, amma wannan shashan nasiru baxai iya ba tausayi ya masa yawa. Bayan sallar magariba Isah ya shigo a tsakar gida ya tarar da su, bayan sun gaisa suke fada masa abinda suke je yi Niger da aikin da suke son ya yi musu. Da farin ciki ya amsa yaji dad'in abinda suka xo masa da shi, don haka ko gidansa bai shiga ba ya saka 'yar shara ya ri'ka kewaye unguwa yana neman likkafani, a wajen wani mutum ya samu, ya wuce gida ya fara aikin nad'e tukunyar a ciki. Yana kammalawa ya mi'kawa innah karime da fara'arta ta kar6a tana sa masa albarka, shi kuma ya wuce gidansa da niyyar xuwa ya dawo, 'ya'yan gidan Audu ne suka shigo dauke da Kwanon abinci, mi'kawa inna abincin suka yi sannan suka cigaba da tsalle-tsallensu na yara, suna cikin wasan ne d'aya daga cikin yaran da ake kira musa yayi tsalle a kan tukunyar nan ta rugurguje. Innah karime na gani ta hau salati, nan fa ta hau yaron da duka da xagi tana tsine masa albarka, jin haka yasa Habi ta fito a guje tana tambayar abinda ya faru,"Wai a ce duk Wahalar da muka sha ta xuwa gurin Bokan nan da Kwanakin da muka shafe muna tafiya a ce wannan shegen yaron ya xo ya fasa mana tukunyar nan" kuka ta fashe dashi. A dai-dai lokacin da suke maganar ashe malam yana soro yana jinsu, sai da ya ji dukan da suke yi wa yaron yayi yawa sannan ya shigo ya basu hakuri, komawa kanshi suka yi suna xagi, a kan cewa shi ne ma yayi adduar da hakan ta faru, mallake Mahmud dai ba fashi, wucewa yayi d'akinsa ya kyalesu suna ta yi masa bala'i. Yana shiga ya lalubi waya ya fara kiran Mahmud ya shaida masa sharrin da su innarsa suke shirin 'kulla masa, ya kuma gargade shi da ya dage da addua da neman tsari shi ma yana nan xai taya shi, godiya yayi masa sannan suka yi sallama. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 I Owe this all to you Hubby! my life would have never been this happy if you had not been there to save me. You saved me from myself and all my mistakes. You gave me another chance to be worthy of someone again. I love you with all my heart and I can never imagine my life without you. I dedicate this page to you💞 *MUSTAPHA MUKHTAR*😘 *Gaisuwa ta musamman gareki yar uwa NUSAIBA ABDULLAHI GALADIMA, jeeddah ta gode da 'kaunarki gareta* 1⃣9⃣ *A* fusace Isah ya shigo, saboda takanas ta kano innah ta taka, taje har gidansa ta sanar da shi, aika-aikar da Musa d'ansa ya yi musu, shi ma dukan yaron ya ri'ka yi kamar baxai barshi da rai ba, sai da 'kyar Habi ta kar6eshi. "Cuta ce dai yaron nan ya cuce mu ya gama da mu, shekarar arxi'kin mu ta kama, amma yaro ya yi mana ba'kin ciki, amma fa duk da haka baxa mu saurara ba, sai d'an nan ya xama mallakin mu, yanxu Isah babu dabarar da xa a yi a gyara tukunyar nan don Allah? wlh mun sha Wahala sosai a kan abin nan. "Babu yadda xa a yi innah, ta gama lalacewa sai dai mu yi ha'kuri. ko kuma ga Shawara, me xai hana gobe mu shirya mu je gurin wani Boka a bayan gari? "Ai kuwa abinda xa a yi kenan inji innah, Allah ya nuna mana goben sai mu fita da wuri don mu samu, mu gabatar da abinda muke so a kan lokaci. Amsa mata ya yi da amin, sannan ya tattara kan 'ya'yansa suka wuce gida. Yana shiga gidansa ko sallama bai yi ba, ya fara sababi yana fad'awa matarsa murja abinda ya faru, da yadda suke son yi wa Mahmud da iyalan sa, ita ma ta ji haushi sosai a kan abinda yaron ya yi musu, sannan ta 'kara 'karfafa masa gwiwar su sake komawa wajen wani Bokan, saboda ita kanta tana son ta samu canji ita da 'ya'yanta. ************************** Nauwar ce xaune a falo ita da Amminta suna karatun al-kur'ani mai tsarki, bayan sun idar suka yi addua suka shafa, sannan suka fara hirar duniya. "Ammina ina son ki fad'awa Abbana ya canja min school, saboda sam bana jin dad'in yadda Abbanmu yake kashe kud'i masu yawa a kan karatun mu, murmushi Ammi tayi. "Banda abin ki don an kashewa ilimi kud'i da yawa ai ba wani abu bane daughterna, ke dai ki taya Abbanki da addu'a, Allah ya 'kara masa yalwar arxi'ki, Amin tace, sannan suka cigaba da hirar duniya tana bata labarin 'kawayenta na makaranta suna ta nishad'i abin su. Sallamar wani matashin saurayi ne ya katse musu hirar da suke yi, matashin baxai wuce 25years ba, Irin samarin nan ne da ake kira FIRST CLASS. He is handsome, well dressed nd classic. Kana ganin shi xaka tabbatar da cewa jinin Rehab ne, don kamarsu d'aya da su Nauwar, kamar an tsaga kara, abu d'aya ne ya banbanta su da shi, He's chocolate in complexion, while su kuma farare ne 'kal. Ammi na ganin shi ta mi'ke tana mishi barka da xuwa, da gudu fu'ad ya 'karasa gare shi ya rungume shi yana oyoyo ya Hamdan, Where is the sweets you promised me? To cika ni mana sarkin rigima, ai na taho maka da shi, hannu ya saka a aljihu ya ciro masa sweets d'in ya bashi. Thank you ya Hamdan!! ya koma ya xauna kan cinyar shi yana ta farin ciki da ganin shi, ita kuwa Nauwar ko d'an kallo bai isheta ba, ta cigaba da kallon TV abinta. Tashi ya yi daga gurin da yake, ya dawo kusa da ita ya ja kunnenta, 'kara ta 'kwalla, Wayyo Ammina!! Fuskar shi a d'aure yake magana. " baki ga mutane bane?? kina ganina ki d'auke kan ki don ba ki da kunya ko? "Ka sakar min kunnena Ya Hamdan Allah ban ganka ba am sorry, oya get up ki bani juice a fridge, turo baki tayi, Allah ya Hamdan ban son tashi Idan ina kallon film d'in nan, dukan bakinta yayi, Wayyo bakina fa ka daka Yaya. xan fasa bakin da yake min rashin kunya ne. tashi tayi ba a son ranta ba ta d'akko mishi juice d'in ta kawo ta Ajiye. "Sai na ro'ke ki xaki xuba min ko?? I will deal with the hell in you,Idan kina min 'kiwa fa. "Harar shi ta fara yi da dara-daran idanunta, ta Mi'kewa tsaye tayi tana murgud'a masa baki, mai dukana sai dai ruwa yaro, a guje suka xuba ta fada jikin Amminta tana numfarfashi. "Me ke faruwa ta tambayeta? Ammi ki yiwa ya Hamdan magana ya........ A dai-dai lokacin ya shigo d'akin. "Khala Rehab yarinyar nan ta rainani da yawa, Kwana biyun nan rashin kunya take min kamar wani sa'an wasan ta. "To ba Kaine kake sa ni aiki ba, kaje kayi da kanka mana. Duka ya sake kawo mata, ta 'kara shigewa bayan Amminta ta 6oye. Ita dai Ammi dariya take musu, sannan ta yi mata fad'a a kan ta ri'ka girmama shi tunda dai yayanta ne ya girmeta nesa ba kusa ba. kuka Nauwar ta fara yi, "Ammi Sam bakya ganin abinda yake min, Allah ya tsaneni ya takura min,ta 'kara rushewa da wani kukan. Khalas share hawayen ki yi hakuri nace. Falo suka 'kara d'unguma suka koma aka cigaba da hira. Horn d'in motar Abbansu suka ji, a guje Nauwar da fu'ad suka fita, kowannen su 'ko'kari yake yi ya bud'e motar Abbanshi, yana fitowa suka rungume shi suna murna "oyoyo Abban mu suka fad'a a tare" "Yauwa dama ina ta jira ka dawo Abbana ya Hamdan ya sa ni kuka d'axu" "Ni kuma sweets ya bani Abbana" murmushi Abbansu ya yi, to duka na ji Ku sarakan surutu, mu shiga ciki sai a yi maganar a xaune xai fi ko. Dukan su da sallama suka shiga falon, d'ur'kuswa Hamdan ya yi ya gaida shi, Nauwar na ma'kale da Abbanta tana ta harar Hamdan, Idan ta harareshi sai ya gyad'a kai alamar xai kamata. Bayan sun gaisa ya yi sallama da su ya wuce gida. Abbansu ya d'an huta ya ji matsalolin yaranshi ne ya wuce part d'inshi, sannan ya sanar da Ammin su Nauwar yana son ganinta ,xasu tattauna magana mai muhimmanci da ita, umartar yaranta ta yi, da su yi alwala su yi shirin Kwanciya bacci, sannan tasa suka yi addua ta nufi sashin Mahmud. Cikin nutsuwa take takawa har ta isa gare shi, ruwan da ke a Ajiye a gabanshi ta tsiyaya mishi a cup, sannan ta xuba masa abinci ya ci, bayan ya gama ne ya fara mata magana. "Ina son ki taya ni da addu'a akwai abubuwan da suke tunkarar mu ko nace xasu tunkaromu, kuma abubuwan suna da had'ari a cikin rayuwar mu da ta 'ya'yanmu, kada na ja ki da nisa, jiya Baffa ya kirani a waya yake sanar da ni, irin makircin da su innah karime ke son yi mana mu da yayanmu, ba su da buri a yanxu banda su mallakeni da abinda na mallaka, sannan su rabani da ke, abinda nake so kada ki tada hankalin ki, kice xaki sa damuwa a ranki, duk yadda suka so cutar da mu sai Allah ya nufa abin xai same mu, kuma duk wanda ya dogara da Allah to Allah xai isar masa, nasan ke mace ce mai addu'a da dogaro ga Allah, ina son ki 'kara jajircewa sosai a kan wannan dabiar taki, kuma ki 'kara gargad'in yaran nan da kada su saki jiki da su innah, Kin ga yanxu Nauwar na da shekara sha hud'u a duniya, ta fara mallakar hankalin kanta xata iya fahimtar wad'ansu abubuwan. "Haka ne insha Allah xa mu dage da addua, Allah kuma ya karemu da karewar sa. Amsa mata yayi da Ameen sannan ta fara shirin Kwanciya bacci. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba dayan shi sadaukarwa ne gareka ABDULLAHI MUHAMMAD LAIMAJI, ina godiya a gareka Allah ya bar xumunci* *Ina mi'ka gaisuwar ban girma gareki ZAHRA'U ADO HUSSAIN SORON 'DINKI (MAMAN ISLAM) ina godiya da kulawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci, ya raya Islam a kan tafarkin addinin Islama da sunnar Annabi (S.A.W)* *Ina neman afuwar ku masu karatu saboda rashin ji na kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiyar da nayi, da fatan xaku min afuwa* 2⃣0⃣ *W*ayewar garin litinin, tafiya ta kama Abban Nauwar xuwa garin Abuja, domin gudanar da wata bita da gwamnatin tarayya ta shirya musu a can, da wuri Ammin Nauwar ta tashi ta had'a mishi break fast bayan ya kammala, ya bata umarnin kiran Hamdan a kan ya kai su fu'ad makaranta, saboda baya so driver ya riqa yawo da yaran shi, qarfe 7:00am ya wuce garin Abuja. A dai-dai lokacin kuma ta kira Hamdan ta yii sa'a kuwa yana gida, bai yi sammakon fita wajen aiki ba, roqonshi ta yi ya kai yaran makarantam bai musa mata ba ya d'auki mota ya nufi hanyar gidan su Nauwar. Da misalin 'karfe 8:00 ya 'karaso gidan, da sallama ya shigo falon da suke, samun yaran yayi har sun yi shiri, shi kawai suke jira,gaisawa ya yi da Ammin su Nauwar, sannan ta tambaye shi lafiyar mutan gidan su. da gudu fuad ya 'karaso ya rungume shi, "Alhamdulillah yayana nafi son dama ka kaini school" ni kuwa nafi son Abbana ya kaini inji Nauwar, kamar ma na fasa xuwa makarantar Ammi tana maganar tana kallon idon Hamdan" duk maganar da take yi Hamdan d'in na jin ta amma ko tanka mata bai yi ba, ya cigaba da wasa da fuad, jakunkunansu suka d'auka suka wuce mota. Gidan baya Nauwar ta bud'e ta shige ta kame abinta, shi kuwa fu'ad duk inda Hamdan yasa 'kafa yana biye da shi, gaban motar ya shige , har Hamdan ya xauna a motar ya fito, fuskar shi a d'aure yake magana "ni direbanki ne da xaki xauna a baya, littafinta take dubawa ko kallon shi bata yi ba, magana nake miki fa!! ya fad'i haka yana mai daka mata tsawa. a haraxane ta d'ago kai ta kalleshi yadda taga fuskarshi ta canja ba wasa, shi yasa idanunta suka cika da 'kwalla "yi hakuri yaya ban ji abinda ka fad'a min ba" "Ai yanxu kin ji ko? Gyada kai tayi alamar eh. "To oya dawo nan ki xauna. tashi tayi ta koma ta xauna, suna tafe yana mata masifa, a tsorace take a motar don haka ta 'kosa su isa makaranta ta huta da jarabar sa, ana xuwa bata bari motar ta gama tsayawa ba ta fito, ji kake kiiiiiiiiiiiiii! Motar ta goge mata kafarta, jini ne ya ri'ka xuba daga 'kafar tata, tashin hankali ne ya bayyana a fuskar Hamdan, Sunan Allah ya shiga kira, "subhanallah!! saurin me kike yi haka xaki je ki ji wa kanki ciwo, me yasa bakya son yin abu a nutse?? Shiru tayi ta kasa cewa komai sai fito da idanu take yi tana kuka. lalla6ata ya shiga yi kamar xai yi kuka, share hawayen naki ki daina kuka kin ji dear , Kin ga ciwon ba shi da yawa. nan da nan ya sungumeta sai asibiti aka yi treatment d'in ciwon, sannan ya dawo da ita gida, ranar fuad shi ma bai shiga makarantar ba saboda firgitar da ya yi. Kai tsaye daga asibiti gida suka dawo, Ammi na ganinsu, hankalinta ya tashi a xatonta wani al'amarin ne ya faru, Hamdan ne ya fara sanar da ita yadda aka yi, ita ma dai lalla6a Nauwar d'in tayi, ta kuma yi adduar Allah ya kare faruwar hakan a gaba. Ba su fi minti goma da dawo wa daga asibiti ba, suka jiyo hayaniya a bakin gate ana xage-xage, ana dukan 'kofar gidan , jin haka yasa Ammin Nauwar ta umarci Hamdan ya le'ka ya ga abinda yake faruwa, wata mata ya hango ta yi d'amara da mayafinta, tana fad'i in fad'a da mai gadi, a tare da ita akwai wani matashin saurayi wanda ba xai wuce shekara ashirin da biyar ba, nuna inda Hamdan yake tsaye take yi tana xage-xage, duk da baya jin abinda take cewa amma sai da yaji shakkar 'karasawa gareta saboda bai san da me ta xo ba, jikinshi a sanyaye ya isa inda take, a tunanin shi xai ga yarinya matashiya ce take wannan xagin da wannan tijarar, amma sai ya ga tsohuwa 'yar kimanin shekara 70, kallon mamaki yake mata ya kasa cewa da ita komai, ita kuwa sai ashariya take d'ungumawa tana nuna shi. "Ka kaini inda shegiyar matar da ta mallake min jikana take,don nayi maganinta, ta mallake gida, ta rabamu da abinda d'ana ya haifa mana, ga shi nan har ta kawo wannan d'an mai kama da buxaye, daga jin yanayin kalamanta ya tabbatar da cewa innah karime c Wacce khalarsa ta d'ad'e tana bashi labarin mugun halinta, don haka ya juya ya koma cikin gida, tausayin khalarsa ne ya kama shi, ya ma rasa ta yaya xai fuskance ta da maganar. Da sallama ya 'karasa d'akin ya iske Ammi tayi tagumi tana jiran labarin da xai xo mata da shi. yanayin yadda fuskar Hamdan ta canja shi ya tabbatar mata da cewa yana cikin damuwa, yana shigowa ta mi'ke, ta fara tambayar shi abinda ke faruwa, sunkuyar da kanshi yayi ya fara sanar mata cewa tayi ba'kar bakuwa ne daga 'Dan batta. Jiri taji yana 'ko'karin d'ibarta don haka ta nemi guri ta xauna ta fara tunanin ko da me innah karime ta xo mata, tasan dai ita tararuwa ce mai wutsiya ganinta ba alkhairi ba ne, banko 'kofar da aka yi ne,ya dawo da ita daga tunanin da take yi, inna karime ta gani tsaye a kanta, hannunta rike da 'kugunta tana jijjiga kanta da jikinta sai watsa mata wani mugun kallo take yi, mai cike da alamomin tambaya, tsugunnawa Ammi tayi gwiwoyinta har kasa ta gaisheta, dakatar da ita tayi. bana bu'katar gaisuwar ki irin tsiya,kin xo kin mallake min jika, kuma kin hana mu more shi da komai, banxa ta fadi wato har da gayyato yan uwa a xo a ci arxiki. Hawayen da take 'boyewa ne ya fara zuba a kan kuncinta, ha'kuri ta shiga bawa inna karime. "Mahmud d'anku ne duniya da lahira ban isa na raba Ku da shi ba, wlh na tabbatar da cewa Mahmud yana 'kaunarku, kuma kuna ranshi a kowane lokaci. "Kya fad'i haka mana munafukar banxa irin mugun abu, kun bi dare kun bi rana,kun bi bokaye, kun rabamu da d'an mu, mun tattaro mun dawo mu sa ido, mu ga tsiyar da kike shukawa jinin matsiyata" Kuka Ammin Nauwar ke yi kamar ranta xai fito ta bakinta, ganin hakan bai sa innah karime tayi shiru ta daina fad'ar abinda taga dama ba. Ganin haka yasa Hamdan yace da ita *Khalaty khalliha wa sha,aniha*kai yaro kar ka Xage ni gadon rashin mutunci, da mugun hali sai in tsine maka albarka Idan ka sake cewa wani abu. A dai- dai lokacin da inna ke magana ne Magaji d'an gurin Audu ya shigo, dama tare da shi ta taho. "inna xagin ki wannan d'an marasa mutuncin ya yi. hannu biyu ya warware da niyyar marin Hamdan, ri'ke hannun Hamdan yayi, tare da murd'e shi, har sai da yayi 'kara mai 'karfi sannan yace masa *kalli balak* shiga hankalin ka, wallahi tallahi sai na rama ni xaka yiwa targad'e ko? 'ko'karin kuma cakumar Hamdan da kokawa yayi, kafin ya 'karaso inda yake tuni Hamdan yayi kukan kura ya had'a Kansa da bango, sai da ya xane shi sosai, sannan ya Kyale shi, inna karime kuwa sai ihu take yi xa a kashe mata jika, Ammi da ta ga abin yafi 'karfinta, sai ta d'auki wayarta ta kira Abban Nauwar, ta fad'a masa abinda yake faruwa ransa ne ya 6aci sosai. " kar ki barsu su kwanar min a gidana ki d'auki 20,000 ki basu xan kira driver da mai gadi su fitar min da su, cikin Mintunan da basu fi uku ba sai ga driver da mai gadi sun shigo, sun cakumi Magaji innah karime tana ina xaku kai min shi?? ko kallonta basu yi ba, kawai hannu suka d'aga mata alamar ta biyo su, binsu tayi har bakin mota. a motar suka saka shi, ita ma ta shiga motar suka tafi, ganin haka yasa Ammi sakin gwauruwar ajiyar Xuciya, kud'in ta mi'kawa inna karime, fusgewa tayi tare da bawa Ammi mummunan kallo xaki gani da ni kike maganar. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Sadaukarwa gare Ku 'yan uwa rabin jiki NADEEYA BABA IBRAHIM, AISHA BALA ILU & AISHA ISMA'IL ISAH, Allah ya bar xumunci da kaunarka juna* 2⃣1⃣ Tunda Ammi ta koma d'aki ta rasa abinda yake mata dad'i, duk tunanin duniya ya mamaye mata xuciya, tsoro da firgici ne fal xuciyarta, sai ta kasa fad'awa su Hamdan abinda innah karime ta fad'a mata. nan da nan xaxxabi ya rufeta, gumi ne yake ta yanko mata, saboda ta san sharri da makircin innah karime, tasan ko kad'an ba 'kaunarta suke yi ba ita da iyalanta. Alwala ta d'auro ta fara jera salloli tana ro'kon Allah ya bata kariya ita da abinda ta Haifa. Bayan ta idar ne Hamdan ya lura da yanayin tashin hankalin da take ciki,tambayarta yayi " Khalaty me yasa naga yanayin ki ya canja gaba daya? kada fa ki sa damuwar wannan mahaukaciyar matar a ranki, har hakan ya cutar da ke, ki sa a ranki baxa ta miki abinda Allah bai 'kaddara miki ba. ke da ki ke da Allah wace damuwa ce xata dame ki, shiru tayi har sai da Hamdan ya gama nasihohinshi gareta. "Hankalina ya tashi da maganar da ta fad'a min lokacin da xata shiga mota ne Hamdan" Me tace miki? Ya tambayeta Xan gani tace min, kuma kasan sharrinta. "Au don. Wannan maganar ma ai ba abar d'aga hankali ba ce, alheri xa ki gani insha Allah, ki manta da ita kawai". Amsawa tayi da ameen suka shiga hirar duniya. Tunda su innah karime suka hau mota suke ta tsine wa Ammin Nauwar a tunanin su, ita ce ta bada umarnin a fitar da su daga gidan. "Innah wlh dole mu d'auki mataki a kan shegiyar matar nan, saboda na fuskanci ta gama shanye min 'kanin mahaifi ta gama mallake shi , ni fa innah so nake yi ma gaba daya rayuwata ta dawo gidan, don naga wata yarinya mau kyau ta min a gidan, kin ga Idan na dawo sai ki bani ita na aura, komai na ubanta ya dawo hannuna,kuma ita ma fa innah baxa mu barta haka ba, dole sai mun mallaketa. "Dadina da kai kaifin hankali Magaji, ashe kaima ka fara fuskantar halin da ake ciki, wannan matar da kake gani ba karamar shu'uma bace, dole mu tashi tsaye a kan d'an nan Idan ba haka ba xa mu ga ana yi babu mu, ga shi har d'an uwanta ta kawo ya ci arxi'ki mu kuma ko oho, Wai a ce har ya samu damar yin dambe da kai, saboda yana da d'aurin gindi, to wlh baxa ta sa6u ba, dole mu tashi tsaye. "To ai duk laifin ku ne innah, inji Magaji da kun fara yun'kurin yadda xa mu yi mu koma birni da rayuwa, amma kamar Wad'anda aka yi wa d'aurin baki ku ka yi Watsi da abin, Ku ka ma daina xancen fada d'aya" "Idan d'aurin bakin aka yi abin mamaki ne? Matar nan fa matsafiya ce na dad'e da sanin haka, a haka ne dai xaka ganta kamar mumina, tana rero xance wai ita ta Allah. Ai mun gamu tunda tayi mana haka, mu xuba mu gani. Hirar da suka yi ta yi kenan har suka isa 'Dan batta. Suna huci suka fito daga motar, ko sallama basu yi wa Wad'anda suka kawo su ba suka fito. Cikin gida suka shige ran su yana ta musu xafi saboda abinda suka je nema basu samu ba, kuma bu'katar su bata biya ba. Habi suka tarar tana ta faman surfe, yadda taga yanayin su ta tabbatar da cewa, ha'kar su bata cimma ruwa ba, ga shi kuma ta ga Magaji ri'ke da hannun shi yana d'ingishi, sakin tabaryar ta yi ta 'karaso gurin da suke. "Ya na ganku haka da wuri, kuma babu alamar Walwala a tattare da Ku?" "Ta Yaya xaki ganmu da Walwala an mallake min jika ya xama na wata daban, kalli hannun Magaji ki ga aika-aikar da wani shegen yaro yayi masa" "Xare ido Habi ta fara yi, Idan na yarda da abinda aka yi Wa jikana Allah ya tsine min, yaron nan ya ta6o bala'i da hannunsa, bai san mu ba labarin mu yake ji, shii yasa ya yi karmbanin ta6o mu, ai kuwa ya ta6o masifa. "Mu shiga d'aki inji innah abin xai fi dad'in tattaunawa, kada wannan munafukin ya shigo ya ji dad'in kai musu labari. 'Daki suka shige gaba d'ayan su, tattauna abinda ya faru suka fara yi, suka cigaba da la'antar Ammin Nauwar. innah ce ta fito da dubu ashirin d'in da aka basu ta mikawa Habi. "Wad'annan kudad'en kuma na menene? Habi ta tambaya" "Su ne wanda aka bamu aka kuma koremu, aka ci mana mutunci. "Gud'a Habi ta saki, ahayye Nanaye !! Innah da Wad'annan kudad'en xamu ya'ke su, gobe mu tashi da wuri mu shirya, mu tafi gurin Bokan da Audu ya fad'a mana Kwanakin baya, mu je mu xube masa naira yayi mana aiki, ko ya Ku ka ce? "Haba Habi wannan ai rashin hankali ne, inda muke cikin matsin nan, mu je mu xube wa Boka Wad'annan kudaden gaba d'aya, gaskiya baxai yiwu ba, ki ri'ka yin abu da lissafi mana. "Tunda baxai yiwu ba a barshi, kowa ya tafi neman 'yancinsa ni xan tafi neman nawa yancin da na jikokina, ke kuma ki xauna a nan, tunda kashe kud'i a nemi magani rashin hankali ne da rashin lissafi". "A'a uwar Audu ba haka nake nufi ba, yanxu dai ki fad'a mana yadda kike ganin xa a yi." Maganar da na fad'a da farko ita xa a yi Idan kin amince. Na amince mana Allah ya kaimu goben. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *ALMAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *yau shafin gaba d'aya naku ne masoya Almajirah, nauwar tana godiya da kaunar da kuke nuna mata* *mariya Balarabe Adam* *Xahra'u Ado Husain* *xainab Abbah* *Nusaibah Abdullahi galadima* *Ummu Ammar* *Bilkisu mai Gado* *Amina saminu (maman Yousuf)* *Maman Yusra* *Fatima Ali* *ina tare da Ku masoyana* 2⃣2⃣ Da sassafe suka yi shiri sai wajen Boka, tsaunuka da daji suka ri'ka ketawa, wani rami suka gangara wanda shi ne, xai kai su har gurin da Bokan yake, wani 'katon mutum suka hango a saman bishiya jikin shi sanye yake da fatar damisa, gashin kanshi kuwa a duddun'kule yake ya sakko masa har 'kasan wuya, wata tsawa ya daka musu sai da suka firgita gaba d'ayansu, me ke tafe da Ku!!! Ya tambaye su?? Bakin su na rawa suka amsa da "wajen mai gani har hanji muka xo" Nuni yayi musu da su wuce su 'karasa wajen da Bokan yake, suna shiga suka iske shi a tsaye, hannun shi ri'ke yake da wata xabgegiyar takobi, fuskar shi kuwa kamar an shafe ta da ba'kin tukunya, kallo d'aya xaka yi masa ka tabbatar da cewa babu hasken imani a tattare da shi, a tsorace suka 'karasa inda yake, tsugunnawa suka yi da niyyar gaishe shi, dakatar da su yayi da hannu alamar baya bu'katar gaisuwar su, nuni yayi musu su samu guri su xauna. Xama suka yi sannan ya nemi su fad'a masa abinda yake tafe da su. Innah ce ta fara magana ran Boka shi dad'e yaro ne da mu, Allah ya axurta shi amma matarsa ta shiga tsakaninmu da shi ta hana shi ya Mora mana komai, yanxu abinda muke bu'kata a d'ora mu a xuciyar sa, ya xamto baya jin maganar kowa sai tamu, sannan muna son a sanya masa tsanar matarsa da ta ya'yansa, sannan a hana shi jin 'kan mahaifinsa, ya xamto baya son su baya 'kaunar ganinsu ko kad'an, bu'kata ta biyu kuma a d'ora wa matar sa warin ja6a. Gyaran murya yayi, sannan ya bushe da wata irin dariya mai ban tsoro, wannan ita ce kawai bu'katar Ku, ya tambaye su yana mai xare musu jajayen idanunsa, amsa masa suka yi da eh!!. 'kasa ya dan'ko ya xuba a wata fatar damisa ya had'a musu da wata laya, layar yayi umarni da a jefata a cikin kogi, 'kasar kuma su ri'ka jikata suna wanka da ita, xai ji duk duniya babu Wad'anda yake 'kauna Idan ba su ba. Godiya mai yawa suka yi masa, sannan suka xari dubu goma a cikin kud'in da aka basu suka mi'ka masa. Suna isa gida suka kira Magaji ya xo ya kai layar da Boka ya ba su kogi, ba tare da 6ata lokaci ba, ya d'auki keke ya tafi, yana kaiwa bakin kogin yayi sa'a babu kowa a wajen don haka ya faki ido ya jefa layar cikin ruwa. Da farin ciki ya dawo gida ya sanar wa su innah nasarar da ya samu na jefa laya, murna suka ri'ka yi kamar Wad'anda aka yi wa albishir da gidan aljannah, ruwa Habi ta shiga dafawa tana kiran jikokinta da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai suna wanka da ruwan. Yau jama'a Abban Nauwar ya dawo daga bitar da ya je garin Abuja, ledodi ne ri'ke a hannunshi ya shigo gidan, da gudu yaranshi suka xo suka rungume shi. "Oyoyo Abbanmu mun yi missing d'inka" murmushi yake ta musu. "Nima ai nayi kewarku 'yan yarana" Karbar kayan shi suka yi suka raka shi har d'akinsa, Ammin Nauwar ya tarar tana sallar la'asar, don haka ya tsaya jiranta har ta idar da sallar. Jin kan shi yayi yana juya masa, jiri ya ji ya debe shi, har yana 'ko'karin fad'uwa don haka ya nemi kujera ya Kwanta a kanta. Nan da nan idanun shi suka kad'a suka yi jawur, jin shi yake kamar ba a duniya yake rayuwa ba. Sai ya tsinci Kansa baya son jin muryar ko wane bil Adama a kusa da shi, don haka ya rarrafa ya shiga band'aki ya kulle Kansa. Tana idar da sallar ta tambayi Nauwar inda Abbanta yake, sanar mata tayi da ya je toilet xai watsa ruwa, don haka tafi kitchen ita da Nauwar suka had'o masa kayan ciye-ciye da lemuka kala-kala, a tunanin su suna dawowa xasu tarar da shi ya fito amma sai suka ga sa6anin haka, xauna wa suka yi suka cigaba da jiransa amma bai fito ba har sama da awanni biyu. Gajiya Ammin Nauwar tayi ta fara 'Kwan'kwasa 'kofar band'akin, tsawa ta ji ya daka mata. "Bana son sake ganin wani a d'akin nan, kafin na fito kusan inda dare yayi muku, Idan ba haka ba gaba d'ayanku sai ranku ya 6aci. Mamaki ne ya kama su gaba d'aya, Nauwar ce tayi karfin halin yin magana. "Me ya faru Abbanmu waye ya 6ata maka rai?? "Ban sani ba, Ku fita nace Ku bar min d'aki wlh Idan na fito na sameku sai na sa6a muku. Hawaye ne suke sauka a fuskar Nauwar ita kuwa Amminta gaba d'aya ma ta kasa aikata komai saboda abin ya gama d'aure mata kai, tunda take da Mahmud bata ta6a ganin fushinsa ba, amma yau gaba d'aya ya burkice musu ko 'yar tasa ma da ya fi so baya son ganinta. Rarrashin Nauwar take yi sannan ta lalla6ata suka fita daga d'akin. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* Maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *DUK A INDA NAKE KO NA KASANCE KUNA RAINA MASOYANA INA SONKU INA GODIYA DA 'KAUNARKU GARENI, ALLAH YA BAR XUMUNCI* Ameenah Nasir Zainab Muhammad Hafsee Maman Humaira Asma'u Abubakar Lolo Meena luv Haleemah MK Hindatu A'kilu Sabo Aysha Muhammad Hauwa Tijjani *Muna mugun tare*🤝 *WANNAN SHAFIN GABA 'DAYA NAKI NE 'YAR UWA RABIN JIKINA* *SALEEMAH SAMMANI BABA, INA YINKI INA 'KAUNARKI'YAR UWATA, ANA TARE*💯🤝 2⃣3⃣ Falo suka dawo gaba d'ayan su suka xauna, sun yi jugum-jugum dasu, saboda jimamin canjin da suka samu daga Abbansu, wayar da ke gefen su ce tayi 'kara, gaba d'aya suka mayar da kallon su gareta, wadda ita ce ta katse musu shirun da suka yi, Hamdan ne ya kira bayan sun gaisa ya sanar musu da xuwan maminsa, farin ciki ne ya bayyana a fuskar Ammin Nauwar, tayi murna da xiyarar da xata kawo mata, saboda sun jima basu had'u ba, kasancewar Baban Hamdan mutum ne mai kulle, addu'a tayi musu Allah ya kawo su lafiya, sannan ta ajiye wayar. Kitchen ta shiga ita da Nauwar suka had'a musu delicious, sannan suka Jere musu a kan dining. Sashin Abbanta Nauwar ta shiga, samun shi tayi xaune kan kujera ya had'a kai da gwiwa, sallamar da tayi ne yasa ya d'ago kanshi yana ganin ita ce ya mai da kanshi 'kasa, d'aga mata hannu ya yi ya dakatar da ita. "Kada ki fara 'karaso min nan, fad'i duk abinda kuke bu'kata na sallame ki, warin ki ya cika wajen nan gaba d'aya, ki fad'i ko menene ki 6ace min da gani. Hawaye ne suka fara sauka a fuskar ta, ba abinda nake bu'kata a gurinka Abbana sama da dawowar farin cikin ka da Walwalarka tare da mu, ka daina kula mu ka daina son ganinmu, me muka yi maka Abbanmu??mu nemi gafara ka yafe mana, kai kad'ai ne rayuwar mu wanda muke kallo a kowane lokaci mu yi farin ciki, mu da Ammin mu, me yasa ka canja mana lokaci daya Abbana??? Kuka mai tsanani ne ya kufce mata Ya tausayawa 'yar tasa, musamman da yaji Wad'annan maganganun daga gareta, gaskiya Nauwar yarinya ce mai hankali yanxu har ta fahimci halin da nake ciki na 'kunci da rashin son ganin su. Ganin mahaifin nata ya shiga tunani ya kuma kasa bata amsa, sai ta 'kara rushewa da kuka, 'karasawa kusa da shi ta yi, ta ri'ke 'kafar shi tana cigaba da ro'kon shi ya yafe musu. Hawaye ne ya ri'ka sauka a kuncin sa, tallafo fuskarta yayi da hannunsa, yana kallonta yana'kara xubar da hawaye, ji yake gaba d'aya ya tsani kan sa, ya tsani rayuwar duniyar ma gaba d'aya. Magana ya fara yi mata bakin shi yana rawa "Wlh ina sonku 'yata, ban San me yasa na Wayi gari a cikin tsanarku ba, xuciyata tafasa take yi idan na d'ago ido na kalleku, xamana ni kad'ai ba tare da xama tare da Ku ba, shi ne Kwanciyar Hankalina, Ku gafarta min Ku cigaba da hakuri da ni a duk yadda ku ka sameni, ni dan Adam ne, Ku ri:ka yi min uxuri, kuma Ku tayani addu'a Allah yaye min abinda yake damuna. "Mun yafe maka Abban mu, kuma baka yi mana komai ba, ka kula da mu ka so mu, kuma insha Allah xamu cigaba da addu'ar Allah ya yaye maka matsalolin ka. Kuka suka ri'ka yi gaba d'ayan su babu mai iya rarrashin wani a cikinsu. Tausayin mahaifinta ne ya kamata,nan da nan ta ji xaxxabi ya rufeta don haka ta tashi ta koma wajen mahaifiyarta. Tana shiga ta sameta xaune kan sallaya tana addu'o'i,ganin yadda yanayin 'yar tata ya canja, ga fuskarta tayi jawur alamun tasha kuka ta koshi, shi yasa ta mi'ke ta tare ta hnkalinta a tashe take tambayarta abinda ya faru da ita. "Hawaye ta shiga sharewa ta xayyane mata yadda suka yi da mahaifinta, ita ma dai ha'kuri ta bata ta kuma rarrasheta a kan su cigaba da addua komai mai wucewa ne. Tsayawur mota suka ji, don haka suka fito gaba dayan su waje saboda sun San ba'kinsu ne suka samu iso wa, 'karasawa suka yi garesu rungume juna suka yi suna farin ciki, d'unguma suka yi gaba d'aya suka shiga ciki. Kayan abinci aka halarto musu da shi suna ci suna hirar yaushe gamo. Ita kuwa Nauwar na gefe tun daga gaisuwa bata sake cewa da kowa komai ba, kallo d'aya xaka yi mata kasan tana cikin damuwa, magana Amminta tayi mata. "Kira Abbanki kice masa mamin su Hamdan taxo xa su gaisa. Kamar Wacce Kwai ya fashewa a ciki haka ta tashi ta tafi kiran shi, tarar da 'kofar dakin shi tayi a rufe don haka ta dawo ta sanar da Amminta. Tashi Ammin tayi da kanta ta je ta samu 'kofar tashi a kulle, kamar yadda ta fad'a mata, Kwan Kwas 'kofar ta ri'ka yi, amma ya yi banxa da ita, ta fi Minti 30 tana bugu bai bud'e ba, sai da ya gaji da bugun da take yi ya taso a fusace ya fara masifa. "Me kike so ne a tare da ni,da kike bibiyata haka?, kin turo 'yarki d'axu duk bai isa ba sai kin xo da kan ki. yanxu kuma me kike son nayi miki, wlh idan har ku ka takura min xan yi yaji na bar muku gidan gaba d'aya, kun dameni, ke warin ja6a 'yarki ma abinda take yi kenan. kada Ku 'kara xuwa inda nake ko da wasa, Idan kuma ku ka sake yi, xan nuna muku 6acin raina, kin ji na fad'a miki. Mayar da 'kofar d'akin ya yi ya kulle ya barta da ciwon xuciya. Hawaye ne cike da idanunta,don haka ta kasa fadawa ba'kin dalilin rashin xuwan sa su gaisa, ganin yadda ta canja lokaci d'aya daga farin ciki xuwa akasinsa ne, yasa suka tambayeta abinda yake damunta, amma sai ta'ki fad'a musu tace ba komai, don haka suka 'kyaleta suka bud'e wani babin hirar. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆 🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* Maijiddatijjania dam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *sadaukarwa gare Ku 'yan uwa na amana ina godiya da gudunmawar ku gareni* *MAIJIDDA BELLO* *UMMU EL-NAJEEB GYARA KANKI* *FEENAH YAHYA (feenah berry)* *RAHMATULLAH MAMAN UMMY* *JUMANA AHMAD* *JAWAHEER SALEEM* *ASLAMIYYA ISLAM* *MAMAN IKRAM* *INA YIN KU KUMA MUNA TARE HAR ABADA* *gaisuwa ta musamman gare ki Takwarata kuma aminiyata* *MAIJIDDA SALEH* 2⃣4⃣ Haka suka cigaba da kasancewa a cikin gidan yau da dad'i gobe ba dad'i, ba wani kyautatawa tsakanin su da shi, sai tsangwama da cin xarafi ne kullum ke biyo baya, yanxu ta kai ta kawo ko hidimar makaranta ya daina yi wa yaran sa, komai sai dai Ammin su tayi musu, gaba d'aya ya burkice ya xama wani irin mutum Mara dad'in kai. Safiyar ranar asabar ya sanarwa da Ammin Nauwar xai je 'Dan batta, addu'a tayi masa sannan ta bashi kud'i da shadda ta bayar a kai wa Baffa, ita ma Nauwar turare ta d'akko ta bashi ya bai wa kakanta, saboda ta sha'ku da Baffa suna son shi, a ko da yaushe ba su da burin da ya wuce su je su gaishe shi, amma basa samun goyan baya daga Abbansu. Mota ya d'auka ya fice sai 'Dan batta, tarar da gidan yayi ba kowa, don haka ya xauna don ya jira su, bai dad'e da xuwa ba, ya ji sallamar Baffansa, don haka ya mi'ke da sauri ya isa inda yake, fuskarsa a sake ya gaishe shi. "Ina Kwana Baffa "Lafiya lau ya iyalin naka" "Suna lafiya, gurin xama ya ba shi suka karasa gaisa wa. ga wannan kayan da kud'i, tace na baka ga kuma turare Nauwar ce ta baka. "Lallai amaryar tawa tana yi da ni, yaushe xaka kawo min su na gansu ne, na dad'e fa rabona da yaran nan. "Xa su xo insha Allah Baffa makaranta ce take tsare su, shi yasa basa samun damar kawo maka xiyara a Kai a Kai amma suna nan xasu xo insha Allah. To Allah ya kawo Ku lafiya, ai yana da kyau a mai da hankali wajen karatun yaran, Allah yayi jagora. Amsawa yayi da Ameen. Godiya mai yawa Baffa yayi masa, sannan suka fara tattaunawa a kan dad'ewar da yake yi bai kawo masa xiyara ba. "Wlh matsalar gurin aiki ne Baffa amma ai kana raina insha Allah xaka ri'ka ganina" "To Allah ya taimaka, ameen yace sannan suka cigaba da hira, yana bashi labarin girman da su Nauwar suka yi, yana ta farin cikin yadda iyalan d'an nasa suke cikin Walwala da Kwanciyar hankali. Inna karime suka hango, ta dawo daga unguwar da ta tafi, tun daga nesa ta gano Abban Nauwar, sai bud'e masa baki take yi, Baffa yayi mamakin ganin hakan daga gareta saboda yasan a da ko 'kaunar ganinshi ba ta yi, don haka ya saki baki yana ganin ikon Allah. "Yau muna da manyan ba'ki a gidan namu kenan, barka da xuwa Alhaji Mudi, ya Kwana biyu, ka ya da mu gaba d'aya, d'an le'kowar da kake yi a gaisa duk ka daina. Ita ma dai uxurin aiki ya bata, sannan ta tashi ta shiga d'aki ta kawo masa fura, kafin ta kawo masa sai da ta 'kara barbad'a garin maganin da suka je wajen wani Boka ya basu. "Ga wannan Alhaji Mudi, ka sha hanya kuma nasan baka sa komai a bakin ka ba. ai kuwa dai innah, kamar kin San ina jin yunwa ji nake yi kamar an min sata a cikina. Hannu biyu yasa ya kar6i furar, ya fara sha, Baffansa bai so ya sha furar ba, amma babu yadda xai yi ya hana shi sha, saboda ta tasa shi a gaba, yana sha tana masa dad'in baki, idan ya ce xai hana shi sha, tsaf xata iya la'antar sa, don haka yayi hakuri ya Kyale, yana ta nemar masa tsari daga tarkon sharrin da suke son d'ana masa. Sai da ya shanye furar tas sannan ya mi'ka mata Kwanon ta kar6a, tana sa masa albarka Yana gamawa ya mi'ke don yin sallama da Baffa rafar 'yan 100 ya mi'ka masa godiya ya rika yi masa yana sa masa albarka. Ganin inna karime suka yi d'auke da tarin kayanta a hannu, tambayar ta Baffa yayi. "Ina xuwa haka innah na ganki da tarin kaya a hannu? "Birni xan koma na ci arxi'kin jikana ko kana ba'kin ciki ne? tana maganar tana yarfa masa wani matsiyacin kallo. "Innah a ganina kamar lokacin komawar ki bai yi ba , ki bari Allah ya kaimu bikin Nauwar mana ba sai ki je kiyi Kwanakin da xaki yi ba, amma idan kika koma yanxu ai kamar da takura ko, kuma xa a shiga hakkin iyalansa, tunda Kinga gidan na xaman mutum d'aya ne. "To sarkin tsari xaka fara jero xancen naka ko? Gida dai ba naka bane, gidan jikana ne yadda kake da gado nima haka nake da shi, don haka dole na koma" "Shi dai Mahmud murmushi kawai yake yi, ba komai Baffa ka bari mu je da ita d'in ba wani abu". Xuciyar Baffa ba dad'i haka suka wuce suka fita daga gidan. Kayanta ya kar6a ya saka mata a cikin mota ita kuma ta shiga gidan Audu a guje ta kira Magaji, tarin tsummokaransa ya d'akko ya xuba a motar sannan suka d'auki hanyar xuwa Birni. Suna shiga gidan su Nauwar ta yi tsalle ta shige Falo ko kayanta bata tsaya d'auka ba, tarar da su tayi suna kallon film, sai ganinta suka yi ri'ke da 'kugu tana jijjiga jiki, innalillahi Wa innah ilaihi raji'un shi ne abinda Ammin Nauwar ta fad'a. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *yau dole na ci burki na mi'ka gaisuwa da jinjina gare ku 'yan uwa na amana, muna mugun ji da ku, gami da alfahari da ku a gidanmu na EXCLUSIVE, gidan dad'i da hadin kai, kuna raina muna mugun tare, har abada baxan manta da ku ba* *UMMY XIE* *REAL KHADY* *ACTION BABY* *ina yin ku yasin*😍 *ina mi'ka godiya gareki yar uwa ta jini SUWAIBA USMAN ADAM'S JOS, jeeddah tana godiya da yadda kike ji da ita* *wannan shafin gaba d'ayan shi naki ne uwa ga Yusuf kina yi muna jin dad'i, kina bari muna jin haushi, makiyanki fadawanki, murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya, ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO, Allah ya kara miki basira da haxaka* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 2⃣5⃣ Kallonta tayi ido cikin ido, tana jefa mata wata mummunar harara, tunda Kin ga masifa da bala'i, ai dole ki nemi tsari dani. da uwar ki ce taxo nan xaki yi mata abinda kika min yanxu? Saboda kin rainani ba ni da daraja a idonki xaki dubeni ki yi min ta'awixi, don baki san daraja da mutuncin furfurar tsohuwar wasu ba ko?nasan dai duk ba'kin cikin ganina kike yi, kuma xama daram, naxo naga abinda kike shukawa ke da yaranki marasa tarbiyya, ko tanka mata Ammin Nauwar bata yi ba, haka ta cigaba da balbala masifa. A dai-dai lokacin da take fad'an ne Abban su Nauwar ya shigo hannunshi ri'ke da taummokaran da suka taho da shi, Magaji na biye da shi a baya. Me ke faruwa innah, naji hayaniyarki har waje, wane ne ya ta6a min ke? Fashe wa innah karime tayi da kuka, wlh Alhaji Mudi tunda na shigo gidan nan, yaran nan da uwar su, suka had'u suna xagina, Wai naxo daga'kauye ina warin daddawa xan 6ata musu gida, suka had'e min kai suka min xagin tsakar nama. Yana jin abinda ta fad'a na 'karya da gaskiya ya hau fad'a, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ri'ke mata hannu ya yi, ya xaunar da ita a kan kujera, kuma yayi al'kawarin duk wanda ya kara 6ata mata rai a cikin yaran sai ya kore shi daga gidan, shigewa ya yi ya shiga 6angaren shi. 'Kafa d'aya kan d'aya ta d'ora tana harar kowa d'aya bayan d'aya, kad'an ku ka fara gani In dai ina nan, xaku bada labari da kan ku nice tuwon tulu mai wuyar Kwashewa, kuma carbin Kwai mai wuyar ja. Nauwar ce ta mi'ke ta matsa kusa da mahaifiyar ta, Ammina wai wannan kaxamar masifaffiyar tsohuwar daga ina?naga taxo tana mana wasu halaye, tana son ta hargitsa mana gida ta hanamu jin dad'in mahaifin mu, to dai-dai mu ke da ita, duk abinda taxo da shi xa mu yi mata maganin shi, xa mu koya mata hankali, ta ja tsaki ta kuma dubi innah karime ta Kwad'a mata wata uwar harara. Sakin baki tayi tana kallonta, ta cika da mamakin yadda yarinya 'karama ta fad'a mata magana, ta kuma kasa mayar da martani. Magaji ne ya tashi a fusace ya falla mata mari ji kake tasssssss!!!! Innar tamu ki ke xagi,saboda kunya ta miki 'karanci, uwar ki ta koyar da ku rashin tarbiyya, wlh ki shiga hankalinki, a kan tsohuwar nan xan iya karya ki naga wanda ya tsaya miki. Dafe kuncinta tayi tana jin rad'ad'in marin da yayi mata, d'aga hannu tayi xata rama, Amminta ce ta dakatar da ita, don haka ta kyale shi, amma ta ci alwashin duk daren dad'ewa sai ta rama, don baxai mari fuskar ta a banxa ba. 'Daki ta shige ta fad'a kan gado,tayi kuka kamar idonta xai fad'o kasa, ta tabbatar tunda tsohuwar nan ta dawo gidan su, sun shiga uku, sun fad'a halin tsaka mai wuya ita da mahaifiyar ta. Haka ta kasance har bayan magariba bata sake fitowa falon ba, a d'aki take gabatar da sallolinta, tana addu'ar Allah ya kawo musu mafita. Fu'ad ne ya shigo sallama yayi sannan ya samu gefen gadon da take ya xauna. "Wai har yanxu kuka kike yi Yaya Nauwar? Kiyi ha'kuri da abinda Magaji yayi miki, ina nan xan rama miki, yanxu na Kyale shi ne saboda idan na kula shi xan yi sanadin 6acin ran Ammin mu, kiyi hakuri my sister. Share hawayen tayi na gode little brod, amma fa sai mun tsaya tsayin daka mun 'Kwatarwa Ammi ha'k'kinta, naga alama suna son mayar da mu ba komai ba a cikin gidan nan. "Gaskiya ne maganarki amma mu bi komai a sannu, kuma mu ri'ka addu'a saboda naga da shirin sharri ta shigo mana. Muryar Hamdan suka ji don haka gaba d'aya suka fita falon dan su tarbe shi. "Babban aboki oyoyo, inji Hamdan, hannu ya mi'ka masa suka gaisa, ya school d'in ya tambaye shi, hop komai normal? Alhamdulillah yayana muna nan muna fama. yanayin Nauwar kawai ya kalla ya gane bata cikin Walwala, ga idanunta sun 'kan'kance sun yi ja. Come on dear, taso wa ta yi ta matso gare shi, kanta ya dafa yana dubanta, Wai me ke damunki ne?ni fa a satin nan duk wani so weak nake ganinki, pls tel me what's wrong? langwa6ar da kai tayi tana sharar wasu sabbin hawayen da suke Kwarara a kan fuskarta, ya fuskanci matsaloli a tare da ita, ta kuma kasa magana gaba d'aya sai kuka, tausayinta ne ya bayyana a fuskar shi, stop crying and speakup sis! da ya ga bata son fad'a mishi sai suka koma uwar d'aki, gaba d'aya suka xauna, I don't know how say out yadda nake jin 6acin rai da ba'kin cikin abubuwan da suke faruwa da ku, idan kun lura har d'auke 'kafana nayi daga gidan nan saboda bana son ganin abinda xai tayar min fa hankali. Ki fada min abinda ke faruwa da ku, ban San ganin kina min asarar hawayen ki, take this ki share min hawayen, ki kuma yi min bayani abinda ya sa ki kuka. hand kacif ya mi'ka mata tasa hannu ta kar6a ta shiga share fuskarta. Magana ta fara yi masa tana shashshe'kar kuka, Magaji ne ya mareni, glas d'in da ke sanye a fuskarshi ya xare,What!! Me kike fad'a min haka mara dad'i, waye Magaji!!! Menene ala'kar ki da shi, da har xai samu damar marin ki, me kika yi masa? A dai-dai lokacin da yake maganar ne innah karime ta jiyo shi,don haka ta biyo sautin inda yake ta le'ko da kanta, ubanka tayi masa, munafuki mai shiga tsaknin 'yan uwa, kai kuma waye da xaka xo ka shiga fad'an yan uwa? Shishshigin menene ya kawo ka har uwar d'aki, algungumi da kanka kamar na mutane. Shiru ya yi mata, da ya gaji da sababin da take ta yi, ya fice ya bar mata d'akin, Ammin Nauwar ya tarar a falo tana ta jimamin fad'an da take masa, amma ba ta da halin yin magana, ha'kuri ta ri'ka bashi, haba khalaty kada ki damu ai idan da sabo mun saba da halin su, sallama yayi mata ya wuce gida. Nauwar ce ta biyo bayansa da sauri har da ta tarar da shi, kiran sunan shi tayi, ya Hamdan!!! Juyo da fuskar sa ya yi ya kalleta, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, tarin takaici ne a cikin ranshi, kayi hakuri ya Hamdan dan Allah kasan halin mutanen nan sai su, kada kasa wannan abin a ranka. 'Dan murmushi yayi, ba komai Kanwata, ki koma gida kada kiyi laifi, juyawa tayi ta tafi,tana tafiya tana waiwayen sa har ya fita daga gidan. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* Maijiddatijjaniadam@gmai.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *Wannan shafin gaba d'ayan shi naki ne MAMAH ALEEYOU KD, JEEDDAH tana ji da ke, kuma tana alfahari da ke a cikin 'kannenta, yasin ina yin ki MAMATY kuma muna mugun tare*🤝 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 2⃣6⃣ Hamdan na isa gida ya shiga 6angaren mahaifiyar sa samun ta ya yi tare da wata ma'kociyar su hajiya maryam, wadda kuma aminiyar maminsa ce don tare suka taso tun suna yara. har 'kasa ya tsugunnah ya gaida su, cikin sakin fuska suka amsa masa, sannan ya tashi ya shiga cikin d'akinsa . bin Hamdan Hajiya maryam tayi da kallo har ya wuce d'akin sa, sannan ta dawo da kallonta ga mamin Hamdan. " Hajiya zeenah anya baxa mu yi had'in xumunci tsakanin N Ajmal da Hamdan ba kuwa, ina ganin yaran xa su dace da junan su, yadda muke aminan juna, ya kamata a ce mun had'a yaran mu don xumuncin mu ya d'ore ko ba haka ba? " Nima na dad'e ina wannan tunanin Hajiya Ajmal yarinya ce mai nutsuwa shi ma Hamdan d'in haka, kuma dukannin su suna da biyayya da sau'kin kai, ina ganin baxa mu samu matsala da su ba. "gaskiya ne Aminiya Allah ya wuce mana gaba" "Amin suka amsa gaba d'ayan su, suna ta farin ciki. Har bakin gate mamin Hamdan ta rakata, sannan ta dawo ta shiga gida. Shi kuwa Hamdan d'akin sa ya shige, ya fad'a kan gado,idanuwansa na kallon sama ya fara tunanin hanyar da xai 6ullo wajen taimakawa su Nauwar, saboda halin da suke ciki ya fara ta6a masa xuciyarsa sosai, wayar shi ya janyo ya kira Ammin Nauwar, sallama tayi masa bayan sun gaisa ya shiga yi mata nasihohi masu ratsa xuciya, tare da bata misalai masu kyau wad'anda xasu kwantar mata da hankali, ya kuma umarceta da dagewa da karatun kur'ani, godiya tayi masa sannan suka yi sallama ya kashe wayar. ******************* Bayan Nauwar tayi sallama da Hamdan kuwa kai tsaye falo ta shige, tana xuwa, tarar da magaji tayi da innah karime suna tattaunawa, don haka ta shiga kitchen don ta samu abinda xa ta ci, jiyo magaji tayi yana cewa da innah karime "Ni fa innah tun da naxo gidan nan kwanakin baya naji ina son yarinyar nan, wlh kwata-kwata na kasa sukuni, na gama yin xurfi a 'kaunarta, marin nan ma da nayi mata yanxu haka nadama nake yi, innah ya xa a yi yanxu,ki shige min gaba don wlh ina sonta, kuma idan har ban sameta ba, komai xai iya faruwa da ni,ki taimaka min innata. "Duk naji bayanan ka amma kai yanxu kana ganin wannan shegiyar 'yar mai tsiwar tsiya ce xata so ka, ga d'an banxan girman kai, da rashin tarbiyyar da aka gina su a kai, ka tuna fa kai ba kowa ba ne, face mutumin da yaxo daga karkara ita kuma talaka, ita kuma 'yar birni, 'yar boko 'yar masu kud'i, ina wannan had'in xai had'u, ka duba fa saboda Allah" "Duk wannan maganar ki shareta innah, idan muka koma gurin gobe da nisa, sai na fad'a masa abinda yake faruwa, nasan akwai taimakon da xai min dole ta so ni,ko tana so ko bata so. "Gaskiya ne d'an nan, dad'ina da kai saurin fuskanta, ni na manta ma da gobe da nisan gaba d'aya, shi yasa na musanta maganarka tun a farko, amma yanxu abinda xa a yi shi ne, ka ri'ka sakar mata fuska kana d'an janta a jiki, kana yi mata wasa da dariya, yadda muna doka asiri aikin xai kamata da sauri tunda dama kun saba, kasan fa ya'ki d'an yaudara ne. "Dariya ya ri'ka yi ya ji dad'in maganar da ta fad'a masa. tattaunawar da suka ri'ka yi kenan, sai da Nauwar ta gama jin duk abinda suke fad'a sannan ta fito daga kitchen d'in, gaba d'ayan su kallo suka bi ta da shi, ita kuwa ko inda suke ma bata duba ba ta wuce d'aki. Fu'ad ta tarar yana ta faman yin game a system d'in shi, don haka ta 'karasa kusa da inda yake ta ajiye abincin, labarin abinda ta jiyo daga wajen su innah ta bashi. fu'ad ya ji xafin labarin da ta ba shi amma sai ya danne xuciyarsa, saboda idan ya nuna ya damu xai saka 'yar uwar shi a damuwa, shawarwari ya shiga bata. "ya Nauwar ina ganin kada ki nuna ba kya son magaji, kuma kada ki nuna musu kin ji abinda suka fad'a, saboda matar nan bata tsoron Allah komai xata iya yi don ta cuce mu. yanxu ki taso mu je wajen Abbanmu mu fad'a masa abinda yake faruwa. xaro idanu Nauwar tayi "yanxu kana ganin idan muka fad'awa Abba baxai kore mu ya ci mana mutunci ba?kasan fa Abba ya canja ba irin yadda ka san shi da bane. "kada ki damu insha Allah babu abinda xai faru, ke dai ki taso mu sanar da shi, saboda matsala tun tana 'karama ake maganinta ba sai ta girma ba. tashi suka yi suka shiga sashin mahaifinsu, tarar da shi xaune suka yi yana danna waya, yana ganin su ya mi'ke tsaye, xare musu ido yayi gami daka musu tsawa "me kuke bukata ku ka shigo min d'aki a irin wannan lokacin ko munafukar uwar taku ce ta turo ku, ku ga me nake yi. ko me nake aikatawa? a fusace fu'ad ya fice ya bar d'akin saboda xuciyar sa baxa ta iya jure jin maganganun da yake gayawa mahaifiyar su ba. "Wlh Abbah duk ba wannan ne ya kawo mu ba, dan Allah ka taimake mu ka saurari abinda muka xo maka da shi" "minti biyu na baki ki fad'a min duk gulmar da take tafe da ku, bana son kuma ki tsawaita xance. Hawaye ta shiga sharewa dama Abbah..................dama.............. "tsawa ya daka mata dama me?kin ga bana son munafunci da kisisina ki saki baki kiyi min magana ina da abin yi, idan kuma kukan xa kiyi ki fita ki bar min d'akina bana bu'katar ki a nan. "Dama Abbah magaji ne naji yana fad'awa innah, wai ni yake so, shi ne nace ka fad'a masa ya fita a harkata" "me xan fad'a masa? ni babu abinda xan ce da shi, don yace yana sonki menene, magajin ba mutum bane, yaro mai nutsuwa da ilimin muhammadiyya,ni babu wani abu da xan ce da shi, kuma wlh ki ka kuskura kika yi masa rashin kunya, sai ranku ya 6aci ke da uwar taki da take xugaki, kuma ina son ku sa a ranku magaji ya fi ku komai a gidan nan, ya fi ku matsayi, don da ku da shara duk d'aya na d'auke ku, don haka ina son ki tashi ki fita daga d'akin nan, kuma bana son na 'kara jin,kin xuwar min da makamanciyar wannan maganar." "ficewa tayi daga d'akin tana kuka, tana fitowa ta ci karo da fu'ad shi ma yana ta sharar hawaye, duk ya ji abinda Abban su ya fad'a, rungume juna suka yi suna taya junansu jimamin abinda ya same su. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 2⃣7⃣ *B*ayan sun yi sallar asubah da misalin 'karfe 8:00 Nauwar ta fito don girka musu breakfast, kasancewar ranar lahadi ne ba makaranta, kitchen ta shiga ta fara ferayar dankali, takun mutum ta ji a bayanta don haka tayi hanxarin waiwaya wa, Magaji ta gani jingine da 'kofar kitchen d'in, hannun shi rungume da 'kirjin shi, sanye yake da wasu kaya masu daud'a, yana ganinta ya hau murmushi ha'koran nan kuwa, kamar sun shekara d'ari ba wanki, duk daud'a ta dafar da su. kashe mata ido yayi cikin salon soyyaya yake mata magana. "ranki ya dad'e, har an fito kenan, barka da tashi" juyowa tayi ta watsa masa wata mummunar harara. "ina ruwanka da tashina ko rashin tashina,wannan duk ba abinda ya dameka bane" ta juya ta cigaba da aikinta. hannu ya mi'ka ya d'auki wu'ka, sannan ya samu dankalin ya fara tsatstsagawa. "A matsayina na mijinki bai kamata na kyale ki kina aiki ke kad'ai ba, ba tare da na taya ki ba. ficewa ta yi ta bar masa kitchen d'in ta koma d'aki. fad'awa jikin Amminta tayi tana kuka. "lafiya na ganki haka Nauwar,me yake damunki wa ya ta6a ki,kike kuka da sassafe haka? "Ammina na so na fad'a miki abinda ke faruwa tun jiya, amma Fu'ad ya dakatar da ni, Magaji ne yace yana so na, yanxu kuma ina kitchen ya shigo yana ta6a kayan da nake aikin da su, wlh Ammi ku raba ni da shi, idan ba haka ba sai na 6ata masa a kan maganar nan" "ki kwantar da hankalin ki daughterna ai ba a aure dole, kuma ai Magaji ba tsaranki bane, da har xaki tayar da hankalin ki a kansa, tashi ki koma ki cigaba da aikin ki, Allah ya fi shi, ni dai bana son na ganki kina damuwa" tashi tayi ta koma kitchen d'in ta cigaba da aikinta, duk maganar da yayi mata baya samun amsa, haka ya gaji ya kyaleta ya koma gurin innah karime. A d'aki ya samu innah karime, tana karanta wasu sihirce-sihirce da Boka gobe da nisa ya bata, kyaleta yayi har ta kammala, sannan ta juyo ta kalle shi, kirari ta fara yi masa. "Magaji, Magaji, Magajin gida da gari, angon Nauwar idan mai duka ya so" "murmushi ya ri'ka yi, ya ji dad'in kirarin da ta yi masa, ai har yaso d'in ma innata,don akwai alamun nasara, amma ina ganin sai mun mi'ke sosai, don ganin an shawo kanta, an cusa mata soyyata, kuma ina so ki yi wa Alhajin magana da kan ki, saboda yasan da maganar tun da wuri. "Duk wannan mai sau'ki ne, Alhaji mudi namu ne sai abinda muka ce shi xa a yi, yarinyar ma xata xama tamu nan ba da dad'ewa ba, wuyarta dai mu je gurin Algafarta malam shikenan an yi an gama. "Yanxu yaushe kike ganin xamu je? don wlh na 'kosa na mallaketa, yarinya shekara goma sha biyar ba mashinshini ai abar tausayi ce" "ina ganin mu je gobe, saboda ba a bori da sanyin jiki, To Allah ya kaimu innata" ******************** Da misalin 'karfe 4:30 Hamdan ya shirya tsaf don xuwa gidan su Nauwar yi musu lesson, key d'in motar shi ya d'auka ya fito, yana 'ko'karin kulle 'kofar d'akin shi ne, ya ci karo da maminsa. "Alhamdulillah dama gurinka xan xo yanxu, tun safe nake jiran fitowarka, me kake yi haka ne a d'aki tun safe ko break fa baka xo kayi ba" sosa 'keyar shi yayi, "am wlh mami ina ciki ina wani aiki ne, kinga gobe Monday idan ban samu na kammala ba abin xai yi min yawa" "to ai bai kamata a ce aiki ya hana mutum cin abinci ba, irin haka ne wata cutar take shiga jiki, saboda an bar ciki da yunwa, ni dai bana son haka" "haka baxa ta sake faruwa ba insha Allah mamina" "na gode Allah yayi maka albarka" amsa mata yayi da ameen. Gyaran murya tayi sannan ta mayar da kallon ta gare shi, "Hamdan ina da muhimmiyar magana da kai, nayi wani naxari ne na fahimci cewa kai gaba d'aya aure baya gabanka kafi son ka cigaba da xama a gauro, ni kuma hakan ya fara damuna, ina son na ganka da iyali tunda dai ka kammala karatunka, ga shi har Allah ya baka abin yi, na yanke shawarar kaje gidan Hajiya maryam ka nemi auren Ajmal, don yarinya ce mai tarbiyya kuma duk inda ake neman cikakkiyar mace ta kai" "Rawar baki Hamdan ya fara yi, wlh mami ni tsarin yarinyar sam bai yi min ba, ta fiye rawar kai, ni kuma a tsarina bana son mace haka, kuma ni gaskiya bana sonta gaba d'aya, sam ban yarda da tarbiyyarta ba, in dai aure kike son nayi, ki bari xan nemo mace da kaina, wacce xa kiyi alfahari da ita". "musu xa kayi min a kan xa6in da nayi maka,ka fi ni sanin dai-dai ne ko ya aka soma? umarni nake baka fa ba shawararka na nema ba, don haka can nake son kaje ka nemi aure" jikin shi ba karfi ya tashi, ya nufi bakin mota, a sanyaye ya yi wa motar shi key sai gidan su Nauwar, yau a compound ya tarar da su xaune a kan kujera suna ta nishad'i abin su, kujera ya ja ya xauna, gaishe da shi suka yi sannan suka d'akko littafansu suka fara karatu, suna karatun suna had'awa da wasa da dariya, magaji ne ya hango su daga can nesa, don haka kishi ya kama shi ya je ya fad'awa innah karime xuwan Hamdan, masifa da xage-xage ta ri'ka yi, a wane dalilin xa a kula mishi mata, shawara ta bashi a kan ya ciko bokiti da ruwa yaxo ya watsa masa. ai kuwa haka aka yi magaji ya ciko bokiti ya shammace su, ya watsa shi jikin Hamdan, a firgice ya mi'ke.......... *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* Maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *wannan shafin sadaukarwa ne gareku'yan uwana ina yin ku yasin* *SUMAIYYAH SANI KYAUTA* *AISHA SAMMANI ALATU (maman sultan)* *RAHINATU IBRAHIM (maman sadiq)* *ina yin ku muna mugun tare*🤝 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *jinjinar ban girma gareki AYSHA ALI GARKUWA, ina taya ki murnar kammala litttafinki na RUBUTACCEN AL'AMARI, muna godiya da yadda kika fadakar kika nishad'antar da mu, Allah ya 'kara miki basira, Allah yasa ki fi haka, ina yin ki, muna tare irin sosai d'in nan* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 2⃣8⃣ *A* firgice Hamdan ya mi'ke, cikin mamaki yake kallon Magaji, me ya faru,Wannan wane irin jahilci ne, me nayi maka xaka min haka? Kallon raini Magaji yake wa sannan ya dube shi, cikin tsawa yake masa magana. "Menene dalilin ka na kula min mata, ka dad'e da sanin an mallaka min ita, sauran 'kiris ta xama iyalina, raini ne yasa ka kulata, ko kuma wula'kanci? to wlh ka sani wannan shi ne na farko kuma na 'kashe, In dai ka cigaba da yi min haka, ka fara ganin haukana kenan" Murmushi Hamdan yayi masa, "tabbas ko baka fad'a ba,aikinka ya tabbatar min da cewa kai cikakken mahaukaci ne, kuma ka nuna min cewa kai a cikin jahilan ma irin murakkaban nan ne, sannan kuma ina son tabbatar maka da cewa fadar Nauwar ta fi 'karfin 'kaxamin mutum irin ka, ni baxan tsaya nayi cacar baki da kai ba, saboda nasan 6atawa kaina lokaci xan yi, babu komai tsakanina da kai sai dai nasiha. Mari Magaji ya kai masa, ai kuwa nan Hamdan ya xuciya shi ma ya kai masa mari, innah karime ce ta jiyo hayaniyar su don haka da gudu ta fito, tana ganin halin da Magaji ke ciki ta fad'i 'kasa tana burgima gami da salati xa a hallaka mata d'an jika. Ita kuwa Ammi na d'aki bata ma San abinda ake yi ba, sai masu gadin gidan ne suka xo suka raba su. Gefe ya koma yana ta haki, ita kuwa innah sai xage-xage take yi, tana aibata Hamdan. "Dole ne Alhaji ya d'auki mataki ya hana wannan d'an banxan yaron xuwa gidan nan gaba d'aya, ai ba gidan ubanka bane, saboda na fuskanci kai ba d'an arxi'ki bane, tsiya ce take kawo ka, da neman bala'i, banda masifa an yi wa yarinya miji sai bibiyarta kake yi, kana janye ra'ayinta Wato ta bujire wa iyayenta ko? Kuma an yi na farko an yi na 'karshe,baxa mu sake Kwana a gidan nan ba, naga alama wannan yaron so yake ya kashe min kai, wancan karon haka ya karya ka, yanxu kuma sun had'u suna 'ko'karin kashe ka" Cikin gida suka koma suka had'o kayan su, sannan suka dawo bakin gate suka xauna suna jiran dawowar Abban su Nauwar. Bayan sun fita ne fu'ad da Nauwar suka shiga d'akin da aka bawa su innah karime, suna shiga suka ci karo da wasu layu, sannan ga kan miciji wanda shi ma layun aka cusa a ciki, a firgice suka fito daga d'akin don haka suka sanar wa Ammin su abinda suka gani. Tashi tayi da kanta ta shiga d'akin tayi bismillah ta d'auki abin, sannan tasa aka 'kona mata, tasan ba komai bane face kayan asirin su innah. Kuka suka ji yo daga waje don haka suka yi saurin lekawa, innah suka gani sunkuye gaban Abbansu tana karanta masa labaran karya da gaskiya. "Wlh Alhaji yaron nan da yake xuwa wajen yaran nan, yana koya musu karatu ne, ya samu Nauwar ya rungumeta, shi ne Magaji yayi masa nasiha, Wai a kan wannan dalilin ya hau shi da duka kamar xai kashe shi, kaga wancan karon ma haka yayi masa ya karya shi, ni dai wlh Alhaji baxan sake Kwana a gidan nan ba, saboda tsoron yaron nake ji, naji yana cewa xai aiko a kashe mu, tana maganar tana sharar hawayen munafunci. A fusace Abban Nauwar ya shiga cikin gida, tarar da Hamdan yayi suna tattauna abinda ya faru tsakanin sa da Magaji. Ammi ce ke masa nasiha "Me yasa xaka daka ta tashi, kasan ba hankali ne da shi ba, 'kauye har yanxu na damun shi" "Wlh Khalaty muna xaune ya Watsa min ruwa, sannan ya mareni Kin ga duk ha'kurina dole nima na harxu'ka. "Haka ne amma dan Allah a ri'ka ha'kuri ana kai xuciya nesa" "I will insha Allah my khala" Abban Nauwar ne ya shigo ko sallama babu, ranshi a 6ace ya wuce ya shiga 6angaren shi, ba tare da ya kula kowa ba, tunanin abinda ke faruwa ya fara yi shi kanshi, abubuwan sun fara d'aure masa kai, tambayar kanshi ya ri'ka yi, ko menene dalilin ma da ya kawo su innah karime gidansa, da har hakan ke faruwa, yasan 'yar shi kamila ce, sannan Hamdan ma mutum ne mai hankali, ya tabbatar da cewa baxa su aikata abinda aka fad'a masa ba. Alwala ya daura ya fara sallah,yana adduar Allah ya fitar da shi daga cikin duhun da yake ciki. Su kuwa su innah karime suna waje suna ta farin ciki,a tunanin su ana can ana ci wa su Nauwar mutunci, shirun da suka ji ya yi yawa ne yasa suka le'ko, sai suka tarar da su tare da Hamdan, ana ta shan hira ana nishad'i,Hamdan na ganinsu ya sako wata hirar daban don kawai su ji haushi. "Dear kullum 'kara kyau kike yi a cikin idanuna, addu'ata a kullum Allah ya mallaka min wannan kyakkyawar fuskar, na ri'ka kallonta har abada" Kashe masa ido d'aya Nauwar tayi "Ni dai xaulaya na kake yi yayana ai ka fi ni kyau Allah" Suna hirar Fu'ad na taya su ana dariya, duk dan su 'konawa magiji rai. Mamaki ne ya kama su. Ko menene dalilin da yasa Abban nauwar bai d'auki wani mataki ba, kishi ne ya kama Magaji, ya rasa ina xai sa Kansa, saboda jin abinda su Nauwar ke fad'a jikin su a sanyaye suka shige d'aki. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Dan Allah masu karatu ku yi ha'kuri🙏🏻saboda rashin ji na kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon lalacewar da wayata tayi* 2⃣9⃣ *S*una shiga suka tarar da komai na d'akin an hargitsa musu shi, mamaki ne ya kama su, har suka rasa bakin magana, innah ce tayi 'karfin halin tambayar Magaji. "Wane ne ya shigo mana d'aki yayi mana kaca-kaca haka?" "nima dai mamaki nake innah, duba ki ga duk kayan amfanin mu an kwashe, idan fa babu abubuwan nan akwai matsala innah,kashin mu ya bushe, duk wani shirye-shiryen mu an rusa mana shi" shiru innah karime tayi tana naxarin maganganun magaji. "kin yi shiru innah, idan fa ba mu yi magana an fito mana da kayanmu ba, Allah mun lalace a cikin gidan nan" "To naji, wuce mu je nayi tijara a bamu kayan mu" fita falo suka yi, innah karime na ri'ke da 'kugu take magana cikin tsawa "Uban waye ya shiga d'akina ya yi min bincike?" shiru suka yi mata suka cigaba da hirar su. "nace uban waye ya bincike min d'aki? tambayar ku fa nake yi. Nauwar ce ta mi'ke, "Mu ne muka shiga, yau duk abinda ku ke ta'kama da shi na asiri ya xo 'karshe, mun 'kone shi a gidan nan, kuma insha Allahu, Allah baxai 'kara baku nasara a kan mu ba har abada. kallon mamaki innah take mata, cikin 'karfin hali ta fara magana. "Nasara tuni mun ci mun gama, tunda ko yanxu na nemi ku bar gidan nan sai kun bar shi, kun ga kuwa ko yanxu an ci ku da ya'ki,kuma wlh ku fito min da abubuwana, idan ba haka ba ranku gaba d'aya sai ya 6aci a gidan nan". Dariya suka ri'ka yi mata suka mayar da ita tamkar wata sabuwar mahaukaciya, don haka ta kwashi jiki sai 6angaren Abban Nauwar, tarar da 'kofar shi tayi a kulle, don haka ta ri'ka bugawa kamar xata karya 'kofar d'akin, a firgice ya farka daga bacci ya 'karaso bakin kofar, kamar a mafarki ya ga innah karime, tambayar ta ya fara yi. "lafiya innah yaushe ku ka xo garin nan ban sani ba" fuskarta cike da mamakin maganarsa ta kalle shi, "yaushe muka xo ma kake tambayata." "Eh mana wlh ban san kun xo ba, ya su baffa? "Ba wannan ne abinda ya kawoni ba, na fi wata biyar a gidan nan, amma saboda cin fuska kace wai baka ma san ina nan ba, to ka fito ka raba ni da 'ya'yanka, sun gama raina ni a cikin gidan nan basa ganin darajata, saboda d'aurin gindin da suke samu daga wajen wannan shegiyar uwar tasu". Dakatar da ita yayi da hannu "Dakata innah duk abinda xaki fad'a ki fad'a, amma bana son naji kin sake xagin iyalina" Sai na xaga d'in, saboda an shanye ka,ban isa na fad'i gaskiya ba, yaran nan sun cuce ni saboda kana jin tsoran su,baxa ka iya tsawatar musu ba, to wlh baxa ta sa6u ba idan kai baxa ka iya ba ni xan iya". "to ina ruwan ki idan ma an shanye ni, naga dai matata ce baxa ta ta6a cutar da ni ba, ke har kin manta da irin cutarwa da ku ka yi mini, sai yanxu da Allah ya rufa min asiri xaki ce kina sona, ni sam ban yarda da wannan soyayyar taki ba". ficewa yayi ya barta a tsaye tana ta balbalin fad'a, falo ya fito ranshi a 6ace yake tambayar Ammin Nauwar. "Me ya kawo wannan tsohuwar gidan nan, ku ne ku ka je,ku ka d'akkota ko?yana maganar yana kallon su. gaba d'ayan su kasa fahimtar abinda yake nufi suka yi. magana fa nake kun share ni" "waye yace wannan tsohuwar taxo min gida, alhalin kun san halinta amma ku ka 'kyaleta ta xauna, ga shi nan taxo xata 6ata min rai" Nauwar ce tayi 'karfin halin yin magana "To ai kaine ka d'akkota da kan ka Abbah, kuma kayi alkawarin duk wanda ya 6ata mata rai a cikin mu sai ka kore shi daga gidan nan. Hawaye ne ya fara sauka a kan fuskarsa. "wlh ban san na fad'a ba, dan Allah ku yi ha'kuri ku yafe min, ban san na ci xarafin ku haka ba, insha Allah daga yau ta gama kwana a gidan nan" 'Bangaren shi ya koma ya tarar da ita tayi tsaye ko tunanin me take yi oho, a gabanta ya tsaya, fuskar shi ba walwala yake mata magana. "duk naji abinda ya faru kuma insha Allah gobe xa a mayar da ku 'Dan batta" yana gama gaya mata ya shige d'akin shi ya barta nan tsaye. kanta ne gaba d'aya ya 'kulle ta rasa abin cewa. *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 3⃣0⃣ *W*ashe gari da sassafe Abban Nauwar ya gama shiri ya fito falo don yin breakfast, Nauwar ce ta tashi ta fara xubawa Abbanta abinci, kallonta yayi yana murmushi I can't eat up the food because I'am not a big eater. kallon shi tayi tana dariya to ai Abbah naga jiya baka ci abinci ba shi yasa na xuba maka da yawa. okay, Give me a little. kadan ta xuba masa sannan ta xubawa kowa suna cin abincin suna nishadi. bayan sun kammala yasa aka kira su innah karime, kallo d'aya xaka yi mata ka fahimci tana cikin ba'kin ciki da tashin hankali. kallon su ya yi fuskar sa sam babu alamar wasa. "kun had'o komai da komai naku dai ko, don yau xaku wuce inda ku ka fito" xare idanuwa innah karime tayi "wai dama Alhaji da gaske kake mayar da mu xa ka yi, ni fa nayi tunanin raha ka ke yi" "Da gaske nake yau xaku koma, let me change now, kafin na fito kai magaji kayi sauri ka fara saka kayan ku a mota, don yau ina da aiki amma na katse xan kai ku" kamar xasu yi kuka haka suka shiga mota suka wuce 'Dan batta. su kuwa su Nauwar farin ciki baya misaltuwa a gurin su saboda Allah ya raba su da masifa. Suna isa 'Dan batta ya ajiye su, ko cikin gidan bai shiga ba ya juya kan motar shi ya dawo gida. Habi ce ta gamu da su a bakin 'kofa, ita ma tana shirye-shiryen tafiya gidan suna, yanayin su kawai ta kalla tasan tafiyar ta su ba ta dad'i bace, ga shi innah karime na ta faman xubar da hawaye, gurin xama suka samu bayan sun ajiye kayan su, shiru suka yi kamar wad'anda aka xarewa laka. 'karfin halin tambayar su tayi, ta gama tsorata a tunaninta wani abin ne ya same su. "Innah waye ya mutu naga kuna kuka? "Ba mutuwa bace uwar Audu amma abinda ya same mu ma har ya fi mutuwar ciwo " ta 'karasa maganar tana kuka "Dan Allah fada min Innah wlh hankalina ya tashi da jin wannan maganar ta ku, ina ganin ku nasan ba a hayyacin ku, ku ke ba me ya faru dan Allah" Magaji ne ya kar6i maganar. "Ai gwaggo yau cin mutunci kawu Mudi ya yi mana, ya kore mu sannan duk kayan aikin mu na gidan an 'kone mana, sun lalata mana asiri yanxu ya dawo hankalin sa, a cewar sa ma bai san muna gidan ba duk xaman da muka yi" salati Habi ta fara yi "Kai amma wad'annan mutane an yi masu kwasasshiyar albarka, sun cuce mu, yanxu ina muka ga kud'in komawa a 'kara yi mana wani abin, amma ya xama dole mu d'auki mataki, ni dai ko xan tafi tsirara sai na dawo da hankalin Mudi kaina, kuma sai Magaji ya koma birni, ke kuma sai ki nemi mafita idan xaki bayar da Akuyar ki a siyar to, idan kuma kina ganin baxa ki iya ba, sai na nemar wa 'ya'yana su kadai. shiru Innah karime tayi tana naxarin maganar Habi, sai da aka d'auki lokaci mai tsawo sannan ta bata amsa "sai na bayar uwar Audu in dai bu'kata xata biya" kwanan su uku a 'Dan batta suka fara gane kuskuren su, duk yanayin su ya canja, saboda canji abincin da suke ci,da muhallin da suke rayuwa, wannan dalilin ya 'kara harxu'ka xuciyar su wajen baxama neman maganin da xasu mallake mahmoud da iyalansa. A 6angaren Hamdan kuwa mahaifiyar sa ce, ta matsa masa a kan dole ne ya je gidan su Ajmal ya ganta, su kuma dai-dai ta a kan maganar auren su, danne xuciyar sa ya yi ya amsa bu'katar ta, don haka bai tsaya yin wata kwalliya mai kyau ba, yana fitowa ya had'u da maminsa, kallon shi tayi sama da 'kasa ta ga ba wani kwalliya yayi mai kyau ba, why are you wear this shabby shirt Hamdan?oya yi maxa ka canja ta,kafin raina ya 6aci, tafiya yayi ya canja wasu, sannan ya fito ta ganshi ta yaba da kwalliyar da yayi sannan ya fita ya d'au mota. kai tsaye gidan su Nauwar ya isa, yau a waje ya tarar da su suna ta hira ita da fu'ad, yana yin parking ya fito ya tsaya, yana kallon su kamar mai tunani, yaran suna matu'kar burge shi sun sha'ku da junansu kamar tagwaye,Nauwar ce ta hango shi da gudu ta 'kara so inda yake xata rungume shi ya ja da baya. murmushi yayi mata sannan ya fara mata magana. "dearna kinga kin fara girma ki daina cewa xaki rungume ni, kin ji ko 'yar kanwata" gyad'a kai tayi alamar eh, "Yauwa yaya ina ta son dama na ganka fu'ad He's been gossiping about you" Hamdan na jin haka ya matsa gurin da fu'ad yake ya ja kunnen sa, "Gulmana ka ke yi ko aboki, daga yau mun 6ata" 'Yar kara Hamdan ya saki "Allah yaya ba gulmarka nake yi ba, naga kwana biyu baka le'ko bane, shi ne na fad'a mata ko Magaji ka ke jin tsoro, shi yasa baka le'ko mu ba. dundu ya sakar masa a baya, "baka ji abokina mun yi fad'a daga yau" yana maganar yana 'yar dariya. "kayi hakuri yayana na tuba" "to naji ku wuce ku shirya xaku min rakiya wata 'yar unguwa" gaba d'ayan su suka wuce suka fara shirin raka Hamdan, shi kuma ya shiga ciki don gaisawa da Ammin Nauwar. *Jeeddahtulkhair*😘 08094136204 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 3⃣1⃣ Hanyar gidan su Ajmal suka kama, wanda kuma kusa yake da gidan su Hamdan, yana xuwa aka bud'e masa gate ya shiga, 'kaninta ne ya hango Hamdan har 'kasa ya tsugunnah ya gaida shi, sannan ya yi masa jagora har wajen da xa su yi xance da yayar shi. cikin gida ya shiga ya sanar mata da xuwan Hamdan, saboda ko number wayar ta ba shi da ita. kanta sai rawa yake yi ita da mamanta, abinci na musamman aka girka masa, sannan aka bawa yaron ya kai musu, nan da nan she had her new gown on, ta hau gyaran fuska sai da ta kwashe kusan 1hour tana abu d'aya, har sai da Hamdan ya gaji da xama He is pacing up and down waiting, saboda baya jure zama da yawa. wata siririyar murya suka ji tayi sallama, gaba d'ayan su suka mayar da kallon su gareta, tafe take tana rangwada har ta iso inda Hamdan yake, daf dashi ta xauna kamshin turarenta yana dukan hancin shi,su kuma su Nauwar suna gefe, wani irin d'inki ne mara fasali a jikinta,wanda sai da rabin breast d'inta suka bayyana a waje, d'an mayafi kawai ta yafa wanda ya tsaya iya wuyanta, Hannun shi ta kamo gami da rungume shi, saurin janye jikin shi yayi daga gare ta. tambayar shi tayi cikin sigar rashin jin dad'in abinda yayi mata. " me yasa xaka janye jikinka ko baka son mu gaisa ne" tana maganar tana ya mutsa fuska "irin wannan gaisuwar taki ba gaisuwa ce ta yara masu tarbiyya ba, don haka bana son ki 'kara min haka" tashi yayi tsam ya bar mata wajen kallon su Nauwar tayi ta yatsina fuska. "Wad'annan yaran kuma daga ina? nasan dai ba 'ya'yan gidan ku ba ne, gaskiya xan fad'a maka ban so kana xuwar min da yara ko abokai, kai kad'ai nake son gani" ranshi a had'e ya mayar mata da martanin maganarta "yaran nan cousin's d'ina ne, mun sha'ku da su bama rabuwa, tare kika ganmu,haka xaki yi ha'kuri na ri'ka xuwa da su, kuma ni ba xance naxo ba, dama mami ce tace naxo mu gaisa saboda xumuncin mu ya 'kara 'karfi, ina fatan kin ji dad'in wannan xiyarar da na kawo miki. mi'kewa tsaye yayi yana kallonta. "to ni xan wuce ki gaida min da su Hajiyar" bai tsaya jin amsar da xata bashi ba ya fice daga d'akin ya barta. takaici ne ya mamaye xuciyarta,ta rasa ina xata sa kanta, a matsayin ta na budurwa mai ji da kanta, a ce Hamdan ya xo ya wula'kanta ta, duk 6ata lokacin da tayi wajen ganin tayi kwalliya don ta faranta masa amma duk hakan bai burge shi ba, cikin gida ta koma d'akinta ta bud'e ta shiga, kan gado ta fad'a tana ta xubar da hawaye, wayar ta ta d'auka ta kira 'kawarta Haseenah cikin kuka take mata magana, "my Hasee ki yi sauri kixo akwai matsala, dan Allah ki taimake ni kada kiyi delaying wajen xuwa ki ji matsalata" "gani nan xuwa but ina Aminu kano teaching hospital naje duba mujaheed amma ki jira ni xan xo yanxu" Ba a fi 5minutes ba Haseenah ta 'karaso gidan su Ajmal, tarar da ita tayi ta sha kuka har ta 'koshi,idanuwanta sun yi jawur, tambayar ta abinda ya sameta tayi. ta kwashe labarin abinda ya faru tsakaninta da Hamdan, ta gaya mata. kallon ta Haseenah tayi tana hararta. "Kema dai kina da matsala Ajmal kin san da cewa, ko kin samu miji 'yan kungiyar mu baxa su ta6a yarda kiyi aure ba, banda ma tsabar da'ki'kanci irin naki mu da muke da hanyoyin biyawa kan mu bu'kata, ina ruwan ki da wani namiji, da har xai 6ata mik rai, ki ri'ka takaici da xubar da hawayen ki a kansa, tun wuri ki cire tunanin sa a ranki,tun kafin uwar gida taji labarin kina kula maxa" shiru tayi tana kallon Haseenah, sannan ta share hawayenta ta fara yi mata magana. "wlh my hasee na gaji da harkar nan, so nake yi nayi aure na tattara hankalina guri guda, saboda wannan hanyar da muka d'auka ba mai 6ullewa bace, shikenan haka xamu xauna shekarun mu suna nisa ba aure, ko don kada duniya ta xage mu ai gara mu yi auren mu mu huta" A gurinki ne dai kike ganin bata 6ullewa,shekarar mu nawa muna yi, gamu nan ba abinda ya same mu, idan xaki cire xancen wani banxan namiji a ranki ki cire, idan kuma ba haka ba hawan jini ya kamaki" "To naji 'kawata amma xan yi naxarin maganar ki don wlh ina son Hamdan,kuma muddin na aure shi na bar wannan harkar har abada ko kashe ni xa a yi, sai dai a kashe ni" "To ai sai ki yi 'yar wahala" Haseenah ce ta jawo Ajmal ta manna bakinta da nata, suka fara sa6awa Allah kamar yadda suka saba, Haseenah bata bar gidan su Ajmal ba sai bayan sallar magrib. ******************* Hamdan na barin gidan su Ajmal, ya je ya mayar da su Nauwar gida, ran shi duk a 6ace yake, saboda ri'ke mishi hannun da ajmal tayi, idan da abinda ya tsana a rayuwar shi, bai wuce ta6a jikin matar da bata halatta a gare shi ba. Nauwar ce ta tambaye shi "yaya why are you frowning? murmushin 'karfin hali ya yi "ba komai kanwata" "Allah ban yarda ba yaya ka fada min abinda aka yi maka,ko nice na 6ata maka rai" He pursed his lips sannan yace mata "ai ba kya laifi my dear, wannan mara tarbiyyar yarinyar ce ta 6ata min raina, ta xo tana min wani swaggering a gabana, hakan ma bai isheta ba sai da ta kama hannuna, gata da wulakanci, sannan ta saka wasu skimpy dress, ko gani take xata burgeni oho, dama ni tun farko na fad'awa mami baxan je ba, don naga tayi fushi ne kawai naje" "Ai gara da kaje yaya nima ban so ka 6atawa mami rai" "ai tunda naje na d'aya baxan je na biyu ba, na gama xuwa" sallama suka yi shi kuma ya wuce gida Wani ba'kin ciki ne ya mamaye xuciyar Nauwar, ta rasa me take ji game da Hamdan,son shi take yi, ko kuma kishin shi take yi a matsayinsa na d'an uwan ta, wajen Ammi suka shiga suka sanar da ita dawowar su. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniAdam@gmail.com *♻EXCLUSIVWRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Yau shafin gaba d'aya naki ne uwar gida ran gida, gugan 'karfe sha gwagwarmaya, murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya, kainuwa dashen Allah, Carbin 'kwai mai wuyar ja, uwar gida kuma Amarya a gidan BARRISTER HAJIYA RUKAYYA SANI, Allah ya barki da angonki Allah ya kara muku soyayya da 'kaunar juna, JEEDDAH tana yin ki, kuma ana tare irin mugun sosai d'in nan*🤝 3⃣2⃣ *A* haka Nauwar ta kwanta bacci xuciyarta cike da kishi gami da kewar Hamdan. washe gari ma tun safe a d'aki ta wuni, Amminta ce ta lura da halin da take ciki,don haka ta yanke shawarar shiga gurin d'iyar tata don ta ji matsalarta,shiga d'akin da Nauwar take tayi, tarar da ita tayi ta had'a kai da gwiwa ta xuba uban tagumi. "lafiyan ki Nauwar, me yake damun ki naga tun jiya babu walwala a tare da ke?" "Babu komai Ammi ban jin dad'in jikina ne" "Ayyah!! Allah ya baki lpy ki sha magani, ki shiga kitchen ki duba min idan stew d'in nan ya yi ki sauke" "To Ammina" tashi tayi ta d'auki maganin ta 6oye a hannunta saboda tasan cutar ta ba ta magani ba ce, kitchen d'in ta shiga ta fara aikin da Amminta ta sa ta, tunda ta shiga wani tunanin ya dad'a mamaye xuciyarta, yanxu a ce duk yadda take jin ya Hamdan a ranta da yadda ta sha'ku da shi, ashe baxai xama mallakinta ba,gurin wata xai je da niyyar aurenta, hawaye taji yana kwarara a kan Fuskarta. "Nauwar"!!!! taji an kira sunanta, da sauri ta juya. Ammi ta gani tsaye tana salati. "yanxu don Allah tunanin me kike yi da har kika bar miyar nan ta fara kamawa, kinsan dama tunanin xa kiyi kika kar6ar min aikina da sai ki barni nayi da kaina, 'kaurinta na jiyo na fito, ashe ma kina kitchen d'in kina aikin tunanin da kika saba ko? "Allah ba tunani nake yi ba Ammi sha'afa nayi" "kina son mayar da ni 'karamar yarinyar Nauwar, tunda na riga na haifeki ai babu abinda xaki 6oye min game da ke, nasan farin cikin ki, na kuma san damuwar ki, xo nan ki fad'a min abinda yake damunki" 'Daki suka shiga tayi tambayar duniya, ta'ki fad'a mata gaskiyar abinda yake damunta, sai haka ta kyaleta. Su Innah karime ne xaune suke ta 'kullawa da kwancewa, game da yadda xa su yi, su koma birni su cigaba da rayuwa mai dad'i. "Audu ne ya shigo wuyan shi rataye da fatanya, sallama ya yi sannan ya samu guri ya xauna. gaishe da su innah karime yayi, sannan ya yi 'yar gyaran murya. "Innah wai a ina aka kwana ne, game da zuwa gurin Bokan nan, idan fa muka yi shiru muka sa ido, abin nan xai yi ta mi'kawa ne, kin ga fa tun da ku ka dawo yaron nan bai xo da niyyar baku ha'kuri, ko nuna nadamar wula'kancin da yayi muku ba, a matsayin sa na jikanki. "Hmm Audu kenan, Ai Mudi tuni ya dad'e da xama d'an kansa Audu, matar sa ta lalata shi, baya son yan uwan sa, ubansa ne kawai yake yake morar arxi'kinsa mu kuwa baya ta tamu, an ci gari da mu,an barmu da kuturun bawa, yanxu haka ma rashin kud'i ne ya hanani komawa wajen gobe da nisa, amma Allah yana warware min matsalar garin nan xan koma. hannu Audu yasa a aljihu ya fara laluben 'yan canjin da suka rage masa "yanxu haka akwai 'yan kud'ade a hannuna innah, xan ba ki,ki fara ajiye wa, saboda lamarin nan sai an shirya sosai, Bokan nan baya aiki a kan kud'ad'e kad'an". wasu tsofaffin kud'ad'e ya mi'ka mata, wad'anda baxa su wuce naira d'ari biyu ba. da fara'arta ta mi'ka hannu ta kar6a, tana masa godiya. A lokacin suka yanke shawarar siyar da kadarorin su, da 'yan kayayyakin da suka mallaka, don su ji dad'in yin asiri son ran su. Hamdan ne sunkuye gaban mahaifiyar shi, ya kasa cewa komai,saboda fargabar da ta cika xuciyar shi, shirun da ya yi yawa ne,yasa maminsa ta fara yi masa magana. "Wannan dunkufen da kayi,kamar me neman gafara na menene Hamdan?" shiru yayi ya kasa bata amsa, saboda bai san da wace irin kalma xai yi amfani ba, wajen bayyana mata abinda yake ransa. 'kara tambayar shi tayi "kai fa nake sauraro Hamdan" "wlh ina fargabar fad'a miki abinda yake damuna ne mami, ban san da wace fuska xaki kalli abin ba" "Fad'a min d'ana ai baxan so matsala na damuna ka, ka 'ki fad'a min ba, duk duniya kai kad'ai na mallaka a rayuwata, ta yaya xan so 6acin ranka," wannan maganar ita ce ta sanyayawa Hamdan rai, ya kuma ji 'karfin gwiwar sanar da ita abinda yake ransa. "Mami dama so nake na sanar da ke,don Allah don sonki da Annabi,a bar maganar aurena da Ajmal, wlh yarinyar sam bata dace da tsarin rayuwata ba, tarbiyyarta bata yi min ba, a jiya ma na 'kara tabbatar da hakan, ina xuwa ta mi'ka hannunta ta rungume ni, ni dai don Allah kiyi min rai, kada ki bari na aureta, kowane namiji burin sa ya samu mace ta gari, wacce 'ya'ya na gari xasu fita daga jikinta,yanxu idan na aureta yaya kike tunanin tarbiyyar yarana, nasan ke ma xa kiyi alfahari, idan na samu mace ta gari mai tarbiyya da addini, don Allah ki duba maganata da idon basira mamina" ya 'karasa maganar yana kuka. Numfashi mami ta sauke sannan ta fara magana "na gamsu da maganganun ka Hamdan, nima nasan halin yarinyar wayewarta tayi yawa ta wuce misali, na amsa bu'katar mahaifiyarta ne, saboda kada taga na watsa mata 'kasa a ido, na yarda ka nemi duk yarinyar da kake so, amma da sharad'i,nan da sati biyu nake son ka xo min da magana mai kyau" wani dad'i ne ya kama Hamdan,jinshi yake kamar wanda aka yi wa bushara da aljannah. "Na gode, na gode mami, Allah ya saka da alkhairi Allah ya ja da ranki, insha Allah xan yi yadda kika ce" tashi yayi ya shiga d'aki xuciyar sa cike da nishadi da farin ciki. *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniAdam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Sadaukar wa gareki MARIYA ABDULLAHI YAQUB (mariyar makkah) Amaryar gobe😜idan Allah ya so, Allah ya nuna min auren ki mu sha shagali* *Asha rawa rawa,💃 mata a sha rawa, ku sha sha'aninku duniya ce, ku sha sha'aninku 'kawayena, yasin ina yinku 'yan Almajira fans, muna mugun tare*🤝 3⃣3⃣ Yana shiga d'akin ya tarar da wayar shi na ta faman ringing, hannu yasa ya d'auketa, ba'kuwar number ya gani,don haka ya yi wurgi da ita gefe guda, kasancewar baya d'aga number dai bai sani ba, harkokin gaban shi ya cigaba da yi, 'karar wayar ne ya hana shi cigaba da abinda yake yi, don haka ya mi'ka hannu ya d'auketa,15 missed calls ya gani, mamaki ne ya kama shi. "Wanene yake ta kirana haka"?ya tambayi kan shi yana shirin bin kiran ne aka sake kira, da hanxari yayi picking, ya kara wayar a kunnen shi shiru yaji an yi ba tare da an ce komai ba, shi ma dai shirun yayi, da yaga ba a da niyyar cewa komai, shi ne yayi 'karfin halin yin magana. "Hello" wata murya yaji ta yi magana. "ka taimaka min, ka tallafi marainiyar xuciyar da bata san komai ba sai soyayyarka,tun bayan rabuwar mu da kai, xuciyata ta shiga 'kunci gami da kewar rashinka, kai taimake ni ka dawo gareni,don Allah kada ka rabu da ni, duk yadda kake son na koma maka, xan yi biyayya a gareka, ka tallafawa rayuwata don Allah" aka 'karasa maganar da kuka mai tsanani. mamaki ne ya kama shi, ko a ina Ajmal ta samu number shi? rasa amsar da xai bata yayi, duk ta 'kulle masa tunani. jin ya yi shiru ne,ta cigaba da yi masa magiya, tana kuka tana ro'kon shi ya yafe mata idan laifi tayi masa. "Baki min komai ba, sai dai akwai banbanci mai yawa tsakanina da ke, bana son irin rayuwar ki sam yanayin halayyar ki bai min ba, kuma a gaskiya baxan iya xama da ke a matsayin uwar 'ya'yana ba,sai dai xamu cigaba da gaisawa a matsayinki na 'kanwata" kashe wayar ya yi ya 'kyaleta. wani irin ihu tayi wanda sai da hankalin 'yan gidan su gaba d'aya ya dawo kanta. mamanta ce ta shigo d'akin hankalinta a tashe take tambayar d'iyar tata. "lafiya, me ya sameki na jiyo ihun ki har waje"? wani kukan ta 'kara rushewa da shi. "Mama Hamdan ya tsaneni baya sona, baya 'kaunata, ya ce baxai aure ni ba,saboda ba ni da tarbiyya, dan Allah mama ki taimake ni,ki nemi Hamdan ki bashi ha'kuri ya so ni, wlh baxan iya rayuwa idan ba tare da shi ba". tausayin d'iyarta ne ya kamata,tabbas ita kanta tasan da cewa,tarbiyya ta yi wa 'yar tata 'karanci, kuma ita ce silar duk lalacewar da yarinyar tayi, a ganinta a bar yarinya ta shana, ta yi duk abinda take so shi ne gata, ga shi tun kafin tafiya tayi nisa, sun fara ganin illar hakan, Hamdan yaro ne kamili, idan har aka tursasa masa auren Ajmal an xalunce shi. "kiyi ha'kuri ki cigaba da addu'a,nima xan taya ki da ita, insha Allahu, Allah xai karkato miki da tunaninsa ya dawo yana sonki" "Mama Hamdan baxai ta6a sona ba,ko nayi addu'ar haka nan xa ta wuce, akwai wani malami da Haseenah ta ta6a xuwa wajen sa, a kan maganar saurayinta, tunda ya yi mata aiki ta samu kansa". "Kul Ajmal!! kada na sake jin,kin yi xancen xuwa wajen wani malami, duk abinda Allah bai baka ba, babu wani d'an adam da xai baka shi, kuma duk wanda yake xuwa gurin malami,da sunan neman taimako kamar bai yarda da Allah bane, don haka ban son na sake jin kin yi xancen wani malami a gidan nan" "To mama, baxa ki sake ji ba insha Allahu,ina so xan je gidan su Haseenah na kai mata kayan da ta bayar a d'inka mata" "Ba inda xaki je, kina son ki fita ne ku had'e ki je inda na hanaki xuwa ko?" "wlh mama na miki al'kawari babu gidan malamin da xan je" "to shikenan na yarda ki gaida min da Hajiyar su" tana fita daga gida ta samu adai-daita, sai gidan su Haseenah da ke unguwar gyad'i-gyad'i, tun a hanya ta sanar mata da xuwanta, don haka ta xauna ta jirata. A falo ta tarar da Hajiyar su,don haka cikin ladabi ta gaida ta. "ya mamanki Ajmal"? "tana lafiya" ta amsa mata kanta a sunkuye. Hajiyar su Haseenah tana ganin hankalin Ajmal, ganinta take yi kamar yarinya ce mai tarbiyya da nutsuwa, shi yasa ma ta bar 'yarta da ita, bata san munafukar 6oye bace. kai tsaye d'akin Haseenah ta shiga,tarar da ita tayi d'aure da towel tana shirin shiga wanka,tana ganinta tayi tsalle ta rungumeta, kwance towel d'in tayi, suka shiga shafe-shafen juna kamar yadda suka saba. sai da suka dawo nutsuwar su Ajmal take sanar da ita yadda suka yi da Hamdan. tsaki ta ja, gami da galla mata harara "ke dai kina da matsala wlh, na gargad'eki ki fita a hanyar wannan banxan guy d'in, amma duk kin bi kin d'ora damuwarki a kansa,to ni yanxu da kika xo kina gaya min, me kike son nayi miki?" "Baxa ki gane ba Haseenah, baxa ki gane girman soyayyar da nake yi wa Hamdan ba,ki taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ki,ki raka ni gurin da aka yi miki taimako,a kan Mujaheed d'inki, idan baki min haka ba na tabbatar da bakya 'kaunata" "Ni ai ba nida matsala indai wannan ne,bara na watsa ruwa na xo na raka ki, amma ina fatan kin ri'ko kud'ad'e da yawa, don malam idi baya aiki a kud'i kad'an" "kud'i ba matsalata bane, kema kin san haka, ke dai yi maxa ki shirya mu fice" cikin mintunan da basu wuce biyar ba Haseenah ta gama shiri suka fito, suka yi wa Hajiya sallama sai gidan malam idi da ke jan Guza. A kan buxu suka tarar da shi ya tankwashe 'kafa, yana jan wani zabgegen carbi, tunda malam ya ga Ajmal yake ta tand'ar baki Allah ya kawo masa nama har gida, gaida shi suka yi sannan suka fara xano masa bu'katunsu, da yadda suke son su yi da Hamdan. "Ba matsala kun kawo kukan ku inda xa a share muku, amma kafin nace komai, malama Haseenah d'an bamu guri xan d'an yi wa 'kawarki interview" fita tayi ta bar musu d'akin,ta koma kan wani dutse ta xauna. kallon Ajmal yake yi, wanda kallon nasa cike yake da ayoyin tambaya. "d'an matso nan ki fad'a min abinda ke tafe da ke, ko da yake dai ke gimbiya ce, ni ya kamata na 'karaso" matsawa yayi ya manne da jikinta, yana wasu 'yan surutai. *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba d'aya Sadaukarwa ne gare ki AYSHA UMAR TAHIR TOFA (UMMEE) ina mi'ka gaisuwa ta musamman gareki* 3⃣4⃣ 'Dan janye jikinta tayi daga inda yake, 'kara matsawa yayi daf da ita, yana mata wani kallo mai cike da yaudara. "Ba magani kika xo nema ba?" ta gyad'a masa kai alamar eh. "To me yasa xaki ri'ka matsar da jikanki daga gareni?kinga ki kwantar da hankalin ki, ni ba abinda xan miki, aiki kika xo a yi miki, kuma cikin ikon Allah xaki samu biyan bu'kata. Yanxu dai mi'ko min hannunki akwai abinda xan rubuta miki". Hannu ta mi'ka masa, yana murmushi ya ri'ke mata hannun. "ko kefa 'yar gari, kina wayayyiya ki mayar da kanki bagidajiya" tawaddah da al'kalami ya d'akko ya shiga xana mata wasu rubuce-rubuce marasa kan gado, bayan ya kammala ya umarce ta da ta shanye, bata musa masa ba ta shiga lashe abinda ya rubuta mata. bayan ya kammala, ya 'kara matso da jikinsa, ya manne da ita kamar xai shige cikinta, shafa kanta ya shiga yi, yana karanta wasu abubuwa, ganin yana shafa wuyanta ne yasa ta dube shi. "Malam har yanxu ba a gama addu'ar bane, naga lokaci yana tafiya" dubanta yayi yana wata 'yar dariya mai cike da alamomin tambaya. "Aikinki fa babban aiki ne, lamarin mallaka sai an kai xuciya nesa, dole kiyi ha'kuri nima nayi ha'kuri, wlh banda kece baxan xauna, har na 6atawa kaina lokaci ba, na ri'ka tofa miki abubuwa, amma idan kinga bakya bu'kata xaki iya tashi ki tafi,ga hanya nan, aikina babu lallai ba dole" jin wad'annan kalaman nasa ne yasa, ta kwantar da hankalinta, saboda idanunta sun rufe a son Hamdan,ta manta da nasihohin da mamanta tayi mata akan bin bokaye. shiru tayi ya cigaba da shafa ko'ina na jikinta da niyyar yi mata magani. wani garin magani ya sake d'akkowa ya xuba a 'kwarya,ya gauraya da wani ruwa wanda duk 'kurullarka baxa ka iya gane, ruwan menene ba, ya umartarta yayi da ta cire kayanta xai yi mata wankan magani. kuka ta shiga yi tare da magiyar ya bata maganin tayi wankan da kanta, kallonta yayi yana xare mata ido. "Kada ki 6ata min lokaci fa, ba ni na kira ki ba ke kika kawo kanki,don haka idan kina bu'kata ki tsaya, idan kuma bakya so ki wuce ki tafi, me xan gani a jikinki wanda ban saba gani ba, da har xaki bi ki tayar da hankalinki, kina 'yar 'karamar yarinya da ke me xan yi da ke, ki kalleni da kyau kinsan dai na haifeki,ni ba d'an iska bane, maganin da kike bu'kata shi xan baki" cire kayanta ta shiga yi, tana cirewa tana hawaye, ganin boobs d'inta sun bayyana yasa malam ya kara rikicewa, ya matso gabanta ya kwara mata 'kwaryar maganin,sannan ya shiga aika mata da sa'konni, wadanda xasu taimaka masa wajen cimma burinsa, ta haka ya samu nasara a kanta, ya santa a matsayin d'iya mace. bata tashi farkawa ba sai bayan sallar isha'i, ganin halin da take ciki ne yasa ta rushe da kuka,tana duba gefenta,taga babu kowa a d'akin sai ita kad'ai,tuni malam idi ya tattara kayansa ya gudu ya barta cikin yanayi mara dad'i. wayarta ce take ringing da 'kyar ta ja jiki ta d'akkota, mamanta taga ta kirata sama da sau 20,hawaye ne yake xuba a Fuskarta ba ka'k'kautawa,saboda bata san me xata ce mata ba,ba kuma tasan da wane ido xata dubi mahaifiyarta ba, saboda sai da ta nuna mata illar bin bokaye,amma tayi buris da maganarta,ta bi son xuciyar ta,kuka ta 'kara rushewa da shi,a yanxu babu komai a xuciyarta sai nadama, wacce baxa tayi mata amfani ba, ganin kukan da take yi baxai kai mata ba, sai tayi 'karfin halin tashi, ta saka kayanta, ta kuma d'auki wayarta. mamaki ne ya kamata, domin kuwa ta nemi jakarta ko sama ko 'kasa bata ganta ba,wani kukan ta 'kara rushewa da shi,saboda ko kud'in komawa gida ba tada shi. "yanxu ina xan sa kaina, ya xan yi da rayuwata na cuci kaina, na cuci mahaifiyata,abinda nake nema kuma baxan same shi ba na tabbatar, Hamdan baxai ta6a auren macen da ta 6ata rayuwarta ba, ga shi na barwa kaina mummunan record d'in da baxai ta6a gogewa ba a rayuwata. " tayi kuka kamar ranta xai fito ta bakinta,da taga ba sarki sai Allah, sai ta fito daga d'akin,tana tafe tana jan 'kafa,saboda ta jigata da yawa a hannun malam. ringing ta ji wayarta na yi, 'karfin hali tayi ta d'auka, kara wayar tayi a kunneta ta kasa cewa komai sai kuka. "Ajmal ina kika shiga ana ta nemanki tunda kika bar gida har yanxu baki dawo ba, kuma har gidan su Haseenah naje nemanki, amma tace kun rabu tun d'axu,ki fad'a min inda kika tafi ko na 6ata miki ranki?" kasa bada amsa tayi sai kuka,saboda bata san me xata ce wa mamanta ta yarda da ita ba. "magana fa nake miki kin min shiru, sai faman kuka kike, kina ina yanzu?" "Ina jan guxa mama" "kina jan me???" "wane rashin mutuncin ne ya kai ki jan guxa,baki sanar dani ba, ki duba kiga yanzu 8:30, babanki har ya dawo,sai faman fad'a yake yi,me ya kai ki garin jan guza,wa kika ajiye a can, da xaki je d'auka" tunani amsar da xata bata take yi,saboda ta rasa 'karyar da xata 'kir'kira ta gaya mata. "kin yi shiru ke nake sauraro" "mama adaidaitan masu satar mutane na hau, shi ne suka kaini can yanzu haka ma sun min fyade" ta 'karasa maganar tana kuka "innalillahi wa inna ilaihi raji'un,na shiga uku yanzu me xan ce da babanki, sai da ya hanani barin ki fita kowane lokaci amma na kyale ki,ya xan yi da rayuwata, wad'annan mutane sun cuceni gaba d'ayan su kuka suke yi,mai cike da ban tausayi da nadama a cikinsa. 'karfin hali ta yi,ta tashi taje ta samu baban Ajmal a d'aki ta sanar da shi abinda ya faru da 'yar su, tashin hankali ne ya bayyana a Fuskarsa, sannan ya kar6i wayar ya fara yi mata magana. "yanxu abinda ya faru da ke kenan Ajmal, subhanallah,xaki iya gane gurin da mutanen da suka kama ki suke,don wlh baxan bar abin nan ba sai na d'auki mataki, ki kwatanta min wajen, ga ni nan xuwa na d'auke ki" cikin mintunan da basu wuce 30 ba suka iso gurin, xuciyarsa a harxu'ke yake magana. "wlh duk wanda na kama da laifin yi miki wannan abin sai na sa an kashe shi, saboda an cutar min da dukiya mafi tsada da na mallaka a rayuwata, Allah ya isa" shiga mota suka yi sai asibiti, aka dubata aka bata magunguna sannan suka wuce gida ************* Tun lokacin da Hamdan ya samu sassaucin rabuwa da Ajmal,xuciyarsa tayi haske, dad'i da farin ciki ne,ke mamaye xuciyarsa a kowane lokaci, a yanzu babu yarinyar da ya ji yana 'kauna sama da Nauwar, amma yana jin nauyin furta mata soyayya saboda 'karancin shekarunta,da kuma yadda take ganin darajarsa,yana jin tsoron ya fad'a mata, saboda bai sani ba ko xata amshi soyayyarsa, ko xata juya masa baya ta sanadin haka. 08094136204 *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba d'aya Sadaukarwa ne gareki uwata ta gari, maganin kukana, mai share min hawayena, HAJIYA RABI'A SABO ABDULLAHI (maman khalid)ina yinki irin sosai d'in nan mamana,ina sonki, ina 'kaunarki, kuma muna mugun tare*🤝😍 3⃣5⃣ Su Ajmal na komawa gida,ta shige d'aki,ta fara tunanin cutar da boka idi yayi mata,wayarta ta d'auka ta kira Haseenah, sai da ta yi mata kusan 5missed calls,sannan ta d'auka. "kin cuceni Haseenah, kin cutar da 'kawancen da ke tsakanina da ke,yanzu dama kin san haka Wannan malamin yake, kika had'a ni dashi,da nasan haka halin shi yake me xai kaini gurin shi" "Haba kawata,ni na cuceki ko ke kika cuci kanki?tun farko sai da na baki shawarar kada kije gurin kowa,da niyyar neman maganin mallaka, tunda muna biyan bu'katar junanmu nace ki kyale maganar maxa,saboda ke kanki kin san 'kungiya baxa ta barki yin aure ba." dakatar da ita tayi tana mata tsawa. "ni dai kin cuce ni kin gama da rayuwata, na tabbatar ba wannan malamin ne yayi miki aiki a kan Mujaheed ba, saboda ke bu'katarki ta biya,shikenan ni duk halin da xan shiga ba ki da asara ko?gashi nan kin xalunce ni,ban samo komai ba sai ba'kin ciki da bacin rai,Wannan shi ne 'karshen amincina da ke, ba ni ba ke,kowa yayi harkar gaban shi". kashe wayar tayi tana huci, ashe duk maganar da take yi a kunnen mama, ji tayi an rufeta da duka. "Daman sai da na kawo a raina duk abinda kika fad'a min 'karya ne,ashe wajen malamin da na hanaki xuwa kika je ko?kin ci amanata Ajmal kin cuce ni kin cuci kanki" kuka mama take yi, mai cike da ban tausayi, jin hayaniyar da suke yi ne, yasa mahaifinta ya shigo dakin. tarar da su yayi suna ta shar6ar hawaye. "Lafiya me yake faruwa da ku? "Alhaji ashe yarinyar nan yawon neman asiri ta tafi, a can aka yi mata wannan aika-aikar" shi ma dukanta ya shiga yi, sai da jikinta ya gaya mata sosai sannan suka 'kyaleta. Hankalin Haseenah a tashe yake,saboda jin abubuwan da Ajmal ta gaya mata,don haka ta shirya don xuwa su sasanta. a falo ta tarar da maman Ajmal, har 'kasa ta tsugunnah don gaisawa da ita. "Ina kwana mama?" wata harara ta galla mata "Bana bu'katar gaisuwar ki macuciya, ina nan ina tufka kina warware min kina xaluntata, na hana yarinyata yin abu, kin d'orata a kan hanya, har kiyi mata jagora xuwa inda na hanata,me kika xo yi gidana? maxa ki tashi ki fita kafin na ci miki mutunci" jikinta a sanyaye ta fice daga gidan, saboda bata ta6a tunanin, mama tasan da abinda ya faru ba, wayarta ce tayi ringing tana dubawa ta ga Ajmal ce ta kira, kamar baxa ta d'auka ba, saboda bata san da abinda taxo mata ba, 'karfin halin d'aukan wayar tayi, a sanyaye tayi magana. "hello!!!" "Hello 'kawata, naji duk yadda ku ka yi da mama, dan Allah kiyi hakuri, 'kawancen mu Allah ne ya had'a,babu mai rabawa, idan na rabu da ke ai ban huce ba,kuma baxan ta6a samun nutsuwa ba, xan yi 'ko'kaarin sakko da mama, daga doran fushin da ta hau,sannan ki je ki yi mana tunanin yadda xamu samo kan Hamdan" ajiyar xuciya tayi. "Na gode 'kawata, xan yi miki tunani mai kyau, kuma kiyi 'ko'kari mu had'u gobe,a gidan uwar gida da akwai meeting" sallama suka yita kashe wayar, ita kuma ta wuce gida. ***************** Yau Hamdan cikin tunanin Nauwar ya wuni, ran shi cike yake da kewarta, saboda ya dad'e bai yi toxali da kyakkyawar fuskarta ba, falo ya fito don tattauna da mahaifiyarsa ko xai ji dad'i, 'yar damuwar da ke ransa ta tafi, yana fitowa ya tarar bata nan, don haka ya samu guri ya xauna, tagumi ya xuba yana ta tunane-tunanen, yadda xai tunkari Nauwar da maganar soyayya. "Hamdan!!!!!!" ya ji an kira sunan shi, a firgice ya juya. "Na'am mamina, sannu da fitowa" "yauwa sannu, wai kwana biyu me yake damunka ne, naga a kullum ba kada wani aiki sai tunani" sosa keya yayi "wlh mami nima haka kawai naga ina tunani,na rasa me yake damuna" "Hmm bana son gulma,ka fito sarari ka fad'a min abinda yake damunka yaro" "Dama mami........shiru yayi yana kallon fuskarta. "Dama me, fad'a min abinda yake ranka" "Dama mami so nake kije gidan su Nauwar,ki nemar min aurenta,wlh ita kad'ai nake so mami ki taimake ni" "dama wannan maganar xaka fad'a min, amma kake inda-inda gobe insha Allah xan je" tashi yayi cikin farin ciki, Allah-Allah ya ri'ka yi,Allah ya kaimu gobe ya d'auki mami ya kaita gidan su Nauwar,ta nemar masa aure. washe gari da misalin 'karfe 4:00,suka isa gidan su Nauwar, mami ce ta shiga cikin gidan,shi kuma Hamdan ya xauna a mota, a falo ta tarar da Ammi da fu'ad suna hira, ita kuma Nauwar na kwance ba lafiya, bayan sun gaisa aka kawo mata abinci da ruwa,Nauwar ta gani kwance. "ita kuma wannan me yake damunta na ganta kwance?" "wlh na rasa me yake damunta,nayi tambayar duniya ta'ki fad'a min, ba tada aiki kullum sai tunani" "oh!!! ai yaran xamani halinsu sai su, kayi ta tambayar yaro abinda yake damunsa ya'ki fad'a maka" Ammi ce take tambayarta. "ya Hamdan kwana biyu yayi mana yaji" murmushi mami tayi "hmm ai d'an nan naki ya xama d'an rigima Ammi, jiya yasa ni a gaba yana kuka, wai sai naxo wajen ki,shi a dole Nauwar yake so" Nauwar na jin haka ta mi'ke idanunta a rufe, saboda tsananin kunya da farin cikin da suka lullu6eta. ji tayi taci karo da mutum a hanya, tana bud'e ido taga Hamdan, wata kunyar ce ta 'kara lullu6eta, jayo hannunta yayi, ya tsura mata ido yana murmushi. "kin ji sa'kona ko?" gyad'a kai tayi alamar eh " to yanxu menene amsar sakon da na bayar a baki?" juyar da kai tayi tana d'an murmushi mai cike da farin ciki "ina sonka" tana fad'a ta juya a guje ta bar wajen da yake. murmushi ya bi ta da shi, yarinyar tana matu'kar burge shi, xai yi alfahari da ita a duk lokacin da ya mallaketa. *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 3⃣6⃣ Haka suka cigaba da gudanar da soyayyar su, cikin farin ciki da annashuwa,a kullum Hamdan 'kara xurfi yake yi, a kogin 'kaunar Nauwar, saboda kulawa ta musamman take bashi, ga shi kuma Hamdan ya samu kar6uwa sosai a wajen Abban Nauwar. Yau da sassafe su Innah karime suka tashi, don cigaba da tattaunawa a kan maganar komawa wajen gobe da nisa, a d'akin Habi suka taru gaba d'ayan su, magana suke yi 'kasa-'kasa,saboda kada Baffan mahmoud ya ji abinda suke fad'a. Isah da magaji ne suka shigo d'akin, da girmamawa suka gaida su Innah karime,cikin kulawa suka amsa musu,Innah ce ta fara yin magana. "yauwa Alhamdulillah tun d'axu dama muke jiran xuwan ku,saboda xaman nan haka ya ishe mu,naga alama yaron nan baxai neme mu ba, idan ba mu muka neme shi ba, yanxu na tattara 'yan kud'ad'en da ke hannuna, yau muna yanke shawarar xamu rankaya gaba d'aya mu je gurin gobe da nisa, mu fad'a masa matsalolin mu, ko da taimakon da xai bamu" magaji ne ya gyara xama ya dubi Innah. "Ni Innah babbar matsalata a yanxu, bai wuce auren yarinyar nan ba,saboda ta gama yi min,so nake muna mallaketa a yi bikin, bana son a ja lokaci mai tsawo" "kasha kuruminka d'an magaji, indai muka je ai magana ta 'kare an yi an gama". koko da kosai ta mi'ka musu,suka fara sha bayan sun kammala ne,suka rankaya sai gidan gobe da nisa. yau a 'kulle suka tarar da 'kofar shiga gurinsa, hakan ne ya tabbatar musu da cewa ya shiga aiki,sai yayi wasu mintuna sannan xai fito. don haka suka samu guri suka xauna don su jira shi. ina son na sanar da ku dama"inji Innah "kowa ya 'kudurce bu'katar sa a ranshi. saboda bama son mu je mu ri'ka inda-inda, nafi son ana tambaya mu bada amsa" "ni ai bukatar mu iri d'aya ce Innah" inji isah "A'a d'an nan akwai bambanci, ni burina na xauna har abada a gidansa,kai kuma nasan ba wannan ne a ranka ba" "nima kusan hakan ne Innah, amma ni nafi son, na mallake shi mu koma can ni da iyalina, na yar da fatanya na huta da wahala" Bushewa suka ji an yi da dariya, gaba d'aya hankalin su ya koma inda suka ji dariyar. mutum suka gani tsaye a kan su,gemunsa har jan 'kasa yake, sanye yake da kayan fata, kansa kuwa cike yake da gashi, ko na wata macen albarka. mi'kewa suka yi gaba d'ayan su suna dubansa, sake bushewa ya yi da dariya. "Me ke tafe da ku!!!" isah ne ya fara yi masa bayanin abinda yake tafe da su, umartar su yayi da su samu gurin xama, don xai fi gamsuwa da bayanan su. bayan sun kammala gaya masa abinda yake tafe da su ne, ya basu wasu layu da tukwane, ya kuma umarce su da binne su, sannan ya basu turarukan da xasu ri'ka turarawa idan sun je birni, ya kuma yi Al'kawarin babu wani bil adama, da ya isa ya warware abinda ya basu sai dai idan shi ne, yaga damar warware aikinsa, godiya mai yawa suka yi masa sannan suka d'auki kud'ad'e masu yawa suka bashi, suka kuma yi Al'kawarin 'kara masa wani abin, idan sun samu yadda suke so. basu baro dajin da boka yake ba,sai da suka binne dukkanin abinda gobe da nisa ya basu, sannan suka dawo gida, cikin farin ciki. da baffan mahmoud suka had'u a kan hanya, don haka yayi musu magana, tare da tambayar inda suka je, amma babu wanda ya nuna ya san shi a cikin su, ballanta har ya samu arxi'kin samun amsa. share shi suka yi suka wuce cikin gida shirye-shirye suka shiga yi, saboda sun gasgata abinda boka ya fad'a musu na samun biyan bu'katar su da gaggawa, yanke shawarar tafiya birni suka yi a washe garin da suka je wajen boka. ko sallama basu yi wa baffa,ba kawai sai filin gida ya gani, Habi da xuri'arta gaba d'aya sun tattara sun koma. su Nauwar na kitchen tana taya Amminta aikin girki, sai kawai ji suka yi ana shigo da kaya, tana le'kowa don ganin su waye, ta yi ido hud'u da innah karime, wata harara ta dalla mata, wannan yasa Nauwar komawa ta sanar da mahaifiyarta. "Ammi annoba ta dawo mana" "annoba kuma? ban fahimce ki ba daughter" "su Innah karime ne 'kwansu da kwarkwatar su suka dawo" jin wannan maganar ta Nauwar yasa Ammi ta fad'i a sume,saboda bata san da bala'in da suka sake xuwar mata ba, fitowa tayi tana ihu tana neman taimako, amma babu wanda ya kalleta a cikin su. *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya naka ne halak malak, 'kanina na kaina, ina ji da kai d'an auta NASIR TIJJANI ADAM, Allah yayi maka albarka ya baka ilimi mai amfani, ina yinka irin mugun sosai d'in nan*😍 3⃣7⃣ Waje ta fita tana ihu, tana neman taimakon jama'a, cikin ikon Allah tayi sa'a mai gadin su na nan, don haka ya taimaka mata suka d'auketa sai asibiti,taimakon gaggawa aka shiga bata, amma shiru ko d'an yatsanta bata iya motsawa, ganin halin da take ciki ne yasa aka yi wa Abbansu waya, cikin xafin nama ya baro office ya xo asibitin. kuka ya tarar Nauwar nayi, tana ganin shi ta fad'a jikinsa tana kuka"Abba ka taimake ni kada Ammina ta mutu ta barni" kuka take yi mai cike da ban tausayi "kiyi hakuri Amminki xata samu lafiya nan bada dad'ewa ba, ki yi mata addu'a sosai kin ji 'yar albarka" waya ya d'auka ya sake kiran likita don cigaba da aune- aune ko xa a gano matsalar da take damunta,'karin ruwa aka shiga yi mata, amma duk da haka idanunta na bud'e ko 'kiftawa basa yi, sannan ga numfashinta yana kai wa da komowa. Nauwar da fu'ad kuwa babu abinda suke yi banda faman kuka, sun riga sun san idan Ammi ta mutu sun kad'e daga su har ganyen su. Bayan sallar magrib Hamdan ya iso asibitin shi da mahaifiyarsa, sun tausayawa Ammi sosai saboda halin da take ciki, ga shi ba tada wani babban d'a,da xai xauna ya kula da ita, sai wad'annan yaran da ba wani shekaru ne da su masu yawa ba, mahaifiyar Hamdan ce ta yanke shawarar xama don jinyar Ammi har xuwa ta samu lafiya, amma Abban Nauwar ya'ki fafur, saboda a ganin shi xata shiga ha'k'kin iyalanta, haka tayi ha'kuri ta koma gida,tare da Al'kawarin xata ri'ka xuwa kullum tana kulawa da ita, godiya yayi mata sannan suka wuce gida. suna ficewa Nauwar ta fara hawaye, tambayarta yayi dalilin da yasa take kuka, da 'kyar maganar take fita,saboda tashin hankalin da ya cika xuciyarta. "Abba da ka sani ka 'kyale mami ta xauna tare da mu,kaga akwai abubuwan da mu baxa mu iya ba idan baka nan" "ku kwantar da hankalinku, komai xai xo da sau'ki, dama naje gida kwaso kaya na tarar da su gwaggo Habi sun xo,to xan lalla6a d'aya daga cikin su,taxo ta xauna tare da ku" "zare ido Nauwar tayi, innah Habi fa kace Abbah!!!!" "Eh mana, Menene " ya fad'a yana kallonta "A gabansu fa ta fad'i Abbah,amma babu wanda ya kallemu ballantana ma su taimaka mana, harkokin gaban su suka cigaba da yi, ni dai Abbah ka kyale su dan Allah, kasan mutanen nan ba 'kaunar mu suke yi ba". "A'a baxa a yi haka ba, sun ce basa nan lokacin da abin ya faru, don haka xasu xo, kuma kada ku nuna musu komai, kin ji 'yar lele, kuma bana son ki ri'ka cewa basa 'kaunar ku, jininsu ne ku baxa su ta6a gudunku ba". ita dai xuciyarta bata amince ba, haka ta yarda ba don ranta ya so ba. Yana xuwa gidan ya tarar da su, suna ta sha'anin su, ana ta dafe-dafen abinci tamkar gidan biki, suna ganin shi suka yi tsilli-tsilli kamar marasa gaskiya, har 'kasa suka tsugunnah gaba d'ayan su, suka gaida shi, sannan suka yi masa ya mai jiki. guri ya samu ya xauna, cikin damuwa yake musu magana "Dan Allah ina son mutum d'aya daga cikin ku, ta taimaka ta xauna da yaran nan a asibiti,saboda akwai abubuwan da baxa su iya yi mata ba" cikin kulawa Habi ta amsa masa. "Ba komai Alhaji Mudi, ai ba sai ka ro'ke mu ba, dama muna da niyyar hakan, ai ba a hana maba da rago fata Alhaji, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ya tashi kafad'a" Amsa mata yayi da ameen. "ki fara shiri idan na dawo daga siyo magani xan biyo mu tafi" "to Alhaji ina jiranka" yana ficewa suka kalli juna ita da innah suka bushe da dariya. "lokaci fa yaxo innah, wanda xa mu yi amfani da damar mu, wajen 'kara kwantar da wannan shegiyar matar, kada mu kuskura mu barta ta tashi, kullum mu ri'ka yi mata turaren da Boka ya bamu, a rasa gane kan ciwonta, daga nan kin ga gida ya xama namu,ko ba haka ba?" "kwarai kuwa Habi haka xa a yi kin xo da magana mai kyau" wani buhu ta d'akko daga gefenta, wani turare ne 'kunshe cikin takarda "Ungo ki tafi da turaren nan asibiti, ki ri'ka turara mata shi,ba dare ba rana idan mai gidan yayi magana,kice maganin mayu ne, ni kuma xan cigaba da turara d'ayan a gidan nan, xan fad'a masa cewa ciwonta yana da ala'ka da jinnu,dole sai an turare gidan sannan xasu fita,a haka har sai mun cire mata son xaman gidan nan,daga xuciyar ta da 'ya'yanta gaba d'aya" kar6a tayi ta 'kulle shi a gefen xaninta, sannan ta shirya tsaf don tafiya asibitin. Abban Nauwar bai dad'e da fita ba, ya dawo don haka suka rankaya xuwa asibiti. *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba d'aya naku ne, ku yi yadda kuke so da shi, NADEEYAH BABA IBRAHIM & MARYAM LAWAL (MAAMA)* 3⃣8⃣ Abban Nauwar ne ya nuna mata d'akin da suke, shi kuma ya wuce gurin likita, da sallama ta shiga d'akin da su Nauwar suke, gurin zama ta samu, babu wanda ta kula sai faman kallon d'ai-d'ai take wa kowa na gurin, a dai-dai lokacin ne Abban Nauwar ya shigo, tare da likitoci don su cigaba da checking na lafiyar Ammi, tana ganin shi ta saki ranta ta hau subad'i, ita a dole sai ya fuskanci tana 'kaunar su. cigaba da juya Ammi suka yi, ana mata allurai gami da bata magunguna, aka yi sa'a ta farfad'o ta fara dawo wa hayyacin ta. kallon Abban Nauwar Habi tayi tana murmushin munafunci. "Alhamdulillah Alhaji, Allah ya taimaka wannan baiwar Allah ta fara samun sau'ki, yanxu kamata ya yi kuma a had'a mata da maganin hausa, saboda da alamar ciwon nan yana da nasaba da aljanu" cikin mamaki likitan ya dubeta. "Hajiya ke xaki nuna mana yadda xamu yi aikin mu, ba wani maganin gargajiya da xa a bata, ki barmu mu gwada ta mu sa'ar, idan aikin mu bai yi ba,sai ku je ku gwada na gargajiyar" girgixa kai Abban Nauwar yayi. "gaskiya ne ni kaina ban so shaye-shayen magungunan gargajiyar nan, gara a yi na asibitin xai fi sau'ki". ganin bata samu goyan baya bane,yasa tayi shiru xuciyarta cike da takaicin, ta samu dama amma bata yi amfani da ita ba. haka suka gama xaman asibitin bata samu damar turara mata komai ba,innah karime ce kawai ta samu damar yin nata turaren,ita ma kuma ba kullum ba, a haka suka kasance har suka dawo gida. A kwana a tashi kullum Ammi na 'kara samun sau'ki, kuma ko da yaushe mamin Hamdan na xuwa tana d'ebe mata kewa, su innah karime kuwa, d'aki aka ba su a cikin falon gidan, don haka duk abinda suke shukawa bata sani ba, kuma babu abinda ya canja na xamantakewar ta tsakaninta da mai gidanta, yana kulawa da ita gwargwadon iko. yau da kasala suka tashi, don ko abincin safe basu samu damar girkawa ba, Nauwar ce ta 'karfafa jikinta don shiga kitchen ta soya musu ko doya ce, innah karime da Habi ta gani,suna barbad'e-barbad'en magani, a cikin kayan abincin su, la6ewa tayi sai da suka kammala, taga duk guraren da suka xuba, sannan ta juya da sauri ta koma d'aki ta sanar da Amminta,bayan sun tafi ne, tasa aka fitar da kayan abincin gaba d'aya aka bai wa mai gadi sadakar su. ganin duk tsafe-tsafen da suke yi baya tasiri ne yasa suka canja sabon salo,saboda a nasu d'an 'karamin tunanin suna ganin ita ma asirin take yi, shi yasa duk abinda suke yi baya kamata, sai suka 'kara yanke shawarar komawa wajen boka, domin a shagalar da ita ga barin yin addu'a, saboda ta haka ne xa su samu damar cinta da ya'ki. wannan karon magaji suka aika don yaje ya kar6o musu maganin, cikin farin ciki ya kar6i aiken, a ranshi ya fad'a banxa ta fad'i xan je na shana son raina kai tsaye gidan magajiya ya xarce, don ya dad'e yana son samun kud'i,don ya hole son ransa, amma hakan ya ci tura, saboda rashin kud'in da ya baibaye shi. yana fi to ya shiga gidan, ya iske magajiya a xaune kan kujera, tana faman busa sigari,tana ganin shi ta mi'ke tana farin ciki, tasan duk lokacin da magaji xai xo da kud'i yake xuwa, d'aki ta shigar da shi ta bashi lemo da abinci, sai da ya ci ya 'koshi sannan ya fara mata magana. "Uwar shagalallu 'yar duma-dumar yarinya nake so yau a nan xan huce gajiyata" busa sigarin da ke hannunta ta cigaba da yi, sannan ta kalle shi tana juya idanunta. "duk 'yan matana basa nan sun fita, amma idan xaka iya jira sai ka jirasu har su dawo, amma fa ka tabbatar kaxo da wadataccen kud'i" "Haba uwar daba, kin san idan ba nida kud'i babu abinda xai kawo ni gidan nan, aljihuna a cike yake" zama yayi har sai da 'yan matan suka dawo, ya gama duk abinda xai yi, da yamma li'kis ya koma gida, suna ganin shi suka ri'ka murmushin farin ciki a tunanin su, yaje ya isar musu da sa'kon da suke so. xama yayi ran shi a 6ace, kamar wanda wani abu ya same shi, tambayar shi innah karime ta fara yi "lafiya naga kaxo ranka ba walwala, me ya faru" idanun shi ne suka firfito waje, alamar rashin gaskiya ya baiyana a fuskar sa. "wlh innah tun da na fita nake ta yawo a garin nan, kudin da ku ka aikeni da shi, sun fadi gaba d'aya,kuma ban san ya aka yi ba". dafe kirji tayi tana duban shi. "sun fad'i!!! kana hauka ne kaje ka xubar mana da kud'ad'e haka"? "kaddara ce innah, wlh bansan lokacin da suka fadi ba nima, kawai gani nayi babu kud'in a aljihuna" "karya kake yi tsohon munafuki, ko dai kaje ka bawa 'yan mata kud'in, don nasan yanxu abinda kasa a gabanka kenan" Habi ce ta le'ko da kai daga d'akin. "A'a innah karime kada ki yi wa jikana sharri,wane mata yaje yana rabewa kud'i, bana son irin wannan maganar ehe" ganin bala'in da Habi take mata ne, yasa ta yi shiru saboda tasan tsiyar Habi ta fi tata. *Jeeddahtulkhair*?[9/9, 9:09 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba d'aya naku ne, ku yi yadda kuke so da shi, NADEEYAH BABA IBRAHIM & MARYAM LAWAL (MAAMA)* 3⃣8⃣ Abban Nauwar ne ya nuna mata d'akin da suke, shi kuma ya wuce gurin likita, da sallama ta shiga d'akin da su Nauwar suke, gurin zama ta samu, babu wanda ta kula sai faman kallon d'ai-d'ai take wa kowa na gurin, a dai-dai lokacin ne Abban Nauwar ya shigo, tare da likitoci don su cigaba da checking na lafiyar Ammi, tana ganin shi ta saki ranta ta hau subad'i, ita a dole sai ya fuskanci tana 'kaunar su. cigaba da juya Ammi suka yi, ana mata allurai gami da bata magunguna, aka yi sa'a ta farfad'o ta fara dawo wa hayyacin ta. kallon Abban Nauwar Habi tayi tana murmushin munafunci. "Alhamdulillah Alhaji, Allah ya taimaka wannan baiwar Allah ta fara samun sau'ki, yanxu kamata ya yi kuma a had'a mata da maganin hausa, saboda da alamar ciwon nan yana da nasaba da aljanu" cikin mamaki likitan ya dubeta. "Hajiya ke xaki nuna mana yadda xamu yi aikin mu, ba wani maganin gargajiya da xa a bata, ki barmu mu gwada ta mu sa'ar, idan aikin mu bai yi ba,sai ku je ku gwada na gargajiyar" girgixa kai Abban Nauwar yayi. "gaskiya ne ni kaina ban so shaye-shayen magungunan gargajiyar nan, gara a yi na asibitin xai fi sau'ki". ganin bata samu goyan baya bane,yasa tayi shiru xuciyarta cike da takaicin, ta samu dama amma bata yi amfani da ita ba. haka suka gama xaman asibitin bata samu damar turara mata komai ba,innah karime ce kawai ta samu damar yin nata turaren,ita ma kuma ba kullum ba, a haka suka kasance har suka dawo gida. A kwana a tashi kullum Ammi na 'kara samun sau'ki, kuma ko da yaushe mamin Hamdan na xuwa tana d'ebe mata kewa, su innah karime kuwa, d'aki aka ba su a cikin falon gidan, don haka duk abinda suke shukawa bata sani ba, kuma babu abinda ya canja na xamantakewar ta tsakaninta da mai gidanta, yana kulawa da ita gwargwadon iko. yau da kasala suka tashi, don ko abincin safe basu samu damar girkawa ba, Nauwar ce ta 'karfafa jikinta don shiga kitchen ta soya musu ko doya ce, innah karime da Habi ta gani,suna barbad'e-barbad'en magani, a cikin kayan abincin su, la6ewa tayi sai da suka kammala, taga duk guraren da suka xuba, sannan ta juya da sauri ta koma d'aki ta sanar da Amminta,bayan sun tafi ne, tasa aka fitar da kayan abincin gaba d'aya aka bai wa mai gadi sadakar su. ganin duk tsafe-tsafen da suke yi baya tasiri ne yasa suka canja sabon salo,saboda a nasu d'an 'karamin tunanin suna ganin ita ma asirin take yi, shi yasa duk abinda suke yi baya kamata, sai suka 'kara yanke shawarar komawa wajen boka, domin a shagalar da ita ga barin yin addu'a, saboda ta haka ne xa su samu damar cinta da ya'ki. wannan karon magaji suka aika don yaje ya kar6o musu maganin, cikin farin ciki ya kar6i aiken, a ranshi ya fad'a banxa ta fad'i xan je na shana son raina kai tsaye gidan magajiya ya xarce, don ya dad'e yana son samun kud'i,don ya hole son ransa, amma hakan ya ci tura, saboda rashin kud'in da ya baibaye shi. yana fi to ya shiga gidan, ya iske magajiya a xaune kan kujera, tana faman busa sigari,tana ganin shi ta mi'ke tana farin ciki, tasan duk lokacin da magaji xai xo da kud'i yake xuwa, d'aki ta shigar da shi ta bashi lemo da abinci, sai da ya ci ya 'koshi sannan ya fara mata magana. "Uwar shagalallu 'yar duma-dumar yarinya nake so yau a nan xan huce gajiyata" busa sigarin da ke hannunta ta cigaba da yi, sannan ta kalle shi tana juya idanunta. "duk 'yan matana basa nan sun fita, amma idan xaka iya jira sai ka jirasu har su dawo, amma fa ka tabbatar kaxo da wadataccen kud'i" "Haba uwar daba, kin san idan ba nida kud'i babu abinda xai kawo ni gidan nan, aljihuna a cike yake" zama yayi har sai da 'yan matan suka dawo, ya gama duk abinda xai yi, da yamma li'kis ya koma gida, suna ganin shi suka ri'ka murmushin farin ciki a tunanin su, yaje ya isar musu da sa'kon da suke so. xama yayi ran shi a 6ace, kamar wanda wani abu ya same shi, tambayar shi innah karime ta fara yi "lafiya naga kaxo ranka ba walwala, me ya faru" idanun shi ne suka firfito waje, alamar rashin gaskiya ya baiyana a fuskar sa. "wlh innah tun da na fita nake ta yawo a garin nan, kudin da ku ka aikeni da shi, sun fadi gaba d'aya,kuma ban san ya aka yi ba". dafe kirji tayi tana duban shi. "sun fad'i!!! kana hauka ne kaje ka xubar mana da kud'ad'e haka"? "kaddara ce innah, wlh bansan lokacin da suka fadi ba nima, kawai gani nayi babu kud'in a aljihuna" "karya kake yi tsohon munafuki, ko dai kaje ka bawa 'yan mata kud'in, don nasan yanxu abinda kasa a gabanka kenan" Habi ce ta le'ko da kai daga d'akin. "A'a innah karime kada ki yi wa jikana sharri,wane mata yaje yana rabewa kud'i, bana son irin wannan maganar ehe" ganin bala'in da Habi take mata ne, yasa ta yi shiru saboda tasan tsiyar Habi ta fi tata. *Jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *Masoya na tafi Kwana da kwanaki ko cigiyata Ma ba a yi ba na gode, kuma Duk nayi fushi da ku* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 3⃣9⃣ Washe garin ranar Asabar suka yi shirin xuwa yawon neman asirin da suka saba, ba su yi wa kowa sallama ba suka kama hanyar Zuwa Dan batta, babu abinda xuciyar su ke musu saka face sharrin da xasu kulla don kawar da Ammi da yayanta Daga doron kasa Domin su samu Farin ciki da Jin dadi na har abada. Da isar su tasha suka samu mota, ba tare da bata lokaci ba suka dauki hanyar garin Dan batta. basu fi rabin awa suna tafiya ba suka isa garin. A tashar garin motar ta sauke su don haka suka kama hanyar gidan boka don Ko gidan Baffa basu nema ba, suka wuce dan gudanar da abinda ya dame su. tafiya Kawai suke yi babu wanda yake iya cewa dan uwansa komai kasancewar dukkansu suna cikin damuwa da alhinin kudaden da suke batarwa ba tare da sun samu biyan bukata ba, isar su wajen ke da wuya suka tarar da kofar Bokan a kulle, mamaki ne ya kama su saboda tunda suke xuwa basu taba tarar da hakan ba. Don haka suka nemi wajen xama, suna jiran tsammanin ganin ta inda xai bullo. Bai fi xaman awa daya suka yi ba, guguwa mai karfi suka ji ta tunkaro inda suke. Tsoro ne ya kama su,suka fara janye jikin su, wani irin gunji gami da gurnani guguwar ke bayarwa tare da dariya mai ban tsoro, ga wani haske mai cike da walkiya da yake tashi, matsawa suka fara yi, amma da sun matsa sai ta kara tunkaro wajen da suke. Sai da ta xo daf da su wani hasken wuta ya bayyana Mutum ne sanye da warki wanda aka hada shi da fatar damisa, hannunsa jere yake da guru da layu, gemunsa kuwa har jan kasa yake, ga wasa layu shirye a kugunsa da dantsen hannayensa idanunsa kuwa tamkar garwashin wuta, da dukkan alamu dai ba Bokan da suka sa ba xuwa wajen sa bane, don wannan na yanxu, ya fi wancan hatsabibanci, ja da baya suka shiga yi. cikin kakkausar murya ya daka musu tsawa "Me ke tafe da ku"?? yana maganar wuta na fitowa daga bakinsa. Cikin rawar murya innah karime ta amsa masa "Dama wajen boka na innah Muka Zo sai kuma Muka tarar baya nan, dama.... Dama....... Nuni yayi mata da hannunsa "bana bukatar Jin komai Daga gareku" Wani mudubi ya dakko a cikin wata salka ya mika musu, murmushi suka yi gami da gyada kai, alamun sun samu gamsuwa da aikinsa, hoton Ammin Nauwar ne ya bayyana da Abbansu da Duk yayansu gaba daya. dago jajayen idanunsa ya yi, ya kalle su "me kuke so a yi musu ? ya fadi maganar tare da fitar da hayaki daga bakinsa. Muna hallaka mutum Muna lalata shi Muna raba soyayya, muna raba mutum da hankalinsa, muna tsinewa mutum. Wannan duk aikina ne wanne Ku ka xaba a ciki ? Innah karime ce ta dago da sauri ta kalle shi Abinda muke so Allah gafarta ran boka, ita wannan matar tasa a haukatata, yar su kuma a sa ta shiga duniya Shi kuma wannan yaron nasu namiji a hallaka Shi, ta haka ne xamu samu mu mallake duk abinda muke so. Ko ya kika ce Habi ?? Tabbas xancen ki na kan tsari innah haka za a yi Bushewa yayi da dariya an gama. Wata laya ya dakko wadda ke kunshe cikin wani tsumma ya mika musu,da hannu biyu suka sa suka karba. Ya xamuyi da ita Allah gafarta Malam? Daka musu tsawa yayi tare da nuna su da hannu. bana son yawan tambaya da karambani. Wannan ku jefata a kogi, kuna jefawa xata haukace baxa ta samu sauki ba har abada, kafin ku isa gida yanxu xan tura uwar daji ta fara aikinta. wannan kasar kuma Ku barbada ta cikin gidan muddin suka taka shi yaron kashinsa ya bushe ita kuma yarinyar ta yi bankawana da rayuwar gidan har abada. Kudi suka mika masa, nuni yayi musu da hannu alamun baya bukatar komai daga gare su. Don haka suka tashi xuciyar su cike da Farin ciki. Haka suka cigaba da keta dajuka da ciyayi a kan hanya suka ci Karo da Audu inda suka kwashe labarin duk abinda ya gudana tsakaninsu da boka, yayi farin ciki kwarai da gaske. ba tare da bata lokaci ba ya karbi layar don yaje kogi ya jefata su kuma suka wuce tasha don hawa mota. Ammi ce kwance a kan gado idanunwanta na rufe ji take kawai kanta na juyawa, bata iya gane komai, addu'a ta shiga yi tare da karanta ayatul kursiyyu, wani duhu take ganin yana kusanto inda take, amma da ta karanta addua sai ya gushe, tana tsayawa sai ya kara kusanto ta, haka suka rika yi har xuwa lokacin da bacci yayi awon gaba da ita, a cikin baccin taji kamar abu ya tsikareta don haka tayi saurin farkawa tare da ambaton Allah, duhun daxu ne ya kara dawo mata, juyawa kanta ya rika yi yawun bakinta ya kafe gaba daya ta kasa karanta komai, wata mata ta hango a cikin duhun ta kusanto inda take, idanunta jawur gashin kanta a tsafe, matsowa ta rika yi inda take tana kawo mata duka, da karfi taja hannunta ta danna mata wasu layu a baki, wani ihu Ammi take yi tamkar haniniyar doki tun daga lokacin bata sake sanin a duniyar da take ba. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 4⃣0⃣ Haka ta kasance cikin matsanancin hali har xuwa lokacin da su innah karime suka iso gidan, cikin gadara da nuna isa, suka tura kofar gidan danna kansu falo suka yi kawai ba tare da sallama ba. ihun Ammi suka ji yana tashi, cikin farin ciki suka karasa dakin da take tarar da ita suka yi kwance cikin mawuyacin hali, hada idanu suka yi suka tafa suka bushe da dariyar mugunta. Guda habi ta shiga yi, Alhamdulillah aiki ya biya,kwance gefen xaninta tayi ta fito da maganin da boka ya basu ta shiga barbada mata a jiki, nan da nan yanayinta ya sake sauyawa kamaninta gaba daya suka juye ta koma tamkar wacce ta fito daga jinsin shaidanu, ihu ta shiga yi tayo kansu a guje suka fice suka kulleta a dakin. barbada maganin suka cigaba da yi a duk lungu da sako na cikin gidan,sannan suka koma dakinsu suka mayar da kofa suka kulle. innah ce ta dubi Habi, "Allah ya amsa rokonmu xamu yi yadda muke so a gidan nan, wannan shekarar har aikin hajji sai mun je mun sauke farali" "ai bokan nan karshe ne innah, ya iya aiki ga shi babu ko sisin mu sai riba da muka samu, jira nake yi yaran nan su dawo daga makaranta, su taka maganin nan, su ma tasu ta kare kowa ya huta, ni yanxu babban abinda ya dameni kada magaji ya dawo daga gantalinsa ya bi, ta kan maganin alhalin ba dan shi aka xuba ba, tashi mu fita mu yi gadin sa a waje kada garin neman gira mu rasa ido. fitowa suka yi gaba daya,suka nufi kofar fita daga falon, xamansu ke da wuya Nauwar da fu'ad suka dawo daga makaranta, sallama suka yi musu amma ko yan kallo basu ishe su ba, don haka basu tsaya gaisawa da su ba suka nufi hanyar shiga cikin gida, tun daga bakin kofa suke jiyo ihu da haniniya kamar na doki, don haka suka saurara don jin ta inda ihun yake fitowa. Nauwar ce ta dubi fu'ad "ni fa ihun nan jinsa nake kamar daga cikin dakin Ammi yake" tsayawa suka yi suka saurara sosai, sannan suka danna kansu falo,ba tare da tunanin akwai abin cutarwa a cikinsa ba, sai da suka kai tsakiyarsa, taji fu'ad ya saki wani ihu mai raxanarwa ya fadi kasa babu abinda ke fitowa daga bakinsa sai dafara, gigicewa Nauwar tayi ta rasa inda xata sa kanta, fadawa kanshi tayi tana kuka mai cike da ban tausayi. "kada ka mutu fu'ad ka barni dan Allah ka tashi ka taimakeni dan Allah kayi magana" da taga alamar dai baya cikin hayyacinsa nan da nan ta fita ta kira mai gadi aka saka shi a mota suka tafi asibiti. da isarsu aka fara duba shi, aka bashi taimakon gaggawa ya fara farfadowa farin ciki ne ya cika xuciyarta sai a lokacin ta tuna bata ga Amminta ba, don haka ta dauki waya ta fara kiranta, wayar na ta ringing amma an ki dauka, sai da tayi mata missed call wajen goma ba a amsa ba, don haka ta fara kiran Abbanta ta sanar da shi halin da ake ciki, ba tare da bata lokaci ba ya dakko mota ya biyo su asibitin, a lokacin da ya iso jikin fu'ad ya kara tsananta ko hannunsa baya iya dagawa, hankalinsa ya tashi sosai, babu abinda yake iya yi banda hawaye. tambayarta ya shiga yi ina Amminta da su innah karime cikin kuka ta fada masa cewa Amminta ta tafi unguwa, su Innah karime kuma suna nan amma basu taho tare da mu ba. A fusace ya dauki key ya fita don yaje ya same su ya ci musu mutunci, yana isa gidan ya tarar da su xaune sun baxa tabarma suna cin abinci, ko sallama bai musu ba ya hau yi musu fada. "yanxu dan Allah innah ya kamata a ce fu'ad yana cikin wani hali kun kyale shi daga shi sai yarinya a wajensa babu wanda xai bisu yaga halin da suke ciki, ya dace abinda kuka yi. innah ce ta karbi xancen kayi hakuri Alhaji, abinda xan fada maka ba mai dadi bane kuma shi ne dalilin da yasa bamu bi yarinyar nan asibiti ba, sbd idan muka tafi tare da ita mu ma abin xai iya ritsawa da mu. cikin mamaki ya dubeta "wane abu ne ya faru, da har ku ke tsoron kada ya ritsa da ku? hawaye innah karime ta shiga sharewa "wlh Alhaji yarinyar nan makiyiyarka ce bata kaunarka bata kaunar ganin cigabanka da farin cikinka, guba ta bawa yaron nan yaci ya shiga wannan halin da yake ciki. kallonta yayi idanunsa cike da kwalla, guba fa kika ce innah, anya Nauwar xata bawa fu'ad guba kuwa, yarinyar nan tana son dan uwanta da yawa fa. wlh ba karya nayi maka ba Alhaji guba ta bashi, tunda ka kyaleta tana xuwa makarantar yahudawa komai ma xata iya aikatawa. Falo ya shiga ya fada kan kujera ya rika kuka tamkar karamin yaro, sai dai har yanxu xuciyarsa bata gama yarda cewa Nauwar ce ta aikata wannan danyen aikin ba. daurewa yayi ya tashi ya tafi asibitin sai dai yana dosar kofar dakin ya jiyo kukan Nauwar da mai gadi, da sauri ya karasa inda suke ya tarar da Nauwar kwance kan gawar fu'ad tana kuka mai cike da ban tausayi, cak ya dauketa yayi jifa da ita gefe guda ya shiga dukanta ta ko'ina, har sai da likitocin suka shigo suka karbeta. tambayarsa suke yi, lafiya Alhaji, kawai nuna ta yake da hannu ya kasa magana sai kuka da yake yi cikin kukan yake fada musu cewa ita ce ta kashe shi. ita ma Nauwar din kukan take yi, kamar ranta xai fita. "wlh bani na kashe shi ba Abbah" mamaki ne ya kamasu don su kansu maganar bata bi jikinsu ba, daya daga cikin likitocin nan ya dafa kafadarsa "Alhaji kabi abin nan a hankali a yi bincike don wannan yarinyar da gani baxa ta aikata haka ba" ture hannunsa yayi,"kaga dakata malam, ba a shedar dan yau, baxan kyale maganar nan ba dole a dauki mataki" wayarshi ya dauka ya kira yan sanda a mintunan da basu wuce biyu ba, yan sanda suka xo suka yi awon gaba da Nauwar don a gudanar da bincike. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* *wannan shafin gaba daya naki ne halak malak kiyi yadda kike so da shi AYSHA AHMAD SANI (YAR LONDON) ana mugun tare* 4⃣1⃣ Tun a motar take ta rusa ihu, ita kam yanxu ji take kamar Allah ya dauki ranta ta bi fu'ad ta huta da bakin ciki da kuncin rayuwar da take ciki. suna isa police station din aka fito da ita daga motar suka shiga ciki domin a fara gudanar da bincike. kuka take yi mai ban tausayi, cikin rarrashi da lallabawa yan sandan ke yi mata magana, "ki kwantar da hankalinki indai babu hannunki a cikin kisan yaron nan xaki fita,kiyi shiru ki daina kuka, yanxu xamu tura wakilin mu Asibitin su tabbatar da cewa guba aka bashi,ko mutuwar Allah da Annabi yayi, baxa mu yanke miki hukunci ba tare da mun bincika gaskiya ba. kalaman dan sandan su suka kwantar mata da hankali ta ji sanyi a ranta, sannan aka umarci wata yar sanda ta shigar da ita jail kukanta ne ya kara tsananta, yau ita ce a cikin mummunan matsayi, kuma da sa hannun mahaifinta aka kawota, yanxu tasan babu wani gata da ya rage mata, banda na Hamdan, tasan da yana gari da duk haka bata faru ba, don baxai taba barinta a cikin mawuyacin hali ba. ji take kamar ta bar duniyar ta huta da bakin cikin rayuwa. bayan yan sanda sun tafi da Nauwar, Abbanta ya cigaba da kiran yan uwa da abokan arxiki yana sanar da su mutuwar fu'ad da abinda ya faru da Nauwar, amma babu wanda ya yarda da maganarsa, saboda yanxu kowa ya fahimci halin kunci da su Nauwar ke ciki ita da mahaifiyarta, kafin a dauki gawar likitoci suka tabbatar masa da cewa yaron ba guba ya sha ya mutu ba, kawai lokacinsa ne yayi, amma duk da haka yaki amincewa don haka suka kyale shi ya dauki gawar don xuwa a yi mata suttura. bayan komai ya lafa hankali ya kwanta, mahaifin Hamdan yaje ya same shi don su tattauna a kan abinda yake faruwa da Nauwar, amma gaba daya ya birkice masa yaki xancen, sai hakura yayi ya kyale shi. A kullum su innah karime sai kara hura wutar bala'in suke yi suna dada xuga shi, wannan dalilin yasa bai sake komawa ta kan xancen Nauwar ba, ko abinci ba ya kai mata, sai dai yan sandan su ji tausayinta su bata, sai da tayi kwana 5 a hannunsu ba tare da ya waiwayi inda take ba. A ranar da fu'ad xai cika kwana bakwai da rasuwa manyan unguwa da baban Hamdan suka hadu suka xo wajensa, domin samarwa Nauwar mafita, a bakin gate suka tarar da shi yana kokarin fita da mota, don haka suka dakatar da shi, bayan sun gaisa suka fada masa abinda ke tafe da su, sai da yayi kamar baxai saurare su ba, ganin yadda suka xo da yawa ne yasa suka yi masa kwarjini ya tsaya. falo ya shigar da su, suka fara yi masa bayani "gaskiya Alhaji abubuwan da suke faruwa a gidan nan basu kamace ka ba, ya xa ai a ce yaro ya rasu ka dorawa karamar yarinya laifi kace ita ta kashe shi, kuma likitoci sun tabbatar maka da ba guba yasha ya mutu ba,me yasa xaka rika irin wannan a matsayinka na babban mutum. sannan mun ji labarin cewa tunda yaron nan ya rasu, ba a sake gani ko jin labarin mahaifiyarsa ba amma baka neme ta ba, ka sani iyalinka amana ne a gareka, kuma sai an tambayeka a kan amanar da aka baka, shin ka kula da ita ko kuma kayi watsi da ita, ya kamata kasan abinda kake yi, kuma mu yanxu mun yanke shawara ko ka yarda ko baka yarda ba, xamu tafi gaba dayanmu tare da likitoci a karbo yarinyar nan sbd kowa yasan babu hannunta a ciki. shiru yayi ya kasa magana, sai dai hawaye da yake sharewa kawai, da dukkan alamu yana jin xafin abinda yake yiwa iyalin nasa. Dakata!!! malamai munafukai. gaba daya daga idanunsu sama suka yi suna ganin ikon Allah, innah karime ce tasha dammara tana xare idanu tana nuna su da dan yatsa. ina labe ina jin duk abinda ku ke kullawa, to babu munafukin da ya haifarwa mudi yarsa a cikin ku, don haka shi yake da ikon yanke duk hukuncin da yaga dama a kanta,me yasa lokacin da ta aikata abin baku xo kun hanata ba, sai yanxu xaku xo da wasu kafafunku kamar an kafawa katako kusa, kuce xa ku yi magana, to wlh baku isa ba, babu wanda ya isa ya hana a daure yarinyar nan ko a dauki hukuncin da ya dace a kanta, munafukan banxa munafukan wofi." kallonta kawai suka yi babu wanda ya tanka mata, kasancewar duk ta haife su, don haka baxa su iya musu da ita ba, amma kuma maganarta bata sa sun fasa abinda suka yi niyya ba. Tashi suka yi gaba daya suka fita daga gidan, kai tsaye police station suka wuce. wajen D.P.O suka shiga suka fada masa duk abinda ya faru, sannan likitoci suka mika masa takardar da take tabbatar da cewa ba guba yasha ba, a daidai lokacin Abban Nauwar din ya shigo inda yace ya janye karar, don haka aka fito da Nauwar "kallo daya xaka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin mawuyacin hali, duk tayi baki ta rame, tana ganin Abbanta ta rushe da kuka mai ban tausayi, ko kallonta bai yi ba, hakuri mutanen wajen suka shiga bata. kiyi hakuri Nauwar kowane bawa da irin yadda Allah yake jarrabarsa ki kaddara cewa irin taki jarrabawar kenan, idan kika yi hakuri da sannu xaki cinye" wadannan nasihohin su suka sanyaya mata ranta ta daina kuka. mota suka shiga suka taho gida, su kuma mutanen suka wuce guraren harkokinsu. yau ma tana nufo kofar gidan taji haniniyar doki irin wacce taji kwanaki, amma ta yau tafi ta kullum don yau din a kusa take jinta, tana sauka daga motar ta fara laluben inda sautin yake fitowa, mutum ta hango daure a cikin gidan da ake saka Gen, bude idonta tayi sosai don ganin wanda aka saka a ciki, da gudu ta karasa wajen tana isa ta iske Amminta ce, kuka mai tsanani ta saki ta fada kan kejin sumammiya. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *wannan shafin gaba daya naki ne LAILA SANI MUH'D (maman teemah) Thnx 4 d love and support* 4⃣2⃣ Mai gadi ne yaji faduwarta ya taho da sauri, tarar da ita yayi ta suma don haka yayi hanxarin lekawa cikin gida ya kira su innah karime ya fada musu abinda ya faru, amma gaba daya suka balbale shi da masifa, suka yi masa korar kare ruwa ya samo ya yayayfa mata, cikin ikon Allah aka samu ta farfado, a hankali ta fara bude idanunta tana salati, hakuri ya shiga bata yana rarrashinta "kiyi hakuri Allah yana sane da halin da kuke ciki, addu'a ita ta kamace ki ba kuka ba" jinta take gaba daya bata cikin hankalinka, a hankali ta karfafa jikinta ta mike, xaunawa tayi don jiri ne ke dibarta, nasiha mai gadi ya cigaba da yi mata,har xuciyarta ta warware daga raunin da ta samu kanta a ciki. yanxu jinta take xata iya karawa da duk wanda ya takaleta da fada, ko ya taba mata mutuncin Amminta, don haka ta mike ta dubi gurin da Ammi take a daure. sunan mai gadin ta kira "malam Ali ina aka jiye mukullin wajen nan, kuma me yasa ka bari aka saka mahaifiyata a ciki" cikin ladabi ya amsa mata "wlh ban sani ba ranki ya dade, su Hajiya ne suka sakata a ciki kuma mukullin yana hannun su" A fusace ta wace gurinsu innah karime ta same su tare da su magaji ana ta hira nuna su tayi da hannunta "abinda ku ke mana ya ishe ku haka, hakuri ba hauka bane, idan tura ta kai bango dan Adam baya jurewa, wane dan iskan ne ya saka min uwa a cikin keji?" dafe kirji innah karime tayi tana mamakin kalaman da ke fita daga bakin Nauwar, gaba daya ta kasa magana sbd bata taba xaton jin hakan daga gareta ba. magaji ne ya mike "wane ne dan iskan a nan, babu wajen da ya dace mahaukaciyar uwarki ta xauna, idan ba xaman turu ba don baxa mu kyaleta a nan, ta bata mana guri da warin kashi ba" bata san lokacin da ta daga hannu xata kwada masa mari ba, rike hannunta yayi. "ko wannan mahaukaciyar uwar taki bata isa tace xata mareni ba, ballantana kuma ke, kuma wlh kin yi na farko kuskure ne idan kika sake yin na biyu ganganci ne, sai kinga yadda xan yi dake a cikin gidan nan, banxa shashasha wacce ubanta bai damu da ita ba" kuka ne ya kwace mata ta fita a fusace ta samu wani katon katako, ta saukewa magaji a kansa, nan da nan ya kamata da kokawa suka rika yi, maigadi ne ya jiyo hayaniya ya shigo ya raba, amma su innah karime cewa suka yi baxa su raba ba, sai ya kasheta su ga abinda xai faru. idanunta a rufe ta fita, gidansu Hamdan ta nufa, kai tsaye dakinsu ta shige ta tarar da momy xaune akan kujera tana isa wajenta ta fada kanta tana kuka, tambayarta ta rika yi. "lafiya Nauwar na ganki a haka me ya faru da ke kike kuka, kiyi hakuri ki fada min matsalar ki" ta kasa fada mata komai sai hawaye gami da ajiyar xuciya da take yi "ki fada min Nauwar dan Allah hankalina ya tashi sosai" cikin kuka take fada mata halin da Amminta take ciki da abinda su innah karime suka yi mata, mayafinta ta dauka suka tafi gidan tare, suna isa ta tarar da Ammi a wannan hali, hawaye ne suka rika xubo mata. "Rehab yanxu kece kika xama haka, kece a wannan halin, gaskiya mahmud yaci amana, bai rike amanar da ya karbo a wajen mahaifanki ba, ya raboki da danginki ya kawo ki wajen da baki da kowa,kuma baki san kowa ba, gaskiya duniya abin tsoro ce" kiran mai gadi tayi tasa ya balle wajen, tunda su innah karime sun hana mukullin, ana budewa tayo kansu da gudu xata dake su,da kyar maigadi yayi ta maxa ya riketa aka shigar da ita daki, gaba dayansu kuka suke babu mai iya rarrashin wani, sbd tausayin Ammi da suke ji. Toilet suka shigar da ita suka canja mata kaya masu kyau, kasancewar tafi sati guda rabonta da taga ruwan wanka, bayan sun dawo da ita daki suka dafa mata abinci mamin hamdan ce take bata,amma da sun bata sai ta furxo da shi ta rika wani ihu kamar na kukan jaki, a haka ta cigaba da bata har ta koshi. mamin Hamdan bata bar gidan ba har sai bayan sallar isha'i Bayan tafiyarta ne Abban Nauwar ya dawo, tana jin karar motarsa ta fito da saurin don ta tarbe shi, amma yana ganinta ya nuna kamar bai ganta ba ya shige bangarensa. bai fi minti biyu da shigowa ba, innah karime ta shiga ta same shi ta xayyana masa abinda ya faru ta hada masa da abinda ya faru da wanda bai faru ba shi kuma ya hau kai ya xauna. A fusace ya fito, yana kiran sunan Nauwar "Nauwar!! Nauwar!! kina ina ne?? jikinta na rawa ta fito don tasan ba alkhairi ne yasa shi kiran sunanta ba. har kasa ta tsugunna, idanunta na kasa tayi masa magana. "gani Abbah" nunata yayi da hannu "kada ki kuskura ki kara kirana da Abbanki ni ba ubanki bane, ni ban haifi wacce xata kashe dan uwanta ba, ban haifi wacce xata ce xata kashe dan uwana ba, daga yau sai yau idan kika kara ikrarin xaki kashe magaji wlh sai na daure ki, sai kin kare rayuwar ki a gidan yari, kuma yanxu yanxu ina son ki tattara kayanki ki fita daga gidan nan, bana son kara ganinku daga ke har mahaukaciyar uwarki" gaba daya ta nemi hawaye a idonta ta rasa, wani daci ne yake taso mata tun daga kasan xuciyar ta, xata bude baki tayi masa magana ya dakatar da ita. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba dayansa sadaukarwa ne ga members na Al-majira fans 1 $ 2 Ina godiya da yadda kuke nuna kulawar ku da kaunar ku ga wannan littafi na gode Allah ya bar xumunci* 4⃣3⃣ Haka ta tashi jikinta a sanyaye ta wuce daki, a hanyar shigarta dakin taci Karo da Habi, bushe mata da dariya tayi Sannan ta dube ta " ba dai ke Mara kunya ba, Kadan kika gani kuma barin gida ya xama dole, sai dai idan rashin xuciya ne xai xaunar da ku" Hawaye masu Xafi ne suka rika kwarara a kan fuskarta, Kai tsaye ta shige daki ta fada kan gado ta fara kuka mai cike da ban tausayi, ta rasa wanda xata ra6a taji dadi ballantana har ta samu damar tattauna matsalarta dashi taji sanyi a ranta. Bugun kofar da ake yi ne yasa ta dawo hayyacin ta a hankali ta tashi don bude kofar dakin,Abbansu ta gani tsaye babu alamar annuri a fuskarsa, suna hada Ido gabanta ya fadi, tasan ba alkhairi ne ya kawo shi ba. Cikin tsawa yake mata magana. "me kike yi har Yanxu baki tattara kayan ki kin bar min gida ba, bana son Ki Kara minti biyu ba tare da kin bar gidan nan ba, Ina nan tsaye Ki hada kayanki Kisan inda dare yayi miki,da ke damu nahaukaciyar mahaifiyarki, bana bukatar na sake bude ido naga giftawar ku a gidana. Fadawa kan shi tayi tana kuka "Haba Abba me Muka yi maka ka tsane mu, idan ka Kore mu ina Kake son mu je, ya Ka ke son mu yi da rayuwar mu ina Kake son mu ra6a mu ji sanyi, bamu da Kowa sai Kai Abbana sai Allahn da ya hallicce mu, Idan kace ka juya mana baya a Yanxu wane hali Kake tunanin xamu fada, na rasa dan uwana, mahaifiyata ta rasa hankalinta,ya zan yi da rayuwata Abbana" ta karasa maganar tana kuka. Saboda tsanin kukan da take yi wasu maganganun ma basa fita.sai da ya gama saurarenta tsaf, ya tureta gefe guda, ya fara mata magana da kakkausar murya. "Ina ruwana da inda xaki, duk inda kika ga ya dace ki tafi mana ba damuwata bace, ai ita duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai sani ba, ku tafi ku girbe abinda ku ka shuka na sharri ke da uwarki" Yana karasa maganar ya fara jefo musu kayan su fall, yana gamawa ya Kira magaji suka fitar da kayan waje Sannan yasa aka jefo Ammi da Nauwar kofar gidan, Sannan ya mayar da kofar gate din shi ya kulle. Kukanta ne ya Kara tsananta Anya kuwa ba mafarki take yi ba, wannan masifa da me tayi kama, ko a mafarki bata taba zaton xata samu kanta a cikin wannnan halin ba, murxa idanunta tayi don ta Kara tabbatar da abinda take ganin ba Gaskiya bane, Yanzu babanta mahaifi wanda yake kaunarsu wanda baya son ganin bakin cikinsu shi ne yayi mata haka, gaskiya asiri bala'i ne, baza ta taba yafewa wanda ya shiga tsakaninta da Abbanta mai kaunar ta ba, kwantawa tayi a kan kayan su tana ta faman kuka, tafi rabin awa tana abu daya, ganin baza ta samu mai taimakonta ba kasancewar dare ya yi, duk makotan su sun kulle gidajen su, wannan yasa ta dago ta fara tunanin nemawa kansu mafita, dagowar da xata yi ta nemi Ammi ta rasa, hankalinta ne ya Kara tashi ta bazama nemanta tana tafiya tana rusa kuka. "Allah ka taimaki rayuwata kaga halin da nake ciki, Allah ka bayyana min mahaifiyata " Tafiya tayi mai Nisa Sannan ta hangota kwance kan wata bola tana tsintar kaxanta tana ci, da hanxari ta karasa ta karbi abinda take ci, dabara tayi mata ta tashe ta daga wajen,suka Kara komawa kofar gidan su ko Allah xai sa Abbansu yaji tausayin su ya bude musu su shigo, abin mamaki tararwa tayi an kwashe kayan da suka Bari gaba daya babu abinda aka bar musu sai kayan jikin su. Haka suka xauna a wajen har xuwa lokacin sallar asubah,yana fitowa ya tarar da su ya sake yi musu sabuwar tijara, maigadi ne ya jiyo hayaniyar sa ya fito don ganin abinda ke faruwa, tunda yasan yanxu gidan ba xaman lafiya ake yi ba. Hakuri ya rika bashi "Gaskiya Alhaji idan aka yi wa bayin Allahn nan haka ba a kyauta ba, kuma ba a yi musu adalci ba, yanxu idan ka Kore su ina xasu je?ka duba fa halin da Hajiya take ciki yanxu gaba daya bata hankalinta, Idan ka koresu Waye xai karbe su, Tunda kaine dolen su, bai kamata kayi musu haka ba, Idan ka kyale su kamar kayi toxarta rayuwar su ne" Tsawa ya daka masa "saurara Malam aikin gadi na dauke ka ko kuma bada Shawara? Bana son munafunci da sa ido, daga Yau ba ruwanka da abinda ya shafi harkar iyalina, ka tsaya iya matsayinka na Mai gadi". Tsugunnawa yayi har kasa "Allah ya huci xuciyar ka Alhaji, na fada maka gaskiya ne Sbd xaman tare bai ce haka ba, Amma kayi hakuri baza a sake ba Insha Allahu" Binsa yayi da harara, wucewa dakinsa yayi ya barshi yana ta balbala fada. Korarsu yayi, sai da ya raka su har karshen layin unguwar Sannan ya dawo. Haka suka wuce suna tafiya Nauwar na kuka tana tuna rayuwa "tabbas duniya abar tsoro ce kuma ba tada tabbas tana iya juya maka baya a kowane lokaci. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *wannan shafin gaba dayansa sadaukarwa ne gareki QUEEN MARYAM (maman surayya)ina godiya da kulawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci ina yinki irin mugun sosai din nan* *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 4⃣4⃣ Haka suka rika gararanba a cikin unguwa har kusan magariba,duk wanda ya Kalli halin da suke ciki sai ya tausaya musu, ya kuma yi Allah wadai da halin mahaifin Nauwar. Tafiya suka cigaba da yi ba tare da sun tsaya ba, saboda tana gudun kada a samu masu tsaigumi su je su fadawa Abbanta, cewa har Yanxu basu bar cikin Unguwar ba, Don haka tayi gaggawar neman hanyar da xata tsira da mutuncinta da na mahaifiyarta, tana tafe tana kuka ita kuma Ammi na kokarin xillewa ta barta kasancewar yanxu bata gane komai ba kuma ta iya fahimtar komai. Sai da suka yi nisa da Unguwar sosai sannan suka tsaya, bakin kofar wani gida ta samu domin sun gaji da tafiya tana son su huta kuma su Kwana a wajen, idan gari ya Waye kuma tayi tunanin inda ya dace su tafi, domin xaman su a haka ba mai yiwuwa bane. tunanin zuwa Dan batta tayi, sai kuma taga cewa idan taje Dan batta Akwai yiwuwar Abbansu Yaje ya Kore su,don haka ta yanke shawarar tafiya tasha duk motar garin da ta samu, Kawai xasu hau tunda Akwai yan canji a a jikinta. A Yanxu babu abinda ya fi damunta Sama da lalurar Amminta,da rashin wanda xai taimaka mata wajen nema mata magani, tana tunanin hawaye na sauka a kan fuskarta. Wata murya mai sanyi taji ta mata Magana, saurayi ne wanda baxai wuce shekara talatin ba xuwa talatin da biyu yayi mata magana, da dukkan alamu yana da nutsuwa da addini. "Assalamu alaikum yan mata" Dago fuskarta wadda ke cike da hawayen bakin tayi, hanxarin goge hawayen tayi ta dube Shi, cikin ladabi ta amsa masa sallamar "wa alaikumussalam wa rahmatullah " Dubanta yayi yana murmushi. "kin burgeni yan mata kin iya amsa sallama, kuma ba kida wulakanci da girman kai, yadda kike mai kyan nan ya kamata a ce Kina da girman kai amma da yake Kin san darajar dan Adam sai kika amsa min cikin sakin fuska, Allah yayi miki albarka " Amsa masa tayi da Ameen, ya cigaba da surutu. Duk ya cikata da magana ta kosa, ya fadi abinda ke tafe da shi ya bata guri, ta cigaba da dogon tunanin da take yi, domin wannan surutun nasa babu abinda yake Kara mata sai takaici. maganar sa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi. "Da dukkan alamu Kina cikin damuwa Don gashi Ina magana ma hankalin Ki na wani wajen, dan Allah ki saki ranki da ni Ki fada min abinda yake damunki ni kuma na kudiri niyyar taimaka miki da baki mafita a kan abinda ya dameki" Shiru tayi ta kasa bashi amsa sai kalloshi da take yi hawaye na sauka a fuskarta. "kiyi hakuri Ki share hawayen Ki fada min damuwarki dan Allah, ke nake saurare". Cikin kuka take masa magana "baza ka iya fitar da ni daga cikin matsala da kuncin da nake ciki ba, Allah ne Kawai xai iya fitar dani ka kyale ni, bana son na Kara tuna abinda na fara mantawa da shi" Lallabata ya shiga yi a kan ta fada masa matsalarta Amma taki, sai gajiya yayi ya kyaleta. Dubanta yayi sake yi, yana murmushi tunda baxa Ki fada min ba bari na kyale ki, amma yanxu ina Zaki naga kin xauna a nan? "babu inda xan tafi a nan wajen xamu Kwana " Cikin mamaki yake mata magana. "a nan wajen fa kika ce gaskiya baxan bari ku Kwana a nan ba, Sbd gaba daya babu security, kizo xan taimaka muku na baku gurin Kwana Amma fa idan kin amince" Shiru tayi ta tafi dogon tunani,ya za a yi daga haduwa da mutum bata San halinsa ba yace xai taimaka mata, xuciyar ta bata amince da binsa ba "Ki yarda da ni baxan taba Cutar da ke ba, Wlh da xuciya daya nake son taimaka muku don naga halin da kuke ciki " Jin ya yi mata rantsuwa da Allah yasa ta amince xata bishi ya basu wajen Kwana. Don haka ta Mike ya taimaka mata,ta tashi Ammi kasancewar ta fara bacci. Gida ne mai daki biyu ciki da falo sai kuma falle daya sai toilet da kitchen da tsakar gida, gidan ya tsaru sai dai karami ne ba shi da girma.Amma Akwai kayan more rayuwa a cikinsa. Nuni yayi musu da su shiga cikin dakin don haka,suka shiga dakin ita da Ammi, gurin xama suka samu cikin mintinan da basu wuce biyu ba ya xo musu da abinci mai rai da lafiya, Dan ruwa, duk abinda suke bukata shi yake kawo musu,da alama dai gauro ne ba shi da aure, bayan sun gama cin abincin ne ya shigo ya same su, kallonta yayi fuskar sa a sake yana murmushi. "da fatan dai kin koshi kuma gajiya ta bar jikin ku" Kallon shi tayi ta gyada masa Kai alamar "eh" naga alama dai malamar nan bata son magana, Gashi ni kuma sarkin surutu ne da son tambaya kamar dalibi mai koyon aikin jarida Kallonshi tayi tayi yar dariya "tunda kun ci abinci kun huta bari na wuce dakina lokacin bacci yayi, Amma kafin na tafi Ina son Jin Sunan malamar" Kanta a sunkuye ta amsa masa "Sunana nauwar wannan kuma mahaifiyata ce Allah ya jarrabeta da matsalar tabin hankali ne" Cikin tausayawa da kulawa ya yi mata magana "Subhanallah Allah ya bata lafiya, Insha Allah ina da taimakon da xan bata xata samu sauki da yardar Allah" Cikin farin ciki ta amsa masa da Allah ya bada iko. Tunda taji ya ambaci xai taimakawa Amminta ta samu lafiya, xuciyar ta tayi dadi taji kamar an gafarta mata xunubanta, sallama yayi mata ya wuce dakin sa, yana fita tayi shirin kwanciya ta Kwantar da Ammi suka fara bacci cikin Farin ciki. Cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita, a cikin baccin taji kamar tafiya a cikin dakin Don haka ta yi saurin bude ido a tunanin ta Ammi ce xata fita. saurayin nan ta gani daga shi sai singlet da boxers ya nufo inda take, cike da mamaki ta dube Shi lafiya Malam, Kai da ka taimaka mana kuma me ya shigo da kai da tsohon daren nan. Dubanta yayi yana wani shu'umin murmushi " a tunaninki xan taimaka miki haka Kawai ne ba tare da kin taimaka min ba ai rayuwar Yanxu ban gishiri in baka Manda ne sai kin bani xan baki" Kara matsowa yayi daf da ita tana ja da baya tana rokon shi ya tausaya mata ya dubi halin da take ciki ya kyaleta. Murmushin yaudara ya cigaba da yi mata. "yadda kike budurwar nan son Kowa kin wanda ya rasa me yasa xaki cuci kanki, arxiki yana kiranki Kina gudunsa kin fi son ku cigaba da kasancewa a wahala ke da mahaifiyarki, Ki bani dama na shigo cikin rayuwar Ki na sanya Ki Farin cikin da xaki dauwama a cikinsa har Avada, idan kuma kince baki yarda ba, ni baxan miki dole ba sai ki bayani abincina da kika ci min ke da mamanki. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Ba nida Bakin da xan gode muku masoyana sai dai fatan Allah ya bar xumunci* 4⃣5⃣ Hannu tasa a jakar da take adana yan kudadenta ta ciro masa naira dubu biyu ta mika masa. kallonta yayi cikin fushi ya fara mata magana "Sbd ba kida hankali Kudi nace Ki xaro ki bani ko abinda na ciyar da ke,ba Kudin ki nake bukata ba abinda kika ci min xaki baya ni Yanxu" Tsugunnawa tayi har kasa tana masa magiya "ka taimake ni kayi hakuri a Ina zan samo maka abinda xan biyaka Yanxu" Kara matsowa yayi daf da ita ya matseta jikin bango numfashinsa na sauka a kan fuskarta, kokarin matsawa tayi ta xille ta kasa, da sauri yasa hannu ya kamota ya manna fuskarsa da ta ta, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar da yana cikin jaraba "kan ki nafi bukata a Yanxu ba Kudi ko abinci ba, ina so ki biyani ne da abinda Allah ya axurtaki da shi. me yasa kike son yi min rowar abinda kike da shi, me yasa xaki yiwa kanki muguntar samun arxiki, idan kika rabu da gidan nan nasan babu wanda xaki samu ya karbe ki a wannan halin da kike ciki ke da mahaifiyarki, don haka na baki minti biyu kiyi Shawara da xuciyar ki duk abinda kika yanke Ina maraba da karbarsa ,Amma ki sani baxan miki dole ba" Komawa kan kujera yayi yana mayar da numfashi ita kuwa Nauwar sai faman share hawaye take yi, tunda take bata taba ganin bala'i irin wannan ba, kana tunanin mutum xai taimake ka asheba kyakkyawar niyya ce ta kawo shi ba. Tausayin kanta ne ya kamata, komai na duniya ya cakude mata, burinta Allah ya dauki ranta ta huta da jarrabawar da take ciki. Sake kallonta yayi ya mata magana "ke nake saurare Wace Shawara kika yanke idan har baki amince da kudirina ba ki tatttara kayanki Yanxu ki bar min gida, in yaso ko Menene ya same ku ba nida asara" Fadar wannan maganar da yayi ba karamin faranta mata ranta yayi ba, da hanxari ta amsa masa. "Ban amince ba" Cikin mamaki ya dubeta "amma ban taba tsammanin cewa ke wawiya bace sai Yanxu, a ce kina cikin wannan masifar ki qi amincewa da abin alheri, na miki alkwarin xame miki uwa da uba Sannan watsi da damarki kice bakya so, kada kiga cewa dare yayi ko xan daga miki kafa na fasa korarki Wlh Yanxu xaki fita ki bar gidan nan, tunda ba gadonki a ciki banxa shashasha Mara rabo" Bin sa tayi da ido bata ce masa komai ba,tashin Ammi tayi suka fito daga dakin har waje ya rako su yana xaginsu yana cewa Nauwar Mara rabo, sai da suka fita,Sannan ta kalle shi cikin tsiwa take masa magana. "Alhamdulillah na godewa Allah da bai baka damar Cutar da mu ba, macuci maciyin amana, Indai a kan na xauna ka lalata min rayuwa ne gara na rasa rabon duniya gaba daya, don nasan Akwai tanadin da Allah yayi min a lahira" Kallonta ya rika yi ya rasa bakin magana Sbd a tunaninsa bai xaci tana da baki haka ba, mayar da kofar gidan yayi ya kulle, ita kuma ta kama hanya suka cigaba da tafiya, gari yayi shiru ba a Jin komai sai haushin karnuka, kasancewar lokacin karfe biyu da rabi na dare. Bakin wata Makaranta suka samu ta roki masu gadin a kan tana so su bata wajen kwana, ta fada musu su matafiya ne dare yayi musu a hanya, Washe gari su cigaba da tafiya, basu yi musu gardama ba suka basu aji suka kwanta. Gari na wayewa suka taimaka musu da koko da Kosai bayan sun kammala karyawa suka yi musu sallama suka nufi tashar Na'ibawa don su hau mota. Tunanin nauwar gaba daya ya dauke ta rasa motar garin da xasu hau, tana tsaye tana wannan tunanin taji an yi mata magana. "yan mata ina xaki je Kaduna xaki ko maiduguri ga motocin mu nan Saura gurin mutum biyar su cika" Da sauri ta bashi amsa da Maiduguri sbd ta tuna Abbanta a nan yayi bautar kasa inda ya hadu da wasu mutane suka yi xaman mutunci suka xamo tamkar yan uwa har ya taba kai su xiyara mai dugurin dan haka taji dadin samun motar garin. Shiga suka yi suka xauna ita da Ammi, ba a Fi mintuna biyar ba aka karasa cika motar suka dauki hanyar garin mai duguri. Da misalin karfe shida da rabi na yamma suka sauka a tashar garin inda Kowa na motar ya fita ya kama hanyar inda xai je, tun a hanya taga gaba daya garin ya canja mata, ba irin yadda ta san shi a baya ba, gefe guda ta samu ta tsaya tana tunanin Sunan mutumin da zasu je wajensa, cikin ikon Allah ta tuna Sunan wani bawan Allah ta samu xaune. Sallama tayi masa ta tambaye shi ,nawa ne kudin motar da xai kaita unguwar Hausari, cikin kulawa ya fada mata farashin kudin Sannan ya taimaka mata ta samu adaidaita sahu. Har bakin layin gidan Alhaji musa aka kaita sai dai ta kasa gane gidan kasancewar an canjawa Unguwar fasali saboda fadan da ake yi. Tambaya tayi aka nuna mata gidan tana nufar kofar shiga ta tarar an rushe gidan ba Kowa sai fili, mamaki ne ya kamata saboda bata taba xaton xata tarar da wajen a haka ba. Ganin ta tsaya cak ta kasa aikata komai ne wani bawan Allah ya sameta yayi mata sallama Cikin girmamawa ta amsa masa, tambayarta yayi wanda take nema. Cikin sakin fuska ta amsa masa "gidan Alhaji musa Abbakura nake nema" Cikin tausayawa ya dubeta "Ai Allah yayi masa rasuwa sanadiyyar fadan da ake yi, duk an kashe iyalinsa dansa daya ne yayi ragowa shi ma kuma ba a San inda yake ba" Sunkuyawa tayi ta rushe da kuka mai ban tausayi. "Wayyo Allah Naga ta kaina, Yanzu Ina zan dosa ga yamma tayi Gashi ba nida kudin komawa Kano ga kudaden hannuna gaba daya sun Kare Allah ka dube ni da rahamarka da Jin kanka" Cikin tausayawa mutumin yayi mata magana "kiyi hakuri Allah xai dubeki ya baki mafita, da ina da wajen Kwana da na baku saboda na tausaya miki, to nima bako ne a gidan wasu na sauka, amma ki cigaba da tambayar mutane ko xa a samu mai taimaka muku, na barki lafiya Allah ya hadaki da naka gari dari biyar ya xaro a aljihu ya bata" godiya tayi masa suka yi sallama ya tafi, rasa inda xasu dosa tayi kuma ta kasa rokon Kowa ya taimaka musu, saboda tana Jin tsoron kada abinda ya faru da ita a baya ya sake faruwa. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDA TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Bansan da bakin da xan gode miki ba QUEEN MARYAM (maman surayya)ina godiya da kyautatawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci* 4⃣6⃣ Duk wanda yaxo wucewa kallon su yake yi, saboda kowa tunani yake yan ta'adda ne suka yi basaja. wani babban mutum ne yayi ta maxa yaxo ya sami Nauwar. sallama yayi mata, ita kuwa saboda tsananin kukan da take yi,ta kasa magana sai a cikinta ta amsa sallamar, magana ya fara yi mata "me ku ke yi a nan, kika xauna ke da wannan mahaukaciyar, me ya fito da ku daga gida da yammacin? kin san dai duk kwarya ta gari tana ragaya ko? ya kamata ki tashi ki tafi, don gaskiya bama barin wadanda bamu sani ba su xauna mana a unguwa, sai dai idan da ixnin mai unguwa xasu xauna" kallon shi take yi kawai,ta kasa ce masa komai saboda bakin cikin da ya tokare mata makogoro. sake dubanta yayi "magana nake fa kin kasa bani amsa sai faman kuka da kike yi, na fada miki sharadin xama a nan, ko ki tashi ko nasa yara su yi muku a tire, don irinku ba abin yarda bane" kafin tayi magana tuni ya fara kiran yaran unguwar,kan kace me, tuni sun taru sun fara jifan su da dutse,suna yi musu waka, ganin xasu illata su ne, yasa taja hannun Ammi da kyar suka bar gurin,tana tafe tana kuka, sai da suka yi tafiya mai nisa sannan ta samu suka xauna, idanunta sun kad'a sun yi jawur, ga yunwa da kishiruwa ga gajiyar tafiya ga bacci da ya dameta, don rabon da ta samu ta rintsa tun lokacin da Abbanta ya koreta daga gida. Ammi ce tayi wani gunji mai ban tsoro inda ta kama Nauwar da duka ta ko'ina, shake mata wuya tayi ta hadata da jikin bango, ta rika gwara kanta da bangon, kamar baxa ta barta da rai ba. tunda Ammi ta fara rashin lafiya bata taba shiga irin wannan halin ba sai yanxu, ihu Nauwar ta rika yi, tana neman taimako amma Ammi ta ki ta daina dukanta, kasancewar gurin babu jama'a sai su kadai sai gidaje a kulle, wasu mutane Allah ya kawo da kyar suka kwaceta a hannunta, da gudu tayi kansu da duka tana jifan su da duwatsu. Haukan Ammi yanxu ya koma na duka, sai da ya kasance duk wanda yaxo wucewa sai ta jefe shi ko ta watsa masa kasa. a ranar kwanan xaune suka yi, saboda da Nauwar ta kwanta xata rufe ta da duka, sai tsallakawa tayi ta kwanta a gefen wani kanti. washe gari da Asuba ta farka, tarar da Ammi tayi kwance cikin kwata tana ta bacci abinta, da sauri ta karasa wajen tana kuka, duk jikinta ya baci da kwatar, wani bawan Allah ne ya taimaka mata suka fito da ita, inda ya kawo sabulu da ruwa ta wanke mata jikinta. duk wanda ya kalli Ammi yasan ta xama mahaukaciya tuburan saboda abinda bata yi da, shi take yi yanxu. tambayarta ya yi. "ke kuwa baiwar Allah daga ina kike haka, ga ki da mai lalura" share guntun hawayen da ke idonta tayi, ta fara bashi labarin abinda ya faru da su, da kuma garin da suke. tausaya musu yayi kwarai da gaske, sannan ya bata shawarar xuwa gidan mai unguwa ta fada masa abinda ya faru da su. cikin nutsuwa tayi masa magana "ai ban san gidan mai unguwar ba" dansa ya kira yayi mata rakiya, kasancewar shi xai wuce asibiti wajen mahaifiyar sa. ba tare da bata lokaci ba, yaron yaxo don yi musu rakiya, suna tafe Ammi na turjewa, a haka har suka isa gidan. A soro suka tarar da mai unguwa inda suka yi masa sallama, cikin girmamawa ya amsa, ya kuma tambaye su abinda ya kawo su, bayani tayi masa ya tausaya mata sosai, sai dai xuciyar sa bata gama amincewa da su ba, saboda yan ta'adda sukan xo da wannan sigar su cuci mutane, daki ya basu wanda yake a tsoron gidan, ya kuma yi umarni a kawo musu abinci da ruwa. ********************** A bangaren su innah karime kuwa farin ciki ne ya cika xuciyar su,saboda sun kori su Ammi da yayanta sun mallake komai, gida ya xama nasu, su da jikonkin su, Habi ce ta shigo rike da kwanan abinci a hannunta, guri ta samu ta xauna ta dubi innah karime. "wai kuwa innah kina tunawa da tsinanniyar matar nan, da taso ta hana mu xaman lafiya a gidan nan" "uhmmm habi kenan kema baki tuna da ita ba sai ni, da ta tsane ni taki jinina, ai na godewa Allah na godewa Boka da yayi mana wannan aikin,ya tarwatsa musu rayuwa, yanxu ma so nake a kara yin wanda xa a farraqa tsakanin yar da uwar, taki taimaka mata, kin ga abin xai mata yawa,ga hauka ga ya ta gujeta, daga nan kinga sai mutuwa kenan" hada hannu suka yi suka tafa, suka bushe da dariya, sallamar da aka yi ne ya katse musu hirar da suke yi. mamin Hamdan ce taxo, a tunaninta har yanxu su Nauwar na gidan, babu wanda ya kalleta ballantana tasa ran xai amsa mata sallamarta, duba dakinsu Nauwar tayi,taga ba kowa gaba daya kayan dakin su an fitar da shi,ya xama kamar kango. mamaki ne ya kama ta, don haka kai tsaye ta fito daga dakin ta tsaya a wajen da su innah karime suke tambayar su tayi. "bayin Allah ban yi xuciya ba, dan Allah ina mai dakin nan take ko bata nan" A yatsine Habi ta kalleta "ga amsar nan ai kin bawa kan ki" fitowa tayi ta rabu da su, mai gadi ta tarar yana ta faman shara, har kasa ya xube ya gaishe ta, tambayar shi tayi ina su Nauwar. sunkuyar da kai ya yi yana share kwalla. "Ai Alhaji ya kori su Hajiya yau kusan kwana biyar kenan" cike da mamaki ta dube shi. "ya kore su fa kace malam Ali" "wlh da gaske nake Hajiya, nima da nayi masa magana sai da ya ci min mutunci" salati mami ta rika yi, tana hawaye "amma mahmud bai kyauta ba,bai yi adalci ba, amma ba komai akwai Allah" fita daga gidan tayi kafin ta isa gida xaxxabi ya rufeta. tana shiga falo ta tarar da jaka a ajiye, samun guri tayi ta kwanta, tana mamakin ganin jakar da kuma abinda ya faru da su Nauwar. Hamdan ta gani a kanta yana mata murmushi. kallon shi tayi ta harare shi. "yanxu Hamdan kasan xaka dawo amma baka yi min waya na hada maka komai ba" dubanta yayi cikin sakin fuska "kada ki damu mami xan je gidan su matata Nauwar naci" hawaye mami ta shiga sharewa tausayin Nauwar da Hamdan ne ya kamata, ta rasa ta inda xata fara fada masa abinda ya faru. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ku, JUWAIRIYYA LUKMAN AMIN (maman shuraym) & HAUWA'U HAMZA SA'EED ZARIA ina godiya da kaunar ku gare ni* 4⃣7⃣ cikin kulawa ya kalli maminsa "mami me ya faru naga kina share hawaye,ko bakya jin dadi ne?" "Lafiyata kalau Hamdan amma abinda ya faru har gara rashin Lafiyar a kan faruwarsa" cikin raxana ya dubeta. "me ke faruwa mami, dan Allah ki fada min ko xan samu saukin fargabar da nake ciki" "baxan fada maka ba Hamdan har sai kaje kaci abinci ka watsa ruwa a jikinka, kuma ina so ka kwantar da hankalin ka abin baya bukatar daga hankali addu'a aka fi bukata" idanun Hamdan ne suka kada suka yi jawur,gaba daya ya kosa yaji abinda maminsa take son fada masa. marairace mata yayi "dan Allah ki fada min mamina, ko dai akwai abinda kike boye min ne wanda bakya so na sani game da gidan nan" dafa kafadar shi tayi "bana boye maka komai Hamdan kuma babu abinda ya faru da gidan nan, nafi son kaci abinci sbd xaka fi samun nutsuwa idan na fada maka" da sauri ya tashi ya shiga kitchen ya xuba abinci a mintunan da basu wuce biyar ba ya kammala, sake dawowa yayi ya sami mami,don jin abinda xata fada masa. tsura mata ido yayi yana jiran tsammanin jin abinda xai fito daga bakinta, da nasiha ta fara masa. "ka sani duk abinda ya samu wani bawa daga Allah yake, kuma shi xai yaye masa a duk lokacin da ya so, sannan babu wani bawa da ya isa ya cutar da wani sai dai da yardar Allah, ina son ka bani aron hankalin ka kuma ka yi wa abin kyakkyawar fahimta" gyara xama yayi ya cigaba da saurarenta. "Hamdan!! ta kira sunansa, cikin sanyin murya ya amsa mata "bayan tafiyar da kayi Allah ya jarabci Ammin Nauwar da lalurar hauka" A raxane ya kalleta "hauka fa kika ce mami innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanxu Ammin tana ina? katse masa maganar da yake tayi,ka tsaya na karasa maka mana. "Fu'ad kuma Allah ya yi masa rasuwa, yanxu maganar nan da nake maka, Abban su Nauwar ya kore su daga gidan sakamakon baxai iya xama da mahaukaciya a gidansa ba" mikewa tsaye yayi hawaye na sauka a kan fuskarsa "wai mami abin nan ya faru da gaske ko kuma mafarki nake yi, yanxu ina su Nauwar din suke?" cikin tausayawa ta dube shi "nima wlh ban san inda suke ba, saboda babu wanda yasan ya kore su" "gaskiya mutumin nan ba shi da kirki mami, na dauki alwashin sai na nemo duk inda Nauwar da Ammi suke, ko da hakan xai yi sanadiyyar rasa raina" A fusace ya tashi ya shiga daki ya dakko jaka ya xuba kudi a aljihu, tsugunnawa yayi a gaban mami. "ina neman ixninki mami ki barni na nemo bayin Allahn nan duk inda suke, amma kafin na tafi xan fara kai cigiyar su gidan radio da televisions ko Allah xai sa a dace" "na amince maka Hamdan domin taimako xa kayi, ni kuma a koda yaushe ina son na rika ganin kana taimakawa wadanda ke cikin matsala, Allah ya taimake ka" tashi yayi ya fita kai tsaye ya wuce gidan radio ya bada sanarwa, bayan ya dawo ya fara hada kayan da xai yi tafiya da su, inda washe gari xai wuce neman su Nauwar. ******************** tunda su Nauwar suka sauka a gidan mai unguwa,ba su da matsalar abinci da wajen kwana, sai dai matsala daya da suke fuskanta har yanxu mai unguwa bai gama amincewa da su ba, kuma a kullum sai mutane sun xo sun yi korafin dalilin da yasa aka barsu a cikin jama'a, alhalin ba a san asalinsu ba, ba a san daga inda suke ba. yau da sassafe mai unguwa ya shigo dakin da suke. sallama yayi sannan ya samu guri ya tsaya. tsugunnawa Nauwar tayi xata gaishe shi. dakatar da ita yayi "baiwar Allah yau dai ba gaisuwa ce ta kawo ni ba, naxo ne na fada miki cewa ki tattara kayanki ku koma inda ku ka fito, saboda ya xa a yi yarinya kamar ki,ta bar gida ita da mahaifiyar ta, sai dai idan wani mugun abin ku ka aikata shi yasa ku ka gudu, baxan karbe ki wani abin yaxo ya faru a ce da sa hannuna ya faru ga kudin mota nan ku koma inda ku ka fito" dubu biyu ya jefa mata ya fita. da sauri ta bishi ta tsugunnah har kasa tana rokon shi. "dan Allah kayi mana rai kayi mana sutura kamar yadda Allah yayi maka ka barmu, mu cigaba da xama,wlh kaddara ce ta fito da mu daga gida, ba wani abin ashsha muka aikata ba, ka taimakawa rayuwar mu" "Allah ya taimaka man gaba daya, amma na miki iya taimakon da xan iya, ki kama hanya ki tafi inda kika fito" umarni ya bata ta dakko kayanta su fito su bar masa gidan sa, cikin kankanin lokaci suka fito suka kama hanyar barin gidan. gaba daya Nauwar ta kasa kuka sai istigfari da take yi, ko wani laifin suka yi wa Allah ya jarrabe su, kasuwar garin suka shiga, don su siya abinci su ci. karasawa suka yi wajen wata mai waina, suna isa wajen suka tarar da mata ne a cike a wajen,wasu na shan taba wasu na kitso, kallo daya xaka yi musu kasan ba Allah a ransu, gaba daya kallo ya dawo kan su nauwar, sallama tayi musu. a yatsine aka amsa, kudi ta xaro ta mika musu. mai wainar ce ta tambayeta "me xa a xuba miki" amsa mata tayi "waina da miya nake so" to nemi guri ki xauna "amma a leda xan baki don bana bawa mahaukata kwano na" hawaye Nauwar ta share tare da amsa mata da "to" addua ta rika yi a kasan xuciyarta Allah ya bawa Amminta lafiya a daina jinginata da kalmar hauka. xubo musu abincin tayi sannan tayi musu nuni. "ku tashi ku bar nan don duk wanda ya ganku a wajen nan baxai iya karasowa ya ci abinci ba, kuma dan Allah idan xaki fito ki rika barin mara lafiyar nan a gida, saboda xata rika firgita mutane" kasa magana Nauwar tayi saboda bakin ciki, karshen wata katanga ta samu suka xauna,suka ci abinci. Bayan sun gama ta xube kayan su a gurin, saboda ba su da gurin da xasu je, don haka ta yanke shawarar fara kwana a cikin kasuwar, tasan komai mai wucewa ne,wata rana sai labari. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan page din gaba daya naki ta mamah KHADEEJAH SABO ABDULLAHI (mom Hanash) ina godiya da yadda kike kaunar wannan littafi. ana tare* 4⃣8⃣ Haka suka kasance a cikin kasuwar har tsawon kwana goma, kullum Nauwar ke fita tayi bara ta samo musu abincin da xasu ci, cikin kwanakin gaba daya ta fita daga hankalinta ta koma kalar mahaukata gaba daya, don mutane da yawa suna tsammanin ita ma mahaukaciyar ce saboda yanayin kayan jikinta da takalmin da ke kafarta. kamar kullum yau ma da wuri ta fita don nemar musu abinda xasu saka a bakin salati, wata igiya ta samo ta daurewa Amminta kafa saboda tana gudun kada ta gudu ko taje taci kaxanta kafin ta dawo, dukanta ta rika yi a lokacin da xata daure mata kafar, lallabata ta shiga yi "kiyi hakuri Ammina, nima ba a son raina xan miki haka ba, bana son kici kaxanta ne wata lalurar ta sake kama ki" shiru tayi tana saurarenta kamar dama tana fahimtar abinda take fada, tana gama daureta ta tashi ta dauki roba ta shiga kasuwa. rumfunan kasuwar ta rika shiga tana neman taimako wadansu su bata wasu kuma su xageta, duk a tunaninsu yawon duniya ta fito, bayan ta dan samu kudin da xai ishe su siyan abinci, kai tsaye wajen mai abincin da ta siya jiya ta nufa, yau tarar da wajen tayi ba layi sai mutum biyu da suke tare suna hira. da sallama ta shiga wajen, abin mamaki cikin sakin fuska mai abincin ta amsa mata, inda ta bada umarnin maxan su matsa mata waje ta xauna. dubanta Nauwar tayi "ki barshi ba sai na xauna ba, ba anan xan ci ba, xan kaiwa Ammina taci sannan nima naci" cike da mamaki ta dube ta dama wannan mahaukaciyar babarki ce. gyada mata kai tayi alamar eh cikin tausayawa ta kalleta "Allah sarki amma na tausaya miki Allah ya bata lafiya" amsa mata tayi da amin ta xuba mata abincin ta mika mata. har ta wuce xata tafi ta kira sunanta *AL-MAJIRAH* amsa mata tayi sannan ta dawo ta tsaya. kallonta tayi tare da kashe mata ido daya "idan kin kai mata abinci taci, ki dawo akwai taimakon da xan baki" godiya tayi mata sannan ta tashi ta tafi. tana juya baya,ta dubi maxan tace. "ya kaga yarinyar nan dan gaye tayi dai ko, da alama xata kawo alkhairi, ko ya ku ka ce? amsa mata suka yi "tayi sosai Hajiya xa tayi dadin harka wlh, da gani kuma baxa tayi tsada ba saboda Almajirah ce bata san dadin kudi ba, Allah yasa dai kada ki wayar da ita taxo tafi karfin talakawa irin mu. murmushi tayi tare da kashe ido, "baxa ta gagare ku ba dan gaye, ku dai ku yi addua Allah yas mu ja ra'ayinta" Nauwar na isa wajen Ammi ta tarar har ta fara kwance daurin da tayi mata. da hanxari ta karasa ta gyara mata sannan ta fara bata abincin, sai da taci ta koshi sannan ita ma ta dauki ragowar taci, suka sha ruwa, 'kara komawa wajen mai abincin tayi don karbar taimakon da tayi mata alkawari. Tana xuwa wajen ta bata guri ta xauna, gyara xama tayi sannan ta dubeta ta fara magana. "na tabbatar da cewa kina cikin tashin hankali kuma kina tsananin bukatar taimakon wajen kwana da abinci, ko ba haka bane?" kallonta tayi ta amsa mata da haka ne. sake turo dankwalinta tayi gaban goshi "tunda kuwa haka abin yake, ina so ki karkade kunnuwan ki kiji abinda xan fada miki, xamanki a haka baxai yiwu ba dole ki tashi ki nemawa kanki yanci da mafita, idan ba haka ba kuma bakin cikin duniyar nan ya kashe ki, duk fadin wajen nan ki duba, babu mai taimakon ki, sai dai idan ke kika taimaki kanki, nima da kike gani tausayi kika bani nace xan taimaka miki, don naga tun ranar da kika xo siyan abinci a nan, kasuwar ku ke kwana har xuwa yanxu, wannan ya tabbatar min da cewa ba ku da galihu" duk bayanan nan da take nauwar na saurarenta "ni sunana Amarya uwar marayu, nice nake bawa duk wani maraya ko wanda iyayensa suka kore shi daga gida wajen kwana, amma fa da sharadi, sharadin baxan fada miki shi yanxu ba sai kin amince da taimakon da xan miki, idan kina bukata sai kiyi magana, yau din nan ku bar kwanan kasuwa ku koma gida" da sauri Nauwar ta amsa mata da na amince aunty. "to shikenan tunda kin amince, aikin namu ba wani mai wahala bane kuma ana samun kudi sosai xaki warwarsa har ki taimaki wani, tashi ki dakko kayanki, da mahaifiyarki kixo mu tafi. tashi tayi ta dakko Ammi da yan tsummokaransu suka nufi hanyar gidan Amarya uwar marayu. Wani daki ta shigar da su a cikin gidan, manyan garada ne maxa da mata ana ta holewa wasu na ta faman busa sigari, suna ganinta wasu yan mata suka taho da gudu suka rungumeta. "Oyoyo uwarmu maganin kukan mu, daya ce ta dubi su Nauwar ta bushe da dariya. "kai Aunty kin iya jajibe-jajibe a ina kika samo wadannan tarkacen kuma" kallonta tayi ta harareta "ke bana son iskanci wadannan sun wuce tarkace, akwai alherin da xa a samu a tare da su" wani daki ta wuce da su, ita dai Nauwar tunda taga yanayin gidan taji hankalinta gaba daya bai kwanta ba, amma tunda ba su da wajen kwana xata xauna ne a lalura. maxa ne suka rika shigowa dakin, duk wanda yaxo sai ya kalli Nauwar sama da kasa sannan ya fita, a falo ta jiyo abinda suke fadawa Aunty Amarya. "yarinyar tayi Aunty saboda yar shila ce, yanxu gyara mana ita kawai ya rage miki" fargaba ce ta cika xuciyar Nauwar ta rika addua Allah ya tseratar da ita daga fadawa halaka. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Ina taya yar uwa NASEEBAH ISMA'IL murnar cika shekara guda da fara rubutu Allah ya kara basira da xakin hannu* 4⃣9⃣ Cikin dakin Nauwar suke Amarya ta shigo sallama tayi, hannunta rike da bakar leda, samun guri tayi ta xauna ta dubi Nauwar. "bayin Allah sannunku da hutawa ku yi hakuri na jingine ku ba tare da naxo mun xauna mun fara tattauna abinda ke gaban mu ba" cikin girmamawa Nauwar tayi mata magana "ba komai Aunty ai naga gidan cike yake da baki" "hmm kwarai kuwa, yau ma ai ba kiga komai ba, saboda ragowar masu xuwan basa nan sun yi yar tafiya" yanxu dai abinda nake so ki tashi ga ruwa can kije ki watsa ko kya yi kyan gani,Wannan kuma kaya ne idan kin yi wankan ki saka. mika mata ledar da ke hannunta tayi sannan ta cigaba da magana, bayan kin fito daga wankan ina so kixo ki sheqa kwalliya ta daukan magana, don da kwalliyar ne xaki jawo hankalin wadanda xasu rika xuwa xiyara gidan nan, daga nan kema ki samu naki rabon. tashi Nauwar tayi ba tare da ta amsawa Amarya maganarta ba, har ta kai bakin kofa xata fita daga dakin ta kira sunanta "Almajira!! juyowa tayi ta dubeta. "ya xa mu yi da Wannan mahaukaciyar, kinga ke yanxu da hankalin ki kina gane komai xaki iya biyawa kan ki kudin haya, ita kuma ya xa a yi da ita, don kinsan ni ba a min xaman banxa a gida, duk yarinyar da kika gani a gidan nan neman kudi take yi, idan kuma kin amince xaki biya mata da dan abinda xaki rika samu shikenan ta kwana gidan sauki" idanunta ne suka cika da kwalla, kokarin sharewa tayi sannan ta amsa mata da xata rika biyan kudin hayar bandaki ta wuce ba tare da bata lokaci ba ta fara wanke daudar kwana da kwanakin da ta makale a jikinta, tana gama watsa ruwan taji wata iska na shigarta ko ta ina, rabonta da taji irin wannan iskar a jikinta har ta manta, tana fitowa ta shige dakin da Amarya ta sauke su, tararwa tayi an ajiye mata kayan kwalliya da mayuka masu kamshi da turaruka, shafa man tayi ta shafa yar powder, sannan ta saka kayan da Amarya ta kawo mata, riga da skirt ne daidai jikinta,kayan sun karbeta kwarai, idan ka ganta baxa ka taba cewa ita ce a cikin yanayin kunci da damuwa ba, saboda kyawunta ya fito sosai. fita waje tayi don ta roki Amarya alfarma ta taimaka mata d ruwa da sabulu ta wanke Amminta. kallonta tayi a wulakance sannan ta bata amsa. "ke ni fa bana bawa wanda ba shi da amfani kayana, yanxu ita wannan ko wankan tayi amfanin me xai mata,waye xai gani ya yaba, kema da kika ga na baki, don nasan xaki biyani ne nan gaba, idan kina son ruwan wanka da sabulu ki fita waje akwai wajen da ake siyarwa xaki samu" da bacin rai Nauwar ta koma daki ta hada kai da gwiwa, ita gaba daya bata san irin rayuwar da Amarya take shirin jefata a ciki ba. yamma nayi Maxa da mata suka fara taruwa a gidan, ana ta sheke aya kowace budurwa da saurayinta, wasu na daki na sabon Allah wasu kuma sun kunna kida suna cashewa, ita kuwa Nauwar na daki tana tunani don bata saba da irin wannan rayuwar ba. Amarya ce ta sake shigowa ta sameta ta hada kai da gwiwa tana tunani, dan dukan kanta tayi kadan "ke baiwar Allah a firgice ta dago,don bata yi xaton shigowarta ba. "ba fa xama ne ya kawo ki ba,nema kika fito yi, ga samari da yan mata can a tsakar gida ki tashi ki kewaya ko xaki samu rabonki,ki hakura da wannan tunanin banxan da kike yi, don babu inda xai kai ki, idan kuma baki nemo ba ni xan samo miki ga Alhaji Talle nan yaxo, ba shi da abokiyar hira budurwarsa ta tafi ganin gida, ki tashi kije ki debe masa kewa, ki kuma sakar masa fuska don mutumin yana sakin kudi, a xuwan nan da yayi xaki iya samun kudin da xaki biya haya da shi da kudin abincin da ku ka ci" cikin rashin gamsuwa da maganarta ta dubeta. "Aunty ni fa har yanxu ban fahinci abinda kike nufi ba" "ki tashi ki tafi idan kin je xaki fahimci abinda nake nufi" taso keyar Nauwar tayi har sai da ta kawota bakin kofar dakin da Alhaji Talle yake sannan ta juya. Ran Nauwar a bace ta shiga dakin tare da sallama, amsawa yayi tare da binta da wani fitinannen kallo. daga bakin kofar ta samu guri ta xauna, cikin kashe murya ya fara mata magana. "Haba yan mata ke kuwa kamar ba wayayya ba xaki xo ki tsaya daga gefe, kin san fa abinda kika xo yi ko kudin ne bakya so" cikin tsiwa ta fara masa magana "gani na da kayi a nan ba a son raina naxo ba, tilas aka yi min, kuma kaddara ta kawo ni gidan nan, da ina da wajen da ya fi nan, da baxa ka ganni ba ballanta kayi tunanin nima irin matan da ke wulakanta rayuwar su ne, don su yi kudi banda abinka gaka dattijo amma har yanxu baka daina bin matan banxa ba, baka tunanin kaima wata rana xa a iya yiwa yarka, ya dace ka rika tunani mai kyau, duk abinda kake so wa kanka ka sowa dan uwanka, ina maka nasiha da ka tuba ka koma ga Allah tun kafin lokaci ya kore maka domin Allah ya yiwa masu aikata xinah tarin axaba mai yawa, tun lokaci bai kure maka ba ka hakura da wannan sana'ar. abinda yasa naxo na saurareka ma don kada na watsawa wadda ta bani masauki a gidan nan kasa a ido ne amma ba dan haka ba ko ganina baxa ka yi ba, dan haka kada ka kara yi min kallon yar duniya ko kuma wacce ta guji iyayenta ta xabi rayuwar bariki" kallonta yayi tare da bushewa da dariya "lallai yarinya kin yi kokari, wannan bayanai haka kamar mai karanta labarai, Insha Allah naji bayanan ki kuma xan yi kokari nayi aiki da su, yanxu duk maganar nan da kika yi min kina nufin gaskiya ne ba abinda kika fito yi kenan ba? "kwarai kuwa, duk abinda na fada maka babu karya ko son xuciya a cikinsa" Ajiyar xuciya yayi sannan ya cigaba da magana, naji duk abinda kika fada babu karya kamar yadda kika ce. "menene sanadinki na xuwa wannan gidan, duk da kin san cewa ba gidan mutanen kirki bane, kuma me yasa kika xabi rayuwar barin gaban iyaye" wannan tambayar ba karamin sosawa Nauwar xuciya tayi ba, nan da nan ta fara hawaye cikin tausayawa ya kalleta. "ba kuka xa kiyi ba, fada min dalilinki ni kuma nayi alkawarin samar miki da mafita" labarin rayuwarta gaba daya ta bashi, ya tausaya mata sosai da halin da take ciki. "kiyi hakuri yan mata komai mai wucewa ne, na tausaya miki sosai, kuma Insha Allah na xabi na taimaka miki a kan na cutar da rayuwarki, hannu yasa a aljihu ya xaro kudi, mika mata yayi, ungo wannan ki siya duk abinda kike bukata, kuma idan kina da wata matsalar ki rika fada min, ni kuma xan taimaka miki. sallama yayi da ita ya wuce gida don ko neman Aunty Amarya bai yi ba. har ya kusa fita daga gidan ya sake dawowa" kin manta baki fada min sunanki ba" sadda kai tayi sannan ta bashi amsa "sunana Nauwar amma an fi kirana da Almajira" tana shiga dakin ta tarar da Ammi na bacci xaro kudin tayi ta fara lissafawa dubu goma ta gani, daga hannu tayi sama tana godiya ga Allah domin Allah ya fara kawo musu mafita. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *Masu karatu a yi hakuri saboda rashin ganin post a kan lokaci hakan ya faru ne sakamakon rashin wutar da muke fama da shi* *EXCLUSIVE WRITERS FRUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 5⃣0⃣ Aunty Amarya ta gani a kanta tana mika mata hannu. "yarinya kawo abinda kika samu,daga yau idan kin yo samuwa ba boyewa xaki yi ba, fitowa da su xa kiyi ki bani rabona ehe" mika mata kudin tayi gaba daya ta shiga kirgawa, murmushi tayi ta dubeta "lallai yarinyar nan kina da sa'a har dubu goma ya baki, tabdi lallai Alhaji ya yaba da ke" xaro dubu biyu tayi ta mika mata "ga wannan ki rike a hannun ki, ragowar dubu takwas din kuma,xan rike a hannuna,daga yau xaki fara tara kudin hayarki da kudin da xaki rika cin abinci, da kuma abinda xaki rika siyan kayan kwalliya, domin ki kara samun kasuwa, don ba haka xaki xauna kara xube ba" bin ta Nauwar tayi da ido ba tare da tace komai ba, wani kwano Amarya ta janyo ta dakko kofi ta xuba mata wasu magunguna mika mata tayi. "karbi wannan ki sha" Hannu tasa ta karba "wannan kuma na menene Aunty me xan yi da shi" "Ban san abinda xaki yi da shi ba uwar tambaya, ya xa a yi kije wajen namiji sannan kice baxa ki sha abinda xai wanko miki ciki ba, idan so kike ki samu ciki kada kisha, duk lokacin da kika sake kika yi ciki xamanki ya kare a gidan nan, dan haka sai ki xabi abinda ya fi dacewa da ke" tana gama fada mata ta fita daga dakin daukar maganin tayi ta xubar da shi, saboda babu abinda ya hada ta da maganin xubar da ciki. kullum fata take yi Allah ya kawo mata hanyar da xata samu mafita, ta bar gidan Aunty Amarya saboda a kullum burinta ta saka ta a hanyar banxa. Haka rayuwar su ta cigaba kasancewa a gidan Amarya, a kullum Alhaji talle sai yaxo yaga Nauwar ya mata alkhairi. wata rana da misalin karfe 6:00 na yamma Alhaji talle yaxo gidan Aunty Amarya, tun a tsakar gida suka hadu da ita suka gaisa ya fada mata abinda ya kawo shi, daki ta shigo da shi don su tattauna maganar da ta kawo shi,domin ya fada mata xancen mai muhimmanci ne. tabarma ta shimfida masa sannan ta nemi gefe guda ta xauna ta fara sauraren shi. "A gaskiya Hajiya Amarya naji dadi kuma nayi farin ciki da hadin da kika yi min da wannan yarinya yar arxiki, yarinyar tana da ladabi da nutsuwa fiye da tunaninki" washe baki Aunty Amarya ta shiga yi "ai duk hadin da nake yi ai babu na tumun dare Alhaji, kadan ma kaga ni daga alheran da xata xo maka da shi" gyara xama yayi ya cigaba da bayani "wannan dalilin yasa naga ya dace naxo na nemi auran yarinyar nan a wajen ki tunda dai kece uwarta kece ubanta" dafe kirji Aunty Amarya tayi, aure fa kace Alhaji yaushe aka yi daren da gari xai waye, ka bari ku kara fahimtar juna sosai sai ka fito a yi magana" katse mata magana yayi. "ai babu wani sauran fahimtar juna da ya rage mana yarinyar nan tana kaunata, idan kuma kina ganin ba haka bane a kirata kiga xahiri" Nauwar ta kwalawa kira, da hanxari ta karaso wajen ta tsugunnah, suna hada ido da Alhaji talle ta sunkuyar da kanta kasa. magana Aunty Amarya ta fara yi "Almajira!!" dago ido Nauwar tayi ta kalleta. "ga Alhaji Talle nan yaxo neman aurenki wace shawara kika yanke" xaro ido Nauwar tayi "neman aure fa kika ce Aunty Amarya, ni ban shirya auren kowa ba yanxu saboda rashin lafiya Ammina har sai ta warke xan fara saurarar samari" dakatar da ita Alhaji Talle yayi "haba yan mata rashin lafiyar mahaifiyar ki baxa ta hana mu aure ba kuma baxa ta katse mana jin dadin rayuwa ba, na miki alkawarin baki kulawa mai yawa fatana kawai ki amince da bukatata a wuce gurin" *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 5⃣1⃣ Shiru Nauwar tayi tana sauraren abinda Alhaji Talle da aunty Amarya ke fada, sai da suka kammala tsaf sannan tayi musu magana. "duk naji abinda ku ka fada Aunty, amma ni ban amince da wannan hadin ba, dama nayi xaton Alhaji ya taimaka min ne saboda Allah, dan ni a matsayin uba na dauke shi, don haka baxan iya auren shi a matsayin abokin rayuwata ba" rike baki aunty amarya tayi tana mamakin kalaman Nauwar. "lallai yarinyar nan kin cika butulu, dama bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage bata mage, yanxu duk mutuncin da Alhaji yayi miki, kin mance har xaki watsa masa kasa a ido kice bakya son shi, to idan baki yi auren ba uban me xaki yi" ganin aunty Amarya nata faman fada, shi yasa Alhaji dakatar da ita. "haba Amarya abin ai bana tashin hankali bane, don tace bata sona ai bata yi laifi ba, saboda ba a soyayya dole amma abinda xa a yi duk abinda tasan nawa ne, ni na bata ko na kashe mata, xan rubuta list yanxu ta tattaro min kayana ta bani, idan ba haka ba kuma xan shigar da kara wajen hukuma" gumi ne ya rika yankowa Nauwar ta ko'ina, ina xata samu kudin da xata biya shi abinda yayi mata, alhalin duk kudin da yake bata aunty Amarya ke karbewa ta kashe abinda yake xuwa hannunta ba mai yawa bane. katse shirun da suka yi Aunty amarya tayi. "wace shawara kika yanke game da al'amarin nan, Alhaji yana da abin yi ke kawai yake jira" hawaye ne ya rika yankowa daga idanun Nauwar, bakinta na rawa ta amsa musu da "na amince" farin ciki ne ya bayyana a fuskar Alhaji Talle ya shiga washe baki. "yauwa ko kefa ai haka ya fi miki, Allah ya min arxiki na samu tsuntsu daga sama gasashshe, ke kuma Amarya Allah ya saka miki da alkhairi da wannan hadi da kika yi" "ba komai Alhaji ai yiwa kai ne" duban Nauwar tayi, tashi ki tafi tunda an gama maganar da xa a yi da ke, mikewa Nauwar tayi ta bar dakin. tana fita Aunty Amarya ta dubi Alhaji. "yanxu abinda ya rage sai a fara shirye-shiryen biki, kudi xaka rika bayarwa ana siyo mata kayan da xa a jera a daki, kasan ba tada kowa sai ni sai kuma kai,don haka duk wani gata da uba xai yiwa yarsa kaine xaka yi mata" duk wannan ba matsala Hajiya hannu yasa a aljihu ya xaro kudade masu yawa ya mika mata, ki fara siyo mata kayan aikin gida, saboda nan da sati biyu nake son a yi komai a gama. Tun daga ranar da Alhaji talle yaxo gidan Aunty Amarya aka yi maganar auren su da Nauwar, ya kara dagewa wajen yi mata hidima, ita kuwa tun daga lokacin ta fada cikin damuwa ta daina walwala, saboda tana cikin tsaka mai yawa, gaba daya rayuwa tayi mata xafi. Ana saura kwana uku daurin aure, Aunty Amarya ta gama shirya mata komai na gida inda aka fara shirye-shiryen tafiya jere, samun Nauwar tayi a daki ta hada kai da gwiwa. "har yanxu baxa ki hakura da damuwar nan ba, aure fa ba fashi saboda Alhaji baxai yafe miki kudin da ya kashe miki ba, dama shi ba a cin kudinsa a kwana lafiya don haka ki kwantar da kai, ki samu rabonki, yanxu xan kira mai kunshi da gyaran jiki tayi miki" "kinga Aunty kada ki fara a kirawo min kowa, ba wani kunshi da xan yi, wlh da ina da kudin da xan biya wannan mutumin abinda ya kashe da tuni na biya shi, na huta da masifa, dan gaba daya bana son auren nan ni ba aure ne a gaba na, idan na aure shi ya xan yi da mahaifiyata" ta karasa maganar tana kuka. "idan ta maganar mahaifiyarki ne mun gama magana yace xai bata dakin a gidan da xaki xauna, ke dai ki kwantar da hankali kici arxiki ki bar arxiki a inda yake" fita tayi ta bar mata dakin tana ta faman share hawaye, ita dai taga masifa daga wannan sai wannan, Allah ya kawo mata mafita. Yamma nayi Alhaji talle yayi sallama gidan da nauwar take, kai tsaye dakin Aunty ya shiga ya tarar da ita xaune ita kadai tana ta sharbar kuka, gefe guda ya samu fuskarsa cike da tashin hankali. "lafiya kike kuka Amaryar Alhaji, kiyi hakuri ki karbi abin nan a matsayin kaddara, na kudiri niyyar baki kulawar da da mahaifi, baxan cutar da ke ba,baxan bari komai ya cutar da ke ba, fatana dai ki soni ki kuma bani kulawa kamar yadda xan baki" share hawaye tayi sannan ta dube shi da jajayen idanunta. "Kayi hakuri ka fita a rayuwata wlh bana kaunarka" murmushi Alhaji yayi "lallai ke yarinya ce, ai ita rayuwa dama ba komai da kake so,kake samu ba wani abin karbar shi kawai ake yi ba dan ana sonshi ba, ki kwantar da hankalin ki kawai" kudi ya mika mata karbi wannan dubu talatin ne kiyi walima ke da kawayenki. hannu tasa ta karba taji wani sanyi a ranta, yana bata ya mike ya fita daga dakin. A ranar ta nemi ixnin Aunty amarya tana son xata kai Ammi chemist saboda tana dan fama da xaxxabi, cikin kulawa ta amsa mata "ayyah Allah ya bata lafiya, kiyi sauri ki dawo xaki taya ni aiki" tana fita ta kama hanyar tasha, ta xabi barin garin ne saboda hakan shi ne samun farin cikinta. motar da xata kai su garin gombe ta samu, ba tare da bata lokaci ba suka kama hanya sai gombe. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 5⃣1⃣ Shiru Nauwar tayi tana sauraren abinda Alhaji Talle da aunty Amarya ke fada, sai da suka kammala tsaf sannan tayi musu magana. "duk naji abinda ku ka fada Aunty, amma ni ban amince da wannan hadin ba, dama nayi xaton Alhaji ya taimaka min ne saboda Allah, dan ni a matsayin uba na dauke shi, don haka baxan iya auren shi a matsayin abokin rayuwata ba" rike baki aunty amarya tayi tana mamakin kalaman Nauwar. "lallai yarinyar nan kin cika butulu, dama bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage bata mage, yanxu duk mutuncin da Alhaji yayi miki, kin mance har xaki watsa masa kasa a ido kice bakya son shi, to idan baki yi auren ba uban me xaki yi" ganin aunty Amarya nata faman fada, shi yasa Alhaji dakatar da ita. "haba Amarya abin ai bana tashin hankali bane, don tace bata sona ai bata yi laifi ba, saboda ba a soyayya dole amma abinda xa a yi duk abinda tasan nawa ne, ni na bata ko na kashe mata, xan rubuta list yanxu ta tattaro min kayana ta bani, idan ba haka ba kuma xan shigar da kara wajen hukuma" gumi ne ya rika yankowa Nauwar ta ko'ina, ina xata samu kudin da xata biya shi abinda yayi mata, alhalin duk kudin da yake bata aunty Amarya ke karbewa ta kashe abinda yake xuwa hannunta ba mai yawa bane. katse shirun da suka yi Aunty amarya tayi. "wace shawara kika yanke game da al'amarin nan, Alhaji yana da abin yi ke kawai yake jira" hawaye ne ya rika yankowa daga idanun Nauwar, bakinta na rawa ta amsa musu da "na amince" farin ciki ne ya bayyana a fuskar Alhaji Talle ya shiga washe baki. "yauwa ko kefa ai haka ya fi miki, Allah ya min arxiki na samu tsuntsu daga sama gasashshe, ke kuma Amarya Allah ya saka miki da alkhairi da wannan hadi da kika yi" "ba komai Alhaji ai yiwa kai ne" duban Nauwar tayi, tashi ki tafi tunda an gama maganar da xa a yi da ke, mikewa Nauwar tayi ta bar dakin. tana fita Aunty Amarya ta dubi Alhaji. "yanxu abinda ya rage sai a fara shirye-shiryen biki, kudi xaka rika bayarwa ana siyo mata kayan da xa a jera a daki, kasan ba tada kowa sai ni sai kuma kai,don haka duk wani gata da uba xai yiwa yarsa kaine xaka yi mata" duk wannan ba matsala Hajiya hannu yasa a aljihu ya xaro kudade masu yawa ya mika mata, ki fara siyo mata kayan aikin gida, saboda nan da sati biyu nake son a yi komai a gama. Tun daga ranar da Alhaji talle yaxo gidan Aunty Amarya aka yi maganar auren su da Nauwar, ya kara dagewa wajen yi mata hidima, ita kuwa tun daga lokacin ta fada cikin damuwa ta daina walwala, saboda tana cikin tsaka mai yawa, gaba daya rayuwa tayi mata xafi. Ana saura kwana uku daurin aure, Aunty Amarya ta gama shirya mata komai na gida inda aka fara shirye-shiryen tafiya jere, samun Nauwar tayi a daki ta hada kai da gwiwa. "har yanxu baxa ki hakura da damuwar nan ba, aure fa ba fashi saboda Alhaji baxai yafe miki kudin da ya kashe miki ba, dama shi ba a cin kudinsa a kwana lafiya don haka ki kwantar da kai, ki samu rabonki, yanxu xan kira mai kunshi da gyaran jiki tayi miki" "kinga Aunty kada ki fara a kirawo min kowa, ba wani kunshi da xan yi, wlh da ina da kudin da xan biya wannan mutumin abinda ya kashe da tuni na biya shi, na huta da masifa, dan gaba daya bana son auren nan ni ba aure ne a gaba na, idan na aure shi ya xan yi da mahaifiyata" ta karasa maganar tana kuka. "idan ta maganar mahaifiyarki ne mun gama magana yace xai bata dakin a gidan da xaki xauna, ke dai ki kwantar da hankali kici arxiki ki bar arxiki a inda yake" fita tayi ta bar mata dakin tana ta faman share hawaye, ita dai taga masifa daga wannan sai wannan, Allah ya kawo mata mafita. Yamma nayi Alhaji talle yayi sallama gidan da nauwar take, kai tsaye dakin Aunty ya shiga ya tarar da ita xaune ita kadai tana ta sharbar kuka, gefe guda ya samu fuskarsa cike da tashin hankali. "lafiya kike kuka Amaryar Alhaji, kiyi hakuri ki karbi abin nan a matsayin kaddara, na kudiri niyyar baki kulawar da da mahaifi, baxan cutar da ke ba,baxan bari komai ya cutar da ke ba, fatana dai ki soni ki kuma bani kulawa kamar yadda xan baki" share hawaye tayi sannan ta dube shi da jajayen idanunta. "Kayi hakuri ka fita a rayuwata wlh bana kaunarka" murmushi Alhaji yayi "lallai ke yarinya ce, ai ita rayuwa dama ba komai da kake so,kake samu ba wani abin karbar shi kawai ake yi ba dan ana sonshi ba, ki kwantar da hankalin ki kawai" kudi ya mika mata karbi wannan dubu talatin ne kiyi walima ke da kawayenki. hannu tasa ta karba taji wani sanyi a ranta, yana bata ya mike ya fita daga dakin. A ranar ta nemi ixnin Aunty amarya tana son xata kai Ammi chemist saboda tana dan fama da xaxxabi, cikin kulawa ta amsa mata "ayyah Allah ya bata lafiya, kiyi sauri ki dawo xaki taya ni aiki" tana fita ta kama hanyar tasha, ta xabi barin garin ne saboda hakan shi ne samun farin cikinta. motar da xata kai su garin gombe ta samu, ba tare da bata lokaci ba suka kama hanya sai gombe. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* *NANAH JUWAIRIYYA, SHAMSIYYA ZAYYANU RIMI, SAKEENAT JIBRIL, naji dadin comments dinku Ina godiya da yadda kuke kaunar wannan littafi na AL-MAJIRA Allah ya bar xumunci* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 5⃣2⃣ Har bayan iska'i Amarya na dakon dawowar nauwar Amma shiru ba Labari, gajiya tayi da jira dan haka ta dauki aikinta ta fara yi, tana aikin tana masifa, jira Kawai take nauwar ta dawo ta sauke mata kwandon bala'i, bayan ta kammala ta dauki mayafi ta fita xuwa chemist din da tace mata xata je. Dan sallama ta shiga shagon inda ta tarar da mai chemist din yana shirye shiryen kullewa, gaisawa suka yi Sannan ta fara yi masa bayani "Malam musa ya gida ya aiki"cikin sakin fuska ya amsa mata "alhamdulillah Hajiya Amarya " "Dan Allah Malam musa tambaya nake" Dakatawa yayi da abinda yake yi ya tsaya don saurarenta "Allah yasa na sani Hajiya" Gyara tsayuwa tayi ta cigaba da magana "Akwai baki da nayi a gidana a cikinsu Akwai wata mai tabin hankali, to mai tabin hankalin aka ce xa a kawo ta wajenka tasha magani tun yamma, har Yanxu ba labarin su" "Subhanallah!! Wlh basu xo ba Hajiya amma ki tambayi mutane ko sun ga inda suka yi" Godiya tayi masa sannan ta fice Daga wajen xuciyar ta cike da mamakin inda su nauwar suka yi. A hanya taci Karo da daya daga cikin mutanen da suke xuwa wajenta har ta wuce bata ganshi ba yaja mayafinta ta dawo da baya. "Haba hajajjaju wuce mu ma xa a yi baxa a kula mu ba" "Wlh ban ganka ba Dan ladi raina a bace yake wai yarinyar nan da take gidana tun yamma ta fita har Yanxu bata dawo ba, ga aikin bikinta ina so ta taya ni" Kwashe wa yayi da dariya "wlh Hajiya yarinyar nan ta fece, yarinyar da na gamu da ita a tasha xata hau mota, ai sai dai ki rungumi sorry Kawai " Salati Amarya ta fara yi"lallai yarinyar nan ta cika yar akuya sakayyar da xata yi min kenan ai kuwa duk inda take sai na Nemo ta" Wucewa tayi a fusace ta shiga gida. Tana shiga ta dauki waya ta kira Alhaji talle ta sanar da shi halin da ake ciki Ashar ya danna mata "Wlh bansan wannan zancen ba Amarya Sam ba haka Muka yi da ke nake, me yasa Kinsan xata gudu kika sa na yarda da ita na gama kashe mata kudade a banxa, Wlh bansan asara ba, ban kuma san hanyar gidansu ba, tun wuri ki nemota kafin lokaci ya qure miki" Har kasa Amarya ta tsugunnah kamar yana kallonta, rokonsa ta rika yi saboda tasan tijararsa da cin mutuncinsa, bai Ki ya toxartata a kan wannan abin ba. Kashe wayar yayi ya kyaleta a tsugunne tana magiya, sake kiran wayar Shi tayi Amma gaba daya yaki dauka sai hakura tayi ta kyale Shi, ta shiga daki tana tsinewa nauwar "amma wannan yarinya ta cuce ni ta gama da ni, ta saka ni a tsaka mai wuya, Ina naga abinda xan biya wannan tijararren kudinsa" ganin mutum tayi a kanta yana ta xare-xaren ido, a sanyaye ta dago "Sannu da zuwa alhaji, ga guri bismillah xauna" Hararta yayi "ba wani Sannu da xuwa alhaji kuma babu wani guri da xaki bani na xauna Don ba xama ne ya kawo ni ba, Ina nauwar take??? A Yanxu ita nake bukata ba Kudi ba, Wlh sai kin fito min da ita ko ranki ya baci Yanxun nan, ni zaki ci wa amana, ni xaki yaudara ki karbe min kudade kice xaki aura min yarinya, Yanzu kuma Ki bata kudin mota ta gudu ta bar garin, wato an ci moriyar ganga ko, to Wlh baxa ta sabu ba, ko ki fito min da Matata ko jikinki ya gaya miki Sannan na mika Ki wajen yan sanda" Tunda lokacin da Amarya ta fara Jin kalaman Alhaji ta tabbatar da cewa ba xai mutunta mata ba ta fara kuka tana rokon shi ya rufa mata asiri. "ka taimake ni Alhaji Kasan baxan danfare ka ba, ban shirya abin nan a matsayin yaudara ba nima yarinyar nan yaudarata tayi ta barni a tsaka mai wuya, dan Allah kayi hakuri ka rangwanta min" Cikin fushi ya mata magana "ba wani rangwami da xan miki Domin Kowa yasan karuwa makaryaciya ce, sau nawa xaki fadi magana ki kuma abin ba haka bane, Ai ke ba abar yadda bace Amarya" Bude baki tayi xatai magana kafin tace komai ya hauta da duka ta ko'ina yana xaginta, ihu ta rika yi kafin kace kwabo tuni Jama'a suka cika gidan suna tambayar su abinda ya faru. Cigaba da dukanta alhaji talle yayi da kyar mutane suka kwaceta. Cikin xafin rai yake musu bayani "wai a ce ni matar nan xata damfara mun yi da ita xata aura min yarinya sai da na gama kashe kudina gaba daya Dan rainin hankali tace min wai yarinyar ta gudu Wlh baxan yarda ba sai na dauki mataki " Rike baki mutanen suka yi suna mamakin wannan cakwakiyar da Amarya ta hadawa kanta, hakuri suka shiga bashi "gaskiya Dan rashin kyautawa Amarya bata kyauta maka ba amma hakuri ya kamata kayi, Tunda Kaima kayi kuskure a matsayin ka na Babban mutum Kazo gidan mata masu xaman kansu kace xaka aure su wannan ai kuskure ne, hausawa sun ce kwarya ta gari tana ragaya, Yanxu ka daga mata kafa ta biyaka kudinka a hankali dama bariki ta gaji haka, garin banxa ne ya tafi a faraufarau din Wofi don haka sai ka rungumi na Annabawa" Duk mutanen da ke wajen babu wanda ya gayi bayan a Kai Amarya wajen yan sanda Kowa hakuri yake bawa Alhaji talle Sannan suka saka shi a gaba ya fita ya bar gidan" ***************** Yau da sassafe baffan Mahmoud ya shirya xuwa wajen sau, saboda ya dade bai xo wajen Mahmoud ba, shi ma kuma gaba daya ya dauke kafarsa Daga Dan batta, baya xuwa baya yi masa aiken komai. kasuwa ya shiga Don siyowa yan jikokinsa mangwaro da gyada, bayan ya siya ya nufi Tasha don Hawa motar Kano. Cikin kankanin lokaci suka shigo Kano inda ya samu adaidaita sahu ya kawo shi gidan Mahmoud. A Bakin kofa ya iske mai gadi yana ganinshi ya tsugunnah har kasa ya gaishe Shi ya karbi kayan da ke hannunsa ya yi masa rakiya har cikin gida. Sallama suka rika yi a Bakin kofar falon babu wanda ya amsa musu duk da cewa suna Jin hayaniyar jama'a, sai da aka dauki mintuna Sannan innah karime ta fito, tana ganin baffan ta hade rai kamar Wacce aka aikowa da naka'ikan mutuwa, har kasa ya tsugunnah xai gaisheta, dakatar da shi tayi. "bana bukatar gaisuwarka tauraruwa mai wutsiya ganinka ba alkhairi ne ba, wane munafuncin ne kuma ya kawo ka, Tunda Muka zo garin nan saboda kana ji da kininbibi baka biyo mu ba sai Yanxu, to me kaxo yi? " Kansa a sunkuye ya bata amsa "dama naxo naga wannan yaron ne da yayansa saboda na Kwana biyu ban gansu ba, Sannan kuma ina so Habi ta koma dakinta saboda Yanxu ina dan fama da rashin lafiya bana samun mai kulawa da ni" Wata shu'umar harara ta watsa masa "to naji abinda ka fada, kana ta xuba kamar wani Dan Kanya, ina san ka sani Habi baxa ta koma cikin wahala ba, muna nan muna Jin dadin rayuwar mu, Allah ya kashe ya bamu, don haka ba inda xata je muna nan a tare" Shigewa tayi daki ta barshi tsugunne, bayan lokaci kadan sai gata da tabarma da abinci watsa masa tabarmar tayi, shi kuma abincin ta ajiye masa shi. "ga tabarma nan ka xauna kafin Dan naka ya dawo, don baxa ka shigar mana daki ba ko da wata jarabar kaxo mana, wannan abincin kuma kaci dama nasan shi ya kawo ka sbd an dade ba a hadu da shinkafa ba" Shigewa daki tayi ta rufo kofa ta bar Baffa xaune yana hawayen Bakin ciki, da baisan innah karime ce mahifiyarsa ba, da cewa xai yi ba ita ta haife shi ba saboda yadda take nuna masa kiyayya kirikiri. Maigadi ne ya ganshi yana kuka don haka ya nufo wajen da sauri ya fara bashi hakuri. " kayi hakuri baba, Wlh da xan fada maka irin abubuwan da suke faruwa a gidan nan da kayi mamaki, ka share hawayenka komai ka barwa Allah xai yi maka magani" *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: Share hawayen yayi ya dubi mai gadi "na gode Malam Ali Insha Allah baxan Kara tayar da hankalina a kan haka ba." Bude masa kwanon abincin yayi "kaci abincin nan baba kada ya huce" Kallonsa yayi ya girgixa masa kai, "bana sha'awar komai Malam Ali Bakin ciki ya gama cika min cikina" Tausayin baffan Mahmoud ne ya kama mai gadi "kayi gefe da komai baba Insha Allah komai mai wucewa ne" Hawaye Baffa ya cigaba da sharewa saboda kukan ne Kawai xai saukaka masa damuwar da yake ciki. Duban Malam Ali yayi "wai ni ina matar gidan nan da yaranta ne Malam Ali tunda naxo banji motsinsu ba, ko sun tafi unguwa ne" Shiru Malam Ali yayi ya rasa amsar da xai bawa Baffa,saboda Idan ya fada masa basa nan ba karamin tashin hankali xai shiga ba, Don haka ya ki bashi amsa ya kawo masa wata hirar. Duk da wannan dabara da Malam Ali ya yiwa Baffa sai da ya sake maimaita masa irin wannan tambayar, dabara ce ta fadowa Malam Ali yace masa sun tafi Makaranta, haka suka xauna har wajen sallar La'asar suna hira suna jiran dawowar Abban Nauwar. Bugun kofa suka ji dan haka Malam Ali ya tashi Don bude kofar, Habi ce tare da magaji sun dawo daga unguwa, tana ganin Baffa tayi turus taja da baya "me xan gani, nafarki nake ko idona biyu" Magaji ne ya karbi zancen idonki biyu Don haka sake bude su Idan Kina ganin mafarki kike yi" Wucewa magaji yayi ya shige daki ko kallon Baffa bai yi ba, ballantana ya samu arxikin Gaisuwa. "Lallai annoba ta xiyarce mu har gida, me kuma kaxo yi nan gidan Malam, me yasa Kai ba kada hakuri duk kokarin da yaron nan yake yi a kanka sai ka biyo shi har gida maula salon ka zubar mana da mutunci ya gaji da mutuncinmu, gaskiya Malam baka kyauta mana ba wlh" Sakin baki Malam Ali yayi yana ganin ikon Allah tunda yake bai taba ganin irin wannan rashin da'ar ba sai yau. Hawaye ne ya cigaba da sauka a fuskar Baffa, saboda Bakin cikin da ya mamaye xuciyar sa da na sanin xuwansa gidan yake, ga Shi bai samu ganin Wadanda Yaxo dominsu ba, tashi yayi ya saka takalminsa xai fita ya bar gidan, da sauri maigadi ya tare shi yana bashi hakuri, Amma Sam yaki hakura ya fita. Tararshi yayi yasha gabansa. "kayi hakuri Baba baxan bari ka fita ranka a a bace haka ba, Yanzu xamani ne na lalura idan wani abin ya sameka fa, kayi hakuri ka jirayi xuwan mai gidan tunda dominshi dama kaxo kaga ba dadi idan baka hadu da shi ba" .saboda kukan da Baffa ke yi ya kasa magana ma gaba daya, baki ya cigaba da bashi amma yaki komawa cikin gidan, suna tsaye a wannan halin suka ji karar mota, saurin waiwayawa mai gadi yayi da sauri ya tafi bakin motar ya tsugunnah.. "Sannu da xuwa ranka ya dade, Ga Baffa nan Yaxo tun daxu yake jiran xuwanka" Da hanxari Abban nauwar ya fito daga motar ya fito, wajen Baffa ya nufa, Tsugunnawa har kasa yayi "Sannu da xuwa baffana" Kukan da Baffa ke yi shi ya hana shi amsa sallamar, shirun da yaji ne yasa ya dago kai don ganin halin da yake ciki. Hawaye yaga na sauka a kan kuncin Baffa Tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa "lafiya naga kana kuka baffana, me yake damunka ko jikin naka ne" "ka Kwantar da hankalinka Mahmoud lafiyata kalau kukan Farin cikin ganinka nake yi shi yasa". Murmushin karfin hali yayi ya sake Duban baffanshi "nasan ba haka bane baffana Kawai ka Boye min ne saboda kada na shiga damuwa amma a xahirin gaskiya Akwai abinda yake danunka" "na fada maka babu komai Mahmoud" Kiran Malam Ali yayi ya fara tanbayarsa abinda ya faru da baffanshi, bayani yayi masa dalla-dallah, a fusace ta wuce xai shiga gidan. Kiran sunanshi Baffa yayi "kada kace xaka yi tashin hankali akan wannan abin, kamar yadda na barwa Allah Kaima kayi hakuri ka barwa Allah, innah mahaifiyata ce baxan iya bari ka yi mata abinda bai kamata ba, kayi hakuri ka kyale su Duk abinda mutum yayi Dan kansa" Dawowa yayi ya Rike hannunsa suka shiga cikin gida Ko sallama bai yi ba, yasa kafa ya doki kofar falon, yana shiga falon su innah karime suka Mike suna masa Sannu da xuwa "Barka da zuwa Alajin Allah Ashe har ka iso bai basu amsa ba ya wuce sashinsa" Mamaki ne ya kama baffan Mahmoud wai Mahmoud din da aka tsana ne har ake kiransa da Alajin Allah Lallai duniya ba gaskiya" Suna shiga dakin ya kunnawa Baffa AC ya shiga kitchen da kansa dan hada masa abinci bayan ya kammala ya kaishi bandaki ya umarce Shi da yin wanka. Yana fitowa ya bashi kaya na alfarma ya saka Sannan suka fara cin abincin suna yi suna hirar Yaushe gamo. A cikin hirar ne ya jefo masa tambaya "wai ni ina matar gidan nan da yayanta ne tunda naxo fa banji motsinsu ba, na tanbayi mai gadi yace suna unguwa gashi har kusan karfe takwas basu dawo ba, kuma ban ji kayi cigiyarsu ba, anya lafiya kuwa Mahmoud" Wannan tambayar ba karamin tayar masa da tabon da ke ransa tayi ba [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* *NANAH JUWAIRIYYA, SHAMSIYYA ZAYYANU RIMI, SAKEENAT JIBRIL, naji dadin comments dinku Ina godiya da yadda kuke kaunar wannan littafi na AL-MAJIRA Allah ya bar xumunci, yasin ina yinku irin mugun sosai din nan* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 5⃣2⃣ Har bayan isha'i Amarya na dakon dawowar nauwar Amma shiru ba Labari, gajiya tayi da jiranta, dan haka ta dauki aikinta ta fara yi, tana aikin tana masifa, jira Kawai take nauwar ta dawo ta sauke mata kwandon bala'i, bayan ta kammala ta dauki mayafi ta fita dan xuwa chemist din da tace mata xata je. Da sallama ta shiga shagon inda ta tarar da mai chemist din yana shirye shiryen kullewa, gaisawa suka yi Sannan ta fara yi masa bayani "Malam musa ya gida ya aiki" cikin sakin fuska ya amsa mata "alhamdulillah Hajiya Amarya " "Dan Allah Malam musa tambaya nake" Dakatawa yayi da abinda yake yi ya tsaya don saurarenta "Allah yasa na sani Hajiya" Gyara tsayuwa tayi ta cigaba da magana "Akwai wasu baki da nayi kwanakin baya, a gidana a cikinsu Akwai wata mai tabin hankali, to mai tabin hankalin aka ce xa a kawo wajenka tasha magani tun yamma, har Yanxu ba labarin su" "Subhanallah!! Wlh basu xo ba Hajiya amma ki tambayi mutane ko sun ga inda suka yi kinsan lamari idan aka ce da mai tabin hankali dole sai hakuri " Godiya tayi masa sannan ta fice Daga wajen xuciyar ta cike da mamakin inda su nauwar suka yi. A hanya taci Karo da daya daga cikin mutanen da suke xuwa wajenta, har ta wuce bata ganshi ba yaja mayafinta ta dawo da baya. "Haba hajajjaju wuce mu ma xa a yi baxa a kula mu ba" "Wlh ban ganka ba Dan ladi raina a bace yake wai yarinyar nan da take gidana tun yamma ta fita har Yanxu bata dawo ba, ga aikin bikinta ina so ta taya ni" Kwashe wa yayi da dariya "wlh Hajiya yarinyar nan ta fece, yarinyar da na gamu da ita a tasha xata hau mota, ai sai dai ki rungumi sorry Kawai " Salati Amarya ta fara yi"lallai yarinyar nan ta cika yar akuya sakayyar da xata yi min kenan, ai kuwa duk inda take sai na Nemo ta" Wucewa tayi a fusace ta shiga gida. Tana shiga ta dauki waya ta kira Alhaji talle ta sanar da shi halin da ake ciki Ashar ya danna mata "Wlh bansan wannan zancen ba Amarya Sam ba haka Muka yi da ke nake, me yasa Kin san xata gudu kika sa na yarda da ita, na gama kashe mata kudade a banxa, Wlh bansan asara ba, ban kuma san hanyar gidansu ba, tun wuri ki nemota kafin lokaci ya qure miki" Har kasa Amarya ta tsugunnah kamar yana kallonta, rokonsa ta rika yi saboda tasan tijararsa da cin mutuncinsa, bai qi ya toxartata a kan wannan abin ba. Kashe wayar yayi ya kyaleta a tsugunne tana magiya, sake kiran wayar tayi Amma gaba daya yaki dauka,sai hakura tayi ta kyale Shi, ta shiga daki tana tsinewa nauwar "amma wannan yarinya ta cuce ni ta gama da ni, ta saka ni a tsaka mai wuya, Ina naga abinda xan biya wannan tijararren kudinsa" ganin mutum tayi a kanta yana ta xare-xaren ido, a sanyaye ta dago kai "Sannu da zuwa alhaji, ga guri bismillah xauna" Hararta yayi "ba wani Sannu da xuwa alhaji kuma babu wani guri da xaki bani na xauna Don ba xama ne ya kawo ni ba, Ina nauwar take??? A Yanxu ita nake bukata ba Kudi ba, Wlh sai kin fito min da ita ko ranki ya baci Yanxun nan, ni zaki ci wa amana, ni xaki yaudara ki karbe min kudade kice xaki aura min yarinya, Yanzu kuma Ki bata kudin mota ta gudu ta bar garin, wato an ci moriyar ganga ko, to Wlh baxa ta sabu ba, ko ki fito min da Matata ko jikinki ya gaya miki Sannan na mika Ki wajen yan sanda" Tun lokacin da Amarya ta fara Jin kalaman Alhaji ta tabbatar da cewa ba xai mutunta mata ba, kuka ta fara yi tana rokon shi ya rufa mata asiri. "ka taimake ni Alhaji Kasan baxan danfare ka ba, ban shirya abin nan a matsayin yaudara ba, nima yarinyar nan yaudarata tayi ta barni a tsaka mai wuya, dan Allah kayi hakuri ka rangwanta min" Cikin fushi ya mata magana "ba wani rangwami da xan miki Domin Kowa yasan karuwa makaryaciya ce, sau nawa xaki fadi magana kuma abin ba haka bane, Ai ke ba abar yarda bace Amarya" Bude baki tayi xatai magana kafin tace komai,ya hauta da duka ta ko'ina yana xaginta, ihu ta rika yi kafin kace kwabo tuni Jama'a suka cika gidan suna tambayar su abinda ya faru. Cigaba da dukanta alhaji talle yayi da kyar mutane suka kwaceta. Cikin xafin rai yake musu bayani "wai a ce ni matar nan xata damfara mun yi da ita xata aura min yarinya, sai da na gama kashe kudina gaba daya Dan rainin hankali tace min wai yarinyar ta gudu Wlh baxan yarda ba sai na dauki mataki " Rike baki mutanen suka yi suna mamakin wannan cakwakiyar da Amarya ta hadawa kanta, hakuri suka shiga bashi "gaskiya Dan rashin kyautawa Amarya bata kyauta maka ba amma hakuri ya kamata kayi, Tunda Kaima kayi kuskure a matsayin ka na Babban mutum Kazo gidan mata masu xaman kansu kace xaka nemi aure. wannan ai kuskure ne, hausawa sun ce kwarya ta gari tana ragaya, Yanxu ka daga mata kafa ta biyaka kudinka a hankali tunda dama bariki ta gaji haka, garin banxa ne ya tafi a faraufarau din Wofi, don haka sai ka rungumi na Annabawa" Duk mutanen da ke wajen babu wanda ya goyi bayan a Kai Amarya wajen yan sanda,Kowa hakuri yake bawa Alhaji talle Sannan suka saka shi a gaba ya fita ya bar gidan" ***************** Yau da sassafe baffan Mahmoud ya shirya xuwa wajen dansa,saboda ya dade bai xo wajen Mahmoud ba, shi ma kuma gaba daya ya dauke kafarsa Daga Dan batta, baya xuwa baya yi masa aiken komai. kasuwa ya shiga Don siyowa yan jikokinsa mangwaro da gyada, bayan ya siya ya nufi Tasha don Hawa motar Kano. Cikin kankanin lokaci suka shigo Kano inda ya samu adaidaita sahu ya kawo shi gidan Mahmoud. A Bakin kofa ya iske mai gadi yana ganinshi ya tsugunnah har kasa ya gaishe Shi ya karbi kayan da ke hannunsa ya yi masa rakiya har cikin gida. Sallama suka rika yi a Bakin kofar falon babu wanda ya amsa musu,duk da cewa suna Jin hayaniyar jama'a, sai da aka dauki mintuna Sannan innah karime ta fito, tana ganin baffan ta hade rai kamar Wacce aka aikowa da mala'ikan mutuwa, har kasa ya tsugunnah xai gaisheta, dakatar da shi tayi. "bana bukatar gaisuwarka tauraruwa mai wutsiya ganinka ba alkhairi ba, wane munafuncin ne kuma ya kawo ka, Tunda Muka zo garin nan saboda kana ji da kininbibi baka biyo mu ba sai Yanxu, to me kaxo yi? " Kansa a sunkuye ya bata amsa "dama naxo naga wannan yaron ne da yayansa saboda na Kwana biyu ban gansu ba, Sannan kuma ina so Habi ta koma dakinta saboda Yanxu ina dan fama da rashin lafiya, bana samun mai kulawa da ni" Wata shu'umar harara ta watsa masa "to naji abinda ka fada, kana ta xuba kamar wani Dan Kanya, ina san ka sani Habi baxa ta koma cikin wahala ba, muna nan muna Jin dadin rayuwar mu, Allah ya kashe ya bamu, don haka ba inda xata je muna nan a tare" Shigewa tayi daki ta barshi tsugunne, bayan lokaci kadan sai gata da tabarma da abinci watsa masa tabarmar tayi, shi kuma abincin ta ajiye masa shi. "ga tabarma nan ka xauna kafin Dan naka ya dawo, don baxa ka shigar mana daki ba ko da wata jarabar kaxo mana, wannan abincin kuma kaci dama nasan shi ya kawo ka sbd an dade ba a hadu da shinkafa ba" Shigewa daki tayi ta rufo kofa ta bar Baffa xaune yana hawayen Bakin ciki, da bai san innah karime ce mahifiyarsa ba, da cewa xai yi ba ita ta haife shi ba, saboda yadda take nuna masa kiyayya kirikiri. Maigadi ne ya ganshi yana kuka don haka ya nufo wajen sa da sauri ya fara bashi hakuri. " kayi hakuri baba, Wlh da xan fada maka irin abubuwan da suke faruwa a gidan nan da kayi mamaki, ka share hawayenka komai ka barwa Allah xai yi maka magani" *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 09077389712 5⃣3⃣ Share hawaye yayi ya dubi mai gadi "na gode Malam Ali Insha Allah baxan Kara tayar da hankalina a kan haka ba." Bude masa kwanon abincin yayi "kaci abincin nan baba kada ya huce" Kallonsa yayi ya girgixa masa kai, "bana sha'awar komai Malam Ali Bakin ciki ya gama cika min cikina" Tausayin baffan Mahmoud ne ya kama mai gadi "kayi gefe da komai baba Insha Allah komai mai wucewa ne" Hawaye Baffa ya cigaba da sharewa saboda kukan ne Kawai xai saukaka masa damuwar da yake ciki. Duban Malam Ali yayi "wai ni ina matar gidan nan da yaranta ne Malam Ali tunda naxo fa banji motsin su ba, ko sun tafi unguwa ne" Shiru Malam Ali yayi ya rasa amsar da xai bawa Baffa,saboda Idan ya fada masa basa nan ba karamin tashin hankali xai shiga ba, Don haka ya ki bashi amsa ya kawo masa wata hirar. Duk da wannan dabara da Malam Ali ya yiwa Baffa sai da ya sake maimaita masa irin wannan tambayar, dabara ce ta fado masa yace sun tafi Makaranta, haka suka xauna har wajen sallar La'asar suna hira suna jiran dawowar Abban Nauwar. Bugun kofa suka ji dan haka Malam Ali ya tashi Don bude kofar, Habi ce tare da magaji suka dawo daga unguwa, tana ganin Baffa tayi turus taja da baya "me xan gani, mafarki nake ko idona biyu" Magaji ne ya karbi zancen idon ki biyu Don haka sake bude su Idan Kina ganin mafarki kike yi" Wucewa magaji yayi ya shige daki ko kallon Baffa bai yi ba, ballantana ya samu arxikin Gaisuwa. "Lallai annoba ta xiyarce mu har gida, me kuma kaxo yi nan gidan Malam, me yasa Kai ba kada hakuri ne, duk kokarin da yaron nan yake yi a kanka sai ka biyo shi har gida maula,salon ka zubar mana da mutunci ya gaji da kulawa da mu, gaskiya Malam baka kyauta mana ba wlh" Sakin baki Malam Ali yayi yana ganin ikon Allah tunda yake bai taba ganin irin wannan rashin da'ar ba sai yau. Hawaye ne ya cigaba da sauka a fuskar Baffa, saboda Bakin cikin da ya mamaye xuciyar sai da yayi da na sanin xuwansa gidan , ga Shi bai samu ganin Wadanda Yaxo dominsu ba, tashi yayi ya saka takalminsa xai fita ya bar gidan, da sauri maigadi ya tare shi yana bashi hakuri, Amma Sam yaki hakura ya fita. Tare shi yayi yasha gabansa. "kayi hakuri Baba baxan bari ka fita ranka a bace haka ba, Yanzu xamani ne na lalura idan wani abin ya sameka fa, kayi hakuri ka jirayi xuwan mai gidan, tunda domin shi dama kaxo, kaga ba dadi idan baka hadu da shi ba" .saboda kukan da Baffa ke yi ya kasa magana ma gaba daya, baki ya cigaba da bashi amma yaki komawa cikin gidan, suna tsaye a wannan halin suka ji karar mota, saurin waiwayawa mai gadi yayi da sauri ya tafi bakin motar ya tsugunnah.. "Sannu da xuwa ranka ya dade, Ga Baffa nan Yaxo tun daxu yake jiran xuwanka" Da hanxari Abban nauwar ya fito daga motar ya fito, wajen Baffa ya nufa, Tsugunnawa har kasa yayi "Sannu da xuwa baffana" Kukan da Baffa ke yi shi ya hana shi amsa sallamar, shirun da yaji ne yasa ya dago kai don ganin halin da yake ciki. Hawaye yaga na sauka a kan kuncin Baffa Tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa "lafiya naga kana kuka baffana, me yake damunka ko jikin naka ne" "ka Kwantar da hankalinka Mahmoud lafiyata kalau kukan Farin cikin ganinka nake yi shi yasa". Murmushin karfin hali yayi ya sake Duban baffanshi "nasan ba haka bane baffana Kawai ka Boye min ne saboda kada na shiga damuwa amma a xahirin gaskiya Akwai abinda yake damunka" "na fada maka babu komai Mahmoud" Kiran Malam Ali yayi ya fara tambayarsa abinda ya faru da baffanshi, bayani yayi masa dalla-dallah, a fusace ya wuce xai shiga gidan. Kiran sunan shi Baffa yayi "kada kace xaka yi tashin hankali a kan wannan abin, kamar yadda na barwa Allah Kaima kayi hakuri ka barwa Allah, innah mahaifiyata ce baxan iya bari ka yi mata abinda bai kamata ba, kayi hakuri ka kyale su Duk abinda mutum yayi Dan kansa" Dawowa yayi ya Rike hannunsa suka shiga cikin gidan. Ko sallama bai yi ba, yasa kafa ya doki kofar falon, yana shiga falon su innah karime suka Mike suna masa Sannu da xuwa "Barka da zuwa Alajin Allah Ashe har ka iso" bai basu amsa ba ya wuce sashinsa Mamaki ne ya kama baffan Mahmoud wai Mahmoud din da aka tsana ne har ake kiransa da Alajin Allah~ Lallai duniya ba gaskiya" Suna shiga daki ya kunnawa Baffa AC ya shiga kitchen da kansa dan hada masa abinci, bayan ya kammala ya kai shi bandaki ya umarce Shi da yin wanka. Yana fitowa ya bashi kaya na alfarma ya saka Sannan suka fara cin abincin suna yi suna hirar Yaushe gamo. A cikin hirar ne ya jefo masa tambaya "wai ni ina matar gidan nan da yayanta ne tunda naxo fa banji motsinsu ba, na tambayi mai gadi yace suna unguwa, gashi har kusan karfe takwas basu dawo ba, kuma ban ji kayi cigiyarsu ba, anya lafiya kuwa Mahmoud" Wannan tambayar ba karamin tayar masa da tabon da ke ransa tayi ba, sunkuyar da kansa yayi saboda ba shi da amsar da xai bawa Baffa, hawaye ne suka rika sauka a kan kuncinsa. cikin tashin hankali Baffa ya dube shi lafiya kake kuka, ko dai sakin yarinyar nan kayi. inda inda ya fara yi, saboda gaba daya ya mance inda su Nauwar suke ya manta da rayuwarsu tunda suka tafi bai sake tunawa da su ba. ganin kukan da yake yi ne, yasa Baffa ya kyale shi da maganar ya kudurce a ransa washe gari xai samu mai gadi ya tambaye shi abinda ke faruwa. kwana Baffa yayi yana tunanin su Nauwar,shi kuma mahmud na jin xafin abinda ya yiwa su Nauwar, amma kuma baxai iya yin komai a kai ba. Washe gari da sassafe Baffa ya fita wajen mai gadi, samun shi yayi yana laximi don haka ya jira shi ya kammala sannan suka gaisa "dama xuwa nayi mu tattauna dangane da matar gidan nan tunda naxo ban ganta ba banga Nauwar da fu'ad ba, na tambayi wannan yaron ya hau kuka ya kasa bani amsa, ko dai sakinta yayi, shi ne yake boye min, dan Allah kada ka rufe min komai ka fada min gaskiyar wannan al'amarin. shiru mai gadi yayi na wasu yan lokuta sannan ya dago ya dubi Baffa. "tunda ka roke ni na fada maka gaskiya Insha Allah xan fada maka baba, babu abinda xan boye maka" "Abubuwa da dama sun faru a gidan nan wanda nasan baka sani ba, kuma ba a sanar da kai ba, amma ina rokonka dan Allah ka kwantar da hankalinka, kada ka bata ranka dangane da abinda xan fada maka" tsayawa yayi yana sauraren sa. "Baba Allah ya yiwa fu'ad rasuwa sakamakon rashin lafiya" dafe kirji Baffa yayi" subhanallah yaushe, wlh basu fada min ba" Ai har an dan kwana biyu "baba kwalla Baffa ya shiga sharewa "kayi hakuri Baba addu'a xaka yi masa Allah ya gafarta masa" addu'a Baffa ya shiga yiwa fu'ad yana roka masa rahma. tambayar mai gadi ya shiga yi "to ina matar gidan da ragowar yaran gidan?" kamar mai gadi baxai bashi wannan amsar ba, amma saboda ya yi masa alkawarin fadar gaskiya, sai ya danne xuciyarsa ya fara yi masa bayani "uwar yaran ta haukace, shi ne mai gidan nan ya kore su" mikewa Baffa yayi yana salati, nan da nan kansa ya rika juyawa, ya fadi kasa sumamme. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 09077389712 5⃣3⃣ Share hawaye yayi ya dubi mai gadi "na gode Malam Ali Insha Allah baxan Kara tayar da hankalina a kan haka ba." Bude masa kwanon abincin yayi "kaci abincin nan baba kada ya huce" Kallonsa yayi ya girgixa masa kai, "bana sha'awar komai Malam Ali Bakin ciki ya gama cika min cikina" Tausayin baffan Mahmoud ne ya kama mai gadi "kayi gefe da komai baba Insha Allah komai mai wucewa ne" Hawaye Baffa ya cigaba da sharewa saboda kukan ne Kawai xai saukaka masa damuwar da yake ciki. Duban Malam Ali yayi "wai ni ina matar gidan nan da yaranta ne Malam Ali tunda naxo fa banji motsin su ba, ko sun tafi unguwa ne" Shiru Malam Ali yayi ya rasa amsar da xai bawa Baffa,saboda Idan ya fada masa basa nan ba karamin tashin hankali xai shiga ba, Don haka ya ki bashi amsa ya kawo masa wata hirar. Duk da wannan dabara da Malam Ali ya yiwa Baffa sai da ya sake maimaita masa irin wannan tambayar, dabara ce ta fado masa yace sun tafi Makaranta, haka suka xauna har wajen sallar La'asar suna hira suna jiran dawowar Abban Nauwar. Bugun kofa suka ji dan haka Malam Ali ya tashi Don bude kofar, Habi ce tare da magaji suka dawo daga unguwa, tana ganin Baffa tayi turus taja da baya "me xan gani, mafarki nake ko idona biyu" Magaji ne ya karbi zancen idon ki biyu Don haka sake bude su Idan Kina ganin mafarki kike yi" Wucewa magaji yayi ya shige daki ko kallon Baffa bai yi ba, ballantana ya samu arxikin Gaisuwa. "Lallai annoba ta xiyarce mu har gida, me kuma kaxo yi nan gidan Malam, me yasa Kai ba kada hakuri ne, duk kokarin da yaron nan yake yi a kanka sai ka biyo shi har gida maula,salon ka zubar mana da mutunci ya gaji da kulawa da mu, gaskiya Malam baka kyauta mana ba wlh" Sakin baki Malam Ali yayi yana ganin ikon Allah tunda yake bai taba ganin irin wannan rashin da'ar ba sai yau. Hawaye ne ya cigaba da sauka a fuskar Baffa, saboda Bakin cikin da ya mamaye xuciyar sai da yayi da na sanin xuwansa gidan , ga Shi bai samu ganin Wadanda Yaxo dominsu ba, tashi yayi ya saka takalminsa xai fita ya bar gidan, da sauri maigadi ya tare shi yana bashi hakuri, Amma Sam yaki hakura ya fita. Tare shi yayi yasha gabansa. "kayi hakuri Baba baxan bari ka fita ranka a bace haka ba, Yanzu xamani ne na lalura idan wani abin ya sameka fa, kayi hakuri ka jirayi xuwan mai gidan, tunda domin shi dama kaxo, kaga ba dadi idan baka hadu da shi ba" .saboda kukan da Baffa ke yi ya kasa magana ma gaba daya, baki ya cigaba da bashi amma yaki komawa cikin gidan, suna tsaye a wannan halin suka ji karar mota, saurin waiwayawa mai gadi yayi da sauri ya tafi bakin motar ya tsugunnah.. "Sannu da xuwa ranka ya dade, Ga Baffa nan Yaxo tun daxu yake jiran xuwanka" Da hanxari Abban nauwar ya fito daga motar ya fito, wajen Baffa ya nufa, Tsugunnawa har kasa yayi "Sannu da xuwa baffana" Kukan da Baffa ke yi shi ya hana shi amsa sallamar, shirun da yaji ne yasa ya dago kai don ganin halin da yake ciki. Hawaye yaga na sauka a kan kuncin Baffa Tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa "lafiya naga kana kuka baffana, me yake damunka ko jikin naka ne" "ka Kwantar da hankalinka Mahmoud lafiyata kalau kukan Farin cikin ganinka nake yi shi yasa". Murmushin karfin hali yayi ya sake Duban baffanshi "nasan ba haka bane baffana Kawai ka Boye min ne saboda kada na shiga damuwa amma a xahirin gaskiya Akwai abinda yake damunka" "na fada maka babu komai Mahmoud" Kiran Malam Ali yayi ya fara tambayarsa abinda ya faru da baffanshi, bayani yayi masa dalla-dallah, a fusace ya wuce xai shiga gidan. Kiran sunan shi Baffa yayi "kada kace xaka yi tashin hankali a kan wannan abin, kamar yadda na barwa Allah Kaima kayi hakuri ka barwa Allah, innah mahaifiyata ce baxan iya bari ka yi mata abinda bai kamata ba, kayi hakuri ka kyale su Duk abinda mutum yayi Dan kansa" Dawowa yayi ya Rike hannunsa suka shiga cikin gidan. Ko sallama bai yi ba, yasa kafa ya doki kofar falon, yana shiga falon su innah karime suka Mike suna masa Sannu da xuwa "Barka da zuwa Alajin Allah Ashe har ka iso" bai basu amsa ba ya wuce sashinsa Mamaki ne ya kama baffan Mahmoud wai Mahmoud din da aka tsana ne har ake kiransa da Alajin Allah~ Lallai duniya ba gaskiya" Suna shiga daki ya kunnawa Baffa AC ya shiga kitchen da kansa dan hada masa abinci, bayan ya kammala ya kai shi bandaki ya umarce Shi da yin wanka. Yana fitowa ya bashi kaya na alfarma ya saka Sannan suka fara cin abincin suna yi suna hirar Yaushe gamo. A cikin hirar ne ya jefo masa tambaya "wai ni ina matar gidan nan da yayanta ne tunda naxo fa banji motsinsu ba, na tambayi mai gadi yace suna unguwa, gashi har kusan karfe takwas basu dawo ba, kuma ban ji kayi cigiyarsu ba, anya lafiya kuwa Mahmoud" Wannan tambayar ba karamin tayar masa da tabon da ke ransa tayi ba, sunkuyar da kansa yayi saboda ba shi da amsar da xai bawa Baffa, hawaye ne suka rika sauka a kan kuncinsa. cikin tashin hankali Baffa ya dube shi lafiya kake kuka, ko dai sakin yarinyar nan kayi. inda inda ya fara yi, saboda gaba daya ya mance inda su Nauwar suke ya manta da rayuwarsu tunda suka tafi bai sake tunawa da su ba. ganin kukan da yake yi ne, yasa Baffa ya kyale shi da maganar ya kudurce a ransa washe gari xai samu mai gadi ya tambaye shi abinda ke faruwa. kwana Baffa yayi yana tunanin su Nauwar,shi kuma mahmud na jin xafin abinda ya yiwa su Nauwar, amma kuma baxai iya yin komai a kai ba. Washe gari da sassafe Baffa ya fita wajen mai gadi, samun shi yayi yana laximi don haka ya jira shi ya kammala sannan suka gaisa "dama xuwa nayi mu tattauna dangane da matar gidan nan tunda naxo ban ganta ba banga Nauwar da fu'ad ba, na tambayi wannan yaron ya hau kuka ya kasa bani amsa, ko dai sakinta yayi, shi ne yake boye min, dan Allah kada ka rufe min komai ka fada min gaskiyar wannan al'amarin. shiru mai gadi yayi na wasu yan lokuta sannan ya dago ya dubi Baffa. "tunda ka roke ni na fada maka gaskiya Insha Allah xan fada maka baba, babu abinda xan boye maka" "Abubuwa da dama sun faru a gidan nan wanda nasan baka sani ba, kuma ba a sanar da kai ba, amma ina rokonka dan Allah ka kwantar da hankalinka, kada ka bata ranka dangane da abinda xan fada maka" tsayawa yayi yana sauraren sa. "Baba Allah ya yiwa fu'ad rasuwa sakamakon rashin lafiya" dafe kirji Baffa yayi" subhanallah yaushe, wlh basu fada min ba" Ai har an dan kwana biyu "baba kwalla Baffa ya shiga sharewa "kayi hakuri Baba addu'a xaka yi masa Allah ya gafarta masa" addu'a Baffa ya shiga yiwa fu'ad yana roka masa rahma. tambayar mai gadi ya shiga yi "to ina matar gidan da ragowar yaran gidan?" kamar mai gadi baxai bashi wannan amsar ba, amma saboda ya yi masa alkawarin fadar gaskiya, sai ya danne xuciyarsa ya fara yi masa bayani "uwar yaran ta haukace, shi ne mai gidan nan ya kore su" mikewa Baffa yayi yana salati, nan da nan kansa ya rika juyawa, ya fadi kasa sumamme. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne a gareki UMMU SULAIM MUHAMMAD LAWAN(hasanatullah) Nauwar na godia da yadda kike son wannan labari nata Allah ya bar xumunci* 5⃣4⃣ A gigice mai gadi ya shiga sashin su innah karime, samun su yayi suna shiryen-shiryen fita unguwa. "Hajiya ku fito baba ya fadi dan Allah ku taimaka masa" A fusace Habi ta dube shi ta bashi amsa "faduwarsa bata shafe mu ba, ka karasa ciki ka fadawa dansa" da gudu ya karasa bangaren Abban Nauwar, tarar da shi yayi yana bacci, dan haka ya tashe shi suka rankayo suka taho wajen Baffa hankalinsa a tashe yake masa magana "Baffa me ya sameka ka fadi, dan Allah ka tashi" da sauri mai gadi ya kawo ruwa aka yayyafa masa, ya fara bude ido sannan ya saka shi a mota suka yi asibiti" suna isa aka fara duba Baffa inda aka tabbatar masa da cewa damuwa ce tayi masa yawa, kuma idan ya cigaba da kasancewa a cikin damuwa, yana da baraxanar kamuwa da hawan jini. suna kammala duba shi suka dawo gida, a daki ya saka shi yana tambayar shi "dan Allah ka daina saka damuwa a ranka Baffa ka dai ji abinda likita ya fada mana" duban shi yayi yana hawaye "dole nayi kuka mahmud, saboda babban bala'i ne ya sameka a rayuwa wanda idan ban yi da gaske ba, xai yi sanadiyyar shigarka wuta, ka dakko amanar yarinya gari i gari, tun daga sudan amma ka wulakanta ta, ka koreta da ita da yar jikata guda daya da na mallaka, wacce ita ce tayi ragowa a yayanka, mahmud dole na cigaba da kasancewa a cikin bakin ciki, jikana ya rasu amma saboda baka ganin darajata duk baka fada min ba" shiru yayi yana sauraren Baffa,maganarsa na shiga kunnesa, duk abinda Baffa yake fada masa yasan ya aikata kuma bai kyauta ba, amma baxai iya daukan mataki a kan haka ba. katse masa tunani Baffa yayi "mahmud idan kana son ganin farin cikina da walwalata ka nemo yarinyar nan tare da yarta idan ba haka ba ban yafe maka ba" a raxane ya dubi Baffa "baka yafe min ba fa kace Baffana" "eh ban yafe maka ba, har sai ka cika umarnin da nayi maka" kuka mahmud ya rika yi yana rokon Baffa gafara, amma yaki yafe masa. A ranar Baffa yace baxai sake kwana a gidan ba,duk da magiyar da mahmud yayi masa yaki hakura, sai daukan shi yayi a mota ya kai shi har Dan batta, suna tafe a mota Baffa na kuka, saboda tausayin halin da dansa ke ciki. Bayan ya kai shi ya xaro kudi masu yawa ya bashi, amma sam Baffa yaki karba, kayan abincin da ya siyo masa ma cewa yayi ya juya dasu, saboda babu abinda xai yi da su, tunda ba shi da mai girka masa. Idanun mahmud cike da hawaye ya dubi Baffansa "Dan Allah ka yafe min Baffa,me yasa xaka ki karbar abinda ya fito daga hannuna gaba daya" fuskar Baffa ba annuri ya dubi mahmud "tunda ka xama mara adalci baka kulawa da iyalinka ka xabi wasu ka barni ka wulakanta amanar da ka dakko, babu ruwana da kai, kaje ka kama mutanen da kake ganin sun fini daraja a wajenka" tashin hankali ne ya bayyana a fuskar mahmud "wlh ban kama kowa ba baffa, nasan kaine kayi min gata, ka soni a lokacin da kowa ke guduna, ta yaya xan ki ganin darajarka, kayi hakuri kayi min afuwa" tausayin dansa ne ya kama shi, yasan duk abinda yake yi ba a hankalinsa yake ba, amma ya kuduri niyyar yi masa addu'a Allah ya dawo da shi hanya madaidaiciya. "shikenan na ji bayanan ka mahmud ka tashi ka tafi kada dare yayi maka a hanya, Allah ya ganar da kai gaskiya, ya fito da kai daga duhun da kake ciki" amsawa yayi da ameen ya mike ya tafi. xuciyarsa cike da bakin cikin Abubuwan da yake aikatawa, mamakin kansa yake,ta yaya ma aka yi hakan ke faruwa? haka ya isa gida da wadannan tunane-tunanen ya kuma kudiri niyyar korar Habi daga gidansa, dole ta koma Dan batta ta kula da tsohonsa. Yana isa gidan ya shiga sashin su innah karime da niyyar fadawa Habi ta shirya gobe xai mayar da ita dakinta, amma abin mamaki sai bakinsa ya kulle ya kasa furta mata komai, sai gaisawa suka yi ya fito ya tafi dakinsa xuciyarsa cike da bakin ciki. Bayan komawar Baffa dan batta da sati biyu, ciwonsa ya kara dawowa saboda kullum ya tuna su Nauwar da mahaifiyarta sai yayi kukan bakin ciki, wannan dalilin ne yasa ciwon nasa yake dawowa danye. A ranar da ciwon sa yayi xafi Audu ya kira mahmud ya sanar da shi, a gigice ya nufi hanyar xuwa dan batta, inda suka dakko Baffa suka dawo da shi asibitin kano, taimakon gaggawa aka rika bashi, cikin ikon Allah ya samu sauki, bayan ya warware ne ya tambayi mahmud. "wai ina malam Abdullahi ne? tunda na fara rashin lafiyar nan banga yaxo ya gaishe ni ba, anya ya sani kuwa?" A kunya ce mahmud ya amsawa Baffa saboda rabonsa da yaje wajen malam Abdullahi har ya manta, ko waya malam din yayi masa baya dauka, gashi kuma shi ne yayi silar xuwansa birni,shi ne silar duk wani arxiki da yake takama da shi. "A'a ban fada masa ba Baffa naga abubuwan ne sun yi yawa bana san na takura masa" cikin fushi Baffa yake wa mahmud magana "bana san shashanci aminin nawa xaka ki fadawa abinda ya dameni, maxa dauki waya ka kira shi ka fada masa kafin na bata maka rai" daukan wayar yayi ya kira malam Abdullahi. "mamaki ne ya kama malam, yau kuma mudi ne aka tuna da ni aka kira ni Allah da iko yake" daukan wayar yayi ya kara a kunnesa, sallama yayi sannan ya kira sunan mahmud "wata sabon gani yau kuma xumuncin ne ya motsa an tuna da ni" kunya ce ta kama mahmud saboda ya dade bai kira shi sun gaisa ba. "dama Baffa ne ba shi da lafiya, shi ne yace bai ganka kaxo dubiya ba" "subhanallah ai ban sani ba wlh, ka fada masa gani nan xuwa yanxu insha Allah" suna gama wayar ya dauki takalmi sai wajen Baffa, da sallama malam Abdullahi ya shigo wajen. Baffa na hada ido da shi ya fashe da kuka mai ban tausayi, karasowa malam Abdullahi yayi yana rarrashin Baffa. "kayi hakuri malam cuta ai ba mutuwa bace, in Allah ya yarda xaka samu sauki" bayan sun dawo hayyacin su ne suka gaisa, ya tambayi Baffa abinda ke damunsa. hawaye Baffa ya share "wlh ba komai ke damuna ba malam sai bakin cikin mahmud" malam Abdullahi ne ya dubi mahmud "kai yaro, yanxu bakin cikinka ne yake son hallaka mahifinka, anya kana san cikawa da imani kuwa? sunkuyar da kai mahmud yayi saboda ba shida amsar da xai bawa malam. Baffa ne ya cigaba da yi masa bayani "yanxu ace malam yaron nan ya kori yarsa da matarsa, dansa ya rasu duk ban sani ba" cikin mamaki malam Abdullahi ya dubi mahmud. "kanka kalau kuwa ka aikata wannan danyen aikin, gaskiya da wata a kasa" tashi ka fita xamu tattauna da baffanka. bayan ya fita malam Abdullahi ya dubi Baffa "wannan abin fa ba na lafiya bane, ka daina saka bakin cikin yaron nan a ranka, ina ganin akwai lauje cikin nadi" "Nima haka nake tunani malam" "Tunda abin haka ne, addu'a ya kamata a yi, Yanxu xansa a yi saukar kur'ani, Allah ya warware duk wata matsala dake damun yaron nan, su kuma Allah ya bayyana su" cikin farin ciki Baffa ya dube shi. "Gaskiya hakan yayi kyau, Allah ya amsa mana adduar da xamu yi, shi kuma Allah ya shirye shi" sallama suka yi da Baffa, yayi masa alkawarin taho wa da mahmud magungunan karya sihiri. godiya mai yawa yayi masa sannan suka rabu *Jeeddahtulkhairhb😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJAN* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gareki AYSHA KABIR (Mrs shehu Murtala) Allah ya qara muku xaman lafiya da yarlawar arxiki, thanks 4 d love and support* *ina bawa Makaranta littafi hakuri saboda rashin ganin post jiya, hakan ya faru ne sakamakon rashin caji, a yi min afuwa kun san rayuwar kauye sai a slow* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 5⃣5⃣ Bayan Baffa yayi sallama da malam Abdullahi ne ya 'kwalawa mahmud kira,da sauri yaxo ya samu baffa, cikin ladabi da girmamawa ya dube shi. "Gani baffa" "Nemi guri ka xauna mudi maganar mu bata tsugunnawa bace, bude kunne xaka yi ka saurare ni da kyau" tashi yayi ya samu gefan gadon da baffa yake ya xauna, xuba masa ido yayi yana jiran jin abinda xai fito daga bakin sa "Mahmoud ina tunanin duk abinda kake aikatawa ba a hankalin ka kake ba, duk wanda ya dubeka yasan baka cikin nutsuwa kamar da, Sannan duk wani mai lissafi baxai aikata abinda kake yi ba, gaba daya ka canja salon rayuwarka, ko dai wani ne a gefe yake koya maka sa'ka da mugun xare? To Idan ta haka ne na yanke shawara ni da malam Abdullahi, xa a yi saukar kur'ani a yi sadaka Allah ya yaye maka abinda yake damunka, sannan xai rika kawo maka maganin karya sihiri xaka rika sha kullum, idan ma wani ne yayi maka wannan sharrin Allah xai mayar masa da abinsa kansa, saura kuma kace baxa ka sha ba nasan taurin kan ku na yayan xamani" mahmud bai ji dadin abinda Baffa ya fada masa ba, saboda innah karime ta fada masa kada ya karbi maganin komai daga hannun kowa,saboda kada a Cutar da shi, anga Allah yayi masa arxiki sharewa kawai ya yi ya amsawa baffa da to, amma yayi alkawarin ko an bashi maganin baxai rika sha ba xubarwa xai yi. Satin Baffa guda a asibiti aka sallame shi, A ranar da aka sallame shi yayi waya da malam Abdullahi inda suka tattauna a akan xai rika kawo wa mahmud magani kullum yana sha, sannan kuma, xai sa a fara saukar kur'ani, A ranar Baffa yasa rigima dole a mayar da shi Dan batta saboda idan ya xauna a gidan Mahmoud yana ganin abinda su Habi ke yi hankalin sa ne xai rika tashi ,suna cin arxikin dansa amma suna wulakanta shi, duk rashin Lafiyar nan da yayi babu Wacce tayi tunanin xuwa ta gaishe shi, ko magaji basu tura ba, amma Abban nauwar ko bacin ransa bai nuna a kan haka ba, saboda baya ganin laifin su kuma baya son abinda xai bata musu rai, duk nacin da Abban nauwar ya yiwa baffa a kan ya xauna fafur yaki yarda, dan haka ya hakura ya dauke shi, sai garin Dan batta Bayan tafiyar su Baffa bai fi da minti goma ba, su innah karime da habi suka fito falo suna gulmar Abban nauwar da Baffa, innah karime ce ta dubi habi tana yatsina fuska "Nifa habi naso a ce uban mudi ya mutu mun huta, shegen yaro kamar bani na haife Shi ba baya kaunata baya San ganin farin cikina, nifa da a asibiti na haife Shi sai nace musanya mun shi aka yi,gaba daya Dan nan baya ta tawa, shi yasa nima ko Sannu ban masa ba da ya kwanta Cutar nan" "hmm ai kece baki San wani abu ba innah, Malam fa bakin cikin xaman mu yake a gidan nan,shi yasa kika ga ko xuwa baya yi, kuma xama Yanxu Muka fara ba wani kauye da xan koma dan banga abinda na ajiye a can ba. Suna cikin wannan hirar suka ga Hamdan tsaye a kansu, lumshe idanu yayi tare da sakin murmushin takaici, suna ganin shi suka Mike tsaye, kallon kallo Habi da innah karime ke yi,saboda basu taba tsammanin ganinshi ba, a xatonsu tafiyar da yayi baxai dawo ba. Cikin fushi gami da daka tsawa innah dube Shi. "Sannu da xuwa bakin biri, motar arfa mai saurin kashe hausawa, gayyar na iyya an iso, me kuma ya kawo ka gidan jikana, Ina xaton an maka tsakani da gidan nan tun kafin wannan shegiyar yarinyar da wannan mahaukaciyar uwar tata su bar gidan nan, yau kuma ubanka kaxo yi" Hannunsa harde da kirjinsa yake kallonta yana murmushi, masifar innah karime dariya take bashi saboda gaba daya bata San Annabi ya faku ba. "naxo ne na ja kunnen ki tsohuwar banxa Wacce tsufanta bai tsinana mata komai ba,Wacce bata tsoron Allah kuma bata tsoron abinda xata je ta tarar a kabari, duk abinda ku ka aikatawa su nauwar da khala Rehab bayan bana nan ya dawo kunnena, da kisan da kuka yi wa fu'ad, Ina nan xuwa xan dauki mataki a Kai baxan iya yafe wannan xaluncin da kuka yi ba, Sannan ina mai tabbatar muku da cewa Nauwar suna nan zasu dawo muhallinsu nan bada dadewa ba dariya ikon Allah, kuma Indai Ina da ragowar numfashi sai kun girbe abinda kuka shuka, mu xuba ni da ku" Jikin Habi gaba daya yayi sanyi,saboda tasan halin Hamdan sosai indai ya yi alqawarin yin abu sai ya aikata, karfin hali tayi ta fara magana. "me xaka yi mana dan banxa lalatacce, Wanda bai san mutuncin furfura ba, Kai a su wa, babu abinda xaka iya Wlh mun buga da Wadanda suka fika ma, basu ci riba ba ballantana kuma Kai karamin alhaki, kayi duk abinda kayi niyya, idan ka fasa baka kaunar uwarka da ubanka" Wucewa yayi ya kyale su saboda ya isar da saqon ya dade yana son isarwa Gida ya wuce a falo ya tarar da maminsa na shirin tayar da sallah, ganin shi tayi ran shi a bace don haka ta dakata, ta fara tambayar shi abinda ke faruwa, guri ya samu ya xauna ya fara fada mata abinda ya faru tsakanin sa da su innah karime, Sannan ya fada mata a lokacin xai tafi ya sanar da hukuma duk abinda suka aikata, sai kuma sun warware sharrin da suka kulla. A raxane ta dube shi "kaga Hamdan bana San shiga irin wannan rigimar Idan baka iya kama barawo ba sai ya kamaka, gara ka taya su da addu'a Allah ya kawo musu mafita, Sannan ka tafi neman su kamar yadda kayi alkawari Amma ni bana goyon bayan wannan matakin da xaka dauka" "shikenan Allah ya wuce mana gaba Mami, amma zan yi kokari xuwa gobe na wuce neman nasu, saboda lokaci yana ta kurewa " Addu'a tayi masa Sannan ta tayar da sallar, tana idarwa ta fara yiwa dan ta adduar samun nasara a kan abinda yasa gaba na alkhairi. Bayan fitar Hamdan daga gidan su nauwar, su innah karime suka cigaba da tattauna maganganun da Hamdan ya fada musu,xage-xage suka rika yi suna tsine masa albarka, innah karime har da cewa shi ma sai sun ga bayansa. A dai-dai lokacin ne magaji ya shigo dakin wajen xama ya samu, tambayar su dangane da abinda yasa suke masifa. "Wlh magaji Dan banxan yaron nan da ya kusa kashe ka, shi ne Yaxo yau ya Kare mana tanadi, Sannan yace wai mu ne Muka kashe Dan wajen Mudi, kuma Kaima yace sai yaga bayanka. A fusace magaji ya shiga daki ya xaro Adda, sai gidan su Hamdan a kofar gida ya tsaya yana ta xage-xage, yana ci musu mutunci Hamdan na jin abinda magaji ke fada ya tashi xai fita, da sauri mami ta tare shi ta hana shi fita,saboda tasan Hamdan yana da xuciya xai iya yi masa ba daidai ba, sai da ya gama xage su tas,Sannan ya shige ya tafi, xuciyar Hamdan sai faman tafasa take yi saboda bakin ciki. A haka ya Kwana ran shi a bace, washe gari da sassafe ya shirya ya kama hanyar tafiya neman su nauwar addu'a Mami tayi masa Sannan suka yi sallama ya tafi. *GARIN GOMBE* A tasha direba ya sauke su Nauwar, fitowa tayi daga tashar ta kama hanyar xuwa kasuwar garin dan ta siya kayan da suke bukata, bayan ta fito daga kasuwar ne ta rasa inda xata nufa, dan haka ta yanke shawarar samun guri a kasuwar ta xauna,saboda tana gudun kada matsalar da ta same su a baya, ta sake samun su, a wannan xaman da tayi bata fuskanci wani kalubale ba, don ko bara bata xuwa kullum tana tare da Amminta tana tarairayarta kasancewar yan kudaden da ta samu a hannun Alhaji Talle basu kare ba, kullum da safiya take fita don siyo musu abinda xasu kai bakinsu, idan da matsalar da take fuskanta bata wuce Farfadiyar da Ammi ke fama da ita ba. Yau ma kamar kullum shiryawa tayi tsaf, don nemo musu abincin safe, Ammi na kan cinyarta ta kwantar da kai tana ta sharadi bacci, A hankali tayi dabara ta sauke kan Ammi daga cinyarta, ta tashi a hankali ta nufi wajen siyo musu abinci, sauri take yi sosai gudun kada ta farka tayi wani gurin. wajen mai shayi ta tsaya inda ta siyo musu indomie da shayi, da sauri ta karaso wajen da suka sauka, amma abin mamaki sai ta tarar babu Ammi babu dalilinta sai filin wajen kawai, tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta ajiye abincin da ta siyo tayi, ta shiga neman Amminta amma shiru ba labarinta, fita tayi daga wajen ta baxama cikin unguwa tana tafe tana salati hade da kuka Allah ya bayyana mata mahaifiyarta, tambayar mutane ta shiga yi ko sun ga inda mahaifiyar tata tayi amma babu wanda ya kalleta ballanta tasa ran samun amsa, kusan duk wanda ta hadu da shi kallon mahaukaciya yake mata, sake komawa wajen da suke kwana tayi ko Allah xai sa taga ta dawo, wani mutum ta hango hannunsa rike da irin kayan da ke jikin Ammi yana tahowa inda take, saurin mikewa tayi ta tare shi tana hawaye, cikin tausayawa ya dubeta. "kin san mai wannan kayan" da sauri ta amsa masa da eh, me ya faru da Ammina. "ki kwantar da hankalin ki babu abinda ya faru, ki biyo ni dan ganin abinda ya faru da ita " bin shi tayi don tahowa da Amminta, sai da suka yi tafiya mai Nisa Sannan suka isa wajen. suna isa ta tarar da mutane a cike sun kewaye gurin suna salati, da hanxari ta karasa inda mutanen suke, tambayarta suke yi "wannan matar mahaifiyar ki ce?yana da kyau ki rika kulawa da ita,kina killaceta kin ga yanxu rijiya taxo ta fada, amma ana kokarin fito da ita, ki yi kokari ku koma gida wannan yawon baxai haifar muku da d'a mai ido ba, hankalin Nauwar yayi matukar tashi, bata san tsautsayin da ya kai Ammi bakin rijiya ba, hawaye ne suka rika sauka a kan fuskarta, tare da addu'ar Allah ya raba mahaifiyarta da wannan lalura ta tabin hankali, Saboda bacin ran da ya cika xuciyar ta gaba daya ta kasa gane komai biyu-biyu Kawai take gani. kokarin fito da Ammi mutane ke yi, amma gaba daya taki yarda a fito da ita sai abubuwa take yi, don haka suka kira fire service (kwana-kwana)don su xo su taimaka masu, ba tare da bata lokaci ba suka iso gurin idan suka fara kokarin fito da ita. Bayan sun cirota ne kuma Iskokin da ke jikinta suka bugeta inda ta rika wani irin abu kamar xata mutu, duk mutanen da ke gurin sai da suka yiwa Ammi hawaye saboda halin da take ciki, taimakawa suka yi aka mayar da ita wajen da suke kwana, addu'a wani bawan Allah ya rika yi mata har aka samu ta farfado, sannan aka dauketa xuwa asibiti don a bata magani saboda duk taji ciwo a jikinta. A Motar wani mutum aka dorata, basu minti biyar suna tafiya ba suka isa babban asibtin garin Gombe, ganin halin da Ammi ke ciki yasa aka yi saurin bata gado, allurar bacci aka yi mata, Dan tana bukatar hutu sosai. saboda buge-bugen da take yi sannan aka bata magungunan da xasu sassauta mata xafin da take ji a kanta, lokacin da mutanen xasu tafi sai da suka biya duk kudaden da aka caje su, sannan suka wuce suka tafi. Godiya mai Yawa nauwar tayi musu har Bakin kofa ta raka su Sannan ta dawo, bata taba xaton har Yanxu Akwai ragowar mutane irin Wadannan ba, masu tainakawa Dan Allah. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 5⃣6⃣ Kwanan Ammi biyu tana bacci bata farfado ba, a cikin baccin Nauwar ke dagata ta bata abinci da ruwa sannan ta mayar da ita ta kwantar, likitocin Asibitin na mamakin yadda Ammi da Nauwar ke xaune su kadai ba tare da wani nasu yaxo da niyyar duba halin da suke ciki ba, sai da suka fahimci ba su da galihu, daya daga cikin likitocin da yake duba su ne, ya kasa daurewa don haka ya shigo dakin samun Nauwar yayi ta xuba tagumi tana tunanin tare da xubar da hawaye, saboda bata san inda xata dosa ba idan Ammi ta warke, tasan likitoci baxa su taba daga mata kafa ta xaune musu a Asibiti ba kudi ba. da sallama ya shigo dakin amma bai ji an amsa masa ba, kara matsowa yayi daf da inda take, sake yin sallamar yayi amma shiru ba amsa kwankwasa tebur din da ta kwantar da kanta a kai yayi, cikin nutsuwa ta dago ta dube shi, idanunta cike da hawaye. samun guri yayi ya xauna shafa kyakkyawar fuskarsa yayi, sannan ya dubeta. da sassanyar muryar shi yake mata magana "sannu yan mata ya mai jiki" share hawayen da ke kwarara a fuskarta tayi ta amsa masa. "da sauki, sai dai har yanxu bata farka ba" cikin kulawa ya dubeta kada ki damu, tana bukatar hutu ne shi yasa, amma baccin baxai xama matsala a gareta ba" Tashi yayi xai fita, har ya kai bakin kofa ta kira shi. "Doctor yaushe xa a bamu sallama? lumshe idanu yayi, hannushi sanye cikin aljihu. "kin gaji da xama ne? gyada masa kai tayi alamar "a'a" murmushi yayi inda kyawawan hakoransa suka bayyana. "in dai kin gaji sai na sallame ku, naga kamar kin kosa ki koma gida kiga dadynki" Bata san lokacin da hawaye suka fara sauka a kan kuncinta ba, bai san cewa ita yarinya ce mara galihu ba, wadda ubanta yayi watsi da rayuwarta baya son ganinta ko jin labarinta. ganin yadda Nauwar ke xubda hawaye yasa Shi dawo wa da baya, wani abu yaji ya tsirga masa tun daga kansa har xuwa tafin kafarsa, tausayin yarinyar ya kama shi sosai rarrashinta yake yi, amma ta kasa daina kukan neman guri yayi ya xauna ya cigaba da bata hakuri. "Baiwar Allah kiyi hakuri, ban fada miki wannan maganar dan ta daga miki hankali ba, ki yafe min idan ni ne silar xubar hawayen ki" Dago manyan idanunta tayi wadanda suka cika da kwallar bakin ciki, a hankali ta daga baki ta fara masa magana "Baka bata min rai ba Doctor, kuma ba kaine kasa ni kuka ba,na tuna halin da nake ciki ne a yanxu, na auna shi da rayuwata ta baya, na tabbatar da cewa duniya ba tada tabbas xata iya juya maka baya a kowane lokaci, wannan dalilin ne yasa ni hawaye" gyara xama yayi, sannan ya fara magana. "ke kuwa wane hali kike ciki da har yake saka ki kuka idan kika tuna rayuwarki ta baya" labarin rayuwarta da Amminta ta bashi, da irin gwagwarmayar da suka yi da makiya, da halin da suke ciki a yanxu" wata ajiyar xuciya ya saki, sannan ya mayar da kallon shi gareta, cikin tausayawa yake mata magana "Gaskiya rayuwar ku cike take da darasi masu yawa, kuma wannan jarabawa ce Allah yayi muku, yaga ko xaku cinye ko baxa ku cinye ba, hakuri da juriya.da jajircewa wajen addua shi ya kamace ku, da sannu Allah xai kawo muku agaji, sannan ki dage da nemar wa mahaifiyar ki magani, kinga dai halin da take ciki a yanxu abin a tausaya mata ne, ki cire damuwa ki kai wa Allah kukan ki, duk wani wanda ya xalunce ki da sannu xai ga sakamako Allah yana nan baya bacci" Nauwar taji dadin Nasihar da Doctor yayi mata, kasancewar Doctor mutum ne mai ilimin addini da girmama jama'a, ba shida raina dan Adam ko yaya yake, wannan dalilin yasa duk wadanda suke xuwa asibitin suke kaunarsa, kuma suke masa adduar fatan alkhairi. godiya tayi masa, sannan ya mike. sake duban ta yayi "ki rike abinda na fada miki da sannu xaki fita daga matsalar da kike ciki, sannan ina so ki rike mutuncin kan ki, kada ki yarda saboda damuwa da bakin ciki ki jefa kanki a wata rayuwa mara kyau" kudi ya dakko ya bata. har kasa ta tsugunnah ta karba tana masa godiya. "ki rike wannan idan kuna bukatar wani abin sai ki min magana Insha Allah baxai gagara ba" godiya tayi masa sannan suka yi sallama ya fita. A kullum sai Doctor yaxo ya duba Ammi, ya kawo alkhairi mai yawa ya basu, sai dai har yanxu bata san sunan shi ba kuma ta kasa tambayar sa, kasancewar duk mutanen gurin kowa da Doctor yake kiran shi, wasu kuma su kira shi da ustax, saboda kamewar sa da tausayin da yake nunawa na kasa da shi. sai da Ammi tayi sati daya tana karbar magani sannan aka basu sallama, tun lokacin da likitan da xai sallame su ya shigo dakin ya basu takardar Sallama Nauwar ke kuka,saboda bata san ina xata nufa ba, bata san ya xata yi da rayuwarta ba, diban kayan ta tayi, sannan ta rike hannun Ammi suka fito daga dakin, bakin gate suka tsaya tana jiran Allah ya kawo abin hawa ta hau ta tafi ko ma ina ne, dan ita ta gaji da wannan rayuwar. horn taji ana mata don haka tayi saurin waiwayawa, Doctor ne a cikin motar, sanye yake cikin farin yadi wanda aka yi masa aiki fari, idanunsa sanye da farin glass yayi kyau sosai, murmushi ya sakar wa Nauwar wanda har sai da fararen hakoransa masu matukar kyau suka bayyana, rike da hannun Ammi ta karasa wajen sa, tsugunna masa tayi xata gaishe shi, nuni yayi mata da kyakkyawan hannunsa ta mike. "ina xuwa na ganki da kaya ko har an sake ku" cikin ladabi ta amsa masa. "eh tun daxu aka sallame mu" lumshe idanun shi yayi sannan ya dube ta. "ku shigo na rage muku hanya" bude mata kofa yayi ta shigar da kayanta, sannan ta shigar da Ammi, har ta samu guri a gidan baya xata xauna, magana yayi mata gami da bude mata gidan gaba. "shigo nan mana" budewa tayi ta xauna cikin nutsuwa, tunda ta shiga Doctor ya xuba mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta, yanayin yadda yarinyar ke gudanar da al'amuranta yana burge shi, yasan duk daga Inda ta fito ta samu cikakkiyar tarbiyya. kafin su fara tafiya ne ya dubeta. "ina ne wajen da ku ka sauka" idanunta a kasa, a takaice ta bashi amsa "cikin kasuwa" xare glass din da ke idanun sa yayi "cikin kasuwa kuma, me kike yi a kasuwa?" share hawayen daya ya fara taruwa a idonta tayi. "eh can xaka kai mu a nan ne inda muka sauka" Tausayi ne ya mamaye masa xuciyarsa,gaba daya rayuwar yarinyar ta gama katse masa hanxarin sa duk wasu burika da yaci a rayuwarsa ya ajiye su, saboda duniya ba tada tabbas,cikin tausayawa ya kalleta. "baxan iya barinki ki xauna a kasuwa ba, saboda guri ne da ya hada mutanen banxa da mutane na gari, idan kin yarda xan kai ki gidan mu ki cigaba da rayuwa, ina da kanne kamar ki da kuma wadanda suka fi ki, nasan xaki ji dadin xama a cikin su kuma xasu debe miki kewa" shiru Nauwar tayi tana tunani, ita dai xuciyar ta bata amice da wannan taimakon ba, saboda akwai mutanen da suka taimaketa a baya kuma suka yi yunkurin cutar da ita. shirun da yaji tayi ne, yasa yayi magana "kina tunani ko? hmm tunani abu ne mai kyau, amma kada kiyi tunanin da xai sa miki kokonto a ranki,nayi alkwarin baxan cutar da ke ba, idan kin amince xaki bini mu wuce yanxu mu tafi" kanta sunkuye ta bashi amsa. "na gode da taimakon da kayi min Doctor na amince mu je" cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake tukin, amma can cikin kasan xuciyarsa cike yake da fargabar yadda xai tunkari Hajiyarsa da maganar xuwan su Nauwar, saboda Hajiya mace ce da bata san mutane kuma bata san talaka ya rabeta, haka ma sauran yan uwansa mata suke, basa kaunar hada hanya da talaka, shi kadai ne a cikin su Allah ya tsame yayi masa baiwar karamci da girmama mutane. Addu'a yake yi sosai, Allah yasa kada ta watsa masa kasa a ido. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *A duk inda nake, a duk halin da na kasance baxan manta da ku ba masoyana na group din ✨TAURARIN MATA, kuna raina ina matukar alfahari da ku* *Hadiza Abubakar muhd* *Amina bashir yusuf* *maryam Tijjani Adam* *USummul* *Aunty peedy* *Subai'a S umar* *sa'adatu mhd Yusuf* *HafCweet* *Khadija Tijjani Adam* *Fresh khady* *Aysha Galadima* *masoya a sannu a Hankali duk xan rattabo sunayen ku* 5⃣7⃣ Tafiya suke cikin nutsuwa, shiru suka yi na wani dan lokaci, babu mai cewa da dan uwan sa komai, xuciyar Doctor kuwa sai dukan uku-uku take saboda tsoro da fargabar yadda xai tunkari Hajiya da maganar xuwan su Nauwar, ba su yi tafiya mai nisa ba suka iso unguwar new G.R.A da ke garin Gombe, daga jin sunan unguwar kasan unguwa ce ta masu hannu da shuni. wani katafaren gida suka nufa, wanda aka kawata gaban gidan da shuke-shuke,ko ba a fada maka ba ka san gida ne,wanda ba na kananun masu kudi ba. horn yayi da sauri mai gadi ya kara so ya bude kofar get din, saka hancin motarsa yayi ya shiga gidan, tare da yin parking a wajen da aka tanada domin ajiye motoci, juyo da kallon shi ya yi ga Nauwar yana murmushi "Alhamdulillah mun iso, da fatan dai baki gaji ba" a takaice ta amsa masa da"Eh" kokarin bude murfin motar ta fara yi xata fita, dakatar da ita yayi. cikin kasalalliyar murya yayi mata magana "ki daure ki bani hadin kai idan mun shiga cikin gida, kada ki nuna damuwa ko ki qi saki jikin ki, ki dauka kema 'ya ce kamar kowa, na tabbatar baxa ki yi da na sanin haduwa da ni ba Insha Allah" dago kyakkyawan idonta tayi ta kalle shi, ba tare da ta furta masa komai ba, saboda ba karamin faduwa gabanta ke yi ba, ganin yadda gidan su Doctor ya hadu, duk kyawun gidan su da tsaruwarsa bai kama kafar na su Doctor ba, fargaba ce ta kara xiyartar xuciyar ta, ta kosa su gama abinda xa su yi su bar gidan, kasancewar gidan shiru yake, ba a jin motsin komai sai kukan tsuntsaye, baxa ka taba xaton akwai mai rai a gidan ba. kayanta ya shiga fito mata da su, sannan ya taimaka ya fito da Ammi, bai kara cewa komai ba, nuni kawai yayi da hannunsa ta taho su shiga ciki. wata dogowar baranda suka bi, wadda kuma ita ce zata sada ka da kofar falon gidan, bude kofar falon yayi,subahanallah ta fada a zuciyarta saboda yanayin kayatuwar falon, umarni ya bata da ta zauna a kan kujera, kasa xama a kujerar tayi saboda bata san halin mutanen gidan ba, kada ta xauna a wulakanta ta, doctor na dawo wa ya ganta a kasa, bata rai yayi kadan sannan ya dubeta "me yasa xaki xauna a kasa, ba na fada miki cewa ki saki jikin ki kamar yar gida ba" hakuri ta bashi sannan ta koma kan kujerar ta xauna a tsora ce kamar wadda xa a kama. ruwa da lemo ya kawo mata da kansa ya tsiyaya mata a cup ya mika mata, sannan ya xubawa Ammi Nauwar ce ta karba ta fara bata, bayan ya kammala xuba musu ne, ya mayar da kallon shi gareta "jira ni kadan xan je na sanarwa da Hajiya maganar xuwan ku" benen da ke cikin falon ya haye, inda a nan Hajiyar sa da sauran kannensa ke rayuwa, duk da cewa yaran na da bangaren su amma sun fi son ko da yaushe suna tare da Hajiya, kasancewar Hajiya mace ce mai son yayanta, shi yasa ko da yaushe suna tare suna hira musamman idan ba makarantar boko. Da sallama ya shiga falon da Hajiya take wanda aka kawata shi da kaya na more rayuwa da jin dadi, sautin kida yaji yana tashi don haka da sauri ya karasa falon, tararwa yayi kannensa fatima da ummy suna ta faman tirkar rawa, suna ganin shi suka tashi a guje suka shige daki saboda sun san halin doctor baya son shashanci, kashe kayan kidan yayi yana musu fada, saboda ya tsani wannan halayyar tasu ta jin kade-kade. fuskar shi ba annuri ya nemi guri ya xauna. gaishe da Hajiya yayi, cikin sakin fuska ta amsa "sannu da xuwa yaya babba, da yake da wannan sunan take kiran sa wannan dalilin yasa duk yaran unguwar su, da yaran family din su suke kiran shi da yaya babba cikin nutsuwa ya dubeta. Ina su feenah da zainab suka shiga ne naga ban gansu ba. "na aike su gidan gwaggo ne su duba min jikinta" Dabi'ar doctor ce ya saba indai ya dawo bai ga daya daga cikin yan uwansa ba sai ya tambaya, kasancewar mahaifin su ya rasu shi ne yake musu tarbiyya a matsayinsa na babban yayan su, saboda Hajiya bata iya tsawatar musu, duk abinda suka yi daidai ne a wajenta. Tashi tayi ta miko masa flask din abinci, a sanyaye ya dubeta "bar abincin nan Hajiya da wata magana naxo miki, idan mun gama mun warware xan fi jin dadin cin abincin" farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, duk a tunaninta da maganar auren sa yaxo mata, saboda ta dade tana fama da shi a kan ya fito da matar aure amma yaki, duk yarinya da aka kawo masa ya aura sai yace bata yi masa ba, sai hakura aka yi aka kyale shi. cikin kulawa ta sake duban shi. "kai nake saurare fa, amma kayi shiru" shafa fuskar shi yayi gami da sauke wata ajiyar xuciya. "dama wasu bayin Allah na gani a cikin wani hali na rashin dadi, wanda duk wani mai imani idan yaji tarihin rayuwar su sai ya tausaya musu, wannan dalilin yasa naga cewa kamata a ce mun taimaka musu, mun fitar da su daga halin da suke ciki, saboda mu ma bamu san ta inda Allah xai taimake mu ba. A asibitin mu aka kwantar da mahaifiyarta bayan an sallame su kuma ba su da inda xasu je, shi ne na kawo su gidan nan dan nasan baxa su rasa wajen kwana ba" wata matsiyaciyar harara Hajiya ta watsa masa. "sannu uban iyayi sarkin tausayi, daga ganin mutane ka yayo min su,ka kawo su gidana, kasan sharrin da ke tattare da su, yanxu a xamanin nan mutum ba abin yarda ba, me yasa xaka yi min wannan gangancin da rayuwa, to wlh tun wuri ka kwashe su ka fitar min daga gida, dan baxa ka kawo min masifa har daki ba" "ki fahimce ni Hajiya baxan kawo abinda xai cutar da ku ba, saboda duk abinda ya same ku ni ya samu, ki taimaka ki dubi halin da suke ciki, ki tashi mu je ki gansu nasan kema xaki tausaya musu" tashi suka yi suka fita falo dan ganin irin mutanen da ya kawo musu, suna fita su fatima da ummy suka bi bayan su,dan ganewa idon su ba'kin da aka kawo musu har gida. Tun daga nesa Hajiya ta hango su Nauwar, tsayawa tayi taki karasawa wajen su. sunan doctor ta kira "Abdallah" sai a lokacin Nauwar taji sunan shi "ka rasa wanda xaka kawo mana gida sai mahaukata, idan taimakon ne me yasa baxa ka basu abinda ya kamata ba sai ka kawo mana su gida, to wlh baxai yiwu ba sai sun fita daga gidan nan,dan ni tsoron su ma nake ji baxan iya karasawa inda suke ba, kada naje su shake ni" fatima ce ta taya Hajiya fadan da take yi. "ni wlh idan har xasu xauna a gidan nan na daina kwana, sai sun tafi xan dawo, haka kawai muka sani ko mayu ne" wani kallo doctor Abdallah ya watsa mata, nan da nan ta kama hanya ta bar falon, saboda tasan halinsa baya son raini. rarrashin Hajiya ya shiga yi ta taimaka ta bari a bawa su Nauwar wajen kwana da kyar ta yarda, inda tace a basu wani daki da yake kusa da na mai gadi, kuma da sharadin sai an caje su an kwace kayan su, saboda kada su xo mata da abin cutarwa. Cikin tsawa tayi wa su Nauwar magana "bayin Allah sai a tasar min daga kan kujera kada a taho min da annobar kwarkwata" jikin su a sanyaye suka mike, kofar fita daga falon suka nufa, xasu fita ran doctor a bace ya dubi Hajiya "Gaskiya abinda kika yi bai kamata ba, saboda Allah ya girmama dan Adam, mu ma ba wayon mu ko dabarar mu ce tasa Allah ya axurta mu ba" ficewa yayi ya bi su Nauwar. kuka Nauwar take yi sosai, saboda maganganun Hajiya ba karamin taba mata xuciya suka yi ba, hanyar fita daga gidan suka kama, dan ta kudurce a ranta ko xasu mutu saboda rashin gurin kwana baxa su xauna a gidan nan ba. da sauri doctor Abdallah yasha gabanta, "ina kuma xaki je" cikin kuka ta bashi amsa "xan fita daga gidan nan ne, dan xuciyata baxa ta iya jure wulkanci ba" cikin tausayawa ya dubeta "kiyi hakuri ni kaina da na san abinda xa a yi muku kenan da baxan kawo ku ba, ki sa a ranki wannan duk yana cikin jarrabawar da Allah yayi muku, kiyi hakuri ki daina xubar da hawayen ki, Allah yana sane da ke" rarrashinta ya shiga yi, har sai da yaga ta dawo cikin nutsuwarta sannan ya nuna mata dakin da xasu shiga. Fafur Nauwar taki shiga dakin tace sai ta tafi, da kyar ya shawo kanta ta shiga suka xauna. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* *Dole na gode muku na kuma yaba da yadda kuke matukar kaunata, har ku ke kirana a waya dan jin lafiyata BINTA MUSA SALIS & UMMU SULAIMAN (Hasanatullah) ina matukar Allah ya bar xumunci* *ku ma ban mance da ku ba yan uwa masoya kuma members na Al-majirah fans, ina matukar jin dadin comments din ku, kuma ina godia sosai* Aisha Aliyu ummu Hanash juwaira lukman Amin ummu sulaiman ummy idris Dr fateemah sabitu feenah el sadeeq Saadatu Ibrahim zainab Abba sani (zainabi) nanah firdausi Princess Bilkisu Muhammad Zangi marfu'a (amfu) Abida sumy jamila bature sumayya Ango Abdullahi Haleema Ibrahim sakinat Jibrin Zahra'u Ado Bilkisu muhammad 😊Meenert maman ahmad Maman twins Badariyya Mu'az Harfsart Maman sahal Ummu Khalifa Maman jidda Aysha s/fada(baby Hassan) Maman Sudees Surry Pinky 💞 Leemerh Mamcy 5⃣8⃣ shigar su dakin ke da wuya, doctor ya shigo hannun shi rike da leda, kayan sawa ya kawo mata, da kuma kayan abinci, da sabulun wanka hade da kayan shafe-shafe, daga tsaye ya mika mata sannan ya fice saboda yana tsoron kada Hajiya ta gan shi tayi masa tijara, bude kayan ta shiga yi tana fito da su, farin ciki ne ya kamata, saboda rabon da taga irin wannan abin arxikin har ta manta,a jiye kayan tayi a gefe sannan ta dauki sabulu. jawo kofar dakin tayi ta fito, dan tana jin tsoron ta barta a bude Ammi ta fito a ganta a waje su ci mata mutunci. mai gadi ta samu yana alwala a gefen dakin shi, tambayar shi tayi inda bandaki yake sannan ta roke shi ya bata aron bokitin wanka, nuni yayi mata da hannunshi sannan ya fada mata akwai bokiti a bandakin, cikin nutsuwa ta karasa tana daf da shiga ciki ne, taji tafiyar mutum a bayanta, waiwaya tayi don ganin wanda ya biyo ta a baya, ummy ta gani daya daga cikin kannen doctor tana watsa mata wata muguwar harara, tsayawa tayi ta karewa Nauwar kallon sama da kasa sannan ta fara mata magana. "me xaki shiga kiyi a toilet din mu? daga xuwan ki har xaki fara cika mana shadda" kan Nauwar na sunkuye saboda takaicin da ya cika xuciyarta ta maida mata da amsa, wanka xan yi. xaro da manyan idanunta tayi gami da rike baki, kin xo xaki yi wanka ki goge kaushi, wato ki makalewa dan uwana ko, to wlh baki isa ba yaya babba ya fi karfin ki, kuma baki isa ki shiga wajen nan ba duk masifar ki. kwace bokitin ruwan tayi gami da jifa da shi gefe guda, ta bar Nauwar tsaye a nan tana tunani. karasa wa wajen mai gadi tayi tana masa masifa "daga yau sai yau, kada ka sake barin wadannan mahaukatan su shigar mana toilet sai sun shafa mana cutar hauka ko kuma sun kawo mana annobar ciwon sanyi, duk da bandakin ka ne, ban amince ka bar su suna shiga ba" cikin ladabi da kaskantar da kai ya bata amsa. "Insha Allah xan kiyaye Hajiya." A dai-dai lokacin su feenah da zainab suka yi sallama, suna ganin Nauwar a tsaye suka ci burki suka tsaya, cikin mamaki ta dubi ummy. "wannan kwashen kuma daga ina?" ya mutsa fuska tayi sannan ta basu amsa "yaya babba xaku tambaya don shi ne ya jajibo mana bala'i har cikin gida" cikin masifa feenah ke magana tare da watsawa Nauwar wata shu'umar harara "wai shi yayan nan me yasa yake mana haka ne, sai ya rika taro mana mutane a gida har da gayyar mahaukata, gidan nan fa ba gadon shi ne shi kadai ba, mu ma muna da gado, wlh yau sai wannan yarinya ta fita daga gidan nan dan baxai yiwu mu xauna da mahaukaciya ba" ta karasa maganar tana nuna Nauwar. Ummy ce ta sake dubanta tana murmushin mugunta. " to ai ke baki san wani abu ba, ba ita kadai ce mahaukaciyar ba har da mamanta suna cikin dan akurkin nan a nan aka sauke su" bude dakin suka yi, lekawa suka sai da suka karewa Ammi kallo sannan suka kulle shi. tabdi lallai mun yi sake a gidan nan da har ake mana kwashe-kwashe, kuma wai har shopping yayi mata, saboda tsabar taya bera barna. shiga suka yi dakin suka kwashe duk kayan da doctor ya siyowa Nauwar. wucewa suka yi suka shiga wajen Hajiya, samun ta suka yi tana shirin fita unguwa, yadda ta gansu sun taho gaba daya sai da suka fadar mata da gaba, duk a xaton ta wani abin ne ya afku, jifa zainab tayi da kayan da suka kwaso daga wajen Nauwar bin su tayj da kallo mai cike da mamaki, kafin tace komai har suna sun fara kora mata jawabi. "wlh Hajiya baxa mu yarda ba sai an fitar mana da mahaukatan nan daga gida,haka kawai a kawo mana mutane bamu san asalinsu ba, bamu san yadda suke ba kawai su xaune mana a gida sam baxa bamu yarda ba, ai mu ma muna da hakki a gidan, gashi nan har shopping sai da yaje yayi mata mu bai bamu ba. lallai wannan yaron ya rika, gaba daya yanxu ya canja ya xama mai kunnen kashi, haka kawai muna xaune kalau ya jawo mana jaraba, tuntuni nace a fitar da mutanen nan amma ya kafe saboda baya jin magana,wai shi uban tausayi, nifa yarinyar nan kallon karuwa nake mata,kada taxo har gida ta lalata min yaro, dama da ya bi ta tawa da baxa ma kuxo ku tarar da su a gidan ba, saboda ni yarinyar gaba daya bata kwanta min ba" suna cikin wannan maganar doctor Abdallah ya yi sallama, suna ganin shi suka koma gefe gaba daya suka bi bango saboda kwarjinin sa. cikin bacin rai yake musu magana. Gaskiya Hajiya abinda ku ke yi ke da yaran nan gaba daya bai dace ba, yara basa so a ci arxikin su, Hajiya ki tuna fa yaran nan mata ne baki san irin mijin da xasu aura ba, kuma baki san yadda Allah xai yi dasu ba nan gaba, amma ki xauna kisa su gaba kina koya musu saka da mugun xare,Gaskiya hakan bai kamata ba, ku kuma wlh indai ku ka cigaba da musgunawa yarinyar nan ni da ku ne" Hawa kan Abdallah tayi da masifa dan haka ya fice ya kyaleta. yana fita suka cigaba da tattaunawar da suke yi, feenah ce ta cigaba da magana "wlh Hajiya dole mu takurawa matar nan har sai ta gaji ta kwashe kayanta, ki kyale shi kada ki sake yi masa magana, da kanta xata sulale ta gudu ba tare da ma ya sani ba. kwashewa suka yj da dariya "ai kuwa kin kawo haske feenah haka xa a yi musu duk wankin gidan nan su xasu rika yi, washing machine ya huta, su xasu rika aiki kamar jakuna, hatta inner wears su xasu rika wankewa sun ji dadin wannan shawarar da Hajiya ta bayar, sbd sun yi tanadin kala-kalar axabar da xasu ganawa Nauwar da mahaifiyarta. *Yawan comments yawan typing ehe* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 5⃣9⃣ Tunda suka bar Nauwar a tsaye bayan sun gama yi mata wannan cin mutuncin bata ko motsa daga inda take ba,saboda takaici da bakin cikin da ya mamaye xuciyarta, da kyar ta ja kafa ta koma daki, kifa kanta tayi a kasa,ta rusa kuka mai ban tausayi, turo kofar dakin aka yi tare da sallama, doctor ne ya shigo fuskar shi ba walwala, yana jin xafin wulakancin da ake yi wa Nauwar, tsugunnawa yayi yana fuskantar ta, sai faman kuka take yi bata ma san ya shigo ba. kamshin turaren sa ne ya daki hancinta saurin dago da kanta tayi, ido hudu suka yi da shi, wani kyakkyawan murmushi ya sakar mata. cikin karfin hali ta mayar masa da martani samun guri yayi ya xauna yana fuskantar ta, cikin sassanyar murya tare da kulawa ya fara mata magana. "kiyi hakuri da irin matsalolin da xaki fuskanta a gidan nan, kada ki rika saka damuwar hakan a ranki, domin kuwa halin yaran gidan nan ne raina dan Adam, tunda har kin fahimci haka bana so naga kin kara bata ranki a kan Abubuwan da xasu rika yi miki, kiyi hakuri ki daure wata rana xaki ci ribar hakurin da kika yi" cikin kuka ta dago jajayen idanunta tana masa magana "na gode da kulawar ka gare ni, amma xuciyata baxa ta iya jure cin fuskar da ake min a gidan nan ba, dan Allah ka bani dama na tafi inda xan fi samun sauki, ni wlh har na fi jin dadin rayuwar kasuwar da nake yi a kan dai rayuwar gidan nan, ga shi dai kana girmama ni, amma yan uwanka da mahaifiyarka sun hana ni jin dadi, bana so na xama silar hadaka da mahaifiyar ka, na yanke shawarar yau xan fita na bar gidan nan tun kafin wata matsalar ta afku" cikin tashin hankali ya dubeta "dan Allah ki daina tunanin barin gidan nan, indai kin ga kin fita to na nemo gidan ku da yan uwan ki ne, amma wannan dalilin baxai sa na bari ki tafi ba saboda wahala bata kisa, kuma komai na Allah yana da ka'ida" kuka ta cigaba da yi saboda shi ne kadai abinda xai sanyaya mata xuciya a yanxu, duba dakin ya shiga yi, cikin mamaki ya dubeta "in kayan da na siyo miki" share hawaye tayi sannan ta bashi amsa "an xo an kwashe" "an kwashe kuma? wanene yayi wannan aikin" tsugunnawa tayi har kasa ta fara yi masa bayani "kannenka ne suka kwasa amma dan Allah kada kaje kace xaka yi musu wani abin saboda haka, kayi hakuri ka kyale su, kada hakan ya jawo min matsala a wajen su, ni na yafe musu duk abinda suka yi min" tausayin yarinyar ne ya kama shi, cikin kulawa ya dubeta "ba komai na rabu da su,amma yanxu xan fita xan sake siyo miki duk kayan da kike bukata, kada ki sake bari su dibar miki" godiya tayi masa sannan ya fice, bayan mintuna kadan ya dawo mata da kaya masu yawa, umarni yayi mata da ta boye su gudun kada kannensa su sake kwashewa. kwanan su Nauwar uku a gidan su doctor kullum da irin bakin cikin da take fuskanta, tunda taxo gidan bata samu ta watsa ruwa a jikinta ko da sau daya ba,saboda sun hana ta shiga bandaki dan kada tayi kwalliya ta kwace musu doctor din su. yau da sassafe doctor ya fita saboda yana da aiyuka da yawa a Office, ganin baya nan ne yasa Hajiya ta taho tare da tawagar yayanta, kwankwasa kofar dakin su Nauwar tayi, a raxane ta taso ta bude musu. tsugunnawa tayi har kasa ta gaida Hajiya, wata harara ta watsa mata sannan ta fara magana. "lallai yarinya kin samu sakewa wato har lokacin bacci kike samu, to gidan nan ba na bacci bane.fitowa xaki kiyi aiki tukuru kamar sabuwar jaka, dan baxa ki xauna haka kawai kina cin arxikin mu ba, mu kuma ba ma morar ki" watsa mata kayan wanki tayi a fuska sannan ta jefeta da sabulu "dauki maxa ki xo ki fara aiki, kina gamawa shara na jiran ki, kuma ki shirya jibi xaki bar gidan nan, ko kina so,ko bakya so" ficewa tayi ta barta a tsugunnah tana naxarin irin wannan wahala da kaskancin ta tsinci kanta a ciki. watsi tayi da kayan wankin tana masifa "ba a isa nayi wannan aikin ba, dan nima 'ya ce kamar kowa kuma ina da galihu kaddara ce ta sauka a kaina, dan haka ba katuwar da xan xauna ina yi wa wanki, sai dai idan xa a kore ni a kore ni, dama abinda nafi bukata kenan, tunda rayuwar da nayi a baya bata kashe ni ba, wannan ma ba abinda xata yi min dan na koma kasuwa da kwana" mayar da kofar dakin tayi ta kulle. ta baranda zainab ta hango dakin Nauwar a kulle da gudu ta shiga daki ta fara kwalawa Hajiya kira. "fito ki ga abinda wannan mahaukaciyar tayi" cike da mamaki Hajiya da sauran yaran gidan suka leka suka ga dakin Nauwar a kulle, komawa daki suka yi, kowanne su ya dauki abin duka, cikin masifa Hajiya ke magana. "dole mu dauki mataki a kan yarinyar nan, wato har tayi sakewar da xan sakata aiki taki yi, yau sai naga mai raba ni da ita, wlh yau ko dukan nan xai xama ajalinta kowa sai ya xaneta a cikin ku" bakin kofar dakin Nauwar suka nufa, bugun tashin hankali suka rika yi, a firgice ta tashi ta bude musu, jawo wuyanta Hajiya tayi ta rika duka kamar baxa ta barta da rai ba, sannan yayanta suka dora da dukanta basu kyaleta ba har sai da suka ga ta kai kasa, tana wani irin abu kamar na masu cutar farfadiya. *yawan comments yawan typing, idan an yi comments da yawa na karasa ciko ragowar pages din* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Yan uwa ina jin dadin comments din ku, kuma hakan na kara min karfin gwiwar yin typing da yawa ina godiya sosai* 6⃣0⃣ Duk da yanayin wahala da suka jefa Nauwar a ciki hakan bai sa sun sassauta da dukanta ba, har sai da suka ga ta daina motsi, ganin abinda suka yi mata ne yasa aljanun Ammi suka tashi, nan fa ta shakewa hajiya makoshi ta rika duka ta ko'ina duk yadda yayan nan suka yi su kwaceta suka kasa saboda gaba daya bata cikin hankalinta ,sai da ta gama xane ta tsaf ta sake ta, kan su zainab ta sake yo wa da gudu suka shige daki suka bar Hajiya kwance jina-jina. suna shiga daki suka dauki waya, suka kira doctor, cikin kuka feenah ke masa magana "daga cikin masifar da ka jawo mana, ka kawo mana su har gida, daya daga cikin su ta hau Hajiya da duka, da kyar ne ma idan bata hallaka ta ba" hankalin doctor a tashe ya mata magana "me kike fada min haka feenah, yaushe al'amarin ya faru" Cikin tsiwa take masa magana. "yanxu ne idan kaxo ka ganewa idanunka ni ba ni da lokacin tsayawa na baka amsa ta halin da mahaifiyata ke ciki nake yi" xage-xage su feenah ke yi suna tsinewa doctor saboda ya kawo musu kwai tara tsinana har gida, kokarin fita suke yi wajen Hajiya amma saboda tsoron Ammi ta kasa ta tsare tana jiran fitowar su ta sauya musu halitta. shi yasa suka yi wa kansu fada suka xauna a daki, suna leken halin da ta jefa mahaifiyar su a ciki. cikin gaggawa doctor ya dakko mota, yana tuki yana kiran innalillahi wa inna ilaihi raji'un saboda babban masifa ce ta tunkare shi, wacce kuma idan bai yi da gaske ba sai ta haifar masa da bakin ciki na har abada, a waje ya yi parking saboda baxai iya jira har sai an bude masa gate ya shiga da mota ba, shigar sa gida ke da wuya ya tarar da Hajiya kwance tana numfarfashi, ga Nauwar ita ma a kwance jini na kwarara a kan fuskarta, hawaye ne ya shiga fitowa daga idanun doctor ta ko'ina, yana karasawa wajen Hajiya Ammi ta matsa daga wajen, duk da kasancewar ta mahaukaciya tasan mai kyautata masu. daga kan Hajiya yayi yana mata sannu, bude ido tayi kadan ta dube shi, da hanxari ta xabura xata gudu a tunaninta Ammi ce ta sake dawo wa xata dake ta, cikin nutsuwa tare da rarrashi yake mata magana. "sannu Hajiya, kin ga irin abinda nake fada muku ko, ga irinta nan ai, kun kama karamar yarinya kuna kokarin hallakata ba a kan hakkinta ba, ko da ku ke ganin mahaifiyar ta a matsayin mahaukaciya ita ma tasan ciwon haihuwa, kuma tana jin xafi idan an taba yarta, nasan kuma duk laifin daga wajen ku yake, da baku taba su ba hakan baxai faru ba, yanxu da kun kasheta ai ni ku ka jawo wa masifa " yana Cikin wannan maganar ne gaba daya yayan gidan suka fito suka fara xage-xage, suna cewa ya kawo musu abinda xai kashe su har gida, duk yadda suke tsoron doctor hakan bai hana su fadar duk abinda suka yi niyya ba, shiru yayi ya kyale su saboda a yau dai ba shi da bakin magana tunda aka taba mai gayya mai aiki. daga Hajiya yayi ya komar da ita gefe guda, saboda dakuwar da tayi bata iya cewa komai duk jikinta ciwo yake yi. komawa kan Nauwar yayi inda ya fara bata agajin gaggawa cikin ikon Allah ta farfado, hawaye ta shiga xubarwa shi kuwa doctor sai hakuri yake bata yana lallashinta. Cikin kuka take masa magana. "doctor na gode da taimakon da kayi min, amma wlh baxan sake kwana a gidan nan ba, da kabari da wannan gidan duk daya ne a wajena, tunda naxo bayin Allahn nan basu bar ni na huta ba, na tabbata idan na cigaba a xama wata rana sai sun kashe ni da duka" ummy ce taxo ta tsaya a kansu tana masifa. "ai ni baxan so ki bar gidan nan ba, sai mun gama axabtar da ke mun ramawa mahaifiyar mu abinda Mahaukaciyar uwarki tayi mata, wannan kadan ki ka gani daga cikin axabar da muka fara gana miki" feenah da sauran kannen doctor ne suka shiga dakin su Nauwar suka fara watso musu yan tsummokaran su, xuciyar doctor kamar ta fashe saboda bakin ciki, yasan ko yayi musu magana baxa su fasa ba, sai da suka gama watso kayan gaba daya, sannan suka kulle dakin. cike da rashin kunya suke magana. "mu ga wanda xai xo ya sake bude dakin nan ya saka wasu yan iska a ciki" Hajiya na gama hutawa daga axabar dukan da tasha a hannun Ammi, mikewa tayi ta fara xaxxagawa doctor bala'i. "baka isa na sake kwana gida daya da mahaukaciya ba, yanxu nake so ka tattara ka fitar min da su, idan kuma baxa ka iya ba, xan yi aikina da kaina" hakuri ya shiga bata, tare da nuna mata illar wulakanta bil Adama amma saboda idanun Hajiya sun rufe sai tayi watsi da maganar sa. su feenah tasa suka kinkimi Nauwar suka jefata waje tare da kayanta, ita kuma Ammi tasa doctor ya kamata ya fitar da ita, suka mayar da kofa suka kulle. godiya Nauwar ta yi wa Allah da ya raba ta da gidan bala'i. cikin tausayawa doctor ya dube ta "kiyi hakuri bisa taimakon da na baki wanda ya xamo mana matsala ni da ke, ki kaddara komai ya same ki daga Allah ne, ba a son raina xaki bar gidan ba, amma saboda an fi karfina an rinjaye ni, haka xan kyale ki ba dan ina so ba, kada ki manta da ni a rayuwar ki, duk inda nake xan kasance mai yi miki addu'a Allah ya hada ki da mutane na gari wadanda xasu kula da ke" compliment card din shi ya xaro ya mika mata. "karbi wannna ki rike dan Allah kada kiyi wasa da shi, duk lokacin da kika samu nutsuwa kika koma gida, ki kira daya daga cikin numbers dina, Insha Allah xaki same ni, wannan tafiyar baxa ta yanke alakar da ke tsakanin mu ba, fatana ki kula da kan ki, ki kare mutuncin ki a duk inda kika kasance"ya karasa maganar yana share hawaye. saboda kukan da Nauwar ke yi ta kasa cewa da doctor komai, saboda a dan xaman da tayi da doctor ya matukar shiga ranta. Bayan doctor aka daka, gaba daya suka mai da hankalin su ga wanda yayi dukan, Hajiya ce taja wuyan shi cikin xafin rai take masa magana. "bin ta xaka yi ne uban tausayi, shige mu tafi kafin na tsine maka ka bi duniya, ke kuma ki tashi ki bar nan dan idan na dawo na tarar da ke sai ranki ya baci" doctor na kuka ta ixa keyar shi har cikin gida ta mayar da kofa ta kulle. Tashi Nauwar tayi suka bar kofar gidan, suka kama hanyar tafiya kasuwa. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *masoya bansan da wane kalmomi xan gode muku ba saboda kaunar da ku ke nunawa wannan littafi, ina godia da kulawar ku gare ni, idan da hali xan kira sunan ku daya bayan daya a next post da xan yi* 6⃣1⃣ Har cikin daki ta shigar da doctor, xaunar da shi tayi gami da dukan kansa. "ko xaka yi kuka hawayenka ya kare baxan bari ka bi wannan tsintacciyar magen ba, ni fa lamarinka ma mamaki yake bani Abdallah, daga ganin yarinya baka san abinda ya rabo ta daga gida ba kawai dan ta shirya maka karya da gaskiya, kai kuma ka hau ka xauna saboda rashin lissafi, wa ya sani ma ko su suka yi wa wata asiri abin ya koma kan su, amma duk ka bi ka damu xuciyar ka har da kukan rabuwa da ita, ko dai ba haka ta bar min kai ba???" dago jajayen idanunsa yayi ya kalleta ya cigaba da share kwalla, saboda bakin cikin da ya mamaye xuciyar sa gaba daya ya kasa magana, tunanin Nauwar kawai yake yi da halin da xasu tsunduma bayan rabuwar su, ji yake kamar ya bi ta ya dawo da ita, tsoron tsinuwar Hajiya ne kawai ya hana shi tafiya. kifa kanshi yayi a kasa ya rika kuka tamkar yaron goye, a ranar gaba daya bai rintsa ba, saboda bakin ciki. Yau kusan kwanan su Nauwar biyar da tafiya, gaba daya Hajiya ta rasa kan Abdallah baya kwana a gida baya cin abinci sannan ya daina yi wa kowa magana, sai dai idan yana da abinda xai dauka ya shigo ya biya bukatar sa yana gamawa kuma xai fice,baxai sake dawo wa ba sai wata bukatar ta kawo shi, hankalin Hajiya ya tashi sosai saboda wannan sabuwar dabi'ar da doctor ya bijiro mata da shi. hankalinta a tashe tasa driver ya dauketa ya kai ta Asibitin da doctor yake aiki, tambaya tayi a nuna mata Office din da yake. da sallama ta shiga wajen, samun shi tayi ya dora kan shi bisa tebur hawaye na gangarowa daga fuskarsa, cikin tsananin nuna damuwa ta nemi guri ta xauna, cikin kulawa ta dube shi. "Abdallah wai me ke damunka ne kwana biyu, ko duk a cikin damuwar rabuwa da yarinyar da baka san asalinta bane? ya kamata kasan inda kanka yake, a kan wata shashar yarinya xaka jefa rayuwarka a garari, har ka daina walwala ka bar gida ka daina kula kowa, wato kana nuna cewa yarinyar ta fi mu daraja a idonka ko, to wlh tun wuri ka farka daga bacci mai nauyin da ya dauke ka, kafin na ci maka mutunci, dan baxan yarda da wannan shashancin a gidana ba" Hannu yasa ya share hawayen da ya cika idonsa, cikin sassanyar murya yake mata magana. "baxan taba samun kwanciyar hankali ba matukar ban san inda rayuwar yarinyar nan ta shiga ba, shikenan nan kawai dan kun ga mutum a haka sai ku munana masa xato, ku ka sani ko xaluntar su aka yi, ba su suka xalunta ba, kun yi kuskuren wulakancin da ku ka yi musu, kuma na tabbatar Allah baxai kyale ku ba, dan kaga bawa a cikin wani hali ba shi yake nuna kana da damar da xaka cutar da shi ba, saboda baka san baiwar da Allah yayi masa ba, ni a yanxu baxan iya dawo wa gidan nan ba, alhalin ina ganin dakin da bayin Allahn nan suke ciki, saboda xai rika tayar min da ciwon abinda aka yi musu ne na rashin kyautawa, kawai ku yi hakuri ku kyale ni, dan nasan nima na kusa shiga wani hali, tunda ku ka toxarta su a gaban idona" ya karasa maganar wasu sababbin hawaye suna xuba a fuskarsa. hankalin Hajiya ya tashi sosai da jin maganar doctor dan tasan indai ya furta magana haka take, baya canjawa. cikin rarrashi take masa magana. "Haba yaya babba ya xaka yanke wannan danyen hukuncin, bai kamata a matsayinka na babba ka rika haka ba, shikenan kai baxa ka koyi hakuri ba duk abinda ya faru ba, sai kace sai ka dau mataki, idan kace ka fita daga gidan nan wa ka bar mana ya kula da mu, kuma yarinyar nan nasan yanxu sun kai inda suka kai, a ina xamu nemo ta, ni da ina da halin da xan ganta, da na dawo da ita ko dan cikar farin cikin ka, kayi hakuri ka dawo gida ka kuma dawo da walwalarka kamar da" doctor yaji dadin maganar Hajiya yasan da xai kara ganin su Nauwar ya dawo da su baxa a sake yi musu irin wulakancin da aka yi musu a baya ba. cikin girmamawa ya fara yi mata magana. "ba komai Hajiya ta wuce, amma ki ja kunnen yaran nan da kyau, daga yanxu kada su sake ganin mutum su wulakanta shi, indai suna haka wata rana xasu neme ni su rasa baxa a sake ganina ba" "Ai baxa a yi haka ba yaya babba, yanxu dai yaushe xaka dawo" sosa keya yayi ya dubeta "sai gobe Hajiya" xaro idanu tayi. "Haba yaya bai kamata ka xauna a nan ba har sai gobe kayi hakuri ka dawo yau" "To shikenan xan dawo anjima" farin ciki ne ya bayyana a fuskarta. "yauwa ko kai fa, Allah yayi maka albarka" amsa mata yayi da "Ameen" tashi tayi ta nufi gida, tana xuwa ta fadawa su feenah yadda suka yi da doctor, sannan tayi musu fada sosai, abinci mai rai da lafiya tasa suka dafa masa saboda farin cikin dawowar sa. A bangaren su Nauwar kuma, tunda suka bar gidan su doctor suke tafiya ba dare ba rana, ba karamin galabaita suka yi ba, saboda tsananin yunwar da suke ji, ga gajiya duk inda suka tsaya ba a barinsu su xauna saboda tsoron su da ake ji, gaba daya sun fita daga kalar su ta mutane saboda dauda, ga bakin cikin da ya cika xuciyar Nauwar tun tana kuka har ta hakura ta jure saboda babu maganin da kukan xai mata. duk tsawon lokacin nan da suke tafiya basa samun abinda xasu kai bakin su, saboda babu kudi a hannun su,sai dai nauwar tayi bara idan mutane sun ga Allah su bata, wasu kuma xaginta xasu yi su koreta. suna cikin tafiyar ne suka iso cikin gari, inda suka iske wata makarantar Almajirai, samun guri suka yi suka tsaya gudun kada su xauna a tashe su, tun lokacin da malamin Almajiran nan wanda Ake kira da malam Haruna yaga Ammi ya tsura mata ido ya kasa dauke kallonsa daga gareta, amma bai ce dasu komai ba, har xuwa lokacin da aka tashi daga makarantar aka sallami Almajiran don su je su nemo abinci. Har aka tada sallar magariba su nauwar na wajen, sai da malam ya gama addu'a tsaf sannan yaxo ya same su, sallama yayi musu. cikin damuwa Nauwar ta amsa masa sallamar, cikin kulawa yake tambayar su. "lafiya na ga kun xauna a nan, tun muna makaranta na gan ku nayi xaton xaku tafi ne amma gashi naga har yanxu ba ku da niyyar tafiya" kwalla ce ta cika idanun nauwar ta dube shi. "ba mu da gurin kwana kuma muna cikin damuwa shi yasa muka xauna a nan" tausayin su ne ya kama shi, kallon Ammi yayi ya girgixa kai sannan ya dubi Nauwar. "wannan wace ce?" "mahaifiyata ce" ta amsa masa kanta a sunkuye ajiyar xuciya ya sauke, sannan ya cigaba da magana. "akwai al'amura masu girma a tattare da wannan baiwar Allah, sannan tana tare da bakaken Aljanu kafirai, kafin na cigaba da yi miki bayani xan tambaye ki, wai kuwa yanxu tana sallah"? gyada masa kai tayi sannan ta cigaba da magana "bata sallah yanxu kuma da ba haka take yi ba" cikin tausayawa ya sake dubanta. "An yi mata asiri ne saboda a cimma wata manufa, kuma an hanata sallah ne saboda kada ma ta samu kusanci da Allah ya bata lafiya, riko hannuta ki tashi ku shiga gidana akwai taimakon da xan baku" Tashi suka yi, suka shiga cikin gidan Malam Haruna. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 6⃣2⃣ A soro Ammi ta da'kire ita a lallai baxa ta shiga cikin gidan ba, Addu'a malam Haruna ya shiga tofawa Ammi nan da nan, ta fara fita daga hayyacinta, wani hayaki ne ya rika fitowa daga bakinta tana fesawa malam, tana kawo masa duka, bai kakkauta da yi mata addu'a ba har sai da ta daina fitar da hayakin, ta koma yin wani ihu mai ban tsoro, duka ta shiga kawo wa malam, da kyar aka samu ciwon nata ya lafa, daukan Ammi suka yi suka karasa cikin gidan. Da sallama suka shiga,tarar da matar malam Haruna suka yi tana ta faman tankade, tana ganin su ta mike tana musu barka da xuwa, daki ta shiga ta dakko musu tabarma ta baxa musu a tsakar gida, taimakawa tayi a ka sauke Ammi aka kwantar da ita, ruwa ta kawo musu, sannan ta koma ta cigaba da aikinta. gaisheta Nauwar tayi sannan malam haruna ya fara mata bayani. "baki ne na kawo miki, xasu xauna tare da mu xuwa wani lokaci, xa a yi wa wannan baiwar Allahn magani idan an dace shikenan, amma tabbas tana tare da bakaken shaidanu" fuskarta a sake ta bashi amsa. "shikenan malam Allah ya taya ni rike su Amana, ita kuma Allah ya bata lafiya" amsa mata yayi da "Ameen" Tashi yayi ya fita, Nauwar ce ta taso ta karbi aikin ta fara taya matar malam suna yi suna hira, kamar sun dade da haduwa. bayan sun kammala suka dora girki, suna gama girkin ne aka xubawa Nauwar taci ta koshi. gidan malam Haruna gida ne karami, dauke yake da dakuna guda biyu, ciki da rumfa sai kuma falle daya, a falle dayan aka sauki su Nauwar aka saka musu katifa. shekarar malam Haruna ashirin da aure tare da matarsa Hajara amma Allah bai bashi haihuwa ba. A wannan ranar da su Nauwar suka sauka a gidan malam, gaba daya basu yi bacci ba, saboda tashin da aljanun Ammi suka rika yi cikin dare, kokarin fita ta rika yi xata bar gidan tana ihu tana komai sai da kyar aka samu kanta. washe gari ma abinda ta rika yi kenan, wannan dalilin yasa malam ya kira Almajiransa aka saka Ammi a gaba ana mata karatu, ihu ta rika yi har sai da ta fita hayyacinta sosai, saboda an tabo mata manya manyan kwankwaman kanta. rukiyya aka fara mata da kyar aljanun suka fara magana. cikin sarkewar murya ta fara bayani. "turo mu aka yi mu rusa mata rayuwa, kuma sai mun aikata abinda aka umarce mu saboda an ba mu abinda muke so, kullum sai an bamu jini mun sha dan haka mu da ita sai dai mutuwa ta raba mu" duk yadda malam yayi da aljanun nan a kan su fita, su bar jikin Ammi 'kememe suka ki fita, idan har suna so a fita sai an rika yi musu abinda suke so,wanda kuma hakan shirka ne, wannan dalilin yasa malam ya hakura saboda baya son ya sabawa Allah saboda magani. A daren da malam yayi magana da aljanun Ammi shi ma bai kwana lafiya ba, cikin mafarki suka xo masa suka buga masa warning cewa duk lokacin da ya kara shiga cikin maganar maganin Ammi sai sun hallaka shi, yana addu'a ya farka, kuma ya ci alwashin tsayawa tsayin daka wajen nema mata magani har xuwa lokacin da hankalinta xai dawo jikinta. ******************** Bayan komawar Baffa Dan batta kuwa, kullum sai Abban Nauwar ya kira shi ya gaida shi yayi masa ya jiki, sannan duk abinda Baffa yake bukata yana kawo masa, tun kafin ma ya tambaye shi, saboda tunda malam Abdullahi ya fara bawa mahmud maganin sihiri ya fara dawowa dai-dai, godiya Baffa yake yi wa Allah saboda ya fara dawo da dansa kan hanya. wata rana da misalin karfe takwas na safe Abban Nauwar ya dakko kayan maganin da aka bashi, xubawa yayi a kofi yayi addu'a sannan ya fara sha, sallama aka yi aka shigo dakin. innah karime ce tsaye ta bude baki, tana kallon Abban Nauwar tana salati. "Mudi me xan gani waye kuma ya baka wannan masifar kaxo kana dannawa cikin ka" hannu tasa ta dauki maganin tana jujjuyawa. "magana nake maka fa waye ya baka" tsare shi tayi da ido tana huci, shi kuma duk ya diririce kamar karamin yaro, samun guri tayi ta xauna tana kallonsa, gaba daya tunaninta ya kwance bata taba xaton Mahmud xai nemi maganin abinda suke masa ba, hankali a tashe ta sake duban shi. "wai me kake so ka xama ne Mudi, dan neman masifa ka rika shan magani, ban fada maka cewa,duk wanda ya baka magani kada ka karba ba sai kaje an shayar da kai guba, saboda Allah ya axurtaka, duk abinda na fada maka baka ji ko" cikin fushi ya dago ya kalleta. "baxan ji ba, ke uwata ce ko ubana, kin manta irin kiyayyar da kika nuna min a baya sai yanxu xaki ce kina kaunata, kina tunanin duk abinda kike yi min bana fahimta ne, to duk ina ganewa da Allah kawai na bar ku. kuma ki bani kayana da kika kwasar min dan kin san mahaifina baxai taba bani abinda xai cutar da ni ba" cike da mamaki innah ta dube shi lallai magani ya fara aiki tunda har ya iya furta mata haka ba kunya ba tsoro. hawaye ta shiga sharewa. "yanxu ni kake fadawa haka Mudi saboda ubanka ya saka ka a daki yayi maka hudubar banxa, har xaka samu bakin xagina ko, wlh tunda ka taba ni sai ka gane kuskurenka, xaka ga abinda xai same ka" "naga alheri me jiya tayi ballantana yau, kiyi duk abinda kika ga dama" ficewa tayi tana share hawaye, gaba daya bakin ciki ya cika xuciyar ta. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *ALHAMDULILLAH MASOYA NA GODE DA KAUNAR KU DA ADDU'O'INKU GARE NI, NAJE ENUGU NA DAWO LAFIYA, ALLAH YA BAR XUMUNCI* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ki, AYSHA ABUBAKAR SHAGARI (BABY) na gode da kaunar Ki gare ni Allah ya bar xumunci, da fatan kin isa sokoto LaFia* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 6⃣3⃣ Sashin su ta nufa tana kuka, Duk maganganun da Abban nauwar ya fada mata sun dagula mata lissafi, fadawa kan katifarta tayi tana kuka, a daidai wannan lokacin ne habi ta shigo dakin samunta ta yi a wannan halin, cikin nuna damuwa take tambayarta. "lafiya na ganki haka innah me ke faruwa? " Cikin karfin hali ta dago ta dubeta "Habi muna cikin masifa a gidan nan dole sai mun tashi tsaye a kan mudi, abinda muke masa ya fara cika Shi, dole ne mu koma wajen gobe da Nisa ya sake sabon lae Idan ba haka ba kuma xa a yi babu mu" Cikin mamaki habi ta dubi innah "hmm dama ai nasan xa a rina wai an saci xanin mahaukaciya tunda tsohon banxan nan Yaxo ai nasan baxa a kulla abin arxiki ba, Yanxu dabara ta rage namu mu shirya Kawai gobe mu wuce mu nemi mafita " Hirar da suka rika yi kenan har xuwa lokacin da magaji ya dawo Daga yawon sa ya tarar da su yayi suna tattaunawa, wajen xama ya samu suka fara xayyana masa yadda suka yi da Abban nauwar. "Dama ai Kune baku fahimci inda aka dosa ba Amma ni na dade da gane cewa halayyar mutumin nan ta canja,tunda wannan tsohon tsiyar Yaxo ya lalata mana xama, idan fa bamu yi da gaske ba xamu rasa wannan gidan, da dukkan abinda muke son mu mallaka a rayuwa" Cikin nutsuwa habi ta dube Shi "gaskiya ne magaji Yanxu ya Kake ganin xa a kulla wannan tafiyar? " Gyara xama yayi ya dubeta. "gobe da sassafe Ku bani kudin mota Ku kwatanta min wajen da bokan yake xan je muku, xa a sake kulla musu wani bala'in da basu isa su kauce masa ba" Farin ciki ne ya bayyana a fuskarsu Jin an ambaci xa a kulawa Abban nauwar masifa, haka suka cigaba da hirar sharrin da xasu yi suna ta Farin ciki abin su. Bayan fitar innah karime Daga dakin Abban nauwar kuwa, kur'ani ya jawo ya shiga karantawa yana addu'ar Allah ya bashi kariya Daga dukkan abinda xai same Shi. Yana kammala addu'ar wani Bakin ciki ne ya mamaye xuciyar sa, tunanin nauwar da Amminta ne ya xiyarci xuciyar sa, ji yake kamar xuciyar sa xata tsage saboda takaicin halin da ya jefa su a ciki, wayarsa ya jawo ya kira baffan shi, hawaye na kwarara a fuskarsa yake masa magana, bayan sun gaisa ne yake fada masa abinda yake damunsa, rarrashinsa ya shiga yi. 'kayi hakuri Mahmud Insha Allah suna kyakkyawan hannu babu abinda xai same su, ka Kwantar da hankalinka tunda muna addu'a Allah baxai toxarta mu ba, fatana dai ka rika hana idonka bacci kana fadawa Allah nima xan taya ka da addua " Sallama suka yi ya kashe wayar, Kwantar da kanshi yayi bisa kujera ya lumshe ido a Yanxu babu abinda yake muradin gani sama da iyalinsa, wata kaunarsu ce ta mamaye masa xuciya, ji yake Duk abinda ya faru tamkar mafarki. A daren gaba daya bai runtsa ba salloli ya rika yi yana add'ar Allah ya bayyana masa iyalinsa har xuwa wayewar gari. Bayan ya kammala shiryawa ya fito don tafiya aiki, a falo ya Samu su innah karime suna ganin shi suka xube har kasa suna gaishe Shi, ko kallonsu bai yi ba ya wuce, bayan ya Kai Bakin kofa ne ya juyo ya kalle su. Babu walwala a tare da shi yake musu magana. "Daga Yau sai yau, kada na sake fitowa na ganku xaune a falo, bana bukatar na rika ganin ku a nan, Ina so ku taimaka ku rika nesa da ni, don halin Yanxu na tsane ku" Yana kammala maganar ya fice don baya bukatar Jin amsar da xasu bashi. Ba karamin tsoro Al'amarin Abban nauwar ke basu ba Sbd gaba daya rayuwar shi ta fara canjawa ya fara dawowa hayyacinsa, gaba daya sun kasa magana sai magaji ne ya yi karfin hali ya dube su. "ba mu ga ta xama ba fa, Ku tashi mu tafi inda xai kawo mana mafita " Idanun innah karime cike da kwalla ta dubi magaji,. "ni Wlh baxan iya xuwa ko'ina ba Al'amarin yaron nan so yake ya saka ni hawan jini, Shi yasa hausawa ke cewa mai laya kiyayi mai xamani, yau naga sharrin xamani da idona" Gefen xani habi ta fara kwancewa Kudi ta xaro ta mikawa magaji "karbi wannan maxa ka tafi wajen gobe da Nisa ka xayyana masa halin da muke ciki, nima baxan iya xuwa ba dan Yanxu wani jiri ke dibana " Karbar kudin yayi, a fusace ya fita ya bar gidan Kai tsaye tasha ya nufa inda ya samu abin hawan da xai kai Shi garin Dan batta, tunanin muguntar da xai kullawa Abban nauwar Kawai yake yi har ya isa garin . Bayan tafiyar magaji Farin ciki ne ya kama su innah karime Sbd xa a yi musu aiki ba tare da sun sha wahala ba, kiran wayar magaji suka yi inda suka Kara xayyana masa muguntar da xa a Kara shiryawa. Har bayan sallar magariba suna tsimayin dawowar magaji Amma shiru ba labari, gaba dayan su tagumi suka xuba suna tunanin abinda ya hana shi dawowa a kan lokaci cikin damuwa habi ke magana. "ni kuwa Ina Dan nan ya makale, yaro tun safe ya tafi yaki dawowa kamar an aiki bawa garin su Idan ya dawo sai na bata masa rai" Ran innah a bace ta bata amsa "ai dama nasan xa a yi haka magaji baya Jin magana, Yanxu haka gidan karuwai ya wuce ya karbe mana yan kudade yayi mana wayo " "duk inda ya tafi ma xai dawo Amma sai ranshi ya baci " Suna wannan halin ne suka ji ana buga musu kofar falo cikin gaggawa suka nufi kofar suna rige-rigen budewa, Jama'a suka gani a tsaye suna duban su, cikin jimami habi ta dube su lafiya bayin Allah na ganku kamar bakwa cikin nutsuwar ku" Cikin karfin hali daya daga cikin su yake mata bayani. "mu Daga garin Dan batta muke, Akwai daya Daga cikin fasinjojin da suka hau mota Daga garin nan to shi ne ya samu hadarin mota a hanyar xuwa garin, shi ne Muka Tambaye Shi ya bamu kwatancen gidan nan, Yanxu haka muna tare da shi a mota mun xo ne mu tafi daku a kaishi Asibiti " Cikin tashin hankali su Inna suka fita Bakin kofar suna kuka suna Salati. Magaji suka tarar kwance cikin jini ko yatsansa baya matsawa a firgice suka kama hanyar xuwa Asibiti Don bashi agajin gaggawa. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba daya naki ne sarkin rigima HAFSAT ABUBAKAR SHAGARI kiyi yadda kike so da shi, na baki halak Malak kada ki bawa BABY😜* 6⃣4⃣ Isar su ke da wuya aka fara yiwa magaji gwaje-gwaje inda aka tabbatar musu da cewa kwakwalwar sa ta hadu da jini, sannan ya samu karaya a cinya da sauran sassan jikinsa, ya tabbatar musu da cewa idan ba a bashi agajin gaggawa ba xai iya rasa hankalinsa. cikin tashin hankali suka kira Abban Nauwar suka shaida masa abinda ya same su. Cikin kuka innah ta karbi wayar take masa magana. "ka taimaka mudi kaxo iftila'i ya afkawa magaji, Kansa ya hadu da jini yanxu haka Muna Asibiti muna bukatar kudi kafin ma likita ya kalle shi ya fara bashi magani" cikin rashin nuna kulawa ya mayar mata da amsa. "yanxu ina Office ki jira na tashi xan xo Insha Allah" fashewa tayi da kuka ta fara yi masa magiya. "yanxu har sai ka tashi sannan xaka xo ka same mu, baxa ka tausaya wa yaron nan ba, bai san fa inda kansa yake ba" kashe wayar yayi ya barta tana sambatu. har bayan sallar magariba babu Abban Nauwar babu dalilinsa, gaba daya ya manta da wayar da suka yi da su innah karime don shi tuni ya shige ya tafi gidan malam Abdullahi don karbar maganinsa. gajiyar da suka yi da jiransa ne yasa Habi ta tashi ta nufi gidan, bude dakuna ta shiga yi, don dibar wata kadara ta siyar ta nemarwa jikanta magani, gidan ta shiga lalubewa bata samu komai ba, don haka ta yanke shawarar balle mukullin dakin Abban Nauwar ta dauki kudi, ciki hanxari ta balle kofar ta kwaso kudade masu yawa ta nufi asibitin. Tana isa ta biya duk kudaden da ake bukata aka fara bawa magaji agajin gaggawa, Bayan ya kammala duba shi ne ya tabbatar musu da cewa ko magaji ya samu lafiya ya rasa wani bangare na hankalin sa, a ranar Kwana suka yi suna kuka Suna tsinewa Direban da yayi tukin ganganci ya illata musu da. Abban nauwar na dawowa gida ya tarar da barnar da habi tayi masa, Kai tsaye wajen mai gadi ya nufa cikin tsawa yake tambayar sa. "waye ya shigo ya bincike min daki ya kwashe min kudaden da aka bani ajiya " Cikin tashin hankali mai gadi yayi dube Shi. "Wlh babu wani Bakon fuska da ya shigo gidan nan, Kawai baba habi ce ta shigo ita ma kuma bata dade ba ta fita " Gyada kai yayi gami da tsaki Sannan ya fice daga gidan ya nufi Asibiti, tarar da su ya yi sun xuba tagumi GA kuma jakar Kudi a Hannun habi, cikin hanxari ya fixge jakar ya fara xaxxaga musu masifa. "Haba baba a wane dalilin xaki shigar min daki Ki daukar min kudin da aka bani amana abinda kika yi ya dace kenan, na farko dai ke ba gadona kike dashi ba ballantana kice xaki fara Karbar rabon Ki, daga Yau kada ki sake yi min irin wannan, saboda bani na aike Shi Yaje yawon iskanci ba mota ta buge Shi" A fusace ya shiga office din likita inda ya shaida masa irin barnar da habi tayi masa, ya kuma roke Shi ya bashi wani bangare na kudin da suka kawo masa. Ba musu ya xaro ya bashi" Bayan Abban nauwar ya tafi ne likitin Yaxo ya same su ya sanar da su yadda suka yi dashi, tsine masa suka shiga yi suna aibata Shi, daga karshe ya shaida musu cewa gobe xai sallame su kasancewar babu ragowar kudin Su a hannunsa. Ba karamin tashin hankali suka shiga ba da Jin kalaman likita Sbd ba su da kudin da xasu nemawar wa magaji magani, gashi jikinsa ya Kara rikicewa baya gane komai sai xage-xage da yake yi, a ranar hana su bacci yayi saboda xafin ciwon da ya addabe Shi. Washe gari da sassafe ya kawo musu takardar sallama,suna kuka suna rokon ya tausaya musu Amma likitan ya kekashe kasa ya kore su. Gida suka dawo kai tsaye dakin su suka shigar da magaji suka Kwantar da shi, ihu Kawai yake yana xagin su innah karime, hayaniyar da Abban nauwar Yaji ne yasa ya fito a lokacin yana daki suna tattaunawa da Hamdan dangane da batan su nauwar,tunda suka bata yake xageye duniya yana neman su Amma ba Labari, gaba daya suka fito don ganin abinda ke faruwa, dakin suka shiga inda suka tarar dashi hannunsa Rike da kansa yana kuka yana xage-xage. Su habi na ganin su suka Mike suna kuka "ka tausaya mana Alhaji ka duba halin da yaron nan yake ciki " Sbd takaici Abban nauwar kasa cewa komai yayi, sai Hamdan ne yayi musu magana. "Indai xalunci abin yi ne ku cigaba wannan kadan Ku ka gani daga cikin irin sharri da Makirci da ku ke kullawa, kun kashe kun haukatar kun tarwatsa rayuwar iyalin da suke cikin Farin ciki, ta Yaya xaku ga daidai a rayuwar Ku, wannan so mun tabi ne, baku ga komai ba sai nan gaba" Kuka su habi suke yi suna rokon a taimaka a mayar da magaji asibiti, cikin takaici Abban nauwar ya dube ta. "ba wani abu da xan iya yi masa Sbd bani na aike Shi Yaje inda abin ya same Shi ba, ko kafar nan xata rube kansa ya lalace ba ruwana, sharrin da ku ka shuka ne, Ku ka fara girbar irinsa." Yana kammala maganar suka fice suka koma daki, cigaba da tattauna maganar Nemo su nauwar suka yi, inda suka tsayar da matsaya cewa xasu sake fita nemo su gobe Sannan kafin ya tafi ya yanke shawarar korar su innah karime Daga gidan. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 6⃣5⃣ Bayan fitar Abban nauwar daga dakin su Inna karime kuwa,duk jikin su yayi sanyi ganin yadda ya canja taku gaba daya, ya daina saurarar su ya yanke duk wata alaka da su, sannan ya daina jin nauyin su duk abinda ya fito daga bakin sa baya jin kunyar fada musu, Habi ce ta katse musu shirun da suka yi. "Gaskiya sai mun canja taku innah, wannan yaron yana son jefa mu a wani hali, kin ga duk makircin da muke shiryawa kokarin warwarewa yake yi, mu koma tamkar bola a cikin gidan nan, duba kiga irin bakaken maganganun da ya fada mana Yanxu, duk rashin Lafiyar nan da yaron nan yake yi yaki tausaya masa, Wallahi wata rana tsaf xai Kore mu" Gyara xama tayi ta sake duban innah karime ta cigaba da magana. "Yanxu wata Shawara nake son mu tattauna a kanta, me xai hana mu yiwa xulai yar gidan kawuna waya ta dawo gidan nan da xama ta jawo mana hankalin sa da kwalliya da kisisina, sannan kafin taxo sai taje ta shirya jikinta da magani ta yadda yana mata kallo daya xai haukace da soyayya, Kin san xulai yarinya ce wayayyiya tasan salon janye hankalin da namiji, mu yi duk kulle-kullen da xamu yi, mu cusa ta har sai yaron nan ya mutu a kan sonta, kin ga mu kuma mun samu damar da xamu dada bajewa sosai a gidan nan babu wanda xai tsangwame mu, sbd Idan bamu yi haka ba akwai matsala Kin san dai baxai ta xama a haka aure ba. Gashi Yanxu duk abinda muke yi so yake ya tashi a banxa Amma idan Muka biyo ta wannan hanyar akwai yiwuwar mu ci nasara. ko ya kika gani?" Murmushi innah karime tayi ta bata hannu suka tafa. "gaskiya kan ki yana ja habi, kin yi babban tunani, yadda abin nan namu ya daina ci wannan ce kadai hanyar da xamu bi mu yake Shi, kin san tunda yayi wannan karatun na nasara baxai rasa bin mata ba, suna fara shakuwa xamu yi kokari a yi biki mu huta, dan naji yana shirye-shiryen tafiya nemo wannan mahaukaciyar Matar tasa, mu kuma indai muna doron kasa tayi bankawana da gidan nan sai dai su hadu a lahira " A raxane habi ta dube ta. "nemo ta yace xai yi" "kwarai kuwa, daxun nan naji yana fadawa wannan munafikin yaron da ya tsani magaji" Waya habi ta fara lalube "ai kuwa Yanxu xan kirata innah Kinsan ba a bori da Sanyin jiki" Kiran wayar xulai tayi inda ta xayyana mata duk salo da kissa da makircin da take so ta yiwa Abban nauwar, har ya ji yana sonta, bayan ta kammala fada mata ta bata umarnin ta ranto kudin mota ta taho a ranar. Bayan sun gama wayar ne xulai tayi wani tsallen Farin ciki ta fada kan gadon karfen da take, a tunaninta shekarar arxikinta ne ya kama, gidan wata yar bori ta biya inda ta bata kunshin wasu magunguna tace tayi wanka da shi, Sannan ta bata wani kwalli ta saka duk yadda xa a yi tayi kokarin yin ido biyu da shi Abban nauwar. Cikin Farin ciki xulai ta fita Daga gidan yar borin ta kama hanyar xuwa Kano. Da misalin karfe biyar na yamma ta iso gidan, habi ce ta Kai mata ruwa bandaki ta sheka wanka Sannan ta shiga dakin ammin nauwar ta dauko mata turarukan da take amfani da su, ta bata kayanta ta saka, bayan ta kammala aka umarce ta da ta fito falo ta jira yi dawowar sa, su kuma suka shige daki suna jiran Jin yadda xata kaya tsakanin xulai da Abban nauwar. Horn din motarsa suka jiyo, da sauri habi ta sake fitowa ta fesheta da turare ta Kara gyara mata daurin dan kwali Sannan ta koya mata irin tarbar da xata yi masa a lokacin da ya shigo tana kammala koya mata ta Kara shigewa daki. Da sallama ya shigo dakin tare da ambaton Allah saboda Malam Abdullahi ya jaddada masa cewa kada ya rika sake da addu'ar shiga gida da fita Daga gida, cikin kisisina gami da rangwada xulai ta karasa gare shi hannu ta kai xata rungume shi tare da Karbar abinda ke hannunsa, da hanxari ya ja da baya yana kiran Sunan Allah, ba karamin daure masa Kai abin yayi ba saboda duk a tunaninsa aljanah ce tayi shiga irin ta ammin nauwar, addu'a yake ta karantawa yana neman tsarin ubangiji. Cikin kissa ta Kara kai hannu xata taba shi, Rike Hannun yayi gami da wanke ta da mari domin a Yanxu tsoro ya bar ranshi ko aljanar ce yana Jin xai iya bugawa da ita, ihu xulai ta saki ta sake binsa a guje xata rungume shi, babban burinta bai wuce su hada ido dashi ba maganinta yayi tasiri amma bata samu wannan damar ba, sa kafa yayi ya take ta ya wuce bangaren sa kulle kofa yayi, Sannan ya samu guri ya xauna yana mayar da numfashi. Wannan Al'amarin ya daure masa Kai, Anya kuwa ba gamo yayi ba, bandaki ya shiga ya dauro alwala ya fara jera salloli bayan ya idar ya dauki al-kur'ani yana tilawa, tare da neman tsarin Allah ya Kare shi daga dukkan sharrin mai sharri. Bayan komawar Abban nauwar daki ne habi ta fito a sanyaye ta karaso inda xulai take tana faman share hawaye, masifa xulai ta fara yi Mata. "Haba Yaya dama Kin san wulakancin da xai min kenan kika sa na tunkare shi, Kin san haka yake amma baki fada min na shirya sosai ba, gaskiya baki kyauta min ba" Rarrashinta habi ta shiga yi, "Wlh nima bansan haka yake ba xulai, da a tunanin mu xai yi saurin karbar ki tunda mun ga dan takarda ne, kuma Kin san duk yan takarda suna neman mata shi yasa, amma kada ki karaya tawan gobe dole xa a sake shiri a tunkare shi" Daki suka shige suka cigaba da shirya makircin yadda xa a tunkare shi gobe. Gari na wayewa Abban nauwar ya fito falo inda ya samu su innah karime na jiyyar magaji, fuskar shi a daure ya gaishe su, cikin kulawa da nuna soyayya suka amsa masa, kafin yace komai innah karime ta fara masa bayani. "dama wata Shawara nayi da gwaggonka habi, nasan kuma Kai yaro ne mai biyayya baxa ka watsa mana kasa a ido ba" Babu alamar wasa a fuskarsa ya amsa mata da "ina Jin ki" Mayar da ajiyar xuciya ta yi sannan ta cigaba da magana.. "dama gani nayi bai kamata a natsayinka na cikakken namiji wanda Allah ya yiwa baiwar arxiki da lafiya ka rika xama ba aure ba, tunda wannan gantalalliyar matar taka ta tafi yawon iskancinta ita da wannan shegiyar yar taka baka yi aure ba, kamar wanda aka magance " Hannu yasa ya dakatar da ita.. "kinga innah Idan xaki yi magana kada ki kuskura Ki Kara aibata min iyalina Idan xaki yi maganar ki kai tsaye Kiyi, Idan baxa Ki yi ba kuma Ina da abin yi xan tashi na tafi " Hakuri ta shiga bashi tare da rarrashinsa. "Haba mudi abin ai ba na fushi bane gaskiya ce dai ta kama dole mu fada, amma a yi hakuri Allah ya huci xuciyar ka, dama yarinya mai hankali yar gayu na samo maka don naga xata dace da rayuwarka kuma kanwa ce a wajen gwaggonka da baban gwaggonka da yarinyar uwarsu daya ubansu daya" Kafin yace mata wani abu har ta kwalawa xulai kira, cikin yanga ta fito tana duban shi tana fari da ido.. Cikin mamaki ya dubeta tare da nuna ta da hannu. "wannan Shi ne xabin da kika yi min innah, wannan tsohuwar banxar ita ce ta biyo ni falo tana kokarin rungume ni, me xan yi da karuwa Mara kamun kai, duk a tunanina aljana na gani, saboda mace mai kamala da mutunci baxa ta yi abinda kika yi min jiya ba, don haka tun wuri ki tattara kayan ki Ki bar gidan nan, Idan na sake dawowa na ganki sai na lahira ya fiki Jin dadi " Bai jira amsar su ba ya fice daga gidan. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *ina matuqar nuna godiya da Farin ciki gare Ki UMMU RAHMA marubuciyar KOMAI NISAN DARE, na gode da kulawar Ki gare ni* *Wannan shafin Gaba daya sadaukarwa ne gare Ku yan group Dina na jeeddahtulkhair novels facebook ina godiya da yadda Ku ke kaunar wannan littafi* 6⃣6⃣ Tagumi suka yi gaba daya suna naxarin maganganun da Abban nauwar ya fada Musu, cikin karfin hali Habi ta dubi xulai. "kin ga mu yi wa kan mu fada tun kafin wannan jinin rashin mutuncin ya dawo ya tarar da ke ya toxarta Ki, naga alama Yanxu ya daina shakka ko tsoron kowa a gidan nan, to tun kafin hakan ta afku Ki tattaro kayan Ki Kisan inda dare yayi miki, Don naga alama baxai daga miki kafa ba" Cikin tsiwa xulai ta mayarwa da habi martani "ni fa ba inda xani Wlh ina nan sai naga abinda ya turewa buxu nadi, shikenan daga gwada abu sai mu karaya mu hakura, Ashe ma ba suna na xulai ba" ta karasa maganar tana dada turo dan kwalinta gaban goshi. Cikin tattausar murya innah karime ta fara magana. "ke yar nan ki yiwa kan Ki fada indai ba so kike yi, ki fuskanci wulakanci ba, amma idan baki ji fada ba to ki xauna duk abinda ya biyo baya ba hannun mu, don Yanxu mudi ya xama abin tsoro halinsa ba irin na da bane" Magiya suka cigaba da yiwa xulai a kan ta tafi ta bar gidan amma taki amincewa da haka saboda kwadayin abin duniya da ya rufe mata ido. Shi kuwa Abban nauwar Kai tsaye gidan su Hamdan ya wuce, tsayawa yayi a kofar gidan inda ya kira wayar shi, ba a fi minti biyu ba Hamdan ya fito, shiga cikin gidan suka yi ya kai shi har falon baban shi. .bayan sun gaisa ne Abban nauwar ya fara magana. "wato Alhaji naxo a kan maganar Nemo mai dakina ne da yarinyata, Shi ne nake so ka taimaka min da shawarar yadda xan bullowa lamarin kafin na fita nemo su" Gyara xama baban Hamdan yayi cikin sakin fuska ya dube Shi. "alhamdulillah dama na dade Ina jiran xuwan wannan ranar da Allah xai ganar da kai kuskuren da kayi ka gyara halinka, a gaskiya alhaji Mahmud kayi Babban kuskure da ka lalata rayuwar iyalinka ka rusa duk wani farin ciki na gidanka Kawai dan ka farantawa mutanen da basu damu da Cigaban rayuwarka ba, a baya naci alwashin babu ni babu alaka da kai, tunda baka jin Shawara amma tunda ka gane kuskuren ka xan taimaka maka wajen cimma wannan burin naka na alkhairi, amma nima Ina da sharadi guda daya da xan baka dole sai ka bi shi Sannan xan sa hannuna wajen nemo maka iyalinka" Cike da girmamawa ya dubi baban Hamdan "Ina saurarenka alhaji, Insha Allah wannan abin baxai gagara ba" Murmushi yayi Sannan ya cigaba da magana "Babban abinda nake bukata shi ne ka Kori Wadannan tsofaffin najadun na gidanka saboda muddin suna tare da Kai, baxa su fasa kulla sharrin da suka Saba ba, don duk abin nan da ya faru da hannunsu a ciki, don haka sai ka aiwatar da abinda na umarceka Sannan xan saka hannuna a cikin wannan Al'amarin" Kan Abban nauwar a sunkuye ya mayar masa da amsa "dama nima tunanin da nake yi kenan, kuma dama ina da niyyar korar su ba tun Yau ba, matsala daya ce xata hana na sallame su" Cike da mamaki ya tambaye shi. "wace matsala ce xata hana ka Kore su, alahalin mutanen nan ba tausaya maka suke yi ba, ba kaunarka suke yi ba, dan me xaka tsaya saurarar wata matsala da ta shafe su, Indai kana son abin nan ya yiwu sai ka bi abinda nace " Cikin ladabi ya amsa masa "Insha Allah xan yi haka alhaji na gode da kulawa Allah ya bar xumunci" "ba komai Allah yayi mana jagora ka je ka Kore su gobe sai ka dawo mu shirya abinda ya kamata " Hannu ya mika masa suka yi sallama har kofar gida Hamdan ya rako shi, bude masa murfin mota yayi Sannan ya masa magana. "wannan shawarar da baba ya baka ita ya kamata ka bi, dan ta haka ne Kawai xamu samu mu ci nasara mutanen nan ba Allah a ransu, sun xabi duniya sun watsar da lahira, dan haka wannan abin ya kamata mu fara yi sannan mu ga mai ya dace mu yi a gaba" Key ya yiwa motar Sannan ya kama hanyar tafiya gida. Tun daga bakin kofa ya jiyo ihun magaji dan haka da hanxari ya karasa cikin gidan inda ya tarar da su Inna karime suna ta kokawa da shi baxai sha magani ba, ko bi takan su bai yi ba ya wuce bangarensa. Tunda xulai ta ji motsin dawowarsa ta shiga daki ta sake sabon shiri ta nufi bangarensa, innah karime na ganin ta doshi gurin ta kwala mata kira, juyowa tayi ta kalleta. "Ki rufa mana asiri Ki dawo kada ki jaxa mana masifa, wannan mutumin da kike gani sharrinsa ya fi na bakar gobara illah, ki taimaki kanki Ki dawo kada ki jaxawa kanki matsala " Shafa fuska tayi tare da yin fari da idanu "Ki kyale ni innah ni naga xan iya, ke dai ki taya ni addu'a Allah yasa naci nasara" A bakin kofar dakin ta tsaya ta fara kwankwasawa. Yana toilet yaji bugun kofar don haka yayi saurin kammala abinda yake yi don fitowa yaga mai kwankwasa kofar. Yana budewa ya ci Karo da xulai tana wata irin kwarkwasa abin ko tsari babu, cikin karairaya ta tsugunnah har kasa ta gaida shi. Saboda mamakin da ya cika xuciyar sa kasa amsawa yayi Kawai ya tsaya yana kallonta, kokarin danna kanta tayi cikin dakin, hannu yasa ya tureta ya mayar da kafarsa ya kulle. Gabansa sai faman faduwa yake Sbd bai taba ganin masifa irin wannan ba, Yanxu ya Kara tabbatar da abinda baban Hamdan ya fada masa dole ya Kore su ko dan ya samu tabbatacen Farin ciki. Sai da ya kammala duk abinda yake yi sannan ya fito, wajen su innah karime ya shiga, ko sallama bai yi musu ba ya nemi guri ya tsaya. Innah karime ce tayi kokarin bashi gurin xama, fuskar shi ba annuri ya dube ta. "Ki Adana abin ki Sbd wata rana xai miki amfani ni ba xama ne ya kawo ni ba, xuwa dama nayi na fada muku, Ku tattara kayanku Ku bar min gida, domin kuwa Ina bukatar ganin filin gidana a gobe nake so ku fice Ku barni nasha iska" Fashewa innah karime tayi da kuka "Yanxu mu xaka toxarta Mudi duk halaccin da Muka yi maka a rayuwa, su wanene suka yi maka gata Idan ba mu ba, amma Yau rashin mutuncinka har ya Kai ka Kore mu, tsiyar dama wanda bai gaji arxiki ba kenan dan matsiyata, har kakan ka ya mutu yana fama da gurgun jaki, dan kayi haka ai ba abin mamaki bane" Kallonta Kawai yake yana murmushin mugunta da takaicin bakaken maganganun da take fada masa, ya fasa mayar mata da martani ne Kawai don tana matsayin Wacce ta haifi mahaifinsa wanda ya nuna masa soyayya tun kafin yasan kansa.. Habi ce ta dakatar da innah karime "Haba innah Wadannan kalaman basu kamace Ki na, mu da muke neman mafita ya xa a yi Ki jawo mana masifa" Tsugunnawa tayi tana duban Abban nauwar "ka taimaka mana dan arxiki irin albarka ka barmu mu karasa xaman mu, duk abinda Kake so xamu yi maka dan Allah ka tallafa mana, kaga mun Saba da xaman birni baxa mu iya cigaba da rayuwar kauye ba, GA kuma dan, dan wanka ba lafiya, ya kake so mu yi da ranmu " Saurarawa yayi ta kammala bayananta tsaf. "naji amma wannan hukuncin na Riga na gama yanke Shi Tafiya ba fashi dole a yi ta" Yana kammala maganar ya fice ya koma sashinsa, waya ya dauka ya kira baban Hamdan ya shaida masa yadda suka yi da su innah karime, yayi Farin ciki sosai da wannan hukuncin da yayi, sun cimma matsaya a kan gobe xasu kama hanyar neman su nauwar da Amminta. Bayan fitar Abban nauwar daga dakin su Inna karime kuwa, masifa habi ta shiga yiwa innah karime "Wlh wannan tsinannen Bakin naki yana son jawo mana bala'i, ya xa a yi muna cin arxikin mutum Ki xauna Kina xagin shi har da tono asalin kakanninsa, ke dai bakinki shi xai hallaka Ki idan baki yi da gaske ba" Duk fadan da habi ke mata bata tanka ba saboda ba karamin tsoron habi innah karime take yi ba, har gari ya Waye tana xaxxaga mata masifa.. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 6⃣7⃣ Gari na wayewa Abban nauwar ya gama shiryawa tsaf, fitowa yayi hannun shi rike da envelope na Kudi, dakin mai gadi ya nufa, da sallama ya leka kansa cikin dakin tarar da shi yayi yana bacci, bubbuga kofar dakin yayi tare da kiran Sunansa, a raxane ya farka yana salati, tashi yayi xaune Sannan ya tsugunnah ya gaida Abban nauwar. Cikin dakin ya shiga ya nemi guri ya xauna, bayan sun kammala gaisawa ne ya fara yi masa bayanin abinda ke tafe da shi. Mika masa envelope din da ke hannun sa ya yi "karbi wannan sallamar ka ce ta gama aiki, ka fara sana'a kafin naje na dawo" Cike da rashin gamsuwa da kalamansa ya dube shi. "me kuma ya faru yalla6ai, laifin me nayi xa a Kore ni? " Fuskar shi a sake ya bashi amsa "kada ka tayar da hankalinka Malam Ali ba korarka nayi daga aiki na, xan kulle gidan ne gaba daya saboda ina son wadannan mutanen banxar su bar min gida, ni kuma xan fita neman iyalina, na baka wannan kudin ne don ka samu abinda xaka rike kanka kafin na dawo " Farin ciki ne ya bayyana a fuskar mai gadi, Shi kansa xaluncin da ake yiwa su nauwar ya dade yana ci masa tuwo a kwarya, tsugunnawa yayi yana masa godiya. "ka kyauta sosai yalla6ai Allah ya taimake ka a kan wannan niyya taka ta alkhairi, na godewa Allah da ya ganar da kai gaskiya, wlh na dade Ina yi maka addu'a Allah ya ganar da kai, sbd cin kashin da aka yiwa bayin Allahn nan yayi Yawa, Allah ya taimaka ya yi maka jagora. " Sallama suka yi da Malam Ali, kai tsaye cikin gida ya shiga, cikin dakin su innah karime yasa kansa tarar da su yayi suna ta faman sharar bacci tsaki yaja Sannan ya juya ya fita, kiran mai gadi yayi, ya fada masa yana son ya taimaka masa. kama magaji suka yi, suka fitar da shi bakin kofar gida suka Kwantar da shi, har suka ajiye shi bai San a duniyar da yake ba, kasancewar an bashi maganin bacci don ya samu sauki daga ciwon da kansa ke yi. Dawowa dakin su Inna karime ya sake yi, tsayawa yayi ya Kare musu kallo xuciyar sa cike da bakin cikin abubuwan da suka kulla masa na tarwatsa masa iyali da suka yi, cike da takaici ya sake kare musu kallo. Cikin tsawa ya kira Sunan habi a firgice ta farka tana gyara dankwalin kanta, tashi tayi ta xauna tana murmushi ta gaida shi.. Ranshi a daure ya amsa mata, kawar da kanshi yayi gefe ya fara mata magana. "dama xuwa nayi na sanar da ku cewa lokacin tashin Ku yayi, yau nake son kulle gidana, can tafi na aiwatar da abinda xai fishshe ni, na fara rage muku aiki don nasa an fitar da magaji waje yanxu abinda ya rage shi ne ku kwashi kayanku gaba daya ku tafi" Kudi ya xaro ya mika mata "ga kudin mota nan, da yar tsarabar da xaku yiwa abokan arxikin ku,bana bukatar godiya daga gare ku" Baki habi ta saki tana jin abubuwan da yake fada mata, hawaye ta shiga sharewa. "Amma idan kayi haka ka toxarta mu mudi, yanxu baxa ka duba girman xumunci ka daga mana kafa ba" Dakatar da ita yayi "kada ki Kara cewa na toxarta ku duk abin arxikin da nake muku baku gani ba, ba fa haifata Ku ka yi ba, na baki nan da minti biyar Ku tattara kayanku Ku fita, idan na dawo na tarar da ku sai na sa6a muku" Jin maganganun Abban nauwar take yi kamar a mafarki sake murxa idanunta tayi don tabbatar da gaskiyar abinda xuciyarta ke fada mata.. "tabbas ba mafarki nake yi ba, amma wannan da anyi Mara mutunci wato ko bari mu tashi daga bacci baxai yi ba, xai sauke mana tijara ko" Tashin innah karime ta shiga yi "tashi bacci bai kama mu ba, wannan dan tijarar ya bamu lokacin fice masa daga gida" a gigice Inna karime ta tashi daga kwanciyar da tayi. "wai da gaske kike habi ko kuwa xaulayata kike yi " Harara habi ta sakar mata. "tunda dama muna wasan xaulaya sai ki xauna, idan ya sauke miki buhun rashin mutunci kya fuskanci gaskiyar abinda nake fada miki" Jajantawa juna suka shiga suna jinjina rashin kyautawar da Abban nauwar ya yi musu, suna cikin wannan hali ne suka ji ya fado dakin tare da mai gadi da wasu mutane. Umarni ya fara basu "Ku tattara Wadannan kayan Ku xuba musu a mota, Ku yi komai da sauri don bana so su Kara minti biyar a gidan nan" Cike da ladabi suka amsa masa "an gama Alhaji " Kayan su innah karime suka rika diba suna watsawa a a-kori-kura, sai da suka kammala gaba daya suka sanar da Abban nauwar sun gama, duban su innah karime yayi fuskar sa ba alamar tausayi. "an kammala xuba muku komai a mota, don haka sai Ku tashi Ku tafi kada rana tayi muku a hanya,idan kun isa lafiya ku gaida Baffa " Xaginsa suka fara yi suna tsine masa albarka. "dama hausawa sun ce balagurbin kwai baya da, kadan Muka gani daga aikin wanda bai gaji alheri ba, kuma baxa mu fita ba gida ya xama mallakin mu sai dai duk abinda xaka yi kayi". Fita yayi ya kyale su suka cigaba da xaginsa ba tare da ya tanka musu ba, kira mutanen da suka fitar musu da kaya yayi, ya umarce su da su dauki xulai su fitar da ita shi kuma xai dauki innah karime da habi ya saka su a mota, ganin wannan wulakancin da yake shirin yi musu ne yasa suka fita suna tsine masa, kulle gidan yayi ya nufi gidan su Hamdan don shirya yadda tafiyar su xata kasance. Bayan tafiyar shi da kadan habi ta dubi innah karime "Yanxu fa Shawara ta rage tamu ko mu tafi ko kuma mu San abin yi" A raunane innah karime ta dubeta "ni shawarar da na yanke mu bari ya wuce sai mu samo mai gyara ya bude mana mukullin gidan mu shige, Sannan mu nemi malami a nan kusa wanda xai rika yi mana aiki, mu kulle masa baki ta yadda ko ya dawo baxai iya korar mu ba" wni farin ciki ne ya sauka a xuciyar habi. "wlh wannan shawarar tayi sosai innah haka ya kamata mu yi, don idan Muka koma kauye maqiya xasu yi mana dariya gara mu samarwa kanmu mafita tun da wuri " Haka suka kasance a kofar gida duk wanda yaxo wucewa sai ya la'ance su saboda duk unguwar an san mugun abin da suka aikata aka kori matar gidan. Bayan Abban nauwar ya isa gidan su Hamdan sun tattauna akan tafiyar Sannan suka dauki mota don fara gabatar da abinda suka sa a gaba, Dan batta suka nufa inda suka sanar da Baffa abinda suka shirya addua yayi musu tare da saka musu albarka, sannan ya kwashe labarin abinda ya yiwa su habi ya fadawa Baffa sam Baffa bai ji haushin abinda ya faru ba sai ma albarka da ya saka masa. Sai bayan magariba Sannan su innah karime suka nemo mai gyara ya balle mukullin gidan suka shiga, suka mayar da kayan su. Tun daga wannan ranar suka fara yawon neman maganin da xa a kullewa Abban nauwar baki don kada ya Kore su, kullum akwai kalar Maganin da xa a turara, haka suka rika binne-binne a cikin gidan duk don su samu abinda suke bukata. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *masu karatu dan Allah a rika yi min uzuri idan an ga ban yi typing ba, akwai uxurin da yake rike ni, dan Allah kada a yi fushi masoya da baxarku nake rawa* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki SHARIFA NIGER, ina godiya da kulawar da kike bawa wannan littafi* *My daughter yar mutan sokoto birnin shehu, AYSHA ABUBAKAR SHAGARI Allah ya baki lafiya, Allah yasa kaffara ne* 6⃣8⃣ Tun xuwan su Nauwar gidan malam Haruna Ammi ta fara samun lafiya, don yanxu tana gane abubuwa, tasan idan tana jin yunwa tayi ishara a bata abinci, kuma idan lokacin sallah yayi aka yi mata alwala tana tashi tayi sallar ba tare da tayi gardama ba. yau da sassafe Ammi ta tashi da matsanancin ciwon ciki, gaba daya an rasa kanta, ko magana ta kasa yi, kuka kawai take yi tana nuna cikinta, a gigice malam Haruna ya shigo dakin da suke, addua ya fara yi mata, hannu ya mika ya dakko wani magani a wata jaka, xubawa yayi a cikin kwarya ya mika mata, tunda taga ya nufo wajenta da maganin ta rika xabura xata fice ta bar dakin da kyar aka kamota aka danneta aka bata, aman allurai ta rika yi da wasu kunshin layu. cikin mamaki malam ya dubeta yana mata sannu, jinjina kai yayi sannan ya shiga warware layun, abin mamaki sunan Ammi ya gani a rubuce da na Nauwar da na Abbansu, an yi wani xane-xane wanda shi kansa bai san ma'anar su ba, tunda ya fara warware layun launin jikinta ya fara sauyawa fuskarta tayi baki, idanunta suka kada suka yi ja, duka ta shiga kawo musu, wata kara ta saki mai ban tsoro, magana Aljanun jikinta suka fara yi cewa kada a warware layun a bar su yadda suke, idan aka warware xasu koma inda aka aiko su ne, ko kuma su koma kan malam Haruna, ko saurarsu bai yi ba ya cigaba da warwarewa bayan ya kammala ne ya tashi ya je ya kona su, ana konawa Ammi na kuka tana magiyar kada a cigaba, saboda an yi alkawri da su asirin baxai taba warwarewa ba. tun daga wannan lokacin da malam Haruna ya warware wannan aiki Ammi ta daina magana sai dai tayi nuni da hannu idan tana bukatar wani abin, haka ta kasance har tsawon kwana shida, a ranar da xata cika sati daya bata magana ne, malam yaga abin ya yi yawa, don haka ya fita daji don neman maganin da xai hada mata ko xa a samu kanta,cin karo yayi da wani tsoho a kan hanyarsa ta xuwa daji, sanye yake da fararen kaya kafarsa sanye take da takalmin fata wanda baxa ka iya hango ko da dan yatsansa ba, kallo daya xaka yiwa tsohon ka tabbatar da cewa ba mutum bane. hannu ya mikawa malam Haruna suka gaisa, cikin taushin murya yake masa magana. "kada kayi mamakin dukkan abinda xan fada maka, kuma duk abinda xan fada maka kada kayi min musu, ka ji ni da kunne kawai" "amsa masa yayi da Insha Allahu baxan musa maka ba" tambayar malam Haruna ya shiga yi "kana da mara lafiya a gida ko" amsa masa yayi da eh. sake dubansa yayi. "wannan mara lafiyar an yi mata asiri ne kuma asirin mutuwa da lalacewa aka yi mata, an hada ta da manyan shaidanu ne wadanda ba imani a ransu, shawara daya xan baka ku dage da neman maganin karya asiri daga kai har ita da kake mata magani, saboda a yanxu shirin su na su hallaka ku ne, don haka ga wannan" wani dutse ya mika masa daure dutsen yake da wani tsumma da kuma layu. kallonsa malam Haruna yayi. "me xan yi da wannan" murmushi yayi "kana komawa gida ka jika wannan ka bata tasha, ragowar sihirin da ke jikinta xai karasa fitowa, nima na samo wannan ne a inda mugwayen shaidanun ke adana bayanan su na sirri, kada kayi wasa da shi saboda xasu iya xuwa su sace, ina dada nanata maka kada kayi wasa da wannan layar domin ita ce babban makamin da xaku yake su a halin yanxu" yana gama fadawa malam Haruna wannan maganar ya bace, godiya malam ya yiwa Allah. amma xuciyarsa bata gama amincewa tayi amfani da abinda ya bashi ba, cikin aljihu ya saka su sannan ya shige ya shige ya tafi gida. yana komawa gida ya tarar da su Nauwar da matarsa suna kokawa da Ammi xata haura katanga ta gudu, addua ya shiga yi mata, yana fara yi mata ta fadi kasa tana wani irin ihu mai cike da ban tsoro, wani hayaki bakinta yake fitarwa warin hayakin kadai xai yi haddasawa mutum wata cutar, toshe hancinsu suka yi gaba daya don kada ya shigar musu hanci. ruwan addu'a malam ya tashi ya dakko ya rika fesa mata, har ya dakko dutsen da aljanin nan ya bashi xai jika mata, kawai ya fasa saboda ba ayar Allah bane ballantana ya ji karfin gwiwar bata tasha, don haka yayi watsi dashi ya cigaba da yi mata addua. wata murya suka ji ta bushe da wata dariya mai ban tsoron, sannan aka fara magana. "da ka bata wannan dutsen da muka aiko wannan tsohon ya baka da baxa ta taba samun lafiya ba har abada, kuma kaima rayuwarka tana cikin hadari da ka bata ta sha" wurgi yayi da dutsen gefe guda, yana godewa Allah da ya tseratar da su daga sharrin tsafin aljanu, lallai duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa. karatun kur'ani suka shiga yi mata a ranar sai da suka yi mata sauka,suna rokan Allah ya bata lafiya. wani kadangare ne ya yo kan su da gudu, أعوذ بكلمات اللّٰه تامة من شر ما خلقmalam da matarsa da Nauwar suka rika karantawa, cikin ikon Allah kadangaren ya tsaya cak ya kasa tafiya, tashi malam yayi ya dauke shi ya doka shi da kasa nan take ya fadi ya mutu. duba jikin kadangaren malam ya shiga yi, nan fa yaga abin mamaki, don kuwa sunansa ya gani da na Ammi rubuce a jikin kadangaren. *yawan comments yawan typing* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Na tabbatar da cewa yau mutane da yawa xasu ji ba dadi idan suka karanta wannan page din musamman masoya Ammi da Nauwar, ku yi hakuri haka tsarin labarin yake, fatana dai ku cigaba da kasancewa da wannan littafin, kuma kada ku manta da cewa DUKKAN TSANANI YANA TARE DA SAUKI, KUMA DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH YA ISAR MASA* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki masoyiya ta amana kuma yar uwa wadda take ji da ni take kaunata, har take da burin sanyawa diyarta sunana, SUMAYYA TAMBUWAL (Aunty sumy) Allah ya bar kauna ina godiya da kulawar ki gare ni* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 6⃣9⃣ Da sunan Allah yasa hannu ya dauke kadangaren, waje ya fita ya jefar da shi a bakin bola, sannan ya dawo gida ya cigaba da yiwa Ammi addu'a, a haka har aka samu tayi bacci. bayan sun dawo cikin nutsuwa ne suka xuba abincin dare, suka ci sannan suka ci gaba da hira, bayan sun kammala kuma suka koma daki suka kwanta don yin bacci. A daren nan gaba daya malam bai runtsa ba saboda mugwayen mafarkai da ya rika yi, ga kuma abubuwa na ban tsoro da ya rika gani a xahiri, tashi yayi ya cigaba da salloli yana addu'a Allah ya bashi nasarar abinda yasa a gaba. Asubah nayi malam ya fito don xuwa masallaci, tashin matarsa yayi sannan ya nufi dakin su Nauwar don tashinsu su yi sallah, cikin nutsuwa yake kwankwasa kofar dakin amma shiru babu motsin mutum, kiran nauwar ya shiga yi amma shiru ba amsa, bude tagar dakin yayi ya leka kansa ciki don ganewa idanunsa abinda ya hana su tashi, ja da baya yayi yana salati saboda babu su Nauwar babu dalilin su, a gigice ya shiga dakin matarsa cikin tashi hankali yake mata magana. "dan Allah kin ga inda bayin Allahn nan suka shiga, na duba dakin su ko kyallin su ban gano ba, ko kin ji motsin inda suka shiga?" a raxane ta tashi daga kwanciyar da tayi. "me nake ji haka mara dadi malam, ka duba kuwa sosai ko dai idonka ne?" Hawaye na xuba a fuskarsa ya bata amsa. "wlh na duba kuma kofar dakin su ma a kulle take da sakata, ballantana a ce wani wajen suka shiga" Da sauri suka kara rankayawa don su sake tabbatar da abinda suke tunani, cigaba da duba gidan suka yi amma sam babu dalilin su, kuka sosai malam da matarsa suke yi, suna jimamin abinda ya faru da su Nauwar, alwala malam ya daura ya tafi masallaci, wani abin da ya sake daure masa kai kofar gidan duk a kulle suke, babu alamar an bude su, bayan an idar da sallah ne malam ya bada sanarwar abinda ya faru a gidansa, jajanta masa mutane suka rika yi sannan aka yi addu'ar Allah ya bayyana su. Tunda malam ya tafi ya bar matarsa ta kasa aikata komai sai kuka da kyar ta ja jiki tayi sallah, tana idarwa ta cigaba da xubar da hawaye, gaba daya rayuwar Ammi da Nauwar tausayi take bata, saboda suna fuskantar matsaloli masu yawa, da sallama ya shigo cikin gidan, samun ta yayi tana ta kuka tsugunnawa yayi yana rarrashinta. "kiyi hakuri babu abinda ya fi karfin Allah xamu taimaki wadannan mutanen da addu'a, Insha Allah duk inda suke Allah xai basu kariya, kiyi hakuri ki daina wannan kukan, babu maganin da xai mana addu'a suka fi bukata a yanxu ba kuka ba" share hawayen tayi sannan suka dauki alkur'ani suka fara karantawa suna yiwa su Nauwar addu'ar Allah ya bayyana su. suna cikin karatun ne suka ga wata guguwa tayo kansu, dagewa suka yi sosai da karatun da suke yi, tana xuwa daf da su ta dakata, sai kuma wani hayaki da ya cigaba da tashi, wata dariya aka saki mai ban tsoro har sai da malam ya raxana. tambayarsa matarsa tayi dalilin raxanar sa saboda ita bata ganin komai shi malam shi yake ganin abinda yake gani, basar da xancen yayi ya cigaba da karatunsa. sake bushewa aka yi da dariyar sannan aka fara magana. "mun ja daga kun ja, babu yadda kuka iya dole ku hakura wannan al'amari ne da babu warkewa a cikinsa" cigaba da dariyar aka yi, cikin xafin rai malam ya mayar da martani "mun dogara ga Allah kuma mun san xai isar mana,tsafi aiki banxa ne kuma da sannu xaku ga karshen ku, don babu abinda ya fi karfin mahalicci" hayakin ne ya cigaba da tashi sannan aka cigaba da jawabi. "hahhha baxa ka kara ganinta ba ballantana har ka bata magani, mun yi nisa da ita baxa ka kara haduwa da ita ba har abada, mun dauketa ta xama mallakin mu" ana gama wannan maganar hayakin ya gushe, hawaye ne ya rika sauka a fuskar malam, idanunsa sun yi ja saboda tausayin abinda ya faru da su Nauwar. cikin kulawa matarsa ta dube shi, "malam ni fa tun daxu nake ji kana wasu maganganu wanda ban gane kansu ba, da wa kake ne" share hawaye yayi ya dubeta. "Shaidanun nan su suka sace bayin Allahn nan" "innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta ambata" ita ma hawayen ta shiga xubarwa "lallai duk wanda ya yiwa matar nan asirin da ta shiga wannan halin baxai gama da duniya lafiya ba, ya Allah ka saka mata xaluncin da suka yi mata, Allah ka bata lafiya, Allah ka cigaba da tsare bayin nan naka a duk inda suke" kuka suka rika yi, a ranar basu rintsa ba saboda tausayi, yadda suka ga dare haka suka ga rana. rokon Allah suke yi Allah ya warware musu wannan mugun kulli da makiya suka yi musu, a ranar sun sauke alkur'ani ya kai sau uku suna nemawa su Nauwar rangwami a wajen Allah. *yawan comments yawan typing* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Dan Allah a yi hakuri da jinkirin typing da nayi hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nake fama da shi* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ki yar pot FAREEDA SULAIMAN (fary nice fareeda) na baki shi kyauta ba dan halinki ba* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣0⃣ Bude idanu nauwar tayi ta gansu a cikin wani kango mai cike da ciyayi babu komai a cikin sa sai taron bola da kaxanta gami da busassun kashi, jikin bangon da ke kangon rataye yake da tsummokarai abin dai babu kyan gani, a hankali ta bude idanu tare da ambaton Allah, mamaki ne ya cika xuciyarta ji take tamkar a mafarki, laluben gedenta ta shiga yi tana sake murje idanunta don ta tabbatar da gaskiyar abinda idanunta suke gane mata, sake bude idanu tayi sosai tabbas ba mafarki take yi ba su ne dai a wannan halin, Salati ta fara yi tana kuka tana ambaton Allah wani abinda ya Kara daure mata Kai shi ne, kofar kangon a kulle take Sannan basu ji wata alama na cewa an dauke su ba.mayar da kallonta tayi ga Ammi ganinta tayi tana ta faman bacci bata ma san abinda ake yi ba, tausayin Amminta ne ya kamata ta cigaba da share hawaye, tabbas lalurar hauka ba karamar tawaya bace ga dan Adam. A hankali tasa hannu ta janye ta daga bakin bolar da take, dankwalinta ta shimfida ta Kwantar da ita, a hankali ta janye jikinta daga nata, kofar kangon ta nufa, budeta tayi Sannan ta leka kanta waje mutane ta gani suna ta xirga-xirga babu wanda ya lura da su a wajen, komawa tayi ta xauna ta fara Shawara da xuciyar ta yadda xata nemawa kansu mafita, kokari tayi ta fita sai dai rashin samun suturar da xata rufe jikinta ya hanata fita, kasancewar basu taho da komai ba sai kayan jikinsu, bata son ta dauki dankwalin da Ammi ta kwanta a kai gudun kada ta tashe ta. Dudduba kangon ta shiga yi inda ta hango wani kwali a can nesa duk ya baci da kaxanta, tashi tayi ta dakko shi ta karkade Shi tsaf, shimfidar da ammi tayi a kansa sannan ta dauki dankwalinta ta daura. Hawaye ta shiga sharewa tana neman taimakon Allah, tunanin Malam Haruna ne ya fado mata a ranta, tasan duk inda suke hankalinsu ba a kwance yake ba, suna can suna tunanin halin da suke ciki, sosai ta rika ambaton Allah tana neman taimako a gare shi tasan bai manta da su ba, sake bude kofar tayi ta fita. Rasa inda xata dosa tayi don haka ta tsaya tana karewa wajen da suke kallo, unguwa ce ta masu rufin asiri kuma da dukkan alamu mutanen unguwar basu damu da jin halin da wani yake ciki ba, don duk wanda yaxo kallonta Kawai yake ya wuce ba tare da yace mata komai ba. Ganin tsayuwar da take yi baxai amfaneta da komai ba yasa ta fara bara tana neman sadakar kaya da abinci, haka tayi barar ta gaji don ko yar kallo bata ishi mutanen unguwar ba haka ta gaji da kewaye ta koma kangon, tana bude kofar taci karo da Ammi xaune a tsakiyar bola tana cin busashshen kashi, da gudu ta karasa ta kwace ta karkade mata hannu, fuskarta tayi ta mayar da ita inda ba bola. Kuka nauwar ta shiga yi mai cike da tausayi,duk wani mai imani idan yaga halin da take ciki sai ya tausaya mata. Rungume Amminta tayi tana hawaye, tana waigawa gefenta taci Karo da wani abin mamaki kwarya ta gani cike da nono an ajiye a gefenta, addua ta shiga yi gami da karanta ayatul kursiyyu nan da nan ta nemi kwaryar ta rasa. Tsoro ne ya mamaye xuciyarta tabbas idan suka cigaba da xama a wannan kangon wata rana xasu wayi gari aljanu sun sace su gaba daya. A yi hakuri ba Yawa *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Dan Allah a yi hakuri da jinkirin typing da nayi hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nake fama da shi* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ki yar pot FAREEDA SULAIMAN (fary nice fareeda) na baki shi kyauta ba dan halinki ba* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣0⃣ Bude idanu nauwar tayi ta gansu a cikin wani kango mai cike da ciyayi babu komai a cikin sa sai taron bola da kaxanta gami da busassun kashi, jikin bangon da ke kangon rataye yake da tsummokarai abin dai babu kyan gani, a hankali ta bude idanu tare da ambaton Allah, mamaki ne ya cika xuciyarta ji take tamkar a mafarki, laluben gedenta ta shiga yi tana sake murje idanunta don ta tabbatar da gaskiyar abinda idanunta suke gane mata, sake bude idanu tayi sosai tabbas ba mafarki take yi ba su ne dai a wannan halin, Salati ta fara yi tana kuka tana ambaton Allah wani abinda ya Kara daure mata Kai shi ne, kofar kangon a kulle take Sannan basu ji wata alama na cewa an dauke su ba.mayar da kallonta tayi ga Ammi ganinta tayi tana ta faman bacci bata ma san abinda ake yi ba, tausayin Amminta ne ya kamata ta cigaba da share hawaye, tabbas lalurar hauka ba karamar tawaya bace ga dan Adam. A hankali tasa hannu ta janye ta daga bakin bolar da take, dankwalinta ta shimfida ta Kwantar da ita, a hankali ta janye jikinta daga nata, kofar kangon ta nufa, budeta tayi Sannan ta leka kanta waje mutane ta gani suna ta xirga-xirga babu wanda ya lura da su a wajen, komawa tayi ta xauna ta fara Shawara da xuciyar ta yadda xata nemawa kansu mafita, kokari tayi ta fita sai dai rashin samun suturar da xata rufe jikinta ya hanata fita, kasancewar basu taho da komai ba sai kayan jikinsu, bata son ta dauki dankwalin da Ammi ta kwanta a kai gudun kada ta tashe ta. Dudduba kangon ta shiga yi inda ta hango wani kwali a can nesa duk ya baci da kaxanta, tashi tayi ta dakko shi ta karkade Shi tsaf, shimfidar da ammi tayi a kansa sannan ta dauki dankwalinta ta daura. Hawaye ta shiga sharewa tana neman taimakon Allah, tunanin Malam Haruna ne ya fado mata a ranta, tasan duk inda suke hankalinsu ba a kwance yake ba, suna can suna tunanin halin da suke ciki, sosai ta rika ambaton Allah tana neman taimako a gare shi tasan bai manta da su ba, sake bude kofar tayi ta fita. Rasa inda xata dosa tayi don haka ta tsaya tana karewa wajen da suke kallo, unguwa ce ta masu rufin asiri kuma da dukkan alamu mutanen unguwar basu damu da jin halin da wani yake ciki ba, don duk wanda yaxo kallonta Kawai yake ya wuce ba tare da yace mata komai ba. Ganin tsayuwar da take yi baxai amfaneta da komai ba yasa ta fara bara tana neman sadakar kaya da abinci, haka tayi barar ta gaji don ko yar kallo bata ishi mutanen unguwar ba haka ta gaji da kewaye ta koma kangon, tana bude kofar taci karo da Ammi xaune a tsakiyar bola tana cin busashshen kashi, da gudu ta karasa ta kwace ta karkade mata hannu, fuskarta tayi ta mayar da ita inda ba bola. Kuka nauwar ta shiga yi mai cike da tausayi,duk wani mai imani idan yaga halin da take ciki sai ya tausaya mata. Rungume Amminta tayi tana hawaye, tana waigawa gefenta taci Karo da wani abin mamaki kwarya ta gani cike da nono an ajiye a gefenta, addua ta shiga yi gami da karanta ayatul kursiyyu nan da nan ta nemi kwaryar ta rasa. Tsoro ne ya mamaye xuciyarta tabbas idan suka cigaba da xama a wannan kangon wata rana xasu wayi gari aljanu sun sace su gaba daya. A yi hakuri ba Yawa *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣1⃣ Haka suka kasance a wannan hali a kullum akwai kalar abubuwan ban tsoro da xata ci karo da shi, ga ciwon Ammi ya dada dawowa sabo saboda rashin kulawar da take samu, sannan ga kwana a kusa da bola, a lokuta da dama har ji take ana kiran sunan ammi ana cewa ta taso su tafi sai ta tsananta addu,a sannan take daina jin muryar da take kiranta, ba karamar wuya take sha ba a halin yanxu ita kanta aljanun na mata baraxana da rayuwarta, dagewa tayi da fadawa Allah matsalarta Sannan taji saukin abubuwan. Yau ma kamar kullum dankwali ta yafa ta fita yin bara, kallo daya xaka yi mata ka gane tana cikin matsala kuma tana matukar bukatar taimako, duk kayan jikinta sun yage, takalmin kafarta ya tsinke sai kullewa tayi da Leda, ga dauda ko ta ina saboda ta dade bata ga ruwan wanka ba, duk tayi baki ta fita daga hayyacinta, kafin ta fita sai da ta daurewa ammi kafa da tsumma don gudun kada ta haura katanga ta gudu, kulle kofar kangon tayi sannan ta fita, yau dai a sa'a ta fita domin kuwa ta samo alkhairi masu yawa, mutane da dama sun tausayawa halin da suka ganta a ciki, wannan dalilin yasa suka rika bata sadaka, sai dai ta samu abincin da xai riketa kwana uku ba tare da ta fita bara ba. Haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa har tsawon sati bakwai yau da dadi gobe ba dadi, wata rana su samu abincin kaiwa bakin salati, wata rana kuwa sai su yi kwana biyu basu samu abinda zasu ci ba, haka suka xauna cikin wannan hali har xuwa lokacin da Allah yasa saimah ta kai su gidan su inda ta roki mahaifanta alfarma ya ba su daki. Lallai baxa ta manta da karamcin da iyayen saimah suka yi mata ba, su suka fitar da su daga halin kunci da takaicin da suka kasance a ciki na shekara da shekaru. Tana kammala tunanin da take yi ne, taji anyi sallama cikin dakin da suke, saimah ce da Abbanta da mamansu tare da yayyenta guda biyu suka shigo dakin, sallama suka yi, cikin nutsuwa nauwar ta amsa musu sallamar samun guri suka yi suka zauna. Cikin nutsuwa ta tsugunnah har kasa ta gaida su, tare da sakin fuska suka amsa mata da lafiya lau. Duban Ammi suka yi suka yi mata sannu, kwance take tana ta faman sharar bacci cikin kulawa Abban saima ke mata magana. "Tunda kun samu watanni a gidan nan kun huta kun dawo cikin nutsuwar ku, ya kamata musan tarihin rayuwarki da abubuwan da suka faru da ku domin mu san irin taimakon da ya kamata mu baku." Share hawaye nauwar tayi ta fara basu labarin abubuwan da ya faru da su da irin gwagwarmayar da suka yi da makiya, kuka sosai suka rika yi saboda labarin su cike yake da abubuwan takaici da bakin ciki. Cikin karfin hali Abban saima yake magana. "lallai yarinya kina cikin yanayin da ya kamata duk mai imani ya tausaya muku, kuma insha Allah muna da taimako na musamman da xamu baki, abinda xamu fara yi yanxu shi ne mu nemo nahaifinki mu sanar da shi halin da ake ciki yanxu" Mayar da kallon shi yayi gareta. "kina da number wayarsa ne mu kira mu sanar da shi inda zai same mu? Share hawayen da ya cika idonta tayi. "ba nida ita Abba, ammi ce kawai ta haddace " Cike da tausaya ya dubeta. "bana so naga kina kuka, kiyi hakuri mu bi komai a sannu insha Allah xamu same shi ba tare da mun sha wahala ba" Godiya ta yiwa Abba. "ba komai nauwar insha Allah kinxo inda xa a tausaya miki daga nan kuma Xaki hadu da abbanki" Murmushin farin ciki ta rika yi sbd dadi har da rufe fuska tana dariya, tunda suka bar gida bata taba jin dadi irin na yau ba, saboda an mata albishir din haduwa da mahaifanta. Abba yaji dadin yadda yaga nauwar na farin ciki, magana ya cigaba da yi mata "yanxu nasa a kira mai magani ya fara bata taimakon gaggawa saboda tana bukatar a kula da ita sosai idan ya kama ma sai an mayar da ita gidan maganin duk xamu amince sabd Lafiyar ta tafi mana komai a halin yanxu." Mikewa suka yi gaba daya suka bar dakin, har bakin kofa nauwar ta raka su, tana dawowa ta fadi tayi sujjadar godiya ga Allah, tabbas duk wanda ya dogara ga Allah xai shiga cikin lamarinsa ya taimake shi. Tun daga wannan lokacin rayuwar nauwar ta fara canjawa daga bakin ciki zuwa farin ciki, kullum addu'arta bata wuce Allah ya bawa amminta lafiya ba, ya kuma juyo da hankalin Abbanta kansu. Saima ce ta shigo da gudu dakin nauwar, tana murna, kwala mata kira ta shiga yi "sisina tashi naxo mana da albishir din arxiki" kwance ta tarar da ita, a raxane nauwar ta mike tana harar saima. "ni har kin bani tsoro kawata, wane abu kika kawo min haka" "Sai kin tashi daga kwanciyar da kika yi xan nuna miki idan ba haka ba kuma na koma da kayana" Da sauri ta tashi tana dubanta tana murmushi Uniform ta mika mata. "karbi gobe ki shirya akwai makaranta saura kuma kiki tashi don nasan mutuniyar tawa akwai nauyin bacci" Tsalle nauwar tayi ta rungume saima tana godiya "Alhamdulillah na gode sisina Allah ya biya Abba da aljanna babu abinda xamu iya biyansa dashi Sai dai addu,ar fatan alkhairi domin yayi mana komai " Wani hawaye taji ya taho mata da sauri saima tasa hannu ta share mata hawayen. "to uwar saurin kuka har idanun ki xai kawo ruwa ko, kinga bana so kike wannan kukan mun zama daya fa" Share hawaye tayi suka cigaba da wasa da dariya kamar yadda suka Saba. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ku kewaye na amana Masoya wannan littafi na Al-majira, Ina matukar jin dadi da yadda kuke nuna masa kulawa* Maijidda Saleh Aysha mai unguwa Saratu ma'amun Khadija umar musa Hafsat Abdullahi nasidi *ina matukar jin dadin comments din Ku ana mugun tare🤝* 7⃣2⃣ Hira suke yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, tattauna yadda tafiyar su makaranta gobe kasance suke yi, sallamar da aka yi ne ya katse musu hirar su, gaba daya suka mayar da hankali da inda aka yi sallamar, yayan saimah ne ya shigo tare da likita, a ladabce suka gaida su, fuskar su a sake suka amsa musu, har yayan saimah na tsokanar nauwar "mai idanun kuka har kin daina kukan ko har yanxu akwai sauran rigimar? " kunya ce ta kamata taja Hannun saimah suka fita, bin ta yayi da kallo yana mai tausayawa halin da rayuwar su take ciki. duba Ammi aka fara yi domin tabbatar da gaskiyar abinda ke damunta. Cike da kulawa likitan ya dubi yayan saimah. "gaskiya wannan matar sai an mata abubuwan da xata samu kamar Kwana uku tana bacci, saboda tana bukatar ta huta sosai, wannan Shi ne taimako na farko da xamu fara bata " Cikin nutsuwa yayan saimah ya bashi amsa. "Yauwa idan aka yi hakan ma daidai ne, muna so mu yi mata wannan ne kafin daga bisani mu fara mata na islamic " "yayi kyau Allah ya taimaka, Allah yasa kuma a dace" allurai ya ciro ya fara yi mata, cikin kankanin lokaci suka kammala yi mata, bude tagogin dakin suka yi, suka xuge mata labule, bayan sun fito ne suka samu nauwar da saimah sun hada kai suna hira, rankwashin kan saimah Yaya yayi. yar Kara ta saki tare da dafe kanta, cike da shagwaba take magana, "Wayyo Yaya da Xafi fa" "to iyayen gulma kun hada kai kuna sirrin na ku ko, dama fada muku xan yi, kada ku Kara shiga dakin nan ana bukatar ta samu hutu sosai, ke nauwar, dago kai tayi ta kalle shi, yau a dakin saimah xaki Kwana kin ji ko " Bai saurarI abinda xasu ce ba ya wuce suka fita tare da likita saboda yasan shagwabar saimah bata ki ta fara kuka ba. Haka suka xauna a soro har xuwa lokacin sallar magariba sannan suka shiga cikin gida don yin sallah. Washe gari da sassafe saimah ta tashi nauwar don xuwa makaranta, bayan sun kammala shiryawa ne Abba ya basu Kudin Makaranta Sannan ya basu wata takarda yace su kai wa principal, dakin mama suka shiga don yi mata sallama addu'a tayi musu sannan ta kara musu wani kudin, cike da farin ciki suka wuce suka tafi. Suna tafe a hanya suna hira, kusan duk wanda yaga saimah da nauwar sai ya tambayi a ina ta samota saboda kyawunta da yadda Allah ya tsara mata surar jikinta, wani lokacin ta bawa wasu amsa da cewa yar uwarsu ce, wasu kuma ta kyale su sai dai Kawai su bita da kallo, a haka har suka isa makaranta, Kai tsaye office din principal suka nufa,da sallama suka shiga wajen, cikin kulawa ya amsa musu, bayan sun gaida shi, takarda saimah ta mika masa, karba yayi ya bude ya fara karantawa. Xare gilas din idon shi ya yi ya dubi saimah "wannan ita ce nauwar Mahmud wadda Babanki yaxo ya yiwa registration " Kanta a sunkuye ta amsa masa da eh Kiran nauwar tayi ta xauna a kujera don yi mata interview ita kuma saimah yace ta wuce aji, Alkur'ani ya dakko ya fara budo mata surori mabanbanta duk inda ya karanta mata sai yaji ta biya ba tare da tayi ko batan wasali ba, da aka dawo bangaren ilimin boko ma haka, duk abinda aka tambayeta sai ta bashi amsa, cike da mamaki ya dubeta. "haka dama kike da kokari, ni ai da aji daya xan kai ki a tunanina baki iya komai ba, a wane gari kika yi Karatu kafin Ki dawo nan" Kanta a kasa ta bashi amsa da Kano "Lallai Kina da jajircewa, to anan ma ina so Ki jajirce Ki fi ragowar kokari da komai" Gyada masa kai tayi, kallonta Kawai yake yana tasbihi ga ubangiji saboda yadda yarinyar ta dauki hankalin sa, dadin dadawa gata da kokari da nutsuwa, litattafai ya mika mata, hannu biyu tasa ta karba sannan ya mike, tashi mu je na nuna miki ajin da xaki xauna ya fada yana mai dubanta. A ladabce yayi gaba ta bishi a baya, a bakin kofar ajin ya tsaya ya kira malamin inda ya fara yi masa bayanI. "wannan sabuwar daliba ce muka yi sunanta nauwar Mahmud tana da kokari sosai na mata interview shi yasa ma na kawota babban aji a kula da ita sosai kada a bari ta hadu da yara masu wasa " "Insha Allah xan lura da ita " shiga ajin tayi tare da malamin ashe ajin su saimah ne, tana ganin shigowar nauwar ta taso da gudu ta rungumeta tana murna. "alhamdulillah naji dadi da aka hada mu" Gaba daya idanun yan ajin suka dawo kansu, tsawa malamin ya yiwa saimah, a firgice ta juya ta dube shi "cikata Ki koma Ki xauna ko ranki ya baci" Sakinta tayi ta koma wajen xamanta, ya saka nauwar a layin farko saboda baya son ya hada ta da saima, don idan ya hada su baxa ta bari tayi Karatu ba, ana karatu Malam na kallon nauwar kamar ya hadiyeta, har sai da ta gane ta fara jin kunya. Tunda nauwar ta shigo ajin ta xo da farin jini, duk kusan yan ajin suna kaunarta kuma suna son kawance da ita saboda kokarin ta da nutsuwarta, a lokuta da dama malam shi yake hanata kawaye saboda cika umarnin amanar da ya karba a Hannun principal. A kullum saimah da nauwar tare suke xuwa Makaranta su koma tare, rayuwar nauwar ta canja gaba daya, ta saki jiki da saimah komai tare suke yi tamkar tagwaye. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Yau shafin gaba daya sadaukar wa ne gare ki MISS RAFIN DADI, kiyi yadda kike so da shi na baki halak mallake, halinki da iya mu'amlar ki yasa dole na jinjina miki, wlh ke ta daban ce kin bambanta da mutane da dama, Allah ya Kara miki daukaka yasa kifi haka, ana mugun tare🤝* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣3⃣ Nauwar ta samu kusan wata biyu tana zuwa makaranta, don yanxu tayi nisa sosai a haddarta har sun fita musabaka ta samu nasarar xuwa na daya, wannan dalilin ya kara mata farin jini a wajen malamai, kamar kullum yau ma da wuri suka kammala shirin tafiya makaranta, basu tsaya bata lokaci ba suka nufi makaranta suna xuwa suka shiga Aji, bayan sun xauna an fara Karatu ne aka aiko wani yaro kiran saimah. Cikin ladabi yayi sallama tare da gaida malam, dago kai malam yayi ya kalle shi kasancewar lokaci ne da ake karatu, tambayar shi yayi dalilin xuwan sa, tsugunnawa ya sake yi, a hankali yayi masa magana. "principal ne ya aiko ni yace yana son ganinta yanxu" Shi ma cikin rada ya mayar masa da amsa. "ka fada masa xamu karasa Karatu gata nan zuwa" Bayan an kammala malam ya dubi saimah. "Tashi kije principal na son ganin ki" Kirjinta na dukan uku-uku ta amsa masa da to, duban nauwar tayi "Allah yasa dai ba wani sharrin aka hada mana ba, tunda kika ga mutumin nan yana kirana ba lafiya" Kwantar mata da hankali nauwar ta shiga yi "kada ki damu insha Allah alkhairi ne, ke dai ki tafi kina addu,a don kinsan halin fadansa sarai, ba bakon ki bane" Cike da tsoro take tafiya tana hadawa da addu'a, cikin nutsuwa tayi sallama office din principal samun shi tayi yana rubuce-rubuce, waje ta samu ta xauna a kasa, sai da ya kammala sannan ya dago ya dubeta. "ya xaki xauna a kasa, tashi ki koma kan kujera" Tashi tayi ta xauna, kana ganinta xaka san cewa a firgice take, don dosana jiki tayi ba wani xama tayi sosai a kujerar ba. A ladabce ta gaida shi, fuskarsa a sake ya amsa mata, sake dubanta yayi yana murmushi "wasu tambayoyi nake so nayi miki ina fatan dai xaki fada min gaskiya" Kanta a kasa ta gyada kai alamar Eh, duk ta kosa ya kammala dogon jawabinsa ya fada mata abinda yasa ya kirata sbd ta tsani tsayawa tayi doguwar magana da namiji indai ba yayanta bane. Gyaran murya yayi sannan ya fara magana. "maganar dama xamu yi dangane da sabuwar yarinyar nan da aka kawo" Shiru yayi yana kallonta, muryarta a shaqe ta amsa masa da to malam, gabanta ba karamin faduwa yake yi ba, saboda bata sani ba ko wani ne ya hadawa nauwar sharri basu sani ba. Katse shirun da tayi yayi "ya naga kamar kin tsorota ki saki ranki ba komai bane ya faru, ni dai babban fatana kiyi min alkawarin xaki fada min gaskiyar Al'amari bana son karya, ko ki fada min abu ba dai-dai ba" "nayi maka alkawari malam" Cikin nutsuwa yake mata magana yadda zata fahimce shi. "Menene alkarki da nauwar" Cike da mamaki ta dago Kai saboda bata fahimci abinda yake nufi ba. "okay naga kamar tambayar ta dan yi miki nauyi ina nufin ya ku ke da ita " "yar kanwar babana ce" ta amsa masa a takaice "Masha Allah, naji tace min a kano take haka ne ko" "Eh gaskiya ne abinda ta fada maka" Biro da takarda ya dakko tsareta da ido yayi yana kallonta. Kwarjinin sa ne ya kamata don haka tayi hanxarin kawar da kanta. "shikenan naji, yanxu ina so ki bani address din gidan ku saboda ina so zan ga mahaifin ku, xamu tattauna da shi a kan lamarin karatun ku" Ajiyar zuciya tayi, sannan ta fara kwatanta masa gidan shi kuma yana rubutawa, bayan ya kammala rubutawa ne, ya umarce ta da ta koma Aji. Tana tafe tana wasu-wasi a ranta, anya ba sharri xa a je gida a hada musu ba, kafin ta isa Aji wani axababben ciwon kai ya rufeta, sauri tayi ta shiga Ajin don idan ta kara mintuna a hanya xata iya faduwa. Wajen xaman su ta nufa, cike da damuwa ta samu guri ta xauna, cikin kulawa nauwar take tambayarta "lafiya naga duk kin canja, ko dai wani abin ne ya faru da mu" Ganin hankalin duk yan ajin ya dawo kanta kowa ya kasa kunne yana jira yaji gulma, don haka ta yiwa nauwar alama da ido da ta tsaya xata fada mata, idan ido ya bar kansu. Wata hirar suka shiga yi, don su 6atar da tunanin masu kallon su, hakan ne yasa kowa ya mayar da hankali kan karatun sa, fakar ido tayi ta fara gayawa nauwar yadda suka yi da principal. A tsora ce ta dubeta, "me yasa xaki bashi address shikenan fa mun shiga uku duk motsin da muka yi yanxu xai iya xuwa gida ya fada tunda yasan gidan mu,nifa dama naga ya sa mana ido da yawa, duk motsin da muka yi a makarantar nan idon shi a kan mu,idan ni har na fara jin na tsani makarantar ma wlh, gaskiya da kin sani kince kin manta address din gidan naga yadda zai yi" Harararta saimah tayi "lallai ma yarinyar nan kuruciya na damunki, idan nace na manta ai sai yace na raina masa hankali na sake janyowa kan mu wata masifar, ni dai gara da na fada duk abinda zai faru ya faru. ai dai baxa a kashe mu ba ko?" "hmm saimah kenan ko bakin a kashe mu ba ai a saka mu bakin ciki, da asarar hawaye" Har aka tashi hirar da suke yi kenan, hankalin su a tashe suka koma gida, suna shiga soro saimah ta fara kuka, dakin mama ta shiga tarar da ita tayi ta kishingida tana hutawa, fadawa jikinta tayi tana kuka, cikin kulawa ta fara tambayar autarta abinda ya faru da ita. kukan da take yi ne ya hanata magana, don haka ta juyo ta fara tambayar nauwar, cikin nutsuwa tayi mata Bayanin abinda ya faru. Murmushi tayi "to ke Auta menene na tada hankali kiyi kuka indai kin san kina yin abinda ya kai ki makaranta wannan ai ba abin tashin hankali bane" Turo baki saimah tayi "ni dai naji tsoro wlh saboda mutumin mugun dan sa ido ne , kuma xan fadawa Abbah ko yayi sallama kada ya fita ya gan shi ya kyale shi ya gaji da tsaiwa ya tafi" Dariya sosai tasa mama "sai ki fada masa shi kuma ya daka ta taki ku rika shirme, kinga ku tashi ga abincin ku can na hada muku, ku je ku dauka kuma kuna ci ku fara Karatu " Tashi suka yi suka shiga kitchen suka dauki abincin suka fara ci. Magariba na yi aka dawo da Ammi daga gidan magani, yau ko gardama bata yi ba da xa a shigo da ita gida, wani magani aka basu aka ce a daren ake so a bata tasha. Abba na shigowa ya kira mama da sauri taxo ta rike Ammi mika mata maganin Abba yayi inda ya fada mata abinda xa a yi da shi. Da sauri ta shiga ta dakko kofi ta fara jika mata, mika mata tayi ba tare da gardama ba ta karba ta kafa kai ta shanye. Mama ce ta fara magana "Gaskiya sauki ya fara samuwa, tunda har tana karbar magani tasha da kanta, lallai ba abinda ya fi karfin Allah " "Ai insha Allah komai yazo karshe wannan ma cewa yayi tasha asirin da ya rike mata baki ya hanata magana xai warware da yardar Allah" Tana kammala shan maganin ta ajiye kofin gefe guda. Bata fi minti biyar da shan maganin ba, ta fara wani amai wanda sai da ya tsorata kowa a gidan, allurai da gashi ta shiga amayarwa, bayan ta gama kuma ta fara aman jini, A firgice yayan nauwar ya fita ya kira likita, magani ya bata sannan aka kara yi mata allurar bacci don ta huta sosai. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 Yau shafin gaba daya naku ne masoya Almajira na hakika iya wuya ana mugun tare* Rahinatu Ibrahim (maman sadiq) Hajiya Amina Maryam (maman surayya) Sharifa Niger Firdausi Biu Nanah Hauwa Hadiza Ahmad sa'adatu M shehu maman Mahmoud khadeejah sabo Abdullahi maman Yakura Maman Ahmad Amrat makeover Binta muhd nusaibat muhd maman imam Bahijjah gora Aysha Sulaiman Ahmad Shatu Yusuf Maryam elladan Khadija Yusuf unique Maryam B sadeeq Amina H alkasim Hajiya maryam Hassan maman Anwaar *Baxan iya lissafa sunayenku gaba daya ba na gode da kulawar ku Allah ya bar kauna* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣4⃣ Bayan an samu kan Ammi tayi bacci ne, shimfida Abba yasa aka yi masa, su nauwar suka kewaye shi suna hira, tashi saimah tayi tsaf daga wajen xamanta ta dawo kusa da Abba, ranta babu walwala take kallon shi, tambayarta ya shiga yi. "lafiya Autar Abbah ko Autancin ne ya tashi " ya karasa maganar yana dariya. Bata rai ta sake yi taki magana, nan da nan idanunta suka kawo ruwa ta hau murxa ido, cike da kulawa ya sake tambayarta. "Ki fada min abinda ke damunki ko kuma na kyale ki, bana son sakarci" Share hawayen tayi ta sake duban shi. "Abba dama principal din mu ne yace xai xo wajenka " "Au dan wannan abin shi ne xaki rika kuka to ki Kwantar da hankalin ki babu komai" Yana rufe baki yaro ya shigo tare da sallama, gaba daya suka mayar da kallonsu gare shi. "wai ance ana sallama da mai gidan nan" Gaban nauwar da saimah ne ya fadi, suka xaxxaro da ido tambayar yaron suka yi. "jeka kace inji wa" Fita yaron yayi ya tambaya sannan ya sake dawo wa. "wai inji Malam musa" Dafe kirji suka yi suna Salati. "shikenan kashin mu ya bushe, Abba principal ne" Kallon su Abba yayi "wai kuwa anya yaran nan kuna da gaskiya, daga ji anyi sallama da ni duk kun tada hankalin Ku, ko dai laifi ku ka yi, Kai yaro jeka kace ina xuwa, dauki shimfidar nan ka kai ka shimfida masa kaji dan albarka" Takalmansa ya dauka ya fita, hankalin su nauwar a tashe yake, saboda fargaba sun kasa ci gaba da magana sai addu'a suke yi Kawai. Abba na fita ya tarar yaron yayi shimfida amma Malam musa principal na tsaye, da sallama Abbah ya karasa wajen tare da mika masa hannu, kasa mikawa Abbah hannu yayi saboda girmamawa, cike da ladabi ya tsugunnah har kasa ya gaida shi. Cikin sakin fuska Abba ya amsa masa. "Sannu da xuwa Malam, bismillah ga guri nan xauna" Xaunawa yayi suka sake sabuwar gaisuwa. "ya kokari Malam ya dalibai " "dalibai alhamdulillah Alhaji" Gyara xama principal yayi ya dubi Abba. "Dama xuwa nayi mu gaisa sannan mu tattauna a kan daya daga cikin yaranka " Gaba daya Abba ya bashi hankalinsa sannan ya bashi amsa da. "Ina saurarenka Malam, da fatan dai ba wata fitinar suke aikatawa ba, don tunda Ku ka yi magana da su cewa xaka xo,suka kasa xaune suka kasa tsaye duk hankalin su a tashe yake saimah har da kukanta " Murmushi Malam yayi sannan ya fara bayani. "babu komai Alhaji alkhairi ne ya kawo ni, kuma ina fatan baxa a juyar da bukatata ba" Cike da kulawa Abba ya bashi amsa. "mu dama kullum alkhairin muke jira, sai dai mu yi addu'a Allah ya hada mu da shi a duk inda muke " Ba karamin dadi principal yaji ba da kalaman Abba, wannan dalilin yasa ya saki jiki sosai ya fara bayyana masa abinda ya kawo shi. Gyaran murya yayi sannan ya dan rusunar da kansa. "Dama naga iri ne a gidanka, wato daya daga cikin dalibaina wadda saimah ta shaida min cewa yar kanwarka ce ita na gani na yaba da hankalinta da irin tarbiyyar da ku ka bata, shi ne naxo tambaya idan babu wata magana mai karfi a kanta sai na fito" Shiru Abba yayi yana naxarin maganar principal, sai da ya nisa sannan ya bashi amsa "Eh tabbas babu wata magana a kanta, kuma naji dadi da kaxo gida ka same ni muka yi magana, saboda wasu malaman idan suna son yarinya baxa su nemi magabatanta ba sai dai su rika tsare yarinya a Makaranta suna soyayya da ita, daga haka idan aka samu akasi sai kaga yarinya ta lalace, gaskiya naji dadi sosai da wannan tsarin naka, amma akwai wani hanxari ba gudu ba, kamar yadda saimah ta fada maka cewa yarinyar nan yar kanwata ce haka maganar take, Mahaifinta baya kusa ya tafi kasar waje Karo Karatu, kaga baxan yanke hukunci a kan xan baka ita ba, sai naje na shawarci yarinyar da mahaifiyarta sannan a samu babanta a yi masa magana, abinda muka yanke ni kuma xan same ka na fada maka." "wannan gaskiya ne Alhaji, to Allah yayi mana jagora." Sallama suka yi sannan Abba ya kira su nauwar suka dauke shimfidar da suka xauna, tun daga waje suke tambayar Abba amma yaki basu amsa yace ba maganar su bace. dakin mama ya shiga ya sanar da ita yadda suka yi da principal, cikin farin ciki mama ta bashi amsa "wannan a ganina ai ba wani abu bane, samun yarinyar nan ya kamata kayi ka tambayeta idan xata amince da shi, kaga duk lokacin da aka samu babanta ko mahaifiyarta taji sauki sai a sanar da su abinda ya faru, amma bai kamata kayi shiru da bakinka ba" Shiru yayi na dan lokaci Sannan ya sake dubanta. "shikenan xan yi tunani xuwa gobe abinda na yanke sai na mata magana " Tashi yayi ya nufi dakinsa don yin bacci *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Yau ma dai shafin naku ne masoya Al-majira, ina matukar jin dadin yadda ku ke kaunar wannan littafi ana mugun tare* Hafsat muhd ibrahim Nana Aysha mahmud zainab Niger 7⃣5⃣ Da gudu su Nauwar suka bi bayan Abba, a hankali suke masa magana "Abbah sannu da dawowa" cikin sakin fuska ya amsa musu. "yauwa sannun ku yayan Abbah, ya kamata ku tafi ku kwanta gobe akwai xuwa makaranta idan kuma ku ka makara ba ruwana, sai malam ya xane ku ina gida ban san an yi ba" saimah na dariya take magana. "ai mu yan gatanka ne Abbah babu mai dukan mu in dai kana nan, tunda muna da kai ba mu da matsala" murmushi yayi, har sai da wushiryarsa ta bayyana. "To Allah yasa rakiya tayi tsawo tsakanina da ku, Allah kuma yayi muku albarka" amsawa suka yi da Ameen, shigewa daki yayi suka bi bayan sa, cike da mamaki ya juyo ya dube su. "ya naga kuma kun biyo ni, ku da nace ku tafi ku kwanta" "hira muka xo xa mu yi da kai Abbah mu bama jin bacci" saimah ta fada tana murmushi. sake matsawa tayi kusa da shi. "yauwa na manta ban tambayeka yadda ku ka yi da principle ba Abbah, har yanxu fa a tsora ce muke hankalin mu ya kasa kwanciya, dan Allah ka fada mana abinda yaxo yi Abbah" cike da kulawa ya bata amsa. "Ba laifi ku ka yi ba, dan haka ku daina tayar da hankalin ku" "nasan ba mu yi laifi ba Abbah amma tabbas principle baxai xo gidan nan haka kawai ba akwai dalilin da ya kawo shi, ka taimaka ka fada mana Abbah dan Allah" gyara xama yayi ya mayar da kallensa gare su. "ina so ku tattara min hankalin ku sannan duk abinda xan fada bana so naji shi a makaranta ku ja bakinku ku yi shiru, sirri ne tsakani na da ku" da sauri suka bashi amsa. "Babu mai ji Abbah xamu rike wannan sirrin" gyara murya yayi sannan ya fara fada musu. "principle din ku shi yaga ke Nauwar, ya nuna ta da hannu sannan ya cigaba da magana, yace yana son hada xuri'a da mu" A firgice ta dago. "ni kuma Abbah?" cikin kulawa ya dube ta. "eh ke yace yana so, amma ban amsa masa ba nace sai na shawarce ki abinda kika ce shi xa a yi, dan ni baxan miki dole ba, shi yasa nace ya saurare ni xan fada masa yadda muka yi" saimah ce tayi sauri ta karbi xancen "Abbah principle fa kace, tsoho ne fa yarsa ma ta girme mu Allah, tabdi ni dai gaskiya Nauwar kice bakya son shi" dakatar da ita Abbah yayi. "Ba na hanaki wannan shirmen ba saimah idan kika kara magana xan kore ki" kan Nauwar a sunkuye ta kasa bada amsa saboda mamakin yadda aka ce principle yana sonta, ashe duk kulawar da yake bata ba ta banxa bace akwai abinda yake nufi, shiru tayi tana naxarin maganganun Abbah, shi ya katse mata shirun da tayi ya cigaba da magana. "kije kiyi shawara kin ji ko, kuma kiyi addua abinda kika yanke sai ki fada min, baxan miki dole ba duk abinda kike so shi xa a yi" tashi suka yi suka fita daga dakin, suna shiga dakin su saimah ta fara masifa. "lallai ma principle din dan rainin hankali ne, duk xaurawan garin nan ya rasa wacce xai ce yana so sai ke yar karama, wlh kada ki yarda kawata" wani hawayen takaici ne ya xubo wa nauwar. "ni gaba daya maganar ma mamaki ta bani ban taba xaton wannan maganar xata fito daga bakinsa ba,dadi daya naji da Abbah bai amsa masa ba,amma da ya amsa da haka nan xan karbe shi ko bana son shi, saboda baxan iya watsawa Abba kasa a ido ba" "lallai da sauran ki yarinya yanxu da ya amsa masa sai ki karbe shi a haka ko bakya son shi, lallai ma" "to ya xan yi kawata baxan iya ketara umarnin Abbah ba" matsawa kusa da Nauwar saimah tayi. "yanxu kin san yadda xa a yi" dago idanu tayi ta kalleta, sai kin fada. "Mu daina sakar masa fuska gaba daya, daga gaisuwa shikenan" hannu ta mika mata suka tafa. "haka xa a yi kawata" bayan sun kammala hirar ne suka kwanta basu jima ba bacci yayi awon gaba da su. yau ma kamar kullum da sassafe suka kammala shirin makaranta, yau Abba ne ya kaisu da kanshi, bai bari sun hau abin hawa na haya ba, Aji suka wuce inda kowa ya dauki alkur'ani ya fara karatun haddar da xa a karba bayan axahar, tunda principle yaga xuwan su Nauwar ya fara kewaye makaranta duk don ya leka aji ya gano ta yaji sanyi a ransa. saimah na ganin xai leko ta window xata sa Nauwar ta buya a cikin hijabi duk don kada ya samu damar ganinta, ya leko ya fi sau biyar amma bai samu nasarar haduwa da ita ba, sake xagayo wa yayi ya tsaya daidai window din da xai hango su, a lokacin su kuma sun shagala da karatu, kiran su yayi duk su biyun suka fito tsugunnawa suka yi a gabansa tare da gaishe shi. fuskarsa a sake ya amsa "yau dai baku xo makaranta da wuri ba ko, kuma, nasan ke kika sa Nauwar ta makara don ta fiki himma" kansu a kasa suka bashi amsa. "da wuri muka xo malam" "shikenan naji ku tashi ku tafi aji, idan kun je gida ku gaida babanku ku ce yau xan dawo mu karasa magana a kan gonar da na gani ina so " tashi suka yi, ya bi Nauwar da wani mayataccen kallo, ba karamin burge shi take yi ba, yanxu babban burinsa bai wuce yaga Allah ya mallaka masa ita ba. saimah ce ta dubi Nauwar, "kawai fa dan ya ganki ne ya kira mu dan rainin hankali a yau din nan nake so mu yi wa tufkar nan hanci, mu fadawa abbah gaskiya ya dakatar da shi, don baxai hana mu sakewa a makarantar mu ba" Har suka shiga Aji saimah na mita saboda abin principal ya fara bata haushi. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki yar uwa aminiya, kuma abokiyar fadana, AYSHA SABO ABDULLAHI (maxumunciya) na baki wannan page kyauta ba dan halinki ba, kiyi yadda kike so da shi* 7⃣6⃣ Su saimah na isowa gida suka ci karo da Abbah xai fita masallaci hannun shi rike da tasbaha yana ja, da sauri suka karasa kusa da shi. "yauwa Abba yau ma principle ya sake bamu sako mu fada maka, wai ya maganar gonarka da ya gani yana so, yace kuma xai xo yau ya ganka" mamaki ne ya cikawa Abbah xuciya, ya ma kasa basu amsar abinda suka fada masa. "to naji ku tashi ku tafi, Alllah ya kawo shi lafiya" jujjuya maganar ya rika yi a xuciyar sa "Me yasa wannan mutumin xai min haka, ai bai kamata ya bawa yara wannan sakon ba sam bai kamata ba, amma xan yi maganin sa" ya fada tare da yin kwafa sannan ya fice ya nufi masallaci. Yau ma dai kamar jiya sake aiko yaro yayi aka yi sallama da Abbah, maganar neman auren Nauwar ya sake yi, Abbah bai bashi wata cikakkiyar fuska ba, saboda yana ganin abin nashi ya fara wuce gona da iri, yana son takurawa yara ya hana su walwala da farin ciki, ba tare da sakin fuska ba yake masa magana. "mun tattauna da mahaifiyar yarinyar nan tace a kyale mata yarta karatu xata yi, baxa ta bari ta fara tsayawa da samari ba sai tayi nisa sosai a karatun ta" yana kammala fada masa ya juyar da fuskarsa gefe . principle bai ji dadin sakon da Abba ya fada masa ba, amma ya daure ya bashi amsa. "ba komai ai hakan yana da kyau, amma a ganina Alhaji ai karatu baxai hana aure ba, kamar yadda aure baxai hana karatu ba, matukar yarinyar nan ta aure ni baxan hanata gudanar da duk wani abu da xai xama cigaba ne na rayuwarta ba, a bani dama na turo a yi maganar aure, idan yaso tana kammala secondry sai a daura auren, ko wata daya baxa tayi a gidana ba xan nemar mata admission ta shiga jami'a, a duba wannan al'amarin Alhaji, domin Allah bai taba jarabtata da son wata ya mace ba sama da wannan yarinyar, da sonta nake kwana da shi nake tashi a duba Alhaji a yi min rai" tausayi principle ya bashi, sakin fuskar shi yayi kadan sannan ya dube shi. "naji duk bayananka xan yi kokari na sanarwa da mahaifiyarta yadda muka yi da kai, abinda tace sai na kiraka a waya na sake sanar da kai, ba ma sai ka kuma dawowa ba kasan waya ta wakilci komai" yaji dadin kalaman Abbah, sallama yayi dashi ya tashi ya tafi Abbah kuwa sai mita yake yi a xuciyarsa. banda ma budurwar xuciya mai dattijo kamar wannan xai yi da yarinya,wani karin takaicin ma har da cewa wai babu yar da ya taba so kamarta, daki ya shige don ko mama bai fadawa yadda suka yi da shi ba saboda haushin da ya bashi. kullum sai principle ya kira Abbah ya tambaye shi game da maganar da suka yi, amsa daya dai yake bashi ita ce mahaifiyar Nauwar taki amincewa, ganin wannan yawo da hankalin da ake masa ne yasa ya roki alfarma a barshi yaje har garin da baban Nauwar yake ya nemi aurenta tunda dai a nan an hana shi motsawa, nan ma dai dakatar da shi aka yi, haka ya kasance kullum a cikin damuwa da shaukin son auran Nauwar, ita kuma yanxu ko gaisuwa bata barin ta hadata da shi,saboda takura mata da yake yi da mayataccen kallon shi. A haka suka cigaba da kasancewa kullum cikin wasan buya, har sai da sauran malamai suka fahimci akwai wani abu a tsakanin su. ******************* A bangaren su Abban Nauwar kuwa tunda suka bar gida basu sake komawa ba, kullum Abban Nauwar a cikin kuka yake da shaukin son ganin iyalansa a kullum ya tuna cewa sharrin su innah karime ne ya hargitsa masa kan family sai ya musu Allah ya isa, Kullum addu'a yake Allah ya hana su farin cikin duniya da na lahira kamar yadda suka hargitsa masa tunani suka hana shi jin dadi suka jefa matarsa da yarsa a mummunan hali. babban abinda ya fi daga masa hankali kuma wanda yake sa shi kwanciya rashin lafiya a duk lokacin da ya tuna, bai san halin da suke ciki ba, a mace suke ko a raye, gashi shi ya kore su da kansa, ba karamar nadama yake yi ba idan ya tuna da haka, wannan dalilin yasa ya matsa da neman su, duk garin da suka sauka sai ya bada cigiyar su a gidajen radio da television ko Allah xai sa a gansu. sun je garuruwa sun fi goma, haka kuma duk garin da yaje sai yasa an yi masa saukar kur'ani an roki Allah ya bayyana su,ya kuma yayewa Ammi lalurar da ya jarabceta da ita. ita ma Nauwar Kullum adduarta bata wuce Allah ya hada ta da mahaifinta ba. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Yau shafin gaba daya naki AUNTY MUNEERA ABBA DANDAGO, Allah ya kara miki lafiya da imani* 7⃣7⃣ Tunda principle ya kasa samun tsayayyiyar magana, daga wajen Abba, ga shi ya nemi a kai shi wajen mahaifin Nauwar anki, don haka ya shiga kulla yadda xai samarwa da kansa mafita, tunanin yadda xai bullowa lamarin ya rika yi, yanxu komai ya damule masa saboda ko samun damar magana da Nauwar baya yi, da ta ganshi xata gudu baxa ta sake barin su hadu ba, tashi yayi da kansa ya shiga aji ya kirata yace taxo Office yana son magana da ita. hanata tafiya saimah tayi sai da yayi kusan aike uku sannan ta tashi ta tafi tana buntsure-buntsure ta tafi, a bakin kofar Office din ta tsaya tare da yin sallama, a hankali ya dago ido ya kalleta, wani lafiyayyen murmushi ya sakar mata gami da kiran sunanta cikin sassanyar murya. "Nauwar karaso mana" kara turo baki tayi, tare da daure fuska, "bar ni a nan ba sai na shigo ba" wani dadi yaji ya mamaye masa xuciya, sassanyar muryarta ba karamin debe masa kewa take yi ba, wannan turo bakin ba karamin burge shi yake yi ba. cikin sakin fuska ya kara maimaita abinda ya fada mata. "ki shigo nace bana son gardama" ya karasa maganar yana lumshe idanunsa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta karasa xaunawa tayi a kasa, nuni yayi mata da hannun shi. "tashi ki dawo nan, daga yau idan kika xo bana so ki kara xama a kasa, ki dauka nan wajen dakin ki ne, domin da mai dakin da kayan cikinsa duk mallakin ki ne" kanta a sunkuye yake tana wasa da yatsunta sam babu alamar wasa a tattare da ita, duk maganar da yayi bata bashi amsa ba, saboda gaba daya haushi yake bata, musamman idan ya kashe mata ido, ji take kamar ta rufe shi da duka. sake dubanta yayi, yana murmushi. "me yasa kike guduna kwana biyun nan Nauwar, ki fada min gaskiya idan laifi nayi miki na baki hakuri, amma har ga Allah raina yana baci idan naga muna wasan buya da juna" har yanxu kanta a kasa yake bata dago ta dube shi ba, muryarta a dashe ta amsa masa da ba komai. kallonta yayi yana girgixa kai. "hakan nan baxa ki rika guduna ba akwai dalili ki fada min gaskiya, saboda har yanxu na gaxa samun nutsuwa da damuwar hakan nake kwana da ita nake tashi" kara bashi amsa da ba komai tayi. wani kallo yayi mata wanda har sai da yasa taji kunyar kanta. "ni nasan akwai wani abu Nauwar kawai kina boye min ne, idan kuma baki fada ba ni xan fada miki dalilin guduna da kike yi, kin yarda na fada" gyada kai tayi alamar ta yarda. sake gyara xama yayi ya dubeta "dago ki kalleni so nake mu yi magana ta fahimta tsakanina da ke" A kunyace ta dago ta kalle shi, sai dai suna hada ido dashi tayi saurin kawar da idanunta saboda abinda ta gani na soyayya a idon principle, wani dan murmushi yayi wanda ya bayyanar da fararen hakoransa. "ko a yanxu nasan kin fahimci sakon da nake son isarwa a gare ki" sake daure fuska tayi don ko amsar tambayarsa bai samu ba. "A yau nake son bayyanar miki da abinda ya dade yana damuna a xuciyata, amma ban san da wace fuska xaki kalli abinda naxo miki da shi ba, fatana dai ki yiwa abin kallo na nutsuwa kuma ki dube shi da idon basira, kuma ina so kiyi min alkawarin fada min gaskiya, domin tsakanina da ke babu yaudara ke diya ce a gare ni baxan yi fatan wani abu ya ta6a rayuwar ki ba" gyada kai tayi alamar ta amince, duk ta kosa taji abinda yake son fada mata ta gaji da wannan dogon turancin da yake mata. "Tunda kin amince xaki fada min gaskiya ni kuma xan fada miki abinda yake raina, Nauwar INA SON KI" A firgice ta dago ta kalle shi ji tayi maganar na mata yawo a kwakwalwa, dafe kirjinta tayi ta kalle shi. "kana sona fa kace malam?" kashe idanu yayi gami da sakar mata wani shu'umin murmushi. "Haba Nauwar ya naga lokaci daya kin firgita akwai fa aure tsakanin malami da daliba, Allah bai haramta haka ba, na miki alkawarin xaki samu soyayya mara yankewa a gidana xaki ji dadin da ba shi da misali,sai kin yi alfahari da ni a matsayin abokin rayuwar ki,baxan taba bari kiyi kuka a gidana ba sai dai idan na soyayya ne" shiru tayi tana jin kalaman principle na shiga ta cikin kunneta, a xuciyarta kuwa cewa take, me xan yi da tsoho kamar ka. cigaba da magana yayi cikin taushin murya. "Tunda na fada miki abinda ke raina,kema ya kamata naji ra'ayin ki a kan haka, amma kafin lokacin xan tambaye ki, kuma wannan tambayar ita nake so ki fada min gaskiya kada ki ha'ince ni ki sa nayi xurfi a soyayyar gonar da baxa ta xama mallakina ba" "na maka alkawari tun daxu xan fada maka gaskiya fa" "Naji ai kuma na gamsu da maganar ki amma ina kara jaddada miki abinda nake so ne saboda bana son a samu matsala" cikin nutsuwa ya fara tambayarta. "an miki miji ko kuma akwai wata tsayayyiyar magana a kan ki, bana son karya ki fada min gaskiya kamar yadda kika min alkawari" Har tayi niyyar fada masa gaskiya ta fasa,saboda muddin tace ba a bada ita ba, shikenan xai yi amfani da wannan damar ya rika takura mata. kanta a sunkuye ta bashi amsa da an bada ni. A raxane ya dago ya kalleta ji yayi kamar ta soka masa mashi, nan da nan idanunsa suka kada suka yi jawuri, bakinsa na rawa yake mata magana. "An bada ke fa kika ce" sake tabbatar masa da amsar abinda ya fada tayi. "wa aka bawa to, kuma yaushe aka bada ke,? amma ko wanene wannan yayi min shigar sauri amma kuma Alhaji bai fada min haka ba" cikin nutsuwa ta fara yi masa bayani. "Dan uwana aka bawa tun kafin mu xo garin nan aka yi mana baiko, Abba ya boye maka ne saboda baya so hankalinka ya tashi" dago jajayen idanunsa yayi ya dubeta. "Amma ban ji dadi ba wlh, saboda na gama tanadin yadda xan gudanar da rayuwata da ke amma ba komai haka Allah ya tsara, duk abinda Allah yayi ba mu da xabi sai dai mu yi biyayya, Allah ya baku xaman lafiya Allah yasa abokin arxikinki ne" amsawa tayi da Ameen, ba karamin tausayi ya bata ba, duk yanayinsa ya canja da ka ganshi xaka tabbatar yana cikin damuwa. tashi tayi xata tafi, kiran sunanta ya sake yi cikin nutsuwa ta juyo ta kalle shi. "wa yace ki tashi ki tafi ai bamu gama magana ba" komawa tayi ta xauna tana dubansa. "Akwai alfarma daya da nake so kiyi min, dan Allah kada ki fadawa dalibai abinda muka tattauna wannan sirri ne tsakanina da ke" "Insha Allah babu mai ji malam" sallama suka yi ta koma Aji, xuciyar principle cike da kauna da shaukin son Nauwar, lokacin da ta fadawa saimah yadda suka yi da shi ba karamin farin ciki tayi ba. hannu ta mika mata suka tafa. "Gaskiya kin yi fasaha kawata, ba karamar basira kika yi ba, gara da kika fada masa haka kinga ya sakar mana mara mu yi fitsari mu huta, haba nacin tsohon nan yayi yawa" tun daga wannan lokacin ta samu lafiya da shi, ya daina damunta da axababben kallon shi, tsakaninta da shi sai dai mutunci. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣8⃣ Nauwar ta shekara guda tana xuwa makaranta, inda ta samu damar haddace ixu ashirin, kuma tana cikin daliban da suka samu damar lashe gasar alkur'ani mai girma, wacce aka gabatar tsakanin makarantu, ita kuma saimah ta haddace ixu talatin, wannan dalilin yasa Abbah ya hada musu gagarumar walima, inda suka gayyato yan uwa da abokan arxiki suka taya su murna, komai iri daya Abbah ya yi musu babu wani banbanci da ya nuna tsakanin Nauwar da saimah, haka suka kasance tamkar yan tagwaye gwanin sha'awa. A tsayin wadannan watanni da aka kwashe kuwa, Kullum Ammi na kara samun lafiya don har magana ta fara yi kuma tana gane Nauwar da yayan gidan su saimah, sai dai yanxu ba komai take iyawa ba sai an koya mata saboda ta manta abubuwa da yawa, amma mai maganin yayi alkawarin a sannu a hankali xata kara samun sauki,kuma xata warke garau kamar bata taba yin ciwon ba da yardar Allah. rayuwa suke yi mai cike da farin ciki da jin dadi, idan har baka san su Nauwar a baya ba, baxa ka taba cewa su ne suka wulakanta suka yi bara ba, ita kuwa Ammi babu wanda xai ce mahaukaciya ce don duk buge-buge da surutan da take yi a da ta daina, gaskiya Abbah a tsaye yake akan al'amarin Ammi sai dai fatan Allah yayi masa sakayya ta alkhairi. yau su Nauwar xaune suke a dakin mamah suna ta hira tare da ita kasancewar an yi hutun makaranta, tashi tayi tace musu tana xuwa, dakin Abbah ta shiga samun shi tayi xaune yana karatun kur'ani, gefe guda ta samu ta xauna sai da ya kammala yayi addu'o'i sannan ya juyo ya dubeta. cike da girmamawa ta gaida shi, ya amsa yana mai sakin fuska. "Alhaji wani tunani nayi game da bayin Allahn nan, yau shekarar su guda a gidan nan amma har yanxu ba a samu, wani nasu da yaxo yayi cigiyar su ba, tunda mahaifiyar yarinyar nan ta fara samun sauki sosai, abubuwan jikinta sun fara warwarewa ya kamata ka bayar da cigiyar su a gidajen radio, ko Allah xai sa yan uwansu su ji, don nasan duk inda suke yanxu hankalin su ba a kwance yake ba" cikin nutsuwa ya dago ya kalleta. "gaskiya ne Hajiya sai da kika yi wannan maganar nima naga ya dace a yi hakan, Insha Allah xamu bada cigiyar su idan Allah yasa an dace sai kiga an samu yan uwansu su ma idan da taimakon da xasu yi musu sai kiga matar nan ta warke gaba daya" wayar da ke gefensa ce tayi 'kara, don haka yasa hannu ya dakkota number ya fara dubawa, murmushi yayi sannan ya dubi mama. "Hajiya sadeeq ne ya kira ni ko dai yana hanya ne" farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, ba mamaki don naji yana waya da yan uwansa yana ce musu ya kusa dawowa" wayar ya kara a kunnensa ya fara magana. cike da ladabi sadeeq yake magana, Abbah na bashi amsa bayan sun kammala ne ya juyo ya kalli mamah. "Ai kuwa dawowar xai yi, yace anjima da misalin karfe biyar a je a dakko shi a airport" cike da farin ciki ta amsa masa da Allah ya kawo shi lafiya amma bai kyauta ba da bai fada mana da wuri ba" yayan Abban saimah su biyar ne yaya Muhammad wanda shi ne babba sai Mahmud mai biye masa sai kuma sadeeq wanda shi ne d'a na uku sai kuma mubarak sai kuma autar su saimah wadda ita ce ya mace daya tilo a wajen mama da Abbah, wannan yasa duk wani abu da xai farantawa saimah suke son shi. Muhammad da Mahmud da mubarak duk sun yi karatun su ne a gida basu fita kasar waje ba,inda yanxu suke aiki a manyan ma'aikatu, yaya Muhammad da Mahmud duk sun yi aure da yayansu yanxu sadeeq da mubarak da saimah ne kawai suka yi ragowa. sadeeq yayi karatunsa ne a kasar England a bangaren likitanci. tashi mamah tayi ta fita daga dakin Abbah, dakinta ta nufa inda ta tarar da su Nauwar sun hada kai suna gulma, tsokanar su ta fara yi. "An hada kai ana gulmar principle ko" A raxane suka dago suka dubeta. "rufa mana asiri mama ina mu ina xancen principle a gidan nan" dariya suka bata don taga alamar sun tsani a ambaci sunan principle, sake dubansu tayi tana murmushi. "To albishirin ku" da sauri suka amsa mata da "goro" "ku shirya yau yayanku xai dawo" tsalle suka fara yi suna murnar dawowar yaya sadeeq, duk da cewa Nauwar bata san kowane ne shi ba,bata taba ganinsa ba amma saimah tana yawan bata labarinsa, mutum ne mai saukin kai da barkwanci ga shi da son mutane, da dukkan alamu kuma jininsu ya hadu da saimah wannan dalilin yasa ita ma ta kosa ta gan shi. wanka suka shiga suka fara shiri da wuri, dan sun san halin Abba baya son jira, shi yasa suka fara komai a akn lokaci. karfe biyar jirgin su ya sadeeq ya iso, ba tare da bata lokaci ba aka tafi dakko shi. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣9⃣ Suna isa gurin da gudu saimah ta karasa ta rungume shi, cike da farin ciki ya karaso wajen su Abbah,xubewa yayi har kasa yana gaida su, fuskar su a sake suka amsa masa, ita ma Nauwar tsugunnawa tayi ta gaida shi, cikin farin ciki ya amsa mata. tambayar saimah yayi "wannan kawar ki ce ya sunanta" tana murmushi ta amsa masa da eh, sunanta Nauwar. kayansa suka dakko aka xuba a mota suka wuce gida. suna isa gida kai tsaye dakin mama suka shiga, tarar da ita suka yi ta shirya masa abinci kala-kala, dakkowa saimah tayi ta fara xuba masa, yana ci suna hirar yaushe gamo, bayan ya kammala ne ya dakko jaka ya shiga ciro musu tsarabar da ya kawo musu, ba kamar siyayya ya yiwa saimah ba, daga cikin kayanta ta debi rabi ta bawa Nauwar. mama ce ta umarce su, da su dauki turaren wuta su saka a dakin yaya sadeeq, tashi suka yi suka fara abinda ta saka su. bayan sun fita ne yake tambayar mamah. "Mama ya kamata kawar saimah ta tafi gida kinga dare ya fara yi kada a neme ta" murmushi tayi sannan ta dube shi. "baka ga dakin soro a bude ba" "ban kula ba ina ta sauri na shigo ciki na ganki" cigaba tayi da magana tana duban shi. "To mamanta ce a ciki, a nan gidan suke kwana don sun fi shekara a nan" cike da mamaki ya dubeta. "A ina kuma ku ka samo su mamah?" labarin Ammi da Nauwar ta kwashe ta bashi, cike da tausayawa ya dubeta. "gaskiya na tausaya musu mamah Allah ya basu mafita, nima kuma akwai kokarin da xan yi mata, idan na huta xan auna kwakwalwarta saboda irin wannan ciwon wani lokacin dole sai an hada da maganin asibiti, amma kamar ba hausawa bane ko mama?" "kai kuwa me ka gani kace ba Hausawa bane" "naga kalar su kamar ta larabawa ce mamah" murmushi tayi masa, to sarkin tambaya ka dawo xaka fara ko, tashi maxa kaje ka watsa ruwa idan ka dawo sai mu dora daga inda muka tsaya. tashi yayi ya shiga bandaki ya fesa wanka, shigar kananan kaya yayi ba karamin karbar jikinsa kayan suka yi ba, kiran saimah yayi, da gudu ta karaso inda yake. "ina kawar taki dakko mayafinku, ku xo ku raka ni unguwa" kiran Nauwar ta shiga yi, da sauri ta shiga daki. "yi sauri ki shirya xamu raka ya sadeeq unguwa" A kasalance ta dubi saimah. "ni baxa ni ba ki tafi kawai" kallonta tayi tana hararta. "ai kuwa baki isa ba, sai kin je kinga malama dauki mayafi ki fito ina jiran ki" fita tayi ta kyaleta a tsaye, Nauwar bata son xuwa haka dai ta dauki mayafi ta bi ta. A kofar gida suka iske shi xaune har ya gaji da tsaiwa. sallama suka yi fuskar sa a sake ya amsa musu, mota ya bude ya shiga, saimah ta shiga gaba Nauwar kuma ta xauna a baya, suna tafe suna hira labarai Saimah ta rika bashi yana dariya, juyowa tayi tana duban Nauwar "yauwa yaya na manta ban baka labari ba, wani principle mu ne tsoho yace yana son Nauwar" duka ta kaiwa saimah, "Allah karya ta fada maka yaya" gwalo Saimah ta rika yiwa Nauwar, ita kuwa saboda takaici ta kasa cewa komai, shi kuwa yaya sadeeq sai dariya yake yi yana kara tunxura Nauwar "to menene dan tsoho ya so ki, ai ba haramci a ciki, idan kinga ya miki ki so kayanki kin ji kanwata" da sauri tayi magana. "Allah ya kiyaye me xan yi da shi" xaulayarta ya rika yi sosai, yana kiranta da amayar pc kamar xata yi kuka idan ya kirata da wannn sunan. super market ya kaisuu yace kowa ya xabi kayan kwalliyar da yake so,kudade masu yawa ya kashe musu sannan suka dawo gida. har Nauwar ta fara sakewa da ya sadeeq saboda mutum ne mai barkwanci da son mutane. A ranar kusan kwana suka yi suna hira. washe gari da sassafe ya shigo dakin mama ya gaida ita, cigiyar su saimah ya yi, inda mama tace masa suna daki suna bacci, kayan aikinsa ya dakko a jaka, cikin nutsuwa yake wa mama magana. "ya kamata a kaini naga mara lafiyar nan na fara binciken abinda yake damunta" tashi tayi ta raka shi dakin, tarar da Ammi suka yi xaune, da sallama suka shiga dakin, kallon su kawai take saboda yanxu gaba daya ta manta menene sallama da yadda ake amsata, wajen xama suka samu, tambayoyi ya sadeeq ya fara yi mata, wasu maganganu ta rika yi marasa kan gado. cikin mamaki ya dubi mama "dama abinda take yi kenan amma ku ka ce ta ji sauki" "hmm lallai sadeeq baka san lokacin da take kan ganiyar cutarta ba, ai yanxu anji sauki sosai da ko magana bata yi, yanxu dai matsala daya take damunta, bata gane abubuwa sannan bata iya komai ba sai an koya mata" cikin tausayawa ya dubi Ammi "Allah sarki sannu mama, Allah ya baki lafiya, insha Allah ni ne sanadin warakar ciwon ki" magunguna ya dakko ya mikawa mama ta bata,sannan ya yi mata wasu allurai. kallon mama yayi yana mata bayani. "wadannan abubuwan da na bata su ne xasu taimaka wajen saita mata tunaninta, sannan a sannu a hankali xan rika xuwa ina koya mata abubuwan rayuwa, amma ku ma sai kun taimaka min, sannan a daina barinta tana xama ita kadai idan da hali nauwar da saimah su dawo nan dakin da xama saboda ta haka ne xata rika koyar magana kuma ta gane komai ba tare da an sha wahala ba" Albarka mama ta shiga sawa ya sadeeq, fitowa suka yi daga dakin ya shiga dakin su saimah yin hira, don a yanxu ba shi da abokan da suka wuce su. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 8⃣0⃣ Shigar da kansa yayi cikin dakin tare da sallama, tarar da su yayi zaune suna hira, Nawwar ce ke bawa saimah labarin yaya Hamdan da irin gudunmawar da ya basu a rayuwar su, da kuma kanin ta fu'ad da irin tuggun da su innah karime suka yi har suka raba shi da rayuwar sa. karasowa gurin su ya sadiq yayi, fuskarsa dauke da murmushi kusa da Saimah ya samu ya xauna. "yan kannena me ku ke tattaunawa nima nazo a yi hirar da ni, ko ba a gayyata ta?" saimah ce tace " la yaya har da kai mana" gyara xama yayi yana facing din Nawwar da Saimah, duk lokacin da suka hada ido da Nauwar sai ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi, sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yan yatsunta, fada tayi a zuciyar ta wannan mutumin me kuma yake nufi da ni ne haka. kiran sunanta da yayi shi ya katse mata tunani da ta tafi, dagowa tayi ta dube shi, sake yi mata murmushin yayi "ko ba'a son ayi hirar dani ne tunda na shigo kika yi shiru Nauwar, ki saki jikinki ni yayan ki ne fa" murmushi tayi "ba haka ba ne yaya, kawai bana jin magana ne yau" dariya saimah tayi gami da dukan cinyar Nauwar. "ita fa wannan yarinyar haka take da miskilanci idan bata ga damar magana ba sai mu wuni a nan bata ce komai ba" tsokanarta yaya ya shiga yi. "ki kyaleta Saimah ni nasan abinda ya hanata magana tunanin tsoho mai ran karfe take yi" da sauri Nauwar ta dago manyan idanunta. "rufa min asiri yaya, ni har na manta da rayuwar shi Allah" "ki fadi gaskiya dai, jiya fa kin fada min shi ne xabin xuciyar ki" ya karasa maganar tare da kanne mata ido daya. "hmm wai a lallai sai kun sani magana ko, to nayi shiru baxan kuma cewa komai ba" hira suka rika yi suna dariya. lekowa dakin mamah tayi. "to sarkin son surutu kana nan kana xuba kamar ruwan famfo ko, taso ka raka ni unguwa xamu karbowa maman Nauwar magani kasan babu damar a tafi da ita yau tunda an bata maganin bacci" da sauri ya mike yana kallon su Nauwar. "to xan je na raka mama me ku ke so na taho muku da shi a hanya?" yana maganar yana kallon idon Nauwar, bata ce masa komai ba sai saimah ce ta bashi amsa. "fura xaka siyo ma ita muke shaawa" sake duban Nauwar yayi. "baki ce komai ba kanwata ta kaina" kanta a kasa ta bashi amsa. "nima ita nake so" A dawo lafiya suka yi masa, sannan ya fita. kai tsaye gidan magani suka nufa, inda suka fada wa mai maganin yadda jikin Ammi yake. cike da kulawa yake musu magana. "kada ku damu da duk abinda xaku gani, a hankali saukin xai samu, cuta ita take shiga lokaci daya amma sauki sai a hankali, fatana kada ku gajiya da nema mata sauki a wajen Allah, da sannu xata samu lafiya Insha Allahu" magunguna ya dakko ya basu. "wannan aje a bata tasha sannan tayi wanka, Insha Allah kafin ku sake dawowa xaku bani labarin yadda jikinta xai koma" godiya mai yawa suka yi masa,kudi ya sadeeq ya dakko ya bashi, cewa yayi baxai karba ba har sai bukata ta biya. sallama suka yi masa suka fito, suna tafiya a hanya ya sadeeq ya dubi mama. "Har cikin xuciyata ina jin tausayin matar nan da yarta jinta nake yi kamar yar uwata, tunda na dawo ban taba yin sallah,ba tare da na yi musu adduar Allah ya bayyana yan uwansu ba" "ni kaina ina tausaya musu wlh, fatana dai Allah ya bata lafiya ta bada labarin inda xa a samu yan uwanta, na manta ma ban tunawa babanku ba yana ta maganar xai kai cigiyarsu gidan radio da televisions har yanxu ban ji ya tuna ba, muna komawa xan kara tuna masa maganar, saboda gara a maida hankali wajen neman yan uwan su" "mamah a nawa tunanin gara ku bari ta warke gaba daya ta dawo hankalinta sai a nemi yan uwansu amma yanxu tana cikin lalura ko an nemi yan uwanta ba wani abu da xasu iya yi mata" "haka ne maganarka amma xan nemi shawarar baban ku abinda yace shi xa a bi" tsayawa yayi ya siyawa su saimah furar su, sannan suka karasa gida. Hannun shi rike da ledar furar da ya siyo yayi sallama dakin su saimah, da gudu ta karasa ta karbi ledar hannun nasa, ita ma Nauwar tasowa tayi tana masa sannu da xuwa, fuskarsa a sake ya amsa musu. gefen gado ya samu ya kishingida yana duban su. "sannu yaya kasha hanya, mun gode da dawainiyar da ake yi da mu Allah ya saka da alkhairi" "babu komai kanwata mun xama daya da ku" ledar suka bude ciro furar suka yi suka fara sha, suna godewa yaya sadeeq. tashi yayi xai fita daga dakin, har ya kai bakin kofa ya kira sunan saimah. "anjima ina so ki same ni a dakina xamu yi wata magana" yana kammala fada ya wuce ya fita. wajen mama ya shiga ya karbi magungunan ya fara hadawa Ammi. "ya kamata a bata abin nan yanxu saboda ni wlh na kosa ta warke, gobe kawai sai a hada mata na wankan tayi nasan kafin sannan allurar ta saketa" murmushi mama tayi tana dubansa. "wai garajen me kake yi ne sadeeq idan an bi komai a hankali ai xai fi ko" "Haka ne mama, amma kin san ba a bori da sanyin jiki, nafi son naga ta warke ta dawo kamar kowa" naci yasa har sai da ta tashi suka tafi dakin Ammi, kiran su nauwar tayi suka xo suka taimaka mata ta dagota aka bata maganin ta sha" *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ku ZAHRA MUSA & HAFZIYYA NASIDI, da fatan kun je gida lafiya* 8⃣1⃣ Bacci Ammi ta cigaba da yi, su mama kuma suka tashi suka bar dakin, addu'a bata bar bakin su ba a Kullum, rokon Allah suke ya wadata Ammi da lafiya. daki ya sadeeq ya shige ya xauna, kira ya kwalawa saimah da hanxari ta nufi dakinsa sallama tayi masa. tarar da shi tayi xaune kan gado ya hada kai da gwiwa, kansa a kasa ya amsa mata sallamar, karasawa gurinsa tayi cikin nutsuwa take masa magana. "lafiya yaya naga ka hada kai da gwiwa ko baka jin dadi ne" A hankali ya dago ya dubeta tare da girgixa mata kai. "babu abinda yake damuna kawai gajiya nayi kin san yau na dan yi xirga-xirga" kusa da shi ta samu ta xauna. "gani yaya" dagowa yayi ya matso kusa da ita yana fuskantar ta. "wani sirri xa mu yi da ke amma bana so ki fadawa kowa, sbd bana son maganar ta fita yanxu sai nan gaba nake da burin kowa ya sani" cikin nutsuwa ta dube shi. "ina jin ka yaya" "na san kin dade da sanin ina jin xafin halin da mutanen nan suke ciki ko" amsa ta bashi da "haka ne yaya" "kuma nasan kin san da cewa duk inda aka samu tausayi dole akwai so a gurin" "maganarka haka take" "bana so na ja ki da nisa ina son Nauwar, saboda yarinya ta shiga xuciyata ta gama yi min, amma ban sani ba ko xata amince ta karbi soyayyata" farin ciki ne ya bayyana a fuskar saimah. "Alhamdulillah naji dadin wannan abin dama ina taso nace maka, dan Allah kace kana sonta, ina son xumuncin mu ya dore sbd tana da nutsuwa kuma da gani ta samu tarbiyya, na tabbatar da cewa idan har na fada mata kana sonta baxa ta ki karbar soyayyarka ba, saboda ai ka hadu yayana ba kada wata makusa" murmushi yayi ya dubeta. "bana son xuga kanwata, amma kin san wani abu" da sauri ta dago ta dube shi. "bana so ki fada mata yanxu, nafi so sai mamanta ta warke saboda yanxu tana cikin damuwa bai kamata a xo mata da wannan maganar ba" murmushi tayi sannan ta cigaba da magana. "banda abin ka yaya ina ruwan soyayya da wata damuwa, ka sani ko hakan ya xama sanadin farin cikinta ni dai sai na fada mata" tashi tayi xata fita da sauri ya jawota ya xaunar da ita. "kin manta mun yi alkawari baxa ki fada mata ba, idan kika fada mata xata daina sakewa a gidan nan ne, Kullum ta rika xaman daki, yar hirar da nake samu mu yi duk xata daina yarda a yi da ita, nafi so na fada mata a lokacin da xa a ce gobe babanta xai xo kin ga a lokacin xamanta a gidan nan ya kare sai dai na rika xuwa wajenta tadi, ko ba haka ba" "shikenan yaya baxan fada mata ba" tashi suka yi gaba daya suka shiga dakin mama, tarar da Abba suka yi xaune suna tattauna maganar kai cigiyar su Nauwar gidan radio, yaya ne ya xauna saimah kuma ta tafi dakin Ammi saboda Nauwar tana can. Abbah ne ya dubi ya sadeeq. "yauwa naji dadi da na ganka yanxu domin xancenka ma muke yi, kaine xaka jagoranci cigiyar da xa a bayar a gidan radio da televisions, yarinyar nan ta bamu duk wani tarihin mahaifinta da abinda ya rabo su da gida, don haka idan kaje ka fada musu a program din da aka fi yawan saurara xasu bada wannan sanarwar" takarda ya mika masa, cike da ladabi yasa hannu ya karba, magana Abbah ya cigaba da yi. "yau fa nake so kaje don bana son abin nan yayi tsawo kaga an fara samun kan mahaifiyar yarinyar nan, sannan sun fi shekara a gidan nan, idan muka cigaba da xama a haka mun xalunci mahaifin yarinyar nan don nasan duk inda yake yanxu hankalinsa ba a kwance yake ba" Abba yana rufe bakinsa yaji hayaniya a soro da gudu su Nauwar suka shigo dakin suna magana. "Abbah ku taso ku ga Ammi" basu tsaya tambayar abinda ya faru ba suka dunguma suka yi soro. Ammi suka gani xaune, tana duban su, hawaye na sauka a kan fuskarta, karasawa suka yi kusa da ita, cike da mamaki mama ta dubeta "sannu maman Nauwar" A hankali ta dago ido ta dube ta. "yauwa Hajiya" dakin ne gaba daya ya hargitse ji kake kowa yana fadin Alhamdulillah sauki ya samu. da gudu Nauwar ta karasa ta rungume Amminta tana kuka. "Allah sarki Ammina ashe kina da rabon jin sauki, Allah na gode maka da wannan ni'imar da kayi mana Allah ya kara miki lafiya" kuka suka rika yi sosai da kyar aka janye Nauwar daga jikin Ammi. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 🎂🎂🎂🎂🎂🎂 *Happy birthday 💃🏽💃🏽to you NASIBAH ISMA'IL(naseeba gawo)washing you many more blessing years and Happy returns* 8⃣2⃣ Idanun Ammi cike da hawaye ta dube mutanen da ke dakin. "nan a ina nake kuma menene dalilin xuwana?" cike da kulawa mama ta dafa kafadarta. "ki kwantar da hankalin ki, kina gidan aminci ne inda babu cutarwa a cikinsa, kina garin kaduna a unguwar Rimi, dalilin xuwan ki nan labari ne mai tsawo ki bari ki nutsu sosai xan fayyace miki komai, yanxu dai ki tashi ki karasa wankan maganinki kici abinci sannan mu fara magana" tashi Ammi tayi ta nufi bandaki saimah da Nauwar ne suka kai mata ruwa bandakin, bayan ta fito aka bata abinci taci sannan ta shiga dakin mama ta fara bata labarin sanadin xuwan su gidan su saimah. kuka sosai Ammi ke yi, tunda take bata taba xaton xata shiga irin wannan rayuwar ba, sai a lokacin ma ta san danta fu'ad ya rasu, ba karamin tashin hankali ta shiga ba, hakuri mama ta shiga bata har sai da ta dawo cikin nutsuwarta. ranar da Ammi ta warke kuwa Farin ciki baya misaltuwa a wajen Nauwar kana ganinta xaka tabbatar da cewa tana cikin farin ciki, alwala ta dauro ta fara jera sallolin godiya ga mahalicci, da ya dawo mata da hankalin mahaifiyarta, sannan ta kudiri niyyar gobe xata tashi da axumi duk don nuna godiya ga Allah bisa wannan babbar ni'ima da ya yi mata. bayan ta idar da sallah ne saimah ta shigo ta sameta xaune tana addu'oi, sai bayan da ta kammala ta fara mata magana. "ba karamin farin ciki nake yi ba da wannan babban arxikin da Allah yayi mana, Allah maji rokon bawa indai ka roke shi wata rana xai amsa maka, matukar baka yi gaggawa ba, Allah ya kare mu daga sharrin mutum da na aljan" dagowa Nauwar tayi ta amsa mata da "Ameen, ban san irin farin cikin da nake ciki ba yau, sbd da na yanke kauna cewa Ammi xata samu lafiya sbd kullum a yanayi daya take" "ai indai ka dage da addu'a a komai Allah xai baka mafita, mu dai mun godewa Allah da wannan baiwar da yayi mana" tashi suka yi suka shiga dakin mama, tarar da su suka yi suna hira Ammi har da dariya, cike da farin ciki Nauwar ta karasa wajen fadawa tayi jikin Ammi tana mata magana. "Ammina sannu da hutawa" dago fuskarta tayi. "to sarkin son jiki daga ni xaki xo ki daddanne min ciya ko" murmushi Nauwar tayi "Haba Ammina yaushe rabon da na hau, yau dai ki kyaleni na hau kin san anjima ba a hadu ba" dariya mama take yi "ai yaran nan haka suke da son jikin tsiya haka nake ta fama da saimah yanxu ta dan rage" suna cikin wannan maganar yaya sadeeq ya shigo, a ladabce ya tsugunnah ya gaida mama sannan ya juya ya gaida Ammi, cike da sakin fuska suka Amsa masa. kansa a kasa yake musu bayani. "mama yanxu nake so na tafi na bada sanarwar nan, amma kafin lokacin ya kamata ku shirya a tafi gidan mai magani nasan xai yi farin ciki idan yaga yadda jikinta yayi, idan na dawo gida sai na wuce wajen bada cigiyar" "To shikenan dan albarka" mayafi suka dauka, sai gidan mai magani, ba karamin mamaki yayi da gani Ammi ba, wajen xama ya basu, fuskarsa cike da fara'a ya dube su. "Alhamdulillah, Allah maji rokon bawa, sannu baiwar Allah kin sha fama" murmushi Ammi tayi ta dube shi. "komai yayi sauki malam yanxu babu abinda nake ji mun gode sosai Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi" hira sosai suka rika yi da Ammi akan rashin lafiyar da tayi, bayan sun gama ne suka yi sallama, kudade masu yawa yaya sadeeq ya bashi, cike da farin ciki mai maganin ya karba, adduar fatan alkhairi ya rika yi musu sannan suka tashi suka bar gidan. kai tsaye gida yaya sadeeq ya mayar da su mamah sannan ya wuce wajen bada cigiya. bai dade da tafiya ba ya dawo, tarar da su yayi a tsakar gida suna cin abinci da sallama ya karasa wajen da suke, cikin kulawa mama take masa magana "sannu da xuwa saddequ har ka dawo amma kayi sauri sosai" takalmansa ya shiga cirewa. " naje na kai mama sun ce Insha Allah xasu bada sanarwar har xuwa lokacin da xa a dace, na bada number wayar da xa a same mu" Albarka ta shiga saka masa sannan ya shiga kitchen ya dakko abinci. ********************** A bangaren Abban Nauwar kuwa, sun yi nema har sun gaji don haka suka yanke shawarar komawa gida kawai su cigaba da addu'a don sun san Allah maji rokon bawansa ne. sallama yayi da Hamdan da Abbansa shi kuma ya wuce gida. Yana nufo kofar gidansa yaga kofar gidan a bude alamun akwai mutane a ciki, da sauri ya doshi kofar shiga gidan, ihu yaji ana yi ana neman taimako, da hanxari ya shiga gidan don ganewa idonsa abinda ke faruwa. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Ina yiwa al'umar musulmin duniya Barka da sallah da fatan anyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ameen* 8⃣3⃣ cikin fushi ya shiga gidan tarar da kofar yayi a kulle, buga kofar ya shiga yi ba kakkautawa amma ba a xo an bude masa ba sai ihu da yake tashi. ganin ba a da niyyar bude masa ne yasa ya fita ya bar gidan, kiran me gyara yayi inda ya balle masa murfin kofar ya shiga. cikin falon ya sa kanshi, ihu dai yake ji amma kuma bai ga komai a ciki ba, dakin Ammin Nauwar ya shiga, da sauri ya ja da baya yana ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un, innah karime ya tarar maciji ya nade mata jiki, ihu kawai take tana neman taimako, jawo kofar dakin yayi ya kulleta, da sauri ya dauki mukullin moto ya fita, kiran masu cire maciji yayi, suna isowa suka shiga dakin da take. kallo daya mai cire macijin yayi wa macijin da ya nadeta ya ja da baya, dafa kafadar Abban Nauwar yayi. "Alhaji wannan ba irin macijin da muke cirewa bane, wannan da gani na iska ne, abinda xa a yi kawai turaren magani xan mata, idan ya saketa shikenan idan kuma bai saketa ba sai a yi hakuri, sbd aikin ya fi karfina" wani gumi ne kawai yake yankowa Abban Nauwar, mamaki yake daga ina ma macijin ya shigo har ya makale mata a jiki bata sani ba. "shikenan ba komai a gwada yin turaren idan an dace shikenan" burgima innah karime take yi, tun tana ihu har muryarta ta dashe, turare ya saka a dakin ya kulle sannan suka dawo falo suka xauna. tagumi Abban Nauwar yayi sbd abubuwan da suke faruwa a gidan sa suna matukar bashi mamaki, a xuciyarsa yake magana. "mutanen nan sai dai idan wani mugun abin suka kunno ya koma musu kansu, kadan ma suka gani daga aikin asiri" bayan minti biyar da saka turaren ya tashi ya shiga dakin, tarar da macijin yayi ya sulale ya gudu, gaba daya innah karime ta galabaita ta fita daga cikin hankalinta, a hankali ya dagota, kiran Abban Nauwar yayi da hanxari ya karaso ciki. "Alhaji abin nan ya illata baiwar Allahn nan saboda duk wata ga6a ta jikinta ya karyata, sannan kuma yayi mata tsattuwa a ido, gaskiya sai tsananin rabo xata samu ta mike, kuma ko ta mike ta rasa idonta biyu" cikin jimami Abban Nauwar ya dubi mai magani. "yanxu babu wani taimako da xa a bata kenan" kallon shi yayi sannan ya mayar masa da amsa. "taimako daya xamu yi mata shi ne mu bata maganin da xata yi aman dafin da ya xuba mata a cikinta, amma idonta gaskiya ya tafi baxai dawo ba sai dai hakuri" magana suka jiyo ana yi a falo don haka suka kasa kunne don jin abinda ake fada, Habi ce ta shigo tana shewa. "innah kina ina ki fito yau nayi ido hudu da gobe da nisa, ya fada min mahaukaciya baxa ta kara samun lafiya ba har abada, kuma shi ma mudi gobe ko jibi xai yi ajalinsa tunda yanxu wulakanta mu yake yi, gara ya hallaka shi kowa ya huta dukiyarsa kuma mun yi alkawarin xamu raba gida biyu mu bashi kaso daya" duk wannan maganar da take yi a tunaninta babu kowa a gidan saboda bata nan Abban Nauwar ya dawo, shirun da taji ba a amsa mata bane yasa ta shigo cikin dakin, tarar da su tayi tare da mai magani sun yi tsaye suna mamakin maganganun da suka ji daga gareta. tana ganin Abban Nauwar ta xube kasa tana borin kunya, shi kuwa kallonta kawai yake ya kasa magana saboda mamaki. mai maganin ne ya buga mata tsawa. "matsa ki bamu guri munafukar banxa munafukar wofi, kina tsammanin duk maganganun da kika fada bamu ji abinda kika ce bane, to yau karyar asiri ta kare wanda kike yi dominsa yaji komai, yanxu ma da shirin da kika taho da shi ki bani abinda kika karbo kafin na tona miki asiri" rawar baki Habi ta fara yi. "wlh ban karbo komai ba Allah ya gafarta malam, babu komai a xuciyata sai alheri" sake daka mata tsawa yayi. "xaki bani ko sai na mayar miki da duk asiran da kika yiwa wannan bawan Allahn da iyalansa kan ki" rufe ido yayi, sannan ya mika mata hannu. "miko min maganin da ya baki kafin na bude idona" rawar jiki ta fara yi nan da nan, ta fara kwance gefen xaninta sai ga magunguna nan suna fadowa, a hankali ya sunkuya ya kwashe magungunan. fuskarsa a daure ya dubeta. "akwai binne-binnen da ku ka yi,ina so ki hako min shi yanxu ki bani" sake duban Abban Nauwar yayi. "wannan matar shaidaniya ce ita da wannan ta kwancen da maciji ya makalewa a jiki, kuma wannan macijin su suka kawo shi gidan nan don ya cutar da kai, sai kaikayi ya koma kan mashekiya, don haka baxan bata maganina ba saboda muguwa ce, gobe kuma xan dawo duk wani mugun aiki da suka yi a gidan nan sai na warware shi, ke kuma" ya nuna Habi da hannu. "gobe ki shirya duk abinda kika yi na sharri sai na mayar miki da shi kanki, xaki bada labarin illar xalunci da kanki" faduwa Habi tayi tana rokon shi ya taimake ta ya rufa mata asiri amma ko kallonta bai yi ba ya fice a fusace ya bar gidan. shi kuwa Abban Nauwar bakin ciki ma ya hana shi magana, kawai wani hayakin bakin ciki ne yake taso masa a xuciyarsa, jiran gobe kawai yake yi ta ga ruwan rashin mutuncin da ya tanadar mata. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 8⃣4⃣ Gwiwoyi biyu Habi tasa a kasa tana rokon shi gafara. "Dan Allah kada ka bari mutumin nan ya maido min da abinda ba nida hakki a kansa, wlh ba nida wani hannu cikin 6atan yayanka, ban san abinda ya faru ba ka taimaka ka tallafi rayuwata, kasan babu yadda xa a yi a hada baki da ni a cuci iyalanka ko dan alkhairin da kayi mana" Hawayen takaici Abba Nauwar ya shiga xubarwa ficewa yayi ya barta a dakin tana ta sambatu, sashinsa ya nufa yana shiga dakin ya fada kan gado ya cigaba da share kwallar bakin ciki. waya ya dauka ya kira baffa, cikin kuka yake masa bayani abinda ya faru. "Baffa ashe duk halin da na shiga da sa hannun Gwaggo Habi da innah karime" salati Baffa ya shiga yi. "Ai dama kaine baka gane ba Mahmud ni na dade da fuskantar hakan, fatana dai kayi hakuri kada ka saka damuwar hakan a ranka kuma ka cigaba da addua komai na Allah yana da iyaka, ya labarin jikat kuwa" gyaran murya yayi sannan ya fara yi masa bayani. "wallahi Baffa nayi neman duniya babu labarin su, mun kai cigiya duk inda ya kamata amma har yanxu bamu ji wata magana mai karfi ba, dan Allah ka taya ni da addu'a ina cikin kunci da damuwa ko bacci bana iya yi, xaka yi mamaki idan kaga yadda na rame na fita daga hayyacina" Hakuri Baffa ya rika bashi yana rarrashinsa har sai da xuciyarsa tayi sanyi, daga karshe Abban Nauwar yake shaida masa abinda ya faru da innah karime, cikin tashin hankali Baffa yake tambayarsa. "yaushe ita kuma wannan ibtila'in ya afka mata" "jiya ne Baffa nima bana nan sai dawo wa nayi na tarar da ita a wannan halin" ba karamin damuwa Baffa yayi da halin da innah karime ke ciki ba. "Dan Allah kada ka duba abubuwan da suka yi maka, ka danne xuciyarka ka kula da ita ko dan tsufanta, na roke ka kayi haka dan Allah Mahmud" "Insha Allah xan yi yadda kace Baffa" sallama suka yi sannan ya kashe wayar, a ranar kwana yayi cikin bakin ciki da jimamin sharrikan da su innah karime suka kulla masa. washe gari da misalin karfe goma na safe mai magani ya iso gidan, bai tsaya an shigo da shi ba ya karaso har cikin falo, kiran sunan Abban Nauwar ya shiga yi cikin xafin nama ya karaso inda yake, bayan sun gaisa ne yake tambayarsa ina Habi take. "ni tun safe ban ji motsinta ba don ko sallah bana jin ta fito tayi" bakin kofar dakin ya nufa, buga kofar ya shiga yi amma shiru ba a bude ba, mai maganin ne ya taso da kansa ya fara bugawa yana yi mata masifa, a hankali ta jawo jiki ta karaso bakin kofar. "Baxan bude kofar nan ba har sai kayi min alkawarin baxa ka tona min asiri ba" dabara yayi mata har taxo ta bude. Bayan ta fito ne yace ta karaso falo su yi magana, bata yi gaddama ba ta fito. "Abinda nafi bukata a yanxu kawai ki tashi salun alun, mu tafi ki nuna min guraren da ku ka binne asiri idan ba haka ba kuma ni xan nuna gurin da kaina kuma sai na toxarta ki a idon duniya" jikin Habi na rawa ta tashi, da farko kitchen ta shigar da su inda ta nuna wani waje tace a nan ma sun binne asiri, ha'ko wajen ya fara yi inda aka fito da layu an sanya su a cikin tukunya, a take ya doka su da kasa ya fasa sannan ya kone layun. sake tasa keyarta yayi ta rika kai shi gurare mabanbanta da suka binne asirai a cikin gidan, har dakin Abban Nauwar sai da suka je nan ma sun yi ajiye ajiye a cikin pillow. Bayan sun gama xageye ko ina na gidan amma bata nuna da dakin Ammi ba, a cewarta tace babu komai a ciki. cikin fushi mai maganin ya dubeta. "kada ki rainawa kan ki hankali, na riga nasan komai game da abubuwan da ku ke yi,kawai ki tashi mu je ki nuna min inda kika binne mugun abin ku" kuka sosai Habi take yi tana rokon shi ya kyaleta bata san wajen da suka ajiye ba, tilasta mata yayi sai da ta tashi ba a son ranta ba. suna shiga ta nuna karkashin gado tace duk Abinda ya faru da Ammi a nan suka xo suka binne. nunata yayi da hannu. "xo ki hako da kanki ki kona tunda ku ka xo ku ka saka" nan ma dai tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta, nan da nan gumi ya rika yanko mata ta ko'ina, rokon shi ta fara yi. "ka taimaka ka kyale ni wlh Aljanu aka turo suka binne abin nan kuma wanda yayi aikin ya fada mana cewa duk wanda ya taba wannan asirin shi ma sai yayi hauka irin wanda matar Mudi tayi,ka rufa min asiri ka kyale ni" Sake daka mata tsawa yayi yace ko tana so ko bata so sai ta hake abin da hannunta. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 8⃣5⃣ Gigicewa Habi tayi hawaye ko ta ina zuba yake a kan fuskar ta, sake tsugunnawa tayi tana rokonsa amma ya toshe kunnuwan sa yaki saurararta, innah karime na kwance duk ta zama abin tausayi da kyar take iya bude baki tayi magana, cikin karfin hali ta fara yiwa mai magani magana. "Dan Allah malam ka dubi girman Allah kayi mana alfarma kada ta taba abin nan, wlh ita kadai ta rage mai kula da ni, jikanta mai jin tausayina ya samu tabin hankali, ni kuma yanxu ba nida ido ita take min jagora ta bani abinci tayi min duk abinda ya kamata, dan Allah ka duba wannan Al'amari kayi mana rangwami " Babu alamar tausayi a fuskarsa ya dubeta. "me yasa lokacin da xaku aikata sharrin baku dubi girman Allah kun fasa ba, kunga kuwa tunda baku ji tsoron Allah kun ki aikata sabo ,nima bazan fasa mayar muku da sharrin ku kanku ba, don haka dole sai ta dakko abin nan da Kanta ta warware, tunda hannunku ne ya ajiye, kema Allah ne ya rufa miki asiri wannan bala'in ya afka miki amma wlh da kinga yadda xan mayar da ke a cikin gidan nan" Jin wadannan maganganun da yake fada ne yasa innah karime taja baki tayi shiru, tun daga lokacin bata sake cewa komai ba. Sake dakawa Habi tsawa yayi jikinta na rawa ta mike ta nufi karkashin gadon Ammi, taimaka mata suka yi suka tayata janye gadon sannan ta fara tono abinda suka binne. Tana tonawa tana hawaye, wani wari ne na tashin hankali ya rika fitowa daga ramin, a hankali ta rika hakowa har sai da taxo dai-dai wajen da aka binne asirin, wata tukunya ta dakko wadda aka nadeta da fata ga kuma layu da aka kewayeta da su, karba mai maganin yayi ya ajiyeta a gefe, cigaba da tonawa tayi sai kuma ga gafiya an saka laya a bakinta duk jikinta ita ma an xagaye shi da layu, sai da ta gama fito da kayan tsafin tsaf, sannan ta koma gefe ta tsaya. Cikin fushi mai maganin ya dubi Habi. Kin fito da kaya saura kuma warware su, ke kika kulla kuma Kece xaki kwance. Nan ma dai tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta saboda tasan matukar ta warware wadannan kaya kashinta ya bushe. Sake dubanta yayi yana xare mata idanu ki warware nace kafin naci mutuncin ki. Cikin kuka ta dubi Abban nauwar "yanzu mudi a gabanka xa a tozarta ni a ci min xarafi amma kayi shiru baka ce komai ba, amma wlh idan ka bari aka ci min mutunci baka cika dan halak ba, ka tuna a matsayin uwa nake a wajenka" Ransa a bace ya mayar mata da martani. "babu abinda zance sai dai Allah ya Kara, dama hausawa sun ce idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, gashi nan kin gina kina tunanin ni kadai da iyalaina ne xamu fada ciki, to gashi nan kema kin fada cikinsa, kuma wannan kadan kika gani daga cikin illar zalunci wata shari'ar ma sai a lahira dan wallahi baxan taba yafe abinda ku ka yi min ba" Ya karasa maganar yana kuka.. Cikin kulawa mai magani ya dube shi. "kada ka damu Alhaji sai fa ta warware abin nan, ko da hakan xai yi sanadiyyar mutuwarta dama irin su ba su da amfani a cikin al'ummah gara ta mutu kowa ya huta " Kuka Habi ta rika yi saboda taji an ambaci mutuwa gaba daya ta gigice sai faman magiya take yi. Umarni ya kara bata a kan tace fara warware asirin da hannunta, wani hayaki ne da duhu suka turnike dakin, ga kuma wari na tashin hankali, tana warware asirin yanayin halittar ta da kamanninta suna juyewa suna komawa irin na dabbobin daji, shi kansa mai maganin sai da abin ya bashi tsoro, sai da ta gama warwarewa gaba daya ya umarceta ta tashi.. A hankali taja jiki ta koma kusa da innah, wani bacci mai nauyi ne ya dauketa dan haka suka fito suka bar dakin.. har kofar gida Abban nauwar ya raka mai magani sannan yayi masa alkhairi mai yawa. Godiya mai magani yayi masa sannan ya dube shi. "Alhaji na gode da wannan karamcin naka ina mai tabbatar maka da cewa mutanen nan sai sun ga karshen su, ka jira xuwa lokacin da matar nan xata farka xaka ga abinda xai faru, fatana dai kada kayi sake da addu'a saboda gidan nan naka sun lalata shi da shaidanu yanzu haka shaidanu ne cike a cikinsa, don haka sai ka dage da karatun kur'ani." Godiya Abban nauwar yayi masa sannan suka yi sallama ya tafi. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 8⃣6⃣ Kai tsaye daki ya wuce ya fara tunanin halin da su habi suka jefa kansu, tashi yayi ya rika kewaye dakin yana jinjina irin mugun halin su, alwala ya dauro ya fara jero salloli yana addu'a Allah ya bayyana masa matarsa da yarsa. A ranar bai runtsa ba addu'a ya rika yi sosai yana neman taimakon ubangiji, bai kwanta ba har sai da yayi sallar asubah sannan ya koma bacci. Cikin mafarki ya jiyo ihu da hayaniya a firgice ya farka,salati ya fara yi, sannan ya dakata don jin daga ina hayaniyar take, sakkowa yayi daga gadonsa yana kewaye dakin, har yanxu dai bai daina jin hayaniyar ba, da gudu ya nufi falo, yana dosar wajen yaci Karo da Habi ta shaqe innah karime tana ta faman dukanta, cikin xafin nama ya karasa wajen. cikin tsawa yake mata magana "ke lafiyar ki cika ta mana, bakya ganin halin da take ciki" Tsawa ta daka masa sannan tayo kansa da duka, kwancewa yayi ta samu bango. duk iya kokarin da yayi don ya kwaci innah karime ya kasa, da gudu ya fita kofar gida yana neman taimakon jama'a, da kyar ya samo mutum biyu suka shigo gidan, kasancewar duk mutanen Unguwar haushinsa suke ji saboda abinda ya yiwa Ammi da nauwar, kokawa sosai suka rika yi da habi a kan ta saki innah amma taki sakinta kasancewar gaba daya bata cikin hankalinta ta xama mahaukaciya tuburan, idanunta sun yi ja, fuskarta ta xama baka kirin, kokawa dai suka rika yi da ita, cikin xafin rai take musu magana. "baxan cikata ba sai na hallakata ita ce ta kashe mana jikoki " Xance take yi mara kan gado, Lallabata suka shiga yi a kan ta kyaleta da kyar aka shawo kanta aka kwaci innah da kyar tana nunfarfashi duk ta galabaita. Cikin hanxari suka tura habi daki suka kulleta, ita kuma innah karime suka dauke ta sai Asibiti, a ranar ko magana bata iya yi saboda wuyar da ta sha a Hannun habi, sai da aka yi mata karin ruwa. Washe gari da sassafe Abban nauwar ya dauketa sai Dan batta, Baffa na ganin yadda innah karime ta koma ya fara hawaye, cikin kuka Baffa yake magana "Me nake gani haka Mahmud lafiya me kuma ya Kara faruwa da ita" Kan Abban nauwar a kasa ya fara yi masa bayani. "Wlh Baffa ina daki ina bacci naji hayaniya ashe wai goggo habi ce ta kamata da duka kamar xata kasheta Yanxu haka daga Asibiti muke " Cikin karfin hali Baffa yake magana. "kayya amma wannan abu bai yi dadi ba, me innah tayi mata haka da xata yi kokarin hallakata" "bata yi mata komai ba Baffa ta samu tabin hankali ne don yanxu bata gane komai" A raxane Baffa ya dago "tabin hankali fa kace Mahmud " "Wlh Baffa, yanxu haka ma sai kulleta nayi a daki sannan na samu na fito, ni kaina kokarin dukana take yi, abin nata ya bani tsoro sosai " Kuka Baffa yake yi sosai. "ga irin ta nan mutum yayi mugun abu ya koma masa kansa, menene amfanin irin wannan ga tarin xunubi a wajen Allah ga Hauka gashi abin duniyar da ake kwadayi ba a same shi ba, yanxu idan ta mutu a haka me xata cewa Allah " Rarrashin Baffa Abban nauwar ya rika, ita kuwa innah tayi shiru sai sharbar kuka da take yi, cikin kuka take magana. "Bahaushe yayi Gaskiya da yace idan xaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, Wallahi wannan sharrin duk mu muka yi ya Koma mana kanmu, mudi ka yafe mana mu ne muka haukata matarka muka kada yarka muka juyar maka da tunani, ka yafe mana nasan idan muka mutu da hakkinka Allah baxai sassauta mana ba, Kaima ka yafe min, ta nuna baffan Mahmoud, na rabaka da danka na hana yaji kanka" Kallon kallo Baffa da Abban nauwar suke yi ji suke kamar a mafarki suke jin wadannan maganganun nata. Cikin nutsuwa Baffa ya dubeta. "na yafe miki innah, Allah ya yafe mana gaba daya" Hawaye Abban nauwar ya mayar mata da amsa "innah ni ba nida abinda xance saboda iya cuta kun cuce ni sai dai nace Allah ya bi mana hakkin mu,duk wanda ya xalunci wani tsakanin ni da Ku Allah ya saka masa" Tashi yayi xai bar wajen Baffa ya riko shi. "Dawo mudi bana so ka fita a cikin bacin rai kada wani abin ya sameka kayi hakuri ko a yanxu sun ga qarshen su,Allah ya huci xuciyar ka, ga babban albishir xan baka, ka sanarwa habi cewa na saketa saki uku kada ta kuskura ta dawo min gida, kuma xan nemi yayanta na Kara jaddada musu, ita ma innah don mahaifiyata ce ita ta kawo ni duniya babu yadda xan yi dole na xauna da ita, ina umartarka dan Allah kana komawa gida ka kori habi duk inda xata tafi taje, ai duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai iya ba" Innah karime kuka take tana rokon gafarar Abban nauwar amma ko kulata yaki yi, rokon Baffa ta shiga yi. "kai kuwa kasa baki ya yafe min mana tunda yana jin maganarka " "gaskiya baxan takura masa ba innah saboda wannan hakkin sa,shi yake da ikon yafe miki, ko ni na xalunce shi Allah sai ya saka masa, don haka ki cigaba da addu'a Allah ya sakko masa da fushinsa ya yafe miki" A take Baffa yasa aka kirawo su Isah yayan habi ya shaida musu hukuncin da ya yanke, kuka suka rika yi suna jimamin halin da mahaifiyarsu take ciki, Audu ne Kawai yayi karfin halin yin magana "Wlh dama Baffa ina Jin ciwon abubuwan da suke wa mudi Kawai don ba nida ikon hanawa ne shi yasa nayi shiru, gashi nan ta jawowa kanta hauka tana xaman xamanta" Isah ne ya hau xage-xage. "Wlh wannan haukan hada ta aka yi da shi, mu babu inda muka gaji hauka" Innah karima ce ta fara magana. "A dakata a saurareni wlh tallahi babu hannun kowa a cikin wannan Al'amrin mu muka jawo shi da kan mu, dan haka kada a Kara xargin Kowa habi ita tayi jagorancin haukata matar mudi gashi nan yanxu ya koma kanta, iyakar mu Allah ya fara nuna mana tun kafin aje lahira" Tana gama jawabin sai kuma kunya ta kama Kowa a gurin wasu na kuka wasu kuma sun kasa magana saboda bakin ciki , haka Abban nauwar ya fito ya barsu suna jimami, Kudi mai yawa ya bawa Baffa sannan ya kama hanyar dawowa gida. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 8⃣7⃣ Tun a hanya yake sake-saken yadda xai bullowa Al'amarin habi, saboda baya jin xai iya cigaba da xama da ita a wannan halin da take ciki na hauka. Yana isa gidan wani abin mamaki ya gani, gaba daya ta karya masa kofofin gidan ta fito waje, kwance ya tarar da ita kan yashi yara na jifanta da duwatsu ta cire dan kwalin kanta, tana bin su a guje tana duka, yana karasawa wajen ta yo kanshi xata dake shi cikin fushi ya fara yi mata magana. "Waye yace Ki karya min kofar gida Ki fito, gashi nan ai kin fito yara na jifanki kamar shaidan" Bata kula shi ba ta cigaba da bin yaran tana dukan su tare da jifansu da dutse, dawowa tayi ta cigaba da birgima a cikin yashin yara na yi mata waka. "Habi mahaukaciya in ta mutu ba ruwan Allah, walakiri ya jibgi kayansa" Suna mata wakar tana tsalle tana juyi, idan kuma ta gaji ta koma kan yashi ta cigaba da jifan su, wani bakin ciki ne ya kama Abban nauwar shigewa gida yayi ya kyale yaran suna tsokanarta. Karasawa cikin gidan yayi, ba karamar barna habi tayi masa ba, a xuciyar sa yake magana. "Lallai wannan shi ake kira da kaikayi koma kan mashekiya, Allah baya xalunci sai dai idan bawa ne ya xalunci kansa, gashi nan ta xama mahaukaciya cikakkiya wacce babu Wanda yasan ranar da xata warke sai Allah " Fita yayi ya kira mai gyara inda ya shiga gyara abubuwan da ta bata, bayan ya kammala ne ya dubi Abban nauwar. "xan tafi Alhaji kuma ina da yar shawarar da xan dan baka, ya kamata ka dauke mahaukaciyar nan daga gidanka idan ka barta ba a san irin barnar da xata yi nan gaba ba, kuma xaman ta a cikin Al'umma ba karamar matsala bace don xata iya cutar da su tunda bata cikin hankalinta" Shiru Abban nauwar yayi sai da mai gyara ya gama jawabin saNyan ya bashi amsa "gaskiya nima naga illar hakan, yanxu dama nake shirin kiran yayanta su xo su tafi da ita" Waya ya ciro a aljihu ya kira Isah, sallama Abban nauwar yayi masa, cikin fushi ya amsa sallamar, bai tsaya yayi masa bayanin makasudin kiransa ba ya haushi da xagi, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, har Yanxu bai yarda cewa mugun abinda suka yi bane ya koma musu kan su. Murmushi Abban nauwar ya yi sannan ya mayar masa da amsa. "dadin abin dai Kowa yasan abinda mahaifiyarka tayi min, abinda tayi a bayyane yake Kowa ya sani ba sharri aka yi mata ba, nayi niyyar na kaita Asibiti a rika bata magani amma tunda naga abin naka ba mutunci kaxo ka dauki uwarka, don baxan bari ta Kara Kwana a gidana ba" Bai jira amsar da xai bashi ba ya kashe wayar. Hakuri mai gyara ya rika bashi a kan ya bari ta Kwana gobe su dauketa amma yaki yarda, kudinsa ya dakko ya bashi sannan ya mayar da kofa ya kulle, ta taga yake jiyo hayaniyar yara da jifan da suke yi mata, duk sun farfasa mata goshi sai jini ke faman xuba, ko kadan bai ji tausayinta ba saboda ita ta jawowa kanta. Bayan ya dan kwanta ne don ya huta yaji ana buga masa kofa, lekawa yayi don ganin wanda yaxo. Hamdan ya hango a bakin kofar yana ta fara'a da hanxari ya karasa ya bude masa kofar, cikin sakin fuska yayi masa magana "Sannu da xuwa Hamdan yau kaine a gidan namu" Tsugunnawa Hamdan yayi ya gaida shi sannan suka shiga cikin gidan, Hamdan ne ya dubi Abban nauwar yana masa magana. "Yau din nan fa farin ciki baya misaltuwa a xuciyata har gida aka xo aka fada min albishir din abinda ya samu matar nan, wlh ba karamin farin ciki nayi da hakan ba, bayan an fada min wannan abin dadin Kuma, sai na sake ganin wani abin alkhairin da idona" Cikin sakin fuska Abban nauwar ya dube shi "wane abin alherin ka gano mana Hamdan " Gyara xama yayi "Yau ina gida ina ganin labarai Kawai naga an saka hoton ammi da nauwar ana cigiyarsu " Cikin Farin ciki Abban nauwar ya rungume Hamdan yana tambayarsa. "alhamdulillah a wane gari suke yanxu" "suna Kaduna unguwar rimi" Godiya Abban nauwar ya yiwa Allah a take ya dauro alwala yayi nifilar godiya ga Allah. Juyo da kallonsa yayi ga Hamdan. "yanxu xamu tashi mu tafi ko" Murmushi Hamdan yayi "A Haba Abba saurin me muke haka mu bari dai sai gobe ko" Da kyar ya yarda suka bar tafiyar xuwa gobe, hirar su innah karime suka rika suna tattauna yadda karshen su bai yi kyau ba. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 8⃣8⃣ Kiran Abban nauwar aka yi a waya cikin nutsuwa ya mika hannu ya dauka, Kara wayar yayi a kunnensa,da sallama ya fara sannan yayi shiru don sauraren abinda xai fito daga bakin mai maganar, gaisawa suka yi sannan mai maganar ya fara bayani "nasan baka gane ni ba Alhaji Audu ne dan uwan ka mun xo tafiya da goggo ne" Cikin sakin fuska Abban nauwar ya mayar masa da amsa. "Allah sarki sannu da xuwa Audu ya hanya, gani nan xuwa na bude maka kofa " Da sauri ya fita don bude masa kofar, a bakin kofar ya tarar dashi tsaye tare da Isah ko kallon Isah bai yi ba ya mikawa Audu hannu suka gaisa. dudduba gurin ya shiga yi mamaki ne ya kama shi da bai ga habi ba. Cikin rashin mutunci Isah yake magana.. "ina ka Boye mana uwar mu mugu axxalumi wanda bai san alkhairi ba, ka fito mana da ita ko ranka yayi mummunan baci" Audu ne ya dakatar da shi daga fadan da yake yi "Haba Isa me yasa Kake yin haka ne, Kawai sai ka hau fada baxa ka tsaya a bi komai a hankali ba" "Sai da aka cuce mu aka haukata mana uwa xaka ce nabi abu a hankali baxan bi ba" Cikin kulawa Abban nauwar ya dubi Audu. "ka kyale shi ya xage ni ba wannan ne Karo na farko da ya fara xagina ba, dama ya riga ya saba" Hakuri Audu ya rika bashi.. "kada ka damu ba komai" Cikin gida suka shiga ya fara nunawa Audu irin barnar da habi tayi masa, bayan ya gama nuna masa ne ya fara yi masa bayani. "kafin na dawo daga Dan batta, na tarar tayi min wannan barnar da yake dama a daki na kulleta na tafi, shi ne ta balle kofofin ta fice, ta koma kofar gida ta xauna, ban yi xaton ta tashi ta sake tafiya wani wajen ba, yanxu abinda xa a yi mu kewaya bayan layi ko xamu ganta" Fita suka yi suka fara binciken inda ta tafi amma babu ita babu dalilinta, tambayar mutane suka shiga yi amma duk wanda yaji batun neman habi ne sai yayi tafiyarsa ya kyale su a tsaye, shi kansa Audu sai da jikinsa yayi sanyi da wannan bakin jini da habi take da shi. Komawa kofar gida suka yi suka tsaya suna tunanin yadda xasu bullowa lamarin, daga can nesa suka hangota ta taho a guje ta dora tarin tsummokarai a kanta, yara na biye da ita suna jifanta, da sauri Audu da Isah suka karasa wajenta, magana suka fara yi mata. "goggo haka kika xama Innalillahi wa innah ilaihi raji'un, ya aka yi haka ta afku da ke goggo" Xare musu ido tayi ta fara jefo musu duwatsu, domin gaba daya bata gane su ba, matsawa kusa da ita Isah yayi ya karbi daurin kayan sannan suka kamata da kyar aka saka ta a mota suka tafi da ita gida. Kudi mai yawa Abban nauwar ya bawa Audu sannan suka yi sallama ya tafi. Wajen Hamdan Abban nauwar ya koma ya sanar da shi yadda suka yi da Isah mamaki ne ya kama hamdan. "Lallai ma Isah ba shida tunani, duk abinda matar nan tayi maka bai gani ba har yana da bakin xaginka, Allah ya kyauta" Bayan sun gama tattaunawa ne Hamdan ya yi masa sallama ya tafi gida. A daren ranar da Abban nauwar xai tafi Kaduna bai ko runtsa ba saboda farin cikin xai hadu da iyalinsa da ya rabu da su lokaci mai tsawo, salloli yake yana godiya ga Allah da wannan niima da yayi masa. Washe gari karfe bakwai na safe ya gama shiryawa tsaf, gidan su Hamdan ya nufa inda yayi sallama da mahaifinsa har cikin gida ya shigar da shi yayi sa'a kuwa sun shirya tsaf suna jiran xuwan sa. Basu wani bata lokaci ba suka dauki hanya sai Kaduna, basu fi awa biyu suna tafiya ba suka isa Kaduna, inda suka tambayi mutane a nuna musu hanyar da xasu yi Unguwar rimi, cikin kankanin lokaci suka isa unguwar inda suka tambayi gidan su saimah aka nuna musu. Yaro suka samu suka aika cewa ana sallama da maigidan, a tsakar gida yaron ya tarar da su suna karyawa, da sallama ya karasa wajen su sannan ya fada musu aiken da aka yi masa. Tanbayarsa Abban saimah yayi.. "wane ne yake sallama da farar Safiya haka? " Cikin nutsuwa yaron ya bashi amsa. "wasu mutane ne su uku, sun ce na fada maka baki ne daga kano" Nauwar na jin an ambaci baki daga Kano ta dubi saimah "Nifa ina ji a jikina Abbana ne yaxo" Saimah na murmushi ta dubeta "to sarkin garaje kya bari dai su shigo a ga kowane ne ko" Suna cikin wannan maganar ne ta jiyo murya Abbanta yana waya, tashi tayi a guje ta fita don ganewa idonta abinda take tunani. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Masoyana na gode da addu,ar samun lafiya da kuka yi min Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci* 8⃣9⃣ Tsaye ta tarar da Abbanta ya tsurawa kofar gidan ido yana shirin ganin wanda zai fito daga ciki, nauwar ya gani ta taho a guje, hannu ya bude mata ta fada jikinsa tana murmushin farin ciki. "Oyoyo Abbana, yaushe rabon da na ganka har na manta, ban taba tunanin xan sake ido biyu da kai ba, nayi zaton na barka har abada, Abba makiya sun saka katanga a tsakanina da kai, mun yi kewarka sosai ni da Ammi, mun sha wuya da bana tare da kai" kafin ta kammala maganar tuni hawaye ya cika idonta. Toshe mata baki yayi hawaye na xuba a fuskar shi. "kiyi hakuri "yata yau Allah ya kawo muna karshen wahalar da muke ciki, kamar yadda ku ka yi kewata haka nayi naku, tun da kuka bar gida ban kara samun nutsuwa ba sai yau, ki daina zubar da hawayen ki, yanxu ba lokacin kuka bane lokaci ne da xamu yi farin ciki da Allah ya hada mu da juna" Share mata hawayen ya shiga yi da hannunsa. Waiwayawa gefenta tayi, sai a lokacin tasan da su Hamdan, har kasa ta tsugunnah ta gaida baban Hamdan sannan ta mayar da kallonta ga Hamdan. Wani tattausan murmushi ya sakar mata gami da kallo mai cike da tausayawa, cikin sassanyar muryar sa ya amsa mata gaisuwar ta, suna cikin gaisawa Abban saimah ya fito da dukkan yan uwanta, Ammi na hada ido da Abban nauwar ta kawar da kanta gefe hawaye ne ke sauka cika idonta, karasowa yayi daf da ita yana rarrashinta. "Kiyi hakuri Raihab ki dauka duk abin nan da ya faru kaddara ce, Allah yana sane da halin da muke ciki" Cikin gida suka shiga gaba dayan su, abinci Kala Kala aka kawo musu, Sai da suka xuxxuba musu sannan suka fita gaba daya suka bar dakin don su samu damar cin abincin. Bayan sun kammala Abban saimah ya shigo dakin. Wajen zama ya samu sannan suka fara tattaunawa, Abban nauwar ne ya fara magana. "Alhaji mun gode da wannan karamcin da kayi mana, nayi farin cikin yanayin da na tarar da iyalaina Allah yayi maka sakamako da aljanna" Murmushi Abba yayi "Ba komai ai d'a na kowa ne, kuma duk wanda ya taimaki wani Allah xai taimake shi, Allah ya kiyaye faruwar hakan a gaba" Gaba daya suka amsa da ameen, Abban Hamdan shi ma addu'ar fatan alkhairi ya yiwa Abban saimah, bisa ga wannan alkhairi da yayi musu. kiran wayar baffa aka yi suka hada shi da Abban saimah shi ma yayi masa addu'a da godiya, hira suka xauna suna yi sosai basu tashi tafiya ba sai wajen karfe hudu na yamma, kira Abban saimah ya kwalawa nauwar cike da ladabi ta karaso dakin. tsugunnawa tayi tare da sunkuyar da kanta kasa. Abbanta ne yayi magana "nauwar kice da Amminki ta shirya xamu tafi yanxu" Idanun nauwar ne suka cika da hawaye sbd jin abinda Abbanta ya fada. "Yau xamu tafi Abba? " Amsa mata yayi da eh Hawaye ne ya ke sauka a kan fuskarta "Abba dan Allah ka kyale mu xuwa wani satin mu taho, ban yi sallama da kawayena na makaranta ba" Murmushi yayi ya dubeta "to shikenan sarkin kuka na bari ki gama sallama da kowa sai naxo na dauke ki " Abban saimah ne yayi saurin tarar numfashinsa. "Aa ka bari Alhaji xan kawota ma da kaina ita da Aminiyar tata" ran Hamdan bai so hakan ba sai dai ba halin yayi magana dole yayi shiru tunda manya sun sa baki. Cike da farin ciki nauwar ta tashi ta fita, fadawa Ammi sakon Abbanta tayi, ran ammi bai so ba ta tashi ta bisu, har bakin mota mutan gidan su saimah suka raka su, sannan suka wuce suka tafi. Kai tsaye Dan Batta suka wuce, suna isa suka shiga dakin Baffa yana ganin su ya Mike ya tarbe su cikin sakin fuska.. "Alhamdulillah Allah mun gode maka sannu da xuwa yata Barka da arxiki" Wajen zama suka samu gaishe shi suka yi cike da girmamawa, cikin sakin fuska ya amsa musu, Abban nauwar ne ya bashi labarin yadda aka samu su Ammi, ba karamin farin ciki yayi da haka ba. "mun gode Allah da wannan abin alkhairi da ya same mu, mun shiga kunci a baya gashi yanxu Allah ya kawo mana sauki, shi yasa dogaro ga Allah yake da riba gashi nan mun ga sakayyar da Allah yayi tun a duniya, 'yata Allah yayi miki albarka bisa ga hakurin da kika yi, Allah ya baki Ladan jarrabawar da kika shiga, dan Allah ina son kada ki rika tuna abubuwan da suka faru a baya ki dauka hakan kaddara ce kuma jarrabawa ce aka Yi miki gashi nan yanxu kin cinye, duk wadanda suka cutar da ke sun xama abin tausayi, innah Mahaifiyata ta makance duk jikinta babu abinda yake matsowa komai sai dai a yi mata, ita kuma dayar abokiyar xaman babar Mahmoud ta haukace yanxu haka ta baxama daji tun shekaran jiya ake nemanta ba a ganta ba, shi ma dayan mai taya su aikin sharrin yanxu haka baya gane komai ya bugu a kansa ga jikinsa ya karye, kafarsa daya ta rube an yanke ta. Duk wadannan abubuwan da suka faru, Allah ne ya miki sakayya tun a duniya kafin kuma a je lahira Allah ya tantance mai gaskiya, ki kwantar da hankalinki ki yiwa mijinki biyayya ku dawo rayuwa kamar yadda kuke yi a da cikin farin ciki da kwanciyar hankali " Sun ji dadin wadannan kalaman na Baffa godiya mai yawa suka yi masa sannan suka tashi suka tafi saboda basa son yin dare a hanya, har xasu bar dakin baffa ya kira sunan su. "Amma dai ba tsohon gidanka xata koma ba ko Mahmoud " Tsugunnawa yayi sannan ya amsa masa. "nan xata koma baffa" Girgiza kai Baffa yayi. "Ba zai yiwu ta koma wannan gidan ba saboda har yanxu baxa a rasa mugwayen shaidanu a ciki ba, ka gyara mata daya gidan naka ta koma " Amsawa Baffa yayi da to Sannan ya bashi kudi masu yawa. Albarka ya shiga saka masa. "Allah ya kula da bayanka kamar yadda kake kula dani Mahmoud na gode dan Allah ku karasa wajen innah ku gaisheta. Wajen innah karime suka shiga tarar da ita suka yi tana ta numfarfashi kamar xata wuce lahira, gaisheta suka yi da kyar take iya magana. Bayani Abban nauwar ya fara yi mata. "innah ga maman nauwar fa taxo ta gaishe ki ta samu lafiya yanxu babu abinda yake damunta" Wani hawaye ne ya rika zubawa daga idon innah karime. Cikin kuka take magana "Allah sarki Baiwar Allah ki yafe min cutar da nayi miki, baki min komai ba na dora miki Karan tsana wlh kuskure ne ki yafe ni dan Allah " Shiru Ammi tayi bata cewa innah komai ba haka ta rika surutai tana sambatun ta yafe mata, amma bata samu amsa daga wajen Ammi ba. Tashi suka yi suka fita suka barta a wannan halin. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣0⃣ Gidan su Hamdan suka wuce cikin farin ciki mama ta tarbe su, abinci kala-kala ta kawo musu sannan suka fara hirar yaushe gamo, cikin tausayawa ta dubi Ammi. "ikon Allah ban taba xaton xaki dawo daidai ba Rehab kin shiga cikin mawuyacin hali sanadiyyar wadannan axxaluman, Allah ya dube mu da idon rahma ya baki lafiya, dole mu gode masa" murmushi Ammi tayi. "Nima nayi mamaki da aka rika bani labarin yadda na xama a da amma gashi yanxu komai ya xama tarihi, Allah ya kara kiyaye mu daga sharrin masu sharri" amsa mata tayi da "Ameen" sallamar Hamdan ce ta katse musu hirar da suke yi, da sakin fuska ya nufo wajen su,wajen xama ya samu yana fuskantar Ammi yana magana. "Yauwa Alhamdulillah dama so nake ku dawo a yi wata magana" gaba daya suka mayar da hankalin su gare shi "wace magana kuma xa a yi" gyara xama ya yi yana dan murmushi. "maganar aurena da Nauwar mana ko xuba min ido xa ku yi nayi ta xama a gauro" Harar shi mama tayi. "lallai xan baka sarautar rashin kunya Hamdan, yanxu a ce ko kunyar idona baka ji ba kake wannan maganar, lallai dan xamani" murmushi Ammi tayi. "ni fa Hamdan dan gidana ne kin san ba jin kunyata yake yi ba, ya saba irin wannan rashin kunyar a gabana" dariya kawai Hamdan yake yana sosa kewa. "to yanxu mama dan nace ina son aure ai ban yi rashin kunya ba, kiga fa abokaina da yawa sun yi wasun su har da yaya" dukan bayansa mama tayi. "ni tashi ka bamu guri mara ta ido, xamu yi magana anjima" mikewa yayi sai da ya kai bakin kofa ya kalli mama yana dariya. "mama yau fa xa a yi maganar nan dan na kosa naji Abinda aka yanke" yana gama fada ya fice. cikin mamaki mama ta dubi Ammi "lallai halin yaran xamani sai dai a kalle su kawai, yanxu yaro har xai iya furta yana son aure dan rashin kunya, Allah dai ya shirya mana yaran mu" Hira suka cigaba da yi sannan suka tattauna maganar auren Hamdan da Nauwar da lokacin da ya kamata a yi, sannan kuma suka yanke shawarar samun maxajen su don su yi musu maganar. A bangaren Nauwar kuwa samun saimah tayi a daki tana kwalliya matsawa kusa da ita tayi, tana murmushin farin ciki. "ni fa ba karamin dadi nake ji ba kawata da Abbana ya bar ni xan karasa hutu a nan,amma da an ce na bi su Ammi, ban san bakin ciki da irin kewarku da xan yi ba" juyowa saimah tayi tare da dafa kafadarta. "wlh nima haka kawata, dama dai Abba xai bar mana ke a nan da naji dadi, yanxu idan ma kin tafi dole mu yi kewar juna,komai fa tare muke yi, ya xamu ji idan wata ra muka wayi gari bamu ga junanmu ba" idanun Nauwar har sun fara kawo ruwa. "Har bana son ranar nan taxo wlh, saboda ban san irin yanayin da xan tsinci kaina a ciki ba" cike da kulawa saimah ta dubeta. "dan Allah mu bar wannan maganar saboda xata iya bata mana farin cikin mu" rada saimah ta yiwa Nauwar a kunne, a xabure Nawwar ta dubeta. "yaya fa kika ce saimah, shi yace ki fada min haka" "Eh mana ya dade da bani wannan sakon amma yace kada na fada miki har sai an samu iyayenki saboda idan na fada miki a lokacin xaki iya shiga damuwa shi yasa na fada miki yanxu" maganar nan bata yiwa Nauwar dadi ba saboda tana ganin girman yaya sadeeq saimah ce ta lira da yanayin da ta tsinci kanta. " ya naga yanayin ki ya canja ko bakya son yayan nawa ne" xare idanu Nauwar tayi. "Haba ni na isa nace bana son yaya sadeeq ko dan karamcin da kuka yi mana, kawai dai ina jin kunyar yadda xan cigaba da kasancewa a gidan nan ne" hararta saimah tayi. "Haba Nauwar sai kace ba yar birni ba, mun xama daya fa da ku, ki dauka kece yar gidan nan shi yaxo bakunta ki saki jikinki nasan yaya baxai takura miki ba dan shi mutum ne mai saukin kai,kuma baxai so ya ganki a damuwa ba" "shikenan kawata na gode da karfafa min gwiwa Allah ya bamu dacewa" Hirar duniya suka fada suna yi suna shewa, a daidai lokacin yaya sadeeq ya shigo dakin, da sallama ya karaso wajen su, Nauwar na ganinshi ta kwantar da kanta a kan gado wai ita a lallai bacci take. kiran sunanta yayi cikin salo mai kayatarwa, shiru tayi ba tare da ta amsa ba, sake kiranta yayi a hankali ta bude ido ta dago ta kalle shi mayar da kanta tayi saboda yanxu gaba daya nauyin shi take ji, murmushi yayi sannan ya sake yi mata magana. "tunda kunyata ake ji bara na tashi na fita kada na hana ki sake wa" mikewa yayi da niyyar barin dakin, yana maganar yana kallon saimah, cikin xaulaya saimah tayi masa magana. "yaya ka kwantar da hankalinka ba kunyarka take ji ba, fuskar masoyinta principle take son a gani" A xabure ta dago ta kaiwa saimah duka "wlh karya take yaya kawai kaina ne yake ciwo" shi dai yaya sadeeq dariya kawai yake, ficewa yayi ya barsu suna abin su. Cikin tunani Nauwar ta kwana xuciyarta sai shawarwari take bata, ta karbi soyayyar sadeeq ko kada ta karba, wata xuciyar tace ta karba wata kuma ta tuno mata da maganar Hamdan da irin gudunmawar da ya basu a haka ta kwana tana wadannan tunanin. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba daya naki ne halak kiyi yadda kike so da shi, SISTER FURERA MUHAMMAD (Maman Hauwa) ina yinki ina kaunar ki, Allah ya bar xumunci da kaunar juna* 9⃣1⃣ Yau tun safe nauwar bata fito ba a daki ta wuni saboda tana jin kunyar fitowa tsakar gida don kada ta hadu da yaya sadeeq ya rika sakar mata wannan asirtaccen murmushin nasa mai sanya mata kasala, don ko gaida mama da Abba bata fita tayi ba, shirun da mama taji ne babu motsin ta a waje shi yasa ta shigo dakin dan jin dalilin da yasa bata ganta ba. Kwance ta tarar da nauwar kanta na kallon sama da sallama ta shigo dakin, tsayawa tayi ta karewa nauwar kallo sannan ta karaso inda take. A hankali ta dago kai ta Kalli mama, tare da tashi xaune. "sannu da gida mama" Cikin sakin fuska mama ta amsa. "yauwa nauwar, lafiyanki yau gaba daya ban ji motsinki ba, ko dai tunanin Amminki kike yi baki fada mana ba" Murmushi nauwar tayi. "A'a mama yau bana jin dadi ne kawai " Cikin kulawa ta dubi nauwar. "Ayya Allah ya baki lafia amma ai bai kamata kiyi shiru baki fada min ba, shikenan da ban shigo ba haka xaki xauna da ciwo a jikinki baki yi magana ba" Kiran saimah mama tayi cikin xafin nama ta karaso dakin Tsugunnawa tayi. "Gani mama" "yanxu dan sakarci Kin san nauwar ba lafiya amma baki fada min ba, sai da na shigo yanxu naga yanayinta nasan ba tada lafiya da ban shigo ba sai dai ciwo yayi ta cin jikinta kenan Allah ya shirye Ku yaran nan" Dariya saimah take yi "Lallai mama Kina cikin gidan nan amma ana binne Ki, duk abinda yake faruwa baki sani ba, to nauwar lafiyarta kalau " Cike da mamaki mama take duban saimah, ita kuwa nauwar kara danna kanta tayi cikin bargo saboda ruwan da saimah ta ballo mata " Magana mama ta cigaba da yiwa saimah "kin fara magana kuma kin yi shiru, ni fa wannan sakarcin ne bana so" Duban nauwar saimah tayi tana dariya. "na fada ko nayi shiru? " Shiru nauwar tayi mata ba tare da ta bata amsa ba, sai hararta da take yi kawai. Cikin kakkausar murya mama ta sake maimatawa saimah tambayar da tayi mata. "xaki fada min ko sai na Saba miki" Murmushi saimah tayi tana kallon mama. "mama ya naga duk kin tashi hankalin Ki abin farin ciki ne fa xai faru ke dai kiyi addu'a kawai " "to naji ko na Farin cikin ne ki fada min yanxu ina saurarenki" Rufe fuska saimah tayi. "da ke da Ammi kun xama surukai mama" Cikin mamaki mama ta jawo saimah ta xaunar da ita tana kallon fuskarta. "da gaske kike ko kuma xancen Ku ne na yara" "Wlh da gaske nake mama yaya Sadeeq yana son nauwar " Farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta. "kai amma naji dadin wannan al'amari ashe xumunci baxai yanke tsakanin mu da Ku ba nauwar, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ai kuwa xan samu sadeeq yanxu yasan da wannan abin alkhairin bai fada min mun yi magana da ammi ba har ta tafi" Saimah ce ta bata amsa. "to ai kunyar ki yake ji ne mama shi yasa bai fada miki ba, kuma baya son a fada miki saboda kada nauwar ta rika jin kunyar ki ta kasa sakewa a gidan nan" Mikewa mama tayi tana magana.. "ni ai nauwar ba surukata bace yata ce duniya da lahira dan haka ni ba wani sarakuta da xa mu yi da ita" Fita mama tayi ta bar dakin xuciyarta cike da Farin cikin faruwar wannan al'amari. Mama na barin dakin nauwar ta dago tana harar saimah. "kin bata min rai wlh me yasa xaki fadawa mama, ni kin jawowa kanki ma gobe xan yi tafiyata gida" A firgice saimah ta dago fuskar nauwar tana bata hakuri. "kiyi hakuri sisina menene amfanin boye abin da xa a yi, gara a fada mata ta sani, Kinsan na kosa na fara xuwa gidanki cin taliya" Duka nauwar ta kai mata. "Ai da yake ke xama xa kiyi ba auren ko, Allah yasa sai an yi bakin ki xa a yi nawa" Murmushi saimah tayi mata. "ni da ko mijin babu gara ke kin samu, naki xa a fara yi duk abin ki yarinya " Juyar da kai nauwar tayi tare da cewa ba amin ba. Tashi saimah tayi. "Nauwar Ki tashi kin manta xamu je gidan kawayen mu ki fara yi musu sallama ko kin manta ne? " A hankali ba dago ta bata amsa. "tunda kika bata min rai na fasa" Rarrashinta ta shiga yi har sai da ta tashi suka tafi. A daren mama ta fadawa Abba abinda taji daga bakin saimah, ba karamin farin ciki Abba yayi ba dama ya dade yana wannan tunanin. Don haka suka yanke shawarar kiran sadeeq don Kara tabbatar da maganar daga bakinsa. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *A yi min afuwar rashin ji na kwana biyu hakan ya faru ne sakamakon abubuwa da suka yi min yawa* 9⃣2⃣ Bayan sallar magariba ya sadeeq ya tafi don dakko su Nauwar, a bakin titi ya tsaya, kiran wayar saimah yayi inda ya shaida mata cewa yana jiran su, cikin sauri suka hada kayan su suka fito inda suka samu rakiyar kawar su Halima, wacce kuma dama gidan su suka je. tun daga nesa ya sadeeq ya hango Nauwar, cikin nutsuwa take taku daya bayan daya, wani kallo mai cike da soyayya yake mata tare da sakar mata kyakkyawan murmushi mai kayatarwa, har sai da taji kunyar kanta, har suka karaso wajen hankalinsa na kan Nauwar bai san ma sun iso ba, gaida shi Halima tayi amma bai san ana yi ba,sai da saimah ta dan taba kafadarsa. "yaya ina hankalinka yake haka, mun karaso amma hankalinka na wani wajen ga Halima na ta gaisheka tun daxu" a raxane ya dago yana murmushi. lafiya lau ya amsa mata dashi, sannan ya cigaba da aikin kallon Nauwar. sake taba shi saimah tayi. "yaya wai yau ina hankalinka yake tafiya ne?" murmushi yayi "Ayya sorry my saimah, nayi nisa a tunanin tauraruwar matan da haskenta ke haske sararin samaniya shi yasa kika ga yau din nan sai a hankali". turo baki saimah tayi. "dama kana da wata tauraruwa ne bayan sisina" murmushi yayi tare da dafa kafadar saimah. "nima ai ita nake nufi sarkin fushi wato har ranki ya baci ko, to ina so kisa a ranki Nauwar ita ce mace daya tilo da na bawa gurbi a wannan xuciyar tawa, kuma har abada baxa ta taba fita ba" tsalle saimah tayi tare da rungume ya sadeeq. "na gode yayana na kaina Allah ya kaimu lokacin auren ku mu sha biki" cike da sakin fuska ya amsa mata da Ameen duk xancen da suke yi a kunnen Nauwar duk nauyi da kunyar ya sadeeq ta mamaye ta, a hankali ta bude murfin motar ta shiga gidan baya, juyowa yayi ya kalleta, cikin sassanyar murya yake mata magana. "Tashi ki dawo nan kusa da ni Nauwar" makale kafada tayi alamar. "aa" cikin rarrashi da lallabawa yace ta dawo ta xauna, kin tashi tayi sai da saimah tayi mata magana a karo na biyu sannan ta tashi ta shiga, kanta a sunkuye yake ta kasa hada ido da ya sadeeq shi kuwa sai janta da hira yake yana mata barkwanci, saimah ce kawai take taya shi, a haka har suka iso gida. A kofar gida suka ci karo da Abba, kiran sunan su yayi gaba daya suka karasa wajensa suka xube don jin Abinda xai fada musu. Fada ya fara yiwa yaya sadeeq. "me yasa baka je ka dakko yaran da wuri ba har sai da suka yi magariba a waje" kasancewar Abba baya son su saimah su yi dare a unguwa shi yasa ma duk inda xasu je yake sawa a kaisu a kuma dakko su. cikin ladabi ya sadeeq ya mayarwa da Abba amsa. "Na biya Office ne Abba kuma ba a tashi da wuri ba shi yasa na makara wajen dakko su" cikin kulawa Abba ya dube shi. "to shikenan sannunku da xuwa" cikin ladabi suka amsa masa da yauwa. magana Abba ya cigaba da yi saddequ!!!! cikin ladabi ya sadeeq ya juyo ya dube shi tare da amsa wa da na'am Abba. "ina son ganinka bayan sallar isha xamu tattauna wata muhimmiyar magana" kansa a sunkuye ya amsa da "to Abba" tashi suka yi suka shiga cikin gida. dakin mama suka shiga inda suka tarar da ita da bakuwa don haka suka koma dakin su don gabatar da sallar magariba, bayan sun idar ne wayar Nauwar ta fara ringing don haka tayi saurin daukan wayar, number Ammi ta gani cikin hanxari ta kara wayar a kunneta. cikin nutsuwa tayi mata sallama. "Ammina barka da dare" cikin tattausayar murya ta mayar mata da amsa lafiya lau daughter ya kowa da kowa" amsa mata tayi da lafiya lau. bayan sun kammala gaisawa ne take tambayarta. "ya kamata fa ki dawo gida daughter akwai muhimman abubuwan da ake so a tattauna da ke, abin baxai tafi daidai ba har sai kina nan" rausayar da kai Nauwar tayi tare da cewa. "to Ammina xan taho jibi, amma me xa a tattauna haka Ammi" "Aa ki bari dai ki dao xaki ji komai" sallama suka yi sannan ta ajiye wayar. saimah ce ta juyo ta kalleta. "ya naji kina cewa xaki tafi jibi Nauwar?" "eh Ammi ce tace nayi sauri na dawo akwai muhimman abubuwan da xa a yi, ni ake jira na dawo" Ajiyar xuciya saimah tayi tana duban Nauwar. "nima kuwa wlh baxan tsaya ba tare xamu tafi, tunda dai ba a koma makaranta ba" murmushi Nauwar tayi. "nima nafi son mu tafi tare dan bana so na tafi na bar ki a nan jin gidan xan yi duk yayi min xafi" Hirar su suka cigaba da yi suna tattauna yadda xasu shirya tafiyar su jibi. da sallama yaya sadeeq ya shiga dakin Abba, a xaune ya tarar da shi yana karatun kur'ani, tsayawa yayi har ya kammala yayi addu'a suka shafa tare, a ladabce ya dubi Abba "Gani Abba" cike da kulawa ya dubi dan nasa "Saddeequ ina so ka tattaro min hankalinka ka bani shi nan" gyara xama yayi. "to Abba ina saurarenka" gyaran murya Abba yayi sannan ya fara magana. "wato na fuskanci akwai alaka mai karfi tsakaninka da wannan yarinyar Nauwar" gaban ya sadeeq ne ya fadi, saboda bai san me Abba xai ce dashi game da nauwar ba, cikin hanxari ya amsa masa da eh "wannan dalilin yasa naga ya dace indai har da gaske kake kana son yarinyar nan kayi mana magana mai kyau, mu kuma mu samu mahaifinta mu nemar maka aurenta" wani dadi ne ya tsirgawa sadeeq tun daga baban yatsansa har xuwa kwakwalwarsa, nan da nan farin ciki ya bayyana a fuskarksa cike da fara'a ya bawa Abba amsa da. "ina sonta Abba" ba karamin dadi Abba yaji da wannan amsa da ya bashi ba, cikin farin ciki ya dube shi. "Alhamdulillah naji dadin jin wannan maganar daga wajenka, don haka baxa mu yi kasa a gwiwa ba xamu nema maka aurenta, fatan mu dai kada ka bamu kunya ka rike yarinyar nan da kyau da amana" kansa a kasa ya amsa masa. "Insha Allahu xaku yi alfahari da auren nan Abba, fatana dai ku cigaba da yi min addua" "Addua Kullum a cikinta muke, fatan mu dai Allah ya tabbatar da alkhairan da ke ciki ya kade dukkan sharri, gobe idan Allah ya kaimu xan kira babanta na shaida masa, daga baya kuma sai mu je mu yi magana ido da ido" xuciyar ya sadeeq fes ya tashi ya bar dakin. da tunanin maganar da Abba ya fada masa ya kwana, ya kosa gari ya waye yaji amsar da ta fito daga gidan su Nauwar duk da cewa dai yasan baxa su hana shi aurenta ba. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣3⃣ Nauwar da saimah ne suka fito da sauri daga dakin su dakin mama suka nufa inda suka mika mata wayar da ke hannun su tare da cewa Ammi ce xa tayi magana da ke, karbar wayar tayi ta kara a kunneta tare da yin sallama cike da annashuwa suke magana, a nan Ammi ta shaida mata cewa Jibi Nauwar xata taho gida, mama bata so tafiyar Nauwar ba amma dole ta hakura sbd yanxu ita ce 'ya daya tilo da tayi ragowa a wajen iyayenta, a ranar mama ta bawa Nauwar kudi inda saimah ta rakata kasuwa suka yi siyayyar tafiya. Ya sadeeq ne xaune a Office gaba daya yau ya kasa sukuni jira kawai yake yaji sakamakon da xai fito daga bakin Abba, gashi har karfe hudu na yamma Abba bai kira shi ba, tashi yayi ya nufi gida don yau yana jin baxai iya aikata komai ba indai bai samu muradin xuciyarsa ba, A hankali cike da nutsuwa yake tuki, addu'a kawai yake yi, Allah yasa yaji alkhairi daga bakin Abba, yana isowa kofar gida ya fito daga motar, sai da ya tsaya yayi tunani na wasu yan mintuna sannan ya karasa cikin gidan, tarar da su saimah yayi suna ta fito da kayan da suka siyo a kasuwa, a hankali ya nemi gefe ya xauna kusa da mamah, jujjuya kayan ya shiga yi yana yaba kyan su, A hankali ya mayar da kallonsa ga mamah, tare da tambayarta ina Abba yake, cikin nutsuwa ta bashi amsa da yana cikin daki. wani farin ciki da dadi ne suka sauka a cikin xuciyarsa, cikin nutsuwa ya mike yana taku a hankali har ya isa bakin kofar dakin, tsayawa yayi ya gyara tsaf, sannan ya taka a hankali ya shiga dakin tare da sallama, a kashingide ya iske Abba yana laxumi, dagowa yayi tare da amsa sallamar. wajen xama yaya sadeeq ya samu, kansa a kasa yake magana. sannu da hutawa Abba ranshi a sake ya amsa masa da yawa Saddeequ ya aikin, ashe har ka dawo dagowa yayi tare da sakin takaitaccen murmushi. eh nima yanxu na shigo Abba. murmushi Abba yayi tare da duban ya Saddeeq. "nasan dai tatsuniyar gixo bata wuce ta koki, a kan maganar nan kaxo min nan, wato kaji shiru har ka kosa kaji abinda muka yi da su ko" dago kai yayi tare da sosa keya. "aa Abba dama naxo ne na gaisheka ne naga tunda na shigo ban ji motsinka ba, amma dai har da wannan maganar ma, ya ku ka yi da su Abba" duban shi Abba yayi yana murmushi. Allah ya shirya mana ku yaran xamani, yanxu yaro da kansa yake xuwa jin labarin auren sa mu kuwa a da sai dai a yi mana komai, har amaryar ma wani lokacin bai fi sau daya xaku hadu ku gaisa ba,daga nan sai aure kawai. numfashi Abba yaja sannan ya cigaba da magana. "na kira mahaifinta mun yi magana da shi ta fahimta, ya fada min cewa........." saurin dagowa ya Saddeeq yayi don jin abinda xai fito daga bakin Abba. Abba ya lura da yanayin yadda ya saddeq ya kosa yaji yadda suka yi. "ya naga har ka tsorata saddeequ tun kafin na fada maka abinda yace dani" A hankali ya dago manyan idanunsa, tare da yin dan murmushi. "ba tsorata nayi ba Abba" "yauwa yaron kirki a harkar aure babu tsoro, kowa rabonsa xai aura babu wanda xai auri matar wani kaji ko" amsa masa yayi da to sannan ya cigaba da magana. "ya shaida min cewa yarinyar nan suna soyayya da wani dan uwanta wanda dashi suka xo gidan nan, nasan ma ka ganshi" wani kishi da bakin ciki ne suka tokare makogoron ya sadeeq da kyar ya iya amsawa Abba da eh. "to wannan yaron shi ne yake sonta tun tana yarinya kuma ita ma ya tabbatar min da cewa tana son shi, dan sun shaku sosai sai dai kawai ba a yi maganar auren su ba, yace idan kana ganin xaka iya shigowa cikin manemanta sai ka shigo yana maraba da kai, ya tabbatar min da cewa babu alfarmar da xamu nema a wajensa ba tare da yayi mana ba,idan kana ganin xaka iya neman aurenta to kofa a bude take" wata Ajiyar xuciya ya sadeeq ya saki, idanunsa sun yi ja, ya dago ya dubi Abba. "to shikenan Abba Allah ya xaba mafi alkhairi amma ina ganin kafin lokacin ya kamata nayi istikhara na nemi xabin Allah ina ganin xai fi sauki" ba karamin dadi Abba yaji ba shi yasa yake son sadeeq sbd hangen nesan sa, cikin farin ciki ya bashi amsa. "hakan yana da kyau sadeeq Allah yayi jagoranci" amsawa yayi da aameen. jikinsa a sanyaye ya fita ya bar dakin, ba karamin tafasa xuciyarsa take yi ba, ya tsani hada taraiya da wani a kan abinda yake so, gashi har wani ya shiga xuciyar yarinyar da ya gama tsara rayuwarsa da ita, tunanin ta inda xai fara bullowa lamarin ya shiga yi, dakinsa ya bude yana shiga ya fada kan gado tare da runtse idanunsa ko xai ji saukin hayakin da ke taso masa daga kasan xuciyarsa, xikirin Allah ya fara yi, sbd shi ne kadai abinda xai saukaka masa damuwrsa domin yanxu ji yake gaba daya duniya tayi masa xafi babu wani abu da xai faranta ransa idan ba xikirin ba. *Jeeddahtulkhair😘🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣4⃣ Kansa ne yake rika juyawa a hankali ya tashi xaune ya dafe kan nasa tare da rungumar pillown da ke hannunsa, innalillahi ya shiga ambata, bai san inda xai tsoma rayuwarsa ba idan har aka ce ya rasa Nauwar, lokaci guda ta shiga xuciyarsa ta samu gurin xaman da fitarta sai an sha wuya, ba karamin axaba rayuwarsa xata fada ba idan aka ce wani ya kwace masa abar kaunarsa, a hankali ya ja jiki ya shiga bayi ya daura alwala ya fara jero nafila rokon Allah yake yi sosai har da xubar da hawaye yana neman agaji, ya bashi nasara a bisa abinda yasa gaba sannan ya xaba masa abinda ya fi xama alkhairi a gare shi, yana gamawa ya shafa ya nemi guri ya cigaba da xurfafa tunanin guguwar da take shirin tunkaro shi. Har bayan sallar magarib yana daki ya kasa yin katabus idanunsa sun yi jawur,da ganinsa yana cikin tsananin damuwa, kamar daga sama yaji mama na kwala masa kira, da hanxari yaja jiki ya shiga cikin gida a bakin kitchen ya sameta, da flask din abinci a gabanta, tunda ya nufo wajenta ta bishi da wani kallo mai cike da ayoyin tambaya jikinta ya bata dan nata yana cikin matsananciyar damuwa, duk wani walwalarsa da nishadinsa sun ragu, ganin kallon da take masa ne yasa ya karfafa jikinsa tare da sakin rai yana fara'a ya karasa wajenta, tsugunnawa yayi yana fuskantarta. "gani mama" cike da damuwa da halin da yake ciki ta bashi amsa. "me yasa yau ka shige cikin daki ban ganka a cikin yan uwanka ba, bana xaton yau a jama'i kayi sallah, sannan ga abincinka har yana shirin salamcewa amma babu labarin xuwanka duk da cewa nasan baka wasa da cikin ka, fada min abinda yake damunka"? hadiye damuwarsa yayi ya saki rai yana mata magana "babu Abinda yake damuna mama kawai dai bana jin nishadi ne yau din nan" hade rai tayi babu alamar wasa a tattare da ita. "ka fada min gaskiya sadeeq bana son boye-boye ni mahaifiyarka ce duk wani abu naka na sani, nasan farin cikinka nasan akasin haka kaga kuwa babu abinda xai canja a tattare da kai ba tare da na gane ba, dan nasn halin dana sarai ba mutum ne mara son jama'a ba" kasa mallakar xuciyarsa yayi, kafin kace me hawaye ya cika idanunsa tuni ya fara kwarara a saman fuskarsa. hankalin mama a tashe ta dago fuskarsa tana tambayarsa. "lafiya Abubakar me ya faru da kai, ko dai korarka aka yi a wajen aiki" saboda bakin cikin da ya cika xuciyarsa ya kasa magana, rarrashinsa mama take yi kamar yaron goye, sai da yayi kukansa ya koshi ya share hawayensa sannan ya fara yi mata bayanin dalilin kukan nasa, cike da tausayawa ta dube shi. "kayi hakuri sadeeq idan Nauwar rabonka ce xaka samu, nayi mamakin yadda yarinyar nan ta shiga ranka haka lokaci guda, kai da baka sa abu a ranka,kuma damuwa bata hanaka walwala, dan Allah ka saki ranka muna nan muna yi maka addu'a Allah xai xaba maka mafi alkhairi, banda abinka ma yarinyar da ba aure aka daura mata ba kawai cewa aka yi fa da wanda yake sonta, kana da damar da xaka bayyana mata soyayya, idan rabonka ce sai kaga ka aureta har ka haifa min yan jikoki" ta karasa maganar tana murmushi. shi ma ya sadeeq murmushin yayi saboda ba karamin faranta masa mama tayi ba da ta ambaci yayan da xai samu a jikin Nauwar, lallaba shi ta rika yi har sai da ya saki ransa ya ci abincin sosai ya manta da duk damuwar da ta dame shi. yau ta kama litinin kuma ita ce ranar da Nauwar xata koma gida, tun safe ta kammala shirye-shiryen da xata yi, tana daki ta xuba tagumi tana kukan rabuwa da gidan su saimah, ita ma kukan saimah ke yi saboda ba karamar shakuwa suka yi da juna ba, kiran sunan su Abba yayi da hanxari suka taso suka fito tsakar gida, cikin kulawa yake musu magana. "kukan me kuke yi Nauwar, ai ba a rabu ba ana tare kuma xa a rika xumunci ku share hawayenku" hannu suka sa suka shiga share hawayen "yauwa ko ku fa, to ku dakko jakar kayan ku yanxu xamu tafi kano,baba son yin dare a hanya" wani sabon kukan suka cigaba da yi, ita ma mama hawaye ne suka cika idanunta amma taki bari su xubo, saboda bata son hankalin yaran ya sake tashi, jakar kayan suka dakko suna tafe suna kuka rungume mama Nauwar tayi da kyar aka cireta daga jikinta, suna kuka suka rabu, kiran ya sadeeq Abba yayi don shi ne xai ja motar da xasu yi tafiyar da ita. fitowa yayi daga dakinsa sanye yake da shadda golden colour wadda aka yiwa aiki da xare kalar shaddar,hularsa ma kalar kayansa ne haka ma takalmin da ke sanye a kafarsa, ya kuma sanya agogo wanda ya kara fitar masa da wankan sa, ba karamin karbar jikinsa kayan suka yi ba, yayi matukar yin kyau sai dai kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa don a yan kwanakin nan har ya dan rame. Abba ne yayi masa magana. "mu shige mu tafi ko sadeeq" A ladabce ya amsa da to Abba. kama hanyar tafiya suka yi, su Nauwar sai faman kuka suke duk irin rarrashin da Abba yayi musu suka ki dainawa sai hakura yayi ya kyale su, sai da suka kusa shigowa kano sannan suka Hakura. kama hanyar xuwa gidan su Hamdan suka yi tunda yanxu a nan Ammi take, kasancewar gidan da ake gina mata ba a kammala shi ba, a kofar gida suka hango Hamdan tsaye yana jiran isowar su Nauwar, hannu shi rungume yake a kirjinsa, kallon motar da ke nufo kofar gidan su yake yi, kamar a mafarki ya hango Nauwar tana masa murmushi, cikin doki da shaukin son ganinta ya karaso wajen, parking ya sadeeq yayi sannan ya matso daf da su, cikin ladabi yake gaida Abba, cikin sakin fuska ya amsa masa, hannu ya mikawa ya sadeeq shi ma fuskarsa a sake ya mika masa suka yi musabaka, juyo da kallonsa yayi wajen Nauwar wani kallo yake mata yana wani kashe mata ido, murmushi ya rika sakar mata,ita ma murmushin take masa cikin shagwaba take masa magana. "Na tafi na dade nasan ko missing dina ma baka yi ba" Cikin marairaicewa yake mata magana "Haba queen ya xa a yi na manta da ke, indai xan manta da ke ai xan mant da kaina" duk maganganun da suke yi a kunnen ya sadeeq, ji yake xuciyarsa kamar ta fito saboda kishi da bakin ciki, da sauri ya fito daga motar ya koma gefe ya tsaya saboda baxai iya jure kallon wannan bakin cikin ba, sai da suka gama maganar su tsaf sannan ya shigar da su cikin gida a sitting room aka sauke su, su kuma su Nauwar suka wuce cikin gida. Ruwa da abinci aka kawo musu, an karrama su sosai,an yi musu karbar mutunci, ruwa Abba ya dauka ya sha sannna ya dubi sadeeq. "ka dauki ruwan ka sha mana sadeeq mun sha hanya ai kana bukatar kasha ruwa" muryar shi a dashe ya bawa Abba amsa. "bana jin kishiruwa na koshi" ji yake kamar ya fashe da kuka sbd abin takaicin da ya gani yanxu,da na sanin xuwansa yake yi da ya xauna a gida duk da bai ga wannan abin takaicin ba, baya jin yau xai iya runtsawa saboda tsananin kishin da ya cika zuciyar sa. Sallamar Ammi da Abban nauwar ne ya dawo da shi hankalinsa, cike da ladabi ya gaishe su, hira suka fara yi da Abba tare da yi masa godiya abisa karamcin da yayi musu, da kulawa da su da yayi na tsawon wani lokaci ba tare da ya nuna gajiyawa ko kosawa a bisa haka ba. fuskar Abba a sake yake basu amsa. "ba komai ai mun xama daya da ku, Allah ya kara mana dankon xumunci" gaba daya suka amsa da ameen komawa ciki Ammi tayi ta bar su da Abban nauwar don tattaunawa dangane da maganar auren sadeeq da Nauwar. Abban nauwar ne ya fara bayani. "naji dadin wannan maganar da ta fito daga wajen ku Alhaji " Cikin sakin fuska Abba ya bashi amsa "ban tari bunfashinka ba Alhaji ni ina ganin mu bar maganar auren nan" gaban ya sadeeq ne ya fadi jin Abba yace a bar maganar aurensa. da sauri Abban Nauwar ya dubi Abba. "ya xaka ce a hakura Alhaji"? "ba wani abu ne yasa nace a bar maganar ba, sai don yarinyar nan tana da wanda take so, shi ma kuma yake sonta, idan aka ce sadeeq ya shigo cikin masu neman aurenta ina ganin ba a yi mata dalci ba, saboda tuntuni da akwai wanda xuciyarta take so ta kuma saba da shi, ni kuma duk abinda yarinyar nan take so wlh ina son sa saboda tamkar 'yata ta cikina na dauketa" "Haka ne Alhaji nima nasan da haka, amma ni a tsarina a kuma yadda na dauke ku, yanxu babu abinda xai sa ku nemi alfarma a gurina nayi watsi da ita, baxan iya hana danka abinda yake so daga wajena ba, saboda haka ne ma nake so a yi maslaha, ko yarinyar nan tana so ko bata so haka xa a yi, Hamdan ya nemi saimah su dai-daita, shi kuma sadeeq ya auri Nauwar haka na yanke" wani farin ciki ne ya xiyarci xuciyar ya sadeeq ji yayi kamar an yi masa albishir da aljannah, duk ya nemi damuwar da ke xuciyarsa ya rasa. saurin dakatar da Abban nauwar Abba yayi. "Aa baxa a yi haka ba Alhaji a bawa yara abinda suke so, mu so muke Yi, su yi aure su xauna lafiya ba so muke su yi mana jeka ka dawo ba, don gaskiya baxan yarda da wannan hukuncin naka ba domin ina son farin cikin diyata, baxan bari a yi mata auren dole ba kawai saboda a farantawa sadeeq,ko yanxu na gani da idona yaran nan suna son junan su,ba karamar matsala xa a samu ba idan aka ce xa a farraqa tsakanin su, shi sadeeq din yayi hakuri mana tunda tun tuni bai yi magana ba, kaje kayi tunani sosai a kan wannan maganar tawa, abinda ka yanke sai mu yi magana ta waya" Ba karmin haushi ya sadeeq yaji ba, da Abba yaki karbar kudurin Abban nauwar, haka suka cigaba da tattaunawa akan maganar amma sam Abba yaki yarda a bawa nauwar ya sadeeq, basu bar gidan ba sai da suka yi sallar la'asar sannan suka tafi, ita kuma saimah a nan suka barta saboda xata karasa hutunta na makaranta. *Jeeddahtulkhair😘*[9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣5⃣ A ranar da su Abba suka koma kaduna bacci mai dadi yaya sadeeq yayi, don har mama sai da ta lura da yadda yake cikin farin ciki ya saki ransa ya daina xama cikin Kadici, addu'a ya rika yi Allah ya tabbatar da alkhairin da ke cikin auren su da nauwar. Su Nauwar ne xaune a falo tare da su Ammi da mama tana basu labarin irin gararin rayuwar da suka shiga kafin su hadu da gidan su saimah, da irin abubuwan da Ammi ta rika yi a lokacin da take cikin rashin lafiya, sai a lokacin take fada mata sharrin da su innah karime suka yi mata cewa ita ta kashe fu'ad.A daidai lokacin Abbanta ya shigo tare da Abban Hamdan xaunawa suka yi aka cigaba da hirar da su, ba karamin tausayawa junan su suka yi ba bisa halin da suka fada a baya, a lokacin Abban Nauwar yake sanar da su cewa sun kusa komawa gidan su sbd an kusa kammala musu ginin da ake yi. ba karamin farin ciki Ammi tayi da jin hakan ba, cigaba da bada labari Nauwar tayi wajen tausayi su tausaya human su wajen dariya kuma a hadu a yi dariyar tare, har suka xo daidai wajen da take basu labarin xaman su a gidan su doctor Abdallah da irin gallaxawa da cin xarafinsu da Hajiya take yi ita da yayanta, tunowa tayi da complement card din da doctor Abdullah ya bata, da alkawarin da tayi na nemansa a duk lokacin da ta samu iyayenta, da sauri ta tashi ta shiga daki ta bude jaka ta xaro card din. Karasowa kusa da Abbanta tayi tare da mika masa card din, cikin sassanyar murya take masa magana. "Abba wannan shi ne mutumin da ya tausaya mana ya kula da mu kamar yadda aka yi mana a gidan su saimah, Shi ne mutum na farko da ya taimaka mana dan Allah ba dan wata manufa ba, sai dai mahaifiyarsa tafi karfinsa domin ita ta kore mu daga gidan, saboda a tunaninta wai mun mallake mata d'a yana ta yi mana wahala" Hannu biyu yasa ya karba tsayawa yayi ya duba katin sosai, dagowa yayi ya kalleta yana maimaita sunan da ke rubuce a jikin katin . "Abdallah Sani fataskum!!!!!" sake dubanta yayi "Wannan mutum shi ne ya taimake ku? " Gyada kai tayi alamar eh "to ai wannan yaron 'kani ne a gurina, ku ne dai baku san shi ba, tunda bama xiyartar juna, mahaifinsa Alhaji sani fataskum, dan uwan mahaifiyata ne, muna xumunci da mahaifinsa sosai yana xuwa gidan mu wajen Baffa,nima a da ina xuwar masa xiyara sai bayan ya rasu alaka ta yanke kasancewar matarsa ba tada kirki bata son kowa ya rabe shi, baxan yi mamaki ba dan kun ce an yi muku haka a gidan su, xasu aikata fiye da haka ma, don wannan kadan ne daga irin mugun halin uwar su" Hannu yasa a aljihu ya ya shiga lalubo wayarsa, copy na lambobin da ke jikin katin yayi sannan ya fara kira, cikin sa'a kuwa bugu daya aka dauka, da sallama ya fara magana cike da tausasawa aka amsa sallamar. bayani Abban Nauwar ya fara yi masa. "kana magana da dan uwanka daga kano garin dan batta" murmushi doctor yayi. "masha Allah naji dadin kiran nan naka, kamar dama kasan ina nan ina fafutukar neman yan uwan mu na kano amma fafur Hajiya ta hana adress, amma dan Allah kayi Hakuri ban gane muryar dan uwan nawa ba" "kana magana da Mahmud nasan kafi sanina da Mudi ko" cikin farin ciki ya amsa tare da yin takaitaccen murmushi "kwarai kuwa, ya gida da yara" amsa masa yayi da lafiya lau, sannan ya fara yi masa godiya da abin arxikin da ya yiwa su Nauwar. "ina godiya sosai da abin arxikin da ka yiwa iyalina Allah ya saka maka da alkhairi" cike da mamaki yake tambayarsa "iyalinka kuma?? yaushe na taimake su" murmushi Abban Nauwar yayi. "nasan ka manta sbd an dauki Lokaci mai tsawo da faruwar hakan, idan baka manta ba akwai wata mahaukaciya da wata yarinya da ka taimakawa ka kaisu gidan ku, ka fara canja musu rayuwa daga bakin ciki xuwa farin ciki, sai da wani dalili yaxo ya gifta sannan ku ka rabu, to wannan mahaukaciyar mai dakina ce, ita kuma yarinyar Nauwar 'yata ce" salati doctor ya fara yi. "ikon Allah ashe ma yar uwata na taimakawa, wlh na tausayawa halin da suke ciki a lokacin shi ne ma yaja hankalina har na kai su gida saboda basa cikin kwanciyar hankali, amma dai yanxu mara lafiyar taji sauki ko?" "Taji sauki har sun dawo gida dama haukan ba nata bane hadata aka yi da shi amma yanxu komai ya dawo daidai, yanxu muke mayar da maganar sai Nauwar ta tuno da card din da ka bata ina dubawa naga sunanka a jiki nace baxan iya jurewa ba har sai na kiraka na gode Maka Allah ya saka da alkhairi" ba karamin dadi doctor yaji ba da Allah ya mayar da su nauwar kyakkyawan hannu dama kullum addu'ar da yake yi musu kenan, tunda suka rabu da su bai taba shiga farin ciki irin na yau ba sbd tunda suka tafi bai kara ji Ko ganin mai kama da su ba. magana ya cigaba da yiwa Abban Nauwar "ina nauwar din take idan tana kusa bani ita mu gaisa" mika mata wayar yayi suka fara gaisawa. "sannu Nauwar ya bayan rabuwa" A ladabce take amsa masa maganarsa, bayan sun gama gaisawa ne ta mikawa Abbanta wayar suka yi sallama. Hannu doctor ya daga sama yana godiya ga Allah, a lokacin ya dauki mukulli ya yiwa motarsa key sai gida a falo ya tarar da hajiya da kannensa suna hira, labarin yadda suka yi da Abban nauwar ya shiga bata "oh!!! amma wlh naji kunya ashe yar ma tamu ce,nayi musu wannan korar karen yanxu da wane ido xan kalli ubanta wlh nayi nadamar abinda nayi musu, shi yasa ba a son wulakanta dan Adam baka son ko wanene shi ba, Allah yasa dai yarinyar nan bata fadawa ubanta irin cin mutuncin da muka yi musu ba" tashi doctor yayi ya bar hajiya tana ta subadi duk ta shiga damuwar rashin mutuncin da tayi musu. A kullum sai doctor ya kira Abban nauwar sun gaisa yanxu xumuncin su ya kara karfi sosai, ita kuwa Hajiya don kunya taki yarda a bata Abban nauwar su gaisa. *jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣6⃣ Haka rayuwar su Nauwar ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki, rayuwa mai dadi suke yi a gidan su Hamdan, a dan xaman da saimah tayi a gidan su Hamdan ba karamin sabo suka yi ba saboda shi mutum ne mai son mutane da saukin kai, tsakanin nauwar da Hamdan kuwa suna gudanar da soyayyar su cikin kwanciyar hankali. wayar da ke gefen Abban Nauwar ce tayi ringing hannu yasa ya dakko tare da kara wayar a kunnensa, cikin sakin fuska ya ambaci sunan mai kiran. "Sadeeq barka da yau, ya ku ka je gida" cikin ladabi ya amsa da lafiya lau..... shiru yayi na wani dan lokaci Abba ne ya katse shirun tare da cewa. "Da alama kana cikin damuwa Sadeeq ka fada min duk abinda yake damunka" shiru yayi ya kasa cewa da Abban Nauwar komai sai da ya sake maimaita masa tambayar sannan ya saki ransa ya fara magana"Abba a kan maganar nan ne da muka yi game da aurena da Nauwar naji shiru baka ce komai ba, Abba ma kuma bai ce min komai ba" Sauke ajiyar xuciya yayi sannan ya fara yi masa bayani. "haka ne Sadeeq nayi shiru da maganar ne sbd ina dan son na gama wasu shirye-shirye, amma yau Insha Allah xan samu Nauwar din nayi mata magana duk yadda muka yi da ita xan fada maka" godiya mai yawa ya Sadeeq ya yiwa Abba sannan suka yi sallama xuciyarsa cike da farin ciki. A lokacin ya shirya ya nufi gidan su Hamdan don sanar da Nauwar abinda yake son fada mata, a sitting room ya xauna inda ya kira Ammi ya sanar da ita yana son ganin su ita da Nauwar, bai fi minti biyu da fada musu ba suka karaso wajensa, A xaune suka same yana jiran isowarsu, kujera Ammi ta samu ta xauna ita kuma Nauwar ta xauna a kasa, cikin ladabi ta gaida Abban nata, sannan suka gaisa da Ammi bayan sun kammala ne ya fara magana. "Nasan xa ku yi mamakin kiran ku da nayi gaba daya, ina so mu yi magana ne a kan auren Nauwar" gaba daya suka bayar da hankalin su gare shi, gaban Nauwar kuwa sai dukan uku-uku yake yi. gyaran murya yayi sannan ya cigaba da magana. "Na duba naga babu wanda ya dace ya auri Nauwar sai Sadeeq saboda irin taimakon da iyayensa suka yi mana, kuma ya nuna yana son yarinyar nan idan har muka ce baxa mu bashi ba ina ganin mun yi butulci" A xabure Nauwar ta dago ta kalli Abba, fuskarta ce ta canja daga farin ciki xuwa bakin ciki, Ammi ta lura da yanayin da yar tata take ciki, ita kanta bata ji dadin hukuncin da yayi saurin yankewa ba tafi son a shawarci yarinyar a ji abinda xuciyarta ta amince da shi. katse shirun da suka yi yayi, "wannan shi ne xabin da nayi miki Nauwar kuma ina so ki xama mai biyayya a kan haka, shi kuma Hamdan xan same shi na fada masa yaje ya nemi auren Saimah" wani hawaye ne ya fara xubowa Nauwar, a hankali ta lallaba ta tashi ta bar dakin, tana xuwa dakin da suke ta samu saimah na ta sharar bacci wannan yasa ta samu damar yin kuka son ranta, Nauwar na fita Ammi ta dubi Abba. "A ganina bai kamata a yiwa yaran nan haka ba, nasan kasan tsayin shekarun da suka shafe suna son junan su, idan aka ce xa a raba su lokaci daya an xalunce su" fada ya hau Ammi da shi. "Haka na yanke haka kuma xa a yi, sai dai idan ke xaki xugata ta bijirewa abinda nake so" Sake duban shi tayi "yana da kyau kayi dogon naxari a kan wannan hukuncin naka, idan aka yiwa nauwar haka Ina ganin ba a yi mata adalci ba idan ka duba tsawon shekarun da ta dauka cikin bakin ciki da kuncin rayuwa, yanxu fa ta fara dandana dadin duniya sannan kuma a ce xa a kara sakata a halin bakin ciki, gaskiya ka duba wannan al'amarin da kyau" fadan ya cigaba da yi ganin ya dau xafi ne yasa Ammi ta bashi Hakuri ta tashi a bar dakin. A ranar ya samu Abban Hamdan suka tattauna a kan batun, shima dai bai ji dadin hukuncin da ya yanke ba sbd yasan irin soyayyarda ke tsakanin Hamdan da Nauwar. washe gari da safe Abban Hamdan ya kira shi ya fada masa yadda suka yi da baban Nauwar ya kuma bashi hakuri a kan wannan babbar jarabawar da take shirin tunkaro shi. Hawaye ne ya shiga fitowa daga idon Hamdan ta ko'ina idanunsa cike da kwalla ya dubi Mahaifin nasa. "yanxu ya ake son nayi da rayuwata Abba duk tsawon shekarun da na dauka ina son yarinyar nan a ce baxa a bani ita ba saboda wani bare da yaxo daga baya" ya karasa maganar yana kuka mai cike da ban tausayi, dafa kafadarsa Abban nasa yayi yana rarrashinsa. "kayi hakuri Hamdan xan yi iya bakin kokarina don ganin na shawo kansa Amma ni kaina banso hakan ba, Kaje ka cigaba da addu'a Allah ya xaba mana mafi alkhairi" Tashi yayi ya bar wajen idanunsa a rufe yake tafiya, daki ya shiga ko xai ji saukin damuwar da ke damunsa, ji yayi yaci karo da mutum saurin dagowa yayi, ashe ya manta ba dakinsa ya shiga ba dakin su nauwar ya fada, ganinta yayi xaune a bakin kofa ta xuba tagumi tana ta faman sharbar kuka, a hankali ya ja kafa ya xauna daf da ita yana fuskantar ta, bude baki yayi xai mata magana Amma saboda tsananin kuka da bakin cikin da ya cika masa xuciya ya kasa magana, sun fi minti biyar a wannan halin sai da xuciyarsa ta dan yi sanyi sannan ya dubeta. "Nauwar"A hankali ta dago ido ta dube shi, tayi mamakin jin ambatar sunanta da yayi kai tsaye ba tare da ya sakaya ba, saboda rabon da ya fadi sunanta kai tsaye har ta manta, wannan dalilin yasa ta bashi hankalinta sosai don tasan maganar da xai mata mai muhimmanci ce. Kallonta yake ya kasa magana idanunsa sun kada sun yi jawur, karfin hali tayi ta fara yi masa magana.. "dearna ka kira sunana kuma kayi shiru, dan Allah ka fada min abinda yake damunka" Sunkuyar da kanshi yayi bai iya cewa komai ba, sake maimaita masa tambayar tayi. Cikin yanayin bakin ciki muryarshi na shakewa yake mata magana "Ina cikin tashin hankali ana so a raba tsakanina da ke, a bawa mutumin da bai san muhimmancin ki gare ni ba, kwanana ya kare a duk lokacin da aka raba ni da ke, na tabbatar da cewa baxan samu mace kamarki ba, baxan taba son wata mace irin son da nayi miki ba, kisa a ranki daga yanxu xaki iya Jin labarin mutuwa ta a kowane lokaci, xuciyata baxa ta iya jure ganin ki Kina soyayya da wani ba ni ba" Tashi yayi ya fita ya bar dakin kai tsaye dakinsa ya wuce, da sauri nauwar ta biyo shi tana masa magiya. "ka tsaya ka saurare ni dearna wlh nima ba a son raina hakan xai faru ba har yanxu da soyayyarka a xuciyata kuma babu namijin da xan yiwa irin son da nake maka" Juyowa yayi yana share hawaye yana Dubanta. "na gode da soyayyarki gare ni, nima xan ji dadi idan kika yiwa Abba biyayya a bisa xabin da yayi miki, na miki uxuri nauwar nasan Kina sona kuma baki yaudare ni ba, kuma har yanxu ban fidda ran Ki xamo mata a gare ni ba, don haka ki share hawayenki, ki daina yi min asarar su ki adana min su har sai ranar da aka kawo ki gidana a matsayin matata nake son naga kin fitar min da su saboda farin ciki, amma akwai alfarma daya da xan nema a wajen Ki nasan kuma baxa Ki qi yi min ba" Dago kai tayi "xan maka ko menene dearna " Cike da tausayawa ya dubeta. "Dan Allah ki nisanta da ni kinga Yanxu a matsayin matar wani kike, bai kamata na rika magana da ke a koda yaushe ba, yana da kyau mu fara koyawa kanmu rashin junanmu tunda mafarkin mu baxai cika ba" ya karasa maganar yana kuka, kulle kofar dakin ya yi ya fada gado yana kuka mai tsanani, a bakin kofar ta tsaya tana kuka tana shure-shuren kafa. "me yasa xaka yi min haka Abba ka tausaya min ka bani xabin da xuciyata ke so, wlh baxan iya yiwa wani da namiji biyayya ba bayan Hamdan ka duba halin da xan fada Abbah ka taimake ni" A gigice saimah ta fito daga daki ta tarar da nauwar a wannan halin dakin su Ammi taje ta sanar da su halin da take ciki, a sume suka tarar da ita cikin gaggawa suka dauketa sai Asibiti ba karamin tashin hankali saimah ta shiga ba, saboda taji abubuwan da nauwar ke fada tun tana bayi tana wanka sannan ta lura da walwalarta gaba daya ta canja, cikin damuwa take tambayar Ammi.. "Ammi wai me aka yiwa nauwar kuma me ake so a bata wanda bata so" Murmushi Ammi tayi "ba komai saimah Kawai shirmen Ku ne na yara" Xuciyar saimah bata amince da maganar Ammi ba don haka ta takura mata da tambaya amma taki gaya mata abinda ke faruwa, kyaleta tayi tare da yanke shawarar neman Hamdan taji abinda ke damun aminiyarta don shi ma ta lura da shi baya cikin walwala Kwana biyu. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣7⃣ A asibitin suka kwana washe gari da safe Ammi ta kira Abban Nauwar ta shaida masa halin da take ciki, cikin mintunan da basu wuce biyar ba ya karaso asibitin tarar da Nauwar yayi kwance tana ta faman numfarfashi a raxane ya karaso wajen da take girgixata ya shiga yi. "me yake damun ki Nauwar, dan Allah ki tashi kada ki mutu ina sonki wlh ina son farin cikin ki, na fasa baxan miki abinda bakya so ba"duk juyatan da yayi ko dan yatsanta bai motsa ba, a daidai lokacin likita ya karaso wajen da yake dafa kafadar Abban Nauwar yayi. "kayi hakuri Alhaji yarinyar nan xata ji sauki Insha Allah akwai sauran shan ruwanta a gaba kada ka damu kanka, tashi ka biyo ni ina son mu yi ganawa ta musamman tare da kai" bin shi yayi har suka isa Office, kujera ya nuna masa ya xuna sannan ya fara yi masa bayani, "gaskiya Alhaji baxan boye maka ba, babu wata cuta da take damunka yarka face tsananin damuwa da bakin cikin da suka mamaye xuciyarta wanda hakan har yana baraxanar dora mata ciwon xuciya mai tsanani,idan akwai abinda ake wa yarinyar nan wanda bata so a yi hakuri a daina,saboda xata iya rasa rayuwarta a kowane lokaci" ya karasa maganar yana kallon Abban Nauwar, a raxane ya dago ya dubi likitan. "gaskiya ne abinda ka fada doctor duk ciwon da yarinyar nan take ciki ni na jawo mata shi da kaina, kuma in Allah ya yarda xan yi kokarin ganin na kawo mata karshen shi" cike da mamaki likitan ya dube shi. "kai kuwa Alhaji me zai sa ka hada yarka da bakin ciki irin wannan, idan har kana son rayuwarta kayi gaggawar warware wannan kullin da ke cikin xuciyarta, ko dan ka ceto rayuwarta daga halaka" Hannu ya mika masa suka yi musabaha sannan suka yi sallama. yana fitowa ya tarar da Hamdan yaxo suna hira da saimah tausayinsa ne ya kama shi, duk yayi baki ya rame ko hada ido da Hamdan din ya kasa yi saboda yana jin kunyar sakon da ya bayar a fada masa, da ganin shi ba a cikin hankalin shi yake ba, kallo daya xaka yi masa kasan yana cikin matsananciyar damuwa, har kasa Hamdan din ya gaida shi, cikin hanxari yayi saurin barin asibitin don komawa gida yayi shawara da Abban Hamdan a kan abinda yake faruwa. saimah ce ta mayar da kallonta ga Hamdan, "ni fa har yanxu na kasa gane kan ciwon Nauwar, na tambayi Ammi tayi min bayani tace min babu komai, kuma a lokacin da Nauwar din ta fadi naji wasu maganganu da take fada, kuma a bakin dakinka na tarar da ita shi ne ban gane dalilin hakan ba dan Allah ka fada min gaskiya ko akwai kokarin da xan yi don ganin na shawo muku kan matsalar" Ajiyar xuciya Hamdan yayi, idanunsa har sun kawo kwalla saurin sharewa yayi tare da dubanta. "Nasan Nauwar ta baki labarin ko ni wane ne a wajenta, da irin shakuwar da ke tsakanin mu na tabbatar da cewa kema kinga xahiri a aika ce, mun shafe sama da shekaru goma muna son junanmu, yanxu kuma Abbanta yace baxai bani ita ba, wani mutum daban xai bawa, wannan dalilin yasa Nauwar ta fada cikin wannan mawuyacin halin, kuma nima daf nake da fadawa irin halin da take ciki na sani" a firgice saimah ta dago ta kalle shi cikin mamaki take tambayarsa, tare da jinjina kai "Amma ban ji dadin faruwar wannan abin ba, kuma nasan daga inda matsalar take, yayana suke so su bawa tunda ya nuna yana sonta, nasan Abban nauwar yasan kuna on junanku kunya yake ji yace baxai bawa yayana ba shi yasa ya dage a kan haka,amma xan samu ya Sadeeq din nayi masa nasiha ya ceto rayukan da suke da baraxanar fadawa cikin wani hali ya hakura tunda dai dan Allah muka taimaka ba dan wani abu ba, kuma ni bana son naga rayuwar nauwar ta kara shuga wani hali saboda bakin ciki da kuncin rayuwar da suka shiga a baya, fatana a gareka ka cire duk wata damuwa,tunda ina tsakiya insha Allah xa mu yi nasarar ganin kun samu junan ku" cikin farin ciki Hamdan ya dago ya dubi saimah. "Na gode miki saimah Allah ya baki ikon cika mana burin mu Allah ya baki duk abinda kike nema na alkhairi" sallama suka yi, sannan ya wuce gida ko samun damar gaisawa da Nauwar bai yi ba,saboda baccin da take yi, a nan take saimah ta kira wayar Abbanta, cike da ladabi ta gaishe shi ya amsa mata cikin sakin fusa. "Autar Abba kin ji dadin kano kin makale ko neman gida bakya yi ko" murmushi tayi "ina nan xan dawo Abba Nauwar ce ba tada lafiya shi yasa ban dawo ba, yanxu haka ma a asibiti muke waya" hankalinsa a tashe ya tambayeta"me kuma ya samu diyar tawa?" "wlh Abba damuwa ce kawai kuma hakan har yana neman ya haifar mata da ciwon xuciya" Hankalin Abba yayi matukar tashi da jin kalaman saimah "subhanallahi amma abu bai yi dadi ba, ko menene dalilin da yasa ciwon yake baraxanar kamata" Ajiyar xuciya saimah tayi, "A kan maganar aure ne Abba, babanta yace baxai bata wanda take so ba sai dai ya bata ya sadeeq ta hakura tayi biyayya a kan haka, kasan kuma idan aka ce xuciya da abinda take so dole sai an shiga wani hali Abba" haka ne autar Abba, xan yi duk mai yiwuwa wajen ganin maganar nan ta rushe saboda ni kaina ban ji dadin hukuncin da ya yanke ba bana son a rika takurawa yarinyar nan, xan samu sadeeq din xan yi masa magana shi ma kuma baban nata xan kira shi nace masa mun janye" wani farin ciki ne ya kama xuciyar saimah. "yauwa Abba na gode da wannan jihadin da xaka yi" xuciyarta fari tas suka yi sallama, bata matsa daga wajen ba sai da ta kira ya sadeeq, da sallama ta fara yi masa magana shi ma dai da alama yana cikin damuwa, cikin sassanyar murya ta fara yi masa magana, "yayana na kaina ina so ka bani hankalinka xa mu yi wata magana mai muhimmanci kuma ina so ka yiwa abin kyakkyawar fahimta dan Allah" gaba daya ya bata hankalin shi "ina sauraronki kanwata ta kaina" gyara tsayuwa tayi sannan ta cigaba da magana "yayana ceton rai xaka yi ko ma nace rayuka daga fadawa cikin halin qaqa na kayi, Nauwar tana cikin wani hali sanadiyyar ka" xaro idanu yayi tare da tambayarta "sanadina fa kika ce saimah?" "kwarai kuwa sanadinka ne yaya, domin kuwa sanadiyyar son da kake mata ne yasa babanta xai tilasta mata aurenka alhalin kuma da wanda take so saboda yana jin kunyarka da ta iyayenmu baxa mu roki alfarma bai yi mana ba don saboda taimakon da muka yi musu, shi ne nake rokon alfarma dan Allah, ka janye daga maganar nan saboda aure idan aka yi shi da soyayya ya fi dadim kuma bana so a ce yau ka auri matar da bata sonka ta aureka ne kawai saboda biyayya kayi mana alfarma ka ceto ta daga wannan bakar rijiyar bakin cikin da xata fada" Ajiyar xuciya yaya sadeeq yayi sannan ya fara magana "nima naga abinda nayi bai dace ba saimah naxo na shiga rayuwar masoya xan tarwatsa musu duk farin cikin su, a cikin xuciyata dama na fara janyewa ina ta addu'a Allah ya cire min sonta ya xaba min abinda ya fi alkhairi, kiyi mata albishir da cewa ina sonta kuma ina son duk farin cikinta kuma xan cigaba da kulawa da ita a matsayinta na kanwata ki fada mata na janye ta auri hamdan Allah ya sanya alkhairi a ciki ya basu xaman lafiya" tsallen farin ciki saimah tayi tana yiwa yayanta godiya a bisa wannan hakuri da yayi sallama suka yi sannan ta koma daki, yanayin yadda ta shiga cikin farin ciki ne yasa Ammi kallonta tare da tambayarta. "saimah albishir aka yi miki haka naga kina fara'a" matsawa kusa da Ammi tayi "wlh babban albishir aka yi min yaya ya janye nauwar ta auri hamdan, na fadawa Abban mu ma duk yace shi ma ta auri hamdan shi yasa kika ga ina dariya saboda bana son abinda xai batawa yar uwata rai" farin ciki ne ya bayyana a fuskar Ammi "Alhamdulillah amma naji dadin wannan abu Allah ya xabawa sadeeq mace ta gari ta kirki" amsawa tayi da ameen sannan ta karasa wajen Nauwar shafa fuskarta ta shiga yi "tashi sisina Abba da ya sadeeq sun janye ki auri Hamdan ki tashi ki taya ni murna" A hankali nauwar ta bude ido rungume saimah tayi suna murna. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki AUNTY RAMLATU ABBA DANDAGO, ina godiya da yadda kike kaunar wannan littafi* 9⃣8⃣ Ranar cikin farin ciki suka wuni kuma a ranar aka sallame su daga asibitin, sai dai gargadi da likitan yayi musu na aguji batawa Nauwar rai saboda gudun sake fadawa cikin halin da ta shiga. gida suka dunguma suka tafi, waya Nauwar ta dauka ta kira Hamdan cikin kashewar murya tare da kissa take masa magana, wani dadi gami da farin ciki ne ya tsirga masa cikin xuciyarsa saboda ya cire ran samun Nauwar a rayuwar sa, Albishir tayi masa da janyewar Sadeeq wani farin ciki ne ya kama shi addu'a ya shiga yiwa Sadeeq tare da yi masa fatan Allah ya hada shi da mace ta gari. a bangaren Abban Nauwar kuwa tunda ya tafi daga asibitin ya kasance cikin bakin ciki gami da bacin ran halin da ya jefa yarsa a ciki, Allah ya sani yana son Nauwar kuma baya son abinda xai taba mata farin cikinta kunya da nauyin Abban saimah ne kawai xai sa ya tursasata ta auri sadeeq, wani bacin rai ne ya lullube shi ya rasa ina xai tsoma ransa, kwanciya yayi ya daga kanshi sama yana tunanin yadda xai bullowa al'amarin saboda baya son rasa Nauwar, runtse idon shi yayi yana ambaton Allah, wayar da ke gefensa ce tayi kara a hankali ya mika hannu ya dakkota, number Abban saimah ya gani ranshi a sake ya amsa wayar, bayan sun gaisa yake shaida masa abinda suka yanke shi da Sadeeq, Abban Nauwar bai ji dadi ba saboda ya so hada xuria da su saimah Allah bai yi ba,ta wani bangaren kuma yayi farin ciki ko don cikawa diyarsa a burinta, tashi yayi ya nufi asibitin don fada musu abinda ake ciki, yana isa ya tarar da gadon ba kowa mamaki ne ya kama shi dan ganin wajen empty hankalinsa a tashe ya shiga Office din likitan, tarar da shi yayi xaune yana rubuce-rubuce cikin nutsuwa ya karasa kusa da shi, bayan sun gaisa ne yake tambayarsa inda su Nauwar suke, fuskarsa a sake ya bashi amsa"ai mun sallame su tun daxu, ashe basu kiraka sun fada maka ba" "eh wlh basu kira ba, da fatan dai ba jikin ne yayi xafi ba" yana fara'a ya bashi amsa. "tuni yarinyar ta samu sauki da kafarta ta tafi gida, fatana dai a gareka shi ne a kula da bata mata rai, duk abinda xai sakata a damuwa a yi kokari a kauce masa, sbd yanxu ma damuwar ce taso haifar mata da wannan ciwon" "xa a kiyaye Insha Allah, yanxu ma albishir naxo musu da shi na janye wannan maganar kuma na tarar basa nan" "ok kayi hanxari ka sanar da su" sallama suka yi cikin sauri ya nufi gidan su Hamdan, dukan su a falo ya tarar da su ana ta nishadi da sallama ya shiga gaba daya suka mayar da hankalinsu gare shi, Nauwar da saimah ne suka mike suna masa barka da xuwa, cikin sakin fuska ya amsa musu sannan suka gaisa da Ammi da maman Hamdan, guri ya samu ya xauna, ruwa su Nauwar suka kawo masa bayan ya sha ne ya fara yi musu bayanin abinda ya kawo shi, ba karamin farin ciki suka yi da jin wannan albishir daga gare shi ba, sannan ya sanar musu cewa gidan su ya kammala gobe xasu koma, a ranar kwanan farin ciki suka yi, Nauwar da Hamdan kuwa kwana suka yi suna waya. washe gari da safe suka yi harmar tafiya gidan don su samu su gyara gidan sosai, a kusa da gidan su aka yi musu ginin ba karamin tsaruwa gidan yayi ba, tararwa suka yi an gyara komai har jere an yi musu, babu abinda ya rage musu sai xama su huta, bangare biyu ne a gidan, bangare na farko shi ne nasu Nauwar dayan kuma Baffa ya ginawa, wanda xai je ya taho da shi nan ba da jimawa ba, Nauwar ce ta dubi Amminta. "Alhamdulillah ban taba tsammanin xamu dawo irin wannan rayuwar da muka yi a baya ba, gashi mun samu canji da cigaba fiye da wanda muka samu a da, Allah mun gode maka ya Allah ka kare mu daga sharrin abokan gaba" gaba daya suka amsa mata da Ameen, sallama Abbanta yayi ya karaso wajen su. "ku shirya yau muna da manyan baki a gidan nan Abdallah xai kawo mana xiyara don ya fada min yanxu haka ya kusa shigowa kano" cikin farin ciki Nauwar ta dubi Abbanta "amma naji dadi Abba dama ina ta tunanin ce maka yaushe xamu je musu xiyara saboda yayi mana mutunci a lokacin da muke bukatar taimako" fuskarsa a sake ya dubeta. "to ai gashi nan yau xai xo ya sada xumunci ya riga mu samun ladan, ku yi sauri ku tashi ku shiga kitchen ku hada masa abinci kafin ya karaso" da sauri suka shiga kitchen suka fara shirya abinci mai rai da lafiya, bayan sun kammala suka shiga wanka sannan suka sanya kaya iri daya masu kyau ita da saimah. bayan mintunan da basu wuce sha biyar ba, suka ji alamar tsayuwar mota Abban Nauwar ne ya fita don taho da doctor Abdallah, a falo aka sauke shi, cikin nutsuwa su Nauwar suka fito a ladabce suka gaishe shi cikin sakin fuska ya amsa musu, bin Nauwar yayi da kallo yana mamakin yadda ta canja da a hanya ma suka hadu ba lallai ne ya ganeta ba, saboda yadda ta canja kamanninta suka koma kamar na larabawa, tashi suka yi suka fara kawo masa abincin sannan suka dan taya shi hira sannan suka tashi suka koma dakin su, Abban nauwar ne ya shigo suka fara hirar yaushe gamo sannan ya bashi labarin irin gwagwarmayar da su nauwar suka shiga bayan rabuwar su da shi, doctor ya tausaya musu halin da suka kasance cike da tausayawa yake masa magana "nima tunda suka tafi hankalina bai kwanta ba saboda ina tsoron duniyar nan amma saboda babu yadda xan yi na bar su suka tafi saboda gudun bacin ran Hajiya, ni kuma gani gauro dama ina da aure ne da sai na kaisu gidana" ya karasa maganar yana dariya, cikin mamaki Abban Nauwar ya dube shi. "kana nufin kace har yanxu ba kada aure doctor lallai turawa sun yi tasiri a kanka" murmushi doctor yayi. "wlh ba haka bane kawai shi aure lokaci ne, kuma a gaskiya tsoron yan matan yanxu nake yi shi yasa ma har yanxu na kasa xaben mata" Abban Nauwar na murmushi ya dube shi. "tunda tsoron yan matan kake ji kaxo ni xan baka yata ka aura" gyara xama doctor Abdallah yayi "Da gaske kake xaka bani?gyada kai Abban Nauwar yayi "idan ka shirya kaxo wlh xan baka" "Ai ni a shirye nake ko yanxu ka bani karba xan yi, Nauwar xaka bani ko yayarta?" dariya doctor ya bawa Abban nauwar ganin yadda ya dauki maganar da muhimmanci. "Nauwar ai an yi mata miji sai dai yayar tata idan kana so" fuska a sake ya amsa. "ina so mana, amma da nafi son karamar, amma tunda kace an mata miji na karbi babbar ya sunanta" "sunanta saimah"ya fada masa a takaice, labarin kulawar da suka bawa su Nauwar ya fara bashi da irin karamcin iyayenta Hannu biyu doctor yasa ya karbi saimah ba karamin shiga ransa tayi ba saboda yadda ta samu kyakkyawan yabo a wajen abban nauwar Hirar duniya suka cigaba da yi har xuwa dare. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *ALLAHU AKBAR DUNIYA LABARI Allah ya yiwa daya daga cikin masoya wannan littafi rasuwa,😭😭😭 kuma member a group dina na sirrin ya mace HASANATULLAH MUHD LAWAN (Ummu sulaiman)Allah ya gafarta mata, halinta na gari ya bita, Allah yasa aljannah ta xamo makoma a gareta* 9⃣9⃣ A gidan su Nauwar doctor ya kwana washe gari ma kayan abinci na alfarma suka hada masa, saimah da Nauwar ne suka kawo masa cikin ladabi suka gaida shi, idanunsa a kan saimah ya yaba da hankalin yarinyar da yadda take gudanar da abubuwanta cikin nutsuwa, wani sonta ne ya kara shiga ransa ya xama wajibi a gare shi ya so ta, suna ajiyewa suka koma daki. bayan ya kammala cin abincin ya fara yiwa Abban Nauwar maganar auren sa. "ni fa so nake a yi a kare komai yau, saboda yau din nake son tafiya gida ina so na kaiwa Hajiya kyakkyawan labari dama ta kosa ta ga jikokinta" murmushi Abban Nauwar yayi "me kake ci na baka na xuba Abdallah yanxu dama nake son na sameta nayi mata magana nasan baxa ta ki karbar ka ba" "ni dai ka tashi ka tafi so nake naji result don nan da karfe12 xan wuce" takurawar da doctor ya rika yiwa Abban Nauwar ne yasa ya tashi, dakin su Nauwar ya shiga inda ya tarar da su suna hira, waje ya samu ya xauna cikin ladabi suke masa magana, "sannu da shigowa Abba" fuskarsa a sake ya amsa musu duban su yayi gaba yana murmushi" ina so ku bani hankalin ku gaba daya xan yi magana da ku" gyara xama suka yi suna dubansa tare da cewa, "muna saurarenka Abba" gyaran murya yayi sannan ya fara magana, kiran sunan saimah yayi tare da tambayarta"an yi miki miji a gida ne ko kuwa"kamar daga sama taji tambayar, kanta a sunkuye ta bashi amsa "ba a yi min ba Abba" "yauwa Alhamdulillah dama na tambaye ki ne saboda bana son a yi neman aure a kan neman aure" bata fahimci abinda yake nufi ba kuma bata tambaye shi ba, shiru yayi na wani dan lokaci sannan ya cigaba da magana. "kinga wannan dan uwan nawa da ku ke kaiwa abinci ko" ya tambayeta a takaice, a hankali ta dago ido ta amsa masa da "eh Abba" "wannan da kike gani dan uwana ne na jini kuma mutumin kirki ne ya nuna yana sonki da aure, idan kin amince xai fito nan bada dadewa ba domin baxa a dauki lokaci mai tsaho ba xa a yi komai a gama, fatana dai ki amince da shi" wani farin ciki ne ya lullube Nauwar taji dadin wannan hadin saboda da saimah da doctor xasu dace sosai saboda mutane ne masu tsari da tsafta, Nauwar ce tayi saurin cewa "ta amince Abba"saurin dakatar da ita yayi "Aa ki kyaleta tayi magana da kanta" sake maimaita mata tambayar yayi a kunyace ta amsa da "na amince Abba" ba karamin dadi yaji da amincewarta ba, dama baya son ya aurar da nauwar ita kadai ya fi son ya hada da saimah a yi komai tare, albarka ya shiga saka mata yana mata fatan samun nasara a rayuwa. Abba na fita Nauwar tayi tsalle ta rungume saimah suna murna dama ita saimah ta yaba da doctor tun kafin ya furta yana sonta kawai ta danne ne saboda kunya. Abban Nauwar na komawa wajen doctor kafin ya karaso gurin shi har ya kosa ya mike nufo shi yayi yana tambayar shi "ya ku ka yi da ita, ta amince kuwa?" murmushi Abban Nauwar yayi yana masa magana. "Haba sarkin xumudi ka bari na karaso dai ko" komawa yayi ya xauna "na kosa naji sakamakon ne shi yasa amma tunda an ce na koma dole nayi biyayya don kada a hanani" ya karasa maganar yana dariya duban shi Abban Nauwar yayi. "kamar yadda na fada maka dama yarinyar ba tada matsala don lokacin da na fada mata ko musu bata yi min ba, kaga da bata so xata dakatar da maganar, don haka yanxu abinda ya rage maka shi ne ka fara shirye-shiryen biki" farin ciki ne ya bayyana a fuskar doctor "kai!! amma naji dadi, na gama komai dama matar ce ta gagare ni sai da yayana ya bani tukunna" dariya Abban Nauwar yayi "Ai da nasan tuntuni haka kake xaune ba aure da tuni na aurar da kai na huta" murmushi kawai doctor ke yi don ya rasa da wane baki xai yi godiya saboda farin ciki"wato komai na Allah yana da hikima da su nauwar ba su shiga halin tsaka mai wuya ba da baxa su sanni ba, kuma baxa su san saimah ba, gashi nan ta sanadin su na samu matar aure" jinjina kai Abban Nauwar yayi "gaskiya ne fatan mu dai Allah ya xaunar da ku lafiya" amsawa yayi da "Ameen" nan take ya kira Hajiya ya fada mata "tayi farin ciki sosai sannan ta sa masa albarka" duban shi Abban Nauwar yayi "tunda ka kira Hajiya nima bara na kira Abbanta na fada masa don ya shirya don baxa a wuce sati uku ba a yi bikin nan ba. kiran wayar abban saimah yayi yana ganin numbersa ce yayi saurin dagawa, cikin sakin fuska yake masa magana bayan sun gama gaisawa yayi masa maganar cewa saimah ta samu mijin aure kuma dan uwansa ne Abba yayi farin sosai cikin farin ciki yake magana "yanxun nan mamanta take sanar da ni sun kirata a waya ita da nauwar sun fada mata, nace lallai yaran yanxu sai dai a bar su kawai wato baxa su iya jira ma ka kira ba" murmushi Abban Nauwar yayi "da Alama doctor ya samu shiga ne tunda kaga haka Alhaji kasan yaran nan idan suna son abu idon su rufewa yake haka ma idan basa so, mu dai sai dai godiya ga Allah xamu aurar da yaran nan gaba daya ga yara yan mutunci" "Haka ne Alhaji Allah yayi mana taimako, wane lokacin kake ganin ya dace a tsayar" Abban saimah ya tambaya gyaran murya yayi "xan shawarci maxajen nasu naji duk yadda suka ce xan kiraka mu shawarta amma ni bana so a wuce wata daya ba a yi komai ba" sallama suka yi sannan ya kashe wayar ya mayar da kallon shi ga doctor "ka samu karbuwa a wajen saimah kaji har ta kira gida ta fada musu" murmushi doctor yayi yaji dadin karbar da saimah tayi masa, a ranar ya koma fataskum don fara shirye-shiryen biki. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya naki ne sarkin rigima kawata, aminiya, yar uwata abokiyar fadana MAIJIDDA BELLO na baki wannan shafin kyauta kiyi yadda kike so da shi* 1⃣0⃣0⃣ Shakuwa mai tsanani ce ta shiga tsakanin doctor da saimah ba karamin son junansu suke yi ba, don kusan duk bayan Kwana biyu sai doctor yaxo xance wajen saimah,Hajiya ma tana matukar kaunarta a kullum sai ta kirata a waya taji muryar surukarta, shirye-shiryen biki sun yi nisa don su doctor har sun tsayar da ranar da xasu kawo lefe don a tsayar da lokacin biki. yau da sassafe suka tashi domin xasu je dan batta gaba dayan su suka tafi, don sanar da baffa lokacin da aka tsayar na auren su saimah, Hamdan ne yaja motar domin yana son xuwa yaga baffa, Abban Nauwar me ya xauna a gaba,Ammi da saimah da Nauwar na gidan baya, misalin karfe takwas na safe suka bar gida basu isa garin dan batta sai karfe tara, tun daga nesa suka hango taron mutane cike da kofar gidan Baffa, saurin dakatawa Hamdan yayi, don ya samu wajen da xai yi parking saboda idan ya karasa baxai samu gurin tsayawa ba, jikinsu a sanyaye suka fito gaba daya suka nufi kofar gidan, duk wanda suka kalla sai su ga yana cikin alhini da jimami, cikin hanxari suka karasa wajen, a taugunne suka tarar da Baffa ya hada kai da gwiwa,gaba daya suka gaishe shi, amma ya kasa amsawa, cikin nuna damuwa da halin da yake ciki Abban Nauwar ya yi masa magana "sannu da gida baffa" A hankali ya dago ya dube shi "yauwa Mahmud sannu da xuwa yaushe ku ka karaso gaba daya haka kamar kun san abinda ke faruwa" cikin damuwa yake tambayar sa"me kuma ya faru Baffa" share kwallar da ke shirin fito masa yayi sannan ya cigaba da magana "Allah ya yiwa innah rasuwa yau da safe"ya karasa maganar yana share hawaye, cikin nuna damuwa ya dube shi, "kayi hakuri Baffa dukkan mai rai mamaci ne fatan mu dai Allah yaji kanta yasa ta huta ya yafe mata kurakurenta" Amsawa yayi da "Ameen" sannan ya cigaba da magana "ina cikin damuwa Mahmud ana so a yiwa innah suttura amma abu ya gagara"cike da mamaki yake tambayarsa "me ya hana a suturtata" girgixa kai Baffa yayi "ba komai ne ya hana ba sai abinda ya faru da gawarta abin xai baka tsoro, shi yasa na shiga damuwa nake jin tsoron abinda xata je ta tarar a lahira tunda gashi tun a duniya Allah ya fara nuna ko wacece ita, wlh Mahmud ji nake kamar na mutu na huta da wannan bakin cikin da nake ciki, wannan abinda ya faru nan gaba xai xame mana abin gori a wannan karkarar tamu yaya da jikoki" cikin rashin gane abinda Baffa ke nufi Abban Nauwar ya sake tambayarsa "Baffa ni fa ban fahimci abinda kake nufi ba tun daxu me ya faru da innar da har aka kasa yi mata suttura a kai ta kushewarta" wasu xafafan hawaye ne suka cigaba da sauka a fuskar Baffa "yanzu a halin da ake ciki fuskar innah tayi bakikkirin tana fitar da hayaki Yanxu haka limamin da xai yi mata wanka ya shaki irin wannan hayakin yanxu haka yana kwance a asibiti sannan kuma maciji ya nade jikinta kowa tsoron shiga inda gawar take yake yi, bansan ya xan yi ba mudi a ce mahaifiyata ce a irin wannan halin, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da kuka mai cike da ban tausayi ya karasa maganar shi ma abban nauwar kukan yake yi saboda yana tausayin baffansa yana jin xafin halin da kakarsa ke ciki a halin yanxu, neman shawarar mutane suka shiga yi wasu su ce a samu wasu su daure su yi mata wankan a haka, wasu kuma su ce a kyaleta a haka, duk wanda aka kama sai ya xille ya gudu sai da aka nemi kowa aka rasa mutum daya ne kawai ya tsaya Shi ma saboda abokin Baffa ne yana Jin kunyar ya gudu ya bar shi, daga karshe dai aka yanke shawarar a barta a cikin dakin ba tare da an tabata ba, shi kuma baffa ya bar gidan tunda abin yaxo da haka ko xaman makoki ba a yi ba saboda gulmar abinda ya faru kawai ake yi a kauyen a tarihin rayuwarsu basu taba gnin irin wannan abin ba sai a kan innah karime, kowa sai tunnin abinda ta aikata yake yi saboda mutuwarta taxo da wani sabon salo na mamaki, A ranar Baffa ya koma gidan su nauwar dama an gina masa bangarensa an gyara masa komai, Kullum Abban Nauwar cikin kwantar masa da hankali yake yana rarrashinsa a kan kada yasa damuwar innah a ransa ya dage da yi mata addu'a watakila sanadin haka taji sauki a wajen Allah Ranar da ta cika kwana bakwai da rasuwa aka kawo lefen Nauwar da saimah kaya aka yi na gani na fada doctor Abdallah akwati sha biyu ya yiwa saimah ita kuma nauwar aka yi mata takwas ba karamin kashe kudi suka yi ba, gaskiya duka bangarorin biyu sun yi barin naira domin dukansu babu wacce aka sakawa suttura ta kasa da dubu ashirin, an yanke lokacin biki bayan sati biyu, kafin lokacin yan gidan su saimah suka taho gaba daya don sun barwa Abban nauwar ragamar bikin gaba daya sun ce yayi komai. Yau da wuri suka shirya don xuwa gidan gyaran jiki da ke unguwar xoo road, basu samu wanda xai Kai su ba kasancewar Ammi na ta xirga-xirgar harkar biki, a bakin titi adaidaita sahu ya sauke su, da kafarsu suka karasa don shiga gidan mai gyaran da xata gyara su, wani mutum suka hango tsaye a bakin mota sanye yake da farin yadi, ba yabo ba fallasa, baxa ka kira shi da talaka ba, haka kuma baxa ka ce masa mai Kudi ba sai dai a saka shi a sahun masu rufin asiri, kallon su yake yi sosai har sai da suka tsargu da kallon da yake musu, har suka kusa karasawa wajen basu gane ko wanene shi ba, sai da suka je daf da inda yake xasu shiga layin gidan da xasu je nauwar ta ja da baya tana masa duban mamaki, cikin sarkewar murya ya kira sunanta "Nauwar kece ashe xan gane ki" Xubewa tayi a kasa tana gaida shi tare da xubar da hawaye "Malam ashe xaka gane ni? " Ajiyar xuciya yayi "ya xa a yi na kasa gane Ki nauwar, mun shiga tashin hankali a lokacin da muka neme ku muka rasa, tun daga ranar da kuka tafi ban Kara samun walwala ba, saboda ina tunanin kada shu'uman aljanun nan su sabauta muku rayuwa amma naji dadi da na ganki, Ina ne gidan ku, ina fatan kuma mahaifiyar Ki ta samu lafiya? " Share hawaye nauwar tayi "da taimakon Allah da taimakon ka da na Wadannan mutanen" ta nuna saimah "ta samu lafiya yanxu ta dawo mutum kamar kowa" Fara'a Malam Haruna ya shiga yi "alhamdulillah Allah ya qara lafiya ya Kare ku daga sharrin masu sharri" amsawa tayi da Ameen tare da tambayarsa "Ina baba da fatan dai tare kuka xo" murmushi yayi "tana gida yanxu haka ma daurin aure naxo kuma Allah ya kaddara haduwar mu da ke" Nan take nauwar ta kira Abbanta cikin farin ciki take magana. "albishirinka Abba" Cikin sakin fuska ya amsa mata da "goro me ya faru yata ta Kaina ?' "Yanxun nan naga Malam Haruna Wanda ya taimaki Ammi ta samu lafiya " cikin kulawa yace ta hada shi da Malam addu'a ya rika yi masa yana godiya a bisa taimakon da ya bawa iyalansa, bayan sun yi sallama da Malam ne suka cigaba da magana da nauwar "Ku je gida tare da Malam din gani nan xuwa yanxu" adaidaita suka sake Hawa suka rankaya suka tafi gidan su nauwar. *jeeddahtulkhair😘* [9/23, 10:10 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *MAIJIDDA TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya tukwici ne a gare ku* *Abdurrahman ibrahim* *Yusuf mas'ud duniya* *Ibrahim (itz ibrahim)* *ina godiya da yadda kuke ta fafatukar ganin wannan littafi ya karbu wajen yin post din shi a facebook na gode Allah ya saka da alkhairi ya bar xumunci* 1⃣0⃣1⃣ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 A dakin saukar baki aka sauke malam Haruna, hannu biyu Ammi ta karbi malam tare da kawo masa abinci kala-kala, bayan ya kammala ya fara bata labarin irin gwagwarmayar da yayi da aljanun Ammi bayan tafiyar su. "ba karamin auna arxiki kika yi ba Hajiya wadannan aljanun basu so barin ki da rai ba, domin kuwa ni kaina Allah ne yayi da kwana na a gaba a zahiri na rika ganin su zasu hallaka ni, da taimakon Allah da addu,a na samu na kore su daga gidana, amma dai Alhamdulillah yanxu komai yazo karshe gashi nan har kin dawo garau da ke, Allah ya kara lafiya wadanda suka yi kuma nasan yanxu abin ya koma kansu, domin asirin da suka yi kaikayi koma kan mashekiya ne" Gyara zama Ammi tayi "mun gode sosai malam nauwar duk ta fada min irin taimakon da kayi mana Allah ya bada lada wadanda suka yi abin kuma yanxu duk sun xama abin tausayi, dayar ta haukace dayar kuma tayi mutuwar wulakanci" mamaki ne ya kama malam, "kinga ai rashin amfanin cutar da mutum gashi nan burinsu bai cika ba, to yanxu ita mai mutuwar nan me zata je ta gayawa Allah, ko da yake su masu wannan mugun abin ba gani suke yi ba, gani suke duk abinda suke yi dai-dai ne" Hirar da suke tayi kenan, har Abban nauwar ya dawo da sallama ya shigo dakin, cikin sakin fuska ya karasa inda malam Haruna yake hannu ya mika masa suka gaisa, sannan ya fara yi masa godiya abisa abubuwan alkhairin da yayi musu, cikin sakin fuska malam ya mayar masa da amsa "ba komai Alhaji ai wanda ya taimaki wani Allah xai taimake shi, mu dai Alhamdulillah da Allah ya bata lafiyarta, sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba, Ashe kuma auren nauwar ya taho, rabon naxo bikin ne yasa muka hadu da ita" murmushi Abban nauwar yayi "Abu ya matso kam dan yanzu saura sati biyu a fara biki" addu,ar fatan alkhairi malam yayi sannan suka fada wata hirar, bai tashi tafiya ba sai bayan sallar la'asar sha tara ta arxiki Abban nauwar da Ammi suka hada masa har sai da ya rasa bakin godiya, Abban nauwar ne da kansa ya dauke shi a mota ya mayar da shi masaukinsa suna isa gurin ya tsaya suka fara magana. "yanxu kuma sai yaushe xaka dawo malam" shiru yayi na dan lokaci sannan ya yi magana "insha Allah zan yi kokarin dawowa bikin diyata duk da dai garin namu da nisa amma zan kokarta naxo" cikin kulawa Abban nauwar yake tambayarsa "ina ne garin da kake malam"? Gyara zama yayi"can cikin wani Kauye ne a garin Gombe amma yan uwana da yawa suna nan garin ni kadai Allah ya zaunar a can" murmushi Abban nauwar yayi "me yasa baxa ka dawo nan din ba malam ko garin namu ne bai maka ba" ya karasa maganar yana murmushi "me zai hana ni xama a kano ni da mahaifata, idan na samu muhalli xan dawo insha Allah" cikin kulawa Abban nauwar ya dube shi. "Malam idan har babu damuwa ina da gidan da xan saka ka sai ka dawo cikin yan uwanka" wani farin ciki ne ya rufe malam Haruna "Ai kuwa na gode Alhaji idan xan dawo biki sai mu taho gaba daya da uwar gidan nawa ba sai mun kara komawa ba" "Yauwa nima abinda nake so nace kenan yanxu xan sa ayi muku duk gyaran da ya kamata kuna xuwa sai ku shiga gidan ku" Godiya mai yawa malam Haruna yayi da xa su yi sallama Abban nauwar ya dakko kudi mai yawa ya bashi sannan ya wuce gida. Kai tsaye wajen mai gyara ya nufa ya xayyana masa irin yadda xa a gyarawa malam Haruna gidansa. Daga nan kuma ya wuce gidan malam Audu ya mika masa mukullin wani gida da ya gina masa, albarka malam ya shiga saka masa yana yi masa addu'ar gamawa da duniya lafiya, cikin girmamawa yake wa malam magana "wajibina ne na kula da kai malam domin kaine silar duk wani arxiki nawa da nake takama da shi, don haka duk abinda nayi maka ban biyaka ba, burina a kullum na kyautata maka kai da baffa saboda irin kulawar da na samu daga gare ku' cigaba yayi da sa masa albarka, washe gari da safe ya aika da mota aka kai malam sabon gidansa. *BAYAN SATI DAYA* Baki daga kasashe daban daban ne suka zo don halarta bikin su nauwar da saimah yan uwan Ammi daga Sudan duk sun xo don shaida wannan aure mai albarka, guraren biki daban daban aka kama don gudanar da wannan bikin da aka dade ana jiran xuwansa. yau ta kama daurin aure da wuri su nauwar suka shirya a dakin Abbansu suka xauna, tun kafin a daura auren nauwar ke faman kuka saboda bata son rabuwa da Amminta, bayan an daura auren ne Abban saimah ya shigo ya fara yi musu nasihohi masu ratsa jiki sannan kuma ya mikawa kowacce a cikin su sadakinta, cikin kuka nauwar take masa magana "Abba na bar maka ka rike kayi duk abinda kake so da shi"tausayin nauwar ne ya kama shi "Aa nauwar ki rike ki siya wani abin mai muhimmanci da shi Allah yayi miki albarka" bayan fitar Abba daga dakin angwaye suka shigo sanye suke da fararen Shadodi komai nasu iri daya Hamdan da doctor Abdallah suka saka, fuskar nauwar a rufe tana ta faman kuka karasowa inda take Hamdan yayi da sauri taja jiki ta matsa murmushi yayi yana mata magana "yau kuma dodo na zama nauwar kike jin tsoro na" Shiru tayi ba tare da ta bashi amsa ba ya rika tsokanarta, sai da suka gama magana sannan mai hoto ya shigo ya fara daukansu, bayan sun kammala suka fita doctor ya kama hanyar tafiya fataskum shi kuma Hamdan yayi gida. A unguwar nassarawa G. R. A Abban Hamdan ya gina masa katafaren gida wanda kuma ba su da nisa da gidan su Hamdan, shi kuma doctor Abdullah a fataskum xai xauna a wani hadadden gida da ya samu gado a wajen mahaifansa, da misalin karfe daya na rana yan daukan Amarya suka zo, wadanda su ne xasu tafi da saimah gidan doctor, ba karamin tashin hankali saimah ta shiga ba kuka gaba daya yaki zuwar mata, amma dai kana ganinta kasan tana cikin damuwa a daki Saimah take iyaye nayi mata fada a dai-dai lokacin nauwar ta shigo ta tarar da saimah na ta faman sharar kwalla da sauri ta karasa wajenta ta rungumeta kuka take yi mai cike da ban tausayi da kyar aka cire saimah daga jikin nauwar aka sata a mota sai gidan doctor. .tunda aka tafi da saimah nauwar ke kuka rarrashin duniyar nan an yi mata ta kasa yin shiru har zuwa karfe shida na yamma wanda a wannan lokacin xa a kaita dakin mijinta, da kyar aka lallabata ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito aka Fara yi mata nasihohi a kan xama da miji, nan ma dai ta shiga tashin hankalin rabuwa da Amminta haka aka tarkatata aka kaita gidan Hamdan. Rayuwa mai dadi suke yi a gidan mazajen su cike da xaman lafiya da kwanciyar hankali duk wanda yaga irin zaman da suke yi sai abin ya burge shi, watan Su nauwar biyu da aure Allah ya azurta su da samun ciki ba karamin lele nauwar ke sha a wajen Hamdan da mamansa ba kowa fata yake Allah ya sauketa lafiya. Sai da saimah ta cika wata uku a gidan doctor sannan taxo ganin gida, sai da tayi sati biyu sannan ta tafi nan ma dai sai da suka sha kuka suka rabu. A ranar da suka cika wata tara dai-dai nauwar ta haifo santalelen jaririnta kamar su daya da Hamdan komai da komai, sunan Abban nauwar aka sanyawa yaron inda suke kiran shi da Adeel, ba karamin gata kakannin Adeel ke gwada masa ba, don bai fiya xama a hannun nauwar ba kusan kullum yana tsakanin gidan mama da Ammi. Yau da sassafe Ammi taji ana kwankwasa mata kofar falo da hanzari ta tashi don budewa tare da cewa "wanene " shiru aka Yi ba a yi magana ba, cikin karfin hali ta saka key ta bude kofar, mace ta gani tsirara haihuwar uwarta fuskarta baka kirin cikin rawar baki take mata magana"Habi Kece lafiya na ganki a wannan yanayin " Hawaye matar take xubarwa "ki yafe min duk abinda nayi miki don Allah mutuwa xan yi na wulakanta naga rayuwa yanxu haka ni nasan irin axabar da nake dandanawa ki yafe min " tana gama fada ta fadi kasa tana wani irin abu a dai-dai lokacin yayan Habi suka yi sallama "yanxu Sai da kika taho baba Inna lillahi wa Inna ilaihi rahi'un" Jujjuyata suka rika yi suka ga bata motsi cikin kuka suke wa Ammi magana. "daga gidan magani ta gudo Hajiya da yake yanzu ana yi mata dan kokari tun jiya take cewa sai taxo ta roke ki gafara dan Allah ki yafe mata Hajiya " suka karasa maganar suna kuka. Ita ma Ammi kukan take. "na yafe mata Allah ya yafe mana gaba daya" Daukanta suka yi suka tafi Dan Batta don yi mata suttura. Sai da Abban nauwar ya dawo take Fada masa abinda ya faru,mamaki yayi da tace ta yafewa Habi "yanxu sai ki yafe Mata duk irin cutarwar da tayi miki. Murmushi Ammi tayi "Menene don na yafe mata Allah yana tare da masu hakuri" Haka suka cigaba da rayuwa mai dadi cikin farin ciki da annashuwa. Lallai duk mai zalunci xai ga yadda Allah xai yi da shi tun a duniya domin Allah da kansa yace ya haramtawa kansa zalunci kuma ya sanya shi abin haramtawa a tsakanin mu, don duk Wanda ya cuci wani Allah bazai saurara masa ba bazai masa rahma ba, sai dai idan bawan Nasa ne ya yafe, don haka nake kira ga yan uwa mu nisanci zalunci da shirka ga Allah, duk abinda Allah bai bawa mutum ba babu wani malam ko boka da zai bashi don haka mu kiyaye. abinda na rubuta dai-dai Allah ka bamu ladan wanda nayi Kuskure Allah ya yafe mana, Allah yasa mutane su yi amfani da fadakarwar da ke cikin wannan littafi. *Alhamdulillah* Taku *jeeddahtulkhair😘* Sai kun sake ji na a sabon littafina.