"[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* 28/8/2020 Wattpad@Rashuna *KATANGA* _Ina matuk'ar godiya ga Allah (S.W.T) da zai ba ni ikon kawo muku wannan littafi mai suna KTG, ina fatan yadda zan fara cikin yalwatacciyar lafiya na kammalashi haka, Amin summa Amin_ _Sak'on gaisuwa ga 'yan uwa da abokan arzik'i, da kuma dukkanin masoyana na kusa da nesa, ina kuma fatan za ku bani had'in kai cikin wannan littafin, kalma d'aya kawai zan gaya muku, alk'alamin ya fi mashi tsini, kuyi k'ok'ari kui nitso ku ninkaya cikin wannan sabon alk'alamin mai suna *KATANGA*_ _Hak'k'in mallaka:_ RABEE'AH SHU'AYB NABABA (RASHUNA) ____________ *ONE* _Bismillahir rahamanir rahim._ *SHIMFID'A* Malam Ahmadu an haifeshi a garin Zaria, asalin malantarsa ya gadota ne a gurin mahaifinsa Malam Buba, kasancewar kuma tun ya na yaro mahaifiyarsa ta rasu, tare ya rayu da mahaifinsa har sai da ya yi aure da matarsa Asabe sannan Allah ya karb'i ran malam Buba, daga nan Malam Ahmadu ya ci gaba da jan ragamar mahaifinsa ta malamta. 'Ya'ya uku Allah ya azurtasa da shi, Abdullahi, Maryam sai autansa Shamsu, Abdullahi shine ya gado mahaifinsa amman kuma ba a iya malamtar ya tsaya ba ya na da shago a kasuwa da yake sayar da kayan awo. Malam Ahmadu shine ya zab'awa Abdullahi mata, 'yar amininsa ce k'ud da k'ud da Allah ya karb'i ransu shi da matarsa shekarun baya da suka wuce, kasancewar gidan nasu gidan yawane, kuma auran zumunci akayi tsakanin mahaifan nata, haka take ta watan gari riya a cikin gidan sai uwar bauta da take musu, tausayinta da duba maraicinta da amuntakar da ke tsakaninsa da mahaifinta hakanne yasa ya nemawa Abdullahi auranta, Abdullahi baiyi musu ba kasancewar ya yaba da d'abiunta kuma ta na yawan burgeshi a duk sailin da zasu had'u hakan yasa ya karb'i tayin auranta da hannu bibbiyu. A gurin Asabe wacce yanzu suke kira da Iya aka fara samun k'alubale, inda ta yi tsalle ta dire akan d'anta ba zai auri 'yar makafi ba, kasancewar mahaifanta duk makafi ne, shikuwa Malam Ahmadu yace ta yi kad'an ta hana wannan auran, idan har taga ba'ayi sa ba to tabbas babu ransa a Duniya. Abdullahi da Maimuna sun aminta da juna sosai ya yin da suka fad'a zazzafar soyayya nan da nan magabata suka shiga lamuran nasu, a lokacin ne kuma wanda yake neman auran Maryam me suna Yusuf ya fito, a kano yake a zaune aiki ne ya kawosa zaria, tun ganin farko da yaiwa Maryam ya aminta da ita, bai fara zuwa zance ba sai da Malam ya yi masa izini, daga bisani kuma yace ya turo magabatansa. An tsayar da ranar auran Abdullahi da Maryam lokaci guda . Anan cikin gidan, Malam Ahmadu ya yanki gefe ya yiwa Abdullahi gini, d'akuna uku ne maka² abinsa a wadace, ya yi musu kuma k'ofar gurinsu da ban, sannan kuma ya had'a masa lefe dai-dai da zamanin da suke ciki. Ansha shagalin biki kafin a kawo amarya sashinta, ita kuma Maryam aka kaita unguwar Sabon gari. Lafiya lau zaman Abdullahi da Maimuna yake babu wata matsala ko d'aya, Malam ya d'ebo soyayyar duniya ya d'orawa surukar tasa, kullum in zai shigo gida da abinda zai aika mata da shi, ya yin da Iya kuwa ta bi ta tsaneta, ko kad'an ba ta sakar mata fuska kyara da tsangwama shine tsakaninsu. Wata d'aya da bikinsu Allah ya azurtata da samun juna biyu, tattali da kulawa fiye da wacce take samu ada Malam yake mata, idan ya fita duk abinda ya san me ciki na sha'awa shi yake siyo mata, Iya kuwa tayi ta sababi a tsakar gida ta na masifar ga d'iyarsa can ta na da juna biyun amma ba ya ta tata ya tare a bayan sirika, ya taka k'afa ma yaje ya gano d'akinta baije ba don tsabar tab'ewa da lalacewa, ci kanki kuwa Malam ba yace mata sai dai yai ta murmushi idan ta na yi ya nai mata uzurin k'wak'walwarta ta goce. Cikin Maimuna na shiga wata tara cif, ta haifi kyakkyawar yarinyarta sankace ciya, da hak'oranta guda biyu na k'asa, tsakanin Abdullahi da Malam ban san wanda ya fi wani farin ciki ba, Malam fad'i yake an haifar masa jika 'Yar baiwa, mutane kuwa da wanda Maimuna ta sani da wanda ba ta sani ba sai tururuwar zuwa barka suke, wasu ma don suga hak'oran ne kawai yake kawo su, don duk wanda yazo sai ya d'aga bakin ya gani, sai dai kawai Maimuna ta yi murmushi. Iya kuwa ko lek'owa taga jikarta ba ta yi ba, illa ma bak'in ciki da take kamar ranta zai fita, saboda yadda taga malam ya na rawar k'afa ya samu jika 'Yar baiwa, don har ya siyo raguna biyu tik'a² ya tirkesu bakin nan yak'i rufuwa, Iya kuwa tace. "Inma za ka daina farin ciki ka daina, shawara nake baku ku d'auki 'yar nan ku kaita bakin ruwa don wallahi 'yar aljanu ce ba 'yar baiwa ba. “ Murmushi kawai Malam ya yi baice da ita komai ba don ya san bak'in ciki ne ya taru yai mata yawa. Ansha shagalin suna yadda ba kwa zato, yarinya taci sunan babar Malam AYSHA, Maimuna tace a dinga kiranta da NUSRAT, yayin da Malam ya d'ebo soyayya,tattali gami da kulawa ya aza akan 'Yar baiwa. Wata d'aya tsira Maryam ma ta haifi 'yarta mace taci sunan babar Yusuf RABEE'AH suke kiranta da HIDAYA. Watan Nusrat uku a duniya Iya ta matsawa Ahmadu number sai ya k'ara aure, wata bazawara ce nan mak'otansu da take shigo mata, mijinta mutuwa ya yi kuma mai bala'in kud'i ne, siyayya take yowa Iya sosai da haka ta siyeta, don dama burinta kenan ta tirsasa d'an nata ya aureta, don ta tareshi da buk'atarta ya yi mata kaca² hakanne yasa ta biyo ta gurin Iya. Don a samu zaman lafiya Malam yacewa Abdullahi ya aureta, itama ya bi zab'inta,ko a samu k'iyayyar da takewa Maimuna ta ragu, don fad'i take yaiwa mahaifinsa biyayya amman ita saboda bai d'auketa a bakin komai ba ya watsa mata k'asa a ido ta ya ya kwa za ta k'aunaci Maimuna? Tun sanda aka saka ranar tarewar Bulki Malam da Abdullahi suke kwantarwa da Maimuna hankali ita kuma ta nuna musu hakan ba komai bane dama ai namiji mijin mace hud'u ne. D'aki d'aya shi ya zama na Maimuna, d'aya na Abdullahi d'ayan kuma na Bulki. Ranar juma'a aka d'aura auransu kuma a ranar ta tare, farin ciki gurin Iya ba'a magana kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, tunda take ba ta tab'a taka gurinsu ba sai a ranar da aka kawo Bulki. To zamansu dai ga shinan da dad'i babu dad'i a haka rayuwar take juyawa. Shekarar Nusrat d'aya Maimuna ta sake haihuwar mace wacce taci sunan mahaifiyar Maimuna SAFIYYA suke kiranta SHUKHURA, wata uku tsira Bulki ma ta haifi 'yarta mace wacce taci sunan Iya na gaskiya ZAINAB suke kiranta da NIMHA, anan fa Iya ta baje kolin gata da soyayya, fad'i take yanzu ne aka haifa mata jika. Tun haihuwar Shukhura sai da Maimuna ta shekara biyar kafin ta haifi wata macen aka saka mata NA'IMA suke kiranta da YUSRA, ita kuwa Bulki ba ta sake haihuwa ba tun daga kan Nimha. Malam yadda kuka san bai da wata jika sai Nusrat, komai ya samu 'Yar baiwa, kayan ciye² kuwa sai ta rage ake samwa k'annenta, ta shak'u da kakan nata fiye da zatonku masu karatu, shima kuma ta shiga ransa sosai da sosai, ya na bata kulawa ne ba wai don fifici ko wani abuba, sai dai shi a ganinsa dole ne jikanka na fari ya banbanta da sauran, saboda gaba d'aya soyayyar da kakewa d'an naka kake 'yebowa ka aza a kansa. Amman a gurin Iya da Bulki cin fuskane kawai, don a nuna ba'a son Nimha, hakan yasa suma suka d'auki dukkanin tsana suka d'ora akan Nusrat. Nusrat Fara ce, amman farinta mai duhu ne, fuskarta siririya ce mai d'auke da siririn dogon hanci, idanuwanta suna da girma matsakaici masu shape d'in k'wan k'walati, cikin idonta fari ne tas ruwa ya kwanta a cikinsa mai maik'o, k'wayar idonta kuwa bak'a ce me silkin brown a ciki, bakinta d'an madai daici ne haka zalika lab'b'anta basu da wani tudu, ko ya ta motsa bakinta wani siririn dimple ne ke bayyana a gefen kumatunta na tsaye wanda yake k'ara fito da zallar kyahunta. Shukhura kuwa fara ce k'al, suna yanayi da Nusrat, amman ta fi Nusrat kyau, kina ganinta kai tsaye za ki kirata kyakkyawa, saboda ita ko ba tai murmushi ba kumatunta a lotse yake, kuma nata irin na kwance ne. Yusra ma fara ce kamar Shukhura, itama ta na yanayi da su, amman kuma ba ta da dimple. A yanzu shekarun Nusrat goma sha biyar a duniya, ta na sss1, su Shukhura kuma shekarunsu goma sha hud'u suna jss 3 auta Yusra kuma shakarunta tara a duniya ta na aji hud'u a primary. Allah ya yiwa Malam rasuwa shekaru hud'u da suka wuce bayan ya yi jinya kad'an, kowa ya ji babu dad'i domin anyi babban rashi mai girma, musamman Nusrat, bayan mutuwarsa ne kuma soyayyar da Abdullahi wanda yanzu suke kira da Baba yakewa Nusrat ta fara bayyana, don har ga Allah ya fi k'aunarta ya na b'oyewa ne saboda kada ya kuma janyo mata bak'in jini. mutum ne me wadatar zuciya, ba wani k'arfi ne da shi ba sai dai rufin asiri na Ubangiji, don sun wuce cin yau da na gobe a gidansa, haka zalika bai bar iyalansa a wulak'ance ba, a ko da yaushe za ka samesu cikin kyakkyawar kamala. Shamsu ya yi aure da matarsa Fiddausi da d'iyarsu Amima sa'ar yusra, sunanta na gaskiya Zainab, shima Iya ya yiwa takwara, a kaduna suke a zaune a saboda anan ne yake aiki, ya ninka yayan nasa sosai a fannin dukiya wanda k'arara Iya ke nuna banbanci tsakaninsu da Baba. Aunty Maryam kuma mijinta ya koma kano da aiki don haka ya d'ebe su suka koma kano da zama, 'ya'yansu hud'u yanzu, Hidaya, Abdul, Hibba, Abbas, suma sosai Iya take ji da su saboda suma mahaifinsu na da kud'i, kuma anai mata aike akan kari. *Wannan kenan* 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK in kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana, duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *TWO* Yau ta kama lahadi, duk da suna cikin hutun makarantar boko, su Nusrat duk sun tsefe kawunansu zasu kitso, sai da Nusrat ta fara wanka ta yiwa Yusra ma ta wanke mata kanta ta taje ta shafe mata shi da mai sannan suka shirya zasu tafi, kallon Shukhura Mama ta yi da ta saka hijabi zasu tafi tace. "Ke yanzu ba za ki wankan ba haka za ki bisu?“ Sai da ta fara turo baki gaba kana tace. "To Mama nan da nan d'in sai na yi wanka, abinda yanzun nan za'a mana mu dawo. “ "Allah ya shirya. “ Mama kawai tace ta na mik'awa Nusrat kud'in kitson nasu had'e da fad'in. "Ta fara yi miki kitson, kuma tai miki manya don kinsan yadda yawan kanki yake, kuma ke zan barwa girkin dare don fita zan yi, saura kuma kice a fara yiwa Yusra don na san hali. “ Murmushi Nusrat ta yi, bayan ta saka hannu biyu ta anshi kud'in kana tace. "Mun tafi.“ Maman tace. "Allah ya tsare, ku dai yi addu'a kafin ku fita. “Tace. "Amin, tom insha Allah.“ Tare da jan hannun Yusra suka bi bayan Shukhura da ta fita tun d'azu. Har sun d'an gota gurin Iya ta hango giftawarsu da sauri ta k'walowa Nusrat kira. "Ke ke A'i zo nan. “ Da yake haka take kiranta tun ma Malam na raye, juyowa Nusrat ta yi, Yusra ta turo baki gaba tace. "Wallahi na san aiki za ta sakaki, kawai kizo mui tafiyarmu mu rabu da ita.“ Murmushi Nusrat ta yi tace. "Bara dai naje na ji kiran da take mini.“ "Tak'i ta rabu da ni d'in, shegiya ifrituwa me zunb'utun baki. “ Suka jiyo muryar Iya daga ciki, kuma turo baki Yusra ta yi ta na hararar gurin kafin ta fice waje da sauri, Nusrat kuma ta nufi gurin Iyan ta na murmushi. Gyaran d'aki tace tai mata da wankin band'aki sai 'yan tsunmokaranta ma da tace ta wanke mata. Kallon Shukhura Nana me kitso ta yi tace. "Ina su Yayar taku?“ "Ga sunan suna hanya. “ "To shiga ciki, gani nan bari na k'arasa sharar nan. “ Rufe bakinta kenan Yusra ta yi sallama, kallon ta Shukhura ta yi bayan ta amsa sallamar ta ta tace. "Ina Yayarmun?“ "Ba Iya ce ta kirata ba, har ta na ce mini ifrituwa. “ Wani haushi ne ya kama Shukhura, ta zura takalminta ta fasa shiga d'akin ta fice a fusace Yusra ta biyo bayanta. Kamar an jefota ta shigo ta na kallon Nusrat da ke zubar da shara. "Sannu" Tace mata, kafin ta shige zuwa gurin Iya, iya na ganinta ta d'aure b'arin goron da ta b'antara a gefen zaninta kana tace. "To rasa kunya b'eran tanka, kinzo kimin rashin kunyar taki ne? “ Kar katar da kai Shukhura ta yi tace. "Ashe 'Yar aljanu na da rana tun da har an iya sakata aiki, me yasa ba ki kirawo 'yar lelen taki tai miki ba sai ita za ki saka, amma in abu zaki bayar babu wanda ke gabanki sai Nimha, amman in aikine sai wacce kika raina, don kin san Nimha ko tsintsiya ba za ta iya d'aga miki ba. Bayan kuma kitso zamu je kina gani kuma Mamanmu na zaman jiranmu“ "Tunda dai ba ke na saka ba, ki shige ki bani guri, kiyi can da rashin kunyarki. “ Cewar Iya "Waa aini kin san abinda bazai tab'a yuyuwa bane, don wallahi bazan bautawa wanda bai san ina yi ba, in cin mutumci ne ya taso azo a tarkace mini, lalalala wallahi, itama ita taga za ta iya.“ "Ni kikewa cin mutumci Safiya, Allah ya dawo da Audu, wallahi za ki gane Ubanki na haifa. “ "Amin, ya dawo d'in ki gaya masa, wallahi duka d'aya yamin kinsan sai na bi ta inda zan rama, Allah ya baki sa'a. “ "Wai da sa'ar ki kikeyi ne Shukhura?“ Cewar Nusrat ta na kallonta, ba ta bata amsa ba ta fice ta na zunb'uro baki, Iya kuwa k'ifi² ta yi da ido tunowa da ta yi sanda ta saka Nusrat a gaba ta na zaginta Shukhura ta amshe ta hayayyak'o kamar za ta daketa har sai da Mama ta fito ta kikkifawa Shukhura mari, shine Baba ya na dawowa Iya ta kwashe ta gaya masa, aikwa ranar Shukhura ta sha duka gurin Baba, ita kuwa ta d'auki aniyar wallahi sai ta rama akan Iya, sai da ta bari duhu ya yi ta kad'a karkashinsu me yauk'i taje ta zuba a band'akin Iya,don ta na da tabbacin yanzu za ta fito ta shiga band'akin ta lab'e a bayan k'ofa, Iya na shiga ta yi sufa ta fad'i Shukhura ta fito ta na ta k'yak'yata mata dariya, tace mata kad'an ta gani muddun ta na sakawa Baba na dukanta, Iya kuwa jiki yai tsami da k'yar ta iya mik'ewa. "Yanzu Mama kina kallo ga Iya can ta saka Nusrat aiki.“ Shukhura ta fad'a ta na turo baki gaba. “ "To meye, don ta sakata aiki?“ Mama ta fad'a ta na cigaba da tankad'en da take. "Amma Mama kefa kikace a fara mata kitson saboda za ki bar mata girki.“ "Yanzu kuma na fasa ba, kije ke a fara miki sai ki baro Yusran a can in Yayar taku tazo sa taho tare sai ki karb'i girkin na samu na fita. “ "Amma Mama....“ Dakatar da ita Mama ta yi had'e da fad'in. "Ban san jin komai ki shige kije kiyi abinda na saki. “ Fita ta yi ta na tutturo baki Mama ta girgiza kai had'e da fad'in. "Allah ya shirya. “ Sai da Iya ta kinta tanci dawowar Baba ta fito babban tsakar gida ta k'wama kujera ta na jiran dawowarsa, aikwa ta na jin sallamarsa ta saki kuka me k'arfi, a gigice ya nufota ya na tambayarta. "Lafiya Iya, me ya faru kike kuka haka?" Face hanci Iya ta yi tace. "Wai ni yau A'i za ta kalli tsabar idona ta zageni ta uwa ta uba. “ " 'Yar baiwa.“ Baba ya k'wallawa Nusrat kira, Nusrat da ke d'aki tun da ta dawo daga kitso kanta ke ciwo shine ta nemi guri ta kwanta, ta na jiyo abinda Iya ke cewa Baba gabanta ya yanke ya fad'i, da ta ji kwa ya k'wallo mata kira nan da nan idonta ya yi rau-rau zai fidda ruwa, a hankali ta mik'e ta fito ba tare da ta amsa kiran ba, kallonta Shukhura ta yi da ke kwashe tuwo ta cika k'atuwar kula ta kai d'akinsu, tace. "Kinga dai da abinda ta saka miki ko? kuma wannan ba shi zai hana gobe idan tace yimin kaza kiyi mata ba. “ Ba tace mata komai ba sai juya idonta da tayi da ya fara fitar da ruwa ta nufi tsakar gidan, Shuk'hura kuwa taci gaba da kwashe tuwonta ta na mamakin sanyin hali irin na Nusrat, ta yi k'wafa a hankali, a ranta tace. 'Iya kenan, ai gara ki tab'ani akan ki tab'a Yayarmu wallahi, don ba ki son son da nake mata bane.' Baba na ganin ta taho a sanyaye ya saki murmushi had'e da fad'in. "Taho mana 'yar baiwa. “ Ganin murmushi akan fuskar Baban nata yasa ta samu k'arfin guiwar k'arasawa gareshi, bak'ar ledar hannunsa ya mik'a mata, me d'auke da d'ata manya-manya kasancewar yasan ta na matuk'ar son d'ata, kana yace. "Ga masoyin naki.“ Murmushi me sauti ta saki tace. "Na gode Babana. “ Baki galala Iya ta saki ta na kallonsu daga bisani ta tafa hannuwa tace. "Yau naga lalacewa ni Asabe, yanzu ina gaya maka abinda yarinyar nan ta yi mini amma kai d'ata ka d'auka ka bata, gani ni wacce na yi silar zuwanka duniya ka san da cewa ina mutuwar son ka'za amma baka tab'a siyowa ka bani ni kad'ai a gidan nan ba, sai dai ka siyo gaba d'aya aci, amman ita da yake shafi da mai ce ka ware ta cikin 'yan uwanta uku, ture biyunma tunda su cikinsu d'aya ai ko Nimha ka siyowa don gudun fitina.“ "D'atan da na siyo mata na tabbata ba za ta cishi ita kad'ai ba, rabawa zasui gaba d'aya da ita da 'yan uwanta, zancen kuma Nusrat ta zage ki wallahi Iya ko jikina duk kunne ne bazan tab'a yadda za ta iya zaginki ba, ko da kuwa dukan mutuwa kikai mata a cikin gidan nan, bare kuma na san halinta ba sawa ba fitarwa, da dai Shukhura kika ce to tabbas wannan zan yadda amma 'yar baiwa lalala, sai dai kice Shukhura ce ta zageki kikace 'yar baiwa ce saboda.... ”Da sauri Iya ta dakatar da shi da fad'in. 'Ni wallahi bance maka Safiya ba, ko sunanta ban ambata a gurin nan ba in ba yanzu ba, jama'a ko kunji na ambaci Safiya? “ Ta fad'a da k'arfi yadda 'yan ciki zasu jiyo ta, murmushi Baba kawai ya yi ya ja hannun Nusrat sukai ciki. "Kedai Mero kin haifi jarabar aljanu a gidan nan, yarinya ta bi ta zamar muku masifa duk kunfi k'aunarta cikin 'yan uwanta, su kuma hakan ko kad'an hakan ba ya damunsu, wannan wata iriyar musifa ce? Kai kuwa Audu k'atuwar asara ce ta hau kanka don zan iya dafa qur'ani kafi son wannan 'yar aljanun ko nace 'yar ruwa akan ni da na diroka duniya, bacin haka har maganata za ka k'aryata ka zab'i d'iyarka, babu komai ai gobe Shamsu zai zo garin, Allah sarki d'an albarka na san gobe miyarmu da ka'ji zan cisu har na ture, don ni ina jin idan yazo ma tattara kayana zan na bisa, don wallahi na gaji da cin shinkafa 'yar hausa da tuwon garin masara kullum suna cushe maka a ciki, don na ji ana rad'e rad'en tuwon masara gini yake a cikin mutum, haka kawai na zauna naje na kashe kaina tun wa'adina bai cika ba. “ Sai misalin k'arfe takwas Mama ta dawo, kallon Nusrat da ke kwance ta yi tace. "Ina Mamana, Yusra taci abinci da kika barta tai bacci?” "Cikin gida tace mini za ta shiga tun d'azu, Yusra kuma sai da taci abinci tukunna tai bacci. “ "Lafiyanki kuwa naga kina yatsina fuska? “ Ta tambayeta duk da a ranta mamakin wai Shukhura ce tace ta tafi cikin gida, bayan ba k'aunar zuwa gidan take ba, aike ma da dole take shiga. "To ki tashi ga fura na taho miki da ita kisha sai ki sha magani.“ Da hanzari ta mik'e don dama yunwa take ji kuma har ga Allah ba ta k'aunar cin tuwon donma ta d'an ci d'atan da Baba ya kawo mata duk da wasu sunce shima ya na faifaye ciki, ita kuwa Mama sanin halin d'iyar ta ta yasa ta yo mata guzurin furar. Sauke idanuwanta ta yi akan kular tuwon da Shukhura ta ajiye, a fili tace. "Allah ya shirya mini ke mamana. Maza Nusrat ki gama kije ki kira mini ita. “ Ta na rufe bakinta ta jiyo sallamarta suka amsa mata. "Laa Mamanmu kin dawo ashe? sannunki da dawowa. “ Fuska a had'e tace. "Yauwa, me kika je yi cikin gida? “ "Nifa ba cikin gida nace mata zanje ba, gidan su Farha nace mata za ni kallo.“ Takai k'arshen maganar ta na kallon fuskar Nusrat. "Ban hana ki zuwa kallo ba?to da Babanku kawai zan had'aki na huta, Ke kuma ai ga shinan kin rufa mata asiri ta tonawa kanta. “ Takai k'arshen maganar ta na kallon Nusrat, yayin da ita kuma ta saki murmushi. "Kiyi hak'uri Mamanmu bazan sake ba. “ "Sau nawa kina fad'in haka? “ "Allah da gaske nake Mamanmu daga wannan bazan sake ba. “ "To wancan uban tuwon da kika ajiye da fatan abincinki ne na sati guda ko?“ "Haba² Mama, sai kace wacce uwarta ta tsine mata duniya ta juya mata baya zan jera sati guda ina cin tuwo, tuwonma ba sabo za'a dinga yi mini ba. “ Mama ta so yin dariya amma ta kanne tace. "Koma me zaki ce kice, amma wancen tuwon sai kinyi sati kina cinsa a gidan nan tun da ke kunnenki na k'ashi ne ba ya jin magana, bacin sau nawa zance ki daina cika mini kula kina kawo mini d'aki? “ Sai da ta fara turo bakin nan gaba kana tace. "To kina dai kallo duk ran girkinta sai ta cika kula fam ta kai d'aki, bacin daga ita sai 'yarta d'aya kamar rai, mu kuwa ta milliro mana, ta cikawa Baba da sirikarta kwano, nima kuwa yau na rama na millira musu na millirawa Iya ma, Baba kuwa na cika masa kwano har ya na zuba. “ Salati Mama ta yi ta saki baki ta na kallon Shukhura. "To don ita ta na cika kula ta kai d'aki ita ta shafa, sune mayunwata ba mu ba, ga shinan yanzu kin sakani a bakin duniya, tijarar Iya ma kad'ai ta isheni, don cewa za tai ina sani na baki girkin shiyasa har ga Allah ban son na bar miki girki na fita. “ "A to don wallahi muddun ni nai girki bazan fasa ciko mana kula na kawo d'aki ba, ko ba za muci ba sai dai mui asararsa. “ "Me kika ce?“ Mama ta tambayeta kasancewar k'asa² tai maganar. "A'a cewa na yi kiyi hak'uri bazan kuma ba. “ "To zo ki fice mini da kular, kije ki k'ara musu tuwon.“ Ta na jin haka ta saki k'ara. "Waishhhhhh Mama kashi² ina zuwa ta fice da gudu zuwa ban d'aki, murmushi Mama ta yi a ranta ta na nemawa Shukhura shiriya ta d'auki kular tuwon ta fita, murmushi ma Nusrat keyi tun fara dramar Maman da Shukhura, don dama sun riga da sun saba...... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biyama ki turo cikinta. 09037093702. In katin wayane 400 Za ku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: https://chat.whatsapp.com/L7ZWZtJoVg39WGbG36r78I. Pls share *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *THREE* Ashe ba kallo Shukhura taje ba, can bakin titi taje gurin me saloon ta siyo farata koraye shar da su, ta biya gurin me zob'o ta siyo, ta sayi cewing gum ta jefa a baki sannan ta yo gida, a wani d'an lokon babban tsakar gida ta ajiye faratan da zob'on kana ta shigo. Sai da ta bari d'aya ta gota ta tabbata a lokacin baccin kowa ya yi nisa ta salallab'a a hankula ta zare sakatar gurinsu ta fice, bayan ta d'auko farar hodarsu, ko tsoron duhun dare ba ta yi, bursuna farar hodar ta yi tun daga fuskarta har wuyanta, ta cire hijabinta sai ta bar wata hula me cibiri cibirin gashi a kanta, rigar jikinta dama ta wani tsohon uniform d'inta na islamiya ne da take bacci da ita. Cikin dabara ta man manna faratan a yatsunta da chewing gum, ta d'aga jarkar zob'on nan ta shanye ta bar d'an guntu a ciki, nan da nan bakinta ya yi jajir, ta guntsi ragowar a bakinta, turmi ta taka ta zira hannunta ta saman k'ofar d'akin Iya a hankula ta zare sakatar kana ta tura ta shiga ta mayar ta rufe, kallon Iya da ke bacci akan gado ta yi, sakamakon haska 'yar k'aramar cocilan d'in da ke hannunta da ta yi a ranta tace. 'Za ki gane kurenki ne.' Kan ruwan cikinta ta hau ta zauna, cikin bacci Iya ta ji masifar nauyi ya ziyarceta, a hankula ta bud'e idanuwanta duk a tunaninta madannin dare ne ya danneta, ido biyun da ta yi da Shukhura nan take wani mugun tsoro ya kamata ta bud'e baki za tayi ihu Shukhura ta yi saurin toshe mata baki da wani tsumma da ta yayibo a gefenta, cikin wata iriyar murya me ban tsoro tace. "Kada ki mana ihu a nan, in ba haka ba zamui daga daga da namanki. “ Nan da nan jikin Iya ya fara rawa kar kar ta fara biya duk wata addu'a da tazo bakinta, son tashi take amma gaba d'aya ta k'asa tashi, hannu Shukhura ta Saka ta karto gefen fuskar Iya had'e da juyar da idanuwanta, rintse ido Iya ta yi kafin ta ji saukar muryar Shukhura a kunnuwanta. "Al'quran kika kuma tsangwamar Nusrat a cikin gidan nan sai mun cire miki k'afa d'aya da hannu d'aya, mu kuma maidar miki bakinki k'eyarki, sannan mu d'aukeki zuwa cikin ruwa, kima gode Allah kin fara manyanta da wallahi yau sai mun sakaki murmushi da hak'ori d'aya.“ Iya firgita Iya ta firgita, wani mugun tsoro ne ya kuma shiga jikinta ko k'wak'k'waran motsi ta kasa, ta na san magana amman ba dama saboda ta toshe mata baki da t'summa kuma ta rik'e da d'aya hannunta, um umm kawai take ta na girgiza kai hawaye na zuba a idonta, tausayi ta bawa Shukhura don tasan ta sha nauyi, don Iya irin siraran tsofaffin nan ne, ita kuwa Shukhura ta na da jiki, d'agata ta yi ta sauka daga kan gadon ta cire hannunta daga bakinta had'e da fad'in. "Kada kuma ki sake ki mana ihu don wallahi zan maidar miki da idonki goshi ki zama mai ido d'aya. “ Ta na maganar ne ta na ja da baya, yayin da Iya tace. "Allah ya baku hak'uri wallahi na daina takura mata, ba iya ita kad'ai ba ma wallahi dukansu na daina shiga harkarsu.“ Wani ihu Shukhura ta yi ta na zaro harshe ya yin da Iya ta yi wani hantsile ta koma k'arshen gado goshinta ya bugi da bango, duk azabar da ta ratsa ta k'wak'wal warta amma haka ta d'inke bakinta saboda tsoron kar ta yi ihu a maidar mata da idonta goshi, ja da baya Shukhura ta ci gaba da yi had'e da fad'in. "Kada kuma ki sake ki juyo sai mun b'acewa ganinki in ba haka ba kuma zamui sama da ke zuwa fadar sarkin aljanu. “ Ta na kawowa nan, ta bud'e k'ofa ta fice, ta taka turmi ta maidar mata da sakatar ta, kana ta d'auke turmin ta mayar da shi mazauninsa, sannan ta d'auki hijabinta ta shige ciki, ta na k'ok'arin mayar da sakata ta ji muryar Baba yace. "Waye nan?“ K'irjinta ta ji ya yi wani irin bugu nan da nan wani mugun tsoro ya kama ta ta fara rawa da bakinta. "Um nice, fitsari na fito naga kamar ba'a saka sakata ba, shine na duba. “ Ta na kawowa nan ta yi saurin fad'awa band'aki don gudun kada ma ya fito ya ganta. Fuskarta ta wanke da sabulu, ta cire faratan ta jefa a shadda, kana ta fito ta koma d'aki, sai bayan da ta kwanta a shimfid'arta wata muguwar dariya tazo mata, fashewa ta yi da dariya sosai ta na hango yadda idanuwan Iya suka firfito gaba d'aya kamar na mayyar da aka kama, wata dariyar ta kuma fashewa da ita, Nusrat da ke gefenta ta farka ta na kallonta a tsorace. 'Anya kuwa babu almutsutsai akan Shukhura kuwa. ' Taji zuciyarta ta jefo mata wannan tambayar kafin ta ji muryar Baba ya na k'walo mata kira. " 'Yar baiwa“ "Na'am Baba. “ Ta amsa, ta tashi ta fita jiki a sanyaye. "Lafiya kuwa nake jiyo dariya a d'akin ku?“ "Wallahi Baba Shukhura ce, kuma ban san me takewa dariyar ba, anya Baba ba za'a nema mata magani ba, ni wasu abubuwan in ta na yi gani nake kamar ba ita kad'ai ba. “ Murmushi Baba ya yi yace. "Shukhura. “ "Na'am.“ Ta amsa cikin muryar shagwab'a ta fito ta na sosa kai. "Me ya sakaki dariya cikin tsohon daren nan? “ Sai da ta fara turo baki gaba sannan tace. "Kawai tuno yadda na tumur mushi hadiza d'azu a makarantar allo na yi, tsokanar Yayarmu ta yi ni kuwa na had'a mata jini da majina ta mik'e da k'yar jiki duk yai tsami kamanninta duk sun sauya bakin nan kamar zunb'utun zakara. “ Ta kuma fashewa da wata dariyar. "To jeki ki kwanta, kinga dare ne kada ki kuma dariyar, kinji Mamanmu. “ D'aga masa kai ta yi, ta koma d'aki, ya bita da idanuwa a zuciyarsa ya na nema mata shiriya, duk da a zuciyarsa shima ya fara tunanin ba ita kad'ai bace, don al'amarin nata akwai ban tsoro, shiyasa ya daina dukanta ko me Iya tace tayi mata, don ya san itama Iyan da laifinta, kuma duk irin dukan da zaiwa Shukhuran ba shi zai hana ta samo ta inda za ta rama akan Iya ba. Duban Nusrat ya yi yace. "Je ki kwanta 'Yar baiwa, zamui maganar da Mamanku da safe.“ "Toh“ Tace had'e da juyawa ta koma d'akin, ta na kwanciya Shukhura ta rungumota ta baya ta na sakin dariya. "Ina sonki Yayarmu, matuk'ar ina numfashi bazan tab'a bari a tab'a mini ke ba na k'yale, da a tab'a ki gara ni a tab'a ni. “ Wasu hawaye ne suka zubo a fuskar Nusrat wa'yenda ba ta san dalilin zubowarsu ba, hannu ta saka ta baya ta rik'e hannun Shukhura gam had'e da fad'in. "Nima ina sonki k'anwata, amma don Allah ki daina fad'a kinji k'anwata. “ "Zan daina, idan har aka daina tab'aki, fatana na saka tsoron ki a zuciyar duk me tab'aki, yadda ko ganinki ya yi sai yai shayin yi miki magana." Ta na kawowa nan ta kuma rungumota a haka bacci ya d'auketa saboda ba ta da wuyar yin bacci, Yusra da ta farka ta jita ba jikin Nusrat ba ta yi juyi ta shige jikinta, hannu Nusrat ta saka ta na shafa kanta, ta na shafo kan Shukhura da d'aya hannun, har lokacin hawaye na zuba a idanuwanta, ta tabbata hawayen k'aunar da 'yan uwanta suke mata ne, kyakkyawar Katanga mahaifiyarsu ta gina musu a zuciyoyinsu na k'aunar junansu, babu ruwansu da k'yashi ko bak'in cikin anyiwa wani abu a cikinsu ba'aiwa d'aya ba, ta na fatan soyayya da k'aunar da sukewa junansu suci gaba da ita har k'arshen numfashinsu, kada Allah ya bawa wani nasarar rusa katangar alak'ar da take ginanna a zuk'atansu. Dubanta ta kai ga mahaifiyarsu da ke baccinta cikin kwanciyar hankali, duk abubuwan da suka faru ba ta san anyi ba, kasancewarta me nauyin bacci, shiyasa ko wani abun Baba ke buk'ata a gurinsu sai dai ya k'wallowa Nusrat kira. A b'angaren Iya kuwa k'wak'wame da bango wani wahalallen bacci ya yi gaba da ita, ba tare da ta shirya zuwansa ba. Washe gari da safe Nimha da taje kaiwa Iya abincin kari, kasancewar girkin Ummanta ne, anan ta samu Iya da kumburarran goshi, gefen fuskarta a karce. "Ayya Iya sannu me ya same ki?“ "Ke dai bari 'yar nan, duhun dare ne irin na damuna, na tashi fitsari na nemi cocilan d'ita na rasa nai shahada na fito haka shine na sha k'asa.“ "Ayya sannu Allah ya kiyaye, ga karin kumallon ki nan.“ Cewar Nimha, daga haka kuma ta juya ta fita kafin Iya tace. "Amin. “ Nimha na zuwa ta gayawa Ummanta abinda ya samu Iya, tab'e baki Umman ta yi had'e da fad'in. "Wa ya sani ma ko karkashin aljanar yarinyar cen ta kuma kad'awa ta zuba mata, ni ban tab'a ganin tak'adiriyar yarinya irin Shukhura ba, Iya na cewa Nusrat 'yar aljanu ai Shukhura ce 'yar aljanu ba Nusrat ba.“ Maganar da Umma ta yi kaf a kunnen Shukhura suka sauka, wani murmushi ta yi a ranta tace. 'Allah ya had'amu za kwa kiyi kallon tak'adiranci.' Kowa na gidan sai da ya shiga ya duba Iya, Nusrat da Shukhura a tare suka shiga duba ta, abinda ya bawa Nusrat mamaki ganin Iya ta kirata da Nusrat abinda tsawon rayuwarta ba ta tab'a kiranta da shi ba, sai dai ta kirata da Ai, ba ma za tace Ayshan ba, duk don Malam ya ji haushi. Sannan kuma har suka fito ba ta sanyata aiki ba, kasancewar duk sanda ta shiga gurin ba za ta fito ba sai ta moreta ko ya ya ne, kuma ta na kallon Shukhura ta na ta sunkui da kai ta na matse dariya, shine da suka koma d'aki ta dubi Shukhuran tace. "Wai dariyar me kike ta matsewa ne a d'akin Iya? “ "Yo ba dole na yi dariya ba, kinga kuwa goshinta kamar mulmuleliyar daddawa sai shek'i yake. “ Ta fashe da dariyar da ke cinta tun d'azu. "Allah ban yadda da ke ba Shukhura, duk yadda akai ta dalilinki Iya ta ji ciwon nan. “ " To ni me ta mun da zan saka ta ji ciwo? “ Ta fad'a ta na d'an turo baki gaba. "Kefe kika ce sai kin saka tsorona a zuciyar duk me takura mini, kuma yau kallon da Iya ta yi mini ya bam bamta da wanda ta ke mini a kullum.“ Rik'o hannuwanta Shukhura ta yi had'e da fad'in. "Tabbas 'Yar baiwa ce ke Yayarmu.“ Kana ta shiga labarta mata yadda sukai da Iya ta na dariya, murmushi Nusrat ta yi tace. "Tabbas Iya tai namijin k'ok'ari da ba ta sume miki ba, don in nice wallahi sumewa zan yi, a gaskiya kin d'au hak'k'in 'yar tsohuwa, don ta tsorata sosai tun da gashi ko labarin ainihin abinda ya faru ba ta bayar ba.“ "Wallahi ba wani hak'k'in ta da na d'auka, in hakane ita sau nawa ta na d'aukar hak'k'unanmu. “ Girgiza kai Mama ta yi, a kwance take duk a tunaninsu bacci take, duk abinda Shukhuran ta fad'a ta jishi, kuma ta na nemawa 'yar tata shiriya, don Baba yace da kansa zai dingai mata rubutu ta na sha, don abin nata ya fara yawa duk abinda akai mata tace sai ta rama ko ta halin k'ak'a. "Kya ci gidanku, bari Babanku ya dawo sai na gaya masa, kuma ki tashi kije yau ke za ki mata shara ki wanke mata band'aki. “ Zunb'uro baki gaba tai ta mik'e, don in ba ta ta shi ba ta san Mama na iya jefo mata duk abinda ke kusa da ita, bayan fitarta Mama ta yi tunanin may be taje ta kumai mata wata muguntar don haka ta shiga k'wala mata kira kafin ta tashi ta bi bayanta....... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *FOUR* Washe gari da safe misalin goma da rabi, zaune suke suna cin jolof in taliya a babban tray, kasancewar Baba ba ya nan ba a gida ya kwana ba kuma girkin Umma ne sai tak'i toya k'osai ta dama zallar kunu kad'ai ta bawa Nimha 200 ta siyo musu iya su da Iya kawai, wannan dalilin ne yasa Mama ta yi musu jolof in taliya saboda kunu kad'ai bazai rik'e cikinsu ba kuma Nusrat ba ta shan kunu sai koko. Muryar Hidaya suka ji ta na k'wallowa Nusrat kira tab'e baki Shukhura ta yi bayan ta zuba taliyar a bakinta tace. "Ga su shafi da mai nan an faso. “ Wata muguwar harara Mama ta jefeta da shi, kawai sai tai murmushi ta sunkui da kai, daga bakin k'ofa Hidaya ta tsaya, ta tsuguna har k'asa ta gaisar da Mama kana ta dubi Nusrat da ke kallonta ta na murmushi, ta yafitota da hannu had'e da fad'in. "Kizo Yaa RJ ne ke kiranki, tsam Nusrat ta mik'e dama jikinta da hijabi saboda ba ta rabo da shi a jikinta ta bi bayan Hidaya suka fice Mama ta bita da idanuwa, Shukhura ce tace. "Nifa Mama sai nake ganin Aunty Maryam kamar ba ta son Yaa RJ ya na kula Yayarmu.“ "Rufe mini baki ko na dakar miki shi da hannuna, na fa gaya miki ba na son irin magan ganun nan ko? Idan ma ba ta son ya kulata naga ta dalilinta duk kuka sanshi.“ "Yi hak'uri Mama, amma kuma in saboda kar wata alak'a ta shiga tsakaninsu ne to ta sha kurumunta in Allah ya yarda mijin Yayarmu ba daga tsatson mijinta zai fito ba ehe. “ Girgiza kai kawai Mama ta yi don zuciya ta kusa ciyota ta k'wala mata mificin da ke kusa da ita, zama Shukhura ta gyara had'e da gyara murya tace. "Mamarmu nidai na gaji wallahi, ko yaushe sai ki dinga hanamu fad'a ana kuma k'wararmu, nidai wallahi idan Baba ya dawo zan kwashe duk abinda matarsa ke mana a gidan nan in gaya masa, haka kawai yanzu da ba dan muna da wannan taliyar ba sai dai fa mu zauna da yunwa har rana da ranar ma ba wani ishashh......“ Dakatawa ta yi da maganar sakamakon mificin da Mama ta rafka mata don taga hararar da take wurga mata ba za ta saka ta rufe mata baki ba sai ta had'a da duka, mik'ewa Shukhura ta yi ta na zunb'uro baki, ta figi hijabinta da ke kan k'ofa, ta na matsar k'wallar k'arya ta fice ta na. "Wallahi na kusa yin maganin wata a cikin gidan nan.“ Ta fad'a da k'arfi yadda Umma da ke d'aki za ta jiyo ta. Aunty Maryam na shiga d'aki ta tarar da Iya da kumburarran goshi. "A'a Iya me ya sameki haka?“ "Zamewa na yi na fad'i na buge da bango. “ "To wannan karcewar ta gefen fuskarki fa?“ "Ke nifa ba na son tambaya, na gaya miki zamewa na yi na fad'i, me kuma kike son ji, kin wani titsiyeni kamar wata uwata sai kinji abinda ya sameni sai kace wani abu za ki iya a kai, mtssss. “ Taja tsaki taci gaba da sababi yayin da Aunty Maryam tace. "Allah ya huci zuciyarki.“ Ta fice daga d'akin, in ba haka ba ba za ta daina sababin ba, ta shiga d'akin Umma don su gaisa. A cikin mota Nusrat ta samu Yaa RJ, tun fitowarta yake sakar mata murmushi ta cikin gilashin motar har ta k'araso gaban motar, a bud'e murfin motar yake don haka ta shiga ciki ta zauna suka had'a ido da Hidaya da ta juya ta koma cikin gidan. Shiru ne ya biyo baya sai kanta da ta sunkuyar k'asa ta na watsa da yatsan hannunta, yayin da shi kuma ya kafeta da idanuwansa, ya na jin wani sabon yanayi a kanta, ya san Nusrat yarinya ce ta yi k'ank'anta ya furta mata kalmar soyayya, amma ya na jin tsoron ya dawo ya tarar wani ya riga shi nasarar karb'ar soyayyarta, sanyin halinta, yanayin tafiyarta, yanayin maganarta komai ya yi dai-dai da yadda yake son matarsa ta kasance. "Ina wuni Yaaya?“ Nusrat ta katse shirun da yake tsakaninsu ta kuma katse shi daga tunanin da ya tafi, rintse idanunwansa ya yi ya busar da wata iska mai sanyi saboda yadda muryarta ta shiga jikinsa ta zauna, wani siririn zoben azurfa ya ciro daga d'an k'aramin yatsan hannunsa. "Muga hannunki. “ Zara zaran yatsunta ta mik'a masa ya zira mata a yatsanta na kusa da babban yatsa. "Daga nan kaduna zan wuce ta nan jirginmu zai tashi zuwa Uk nan da shekara uku zan kammala karatuna na dawo, ki mini alk'awari ba za ki bawa ko wani saurayi damar k'ulla soyayya da ke ba. “ Ba ta gane inda maganarsa ta dosa ba, don haka ta tsira masa idanuwanta kamar me karantar amsoshin tambayoyin da ke dank'are a zuciyarta, yayin da shi kuma yake jin kallon da take masa har tsakiyar zuciyarsa. 'Meye dalilin da yasa ka bani zobe, me yasa zan maka alk'awarin k'in kula ko wani saurayi bayan ba ni da tabbacin sona kake, idan ma sona kake anya auranmu zai yuhu kuwa, kana ganin Aunty Maryam za ta bar Katangar alak'ar da take ginanna a tsakaninsu taci gaba da ginuwa?' Wa'yannan tambayoyin sune cunkushe a ranta amman ta k'asa furta ko da kalma d'aya, ji take bakinta yai mata matuk'ar nauyi. Hannunta ya matsa had'e da fad'in. "Pls Nusrat. “ Tsintar kanta kawai ta yi da d'aga masa kanta, ya saki kyakkyawan murmushi, ya d'auko wata leda ya d'ora a kan cinyarta. "Na gode Nusrat, Allah ya baki ikon cika mini alk'awarina, bari ni zan wuce, ki gaida mini da su Mama. “ "Za su ji insha Allah, Allah ya kaika lafiya, ya kuma baka sa'a akan karatun naka.“ "Aminnnnn“ Yace yana me jin dad'in addu'arta yayin da ita kuma ta fice ba tare da ta d'au ledar da ya ajiye mata ba, murmushi ya yi don ya san za'a rina, a dai-dai lokacin Shukhura ta fito ta na zunb'uro baki, da hannu ya yafitota tazo gareshi, d'an risinawa ta yi ta gaisheshi yace. "Ga leda nan d'auki ki kaiwa Mama kice ina gaisheta.“ "Tom, an gode. “ Ta d'auki ledar shi kuma ya ja motarsa yai gaba. _RIDWAN JIBRIL shine cikakken sunansa yayin da ake masa inkiya da RJ, mahaifinsa da Yusuf mijin Aunty Maryam uwarsu d'aya ubansu d'aya, mahaifinsa ya rasu tun ya na yaro a gurin mahaifiyarsa yake da take aure a kaduna, tun bayan auran Yusuf da Aunty Marya ya d'auko RJ ya dawo gurinsa da zama suka rik'eshi tamkar d'ansu na cikinsu, bayan gama karatunsa na_ _secondary ya turasa Uk acan yake had'a karatunsa a fannin jarida._ _Hidaya da Nusrat tasu tazo d'aya sosai, suna k'aunar junansu hakanne yasa Nusrat take yawan zuwa hutu gidansu, yayin da shak'uwa me k'arfi ta shiga tsakaninta da Rj, har ta rikid'e ta koma soyayya a zuciyar RJ, idan har zaije kaduna gurin mahaifiyarsa sai ya fara tsayawa gurin Nusrat ya yin da k'arara Aunty Maryam ke nuna ba ta son alak'arsa da Nusrat saboda akwai wani buri da suka ci a kansa ita da mai gidanta._ Kwata² Shukhura tak'i yadda ta shiga ko gurinsu, ta na filin babban tsakar gida a zaune ta na dakon zaman jiran Baba ya dawo, don kada ma Mama ta hanata aikata abinda tai niya, ledar da RJ ma ya bata a bakin k'ofar d'aki ta ajiye ta fito don duk kada Mama ta ruguza mata shirinta, ta san dai duk tsiya Baba bazai wuce 12 na rana bai dawo ba saboda ba a gida ya kwana ba. Har kusan k'arfe d'aya Baba bai shigo cikin gidan ba, har ta fara tunanin tashi ta jiyo takun tafiya don haka ta maida idanuwanta kan k'ofar shigowar, aikuwa Baban ne ya yi sallamar ta amsa masa ta nufeshi had'e da d'ora damuwa akan fuskarta, har da fara taro k'walla, gaban Baba ne ya yanke ya fad'i yace. "Lafiya Shukhura me ya faru? “ "Baba.“ "Na'am fad'a mini me ya faru? “ "Dama kullum Mama ce ke hanani gaya maka.“ "Ina jinki.“ "Duk ranar girkin Umma ba ta bamu abinci ishashshe, da kai da Iya da su ta ciccika muku kwano, kuma har d'anye take ragewa ta b'oye, to yau da safe ba ta toya mana k'osai ba zallar kunu kawai ta dama, ta bawa Nimha ta sayo musu su da Iya. “ Ran Babane ya yi mugun b'aci, ya tabbata Shukhura ba za tai masa k'arya ba, shafa kanta ya yi yace. "Jeki ciki zanwa tufkar hanci. “ Cike da murna ta shige ciki ta na jin kamar ta sauke abu me nauyi a zuciyarta ko kad'an ba ta damu da hararar da Mama ke ta zabga mata ba. Sai da ya bari Umma ta gama girki ta raba kowa ta kai masa shima ta kawo masa nasa sannan ya k'wallowa Shukhura kira, ta amsa ta fito da saurinta. "D'auko mini abincinku.“ "Toh." Tace da hanzari ta juya ta d'auko. "Jeki ki anso mini na Iya. “ "Ai yau Iya ba ita kad'ai bace su Aunty Maryam sun zo. “ "Af na sha'afa, da na shiga gurin Iyanma mun gaisa, bar na tan. “ Ya dubi Umma yace "D'auko mun naku, kuma bance ki rage komai ba, inma kin rage da kaina zanzo na duba.“ Tsuru² Umma ta yi da ganinta ka san ba ta gaskiya taje ta d'auko ta kawo masa duban Shukhura ya yi yace. "Je ki d'aki, ki turo mini Mamanku. “ Shukhura na barin gurin Baba ya dubi Umma yace. "Yanzu wannan adalci kenan? Kalli abincin da rai d'aya zai ci, ki dubi na rai biyu duk sun taka wanda rai hud'u zai ci kinwa kanki adalci? Ko iya Nimha kad'ai ai sai ta tashi da wannan abincin, idan ni ba na gani ai Allah ya na ganinki kuma hakk'insu bazai tab'a barinki ba. “ Fad'a sosai Baba ya shiga yiwa Umma kamar zai ari baki, ya shaida mata muddun ta kuma irin rabon nan to sai ta bar masa gidansa, Mama da tazo fad'an ya rufe ta da shi akan me za ta hana a gaya masa irin haka na faruwa a cikin gidansa ya d'au mataki tunda ita ba ta gaya masa ba, ita dai Mama hak'uri ta bashi don sosai Baba ransa ya b'aci, ranar huni ya yi ya na surfawa Umma fad'a, abincinma ya yi zuciya ya k'i ci ya juyewa su Shukhura akan nasu na su Umman ma ya datsi rabi ya k'ara musu akai ya kira Shukhura ta d'auka, Umma kuwa sai huci take kamar ta janyo Shukhura tai ta jibgarta. _____________ Bayan sati guda Baffa Shamsu yazo garin zariya, a lokacin su Aunty Maryam sun koma kwana uku sukai suka tafi. Transfer yake nema zai dawo zariya gaba d'aya hakanne yasa yazo don neman gidan da zasu samu su zauna, duk da nan kusa da gidansu an masa tallansa to dai ya na son siya amman dai ba su gama cininki ba, tun zuwansa Iya tace. "Nidai yau aradu shinkafar gwamnati zanci, don wallahi na gaji da cin shinkafar hausa ina karo da tsakuwa ta na farfasa mini hak'ori, kalli nan kaga yadda duk hak'orina ya farfashe, don haka ma ni wallahi in za ka tafi binka zan, don na gaji da cin tuwon masara kullum da daddare na kwanta, gara a dinga dafa mini taliyar nan ta gwamnati me dad'in gaske.“ Murmushi kawai Baffa Shamsu ya yi yace. "Haba Iya ba na son kina irin wa'yan nan magan ganun kema dai kinsan Yaya yana matuk'ar k'ok'ari, idan yaji abinda kike cewa bazai tab'a jin dad'i ba.“ "To kar ya ji dad'in mana ni ina ruwana, wani k'ok'ari yake banda son 'yarsa da ya fifita a kaina. “ Ko me ta tuna kuma sai tai shiru kana tace. "Mubar ma maganar d'an arzik'i maza je ka siyo mana shinkafar, ka kuma siyo mana kaji don yau mu d'an wasa bakinmu, don rabona da ci nikam ina jin tun kan rasuwar Malam. “ Girgiza kai kawai Baffa Shamsu ya yi ya na mamakin halin mahaifiyar tasu sam ba ta da godiyar Ubangiji, duk zuwan da zaiyi sai sunci kaji a gidan, haka zalika Baba ma idan ya ji aljihunsa da nauyi ya na siyo musu su ci amma wai kunji rabonta da ci tun kan rasuwar Malam. Buhun shinkafa biyu da katan na taliya da macaroni biyu Baffa Shamsu ya siyo musu ya ajiye su a d'akin Mama, ya siyo musu kaji guda biyar manya ² gashi kuma aka taki sa'a girkin Umma ne, don haka Shukhura ta na da 1000 tace bari taje titi ta siyo don ta san 'yar kad'an za'a sanmusu, Nusrat ma na da 1000 sai ta bata ta siyo musu guda biyu kuma manya da su. Ilai kuwa cinya d'aya fukafiki aya sai wuya aya aka saka musu, ko kad'an ba su damu ba Shukhura ta wanke nasu ta tafasa ta fara suya. K'amshin suyar naman Iya ta ji a ranta tace kaddai matar nan ragewa ta yi take soyawa da hanzari ta fito don ta ganewa idonta, ganin Shukhura ce me suyar ta kai hannu za ta d'auka a cikin wa'yanda ta kwashe, Shukhura ta yi saurin d'auke robar hannun Iya ya sauka a k'asa har sai da ya yi k'ara tace. "Auchhhhh“ Don ta ji zafi sosai, Shukhura kuwa ko a jikinta ta murgud'a baki tace. "Ai ba taku bace, wannan tamu ce naje na siyo, da za ki d'auko yamutsats tsan hannunki ki saka mini a ro....“ Ba ta k'arasa ba taji saukar mari a kuncinta, dafe kuncin ta yi ta tsaya ta na kallon Mama da ta fusge robar naman a hannunta ta d'auki cinya manya² guda biyu ta bawa Iyan, sai da Iyan ta ansa kana ta tab'e baki. "Ai da ba ki daketa ba ai na san duk makirci ne irin naki, ke kitsa mata dukkan abinda takeyi a gidan nan, amma ai Shamsu yazo zai mini maganinta. “ Ta na kawowa nan ta fice daga gurin Shukhura ta bita da d'an iskan kallo, Mama ba ta iya cewa komai ba ta koma d'aki Shukhura ta k'wallowa Nusrat kira. "Yayarmu zo ki kama mini na shiga band'aki. “ Nimha tace. "Kawo na miki kan ki dawo. “ "Don aji dad'in d'iba akai d'aki ba, a'a basshi na gode ga Yayarmu nan za ta ansa. “ Umma ta gallawa Nimha harara. "Maganin shishshiginki kenan ga shinan an gab'a miki magana.“ Memakon Shukhura ta shiga band'aki sai ta fice ta yi gurin Iya. "Kina ina yau in kinci naman nan ba Mama ce ta kawoni Duniya ba. “ Iya na jin haka ta yi saurin nad'e shi a leda ta saka a k'ark'ashin gado, dama ajiyeshi ta yi sai ta gama da na cikin miyar. A bakin k'ofa ta cage tace. "Ki fitomun da namana.“ Sai ki d'auka in kin ganshi ai. “ Bin d'akin tai da ido ta na nazarin inda Iyan za ta ajiye naman, ganin kamar idon Shukhuran ya na sauka a k'ark'ashin gado Iya ta yi saurin d'aukewa ta mik'e tsaye. "Sai kizo ki k'wata in baki da kunya. “ Kanta Shukhura ta yi gadan² ta kama hannunta za ta murd'e. "Ke ke ba ki da hankali wai. “ "Eh bani da shi d'in, ta d'auka ta baki naman sannan ki yab'a mata magana kuma kici alqur'an ba ki isa ba. “ Taci gaba da k'ok'arin k'watar naman dai-dai nan Baffa Shamsu ya shigo. Kyakkyawan maruka ya saukewa Shukhura kana ya tambayi ba'asi Iya ta koro masa bayani, hararar Shukhura ya yi da ke tsugune dafe da kuncinta. "Dama ance ba ki da kunya to yau zanyi maganin rashin kunyarki. “ Ya zari cagar radio ya yo kanta ta saki ihu ta yi bayan Iya dai- dai lokacin ya kawo mata duka ya sauka a jikin Iya, Iya ta zunduma ihu tsabar azaba. "Shamsu ka rabu da yarinyar nan dan Allah kar ka daketa, bai saurari Iya ba ya b'anb'aro Shukhura daga jikinta ya hau zuba mata wayar ko ta ina, aikwa ta bud'e murya ta dinga zunduma ihu, Mama ko motsi daga inda take ba tai ba, kuma ta hana su Nusrat zuwa, tace ai gara taji a jikinta gobe ma ba za ta sake ba, Umma kuwa da gudu ta nufo gurin ta na shewa dama a ciki take da ita. Sai da ya yi mata lilis sannan ya k'aleta,ya fice, Iya na gefe ta na ta matsar k'walla don ta san yau kashinta ya bushe gurin Shukhura, yayin da Umma ke ta shewa ta na fad'ar magan ganu. "Yau dai an mana maganin mara kunyar gidan nan, aiyiri yiri yiri yiri. “ Wani kukan kura Shukhura ta yi ta saki wani ihu ta yo kan Umma da gudu, tsoro ne ya kama Umma ta mik'e za ta fice ta yi tuntub'e ta fad'i, yayin da Shukhura ta shiga aljanun k'arya ta dinga cin uban Iya da Umma da sanda dukkanninsu sun jigata sosai, har sai da Mama tazo ta janyeta, suna shiga d'aki ta fashe da dariya a ranta tace. 'Saura Baffa Sham sun.' Mama kuwa zuba mata ido kawai ta yi, don ta d'auki alk'awarin ta daina dukanta daga yau, addu'ar nan ita za ta cigaba da yi mata anai mata rubutu ta na sha. Da jan jiki Umma ta samu ta komo gurinta, ta na jin mugun shakkar Shukhura a ranta, Iya kuwa kuka ta dinga rusawa don yau babu abinda zaisa ta kwana a cikin gidan nan Shamsu yazo su tafi Kaduna ta wuta da wannan jaraba da masifar da Audu ya haifa. Hankalin Shukhura bai kwanta ba har sai da ta sakawa Baffa Shamsu cinnaku biyar manya² a riga ai kuwa ya sha muguwar azabar da ta wuce dukan da yai mata. 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *SIX* Ta b'angaren Alhj Faruoq Fanda kuwa ya na zuwa gida ya sanar da matarsa Hajiya Suwaiba wata yarinya ta yi wuff da zuciyar yaronsu, farin ciki tsanta H.Suwaiba ta shiga had'e da fad'in "Wata yarinya ce wannan mai matuk'ar sa'a Alhaji?“ "Ai ban baro gurin saukar nan ba sai da na saka aka samo mini bayanai a kanta. A nan unguwar cikaji suke zaune, mahaifinta ba wani mai hali bane sai dai rufin asiri na Ubangiji, itace 'ya ta biyu a gurinsa, ta na matakin aji biyu a sss, an shaidu 'yan gidan gaba d'ayansu da tsantsar tarbiya, sunanta na gaskiya Safiyya, amma da Shukhura ake kiranta.“ K'awataccen murmushi H.Suwaiba ta saki tace. "Kai amman na ji dad'i, Allah yasa itace abokiyar arzik'insa, ai banda hidimar saukar nan da muke ta Maryam da ba abinda zai saka ni zuwa naga sirikata a yau.“ Murmushi Alhj ya yi yace. "Don zumud'i irin naki, gobe in sha Allah dai zamu je gaisuwa, da kayan na gani ina so, don har ga Allah na yaba da zab'in yaron nawa, don dama ina gudun ya d'auko mana irin wayayyin yaran nan marasa tarbiya, fatanmu dai Allah yasa ba maganar wani a kanta.“ "Amin., amma ka dai sanar da Hajiya Inna ko, don gara a gaya mata tun wuri za'a yo mata kishiya. “ Ta kai k'arshen maganar ta na dariya, dariyar shima Alhajin ya yi yace. "Ita ai na fara gayowa ta na nan ta cika fam ta na jiran shigowarsa, na san yau dai ba za'a bashi abinci ba nan za'a koro mana shi. “ Alhj Farouq Fanda asalinsa d'an garin Fanda ne, neman kud'i mahaifinsa yazo yi tun Farouq na yaro, a garin kano suka fara zama ya na yin kasuwancinsa kuma Allah yasa masa albarka a ciki, nan da nan ya tara dukiya me d'imbin yawa, Farouq shi kad'ai ne d'ansa wannan dalilin ne yasa ya bashi gata mai yawa, ranar da Faruoq ya gama karatunsa na shari'ah a ranar mahaifinsa ya rasu, sunyi kuka iya kuka da shi da mahaifiyarsa Fatima (Hajiya Inna. ) Bayan rasuwar mahaifinsa ne dukiyoyinsa duk suka dawo k'ark'ashinsa, sannan kuma ya fara aiki a matsayinsa na babban alqali, nan da nan dukiyarsa ta kuma bunk'asa, ga kuma harkokin kasuwancin mahaifinsa hakan ne yasa ya nemi mataimaka kuma ya samu masu aminci, daga kano suka tarkata suka koma zariya da zama a unguwar sabon gari, gida ya dank'ara ba na wasa ba, ya yiwa Hajiya Inna sashinta da ban, zuwansa zariya anan ya had'u da Hajiya Suwaiba suka fara soyayya itama 'yar garin zariyan ce anan unguwar cikaji, ba'a d'au wani lokaci ba akai bikinsa da Suwaiba, Hajiya Inna na mutuk'ar k'aunar sirikar tata, ko kad'an ba ta san wani mugun hali na uwar miji da ake fad'a ba, ta rik'eta tamkar 'yar cikinta, wannan dalilin ne yasa tai alqawarin idan Allah ya azurtata da 'ya'ya maza za ta k'aunaci matansu kamar 'ya'yan cikinta, don a ganinta babu bambamci tsakanin d'anka da sirikar taka tunda an riga an zama d'aya. 'Ya'ya biyu Allah ya azurtasu da su, Mustafa,sai Maryam, sunga gata sosai gurin mahaifan nasu. Mustafa Faruoq Fanda, wanda abokansa ke kiransa da Fanda ya kammala karatunsa na low har ya zama Barrister mai zaman kansa, komai na shi na rayuwa a sashin Hajiya Inna yake don ta na matuk'ar k'aunarsa, Maryam kuwa rayuwarta ta fi k'arfi a gidan kakanninta na uwa acan cikaji, da yake suma da rufin asirinsu, zamanta a cikaji shiyasa islamiyarsu tazo d'aya da su Shukhura, ba ajinsu d'aya ba, da yake aji biyu ne aka had'e akai saukar, itama Maryam ta yi candy ta na jiran sakamako don ta d'ora daga inda ta tsaya. Wannan kenan. Washe gari da safe Iya ta sami Mama a lokacin ta na toya k'osan da zasui kari da shi tace. "Waini Maimuna ba'a kasafta kud'in nan bane? Na ji shiru ba'a ce Iya ga naki ba. “ "Wani kud'i?“ Mama ta tambayeta don ita a tunaninta wasu kud'i ne Baba ya samu da ban. "Ban gane wani kud'i ba, ki jiki da wata iriyar tambaya, to kud'in da jikokina suka samo.“ D'an k'aramin murmushi Mama ta yi tace. "To ki bari in Babansu ya tashi sai ki tambayesa, in kuma in taso miki shi to? “ "Aini na san ba za ki bari a bani ko ficika a kud'in nan ba Maimuna, na rasa me na yi miki a duniyar nan kika bi kika tsaneni daga ke har 'ya'yanki bare ma waccan me tak'adiriyar k'irar samudawa, da fari kamar arnan zabiya, na tabbata da Nimha ce ta samo kud'in nan biyu za'a raba a bani, amman da yake ku mugaye ne an halicci rowa a jininku biyar kun gagara ba ni, kuje kui ta ci insha Allahu sai kun shekara kuna zabga gudawar da ba ta da comlayin, tuban sardauna kawai.“ Shukhura da Nusrat da ke kallo a 'yar k'aramar wayar Mama, duk suna jin abinda Iya ke cewa, zumbur Shukhura ta mik'e ta fito. "Ki gani a kanki me mugun alkaba'i, insha Allahu kanki bakinki zai komo, naga kud'i namu ne ko, to ba za'a bayar d'in ba kiyi abinda za ki, rowa kuwa mu muka yanke mata cibi, kuma zan nuna miki ni babbar tak'adirya ce don naga kwana biyu kin manta da tak'adirancin nawa, inma tuban galadima ne ko wambai tunda mu musulmai ne Alhmdlillh. “ Tun fara maganar Shukhura Baba ya fito, shi yaiwa Mama alamar ta yi shiru daga k'ok'arin dakatar da Shukhura da take har sai da Shukhuran ta kai aya ya ja hannun Iya suka fice da ke neman fisgewa ta na d'an kuka, sai da sukaje d'akinta sannan ya sake ta yai k'asa da muryarsa sosai yace. " Tun da na auro Maimuna gidan nan take d'aukar cin kashinki Iya, ba ta tab'ai miki kallon banza bare musu da ke, amman har ta haihu kina yi a gaban 'ya'yanta wanda Shukhura ba ta iya d'auka har sai ta rama sannan kuma kisa in daketa k'arshe kuma kanki abin zai dawo, amman har yau kink'i daina abubuwan da kike, maganar kud'i kuma da kike yaran nan daga su har mahaifiyarsu biyar basu karb'a ba ni suka barwa saboda hidimar gida da kuma auransu in ya taso amman kuma kinzo kina fad'ar maganganu a kai, yanzu meye ribar sa'insa da jikarki? Dan Allah Iya ki canja, ki dinga jan girmanki.“ Kuka iya ta ja had'e da fad'in. "Tashi ka fita Audu, tashi ka fita nace tun kafin na tsine maka ka bi duniya, har ni za kazo ka gayawa maganganun banza, a gabanka 'yarka tai mini cin mutumci ka kasa d'aukar mataki saboda an baka kud'i? Jeka kawai Audu na barwa Maimuna da 'ya'yanta kai.“ "Kiyi hak'uri Iya, yanzu zanje na lillisa mata jikinta. “ Kukan Inna ne ya tsaya cak tace. "Idan har kana son albarka a gurina kada ka tab'a lafiyar tak'adiriyar yarinyar nan, don wallahi kaf tak'adirancinta za ta sauke mini yau.“ B'oyayyen murmushi Baba ya yi ya tashi ya fita. Yusra da ta dawo daga siyo sikarin da Mama ta aiketa tacewa Mama. "Wasu a mota sunce suna sallama da Baba. “ Baba da shigowarsa kenan maganar ta sauka a kunnensa ya juya had'e da fad'in. "Bari naje naga su waye.“ Sai kuma gashi ya dawo yace Yusra ta d'auko tabarmi, ta d'auko taje ta shimfid'a a soro. Bayan gaishe² Alhj Faruoq ya gabatarwa da Baba abinda ke tafe da su, sannan ya d'ora da cewar. "Da fatan ba maganar wani a kanta. “ Baba yace. "Ba maganar kowa a kanta, kuma na yi masa izini yazo ya nemi soyayyarta idan har ta amince mishi babu abinda zai hana na bashi ita, Allah ya tabbatar mana da alkhairi. “ Godiya Alhj Faruoq sukai da shi da abokinsa da suka zo tare, sannan ya sanya driver d'insa da ya tuk'osa ya fito da akwatin da suka zo da shi, akwati ne mai kyau madai daici, Alhj Farouq yace. "A bawa Shukhura, kayan sun gani suna so ne. “ Baba yace bazai karb'a ba suka ce ai 'yarsu suka kawo, idan kwa bai ansa ba to baiyi na'am da su ba, daga haka sukai masa sallama suka tafi shi kuma ya ja akwatin ya nufi cikin gida...... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *FIVE* A haka rayuwa take juyawa cikin d'an k'aramin familyn nan, Nusrat ta yi candy, su Shukhura kuma saura shekara d'aya su yi, a lokacin ne kuma aka saka musu ranar saukarsu ta islamiya da yake duk ajinsu d'aya har Nimha. 3/4/2014 shine ya kama ranar saukar tasu. Iya ba ta sauya daga halinta na nuna banbanci tsakanin jikokinta ba har ma ga 'ya'yan nata, don yanzu Baba bai samun cininki sosai a kasuwa sai ya zamto abinci ma Baffa Shamsu ne ke ajiye musu duk wata, saboda ya dawo nan kusa da gidan nasu da zama. Hakan da matarsa ta gani ne yasa ta d'au babban mataki a kansa, abincin da yake sauke musu sai ya koma saukewa gidan su matar tasa duk wata, gaba d'aya ta bi ta mallake shi ta kanainaye shi ba ta bari ya morawa kowa abin biyar face 'yan uwanta, zagi da tsinuwa kuwa ta na shan shi gurin Iya amma a bayan idonta, in a gaban idonta ne kanzil ba ta iya tofawa, saboda abincin da take kawo mata rana da dare kar taje a daina kawo mata ta shiga uku da cin tuwo don yanzu sai su jera sati suna cinsa huni sir, don yanzu rayuwar gidan lallab'ata suke duk abinda Baba ya samo ciki ake k'ok'arin bawa hak'k'insa. 3/4/2014 Ta kama ranar lahadi kenan, ranar da zuk'ata da yawa ke cikin farin cikin kammala saukar karatun alqurani mai girma, za'a bawa kowa allonta na shaidar saukarta, irin wannan ranar ce ko wani bawa ke burin ta riskesa. Tun daga farkon layin makarantar tasu mak'il yake da mutane ko 'yan saukarma ba'a hangowa saboda suna tsakiya a cikin rumfa,banda sautin qira'ar Shukhura mai matuk'ar dad'i babu abinda kake juyowa a gurin mutane da dama sun nutsu suna saurarar karatun da ke saukar da nutsuwa a zuk'ata. Bayan kammala karatun Shukhura ta taso a hankula ta koma gurin zamansu, tun tasowarta FANDA ke binta da kallo, duk da kasancewar ga tsantsar yarinta nan a fuskarta ya na kallo amman kuma ta kama zuciyarsa sosai, tabbas idan ya bari lokaci ya shud'a wani ne zai riga shi mallakarta, don irin su Shukhura ba wanda ake kalla a kau da kai bane, bare nan gaba ta k'ara girma, har ta zauna idonsa ya na kanta, a hankali ya sauke idonsa akan wacce ke Kusa da ita, tabbas ya gano kama a tattare da su ya na kyauta zatan 'yan biyu ne, duk kallon da yake binta da shi mahai finsa Farouq Fanda na lura da shi, ko ma wacce yarinyace wannan tabbas ta taki sa'a gurin d'an nasa, kallo d'aya idan yaiwa mace to tabbas ta taki babbar sa'a, tun kammala karatunsa yake masa zancen aure amma yake tai masa kwana kwane, amman yau yaga alamun d'an nasa yayi kamu, idan kuwa hakane zai fi kowa farin ciki, bare kuma mahaifiyarsa ta ji labari da Hajiya Inna, murmushi ya yi ya na gano yadda Inna za ta d'auki zancen. Kallonsa ya yi har lokacin idonsa na kan Shukhura, wani kyakkyawan murmushi ya saki ya saka bakinsa dai² kunnansa yace. "Da dukkan alamu dai yau yarona yaga matar aure. “ Kunya ce tai mugun kama shi, ashe dai duk abinda yake mahaifinsa na lura da shi, shafa kansa ya yi ya na mai sunkui da kai, shafa kansa Abban nasa ya yi yace. "Soyayya ta na da kyau yarona, Allah yasa matar arzik'i ce. “ A can k'asan mak'oshi ya amsa da "Amin“ Ya na mai jin muguwar soyayyarta a zuciya wannan shi ake kira love at first sight. Bayan kammala saukar aka fara kiran d'aliban da sukai na d'aya zuwa na goma don a basu kyauta. Aysha Abdullahi Ahmad aka fara kira wacce tai na d'aya sannan aka kira Safiyya Abdullahi Ahmad ita tai ta biyu sai Maryam Farouq Fanda da tai na uku daga haka har aka kai na goma duk aka basu Kyaututtukansu, anan Alhaji Faruoq Fanda ya karb'i speaker yai magana akan ya bawa makaranta kyautar million d'aya, sannan ya bawa Aysha Abdullahi Ahmad da Safiyya Abdullahi Ahmad kyautar million d'aya, saboda yaba k'wazonsu, cikin d'alibai kusan 100 su suka d'au matakin na d'aya da na biyu. Nan gurin taro ya hautsine kowa na fad'in albarkacin bakinsa, yayin da wasu ke cewa ai kyautar million biyu gurin Alhaji Farouq Fanda ba komi bace kamar biyar haka yake jin ya cire daga aljihunsa. Iya kuwa sai dashe baki take ta na kuma b'antarar goronta, ta kalli Umma da ranta yai bak'ik'k'irin saboda bak'in cikin Shukhura da Nusrat, harara Iya ta galla mata tace. "An dai yi asarar haihuwa, ace duk kyaututtukan nan da ake rabawa babu sunan Nimha ko d'aya, saboda k'wak'walwarta irin ta jaki ce, amma kalli 'ya'yan albarka, gaskiya Maimuna ta iya haihuwa banda kyaututtukan da suka samo har kyautan million d'aya suka samo mana saboda 'yan arzik'i ne su irin albarka, don ni har ma na fara kasafta nawa kason da za'a bani, na san dai zan samu kamar dubu d'ari biyu, kinga dubu d'ari zan sayi kayan abinci har da su maltina da madara da su k'wai, da taliyar nan me kanannad'ewa ta gwamnati, d'aya dubu d'arin kuma na ajiye a hankula ina zara ina siyo gasashiyar kaza da youghot ina ci da daddare in tayar da kai, wayyo ai a cikin satin nan ma sai an k'asa gane ni zan canja kala saboda cin dad'i, fatar nan tawa da ta fara yamutsewa saboda wahala za ta gyaru, kai Allah dai ya shiwa Maimuna albarka da ta haifo wa'yannan 'yan albarkar, tun da nake ban tab'a rik'e dubu goma ta kaina ba, amman gashi dalilinsu zan rik'e,har dubu d'ari biyi, ni ban san ma tun tuni me ya hanani nuna musu k'auna ba wallahi, amman duk cikin jikokina Allah na gani na fi son su.“ Duk zubar nan da take ita kad'ai take yinta, don Umma ta bar gurin saukar tun sanda ta fara maganar, saboda ganin za ta d'ora mata wani bak'in cikin ne kawai, da ta jujjuya ba taga Umman ba itama sai ta nufo gida ta na tafe ta na kuma kasafta dubu d'ari biyun da za'a bata. Sai kusan k'arfe uku suka baro gurin saukar, saboda an yiyyi hotuna acan, a matuk'ar gajiye dukkaninsu suke, don haka ko waccensu sai da tai wanka kafin su kwanta zuwan jiran yamma ta yi, duk da gidan nasu a cike yake da 'yan hidimar saukar. Da yamma sukai walimarsu anan cikin gidan, kaya iri d'aya suka saka dukansu, Aunty Maryam ce ta d'inka musu, itace ma ta d'au nauyin kayan snacks d'in da suka raba a walimar. Har kusan dare Iya na d'akin Mama tak'i tafiya sai jan Mama take da hira, Mama kwa sai dai tai ta binta da um da umum saboda rashin sabo. "Aini fa ko, tun tuni dama ina sonki da 'ya'yanki dama duk makircin shegiyar matar can ne wallahi, kullum ita kenan kawo mini b'atanci akanku, ai gashinan ta haifi yarinya mai k'wak'walwa irin ta jaki, da k'afafuwanta kamar na babyn roba. “ "Uhm“ Mama tace kawai, ta na mik'ewa don jin ana kiran sallar isha, in ba sallar ta tayar ba Iya ba za ta k'yaleta da wa'yannan zantuttukan nata mara sa kan gado ba, ganin Maman ta tayar da sallah yasa Iya ta tashi ta fice ta na jifan d'akin Umma da banzan kallo, Umma ta na hangota ta labule a ranta tace. 'Makirar mata kawai, insha Allahu k'wandala ba za'a baki cikin kud'in ba inga ta tsiya, ina nan kuma za ki dawo jikina in miki rashin mutumcin da har ki koma ga mahaliccinki baza ki manta shi ba, tsohuwar banza kawai.' Iya tun ta na jiran shigowar Baba yazo a kasafta kud'in, har bacci yai gaba da ita ba tare da ta sani ba, Baba kuwa sai gurin 11 na dare ya shigo, bayan ya rufe gurinsu ya kirawo Mama da su Shukhura anan ya ke gaya musu. "Na kai Accaunt number d'ina makarantarku, Alhmdlillh d'azu na ji kud'inku sun shigo har million d'aya, yanzu me kuke gani za'ai da kud'in?“ Shiru dukkaninsu sukai su na kallon Mama, ganin Maman ba za tai magana ba yasa Nusrat tace. "Nidai Baba a shawarata kawai ka bar kud'in a Accaunt d'inka, in yaso sai a 'yebi wasu daga ciki a siyo kayan abinci, duk wata lalaura da za ta taso sai a magance da kud'in ko kuwa? “ Ta fad'a ta na kallon Shukhura. "Eh Yayarmu, nima hakan nake shirin fad'a kika riga ni. “ Murmushi Mama ta yi, ta na mai yabawa da hankalin yaran nata, kuma taji dad'in abinda suka ce da mahaifin nasu tace. "Na ji dad'i matuk'a da abinda kuka yanke, dama nak'i maganane don na ji ta bakinku, ku tashi maza kuje d'aki, Allah ya yi muku albarka. “ "Amin.“Suka amsa a tare suka tashi suka fita, bayan fitar tasu Mama ta kalli Baba tace. "Ta bakin nasu nima zanyi, ka d'ebi wasu kud'in ka siyo mana kayan abinci, kabar ragowar a asu sun naka, in yaso duk abinda aka d'an samu sai ka dinga ajiye su, saboda kwanan nan za ka ji auran yaran nan ya tashi, kuma duk su ukun nake magana, don Nimha da Shukhura sun fi Yayartasu gab'b'an girma, in suka jero sai ka rantse itace k'aramar su, shiyasa ma ita Yayartasu d'in ba saurayin da ke zuwa gurinta, sab'anin Nimha da Shukhura, bare ma Shukhura babu ranar banza da ba za'a zo ace ana sallama da ita ba, sai na tursasa ta take fita, sai tace ai wai ita Yayarsu ba ta zance. “ "Da gaskiyarki Maimuna, nima ina tunani idan akace mini auran yaran nan ya taso, duk dai da Allah na dogara shi na mik'awa lamurana, tabbas kuma da ace Nusrat na da tsayayye a yanzu zan aurar da ita, tunda ta yi candy tai sauka me kuma za'a jira, amnan tunda babu sai muyi rok'on Allah ya kawo mata na gari, su Shukhura kuwa babu zancen ai yayarsu ba ta zance, shi aure ai lokaci ne ba'a jiran sai yaya tayi sannan k'anwa za tayi, duk wacce ta samu miji zan aurar da ita, fatana dai Allah duk ya had'a su da mazaje na gari, kuma na ji dad'in shawararki hakan kuma za'ai Allah ya shiga lamarinmu ya kuma dafa mana. “ Mama ta amsa masa da. "Amin. “ 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ *KATANGA* ____________ *EIGHT* Tun kan ta k'arasa soro k'irjinta ke dukan uku² shikuwa Mustapha alamun tafiyar da ya jiyo ne yasa shi k'urawa k'ofar da za ta fito ido, sai da ta janyo mayafinta ta rufe fuskarta kafin ta tako a hankali zuwa gurin da akai masa shimfid'a da tabarma zuciyarta na harbawa da gudun gaske, can gefe da shi ta samu ta zauna ta sunkui da kanta k'asa kafin tace. "Ina wuni.?“ "Nima ban ganshi ba, tun da dai ba ajiyarsa kika bani ba, idan kwa kina son na amsa miki to ki tabbata kin yaye rufin da ya Katange mini kyakkyawar fuskar da nake da muradin kallo a ko da yaushe. “ K'asa ta kuma yi da kanta ta na murmushi. "Please nidai a taimaka mini, yau kusan sati guda rabon da na ganta, tun a ranar da ta samu babban guri a zuciyata, idanuwana suka aminta da ita, suka tabbatar da itace sanyinsu kuma haskensu.“ "To aini kunya nake ji." Ta fad'a kamar a shagwab'e. "Idan kika sShukhuraki cikin nawa za ki daina jin kunyar. “ 'Cif, na ma kasa bud'e mayafina na ganshi, duk da zuciyata da take ta azalzalata na gansa shine har zan saka idona cikin na, hod'ijam aikam dai sai dai kar na daina jin kunyar' Muryarsa ce ta dawo da ita daga d'an k'aramin guntun maganar zucin da ta tafi. "Zan fa zo da kaina na cire mayafin gaba d'aya wallahi idan har ba ki d'aga sa ba.“ 'Cif saboda kai d'an ikka ne haka kawai ka ciren mayafina, hod'ijam aikam dai da kaga tsigalewa.' K'irjinta ne ya buga, zuciyarta tai wani irin harbawa yayin da ta jisa ya matso dab da ita. 'Laa kaddai ciren mayafin zaiyi kuwa, na shige yau na had'u da mara kunyar mutum.' Da sauri ta yaye mayafin da ke fuskarta, wani kyakkyawan murmushi Mustapha ya saki da yayi sanadiyar motsawar zuciyar Shukhura, wani fitinannen kyahu ta gani a tattare da Mustaphan wanda ba za ta iya bayyana muku shi ba saboda tsabar rud'ewa da cikar kyahunsa. Gira d'aya ya d'age mata had'e da fad'in. "Na miki ne? “ Lumshe idanuwanta ta yi don jin bak'on yanayin da ke sauka a ilahirin jikinta, ta d'au tsayin lokaci a haka yayin da shi kuma yake morewa kallonta son ranshi. Hira suka d'an tab'a kad'an, k'ofofin zuciyar Shukhura sun bud'e gaba d'aya suna d'iban sak'onnin da ke samun babban matsuguni a cikinta, da ya tashi tafiya ya dubeta yace. "A taimaka mini a tura mini hotunan da zasu dinga d'ebe mini kewa. “ Ya fad'a ya na me mik'o mata kyakkyawar wayarsa kamar shi, ta fuskanci yadda yake me kyau haka komai nasa yake me kyau. "Aini bana da hoto ko d'aya.“ "Ko a wayar Yayarmu ne a d'an samo mini mana. “ Don a d'an hirar nan da sukai ta ambaci Yayarmu ya kai wajen sau nawa, anan ya gane da wacce take zaune kusa da ita yai tunanin 'yan biyune itace Yayarmun, kuma ya fuskanci akwai soyayya me matuk'ar girma a tsakaninsu. "Yayarmu ba ta da waya ai. “ "Kawai dai rowa za ki mini, tom shi kenan a gaishe mini da su Mamarmu da Yayarmu da kuma k'annenmu. “ "Tom shikenan zasu ji insha Allah, nima a gaisar mini da so Hajiya, da kuma Hajiya Inna.“ Dariya ya yi had'e da fad'in. "Hajiya Inna za ta ji da kyau. “ Tunowa da ya yi darun da ta saka da Hajiya ta sanar mata su Shukhura ba 'yan biyu bane, Hajiya Inna har da kuka don ita har ga Allah ta saka ran samun tattab'a kunnenta 'yan biyu da zasu dinga sanyata farin ciki, sai da Hajiya ta lallab'a ta tace ai ba dole sai 'yan biyu ne ke haifar 'yan biyu ba, sai kiga ma 'yan biyun basu haifa, ita kuwa idan da rabo sai kiga ta haifa mana, Hajiya Inna tace. "To Allah yasa, amma 'yan biyunne suma suna tafiya da gado, shiyasa na fi samun tabbacin da 'yan biyu ce za ta haifa mana 'yan biyu.“ Zaune suke suna fuskantar juna da wani kyakkyawan bafulatani hannuwanta ya rik'o yace. "Yarinyata hak'ik'a ke haske ce a cikin rayuwar TURAKI ke za ki masa Katanga da damuwar da yake ciki a yanzu, za ki zame masa alkhairi, farin ciki, kuma madubin rayuwarsa. Hak'ik'a Turaki ya na cikin matsananciyar damuwa, kuma ina da tabbacin kece kad'ai za ki iya fiddashi daga ciki, kece za ki d'ora murmushin da ya dad'e da barin kan fuskarsa, ina mai kuma tabbatar miki ke haske ce cikin rayuwarsa domin kece kad'ai za ki yaye duhun da ke lullub'e da shi. “ "To ta ya'ya kake ganin zan zame masa haske bayan ban sanshi ba ban san a ina yake ba, ban kuma san a ina zan same sa ba. “ "Nima ban sani ba, amman kuma ina so ki mini alqawari guda d'aya. “ "Wani alqawari ne ka fad'a ina jinka, zan cika maka shi domin ina maka kallo tamkar mahaifina. “ Shafa kanta ya yi had'e da fad'in. "Na yi matuk'ar farin ciki yarinyata, Allah ya yi miki albarka.“ "Aminnn, ina jinka gaya mini alqawarin.“ "Kada ki bud'e k'ofofin zuciyarki ga kowa bare har ki basu muhalli, har sai lokacin da zai bayyana gare ki sai ki bashi gurbi a ciki ki kuma rufeta gaba d'aya, idan kwa ba haka ba akwai wani abu da zai muku Katanga a tsakani. “ "To amma. “ "Ba na so kice komai, tun da kin riga kin amsa mini tun a farko. “ Shiru tayi, ta na son ta sanar da shine ta riga ta yiwa wani wannan alqawarin, gashi kuma ya katseta, yanzu ya za ta yi, meye mafita gareta? "To meye alak'arka da shi, kuma meye sunansa na gaskiya? “ "Kafin na amsa miki tambayar zan sanar da ke ba za ki sake ganina ba daga yau, kuma ansar wannan tambayar da zan baki itace maganarmu ta k'arshe. D'ana ne shi, amman kuma mutuwa tai mana Katanga a tsakani tun shud'ad'd'an zamani, sunansa na gaskiya ALIYU ana kiransa da Aa............ Girgizata Shukhura ta yi had'e da fad'in. "Yayarmu.“ Wanda hakan ya yi sanadiyar farkawarta daga baccin da take wanda tai mafarkin nan a ciki. "Mtsss kin kama kin tashe ni, gashi ban samu ya fad'a mini sunan da ake kiransa da shi ba yadda in ya bayyana gareni zan ganesa, gashi yace daga yau bazan kuma ganinsa ba. “ Ta fad'a ta na me jin haushin yadda Shukhura ta katse mata mafarkinta ba tare da an gaya mata sunan da ake kiransa da shi ba, to kuma da yake ce masa Turaki waye ke kiransa da hakan? Oho ta bawa kanta ansa. "Kiyi hak'uri, Mama ce tace na taso ki ki k'arasa wanke-wanken yankewa na yi a hannuna in omon ya shiga zafi yake mini kuma bakwan ta kusa da kikace a tashe ki, to amman kuma waye kike kiran ba'a gaya miki sunan da ake kiransa da shi ba? “ "Mafarkin da na gaya miki ina yi ne Shukhura, gashi kuma yace daga yau ba zan sake ganinsa ba, bansan ta inda zamu had'u da Turaki ba Shukhura kuma ban san da wata alama zan ganesa ba. “ "Yayarmu na gaya miki fa ki watsi da lamarin mafarkin nan na ki mafarki fa ba gaskiya ba ne. “ "Wani mafarkin gaskiya ne Shukhura, don na ji ance wasu malaman sunce duk mafarkin da za kayi shi da daddare ka sake yinsa bayan sallar asuba gaskiya ne, wannan dalilin ne nake jin nima nawa gaskiya ne, kuma ina jin hakan a jikina.“ "Wai Shukhura Ina Yayar takun take ne.” "Gani nan Mama. “ Nusrat ta fad'a had'e da ficewa daga d'akin Shukhura ta bita da kallo. Washe gari Mustapha ya dawo ya kawowa su Shukhura ita da Nusrar wayoyi sababbi fil a kwalinsu sai walwali suke da shek'i, murna gurin Shukhura da Nusrat ba'a magana yayin da Umma bak'in ciki kamar ya karta, ta sanya Nimha a d'aki tace. "Kin gani ko, sun fara tura ki a gefe tun kan arzik'in ya ratsasu, yanzu in da da kara ai har da ke za'a kawo wayar. “ " Ni ban ji komai ba Umma, nima Saminu yace k'arshen watan nan zai siya mini. “ "Au yanzu yarinyar nan ba ki sallami Saminun nan ba, yanzu ki rasa wanda za ki mak'alewa sai matsiyacin da babu abinda zai iya tsinana mana.“ Turo baki gaba ta yi ta na had'e rai tace. "Wallahi ni Umma shi nake so ba abin hannunsa ba, idan har zai bani soyayya da farin ciki ya gama mini komai, kuma k'arshen satin nan zai turo magabatansa gurin Baba. “ Ta na kawowa nan ta fice daga d'akin don ta san maganar da za ta fito daga bakin Umman ba mai dad'i bace. "Amman ke dai anyi gantalalliyar yarinya, to wallahi tun wuri kije ki sami Babanku ki sanar masa ba kya sonsa don wallahi muddun rai ba za ki auri matsiyacin yaron nan ba, dudu nawa ne albashinsa da zai iya rik'eki, aike wallahi zubin matan manya ne da ke, amman da yake ba ki san ciwon kanki ba kin lik'ewa wanda babu d'igon arzik'i a tattare da shi, banda haka da kin samo mana wanda zamu shiga cikin dukiya mu kwantar da kai a cikinta a kuma daina mana d'agawa da dukiyar da babu tabbas d'in za'a ji dad'inta.“ A haka rayuwa take tafiya har aka shiga watan azumi, soyayyar Shukhura da Mustapha kuwa ta yi k'arfin da ba kwa zato, har an kawo kud'i an saka rana ta na yin candy, Nimha ma Saminu ya kawo kud'inta tare za'a had'asu da Shukhura, babu haukan da Umma ba ta yi ba, Baba kuwa yace ba ta isa ba, ai arzik'i na Allah ne. Nusrat dai har yanzu babu wanda take saurara har ta kaima yanzu in za ta fita nik'af d'inta take mak'alewa a hammata sai taje soro ta d'aura don kar ma a ganta ace ana sonta, sun sha fad'a sosai da Shukhura har tace sai ta gayawa Mama, sai kuma ta kasa fad'a, ita tausayi ma Nusrat d'in take bata gani take kamar da aljani take yin mafarkin nata da take kira gaskiya. Iya da Nimha kuwa sun dinga mata habaici kenan wai Allah ya yi mata nauyin k'afa gashi har za'a aurar da k'annenta biyu ita ko mashin shini ba ta da, ita kuwa ko kad'an hakan ba ya damunta lokacin auran nata ne bai zo ba idan yazo kowa zai sha mamaki. Mama da Baba kuwa Nusrat d'in tausayi take basu, don Baba har rubutu yake yi ya na bata ta sha na taimako ko Allah zai fito mata da nata mijin itama ya had'asu gaba d'aya ya aurar. Yau aka kai azumi na goma, kuma yaune Mustapha ya kawowa Shukhura kayan Shan ruwa, madara ce peak ta ruwa katan uku sai bomvita babban robar uku milo babban gwangwani uku, sai suger k'aramin buhu, k'wai kiret biyar, sai kuma kayan fruit, Iya kuma ya aiko mata da katan d'in maltina da madara, saboda kullum yazo zance har soro take zuwa su gaisa ya d'an bata hasafi, tun Shukhura na jin takaicin hakan da kunya har tazo ta sake gaba d'aya, don lamarin Iya sai du'ai son abun duniyarta har ya fi na daa. sai tsalle take ta na murna, da yazo da daddare tun kafin Shukhura ta fita ta riga ta fita don ta na ankare da hararar da take zabga mata in taje, har k'asa ta tsuguna ta nai masa godiya kamar za ta ari baki. Umma bak'in cikin duniya ya isheta, ta na kallo aka shige da wa'yannan uban kayan d'akin Mama, ita kuwa Saminu kayan fruit kawai ya kawo sai k'wai kiret uku, takaicin duniya duk ya bi ya isheta ta dinga tsine masa albarka, ji take kamar ta rufe Nimha da duka don ta kaici, amman ta ci alwashin daga bikin Nimhan har na Shukhuran babu wanda muddun rai ba za ta zuba ido 'yarta ta fad'a gidan wahala ba 'yar kishiyarta ta tsunduma gidan hutu ai taci baya, za ta yi duk yadda za tai taga wannan auran bai yi ba, ko na Nimha ya yi to tabbas na Shukhura bazai yuyu ba za ta shiga duk inda za ta shiga ba tare da ta nemi taimakon kowa, saboda daga k'arshe wanda ka nemi taimakonsa shine wanda yake k'ok'arin ganin bayanka, tun da ga shinan a fina finan hausa ana yi da kuma littattafan hausa.......... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ *KATANGA* ____________ *SEVINE* San da Baba ya shiga cikin gidan Umma kad'ai ya tadda da Nimha a tsakar gida suna karyawa, tun shigowarsa Umma ke bin akwatin hannunsa da kallo, ganin ya nufi d'akinsa zai ajiye tace. "Babansu wannan akwatin fa? “ Bai magana ba ya shiga ya ajiye kana ya fito ya k'wallawa Mama kira, ta amsa ta fito. "Kin kai mini ruwan wankan?“ "Eh na kai.“ "To bani kwandon da jallabiyata. “ Duk na kai suna can.“ "To sannu Allah ya yi albarka. “ "Amin.“ Tace ta juya ta koma d'aki, har zai shiga band'aki Umma tace. "Babansu magana fa nake kaimin shiru. “ "Ko ma dai ta meye idan kinyi hak'uri za kiji.“ Daga haka yai shigewarsa band'akin. Sai da yai wanka ya shirya, kana ya karya, sannan ya k'wallowa Nusrat kira, da tazo yace. "D'auki wannan akwatin ki kaimin ita gurin Iya. “ Tace."To“ had'e da d'aukar akwatin ta nufi gurin Iya, shi kuma yacewa su Mama da Umma suzo su same shi gurin Iyan ya biyo bayan Nusrat d'in, Iya na tambayarta wannan akwatin fa dai dai lokacin Baba ya shigo yace. "Ni nace ta kawo, ajiye kiyi tafiyarki. “ Ajiyewa ta yi ta juya ta fita, kafin zuwan su Mama Baba har ya farawa Iya bayani da suka zo kuma ya had'u ya d'ora musu bayanin yadda sukai da su Alhj Faruoq, kafin su bud'e akwatin suga meye a cikinta, lesuka ne 'yan ubansu masu matuk'ar kyau da tsada har kala uku, atamfofi ma uku, sai mayafansu da takalma da jaka, Iya murna da farin ciki kamar ta yi me, sai gud'a take. "Kai Amma wannan yarinya akwai goshin arzik'i, duk inda tai arzik'i binta yake da gudu ya na kamota, gashi har yau mune zamu had'a zuri'a da familyn Fanda, ai abin sam barka ne wannan.“ Umma kuwa bak'in ciki kamar ta yi me kawai yak'en dole take don kar ace ta na bak'in ciki, Mama kam shiru tai ba tace komai ba, Babane yacewa Mama. " ga su nan ki ajiyesu kar tai amfani da su, har sai yaron yazo sun fahimci juna, idan ta aminta da shi to, idan ba ta so ba zan mata dole ba, don haka kece mahaifiyarta ke kika san ta yadda za ki biyo mata. “ "Ai ta aminta da shi ma Audu, wace sakaryar ce za ta k'i zuk'ek'en saurayi d'an gidan Fanda, ga kyau ga kud'i ga ilimi ga kuma ladabi da biyayya, ko ni da nake tshohuwa wallahi ya na mugun birge ni, ai ku kwantar da hankalinku aure kamar anyishi an gama. “ Baba baice komai ba ya yi musu sallama ya tafi kasuwa, sai Umma ce tace. "Iya dama kin sanshi ne? “ "Inma ban sanshi ba tun da ya na son jikata aikwa saninsa ya zama dole. “ Shukhura da Nusrat suka d'ago suka kalli mahaifiyarsu bayan sun gama kallon kayan suka had'a baki gurin fad'in. "Mama kayan waye to?“ "Naki ne Shukhura. “ "Nawa kuma Mama?“ Ta fad'a ta na kallon fuskar Nusrat kafin ta mayar dubanta kan Maman, ita kuma tai musu bayani kamar yadda Baba ya yi mata ta d'ora daa. "Ba dole za'a miki ba Shukhura, ba kuma za'a tab'a musu kaya ba har sai kun fahimci juna kin kuma aminta da shi, sunzo sun nemi izini ne sun kuma kawo kayan na gani ina so. Ki tsayar da zuciyarki guri d'aya, kada dukiyarsu ta rud'e ki ko wani abu na k'yale² idan har bai kwanta miki a rai ba, ki same ni ki gaya mini ni kuma zan gayawa Babanku sai a mayar musu da kayansu a basu hak'uri.“ D'aga kai kawai Shukhura ta yi ta na sunkui da kai k'asa, Mama ta mayar da kallonta ga Nusrat tace. "Yayarsu babu wani wanda ya tab'a tunkararki da zancen soyayya ne?“ Kai tsaye tace. "Eh babu Mama. “ Shukhura ce tai saurin d'ago kai ta kalli Nusrat d'in yayin da Nusrat d'in ta galla mata harara, ganin hakan da Mama ta yi ne yasa tace. "Gaya mini Shukhura waye? In ita kunya ta hana ta fad'a. “ "Babu kowa Mamanmu. “ Shukhura ta bata amsa. "To shikenan tun da ba za ku gaya mini ba, idan Babanku ya dawo kwa gaya masa, Allah dai ya had'aku da mazaje na gari.“ Suka amsa da. "Amin." A tare. Da yamma Hajiya Suwaiba tazo gidan su Shukhura, Mama tai mata tarb'a ta mutumci da girmamawa dai² da k'arfinsu, yayin da Hajiya Suwaiba take ta yabawa da karamcinsu, ta kuma samu sirikartata 💯. Kayan kwalliya ta kawo mata tace ita da 'yar uwarta, don Mustafa yace mata ya na jin fa 'yan biyu ne, Inna kuwa daga jin haka har ta fara murnar za'a haifo musu tagwaye. Tun daga kan mayuka na gyaran fata babu abinda babu a ciki, godiya sosai Mama tai mata, ta rakata gurin Iya suka gaisa, Iya yadda kuka san ta gurfana a gabanta tai mata sujjada aikwa da ta tashi tafiya ta ajiye mata then thauthand, murna gurin Iya ba'a magana ta taho filin tsakar gidansu ta na ta rangad'a gud'a ta na shiwa Mama albarka don ta iya haihuwa tunda ta haifo Shukhura jinin arzik'i. Umma na d'aki takaicin duniya ya bi ya isheta, wani malulun bak'in ciki ne ke damunta, yanzu ta na gani su Maimuna zasu fandama cikin daula, don had'a zuri'a da Familyn Fanda kamar ka tako arzik'i ne, haka za'a mashaheta bora a cikin gidan nan da ita da 'yarta, don Shukhura ba kunya ce da ita, idan ta auri jinin Fanda kanta zai k'ara girma ta kuma taka wanda taga dama, tazo ta na d'agawa k'arshe ma komai na gidan ya dawo hannunta, da ace Nusrat ce ta san ba ta da matsala za ta dubeta tamkar mahaifiyarta, Shukhura kuwa babu abinda take hanga cikin idanuwanta banda tsantsar taya mahaifiyarta kishi, idan kwa ta samu wannan power ta riga ta zama sorry a cikin gidan nan daga ita har 'yarta, don haka dole ne ta nemi mafita tun lokaci bai nemi k'ure mata ba. "Wai meyasa kika cewa Mama ba ki da saurayi? Bayan ga Malam Tajo nan kamar zaiyi hauka a kanki kin kuma k'i ki bashi damar da zaizo ya fallasa asirin zuciyarsa. “ "Bazan tab'a bashi damar hakan ba Shukhura. “ "Saboda me? “ "Saboda girman alk'awari. “ "Hmmm Yayarmu kenan, na tambayeki.“ "Tom Allah yasa na sani.“ "Wai Yaya Rj yace yana sonki ne? “ "A'a baice ba, amman na san ya na dawowa zai gaya mini.“ "Baice ya na sonki ba, amman kike wahalar da kanki gurin zaman jiranshi, baki da tabbas d'in soyayyarki a zuciyarsa, bacin haka Aunty Maryam ba za ta tab'a bari ki auresa ba, domin Hidaya take da burin ya aura. Dan Allah Yayarmu kiyi watsi da lamarin Yaa RJ, ki tsayar da zuciyarki guri guda, kina da samarin nan ki basu dama har ki samu gwani a cikinsu, don ni a ganina Yaa RJ b'ata miki lokaci kawai yake yana kuma wasa da hankalinki, tun da shekara uku yace miki zaiyi ya dawo, yanzu a k'aida saura shekara d'aya kenan amman me Hidaya tace, cewa tai saura shekaru biyu ya dawo, ke a tunaninki Baba zai barki har nan da shekaru biyu a cikin gidan nan, ko kuma za ki cigaba da nuna babu wanda ke zuwa yace ya na sonki? Ta yaya kike tunanin zan karb'i lamarin aurena da muhimmanci bayan ke ba kiyi aure ba, har ga Allah ba na son na yi aure na tafi na barki.“ Hannuwan Shukhura Nusrat ta kama ta rik'e da hannu biyu kana tace. "Ni yanzu ba lamarin Yaa RJ ne ke damuna ba, akwai abinda ke damuna, kuma shi yake hanani karb'ar soyayyar kowa. Kada ki damu da lamarin aurena Shukhura, shi aure lokaci ne, kowa da akwai lokacin da Allah ya rubuta mata, babu ruwansa da wannan yaa ce ko k'anwa duk wacce lokacinta ya yi shikenan, haihuwa, aure da mutuwa duk tafiyarsu d'aya ne suna zuwar maka ne a sanda ba kai zato ba ba kai tsammani ba, don haka kada ma ki sake ki saka a ranki don banyi aure ba kema ba za ki ba, kin san Baba ba zai d'auki hakan ba, kar kuma ki amfani da hakan kice Mustapha bai miki ba, za ki cuci kanki ne don ni ba na hango aurena a nan kusa, ina ji a jikina akwai wasu abubuwa da zasu faru, amman bansan meye su ba.“ "Wani lamari ne ya hana ki karb'ar soyayyar kowa a zuciyarki. “ Wayar Mama ce tai k'ara alamun an kira Nusrat tace. "Kinga har ya k'araso ba ki gama shiryawa ba, maza kiyi² ki k'arasa shirin in kin dawo ma k'arasa maganar, kuma ina fatan k'anin nan nawa ya dagargazo miki zuciyarki kafin ki dawo, kizo kiy tai mini hirarsa ina saurare don naga alamun hakan ma tun a waya. “ Murmushi kawai Shukhura ta yi, don har ga Allah muryar Mustapha ta tafi da ita, sakamakon wayar da suka dunga yi, Maryam k'anwarsa ya turo ta anshi number Mama shine yake kiranta suna gaisawa, burinta kawai ta ganshi a fili don ta na fatan ganinsa ya fi jinsa shikwa ya dinga ja mata aji har sai yau da aka kusa cin sati suna wayar sannan yace mata zai zo. Shi d'inne kuwa yazo, don haka a gaggauce ta k'arasa shiryawa ta fita, Nusrat na ta zolayarta, don sun zamo tamkar wasu k'awaye aminai, don dukansu babu wacce za ta daki k'irji tace ta na da k'awa aminiya sai dai k'awar da za'a gaisa a wuce, sune k'awayen kansu, kuma hakan baisa Shukhura ta raina Nusrat d'in ba........ 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ *KATANGA* ____________ *NINE* Shukhura ta rasa yadda za ta yi da Iya, don abin nata kullum k'ara gaba yake, don idan taje su gaisa bai bata ko ficika ba samun guri take ta zauna, ranar da tai mata haka kuwa mantawa ya yi ya fito babu kud'i a jikinsa, ba ta tashi ba har sai da yace. "Iya a mini afuwa ban fito da kud'i ba yau, amma gobe insha Allah za kiga sak'o. “ Takaicin duniya ya ishi Shukhura ji tayi kamar ta nitse a gurin da take a zaune don tsabar kunya yayin da Iya kuwa ta wangale baki tace. "Tom shi kenan jikana babu komi, da yau da gobe duk d'ayane.“ Kunji sai kace ajiya ta bashi, wani d'an iskan kallo Shukhura ta bita da shi a ranta kuwa tace. 'Zanyi maganinki wallahi, yadda ko shi kansa Fandan aka ce gashi a soro ba za ki fito ba, ke ko govnor garinnan El Rufa'i akace gashi yazo zance gurina ba za kiyi gigin fitowa ba.' Fuska taje ta siyo me mugun abun tsoro, sai dagurintaa ruwa bayan an idar da sallar asham, dama lokacin ne dai² zuwansa, tun yamma da tai wanka ta saka riga da wando dama, don haka sai ta d'auko hijabinta har k'asa ta sanya, Mama dama ta na d'akin Baba don haka sai ta cewa Nusrat. "Yayarmu bari na fita soro.“ Tace mata. "Tom. “ Iya na ganin giftawar Shukhura ta fasa tayar da sallar da za tai, don yau ta makara ba ta samu bin jam'in asham ba wani bacci ne ya kwasheta ta na zaune. Murmushi ta yi ta ziro silifas d'inta ta biyo bayan Shukhura ta na k'iyasta yau sallamar da za'ai mata me matuk'ar nauyi ce, don ta na bin bashin wancen zuwan. Shukhura na fita soro ta cire hijabinta ta sak'ala shi jikin k'ofa sannan tai saurin d'aura fuskar ta juya baya. Bakin Iya ya k'asa rufuwa har ta doso soron, dama soron gidan gashi da mugun duhun tsiya, ko hucewa za kai sai ka haska saboda gudun masu lab'ewa, zance ma in zasui sai sun kunna fitila. "A'a yau kuma ba ku kunna fitilar ba ne? “ Cewar Iya ta na tsayawa a dai-dai tsakiyar soron gidan don ba ta hangar komai kar taje ta taka wani daga cikinsu shiyasa tai maganar don su kunna fitila, wani irin dank'a Shukhura taiwa kanta ta had'a fuskokinsu guri d'aya ta sauya magana zuwa me abun tsoro. "Ke wata iriyar nanatacciyar tshowa ce, mu ba ma son mutum me son abun Duniya, daga yau idan Mustapha ya k'ara zuwa kika fito sai mun karya tsila tsilan k'afafuwan nan naki masu kama da Babyn roba, kuma mu shanyar miki da b'arin jikinki gaba d'aya. “ Kar kar kar kawai jikin Iya ke yi uwa mazari ihun da taso ta yi ma ta k'asa wani mugun tsoro ne ya shigeta wanda ba ta tab'a jin irinsa ba. Allahumma inni auzu bika minal kubsi wal kaba isi, kawai take karantawa a ranta kafin Shukhura ta buga mata razananniyar tsawa had'e da fad'in. "B'ace mana da gani tun kafin mu mayar miki da k'afafuwanki a sama kanki a k'asa.“ Fitsari ne zirrrr ya fara bin k'afafuwan Iya kafin ta juya a guje sai ji kake k'um ta bugu da bango ta dawo baya, wata wahalalliyar k'ara ta saki, ta na so ta rarrafa ta bar soron ma ta k'asa anan ta zube a sume tsabar tsoro da rikirkicewa. Umma ce ta jiyo k'arar, don haka ta nufo soro da 'yar fitilarta, ta na haskawa taga Iya a sheme cikin fitsari. "Subhanallahi.“ Shine abinda tace kafin ta juya taje ta kirawo su Baba, ruwa aka watsa mata ta farka a mugun tsorace ganin su Baba kawai ta fashe da mugun kuka, Baba na tambayarta abinda ya faru, kawai cewa take su kamata su kai ta gurinta. Babu yadda Baba baiyi da Iya ba akan ta fad'i abinda ya faru da ita tak'i, k'arshe tace ina ruwansa ya rabu da ita don dole ya k'yaleta Mama ta dubi Nusrat tace. "Kika ce Shukhura na soro, ya kuma ban ganta ba?“ "To nidai Mama haka na ji tace mini, to ina kyauta zaton ban jita dai² ba tun da banga ta d'auki tabarma ba ma.“ Ta na rufe bakinta Shukhura na sallama Nusrat tace. "Yauwa ga ma ta nan.“ Kafin su amsa mata sallamar. "Ina kika je? “ Shine tambayar da Mama ta jefeta da ita, sosa kai tai kafin tace. "Mustapha ne ya kirani gashi a k'ofar gidanmu na fito na anshi sak'o, kuma da na fito ban ganshi ba ina jin zolayata yake, shine muka had'u da 'yar ajinmu muka tsaya muna d'an tattaunawa. “ "Ya yi miki kyau." Mama tace mata, Nusrat kuwa ta kafe ta da idanuwa, ita ta san dalilin kallon da take mata akan abinda ya samu Iya ne ta na zargin Shukhuran ce tai mata wani abu, murmushi kawai Shukhura ta yi, don ta san in ta ritsa ta dole ta gaya mata gaskiya. Tun daga wannan ranar Iya ba ta k'ara gigin fita in Mustapha yazo ba, saboda ita kad'ai ta san azabar da ta sha na jinyar goshinta, shi kuwa da yaga kwana biyu ba ta fitowa shine ya cewa Shukhura zai shiga su gaisa da Iya taje ta gayo mata, ko da Shukhura taje kuwa, iya tace ba ta san zance ba, ta yiwa Allah ta yiwa Annabinsa tace masa yasha zamansa ta yafe duniya da lahira, Shukhura kuwa tace ai kuwa sai ya zo ta fita ta na dariya Iya ta banko k'ofarta ta saka sakata tace sai dai yazo ya gaisar da k'ofa alk'ur'an. Kayan toshi ma da aka kawowa Shukhura k'arara Umma ta nuna bak'in cikinta a gurin, duk da Saminu ma ya yi dai² k'ok'arinsa amman ta raina ta na ta tsine masa albarka, ta na kiransa me kantar talauci, azumi kawai take jira ya k'are ayi sallah ta dugunzuma neman mafita, cikin k'udurar Ubangiji akai sallah lafiya aka gama lafiya, aikuwa ta shiga can cikin k'auyen zariya acan ta samo wani malami, ya shaida mata kud'in aikinta dubu ashirin idan har ta kawo dubu ashirin d'innan to tabbas wannan aure bazai tabbata ba, jiki na rawa ta dawo gida ta sayar da kayan gadonta gaba d'aya ta koma ta kai masa yace to yanzu ta koma taje ta kawo masa k'asar da Mustapha ya taka, idan ta kawota to tabbas da kansa zai zo yace ya fasa wannan aure, shi kuma Saminu za mu juyar masa da ra'ayi da kansa zaice ya fasa auran Nimha, kinga daga nan sai mu juyo da hankalin Mustapha kan Nimha. Farin ciki sosai Umma tai da jin jawabin Malamin, aikuwa ranar da Mustapha yazo ta k'asa ta tsare ta na jiran shigowar Shukhura ta yi sauri ta fice ta d'ebo k'asar da Mustapha zai taka, aikuwa ta na ganin shigowar Shukhuran ta yi saurin ficewa ta 'yebo washe gari taje ta kaiwa malamin aikuwa yace ta na kwance za ta ji kyakkyawan labari... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *KTG* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ ____________ *TEN* KWANCI TASHI Gurin Ubangiji ba wuya, su Shukhura har sun yi candy, sati d'aya da yin candynsu aka kawo lefen su. Akwatina 6 haka Saminu yaiwa Nimha, kuma ya yi iya k'arfinsa kayanta babu kushe ko d'aya, Shukhura kuwa akwatina goma sha biyu dank'are da kaya na alfarma, sark'ok'in daham kuwa zasu kai 6 a ciki, nan da nan hankalin Umma ya k'ara tashi, ta fuskanci wannan malamin kawai kud'inta yake ci dole ta canja shik'a. Wani k'ungurmun boka ta kuma samowa shi ya sanar mata. "Duk wanda yace miki wannan aure bazai tabbata ba to tabbas yai miki k'arya, kud'inki kawai yake ci, wannan aure muk'addari ne daga Ubangiji kuma babu makawa sai ya faru, don haka kije ki rungumi k'addarar da tazo miki da hannu bibbiyu.“ "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu babu wata mafita? “ " Babu wata mafita indai akan hana auran nan ne, sai dai wani da ban kuma, don wannan ba makawa sai ya tabbata. “ Shiru Umma tai hankalinta in yai dubu ya tashi, yanzu dole ta koma ta d'ebi cin kashi gurin kishiyarta, haka za ta zauna ta na kallon Shukhura na d'agawa da fariya ta na auren me kud'i, komai ta yayibo ta kaiwa uwarta ta na zaune kamar jaka, 'yarta kuwa sai dai ta yayibo kantar talaucinsu ta juye mata, ina bazai yuyu ba da sake, to kuma ta ya ya? Koma ta yaya ne ta bawa zuciyarta amsa daga bisani ta kalli bokon za tai magana ya dakatar da ita da hannu d'aya. "Kud'in aikinki dubu d'ari biyu, za ki kawo mini dubu hamsin da bak'ak'en kaji guda shida, idan aiki ya tabbata sai ki ciko dubu d'ari da hamsin, amman idan har kina so aikin ya kama jikinta sosai sai idan babu ran mahaifiyarta. “ 'Ta yadda da ingancin aikin bokan nan, tun da har ya san abinda ke zuciyarta, to amman kuma ta ya ya mahaifiyarta za ta rasu bayan ranta ba a hannunsu yake ba?.' Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi. "Zan tura mata ciwon da zaiyi sanadiyar mutuwarta, daga nan ba ki da sauran Katanga tsakaninki da Shukhura, ke za ta dingaiwa kallon mahaifiyarta, amman kafin nan sai an fara raba tsakaninsu da me gidanku, a kuma rufe bakinsa, babu case ga wannan tsohuwar matar idan har kina sakar mata abin Duniya. Su kuma 'yan uwanta za'a raba soyayyar da ke tsakaninsu, saboda ta na matuk'ar son su fiye da son da takewa kanta.“ Farin ciki ne ya dabaibaye zuciyar Umma, ta dinga sharara masa godiya, suka rabu akan za ta dawo ta kawo masa abinda ya Buk'ata.“ Akwatinan Nimha ta kwashe da wasu kaya daga ciki taje ta sayar ta kai masa kud'in da kajin da ya buk'ata, ya bata wani ku'ullikan magani, d'aya ta zuba a cikin abincin da Mama za ta ci, d'aya ta zuba cikin ruwan turaren da za'aiwa Shukhura kamu da shi, d'aya cikin abincin da Baba zai ci, sai laya da za ta saka a bayan gadon Shukhuran, babu wanda zai lura da layar sai ita da ta saka da kanta, sauran abubuwan kuma shi zai ji da komai. Shirye²n biki su Mama suke hankali kwance, don yanzu saura sati guda a fara shagul gulan biki, duk da Mama ta fara fuskantar wasu sauye² daga Baba hakan baisa ta tayar da hankalinta ba, da Allah ta dogara shi kuma taci gaba da mik'awa buk'atunta, don a 'yan kwanakin nan wasu mugayen mafarkai take mara dad'in ji ko kad'an, kawai ta na danne damuwarta ne saboda yaranta, don wani abu da Shukhura kuma ta tsira shine, duk dare sai ta sanyata a gaba ta na kuka ta na rok'onta akan a fasa wannan bikin, ta na jin kamar wani babban al'amari zai tunkaro su idan har akayi wannan auran, sai dai ta lallasheta da nasihohi masu ratsa jiki, don babu damar tunkarar Baba da wannan maganar, bare ya dube su, don ita kanta Mama yanzu ba ta buk'atar auran, to Baban gaba d'aya yanzu ya sauya musu da Nusrat kad'ai yake zama ya yi hira, hakan ya kuma tayar da hankalinsu gaba d'aya amman a haka suka daure suka cigaba da shirye shiryen da ba'a rasa ba. Ranar juma'a akai kamu anan cikin gidan, Iya ce ta kama duka amaren guda biyu, yayin da taiwa Shukhura amfani da turaren Nimha, taiwa Nimha da na Shukhura wannan kuma duk tsarin Umma ne. Ranar juma'ar da daddare akai Dinner d'in gidan su Mustapha, da Baba yace Shukhura ba za ta ba, da k'yar Nusrat ta lallab'a shi ya barsu suka je, kuma diner d'in ta k'ayatar da dukkan wanda ya halarci gurin. Washe gari asabar sukayi walima anan cikin gidan don Baba ya hana DJ kuma walimar ta yi gwanin ban sha'awa. Washe gari lahadi kuma aka d'aura auran. Safiya Abdullahi Ahmad da angonta Mustapha Faruoq Fanda Zainab Abdullahi Ahmad da angon ta. Saminu Yusha'u Hamza. Tun da aka d'aura auran Shukhura da Nusrat ke kuka, gaba d'ayansu suna jin wani miki a zuciyarsu ya na musu ciwo amma ba su san dalili ba, Mama ce tai k'ok'arin rarrashinsu duk da itama ba ta jin dad'in jikinta, amman saboda mutanen da ke shigowa ana kallonsu shiyasa ta rarrashesu, su d'aki falle d'aya bare tace su shiga ciki suyi kukan nasu babu wanda ya gansu, ta san dai kukan rabuwa suke, wannan kuka kuwa dole su yishi, sun taso tamkar 'yan biyun da suka zauna a mahaifa d'aya, suna matuk'ar son junansu ko kyauta za'a yi musu sun fi son ayi musu a tare, idan kwa aka bawa d'aya to tare zasui amfani da shi, musamman Shukhura da ki mata kyauta gara kiyiwa Nusrat za ta fi matuk'ar farin ciki, hakan da Mustapha ya gani ne yasa komai zai yiwa Shukhura sai ya yi musu tare da Nusrat , wataran ma Nusrat d'in kad'ai yakewa kyauta don kawai yaga farin cikin sahibarsa. K'arfe biyar dai² aka kawo motocin d'aukar amarya Shukhura, ita Nimha sai bayan sallar Isha saboda babu nisa, a lokacin kukan Nusrat da Shukhura ya k'ara k'arfi suka rungume juna suna kuka kamar ba sa rabu ba, Iya ce tazo ta janye Shukhura ta na sababi. "Meye kuma na kuka bayan Allah ya 'yanta ki ya kaiki gidan daula, ki daina biyewa Nusrat bak'in ciki take miki don ita Allah ya yota me nauyin k'afar tsiya har yau ko mashin shini babu. “ Shukhura kukanta kawai take, Iya ta dank'ata hannun Aunty Maryam suka shiga da ita d'akin Baba, yayin da Mama ta rungume Nusrat ta na jin itama kamar ta fashe da kukan, takai dubanta ga Yusra da take ta aikin matse k'walla, da hannu ta yafito ta itama tazo gareta ta rungumesu ta na jin wani iri a zuciyarta. Nasihu masu ratsa jiki Baba ya yi mata, ban da kuka babu abinda take ta cikin mayafinta daga k'arshe Baba ya sanya mata albarka aka fito da ita, ganin ana k'ok'arin fita da ita yasa ta fisge hannunta ta ruga d'akinsu da gudu, jikin Mama ta fad'a ta ruk'unk'umeta ta na kuka me ban tausayi, ta na jin kamar shi kenan daga yanzu sun rabu rabuwa ta har abada, shafa kanta Mama ta yi, don ta kusa sanyata zub da k'walla kawai ta na jajircewa ne. "Allah ya yi miki albarka Shukhura, kije kiyi hak'uri ki kuma rik'e gaskiya a duk in da kike. “ "Mama ki yafe mini.“ "Babu abinda kika tab'a yi mini Mamana, ko da kinyi mini nan gaba na yafe miki Shukhura Duniya da lahira, fatana ki rik'e 'yan uwanki da daraja, kada ki bada damar da za'a rusa ginanniyar katangar k'aunar da na gino a tsakaninku tun kuna yara, idan kikai mini haka kin biyani Duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka baki d'ayanku, Amin, muje maza ana jiranki. ” Ta rik'o hannunta had'e da na Nusrat, don Yusra tun d'azu ta fice k'ilama har ta samu mota, a hannun Aunty Maryam Mama ta kuma dank'a ta had'e da fad'in. "Allah yasa ki shiga a sa'a, insha Allah mutuwa ce za ta fito dake daga wannan gida cikin salama da aminci, Allah kuma ya baku zaman lafiya na har abada amin, Yayarsu kije ki raka 'yar uwarki d'akinta. “ Daga haka ta saki hannun Nusrat d'in ta shige d'aki, daga jin k'arshen maganarta ka san kuka take. Sai da aka kai Shukhura gurin Hajiya Suwaiba da gurin Inna kana aka huce da ita sashenta dake gefen gidan. Sashen Shukhura gaskiya ya had'u iya had'uwa, komai walwali yake da k'yalli, bed room d'inta ma ciki da falo ne, anan aka yi amfani da kayan da Baba ya siya mata, don cewa sukai ba sai an mata komai ba, Baba yace a barshi dai ya siyawa 'yarsa mutumci, ko ba komai itama za tayi alfahari da haka, kamar yadda ko wace amarya ke yi. Kayan da Baba ya yi musu suma ba laifi sun yi kyau iya kyau. Kowa ya watse daga Shukhura sai Hidaya da suke jiran angwaye su zo suma su kama gabansu, tara dai² Mustapha ya kira Shukhura yace gasu a k'ofar gida zasu shigo don haka sai suka k'ara d'an kimkimtsawa suka fito da ita babban falo suka zauna, abokan nasa biyune sai shi cikon na uku, addu'oi aka yi akan Allah ya basu zaman lafiya kana abokan sukai musu sallama suka fita yabi bayansu don ya yi musu rakiya, su Nusrat ma suka tashi zasu tafi, rik'o hannunta Shukhura ta yi gam tace. "Dan Allah Yayarmu kar ki tafi ki barni.“ Ta fad'a jikinta na rawa, hawaye ne ya zirarowa Shukhura haka zalika Nusrat d'inma suka rungume juna suna kuka, karo na farko kenan da zasu nesanta da juna tun tasowarsu, gurin kwanciyarsu d'aya, filon da suke d'ora kai guda d'aya a haka zasui bacci Shukhura ta rungumo Nusrat ta baya, ta gaba kuma Yusra ta rungumeta, gashi yau zasu kwana ba tare da Shukhuran ba, aure kenan me kawoka wata sabuwar bigiren rayuwa. "Kar ki tafi ki barni, ba na son ki barni, ki zauna tare da ni kinji Yayarmu don Allah.“ "Ai muna tare Shukhura, ba wai mun rabu kenan ba, gobe ma insha Allahu zamu zo, ke dai ki rik'e nasihohin da akai miki, azkhar d'in nan na safe da yamma kada ki sake ki wasa haka zalika nafil fili ma. “ Daga haka ta zare jikinta daga nata ta bi bayan Hidaya saboda tun d'azu Mustapha yace su fito abokansa su sauke su a gida, ledar kaza da youghort Mustapha ya bawa Nusrat ta yi godiya ta shiga motar suka tafi shi kuma ya juya cikin gidan. Ya sha rikici sosai da lallami ya lallamata har sukai sallah suka mika godiyar su ga Ubangiji, daga bisani suka d'an tab'a kazar amarcin don dukkaninsu basu saki jiki sun ci ba, sun d'an jima a zaune, ta na kwance a jikinsa ya kanainayeta kana sukai shirin bacci suka kwanta, Mustapha ya hankad'o ni daga d'akin yace mini. "Asuba ta gari kema kije ki huta. “ Don haka na tafi hutawa sai kuma gobe in kun jini...... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #N.W.A #Team KTG #Sonso fisabilillah [10/8, 3:43 PM] Binta Lawan: *KTG* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ ____________ *ELEVEN* (ZANEN K'ADDARA) A wannan dare su Nusrat basui bacci ba, zazzab'i ne me zafin gaske ya rufe Mama da kuma matsanancin ciwon kai, wanda bacci ya k'auracewa idanuwanta, haka zalika ma Nusrat ba ta iya rintsawa ba ko kad'an har garin Allah ya waye. Fitowa ta yi ta nufi d'akin Baba don ta sanar da shi sai taji muryar Umma tace. "Nusrat.“ Juyowa ta yi ta na kallonta don ba magana ce ke had'asu ba, face gaisuwa idan Nusrat d'in ta gaisheta. "Cewa na yi Shukhura kuwa ta kiraku? Kinga ni har ta kirawo ta gaisheni." "Ai tun da nai sallar asuba mukai waya da ita. “ Nusrat ta ba ta amsa, don yanzu ba lokacin da za ta tsaya yin tunani akan maganar ba ne, d'akin Baba tai shigewarta, ya na kishin gid'e bacci har zai fara fusgarsa ya ji alamun shigowar mutum, a hankula ya sauke idanuwansa akan fuskar Nusrat yace. " 'Yar baiwa lafiya? “ "Baba, Mama ce ba ta da lafiya tun cikin dare. “ "To sai akai ya ya kuma. “ Tsura masa ido Nusrat tai, kamar ba Baban nan nasu ba, mai k'aunar mahaifiyarsu, ta hango lokacin da tai wata rashin lafiya yadda duk ya firgice ya fita daga hayyacinsa, ya zamo tamkar shine mara lafiyar. Wani yahu me tauri ta had'iye tace. "Dama chamise zamu je. “ "To sai kun dawo don ni ficika ba na magani. “ Ba tace komai ba ta juya ta bar d'akin, dama ba kud'insa suke buk'ata ba, kawai dai ta gaya masa ne a matsayinsa na me jagorantarsu gaba d'ayansu. Umma kuwa bak'in ciki ne yai mugun kama ta da taji wai Shukhura sun yi waya da Nusrat, a yadda bokanta ya sanar mata idan har Shukhura ta kwana a kan gadon nan to sunyi rabuwa ta har abada ita da 'yan uwanta, tsakaninsu kuwa sai dai kallo, ita kuwa Mama na mutuwa, to tabbas ita za ta zamo mahaifiyar Shukhura kuma babu wanda ya isa yai magana akan hakan, dad'inta d'aya ne da ta fuskanci Mama ba ta da lafiya, tsakanin Shukhura da Nusrat kuma za ta zuba ido ta gani. Sun ci sa'a me chamise d'in ya fito, ya yi mata allurar zazzab'i ya bata kuma magun guna, kud'i ya kama 1500 Nusrat ta bashi 2000 ya basu cangin 500 suka kamo hanya suka taho gida. To Alhmdlillh sai jikin nata ya d'anyi sauk'i kad'an, har Nusrat ta had'a mata shayi me kauri ta sha, ganin jikin Maman ya yi sauk'i sai a sannan ta yi tunanin Shukhura har yanzu ba ta kirasu ba, amman gashi ta kira Umma sun gaisa, ta na cikin wannan tunanin sai ga Hidaya ta shigo tace mata tafiya zasuyi, amman zasu fara biyawa gidan Nimha da Shukhura in da sak'on da za'a kaiwa Shukhura a bada, kafin Nusrat ta mik'e ta bawa Hidaya sak'on sai wayar Hidayan ta yi k'ara sai Hidayan cewa ta yi. "Kinga ma Shukhuran na kirana bari muji meye to. “ Ba ta jira me Nusrat d'in za tace ba ta d'aga wayar, ta can b'angaren Shukhura tace. "Hello Hidaya kice a had'o mini duka akwatinana ku taho mini da shi.“ "To, shi kenan za'a taho da su, ga Nusrat za tai miki magana. “ Hidaya ta fad'a don ganin kallon da Nusrat d'in take mata, alamu ne na ta na son magana da 'yar uwar ta ta, k'ittt kike ji Shukhura ta kashe wayarta mamaki gaba d'aya ya kama su, a haka Nusrat ta shiga had'awa Shukhura duka akwatinanta da abubuwan da ba'a rasa ba, suka samo yara duk suka fita da su aka zuba a mota, kana sukai sallama da su Hidayan Nusrat tace. "Ku gaishe mini da Shukhuran ku gaya mata Mama ce ba taji dad'i ba." A tunanin Nusrat idan aka cewa Shukhura Mama ba taji dad'i ba za ta kira waya, in ma fishi take da ita ko tai mata wani laifin da ba ta sani ba ai ta kira layin Maman ta ji, amman har dare Shukhuran ba ta kira ba, ganin yadda duk Nusrat d'in ta bi ta damu yasa Mama tace. "Bani wayata na kirata. “ Saboda tun d'azu Mama tace ta kirata tak'i, saboda ta na ganin kamar ta na da dalilin da yasa tak'i nemansu gara su d'an d'aga mata k'afa su gani. “ Ringin d'aya Shukhuran ta d'aga da murnarta tace. "Hello Ma.......“ Cak taji maganarta ta tsaya ta kasa furta Maman da take buk'atar fad'a, Mama ji tayi gabanta ya yanke ya fad'i a hankula ta furta. "Innalillahi wainna ilaihir raji'un.“ Kafin taji saukar kukan Shukhura a kunnenta. "Shukhura lafiyarki kuwa?“ Cikin kuka tace. "Nima ban san me ke damuna ba, daku na kwanta a raina da ku kuma na tashi, tun da mukai sallar asuba nake son kiran wayarku amman na k'asa, sai na ji ana rad'a mini a kunnena wai ke ba mahaifiyata bace, Umma ce mahaifiyata ko kuma ace su Yayarmu ba 'yan uwana bane Nimha ce kad'ai 'yar uwata, na san Yayarmu ta damu sosai amman wallahi ko muryarta ba na son jin, ina cikin damuwa zuciyata ta na mini zafi, da na san haka auren zai zo mini da babu abinda zai sakani yinshi. “ Ta na kawowa nan ta fashe da wani matsanancin kuka, Mama kuwa Innalillahi kawai take ambata a zuciyarta, yayin da Nusrat duk ta na jin abubuwan da Shukhuran ta fad'a, had'a kanta tai da guiwa ta fashe da kuka me ciwo, 'yar uwarta da take sonta fiye da son da takewa kanta yau itace ta furta ba ta son jin muryarta, me yake shirin tunkaro rayuwarsu ne, waye me buk'atar rusa Katangar farin cikin da suka dad'e da ginata a zuciyoyinsu? Majina Shukhura ta jaa taci gaba da cewa. "Mama kicewa Umma me mukai mata take son rusa rayuwarmu gaba d'aya, in wani abu mukai mata sai mu nemi yafiyarta, na san dai itace ta shiga tsakaninmu saboda da sassafe ita na fara kira na gaisar, bayan ko anan cikin gidan ba kullum nake gaisheta ba. “ Numfasawa Mama tayi tace. "Umma ba ta isa ta miki komai ba Shukhura, ki saka hakan a ranki, babu wani abu wanda yake faruwa a rayuwa face dole sai da wani zare da ya haddasa hakan, kuma bama iya ganin zaren, shi wannan zaren shi ake kira ZANEN K'ADDARA. Dan haka kada ki kuma danganta abinda ya same ki da wani d'an adam, duk abinda ya sameki to ki tabbata yana cikin k'addararki, ki kuma kai kukanki ga Ubangiji domin shi kad'aine zai baki ikon cinye jarabawar da yai miki har ya yaye miki abinda ke damunki, yanzu kije kiyo auwala ki d'auki qur'ani ki karanta za kiji sanyi a ranki, maza jeki, Allah yayi miki albarka, ki kuma daina wannan kukan.“ Muryarta can k'asa tace. "Tom“ Mama ta kashe wayar ta lumshe idonta kana ta bud'esu akan Nusrat da ke gurshek'an kuka...... Jiya ba ku jini ba, chargi ne ban samu ba wutarmu ta lalace, gobe da jibi ba lallai ne ku jini ba saboda muna hidimar biki. 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #N.W.A #Team KTG #Son so fisabilillah[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* 28/8/2020 Wattpad@Rashuna *KATANGA* _Ina matuk'ar godiya ga Allah (S.W.T) da zai ba ni ikon kawo muku wannan littafi mai suna KTG, ina fatan yadda zan fara cikin yalwatacciyar lafiya na kammalashi haka, Amin summa Amin_ _Sak'on gaisuwa ga 'yan uwa da abokan arzik'i, da kuma dukkanin masoyana na kusa da nesa, ina kuma fatan za ku bani had'in kai cikin wannan littafin, kalma d'aya kawai zan gaya muku, alk'alamin ya fi mashi tsini, kuyi k'ok'ari kui nitso ku ninkaya cikin wannan sabon alk'alamin mai suna *KATANGA*_ _Hak'k'in mallaka:_ *RABEE'AH SHU'AYB NABABA* (RASHUNA) ____________ *ONE* _Bismillahir rahamanir rahim._ *SHIMFID'A* Malam Ahmadu an haifeshi a garin Zaria, asalin malantarsa ya gadota ne a gurin mahaifinsa Malam Buba, kasancewar kuma tun ya na yaro mahaifiyarsa ta rasu, tare ya rayu da mahaifinsa har sai da ya yi aure da matarsa Asabe sannan Allah ya karb'i ran malam Buba, daga nan Malam Ahmadu ya ci gaba da jan ragamar mahaifinsa ta malamta. 'Ya'ya uku Allah ya azurtasa da shi, Abdullahi, Maryam sai autansa Shamsu, Abdullahi shine ya gado mahaifinsa amman kuma ba a iya malamtar ya tsaya ba ya na da shago a kasuwa da yake sayar da kayan awo. Malam Ahmadu shine ya zab'awa Abdullahi mata, 'yar amininsa ce k'ud da k'ud da Allah ya karb'i ransu shi da matarsa shekarun baya da suka wuce, kasancewar gidan nasu gidan yawane, kuma auran zumunci akayi tsakanin mahaifan nata, haka take ta watan gari riya a cikin gidan sai uwar bauta da take musu, tausayinta da duba maraicinta da amuntakar da ke tsakaninsa da mahaifinta hakanne yasa ya nemawa Abdullahi auranta, Abdullahi baiyi musu ba kasancewar ya yaba da d'abiunta kuma ta na yawan burgeshi a duk sailin da zasu had'u hakan yasa ya karb'i tayin auranta da hannu bibbiyu. A gurin Asabe wacce yanzu suke kira da Iya aka fara samun k'alubale, inda ta yi tsalle ta dire akan d'anta ba zai auri 'yar makafi ba, kasancewar mahaifanta duk makafi ne, shikuwa Malam Ahmadu yace ta yi kad'an ta hana wannan auran, idan har taga ba'ayi sa ba to tabbas babu ransa a Duniya. Abdullahi da Maimuna sun aminta da juna sosai ya yin da suka fad'a zazzafar soyayya nan da nan magabata suka shiga lamuran nasu, a lokacin ne kuma wanda yake neman auran Maryam me suna Yusuf ya fito, a kano yake a zaune aiki ne ya kawosa zaria, tun ganin farko da yaiwa Maryam ya aminta da ita, bai fara zuwa zance ba sai da Malam ya yi masa izini, daga bisani kuma yace ya turo magabatansa. An tsayar da ranar auran Abdullahi da Maryam lokaci guda . Anan cikin gidan, Malam Ahmadu ya yanki gefe ya yiwa Abdullahi gini, d'akuna uku ne maka² abinsa a wadace, ya yi musu kuma k'ofar gurinsu da ban, sannan kuma ya had'a masa lefe dai-dai da zamanin da suke ciki. Ansha shagalin biki kafin a kawo amarya sashinta, ita kuma Maryam aka kaita unguwar Sabon gari. Lafiya lau zaman Abdullahi da Maimuna yake babu wata matsala ko d'aya, Malam ya d'ebo soyayyar duniya ya d'orawa surukar tasa, kullum in zai shigo gida da abinda zai aika mata da shi, ya yin da Iya kuwa ta bi ta tsaneta, ko kad'an ba ta sakar mata fuska kyara da tsangwama shine tsakaninsu. Wata d'aya da bikinsu Allah ya azurtata da samun juna biyu, tattali da kulawa fiye da wacce take samu ada Malam yake mata, idan ya fita duk abinda ya san me ciki na sha'awa shi yake siyo mata, Iya kuwa tayi ta sababi a tsakar gida ta na masifar ga d'iyarsa can ta na da juna biyun amma ba ya ta tata ya tare a bayan sirika, ya taka k'afa ma yaje ya gano d'akinta baije ba don tsabar tab'ewa da lalacewa, ci kanki kuwa Malam ba yace mata sai dai yai ta murmushi idan ta na yi ya nai mata uzurin k'wak'walwarta ta goce. Cikin Maimuna na shiga wata tara cif, ta haifi kyakkyawar yarinyarta sankace ciya, da hak'oranta guda biyu na k'asa, tsakanin Abdullahi da Malam ban san wanda ya fi wani farin ciki ba, Malam fad'i yake an haifar masa jika 'Yar baiwa, mutane kuwa da wanda Maimuna ta sani da wanda ba ta sani ba sai tururuwar zuwa barka suke, wasu ma don suga hak'oran ne kawai yake kawo su, don duk wanda yazo sai ya d'aga bakin ya gani, sai dai kawai Maimuna ta yi murmushi. Iya kuwa ko lek'owa taga jikarta ba ta yi ba, illa ma bak'in ciki da take kamar ranta zai fita, saboda yadda taga malam ya na rawar k'afa ya samu jika 'Yar baiwa, don har ya siyo raguna biyu tik'a² ya tirkesu bakin nan yak'i rufuwa, Iya kuwa tace. "Inma za ka daina farin ciki ka daina, shawara nake baku ku d'auki 'yar nan ku kaita bakin ruwa don wallahi 'yar aljanu ce ba 'yar baiwa ba. “ Murmushi kawai Malam ya yi baice da ita komai ba don ya san bak'in ciki ne ya taru yai mata yawa. Ansha shagalin suna yadda ba kwa zato, yarinya taci sunan babar Malam AYSHA, Maimuna tace a dinga kiranta da NUSRAT, yayin da Malam ya d'ebo soyayya,tattali gami da kulawa ya aza akan 'Yar baiwa. Wata d'aya tsira Maryam ma ta haifi 'yarta mace taci sunan babar Yusuf RABEE'AH suke kiranta da HIDAYA. Watan Nusrat uku a duniya Iya ta matsawa Ahmadu number sai ya k'ara aure, wata bazawara ce nan mak'otansu da take shigo mata, mijinta mutuwa ya yi kuma mai bala'in kud'i ne, siyayya take yowa Iya sosai da haka ta siyeta, don dama burinta kenan ta tirsasa d'an nata ya aureta, don ta tareshi da buk'atarta ya yi mata kaca² hakanne yasa ta biyo ta gurin Iya. Don a samu zaman lafiya Malam yacewa Abdullahi ya aureta, itama ya bi zab'inta,ko a samu k'iyayyar da takewa Maimuna ta ragu, don fad'i take yaiwa mahaifinsa biyayya amman ita saboda bai d'auketa a bakin komai ba ya watsa mata k'asa a ido ta ya ya kwa za ta k'aunaci Maimuna? Tun sanda aka saka ranar tarewar Bulki Malam da Abdullahi suke kwantarwa da Maimuna hankali ita kuma ta nuna musu hakan ba komai bane dama ai namiji mijin mace hud'u ne. D'aki d'aya shi ya zama na Maimuna, d'aya na Abdullahi d'ayan kuma na Bulki. Ranar juma'a aka d'aura auransu kuma a ranar ta tare, farin ciki gurin Iya ba'a magana kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, tunda take ba ta tab'a taka gurinsu ba sai a ranar da aka kawo Bulki. To zamansu dai ga shinan da dad'i babu dad'i a haka rayuwar take juyawa. Shekarar Nusrat d'aya Maimuna ta sake haihuwar mace wacce taci sunan mahaifiyar Maimuna SAFIYYA suke kiranta SHUKHURA, wata uku tsira Bulki ma ta haifi 'yarta mace wacce taci sunan Iya na gaskiya ZAINAB suke kiranta da NIMHA, anan fa Iya ta baje kolin gata da soyayya, fad'i take yanzu ne aka haifa mata jika. Tun haihuwar Shukhura sai da Maimuna ta shekara biyar kafin ta haifi wata macen aka saka mata NA'IMA suke kiranta da YUSRA, ita kuwa Bulki ba ta sake haihuwa ba tun daga kan Nimha. Malam yadda kuka san bai da wata jika sai Nusrat, komai ya samu 'Yar baiwa, kayan ciye² kuwa sai ta rage ake samwa k'annenta, ta shak'u da kakan nata fiye da zatonku masu karatu, shima kuma ta shiga ransa sosai da sosai, ya na bata kulawa ne ba wai don fifici ko wani abuba, sai dai shi a ganinsa dole ne jikanka na fari ya banbanta da sauran, saboda gaba d'aya soyayyar da kakewa d'an naka kake 'yebowa ka aza a kansa. Amman a gurin Iya da Bulki cin fuskane kawai, don a nuna ba'a son Nimha, hakan yasa suma suka d'auki dukkanin tsana suka d'ora akan Nusrat. Nusrat Fara ce, amman farinta mai duhu ne, fuskarta siririya ce mai d'auke da siririn dogon hanci, idanuwanta suna da girma matsakaici masu shape d'in k'wan k'walati, cikin idonta fari ne tas ruwa ya kwanta a cikinsa mai maik'o, k'wayar idonta kuwa bak'a ce me silkin brown a ciki, bakinta d'an madai daici ne haka zalika lab'b'anta basu da wani tudu, ko ya ta motsa bakinta wani siririn dimple ne ke bayyana a gefen kumatunta na tsaye wanda yake k'ara fito da zallar kyahunta. Shukhura kuwa fara ce k'al, suna yanayi da Nusrat, amman ta fi Nusrat kyau, kina ganinta kai tsaye za ki kirata kyakkyawa, saboda ita ko ba tai murmushi ba kumatunta a lotse yake, kuma nata irin na kwance ne. Yusra ma fara ce kamar Shukhura, itama ta na yanayi da su, amman kuma ba ta da dimple. A yanzu shekarun Nusrat goma sha biyar a duniya, ta na sss1, su Shukhura kuma shekarunsu goma sha hud'u suna jss 3 auta Yusra kuma shakarunta tara a duniya ta na aji hud'u a primary. Allah ya yiwa Malam rasuwa shekaru hud'u da suka wuce bayan ya yi jinya kad'an, kowa ya ji babu dad'i domin anyi babban rashi mai girma, musamman Nusrat, bayan mutuwarsa ne kuma soyayyar da Abdullahi wanda yanzu suke kira da Baba yakewa Nusrat ta fara bayyana, don har ga Allah ya fi k'aunarta ya na b'oyewa ne saboda kada ya kuma janyo mata bak'in jini. mutum ne me wadatar zuciya, ba wani k'arfi ne da shi ba sai dai rufin asiri na Ubangiji, don sun wuce cin yau da na gobe a gidansa, haka zalika bai bar iyalansa a wulak'ance ba, a ko da yaushe za ka samesu cikin kyakkyawar kamala. Shamsu ya yi aure da matarsa Fiddausi da d'iyarsu Amima sa'ar yusra, sunanta na gaskiya Zainab, shima Iya ya yiwa takwara, a kaduna suke a zaune a saboda anan ne yake aiki, ya ninka yayan nasa sosai a fannin dukiya wanda k'arara Iya ke nuna banbanci tsakaninsu da Baba. Aunty Maryam kuma mijinta ya koma kano da aiki don haka ya d'ebe su suka koma kano da zama, 'ya'yansu hud'u yanzu, Hidaya, Abdul, Hibba, Abbas, suma sosai Iya take ji da su saboda suma mahaifinsu na da kud'i, kuma anai mata aike akan kari. *Wannan kenan* 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK in kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana, duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *TWO* Yau ta kama lahadi, duk da suna cikin hutun makarantar boko, su Nusrat duk sun tsefe kawunansu zasu kitso, sai da Nusrat ta fara wanka ta yiwa Yusra ma ta wanke mata kanta ta taje ta shafe mata shi da mai sannan suka shirya zasu tafi, kallon Shukhura Mama ta yi da ta saka hijabi zasu tafi tace. "Ke yanzu ba za ki wankan ba haka za ki bisu?“ Sai da ta fara turo baki gaba kana tace. "To Mama nan da nan d'in sai na yi wanka, abinda yanzun nan za'a mana mu dawo. “ "Allah ya shirya. “ Mama kawai tace ta na mik'awa Nusrat kud'in kitson nasu had'e da fad'in. "Ta fara yi miki kitson, kuma tai miki manya don kinsan yadda yawan kanki yake, kuma ke zan barwa girkin dare don fita zan yi, saura kuma kice a fara yiwa Yusra don na san hali. “ Murmushi Nusrat ta yi, bayan ta saka hannu biyu ta anshi kud'in kana tace. "Mun tafi.“ Maman tace. "Allah ya tsare, ku dai yi addu'a kafin ku fita. “Tace. "Amin, tom insha Allah.“ Tare da jan hannun Yusra suka bi bayan Shukhura da ta fita tun d'azu. Har sun d'an gota gurin Iya ta hango giftawarsu da sauri ta k'walowa Nusrat kira. "Ke ke A'i zo nan. “ Da yake haka take kiranta tun ma Malam na raye, juyowa Nusrat ta yi, Yusra ta turo baki gaba tace. "Wallahi na san aiki za ta sakaki, kawai kizo mui tafiyarmu mu rabu da ita.“ Murmushi Nusrat ta yi tace. "Bara dai naje na ji kiran da take mini.“ "Tak'i ta rabu da ni d'in, shegiya ifrituwa me zunb'utun baki. “ Suka jiyo muryar Iya daga ciki, kuma turo baki Yusra ta yi ta na hararar gurin kafin ta fice waje da sauri, Nusrat kuma ta nufi gurin Iyan ta na murmushi. Gyaran d'aki tace tai mata da wankin band'aki sai 'yan tsunmokaranta ma da tace ta wanke mata. Kallon Shukhura Nana me kitso ta yi tace. "Ina su Yayar taku?“ "Ga sunan suna hanya. “ "To shiga ciki, gani nan bari na k'arasa sharar nan. “ Rufe bakinta kenan Yusra ta yi sallama, kallon ta Shukhura ta yi bayan ta amsa sallamar ta ta tace. "Ina Yayarmun?“ "Ba Iya ce ta kirata ba, har ta na ce mini ifrituwa. “ Wani haushi ne ya kama Shukhura, ta zura takalminta ta fasa shiga d'akin ta fice a fusace Yusra ta biyo bayanta. Kamar an jefota ta shigo ta na kallon Nusrat da ke zubar da shara. "Sannu" Tace mata, kafin ta shige zuwa gurin Iya, iya na ganinta ta d'aure b'arin goron da ta b'antara a gefen zaninta kana tace. "To rasa kunya b'eran tanka, kinzo kimin rashin kunyar taki ne? “ Kar katar da kai Shukhura ta yi tace. "Ashe 'Yar aljanu na da rana tun da har an iya sakata aiki, me yasa ba ki kirawo 'yar lelen taki tai miki ba sai ita za ki saka, amma in abu zaki bayar babu wanda ke gabanki sai Nimha, amman in aikine sai wacce kika raina, don kin san Nimha ko tsintsiya ba za ta iya d'aga miki ba. Bayan kuma kitso zamu je kina gani kuma Mamanmu na zaman jiranmu“ "Tunda dai ba ke na saka ba, ki shige ki bani guri, kiyi can da rashin kunyarki. “ Cewar Iya "Waa aini kin san abinda bazai tab'a yuyuwa bane, don wallahi bazan bautawa wanda bai san ina yi ba, in cin mutumci ne ya taso azo a tarkace mini, lalalala wallahi, itama ita taga za ta iya.“ "Ni kikewa cin mutumci Safiya, Allah ya dawo da Audu, wallahi za ki gane Ubanki na haifa. “ "Amin, ya dawo d'in ki gaya masa, wallahi duka d'aya yamin kinsan sai na bi ta inda zan rama, Allah ya baki sa'a. “ "Wai da sa'ar ki kikeyi ne Shukhura?“ Cewar Nusrat ta na kallonta, ba ta bata amsa ba ta fice ta na zunb'uro baki, Iya kuwa k'ifi² ta yi da ido tunowa da ta yi sanda ta saka Nusrat a gaba ta na zaginta Shukhura ta amshe ta hayayyak'o kamar za ta daketa har sai da Mama ta fito ta kikkifawa Shukhura mari, shine Baba ya na dawowa Iya ta kwashe ta gaya masa, aikwa ranar Shukhura ta sha duka gurin Baba, ita kuwa ta d'auki aniyar wallahi sai ta rama akan Iya, sai da ta bari duhu ya yi ta kad'a karkashinsu me yauk'i taje ta zuba a band'akin Iya,don ta na da tabbacin yanzu za ta fito ta shiga band'akin ta lab'e a bayan k'ofa, Iya na shiga ta yi sufa ta fad'i Shukhura ta fito ta na ta k'yak'yata mata dariya, tace mata kad'an ta gani muddun ta na sakawa Baba na dukanta, Iya kuwa jiki yai tsami da k'yar ta iya mik'ewa. "Yanzu Mama kina kallo ga Iya can ta saka Nusrat aiki.“ Shukhura ta fad'a ta na turo baki gaba. “ "To meye, don ta sakata aiki?“ Mama ta fad'a ta na cigaba da tankad'en da take. "Amma Mama kefa kikace a fara mata kitson saboda za ki bar mata girki.“ "Yanzu kuma na fasa ba, kije ke a fara miki sai ki baro Yusran a can in Yayar taku tazo sa taho tare sai ki karb'i girkin na samu na fita. “ "Amma Mama....“ Dakatar da ita Mama ta yi had'e da fad'in. "Ban san jin komai ki shige kije kiyi abinda na saki. “ Fita ta yi ta na tutturo baki Mama ta girgiza kai had'e da fad'in. "Allah ya shirya. “ Sai da Iya ta kinta tanci dawowar Baba ta fito babban tsakar gida ta k'wama kujera ta na jiran dawowarsa, aikwa ta na jin sallamarsa ta saki kuka me k'arfi, a gigice ya nufota ya na tambayarta. "Lafiya Iya, me ya faru kike kuka haka?" Face hanci Iya ta yi tace. "Wai ni yau A'i za ta kalli tsabar idona ta zageni ta uwa ta uba. “ " 'Yar baiwa.“ Baba ya k'wallawa Nusrat kira, Nusrat da ke d'aki tun da ta dawo daga kitso kanta ke ciwo shine ta nemi guri ta kwanta, ta na jiyo abinda Iya ke cewa Baba gabanta ya yanke ya fad'i, da ta ji kwa ya k'wallo mata kira nan da nan idonta ya yi rau-rau zai fidda ruwa, a hankali ta mik'e ta fito ba tare da ta amsa kiran ba, kallonta Shukhura ta yi da ke kwashe tuwo ta cika k'atuwar kula ta kai d'akinsu, tace. "Kinga dai da abinda ta saka miki ko? kuma wannan ba shi zai hana gobe idan tace yimin kaza kiyi mata ba. “ Ba tace mata komai ba sai juya idonta da tayi da ya fara fitar da ruwa ta nufi tsakar gidan, Shuk'hura kuwa taci gaba da kwashe tuwonta ta na mamakin sanyin hali irin na Nusrat, ta yi k'wafa a hankali, a ranta tace. 'Iya kenan, ai gara ki tab'ani akan ki tab'a Yayarmu wallahi, don ba ki son son da nake mata bane.' Baba na ganin ta taho a sanyaye ya saki murmushi had'e da fad'in. "Taho mana 'yar baiwa. “ Ganin murmushi akan fuskar Baban nata yasa ta samu k'arfin guiwar k'arasawa gareshi, bak'ar ledar hannunsa ya mik'a mata, me d'auke da d'ata manya-manya kasancewar yasan ta na matuk'ar son d'ata, kana yace. "Ga masoyin naki.“ Murmushi me sauti ta saki tace. "Na gode Babana. “ Baki galala Iya ta saki ta na kallonsu daga bisani ta tafa hannuwa tace. "Yau naga lalacewa ni Asabe, yanzu ina gaya maka abinda yarinyar nan ta yi mini amma kai d'ata ka d'auka ka bata, gani ni wacce na yi silar zuwanka duniya ka san da cewa ina mutuwar son ka'za amma baka tab'a siyowa ka bani ni kad'ai a gidan nan ba, sai dai ka siyo gaba d'aya aci, amman ita da yake shafi da mai ce ka ware ta cikin 'yan uwanta uku, ture biyunma tunda su cikinsu d'aya ai ko Nimha ka siyowa don gudun fitina.“ "D'atan da na siyo mata na tabbata ba za ta cishi ita kad'ai ba, rabawa zasui gaba d'aya da ita da 'yan uwanta, zancen kuma Nusrat ta zage ki wallahi Iya ko jikina duk kunne ne bazan tab'a yadda za ta iya zaginki ba, ko da kuwa dukan mutuwa kikai mata a cikin gidan nan, bare kuma na san halinta ba sawa ba fitarwa, da dai Shukhura kika ce to tabbas wannan zan yadda amma 'yar baiwa lalala, sai dai kice Shukhura ce ta zageki kikace 'yar baiwa ce saboda.... ”Da sauri Iya ta dakatar da shi da fad'in. 'Ni wallahi bance maka Safiya ba, ko sunanta ban ambata a gurin nan ba in ba yanzu ba, jama'a ko kunji na ambaci Safiya? “ Ta fad'a da k'arfi yadda 'yan ciki zasu jiyo ta, murmushi Baba kawai ya yi ya ja hannun Nusrat sukai ciki. "Kedai Mero kin haifi jarabar aljanu a gidan nan, yarinya ta bi ta zamar muku masifa duk kunfi k'aunarta cikin 'yan uwanta, su kuma hakan ko kad'an hakan ba ya damunsu, wannan wata iriyar musifa ce? Kai kuwa Audu k'atuwar asara ce ta hau kanka don zan iya dafa qur'ani kafi son wannan 'yar aljanun ko nace 'yar ruwa akan ni da na diroka duniya, bacin haka har maganata za ka k'aryata ka zab'i d'iyarka, babu komai ai gobe Shamsu zai zo garin, Allah sarki d'an albarka na san gobe miyarmu da ka'ji zan cisu har na ture, don ni ina jin idan yazo ma tattara kayana zan na bisa, don wallahi na gaji da cin shinkafa 'yar hausa da tuwon garin masara kullum suna cushe maka a ciki, don na ji ana rad'e rad'en tuwon masara gini yake a cikin mutum, haka kawai na zauna naje na kashe kaina tun wa'adina bai cika ba. “ Sai misalin k'arfe takwas Mama ta dawo, kallon Nusrat da ke kwance ta yi tace. "Ina Mamana, Yusra taci abinci da kika barta tai bacci?” "Cikin gida tace mini za ta shiga tun d'azu, Yusra kuma sai da taci abinci tukunna tai bacci. “ "Lafiyanki kuwa naga kina yatsina fuska? “ Ta tambayeta duk da a ranta mamakin wai Shukhura ce tace ta tafi cikin gida, bayan ba k'aunar zuwa gidan take ba, aike ma da dole take shiga. "To ki tashi ga fura na taho miki da ita kisha sai ki sha magani.“ Da hanzari ta mik'e don dama yunwa take ji kuma har ga Allah ba ta k'aunar cin tuwon donma ta d'an ci d'atan da Baba ya kawo mata duk da wasu sunce shima ya na faifaye ciki, ita kuwa Mama sanin halin d'iyar ta ta yasa ta yo mata guzurin furar. Sauke idanuwanta ta yi akan kular tuwon da Shukhura ta ajiye, a fili tace. "Allah ya shirya mini ke mamana. Maza Nusrat ki gama kije ki kira mini ita. “ Ta na rufe bakinta ta jiyo sallamarta suka amsa mata. "Laa Mamanmu kin dawo ashe? sannunki da dawowa. “ Fuska a had'e tace. "Yauwa, me kika je yi cikin gida? “ "Nifa ba cikin gida nace mata zanje ba, gidan su Farha nace mata za ni kallo.“ Takai k'arshen maganar ta na kallon fuskar Nusrat. "Ban hana ki zuwa kallo ba?to da Babanku kawai zan had'aki na huta, Ke kuma ai ga shinan kin rufa mata asiri ta tonawa kanta. “ Takai k'arshen maganar ta na kallon Nusrat, yayin da ita kuma ta saki murmushi. "Kiyi hak'uri Mamanmu bazan sake ba. “ "Sau nawa kina fad'in haka? “ "Allah da gaske nake Mamanmu daga wannan bazan sake ba. “ "To wancan uban tuwon da kika ajiye da fatan abincinki ne na sati guda ko?“ "Haba² Mama, sai kace wacce uwarta ta tsine mata duniya ta juya mata baya zan jera sati guda ina cin tuwo, tuwonma ba sabo za'a dinga yi mini ba. “ Mama ta so yin dariya amma ta kanne tace. "Koma me zaki ce kice, amma wancen tuwon sai kinyi sati kina cinsa a gidan nan tun da ke kunnenki na k'ashi ne ba ya jin magana, bacin sau nawa zance ki daina cika mini kula kina kawo mini d'aki? “ Sai da ta fara turo bakin nan gaba kana tace. "To kina dai kallo duk ran girkinta sai ta cika kula fam ta kai d'aki, bacin daga ita sai 'yarta d'aya kamar rai, mu kuwa ta milliro mana, ta cikawa Baba da sirikarta kwano, nima kuwa yau na rama na millira musu na millirawa Iya ma, Baba kuwa na cika masa kwano har ya na zuba. “ Salati Mama ta yi ta saki baki ta na kallon Shukhura. "To don ita ta na cika kula ta kai d'aki ita ta shafa, sune mayunwata ba mu ba, ga shinan yanzu kin sakani a bakin duniya, tijarar Iya ma kad'ai ta isheni, don cewa za tai ina sani na baki girkin shiyasa har ga Allah ban son na bar miki girki na fita. “ "A to don wallahi muddun ni nai girki bazan fasa ciko mana kula na kawo d'aki ba, ko ba za muci ba sai dai mui asararsa. “ "Me kika ce?“ Mama ta tambayeta kasancewar k'asa² tai maganar. "A'a cewa na yi kiyi hak'uri bazan kuma ba. “ "To zo ki fice mini da kular, kije ki k'ara musu tuwon.“ Ta na jin haka ta saki k'ara. "Waishhhhhh Mama kashi² ina zuwa ta fice da gudu zuwa ban d'aki, murmushi Mama ta yi a ranta ta na nemawa Shukhura shiriya ta d'auki kular tuwon ta fita, murmushi ma Nusrat keyi tun fara dramar Maman da Shukhura, don dama sun riga da sun saba...... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biyama ki turo cikinta. 09037093702. In katin wayane 400 Za ku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: https://chat.whatsapp.com/L7ZWZtJoVg39WGbG36r78I. Pls share *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *THREE* Ashe ba kallo Shukhura taje ba, can bakin titi taje gurin me saloon ta siyo farata koraye shar da su, ta biya gurin me zob'o ta siyo, ta sayi cewing gum ta jefa a baki sannan ta yo gida, a wani d'an lokon babban tsakar gida ta ajiye faratan da zob'on kana ta shigo. Sai da ta bari d'aya ta gota ta tabbata a lokacin baccin kowa ya yi nisa ta salallab'a a hankula ta zare sakatar gurinsu ta fice, bayan ta d'auko farar hodarsu, ko tsoron duhun dare ba ta yi, bursuna farar hodar ta yi tun daga fuskarta har wuyanta, ta cire hijabinta sai ta bar wata hula me cibiri cibirin gashi a kanta, rigar jikinta dama ta wani tsohon uniform d'inta na islamiya ne da take bacci da ita. Cikin dabara ta man manna faratan a yatsunta da chewing gum, ta d'aga jarkar zob'on nan ta shanye ta bar d'an guntu a ciki, nan da nan bakinta ya yi jajir, ta guntsi ragowar a bakinta, turmi ta taka ta zira hannunta ta saman k'ofar d'akin Iya a hankula ta zare sakatar kana ta tura ta shiga ta mayar ta rufe, kallon Iya da ke bacci akan gado ta yi, sakamakon haska 'yar k'aramar cocilan d'in da ke hannunta da ta yi a ranta tace. 'Za ki gane kurenki ne.' Kan ruwan cikinta ta hau ta zauna, cikin bacci Iya ta ji masifar nauyi ya ziyarceta, a hankula ta bud'e idanuwanta duk a tunaninta madannin dare ne ya danneta, ido biyun da ta yi da Shukhura nan take wani mugun tsoro ya kamata ta bud'e baki za tayi ihu Shukhura ta yi saurin toshe mata baki da wani tsumma da ta yayibo a gefenta, cikin wata iriyar murya me ban tsoro tace. "Kada ki mana ihu a nan, in ba haka ba zamui daga daga da namanki. “ Nan da nan jikin Iya ya fara rawa kar kar ta fara biya duk wata addu'a da tazo bakinta, son tashi take amma gaba d'aya ta k'asa tashi, hannu Shukhura ta Saka ta karto gefen fuskar Iya had'e da juyar da idanuwanta, rintse ido Iya ta yi kafin ta ji saukar muryar Shukhura a kunnuwanta. "Al'quran kika kuma tsangwamar Nusrat a cikin gidan nan sai mun cire miki k'afa d'aya da hannu d'aya, mu kuma maidar miki bakinki k'eyarki, sannan mu d'aukeki zuwa cikin ruwa, kima gode Allah kin fara manyanta da wallahi yau sai mun sakaki murmushi da hak'ori d'aya.“ Iya firgita Iya ta firgita, wani mugun tsoro ne ya kuma shiga jikinta ko k'wak'k'waran motsi ta kasa, ta na san magana amman ba dama saboda ta toshe mata baki da t'summa kuma ta rik'e da d'aya hannunta, um umm kawai take ta na girgiza kai hawaye na zuba a idonta, tausayi ta bawa Shukhura don tasan ta sha nauyi, don Iya irin siraran tsofaffin nan ne, ita kuwa Shukhura ta na da jiki, d'agata ta yi ta sauka daga kan gadon ta cire hannunta daga bakinta had'e da fad'in. "Kada kuma ki sake ki mana ihu don wallahi zan maidar miki da idonki goshi ki zama mai ido d'aya. “ Ta na maganar ne ta na ja da baya, yayin da Iya tace. "Allah ya baku hak'uri wallahi na daina takura mata, ba iya ita kad'ai ba ma wallahi dukansu na daina shiga harkarsu.“ Wani ihu Shukhura ta yi ta na zaro harshe ya yin da Iya ta yi wani hantsile ta koma k'arshen gado goshinta ya bugi da bango, duk azabar da ta ratsa ta k'wak'wal warta amma haka ta d'inke bakinta saboda tsoron kar ta yi ihu a maidar mata da idonta goshi, ja da baya Shukhura ta ci gaba da yi had'e da fad'in. "Kada kuma ki sake ki juyo sai mun b'acewa ganinki in ba haka ba kuma zamui sama da ke zuwa fadar sarkin aljanu. “ Ta na kawowa nan, ta bud'e k'ofa ta fice, ta taka turmi ta maidar mata da sakatar ta, kana ta d'auke turmin ta mayar da shi mazauninsa, sannan ta d'auki hijabinta ta shige ciki, ta na k'ok'arin mayar da sakata ta ji muryar Baba yace. "Waye nan?“ K'irjinta ta ji ya yi wani irin bugu nan da nan wani mugun tsoro ya kama ta ta fara rawa da bakinta. "Um nice, fitsari na fito naga kamar ba'a saka sakata ba, shine na duba. “ Ta na kawowa nan ta yi saurin fad'awa band'aki don gudun kada ma ya fito ya ganta. Fuskarta ta wanke da sabulu, ta cire faratan ta jefa a shadda, kana ta fito ta koma d'aki, sai bayan da ta kwanta a shimfid'arta wata muguwar dariya tazo mata, fashewa ta yi da dariya sosai ta na hango yadda idanuwan Iya suka firfito gaba d'aya kamar na mayyar da aka kama, wata dariyar ta kuma fashewa da ita, Nusrat da ke gefenta ta farka ta na kallonta a tsorace. 'Anya kuwa babu almutsutsai akan Shukhura kuwa. ' Taji zuciyarta ta jefo mata wannan tambayar kafin ta ji muryar Baba ya na k'walo mata kira. " 'Yar baiwa“ "Na'am Baba. “ Ta amsa, ta tashi ta fita jiki a sanyaye. "Lafiya kuwa nake jiyo dariya a d'akin ku?“ "Wallahi Baba Shukhura ce, kuma ban san me takewa dariyar ba, anya Baba ba za'a nema mata magani ba, ni wasu abubuwan in ta na yi gani nake kamar ba ita kad'ai ba. “ Murmushi Baba ya yi yace. "Shukhura. “ "Na'am.“ Ta amsa cikin muryar shagwab'a ta fito ta na sosa kai. "Me ya sakaki dariya cikin tsohon daren nan? “ Sai da ta fara turo baki gaba sannan tace. "Kawai tuno yadda na tumur mushi hadiza d'azu a makarantar allo na yi, tsokanar Yayarmu ta yi ni kuwa na had'a mata jini da majina ta mik'e da k'yar jiki duk yai tsami kamanninta duk sun sauya bakin nan kamar zunb'utun zakara. “ Ta kuma fashewa da wata dariyar. "To jeki ki kwanta, kinga dare ne kada ki kuma dariyar, kinji Mamanmu. “ D'aga masa kai ta yi, ta koma d'aki, ya bita da idanuwa a zuciyarsa ya na nema mata shiriya, duk da a zuciyarsa shima ya fara tunanin ba ita kad'ai bace, don al'amarin nata akwai ban tsoro, shiyasa ya daina dukanta ko me Iya tace tayi mata, don ya san itama Iyan da laifinta, kuma duk irin dukan da zaiwa Shukhuran ba shi zai hana ta samo ta inda za ta rama akan Iya ba. Duban Nusrat ya yi yace. "Je ki kwanta 'Yar baiwa, zamui maganar da Mamanku da safe.“ "Toh“ Tace had'e da juyawa ta koma d'akin, ta na kwanciya Shukhura ta rungumota ta baya ta na sakin dariya. "Ina sonki Yayarmu, matuk'ar ina numfashi bazan tab'a bari a tab'a mini ke ba na k'yale, da a tab'a ki gara ni a tab'a ni. “ Wasu hawaye ne suka zubo a fuskar Nusrat wa'yenda ba ta san dalilin zubowarsu ba, hannu ta saka ta baya ta rik'e hannun Shukhura gam had'e da fad'in. "Nima ina sonki k'anwata, amma don Allah ki daina fad'a kinji k'anwata. “ "Zan daina, idan har aka daina tab'aki, fatana na saka tsoron ki a zuciyar duk me tab'aki, yadda ko ganinki ya yi sai yai shayin yi miki magana." Ta na kawowa nan ta kuma rungumota a haka bacci ya d'auketa saboda ba ta da wuyar yin bacci, Yusra da ta farka ta jita ba jikin Nusrat ba ta yi juyi ta shige jikinta, hannu Nusrat ta saka ta na shafa kanta, ta na shafo kan Shukhura da d'aya hannun, har lokacin hawaye na zuba a idanuwanta, ta tabbata hawayen k'aunar da 'yan uwanta suke mata ne, kyakkyawar Katanga mahaifiyarsu ta gina musu a zuciyoyinsu na k'aunar junansu, babu ruwansu da k'yashi ko bak'in cikin anyiwa wani abu a cikinsu ba'aiwa d'aya ba, ta na fatan soyayya da k'aunar da sukewa junansu suci gaba da ita har k'arshen numfashinsu, kada Allah ya bawa wani nasarar rusa katangar alak'ar da take ginanna a zuk'atansu. Dubanta ta kai ga mahaifiyarsu da ke baccinta cikin kwanciyar hankali, duk abubuwan da suka faru ba ta san anyi ba, kasancewarta me nauyin bacci, shiyasa ko wani abun Baba ke buk'ata a gurinsu sai dai ya k'wallowa Nusrat kira. A b'angaren Iya kuwa k'wak'wame da bango wani wahalallen bacci ya yi gaba da ita, ba tare da ta shirya zuwansa ba. Washe gari da safe Nimha da taje kaiwa Iya abincin kari, kasancewar girkin Ummanta ne, anan ta samu Iya da kumburarran goshi, gefen fuskarta a karce. "Ayya Iya sannu me ya same ki?“ "Ke dai bari 'yar nan, duhun dare ne irin na damuna, na tashi fitsari na nemi cocilan d'ita na rasa nai shahada na fito haka shine na sha k'asa.“ "Ayya sannu Allah ya kiyaye, ga karin kumallon ki nan.“ Cewar Nimha, daga haka kuma ta juya ta fita kafin Iya tace. "Amin. “ Nimha na zuwa ta gayawa Ummanta abinda ya samu Iya, tab'e baki Umman ta yi had'e da fad'in. "Wa ya sani ma ko karkashin aljanar yarinyar cen ta kuma kad'awa ta zuba mata, ni ban tab'a ganin tak'adiriyar yarinya irin Shukhura ba, Iya na cewa Nusrat 'yar aljanu ai Shukhura ce 'yar aljanu ba Nusrat ba.“ Maganar da Umma ta yi kaf a kunnen Shukhura suka sauka, wani murmushi ta yi a ranta tace. 'Allah ya had'amu za kwa kiyi kallon tak'adiranci.' Kowa na gidan sai da ya shiga ya duba Iya, Nusrat da Shukhura a tare suka shiga duba ta, abinda ya bawa Nusrat mamaki ganin Iya ta kirata da Nusrat abinda tsawon rayuwarta ba ta tab'a kiranta da shi ba, sai dai ta kirata da Ai, ba ma za tace Ayshan ba, duk don Malam ya ji haushi. Sannan kuma har suka fito ba ta sanyata aiki ba, kasancewar duk sanda ta shiga gurin ba za ta fito ba sai ta moreta ko ya ya ne, kuma ta na kallon Shukhura ta na ta sunkui da kai ta na matse dariya, shine da suka koma d'aki ta dubi Shukhuran tace. "Wai dariyar me kike ta matsewa ne a d'akin Iya? “ "Yo ba dole na yi dariya ba, kinga kuwa goshinta kamar mulmuleliyar daddawa sai shek'i yake. “ Ta fashe da dariyar da ke cinta tun d'azu. "Allah ban yadda da ke ba Shukhura, duk yadda akai ta dalilinki Iya ta ji ciwon nan. “ " To ni me ta mun da zan saka ta ji ciwo? “ Ta fad'a ta na d'an turo baki gaba. "Kefe kika ce sai kin saka tsorona a zuciyar duk me takura mini, kuma yau kallon da Iya ta yi mini ya bam bamta da wanda ta ke mini a kullum.“ Rik'o hannuwanta Shukhura ta yi had'e da fad'in. "Tabbas 'Yar baiwa ce ke Yayarmu.“ Kana ta shiga labarta mata yadda sukai da Iya ta na dariya, murmushi Nusrat ta yi tace. "Tabbas Iya tai namijin k'ok'ari da ba ta sume miki ba, don in nice wallahi sumewa zan yi, a gaskiya kin d'au hak'k'in 'yar tsohuwa, don ta tsorata sosai tun da gashi ko labarin ainihin abinda ya faru ba ta bayar ba.“ "Wallahi ba wani hak'k'in ta da na d'auka, in hakane ita sau nawa ta na d'aukar hak'k'unanmu. “ Girgiza kai Mama ta yi, a kwance take duk a tunaninsu bacci take, duk abinda Shukhuran ta fad'a ta jishi, kuma ta na nemawa 'yar tata shiriya, don Baba yace da kansa zai dingai mata rubutu ta na sha, don abin nata ya fara yawa duk abinda akai mata tace sai ta rama ko ta halin k'ak'a. "Kya ci gidanku, bari Babanku ya dawo sai na gaya masa, kuma ki tashi kije yau ke za ki mata shara ki wanke mata band'aki. “ Zunb'uro baki gaba tai ta mik'e, don in ba ta ta shi ba ta san Mama na iya jefo mata duk abinda ke kusa da ita, bayan fitarta Mama ta yi tunanin may be taje ta kumai mata wata muguntar don haka ta shiga k'wala mata kira kafin ta tashi ta bi bayanta....... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *FOUR* Washe gari da safe misalin goma da rabi, zaune suke suna cin jolof in taliya a babban tray, kasancewar Baba ba ya nan ba a gida ya kwana ba kuma girkin Umma ne sai tak'i toya k'osai ta dama zallar kunu kad'ai ta bawa Nimha 200 ta siyo musu iya su da Iya kawai, wannan dalilin ne yasa Mama ta yi musu jolof in taliya saboda kunu kad'ai bazai rik'e cikinsu ba kuma Nusrat ba ta shan kunu sai koko. Muryar Hidaya suka ji ta na k'wallowa Nusrat kira tab'e baki Shukhura ta yi bayan ta zuba taliyar a bakinta tace. "Ga su shafi da mai nan an faso. “ Wata muguwar harara Mama ta jefeta da shi, kawai sai tai murmushi ta sunkui da kai, daga bakin k'ofa Hidaya ta tsaya, ta tsuguna har k'asa ta gaisar da Mama kana ta dubi Nusrat da ke kallonta ta na murmushi, ta yafitota da hannu had'e da fad'in. "Kizo Yaa RJ ne ke kiranki, tsam Nusrat ta mik'e dama jikinta da hijabi saboda ba ta rabo da shi a jikinta ta bi bayan Hidaya suka fice Mama ta bita da idanuwa, Shukhura ce tace. "Nifa Mama sai nake ganin Aunty Maryam kamar ba ta son Yaa RJ ya na kula Yayarmu.“ "Rufe mini baki ko na dakar miki shi da hannuna, na fa gaya miki ba na son irin magan ganun nan ko? Idan ma ba ta son ya kulata naga ta dalilinta duk kuka sanshi.“ "Yi hak'uri Mama, amma kuma in saboda kar wata alak'a ta shiga tsakaninsu ne to ta sha kurumunta in Allah ya yarda mijin Yayarmu ba daga tsatson mijinta zai fito ba ehe. “ Girgiza kai kawai Mama ta yi don zuciya ta kusa ciyota ta k'wala mata mificin da ke kusa da ita, zama Shukhura ta gyara had'e da gyara murya tace. "Mamarmu nidai na gaji wallahi, ko yaushe sai ki dinga hanamu fad'a ana kuma k'wararmu, nidai wallahi idan Baba ya dawo zan kwashe duk abinda matarsa ke mana a gidan nan in gaya masa, haka kawai yanzu da ba dan muna da wannan taliyar ba sai dai fa mu zauna da yunwa har rana da ranar ma ba wani ishashh......“ Dakatawa ta yi da maganar sakamakon mificin da Mama ta rafka mata don taga hararar da take wurga mata ba za ta saka ta rufe mata baki ba sai ta had'a da duka, mik'ewa Shukhura ta yi ta na zunb'uro baki, ta figi hijabinta da ke kan k'ofa, ta na matsar k'wallar k'arya ta fice ta na. "Wallahi na kusa yin maganin wata a cikin gidan nan.“ Ta fad'a da k'arfi yadda Umma da ke d'aki za ta jiyo ta. Aunty Maryam na shiga d'aki ta tarar da Iya da kumburarran goshi. "A'a Iya me ya sameki haka?“ "Zamewa na yi na fad'i na buge da bango. “ "To wannan karcewar ta gefen fuskarki fa?“ "Ke nifa ba na son tambaya, na gaya miki zamewa na yi na fad'i, me kuma kike son ji, kin wani titsiyeni kamar wata uwata sai kinji abinda ya sameni sai kace wani abu za ki iya a kai, mtssss. “ Taja tsaki taci gaba da sababi yayin da Aunty Maryam tace. "Allah ya huci zuciyarki.“ Ta fice daga d'akin, in ba haka ba ba za ta daina sababin ba, ta shiga d'akin Umma don su gaisa. A cikin mota Nusrat ta samu Yaa RJ, tun fitowarta yake sakar mata murmushi ta cikin gilashin motar har ta k'araso gaban motar, a bud'e murfin motar yake don haka ta shiga ciki ta zauna suka had'a ido da Hidaya da ta juya ta koma cikin gidan. Shiru ne ya biyo baya sai kanta da ta sunkuyar k'asa ta na watsa da yatsan hannunta, yayin da shi kuma ya kafeta da idanuwansa, ya na jin wani sabon yanayi a kanta, ya san Nusrat yarinya ce ta yi k'ank'anta ya furta mata kalmar soyayya, amma ya na jin tsoron ya dawo ya tarar wani ya riga shi nasarar karb'ar soyayyarta, sanyin halinta, yanayin tafiyarta, yanayin maganarta komai ya yi dai-dai da yadda yake son matarsa ta kasance. "Ina wuni Yaaya?“ Nusrat ta katse shirun da yake tsakaninsu ta kuma katse shi daga tunanin da ya tafi, rintse idanunwansa ya yi ya busar da wata iska mai sanyi saboda yadda muryarta ta shiga jikinsa ta zauna, wani siririn zoben azurfa ya ciro daga d'an k'aramin yatsan hannunsa. "Muga hannunki. “ Zara zaran yatsunta ta mik'a masa ya zira mata a yatsanta na kusa da babban yatsa. "Daga nan kaduna zan wuce ta nan jirginmu zai tashi zuwa Uk nan da shekara uku zan kammala karatuna na dawo, ki mini alk'awari ba za ki bawa ko wani saurayi damar k'ulla soyayya da ke ba. “ Ba ta gane inda maganarsa ta dosa ba, don haka ta tsira masa idanuwanta kamar me karantar amsoshin tambayoyin da ke dank'are a zuciyarta, yayin da shi kuma yake jin kallon da take masa har tsakiyar zuciyarsa. 'Meye dalilin da yasa ka bani zobe, me yasa zan maka alk'awarin k'in kula ko wani saurayi bayan ba ni da tabbacin sona kake, idan ma sona kake anya auranmu zai yuhu kuwa, kana ganin Aunty Maryam za ta bar Katangar alak'ar da take ginanna a tsakaninsu taci gaba da ginuwa?' Wa'yannan tambayoyin sune cunkushe a ranta amman ta k'asa furta ko da kalma d'aya, ji take bakinta yai mata matuk'ar nauyi. Hannunta ya matsa had'e da fad'in. "Pls Nusrat. “ Tsintar kanta kawai ta yi da d'aga masa kanta, ya saki kyakkyawan murmushi, ya d'auko wata leda ya d'ora a kan cinyarta. "Na gode Nusrat, Allah ya baki ikon cika mini alk'awarina, bari ni zan wuce, ki gaida mini da su Mama. “ "Za su ji insha Allah, Allah ya kaika lafiya, ya kuma baka sa'a akan karatun naka.“ "Aminnnnn“ Yace yana me jin dad'in addu'arta yayin da ita kuma ta fice ba tare da ta d'au ledar da ya ajiye mata ba, murmushi ya yi don ya san za'a rina, a dai-dai lokacin Shukhura ta fito ta na zunb'uro baki, da hannu ya yafitota tazo gareshi, d'an risinawa ta yi ta gaisheshi yace. "Ga leda nan d'auki ki kaiwa Mama kice ina gaisheta.“ "Tom, an gode. “ Ta d'auki ledar shi kuma ya ja motarsa yai gaba. _RIDWAN JIBRIL shine cikakken sunansa yayin da ake masa inkiya da RJ, mahaifinsa da Yusuf mijin Aunty Maryam uwarsu d'aya ubansu d'aya, mahaifinsa ya rasu tun ya na yaro a gurin mahaifiyarsa yake da take aure a kaduna, tun bayan auran Yusuf da Aunty Marya ya d'auko RJ ya dawo gurinsa da zama suka rik'eshi tamkar d'ansu na cikinsu, bayan gama karatunsa na_ _secondary ya turasa Uk acan yake had'a karatunsa a fannin jarida._ _Hidaya da Nusrat tasu tazo d'aya sosai, suna k'aunar junansu hakanne yasa Nusrat take yawan zuwa hutu gidansu, yayin da shak'uwa me k'arfi ta shiga tsakaninta da Rj, har ta rikid'e ta koma soyayya a zuciyar RJ, idan har zaije kaduna gurin mahaifiyarsa sai ya fara tsayawa gurin Nusrat ya yin da k'arara Aunty Maryam ke nuna ba ta son alak'arsa da Nusrat saboda akwai wani buri da suka ci a kansa ita da mai gidanta._ Kwata² Shukhura tak'i yadda ta shiga ko gurinsu, ta na filin babban tsakar gida a zaune ta na dakon zaman jiran Baba ya dawo, don kada ma Mama ta hanata aikata abinda tai niya, ledar da RJ ma ya bata a bakin k'ofar d'aki ta ajiye ta fito don duk kada Mama ta ruguza mata shirinta, ta san dai duk tsiya Baba bazai wuce 12 na rana bai dawo ba saboda ba a gida ya kwana ba. Har kusan k'arfe d'aya Baba bai shigo cikin gidan ba, har ta fara tunanin tashi ta jiyo takun tafiya don haka ta maida idanuwanta kan k'ofar shigowar, aikuwa Baban ne ya yi sallamar ta amsa masa ta nufeshi had'e da d'ora damuwa akan fuskarta, har da fara taro k'walla, gaban Baba ne ya yanke ya fad'i yace. "Lafiya Shukhura me ya faru? “ "Baba.“ "Na'am fad'a mini me ya faru? “ "Dama kullum Mama ce ke hanani gaya maka.“ "Ina jinki.“ "Duk ranar girkin Umma ba ta bamu abinci ishashshe, da kai da Iya da su ta ciccika muku kwano, kuma har d'anye take ragewa ta b'oye, to yau da safe ba ta toya mana k'osai ba zallar kunu kawai ta dama, ta bawa Nimha ta sayo musu su da Iya. “ Ran Babane ya yi mugun b'aci, ya tabbata Shukhura ba za tai masa k'arya ba, shafa kanta ya yi yace. "Jeki ciki zanwa tufkar hanci. “ Cike da murna ta shige ciki ta na jin kamar ta sauke abu me nauyi a zuciyarta ko kad'an ba ta damu da hararar da Mama ke ta zabga mata ba. Sai da ya bari Umma ta gama girki ta raba kowa ta kai masa shima ta kawo masa nasa sannan ya k'wallowa Shukhura kira, ta amsa ta fito da saurinta. "D'auko mini abincinku.“ "Toh." Tace da hanzari ta juya ta d'auko. "Jeki ki anso mini na Iya. “ "Ai yau Iya ba ita kad'ai bace su Aunty Maryam sun zo. “ "Af na sha'afa, da na shiga gurin Iyanma mun gaisa, bar na tan. “ Ya dubi Umma yace "D'auko mun naku, kuma bance ki rage komai ba, inma kin rage da kaina zanzo na duba.“ Tsuru² Umma ta yi da ganinta ka san ba ta gaskiya taje ta d'auko ta kawo masa duban Shukhura ya yi yace. "Je ki d'aki, ki turo mini Mamanku. “ Shukhura na barin gurin Baba ya dubi Umma yace. "Yanzu wannan adalci kenan? Kalli abincin da rai d'aya zai ci, ki dubi na rai biyu duk sun taka wanda rai hud'u zai ci kinwa kanki adalci? Ko iya Nimha kad'ai ai sai ta tashi da wannan abincin, idan ni ba na gani ai Allah ya na ganinki kuma hakk'insu bazai tab'a barinki ba. “ Fad'a sosai Baba ya shiga yiwa Umma kamar zai ari baki, ya shaida mata muddun ta kuma irin rabon nan to sai ta bar masa gidansa, Mama da tazo fad'an ya rufe ta da shi akan me za ta hana a gaya masa irin haka na faruwa a cikin gidansa ya d'au mataki tunda ita ba ta gaya masa ba, ita dai Mama hak'uri ta bashi don sosai Baba ransa ya b'aci, ranar huni ya yi ya na surfawa Umma fad'a, abincinma ya yi zuciya ya k'i ci ya juyewa su Shukhura akan nasu na su Umman ma ya datsi rabi ya k'ara musu akai ya kira Shukhura ta d'auka, Umma kuwa sai huci take kamar ta janyo Shukhura tai ta jibgarta. _____________ Bayan sati guda Baffa Shamsu yazo garin zariya, a lokacin su Aunty Maryam sun koma kwana uku sukai suka tafi. Transfer yake nema zai dawo zariya gaba d'aya hakanne yasa yazo don neman gidan da zasu samu su zauna, duk da nan kusa da gidansu an masa tallansa to dai ya na son siya amman dai ba su gama cininki ba, tun zuwansa Iya tace. "Nidai yau aradu shinkafar gwamnati zanci, don wallahi na gaji da cin shinkafar hausa ina karo da tsakuwa ta na farfasa mini hak'ori, kalli nan kaga yadda duk hak'orina ya farfashe, don haka ma ni wallahi in za ka tafi binka zan, don na gaji da cin tuwon masara kullum da daddare na kwanta, gara a dinga dafa mini taliyar nan ta gwamnati me dad'in gaske.“ Murmushi kawai Baffa Shamsu ya yi yace. "Haba Iya ba na son kina irin wa'yan nan magan ganun kema dai kinsan Yaya yana matuk'ar k'ok'ari, idan yaji abinda kike cewa bazai tab'a jin dad'i ba.“ "To kar ya ji dad'in mana ni ina ruwana, wani k'ok'ari yake banda son 'yarsa da ya fifita a kaina. “ Ko me ta tuna kuma sai tai shiru kana tace. "Mubar ma maganar d'an arzik'i maza je ka siyo mana shinkafar, ka kuma siyo mana kaji don yau mu d'an wasa bakinmu, don rabona da ci nikam ina jin tun kan rasuwar Malam. “ Girgiza kai kawai Baffa Shamsu ya yi ya na mamakin halin mahaifiyar tasu sam ba ta da godiyar Ubangiji, duk zuwan da zaiyi sai sunci kaji a gidan, haka zalika Baba ma idan ya ji aljihunsa da nauyi ya na siyo musu su ci amma wai kunji rabonta da ci tun kan rasuwar Malam. Buhun shinkafa biyu da katan na taliya da macaroni biyu Baffa Shamsu ya siyo musu ya ajiye su a d'akin Mama, ya siyo musu kaji guda biyar manya ² gashi kuma aka taki sa'a girkin Umma ne, don haka Shukhura ta na da 1000 tace bari taje titi ta siyo don ta san 'yar kad'an za'a sanmusu, Nusrat ma na da 1000 sai ta bata ta siyo musu guda biyu kuma manya da su. Ilai kuwa cinya d'aya fukafiki aya sai wuya aya aka saka musu, ko kad'an ba su damu ba Shukhura ta wanke nasu ta tafasa ta fara suya. K'amshin suyar naman Iya ta ji a ranta tace kaddai matar nan ragewa ta yi take soyawa da hanzari ta fito don ta ganewa idonta, ganin Shukhura ce me suyar ta kai hannu za ta d'auka a cikin wa'yanda ta kwashe, Shukhura ta yi saurin d'auke robar hannun Iya ya sauka a k'asa har sai da ya yi k'ara tace. "Auchhhhh“ Don ta ji zafi sosai, Shukhura kuwa ko a jikinta ta murgud'a baki tace. "Ai ba taku bace, wannan tamu ce naje na siyo, da za ki d'auko yamutsats tsan hannunki ki saka mini a ro....“ Ba ta k'arasa ba taji saukar mari a kuncinta, dafe kuncin ta yi ta tsaya ta na kallon Mama da ta fusge robar naman a hannunta ta d'auki cinya manya² guda biyu ta bawa Iyan, sai da Iyan ta ansa kana ta tab'e baki. "Ai da ba ki daketa ba ai na san duk makirci ne irin naki, ke kitsa mata dukkan abinda takeyi a gidan nan, amma ai Shamsu yazo zai mini maganinta. “ Ta na kawowa nan ta fice daga gurin Shukhura ta bita da d'an iskan kallo, Mama ba ta iya cewa komai ba ta koma d'aki Shukhura ta k'wallowa Nusrat kira. "Yayarmu zo ki kama mini na shiga band'aki. “ Nimha tace. "Kawo na miki kan ki dawo. “ "Don aji dad'in d'iba akai d'aki ba, a'a basshi na gode ga Yayarmu nan za ta ansa. “ Umma ta gallawa Nimha harara. "Maganin shishshiginki kenan ga shinan an gab'a miki magana.“ Memakon Shukhura ta shiga band'aki sai ta fice ta yi gurin Iya. "Kina ina yau in kinci naman nan ba Mama ce ta kawoni Duniya ba. “ Iya na jin haka ta yi saurin nad'e shi a leda ta saka a k'ark'ashin gado, dama ajiyeshi ta yi sai ta gama da na cikin miyar. A bakin k'ofa ta cage tace. "Ki fitomun da namana.“ Sai ki d'auka in kin ganshi ai. “ Bin d'akin tai da ido ta na nazarin inda Iyan za ta ajiye naman, ganin kamar idon Shukhuran ya na sauka a k'ark'ashin gado Iya ta yi saurin d'aukewa ta mik'e tsaye. "Sai kizo ki k'wata in baki da kunya. “ Kanta Shukhura ta yi gadan² ta kama hannunta za ta murd'e. "Ke ke ba ki da hankali wai. “ "Eh bani da shi d'in, ta d'auka ta baki naman sannan ki yab'a mata magana kuma kici alqur'an ba ki isa ba. “ Taci gaba da k'ok'arin k'watar naman dai-dai nan Baffa Shamsu ya shigo. Kyakkyawan maruka ya saukewa Shukhura kana ya tambayi ba'asi Iya ta koro masa bayani, hararar Shukhura ya yi da ke tsugune dafe da kuncinta. "Dama ance ba ki da kunya to yau zanyi maganin rashin kunyarki. “ Ya zari cagar radio ya yo kanta ta saki ihu ta yi bayan Iya dai- dai lokacin ya kawo mata duka ya sauka a jikin Iya, Iya ta zunduma ihu tsabar azaba. "Shamsu ka rabu da yarinyar nan dan Allah kar ka daketa, bai saurari Iya ba ya b'anb'aro Shukhura daga jikinta ya hau zuba mata wayar ko ta ina, aikwa ta bud'e murya ta dinga zunduma ihu, Mama ko motsi daga inda take ba tai ba, kuma ta hana su Nusrat zuwa, tace ai gara taji a jikinta gobe ma ba za ta sake ba, Umma kuwa da gudu ta nufo gurin ta na shewa dama a ciki take da ita. Sai da ya yi mata lilis sannan ya k'aleta,ya fice, Iya na gefe ta na ta matsar k'walla don ta san yau kashinta ya bushe gurin Shukhura, yayin da Umma ke ta shewa ta na fad'ar magan ganu. "Yau dai an mana maganin mara kunyar gidan nan, aiyiri yiri yiri yiri. “ Wani kukan kura Shukhura ta yi ta saki wani ihu ta yo kan Umma da gudu, tsoro ne ya kama Umma ta mik'e za ta fice ta yi tuntub'e ta fad'i, yayin da Shukhura ta shiga aljanun k'arya ta dinga cin uban Iya da Umma da sanda dukkanninsu sun jigata sosai, har sai da Mama tazo ta janyeta, suna shiga d'aki ta fashe da dariya a ranta tace. 'Saura Baffa Sham sun.' Mama kuwa zuba mata ido kawai ta yi, don ta d'auki alk'awarin ta daina dukanta daga yau, addu'ar nan ita za ta cigaba da yi mata anai mata rubutu ta na sha. Da jan jiki Umma ta samu ta komo gurinta, ta na jin mugun shakkar Shukhura a ranta, Iya kuwa kuka ta dinga rusawa don yau babu abinda zaisa ta kwana a cikin gidan nan Shamsu yazo su tafi Kaduna ta wuta da wannan jaraba da masifar da Audu ya haifa. Hankalin Shukhura bai kwanta ba har sai da ta sakawa Baffa Shamsu cinnaku biyar manya² a riga ai kuwa ya sha muguwar azabar da ta wuce dukan da yai mata. 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *SIX* Ta b'angaren Alhj Faruoq Fanda kuwa ya na zuwa gida ya sanar da matarsa Hajiya Suwaiba wata yarinya ta yi wuff da zuciyar yaronsu, farin ciki tsanta H.Suwaiba ta shiga had'e da fad'in "Wata yarinya ce wannan mai matuk'ar sa'a Alhaji?“ "Ai ban baro gurin saukar nan ba sai da na saka aka samo mini bayanai a kanta. A nan unguwar cikaji suke zaune, mahaifinta ba wani mai hali bane sai dai rufin asiri na Ubangiji, itace 'ya ta biyu a gurinsa, ta na matakin aji biyu a sss, an shaidu 'yan gidan gaba d'ayansu da tsantsar tarbiya, sunanta na gaskiya Safiyya, amma da Shukhura ake kiranta.“ K'awataccen murmushi H.Suwaiba ta saki tace. "Kai amman na ji dad'i, Allah yasa itace abokiyar arzik'insa, ai banda hidimar saukar nan da muke ta Maryam da ba abinda zai saka ni zuwa naga sirikata a yau.“ Murmushi Alhj ya yi yace. "Don zumud'i irin naki, gobe in sha Allah dai zamu je gaisuwa, da kayan na gani ina so, don har ga Allah na yaba da zab'in yaron nawa, don dama ina gudun ya d'auko mana irin wayayyin yaran nan marasa tarbiya, fatanmu dai Allah yasa ba maganar wani a kanta.“ "Amin., amma ka dai sanar da Hajiya Inna ko, don gara a gaya mata tun wuri za'a yo mata kishiya. “ Ta kai k'arshen maganar ta na dariya, dariyar shima Alhajin ya yi yace. "Ita ai na fara gayowa ta na nan ta cika fam ta na jiran shigowarsa, na san yau dai ba za'a bashi abinci ba nan za'a koro mana shi. “ Alhj Farouq Fanda asalinsa d'an garin Fanda ne, neman kud'i mahaifinsa yazo yi tun Farouq na yaro, a garin kano suka fara zama ya na yin kasuwancinsa kuma Allah yasa masa albarka a ciki, nan da nan ya tara dukiya me d'imbin yawa, Farouq shi kad'ai ne d'ansa wannan dalilin ne yasa ya bashi gata mai yawa, ranar da Faruoq ya gama karatunsa na shari'ah a ranar mahaifinsa ya rasu, sunyi kuka iya kuka da shi da mahaifiyarsa Fatima (Hajiya Inna. ) Bayan rasuwar mahaifinsa ne dukiyoyinsa duk suka dawo k'ark'ashinsa, sannan kuma ya fara aiki a matsayinsa na babban alqali, nan da nan dukiyarsa ta kuma bunk'asa, ga kuma harkokin kasuwancin mahaifinsa hakan ne yasa ya nemi mataimaka kuma ya samu masu aminci, daga kano suka tarkata suka koma zariya da zama a unguwar sabon gari, gida ya dank'ara ba na wasa ba, ya yiwa Hajiya Inna sashinta da ban, zuwansa zariya anan ya had'u da Hajiya Suwaiba suka fara soyayya itama 'yar garin zariyan ce anan unguwar cikaji, ba'a d'au wani lokaci ba akai bikinsa da Suwaiba, Hajiya Inna na mutuk'ar k'aunar sirikar tata, ko kad'an ba ta san wani mugun hali na uwar miji da ake fad'a ba, ta rik'eta tamkar 'yar cikinta, wannan dalilin ne yasa tai alqawarin idan Allah ya azurtata da 'ya'ya maza za ta k'aunaci matansu kamar 'ya'yan cikinta, don a ganinta babu bambamci tsakanin d'anka da sirikar taka tunda an riga an zama d'aya. 'Ya'ya biyu Allah ya azurtasu da su, Mustafa,sai Maryam, sunga gata sosai gurin mahaifan nasu. Mustafa Faruoq Fanda, wanda abokansa ke kiransa da Fanda ya kammala karatunsa na low har ya zama Barrister mai zaman kansa, komai na shi na rayuwa a sashin Hajiya Inna yake don ta na matuk'ar k'aunarsa, Maryam kuwa rayuwarta ta fi k'arfi a gidan kakanninta na uwa acan cikaji, da yake suma da rufin asirinsu, zamanta a cikaji shiyasa islamiyarsu tazo d'aya da su Shukhura, ba ajinsu d'aya ba, da yake aji biyu ne aka had'e akai saukar, itama Maryam ta yi candy ta na jiran sakamako don ta d'ora daga inda ta tsaya. Wannan kenan. Washe gari da safe Iya ta sami Mama a lokacin ta na toya k'osan da zasui kari da shi tace. "Waini Maimuna ba'a kasafta kud'in nan bane? Na ji shiru ba'a ce Iya ga naki ba. “ "Wani kud'i?“ Mama ta tambayeta don ita a tunaninta wasu kud'i ne Baba ya samu da ban. "Ban gane wani kud'i ba, ki jiki da wata iriyar tambaya, to kud'in da jikokina suka samo.“ D'an k'aramin murmushi Mama ta yi tace. "To ki bari in Babansu ya tashi sai ki tambayesa, in kuma in taso miki shi to? “ "Aini na san ba za ki bari a bani ko ficika a kud'in nan ba Maimuna, na rasa me na yi miki a duniyar nan kika bi kika tsaneni daga ke har 'ya'yanki bare ma waccan me tak'adiriyar k'irar samudawa, da fari kamar arnan zabiya, na tabbata da Nimha ce ta samo kud'in nan biyu za'a raba a bani, amman da yake ku mugaye ne an halicci rowa a jininku biyar kun gagara ba ni, kuje kui ta ci insha Allahu sai kun shekara kuna zabga gudawar da ba ta da comlayin, tuban sardauna kawai.“ Shukhura da Nusrat da ke kallo a 'yar k'aramar wayar Mama, duk suna jin abinda Iya ke cewa, zumbur Shukhura ta mik'e ta fito. "Ki gani a kanki me mugun alkaba'i, insha Allahu kanki bakinki zai komo, naga kud'i namu ne ko, to ba za'a bayar d'in ba kiyi abinda za ki, rowa kuwa mu muka yanke mata cibi, kuma zan nuna miki ni babbar tak'adirya ce don naga kwana biyu kin manta da tak'adirancin nawa, inma tuban galadima ne ko wambai tunda mu musulmai ne Alhmdlillh. “ Tun fara maganar Shukhura Baba ya fito, shi yaiwa Mama alamar ta yi shiru daga k'ok'arin dakatar da Shukhura da take har sai da Shukhuran ta kai aya ya ja hannun Iya suka fice da ke neman fisgewa ta na d'an kuka, sai da sukaje d'akinta sannan ya sake ta yai k'asa da muryarsa sosai yace. " Tun da na auro Maimuna gidan nan take d'aukar cin kashinki Iya, ba ta tab'ai miki kallon banza bare musu da ke, amman har ta haihu kina yi a gaban 'ya'yanta wanda Shukhura ba ta iya d'auka har sai ta rama sannan kuma kisa in daketa k'arshe kuma kanki abin zai dawo, amman har yau kink'i daina abubuwan da kike, maganar kud'i kuma da kike yaran nan daga su har mahaifiyarsu biyar basu karb'a ba ni suka barwa saboda hidimar gida da kuma auransu in ya taso amman kuma kinzo kina fad'ar maganganu a kai, yanzu meye ribar sa'insa da jikarki? Dan Allah Iya ki canja, ki dinga jan girmanki.“ Kuka iya ta ja had'e da fad'in. "Tashi ka fita Audu, tashi ka fita nace tun kafin na tsine maka ka bi duniya, har ni za kazo ka gayawa maganganun banza, a gabanka 'yarka tai mini cin mutumci ka kasa d'aukar mataki saboda an baka kud'i? Jeka kawai Audu na barwa Maimuna da 'ya'yanta kai.“ "Kiyi hak'uri Iya, yanzu zanje na lillisa mata jikinta. “ Kukan Inna ne ya tsaya cak tace. "Idan har kana son albarka a gurina kada ka tab'a lafiyar tak'adiriyar yarinyar nan, don wallahi kaf tak'adirancinta za ta sauke mini yau.“ B'oyayyen murmushi Baba ya yi ya tashi ya fita. Yusra da ta dawo daga siyo sikarin da Mama ta aiketa tacewa Mama. "Wasu a mota sunce suna sallama da Baba. “ Baba da shigowarsa kenan maganar ta sauka a kunnensa ya juya had'e da fad'in. "Bari naje naga su waye.“ Sai kuma gashi ya dawo yace Yusra ta d'auko tabarmi, ta d'auko taje ta shimfid'a a soro. Bayan gaishe² Alhj Faruoq ya gabatarwa da Baba abinda ke tafe da su, sannan ya d'ora da cewar. "Da fatan ba maganar wani a kanta. “ Baba yace. "Ba maganar kowa a kanta, kuma na yi masa izini yazo ya nemi soyayyarta idan har ta amince mishi babu abinda zai hana na bashi ita, Allah ya tabbatar mana da alkhairi. “ Godiya Alhj Faruoq sukai da shi da abokinsa da suka zo tare, sannan ya sanya driver d'insa da ya tuk'osa ya fito da akwatin da suka zo da shi, akwati ne mai kyau madai daici, Alhj Farouq yace. "A bawa Shukhura, kayan sun gani suna so ne. “ Baba yace bazai karb'a ba suka ce ai 'yarsu suka kawo, idan kwa bai ansa ba to baiyi na'am da su ba, daga haka sukai masa sallama suka tafi shi kuma ya ja akwatin ya nufi cikin gida...... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna *KATANGA* ____________ *FIVE* A haka rayuwa take juyawa cikin d'an k'aramin familyn nan, Nusrat ta yi candy, su Shukhura kuma saura shekara d'aya su yi, a lokacin ne kuma aka saka musu ranar saukarsu ta islamiya da yake duk ajinsu d'aya har Nimha. 3/4/2014 shine ya kama ranar saukar tasu. Iya ba ta sauya daga halinta na nuna banbanci tsakanin jikokinta ba har ma ga 'ya'yan nata, don yanzu Baba bai samun cininki sosai a kasuwa sai ya zamto abinci ma Baffa Shamsu ne ke ajiye musu duk wata, saboda ya dawo nan kusa da gidan nasu da zama. Hakan da matarsa ta gani ne yasa ta d'au babban mataki a kansa, abincin da yake sauke musu sai ya koma saukewa gidan su matar tasa duk wata, gaba d'aya ta bi ta mallake shi ta kanainaye shi ba ta bari ya morawa kowa abin biyar face 'yan uwanta, zagi da tsinuwa kuwa ta na shan shi gurin Iya amma a bayan idonta, in a gaban idonta ne kanzil ba ta iya tofawa, saboda abincin da take kawo mata rana da dare kar taje a daina kawo mata ta shiga uku da cin tuwo don yanzu sai su jera sati suna cinsa huni sir, don yanzu rayuwar gidan lallab'ata suke duk abinda Baba ya samo ciki ake k'ok'arin bawa hak'k'insa. 3/4/2014 Ta kama ranar lahadi kenan, ranar da zuk'ata da yawa ke cikin farin cikin kammala saukar karatun alqurani mai girma, za'a bawa kowa allonta na shaidar saukarta, irin wannan ranar ce ko wani bawa ke burin ta riskesa. Tun daga farkon layin makarantar tasu mak'il yake da mutane ko 'yan saukarma ba'a hangowa saboda suna tsakiya a cikin rumfa,banda sautin qira'ar Shukhura mai matuk'ar dad'i babu abinda kake juyowa a gurin mutane da dama sun nutsu suna saurarar karatun da ke saukar da nutsuwa a zuk'ata. Bayan kammala karatun Shukhura ta taso a hankula ta koma gurin zamansu, tun tasowarta FANDA ke binta da kallo, duk da kasancewar ga tsantsar yarinta nan a fuskarta ya na kallo amman kuma ta kama zuciyarsa sosai, tabbas idan ya bari lokaci ya shud'a wani ne zai riga shi mallakarta, don irin su Shukhura ba wanda ake kalla a kau da kai bane, bare nan gaba ta k'ara girma, har ta zauna idonsa ya na kanta, a hankali ya sauke idonsa akan wacce ke Kusa da ita, tabbas ya gano kama a tattare da su ya na kyauta zatan 'yan biyu ne, duk kallon da yake binta da shi mahai finsa Farouq Fanda na lura da shi, ko ma wacce yarinyace wannan tabbas ta taki sa'a gurin d'an nasa, kallo d'aya idan yaiwa mace to tabbas ta taki babbar sa'a, tun kammala karatunsa yake masa zancen aure amma yake tai masa kwana kwane, amman yau yaga alamun d'an nasa yayi kamu, idan kuwa hakane zai fi kowa farin ciki, bare kuma mahaifiyarsa ta ji labari da Hajiya Inna, murmushi ya yi ya na gano yadda Inna za ta d'auki zancen. Kallonsa ya yi har lokacin idonsa na kan Shukhura, wani kyakkyawan murmushi ya saki ya saka bakinsa dai² kunnansa yace. "Da dukkan alamu dai yau yarona yaga matar aure. “ Kunya ce tai mugun kama shi, ashe dai duk abinda yake mahaifinsa na lura da shi, shafa kansa ya yi ya na mai sunkui da kai, shafa kansa Abban nasa ya yi yace. "Soyayya ta na da kyau yarona, Allah yasa matar arzik'i ce. “ A can k'asan mak'oshi ya amsa da "Amin“ Ya na mai jin muguwar soyayyarta a zuciya wannan shi ake kira love at first sight. Bayan kammala saukar aka fara kiran d'aliban da sukai na d'aya zuwa na goma don a basu kyauta. Aysha Abdullahi Ahmad aka fara kira wacce tai na d'aya sannan aka kira Safiyya Abdullahi Ahmad ita tai ta biyu sai Maryam Farouq Fanda da tai na uku daga haka har aka kai na goma duk aka basu Kyaututtukansu, anan Alhaji Faruoq Fanda ya karb'i speaker yai magana akan ya bawa makaranta kyautar million d'aya, sannan ya bawa Aysha Abdullahi Ahmad da Safiyya Abdullahi Ahmad kyautar million d'aya, saboda yaba k'wazonsu, cikin d'alibai kusan 100 su suka d'au matakin na d'aya da na biyu. Nan gurin taro ya hautsine kowa na fad'in albarkacin bakinsa, yayin da wasu ke cewa ai kyautar million biyu gurin Alhaji Farouq Fanda ba komi bace kamar biyar haka yake jin ya cire daga aljihunsa. Iya kuwa sai dashe baki take ta na kuma b'antarar goronta, ta kalli Umma da ranta yai bak'ik'k'irin saboda bak'in cikin Shukhura da Nusrat, harara Iya ta galla mata tace. "An dai yi asarar haihuwa, ace duk kyaututtukan nan da ake rabawa babu sunan Nimha ko d'aya, saboda k'wak'walwarta irin ta jaki ce, amma kalli 'ya'yan albarka, gaskiya Maimuna ta iya haihuwa banda kyaututtukan da suka samo har kyautan million d'aya suka samo mana saboda 'yan arzik'i ne su irin albarka, don ni har ma na fara kasafta nawa kason da za'a bani, na san dai zan samu kamar dubu d'ari biyu, kinga dubu d'ari zan sayi kayan abinci har da su maltina da madara da su k'wai, da taliyar nan me kanannad'ewa ta gwamnati, d'aya dubu d'arin kuma na ajiye a hankula ina zara ina siyo gasashiyar kaza da youghot ina ci da daddare in tayar da kai, wayyo ai a cikin satin nan ma sai an k'asa gane ni zan canja kala saboda cin dad'i, fatar nan tawa da ta fara yamutsewa saboda wahala za ta gyaru, kai Allah dai ya shiwa Maimuna albarka da ta haifo wa'yannan 'yan albarkar, tun da nake ban tab'a rik'e dubu goma ta kaina ba, amman gashi dalilinsu zan rik'e,har dubu d'ari biyi, ni ban san ma tun tuni me ya hanani nuna musu k'auna ba wallahi, amman duk cikin jikokina Allah na gani na fi son su.“ Duk zubar nan da take ita kad'ai take yinta, don Umma ta bar gurin saukar tun sanda ta fara maganar, saboda ganin za ta d'ora mata wani bak'in cikin ne kawai, da ta jujjuya ba taga Umman ba itama sai ta nufo gida ta na tafe ta na kuma kasafta dubu d'ari biyun da za'a bata. Sai kusan k'arfe uku suka baro gurin saukar, saboda an yiyyi hotuna acan, a matuk'ar gajiye dukkaninsu suke, don haka ko waccensu sai da tai wanka kafin su kwanta zuwan jiran yamma ta yi, duk da gidan nasu a cike yake da 'yan hidimar saukar. Da yamma sukai walimarsu anan cikin gidan, kaya iri d'aya suka saka dukansu, Aunty Maryam ce ta d'inka musu, itace ma ta d'au nauyin kayan snacks d'in da suka raba a walimar. Har kusan dare Iya na d'akin Mama tak'i tafiya sai jan Mama take da hira, Mama kwa sai dai tai ta binta da um da umum saboda rashin sabo. "Aini fa ko, tun tuni dama ina sonki da 'ya'yanki dama duk makircin shegiyar matar can ne wallahi, kullum ita kenan kawo mini b'atanci akanku, ai gashinan ta haifi yarinya mai k'wak'walwa irin ta jaki, da k'afafuwanta kamar na babyn roba. “ "Uhm“ Mama tace kawai, ta na mik'ewa don jin ana kiran sallar isha, in ba sallar ta tayar ba Iya ba za ta k'yaleta da wa'yannan zantuttukan nata mara sa kan gado ba, ganin Maman ta tayar da sallah yasa Iya ta tashi ta fice ta na jifan d'akin Umma da banzan kallo, Umma ta na hangota ta labule a ranta tace. 'Makirar mata kawai, insha Allahu k'wandala ba za'a baki cikin kud'in ba inga ta tsiya, ina nan kuma za ki dawo jikina in miki rashin mutumcin da har ki koma ga mahaliccinki baza ki manta shi ba, tsohuwar banza kawai.' Iya tun ta na jiran shigowar Baba yazo a kasafta kud'in, har bacci yai gaba da ita ba tare da ta sani ba, Baba kuwa sai gurin 11 na dare ya shigo, bayan ya rufe gurinsu ya kirawo Mama da su Shukhura anan ya ke gaya musu. "Na kai Accaunt number d'ina makarantarku, Alhmdlillh d'azu na ji kud'inku sun shigo har million d'aya, yanzu me kuke gani za'ai da kud'in?“ Shiru dukkaninsu sukai su na kallon Mama, ganin Maman ba za tai magana ba yasa Nusrat tace. "Nidai Baba a shawarata kawai ka bar kud'in a Accaunt d'inka, in yaso sai a 'yebi wasu daga ciki a siyo kayan abinci, duk wata lalaura da za ta taso sai a magance da kud'in ko kuwa? “ Ta fad'a ta na kallon Shukhura. "Eh Yayarmu, nima hakan nake shirin fad'a kika riga ni. “ Murmushi Mama ta yi, ta na mai yabawa da hankalin yaran nata, kuma taji dad'in abinda suka ce da mahaifin nasu tace. "Na ji dad'i matuk'a da abinda kuka yanke, dama nak'i maganane don na ji ta bakinku, ku tashi maza kuje d'aki, Allah ya yi muku albarka. “ "Amin.“Suka amsa a tare suka tashi suka fita, bayan fitar tasu Mama ta kalli Baba tace. "Ta bakin nasu nima zanyi, ka d'ebi wasu kud'in ka siyo mana kayan abinci, kabar ragowar a asu sun naka, in yaso duk abinda aka d'an samu sai ka dinga ajiye su, saboda kwanan nan za ka ji auran yaran nan ya tashi, kuma duk su ukun nake magana, don Nimha da Shukhura sun fi Yayartasu gab'b'an girma, in suka jero sai ka rantse itace k'aramar su, shiyasa ma ita Yayartasu d'in ba saurayin da ke zuwa gurinta, sab'anin Nimha da Shukhura, bare ma Shukhura babu ranar banza da ba za'a zo ace ana sallama da ita ba, sai na tursasa ta take fita, sai tace ai wai ita Yayarsu ba ta zance. “ "Da gaskiyarki Maimuna, nima ina tunani idan akace mini auran yaran nan ya taso, duk dai da Allah na dogara shi na mik'awa lamurana, tabbas kuma da ace Nusrat na da tsayayye a yanzu zan aurar da ita, tunda ta yi candy tai sauka me kuma za'a jira, amnan tunda babu sai muyi rok'on Allah ya kawo mata na gari, su Shukhura kuwa babu zancen ai yayarsu ba ta zance, shi aure ai lokaci ne ba'a jiran sai yaya tayi sannan k'anwa za tayi, duk wacce ta samu miji zan aurar da ita, fatana dai Allah duk ya had'a su da mazaje na gari, kuma na ji dad'in shawararki hakan kuma za'ai Allah ya shiga lamarinmu ya kuma dafa mana. “ Mama ta amsa masa da. "Amin. “ 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ *KATANGA* ____________ *EIGHT* Tun kan ta k'arasa soro k'irjinta ke dukan uku² shikuwa Mustapha alamun tafiyar da ya jiyo ne yasa shi k'urawa k'ofar da za ta fito ido, sai da ta janyo mayafinta ta rufe fuskarta kafin ta tako a hankali zuwa gurin da akai masa shimfid'a da tabarma zuciyarta na harbawa da gudun gaske, can gefe da shi ta samu ta zauna ta sunkui da kanta k'asa kafin tace. "Ina wuni.?“ "Nima ban ganshi ba, tun da dai ba ajiyarsa kika bani ba, idan kwa kina son na amsa miki to ki tabbata kin yaye rufin da ya Katange mini kyakkyawar fuskar da nake da muradin kallo a ko da yaushe. “ K'asa ta kuma yi da kanta ta na murmushi. "Please nidai a taimaka mini, yau kusan sati guda rabon da na ganta, tun a ranar da ta samu babban guri a zuciyata, idanuwana suka aminta da ita, suka tabbatar da itace sanyinsu kuma haskensu.“ "To aini kunya nake ji." Ta fad'a kamar a shagwab'e. "Idan kika sShukhuraki cikin nawa za ki daina jin kunyar. “ 'Cif, na ma kasa bud'e mayafina na ganshi, duk da zuciyata da take ta azalzalata na gansa shine har zan saka idona cikin na, hod'ijam aikam dai sai dai kar na daina jin kunyar' Muryarsa ce ta dawo da ita daga d'an k'aramin guntun maganar zucin da ta tafi. "Zan fa zo da kaina na cire mayafin gaba d'aya wallahi idan har ba ki d'aga sa ba.“ 'Cif saboda kai d'an ikka ne haka kawai ka ciren mayafina, hod'ijam aikam dai da kaga tsigalewa.' K'irjinta ne ya buga, zuciyarta tai wani irin harbawa yayin da ta jisa ya matso dab da ita. 'Laa kaddai ciren mayafin zaiyi kuwa, na shige yau na had'u da mara kunyar mutum.' Da sauri ta yaye mayafin da ke fuskarta, wani kyakkyawan murmushi Mustapha ya saki da yayi sanadiyar motsawar zuciyar Shukhura, wani fitinannen kyahu ta gani a tattare da Mustaphan wanda ba za ta iya bayyana muku shi ba saboda tsabar rud'ewa da cikar kyahunsa. Gira d'aya ya d'age mata had'e da fad'in. "Na miki ne? “ Lumshe idanuwanta ta yi don jin bak'on yanayin da ke sauka a ilahirin jikinta, ta d'au tsayin lokaci a haka yayin da shi kuma yake morewa kallonta son ranshi. Hira suka d'an tab'a kad'an, k'ofofin zuciyar Shukhura sun bud'e gaba d'aya suna d'iban sak'onnin da ke samun babban matsuguni a cikinta, da ya tashi tafiya ya dubeta yace. "A taimaka mini a tura mini hotunan da zasu dinga d'ebe mini kewa. “ Ya fad'a ya na me mik'o mata kyakkyawar wayarsa kamar shi, ta fuskanci yadda yake me kyau haka komai nasa yake me kyau. "Aini bana da hoto ko d'aya.“ "Ko a wayar Yayarmu ne a d'an samo mini mana. “ Don a d'an hirar nan da sukai ta ambaci Yayarmu ya kai wajen sau nawa, anan ya gane da wacce take zaune kusa da ita yai tunanin 'yan biyune itace Yayarmun, kuma ya fuskanci akwai soyayya me matuk'ar girma a tsakaninsu. "Yayarmu ba ta da waya ai. “ "Kawai dai rowa za ki mini, tom shi kenan a gaishe mini da su Mamarmu da Yayarmu da kuma k'annenmu. “ "Tom shikenan zasu ji insha Allah, nima a gaisar mini da so Hajiya, da kuma Hajiya Inna.“ Dariya ya yi had'e da fad'in. "Hajiya Inna za ta ji da kyau. “ Tunowa da ya yi darun da ta saka da Hajiya ta sanar mata su Shukhura ba 'yan biyu bane, Hajiya Inna har da kuka don ita har ga Allah ta saka ran samun tattab'a kunnenta 'yan biyu da zasu dinga sanyata farin ciki, sai da Hajiya ta lallab'a ta tace ai ba dole sai 'yan biyu ne ke haifar 'yan biyu ba, sai kiga ma 'yan biyun basu haifa, ita kuwa idan da rabo sai kiga ta haifa mana, Hajiya Inna tace. "To Allah yasa, amma 'yan biyunne suma suna tafiya da gado, shiyasa na fi samun tabbacin da 'yan biyu ce za ta haifa mana 'yan biyu.“ Zaune suke suna fuskantar juna da wani kyakkyawan bafulatani hannuwanta ya rik'o yace. "Yarinyata hak'ik'a ke haske ce a cikin rayuwar TURAKI ke za ki masa Katanga da damuwar da yake ciki a yanzu, za ki zame masa alkhairi, farin ciki, kuma madubin rayuwarsa. Hak'ik'a Turaki ya na cikin matsananciyar damuwa, kuma ina da tabbacin kece kad'ai za ki iya fiddashi daga ciki, kece za ki d'ora murmushin da ya dad'e da barin kan fuskarsa, ina mai kuma tabbatar miki ke haske ce cikin rayuwarsa domin kece kad'ai za ki yaye duhun da ke lullub'e da shi. “ "To ta ya'ya kake ganin zan zame masa haske bayan ban sanshi ba ban san a ina yake ba, ban kuma san a ina zan same sa ba. “ "Nima ban sani ba, amman kuma ina so ki mini alqawari guda d'aya. “ "Wani alqawari ne ka fad'a ina jinka, zan cika maka shi domin ina maka kallo tamkar mahaifina. “ Shafa kanta ya yi had'e da fad'in. "Na yi matuk'ar farin ciki yarinyata, Allah ya yi miki albarka.“ "Aminnn, ina jinka gaya mini alqawarin.“ "Kada ki bud'e k'ofofin zuciyarki ga kowa bare har ki basu muhalli, har sai lokacin da zai bayyana gare ki sai ki bashi gurbi a ciki ki kuma rufeta gaba d'aya, idan kwa ba haka ba akwai wani abu da zai muku Katanga a tsakani. “ "To amma. “ "Ba na so kice komai, tun da kin riga kin amsa mini tun a farko. “ Shiru tayi, ta na son ta sanar da shine ta riga ta yiwa wani wannan alqawarin, gashi kuma ya katseta, yanzu ya za ta yi, meye mafita gareta? "To meye alak'arka da shi, kuma meye sunansa na gaskiya? “ "Kafin na amsa miki tambayar zan sanar da ke ba za ki sake ganina ba daga yau, kuma ansar wannan tambayar da zan baki itace maganarmu ta k'arshe. D'ana ne shi, amman kuma mutuwa tai mana Katanga a tsakani tun shud'ad'd'an zamani, sunansa na gaskiya ALIYU ana kiransa da Aa............ Girgizata Shukhura ta yi had'e da fad'in. "Yayarmu.“ Wanda hakan ya yi sanadiyar farkawarta daga baccin da take wanda tai mafarkin nan a ciki. "Mtsss kin kama kin tashe ni, gashi ban samu ya fad'a mini sunan da ake kiransa da shi ba yadda in ya bayyana gareni zan ganesa, gashi yace daga yau bazan kuma ganinsa ba. “ Ta fad'a ta na me jin haushin yadda Shukhura ta katse mata mafarkinta ba tare da an gaya mata sunan da ake kiransa da shi ba, to kuma da yake ce masa Turaki waye ke kiransa da hakan? Oho ta bawa kanta ansa. "Kiyi hak'uri, Mama ce tace na taso ki ki k'arasa wanke-wanken yankewa na yi a hannuna in omon ya shiga zafi yake mini kuma bakwan ta kusa da kikace a tashe ki, to amman kuma waye kike kiran ba'a gaya miki sunan da ake kiransa da shi ba? “ "Mafarkin da na gaya miki ina yi ne Shukhura, gashi kuma yace daga yau ba zan sake ganinsa ba, bansan ta inda zamu had'u da Turaki ba Shukhura kuma ban san da wata alama zan ganesa ba. “ "Yayarmu na gaya miki fa ki watsi da lamarin mafarkin nan na ki mafarki fa ba gaskiya ba ne. “ "Wani mafarkin gaskiya ne Shukhura, don na ji ance wasu malaman sunce duk mafarkin da za kayi shi da daddare ka sake yinsa bayan sallar asuba gaskiya ne, wannan dalilin ne nake jin nima nawa gaskiya ne, kuma ina jin hakan a jikina.“ "Wai Shukhura Ina Yayar takun take ne.” "Gani nan Mama. “ Nusrat ta fad'a had'e da ficewa daga d'akin Shukhura ta bita da kallo. Washe gari Mustapha ya dawo ya kawowa su Shukhura ita da Nusrar wayoyi sababbi fil a kwalinsu sai walwali suke da shek'i, murna gurin Shukhura da Nusrat ba'a magana yayin da Umma bak'in ciki kamar ya karta, ta sanya Nimha a d'aki tace. "Kin gani ko, sun fara tura ki a gefe tun kan arzik'in ya ratsasu, yanzu in da da kara ai har da ke za'a kawo wayar. “ " Ni ban ji komai ba Umma, nima Saminu yace k'arshen watan nan zai siya mini. “ "Au yanzu yarinyar nan ba ki sallami Saminun nan ba, yanzu ki rasa wanda za ki mak'alewa sai matsiyacin da babu abinda zai iya tsinana mana.“ Turo baki gaba ta yi ta na had'e rai tace. "Wallahi ni Umma shi nake so ba abin hannunsa ba, idan har zai bani soyayya da farin ciki ya gama mini komai, kuma k'arshen satin nan zai turo magabatansa gurin Baba. “ Ta na kawowa nan ta fice daga d'akin don ta san maganar da za ta fito daga bakin Umman ba mai dad'i bace. "Amman ke dai anyi gantalalliyar yarinya, to wallahi tun wuri kije ki sami Babanku ki sanar masa ba kya sonsa don wallahi muddun rai ba za ki auri matsiyacin yaron nan ba, dudu nawa ne albashinsa da zai iya rik'eki, aike wallahi zubin matan manya ne da ke, amman da yake ba ki san ciwon kanki ba kin lik'ewa wanda babu d'igon arzik'i a tattare da shi, banda haka da kin samo mana wanda zamu shiga cikin dukiya mu kwantar da kai a cikinta a kuma daina mana d'agawa da dukiyar da babu tabbas d'in za'a ji dad'inta.“ A haka rayuwa take tafiya har aka shiga watan azumi, soyayyar Shukhura da Mustapha kuwa ta yi k'arfin da ba kwa zato, har an kawo kud'i an saka rana ta na yin candy, Nimha ma Saminu ya kawo kud'inta tare za'a had'asu da Shukhura, babu haukan da Umma ba ta yi ba, Baba kuwa yace ba ta isa ba, ai arzik'i na Allah ne. Nusrat dai har yanzu babu wanda take saurara har ta kaima yanzu in za ta fita nik'af d'inta take mak'alewa a hammata sai taje soro ta d'aura don kar ma a ganta ace ana sonta, sun sha fad'a sosai da Shukhura har tace sai ta gayawa Mama, sai kuma ta kasa fad'a, ita tausayi ma Nusrat d'in take bata gani take kamar da aljani take yin mafarkin nata da take kira gaskiya. Iya da Nimha kuwa sun dinga mata habaici kenan wai Allah ya yi mata nauyin k'afa gashi har za'a aurar da k'annenta biyu ita ko mashin shini ba ta da, ita kuwa ko kad'an hakan ba ya damunta lokacin auran nata ne bai zo ba idan yazo kowa zai sha mamaki. Mama da Baba kuwa Nusrat d'in tausayi take basu, don Baba har rubutu yake yi ya na bata ta sha na taimako ko Allah zai fito mata da nata mijin itama ya had'asu gaba d'aya ya aurar. Yau aka kai azumi na goma, kuma yaune Mustapha ya kawowa Shukhura kayan Shan ruwa, madara ce peak ta ruwa katan uku sai bomvita babban robar uku milo babban gwangwani uku, sai suger k'aramin buhu, k'wai kiret biyar, sai kuma kayan fruit, Iya kuma ya aiko mata da katan d'in maltina da madara, saboda kullum yazo zance har soro take zuwa su gaisa ya d'an bata hasafi, tun Shukhura na jin takaicin hakan da kunya har tazo ta sake gaba d'aya, don lamarin Iya sai du'ai son abun duniyarta har ya fi na daa. sai tsalle take ta na murna, da yazo da daddare tun kafin Shukhura ta fita ta riga ta fita don ta na ankare da hararar da take zabga mata in taje, har k'asa ta tsuguna ta nai masa godiya kamar za ta ari baki. Umma bak'in cikin duniya ya isheta, ta na kallo aka shige da wa'yannan uban kayan d'akin Mama, ita kuwa Saminu kayan fruit kawai ya kawo sai k'wai kiret uku, takaicin duniya duk ya bi ya isheta ta dinga tsine masa albarka, ji take kamar ta rufe Nimha da duka don ta kaici, amman ta ci alwashin daga bikin Nimhan har na Shukhuran babu wanda muddun rai ba za ta zuba ido 'yarta ta fad'a gidan wahala ba 'yar kishiyarta ta tsunduma gidan hutu ai taci baya, za ta yi duk yadda za tai taga wannan auran bai yi ba, ko na Nimha ya yi to tabbas na Shukhura bazai yuyu ba za ta shiga duk inda za ta shiga ba tare da ta nemi taimakon kowa, saboda daga k'arshe wanda ka nemi taimakonsa shine wanda yake k'ok'arin ganin bayanka, tun da ga shinan a fina finan hausa ana yi da kuma littattafan hausa.......... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ *KATANGA* ____________ *SEVINE* San da Baba ya shiga cikin gidan Umma kad'ai ya tadda da Nimha a tsakar gida suna karyawa, tun shigowarsa Umma ke bin akwatin hannunsa da kallo, ganin ya nufi d'akinsa zai ajiye tace. "Babansu wannan akwatin fa? “ Bai magana ba ya shiga ya ajiye kana ya fito ya k'wallawa Mama kira, ta amsa ta fito. "Kin kai mini ruwan wankan?“ "Eh na kai.“ "To bani kwandon da jallabiyata. “ Duk na kai suna can.“ "To sannu Allah ya yi albarka. “ "Amin.“ Tace ta juya ta koma d'aki, har zai shiga band'aki Umma tace. "Babansu magana fa nake kaimin shiru. “ "Ko ma dai ta meye idan kinyi hak'uri za kiji.“ Daga haka yai shigewarsa band'akin. Sai da yai wanka ya shirya, kana ya karya, sannan ya k'wallowa Nusrat kira, da tazo yace. "D'auki wannan akwatin ki kaimin ita gurin Iya. “ Tace."To“ had'e da d'aukar akwatin ta nufi gurin Iya, shi kuma yacewa su Mama da Umma suzo su same shi gurin Iyan ya biyo bayan Nusrat d'in, Iya na tambayarta wannan akwatin fa dai dai lokacin Baba ya shigo yace. "Ni nace ta kawo, ajiye kiyi tafiyarki. “ Ajiyewa ta yi ta juya ta fita, kafin zuwan su Mama Baba har ya farawa Iya bayani da suka zo kuma ya had'u ya d'ora musu bayanin yadda sukai da su Alhj Faruoq, kafin su bud'e akwatin suga meye a cikinta, lesuka ne 'yan ubansu masu matuk'ar kyau da tsada har kala uku, atamfofi ma uku, sai mayafansu da takalma da jaka, Iya murna da farin ciki kamar ta yi me, sai gud'a take. "Kai Amma wannan yarinya akwai goshin arzik'i, duk inda tai arzik'i binta yake da gudu ya na kamota, gashi har yau mune zamu had'a zuri'a da familyn Fanda, ai abin sam barka ne wannan.“ Umma kuwa bak'in ciki kamar ta yi me kawai yak'en dole take don kar ace ta na bak'in ciki, Mama kam shiru tai ba tace komai ba, Babane yacewa Mama. " ga su nan ki ajiyesu kar tai amfani da su, har sai yaron yazo sun fahimci juna, idan ta aminta da shi to, idan ba ta so ba zan mata dole ba, don haka kece mahaifiyarta ke kika san ta yadda za ki biyo mata. “ "Ai ta aminta da shi ma Audu, wace sakaryar ce za ta k'i zuk'ek'en saurayi d'an gidan Fanda, ga kyau ga kud'i ga ilimi ga kuma ladabi da biyayya, ko ni da nake tshohuwa wallahi ya na mugun birge ni, ai ku kwantar da hankalinku aure kamar anyishi an gama. “ Baba baice komai ba ya yi musu sallama ya tafi kasuwa, sai Umma ce tace. "Iya dama kin sanshi ne? “ "Inma ban sanshi ba tun da ya na son jikata aikwa saninsa ya zama dole. “ Shukhura da Nusrat suka d'ago suka kalli mahaifiyarsu bayan sun gama kallon kayan suka had'a baki gurin fad'in. "Mama kayan waye to?“ "Naki ne Shukhura. “ "Nawa kuma Mama?“ Ta fad'a ta na kallon fuskar Nusrat kafin ta mayar dubanta kan Maman, ita kuma tai musu bayani kamar yadda Baba ya yi mata ta d'ora daa. "Ba dole za'a miki ba Shukhura, ba kuma za'a tab'a musu kaya ba har sai kun fahimci juna kin kuma aminta da shi, sunzo sun nemi izini ne sun kuma kawo kayan na gani ina so. Ki tsayar da zuciyarki guri d'aya, kada dukiyarsu ta rud'e ki ko wani abu na k'yale² idan har bai kwanta miki a rai ba, ki same ni ki gaya mini ni kuma zan gayawa Babanku sai a mayar musu da kayansu a basu hak'uri.“ D'aga kai kawai Shukhura ta yi ta na sunkui da kai k'asa, Mama ta mayar da kallonta ga Nusrat tace. "Yayarsu babu wani wanda ya tab'a tunkararki da zancen soyayya ne?“ Kai tsaye tace. "Eh babu Mama. “ Shukhura ce tai saurin d'ago kai ta kalli Nusrat d'in yayin da Nusrat d'in ta galla mata harara, ganin hakan da Mama ta yi ne yasa tace. "Gaya mini Shukhura waye? In ita kunya ta hana ta fad'a. “ "Babu kowa Mamanmu. “ Shukhura ta bata amsa. "To shikenan tun da ba za ku gaya mini ba, idan Babanku ya dawo kwa gaya masa, Allah dai ya had'aku da mazaje na gari.“ Suka amsa da. "Amin." A tare. Da yamma Hajiya Suwaiba tazo gidan su Shukhura, Mama tai mata tarb'a ta mutumci da girmamawa dai² da k'arfinsu, yayin da Hajiya Suwaiba take ta yabawa da karamcinsu, ta kuma samu sirikartata 💯. Kayan kwalliya ta kawo mata tace ita da 'yar uwarta, don Mustafa yace mata ya na jin fa 'yan biyu ne, Inna kuwa daga jin haka har ta fara murnar za'a haifo musu tagwaye. Tun daga kan mayuka na gyaran fata babu abinda babu a ciki, godiya sosai Mama tai mata, ta rakata gurin Iya suka gaisa, Iya yadda kuka san ta gurfana a gabanta tai mata sujjada aikwa da ta tashi tafiya ta ajiye mata then thauthand, murna gurin Iya ba'a magana ta taho filin tsakar gidansu ta na ta rangad'a gud'a ta na shiwa Mama albarka don ta iya haihuwa tunda ta haifo Shukhura jinin arzik'i. Umma na d'aki takaicin duniya ya bi ya isheta, wani malulun bak'in ciki ne ke damunta, yanzu ta na gani su Maimuna zasu fandama cikin daula, don had'a zuri'a da Familyn Fanda kamar ka tako arzik'i ne, haka za'a mashaheta bora a cikin gidan nan da ita da 'yarta, don Shukhura ba kunya ce da ita, idan ta auri jinin Fanda kanta zai k'ara girma ta kuma taka wanda taga dama, tazo ta na d'agawa k'arshe ma komai na gidan ya dawo hannunta, da ace Nusrat ce ta san ba ta da matsala za ta dubeta tamkar mahaifiyarta, Shukhura kuwa babu abinda take hanga cikin idanuwanta banda tsantsar taya mahaifiyarta kishi, idan kwa ta samu wannan power ta riga ta zama sorry a cikin gidan nan daga ita har 'yarta, don haka dole ne ta nemi mafita tun lokaci bai nemi k'ure mata ba. "Wai meyasa kika cewa Mama ba ki da saurayi? Bayan ga Malam Tajo nan kamar zaiyi hauka a kanki kin kuma k'i ki bashi damar da zaizo ya fallasa asirin zuciyarsa. “ "Bazan tab'a bashi damar hakan ba Shukhura. “ "Saboda me? “ "Saboda girman alk'awari. “ "Hmmm Yayarmu kenan, na tambayeki.“ "Tom Allah yasa na sani.“ "Wai Yaya Rj yace yana sonki ne? “ "A'a baice ba, amman na san ya na dawowa zai gaya mini.“ "Baice ya na sonki ba, amman kike wahalar da kanki gurin zaman jiranshi, baki da tabbas d'in soyayyarki a zuciyarsa, bacin haka Aunty Maryam ba za ta tab'a bari ki auresa ba, domin Hidaya take da burin ya aura. Dan Allah Yayarmu kiyi watsi da lamarin Yaa RJ, ki tsayar da zuciyarki guri guda, kina da samarin nan ki basu dama har ki samu gwani a cikinsu, don ni a ganina Yaa RJ b'ata miki lokaci kawai yake yana kuma wasa da hankalinki, tun da shekara uku yace miki zaiyi ya dawo, yanzu a k'aida saura shekara d'aya kenan amman me Hidaya tace, cewa tai saura shekaru biyu ya dawo, ke a tunaninki Baba zai barki har nan da shekaru biyu a cikin gidan nan, ko kuma za ki cigaba da nuna babu wanda ke zuwa yace ya na sonki? Ta yaya kike tunanin zan karb'i lamarin aurena da muhimmanci bayan ke ba kiyi aure ba, har ga Allah ba na son na yi aure na tafi na barki.“ Hannuwan Shukhura Nusrat ta kama ta rik'e da hannu biyu kana tace. "Ni yanzu ba lamarin Yaa RJ ne ke damuna ba, akwai abinda ke damuna, kuma shi yake hanani karb'ar soyayyar kowa. Kada ki damu da lamarin aurena Shukhura, shi aure lokaci ne, kowa da akwai lokacin da Allah ya rubuta mata, babu ruwansa da wannan yaa ce ko k'anwa duk wacce lokacinta ya yi shikenan, haihuwa, aure da mutuwa duk tafiyarsu d'aya ne suna zuwar maka ne a sanda ba kai zato ba ba kai tsammani ba, don haka kada ma ki sake ki saka a ranki don banyi aure ba kema ba za ki ba, kin san Baba ba zai d'auki hakan ba, kar kuma ki amfani da hakan kice Mustapha bai miki ba, za ki cuci kanki ne don ni ba na hango aurena a nan kusa, ina ji a jikina akwai wasu abubuwa da zasu faru, amman bansan meye su ba.“ "Wani lamari ne ya hana ki karb'ar soyayyar kowa a zuciyarki. “ Wayar Mama ce tai k'ara alamun an kira Nusrat tace. "Kinga har ya k'araso ba ki gama shiryawa ba, maza kiyi² ki k'arasa shirin in kin dawo ma k'arasa maganar, kuma ina fatan k'anin nan nawa ya dagargazo miki zuciyarki kafin ki dawo, kizo kiy tai mini hirarsa ina saurare don naga alamun hakan ma tun a waya. “ Murmushi kawai Shukhura ta yi, don har ga Allah muryar Mustapha ta tafi da ita, sakamakon wayar da suka dunga yi, Maryam k'anwarsa ya turo ta anshi number Mama shine yake kiranta suna gaisawa, burinta kawai ta ganshi a fili don ta na fatan ganinsa ya fi jinsa shikwa ya dinga ja mata aji har sai yau da aka kusa cin sati suna wayar sannan yace mata zai zo. Shi d'inne kuwa yazo, don haka a gaggauce ta k'arasa shiryawa ta fita, Nusrat na ta zolayarta, don sun zamo tamkar wasu k'awaye aminai, don dukansu babu wacce za ta daki k'irji tace ta na da k'awa aminiya sai dai k'awar da za'a gaisa a wuce, sune k'awayen kansu, kuma hakan baisa Shukhura ta raina Nusrat d'in ba........ 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ *KATANGA* ____________ *NINE* Shukhura ta rasa yadda za ta yi da Iya, don abin nata kullum k'ara gaba yake, don idan taje su gaisa bai bata ko ficika ba samun guri take ta zauna, ranar da tai mata haka kuwa mantawa ya yi ya fito babu kud'i a jikinsa, ba ta tashi ba har sai da yace. "Iya a mini afuwa ban fito da kud'i ba yau, amma gobe insha Allah za kiga sak'o. “ Takaicin duniya ya ishi Shukhura ji tayi kamar ta nitse a gurin da take a zaune don tsabar kunya yayin da Iya kuwa ta wangale baki tace. "Tom shi kenan jikana babu komi, da yau da gobe duk d'ayane.“ Kunji sai kace ajiya ta bashi, wani d'an iskan kallo Shukhura ta bita da shi a ranta kuwa tace. 'Zanyi maganinki wallahi, yadda ko shi kansa Fandan aka ce gashi a soro ba za ki fito ba, ke ko govnor garinnan El Rufa'i akace gashi yazo zance gurina ba za kiyi gigin fitowa ba.' Fuska taje ta siyo me mugun abun tsoro, sai dagurintaa ruwa bayan an idar da sallar asham, dama lokacin ne dai² zuwansa, tun yamma da tai wanka ta saka riga da wando dama, don haka sai ta d'auko hijabinta har k'asa ta sanya, Mama dama ta na d'akin Baba don haka sai ta cewa Nusrat. "Yayarmu bari na fita soro.“ Tace mata. "Tom. “ Iya na ganin giftawar Shukhura ta fasa tayar da sallar da za tai, don yau ta makara ba ta samu bin jam'in asham ba wani bacci ne ya kwasheta ta na zaune. Murmushi ta yi ta ziro silifas d'inta ta biyo bayan Shukhura ta na k'iyasta yau sallamar da za'ai mata me matuk'ar nauyi ce, don ta na bin bashin wancen zuwan. Shukhura na fita soro ta cire hijabinta ta sak'ala shi jikin k'ofa sannan tai saurin d'aura fuskar ta juya baya. Bakin Iya ya k'asa rufuwa har ta doso soron, dama soron gidan gashi da mugun duhun tsiya, ko hucewa za kai sai ka haska saboda gudun masu lab'ewa, zance ma in zasui sai sun kunna fitila. "A'a yau kuma ba ku kunna fitilar ba ne? “ Cewar Iya ta na tsayawa a dai-dai tsakiyar soron gidan don ba ta hangar komai kar taje ta taka wani daga cikinsu shiyasa tai maganar don su kunna fitila, wani irin dank'a Shukhura taiwa kanta ta had'a fuskokinsu guri d'aya ta sauya magana zuwa me abun tsoro. "Ke wata iriyar nanatacciyar tshowa ce, mu ba ma son mutum me son abun Duniya, daga yau idan Mustapha ya k'ara zuwa kika fito sai mun karya tsila tsilan k'afafuwan nan naki masu kama da Babyn roba, kuma mu shanyar miki da b'arin jikinki gaba d'aya. “ Kar kar kar kawai jikin Iya ke yi uwa mazari ihun da taso ta yi ma ta k'asa wani mugun tsoro ne ya shigeta wanda ba ta tab'a jin irinsa ba. Allahumma inni auzu bika minal kubsi wal kaba isi, kawai take karantawa a ranta kafin Shukhura ta buga mata razananniyar tsawa had'e da fad'in. "B'ace mana da gani tun kafin mu mayar miki da k'afafuwanki a sama kanki a k'asa.“ Fitsari ne zirrrr ya fara bin k'afafuwan Iya kafin ta juya a guje sai ji kake k'um ta bugu da bango ta dawo baya, wata wahalalliyar k'ara ta saki, ta na so ta rarrafa ta bar soron ma ta k'asa anan ta zube a sume tsabar tsoro da rikirkicewa. Umma ce ta jiyo k'arar, don haka ta nufo soro da 'yar fitilarta, ta na haskawa taga Iya a sheme cikin fitsari. "Subhanallahi.“ Shine abinda tace kafin ta juya taje ta kirawo su Baba, ruwa aka watsa mata ta farka a mugun tsorace ganin su Baba kawai ta fashe da mugun kuka, Baba na tambayarta abinda ya faru, kawai cewa take su kamata su kai ta gurinta. Babu yadda Baba baiyi da Iya ba akan ta fad'i abinda ya faru da ita tak'i, k'arshe tace ina ruwansa ya rabu da ita don dole ya k'yaleta Mama ta dubi Nusrat tace. "Kika ce Shukhura na soro, ya kuma ban ganta ba?“ "To nidai Mama haka na ji tace mini, to ina kyauta zaton ban jita dai² ba tun da banga ta d'auki tabarma ba ma.“ Ta na rufe bakinta Shukhura na sallama Nusrat tace. "Yauwa ga ma ta nan.“ Kafin su amsa mata sallamar. "Ina kika je? “ Shine tambayar da Mama ta jefeta da ita, sosa kai tai kafin tace. "Mustapha ne ya kirani gashi a k'ofar gidanmu na fito na anshi sak'o, kuma da na fito ban ganshi ba ina jin zolayata yake, shine muka had'u da 'yar ajinmu muka tsaya muna d'an tattaunawa. “ "Ya yi miki kyau." Mama tace mata, Nusrat kuwa ta kafe ta da idanuwa, ita ta san dalilin kallon da take mata akan abinda ya samu Iya ne ta na zargin Shukhuran ce tai mata wani abu, murmushi kawai Shukhura ta yi, don ta san in ta ritsa ta dole ta gaya mata gaskiya. Tun daga wannan ranar Iya ba ta k'ara gigin fita in Mustapha yazo ba, saboda ita kad'ai ta san azabar da ta sha na jinyar goshinta, shi kuwa da yaga kwana biyu ba ta fitowa shine ya cewa Shukhura zai shiga su gaisa da Iya taje ta gayo mata, ko da Shukhura taje kuwa, iya tace ba ta san zance ba, ta yiwa Allah ta yiwa Annabinsa tace masa yasha zamansa ta yafe duniya da lahira, Shukhura kuwa tace ai kuwa sai ya zo ta fita ta na dariya Iya ta banko k'ofarta ta saka sakata tace sai dai yazo ya gaisar da k'ofa alk'ur'an. Kayan toshi ma da aka kawowa Shukhura k'arara Umma ta nuna bak'in cikinta a gurin, duk da Saminu ma ya yi dai² k'ok'arinsa amman ta raina ta na ta tsine masa albarka, ta na kiransa me kantar talauci, azumi kawai take jira ya k'are ayi sallah ta dugunzuma neman mafita, cikin k'udurar Ubangiji akai sallah lafiya aka gama lafiya, aikuwa ta shiga can cikin k'auyen zariya acan ta samo wani malami, ya shaida mata kud'in aikinta dubu ashirin idan har ta kawo dubu ashirin d'innan to tabbas wannan aure bazai tabbata ba, jiki na rawa ta dawo gida ta sayar da kayan gadonta gaba d'aya ta koma ta kai masa yace to yanzu ta koma taje ta kawo masa k'asar da Mustapha ya taka, idan ta kawota to tabbas da kansa zai zo yace ya fasa wannan aure, shi kuma Saminu za mu juyar masa da ra'ayi da kansa zaice ya fasa auran Nimha, kinga daga nan sai mu juyo da hankalin Mustapha kan Nimha. Farin ciki sosai Umma tai da jin jawabin Malamin, aikuwa ranar da Mustapha yazo ta k'asa ta tsare ta na jiran shigowar Shukhura ta yi sauri ta fice ta d'ebo k'asar da Mustapha zai taka, aikuwa ta na ganin shigowar Shukhuran ta yi saurin ficewa ta 'yebo washe gari taje ta kaiwa malamin aikuwa yace ta na kwance za ta ji kyakkyawan labari... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #Team KTG #N.W.A [10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *KTG* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ ____________ *TEN* KWANCI TASHI Gurin Ubangiji ba wuya, su Shukhura har sun yi candy, sati d'aya da yin candynsu aka kawo lefen su. Akwatina 6 haka Saminu yaiwa Nimha, kuma ya yi iya k'arfinsa kayanta babu kushe ko d'aya, Shukhura kuwa akwatina goma sha biyu dank'are da kaya na alfarma, sark'ok'in daham kuwa zasu kai 6 a ciki, nan da nan hankalin Umma ya k'ara tashi, ta fuskanci wannan malamin kawai kud'inta yake ci dole ta canja shik'a. Wani k'ungurmun boka ta kuma samowa shi ya sanar mata. "Duk wanda yace miki wannan aure bazai tabbata ba to tabbas yai miki k'arya, kud'inki kawai yake ci, wannan aure muk'addari ne daga Ubangiji kuma babu makawa sai ya faru, don haka kije ki rungumi k'addarar da tazo miki da hannu bibbiyu.“ "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu babu wata mafita? “ " Babu wata mafita indai akan hana auran nan ne, sai dai wani da ban kuma, don wannan ba makawa sai ya tabbata. “ Shiru Umma tai hankalinta in yai dubu ya tashi, yanzu dole ta koma ta d'ebi cin kashi gurin kishiyarta, haka za ta zauna ta na kallon Shukhura na d'agawa da fariya ta na auren me kud'i, komai ta yayibo ta kaiwa uwarta ta na zaune kamar jaka, 'yarta kuwa sai dai ta yayibo kantar talaucinsu ta juye mata, ina bazai yuyu ba da sake, to kuma ta ya ya? Koma ta yaya ne ta bawa zuciyarta amsa daga bisani ta kalli bokon za tai magana ya dakatar da ita da hannu d'aya. "Kud'in aikinki dubu d'ari biyu, za ki kawo mini dubu hamsin da bak'ak'en kaji guda shida, idan aiki ya tabbata sai ki ciko dubu d'ari da hamsin, amman idan har kina so aikin ya kama jikinta sosai sai idan babu ran mahaifiyarta. “ 'Ta yadda da ingancin aikin bokan nan, tun da har ya san abinda ke zuciyarta, to amman kuma ta ya ya mahaifiyarta za ta rasu bayan ranta ba a hannunsu yake ba?.' Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi. "Zan tura mata ciwon da zaiyi sanadiyar mutuwarta, daga nan ba ki da sauran Katanga tsakaninki da Shukhura, ke za ta dingaiwa kallon mahaifiyarta, amman kafin nan sai an fara raba tsakaninsu da me gidanku, a kuma rufe bakinsa, babu case ga wannan tsohuwar matar idan har kina sakar mata abin Duniya. Su kuma 'yan uwanta za'a raba soyayyar da ke tsakaninsu, saboda ta na matuk'ar son su fiye da son da takewa kanta.“ Farin ciki ne ya dabaibaye zuciyar Umma, ta dinga sharara masa godiya, suka rabu akan za ta dawo ta kawo masa abinda ya Buk'ata.“ Akwatinan Nimha ta kwashe da wasu kaya daga ciki taje ta sayar ta kai masa kud'in da kajin da ya buk'ata, ya bata wani ku'ullikan magani, d'aya ta zuba a cikin abincin da Mama za ta ci, d'aya ta zuba cikin ruwan turaren da za'aiwa Shukhura kamu da shi, d'aya cikin abincin da Baba zai ci, sai laya da za ta saka a bayan gadon Shukhuran, babu wanda zai lura da layar sai ita da ta saka da kanta, sauran abubuwan kuma shi zai ji da komai. Shirye²n biki su Mama suke hankali kwance, don yanzu saura sati guda a fara shagul gulan biki, duk da Mama ta fara fuskantar wasu sauye² daga Baba hakan baisa ta tayar da hankalinta ba, da Allah ta dogara shi kuma taci gaba da mik'awa buk'atunta, don a 'yan kwanakin nan wasu mugayen mafarkai take mara dad'in ji ko kad'an, kawai ta na danne damuwarta ne saboda yaranta, don wani abu da Shukhura kuma ta tsira shine, duk dare sai ta sanyata a gaba ta na kuka ta na rok'onta akan a fasa wannan bikin, ta na jin kamar wani babban al'amari zai tunkaro su idan har akayi wannan auran, sai dai ta lallasheta da nasihohi masu ratsa jiki, don babu damar tunkarar Baba da wannan maganar, bare ya dube su, don ita kanta Mama yanzu ba ta buk'atar auran, to Baban gaba d'aya yanzu ya sauya musu da Nusrat kad'ai yake zama ya yi hira, hakan ya kuma tayar da hankalinsu gaba d'aya amman a haka suka daure suka cigaba da shirye shiryen da ba'a rasa ba. Ranar juma'a akai kamu anan cikin gidan, Iya ce ta kama duka amaren guda biyu, yayin da taiwa Shukhura amfani da turaren Nimha, taiwa Nimha da na Shukhura wannan kuma duk tsarin Umma ne. Ranar juma'ar da daddare akai Dinner d'in gidan su Mustapha, da Baba yace Shukhura ba za ta ba, da k'yar Nusrat ta lallab'a shi ya barsu suka je, kuma diner d'in ta k'ayatar da dukkan wanda ya halarci gurin. Washe gari asabar sukayi walima anan cikin gidan don Baba ya hana DJ kuma walimar ta yi gwanin ban sha'awa. Washe gari lahadi kuma aka d'aura auran. Safiya Abdullahi Ahmad da angonta Mustapha Faruoq Fanda Zainab Abdullahi Ahmad da angon ta. Saminu Yusha'u Hamza. Tun da aka d'aura auran Shukhura da Nusrat ke kuka, gaba d'ayansu suna jin wani miki a zuciyarsu ya na musu ciwo amma ba su san dalili ba, Mama ce tai k'ok'arin rarrashinsu duk da itama ba ta jin dad'in jikinta, amman saboda mutanen da ke shigowa ana kallonsu shiyasa ta rarrashesu, su d'aki falle d'aya bare tace su shiga ciki suyi kukan nasu babu wanda ya gansu, ta san dai kukan rabuwa suke, wannan kuka kuwa dole su yishi, sun taso tamkar 'yan biyun da suka zauna a mahaifa d'aya, suna matuk'ar son junansu ko kyauta za'a yi musu sun fi son ayi musu a tare, idan kwa aka bawa d'aya to tare zasui amfani da shi, musamman Shukhura da ki mata kyauta gara kiyiwa Nusrat za ta fi matuk'ar farin ciki, hakan da Mustapha ya gani ne yasa komai zai yiwa Shukhura sai ya yi musu tare da Nusrat , wataran ma Nusrat d'in kad'ai yakewa kyauta don kawai yaga farin cikin sahibarsa. K'arfe biyar dai² aka kawo motocin d'aukar amarya Shukhura, ita Nimha sai bayan sallar Isha saboda babu nisa, a lokacin kukan Nusrat da Shukhura ya k'ara k'arfi suka rungume juna suna kuka kamar ba sa rabu ba, Iya ce tazo ta janye Shukhura ta na sababi. "Meye kuma na kuka bayan Allah ya 'yanta ki ya kaiki gidan daula, ki daina biyewa Nusrat bak'in ciki take miki don ita Allah ya yota me nauyin k'afar tsiya har yau ko mashin shini babu. “ Shukhura kukanta kawai take, Iya ta dank'ata hannun Aunty Maryam suka shiga da ita d'akin Baba, yayin da Mama ta rungume Nusrat ta na jin itama kamar ta fashe da kukan, takai dubanta ga Yusra da take ta aikin matse k'walla, da hannu ta yafito ta itama tazo gareta ta rungumesu ta na jin wani iri a zuciyarta. Nasihu masu ratsa jiki Baba ya yi mata, ban da kuka babu abinda take ta cikin mayafinta daga k'arshe Baba ya sanya mata albarka aka fito da ita, ganin ana k'ok'arin fita da ita yasa ta fisge hannunta ta ruga d'akinsu da gudu, jikin Mama ta fad'a ta ruk'unk'umeta ta na kuka me ban tausayi, ta na jin kamar shi kenan daga yanzu sun rabu rabuwa ta har abada, shafa kanta Mama ta yi, don ta kusa sanyata zub da k'walla kawai ta na jajircewa ne. "Allah ya yi miki albarka Shukhura, kije kiyi hak'uri ki kuma rik'e gaskiya a duk in da kike. “ "Mama ki yafe mini.“ "Babu abinda kika tab'a yi mini Mamana, ko da kinyi mini nan gaba na yafe miki Shukhura Duniya da lahira, fatana ki rik'e 'yan uwanki da daraja, kada ki bada damar da za'a rusa ginanniyar katangar k'aunar da na gino a tsakaninku tun kuna yara, idan kikai mini haka kin biyani Duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka baki d'ayanku, Amin, muje maza ana jiranki. ” Ta rik'o hannunta had'e da na Nusrat, don Yusra tun d'azu ta fice k'ilama har ta samu mota, a hannun Aunty Maryam Mama ta kuma dank'a ta had'e da fad'in. "Allah yasa ki shiga a sa'a, insha Allah mutuwa ce za ta fito dake daga wannan gida cikin salama da aminci, Allah kuma ya baku zaman lafiya na har abada amin, Yayarsu kije ki raka 'yar uwarki d'akinta. “ Daga haka ta saki hannun Nusrat d'in ta shige d'aki, daga jin k'arshen maganarta ka san kuka take. Sai da aka kai Shukhura gurin Hajiya Suwaiba da gurin Inna kana aka huce da ita sashenta dake gefen gidan. Sashen Shukhura gaskiya ya had'u iya had'uwa, komai walwali yake da k'yalli, bed room d'inta ma ciki da falo ne, anan aka yi amfani da kayan da Baba ya siya mata, don cewa sukai ba sai an mata komai ba, Baba yace a barshi dai ya siyawa 'yarsa mutumci, ko ba komai itama za tayi alfahari da haka, kamar yadda ko wace amarya ke yi. Kayan da Baba ya yi musu suma ba laifi sun yi kyau iya kyau. Kowa ya watse daga Shukhura sai Hidaya da suke jiran angwaye su zo suma su kama gabansu, tara dai² Mustapha ya kira Shukhura yace gasu a k'ofar gida zasu shigo don haka sai suka k'ara d'an kimkimtsawa suka fito da ita babban falo suka zauna, abokan nasa biyune sai shi cikon na uku, addu'oi aka yi akan Allah ya basu zaman lafiya kana abokan sukai musu sallama suka fita yabi bayansu don ya yi musu rakiya, su Nusrat ma suka tashi zasu tafi, rik'o hannunta Shukhura ta yi gam tace. "Dan Allah Yayarmu kar ki tafi ki barni.“ Ta fad'a jikinta na rawa, hawaye ne ya zirarowa Shukhura haka zalika Nusrat d'inma suka rungume juna suna kuka, karo na farko kenan da zasu nesanta da juna tun tasowarsu, gurin kwanciyarsu d'aya, filon da suke d'ora kai guda d'aya a haka zasui bacci Shukhura ta rungumo Nusrat ta baya, ta gaba kuma Yusra ta rungumeta, gashi yau zasu kwana ba tare da Shukhuran ba, aure kenan me kawoka wata sabuwar bigiren rayuwa. "Kar ki tafi ki barni, ba na son ki barni, ki zauna tare da ni kinji Yayarmu don Allah.“ "Ai muna tare Shukhura, ba wai mun rabu kenan ba, gobe ma insha Allahu zamu zo, ke dai ki rik'e nasihohin da akai miki, azkhar d'in nan na safe da yamma kada ki sake ki wasa haka zalika nafil fili ma. “ Daga haka ta zare jikinta daga nata ta bi bayan Hidaya saboda tun d'azu Mustapha yace su fito abokansa su sauke su a gida, ledar kaza da youghort Mustapha ya bawa Nusrat ta yi godiya ta shiga motar suka tafi shi kuma ya juya cikin gidan. Ya sha rikici sosai da lallami ya lallamata har sukai sallah suka mika godiyar su ga Ubangiji, daga bisani suka d'an tab'a kazar amarcin don dukkaninsu basu saki jiki sun ci ba, sun d'an jima a zaune, ta na kwance a jikinsa ya kanainayeta kana sukai shirin bacci suka kwanta, Mustapha ya hankad'o ni daga d'akin yace mini. "Asuba ta gari kema kije ki huta. “ Don haka na tafi hutawa sai kuma gobe in kun jini...... 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #N.W.A #Team KTG #Sonso fisabilillah [10/8, 3:43 PM] Binta Lawan: *KTG* Wattpad@Rashuna https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_ ____________ *ELEVEN* (ZANEN K'ADDARA) A wannan dare su Nusrat basui bacci ba, zazzab'i ne me zafin gaske ya rufe Mama da kuma matsanancin ciwon kai, wanda bacci ya k'auracewa idanuwanta, haka zalika ma Nusrat ba ta iya rintsawa ba ko kad'an har garin Allah ya waye. Fitowa ta yi ta nufi d'akin Baba don ta sanar da shi sai taji muryar Umma tace. "Nusrat.“ Juyowa ta yi ta na kallonta don ba magana ce ke had'asu ba, face gaisuwa idan Nusrat d'in ta gaisheta. "Cewa na yi Shukhura kuwa ta kiraku? Kinga ni har ta kirawo ta gaisheni." "Ai tun da nai sallar asuba mukai waya da ita. “ Nusrat ta ba ta amsa, don yanzu ba lokacin da za ta tsaya yin tunani akan maganar ba ne, d'akin Baba tai shigewarta, ya na kishin gid'e bacci har zai fara fusgarsa ya ji alamun shigowar mutum, a hankula ya sauke idanuwansa akan fuskar Nusrat yace. " 'Yar baiwa lafiya? “ "Baba, Mama ce ba ta da lafiya tun cikin dare. “ "To sai akai ya ya kuma. “ Tsura masa ido Nusrat tai, kamar ba Baban nan nasu ba, mai k'aunar mahaifiyarsu, ta hango lokacin da tai wata rashin lafiya yadda duk ya firgice ya fita daga hayyacinsa, ya zamo tamkar shine mara lafiyar. Wani yahu me tauri ta had'iye tace. "Dama chamise zamu je. “ "To sai kun dawo don ni ficika ba na magani. “ Ba tace komai ba ta juya ta bar d'akin, dama ba kud'insa suke buk'ata ba, kawai dai ta gaya masa ne a matsayinsa na me jagorantarsu gaba d'ayansu. Umma kuwa bak'in ciki ne yai mugun kama ta da taji wai Shukhura sun yi waya da Nusrat, a yadda bokanta ya sanar mata idan har Shukhura ta kwana a kan gadon nan to sunyi rabuwa ta har abada ita da 'yan uwanta, tsakaninsu kuwa sai dai kallo, ita kuwa Mama na mutuwa, to tabbas ita za ta zamo mahaifiyar Shukhura kuma babu wanda ya isa yai magana akan hakan, dad'inta d'aya ne da ta fuskanci Mama ba ta da lafiya, tsakanin Shukhura da Nusrat kuma za ta zuba ido ta gani. Sun ci sa'a me chamise d'in ya fito, ya yi mata allurar zazzab'i ya bata kuma magun guna, kud'i ya kama 1500 Nusrat ta bashi 2000 ya basu cangin 500 suka kamo hanya suka taho gida. To Alhmdlillh sai jikin nata ya d'anyi sauk'i kad'an, har Nusrat ta had'a mata shayi me kauri ta sha, ganin jikin Maman ya yi sauk'i sai a sannan ta yi tunanin Shukhura har yanzu ba ta kirasu ba, amman gashi ta kira Umma sun gaisa, ta na cikin wannan tunanin sai ga Hidaya ta shigo tace mata tafiya zasuyi, amman zasu fara biyawa gidan Nimha da Shukhura in da sak'on da za'a kaiwa Shukhura a bada, kafin Nusrat ta mik'e ta bawa Hidaya sak'on sai wayar Hidayan ta yi k'ara sai Hidayan cewa ta yi. "Kinga ma Shukhuran na kirana bari muji meye to. “ Ba ta jira me Nusrat d'in za tace ba ta d'aga wayar, ta can b'angaren Shukhura tace. "Hello Hidaya kice a had'o mini duka akwatinana ku taho mini da shi.“ "To, shi kenan za'a taho da su, ga Nusrat za tai miki magana. “ Hidaya ta fad'a don ganin kallon da Nusrat d'in take mata, alamu ne na ta na son magana da 'yar uwar ta ta, k'ittt kike ji Shukhura ta kashe wayarta mamaki gaba d'aya ya kama su, a haka Nusrat ta shiga had'awa Shukhura duka akwatinanta da abubuwan da ba'a rasa ba, suka samo yara duk suka fita da su aka zuba a mota, kana sukai sallama da su Hidayan Nusrat tace. "Ku gaishe mini da Shukhuran ku gaya mata Mama ce ba taji dad'i ba." A tunanin Nusrat idan aka cewa Shukhura Mama ba taji dad'i ba za ta kira waya, in ma fishi take da ita ko tai mata wani laifin da ba ta sani ba ai ta kira layin Maman ta ji, amman har dare Shukhuran ba ta kira ba, ganin yadda duk Nusrat d'in ta bi ta damu yasa Mama tace. "Bani wayata na kirata. “ Saboda tun d'azu Mama tace ta kirata tak'i, saboda ta na ganin kamar ta na da dalilin da yasa tak'i nemansu gara su d'an d'aga mata k'afa su gani. “ Ringin d'aya Shukhuran ta d'aga da murnarta tace. "Hello Ma.......“ Cak taji maganarta ta tsaya ta kasa furta Maman da take buk'atar fad'a, Mama ji tayi gabanta ya yanke ya fad'i a hankula ta furta. "Innalillahi wainna ilaihir raji'un.“ Kafin taji saukar kukan Shukhura a kunnenta. "Shukhura lafiyarki kuwa?“ Cikin kuka tace. "Nima ban san me ke damuna ba, daku na kwanta a raina da ku kuma na tashi, tun da mukai sallar asuba nake son kiran wayarku amman na k'asa, sai na ji ana rad'a mini a kunnena wai ke ba mahaifiyata bace, Umma ce mahaifiyata ko kuma ace su Yayarmu ba 'yan uwana bane Nimha ce kad'ai 'yar uwata, na san Yayarmu ta damu sosai amman wallahi ko muryarta ba na son jin, ina cikin damuwa zuciyata ta na mini zafi, da na san haka auren zai zo mini da babu abinda zai sakani yinshi. “ Ta na kawowa nan ta fashe da wani matsanancin kuka, Mama kuwa Innalillahi kawai take ambata a zuciyarta, yayin da Nusrat duk ta na jin abubuwan da Shukhuran ta fad'a, had'a kanta tai da guiwa ta fashe da kuka me ciwo, 'yar uwarta da take sonta fiye da son da takewa kanta yau itace ta furta ba ta son jin muryarta, me yake shirin tunkaro rayuwarsu ne, waye me buk'atar rusa Katangar farin cikin da suka dad'e da ginata a zuciyoyinsu? Majina Shukhura ta jaa taci gaba da cewa. "Mama kicewa Umma me mukai mata take son rusa rayuwarmu gaba d'aya, in wani abu mukai mata sai mu nemi yafiyarta, na san dai itace ta shiga tsakaninmu saboda da sassafe ita na fara kira na gaisar, bayan ko anan cikin gidan ba kullum nake gaisheta ba. “ Numfasawa Mama tayi tace. "Umma ba ta isa ta miki komai ba Shukhura, ki saka hakan a ranki, babu wani abu wanda yake faruwa a rayuwa face dole sai da wani zare da ya haddasa hakan, kuma bama iya ganin zaren, shi wannan zaren shi ake kira ZANEN K'ADDARA. Dan haka kada ki kuma danganta abinda ya same ki da wani d'an adam, duk abinda ya sameki to ki tabbata yana cikin k'addararki, ki kuma kai kukanki ga Ubangiji domin shi kad'aine zai baki ikon cinye jarabawar da yai miki har ya yaye miki abinda ke damunki, yanzu kije kiyo auwala ki d'auki qur'ani ki karanta za kiji sanyi a ranki, maza jeki, Allah yayi miki albarka, ki kuma daina wannan kukan.“ Muryarta can k'asa tace. "Tom“ Mama ta kashe wayar ta lumshe idonta kana ta bud'esu akan Nusrat da ke gurshek'an kuka...... Jiya ba ku jini ba, chargi ne ban samu ba wutarmu ta lalace, gobe da jibi ba lallai ne ku jini ba saboda muna hidimar biki. 300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i. 0567838462 NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta. 09037093702 In katin wayane 400 zaku biya. Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin. #N.W.A #Team KTG #Son so fisabilillah