*TSAKA MAI WUYA.* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *01* *SHIMFID'A* *KADUNA_Zaria* _Samaru_ Dogon gida. Tun wayewar garin ranar Asabar nake cikin Fargaba da tsoro, Wani irin sanyin jiki da faduwar gaba. gabad'aya gabbaina sunyi sanyi, gabana kuma bai daina tsananta fadi ba. Duk lokacin da na tuna halin tsaka mai wuyar da nake ciki. Fargaba na da tsoro sun karu ne tunda naga sha biyu na rana ta gota, sai na kasa zama duk yadda naso natsuwa ya samu muhalli a jikina da zuciyata na kasa. Sai faman Safa da marwa nake yi a tsakiyar Dakin Maman Boy, tunda a dakinta na shirya cikin Riga da zani na Atamfata English mai kalan Duhuwa. Sabuwa ce domin duka duka bai fi sau uku na taba sakata ba, kuma sau d'aya na tab'a wanketa. Tana daga cikin kayan aure na da Abubukar, ban yi kwalliya ba saboda ba na cikin wannan sukunin, Daga ni sai kanwata Habiba ne a Dakin da Safe itama d'azu shigowar Ramatu ta jata sun fita tare. Dakin mu nake son na leka ammh kuma Kafafuwana sun yi sanyin da sun kasa daukata zuwa Tsakar gidan namu. Tsorona na raguwa ne in na tuna da yau Amma ta tashi jikinta da Sauki har tayi wanka ta saka kayanta masu kyau, tunda yan gidan su marigayi Alhaji Mammandi limancin kona sun zo, gidan da aka haifi mahaifin Babanmu kenan. Duk da ina da tabbacin suma din ba domin taya Amma murna suka zo ba, sun zo ganin yadda za'a kare ne kamar yadda Hasashen su ya saba gaya musu a kaina. Ina jin Hayaniyar su Adda Fati a tsakar gida duk da ba wani taro zasu yi ba, ammh dai suna Dafa abinci saboda makota da yan'uwan da za su zo ko ba da yawa ba. Kamar ma sun gama ne saboda naji ana mganan matan gidan duk su kawo kwanukan su, Hassana ta zo ta Dauki kwanon Maman boy. Sanda ta shigo sai da ta ce min"Sannu Adda HASIYA.." Sai da ta fice ne na dawo hayyacina domin nayi zurfin acikin Tunanin da nake yi, kowani Dakika na Bugawar agogon dake kafe a dakin Maman Boy tare ya ke da Bugawar zuciyata. Gif gif! Gabadaya a tsorace nake na kasa kuma addu'a a fili nake fad'in"Ya Allah! Ya Allah!." Daganan sai bakina ya yi nauyin da nake gaza fad'in komai. To me zan ce? Ko me zan roka? In dai rayuwar da nake ciki ita ake Kira TSAKA MAI WUYA to zan iya cewa ni Hasiya tun haihuwata nake cikin Rayuwar Tsaka mai wuya. A kan idanuwana Karfe d'aya ta Buga, daidai da wani irin fad'uwa da gabana ya yi Ras!. Kafafuwana suka fara rawa, Tsoro nake ji ina ji ajikina kamar abubuwan dake faruwa a kaina ba Canfi ba ne, sannan ba Kuskure ba ne. Da gaske ni ina da Kashin da Rab'ata kada'i kan iya Sanadin Ruguza rayuwaka da Dama. Hannanuna guda d'aya na saka na Dafe kirjina da nake jin yana tasowa kamar zuciyata zata fito. Wlh ina jin Tsoro, tsoro nake ji tsoron da ya bayyana har a cikin jikina zuwa saman Fuskata. Ramatu ce ta fad'o dakin da gudunta ko Nauyin cikin jikinta da ya tsufa bata ji, Gud'a ta daidaici kunnina na Dama ta Rangad'amin da ya yi sanadiyar da naji ni kamar na suma ne, wani irin Shuuu! Naji na wucewa na cikin kunnuwana, ban dawo cikin Hayyacina ba naji muryanta cikin Zak'i daman Ramatu akwai zak'in murya tana Fadin"Ta zama..ta zama matar Salisu" Kin zama..kin zama Amaryan Salisu. An daura auran ki yanzu Hasiya, Salihi ya shigo da gudu yana fad'a'" Kalamanta sun yi daidai da lokacin da sanyayyin kafafuwana su ka gazamin sai na bi umarninsu wajen zubewa a kasan ledan Dakin Maman Boy da karfi, ina haki kamar wacce tayi Gudun Tsere. Hawaye na ji sun cika kwarmin idanuwana, na dago ina kallon Ramatu da ke kallona ina jin hayaniyar fad'in an daura aure daga matan dake tsakar gidanmu, Ramatu nake kallo kamar ban ji daidai ba nace"An daura? Da gaske Ramatu an Daura aure na da Salisu? Na fad'a cikin Sigar kokwanto da Tambaya. Mirmishi ta sakarmin mai cike da kaunar da take yi min tun ranar da ta fara ganina. Gefena ta zauna itama ko Cikin jikinta bai damunta, cikin son kwantar min da Hankali ta Dafa Kafad'ata tana fad'in"Da gaske an Daura auran ki da Salisu. Kuma in sha Allahu wannan auren mutuwa ce zata rabashi Hasiya" Sai ta d'an dakata tana lura da kuma nazarina ganin na Runtse idanuwana hawaye suka zubomin sharr! Kamar an Bud'e famfo. Da irin baiwar da Allah ya bata na Tattausan lafazi ta kira sunana cikin Zakin muryanta "Hasiya..Hasiya D'ako ki kalleni don Allah" A raunane na D'ago ina kallonta kuka na son kwacemin. Da sauri ta saka hannunta guda d'aya tana sharemin Hawaye da suka bata Farar Fuskata. Cikin irin kalaman ta Tausasawa ta cigaba da Fad'in"To kuma me meye na kuka? In sha Allahu wannan auren sai ya shafe mganganun mutane a kanki Hasiya sai yasa sun yi nadaman kiran ki da mabambamta sunaye" Kalamanta suka sake Raunana ni. Cikin karfin Hali na Bud'e bakina nace"Ramatu anya gaskiya kike fad'amin? Ta ina bak'in bakin Fentin da tun haihuwata yake bibiyata sannan kuma kice zai gogu a lokaci d'aya? Na fara girgiza kaina Lokaci d'aya Hawaye suna zubomin nace"Ki na dai Fad'amin hakane saboda naji Dad'i kuma saboda kada na damu" Na karishe fad'a cikin gunjin kukan dake fitowa daga kasan raina. Gabadaya na fad'a jikin Ramatu na saki kuka na, sai naji cikin jikinta ya Tokare ni,Sai kuma naji sanyi ya mamayeni na Dora hannuna saman cikin ina Fad'in"Ko ban yi aure ba..ko ban haihu ba. Na tabbata yar da zaki haifa ko d'a zai kira ni Mama watarana Ramatu" Duk dauriyan Ramatu sai da naji Muryanta na rawa tana fad'in"In sha Allahu ki Dauka duka ya'yan da zan Haifa naki ne Hasiya" Ta fad'a tana rumgumeni gabadaya sai kuma muka had'e kai muna ta kuka, kukan tuna rayuwar mu tunda Fari Lokacin da Ubangiji ya hallicemu. Kai bawa ba'a bakin komai ya ke ba, kuma shi mutum tun daga Haihuwarshi a mutuwarsa yana cikin Kalubalen Rayuwa ne da Jarabawa. Sai da muka yi kukan mu muka gaji sannan muka yi shuru shima Maman Boy ne ta d'ago labule ta ganmu muna ta Rafzan kuka. Baki ta rike kafin tace"To kuma miye na kuka? Aure dai ai an Daura shi sai dai Fatan Allah ya fidda auren ku a bakin yan bani na iya" Tana gama fad'in haka ta saki Labulan D'akin ta juya, kalamanta yasa muka saki juna tana sharemin hawaye nima ina share mata Fad'i take yi"ki kwantar da Hankalin ki in sha Allahu babu abunda zai faru" Kaina na Dagamata ba domin na yarda da ba abunda zai faru d'in ba. Ko sauran Lokutan baya da abubuwan ke faruwa ba sani nake yi ba kawai zuwa suke yi ba zato ba Tsammani. Hira Ramatu ta cigaba da yi min saboda na warware, sai na bi yunkurinta ban gwale mata, ina biye mata cikin Hirar nata. Habiba ce ta kawomana Jalop din shinkafar da suka Dafa, da ruwa tace in ji Adda Fati har zata fice na daga ido ina kallonta cikin Dashewar murya nace"Habiba Amma fa? Ta juyo tana fad'in"Amma na lafiya,wani abu za'a karb'o miki a abu a wajenta ne? Sai na kasa mgana to me zan ce? Ganinta kawai nake son yi ,ban samu damar mgana ba Ramatu tace"Kin ji Habiba jeki abun ki" Sai ta kad'a kai tayi ficewarta. Duk yadda na so na nuna komai ba komai ba ne na kasa. A saman fuskata zaka hango tsoro da wani irin Fargaba. Har sanda Adda Fati ta leko ta kira Ramatu kafin fitarta sai da takara jadaddamin kada na damu babu abunda zai faru. Kai kawai na Daga mata, sanin da nayi komai zan fad'a zata ga kamar na raina kokarinta a kaina ne. Kasa zaman Dakin nayi, hankalina na wajen Amma yasa na mike dakyar kafafuwana sun yi tsami sosai. Abincin ma da aka kawomana idon Ramatu yasa na ci kad'an ammh a kirji na ya tsaya tunda ga shi nan ina jinsa, Kirjina suya yake yi min. Daman tun a kwanaki nan nake fama da ciwon kirji da baya, nasan Ulcer d'ina ce ta tashi ammh halin da nake ciki yasa ban tsaya bi ta kanta ba. Jan kafa take yi saboda ta yi min Tsami ga wani sanyi da jikina ya yi a haka na fito daga Dakin Maman Boy. Gidanmu irin Dogon gida ne ba shi da Fili ko kad'an a tsuke yake ga kuma Jerin gwanon Dakuna reras fin goma shiyasa in dai ka shigo anguwan Samaru kace a kawo ka DOGON GIDA ko yaro ko Babba zai kawo ka har Kofar Gidanmu. Ko sha'ani ake yi a kofar gida ake yi girki saboda ba fili ko a shiga makota ayi, Matan ne aure reras Goma sha uku ne a gidan Amma ce ta sha Hud'u da bata da miji. Kuma kowacce na da Tarin ya'ya kamar tsaki shiyasa kowani babban gidan albarka bayan yaran gidan ma har da na makota. Gida kuma gidan Haya ne, shiyasa bakomai ba ne zaka ganshi cikin Tsari a ire iren gidajen da rayuwa ta kan jeho ire iren mu. Koda na fito duk matan gidan suna waje ana ta cin shinkafa ana Hira, Yaran kuma suna ta guje gujen su, suna ta Hayaniya ni fa ba domin su Addaa fati ba, ba taro na so ayi ba, Tunda nasan da yawansu taron su ci abinci ne su koma suna Dariya da Kaddarata. Ko Amma sai da tace bata son Taron nan Adda Fati ta roketa tace adai yi ko yaya ne yafi ace ba'ayi gayya ba. Har ga Allah ban so ma wata ta ganni ba naso ne na sulale na shige Dakin Amma ammh ina sai da Maman Salihu ta ganni ta ko Rangad'a gud'a tana Fad'in" Amarsu ta ango" Sai kallo ya koma kaina, nan fa suka taru a kaina suna ta min Shegentan ka da suka saba,ni dai ina kauce musu saboda hayaniyar tayi min yawa tana kuma kara tafiya da Fad'uwar gabana. Dakyar na yakice su na Fad'a Dakin Amma tana zaune gefen katifar da waje wajen zamanta shekaru masu yawa, bayanta an kara mata Filo guda Biyu saboda ta zauna Dakyau. Gefenta kuma Wasu abokan wasa suke wajen Babanmu. ni sauran ma ban tsaya kallon su ba kafafuwana ke Hard'ewa kamar zan fadi ganin ina shigowa kallo ya Dawo kaina. Suma din kamar matan gidan namu Gud'a suka saki suna kirana da Amarya sunan da in sun kirani da shi nake jin wani rauni ya lullubeni a shekaru biyun da suka gabata an kirani da suna Amarya, ammh bai Dore ba na tashi daga Amarya na koma Bazawara da wasu jerin sunayen da bazan iya fad'an su ba. Ni dai ban tsaya biye musu ba, samun kaina nayi da karisawa in da Amma take zaune tunda na shigo ta Dago tana kallona da Mirmishin da ya kasa bace mata a saman fuskarta. Bansan na zube a gabanta ba sai da naji kafafuna sun gamu da siminti har yar kara sai da suka ba da Kas!, Cikin Fara'ar da ta boye tsoron dake kan Fuskata nace'"AMMA.." Kai tsaye tace"HASIYAA."! ta kirani cikin muryan ciwo ammh cike da karsashi da Fata. Da Rarrafe na karisa gabanta ina mai riko hannunta guda d'aya, ganin haka yasa ta dora dayan hannunta nata Gabadaya ta jimke hannayena cikin nata. Kwallah suka cikamin kwarmin ido ammh ina kokarin maida su cikin yanayin muryanta tace"Allah ya albarkaci wannan auran naki Hasiya. Fitinar Duniya ya kare ki da shi, Allah yasa gidan zamanki ne Yasa mutuwa ce zata rabaku" Su na d'akin ne ke amsawa da Ameen koda bai kai zucci ba, ni kuma duk yadda naso kada hawaye su kawomin sai da suka zubo kar kan hannayen Amma, itama kamar zatayi kukan tace"Ba kin ce Allah ba? Ai shikenan Hasiya kin gama mgana share hawayen ki kin ji" Sai na zare hannayena cikin nata ina Share hawayen da suka faramin Tsere a saman fuskata. Kamar Daga sama naji wata mata na Fad'in"To an dai Daura auren Allah yasa zuwa anjuma kada mu ji wani bala'in ya afkama angon" Da rinanun idanuwana na kalleta Gambo ce a matsayin y'a take wajen Babanmu. Na kasa mgana to me zan ce? Gaskiya ta fad'a nima Fargaban dake damuna kenan tare da Tsoro. Kafin ma mganarta ta sha iska Inna Talatu Mahafiyar Ramatu tace"Da ikon Allah ba abunda zamu ji sai alheri" Sai kuma Dakin ya Dauka da Insha Allahu cikin yakinin da su kansu ba su Tabbas din hakan zai kasance ko abunda ya faru a baya ne zai maimaita kansa. Had'a ido mukayi da Amma sai ta gyada min kai cikin yakinin da nagani a kwayar idanuwanta, sai na jinjina mata kai Lokaci d'aya ina goge fuskata. Na mike a kasalance ina jan Kafa zan fice Inna talatu ta taidani da Fadi'n"Kada ki ga baki ga Ramatu ba Fati ta kirata suka tafi gidan Dilalliya Jummai, mganar sauran kayanki dake Hannunta" Da kai na amsa mata ina Ficewa, acikin jikina nake jin wannan karon kayan ba zasu dad'e kamar baya ba zasu sake komawa Dilalliya Jummai kamar baya dai. Wannan karon ba Dakin Maman Boy na koma ba,na maman Salihi na shige tunda shi ke kusa da Dakin mu. Kan kujerata na samu na Kwanta ina Numfarfashi. Rufe idanuwana nayi kamar mai barci nan ko ba barci nake yi ba,Tunani ne suka Daibaye Duniyata Gabadaya. In tunanin in na samu zama gidan Salisu Matarsa fa? Wacce tayi ikirarin duk abunda ya samu mijinta sai ta Kasheni. Na tuna labarin da Habiba ta bani da sukaje min jere ita da yan'uwanta haka suka taru suna zagin su da Tijara iri iri, Tunda gida D'aya zai Had'amu da Matarsa uwar ya'yansa. Tunanina ya tsaya cak da tuna in kuma Abunda ya faru da Abubakar ya Faru da Salisu fa? Jikina sai da ya Dauki Dumi da Tuna da Abubakar da abubuwan da suka Faru a baya, har kwanan gobe duk inda wani Dangin Abubukar ya ganni ko ya ga d'aya daga cikin yayyina ba'a rabuwar arziki ba irin sunan da ba su k kirani da shi ba, mugun bala'i kuma sun jima suna rokarmin shi, sun yi kuma ikararin yadda na nakasa Rayuwar Dan'uwansu nima sai sun nakasa ni. Tuna hakan da nayi bansan Dumin da naji a saman fuskata dumin hawaye ba ne, sai da naji digarsu har dogon wuyana da ko Sarka Babu. Yanzu in wani abu ya Faru da Salisu fa? Me zan ce ma mutane da suke kallona da Tabon kashin Tsiya?Da masu cewa Naman jikina ba shi da kyau kuma Rab'ata ma kawai in mutum ya yi da sunan neman aure na shi da arziki har Abada sai dai yaga anayi, ni da akayi min canfi dalilin Haihuwata ne karyar Arzikin marigayi mahaifinmu Alhaji Mamman Mammadi Kona. Ba kuma a bakin bare ba ne wannan mganar abakin Dangin Mahaifin mu ne. Har ciwon Amma da aka kasa gane kanshi an ce duk Sanadina ne, duk in da na zauna na Rayu wajen bazai kara zama mamaro mai amfani ba. A cewar su ni wutsiyar Rakumi ne gani na ba alheri ba ne. Bansan ina kuka ba sai da naji Shesshekan na fita sannan nasan kuka nake yi, ba zan iya hana kaina kuka ba shiyasa sai da nayi ya isheni sannan na hakura na share hawayena. Ba na sallah ina fashi shiyasa na kara gyara kwanciya Barci na neman saceni naji Muryan Ramatu na kiran sunana, daga cikin Dakin na kwala mata kira sai ta jiyo ta shigo. Tashi nayi zaune na matsa mata ta zauna a gefena labari take ba ni yanzu Daga gidan Salisu suke sun je sun kaimin sauran kayan da suka amso wajen Jummai Dilalliya. Kamar da mgana a bakinta yasa na kalleta ina fad'in"Me ya faru? Da sauri Ramatu tace"Babu abunda ya faru kinga Dakin ki? Yayi kyau sosai. Da ya ke kinsan kayanki ba su yi komai ba sai suka kara haska wajen gashi Salisu kamar ya sani ya yi mana Fenti kalan kayanmu" Ta karishe Fad'a cikin Dariya, kallonta kawai nake yi ban yi mgana ba ta cigaba da fadin"A kofar gida muka had'u da Salisu da abokan sa kin ga bakin Mutumin naki kuwa?kamar gonar Auduga" Sai a lokacin nayi mirmishi Da ya fito daga kasan zuciyata. Da gaske ina son Salisu domin kamar Abubakar sun so ni da dukkan zuciyan su, sannan sun toshe kunnuwansu da duk wata mgana mara kyau ko Dad'i a kaina. Lura tayi da Labarin Salisu na Farantamin rai yasa ta cigaba da bani Labarin shi tana fadin"Yana ganin mu ya fara washe mana baki. Ganin Adda Fati yasa bai kwafsa ba, sai da tayi gaba ya bini yana fad'in ki kularmin da Matata. Kin ji yadda yaja kalmar Matata kuwa? Tafad'a tana Dariya nima sai da na Dara, ba ni da waya a hannuna kwanaki ita na Saida da Jikin Amma ya tashi, Salisu ya so ya siyamin na Hanashi ganin Hidimar biki na kanshi, da niyar sai bayan biki zai kara siyamin wata. Daga mganar Salisu muka koma hirar Haihuwarta da zatayi watan gobe, Tana Fad'amin duk ta gama siyan kayan Haihuwa. Cikin karfin jiki da na Zuciya nace"Ai Nura ba daga baya ba. Akwai son kyautatama iyalansa Namiji ne samun kamar sa a wannan zamanin sai an tona" Tayi wani kayattacen Mirmishi kafin tace"Na ma manta ya kirani Dazu muna Hanya. Yace na yi miki Fatan alheri" A d'okance na amsa da Nagode. Domin kaf cikin layin masoyana bayan Iyayena da yan'uwana Ramatu ta Biyo baya wlh Nura na sahun su Salisu da Abubakar su din shakikan Masoya na ne da har addu'ata ina sakasu da Fatan Allah ya had'amu da su a aljannah Firdausi. Mun cigaba da Hira da yasa na saki jikina, muna tare da ita har yammah lokacin mun yi mgana da Salisu da wayar Ramatu yace ba da jimawa ba abokan sa zasu zo Daukana, da yake ba nisa gaban anguwan mu ne da Kad'an. Ramatu ta sanar da su Adda Fati suka fara shirin mika ni gidan mijina a karo na biyu. Da farko tsoro ya hanani sakewa ammh da naga har yammah tayi ban ji wani abu ya taso ba sai na saki jikina, ammh in na tuna na Abubakar shi har an kai ni gidansa. Ya shigo Dakina kenan da ledojin kajin sa na amarci aka kirasa a waya,wayar da ta tarwatsa duka farincikinmu har ma da auran Gabadaya. Wanka Ramatu ta matsamin na sake yi na sauya kaya zuwa wata Shadda milk, ita ta dinkama ni da ita da sunan in ta haihu mu saka ammh da auran nan ya taso sai tace mu yi amfani da shi. Ban yi kwalliya ba na dai shafa Hoda na saka man baki. zuwa Lokacin hayaniyar gidan ta ragu, Kayana na sawa Ramatu ta had'amin su a wata karamar akwatina tun na aurena da Abubakar ne. Dakin Amma a ka kaini bata tawaita nasihan ta ba, Albarka ta sakamin kamar yadda ta saba. kuka nake yi kukan da har ya fito ana jin Sautin shi Ina ji Gambo na sake fadin"Kuka kuma Hasiya? Ke da ba auran Farko ba? Ina cikin Babban mayafin da Ramatu ta sakani sawa, na ke kallonta tunda Shara shara ne ana ganin na waje,ban sa waye ya bata amsa ba tunda akwai muryoyi da yawa a dakin Har da Gabadaya matan gidanmu suna Dakin. Daga karshe naji Muryan Ramatu na Fadin"Ko ba auran Farko ba ne ai aure dai sunan shi Aure" Ni dai ina hawaye muka baro Dakin Amma zuwa Dakin Maman Boy, Adda Fati ta shigo tana fad'in"Ramatu ina ga dai sai bayan mangriba angayen zasu zo ko? Domin naji ana ta kiran sallah" Ramatu tace"To kila dai sai an yi sallar" Adda Fati ta fice tana fad'in"Gaskiya dai mu ma bari mu yi sallar kafin su iso" Tafad'a tana ficewa Daga Dakin sai alokacin Tunanin ina Adda Rukayya ya Fad'omin tun safe da na ganta sau d'aya ban kara ganinta ba. Ko ya'yanta ban ga ko D'aya ba, sai yaron Adda Fati nagani kuma shima zuwa ya yi ya gaisheni. Sai na kalli Ramatu da ke faman latsa wayarta ina fad'in"Ramatu wai ni ina Adda Rukayya ne? Ko ta koma gida ne? Tsam naga tayi kamar tana nazari ni ko na kafeta da ido ina nazarinta, taasan na santa sarai bata isa tamin alaye ba. Sai kawai nayi mirmishin takaici nasan amsar shurunta. Adda Rukayya ce fa ita ce jini na uwa d'aya uba D'aya ammh in ba'a fad'a maka ba sai kace bamu Had'a komai da ita ba. Cikin karyewar murya nace"Ba sai kin ce min komai ba Ramatu na Fahimta. Allah ya sa mu dace" Sai ta kasa amsamin, kallona take yi a sanyaye ni ko sai na kauda kaina. Adda Rukayya ce fa ta kalleni ido cikin ido tace'"Gaskiya Hasiya ki daina zuwa gida na. In wani abu kuke da Bukata ki kirani kawai. Baban su Amna ma baya so yace tsoro yake ji. Baya son zuwan ki gidan shi" Tunda ranar da ta fad'amin wannan mganar na san in da na sauke Matsayin Adda Rukayya a wajena. Ko Amma ta na fad'a ta kuma sha Fad'amin cewa"Hasiya ku yi hakuri da Rukayya. Kaf cikin ya'yana tana da Bambamci ba D'aya take da ke ba, sannan ba D'aya take da Fati ba. Ku yi mata addu'an da Fatan Allah ya Daidaita rayuwarta. Rokona shine kada ku yanke zumumci da ita ko bayan kasa ta rufe idona" Nasan ta zo ne ma da Safen gudun Fad'an Amma, ba sabo da ni ba. Gabadaya Hidiman auran nan Ramatu ne da mahaifiyarta sai Adda Fati kan lamarin ni ko sau d'aya ban ma sakata aciki ba. Ni fa ko ciwon Amma ya tashi bana jiranta tun kiran ta da na tab'a mata kan kan jikin Amman ya tashi ta fara min Fad'a da cewa komai ya ke faruwa ni ce Sila tun haihuwata Rayuwan mutane da Dama ba su wuta ba ciki har da su da Amma ni ce silar Cutar Amma da bata da mgani. Tun daga ranar na kiyaye mata, sai Amma ta sha ciwonta bata sani ba. Sai in taji daga baya ta fara kumfar bakin ba'a Dauketa bakin komai ba tunda Ba'a fada'a mata ba. Har tutiya ta tab'a yi a asibiti Lokacin da aka kwantar da Amma. Ban kirata ba Adda Fati na kira ta zo muka taho asibitin sai bayan an ba ma Amma gado ta kirata ta Fad'amata. Shine da tazo ta rika fad'an meyasa ban kirata na fad'a mata ba? Kuma a lokacin kai tsayen ta kalli Adda Fati tace"Naga kamar sun fi daukan ki wata Tsiya. Allah na tuba me kike da shi Ballatana shi Habibun? Ni dai da kuka raina ni nake da shi,kuma nake rufa muku asiri ni da Mijina" To me wad'anan kalaman ne kuma don in bata zo ba meyasa zan damu? Ina ta kokarin nuna yanayina ba komai ganin haka yasa sai Dakin ya Dauki shuru daga ni har ita ba mai wani mgana kowa na saka wasu abubuwan acikin ransa. Sallar mangariba ya Tada Ramatu ta fita tayo alwala tazo ta gabatar da sallaar tana cikin sallar ne kafin ta Idar, wayarta dake gefena ta Dauki neman Dauki. Ina dubawa naga Salisu ne sai da gabana ya Fad'i. A kasalance na dauki wayar ganin ya sake kira bayan kiran D'azu ya katse. Na latsa koren alamun Dauka na kara kunne ina jin muryansa cikin Shauki da murna yana Fad'in"Ramatu ga mu nan zuwa. Kada ku ji mu shuru mun bari mu yi sallar mangariba ne" Numfashina ne ya kwace min batare da na shirya ba, kuma da hakan ya fallasa ma da ni ce na Dauki wayar. Cikin Shauki da Soyayya yace min"Hasiya..! Hasiya. Numfashin ki Kad'ai ya isa ya shaida min da ke kika Dauki wayar nan" Sai na kara sakin Numfashin cikin Rashin Mafita tsoro nake ji kada wannan Shaukin da Muryan Salisun ta Rikid'e ta koma shaukin bakinciki da takaici. shiyasa na kasa mgana Dakyar na iya bude baki nace"Sai kun kariso. Allah ya tsare" Daga haka na yanke wayar ina jin kamar ana Saremin gwiwoyina. Daidai Lokacin da Ramatu ta Idar da sallar ko kafin ma ta nemi ba'asi tace"Salisu ne ko? Sun taso ne? Dakai na amsa mata sai ta mike Dakyar ta fice tana fadin bari tayi ma su Adda Fati mgana. Ni dai in da ta bar ni nan nake zaune wani Lokacin ina jin yayan mutane alamun ina cikin duniyarmu. Wani Lokacin kuma sai na tafi dogon zangon Tunanin da zan ji kamar komai ya tsayamin Dif! Bana jin yayar wannan duniyar tamu. Da mganar mu da Salisu an fi minti talatin kafin naji Hayaniyar cikin gidanmu tafi ta kowani Lokaci karfi. Tabbas ba Lafiya in dai hayaniyar gidanmu ta rika amsa kuwwa acikin Dakuna. Gabana ya yanke ya Fad'i ras!. Kaina ya saramin a lokaci d'aya, mikewa nayi da sauri jikina da gabbaina sai da suka amsa saboda karfin da na saka wajen tashi. Habiba ta fad'o dakin da sauri sai muka kusa cin karo da juna cikin Fitan hayyaci Tace"Salisu..Salisu ya yi hatsari.! Kamar saukan Aradu haka naji kalamanta,Shuu! Naji kunnuwana sun yi kafin naji Habiba na jijjigani, kafafuwana sun yi sanyi kalau din da suka kasa Daukata,sai ji nayi na tafi luu numfashi na tare da ji na da ganina suka Dauke gabad'aya. Ammh zuciyata harbawa ta ke yi da tunanin Ni HASIYA tabbas ina cikin TSAKA MAI WUYA..! Ba suma nayi ba,ina cikin Hayyacina sai dai ji nayi kamar na samu cutar shanyewan duka jikina, Tunda ina jikin Habiba ne, ammh gabbaina ba inda yake iya motsi wani irin mutuwar jiki ce ta kamani kamar wacce likitoci suka yi ma alluran kashe jiki. Naji mutane nata shigowa Dakin, a na ta maganganu a saman kaina ina jin Muryan Adda Fati tana Salati tare da Fadin"Mun shiga uku. Allah yasa ba abunda ya faru akan Abubakar ba ne zai maimaita kansa a kan Salisu ba" Shine ma! Naji na amsata a raina ai ba bu wani bambamci balle da naji Muryan Ramatu cikin Damuwa tana Fadin"Yanzu abokinsa Musabahu ya kirani cikin damuwa yana fad'amin. Ashe suna kokarin tahowa nan Daukan mu sai ga waya Shagon Salisu ya kama da wuta ga kayan mutane aciki. Shine a rud'e ya hau mashin din kaninsa ya tafi,to ya ce min bai ko karisa ba Mota ta tureshi ya Fad'a ma wani mai adaidaita suka yi fadin anrigizo tare" Sai salati ke tashi a dakin da Hayaniya. Muryan Inna talatu naji tana fad'in"Wani hali Salisun ke ciki? Ramatu tace"Yace suna Emergency har yanzu likitoci na kanshi ammh shi Direban adaidaitan ance nan ta ke ya rasu" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Su Adda fati ke ta faman maimaitawa. Gidan Gabadaya ya Hargitse har da makota masu shigowa jin gulma da ganin yadda za'a kaya. Muna nan ana ta maida zence ni dai tun bayan da Habiba ta jinginar da ni jikin garun Dakin Maman boy ban kara motsi ba, kuma ba Hawaye acikin Idanuwana. Ramatu ta zauna a gabana tana fad'in"Don Allah Hasiya kada ki damu Musbahun ya tabbatar min komai zai zo da sauki" Kallonta kawai nake yi ina jin kamar karo na farko da Naji kalaman Ramatu ba su burgeni ba. Tunda karya take Fad'amin babu abunda zai yi daidai karya take min. Na sani! Itama ai ta sani komai zai kwabemin ne kamar yadda ya kwabemin Lokacin aurena da Abubakar. Yana sona ina son shi ammh Kaddara da Tsaka mai wuyar da Rayuwata take ciki ta yanke aurena tsakanina da shi Har Abada. Daga kofar D'akin Maman Boy ma muna jin kururuwa da Muryanta, tare da mganan wasu suna fad'in"Ku rike ta mana" Ammh ina kururuwa take yi,kamar tsohuwar mahaukaciya, kamar an samin magad'isun mganin a jikina sai gani na mike kan kafafuwana, ko mutuwa nayi na dawo nasan muryan Sahura Matar Salisu, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha zuwa ta min kashedi kan mijinta. Ramatu na kokarin rikeni na Fizge jikina na fice,ina ratsa matan gidanmu da suka yi Dafifi kofar Dakin Amma. ba wuta ammh akwai hasken Farin wata ya haske tsukakken tsakar gidan namu Tarwai ana ganin komai. A gabanta na tsaya ana rike da ita, ihu take tana kuka tare da kuruwan ina nake sai ta kashe ni. Ba zato ba tsammani taji muryana a saman kanta ina Fad'in"Gani..Gani Sahura" Na fad'a cikin wani yanayi a muryata,gabadaya sai kallo ya Dawo kaina har da Ramatu da ta biyo bayana. Adda Fati a rude' ta riko ni tana Fadin"Ke Hasiya lafiyan ki kuwa? Amma na da cikin Daki tunda Labarin ya shigo gidan taji zazzabi mai zafi ya Rufeta ammh kiran sunana da Fati tayi sai ya tafi da kaso mafi girma na cikin sauran kuzarinta sai ga shi ta kife saman katifar da ta ke zaune tana makyarkyatan Sanyi. Adda Fati na kokarin janyeni Sahura ta kyalla ido ta ganni tayi kukan kura kwace rikon ta da kannenta mata suka yi mata,ta nufeni gadangadan tana zuwa ta shakemin wuya, shakar da har ina kakari da gaske take yi Halakani zatayi kuma Daman ta Dauki alwashi. Idanuwanta Jajir kanta ba ko Dankwali gashin kanta ya mike tsaye kamar mahaukaciya sabon kamu Cikin kuka ta jijjigani tana Fad'in"Daman sai da na ce kada ya aureki. Ga mata nan kala kala Dole sai ke? Ina zaman zamana da mijina zaki kashemin shi. Na rantse da Ubangijina in Mijina ya mutu sai nayi ajalin ki Hasiya ni zan kashe ki da Hannuna" Cikin ido na kalleta kafin nace"Nima zan so haka. Zan so ki kashe ni kamar yadda kika ce" Na fad'a cikin muryata mai cike da yakinin nima mutuwar ce ta Dace da ni. Kara makureni tayi tana ikirarin sai ta kasheni. Naji hannaye da yawa suna kokarin bambare hannayenta daga saman wuyana da kuma masu janyeni daga gareta. Ammh ni na kasa wani yunkuri na kwatan kaina. Na riga na gama sadaukarwa Rayuwa ta bata da amfani in dai zan rika zame ma duk wani mai sona Tashin Hankali da Bakinciki. gwara na Mutu kowa ma ya Huta. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *Friday 11/08/2023* *1:30pm* *Post on 01/01/2024* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabooks:JamilaUmarjanafty* *GAISUWA BAN GIRMA ZUWA GA IYAYEN D'AKINA.* *HAJIYA HADIZA MAHE MUHAMMAD* *HALIMA DALHA SHEHU(MAMA)* *ANTY ZAINAB ABDULWAHAB* *HAJIYA AISHA AHMAD IYA* *HAJIYA LUBABATU MUSA* *ANTY FIRDAUSI KABIR* *ANTY FADILA KABIR* *ALHERIN ALLAH YA LULLUB'E RAYUWARKU GABADAYA AMIN* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V +201123302418 *02* Dakyar mutanen da ke zagaye damu suka samu nasaran raba hannayen Sahura da wuyana. Ammh kafin su samu nasaran raba hannayen nata da Wuyana na jigata, domin shaka ne ta yi min da niyar da ke zuciyarta da kuma kalaman bakinta na sai ta kashe ni. Ko bayan an samu ta sakeni karin kokarinta kuma ta kara rike wuyana. Da gaske take yi sai ta kasheni ni ko gabbaina sun yi sanyi da ba na iya ma wani motsi Adda Fati ne da Ramatu ke faman ja na. Ammh na kasa kokarin Tallafa musu wajen kare kaina. Kafin kace me? Gidanmu ya cika Damkam da mutanen anguwa har da Maza magidanta da Samari, ana ta faman maida zencen abunda ke faruwa. Ko ba'a maida ba irin zage zagen da Mugun alkaba'in da Sahura ke jifana da shi kada'i ya isa mutane su gane abunda ke faruwa. Sahura ta haukace ko na ce ta fita daga Hayyacinta ihu take yi tare da kwakwazo tana Fad'in duk mganar da tazo daga bakinta a kaina mara kyau da mugun Fata. An yi an yi a fitar da ita daga gidanmu ammh abun ya ci tura kannenta bazasu iya ba. Sai da suka kira wasu daga chan gidan ba jimawa sai ga su ciki har da yan'uwan Salisun. Wata mata kamar yayar mahaifiyar Sahuran ce sai da ta tsinke Sahura da kyakyawan maruka har guda Biyu. sannan ta dawo cikin hayyacinta ta koma ta zube a kasa tana sakin wani Gunjin kuka mai fitowa daga karkashin zuciya. Buda'r bakin Matan cikin Fad'a tace" ashe baki da Hankali ban sani ba Sahura? Mijin ki na asibitin rai ko mutuwa ammh ke kina nan kina Hauka da Shirme? In yau Salisu ya mutu babu wacce tayi asara sai ke, kin zama bazawara sannan ya'yanki sun zama marayu" Kalamanta suka sanyayyar ma da kowa jiki ciki har da ni da nake tsaye cikin Halin Tsaka mai wuya. Jikin Sahura sai ya yi sanyi ta koma ta na kuka Kasa kasa, Umarni taba ma sauran aka kamo Sahura daga zaune ta mike tana Sharbe kuka cikin Kaushin murya tace"Mu je gida Sahura. addu'a mijin ki ke bukata ba wannan hayaniyar ba, kina mganar zaki kasheta in kika Fad'a gaban yan Amin fa? Kika kashetan fa? Ke ma kina da Labarin kashe ki za'ayi? Sai sahura ta kasa mgana sai Kuka, Wata kanwa ga Salisu ta na matsayin Diyar kanwar mahaifiyarsa ne Zaliha ta kyabe baki tana Fadin"To ba gwara ta kashe mugun iri ba. Ban da Abun Namiji me Salisu ya gani ajikin wannan abar da ya kasa sukuni sai ya aureta? Ta fad'a tana nuna ni sama da kasa kafin ta cigaba da fadin"Ba yadda yan'uwa ba su yi da Salisu kan ya hakura da yarinyar nan ba ammh yak'i Yarinyar da akace ko iyayanta kan Dole suke zaune da ita tun haihuwarta bala'i ke fad'a ma Ahalinta tayi auranta na Farko ta Tsiyace mijin da Ahalinsa gabadaya, ammh kasan da wannan abun kace kai ma sai ka aura ? Haba haba ai wlh ba haka nan ba ne wannan al'amarin da wata a kasa" Karaf wata tace"Kila farar fatan ta ke Rud'an su. Ko lange langen jikin nata? Ammh ni ban ga abun sha'awa a tare da wannan abar ba sai jaraban tsiya da Bala'i" Sai kuma da suka Fad'an na kara bin kaina da kallo duk mganganun da suka Fad'a gaskiya suka fad'a. Ba ni da kyau na azo a gani sai farin fata ,ammh ko dirin nan na mata ba ni da shi siririya ce ni sosai kamar a hureni na Fad'i. Sun yi ta Fad'an mganganu marasa Dad'i su Adda fati da matan gidanmu ke basu hakuri. Shudewar awa d'aya sannan balataliyarsu ta bar gidanmu sai gidan ya yi tsit sai dai tashin yan kananun mganganu. Ni dai juyawa nayi kafana na taku daya bayan d'aya cikin sanyi da wani irin yanke kauna zuwa Dakin Amma. Duk girman tashin hankalin da zan shiga Amma ce mace ta farko da kan Fad'omin araina a irin wannan yanayin. Ina shiga Dakin Duhu ne ya fara mamaye ganina, ana cikin wannan halin waye zai tuna da kunna yar karamar Fitilar mai chaji din da Adda Fati ce ma ta siya mana ita. Sakamakon Dakin namu falle daya ne karami yasa ina shiga ko da Duhun dakin nasan mazaunin katifar Amma chan na nufa kai tsaye gabana na Fad'uwa. Sai dai naji gwiyoyina sun yi sanyi ne sanda na isa gefen katifar na ji tashin nishin Amma da kuma rawan sanyi mai had'uwa da sautin karan Bugawar Hakora. Cikin Daburcewa na Fara lalubanta da Hannayena Lokaci daya ina fadin"Amma..! Amma..! Jin muryata yasa ta Dago daga kifewar da tayi a tsakanin Wuyanta zuwa cikinta, Da sauri itama ta fara mikomin hannunta guda Daya ta na so ta tab'ani cikin ikon Allah naji Hannunta cikin nawa,sai na kara Firgita jin Dumin hannunta Rau har ya Gauraye da Sanyin na wa Hannun Bakina da Jiki na rawa da Tuni na manta da Halin da nake ciki na Fara fad'in"Amma jikin ne ya tashi? Ta shi muje asibiti jikin ki ya Dauki Zafi" Na ke fad'a cikin Fitan Hayyaci, na mike kenan da karfin gwiwata Amma ta yunkura ta mike zaune Lokaci D'aya tana riko hannuna, sai da na dagata na juyo ina kallonta ta cikin Duhun Dakin muryanta a shake tace"Dawo ki zauna Hasiya" Musu ba Halina bane balle Musu da Amma sai na dawo gefenta na zauna ammh ban saki hannunta ba Zafin jikinta na shiga jikina ta Dalilin hannayenta da ke cikin nawa na Jimke. Sai da ta ja gauron numfashi sannan ta kira sunana cikin karyayan Sauti na amsa mata da Sauri cikin Fargaban jin yadda take sauke numfashi, ina tsoron tashin hankali ammh na fi tsoron Tashin hankalin tashin Ciwon Amma da bai da mgani. Tayi ta wahala ko mun je asibiti sai dai su bata allurai da Ruwa shikenan ya lafa mu dawo gida ammh ni kad'ai nasan a irin yanayin da Amma take kwana ta na tashi in ciwon ta ya tashi. Shiyasa nake a firgice ko tari mai karfi naji tayi sai Hankali ya tashi matuka. Cikin Tattausan lafazi ta fara fadi'n"Kiyi hakuri da Kaddaran ki Hasiya. Watarana zaki ji dad'i in sha Allahu" Kallonta na ke yi ina laluban Fuskarta ta cikin Duhun Dakin, tunani ya tafi nesa da mganar ta ina tunanin yaushe ne Ranar jin Dad'in? Sai naji mganar Amma daga sama tana Fad'in"Kada ki sake ki saka Tunanin da mutane suke yi a kan ki. Kada ki kuskura ki yarda da su karya suke yi. Abunda suke Alakanta ki da shi Jahilci ne ba Farar Kafa a addini mu Kambun baka kada'i Annabin Rahma ya sanar damu, ko maita babu shi a addininmu saboda haka kada ki damu da duk abunda ke faruwa, Allah ne ya Saukar ma Abubakar duka kaddarorinsa. Sannan shi ya kara Dauro ma Salisu na shi Jarabawan, Ba ke ba ce Hasiya ke baki isa ki zama silar kaddara ko Jarabawan bayin Allah ba. Ba ke ba ce baki da wannan Hurumin komai da ke faruwa da sanin Allah kuma ikon shi ne" Ta karishe Fad'a tana faman jan Numfashi Lokaci daya Jikinta na kara makarkyata. Na rude hankalina ya kara tashi sai kawai na fashe da kuka ina Fadin"Amma jikin ki na rawa ga shi Zazzabi ya rufeki ki bari mu je asibiti" ko da ba na ganinta nasan mirmishin nan nata na karfin Hali tayi min kafin ta saki hannayena ta koma ta kwanta tana fadin"Bafa wani abu Hasiya.. dubamin dai panadol na sha Zazzabin zai sauka" Kafin ta gama mgana ma na bazama Bangon yammah na Dakin saboda Tsabar yadda nasan kowacce kusurwa na Dakin yasa ko cikin Duhu nasan inda muhallin komai ya ke. Wata jaka ce tawa a rataye nan nake saka Tarkacen magungunan Amma in ciwon ta ya tashi kafin mu tafi asibiti. A cikin Duhun na Dauko mganin, ammh ganin ba na gani yasa na lalubo fitilar na kunna haske ya gauraye Dakin. Da ita na samu na Haska na Debo ma Amma ruwa cikin wani karamin kofi na kuma ballo mata panadol guda Biyu, na tada ita na kuma bata tasha sannan ta koma ta kwanta tana Fad'in"Nagode Hasiya. Allah ya miki albarka Allah ya warware miki kaddarorin da suka Zagaye rayuwarki" a cikin zuciyata na amsa da Amin ganin ta koma ta kwanta ta na sauke Numfashi yasa na mike a kasalance na karisa wajen ma'ajiyar kayan sawanmu na dauko mata zani cikin zannuwan ta na rufa mata daga kafafunta zuwa kugunta. Sannan ni kuma na koma gefenta na jingina da Bango ina faman kokuwa da Numfashi na. Ammh kuka ko Hawaye gabadaya sun kafe a idanuwana. Kirjina na ke wani irin suya,ga harkarina duk ya rike nasan kuma Ulcer ce ammh ba ni da kuzarin mikewa domin na taimaki kaina Ahalin da nake ciki ba na bukatar komai ma duniya komai ya ficemin a raina. Ina jin tashin Hayaniyar su a tsakar gida, ana ta uban maida zence da Hayaniya kafin Daya bayan daya su fara shigowa dakin Amma, ina jAdda Fati da Ramatu na tambaya ta ko jikin Amma ne ya tashi? Da kai kawai na iya amsa musu na kasa mgana sai bin mutane da kallo, abun mamaki duk sun ki tafiya har da yan gidan su Babanmu. Su da basa kaunar su Rabemu Daurin auran ma Alhaji Tanko da ya kasance Shakikan Mahaifin mu guda daya daya ragemana, da Adda fati taje har gida ta Fad'a masa mganar Salisu lokacin da yace zai turo. Ammh Bude bakin sa sai cewa ya yi"Ai kawai Fati ku samu Limamin anguwan ku ya amshi mganar har Daurin auran ma. Wahala ce sai an zo har nan d'in" Ba nisa fa, ina Samaru ina Dirimi chan gidansa yake ammh a bayyane ya ke kowa baya son Rabarmu saboda ni Hasiya. Ko su Gambo da suka k'i tafiya saboda jin kwakwaf ne da samun abunda za'a koma ana ba da Labarinsa. Duk maida zencen da Ramatu da Adda Fati suke a kunnena ammh na kasa wani motsi, sai da naji Ramatu na waya bayan ta gama. Na kura mata ido ina neman karin bayani sai dai kafin na kai ga muskutawa ta fara fad'in"Musbahu ne" Gabana sai da ya fad'i na Runtse idanuwana ina jin kaina na wani Gif Gif jira kawai naji Ramatu tace Salisu ya rasu. Ammh sai ajiyar zuciya ta kwacemin sanda naji Ramatu na Fad'in"Ya ce likito su ce karaya ce guda biyu ya samu, kafa da cinyarsa ta Dama sai kuma yan Rauninka. Ammh ya tabbatarmin da Sauki" Bansan ajiyar zuciya ta kwacemin ba sai da naji ta fito sarari sannan da kuma kallon da kowa ya bi ni da shi. Sai na samu kaina da Sadda kai na kasa ina jin yar salama da Natsuwa kad'an suna shigata. Bazan iya sanin iya tsawon Lokacin da na Dauka ban yi barci ba. Abu d'aya na sani shine sai da gabadaya kowa ya yi barci ya barni Har Amma ta samu barci, ta kuma kara farkawa Zazzabin ya sauka tace na bata ruwa ta sha na Dauko mata. Bayan ta sha ta koma ta kwanta tana ce min"Hasiya ki kwanta ki yi barci kin ji ko" Da kai na amsa mata,ba domin ina jin barcin ba, Hatta Ramatu da Innarta nan suka kwana Dakin bazai Daukemu ba ita da Adda Fati Dakin Maman Boy suka kwana Tunda ita Mijinta Direba ne baya nan. Nasan ba ni da kokarin Ibada bar ni da Khamsil Salawati da nake yi a kullum, ammh bangaran Dagema Sallar Dare da Sauran Ibadu ina da wannan Raunin Shiyasa har barci ya Daukeni gabanin asuba ban iya tashi na Raya wannan daren ko don rokon Sauki daga wajen Allah a kan Halin Tsaka mai wuyar da ta ke ciki. Tare da Fatan samun waraka ga Salisu ni ba ma Aurena na ke ji ba. Lafiyar Salisu ta fi damuna fiye da aurena da ni da shi. ***** Washegari ma abubuwan da suka faru duka ba masu dad'i ba ne. Daga iren mutanen da suka rika shigowa da sunan Jaje ana maida zence tare da nuna ni, da kuma watsewar da taron biki da Salisu ya yi ba wani armashi. Ramatu ta koma gida Daman a Tukur-Tukur take aure Inna Talatu kuma Sabongari take da zama da Gida d'aya muka zauna da su kafin Yayan Ramatu ya yi gidan kanshi su koma chan Gabad'aya. Su Gambo kuwa sai yammah suka koma, bayan sun gama ganin duk abunda ya faru,suka yi ma Amma sallama suka kara gaba. To gwara su sun zo din ko da na ganin ido ne, A gidan su Babanmu su shida ne yan Daki daya Hudu sun rasu ciki har da Babanmu Alhaji Tanko shi ne babba sai Mahaifimmu, sai karamarsu Halima ita tana Birnin Ikko tana auran wani Babba ne a aikin Costume. Suna da tarin ya'ya da Jikoki kaf garin Zaria da kewayanta ba wanda bai san gidan Alhaji Mammadi kona ba. Ammh an wayi gari ba bu mai son Huld'a da mu saboda rashi da babu, Tare da Tsoron kada su rab'emu na shafa musu tsiyata kamar yadda suka sha fad'i a kaina. A kwana uku da Faruwar abun da na Fita sai da na raina kaina. Da kuka na dawo gida haka ake nuna ni dandalin matasa har da Dattawa. Chemist naje siyan mganin Ulcer saboda ta tasan min a kwanakin nan. ganin kuma Jikin Amma ya yi sauki yasa na Dauki Dubu Daya cikin Jarin Danwake da nake yi ne naje siyan mgani. Har achan Chemist din a gaban idona wani ya nuna ni yana fadin"Wannan ce mai Farar kafa da ake mgana? A aureta a auri bala'i ance mijinta na Farko mai kudi ne ammh yanzu ko keke bai da shi, yadda ma naji Biyar ma na bashi sha'awa yanzu" Wani na gefenshi ya karb'e da fadin"To shi wanda aka daura musu aure cikin Satin nan fa? shagonsa ya kone ko tsinke ba'a fita da shi ba. Ga karaya har biyu ga rauninka naji ma ana labarin Kano za'a kaisa ayi masa Dauri wajen miliyan Biyu ake nema kaga shima karshenta Sanadin Jinya ya rasa komai na shi" Ina kallon cikin idanuwan matashin ya kalleni ya tsintar da yawu yana Fadin"Tab.. irin su ai bala'i ne ga al'umma. Allah ya yi mana Tsari da Dangin tsiya" Mganin da ban karba ba kenan na Dawo gida da kuka. Ina zuwa kuma na kara cin karo da wani abun takaicin Adda Rukayya na samu tazo ina shigowa Dakin Daidai tana ce ma Amma" Ni fa ba wanda ya kirani ballatana ya fad'amin abunda ke faruwa. Sai da Babansu Amna ya dawo ya ke fad'amin a gari yaji ana ta Fadin Labarin da yazo yana tambayanta nace ban sani ba. Amma tsakani ga Allah mganar mutane akan Hasiya ba Canfi ba ne gaskiya ki fa Duba Abunda ya faru da Abubakar ga wannan ma, to ko karayar arzikin Baba da Jinyarsa duk itace sila kema ga naki ciwon matsaloli sun ki su kare mana. Ni fa Matsalanta har neman Shafan zaman aurena ya ke so ya yi Tunda Har Baban su Amna ya ce shi ya fara jin tsoro, Mamanshi har mgana ta tab'amin nace mata kashin Tsiyar Hasiya kad'ai ke da ita ban damu ahto kada dalilinta aurena ya Mutu na shiga Uku" Ta fad'a kai tsaye babu kuma alamun Tausasawa a muryanta. Kamewa nayi a kofar dakin Amma na kasa karisawa ciki Amma na zaune kawai tana kallonta, dukkansu ba su san ina Kofar dakin ina Sauraransu ba. Adda Rukayya ta gyara zama tana Fadin"Shine na kawo shawara Amma. Me zai hana tunda dai nasan shima auran nan sunan shi Sakakke. Saboda ba iyayen da zasu bari D'ansu ya zauna da Hasiya mganar gaskiya kenan. Ki tarkata ki kaita Dangin ki chan gada wajen Adda ta zauna tunda chan ba wanda yasan abunda ke faruwa yafi nan da labari ya gama Zaga gari. A chan sai tafi samun kwanciyar Hankali ta samu mijinta tayi aure zai fi ye mata kwanciyar Hankali daga ita har mu Amma" Amma kallonta kawai take yi idanuwanta har sun kawo ruwa. Takaici da bakinciki sun saka ta kasa mgana. Ni kuma sai naji kamar takaicin nawa ma ya Dauke gabadaya, hawayen da duka rage a cikin idanuwana na Share sannan na kariso cikin Dakin ina Danne yanayina. Naso na shareta ne ammh kuma Son nuna mata naji mganganunta yasa na kalleta ina Fadin"Sannu Adda Rukayya? Sai yau aka zo mana? Sai ta kasa mgana Daga ita har Amma ni suka kurama ido suna nazarina yanayina sai kawai nayi mirmishin karfin Hali kafin nace'"Amma shawaran Adda Rukayya ta yi. Gwara na koma wajen Adda na zauna tabbas zai min kwanciyar Hankali da ku kanku Gabadaya. Ga Habiba nasan zata kula Dake Amma." Na fada ina kwaso jarumta zuwa saman Fuskata. Jin kalamai na yasa Adda Rukayya ta samu kwarin gwiwa gyara zama tana Fadin"Ahto nima haka nagani. Amma kada ki dauki mganar nan da wata Manufa mafita na samo ma Hasiya da mu kanmu" Sai Amma ta kauda kai kafin tace"In kinga Hasiya ta bar garin nan to ki tabbatar ma kanki Rukayya kafata kafar Hasiya. sannan kafar Habiba. Nasan Fati zata rika zuwa Dubamu sannan Adda bazata gujeni ba, sannan bazata kyamaci Hasiya ba, har Abada ita din mafaka ce gareni da Ahalina" Mgana ce ta fad'a ba masu yawa ba ammh masu harshen damo ga mai Hankali. Adda Rukayya dai sai jikinta ya yi sanyi kafin ta tabe baki tace"Amma ni fa ba bakuwar zafi ba ce. Ki yi hakuri in mgana ta ta b'ata miki rai" Daga haka ta kakkabe jakarta ta fice daman abunda ya kawota kenan. Duk yadda Amma taso ta fahimci yanayina ban bata Damar haka ba Dakin na kakkabe na share Habiba na makaranta. Bayan na gama na kwashi wankin Amma na fita da shi na Daureye mata, Ruwa ma almajirai na saka suka Dibomin ruwan tunda Bohol din na kofar gidan mu, Fita na kuma ba zai yuyu ba. saboda ko'ina yi da ni ake yi na zama abar kwantace da nunawa. Kwana biyar tsakani Adda Fati da Ramatu suka dawo a bakinsu nake jin Salisu da gaske kano za'a kai shi Asibitin Dala ayi mishi Daurin asibiti. Hankalina duk ya tashi Daman a kwanakinan yana raina kamar naje asibitin na dubashi ammh ina tsoro tare da Fargaban me zuwa na zai iya Haifarwa. Ammh ban duba abunda zai iya zuwa ya dawo ba nayi ma Ramatu mganar zuwa asibiti na Duba Salisu. Itama ta jima bata ce min komai ba tana nazarin abunda zai faru, ammh bata min gaddama ba ta shawarci Adda Fati itama sai da ta jinjina kafin ta kalli Amma tana fadin"Amma kin ga ya dace Hasiya taje ta duba Salisu? Amma tace"Sosai ya dace ai mijinta ne. kuma rashin zuwan ma wata mganar ne in zai samu ki shirya har da ke aje a duba shi" Da wannan shawaran ta Amma yasa har Inna talatu da taji tace zataje itama muka Shirya Tafiyar. bansan yadda mganar ta fita har matan gidanmu suka ji ba, sai suma suka Daka Tsallen zasu je,nasan dai bai wuce ganin abunda zai faru achan ammh ban magantu ba. Ramatu ta yo lafiyayyen Ferfesun kifinta daga gida muka tafi da shi. Mota guda muka samu Bus,Tunda matan gidanmu su tara duk da zasu je, Son ganin Salisu da Halin da ya ke ciki ya Boye tsoron dake cikin Raina. Na shirya cikin Atamfata wata ja riga da Sikat duk cikin kayan aurena da Abubakar ne tunda lokacin akwati shidda ya yi min Shake da kayan alfrma. Sai na saka Jan Hijabi har gwiwana, fuskata fayau daman gata karama sai Zullumi ya kara kankantar da ita. Bayan La'asar muka tafi, tunda Lokacin Musbahu da Ramatu ta kira yace ana bari shiga. Mun shiga asibitin Chika Hud'u da minti Arba'in muna tafe tiri tiri har Emergency bayan mun yi tambayan shashen yan Hatsari aka nuna mana. Duk jikina sai ya kara mutuwa sai ya kasance na koma baya ina bin tafiyar Ramatu tamkar nima tsohon cikin gareni. Bansan wanda ya hangemu cikin yan gidan su Salisu ba ya je ya gayama sauran yan'uwan nasu dake chan wani gefe suna zaune. Mu dai muna tsaye ne Ramatu na kokarin kiran Musabahu muka ji muryan wani kanin Salisu yana fadin"Wa kuke nema? Gabana sai da ya amsa ganin su Ritutu, wasu ma ban san su ba. Nasan dai Salisu ba shi da mahaifiya ta rasu ammh suna da yawa a dakinsu. sannan mamanshi na da abokiyar zamanta itama da nata gayyar. Inna Talatu ne ta sanar da shi munzo Duba Salisu ne, sai naga sun fara kallon kallo kafin su yi mgana sai ga Musbahu yana fadin"Hasiya ne da yan'uwanta daman sun min waya zasu zo duba Salisu da jiki" Sunana kad'ai da aka ambata ya Rushe sauran Annurin su. Kafin ma mu yi wani motsi wata cikin matan nan mai Kiba ta bake kofar Emergency tana Fadin"A'a kuje kawai mun gode. Ammh bazaku shiga da gayyar tsiyarku ku karisa mana Dan'uwa ba" Inna talatu da Adda Fati suka kalli juna kafin Inna talatu ta Tausasa murya tana Fadin"Asshaa baiwar Allah meya kawo wannan mganar? Daga Dubiya sai kuma zencen mu karisa shi? Ai bamu muka sakashi cikin wannan Halin ba ballatana kice zamu karisa shi" Ta fad'a tana mai kwantar da kanta. Ba wacce ta tare kofar ba ce tayi mgana wata mai karamin jiki ne sai dai kallo farko zakayi mata kasan jinin Salisu ne domin suna kama sosai tace"ku ne silar shigar sa wannan Halin mana. Tunda silar auran yarku ce mai kashin Tsiya da bala'i. Ta nakasa mana Dan'uwa ga kuma asaran dukokiyon al'umma duk ta sanadin auranta me zamu ce da wannan auran? Ta bakin kofar Emergency tace"Sai Allah ya tsine ma auran kawai zamu ce Ikilima" Sai gabad'aya matan gidanmu suka saka salati na jimami har da masu gulma Ramatu taji jikinta ya yi sanyi ni take kallo ammh sai na samu kaina da jin kunyarta kaina na kasa ina kallon kasan asibitin cikin bushewar ido da na zuciya. Adda Fati da Inna talatu tare da Musbahu ba yadda ba su yi su barmu mu shiga ba ammh Su ka ki, bayan kuma suna ta bin mu da mugayen mganganu, Har hankulan mutane ya fara dawowa kanmu. Kallon Ramatu kawai nayi ina Fadin"Ramatu ku taho mu tafi kawai. Allah ya bashi lafiya" Kasa min mgana ta yi, ta tsaya tana ce min"Hasiya wannan abun da nayo fa? Sai da na kalli kwandon hannunta sannan nace"Ki ba wa Musbahu in kuma zai zama matsala mu koma da shi" Ba ta yi musu ba taja Musbahu gefe ta mikamasa kwamdon hannunta bayan sun yi mgana, yana ta bata hakuri tace bakomai, su Adda fati tayi ma mgana yasa muka fito daga wajen da niyar Tafiya. Matan gidanmu suna baya suna ta Gulma daman abunda ya kawosu kenan. A haraban asibitin muka had'u da Sahura da yan gidansu kallo kallo akayi tsakanimmu an rasa mai mgana, ganin tare take da wata yar Dattajuwan Mata Ramatu ke shaidamin Innar Salisu ce. Ina kallonta suka gaisa da Inna talatu da su Adda Fati cikin sakewa daga yanayinta yasa na Fahimci zatayi saukin kai ba kamar sauran ba. Cikin Fara'arta tace"kun samu ganin Salisun? Inna talatu tace"A'a ba'a barmu mun ganshi ba" Cikin mamaki tace"ah kuma la'asar ai ta gota. Lafiya kuwa.? Adda Fati Zatayi mgana Inna Talatu ta rike mata hannu tana fadin"Gudun Fitine kawai. Ayi masa sannu Allah ya bashi lafiya" Ni dai sai na samu kaina da Jawo hijabina ta sama ina Rufe fuskata. Nima yanzu kunyar nuna Fuskata nake yi ga Mutane da gaske ni din Annaba ce ko kuma nace gobara Daga kogi mganinta sai Allah. Inaga ta Fahimci mganar Inna Talatu yasa tayi ajiyan zuciya kafin tace"Rayuwar ne sai hakuri. Abubuwwn duk sun rikice ni na rasa ina zan kama. Ku yi hakuri don Allah gobe ma za'a wuce da Salisu kano ayi masa Daurin asibiti. Ku yi hakuri da duk abunda zai biyo baya don Allah" Inna talatu tace"Bakomai Allah yasa ayi a sa'a" Ta amsa da Ameen sannan muka wuce itama ta wuce, Tunda Sahura da gayyarta sun yi gaba suna harare harare da yada mganganu. Har muka isa gida ban tofa komai ba duk da ana ta maida zence a cikin motar. Amma ma Adda fati ta zayyanemata komai ta sauke numfashi kafin tace"Allah ya kyauta" Kowa jiki ba Dadi' haka Ramatu ta tafi tana kara bani baki nace mata bakomai Inna Talatu ne sai dare ta tafi gida Adda Fati kuma mijinta yazo Daukanta bayan ya shigo ya gaida Amma. Har ya bata dubu daya. Washegari wajen misalin karfe sha daya na Safe sai ga Musbahu abokin Salisu ya yi sallama da ni a kofar gida. Daman tunda naji ance Musabahu na kira na na saka faruwar abubuwa Biyu zuwa gareni. Ina fita kuwa dayan da na saka ne ya faru Takarda ya mikomin cikin sanyin jiki na saka hannu na karb'a tunkafin na Bude na san me ke ciki ba wannan ne karo na farko, da na taba amsar irin ta ba. Karfin halina Musbahu ya gani yasa ya ce"Kiyi hakuri Hasiya..Kiyi hakuri iya shi kawai zan iya ce miki. Ammh ki sani Salisu ba shi da laifi har ga Allah fin karfinsa akayi" Mirmishi nayi mai ciwo kafin nace"Bakomai Musabahu. Ka gaishe shi Allah ya bashi lafiya" Ya amsa da Ameen kafin yace"Yanzu zamu dauki hanyar kano." Na jinjina kai ina musu fatan Sauka lafiya. Har na shiga Dakin Amma bata Fahimci yanayina ba, ko bud'e takardan ban yi ba. Na turata cikin jakata ta ajiyan karikitai. Na fita tsakar gida na samu Habiba na Hura gawayi zata Damama Amma koko. Sai na Leka dakin Maman Boy nace ta aramin wayarta. Ta dauka ta bani chan wajen bayi naje na saka lambar Adda Fati da na riga na Haddace na kirata ta na Dauka nace"Adda fati Hasiya ce! Ban jira cewarta ba na cigaba da fadin"ki kira Inna talatu kuje ku yi mganar kwaso kayana gidan Salisu. Saboda ya sake ni d'aazu" Ina jin ta fara salati na yanke kiran. Lambar Ramatu na saka na kirata sai kudin suka kare ashe ya shiga sai ga shi ta biyo bayan kiran. Ina Dauka ko cewarta ban jira ba nace"Ramatu shima Salisu ya sake ni" Cikin Firgici Ramatu tace"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Kina ina ne? Ina danne kukan da naji ya tasomin nace"Ina gida. Wayar maman boy ce" Kashe wayar nayi saboda Duhu naji yana mamaye ganina. Ina juyowa muka had'a ido da Kaltume itama matar gidanmu ce tana kallona da alamu ta gama labemin taji duka mganata. Cikin son gulma tace"Ba dai shima Salisun sakin ki ya yi ba? Da kai na amsa mata. Ba na son kwakwazonta yasa na wuce ko kafin na kai Dakin ta fasa kururuwa tana Fadin"Shikenan shima Salisun ya saki Hasiya" Salisu ya saki Hasiya" Wancan ta karba wanchan ta karb'a har kunnen Amma. Ina shiga Dakin tace"Zo nan Hasiya" Ina kauce ma kallonta na zo na zauna agabanta. Cikin kallona tace"Salisu ya sake ki? Kai na gyad'a mata ban yi mgana kawai sai ta ce"Saki nawa ne? Ba musu na mike naje na Dauko Takardan na mikamata Ammi,tayi karatun boko da na addini. Kai tsaye ta warware takardan ta karanta kafin ta ninketa yadda take. Ni ta kallah cikin nazarina kafin tace"Allah yasa haka shi yafi zama alheri gareki damu gabad'aya Hasiya" Ciki ciki na amsa mata da Ameen kafin nace"Na kira Adda Fati,da Ramatu na fad'a musu" Kai Amma ta jinjina min kawai ni kuma sai ma mike na fice. Duk suna Tsakar gida kamar jimamin gaske suke yi na mikama Maman Boy wayarta na juya na koma Daki. Sai na tsiri gyara jakar kayana ina jin abunda ke sukan raina ya na tab'a har kashin bayana. Da gaske kenan abunda mutane ke fad'a a kaina ya tabbata? Tabbas ina da Farar kafa. Sannan zamana ko rab'ar mutane ba alheri ba ne. Salisu da Abubakar sun shud'e daga Duniyata gab'adaya, sun zama Tarihi kamar ma ba'a yi su ba. Sun shud'e saboda ba su ne daman Mahadin kaddaran ki ba HASIYA.! *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabooks:JamilaUmarjanafty* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki. *03* Sunana Hasiya Mamman kona, sunan mahaifiyata kuma Aisha-Jari. Bafullatar Garin gadan mallam mamman da ke hanyar Abuja. Mahaifina Alhaji Mamman Haifaffan garin zariya ne dake jahar kaduna, a cikin kuma tsangayar zariya wato anguwan limancin kona. Sunan mahaifin shi wato kakanmu kenan wanda shine asalin Tushen mu, Alhaji Mammadi Mamman kona. Shima tun asalin tale talen iyaye iyayen su haifaffun garin zariyan ne ma'ana gaba da baya jinin zazzagawa ne su d'in. Alhaji Mammadi Mamman kona Manomi ne kuma sannan masaki ne yana dinkin Sakan aikin hannu na manyan mutane har da sarakuna. Sannan yana saka hula shima na hannu kala kala, Dalilin da yasa ya yi suna shine Aikin hannu da kuma Hulan da ya kan saka ma manyan mutane da Sarakun gidan Sarautar zazzau. shiyasa duk wanda ke garin zariya ya san tarihin tsohon gida na Alhaji Mammadi mamman kona. Tunda a zamaninsa da kudin Sakan sa yaje makka sannan ya mallaki gida kuma ya auri mataye har guda biyu a rana d'aya. Salamatu da Lauratu sune matan na shi suma kuma duka haifaffun garin zariya ne. Kafin rasuwarsa ya tara ya'ya goma cif,Lauratu ke da Hud'u. Salamatu ita tayi shida, ciki har da mahaifin mu wanda aka maida masa sunan Muhammad, sai a ke kiransa Mamman kamar yadda sunan ya ke. Alhaji Tanko ne Babba sai Mamman, sai Hasiya, akwai muhammad Sani, Hajara sai Halima ita ce karamar su wacce yanzu haka take aure a garin ikko tana zaune tare da iyalanta da mijinta. D'akin Lauratu kuma akwai Jibril shine Babba yanzu haka kuma yana nan da Ranshi yana aiki da babbar ma'aikata a kaduna sai Saratu, Goggon Kona kenan itama tana da ranta a garin zariya sai Saminu da Muhammad Auwal shi yana saurayi ma ya rasu ko aure bai kai ga yi ba. Labarin mahaifina na ke baku, ammh zan tabo bangaran dangin babanmu ne saboda kusan ta ko'ina cikin gata na taso kafin tsaka mai wuyar da nake ciki ta jefani ni da iyayena da yan'uwana cikin halin k'ak'ani k'ani. Babanmu Alhaji Mamman kona, ya yi karatun boko zuwa na arabi tunda Mahaifinsu mutum ne mai yalwata ma iyalansa kafin mutuwarsa. Ya yi kokarin had'e kan iyalansa kafin mutuwarsa kuma Alhamdulillah a lokacin kawunansu a had'e suke kafin mutuwarsa ta yi sanadiyar tarwatsa komai. Tun bayan rasuwarsa aka raba iya abunda ya bari kowacce taja barayinta ita da ya'yanta daga lokacin sai zumunci ya samu Rauni, kowacce ita tayi fad'i tashin ta ita da ya'yan da aka mutu aka bar mata. Ita lauratu da ya'yanta su suka ci wannan gida na limancin kona,ita kuma salaamatu ta samu na anguwan Madaka itama tare da ya'yanta. Shiyasa sai kowacce ta koma inda ya'yanta da ita kanta suka gada suka zauna. Daga lokacin sai abun ya koma in na samu ya'ya na. In na samu dan'uwa da muka fito ciki D'aya sai had'uwa ta yi wahala abubuwa suka yi ta faruwa batare da Sanin junansu ba. Alhaji Tanko shi ya gaji Alhaji Mammandi wajen saka huluna da Aikin hannu na riguna Darajar Mammandi kona yasa shima sana'ar ta karbesa sosai. Babanmu kuwa d'an boko ne tunda tun alokacin sai dai ya yi NCE. Sannan ya fara kasuwancin saida taki, tare da Dillanci sai da Filaye da kuma kama Hanyar gona in za'ayi Noma. Da wannan sa'anar ya yi karfi kuma da ita ya yi aure da mahaifiyar mu. A rugar da ke Gadan mallam Mamman ya ganta Farar Doguwar bafullatana da bata jin eh na ko da ilimin boko da arabiya, yana ganinta ya ji kuma ya gani ya na so. Sun je du ba wata gona ne ta wajejen ya ganta tana tallar Nono shikenan ya ga mata. Amma a gidan auranta ta samu ilimin addini da mu'amala da mutane, Marainiya ce daga ita sai ya yarta Hannatu_Hari Adda. Sai baffan su da ya rike su ya rasu shekarun baya. Mu dai mun taso mun bud'e ido mun ga rayuwarmu cikin gata da jin dad'i. A anguwan alkali na bude ido na ganmu muna rayuwa cikin gidan mahaifin mu tare da mahaifiyarmu da muke kira Amma da Sauran yan'uwana. Mu hud'u Amma ta Haifa Adda Rukayya ce Babba sai Adda Fati, sai ni Hasiya da Amma ta ce sunan kanwar baba ce da ta fad'a rijiya ta rasu aka maidamin. Sai Habiba da ita ce karamar mu. Tun tasowar mu bamu san wani wahalan rayuwa ba har mota babbanmu ya mallaka sannan daidai gwargwado za'a sakamu cikin masu rufin asiri. Na taso naga kowa a dangi na son mu da kaunarmu. Na kuma san babban mu ya rasa wasu daga cikin yan'uwansa ammh na san Alhaji Tanko Baban mu ne,Sai Goggo Halima dake aure a garin Lagos, muna kiranta Baaba. Na kuma san gidan Baba saminu da ke Limancin kona gidan da bayan Rasuwar mahaifiyarsu Lauratu suka gyara shi Baba Saminu ke zaune aciki da iyalansa. Baba Jibril kuma yana garin kaduna yana aiki chan ya ke zaune tare da iyalansa. Tunda muna zuwa in aka yi haihuwa ko auren. Amma ta fi zuwa anguwa da ni, ni ma kuma tun ina yarinya ina da son yawo duk inda za'a je sai na saka Rigiman sai an je dani. Ko da muka taso kakarmu Salme ta rasu. Amma tace auran su ba jimawa Allah ya yi mata rasuwa. Lokacin da na taso ba ni da wayau bansan me ake kira da rayuwa ba shiyasa ban taba kawo ma kaina a dangin Babbanmu kowa kansa ya sani ba Daga kafa sai kauri. D'ana nawa ne D'anka kuma na ka ne. Doguwa ce ni sambal ba ni da kiba kamar a hureni na fad'i ne. Ammaa na biyo har ta farar fatarta domin jajir take to ni har na fita Fari ma. Kaf a dakin mu na fi su fari su kuma sun biyo Duhun Fatar babbanmu sai suka Sirka ammh ni Farina har yana Daukan ido, mutane in suka ganni sun sha tambaya ko iyayena Zabiya ne? Suna tunanin kalan Fari na kad'an ne ya rage ban zama zabiya ba. Ga ni ba kiba sai farin kawai da Doguwar Fuska sannan ina da ga shi, wanda sai daga baya na same shi Amma tace ina yarinya kaina kwaikwai ne duk su Fati sun fi ni sumar gashin kaina ammh daga baya da na Fara girma sai duk nazo na Kire su sumar kai da cika. Wani abun mamaki kuma komai na jikina karami ne kafafuwana sanda ne sirara, haka hannayena da kaina kamar kwai in ji su Adda Fati. Na san mun samu ilimin zamani da na addini daidai gwargwado. Ban san wahala ba kuma ko labarinta ban taba ji ba, sai shekarar da na kamallah karamar sakandiri gobara ta tashi a gidanmu da komai sai da ya kone dagamu sai kayan jikin mu muka fita da shi. Daman Amma ta taba bamu labarin Ranar da ta haifeni gobara ta kama Dakin da Babbanmu ke ijiyan Takinsa ba'a fitar da komai ba. Dalilin wannan gobaran ma ya tafka asara mai yawa. Ban taba kawo kaina gobaran da ke faruwa da mu na da alaqa da ni ba, sai da bayan Baba ya kama mana Hanyar wani gida yana ta fad'in tashin neman yadda zai yi tunda asarori ya tafka ba kad'an ba. Wata gobarar ta kara tashi a inda muka koma,shi dai Allah ya takaita Daki d'aya ta ci wato dakin Babbanmu itama ta lashe kudad'e da wasu takardun filaye. To fa daga Lokacin aka fara mganganun a nemi taimako ana tunanin ko Aljananu ne. Babbanmu duk ya toshe kunnewansa daga mganar mutane ciki har da yan'uwansa. Sai ya kasance Gobara ta zame mana jnin jiki. Ba'a daukan wata uku gobara bata Lashe wani abu na Kudi ko kaddara ba kuma arasa ta ina Gobaran ke tashi. Tun ana Fad'i daga nesa har ya zo kusa ballatana da karayan arziki ta samu babbanmu komai da ya mallaka sai da ya kare ya dawo gida ma yana jinya ciwon kafa haka kurum ta rika Duran ruwa ta kumbura fita ma ya gagaresa. Ni bansan daga ina mganar ta fara fita ba ammh na san rana tsaka na zama abun gudun mutane da sunan cewa ina da Farar kafa haihuwata ita ce silar Komai sannan duk in da nake gobara bazata daina tashi ba. Sannan baza'a daina saran dukiya ba. Daga karshe ma har da rai sakamakon rasuwar babbanmu sai mganar ta fito fili kowa ya jita. Da rasuwar babanmu da Ciwon Amma duka acikin shekara d'aya komai ya faru. Da kuma tsarwatsewar rayuwarmu daga sama zuwa kasa. Tsangwama da Hantsara ba bu wanda ba mu sha ba a wajen Dangi da Mutanen gari ba duk saboda ni, Naman jikina ma sun ce ba mai kyau ba ne jini na ba jinin alheri ba ne. Dalilin da yasa zama a ganuwar zariya ya gagaremu muka koma Samaru da zama a gidan haya. Ba'a dogon gida muka fara zama ba sai da muka zauna a wani gida dake Anguwa y'an Randa, shima watanmu biyu akayi gobara maigidan ya tadamu, sai muka koma layin tsamiya Dogon Gida. Fad'in irin fad'i tashin da Amma ta yi bazai fad'u ba, tana halin ciwo yau ciwo gobe sauki ta rika sana'o'in hannu domin inganta rayuwarmu. Ta yi saida abinci alale, Alkubus, Danwake da kayyyakin gidajen na mata duka Amma ta yi shi tunda Dangin Babbammu sun gujemu saboda ni kowa ya ce bazai Dauki bala'i ya kai gidan shi ba. Kafin mu samu gida a samaru gidan Baba Saminu muka zauna Satin mu daya ya koremu saboda Gobara ta tashi a kitchen ranar ya ce Sanadina ne. Tundaga lokacin Amma ta tsame kanta da mu daga rab'ar zuru'armu. Da taimakon Amma da kuma Jajircewan Adda yayar Amma muka cigaba da rayuwa, bayan Amma ta gama Saida komai na gadonta Adda bata barta haka ba taimako daidai misali tana kawo mana. Komai a ke fad'a a kaina Amma bata yarda ta kan ce"Hasiya ki kwantar da Hankali Canfi karya ne kambun baka Annabi ya sanar da mu. ba bu farar kafa ba bu maita" Tun kalamanta na tasiri har suka Daina min tasiri na Fahimci da gaske dai ni Hasiya ina da Farar Kafa. Abubuwa sun yi san yi da Had'uwar Amma da Inna talatu a Dogon gida ni kuma muka kulle da Diyarta Ramatu sannan tun dawowarmu sai gobara bata kara bin mu ba, Na samu na cigaba da makarantar gwammati Adda Fati ce gwammati ta biya ma Neco. Adda Rukayya daman ta gama ita. Amma bata kwanta ba tana sana'ar sai da Danwake da wake da shinkafa da wake da mai da yaji kuma tana samu tunda ga Adda fati na tayata,nima kuma ba ni da kiyuwa ina da son aiki. Da farko rayuwar ta juya mana baya ammh daga baya sai ta waiwayo mu. Adda rukayya ta samu miji mai hali ma'aikacin gwammati. Sai da mganar aurenta ne Amma ta nemi dangin su Babanmu suka shiga mganar, muna tunanin In Adda Rukkya tayi aure zata ji kanmu ashe ba haka ba ne. Shanun Adda aka saida akayi mata yan kayan Daki tare kuma da sana'ar Amma na ba dare ba rana. Adda Rukayya ta na da wani Hali bata da son yan'uwa kuma bata da Kulafacin uwa ballatana damuwa da Halin da muke ciki,bkomai daga bangaranta ba ma samu tun Amma na Damuwa har ta daina ni daman ban wani shaku da ita ba, tunda ta sha Hantarata da mai Farar kafa har tab'a ce min tayi"Wannan Farin fatar naki ba na banza ba ne. Yanzu haka na tsiya ne da Talauci." Sai da Adda Fati ta yi aure ne sannan muka san taimakon daga bangaran gidan surukai, Habibu mijinta Bakanike ne, kuma yana da Rufin asiri yana sonta,shiyasa mu ma ya ke rikemu da Daraja alherai kala kala yana yi mana sai godiya. Adda Rukayya kuwa ba ta ma Dauke mu da Daraja ba ballatana shima mijinta da Danginsa su darajamu. Mijinta ma kwata kwata zuwansa gaida Amma bai kai sau biyar ba. Kamar ma kyama muke ba shi. Ni ko daman Adda Rukayya ta sha fad'in ni ce na saka Baba ya rasa komai na shi muka talauce kuma kafin mutanen gari su fad'a masa ita ta gayamasa. Shiyasa bai taba amsa gaisuwata ba acewarsa irin mu ko mgana da Fatar baki ce sai ya bi mutum ya Lalace. Bazan ce ban da mu da karatun boko ba,ga yanayin da mu ke ciki yasa ban zurafafa ma kaina sai na yi karatun boko ba, Na san na iya karatun Hausa da Rubutu sannan na iya karanta Turanci iya inda zan iya, Karatun addini kuma ban zurfafa ba,na yi islamiya a anguwan Alkali bayan dawowarmu Samaru na shiga makarantar Dare ta mallam Habu tare da Ramatu na san addinina daidai gwargwardo. Sallah da yadda zan gyara ibada ta gabadaya da sanin hukunce hukunce tsarki da sallah,sanin abu mara kyau da mai kyau, sannan ina iya karanta bakin karatu a duk in da na ganshi. Tun tasowata bazan ce ina da Farinjini ba, ballatana ga yanayina ba kowa ne in ya ganni yake jin ina Burgesa ba ko kawa ban taba yi ba sai akan Ramatu shiyasa har gaban Abada na ke jinta a raina. Sannan na ke sakata cikin farkon Farkon jerin masoyana. Ko a cikin dangin mu ana Hantara na ballatana ga jama'ar gari shiyasa kasancewa ta, mai farin jini bai dameni ba. Ban san me ake kira Saurayi ba sai dai in ga ana zuwa wajen Ramatu ni kuwa bai dameni ba na fi damuwa da lafiyar Amma tare da sana'o'in da muke yi domin rike kanmu. Amma ciwon ta ba shi da suna ko sanadi, ta fara shi daga zazzabi mai zafi sai kuma karkawa da ciwon kai mai tsanani da abun ya yi girma sai ya ke had'a mata har da Ciwon duka gabbanta,kafa, Hannaye, baya da sauran su in ta farashi kamar bazata ta shi ba, sai an kai ta asibiti an mata allurai da ruwa sannan ta ke dawowa hayyacinta. An yi gwaje gwaje har an gaji an rasa gane sanadi ko ciwon, mgana D'aya ce Typoid da Maleria ne, ammh kowa ya ga yadda Amma ke jin jiki sai ya ce ciwonta ya fi karfin maleria. Ta rame ta Lalace ga ciwo ga wahalar rayuwa. Ni da Habiba mu ne karfin sana'ar Danwake da shinkafa da wake,sau biyu muke yi a rana da Safe da yammah, ni na ke yin na safe da yammah kuma Habiba in ba makarantar yammah sai ta kama mun, Amma kuma ba ta iya zama sai dai in ciwon ta ne ya yi tsanani. Mace ce mai kazar kazar da son kai da kawo ta na da karfi na Fulani acikin jikinta kamar yadda Adda ta ke, itama mace ce kamar maza a tsaye take kan kafafunta ta fi Amma Lafiya tunda ita har yau har gobe bata da wani ciwukan wannan zamanin. Ba mu da kowa sai kawunan mu sai Allah, sai Adda fati da ta ke taimako mu, sai Inna talatu tunda Yayan Ramatu tela ne na mata kuma yana samu sosai, tabbas zaman su a gidan nan sun taimaka mana matuka. Adda Rukayya kuma ba ta cikin Lissafi ita wannan da ita da ba bu duk D'aya ne sai ta jima ba ta zo ba, in ma tazo ba ta zuwa da komai, matar da ko haihuwa zata yi sai dai ta kira kawayenta ko Dangin miji sai daga baya ma muke samun Labari. Adda fati ke zuwa ni tun sunan Yarta ta Biyu Madina. Da muka je dangin mijinta suka rika nuna ni suna mganganu. Har suna fad'in daga ganin fari na daman na cuta ne ba na lafiya ba, Allah ya sa ma ba maita na ke da shi ba, a gabanta kuma bata tsawarta ba Da Adda Fati ta yi mgana sai ta fara Fad'an in mun zo mu watse mata taro nata ne, mu kara gaba ta gode. Tundaga ranar ban kara kafafuwana ba su kara taka gidanta ba sai jikin Amma da ya tashi na je na gayamata ta fito ta ce min kada na kara zuwa saboda Mijinta ya ce ba ya son ina zuwa masa gida. Ba ni da Fad'a ina da mgana ni d'in ba Shuru Shuru ba ce sai dai na san a inda na ke yin sa, Ina da wani Hali na zuciya da Taurin kai ko dan'uwana ne ya nemi ya wulakanta ni ina janye jikina Daga garesa wulakanci ne babban abunda zaka yi min kaga bacin rai na. Ko ka taba Amma to a nan ne zaka ga ainihin wacece Hasiya Mamman kona. Bazan iya fad'in wani lokaci ne Abubakar ya shigo rayuwata ba. Ni dai nasan watarana na je kasuwa siyo ma Amma dawa da rogo na garin Danwake, muka had'u da shi a bakin Hanyar cikin motar abokinsa,ya yi min mgana ya nemi lambar wayata na ce masa ba ni da waya sai ya nemi na kwatanta masa gidanmu. Na kwatatan masa, a daran ya zo ya ganni mganarsa ta farko da bazan taba mantawa ba ita ce"Hasiya ni fa son ki na ke yi da gaskiya. Kuma in sha Allahu Auran ki zan yi" Tabbas mganganun sa sun yi tasiri a raina yadda ya ke d'an gayu dan boko dan gidan manyan mutane. Gidan su gidan arziki ne,tunda Mahaifinsa dan kasuwa ne shima Abubakar din Shaguna garesa na kayan yara a kasuwar sabon garin Zariya. Fari ne tas Bakano ne tunda Mahafinsa bakano ne mahaifiyarsa yar Danja ce da ke jahar katsina. Ni da bakina na fad'amai komai da ya danganci Rayuwata saboda naga kamar yanayinsa ya yi nisa da tawa rayuwar ammh ya ce yaji ya gani. Har ga Allah kyakyawan dabi'unsa mu'amalansa ya sa na fara son shi ban sani ba. Abubakar ya yi min komai a rayuwa in nace komai ina Nufin komai!. Ya so ni,ya kaunace ni a yadda na ke ya kuma toshe kunnuwansa da duk wasu suka ko yarfe a kaina shi dai ya ce yaji ya gani. Abun da ya yi min da har gobe na ke jin sa a raina ya Daraja abunda ya ke a kusa da ni. A lokacin ko ni ban kaisa kula da Lafiyar Amma ba. Ba ni da fargaba ciwon ta ya tashi Ina da Abubakar. Cikin Lokaci ya maidani mace mai aji da alfarma ya siyamin waya da kayan kwalliya da Suturu ban san iyaka ba. harta Kanwata Habiba yana yi mata Hidima Amma ko har yau ta na Daura d'aya daga cikin irin kayan da Abubakar kan siyo ya bata. Adda Fati har gobe ta kan ce bazata daina min bakincikin Rabuwa da Abubakar ba Masoyi ne da ya amsa sunan masoyi a gareni. Har gidanta mun sha zuwa tare, Har gadan mallam Mamman mun je na kai ma Adda shi sun gaisa ta na ta saka albarka bakinta ya ki rufuwa. Ban tab'a tunanin watarana soyayyata da Abubakar zai iya kasancewa a tsaka mai wuya ba. Na riga na gama sakin jiki da shi ban sani ba ashe sanda ya kai mgana ta gidansu a kayi bincike komai nawa sai da aka warware har da Kagen abunda ma bai faru ba. Mahaifiyarsa ta yi tsalle tace Allah ya tsareta Abubakar ya auro mai Farar kafa Rigima ta yi tsami domin Abubakar ya ce sai ni Hasiya. Gaddama ta farko da ya taba yi ma iyayen shi a kaina, ni bansan Halin da ake ciki ba tunda baya Fad'amin. Sai da Mahaifinshi ya tsawarta da mganar yace abunda Abubakar ya ke so shi za'ayi mishi. Shi ya jagoranci neman auran wajen Dangin Babbanmu Alhaji Tanko shi ya karbi mganar Tunda shi ne waliyin mu. Kuma ba kunya ba tsoron Allah. Ya ke karb'an mgana ba tare da sanin ya muke rayuwa ba. Ammh yana karb'an mganar ne sisin shi in bai ga Dama ba, bazai ba da ba. In sha'anin ya tashi matansa su zo in kuma bai ga dama ba, ba wanda muke gani. Ballatana ya'yan sa da suke ganin kansu suma wasu ne. An saka mana Rana da Abubakar wattani bakwai. Dalilin da ya kawo Kannen Abubakar gidan mu. Har tsakar gidanmu suka ci mana mutumci, sai ga sirrin mu A bakinsu suna mana maimaici. Sai alokacin nasan Dangin Abubakar ba su sona. Da nayi masa mgana sai yace kada na Damu shi dai yaji ya gani. Na tab'a masa tambayar "Haka zai aureni Ahalin ina da farar kafa? Kada wani abu ya same shi fa? Dariya ya yi kafin yace'"Farar kafa ba shi cikin addini ban yarda ba Hasiya ki bar ma wannan Tunanin Allah ne ya isa ya yi komai ba Mutum ba'" wannan yakinin na shi yasa na kara sakin jikina a kan Abubakar ballatana da Mahaifin shi ya zo har gida ya ba ma Amma Hakuri sannan ya Tursasama kannen Abubakar suka Dawo har gida suka ba ni Hakuri ni da Amma. Sai mgana ta wuce zukata suka samu natsuwa da kwanciyar Hankali. Komai da akayi min na aurena Amma ce da Adda Hari, sai Adda Fati da ni kaina Tunda ina samun kyatuttuka wajen Abubakar na kudi da Suturu, sannan ga Ramatu a gefe lokacin itama ta Had'u da Nura shima ba laifi yana sonta sannan Hidima Daidai misali ya na yi mata. Ga Inna talatu ita ce kamar Aminiya wajen Amman mu, an yi min kaya Daidai misali na yar talaka. Gidan da Abubakar ya na a Hanwa ne 2bedroom da falo sai kitchen an samu dai an yi min gado d'aya. Shi ne wajibi wadanda sukeje jere sun dawo suna Santin Muhallina. Akwatuna Bakwai Abubakar ya yi min shake da kayan alfarma kayan da aka jima ana zencen su a gidanmu da anguwan gabad'aya har ta da dangin baban mu da ban san ta ina labari ya je musu ba, sannan sunzo ganin ma idon su. Ko acikin Dakin ku akwai wada'anda basa son Cigaban ka. Irin Adda Rukayya ce kiri kiri ta kalleni tace" ina fatan kin fad'a masa gaskiyan yanayin ki? Sai na kasa bata amsa Adda Fati ce ta mata mgana sai ta tabe baki tace"Ahto gwara dai a fad'amai tunda wuri kada wani abu ya biyo baya. " Ni fa na jima da cire Adda Rukayya a matsayin yar'uwata na riga na gama Fahimtar ta, bakinciki ta nuna da Hassada ga nin ko ita albarka. Ta rika Fatan wani Sanadi ya yanke wannan jin Dadin da zan shiga Tunda tun asali bata kaunata. Shiyasa ba zata so Cigaba naba. Tunda ta na Dauka komai ya faru damu ni ce sila. Tun Amma na Dauke mata kai, har sai da ta dawo tana mata Fad'a in ta yi wani abun gaban mutane. A chan gidan Marigayi Mammadi Mamman kona aka daura aurena da Abubakar. Auran da ya zo cikin Tarin kalubale da ban tab'a tsammanin Farincikina zai koma bakinciki da kuka ba. Lafiya lau muka yi taron biki na tara yan makarantar mu ta Dare sai makota ma su zuwa ganin kwakwaf. Sai Adda da iyalanta sai matan gidanmu sai Matan Baba Saminu da iyalansu sai Goggon Kona Baaba ta Lagos sako ta turo ma Adda Fati dubu ashirin tace a ba ma Amma ba yawa. Alhji Tanko da Baba Jibiril ba sako ba aike ba kuma iyalansu. Amma daman bata jira su ba. Har gwara Baba Saminu bayan Daurin aure ya zo har gida ya yi ma Amma Murna shi daman ko matansa na kukan Son abun Hannunsa ba ya kwantuwa. Na dauka sanda aka kaini gaban Amma ta min nasiha na yi kuka na har abada kenan. Ashe ban ma yi kukan ba, An kai ni gidana a d'aya daga cikin Tsala Tsalan Motocin da abokan Abubakar suka kawo mana. An je da yawa kuma duka motocin sun Dauke mutane da Kafar Dama na shiga gida tare da Rikon Inna Adda da Goggon kona. Na samu salama da farinciki Lokacin da na ji ni saman gadon aurena. Daga lokacin hayaniya da Mganganun mata ya rika tashi an kawo mana abinci da nama da Ruwan gora sai lemuka an ci an sha har mutane sun yi guzarin sa. Zuwa Tara na dare suka maida mutane gida Ramatu kad'ai a ka bar min sai da Angaye suka shigo. Bayan yan Nasihu da barkwanci suka mike suka tafi. Ina kuka Ramatu na kuka muka Rabu. Na san Abubakar ya raka su ya kuma dawo bayan ya Rufe gida, ya zauna a gefe na yana kiran Sunana da Hasiya Amarya. Na ga sanda ya cire Babban Rigansa ya fita sai ga shi ya dawo da Filet da Kofuna ya baje kazan da ya shigo da shi. Shi ya rika ba ni a baki har na koshe daganan duk wata Hidima shi ya yi a wannan daran ya jagoranci sallar Nafilan albarkan aure. Daganan ya bi da ni cikin Salama har ya maidani Cikakkiyar mace mun yi kwanan Farinciki da Annushuwa. Daga wannan Daran har rabuwata da Abubakar bamu kara kwanan Farinciki ba. Da asuba wayar sa ta tashemu da mummunan Labari da ya yi silar Rugujewar aurena. Labarin Shagunan Abubakar sun kama da wuta cikin Dare ko Tsinke ba'a fitar ba. Abubakar ya fita cikin tashin Hankali ya baarni cikin Zullumi. Zullumin da har na yi wata uku gidan Abubakar ina cikin shi. Da D'aya da D'aya komai na Abubakar ya ke karewa Wuta ba'a san ta ina ta ke fitowa ba ita ke lashe komai. Bayan konewar shagunansa Mahaifinsa ya Farfado masa da Shago daya shima ko wata bai yi ba wuta ta lashe komai. Kuma duk inda wutar ta tashi tsinke ba'a Fitar da shi. Dangin sa suka taso min caa akan ni ce sillar duk abunda ke Faruwa. Tun Abubakar na Boye min Damuwarsa har ta kasa boyuwa ta bayyana. Abubakar ya yi shaguna sama da Biyar Gobara na lashe su na karshen ya tafi kano siyayya a hanya bata gari suka masa dukan kawo wuka suka karbe kudin suka watsar da shi a bakin Hanya. Sanadin da Abubakar ya rasa komai na shi. sannan shima Mahaifinsa ba shi da shi, tunda shi ya rika tallafama Abubakar jari. Shigowar Abubakar duniyata yasa na aminta da Mganar Ammi na ba mai yi sai Allah. Ammh daga Lokacin da abubuwan suka yi ta faru dani na aminta da cewa ni Hasiyar Bakar tsiya ce. Tabbas na zama Sanadin Lalacewar arzikin Abubakar na yi kuka kamar raina zai Fita auran mu na da wata uku Mahaifiyarsa ta zo har gida ta saka shi Gaba sai da ya Rubutamin Saki biyu. Yana kuka ina kuka. Har kuma gobe ban kullaci Abubakar ba na san shi din mai sona ne duk mganganun da gari ya dauka a kaina bai taba aminta ba in nace ni ce sanadin komai sai yace ba ni ba ce daga Allah ne shi ke da Jarabawa da Kaddara. Rabuwar aure na da Abubakar da abubuwan da suka biyo baya. Sai Tambarin sunana ya amsa kuwwa a gari, Hasiya na da Farar kafa Hasiya Bakar tsiya ce, Hasiya ba Alheri ba ce. Ban isa na hana Mutane fadin abunda suka gani a kaina ba. Na san har na gama Idda ina kukan Rabuwa da Abubakar. Mun rabu rabuwar da har yau ban kara ganinsa ba. Na dai ji labarin ya bar zariya ya koma kano wajen yayan babansa ya na tayashi kasuwanci. Gama iddata ba Dadewa aka yi auran Ramatu, sun koma sabon gidansu da Sati d'aya aka yi bikinta da Nura sai Kadaici ya yi min yawa. tunani da mganganun mutane duk ya isheni ba'a waje ba acikin gidanmu ma ana yadamin mgana. daga kuma Lokacin sai jikin Amma ya rika rikicewa ba'a wata bata ziyarci asibiti ba sai karfin Sana'ar da duk wata Dawainiya ya koma kaina. Kayan aurena kuma Wata Dilalliya da ke kusa damu aka baiwa ajiya tunda ba mu da wajen Ajiya. Har ga Allah na cire rai da kara wani auran na Dauka kowa yasan me ke faruwa da ni in wani namiji ya Rabe'ni ma manta Allah ke yin komai a lokacin da yaso. Ba zato ba tsammani sai ga Salisu ya shigo Rayuwata. Da ya yi sanadiyar wanke duk wani bakin Fentin da Auran Abubakar ya shafamin. Salisu shima ya kaunace ni. Ya so ni da dukkan Zuciyarsa. A auran Salisu ban saki jiki ba. Nasan abubuwa da dama za su iya Faruwa ammh ban tsammace su yadda suka faru d'in ba. Aure na da Salisu ya zama kamar ba'ayi ba. Cikin lokaci Allah ya raba wannan auran da shi da kanshi ya Kulla shi. Ina tunanin tunda Rayuwata ta na cikin Tsaka mai wuya mafi al'ala na cire mganar aure a raina na tsaya na kula da Amma tare da Habiba. Ammh tabbas na Fara Tunanin na Lallashi Amma mu koma Wajen Adda Hari in da ba kowa yasan ni Hasiya Bakar tsiya ba ce. Na cigaba da Bautar Ubangiji da kula da Amma, har ta Allah ta kasance dani. Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari. Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah. Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari. Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah. Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus *04* *Bayan Sati D'aya* Bayan Sati d'aya da sakin da Salisu ya aiko min da shi, Kamar ba'ayi ba. labarina tsakanina da Salisu ya Shud'e kamar bamu taba Had'uwa ba, Kayana da aka riga aka jera tun kwana biyu da sakin su Adda fati suka je suka kwaso min kayana. Maganganu da mugayen bala'i ba irin wanda Sahura da danginta ba su jefani da shi ba. Wannan karon ma Dilalliya aka bawa ajiyan kayan sauran kuma Adda Fati ta tafi da su gidanta. Sauran kayan kitchen kuma gidan Ramatu na kai mata ajiya,tunda ita kad'ai ne a gidan kuma 2bedroom gareta, guda daya ne ke da gado d'ayan tarkace ne aciki. Ko sau d'aya ban bari damuwar da na ke ciki ta bayyana saman Fuskata ba. Saboda Amma nasan irin ciwonta nasan irin tashin hankalin da na ke shiga in Amma na ciwonta, shiyasa na ne kafa kafa da lafiyarta. Ni kaina nasan na yi dauriya sosai ban zauna nayi kuka ba, ko hakurin Adda Fati da Ramatu suka rika ba ni, ko a fuskata ba su ga alamun na damu ba. Duk da mgana ta zaga gari har gida ake zuwa da sunan yi ma Amma jaje, saboda kawai a ganni a fita ana nuna ni, a dangin Babanmu Baaba ce kad'ai ta lagos ta kira Adda fati suka yi mgana. Tace Goggon Kona ta fad'a mata aurena ya sake mutuwa, Kuma ta saka bayan Adda Fatin ta zo gida ta mata Flashing ta kira suka yi mgana da Amma. Nima an bani tayi ta ba ni baki, Sai Baba Saminu da ya zo da safe Ana sati da abun ya share kafa yana ce ma Amma abun nan fa ya yi yawa,ya kamata a nema min mganin Farar kafa har da na maita ma. Amma kamar ta yi kuka cikin Dauriya tace"Hasiya ba ta da Farar kafa, sannan ba ta da maita. Ba ta gaje ta ba, ni ba mayya ba ce sannan uban ta ma da Maye ne da kun sani" Kalaman Amma yasa ya fara kame kamen mganganu kafin ya yi mata sallama ya shura takalmansa ya fice. Ranar Amma ta sha kuka, ni kaina mganar tasa ta dakeni Maita fa? Zargin maita ai abu ne mai wahalan sha'ani. Saboda damuwar da na ga Amma ta shiga yasa na ce mata mu koma ga sana'armu tunda dai komai ya wuce, Da ya ke jarin duk ya lalace saboda sha'anin bikin nan, sai muka fara da Danwake ,shinkafa da waken sai zuwa gaba in jarin ya tarfu sauran siyayyan rogo da dawan ma Habiba taje kasuwa ta siyo komai ni ba ni da Damar Fita, Tunda in dai na fita sai na zama abun Nuniya. Ni na ke jefa Danwaken Amma na taikamin da zubawa, kuma ana ciniki sosai, Saboda matan gidanmu suna siyan ma ya'yan su har da mazajen su. Da kuma makota tunda a irin gidajen da muke zaune ba kasafai akan Dora abinci ba yawanci an fi siyan irin su Danwake da Shinkafa da wake na Saidawa sai su awara a samu a ci a sha ruwa. Duk da ina nuna komai ba komai ba ne ni kada'i nasan Halin da na ke kwana ina tashi, Kirjina suya ya ke yi ji na nake yi kamar ba ni da Sauran amfani,ammh in na Tuna Amma sai naga ina da amfani a wajen Amma bayan ni bata da kowa. Salisu na raina, ba ni da in da zan samu labarinsa shiyasa na ke masa addu'an Allah ya bashi lafiya ya dawo da kafafunsa cikin koshin lafiya. Habiba sai asabar da Lahadi take zama a gidan ranakun Sati kuma tana zuwa makarantar Boko da Safe, da yammah kuma taje islamiya, da Daddare kuma ta je makarantar Dare. Shiyasa yawancin ayyukan gidan suna kaina, Daman kula da Amma ni na Daukeshi a wuyana da kaina ina Kafa kafa da lafiyarta fiye da tawa lafiyar. Adda Rukayya sai sati uku da Faruwar abun ta zo gida tana ta yamutse yamutsen Fuska tazo ta sameni ina Dafa shinkafar yammah, tunda mun fara satin da ya shige lokacin da ta shigo ina kofar Dakin Amma ina gyaran shinkafa. Sama da kasa ta kalleni ba ta tankani ba sai ni ce na yi mata mirmishi ina fadin"Adda Rukayya ke ce tafe?Sannu da zuwa." A saman lebe ta amsani ta rab'ani ta shige ciki ina jinta Suna gaisawa da Amma. Shuru na dan wani lokaci kafin naji ta ta na fad'in"Amma ya mganr da muka yi? Tunda Fati ta fad'amin Shima Salisun ya saki Hasiyar" Kai Tsaye Amma tace"Wata mgana kenan? Yaya Rukayya tace"Mganar tafiyar Hasiya wajen Adda Hari mana. Amma shawarar nan ita ce Mafita haka ma Baban su Amna ya ce da na Fad'a masa." https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V +201123302418 Ban ji me Amma ta ce mata ba sai dai naji Muryan Adda Rukayya a harzuke tana fad'in"To shikenan Amma ni mafita daman na kawo ai shikenan" Ban tsaya jin sauran mganganun ba na tashi daga wajen zuwa wajen ma zubar ruwa na wanke shinkafa, acikin raina ina ta kokarin karfafa kaina, sanda ta fito ina zuba shinkafan ne cikin Tukunya. Tunda waken Dabam mu ke dafa shi,Haka ta wuce ni Fuu ko kallo ban isheta ba ni ce na bita da cewa "A sauka lafiya" Ina mirmishin takaici, matan gidanmu suka bita da kallo tunda duk suna waje ana hada hadan d'ora na dare, Masu d'orawan kenan irin su Maman Boy sai zaman gulma da yi da mutane tana fita suka fara kuskus ana kallona ana mgana, komai za su Fad'a bazan damu ba tunda sai bango ya Tsage kadangare ke samun wajen shiga. Sai da Ramatu ta leko ni Daga awo take tazo Dubani, a bakinta na ke jin Salisu an yi masa aikin an daure inda ya samu karayan Musbahu ya kirata ya ke Fad'amata kuma yadda ya ke Fad'a jikin Salisun da sauki tunda yana cin abinci sannan kuma yana mgana. A raina na yi Hamdala a fili kuma nace"Allah ya kara masa lafiya" Ramatu ta amsa da Ameen sai yammah ta tafi, Muna ta zencen haihuwanta tunda ta shiga wata na Tara, Har ina mata Fad'an ta daina Fita hakanan kada ta haihu a Hanya. Muka yi wasa da Dariya na Saba Rakata har bakin Titi ta samu adaidaita ko mashin, ammh yau ban fita ba saboda ina kauce ma idanuwan mutane a kaina. Itama sanin haka yasa ba ta damu ba Habiba na saka ta rakata har bakin Titi, tunda Ranar ba islamiyan yammah jumma'a ce. Ba mu da matsalan abinci Tunda muna ci cikin sana'ar mu, dagani sai Habiba Amma ce ta kan bukace koko ma wani lokacin amm ni in na ci Danwake na da Safe sai wani Daren kuma inna ci sauran Shinkafan da na kan rage mana ni da Habiba, Amma koko na kan Damata da Daddare ta sha, da Safe kuma wani Lokacin Add Fati na kawo mata kayan tea. Bata cika sha ba, in dai ba duka Zan had'a mana mu sha ba. Ranar asabar da Safe ina Hada had'ar kwabin Danwake sai ga kiran Adda Fati ta wayar Maman boy, sai da gabana ya fad'i da Maman boy ta kawomin sai dai Hankalina ya tashi da naji ta na Fad'amin Ramatu ce ta kirata taje asibiti tun jiya maranta ke ciwo to sun Riketa sun ce Haihuwa ne, tana asibitin Abu na Tudun wada naje na sameta. Ina jin haka na ruga Daki na Fad'a ma Amma cikin Sauri tace"Maza ki hanzarta ki je ki sameta. Allah Sarki Ramatu Allah ya raba lafiya" Cikin Saurin na Sauya kaya ko wanka ban tsaya yi ba, Habiba na bar ma kwabin Danwaken tunda ta iya cikin kudin Ciniki na Dauki 1k na mota na Zurma hijabina har kasa mai ruwan kasa,Fuskata Fuskata kozai kozai haka na fita Maman boy har ta gama yee kuwa da mganar sai fad'i suke yi Allah Sarki Ramatu Allah ya Raba lafiya. Sai ga shi har na kai bakin Titi ina ta Faman rufe fuskata da Hijabina, adaidaita na samu zuwa Pizzet, Dagachan na samu na Tudun wada,na sha wahala kafin na gano Ramatu. Haihuwa ce ammh sai zuwa Dare sukace sun dai riketa ne tunda Maran na Damunta nayi mata sannu ta amsani cikin yanayin ciwo. key din gidanta ta bani tace na je na kwaso kayan haihuwan da ta had'a acikin karamin akwatinta,vsai zannuwa da zan Dauko mata. Sai Fulas da Filo da kayan tea duk ta ce na Dauko. Sauri Sauri ko na sake hawa mashin naje na Dauko mata komai da komai na iske Fulas din cike da ruwan zafi Daukowa kawai nayi, kayan tea din kuma a kitchen dinta na gani na kwaso su duka. Tunda Nura kam ba abunda ya Rage Ramatu da shi. Sanda na dawo naguda gadan gadan,ina asibitin Inna talatu tazo bata jima ba tatafi, tunda kannen Nura da mahafiyarsa sun zo duk muna tare da su,bRamatu ta sha wahala sosai Nura baya nan sun tafi aiki Abuja Hankalinsa duk ya tashi yana ta kiran kannensa a waya domin jin ko ta haihu? ba ita ta samu bud'e ido ba sai Dare misalin goma. Ni Daman ban ma yi tunanin komawa gida ba,hankalina bai kwanta ba sai da Nurse ta fito tace Ramatu ta sauka an samu y'a mace sannan ni da kannen Nura muka saki Hamdala. Cikin lokaci kalilan Labarin Haihuwar Ramatu ta yi Tambari ni dai ba waya a hannuna ammah na san Inna talatu ta Kira Adda Fati, ita kuma zata sanar da Amma ko ta wayar Maman Boy ne. Ni nace ma Kannen Nura su tafi gida ni na kwana da Ramatu ,sai Daukan bby na ke yi farinciki ya cikani Yarinyar mai kyau da ita, gaskiya jarirai na da ban sha'awa Ramatu sai Faman dariya ta ke yimin, duk ta rame Lokaci d'aya lalle Haihuwa yakin mata. Ranar asibitin ya cika da Mutane Dangin Nura, shima adaran ranar ya Dawo, Bakinsa har kunne ni kuma ina masa tsiyar angon karni yana kwasar Dariya,komai da zamu bukata Nura ya siyama na. Sannan abinci daga gidansu Nura ake kawo mana Tunda suna Wajen Danmagaji ne. Ramatu tayi ta yi naje gida na yi wanka nace mata bazani ba sai ta kyaleni, Washegari sai ga su Inna talatu har da Adda Fati da Amma, bakina ya ki rufuwa ganin Har da Amma akazo. Zuwa chan kuma sai ga mutaan gidanmu Maman boy ce Jagoran su. Sun jima sai yammah suka tafi Amma ta zo min da kaya kala Biyu da Hijabi tunda tasan gidan Ramatu zan wuce,vkamar ko ta sani a daran aka sallame mu muka koma gidanta,Sai bayan suna zata koma wajen Inna talatu ta yi jegonta. Ramatu ba kawa ba ce a wajena yar'uwa ce shiyasa komai na yi mata ban Fad'i ba, kan jikina na ke Hidima da ita ko ruwan wankan ta Safe da yammah na Dauke ma Kannen Nura ni nake yi girki ne suke taikamin wani Lokacin, ammh har wankan Bby na iya sai dai Kanwar maman Nura ke zuwa da Safe ta yi mata wanka Ramatu kuma Amma ce yakamata ta zo ta yi mata to bata da lafiya sai aka Dauketa mata,wata abokiyar wasan Ramatu ke zuwa ta yi mata Safe da yammah. Ni kuma na ji da yan wanke wanken kayan Ramatu da baby, Nura kam ya shirya ma Ramatu sunanta daidai karfinsa, Shinkafa aka Dafa da wake Jalop,har da zobo Ramatu ashe ta yi mana Dankin wata Atamfa Cinghamvi, iri d'aya sai dai na yi hawaye,ita na saka na ci suna ba ni da Dan kunne da Sarka nata ta bani na akwatinta da ya rage guda d'aya bata yi amfani da shi ba. Na fito tsab da ni nima ina walwalina ni ce kuma kan komai na abincin, Adda Fati tun Safe tazo nan ta kwana ita da kanwar Inna Talatu Rahane daga Soba tazo. An yanka Raguna Guda Biyu Yarinya taci sunan mahaifiyar Nura, Khadija Ramatu tace zamu rika kiranta Noor haske. Washegari su Adda fati suka yi soye aka raba naman gida uku kashi Daya na dangin Nura D'aya kuma na Nura da Ramatu,D'ayan kuma na danginta, duka Ramatu tace kashi d'ayan a kai ma Inma talatu ta ba wa wad'anda suka kamata cikin na su ta Dibarmin nawa, sai da ta kwana Goma ta koma sabon gari gaban Inna talatu sai na rakata har chan sannan na wuce gida da sha tara na arziki daga Ramatu da mijinta. Atamfa ta bani tare da su manshafawa, kayan kwalliya takalmi Sabulan wanka da na wanki, Hijabai kala biyu sabbi,ta kuma had'amin da kayan abinci tace na kaima Amma tunda gida zata koma kuma daidai gwargwardo sun fi mu rufin asiri. Nura kuma Dubi biyar ya bani nayi ta godiya har ina kwallah da na koma na nuna Amma itama tace an kawo mata nama mai yawa da yajin jego har da Fallen zani da Omon wanki. Amma ta kalleni bayan ta gama Daga kayan da na zo da su Habiba ta Dauki Hoda da Jan baki tana fadin"Adda Hasiya ni dai ina son kayan kwalliyar kin ji don Allah" Ina mirmishi nace"Ke daman nace zan ba ma wa dauka Habi" Ta fara tsallen Murna muna yi mata Dariya ni da Amma. Dubi biyar d'in da Nura ya ba ni na mikama Amma ina fadin"Amma sai mu kara a jarin shinkafa ko? Amma ta ki karb'a Lokaci daya tana Fadin"A'a kudin ki ne, ki rike a hannun ki Hasiya" Ban samu zarafin mgana ba mukaji Ana maraba a tsakar gida, kamar Muryan Adda hari na rika ji sai da Habiba ta fita sai ga ta ta shigo da Buhu a hannunta bakinta har kunne tana Fadin"Adda ce da Badd'o' Amma ta washe baki tace"Harin ce da yamman ne? Maraba da Hari ta Jari" Hakan ta kan Fad'a daman Saboda chan Gada kowa da haka ya san su,in aka ga Amma ace mata Jarin Hari, in kuma aka ga Inna sai ace mata Harin jari. Adda Hari bakinta har kunne Saboda Murna ni kaina murna duk ta cikani Yarta autarta Badd'o kuwa haka ta nade jikin Amma ta na mata oyoyo da Gurbattacen Hausanta,Tunda su sun fi jin Fullanci hausan na su sai a hankali ko Amma da zama ne ya yi zama bakinta yaji Hausa, ammh duk da haka akwai fullanci a harshenta mu kam mukan ji iya sunayen abubuwa da baza'a rasa ba. Amma ta kasa zaune ta kasa tsaye,Sai da suka yi sallah suka natsa Ruwan zafi na dafa musu suka sha Tea da Buredi sannan aka zauna saman Hira bayan Inna Hari ta kwance Buhun tsarabanta,su Daddawa ne sai Fura da Nono da manshanu,sai garin kuni da yawa,Amma nata godiya ina tayata Habiba da Baddo na gefe suna ta shan Hira. Adda Hari bata sako mgamar aurena ba ko kad'an ba Duk da Amma ta kirata ta wayar Adda Fati ta fad'amata mutuwar aurena da Salisu. Daman tace tana tafe in ta samu dama sai da Safe ta yi ma Amma zencen Lokacin ina waje ina Hidimar danwake, Habiba da Baddo suna taimakamin da Zubawa suka yi mganganun su adaki da yar'uwanta sai da muka gama na koma Daki sannan Adda Hari ta kirani nazo gabanta na zauna Kaina ta Dafa kafin tace"Ki kwantar da Hankalin ki Hasiya. Babu wani farar kafar da kike da shi, sannan ke baki gaji Maita ba. Watarana sai labari haka Allah ya Tsara" na kalleta ina gyad'a mata kai Duk da tana cikin Rugga Adda tana da iliminta daidai gwargwardo. Sun cigaba da mgana da Amma duk a kaina ni ko ina chan gefe ina gyara kayana, ina ji Amma na fad'ama Adda Hari mganganun Adda Rukayya. Adda tayi Dariya kafin tace"Kyaleta Jari. duniya ce zata gayama Rukayya gaskiya. Mganar Hasiya kuma ni kin ki min ne Jari da Tuni ta na hannuna." Amma tace"sai dai ki dauke mu gabad'aya" Inna Hari na Dariya tace"Duk zan iya da ku kin sani. Tun yaushe na ke hakilon ki dawo wajena? Amma ta kad'a kai kafin tace"Saboda yaran nan ne Hari" Inna Hari tace"Yara suna ina? Fati na gidan mijinta Rukayya ma haka. Hasiya da Habiba ne kuma na ce dukkan ku zan iya rike ku jari zaman ki anan bai da wani amfani ga shi ba ki da ishashiyar Lafiya. Hasiya ce kuma kinga ga irin jarabawarta in zaki amince duka sai mu tattara mu koma da ikon Allah Hasiya zata yi auranta achan ta kuma zauna lafiya" Amma ta yi shuru ba ta yi mgana ba ni kuma saboda ba da ni ta ke mgana ba yasa ban saka musu baki ba. Ammh ni kaina zan so mu koma chan da Rayuwarmu kila Hankalin mu zai fi kwanciya. Adda Hari sati tayi mana sannan ta koma, kafin ta koma na rakata gidan Inna talatu ta yi ma Ramatu barka da yar Dubunta tace a siyama Noor kwalli, Sannan har gidan Adda Fati mun je itama tazo ita da mijinta sun gaisheta Adda Rukayya ce bata zo ba kuma bata kira waya ba, sannan ba wanda ya damu da ita. Cikin Dubi biyar din da Nura ya ba ni na cira 1k na bama Baddo, Adda Fati ko 8k ta kawo ma Amma tace a bama Adda Hari tayi na Mota sannan ta siyama Baddo kayan kwalliya da Hijabi. Adda Hari ta koma akan Amma tace in ta shirya zata kirata tace ita ba ta da matsala. Sauran Dubu hudu kuwa saka na ba ma Kultumen gidanmu tunda sana'arta ne, ta sakama Noor Huluna guda hud'u masu kyau, da ta gama naje da kaina na kaimata duk da sai da ta yi min Fad'an me yasa na kashe kud'ina? Na harareta ina fadin"Bansani ba" Dariya ta yi har kuma a ranta taji Dadi, shi alheri komai kankantar shi yana da dadi sosai. Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji, Har Ramatu ta gama jegon arba'in ta koma gidan ni naje na yi mata kwana biyu na tayata gyaran gidan,sai da Nura ya dawo sannan na koma gida Amma jiki ya yi kyau tunda in ba na nan ita ke Danwake,da yammah kuma ta yi shinkafa da wake, Mganar komawar mu wajen Adda Hari kuma ta sha ruwa tunda har Haya naji Amma ta yi ma Adda Fati mganar sake biyan na shekara. Wannan D'akin dubu Talatin muke biya duk shekara. Tunda naji haka sai na cire ma raina Sauyin muhalli na kuma san dalilin Amma na kada ace da gaske zargin da ke kaina Shiyasa muka bar gari, tana danne komai ne saboda ni. Adda Rukayya sai bayan Tafiyar Adda Hari tazo ita da ya'yanta kuma ma aranar sai da ta kara yi ma Amma mganar nan dai Amma ta kalleta ido cikin ido kafin tace"Ke Rukayya ki fita idona. Na ce ki fita idona na rufe ina ruwan ki da Hasiya ko akan ki take? Kina ci da ita ne ko kuwa akwai abunda kika Dauke mata ne da kika Kwazzabi kan ki sai ta bar miki garin nan ne? Sai Adda Rukayya ta Fara kame kame Ran Amma ya baci ta nuna mata kofar fita tana fadin"Daga yau sai yau in dai kin san mganar Hasiya zata kawo ki to na gode ki zauna gidan ki ba sai kin zo ba, da ke ko baki zamu cigaba da Rayuwa Rukayya shi ruwa cikin cokali ya isa mai Hankali wanka" Sum sum ta yi ta kai ta fara ba ma Amma Hakuri ganin ranta ya baci yasa har ta jima agidan, ganin har da yaranta suka zo yasa na yi jallop din shinkafa da rana mai allayahu yaranta ta koya musu bakin Halinta ko cin abinci ba su yi sun raina. Amma ko har ta tafi bata kara kallonta ba, Kunya taji ta zaro dubi biyu ajaka ta sauke Gaban Amma tana Fadin"Amma ku kara wlh Baban su Amna ne ba su yi albashi ba." A ciki Amma ta amsa da cewa"Allah ya ba da lada" Har ja ya'yanta suka fice Amma bata kalleta ba ni ce ma ma aiki Habiba ta siyoma yaran Biskit, a rene Adda Rukayya ta amsa ba ko Nagode ni kuma bai dameni ba saboda nasan Har Abada Adda Rukayya ba ta isa ta sauya jinin da ke Tsakanina da ita ba Ashe taji Haushin mganar Amma ta taka har Gidan Adda Fati ta na Fad'amata tazo Amma ta rufeta da Fad'a sabo da ni. Sannan har su Anma ba ta ja ajiki ba ta na jin haushinta domin ta kawo mafita. Har ta na fad'in"Fati nima fa ina son Hasiya ai kanwatace kamar yadda ta ke kanwarki. Bana jin dadin zarge zargen da ke kanta ne, ni wlh ina mata Fatan Rayuwa mai kyau in ta koma gaban Adda Hari" Adda Fati dai ta bata baki, ammh ta rike Amma ta ki kula ya'yanta Saboda ni,ita kuma tana so na ne ta nemar min mafita da Adda tazo tana gayama Amma,vkyafci ta yi kafin tace"Fati bar ni da Rukkyya Mutuniyar wofi ce. Ta zabi miji da danginsa da mutanen Duniya akan uwarta da danginta. Ba inda zamu koma tunda ba mu gagara lallaba rayuwarmu anan ba Fati. Adda ba shi gareta ba karfin Hali ne bazan kwashi jiki na koma na D'orata mata nauyi ita da ya'yanta ba. Sannan bazan bar Hasiya ta koma ba tunda nan aka Haifeta akwai nakasu in har na ce ta koma chan da zama" Da haka Amma ta kashe mganar komawata wajen Adda, da Addan ta kira ce mata kawai ta yi"Adda zan zo dai na miki kwana biyu gabadayanmu in Habi ta yi Hutun makaranta in sha Allahu" Adda bata damu ba tace tana jiran mu duk sanda muka zo. Tundaga Lokacin Adda Rukayya ba ta kara ma Amma mganar ba ko ta zo gidan sai ta koya ma kanta kame bakinta. Ni ko na kama mutumcin kaina Daga gaisuwa ba na shige mata Hankalina na kan sana'ar da muke ci da kanmu da Rufin asirin mu, tare da Kula da Amma cikin wattani uku duk abubuwanan suka faru sai abunda ya Faru na aurena da Salisu ya lafa tunda har ina Fita Diban ruwa ko zuwa kasuwa ko chemist siyo mgani. Ba fargaba tunda daman abun na Lokaci d'aya ne yana wucewa shikenan kamar komai bai Faru ba. A bakin Mutanen gidanmu naji Salisu ya dawo gida an saka masa karafa a kafafunsa na Dori da Karafan asibiti guda biyu ya ke tafiya. Ammh duk bayan wata daya suna komawa sannan ana masa Dressing a gida. Ni dai nawa yi masa fatan alheri da Fatan samun waraka komai tsakanina da shi ya jima da karewa kamar bai faru ba. Na kuma tabbata daga kan Salisu kila na gama aure tunda yanzu dai ko daga nesa wani ya zo da sunan aure na, zuwa daya zai yi bazai kara Dawowa ba tunda za'a karanta masa komai a kaina har da karin gishiri da maggi. Nasan kaddara ce ko in ce Jarabawata ce haka. Ammh ban taba Tunanin Wata Kaddaran zata sake bibiyata nan kusa ba. Bani kuma da masaniyar zanen kaddara ta na kusa da ni ban sani ba. Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086 *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki. *05* *GUSAU_ZAMFARA.* _Area:Tudun wada_ *Lahadi, 10:40am* "Wai wani shegen ne ke min burutun a shashe na da Safiyar Allah nan? Ta fad'a cikin kufula da takaicin yadda aka maida ita banza tana ta mgana ita kad'ai. Kokarin mikewa take daga zaunen da take lokaci d'aya tana Laluban sandar ta, tana cigaba da fad'in"Ko wani d'an jakar uba ne ya bari na fito mu ga juna yau sai na Deb'e masa albarka" Ta samu mikewa kan kafafunta, ta kuma samu nasaran ganin Sandarta ta karfe a gefenta sai dai kamar akwai sauran rina akaba, tunda sai faman lalube take yi kamar ganinta na da rauni. Garin lalubenta ne hannunta ya kai kan wani bakin gilashi ta dauko shi tana fad'in'"kaji rashin tabbas na Abun nasara yanzu gilashi na fuskata na nemesa na rasa. Mtswww aikin banza da wofi" Bum! Taji kamar an fad'o dakin nata a rashin sukuni a zafafe ta saka gilashin nata cikin Masifarta da tun tana matashiyarta ya zame jiki har tsufanta tace"Nace wai waye zai zo ya Dameni da burumtu ne? To ko waye in bai yi mgana ba Allah ya tsinee..." "Innani ni ce". A kafad'a da wata sanyayyiyar murya mai cike da yarinta da kuruciya. Wacce aka kira da Innani ta d'ago kanta a masifan ce tana yamutsa Tace"Ke ce wa? Baki da suna ne? Ina na ke iya gane muryoyin yaran gidan Sulaimanu, ku rika wani make murya kamar wasu ya'yan gyare" Ta fad'a lokaci d'aya ta na kara gyara zaman gilashin da ke fuskarta sosai ya cika mata fuska kir kuma ta sauke ganinta kan yar yarinyar dake gabanta sanye da Hijabi mai ruwan kasa. Kanta na kasa tana wasa da yatsun hannunta. "Sultana ce. Sultana ce Innani" Baki Innani ta washe kafin tace"Au ki ce Sulsana ce ta wajen Salamatu ko nace Matar MAGAJIN GIDA. uwargida Sarautar mata a gidan Abubakar Saddiqu alkawarin Allah sai ya cika da yardan Allah, ya ki nan yar nan taho ki zauna kusa da ni" Ta fad'a tana ya fito ta da Hannu. Jikinta kamar ba karfi ko na ce wacce ta tashi matsananciyar jinya ta karisa gefen Innani ta zauna. Innani ta gyara zama tana fad'in"Ke kam ki rika kama jikin ki mana Sulsana. Ayi mace kamar wahainiya saboda rashin kuzari" Ita dai kanzil bata kara ce mata ba, kanta na kasa tana wasa da yatsun hannayentaa. Innani ta kara kallonta cikin nazarinta kafin tace"Daman kece kika zo kina min bare bare a sasana? Tsiyana da ke wauta ko rashin wayau ne ma zan ce ni Dije? Ayi yarinya sai shegen tsoron mutane. Allah dai ya yaye miki kin ji ko" Wannan karon ne ta murmusa ammah ba tayi mgana ba, ganin haka yasa Innani ta washe wawulan bakinta da babu Hakora ko d'aya duka sun gama barewa, Daman na Roba take makalawa in zata ci abinci abubuwa masu tauri kuwa sai dai ta saka wuka ta yi gutsi gutsi da shi, Kwad'ayi ne da Innani komai na Duniya ba bu abunda bata ci. Tace da wuya ta kasheta gwara dad'i ya kasheta. https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V Cikin Dariyanta tace"ina lafiyar ita uwar taki? In ji dai lafiyanta lau? Ina shi Baban naku? Tun asuba da ya leko muka gaisa ban kara ganinsa ba." Muryanta a sanyaye tace"Umma tana lafiya. ABBA kuma yana bangaransa shi da Mama" Nan da nan Annurin fuskar Inanni ya Dauke ta wani Dauke kai kafin tace"Uhm ko da naji." Daganan tayi Dif tana faman girgiza sadan dake gefenta. Sultana sai satan kallonta ta ke yi tana danne mirmishinta. Sai jin mangari ta yi a kai lokaci d'aya Innani tace"Munahika yi dariyar taki mana a sarari yarinya sai bakar gulma kamar haihuwar Ssuwaiba. Da sauri ta kalleta cikin mamaki Lokaci daya tana dafe kanta in da Inanni ta mangareta. Innani ta yayyako mata cikin masifa tace"Miye kuma kike kallona? Ko na fad'a a bakin yan baka ne ko ke ma kin koyi halin ya'yan Suwaiba ne ban sani ba?Allah to ya sauwake kin cuci Salamatu da Sulaimanu domin ba haka suka tarbiyantar dake ba" Ko gajiya da mgana Innani ba tayi, haka Sultana ke fad'i a cikin ranta. Mirmishi ta yi kafin tace"Innani.." Innani ta kalleta batare da tayi mgana ba, ganin Sultana taki mgana sai kuma wasa da gefen hijabinta take yi yasa Innani ta yi tsaki kafin tace"Nace miye ne kika tasani kina faman kiran sunana? Shuru Sultana taki mgana kanta na kasa sai wasa da gefen hijabinta ta ke yi, Innani tayi sakate kafin ta juya cikin jin haushi goronta da ke cikin wani karamin kwano ta jaho,ta fara yayyankashi a saman tafin hannunta. Chan kasa kasa taji Sultana ta kara kiran sunanta"Innani.." "Kina kara kiran sunana zan kwad'a miki mari, bar ganin ina raga miki,sai naci mutumcin ki. Yarinya kin zo kin tasani kina faman kiran sunana, kuma ki yi mgana kin ki yi to uban waye shashasha irin ki? Mtswwww.." Bayan taja tsaki ta cigaba da bambare gorinta tana watsawa cikin bakinta. Sultana sai kallonta ta ke yi ta kasa mgana sai daga baya ta kara kiran sunanta ta juyo a zafafe da niyyar kara sauke masifarta. Sultana ta lamgwabe kai lokaci d'aya tana mika mata siririn hannunta cikin Shagwaba tace'"Innani san min goron" Innani tayi kwafa kafin ta dauko goro karami cikin kwanon gabanta ta dangwara ma Sultana a hannu Lokaci daya tana fadin"Na shige su da kwazzaban ki Sulsana. Wannan yarinya Magajin gida zai yi fama" Fad'ar sunan yasa dukkansu suka kalli juna Sultana ta kauda kanta. Innani kuma kamar an tunasar da ita ta gyara zama tana fad'in"Ke sulsana kun yi mgana da Magajin gida ko kwanaki nan? Ni wajen kwana uku kenan bana samun sa a waya kuma bai kirani ba, Allah yasa lafiya ina ta zuci zuccin in yi ma Sulaimanun tad'insa sai sha'anin duniya ya mantar da ni." Da kai sultana ta yi mata mgana da girgiza mata kai alamun itama ba su yi mgana ba. Nan da nan Innani ta kara Harzuka cikin daga murya tace"Ke uwarki. Baki zaki bude ki yi min mgana ba ne Sultana tace" A'a Innani" Nan da nan Hankalin Innani ya tashi ta fara salati tana Direwa kafin tace"Wayyo jikana. Yana chan wata uwa duniya ba uwa ba uba. Ba kuma dangi ko wani hali yake ciki? Ke sulsana dubamin wayata cikin daki ki zo ki kara kiramin shi Allah yasa jikana yana lafiya. Magajin Sulaimanu bayan shi ba shi da wani magaji anan duniya" Ta ke fad'a tana kokarin fashewa da kuka. A sanyaye Sultana ta mike tana wannan tafiyar nata Innani ta kalleta cike da takaici tana fad'in"Zaki yi sauri ko sai na turaki da wannan Sandar ta hannuna? Ta fad'a tana kokarin dauko sandan nata da gudu Sultana ta shige cikin Uwar Dakin Innani, ta fara neman wayar na ta. Ta duba ko'ina bata gani ba, ga shi daga Falo Innani sai faman kiran ta take yi sai da ta gaji ta fito ammh Daga gefe ta tsaya tana fad'in"Ni fa ban ga wayar taki ba Innani" Yadda Innani ta kalleta da tana kusa sai ta sha duka da sanda, shiyasa ta tsaya daga baya baya. Tsaki tsaki tsut.! Kafin tace"Ko ke ma idon naki na da Rauni ne na saka Sulaimanu ya kai ki in da ya kai ni aka ba ni wannan gilashin? Ammh ace waya na barta saman katifar da na kwanta ki zo kina ce min wai baki gani ba? Ta fad'a tana nuna ta da Sanda,kamar zata daketa. Sultana ta tura baki tana kallon gefen kwanon Innani ga wayar nan kirar kamfanin Tecno karama, ammh tana ta kumfar bakin a saman katifa ta barta. An ci sa'a ne da tana cikin Lalinta ne zata rika bala'i tana tsine tsinen an sace mata waya. Yanzu ma ido ta mutsike tana fad'in"Baki gani ba fa da gaske Sulsana? Allah dai ya tsine ma barawo da uwar barawo wlh" Sultana ta zaro ido kafin ta karisa gaban Innani ta duka ta Dauki wayar ta mika mata tana fad'in"Ga fa wayar taki nan a gaban ki Innani" Innani ta bi hannun Sultana da kallo kafin ta karbi wayar ta jujjuya tana Fadin"Ikon Allah! Ni fa saman katifata na barota. Ni fa daman na dad'e da sanin abun nasara ba shi da tabbas, sai ka ijiye abu ka nemeshi ka rasa sai chan ka ganshi a wani waje mtseww" Ta karishe da tsaki daman Tsina da Tsaki a bakin Innani Allah ya fissheta kada ta zo mutuwa su kama bakinta. Sultana ta kara damgwara ma wayar tana Fad'in"Maza kiramin magajin gida. Allah yasa yana hannu nagari." Sultana ta dukufa kiran Magajin Gida kamar yadda Innani ta saka akayi mata Saving a lambarsa. Itama cikin mazari ta latsa lambar nasa sai dai kuma kuzarinta ya ragu da wayar ta ke kara duui! Sai kuma ta yanke, tayi haka har sau uku duk tafiyar d'aya ce tana ji Innani na fad'in"Kin samu magajin gidan ko? Ta kasa bata amsa Dagowa ta yi ta kafe Inanni da ido. So ta ke yi ta ce mata ya yi blooking dinta ne,ammh tasan Innani ko za'a shekara bazata gane komai ba. Shiyasa ta mikama Innani wayarta ta ki mgana, da kallon mamaki ta bita baki bude kafin tace"Ke na ce kin samu magajin gidan a waya? Sultana ganin Innani ta ki karban wayanta sai ta dungure mata a saman cinyarta ta mike tana fad'in"Innani wayarsa ba ta shiga." Inna ta rafka salati tana fadin"Na shiga uku na lalace ni Dije. Ke kinga Sulsana maza jeki ki gayama Babanku yazo ina nemansa" Sultana tace"Innani Abba kuma? Barci fa ya ke kinsan yau weekend ne" Innani ta rarumi sandarta tana fadin"Ko barcin mutuwa ya ke nace ki taso min shi kaji min ja'irar yarinya tabbattaciya. Ba gwara ya tashi da wannan barcin da tashin hankalin da ke Tunkaromu ba, Magajin gidan ne gabadaya ba'a san inda ya ke ba yanzu kai co na Dije, daman wlh ban so tafiyar yaron nan ba, ya lallameni da Kalamansa na bayan ya had'a da su jawomin manyan ayoyin Allah Sai na amince ammh har cikin raina Hankalina bai kwanta ba" Ta karishe fad'a tana face majina,Sultana ta yi tsaye tana kallonta ganin yadda Lokaci daya ta rikice, To daman ai shi kad'ai ne ke rikitar da Innani sannan kuma cikin Mintina ya ke dawo da ita saiti, wanda ko Abba da ta haifa sai ya Dauki awa Biyar Innani ba ta ji mganarsa ba. Bata sani ba Inanni ta daga Sandarta sama tana fad'in"Zaki wuce ki taso min shi ko sai na Rafke ki? Sakarya mara wayau in kina da Tunani da Hankali ai kema abun kukan ne ya same ki, in da kara zama zaki yi mu taru mu tashi gidan da koke koken mu" Sultana dai da gudu ta fice daga Shashen Inanni tana haki kamar ta yi wani gudun tsere. Babban gida ne mai shashena biyar,bi da bi, biyun na jikin juna suna da girma,Karamin ne ke chan gefe shashen Innani kenan, wanda ya fi girma gabadaya shine na jikin wani karamin Shashe shima. Sai da ta tsaya a wajen ta kallah kamar zata ganshi ya fito. Sanin ba Fitowar zai yi ba yasa ta juya ta tunkari shashe guda biyun da suka fi girma. Na farkon ta bude kofa ta shiga, Sad'af Sad'af kamar barauniya. Ta kawo Tsakiyar Falon taji an ce"Sultana." Cak ta tsaya ko ba ta juyo ba. Ta san Muryan wacece Umma ce! Cikin sanyin jikinta na Hallita ta juyo kanta na kasa tana had'e kafafunta alamun ba ta da gaskiya. Doguwar mace ce,mai dan kaurin jiki baka zaune kan kujera remot a hannunta. Sanye ta ke da Atamfa super aura mai kalan Duhuwa ta ci Daurinta kamar wata matashiya. Alhalin zata ba ma Shekarun Hamsin baya. Sama da kasa ta kalleta kafin tace"Daga ina kike da sassafe daga tashin ki a barci na duba ki ban ganki ba? A sanyaye tace'"Shashen Innani na je" Hajiya Umma ta gyad'a kai kafin tace"Ta na lafiya ko? Da kai ta amsa mata bata damu ba sanin Halinta. Mirmishi ta yi mata kafin tace"Sai ki wuce ki je ki yi wanka ki zo ki mu karya" Kamar tana jira ta amsa da Toh ta wuce da Sauri Umma ta bita da kallon mamaki a ranta tana Tunanin Saurin me Sultana ke yi haka? Tunaninta ya tsinke ni Lokacin da taji mganar Innani da karfi tana kwalamata Kira. "Salamatu.. salamatu.." Kina ina ne salamatu,? Zumbur ta mike lokaci d'aya tana watsar da Remot din hannunta. Zata iya banzarta da kiran kowa ammh ba zata iya kyale kiran Innani ba. Uwar mijin da ta yi mata rikon uwar da ta rasa tun a zamanin baya. Uwar da ta Fifita son da take yi mata sama da d'anta data haifa. Ita ko mai zata saka ma Innani? Ba bu ban da ta rika yi mata Biyayya da yi mata duk abunda take so har ma da wanda ba ta ce tana so ba. Da sauri ta fita daga Falon a kofar shigowa suka ci karo da Inanni ta fito tana dogara sandarta. Kai wannan tsohuwa da Jaraba ta ke, ta tsufa har ta duke sai ma da taimakon sanda ta ke iya tafiya, Kanta gabad'aya ba baki sai Furfura. Fuska duk ta tamuke sai dai Fatar taushi da hutu tare da jin Dadi ammh mganar gaskiya Inanni zata bama Chasa'una baya. Umma ta tsorata da taga Inanni na kuka yarkace yarkace. Da Sauri ta riko hannunta tana fad'in"Ga ni nan Inanni lafiya? Ko yunwa kike ji ne? Domin a tunanin Umma, Hajiya mama bata kai ma Innnani abun karyawanta ba. Tunda yau lahadi megidan na nan kuma ba da wuri suke karyawa ba. Tasan Innani da abinci kamar mai tsotsan ciki. Shashenta baya rabo da abinci har cikin Dare sai ta tashi in ba abinci ta fashe da kuka. Innani jin Muryan Umma sai taji sanyi ammh jin Abunda tace ne yasa ta kwace hannunta tana fadin"Matsa ba ni waje. Hala bani da aiki ne sai cin abinci kamar wata tsutsa!? Ana ta rai mai Daraja wa ke ta abinci? Umma ta sauke muryanta kasa tana Fadin"Yi hakuri Innani mu je ciki sai ki fad'amin me ke faruwa? Ta fad'a tana kokarin kamo Sandan hannun Inanni, ganin haka yasa Innani ta turje tana fad'in"Ina naga ta shiga ciki Salamatu? Ina nan tsaye har sai Sulaimanu ya fito" Umma ta kalleta cikin mamaki kafin tace"Wani abu ne ya faru Innani? Sai kawai Innani ta kalli Umma ta faahe da kuka da karfi tana Fad'in"Ina zan iya fada miki. Ai sai hankalin ki ya tashi bari dai shi Sulaimanun yazo shi Tunda namiji ne ya na da Dakiya zai iya saurarana" Kafin Umma tace wani abu Mallam Tajuddeen maigadi ya zo in da suke da Sauri yana fad'in"Subhanallah Hajiya lafiya kuwa? Ya fad'a yana kallon Inanni cikin damuwa ganin tana kuka, duk da kukan Innani in dai kana gidan Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi to ya zame maka jiki. Innani ko kallonta ka yi in bai yi mata ta ga daman ta fashe da kuka. Innani na jin muryan Mallam Tajudden ta watsake ta daina kuka Umma ko ce masa tayi"Bakomai Mallam. Koma bakin aikin ka kawai" Har ya juya Inanni tace"Ya koma ina Salamatu? Ai gwara ya tsaya in Sulaimanu ya fito aji in dole sai an had'a da ayoyin Allah. Mallam Saju tsaya tsaya Sulaimanu ya fito" Umma ta rike haba cikin mamaki kafin tace"Innani Abban Su siyama fa bai fito ba! Ko kin kirashi ne? Innani tace"Na aika yarinyar taki Sulsana ta taso min shi. Ina ya ga ta barci Magajin gida gabad'aya ba'asan inda ya ke ba" Umma ta bude baki, kafin ta rufe Mallam Tajudden ya kalleta ta kalleshi kafin ta juya tana kallon Inanni da ke fad'in"Wai ina Sulaimanun ne? Kaji min watsewa ni Dije ni uwarsa ma na taso kan kafafuna shi uwar me ya ke yi da bai fito ba har yanzu? Kada fa na zama uwar banza ne yasa ban je har shashen na shi na taddo shi ba, na tsaya a bangaran salamatu" Sai da Umma ta Murmusa kafin tace"Innani wata Sultanan? Sultanan da ke cikin daki tun dazu? Da wani kallon Innani ta bita da shi kafin ta yi kwafa tace"Lalle ja'irar yarinyar nan da ni take mgana. Tunda taki zuwa ke uwarta je ki taso min Sulaiman." Umma ta yi kokarin riko Innani tana Fadin"Mu shiga ciki Innani. Magajin gida kuma lafiyansa kalau. Kin manta yana Zariya yaje makaranta? Innani ta yi shuru alamun Nazari kafin tace"Tsakaninki ga Allah Salamatu kwananki nawa baki yi mgana da Magajin Gida ba? Umma tace"Na yi mgana da shi jiya ma Innani" Innani ta kalleta kafin tace"Sai kin Rantse zan yarda da ke Salamatu." Umma ta yi mirmishi Tana kallon Mallam Tajuddeen. Wanda ya juya shima yana mirmishin Diraman Innani da mutum ba ya gajiya da Dariya. Umma sai da ta rantse sannan Innani ta amince da ita ta shiga Shashenta. Ta zauna kan kujera ta na share hawaye da Haban dankwalin kanta. Umma ta zauna gefenta ta ja Haban zaninta mai kyau da Tsada tana Share ma Innani hawaye cikin Sigan lallashi ta ke fad'in"Ki yi hakuri Innani. Magajin gida yana nan lafiya zai zo ya ganki kwananan in sha Allahu" Innani ta yi mirmishi kafin tace"Shikenan tunda kin tabbatar da yana lafiya. Ni daman rashin samun sa ta wayar zamanin nan ne ya Dagamin Hankali. Ammh tunda ke uwarsa kin tabbatar da yana lafiya ba ni da tacewa" Umma ta yi mirmishi kafin tace"Yana lafiya Innani in sha Allahu. Zan kuma sa ya kiraki in sha Allahu. Innani ta gyada kai batace komai ba. Umma ta mike tana fad'in"Innani me zaki ci in kawo miki? Innani ta yamutsa fuska kafin tace"Na riga na ci goro salamatu zauna abun ki. Nagode sosai Allah ya shirya miki zuru'a, yadda kike kula da lamarina kema Allah ya shiga lamarin ki" Umma ta mike ta na ta amsawa da Ameem Ameen. Duk da yadda Inanni ta ke da Tsine Tsine akwai saka albarka da kyawawan addu'o'' a bakinta. Umma kitchen taje ta hado abun karyawan su,Ta leka da kanta ta kira Sultana wacce har ta yi wanka ta saka Doguwar riga baka. Kai tsaye tace"Kina Fiki fiki da ido. Sai ki fito mu karya" Dakyar ta fito tana Tafiya sannu Sannu taki dagowa su had'a ido da Inanni, ita ko sai faman Hararanta ta ke yi tana kyafci. Umma na kallon su tana Dariya. Bata yi mgana ba sai da Innani ta tabe baki tace"Bar wani rabe rabe. Kiyuwa ko? Kin koyi bakar Dabi'a wajen yaran chan na Suwaiba kamar ni na aike ki ki k'i zuwa ko? Sultana ta zauna ta rab'e bayan Umma tana fadin"ki yi hakuri Innani" Innani ta washe baki kafin tace"Me kika yi min yar nan? Ke dai bari Uwar ki tace magajin gida na lafiya. Ni daman lafiyarsa ya dameni in ta ni ce ai Sulaimanu ya kwana ya na barcin asara Mutumin banza kawai zai ce duk koken koken da nayi bai ji ba ne Salamatu? Umma na Had'a tea tace"Bai ji Ba Innani. In da yaji kinsan zai fito shi da baya son ganin ki cikin damuwa." Innani ta tabe baki bata kara mgana ba, sai dai Umma na janta da mgana Jefi jefi. Suna gama karyawan Sultana ta kwashe komai zuwa kitchen. Daganan tana fitowa ta koma Daki ta dauki aikin makarantarsu tana Dubawa. Umma da Innani na Falo sun tsinke da Hira. daga dakin tana jin muryan Innani a sama tana mgana da Anty Surayya sai faman bude murya ta ke yi. Sultana ta Dafe kanta a fili ta Furta"Innani Hayaniya da kanta" ***** Alhaji Sulaaiman Abubakar Shinkafi Bakin Dattijo Dogo baki. Ya yi sallama Shashen Hajiya Umma, Bayansa kuma Hajiya Mama ce Farar mace alkyabban mata. Ta ci kwalliya sai faman tashin kamshi take yi. Suna tafe, wasu yara guda biyu mace da Namiji suna bin su a baya. Da sallama suka shigo falon. Shashen Innani suka fara isa bata nan. Su san ba inda zasu sameta sai Shashen Hajiya Umma. Shiyasa suka garzayo da sauri. Umma ce ta mike tana musu sannu da zuwa cikin natsuwa tace"Abban su siyama barka da Safiya.! Ina kwana Maman yara? Afiya Gud mrning" Umma ta fad'a ta na rike yar mace ajikinta. Namijin ya karisa gabanta tana fad'in"Umma" Kansa ta shafa tana fad'in"Abadallah bawan Allah" Wacce aka kira da Maman yara ta saki fuska sosai ganin Umma cikin Dariya tace"Hajiya Umma mun tashi lafiya? Ya kwanan Sultana? Umma tace"Sai hamdala ya kwanan su Abdallah? Mama tace"Ga su nan rigiman mu. Su Salima sun fara tsuwwaa sun gaji da su a maida su gidan su" Umma na dariya tace" Nan ma ai gidan su ne. Ban da abun su salima." Matan kadai ke hiran su Alhaji Sulaiman ya gurfana gaban Inanni yana gaisheta. Sai da ta dafa kanshi Sannan ta amsa lokaci d'aya tana fadin"Allah ya yi maka albarka Sulaimanu. Allah ya albarkaci samun ka,da arzikin ka. Ya raya maka zuru'a ya shirya maka su. Allah ya tsole idon makiya a kan ka yarona." Cikin jin dad'i ya ke ta amsawa'"Ameen Ameem Innani." Sannan ya koma gefenta ya zauna yana gyara zaman shaddan jikinsa. Inanni kasa kasa take kallon Mama ganin haka yasa itama ta bi bayan mijinta ta zube tana gaisheta ta amsa a Kirne kafin tace"Yaran ki hala basu gidan nan ne Suwaiba? Mama ta dago tana fad'in"Suna nan Mana Innani. Da Safe ma ai Siyama ce ta kawo miki abun karyawan ki" Innani ta tabe baki kafin tace"Au ita ce? Ai ba ta jira na ganta ba afalo ta Damkwafar min da shi ta kara gaba." Mama kanta na kasa tace"ki yi hakuri Innani zan yi musu mgana za su gyara." Innani ta kauda kai ta maida wajen Danta da ke wasa da jikokinsa,Takaici ya isheta shi kuma ganin haka yasa da Sauri ya tura su gabanta yana fadin"Ku je ku gaishe da Inanni" Gabanta suka tsaya suna kallonta. Ta dafa kan Afiya tana fadin"Yaran nan yaushe zasu koma gidan Uban su ne? Falon shuru ya yi daga Umma har Mama an rasa mai mgana sai Abba ne ya yi gyaran murya kafin yace"Sa'imar ba su dawo ba ne. Da sun dawo zata zo ta Dauke su ko Sauwaiba? Mama tace"Eh Innani da zarar sun dawo zata zo ta Dauke su' Innani ta kallesu tsab har ta na wani gyara zaman gilashinta kafin ta tabe baki tace"ai shikenan. Sulaimanu nace baka ji kuka na ba ne yau? Da Sauri yace"Subhanallah me ya faru Innani? Innani tace"To magajin gida ne ban ji sa ba kwana biyu. sai hankalina ya tashi na zata ko ya fad'a hannun banza ne, Sai da salamatu ta lallashe ni da cewa sun yi mgana sannan na yarda itama sai da ta rantse na yarda kasan karya ba ta da wuya a wajen Babba." Abba ya nmurmusa kafin yace"Ya na nan lafiya Inanni. Jiya da Daddare ma mun yi mgana" Innani tace"Shikenan tunda yana lafiya. Sati mai zuwa na fasa zuwa sha'anin nan na yar gidan Sammani Wajen jika na zani na gansa ko Hankalina ya kwanta" Abba ya kalli Matansa suka kallesa sigina ya yi ma Umma shiyasa ta gyara zama tana fad'in"A'a Inanni ai basai kin je ba. Da kanshi zai zo ya ganki" Innani ta yi shuru ta na kallonta ta cikin gilashinta kafin tace"In ma bai zo ba ke kika sani Salamatu. Alhakin rashin zuwa Duba magajin gida na kanki" Umma na mirmishi tace"shikenan innani. Sai kuma ta juya tana mgana da Abba kan bikin diyar kaninsa Sammani da za'ayi a Shinkafi Sati na sama Innani tace ita zata wakilceshi ba sai yaje ba. Abba na fad'in"Innani tare zamu. Ina so na samu Daurin aure" Kai tsaye tace"To da an gama Daurin auran ka dawo gida kaji ma na Fad'a maka" Mirmishi ya yi kafin yace"Naji Innani." Umma na jin su duk da Hankalinta na wajen su Afiya, sannan suna taba Hira da Mama. Sai dai ita tasan Dalilin Innani saboda kada yan'uwa su gansu su kawo bukatotunsu ba ta son D'anta na fitar da kudi. Abunda Inanni bata sani ba ko mako da son kudi Alhaji Sulaiman Shinkafi ya fita. Mutum d'aya ne shi kadai jalli Tal ke iya saka shi fitar da kudi ko da bai yi niyya ba. Kuma shi ke iya yanke Hukuncin da Ko Innani bata isa ta ce A'a ba ballatana shi. Innani mikewa ta yi tace zata koma Shashenta ta kwanta Harkarkarinta na ciwo. Abba Da Umma har Mama suka mike suna rawan jikin kamata. Abba ya rike mata Hannu Umma ta kama Sandarta. Ita kuma Mama tabi bayansu bayan tace ma su Afiya su zauna su dawo. Ko da batayi niyya ba dole ta raka su in ba Haka ba yanzu Innani zata hau ta kanta ta zauna. Suna fita Haraban gidan Haushin kare Huhuhuu!!! Innani ta razani ta kamkame Abba tana Fad'in"Innalillahi ni Dije? Yanzu daman Sulaimanu baka fita da wad'anan bakaken Halitun da ke Firgitani mutane da makota ba? Har ni uwarka suna hanani barci. Nan fa na gayama mala'ikun Allah basa ta kan mu tunda ka ke ijiye karnuka a cikin gidan ka" Cikin ladabi yace"Inanni ai sabo gadi ne, kinsan irin Sana'ata" Kai tsaye tace"Ka ci uwaka kai da sana'ar taka. Allah dai ya tsine ma wad'anan karnukan gabadaya" Umma na Danne Dariyanta tace"Innani Kin manta Magajin gida yace miki a bar su yana so" Nan da nan Innani tace"An yi haka kin ga ko na sha'afa salamatu. Sulaiman to kaji Magajin gida yace yana so. Kuma tunda magajin gida yace yana so an gama mgana maza ka barsu, sannan a rika basu abinci kada ya dawo kuma yaga an yi masa ba Daidai ba." Kai tsaye yace"In sha Allahu Innani." Yana mirmishi. Mama na baya sai bata rai take yi, har shashenta suka rakata nan din ma sai da suka gurfana gabanta har sai da tace su je su barta zata kwanta huta. Dalilin da yasa suka yi mata sallama kenan suka fita. Yau lahadi ce daman a ka'idan Alhaji Sulaiman akan had'u a falon Shashen sa shi da matansa su yi su tattaunawa yaji matsalolinsu. Yau ma shashen nasa suka wuce bayan Mama ta koma Falon Hajiya Umma ta damkama Sultana su Afiya ta fice ta barta tana Tura baki. Sam bata son Hayaniya gashi kuma Mama ta had'ata da wad'anan yaran. Alhalin su Salima na chan kwance suna hutawarsu. Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086 *Janafty* *Sep 09/2023* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V +201123302418 Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086 *06* *Zaria* Samaru_Tsamiya. 8:11am. A cikin anguwan samaru Layin Tsamiya, Ire iren gidajen su na b'arayin wajen zaku ga akwai d'akuna a waje saboda anguwa ce ta yan makaranta, Makaranta kuma Babba a Africa wato ABU ZARIA. Ko bayan makaranta akwai y'an kasuwa da masu huldar arziki da neman na kansu, iren iren gidajen wajen duk akwai dakunan a waje domin ba da Haya na maza matasan yan makaranta. A irin hakane na hango wani gida mai Damdamali a kofar gidan har da Rumfa sai Dakunan waje jere a layi Guda biyar, Daga gefe har da makewayin su na lalura. Gidan na marasa karfi ne ammh kuma bai lalace sosai ba, yanzu haka kila ma megidan ya rasu dakunan magada ne. Dakunan duka suna Rufe ne,Sai guda d'aya na farko ne a bud'e har da Labule, Kai tsaye sai ga wani Dogon Saurayi ya fito Sanye da kayan yan Bautar kasa completed, a jikinsa Farar Riga da Green din wando,sai Falmaran din su Green sai Facin cap itama kalan green mai haske. Kafarsa sanye da Booth din takalminsu mai ruwan goro. Bayansa goye da wata Bakar Jaka karama ta baya. Dukawa ya yi yana kara tamke igiyan takalminsa duk da yana Duke ne ammh Dole za'a kirasa ingarman Namiji Tunda ya had'a tsawo da Fad'i na Budewar cikakkun maza. Ya nan nan a duke Wani farin Saurayi ya sake Fitowa daga Dakin shima da irin shigar sak, Daga gani ni masu yi ma kasa Hidima ne ma'ana Corpers. Kofar Dakin ya Rufe ya saka makullin yana kullewa lokaci d'aya yana fadi'n"Hala yau tafiyar kasa zaka yi? Ya fad'a daidai Lokacin da ya gama kulle Dakin, Shima yana da jakar baya kalan kayansa wato green. Sai ya kara gyara zamanta a saman kafad'ansa na Hannun Dama Key din kuma sai ya zura a aljihun wandonsa. Wanda ke duke kuma bai tankasa ba,Illah cigaba da tamke igiyoyin takalminsa da ya yi, na tsayen ya kara kallonsa lokaci d'aya ya duba Bakin agogon Fatan da ke hannunsa cikin Kosawa yace"Mallam mun fa makara. Ka tsaya sai faman tamke igiyoyin takalmi ka ke yi." Sai a lokacin ya mike yana kara Dage wandonsa sama har ana ganin sawowin kafarsa mai cike da gargasa ga su nan duk sun kwanta. kai tsaye ya kai duban shi kan agogon Silban da ke hannunsa 8:20am na safe kuma ya kamata By now ya isa inda zashi. Yana shirin mgana wayarsa da ke aljihun wandonsa ta Dauki Vibration alamun ana kiran shi,Hannu ya saka ya ciro wayar yana duba mai kiran duk da yasan Daga gida ne, Tunda itace wayarsa da kowa ya san layin. Babbar waya ta makaranta ce da aiki ba kowa ya san shi da ita ba. Sunan UMMA da ya gani ne yasa ya yi kasake shi bai dauki wayar ba, shi kuma bai maidata aljihu ba. Saurayin da ke bayansa ya yi Dage tunda ya fishi tsawo ya leka yana Fad'in"Waye ke kira? Ko SULTANA ce? Da sauri ya kauce bayan ya jimke a wayar a hannunsa yana sauke numfashi, Dariya na gefensa ya saka kafin yace"Yarinyar nan na bala'in ji da kai, tana kulawa dakai kai kuma ga shi ban ga kana kula da ita ba" "Tahir..." Muryansa cikin Kaushi da asset din Zamfaranci acikinta ta katse Tahir da ke masa Tsiya. Rai ya bata kafin yace'Tahir me? Ba gaskiya na Fad'a ba. Ina fa lura da kai tun satin nan ta ke kiran ka da wayar Umma ba ka Dauka" Mirmishi ya saki kafin ya juyo suna kallon juna. Fuskarsa Ma'abociyar Haiba da zati ta bayyana, Baki ne mai ruwan kalan haske doguwar Fuska garesa Dauke da Dogon Hanci da idanuwansa matsaikata. Yana da Zagayyen Saje da gemunsa baki Suluf Cikin Yanayin Mganarsa ta cikakkun maza yace"Au ashe? wa ya saka ka aiki a kaina? Tahir yace"Sai an sakani? Kasan dai tare muke kwana nasan komai da ya Danganceka" Kai ya jinjina masa kafin yace"Ka sani mana Tunda ka na sakamin Ido" Ya fad'a yana hararansa Dariya ya yi lokaci d'aya ya Dafa kafad'ansa yana Fad'in"Na gaida Magajin gida" Wani mugun kallo ya yi masa. Da yasa da Sauri ya Daga Hannunsa sama yana Fadin"Afuwan. SADIQ.. " Kokarin maida hannunsa ya ke saman kafad'arsa ya yi saurin tureshi ya wuce gaba. Da gudu ya bi bayan shi yana Dariya. Duk da ya so kada Tahir ya yi masa shakiyancin Dafe nan sai da ya Dafa shi suna tafe suna Rangaji kamar wasu yara. Suna tafe zuwa bakin Titi Tahir ya kallesu ganin Sadiq s ya fisa tsawo shi kansa wajen kafad'arsa ya ke. Yasa ya ce"Tabdijam. Gaskiya ka na da Tsawo kamar wani Samudu" Kai tsaye Sadiq yace"Shi ne.." Tahir ya yi shegiyar Dariyan sa da Sadiq ya tsana kafin yace"Kai ma ka sani kenan? Kallon juna suka yi kafin Sadiq ya jinjina kai yana Fad'in"Ina maka Fatan samun lafiya Tahir yusuf Daura" Tahir na Danne Dariyansa yace"Ba ni lafiya ne? Sadiq ya gyada masa kai kafin yace"Eh mana. ai ciwon ka ba shi da mgani saboda Dariya soso min Hauka ne" Tahir ya dauke Dariyan sa ya na kallon Sadiq shi ko ya sha Mur ko kara kallon su bai yi ba,Tahir ya daga kafa ya bisa ganin ya yi gaba ya barshi sai da ya bari sun jera sannan yace"Nasan mganin ka. Innani zan gayamawa abunda kace a kaina. wato ina Hauka ko Sadiq? Mirmishi ya saki mai tsada ammh bai yi mgana ba. Tahir ne ya cigaba da zuba mganarsa yana jinsa ammh ba kowacce mgana ya ke bashi amsa ba. Duk da shi ba miskili ba ne ammh mganarsa Ra'ayi ce akwai Lokacin da Ra'ayin hakan baya zuwa masa. Suna tafe in sun ga gungun matasa Sadiq zai daga musu hannu ya yi musu sallama, in Dattijai ne kuma ya gaishe su da kwana bayan ya yi musu sallama. Tahir ma dolensa ya ke yi Tunda yasan Halin Sadiq suna yin gaba zai fara masa wa'azin yad'a sallama a tsakanin Mutane na tsaye ya gaida na zaune har ya Haddace wannan Mganar. Suna tafe Rai rai har bakin Titi suna zuwa Tahir yaga Sadiq na kokarin sama musu adaidaita, da Sauri Tahir yace"Mu hau mashin mana. mun makara fa." Ya fad'a yana kara Duba agogon Hannunsa Tara saura. Bai tanka sa ba sai da ya tsare musu adaidaita sannan ya kallesa lokaci d'aya yana Fadin"A daidaita zamu hau Tahir" Tahir ya bata rai kafin yace"Haba don Allah. Kamar wasu mata? Mu hau mashin mana Sadiq" Sadiq ya ja sa yana Fad'in"Adaidaita nace zamu shiga Tahir. Kuma da ka ke mganar Mata daman kai namiji ne? Yana mgana ya na Tura Tahir cikin adaidaita shima ya bi bayansa lokaci d'aya yana fadin"Ni kwangila za ka sauke ni. Shi kuma" "Pizzet zan sauka mallam" Tahir ya katse shi da Sauri yana kunkuni,;Sadiq sai da ya yi dariya kafin yace"Mallam mu je" Mai adaidaita yaja suka Fara tafiya Tahir ya sha kuni, yaki mgana ballatana Dariya sai ma ya fiddo wayarsa yana Famam dannawa shi kuma Sadiq na kallon Hanya. Sun kawo Bakin ABU aka tsaida shi wata mace ta shiga. Tahir ya matsa kusa da Sadiq ya na Hararansa cikin kunkuni ya yi tsaki. Sadiq na jinsa bai yi mgana ba yana dai ta mirmishi kafin su isa in da Sadiq zai sauka an dauka an ijiye yafi sau biyar Ran Tahir ya baci sai masifa ya ke wai yana Duba agogo wai ya makara Saboda Sadiq ya tankasa su yi tsiyar a hanya sai kuma bai kulasa ba har ya sauka, ana sauke shi ya ba da kudin gabadaya bayan ya fito da Wallet dinsa. Ta baya ya dawo ya Dafa kafadan Tahir ya na Fad'in"Abokina sai mun had'u ko? Da Sauri Tahir ya fizge kafad'ansa yana Fad'in"Mu je don Allah mutane sun makara ka tsaya kana ta share share a kan hanya." Mai adaidaita ya tada Napep dinsa yana fadin'"Bawan Allah adaidaita ta haya ce in da baka san share share sai ka dauki Drop. Kare da kud'insa ya sha lahaula.". Sadiq sai da ya yi dariya har Fararan Hakoran sa suka bayyana a waje. Daganan titi ya tsallaka zuwa Ofishin Road Safety. Chan ya ke C.D.S. dinsa shi kuma Tahir Fada zai je a secateria za su had'u da yan team din su dagachan zasu wuce in da suke na su C.D.S. d'insu kuma rana d'aya su ke yi duk Ranar Talata. Sai bayan La'asar ya baro wajen yunwa ya ke ji,cikinsa har wani kara ya ke yi, Yau furan da ya ke siya ya sha ya siya yaji nonon da karni ya kyutar da shi. Matar da ta ke kawo nonon bafullatana ne to ba ta zo ba yau sai wata ce ta kawo kamar Nononta ba pure ba wani iri ya yi masa baki da ya bata masa Yanayin bakinsa. Ba shi da matsalan siyan duk abunda ya gani yaji yana sha'awa. Bayan nan ya siyi zogala aka kwad'an ta masa shima yaji Bakinsa ba Dad'i ya kira almajiri ya ba shi. Sai rogo da gyada ne ya siya bayan ya kamo hanya. In dai ya zo ranar shi ya ke ba da sallar Azahar da La'asar a wajen in bai zo ba kuma wanda ya saba jan su sallah sai ya ba su. Adaidaita ya sake tara har samaru ya kuma gangaro da kafarsa har inda suka kama domin zaman bautar kasar su a garin Zariya. Yasan Tahir ya dawo tunda yasan ba sa Dad'ewa. Tura Dakin ya yi yaji a rufe bai damu ba ya na da key a hannunsa. Kuma yasan ya rufe ne ta ciki tunda aka taba musu sata suke kulle dakin su ko da suna ciki. Ya na ko budewa sai ga shi ya shiga yaga Tahir kwance share share akan katifa kamar ya mutu daga shi sai gajerun wando, ga kayan da ya cire nan watse a kasa takalminsa har da agogo jakarsa ga wata bakar leda nan a kasa itama ana ta muhallin. Sadiq yq bi sa da kallon Takaici. Tsallake kayan ya yi zuwa chan kurya ya zauna gefen katifar,Tahir cikin barci ya mulmula ya maka ma Sadiq kafarsa, shi ko cikin fusata ya juyo ya Hauresa da Kafarsa shima bayan ya mike. Tahir ya kara juyawa zai koma Barci Sadiq ya sa takalminsa ya taka masa kafa yana Fad'in"Dilla ta shi mallam. Yanzu haka ko sallah baka yi ba ka kwanta kamar wani gawa" Tahir ya bude ido dishi dishi yana kallon Sadiq kafin ya yi mika ya mike zaune tare da Hamma haaaaa..! Sadiq ya ji haushi cikin kufuluwa yace"Ka tashi daga barci ba Salati ba kiran sunan Allah. Sannan ka yi hamma ba Alhamdulillah ka bud'e baki kamar wani sakarai yanzu ko yara sun san in sun tashi daga barci su kira sunan Allah. Sannan sun san in sun yi Hamma su Rufe baki" Tahir ya bisa da kallo da Shanyayyun idanuwansa da alamun barci bai ishe shi ba. Sadiq ya shure kayansa da kafarsa yana Fad'in"Kai dai mugun kazami ne Tahir. Miye haka? Tahir ya mike yana mika lokaci d'aya yana Fadin"Kar ka isheni fa. Na dawo a gajiya me ka ke tunanin zan iya tsinana ma kaina? Sadiq ya kalli Tahir cikin takaici ya ma kasa mgana illah kad'a kai kawai da ya yi yana fad'in"Biyar saura ka je ka yi sallah Mallam" Ba musu Tahir ya ja wandonsa ya zura ya saka wata karamar riga da ya Dauko saman akwatinsa,:sannan ya fice Daga Dakin bayan ya zuba ruwa a buta . Sadiq ya bishi da kallon Haushi. Ba ya iya zama da kaya a watse a daki shi Mutum ne da ke son kimtsi. Karshenta shi ya kare da tattara ma Tahir kayansa ya ninke masa ya Bude akwatinsa ya saka masa. Sannan ya fito masa da karamin wando da Riga na shan iska. Yasan waye Tahir da Hauka wajen dauko kaya sai ya kara watsar da wasu kayan kuma bazai maida ba ko ya yi mgana kunnen uwar shegu ya ke yi da shi. Bakinsa har tsini ya ke yi saboda mgana ammh in dai akan Tahir ne a banza ne. Shima kayan jikinsa ya cire ya shanyasu saman Hanger saboda su sha iska, Akwatina uku ne a Dakin Biyu na Sadiq d'aya na Tahir ne shima karamin ciki ya Bud'e ya Dauko Jallabiya ya saka Mai ruwan kasa. Ya zura ya kuma kai komai nasa a muhallinsa Dakin Tsaf kamar na mata,komai yana muhallinsa. Gefe katifarsu ce Babba na kwanciya Sai wajen kayansu, Kayan kwalliya na maza sannan sai wani Dirowa kasa kuma inda suke jera takalmansu. Daga gefe kuma Gas din girki. Sai kayan abinci da kayan girki. Sai botikan wanka guda Biyu sai babban roba in da suke Tara Ruwa. Daga kusurwa kuma ga karamin Fridge din su tunda suna zuwa da miya ko wani abun da zai lalace shiyasa suke da Fridge din. Kafin Tahir ya shigo har ya gyara gadon ya share Dakin. Sai da ya gama Hiran sa da Matasan da ke gefen dakinsu suna waje suna wanki sannan ya shigo ya ta da Sallah. Sadiq na zaune a gefe yana kallon shi har ya Idar ya mike yana ninnike Darduman Lokaci d'aya yana fad'in"Sultana dai ta huta in dai ta bangaran gyaran Daki ne" Yana jinsa ya yi masa banza sai ma ya jaho Ledan Rogonsa ya Dauko ya Bude ya fara ci. Gefensa Tahir ya zauna yana leka ledan gabansa kafin yace"me ka ke ci ne?Rogo da aya? Tab! A ci lafiya" Tashi ya yi ya bude fridge ya Dauko bakin Coke dinsa guda d'aya da ya siyo da zai dawo ya saka a Fridge ne Tunaninsa za'a kawo wuta kuma yau suna jin Halin na su. Gefen Sadiq ya kara komawa ya zauna ya jawo ledansa da Sadiq ya ijiye masa nan gefen Littafansa tunda kowa bangaran da yake kwanciya yana ajiyan littafansa masu muhimmanci. Cake ne babba aciki ya fito da shi yana ci yana korawa da lemu gefe d'aya kuma yana Faman chart ta wayarsa. Sadiq bai ci rogon da yawa ba yaji ya Chusemai ciki sai kawai ya Ture ya kalli Tahir yana fad'in"Ka ci." Tahir yace"A'a Arammah kai dai kaci ni nagode" Sadiq ya yamutsa Fuska kafin yace"Ya cushemin ciki ne." Tahir ya kallesa a karkace kafin yace"Ka ma ci sa'a a irin yameyamen da ka ke yi ma cikinka baka fara ciwon Tsakuwar ciki ba" Sadiq ya kallesa kafin yace'"Fatan da ka ke yi min kenan? Tahir ya Daga lemun hannunsa da Cake yana fad'in"Afuwan" Daganan ya cigaba da shan lemunsa yana had'awa da Cake Status ya ke kallo an saka wakar Turanci har yana bi. Sadiq ya koma ya kishingid'a yana Fad'in"Ka dafa mana abinci" Tahir ya yi masa banza sai da ya kara maimaitawa sannan yace"Wani abinci kuma? Baka ci rogon ka ba. Ni kuma kaga iya wannan ni da wani abu sai gobe in muna raye" Sadiq ya yi kasake yana kallonsa yasan rashin Mutumcin Tahir saboda yasan girki na da D'aya daga cikin abunda ke ba shi Wahala baya ma kwantatanwa Tahir din ke musu abinci. Shiyasa wani Lokacin bai juran wulankancin Tahir ya ke fita ya samu wani abu yaci. Tahir kuma kamar da gayya sai yaga Dama ya ke d'ora abinci ko ya yi ta abubuwa ya na bata Lokacin barin ma in yaga ya yi mgana ko ya Lura yana jin yunwa. Yadda ya Fahimci Tahir ya so ya wulakanta ne yasa ya mike ya saka Dogon wando ya Dauki kudi cikin Wallet dinsa ya fice. Yana ji Tahir na Fad'in"Me zamu Dafa? Ko amsa shi bai yi ba ya zura Takalminsa masu taushi ya fita,Sallama ya yi ma matasan da ke waje yan makaranta ne su. Ganganrawa ya yi cikin Layin Tsamiya in da yake siyan awara. Yaje da kansa ya siyo aka saka masa yaji da kabeji har da albasa Dabam sun san shi Custumer din su ne Sosai Sadiq yasan muhimmancin awara. Sadiq ba bu abunda ba ya ci shi mutum ne kamar Social kamar kuma ba Social ba. Rayuwarsa Sannu sannu ya ke binta yadda ya Dauki al'amuransa sai ya baka mamaki a irin matsayinsa na Rayuwa. Ababen duniya masu dadi da kawatuwa ba su dameshi ba ya fi son na Mutanen da suka Dauki Rayuwa a sannu. Duk wani abu na gargajiya Sadiq na Cinsa su ne cimarsa ma tun zamanin suna Hostel a Cikin Abu zariya. Tunda daga shi Tahir nan suka samu Shedar Degree din su na Farko. Ko da ya koma Daki Tahir na zaune in da ya barshi da waya a hannunsa ammh ya gama shan lemunsa da Cake dinsa ya kuma watsar da ledojar da goran anan bai kwashe ba. Ko mgana Sadiq bai masa ba ya tattara dattin ya fita waje ya watsa cikin Abun shara. Yazo ya Dauko Filet karami ya juye awaransa da yajinsa tana tashin Tiriri ya samu gefe ya shimfid'a Darduma ya zauna. Daman ya wanko Hannunsa da ya fita waje ya yi bismillah ya fara cin awaransa Hankalinsa kwance. Tahir na kallonsa Jefi Jefi shuru dakin ya Dauka na wasu mintina kafin Tahir ya kauda shurun da cewa"Jb na gaisheka." Sadiq ya jinjina kai bai yi mgana ba sai da ya cinye awaran bakinsa. Sannan yace"kun had'u ne? Tahir ya ce"A ina? a Chart muka yi mgana da shi." Daganan Sadiq bai kara magana ba sai da Yaji cikinsa ya kusa cika, sannan ya mike ya isa ga Fridge ya Bude ya Dauko Ruwan gora guda d'aya yana juyowa yaga Tahir gaban a waransa ya Dauka yana Fad'in"A ina ka siya awaran nan? Allah ya sa ba wajen kazaman masu awaran nan na bakin Titi ba ne? Sadiq ya tsaya kyam yana kallon Tahir bai samu masa mgana ba illah ya Duka ya ja Filet din awaransa yana Fad'in"Ko ma nan ne ina ruwan ka? Baka ce ka koshi ba? Tahir yace"kamshinta ne ya yi min Dadi. Mu ji Allah ya sa da Dad'i" Sadiq ya Daure fuska kafin yace"Kasan Allah? Bazaka ci ba." Tahir ya yi dariya ya tura na Hannunsa baki ya tauna yana lumshe ido Kafin yace"Kai..Wow. da'di k'aramin don Allah" Sadiq ya ce" ka fita ka siya in ka matsu" Tahir yace"Ga shi ka siyo mana. kasan Allah? Nima sai na ci" Tahir ya mike Sadiq ya mike suka Fara kokuwan awara Tahir na sai ya ce Sadiq na bazai ci ba. Suka Fara Zagayen Dakin da gudu Tahir na Bin Sadiq a baya. Daman so ya ke ya gajiyar da Sadiq din ya yi fushi ya ba shi awaran ahakan ce ta Faru daga karshe ya dungura masa Filet din yana Fadin"Tahir.." Da Sauri Tahir ya katse shi da Fadin'"Nagode Abubakar Sadiq Sulaiman Shinkafi." Karamin tsaki yaja ya koma saman katifa ya kwanta ya juya ma Tahir baya. Yana jinsa yana Fad'in"Awaran nan ta yi dadi a ina ka siya hala? Yasan bazai tankasa ba shiyasa yace" ina Tunanin me yasa aka haife ka a zamfara ba'a shinkafi ba? Kafi dacewa da gayun kauyen nan abokina." Da Sauri Sadiq ya juyo yana Fuskantar Tahir cikin mirmishi yace"Da Sauki tunda ba'a Daura za'a Haifeni ba." Tahir ya fashe da Shegiyar Dariyarsa. Sai kuma me? Kawai sai ya shake ya fara Tari Sadiq ya yi kwafa kafin yace"Tahir Allah ya kara" Tahir idanuwansa Jajir ya Dago yana Fadin"Ruwa Sadiq. Ruwa.." Sai da yaga Tahir ya ji jiki sannan ya mike ya Dauko masa ruwa ya mika masa ya bude ya kwankwad'a kusan Rabi, sannan ya koma ya kwanta a kasan cafet din dakin yana maida Nunfashi cikin azaba. Shakewar yaji ba ta da kyau ko kadan Tahir har ya Fita Hayyacinsa Yana jin Mirmishin Sadiq yana Fad'in"Nan gaba ka koyi ladabin cin abin Tahir." A wahale Tahir ya ce"To ya Alarramma Abubakar Sadiq." Sadiq yace"Ba gatse ba ne Sunana kenan" ******* Yanzu kam ba abunda zance ma Allah sai godiya, Rayuwa ta yi mana kyau da inganci, Ciniki mu ke yi sosai na kan sana'o'in mu, musamman ma Danwake na Safen nan shinkafa da wake ne cinikin sai a hankali. Sai muka dawo da yin Danwake tare da Daffafen wake, Sai man kuli da manja duk wanda ka ke so a saka maka. Matasa sun gane ma Danwaken da yan makaranta sosai a ke siya. Ayyukan sai suka maidani mai yawan Aiki ya kasance na kan jima ban Tuna Tarin kaddarorin Rayuwata ba. naa kan manta cewa Rayuwata ta na cikin Tsaka mai wuya ne. Amma jikinta ya yi kyau bata kara ko Zazzabi ba, ni ne karfin duka ayyukan Habiba Saboda makaranta, Sai dai ta na taimakamin in tana gida sannan ita kan Shiga kasuwa in bukatar haka ta taso, duk da ina Fita ammh ba kasafai ba na tsame kaina da shiga Cikin mutane saboda Gudun gori da Habaici. Ko acikin gidanmu ban tsira ba haka ko yan'uwan su suka zo a fito ana nuna ni ana mgana kasa kasa. To menene sabo a abunda suke Fad'a kaina duk abunda zasu fad'a an riga su Fad'an sa. Yau ni kadai ke ta aikace aikace ne, Habiba bata nan tana gidan Adda Fati tun jiya. Ita ta kira tace Habiban ta zo bata jin dadi suna ta Fama da zazabi ita da yara. Sau tari Mutanan gidanmu na yawan Fad'in ina ba su mamaki. a yanayin jikina kamar bazan yi kuzari ba ammh kuma ni macece mai zafin Nama ko aiki ne mai wuyan Ban fara ba, da na fara shikenan cikin Lokaci kad'an zan gama shi. Amma ta na yawan fad'amin cewa yanayina yanayin Adda Hari ce itama mace ce mai zafin Nama da komai cikin Hanzari da Kazar kazar. Sai goma na Safe na gama Saka Danwake kuma ya kare duka bayan na gama ana ta aikowa na ce babu,Bayan na gama kankanta abubuwan da na bata na kawowa Daki na kawo na wankewa na wanke,Sannan na shiga daki na samu Amma na Sallar Walha. Zama nayi gefen katifarta na Bude kwanon shan da ke cike da koko, ni da Dama mata da Safe, na saka karamin kofin da ta gama sha na zuba na koma gefe ina sha tas na shanye tunda ba tsami bazai min matsala ba. Daidai Lokacin Amma ta Idar da addu'anta ta Dago tana kallona kafin tace"Ki kara mana in bai isheki ba" Kai na girgiza mata kafin nace"ya isheni Amma kwarnafi na ke gudu. Don ma naji ba shi da Tsami ne na sha da yawa" Amma ta jinjina kai kafin tace"To ai baki ci komai ba Hasiya? Cikin Tabbatarwa nace"Na ci wake da mai da yaji Amma" Amma ta kuramin ido kafin tace"Kin tabbatar? Kin san kina da lulura kuma ki rika wasa da cikin ki" Dariya na yi kafin nace"Amma kada ki damu a koshe na ke" Bata kara mgana ba ta fara jan Casbahan da ke hannunta ni kuma na isa ga jakar da nake tara kudin ciniki na Dauko na zube su a tsakar Dakin ina Kirgawa bakina har kunne na ce ma Amma Danwaken ana samu da shi Sosai. Amma ta gyada kai kafin tace"Sai mu godema Allah" Sai da na gama kirga kudin na ware na wanda za'a je kasuwa ina cewa"Amma garin Danwaken mu ya kare ga Habi bata nan" Amma tace"Ki je da kanki mana. Tunda baki da tabbacin yau zata dawo kada ki jirata kuma gobe babu garin a hannu." Da shawaran Amma na yi amfani sai da nayi wanka sannan na yi shirin Fita. Tunda Amma tace sai anjuma zatayi wanka ni na fara yi tunda fita zan yi, Hijabina na saka har kasa akwai Nikab na Habiba ne shi na ara na saka bana son a samu wata matsala ne. Amma na gefe tana kallona har na Soke yar wata jaka mai igiya ta Habiba ce na ara saboda saka kudi nayi ma Amma sallama tayi min fatan Dawowa lafiya na fita. A tsakar gida na ci karo da Maman Boy da maman salihi nasan sun yi da ni Saboda naga suna nunani da baki ban damu ba na fice ina Fad'in"Zan shiga kasuwa" Da Sauri Maman Boy ta mike tana Fadin"Tsaya Hasiya. Daman ina son Citta da kunafari nawa sun kare" Dole na Tsaya,Ammh Maman boy sai da tayi min taron mutane sako wajen na mata biyar suka hadamin ga shi kuci kuci hakanan na karb'a bani da Mafita. Har na kai bakin Titi ba bu wanda yaa ganeni bakina alaikum na shiga kasuwa wajen masu had'a garin Danwake naje na fad'i iya adadin za'a hadamin sai na shiga cikin kasuwa na siyo wayan murhu da gawayi. Sai na siyo wake da mangyad'a da Borkonu sai kayan maggi da kayam kamshi, sai sakon su maman Boy na jima a kasuwar sannan aka gama Had'amin komai tunda sai da na jira akayi nika. Aka had'amin komai cikin wani karamin Buhu mangyadan ne kawai na rike a hannu kada ya fashe. A bakin Titin Tsamiya na Sauka Tunda bazai shigo dani ba. Na Dauki Buhuna a saman kaina mangyada kuma yana Hannuna Lokacin Rana tayi Biyu har ta wuce. Ta layin da zai kai mutun har gidanmu na bi inda masu awara ke layi wajen su biyar suna ta siyan su har da masu Dankali da kosan manja. Da zan wuce naga matasa a wajen tunda daman wajen zamansu ne. Naji muryan wani Saurayi yana Fad'in"Ke mai awara nan barayin ina ake saida Danwake mai Dad'i da Safe haka? Na ji sanda wata yarinya tace"Nan dogon gida ana Danwake da Safe mai Dad'i Da wake in mutum na so, sannan mangyada ko manja sai wanda ka zab'a". Na wuce acikin raina ina jin dadin ko bakomai akwai jin Dad'i a yabi sanar mutum, har na isa gida bakina yaki Rufuwa ina ko sauke kayan saman kaina na fara gayama Amma. Tayi dariya kafin tace"Hasiya manya.." Ina Dariya nace"Amma baki ji dadin da naji ba" Ammh ta yi mirmishi. Sallah nace zan yi sannan na warware kayan na mikama su Maman boy sakon su har sun fara lekowa suna Fadin"Hasiya nace dai baki manta da Sako na ba ko? Tafarnuwa da ungurnu ne ni dai Sakona" Har sai da nace musu Sai na yi Sallah zan Fito da sakon su na basu, sannan suka shafamin lafiya. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *10/09/2023* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari. Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah. Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus *07* Shi Sadiq a kan Quantity Surveying ya samu shaidar Degree d'insa na farko. Ma'ana sani kan harkan shimfid'a Titina da sauran su. Shiyasa ya ke bautar kasar sa a Dismento Nigeria limited Old Sokoto Road, Samarun Zaria. Shi kuma Tahir Politcal Sciences ya karanta wato harkan abunda ya shafi Siyasa. Ya na bautar kasar sa ne shima a wata goverment secondary na cikin Samarun zaria. Yau litini tun bakwai da Rabi ya fita ya bar Tahir a gida ya na faman nuku nukun sa, Sai da ya biya in da ya fara siyan Danwake mai d'an karen Dad'i ya mika karamar kularsa da ya ke zuwa da ita ga yaran da ba'a rabasu da wasa a kofar gida suka shiga suka amso masa. Dashi ya tafi wajen aikin nasa. ya riga ya saba tunda ya samu Danwaken nan da shi ya ke tafiya wajen yana karyawa har kuma wani Lokacin ya yi ragowa ya dawo da shi gida. Watarana kuma wani wanda suke aiki a wajen shima hidimar kasar ya ke yi suke ci tare. Karfe biyu saura ya baro kamfanin kamar yadda ya saba adaidaita ya hayo zuwa anguwar Tsamiya aka sauke sa a bakin Titi ya gangaro da kafarsa. Yasan Tahir na rigashi dawowa tunda makarantar sa ta fi kusa gida. Sannan ba tsayawa ya ke a tashi ba da ya gama Darasinsa ya ke gudowa gida Tahir dan Shiririta ne ba komai ya ke ba ma Muhimmanci ba shi dai wayarsa kamar tafi komai muhimmamci a rayuwarsa. In kaga ciwon da Tahir bai Dauki waya a hannunsa ba to kila sai dai ciwon Ajali mutun ne mai mu'amala da kafafen yad'a zumunta sosai ba irin Sadiq da waya ko hawa irin kafafen nan ba su dame shi ba, Shi dai barsa da kallon Fina Finan korea da turkish Drama suna nan cike a Laptop dinsa ko Tab dinsa. Sai kuma sanin kan Na'ura mai kwakwala wannan tun yana karami ya iya sarrafata tunda ya taso ya gansu ne shima agidan su. Dakin a bude Tahir ya barshi Saboda Sabon Iskanci har da su Dage Labule sama a dakin na Fuskantar waje, ga shi cikin Anguwa mai cike da Mutane sai wucewa ake yi ana ganin musu asirin dakin Ba wannan ya fi bata ma Sadiq rai ba sai ganin yadda Tahir ya yi kaca kaca da Dakin Alhalin kafin fitarsa da Safe sai da ya kimtsa dakin shara ne kad'ai bai yi ba yace sai ya Dawo. Tun kafin ya shigo ya gimtse fuskarsa Sanye ya ke da Riga da wando,Rigar mai Dogon hannu ce mai ruwan Ash da layi layin blue. Wando kuma jeans ne mai ruwan kasa sai Rufaffen baki takalmin da ke kafarsa bayansa Rataye da Jakar laptop d'insa sai karamar kular da ke hannunsa. Yana shigowa ba domin sanin Darajan Sallama ba, da ba zai yi ba sai dai yasan Darajanta tunda shi Musulmi ne Murya ba Dad'i yace"Assalamu Alaikum.." Bai ko jira Tahir dake kwance kan Katifa da ya yi wani da'i da'i ya amsashi ba cikin Fusata yace"Haba Tahir. Haba Tahir meye haka? Ya fad'a yana kallon Tahir din cikin Takaici. Tahir da ke kwance daga shi sai dogon wando ko Riga ba bu ajikinsa wayarsa na Hannunsa yana Dannawa ya yi matashi da d'aya hannun na shi Cikin kosawa da irin ka katsemin aikin gabana ya Dago yana kallon Sadiq kafin yace"Miye wai? Kai dai baka raina abun korafi wlh. Zafi ne ya isheni ga shi ba wuta shiyasa na bude kofar na kuma D'age labulen mu samu iskar Duniya ya shigo mana" Daga haka ya koma ya cigaba da Dannan wayarsa yana ta faman mirmishi. Sadiq ya tsaya kawai ya na kallon Tahir bakinciki ya chuse ranshi. Kai tsaye ya sauke jakar hannunsa tare da kulan ya dago cikin Zaro ido yana nuna Dakin da kallo kafin yace"Au baka san me kayi ba ko Tahir.? Ba ka san ma me ka yi ba ko Tahir? Tahir Hankalinsa na kan wayarsa yace"Me na yi kuma? Da muryan ko ajikinsa. Sai kawai Sadiq ya yi kwallo da Takalmin Tahir da ya cire nan tsakar dakin sai da ya Daki bango ya Dawo Tahir ya Dago yana kallonsa baki Bude kafin yace"Me ya yi zafi Alarammah? A fusace Sadiq yace"Ban sani ba. na gaji da kazantar ka Tahir na gaji. Kai yaro ne? Komai sai an gayamaka zaka yi? Bakina kullum akan mgana d'aya ne ehe? Ya karishe fad'a har jijiyon kansa na tashi alamun ranshi ya baci ganin haka yasa Tahir ya ijiye wayarsa nan saman gado ya mike yana fadin"Yi hakuri to. Kasan gajiyan da nayi yau? Daman fa ina da shirin na mike na kwashe na share dakin ne ka shigo" Ya na fad'a lokaci d'aya ya duka yana kwashe kayansa da ya cire watsar da su anan. Sadiq sai faman Hararansa ya ke yi kamar idanuwansa za su fad'o kafin yace"mgana d'aya ba zaka Dauka ba Tahir. Shikenan ka cigaba" Daga haka ya karisa gaban Fridge ya Bude ya Dauko ruwa ya sha anan duka ya shanye ya fita waje ya jefar da Goran sannan ya dawo. Tahir dai dole ya kwashe duka kayansa ya kimtsa wajen saboda yaga Ran Sadiq ya baci yasan Halinsa haka ya ke ba shi da Saurin fushi ammh kuma ya tsani ya rika maimaita mgana Daya. Sai ga Tahir har da Shara, sai bayan ya gama ne ya yo alwala ya zo ya yi sallah Lokacin da ya idar Sadiq na kan katifa barayin da yake kwanciya tunda Kafitar tsakiya Dakin suka sakata kowa farko ya ke so ba Lungu ba, sai suka raba Gardama suka sanyata a Tsakiyan Dakin. Ya na sallame sallan yaga Sadiq da ke danna laptop dinsa har ya sauya kaya zuwa saukkaku na zaman gida. Yanayin kallon kad'ai da ya gani ya sha jinin jikinsa da Sauri yace" kana wani kallo na kamar na yi sabo? Lalurin sallar azahar har sai la'asar ta gabato." Sadiq kamar ba zai yi mgana ba sai kuma ya jinjina kai kafin yace" kai dai ka sani. Kai ba yaro ba ne in daidai ka aikata ma ai ka sani Tahir ba ruwan Sadiq aciki ni dai tsakani ga Allah na fita hakkin zaman tare" Daga haka ya cigaba da kallon allon Laptop dinsa shi kuma Tahir ya mike yana Hamma kafin yace"Abokina yunwa na ke ji. Kuma miyar nan fa ta kare ita kenan jiya na yi mana shinkafa da Miya." Banza da shi Sadiq ya yi ganin haka yasa ya nufi kular da ya shigo da shi ya jawota yana fad'in"Wai miye a kulan nan ne da ko da yaushe ka ke fita da ita kuma ka dawo da ita? Sai dai me? Ya kasa mgana da ya ga Sauran abunda ke ciki Danwake da wake da Manja an chakud'a an ci an rage kad'an. Da sauri Tahir ya kauda kansa kafin ya Dago yana kallon Sadiq cikin Jin haushi yace"Haba Sadiq. Tsakani ga Allah abunda ka ke yi yanzu ka kyauta kenan? Ba tare da Sadiq ya kalleshi ba yace" me na ke yi? Tahir yace"Gidadanci mana. Eh mana Gidandanci mana ban da haka miye ribarka na zuwa da Danwake wajen aikinka Tsakani ga Allah? maganar gaskiya wannan dabi'ar taka ta katon bagidajen Kauye ne" Mirmishi Sadiq ya yi kafin yace"To miye bambamcin Tahir? Ai bagidajen kauyen ne ko baka sani ba? Ya fad'a yana saka kallon wajen Tahir wanda ya rufe kular ya dawo gaban Sadiq ya zauna saman katifa yana Fadin"Danwake a kula kamar wani yaro dan firamari Sadiq? Ina laifin in Danwaken ka ke son kaci ai akwai a Restaurant sai ka shiga ka siya kaci tunda kai dai ka san nasan abinci ko wani Restaurant in kana Ra'ayi zaka ci bai fi karfin aljihun ka ba" Yadda Tahir ya ke mganar zaka san abun ya mishi ciwo, duk da yasan Waye Sadiq ta wannan bangaran bai taba Tunanin abun na shi ya kara Lalacewa kamar haka ba. Wai Danwake a kula abun ma ba shi kunya ya ke yi wlh in ya tuna kuma wai ka shiga cikin mutane da shi kamar wani karamin yaro. Lura da Hakan da Sadiq ya yi shiyasa ya ture Laptop din gabansa ya Fuskancesa kafin yace"Rayuwa ce. Kowa da irin yadda ya ke tafiyar da tasa Rayuwar Tahir. Miye aibu aciki don na siya abunda nake so na tafi da shi wajen aiki na? Da Sauri Tahir yace"Wlh akwai aibu. Babban aibu ma kuwa. Aikin yara fa ka ke yi? Yaran ma kanana Sadiq. Haba don Allah" Tahir ya fad'a har yana wani juya Fuska irin yaji kunyan nan. Dariya Sadiq ya yi kafin yace" A wajen ka kenan ya ke aibu ni dai a wajena a daidai na ke kallonsa kasan Hausawa na cewa Daidai wani.." " Karkatan wani.." Tahir ya karishe cikin mamaki kawai yana kallon Sadiq. Shi kuma yana yi masa mirmishi sai kawai ya rike Haba yana fad'in"Ikon Allah.. Allah mai mutane kala kala kawai sai aka ganka ka fito da kula ka bud'e ka na cin Danwake da wake da Manja." Sadiq yace"I sata na yi? ni zan ci kayana ra'ayi na ne. Ban kuma takurama Ra'ayin wasu ba." Tahir yace"Ni tsaya ma a ina ka ke siyan Danwaken nan ne? Sadiq ya ce"chan ne wani gida a kasan layin wajen masu awaran nan da Dankali" Cikin takaici Tahir yace"kai ko a ina kasan gidan? Ko da ya ke in wajen ciye ciye irin wannan ne kai tsuliyan gari ne" Sadiq yace"Ni fa ranar naje siyan awara a wajen naji wani na tambaya ina ake saida D'anwake mai dad'i? sai wata mai awara ta kwatanta masa gidan kuma ta yabi Danwaken shiyasa nima nake zuwa ina siya. Kuma Alhandulillah akwai dadi ga tsafta" Tahir ya karkace baki kafin yace"A ina kasan ya na da Tsafta? Hala a waje ne a ke d'anwaken? Ko kasan me yin Danwaken ne? Sadiq cikin kosawa da Tambayoyin Tahir yace"ba'a waje ba ne acikin gida ne. Ta ya za'ayi na san mai yin Danwake Tunda ba gidan na ke shiga ba" Tahir ya ce"Uhm sai kaga yadda ake D'anwaken ka raina kanka Sadiq. ba fa kowa ke tsaftace abun sana'arsa ba, barin ma irin gidajen anguwannin nan. Wani abun wlh in kagani kamar kayi Amai.." "Tahir.. Tahir don Allah.." Sadiq ya katseshi bayan ya Daga masa hannu Dariya Tahir ya kwashe da shi kafin yace"Wai don nace Amai..Amai..!" Sadiq ya ce"Daman kazami ne kai. na sani" Tahir yace"Tabdijam! Ai dama a Shinkafi a ka haife ka zaka fi Dacewa da Katon kauyen Shinkafi ba na Birnin Zamfara ba." Sadiq ya yi dariya har sai da ta yi Sauti lokaci d'aya kuma ya kimtse fuska ya kurama gefe d'aya ido kamar mai Nazari. Kansa ya jinjina kafin yace"To ai ban yi maka karya ba Tushena kauye ne. Kuma kauyen Shinkafi. Ko ba'a Haife ni achan ba chan aka Haifi Abba. Sannan lokacin da aka haifeni Umma ta fara rashin lafiya ko arba'in d'ina ba'ayi ba Abba ya ce Innani ta tafi da ni da Umma Shinkafi ta na kula da ni, Sannan ina da wata Takwas saboda Laluran Umma Innani ta yayeni babu abunda bata ba ni na ci Saboda inganta lafiyata ba, Tahir ban sha Nonon uwa kamar yadda ka sha ba. Hannun Innani na zauna har na tsawon Shekara Shidda sannan Abba ya karbo ni na dawo zamfara Ka ga kuwa ka daina mamaki in kaga ina cin wani abu akwai sabon haka Tun ina da kuruciya da su na Saba, kuma ni Inanni ta yi min Renon uwa ka sani ko a yanzu ta mini gatan da ko Abba da ke d'anta ba ta yi ma shi ba" Tahir da ya yi Tagumi yana kallon Sadiq ya na jinsa ya Sauke ajiyar zuciya kafin yace"Shiyasa ko Hajja na je gida ta rika rawan jikin kawo min abubuwa taga na fara cewa ba na cin kaza sai ta fara fad'a tana fadin kai dai ka cika kircin tsiya shiyasa nake son abokin nan naka Saddiqu yaron nan har mamaki ya ke ba ni ga shi Dan gata gaba da baya ammh a irin Rayuwarsa kamar wanda baisan gata ba komai ci ya ke har kaji ya na fad'in Hajja zogalen nan ki ijiyemin zan ci da Daddare ammh kai sai shigen iyayin banza da Wofi tafi mara wayau shiyasa baka kiba kullum lange lange kamar iska" Gabadayan su suka kwashe da Dariya Tahir yace"Ina shan gori wajen Hajja komai sai tace Saddiqu ya fi ka Tahir kai kam sai fatan Shiriya." Sadiq yace"Allah sarki Hajja na yi kewar Dambunta da kwad'en Zogalenta yaushe zamu je Daura? Tahir yace"Kasan ko kwanaki ta yi ta fama da Zazzabi." Sadiq ya kallesa kafin yace"Subhanallah yaushe? Shine baka Fad'amin ba? Tahir yace"Kawu ya ce da Sauki shiyasa kaji ban Fad'a maka ba. Kasan Hajja da kafiya ga shi ta na ciwo ammh taki bari aje asibiti wai ita ta warke." Sadiq yace"In na ganta Innani na nake gani a tare da ita. Bambamcin kad'an ne ita Hajja ba ruwan Tsine tsine a bakinta.". Tahir ya fashe da Shegiyar Dariyansa yana Fadin"Allah Sarki Inanni gaskiya ina missing nata. Yaushe zaka gida na bika nima? Sadiq yace"mu bari weekend, Jiya Abba ke fad'amin Innani na Shinkafi chan ya barota wajen sha'anin Diyar Baba Saminu da akayi, So kuma ba na son zuwa ba ta gida. Abba yace dakyar suka lallasheta da ta ce sai tazo ta ganni ina nan ba uwa ba uba Allah yasa ina Hannu nagari" Tahir ya kara kwashewa da Dariya kafin yace"Allah ya ja da ran magajin gida da girman kujeran ka.." ya fad'a har yana daga masa babban yatsansa alamun jinjina. Sadiq ya make hannun yana Fadin"Ka bari Tahir." Shi ko sai fadi' ya ke"Takawarka Lafiya Autan Umma dan gatan Abba. shalelen Innani. Angon SULTANA" wata uwar Harara Sadiq ya sakar masa kafin yace"Tahir sunan Sultana ya fita a bakin ka? Inanni bata kyautamin ba" Ya fad'a yana yamutsa Fuska Tahir ya Dafa kafad'arsa yana Fad'in"Mutumina kaji dadin ka. Kai dan gata ne irin wannan zukekiyar Yarinyar duk ka kai kadai? Ya ke fad'a yana Dariya Lokaci daya yana kashe masa ido d'aya. Ture hannunsa Sadiq ya yi yana fadin"Tahir Allah ya shirye ka." Tahir yace"Ni dama Hajjo nima ta kamamin wata achan Daura yar Fara haka Danya Sharaf mallam" Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Ai tasan halin yan kayanta ne. In ko ta kama maka zaka iya kunya tat Tahir." Cikin Magiya da Fuskar Tausayi Tahir yace"Wlh a'a. Kaga da mun gama Hidiman kasar nan muka kama aiki sai kawai kaji mun angwance Rana Daya da yan Shillan mu Abokina." Dukkansu Dariya suka saka har suna Tafawa kafin Sadiq yace"A'a in muka angwance Rana d'aya wa zai rakani Dakin Sultana? Tahir ya bushe da Dariya ya Daki kafadar Sadiq da karfi yana Fadin"Shige abokina ashe kana son yarinyar nan sai ka rika wani basar da ita? Sadiq na mirmishi yace"Tahir ba komai ke bukatar bayyanawa ba. Sultana Zabin Umma ce. Sannan Burin Innani ne, ni kuma kaga matan nan biyu suna da Muhimmamci a Rayuwata da ko wuta suka ce na shiga wlh zan shiga. Sun gama min komai a Rayuwata. Sultana a gaba na Umma ta Reneta yarinya ce karama fa Tahir sai na zauna ina Biye mata? Ni ma yaron ka ke so na koma? Tahir ya ce da Sauri"ko ba ka koma yaro ba akallah dai ka Damu da ita kamar yadda ta damu da kai." Sadiq ya mike tsaye yana gyara zaman 3Quater da ke jikinsa lokaci d'aya yana Fad'in"Tahir har yanzu da Sauran Lokaci. Baka gane abunda na ke gayamaka ne? Shekarata Talatin wannan Shekaran Sultana ba ta wuce sha Shidda ba Jss3 fa take. Ba ta ko gama socondary ba, Sannan ni ma ina son Dora Masters dina bayan mun gama Servise din mu, ina da abubuwan yi a gababa ma su tarin yawan da ba na so wani abu ya Daukemin Hankali itama ba na so na zama Silan samun matsala a bangaran karatunta shiyasa kaga ina mata haka kuma mganar kira muna gaisawa, daga gaisuwa da tambayan makaramta bata iya fa mgana da ni,wani Lokacin ma in ta kirani da wayar Umma ina Dauka sai dai ta ce bari ta kaima Umma. Ka kyale yariyanan Kuruciya ne da Wauta ke Dawainiya da ita fa" Tahir na yar Dariya yace"Kuruciya da Wauta ko dai Soyayya? Wlh Sultana ta na sonka Sadiq" Sadiq yaja tsaki kafin yace"So? Tahir kai ma shekarunka ba su yi maka amfani ba. Ina yarinya kamar sultana ta san wani So? Tahir yace"Wad'anda ma basu kaita ba susan So mallam. Ni ka manta yarinya yar Jss2 ta turomin wasikar tana so na? Sai kace me kuma? Sadiq yace"Abun ya na faruwa ne da yanayin In da mutum ya taso. Rayuwar Sultana ba daya ya ke da matan wajejjan nan ba Tahir. Kawai dai kace ta san ni zan aureta haka iyayenmu suka tsara to na yarda akwai wannan Shaukin na sanin haka Tun da karuciyarta ammh ba zencen so ba Tahir" Tahir zai yi mgana Sadiq ya kallesa yana Fadin"Tahir.." Sai ya yi shuru yana jinjina kai kafin yace"Shikenan zamu maimaita mganar nan watarana in da rai da Rabo abokina." Sadiq ya sauka Daga kan katifar yana Fadin"Ranar jumma'a zamu tafi Daura mu kwana Asabar, Ranar Lahadi mu je zamfara sai mu dawo talata da safe." Tahir ya mike ya Daka tsalle akan katifa yana fadin"Ehhyeee..Gida gida Dad'i" Sadiq ya girgiza kai bai yi mgana ba Buta ya dauka ya zuba ruwa yana Fadin"La'asar ta kusa Tahir" Tahir ya duba agogon wayarsa kafin yace"Da sauran lokaci." Sadiq ya shafa cikinsa kafin yace"Cikina ya lalace yau ina ta shiga bayi a kamfani" Tahir ya kwashe da Dariya kafin yace"Ba dole ba. Danwake da wake fa kake ci? Ga yaji. Ai cikin ka ma na baka lafiya a irin yame yamem da ka ke masa ya ci ace kashin ka ya Daina karfi ya koma zawo ma" Sadiq ya yamutsa fuska kafin yace"Da gaske fa Tahir. In na fito wannan na biyar fa kenan" Tahir ya zaro ido kafin yace"Ka sha mgani? Sadiq ya fita da Sauri yana Fadin"Duba in muna da sauran filajin in kuma babu Tahir ka fita ka siyomin. Wlh cikina sai kartawa ya ke yi" Y na fad'a ya zura a guje ya shige makewayin su na waje Allah yasa ba kowa a baranda sauran masu Dakunan ba su dawo daga cikin makaranta ba. Tahir na dariya ya saka Rigarsa Fara T.Shirt ya Dauki 500 cikin Jakarsa da ya Dawo da ita daga makaranta ya fita. Chemist din ba nisa shiyasa ya jawo kofar sai dai ya isa gaban Makewayin da Sadiq ke ciki ya Daga Murya yana Fadin"Na fita ban kulle kofar ba. Ka kula da motsi" Sadiq na ciki sai ji ya yi ya ce"Uhmmm... Tsuwww..! Zawo na fita Tahir ya Fashe da Shegiyar Dariyarsa ya tsallaka Baranda yana fadin"Eh lalle dole in nemo maka mgani. kada cikin Dare ka zame min kaya na shiga uku" ******** *Dogon gida*. Alhamis_8:30am. Habiba na ke sakawa Danwake a roba, tana tsaye a kaina ta na Fad'in"Adda kada ki sa min da yawa. Ki ijiyemin na anjuma don Allah" Kai na jinjina kafin nace"ke kam da Danwake Habi" Dariya ta yi bata yi mgana ba na gama saka mata mai da yaji na mika mata ta karb'a. Sauri ta ke yi ta makara Daki ta shige da gudu. Ni kuma ta barni ina kiciniyar kwashe wanda na saka a wuta ga mutane suna jira na cikin gida da waje. Abun ne yanzu na wannan rayuwar sai godiyar Allah. Farko an fara da cire tallafin man Fetur ne, takala ya shiga wani Hali na Babu da k'anik'ani. Sannan sai man fetur ya rika tashi ya na Hauhawa, sai kuma ababen rayuwa da yau da kullum su ka rika tashi suna Hauhawan Farashi komai yanzu ya zama dan zani. Masu kudin ma suna ji ajika ballatana mu talakawan da ba tallafi sai mun tallafama kanmu da ire iren sano'i'on cikin gida. Shiyasa komai ya yi tsada har Danwaken yanzu na 400, bai iya kosar da Mutum sai dai aci kawai a gode Allah. Godiyar da na ke yi ma Allah da Sana'ar ba ta kwace a hannun mu, duk da ciki muke wasu Hidimdimun ammh kuma da Sauki acikin lamarin ba ma abinci, mu ci danwake da Safe ko mu ci wake,Da yammah mu ci shinkafar da muke siyarwa. Amma kuma daman yar koko ce da Farau Farau. Ko ayi mata Faten Tsaki da Shuwaka, sai bangaran ci da shan mu ya samu sauki bangaran Sabulun wanka da na wanki sai kuma in Adda Fati ta yi nukasanin kawowa ammh ta Dauke mana wannan bangaran. Duk da ina gajiya ammh ba na nunawa ko a fuska aiki na ke yi kan jikina kan karfina ni ce saka Danwake, juyawa kwashewa. Zuzzuba ma Mutane tare da sallamansu Layi a ke yi min abun sai godiya kawai. Sakamakon ya kasance Safiya sai ki ga babu chanji a Hannuna in aka zo siya nakan ce aje a dawo lokacin na tara yan canji. Ina cikin Kwashe Danwake Datti yaron Maman Salihi ne ya iso gabana da kyakyawan Kular da tun kwana goma da suka gabata ake zuwa siyan Danwake da ita. Ya na zuwa tun kafin ya yi mgana na ce"Na Dari takwas ko? Waken Dari hud'u Danwaken D'ari Hud'u sannan manja za'a saka" naa Haddace lissafin koma waye mai siyan Danwaken nan yana da ka'ida da Tsari ne. Dariya Datti ya yi lokaci d'aya yana mikamin Dubu daya lokaci d'aya da Fadi'n " ya ce ayi sauri" Kai na jinjina kawai batare da na yi mgana ba. Bansan meyasa na ji na Damu da ma ko waye mai siyan Danwake a kyakyawan kular nan ba. Ko saboda kirkin da ya ke min ne bansani ba? Tun ranar farko da ya fara siya ba chanji nace ma yaron da ya aiko ba chanji sai anjuma. Sai ya ce bakomai zai dawo gobe, washegarin da ya dawo na bashi chanjinsa bai karba ba. kuma Tun daga ranar dubu daya yake zuwa da shi cinikin 800 ya ke yi min 200 kuma chanjinsa baya taba Karb'a. Ko na aika da shi zai dawo da d'an aiken ne, kuma yaran gidan mu na son zama akofar gida da Safe haka saboda in ya aike ka ka fito sai ya baka Kudi. Ba ma su ba ni kaina ina jin dadin haka har acikin raina sannan sau biyu ina Tambayan Datti Yaro ne ko Babba ke aiko shi? Kai tsaye yace"Babba ne fa Tab" Sai da na yi Dariya ranar da ya Fad'amin haka. Jin yace ya na sauri ne yasa na ke hanzarin gama kwashewa na Fara sallaman shi, bansan fitowar Amma ba sai jin mganarta na yi a gefe na. "kawo na rika taimaka miki da zubawa" Na juyo da sauri ina fadin"Amma.." Bata samun zarafin mgana ba Habiba ta fito da shirin ta na tafiya makaranta, Ta na Fadin"Adda kudin tara zan tafi" Amma ce ta kwance hab'an zaninta ta Dauko mata naira Hamsin ta ba ta ta karb'a ta na fadin"Sai na dawo" Ni da Amma muka had'a baki muka yi mata Fatan dawowa lafiya. Robobin na mutane na tura ma Amma gabanta lokaci daya ina gayamata adadin yadda zata saka musu ni kuma na jawo kular nan mai kyau mai hawa uku yar doguwa da ita. kullum aka zo da ita sai na Dagata na kallah tana Burgeni ban taba ganin kula mai kyan ta ba. Ashe Amma na lura da ni har na gama kallo na saka Danwaken na bi kuma Tsarinsa,Wake Dabam, Danwake Dabam sannan yaji dabam da mai. Ina gamawa na mikama Datti da ke Tsaye yana jirana kafin na yi mgana yace '"ya ce in ba chanji a bar shi kawai.." Mirmishi na yi na mika masa ya fice da gudu har ina lekensa Amma ta kalleni ta kara kallona batayi mgana ba sai da muka sallami mutanen da ke kanmu sannan ta kalleni tana Fad'in"Hala Danwaken waye? Cikin ko in kula nace"Bansani ba Amma. mee barin chanjin nan nasa ne ban taba ganinsa ba" Amma ta yi shuru kafin tace"To koma waye Allah ya yi masa albarka." na amsa da Ameen Ameem. Amma bata barni ba sai da muka gama Duka. Sannan ta barni ina Had'a kayan ita kuma ta tafi raban Fad'a Tsakanin Maman boy da Kaltume. Ire iren rigimrigimun gidanmu ba sa Damuna wlh na riga na saba. To abunda ya ke kamar Ibada ayi da Safe ayi da rana ayi da Daddare. Dambe ko tun zamanin baya an sha cin uban Dambe ballatana Dogon gida yana da karfin suna na Dabi'ar Fad'ace Fad'ace. Fad'an dai Kaltume ce bata da gaskiya Kuma tsakani ga Allah halinta ne na Munafunci yi ma Mutane Labe in suna waya ko in sun yi baki. Shine ta yi ma Maman boy labe tayi wayarta da mijinta ta zo tana yad'ama su Maman Salihi wai mijin Maman boy neman mata ya ke yi. Taji maman boy nata fad'a a waya. Mgana ta famtsama agida har Maman boy taji shine ta Tada Rigima. Kaltume sai Rantsuwa ta ke yi ba ita ta Fad'a ba. Maman Salihi ma na Rantsuwan ita ta fad'a mata sauran na maida yadda akayi, Ina jin Amma na ta ba da hakuri Maman boy taja Daramam sai ta yi ma kaltume jina jina,abun takaici mijin kaltume fa na gidan bai riga ya fita ba ake wannan jidalin sai Dura manyan asharai suke yi ba dad'in ji, zagi Irin na ma su b'ata Tarbiyan in yaro yaji su. Shiyasa yaran su ba su da Tarbiya sai kaji munanan zagi a bakinsu ga rashin kunya. In ana irin haka Daki na ke shigewa yau ma haka nayi ina gama wanke wanke na kwashe komai na kai Daki Sauran Rushin kuma na saka mana Ruwan wanka. Ya zamu yi? Ba mu da wata mafita ammh gidan Haya ai ba gidan zama ba ne wlh. Ina fata da addu'an duk wad'anda ke gidajen Haya Allah ya Hore musu su yi na kansu. Mu kuma irin mu da muka d'and'ana rayuwar gidan kai kaddara ta kawo mu in da muke yanzu sai nayi mana Fatan ganin karshen lamarin. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *08* Ranar Jumma'a tun safe suka shirya tafiyarsu a son samun Sadiq ma tun 6:30am na safe su bi motar Katsina. Ammh nukun nukun Tahir yasa sai dai suka wuce takwas na Safe a zariya. Kamar shima bai son Halin Tahir ba, da yace su had'a kayansu waje d'aya ya yarda da batunsa. Sai da ya gama zama ya shirya musu kayansu na tafiya a karamar akwatinsa. Da duk abunda zasu bukata na tafiyan kwana Hud'u, Ammh Tahir da iskancin sai bayan an gama shiryan kayan ya ke fito da Tsirfe tsirfe daga yace ya manta ba'a saka masa kaza ba, sai ya ce ba kaza zai je da shi ba Sadiq yaji kamar ya cire kayansa ya sauya jaka. Sai dai makaran da suka yi yasa ya yi Hakuri Tunda ya san Halin Tahir ya had'a kaya da shi. Motar katsina suka samu Direct sai sun je ne zasu Hau na cikin garin Daura. A motar KST irin mu cin mutane sha takwas din nan ne, Tahir gaban Mota ya shiga. Shi kuma Sadiq baya son matsuwa sai ya shiga kujerun baya na daga su sai Direba. Sun Dauki Hanya aka fara Hirarraki na cikin motar haya na abubuwan da ke faruwa a kasarmu. Tsadar Rayuwa da yadda komai ya sauya sai kuma aka gangaro kan yan sace sace da ake fama da shi na Mutane a hanyoyin mu na tafiye tafiye. Sadiq na jinsu bai saka baki ba. Saboda shi bai cika saka baki a irin wad'anan hirarrakin ba. Ammh Abun mamaki Tahir har yana zakewa ana Hiran yan kidanafin ya Dage yana ta zagin su yana Fad'in cewa ai yan iska ne sai sun ce a basu kudin fansa an gama Biyansu kuma sai su kashe rai. Duk a motar Tahir ya fi kowa Zakewa muryansa tafi ta kowa amsa kuwwa acikin Motar. Har yana wani Tada jijiyan wuya Sadiq na ta so ya Juyo su had'a ido ya yi masa gargad'i ta cikin idanuwansa ammh ina Hira ta Rufe masa ido. Yasan mafita daya ce itace wayar Tahir yasan ba ta subucewa daga Hannunsa. Da Sauri ya tura masa da sako kamar haka "Tahir.. Tahir wlh ka kiyayi kanka ka na Daga murya in akwai su acikin motan nan fa? Ganin Sakon Sadiq yasa Tahir ya Dawo cikin Hayyacinsa. Sai ga bakinsa ya yi gum wani na gefensa har ya na tabosa irin acigaba da Labarinan ammh ina Sai Tahir ma ya fara barcin karya ganin Dannan wayar tasa ma bazai fisheshi ba. Kuma ya na kama bakinsa sai Hirar ta Sauya daga baya ma kowa ya cigaba da Harkan gabansa Daman Tahir ne uban yan Zakewa. A haka har suka isa katsina sha d'aya na Safe daganan suka sake samun motar Daura. Sai daya saura na rana suka iso Daura. Gidan su Tahir babban gida ne, na ginin kasa Inda yayyensa da matansa ke ciki da Sauran iyayansu da kawunansa. Tahir maraya ne ba uwa ba Uba hannun Kakarsa ya taso Hajja. Suna sauka da kayansu yaran yayyyen Tahir suka kyalla ido suka gansu suka zura cikin gida da Gudu suna murna Fad'i suke yi"Ga Baba Dahiru chan yazo. Hajjo ga Baba Dahiru." Kafin su ce me wasu yaran sun yayyayemesu har sun dauki akwatinsu zuwa cikin gida. Sai dai suka bisu a baya suna shiga gidan Shashen Hajja na daga ciki ne sai sun wuce shashen matan gidan. Suna shiga sai tashin oyoyo Dahiru ke tashi sai dai kaji ana oyoyo Baba Dahiru mutanen Zaria. Sadiq Dariya ta kusa Shakesa yana kannewa da ganin yadda Fuskar Tahir ke yi in akace masa Baba Dahiru. Sai da suka gaggaisa da su sannan suka karisa Shashen Hajja. Allah Sarki tunda taji zuwansu ta kasa zama ta na Tsaye kofar dakinta tana Duban Hanya Tunda an shigo da kayansu dakinta. Suna shigowa ta washe bakinta cikin Tsananin Murna ta ke fad'in"Maraba da bakin Zazzau. Ah'a har da Saddiqu a she? Maraba lale da Saddiqu" Sadiq ya yi mirnishi ya karisa har gaban Hajja shi da Tahir ya rankwafa zai gaisheta ta saka Hannu ta rikosa tana Fadin"Haba Saddiqu mike mike..Ku shigo ciki maraba" Tahir ta kallah kafin tace"Dahiru maraban ku da zuwa' Tahir ya hura hanci kafin yace"Hajja wani irin Dahiru don Allah? Sunana Tahir..Sunana Tahir Hajja Ahto" Hajja ta make kansa tana Fad'in"Tafi d'an nema Dahiru muka sani mu dai ba wani Attahir ba" Me Sadiq zai yi in ba Dariya ba ya juyo yana kallon Tahir kafin yace"Dahiru shiga gaba mu je" Tahir ya balla masa Harara shi kuma yana Dariya ya bi bayan Hajja zuwa cikin Dakinta. Allah Sarki yar tsohuwar nan ta kasa zama saboda su kawo musu wannan kawo musu wannan Farinciki ya kasa barin Fuskata sai faman tambayansu take ya karatun ya'yan nan? Tahir na jin Haushin Daman sunan da ta daina kiransa da shi yace"Hajja sau nawa zan fad'a miki mun gama karatu Hidimar kasa muke yi yanzu..? Hajja ta ce'Yo ina ce duk karatun ne ko? Tahir bai kara mgana ba Sadiq ya bari da kara yi ma Hajja bayani. Ta washe baki kamar ta gane tana fadin"Yauwa na gane yanzu. Saddiqu ya wajen iyayen naka da sauran yan'uwanka? Ina kakarka? Sadiq yace"Duk suna gaishe ku Hajja." Daga nan suka bude hira tsakaninsu, Hajja da karfinta ba kamar Innani ba, Domin a shekarunta kasa da na Innani ne, ba ta wuce 70 haka shiyasa da karfi a jikinta sannan jiki ya saba da Wahala tuntuni ba kamar Inanni ba, duk dai itama ta yi zaman kauye ammh bata cikin Wahala. Ruwa kawai su ka sha sai Furar da ta Dama musu saboda jumma'a ne yasa suka yi alwala zuwa masallacin jumma'a suka yi sallah. Sai wajen uku suka dawo gidan chan suka had'e da yayyen Tahir suka gaggaisa suka kuma Dungumo zuwa Dakin Hajja a tare da aka gama cika shi da abinci kala kala na tarbansu. Sadiq ya saba zuwa gidan su Tahir tun suna makaranta ya saba da duka Ahalin Tahir kamar yadda shima ya saba da na shi Dangi. Kowa a gidan su Tahir yasan waye Sadiq kamar yadda Sunan Tahir ya yi tambari a gidan su Sadiq, tare suka had'u suka ci abinci Shi dai Sadiq Dambun Zogale ya ci Tahir kuma ya ci Taliya da Miya da Nama,Sadiq Naman kadai yaci saboda Nama na daga cikin abunda ya fi so duk Duniya. Sallar La'asar ya tada su suka tafi masallaci bayan sun fito kuma ba su dawo gidan ba, sun had'e da abokan Tahir tun na kuruciya suka zauna akofar gidan su Tahir suna ta Hira sai da aka kira sallar mangariba sannan suka tafi masallaci ba dai su suka dawo gidan ba sai bayan Sallar Isha'i. Suna shigowa suka iske kanwar Tahir mai bi masa Zulaihat tazo har da Girki ta yo musu. Tana ganinsu ta washe baki tana Fadin"Yaya Dahiru sai yanzu? Tun dazu nazo Hajja tace kun je masallaci' Tahir ya ware mata ido kafin yace"Ke.. ina wasa da ke ne? Ba na gayamiki ki daina kirana wani Dahiru ba Sunana Tahir" Hajja na saman Darduma ta na lazimi tace"Kaji tsirfan banza, da Dahiru ubanka ya yanka maka Rago. Shi muka sani kuma Shi zamu cigaba da kiran ka" Sadiq ya yi mirmishi yana Rufe baki ganin Tahir ya yi wani Fuska yana Huci Jikin Zulaihat ya yi sanyi sai ta Juya tana kallon Sadiq kafin tace"Yaya Sadiq sannun ku da zuwa" Ya amsa mata cikin sakewa yana Tambayanta ya gida da yaran. Tahir da kansa ya gaji ya saki Fuska, ballatana da ya Zulaihat tace alele ta yi ta kawo musu sai ya warware suna ta fira ballatana da yayyensa suka shigo suma aka had'e ana ta Hira ko da ba ma su kudi ba ne ammh akwai kaunar junansu da kyakyawan zumunci a Tsakaninsu. Sannan da shakuwa da kaumar junansu musamman Tahir da suke ganin shine karamin su Tunda Zulaihat ta yi aure ta gina na ta iyalan. https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V Sai karfe sha daya suka watse su ma sallama suka yi ma Hajjo suka dauki kayansu zuwa Dakin Tahir na cikin Shashen Hajja daman nan suke sauka Daki ne irin na yan kauye dai. Tsaf an gyarashi Inda Sadiq ke da Tabbacin Hajja ta gyarashi ammh Tahir ai son jikinsa da kazanta bazai barshi ya tafi ya barki Dakin a gyare ba. Sakamakon sun gaji kuma ba su samu Hutu ba yasa ba su bata Lokaci ba suka bi lafiyan Katifar Tahir wata yar yaloliya da ita. Ba su farka ba sai asuba Da asuban ma Sadiq ne ya tashi Tahir kamar yadda suka saba ko achan baya. Bayan sun dawo sallar asuba suka koma barci ba su tashi ba sai goman Safe shima Hajja ce tazo dubasu tana Fadin barcin su ba na lafiya ba ne su tashi hakanan, ita ta saka musu ruwan zafi dukkansu suka yi wanka suka sauya kaya sannan suka shiga Dakinta suka karya. Sun iske kayan karyawan su kala kala daga Dakunan matan yayyen Tahir har Zulaihat ta yo musu kunin gyada da Fanke shi Sadiq ya ci Tahir kuma Tea ya sha da Buredi. Sannan suka kwanta Dakin Hajja suna ta Hira. Tahir kan gadon karfen Hajja ya yi Dare dare yana charting shi kuma Sadiq na zaune samar Darduma a tsakar daki yana taya Hajja bare gyada suna ta hira in ka shigo ka gansu sai ka yi Tunanin shine jikan nata Tahir ne bakon. Sai da abokin Tahir Jamilu yazo ya jasu suka fita zuwa gidansa ya yi aure Tahir din na Zaria. Chan suka je amarya ta yi musu abinci sai a hankali Tunda karamar yarinya ce Tahir sai shakiyanci ya ke yi ma abokinsa wai ya auri kwaila. Sadiq na kare ma Jamilu Tahir ya kallesa yace"Dole ka kare masa mana. Tunda duk tafiyar ku daya ce" Sadiq yace"Eh mun ji din". Ya na da sakin jiki sosai Tun farkonsa Daman mai son mutane ne kuma ba shi da Bakunta ballatana amincin da ke Tsakaninsa da Tahir ya wuce duk yadda Mutane ke Tunani a kansu. Ranar yini suka yi ziyarce ziyarcen gidajen yan'uwan Tahir har gidan Zulaihat sun je ta yi ta rawan jiki da su Sadiq yace Danwake zata yi masa. Shi kuma Tahir yace ta Dafa masa kwai. Sadiq ya zunguresa ya na fadin"Wai ajiyan kwan ka bata da zaka ce ta dafa maka? Tahir yace"Kai ajiyan Garin Danwaken ka bata da kace tayi maka"? Da ya ke ta na jinsu sai ta yi Dariya kafin tace"Kowa zan yi masa abunda ya ke so" haka ko akayi kowa ra'ayinsa ta yi masa Mijinta ne kuma yace duk abunda suke so ta yi musu Daga karshe Tahir nata Fad'an meyasa ta yayyaka ma Sadiq kwai a cikin danwakensa Tunda yace shi baya cin kawai Sadiq yayi masa bakam yana cin Danwakensa yana Santi. Sai Dare Hajja ta gansu sai fad'a take yi tana fadin"ina kuka shiga ne yau? Tun dazu na gama Tuwon. Yan'uwanka sai zuwa neman ku su ke yi bakwa nan" Sadiq ne ya ke fad'amata inda suke je yau tace sun kyauta sun yi ziyara. Ba su ci tuwon ba sun koshi sai dai Sadiq yace ta yi masa Dumame da Safe. Sai adaran Sadiq ke fad'ama Hajja da Safe Gusai zasu je. Ta fara fadan ba su gayamata da wuri ba nan da nan ta mike ta fara had'a abunda ta ke da shi Wanda zata bama Sadiq ya kai ma iyayensa. Tun safe suka shirya kafin Takwas sun karya ,sun kuma shirya tsab Hajja ta bama Sadiq leda cike da su kuka,kubewa garin kuni,zogale danya da wacce ta bushe kayan kamshi sai aya mai kyau ta ce a kai ma Innani. Yayyen Tahir har tasha suka rakasu suka ba su 10k. Sadiq dai bai isa ya ce komai ba tunda ko ya yi mgana ba za su saurareshi ba. Da zasu tafi Kasim wanda shine Babba ya Dafa kafad'ar Sadiq yana Fadin"Ku kula Sadiq. Allah ya tsare ku mungode Allah ya bar zumumci" Sai da Motarsu ta tashi sannan suka koma gida. Da wuri suka isa Gusai, Sadiq sai yaji wani irin iska farinciki na shiga jikinsa da gaske ne ba gida kamar gidan ku. Ba kuma gari kamar garin ku, daga nan suka samu abun hawa zuwa Tudun wadan Gusai. Lokacin da Sadiq ya Buga makeken get din gidansu Mallam Tajudeen ya Bude get din ya gansa sai ya washe baki cikin Tsananin Farimciki yace"Ma sha Allah. magajin gida barka da sauka. Mallam Attahiru maraban ku da zuwa.." Sadiq ya yi mirmishi ya na Dafa kafad'an Mallam Tajudden kafin yace"Mallam mun same ku lafiya? Daidai Lokacin da ya ke kokarin karban Jakar hannunsa sai ya hanasa ya noke yana fad'in"A'a kai fa malamina ne me yasa zan bari ka karban min kaya? Mallam Tajudden ya yi dariya kafin yace"Ammh ni a karkashin mahaifinka na ke. Biyayyata a gareka Dole ce" Sadiq bai ce komai ba ya mikamasa Akwatin ya karba da Sauri ya sake Bude musu kofar suka shiga Tahir na Binsa a baya Lokaci daya yana fad'in"Mallam Taju Tahir fa sunana ba Attahir ba." Da Sauri Sadiq yace"Ko Dahiru zai ce? Tahir ya tokare shi da takalminsa ta baya yana Fadin"Uban Dahirun" A tare suka saka Dariya shi ko Malam Tajudden da gudu ya shege shashen Innani Saboda yasan itace ta Farkon da ya kamata tasan magajin gida ya dawo. Suna tafe a haraban Gidan Sadiq na kallon Motocin da ke fake a Haraban gidan cikin Tsananin kewa ya ce"Abba na gida kasan yau weekend ko zai fita sai yammah." Tahir ya bi motocin da kallo. Shi fa har mamaki yake in yaga Sadiq a wani wajen na wata irin rayuwa. Sai ya Tuna mahaifinsa da gidansu da Duka Danginsa sai ya rika mamaki gata iya gata ba wanda Sadiq bai mallaka ba Motar hawa ko wace iri ya ke so zai hauta ammh in ka ganshi a yana yawo da kafarsa a layi sai ka rantse bai taba ganin Mota ba. Muryan Sadiq dai ta katsesa sanda ya ke fad'in"Kaga fa Tahir akwai baki a gidan nan. Wacan kamar Motar Yaya Sa'im" Tahir dai sai dai ya kallah baya mgana suna tafe suna bangazan kafad'an juna kuma suna tafiyan wahainiya. Tahir ya juya baya ya kara kare ma girman gidan kallo da girman Shashe shashe na gidan da irin kayan alatun da ke cikin gidan sai ya koma ya bi Sadiq da kallo da ke tafiya zuwa Shashen Innani. Kawai sai ya girgiza kai ya kara d'an gudu ya cimmasa lokaci daya yana Fad'in"kamar ba daga gidan nan ka fito ba" Sadiq sai ya murmusa kafin yace"Mutane da yawa haka suke dauka" Tahir ya kallesa kafin yace"Dama ni ne kai Sadiq" Da Sauri Sadiq yace"Tahir ka zama mai godema Allah da Ni'imarsa sai ya kara maka." Tahir ya yi mirmishi kawai bai yi mgana ba. Sun kusa isa kofar Shashen Innani kenan sukaji mganarta fad'i take yi"Kai Mallam Saju ba'a san malamai makada Annabawa da karya ba. Ka Rantse Kwarankwatsa Magajin gida ne ka gani" Sadiq ya kalli Tahir shima ya kalleshi suka fashe da Dariya. Da sauri sauri suka nufi Shashenta suna shiga suka isketa Tafe da Sandarta ga gilashinta a Fuska Mallam Tajudden na gefenta. Daga bayanta kuma Siyama ce da Sultana sai yaran Sa'ima su Abadallah. Daman suna Shashen nata ne Tun Safe da Abba da Umma tare da Mama suka shiga gaisheta bayan Taba Hira sai suka tafi Shashen Abba suka barta da Sultana Daman yar gidanta ne ko Innani bata ga kowa ba bata cika Damuwa ba. Tafi damuwa da in bata ga Sulsana ba acewarta ba. Sa'ima ce tazo tafiya da yaranta da tazo gaishe da Innani suka zo tare da Siyama shikenan ta bar su nan ta koma Shashen uwarta. Ko da Mallam Tajuddeen ya shigo da akwatin Sadiq yana ma Innani albishir ga Magajin gidan ne sai Masifa take yi da faman tambayan ba Sa'imar ta zo ba? Ta kwashi ya'yanta ta tafi mana sun gaji da su. Siyama yarinya ce sa'ar Sultana sun riga sun san Halinta ba su bi ta kanta ba. Innani duk son ta da bako to in yazo gidan Sulaimanu kada ya wuce kwana uku komai mutumcinku da taga ka share kafa zata fara sakin Manganganun an zo an dora ma Sulaimanu nauyi Allah na Tuba shima Rufin asirin Allah ne ba shi da shi. Ko da kuwa jikokinsa ne tace ai suna da Gidan Ubansu su zauna chan mansa. Innani ba ta yarda da Mallam Tajuddeen ba shiyasa ta mike kamar ta kifa tana ya rantse dai da gaske Magajin gida ya gani. Ko a yanzu din ma bata lura da shi a gabanta ba, sai Faman fadi ta ke Mallam Saju ya rantse kada yazo karya ya ke mata. Sultana ta bayan Innani ta ke lekowa tana kallon Yaya Sadiq shi kuma Hankalinsa na wajen Innani yana ta mata mirmishi Siyama ta Buga Ihu ta nufesa tana Fadin"Wlh Innani da gaske Yaya Sadiq.." Ta fad'a jikinsa cikin Tsananin murna Su Abdallah ma suka nufesa suna fadin"Uncle.." Rikesu ya yi gabadayansu yana Dariya Innani sai ta rikice ta fara fadin"Ke don uwarki Siyama Ina magajin gidan" Sadiq ya saki su siyama ya karisa ya rike Sandar innani ya saka Hannu ya ciro glass din idonta ya goge mata sannan ya maida mata Lokaci daya yana Fadin"Ga ni nan fa Tun dazu a gabanki Innani ko dai har yanzu Idanuwan naki da sauran gyara bakya gani Innani" Ai jin muryan Magajin gida ya Rikita Innani ta rikesa gam cikin Lalube tana Fadin"Allahu Akbar Abubakar Saddiqu dai a gabana."Sai ta fashe da kuka tana fadin"Yau dai ga magajin Sulaiman ya dawo. Dole na damu kwana nawa bamu yi mgana ta wayar zamanin nan ba. Sulaimanu fa kai kadai garesa magajinsa Dole na shiga Damuwa in ban jika ba" Rumgumeta ya yi yana Fadin"Innani ina nan lafiya. Ai na gaya miki Hidimar kasa na ke yi achan Zariya ko..? Innani tace"Eh haka kuma kace to yanzu daga chan Zariyan ka ke? Kai tsaye ya juya yana kallon Tahir wanda ya Dauki Afiya. Ya nuna mata Tahir kafin yace"Daga Daura muke. Tare da Tahir muke" Innani ta yi shuru ta na bin Tahir da kallo kafin ta yamutsa fusaka tace"Waye kuma wani Sahir? Sadiq na Dariya yace"Attahiru abokina Innani" Ai sai ta washe baki tana Fadin"A'a dan kwalba uba kace Attahiru naga ya yi wani fari ne kuma shine don sheganta bai zo ya rumgumeni mun yi masa Oyoyo ba." Sadiq ya kalli Tahir ya na Dariya Shima Dariyan ya ke ya Sauke Afiya ya Nufi Innami ya Rumgumeta yana Fadin"Allah ya bar mana Ran Innaninmu" Ta make kansa tana Fadin"Kaji dadin Tsokana ta ko" Dariya ya saka idanuwansa na kallon Sultana da ke bayan innani kanta na kasa ta na wasa da gefen Hijabinta. Da karfi yace"Sultana daman kina nan? Ya makaranta" Sai alokacin Sadiq ya ganta kallo Daya ya yi mata bai yi mamakin Tana wajen bai sani ba. Yarinyar ba ta da Hayaniya ko kadan. Yana mamakin yadda ta so ta zo daya ma da Innani. Sai a lokacin ta gaishe shi ya amsa cikin Sakewa kadahan kadahan. Ta kuma gaida Tahir ya amsa yana Tsokarta da Matarmu.. Tana jin haka ta ruga da gudu tana jin kunya Sadiq ya Take kafar Tahir yana Hararansa da ido shi ko ya yi kamar bai gani ba. Innani ta tattara su sai Shashenta bayan ta ce ma Siyama"Maza je ki gayama iyayen ki ga Magajin gida nan da Attahiru a kawo musu abinci. Ta juya ta na kallonsu suna zama a kujerun falonta domin Dakin Innani ko amarya ta sameshi to sai Hamdala. Sadiq ta kalla kafin tace"Magajin gida me zaka ci ne a kawo muku? Kai ne baka fadi kuna hanya ba da Tun Safe na hana kowa zaman lafiya a gidan nan" Sadiq yace"Innani sai anjuma ko zamu iya cin wani abu. Sai da muka karya sannan Hajja ta bari muka kamo Hanya" Innani ta washe baki tace"Shiyasa na ke kaunar kakar Attahiru. Ta na kular min da kai kamar yadda na ke kula da kai, To ya kuka baro su? Attahiru ya wajen yan'uwa ka na chan Dauran? Tahir ya bata amsa da suna gaisheta lokaci daya da Tura mata ledan gabansa yana Fad'in"Hajja tace a kawo muku Innani. Ayar ciki tace taki ce" Innani ta ja ledan ta kara gyara zaman gilashin idanuwamta Lokaci daya tana Fadin"Kai naji dadi kamar tasan ina son wasa hakora na kwanakinan" Sadiq ya kalleta yana mamakinta matar da kullum cikin cin nama take da kayan dadi ammh tana Fad'in kwana Biyu bata wasa hakora ba. To ina ma taga hakoran? Ta na washe bakin yaga na Robanta das a bakinta suka kalli juna da Tahir suka saka Dariya. Sultana kunya yasa ta kasa zuwa Falon Abba ta fad'a musu dawowan Yaya Sadiq sai Siyama ce taje ta Fad'a. Umma ta mike da Sauri ta na Fadin"Auta na yazo ganin gida kenan" Haka ma Abba ya mike har jikinsa na Rawa Fadi ya ke yi"Mun yi mgana da shi jiya kuma bai ce min zai zo ganin mu ba. Ke Suwaiba a shirya ma Magajin gida abun karyawa." Siyama ta yi saurin cewa"Abba shi da Ya Tahir ne" Abba na bin bayan Umma yace"To daman duk in da kika ga Magajin gidan zaki ga Attahiru a wajen.. ki yi kokari Suwaiba kafin Innani ta fara fadan an barsu da yunwa." Mama ta ce"To Alhaji ammh mu je nima mu gaisa da su. Siyama zata yi ma Salima mgana zata ji da abun karyawan na su" Abba yace"A'a ba na son korafin Innani kinsan Halinta kije kawai ki yi abunda na saka ki" Mama bata da mafita illa juyawa zuwa Shashenta tana Danne abunda ke ranta. Tana shiga ta ga Sa'ima da Salima suna Hira afalo ganin yanayinta yasa suka hada baki wajen fadin"Mama lafiya? Sai ta saki Fuska kafin tace"Magajin gida ya zo. Kuje shashen Innani ku gaisa da shi kafin kakarku ta fara tsinan ku." Salima ta mike da Sauri tana Fadin"Bros ya zo? Kafin mama ta kara mgana ta fice a guje Sa'ima ta mike ta na gyara Lullubinta tace"Mama bari na je mu gaisa da kanina na yi kewarsa sosai." Mama ta murmisa tana fadin"Ki turomin Siyama ta taimakamin wajen hada musu abun kari" Sa'ima ta amsa ta na Ficewa. Tunda Mama ke da girki sannan Ranar asabar da Lahadi yan aikin su basa zuwa tunda yaran nan na gida kuma a Tsarinsu a karshen sati duk mai girki ita zata yi da kanta saboda Alhaji na gida. Ko da Sa'ima ta isa Shashen Innani ta iske Abba rike da Hannun Sadiq kamar wani zai kwace sa gefensa Umma kuma ce ya d'ora kansa saman kafadanta ya narke kamar yaro. Gabansa kuma su siyama ne da Salima sai su Afiya kowa sai mgana ya ke yi Salima fadi ta ke yi"Yaya Sadiq tun wata daya da ya wuce na yi chart dinka a wsop baka duba ni ba" Ta fad'a cikin shagwaba Siyama kuma fadi take yi"Yaya Sadiq mu ma a siya mana waya ni da Sultana" Sai dai aka fadi Sultana ya Daga kai yana kallonta tana gefen Innani ta Rakube kanta kasa kamar wata marainiya. Tahir ya kallah da ke kallonsa gira ya daga masa shi kuma ya balla masa Harara. Innani sai msifa ta ke yi"Haba don Allah ku bar min jika ya Huta daga Dawowarsa kun fara damunsa da Korafe korafe." Sa'ima ta yi mirmishi sannan ta yi sallama Falon Innani Tunda ba wanda yasan da Tsayuwarta.. Tana shigowa Sadiq ya mike yana Fadin"Ya Sa'im" Kai tsaye ya mike ya Nufeta suka Rumgume juna cikin Farin ciki ta shafa kan shi tana Fad'in"Dan kanin mu min yi kewarka" Yana Dariya yace"Bakwa kai min ziyara Shiyasa" Ya fad'a cikin Shagwaba da Sauri tace"Kada ka damu zamu rika zuwa..Sannu da hanya Tahir sai tare da Sadiq muke ganinka ko? Tahir na mirmishi suka gaisa ta na masa Tsiyan baya zumunci sai da Sadiq ko. Umma da Abba bakinsu ya ki Rufuwa duk wani walwalan gidan Alhaji Sulaiman yana tafiya ne tare da Farincikin Abubakar Sadiq. Dakyar ya kwaci kansa zuwa Shashensa shi da Tahir suka yi wanka sannan suka kwanta su huta. Tahir na kwance saman makeken gadon Sadiq a cikin Bedroom dinsa. ya na kuma kare ma Dakin kallo ba bu abunda babu na more rayuwa. kaya ga su nan kala kala takalma shurfa ne guda kamar wadrope,Shi bai ga abunda Sadiq ya nema ya rasa ba abunda ma bai nema ba ya samu. Har cikin Bedroom dinsa akwai karamin Tibin bango bayan faskekiyar plasma da ke falo, Sadiq gajiya tasa ya fara barci shi kuma ya kasa sai kawai ya tashi ya koma falo ya yi flat saman Daya daga cikin kujerun Falon Sadiq bayan ya kunna kallo remot a hannunsa yana Sarrafa tashoshi. Iskar A.c na kala shi sanye yake da karamin wando da riga mara Hannu kayan Sadiq ne sabbi yana ma Tunanin bai Taba saka su ba. Yana nan kwance Siyama da Sultana suka shigo da basket cike da kayan karyawan su. Suka masa sannu da hutawa suka fita. Tarbiyan gidan su Sadiq mai kyau ce duk da sun taso cikin gata. Ko da Sadiq ya ke yayansu ba'a ba su daman su shigo shashen kai tsaye ba. yanzu ma sai da ya ba su izini sannan ba su zauna ba suna kawo abunda aka aikosu su ke tafiyarsu, gwarama yayenshi su Yaya Surayya su kan shigo su zauna ayi ta Hira. Tahir dai ya mike ya jawo kwandon gabansa Ferfesub kayan ciki ne, Sai Ruwan Zafi soyayyan kwai da buredi sai Ferfesun kaza yana Turiri. Shi ya zuba ya ci har ya na Dankwale da Buredi bayan ya gama ya sha lemun kankana mai sanyi. Ya koma ya kwanta ya na Hamdala. Tun yana kallo sama sama har barci ya kwashe shi wayarsa ba chaji ne sai ya sakata chaji cikin Bedroom din Sadiq. Ba su suka tashi ba sai Azahar. Shima din Sadiq ne ya tashe shi sun makara sai jam'i suka yi a daki. Suna cikin sallar a ka sake kawo musu wani kwandon abincin na safe ya Tadda na rana kenan. Sadiq ne kadai ya ci Jallop din shinkafa Tahir ya ce sai anjuma. Ashe suna barci ba su sani ba Innani ta saka Sultana ta yi ta kiran mata yan'uwan Sadiq ta na fadin kowacce tazo Magajin gida ya zo. Ko da suka sauya kaya suka isa Shashen Innani cike da ya'ya da Jikoki daman sun kosa su gansa Innani ta Hana su zuwa Shashensa tace yana barci kada adamar mata jikanta. Suna shigowa Dakin Innani ya Dau Sowan ga Bros. Har da Abba da Umma da Mama yau Shashen Innani suke tunda daman in dai Sadiq na gida wajen zamansa Shashen Innani ne. In yaje shaahen Umma sai domin kebewa ta uwa da Abunda ta Haifa, shashen Mama kuma yana shiga su gaisa su yi hira da Kannensa Shashen Abba kuma yana shiga in mganata sirri ta had'a su ko yana son ayi wani abun. Hajiya Surayya ce ta fara tasowa itace babba a dakin Hajiya Umma. Cikin Annuri tace"Autan Umma ya zama Saurayi" Tafada tana Dariya. sadiq sai mirmishi ya ke yi ya nufi yan'uwansa. Surraya ce da Sadiya,Sajida,da Sa'adatu. Subai'atu da Saddiqa ba'a garin Gusai suke aure ba. Sai bangaran Dakin Umma Sa'ima Sakeena,Shahida na Umra Saliha ta raka mijinta Seminar a lagos. Tsakiyarsu ya zauna suka yayyameshi suna sa kawai ke tashi. Tahir kuma na gefe shima cikin Farinciki suka karbeshi suka gaisa a Mutumce da Tambayan mutanen gida. Sai ya juya suka gaisa da Mama, Umma da Abba daman sun gaisa tun dazu, Innani ko na gefe sai Taunar ayarta take yi da ance Innani mu ji ayan sai ta fara masifa tana Fadin"Ba zan bada ba. Ba wacce ta siyo ta kawomin. Sai kakar Yaron nan Attahiru saboda haka ba Shegiyar da zata ci wlh" Sadiq ya kalleta kafin yace"Innani ba na hanaki zage zagen nan ba" Da Sauri Innani tace"yi hakuri Magajin gida raina ne ya baci. Haba duk abunda yaran nan suka ganni da shi sai sun yi kokarin rabani da shi.. nima D'an nawa ba arzikin garesa ba Rufin asiri ne kowace ta na da Miji taje mijinta ya siyamata mana" Kai tsaye ya juya yana kallon yan'uwansa kafin yace"To kun ji. Kada wacce ta kara rokar Innani abunta. Kowacce ta na da miji ya siyamata itama d'an nata da ke siyamata ba shi da wani kudi sai Rufin asirin Allah" Innani na Dariya da Hakoranta tace"Allah ya tsaremin kai Jikana." Dariya aka saka gabadaya Falon na Diraman Innani an samu dai bata Fashe da kuka ba ko ta yi tsine tsinen da ta saba ba. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki. *09* Kowa kokarinsa ya faranta ma Sadiq rai, maganganu kawai ke tashi kowa kokarinsa ya fad'i bukatunsa Sadiq ya cika masa. Ga Abba zaune ammh kowa ya tashi sai dai yace Yaya Sadiq ina son abu kaza. Ina son a chanzamin kaza don Allah. Salima cikin Shagwaba ta ke fad'in"Bros wayata duk ta tsufa don Allah a sauya min wata." Ta karishe fad'a cikin Shagwaba. Siyama ko gefen hannunsa na hagu ta makale kamar wata yarinya fuskar nan a tabe kamar zatayi kuka tace"Ya Sadiq mu ko wayar ba mu da shi. A siya mana ni da Sultana" Dariya ya yi yana shafa kanta kafin yace"ba yanzu kuka ka gama Jsce ba? Ku bari in kun shiga SS1 sai a siya muku ko? Nakwa nakwa ta yi da Fuska ganin haka sai ya ja kumatunta yana Fadin"Haba Autan mu Smile mana. Za'a siya muku waya wannan cewar Magajin gida ne" Jin haka yasa ta saki mirmishi ta juya tana kallon Sultana kafin tace"Sultana kin ji mu ma mun kusa zama manyan yara su Yaya Salima a daina mana wukalamci kan waya.". Ta fad'a tana nuna ta da baki Salima ta zaburo ta na fad'in"Ni sa'arku ce da kike gasa da ni? Yaya Sadiq ya kalleta kafin yace"Salima.." Ta kallesa sai ya girgiza mata kai. Ta gefen idanuwansa Sultana ya ke kallo da har lokacin ko Tarinta bai ji ba. Yarinyar nan ta na da aiki. Innani na jin su bakam kawai tayi bata kara mgana ba. Umma kuma da Mama suke taba Hira Abba kuma an kira wayarsa ya fita. Tahir na gefe ya na duba wayarsa ammh kacokan hankalinsa na kan Sadiq da yan'uwansa da irin kauna da Gatan da suke nuna masa a ransa yana jin Dama ace Dama ace, Dama ace Shine Sadiq da Duniya ta jima da Shaida wannan gatan da ya ke da shi. Big sis Hajiya Surayya ta kalli kaninsu kafin tace"Autan Umma sati na sama Muhsin zai dawo" Kallonta ya yi yana nazarin waye kuma Muhsin ganin haka yasa tace"kanin mijina mana da na so ku tafi waje karatu tare." Sai alokacin ya tuna da shi cikin Mirmishi yace"Oh Allah Sarki. Sai yanzu ya gama karatun na shi? Hajiya Surayya tace"Eh ammh zai koma ya samu kwarewa kan bangaran da ya karanta. Da yanzu ka tafi da muna nan muna shirya maka kyakyawan Tarba Shalelenmu" Kamar bazai yi mgana ba sai kuma ya yi mirmishi kafin yace"Big sis. Sunaanshi Muhsin ni kuma sunana Abubakar Sadiq. Ba zai zama Dole Ra'ayina ya zama na shi Ra'ayin ba. Shima ba lalle nawa Ra'ayin ya zama iri d'aya da na shi ba. Shi kanin mijin ki ne ni kuma kanin ki ne akwai bambamci Tsakanina da shi." Sa'ima ce ta yi karaf tace"To gaskiya in zaka yi masters dinka waje zaka fita ka zabi duk kasar da kake so kaji? Sadiq ya kalleta kafin yace"Yaya Sa'ima.". Da sauri tace"A'a mun gaji da ganinka kana gararanba a tsakanin Zariya da gusai kamar wani mara gata.". Sadiya tace"Kuma Alhalin ina Tunanin kaf set din su ba wanda ya kai shi gatan ba". Shahida ma ta saka bakinta gabadayansu suka yi masa caa da zencen zaman da ya ke yi a zariya. Sajida tace"Ni abun haushin ma haya fa ya ke mganar ya kama a chan wani gida suna zaune. In da ya yarda ba sai Abba ya siya masa gida achan ya zauna ba." Sakeena ta karbe da Fadin"Autan Umma mu dai ka dawo gida don Allah wlh muna kewarka ka bar garin nan sam ni Hankalina bai kwanta da zaman ka achan ba." Hannayensa ya Hard'e a kirji yana kallonsu yana faman mirmishi. Salima ta karishe mganar da cewa"Big bros kawayen mu duka yayyensu a kasar waje su ke karatu ni in suka Tambayeni rasa ma me zan fad'a musu na ke yi" Ta fad'a kamar zatayi kuka Dariya ya yi har Fararan Hakoransa na bayyana kafin yace"sai kice mu su a zariya ya yi karatu kuma yana chan yana Hidimar kasa." Salima ta Zaro ido kafin tace"Bros..". Kai ya gyada mata alamun eh hakane sai ta jime fuska ta yi mgana su Sakina suka saka Dariya. Tahir na gefe ya tsoma baki karo na Farko kafin yace"Sai ma kunga ire iren abincin da ya ke ciki.." Tahir bai tsaya ba ya shiga ba su labarin irin cimar Sadiq ke yi a zariya harda Danwaken da ya ke siya yana Tafiya da shi wajen aiki. Gabadayansu suka Bude baki suna kallon Sadiq shi kuma ko ajikinsa. Tahir yace"Abun haushin ma masu saida abubuwan ba su da Tsafta wani abun ma baisan da ga ina aka Sarrafashi ya siya yana ci ba. Ko ni ba na irin Rayuwar da Sadiq ya ke yi kamar wanda ya fito daga Daji." Sadiq ya kallesa kafin yaace"Daman daga ina na fito.? Surayya ta kalli Sadiq kafin tace"Why Autan Umma? Nan fa suka taso masa suna ta mganan gaskiya gwara ya dawo gida ya yi Bautar kasarsa. Su ka gama mganganunsu bai tankan su ba sai daga karshe Umma ta shigar masa ta na Fadin"Ku kyalemin Auta ya yi irin Rayuwar da ya ke so haba. ai ba kauce ma Hanya ya yi ba Ra'ayi ne kowa da irin na shi" Sai Lokacin Sadiq ya yi mgana cikin Halin ko in kula yace"Yauwa Umma Fad'a musu ba mai zab'amin abunda zan ci, cikina ne rayuwata ne ok.! Sannan in kun ga na baro Garin Zariya na gama abunda ya kaini ne sai ko in mutuwa." Kawai sai ji akayi Innani ta fashe da kuka Tana fadin"Allah ya tsine ma duk wanda ke jifan jikina da kalmar mutuwa. Sulaimanu ba shi da wani magaji yau in magajin gida ya mutu ina zamu saka kanmu.? Allah dai ya tsine ma duk mai yi masa fatan Mutuwa akansa wlh." Ta karishe fad'a lokaci daya kukan nata ya Dauke ai sai falon ya dau shuru kada wata ta tofa Innani ta Sauke mata Tsine tsinen da ke bakinta. Sai Dakyar Sadiq ya lallabata ta yi shuru ta hakura, Shima tunda ya ce bazai bari ba suka kyaleshi sanin Halinsa na kafiya da Shegen girmama Ra'ayinsa saman na kowa. Hira suka cigaba da yi na zumunci sallar la'asar kadai ya ta da su kafin nan sun yi masa bakin me zasu kawo masa? Kowacce na masa magiyan ya kawo mata ziyara kafin ya tafi tare da Tambayanshi me dame me dame zasu had'a masa in zai koma? Kai tsaye yace"Kowa ya san abunda na fiso ko? Salima ta yi tsalle tace"Nama." Suka saka Dariya gabadaya su san Sadiq kamar kura ya ke wajen cin Nama. Innani ce ta fattakesu da Masifarta fad'i ta ke yi"Kai dilla kowacce ta ja ya'yanta ta tafi gidan mijinta kun zo kun cikama D'ana gida zaku cinyemasa dan abunda ya tara to shima ba shi da komai Rufin asirin Allah ne" Surayya tace"Innani ke fa ki rika kiran mu kina fadi'n mu zo ga magajin gida yazo sannan yanzu kuma munzo, kina korarmu" Innani tace"fisabilillah an yi na mutumci da arziki. Ba sai ku tattara ya'yan ku ku tafi ba? To billahillazi in ma bazaku tafi ba ku fice min daga Shashena kun isheni yarinyar nan Sulsana na so ta kebe da magajin gida kun bi kun kankane, ku fa wani Lokacin girma ne kawai ammh ba ku da wayau kwata kwata ba ku san ya kamata ba" Ta fad'a ko ajikinta ta na kara ma zaman gilashinta zama a idanuwanta. Sultana da ke gefenta ta Dago a tsorace ta kalleta baki Bude tace"Innani.." Innani ta juyo a masifan ce ta na Fad'in"Innani me? Don ubanki ai ba karya na yi miki ba? In ba mgana kike son yi da shi ba uban kike min a baya kamar wata yarinya? Ko ni ce uwarki? Ba ga salamatu chan ba meyasa baki je kin nanike ta ba. ni tashi daga baya na tsufa haba fisabillahi ai na yi wahala da ya'yana ya isa haka wani shegen jika ya yi ta kansa ni ma ta kaina nake yi." Ga dariya ba Halin ka yi Dariya Salima ta saki dariyanta ganin yadda Sultana ta yi kamar kazar da aka Tsoma a ruwan zafi da Innani ta Tureta. Innani ta ji tashin Dariya ta Daga Sandar ta tana fadin"Wata shegiyar ce ina mgana ta na min Dariya? Salima ta Rufe baki tana zaro ido aka yi shuru ba wanda ya tanka ta Surayya taje ta dago Sultana da har ta fara hawaye ta riko hannunta tana Fadin"Karki damu da Innani an juma sai tayi cigiyarki.." Innani taji an yi banza da ita ana ta mgana sai kawai ta karkace baki kafin tace"Ko wacece ta yi dariya nan Allah ya tsine.." "Innani.." Sadiq ya katseta da karfi jin Muryansa yasa ta yi shuru ta kama Jan hanci kamar zatayi kuka ta na Fad'in"yaran nan na sulaimanu na arzikin dai duk sun kare yanzu duk diyan banza ne" Sadiq ya bude muryansa ya na Fad'in"Innani wlh in na fita daga Shashen nan har na koma bazan kara dawowa ba. Sau na wa zan hanaki tsine tsine nan? Ki na ta aibata jikokin ki da kanki..? Sai Innani ta kasa mgana, jin ya yi shuru yasa ta dago ta na kallonsa kafin tace"Ka yi hakuri magajin gida Raina ne ya baci. Ka yi hakuri in ka gujeni ina zan saka raina ni Dije ba ni da kowa sai kai anan duniya nan" Kai Tsaye yace"Ba ki na da D'a ba. ga Abba nan mu ba kin gama tsine ma na ba? Da sauri Innani tace"Wlh ban tsine muku ba. Dukkan ku ya'yan nan Allah ya yi muku albarka ya tsare gabanku da bayanku ya kare min ku. Allah ya shirya muku zuru'an ku gabadaya." Sadiq ya yi mirmishi ya karisa gaban innani ya zauna ya Rungumota yana Fadin"Ameen Ameen Innani na." Suma Sauran da Ameen suka amsa saboda Sadiq an samu Innani na ta zabga musu addu'o'i kafin su fita daga Shashenta dukkansu sai da suka sauke mata kudade Inanni na Hawaye tana fadin"Kai duka ya'yan Sulaimanu yan albarka ne. Allah dai ya yi muku albarka ya kare ku da Sharrin makiya. Ke sulsana ina kike ki kirgamin kudin nan muga nawa na samu? Surraya tace"Innani wata Sulsanan? Wacce kika ture kika kora.? Innani tace"Kaji sharri da karya abakin manya ni Dije yaushe na Taba Sulsana? Kai Saddiqu maza kaje ka tahomin da Matarka nan" Ba shi da mafita illah yace mata toh ficewa suka yi suka barta da Siyama itama din Innani sai fad'a take yi tana Fadin'Uban wa yace ki zauna min afalo? Ni fa Sulsana nace magajin gida ya kirata so na ke yi su samu kebewa tunda dai nan da wata Shekaran zan ce Sulaimanu ya yi musu aure nagaji da ganin wannan watsewar aciikin gidan D'ana yara sai rashin kunya da Rashin Tarbiya gwara kowwcce tayi ta kanta shima d'ana ya yi ta kansa" Siyama dai karshenta Fattakanta Innani ta yi ta fito tana fadin"Ga shi nan kici falon gabadaya. In ma kin kara ganin kafata." Innani ta Daga sandarta tana Fadin"In kika kara Dawowa sai na ci Ubanki. Lallataciyar yarinya mara tarbiya kawai. Kai Suwaiba dai bata iya Haihuwa ba duk ya'yanta ne suka batamin zuru'ar d'ana." Kowacce shashen uwarta ta shige kafin mangriba Sakina da Shahida suka hau motocin su suka tafi,bayan mangariba kuma Surayya da Sa'ima da Sadiya ma suka tafi da cewa gobe Zai ga Sakon su. Shi daman ya na waje tare da Mallam Tajudden suna karatun Bukhari da Musulim, Mallam Tajuddeen malami ne sosai mahaddaci masanin Hadisa shiyasa Sadiq in dai yana gida baya wasa da daukan karatu a wajensa. Tahir na cikin Shashensa yana fama da waya bai ma gayyacesa ba sanin Halinsa. Suna karatu karnukan Abba suna Damunsu da Haushi Sadiq ya kalli Mallam Tajudden kafin yace"Abba bai rage karnukan ba ko? Mallam Tajudden yace"an fita da wad'anda ka sani wad'anan manya ne guda biyu aka kawo su kwanaki." Shuru ya yi bai yi mgana ba ba domin Hujjar Abba ba. Da bazai bari ya ijiye karunuka a cikin gida ba. Sai da aka kira sallar Isha'i sannan suka Rufe karatun alwala suka Daura suka fita zuwa masallaci nan kusa da su. Bayan sun dawone suka yi musabaha tare da sallama Mallam Tajudden ya shige muhallinsa shi ma Sadiq ya koma shashensa. Ya na shiga ya ga Tahir rashe rashe kan kujera ga basket din abinci nan a gabansa ya ci duk ya watse komai. Kuma ya kure karan Tv kuma alokaci daya yana amfani da waya.. Sanye Sadiq ya ke da Jallabiya Mai ruwan kasa da Hula. Hannunsa kuma littafin bukhari da Musulim ne a Hannunsa. Yana shigowa kallo daya ya yi ma Tahir ya Dauke kanshi kafin ya cigaba da Tafiya zuwa Bedroom dinsa. Kamar daga Sama yaji Tahir na Fad'in"Alarammah barka da Dawowa." Sadiq ya juyo kafin yace"Yauwa. Ka yi sallah? Tahir yace"Wace sallar? Kai Tsaye Sadiq yace"Isha'i.." Sai Tahir ya zaro ido kafin yace"Wai kana nufin har an yi isha'i.? Sadiq ya yi karamin tsaki kafin yace"Ana ta jiran ka Tahir kaji ana ta jiran ka. Ka na da rauni wajen ibada ammh wajen Shagalan duniya baka da wannan Raunin Tahir ka gyara ka gyara Rayuwarka." Tahir ya yi dariya kafin yace"Ka na ba ni mamaki ko da yaushe sai ka na mganar na gyara Rayuwata?. Shin rayuwata ba ta akan hanya ne ko ya ya? Sadiq haushi yasa bai kara mgana ba ya Juya ciki ya na ji Tahir na Fadin"Naji yanzu zan ta shi nayi shikenan". Shi dai Shigewarsa ciki ya yi ya adana Littafinsa a muhallinsa. Wanka ya shiga bayan ya fito ne Tahir ya shigo ya shiga ya yi alwala sama sama ya yi sallar tasa kamar yadda ya Saba ya fita ya koma Falo kan waya kai kawai ya girgiza Tahir sai Allah kawai. Riga da wando ya saka Fari da baki yana son ganin Abba Kafin ya kwanta akwai mganar da ya ke so su yi. Falo ya fito kujeran da ke fuskantar Tahir ya jawo basket din gabansa. Pepe kitchen din da akayi domin sa ya ci duk da Tahir ya ci ammh ko Rabi bai ci ba naman kawai ya ci ya kora da lemu ya yi hamdala. kayan da Tahir ya bata duk shi ya tattara ya ijiyeshi nan gefe yasan su siyama zasu zo su dauka. Sai alokacin ya Dauki wayarsa ya na Dubawa. shi waya ya Dauketa kawai a kira ka kira Mutum ba shi da Juriyan Chart gwara ma karanta labaran abunda ke Faruwa. Ammh Tahir har mamaki ya ke ba shi baya gajiya Tahir na daga cikin mutanen da waya ta ke hanasu koomai ciki har da cikakkiyar Ibada ta shiga ransu da ta sanya suka Shagala. "JB na gaishe ka.." Tahir ya fad'a Hankalinsa na kan wayarsa. Sadiq ya Dago ya na kallon sa cikin mamaki yace"JB..? Tahir yace"Yes yanzu ma haka da shi muke chart na fad'a masa muna Gusai. Shine ya ke mganar bamu tab'a kai masa ziyara kano ba." Karamin Tsaki Sadiq ya yi kafin yace"Haka kawai sai mu bar abunda ke gabanmu mu kai masa ziyara Tahir? Tahir ya kalli Sadiq kafin yace"Yes ofcourse. Abokin mu ne fa Sadiq. Ba bu illah domin mun kai masa ziyara ba bu laifi a hakan.." Sadiq ya ce"Da laifi. Mutane irin JB a ga kana mu'amala da su kai ma kimar ka zata iya tabuwa." Tahir da mamaki yasa ya bar Danna wayarsa ya Dago ya na kallon Sadiq da ya cigaba da fadin"Tunda na Fahimci Halayyarsa na janye daga gareesa kaima Kuma na maka mganar Ka janye masa ammh baka ji Tahir. Jb ba rayuwarku daya da shi ba kuna da Tarin bambamci." Kai Tsaye Tahir yace"Ko zaka iya gayamin bambamcin? Ya tambaya cikin wani yanayin. Ganin kamar Tahir din ya ba shi Hankalinsa ya sa ya sauke wayarsa hannunsa ya gyara zama ya na Fuskantar Tahir lokaci d'aya yana Fadin"Jb irin ya'yan musu kudin nan ne da gata ya bata su Tahir. Jb na neman mata shine shaye shaye duk ba wannan ba Kasani na sani JB baya sallah Tahir sannan har zarginsa ake yi da neman maza fa! To duk munsan wannan meyasa zamu rika Huld'a da shi Tahir? Tahir ya kurama Sadiq ido kafin yace"Duk na san wannan bayan su fa? Sadiq yace"Kuma ba irin rayuwarka Daya ba. tahir kai maraya ne ya kamata ka iya rike maraicinka ko Domin Hajja ka tuna da sauran yan'uwanka ka tayasu kula da kanka." Sai kawai Tahir ya yi mirmishi kafin yace"Daman nasan zaka zo wajen nan. Wato JB yaron masu kudi ne ni kuma yaron Talakawa maraya da bai mallaki komai ba. Bai dace na yi abota da shi ba ko Sadiq? Sadiq ya yi kasake ya na kallon Tahir ya bude baki zai yi mgana ya Daga masa lokaci daya yana fadin" Nagode da ka Tunasar da ni matsayina., Na fahumci Jb da irin ku ya dace ya yi abota ya'yan masu kudi dan gata kai ma nagama Fahimtar zama da kai ganganci ne. Nagode da duka alfarman da ka yi min." Sadiq ya bude murya yana Fad'in "Tahir.." Shima A fusace ya ce"Abubakar Sadiq Sulaiman Shinkafi na san matsayina yanzu nace.." Daga haka fuu ya shige ciki bayan ya Dauki wayarsa, Sadiq ya bisa da kallon mamaki ya na nazarin wani abun. Tare fa suka zauna da Jb a Abu Hostel ya san halinsa sosai wannan mganganun ma na Tahir ba nasa ba ne, Na Jb ne shi ya ke zugasa ya na Fad'a masa mganganu a kansa Tunda yasan in dai yana Tare da Tahir bazai taba barinsa ya ja Tahir ga halakar da ya ke ciki ba. Shima ransa a bace ya ke shiyasa bai bi Tahir din ciki ba nan ya bata Lokaci daa yaji yana jin barci sannan ya shiga ciki. Ya iske tahir ya kwanta a kasan cafet yana danna wayarsa ga akwatinsu nan ya kwashe kayansa ya zube su a kasa. bai ce masa komai domin shima a yanzu ya riga ya san wani matsayi ya sauke Tahir. Da asuba shi ya tashi Tahir su je masallaci ammh sai ya Fahimci ba shi da Niyar zuwa sai ya tafi abunsa da suka Had'u da Abba a masallaci sai da ya tambayesa ya ce Tahir din ya makara ne. Haka da yaje gaida Umma da Mama tunda sun saba in dai tare suka zo to tare suke shigowa gaida su. Hatta Innani sai da tace"Ina Attahiru ne tun jiya ban gansa ba? Sai ya ce yana barci Innani ta tabe baki batayi mgana ba. Nan ya bata lokaci sai da gari ya yi haske ya koma bangaransa ya iske Tahir ya yi wanka ya shirya har ya zuba kayansa acikin wata babbar leda wacce ya fita da kansa shago ya siyo. Mamaki bai barshi ya yi masa mgana ba, sai ma ya fito falo ya bar masa Dakin Siyama da Sultana sun shigo da Basket din abun karyawansu kenan Tahir ya fito ya na wani cin mgani ganin su Siyama yasa ya saki Fuska suka gaisa. Sun fahimci duka abokan ba su da walwala Sadiq ma dakyar ya amsa gaisuwarsu suka sauke na Hannunsu suka Dauki na jiya da suka yi amfani da shi. Suna Fita Siyama tace"Sultana me ya faru da yaya Sadiq ne? Sultana ta girgiza kai alamun bata sanu ba ammh ita kanta taga alamun bacin rai a tare da su gabadayansu. Tahir kallon Sadiq ya yi ya na Fadin"Zan ta fi. Nagode da alfarman ka." Sadiq ko kala bai ce masa ba sai kawai ya mike sannan yace"Ka tsaya ka karya sai ka tafi. Domin ni bazan haka ka yi abunda ranka ke so ba Tahir" Sai da ya harari kwandon abinci kafin yace"Nagode Sadiq na iya da maraicina kaji ko" Daga haka ya fice daga Falon Sadiq ya Zura hannayensa A aljihun wandonsa ya bi bayan Tahir da kallo yana mirmishi ya na da kyakyawan Tabbacin ba Zariya Tahir zai koma ba Wajen Jb zai tafi. Tahir bai tafi ba sai da ya shiga ya yi sallama da Umma da Innani Abba ne bai samu ba fitan gaggawa ta same shi. Umma ta ganshi shi kadai tace"Ah ba Auta yace tare zaku tafi ba.? Sai Tahir ya sosa kai yana Fadin"Umma kiran gaggawa ne ta sameni daga wajen aikina. Shi sai gobe zai taho" Umma dai kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa 10k ta bashi tace ya yi na Mota, in Sadiq zai dawo gobe zai taho musu da Miya da Sauran kayan abinci ya amsa ya na ta godiya. Har Mama yaje ma Sallama itama sai da tayi mamakin tafiyarsa ammh bata Damu Tunda daman wani lokacin Tahir na fara biyo Sadiq nan ko Hutu suka yi daganan sai Direba ya kaisa har Daura watarana tare da Sadiq watarana kuma shi kadai. Innani ce ta basa 500, ta yi ta dai saka masa albarka bata damu ba jin ba da Sadiq zasu tafi ba daman bata son tafiyarsa. Sadiq ko a fuska bai nuna ma iyayensa wani abu ya taba had'ashi da Tahir ba. Ba wannan ba ne na Farko an yi haka kusan sau uku kenan. Tahir ya na da wawanci wani Lokaci zai nemesa lokacin da yasan shi Abotar gaskiya ya ke tsakaninsu ba ta Sharri ba. Kafin Dare duk abunda zai tafi da shi Umma ta had'a masa, Miya mai yawa da taji Naman kaza,sai soyayyan Naman sa da yawa. Surayya ta yo masa pepe chicken da Cake,Sauran kuma daga mai Dunout sai mai samosa,Cincin Cookies Nama ba abunda basu had'a masa ba. Mama kuma ta yi masa Cincin manya na ci da Tea mai yawa tare da Tuwon madara. Daman shi yasan dan gata ne wasu abubuwan ma sai yana ma barinsu a gida, Saboda sun masa yawa kowa dai burinshi yaga ya kyautata masa. Da daddare suna Shashen innani Siyama da Sultana suna Shashen Umma, Salima daman akwai son girma ta na shashen Mama. Hiran mutanen Shinkafi a ke yi da mganar Mahaifin Sultana Umma tace ya kirata sun gaisa ya fi sau biyar cikin Satin nan kamar dai yana son Sultana taje wajensa ne tunda yana ta mganar sauran kannenta suna ta kewarta. Innani ta yi karaf tace"Kaji wani tsirfa to ta yi masa uban me in taje chan! Ban da abun mutum ba ma kasamu an Dauke ma Laluranta ammh ka na wani lalacewa" Abba ya yi mirmishi kafin yace"Innani ai ba'a sauya ma Tuwo suna Sultana yarmu ce ammh kuma Shitu ne Hallatattacen mahaifinta." Innani ta tabe baki kafin tace"Shitun me? Maketancin Mugu Allah dai ya isa tsakanina da shi Sanadinsa Hauwata ta bar gidan duniya.". Ta fara jan Hanci zata fara kuka Sadiq ya ce"Innani.." Tana jin haka tace"Na yi shuru magajin gida nayi shuru." Kai ya gyada kafin ya kalli Abba yana fadin"Abba a sha'anin Baba Sammani nawa ka ba shi Gummuwa? Abba yace"Dubu talatin Innani ta ce na ba shi da Hamsin na yi Niyya. Innani tace ya yi yawa ko ba haka ba Innani.? Innani ta yamutsa Fuska kafin yace"Yo ina laifi Allah na Tuba a wannan marar da muke ciki na Tsadawan Rayuwa da farko yace Hamsin nace a'a bayan Sammani akwai yan bani bani irin su Husai da Hassu su sai ya kacachala musu ahirin din ba shi kenan ba." Sadiq ya kalleta ya kalli Abba takaici ya ishe shi Dole Baba Sammani ya kirashi ya na kukan ya ci basussuka Lokacin sha'anin ya taimaka masa. Ta ina wanda zai aurar da ya' ba shi da shi ya na kallon ka a wanda zai masa komai kuma kace ka bashi Dubu Talatin. Umma ya kalla kafin yace"Umma kinsan da haka kuma baki kirani kin Fad'amin ba.? Umma tace"Bansani ba Auta. Ban samu zuwa bikin ba, da Maman yara suka tafi sai da ya dawo ya ke Fadamin nace gaskiya bai kyauta ba, kuma ita kanta Maman Aishar sai da ta kirani ta na min kuka suna Bukatar taimako" Innani ta tareta da Sauri da cewa"Uban me tace ita Madihan? Au sun raina talatin din ne? Sulaimanu fa ba mai kudi ba ne shima din Rufin asirin Allah ne in ya biye ma mutanen nan wlh kaf sai sun talaautamin d'ana ya koma ya na bara kamar yadda suke bara" Mama da Umma suka kalli juna kowacce ta kasa mgana. Abba yace"Wlh Innani kinsan Dan kauye in ya ganka a birni sai ya yi tunanin Duniya ka tara. Abunda suke zato ba su san ba haka ba ne nima din buga buga ce kawai." Sadiq ya kasa mgana kawai ya zama dan kallo yana jin Innani ta zauna sai zuga Abba ta ke yi tana hanashi yin alheri daman shi ya jima da Sanin wasu halin Abba marasa kyau wajen Innani ya gajesu. Bai damu da ita ba kai tsaye ya kalli Abba kafin yace"Gaskiyan mgana Abba kudin da ka bashi ya yi kad'an kada ka manta ba shi da hali nomar ma da suke yi kai ka ke tallafa musu shima na iya ci da iyali ne. Y'a fa ya aurar Abba ta ina dubu talatin zatayi masa? Ya kirani yana gayamin yacci bashi Saboda haka zamu biya masa duka ba shin da ya ci Abba." Abba sai ya kasa mgana ya na ta zaran ido,Innani ta yi galala galala kafin tace"Yau na ji tsiya da wasila ta ina zai fara biyan bashin da bashi ya ci ba? Sulaimanu fa ba bawan su ba ne ai ya na da ya'ya su biya masa ba shin mana." Ran Sadiq ya baci yace"Innani kada ki kara sakamin baki in ina mgana da Abba na." Innani ta saki baki ammh kuma ta kasa mgana jin muryansa cikn kaushi yana Fad'in"Sai Baba Hassu ta kirani kan yaronta ya samu makarantar nan ta police acadamy wudil tana neman a tallafa masa Abba. Shima zamu taimaka mata." Abba ya kasa mgana har yanzu Sadiq ya cigaba da fadin"Sannan Baba Husau ma ta kirani yarta zata yi jarabawan fita ba kudi tana son don Allah a tallafa mata.!" Ganin Abba ya kasa mgana yasa ya ce"Abba dukkansu zamu taimaka musu.". Da sauri Abba yace"Eh.. Eh zamu taimaka musu za'a taimaka musu." Innani na jin haka ta fashe da kuka tana Fad'in"shikenan zasu talautamin Dukiyan yaro. Kai su Sammani dai ba su ji dadi ba Allah dai ya tsine musu albarka dukkansu. Tunda ba su da Godiyar Allah.". Sadiq a fusace ya kalli Innani ya na fadin"Allah bazai taba tsine musu ba sai dai ke ce in baki gyara halin ki tun a duniya ba wlh ki ka je lahira tsinuwan Allah sai ta kamaki." Sai Innani ta razana ta Dafe kirji tana Fadin"Na shiga uku ni Dije? Anya magajin gida ne wannan? ni ko me nayi da Allah zai la'ance ni" Kai Tsaye yace"Kina hana alheri. Kin ba da taimakon wajen maida Abba haka. kinsan yana da halin taimakawa ammh sai ki rika hanashi meyasa haka Innani? Ka yi alheri a duniya ka tsince shi a lahira yau in Abba ya Mutu ni da ke da su Umma ko dukiyar da kike kareta bamu isa mu hana shi karban hukuncin Allah kan yadda ya tafiyar da Dukiyarsa ba. In za'a fitar da zakka ki rika masifan danki ba shi da kudun Rufin asirin Allah ne, in zai yi kyauta ki hanashi kice ba shi da shi haba Innani ki sani fa wannan abubuwan da na ke saka shi yana aikatawa Sune Zasu bibiyeshi acikin kabarinsa Ranar da ya Mutu. Ki sani wannan aikin Alherin shi zai zama gatanmu bayan ba bu Abba. Ki sani Akwai mutuwa zaki mutu, Abba zai Mutu Umma ma zata mutu mama ma haka nima zan mutu watarana duka bamu a wannan duniyan to gwara mu aikata alherin da zamu je kabari muna jin daman mun ninka aikin alherin da muka yi a duniya Saboda yadda Ni'imar Allah zata rika ziyartamu acikin kaburburan mu ki Sani wlh tallahi duk abunda ka aika na Alheri zaka girbeshi in na Sharri ne ma hakan. To ki gyara kada ki mutu cikin wannan Halin Tsinuwar da kike kira ma Mutane ta Sauka akan ki" Ya karishe fad'a fusace Lokaci daya ya na mike ya kama hanyar barin Falon yana fadin"Zan kira su Abba. In na ji adadin kudad'en da za'a taimaka musu zan gayamaka." A yadda ya ke mgana suka Fahimci ran Maza ya baci. Jikinsu Abba duk ya yi sanyi sun kasa mgana Umma ta kalli Abba ta kalli Innani da ke sharan kwallah tana Fadib"Sulaimanu ka yi aikin Allah kaji ko ? Ka yi ta alheri da taimako ko na mutu, ba cikin tsinuwan Allah ba duk wannan shekaran ka kai su Samnani Hajji kai duk ma su dawo nan gidan da zama wlh bazan kara mgana ba." Umma da Mama suka kalli juna suna Mirmishi Abba ne ya koma ya na ta lallashin Innani.. daman Umma tasan mai gayya mai aiki in yazo to kamar zanen kaddara ne komai da yace a yadda ya ke so haka zai faru. Duk yadda ka ke nakasun ta wani bangaren to Allah na haskaka ta wani Bangaran Washegari fuskar cunkushe ya tashi sallama ma tsakaninsa da Innani sama sama ne, Sai faman ba shi hakuri ta ke yi tana fadin"Ai nace dukkasubsu dawo nan da zama an zama daya. To menene ma Duniyan nan Allah na Tuba magajin gida? Sulaimanu fa da ka ke gani ya na da arzikin nan duk su zo mu ci arzikin tare" Kamar zai yi dariya sai dai ya fasa ta bashi kuli mai siga da yawa da ta samo a Shinkafi da gyad'a soyayya daman shi ta ijiyemawa ya karb'a yana Fadin"Nagode innani Insha Allahu zaki mutu cikin salama kuma ba bu tsinuwar Allah a kan ki." Innani najin haka ta washe baki tana Fadin"Yauwa har naji Hankalina ya kwanta. To nace ba ka samu kun kebe da Sulsana ba? Kaga ina so nan da Bad'i Sulaimanu ya aurar da ku.". Kai tsaye yace"Innani.." Ta amsa ya cigaba da fadin"Innani ba Ruwan ki da aurena da Sultana. Ko da kuka zabamin ita Ra'ayina ya sa na karbeta saboda haka yaushe zamu yi aure wannan na Ubangiji ne ki daina katsaladan a Sha'anin Allah kada ki Mutu kasa taki karban ki.". Hankalin Innani ya tashi ta rika Fadin"N shige su alqur'an na bari. Wlh magajin gida bazan kara shiga ba." Ya na mirmishi ya Rumgumeta yasan ya gama Firgitata Innani na Tsoron azaban Allah. Direban Abba ya kaisa har zariya Tunda ya na da kaya. Har da lemuka duk daga gida Umma ta saka ya Dauko. Ko da ya koma Daki duk ya yi kura. Da yake daga shi har Tahir suna da key a hannunsa. Bayan ya gama shiga da kayan ya zage ya gyara daki tas ya tsaftaceshi. sannan ya yi wanka ya sauya kaya. Bai fita ko'ina ba yaci Nama ya kora da Ruwa ya koma ya kwanta yana barcin gajiya. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V *10* Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi haifaffan garin Shinkafi ne da ke Jahar Zamfara. Asalin sunan Innani Dije ne kuma ta yi aure aure kamar uku kafin ta auri Abubakar mahaifin Sulaimanu, Innani Tun tana matashiyarta irin matan nan ne masifaffu tijararru an yi mata irin auran gida tun da fari ta rika guje guje auren ya lalace bai je ko'ina ba. Iyayen Innani masu kudi ne, ko a baya Tunda suna Noma sannan suna da Tarin Dabobbi. Innani itace Matar Abubakar ta biyu ko da akayi auran su taje ta iske shi da uwargidansa kuma uwar ya'yansa Barira. Wacce ta yi ta hauka sanda za'a auro mata Innani tunda a lokacin Mallam Abubakar ya nuna matukar kaunar Innani a Zahiri kuma ya ke nunawa da ya sanya tsananin kishinta a zuciyar Barira. sannan sanda zata zo iyayenta sun yi mata kayan gata na alfarma tunda ita kadai suka haifa ga shi kuma sun kwana biyu a duniya. Shiyasa dukkan gata suka tattara suka ba ma Innani komai ta ke so ta na samu har da ma wanda ba ta so duka iyayenta na cika mata shi. Shigowarta gidan Abubakar ya sauya komai saboda ta na son shi tunda ya na lallabata ya na kuma ji da ita. Sannan kuma ya na ji da Masifarta kuma ya na yi mata abubuwan da ta ke so. Sai sanadin haka ya kara hura wutar kiyayya da Tsakanin kishi a gidan Abubakar, komai Barira ta ga Innani da shi sai tace mijinsu ne ya siya musu sannan ta na zargin shi da Nuna bambamci a tsskaninsu. Har kuma ta jawo ya'yanta cikin kishin ba su dauki Innani a matsayin uwa ba, sai itama kuma ta ce kowa ya yi ta kansa. Haihuwanta ta farko Namiji ta Haifa aka samu Sulaimanu, bayan shi ta jima bata haihuwa ba,Sai daga baya ta samu mace mai suna Hauwa Kulu. Kuma har alokacin Barira da ya'yanta ba saa raba'ar Innani da ya'yanta duk ko yadda Abubakar ya so ya had'a kan zuru'arsa bai samu ba har ya bar gidan Duniya. Ya tafi ya bar Barira da ya'ya Biyar,Sammani ne babba Gaddafi ,Sai Hassu sai Husai sai karamar su Zuwaira. Kuma ya mutu bai bar komai ba sai gidan da suke ciki ita kuma Innani sai ta koma gaban iyayenta da zama ta cigaba da renon ya'yanta a kan nata Tunanin na kada su taimaki wanda bai taimake su ba, kamar yadda Barira ta janye ya'yanta daga Ya'yan Innani ita Innani haka tayi na bakinta tace kowa ya yi ta kansa. Haka Rayuwa ta mika Innani ta rasa iyayenta komai na su ya dawo hannunta da shi ta zama yar kasuwa mai saida Hatsi, lokaci d'aya kuma ta na kula da su Sulaiman. Sulaiman ya yi karatun zamani har matakin Diploma a garin zamfara Hauwa kulu kuma iyakarta Jss Innani ta yi mata aure da Shitu shima dan asalin garin Shinkafi ne,ammh wajen shekaru goma da auran su ba ta haihu ba,sai ya kara aure ya haihu sai aka fara Tunanin Hauwa kulu ce bata Haihuwa mgana tayi Tambari a gari Innani ko gida gida take bi ta na Tsine ma duk wanda yace yarta bata Haihuwa. Sulaiman kuma bazai ce ga Silar Arzikinsa ba, sai dai yasan ya fara da bin wani dan'uwan Innani da ke sana'ar Siyar da kayan wuta a garin Zamfara, Daganan shima sai ya kafa nashi sana'ar ya na saida komai na kayan wuta Daga baya da yayi karfi har na'ura mai kwakwalwa ya ke sarowa ya na Saidawa. itace sana'an da ya fara samu da shi, Sannan da ita ya yi auransa na Farko da Salamatu yar garin Gummi ce yayarta ke auran Dan'uwan Innani anan suka Had'u. Tsakanin Salamatu da Sulaiman auran Soyayya ce tsantsan da kuma amincewar Innani tunda ta ga Salamatu Allah ya Dora mata kaunarta acikin ranta saboda Ladabinta da Biyayyarta. A garin zamfara suka fara zama a gidan Haya da ya kama lokacin. Innani kuma ta na Shinkafi ta na gudamar da sana'arta ta saide saide hatsi, da farko wani Alhaji ne ya fara haskamai saro na'urori daga kasar waje saboda an fi samun masu inganci da taimakon Innani ya fara zuwa kasar China saro computoci kuma yaji dadin zuwa sosai Tunda ya samu riba matuka gaya. Daganan kuma sai ya ga waje bayan China har India ya ke shiga domin Saro kayayyakin wuta. Da shawaran abokan sana'arsa suka haskamai ya fara sana'ar saida Danyan gold kuma ya shiga da kafar Dama cikin Lokaci kad'an ya samu kudin da zai rufa ma kansa asiri tare da innani da kanwarsa. Lokacin da ya yi ginan gidansa na Gusai sai ya koma tare da Amarya Suwaiba Hajiya Mama kenan, dalilin Ya na neman Haihuwan d'a Namiji ido Rufe,Tunda Hajiya Umma Tunda aka yi auran su ya'ya mata ta dinga Haihuwa kuma haihuwan nata akai akai take yin shi, Duk da Innani na son Umma bai hana saka Sulaiman ya kara aure ba tunda babban Burinta Sulaimanu ya samu Magajin da zai gaje shi watarana Suwaiba asalin yar Birni ce agarin gusai aka haifeta kuma anan ta Girma ganin Alhaji Sulaiman na da abun hannunsa yasa mganar auren ma bata Dauki tsawon Lokaci ba akayi komai aka gama sai dai ba ta zo da Farinjini ba ganin Farko da Innani ta yi mata ta tabe baki tace bata da D'a saboda ta na ta kallon Mutane a yatsine tun kuma daga Lokacin har gobe Innani ba ta wani yin Mama sai dai bata Zafafa ba, ammh ko ya'yanta suka yi wani abun sai tace"Ya'yan suwaiba dai jarabbabu ne." Itama sai al'amarin bai sauya zani ba, Itama ta na zuwa ta fara zazzage haihuwan ya'ya mata ba ta fara da Magajin kamar yadda Burin Innani ya ke ita da Alhaji Sulaiman ba. Tashin Hankalin Innani kada yau sulaiman ya fad'i ya Mutu su Sammani su gaje abunda ya ke da shi ba shi da Magajin da zai gaje shi. Sai Hankalin Innani ya tashi sannan ta tusa ma Sulaiman tunanin cewa in bai haifi Namiji ba kamar bai haihu ba ne ya'ya mata ba su da wani amfanin da za su yi masa namijin da zai Haifa shine asalin Magajin gida. Sannan da karancin ilimin addini a barayin Innani shima Alhaji Sulaiman da sauki ammh duk da haka ya na matukar kaunar Innani har da dalilin yasa baya iya saba mganarta sannan har yau har gobe da cewarta ya ke amfani sai dai in mganar Magajin gida ne zai Ture nata. Da Farko da Alhaji Sulaiman ya gina ma Innani shashenta kin komawa ta yi tace saboda Hauwa bata son ta baro ta ita kad'ai sai yan uba ta shiga uiu Shiyasa ta yi zamanta a shinkafi sai dai ko da wani lokaci ta na Hanyar gusai kawo ma su Umma Rubutu da jike jiken magunguna saboda dai su haifi Namiji Sulaimanu ya samu magaji. Umma da na iliminta wani lokacin sai ta kalli Innani ta na fadin"Innani Haihuwa ta Allah ce. Ko ya baka d'a Namiji ko ya baka mace duka Tsarinsa ne bawa bai isa ya kauce ma Kaddaransa ba wasu ma na neman Haihuwan ba su samu ba mu kuma mun fa samu ba sai mu gode masa ba? A lokacin Innani hararan Umma ta ke yi kamar idanuwanta zasu fado kafin tace"Kaji min wani tsirfa da jaraba yo har mu zaki gayama Allah Salamatu? Tun kafin a haifeki na ke sallah Saboda haka baki isa ki gayamin komai ba" Dole Umma ke kama bakinta duk Abunda Innani ta bata sha take yi, ita ko Mama sai ta yi gaddama da ya ke ta yi karatun aikin jinya bata cika shan jike jiken magungunar gargajiya ba. Sai In tace bazata sha ba Innani ta fara bala'i ta na tsine tsine har cewa mata ta taba yi ko ta sha ko kuma ta kara gaba bazata zauna a gidan Danta ba ta sha mganin da zai kawo mata jikanta Namiji ba. Mama Da Umma da mijinsu kamar makunnin wuta ne, Innani ce ke rike da Makunnin ta na Sarrafa shi, ya ce duk wacce bazata bi mganar Innani ba to zata kara gaba tunda shima Umarninta ya ke bi, a kauyen kuwa da ke zagaye da Shinkafi ba inda kafar Innani bai taka ba wajen neman taimako ba, duk in da taje mganarta kenan"Sulaimanu ba shi da magaji ga shi ya na cikin yan Uba wad'anda ba sa kaunarsa." Tunda su ya'yan Barira sun saki ganin mahaifiyar ta su Barira Allah ya yi mata rasuwa. Ganin haka sai Innani ta ke mganar saboda sun ga Allah ya Daukakan Sulaiman ne shiyasa suke bibiyansa yanzu. Su kuma duk rayuwa ta koma sai a hankali suna Biyo dan'uwansu domin zumumci kuma da Taimako ammh Innani ta Tsare gaba ta tsare baya. Ko zuwa suka yi Innani zata tattare ta saka ya ba su kudi kad'an da ko na maida su gida bazai isa ba sannan ta hana su kwana acewarta shima Sulaiman ba kudin garesa ba Rufin asirin Allah ne. Za'a iya cewa wani abun na Abba ya Tadda Hali ammh kuma da zugan Innani da irin Tarbiyanta. Hauwa kadai ta ke bari Abba na tallafa mata itama haka take tsine ma shitu tunda yanzu matansa biyu kuma dukkansu suna ta Haihuwansu Hauwa ce aka bari cikin gorin dangin miji da kishiyoyi sannan Innani ta so ta raba auran Hauwa tace sai Shitu shima ya ce sai Hauwa daga karshe Innani ta fita batunta ta koma neman ma matan Sulaiman mganin Haihuwan Magajin gida. Lokacin da Magajin gida ya zo Duniya komai na Rayuwa Alhaji Sulaiman ya gama mallaka ya yi karfi a sana'ar gwalagwalai sannan tare da Shigo da kayan wuta, da su kamfutoci a lokacin kuma ya'yan shi goma sha d'aya duka Mata ne innani ba inda bata shiga ba, ammh har alokacin Kum fayakum. Umma ke da Shidda, Mama kuma na da Hud'u. Surayya ce itace Babba, sai Suba'atu,Sadiya,Sa'adatu,Saddiqa,Sajida,Sai dakin Mama kuma Sa'ima ce babba sai sakeena,Saliha,da Shahida. Kaf din su sunayensu da Harafin S ya fara kamar yadda na iyayensu ya fara Shiyasa ko a makaranta in za'a kira sunansu da SS Shinkafi a ke kiransu. Kuma a zuwa Lokacin Innani ta Dawo Gidan d'anta da zama saboda ta ce ta rika lura da wasu abubuwan tunda har yanzu Allah bai kawo magajin gidan ba, Sai dai har alokacin bata Saduda ba Duk in da taji ana ba da taimako sai kafarta taje bata Hakura ba. Umma ta samu cikin da tunda ta same shi ta ke wahala ba'a taba sanin ta na da Junnu ba sai alokacin suka tashi zabuban sai dai aka yi ta mgani Innani ce ta tsaya kan Umma alokacin ta rika kula da ita, sai dai ta sha Uban jike jike da Ruwan Rubutu a shashenta akayi renin cikin Sadiq wanda ko Innani bata sakama Ranta magajin gida ke tafe ba Ciwon Umma ya Dauke wannan Tunanin daga kanta. Sadiq ya zo duniya cikin wani irin Hali da tsaka mai wuya Umma ta Haifeshi ba ta san wanda ke kanta ba, bata kuma san abunta ta haifa ba Kamar mahaukaciya haka ta koma ta na mganganu marasa ma'ana da kokarin tashi ta fita da gudu kamar wacce ta zare Abba ya so a yi na asibiti Innani ta hana Sannan Dangin Umma daga Gummi sun kasa mgana saboda ganin Kulawar Innani akan Umma sai suka kauda idanuwansa. Tun da Sadiq ya fad'o duniya Daman Innani ta karbi haihuwarsa tace an samu Abubakar Sadiq,Magajin gida yazo tun kuma daga Lokacin Innani ta karbi Ragamar kula da Sadiq a hannunta tare da Umma Gabadaya. Da abun ya ki yi ne tace za su koma Shinkafi da zama saboda nema ma Umma magani. Abba ba shi da mafita saboda Umarnin Innani ne, haka ta koma Shinkafi da zama tare da Umma da Sadiq tana kula da Umma gefe daya ta na kula da Magajin gida. Shiyasa Sadiq yace Innani na da Muhimmanci a Rayuwarsa yana da wata takwas ta cireshi a nono saboda daman sai da Dubara Umma ke iya ba shi Nonon Tunda har Lokacin sai a hankali. Shiyasa Sadiq ya gini da ciye ciyen abincin gargajiya tunda duk shi Innani ta rika Dura masa. Ya taso ya gansa a Shinkafi ne tare da Umma da Innani, sai dai Abba da Sauran yan'uwansa na zuwa dubashi a kai akai ko da suke a shinkafi ba bu gatan da Sadiq bai gani ba Abba da Inanni kamar zasu lashe shi Saboda so da kauna in kana son su soka to ka so magajin gida sai suma su soka. Umma sai da ta kusa shekara Biyar cikin wannan Halin sannan ta warke da taimakon magungunar musulumci,da addu'o'in malamai lokacin da ta warke ita kuma Sai Hauwa ta fara ciwo daga zazzabi ta fara sai rama kuma Sai Innani bata koma Gusai ba sai Umma ce ta koma Gidan Mijinta aka kuma bar ma Innani Sadiq a hannunta. Shekara takwas ya kwashe a shinkafi sannan ya dawo gusai wajen iyayensa da zama tare da Innani wacce ta kasance itace komai na shi. Tun yana karaminsa ya ke da katon bangare shi kadai kuma ya mallaki komai da yan gata ke mallaka. Sai dai shi ra'ayinsa ba shi kan Sauran Ra'ayin wadanda ke zagaye da shi. Ra'ayinsa Dabam ne da na kowa sannan Rayuwarsa mai Sauki ce ba kamar yadda akayi Tunanin Magajin gida zai kasance ba. Sultana Diyar Hauwa ce wacce ta Haifeta ko ganinta ba ta yi ba Allah ya yi mata rasuwa,Umma na ganinta ta ji ta na sonta ta Dauketa Innani ta Daurre mata Gindi Dole Shitu ya bar musu Sultana yasan Tijaran Innani bai isa ya musa ba. Dalilin da zamanta ya Dawo gidan su da Sadiq kenan Hannun Umma. Sadiq tun yana karaminsa mutum ne mai sanyin Hali Tausayi da jinkai, ga Abba da mako da son abun duniya shi da Innani ammh kuma shi ba su iya masa gaddama. Tun yana da sha wani abu a duniya yasan ya taimaki wadanda ba su da shi, ko a hanya yaga mutum na neman taimako zai ce ka Biyosa sai gida sai dai Abba yaji sallama kuma ba shi da ikon cewa a'a kai tsaye Sadiq zai ce Abba a taimaka masa don Allah. Sannan shi Yaro me da ke son zama cikin mutane ko da bazai Rabesu ba, ammh yana son zama cikin Anguwan da ke da cikowar Mutane shi dai ya kasance ya na ganin Mutane kowa na Harkan gabanshi. Mutum ne da ke son Rayuwa daidai misali bai cika son Dora Rayuwarsa kan Babban mizanin da kowa ya Dauke shi ba. Ya san shi dan gata ne gaba da baya. Ba Iya Innani ba kaf Dangi kowa shi ya ke so burin shi ya farantamasa rai. Tausayinsa ya siya masa soyayyan Mutane tun kafin ya zama Saurayi su Baba Sammani suka rike shi kamar shine Abba Tunda in ka fad'amasa matsalanka to kaje gida ka kwanta ka gaddara ma matsalarka ta kare. Ya na son Mutane da son yan'uwa mafi girman abunda ke ranshi Shine Tausayi Sadiq ba ya so yaga Mutane na cikin wani Hali ya kasa taimakawa baya so yaga wani cikin halin Babu ko Damuwa in dai yana da Halin taimakawa shiyasa in kaga Abba ya yi kyauta to Sadiq shi ne in yace ba'a iya Saba mganarsa Innani ta kan ce yi masa komai ya ke so tunda komai da ka mallaka na shi ne magajin gida. A shinkafi ya fara Fimari dinsa sannan yazo gusai ya karisa secondary school dinsa wata makaranta ya yi mai hade da boko da arabi saboda son addininsa. Yana da naci kan abunda ya ke so ya koya,yan'uwansa ba su so ya yi karatu ma a Nageria ba, sai dai kuma Uban gayyar baya Ra'ayin haka. Sannan ga Mallam Taju da ya ke Daukan karatu a wajensa. A makaranta suna hadda sannan in ya Dawo gida yana yi wajen Mallam Taju shiyasa cikin Lokaci ya samu ilmin da ko iyayensu ba su taba Tunanin yana da shi ba. Kafin ya gama Secondary School ya Sauke Qur'ani sauran littafai ya Durfafa kowa ya san shi yana da Saukakkiyar Rayuwa. A kallo daya in kayi masa bazaka ce yana da wani gata ba saboda yana Daidaita Rayuwarsa daidai da ta kowa. An sha Fama da shi akan ya je waje ya yi karatun Likitanci ammh Sadiq fur yace baya Ra'ayi shi Quantity Surveying zai karanta masu kula da harkan Shimfid'a tituna kuma kowa yasan Ra'ayin shi ne gaba da na kowa hatta da Abba da Innani. Suna ji suna gani ya tattara kayansu ya tafi zariya, in da ya samu Admission a ABU ZARIA zai karanta Ra'ayinsa. Abba ya so ya kama masa gida ya zauna yace baya so a Hostel zai zauna cikin Dalibai yan'uwansa. Wannan shine Mafarin Haduwarsa da Tahir kenan. Tahir ya zo daga Daura ne d'an talakawa maraya da taimakon yayyensa da Kakarsa ya samu makarantar, Daki daya suke mafarin Zamansu kuma abokai duk cikin Dakin Sadiq ya fahimci Tahir ya fi su maida kai ga karatu, Su hudu ne Shi da Tahir sai Jabir sai Usman Muhammad Balarabe Mb kenan. To har gwara Usman akan Jb da shima yaron mai kudi ne babanshi dan siyasa ne, kuma daga kano yake daga ganinsa zakasan ba karatu ya zo yi ba illah Shagala. Da Farko Sadiq da Tahir fad'a suke yi kan gyaran Daki Tunda Sadiq baya son yaga Shirgi a Daki yana son Tsafta daga baya kuma sai suka zama abokai duk da ba Course daya suke karanta ba. Cikin Lokaci kadan suka Fahimci Hallayan juna. Suna shekara ta uku Jb ya bar Dakinsu ya koma ya kama daki a wajen makaranta yana cigaba da watsewarsa. Sadiq ya yi suna Abu zaria saboda Tausayinsa da taimakonsa Abba ya sha Biyama Dalibai kudin makaranta bai san iyaka ba. Sai dai Sadiq ya kirashi yace"Abba akwai wani a makarantarmu bai biya kudin makaranta ba gashi za'a fara Jarabawa. Abba zamu taimaka masa." Abba ba shi da mgana illah yace"Za'a taimaka musu Magaji gida zamu taimaka musu in sha Allahu" Tahir ko da Usman shekaran ta kusa da ta karshe duk Sadiq yasa Abba ya Biya musu kudin makaranta. Shi Usman dan gangare ne, yana da kokari sosai phamarcy ya karanta da suka gama ya samu Scoolarship zuwa kasar Ughanda domin cigaba da karatunsa. Rabuwarsu kenan, Jb kuma daman Sadiq ya yanke alaqan sa da Jb Tahir ne ya kasa Rabuwa da shi. Sadiq akan kirashi da sunan Alarammah Saboda Addininsa sannan masanin Qur'ani ne da Sauran littafai kuma yana cikin malaman MSS na makaranta yana kuma limanci a masallacin makaranta, Sannan duk karattukan da ake yi da Sadiq a ke shi Yazo karatun boko ammh kuma ya samu har da karin na addini kuma in ya koma gida Hutu ya rika Daukan Wajen Mallam Taju. Sadiq ba bu abunda ya taba nema ya rasa a makaranta sai dai ma ya kyautar shine siyama marasa karfi Handout sannan ya dinga Rabon kayan abincinsa ga duk wanda yasan yana Bukata. Sadiq tausayinsa ga Mutane mai yawa ne. Duk da Abba da mako da son abun duniya ammh Sanadin Sadiq yasa ya ke alheri a chan Shinkafi sai kiga Mutum na da lambar Sadiq ammh kuma ba shi ta Abba. Saboda abunda Sadiq zai yi maka Abba bazai iya yi maka ba shiyasa shi ba iya magajin gida ya ke ba, shi magajin kowa ne. Shi kuma yasa Abba ya jawo yan'uwansa ajiki ya kuma ba da Kofar kowa na zuwa gidan Abba ayi zumumci. Shi kuma ya saka Tsarin zuwa Shinkafi zumunci da kuma in sha'ani ya tashi Duk bala'in Innani bata iya ma Magajin gida shi ma kuma ya Fahimci har da Jahilci ke damun Innani shiyasa ya ke kokarin Gyara mata in tayi kuskure. Maganar auran sa da Sultana kuma Umarnin Umma ce, Sannan Innani ta Dora Burinta shi kuma Umma da Innani suna da Daraja a wajensa shiyasa batare da Tunanin watarana zai iya shiga tsaka mai wuya ba ya amince. Sultana ta taso ne da mganar Sadiq shine mijinta a bakin kowa. Yarinya ce shiyasa ba zata daura mizanin komai a yanzu ba ammh Abu daya ta sani Sadiq shine mijin da kowa yasan zata aura hatta iyayenta sun sani da Yan'uwanta, ta na zuwa Hutu ganin su ammh fa In innani ta yi ra'ayi har a yanzu Innani Tsine ma Shitu ta ke yi tace bakincikinsa da na matansa ya yi Sanadiyar Rasuwar Hauwa kulu. Sadiq ya zabi ya yi karatu a zariya saboda Dalilinsa na zama in da Mutane ke harkokinsa ya yi kuma rayuwarsa kamar yadda daidai da yanayin da ya ke so Rayuwarsa ta kasance sannan ya zabi zama a Hostel saboda halinsa na son Mutame da mu'amala in da Mutane suka fi yawan zama. Bai cika son zama gidan su ba saboda anguwa ce da ba ta cika Hayaniya ba. Allah ma yasa yana da yayye mata kadaici bai cika Damunsa ba in dai yana gida to kowa Burinsa ya faranta masa. Suna kaunarshi kamar yadda ya ke kaunarsu. Duk da Mama na taba kishi da Umma ganin Innani ta fi sonta sannan ita ce uwar Magajin gida ammh bata isa ta raba kan ya'yan gidan ba. Ba bambamci Tsakaninsu duk Daya suka Dauki junansu musamman Sadiq ko da ya ke karami a acikinsu yana da kyakyawan Tunani mai kyau tunda ya karanta kuma ya gani. Bayan Sadiq Mama ta kara Haihuwan Salima da Siyama wacce itace karama daga ita aka rufe haihuwa agidan Siyama ta zama autan Gidan. Sadiq kuma ya kasance Autan Umma Shalelen Abba da Innani. Dukkansu matan sun yi aure a garin Gusai, Suba'atu ke aure a kano sai Saddiqa da ke kebbi. A dakin Mama kuwa Sa'ima da Sakeena suma suna Gusai ne suna aure. Sahida na aure a katsina ita kuma Saliha na auran yaron yayar Mama ce suna garin Ibadan da zama in da ya ke aiki a kamfanin Dangote. Kuma kowacce ta na jin dadi agidan da mijinta sun kuma hayayyafa da ya'yen su turbarkallah masha Allah. Lokacin da Sadiq ya kamallah makaranta cikin yan'uwan sa ba wacce ta so ya yi bautar kasa a zariya ammh kuma Tunda yace chan zai yi ba su da tacewa barin ma Surayya da suke kira Big sis taso yaje kasar waje ya yi karatun liktanci tare da kanin Mijinta Sadiq yace baya ra'ayin haka. Da farko Har Abba da Umma sun Amince Innani ma ta samu ta shawo kanta ammh A'a din Sadiq kad'ai ya isa da ya Rusa komai. Dole a kabarshi ya tafi zariya again Bautar kasa. A wannan karon ma Abba yaso ya siya masa gida yace shima baya Ra'ayi sai haya ya kama da Farko a Daura Tahir ya so ya yi nasa Hidimar kasar ammh Ganin Sadiq ya koma zariya shima ya nema ya koma Saboda Abotan da ke tsakaninsu ta yi nisan da har Ahalin juna sun sani. Sadiq yadda ake son shi yasa ko Kashi ya kai gida ya ke da Daraja. Shiyasa Tahir ya ke kamar dan gida a gidan su Sadiq duk kuma abunda Sadiq yace ayi masa Abba ba gaddama ya ke yi masa. Ranar farko da Tahir yazo yaga irin gatan da Sadiq ke ciki bayan sun koma Zariya ya kallesa yace"kai ko wani irin abu ka ke samu a garin nan da ka zabi irin wannan Rayuwar Alhalin kai dan gata ne? Sadiq mirmishi kawai ya yi masa bai ce komai ba, Sadiq ya je ya sauke Farali kafin su gama makaranta shi da Innani Umra kam ya sha zuwa tun yana matashinsa. Shekaran da suka dawo ne Innani ta fara fama da matsalan idon da yasa aka kaita asibitin ido Makka na larabawa da ke kano. Aka yanka mata gilashi Tunda ganin nata ya koma sai hankali sannan ga tsufa ammh bazata bar Halinta ba. A rayuwar Abba in da ace yau ba Sadiq da Tuni lamarinsa ya wuce Tunanin mai karatu abunda ya zama Dole kawai ya ke yi. Ko zakka baya Fitarwa sai tasowan Sadiq yasa duk Shekara sai an fitar da Zakka sannan kuma yasa yana taimaka ma su Baba Sammani da kudi duk Damina suna yin Noma domin ci da iyalansa sannan in zasu tafi sai an cika booth da kayan abinci. Gidan Innani da ta gada Tun iyayenta Abba ya gyara nan suke sauka in sun zo garin ,Sadaka ko akai akai Sadiq kan saka Abba na yi, ko a masallaci yaji ana neman taimako zai ce Abba zamu ba da namu taimakon Abba bashi da mgana sai dai yace zamu taimaka musu magajin gida. Shiyasa yadda Mutane ke ganin kima da Girman Magajin gida wlh Alhaji Sulaiman ba shi da wannan kimar. Kannenshi Mata su Hassu dalilin Sadiq su kan sazo gidan su da iyalansa su yi kwanaki sai dai zasu sha Mgana da Habaici bakin Innani ta yi ta fadin Sulaimanu ba mai kudi ba ne Rufin asirin Allah ne. Wayar Sadiq ko da yaushe cikin kiransa yan'uwa suke yi, Alhaji Sulaiman kuwa wani sai ya jima bai kirashi ba Ammh Sadiq sha yanzu ne kuma mganin yanzu. Da ka kira shi ka gayamasa matsalan ka shikenan. Ko'ina ka je addu'a ce da Fatan alheri ga Alhaji da iyalansa Sanadin Sadiq Magajin gida. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *11* *Zariya* Laraba. Abubuwa biyu ne suka min tsaye a kahon raina a kwanaki nan. Na farko yau kwanaki biyar cur mutumin da ke siyan Danwaken Sannan kuma ya kuma bar min chanjin naira na gugan naira har Dari biyu ya daina zuwa. ina lissafe tun Alhamis da ya aiko aka siya masa bai kara dawowa ba har ga shi yau talata. Tun safe na ke duban hanya ammh shuru har su datti na kira na tambaye su sukace suma sun daina ganinsa yana zuwa. Acikin raina na ke ta faman wasi wasin to lafiya? Wata zuciyar kuma ta kwab'eni da cewa"Hasiya kada zak'ewar ki ta cika yawa fa." Nima sai daga baya naga na zak'en gaskiya mutumin da ban taba sani ba me yasa zan damu kaina Saboda shi? Sai wata zuciyar tace min ko ban san shi ba Cinikayar ya had'amu kuma sanin Mu'malace ka yi cigiyar abokin Cinikaryar ka. Tun Safe da na zauna kujeran saka Danwake a tsakar gida na ke ta faman duba kofar gida da naga yaro ya shigo sai na Dauka shine, ammh kuma rashin ganin yar kular da ya saba aikowa ke sakarmin da gwiwa. Maganar gaskiya ina cikin zullumi Ajiyar rai na sauke lokacin da Goma ta gota na gama Saka Danwake gabadaya har ya kare iya wanda zan ci kad'ai na rage. Shi kuma abu na biyun da ke damuna Salisu ne! Ya na yawan Fad'omin a rai a kwanaki nan jiya har mafarkin sa nayi. Wai mun had'u na gaishe shi ya ki amsawa naga Musabahu a wajen da ya ce masa"Salisu Hasiya ce fa ke gaisheka ka yi kamar baka ji ba." Kai tsaye naji muryan Salisu na Fad'in"Bazan amsa mata ba Musbahu koma miye faru. Bai kamata na kwanta Jiya Hasiya taki gaisheni ba." Daganan na farka ina ta faman zufa. Tun daga lokacin zullumi na ya karu akan na baya. A bakin Mamam boy nake jin sun koma asibiti an kara Dubashi an ce sai karfen jikinsa ya shekara za'a cire masa. Maman boy Idon gari ce ka rasa ina take samun wasu labaran, ko da ya ke Gantali ce da ita ba inda kafarta baya shiga da mijinta ya fita itama ta ke saka kafa ta fita kusfa kusfa a samaru nan anguwar Tsamiya Da'i da'i kun gidaje ne Maman boy ba ta shiga ba. shiyasa akwai labaran gidajen mutane da dama abakinta. Nasan ko giyan wake na sha ban isa na dauki Siraran kafafuwana zuwa gidan Salisu da sunan gaishe shi ba. na tabbata Sahura sai ta kasheni kamar yadda ta kudurta in kuma ban mutu ba to tabbas zan samu manyan Rauninka da zan jima cikin Doguwar suma. tuna haka kad'ai kan kwabar da Niyyata ko Amma na kasa gayamata zuciyata duk da ta ganni suku suku da ta tambayeni sai na ce mata ban jin dad'i da Safen ne. Amma na da wani irin hali ko ya ya na ke cikin damuwa ta sani sai da ta kalleni cikin Nazarina kafin ta kad'a kai tana fadin"Ko ulcer d'in ki ce zata tashi? Kai tsaye nace mata"In ma itace ina da Sauran magunguna na ruwa da na kwayar sai na sha." Kai tsaye itama tace min"In bazaki Jefa Danwaken nan ba a hakura yau Hasiya." Ban bari ma na ja mganar da ita ba. Taga na mike na fara had'a kayan yin Danwaken sai ba ta kara mgana ba Ammh ta jima ta na kallona ta kuma san tabbas wani abu na Damuna to ta ina ma zatayi Tunanin bazan damu ba. Damuwa a gareni ta zama Tilas ko domin yadda na zama abun gudu da kyama wajen jama'a. Ramatu na ke son gani ko zan gayamata cikina ta ba ni shawara, Shiyasa ina gama wanke wanken kayan da na bata, bayan na kai Daki na zo na saka ruwan zafi a rushin da na rage na leka Dakin Maman Boy nace ta aramin wayarta zan kira Ramatu. Kai tsaye tace min"Gaskiya ba kudi acikin wayar" Cikin mamaki nace mata"Ba kud'i? Ba shekaranjiya na saka Dari da zan kira Adda Fati ba? Kuma ba mu jima mu na mgana ba. Na dai san ban isa cinye wannan Darin ba." Cikin tabe baki tace"To ni dai bansani ba, ban kira kowa da shi ba." Ban kara mgana ba Na karb'i wayar na juya ban ko tsaya duba kudin wayar ba na leka kofar gida na kira Salihi na Dauki Naira dari da goma cikin cinikin Danwake na ce ya ruga ya siyomin Katin Mtn ya yi Sauri. Sanin Halin Salihi da aikensa da sai ka mamta da shi ya ke dawowa yasa na koma Daki na fara kanta shi zan gyara Amma na saman gadonta barci ya kwasheta itama duk sai a hankali kwanaki nan da zazzabi ta ke kwana. Har sai da na gama na share daki na wanke bayi saboda bazan iya shigarsa haka batare da na wanke ba. Na juye ruwa na yi wanka na fito na sauya kaya sannan Salihi ya dawo, Allah ya taimakeni ma ya kawomin katin lafiya. Ina gama Loda katin na kira Ramatu daman na Haddace lambarta bayan ta Dauka mun gaisa da tambayan su Amma da Noor nace"Ke ina son ganinki kina gida gobe..? Da zumud'i tace"To ni kuma ai goben nake shirin zuwa miki Yini ni da Noor. Gidan Inna zan kwana da Sassafe tahowa kawai zan yi" Cikin jin dad'i nace"To shikenan ma sai kin zo d'in. Ki gaida inna Talatu" Kai tsaye tace"Zata ji nima ki gaidamin da Amma da Habi auta." Daganan muka yi sallama. Jin tace zata zo sai naji dadi a raina. Ban koma na zauna ba sai da na Mayar ma Maman boy wayarta sannan na dawo na saka Danwake da manja da maggi naci. Ganin Amma nata barci yasa na kwashe yan kayanta da suka yi datti na Daureye mata da nawa na aikin Danwake. Kayan ba su da yawa tunda wanchan Sati Habi ita tayi mana wankin kayan duka ranar Sati tunda ba makaranta. Su datti na bama goma goma suka Debemin ruwa a waje. Ina mamakin yadda matan gidanmu ba su damu da sanya yaransu a makaranta ba sai dai su bar su su yi ta gararamba a gari ba arabi ba boko. Na taba yin musu mgana Maman Salihi tace min da na abinci za su ji ko da na kudin makarantarsu daganan sai na Rufe bakina. Duk da sai ayi abu Dari ban saka bakina ba yanzu sai kiji gori na tashi ni da ke da ababen gori gasusan kaca kaca. Kwanakin nan ma da na ga Kaltume na jin Haushina daga ni har Amma bata kulamu kawai saboda mijinta na son Danwake na,ya kan siya ya ci kafin ya fita sai ta fara adawa da ni kai Tsaye kuma ta same ni ta min mgana cewa bata son na kara saida ma Mijinta Danwaken mu in tace bata so kawai a barshi kada rayuka su baci. Amma na jin haka tace a barshi kawai saboda Kaltume ba ta tsoron Tijara Tundaga ranar ban kara saida masa ba ko ya aiko zan ce gabadaya an siye shi ba bu. Daganan na samu lafiya,ammh har alokacin bata daina min gani gani ba ita a tunaninta kada Mijinta yace ya na sona na saka ta uku ni kam a raina nace ta ya ya zai ce ya na sona? Shi kan shi ai baya so ya shiga cikin ukun ba. ***** Washegari saboda zuwan Ramatu sai ban kwab'a danwake da yawa ba. Tunda tace min sabon gari ta kwana kenan zata iso nan da wuri, shiyasa tun safe na tashi na fara aikin Habiba ta taimakamin da wura gawayi ni har ta sakamin tukunyar Farko. Daga baya na amsheta ta shiga wanka Saboda tafiya makaranta. Cikin ikon Allah yau sai ga Mutumin ya aiko Datti da gudunsa ya zo min da kular ya na washe baki ya ce"Adda Hasiya ga Mutumin nan ya zo" Bansan dalili ba sai da naji wani sanyi a raina na karbi kular da Sauri tare da dubu d'ayan da ya ke ba ni. Ga mutane na layi ammh sai da na saka masa sannaan na mika ma Datti ina Fad'in"Ka ce masa mai Danwake tace lafiya kwana biyu bai zo ba? Sai Faman mirmishi na ke yi ni kadai Har sai da Datti ya Dawo yana cemin"Yace tafiya ya yi shiyasa." Kad'a kaina na yi a fili nace"Haba shiyasa naji sa shuru ashe.." Har Datti ya juya na sake kwalamasa kira ya dawo na kallesa kafin nace"Tambayarka zan yi. Mutumin nan da ke aiko ka yaro ne ko babba? Da Sauri Datti yace"Kai Babba ne fa." Ya fad'a cikin nuna yarintarsa. Da gudu kuma ya fita ya barni ina mamakin kaina na miye nawa na son sanin yaro ne ko Babba?. Yau cikin Nishad'i na cigaba da Saka Danwake na zuwa tara na gama komai na share wajen, sannan na wanke kwanukan da na taba girki zan yi saboda zuwan Ramatu. Ammh sai nace bari sai tazo kada na Dafa ya yi sanyi. Amma na fara saka ma ruwan wanka na juye mata ta yi tunda jiya bata samu yi ba, kokon da na Dama mata na sha nima tunda ba shi da Tsami sai waken da na saka masa manja kadan naci saboda kumburin ciki. Kafin ta fito wanka na gyara dakin na Share ta na fitowa nima na shiga na yi, koda na fito na isketa ta shirya ta na zaune ta na shafama kafafuwanta man zafi. Cikin yanayin mganarta tace"Hasiya nace ki siya ko karamar waya ce. Ta na da amfani tunda ga shi ina ta son na kira Adda mu gaisa ba wayar da zan kirata." Ina shafa ma jikina Vaselin nace"Amma zan siya. Ki bari riban ya kara taruwa ba na so na taba ne kuma mu shiga har uwar kudin" Amma ta yi mirmishi kafin tace"Hasiya ina zaki kai wannan tattalin naki? Dariya na kyalkyalce da shi kafin nace"Amma rayuwar nan sai mutum ya iya tattali ballatana yadda Tsadar rayuwa ya kara Hauhawa." Amma ta jinjina kai kafin tace"Hakane ina miki Fatan watarana mijinki ya Mori wannan Tattalin naki da hangen nesan da Ubangiji ya mallaka miki su Hasiya." Na ji add'aunta acikin raina na amsa da Ameen batare da na ji acikin raina hakan zai iya kasancewa ba. Na riga na Sadakar na gama aure a Duniya baxan kara yarda na auri wani ba. Ballatana nazo na zame masa matsala a rayuwarsa. Iya bakin Fentin da shafa ma kaina Dalilin Aure ya isheni ba na kuma Bukatar karin wani Tozarcin. Amma itama ta Fahimceni sai ta sauya Hirar zuwa ta Adda Fati ta na Fadin"Oh Fati shuru kwana biyu bata zo ta dubamu ba." Ina Zura Doguwar riga a jikina nace"kinsan ta yi ta fama da Zazzabi ita da yara. Ta na samun Sarari zaki ganta, Adda Rukayyace ma naga kwana biyu yan ganin Damanta ba su turo ta zo ba." Amma tace"Itama sai da nayi mganarta a raina. Allah yasa suna lafiya su da iyalansu" Ina Daura Dankwali nace"Amma lafiya ke shuru fa. Suna nan lafiya da wani abu ya faru da mun sani." Amma na shirin mgana mukaji sallamar Adda Fati suna gaisawa da su Maman Boy. Na kalli Ammi ta kalleni kafin nace"Amma Muryan Adda Fati ce fa." Amma tace"Baiwar Allah ina ta zencen ta sai ga ta" Ta na ko dago labule ta shigo nace"Kinsan yanzu Amma ke mganar ta ji ku shuru ke da Adda Rukayya Allah yasa kuna lafiya" Ta na Sauke goyon Hanifa da ke bayanta gefen Amma lokaci daya ta na Fadin"Zazzabin da muka sha ne da yara duk jikina ba Dadi. Babansu ma sai yau ya fara fita aiki. shi har da Basir ne ya tasar masa." Ni da Amma muka had'a baki wajen fadin"Subhanallah." Na dauki Hanifa sai naga barci take yi na mikama Amma ina Fadin"Habi ai tace har Hanifa ta sha Zawon hakuri." Adda Fati tace"Sosai ammh duk mun samu sauki su har sun tafi makaranta shima yau ya tafi na gaji da zaman gidan nace bari na biyosa ya saukeni agida kawai na duba ku." Ledan da ta shigo da shi ta mikama Amma tana fadin"Sabulai ne da Manshafawa Amma. Ba kudi ne duk mun cinye a asibiti" Amma tace"Bakomai Fati. Allah ya yi albarka ya azurta mijinki da kudin Halal ya shirya muku zuru'a." Muka amsa da Ameen Ameen. Kallona ta yi kafin tace"Hasiya wlh rashin wayarki na damuna kana son mgana da ku ammh sai ka kira makota." Amma tace'Nima tsiyar da na ke mata ko da yaushe kenan. Kinsan ta da rashin son kashe kud'i ba Dalili." Adda Fati tace"Kamar wata ma'aikaciyar gwammati ba. Komai ace sai an yi shi cikin Tsari." Dariya kawai na yi bance komai ba. Ina kusa da Amma ina kallon Hanifa da ke hannunta ta na barci. Adda Fati ashe kallo na ta ke yi sai da na Dago muka had'a ido cikin ware mata ido nace"Na yi miki kyau ne wannan kallon fa Adda Fati" Adda Fati tace"Kin kara fari ne sannan atamfar nan ta na yi miki kyau in kika sakata" Na bi Atamfar jikina da kallo wata Bakar Atamfa ce Chiganvy baka da Fara ce tun ta akwatin aurena da Abubakar ne. Ba tun yau ba in dai na saka Atamfar ne sai mutane sun ce ta na yi mini kyau. Dukkansu ni suka bi ni da kallo, ni kuma tuna Abubakar yasa yanayi na kawai ya sauya Amma ce ta ce"ki gayamata ta rage tunani baki ga ta na ta ramewa ba ne" Adda tace"Amma Hasiya fa daman ka shi da rai ne. Tunanin rayuwa kuma Dole ne Amma. hasiya ki yi hakuri In sha Allahu Mijinki na Har Abada ya kusa zuwa. Wanda zaki Daura kayansa ki yi ta Daurawa har Abada." Mirmishi kawai na yi ban yi mgana Ameen din ma wannan karon ban ce ba. Hira Amma da Adda Fati suka cigaba da yi ni kuma sai na jingina da Bango na fada kogin Tunanin irin Rayuwar da muka shinfida da Abubakar. Sai ga shi cikin wattani uku komai ya zama Sai Tarihi. Tunanin da na lula yasa ko sallamar Ramatu ban ji ba sai da naji Challara kukan Noor sannan na san har ta iso. Na bita da kallo har ta zauna kusa da ni ta na gaida Amma Noor kuma na Hannun Adda Fati har ta fara kuka. Cikin kasalan da ya Rufeni nace"Yaushe kika shigo.? Tana mirmishi ta kalleni kafin tace"Lokacin da kika shiga kogin Tunani mana" Sai kawai na yi mata mirmishi. Ta shi nayi na je na Debo musu ruwa. Na Dauki Dubu daya na fita tsakar gida ba yaran sai na leka waje Hamisu na gani yayan Salihi shi na ba ma wa nace ya siyomin lemun panta guda Biyu. Ban dawo ba sai da na jirasa ya dawo sannan na Dawo Dakin. na ijiye mata a gabanta duka ta kalleni ta na fadn''Ji don Allah kamar wata bakuwa." Ina Hararanta nace"Eh mana ke ai bakuwa ta ce mana ko Amma? Amma tace"Ni ma Ramatu bakuwatace. Ammh kuma yar gida ce Tunda diyata ce" Adda Fati tace"Kwarai kuwa. Hasiya karbi yarku mai kiyuya." Ina Dariya na karbi Noor ina mata wasa. Fita na yi waje in da su Maman Salihi suke ganina da Noor yasa maman Boy ta karbeta tana Fadin"Yarinyar ta yi yawo fa". Yake nayi kafin nace"In ba damuwa zamu zauna a dakin ki ni da Ramatu maman boy." Cikim Fara'a tace"Haba Hasiya me zai hana? Na taba miki shamaki da Dakina ne? Karaf Maman Salihi ta karbe da Fadin"Ballatana ni. Ko ya'yana ban muku shamaki da su ba, aike ko gaban anguwan nan ne ta aike su zasu je." Mirmishi nayi kafin na karbi Noor ina Fadin"To nagode" Na juya naji Kaltume da ke jajjagen kayan miya tace"Uhm ku dai bi a Hankali kada mu ji gobara ta fara bin Dakuna." Ina mamakin meyasa Kaltume ta ke wasa da Kaddara ta? Ko don ita yarinyace domin ko haihuwa bata tabayi ba shekararta daya ne da wani abu a gidan bata wuce sa'ata ba ga rawan kai ga munafunci ga Gulma. Ni dai shigewata daki nayi ban biye mata ba na iske Ramatu da Adda Fati na ta Hira. Zani na Dauka na goya Ramatu na Dauki mata lemonta nace tazo muje Dakin Maman Boy. Ba musu ta taso ta na ce ma su Amma'"Adda bari mu je" Suka amsa mana da Toh. Dakin Maman Boy muka shige na saki Labule na san su da Dabi'an labe. Daman mun shige mun bar su da mgana a bakinsu. Zama muka yi a kujera d'aya ina ta kallon Ramatu ta yi kiba kamar ba ita ba Taga kallon ya yi yawa ta Zungureni ta na fad'in"Kallon fa kinga na sauya miki ne? Kai Tsaye nace"Kin yi kiba Ramatu kin yi fari sosai ma sha Allah." Ramatu tace"Alhamdulillah. Ammh kinsan har da Jego ko? Ina Hararanta nace"Wani jegon? Mata kina neman wata biyar da Haihuwa kina kiran Jego kawai dai yayana ya iya kiwo ga Noor ma ta yi bulbul ta yi yawo." Ramatu tace"Gaskiya kam baza'a raina ma yayanki ba. Yana ji damu sannan ya na kula damu yace na gaisheki ma sosai." Ina mirmishin jin dadi nace mata ina amsawa. Nan muka shiga Hira har da Shewa sallah kadai ya tadamu girki ma Adda tace na bari zata girka. Me zata Dafa? Nace muna da Sauran Taliya ta Dafa mana Amma na son ta da wake ta manja. Tace to kafin ma ta Dora Biyu tayi sai ga Habiba ita ta karbi girkin. Cikin lokaci ta gama sai da muka ci muka natsa Noor ma Habiba ta karbeta mayya yara ne ina ta mata Fad'an ina zata kai yara har Biyu ga Hanifa ga Noor ta na Dariya tace"Kai Adda na iya fa renon yara kema ki bari ki Haihu ni zan renan miki ya'yan ki." Mirmishi kawai na yi kafin nace"Habi ni ai bazan haihu ba ballatana ma ki renin ya'ya na ammh dai ga na su Adda da su Ramatu sun isheki Reno." Ba Ramatu kadai ba Hatta Habiba sai da ta tsaya ta na kallona. Ramatu ne tace taje kawai ta na Fita ta juya kaina ta na min Fad'a cikin Masifanta tace"Haba Hasiya. Shikenan sai ki cire rai da Rahmar Allah? Wa ya fada miki bazaki yi aure ba? Sannan wa ya fad'a miki ke ma bazaki Haihu ba? Kai Tsaye nace"Komai a bayyane ya ke Ramatu kada ki yi kokarin Lullube abunda bazai taba lullubuwa Saboda ina taki ba. na sani kin sani, Ba bu wani Namijin da zai so ya aure ni ya auri Bala'i masifa da shiga uku da kudinsa ba Ramatu, ba bu wannan Namijin" Kai Tsaye Ramatu tace"Akwai shi. akwai shi Hasiya." Cikin Idanuwana da suka cika da kwallah na kalleta kafin nace"Akwai shi fa kika ce? To in akwai shi yana ina? Shuru ta yi cikin wani yanayi kafin tace"Ya nan a inda Allah ya ijiyesa Hasiya. Kila kusa dake ko kuma nesa da Duniyarki. Ammh tabbas nasan akwai wannan Namijin. Namiji irin Salisu sannan wanda ya fi Abubakar Jarumta da Tausayi namijin da yasan Babu mai yi sai Allah ya kuma san Kaddara ce ke bibiyan Rayuwarki ba Canfi ba" Kalamanta suka sakani sai da na Murmusa kai tsaye nace"Kada mu yaudari kanmu Ramatu ba bu wannan Namijin. ko zai amince da ni Ahalinsa bazasu taba bari D'ansu ya auro Jaraba da kudinsa ba." Ramatu tace"ni kuma ina ji ajikina Hasiya bazaki Dauwama ahaka ba. Namijin da na Fada miki koma waye zai zo. Zai zo in sha Allahu" Cikin Sauri nace"Zai zo? Yaushe..? Ramatu ta kalleni cikin Rauni kafin tace"Bansani ba Hasiya.. ammh nasan Allah zai kawo sa." Ina jin kalamanta sai nima nawa kalaman bakin suka kare cigaba da bani baki tayi ta na ta faman Lallashina. Shine ma na sake har na gayamata mafarkin da nayi na Salisu. Kai Tsaye tace"Kada ki damu Salisu bazai taba Zargin ki ba ai yasan abubuwan da suka Faru ya tabbata ke ma kina kokarin kokuwa da Kaddaran ki ne." Sai na gyad'a mata kai alamun gamsuwa shiyasa ta cigaba da Fad'in"Saboda haka ki kwantar da Hankalin ki Salisu zai warke kamar wani abu bai taba samunsa ba." Da Sauri nace"In sha Allah.." Muna nan muna mgana sai da aka kira la'asar muka koma Dakin Amma muka yi sallah mun idar kenan sai ga Kiran Adda Rukayya ta wayar Adda Fati bayan sun yi mgana aka bama Amma suka gaisa suka yi mganan da za su yi sannan suka yi sallama. Sai alokacin Adda Fati ke fad'amana Ranat asabar Adda Rukayya zasu tare a Sabon gidan da Mijinta ya gida anan Gaskiya. Sannan tare da Birthday din Cikar Amna shekara Shidda Shine ta ke fad'ama Adda Fati tace ta fad'amana jin ma tana gidan sai tace ta bama Amma ta yi mata mganar Habiba tazo Ranar Jumma'a ta tayata parking. Dukkanmu mun yi mata Murna. Adda Fati tace"Ramatu ki fad'ama Inna Talatu Ranar sati sai mu je mata Murna." Ramatu tace"Zan fad'a mata Hasiya ki shirya muje.." Zan yi mgana kenan in ce bazan je ba Amma ta yi saurin cewa"Zaki je mana Hasiya. Yanzu ma sai da tace na fad'a miki tana jiran ki." Na sha mamakin wai Adda Rukkaya na jira na, matar da Tsoron fad'an mijinta ta ke yi sama da ni yar'uwanta. Ganin yadda na yi ne yasa Adda Fati da Ramatu suka rika Tausana da kada na Damu yar'uwata ce Rukayya ban isa na sauya ma wannan alakar tamu suma ba jinina ce. Da kalaman bakinsu yasa nace na amince zan ce batare da Tunanin wani irin Tozarci ke jirana in na shiga cikin sha'anin da ban saba shiga ba. Sai Yamma Adda Fati ta tafi, Ramatu ta riga ta tafiya tunda ita gida zata koma. Naji dadin zuwan Ramatu ko banza ta Debemin kewa tare da Shawarwarinta masu amfani. **** Tahir bai dawo ba sai Ranar Jumma'a Da Safe ya je wajen aiki ko da ya dawo ya iske shi. Ya san muhimmamcin sallama a musulunci an kuma ce in kai kaje to kayi ma wanda ka iske sallama. Shiyasa ya yi masa sallama ya kuma ba shi Hannu suka yi musabaaha. Yadda Tahir bai sakar masa Fuska ba shima haka ya yi masa gim da ransa. Abu d'aya ya Kudurta ko kwashe kayansa Tahir ya yi zai sauya wajen zama bazai taba ce masa don me ba? Saboda sanda ya zo suka zauna Tare ba shi ya Kirasa ba Ra'ayinsa ne yanzu ma in yace zai sauya wajen zama bazai taba zama Takura ga Ra'ayin Tahir ba. Shi dai hakkin zaman tare ya Cire sannan ba zai fasa gayama Tahir gaskiya ba. Duk da yasan shakuwa da Amintar da ke Tsakaninsu bazai saka su yi nesa da juna ba. Dole daya zai nemi daya kuma ya na Tabbacin ko kwashe kayansa Tahir ya yi ya na da tabbacin sai ya Dawo Domin bai saba da kowa ba sama da shi shiyasa bai damu ba ya shiga Harkan gabansa. Yau da Danwakensa yaje wajen aiki ya ci a chan bai dawo da Saura ba Duka ya cinye. Ya ji kimar mai Danwaken nan ta karu a idonsa Matar mai mutumci ne tasan Daraja Costumominta tunda har ta iya lura da ya yi kwanaki bai zo siyan Danwake ba har ga Allah abun ya yi mishi dadi a ranshi. Wata zuciyar ta fad'a masa ka sani ko itama ta na da manyan ya'ya dole ta damu da ya'yan wasu. Kawai Tunaninsa ya fi ba shi mai Danwaken nan Dattijuwa ce uwa kuma Rayuwa da yanayin da ake ciki ballatana ga ire iren anguwan nan sai a hankali zaka ga kowa na sana'a domin Dogara da kansa. Kuma a tunanin Sadiq a irin su Sana'an Danwake, Kuli abinci haka na Dattijai ne yara kuma sai dai in su awara, Dankali da Sauransu. Bai taba kawo ma kansa matashiyace ke Danwaken da ke siya ya na jin Dadinsa ba. Tahir da kansa tun a daran ya gaji da cin mganinsa ya sauko ya na masa mgana bai kuma tambayeshi ba ya fad'a masa kano yaje gidan Jb. Sadiq bai yi mamaki ba daman ya na kallon Wani Turkish Drama ne a laptop dinsa ya Tsaida yana Sauraransa Tahir din. Cikin Tattausan lazafi yace"Fatan ya na lafiya..? Tahir ya sauke wayar Hannunsa ya na Fadin"Uhm kai kasan me? naga abunda ka ke gayamin Jb fa ya lalace mata haka ya ke kawowa gidan ana shaye shaye ana lalacewa." Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Ba sabon abu ba ne." Tahir yace"Ni ai ban zata haka ya lalace ba. Wlh da gudu na had'o kayana na dawo nima ya fara kokarin Tusamin lalacewarsa har da cewa zai kawomin yan mata Biyun da zasu rika tayani kwana kafin na dawo." Sadiq ya gyada kai ya na kallon Tahir kafin yace"Me yasa baka karbi' tayinsa ba.? Tahir ya harareshi kafin yace"Ni dan iska ne Sadiq? Haba haba dai." Sadiq ya ce"Ok ashe yanzu ka Fahimci mganata. Da nace ba matsayin ku d'aya da Jb ba." Tahir yace"Na Fahimta. Sorry Abokina Sharrin Shedan ne." Sadiq yace"Is ok.." Daga haka ya cigaba da kallon Tahir kuma ya Dauki wayarsa ya na Fadin"Usman Mb na gaisheka." Kai Tsaye Sadiq yace"Mun yi chart da shi dazu ina wajen aiki." Tahir yace"Oh nima jiya muka yi mgana da shi." Daga haka Sadiq bai kara mgana ba, ya cigaba da kallonsa Tahir kuma ya cigaba da latsa wayarsa. Washegari asabar da gyaran Daki Sadiq ya tashi da kuma wankin kayansa. Tahir na kofar dakin kan jakar ruwan da suka siya ya na kallon Sadiq ya tube dagashi sai 3Quater wando da Karamar riga ya na wankin kayansa. Cikin takaici yace"gaskiya ka na cutar da Magajin gidan nan da ake kiran ka. Wanki fa ka ke yi da kanka." Sadiq kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Eh mana ai ban fi karfin wanki da kaina ba. Ko daman chan lalacewa ne ace mutum ya zauna yace komai sai an yi masa, kuma nagaya maka mai wankin nan baya min wanki mai kyau. Sannan ga batar da kaya wanduna na nawa ya ce bai gani ba? Har fa wannan wandon farar shaddar tawa ya bace kuma zencen kenan." Tahir yace"To ba sai ka yi masa kashedi ba..? Sadiq ya yi tsaki kafin yace"Sai dai in a cikin kunnensa zan zuba kashedin sannan sai ya ji." Tahir ya kwashe da Dariya kafin yace"Tsiyana da kai fushi. ni kam bazan iya ba. Ga ruguna na had'e da boxers dina na kawo ka wankemin? Sadiq ya dago ya na nuna ma Tahir kwatan dake gabansu lokaci d'aya yana fadin"Kawo Tahir. Kwata ta kwashi nata rabon." Tahir ya dage baki kafin yace"Mugunta phone store Abubakar Sadiq Sulaiman Shinkafi." Sadiq yace"ba ka ga mugunta ba sai kaga fararen rigunanka acikin kwata." Dariya suka saka gabadaya. Tahir na zaune har Sadiq ya gama wankinsa ya shanya suna da Igiya nan bakin barandansu saura kuma kananun kaya a daki ya baza saman akwatinsu tunda igiyan bata da girma. kuma ba shi kadai ya yi wanki ba Tahir dai bai yi ba son jiki shi dai ya fi gane ma ya kai wanki a kawomasa a goge acikin Leda shi kuma Sadiq yace ya gaji da Hannunsa ba mai kara saka shi ciwon baki. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabooks:JamilaUmarjanafty* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086 *12* Haka kurum na ji na kwana da zumud'in tafiyar mu tarewar Adda Rukayya. Abunda bai cika Damuna ba kenan wato shiga Mutane, shiyasa ko D'anwake ranar asabar d'in ban yi ba nace ma Amma zamu huta. Amma tace daman ai ni ce ba na son jikina ya Huta ammh tuni tace na rika Hutawa ko sau d'aya a sati. Tun safe na yi wanka na shirya Tunda Habiba tun jiya ta tafi, sai da na tsaya na yi ma Amma abinci na gyara daki wanka ne kada'i ba tayi ba tace min jikinta sai a hankali bazata iya wankan nan ba kila sai zuwa gobe. Sai na Rabu da ita kawai daman mun yi da Ramatu zan biya mata mu wuce tare. Inna talatu kuma tare zasu tafi da Adda Fati da zata biyo ta nan gidan su wuce. ina gidan kafin na wuce Suka iso gabad'ayansu da na so ma mu tafi tare sai nace ma Ramatu mu had'u achan kawai sai kuma na sauya Ra'ayi jin su Maman Salihi sun buga tsalle sun ce zasu je ma Adda Murna. Ban san a ina ma suka ji labarin ba Kawai sai na ce musu sai sun zo. Kayana na saka wanda Ramatu ta yi mana ranar sunan Noor. Sai na yi amfani da Farin Hijabina sabo ne lokacin Bikina da Salisu na d'inkashi. Na saka takalmina mai saukakken Tudu tunda ina da tsawo ba na jin Dadin saka takalma masu Tudu. Sai ga shi na yi yar kwalliyata har da Shafa hoda da kwalliya tare da man lebe Amma da su Adda suna ta fad'in na yi kyau da na kalli madubi sai da na yi dariyan kaina Fuskarta yar Sirit ce gaskiyan mgana komai na jikina karami ne ba Babba ba, hatta ko da kaina duk da tarin gashin da na ke da shi kana kallona zaka san ina da karamin kai. sai dai fuskar ta yi fasali Farar Hoda na saka daman ita nake shafawa,tunda ga yanayin Fatar Jikina ina da Haske sosai kamar wata zabiya. Adda Fati na ta yi min d'an bikin na jirasu nace Wlh bazan tsaya jiran wannan gayyar tafiyar na su ba. Na ko yi tafiyata bayan na yi ma Amma sallama tace a dawo lafiya. Na riga na yi yak'i da kaddarata shiyasa na yi Gundunbalan fita ba Abun rufe Fuskaa duk da ba wanda ya tareni da wata mgana ammh na sha nu ni da baki da Hannu ana zud'ena. Adaidaita na samu zuwa pizzet daganan na samu na D'anmagaji tunda yanzu ta cikin Titin Tukur Tukur suke bi. Karfe sha d'aya da wani abu na isa gidan Ramatu na iske Nura na gidan ashe ya dawo yana gari. Na ganshi sai fama ya ke da Noor itama kuma Ramatu na ciki ta na Shiryawa. Shigowata na karb'eshi ina Fadin"Kawata muguwa ce. Shikenan sai ta barka da reno kai da ka dawo ka na Bukatar Hutu." Yana dariya yace"Yauwa Hasiya ki yi mata Fad'a bata Tausayamin da na dawo kamar ta samu D'an reno" Ramatu na daki ta daga Murya ta na Fad'in"In baka nan zan rena ammh fa in ka dawo kaima zaka Tab'a" Kai ya girgiza kafin yace"Kin ji ta ko? Ina sabata saman kafad'ata nace"Kyaleta da ni, zan yi maka mganinta." Ramatu ta fito cikin Shirin Fita ta wurgamin zanin goyo tana Fad'in"Goya yarki mu tafi mun yi rana." Ba musu ko na goyata Nura kuma ya shige ciki Ramatu ta bi bayansa sai chan suka fito tare. Tunda yana nan shi ta bar ma gidan Ammh har bakin Titi ya rakomu muka samu abun hawa zuwa gaskiya Bayan Ramatu ta kira Adda Rukayya ta yi ma mai adaidaita kwatance wajen. Cikin Lokaci ko sai gamu a sababbin anguwannin Gaskiya ne gida mai suna gida Baban su Amna ya gina Tunda babba ne a ma'aikatan MBAIS. ko da muka isa mun iske gida cike da yan'uwa kamar ana wani Biki Adda Rukayya daga ita sai Habiba ne sai makotanta inda suka taso. Gidan Babba ne shashen Adda Rukayya dakuna Hudu ne kowanne da Bayuka sannan ga Falo ga kitchen. shashen mai gidan ma babban waje ne sai kuma wani bangare da ba'a gama ba. Tunda muka shigo na lura da yanayin yan'uwan Mijin sai faman nuna ni suke yi ana kus kus. Wanda ma bai sanni ba duk an gayamasa komai a kaina ban maida kai ba muka wuce cikin Dakin da Adda Rukayya take. Abun mamaki ta yi maraba damu sosai ta saka wani leshi sabo ta ci kunshi da kitso kamar wata Amarya. Kai tsaye ta kalleni tace"Hasiya sai yanzu.? Ba fa kowa sai ni kad'ai Allah yasa ma Habiba na nan" Mirmishi kawai na yi ban ce mata komai ina ta kallon wajen gadajen duk Sabbi ne falon ne bakomai Kila ba'a kawo kayan ba ne. kafin ma mu tambayeta ta shiga gayamana masu kujrun ne ba su kawo ba sai an juma Gadaje kawai aka kawo sai kayan kitchen data siya tunda munzo muje mu tayata jera komai. Hijabina na cire ban sauke Noor ba Duk da tayi barci yanzu ina Sauketa zata Farka. Habiba sai faman mopping din Tayels ta ke yi ta gama wankin bayi wai a hakama sun Rage ayyukan tunda tun jiya da Daddare duka dawo nan suka kwana. Dangin mijinta kuwa suna tsakar gida ba abunda suke yi sai shewa da Hira. Tare da Adda Rukayya da makotanta muka gyara mata kitchen d'inta wasu kayan duk Sabbi ta siya muna ji suna hira da makociyarta adashen dubu Dari Biyu ta shiga aka bata kwasan farko. Kallona ta yi kafin tace"Hasiya na ware muku wasu kaya suna chan gidan. Har da wasu kayan amfani na cikin gida in Habiba zata dawo zata Taho muku da shi." Kai na jinjina kafin nace"Mungode Adda Congrat Allah ya sanya alheri yasa an yi ma rai ne." Ta amsa da Ameen cikin Fara'a kafin tace"Ina Adda Fati ne wai? Kai tsaye nace"Suna tafe sai da ta biya ta gida ita da Inna Talatu da mutan gidanmu ne su Maman boy." Adda Rukayya tace"Munafukai za'a zo ganin kwaf." Ramatu tace"Su zo ai arziki ne sai su dagwala su kara gaba" Adda Rukayya cikin Farinciki ta saka Shewa suka kashe da Ramatu ta na Fadin"Wlh kuwa su zo su sha kallo." Nan suka cigaba da Hirar su da Ramatu tare da makotanta ni nawa kawai Mirmishi da eh ko a'a. Babu wani sakin jiki ko shakuwa Tsakanina da Adda Rukayya yau ma na Fahimci tana cikin Tsananin Farinciki ne shiyasa. Sai bayan azahar su Adda Fati suka iso lokacin har an kawo abinci daga Gidan su Baban Amna cikin gari. Ba su da nisa da Babban gidanmu na marigayi Mammadi kona. Sun san mu kamar yadda mu ma muka san su. Abincin ma kula Hud'u ne suka Dauki Biyu suka ba ma Adda guda Biyu. Ni na zuzzuba mana muka ci muka sha Ruwa da lemu tunda Walima ce aka yi. Amna da Aslam na ta tsallen Murna sun yi sabon gidan. Yaran sun fi sabawa da Dangin Ubansu shiyasa ma suna tare da su. Ni dai tunda na Fahimci yadda na zama mujiya da abun nunawa sai na kama kaina acikin Dakin Adda ko Fitowa ban karayi ba tunda muka gama gyaran kitchen. Su Maman Salihi sai zaga gidan suke yi suna santi bayan sun gama ci sun sha abun mamaki har Kaltume da nasan gulmar da ta kawo ta ta fi wacce ta kawo su maman Salihi. Sai Gabda La'asar Baban Amna ya kira yace ga masu kawo kujeru nan da wasu kayanbA gyara waje jin haka yasa muka mike muka kara gyara Falon da Sauran Dakunan. Kawo kayan yasa Danginsa suka shisshigo mazan su suka rika shigowa da kujeru ne sai katifi da cafet sai tv bango guda Biyu da sauran tarkace. Sai Falon ya yamutse kowa na fad'in yadda Setin kujerun suka yi kyau da cika ido. Adda Rukayya sai faman washe baki take yi tana fadin"bangare na za'a fara gyarawa, na shi yace sai daga baya" Shagala da ganin abun arziki yasa na fito nima na Tsaya cikin mutane ana santin ganin kayan da ni. Noor ta tashi ta na Hannun Habiba. alokacin ba ni da Hijabi Domin Tunda na cire ban maida ba, sallah ban yi ba Tunda ina Hutu. Kamar Daga sama naji an kira sunana da Karfi "Hasiya.." Sai na juyo sai da Gabana ya fad'i ganin Jummai kanwar Abubakar ce itace Autar su. Kallonta na ke yi ina kokarin daidaita yanayina jin ban amsa ba yasa da ta shiga Tafa Hannu ta na Fad'in"Na shiga uku na lalace wa na ke gani haka kamar Hasiya Jaraba da Masifa da bala'i.? Jin mganarta yasa sai Hayaniyar ta Tsaya kallo da Hankali ya Dawo kanta. Ita ko kai tsaye ta shiga nuna ni ta na kuma kallon kanwar Baban Amna Tunda ta dalilimlnta tazo gidan. Ita jummai tana auran kanin mijin Kanwar Baban Amna ne su d'in Facalolin juna ne. Cikin mamaki tace"Me ye had'in ku da wannan Jarabar? Ta fad'a ta na nuni Kamwar Baban Amna mai suna Zainab tace"Wannan wai? Kanwar Ya Rukayya ce matar Yaya Adamu." Ai sai jummai ta Rafka salati tana Fadin"Me ya kai ku jawota nan wajen? To Allah ya kyauta mu gama taron nan lafiya wani bala'in bai afka ma dan'uwan ku ko wannan gidan ba." Duk na Tsure na kasa ko kwakwaran motsi kamar yadda su Ramatu suka yi. Da yake Abubakar suna da Tarin zuru'a a gidansu nima ba duka na san su ba su Adda Rukayya ba su san Jummai ba sun fi sanin manyan. Ramatu ce ta kalleni ta na Fad'in"Wacece wannan Hasiya? Dakyar na Hadiye miyan baki na kafin nace"Jummai ce k'anwar Abubakar.". Ramatu ta zaro ido Adda Fati na gefe tace"Subhanallah Allah yasa kada ta watse taron nan" Ai bata gama Rufe baki ba Zainab kanwar Baban Amna tace"Mun santa sarai Jummai ni kaina da na ganta tazo sai da nayi mgana to ammh gudun ka yi mgana ace ka tada Fitina yasa ban ce komai ba." Jummai ta ce"Kin ko yi kuskure. Wannan matar ba Mutum ba ce ina zargin Mayya ce." Su Adda suka saka Salati Inna Talatu ta shiga Tsakiya ta na Fad'in"Ashas. Wani irin maita kuma baiwar Allah? Kai Tsaye Jumma tace"in ba maita ba menene? In ta kama kurwan mutum sai ta Allah kawai. yaya Abubakar sai da zaman zariya ta gagareshi ya koma kano komai ya taba da sunan sana'a sai ya lalace ta gama lalata masa Rayuwarsa gabad'aya muma ta lalata mana Rayuwar mu tunda ta dalilinta Ubannu shima ya rasa komai na shi in ba Maita ba mene wannan? Ki sake mana kurwan d'an uwa don girman Allah Hasiya." Tun kafin ta gama mgana na Fara Hawaye cikin murya ta nace"Wlh ni ba na maita. Dangin mu kuma ba Mayu." Da sauri Zainab kanwar Baban Amna tace"Kina fa da Maita Hasiya. in ba maita ba menene? Ina ce a auran ki na Biyu ma abuunda ya faru kenan? An ce shima sai da aka rasa Dukiya sannan shima har tana neman ransa Tunda yana chan yana jinya da karaya uku ajikinsa ko'ina kika shiga Bala'i ne da Masifa zai faru to in ba Maita ba ne, sai ki fad'ama na uban me kike da shi..? Kalmar maitan da suke jefana da shi yasa na Fashe da kuka. Ramatu ta rikeni ta na Fadin"Wani irin maita kuma? Hasiya ba mayya ba ce in da mayyace da Tuni kun sani ai kunsan tushenta asali ma kusa kuke da su" Nan fa mganganu ya rika tashi kannen Abubakar suna ta cewa a bakin ya'yan Baba Saminu suke jin Labarin su ma sun ce maitan gareni. Adda Fati tace"Mu ba mu da Maita. Ba mu yi gadon shi ba. Da muna da shi da kunga Rukayya da shi." Kai Tsaye Zainab tace"Ai an ce ana siya kuka sani ko itama siyan tayi." Adda Rukayya da ta kasa mgana Tun dazu sai yanzu ta dakama Zainab Tsawa kafin tace"Ya isheki Zainab. Kina wuce gona da iri ya kuma isheki jifar yar'uwata da kalmar Maita." Zainab ta Saki gud'a kafin tace"Ku na kokarin Boye abunda bazai Boyu ba Yaya Rukayya. To in ba maita ba ce ku fad'a mana ko menene muna son ji." Adda Rukayyah sai ta kasa mgana Ramatu ce tace"kaddaran Allah ce. Hasiya ba Allah ba ce ba ta da masanin gaibu. Kuma wannan mganar da kuke yi kamar kuna Jayayya da Kaddaran Allah kuma Daidai ya ke da Baku yarda da Allah ba." Maganganun Ramatu yasa suka yi Shuru Jummai ta tab'e baki kafin tace"Wlh kada ku yarda da mganar su. Gwara ta tafi tun kafin mugun abunda ta tsara ya saukar mana." Jin maganganunta yasa kannensa suka fara cecekucen sai na bar gidan kada na jawo musu wata asarar. Kuka na ke yi da Bakina da zuciyata. Adda Rukayya ta ba ni mamaki yadda ta shiga ta na masifan sun zo sun tozarta ta tunda suka Tozartani. Tabbas jini jini ne, Dan'uwanka zai iya maka abu ammh shi bazai iya Daukan wani ya yi maka ba. Mgana taki karewa suna ta Tafka bala'i kan sai na bar gidan har suna Hakilon za su fita da ni ita kuma Adda Rukayya tace ba zan tafi ba ba su isa ba. Ganin abun na neman ya yi yawa yasa nace ma Adda Rukayya bari na tafi kawai. Idanuwanta jajir tace"Ba fa zaki tafi ba. Ko da suke tunanin nan gidan Dan'uwansu ne. Ni ma su yi Tunanin Ni matarsa ce ina da iko da komai na shi." Inna Talatu ta ga Hayaniyar ta yi yawa ga maza masu kawo kaya yasa ta ce ma Adda ta bari na tafi kawai ta kalli Ramatu ta na fad'in"Ramatu ku je gidan ki da ita." Ramatu ta gyad'a mata kai sai ta Rikemin hannu na koma Dakin Adda ina sharan kwallah na saka Hijabina Da takalmina Habiba sai kuka ta ke yi ta na fad'in"Adda Hasiya ki yi hakuri." Ban iya mata mgana ba. Ramatu ta karbi Noor ta goya muka fito ammh duk da Haka Rigimar bata kare ba. Kamar wasa zamu fita muka bangaji juna da bakin da suka shigo ni ban san yadda abun ya faru ba sai gani na yi d'aya daga cikin su ta fad'i a kasa tana ta faman birgima da ihu. Suna ganin haka wata mata ta kwalla kara ta na fad'in"Ku riketa ta tabatta mayyace ta kama Ladidi" Ta fad'a cikin karaji ni dai na juya ina son sanin meke faruwa ba zato ba tsammani naji an cakume an yo baya dani ana fad'in bazan tafi ba sai na Tsallaka matar dake kwance tana Fizga kamar mai aljanu. Ramatu na ja na ta na fad'in"Hasiya ba mayya ba ce don Allah ku bari mana.". Ta na yi su Adda na yi Inna Talatu fad'i take"Shed'an ya shigo gidan nan don Allah ku bari mana." Ba wanda ya Saurare su rikeni yan'uwan Baban Amna suka yi suna Rantsuwan sai na Tsallaka matar da ke kwance sannan zasu kyaleni. Na rude na Dimauce domin ban tab'a ganin wannan tashin Hankalin ba. Ganin su Adda Fati suma sun taso sun Tare ni yasa Zainab tace ma mazan da suka kawo kaya su Rufe kofa su zo su kama mu su ni. Innalillahi wa'inna alaihirraju'un Ban taba zaton haka Rayuwa ta ke cikin Tsaka mai wuya ba sai ranar. An ce sarki yawa ya fi sarkin karfi. Sun fi mu yawa su Adda baza su iya da su ba sannan ga Maza. Haka wani Namiji ya rikeni daman ni ba auki ba, Matan kuma suma kaimun duka ta ko'ina Hijabin jikina haka aka yagashi a ka yar, A na jamin Rigan jikina Dankwalina ko Tuni ya yi ta kan shi Gashina ya bazu haka suke jamin ga shi suna Tunkud'a ni su Ramatu na Faman tareni ammh sun fi karfin su. Bana so na tsallakata Saboda ni ba Mayya bace, gida ya cika da iface iface da Hayaniya wasu suka fita waje suka rika Ihun an kama mayya kafin kace me gida ya cika da Mata da maza. Sai da suka min duka suka yayyagamin kayana dagani sai siket sai Bra a gaban Mutane mata da Maza Ramatu ta rufanin Hijabinta suka Cire suka watsar Adda Rukayya na ta Ihu sai kiran Wayar Baban su Amna take yi baya Dauka. Su kuma sun yi Rantsuwan Wlh tallahi sai na Tsallakata ko su halakani,Tozarcin da ban taba ganin irin shi ba. Tsirara suka kusa yi min dagani sai siket. Haka na ke wani irin kuka zuciyata na zafi kamar zan Mutu Adda Fati kuka Adda Rukayya ma. Habiba ma kuka Ramatu kuka, duk wani mai imani da idon shi bai Rufe ba sai da ya Tausayamin. Na tsugunna na Rufe kirjina ina kuka ina Fad'in"Wlh ni ba mayya ba ce.". Wani Saurayi yace"Ki ta shi ki Tsallakata sai mu tabbatar da ke ba Mayya bace" Ban yi shawara da kowa ba na mike ina Duke jikina na tsallaka matar nan dake numfarfashi. Ba ta tashi ba suka ce sai na kara na kara shima bata tashi ba. Suka ce sai na kara cikin ikon Allah ina kara yin na uku sai gata ta mike ta na faman zare ido ganin Mutane a kanta yasa ta ke fad'in"lafiya me ya faru.? Kawai wajen ya Rud'e da Hayaniyar "Laa! Wlh da gaske Mayya ce." Ko kafin na yi wani yinkuru sun Rufeni da Duka Inna Talatu ta fita da Gudu waje tana neman agajin jama'a. Adda Rukayya ta shiga cikin su tana Ihu ta na Fad'in"Kai kai ku bari mana." Ramatu ko wayarta ta Dauko ta Kira mijinta ita kanta garin kareni dukanta ake yi Noor sai sai Faman Tsala kuka take yi. Inna talatu na Kofar gida ta ga zuwan Mijin Adda Rukkayya a mota. Daman yana Hanya zuwa ne bai ga ko kiran Adda Rukayyan ba inna Talatu ta nufe shi cikin tashin Hankali tana fadin"Za su yi kisa wlh zasu kasheta." Hankalin sa ya tashi jin hayaniya ya Fad'a gidan a guje. Shi kanshi ya shiga Tashin hankali ganin gida cike da mata da Maza daman tare ya ke da abokinshi. Adda Rukayya na ganinshi ta Nufeshi ta na kuka fad'i ta ke yi"Wlh wani abu ya samu Hasiya ba ni ba kai har Abada Adamu." Bai tsaya jin ba'asi ba suka fara watse taron da Kai kai ku bari mana Jumai da Zainab sun fi kowa zakewa wajen dukana. Baban Amna da Abokinsa suka kwaceni lokacin sun gama Min lilis bakina da jini hancina na jini kaina daga goshi na sun fasamin har da masu tsigemin gashin kaina. Sun samu nasaran balle zaren bra dina ta baya Dalilin da yasa na kwanta a kasa na Rufe kirjina da Hannayena ina wani irin kuka mai Cin rai kamar ba ni ba. Baban Amna yace"Subhanallah.." Ramatu ta kwance Noor ta zo ta lullunbamin zanin goyon nata Adda Fati kuma ta cire hijabinta ta Dagoni ta sakamin ta na kuka. Baban Amna yace"Meke faruwa ne?miye haka..? Nan zainab ta shiga warware masa komai ta karishe da fad'in"Ladidi fa ta kama sai da muka sakata ta tsallaketa sau uku sai ga shi ta tashi." Ladidi cikin mamaki tace"Ni fa Inaga Lalurata ce ta tashi. Ina da Aljanu kuma suna yawan bugeni na Fad'i." Sai wajen ya yi shuru. Baban Amna yace"fisabillahi me ye haka.? Sai ku ce ta tafi gida menene amfanin wannan tozarcin? Ni dai kuka kawai na ke yi, Ramatu ta kalli Inna Talatu ta na Fad'in"Inna Nura yazo zan tafi da Hasiya na wuce da ita gidana.? Inna Talatu tace"Eh kada ta koma ta tadama Amma hankali kuje chan gidan ki kawai." Ta amsa da Toh Adda Fati da Habiba suka taikamin na tashi zanin goyon noor na yi Daure gaba da shi, na saka Hijabin Adda Fati dakyar na ke tafiya Fuskata ta Suntuma saboda duka. Adda Rukkaya kuwa fad'i ta ke yi"Wlh ni kuka Tozarta. Ba dai ni zaku yi ma wannan Tozarcin ba.! Ta ke fad'a cikin Tsawa da karaji. Ba wanda ya kulata sai mijinta da ke ta ce ma Inna talatu ayi hakuri. Ko tankashi ba wanda ya yi tunda yana mganar da an koreni ne ba sai an Dakeni ba kenan shima ya amince da komai da ake fad'a kaina. Nura da mai adaidata yazo Tunda Ramatu tace yazo da abun hawa. Nura sai sallalami ya ke yi yana Fadin"Inna yanzu haka Mutane suka zama Jahilai.? Miye haka don girman Allah." Inna Talatu ta girgiza kai ta ma kasa mgana kafata ba ko takalmi ana ta kai wa ke ta kaya. Dagani sai Ramatu muka shiga cikin Adaidata muka tafi Inna Talatu tace yanzu suma zasu tafi chan gida. Abunda ba su sani ba Tuni su Maman salihu sun zame jiki sun koma gida sun kai Amma Labarin duk abunda ya Faru. Suma muna wucewa ba su koma gidan ba suka wuce sun ma mamta da wasu mutanen gidanmu tashin Hankalin da suke ciki ya ishe su. Suna Hanya Inna Talatu na Tunanin me zasu Fad'a Amma in ta tambaye su ni? Adda Fati tace"Mu ce kawai ta na gidan Ramatu zata kwana biyu" Inna Talatu ta girgiza kai kawai tana Uhm.! Kai jama'a. Ni ko muna tafiya ina ta kuka , kuka da Karfi kamar zan Tsaga Adaidaitan Nura na gaba sai juyowa ya ke yi yana Fadin"ki lallasheta ke kuma mana.." Ramatu na matsan kwallah tace"Ba ni da sauran kalamai Nura a gaban idona aka Tozarta Hasiya kan kaddaran da ba ita ke da iko a kan shi ba." Nura yace"Ni kaina abun ya Tab'ani wlh wai ya abun ya faru ne.? Cikin Damuwa ta fara ba shi labari. Ya saka Salati yana fad'in"Kamar wasu Jahilai." Mai adaidaitan da muke ciki yace"ai yanzu mutane sai Allah ba su da yarda da Allah komai ya faru da Mutum sai kaji ana Fadin jifa ne. Wannan Dabi'ar ta canfe canfe wlh ana Fama da ita yanzu nima akwai wata yar'uwata da tayi aure mijinta ya Talauce ya yi ta shiga bala'i itama a karshe an ce Farar kafa gareta ya sakota wajen shekara tara kenan duk wanda yazo neman auranta da ya samu wannan Labarin baya Tsayawaa. Sun kasa gane mutum bai isa ya san gaibu ba. Allah ke da arziki da Talauci." Nura yace"Rashin yarda da Kaddara ne. Shi kuma rashin yarda da Kaddara Daidai ya ke da rashin yarda da Ubangiji. Mutum bai isa ya yi ma Mutum abunda Allah bai yi masa ba." Mai adaidaita yace"Sosai ka ga anan wajen Tauhidi ya raunana. Sannan kuma a musulunci babu maita babu kuma Canfi ammh Mutanen wannam zamanin basa ganewa komai ya Faru da Mutum sai kiji ance ba Daga Allah ba ne akwai sanadi." Nura ya gyad'a kai kafin yace"Abunda ke Faruwa kenan. Kuma malamai na iya bakin kokarin su mutane basa ji kwata kwata." Mai adaidaita yace"Yanzu ai ko mutuwa ba ta zame ma Mutane wa'azi ba. kaga kuwa tunda Mutuwa ba ta zame mana wa'azi ba wlh tallahi ba bu abunda zai zama aya kuma agaremu." Ina jin su suna ta mganganunsu su da suka gane haka kenan su ke kuma Fad'in haka. Muryata bud'e na ke kuka kukan bakincikin yadda aka yi min Tsirara gaban Mutane. Ganin zamu tsaya gidan Ramatu yasa cikin kuka nace"Ku kaini gida. Don Allah ku kaini gida." Ramatu tace"Amma Hasiya" Cikin kuka nace"gida zan je Ramatu..na ce miki gida zan tafi." Na fad'a cikin karaji da kuka Nura ne yace mu tafi gidan gabadaya. Ni dai tunda na ganmu a kofar gidanmu ban tsaya jiran Ramatu ba na Diro daga adaidaita. Ko ganin gabana ba na yi kafata ta yi tsami ina dingishi. Fuskata ta sumtuma ga jini duk ya bata gaban hijabin da na saka ba Takalmi haka na Fad'a cikin gidan cikin kuka da Muryan karaji na ke kwalama Amma kira. Wacce daman tun sanda su Maman Salihi suka zo da Labarin Amma ta kasa zama adaki tana Tsakar gida tana Safa da marwa labari kuma ya shiga kunnen matan gidanmu suna Tsaye cirko cirko. Ina shigowa na zube gaban Amma ina wani irin kuka. Amma jikinta ya fara rawa ta durkushe itama a gabana ta na Fad'in"Hasbunallahi wani'imal wakeel Hasiya yanzu abunda suka yi miki kenan.? Itama sai kuka, daidai lokacin da Ramatu da Nura suka shigo. Ni ko fad'i na ke yi"Amma menene laifina? Wani abu na aikata da na chanchanci shiga cikin wannan matsanancin tsaka mai wuyan? Amma na tsiyayan Hawaye tace"Ba ki da wani laifi Hasiya. Ba ki da laifi har a wajen Ubangiji." Cikin kuka na ce"Amma da gaske to ni Mayya ce? Da Sauri Amma tace"Wlh ke ba mayya bace, kaf zuru'armu ba mu da maita haka zuru'ar mahaifin ku. Ba ki gada ba sannan baki siya ba Hasiya." Ina rike hannun Amma nace"To miyesa haka ke faruwa da ni? Farko Abubakar daga baya Salisu Amma.? Me yasa.? Me ke faruwa da Rayuwata ne..? Na karishe fad'a ina jin Numfashina na cijewa ya na sama da kasa kamar zai yanke. Cikin kuka Amma ta rikeni ta na fad'in"Bansani ba Hasiya. Abu daya na sani ke mutum ce kamar kowa. Baki da bakin fenti a tare da ke, Komai da ke faruwa Hukuncin Allah ne da mutum bai isa ya ja da shi ba." Amma na mgana ina jin amai na tasomin na fara tari ina rike kirjina Lokaci d'aya ina fadin"Amma kirjina, Mutwa zan yi ko? Dama na Mutu na Huta." Sai amai na fara kelaya shi a jikin Amma ina wani irin rawan jiki kamar zan mutu. Na fita daga hayyacina da bansan su waye ke kaina ba naji dai hayaniya. Ramatu ta wankemin jiki bayan na gama Aman suka kai ni daki. Daga lokacin kwance kawai na ke ina Numfarfashi kamar wacce numfashinta zai bar gangar jikinta. Har dawowan Su Adda Fati ban sani ba. jikina ya yi zafi ashe sai da Nura ya kira wani abokinsa mai Chemist yazo ya yi min alluran ulcer sannan ya sakamin Drip na samu barci. Duk nan suka kwana Ramatu ce kad'ai ta tafi gida sai wayan gari na yi na ganni kwance an gama min karin ruwa. Tun kuma wayewan garin na ke kuka lallashi da ban baki ba wanda Adda Fati da inna talatu ba su yi min ba sun yi har sun gaji sun kyaleni. Amma ko bata mgana, ita kanta in da zata kwanta sai ta fi Hasiya jin jiki saboda yanayin da ta ke ji ajikinta. Zuciyarta na zafi da rad'ad'i in ta tuna yadda Rayuwata ke cikin TSAKA MAI WUYA.! *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari. Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah. Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus *13* Duk lallashin da suke yi min Ina jin su ammh kuma ba na daukan duka magangansu, domin nasan irin kalaman na su na kuma jima ina jin irin su, ammh har yau har gobe babu al'amarin da ya sauya. Gayamin suke na daina damuwa komai da ya faru daga Allah ne. Ni ban isa na tsara kaddaran mutane a Hannuna ba, to a irin yanayin da na ke ciki na gaji da jin irin kalamansu Tunda ba za su taba sama mun mafita ba. Duk maganganun da suke yi ban bude baki na nace Tak ba. Kuka kawai na ke yi na had'a kai da gwiwa ina rafzan kuka. Ko ruwa ban bari ya shiga bakina ba duk ko da magiyan da suke yi min da na ci wani abu ko zan samu karfin jikina. Haba rayuwar nan duk ta isheni in har mganar mutane ba gaskiya ba ne meyasa abubuwa suke faruwa da ni daki daki haka? Farko Babanmu na biyu an ce ciwon Amma ni ce Sanadinsa halin da muke ciki duka Laifin na kaina, Sabo da ni Dangin mahaifin mu suka Gujemu kowama ya gujemu Abubakar ya aureni ya sakeni Salisu ma haka. Duk kuma ace haka kurum abubuwa ke faruwa dani kamar ni kad'ai ce Y'a a wannan Duniyan? Tabbas akwai kamshin gaskiya. na fara Tunanin tunda na zama Annoba ga al'umma to banga amfanin Rayuwata ba ko na Mutu, ko kuma na yi nesa da Rayuwar da ni ke ciki. Ina ji Adda Rukayya ta kira Adda Fati sun yi mgana sannan an ba ma Amma ta na ta bata Hakuri. Adda Fati ta dafani ta na Fad'in"Rukayya na gaishe ki. Tace a yi miki sannu gobe kila ta shigo ita da Habiba." Ban so na yi mgana ba Saboda ba na jin yin mgana da kowa ammh a wannan gabar ina bukatar wani karin bayani, idanuwana jajir na dago ina kallon Adda Fati fuskata duk ta kumbura saboda kuka da duka cikin Dashewar murya nace"Adda Fati ban gane wani abu ba? Me yasa Adda Rukayya ta damu saboda dangin Mijinta sun Tozartani." Adda Fati tace"Kada ki manta Rukayya jininki ne Hasiya. Duk in da aka kai aka kawo ba ta da kamarki kamar yadda ke ma baki da kamarta." Na yi mirmishi ina jin yadda bakina ya Bushe da makogwaro na. Ban ce komai ba na maida kaina cikin gwiwoyina na suke. Inna Talatu ne tace"Ita Halin Rukayya Wauta ne da rashiin wayau. Ammh ba ka budema miji sirrin yan'uwanka ka rika bata su a idon sa saboda gudun watarana ga shi yanzu sun yi abu kuma ya zo ya na Damunta." Sai alokacin Amma ta saka baki jikin Raunin zuciya da na jiki tace"Kuma shi wannan dan'uwa da ka ke Tunanin wani ya fisa. To duk duniya shi ne naka akwai kuma bangaren da Dole naka ne zai iya kare maka shi. Baren bazai iya ba. Ina Fatan wannan abun ya yi sanadin dawo da Rukayya cikin Hayyacinta." Adda Fati ta amsa da Ameen kafin tace"Kuma fa Amma ita zata iya yima Hasiya. ammh in wani ya ci zarafinta sai abun ya fi yi mata zafi kamar yadda ya faru. Wani kuma Tozarcin da suka yi har da zugan Kanwar Abubakar din nan tare da maganganun dangin mu muma." Adda Fati ta sauke ajiyar rai kafin ta cigaba da fad'in"Tunda da bakinsu suke fad'in ga abunda suke fad'i a kan Hasiya. Har suna fad'in suma Dalilin haka suka gujemu, Kuma da gaske ne sun gujemu ba mai neman mu ko sha'aninsu wani Lokacin bama sani suna yin shi. Yanzu Baaba ta lagos sai ta zo garin nan sau biyar dakyar zata zo gidan sau d'aya to wai har gwara ita akan su Baba Tanko shi Baba Jibril karshe da shi da iyalansa ma ba su san inda muke Rayuwa ba. Sai Baba Saminu shi kuma daman tsegumi ke kawosa ya zo ya fad'i mganganu ya kara gaba gabadyansu ba mai Mu'amala mai kyau damu." Amma ta jinjina kai kwarmin idanuwanta sun cika da ruwa cikin wani yanayi tace"Uhm. Ni kaina sun ba ni mamaki kuma lokacin da Alhaji ke Raye wlh ya yi musu komai ya samu na yan'uwan shi ne da iyalansa, ammh yanzu in da zai dawo Duniya yaga Halin da suka barmu a ciki na Tabbata zai yi bakinciki mai yawa." Inna Talatu tace"Ai Allah ne ya kawo mu zamanin Zumuncin zamani. Daga kai sai kauri, in kana da shi ayi da kai in baka da shi kuma kai da banza duk Daya." Amma na sharan hawaye da Gefen zaninta Lokaci daya ta na fad'in"Akwai Allah. Watarana sai Labari komai zai zo ya wuce Rayuwa zata fita daga cikin Tsaka mai wuya, komai kuma zai yi daidai in sha Allahu." Duk ina jinsu ammh ban tankan su ba na riga na samar ma kaina mafita da ni ke ganin shine daidai da Rayuwata da rayuwar kowa sai dai na zabi na yi shuru da bakina ba na son ma wani ya Lallasheni ballatana ya bani baki. Adda Fati ita tayi aikace aikace ta yi abinci ni kam ko a bakina sun yi sun yi nace na ce na koshi ina nan kwance ina kukan zucci da na Sarari jiya an yi min Tozarcin da bazan taba mantawa da shi ba Tsirara a kayi min ana dukana da Zargin maita da kananun Shekaruna na ashirin da Biyar Shekaruna na Duniya, na Dand'ani Dacin Sakin aure har sau biyu bayan Tarin Tozarcin da ke bibiye da Rayuwata. Adda Fati da Inna Talatu sai da Yammah suka tafi, Adda ta yi ta ba ni Hakuri kan ta tafi, inna Talatu kuma roko na ta ke yi kan naci abinci toh kawai na ce musu ba domin na amince da duka mganganunsu ba. Zama a iren gidajen haya irin Gidan mu mtsala ne duk abunda ya faru in dai sun sani sai mutanen gari sun gama ji ballatana ni da Labarina ya yi Tambari a gari. Magana har ta yad'u a gari makotana nata shigowa yi ma Amma jaje da ganin Halin da na ke ciki, abun sai ya kara tabani batare da Tunanin komai ba su Adda na tafiya na mike ina ganin jiri ammh ban damu ba na fara Had'a kayana cikin akwatina babba tun ta auran Abubakar ne, Tunda ya barmin komai da akwatin da duka kayan gidan Gabadaya. Amma na kallo na ta kasa mgana sai da taga shirin nawa ya fi karfin hankali sannan tace"Hasiya lafiya.? Me yasa kike had'a kaya.? Kai Tsaye nace"Amma wajen Adda zan koma bazan iya juran zama na anan ba." Da Sauri Amma tace"Hasiya ba na kashe wannan mganar ba? Ba inda zaki koma nan zaki zauna tare da ni." Kai Tsaye nace"ni kuma ba zan zauna ba Amma ko ki barni na koma wajen Adda ko kuma na shiga Duniya." "Hasiya..!" Tsawa Amma ta dakamin da yasa na Fashe da kuka ina Fad'in"To miye amfanin Rayuwata tun bazan sama ma kaina sukuni da mutanen da ke Zagaye da Duniyata ba? Amma ki Fad'amin meye amfaninna? Ai gwara na Mutu ko kuma na yi nesa da ku gabadaya hankalin ku ya kwanta nima nawa ya kwanta.." Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Juyowa na yi ina kallon Amma Lokaci D'aya ina nuna saitin zuciyata na cigaba da fad'in"Anan daidai wajen na ke jin kuna Amma. Jiya fa Tsirara a ka yi min ana kira na da sunan Maita. Amma ki fad'amin akwai Tozarcin da yafi wannan ne? Ki fad'amin ta yadda zan iya yaki da Tsaka mai wuyar da ni ke ciki? In ban yi tunanin kashe kaina ba, ban yi kuma yi tunanin shiga Duniya ba. To Amma ki bar ni na koma wajen Adda zan fi samun kwanciyar Hankali." Kuka na ke yi har sai da na Durkushe Amma ta kasa tasowa itama jiri ta ke gani in ta mike cikin karfin Hali tace"Hasiya na ce miki ba zaki koma ko'ina ba ko? Tare zamu zauna Mutuwa ce ko aure kad'ai zasu Rabamu." Cikin Ihu nace"Ni kuma in na cigaba da zama anan mutuwa zan yi Amma don girman Allah ki bar ni na tafi." Amma na kuka ina kuka kafin tace"Sai dai ko mu tafi Gabadaya ammh bazan barki cikin wannan rayuwar ta tsaka mai wuya ke kad'ai ba." Jin haka yasa na kasa mgana na koma na dora kaina kan akwatin da na cika da kaya ina ta kuka Halin da nike ciki yasa ko Danwake ban tuna da shi ba. ina ji da Safe ana ta zuwa Nema su maman Boy suna fad'in babu mai Danwaken ba ta da lafiya. Bayan mangriba sai ga Ramatu da Nura sun zo Dubani ita tazo min da Su maltina da Madara sai kayan Marmari da magungunan jiya da Aka Rubuta suka siyomin. Zuwan Ramatu yasa Amma tace duk yau ban ci wani abu ba Ramatu ta fara lallashina da Fad'in"Haba Hasiya kin san kina da lalura me yasa zaki zauna da yunwa.? Hannunta na Dauka zuwa Saitin zuciyata ina fad'in"Daidai nan ne ke min ciwo Ramatu. Wlh na zabi mutuwata da wannan Rayuwar." Da Sauri ta Rufemin baki ta na Fad'in"Ki daina fad'in haka Hasiya. Allah na sane da ke kuma shi ya zaba miki wannan Rayuwar. Fad'in haka kuma Daidai ya ke da nuna masa baki yarda da kaddaransa ba." Kuka ya kwace min na kwanta akan Cinyarta na fashe da kuka ina Fadin"Kaddaran ne tamin nauyin Dauka Ramatu ya zan yi? Ki fad'amin ya zan yi? Wlh ina so na mutu mutuwa zan yi." Na ke fad'a ina wani irin Gunjin kuka Ramatu ma sai kukan Nura ne ya ke ta lallashin mu ya karishe da kallon Ramatu ya na fad'in"Ke kuma miye haka? In kina kuka wazai lallashe ta.? Jin haka yasa ta daina kuka,ni kuma kukan da Amma ke yi yasa na tsaigata nawa Ramatu ta had'amin maltina da Madara na sha ta kuma saka sai da na sha Kayan marmari,sannan ta bani magunguna na sha. Amma ta kalli Ramatu ta na fadin"Ramatu ki kara lallasamin kawarki. Ta kafe Wajen Adda ta ke son komawa" Ramatu ta kalleni ina Runtse ido kafin tace"Hasiya Amma ba ta son tafiyarki. Kuma in kika duba duk in da kike je ba zaki samu sukuni ba in dai ba kina tare da Amma ba ne. Don Allah ki yi hakuri watarana sai Labari." Kai kawai na gyada mata bawai don na aminta da mganarta ba. Ai nasan Hanya Amma sai dai ta tashi taga na tafi bazan zauna ina Kara Rusa mata Rayuwa ba. Ga ciwo ga kuma jikin girma. Haka Ramatu da Nura suka tafi akan gobe zasu dawo. Bayan sun tafi Amma ta zauna ta na ta min nasiha ina sharan kwallah itama ta na sharan kwallah acikin raina ina Tunanin ita Rayuwa meyasa ba ta cika ne sai da Kalubale.? Sai dai ni nawa kalubalen mai girma ne, mai tafiya cikin Tsaka mai wuya. Na firgita ne Lokacin da Amma ta mike zata fita ta Dauro alwala jiri ya kwasheta saura kad'an ta fad'i sai da ta Dafa Bango ta na salati. Duk da nima ba jin dadin na ke yi ba. Sai dai Amma ce komai nawa gwara ni na Raunana da ita ta Raunana Haka na mike na rikota ina Fad'in"Amma. Me ya faru..? Cikin Damke Hannuwana tace"Bansani ba, tun safe na ke ta fama da jiri ga ciwon kai" Jikinta na taba na ji zafi sai gabana ya fad'i cikin wani yanayi nace"Amma Akwai zazzabi a jikin ki fa." Tsoro daya kada ciwonta ya tashi zaunar da ita nayi, baho na samo da Ruwa a buta na yi mata alwala nace ta yi sallar a zaune Tunda ta na ganin jiri. Mangariba da Isha'i ta had'a Lokaci daya Bayan ta idar na sakamata abinci taci na bata panadol ta sha ina Fadin"Amma ki kwanta ki Huta." Kallona ta yi lokacin da na kwantar da ita ina lulluba mata zani a wajen kafafunta. Hannuna ta rike guda d'aya lokaci d'aya ta na kallona cikin wani yanayi. Cikin sanyin murya nace"Amma menene..? Cikin wani sauti tace"Don girman Allah kada ki je ko'ina Hasiya. Ina tsoron na kwanta barci ki aiwatar da Kudurin ki." Sai Amma ta bani Tausayi da Sauri na jinjina mata kai Lokaci daya ina jimke hannunta kafin nace"in sha Allahu bazan je ko'ina ba Amma. Ina tare da ke." Da Sauri tace"Kin Tabbata.? Jinjina mata kai na yi ina Fadin"Na Tabbata Amma." Sai taji dadi ta saki hannuna ta koma ta kwanta tana sauke ajiyan rai. Ni kuma matsuwa sai ta kamani na Zuba ruwa a buta, na fita zuwa makewayi sanda na dawo har Amma ta samu barci sai nima na samu gefenta na kwantar da kaina Saman katifar jikina na kasan leda ina Tunanin makomar Rayuwata. ******* *9:30pm* Jiya bai ci Danwake ba yau ma ga shi bai ci ba, Jiya saboda wankin da ya yi ne yasa bai je ya siya ba. Yau kuma barci suka yi tayi dagashi har Tahir sai Sha daya na Safe suka tashi kuma yana da Tabbacin ko yaje Danwaken ya kare sai ya Hakura. Gyada ya fita ya siya da rogo chan Babban Titi. Tahir kuma Taliya da wake ya Dafa mai kifi duk ya karnace musu Daki. Shi kuma baya Shiri da kifi kwata kwata in har abinci da kifi ba ya ci Tun yana yaro haka ya ke. Ko yaya ya ci abinci da kifi to ranar yini zai yi amai ba sukuni. Kuma ko karnin kifi yaji yanzu sai zuciyarsa ya tashi. Kuma Tahir yasan da haka ammh Saboda ya saka shi mgana yasa ya kirkiri dafa Taliya da kifi. Gabadaya Dakin sai da ya Dauki karnin Tsabar wulakanci irin na Tahir akwai nama acikin Miyan da Umma ta yi masa ya zo da shi da ya yi masa mganar ya yi amfani da shi cewa ya yi shi fa yau ji ya ke yi in bai ci taliya da kifi kamar dan cikinsa zai Zube. Sanin Halin Tahir na wulakanci yasa ya fita batun shi. Yinin Ranar a rashin sukuni ya yi shi da Daddare zuciyarsa ta rika ta shi cikin Masifa ya kalli Tahir da ya gama cin taliyarsa ga farantin nan a gabansa da abun maltinan da ya gama sha, shi kuma yana ta faman Danna wayarsa cikin Nishadi. Kai Tsaye yace'Tahir kasan me wannan abun da ka yi ya jawo min? Dakin nan gabadaya sai karnin kifi ya ke yi kuma kasan yadda na ke da Kifi ko? Kai Tsaye Tahir yace"Sorry Abokina wlh yau da ban ci taliya da kifi ba, da kaga Hanjina ta waje." Ran Sadiq ya baci yace"Na kasa cin komai yau a dakin nan Tahir karni na shiga min ciki cikina." Tahir ya Dago ya na kallonsa kafin yace"Is That Serious..? Saboda Takaici Sadiq bai kara mgana ba jin garin akwai sanyi sanyi yasa ya mike ya nemo Jaket din sa ya saka saman Rigar da ke jikinsa. Ya shuru takalminsa ya fice ya na jin Tahir na fad'in"Ina zaka kuma..? Ko Tankashi bai yi ba ya Fice karamar wayarsa ke jikinsa da ita ya yi amfani ya haska tunda ba wuta anguwan ta yi Duhu. Ba domin siyan wani abu ya fito ba iskar gari ya ke so ya shaka Tunda Tahir ya sauya iskar Dakin gabadaya. Tafe ya ke kawai ya na kallon zirga zirgan Mutane kamar rana sai kuma yaji ya samu natsuwa har bakin Titi yaje sannan kuma ya sake kwana ya Juyo yana cikin tafiya ne ya hangi dandalin Samari a wani Rumfa sai da karisa yaga mai Shayi ne matasa da magidanta an taru ana ta shan Shayi ana Hiran Siyasa da yadda kasa ta ke ciki na Hauhawan man Fetur kowa na fad'in Ra'ayinsa. Sai kawai yaji abun ya Burgesa Sallama ya yi musu suka amsa kafin ya ba su hannu dukkansu suka yi musabaha. Shima ya samu gefen wani matashi ya zauna. Mai Shayin da bai taba ganinsa a wajen ba ya kariso ya na Fadin"Yallabai me za'a yi maka? Shayi ka ke so ko kwai za'a soya maka ko kuma wainar kwai? Sadiq ya dago ya na kallonsa matashi ne ba Wani babba ba shi fa a Tunaninsa Masu yin shayi sai magidanta sai daga baya ya Fahimci matasa suma sun mike da neman na kansu. Saboda yadda Kasar tamu ta koma aikin Gwammati sai wane da wane. Aljihunsa ya laluba ya ciro wallet dinsa duka duka 2k ne a ciki sai ya Dago ya na kallon mai shayin kafin yace"Tea zaka had'amin." Sale mai Shayi ya ce"An gama yallabai sikari da yawa ? Madara ko melo? Sadiq yace"Madara. Sugar din ba da yawa ba." Ya juya kawai ya wuce wajen tukunyar Shayinsa. Su kuma sauran suna ta labarinsu, acikin Hiran na su ne yaji wasu duk sun yi karatu ammh ba bu aikin yi sai Buga Buga mai shayi na Had'a masa Tea ya Daga Murya yana Fad'in"Yallabai a had'o da Buredi.? Sadiq bai san ma da shi ake mgana ba sai da na kusa da shi ya tabashi sannan ya amsa masa da kadan ba da yawa ba. Cikin Lokaci ya hado masa Tea dinsa mai kauri ya kawo masa. Ruwan ya yi zafi da ya sa yaji dadinsa ya gasa masa ciki. shi kanshi da ya kalli kansa a Teburin mai shayi sai da ya Murmusa Sadiq mai abun mamaki suna da kayan Tea a gida ammh sai yaji kamar yafi samun jin dadi da sukuni shan shayi a cikin Mutane daman haka ake ji? Abun mamaki ya sha da yawa kadan ya Rage saboda ya na sha ne ya na jin Hiran matasan da ke wajen. Anan kuma ya ke jin ashe Sale mai Shayi Degree garesa a BUK ya yi karatu bai samu aiki ba ya fara sana'ar Shayi ya na Rufa ma kansa asiri da iyayensa. Tambayan kudinsa ya yi aka gayamasa 600 sai ya ba shi Dubu Daya yace ya rike chanjin Sale na ta Godiya baisan ya Dauki Lokaci ba sai da ya Duba agogon wayarsa ya ga sha daya saura na Dare Dole ta sakashi ya mike ya yi ma matasan sallama ya wuce. Tunda ya zo garin zariya bai taba wuce tara a waje ba. Ba shi da Dabi'ar yawo hatta Tahir da ke da Rawan kai baya yawo Tunda ba su san kowa a garin ba. *** Bansan Lokacin da Barci ya kwasheni ba chan cikin barci naji Nishi da wani irin kakari. Na mike a firgice jin Sautin daga wajen da Amma ke kwance ya ke fitowa da sauri na mike ina Fad'in"Amma. Amma.." Na ke fad'a ina Yin kanta da Sauri na Dagota ammh ina Amma bata hayyacinta numfashinta na fita da Sauri Sauri jikinta ya Dauki Zafi sai makyarkyata ta ke yi kamar wacce aka Jona ma Shooking. Bude Murya na yi ina Kiran sunanta Ammh ina Amma ba ta jina kamar ta yi nesa da Duniyarmu gabadaya. Jikinta ya saki Gabadaya ga Zufa na uban keto mata ta ko'ina. Zufan da nagani da kuma nauyin da ta sakarmin yasa na Tsorata tunda na sha jin ance in mutum ya mutu ya na yin nauyi sannan ya na jikewa da Zufa ya yin Daukan rai sai na gigice. Na fara girgiza Amma ina kiran sunanta cikin kuka da wani irin Tsoro ta ina zan iya daukan rasa Amma a wannan Lokacin? Fadi' na ke yi"Amma don Allah kada ki mutu ki bar ni. Ka da ki tafi ki barni cikin wannan rayuwar ni kad'ai bazan iya ba. Wlh bazan iya ba." Na ke fad'a ina kuka ammh sai naga kamar Amma ba ta Numfashi ji nayi zuciyata ta tsinke da Gudu na Saketa na fice ina haki nima kamar Shed'ata zata Dauke. Dakin Maman Boy na tafi ina Bugawa Cikin kuka nake fad'in"Ku taimaka min Amma Amma kada ta mutu" Duka Dakunan gidanan ba in da ban buga ba. Na tabbata in wasu ba su ji ba, wasu sun ji kuma lokacin dare bai Raba ba duk da ban kalli Lokaci ba ammh ba wanda ya fito ballatana ya taimakamin. Ganin haka yasa na kwashi gudu na koma Daki na kara tarairayo Amma jikina na kara kunnena saitin zuciyarta ta ji dif kamar bata Numfashi, sai naji kamar wani abu ya Sare daga baya na. Tashi na yi ina Haki kafata ba takalmi zanin Amma na Raruma na yafa na fice daga Dakin da gidam ma gabadaya domin neman agajin nutane. Kamar an yi ruwa an dauke ban ga kowa a waje ba shiyasa na Dauki Hanya ina tafiya gudu gudu tunanina na tafi Chemist din gaban gidanmu na nemo Taimako ba na ko ganin gabana jefa kafafuwana kawai na ke yi ina ji kamar zuciyata zata fashe. Sai ji nayi na bangaji mutum da karfin da yasa ya yi baya nima na yi baya ina rawan jiki. Sadiq da yaji ya sha bangaza kamar wasa ya ja baya cikin mamaki gabansa bai Fad'i ba sai dai ya yi kokarin kiran sunan Allah. Ni ko yamayin da na ke ciki yasa ban ko Tsaya ba sa Hakuri ba na kama Hanya zan wuce da fitilar wayarsa yasa ya haske Fuskata daga sama har kasa ya ke bi na da kallo ganin kafafuwata ba Takalmi da kuma yanayin da ta ke ciki yasa da Sauri ya ce"Ke ke Baiwar Allah." Jin ya kirani yasa na juyo ina kallonsa da idanuwana da suka Kumbura. Cikin Wata irin murya naji yace"Lafiya kike tafiya ba takalmi? Har zan wuce sai na Tuna Amma kawai sai na dawo gabansa na Duka ina Fad'in"Amma Amma ce. Don girman Allah bawan Allah ka taimakamin Amma ce ga ta chan. Kamar ta mutu bata Numfashi." Na fad'a cikin gunjin kukan da yasa na Duka na Dafa kafafunsa ina Cigaba da Fadi'in"Bawan Allah ka taimakamin don Darajan Allah. Don Daraja da kaunar da ka ke yi ma iyayenka ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka. Ka taimaki mahaifiyata kada ta mutu." Sadiq ya ja baya da Sauri cikin in ina ya ce"Kinga yi shuru yanzu ina mahaifiyar ta ki ta ke? Ina jin haka na mike jikina na rawa nace"Ta na. Ta na gida." Sai kawai yace"Mu je na gani." Jin haka yasa na yi gaba da Sauri ina Tafiya ina Hardewa shi kuma ya bi bayana har acikin zuciyansa Lokacin da nake tafiyan nan ya Tsorata. Wata zuciyar tace"To in Aljana ce fa Sadiq? Tuna haka yasa ya rage tafiya har sai da na yi masa nisa sannan na juyo ina kallonsa ba na wani ganin Fuskarsa akwai Duhu daga nesa yace"Ina ne gidan? Da hannu na nuna masa gidanmu ina Fad'in"Ga ga gidan chan." Jim Sadiq ya yi kafin ya kad'a kai yace "Muje.." A ransa yace Allah kaga Niyyata na Tausayi da taimako kada ka bari wannan yarinyar ta Cutar da ni in ta na da Niyyar haka. Yadda da Allah da kuma addu'a yasa ya bi Bayan Hasiya har cikin gida saboda dare da kuma yanayin da Sadiq ya ke ciki yasa bai iya gane gidan da ya ke zuwa Siyan Danwake ba ne. Bai ji hankalinsa ya natsu ba sai da Hasiya ta yi masa Jagora har cikin Dakin Yaga Amma kwance kamar ta Mutu. Cikin kuka na Nuna masa Amma ina Fadin"Ka duba ta. Ta mutu ko? Da Sauri ya isa gabanta ya rike hannunta na wani Lokaci kafin ya Dago ya na kallona cikin kuka nace"Ta mutu ko? Da Sauri yace"A'a ta na numfashi sai dai muna bukatar kai ta asibiti da gaggawa." Kawai sai na sulalle ina wani irin kuka bai Saurareni ba ya fice daga Dakin da sauri ni kuma sai na Dora Hannuna a saman kaina ina Fadin"Wayyo Allah na shiga ni Hasiya na lalace" Na Dauka ya tafi ne shiyasa kawai na koma na zauna ina Rafzan kuka babu wanda zai taimake ni a wannan Halin da muka samu kan mu aciki. Sai dai me sai ga shi Mutumin nan ya Dawo da Sauri ya na fadin"kama min ita ga adaidata chan na samo mu kaita aaibiti." Ina jin haka na mike jikina na rawa na tayasa ya daga Umma sai ya Fahimci nima sai a Hankali Tunda jiri ya kwasheni na kusa Fad'i sai da ya Rikemin hannu da hannunsa Guda daya cikin Tausayawa ya ce"Ki na lafiya.? Kai na gyad'a masa ina sharan Hawaye ganin bazan iya ba yasa ya ba ni wayarsa ya na fadin"Rike min ki gani" da Sauri na karb'a sai ga ni nayi ya ciccibi Amma da dukan Karfinsa yana fadin"Ki biyo ni a baya ki rika haskamin hanya." Da Sauri ko na bi bayanshi wai sai da muka fita ne sai ga matan gidanmu suna Bude kofa suna Fitowa ganin an Dauko Amma kamar ba rai yasa su Maman Salihi ke fad'in"Wayyo jikin Amma ce ya tashi? Ko kallonsu ban tsaya yi ba daman shi Tuni ya yi gaba. Da muka fita mai adaidaitan ya taimaka muka sakata a adaidaitan shi gaba ya shiga ni kuma na shiga baya na rike Amma. Mun fara Tafiya mai adaidaitan yace"Wani asibiti zamu je yallabai? Juyowa ya yi ya na fadin"Wani asibiti ku ke zuwa.? Cikin kuka nace"Kowanne muna zuwa." Tsayawa ya yi kawai ya na kallona ina kuka ba haske acikin adaidaitan shiyasa baya ganin Fuskarta. Cikin natsuwa ya maida Hankalinsa wajen mai adaidatan Lokaci daya yana Fadin"Asibitin da ya fi kusa ka kaimu chan." Kukan ne baya so ya na da Raunin zuciya bangaran Tausayi. Wani asibitin kudi da ke samaru ya kaimu muna zuwa ya fita ya kira Nurses suka zo da abun Daukan marasa lafiya suka Dauki Amma suka yi ciki da ita. Mu kuma muna waje muna jira yadda bai zauna ba nima ina Tsaye ina Tsiyayan hawaye. Kaina na rufe shi da zanin da Lallube jikina baya ganin Fuskata Tunda muka kawo Amma aka shiga Emergeny da ita ba su fito ba sai daya da wani abu na Dare shima ta agogon asibitin na Fahimci haka. Mutumin suka yi ma bayani sannan shi naga ya na ta shi ya fita ashe fita ya yi ya siyo mganguna da allurai a wani kwali suka amsa suka shiga ciki. Ni ko ina Tsaye jiri na ke gani ammh na kasa zama sai da naji ina barazanar zubewa yasa na samu kujera na zauna ina kara Fashewa da kuka. Bansan ya zo kusa da ni ba sai da naji Tattausan muryansa yana fad'in"Ki yi hakuri ki daina wannan kukan. mahaifiyarki na nan da Ranta bata Mutu ba." Da Sauri na Dago Fuskata muka Had'a ido Hudu da shi. Akwai haske a asibitin tunda akawai wuta da Farin kwai. Tar fuskata ta haska shima haka tashi. Kallona ya ke yi yana ganin Fari na da haske kamar wata zabiya ashe ma yarinya ce bai dauka haka ba. Ni kuma ba ma shi na ke kallo ba Tunani na da ya ce Amma na da ranta ba ta Mutu ba. Cikin Dashewar murya nace"Amma ba ta Mutu ba? Kai ya gyadamin kafin yace"In sha Allahu." Da Sauri nace"To ta na ina? Kai Tsaye yace"Ta na ciki sun ce jininta ne ya yi kasa sai low sugar ammh sun samu nasaran ceto numfashinta." Sai kawai na Rumgume hannuwana a kirjina ina fadin"Alhamdulillah.." Hawaye na Diga bisa zanin jikina. A jikina naji gir! Har sai da na tsorata sai daga baya na Fahinci wayace na daga zanina na Dauko wayar bawan Allah nan ne. Na mika masa lokacin shi kuma ya na kallon gefe na ya na Tsaye ya saka Hannayensa duka cikin Aljihun wandonsa. Cikin wani yanayi na ce"Bawan Allah." Kai Tsaye ya juyo sai na mika masa wayar ina Fad'in"Ga wayar ka ana kira." Bai karb'a ba sai da yace"Sunana Abubakar Sadiq. Ba bawan Allah ba." Da Sauri na kallesa jin sunan da ya ambata suna mai Daraja a wajena. Shi kuma bai Kara kallona ba sai kawai ya juya ya d'an yi nesa da ni ya na amsa wayarsa. *Wattpadian Family kuna da yawa masu karantawa, ammh kun rage comments da Vote* *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332. mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki. *14* Tahir ke kiransa ya na Dagawa yaji Muryan Tahir cikin Firgici yana fad'in"Sadiq ka na ina ne? Har daya saura na dare baka dawo ba? Wlh na zata ka dawo gida barci ne ya kwasheni sai farkawa na yi naga baka dawo ba." Sadiq ya shafa kansa da Hannunsa guda d'aya kafin yace"Eh ban dawo ba." Cikin Tashin Hankali a muryan Tahir yace"Sadiq ba ka dawo ba? To ka na ina ne? Kamar bazai yi mgana ba sai kuma dai yace"Ina asibiti ne." A firgice Tahir yace"Asibiti? Innalillahi me ya faru da kai? Tahir ya fad'a gabansa na fad'i saboda Matukar Razana ya razana da rashin Dawowar Sadiq abunda bai taba Faruwa ba ne. firgicinsa kada wani abu ne ya samu Sadiq din ya shiga Uku. Sadiq yace"Eh ina asibiti ne nan cikin Samaru." Tahir yace"Baka da lafiya ne? Sai da ya juya ya kalleta ta na zaune ta had'e kai da gwiwa daga ganinta ta na son mahaifiyar nan nata shiyasa ta ke cikin Damuwa da kuka. Kafin ya yi ajiyar rai ya ce ma Tahir"ba ni ne ba ni da lafiya ba Tahir." Tahir cikin kosawa yace"Ka na so ka kasheni da Zullumi ne Sadiq? Waye ba shi da lafiya.? Sadiq yace"Taimako na yi Tahir. Wata baiwar Allah ce." Tahir ya jinjina kai kafin yace"Zaka dawo ne? Shuru Sadiq ya yi Kara kallonta ya yi ita kad'ai ne bai kamata kuma ya tafi ya barta ita kadai ba. Ga ta karamar yarinya ba bu mataimaki a kusa da ita. Kai Tsaye ya ce"An ya? Ban tunanin haka." Tahir ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Wani asibiti ne? Sai na zo na same ka." Sadiq yace"Ka yi zaman ka Tahir lafiyata kalau fa." Tsaki Tahir ya ja kafin yace"Dilla ka Turomin sunan asibitin gani nan zuwa.." Daga haka ya kashe wayarsa. Sadiq ya Sauke wayar daga kunnensa shi kanshi bazai iya fad'an sunan asibitin ba. Sai da ya fita daga Haraban Asibitin ya ga sunan asibitin sannan ya Rubutama Tahir ya tura masa. Dawowa ya yi cikin asibitin ya isketa har ta yi barci ta d'ago kanta saman masagin kujerun da ke wajen domin zaman masu jinya. Daga gani a wahale take numfashin ma nata a wahale ya ke fita, kauda kansa ya yi ya na kallon gefe. Bayan ya zura duka hannuwansa a aljihun wandonsa yana nazarin wasu abubuwan. Kudad'en hannunsa gabadaya sun kare, Allah yasa ma ya na yawo da Atm dinsa da baisan yadda zai yi ba kudin bankinsa sun yi kasa akwai bukatar ya kira Abba ya sake Turo masa kudad'e. Jiya ba su yi mgana ba Shekaranjiya ne ya kirasa da kansa saboda Matsalan Innani tsohuwar nan matsala ce mai zaman kanta a gidan Abba. Wai sultana babanta ke son taje shinkafi ta yi hutu tunda ta gama Jss3 zasu shiga Ss1 ita da Siyama. Umma ta shirya mata Tafiya Abba kuma daman bai da matsala, Ammh Innani naji ta fara Tsine ma Mahaifin Sultana ta na kawo Labaran da bata san Tushen su ba ballatana makamar su ba. Akan Sultana bazata je wajen Mahaifinta ba, ban da Innani da Shegen kafiya da Rikicin Tsufa ta ina zaki raba y'a da mahaifinta? Duk da Sultana yarinya ce tasan Mahaifinta kuma ta na son shi tare da Sauran yan'uwanta. Umma ta kirasa ta fad'a mai Abba ya ce Sultana ta zauna Tunda Innani ba ta so taje. Shi kuma sai ya kira wayar Innani ba ta shiga sai ya ce ma Umma ta kai ma Innani wayar zai mata mgana Umma tace ya Rufa mata asiri kada Innani ta ce ita ta kai kararta wajen Magajin gida. Dalilin haka yasa ya kira Abba ya ce in ya shiga wajen Innani ya kirasa zai yi mgana da ita. Innani dole ta yi shuru da bakinta Tunda ya ce mata Sultana zata tafi Shinkafi taga Babanta da yan'uwanta Dole Innani ta amsa, ammh kuma jiya sun yi mgana da Umma tana fad'a masa Innani ma ta shirya kayanta tace kafarta kafar Sultana kada shitu ya cuta mata ya ganta marainiya. Shi ko kara bi ta kanta bai yi ba innani case ne mai zaman kanta a wannan gidan in ka toshe nan ne sai kaji ta kara balle wata kofar, yasan zuwa zatayi ta yi ta rashin Mutumci sannan ta hana yarinya sakewa a gidan Ubanta tare da sauran yan'uwanta. Ga shi ya lura Mahaifin Sultana Tsoron Innani ya ke ji in ta zaunar da shi ta na ta zage zage Har Allah ya isa ta sha masa ammh iyakarsa ya ba ta Hakuri ammh Tsohuwar nan har yau ba ta Saduda ba. Kila sai ranar da Ciwon Ajali ya kamata ba, ammh ki na Tafiyar da kyar ga makanta kice sai kin je, Haushi ma yaji yasa ya ce ma Umma ta barta taje din taci abunda zata ci achan. Fitowar Nurse shi ya katse masa Tunanin da ya lula. Ta na gayamasa jikin Amma da Sauki nan da zuwa anjuma zasu kawota dakin da zata Huta. Ni kam mafarki na yi naga su Adda Fati sun zo asibiti suna ta kuka sai na Farka a firgice ina kiran sunan Amma. Sai na hange shi yana mgana da ma'aikaciyar Jinya. Daidai lokacin da na mike baya na ya amsa na duka ina wash ita kuma Nurse din ta tafi,da Kyar na karisa gabansa ina dingishi kallonsa na ke yi da Kumburarun idanuwana Tun kafin na yi magana da Sauri yace"Ta na samu sauki. sun ce zuwa anjuma zasu dauko ta zuwa Dakin da zata Huta." Sai da yaji karfafan ajiyan zuciyan da na Sauke kafin hawaye su gangaromin ban damu da Sharewa ba na kallesa ba ni ya ke kallo ba na Fahimci ba shi da Dabi'an yawan kallo shi,cikin Shakkiyar muryata nace"Nagode sosai. Allah ya saka da Alheri Allah ya jikan magabata." A hankali ya amsa da Ameen kafin kai tsaye ya kalleni ya na fad'in"Ki je ki zauna naga kina dingishi ne" Da kai na amsa masa kafin na juya ina Tafiya sannu kafata ba takalmi sai lokacin ya lura da haka. Da wani irin kallo ya bi ni, kallon da ko Sultana da taso a cikin gidan su a gabansa bai taba mata irin shi ba. Kallo daga sama har kasa, Tabdijam ya dad'e ya na mamakin sirantarka Sultana sai yau da ya ga wannan yarinya ya san Sultana gwaiwa ce kafafunta ya kalla kanana sirara kamar na yara kanana. Ta ya mutum zai rika yawo ba takalmi kuma ta na mace? Macen ma acikin asibiti kafarsa ya kallah yaga takalminsa mai hanci ne sannan in ma ya bata bazata iya sakawa ba. Yana da Babban kafa da Tsawo da Tudu lamba arba'in ne ya ke sakawa. In ta saka takalminsa saboda Siranta bazata iya daga kafarta ba ma. Har taje ta zauna ya na kallonta ta gefen ido yana kiyasatawa a tunaninsa bazata wuce sa'ar Sultana ba. Yarinya karama a barta da mara lafiya haka? Ina babansu da sauran yan'uwanta? Shi kadai ya ke ta wannan Tunanin a ranshi, ya na kallonta ta na ta share hawaye daga gabanta ya matsa saboda baya son kuka barin ma na mace Raunana masa zuciya ya ke yi saboda shi mai Tausayi ne. Kujerun da ke gefe chan da shigowa babban falon asibitin kusa da ma su ba da kati ya samu kujera ya zauna yana jin sanyi sanyi yasa ya saka hannayensa cikin Aljihun Jaket din da ke jikinsa. Ita ya ke kallo yaga ta kara Dunkulewa cikin zanin da ta yi mayafi da shi ta Dauki kafarta ta dora saman kujeran ta dunkule jikinta waje daya daga alamu itama ta na jin Sanyin da ya ke ji. Muryan Tahir yaji ya na Tambayan ma su ba da kati. Sai ya saka baki ya kira sunan shi ya juyo ya na kallonsa kafin ya yi mgana da su kila ya na fad'a musu ga wanda ya ke nema chan. Wajensa ya zo ya na fad'in"Ka ji ni shuru ko? Kasan dare ne na jima ban samu abun hawa ba." Sadiq ya matsa masa gefensa ya zauna ya na fadin"Ai sai da nace ka yi zaman ka ba sai ka zo ba." Tahir ya kallesa lokaci daya yana kara bin asibitin da kallo. Har bangaran Hasiya dake dunkule waje daya cikin Sigar Tambaya ya kalli Tahir kafin yace"wannan ce mara lafiyam? Ya fad'a ya na nuna Hasiya, Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Mahaifiyarta ce.". Tahir ya jinjina kai kafin yace"Uhm Allah ya sauwake." Sadiq ya amsa da Ameen shuru na wani Lokacin Tahir ya gaji yace"Yanzu ina mara lafiyan? Sadiq yace"Ta na ciki sai anjuma zasu kawota dakin da zata huta suka ce." Tahir yace"To ai shikenan ma sai ka tashi mu tafi gida. Tunda ga yarta sai ta zauna da ita." Wani kallon baka da Hankali Sadiq ya yi ma Tahir kafin yace"Sai mu tafi mu barta ita kad'ai a asibitin nan? Baka ganin yarinya ce karama" Tahir ya ce"To mene? Ba taimakonsu kayi ka kawo su asibiti ka kuma biya musu komai to me ya rage Sadiq? Sanin Halin Tahir yasa ya yi masa Banza Tahir yace"Ba dai tunanin kwana a asibitin nan ka ke yi ba? Sadiq yace"Shiyasa nace maka ka yi zamanka ba sai ka zo ba." Tahir ya bude baki ya Rufe saboda mamaki kafin ya sake budewa ya na fadin"Nufinka anan zaka kwana Sadiq? Sadiq yace"Anan zamu kwana dai. In ma ka fita yanzu bazaka samu abun hawa ba." Takaici yasa Tahir ya kasa mgana Sadiq ya kallesa ya na Danne Dariya kafin yace"Allah yasa a mizani Tahir Yusuf Daura." Tahir ya kallesa cikin jin haushi takaici duk ya ishesa ya ma kasa mgana Saboda haushi. Sadiq ne fa sanda suna makaranta ya sha kwana da Dalibai in ba su da lafiya a Clinic din makaranta, ya na mamakin wata irin zuciyaa Allah ya ba ma Sadiq. Zuciyarsa ba irin ta kowa ba ne ya na da zuciyar Tausayi Imani da jinkai, zai yi maka wahala da Aljihunsa sannan ya taimake ka da karfinsa shi kam bazai iya wannan aikin ba. Bai kuma taba Fatan ya kwatanta ba ai aikin Allah suna da yawa. Shuru suka zauna kowa na saka abunda ya ke sakawa a ranshi Tahir ya gaji da latsa wayarsa bayansa ne har ya kage yasa ya kalli Sadiq kafin yace"To a ina zamu kwana? Sadiq bai kallesa ba yace"A bayana zaka kwana Tahir" Tahir ya hararesa kafin yace"Dole kace haka mana. Yanzu nufin ka anan kan wannan kujeran zamu kwana? Sadiq yace"Sai ka sauka kasa duka zabi ne" Tahir ya kule kamar ya yi kuka ya gyara zamansa kan kujeran yadda Wuyansa bazai samu matsala da Safe ba yace"Wlh baka kyautamin ba ina zaman zamana ka taso ni zan kwana cikin Takura. Wannan ko Sultana ce zata haihu sai haka" Sadiq na jinsa bai yi mgana ba sai da ya Murmusa. Tahir ya rigasa yin barci sai faman buge bugen sauro ya ke yi yana Tsaki shiko daman ba ya iya barci a asibiti ko ya ci wani abu ko ya sha wani abu. Ya dad'e bai yi barci ba har wajen uku na Dare sannan barci ya kwasheshi sama sai biyar da rabi ya farka shima Tafiya ya rika ji ashe Nurses suka fara Zirga zirga shi ya tada Tahir wanda ya tashi yana Faman soshe soshe da Taba wuya alamun dai kwanciyar ba ta yi masa Dad'i ba. Fuskar nan ta shi kamar Buredi saboda kumburi. Sadiq ya kallesa kafin yace"Mu tafi masallaci." Tahir ya mike yana fad'in"Wash baya na ya 'kage." Sadiq yace"Daman kai ai ba Namiji ba ne" Tahir yace"Dole kace haka tunda ka Halakani da kwanan asibiti. ni dai ina Fatan wannan zuciyar taimakon naka ya yi sanadiyar Shigan ka Aljanna Sadiq." Sadiq yace"Ameen tare da kai da ka ke taimakamin wajen kwanan asibiti." Ya fad'a ya na Dariya Tahir ya Tureshi yana Hararansa har zasu fita sai ya ja ya Tsaya ya juya ya na kallonta barci ta ke sosai abun mamaki a yadda ta kwanta ko motsawa ba ta yi ba ta na nan a yadda ta Dunkule. Tahir ya juya ya na kallon in da ya ke kallo kafin ya samu zarafin mgana yaga kawai ya fara tafiya har zuwa gabanta mamaki bai barsa ya yi mgana ya bi bayan shi yana Taba wuyansa da yaji ya sage. Sadiq kujeran ya duka ya na Dan Bubbugawa ya rasa da wani suna zai kirata Tunda bai san sunanta ba. Daman barcin nawa a cikin tsoro na ke yin shi mai cike da mafarkan Amma, shiyasa ina jin ana Buga gefena nayi zaraf na tashi. Kai na D'ago cikin Firgici Fes sai acikin idanuwansa na kallesa shima ya kalleni. Mikewa ya yi kafin yace"Armm ki tashi ki yi sallah." Kai na gyad'a masa kafin na Sauko da Siraran kafafuna a kasan Tayels din Asibitin kamar yadda na bi kafar tawa da kallo haka shima ya bi ta da kallo kafin yace" Kada ki yi yawo haka ba takalmi acikin asibiti" Cikin sanyin murya nace"ban zo da takalmin ba ne." Na fad'a daidai ina ta shi Tsaye kuguna ya amsa da bayana jikina ya yi tsami na cije baki ina kara Daidaita natsuwata tare da gyara Lullubin zanin jikina ko D'anwali ba bu a kaina Tarin suma na ko gyara babu shi ya saka kan nawa ya cika. Ba tare da Tunani ko shawara ba Sadiq ya cire takalmin kafarsa ya mika min ya na fadin"Zaki iya saka nawa? Yadda na dago kumbararun idanuwana na kallesa haka Tahir shima ya kallesa cikin mamaki da Al'ajabi lalle Sadiq kullum cikin yin abubuwan ban mamaki ya ke yi. Ni kuma na kasa mgana Alherin bawan Allah gareni mai girma na kalli Takalmin har ya ciresu ya Turomin gabana kafin nace"sun yi min yawa." Kai Tsaye yace"Ki saka hakanan in na fita sai na siya miki ko silifas ne.". Dago kaina nayi na kalleshi idanuwana cike da kwallah nace"Nagode sosai Allah ya jikan magabata." Bai amsa ba ni kuma sai na zura kafafuwana cikin takalmin ina Ruwan Sauro ko kwatan takalmin ban ci ba, Ina da Doguwar kafa sai dai ba kauri ne ina kallon kafata sai da dariya ta kamani cikin mirnishin nace"Kafata karamace ka ga ni ban ci ko Rabi ba." Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Nagani." Sai alokacin da na kara Dagowa na kula da Tahir ya kafeni da ido ya na kallona cikin mamaki na kallesa na kuma kallon Sadiq ganin inda na ke kallo yasa ya juya ya na fadin"Abokina ne Tahir." Sai na jinjina kai cikin sanyin murya nace"Ina ina kwana." Tahir ya amsa da Lafiya lau. Ya na kara kallona daga sama har kasa. Hasken Fatata sai ya fara kashe masa ido ballatana ga hasken fararan kwai sai Fuskar ta yi wani 'Dau da ita. Sadiq yace na samu wata Nurse in tambayeta in da zanyi sallah. Sai na amsa masa suka fice suka barni kamar yadda yace haka nayi d'in wata Nurse na tambaya ta nuna min bayi na shiga na kama ruwa na yo alwala. Duk da ba na sallah gwara na wanke jikina da kafafuwana da suka yi min tsami. Dawowa na yi na zauna in da na tashi Amma na ke son gani kamar sun sani sai ga shi wata nurse tazo tace na biyota da Sauri na tashi na bita zuwa wani Daki akwai gadaje uku ne adakin Guda d'aya akwai mutum Ashe Amma ce har an kawota dakin da zata Huta. Ba ta dai Tashi ba ta na barci na karisa kusa da ita ina kiran sunanta jikina ya na rawa Nurse din da ta kawoni tace"Alluran barci na tare da ita saboda ta samu hutu. Jininta ya yi kasa ne sannan akwai low sugar" Bayanin da mutumin nan ya yi min kenan au Abubakar Sadiq yace sunan sa daman ma su suna Abubakar masu Tsausayi ne da jinkai. Nurse tace min na zauna ammh kada na yi hayaniya ko Surutu. Na gyada mata kai har zata fita ta dawo ta na fad'in"Ina yayanki da kuka zo jiya tare? Kallonta na yi cikin mamaki kafin na Tuna wanda ta ke mgana da Sauri nace"Sun ta fi masallaci." Sai ta gyada kai ta fice. Farar kujeran da ke wajen na ja na zauna ina kallon Amma cikin Dare daya ta rame ta Fita Hayyacinta ruwan da aka saka mata na rika lekawa naga yana tafiya ita kuma sai barci ta ke yi cikin sukuni da salama. Shuru ba su dawo ba har gari ya waye sai na fara Tunanin ko sun tafi ne,sai chan sai ga su sun shigo again wannan Nurse din ta kawo su dakin. Suna shigowa na mike ina kallonsu yana rike da Leda baka a hannunsa shi abokin ya na daga baya kamar bai da son mutane. Ni ya mikama ledar na saka hannu na karb'a lokaci daya ya na fadin"Ashe sun bata daki" Kai na gyad'a masa batare da nayi mgana ba. Cikin natsuwarsa da lura ya na dashi Tun jiya yace"Waina ne sai ruwan zafi ki samu ki sha tun jiya baki ci wani abu ba." Kai na gyad'a masa kafin nace"Nagode sosai Allah ya saka da Alheri." Bai amsa ba sai ma ya karisa gaban Amma ya na kallonta kafin yace"Allah ya bata lafiya." Na amsa da Ameen. Tahir daga chan baya yace"Zamu makara fa Sadiq." Jin haka yasa ya kalleni sai kuma ya Duka ya cire silifas din kafarsa da ya siya a waje ya mikamin ya na fadin"Saka wannan shi zai fi yi miki daidai." Da Sauri na cire na kafata na saka Silifas din, lokaci daya ina fadin"Sannu da kokari nagode.". Ya jinjina kai kafin yace"Zamu tafi. In da wani abu ki kirani kin ji ko? Ina so nace masa ba ni da waya ballatana ma lambarsa. Ban samu damar mgana ba Abokinsa ya kara fad'in"Sadiq." Da Sauri ya juya ya na Fadi'n"Mu je Tahir sai mun dawo." Kokarin Biyosu na yi har wajen Dakin da Sauri ya juyo ya na fadin"Ki koma ciki." Ya fad'a ya na kallona sai na kasa masa gaddama cikin ladabi nace"To." Na juya na koma sai da yaga shigata sannan ya wuce ya bi bayan Tahir. Har suka samun abun hawa ba wanda ya yi mgana sai da suka kusa Sauka sannan Tahir yace"Wai yarinyar nan wani irin fari gareta? Albinion ce.? Sadiq ya yi kamar bai jisa ba sai da ya kara maimaitawa sannan yace"Ina zan sani Tahir. Me yasa baka tambayeta ba? Tahir ya tabe baki kafin yace"Ina ruwana da ita wai a ina ka had'u da su? Na ganta ne kamar buzayen nijar masu gudun hijara." Sadiq ya yi mirmishi kafin yace"Bansani ba fa Tahir nima jiya na fara ganinta." Daganan ya fara ba shi labarin yadda ya Had'u da Hasiiya jiya.. Ya karishe da fad'in"Ni ko sunanta ban sani ba jiya na fara ganinta." Tahir ya rike baki kafin yace"Sadiq anya ba gamo ka yi ba? Sadiq bai bashi amsa ba sai da suka Sauka sun fara takawa sannan Sadiq ya ba shi amsa da cewa"Nima na yi tunanin haka da farko, sai daga baya na gane mutane ne" Dariya suka saka gabadayansu. Tahir yace"Ni dai ina fatan kada garin wannan Shegen son taimakon nan naka watarana ka kai kanka da kanka a saida ka." Sadiq yace"To Ameen" yana mirmishi, Koda suka isa Dakin su Takwas saura a gurguje Tahir ya kunna musu gas ya dora Ruwan zafi, Shi kuma Sadiq ya saka a kettlo tunda akwai wutar nepa. Saboda suna Sauri Tea suka sha Tahir sai Kunkunin ya ke yi Sadiq ya ja masa kwanan wahala ga shi yanzu maimakon ya huta zai kara fita kuma. Sadiq dai bai tankasa ba Tahir ya rigasa fita shi ne karshe ya kulle dakin na su saboda ya makara yasa ya hau mashin Saboda ya isa akan Lokaci. Ko achan wajen aiki yarinyar na yawon fad'o masa arai. Sai biyu ya taso daga wajen da ya ke Hidimar kasa. Saboda yanayin da ya kwana aciki yasa bai tuna da Danwake ba. Ko da ya dawo ya iske Tahir na ta sharan barci zafi ya ke ji yasa ya Dibi Ruwan sanyi ya yi wanka ya Sauya kaya ya iske Tahir ya Dafa Farar shinkafa shi Tahir da kifin gwangwani yaci ya rasa me ya ke had'a Tahir da cin kifi. Shi kuma sai ya Dumama miyar da Umma ta yi musu akwai saura ya ci da Naman sa. Sai da ya koshi sannan shima ya bi lafiyan gado ya kwanta sai la'asar ya tashi ya Bugi Tahir ya na fad'in"Sai ka tashi an yi la'asar." Tahir yace"ni ka kyaleni bayan duk kai ka kai ni in da nagaji." Sadiq bai kulasa ba ya tashi ya fita waje ya kama ruwa ya yi alwala ya tafi masallaci Tahir sai ana Tahiyar karshe ya shigo masallacin Da suka idar shi ya tsaya addu''a Har Tahir ya gama na shi Sallar suka fita tare. A hanya Sadiq ya kalli Tahir ya na Fadin'"Sai yanzu na tuna. Dazu nace ma yarinyar nan ta kirani in suna bukatar wani abu ammh Kasan me? Tahir yace"Sai ka Fad'a.? Sadiq yace"Ban ko karbi lambar wayarta ba. Itama ban bata nawa ba." Tahir ya kallesa kafin yace"Allah yasa ma ta na da wayar." Sai Sadiq ya yi shuru kafin yace"Kuma fa domin ni dai ban ganta da waya ba. Ko kuma zai iya yuyuwa rudewa yasa ba ta zo da ita ba." Tahir ya jisa ammh bai tankasa ba. Suna komawa yaga Sadiq na shiri har da saka manya kaya cikin mamaki yace"Ba dai asibitin zaka koma ba? Sadiq yace"Eh ai tare zamu koma? Da Sauri Tahir yace"Wlh tallahi ba in da zani. Kai dai da ka siyan ma kanka Allah ya kiyaye Hanya." Sadiq yace"Ameen addu'ar da ka yi ma ta wadatar." Shigan manyan mutane ya yi har da Hulansa kube mai kyau zanen aikin jikin Shaddarsa mai ruwan madara ya yi ma Tahir sallama ya fice. A hanya ya kira Abba ya ce ya na son kudi Abba yace to zai turo masa. Kai Tsaye yace"Abba wasu bayin Allah ne ke bukatar taimako na lafiya shi ne na ke son na taimaka musu." Abba yace"Shikenan Magajin gida a taimaka musu." Sadiq yace"Nagode Abba. Allah ya kara girma ina Innani.? Abba yace"Sun tafi Shinkafi ita da Sultana tun jiya." Sadiq yace"Abba Innani fa ba ta da wani karfin jiki ga Tsufa Tsakani ga Allah tafiye tafiye ai ba nata ba ne." Abba yace"Kasan Innani da Kafiya. Ta kafe kuma kasan ko nace ta zauna bazata zauna ba. Da ma kai ka yi mata mgana to da zata ji maganarka." Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Allah ya dawo da su lafiya." Abba yace Ameen tambayan Su Umma ya yi da su Salima sun d'an taba hira da Abba sannan suka yi sallama. Ya isa abitin Biyar Daidai, Shi bai yi tunanin siyan komai ba, kai tsayensa ya shiga har Dakin sai dai abun da ya basa mamaki ta nan zaune ita kadai kamar yadda ya barta. Bata ma san ya shigo ba sai da ya yi sallama sannan taji shigowarsa. Zumbur na mike ina kallonsa shima ni ya ke kallo sai naji nauyi na dukar da kaina ina Fadin"Ina yi ni." Cikin Natsuwarsa ya amsa da Lafiya lau ya mai jiki? Na amsa da sauki cikin kulawa ya karisa gaban gadon Amma kafin yace"ba ta tashi ba ne? Da sauri na ce"Ta tashi dazu, sai dai kuma ba dadewa ta koma." Kai tsayen shima yace"Bata ci wani abu ba kenan? Da kai na amsa masa kafin nace"Ruwa kawai tace na bata tasha sai kuma ta koma." Jinjina kai ya yi lokaci daya ya na harde hannayensa saman kirjinsa. Ya na kuma bin nazarin dakin da kallo daga alamun dai ba wanda yazo. Ga sauran wainar da ya siyo mata da Safe nan ta rage. Sai ruwa wanda ya ke tunanin kila siya tayi tunda shi dai bai siyo musu har da ruwa ba. Cikin mamaki yace"likita ya zo ne? Kai Tsaye nace"Eh ya zo ya dubata ya tambayeka nace ka je ka dawo. Sai ya ba ni wata takarda yace na baka." Na fad'a ina dauko masa Takardan saman dirowan da ke wajen na mika masa. Karb'a ya yi ya duba magunguna ne shiyasa kawai ya fice bayan yace yana zuwa Phamarcy yaje ya siyo mgangunan Atm dinsa ya ba da aka cire akwai sauran kudi kafin Abba ya Turo masa daganan ya fita waje ya siyo katan din ruwa da maltina ya had'o mata da kayan marmari sannan ya Dawo daki. Yana shigowa na taso na karbi' kayan hannun nasa ina masa sannu. Ledan mganin ya sakarmin shi kuma sauran ya karisa ya sauke da Hannunsa. Sannan ya juyo ya na fadin"Mgangunanta ne in likitan yazo ki nuna masa." Sai na gyad'a kai kaina a kasa ina fadin"Allah ya saka da alheri." Ya amsa da Ameen. Gefe ya koma ya jingina da Bango ni kuma sai na koma na zauna Shuru na wani Lokaci kafin yace"ba ki kira gidan ku ba ne? Kaina na kasa nace"Ba ni da waya ne shiyasa." Bai yi mamaki ba illah wayarsa da ya fito da shi ya na fadin"Ga wayata in dai kin haddace lambar." Da Sauri nace"Eh na haddace." Mikewa na karisa na karb'a ina fadin nagode ya amsa min da gyad'a kansa. Gefe na koma na saka lambar Adda Fati na kirata har ta katse bata Dauka ba. Sai na kara kira sannan ta Dauka ina jin Hayaniya ta cikin wayar kai Tsaye nace"Adda ni ce Hasiya." Dagachan bangaran tace"Hasiya. Hasiya kuna ina ne? Ga mu nan hankula tashe tun safe Maman Boy ta kirani tace Amma ba lafiya kun tafi asibiti ga shi bamu san asibitin da kuke ba kina ina ne yanzu!? Ina Amman ta ke? Cikin Sanyin murya nace"Adda muna asibiti tun jiya. Amma kuma an bata gado." Da Sauri Adda Fati tace"Kuna wani asibiti ne? Ga ni ga Inna Talatu ga Ramatu zamu taho." Kallonsa na yi shi kuma hankalinsa na kan tagar dakin. Tunani sunan da yaji ta ambata ya ke yi. "Hasiya.? Hasiya suna ne? Sai kuma yaji tana fad'in bata san sunan asibitin ba. Sai ya kalleta nima daidai na juya ina kallomsa sai ya lumshe min ido kafin ya Bude kai Tsaye yace"Ba ni wayar na fad'a mata." Ba musu na mikamasa baayan na ce ma Adda ga shi za'ayi mata kwantance. Karban wayan ya yi, bayan ya yi sallama sun gaisa da Adda sannan ya Fad'a mata sunan asibitin sannan suka yi sallama. Tun bayan gama wayar sai Dakin ya Dauki shuru sai da aka kirasa a waya ya fita ya jima bai dawo ba. Sai ga shi an bude kofa ina juyowa naga Adda Fati kan gaba sai Ramatu sai Inna Talatu sai maman boy da maman Salihi da kaltume. Ni ba ta su na ke ba mikewa na yi ina musu maraba. Ina jin Maman boy na fadin'Sannu Hasiya." Takaici yasa ban amsa ba sun san da Sannu ne ina neman taimakon su ba su taimakamin ba. Duka suna Tsaye gaban gadon Amma na ce ma Adda"Wa ya nuna muku dakin? Adda Fati tace"da wayar da kika kirani, na kira sai ga shi wani Saurayi ya fito ya shigo damu har nan likita ne? Sai na girgiza kai kafin nace"Shi ne wanda ya taimakamin aka kawo Amma asibiti. Adda tare muka kwana sai da safe ya tafi dazu nan ya dawo shi ya kashe komai da a ke bukata." Inna Talatu tace"Allah Sarki Allah ya biyasa." Su Adda suka amsa da Ameen su Maman boy suka fara daidaiciyar mgana wai ba su ji bugun kofata ba sai daga baya. Ramatu ko kusa da ni ta dawo ta na fadin"Hasiya kin ci abinci!? Na gyada kai kafin nace"Ya siyamin waina yanzu kuma ya kawo wad'anan kaya da mgangunan Amma." Ramatu tace"Angode masa. na zo da abinci fulas ne bamu yi tunanin Daukowa ba." Adda tace"Sai na koma na Dauko ba matsala." Inna Talatu ta kalleni tace"ba ta farka ba ne.? Kai tsaye nace"Ta farka ta sha ruwa ta koma sun ce jininta ne ya yi kasa." Suka jinjina kai suna mata fatan samun lafiya. Ba mu ji turo kofarsa ba sai jin sallamarsa muka yi. Gabadaya mu ka juya muna kallonsa. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj *15* Cikin takun natsuwarsa ya karisa shigowa cikin D'akin. Yadda muka zuba masa ido ne yasa ya da'n dukar da kansa ya na fad'in"Sannun ku. Ya mai jikin? Sai suka amsa gabadaya da sauki kafin su shiga gaishe shi ya amsa cikin sakewa Adda da Inna talatu ne suka fara masa godiya. Kansa na kasa yace"Bakomai.." Ni ya kallah nima daidai lokacin na Dago ina kallonsa da Sauri nace"Uhm wannan yayata ce Adda Fati. Sauran yan gidanmu ce wannan kuma kawata ce." Na fad'a ina nuna Masa Ramatu kallonta ya yi lokaci d'aya ya na fadin"Sannun ku zuwa." Suka amsa masa sai dakin ya dauki Shuru Adda Fati sai ta katse shurun da Fad'in"A nan garin ka ke? Kai tsaye ya kalleta kafin yace"A'a." Daga haka bai kara cewa komai ba. Inna talatu tace"Angode sosai Allah ya saka maka da alheri." Bai amsa ba kansa na kasa sai dai ya na ta faman mirmishi. Karisawa ya yi ya duba Amma na d'an lokaci kafin yace min zai tafi. Adda ta fara jero masa addu'o'i ita da Inna Talatu. Baya amsawa sai dai yace bakomai kawai ammh da Inna Talatu tace"Allah ya jikan magabata. In iyayenka na raye Allah yasa su gama lafiya. In kuma ba sa raye Allah ya ba su Aljannah." Ya na gabda zai fita ya juyo cikin mirmishi sannan ya amsa da"Ameen Ameen Nagode." Daga haka ya fice Ramatu ta zungureni ta na fad'in"Ki raka shi mana" Kallonta na yi sai ta gyad'a min kai daidai Lokacin da Adda ke kara fad'in"Hasiya bi shi mana. Ki kara masa godiya." Maman boy da gulma tace"Wlh kuma daga gani asibitin akwai cacan kudi. Tunda ba ta gwamnati ba ne" Jin haka yasa na bisa da Sauri har ya kai Haraban asibitin ya na tafiya. Sai na kasa kiran sunansa illah sauri sauri da na rika yi har na cimmasa. Tsayawa ya yi ya na kallona kafin yace" Me yasa ki ka fito? Kaina na kasa nace"Na zo ne na kara maka godiya." Mirmishi ya yi kafin yace"Godiyar nan ta isa hakanan HASIYA.." Kallonsa na yi cikin mamakin kiran sunana da ya yi sai ya ware min ido ya na fad'in"Ko ba sunan ki kenan ba? Kai na gyad'a masa cikin kunya alamun hakane cikin yar mamaki ya kalleni ya na fad'in"Hasiya sunane? Sunan ba Asiya ba ne? Kai na girgiza masa kafin nace"Hasiya ne sunan." Shima cikin girgizamin kai yace"To ko dai sunan Fulani ne? Kallonsa na yi kai tsaye kamar yadda ya ke kallona. Ya ga mahaifiyarmu da zanen Fulani a gefen bakinta, Da kuma gefe da gefen fuskarta. Sannan yaga Adda Fati da nace yayata ce itama sai yaga yanayinta kamar na Fulani ko buzaye so ya ke ya tabbatar. Na rasa me zan ce masa ne yasa nace"Amma ce bafullatana. Baba kuma bazazzagi ne, Sunan Hasiya kuma kanwar Baba ce da ta rasu, sai ya maida min sunanta." Kai tsaye yace"Kenan ki na jin Fullanci.? Kai Tsaye nace"ba na ji fa sai abunda ba'a rasa ba." Mirmishi ya yi kafin yace"Na sha kina ji ne nace ki koyamin. ni ban iya kowani yare ba." Baki na bude kafin nace"Wlh ni ma ban iya ba." Yadda na yi saurin rantsewa yasa ya yi mirmishi kafin yace"Ban ce ki rantse ba. Yanzu ammh gida zaki koma ki yi wanka ki huta ko? Ni ban yi wannan Tunanin ba sai da ya fad'a sai na kara bin kaina da kallo yarkace yarkace kamar yar gudun Hijira. Sai naji kunya na dukar da kaina ina wasa da gefen zanin Amma da na yi Lullubi da shi. Shi ko bai damu ba kai tsaye yace"Gaskiya ya kamata ki je gida ki Huta." Da toh na amsa shi har mun yi sallama akan gobe zai dawo ya kara Duba Amma da jiki. Na juya zan koma cikin asibitin sai ya kawai naji muryansa cikin kaushi ya kira sunana. "Hasiya.." Da sauri na juyo ina fad'in"Na'am.." Ya na daga in da ya ke yace"Ki kwantar da Hankali zata warke kin ji ko? Sai na gyada masa kai. Mirmishi ya yi ya juya ya fara tafiya sai ga shi na Tsaya har sai da ya bace ma ganina. Mirmishi na yi acikin raina nace"Daman ma su suna Abubakar suna da kirki da jin kai." Cikin asibitin na koma na iske duk sun fito waje Adda Fati ne ke tare da Amma aciki sai na karisa kusa da Ramatu na zauna muka kara gaisawa. Nura na tambaya tace min da Safen nan ya wuce na gyada kai ina masa Fatan isa lafiya. Noor ta ke ba ma Nono sai da ta gama na karbeta ina yi mata wasa. kallona ta yi kafin tace"Ya jikin ki ke ma? Kai tsaye nace"Ni ai na warware." Da sauri tace"Sai kumburin Fusakarki bai sabe ba." A hankali nace"Zai washe shima." Ramatu tace"Ki ci abinci ga shi nan na Fito miki da shi." Na amsa mata da toh. Tazo da filet da cokali sai na Dibi abincin naci Faten wake ne da kifi kadan ma naci saboda cikina ba ya min dad'i. Ramatu tace"Yakamata ki je gida ki yi wanka ki sauya kayan jikin ki." Kai Tsaye nace"Shima haka ya ce." Ramatu tace"Shi wa? Cikin sigar mamaki. Mirmishi na yi kafin nace "ABUBAKAR SADIQ.." daga kasan raina na fad'i sunan saboda Muhimmanci da sunan ke da shi a Rayuwata. Ramatu tace"Au Abubakar Sadiq sunansa? Ma sha Allah wai a ina kuka had'u? Kallonta na yi kafin na fara bata labarin hadu'warmu na karishe da fad'in"Saboda Rudewa haka na zo asibitin nan ba takalmi. Bawan Allah nan takalminsa ya bani na saka sai da ya fita ya siyomin wannan sannan ya karb'i na shi. Ramatu gaskiya ya na da kirki tare da abokinshi suka kwana a asibitin nan da Amma fa." Ramatu tace"Gaskiya ya na da kirki. Allah ya ba shi lada." Na amsa da Ameen. Mun cigaba da Hiran kirkin Sadiq. Kafin Adda ta fito tace Amma ta farka gabdaya muka Dumguma cikin dakin. Amma ta bude ido tas ta na kallon kowa ta na gane kowa duk wanda ya gaisheta sai ta amsa sannan ta ambaci sunansa. Ina zuwa kusa da ita na riko hannunta ina Fad'in"Amma kin bani Tsoro na zata tafiya za ki yi ki barni." Amma ta yi mirmishi cikin muryan ciwo tace"ke ce ki ka ba ni Tsoro, Ba na so ki yi nesa da ni Hasiya." Kai na gyad'a mata ina fad'in"In sha Allahu ba in da zan je Amma. Ina nan tare da ke sai mutuwa." Amma na dariyan jin dadi murya a sanyaye tace"Sai aure dai ko Hasiya.? Sai naji kunya na dukar da kai Inna Talati ke fad'in"In sha Allahu sai aure zai Rabaku." Gabadaya Murna ta cikani ganin Amma ta samu lafiya. Cikin muryan ciwo Amma tace"Wa ya kawo ni asibiti? Muka kalli juna ni da Ramatu kafin ma nayi magana Adda tace"Wani bawan Allah ne Amma. Yanzu ya fita ba da jimawa ba." Amma ta jinjina kai kafin tace"Allah ya biyasa da Aljannah." Muka amsa da Ameen Ameen. Adda Fati na fad'ama zan je gida na Dawo tace ya kamata kan naje na gyara jikina. Nan na bar Adda Fati da Ramatu tare muka fita da Inna Talatu da su Maman Salihi Inna talatu ta samu abun hawan zuwa sabon gari. Mu kuma muka samu na anguwan mu. Suna ta min daidaiciyar mgana ko kallonsu ban yi su kan su susan ba su kyauta ba kowa ya yi nagari ai ya sani. Ina komawa gida na iske dakin sakayashi kawai akayi, Gawayi na fara Hurawa na saka ruwan zafi sannan na gyara dakin na Share. Matan gidanmu sai fad'a min su ke yi an yi ta zuwa neman Danwake babu. Ya ke kawai na yi musu ana ta rai wa ke ta wani Danwake. Sai da na yi wanka na cire kayan jikina na saka wata atamfa Riga da Sikat na siya kamu na Dama na sha, sannan na Dorama Amma ajug zan kai mata asibiti na kuma Daukan mata zannuwa da Hijabi nima na Dauki kaya kala d'aya da Hijabi sai abunda zan gyara jikina Tunda ba na Sallah. Sai yammah na Rufe Dakin Amma da makulli na koma asibiti. Adda kad'ai na iske Ramatu ta tafi, itama ina Dawowa ba Dadewa ta tafi akan sai gobe zata dawo. Ni na kwana da Amma wacce ta ji sauki sosai likita ya zo ya dubata sannan Nurse suna zuwa bata mgani da saka mata ruwa. Washegari na yi ma Amma wanka Tunda ga bayi sannan akwai Ruwa. Da ya ke na Tsaftace makewayin yasa nima na shiga na yi wanka na gyara jikina. Har rana ba wanda ya zo. na zo da kudi a hannuna na fita waje na siyo ruwan zafi da kayan tea na zo muka had'a tea ni da Amma muka sha ni kuma sai na had'a da waina. Nazo da magunguna nima na balla na sha Amma ta na yawan yin barci Saboda inaga allurai da magunguna da suke bata tunda sun ce Hutu ta ke Bukata. Wani abun mamaki da na ji karan Bude kofa sai na juyo da Sauri na zata ko Shine sai naga bashi ba ne. Har Adda Fati ta zo da rana, zuwa la'asar sai ga Adda Rukayya da Habiba sai bani Hakuri ta ke yi da abunda ya Faru ta na gayamana ta yi ma Babansu Amna Hauka da yasa Dole sai da yaje ya ja ma yan'uwansa kunne. Ban ce komai ba sai da ta Dafani ta na Fad'in"Ki yi hakuri don Allah Hasiya." Sai na girgiza kai kafin nace"Bakomai Adda." Amma na barci sai daga baya ta tashi. Maltina na bata tasha na rakata bayi tunda sun cire mata karin ruwa alwala ta Dauro. Tazo ta yi sallolinta daga zaune daman da Safe haka ta yi ammh Alhamdulillah jiki da sauki. Adda Fati ne tace"Amma ko na kira Adda na fad'a mata? Amma tace''A'a kada ki tada mata Hankali kyaleta kawai." Daman nasan haka Amma zata ce, ko ciwo ta ke yi bata son a kira mata Adda kada wai a tada mata Hankali. Adda Fati da Adda Rukayya tare suka tafi sai aka bar min Habiba tare da ni. Ba matsalan abinci Adda Fati ta zo min da Fanten doya da allayahu. Har na cire rai da zuwansa sai ga shi da Daddare bayan isha'i sun zo da abokinsa mara sakewa da Mutane sai akaci sa'a Amma na farke ba ta koma barcinta na fama. Sanda suka shigo ina bayi sai Habiba kadai suka iske kallon rashin sani Sadiq ya yi mata. Ita ma haka ta yi masa sai dai ya ga kamarta da Amma da Adda Fati su suna da jan fata ba irin Fari na garesu ba. Habiba ta gaishesu suka amsa suna tambaya ya mai jiki? Habiba tace ta samu sauki gata nan ma ba ta koma barcin ba. Tahir dai na daga baya Sadiq ne ya karisa gaban gadon Amma. Sanye ya ke da kananun kaya Riga da wando. Rigar mai kalan Ruwan kasa da layi layi ta na da Dogon Hannu. Wandon kuma mai ruwan kasa ne kafarsa cikin Rufaffen takalmi. Amma tunda ta gansa jikinta ya bata Bawan nan ne Allah da ya kawota asibiti. Daman tun dazu ta ke ma Hasiya mgana sai tace mata bai zo ba. Yana gaisheta ta amsa cikin Sakewa lokaci d'aya tace"Abubakar ne? Cikin mamaki ya ce"Eh ni ne Mama." Amma ta muskuta ta na son mikewa da Sauri ya kamata ya na kara mata Filo ta baya. Amma ta kallesa haka kurum taji Saurayin ya shiga ranta. Cikin Mirmishi da muryan ciwo tace"Nagode Allah ya yi maka albarka." Ya amsa da Ameen sai lokacin Tahir ya kariso ya na mata sannu ta amsa masa shima cikin sakewa. Sadiq yace"Abokina ne." Amma ta jinjina kai kafin tace"Allah Sarki nagode sosai Hasiya ta ba ni labarin irin taimakon da kayi mana. Allah ya ba ka lada. Allah ya biya ka da gidan Aljannah" Da Ameen Ameen ya ke ta amsawa. Tahir ko na gefe ya na bin ko'ina da kallo fuskar nan dihim. Ya rasa dalilin Sadiq na matsa masa sai ya rakosa asibitin nan. Ka taimaki mutane to ba sai ka rabu da su ba ina laifi? Ammh lamarin Sadiq sai Allah kawai da ya Hallicesa game da maida lalura da Damuwan Mutane na shi. Amma ta kalli Habiba ta na fad'in"Habi Hasiyan ba ta fito ba ne? Habiba tace"Ba ta fito ba Amma." Sai Amma ta kallesu ta na Fad'in"Hasiyan ta shiga makewayi ne." Sadiq ne ya gyad'a mata kai, Suna Tsaye dai daga gefe ledan da Sadiq ya shigo da ita a hannun ya mikama Habiba ta karb'a ta na fadin"Angode." Sai ta duba abunda ke ciki Taga Tsire ne mai yawa da Sauri tace"Amma nama ne." Ta fad'a cikin jin dadi. Daman Habi da son Nama kamar wata kura. Amma ta yi mirmishi kafin tace"Allah ya ba da Lada. Allah ya yi shi albarka" Dukkansu ba su amsa ba Tahir sai danna wayarsa ya ke yi shi kuma Sadiq ya harde hannayensa saman Kirjinsa. Kai tsaye na fito daga makewayin. Tabbas na ji mganganu ammh ban Dauka shi ba ne. Na zata nurses ne ko Likita sai da na fito dagani sai Doguwar rigar jikina da Dankwali. Kuma ta facing dinsa na fito daidai ya Dago nima na Dago mu ka had'a ido. Wlh sai na ji kunya. na dukar da kaina kafafunawa na rawa na fara takowa cikin Dakin. Amma ta tareni da Fadi'n "Sun zo tun dazu Hasiya." Tahir a ransa ya maimaita Sunan Hasiya a ranshi. Tabe baki ya yi yace daman ai daga ganinsu kauyawa ne. Kuma ta dace da sunan nata Hasiya. Ban samu natsuwa ba sai da na Rarumi Hijabina na zura sannan na gaishesu Abubakar ne kad'ai ya amsa cikin Sakewa Tahir daga lafiya shikenan bai kara ba. Habiba ta nuna min Naman da suka zo da shi,godiya na yi masa bai amsa ni ba illah cewa da ya yi"Kuka ya kare ko? Tunda naga jikin Maama ya yi Sauki ko? Ban ce komai ba sai dai na Rufe Fuskata da Tafin hannayena. Amma ce ta amsashi da cewa"Hasiya ai sarkin kuka ce. Ita dai in dai ta ganni ina ciwo bata kara sukuni sai ta ganni na warke tukunnah." Sadiq yace"Allah sarki. To ta kwantar da Hankalinta kin samu lafiya." Amma tace"Ah Alhamdulillah. Jikina ne kawai ba karfi." Sadiq yace"Shima a hankali zaki ji ki warware." Amma tace"In sha Allahu." Shuru na wani lokaci ba wanda ya yi mgana Tahir na kuncin ya gaji da Tsayuwa Sadiq kuma na Tunanin Jikin Hasiya da yanayinta ya boye Shekarunta. In dai ya canka daidai Yarinyar nan kanwarta ce kenan ta girmi Sultana sai dai kila sa'ar Salima. Amma ce ta katse masa da Tunani da Fad'in"A nan garin ku ke ne? Sadiq yace"A'a Mama karatu mu ke yi anan d'in." Amma tace"Allah Sarki Allah ya taimaka." Sadiq ya amsa mata. AMMA bata gaji ba ta kara kallonsu ta na Fad'in"To a wani gari ku ke ne? Tahir ya kallesa shima ya kallesa ganin Haka yasa Amma tace"ku yi hakuri ina son sani ne saboda taimakon da ka yi mana." Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Ni d'an kauyen Shinkafi ne da ke zamfara. Abokina kuma mutumin Daura ne." Tahir ya kura masa ido ya na mamakin meyasa Sadiq ke son boye kansa. Bai gama mamaki ba yaji Amma na tambayan akwai iyaye ko babu? Bude ido ya yi da hanci ya na kallon Sadiq sanda yaji ya na fad'in"Ba bu Mama a kauyen mu na taso hannun Dangin mahaifina" Amma cikin Tausayawa tace"Allah sarki.Allah ya jikansu da Rahma kada ka damu ni ka Dauke ni a matsayin uwa kaji ko? Sadiq ya jinjina kai ya na fadin"Nagode Mama." Tahir mamaki bai barsa ya yi mgana ba. Yana jin Amma na ta yi ma Sadiq tambayoyi yana amsa mata da cewa sun gama karatu suna Hidimar kasa ne a zariya d'in. Suna cikin mganar ne Likita ya shigo ya duba Amma ya na fad'ama Sadiq bayan sun gaisa cewa Amma zata kai sati anan suna Bukatar ta kara Hutawa ya ce bakomai. Bai jima ba ya fita bayan ya yi ma Amma yan Tambayoyi. Bayan fitan likita ba su jima ba suka yi mana Sallama suka fita Amma na ta saka albarka da addu'o'i. Har waje na rakasu Tahir haraban Asibitin ys fita ya na jiran Sadiq da Tarin mamakin da ke ransa. Nima dai godiyar na sake masa bai amsa ba kai tsaye yace"Kannen ki nawa ne? Cikin mamaki nace"Ni? Sai ya gyad'amin kai cikin natsuwa nace"kanwata d'aya ce Habiba wacce kuka gani. Mu hud'u Amma ta Haifa Adda Rukayya baka ganta ba sai Adda Fati wacce ka gani jiya sai ni sai Habiba." Kai ya jinjina kafin yace"Ashe ba yarinya bace. Da kallon yar ficika na ke yi miki." Maganarsa sai ta sakani Dariya kafata ya bi da kallo. Nima sai na bi in da ya ke kallo sanye na ke flat shoe baki na Habiba ne ma ya yi min yawa Tunda Habiba ta fi ni cikar tsokar kafa. Kai tsaye yace"Wannan takalmin ba naki ba ne ko?? Ina yar dariya nace"eh na Habiba ne. Ammh ya aka yi ka gane ba nawa ba ne? Yana mirmishi yace"Saboda kafarki ba ta boye takalmin ki." Dariya na yi har hakora suka bayyana waje. Shima sai naga ya yi dariyan sai na shagala da kallonsa ganin yadda ya yi kyau kamar wata Daran goma sha Hud'u. Cewa ya yi na koma ciki bari ya tafi muka yi sallama sai da na juya yaga wucewa sannan shima ya tafi. Ko da yaje Tahir ya cika saura kadan ya fashe ya na cewa"mu je.' Tahir ya balla masa Harara ya na Fad'in"Wai son zabiyar yarinyar nan ka ke yi ne Sadiq? Cikin mamaki Sadiq yace"Sunanta Hasiya ba Zabiya ba." Tahir ya yi dariya kafin yace"Wai Hasiya. Juz imanging fa, Sadiq ka fara son wannan yarinyar ne? Sadiq ya yi gaba ya na fadin"Wani irin so kuma? Tahir ka rika saka Tunani in zaka yi mgana pls" Tahir ya bi bayanshi ya na fadi'n"To na rasa gane maka. Yadda ka rasa sukuni Saboda Mutanen nan da yadda ka ke washe ma yarinyar nan baki Sadiq Sannan har da karyan su Umma da Abba sun rasu fa! Duk saboda menene ka ke aikata haka? Kamar bazai yi mgana ba sai dai ya juya ya na kallon Tahir suka Tsaya a bakin asibiti suna kallon juna kafin yace"Tahir kasan taimako dabi'ata ce ba su ne na farko ba. kuma baza su zama na karshe ba. Baka ga su na bukatar neman taimako ba ne?sannan da ka ke mganar so? Son wa? Wannan yarinyar ne zan so? Bata cikin Tsarin matan da ni ke so Tahir." Tahir yace"Na ji ba sonta ka ke yi ba. Taimako ne. To kashe su Umma da kayi da ran su ba da karyan asalin da ka yi musu fa? Sadiq yace"Ba karya na yi ba ni asalina dan Shinkafi ne tunda nan ne Tushena. Su Umma kuma ban san Dalili ba kai ma kasan ba kowa ya ke sanin hakikanin waye ni ba." Daga haka ya wuce Tahir ya rike kugu ya na bin bayansa da kallo cikin mamaki. Haka kurun ya ke ji aransa Wani abu zai faru wanda ba Daidai ne ba shi fa mutanen ba su yi masa ba. Wasu kamar yan gudun Hijira ita kuma yarinya farinta ne baya so kamar wata Zabiya. Bayansa ya bi ammh ba su kara tada mganar ba. Mashin suka samu zuwa gida kuma har suka kwanta Tahir bai kara yi ma Sadiq mgana ba sai dai ya na kallonsa ya na nazarinsa. Yana fatan Allah yasa ba garin taimako Sadiq zai jajbo ma kansa Wahala ba. Washegari kafin Sadiq ya tafi wajen aiki yaji yana jin cin Danwake kamar yadda aka saba da kansa yaje da karamar kularsa. Da datti ya ci karo tun kafin ya kirasa yazo da Sauri ya na Fad'in"Danwake zaka siya? Ya gyada masa kai da Sauri Datti yace"Ba'a yi mai Danwaken mamanta ba ta da lafiya. Suna asibiti har yanzu ba su dawo ba." Shuru ya yi ya na nazari kafin ya yi mirmishi ya Dafa kan Datti naira Dari ya zaro daga Aljihunsa ya bashi ya tafi ya na tsallen Murna. Bai damu ba har ya juya zai tafi sai mganar yaron ta kara Dawo masa sai ya tsaya bayan ya juyo ya na kare ma gidan kallo kamar gidan kamar kuma ba nan ba ne.! Domin kore mamaki ya ga Salihi na gara taya zai shiga gidan sai ya kwala masa kira sannan ya fitosa da Hannunsa. Saninsa ya na ba da kudi yasa Salihi ya zo da Sauri bakinsa washe yace"Ba'a Danwake yau." Da Sauri yace"Na sani. Y ya sunan mai yin danwaken? Salihi yace"Adda Hasiya." Sadiq ya maimaita"Hasiya." Salihi yace"Eh mamanta ba ta da lafiya suna asibitin in ji mamanmu." Sadiq ya cika da mamaki sai dai bai bari Salihi ya tafi haka ba shima darin ya ba shi ya tafi ya na ta murna. Sadiq na tafiya a hanya ya na Mirmishi har da Dariya shi kad'ai. "Hasiya mai danwake." Tabdijam. Daga alamunsu daman ba su da Hali Talakawa ne. Ammh ina mahaifin su? Me ya asalin su? Duk wad'anan amasoshin ba shi da mai amsa masa shi. Ammh har ya koma dakin su yana Dariyan sunan Hasiya da ya maida mata da Hasiya mai Danwake. ******* Sai da Amma tayi sati Cur sannan aka sallameta Lokacin ta samu sauki sosai ta na zuwa bayi da kanta. Sannan ta sallolinta a Tsaye ta samu karfin jiki. Ba bu abunda zan ce ma Abubakar sai Godiya. Domin komai na laluran asibitin nan shi ya yi mana shi hatta kudin gado da sauran magungunan da aka sake rubutama Amma shi ya siya. Sannan ya samo mana adaidaita ta Dauke damu da kayanmu har gida shi kuma yabi bayanmu a kan Babur. Da farko ya ki shiga ciki sai da na matsa sannan ya shiga har daki ya Duka ya kara gaida Amma. Amma ta rike hannuwansa ta na fadin"D'an nan ina ka samu kudade da ka yi ta mana wannan Hidimar?. Kai tsaye yace"Amma ba na gaya miki ina Hidimar kasa ba? To ai gwammati na ba mu wasu kudi duk karshen wata." Ina zai gayamusu Abba ne komai na shi tunda ya riga yace ba shi da iyaye shi maraya ne. Amma ta shiga kwarara add'au tana ma iyayensa da suka rasu addu'a da samun salama. Har sai da ta yi hawaye ganin haka yasa ya ce"Amma bakomai. Ki daina kuka." Dole Amma ta yi shuru ta na ta saka masa albarka. Da zai tafi ni na rakasa ina ganin Matan gidanmu kallo kamar zasu fad'i. Sai da muka fito ya kalleni ya na Fad'in"Gidan ku kuna da yawa haka ne? Kai tsaye nace"Gidan haya ne .mata goma sha uku ne aciki, Dogon gida kenan." Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Dogon gida kad'ai ake kiransa? Na gyada masa kai ina fad'in"Eh." Kai Tsaye ya na kallo na yace"ba'a cewa gidan su Hasiya mai Danwake." Zaro ido na yi ina kallonsa shi kuma yana Dariya yace"Amma ta ji sauki a cigaba da yi ma na Danwaken mu" Cikin mamaki nace"Ya aka yi kasan ina Danwake? Kai Tsaye yace"Ina siya ne." Cikin kura masa ido nace"Ka na siya? Kai ya gyad'amin ya na mirmishi. Kamar an tunamin na nuna sa ya na Fad'in"Kai ne daman me zuwa da kula da Dubu daya har ka ke barin min chanji." Bai amsani ba sai da ya yi mirmishi da yasa na gane shi ne. Kallonsa na ke yi nima cikin jin dad'in kafin nace"ka ci sunan ka. Masu suna Abubakar Sadiq ma su tausayi ne da yakana ma su jinkai ne da Taimako." Na fad'a kai na Tsaye ina kallonsa Idanuwana suna faman cika da kwallah da tuna wani bangare na Rayuwata. Shi kuma sai ya tsaya ya na mamakin mganata cikin sigar tambaya yace"Kin san wani mai irin sunana ne? Kai na gyad'a masa ina fadin"Sosai ma kuwa. Shima kamar ka ya ke ga Kirki ga Tausayi Fara'a sanin ya kamata yakana jin kai da Dattako. Duka ya na da shi shima." Na fad'a hawaye sun cikamin kwarmin idanuwana ina son Abubakar ammh kaddara ta rabani da shi. Kai tsaye yace"Saurayin ki ne? Sai lokacin na dawo Tunanina da Sauri nace"A'a.." Na kauda fuskata ganin yasa bai tsawaita mganar ba. Ya yi min sallama zai tafi nima kuma daman na kosa na koma gida an fara wucewa ana kallon mu. Kuma nasan mamakin ganina da wani ake yi wasu har suna yi ma Abubakar kallon Tausayi. Sun zata Saurayina ne. Ko da na koma gida sai kuzarina ya Ragu bayi na shiga na ci kuka na kamar bazan daina. Ina kewar Abubakar kewa mai yawa sai dai ina yi masa Fatan alheri a duk inda ya samu kansa. Tunda har Sadiq na son Danwake yasa na gayama Amma zan cigaba Saboda shi. Amma tace ko shi kad'ai sai a rika yi masa ya na zuwa ya karb'a ya Chanchanta. Washegari kad'an na yi namu na gida da na shi ina ta Allah Allah yazo to bai dawo ba sai bayan kwana Biyu ya zo Duba Amma. Amma da kanta ta fad'a masa na yi masa Danwake shekaranjiya bai zo ba. Cikin natsuwarsa yace"wani uzuri ne ya hanani zuwa Amma." Ni kuma da na fita rakashi da yi masa godiyan ruwa da maltina da kayan marmarin da ya kawo ma Amma sai yace kada na kara wahalar da kaina. Na cigaba sa sana'ata in yana so zai aiko a siya mishi. Lura da na yi bayason gaddama yasa na amsa masa da Toh. Habiba na Tura kasuwa ta yi mana Cefane tunda da Adda Rukkaya ta zo gida kara Duba Amma dubu biyar ta bani Adda Fati kuma ta kawo mana kayan abimci. to da su na had'a aka siyo kayan Danwake. Amma na da kwana biyar da Dawowa gida na cigaba da sana'armu ta Danwake ranar farko da ya aiko sai nace a maida masa da kudinsa. Ya ki karba yace a dawomin da shi sai na saka Hijabi na fita da kaina nace masa don Allah ya bar kudinsa. Kai tsaye yace"Hasiya duk sanda zan aiko siyan danwake ki karbi kudi nace." Yadda ya yi mganar ne yasa ban isa na yi gaddama ba a muryansa ya na da wani abun da in ya ce abu baka iya masa gaddama. Ya rage yawan shigowa Duba Amma bai wuce a sati sau daya ba. Sai dai in ya aiko siyan Danwake sai yace"a gaida masa Hasiya mai Danwake" In ko bai aiko ba ranar haka zan wuni cewa ma Amma''Yau fa bai zo ba Amma ko lafiya? Sai Amma tace ya na lafiya kila wani abu ne ya tsaidasa. Ina jinsa a raina kamar wani yayana Ban ko iya kiran sunansa sai dai nace shi. Habiba ko Hamma ta ke kiransa Sosai muka saba da shi. Matan gidanmu har sun fara Tsegumi tunda Kaltume har tareni tayi da tambayan shine Sabon Surukin na su?. Kai Tsaye nace mata"A'a wannan Dan'uwan mu ne" Daganan na kashe bakin munafukai ammh nasan ana nan ana lura da ni ana jiran aji wata mgana ne a tare shi da Labarina. Bai taba tambayanta komai game dani ba, sai dai ya taba cewa"ina baban ku? Nace masa ya rasu da Dadewa." Sai yace"ina dangin mahaifin na ku? Sai nace masa suna nan. Daganan bai kara min wata tambaya ba, sai dai suna Hira da Amma har sunan gidanmu ta fad'a masa na Anguwan Kona. Sannan in suna Hira ta kan fad'a masa ita bafullatanan Gadan mallam mamman ce, aure ya kawota zariya. Sannan mu mun dauka da gaske Abubakar maraya ne ba shi da kowa. Ina jin dadi in nagansa ya zo ina jinsa kusa da zuciyata. Ban san me yasa na Damu da shi Fiye da kaina ba. Bansan wata irin kaddara ce ke shinshina a tare da Mutumin da ban Dade'da sanin sa ba. Kaddarace mai girma Hasiya. Girman kaddaran da zata iya sanadiyar shigan ku Tsaka mai wuya. .*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari. Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah. Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* _Masu bukatar a tallata musu Hajojojinsu cikin Farashi Saukakakke 09069067488_ *16* *GUSAU.* Dakyar Innani ta bari Sultana ta yi sati daya a gidan mahaifinta tare da yan'uwanta. Dafe ta yi ta kasa ta tsare yarinya taje domin ganawa da mahaifinta sannan ta samu zama da yan'uwanta, Ammh innani ba ta bari ba, ta na tare da Sultana kafa kafa kamar wacce za'a yi ma wani abun cutarwa. Daga matan har shi kan shi Shitun ba su da mafita sun fi kowa sanin Halin Innani don ta fito ta tara su ta tsine musu to abu ba ne da zai zama mai wahala awajenta ba. Hakanan suka rika Hakuri da ita ammh abu kad'an sai ta yi Allah ya isa akan Bakincikinsa da na matansa ya kashe mata Hauwa kulu akwai Hisabi Tsakaninsu Ranar gobe kiyama. Sannan ta hana Shitu ya gana da yarsa da ya saka a ka kirata zai ga Innani tare da ita kafa kafa. Sai masifa ta ke yi ta na fad'in uban me zai kuma gayamata? Ba ta son iskanci da neman mgana da munafunci. Dole Shitu ya kama kansa ya na ji ya na gani Sultana ta koma batare da mgana ta tsakanin Uba da yarsa ta shiga Tsakaninsu ba. Sannan ranar da zasu koma Gusai Abba ya Turo Direba ya Dauke su Mallam Shitu iya karfinsa ya yi ma Innani da Sultana Hidima ammh sai Innani ta rika fad'in" Dama baka wahalar da kanka ba Shitu. komai da ka sani Sulaimanu na yi ma yarinyar nan babu abunda ta nema ta rasa, Sulaimanu da ka ke gani kudi garesa shiyasa ba mu rasa komai ba." Ammh ta na jin kannen Sultana na fad'in zasu zo suyi mata Hutu wani Lokacin in suka samu Hutun makaranta karaf Innani ko tace"A'a ku yi zaman ku, wannan ai dora ma mai kokari wahala ne. wato kun ji nace Sulaimanu na da kudi shine za'a zo kwada'yi ko? To shima ba shi da komai Rufin asirin Allah ne ina ma laifi an Dauke muku wani Laluran? Wannan yarinyar Sulsana ko bante ubanku bai taba siya mata ba Sulaimanu ne da Salamatu. Allah dai ya biya su da Aljannah" Shitu da Matansa da suka amsa da Ameen Innani dai ta rika masifan kada su so zl sulaimanu ba shi da komai sai Rufin asirin Allah. Ammh tace su bari Bad'i in an tsaida lokacin bikin Magajin gida da Sulsana sai su zo. Ba wanda yasan da labarin yanzu za'ayi auran Sadiq da Sultana ammh zuwan Innani Shinkafi labari ya bazu a kunnen kowa. Har gidan su Baba Sammani da ta je duk haka ta rika ce musu bikin Magajin gida da Sulsana bad'i in sha Allahu. Shitu ma daki ta saka shi ta na fad'a mai cewa gwara ya fara Tanadi tun yanzu Sulaimanu dai ya yi masa na Allah ya yi masa na Annabi. In kuma ba na Shed'an ya ke jira ba sai ya nemi kudin aurar da yarsa Ina za su iya? Tunda shi Ubanta ya na raye? Daman ya mutu ne sai su Dauki na Musulunci su yi." Shitu dai mamaki ya kamasa ya san da mganar auran Abubakar da Sultana ammh bai san da mganar nan kusa ba. Suna yawan mgana da Abubakar yaro ne mai hankali natsuwa da sanin yakamata wanda ko Alhaji Sulaiman ba su cika mgana da shi kamar yadda suke yawan mgana da Sadiq ba. Ya na da tabbacin Innani ta zauna ta Tsara mganarta. Shiyasa a lokacin ya kalli Innani ya na fad'in"Ammah Innani Alhaji Ya fad'amin sai Sultana ta gama makaranta za'ayi bikin Lokacin shima Abubakar din ya gama karatunsa har ya kama aiki." Ai sai Innani ta Zabga masa Dakuwa kafin tace"Allah ya tsine ma karatun albarka. Ka ji min ja'iran ci da lalacewa irin ta Shitu? A na mganar sunnar ma'aiki ka na mganar karatun Bokon tusa da tsiya? Maza ka yi istigifari domin ka yi sabo wajen Ubangiji." Shitu dai ya ga abun mamaki ta wani bangaren kuma bai yi mamaki ba Tun kuluwa na raye sun sha zuwa Innani ta saka su a gaba ta yi masa wankan Tsarki. Wani lokacin tun Safe ta ke musu Dirar mikiya ka yi mgana ta tattara Tsinuwan bakinta a kanka shiyasa da yasan halinta sai yaci mganin zama da ita. Haka sauran matan masa ma tunda ba yau suka san Innani ba. Haka suna mota da zasu koma Innani sai faman ciye ciye ta ke yi. ta na cewa su Hassu ba su da kirki sai ga shi ita ba ta kai musu komai ba ammh duk abunda suka bata sai da ta amsa. Aya ko ta yi tiya uku Wacce Innani ta zo da shi. Tsohuwar nan yar bala'i ce ba ta da hakora ammh sai Uban kwad'ayi da son abun duniya. Innani fa har goriba da rake ta ke sha, Wuka ta ke samu ta yi ta kankarewa ta na afawa a baki da hakoranta na Roba ta ke Taunawa. Yanzu ma Aya ta ke ci sai faman mayau mayau ta ke da baki Direba ya fara Gudu Innani ta fara salati ta na Ihun ya rage gudu. Kuma ba fa gudu ya ke yi ba. Innani ta rika masifa har ta na kukan sai ta gayama Sulaimanu zai kashe masa uwa. Sai Direba ya juyo ya na fad'in"Innani ba fa gudu na ke yi ba. a tamanin fa na ke tafiya." Innani ta dake ta karfi tace"Allah ya Tsine ma maka kai da tamanin din. ni zaka raina ma wayau? In ni ba tsohuwar ka bace ka raina ni ai ka Daraja Furfuran tsohon ka ko? Ya na jin haka bai kara mgana ba Sultana da ke ta kuka tun tahowarsa ta kallah cikin kufuluwa tace"Ke kuma kukan Uban me ki ke yi? Sultana ta kalli Innani cikin Takaicinta kafin tace a hankali"Sati uku Fa Umma ta ce zan yi Innani.." Innani sai ta saki baki ta na kallonta cikin mamaki kafin ta Dungure mata kai lokaci daya ta na fadin"Ta fi chan mara wayau ni gata na yi miki baki sani ba. Shitu da ki ke gani mugun bawa ne, da matan nan nasa ina barin ki cikin su sai kuma abunda Allah ya yi." Sai ta fara kuka ta na fad'in ke kad'ai kuluwa ta mutu ta barmin ta ina zan bari a nakasa min ke." Bakinciki suka Hana Sultana mgana. Ko da ta ke da kananun Shekaru ta san Ubanta ta kuma san yan'uwanta kuma ta na son su da kaunar su ba tun yau ba tasan Innani ba ta kaunar Abbanta ta sha zaginsa a gabanta tun bata damuwa har ta kai ga yanzu abun na yi mata ciwo. Har suka iso Gusai Innani sai mugun Mgana ta ke fad'i akan Shitu har da tsohon Labarin aura auren da ya kara Saboda Kuluwa bata Haihu ba. Sultana kunnenta ta toshe ba ta son ji. Saboda in dai Hadda ce ta rika gama haddace wad'anan Labaran. Ko su kan su Umma sun sha mamakin ganin dawowarsu Sati d'aya kacal. Da Umma ta yi mgana Innani ta harzuka tace"To uban me zamu tsaya yi!? Ina laifi ma an yi zumunci." Daganan ta kama bakinta Mama ko tak bata ce ba Tunda taga yar gaban goshi Umma ta samu rabonta ta tabbata ta yi mgana sai Innani ta Taso mata. Da Abba ya dawo bai ko yi mgana ba. Shi fa Ra'ayin Innani ne na sa Ra'ayin Magajin gida ne kawai cewarsa da Ra'ayinsa ke kan na Innani. Innani bata yi mganar bikin Magajin gida da Sultana da ta gama bazawa a Shinkafi ba. Ta bari ne sai ta samu zama da Sulaimanu kawai ta gayamasa bad'i ta ke son ayi auran nan ta matsu ta ga ya'yan Magajin gida hakanan Umma ta fara ji tunda Matar Baba Sammani Madiha ta kirata ta ke tambayan ya su Innani su ka koma gida? Daganan kuma sai ta ke tambayan Umma ashe biki kuma ya zo. Cikin mamaki Umma tace bikin wa? Madiha tace na Magajin gida da Sultana mana, nan ta kwashe mganar Innani ta fad'aa mata Umma tace to bata san da mganar ba ammh za ta yi ma Abba mgana in ma da bikin za su fad'a musu. To shima Abba Shitu ya kirasa ya masa zencen yace masa sai ya koma gida sun yi mgana da Innani Tukunna. Sai a kayi sa'a Umma ke da Turaka ranar sai ta samu lokacin Tambayansa ko sun yi mgana da Innani? Abba yace a'a. Me ya faru? Sai da ta gayamasa ne shima yace sun yi mgana da Shitu. Umma ta yi shuru kafin tace"Abban Siyama ka na ganin in muka ce Auran nan ya taso ba mu yi gaggawa ba? Sannan ba mu ji Ra'ayin Auta akan mganar ba." Abba yace"Kada ki damu. Abunda Innani ta ke so shi za'ayi Salamatu. Innani ta tsufa a kwai rikicin Tsufa tare da ita gwara na samu na Rabu lafiya da ita." Umma ta jinjina kai kafin tace"Duk na san da wannan. Ammh ta ya ya za su yi aure Sultana karamar yarinya ce. sannan Auta bautar kasa ya ke yanzu bai ko kama aikinsa a hannu ba. Sannan bamu san Wani Tsari ya ke da shi nan gaba ba. ni na dauka sai ta gama makaranta shima kafin lokaci ya san in da ya kama Abban Siyama." Abba ya yi mirmishi kafin yace"Nima haka na so da farko. ammh ya zan yi da Innani salamatu? Umma sai ta yi shuru ammh tasan in su ba su isa ba. Wanda ya isan zai ji kuma zai dakatar da ita, Shiyasa ta bar mganar. Washegari da Safe gabadayansu a Shashen Innani suka karya daman Haka suke yi ranar aikin Umma. Salima ce kad'ai ke zuwa makaranta ita Direba ya dauka Sultana kuma da Siyama SS1 zasu shiga Tukunnah. Bayan sun gama Sultana da Siyama suka kwashe komai suka fita suka bar iyayen na su su zanta. Innani tun safiyar Allah sai Bare naman kaza take sala sala ta na ci Kai Tsohuwar nan akwai rikici a lamarinta. Gabadaya a gabanta suka Durkushe Umma da Abba sai Mama achan gefe. Abba ne ya fara kora mata jawabin kiran Shitu Innani ta saki naman kazan hannunta ta na salati har da tafa Hannu ga gilashinta da ya kusa cika mata Fuska ta na fadin"Na shige su ni Dije? Ashe Shitu Annamimi ne ban sani ba? ni zai yi ma makirci da Tuggu? Umma tace"Subhanallah Innani ba Makirci ba ne ya kira ne yaji tabbaci." Innani tace"Tabbacin Uban me? Zan masa karya ne shi Sulaimanun ina ce ba ni ce uwarsa ba? Umma tace"ke ce Innani har mu ma ke ce mahaifiyar mu ba mu da kamar ki." Sai Innani ta ji sanyi ta Sassauta Murya ta na fad'in"To shi ne shi ya ke Tunanin na yi masa karya ko? To ba karya ba ne da gaske ne Bad'i na ke son a yi auran magajin gida da Sultana." Falon na Innani ya Dauki Shuru Umma ta kalli Abba ta na masa inkiyar ya yi mgana. Sai ya muskuta ya na fad'in"Innani..Dama.." Innani ta Dakatar da shi da Fad'in"Sulaimanu nace bad'i uwar haka naga Yarinyar nan Sulsana a dakin magajin gida ba na son wata mgana." Da Sauri yace"Shikenan Innani yadda kika ce haka za'a yi." Umma ta kallesa shi kuma sai ya kasa kallonta. Mama ta matsonta mata mgana a Hankali" Umman su ki yi mgana mana." Karaf ko Innani ta gani ta balla mata Harara ta na fadin"wata gulmar kuma ki ke gayamata? Kin ga Suwaiba ki Fita idona kafin na ci miki Mutumci." Da Sauri Mama tace"A'a Innani ina ce mata ne ta tambayeki wani wata ne za'a saka na bikin? Innani ta kura mata ido kafin ta tabe baki tace"ke dai kika sani." Daga haka ta cigaba da zare sala salan kazanta ta na tura a baki ta na ci. Umma taga gwara ta yi mgana kafin komai ya zo ya kwabe. Sai ta gyara zama ta na fadin"Innani.." A Fusace tace"Mi ye wai ku ke ta kiran Sunana.? Umma tace"Daman naga kin sauya ra'ayi ne. ni dai nasan a baya mun gama sai Sultana ta gama makaranta lokacin ta kai shekara sha takwas shima Auta ya gama bautar kasarsa har kila ma ya fara aiki kafin mganan auran na su ya taso." Innani ta rika ballama Umma Harara ta na tabe baki kafin tace"Suwaiba ce ta kitsa miki ki ce min haka ko Salamatu? Mama ta zaro ido ta na kallon Umma ita kuma da Sauri tace"Wlh a'a. innani." Innani kamar bazatayi mgana ba Abba ta kallah kafin tace"Baka gayama matanka Umarnina na gaba da Umarnin kowa ba ne? Da Sauri yace"Haba sun sani Innani. Su san Umarnin ki shine nawa Umarnin." Kai ta gyad'a kafin tace"To ashe sun sani ke salamatu ban san me ya shiga kanki ba ki ke biyema Suwaiba da Munafuncinta ba, Ki yi ma murna magajin gida zai yi aure ko kema zaki ga jokokin ki." Umma tace"Innani jikoki nawa garemu a gidan nan? Kai Tsaye Innani tace"Ban gan su baa" Mama ta yi karaf tace"Innani ba ki gan su ba? Kaf ya'yaan mu duk sun haiyyafa. Suma ai jokokin ki ne.". Innani ta Daka mata tsawa ta na fadin"Ke ne zaki wani gayamin ya'yan ku sun haiyayyafa ce miki na yi ban san sun haihun ba ne? Ba na son tsirfa da Tsugudidi Suwaiba ba na so na gaya miki. Sai Mama ta koma gefe ta na fad'in"Allah ya baki hakuri Innani." A fusace tace"Ameen in da gaske kike yi." Sai falon ya Dauki Shuru Umma na Tsoron sake mgana a taso mata Abba kuma na zaune kanzil bai kara cewa ba. Ganin Umma ta yi shuru yasa Innani ta kalleta ta na saussauta Murya ta ce"Kwantar da Hankalin ki salamatu. Nasan sauran ya'yan ku sun haihu ammh su din ya'yan su ba jikokin sulaimamu ba ne halas malak . Duk tsiya suna da wani gidan kakanin na su magajin gida fa? Har abada ya'yan su shi da Sulsana ba su da kamar gidan nan. Duk duniya mu ne na su ba su kuma da kamar mu kuma jokokin ya'ya mata na gidan wasu ne jikan D'a Namiji shi ne Jika Salamatu." Har ta gama maganata ba wanda ya yi ko tari Abba ne yace"Gaskiya ne Innani.." Innani ta rausayar da kai kafin tace"Ku tashi ku je na gama mganata bad'i za'ayi auran magajin gida da Sulsana." Abba ya mike ya na fadin"Allah ya kara girma Innani zan fita." Kai tsaye tace"Allah ya tsare ka. Allah ya kiyaye min kai. Ya rabaka da Sharrin makiya da Mahassada ya Tsare maka dukiyarka" Abba na ta amsawa da Ameen. Ficewa ya yi ya na ce ma su Umma ya fita suka rakasa da Allah ya Tsare. Su dai suna gaban INNANI sun kasa tashi. Innani ta gama cin Namanta ta na so ta shiga ciki ta huta ta kalli su Umma ta na fadin"Wai lafiya ku ka sakani a gaba haka? ni ku tafi ku ba ni waje zan Huta ne" Umma ta marairace kafin tace"Innani Auta bai gama bautar kasa ba. Sultana maka.." Innani ta katse ta da fad"in"Allah ya tsine ma karatu da bautar kasar. nace Allah ya tsine musu tunda su zasu hana A cika sunar ma'aiki Salamatu." Umma sai ta yi shuru Mama ko Dariya ta ke ta dannewa sai da Innani tace"Ba Magajin gida ba hatta jikokinsu Sulaimanu na da arzikin da zai yi musu komai a cikin gidan nan." Dariyan da Mama ke dannewa ta Fito fili Innani ta tsaya ta na kallonta cikin mamaki da takaici. Da Sauri Mama ta danne bakinta na zare ido. Innani ta yi kafyci kafin tace"Ki yi dariya mana Tunda kin raina ni baki san Darajan Furfura ba. In wannan gajeran matar ne mai katon hanci zaki yi mata Dariya in ta na mgana? Nace zaki yi mata Dariya in ta na mgana Suwaiba? Mama sai ta dawo cikin natsuwarta jin Innani ta yi kwantancen Uwarta. Da sauri tace"Yi hakuri Innani ba da gangan ba ne." Innani tace"Da hakurin ya mutu sadakan nawa kika ba ni? Nace sadakan nawa kika bani? Iskancin banza da wofi nasan ai maganinki Allah yasa naga masu faska faskan kafafun dangin ki sun kara zuwa gida d'ana wato ana zuwa aci arziki gida babu ko? to wlh Karnukan nan na Sulaimanu ma su kama da Mutane zan saka mallam Saju ya sakar musu duk su farraka yan banza." Innani ta fad'a ta na kumfar baki. Tasan karonta da karnukan ranar da likita ya zo duba su aka fito da su Innani ta gansu kamar wasu mutane Saboda girma sai da Suma. Da ta farfad'o ko Har sulaimanu sai da ya sha Allah ya isa mallam saju da likita kuwa har da tsine musu sai da aka yi ranar. Jawo sandarta ta yi lokaci d'aya tana mike ta ke fadin"Sai ku bar min falo. Tunda ba Sulaimanu ya gyaramin shi ba. nima mai kudi ce iyayena sun bar min gado Ehe." Haka suka mike sumu sumu suka fice bayan Umma ta ce"a huta lafiya Innani." Innani ta amsa a Dakile sai da suka Fice tace a fili"Salamatu ba wayau. Duk ba ta Fahimci bakincikin Suwaiba." Daga haka ta tabe baki kafin tace"Sai dai ko bakinciki ya kasheta auren magajin gida da Sulsana ba fashi." Da haka ta dogara sandarta ta shige ciki ta nemi gado ta kwanta da gilashinta a ido tunda tace in ta ijiye bacewa ya ke yi. Wayarta ma ta gama Tsine tsine tace Allah ya tsine ma barawo da uwar barawo. Ahalin wayar gefen gado ta fad'a shikenan da ta nema bata gani ba tace an sace. Wasa wasa karamar mgana ta zama Babba Domin washegari Innani Sashen Umma ta yini ta rika sata ta na kiran mata su Surayya da kanta ta ke musu mgana ta na fad'in su fara shiri auran Kaninsu da kanwarsu bad'i kowacce haka taji mganar Daga sama ba sanarwa. Sai bayan Innani ta koma Shashenta suke ta kara kiranta suna Tambayan ba'asi ta na kora musu jawabi. Surayya tace"Umma gaskiya abun bai yi ba me sultana ta sani na aure yanzu? Sadiq ma nasan ba shi da Ra'ayin aure yanzu." Umma tace"To ya muka iya. Kun san dai Halin kakar ku." Surayya tace"Umma kin gayama Sadiq? Umma tace"A'a na kasa gayamasa ko yau mun yi waya da Safe. Tsoro na ke ji Innani ko Abban ku susan ni na Fad'a masa." Surayya tace"Ummi ni zan kirasa na fad'a masa gwara ya dakatar da abun kafin ya yi nisa." Umma tace"To Allah yasa kada sunan ki ya fito." Surraya tace"ban damu ba Umma. Bikin Kaninmu so mu ke a yi shi one in Gusai in sha Allahu." Surayya ita ta kira Sadiq ta gayamasa Halin da ake ciki. Bai yi wani mamaki ba sai dai ya tausayama Innani da ta ke masa shisshigi a rayuwarsa. Mgana ta waya bazai yuyu ba yasa ranar asabar ya ce ma Tahir zai je Gusai Tafiyan Ujila ya taso masa. Tahir ya tambayesa kwana nawa zai yi? Yace daya gobe lahadi zai dawo. Tahir ya yi masa fatan dawowa lafiya. Domin kwanaki nan fad'a su ke yi akan mutanen da Sadiq yaga ya daukesu da Muhimmanci Fiye da Sauran mutanen da yasan ya na taimako. In yau bai je gidan ba to gobe sai yaje bayan kullum ya na hanyar zuwa siyan Danwake da ya ke da tabbacin in ma wani tsafin ne ta nan aka saka masa. Tunda har ka taimake su kuma matar nan ta samu lafiya ka rabu da su mana ammh ya lura Sadiq na so ya saka kanshi a abunda zai zo ya na danasani daga baya. Shi fa tsoronsa kada Sadiq ya fara son zabiyar yarinyar nan. Tunda yaji Sadiaq din na fadin"kamar kanwarsa ya ke ganinta sannan suna ba shi Tausayi." Tunda suna son su jaawosa a jiki ne komai ma zasu iya yi. Haka kurum ya ke jin baya son wannan alaqar ta Sadiq da Sabbin mutanen da garin Tausayinsa ya jajibo ma kansa. Har Sadiq ya tafi shi kad'ai ya rika Tunanin hanyar da zai raba wannan Alaqar da ta fara kulluwa. Ammh kuma ya kasa samun mafita in dai ta mgana ce har ya yi ya gaji Sadiq bai sauraresa ba. ****** Ba wanda yasan da zuwan magajin gida sai da aka ganshi kawai. Kuma zuwan daman na Innani ne wanka kawai ya yi ya sauya kaya ko Shashen Umma bai shiga ba ya yi ma Falon Innani Tsinke da ta Rud'e da jin zuwansa Yana shigowa ta fara "Maraba maraba da Magajin gida." Fuskar nan ba Fara'a Siyama da Sultana ne tare da Innani lokacin ma mganar auran ta ke karanta musu. sannan kuma wai ta na koyama Sultana Dubarun zama da miji Siyama na gefe ta na shan Dariya. Fuskarsa ba Fara'a suna gaishe shi bai amsa ba yace"Ku ba ni waje zan yi mgana da Kakar ku." Jin sunan da ya kira Innani yasa suka san ba lafiya da sauri suka fice. Suna Fita Siyama ta kalli Sultana ta na Fadin"Sultana ko Ya Sadiq zai ce ba za'ayi auran ku yanzu ba ne? Sultana a sanyaye ta ce"Bansani ba. Ammh da hakan ta faru da zan so haka." Siyama tace"Me yasa kika ce haka? Kai Tsaye Sultana tace"Na fi so sai na gama makaranta Siyama. na kara wayau tukunna" Siyama ta jinjina kai kafin tace"Eh kuma fa hakane gwara da wayan ka an fi sanin Darajan ka." Suna tafe suna Hira har shashen Umma taga gansu ne ta ce suka bar Innani ita kadai Siyama tace suna mgaana da Ya Sadiq ne. Umma ta yi mirmishi a ranta ta na jin Dadi tasan Dole kanwar naki Innani ta bar mganan auren nan. Ilai kuwa Sadiq achan Falon Innani Wuta ya bud'e mata. Kamar bai taba saninta ba sai ta fara kuka ta na fadin"Ni daman in ga ya'yan ku ne kafin na mutu." Sadiq yace"Duk ya'yan su big sis da ki ke da shi baki godema Allah ba.! In kuma nazo Allah bai bani haihuwan ba fa ya zaki yi.? Da Sauri Innani tace"Allah ba amin ba. Da ikon Allah sai ka tara zuru'a" Tsaki ya yi kafin yace"To tunda kinsan Allah me yasa kike yi ma Allah Shisshigi? Aure da mutuwa da Haihuwa al'amarinsa ne na kuma sha miki gargadin cewa in kina so ki Mutu cikin salama ki kiyayi shiga Hurumin Allah." Innani tace"Na bari alqur'an bazan kara shiga ba." Kai Tsaye yace"Kin shiga mana. Ina ruwan ki da mganar aurena. Ke zaki zauna da matar in kika aura min ita yanzu? Ko ce miki akayi na gama karatun kenan? Ina gama bautar kasata zan dora masters dina. Mganar aure kuma na Soketa sai ranar da na Shirya Innani." Innani ta yi shuru bata yi mgana ba. Ganin haka yasa ya taso daga in da yake zuwa gabanta ya zauna ya rike Hannayenta ya na fadin"Innani ki kwantar da Hankali in sha Allahu ke zaki rakani Dakin Sultana ranar angwancina." Jin haka yasa Innani ta washe baki ta na fadin"Allah ya nuna min wannan ranar. Allah yasa ina raye ban mutu ba." Hawayenta ya ke share mata da Hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"In sha Allahu bazaki mutu yanzu ba Innani sai kin Dauki ya'ata ko d'a na ni da Sultana." Sai Innani ta Rumgumesa ta na fad'in"Idon makiya a tsiyaye a kan jikana. Yadda kace haka za'ayin magajin gida" Shima Rumgumeta ya yi ya na fadin"Yauwa Kakata mai kyau." Shikenan mgana ta mutu murus. Kwana daya ya yi washegari lahadi ya Dawo zariya. Innani haka ta tara su Abba akaro na Biyu tace mganar aure bata sai magajin gida ya yi masta dinsa. Haka yaran ma duk ta kirasu ta na fad'a musu sai magajin gida ya samu masta za'ayi auransa da Sulsana. Kowa yaji sai ya Dara, Duk wanda yace aikin waye haka da Innani ta Sauya mgana." Umma na dariya ta kan ce"Aikin waye kuwa ban da na magajin gida magajin kowa." To in ba magajin gida ba, Waye ya isa ya sauya wannan mganar ai sai shi kad'ai ne wanda mganarsa ke saman ta Innani da ta Abba shi kan shi. ***** Ya dawo a gajiye dalilin da yasa bai leka gidan su Hasiya ba kenan. Sai washegari litini bayan ya dawo daga in da ya ke hidimar kasar sa. Ya na jin Amma a ransa in ya ganta Umma ya ke gani Hasiya da Habiba kuwa tamkar Siyama da Salima ya ke kallonsu. Ya kuma san zasu damu da rashin ganinsa tunda bai fad'a musu zai yi tafiya ba. Sanin Tahir baya son ya ji zai je gidan nan sai ya fara maganganu yasa bai fad'a masa ga in da za shi ba, ce masa kawai ya yi zai je ya dawo Takaici suka saka Tahir ya kasa mgana Sadiq ya fita ba Dadewa sai ga wani Mutum ya zo ya na masa sallama a kofar dakinsa. Ya ma zata abokan zaman su ne Tunda in suna bukatar wani abu suna yi musu mgana. Tun ballatana sun san Halin Sadiq abun sa na mutane ne. Ya na fitowa sai ya ga bakuwar Fuska da bai taba gani ba mutumin zai kai shekara arba'in dattijon matashi ne. Hannu ya basa suka yi musabaha, cikin mamaki Tahir yace"Lafiya? Kamar ban gane ka ba? Mirmishi ya yi masa kafin yace"Baka sanni ba shiyasa baka gane ni ba.? Tahir yace"Oh to ko wani ka ke nema? Da sauri yace"Ai naga wanda na ke nema dazu ya fita ko? Tahir yace"Sadiq? Cikin alamun tambaya kai ya gyad'a masa kafin yace"Abubakar Sadiq sunansa kenan shima." Tahir duk bai gane ba yasa ya kankance idanuwana kafin yace"mallam wai lafiya? Kai tsaye yace"Taimako ne yasa na zo gareka. na fahimci kai ne abokinsa da ku ke zama tare. To in dai har kana son abokin ka ya cigaba da Rayuwa ya kamata ka dakatar da shi da Rab'ar in da yarinyar nan ta ke." Tahir ya saki hancinsa ya na shakan Iska kafin yace"Wata yarinya kenan.? Kai Tsaye yace"Hasiya mai Danwake wata Fara farinta mai haske haka Siririya." Tahir yace"Oh na ganeta lafiya? Da wani abu ne? Mutumin yace"Sosai ko da matsala dan Samari ganin ko ba yan garin nan ba ne kada a cutar da ku ba ku sani ba. Kada ka bari abokin ka ya auri wannan yarinya ta na da bakin jini da bakin kashi mai kashe rai da asaran Dukiya." Tahir ya ware ido kafin yace"Bawan Allah ban ga ne ba? Wa ya fad'a maka Sadiq auran wannan yarinyar zai yi? Taimakon su kawai ya yi shikenan ba wata mgana." Shima kai tsayen yace"Duk da haka dai ya yi nesa da ita gudun matsala abu ne ya faru ba sau d'aya ba sau biyu ba kowa a anguwan nan yasan da labarinta gwara ka ba shi shawaran ya kiyaye domin tsira da Lafiyarsa." Tahir ya gaji da jin mganar da ya kasa ganewa kai tsaye yace"Mallam ka tafi kai tsaye kan mganar ka. Ba na son wannan zagaye zagayen naka." Jin haka yasa ya shiga warware ma Tahir komai da ya Dangancin Hasiya. Har da mutuwar babanta ma itace cutar mahaifinta karayan arzikin su. Gujen su da Ahalin babansu suka yi. Auran ta da Abubakar da abunda ya faru da kuma na Salisu ya karishe da Fadin"yarinyar ba'a san mayya ba ce ko wani abu. Ammh tabbas duk wanda ya Rabe'ta akwai asaran rai ko Dukiya in ba'a Mutu ba za'a wahala sannan a rasa komai irin su zama da su bala'i ne da Masifa." Har Mutumin nan ya tafi Tahir na Tsaye rike da kugu baki bude mamaki ya Rufe shi. Lalle biri ya yi kama da Mutum yarinyar nan shiyasa farinta ya yi masa wani iri ashe ashe bakar daga ce Gobara daga kogi mganinta sai Allah. Bari Sadiq ya dawo in yaji haka don Dolensa sai rabu da huld'ar da duk abunda ya shafi wannan yarinyar. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj *17* Shi ko Sadiq gidan su Hasiya ya je. Daman ya saba in dai yaje a waje ya kan tsaya ya aika yara sai Hasiya ko Habiba su fito su shiga da shi ciki. Saboda akwai mata a gidan sannan a tsarin addini shi balaggage ne babu tsari ya rika shiga gidan matan aure kai tsaye batare da izini ba. Duk da matan gidan na su Hasiya kallo garesu ba wani abu ba ne, kamar ba matan aure ba. Shi dai har ya shiga ya fito kansa na kasa ba shi da dogon kallo a rayuwarsa koda da wanda ya sani ne, ko da akwai sabo a tsakaninsu. Yau ma d'in Habiba ce ta fito ta shiga da shi ciki har dakin Amma ya na shigowa da Hasiya ya ci karo ta na ganinsa ta sakar masa mirmishinta shima sai ya maida mata martani cikin zolayar da ya fara mata kwanaki nan yace"Hasiya mai Danwake." Baki ta tura kafin na juya ina kallon Amma lokaci d'aya ina fad'in"Amma kin gan shi ko? Wai Hasiya mai Danwake ya ke kirana." Amma na zaune ta na mirmishi na ganin Abubakar d'in, Allah ya sani haka kurum ta ji Allah ya Do'ra mata kaunar wannan bawan Allah, har cikin ranta komai na shi ya yi mata. Cikin Annurin da kan bayyana saman Fuskarta in har ta ga Abubakar tace"Ke ma ba sai ki rama ba. Da ya kira ki Hasiya mai Danwake sai ke ma ki ce masa Habu mai siyan Danwake." Gabadayan su suka fashe da Dariya Habiba na rufe bakinta tace"Amma Hamman ne Habu mai siyan Danwake.? Da ya ke Hamma ta ke kiransa. da Ladabin Fulani yaya kenan. Abubakar ya yi dariya har sai da Fararan Hakoransa suka bayyana awaje Hasiya ce tace,"Shikenan ko Amma ta kawo shawara." Sai da ya zauna gaban Amma sannan yace"Hasiya mai danwake ya fi dad'in fad'a ko a baki Amma" Amma ta yi dariya ba ta ce komai ba gaisawa su ka yi a mutunce kamar yadda suka saba. Habiba ta kawo masa ruwa a jug. Hasiya kuma ta kallesa ta na fad'in" a kawo abinci..? Kai ya girgiza Lokaci d'aya ya na Fad'in" na sha fura a wajen aiki. Cikina ya cika Sosai." Amma tace"ko aikin ne ya hana ka zuwa kwana biyu Abubakar? Ya na sosa kansa yace"A'a Amma kauye na je. kuma tafiyar ta gaggawace shiyasa ban Sanar da ku ba." Amma tace"Ayya. Ka same su lafiya ko? Ya ce"Eh duk sun ce suna gaishe ku Amma" Amma ta amsa cikin sakewa. Kafin su cigaba da Hira kan rayuwa da sauran su. Rabin Hiran duk na Amma ne shi na shi eh a'a ne sai ko in ta yi masa wata Tambayar. Habiba islamiya ta shirya ta tafi ni kuma sai na fita waje na Hura gawayi na Dorama Amma ruwan wanka tunda ba ta yi ba. Daman ban cika zama adakin ba in ya na nan saboda gudun zargin mutane. Yan gidanmu sun ta bin kwakwafin ko saurayina ne to ganin ya na shiga har Daki kuma su jima su na mgana da Amma sai suka aminta da cewa da gasken dai kila d'aan uwan mu ne. Kila kuma cikin Dangin Babanmu da suka watsar da mu ne. A cikin raina na ke jin Abubakar a chan kasan raina na saka shi cikin Layin masu kaunar mu. Ina shiga Damuwa in bai zo ba, Saboda shi ma ina Fargaban kada watarana a rabamu da shi ina jin Tsoron faruwan hakan shiyasa in bai zo ba na rika shiga Damuwa kenan ina faman ce ma Amma" yau fa bai zo ba" Amma kan tausheni da cewa"Zai zo Hasiya. A jikina na ke jin yaron nan ba irin sauran ba ne. Zai zo in sha Allahu." Yau ma sun jima suna Hira da Ammah sai da yammah ta yi ana gabda kiran mangariba sannan ya yi ma Amma sallama ya tafi. Bayan ya ba ta dubu uku Amma ta ki karb'a ta na Fad'in"Kai da ka ke d'an makaranta Abubakar kuma ka ke Hidima damu? Ai sai abun ya yi maka yawa." Haka ta ke fad'i duk sanda ya yi mata wani karamin kyauta. Shi kuma kai tsaye ya ke cewa"Amma kin manta na fad'a miki ina Hidimar kasa ne? Suna biyan mu duk wata kuma Dubu uku ai ba Hidima bace." Amma ta amsa lokaci d'aya ta na Fad'in"Allah ya yi albarka. Allah ya jikan iyayen ka, Allah ya haskaka makwancin su Allah yasa suna cikin Dausayin Aljannah. Nagode sosai Allah ya tsare ka duniya da Lahira." Shi dai na shi amsawa da Ameen ne cikin jin dadi. Ko da ya fito da niyyar tafiya samuna ya yi ina ta fama da fifitan gawayi ya ki kamawa saboda nayi rashin sa'a ya na da Sanyi a jikinsa. Ban san ya zo kusa da ni ba sai da naji ya na fad'in"Wutar ta ki kamawa ne? Da sauri na juyo ina kallonsa. Ya na tsaye a gefena sanye da riga da wando masu ruwan toka rigar ta na da Layi layi sannan tare da dogon hannu na Fahimci ya na son saka riguna masu Dogon hannu. Sannan Dabi'arsa ne ya na tsaye ya tura Hannayensa cikin Aljihun wandonsa. Yau ma haka d'in ya yi sai naga ya yi min kyau. Haka daman masu suna Abubakar su ke da gayu da kyau tare da Tsari? Shagalar da na yi ina kallonsa yasa har ya Durkusa a gabana ban sani ba sai ji kawai na yi ya na fad'in"Kawo na tayaki fifita wutar." Da sauri na dawo Hayyacina da Sauri na tashi ina kallon bayana ganin matan gidanmu a tsakar gida an zuba mana ta mujiya musamman ma Kaltume. Da sauri nace"Don Allah ka bar shi. Kayan ka za su yi hayaki? Ya na kallona yace"kin tabbata zaki iya hura wutar? Da sauri na gyad'a masa. Shiyasa ya mike ya na fadin"Bari na tafi" Ban san bakina ya kubce ba sai da na jini ina fad'in"Tun yanzu? Agogon Fatan da ke hannunsa ya kai ma Duba kafin yace"Mangariba ta kusa ne" Jinjina kai na yi kafin na yi mgana ya rigani da fad"in"Zo mana Hasiya." Ba musu na amsa masa. Daki na koma na dauki Hijabina ina ce ma Amma Abubakar na kirana a waje ta amsamin ta hanyar d'aga kanta sama. Ina fitowata matan gidanmu suka sakarmin na mujiya Har na fice suna kallona na kuma san ina fita za'a dasa yi dani. A kofar gidan na ganshi ya jingina da garu ya na kallon hanya. Ina fitowa ya tashi daga jingina da ya yi da garu ya na kallona. Kallo ba Dabi'an sa ba ne ammh sai ya samu kansa da karemin kallo, Fuskata ta kara masa Fayau saboda jan Hijabi ne ajikina in ba sanin fatata ka yi ba sai kayi Tunanin ba ni da jini ne saboda yadda Fata ta dashe fari sol ba alamun ja ja a jikina. Ni kuma sai na Tsargu da yanayin kallon na shi. Barin ma da mutane ke ta wucewa suna kallon mu har da ma su waiwayowa suna cin Tuntube saboda Gulma. Shi kuma kallona ya ke yi ammh kuma Tunaninsa ya tafi ga Tunanin sunan da Tahir ke kirana wato Zabiya kuma sai yaga gaskiyan shi kad'an ne ya ragemin ban zama Zabiyar ba. Ko Amma fara ce Ammh ba kalan fari na ba ne Habiba ma haka kalan haskenta mai ja ne ba irin na wa ba ya na da tabbacin duk da bai ga sauran yan'uwana duka ba kalan Fatata ta fita Dabam da na su. Gyara murya na yi dalilin da ya sa ya sauke kallonsa a kaina lokaci d'aya ya na fad'in"Hasiya mai d'anwake " Ya fad'a cikin Zolaya. ni ma kai tsaye Nace"Habu mai siyan Danwake ba." Dariya ya yi ya na girgiza kai kafin yace"Sunan ki Asiya ne ba Hasiya ba.' Kai tsaye nace"Na fad'a maka ni sunana Hasiya ba Asiya ba ce." Kai ya jinjina kafin yace"Daman an ce bafullatani da kafiyar tsiya." Baki na tabe kafin nace"Da Amma ka ke ni bazazzagiya ce tunda Babanmu mu haifaffan garin zariya ne." Shima kai tsayen yace"Ammh kin yarda ke Ruwa biyu ce Hausa Fulani. Wani ma in ba kin fad'a masa ba kin fi kama da buzayen yamai." Cikin mamaki nace"Ina ne kuma Yamai.? Ya na Bude ido yace"Baki san yamai ba? Na gyad'a masa kai. Kai tsaye yace"Ke bakauya ce a she ban sani ba." Ina yar Dariya nace"Kuma bak'auya ta had'u da bak'auye ba." Baki ya rike ya na fad'in"Hasiya ashe haka ki ka ji Hausa ban sani ba.? Ban ce masa komai ba sai dai na Murmusa. Shuru ya yi na wani lokaci kafin yace"Bari na zo na tafi. An fara kiran sallah." Ina dagowa nace"Kwana biyu ba ka zo ba? Ba tare da ya ba ma mganar Muhimmamci ba yace"Eh na yi tafiya ne." Iduwana na kallonsa nace"Garin ku ka je? Wannan karon da kai ya amsamin kafin ya yi mgana da sauri na tare shi da cewa"Gobe za ka zo? Cikin mamaki ya kalleni sai na ji kunya da nauyi da sauri na gyara maganata da fad'in"Amma ce ke damuwa in baka zo ba." Mirmishimsa mai Tsada ya saki kafin yace"Ko ban zo ba. zan aiko a siyamin Danwake." Cikin marairaicewa nace"Don Allah kada ka aiko da kud'i" Kai tsaye yace"Nima don Allah ba na son gaddama." Ganin yadda ya yi mganar yasa ban kara cewa komai ba. Sallama mu ka yi ya wuce ni koma na koma cikin gida ina shiga Maman Boy ta washe baki ta na fad'in"Ai na jiki shuru nace Hira ta yi dad'i. naga rushun ya ruru sai na aza miki Ruwan." Ban sakar mata Fuska ba nace Nagode. na shige dakin Amma ina kallonsu suna had'a ido da Maman Salihi za'ayi gulma. Acikin raina nace"Tunanin abunda bazai taba faruwa ba ku ke yi." Ko da Allah ya ce zai Farun Hasiya? ****** Bai koma Daki ba sai da ya tsaya masallaci ya yi sallar mangariba ana wa'azi da Fadakarwa kan mutuwa yasa ya zauna har aka kira Isha'i. Sai da sallar isha'in sannan Tahir ya zo bayan an idar da salla suka koma Daki tare. Bai masa mganar ba sai da suka yi shirin kwanciya. Tahir wayarsa na Hannunsa shi kuma Sadiq Laptop dinsa ya jawo bai ma kai ga kunna ta ba yaji Tahir na fad'in"Wai dazu ina ka je.? Ba tare da ya kallesa ba yace"Gidan su Hasiya na je." Tahir takaici ya sa ka shi ijiye wayarsa duk ko abunda zai sa Tahir sauke waya lalle muhimmancin al'amarin ya girmama. Sadiq bai ma san ya na yi ba kokarin Sarrafa Na'urar hannunsa kawai ya ke yi Lokacin da yaji Tahir na Fad'in"Sadiq ko dai ka fara son Zabiyar yarinyar nan da gaske ne? Ba tare da ya bama tambayan Tahir Muhimmanci ba yace"So kuma? Ka cika maimaita mgana D'aya ina ce mun rufe wannan mganar da kai ko Tahir? Tahir ya katseshi da Fad'in"To in baka so nayi zargin haka ka rabu da su mana. Yan'uwan ka ne da dole sai ka rika zuwa in da su ke? Ina ce daga Taimako ba shikenan ba? Sadiq ya yi shuru kamar bazai yi mgana ba sai kuma chan yace" Tahir na fad'a maka Tausayin su na ke ji. Kuma ni wajen mahaifiyar su na ke zuwa matar na so na wlh." Tahir ya yi wata Dariyar renin wayau kafin yace"Ta na sonka? Eh dole ta soka Tunda ta na son kaima ta jefa rayuwarka cikin gagari ta sanadin yarta kamar yadda ta jefa Sauran." Sadiq bai Fahimci in da Tahir ya dosa ba shiyasa ya ce"Naji ka bar ni. Rayuwata ce ba taka ba Tahir." Tahir yace"Kasan me naji a kan wannan yarinyar da Ahalinta? Sadiq kai tsaye yace"Sai ka fad'a." Ya fad'a hankalinsa na kan Allon Na'urar da ya ke kallo. Tahir yace"ka na fita wani Mutum ya zo can u just imaging yarinyar da ka ke ma kallon yarinya karama auranta fa Biyu bazawara ce." Sadiq ya yi shuru kafin ya Dago ya na kallon Tahir cikin mamaki yace"Me ka ce? Bazawara ? Tahir yace"Yes ofCourse Bizet ba. Abunda zai kara baka mamaki ma shine Bayan mganar auran nata yarinyar ta na da wani abu a tare da ita na Dabam kuma" Sadiq ya yi saurin cewa"Kamar na me? Nan Tahir ya shiga zayyanemasa har da kari ya karishe da fad'in"An ce duk arzikin mutum in ya rabeta sai ya talauce in ma bai rasa rai ba. Mijinta na farko da shi da iyayensa sai da suka rasa komai nasu, na Biyun kuma ya na chan ya na jinya. To wai yarinyar da ace itace silar karyan arzikin Ubanta ta yi kuma sanadiyar mutuwarsa da ciwon uwarta da duka Halin da suke ciki itace Sila kasan wasu haka Allah ke yin su da Farar kafa ba bu albarka ko wani nasibi a tare da su." Tahir ya tsagaita ya na kallon Sadiq ya na so ya Fahimci yadda ya karb'i mganar sai yaga hankalinsa na kan abunda ya ke kamar ma bai ji abunda ya ke fad'i ba. Kai tsaye Tahir yace"Baka ce komai ba? Sadiq kai tsaye yace"Me zan ce maka Tahir? Cikin mamaki ya ce"Baka ji mganata ba ne? Sadiq yace"Na ji mana. Me ka ke so ayi yanzu? Tahir ya gyara zama ya na fad'in"Ka yi nesa da su don Allah Sadiq. Ka na da wad'anda in wani abu ya sameka za su shiga wani Hali." Sadiq ya yi kamar bai ji Tahir ba sai da shi ya gaji da jiran jin ta bakinsa ya kwace laptop d'in ya na fadin"Sadiq mgana fa mai muhimman na ke yi maka ka yi min banza" Sadiq ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce"Tahir me ka ke so nace.? Tahir yace"Au me ma zaka ce ka ke tambaya ta Sadiq? Lafiyar ka Dukiyarka ka tseratar da su mana." Sadiq ya goya hannayensa a saman kirjinsa lokaci d'aya ya na fad'in"To naga ai ni ba mai dukiya ba ne ballatana ace zan talauce." Ya fad'a lokaci daya ya na kyalkyacewa da Dariya. Galala Tahir ya yi ya na kallon Sadiq ganin ya na dariya kamar wanda ya fad'i wani abun dariya. Tahir ya shaka da yasa a fusace yace"Sadiq abun dariya ne wannan? nace abun dariya ne wannan? Sadiq ya tsagaita da Dariyan ya na Fad'in"Gaskiya abun dariya ne Tahir. Ta ya ya zaka yadda da wannan mganganun kamar almara? Daman mutum ya isa ya yi ma wani mutum wani abu batare da Allah ne ya yi masa ba? Ya tambayi Tahir Lokaci d'aya ya na kallonsa. Tahir yace"Ba wannan bane, Ka fara tunanin janye jikin ka daga wannan yarinyar Sadiq in dai ba sonta ka ke yi ba." Sadiq yace"Wlh tallahi ba sonta na ke yi ba. Mganar kuma na janye jikina bai taso ba ban fara domin na daina ba Tahir." Tahir yace"Sadiq ka na jin fa an ce ga abunda ke faruwa a rayuwar yarinyar nan. Daman ni tunda naganta ba ta min ba tsoron ganin Fuskarta ma na ke yi farin ta ya yi yawan da zai iya zama matsala." Sadiq ya kara Bushewa da dariya kafin yace"ina ruwan ka da farinta. Fari ko baki wani hallita ne na ubangaji. Kada ka danganta haka da yanayin da Allah ya halliceta." Tahir yace"Sauran mazajen da ta aura fa? Me zaka ce a hakan haka.? Sadiq ya gyara zama kafin yace"Ni ban zan ce komai ba. Saboda ni musulmi ne na yi imani da Allah da Annabawansa tare da Sahabansa da Littafansa. Sannan na yi imani da Tauhidi da iklasi na kuma san akwai kyakyawan kaddara da Mummuna shiyasa bazan ce komai kan mganganunka ba Tahir, Basu da ma Tushe ballatana makama kai ma ban yi tsammanin jin irin wad'anan maganganun daga bakin ba Tahir." Ya na gama fad'in haka ya karb'e laptop dinsa ya na fad'in"Ni ga Allah na Dogara nasan kuma shi ke aikata mai kyau ga bawa da akasin sa ba Mutum ba." Tahir ya saki baki kawai ya na kallon Sadiq bai taba zaton zai iya Ture wannan mganar ba. Sai yanzu da ya maida abun wasa yasan raba Sadiq da wannan yarinyar nan aiki ja ne. Tahir bai hakura ba yace"Sadiq ba Rayuwarku d'aya ba. Ku na da tarin bambamce bambance don Allah ka bar su ana su Duniya kai ma ka koma taka Duniyan." Sadiq ya amsa shi cikin Sakewa ya na Fad'in"musulmi dan'uwan musulmi ne Tahir. Kuma taimako ai ba laifi ba ne ni ban ga wata matsala ba aciki." Cikin kumfar baki Tahir yace"To aure auren nata ka san da shi? Ka daa garin Taurin kanka ka siya ma kanka wahala Sadiq." Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Abunda ya shafe su sai nace sai na sani? Nima ai ba su san komai a kaina ba, Kaga Tahir plz ka kyaleni da wannan mganar bata da asali ballatana Tushe." Sadiq ya fad'a ya na cigaba da Sarrafa Laptop dinsa Wani Turkish Drama ya ke kallo shi ya ke kokarin kunnawa, sanda Yaji Tahir na fad'in"Ammh kasan akwai farar kafa acikin mutane ko? Kamar Sadiq bazai yi mgana sai kuma ya Ture Na'urar gabansa ya na kallon Tahir na wani Lokaci kafin yace"babu Farar kafa a cikin Mutane Tahir. Kuma babu Farar kafa a musulumci Duk canfi ne kuma Canfi karya ne addini baizo mana da shi ba kai ko Maita ma Annabi bai sanar damu ba kambun baka kad'ai Annabi ya sanar damu akwai shi a acikin musulunci." Ya fad'a cikin Tarin natsuwarsa. Tahir ya yi kasake ya kasa mgana. Sadiq ya cigaba da fad'in" Babu wanda yasan gaibu sai Allah Tahir. Allah Fa'alim lima yarud_ shine mai aikata abunda ya ke so alokacin da ya so. babu Canfi ko farar kafa a musulumci, lamyasiduna_ Babu abunda zai same mu a wannan rayuwar Illama katabullahi lana_ sai Abunda Allah ya Rubuta zai faru same mu. Wahuwa maulana_ kuma Allah shine majibancin dukkan lamuranmu. Wa'allallahi falyatawakkalu mu'uminun_Ga Allah kad'ai ne mu mumumai ne zamu dogara." Sadiq ya karishe fad'a ya na kallon Tahir kafin ya Dora da fad'in"Saboda haka ka kiyaye irin wad'anan mganganun. Ko wani kaji ya na yi ka fad'a masa Allah shine masanin gaibu ba Mutum ba." Daga haka ya cigaba da abunda ya ke yi ya bar Tahir ya na kallonsa. Ba domin wa'azin Sadiq ya wani Shigesa ba. Dole fa akwai ayar tambaya acikin Rayuwar yarinyar sai ace haka kawai komai ke faruwa kai ina da walakin Goro a miya. Dole sai ya yi kamar ya na yi Ko saboda abotan da ke Tsakaninsu da Sadiq ba zai taba bari ya saka Rayuwarsa acikin Tsaka mai wuya ba. Tun daga ranar bai kara yi ma Sadiq mganar ba saboda yasan ko ya yi masa bazai Sauraresa ba. Sai ma karin wasu ayoyon da za su biyo baya da tarin Hadisan da Sadiq zai rika gayamasa ya na fassara masa. Kuma ya na gani Sadiq bai fasa zuwa gidan ba sannan bai fasa zuwa siyan wannan munafukin Danwaken da ya ke Tunanin koma wani Mugun abu ne ciki ta saka ma Sadiq din domin ta ja Ra'ayinsa a kanta. Har so ya yi ya kira Umma ya fad'a mata sai kuma ya kasa. Ba sa taba irin haka da Sadiq ba duk da shima kamar dan gida ne bazai kyautu ya kai karar Sadiq gidan su ba. Ya na cikin neman mafita ne Makarantar da ya ke Hidimar kasa su ka yi Hutu yace ma Sadiq zai tafi gida ko shima zai tafi Gusai? Bai tab'a zaton Sadiq din zai ce za shi ba. Ammh sai ya ce masa shima zai tafi gida ya yi sati biyu sannan ya dawo. Tahir ya ji dad'i sosai tare da Fatan Allah yasa kafin Sadiq ya Dawo ya manta da zabiyar yarinyar. Rana d'aya suka tafi kuma abunda Tahir bai sani ba Sadiq a daran ana gobe Tafiyarsu sai da yaje ya yi ma Amma sallama a kan zai je kauye zai jima kafin ya dawo. Har Amma na fadin ko dai in ya tafi bazai dawo ba ne? Yace mata in sha Allahu zai dawo ai bai gama hidimar kasar ba. Hasiya ta rakosa har waje in ba idanuwansa suka ga masa karya ba yaga damuwa da kewa acikin Idanuwantaa. Ya na cikin motar zuwa Gusai ya ke tunawa da mganar ta cikin sanyi in da ta ke cewa"Ammh zaka dawo ko? Kai ya gyad'a mata kafin yace"In sha Allahu SIYA." Sai ta d'aga masa hannu alamun bye bye kafin tace"Allah ya kiyaye hanya. Ya kuma dawo da kai Lafiya ASSADIQ." "ASSADIQ.." Sunan ya daki zuciyarsa har sai yaji ya amsa acikin jikinsa. Lumshe ido ya yi ya na kallon siraran hannunta lokacin da ta ke d'aga masa hannu da Sanda ta juya siraran kafafuwanta ta koma cikin gida. Sake Bude' idanuwansa ya yi yana jin wani iri aransa In da gaske ne auran Hasiya Biyu me ya faru da ita ta yi aure aure a kananun Shekarunta? Tabbas akwai wani abu shi kuma mutum ne da ba ya cika Takura ma Mutumin da ke tare da shi akan sanin wani abu na fanni Rayuwarsa. Ammh zai so ya ji garin ya ya da kananun Shekarunta ta yi aure har Guda Biyu kuma ta na fitowa? Ya tuna kwanaki har Amma ya taba ma tambayar Ko Hasiya Sikila ce? Amma sai da tayi dariya kafin tace"Hala sirintar ta ka gani ko? Haka na Haifeta lafiyanta kalau Abubakar." Abun mamaki har ya kai Gusai duniyarsa da Tunaninsa akan Hasiya ne. Acikin ransa Tausayinta ya ke ji tun kafin yaji me ya faru da ita. Tausayin yadda ta na karamar yarinya ta Fuskanci Kalmar Saki har sau biyu. Da rana ya sauka agida. Murna wajen iyalan gidan Alhaji Sulaiman ba'a mgana. Kada su Innani ta ji labari ta kasa zama ta kasa tsayuwa Magajij gida ya dawo. Abba baya nan sanda ya dawo ya gaji shiyasa shashensa ya wuce ya yi wanka. Kafin yaci abinci Tahir ya kirasa yace shima ya sauka gida Tun dazu ba su jima suna mgana ba suka yi sallama. Salima ta kawo masa abinci ya ci ya sha sannan ya kwanta ya na warware gajiya." ****** Tafiyar Sadiq da kwana Biyu Adda ta zo Dalilin ta kira Adda Fati ta na tambayan lafiyan Amma. Ita kuma ta gayamata Ciwon da Amma ta yi kwana Biyu tsakani sai gata tare da d'aya daga cikin ya'yanta Isuhu Jauro. Ko alama Adda bata nuna ma Amma da mganar tafiya da ita tazo ba Jauro nan ya barta ya koma sai da ta kwana sannan ta zaunar da Amma da mu tare da Adda Fati da Adda Rukayya. Domin Adda Fati na zuwa tace ta Kira mata Rukayya jin Adda ke kira yasa ta zo da sauri a tunanin ta ba lafiya. Sai da taga kowa lafiya har Amma sannan ta kwantar da Hankalinta. Maganar da Adda ke fad'i ne ta girgizamu ba Shawara ba ce wannan karon tace Umarni ne zata Dauki Amma su koma gida. Adda Fati ta zaro ido kafin tace"Adda mu kuma fa? Mu kadai anan ba mu da kowa fa" Adda tace"Ba ku kad'ai ba ne. Ku na da mazajen ku sannan nan ne Tushen ku ga kuma Dangin Uban ku duk suna garin nan, Aisha kuma aure ne daman ya kawota kuma wanda ya yi silan zuwanta ba shi Tuntuni ya dace na tafi da ita mu zauna tare saboda ku na kauda kai. Ammh yanzu komai ya zo karshe Da Aisha da Hasiya da Habiba duka zan iya rike su, na saka Tuni an gyara muku muhalli ci da sha bazai gagaremu ba in sha Allahu." Ta fad'a kai tsaye ta na kallon mu. Cikin mu sai aka rasa mai kara cewa wani abu tun bayan mganar Adda Fati. Adda ta kalli Amma da ta dukar da kai kafin tace"Wannan karon ba karb'an uzuri. In Hasiya ki ke ji ki daina damuwa achan ma zata samu miji in sha Allahu." Adda Rukayya tace"Ammh Adda rayuwar ce ba d'aya ba kina ganin akwai takurawa gareki kema ki na Fama da kanki.? Da Sauri Adda Fati tace"Eh nima shi na ke Tunani." Adda ta yi mirmishi kafin tace"Ni fa da Aisha muka taso tun bayan rasa iyayen mu. Kuna tunanin bazan iya rike ku ba ne? Kamar yadda na tara ku suma yarana haka na Tarasu kuma suka bani goyon bayan Tahowa da ku kuma in sha Allahu sun ce baza su gaza ba, Naga nan din da ta ke zaune ba wani mai kula da ita. Dangin babanku kuma sun yi butulci da Hankalina ke chan a tashe gwara na Dawo da ita a kusa da ni zai fi min kwanciyar Hankali. Ba shawartanku na ke yi ba Umarni ne. Ke Hasiya ku fara shiri kin ji ko? Cikin sanyin jiki nace"To Adda." A baya na fi kowa Murna da komawar mu gadan mallam mamman. Ammh abun mamaki yanzu sai naji kamar in na tafi zan bar wani abu mai Muhimmamci anan to menene shi wannan? Wata zuciyar ta tunasar da ni shi. "ASSADIQ." shine na ke jin wani iri ya ya zai ji in ya dawo akace masa ga in da muka koma? Maimakon na yi murna sai naji na kasa yin farinciki ko kad'an. Ammah kuma ba ta iya ma Adda Gaddama ba tace duk yadda tace haka za'ayi. Su kan su su Adda jikinsu duk ya yi sanyi haka suka tafi. Washegari mun tashi da had'a kaya duk da bamu gayama kowa ba sukola muka ta shi da shi Tun Safe ni da Habiba. Sai da yammah sai ga Adda Fati da mijinta. na zata yazo gaida Adda ne sai bayan sun Fati Adda ta kalleni ta na fadin"Fati da mijinta sun roki a ba su Habiba ta zauna tare da su saboda karatun ta. to ganin yadda ta damu yasa na amince sai ke ki shirya tare da ke zamu tafi." Gabana sai da ya fad'i na kasa ma mgana Habiba na jin haka ta fara tsallen Murna, daman karatunta ta ke ji in ta koma chan ammh jin haka sai ta fara murna. Amma ba ta ce komai ba sai dai a kasan ranta ni ta ke Tausayi. tun jiya da Adda ta yi mganar nan ta ke ta nema min mafita ammh bata samu ba. Habiba ta samu nata mafita saura Hasiya. Ita da Rayuwarta ke cikin Tsaka mai wuya ta na bukatar Farinciki da jin dad'i. Ta na bukatar wata rayuwar da ta fi wannan da ta ke ciki. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki. *18* Kamar wasa sai ga karamar magana ta zama babba, Adda ta dage tare da ni da Amma zata koma kafarta kafarmu tun ina ganin lamarin wasa har na sare na Saduda da cewa tafiya ta zama Dole. Tuni har Amma ta sanar ma da matan gidanmu saboda rayuwa. An yi zaman Amana tun zamanin zaman mu acikin gidan nan ko cacar baki bata taba yi da kowa ba. Mu ma haka babu ruwan mu tun ballatana ma da ba su cika Rab'ar mu ba, mu ma sai mu ka kama kan mu da Maraicin mu. Adda Fati da Adda Rukayya matuka sun shiga damuwa. Adda Rukayya ta fi bani mamaki ita da ni ke ganinta ba ta damu da mu ba, sai ga shi ta nuna jimaminta sosai. Daman tun faruwar abunda ya faru a gidanta ta yi sanyi yanzu lafiya lau mu ke da ita sai dai duk da haka babu shakuwa Tsakanina da ita kamar yadda muka Shaku da Adda Fati. Dukkansu ba su da mafita ne Gwara ma Mijin Adda Fati zai iya rike mu ni da Amma. Ammh mijin Adda Rukayya ba shi mutumci ko Habiban Adda ta ce zata rike wlh bazai rike ba. Mutumin da bai san kowa ba sai kan shi itama don ya na sonta ne shiyasa ya ke yi mata abunda ta ke so. A baya ne na so na koma wajen Adda da abubuwa suka rikicemin ammh a yanzu kuma sai naji ba na son barin nan d'in. Amma ma ta gama iya nazarinta ta san ba mafita sai ta bar ma Allah duka zabinsa. Adda Fati ta kira Ramatu ta sanar da ita ta kuma ce ta sanar da Inna Talatu. Washegari sai ga su sun zo Hankula ta she, Inna talatu ta ce"Yanzu shikenan kuma Amma zaki bar mu? Kafin ma Amma ta ba ta amsa Adda ta karb'e da cewa"Ba ta bar ku ba. zumunci ai Allah ya riga ya had'a. In bukatar hakan ya ta so zamu zo. Kuma in wani sha'ani ya taso ko auran Hasiya duk za ku zo in sha Allahu." Daganan Inna talatu tasan Adda ta riga ta yanke hukunci ba mai tada wannan mganar. daman ta dad'e ta na so ta Dauke Amma d'in ta koma wajenta. Ni kuma Ramatu sai nanata tafiyarmu ta ke yi ta na fad'in"Yanzu Hasiya in kika tafi ya zan yi? Kinsan fa ba ni da wata kawa wacce ta wuce ki." Cikin sanyin murya nace"Zamu rika waya Ramatu kada ki damu ba bu abunda zai sauya." Ramatu ta yi tagumi ta na kallo na ina yi ma Noor rawa ta na bangala Dariya. Cikin muryan kamar za ta yi kuka tace"Hasiya sai na ke ganin kamar rayuwar zata yi miki wahala. nan aka haifeki kuma anan kika ta shi chan kuma bakon waje ne a wajen ki. Akwai chanjin Rayuwar da kafin ki saba sai kin sha wuya." Mirmishi na yi kafin nace"Zan saba Ramatu. a yanzu dai banga irin rayuwar da Hasiya bazata iya zama acikin ta ba." Ramatu tace"Ni da zaki amince da na yi ma Nura mgana tunda ina da Daki sai ki zauna tare da mu." Ido na waro ina kallonta kafin nace"Ramatu anya ki na da Hankali kuwa.? Ramatu tace"Ras na ke Hasiya. Allah da gaske na ke in kin amince na yi masa mgana sai ki saka baki mu lallashi Adda da Amma" Dariya na yi kafin yace"A'a ba da ni za'ayi wannan aika aikar ba. Bazai yu yu ba Ramatu ai ba mutuwa zan yi ba, Wajen zama kawai zan sauya kuma zumuncin mu na nan har Abadan" Ramatu sai ta kasa magana sai kallona ta ke yi cikin Rauni. Da alamun so ta ke yi ta yi kuka ni kuma sai naki kallonta na cigaba da yi ma Noor wasa ina fad'in"Kinga Noor ta kara wayau sosai." Ramatu ba ta ce komai illah tagumin da ta zabga ta na kallo na. Noor ce ta fara kuka na tashi na goyata na fara zagaye dakin Maman Boy da ita ina jijjigata. Sai ji na yi Ramatu tace"Shikenan sana'ar Danwake ya tsaya? Juyowa na yi ina fad'n"Ya jima da Tsayawa tun kafin zuwan Adda rabo na da yi." Ramatu ta sauke ajiyar zuciya ganin yadda ta damu yasa na karisa na zauna gefenta ina Dafa kafad'arta Lokaci d'aya ina fad'in"Ki daina damuwa ba mutuwa fa zan yi ba." Ramatu ta kalleni kafin tace"Ko ba mutuwa zaki yi ba. Zaki yi nesa da ni ko? Sai na kasa mgana zuciyata sai naji ta matse ni kaina ba na son yin nesa da su musamman wani da zuciyata ta saba da shi. Cikin fitan hayyaci nace"Ni kaina ba na so na yi nesa da shi Ramatu." Ban san me na fad'a ba sai ji nayi Ramatu tace"Shi wa? Kallonta na yi ina tunanin me na fad'a. Ganin haka yasa Ramatu tace"Shi waye baki son ki yi nesa da shi? Ajiyar zuciya na sauke Ramatu ce wacce ba abunda na ke boye mata ita D'in Sirrina ce kamar yadda na ke Sirrinta. Cikin sanyin muryata da ta kara yin kasa nace " ASSADDIQ..." Ramatu ta bud'e ido ta na fad'in"Assadiq kuma? Na ina? Mikewa na yi jin Noor ta fara kuka ina jijjigata nace"ina wanda kwanaki ya taimaka ya kai Amma asibiti? Ramatu ta yi shuru kafin ta ce da sauri"Na gane shi wannan Saurayi baki dogo ko? Wanda ya rakamu dakin da ku ke ciki lokacin da aka kwantar da Amma? Kai na gyad'a mata batare da na yi mgana. Ramatu ko mikewa ta yi jiki na rawa ta iso kusa da ni ta na fad'in"Gayamin naji. Ya ce ya na son ki ne? Ta fad'a lokaci d'aya ta na Dafa kafad'ata. Sai ta ba ni dariya da sai da na Dara cikin Dariyan nace"Wani irin so kuma Ramatu? Ramatu ta harareni kafin tace"To in ba soyayya ba me yasa baki son nesa da shi? Kuma ma ban da abun ki Hasiya ai garin masoyi ba ya nisa." Mirmishi na yi kafin nace"Ba fa soyayya mu ke yi ba. Tun bayan taimakon da ya yi mana sai muka saba yana zuwa gidanan sosai wajen Ammah. To cikin sati nan da ya fita ya zo ya yi mana sallama zai tafi kauyen su shine abun ya ke damuna zamu tafi bai sani ba Ramatu." Ramatu ta kuramin ido cikin mamaki kafin tace"Sai ki kirasa a waya ku yi sallama" Kai Tsaye nace"Ba ni da lambarsa." Ramatu ta yi shuru ba ta yi mgana ba. Ni ma na yi shuru na wani lokaci kafin nace"Ko Amma ta damu tace da ta san da tafiyar da ta yi masa sallama." Ramatu tace"Ba a nan garin nan ya ke ba? Kai tsaye nace"Eh shinkafi ko yace sunan garin su." Ramatu tace"Bazamfare ne kenan" Ban amsa mata ba ta cigaba da fad'in"Damuwarki akanshi ta ba ni mamaki kad'an Hasiya." Kallonta na yi kafin na yi mgana ta yi saurin Tareni da cewa"Daga gani kina jinsa kusa da zuciyar ki ko? Kamar wata gaula haka na gyad'a mata kai ina fad'in"Ban san meyasa ba. Ina yawan tuna shi sannan ina jinsa sosai a cikin wani lungu acikin zuciyata." Ramatu yar dariya ta yi kafin taje ta zauna ta na fadin"Fata na Allah yasa shima ya na jinki a cikin zuciyarsa kamar yadda ke ma kike jinsa." Sai alokacin na Fahimci inda ta Dosa da Sauri nace"Ke ba fa wannan ba. Kawai taimakon da ya yi min ne yasa na kasa manta alherinsa." Ramatu tace"Nima na sani." Daga haka bata kara mgana ba ta bar ni ina Tunanin mganarta. Ramatu wai ta na Tunanin Ina son ASSADIQ Ne? Tuna haka yasa sai da gabana ya fad'i Haramun ne na so wani acikin Rayuwata in dai zan yi duba da Halin da ni ke ciki to aure ko soyayya ta Haramta a gareni ni Hasiya. Kawai girman Alherinsa na ke Tunawa tare da kirkinsa natsuwarsa da taimakonsa zuwa garemu yasa zuciyata ta bashi waje na musamman. Ammh ni kaina nasan Assadiq ya fi karfina ko a kafad'an gwada tsara bazan iya tsayawa da shi ba. Saboda na kauda Tunanin haka acikin Zuciyar Ramatu yasa na kalleta ina Fad'in"Kin samu Labarin Salisu kuwa? Ya jikinsa? Ramatu tace"mun yi mgana da Musbahu kwanaki yace da sauki ya na tafiya da Sanduna guda biyu." Kai na gyad'a a hankali kafin nace"Allah ya kara masa lafiya." Ta amsa da Ameen. Daganan muka yi shuru kowa na ta sake sake, ita daga baya Mijinta ya kirata sai na fita na ba su waje suna mgana ta waya. Sai Dare Ramatu da Inna Talatu suka tafi da Niyar sai jibi in zamu wuce za su zo sallama. Gabadaya mun gama had'a kayan mu. Adda tace komai kada mu bari Isuhu zai dawo gobe ya samo mana motar da zata kwashe kayan duk da ba su da wasu yawa. Habiba kuma aranar ta had'a kayanta Adda Fati da tazo suka tafi Tare sai Murna ta ke yi. Ammh da niyar gobe in zamu tafi za su zo mu yi sallama da Safe. Matan gidanmu da makota sai jajanta Tafiyar Amma suke yi. Sabo shi a ke yi ma kuka daman duk sai suka ji ba Dad'i muma haka. Mun kwana da shirinmu sai ga shi Allah mai sauya lokaci Da safen Isuhu ya kira Adda a waya yace matarsa na kan gwiwa zata haihu tun daran jiya ya kawota asibiti shuru har lokacin bata Haihuwa ba. Kuma ba kowa a wajenta ba yar garin ba ce yar kwanar farakwai ne da ke nan kaduna. Jin haka yasa sai Hankalin Adda ya tashi ta yi shirin tafiya mu kuma tace zata je ta gani in an sauka Lafiya Isuhu zai dawo ya tafi damu. Har acikin raina ban dauka wani Shafin kaddara rayuwa zata kara Bud'emin ba. Sai ga shi ko da yan Sallama su ka zo Adda ta kusa isa gida ma. Mu kuma muna nan bamu tafi ba sai dai kawai su ka sha yinin su tare damu Ramatu na ta murna harda addu'an Allah yasa Adda ta fasa tafiya ta hakura ta barmu anan. Amma kuma acikin ranta addu'a ta ke yi Allah ya sa wannan tsaikon da aka samu Mafitan da ta roki Allah ne ya fara sama mata ta yi ta addu'an Mafita a wajen Ubangiji ga Hasiya ba ta son ta tafi da ita ammh in har Hasiya ta samu inda zata zauna na Har Abada zata koma gaban Adda ta zauna cikin salama har mai kasancewa ta kasance tare da ita. Ba zata rika kwana cikin Fargaba da Damuwa ba. Habiba dai tunda Adda Fati ta riga ta tafi da ita bata dawo ba sai ya rage daga ni sai Amma. Tunda nasaka tafiyar a raina sai na cire sana'ar Danwake a raina tun ballatana da Assadiq ba ya nan sai sana'ar ta fita raina. Sai dai ana ta zuwa neman Danwaken sai nace ma Maman boy ko zata fara yin Danwaken ne kada ma su siya su gudu. Nan da nan ko tace zata had'a jari ta fara, ni na zauna na nuna mata Tsarin komai sannan na bata shawaran ba sai ta tara jarin ba. Ta fara da kad'an a sannu sannu dai zata ga jarin nata ya taru. A rana sau d'aya na ke girki tunda dagani sai Ammah wani lokacin ma ba na yin girkin sai da Daddare da Safe ko Tea ko kuni mu ke sha sai Dare mu ke kara neman abinci. Tun tafiyar Adda ba mu yi waya ba tunda ba ni da waya sai da Adda Fati ta kira wayar maman boy mu ka yi mgana tace Adda ta ce a fad'a mana matar Jauro ta sauka mu duba Isuhu cikin Satin zai zo mu tafi tare. Tunda naji haka sai muka zama cikin shiri daman kuma ba mu wargaze duka shirin kayammu ba tunda ba fasawa muka yi ba. A daran muna zaune da Amma ina yanke mata farcenta tace"Hasiya ni ko kwana nawa Abubakar yace zai yi achan garin su? Kai Tsaye nace"Ban sani ba Amma. Nasan dai yace zai kwana biyu kafin ya dawo." Muka yi shuru dukkanmu ina ajiyar Zuciyar Amma sai kuma chan tace"Na so a ce yaron nan ya dawo ko godiyar irim Dawainiyar da ya yi damu na samu na yi masa. bazai ji dadi ba duk ranar da ya zo ya iske ba ma nan" Shuru na yi ban yi mgana ba saboda abunda ke raina ne Amma ta fad'a. Da safe mai gidanmu yazo Daman Amma ta aika a fad'a masa zamu tashi akwai ragowan kudin mu tunda bamu cike Shekara ba. Da ya nemi ya bamu ragowan kudin sai Amma tace ya barshi kawai mutumcin sa a gareta ya fiye mata komai alokacin duk in da muka je neman haya a hanamu a ke yi saboda Hasiya ammh shi ya ba su wajen zama tagode sosai Allah ya jikan magabata. Suka rabu cikin amimci ta na masa addu'a shima ya na yi mata Fatan alheri. Na riga na Sadakar tafiya ba fashi sai na saki raina kawai Acikin raina na ke jin shima Assadiq ya na daga cikin Mutumen da na ke had'uwa da su a rayuwata ammh kuma na d'an Lokaci ne zasu fita daga Rayuwata batare na so ba sai dai nayi addu'an a duk inda ya ke Allah ya biyasa sannan ina Fatan Allah ya had'amu a Darussalam. Ina da tabbacin a wajen Adda bazamu sha wahala ba tunda ta baro Rugga da jimawa domin isuhu ya gina gida acikin gari ya Daukota suka dawo. Sannan daman ya'yanta duk maza ne tafi Amma yawan haihu. Matan nata guda Biyu ne Halima(Tumba) sai Fatima( Baddo') da itace Auta yanzu a gabanta. Shiyasa na cire damuwa Assadiq a cikin raina ammh na kasa daina jinsa a chan kasan zuciyata. ****** GUSAU. Da gaske Sadiq ya ke yi da yace Hutu zai je gida ya yi. Saboda tunda ya zo ko kofar gida bai fita ba iyakarsa cikin Shashensa ko Shashen Innani ko Bakin get wajen Mallam Taju in za su yi karatu ko yan'uwansa da suka Damu da ya kai musu ziyara bai je gidan kowa ba. Ko bangaren Umma daman bai cika zama ba saboda su Sultana in ya na son mgana da ita ne ya kan shiga. Shashen Mama kuwa sai dai in ya shiga su gaisa. Daman bangaren Innani ne wajen zamansa kowa ya sani ba shi da in da yafi nan. Har acikin ransa ya na kaunar Tsohuwar nan duk ko da Tarin Rikice Rikcenta. Sai ko Shashen Abba in wani lissafin kud'i ya had'a su. Ko wata mgana da ya shafi Dukiyar Abba tunda komai Sadiq na da masaniya a kan su. Duka kaddarorin Abba da Filayensa tsabar kudad'ensa., Akwai ma wasu kaddarorin da Alhaji Sulaiman da Sunan Sadiq ya siye shi daga shi sai Sadiq sai Lauyansa Barrister Tafida suka sani. Ko Pin dinsa na akwatunan bankinsa duka Shekarar da aka haifi Sadiq ne mabud'in su. Yau ma tun safe Barrister Tafidan ya zo suna Shashen Abba suna lissafin kudade da zakkar da za'a cire wannan Shekarar. Abba na gefe komai da Sadiq a ke yi Tunda shine Dan boko. Wani Alfahari ke mukurkusan Abba in yaga yadda Sadiq ke sauya yare ya na Turance Barristet sannan ga Lissafi a kansa da kuma iya Sarrafa Na'ura. Haba duk wanda ke gidan SS SHINKAFI bai iya sarrafa Na'ura ba ai yaji kunya tunda kowa tasowa ya yi ya gansu agidan tunda kasuwancin Abba ne na tun Tale tale ne. Lissfin ya Dauke su har Yamma tunda Sadiq yasa Abba ya ware wasu kudad'e saboda yan'uwansa da ke kauye tare da yan'uwan Umma da Mama. Bangaran abincin gida daman na Shekara suke ajiye sai wata Shekaran kuma ta zagayo. Sai bangaran sauya motocin gida Umma da Mama suna da Motocin su sannan yara ma na da shi ta zuwa makaranta Abba kuma baya sauya Mota sai Sadiq yace ya kamata a sauya su. Sadiq kuma har yanzu ba shi da ko keke yace ba yanzu ya ke Ra'ayin Mota ba tunda shi ba mazauni ba ne. In fita zai yi ya fi bin Abba wajen harkokinsa ko ya Tukasa ko kuma Direba ya tukasa. In kuma zai shiga gari ne sai ya hau ta Umma wani lokacin d'ayar ta Abba ya ke hawa Benz dinsa baka da bai cika Fita da shi ba. Sannan yasa an ware ma ma'aikata na su albashin sai Hidiman makaranta su Siyama. Daganan sai aka cire Riban Shekaran sai kuma zakkar da suka fita Daman Abba yasan wad'anda ake ba ma Zakkar mabukata ne da takalawa yan'uwansa daman Sadiaq na so kason Dabam ya ke cire musu Abba bai isa ya ce Uffan ba. In magajin gida yace haka za'ayi Abba jiki na rawa zai ce ayi haka d'in magajin gida. Sai ana gabda mangariba suka gama Barrister Tafida ya tafi shi kuma yace bari ya koma Shashensa ya yi wanka saboda zuwa masallaci. Abba ma yace wankan shima zai yi yinin ranar duk anan suka yi shi abinci ma sai dai aka shigo musu da shi. Sadiq shashensa ya koma ya yi wanka ya saka Jallabiya bata kai masa kasa ba sosai sai ya saka wando baki. Tare da Abba suka tafi masallaci ba su dawo ba sai da aka yi isha'i. A masallacin ma ana ta neman taimako gyaran speeker masallaci Sadiq ya ce ma Abba za su ba da na su Taimakon. Abba yace ya ba da nawa yaga ya kamata yace Dubu ashirin za su ba da, Sadiq yasa Abba ya yi mgana da Liman suka ba da acct lamba za'a Tura musu sai godiya su ke yi daman in dai Sadiq na gari yaji ana neman tainmkon masallaci sai in da karfinsa ya kare. Suna dawowa kai Tsaye Shashen Innani suka nufa suka isketa ta na sallah sai da ta idar suka gaisa. Ta kalli Sadiq ta na fad'in"Magajin gida duk yau ban gan ka ba tun Safiyar Allah da ka shigo mun gaisa in jin dai lafiya ko? Kai Tsaye yace"Lafiya ta kalau aiki muka yi da Abba." Sai ta washe baki ta na fad'in"Au ho to Allah ya yi albarka." Abba ne ya zauna yana karanta ma Innani abunda suka cire na kudade. Ta na jin ance an cire ma Mama da yan'uwanta ta tabe baki kafin tace"Daman kwadayyayu ne ba domin Allah Suwaiba ta auri Sulaimanu ba." Sadiq ya yi dariya kafin yace"Ke da ki ka ce d'an ki ba mai kudi ba ne Rufin asirin Allah ne,.Kuma wata mgana ki ke yi haka Innani.? Kai Tsaye tace"Uhm to karya nayi? Ya na da kudin ne ba domin Rufun Asirin Allah ba, kaima kasan komai akan Suwaiba da Danginta yi shurun ka Magajin gida." Sadiq ya gyara zama ya na fad"in"Koma menene wannan ya wuce innani. Mama matar Abba ce sannan sun tara zuru'a atsakani ya kamata ki iya bakin ki, Suma jikokin ki ne kamar yadda mu ke jikokin ki. Ba kyau ki na nuna wariya Hakan ba Daidai ba ne." Innani sai ta yi shuru taki mgana. Ya na kallonta yace"Baki ce min kin bari ba yar kakata mai kyau? Innani ta washe baki kafin tace"Na bari magajin gida mganar ka ai itace akan gaba." Mirmishi ya yi bai ce komai ba karamar wayarsa ya ke dubawa d'azu Tahir ya kirasa bai dauka ba ya bari sai ya natsu sai ya kirasa. Shigowar Umma da Mama ya katse Mganar da Abba ke fad'ama Innani. Kasa suka zauna suna gaishe da Innani ta amsa kai tsaye. Sadiq ya juya ya gaida iyayen nasa su kuma suka yi ma Abba sannu da gida. Batare da damuwa ba Sadiq yace"Umma yaushe zaki je Gummi? An ware mu su na su zakkar. Ke ma Mama har da na wajen naki." Mama ce ta fara fad'in"Angode Allah ya kara girma." Umma kuma cewa ta yi"Tunda kana nan sai kaje ka kai musu daman Mallam sai mganar ya ke yi nace baka dawo ba." Innani najin haka ta yi Zaraf tace"Ni ma zani na jima ban je mun gaisa da Mallam Zakari ba." Sadiq ya kalli Innani cikin mamaki kafin yace"Ba inda zan je da ke. Kalle ki fa tafiya ma dakyar kike yi ammh da kin ji zencen yawo jikin ki na rawa." Innani na jin haka kawai sai ta fara Sharan kwallah ta na fad'in"Ai Shikenan sai na hakura. daman na so na sada zumunci ne." Abba na jin haka ya kalli Sadiq ya na Fad'in"Magajin gida ka tafi tare da ita tunda ta na son zuwa." Sadiq ya kasa mgana shi fa ba zuwa da Innani ba Fad'i ba'a tambayeta ba. Innani na jin Abba yace a tafi da ita ta washe baki ta na Fad'in"Bari na kira Sulsana ta had'amin kayana a jakata kwana nawa zamu yi ne magajin gida? Baki ya Bude kafin yace"Ba kwana zan yi ba. Sai dai ke in zaki Tsaya ki kwana." Ya fad'a kai Tsaye Innani tace"Kaji min Sharrin yaran zamani. Ina laifin mun kwana dangin duk su zo su ganka ayi zumumci." Sadiq ya mike ya na fad'in"Innani ba zamu kwana ba shikenan." Innani rai ba dadi tace"Shikenan..salamatu Allah na gani na so na sada zumumci Magajin gida yace a'a." Ta fad'a ta na wani gyara zama gilashinta kamar ta Allah. Abba ne ya ke tambayanta wayarta ya daina ganinta kwana biyu. Innani ta karkace baki tace"Allah dai ya Tsine ma barawo da uwar barawo an sace ta. Tun kwanaki na daina ganinta ballatana ihun nan da ta ke yi in ana kirana." Sadiq da ya so ya fita sai ya fasa ya Juyo ya na kallon Innani ya na fad"in"Wai ke tsohuwar nan bakya jin mgana ko? Ba na hanaki Tsine ma mutane ba? Ki tsine ma ya'yan wasu da jikokin wasu mu ma wasu su tsine mana." Da Sauri Innani tace"Arr. Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu. Jikokina y'an albarka ne haihuwan Sulaimanu haihuwan kwarai." Kai kawai ya girgiza ya fice ya na fadin"Umma ina bangaren ki." Da toh ta amsa shi. Shi dai na ya bar su da Innani ta na musu wani Toshon Tarihi tun Abba na yaro irin labaran Innani kenan in ba labarin Abba ba, Labarin kowa a wajenta bamai kyau ba ne ta kan ba da shi ba wani ma yasan harda karin maginta. Sanda ya shiga Falon Umma ba kowa sai tashin kamshin Turare. Kan d'aya daga cikin kujerun falon ya zauna ya Dauko wayarsa ya kira Tahir Sun jima suna mgana har ya ba shi Hajja suka gaisa ta na tambayan Innani yace yanzu ya baro bangaranta. Shi fa ya kiyaye had'a Innani waya da Mutane in ta shiga Surutun da ba'a saka ta ba sai ta kunyata Mutane. Kafin su yi sallama sai da Tahir yace yaushe zasu koma zariya. Sadiq ya yi shuru kafin yace zai fad'a masa in ya saka rana. Bayan ya gama wayar ya koma ya kishigid'a saman kujeran Umma hankalinsa ya koma kan Tv a tashar Mbc3 Cartoon. Ya na mamakin waye ya ke kallon Cartoon Umma da ba ta da yara sai kamar an yi masa wahayi ya ce"Sultana." Kamar ta na jinsa sai ga ta ta fito daga Daki dauke da karamin Kofin Tangara a hannunta kamar kitchen zata je. yadda ta fito kanta Tsaye yasa yasan bata san ya shigo Falon ba. Duk da tasani shima ya san alaqarsu ta wuce ta yaya da kanwa ammh ba wani sakewa Tsakaninsu. Illah girmamawa da Sanin Darajan juna bai taba wani Hira da Sultana ba bayan gaisuwa ko Hiran makaranta. Har ta kawo Tsakiyar falon bata gan shi ba shi kuma sai ya yi lamo ya na kare mata kallo. Doguwar rigar jikinta ta Roba ce ta Lafe ajikinta abunda ba dabi'arsa bace yau ya yi kallon Sultana Tundaga samanta har kasanta. Ido ya waro ya na kallon manyan kaya wajen karamar yarinya. Sultana ta na da cikar kirji duk da siririya ce daga kasanta ta na da Fad'i Fuskarta ya kallah ta na da cikar Fuskar sannan kafafunta da hannayenta suna da kauri ba kamar na HASIYA BA. ashe abun ba Shekaru ba ne tunda Sai yanzu yasan Hasiya zata girmema Sultana ammh ita ba ta da komai. Bai taba ganinta ba Hijabi ba ammh acikin Hijabin ya ke ganin komai nata ba babba ba ne karami ne. Yaji matsanancin kunya Lokacin da Sultana ta kamasa dumu dumu ya kura mata ido. Sai da yaji muryanta ta na Fad'in"Ina yi ni ya Sadiq" Sannan ya dawo cikin hayyacinsa. Basarwa ya yi da sauri ya na amsa mata. Ya na gani ta wuce kitchen a kunyace duk yadda ya so kada ya bita da kallo sai zuciyarsa ta rinjayesa ya bi bayanta da kallo har ta shige Kitchen. Sannan ya sauke ajiyar rai har da Sarke hannuwansa a saman kirjinsa ya na sakin mirmishin da ya ke fitowa daga kasan ran shi. Ta jima kafin ta fito kila ta na Tunanin ko zai tafi ne sai dai ta fito ta tarar da shi kunya take ji ya ganta ba Hijabi. Ko da mganar aure a tsakanin su Umma bata barinta ta na zama kusa da shi ba Hijabi. Ta na kame jikinta ta fito kanta a kasa ta na wasa da yatsun hannayenta. Daki ta ke shirin komawa ya sa ya gyara zama cikin muryan kasala ya kira sunanta. "SULTANA." Tsayawa ya yi kafin ta juyo ta na kallonsa da kai ya yi mata mgana kafin yace"Zo nan." Kamar tace Bari ta Dauko Hijabi sai kuma ta fasa shi ko aransa mamakin yarinyar ya ke duk da ba shi da Dabiar yawan kallo ai bazata ce bai santa ba yarinyar da ya sani Tun tana jaririya. Kujeran gefensa ta zauna ta kasa kallonsa daga gani a matukar takure ta ke. Sai da ya sha iska sannan ya kalleta yace"Kun gaji da zaman gida ko? Da kai ta amsa masa bai damu ba ya cigaba da fad'in"da an koma Hutu zaku fara zuwa makaranta in sha Allahu ke da Siyama." Cikin murnan da ya bayyana akan Fuskarta tace"Allah ya kai mu." Ya na kallonta kai Tsaye yace"Sai ku dage da karatu ban da wasa. In naga kun maida Hankali wata Shekarar sai a siya muku wayoyi ko? Da Sauri ta Dago kanta ta na washe baki tace"Da gaske? Kai ya gyad'a mata kafin yace"In sha Allahu." Hakoranta sai da suka bayyana awaje daga gani taji dadi. Cikin mamaki yace"Kina son waya ashe? Wa zaki rika kira? Cikin jin dadi tace"Baba da su Ma'u" Bude ido ya yi ya na fad"in"Ku kad'ai Sultana? Sai ta gyad'a kai alamun eh. Cikin marairacewa yace"Ban da ni ko? Shikenan.". Sai taji kunya ta Rufe Fuskarta da Tafukan hannayenta ta na yar dariya Lokaci daya tace"Kai ma zan rika kiran ka." Tabe baki ya yi kafin yace"A'a ai mganar Farko sarki ke fara kamawa. Na gane kin fi son Baba da Ma'u a kaina shikenan na zama maraya Sultana bata so na." Ba zato ya ji tace"Kai ma ina SONKA wlh." Sai da ya kalleta ta san abunda tace ai da Gudu ta tashi ta shige daki. Bai san Lokacin da ya kyalkyace da Dariya ba. Yarinta akwai dadi cikin lokaci ya yi mata wayau ta fad'i abunda ke ranta. A fili ya Furta"Sultana ta fi Hasiya Auki." Sai kuma da ya fad'i sunan Hasiya ya yi tsam me yasa ko lissafin zai yi sai ya kawo sunan Hasiya? ya na kuma da Tabbacin ba ta inda Sultana zata iya Had'uwa da Hasiya. Ko da Allah zai had'a su ta sanadin ka? Saboda jiran Umma yasa bai koma bangaransa ba. ita kuma Sultana Tunda ta gudu bata dawo ba. Sai chan da jimawa Umma ta shigo ba su jima suna mgana ba gajiya ta sauko masa yace zai je ya kwanta. Ammh sun bari akan gobe za su tafi Gummi shi da Innani tunda yace ya kusa tafiya. Baisan bayan Innani har da Sultana za'a tafi ba sai da safe bayan sun shirya ana zuba kayan abinci acikin Booth din mota. Innani ta sha lullubinta da kayanta ma su kyau da wani faskeken gilashinta. Har da uban kaya domin ta rantse ita sai ta yi kwanaki. Sai da yaga Sultana ta shirya itama Dauke da Jakar kayan Innani tun wacce taje Saudiya ne. Yadda Innani ta ke ji da jakar nan ana tabata sai Tsine tsine ya fara tashi. Ciki Sultana ta saka kayanta kala Biyu. Umma ke fad'amai Sultana tace itama Zataje shiyasa tace ta shirya. Ko mgana bai yi ba yana ji ta na gaisheshi ya amsa a tamke kamar ba shi ba ne jiya ya sake da ita ba. Kafin su tafi sai da suka kara samun wata abokiyar tafiyar Siyama tace zata je Innani tace ta shirya Salima dai ita da Mama za su tafi Gidan su acikin gari. Sadiq na gidan gaba Innani da jikokinta na baya gabadaya ta cika Motar da Surutunta kuma komai tagani a hanya sai tace an Tsaya an siya ko gajiya da ciye ciye ba ta yi. Takaici yasa Sadiq bai yi mgana ba har suka isa Gummi. Gidan su Umma babban gidan ne mahaifinta malamai ne a garin. Mahaifiyarta ta rasu ammh Babanta Mallam zakari na nan da ransa da Inna Meri matarsa. Da ya ke an san da zuwan su sun samu Tarba shi dai Sadiq ya na dakin Mallam zakari suna Hirar jika da kaka su Innani na cikin gida. Sai da suka natsa sannan ta shigo su gaisa. Sai ga Innani ta zauna ta na rattaba bayanin ta so ayi auran su bad'i nan ammh Sadiq yace sai ya samu masta dinsa sannan za'ayi auran. Mallam zakari yace"Me wani masta kuma Dije? Aure ai sunnar ma'aiki ne tunda yara sun hada kansu me ake jira? Kai Saddiqu ko baka so ne na shiga cikin Layin nameman daman fin karfi ka yi min" Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba. Innani ta saka ana la'asar suka kamo Hanya shi da Direba. Duk wanda ya shigo sai ta nuna sa shi da Sultana ta kuma ba da labarin komai Tun daga Tushe. Da zai tafi yace yaushe za'a zo a Dauketa ya na so su je shinkafi kafin ya koma. Innani tace sai yadda tafiya ta yi da su, Tunda yanzu sha'anin Tafiya na Allah ne. Yana jin haka ya kama kanshi shi da Direba suka Dauki Hanya Shima Mallam zakarin irin Innanin ne biye mata ya ke yi su ta yi basa gajiya. Shi dai tunda ya ba su sakon Abba ya sauke nauyi suka kamo hanya sai mangariba suka iso Gusai. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki. *19* Koda su ka dawo babu Innani ba wanda ya damu sanin halinta. daman tunda aka ganta da wannan uwar jakar an san sai ta hantse zata dawo. Kuma daman ta na son garin su Umma tunda Mallam zakari da iyalansa suna biye mata shiyasa ta ke matukar son zuwa garin Gummi fiye da zuwa Shinkafi. Sadiq ya na so ya koma cikin Satin nan mai shiga daga kamfanin da ya ke Hidimar kasa sun kirashi. Shiyasa ya shirya tafiya shinkafi ya jima sosai bai je ba tun wani rashin Lafiya da mahaifin Sultana ya yi ya matsa ma Abba suka je tare kuma za'ayi shekaru biyu da faruwar abun. Wannan karon ma yace Abba ya shirya su tafi ba shi ta cewa illah Toh. Yaje Gummi da kwana uku su ka tafi Shinkafi shi da Abba. Tafiyar ta su da Sassafe ne saboda a ranar zasu dawo ba za su kwana ba. Gidan Baba Sammani suka fara sauka aka rika ina za'a saka da su. Da kansa ya aika ma su Hussau sai ga su kowacce ta zo gaishe da Abba. In kunga yadda su ke girmama Sadiq ko Abba albarka. Ga shi matashi ne ammh yadda su ke kallonsa ya wuce tunanin shi. Dalilin Sadiq yasa Abba ya yi ziyara sosai a garin Shinkafi. Sannan ya kuma Fitar da kudade. Tunda aka ji yazo garin mutane sai zuwa su ke da bukatun su. Su Baba Sammani kuwa an ba su na su zakkar har da karin kudad'en da Sadiq ya ware musu. Kowa ya zo sai yace yaushe ne bikin Magajin gida da Sultana? Abba ke rattafa bayanin sai lokacin da Sadiq ya gama karatunsa ya baro Zariya gabad'aya. Gabadaya labaran daga bakin Innani suka fita Sadiq acikin ransa sai fad'i ya ke yi Tsohuwar nan bazata daina karya ba, ta tsufa ammh ba ta san Darajan Tsufan ta ba. Su ne har gidan su Sultana kowa ya san Sadiq Surukin gidan ne shiyasa karramawan da aka yi musu suma din dai duk mganar Innanin ne na bikin Sadiq da Sultana. Nan ma Abba ne ya yi musu bayanin ba yanzu ba in Lokaci ya yi zasu sanar da su. Sun jima nan suka yi Sallar la'asar su ka kuma ci abinci sannan suka yi shirin Tafiya. Sun kamo Hanya Booth dinsa cike da abubuwa irin ta mutanen kauye. irin su gyad'a aya da su kuka da kubewa,goriba da sauran su, suka baro Mutanen Shinkafi suna ta zamabad'a musu godiya tare da addu'an Fatan alheri ga Alhaji Sulaiman da Magajin gida. Ranar da suka dawo har washegari barci Sadiq ya yi ta sha ya na Hutawa duk da wayoyin yan'uwansa sun cika masa waya da kira suna rokon sa don Allah yazo gidajen su. Kowacce Burinta yaje gidanta kuma bai cika zuwa ba sai dai su suzo su same shi a gida. Gwara ma gidan Surayya tunda itace Big Sis kuma ta su tafi zuwa daya da Sadiq daga ita sai Sa'ima sai kuma Shahida da ke aure a katsina ita in suka shiga katsina za su je Daura sun sha biyawa shi da Tahir. Sajida sakonsa ne domin Umma tace kwata kwata shekaru biyu ne a Tsakanin su. Bayan fad'a tsakanin Sako da Sako jininsu kuma bai had'u ba. Saboda Sajida na da Surutu da son jin gulma sannan ta na diban mgana sai ayi mgana da ita ta sirri sai aji ta a bakin wata a cikin su, Mace ce mai kishi da son komai ya zama ita kad'ai ta mallaka shi kuma Sadiq baya son halinta na Surutu shiyasa ba su cika Shiri ba, zai iya kirga saunawa ya taba zuwa gidanta duk da ta na kusa ba ta da nisa da gidan tsakaninsu bai wuce Naira Dari ba. Yafi yarda da Surayya fiye da kowa a dakin su da gidan su. Saboda ta na da kirki da kamewa sannan cikin Nasiha da Lallashi zata yi maka mgana har ka Fahimta. Ya na zuwa gidanta sosai barin ma in yazo garin Hutu ya jima. Shiyasa wannan karon ma ita kad'ai yace mawa zai zo mata kafin ya tafi. Ranar da ya cika sati biyu a garin Gusai ya shirya ya je gidanta. Umma kad'ai ta san ga inda zai je Abba ya fita da wuri Mama kuma bai shiga shashenta kafin ya wuce ba, innani kuma ta na chan bata dawo ba daga ita har su Sultanan. Umma ce ma da ta kira Mallam zakari tace a ba ma Innani su yi mgana. Bayan an bata sun gaisa ta tambayeta yaushe za su dawo? Innani tace uban wa ta ijiye a gidan Sulaimanun da za'a dameta sai ta dawo? Ita ba d'a ba ita kuma ba jika ba kada a dameta sai taga dama zata Dawo tunda Umma taji haka ta kama bakinta Sanin Halin Innani yanzu sai cibi ya zama kari in ma batace ta na so ta yi mata gorin gari tunda taga gidansu ne. Da ta fad'ama Sadiq karamin Tsaki yaja a fili ya Furta"ku kyaleta Umma ranar da ta gaji kuna zaune zaku ganta. Yaran nan dai su dawo saboda ana komawa Hutu zasu fara zuwa makaranta." Umma tace"Wa ya isa ya ce su Sultana su dawo Innani ta tsine masa." Sadiq kai tsaye yace"Ni na isa. Kuma zan kira mallam d'in da kaina nace a bata wayar na fad'a mata." Umma na Dariya tace"Sai dai kai d'in." Haka ya ke maida ma Surayya yadda suka yi da Umma da ta tambayesa Innani ta dawo? Shine ya ke gayamata yadda suka yi da Umma. Surayya ta yi dariya kafin tace"Innani Rigima. Ai in kaine bazata yi fad'a ba tunda Shalele ne." Bai yi mgana ba sannan bai ko yi mirmishi ba. Suna zaune ne a falon Surayya ta cika gabansa da kayan makulashe yaranta duka basa nan suna gidan kakaninsu na bangaran uba sun je Hutu. Daga ita sai yar aikinta a gidan sai zuwan Sadiq maigidanta sunansa D'aya da Sadiq wato Dr. sadiq. Dacta ne a bangaran ilimi. Ba iya a gidan su Sadiq ke da gata ba har a wajen mazajensu tunda har Sun haddace sunansa komai Sadiq ko magajin gida. Ballatana shi Sadiq da ya ke yawan zuwa gidan Surayya akwai Sabo sosai a Tsakaninsa da Dr.Sadiq Da wuri yaje sun dade suna Hirar rayuwa suna Tattauna wasu abubuwan da suka Shafe su na yan'uwa masu kaunar juna. Sai ta gangaro masa mganar auransa da Sultana. Kai tsaye ya kalleta ya na fadin"Big Sis aure na ba yanzu ba sai na gama bautar kasa, na kuma taba fad'a miki zan koma Masters dina. Kuma burina shine sai na Fara aiki kafin na yi aure.'" Surayya ta kallesa cikin mamaki kafin yace"Nan da shekaru nawa kenan? Sadiq ya gyara zama ya na fad'in"Ni bazan kayyade ba. Allah shi ke da komai Tsarin ne kawai na Dan adam. Surayya ta katseshi da Sauri lokaci d'aya da fadin"Mu kuma har muna cewa nan da Shekaru uku lokacin Sultana ta gama makaranta." Mirmishi ya yi kafin yace"To ki yi fatan na samu aiki kafin Lokacin." Surayya na dariya tace"Aikin me? Kai ai dan gata ne dukiyar da Abba ya tara maka kila Har ya'yan Jikokin ka ma sai su iya ci" Ido ya zaro ya na kallonta kafin yace"Kudin Abba ba kud'ina ba ne big sis. Kudin Abba amfanina da su shine na yi karatu na tsaya ga kafafuna." Tasan ya na da Tattausaran Ra'ayi ammh bata taba zaton Ra'ayinsa ta wannan bangaran ya yi tsanani ba. Kai tsaye tace"Wannan ba matsala bace ko baka samu aiki ba sai ka cigaba da Tafiyar da Business din Abba na shigowa da Cumputers" Sadiq yace"A'a ni kasuwanci baya burgeni. Ku barni na tsaya da kafafuna a bisa ra'ayina." Surayya ta lamgwabar da kai kafin tace" mu dai kada garin tsayuwa da kafafunka wata ta zo ta yi ma kanwarmu kafa fa Autan Umma." Dariya ya yi har sai da Hakoransa Farare suka bayyana. Cikin Tattausan lafazi yace"Baku yarda da kan ku ba kenan? Surayya ta bushe da Dariya kafin tace"Wa ya fad'a maka? mun yarda da kanmu shiyasa muka ce a bari sai kanwarmu ta kara girma mun koya mata komai ta yadda zamu kama Autan Umma a hannu ba wacce kuma ta isa ta nuna mana yatsa." Shi dai dariya kawai ya yi bai yi mgana ba ita kuma ta cigaba da fad'in"Ni fa tsoro ma na ke yi kada wata yar zariya taga dogo autan Umma Shalelen Innani ta lafe maka mu muna nan hamgame da baki." Sai a wannan karon yace"To miye? In naga ta yi min sai na aureta." Surayya ta bude baki kafin tace"Ka aureta kuma? Kai Sadiq fita daga idon mu." Ya na yar dariya yace"To ai naga ni ba Mijin Sultana ita kadai ba ne. Ni sadiq mijin Mace ne har guda Hud'u." Surayya tace"Uhm ai fa." Ta fad'a ta na mele baki. Mirmishi ya yi kafin yace"Yes kin ga ko bayan kanwar ku akwai wajen mata uku so gwara ku bi a sannu." Surayya tace"Mu zamu cike gurbin wajen mata ukun in sha Allahu." Sadiq yace"Zaku iya? Surayya tace"Sosai ma." Sadiq na dariya yace"Shiyasa ki ka hana Dr kara aure ko? Ke kadai ki na wahalar da shi ko? Fari ta yi da ido kafin tace"ni ban hana shi kara aure ba. Gurbin sauran matan ne na cike masa kaga kenan baya bukatar kara auran" Nan fa suka fara musu ya na cewa ta sakar ma Dr. Kanbun da ta daureshi ya kara aure ita kuma ta na rantsuwan cewa ita bata hanashi kara aure ba ya yo auran ya gani ko a jikinta ita dai Tunda tasan kanta kishiya in dai ba ta karkashin kasa zata bi bazata taba kada ita ba. Da ta ga ya dage ne kawai sai ta karkace baki ta na kallon shi kafin tace"Tsaya Tsaya. Wai ko ka samu wata ne a zariya ka ke min sharan Fage? Wannan karon sosai ya yi dariya kafin yace"In na samu wata a zariya ai ba na bukatar wani sharan Fage Big Sis. Ina ce ni ne mai auran kuma naga shi auran Sunna ne da Ra'ayi ba na Tunanin in ina Ra'ayi wani zai iya Dakatar da ni." Surayya ta kura mishi kafin tace"Ka tabbatar ba wata ko Sadiq? Kai Tsaye yace"Wlh ba wata Bigs Sis in da ita da tuni kun sani." Sai alokacin ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Yaushe zaka baro zariyan nan ne? Kai tsaye yace"Nan da wata shidda. Ko kilama na yi masters dina achan." Surayya ta zaro ido kafin yace"A'a wlh bamu yarda ba. Tunda bakasan waje ga BUK ta garin kano" Kai Tsaye Sadiq yace"Ni kuma Duk wata makaranta bayan ABU ne a wajena Big sis." Cikin mamaki tace"Na rasa me ka ijiye a garin nan ne Sadiq baka san barin shi ko sultanan ma chan zamu kai ma maka ita? Sadiq ya yi shuru kafin yace"A'a." Tabe baki ta yi kafin tace"Allah yasa da gaske ka ke yi." Dariya Sadiq ya yi kafin yace"Da gaske na ke yi ma in nagama abunda ya kaini dawowa zan yi nan ne asalina Big sis. Sultana kuma in da na samu aiki nan zan ijiyeta." Jin abunda yace ne yasa Surraya taji dadi suka cigaba da Hira. Yana gidan har bayan La'asar ya na ma shirin tafiya sai ga Dr ya shigo. Sai ya tsaya suka gaisa har ya rika jansa da Hira da yasa ya bata lokaci sai gabda mangariba ya fita. Da d'aya motar Abba yaje ya shigo anguwan kenan aka kira sallar mangariba sai da ya tsaya ya yi sannan ya karaso gida. Akwai sakon Umma Dambun kaza ita da Mama sai na Abba kuma yamball ne. Shi kuma na shi pepe chicken ne abunda ya fiso tace in zai koma ya gayamata ta yi masa kayan Fulawa ya tafi da shi. To a daran Tahir ya kirasa yace gobe zai dawo Zariya. Ganin shi bai shirya ba yasa yace ya fara yin gaba shi sai jibi sai ya dawo da haka suka rabu. Sai da Safe da yaje shashen Umma ya gaisheta ya sanar da ita gobe zai koma Ita ta kira yan'uwansa ta sanar da su tafiyarsa. Zuwa Dare sai ga sakonnin su dukkansu har Sajida ita Dambun nama ta yi masa mai yawa sauran kuma kayan Fulawa ne soyayyan Nama tunda susan ya na so. Umma kuma ta yi masa miya mai yawa daman ita ta saba yi masa mama ta saka Salima ta yi masa Cookies da yawa na tafiya tunda yace in ya tafi zai jima bai dawo ba. Innani dai bata dawo ba har ya tafi Abba 100k ya saka masa ta acct dinsa bayan Direba ya kaisa har zariya. Da kaya niki niki tunda harta kayan abinci da su Ruwa da Drinks da su ya ke tahowa daga gida tun baya Dauka Umma ke matsawa ya ke tafiya da shi. Wasu kayan maggi mangyada Duk Umma ke sakamai sai ya je ne ma in Tahir na duba kayan sai yace abu kaza ne da kaza ne shi tunda ba Dubawa ya ke yi ba. Ya dawo zariya daidai ya yi kwana sha shidda baya nan ya iske Tahir da yadawo ba abunda ya yi sai ma Datti da ya karama Dakin dole ya Tube ya gyara Dakin sai Dare ya gama wanka kawai ya yi ya kwanta. Koda ya tashi Tahir ya dafa musu Farar shinkafa sai suka ci da miyar nan da Nama. Sai da suka je sallar Isha'i suka dawo sannan suka zauna saman Hira. Tahir na ba shi labarin yadda yaji dadin zuwa gida hutu da sakon gaisuwarsa Sadiq daga Hajjo da Sauran yan'uwansa. Tahir ne ya tambayi Innani shi kuma ya fad'a masa ta na Gummi gidan su Umma har ya dawo bata dawo ba. Ranar raba dare suka yi suna Hira kafin su kwanta da gari ya waye kuma da wuri suka tashi suka yi shirin fita wajen aiki. Sadiq ya zo da sabbin T.Shirt da Jeans daga gida harda Sabbin Yadika dikkaku da Shaddodi kayan da ya tafi da su bai dawo da su ba Shinkafi ya tsinta yaje da su ya bama su Goggo Husai yace ta bama ya'yansu tunda kayan su chan sai a hankali. Sabbin da ya zo da su rabi ya raba rabin kuma ya ba ma Tahir daman ya na masa haka ya karb'a ya na ta godiya. Tare suka fita saboda sun makara yasa suka hau mashina kowa ya nufi inda za shi. Sadiq ya riga Tahir dawowa yau shiyasa har sai da ya yi wanka sannan Tahir ya shigo. Shi ya Dafa musu macaroni da wake suka ci da Miya suka kora da lemu da Safe Tea suka sha da Cakes har kuma Diba Suka yi da za su fita. Sadiq ya fara d'iba Tahir ma ya gani shima yace tunda zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai bari shima ya D'iba. Sai da sukaje masallaci suka yi sallar la'asar suka dawo sannan Sadiq ya sauya kananun kaya jikinsa zuwa wani yadi mara nauyi. Tunda Tahir yaga haka ya sha jinin Jikinsa kai tsaye ya kallesa ya na fad'in"Ina zaka je? Kai tsaye yace"Gidan su Hasiya" Tahir ya yi shuru batare da ya yi mgana ba jin haka yasa Sadiq ya juyo daidai ya na fesa Turare ya ke fad'in"Ko zaka rakani ne muje tare? Sai da Tahir ya ja karamin Tsaki kafin yace"Allah ya tsareni." Sadiq ya yi dariya bai ce komai ba ya gama fesa Turarensa ya zura Hula sannan ya zo wajen ma'adanan takalmansa ya Dauki wani baki Budade ya saka lokaci d'aya ya juyo ya na kallon Tahir Kafin yace"Sai na dawo." Har ya fice Tahir bai ce masa komai ba ammh ko dannan wayar da ya ke yi alokacin ya dakatar. Har ga Allah ya dauka Tafiyar su gida yasa Sadiq ya manta da wannan zabiyar yarinyar ashe ashe bai manta da ita ba. Har Sadiq ya fice ya na chan ya na saka Tunanin yadda zai raba Sadiq da wannan yarinyar da ya ke tabbacin mayyace daga labaranta marasa Dad'i. ******* Har acikin raina na cire rai tare da Tsammani zan kara had'uwa da Assadiq. Shiyasa har acikin raina ban kawo ma tunani zan kara ganinsa ba. Na riga na sakama rai na zan bar wannan muhallin zuwa wani waje na dabam. Duk da har lokacin Isuhun bai zo ba bamu kwance shirin mu ba Tunda Adda Ta tabbatar mana da cewa zai zo kuma zai taho damu. Musan yanayin Rayuwa ballatana kuma da ga shi an masa haihuwa akwai tarin Hidima a gabansa. Adda ta sake kiranmu tace mu zama cikin shiri ko gobe ko jibi Isuhu zai zo mu tafi satin chan da ya fita abunda yasa bai samu zuwa ba matarsa suka mayar asibiti daga baya jini ya balle mata ammh taji sauki har ta koma gida Adda na kula da ita. Tunda Habiba ta koma wajen Adda Fati ni kuma na zama shuru shuru tunda ba Danwake na ke yi ba. Sai ya kasance ba na fita tsakar gida sai in ko zan yi girki ko kuma zan Dafa mana Ruwan zafi gabadaya komai na Rayuwar ne ya daina min dadi. tuni Maman boy ta fara sana'ar Danwake ni na fara kwaba mata ranar farko ga shi har ta kware. Kuma mutane na siya duk da wasu in akace musu na daina Hakura suke yi saboda sun fi son nawa. Ammh duk da haka ta na samun Ciniki daidai gwargwardo. Yau tun safe da Fad'uwar gaba na tashi ko mgana akayi sai naji gabana ya ba da wani Ras! Har sai na fad'a ma Amma tace na karanta Falaqi da nasi da Ayatul kursuyi kafa uku uku da Amanar Rasuli. Shawaranta na bi na karanta sai abun ya yi sauki ammh Suku suku na tashi har ina zaton ko Ulcer dina ce ta tashi jin baya na da kugu duk ya rike, Kuma da Safen na sha mgani ammh jikina kamar an yi min duka ko Amma ta fi ni karfi da Kuzari. Ita na kai ma ruwa ta yi wanka ni ce ban yi ba saboda naji ba na ra'ayi. Da Safe kunu na dama muka sha da rana kuma na siyo mana Alala. Shiyasa na yini kwance kamar ruwa Amma dai har ta gaji ta kalleni bayan na idar da sallar la'asar taga na kara bin leda na kwanta tace"Hasiya lafiyar ki kuwa? Ina daga kwance nace"Amma ni yau bansan me ya sameni ba. Faduwar gaba da mutuwar jiki." Amma ta yi shuru kafin tace"To Allah ya sauwake." Nace mata Ameen a Hankali. Lumshe idanuwana nayi kamar baeci na son fizgata Amma na daga gefe ta na jan cashaba Naji muryan Salihi ya fad'o dakin mu ya na fad'in"Adda Hasiya ga mai siyan Danwaken nan da safe, a waje ya ce ki zo." Sai naji kamar a mafarki naji mganar da Sauri na Bude idanuwana. Sai dai ban tashi ba sai da naji Amma na fad'in"Ke Hasiya Abubakar ne inaga" Sannan na yi zaraf na mike jikina ba inda baya rawa. Da Hijabin da nayi sallah takalman Amma silafas na wajen na zura na fice da gudu. Ban zarce ko'ina ba sai kofar gida Fata na da Muradina na ci karo da abunda Zuciyata ta gama yanke kauna da sake gani. Shi ne ko yana Tsaye daga gefe rike da Hannun Datti da ya ke ta zuba masa uban surutu. Ganin fitowata da yadda naja na tsaya ina kallonsa ko Kiftawa ba na yi yasa ya zaro walet dinsa ya Dauko 200 ya bama Datti ya karb'a ya na ta washe baki da tsalle ya shige cikin gida. Da kansa ya kariso gabana hannuwansa duka zube cikin Aljihun wandon da ke jikinsa. Kallonsa na ke yi ko kiftawa ba na yi kamar wacce ta warke makanta. Shi kuma ganin haka yasa ya ciro hannunsa guda d'aya ya murza a saman Fuskata lokaci d'aya ya na fadin"Kin yi mamakin ganina ne? Da sauri na Dawo hayyacina sai kuma naji dariya ta kwacemin. Shima Mirmishin ya yi kafin yace"Baki zata zan dawo kwanakin nan ba ko? Daman nace miki bazan wuce sati biyu ba in ma na wuce bazan kai uku ba" Cikin shagwaban da bansan sadda ta kwace min ba nace"Ban zata zan sake ganinka ba ASSADIQ." na fad'a idanuwana na kawo Ruwa kai Tsaye yace"Da sai ku tashi ku koma wani garin Batare da kun jirani ba HASIYA.? Kallonsa na yi ina mamakin ina yaji labarin tashin mu sai ma Tuna Datti nasan bani da haufi shi ya fad'a masa. Rufe fuskata na yi da Tafukan hannayena ina yar dariya wani Farincikin da bansan daga ina ya ke Tunkudo'wa daga kasan raina ba. Cikin sanyin murya nace"Shiyasa muka kasa tafiya ko'ina har sai da ka dawo ka ganmu." Kai ya jinjina kafin yace"Ina Amma? kanwata Habiba ta na lafiya? Fuskata na bude ina fadin"Bismillah mu shiga." Ina gaba ya na baya har zuwa Dakin Amma bayan ya gaisa da matan gidanmu. Gulmammu kafim ma ya fara gaishe su su suke fara gaishe shi suna washe bakin munafunci da Gulma. Amma ma bakinta yaki rufuwa ganinsa a gabanta a duke ya na gaisheta ta amsa ta na fad'in"Abubakar idanuwanka kenan?har na fidda rai da zamu sake Had'uwa ga shi Hasiya ba ta da lambar wayarka." Kansa na kasa yace"Haka yaron chan ke fad'amin zaku tashi Amma" Amma tace"Wlh kuwa ba domin an samu Tsaiko ba da tuni muna chan da yanzu baka same mu ba." Cikin mamaki yace"Me nan gidan ya tada ku ne Amma.? Amma ta girgiza kai kafin tace"A'a wlh. Mu zamu tashi da kanmu" Shuru ya yi jin Amma bata warware mgana ba. Ni ina daga gefe ina Sauraransu sai ya waiwayo ya na fadin"Habiba na makaranta ne? Amma ce ta amsa shi da cewa"Habi ta koma wajen Fati da zama gabadaya." Cikin mamaki yace"Me yasa Amma? Sai da ta kalleni na wani Lokaci ni kuma sai na daga mata kai sannan ta jiya ta na fuskantansa tace"Saboda zamu koma mahaifata da zama gabadaya." Sadiq ya dago ya na kallon Amma kafin yace"Ina kenan? Amma tace"Gadan mallam Mamman chan hanyar kaduna zuwa Abuja." Ni ya kallah kafin ya kalli Amma lokaci d'aya ya na fadin"Har da Hasiya? Sai Amma ta kasa mgana Idanuwanta suka ci ko da kwallah. Ni ce na ba shi da amsa da cewa"Eh harda ni. Gidan Adda zamu koma yayar Amma ce can take da zama ita da iyalanta." Gabadaya Dakin sai ya Dauki Shuru shi bai yi mgana ba nima ban kara mgana ba. Kaina na kasa ina wasa da gefen Hijabin jikina kawai sai ji nayi Amma ta fashe da kuka da sauri na Dago ina kallonta a tare da ni da shi muka isa gabanta cikin rawan jiki da na murya muke tambayamta me ya faru? Amma ta kalleni hawaye Jage jage haka shima ta juya ta na kallonsa ko Kiftawa ba ta yi na tsorata na kalleshi shima ya kalleni a tare muka Dora hanmu a kaf'adan Amma muka girgizata kuma bakin mu a tare ya Furta sunanta. "AMMA.." Kuma a tare hannumuwan mu suka had'u waje d'aya sai da muka ji wani Zir kamar wutar lantar yajamu da kuma Sauri muka saki hannun juna. Amma ta kallemu kafin ta murmusa da haban zaninta take sharewa. Ni kuma na durkusa gabanta ina fadin"Amma baki da lafiya ne? Sai ta girgizamin kai shi kuma sai yace"Taba jikinta ko da zafi sai mu tafi asibiti." Ba gaddama na taba goshinta naji sanyi sai na juya ina masa motsi da ido alamun lafiyanta kalau. Kallona na maida kanta kafin nace"Amma me ya same ki? Cikin mirmishin karfin Hali tace "Bakomai Hasiya. Ina so ki bamu waje zan yi mgana da ABUBAKAR." Dagani har shi juna muka kallah cikin mamaki kafin na kalli Amma zan yi mgana kenan tace"Gaddama ba Halin ki ba ne Hasiya kada ki fara Daga yau." Jikina ne ya yi sanyi ina jin haka sai na mike shi na kallah shi kuma kansa na kasa daga gaban Amma inda ya Durkusa. Har zan fice Amma ta kira sunana na waigo kafin tace"Matso ma da Abubakar Darduman nan ya zauna dakyau." Ba musu ma matsar masa da shi gabansa yaja ya zauna ya tankwashe kafa ya na Fuskantar Amma. Ni kuma sai na fita waje na koma bakin kofar Maman Salihi na zauna. Wake take tsinta sai na saka hannu in tayata domin kada na zauna shuru Tunani ya yi min yawa. Kallona ta yi kafin tace"Bakon ya tafi ne? Bakinta washe cikin basarwa nace"Suna mgana da Amma." Sai ta shuru nima daganan ban kara mgana ba duk ko da suna sako ni cikin Hiransu sai kiji suna ko ba haka akayi ba Hasiya? Iyakata mgana da kai ko na yi gum suna ganina zaune ne ammh gabadaya Tunanina da Hankaluna suna dakin Amma ina Hasaso wani irin mgana ne Amma zata gayama Assadiq ya sa sai da tace na basu waje? Wata zuciya tace ya wuce Labarin ki" Daman nasan ai Tsatsuniyar gizo bata wuce ta kogi. Har aka kira sallar mangariba Assadiq bai fito ba. Ganin duk sun watse sun shige dakanunsu yasa na ari butar maman Boy na yi alwala na yi sallar mangariba adakinta. Ina cikin azkar naji na kasa natsuwa a Daddafe na gama na mike na fita. Ganin ba takalminsa kofar dakin Amma yasa nasan ya tafi. Da sauri na fad'a dakin Amma sai na yi Turus ganinta ta na sallar mangariba. gefenta na koma na zauna gabana naji ya na Di' di' Bakina kuma ya kasa Furta komai. ******* Tunda ya baro gidansu Hasiya ya fara ganin Duhu Duhu. Kansa ko da ya ke sara masa daman tun yana gaban Amma ya fara sara masa. Ko da ya iso dakinsu jikinsa ne ya saki kwata kwata kwakwalwarsa ta daina amfani ballatana ta kaisa ga wani Tunani na Dabam. Yaraf ya fad'a kan katifa ko takalminsa bai cire ba. Tahir na Dakin Ammah ko kallo bai ishesa ba ballatana ya fahimci halin da ya shigo, ya na jinsa ya fita ya je ya yi alwala yazo ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci ammh shi duk yadda ya so ya yunkura ya mike domin ya fita ya Dauro alwala ya tafi masallaci ya kasa. Gabbansa yaji kamar an sauke masa su ko'ina na jikinsa ya saki kamar ba shi da lakka ajikinsa. Kansa na sara masa ammh kuma kwakwalwarsa ta tsaya cak din da ya kasa Dora wani sabon Tunanin tun bayan fitowarsa daga gidan su Hasiya. Halin da ya ke ciki shi ake kira TSAKA MAI WUYA halin da ya kasa sarrafa Tunaninsa ma gabadaya. Tahir sai da tara ta wuce ya shigo Dakin yana jin tashin muryansa a waje yana hira da yan makaranta da suke zaune tare. Har kuma alokacin bai iya ko motsi da kafarsa ba. Yana jin Tahir har takasa ya yi ammh bai iya tashi ba. Shi kuma Tahir haushin Sadiq yake ji shiyasa ya yi kamar bai gansa ba. Da farko ya zata gajiya ce ta kwantar da shi sai da yaga bai je sallar mangariba sannan aka yi isha'i ma bai je ba sai yasan ba lafiya. Lafiyar Sadiq kalau baya fashin sallah Ko da ba shi da lafiya ne sai dai ciwon da ya kasa tashi shine zai hanasa zuwa masallaci. Sannan ya shigo yagansa yarda ya barshi da gangan ya takashi Saboda ya yi mgana ya Fahimci Halin da yake ciki ya ji shuru daganan yasan ba lafiya Kusa da Sadiq ya matsa ya na Taba kafarsa lokaci daya ya na kiran sunansa "Sadiq Sadiq. Kai Sadiq" Har Tahir ya fara tsorata ganin bai yi motsi ba sai kuma yaga ya juyo idanuwansa suna rufe bai bude su ba sannan bai yi mgana ba. Da sauri ya kara kiran sunansa ya na fad'in"Kana jina? Sai alokacin Sadiq ya bude idanuwansa da suka koma gauta saboda ja. Cikin Tsoro Tahir yace"Baka da Lafiya ne? Sai Sadiq ya samu kansa da Dagamai kai Lokaci d'aya ya na fadin"Ba ni da lafiya Tahir. Ba ni da lafiya." Cikin wata irin murya da ta kara Tsorata Tahir da Sauri yacr"Me ke damunka Zazzabi? Ya fad'a lokaci daya ya na Tattaba jikin Sadiq. Shi kuma sai ya kara mulmulawa saman kafita cikin nishi yace"Rufamin abun rufa sanyi nake ji." Jiki na rawa Tahir ya mike ya Dauko Bargon Sadiq ya lulluba masa ya na fadin"Maleria ce inaga. Ka dan huta zuwa anjuma sai ka tashi ka sha magani bari na fita na karbo maka a wannan chemist din" Bai jira cewar Sadiq din ba ya mike bayan ya zare ma Sadiq din takalmin kafarsa ya maida ma'ajiyar takalman sannn ya dauki kudi a jakarsa ya fita Lokaci d'aya ya na jawo ma Sadiq kofar dakin Sadiq ya dago ya na bin kofar da kallo kansa ya Dafe da hannu bibbiyu lokaci d'aya ya na fadin"Dama ace. Dama ace. Daman tun farko na fad'i gaakiyata da duk ban shiga wannan halin na Tsaka mai wuya ba." Ya karishe fad'a kamar ya fashe da kuka. A lokacin tunani da Hankalinsa ne ya ke jin ya rasa gabadaya. FAA'ALUL LIMA YURID LAIN YUSIBA NA ILLAMA KATABALLUHU LANA. Kuyi hakuri an samu kuskure a shafi na sha bakwai wajen Rubutawa, keyboard d'ina ke sauyamin Haruffan rubutuna. Da masu ganin Gusai suna tunanin wani gari ne, suma su kula Gusau ne ba Gusai ba. Nagode. *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *FATAN ALHERI DA SAKON GODIYA ZUWA GARE KU* *AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH)* *MARYAM JUMARE* *NANA HALIMA(MASOYIYA)* *HAFSAH HAFNAN(SAHIBATU)* _*Nagode muku bisa yadda kuka yi ta Hidima da wannan littafin, HasiyarAssadiq tace ta gani kuma ta yaba, Innani kuma tace dukkan ku Allah ya yi muku albarka Amin*_ *20* Sai bayan Fitar Tahir yaji wani mugun zazzabi ya kara rufeshi. Nan da nan ya fara rawan Sanyi Hakoransa na had'uwa waje d'aya. Kansa kuwa kamar zai Tsage gida Biyu Tsabagegen yadda ya ke sara masa, jijiyon kansa sun mike gabadaya Rad'au a saman kansa saboda Halin da ya ke ciki. Idanuwansa biyu Tahir ya dawo da magangunan da ya siyo masa. ba domi Tahir ya taimaka ya tada shi zaune ba ji ya yi kamar bazai iya ma tashi ya zauna da kansa ba. Tea mai kauri Tahir ya had'a masa yace bazai sha ba , shi kuma ya lallabeshi kan ya samu ya sha saboda ya samu sha mgani. Dalilin haka yasa ya sha kad'an ammh ji ya yi ba dad'i kamar ya na shan mad'aci saboda bakinsa da ya zama wani takaf kamar wanda ya yi shekaru cikin jinya. Tahir ya ballo masa magungunan Paracetamol ne sai maganin maleria d'in nan mai warin kudin cizo. Shi ba ya son magani ya fi shiri da Allura ammh Bala'in Tahir yasa sai da ya sha magungunan gabadaya sannan ya kyalesa ya koma ya kwanta Lokaci d'aya ya na kara taba goshinsa jin har lokacin da zafi. Ya dad'e barci bai daukesa ba ya na jin Tahir bi ni bini sai ya lekosa ya na masa sannu tun ya na daga masa kai in yajisa har wani wahallalen barci ya Daukesa mai cike da Tararradi da zullumi. Bai san haka ya yi barci sosai ba sai da ya farka cikin ikon Allah yaji zazzabin jikinsa ya sauka sai dai sarawan kan kad'an. lokacin da ya yunkura ya mike sai yaji ba jirin Tunda ga shi har ya iya mikewa da kansa batare da taimakon kowa ba. Tahir ya kallah da ya kwanta a kasa wayarsa na saman cikinsa kila wajen Dannan wayar ne barci ya Daukesa bai sani ba. Yasan ba shi da laulayin yawan ciwo sai ya jima bai yi ciwo ba, in ko ya yi Ciwo sai dai ko ciwon kai in ya yi Tsanani ne zazzabi shi Allah ya Tsare shi da ciwukan zamani irin su Ulcer ko Typiod. Jin ya samu karfin jiki yasa ya dibi Ruwa a buta bayan ya Dauki karamar wayarsa ya kunna Fitila. Ruwa ya zuba a karamar buta sannan ya yi addu'a ya bude kofa ya fita daidai lokacin da karfe uku na dare ta cika a wayarsa. Ba shi da tsoro daman Tahir ne ke tsoron Fitan Dare ba Sadiq ba shi da ko a gida ko karfe nawa ne zai iya fitowa Haraban gidan su in yaji wani motsi to anan ma shi ke raka Tahir in lalura ya tashe shi cikin Dare. Kai Tsaye makewayi ya haska ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito a tsugunna a kan damdamali ya yi alwala sannan ya koma Daki har Lokacin Tahir na ta barcin bai ma san ya tashi ba. Darduma ya shimfida bayan ya cire kayan jikinsa ya saka wata farar Jallabiya ta mutanen Saudiya. Yasan akwai sallar mangariba da isha'i da ke kansa ba shi su ya fara yi kafin ya mike ya yi salla raka'a Biyu ya jima acikin Sujjuda ya na ta addu'a sannan ya Dago ya yi tahiya ya sallame nan ma d'in ya jima ya na kirga da hannunsa kafin ya daga hannunsa sama ya na addu'a na tsawon wani lokaci sannan ya shafa. Bai koma kan katifar ba sai ya kishigid'a saman darduma ya na jin Kwakwalwarsa ta na shiga wasu Tunane Tunanen da a dazu kwata kwata ta tsaya cak. Iya hangen nasa ya gama Hango masa aikata Rokon Amma daidai ya ke da rasa goyon bayan wasu daga cikin Ahalinsa. In yace kuma ya shawarce su ya bata komai domin ba bu wanda zai rama masa baya acikin wannan Halin da ya ke ciki. A cikin zuciyarsa ya cika da Tausayinsu kuma ya na so ya taimaka musu ammh bukatar Amma ta yi tsauri ta kuma saka masa wani irin Dabaibayi ne mai wuyan fita. Ga shi ya riga ya furta tun farko shi maraya ne babu yadda za'ayi kuma daga baya ya sauya mgana. Tunanin mafita kwakwalwarsa ta Zurfafa aciki ammh sai dai har barci ya kwashe shi bai samu wata mafita mai kyau ba duk Mafitan da ya hango sai yaga bazata bulle da shi ba. Acikin barcin nan da ya koma sai ya yi mafarki ko nace kamar Allah ne ya nuna masa sakamakon zabin da ya mika garesa. Ganinsa ya yi a wani Daji ba gida gaba ba gida a baya. Shi kad'i ya na ta faman bulayi ya rasa hanyar da zata fitar da shi Kamar daga sama yaji an kwala masa kira ya na juya sai ya ganta wata Doguwar mace ammh kuma ta saka mayafinta ta yane Fuskarta ba ya iya ganin kamaninta sai dai kwayan idanuwanta. abun mamaki kuma da Tsohon ciki a jikinta. Ya na ganinta sai ya yi Saurin karisa gareta ya riko hannunta suka fara tafiya tare. Ba zato kawai sai ga Sultana ta sha gabansu ba ta tsaya ba ita ta saka karfinta ta raba Hannunsu waje daya ma'ana ta raba tsakaninsu ita ta shiga Tsakiyarsu ta jimke hannunsa ta ja shi suka cigaba da Tafiya. Waiwaye ya ke yi ya na kallonta ta na kuka ta na nuna masa bata da kowa da ita da abunda ke cikinta sai shi kada ya tafi ya barta. A cikin mafarkin yaga sanda ya kwace hannunsa acikin na Sultana ya ruga a wajenta ya riketa gam! Sultana na ganin haka sai ranta ya baci ta kara Dawowa zata rab'asu sai ba ta yi nasara ba, shi baisan ko daga ina ba ne? Yaga dai gabadaya yan'uwansa sun yi layi a gabansa da taimakon su suka raba hannayensu suka saka masa a na sultana shi kuma sai ya had'a da hannun wacce bai ga Fuskarta ba ya rike tare da na Sultana. Umma ce ta bayyana gabansa ta kwace hannun Sultana ta fara tafiya da shi sai sauran yan'uwansa suka mara mata baya. Yaga har da Abba shima bai bi bayansa ba ta karshen itace Innani ita ta jima a tsaye ta na kallonsu sannan ta juya ta bi bayan su Abba suka bace masa daga Daji nan da ba kowa daga shi sai wannan yarinyar da bai ga fuskarta ba. Gudu ya ke yi ya na ta kiran sunan Abba da Umma ammh ko me kama da su bai gani ba Sai yaji wata murya da ya na jinta yasan ya santa ta kira shi da karfi. "ASSADIQ.." Yana juyowa sai idanuwansa ya gane masa itace. Abunda ta yane fuskarta da shi ya yaye da kansa ta bayyana a gabansa ta na masa mirmishi. Har gabansa ta kariso ta dauki hannuwansa guda d'aya ta Dora saman cikinta sai yaji motsi kamar abunda ke cikinta ne ya motsa a fizge yaji kalaman ta" Ni da abunda ke cikina ba zamu taba barinka ba. Zamu zauna tare da kai sannan zamu tayaka dawo da sauran Ahalin ka." Hasken Fatar ta ya haske masa ido da yasa ya farka a firgice gabadaya jikinsa ya jike da Zufa. Cikin Fitan Hayyaci ya Furta "HASIYA." tabbas Hasiya ya gani da Tsohon ciki? Me wannan mafarkin ya ke nuna masa. Wannan mafarkin ya na nuna masa Zahirin abunda zai faru matukar ya aminta da bukatar Amma zai rasa Sultana sannan zai rasa duka Ahalinsa gabadaya. Sannan ya nuna masa amsa Bukatar Amma zai iya zama alheri garesa ammh kuma kafin cimma haka akwai tarin kalubale sannan zai iya jefa rayuwarsa cikin Tsaka mai wuya da Halin k'ak'ani k'ak'ani. Ajiyar zuciya ya sauke lokaci d'aya ya na Share zufan Goshinsa. Wayarsa da ke gefe ya laluba ya kunna sai yaga biyar da minti goma na asuba shiyasa yaji ana kiran salla a wasu masallatan. Kansa ya koma ya dafe a fili ya sake Furta"Hasiya." Wanda kamar acikin barci Tahir yaji sunansa ya mike a razane ya na fadin"sai naji kamar kana ambatan sunanta? Ya fad'a ya na haske Sadiq din da fitila a saman gado sai kuma ya tsince shi shima a kasa kusa da shi. Cikin alamun barci a idon Tahir yace"Sunan Zabiyar yarinyar nan naji kana ambata. Na shiga uku Allah yasa ba itace ta ka maka ka ke kwance ba Lafiya ba." Cikin mamaki Sadiq yace"Ita wacece ta ka mani? Tahir ya mike ya na mutseke ido kafin yace"Ita Hasiyar da naji ka na kira ko ba sunan wannan zabiyar yarinyar kenan ba.? Karamin Tsaki Sadiq ya ja kafin ya yunkura ya mike Lokaci daya ya na Fad'in"Man ni naji sauki fa." Tahir ya dafa sa lokaci d'aya ya na Tattaba goshinsa da wuyansa lokaci d'aya ya na fad'in"Eh naji jikin ka ba Zafi sosai kila taga bazaka ciwun mata ba ne yasa ta sake ka" Sadiq ya kyalkyalce da Dariya lokaci d'aya ya na Dafe kansa saboda Saramai masa da ya yi. Tahir ya kallah kafin yace"Tahir.. Tahir.." Ya ke fad'a ya na kallonsa Tahir yace"Wlh da yanzu zan nemota duk inda ta ke ta tsallaka ka muguwa kawai." Ya na wucewa wajen kayansa ya ce ma Tahir"Ba fa mayya bace Tahir. Kowa da irin tashi kaddaran" Tahir ya karkace baki yace"Maita fa gaskiya ne." Kai Tsaye Sadiq yace"bamu san maita a addininmu ba. Mu kambun baka kad'ai muka sani maita kuma da ka ke mgana duk Aljanu ne su ke yin abun su da aikin Tsaface tsaface irin nasu" Daganan bai kara mgana ba ya Dauki Buta da Sauran ruwa ya bude kofa ya fice ya bar Tahir na mgana bai tsaya jinsa ba yasan ko kwana ya yi ya na mgana Tahir bazai aminta da mganarsa ba ya riga ya gama aminta da duk abunda aka Fad'a masa. Shi kuma cikin bayanan Amma ya Fahimci Rayuwar Hasiya ba komai cikinta sai Kaddara da ke Dawainiya da ita haka Allah ya tsara mata komai in zai Faru da mutum daman akwai Sanadi. Kuma ita sai ta kasance itace Sanadin na su kaddaran shiyasa ta ke Fuskatar kyama da Tsagwamma. ******** Na gama zura ma Amma ido ko zata min mganar abunda ta tattauna da Assadiq ammh kuma har muka yi shirin kwanciya ba ta ce min komai ba. Sai da na yi mata shirin kwanciya sannan na zauna a gefen kafafunta ina Shafa mata man zafi a kafafunta tunda tace sun rike mata. Ina cikin Shafa mata ina ta so na yi mata mgana ammh na kasa sai na yi kamar na yi mata mgana sai kuma na kasa. Dakyar na yi karfin halin kiran sunanta"Amma.." Ta amsa da cewa Umh. Kallonta na yi cikin wani yanayi kafin nace"Amma me kika fad'a ma Assadiq? a kaina ne? Amma ta yi shuru ta na kallona kafin tace"Me yasa ki ke son sani? Kai Tsaye nace"Ina Son sani ne kawai Amma." Mirmishi ta yi kafin ta Dafa kafad'ata ta na Fad'in"Kada ki damu. In abunda na rokesa ya ji rokona ya amshi Bukata ta zaki ji komai zuwa da Safe. In kuma bai amimce da Rokona ba har Abada bazaki taba sanin me muka Tattauna ba." Cikin mamaki na kalleta kafin nace"Amma." Kai ta gyad'amin tare da mirmishi da ya Kashe min baki. A sanyaye na gama shafa mata man zafinta sannan na gyara mata kwanciya. Hannuna ta rike ta na fad'in"Khairan in sha Allahu Hasiya." Jinjina mata kai na yi batare da mganarta ta shiga jikina ba. Mamaki na ke yi wata mgana ce wannan da Amma ta kasa Fad'amin? Da farko na dauka Labarin abubuwan da suke faruwa da ni ne sai daga baya kuma na Fahimci wata mgana ne ta Dabam. Barci na a ranar rabi da rabi ne duk sanda na farka sai na hangi Amma saman Darduma ta na sallah. Na fad'a daman ba ni da kokarin sallar Dare shiyasa har akayi asuba ban iya tashi ba har sai da Amma ta tasheni sannan na iya tashi ina kallonta ina jinjina abunda zai hanata barcin na tsawon Dare duk da nasanta ta na daga cikin mata masu kokarin Ibada ammh bata kaiwa har dare ya fara ya kare bata yi barci ba Sai zargina ya tabbata da cewa tabbas akwai wani abu da ke faruwa wanda bansani ba. Jikina a sake na tashi da shi, Amma kuma ta lura ammh kuma ba ta min mgana ba sai dai na lura da wani abu tunda garin Allah ya waye Amma ke duban hanya kamar ta na jiran wani ko wata. da ta ji sallama sai ta leko har na nagaji nace mata wa ta ke nema tace min bakomai. Cikin ikon Allah mun gama karyawa kenan sai ga Hamma Isuhu ya diro ba makawa tafiya ta tabbata a ranar kenan Tunda yace tare da wani mai Motar da zai daukan mana kaya suka Taho dagachan ya Dauko Itace ne zai shiga cikin gari ya sauke sannan sai yazo ya kwashemu mu da kayanmu. Jin haka yasa Amma tace na kira su Adda na fad'a musu su zo mu yi sallama. Da wayar Maman Boy na kira su, nace Adda Fati ta kira Inna Talatu da Ramatu ta sanar da su. Daganan sai na fara wanke yan kanukan da muka bata da Safe daman kayammu suna kammale waje d'aya. Isuhu ko na ciki suna Hira da Amma na wani Lokaci kafin yace Amma bari ya shiga cikin gari ya dawo lokacin mun gama fitar da komai zai kira mai Motar in ya gama sai su dawo tare. Na kasa Fahintar yanayin fuskar Amma a lokacin. Ta na dai zaune ta na jan Cashaba ni ce na ke kazar kazar ina had'a mana sauran kayan sawan mu da kayan amfanin da na fito da su. Su Adda ba su tsaigaita nan da nan sai ga su sun taho cikin Damuwa da jimami. Adda Rukayya ma ta riga Adda Fati zuwa ita da ya'yanta duka haka itama Adda Fati har da mijinta Inna Talatu ce ta zo daga baya sai Ramatu ma ta rigata zuwa. Kowa kagani jikinsa duk ya yi sanyi na ganin tafiyar fa da gaske ne. Ni na had'a gawayi na saka mana Ruwan zafi Amma ta fara yin wanka sannan ni nayi daga baya. Na saka wani leshi na cikin kayan Abubakar ne mai Riga da zani, Amma kuma ta saka wata atamfarta da Adda Fati ta Dinka mata, ta kuma koma ta zauna ta cigaba da jan cashabanta duk hiran da su Adda ke yi bata saka musu baki ba. Tuni har yan gidanmu sun aikama Makota cewa yau zamu tashi sai shigowa su ke suna mana sallama. Ba wanda ya damu da yanayin Amma kowa ya na zaton cewa Saboda sabo me yasa jikinta duk ya yi sanyi ba ta walwala. ****** Ya gama Had'a duka Tunaninsa da Hangensa mafita d'aya ce kuma ita ya Tsaida har acikin ransa yasan Allah yaga kyakyawan Niyyarsa na Alheri da taimako kuma ya na da yakinin bazai barsa ya tabe ba. Bai yi wani yunkuri ba sai da suka dawo sallar azahar shi da Tahir saboda saboda zazzabin da ya yi yasa shi bai je wajen aiki ba Tahir ma bai Fita ba. Suna dawowa sallah daman akwai wuta ya saka ruwan wanka a Kittle sai da ya yi zafi sannan ya juyo ya yi wanka Tahir na kwance ya na ta Chart a wayarsa. Sai da ya fito yaga ba shi da Niyyar tashi sannan ya ce masa bazai yi wanka ba ne? Tahir ya dago ya na kallonsa kafin yace"Sai anjuma zan yi." Sadiq ya kallesa kafin yace"Ka tashi ka yi zaka rakani wani waje ne." Tahir yace"Ina.? Sadiq sai ya yi masa banza bai yi mgana ba Tahir ya mike ya na mika kafin yace"Ka samu kanka kenan za'a fita? Da Eh Sadiq ya amsa masa daidai Lokacin ya na bude akwatinsa. Tahir shi kuma sai ya juyo ruwan da Sadiq ya saka masa shima ya fita zuwa wanka. Ya yo wanka kenan ya shigo Dakin ya iske Sadiq ya ci gayunsa cikin wata shadda mai ruwan madara sabuwa ce ya na Tunanin ma bai taba sakata ba. Abun mamakin har da Hula dara mai yanayin aikin jikin kayan sannan ya sanya takalmi budadde na Fatar damisa sannan ya na tashin kamshin Turare. Yana cikin karya Hulan kansa Tahir yace"Daurin aure zamu je ne? Kai Tsaye Sadiq yace"Kamar ka sani." Tahir yace"Ikon Allah Daurin aure ranar Laraba ko dai Bazawara ce.? Kai Tsaye Sadiq yace"Eh.!" Tahir ya tsaya ya na kallonsa kafin yace"Eh fa kenan bazawara ce? To kai ya aka yi ka santa? Sadiq yace"Zan sani mana." Tahir na goge jikinsa da Towel yace"Nagane kila abokin aiki ka ne ko? Sadiq ya daga masa kai Lokaci d'aya ya na Dora wani brown din Agogo na Fata mai kyau da yarari lokaci d'aya ya na ce ma Tahir"Ka yi sauri.." Tahir yace masa Toh yanzu zai shirya. Jin haka yasa Sadiq yace bari yaje ya ciro kudi ya dawo fita ya yi ya ganganra bakin Titi wajen masu POS ya ciro kudi ya Tura cikin Aljihun wandonsa. Ya jima Tsaye a wajen ya na sauke Numfashi kamar mai ciwon Asthma. Wata zuciyar tace"Anya Sadiq abunda zaka aikata daidai ne? Baka ganin cin Amanar yardan iyayenka ne? To ammh ya zai yi? Tausayi ne ya cikamasa Kirjin da ya kasa tankwafar da wannan Rokon sai dai yana da nashi lTsarin da Sharadin har ya yi wannan abun ya gama shi babu wanda zai sani daga cikin wani Ahalinsa sai Tahir shi kuma yasan in ba shi yace ya yi mgana ba Tahir bazai taba cema kowa komai ba. Da haka ya gangara ya koma ya na zuwa ya ga Tahir har ya fito shima cikin Shigan manyan kaya. Kofar su suka kule sannan suka fara Tafiya Tahir ya dauka bakin Titi suka nufa ammah sai yaga sun nufi cikin anguwa. Kai Tsaye yace"Ya na ga haka? Ba abun hawa zamu hau ba? Sadiq na cin mgani yace"A'a." Tahir ya kallesa bai samu zarafin mgana ba yaga Sadiq ya ciro wani bakin glass mai Duhuwa ya kwafa a Fuskarsa saboda batar da k'wayan idanuwansa da zasu bayyana asirin yanayin da ya ke ciki. Tahir ya saki baki kafin yace"Wannan bakin Gilashin fa? Sadiq ya yi kamar bai ji sa ba ya cigaba da Tafiya, shi dai Tahir yaga an zo wajen Taron jama'a bai gani ba sai da yaga sun tsaya a kofar wani Rubabben gida Dagargajajje. Cikin mamaki ya kara kallon Sadiq kafin yace"Ina ne nan? Kai Tsaye Sadiq yace"In da zamu zo mana." Tahir ya bude baki kafin yace"Nan ne wajen daurin auren? Sadiq ya gyad'aa masa kai lokaci d'aya ya na kwalama Salihi kira da ya gansu suna wasa a kofar gida ganin shi yasa har da Datti suka Rugo da gudu Sanin ya na ba da kudi. Suna Rige rigen gaisheshi ya amsa ba Sakewa kai tsaye yace"Ku shiga ciki ku fad'ama Maman Hasiya Abubakar na mgana a waje." Yaran suka kwashi gudu zuwa cikin gida Tahir ko mamaki ya sandarar da shi jin sunan da ya ambata kara bin gidan ya yi da kallo kafin ya Dawo da kallon kan Sadiq da baya ganin kwayar idanuwanshi saboda gilashin da ya saka. Cikin mamakinsa Tahir yace"Nan ne gidan su Hasiyan kenan? Sadiq ya gyad'a masa kai Tahir ya yi kwafa kafin yace"Tsakani ga Allah mu da zamu Daurin aure me ya kawo mu nan? Sadiq ya yi shuru kafin yace"Nan ne wajen Daurin aure" Tahir yace"Nan ne wajen Daurin auran? Ya fad'a cikin Sigan Tambaya again kuma Sadiq ya gyad'a masa kai. Mamaki dai ko takaici zan ce ya kusa kashe Tahir a tsaye. Cikin karin mamaki ya kara cewa"To waye zai yi aure? Sadiq na kallon kasa muryansa ta yi kasa kafin yace "NI.." A Firgice Tahir ya Dago ya na kallonsa Daidai Lokacin da Amma ta fito ba ko Hijabi sai zaninta da tayi lullubi da shi Domin ta na zaune ne daman tana zaman jiran Tsammani sai ga su Salihi da sako. Duk muna zaune adakin Amma Sakon yazo abunda ya bamu mamaki tashin Amma da Sauri da fitan ta batare da ta jira cewar komai ba yasa ta fita ta barmu baki sake cikin zullumi da Tunanin lafiya. Ni kuma Tunda naji sunan wanda aka ambata gabbaina suka saki a tare. Abunda bai saba gani ba ne na gani yau ya saba indai yazo sai dai yace a kirani ammh yau Amma yace a kira kai Tsaye kenan tabbas akwai wani abu a kasa wanda ban sani ba. Achan waje kuwa Amma na fita Taga Sadiq ba ta ko tsaya lura da Tahir ba ta karisa gabanshi ta na fad"in"Daman na sani. Ina da kyakyawan tabbacin zaka Dawo Abubakar" Ta fad'a Lokaci d'aya ta na mirmishi. Dagowa ya yi ya na kallonta sai dai Rauni da kukan UWA shi ne suka Dawo da shi sai kuma Tausayinsu gabadaya. Cikin wani irin yanayi yace"Nazo da abunda kika bukata Amma meye abu na gaba? Amma ta daga hannuwanta sama tace"Alhamdulillah. Alhamdulillah.! Allah na gode maka" Sai kawai ta fashe da kuka ta na neman zubewa a kasa da Sauri Sadiq ya riketa kafin ta kai kasa kada ta tara masa Mutane. Cikin kukan ta ke fad'in"Nagode Allah ya yi maka albarka. Yadda kaji kaima kaima Allah ya jikan ka, Allah ya haskaka Rayuwarka da Alheri Allah ya baka abunda kake nema Duniya da Lahira Allah ya tsareka a duk in da ka ke Allah ya sanya albarka acikin Niyyar ka ta Alheri." Amma ta ke fad'a ta na kuka ga hawaye Shabe shabe Sadiq yasa Hannu ya share mata hawaye ya na fadin"Bakomai Amma." Amma ta rike Hannuwansa ta jimke ta na fadin"Yadda ka share ma wannan UWAR hawayenta Allah ya share maka naka. Yadda ka sanyaya ma wannan Uwar zuciya kai ma Allah ya sanyaya maka taka zuciyar, Yadda ka duba lamarin wannan Uwar kai ma Ina Rokon Allah ya cigaba da Duba Lamarinka har Abada." Sadiq na ta amsawa da Ameen Tahir ko ga shi nan Tsaye ya na ji kuma ya na gani ammh ya rasa gane ina aka dosa. Amma ta na share hawayenta ta juya ta na fadin"Ina zuwa." Cikin gida ta koma da Sauri duk muma Daki ta daga labule ta na kiran Sunan Adda Fati, ta mike ta na Fadin"Na zo ne Amma? Kai ta gyada mata da Sauri ta mike ta fita ni da Ramatu muka kalli juna bamu da amsar da tambayar da ke zuciyarmu. Suna Fita Gefe Amma taja Adda Fati tace ta yi maza ta kira mata Babammu Tanko ta na so ta yi mgana da shi. Ba musu Adda fati ta latso lambarsa ta kirasa daman wayar na Hannunta sai da ta kira kusan sau uku sannan ya Dauka daman ita ta na da lambobin su ta na kiran su ta na gaishe su ko da su sun yada mu suna da Hakki muma mu bi mu yi zumumci da su. Bayan sun gaisa tace masa Amma ke son mgana da shi nan da nan ya bata rai duk da ya jima rabon da yaji ta nemesa yasan kila wani abu take Bukata sai dai zencen ya sha Bambam ta na karban wayar ta yi ma Adda mgana da Hannu alamun ta bata waje. A gurguje suka gaisa har ya fara Tsumewa ya zata ko wani taimako ta ke nema sai yaji ta fara rattaba masa wani jawabin da yasa ya d'an Saki Fuska cikin Sauri yace"Ina gida za su iya karisowa Aisha." Daga haka Amma ta yi masa godiya suka yi sallama. Abun mamaki Amma ta shigo Dakin nan bakinta a washe Adda Fati ta mikama wayarta Lokaci daya ta na Fadin"Fati ta shi ki shirya akwai baki a waje gidan Babanku Tanko zaki raka su yanzu." Ni da Adda Rukayya muka had'a baki wajen fad'in"Gidan Baba Tanko kuma? Cikin Alamun Sigar Tambaya. Amma ta gyada kai fuskarta na bayyanar da Annuri Adda Fati ba musu ta mike ta na Saka Hijabinta Hanifa na Hannuna ta yi barci sai tace na riketa bari ta Dawo Ta na fita Inna Talatu ta kalli Amma ta na fadin"Lafiya dai ko? Amma na mirmishi tace"Sai Alheri in sha Allahu." Adda Rukayya tace"Amma ko an fasa Tafiyar ne? Amma ta kalleta kafin tace"A'a ban fasa ba sai dai kila tafiyar ne zata sauya daga ni da Hasiya zuwa ni kad'ai." A tare muka kalleta ni dai sai da gabana ya amsa Ramatu ta washe baki kafin tace"Yauwa Amma ki bar mana Hasiya tare damu" Amma na mirmishi tace"In sha Allahu Ramatu." Amma fa ta bama kowa mamaki kudi tace na bata naira Dubu biyu na Dauko na bata ita kuma ta aiki Habiba shago ta siyo mata Cimgam da Minti. Inna talatu ne sai da ta maganta cikin mamaki tace"Tashin ne har da rabon su Minti? Amma tace"Wannan na Dabam ne Talatu." Ni dai zaune na ke rike da Hanifa ammh ba na cikin Hayyacina. Ina jin Ramatu na fad'in"Kawata nan Amma zata bar min ke" Ta fad'a cikin Farimciki da Annushuwa kallonta kawai na yi ammh ni nasan a raina ba abunda take tunanina ba ne. Abun mamaki me yasa Amma tace a raka su Assadiq wajen Baba Tanko? ******* Ita kanta Adda Fati ta yi mamakin ganin Sadiq sai dai ba ta samu zarafin jin ba'asi ba gaisawa kawai suka yi tace su je Amma tace ta yi musu jagora zuwa gidan Babansu Tanko. Sadiq sai da ya riko hannun Tahir da ya tsaya ya kasa bin su saboda ya na neman karin bayani. Adaidaita suka samu suka hau har Babban Dodo. Ita ta fara shiga cikin gidan zuwa wani Lokaci sai ga Baba Tankon ya fito da kanshi. Sadiq bai tsaya ma kallonsa ba yadai san Datiijo ne Hannu ya ba su suka yi musabaha kafin ya jazasu zuwa cikin Falon gidansa da ke da kofa ta waje. Suna shiga ya fita ya barsu Tahir ya juyo ya na kallon Sadiq kafin yace"Zaka yi min bayanin meke faruwa ne ko zaka cigaba da barina cikin Duhu.? Sadiq Kai tsaye yace"An kusa zuwa gabar da zaka san komai." Shuru suka Cigaba da zama sai chan kuma sai ga shi ya dawo da wasu mutane kamar goma haka. Shima Sadiq zuwan su wajen Tahir na jinsa ya na waya ya na kuma kwatancen inda su ke Ba jimawa sai ga wasu samari suma bazasu wuce sa'aninsu ba. Sadiq ya gabatar da su da cewa abokan aikinsa ne sai Tahir ya Fahimci daga inda ya ke Hidimar kasar sa ne to ammh me ya kawo su nan wajen? Yaji ana kora jawabin bai tsaya Saurara duka ba ya dai fahimci kamar Aure za'a Daura? Ammh abun mamakin Daurin auran wa? Ya na cikin wannan Tunanin yaji ana Fadin"Ina Sadakin na ku? Sadiq ya karkato aljihu ya fiddo kudi ya mika nan da nan aka kirga Dubu Talatin cif. Baba Tanko ya mika ma Saminu da ke gefensa Lokaci daya ya kallesu ya na Fad'in "Waye zai auri Hasiyan a cikin ku? Tahir yaji kamar kunnensa ya Toshe ya na shirin mgana Sadiq yace"Ni ne." Baba Tanko ya kallesa daga sama har kasa kafin yace"To ka dai san komai da ya shafi yarinyar ko? Sadiq ya gyad'a masa kai batare da ya yi mgana ba. Baba Tanko yace"Kai ko saurayi a haka kuma zaka zira jikin ka? Ko baka duba asaran Dukiya ba ka Duba ta lafiyan ka." Sadiq ya dago ya na kallon Baba Tanko na wani Lokaci kafin yace"Ni ai ba ni da arzikin ma ballatana na duba hakan. Mganar lafiya kuma Allah shi ke da ciwo kuma waraka daga wajensa ta ke." Baba Tanko ya kalli Baba Saminu shima ya kallesa suka had'a ido. Kafin Baba Tanko ya yi gyaram murya yace"Shikenan daman shawara ce. Waliyin ka ya matso kusa tare da Shaidun ka." Sadiq ya nuna Tahir ya na fad'in"Shi ne Waliyina. ya nuna sauran ya na karishe fad'in"Su ne Shaidu na." Baba Tanko ya kalli Tahir kafin yace"Shikenan daman Uwar ta su ta gayamin kai maraya ne ko? Sadiq ya kara gyad'a masa kansa. Tahir magana ya ke so ya yi ammh Sadiq ya hana shi yana ji ya na gani aka fara gudanar da Sigan Daurin aure. Sadiq ya masa Rad'a a kunnensa da fadin"Kayi abunda ya dace. Zan yi maka karin bayani in muka fita." Tahir ya na ji ya na gani ya karb'an ma Sadiq auran Hasiya akan Sadaki naira Dubu Talatin auren da ya samu Shaidu sama da Ashirin saboda kafin a Daura auran wasu mutanen sun karu ciki har da Isuhu Yaron Adda. Domin bayan Fitan su Sadiq ya koma da mai motar domin kwashe kaya Amma tace maza Habiba ta rakasa chan shima. Adda Rukayya ce ta kasa Hakuri ta kalli Amma ta na fadin"Amma wai me ke faruwa achan gidan Baba Tankon ne? Amma ta juya ta na fadin "Auran HASIYA za'a daura" Ba ita kadai ba hatta mu sai da muka girgiza gabadaya muka juyo muna kallonta bakina ya fara rawan da na gaza Furta komai. Inna Talatu ne tace"Da wa kuma? Sannan ba mu da labari? Amma tace"Abun ne yazo a lokaci kurare." Yadda na sandare a zaune haka su Adda Rukayya suka sandare sun kasa mgana Amma ko sai kasa Minti ta ke yi da Cimgam hankalinta kwance. Muna nan zaune muna kallo kallo Ramatu ta kalleni yafi sau goma ta kasa mgana. Sai kawai ga wayar Adda Fati a wayar Adda Rukayya ta na Dauka sai ta saka a Amsa kuwwa cikin mamaki tace"Rukayya Auran Hasiya fa aka Daura yanzu nan" Adda Rukayya taja Numfashi kafin tace"Uhmm da wa? Adda Fati tace"Da wanda in nayi miki bayani bazaki gane shi ba. Wani SADIQ ne, Wanda ya taba kai Amma asibiti kwanaki da Ciwonta ya tashi." Gabana ya fad'i ras! "ASSADIQ.." naji zuciyata ta bani, Wani Dum naji acikin kaina ina jin suma mganganu ammh kuma bana fahimtar abunda suke fad'a. Naji dai sanda Amma tace a fara fita da kaya ita kuma ta fita tsakar gida ta na Rabon minti lokaci d'aya ta na fad'in"Na daurin Auran Hasiya ta ne, yanzu aka Daura mata aure a gidan babansu na Dirimi." Ni ko ina zaune rike da Hanifa na kasa tashi sai da naji Ramatu ta jijjigani ta na fad"in"Hasiya me na ke ji haka? Na bita da kallo da idanuwana da suka Juye kamar yar maye. Sai kuma na koma ina bin Dakin namu da kallo da yara ke ta shiga suna fita da kaya. Yanayin da na ke ciki yasa na kasa ma yin wani kakkwaran motsi. ****** Kamar yadda Ramatu ta jijjigani haka Tahir ya Jijjiga Sadiq bayan sun fito daga Falon da aka Daura aure. Cikin Fitan Hayyaci yace"Sadiq me na ke ji haka ne? Na kasa Fahimtar komai ka yi min bayani." Sadiq ya kasa mgana sai da komai ya tabbata kuma ya fara jin wani irin Nadama da Tsoro. Aure fa ya yi batare da sanin Abba da Umma ba. ba tare da sanin wasu daga cikin Ahalinsa ba. Anya bai yi kuskure ba? Tabbas bai yi Tunanin faruwar haka ba sai yanzu ya zai yi da ita? Wannan shi ake kira Halin Tsaka mai wuya. Sadiq ya Runtse ido ya bude shiyasa yasa ka bakin glass saboda kalan idanuwansa sun sauya daga fari zuwa Jajaye. Tahir ne ya kara masa wani jijjiga mai yawa ya na kara fad'in"Sadiq aure ka yi? Aure ka yi batare da sanin Yan'uwan ka ba? Kasan me ka aikata kuwa Sadiq? Sadiq ya kwace jikinsa da Sauri ya na Fadin"Na sani..na sani Tahir Aure na yi. Aure na yi batare da sanin kowa ba" Ya fad'a cikin karaji, Tahir ma cikin karajin yace"meyasa ka yi haka? Kasan ko me ka aikata? Kasan wani irin girman zunubi ka aikata? Sadiq ka na cikin hayyacinka kuwa? Sadiq ya ji kansa ya sara ya Dafe kanshi lokaci d'aya ya na fad'in"Na sani Tahir na auri Hasiya saboda ina jin Tausayinta. Sai dai ban aureta domin na yi zaman aure da ita ba. Zan SAKE TA da zarar na inganta Rayuwarta ta yi tafiyarta ni kuma salin alim ba wanda ya sani zan koma gida na auri zabin iyayena." Ya na mgana ne Ammh Tahir ya saki baki kawai ya na kallonsa ya fara Tunanin kamar Sadiq ya zare ko ya Haukace. Daman shi ya sani wani abu zai faru mutanenan ba su bar Sadiq haka ba. Ganin al'amarin ya yi kamar almara kamar a mafarki. Sadiq ya yi aure? Kuma ba Sultana ya aura ba wata zabiyar yarinya mai mummuna kaddara a cikin Rayuwarta. Yana tunanin Sadiq ba kanshi daya ba gaskiya to ko ya na sane ya aikata haka bakin Alkalami ya riga da ya Bushe. ba bu wanda ya isa ya sauya wannan Kaddaran. Kaddaran SADIQ ya auri HASIYA. Alhamdulillah. *Karshe littafi na d'aya* Turka turka kenan, Miye makomar auran Hasiya da Sadiq? Ina sultana? Iyayensa fa? Tahir zai rufa masa asiri? Zai saki Hasiya kamar yadda yace? Ko zai gayama iyayensa labarin Hasiya? Hasiya zata samu daidatan kaddaranta tare da Assadiq? Zata samu farincikin? Shin za su yi zaman aure? Ko zata kara zama bazawara a karo na uku? Daga karshe wani irin Kalubale da TSAKA MAI WUYA ke jiran Sadiq, ga shi dai ya tabbata MIJIN HASIYA? Sadiq zai auri Sultana? In ya aureta ya matsayin Hasiya a wajensa? *Duk tarin wad'anan tambayoyin suna cikin Littafi na biyu da na uku, zaku same shi a kan manhajar AREWABOOKS#Jamilaumarjanafty 09069067488* *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Zamu fara littafi na biyu gobe in sha Allahu a Arewabooks, yan WhatsApp kuma sai kun cike limit din mutane 300 in sha Allahu sannan zamu dora, Nagode kwarai da soyayyarku Allah ya Hore ma kowa halin biya Amin.* *Janafty* *12/01/2024*