Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕 💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Allah ka bani ikon rubuta Abunda zai anfani Al,ummarka,Allah ka kiyaye mani harshe na ka bani ikon rubuta alkairi Ameen summa Ameen.* 1. *1998* Wani yaro ne da ba zai ga za shekara tara zuwa goma bah, ya tusa mahaifiyarsa ga ba kuka kawai ya ke saboda irin yadda ya ga halin da take ciki na tsananin labour...........murk'ususu take duk ta fice da ga hayyacinta, fita ya yi karo na babu iya ka tsakar gidan,wani d'aki Ya shiga Ya na kuka. "Antu lantana ki yi hakuri ki zo ki taimaki Maah kar ta mutu......ga ta can ta na yin irin abun nan kamar na mutuwa.........Cikin Wata irin tsawa da tun da ya zo duniya bai tab'a jin irin ta bah....... Tace, "Idan na sake ganin bak'ar fuskar ka Cikin d'akin nan wallahi sai na yi maka dukan da za, a kasa ganeka.......fita anan shegen yaro Mai shegen naci, nima halin da nake ciki kenan fita." Haka ya juya ya na kuka bai koma d'akin ba waje ya fita ya shiga wani gida da ke kallon na Su da kukan sa......tun kafin ya fad'i abunda ya ke so matar ta tare shi cikin kulawa......... "ya a Kai *Areef*?lafiya kuwa? me ya faru gidan naku?maman ka tana lafiya kuwa?." Duk lokaci d'aya ta jera masa wad'annan tambayoyi kamar tana yiwa wani babba. Yana shashshekar kuka muryar ta kasa fita sosai yace, "Maah.......maah.......za ta mutu...... Ki taho karta mutu....." Cikin tashin hankali ta jashi suka fice ko gidan bata tsaya rufewa ba. Sadda Su ka je har faya ta fashe tana nishin wuya d'an na son fitowa........waje ta kora shi ta shiga tai makonta Cikin yar dar Allah sai ga jaririya ta fad'o wani wahalallen nishi ta sauke........dan danan jaririyar ta fara tsanyara kuka asan dai ta iso duniya.... Cikin lokaci k'an k'ane aka gyare su sannan aka d'ora sanwar wanka..........Areef sai tsallen murna ya ke kamar ya anshe ta hannun maah da ke bata nono, d'akin da Areef ya fara shiga ne Wata mata ta fito Cikin tashin hankali tayi waje.........duk kiran da Anni ke kwala mata ba ta saurare ta bah, zuwa can ta dawo nan ma Anni sai tambayarta take ta yi mata banza.........ita sai ma ta k'yaleta.... Lantana aka fiddo aka Kai Asibiti. Alhaji farouk haifeffen garin Katsina ne,ne man Arzik'i ya kawo sa gari Abuja. Alhamdulillah an same shi kuwa don yanzu ya na zuwa Dubai da Sudan sarin kaya,matansa biyu Saudah ita ce mace ta farko da Allah ya bashi wacce A kullum ya ke Alfahari da ita, saboda aurenta shine Abun da ya d'aukaka shi har ya samu rufin asirin Allah,ya na masifar son matar sa sai dai matsalar farko da suka fara fuskanta, ita ce matsawar danginsa akan rashin haihuwarta da wuri, don alokacin sai da suka shekara goma da Aure Saudah ba ta yi ko b'atan Wata ba.......tsegumi dacece kuce ya ringa tashi akan wannan lamarin Idan ta shiga mutane an ringa harararta kenan, gashi Saudah ba mafad'aciya bace za ka jima ka na mata abu ba za ta tab'a tan ka ma ba,sai dai ta sha kukanta idan ya na kusa ya lallasheta ya ba ta hakuri, don idan ba shi ya bata ba bai San me zai ce mata ba, ana Cikin hakan tafiya ta same shi, bai saurari kowa bah ya d'auki matarsa suka cana Dubai............wannan tafiyar ta tun zura mahaifiyarsa. "tace Don nayi ma ka Maganar k'arin aure shine ka gudu kaida matarka ko, to kaje ko inane ka dawo Ina nan Ina jiranka." Basu dawo ba sai da suka shekara biyu. Abun mamakin shine ganin Saudah da su Kai da yaro, Areef Kenan. nan ma wata maganarce tai ta tashi, matar farouk ta haihu saboda bai d'auke mu bakin komi ba shine babu Wanda ya sanar ma. ...........hakan bai hana wannan auren ba Saudah tayi kuka kamar idon ta zai fita saboda bak'in Cikin halin da ta ke ciki, me ta yi masu su ke mata irin wannan k'iyayyar haka mai zafi. Haka saudah ta ci ga ba da zaman hakuri da dangin mijinta, ta na ci gaba da kulawa da yaronta Areef wanda ta ke ma wata kalar soyayya, Wanda idan so samunta ne ko k'uda karya ta b'a mata shi.............wata biyu da da wowarsu akai bikin Alhaji farouk da d'iyar k'awar mahaifiyarsa........ko kad'an ba ya son lantana, ba ma lantana kad'ai ba shi duk wata mace kallon na miji ya ke mata idan ba saudar sa ba, jinta ya ke har Cikin *RUHINSA* kuma ya yi alkawarin har abadan ita ce *ABIN CIKIN RUHINSA* bai tab'a cewa ba ya son lantana ba,Ya barwa ransa don Annabi Muhammad [S A W ] Ya yi hani akan furta k'iyaya ga wanda baka so. Zaman lantana da Saudah kamar zaman doya da manja,ko misk'ala zarratin lantana ba ta Kaunar ta,haka ko ya Areef ya rab'eta sai dai duka shi yasa Saudah ke kaffa kaffa da Yaronta.......Areef na da shekararsa hud'u Saudah ta sake samun wani Cikin, y'an uwanta sun ta ya ta murna da mijinta, mace da namiji ta haifa aka sa ma macen *SHAHIDA* namijin kuma *SHAHID* zan iya cewa wannan haihuwar ta janyo ma sauda wata irin kauna wajen dangin mijinta, Aka fara juya ma lantana baya, yayin da su ka ta so ta gaba kan cewar bata iya komi ba sai dai taci ta yi kashi. wasa wasa sai da lantana ta shekara biyar ko b'ari ba ta yi ba, nan fah kuma tsanar da ake ma Saudah ta dawo ga lantana,saboda daman ko kad'an ba ta ganin girman innah mahaifiyar Alhaji farouk,sai ta yi wata uku ba ta je ta gaida ta bah, idan gidan ta zo a wulak'ance ta ke kallon ta..........su ma sauran dangi duk haka take masu....... Kan Ka ce me sun dawo da kulawarsu A kan Saudah wadda Su ke ganin da can zalintar ta Suke. ......yanzu kuwa kamar su goye ta su ke ji...........haka lantana ta ko ma saniyar ware saboda bak'in halin ta,wanda hakan da ta ga su na mata bai sa ka ta canza hali bah..........haka rayuwar ta ci gaba da tafiya Areef ya na ji da y'an uwansa nan mak'otansu akwai matar abokin Alhaji farouk........lawisa yaran ta biyu, namijin sa,an Areef ne Macen kuma sa,ar Su SHAHIDA,tun da aka auri Saudah su ka kulla k'awance,don Mazajen su ma aminnan juna ne shiyasa su ma su ka had'a kansu abun gwanin sha,awa.........wanda takai har dangin Saudah sun san da lawisa,ita ma lawisa danginta sun san Saudah, Akwana A tashi ba wuya wajen Allah, lantana su ka samu Ciki kusan lokaci d'aya da Saudah............wanda shine yanzu sauda ta sauka, ita kuma ta na kan hanya da sauran Aiki tukun..........Alhaji farouk ba yanan ya je Dubai akan wani kasuwanci da yake Fatan ya tabbata, Wanda idan hakan ta samu ba karamar nasara ya yi bah,don arzikin sa zai linka na da fintinkau..........da zai tafi twins suka matsa akai Su wajen ummin Dubai [yayar saudah ce d same father d same mother] Dole ya tai da su don ganin halin da Saudah ke ciki na haihuwa yau ko gobe, koda akai ma Areef tayin zuwa yace Aa shidai ya na tare da Maah d'insa............. *wannan kenan* [Mrs bb]ce kuma Mom muhsen [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 2. Sai dare Saudah ta San cewar lantana tana Asibiti labour ta ke, lawisa ke sanar da ita Abun da ya faru da yamma. Sai da suka natsu sannan Saudah tace, "Annin Muhajid ya kama ta akira Abun Areef a gaya masa." "tun d'azu na so inyi masa albishir to na duba wayar taki babu Kati, hankalina ya ya d'auku ga wannan tsaleliyar babyn,wallahi ba batun son kai bah Saudah baki tab'a haihuwar k'yak'k'yawar baby irin wannan ba, tun yanzu ma angane kyanta inaga ta girma." Murmushi tayi tana gyara ma babyn kwanciyar ta. tace, "Anni kenan ai kuwa duk wanda zan haifa to saidai ya biyo bayan Areef A komai ma,don yaro na kin san indai ta nan ne to sai dai Ashafa fatiha." "Ai nasan da shi nace haka nufina Cikin wad'anda kika hai...............innalillahi lawisa! Don Allah kiyi shiru Meyasa zakiyi maganar nan please na rok'eki karki k'ara irin haka,yanzu Idan Areef idonsa biyu kikai wannan maganar wallahi akwai damuwa, kin san shi da kaifin basira Abun zai zauna masa karshen ya titsiyeni akan maganar." "yi hakuri Qawata wallahi na shafa,a Amman bazan sake wannan maganar ba nai maki alkawarin hakan." Ajiyar zuciya ta sauke tace, "Qawatah,wallahi son da nake ma Areef shahid da shahida bana masu irin sa,duk da kuwa haihuwar su nayi da cikina Amman ba na jin Su irin yadda na keji da Areef, saboda shine silar kawar mun da duk wani k'unci da nake ciki na rashin haihuwa,ta dalilin sa dangin mijina da surukata Su ka fara martaba ni, Ya fitar dani halin kuka da damuwar da na fuskanta don haka ko zan haifi singa da sabon gari wallahi bayan Areef suke,kuma insha Allah Cikin yara na babu maijin wannan sirrin,ke ma don na yarda da ke ki taya ni b'oyon sa don Allah." "insha Allah Qawata daga bakina dai babu maijin wannan sirrin." 💕💕💕💕💕💕💕💕 Sai washe gari aka sanar da y'an uwa da abokan arzik'i wannan haihuwar, Wanda Alhaji farouk ya kejin kamar an masa albishir d'in gidan Aljannah. Saboda ana gama sanar da shi wannan labarin, abokin kasuwancinsu yayi masa albishir d'in burinsa ya cika, nan take ya yi sujjadar shukru, yana mai tsananin godiya ga Allah Lallai Saudah alkhairi ce garesa,haka zalika wannan Yarinya tazo da arzik'i,nan take yake sanar da Amininsa mijin lawisa cewar asaka ma yarinyar *UMMUL— KHAIRI*. Saida lantana tayi kwana hud'u tana labour baiwar Allah,duk ta fice daga hayyacinta Akwana na biyar likita yace saidai aimata aiki, ranar Alhaji farouk ya dawo duk yadda lantanar take k'unziga mashi hakan bai hana yaji tausayinta ba, nan yasa hannu aka shiga da ita theater room y'an uwanta kuka kawai Suke da iyayenta. Saudah Kanta taji tausayin halin da take ciki saboda duk taurin zuciyarka idan kaganta sai ka tausaya, har kuka tayi Areef kansa yaji babu dad'i. Ba,a fito da ita ba sai bayan awanni biyar, ansamu nasarar fiddo jaririyar wadda ke kama da babanta kamar Alhaji farouk yayi kaki,anyi murnar sosai kafin ashiga nemo ran uwar saidai tun abun suna ganin baida wuya har hankalin Su ya fara tashi, don duk wata kafa ta sadarwar jikinta sun duba Amman babu alamun tana da rai.............sun kwashe awa biyu akanta Amman babu wani alamun zata tashi..........dole suka fito jikinsu yayi sanyi k'alau,da gudu y'an uwanta suka tare shi yaya lantanar. Girgiza Kai likitan yayi yace kuyi hakuri Allah ya amshi Abunsa.............inna lillahi wa Inna ilaihir taju,un hazbunallahu wani imal wakil...........abunda Alhaji farouk ke ta Nana tawa kenan babu ji babu gani sauran kuwa banda ihu da kururuwa babu abun da suke, daga mai suma sai mai fad'uwa haka wannan rana ta zo babu dad'i,duk wani wanda keda alak'a da lantana yayi kuka kamar idonsa zai fita, na yarda da maganar hausawa da akace ko naman jikinka mutun yake yanka kullum,duk randa babu shi za kaji babu dad'i balle ace ma ya rasu.....hazbunallahu wani imal wakil Allah ya jikan lantana Allah ya yafe mata tayi shahada Allah ya haska kabarinta. Abunda Saudah ke ta fad'a kenan, Areef ganin halin da maah d'in sa take ciki Shima sai ya kama kuka, Duk yinin ranar ummul kairi tana wajensa sai idan tayi kuka ya kaita ta sha mama. Haka akai sadakar uku Saudah ta anshi yarinyar tace zata shayar dasu tare, Allah ya bata ladar shayarwar, babanta yayi mata hud'uba da *ummu salma* Haka aka share zaman makoki kowa rai babu dad'i, yayin da Saudah kejin gidan yayi mata girma, daga ita sai yaranta guda biyar ikon Allah kenan, kamar ba itace ke kukan rashin haihuwa bah shekarun baya, sai gashi yau Allah ya azurtata da yara biyar Cikin shekaran da basu Gaza bakwai bah. Babu wani taron suna da akai, Alhaji farouk yadai yanka ma yaransa ragunan suna daga nan suka cigaba da kalawa da Yaransu. Rayuwar taci gaba da gara wa yayin da Areef yake primary 5 zai zana common interest yaje js one, shahid kuma shida shahida suna primary 2 sai twince Dake da y'an watannin,kulawa Suke samu sosai shiyasa suke Wata irin kib'a tajin dad'i, Abunda Saudah ta lura shine Areef yafi nuna kulawarsa ga UMMU SALMA saboda acewarsa UMMUL KHAIRI ta cika kuka da fitina,da ya dawo daga makaranta ita zai fara d'auka yana mata wak'a, yana mata rawa duk kuwa ba wai yana k'in d'aukar UMMUL KHAIRI ba Aa yana d'aukarta Amman da ta fara kuka zaice, "Maah wallahi *khairy* nine bata son na d'auketa kowa yana mata wasa lafiya lau Amman ni da nazo zan mata sai ta yi tayin kuka." Sai tace, "haba babban yaya ai shi yaya babba hakuri aka sanshi dashi, dukansu k'annenka ne kowa ce kuma tana buk'atar kulawar yayanta." Tun daga nan komi zai ma guda to zaima d'ayar,har takai yanzu khairy ta daina masa kuka, har bata yarda da kowa saishi haka Itama SALMA. Alhaji farouk likafa tayi gaba don yanzu ya bud'e sabon kamfanin sa na sarrafa yadiddika materials, boyels ne Gasunan wasu ma bazan ce ga sunan Su ba,ya zuba ma akata da yawa hada amininsa jafar mijin lawisa. Hakan ya ka'ra karfafa zumuncinsu sosai har iyalinsu, don wata sa,in idan su shahida basu nan to tabbas suna gidan Dadyn Muhajid da Meenah,mujahid abokine ga Areef don babu Nisa tsakaninsu ashekaru,Areef zai bashi shekara biyu Meenah kuma kanwar Su shahid ce zasu bata shekara uku........don yanzu duka shekarar ta uku. Gida Alhaji farouk ya fara ginawa na nuna ma sa,a yayin da zai gyara ma mahaifiyarsa wannan da suke ciki. *shekara kwana inji y'an k'arin magana har gashi y'an yaran Maah sun girma, don yanzu kowace nada 12 years* Mrs bb ce kuma mom muhsen. 💕💕💕💕💕💕💕 [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 4. Duk yinin yau Khairat bata fito ba,saidai salma ta ringa kawo mata abinci har d'aki,tunda ta dawo daga makarantar ko salma bata nuna ma result d'inta na,yah Meenah kawai ta gani Itama don tasan bazata fad'ama kowa bah, duk yadda shahida tayi akan ta bata ta gani cewa tai wai nata yab'ace idan ankoma hutu za,a sake dubawa. Shahida bata yarda bah haka ta rabu da ita saboda sanin Khairat badai taurin kaiba. Kwance take ta gama sallar isha,i tana saman abun sallar salma ta shigo jikinta yayi mugun sanyi, ta samu gefen gadonsu ta zauna kallon Khairat kawai take,zuwa can tace. "sweetheart wai kina lafiya kuwa?." Tana daga kwance bata ko d'ago ba tace, "lafiyar kenan mekika gani." Isowa tayi wajenta ta na tadata zaune, "wallahi sweetheart baki da lafiya, bafa tun yau kike wannan Abunba I think tun fad'an................ "bana son tada abunda ya wuce kinarni na huta pls sweetheart." "Shikenan kiyi hakuri, daman Abbu ne yake neman mu mu duka,ke kawai akejira." Runtse idonta tayi tanajin Wata matsananciyar fad'uwar gaba,tabbas maganar result d'inta za,ai kuma tasan Yah Aree ya binciko repiting d'in da akai mata...........yau ita tashiga uku idan ya kamata, babu abunda ya tsana sama da kafad'i exams,ko Su yah shahid idan yaga sun fad'i suna gane kurensu, zai kawar da komi ya baka punishment. "sweetheart karfa yah Areef ya biyo mu,naga yau cike yake damu bama mu ba wallahi har su Anty ma haka." Tashi tayi tana jin wata masassara mai zafi na ratsa dukan jikinta, Ko hijab d'in dake jikinta har k'asa bata cire bah tace, "muje" Haka suka jera suka tafi,yayinda Khairat duk taku d'aya gabanta yake tsananta fad'uwa, ji take kamar tayi fuffuke ta tashi ko kuma tayi Samara anemeta arasa. Koda suka zo bakin k'ofar babban falon Abbu sai ta tokare ta k'ishiga, salma tayi tayi ta shigo ta k'iya dole ta kyaleta ita tashiga. Zama tayi Maah tace, "Ina Khairat d'in yo." Cikin karyewar murya tace, "Maah don Allah Kice kar yah Aree karya doki sweetheart,wallahi kingan ta can ta kasa shigowa tsoro take ji." Dariya kawai Maah tayi don yau zata ga yadda za,a kaya Areef zai iya hukunta kannen nashi. Abbu Ya kwala mata kira, " *ta Alkairi* shigo kinjiko yayanki bazai maki komi bah." Dayake haka yake ce mata tun da aka haifeta. kasa shigowa tayi ganin tak'i shigowa yasa ya bud'e deep voice d'insa yace mata. "wallahi Idan na iso wajen nan jikinkine zaiyyi tsami,dani kike bayani yau Allah kuwa." shahid yace yana dariya, "oga sweetheart ce fah." Harararsa yayi yace" to ina ruwanka y'an saka ido." Anty shahida da Yah meenah Su mujahid duk dariya suke mashi, Kamar wadda k'wai ya fashe wa aciki haka ta fara bin bango kamar gizo gizo, sosai ta bashi tausayi, Amman baijin zai rangwanta akan wannan saken da tayi,tunda yasha fad'a masu cewar karsu had'a karatunsu da komi, karsu yarda damuwa ko wani Abu ya d'auke masu hankali akan karatunsu. Kusada Anni ta zauna idonta ya cika tab da kwallah, k'iris take jira ta fashe kuka. Abbu ne yace yah shahid ya bud'e taron da Addua Yakaranto muka shafa. Kasa Kallonsa tai don tasan had'a idonsu Wata masifar ce wajenta, Jitai Abbu yace. "Kai shahid muga naka." Ba musu ya mik'ama Abbun yayi ba tare da wata damuwa ba, don yasan baida matsalar komi. Yaba mashi yayi sosai tare da mashi kyauta ta musanman, key aka bashi na sabuwar mota y'ar yayi, nan Yashiga murna kowa yana taya shi,ita kuwa ta kasa cewa Uffan.......Anty shahida ma kusan duk iri d'aya ne sakamakon, don naga Itama anbata kyautar motar saidai yah Aree ya ansa ya ba Anni yace, "gashinan Anni ki ajiye wajenki har sai ta natsu sannan ki bata, wallahi ko bayan bani nan naji labarin kin hau mota batare da izinina ba kingama hawan mota saidai Idan tukaki za,ai understand." Cikin rashin jin dad'i tace, "yes." Iri d'aya ce ita da Yah shahid,yah meenah Abbu yace ta mik'o nata, hannunta yana rawa ta mik'ama shi, shirun da sukaji yayi yasa kowa ya tsareta da ido. Abbu yace, "meenah garin ya haka,kinsan wancan Karon ma saida mukai fad'a dake akan hakan ko, to donme zaki sake kawo mani irin sa,ok don wancan na hana Adokeki shiyasa yanzu ma kika sake ko." Hawaye keta zarya akan fuskarta, bakinta rawa yake tace, "wallahi Abbu ba laifina bane wannan Karon, Yaron gidan Alhaji garba ne duk sanda nake rubuta exam d'ina sai yayita copying d'in nawa, nace masa yadaina yak'iya har yaja Anty cire mani rabin mark d'ina,kuma duk sanda na hana shi Idan akai break sai ya d'aukar school bag Ya sace mani books,ya yaga ko nakai shi k'ara ni ake duka........ta fashe da kuka." Taba kowa tausayi wajen shiyasa Areef ya ki hukuntata ba, yace zaije yaga principal d'insu idan akai hutu. "salamatuna ingani naki nasan bazan samu matsala dake ba." Jikinta duk yai la,asar saboda tana gudun atab'amata y'ar uwarta. "Aaaaaa Lallai salamena irin wannan cinyewa haka, gaskiya kin cancanci rakiyar yayanku zuwa UK.......kagani Areef wallahi result din yayi kyau sosai, itace overalls d'insu duk term wallahi naji dadi." Ansa yayi yana k'ayataccen murmushi wanda daka gani Kasan yana cikin farinciki,jinjina kai yayi yace, "please don Allah Mu bata clap." Aikuwa duk aka tab'a mata Amman banda ni saboda bana cikin ma hayyacina,saida naji yace man. "ke ba zaki tab'a ba ko,oya clap for her." Jikina yana rawa na tab'a mata. Abbu yace na bashi nau, Nayi fik'ik'i ina raba idon wanda har kwalla sun fara zaryar Su, Maah ce tace, "wallahi Khairat ko kukan jini zakiyi sai kin fiddo result din nan idan ba haka ba, wallahi kashin tsiya yayanku zai baki." kuka na fashe da shi nace, "Maah bafa abani bah formerster d'in mu ne yace Idan andawo hutu zai duba Mani nawa." Dariya duk suka saka mani banda shi da salma, Wanda ita jitake kamar ta tayani kukan, shikuwa bazan iya sanin meke zuciyarsa ba lokacin. Abbu yace, " ta Alkhairi,kinga dai nan babu abokin wasanki ko, to bani." Ya mik'amata hanunsa ta bashi Amman saboda taurin kai Irin nawa gashi fah ga hannuna cikin hijab, Amman na k'i fiddo wa.......sai sharab'en majina da hawaye nake ai kawai jinai an kasheni da wani zazzafan mari,cikin kakkausar muryarsa yace, "bani" hannuna alokacin wata irin karkarwa yake haka na fiddo shi cikin hijab d'ina na bashi, duk ya jik'e da zufah.........fizga yayi ya mik'ama Abbu. Salma kuka take tayani wanda ni jinai kamar andauke nawa,ashe kuka ma rahma ne don har kwallah din sun k'afe.........sai zuciyata dake wani irin masifar zafi, ga masassarar ta sake rufeni dan danan idona ya fara dishi dishi,don banajin ma abunda Abbu yake fad'a sosai. "kin bani kunya ta Alkhairi,ina yabonki sallah Amman kin kasa Alwallah ban sanki da haka ba, kina yo first position duk term d'in duniya, Amman wannan Karon kirasa ko na nawa zakiyi sai second to d last.........banji dadi ba wallahi ko kad'an banji dad'in haka ba,shiyasa sukai maki repiting abun kunya tun kuna keji da yar uwarki kuke class mate d'in juna gashinan zatai gaba tabarki,anshi nan Areef duk hukuncin da ka ga yadace da ita kayi mata." Tashi yayi yabar shige bed room d'insa, Maah ta rufa masa baya. Anni tace, "Areef karkai saurin yanke mata hukunci ka tambayeta damuwarta, wata kila akwai abunda ya faru,yaro mai hazak'a kullum don ya fad'i irin haka bincika ake bawai hukunci bah nidai shawarar da zan baka kenan." Mujahid yace, "haka ne Anni tunda Kinga meenah ma tayi bayanin abunda yasa hakan ta kasance." salma ta rungumeni tana kuka sai lokacin nawa ya dawo, babu sauti saidai kwalla dake kwarara, da shashshekar kukan. haka kowa ya kwatse yabarmu nan nidashi da salma, mik'ewa yayi yace musamai d'akinsa. Haka muka rufa masa baya salma kamar itace tayi laifin. Koda muka shiga yana kan one seater Ya mikar da kvafafunsa kan table, idonsa arufe, salma ce tace gamu yah. bud'e idonsa yayi Sunyi fitinennen jaa ko na Miye oho. Banzan iya kallon sa ba wanda nasan ni yake kallo, naki d'ago idona,ya maida Kallonsa ga salma yace Cikin muryarsa ta sauko ba kamar d'axun ba. "me ye matsalar swee.......Khairat." Tabbas da sweetheart yazo fad'a sai ya fasa, tunda mukai wayau ban tab'a jin Inda yace Khairat ba, saidai sweetheart shine yau ya canza don yana jin haushina. Salma tana kwalla tace, "wallahi yah Aree ban sani ba, ni ma nayi nayi da ita ta sanar da ni anfi Wata Anma tak'iya,don Allah Yah kayi hakuri karka daketa." goge mata kwallah yayi yace, "idan ta sanar da ni abunda yasa ta fad'i exams zan mata hakurin Idan kuma har ta saka taurin kai irin na d'azu Kinga wannan,ya nuna dorina sabuwa mik'ak'k'a, to da ita zan Zaneta." Hankalin ta ya tashi don tana masifar tsoran dukan dorina, haka bata son duki sweetheart dinta. "ina jinki meye dalilin fad'uwarki jarabawa." Shiru nayi masa don nayiwa zuciyata Alkawarin ko zai kashe ni bazan fad'a bah, kukana nakeyi silently ina zubar kwallah.......saida yamun tambaya sau uku bance komi ba. Yace salma ta tashi tatafi don bazai iya dukana gabanta ba, zata Karya masa zuciya. Tana kuka tatafi takaice dai taurin kaina ya kaishi bango yayi mun dukan da na kasa motsi, ga masassara kamar ta kasheni saida Yah shahid yazo ya kwaceni,wannan dalilin shine babban dalilin da ya saka na janyewa yah Areef, kwana nayi banyi bacci bah wanda salma ma haka tayi,amai kawai nake Shek'awa har na galabaita,nace kuma karta kira kowa haka muka ga wannan daren, ganin abun zai wuce tunani yasa ta fita Aguje taje ta sanar ma da Maah, lokacin karfe shidda na safe Abbu Ya ma tafi waje aiki. Haka Maah suka zo suka saman ban iya ko motsa d'an yatsana......Ai yah Aree kamar zai haukace suka kwasheni sai asibiti,duk tashin hankalin da suke ciki basu Kai yah Aree ba, don afirgice duk yafita natsuwar sa........Anni ce ke kwantar masa da hankali har aka gama bani agajin gaggawa. Mom muhsen ce Mrs bb👌🏻 [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 5. Hana kowa shiga akai har sai nafarka daga baccin dasu kai Mani Allurarsa. Anni aka bari wajena da Anty shahida sauran yah mujahid yakoma dasu,salma hada kukan ta bazata tafi ba saida Yah Aree yayi mata jan ido sannan. Shima d'in bai tafin ba zamanshi yayi duk yadda Anni ke fama dashi yak'iya,dole ta kyaleshi haka sukai ta zaman zuru har ten thirty,sannan nurse din ta lek'o tace shishiga na tashi,Amman wani Cikin su yaje doctor nason ganinsa. Areef ya tafi Anni da Anty shahida suka shiga, Gaisawa sukai da likitan sannan ya zauna, Bayani yayi mashi akan abunda ke damunta. "cewa damuwa ce ta sakar mata masassara sannan da alama ma andoketa ne hada wannan dalilin yasa fever d'in tayi zafi, sannan dole akula da cin abincinta don bata cin abinci sosai,idan ba haka ba ciwon ulcer zai iya kamata, ga magani kasiya can phamercy." Godiya yayi mashi sannan ya fito yaje yasiyo maganin ya jiyo zuwa d'akin da aka kwantar da ita,jiya ke kamar ya kama dukan kanshi haushin kansa yakeji sosai akan abunda yayi wa sweetheart d'insa, tsoro yake kar tayi dogon fushi da shi, don yasan halinta akan rik'o.......sallama yayi Yashiga Ya ajiye magungunan gefe ya kalli Anni, "lafiya dai ko Anni." "da sauk'i dai tunda muka shigo ta k'iyiwa kowa magana, sai kuka da take duk lallashin munyi Amman taki yin shiru." Kallona yayi nayi saurin kawar da idona, Ina shashshekar kuka k'asa_k'asa yana son lallashin ta Amman Idan ya yiwa Khairat saku saku babu tantama raini zai shiga tsakanin su, so yake ya koya mata tsoransa wanda nan gaba baza ringa yi masa taurin kai bah,ya nason bata hakuri dukan jiya da yayi mata, Amman ya girmansa zai kasance a wajenta ba makawa raina shi zatai, Wanda shi bazai so haka ba zai nuna yama manta da abunda ya faru, Shan mur yayi wanda dole idan ta ganshi haka tashiga fargaba...... Cikin dakakkar murya yace, "jiyo nan nace." Jiyowar tayi gabanta na fad'uwa yace, "goge wannan kwallar banzai, me akai maki yanzu da zaki kama yiwa mutane kuka, kin ma gaidasu tukun koko islanci ya hanaki." Bani kad'ai ba su kansu sunsha mamakin Areef d'in,don basu tab'a ganin yayi mana irin wannan kakkausan lafazin, sab'anin y'an kwanakin baya ko fad'a zai mana cikin taushin murya da lallashi yake yi mana, baison ma wani yaji idan kuwa d'ayan mu tana kuka kamar ya taya ta saboda baya son kukanmu,amman yau shine ke d'aga mani murya yana kwatsata dole kowa yayi mamaki katseni yayi da cewa. "maza ki goge wannan kwallar ki gaidasu Idan kuma na dawo baki saki jikinki kamar da ba nida ke ne." Ya maido dubansa ga Anni yace, "Anni bari naje na kawo maku abun break, zo muje *shidah*." sunan da shikad'ai yake ce mata kenan. Fita sukai suka barni da Anni, matsowa tayi jikin gadon da nake ta rik'o hannun da aka cire mani drip, tana kallona kallon da ban tab'a ganin Anni tayi Mani shiba jinai tace mun. "y'ar gidan Anni yajikin naki." idona ya ciko da kwalla nace, "Anni Ina kwana." Murmushi tayi tace, "lafiya lau yajikin naki." "da sauk'i Anni saidai inda yah ya dokeni jiya Anni ciwo yake mun ko zaki gasa mun." tausayi ta bata Amman ta danne bata nuna hakan sosai bah tace, "Ayya sannu kinji bari Antynku ta kawo ruwan zafi sai agasa maki." "nagode Anni nah ke kad'ai ke sona ko." Murmushi tayi mata tace, "Aa y'ar gidan Anni kowa yana sonki, meyasa kikace haka. " "Anni yah Aree baya *kaunata* yafison salma akaina." Gabanta ya fad'i meke faruwa haka, Khairat yarinyar da bazata Gaza shekara 13 ba tasan kishi, danne fargabanta tayi tace, "Haba y'ar gidan Anni Waye yace maki haka, aduk cikinmu in banda Abbu da Maah babu mai son farincikin ku sama da Areef." Hawaye suka zubo mani nace, "no Anni wallahi yah baya sonah jiya naga haka yau ma naga haka, nidai daga yau babu ni babushi, Anni kinsan abunda yasa na fad'i jarabawa ta." Tana kuka take maganar hawaye share_share ga fuskarta,Anni gabanta banda duka babu abunda yake, sunan Allah kurun take anbata,don wannan lamarin na Khairat to saidai akira sunan Allah kurun. sake danne yanayin da take ciki tayi tana yak'e tace, "Ina jinki y'ar gidan Anni,meyasa kika fad'i exam dinki har kika bari aKai maki repiting." Wani kukan ta rushe dashi saida tayi iyakar Inda take so sannan tace, "Anni don Allah karki gaya ma kowa kinjiko idan yah yasani sake dukana zaiyyi." Ai Anni jitake kamar ta zura Aguje, (😂😂😂😂 yo baki bari Kiji komiye tun yanzu har kin shiga rud'u.) "Namaki Alkawarin babu Wanda Zaiji wannan maganar sanar da ni kinjiko." share hawayena nayi nace, "Anni tun daga ranar da Abbu yace su Yah zasu tai wata k'asa karatu nashiga cikin bak'in ciki, kullum saidai na b'oye toilet nayi ta kuka, ko idan naje makaranta inyi, har Cikin dare yi nake Anni saboda banson ya tafi, gashi maah tace idan suka tafi sai sunyo shekara shidda ko bakwai zasu dawo, Anni banson yah yayi mun nisa inaji kamar inbishi ko ince karya tafi, Anni kinsan abunda yake bani tsoro har yasa naki sanar da kowa." Anni tayi Wata irin zufah duk AC din dake sambad'owa ad'akin kuwa, daker ta had'iye wani kakkauran miyau amak'oshin ta tace, "Aa ta Alkhairin Abbu meke baki tsoron." Sake share hawayena nayi Ina cewa, "akwai ranar da sweetheart bata je makarantar islamiya ba, malamin mu ya gama mana darasin sa akan mutanen da ya halitta ka aura, da kuma wanda bai halatta ka aura bah, ban fahimce shi sosai bah Anni sai na bari da aka tashi naje har office d'in Su nasa meshi nayi masa tambaya, "malam don Allah ko mutun zai iya Auren yayansa wanda suka fito ciki d'aya." Kallona yayi yace Meyasa nai masa wannan tambayar nace, "wata ce tace na tambayar mata Kai." Jinjina Kai yayi yace mun, "Aa Khairat haramun ne babu aure tsakanin su har abadan." Banjira sauran bayanin sa ba na tashi na taho, Ko drivern mu banjira ba ranar nataho ina kuka, gida ban bari ko salma tasan me yafaru bah." "kinsan me yasani kukan Anni." Kallonta take tana jinjina kaifin tunani irin na Khairat,kafi tace"Sai kin fad'aman." Wani kukan ya kucce mani Nace, "Anni ba komi ne ya sani kukan bah illah yadda nakejin yah Areef acikin raina, Anni ni Yarinyace nasan da hakan, Amman nima ina mamakin yadda akai har nasan *so* Anni bansan tsawon lokacin da na samu kaina tsundum cikin *kaunar yah Areef* ba, wallahi ban saniba kuka yaci k'arfina naci gaba da cewa, wannan abun da nakeji yasa nayi ma malam tambaya, sai kuma naji cewar babu aure tsakani da shi har abadan,kinji dalilin fad'uwata jarabawa na gaza sanar da kowa saboda dai wannan Abun kunya ne awajen kowa............kuka yaci k'arfina Anni kiyiwa Allah da manzon sa karki gaya ma kowa, don nayarda dake ke bazaki dakeni ba shiyasa na sanar dake.........." Tabbas wannan lamarin ya hargitsa kan Anni, duk ta diririce Lallai Allah mai hikima tunda har hakan tafaru akwai abunda da Allah ya b'oye,amma Duk da haka yarinyar na buk'atar lallashi da ban baki,zatayi wannan k'ok'arin Insha Allah. lallashina take cikin kalamai masu kwantar da hankali,tare da cewa"ki fawwala ma Allah tunda shine ya sanya maki hakan, kiyawaita sallar dare nasan ki da wannan k'ok'arin,to kici gaba sannan kiyi yak'i da zuciyarki akan shi kiringa jarumtar danne komi kikeji Akansa, Allah zai yaye maki kinjiko y'ar gidan Anni,ki rage kuka ki rage taurin kai sannan yanzu so nake ki janye daga gareshi,ban kuma ce kidaina gaidashi ba Amman kijanye mashi idan bashine yakiraki ba karkije,hakan zai saukaka maki komi kinjiko y'ar gidan Anni." "to Anni nah Nagode zanyi Insha Allah daman ina tsoran gaya ma wani ya bigeni shiyasa nace bari ke in gaya maki, dama na yanke shawarar janye mashi." Haka taita lallashina har naji duk damuwata ta ragu sosai. Bajima wa Anty shidah ta shigo da Kayan break tayi mamakin ganina cikin walwala, har ina yimata dariya ruwan zafin Anni ta had'a ta d'age mun rigata na yi kwanciyar rufda ciki take Gasa mun, tana cewa ai dole yamaki zafi duba kiga yadda ya fasaki.......tana Cikin gasawar Ya shigo....... Lumshe idona nayi inajin dadin gasawar. Gabansa ya fad'i duk ni nayi mata wannan dukan, innalillahi dole kiyi fushi dani sweetheart,amman afili sai dai yace mun sannu kawai, tunda nace Yawwa ban sake ko kallon shiba komi Anni tayi mun, brush da wanka ta kuma bani abinci naci, Zuwa can saiga Maah da Dadyn meenah sai Abbu, sunjima kafin Su tafi sunata tsokana ta. Har aka sallameni ba muyi wata magana da shiba, haka muka koma gida salma sai nan nan take Dani, idone nawa kawai............. Na warke sumul Amman na shigo da Wata sabuwar d'abia ta rashin magana, bana shiga shirgin kowa haka duk maganar da zakai mun zan tarasu in baka one ansa. Anni ce kurun nake hira da ita ko salmar na banzatar da ita,duk Inda hankalin Areef yake yakai k'ololuwar tashi saidai duk maitarka bazaka gane halin da yake ciki bah. Kwamci tashi ba wuya wajen Allah har Gashi jibine tafiyarsu UK............. mom muhsen ce Mrs bb 👌🏻 love u fan's 💕💕❤💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 5. Hana kowa shiga akai har sai na farka daga baccin dasu kai Mani Allurarsa. Anni aka bari wajena da Anty shahida sauran yah mujahid yakoma dasu,salma hada kukan ta bazata tafi ba saida Yah Aree yayi mata jan ido sannan. Shima d'in bai tafin ba zamanshi yayi duk yadda Anni ke fama dashi yak'iya,dole ta kyaleshi haka sukai ta zaman zuru har ten thirty,sannan nurse din ta lek'o tace shishiga na tashi,Amman wani Cikin su yaje doctor nason ganinsa. Areef ya tafi Anni da Anty shahida suka shiga, Gaisawa sukai da likitan sannan ya zauna, Bayani yayi mashi akan abunda ke damunta. "cewa damuwa ce ta sakar mata masassara sannan da alama ma andoketa ne hada wannan dalilin yasa fever d'in tayi zafi, sannan dole akula da cin abincinta don bata cin abinci sosai,idan ba haka ba ciwon ulcer zai iya kamata, ga magani kasiya can phamercy." Godiya yayi mashi sannan ya fito yaje yasiyo maganin ya jiyo zuwa d'akin da aka kwantar da ita,jiya ke kamar ya kama dukan kanshi haushin kansa yakeji sosai akan abunda yayi wa sweetheart d'insa, tsoro yake kar tayi dogon fushi da shi, don yasan halinta akan rik'o.......sallama yayi Yashiga Ya ajiye magungunan gefe ya kalli Anni, "lafiya dai ko Anni." "da sauk'i dai tunda muka shigo ta k'iyiwa kowa magana, sai kuka da take duk lallashin munyi Amman taki yin shiru." Kallona yayi nayi saurin kawar da idona, Ina shashshekar kuka k'asa_k'asa yana son lallashin ta Amman Idan ya yiwa Khairat saku saku babu tantama raini zai shiga tsakanin su, so yake ya koya mata tsoransa wanda nan gaba baza ringa yi masa taurin kai bah,ya nason bata hakuri dukan jiya da yayi mata, Amman ya girmansa zai kasance a wajenta ba makawa raina shi zatai, Wanda shi bazai so haka ba zai nuna yama manta da abunda ya faru, Shan mur yayi wanda dole idan ta ganshi haka tashiga fargaba...... Cikin dakakkar murya yace, "jiyo nan nace." Jiyowar tayi gabanta na fad'uwa yace, "goge wannan kwallar banzai, me akai maki yanzu da zaki kama yiwa mutane kuka, kin ma gaidasu tukun koko islanci ya hanaki." Bani kad'ai ba su kansu sunsha mamakin Areef d'in,don basu tab'a ganin yayi mana irin wannan kakkausan lafazin, sab'anin y'an kwanakin baya ko fad'a zai mana cikin taushin murya da lallashi yake yi mana, baison ma wani yaji idan kuwa d'ayan mu tana kuka kamar ya taya ta saboda baya son kukanmu,amman yau shine ke d'aga mani murya yana kwatsata dole kowa yayi mamaki katseni yayi da cewa. "maza ki goge wannan kwallar ki gaidasu Idan kuma na dawo baki saki jikinki kamar da ba nida ke ne." Ya maido dubansa ga Anni yace, "Anni bari naje na kawo maku abun break, zo muje *shidah*." sunan da shikad'ai yake ce mata kenan. Fita sukai suka barni da Anni, matsowa tayi jikin gadon da nake ta rik'o hannun da aka cire mani drip, tana kallona kallon da ban tab'a ganin Anni tayi Mani shiba jinai tace mun. "y'ar gidan Anni yajikin naki." idona ya ciko da kwalla nace, "Anni Ina kwana." Murmushi tayi tace, "lafiya lau yajikin naki." "da sauk'i Anni saidai inda yah ya dokeni jiya Anni ciwo yake mun ko zaki gasa mun." tausayi ta bata Amman ta danne bata nuna hakan sosai bah tace, "Ayya sannu kinji bari Antynku ta kawo ruwan zafi sai agasa maki." "nagode Anni nah ke kad'ai ke sona ko." Murmushi tayi mata tace, "Aa y'ar gidan Anni kowa yana sonki, meyasa kikace haka. " "Anni yah Aree baya *kaunata* yafison salma akaina." Gabanta ya fad'i meke faruwa haka, Khairat yarinyar da bazata Gaza shekara 13 ba tasan kishi, danne fargabanta tayi tace, "Haba y'ar gidan Anni Waye yace maki haka, aduk cikinmu in banda Abbu da Maah babu mai son farincikin ku sama da Areef." Hawaye suka zubo mani nace, "no Anni wallahi yah baya sonah jiya naga haka yau ma naga haka, nidai daga yau babu ni babushi, Anni kinsan abunda yasa na fad'i jarabawa ta." Tana kuka take maganar hawaye share_share ga fuskarta,Anni gabanta banda duka babu abunda yake, sunan Allah kurun take anbata,don wannan lamarin na Khairat to saidai akira sunan Allah kurun. sake danne yanayin da take ciki tayi tana yak'e tace, "Ina jinki y'ar gidan Anni,meyasa kika fad'i exam dinki har kika bari aKai maki repiting." Wani kukan ta rushe dashi saida tayi iyakar Inda take so sannan tace, "Anni don Allah karki gaya ma kowa kinjiko idan yah yasani sake dukana zaiyyi." Ai Anni jitake kamar ta zura Aguje, (😂😂😂😂 yo baki bari Kiji komiye tun yanzu har kin shiga rud'u.) "Namaki Alkawarin babu Wanda Zaiji wannan maganar sanar da ni kinjiko." share hawayena nayi nace, "Anni tun daga ranar da Abbu yace su Yah zasu tai wata k'asa karatu nashiga cikin bak'in ciki, kullum saidai na b'oye toilet nayi ta kuka, ko idan naje makaranta inyi, har Cikin dare yi nake Anni saboda banson ya tafi, gashi maah tace idan suka tafi sai sunyo shekara shidda ko bakwai zasu dawo, Anni banson yah yayi mun nisa inaji kamar inbishi ko ince karya tafi, Anni kinsan abunda yake bani tsoro har yasa naki sanar da kowa." Anni tayi Wata irin zufah duk AC din dake sambad'owa ad'akin kuwa, daker ta had'iye wani kakkauran miyau amak'oshin ta tace, "Aa ta Alkhairin Abbu meke baki tsoron." Sake share hawayena nayi Ina cewa, "akwai ranar da sweetheart bata je makarantar islamiya ba, malamin mu ya gama mana darasin sa akan mutanen da ya halitta ka aura, da kuma wanda bai halatta ka aura bah, ban fahimce shi sosai bah Anni sai na bari da aka tashi naje har office d'in Su nasa meshi nayi masa tambaya, "malam don Allah ko mutun zai iya Auren yayansa wanda suka fito ciki d'aya." Kallona yayi yace Meyasa nai masa wannan tambayar nace, "wata ce tace na tambayar mata Kai." Jinjina Kai yayi yace mun, "Aa Khairat haramun ne babu aure tsakanin su har abadan." Banjira sauran bayanin sa ba na tashi na taho, Ko drivern mu banjira ba ranar nataho ina kuka, gida ban bari ko salma tasan me yafaru bah." "kinsan me yasani kukan Anni." Kallonta take tana jinjina kaifin tunani irin na Khairat,kafi tace"Sai kin fad'aman." Wani kukan ya kucce mani Nace, "Anni ba komi ne ya sani kukan bah illah yadda nakejin yah Areef acikin raina, Anni ni Yarinyace nasan da hakan, Amman nima ina mamakin yadda akai har nasan *so* Anni bansan tsawon lokacin da na samu kaina tsundum cikin *kaunar yah Areef* ba, wallahi ban saniba kuka yaci k'arfina naci gaba da cewa, wannan abun da nakeji yasa nayi ma malam tambaya, sai kuma naji cewar babu aure tsakani da shi har abadan,kinji dalilin fad'uwata jarabawa na gaza sanar da kowa saboda dai wannan Abun kunya ne awajen kowa............kuka yaci k'arfina Anni kiyiwa Allah da manzon sa karki gaya ma kowa, don nayarda dake ke bazaki dakeni ba shiyasa na sanar dake.........." Tabbas wannan lamarin ya hargitsa kan Anni, duk ta diririce Lallai Allah mai hikima tunda har hakan tafaru akwai abunda da Allah ya b'oye,amma Duk da haka yarinyar na buk'atar lallashi da ban baki,zatayi wannan k'ok'arin Insha Allah. lallashina take cikin kalamai masu kwantar da hankali,tare da cewa"ki fawwala ma Allah tunda shine ya sanya maki hakan, kiyawaita sallar dare nasan ki da wannan k'ok'arin,to kici gaba sannan kiyi yak'i da zuciyarki akan shi kiringa jarumtar danne komi kikeji Akansa, Allah zai yaye maki kinjiko y'ar gidan Anni,ki rage kuka ki rage taurin kai sannan yanzu so nake ki janye daga gareshi,ban kuma ce kidaina gaidashi ba Amman kijanye mashi idan bashine yakiraki ba karkije,hakan zai saukaka maki komi kinjiko y'ar gidan Anni." "to Anni nah Nagode zanyi Insha Allah daman ina tsoran gaya ma wani ya bigeni shiyasa nace bari ke in gaya maki, dama na yanke shawarar janye mashi." Haka taita lallashina har naji duk damuwata ta ragu sosai. Bajima wa Anty shidah ta shigo da Kayan break tayi mamakin ganina cikin walwala, har ina yimata dariya ruwan zafin Anni ta had'a ta d'age mun rigata na yi kwanciyar rufda ciki take Gasa mun, tana cewa ai dole yamaki zafi duba kiga yadda ya fasaki.......tana Cikin gasawar Ya shigo....... Lumshe idona nayi inajin dadin gasawar. Gabansa ya fad'i duk ni nayi mata wannan dukan, innalillahi dole kiyi fushi dani sweetheart,amman afili sai dai yace mun sannu kawai, tunda nace Yawwa ban sake ko kallon shiba komi Anni tayi mun, brush da wanka ta kuma bani abinci naci, Zuwa can saiga Maah da Dadyn meenah sai Abbu, sunjima kafin Su tafi sunata tsokana ta. Har aka sallameni ba muyi wata magana da shiba, haka muka koma gida salma sai nan nan take Dani, idone nawa kawai............. Na warke sumul Amman na shigo da Wata sabuwar d'abia ta rashin magana, bana shiga shirgin kowa haka duk maganar da zakai mun zan tarasu in baka one ansa. Anni ce kurun nake hira da ita ko salmar na banzatar da ita,duk Inda hankalin Areef yake yakai k'ololuwar tashi saidai duk maitarka bazaka gane halin da yake ciki bah. Kwamci tashi ba wuya wajen Allah har Gashi jibine tafiyarsu UK............. mom muhsen ce Mrs bb 👌🏻 love u fan's 💕💕❤ [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 3. Alhamdulillah gida ya tsaru iyakar tsaruwa,babban gidane mai fat Kala Kala wanda saboda girman Abota irin ta su Alhaji farouk yace da Amininsa jafar yazo su zauna tare,har kuka yayi saboda farin ciki haka suka dawo gidan rana guda, komi sabo aka loda masa yayinda tuni angyaare ma Inna wancan gidan ba zaka tab'a cewa shine bah. Rayuwar ta cigaba da kasance masu Cikin jin dad'i da kwanciyar hankali,yayin da Wata irin shak'uwa mai K'arfin gaske ta shiga tsakanin *AREEF* da k'annensa *khairat da salma* idan Sun dawo makaranta shine wankansu ya shiryasu ya zubo abinci yaringa basu har sai sun koshi, sannan assessment d'insu zai zauna ya tusasu gaba yana guarding d'insu yaga Sunyi shi lafiya lau, Areef saboda k'annensa ko fita baya yayi, Duk nacin *mujahid* haka zai rabu dashi, haka shahid da shahida Duk yadda suka so Cikin weekend ya ringa binsu shopping sai yace bazai bisu bah, saboda suna cin zalin sweetheart dinshi,dole sukai hakuri saidai driver ya kaisu shikuma Ya ware rana ya kaisu da kanshi.........wata guda kenan da kammala secondary d'insa,tunda twince suka girma Maah ta hana yaringa masu wanka da shiryawa,tunda yanzu ko wacece zata iya yiwa Kanta wanka da shiryawa, yanzu suna js one yayinda shahid da shahida Suke ss2, Muhajid tare sukai graduation da Areef, Neenah ce take js3. Shirye shiryen tafiyar Areef da Muhajid ake zuwa UK jamia,wanda idan suka tafi baza su dawo bah sai Sunyi har masters d'insu........ Motarsu na tsaya wa suka fito Aguje suna kyalkyata dariya,kowa so take ta riga y'ar uwarta isa cikin gida wajen yah Areef kafin Su shiga saiga su sun fito shida mujahid Aguje sukai kanshi, dariya suke masu shida mujahid......kafin ya ankare *salma* ta mamuk'eshi tana dariya har da yiwa *khairat* gwalo aikuwa me zatayi banda kuka, bilhakki da gaskiya ta shige gidan tana rera kukan shagwaba,duba Maah tayi bata ganta ba yasa ta nufi b'angaren Anni tana shiga sukai kacib'is Anni ce ta tatareta. "lalalala kairyn Anni waya tab'aki zo zo taho muji." Ta jata jikinta Maah tace, "Uhm bai wuce rigirmarsu ita da salma, yanzu haka riganta tayi isa wajen Areef." Annin tace, "wai haka ne yar gidan Anninta." Wani kukan ta sake fashe wa dashi tana cewa, "Anni kingani salma ko, kullum sai ta ringa rigana wajen Yah Aree,kuma nace mata yau ta barmun in rigata shine ta k'iya,gasu can suna mun dariya." ..........ta sake rushewa da kuka. Dariya Maah tayi tace, "ai na gaya maki kullum rigimar kenan, salma ta rigani,salma ta rigani tunda ke lusara ce komi babu hanzari,ba dole komi salma ta rigaki ba ko wanka da shiryawa sai bakina yayi tsawo kike gama wa inhar Areef baya nan." Anni zatai magana Areef ya shigo rik'e da hannun salma, har tayi wanka da ga dawowar ta ga lollipop nan Areef ya bata tana ta sha. "Ayya sweetheart gamu munzo biko,ke baki yin zuciya kiringa riganta kema, Amman kullum sai Kinyi kuka, Kinga zo zo mu shirya." Maah dai ficewa tayi tabarsu Inda sabo sun saba wannan fad'an basu wuce d'an lokaci kad'an sun shirya. Anni ta mik'e tace, "sorry y'ar gidan Anni kije yayanku zai shirya ku,sanan kiyi wanka anjima ma zaku rakani unguwa." Salma tace, "Anni irin wannan gurin da kikaje damu rannan,har aka bamu chocolate." Dariya tayi tace, "shazumamu sarkin Shan zaki bacan ba,wani wajene kama hannun y'ar uwarki kuje ki taya ta shiryawa. " Kan ma salma ta iso wajenta ta fashe da kuka, "ba zanje wajensu bah." Ta ruga can cikin gidan Annin ta barsu sake da baki." Don irin hakan bai tab'a faruwa ba, Duk yadda suka b'ata da juna to kafin anjima sun shirya kansu, ko kuma wata sa, in Yah Aree ya shiryasu. Salma tace kamar zatayi kuka, don idan sukai fad'an duk rud'ewa take ko kau itace aka kwara. "Yah Kaga sweetheart ko." Idonta ya cika da kwallah Murmushi yayi ya d'an sunkuyo yace"kar kidamu my Angel, sweetheart dinki zata huce zo muje muci abinci." Anni tace, "zan lallasar maki ita kinjiko salma yar albarka." D'aga Kai tayi tana sake goge kwallarta,janta yayi suka fita, Annin ta wuce wajen Khairat d'in. 💕💕💕💕💕💕💕💕 Wasa wasa Khairat ta k'i shirya wa da salma, haka Shima Areef d'in ta daina shige masa,tama koma gaba d'aya wajen Anni bacci ne kurun yake maido ta cikin gidansu, hakan ya saka salma cikin damuwa saboda tunda suka taso irin haka bata faruwa tsakaninsu. shi kanshi Aree ya shiga damuwa ba kamar k'iriniyarta da tsalle tsallenta, da rigimar ta. Amman duk yadda yaso ya jawota jikinsa ta k'iya,don da ya tunkarota zata fashe da kuka,dole zai barta don subiyun baya son kukansu. shahida ce ta sameta b'angaren Annin tace tazo Yah Aree yana kiranta, Dole tataso suka taho shahidar nayi mata fad'an fushin da take da salma, wadda gata can bata da lafiya saboda taurin kanki Khairat. Cikin muryar kuka tace, "da gaske kike Addah." "gata can ma tak'icin Abinci har yah Aree yayi yayi Amman ta k'icin komi. " Aguje ta k'arasa cikin gidan falon farko ta same su, Zube wa tayi gabanta tana kuka tace, "sweetheart Miye haka, don kawai Ina fushi shine zaki wani sheme kina wani pretending,kinga ki tashi na huce bazan sake fushi da sweetheart d'ina ba,tashi kici kinjiko inhar baki son na cigaba da fushin." Kamar almarah haka suka ga salma ta Mike tana cin abincin,suna hirar su cike da so da kauna. Areef wani sanyi yaji don ko kad'an baya son fushin ko wace cikinsu. Cikin k'an k'anen lokaci komi ya daidai ta, saidai fah Khairat ta canza salo ta daina shigewa Areef, ko assignment ne ta k'asa yah mujahid shine zata je ya koya mata, ta daina rigima da salma akan Areef, ko k'iriniyarta da take masa ta daina Magana ma sai ta Kai makura take masa........gashi lokacin tafiyarsu ya taho don yanzu bai wuce 2 weeks masu zuwa. Amman gefe guda Khairat kullum cikin lissafin tafiyar take, duk kwanan duniya sai tayi kuka ahankali ta fara ramewa duk ta fice hayyacinta,haka akai jarabawa tashiga js3 aman saboda rashin maida hankali saida aka mata repiting......wannan dalilin ya jawo b'atawar *Khairat da Areef* Taufah ana wata ga wata. Mrs bb ce Mom muhsen [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 6. Nasan da labarin tafiyar su Amman ko Anni ban nuna ma halin da zuciyata take ciki ba, tabbas inajin babu dad'i ba kamar jin danai wai salma zata yi masu rakiya har can, ita da Abbu da Dadyn meenah. Wanda da sanda ana maganar tafiyar Abbu cewa yai hada ni za,a rakiyarsu shine yanzu don banyi k'ok'ari ba za,atai abarni basu san yanzu duk abunda zai had'ani da Yah Areef ba bana sonsa, ko sunyi mun tayin zuwa zance bana zuwa. I think kun san yadda feeling d'in missing yake, Wanda da kaji wannan yana yin gara kayata rusa kuka, to haka Khairat takeji,duk yadda taso yin kukan abun yayi mata wuya saidai zafin da takeji cikin ranta, haka tak'i bari Anni ta fahimci komi akan tafiyar tasu,wanda hakan halin Khairat ne inhar bakaso gane abu ba is hardly ka fahimci yana yinta. tana kwance kan gadon meenah wanda yanzu d'akin ya koma nasu su biyu,karatun English novels nake na soyayya, jin abud'e k'ofa yasa nayi saurin b'oyewa don yah mujahid ya hanani ni kuma sun shiga jikina bazan iya daina waba. Ganin salma ce yasa nafiddo naci gaba daga Inda na tsaya, suna rage mun k'uncin da nake ciki,zama tayi kusa da ni ban kulata bah ganin kuma ba kulatan zanba yasa tace, "sweet............" Katseta nayi da cewa, "pls idan kinsan takura ce ki barni don Allah." Shiru salma tayi don iya wuya yau Khairat ta kai salma, wannan halin ko inkulan da take mata ya isa haka, ba ita takar zomon ba rataya aka bata.......cikin k'uluwa tace man. "enough is enough *Khairat* haba ko ni nayi maki laifin iyakar horan da zakiyi mun kenan, Amman taya zan ringa binki kina mun wulakanci,to nagaji nagaji haka nan idan kin gadama Kizo yah Areef na kira." Anni ce tashigo taga ficewar salma rai b'ace abunda zaka jima baka gani tare da ita ba, mutunce mai hakuri sosai Idan don ita zata jaka fad'a zaku shekara aru aru bakuyi bah, tabbas tasan Khairat ce ta tun zurota. Cikin fad'a Anni ke tambayarta abunda ya had'asu, banji komi ba nayi mata bayani fad'a tashiga yimun tana cewa tunda banjin magana tafita harkata, gashinan naja wadda keta son ganin farinciki na tayi fushi dani, kuma intashi maza inje kiran kafin raina ya b'aci, muddin naci gaba da wannan halin zamu b'ata da ita sosai. Ganin duk yadda ta tada hankali tana fad'a yasa na bata hakuri ashe k'ara kular da ita nayi,moper ta d'auko zata maka mun na tashi na rugo ina dariya, ban tsaya ko Ina ba sai falon su Yah mujahid shida yah Areef. Kuka na samu salma nayi tana gaya masu,abunda ya faru, sai naji tabani tausayi matuk'a jiki babu kwari na shiga can gefe na zauna na gaida yah mujahid sannan Shima Nace masa, "yah ina wuni." Kallona yake bazan iya fassara shiba, kawai dai nasan kallon mai laifi yake mun kafin ya Kauda idonsa yace, "haka zan tafi kuna fad'a da junan ku ko,na lura kin fara rainani *Khairat* sunan da ya anbata yasa babu shiri na kallesa, akai sa,a idonsa na kaina kallon Cikin ido mukai ma juna, sai naji ko kad'an banji dad'in sunan da yakira ni dashi bah, sadda kaina nayi naji kamar kwallah zata zubo mun,danne wa nayi daker ta tsaya. Yace, "kiba ta hakuri abunda kika mata, idan kuma kuka sake naji labarin kun sake b'atawa Allah takakkiya zan maku oya maza Kunshirya ina gani." "tabarshi kawai Yah bana so." Cewar salma. B'ata fuska yayi. yace, "bana son taurin kai Kin sani salma ban sanki da haka ba, don haka karki fara kwai kwayon halayen da basuyi maki kyau kinji *my Angel*." Saida kirjina ya yi Wata irin bugawa na runtse idona kawai jinai ya dakan tsawa. "zaki bata hakurin kokuwa sai na tattakaki awajen nan." Yah mujahid yace, "haba Areef Meyasa Kwanan nan kakoyi yiwa yarinyar nan tsawa ne,ehyi ba halinka bane kadaina." Bai kula saba jikina yana rawa kaina na k'asa Ina zubar da kwallah ba tare da Sunyi shawara dani bah,bakina yana rawa Amman na kasa furta komi........ Azafafe ya tashi ya d'auko dorinarsa jinai zau zau ga bayana..........k'ara na fasa inafashewa da kuka Yah mujahid ya anshe dorinar yana masa fad'a,kamar zai dakesa Shima Cikin zafin ran da bansan yana da shiba yace. "wallahi muddin ba ta bata hakuri ba jikinta sai ya gaya mata, raini ya fara shigowa tsakani da ke ko, to mun k'ulla kenan nida ke daga yau wlh, zan saukar maki da wannan girman kan naki." jikina rawa yake kamar mazari, sosai na tsorata da dukan sa yanzu kam tsoran sa yafara shiga ta tabbas,don babu abunda yake firgita ni kamar duka, ganin zai fizge ya yo kaina yasa na sake rushewa da kuka ina mamuk'e kujera. Saida Yah mujahid yace, "oya Khairat ba y'ar uwarki hakuri kinjiko ai ba fad'uwa kikai bah." Bawai inajin k'yashin bada hakurin bane taurin kai ne irin nawa, Amman ganin zai sake dukana yasa nace ina kuka. "kiyi hakuri bazan sake bah." Amman salma tai mun shiru jin haka yasa yace sai nayi ta bata har sai tayi magana. saida na bata sau uku sannan tace tayi. Zuwa lokacin fuskata tayi jajawur kamar tumatur, tashi nayi zan tafi ya fizgoni nayi wata irin fad'uwa saida yah mujahid ya tadani........saboda haushin abunda yayi fita yayi yabar falon. d'akin yayi shiru sai shashshekar kuka nakurum, da karar AC. Ina jin sanda Ya ke Ajiyar zuciya kamar mai iska naji ya fara magana Cikin taushin murya,abun mamaki yabani yanzu fa yake kamar zai tashi sama saboda zuciya, Amman jibeshi kamar bashi bah. "zan tafi na barku don haka kusan mekuke ciki, kar na sakejin wai kunyi fad'a,sanan maganar karatunku karkuga ban nan kuce zakuyi abunda kakeso, wallahi Ina biye da duk motsinku don haka amaida hankali a ajiye mun k'yak'k'yawan results,ke kuma da akama repiting sai ki maida hankali agaba kuna iya tafiya........salma ta fara mik'ewa sannan ni bazan Iya kwatanta yadda zuciyata ta keba, nasan dai ina cikin kunan zuciya da wani irin yanayi marar misltuwa,daker nakai k'ofar har salma ta wuce jinai yace, "zonan" Tsaye nayi na kasa juyowa kuma na kasa tafiya,saida ya dakan tsawa sannan jiki na rawa na isa gabansa na sadda kaina..........shiru tsawon lokaci baice komi ba, nima ban motsa ba, na sadda kaina kurun kwalla na zuba suna d'iga ga hijabina. Jinai dai kawai ya d'ago fuskata nayi hanzarin rufe idona yayin da wasu kwallan suke zuba, handcif ya saka mai fitinennen k'amshi ya na goge mun kwallar.............amman wasu na sake silalowa bai daina gogewar ba har saida suka k'afe, sannan ya saki fuskar. Yace Cikin muryarsa da tayi matukar sanyi, "idan kika sake kukan nan ko bayan kin tafi d'aki nida kene swe.....Khairat." Fita nayi inajin k'afafuna kamar ba zasu iya d'aukata ba, wannan ranar yadda naga rana haka naga dare, tun asuba akafara shirin tafiyarsu, inajin sadda salma tatashi nayi kamar bansan me take bah.......sai tara na tashi nafito wanka kenan Ina tsane jikina naji muryarsa yana tambayar meenah Ina nake, tace ina d'aki.........yana bud'e k'ofar ina shigewa toilet na da tse k'ofar................... Mom muhsen ce Mrs bb 👌🏻 love u wujiga wujiga fan's d'ina ❤❤❤❤❤ [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 7. Jingina nayi da k'ofar toilet d'in Ina sauke numfashi k'asa k'asa, jikin k'ofar yazo ya Jingina bayan sa Shima, murya can k'asa k'asa yake magana, tayi rauni sosai sai kayi tunanin kuka yake. "zamu tafi *sweetheart* saidai abun haushin zamu rabu kina fushi da Ni,pls kiyi hakuri ki fito ko dukana kiyi Wanda zan ringa tunawa da shi." Kuka ya kucce mun mai tab'a zuciya,kamar numfashina zai fice runtse idonsa yayi yana jin babu dad'i, duk yadda yaso yasake ganinta k'iyawa nayi, haka yafita jiki babu kwari........daman shikad'ai akejira gab'a d'aya gidan aka tafi masu rakiya banda Maah da Khairat. Ina bayin nan har suka tai saida nasha kukana kamar ba gobe sannan nafito daga bayin,daidai shigowar Maah d'akin. Zama tayi bakin gadon mu tana kallona bata dai ce komi ba har na gama shiryawa, nazo nayi walha da nake yi na gama sannan na kalleta nace. "Maah ko wani abun zanyi naga tunda kika shigo baki ce komi ba." Wani kallon banza tayi mun kafin tace mun, in biyota d'akinta. Jikina yayi sanyi Allah yasa ba laifi nayi mata ba, Ina tsoran fad'an ta Maah babu sauk'i indai wajen fada ne,duk na tsure tsoro nake kar ta dokeni gashi mai cetona bainan,don wata sa,in idan na mata taurin kai jibgata take kamar jaka, sai shine zai kwaceni. Zama nayi k'asa wajen k'afafunta, na sadda kaina kamar munafuka. Sunana ta kira. " *UMMUL KHAIRI*" D'agowa nai na kalleta nace, "Na,am Maah." "Miye matsayina wajenki." "Maah ke mahaifiya tace." "idan ance mahaifi me ake nufi kenan." "ana nufin wanda ya yi silar kawoka duniya, kuma wanda nauyin kulawarka ci da sha da sutura suka rataya akansu, idan baka lafiya akaika Asibiti tarbiyyarka tana kansu." Wani dad'i ya kama maah lallai duk cikin yaranta babu kamar Khairat wajen komi, Amman sai ta sake Shan mur tace. "sab'amasu yana nufin mekenan." "yana nufin ka sab'ama Allah [S W A] kuma duk mai ja dasu bazai tab'a ganin daidai bah." Jinjina Kai ta sake yi sannan tace. "madallah da malamin islamiyyarku,tunda har duk kinsan wad'annan bazan sha wahalar yi maki bayani bah, kallani nan Khairat." Banyi musuba na d'ago Ina Kallonta ina ganin wasu maganganu masu tsananin nauyi cikin idonta, jinai taciga da cewa. _*"matsayina na mahaifiyarki, na umurceki da cire duk wani Abu dake ranki akan yayanku AREEF,sannan na haramta Aure tsakaninki dashi har gaba da abadan, duk Yarinya ce ke nasan kinsan me ake nufi da haramci,to na haramta maku junan ku, kuma muddin kika take doka ta wallahi ummul khairi BAN YAFE MAKIBA."*_ Iya dauriya nayi bansan ni d'in jaruma ce ba sai yau, ilahirin jikina rawa yake amman nadanne na k'i bari Maah ta gane, idona k'em akanta nace. "insha Allah nayi maki wannan alkawarin,saidai tambayar da nake da ita itace..........." "Bana sonjin tambayar,duk motsinki na sani Khairat karkiga ina nuna halin ko in kula akan lamarin ku, wallahi kar nake kallonku, don haka idan na sakejin kun samu sab'ani da juna keda salma billahil azim zanar tsiya zan maku,kiyi k'ok'ari idan ta dawo ku sasanta kanku,sannan kan karatunki, wallahi Khairat idan kika sake barin damuwa tayi gala ba kanki nida kene." "don haka idan kunne yaji.......... Kaina k'asa Nace, "jiki ya tsira." Tace, "good girl,sannan kidawo da walwalarki, bana son wannan d'ari_d'arin da kike bance kuma kidaina yi masa magana ba,ko kuyi fira, Aa zakuyi duk wannan amman muddin kika sakejin wani yana yi kanshi.........basai na ida ba kinsan sauran tashi Kibani waje." Jiri ke neman kada ni na dafa bango zan fita,sai kuma na juyo Nace, "Maah." kallona tayi alamun tana jina. Cikin karyewar murya kad'an ya hana kuka na bayyana nace, "Maah, don Allah kiyi mun hakuri bazan iya cigaba da magana mai tsawo dashi ba,idan nayi hakan bazan iya hana zuciya ta jin wani abuba, kibarshi murinka gaisawar ya isa,sannan kiman afuwar yau bazan iya warware wa lokaci guda ba,amman namiki alkawarin bazan Kai lokacin da salma zata dawo ahaka bah.......plss Maah." Wani marayan Tausayin y'ar tata ya rufeta,jawoni tayi ta rungume,wanda ba zance ga tsawon lokacin da Maah ta d'auka rabon da ta rungumeni. Cikin muryar lallashi tace, "nayi maki wannan uzirin Khairat,badan na cuta maki nai hakan ba, gata ne nayi maki, ko ince nayi maku keda yayyenki, na kausasa kalamaina ne don na tsorata ki akan abunda kikeji kan AREEF,amman bazan iya hana Allah ikonsa akanku ba, kiyi k'ok'arin kiyayewa kinjiko ta alkhairin Abbunta. Wannan kalamin yasa nasamu natsuwa, nasake mata alkawarin kiyayewa,k'arshe ajikinta nayi bacci, ta kwantar dani ta fita................ Mom muhsen ce Mrs bb 👌🏻 [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 9. Shirye shiryen dawowar Su kawai ake babu ji babu gani,b'angarensu angyaare an cire komi ansa sabo, har kaya sawa saida Abbu Ya siya masu, Manya da k'anana. Abun har mamaki yake bani, saikace shugaban k'asar mu ne zaizo,amman sai ban nuna ba nayi kamar ban san me Akeba,ban shiga mamaki ba saida naga ana sake fentin gidan, nace Eh gaskiya lamarin azimun ne. Sweetheart kuwa duk tafi kowa zak'alk'alewa, banga wanda yayi mata magana ba,saidai suyi ta yi mata dariya. Ranar da ta kama jirginsu zai sauka,washe garin muka tai registration,sweetheart cewa tayi zatayo daga baya, Amman bazata iya fita gida ba har sai sun iso. Haka muka tai nida meenah wadda abun ya isheta har tace, "rawan kan sweetheart d'inki tayi yawa Khairat,ba zaki ringa kwab'arta bah." Murmushi nayi Ina danna wayata, kasancewar itace ke driving d'inmu ni ina gefenta. "Uhm yah meenah kenan, ni asuwa ince ma sweetheart ta rage rawar Kai, wai kokin San yadda take ji dashi kuwa!uhmmm muddin nayi mata Wata magana fad'a zamuyi, kibarta tayi tunda yanzu babu haramcin hakan,duk da har yanzu basan ainahin abunda ya faru ba." "Shikenan,Allah yasa mudace amman hakan babu kamun Kai gaskiya, koshi yana sonta yadda take masa zai ji tana sire mashi." "can su gane banda Wata matsala dasu, ni yanzu fata nake Mu gama registration d'in nan lafiya,so nake muje Dubai." "murmushi tayi mun tace, Kedai kawai Kice wajen heartbeat d'inki zaki." Dariyar da ban shirya mata ba nayi, "kina da ban dariya,wai kin mance cause d'ina ne haba yah meenah wallahi ni ban shirya ma soyayya yanzu ba, saboda ita tana da zak'in da zata shagaltar dake daga komi ma,haka zalika tana da rad'ad'in da zata hana ki dukan wasu abubuwa masu muhimmanci,cikinsu kuwa harda karatunki, tsaf zata k'arar da farincikinki Arudun Allah." Dariya meenah taringa yi harda dukan Sikiyarin motar, haka suka cigaba da hirarsu har sukaje. Kasancewar ranar farko ce shiyasa suka tadda wajen acike,kamar ana rabon kud'i shiyasa basu samu kansu ba sai anata salar magruba, wai ahakan ma basu gama ba sai sun sake dawowa gobe........a matukar gajiye suka iso don yanzu Khairat kejansu,kamar tayi kuka don gajiya tana shigowa harabar gidan gabanta ya yanke ya fad'i........ras ras kallon juna mukai nida yah meenah. "yah meenah Bazan iya shiga gidan nan bah." Idona ya canza Kala kuka nake so nayi Amman Ina danne halin da nakejin zuciyata. Dafa kafad'ata tayi cikin kwantar da hankali tace, "come down Khairat,babu abunda zai faru, kiyi ta karanta duk adduar da tazo bakinki,Allah yana sane dake." Kwallah sun cika idona nace, "yah meenah,inajin tsoran tashin wani miki acikin zuciyata,maah tace mun Idan nasake jin wani feelings Akansa bata yafe bah,yazanyi Idan zuciyata ta k'i saurarena hakan yana nufin na sab'a umurnin Maah, kuma Allah zai tsine mun." Na fad'a ina goge kwallah. Ajiyar zuciya meenah tayi ta anshi key din ta kashe motar,sannan ta zagayo Inda nake na bud'emun,kallonta nayi ta jinjina mani Kai sannan nafito. "Allah bazai kama ki da laifin da bakida tsumi ko dubara Akansa, shi ai yasan abunda yake zuka tanmu,bazai yanke mana hukuncin da yasan bamuda laifin saba, saboda bake kika sama kanki bah Khairat,don haka kiyi iyakar k'ok'arin ki kiyi wa Maah biyayya,sauran kuma kibarwa Allah,idan mun shiga ki saki ranki kamar babu wani Abu,kiyi mashi irin na y'an boko ke kanki zaki samu natsuwa,ok." Murmushi nayi inajin Wata natsuwa na Shigata,ina k'arajin Yah meenah cikin raina itace mai kwantar mun da hankali koda Yaushe sai fah Anni, don sweetheart bama ta natsuwa balle har tasan damuwata ta lallasheni. Cikin kwarin guiwa muka nufi cikin gidan.......... [Wayyo tsoro nakeji😟 anya kuwa Khairat,🤔 Amman duk da haka kin bani tausai😢] Tunda da kan Yah Areef d'in har kawo kan salma babu Wanda babu falon,kirjina kamar zai fito wajen daker nake yak'e, har muka k'arasa Cikin falon tsundum. "Aaaaah kaga mutanen turai,iyyen bah wai kun ganku kuwah yah Areef,yah Muhajid kaine kuwa anya ba musanya mana ku akai ba." Duk ni nake fad'ar haka inajin dukan kirjina yana yawaita,amman duk da haka murmushi mai kyau akan fuskata. Harara ya wurgomun cikin sigar wasa ya d'auke kai yana ma Yah meenah magana. Murmushin na sake k'awata wa na isa ga Yah mujahid,zama nayi gefensa Ina lank'washe k'afafuna Nace ina rik'e ha6ata. "wallahi yah mujahid idan a Wajene naganku zagaye ku zanyi in wuce saboda ko k'an wanda yasanku shekarun baya, yanzu bazai iya gane ku bah." Duk dariya aka saka mana, Salma ce ta shigo d'auke da tiren dinner d'insu. "sweetheart Kinga yah Aree, Kinga yadda ya koma wallahi nayi zaton irin turawan nan ne da ya shigo, ban zaci shine bah." nan ma dariyar ake na kalleshi Shima ni ya kallah, muna had'a ido ya sake harara ta,dariya nayi kafin na shagwa6e fuska na Kalli Anni nace, "Kinga Anni tunda na shigo yake ta harara ta, kofa ansa sannu da zuwar da nayi masa baiba." Annin tace. "Haba babban yaya laifin me yar gidana tayi." Wata murya naji tana magana kamar Ana busa sarewa, cike da tsananin taushi,laushi Kai harda wani sino take fitarwa,saurin Kallonsa nayi Ina sake baza kunnena donjinta da kyau. "Anni,karkice komi wallahi don tunda kika ga nayi shiru kibari kawai, don Kinga Abbu baice komi ba don yasan ta Alkhairin tashi tayi mun laifi." Lumshe idona nayi na kalli maah cikin langa6ar da fuska. "Maah, ba zaki ce komi bah." Murmushi tayi mun tace, "ba ruwana Khairat,kema fa kinsan bakiyi daidai bah." Maida kallona nayi wajen Abbu nace, "Abbuna Kace yayi hakuri." Tashi yayi yana ceman, "ta Alkhairi Kinga nayi nan zanje wani waje sai ten zan dawo, ai da nayi maku sharia." Duk wanda na nufa sai ya zare kanshi, daga mai yimun dariya sai mai tashi ya fice. Yah meenah tace, "yah taci albarka cina ayi mata hakuri, wallahi registration mukaje, munso dawowa kan lokaci kodan mu tarbeku,Amman wallahi wajen a cike daker muka samu aka fara mana, kuma ba agama ba dole sai mun koma gobe." "Shikenan Aminatu jeki abunki." Kallona tayi tace, "saikin taho Khairat bari naje nayi wanka yunwa ma nakeji." Ta fice daga ni sai shi da yah mujahid sai sweetheart,dake ta wani narkewa. Yana biyewa shirmenta,tab'e baki nayi ganin ita tak'i ce masa komi, yah mujahid nayi ma magana,ganin shi ya shareni. "yah mujahid bari naje na dawo kabani labarin UK." Murmushi yayi mai kyau don yah mujahid badai kyau bah,shida Yah Aree saidai suzo tangal. Har na fice banji Yace mun komi ba, sai hirarsu suke da salma ita ce ma tafi bani mamaki, ganin tak'i saka baki ya kulani. [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 8. Rayuwa mai cike da k'alubale, wannan haka yake dukan nin wanda kake gani, to fah kowa da irin yadda rayuwar take zuwa mashi,don babu Wanda zaice tana yimashi 100%,babu shi wallahi dole akwai ta Inda Allah zai jarabceka. Haka yake ga Khairat Allah ya jarabeta da matsanancin son yayanta, Wanda ita kanta bata san lokacin da hakan ta faru da ita ba,gashi bata da masaniyar wace irin ak'akace tsakaninsu, shin ita dashi Waye bare kuma Waye d'angida,idan ta fahimci Maah yadda tayi mata magana ya nuna akwai aure tsakaninsu, Amman to Miye dalilin yi mata shamaki da shi. bata da mai bata wannan ansar, zata bita yadda tace tayi alkawarin bazata sab'ama umurnin taba, zata yi iyakar iyawarta don ganin duk wasu feelings da takeji nashi ta yi yak'i dasu. Tsakanin ta da salma yanzu zakayi mamaki, sun koma y'an biyunsu sak,kaya kansu Iri d'aya suke saka wa,duk wani Abu na shawara zasuyi da juna, kowace nayin iyakar k'ok'arinta wajen ganin ta guje b'acin ran y'ar uwarta. B'angaren karatunsu yanzu komi successful duk da ba class d'aya suke bah,suna tsananin taimakon juna wajen karatu, shahid da shahida Suke guarding d'insu sosai Idan suka dawo gidan, koda salma zasuyi jsce Khairat ce tayi mata time table tana sake fahimtar da ita wasu abubuwan da bata gane bah,hakan ba k'aramin dad'i yayiwa su Maah da Abbu ba, ganin haka yasa yace zai saka asa sunan ta cikin masuyin jsce d'in. Amman tace Aa yabarta ita ba tajin komi, hakan ma yana mata dad'i don tana koyar da y'an class d'in su, dole suka k'yaleta haka salma tazo tayi jsce d'inta cikin sa,a. B'angaren yayansu kuwa babu ranar banza da baya bugo waya, kuma kowa Ana gaisawa dashi banda Khairat,duk yadda Abbu zai yi ta ansa su gaisa saidai tace Aa Abbu Kace dai ina gaidashi. Salma kuwa saboda Shak'uwar su da Areef yasa Abbu Ya siya mata waya 7+ da tayi jss d'inta, tun mutanen gida na mamakin shak'uwarsu har suka daina, don idan suna Waya kamar wata zararra dariya da shagwaba,idan kuwa sukai fad'a Khairat ce ke gaya mata yadda zasu shirya. Yawan sanar da ubangiji damuwarta da take, yasa cikin ikon Allah duk wani zafi da kunan zuciya da takeji idan taga yadda salma Suke waya dashi yanzu ta samu sauk'i sosai, don wata sa,in ma dariya take musu. Cikin k'ank'anen lokaci salma ta rufta tarkon kaunarsa,wanda ita kanta bata sani ba Amman Khairat ta Ganota,mamaki take tana jiran taji Maah tayi ma salmar gargadin hakan amman taji ko Uffan batace mata ba, tambayoyi ne cike cikin cikinta,amman baiyuwa tayi ma Maah su don bazata fad'a mata bah. Ta tattara duk wasu abubuwa ta watsar da su gefe guda, ta d'auki karatunta da muhimmanci,indai ka ganni Zaune to ko dai karatu nake ko kuma ina duba wasu words ga dictionary,na saka Kaina busy da ko hirarshi da salma kemun some times bana ma zaman d'akin balle tayi mun, Ina falo cikin mutane Ina d'an saka baki cikin hirarsu Anni. Su Anty shidah da Yah shahid Sunyi candy,yanzu su Yah kusan shekararsu d'aya da rabi da tafiya, Yah meenah yanzu mate d'in juna muke,shiyasa k'awancen mu yazo d'aya,komi tazo wajena Khairat kaza Khairat kaza, har karatu meke tare. *shekara kwana inji y'an hausa.* Har y'an matan uku sun kammala secondary school d'insu, don har Dadyn meenah ya fara hidimar samar masu admission xuwa jamia,yah shahid yana spain yana karantar engineering,Anty shahida tana katsina tana karantar business administration,ta dad'e tana masifar son harkar kasuwanci,maah taita fad'a akan me zata ce shi zatai, saida Anni ta fahimtar da ita cewa, yaro idan yace zai iya had'iye gatari sai asakar masa k'ota,saboda idan aka matsa mata kan wanda ba taso baza tayi karatun bah, wannan maganar ta anni ce yasa su Abbu suka barta tatafi, y'ar aduwa takeyi amman wajen kanwar Abbu take zaune, don dama goggo baraka tana son Anty shidah. Manyan k'asa su Yah mujahid da Yah Areef suna can UK an rik'esu tunda suka gama, wai sai Sunyi masu aikin shekara uku,yanzu cikin ta biyu Suke next year suna gida war haka. Salma kamar tayi tsuntsuwa taje inda suke,zuwa yanzu Anni tayi mun bayanin yadda muke da yah Areef, sai hankalina ya kwanta, ganin yadda sweetheart d'ina ke masifar kaunarsa Idan aka rabasu inajin tsoron halin da zata shiga,don ba zata iya jure abunda nake jurewa bah, yanzu kam zance Alhamdulillah duk wasu feelings da nakeji nashi narasa, saboda na farko bana ganinsa, ko waya ba muyi, don cikin shekarun nan da basu nan sau d'aya mukai waya Shima ina kwance kan cinyar Maah, naji suna Waya yake tambayata da yi mata k'orafin bana gaidashi,tunda nai waya shine ta bani Shima kuma bai wuce y'an seconds ba. "yah ina wuni." muryarsa ta sake zama ta y'an Gayu yace, "ai da fushi nake dake Khairat,amman dai na huce ya kike ya karatunku." Nace, "Alhamdulillah karatu ka gaida yah mujahid." Na mik'a mata wayar, ita kanta tayi mamakin yadda Nayi, bata ce komi ba, suka cigaba da wayarsu har nayi bacci. Nida salma kowa ji yake da kyansa,bawai batun son kai bah, zan iya cewa nata b'angare d'aya ne, ni kuwa duka b'angaren biyu na d'auko, don Maah fulanin yola ne na usil, Abbu kuma buzune Amman kuma k'ar yake kamar Jini zaifito jikinsa, yayinda Maah take ruwan tarwad'a amman hutu dajin dad'i yanzu yasaka takoma jawur, Na biyo Abbu ta wajen haske da manyan idanu wanda idan ina magana suke kunshewa,ga zara zaran eyelashes har wani kwanciya suke, sai tsawonsa don Maah bazadai Kace mata guntuwa ba, kuma ba gajeraba. Amman am sure ni doguwace kuma tsayina ma daidaici, komina mai tsarine,amman cikar fuskata da cikar halittar jikina duk na Maah ne,da kyawawan hakoranta,da wushirya,masha Allah dai kawai za,ace komi yaji. Sweetheart kuwa komi na Abbu ne har rashin kib'arta, Idan tayi dariya sak Abbu. sweetheart kamar kwalin omo take ba nauyi,ga kuma fara,a ko bacci take. Shiyasa tafini qawaye dayawa don ni k'awayena basu wuce biyar bah, itako lodi lodi haka zaka gansu,in fita mukai kan na had'u da Wanda na sani ta had'u da mutun goma........ Kai sweetheart akwai kwashe kwashe wallahi. yah meenah ma ba laifi don Itama tubarkallah, Allah yayi mata halitta maikyau, komi yaji kenan don tun yanzu har samari sun fara mata yawa,saida na bata shawarar korarsu don inhar tace yanzu zatai soyayya ba makawa Dady aure zai mata, duk ta firgice don tana son boko kamarni. An tambayeni me zan karanta nace I like medicine Shima kuma b'angaren hakori,da farko Abbu da maah sunce Ina karatun yayi tsawo,kuma zansha wuya, saida nayi masu kuka sannan suka barni, Shima saida sweetheart taga dagaske baza su barni ba,yasa ta kira Yah Areef tana kukan shagwaba take sanar mashi, dafari cewa yai tabani wayar ya lallasheni, Amman nace tace nafita. Shi yayi magana aka barmun cause d'ina, Yah meenah kuma, nursing. kuma nace bazan je wata k'asa ba anan gida Nigeria zanyi. Yanzu har mun cike komi an bamu admission anan Abuja zamuyi karatun, kuma day zamuyi, sweetheart kasancewar karatun bai wani d'a d'ata da k'asa ba bata wani d'auki cause mai wuya ba, don education ta d'auka fanin intergrated science. Yanzu registration za muyi mu fara zuwa,b'an gare guda kuma cikin satin nan su Yah mujahid zasu dawo,sweetheart kamar tayi hauka don dad'i nikuwa da naji Ana maganar ma gabana fad'uwa yake sosai. *wannan kenan.* Mu had'u next page. Mom muhsen ce Mrs bb. [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *NI AISHA ABUBAKAR (MRS BB) INAYIWA D'AUKACIN MASOYANA BARKA DA SALLAH FATAN MUNSHA RUWA LAFIYA UBANGIJI YASA MUNA DAGA CIKIN Y'AN TATTATUN BAYI, ALLAH YANUNA MANA WATA SHEKRAR LAFIYA.* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 10&11. Har na isa b'angaren Anni tunani ya cushe Mani k'walwa, ni banga abun fushi anan ba, to mema nayi masa har haka koko don na tafi wani waje bayan nasan zai dawo, to in nasan zai dawo goyashi zanyi, koko mezan masa. Tsaki naja sanda nake ajiye mayafi na, kallona yah meenah tayi tace. "Lafiya dai, ya kuka k'are dashi." Raina 6ace na wurgar da jikkata nace, "Wai yah meenah ni za,a dizga kiga fa yadda yake ta shan k'amshi, kodai ubana in yaje unguwa ya dawo iyakar abunda zan mar kenan, to d'aukarsa zanyi don murna shine zai banza dani, to gidan ya tarar bazan lamunci wulakanci ba, idan wancan karon anyi nashanye yarinta Ce yanzu kuwa da girmana bazan jura ba wallahi." Mai yah meenah take shafawa tace mun, "Ban son wanan zafin ran naki khairat, ki ringa bin komi ahankali." "Haba yah meenah kina ganin yadda yayi Mani halin ko in kula, ita kuma salma kowa yana magana Amman ita uffan ta kasa cewa." "Nadai ce maki kiyi hakuri ki sama kowa ido, karki nuna b'acin ranki afili, ki share inkikai hakan wallahi zakisha mamaki, oya shiga kiyi wanka kizo kiyi sallah ko mangaruba bakiyi ba ga isha,i anata kira." Haka na d'auki maganar yah meenah saboda koba komi ita kad'ai ke kulawa da lamarina. Yadda tace nayi haka nayi, sai gashi cikin ikon Allah nasamu yar natsuwa, wanka nayi nazo nashirya cikin kayan baccina masu shegen kyau, ummin Dubai ta aiko mana dasu kala uku uku mu uku, ba k'arya ummi naji damu, more exspicialy ni bama yini guda bata kirani bah, haka d'anta yah imran jininmu y had'u da juna, don sosai yake ji dani don duk dare idan bana komi, shima yagama duk abunda zai zaikirani video call, nan zamu d'au lokaci muna hira har wani zubin yah meenah ta zo ayi da ita, har sun saba dashi itama. Sallah nayi na gama na jawo system dina ina cireta daga caji, yah meenah tashigo. "Khairat kifito muci Abinci inji yah mujahid." "Wallahi da kwanciya zan, inyaso inci abincin anan d'aki, Amman tunda yah mujahid ne muje." Abaya doguwa har k'asa nasa mukafito, ina cigaba da danna system din, muna hira har cikin falon maah. Salma ta tusa shi gaba yana cin abinci, ga uban juice da ta had'a mashi, itace keta zuba mashi surutu kamar kanyar da babu dadi. Bama tasan mun shigo ba, mu kad'aine falon maah na wajen Abbu nasani, don baka ganinta irin wannan lokacin, idan ba tazo duba muba, don duk dare zata zo taduba idan munyi baci, in bamuyi ba tace komi muke a ajiye akwanta. Zama nayi kusada yah mujahid k'asa nida yah meenah. Murmushi yayi mana yace, "Kun zama y'anmata khairat, nan bada jima wa ba zamu badaku ko." Dariya nayi ina danna laptop dina nace, "Haba yah janmu kake kaima, duka nawa muke ai mun samu muma muyi yar bokon nan da ake mana yanga kanta. Har ga Allah ni ban fad'a da wata manufa ba Amman Ashe na jawo ma kaina fitina, jinai ya ajiye spoon dinsa yace mun, " ke!" Cikin wata tsawa da ta firgitani bama ni kadai ba, har yah meenah ta tsorata. Juyawa nayi ina kallonsa gabana kamar zai fito waje. Cikin kakkausar murya yace Mani, "Da ubanwa kike wannan maganar, watau kinga na kyaleki shiyasa zaki gaya mun magana ko." Yah mujahid yace, "Look Areef, ya daga dawowarka zaka fara halinka don Allah Ka daina, ba dakai take ba, karka tada mata hankali." " jahid kafita cikin maganarnan kana so kace man na kyaleta, bacin maganar da tafad'a d'azu bai isheta ba shine yanzu ma tasake yin wata, shin ni abokin kine khairat, koko kakanki ne ni to zangyara maki zama, ko inuwata kika hango zaki ruga." Idona ya cika da kwallah nace cikin karyewar murya, "Yah........wata tsawar ya dakan data saka na zabura zan ruga, saida yah meenah ta rik'eni........rawa jikina keyi hawaye nata zarya akan fuskata. " tashi bar nan falon, idan na sake ganinki inda nake sai na b'ab'b'alla k'afafunki stupid girl kawai, kenan don ubanki har kin girma ko, to daga yau karna sake ganinki inda kikasan ma zan zauna, aguje nafice ina jin wani irin kuka yana kuccemun, Wanda har numfashina jinake yamun kad'an...........kafin na idasa d'aki ban san sanda najini yashe k'asa ba, saboda wani kullutun bak'in ciki ne ya tokaremun mak'oshi, numfashin ya d'auke.................fitowar maah daga d'akin Abbu kenan saboda tsawar da takejin Areef na kwatsawa, taga fad'uwar khairat.........aguje ta rugo tana kwalaman kira da mugun k'arfi, Amman ina numfashin ya tafi, aguje ta koma suka taho da Abbu.....kankace me gidan kowa ya taru tuni Abbu ya ruga dani asibiti, donjin duk wasu hanyoyin sadarwa na sun daina aiki, kuka riris maah keyi Wanda ya ba kowa mamaki don Abu bai tab'a samun khairat tayi kuka ba, don wani lokacin ma tafi nuna damuwarta kan salma. Amman kuma abun mamakin salma ko gezau batayi ba, don kowa yashiga halin damuwa Amman danna wayarta kawai take, yah meenah kuka take. Tuni yah jahid da anty shidah sun tafi asibitin. Abbu da yah jahid gaban likitan da ya gama duba ni, fad'a yake yi kamar zai ari baki, hakuri suketa bashi daker ya yi masu bayani. "Kasan yarka na daf da kamuwa da ciwon zuciya kuwa, tun sadda na duba ta lokacin baya nasanar dakai,na kuma cema adaina fusata ta da yawa, to gashinan zuciyar ta na mataki na second to the last, muddin irin haka ta cigaba da faruwa, to bazan iya kareta daga abunda zai biyo baya ba. Don haka ruwanka ne kasama mata farinciki, ruwanka ne kabarta damuwa ta kasheta." Maguguna ya rubuta tare da sallama, idan tatashi baccin wuyar da tashiga. Suduka jikinsu yayi masifar yin sanyi,koda suka fito kowa da irin abunda yake sak'awa. Mutan gidan duk sunzo Anni kad'ai suka baro, meenah idonta yayi jawur, Areef kuwa karkaso hada ido dashi, don kamar jangauta haka yakoma, babu wanda yabi ta kanshi tsakanin Abbu da jahid. Ban farka ba sai wajen shabiyu na dare, dole saida nakai washe gari sannan muka koma gida. Kowa sai nan nan yake dani maah kuwa inakan cinyarta, abinci kanshi da kanta take bani, har yanzu Abbu baice komi ba, yah jahid baya yin cikakkar one hr baizo ya duba niba wata sa,in ina bacci wata sa,in ina danna waya komuna fira da maah. Gogan naku kuwa har yanzu banga keyarsa ba, haka zalika nima kuma ko inuwarsa bana kaunar gani, don yanzu wata irin tsanarsa nakeji har kasan zuciyata. Salma kuwa yanzu duk ta canza Mani, bama niba kowa na gidan ta canza mar fuska, maah kuwa ta yi iskar kare da ita, ban sa mekefaruwa ba abun yana cimun tuwo a kwarya, shiyasa nace zan mata magana yau. Yah meenah ta gama mana registration dinmu, tun kwana uku da suka wuce. Ranar Monday zamu fara zuwa makarantar, dadi ya kamani ko banza nashafe babin wanan gayen mai bakin hali. B'angaren Abbu na nufa don kiran maah tazo muci abinci, insamu damar tambayarta. Saidai ina shiga nafara jiyo sautin magana da d'an karfi yana tashi, saika kasa kunne sosai zakaji maganar kamar ana fad'a.........gabana ya yanke ya fad'i abunda ban tab'aji ba iyakar tsawon rayuwata. Ahakali da najuya zanfita, saidai ambaton sunana danaji anyi yasa dole matsawa jikin k'ofar bedroom dinsa na kanga kunnena. "Saudah baki tab'a neman wani Abu arayuwata nace bazan iya maki shiba, duk kanin abunda kike buk'ata ko ina dashi kobani dashi saina nemo na kawo maki don inga farinciki cikin akan fuskarki, ban tab'a zuwa maki da wata bukata ba tunda mukai aure, tsawon shekara talatin yanzu sai yau, Amman kirufe idonki ki watsa mani k'asa ga ido. Ban boye maki halin da y'arki keciki ba, na sanar maki don musamu mafita, mufitar da ita daga halin da take ciki shekara goma sha, Ashe ke kina can kin saka takunkumi mai tsananin girma tsakaninsu, kinjefa yarki cikin halin damuwa, kin jefata cikin masifar da zata iya rasa ranta abisa wannan dalilin, shin idan Areef ya Auri Khairat yana nufin ya tashi daga d'anki kenan, ko yana mufin kin rabu dashi kenan." Kuka take tana cewa Abbun khairat shin wai kamance alkawarin mu da anty hafsat, agabanka tayi magana aranar da ta bani Areef, cewa tabani halak malak, kuma bata yafe ba idan na banbantashi da yarana, sannan gudun son juna ya kama guda, yasa tace na haramta masu juna, idan ba haka ba babu ta yadda za,ai areef ya cigaba da zama matsayin d'an dana haifa, inhar yasan wannan babu makawa duk girman da yayi wajena zata anshi abunta, don tana son Areef ya d'auka nice uwarsa har iyakar karshen rayuwarmu nidashi, ina son Areef Abbun khairat, wallahi ko shahid da shahida, da ita khairat din banajin kaunarsu irin yadda nakejin sa, saboda shine mutumin daya samomin kima da mutunci waje mutanen da suka gasa mun aya ga hannu, akanshi suka fara yimun kallon rahama, taya kuma yanzu saboda yar cikina in fallasa wanan abun, yaka keson suringa kallona bazan iya barin wannan abun ya fito bah, khairat tayi hakuri Allah zai yaye mata, ko salma ba zata aurai ba ta gama haukan nata. " "Na gode maki saudah, akan wannan kikeson y'ata ta mutu ko, saboda kar Yayarki tace zata anshi yaronta ko, to shikenan ni zan Sanar da wanna sirrin ga kowa, zan kuma yiwa Areef tayin Auren khairat, saidai idan shine yace baya sonta bazai aureta ba, zan hakura kuma zan yiwa khairat Addua Allah ya bata Wanda yafishi Alkhairi, inhar khairat bata samai ba babu Wanda zai auresa daga salma har shahida da meenah, nagode." Jin alamun zai fito yasa nafice aguje, kewaye na shige nayi kuka kamar idona zaifita, nayi kukan da ban taba irin saba, Wanda har saida nayita amai akewayen....... Mom muhsen ce Mrs bb[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 12&13 Ganin halin dana shiga zai iya saka aganoni, shiyasa nayi iyakar kokarina wajen ganin na dawo cikin natsuwata, ina nan kwance salma tashigo tana wani taunar cingam cikin yatsina fusma, mamaki nake yadda salma ta canza sosai daga dawowar su yah Aree zuwa yanzu, kokadan yanzu salma bata damu da damuwata ba, sai gari ya waye har rana ta koma ga ubangiji, salma ko kallon banza ban isheta ba, idan ma ni nayi mata magana baza ta kallan ba zata ban ansa, tabbas ina hasashen wani Abu dangane da ita, salma ba haka take ba inson sanin dalilin canzawarta. Wayarta ta ajiye ta shiga wanka ta fito tahau shirin bacci, Amman sai ka d'auka miji gareta sai kwalliya take yi, tana ta feshe jikinta da turaruka, kallon ta nake ina mamakinta. Har ta gama bata cemun uffan ba, saida zata fita har takai kofa ta juyo cikin rainin hankali tace, "Oh na manta fah kifito can babban falon Abbu ana nemanki." Ta juya bin bayanta nayi da kallo kafin na yuk'ura na tashi, sake wanke fuskata nayi nafito, tabbas nasan wannan maganarce za,ai gaba na yana fad'uwa na isa kowa nanan har dadyn yah meenah, dasu Anni da yah jahid kowa dai yana nan banda yah shahid da sai karshen wata zaizo hutun karshen shekara. Zama nayi can gefe bakin kofa, saboda irin kallon k'ask'ancin da yayi min muna had'a ido, bacin tsoronsa da yacika zuciyata ai dana rama. Yah jahid ne ya bude mana taro da addua,kafin kowa ya shafa muka maida hankalinmu kan Abbu, gyaran murya yayi ya fara da cewa. "Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata,ala da yanuna mana wannan rana, ya kuma nuna mana girmanku, Wanda da ba haka kuke ba, an wayi gari kowa ya mallaki hankalin kanshi, zuwa wannan lokacin nasan wasu daga cikinku kanku yatoshe, abisa wasu al, amurrah watau abunda kefaruwa shine, azahirin gaskiya Yayanku areef ba mune muka haifeshi ba, bamune mukashayar dashiba, saidai kuma mune iyayen rikonsa, konace ahalin yanzu dai Areef namune, watau Abunda ya kawo wanan magana shine babu batun b'oye b'oye, Areef kanwarka khairat tataso tun bata san kanta ba, take kaunarka Wanda data kara girma ta fahimci cewar babu aure tsakaninku, tayi kuka tashiga damuwa Wanda wannan damuwar itace ta ja har aka mata ripeting makaranta, karshe ta kasa rikewa ta sanar da Annin Ku, ganin wannan ba abunda za, a kyale bane yasa ta sanar dani, bata gaya ma mahaifiyarku ba saboda taji irin furucin da tayi wa yarinya k'arama, cewar inhar ta sake jin wani yanayi na soyayyarka aranta bata yafe mata ba, alokacin ta nuna cewar akwai alakar aura tayya tsakaninku, Amman ta haramta mata kai, saboda wani dalili. Ban tab'a d'aukar hakan zai kawo ma khairat matsala ba, sai gashi lokacin da ta kwanta asibiti likita ya sanar dani tana da damuwa, idan da hali a San yadda akai akayi mata maganinta, saboda zuciyarta ba zata iya d'auka ba, ban d'auki wani mataki ba, saboda ina ganin abari zuwa sadda zaka kammala karatuka sannan itama tafara hada hadar shiga jamia,sai na sameka da maganar in ka amunce na aura maka ita." Shiru falon yayi sai shashshekar kukana dake tashi cikin falon, duk na jike hijabita da majina da hawaye. Cigaba yayi da cewa, "Sanda kuka dawo nayi farinciki saboda ganin kamar abunda nake tunani zai tabbata,saidai kuma naga kamar ba haka ba, saboda kulawarka kaf akan salma kake yinta, sai kwatsa da kyara da kakewa khairat, har dalilin haka yaja zuciyarta hau hauwa, Wanda likita ya tabbatar mun da cewar wanan matakin shine na karshe data sake ta wuce shi babu makawa zata kamu da ciwon zuciya, shiyasa hankalina ya tashi na kasa natsuwa, gani nake duk sakacina ne, Amman sai naga wannan damar ce kawai zata warware komi." "Na samu saudah da maganar hadaku aure Amman Kalmar farko data furta mun itace cewa ta haramta maku juna kaida ita,saboda alkawarin da tayiwa ummin Dubai cewa cikin yaranta babu mai auren wani, ma,ana khairat ko shahida bazasu aureka ba, kai matsayin wansu kake uwa daya uba daya, alakar aure bazata tab'a shiga tsakanin kuba, don haka khairat saidai tayi hakuri Allah ya bata wani Amman ba kaiba." "Nikuma nace muddin ka amunce da tayin da nayi maka akan khairat, to kuwa wanan auren babu fashi saidai idan mahaifiyarka ta Dubai ce tace aa ko mahaifinka, kokuma kai da bakinka kace bazaka aureta bah." Shiru ya k'ara yawaita cikin falon zuwa yanzu kukana ya karu, don sonjin ansar da zai bayar, har ga Allah duk irin abunda yah Areef yake mun banji zan iya hakura dashi ba ina jinsa shine ABIN CIKIN RUHINA Amman ya na iya da hukuncin ubangiji, muddin yace zai auran, inkuma har naji sab'anin haka nayi alkawarin yafeshi har iyakar karshen rayuwata, haka zalika bazan sake tada hankalina akanshi ba zan d'auke shi matsayin yayana uwa d'aya uba d'aya. Tsawon lokaci baice komi ba Wanda kowa sonjin ta bakinsa yake, har saida dady yace masa. "Areef dakai ake kayi shiru." Ajiyar xuciya yayi yace, "Abbu meye dalilin da yasa maah ta furta hakan." Baidamu da tambayar da yayi ba yashiga bashi ansa. "Watau Areef bari nayi maku dalla dallah." Shekarun baya tun da mukai aure da sauda saida muka shekara goma ko b'ari bayi ba, nan yashiga sanar dasu halin da suka shiga, da irin takurawar da dangin Abbun suka mata, har sadda suka bar kasar.......... "Ranar da muka sauka kasar gidan ummin Dubai muka sauka, Wanda aranar aka haifeka Areef, tun da aka sallamoku asibiti nida saudah muka nuna sha,awar abamu kai, to sanin cewar suma kaikad'ai garesu yasa bamu rok'aba, to Ashe da saudah suka kebe da hafsat, ta sanar da ita halin da take ciki na rashin haihuwa, har gashi ance na k'ara aure saboda bata haihuwa. Saboda son juna da tausayin halin da saudah keciki yasa umminku ta nemi iznin mahaifinka, akan zata barma saudah kai, koda yaji halin da muke ciki baiyyi jaa ba, yace har duniya tatashi Arref na mune halak makal, wannan yasa bamu dawo ba saida aka gama shayar dakai, ta dalilinka komi ya canza Duk da saida kaddarar haihuwar salma tasa na sake wani auren, da marigayiya lantana uwa gareki salma, ranar da aka haifeki ranar mahaifiyarki ta koma ga Allah, saudah ta had'aki da khairat ta shayar daku batare da banbanci ba, kaji tushe mafari komi yanzu INA son ji daga gareka, shin zaka auri kanwar ka khairat kokuwa." Idona akansa hawaye kawai kefita, yayinda kirjina yake wata irin duka, gyara zamanshi yayi yace. *"Abbu kamar yadda maah tace nima ina ganin hakan din ne, kayi hakuri ni nadauki khairat kanwata ta jini ban tab'a jin sonta ba, koda na minty gudane idan nace zan amunce da auren zan iya kwararta, saboda bana son ta, gaskiyar magana ma SALMA NAKE SO BA KHAIRAT BA."* INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU, UN HAZBUNALLAHU WANI IMAL WAKIL.............kala man da nake ta nanata wa kenan cikin zuciya da kan bakina, duk iyayen AC din dake cikin d'akin sunkai shidda Amman zuface nakeyi ta fitar sharia, jikina har karkarwa yake gaba d'ayan falon yayi tsit bakajin motsin komi. Abbu ne yayi karfin hali yace, "Salma kina son yayanku." Kallonta nayi naga ta sadda kai tana wasa da yatsun hannunta, kafin Anni tace, "Ansarta kenan Abbun khairat alamun ta amunce kenan." Jinjina kai yayi duk yana yinsa ya canza sosai, daka kalli fuskarshi zaka gane ranshi ab'ace yake. "Kowa na iya tashi zan nemeku idan bukatar hakan tatashi." Daya bayan daya haka kowa kefita jiki babu kwari, maah duk jikinta yayi mugun sanyi, ta kasa yiwa Abbun magana. Tashi nayi zan fita don har wata juwa ke kwasata, jinai Abbun yace, "Yaki nan ta alkairi, kisameni da safe kafin nafita aiki, kinjiko." Ban iya bashi ansa ba kawai jinjina kai nayi nafita................ Mom muhsen ce Mrs bb [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition isV to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 14&15 Basai na kwatan ta muku yadda daren ya kasancewa khairat ba,domin kuwa bacci duk yadda ya kware wajen sata to fah wannan ranar ya gagara satar khairat,yadda taga rana haka taga dare,don kasa kwana tayi dakin su itada salmar,kuka tun tanayi da hawaye har ya dawo idon ya bushe,wani irin zafi takejin kirjinta nayi kanta kamar zai rabe gida biyu,haka meenah tayi lallashin tagaji tayi bacci ta barta. Duk wani tashin hankali da na kejin zuciyata aciki, nayi iyakar yina nayi control din kaina kafin gari ya waye,don nayi wa kaina rantsuwa da alkawarin idaniyata ta gama kukan *SO* kuma insha Allah zanba marad'a kunya. Shirin bacci jahid keyi yana yi yana kallon Areef da ya kwanta kasa saman kafet din dake malale tsakiyar dakinsu,ko combus din dake kafarsa bai cireba balle ya samu damar fara canza kaya,girgiza kai kawai Jahid keyi don lamarin Areef abun yana kaishi Bango,tsaki yaja wanda Areef baisan ma yana yi bah.......... "Dallah malam tashi anan,kawani sheme kasa kamar Wanda aka aikowa sakon mutuwa." Kallon jahid din yayi yana sauke ajiyar zuciya,lumshe kyawawan idanunsa yayi yana sake yin filo da hannayenshi,baice ma jahid komi ba. Haushi ne ya sake turnik'e jahid,don ganin yaki kulashi wani tsakin ya sake ja yana hayewa gadonsu wayarsa yafiddo yana danne danne........tsayin mitina babu wanda ya sake kula kowa har jahid ya gama abunda yake yayi addua ya kwanta. Sai lokacin yyi magana. "Jahid baka ga kamar Abbu ransa ya baci sosai ba." Cikin kuluwa yajuyo yana cemashi, "Au sai yanzu kagane haka ashe,ai babu anfanin hakan wallahi kabani mamaki Areef,yadda ka bashi kunya ka nuna cewar kana bayan maah,kasan me hakan kenufi kuwa.?to bari ni na gaya maka,kanuna cewar bai isa dakai ba,kuma shi ba matsayin mahaifi yake wajenka ba." Sai lokacin yayi saurin tashi zaune idonsa ya canza kala saboda damuwa yace, "Karka fassarani haka jahid,taya zan dauki mutumen da ya haskaka rayuwata irin haka,kasan matsayin da naba Abbu ciki zuciyata kuwa." Wani tsakin yaja yace mashi, "Duk irin matsayin da kabashi baida wani anfani,tunda har ka wulakanta bukatarshi gaban kowa,kadaina cewa yana da babban matsayi wurinka." Rutse idonsa yayi da karfi yana jin kamar ya kama jahid da mugun bugu,don jin irin kalaman da yake anbata mashi. Cikin muryarsa data canza sauti saboda bacin rai yace, "Karka sake anbata mani irin haka,na fadi iyakar gaskiyata ne saboda banson ya dauki amanar ta yabani inakasa rikewa,because i don't love her salma nakeso itace wadda na zabarwa kaina matsayin abokiyar rayuwata,akanme zanyi karyar yin abunda nasan ba zan yiba,idan kadamu ne saboda nace bason pls and pls jahid marry her." Murmushin takaici yayi yana kallonsa kafin ya gyara jinginarsa jikin gadon yace, "Areef kenan wallahi tallahi kaji rantsuwar dan musulmi ko,da ace babu wata acikin raina ban riga na furta inasonta ba,jiya dana baka mamaki gabankowa zan ce ni yabani aurenta,saboda khairat matan dake ma maza wuyar suce,kuma kaima nan gaba am sorry 2 say wallahi u will regretting." Wani wawan tsaki yaja ya mike yashige toilet yana cewa, "U are not in ur sense wlh,nidin zanyi regretting akan wannan yarinyar marar hankali,mtsss amman babu wanda ya kasheni irinka Allah ya isana wallahi." .......yashige warshi. Jinjina kai kawai jahid yayi yana hango yada lamarin zaikaya. ************* Tun da na tashi da asuba nayi sallah nake karatun qur,ani saboda in kara samun kwarin guiwa,saida naji zuciyata tayi sanyi sannan na tashi yah meenah har ta koma bacci,fita nayi don har lokacin banajin bacci sosai saidai kaina da yayi nauyi saboda rashin baccin,kitchen nasamu anni tana had'a break dinsu Dady don dashi suke tafiya,itada maah idan yau wanan yyi gobe wannan yyi,tsarinsu gwanin burgewa. "Annie ina kwana,ai ina cewa sadaqallahul azim nayo nan,saboda k'amshin girkinki d a ya hana hancina sak'at." Murmushi a kan fuskarta tana motsa fruit salad da ta gama had'awa tace, "Lafiya lau yar gidan Annie,Amman dai kinsan ko lashe bazan y'an maki ba ko." Ansa nayi ina zubawa cikin mazubin da take niyar zubawa nace, "Ba komi k'amshin ma da naji is okay for me,zai cika mun cikina." Kallona tayi ina cigaba da idasa hada basket din break din nasu,cikin tausaya wa tace mun. "Y'ar gidan Annie kallanni." Banyi musuba na d'ago ina kallonta. Hannuna ta rik'o dana gama saka komi tace, "Bakiyi bacci ba khairat,karkice mani abunda yafaru jiya shine ya hana idonki runtsawa,idan kuwa haka ne to banji dadi ba,khairat shin ko kin manta da cewar yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau imani ne,ladace mai tarin yawa karki soma yin halin irin na marasa ilimi,ke yarinyace mai ilimin addini dana zamani,zanso aduk sanda kika tsinci kanki acikin wannan halin kiyi anfani da iliminki,don haka kiyi mani alkawarin wannan shine karon farko kuma na karshe." Kaina yana k'asa nace, "Annie nayi maki alkawarin haka insha Allah." "Yawwa diyar albarka naji dadin haka,nasan kuma tunda kikayi man alkawari bazaki karya ba,Allah yayi maki albarka ya kuma cigaba da karfafa maki akan komi,dauki break din kikai falon Abbunku shizai wuce dashi,dadynku sabko yayi don suna da bak'i." Dauka nayi na nufi cikin fat dinmu, Kowa bacci yake don lokacin karfe bakwai da rabi,falon na sameshi yana karanta jarida,maah na zaune gefenshi, yana yin dana gansu ya nuna akwai damuwa. Sallama nayi na ajiye ina gaida maah,ta ansa cikin kulawa shima na gaidashi. Nai zaune ina jiran ya fadan abunda yasa yace in sameshi da safe,jinai yace mum. "Ta alkairi kije zuwa dare mun hadu,amman ki tabbatar kiyi baci isashe don idonki ya nuna jiya bakiyi bacci ba." Ina wasa da hannuna nace, "Insha Allah Abbu,saika dawo Allah ya kiyaye." Cikin kulawa yace, "Amen Allah yayi maki albarka." Nace"ameen"na baro falon Mom muhseen ce. Mrs bb. [5/27, 8:12 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 16. Daki na koma nayi dakin yah meenah na sameta tashin ta kenan,tana mik'a da salati. Murmushi nayi mata ina hayewa gadon nace, "Morning my dear." Hararata tayi kafin ta sauka daga gadon tana cewa, "Mai kukan banza kawai,wallahi saboda kuka wataran sai kin makance rab'o kawai." Dariya nayi don yadda ta dage sai hararata take tana fad'a, "Kinyi dariya mana ni kinga shigata wanka,kinsandai yau muke fara attending lectures ko." Kwanciya nayi ina jan bargo tare da cewa, "Wallahi yah meenah ko bature bazai nuna maki biting time ba,kiga fa kwata 2 eight muda keda lectures ten thirty." Ta na daga cikin barth room din tagama wankeshi tana hada ruwan wanka tace, "Kanki akeji don wallahi bazan ringa let ba,dana gama inhar baki tashiba saidai kisaman can,don na lura nawarki is too much wlh." Dariya nayi nashige bargo don sanyi akeyi kwanan kamar kamarme. Dandanan bacci yayi gaba dani don dama idon sai lumshewa yake saboda tsabar baccin dake cina. ********** Areef ne da jahid suna wajen exercise dinsu,don wajene keb'entacce wanda aka k'awatashi da abubuwan more rayuwa,babuce babu awajen Abbune yafito zaiwuce ya hangi k'ofar wajen abude,yafasa shiga ya cewa driver yasaka mashi jikarshi baya yana dawowa. Shiga yayi ya samesu duk sunyi gumi,jahid na kan machine din gudu Areef na gefe yana kan na keke......hira suke jefi jefi saida yagama kallesu sannan yayi gyaran murya,duk juyowa sukai suka kallo wajen...........da sauri areef ya sauko daga inda yake ya iso inda Abbun yake,ya dan rugumeshi yana cewa. "Good morning Abbu." D'agoshi yayi yace, "Morning." Jahid ma yazo ya rungumeshi ya gaidashi,don wannan salon tun suna yara sukeyinshi kuma Abbun ne ya koyar dasu hakan,don yanajin dadin jin yaransa ga jiki,Allah kadai yasan irin son da yake masu. Duk suna zaune kasa shi yana tsaye, "Ya kamata dai kamar yanzu kunfara zuwa office,ai kun huta haka nan ko." Areef ya langab'ar dakai zaiyyi shagwabar da ya saba,Abbu yace. "Karkace komi,sarkin son jiki kaikuwa wata macen ma tafika jarumta,don haka banason korafi idan na dawo am talking about that issue OK." Duk suka ce yes Abbu tare suka fito suka rakoshi har mota,Areef ya bude mashi baya yashiga sannan yarufe,daga mashi hannu sukai har yafita........... Komawa sukai suka cigaba d aikinsu,Jahid yace. "Don Allah bakaji kunya ba." Kallon haushi yayi mashi yace, "Kunya! For what." Jinjina kai yayi yaci gaba da abunda yake,saida yadauki lokaci sannan yace, "Ka wulakanta bukatarsa jiya sannan yanxu ko kunyar had'a ido dashi bakayi,meyasa akullum baka damuwa da damuwar wani sai taka,wallahi Areef ur Always selfishness gay ka gyara wannan ba rayuwa bane." Ran Areef yayi masifar b'aci ko kallon da yake ma jahid kad'ai zai tabbatar maka da hakan,cikin muryarsa data zama so deef yace, "Duk Akan wannan yarinyar kake gaya mun magana yadda ranka yaso ko jahid,to bari kaji wani abu wallahi kalma guda da kake fadan marar dadi akan wannan vellege girl din karajin tsanarta nake cikin zuciyata,don haka ba zance ka daina ba plss continue." Shi ma cikin tsananin bacin ran yace, "Uhmmmmm Areef kenan i know u hate her very much,kawai don baka da rabone Allah yajuyar da lamarin,domin kuwa khairat ta fi karfinka don class dinta bana irinku bane,Amma kasani wallahi ba ayin shishshigi cikin lamarin ubangiji,ni bansan gaibuba shiyasa bazan yanke maka hukunciba,Amman insha Allah very soon sai khairat tazamema *dan hakin daka raina* sai khairat ta saka idaniyarka kuka,sai khairat ta saka ka jinyar da tunda kazo duniya baka tab'a yin ir......... *stop jahid.......* stop stop Areff ya fada cikin tsananin tsawa da b'acin rai.........takowa yyi har gabanshi ya daki kafad'arsa yace, "Stop said that,because har abadan hakan bazai faruba,khairat k'anwata ce kadauka ciki daya muka fito,aure ya haramta agaremu,plss don't said that again banson b'acin raina yasa nayi ma yarinyar abunda har ta mutu zata tsaneni akanshi,don haka daga yau karka sake mun maganar that girl." Janyewa jahid yayi yafice Areef ya silale kasa jikin bango dafe da zuciyarsa,ya lumshe idonsa shikad'ai yasan feeling din da yakeji ahalin yanzu,ya dauki almost thirty minutes awajen kafin yatashi ya fito. Meenah ce tafito sauri kawai take don ganin goma saura minty goma, kad'an ya hana basuyi karo da Areef din ba,tayi saurin jaa baya cikin tsoro tace, "Am sorry yah ban gankaba ne ina sauri,ina kwana." Saida ya gama kalleta duk da har lokacin fuskarnan turb'une,sannan yace. "Lafiya,Ina zaki kike sauri." Kallon agogon hannunta tayi tace, "Wlh yau muke fara attending lectures shine nake sauri." "OK u can go." Har ta juya tayi taku uku ya juyo cikin dakakkar voice nashi yace, "Meenah" Saurin dawowa tayi ta tsaya, "Ke kadai zaki school dinne ina sweetheart." Jin abunda yace ne yasa tasan bada khairat yake ba yasa tace, "Ita sai offer monday suke farawa nida khairat ne muke starting." Shiru yayi kafin yajuyo yace. "Ta na Ina." "Bata idasa shiryawa ba shine zanyi gaba,gudun yin let." Jinjina kai yyi ya shige gidan ciki tafiyarsa ta takama,tasan tasota gaba zai shiyasa ta d'an jira A little bit. Wanka na fito inata sauri tsane jikina nashiga yi kafin nafara mulke jikina da cream,idan kuka ganta sai ku rantse yanga take,Amman nan iyakar iyawarta take sauri,farar powder na saka da lipstick sai kwalli daya fito da ainahin kyawun idona,sunyi k'ar k'ar kamar farar takada kaya na fara kokowar cirowa,don aron kayan yah meenah zanyi,kasacewar size dinmu daya har shoes,kayan sunyi mun nisa yasa na jawo stool na taka,Ina cikin jawo kayan aka banko k'ofar dak'arfi wanda tsoro yasani fasa k'ara............stool din ta jurgud'e muka taho tare k'asa...............na sadak'ar karairayewa zanyi kawai.........amman sainajini nafado jikin mutun,jinai yace washhh..........wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke nafara bud'e idona surprise fuskarshi nayi tozali da ita..........idona cikin nashi ga towel dina ya gama tattarewa cinya waje,har d'an pant dina ana gani........babu alamun sakin fuska tare dashi,ganin kallon yaki karewa yasa ya sakeni k'asa timm.......wata kara na saki ta azaba,don k'uguna har saida ya ansa........kuka nafara ina murza bayana katseni yayi da tsawa....... "Tashi anan ko in makeki ubanwa kikeyi har yanzu baki fitaba,ok tun yanzu kin fara wasa da karatu ko,to wallahi kika sake naga spill over ga result dinki kinshiga uku gidan nan,zaki tashi ki shirya ko saina tattakaki." Kukana nake silently ina mik'ewa da k'er kayan nake kokarin komawa in dauko,don bankai ga jawosuba ya kallan yaja tsaki,hannu ya mik'a kurun ya fiddosu ya watso mani ga fuska.........ya fita yana cewa kisake na sake dawowa." Haka nasaka na dauko log hijab dina nasaka da takalmi,matching color nayi na pink anda red........babu wanda nayiwa bankwana nafita......amman kafin na isa compound din gida na gyare fuskata,kamar komi bai faruba. Koda muka shiga mota tace me yayi mani cewa kawai nayi fada yayi mun infito.........munje kan lokaci kowa ya nufi department dinsu,Alhamdulillah lectures din sunyi mani dadi nesa ba kusaba,don yawancin abubuwan duk i knowing them,Amman fa da alama zamusha lectures harsai munce masha Allah,ga azumi tafe kuma cikinshi zamu fara test,natsinci kaina cikin farincikin dana jima banjiba,nayi friend guda husna ladan........d'an zaman da mukai da ita na lura tanada natsuwa sosai,zanji dadin friending da ita,koda muka samu hutun thirty minutes mukaje capteria na nemi yah meenah ban ganta ba,na tambayi ko yan department dinsu sun fito akace sai four,wanda lokacin mu zamu koma sai six zamu tashi. Husna ta siya mana lemo nikuma na siya mana pizzer da shawarma.......sannan muka koma muka cigaba da attending,na lura itama hazik'ace wajen karatun,shiyasa zan zage bazan yarda tafiniba.don inda kishi kan hakan,bazan yarda kafiniba saidai muzo tangal.. Muna class naga miss call din yah meenah,alamun sun tashi,saidai namata text cewar mu sai six tatafi da motar zanhau taxi. Husna hostel take sai naji inama nima Abbu zai barni na zauna hostel din da nafi samun natsuwar karatun.......amman yau zan mashi magana Allah yasa ya yarda. Koda muka tashi nayi wata irin gajiya,har wata juwa nake gani yasa nazauna na fiddo phone dina nayi dialing number yah jahid...........muna zaune da husna ta rakoni bakin get. "Plsss yah don Allah kazo kad'aukeni wallahi bazan iya kawo kaina gidaba,wallahi nagaji." Dariya yakeyi yana daidai fitowa daga gida yayi wani matsiyacin wankan yamma,dama fita zaiyyi takira daidai lokacin. "OK my dear am coming now." Godiya nayi ina kallon husna tana murmushi, "Kincika rangwanta kinga mu mun d'an saba tunda tun satin akafara." "Uhm tunda nake wallahi ban tab'a shan irin wannan wuyarba,lectures fah akwai dadi amman akwai gajiya wallahi." Hira muke ahankali tana k'ara nuna man sauran abunda akai ban nan.....har sanda yah yashigo da motarshi da tasha wanki sabuwar prado dinsu shida yah Areef,don itace gift dinsu sanda suka dawo daga UK.......sun gaisa da husna tayi mun bankwana tatafi. Har mukaje gida ina bashi labarin karatun mu yana kara karfafamu guiwa,anata sallah muka iso gidan yah Areef yana Alwallah bakin get da gani unguwa yaje yau,kafin motar tayi parking yah jahid yake cemun. "Dear matsayin yayanki zan baki shawara kinjiko." Na maida duk hankalina kanshi, "Karki kullaci Areef akan abunda ya faru kinjiko,ki d'auka hakan damace Allah ya baki kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali,kicire shi daga cikin ranki kidaina kallonshi irin kallon dakike masa baya,ki kalleshi irin kallon da kikeman kikewa shahid,zaki samu kwanciyar hankali da natsuwar zuciya kin fahimceni." Ina wasa DA azurfar hannuna nace, "Nagode yah Kuma nayi maka alkawrin hakan,daman wallahi yah Jahid tun ajiyan banyi bacciba saida nayi ma kaina karatun ta natsu,nasan cewa samu da rashi duk na Allah ne,haka zalika wani baya auren matar wani,nasan cewa wata kila daman badanni akayishiba rabon yar uwatane,har abadan zancigaba da yi mashi kallon da yakeman matsayin k'anwarsa ciki guda,nima matsayin yaya shahid zan cigaba damai namaka alkawarin cire wannan feeling din." Murmushi yayi mani yace, "That my dear khairat" ya bani hannu muka tab'a sannan muka fito angama sallah lokacin,har yah Arref yafito daga masallacin cikin gidanmu....kallonmu yayi yana ma yah jahid alamar baiyyi sallaba,yace"sorry oga yanzu zanyi ai,dear jeki gida ayi sallah da wanka ahuta ko." Nace to tare da bin bayan yah Areef har na cinmmashi naji yace mun"ba gaisuwa ta Alkairi." Mamakinsa ya kasheni amman sai ban nuna bah nayi murmushi nace masa"sorry yah ina wuni." Gaba yayi yana cewa"lafiy ya school din". Answa nayi nima na shige d'akinmi don duk yau banga salma ba,da maah. Mrs bb ce 09034722970 [5/28, 2:22 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 17. Salma ce da k'awarta raihana suketa kwasar dariya cikin d'akin,har basujin sallamar da nake.......abayar na cire ina cewa, "Sai Ihu kuke har ba ma kujin sallama ko." Wani kallo naga raiha nayi mun kafin ta sake kwashewa da dariya,salma na taya ta binsu nayi da kallo tsayin lokaci kafin na shige toilet,don na lura wanan dariyar dani suke kuma babu tantama salma labarin abunda yake faruwa ta bata,nasan kuma wannan labarin kaf k'awayenta ta basu shi........wani takaici ya kamani har naji k'wallah ta taru idona........sharewa nayi nayi wanka na tare da alwallah nafito har lokacin hirar su suke ta samari,wani zubin sai su yab'oma gana wanda daji dani suke,ban sake kula suba na hau yin sallata nagama nafara shafa mai inaji raihana nacewa, "Saiki kula kinsan ana iyayin komi don aga anrabaki dashi,don kinsan y'anmatan yanzu sun b'aci da bin maza kina zaune da saurayinki lafiya saidai kiji wuf anfige,kinsan ma wani abun haushin wallahi nakusa dakai shine zaki samai da wannan hali,kidai kula wallahi." Kad'an ya hana ban tankaba,saboda maganar takai mani mak'ura don har zuciyata wani irin ciwo take,haka suka cigaba da hirarsu turarena nashafa duk jikina,sanan na saka kayan doguwar rigace marar nauyi ina gama wa ana kiran isha,i sai kawai na tada sallah sai lokacin tayi niyyar tafiya.......fita sukai naci gaba da salla ta ban fito ba sai wajen takwas,d'akin maah na shiga na sameta suna waya da ummin Dubai........zama nayi gefe injiran su gama har nafara bacci sannan naji tana gyaraman kwanciya,tashi nayi ina mik'a tare da hamma,hannu tasa tarufe mani baki"akwai gajiya ko,gashi da ganin wannan cikin baici abinci ba" "Nayi missing d'inki duk yau maah,wlh school akwai wuya amman fa lectures akwai dad'i maah." Murmushi tayi tana shafa kaina tace"oh my angel kibar dai cika baki kwanan nan za kifara mana kukan kingaji." Shagwab'e fuska nayi ina sake narke mata nace"maah kinga dai salma ko." Maido hankalinta tayi kaina tana sha fa kaina tace"mekuma tayi maki dear." Na gaya Mata abun da ya faru d'azu..........shiru tayi na d'an lokaci kafin tace"my angel karki biyeta,bake ba harni nan salma ta canza mani daga halin dana d'orata akai,tabbas akwai abunda yake faruwa,fatana kici gaba dayin hakurin dana sanki dashi,karki ga don na hana Aurenki da yayanku kiga kamar ban sonki,aa my angel ilove u more than expected,haka kuma ina duba abunda yadace daku ne,inason har bayan raina Areef ya kasance yayanku mai share maku kukan ku,koda aure kukai kunada babban yaya da zai kula da lamarinku.........kid'auka dama babu aure tsakaninku kinji ko angel d'ina.......karki saka damuwar komi cikin ranki Allah zai kawo maki miji nagari na nuna ma sa,a sannan kiyi kokari ki nuna ma Abbunku cewar komi ya wuce wajenki hakan zai saka ya daina fushi dani,ko kinason yayita fushi dani." "Bana so maah insha Allah zan bashi hkr yadaina fushi dake,aman maah kija ma salma kunne wallahi kar wataran takaini k'arshe,ni wallahi maah tun daga randa akai abun nan nituni na yafe shi cikin zuciyata,to akan me zata ringa yayatani cikin friends d'inta.........wannan cin mutuncine.......sallamarsa tasaka nayi shiru ina kwance har lokacin kan cinyar maah tana shafa kaina...........idasa shigowa yayi yazauna gefen da nake........yadda ya canza fuskarshi daga shigowar sa yasa ni tashi daga kan cinyar maah,kallon k'asan ido yake mun bansan fassarar da zanba kallonba.........gyara kallabina nayi har lokacin idonsa na kaina nace batare dana sake kallon inda yake ba. "Maah bari naje Wajen abbu inci abinci dama wajenshi zanje na biyo in gaidaki." Kallon Areef tayi ta b'allamai harara tace"haba my angel daga shigowar yayanki zaki ruga." Ina nu far k'ofa nace"Aa maah dama yanzu zan tashi idan ya tafi anjima mun ida maganar,saida safe." Nafice inajin dukan da gabana keyi yana sassauta,don yanzu wani irin tsoransa nakeji har cikin k'ok'on raina.....wajen Abbu naje nayi sa,ar kuwa lokacin yake cin Abinci.......zama nayi nasaka hannuna kamar yadda yasa nashi,kasancewar Abbu baya cin tuwo da spoon muna hira muna ci har muka gama,nan yake gaya man yah shahid ranar monday zaidawo Anty shida kuma sai Tuesday zata zo weekend........naji dad'i sosai don nayi kewarsu sosai.....nasiha yashiga yimun cikin hikima da jan hankali har yazo kan batun shekaranjiya......cikin tattausan lafazi yace"ta alkairi kinsan cewar duk abuna kaga baka samu ba da hakan ba alkairi bane,don haka kid'auka cewa yayanku dama ba mijinki bane,kiyi hkr insha Allah mijinki zaizo nagari mai nagarta,fatana kisaka tawakkali da hakuri kinjiko inhar kinada damuwa kisanar dani karkice kibar abun ga zuciyarki,don zai illataki karkiji komi ta alkairi na komi kikeso sanar da Abbunki inhar ina dashi zan maki." Godiya nayi mashi tare da yi mashi alkawarin cire damuwar,sannan nace yajawa salma kunne akan abunda takeyi,na gaya mashi abunda ya faru don gudun abunda zaije yadawo.......shima ransa ya b'aci yace inbarshi da ita,har zan mashi maganar zaman hostel su yah jahid suka shigo shida dodona don yanzu sunan dana rad'a mashi kenan cikin zuciyata......tashi nayi nayiwa Abbu saida safe,don banson abunda zai ringa had'amu waje guda. Mrs bb ce👌🏻[6/1, 10:22 AM] Anty Ushe: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 18. Har nakai k'ofa Abba yace"ta Alkairi zonan." Kamar in zura aguje haka naji.......Amman babu damar hakan,kamar wadda kwai ya fashewa aciki haka nake tafiyar,inda na tashi na koma ina jin bugun kirjina yana sake yawa,don har ga Allah atsorace nake gani nake kamar zai kawo man duka......... "Kamar kina son fad'an wani abu ko." Yak'e nayi nace"aa Abbu babu komi." "Banson gardama kinsani don haka menene." Lagab'ar dakai nai kamar zanyi kuka nace"Abbu sonake na koma hostel da zama,idan ina can sai nafiyin karatun sosai,nan gida wani zubin inason yi wani abun zai d'auke man hankali." Kafinma Abbun yabani ansa yayi zak'al yace"Abbu babu wani hostel da zata zauna,duk salon ta biyewa abokan banza aringa yawo ga gari,idan ma na sake jin kin anbaci zaman hostel saina tattakaki,tashi kibamu waje." Kuka nafita inayi saboda haushin abunda yace.........yauma wajen yah meenah nakwana,mun raba dare kowa na bin abunda akamana jiya,nice searching ga computer banyi baci ba sai daya da rabi nayi bacci..yah meenah ta rigank kwanciya............ ******** Rayuwar ta mik'a taci gaba da kasancewa yayinda karatunmu yake tafiya successfully,duk da irin yadda lectures suke zafi hakan bai hana ni jin dadin suba,agajiye lik'is muke dawowa don yah meenah tana rigana,su sunyi gudun duniya sukai 4:35 pm mukau 6:oo pm wani zubinma idan abunyayi zafi har lectures din 8:oo to 9:30 muke........kuma haka zan dawo gida sex in yi wanka da sallar magaruba inci abinci sannan in koma,duk wannan wuyar yah baijin tausayina na zaun hostel,shiyasa gashinan duk na rame cikin abunda bai gaza 2 to 3 weeks ba.......suma yanzu ba zaune suke ba kasancewar sun samu aiki yah jahid dama engineering yayi to yanzu b'angaren yake aiki,cikin wata guda sun sake komawa wasu handsome gays......duk wanda ya gansu yasan suna kwanta kudi Yah Aareef kuma Act ya yi zane zanen gidaje da sauransu..........tsakanin sa da salma kuwa bazance komi ba,don wata irin kulawa sukewa juna,itace abincin safenshi idan zaitai ofis itace lunch nashi itace dinner,gyaran b'angarensu ko karatunta bata bawa muhimmanci ba kamar yadda take kaffa kaffa da duk abunda ya shafeshi,zuwa yanzu babu laifi ni da ita muna magana tunda Abbu ya kirata gani gata yayi mana nasiha da fad'a,har hira munayi babu laifi Amman ba kamar da ba,sosai suke buga soyayyarsu yah shahid yazo hutu satinsi biyu yakoma don sun kusa kammalawa.......Anty shida ma tazo kwananta biyar ta koma zuwanta na fahimci wani abu,akwai boyayyar alka itada yah jahid....nadai yi shiru don nasan basu son asani sai nan gaba,bai wuce kuma kammala karatunta. Don inna mahaifiyar Abbu tafara maganar ya kamata a aurar da su yah Areef hakanan,karsu tsohe agida..........nasan har yanzu ba agaya mata zancen shi da salma ba,sai nan gaba. Nida yah Areef kamar mage da b'era dana hangoshi zan kama gudu,ko muryarsa najiyo zanfece wanan abun yana konama shi rai,haka Anni abun yana bata haushi...tayi man fad'an har ta gaji ta rabu dani,haka maah tayita lallashina tana cewa"haba my angel dina kidaina gudunshi yayankine badodo bane,kinsan hakan haushi yake bashi,idan ya waiwayoki tau babu ruwana,kisaki jiki dashi babu abunda zai maki." Wani zubin ina kuka zance"wallahi maah ko had'a ido mukai hararata yake,tsoran kallonsa nake bazan iya zama inda yake ba,kiyi hkr maah." Hardai Abbu Da da dady maah ta gaya mawa aman babu abunda ya canza. Yau ban samu halin dawowa sex ba,kawai nayi zama na wajen husna har mukai lectures na 8 muka gama lokacin goma saura minty ashirin......duk tsoro ya kamani Abbu nakira nace ya turo driver ya d'aukeni........"ta Alkairi ai hamza yatafi gida tun d'azu bari naturo maki yayanku." Ya kashe tunani nafara to wane yayan kenan,Allah yasa yah jahid ne, don nasan shikad yake zuwa d'aukana. Hira muke da husna tana cewa ingaida mata yah shashid. Dariya nayi nace"yarinya takamu da son the handsome din gidanmu,nama manta ai ingaya maki tun last week yakoma,saidai inbaki no dinsa." Murmushi tayi tace"uhm kawai dai tun randa naje maki yawo naji ya burgeni,jinina ya had'u danashi." "Don't mind friend Zan had'a wannan kaunar insha Alah." Dariya sukai suna cigaba da hirar. Abbu suna hira da Dady kairat ta kira yace, "Bari naje na d'auko khairat,yaran nan nasan basu shigo gida ba.." Dady yace"inhar kana son daidaita tsakanin yaran nan biyu Areef da khairat dole sai kana had'asu wuri guda,ma,ana kana kusanta su da juna misali kaga yanzu babu mai daukota to katura areef yaje ya taho da ita,kirashi awaya nasan zuwa yanzu yana kan hanyar isowa gida." Jinina kai Abbu yayi yace"shawara mai kyau." Wayarsa yaciro yafara kiranshi, "Abbu gashinan na kusa isowa wallahi yau bak'i nayi daga canada." "OK ba damuwa Amman kabiya school dinsu khairat ka d'aukota babu driver yatafi gida." Jiyai jijiyoyin jikinsa sun tsinke,bazai iya musuba dole yace"to kawai." Mrs bb ce👌🏻 [6/1, 10:22 AM] Anty Ushe: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 19&20. Kwana yayi yanajin gabansa yana fad'uwa,lumshe ido yayi ya bud'e ya najin gajiya na bin duk kanin gab'anshi,shiyasa yake tafiyar a slow kamar maijin bacci,garin akwai duhun dare ga iska mai dadin shak'a da ratsa jiki,ga dukkan alamu ma hadarine don su weather su haka take,ayi sanyi ayi zafi wataran ma ruwa zakaga anwuni anayi.......get din makarantar yashiga duk sai y'an tsiraru ke yawo......muna bakin wani department na hango motar yah jahid,don duk tunanina shine saboda motar irid'a yace. "Kinga husna labarin gay din nan bazai k'areba bari kiga ni ga yah jahid can yashigo." "Aikuwa sweetie daga nan zanjuya don idan nace rakaki zanyi toni babu mai rakoni,don wallahi tsoro ake badawa irin wannan time d'in." Sara mata nayi nace"bakida case sweetie,good night ayi mafarkin yah shahid." Dariya tayi tace"ok kekuma kiyi na Dr MK." Murmushi nayi najuya ina tafiya sauri sauri,don daga inda yake hangena nima nake hangenshi akwai d'an nisa babu laifi,hakanan naji kafafuna suna hard'ewa,jikina yacanza gab'a daya gabana yaringa fad'uwa.........innalillahi wa inna ilaihir raju,un na anbata,saboda aduk sanda najini cikin wannan condition din to tabbas dodona nawajen,saboda tsabar tsoransa dana sawa raina jikina har ya saba muddin yana kusa da inda nake tunkan idanuwata suyi tozali dashi jikina zaifara rawa gabana yana faduwa.......jikina amace na isa bakin motar hannuna karkarwa yake,Allah yasani inajin tsoronsa fiye da kima,more excspcialy tsawarsa idan ya kwatsa man ita. Murda kofar nake tak'i bud'uwa.......shikuwa kallonta kurun yake,kafin yaja k'aramin tsaki yabude mata da kanshi.....ina kerma nazura k'afata na dosana duwawuna na zauna dandanan naji idona yacika da ruwa,kuka keson kucceman bansan daliliba,kodan banson abunda zai kusantani dashi daidai da second banson mu had'u.....tada motar yayi yafice cikin sanyinsa kamar baison tukin,tafiya suke iska na kad'asu don glass d'in tagar wjena sauke yake k'asa,dama kuma sauken na ganshi. yayyafi akafara iska yafara man yawa,amman banda halin cewa zan kulle rawar sanyi nake tunda amotar ma AC ya kunna kuma k'arshe take.......jinai yadakan tsawar danake tsoron karyamun har muje gida.........."ubanwa yace kisauke man glass,zaki maidashi kosai naci ubanki,stupid girl." Hannu na yana karma nasaka namaida hawaye suka wankemun fuska,inasharewa karyaga ina kuka nan ma wata masifarce......ina gogewa wasuna zubowa."zanci ubaki wallahi kukan ubanme kikeman dukanki nayi,ko yankar naman jikinki nake,ohhh ga mala,ika aza,ilunki ko dake nake kinaman banza." Yafad'a cikin tsawa.....daidai sanda aka shek'e da ruwa dama kuma muna gaf da gida. Bansan sanda wani kukan ya kucceman ba,dukewa nai nasa kaina cikin cinya naita rera abuna.......kuka nake sosai mai cin zuciya......banza yayi mun har muka iso gidan,nibanma saniba najidai ya tsaya ban d'agoba kukan kirun nakeyi.........fita yayi ruwan yafara dukanshi ya lumshe idonshi,yanajin dadinshi kamar yaita tsayuwa cikinshi har ya kare......zagayowa yayi ina nake zaune yabude k'ofar jinai kurun ya kamo hannuna nafito,rufe motar yayi yajani muna nufar cikin gida.......hannunsa cikin nawa ga ruwa yana sauka kanmu har lokacin kuka nake amman can k'asan makoshi,saboda muryar kanta ta dishe.......idona rufe yake nasa hannuna da abayata na rufe fuskata,shike yiman jagora wannan halin damuke naji tsikar jikina tayashi yarrrrr....... Sanda mukaje wajen hawan step din shiga main falon......jinai kirun an sab'eni baidirnine ko inaba sai d'akin yah meenah......idonta biyu lokacin kallonmu tayi tace"yah me yasameta" Direni yayi kan gado yace"gatanan ki tambayeta" yafice tashi nayi nai jifa da abayata dake k'amshin turarenshi,har lokacin kuka nake sosai jin har lokacin mayataccen k'amshin baibair jikina ba yasa nahau cire doguwar rigar jiina ina cewa, "Tsinanne wallahi sai kabar jikina,tunda banan aka haliccekaba.......ga hawaye share share.....yah meenah kallona kurun take,ganin nacire kayan ma bandaina jinshiba yasa nashiga wanka.....naita dirjar jikina saida nagaj nafito.......dariya kurun yaya meenah kemun babu sassautawa,haushinta ya kamani shiysa har nayi bacci ban tanka mata ba. ************ Koda yaje d'aki takalmanshi kurun yacire ya zube ga kujerar falon su,kanshi sama idonshi kulle,iskar bakinshi kurun yake fesarwa,kasancewar wannan dabi,arshi ce idan yana cikin halin damuwa. Jahid daya fito wanka ya samai awannan hali,sai bai kulashi ba,don yasan halin kayanshi har yagama shirinsa Areef nanan inda yake,karshe sallah kurun yayai yazo ya kwanta kan kujearat,daya tashi.......jahid kallonsa kurun yake don wannan ba sabon abubane wakenshi,saidai nayau yasha banban dana sauran lokutan,don Areef baya kwanciya da kayan jikinshi,duk runtsi zai canza kaya amman yau gashi ya kwanta dasu,bama manya bane masu sauk'in bacci jeans ne da t shet jikinsa,da wannan mamakin yayi bacci. 💕💕💕💕💕💕💕 Washe gari bantashi ba sai twelve,kasancewar banda lectures sai 2:00 pm Abbu nanan tunda nai wanka n shirya najena gaido Annie har take tambayata meya saman jiya taga Areef yashigo dani. "Annie turgud'ewa nayi nazo shigowa k'ofar falo,kinsan daman wannan wajen ba,a wuceshi da sauri,sai kurun na fad'i shine ya taimakeni." Nasan idan ba haka nace bah banda wata karyar data wuce wannan. "Aikuwa nasani tunda nima yasha kadani,kiringa bi sannu da yarintarki karya gurguntaki,dasauki k'afarko." "Eh naji sauk'i sosai nashafa man zafi awajen ." Daga wajen annie wurin maah na wuce, bata falonta na wuce uwar dakarta.......maah ce zaune kan dardumar tsakar dakinta kafafunta mik'e yah Areef ne kwance kan k'afafunta, salma na gefe tana dama mashi fura,gallala nayi ina kallon ikon Allah,dukda bawani abubane da bantab'a ganiba,amman nai zaton zuwa yanzu yah yagirma da wannan alon na yara,ai sai yabarmamu.....kamar injuya naji amman ganin duk sun ganni yasa na idasa,gefen maah na zauna ina gaidata,nacewa salma"yau bakije makaranta bane." "Fuskar ta duk ta yamutse kamar tayi kuka,tave"wallahi banjeba yah nebaida lafiya,bazan iya zuwaba." Kallonshi nayi idonsa rufe ruf,eyelish dinsa sun kwanta kamar na mace, Can k'asan muryata nace"sannu yah Allah yasa Wake." KO ma ah dake musadani banyi tunanin zatajiba balle salma dake d'an nesa damu,amman shi dake kwamce kan cinyarta rasss cikin kunnensa,yace"Ameen." Lab'b'ansa kurun zaka gane kasan yayi magana,duk da haka ni naji jinai maah tace"baki gaidashi da jiki." Mik'ewa nayi nace"ai nayi mashi bari nake waken Abbu kafin time yayi." Banjira cewarta ba nafice,ina mamakin salma saboda wani ta kizuwa makaranta,nalura yanzu saboda shi kokadan bata son karatun.....wata zuciyat tace ita tasani. Waken Abbu mu kayi lunch dina,ganin yana cikin yanayin jin dadi yasa nace"Abbu dongirman Allah kayiwa yah Arref magana yabarni nakoma hostel,wallahi sainafi jin dadin karatun kagafa wataranar har ten nake kaiwa ban iso gidaba,plsss Abbu don Allah kayi amshi magana." Murmushi yakeyi yace"ta Alkairina kean,kindai aida yayanki kamar wani dodonki ko." Kaina na k'asa ina wasa da yatsuna nace"Aa Abbu ba haka bane wallahi shine yake mun tsawa,Kuma ni banaso ko had'a ido mukai sai ya hararenifa,wallahi Abbu yah Areef ya tsaneni yanzu." Girgiza kai yayi yace"Aa ta alkairi karna sake jin haka daga bakinki yayanku bazai tab'a tsanarkiba,kin kasa fahintarsa ne kisaki jikinki dashi kudawo kamar da keda shi." Icon dandanan ya kawo ruwa,don basusan irin tsanar dayake mun ba,cikin karyewar murya nace"Abbu pls" Yah jahid ne yashigo yace"ta alkairi ta shirya in sauketa makaranta." Goge kwallata nayi ina gaidashi, Abbu yake gaya mashi abunda nakeso. Murmushi yayi yace"karki damu inhar hakan shine mafita tokiyi don koni ina baki goyo baya zaman hostel din fiye da kima,don inason ganin ta Alkairin Abbu tayi karatu sosai dazai saka tayi passing." Murushi nayi mai kyau naji dadin kalamanshi nace shikenan zan mashi maganar inkuma baiyarda bafah. "Abbu yace zaima yarda ai Areef nakine babu mai shiga tsakaninku ko ko jahid." Dariya yayi yace"sosai kuwa Abbu." Ahaka nabaro wajen natai nashirya yah jahid ya wuce dani makaranta. Mrs bb ce👌🏻 Mom muhseen [6/2, 8:21 PM] Anty Ushe: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by [Mrs bb] Mom muhsen ce *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 21. Yau lecture biyu garemu sai pratical d'aya,shiyasa muka tashi da wuri.......husna da wata qawarta rahma suka rakoni bakin get muna tafe muna fira,rahma tace"kin san khairat DR MK fa yana ciki,don wallahi ydda nakejin labarinsa wajen wad'anda suka fita abu babu sauk'i,baida kirki ko kad'an kuma ga tsanani wajen test ko exam,amman abun mamakin shine yau da ya kama mu muna noise nai zaton walh korar mu zai sai naga baice mana komiba." Jaki naja nace"shine kuma yace maki rahma inason khairat." Husna dai dariya take ba tace komi ba, "Ni bance yace haka ba,Amman kina dai gani yadda muke addabarsa da surutu class bacin ko ranar da yafara zuwa yayi mana kashedin cewar babu abunda yatsana sama da makara da noise,kuma duk wnda yshiga cse dashi yabani." Girgiza kai nayi nacewa husna"wannan qawartaki bata da kan gado pls kina ringa kwatanta mata pls." Me husna zatai ba dariya ba,rahma ranta ya b'aci rakiyar da batai ma kairat kenan ba.......munata dariyar tare nace"haba wlh kina fama da kwashe kwashen abokai marasa kan gado,shiyasa fa ni kinganni nan ban wata qawa data wuce ke,kema don naga kin zo daidai dani ne,inbacin iskanci ko ya akai tasan haka." Husna na dariya tace"kika sani tashiga zuciyarsa ta gano." Tsaki naja daidai munzo bakin get nace''ki koma yamma tayi sosai.......motar dake shigowace ta katseni. Duk makarantar babu mai irin motar in bashi ba,motace ta gani ta fad'a kowa santinta yake school din. D'auke kaina nayi nayiwa husna sallama na nufi fita,driver baizo ba kuma banzo da mota ba,daman yah jahid ne ya kawoni.......tracking nakeyi ina dub hanya kozan samu taxi,don hanyar ana wuyar abun hawa,duk yadda naso inje gida kan mangruba da alama hakan zai wuya........ban gama tunani naba motar nan tayi parking gabana. Tsoro naji ni dafarko kafin ya sauke glass din tagar gefen shi..... "Shigo mine in kika tsaya jiran taxi zakiyi dare." Fuskarshi bbu alamun wasa ban iya musu da malamina ba shiyasa kurun nashiga,shima kuma don nasan yasan gidanmu nasan bazai cutar dani ba,don Abokin yah Areef ne sosai. Shiga nai kurun ya cigaba da tafiya saida muka hau titi sosai yace"ina motar ne yau" Ina danna wayata nace"banzo da itaba daman Yah jahid ne ya kawoni." "Oky,Amman ya kamata abaki mota saboda irin haka,idan kuma Abbu yana ganin kinyi k'aranta yabarki ki dawo hostel inaga hakan zaifi,don irin haka akwai risk gaki mace." Shiru nayi ina sauraren sa,hakika yana da zak'in murya sosai ga natsuwa komi cikin natsuwa yake har maganarsa. "Nace insha Allah zan masa magana." Daga haka bamu sake cewa komi ba har mukaje gida........ban yarda yashiga ciki ba nace yasaukeni nan ma bakin get is oky. Fitowa nayi nace" thank u sir." Gajeran smile yayi yace"ur welcome, kigaida Maah." Nada"zataji." Sauri sauri nake don kar wanda ya ganni nashige ina ajiyar zuciya,don bansan yazance ba idan aka ganni ya saukeni,duk da ansashi cikin gida hakan bazai hana su tabayeniba. B'angaren Annie na wuce in tajin dadin babu wanda na gamu dashi,yah meenah na ta gyara kayanta na wadrop tayi guga nashiga dakin, " sannu dr kairat." Murmushi nayi nace"me akayi da maza yah meenah kofa first semister bamu gama bah." Kaya nahau cirewa tace"kamar gobene insha Allah." "To Allah ya Nuna mana lokacin lafiya,bari nayi wanka inyi sallah zaki rakani wajen boss." Dariya tayi tana tambayata waye boss, Inacewa idan nafito zakiji. Ban wani d'auki lokaci ba nafito shaf shaf nayi shafa nazura kaya,Allah yayini ba gwanar kwalliya bace,don ni sometimes ko powder bana sawa in zan fita school,amman i wonder nake ganin yadda wasu ke daukar heavy make up suna shiga school....... Saida na gaido Annie sannan nafita cikin gida wajen maah,Falo na sameta itada mai aiki suna hira,na zauna ina gaidata. "Ashe kin dawo,ya test d'in." Na yamutsa fuska"to da sauk'i dai kiyitayi man Addua kar nasamu fail,saboda wlh yau nayi ma lecturan laifi." Fada tayi man kamar zata dakeni,har nai nadamar sanar da ita. Hakuri nabata take cewa idan nayi wasa wallahi karatun zan aje ayiman aure. Wata irin zabura nayi ina kallonta,nace"maah aure fa kikace me yakawo wannan maganar." Sallamar mai aikin tayi tace idan zan kwanta in sameta d'akinta,nace to kurun tatashi tabar falon. Abbu bainan shiyasa banma je inda yake ba,maganarta tayi man tsaye ga makoshi "Aure,ni za,awa auren,tabdijam." Tashi nayi nawuce d'akinmu salma bata nan nasan tanacan ta kasa ta tsare. Tsaki naja nace"Allah yarabani da wanan wahalallar soyayyar." Kaya na fara had'awa cikin trolley,tun kan in tabbatar da anyarje man ko akasin haka harna hada kayana,inaba zuciyata tabbacin ai yama yarda yagama,saida na had'a akwati uku harda jakunkuna takalma dadai sauran abunda zan buk'ata. Nafito na wuce wajen yah meenah nace tataso muje,tayi dani inzo muci abinci nace sai mundawo banda natsuwa harsai na samu abunda nakeso. Fita mukai Annie nacewa Allah yabada sa,a muna dariya mukace ameen. Tunda muka doshi b'angaren nasu zuciyata take bugawa kamar zata fito waje,na rik'e hannun yah meenah gagam har tana cewa"zaki karyani fah." Banmasan nayi ba bansan dalilin dayasa nake masifar tsoran saba,nidai banson had'uwa dashi harcikin zuciyata kuma haka yake,nidai yanzu ko kad'an banajin wani sonsa saboda yariga ya koya man tsoransa ya cireman duk wani feelings akanshi,amman ina mamakin abunda naji shekaranjiya........wanda har yau inajin abun idan natuna da ranar......tura k'ofar falon yah meenah tayi nayi saurin b'oyewa natoge nakasa shiga,da alamun suduka suna nan,inajinma harda salma jinai yah jahid yace"waye nan." Yah meenah tace"yah mune." "To kushigo mana kuke lab'ewa." Jana take ina togewa don har jikina ya fara rawa,saboda tsananin tsoro........dole tashige tabarni ina rawar sanyi. "Ina kairat d'in." Cewar yah jahid "Gata can bakin k'ofa ta k'i shigowa." Murmushi yayi ya kalli Areef dake kwance kan three seater yalumshe idonshi,ga salma zaune gabanshi da alama fad'a sukai. Muryarsa yadaga yace"kishigo my dear bacci ma dodon naki yake." Aikuwa nai zuf nashiga na rakub'e bakin kujerar farko ta wajen k'ofa. Duk nai tsuru tsuru me zasuyi ba dariya ba,har salma dariya take can kasa kasa.......hawaye suka silaloman natashi nayi hanyar fita naji muryarsa irin ta marasa lafiya yace"zo nan." Kasa fitar nayi najuyo ya kalli yah meenah yace"kubarnan." Kankace me taruga salma tatsaya nuk'u nuk'u yadallah mata harara sannan tatashi tafita,yah jahid yaketa jana nakasa biye mashi don jina nake kamar saman gajimare ina lilo. Lumshe idonsa yayi bai sake kulani ba,saida naji zaman ya isheni nace"yah." Jahid murmushi kurun yake yanason wannan dramer tasu, Jin yaki ansawa nasake cewa" *YAH AREEEF*" Tsintar kwayar idonsa nayi cikin tawa,sai bakina yayi nauyi na kasa cigaba da maganar.........sadda kaina nayi ina sharar kwallah,nidai narasa gane kaina,dan danan idan ina gabanshi sai kuka.........."idan kuka zakiyi man get out." Jinai kukan ya kucceman nadunkule waje guda kaina cikin guyawuna,yi kawai nake ina sauke ajiyar zuciya. Yah jahid da tasowa yayi zai lallasheta sai yayi wani tunani kurun sai yafita yabarsu. Tashi yayi zaune yanajin kanshi yana tsananta ciwo,daker ya fizgo maganar yace"zonan." Kasa motsawa nayi jikina rawa kurun yake kamar anjonaman wuta......dafe kanshi yayi da duk hannunsa,cikin tsawar dabaisan ma zai iyayintaba tace"I said come here." Ina makerketa na isa wajenshi,rawa kurun jikina keyi hawaye kau kamar anbude famfo.......hannunsa yasa guda d'aya ya rikoni yana kallona da jajayen idonsa dasuka rine. "Menene,mekike so." Muryata na rawa ina shashsheka nace"dama........dam.....a..cewa za......nyi.......ka....barni na koma hostel." Tsaki yaja kafin ya saki hannuna yace"is that All" D'aga kai kurun nayi yace"waye ya kawoki d'azun." Ai jinai fitsari zai kucceman girgiza kai nayi inaja baya.....fincikoni yayi ya zaunar yana kallona "I said waye yayi dropping naki d'azun." Fashewa zanyi da kuka ya tashi ya shiga d'aki belt ya d'auko yace"answer my question." Saboda tsananin firgitar danake ciki yasa bansan sadda idona yayi looooooo nazube k'asa bah........... Mrs bb ce👌🏻 Love u All my fans [6/4, 9:18 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by (mrs bb) Mom muhseen ce *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 22. Dafe kai yayi yana jin kan nashi yana sarawa,ruwa ya bud'e ya d'auko cikin frig mai sanyi yashiga shafa mata ga fuskarta,wata ajiyar zuciya na sauke mai nauyi.......lumshe ido yayi yana sauke tashi ajiyar zuciyar.....tashi nayi nafice ban sake mai magana ba,harna wuce bangaren maah nadawo don nasan munyi da ita zamuyi magana. Ta na ta shirin kwanciya don Abbu sai yakwana biyu yaje wani taro libiya,idasa shiga nayi na zauna gefen gadon,idona rufe ajiyar zuciya kurun nake,ina mamakin yadda nakejin tsoronsa har cikin yan cikina,abun yana d'aure man kai......."lafiyar kalau." Bud'e idona nayi nace"maah tsoron da nakewa yah Areef yana ban mamaki,inhar zan kusanci inda yake jinake kamar zan sik'e,maah bansan dalili ba tun ina ganin abun ba komi ba maah yanzu yana ban mamaki,yanzu fa zuwa nai kurun na tambayeshi idan yabarni nakoma hostel,amman karkiso kiga yadda jikina yake b'ari,karshe kan nafito har suma nai nadawo." Kallona take tana nazarina tsawon lokaci,kafin ta girgiza kai kurun tace"akwai wani abun,Aman kibar hakan cikin ranki zanyi wani abu akai,sannan kinyi sanyi da azkar dinki khairat,ki zama jaruma akoda yaushe karkibari wani yaga rauninki Addua takobin muminice kizage dayinta,sannan duk sanda zaki kusanci inda yake ya zamo kina karanta hazbunallahu wani imal wakil......kiyita nana tawa har kurabu understand." D'aga mata kai nayi ta cigaba da shirinta,nace"maah shikenan." Have"aa,saurin me kike." Shiru nai inajiranta don dajin maganar tana da matukar muhimanci. Saida ta gama ta hau gadon sannan tace man, "Salma taje ta samu Inna tagaya mata komi akan yayanku,harda soyayyarsu sannan ta k'ara dacewa ita bata son karatun aure takeson yanzu ayi mata." Kallon maah nake kamar itace innar ko salmar......gaba d'aya nayi huking,salmar da kanta tafadi wannan maganar, "shin wai me salma keson zama shin meyashiga kanta,anya wannan tunaninta ne kuwa maah." Murmushi tayi tace"maganarki abun dubawa ce wannan ba tunaninta bane,karanta mata akai,ita kuma tahau ta zauna,salma data sha nonona zubarwa tayi,don banyi zaton hakanba Amman nasan mezanyi." "Maah karkice nafadi haka saboda kishi ko har yanzu inason yah,Anya salma ta dace da yah Areef,maah kar azo abubuwa su dagule." Gyara zamanta tayi takallan tace"kema ai Auren takeson aimaku kudukan ku harda shidah......." Zaro dara daran manyan ido na nai ina kallon maah,murmushi tayi tana kallona"maida idon karsu fad'o,wannan maganar bamai yuwu wa bace khairat kwantar da hankalinki,itadai dakeson auren za,ai mata amman ba d'anaba saidai tanemo wani,duk abunda yarinyarnan take ciki khairat wlh i know,I know everything about her." Jinjina kai nake kamar kadangaruwa,lallai mutun mugune duk da bansan me maah take nufiba,naji ajikina salma ba alkairi take shiryawa ba,cikin karyewar murya nace"maah me mukai mata,bamuyi mata komi ba,yadda kowa yake da yanci cikin gidannan haka takeda,akan me salma zatai haka." "Come down my angel,don't mind her,everything will be Alright." Ganin dare yayi tace inzo yau tare zamu kwanta,dadi yakamani,yau zan kwana jikin maah d'ina after long time. Naje na canzo kayana nazo na kwanta tayi mana Addua tashafemu mukai baccinmu. 💕💕💕💕💕💕💕 Washe gari inada class 7:00 am. Tun wuri maah ta tasheni nashirya taje ta hadoman break dakanta,wani jidani take sosai nikuwa kamar na tashi sama don dadi,Annie tashigo ta ganmu tace"yau kuma shan nono ake,na b'oye ina dariya hira mukai tayi har nagama,yah meenah sai 4:00 pm takeda ita,don yanzu mawiyaci ne mufita tare,hka ma wajen dawowa.......yah jahid ne ya lek'o yace"ko my dear ta shirya zan sauketa makaranta." Nai saurin tashi nace" muje yah jahid." Muka fito ina yiwa yah meenah saita taho......muna dosar motar naji gabana ya fad'i rasss,jikina ya fara rawar da yasaba na kalli yah jahid ya girgiza man kai,adduar da maah tace nayi nacigaba da yi,harda karin wata yana zaune kujerar zaman banza,na shiga baya na zauna cikin kwarin guiwa yah jahid yatada mukatai. Saida nayi jarumta sosai sannan nace"yah Aree ina kwana." Bai juyoba yace"lafiya lau." Har mukaje bai ce komiba kad'an kad'an yah jahid ya jani da hira har mukaje school d'in. Fitowa nai inayi masu sai anjima harna juya naji yace"kayanki fah." Sororo nayi ina kallonsu murmushi yah jahid yayi yafito yana bude but,kayana nane kuwa wad'anda na had'a.....bansan sadda wani k'ayataccen murmushi nayi har dumful dina duka biyin suka bayyyana,kallona naga yanayi kamar ya samu tv,na sadda kai nace"thank u yah Areef." Wayata na fiddo cikin d'oki nakira husna tazo ta tayani d'aukar kayana. Sunanan har ta iso muka kwashi kayan sai hostel,ranar inacikin farin ciki sosai,munfito break nakira maah na gaya mata, tace ai tasani kin gaya man tayi,nasiha sosai tayi mani maishiga jiki,sanan tace inri'e ibadata da azkar dina,idan na kwana biyu zata kawo man ziyara,aikuwa naita jin dadina. *(YANZU WASAN ZAI FARA,MASOYANA KUBIYONI DON JIN YADDA LAMARIN ZAI KASANCE.)* Zama na hostel tare da husna ba k'aramin dadi yake man ba,gashi karatunmu yana kara zurfi,komi yana kara gaba sai inyi wata banje gidaba wani zubin saidai Annie da maah su suzo su ganni,saboda munfara zama busy tsakanina da yah Areef kuwa zan iya cewa ni hakan ma yafiye man kwanciyar hankali,duk da yanzu alhamdulillah tsoron da nakeji nashi yayi mugun raguwa,duk da ba had'uwa mukeba amman sometimes yana kirana yaji ya karatun,ya kuma jaman kunne akan wasa da karatun,daga haka shikenan sai muyi sallama,rabona dashi tun randa suka kawoni,yah jahid ne duk weekend zaizo ya d'aukemu nida husna muje yawo,wani zubin kuma muyita fira har yamma sannan yatai. Yah meenah ma takusan dawowa hostel din,sai dady ya dawo idan yabari zata zo d'akinmu muhadu mu uku. Salma kuwa zuwa yanzu bansan wace take ciki ba,saboda koda wasa ban taba ganin ta kawo man ziyaraba,kuma konaje gidan bana ganinta......Anty shidah tadawo sunyi graduation,yah shahid ma yadawo,gidan yanzu gwanin sha,awa. Husna duk ta rud'e da ganinshi yayinda shi baisan ta nayiba, zanso ace had'in yayuwu saidai yah shahid ba,amai cusu irin wannan bakke ince zan mashi maganarta,amman inanan ina tsara plan dina,don nasan yah zaiso ta kodan bata rasa komiba husnar. Akwai wani abu guda dake faruwa dani,tsakanina da DR MK mutumin duk school d'inan yawancin yanmatan dake ciki bawacce bai burgeta,cikinsukuwa hardani eh sosai Dr yana burgeni ta b'agarori da daban daban,kamar natsuwarsa kamewarsa daga kula yanmata,rashin maganarsa,tsaftarshi gayunshi da kuma tsayuwa akan ra,ayunshi........tun bayan da maah ta rabani da yaj Areef nayi jinyata na warke sainaji kamar anzareman sonshi dake cikin zuciyata,ko miskala zarratin banajinsa irin yadda nakejinsa dacan,inamashi kallon danakewa yah shahid.......Tun bayan dawowata hostel na kula da wani abu,DR mk lectura mune yana d'aukarmu course biyu,baya kula kowa amman ni sai yazamar mashi kamar jiki idan bai kulaniba,bakuma kulawa irin magana cikin mutane ba,koyace insamai office aa ba haka ba. Idan yashigo class idonshi akan sit dina,idan yafara darasi bayafara tambayar kowa saini,dana san ansa da ban saniba, inharkuma banganeba bayagajiya zai tuso darasin tundaga farko harsai nace nagane,idan na makara zaita kallona harsai ni dakaina nafad'i dalilin makarar,inkuwa nasake nayi fashin zuwa class nabani duk da bazai mun maganaba amman fa ranar danazo bazai barmu mutashi ontime ba,duk abunda akai ban nan sai ya maimaitashi,bayajin komi. Wannan abun dayake yasaka husna ankarewa kuma ta isheni da maganarsa,hakika nima nasan something behind,Amman kamar mekenan bansaniba nakanji babu dadi duk randa bamuda lecture dinsa,saboda gaskiyar magana Dr ya iya koyarda mutun yagane,kokai kwalwar kifine dakai dole zaka fahimci wani abu ko baka gane duka ba. Yah Areef bai tab'a zuwa wajena ba kuma nima ban tab'a mashi complain din hakanba,kwana biyu banjin dadi kokadan masassara nake fama da ita saidai husna tayiman atendance,yau da yamma tadawo daga class bayan tayi man sannu tace"khairat kitashi fah yau wlh DR yayi magana akan rashin zuwanki,don bayan anfito yakirani yace ince maki kuhad'u *sahad guiden* 5:30. Anjima." Kallonta nake na kasa cewa komi, Zama tai kusadani tace"khairat inhar maganar soyyyace yazo maki da ita pls,don't reject,bance karkija ajinkiba amman karki nunamai wulakanci yacancanci asoshi baida wata mummunar halayya ." Wayata tayi vibration ina dubawa sunan yah Areef ne text ne yayoman. Budewa nai naga yasa. *meet me in sahad guiden 5:30pm* Kallon juna muke dandanan naji masassarar ta bar jikina,husna ta d'auki wayar tana duba sak'on. Kallona tayi ganin na buga tagumi. "Nikuwa khairat ban tab'a kokarin sanin wani abu dangane da yan gidankuba amman kiyi hkr yau inason sanin ya kuke da wannan yayan naki Areef." Maimakon na bata ansa sai kurun natashi nashige barth room. Mrs bb ce👌🏻[6/4, 7:16 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* WRITTEN BY (MRS BB) MOM MUHSEEN. *(AGASKIYA MASOYANA BANDA KALAMAN DA ZAN GODE MAKU,ILLA IYAKA INCE ALLAH YABAR KAUNA DA ZUMUNCI,HAKIKA IN BABU KU BABU MU HAKA IN BABU MU BANU KU,KARKU KAMAN TA COMMENT D'INKU SHINE K'WARIN GUIWARMU,ALLAH YASHIGE MANA GABA YA BAMU RAI DA LAFIYA.)* 🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSO......._* 23. Husna sororo tayi da wayar ga hannu tana bin hanyar ban d'akin da kallo,tabbas wannan abun ya sake tabbatar mata da cewar akwai wani abun,inbacin haka daga yin simple question sai ki canza,karshe kibarni nan zaune. Tashi tayi ta d'ora sanwar indomi don tasan Khairat ba dora komiba,tunda nashiga barthroom din nai zaune kan abun bayaha,nadafe kaina dake mun masifar sarawa. Nashiga ukuna ni khairat,idan yah yaganni da Dr mezan gaya mai shin zaima saurareni kuwa,mik'ewa nai cikin azama ina sabbatu"kai ina wallahi bazai saurareni ba,wannan b'akar zuciyar bazata barshi yaji komi daga gareniba,nabani yazanyi." Tunawa nai da Husna dana baro d'akin,idan ba itaba wazai bani shawarar yadda zanyi to kenan hakan nanufin saitasan komi kan family issue d'ina,wata zuciyar tace to menene Husna cefa tazama yar uwarta,kuma tana da tabbacin bazata bata shawarar banza ba kuma babu maijin sirrinta wajen wani.Dole na yanke shawarar sanar da ita komi akaina da gidanmu. Wanka nai nafito ina kallonta tana cin abincin tana danna system,kamar komi bai faruba tace"kinga ma zaman kewayen kenan." Murmushi nai ina zaman kusada ita nace"bakiyi fushi bakenan." Tab'e baki tayi tace"kinsan dai ba halina bane ko,akanme zanyi fushi bayan nasan kina da dalilinki na kin gaya man a bunda ya shafeki,don kar husna soda uwar surutu ta zagaye school tana sanar da mutane." Dariya nayi nagane cewar abun yabata haushi nace, "Karkice haka kema kinsan cewa ba haka bane,kiyi hkr insha Allah 2day am telling u everything about khairat,hakan yayi maki ko." Harara ta wurgoman bansaniba kusada ita na matsa"haba mrs shahid farouk ai bazakiyi fushi daniba nasani,yanzu kiban shawarar yadda zanyi inhad'u da kowanensu batare da guda ya ji haushina ba." Ajiye plet d'in da kate cin indomin tayi tana kallona some seconds,sannan tace"ki kira yayan naki kice dashi baki fito lecture lokacinba,amman ya sameki school 7:00pm lokacin kinga kin dawo harma kin natsu." Rungumeta nayi inajin dadi, "Thanks my d besty friend in d world." Murmushi kurun tayi mun tatashi tana had'a kwanonin wanke wanke. Shiryawa nikuma nafara yi cikin natsuwa amman duk da haka ina kokonta yaya,nasan halinshi amman bari najarava wannan shawarar ta husna,ance da jarabawa jirgi ya tashi amman zuciyata sai bugawa take. Nagama shafa mai najawo phone dina nashiga kiran sa,tunda na mallaki waya ban tab'a kiranshiba,ringinga take ba ai picking ba harna sare husna tayun zuru da ido, ganin duk nayi wata iri dani ajiye wayar nayi nace"kingani bai d'auka ba." "To kiyi mashi text mana" Dafe kai nayi cikin rashin jin dadi na shiga typing text d'in kamar haka. *"yah ina class around 5:30,pls KO zaka zo school din 7:00 lokacin i'm free."* Ajiyar zuciya nai ganin ya tafi,tashi nai naciba shiryawa. Bawata kwalliya nayi ba don nibata damanba kyauna haka ya isan,asai na k'ara da waniba farar powder nasa itama don husna ta isan,sai kwalli turare nasa kad'an tunda nasan babu kyau tunda ga inda zanje. Sai jana take wai nayi kwalliya don zanje tad'i da ai bayi nakeba ko hoda bana sawa idan zanje class,murmushi kurun nayi mata nace"babu rakiya kenan." "Wah! Kyaleni research ma zanyi wlh saikin dawo kiyoman tsaraba." Fita nai inajin kirjina yana duka. Nai sa,ar samun taxi ta kawo wani student,natsayar da it nashiga na gaya mai inda zaikaini...........kallon wayar nake ba komi nake kalloba sai time,biyar da sha biyar jingina nai jikin kunerar har mukafice daga makarantar. Minty talatin ya kaimu wajen,wurine na alfarma wanda sai wane da wane ke zuwa wajen,an k'awatashi da abubuwan sha,awa da more rayuwa,ni,ima ce wajen sosai iska mai dadi da fitulu burjik,idan dare yayi sai kace safiyace bazan kwantanta maki yadda tsarin wajen yakeba don yafi karfi alkalamina. Tun daga bakin get d'in wajen nake baza idon ina zan ganshi,don baka shiga saida get fast,wanda duk zaishiga saiyabada kid'i sannan subashi get fast din,idan kuma kagama zaka barmasu abunsu nan. Tsaye nayi ina kallon masu shige da fice,wani daga cikin masu kula da waje ne ya iso inda nake yace"madam bismillah,ga yallaban can yace ayi maki iso." Bin bayanshi nayi abayace jikina har k'asa saboda fakistan ne jikina riga da wando...........wajen babu yawaitar jama,a don inajin akwai ranakun da zakazo kasamu mutane fiye da haka. Wani waje muka nufa naji zuciyata tana bugawa fast,runface maitsananin kyau wajen grass capet yakara fiddo kyan wajen,saidai zuwa yanzu bn ganin kyan wajen,saboda abun nani da firgtni,kocikin miliyoyi mutane naganshi dole shaida shi.....duk tuku guda danake jinake kirjina zaifad'o saboda tsabar fargaba da firgici........bayashi kurun nagani Ammn zuciyata kakarwa take,meya kawosji wajen nan nashiga ukkua ni khairat. Wlh ngaji pls sorry mu hadu gobe. Mrs bb ce.👌🏻 [6/5, 11:43 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕 *ABIN CIKIN RUHINA* WRITTEN BY (MRS BB) MOM MUHSEEN. *GODIYA TA BATA DA IYA KA AKAN KU MASOYANA,HAKIKA KUNE JIGON LITTAFINAN,INA MATUKAR ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE,ALLAH KUMA YASAKA MAKU DA MAFIFICIN ALKAIRINSA,INASONKU KAMAR YADDA KUKE SONA.* *JINA GAREKI UWARIDAN SARDAUNA FATIMA,MARUBUCIYAR SOORAJ ALLAH YABAR KUNA KEDA MAIGIDANKI*😂😉 *not editing* Idan kunga mistake kuyi hkr👌🏻 24. Wani irin tuntub'e ne nayi daya yi silar fad'uwar pos dina,dama d'an rakiyar tunda yashigo dani wajen yajuya tunda naga inda zanje,duk'awa nai na d'auka inajin d'an yatsana yana jinga babban,d'agowar da zanyi naga wayam inda yake zaune su biyun saura Dr amman shi banganshi ba,murje idona nayi sosai amman ban ganshiba ko iskar da ta d'eboshi ban ganiba,waige waige nake amman ko b'urbushinsa ban ganiba.......jikina yayi wani irin sanyi nabani uku wai k'alau nake kuwa kodai tsoron sa ne yasa naga kamar shine awajen da farko,k'arfafa zuciyata nayi na karasa wajen ina ajiyar zuciya k'asa k'asa. Tun kafin na zauna yake kallona yana zaune kan kura ga table gabansa an k'awata shi da yan kayan ci kadan,yad'ora kafarsa kan d'aya yarik'e hab'arsa da hannunsa,fesincap ce kansa wadda ba sosai nake kallon cikin idonsa ba,tabbas Dr ya hadu hadedden guy ne,wanda ya iya daidaita wankanshi,jeans ne dark blue sai light blue d'in shirt tabi jikinshi ta kwanta,agogoce d'aure ga hannunsa na hagu sai daukar ido take,kamshi ketashi mai tsananin shiga rai da kwantar da hankali,har lokacin kallona yake nikuma ina tsaye,da hannunsa ya yi man nuni da na zauna,kujerar dake kallonsa jikina yayi wani lakwab haka na jaye hijab dina na zauna ina wasa da yatsuna,nakasa kallonshi,don bazan iya had'a ido dashi yana mun irin wannan kallonba. Cap din naga ya ajiye gabanshi ya tashi zaune sabanin da dayake kwance cikin kujerar. "Ina wuni." Wayyo kamar zan nitse haka nakeji,kunya ta kamani mema yasa tunda nazo ban gaidashi ba,kasa ansawa nayi inata matsar yatsuna kamar zan tsinkasu,kozafi banaji wanda da kalau nake bazan iya sarrafasu irin haka ba. "Karkijima kanki ciwo,yana zuba lemo cikin cup fuskarshi da murmushi wanda kokad'an baya yinsa cikin class. Mik'omun yayi "bismillah,ance in kayi bako first abunda zaka taryeshi dashi shine abunsha,kafin komi yabiyo baya." Duk na kasa sakewa gashi sai kallona yake ni kallonne bansaba dashiba,yana ban kunya kuma idaniyata bazata zureba. Cikin low voice dina da bansan dalilin sanyinta ba nace"sorry sir good evening." Sautin murmushin sa naji yana rik'e da cup din ruwa saida ya kurba sannan yace"bazan ansa ba tunda nima baki ansa tauba." D'agowa nai nad'an kallai kafin nasadda kai nace"sorry sir bazan it ansa gaisuwarka ba,bacin ni yadace nafara gaidaka kuma banyiba,I'm sorry na shafa,a ne." Ajiye cup d'in yayi yana tattara duk hankalinsa kaina, "Me ya shagaltar dake,nagadai ko kallona ma bakiyiba balle nasaran ko *Muhammad kamees* ne ya d'aukar maki hankali." Innalillahi wayyo Allahna wannan guy din ya iya bada kunya,jinai kamar inzura aguje. (😂😂😂basaban ba khairat) Shiru nai inata murzar hannuna nakasa cewa komi,to mekuwa zance mai jinai yace"kinyi shiru,kisaki jikinki bafa sace ki zanba wallahi ban iya satar mutane." Dariya yaban bashiri murmushi ya kubcemun mai had'e da dariya,rufa bakina nayi nakara sadda kaina inayin abuna. Inajinsa yana tayani amman nashi babu sauti sosai. Saida nagaji nadaidaita kaina yace, "Haka kika iya dariya, Aikuwa zaki koya man nima naringa yiwa budurwata." Kallonsa nai bance komiba murmushi dai nake yi. "Meya hanaki zuwa class 2days,anyi abubuwa dayawa bakyanan." Nad'an saki jikina nace masa "Wallahi bana da lfy kwana biyu amman nasamu sauk'i,husna tana mun bayani idan ta dawo." "Kin tabbata tana yi maki," D'aga kai nayi murmushi yayi yace "to bari mugani idan bayanan sunzauna kanki." Tambayoyi yashiga yiman ina bashi ansa tare da bayani sosai. Tab'i yashiga yimun yana cewa "good,very nice gaskiya husna ta cancanci kyauta kibata wannan inkin koma." Wata envelop ce ya mik'omun. Kallosa nai nace"sir kabarshi ai basai kabata wani abuba." Gabana ya ajiye yana kallon cikin idona yace"don me basai anbata ba,bayan tayi abunda ya farata man,kefa ta yiwa taya bazanji dadiba." Sadda kaina nayi nama rasa mezance masa wlh Dole na k'akaro smile nace"to tagode." Shiru muka sake yi na tsayin lokaci,kuma har yanzu idonsa akaina wlh jinake kmar in bace sabod wannan kallon nashi. Ga magaruba tataho dandanan hankalina ya tashi,saboda ganin bakwai saura minty talatin. "Da alamun dai kin k'osa kibar nan ko,ban tunanin wajen bazai burgekiba aida munje *kalam guiden*." Yak'e nayi nace"Aa wlh yayi kyau,sosai wajen akwai nishad'i." Mik'ewa yayi yana cewa"musanman idan akwai wanda ya sace mka zuciya awajen ba." Ban tashiba nabishi da kallo,shima ni yake kallo wanda bazan iya jure shiba,inda nake ya iso yad'an sunkuyo ta gefen fuskata kamar zai sunbaci kuncina,dandanan jikina ya kama kerma runtse idona nai injin kashin turarensa yana huda gashin jikina,i wonder nakejin something akanshi,mekenan nashiga ukkuna. Cikin wata murya da tayi masifar tada tsikar jikina yace" *ummulkhair,why kika mun irin wannan satar plsss ko kinsan kin kassarani akanta,na zama zero tundaga lokacin da kika yimun wannan satar,plsss ki maido man kayata in samu relief.*" Tunda yafara magnar kirjina ke bugawa babu k'ak'k'autawa,na k'an kame jikina da nakejin kamar yana zarar raina kamar yana fiddamun duk wani kuzari dayayi saura cikin jikin. Wata ajiyar zuciya nasauke mai mugun sanyi jin yatashi daga inda yake,bud'e idona nai ina jin kamar na fasa ihu akan yanayin danaji. Pos din ya d'aukarmu namik'e shikuma ya jaye kujerar nafito,tare muke tafiya zuwa inda yayi parking. "Bakice komi ba." Fuskata kamar zanyi kuka na kallai nace'pls wlh bansan abunda na satar makaba kayi hkr." Dariya yashigayi yana shafa kanshi,hannunsa yana rik'e da cap dinsa, "Gaskiya ba zanyi hkr ba sai kin biyani,idan kuma baki biyaniba zan rama idan na tashi ramawa naki sai yafi zafi,don ko har kuka saina saki." Shiru nai banda ansar bashi,a matsayina na yar jamia wacce ta waye tasan kuma me ake kira da so,to dole nasan me dr yake nufi da kalamansa akaina,nagane komi yke nufi dani nagane kenan yadda na sace mashi zuciya shima yna nufin zai sace tawa. Hakika zan iyacewa zuciyata babu kowa aciki,empty set take amman kuma inajin can k'asan raina wani gurbi da wajen yake yawan bugawa,muddin naji wani feelings akan DR hakan meyake nufi,basan me hakan yake nufiba nabarwa Allahn daya halittamun wannan zuciyar. Bud'emun gaba yayi nashiga yazagayo yashiga,fita mukai mukai mukanufi school,jana yake da fira anman nakasa sakin jikina nabiyeshi,saboda maganarmu dashi ta karshe itace kemun yawo akai,wani gefen zuciyata inajin tsoron Kamuwa da sonsa,wani shashen yana nuna man idan nakamu da son nashi menene,wanda kikemawar dai akwai babban ginshik'i tsakaninku,duk yadda kikakai ga son kasancewa dashi yariga ya zama haramiyarki. Rutse idona nayi inajinsa yana ta gayaman wsu kalamai wanda babu tantama dr zai iya yin nasarar sacemun zuciya cikin d'an karamin lokaci,kamar yadda yafad'a man. Bakin get d'in hostel ya saukeni saida nayi dagaske sannan yabarni nashige..........Allah Allah nake na isa d'aki,don inji shin an aiko nemana,inhar an aiko to tabbas yah yazo,inkuma bai aikoba hakan nanufin baizoba. Don yanzu takwas harda minty ashirin. Husna na tadda tana bud'e wata katuwar ledar shooping,kayane gasunan birjik kamar ba,asan zafin kudiba aka siyosu,tsayenai ina kallon kayan,nidai nasan Dr bai ban komiba ,haka bai aiko kowaba to waye zai kawo,kodai husna aka kawomawa. Jinai tace"sai yanzu kenan,da alama Dr yasamu karb'uwa." Banbi takan kalaminta ba nace"bak'o kikai husna." Mik'ewa tayi tana jingina d bango tace"aa,ke aka kawowa yayanki ya zo bazan iya lissafa adadin mutanen daya turo nemankiba,inacewa baki fito lecture ba,karshe hardai nace bakidawo d'akiba. Baiyi minty goma da tafiya ba ga kaya nan ya aiko dasu abaki,hada wasu cards idan kin duba duk zaki gani." Silalewa nayi k'asa wata zufa na karyomun zuciyata da sauri take bugawa............ Mrs bb ce👌🏻 Mom muhseen 09034722970. [6/6, 12:48 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by (mrs bb) Mom muhseen. *Dedicated by ZAUREN MRS BB* 😉💕 *watt pad* *HUMAIRA 7531* *GODIYA MARAR IDADI GAREKU MARANTA LITTAFINA,INA MAKU FATAN ALKAIRI.* *not edited* 25. Duk nayi zufa hijab din tajik'e sharkaf,wallahi inajin tsoran yah inajin tsoron yasan wani abu tsakanina da dr,shin idan ya tambayan inda naje inazance mashi,bayan nidakaina nace ya saman school at 7:00 pm gashi kuma yazo ni bandawo ba,damuwata wannan karyar danayi cewar naje lecture bayan kuma tabbas yah ne nagani tareda dr wajen sahad guiden,nabani nalalace yazanyi. Hus na ce tatako har gabana,ta durkusa tana cireman hijab dina da gyalen fakistam dina. Cikin kulawa da nuna damuwa tace taso saga nan zauna nan,ta kamani muka zauna kan katifar mu. "Meye faru,duk wannan tashin hankalin nameye,shin mala,ikane yayan naku da har kika tsorata dashi haka,haba khairat ki dawo natsuwarki mana,kefa yar jamia ce babbar budurwa mai daukar overaller na department dinmu,kyakkyawa maiji da wayewa da kudi da kokari,taya zaki ringa jin tsoron namiji irin haka duk da bansan dalilin tsoron nakiba amman yayi yawa,kozan iya sanin alakarku dashi." Jingina nayi jikin bangon dake bayana,ina dunkule kafafuna nasauke ajiyar zuciya maikarfi sannan na kalleta, Cikin karyewar murya da low voice dina nace"husna,idan nace maki yah badan gidan mu bane hakan ba gaskiya bane,saidai zan iya cewa shid'in ba uwarmu daba haka ba ubanmu dayaba,shid'in dane ga yayar mahaifiyata maah. Nabata labarin abunda nasani da wanda naji bakin su Abbu,da yadda nakamu da sonsa shekarun baya harda ciwon zuciyata,komi nasanar da husna har kan abunda kefaruwa yanzu da abunda salma keman. Jinjina kai kurun take tana kallona,kafin ta nisa tace"tabd'ijam,yanzu ya kenan kina ganin cewa yanzu zai iya dawowa yanuna yana sonki,kokuma mekike tunanin ya kawoshi wajenki. Ban bude komiba cikin ayancan akawai ina fiddo kayan ne,akwai cards ciki idan kika duba muna iya samun ansar abunda mukenema,kuma yanzu ke yakikeji cikin ranki akanshi." Zamewa nai na kwanfa ina kallon sama nace"banajin komi kanshi banajinsa irin yadda najisa shekarun baya,bana jin feelings akanshi irin shekarun dasuka wuce,husna saidai abu guda inajin tsananin tsoronsa wanda nikaina bansan daliliba,daidai da second idan muka keb'e ko nake kusada shi in takaice maki har suma ina iyayi. Basan why ba inson daidaita alak'ata dashi kamar sauran yan uwana,amman nakasa wallahi bazan iya cemaki da reason guda dayaba dayasa nake mashi wannan tsoron,.............. "Lallai na maganar maah,datace maki something behind,tunda ada kince ba haka kuke ba dole akwai dalili kece baki saniba,amman nasan maah tasani bazadai ta sanar dakeba." Kallon husna nayi nace"kin tabbatar da haka kuwa." Murmushi tayi mun"na tabbatar saboda tace maki tana ankare da duk abunda kowa keyi,kuma zata san abunyi. Kishirya kije gida kuyi magana zaki tabbatar da maganata,ance zato zunubine koda ya kasance gaskiya,ina zargin yar uwarki da yin wani abu duba da yadda kika gayaman soyayyar da takewa yah Arref din." Tashi nai zaune ina kallonta kamar yau nafara ganinta, "Husna mekike cewa,wace yar uwar tawa karkice salma salma duk son da takema yah bazata cutar daniba,tana sona bazata so abunda zai tab'aniba." Murmushin tayi mun"ada kenan khairat,kibude idonki kifahimci reality,ki auna abubuwa da yawa ada da kuma yanzu d'aya suke,son da kikace tana maki da yanzu tana makishi? Yaushe rabon da ta zauna kuyi hira,tunda kikazo school konace tunda kika dawo hostel ta tab'a kiranki awaya?ta zo inda kike common text wannan tayo maki?,ki bud'e kwalwarki dakyau kifuskanci gabanki makashinka na tare dakai salma bata sonki,zatayi komi don raba wannan kaunar. Karkiyi mamakin idan nace maki yah Areef he love u he love everything for u,amman akwai abubuwa dasukai discouraging power nashi,kiyi mai uziri kisama ranki cewar yayanki bai tsanekiba,bai kikiba hasali kece wacce yabinne cikin zuciyarsa,bance kiyardaba amman wannan shine gaskiyar magana. Wannan dalilin zaisaka salma taga tayi komi don ganin ta sameshi,don ba ita yakeso baba itace dreaming d'insaba thats why." Kamar Tv haka nake kallon husna,kamar almara haka nakejin kalamanta cikin kunnena,jinake ban tabajin magana data d'aure dukkan tunani ba irin wannan,zuciyata tanason yarda da kalan Husna,yayinda wata takeson karyata hakan shin da wace zan yarda. (YAN ZAUREN MRS BB KHAIRAT NA BUKAYAR ZABINKU.😉👌🏻) Tashi husna tayi tashiga tayo Alwallah tafara sallah,don har tara tayi gashi ko magruba bataiba,khairat daman ba sallar takeba. Tunani yayi man sallama nayi zurfi cikinsa,narasa inda zan kama dole zanje gida dole maah ta tabbatar mun da maganar husna. Ranar haka nai bacci da tarin tunanika,kasancewar yau lecture dare garemu dukda weekend ne. shiyasa tun safe dana tashi nai wanka,banma jira cin komiba muka fito da husna tace itama gida zata,saida nashiga muka gaisa da mama sannan mai taxi d'in yawuce dani gidan. Duk motocin kowa nanan,harabar gidan Alamun dai babu Wanda yafita. sosai muka gaisa da maigadinmu,sannan na isa cikin gidan falon mai aikinmuce keta mopping cikin mutunci ina fara,a muka gaisa da ita,nace"basu tashiba ko." "Tace aa suna wajen yin karin kumallo,ai dayake yau ranar hutuce da shad'aya tayi suke tashi." Jinjina kai nayi na wuce dinning room din,fun Karin na isa najiyo uryar Abbu yana fad'a. Cikin sauri na idasa shiga tare da sallama. Annie,dady,maah,Abbu,yah Areef,yahjahid,Anty shida,Yah shahid,sai Yah meena da salma dake durk'ushe kasa gaban Abbu,duk ta kare itce yakewa fadan..........Annie ta tareni tare da rungumeni,sannan na gaidata tana ta murnan ganina,najega yah menah rungume juna mukai inajin kewarta sosai tare dani,duk daina gaida kowa Anty shida tace"ta alkairi kinga yadda kika kara girma,kinyi hankali sosafah." Yah shahid yace"ba,a yabon d'an kuttru sai ya shekara goma da yatsa." Tab'e baki nai ina kallon Abbu, "Kagansu KO yanzu kenan Abbu ni banyi hankaliba gaskiya kaja masu kunne." Dariya yayi yace sudaina jana,salma na kalla sai share kwallah take nace"Lafiya salma kuka kuma." Maad dai dauke kai tayi itama salmar bata ban ansa ba,yah meenah dai tace"itada Abbune." Yah Areef ne ya mik'e yana goge bakinsa da tushu,fuskarsa babu alamun faraa ko kadan,don daman tunda na gaiashi bai ansani ba. Sorry WLh nagaji ajima zanamuku wani. Mrs bb ce 👌🏻 [6/6, 7:44 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by mrs bb. Mom muhseen. *Dedicated to ZAUREN MRS BB* 😘💕💋 *watt pad* *HUMAIRA7531* 26. Muryarsa adake yace ma Abbu, "Zan wuce Abbu." Kallonsa yayi yace"sai yaushe kenan." Agogonsa ya kallah yace"wallahi bansan lokacin ba anma ina kyautata zaton zamuyi aikin 2month a paris,kafin nan mu wuce japan muyo 2 month da ko sati biyune,banda tabbacin zamu dawo kan lokaci gaskiya." Shiru duk akai anan na fahimci tafiyace zaiyyi,kuma bazai dawo nan kusaba. Dady yace"maganar salmar fah." Fuskarsa na kalla yasake d'aureta tam,yace"Dady munyi maganar daga baya,jahid muje kasaukeni time na tafiya." Duk tashi akai don yi mashi rakiya zuwa mota,da alama akwai abunda yafaru kowa naga fuskarshi babu dad'i.ina tsaye yaketa sallama da kowa ina gefe guda na rungume hannu. Maah rungumeshi tayi harda kwallanta,wai zatai kewarshi murmushi nai ina jinjina kaunarta tsakaninta dashi,kamar bazai bar jikintaba haka yaisa ga Annie itama ya rungumeta,su Anty shida da su yah jahid namai dariya wai kuka zai,ina ganin sadda ya hararesu sannan ya mikama yah shahid hannu sukai musaba ha,ya kalli yah meenah yakama kunnenta yace"karatu tukuru." Duk dariya akai masu salma ya mik'ama hannu,isowa tayi yajata gefe bansan me yace mata ba,naga dai tana d'aga kai sannan ya shiga mota. Abbu ne yace mashi"Areef ka gaisa da kowa banda ta alkairi,laifin me tayi maka haka." Shafa kanshi yayi yana murmushi baice komiba,Abbu ya juyo ya yafitoni da hannu. Jikina asanyaye na nufi inda yake,i wonder banji tsoron da nake jiba idan na tunkareshi,isa nai gani nai yabud'e bayan motar yace"shiga." Kallon Abbun nake nama rasa mezance mashi daga man kai naiyayi,dole nashiga Anty shida ma tataho "Abbu inazuwa." Bai musuba tashiga tana dariya,yah jahid na satar kallonta ta mirrow jan motar yayi muka fita,yah jahid da Anty shida kurun suke firarsu anman ni bakina ma yayi nauyi,waimeke faruwane yau gani ga dodona amman narasa inda tsoran ya tafi,yanayin dana shekara uku ko nace hudu banjiba shine nakeji,duk wani yanayi da da nake tsintar kaina cikinsa idan ina tare dashi yadawo,mekenan mamaki da al,ajabi sun rufeni. Har mukaje filin jirgin bance komiba,yah jahid da anty shida suka fita can wajen zama suka samu suka cigaba da firarsu,shiru motar tayi na kasa yin magna gashi lokaci yana ta tafiya,don nasan karfe d'aya zasu tashi,gashi shabiyu da rabi. Ganin yak'i tankaman don yadda duk yabi yasha mur natabbata in nabiyeshi har yatai bzai ceman komi ba,cikin sanyin muryata nace"yah kayi hkr kazo baka saman ba wallahi............"shot up." Ba shiri naja bakina nayi shiru. Cikin muryarsa dakakka yace batare da yajuyoba "Aure dai kikeso dai ko,to ki kwantar da hankalinki nasanar da Abbu kafin nadawo ya aurar dake,idan yaga dama shi masoyin naki sai yabarki ki k'arasa." Atsorace nake kallonsa daga inda nake zaune,zuciyata bugawa take babu kakkautawa, "Yah dongirman Allah kayi..........."karki sake kiyi man magiya,kenan don uabanki har kinyi girman kiyimum karya don kije ki had'u da saurayi,to gara da Allah ya nuna man,insha Allah end of this month keda salma duk zaku idashi gidajen mijinku,tunda har taurin kanku yakai haka ga yayarku nan tunda tafara karatunta ba,asameta da wata matsalaba harta gama saiku *kwalaye daku berori da bakusan kankuba.* zakugane bakuda wayau badai aure kukeso ba. Ai bansan sadda kuka ya kubcemun ba ina kukan ina cewa"yah kai mun rai.......inkika sake magana makeki zanyi fita anan sakara kawai." Dana zoyin mgana sai ya kwatsa man tsawa duk yadda naso yasaurareni abun yaci tura,,. Gashi bakina yakishiru inacewa"wallahi ni banda saurayi Allah yagani ni banyi komiba karatuna nake yadda akasani,shine zakace aimun aure wallahi banso inkuma akayishi saina gudu wallahi........jinai kurun ya faskeni da mari. "Nikike ma musu ni zakiyiwa gardama,khairat duka nawa kike atafin hannuna fa kika girma,karya zan maki kina nufin kocikin biliyoyin mutane kimashiga bazan shaidakiba,balle wajen da babu kowa. Uhmmm yayi kiyi duk abunda zakiyi intakama kikashe kanki amman tabbas Aurenki da............kasa anbatar sunan yayi yanajin kirjinsa yana duka,zuciyarsa tana zafi,idan kakalli idonsa zakasan zafin da yakeji ga ranshi. "Fitarmun anan karkija nayi kasa kasa dake awajen anan." Kuka nake wanda bazan iya tuna lokacin da nayi shiba,haka nafito jikina yana kerma kafafuna sun kasa d'aukata,can gefe nasamu na durkushe ina cigaba da kukana mai cin xuciya.........jinake kamar zan sike ni za,ama aure saboda nayi me kawai don na ansa gayyatar malamina,banyi iskanciba banyi fasikanciba babu abunda aka kamani dashi na haramci shine zasu tsigeni daga karatun da nake so fiye dakomi...............kiransu aka farayi na minty biyar har akafara sanarawar rufe jirgi......inanan durkushe kuka kurun nakeyi. Taku naji abayana ahankali kamshin sa yna sake nufoni,har sanda ya tsaya gabana,durkusawa yayi ya d'agoni tsaye kokrin cire hannuna yake ina bige hannun nashi dake tab'ani,don wani irin haushin sa nakeji,hakan bai hanashi son ganin na bude fuskataba,karshe dole nasaue hannun ina shashshekar kuka idona rufe,duka hannayena ya rik'e da hannu guda dayan kuma yadago hab'ata,kada kaina nayi yasake juyo da fuskar tawa gabanshi,uffan baice ba illa iyaka sakin hnnuna yyi yasaka handchif yana tsane mun hawayena,amman still wasuna biyo baya. Jinai wani irin feelings ya taso mun form some where,wanda bazan mance iri a ba ranar daya daukan yakai har daki.........tun daga yatsan kafata nakejin wani yanayi har cikin jinin jikina,numfashi nake saukewa zuwa yanzu kukan ya tsaya,saidai ajiyar zuciya kuma har lokacin banbude idonaba,kallon fuskata kawai yake jinai anata neman shi jirgi zai tashi amman shinko ajikinsa,sai lokacin na bude idona ahankali idonsa ya sauya launi yakada yayi ja,amman hakan bai hana wani abu fitowa ba yana shiga cikin nawa idon. Jinai kafafuna bazasu iya daukata ba,silalewa zanyi kasa yayi azamar rikeni,saidai najini yayi mun wata kyakkyawar runguma. Fashewa nai da kuka wanda yafi nafarko,bubbuga bayana yake yakasa magana,injiyo yadda zuciyar sa ke duka dagoni yayi yasunbaci goshina,kuncina da tafin hannuna. Saida na rutse idona kafin ya yimun rad'a ga kunne *INA MAKI FATAN ALKAIRI MATAR MUHAMMAD KASEEM,SAI WATARANA BAZAKI SAKE GANINA BA,KIYI HKRI DANI MUN HARAMTA GA JUNA HAR ABADAN,BAZAN IYA KARYAWA MAAH ALKAWARINTA BA.ZANJE NAYI JINYAR XUCIYATA KIKULA DA KANKI AND PLSSSS FORGET ABOUT AREEF FAROUK,GOOD BY UMMULKHAIR.* (Wayyo nasan YAN ZAUREN MRS BB ZASUYI MISSING AREEF.) MUHADU GOBE LOVE U ALL MY MASOYA 😂😘😘😘💕💕💕 MRS BB CE 👌🏻 09034722970 [6/8, 1:14 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕 💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_* Written by mrs bb Mom muhseen. Wattpad Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. NOT EDITED:INKUNGA MISTEK BE SORRY😉 27. Missing page💕 Silalewa nazoyi zan zube sabo yadda jikina gaba ki dayanshi babu kuzari,babu karfi tare dani jinai anyi azamar rikoni,bazan iya gane ma kowaye ba nadaiji muryar yah jahid yan cewa abude mota,kilan shine yatareni. Motar aka sakani sannan nafara gawowa natsuwata,ina hango jirgin ya lula cikin sararin samaniya,wani kuka ne ya kubceman mai rikitarwa,na dunkule waje guda inayin abuna.........Anty ce tarungumoni jikinta tana lallashina, "Kiyi hkr mana ance makine yatafi kenan,duka wata nawane in Allah yakaimu." Jinai yah jahid yace"nima cikin satin nan zantafi ai." Cikin rudewa tace"rufaman asiri kabari idan anyi auren saimutai duk inda kakeso,amman wlh banda yanzu azan iya jurewa ba." Murmushi yayi yace"to taya kike tunanin ita zata iya jurewa,kinsan irin d'acin da takeji cikin zuciyarta kuwa." Daina kukan nai don inason tabbatar wa shin dagaske auren za,aimun don maganganunsu sun nunaman cewa ansan da kaunarsu agida. "Anty,wai dagaske aure Abbu zaiman." Kallona tayi tace"ina kiji maganan nan,bacin anhana kowa yi maku ita." Jinai wani kullutu yazo man wuya ya tokare,shiru nai ban sake tankawaba. Don wani abun yafi gaban kuka sonake naje naji shin dalilin dazaisa atsigeman karatu ayiman aure,bayan ni nace baso banasoshi yanzu abarni nayi karatuna mana,wallahi duk wanda yayi dalilin wannan maganar Allah ya isarmu. Muna isa gida afusace nafito na wuce bangaren maah,bata nan na zube kan gadonta ina sharar kwallah jinake kamar nayi tsutsuwa na bishi,wani irin yanayi nake ciki rashisa yafi mun ciwo matuka akan auren da akece za,aimana,jinake banda wani sauran farinciki ko annashuwa akan tafiyarsa,duk wani feeling's dinsa danakeji ada can baya,na yanzu yalinkashi goma kirjina nakejin yana mun nauyi,jinake bazan iya kaiwa har wannan lokacinba,wata hudu koma fiye dahaka wannan abun danake ciki zaibarni kuwa. Maah ce tafito daga bandaki tayo wanka,kallona take yi batace komiba. Ina ganinta natashi na fada jikinta narushe dawani irin kuka mai tsananin cin rai.............bata kokarin lallashina ba kuma tabace mun komiba yinake yi har inajin kamar numfashina zai dauke,cikin kukan nake cemata"maah Meysa zaki yarda aiman aure nan,maah kinfi kowa sanin banso ni banso karatuna nakeso ayazu nakeson aurenba,maah wallahi in akayishi zanshiga wani hali kitai amakeni,kiyiman rai............rungumeni tayitsam jikinta muka kara sa saman gado da ita sai lokacin tashiga lallashina, "Ya isa haka kidaina kuka,inkinason nayi maki bayani idan kuma bakyaso to kiyita kukan." Dole nayi shiru ina sauke ajiyar zuciya sai shan majina nake,shiru duk mukai ina sauraronta. Cikin taushin murya da lallami tafara man bayani. "Bayan tafiyarki makaranta kinkoma hostel,zuwan inna gidannan yafi biyar tana zuwa wajen mahaifinku bai dawo ba,bayan yadawo tasake zuwa muna tare lokacin ko ansa gaisuwata bataiba,take yiwa Abbunku magana akan tana bashi umurnin cikin wata uku ya aurar da duk yaran dake gidannan,don salma taje tasameta akan cewa itafa batason karatu,aure takeso kuma wanda takeson ni nahana shi ya amunce da ita,ina son dole sai nabashi aurenki." Anan tasan cewar Areef banau bane,tayi fada tatashi hankalin kowa agidannan,har takecewa sai yabar gidan tunda bana uban shi bane,wallahi idan baibar gidanba saita tsinema mahaifinku. Ananfa shima yanuna mata nashi b'acin ran,yace Areef bazai tafi ko inaba shine ubanshi har duniya tatashi. Tace to kuwa wallahi zaiga bacin ranta kuma muddin bai aurar dakuba tasan matakin da zata dauka akai,kuma wallahi muddin tana raye cikin ku jikokinta babu wacce zata auri Arref,. Anan nace ta kwantar da hankalin duk cikin yarana baida mata,domin Areed dana nacikina nake kallonsa,yayansune shi tsayyae kan lamuransu,nan tace naimata rashin kunya ke tashin hankali babu kakkautawa,saida ker Annie tafiddata gidannan. Ranar salma bata kwana gidanba don wallahi nai alkawarin tashigo hannuna sai na lahira yafita jin dadina,bayan wannan yawuce Abbunku yazaunar dani mukai magana kan issue din,cewa salma fa ta dge akan muddin bata samu Arref ba to kuwa babu wadda zata zauna dashi,kuma Khairat bazata zauna lafiya dashiba,don wannan tsoron dakikemai salma ce takai sunanku wajen malamin zaure,akan ya shiga tsakaninku yamaki tsoronshi,yafidda maki duk wani yanayi da soyayyarshi cikin ranki,kinji dalilin jin tsorsnki. Abbunku yaje yayi bincike sosai yagano hakan daman ni tun tana nan gidan nalura da ita,bandai cewa kowa komiba. Anan dai yace mun kowacenku bazata aurai ba kuma aurar daku shine yfiye mashi kwanciyar hankali,yanajin tausayinki don yadda yaga kinason karatunki yanajin takaicin tsigeki yayi maki aure. Amman Baida mafita sai wannan,da har yace akwai yaron abokinsa zai hadaki dashi,to kwatsam saiga yayanku yazo yake sanar da Abbun cewa ai kinada ma wanda kikeso karyayi maki wannan auren nahad'i............Saboda son da areef kemaki yasa Abbun ku canza ra,ayi kan hakan,yace zayi bincike akanshi kuma yayi ya tabbatar da natsuwarshi da gidansu,." Zuwa yanzu idona yabushe saidai wani irin masifar zafi dasukeman,zuciyata duka kurun take nace"maah wallahi ni bason shi nakeba kawai mutunci yakeman saboda yasan ni kanwar yah Areef ce baice yana sona ban." Kallona tayi yace"nasani khairat,duk abunda kefaruwa yayanki ya gayaman,yaban shawarar kuma data dace dake." Kallonta nake cike da mamaki "wace shawara ken maah." "Yace in tsaya tsayin daka don ganin kin auri Dr,domin hakan shizai kawarda tsananin kishin da salman keyi dake,hakan zai dauke idonta daga kanki tabarki kiyi rayuwarki cikin aminci,saboda yanzu ta hakura dashine saboda tasan kema bazaki samaiba. Saboda Areef yatafi kenan harsai anyi aurenku kuntare kozai dawo,don haka kiyi hkr kiyi hkr kiyi hkr khairat,duk abunda yau kaga kanata haukan sonshi baka samaiba to Allah yasan hakan shine alkairinka,bansan dalikin dayasa Allah yasa lamarin yazo ahakaba,nidai nasan zabi nabashi kuma wannan shine zabindaya bamu nidake,don bantaba hutawa ba wajen yimaku adduar samun abokan zama nagariba,don haka karki bani kunya karkibiyewa zuciya takaiki tabaro kirungumi kaddararki hakan shine Alkairinki." Shiru nai narutse idona ydda nakejin kirjina yana suya injin bakina yana d'aci,yasa nakama ambaton sunan Allah,ina karanta hazbunallahu wani imal wakil. Munfi minty talatin shiru babu maicewa komi,sai lazimi nake ita kuma tana shashshafa kaina har naji abunda ya tsayaman ga makwogworona ya rage kaifi. Nace"ita salmar waza ta aura maah." "Wanine d'an uwan mamanta,sun ma daidaita kansu dazu fadan dakikaji Abbunku namata kancewa ita bazaitayi karatuba ne." "Ita ma Antynku ai sun daidaita ita jahid,abun yayi man dadi sosai,da ace yayanku zai yarda sai y auri meenah." Saboda bugawar da zuciyata tayi yasa dole na rutse ido. Tacigaba dacewa"amman bazan masa tutsuba nabarshi ya huce daga rashin samunki,sai yanzu nasan bankyaita mashiba khairat saboda tunfarko bak'inki yakeba saboda ni yakoyawa kanshi shamaki mur,baya wasa dake bayan yanayi dakowa,yanayine don kema kicire abunda keranki akanshi,yana ganin idan kunmani biyayya zanji dadi. Inason Areef saboda biyayyarshi gareni,indai zanyi farinciki tokuwa komiye zaiman,zanyi kewarshi sosai dalikin kukana kenan dazun,don nasan wallahi bazai dawo don yanzuba,nakira yaya hafsa nayi mata bayanin komi takuma fahimceni,nace tayi kokari bayan bikinku ta sashi yadawo,takuma tabbatarmun da hakan." "Ya matsayin karatuna yanzu kenan." Ajiyar zuciya tayi tace"yananan,kuma kobayan anyi bikin zaki cigaba insha Allah,ai muhammad bazai hanaki karatunkiba kiyi kokri kiyinashi biyayya kikoyama kanki sonshi,nasanma zaki soshi don yanada komi da yadace asoshi. Anty shida tashigo mun da abinci,don sai yanzu natuna da ashefa ko break banba,tashin hankalin danake ciki yadanne yunwar danakeji,dukda haka wanda naci baia yawa wanka nai nazo nakwanta daker nsau bacci. Karfe shidda nayi shirin komawa school,gaba d'aya bana cikin yanayi najin dadi,xuciyata ciwo take anya zan iya jure rashin yah tare dani,wai wannan wane irin lamarine,yah Allah kaine ka halittamun wannan zuciyar,kafini sain halin data keciki ka kawo mata agaji.........basan ta yadda zan sarrafa taba goge kwallana nayi bayan nagama shiryawar,fitowa nai na samu duk suna falo,wajen Annie naje narungumeta naji kwallah sun cika man ido,nai saurin sharewa nace masu zanwuce. Yah meenah tace"saina biyoki gobe,munyi magana da dady ya amunce saigobe idan nagama shiryawa zakiganni,koma kibari mutai tare." Murmushin dole nayi nace"inada class karfe takwas,bazanso nayi missing ba,saboda lecture tana da muhimmanci sosai." Jinjina kai tayi tace"da kyau DR KHAIRAT anason irin haka." Duk dariya sukai Anty tace"dr dama wlh inason inganki,tashi nai banda lfy kozaki dubani." Dariya ma tabani nawucesu suna ta dariya,nalura sosuke su rageman radadin da nake ciki. Jikkata na dauko nafito nacewa maah"maah don Allah aban mota hakanan wlh nagaji da yawo kan taxi." "Kibari kiyiwa Abbunku magana idan yayarda sai abaki." Sallama nai dasu nafita saboda tunani bansan ma nazo bakin titiba,haka dai na isa makarantar husna bata kai ga isowa ba,zubewa nai kan katifarmu nahau tunanin dai da yanzu nasan mun kullah kawance dashi. Saidai a class muka hadu da Ita,tace shigowarta kenan wlh da bataso dawowa ba don dai tanason taji yadda akecikine. Ganin yadda idona yayi raurau zanyi kuka yasa tace"aa karkiyi anan bari agama komi kenan saiki gayaman." Ranar ba komi nagane ba sosai amman inayin bakin kokarina ganin nafahimta,don akan darasin zaimana test gobe. Koda muka koma hostel kuka na naitayi sai daker na iya gaya mata duk abunda kefaruwa,ina kuka ina shashsheka ita kanta saida tariga kwallah,rungumeni tayi tashiga bani hakiri,kamar yadda maan tayi,don yanzu babu wata mafita data wuce hakurin. Wannan dare ban iya samun bacci ba,har garin Allah yawaye sadda za,ace rana tayi wani mugun zazzabi yasauko man,har wata makerketa nake,hakorana suna gugar juna.......duk inda hankalin husna yake yayi masifar tashi,kuma na hana ta takira wani dan gidanmu......karshe dai saboda dole gida nakoma saboda ciwon yaki sauki,zuciyata ciwo take babu kakkautawa saida na dangana ga asibiti,kwana na biyar cikin kwanakin nan kuwa Dr mk zaruarshi bata kilguwa safe rana har da dare ma zaka ganshi,har mahaifiyara yakawo tadubani. Saida nakara kwana biyu aka sallaman. Mrs bb ce👌🏻 [6/9, 7:32 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 *ABIN CIKIN RUHINA* Written by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name. Humaira7531 DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *GODIYATA GA MASOYANA BATA DA IYA KA,SAIDAI NACE MAKU ALLAH YA BIYA MAKU BUKATUNKU,HAKIKA BANDA KAMARKU INAMATUKAR ALFAHARI DAKU.* LOVE U SAHIBA TA ALLAH YA RABA LFY😉💕 28. Gida na koma bayan an sallaman,don maah kin yarda tayi danace abarni makaranta na samu sauki,wai ita aa tafison ina gabanta har na idasa wartsakewa. Yah meenah kamar ita ke ciwon duk tabi ta damu,kin komawa tai hostel wai saina warke mukoma tare,Abbu kanshi yashiga damuwa matuka inhar yana gida yini yake zarya dakin maah yana dubani,in yatadda ina bacci zai sunbaci goshina yace"Allah yayaye maki ta alkairi,Allah yana tare dake." Cikin ikon Allah nasamu sauki sosai,har nakan fito falo adanyi fira dani,sabanin kwanakin baya da ko magana banson yi,kuma banson aiman,don idan aka cika man magana zan fashe maka da kuka,dole suka kyaleni amman yanzu ni da kaina nake fita can. Dr yau yace zai zo ya sake dubani,kasancewar yanzu muna waya ba laifi,don anyi komi game da maganar auren mu,manyan shi sunzo anyi komi cikin mutuntawa. Han itama salma nata sunzo duk rana daya za,a daura amman nasu Anty shida ba yanzu ba,yajahid yace ayi mashi hkr sai nan gaba akwai abun da yake maimuhimanci. Nayi kokari matuka wajen ganin na cire damuwa da tunaninsa,amman lokaci lokaci nakan boye nayi kukana don shine abunda zai rageman radadin da nakeji na rashinsa. Na fawwalama Allah komi na anshi dr matsayin mijina,tunda na lura son da yakeyi man maigirma ne,soyayyar sa mai sanyi da shiga ran duk wanda akemawa,hakika nayarda da maganar maahda take cewa ya nada duk abunda za,a soshi,nafarko dr handsome guy ne dan gayune sosai,daga ya nayin shigarsa zaka gane hakan, sannan ma,abocin son kamshine kamar dai yah Areef,don shi kafinma ya iso waje turarensa ne d first dazai sallama wajen,to shima dr haka sannan ga fara,a ban taba ganinsa yana shan murba ko cikin aji fuskarsa asake,baza kace yana dariya ba kuma ba zakace yana shan mur ba,kadaran kada han,ya iya barkwaci,duk yadda kake cikin bacin rai zai iya saka ka dariyar dabaka shirya ba. Dr Ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin ya daidaita natsuwata,nadawo cikin hayyacina shiyasa maah takejin dadi duk randa yazo,itace hada wannan itace hada wancen,haka Annie kai duk yan gidanmu kowa yana son dr sosai,amman banda salma don har yau salma bata shiga sabgar kowa. KO Ameer dinta yazo babu mai wani rawar jiki,idanma ya samu gaisuwar kirki wajen yan gidanmu,saboda shima halinsu guda da ita,daidai gwargwado maah tana kwatanta adalci tsakaninmu duk da cewa ba itace ta haifeta ba,amman duk abunda ta siya man to zata soya mata itama,saboda tace har gobe salma diyace wajenta haihuwarta ne kurun ba taiba,don haka zatai mata duk abunda uwa take ma yarta. Duk da wannan abun bai saka salma taringa gaida maah ba,bata gaidakowa yanzu,har gara idan yah shahid nanan zai ci ubanta yace kuma sai ta gaida duk wanda ke saman ta,duk randa akai irin haka bata kwana gidan sai tayi tafiyarta gidan inna,wannan abun da ta keyi ya kara sakaman salma tafita raina,don duk wanda bai girmama mahaifana ba nayi dashi. Abbu duk yasan wainar da ake toyawa baidaice komiba,don inajin inna tayi kalami mai kaushi akan salmar,bansan dai me tace mashi ba. Rannan Abbu yazo har dakin maah yayi man ya jiki,ya saman ina bacci hirar su ta tadani,sai ban nuna na tashin ba,naji maah tana mashi complain din salmar yace"saudah,kiyi hkr kibar yiman zancen yarinyarnan,tunda kinsan bazan iya yin komi ba,akan kunnenki inna tayi man Allah ya isa idan na sake takurata ko nayi mata wani abu daya bata ranta,kibarta tayi duk abunda ta ga dama kowa rai yaima dadi baya ga maishine,Godiyar danake ma Allah daya bata miji daidai ita,munanan daku Allah shine zaiyyi maganinta." Maah bataji dadi ba tace"karkayi mata baki Dear,hannunka baya rubewa ka yanke kayar,ya kama ta kayi mata addua kurun." Murmushi yayi yace"hakika samun mace kamarki mai tsarkakakkar zuciya sai antona,Allah yai maki Albarka Addua kuma ai tunda aka haifeta nake mata ita,don haka kifita batun salma karki ma sama ranki damuwa." Hakan baisa maah ta daina duk wani shiri ba akan bikinmu,wanda yarage sauran sati uku. Halin da ake ciki kenan. tunda yah yatafi baya waya dakowa sai maah da Abbu,kilan kuma sai yah jahid. Sau daya naji sunyi waya har take gaya mashi nayi ciwo har nakwanta asibiti,sanda na same ta suna wayar zama nai kusa da ita nace taban mugaisa. "Tace ga shima zata gaidaka." Sai cewa yai Kyaleta maah kidai ce inamata yajiki. Wannan abun ya tsaya man garai ranar yini nai in kuka kamar bazan kai ba,sai daker na samu kaina. Tunda na sanar da maah cewa dr zaizo taita shige da fice nidai iyakata shirya kaina idan yazo,babu laifi dr ya samu gurbi cikin zuciyata,saidai gaskiyar magana soyayyar da nakewa dr ko kwata kwatar wadda nakewa yah Areef bata kamoba,saidai inayin iyakar kokarina naga nanuna mai tawa soyayyar,kuma hakan yana matukar faranta mashi. Zuwan husna uku gidanmu dubani,saida nayi yadda nai na had'ata da yah shahid har naroki ya maidata makaranta,to sonake na koma naji yadda suka kare don naga tunda ta gaida shi naga yaki tashi daga falon,yana satar kallonta nasan sai wani abu yabiyo baya. Wanka nashiga ganin yamun text yana hanya,inaji maah tashigo tana fad'a "kullum sai kinga yakusan zuwa zaki tsiri wankan iskanci,kiyi ta shegiyar nawa kishanya bawan Allah yana jiranki,wallahi kishiga taitayinki kafin wata tayi maki kafa." Dariya ma tabani ina shigewa kurun bance mata komi ba,maah nason dr sosai,tana son aurena dashi. Yah meenah tashigo kirana lokacin ma nake shafa mai,itama fadan tayi man wai ina gasa shi dayawa,don naga yana sona sosai. Murmushi nayi mata kurun,don danayi magana zatace nacika gardama,ita tafiddo man kayan dazan saka,riga da siket sunyi mun kyau sosai,kasancewata mace mai dirarran jiki tako ina jikina adire yake,don namafi duk yan matan gidanmu kirji masha Allah,don cib da cib sukaiman,salma kuwa saita had'a da breziya mai soso. Hips dina shima daidaidani baiyi yawa ba haka baiyi kadanba. Itace tayi man d'aurin kallabi don yah meenah gwanace indai nan bangaren ne,gyale kalar kayana ta fiddo man sannan tafesheni da turare maishege kamshi,sanna taja ni muka fito falon bakin dake bangaren Annie,don acan ta saukeshi saida taga shigata takoma don kawo mashi abun tab'awa. Tunda nai sallama ya mike yana wani irin killer smile,ya saka hannayenshi cikin aljihun wandon jeans dinsa,ya karkace kai kallona kurun yake babu kakkautawa. "Wow wow my princess,irin wannan hadewa sai kija miyauna yayita zuba babu kakkautawa." Dariya nayi ina sadda kaina don dr badai sakin layiba,isowa yayi gabana yana bude duk hanayenshi,kallonsa nai ya daga a gira yace"yes come in" Girgiza kaina nayi ina murmushi"Aa nagode da tayinka bismillah kazauna." B'ata fuska yayi yana zama saman hannun kujerar danake"bakison welcoming dina ko princess." "Aa ba haka bane kabari irin wannan welcoming din sai munje can sainayi maka amman pls not now." Gyara zaman shi yayi yana dubana cike da so, "Dagaske." D'aga kai nai murmushin yasake yi yace"karkisa inje in samu Abbu ince pls Abbu amaido daurin auren nan gobe ta alkairinka tayi man alkawarin something sweet nikuma bazan iya jira har sai nan da 3week ba." Dariya yaban ganin yadda yake maganar cikin karya murya kamar mai shirin kuka., Dariyar yake taya ni yace"wallahi kin iya dariya rannan nace ki koya man kika kiya ko." Yah meenah ce tashigo hakan baisa ya tashi daga inda yake ba,saima murmushi yake yana yimata sannu. Tana fara,a tace"yah muhd sannu da zuwa." Cikin sakin fuska yace"yawwa Anty Meemah sannunki da kokari,kina ji dani kullum bakya gajiya." "Wallahi babu komi ai kai nagida ne." Nan fa ya samu yar tayin surutu,don dr akwai zafin surutu saida tayi daker ya barta tatafi. Jiyo wa yai kaina cikin salon kauna lemu ya zuba ga cup yanufo bakina,dole na bude na kurba har shatin jan bakina ya fito........saida yalashe shi tas sannan ya aza bakinsa wajen dana sha,kunya ta rufeni duk da bayau yafara irin wannan abunba. Nayi serving dinsa komi yadda yadace sannan nasauko kusa dashi k'asan don yace yafi jin dadin zaman kasan,yadanci yana jana dafira yaudai duk karatu yafi yawa. Ya jima sosai don nan yayi sallar mangaruba,har suka gaisa da dady da Abbu.najashi cikin gida suka gaisa da maah,har ya ajiye mata rafar yan dubu guda gabanta. Sanda na rakoshi salma tadawo daga rakiyar Ameer don yau yazo,ko kallon inda muke batai ba ni kunya ma naji don saida yace"kamar salma ko." Yake nayi nace "itace" Bai sake cewa komiba Har bakin mota na rakashi yabude baya ya miko man wata leda, "Turarenki yana burgeni ummlkhair,kamshin sa yana sakani shauki matsananci,pls matso na sake jinsa." Matsoni yayi sosai har numfashin mu yana haduwa,dandanan naji tsikar jikina tatashi,sunkuyo da kanshi yayi gefen wuyana ya sauke numfashi mai zafi,saida na runtse ido, nai saurin ja baya. Rungume hannuwa yayi yana kallona da idonsa daya canza yanayi,wani abu nakejin yana shigata bansan komeye ba,kauda idona nayi. Yace"pls just a kiss." Ba arziki na Ruga nabarshi, don wallahi idan natsaya dr yau saiya tsotse man baki,har mamakin sa nake soyayyarsa dandanan take shigar mutun,ya iya tafiyar da ita yadda yadacesaidai idan kabiye zuciya taufa tuni zaku canza ma soyayya mazauni. Mrs bb ce👌🏻😉💕 [6/11, 12:28 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED BY ZAUREN MRS BB _SABODA KAUNAR DA KUKE MAN YASA ZANYI UPDATE YAU,DON DA SAI GOBE INA ALFAHARI DA KAUNARKU DA ADDUOIN KU ALLAH YABAR KAUNA_ 💕💕😘 Not edited. 29. Washe gari mukai shirin koma wa school,nasa rigima dole yah shahid zai kaimu don inada wani plan..........saida yabiya damu mukai shopping sosai saboda semister mai tsawoce,duk da dai Auren yakusa inso samuna nane abarshi nagama aji ukuna,sai ayi lokacin mana cikin hutu,zan ma dr magana yayi wa su Abbu magana abarmu mukarasa wannan semister. Hira muke tayi yana taya mu,ahaka har na sako batun husna inacewa. "Wallahi yah meenah ban tab'ayi kawa irin Husna ba,tana da kirki ga kokari,kisan idan akai abu class tasan ban ganeba muna dawowa hostel mungama duk abunda zamuyi zata ce inxo muyi bita.....bata barina har saina gane,ina sonta sosai gashi akwai natsuwa." Ina maganar ina satar kallon fuskarshi murmushi yake amma baice komi ba,nace"yah kaima ai ka lura da haka ko rannan daka sameta gida." Shan mur yayi yace"don ubanki zama zanyi inta kallonta har naga wani abu tattare da ita." Shiru nai ina kunshe dariyata yah meenah na tayani, Sai kuma yace"kawai dai tana da tarbiyya akwai girmama nagaba." Dadi naji ya kamani nace"sosai kuwa wallahi husna tayi,shiyasa cousin dinta dake sonta yake bala,in jida ita bayason kowa yana rab'arta kishinta yake sosai." Kallon fuskarsa nayi naga dandanan ta canza yah meenah banda dariya babu abunda take,ni kuwa na sha mur irin dagaske haka maganar take,bacin karya ce kurun na shatata don ingane yana ciki ko haukana nake. Bai sake ce mana komi ba amman yanayin sa gaba daya ya canza,magana zan ciga gaba dayi ya dakan tsawa dole naja bakina naguntse,banji haushiba nasan kishine yake damunsa dadi yakamani na kaga mu isa in fesa mata albishi. Har bakin get din hostel ya kaimu muka tsaya fiddo kaya,don suna da yawa saboda kayan yah meenah. Kin tafiya yayi yana ta danna waya,zuwacan yace "kikirata ta taya ku daukar kayan mana." Wayyo dadi haka naji aikuwa nai maza na shiga contact dinta na danna mata kira. "Besty nah gamu bakin get pls kizo ki taya mu kwasar kaya tare muke da yah meenah." "Besty ina hangenku ganin bayanku yanzu nadawo daga cefane bari in karaso." Dadi kamar yayi yaya dani don inson wannan kaunar ta jone, Kamar wasa sai gata sai fara,a take tunma kafin ta san waye amotar, "Yah meenah oyoyo,wallahi naji dadin zuwanku zaman nika dai ya isan,kewa tayi mun yawa." Rungume juna mukai ina mata oyoyo. A kunne nayi mata rad'a nace"kalli gefenki pls." Juyawa tayi ta ganshi zaune cikin mota,kirjinta yabada rassss duk ta diririce daker tace tana yar fara,"yah shahid ur welcome." Dagowa yai ya kawata fuskarsa da murmushinsa mai kyau yace"Asma,u ykk ya makarantar." Tana wasa da hannunta tace"dasauki makaranta yah angode Allah." Jinjina kai yayi yace"Allah ya bada sa,a ga friend dinki nan na maido maki na fita ko." Dariya tayi kadan ta kalleni na kashe mata ido guda tace"ka kuwa kyauta wallahi thank you." Murmushin yayi mata yana tada motar, "Ga wannan akara kudin siyen garin rogo." Dariya tayi ta ansa tana godiya tace"ai mu bama cin irin wadannan yah mu fa inkaga dish din damuke ci zakaso kazauna dakinmu." Yana dariya yace "ok zan gani wataran zan maku shigar bazata." Matsowa mukai muka mashi sallama yayi mana jan hankali kan karatu sannan yafita. Ihun murna nake harda taka rawa,bada dariya babu abunda suke man har mukaje daki............nan fa na sata gaba da tsokana badai tace komiba wai kunyar yah meenah take, "Nace bur wallahi lallai kin ma daina wallahi,wai besty ya kuka kare rannan." Mikewa tayi zatabar dakin nai saurin rikota, Yah meenah tana dariya tace"husna ya haka mun zama daya fa ki bar jin kunyata ni banajin taku,inkuwa haka ne daki zan canza." Dole ta dawo na matsa mata saita gaya man yadda sukai. "Wallahi besty kinfi ciwon ciki katsawa,bafa wani abu ya faruba kawai ya na ta jana da firar school ne tare da cewa kardai na biye samarin makaranta su hanani karatu,shikenan fah." Murmushi nayi nace"soon zakiji ya kiraki yana cewa Asma,u in bakeba sai rijiya mai kwalabe." Gaba daya muka saka dariya,tun tana nokewa taki sakin jiki da yah meenah har ta sake,ranar munsha fira don babu mai lectures cikinmu sai tomorrow morning. 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 A hankali rayuwar take gurgurawa har gashi fara shirin exams,saboda nayiwa dr magana yayiwa Abbu magana yabarni na gama aji uku na,ya kuma yi mashi yayarda ga shirye shiryen biki ga na exams,dole dr ya hakura da takura man kan kira da kuma zuwa,don ma ba sosai muke haduwa ba ko acikin schol din. Saidai koran weekend yazo ya dauke mu muje yawo da shopping. Duk abunda nakeyi ba wai na mance da *ABIN CIKIN RUHINA* ba ne Aa babu second ko awa da zuciyata bata bugawa dashi,daidai darana guda bai tab'a barin zuciyata da *ruhina* huta wa ba,banda wani abun tunawa dashi,illa kalaman sa na karshe nidashi airport. _ina maki fatan Alkairi matar muhammad kaseem,sai wata rana bazaki sake ganina ba,kiyi hkr dani mun haramta ga juna har abadan,domin bazan iya karya wa maah Alkawarin taba,zanje nayi jinyar zuciyata kikula da kanki And plsss forget About Areef farouk,good by ummulkhair._ Wadannan kalaman sun zamar mani kamar fatiha cikin sallar farillah,duk daren duniya sune suke amsa kuwwa cikin kunnena,juriyace da karfin hali kawai suke rike dani,don nayiwa Abbu Alkawarin hakuri da kaddarata,yace man na tai makeshi karya rasani,in nabiye shiga damuwa komi zai iya faruwa dani,don ciwon zuciyata zai iya tashi kuma likita ya sanar da su cewa inhar nasa ke irin wannan kwanciyar,komi zai iya faruwa dani don haka inyi hakuri kowa da kalar jarabawarsa ke kuma taki haka tazo,don haka ki yi wa Allah godiya tare da kokarin ganin kin cinye jarabawar. Kalaman Abby kenan ranar dazan dawo makarnta,naji nasihar sa sosai don inason Abbu na ba zanso ya shiga wani hali ba saboda ni. Zuciyata ta azalzaleni akansa har nakusan shiga wani yanayi,kalamnasa da ya gaya man ranar kafin mufita mota sune suke tunzura bacin raina,har ma inji to miye na kwallafa raina dashi tunda koda babu dr nasan yadda ya fadi kalaman hakan nanufin nai mashi kadan. _k'wailaye daku berori da bakusan kanku ba._ Wadannan kalaman sunfi komi kona man rai,har nakan kalli kirjina dake cike masha Allah,wanda nasan idan za,a tara mata goma cinkinsu da wuya asamu biyu masu irin breast dina,shine yake ceman k'waila,to nayarda dai salma k'walarce Amman ni wallahi ba ita bace. Haka dai nake ta abuna abu wanda yasan halin nake ciki,illah yah meenah da besty husna. Suma ba suda abun yi man face lallashi da ban baki,insuka na yini daki ko lecteres ban jeba nakicin abinci sosai sun san abunne ya tukoni,zasuyita lallashina suna gaya man kalamai masu kwatar da hankali,sai inji nasamu natsuwa. Rannan dai nazauna nayi wa kaina karatun ta natsu,nace shifa wanda nake wannan haukan donshi yana can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali,wata kila man ya shafe babina ya bude wani sabon shafin,kilama yayi budurwa ko ince yayi yanmata don nasa shi gwanin farin jinine akansu. Tunda natuna haka nacire ma raina yah Areef,ganin gamai sona kamar yayi mani sujada saboda tsananin kaunar da yake mani,to akan me zan dorama kaina damuwar wanican da ko kirana mu gaisa baiyi,saidai najishi suna waya da yah meenah amman ko agaidani baicewa,to kan wane dalili wata jotter ta sabuwa da ban fara komi cikin taba nayi rubuta kamar haka. *_NI UMMULKHAIR FAROUK,NAYI ALKAWARIN SHAFE BABIN SA CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN MAN TASHI CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN DAINA YIN CIWO SABODA SHI,BAZAN SAKE SAKA YAN UWANA DA IYAYENA CIKIN HALIN DAMUWA BA SABODA SHI,ZAN FARA SABUWAR RAYUWA DA MASOYINA KUMA MIJINA INSHA ALLAH._* na jefata cikin tarkacena ban sake bai takan taba,don promise ne bazan karya ba zanba marad kunya inaha Allah. Cikin yardar Allah muka gama exams,kuma muduka muna fatan samun sakamako mai ktau,daga wannan hutunne zamutai pratical sai munyi six months sannan mudawo makaranta. Shirye shiryen bikinmu ake babu kama hannun yaro,duk kullum husna nagidan mu sai dare yah shahid yamaida ta,kasancewar yanzu babu laifi sun saki jiki dajuna amman ban tunanin yafurat mata yana sonta,suduka dai idan kagan su tare kasan akwai soyayya mai karfi,amman kowa jinkai dajan class ya hanashi,amman inanan ina hada masu tarko sai yah shahid yafurta da tsiya ma bada arzikiba. Mrs bb ce😉👌🏻 [6/12, 6:28 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira753. DEDUCATED BY ZAUREN MRS BB. NOT EDITED. 30 Komi aka sama rana sai yazo,cikin ikon lillahi gashi dai bikinmu yarage saura kwana uku,yau mutanen dubai suka sauka,da iyalanta yah imaran da kanensa saifudden,sai yar auta mimi taci sunan mahaifiyarsu maah watau zahra,u shine ake kiranta da mimi. Ummi kamar ta goyani don tsananin murnan ganina,nima haka nakeji don yinin ranar muna tare da ita,sai jana take wai ina surukinta yazo ya kawo gaisuwa. Nace metake ci nabaka na zuba zaizo,har sata gaji dashi. Wasu irin kayan kitcheen tazo man dasu new moden,kai daka gansu kasan an narkar da kudi waken,kuma abun jin dadin bani kadai ba harda sweetheart dina salma. Naji dadin kayan sosai naita mata godiya, dun gureman kai tayi wai ai miye na godiya bacin hakkinta ne matsayinta na uwa,kuma haka batunta yake saboda ummi na sonmu tana kaunar maah batajin tsadar abu inhar mune zata yiwa alkairinsa. Mimi tsararmuce amman mun dan girmeta da shekara guda,amman inka ganta zakace itace ta girmimu. Don girman jikine da ita sosai,banyi mamakin rashin ganin *ABIN CIKIN RUHINA* ba don daman naji ajikina bazai halarci daurin aurena ba,ganin kamar zanji babu dadi yasa nai saurin kawar da tunanin hakan cikin raina, Dadaddare Dr yazo gaida ummi sai nokewa yake tana masa dariy,don ummi babu ruwanta da jin kunya,maah cema kejin nauyinsa sosai Annie ma batajin kunyarsa sosai. Gida ya dauki harami don yan gidansu Annie sunzo hada hajiyarsu,da kanwarta da yayarta sai hidima ke dasu,dangin maman salma kuwa basu zo nan gidaba sunacan wajen Inna,hakan yafi don sai anyi rigima yadda nasansu basuda hakuri kona kwabo. Gyaran jiki muke zuwa tunda yarage saura sati biyu,shiyasa gamunan ko ince ganinan nayi wata irin canzawa,don salma bansan wace take cikiba,taki shigowa cikinmu ko kadan,itada kawayenta su raihana kurun suke hidimarsu,har kararta nakai wajen Abbu yace in kyaleta tunda ta janye daga gareni nima injanye mata,idan nacigaba da cusa kaina wajenta zata yi kokarin ganin ranki ya baci,nikuma bazanso abunda zai taba rankiba har agama bikinku ta Alkairi. Rungume Abbu nai ina fashewa da kuka,don tun yanzu nafara jin kewarsa inajin sa har cikin kokon raina,yadda yake tattalina yake gudun duk abunda zai shigar dani cikin damuwa,lallashina yake sosai daker nayi shiru. Kallona yake yana murmushi yace"Kinyi kyau ta Alkairin Abbu,Allah ya kawo ranar da ta alkairina tazama babba zata tai gidan miji itama." Sadda kaina nayi inajin kunyarsa. Dagoni yayi yana dariya yace"kiyi man alkawarin kulawa da mijinki da danginsa da yan uwansa abu mai muhimmanci ma ace mahaifansa,don hakan zai kara maki daraja da kima ga idon su da idon duniya,hakan yasaka mahaifiyarki kullum Allah yake daukaka darajarta akan sauran mutane,saboda tsaye take kan dangina da mahaifiyata,sujjada ce kurin bata yi masu,don haka kizama jaruma mai jajircewa acikin gidanta,hakuri shine babban jigo ga rayuwar Aure idan kika rikeshi kingama dacewa,sannan kizama mai rike sirrin gidanki,sirrin mijinki bakomi akeji da bakin matar gidaba,nasihata kenan wajenki ta Alkairi,ubangiji yasaka Albarka acikin rayuwar aurenku,Allah ya kareku daga sharin masu sheri,kiyi riko da Addininki kirike ibada,duk Abunda ya dameki ki gayawa Allah shi zai jibanci ramurranki." Kuka nake don hakika nasihar shi tashigeni,naji duk wata natsuwa tashigan,naji hankalina ya natsu da auren saboda kalaman abbu,yayi man addua ya sakaman Albarka wannan ma kadai ya isheni,don kowace amarya konace budurwa zataso ta rabu da yayenta lafiya yayinda zata gidan miji,su rabu suna samata Albarka. Haka na fito ina share hawayena. Yah imran tunda ya kyella ido yaga yah meenah shikenan ya zama kamar bindinta,saita boye idan zamu fita yo wani abun,don duk ya hanata samun sukuni,ga yah imran badai iya love ba duk yarudar man da yah meenata. Yaune akagama man gyaran jiki,gobene daurin aure,don nidai nace banason kowane irin event,sai angama daura Aure sai ayi dinner gidan iyayen dr. Mun shigo gidan kenan mukai karo da yah shahid,duk ya fita natsuwarsa murmushi nai don duk yau banbari sun hadu da mutuniyarba,kallonmu yai yasha mur. "Ina Asma,u." Da yake sunsan kanun zancen sainai saurin cewa, "Au nafa manta,yah shahid wannan wanda nace maka yana sonta din nan, yah kamal cousin dinta. ya samemu wajen gyara,ana gama mata ya dauketa inajin sai anjima kadan zaka ga tashigo." Gani kawai nai yadafe kai cikin masifa yake ceman, "Donme zaki bari wani yatai da ita wani waje,bayan kinsan amana mominsu tabaki,ehye maza kirata yanzun nan ta dawo." Mimi da yah meenah sabewa sukai suna dariya kasa kasa,don sun san idan ya kama su suna mashi dariya ran sune zai baci. Sake shan mur nai nadanne dariyata nasake tun zurashi da cewa, "Yah nace maka cousin dinsu ne,ansanshi gidansu,ko ita momin nasan bazatai fad'a ba don antsayar da ranar aurensu bayan sallah babba." Wayyo kuzo kuga tashin hankali karara kan fuskar yah shahid, Cikin tsawa yace. "Sa ranar banza da wofi, aure akai masu dazai bita wani waje ya dauke ta ehy,laifin kine da kikajata. maza maza nace kikirata yanzun nan tabaro duk inda take ta dawo,inba haka ba daga ke har itan sai rayukanku sun b'aci." Ya bar wajen kamar zararre. Saboda dariya har duke wa nake lallai yah ya kamu over,haka nakeso daman,dole ya sauke girman kanshi yafurta tunda shine namiji,wayata na fiddo ina cigaba da dariyata nakirata, "Plan dinmu yayi Husna maza kishigo kafin yah shahid yasama gidan nan bom yatashi.....ina dariya." Itama dariyar takeyi tace, "Ganinan tahowa ina cikin taxi,dama nasan za,ai haka saina iso kiban insha." Kashe wayar nai ina dariya sakon dr ya shigo man. _AMARYAR GOBE YAUDAI D'AYA ABARNI NAZO NAGA KWALLIYARNAN DA AKETAYI KUSAN WATA GUDA._ Murmushi nai inatura mashi sakonsa cewa saikazo. Dakin yah meenah nanne madaddalarmu,can nanufa,. Ina shiga kofar falon Annie naji munyi mugun karo da wani abu,har wayana tana faduwa.......duka wanai na daukota ina murza kaina,saidai sadda zan d'ago banga kowaba........kirjina naji yace dammm saboda wani k'amshi da ko mutuwa nai nadawo bazan iya mance shiba,..........bin hanyar nayi da kallo jikina yana wata irin rawa............. Taufah.🤔 Wani irin sanyi jikina yayi kamar ansakani cikin frig,ina waigen hanyar na karasa cikin daki,hayaniyar suce kurin ketashi,daki suna kyalkyala dariya suna maida yadda kai. Kamar wadda akazarewa kuzari da lakkar jiki haka naji,ina sando na shiga dakin ina bin bango. Silalewa nai kasa bakin kofar shiga bayi,wani irin kerma jikina yake...........wayata na ajiye kan madubi babu wanda ma ya lura dani saboda daroyarsu suke suna ta hirarsu. Rungume kafafuna nayi ina dora kaina saman guiyawuna,ina sauraren bugun zuciyata. Bazan iya cewa ga halin da zuciyata take cikiba,runtse idona nayi ina dauke numfashina na wucinngadi kozan daina jin wannan mayataccen kamshin,amman ina kamar ma hade yake da numfashina,duk sanda zan shakesa tare nake jinsu. Husna ce tashigo tana sauke numfashi,duk suka juyo suna kallonta,mimi ce tai saurin jawota "Ya kuka kare husna na matsu inji wannan dramer." Harararta tayi tana dariya yah meenah tace"Ai da kin jima baki dawo ba kilan yah shahid bulala zaisa ya zanemu tas har amaryar." Cu dariyar suke husna tace, "Ina Amaryar take.......shiru tayi ganina zaune bakin toilet na kudundune kafafu,duk wajen suka kalla. Husna ta ajiye jikarta ta iso wajena. "Khairat,meye haka lafiya kike,yanzu fa muka rabu dake awaya lafiya lau,meya faru daga baya." Duk sun shiga damuwa kowa so yake yaji abunda ya saman,taya zan iya yi masu bayani mezance masu,karo nai da wani mai kama dashi,koko kamshin sa naji,wane daga ciki zan fada. Nashiga ukuna miye haka zuciyata ya ina cikin farin ciki zaki yiman haka,gobene fa daurin aurena inkikamun haka kin zalinceni kin cutar dani da masoyana,plsss na rokeki kifitar mun da wannan masifar,bazan iya cigaba da jurewa ba,inason cigaba da ganin farinciki afusar iyayena............ji sukai kurun na fashe da kuka maitsuma rai,suduka duk jikinsu duk yayi sanyi.......don dajin kukan kasan maiyinsa nacikin kunci da damuwa. Mrs bb ce👌🏻 Love u All 💋💕😉 [6/13, 8:47 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. Not edited 31&32 Saida nayi iyakar yina sannan nayi shiru,shigewa toilet nayi nashige cikin ruwan sanyi,ko sirkashi banba,shaya ce keta zuba bisa kaina nafi minty goma haka.........injin karar wayana yah meenah na cewa, "Wannan wankan ya isa haka ga dr nan nata kiranki yanzu haka zowa yayi." Wani kulutu ne ya tokare man ga makoshi,jinai banson ganinsa bana son jin sunansa..........zafin da zuciyata keman harga jikina don wata irin masassara nakejin tana saukoman. Dole na jawo towel na daura nafito,kowace ta kama waya sai yitake......tsaki naja nafara shiryawa. Doguwar rigace nariza nadan shafa lotion,da body spray na zuba abayata har kasa,don inason dogon hijab rayuwata,kocikin lefena da aka kawo akwatinsu daban wajen kala goma shabiyar.......wayar na dauka nafito compound din gidan,motarsa nacan gefe guda kasancewar filin wajen badai girma da fadi ba,mota goma saita shige har asamu sauran waje. Fitilar ya kunna don nagane shine,tafiya nake kaina kasa inajin babu dadi,bazanso yaga damuwa tare da niba don ban san mezan ce mashi ba,dole na kakaro murmushi nasa ma fuskata........ Budeman gidan gaba yayi yana murmushin sa mai kyau,yasha shadda gizner sai daukar ido take. Shiga nai ina sallama. "Wa alaiki salam,gimbiya Amarya da girman kujerarki,Amarya bakya laifi koda kin kashe dan masu gida." Bansan sadda dariya ta kucce man ba yana tayani, Nace"irin wannan kirari haka,karkasa kaina ya fashe sir." B'ata fuska yayi kamar karamin yaro zai kuka, "Ba nace banson wannan sir dinba,nace maki da munbar school to sir ta kare,saidai my only." Murmushi nai ina jin nauyin sunan sosai,shiru nai ina wasa da tsuna da suka gaji da kyau,don mai kunshi musanmman yayar Annie tazo mana da ita,ta zane mana kafafu da hannuwa,sai daukar ido suke. Hannun ya kalla yace"bakiji wani miyau daya wuce man ba,inso samune wannan yan yatsun in tsotsesu." Bansan sadda nasa abayata na boye fuskata ba. dariya yake sosai yana sake karkacewa yana kallona yace, "Aini ban maga kwalliyarba my love,kidan cireman abayar ingani mana,wallahi tunda kikashigo kamshinki yaketa dukan hancina,ni ko wuyanki kibani in shinshina........." Wayyo kunya kamar zan nitse don kunyar kalamansa, Shagwabe fuskanai nace"pls si........" Wallahi dakin ida saina cinye wannan bakin tunda baijin magana. Shiru nai inajin kunyar fadar sunan da ya keson in fada,jinai yace inajinki. "Cewa nai pls kabari inkana irin wannan guduwa zanyi Allah ni kunya kake bani." Juyowa yai gaba daya gabana,ya riko duk hannayen nawa yace"sa idonki cikin nawa,yau kwana nawa rabon dana saki idona,kullum kina man wayau gyaran jiki kike,to tunda angama yau kibarni na mora ganina pls." Ya karashe maganar yana sunbatar hannayen,har wani lumshe ido yake. Wani iri naji don dr akwai iya salon kauna. Jaye hannun nayi inacewa"pls mekakewa sauri gobene fah." Murmushi yayi yace"shikenan,aidai daga gobe andaina man iyaka da halalina." Hira mukai tayi dashi duk wata damuwata dana taho da ita ya kawar mun ita,dr mutunne mai sanyin hali,hakurinsa mai girmane tsawon tarayyar mu ba taba ganin bacin rans ba,ko abu nai mashi na bacin rai bazai taba nunaman ba,zaidai ce kibaryin abu kaza babu kyau. Any time ever moment fuskarsa dauke da murmushi,tabbas nasan na auri dr na gama damuwa,duk irin halin da nake ciki muddin mukai waya or muka hadu ban sanin inda damuwar take rugawa,tabbas maganar Abbu gaskiyace da yace dr shine ya dace dani,nima nayarda na amunce kuma ashirye nake nayi zaman aure dashi mai dadi,nayi damarar faranta mashi har iyakar karshen rayuwarmu. Zamu yi rayuwa mai kyau da yardar Allah,hakika 100% na yarda dr ya zama mijina uban y'ay'ana. 💕💕💕💕💕💕💕💕 *RANA BATA KARYA SAIDAI UWAR DIYA TAJI KUNYA* *RANAR WANKA BA,A BOYON CIBI,ALKWARIN ALLAH YA TABBAT,UMMULKHAIR FAROUK TA ZAMA MATA GA DR. MUHAMMAD KASEEM,TAREDA MATA GA SHAZALLI YUSUFA DA AMARYARSA UMMUSALMA FAROUK.* dubunan mutane da bazan iya kwatan ta maku iyakar adadinsu ba suka shaida wannan Auren,Amare sunyi kyau har sungaji. domin khairat musanman ummi tayo hayar maiyin kwalliya daga dubai,khairat tahadu iyaar haduwa,saidai muce Allah ya tabbatar da Alkairinsa........tunda labarin daurin auren yazo ga kunnena nake kuka,badan komi ba sai don kawai cewar yanzu fa nazama matar Aure,wacce zata tashi daga gidansu zuwa wani gidan,zan fara sabuwar rayuwa da sabbin mutane,shin wace irin rayuwa zamuyi. Shikenan babuni babu zama gidanmu kenan saidai nazo yawo,lallai Aure abune maigirman gaske,kaduba abunda zai raba uwa da yarta yaraba uba da yarsa,wane abune wanan inbada mutuwa da Aure. Ina falon Abbu ankirani na gaisa da bakinsa,nasamu kyaututtuka har basan iyakaba,vanyi zaton friend dina zasuzo ba saigashi harda mazan department dinmu sunzo man daurin aure. Durkushe nake nasha wani dankareren less,sky blue da pink color,nasha takalma na da jikkata duk farare sai mayafina babba da aka rufaman bisa kaina har fuskata.......majina kurun nake gogewa don kukan tunyaa zuwa da sauti har ya barfita da sautin,falon yarage mutane Abbune da daddy,sai maah Annie da ummi,sai yah jahid da yah shahid..............wanine daga can bakin kofar shigowa,takalmansa sawu ciki kurin nake gani farare tasss,tabbas shine yanayin da zuciyatabtake bugawa ya tabbatar mun shine......hakanan banji dadin zuwansa ba hakika rashin zuwansa sai yafimun kwanciyar hankali,domin samun natsuwar zuciyata. Alamu dai ya nuna fada za,aimun salma akejira tun dazun. Abbune yake waya da driver da ya aika gidan inna dauko salam, "Kashiga kace nina turo azo adaukota za,ai masu fada ita da khairat,..........muryar innar mukaji tafito sosai ciki wayar. "Faruku kafita idona,dolene fad'a tace mun tsoron zuwa take kana iya dukanta,to nima na hana anan za,a dauketa akaota gidan mijinta,ruwanka ne kasamata albarka ruwankane ka tsine mata,inace saudah ce mai yinfadan itada yar uwarya,to itama ga nata dangin uwar nan suna mata,bazata zoba." Baice komiba ya sauke wayar,ummi ranta yabaci don daman ummi badai fada ba,inhar akatabota. Yo ba,a tabota din bama wace allah ciki balle antabo........cikin banbami tace, "Wace irin yarinyace wannan kahaifa farouk,ace yau aurenki zakitai dakin miji bazakizo kiyi sallamar mutunci da iyayenkiba,idan ita wannan ta nuna maah,sannan tacigaba idan ita bata haifetaba kai aikaine ubanta,tazo kasamata albarka. Kumaninda kara da mutunci saudah ba itace tashayar da itaba tsawon shekara biyu,tatarbiyantar da ita,amman dayake nonon datasha fitsarar dashi tayi ta nuna maku cewar itafa diyar lantana ce Allah yajikanta,ai saudah uawartace idan tasan kanta tasan mutunci,kuma inna saita biyeta inbacin kurun dama jiranmu take......" Maah ce tai saurin katseta dacewar, "Don Allah yaya kiyi shiru hakanan,kowa yaza ma nagari don kanshi,ni wallahi taje nayafe mata duk abinda tayi man,Allah yasa Albarka cikin auren." Magana zata sakeyi ummin dady yace"pls hafsat abar maganar kaima kuma kayi hkr duk yadda ranka yakai gabaci dole zakayi hakuri kabisu da Allah yabada zaman lafiya shi ake fata,shine kawai." Nanfa suka rufu kaina kowa da abunda yake fada,kukana kurun nake don jinake baza iya barin maah da abbuna ba. Cikin yayyaena akace idan damai magana yayi mani ga mototci can zuna jiranmu. Yah jahid yayi man nasiha sosai akan hakuri,yac"nasanki indai akan nan wajenne to kikara domin zamane baa yauba bana gibe ba,Allah yayiwa rayuwarku Albarka yakuma kareki daga makiya." Kowa yace ameen,yah shahid ma yayi man Anty shidah kiwa kwallah take tayi tama kasa cewa komi,duk ta kwakwumeni,itada yah meenah. Har yanzu yananan inda naganshi,bai motsaba bai kuma tashiba kuma baice komiba, Ummi ce tafita don wasu baki da sukazo mata biki,tare da maah suka fita tana cewa yah imran yaje yacewa masu daukar amaryar sukara hakuri gatanan za,afiddota. Wannan kalamin yasake tunzura kukana har muryata bata fita,sumabyah meenah kukan suke,don Anty shidah yah jahid yajata sunfita. Abbu da Dady daman suma bakin garesu dayawa zasu sallamesu,don yama tayi wajen biyar harda rabine. Husna ce taje tasake tattaro man kayana danayi using dasu,babu kowa dakin dani sai yah meenah saishi dake can zaune har lokacin. Munanan zaune tsawon lokaci banda shashshekar kuka bana yin komi wata irin kewar yan gianuce akejin tana kamani,sonake yayiman magana yakiya,yaki motsawa yaki kallona,yaki zuwa inda nake kowa yana furta albarkacin bakinsa akan aurena,Amman shi ko tanke baice komiba,hankalina bai sake tashiba saida naga ana jana za a fitar daga cikin gidan.......kua nake ina rike Maah da Annie amman babu mai saurarena,Abbu dakanshi ya kamani yasa motar,sanan yashiga gaba dady shike tukamu,sauran motocin suka rufa mana baya.......inaji ina gani nabar gidanmu zanfada wata duniyar daban,bansan kuma wace rayuwar zanyiba........lallashina kirun Abbu keyi har muka isa,baibari nasaka kafata ba saida nayi addua sosai,har yana aranto man ina ansawa sannan adagaafatta dama asakatare *BISMILLAH.* Mrs bb ce👌🏻💕💕💕😘😘😘ina Alfahari daku [6/16, 11:11 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *I need ur prayers Am not feeling fine.* Not edited. 33. Iyayena maza sune suka kawoni har cikin gidan mijina,nayi kuka kuka mai sunan kuka har jinake kaina zai rabe gida biyu,dandanan zazzabi ya rufeni ruf rawar sanyi kurun nake su yah meenah da suka shigo motocin Abokan ango duk sun rude da halin dana ke ciki,don jikina har wani siraci yake fitarwa.......hakika ban taba dauka haka ake jin dacin rabuwa da iyaye ba in aure ya tashi,lallai ajinjina ma Aure. Anty shidah bata kwana ba yah jahid ne yazo ya dauke ta,Husna dai nan zamu kwana da ita da yah meenah.........sauran kawayen mu duk sun tafi gida suna cewa sai sun dawo gobe walima. Ganin jikin nawa yayi tsanani yasa suka kira dr suka sanar dashi,aikuwa sai gashi kamar daga sama duk yarude.......waya ya ciro ya shiga kiran dr su ganin dr baima ganin su yah meenah rungumeni yayi abunsa babu abunda ya damai,dole suka bar dakin suka koma daya daga cikin bedroom dina,don babu karya iyayena sunyi matukar komari,Abbu gado biyu duk yayi mana da set din kujeru biyu,amman ni maah da annie da ummi suka hadu suka kara man kala guda,duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni ganin kyan bedroom din da nake ciki ba. Komi maroom dakin sai walwalin fitilu yake,gadon kanshi cycle ne kuma juya wa yake,kana iya tsayar dashi kana iya barinsa. Abun gwanin burgewa da ban sha,awa. Ina jikinsa nayi lamo sai ajiyar xuciya nake,kaina kurin yake shafawa yana jeraman sannu,tuni dama ya rabani da gyalena.......saida likita zai shigo ya rufa man shi. Dubani yayi sosai yace"damuwa ce da kukan da tasha suka sakar mata wannan zazzabin,da tasha pen relief zai sauka kuma tayi kokarin cire damuwa insha Komi zaizama successful." Godiya yayi mashi ya tafi kwance nake na kudun dune wuri guda,na lumshe idona ina jin kamshinsa kusa dani. Waya yake idonsa akaina don inajin su suna sakani takurewa. "Ummi jalila ta hado abinci maidan saukin ci sai taci kafin a kawo na sauran,eh ummi to insha Allah, jikin ai da sauki gata nan oky to." Ajiye wayar ya yayi yana tab'a goshina........ajiyar zuciya nai yace, "Sorry my dear tashi ga abinci nan sai kici kisha magani,bazan so wannan ciwonba muna tsaka da farinciki,kokin manta yau wace rana ce bari na tuna maki,yau ranace ta farin ciki agaremu da duk masoyan mu baki daya,burin mu ne ya cika na mallakar juna Allah ne ya nuna mana don haka plss my love,ki tashi mu fuskanci sabuwar rayuwa." Sake lafewa nai cikin gadon mai dauke da wata irin katifa mai laushin tsiya. Kofar aka bude aka shigo tare da sallama, "Wayyo Antinmu kina nufin wannan dinner ba za,ayitaba gaskiya kitashi ki wartsake gidan masoyinki fa aka kawoki..........muryarsa cike da annashuwa yace"Jalila kin raina niko." Tashi nai ina gyara kallabina dana rufa ma kaina shi,kokarin sakin fuskata nai nace mata. "Inayini." Dariya tayi tace"lafiya Anti tunda kinbarmun girman." Harararta yayi yaceman "Karki sake gaidata inba haka ba rainaki zatai,kanwarki ce itace zata ringa gaidaki." Murmushi nake bance komi ba, Tace"ga Abinci nan Anty amarya aci awartsake mutai party." "Jalila babu wani party da za,ai matata bata lafiya kibari inkingama ruwan idon zaben saurayi inbikinku yazo saikuyi koma miye ko love dina." Wayyo kunya kamar tasan yadda zatai dani, Sunkuyar da kai nai ina wasa da gefen kallabina. Dariya tayi tace"ashe kuwa zaki sha kunya don bakiga komiba wajen Dr sai ya rungumeki gaban ummi." Zaro ido nai ina kallonta mezasuyi ba dariya ba har suka bani dariyar nima. Mikewa tayi tace"nayi nan amarya Allah yabada lafiya,ummi na miki sannu." Muryata tayi wani irin sanyi sosai nace, "Nagode kice mata ina ansawa sosai." Kallona kurun yake duk naji na takure shagwabe fuska nai nace"plss d........jin lips dinsa kurun nai kan bakina........daskare wa nai kamar nayi kankara saida ya tsotsa iyakar yinsa sannan ya dago yana kallona, Murmushi yayi yace"Aina gaya maki duk randa kika sake ceman wani dr ko sir saina cinye baki,to yanzu ma arzikinki daya baki daafiya da kinsha mamakina tunda bakijin magana." Juya mashi baya nai kamar zan kuka saboda wallahi rashin kunyar dr tayi yawa, "Nidai kadaina bana so." "OK naji wannan juyo maza nabaki inada baki nabarosu ban sallamesuba.," Yada yayi alamun babu wasa dole yasa na juyo yana bani yana man hira,yana gaya man irin mutanen da suka halarci bikinmu.........ashe daman yunwar nakeji sosai don kwana biyu bana cin komi sai dan abu me ruwa,saida yaga ina shirin sheka mashi amai yasa ya kyaleni.........ya sunbaci goshina yace, "Sai da safe ko in dawo mukwanta tare." Jifarsa nai da filo ya cab'e yana dariya yace"ohodai duk wayon amarya sai ansha manta,kishirya gobe anagama walima zanfara kora don nan gidan zanyi magrib." Dalalo ido nai baki bude dariya ya kwashe da ita yafice bayan ya jehoman filon. Komawa nai jagwaf kan gadon,ina ajiyar zuciya tunda nake ba,a tab'aman kiss ba sai yau har yanzu jinake kamar bakin nasa yana kan nawa,numfashi na sauke ina jinjina soyayyar dr,ya iya tafiyar da ita yadda ya kamata.........tashi nai na gama kalle bedroom din sannan nafito na shiga wanda su husna suke ciki ita da yah meenah. Hira suke konace kowace hira take awaya da masoyinta,don yah meenah tuni tayi nisa wajen kaunar yah imran,love kurun suke bugawa mimi ce keta chat tana ganina tarungumeni. "Allah sarki Amaryarmu sannu kinjiko yajikin,yayi sauki." Murmushi nayi nace"nasha magani na samu sauki,kunci abinci kuwa." Tace"yanzu muka dawo daga cikin gidan,munci mun koshi wallahi khairat kinyi dacen dangin miji kowa maganarki yake,yana yabon halinki ki zauna dasu lafiya kinga wai yadda sukaita hidima damu,abincin nan nama yafishi yawa ferfesun naman kai,gasassun kaji,yan ciki soyayyen naman rago sai wanda mutun yaga damar ci.......mahaifiyarshi tana ta tambayar jikin naki." Wata natsuwa ke shigata "tabbas ina fatan hakan ya dore,Allah ya kawar da shedan tsakanin mu nidasu." Tace "ameen muje na rakaki kiga gidanki khairat,wallahi su Abbu sunyi kokari sai fatan Allahb yabiya su." Tare muka fita dayan bedroom din dake tsakiya muka shiga,Italian bed ne golding color komi golding har fentin kanshi,sai daukar ido yake don yama fi wanda aka saukeni ciki,wanda su Husna keciki kuma komi purple ne da dark pink.........palona biyune babba da karami babban set biyu na royel chairs aka saman,karamin kuma wasu kujerune yan gaske har wani malatsi garesu inzaka zauna zaka danna,wanda zai bakujerar wani irin sanyi ni,ima har haske suke fiddawa da daddare.......saboda farinciki har kuka nai ina gode wa iyayena. wani abun mamakin shine wadannan kujerun wai yah Areef ya siya man su cewar mimi. "Bawan Allah gaskiya Khairat yah yayi jarumta yayi karfin hali sosai,kinsan tunda yabaro nigeria yazo nan gida wlh baida lfy in takai ce maki yah baya cin abinci tsawon sati baici komiba,amai dai kurun karshe saida ya kwan ta asibiti,da fadan ummi da hargaginta ya daure ya karfafa zuciyarsa,amman har gobe ke har abadan yah bazai taba son wata mace kwatankwacin wanda yake makiba,ina rokonki kiringa mashi Addua Allah ya sassauta mashi yana cikin yanayi,don baiso zuwa bikin nan ba ummi ce kamar zata cinyeshi danye yasa dole yazo,to gashinan zuwan ya tado aiki don yanzu haka yana asibiti,gobe zasu koma don yaga likitanshi dake dubashi." Silalewa nai na zauna kan kushin din dake tsakiyar babban falona,hawaye masu zafi suka shiga zubarmun inajin wani ciwo cikin zuciyata. Zamatai kusa dani ta dafa kafadata tace"kiyi hkr ban gaya maki bane don kiyi kuka ba ko kishiga damuwa ba,nagaya makine don kisashi addua Allah yaba shi lafiya ke yanzu kinriga kin zama ta wani tunanin wani ma inkikai haramunne,ki fawwalama Allah komi shikadai yasan me hakan yake nufi,Amman wallahi nidai idan nice koza,a mutu sai an aura man wanda nakeso,ni banson irin wannan rayuwar taya Allah bai haramta abuba amman mutane su maidashi haramci wannan badaidai bane,ana shiga hakkin mutane wallahi." Ina share hawayena nace mata"mimi wannan abun babu wanda keda laifi cikinsa saishi,saboda gaban kowa Abbu yake sanar dashi halin da nake ciki akansa,Amman ya sha mur yace wai shi bama ni yake so ba,shibazai iya aurena ba wannan dalilin shine duk ya jawo komi,har mai aukuwa ta auku,wallahi bazan tab'a yarda da cewar ba laifinsa bane mimi,don haka ni kibar ma yiman maganarsa,don nariga na shafe babinsa zanyi sabuwar rayuwa da maisona." Murmushi tayi tace"kiyi hkr Amman wallahi duk duniya inbanda iyayenmu bakida mai kaunarki sama da yahna,ki dauka haka kaddararku take wani baya auren matar wani." Mikewa nai nace "nayi nan inje nai sallah na kwanta goma saura," Biyoni tai tana cewa"karki tsani yaya ba laifinsa bane." Afusace na juyo kanta nace"nawaye inba shiba nace laifin waye,inda yana sona da gaske mai yahana shi furtawa tun kafin atsayar mun da mijin aure,plsss mimi karkija najuye maki haushin da bana kiba,kibarni haka kibarni na jida kuncin da nake ciki ehy." Bata wani ji haushiba don ko itace wanda ma yafi haka zatai,don bata yarda da auren da babu soyayya ba imfact inta sai wanda ma take masifar so yake masifar sonta zata aure.......tace"Allah ya huci zuciyarki nabari,ammafa duk sanda mukai wya dake ko bayan mun tafi zan ringa baki news din halin da yake ciki." Banza nai mata nashige dakin na banko kofa. Mrs bb ce👌🏻💋💕😘😘 [6/19, 12:43 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *Nga sakonnin gaisiwarku gareni Allah yasaka maku da Alkairinsa* Not edited. 34. Alhamdulillah biki ya tashi anyi walima lafiya amarya tasha kyau,anyi hotuna kala kala har kuka nai da su ummi suka zo yiman bankwana........lallashina taitayi tana shiman Albarka nan akabar mimi wajen maah zata kara mata sati biyu,yah imran kamar yayi kuka baison tafiyar,sai tsogumi yake mata har ya kureta ta haushi da fada, dama ummi abu kadan zai tun zurata taita masifa, "Tun yaushe kake man maganar inace maka dan uwanka ne zaiga likita amman kaki fahimta,ko so kake ya mutu anan ne." Hakuri yaita bata don ya manta shaf da batun ganin likitan Areef din. Kowa ya watse dagani sai husna da yah meenah,suna jiran Ango sai su wuce gida. Hirarsu suke nikuwa nayi tagumi,duk na firgice nasan dr bazai daga man kafa ba yau,yadda yake wannan rawar kafar tun kan akawoni abun tsoro yake ban,duk jikina yayi sanyi harga Allah inason dr Amman banson making love dashi,hakanan nidai zuciyata bata son bashi kaina........jinake kamar ace ba yau banezai tare,sai kuma naga ai koma yaushe ne dole zai tare ni nabani wlh bana so. Hawaye na share husna ta ankare dani tayi murmushi tace, "Yah meenah mutuniyarfa da alamu dai atsorace take,wallahi nikaina tausayi take ban,ganin yadda dr ba sauki ne dashiba." Murmushi tayi ta matso kusa dani tace, "Sorry my qanwa,babu fah wani abu idan baki saki jikinki bane zakija har wani abun ya sameki,amman inkin sake lafiya lau dan zafin baida yawa." Kallonta nai idona yana zubar da kwallah nace, "Yah meenah ni wlh banson ya kusanceni kwata kwata,nidai bana so wlh." Ajiyar zuciya tayi tace"bakison shi kenan." Girgiza kai nai "aa ina son shi kwai banson making love dashine pls ya zanyi wlh ina iya mutuwa akan hakan." "Subhanallahi!khairat kina cikin hankalin ki kuwa,kinsan mekike fada,mijinki nefa halal dinshi ce ke komi yayi dake baida zunubi sai tarin lada,kifitar da duk wani tunani cikin ranki kicire son zuciya ki cire wani can kisaka mijinki cikin zuciyarki, Na riga na ganoki khairat kina son ki kaurace ma mijinki saboda wani ko, kiji tsoran Allah. kinsan kuwa tarin zunubin da kike shirin kwasar ma kanki,shi wanda kike shirin yin wannan wautar yayi biyayya ya dauki kaddara saike,kike shirin wargaza rayuwarnki kansa, auren da kwanansa guda,to ki maida hankali,wlh muddin bakiji maganata bakika aikata har wani abun yabiyo baya,wallahi khairat bakina dana Abbu zan fesa mashi komi." Kuka nake ina cewa "Yah meenah ni wallahi badan shi zanba kuma ni bakiji nace zan kaurace mashi ba,kawai na gaya maki abunda yake raina ne,banson kusancina dashi ba kuma don bansonsa ba.....katseni tayi cikin fad'aa. "Dallah can rufe man baki,keda bakida hankali bakida wayau,to inba haka kike nufi ba mekike nufi kenan ehy,so haukane kanki akafara irin wannan,to ki bada himma,shida yake namiji har zai iya danne son da yake maki ya bi maganar iyayensa,saike ce zaki bijire to Allah yabaki sa,a." Ranta yayi matukar baci da khairat din shiyasa ta cewa husna tatashi su wuce,inba haka ba nan zata barta bata ga anfanin zamansu ba. Kuka riris nakeyi ina rokonsu karsu tai amman basu sairareni ba husna dai tace "inyi hkr inyi biyayya,ba kowa yake samun abunda yake soba inkika kwantar da hankalinki khairat zakisha mamakin irin dadin zaman da zakiji da shi,daurewa ake cijewa ake kiyi hkr kiyi biyayya." Inaji ina gani suka barni nan sukai tafiyarsu,haka nasha kukana har kaina yafara wani azabebben ciwo,gawata masassara ta sauko man dandanan..........haka na koma cikin gidan na shege bedrom dina inda aka fara saukardani,kuka nacigaba dayi har baccin wuya ya saceni. *********** 11:00pm. Abokinsa daya tal ya rakoshi shima yana saukeshi yayi masa saida safe yatafi,saida ya shiga ya gano mitanen cikin gidan sannan yadawo,bangaresa daban acikin gidan shima yasha kayan alatu,abun ba,acewa komi murmushi da annashuwa ne kwance kan fuskarsa yana wanka tare da fefdesa turare,kayan baccine yasaka dogon wando mai taushi fari tas da rigarsa itama fara tass......yagyara gashinsa sannan ya dauki wayarsa yanufi bangarenta. Karar wayata ya tasheni ganin sakon husna na cewar sun isa gida lafiya,lokacin karfe goma da rabi kayan jikina na cire na shiga na watsa ruwa,cikin kayana na lefe na lalalubo rigar bacci saisa saisa bamai nuna jikiba,lotion na shafa ina yi ina tunano maganganun yah meenah,tabbas duk gaskiya take fada,kuma insha Allah bazan sake maimaita irin wannan wautai ba,rigar har kasa take nasaka hulata nasaka body spray........daman nayi isha,i sai kawai na kwanta ina tunanin rayuwata...........kamar daga sama naji motsin kofa, Tsaye yake ya rungume hannunsa yana kallona daga inda nake, Sadda kaina nai ina jin kirjina yana duka,isowa yake yayinda zuciyata take kara bugawa.........zama yai gefena yana murmushi sosai har yana fitar da sauti. "Amarya bakya laifi Allah yasa bakiyi fushiba." Kaina kasa ina murtsikar yatsuna, Hannun yariko saida naji kirjina ya buga....... "Sorry my love abokaina suka rikeni,don duk gobe zasu wuce wasu tunjiya wasu yau,fatan zakiyiwa angonki hkr baiyyi d niyya ba." Shiru nai ganin zai jawoni nai saurin cewa"eh eh.....nayi hkrn." Dariya yayi mai kyau,yace"ok love dina tashi muje kitai maka man nasaka wani abu ga cikin nan,don bazan iya tabuka kowa miba inbanciba." Jinai cikina yabada kululululu Jana yai har babban falonmu wajen dinning table,wata madara ya zuba ga cups guda biyu,kakkaurace ban taba ganintaba da alamun ba yar kasar nigeria bace,irin madarar larabawan nan ce. Sai wata kula hadadda cike da gasassun kaji,sai maiko suke ga wani gashin naman harda romo,zuba mana yayi yana ta jana nakasa sakewa ko kadan,haka ya tusani gaba yaringa danna man naman da madarar nan saida nafara yunkurin amai sannan ya kyaleni. Ya cika nashi cikin yajani muka fara zaga gidan,yana sake nuna man komi da hanyar shiga cikin gida wajen umminsa kitcheen muka shiga yace an tanadi komi insakeduba abuna babu zuwa safe sai anemo,komi akwai kaya miyane kurim babu da vegetables,tun a kitchen din yafara canza layi......jikina banda karkarwa babu abunda yake man Amman na dake saboda banda yadda zanyi. Daker na takura mai mukai sallar nafila,munyi adduoi sosai wanda da matsantawa ta akayisu,sannan muka shafa kan nayi wani yunkuri yakashe fitila,ya kunna dumlight........bansan jikina yana karkarwa ba saida najisa yana kokarin rabani da rigar jikina.........tuni dr ya hade bakinmu yashiga wata irin tsotsa kamar yasamu abincinsa..........basamu nasarar kukaba balle roko,ya dad'e bakina gam banda tsotsa babu abunda yake.........wannan dare yazoman abazata konace yazo man ahalinda bana so,bana ra,ayi ban sani ba kodan badashi nakeson kasancewa ba nidai iyakar sanina inason dr,aman banda dalilin dazance donshi ne ban son making love dashi,..........nasha kuka nasha bakar azaba,duk yan gidanmu babu wanda ban kiraba,tundaga kan Abbu dady har zuwa kan salma yau ranar har ita nakira. Abunda nake gudun dai shine yafaru,dr ya mayar da khairat cikakkar mace yayinda yayi man wani irin rauni.......har waye war gari banniya bacci ba,shimfidarmu kamar anyanka karamar dabba awajen,jagejage da jini wani bakin cikinsa da haushinsa ya dirar mun ga zuciyata,dr baisaka tausayi ba kokadan wajen mu,amala dani bai duba cewar nidin budurwace ba,basan komi akan harkar ba hakayasaki jiki ya dirjeni son ransa............washe gari kuwa yan cikin gidansu babu wanda baisan abunda dr yayi man ba,kunya haushi takaici sune suka cike dan gurbin son da nake mashi. Dakin umminsu na koma saboda saida akakira wata dr mace tayi amn dressing.......ita kanta tayi fada sosai taita ban hkr tana tausaya man,nasha kuka har bansan iyakaba nai dana sanin wannan auren yafi cikin duhu,Amman umminsu hkr taita bani tana lallashina tun ina kin sakewa danita har nasake na maidata kamar maah dina,ban sake komawa cikin gida naba inanan wajen umi da su jalila,dayake kannensa duk basu wuce huduba shine babba. Akwai ishaq mai bi mashi sai jalila da fadima sai autansu namiji sadam. Suduka kowa sona yake kowa son faranta man yake,mahaifinsu kanshi kamar ya goyani,amman kunsan ance ba lallai kasamu 100% soyayyar dangin mijiba tabbas wannan haka yake,in wancen da waccen sun soki tofa ba lallai wancen da waccen su sokiba,haka yake kuwa don fadima da wata yar uwar dadynsu ko inda nake basa son kalla........wannan bai damanba ni banma nuna nasan sunayi. Saida nayi sati biyu dakin ummi da dr yashigo zan ruga ina boye,,,idan ya matsanta infito kuka nake samai dole ya kyaleni.......muna waya da mutan gida sosai ba kamar Annie sau uku take kirana,maah kuwa sai daya inma takiranin,Abbu kuwa har gajiya nake da daga kiranshi,yadai ce babu komi ko ta alkairin Abbu ince eh Abbu komi lafiya. Mimi tazo man nan sau biyu kafin tatafi,husna ma tazo itada momin su har take sanar mun ai manya sunshiga maganarsu ita da yah shahid. Abin yayi man dadi sosai nayi mata murna,koda muka shige daki taita kallona wai duk na rame ita da zata zo ta ganni nayi bulbul gwanin sha,awa amman sai ta ganni haka. Girgiza kai kurun nai ina goge kwallah ta nace, "Husna bazaki gane ba,kiyi fatan kar Allah yasa yah shahid yayi maki irin abunda dr yayi man,wallahi husna ko ganinsa banson yi dr bai tausaya man ba ya saki jiki ya faffarkani,dinki biyu akaiman,har yau idan zanyi fitsari kamar zan fasa ihu azabar da nakeji wajen........gashi umminsu ta fara maganar koma wata bangarena wallahi nidai bana so." Kuka na fashe dashi ta jawoni tana lallashina,sosai nabata tausai gabanta ya fadi wai daman haka auren yake, "Walh khairat friends dina da sukai aure ba haka sukaji ba kuma lafiya lau zaki gansu inkikaje har wata kiba suke,amma i wonder na ganki haka kuma naji something like this abakinki." Ina kan cinyarta nace"husna idan kayi dacen miji mai tausayi wanda yake sonka tsakaninsa da Allah na tabbatar maki hakan bazata faruba,duk da maa kowa da yanayin halittar desire dinsa,amman abun ai ba hauka bane,banso fallasa maki ba dole tasa don idanban samu wanda ya lallasheniba bazan iya samun dadin rainaba,ina mamakin yadda dr zaiman haka kofa dan wasannana baiyi daniba taya zanji dadin akin jikina dashi.,,,, Hakuri taringa bani tana kara man kwarin guiwa,da shawarwari masu anfani takuma ce indaure indaina gudunsa babu kyau kua duk randa ummin tace in koma dakina to kar nayi gardama na koma,wannan shine auren kawai dai nasama raina dauriya da juriya akan bukatarsa. Banso tafiyarsu ba haka sukatai suka barni. Bayan kwana biyu ummi da kanta ta hada man kayana muka koma cikin gidana,jalila nata man dariya kamar inyita kuka haka umi ta tusani gaba muka tai. Ranar dr kamar yazuba ruwa kasa yasha don dadi,sai nan nan yake dani sai jana yake da wasa naki sake mashi fuska,koda yafita jinai kamar kar ya dawo. Haka nashiga gyare idan dukda ana gyarawa saina kara,nasaka tiraren wuta na turate ko ina nai wanka nai sallah isha,i sannan nafara kokarin hada mashi dinner. Sadda ya dawo da tsaraba yadawo man kayan zakine ya kwaso,kamar baison zafin kudin ba,daker na lallashi zuciyata na sake mashi har mukaci abunci tare. Mungama muna kallo yake ceman. "My love" Shiru nai ban ce komiba. Yacigaba da maganarsa "Kiyi hkr akan abunda yafaru,karkiyi tunanin da niyya nayi wallahi bansan nayi ba,ban cikin hayyacina bansan ya akai har haka ta faruba,kiyafe man plsss nima nasan banyi maki daidai ba,kuma kina fushi dani har yanzu plsss kiyi hkr kinjiko bazan sakeba." Wasa nake da hnnuna nace "shikenan na yafe maka ya wuce." Cikin murna yace"tnx my baby yanzu ina kikeson muje yawon honeymoon." "Aa kabarshi basai munjeba pls." "Karkiyi man haka ki fadi ko inane insha Allah zamuje shine as gift dinki na daren farko." Rufe fuskata nai ina murmushi, Yace"yes my wife,kin cancanci fiye da haka don haka inkinason kiga banyi fushiba pls ki fidda country uku dakike sha,awa nikuma i promise 2 u i will take it." Shiru nai ina tunani tabbas ina son zuwa kasar turkey and saudiyya da london,ina son birnin london sosai. Jinai yace"u like makkah,turkey,and london (US)." Dalalo ido nai ina kallonsa ta yadda akai yasan choice dina,murmushi yake hade da dariya yana kaklona shima, Kafin ya jawoni ya dorani kan cinyarsa yace, "Nasan zabinki my love,na tambayeki ne don inji idan zaki fada da bakinki." Murmushiin nima nake yafara man chakulkuli na dunga dariya saida yaga ina niyyar sikewa ya kyaleni, "Plsss kisaki jikinki dani banson wannan dari darin kinjiko,insha Allah cikin kwanannan zamu dage kasa mai tsarki muyo ummarah ta wata guda, sannan mu wuce turkey muyo one month,and last sai muje Us muyo one month,hakan yayi maki." Kwantowa nai jikinsa kirjina yana duka cikin dakiya nace ina murmushi, "Yayi man,an thank you very much my one and only in my heat." Saboda murnan kalaman dana yi mashi matseni yai yana shuking kunnena ,nan take naji wani ziririn abu yana bin dukkannin jikina,.duk yadda naso nayi mashi wayau kiyawa yai,atai kaice dai wannan dare mun rayashi cike da annashuwa,duk da kukan dana sha na zafin da nakeji,sai shiman albarka yake ni nagaza gane wane irin dadine dr yakeji har haka,har ga Allah ni banjinsa kodan tsoron dana sa kama raina ne oho. *Bari mu leka wajen amarya salma.*😉 ************* Amarya salma babu laifi kam gidan yayi kyau,gidane flat house mai dauke da bedrooms uku sai babban falo daya da kitchen,daga can waje inka shigo public toilet yana kalloka,sauran bedroom din kuwa kowane da kewayensa cikin dakin,dayane na mijin biyune nata. Amman kasancewar shi baisaka komi cikin nashi ba,yace set guda na kayan dakinta ajera mashi su,masu jeren duk dangin mamarta ne,da nashi tunda da mamanshi da mamanta uwa daya ubane kowa danshi.......basuyi jaa da magamarb suka saka,yazama salma bedroom dintaguda kujerun da Areef yasiywa khairat,itama yasiya mata amman saboda kishi ko nace bakin hali irin na Ameer din nata yace sam shi bazai iya kallonsu ba don haka asaida abashi kudin yayi mata kasuwanci dasu,haka iyayen mata suka siyar dasu suka cinye rabin kudin suka bashi sauran,bakuma don wai kasuwancin zaiyi mata dasuba aa cinyewa zai, Haka aka kawo amarya salma,da zugar kawayenta babu inda basu shiga bacikin gidan,sai rena mata suke wai duk surutun ahaka aka tsaya,ai sunyi zaton gidanta yafi haka duk labarin kayan dakin ashe ma set gudane kai allah yatsine mai karya,haka suka runga mata wulakanci gaban iyayenta mata,don cikin dangin Abbu babu wanda yaje kai amarya........tun lokacin salma taji wata irin nadama da dana sani sun rufeta,tasha kuka mai sunan kuka haka kuma suka barta takwana ita daya gidan kamar mayya. Hakika sai yanzu takejin abubuwan datayi kokadan bata kyauta ba,taya zata gyara ta saka bacin rai ga zuciyar mahaifinta,ta butulcewa matar data dauketa matsayin diya,tashayar daita tareneta bata banbanta ta da yaranta ba,amman saboda son zuciyarta da biyewa shawarar qawa ta jefa kanta cikin dana sani. Haka washe gari akai walima kowa ya watse yabarta dagabita sai angon da tagaza gane kanshi,sai halinta. Tun tana sakanran ganinsa har bacci ya sace ta,sai washe gari ta ganshi. Gaba daya ya canza mata ace tana amarya amman konkofar dakinta bai nufa ba,cikin kwantar da murya take mashi tambayar inda yaje jiya. Cikin masifa da hargowa yace, "Ban sani ba salma,tunda uwata ce ke ai dole ki tuhumeni da maganar inda naje." Hankalinta ya tashi matuka don abun nashi ya yi yawa,tun saura sati biyu bikinsu yake mata behaving irin haka,tayi mashi tambayar duniyar nan akan laifin da tayi mashi,yace shi atai ashi komiba. To meyake nufi da ita kasancewar salma bata iya hakuri ba,bata jure wulakanci saudubu zaka mata saudubu saita rama.........cike da masifa da bala,i itama tace, "Ya isheni Ameer ya isan,mekake shirin maidani ehy,nace kafadan abunda nai maka amman kace man babu komi,amman still kana mun wanna halayyar kagayan abunda naimaka." "Karki man ihu bisa kai salma,ranki zai mummunan baci wallahi," Cike da bakin ciki tace, "Naje nayi maka ihun Ameer,karfa ka raina man hankali, oh ka kawoni gidanka don ka gana man azaba,kokuwa yar gadin gida ka daukini to baka isaba aure nazo yi kuma da tsiya shizamuyi, ai kaika nace kace aini ko to kuwa dani din zaka rayu wallahi baka isa ba." Dariya yayi yace, "Yanzu nagane inda kika nufa,kina son in kusanceki ban kwana dakin kiba jiya shiyasa kike ta fada haka ko kamar zaki cinyeni danye, aibansan hajira na auraba sai yanzu kiyi hkr kwantar da hankalinki yanzu zan maki yadda kikeso." Ganin ya nufata yasa tafara ja baya tana kermar baki tace, "Kai,kai....karka tabani niba haka nake nufiba wlh niba nufina ba kenan, kawai naga kana niyar canza mana rayuwa ne shiyasa ,plsss Ameer karka yiman komi ban shirya ba,wlh ban shirya ba na rokeka.............inaaa baima sauraretaba sab'arta yayi dama kuwa salma ba wani nauyiba, jefata yai kan gadon yaringa barke kayan baccin dake jikinta,har saida yaga babu komi jikinta,kamar tsohon maye haka yake lasheta yana sauke numfashi,ihu take tana rokonsa amman ina baisanma metake cewa ba,ganin zata tara mashi mutane ya daure bakinta da kallabinta,ya cigaba da gashi kamar wani mahaukaci haka Ameer yake sex da salma , Run tana sanin me yakeyi har tasume babu ruwansa aikinsa kurun yake babu kakkautawa,saida yayi cikakkar awa hudu akanta kamar wani jaki. Sannan ya tashi kobi takanta baiba ya wuce yayi wanka yabar dakin................iya wuya mai sunan wuya salma tasha ta, Don babu wanda yasan hakin da take ciki,shikuwa baisa ke dawowa gidanba sai dare,sai lokacin ya tuna da ita ada yaje dakin har lokain bata farfadoba,sai lokacin hankalin sa ya tashi,ya sungumeta sukai asibiti,atakaice dai salma saida tayi kwana biyar asibiti,itama tasha dinkin har babu adadi,babu kuma wanda yasani balle yazo ya dubata. Ameera yasha tsinuwa da alkaba,ira bakin salma har abun yazo yana bashi dariya.......ciin qawayenta Raihana ce kurun kezuwa gidanta. Dafarko zaman nasu yafara dadi sun shirya kansu bayan tawarke, Har suka zaga dangi Har gida sukaje wajen Su maah a abbu babu wani nuna sun rikesu suka anshesu cike da murna. Yinin su guda suka komavgida,babu alifi sunyi amarcin sati uku. Amman cikin nahufun Raihana tashigo rayuwarsu. (KOME HAKAN KENUFI?) *KUYI HKR KUNJINI KWANA BIYU BANA JIN DDI E AMAN NASAMU SAUKI,PLSS KURINGA SHARE DINSA SOME GROUL PLSSSS DON YA ISA GA MASOYANA NAGODE MAKU SOSAI.* MRS BB CE👌🏻😉😘😘🌹💕 Commen and share's pls [6/22, 9:03 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *sorry for keept waiting,zauren mrs bb sunyi disappointing dina*😢 Not edited. 35&36. Da farko Raihana bata wuce kwana uku kulum idan tataso school tana gidan sasalma itace shiga nan itace shigacan,babu inda bata kurdawa acikin gidan,salma tun tana ganin abun bakomi ba tunda tana ganin ai Raihana kawartace ta Amana,duk da wasu halayen itace ta dorata bisan su,to Amman yanzu abun nata gaba yake wata sa,in in tazo saitace zatayiwa Ameer girki ni naje nahuta,to hutunme garan bawani surfe ko nik'a nikeba,aisune dai za,ace kana gajiya aikin gidane kamar ko taushe yan share share da goge goge,saifa sanwar da gyaran dakuna. Hankalinta ya gaza kwanciya da halin data bullu dashi,gashi bata tafiya har sai yadawo taringa jansa da hira kenan har sai yabiye mata,. Karshe tace shine xai maidata gida idan suka fita Ameer shida dawowa kuma,saidai nafarka tsakar dare inganshi........wata ranar zan jiyosa yana wanka karfe daya ko biyu,babu kyau zargi amman tabbas ina zarginsu shida ita,kasancewar nasan halinsu suduka,Raihana ba tun yanzu take bin maza ba,........shikuma rauni garai indai kan mace ne nan take tana iya jawo hankalinsa kanta,hatsabibiyace ta kin karawa idan ta saka abu gaba babu ubanda ya isa ya hanata,ba gaban iyayenta takeba hannun kakarta take kuma bata son laifin jikar tata,salma bata da natsuwa cikin kwanakin,da yadda suke da Ameer abun gwanin sha,awa Amman yanzu ko kallon dakinta baiyi balle yace zaishiga,yafi sati uku rabin daya kusanceni. Abincina yadaina ci killum kuma da sassafe za fita office,bai dawowa sai taltainin dare..........wannan abun ke azabtar da ita duk ta kara lalacewa,tashiga tashin hankali marar misaltuwa,tarasa waye zata kira yayi mata soving wannan problem din...........ta tuna yar uwarta khairat,irin abubuwan dasuka shirya mata itada raihanan,gashinan to yanzu ta juyo kanta.kuka ta fashe dashi tana nadamar abunda tayi,wai itace har gaban malamin tsubbu takai yar uwarta wadda suka sha nono guda suka rayu tare,suke son junansu kamar rai da ajali,Amman tabiye shawarar qawa ta kaita ta baro,ta rabata da wanda takeso itama kuma yar uwar tata bata samai ba. Wannan kadai ya isheta ishara ga ta bata ma iyayenta rai,Allah bazai barta ba......haka take ta kukanta kamar idonta zai fito. *wannan kenan* *********** Amarya khairat sun d'age kasashen turai,kafin sutai ya zaga da ita dangi ta gaida iyayensa,da nata duk inda sukaje sai sambarka banda gidan yar uwar dadysa yayar dadysu,ko ruwa wannan comon ba abasu ba ba asake bi takan su ba,shi dr yasan dalili nice ban saniba,shiyasa bamu wani jima ba muka baro gidan koda yaga fuskata ta canja ya kama jana da labarin ban dariya har saida na saki fuskata..........gaskiya babu laifi dr ya iya love saidai bansan meyasa baya nuna man shi kan gadoba,duk yadda nake sha,awar sex to daya tun karoni yafara abunda yake zanji yafita raina,because baya wasanni dani shidai kawai yajishi yashige shine muradinsa,nikuma bana so bansan kuma tayadda zan nuna masa ba,inajin kunya gaskiya gashi da dadewar bala,i tun inashan kukan har nazo na hakura na dai kukan,saboda nidai ban tabajin wani dandano ba ckin harkar,kullum sai bakar azaba gabana yaringa wata irin zafi saina kwana na yini yana zafi. Na rasa yazanyi Husna kurun muke wannan maganar,don yah meenah bata barina ma ina dauko maganar balle ta fahimceni,maah da Annie kunyarsu nakeji matuka bazan iya dizcousing wannan issue din dasuba,dole nabar abun matsayin kalar tawa rayuwar kenan ni bazan tab'a jin dadin Aureba har abadan. Munje gida sallama yace nayi masu kwana biyu,wayyo dadi jinai kamar yajefani aljannah.......da Abbu yace aa saida yaga ina kuka sannan ya kyaleni. Inajikin maah bana matsawa ko ina don nayi missing nata sosai,Anty shida tana dubai itada yah jahid,yah meenah ce kurun musha hirar mu tunda har yanzu hutu muke,sai mun dawo daga yawon honeymoon sannan hutun yake karewa. Dadaddare dakin maah zan kwana ta nata bani labarin abunda yafaru bannan,har tazo kan *ABIN CIKIN RUHINA* tace, "Umminki nata cewa tunda kika gama makaranta secondary bakijeba har kikai aure,ince maki idan kun samu lokaci keda dr kuje kugaidata,dama kuma Abbi dinsu imran baida lafy kinga idan kuka tai wannan yawon sai ku biya kudubashi,babu dadi tana sonki kina gudunta." Shiru nai ina tuna wasu abubuwa dasuka wuce ba wai banson ummina ba,inasonta sosai saidai dole yanzu matsayina na matar aure matar wani naguji abunda zai tada man feeling din wani cikin raina,hakika ban taba mancewa dashiba amman me ina ciresa da karfin bala,i saboda gudun jefa rayuwata halaka,ai halakace kana auren wani zuciyarka tana tunanin wani,bazaka taba samun kwanciyar hankali ba ga tarin zunubai kuma,dannewa nai kawai bance mata aa bazamu ba nace, "Allah ya kaimu lokacin maah,insha Allah zanje wajen ummi ko yini muyi mata." Hararata tayi tace"aa karma kuje kawai,yinin banza yaushe har kuka gama gaisawa na lura bason zuwa kikeba." Hkr nabata nace"sorry maah kwana nawa kike son nayi mata to." Ganin zata tashi taji haushi yasa nai saurin rikota ina dariya,naita lallashinta harta sauko tace"ina laifin kiyi mata sati guda." Maimakon nayi gardama sai nace "to insha Allah,kilan ma mu tadda Anty shida can ko." Tace "Aa inajin jibi zata dawo don katsina zata ta anso ko me,kinsan ta samu aiki,shahid ma ya samu shiyasa za,a hade bikinsu dana meenah lokaci guda." Farinciki ya kamani nace"abu yai kyau wlh naji dadi Allah yasa Alkairi,,,,,nan mukai ta tattauna maganar har mukai bacci. Washe gari Abbu saboda ni baije office ba muka zauna mukaita hira kamar anyi shekara ba,a haduba. Kwatsam saiga salma wurjan wurjan,da ganin idonta ma kuka tasha,na mance daduk abunda yafaru na rungumeta ina matsar kwallah,haba itama saita kama kukan,mukaitayi daker mukai shiru zubewa tai gaban maah tarike kafafunta tana kuka tace "Kiyi man rai maah kiya fe man,wallahi nayi danasani,ban kyautata maki ba wlh sharrin zuciyane dana qawa kiyi hkr ke mahaifiyata ce kiyafe man......"sai kuka kowa tabashi tausayi wajen Amman banga hakan ga Abbu ba,shan mur yayi matuka maah dagota tayi tana lallaashi "Daina kuka salma ai hannunka baya rubewa ya yanke kayar,duk abunda kikai mun yafe kinjiko daina kukan haka,ai mungode Allah ma dakika gane gaskiya." Cikin dakakkar murya Abbu yace" mekikazo yi gidan yanzu,bacin sanda kika barshi kina farinciki har bakinson zuwa neman Albarka mu da muka haifeki." Rarrafawa tayi wajensa tana kuka take bashi hkr kuka fake sosai,Aman Abbu ya rude idon sa yace baisan wannan ba tatashi tatai gidanta tunda ta nuna bata ra,ayin wannan. Saida Annie ta saka baki sannan ya kyaleta yana tambayarta lafiya tashigi gidan haka kamar wadda aka koro. Ta na kuka take basu labarin Raihanna"tun wancan lokacin ashe neman juna suke ban saniba,sai dana gansu da idona agidana na nuna bacin raina shine tasashi ya yi man dukan tsiiya,saida na kwanta asibiti bacinan kuma ta dawo gidan da zama wai ai tunda aure zasuyi,nanda sati biyu.............kuka yaci karfinta takasa karasawa gaba daya munshiga tashin hankali,wace irin rayuwace wannan salma keyi Ameer din zaiyi haka,duka auren kwanan sa nawa dazai wannan lalacewar anyi gudun duniya yayi wata uku. Salati da sallallami kawai ketashi falo,salma najikin yah meenah kukan kurun take. Abbu yace"shine kika taho." Tace"Aa don nace ban yarda ta zauna man giba ina kallonsu suna abunda bai dace ba shine tasashi ya dakan yace ina taho gida sai yaneman." "Lahaula walla quwwata illa billah,naga abunda ya isan bai ishi ubangijinaba ni saudah,shi ameerun yayi mai wannan tozarcin lallai yacima dan iska." "Kanaji Abbukhair,bazaka ce komiba gaskiya ka kirashi yazo kadauki mataki mummuna kanshi,taya zai kamata yaringa duka kuma duka yaushe akai auren har da zaice zai karo mata kishiya,kishiyarma qawarta wadda tasan ta tasan komi kanta,gaskiya kayi wani abu." Tashi yayi yace"ga dakuna nan sai wanda ta zab'a ni banda lokacin saurarensa yanzu tukun."yan gama fada yafice ya barmu. Wannan rana batazo mana dadadi ba,kwana mukai mu uku muna tattauna maganar,nida ita da yah meenah,nasha kuka don har yanzu ina son yar uwata tausayinta ya kamani,sainaga ni ai ba komi bane tunda bana fusantar irin wannan rayuwar, Bamu samu bacci ba sari gaf da asuba gashi jirgin karfe tara zamubi muwuce (US) dama na hado kayana tass,daker na tashi nai salla sannan nafita ina taya maah girkin safe. "Kinga dai abunda yafari da yar uwarki,to kadan daga cikin cin amana kenan dakuma sab'ama iyaye kidauki darasi kanta,ina maitabbatar maki bama gamawa akaiba,ba fata naked mata ba amman tabbas duk wanda yasai rariya ya San zata zubar da ruwa,don haka kisan wacce kike ciki duk da nasan duk aure yana da kalubale,haka yake kuma nasan kina taki matsalar,ina sane ban tambayekiba don nima inson ki koyi rike sirrin gidanki,komuma zamuji dadi iyayenki,kicigaba da hkr kowa shine yake zaunar dashi gidan mijinsa tare da iyalinsa,babu wani waje yanzu da zakije kizauna da yafiye dakin mijinki,don haka kikara hkr kinajina." Jinjina kai nai ina cewa"hakane maah insha Allah zanyi duk yadda kikace amman ina tausayin salma,kisa baki Abbu yakirashi adaidaita komi." "Karkidamu ni kaina bazanso zamanta gidanba zanyi duk yadda zanyi komi yadaidai ta,amman kinsan wancen auren saiyayishi,bafa mutuncine dashiba dan iskan yarone na bugawa jarida shafin farko." Dariya nai tace"wallahi kuwa,kuma karkiyi mamakin idan shima baga bokan ta kai shiba,saboda ai kinji tace farko lafiya lau suke." "Hakane ma ah babu tantama wlh,amman kisata Addua nima innaje saudiyya zan akata,kiyi mata nasiha kikara kwatanta mata maah nasan zata gane." "Shikenan kije kishirya lokaci na tafiya,kardai ki manta da zuwa wajen umminki." Dariya nai knacewa "insha Allah maah." Karfe takes da rabi dr yazo nan yayi break,yanata jan yah meenah wai ta kusan tsufa agida........gardai ayi bikin itama tatare gidanta tana cinyewa su abbu abinci,dariya ta kamayi harda salmar aka rakamu airport duk sai naji kewarsu......rungume juna mukai muna share kwallah,aka kiramu muka shige. Sai birnin london ta alkhairin Abbu. #mrs bb ce 😉💕💕😘😘 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *_ABOUL-NASSER (ALFAH) COMING SOON INSHA ALLAH._* FATAN ZAKU JIRAYE SA NAN BADA JIMA WABA INSHA ALLAH.😉🌹🌹 GODIYATA BATA DA IYAKA GAREKU FANS BANSON HAKA KUKE SONABA,ALLAH YABAR MUNKU LOV U ALL. 😘😘😘💕💕💕🌹🌹 Not edited. 38&39. Waje na samu na zauna inajin kafafuna baza su iya daukata no ba,banson had'uwarmu banso ko kadan,shiyasa tun farko naso bujirewa maah badan banson zuwa wajen ummin ba,saidon gudun irin hakan jikina rawa yake saboda wata irin yunwa da nakeji.........youghout ko ice cream kurun nake son sha don sune kayan shana bana iya cin komi har gara cake amman ban dashi saifa kayan zak'i. Wayata na sake dauka in kira ummin in roketa taturo man yah imran din...........saidai wata tsaleliyar mota data shigo ta shagaltar dani,farace k'al tayi masifar yin kyau dagani new modan ce. Fasa kiran nai na zuba ma motar ido inson ganin waye ciki,zuwa wani lokaci na hango wani mutun yana nufo inda nake,hankalina yatashi ainun. Tashi nai na fara neman guduwa don wallah mutumen ma ni tsoro yakeban,gashi dai gabjeje kuma baki kamar dai dan africa. Ganin zan ruga mai yakara sauri nima na kara nawa saurin ina jin kamar zan saki fitsari,,,,,nayi wata irin zufa addua kurun nake ina rokon Allah ya tai makeni.........jinai na karo da mutun dagowar da zan ashe mutumen nan ne wata kara na fasa na ina kwasa wa aguje........ninai kurun anfizogoni anjefa cikin mota.......duk na gigice jikina tsuma kurun yake.......figar motar akai kamar zamu tashi sama muka bar fikin jirgin. Saida mukai nisa sannan na dawo cikin hayya cina na tuna ban kwaso akutunana ba,cikin tashin hankalii nace. "Driver wait na manto jakunkuna na filin jirgin don Allah kamai dani na dauko." Kamar daga sama naji muryannan da ko doguwar suma nai zan ganeta,saidai wannan ta shabanban da wadda na sani watannin baya,,,,wanan kamar an kara mata suger muryar jinake har sino take fitarwa don tsananin sanyi da zak'i. "Uban waye drivernki." Shiru nai don tabbatar da shine naji zafi zagin,rabon da azagan harna manta dama shine keda sana,ar zagin to tunda yatai ban sakejin wandanyace don ubanki ko dan uwarkiba..........shiru nai na hkr nasan dai nayi asara don duk kayana dana siyo nawa dana tsarabar da zan koma dasu suna can cikin jakunkunan,.......har mukaje bakina bai sake maganaba illa skakar kamshin dake gauraye da motar danake inajin dadinsa,tunda nafara laulayi bayan kamshin turaten Dr babu wani turare da yadauki hankalina irin wannan danake shak'a, bazan iya tantance nashine ba ko na motar ba.......zanso insani.........idona rufe yake banma kallonsa balle har nasaka ma raina wani abu tafiya ce maidan nisa mukai kafin muka isa,rabona da Dubai tun na gama primary nazo nai hutun wata biyu daganan sai fa yau,duk garin ya canza man ansake samun cigaba ta ko ina........har naso inzama bakyauya duk da dai naje knda yafi nan din kyau datsari......... "Kina iya fitowa." Yafice yabarni tsaye bin bayansa nai da kallo mamaki ya cikani,kayana nagani zube ya fiddo daga but koyaushe aka saka su oho. Ummi da Mimi da sadam suka iso suna man oyoyo sai na manta da bacin raina na rungume ummi ina murna nima,mimi da sadam suka kwaso mun kayana muka k'arasa ciki. *********** Zuwaa dabai wani canjin yana yine gareni,tunda ummi tagane inda ciki ta shagwab'ani,sai abunda nace inso zanci,tunda Allah yasa yah Areef ya ajiyeni ranar dana zo ban sake ganin saba, sai bayan kwana biyu shima kuma a daining muka had'u na gaidashi ko kallona baiba bakke ya ansa,raina yayi babu dadi ai tunanina yanzu babu sauran takun sak'a,sai yasaki ranshi muyi zumunci,Amman duk wannan bobbotan ban san ko nameye bah........har mimi tasan banji dadi ba ina daki mun gama waya da Dr yace daya gama abunda yake zai iso mukoma. "Nazo ma dad I yya inba yar da hkr." Harara na banka mata na juya ina danna wayata waje ta samu tana cewa, "Bari Kik dalilin jin haushinki da yake,duk baki son sani." Yinai kamar banson me take cewa ba amman kuma nan kunnena na saurarenta. "Tunda yah yadawo daga bikinku kwance yake khairat,aikin da yazo yi saidai wani yake ashi shi,yafi wata asibiti anrasa gano kanshi.....yau sauki gobe ciwo,duk ya tashi hankulan mu Abbi kanshi kamar ya zauce akan ciwonsa,ummi kam wani sa in kuka take mashi akan ya tausaya masu yayi hkr da kaddara ita tasan duk dan bai sameki bane,to kanshi farau rashin masoyiya......wasu ma iyayensu suke rasawa duniya gaba daya sukuma hkr balleshi don kawai baisamu wacce yake so ba,to ita dayake tana jin maganar iyayanta kuma ta yarda da kaddara mai kyau da marar kyau ai gashi can tana zaune gidan mijinta lafiya lau bata dorama kanta wannan masifar ba,saikai kana namiji kakasa jurewa. Banga anfanin kasancewarka namijiba Areef. tunda har baka iya sadaukar da soyayyarka ga waninka,to ko kaki ko kaso khairat dai ta haramta gareka,kuma har abadan bazaka sameta ba,don ina mata fatan kasancewa da mijinta har karshen rayuwarta,don kuwa mijinta yafika sonta idan zaka tashi ka fuskanci gabanka to idan kuma nan zakai ta kwanciya bismillah ga wajenan iyaka abincine in daho inba kanwarka ta kawo maka, da kaci da karka ci uwarsu daya ubansu daya,wahalalle kawai." "Gaban yah jahid lokacin ya biyo shi shima zaiyyi wani aiki nan,ina gefe nima duk ummi take fadar wadannan maganganun,koda na kalli fuskar yah wallahi khairat kuka yake amman babu sati saidai hawaye dake zuba,fita nai inbasu waje don naga yah jahid yana son magana dashi.........dama ummi tana gama fadan ta tafice rai b'ace. Ina jikin k'ofar naji yah jahid yana lalashinsa,yana cewa, "Areef ya kamata ka tashi hakanan,duk abunda ummi ta fad'a gaskiyane kaifa namijine kaine yadace ace kana yin juriyar da khairat keyi,barifa kaji itama fa badan tan soba,bata da yadda ta iya ne dasu Abbu........"karya take jahid bata sona shi take so.ya katseshi da fadar haka. Murmushi yayi yace"kishinka bazai barka kayarda da haka ba,amman kasani itama tana cikin irin wannan halin,tadai fika juriya ne." Wannan maganar ta sake har zuka yaya yace"shikenan aina an fad'a hakaan nai aka alkawarin baza sake kwaniya aka rashinta ba,ama abu guda da zakai mun shine kasanar dasu kar wanda ya sake anbata mun sunan ta gabana,,,,idan ba haka ba zasu neman su rasa,naji ma ni duk natsaneta wallahi banson maganinta yanzu,..... Tun daga lokacin yah yadawo kamar bai taba ciwo ba arayuwa,saidai lokaci lokaci zaisha mgani saboda ciwon zuciyarsa.......ranar da kikazo dana sanar dashi ummi tace yaje yadauko ki kinga yadda ya har zuko man kamar zai makeni,aguje nabar wajen nai zaton bazai jeba sai muka ga yadawo tare dake.......tun daga ranar baya zama gia saidai gida uncle jabir (kanen su maah ne shine autansu shima baitab'a haihuwa ba)kinji haushinki da yakeji ." Tsaki naja nace"ya dade baiji haushina ba angaya mashi ni tashi nake, ni ko tunashi banyi kimaji in gaya maki." Dariya tayi tana cewa"eh gaskiya ne naga alama. haba mata wazaki maida shashasha kawaidai kina waskewa ne saboda kina da aure nima kuma zanso kina yin hakan,yadda yake shareki baya ansa gaisuwarki kema kibar gaidashin,hakan zai bashi haushi,saboda ke duk yazama dan bala,i wlh." Dariya nai nace"dama shine wlh dama fitinannene ne,saidai kice karuwa yayi ninan nizan gaya maki masifarshi wlh. Gyara kwanciya nai ina sake cewa"inyayi hkr na kusan tafiya don ma ummin tace saina k'ara sati wlh da da dr yazo zanbi mijina inkoma." "To masu miji muma dai ai mun kusan yin auren adaina mana gori harda goruba." Dariya nai mata mukahau wata hirar. ******* Yau mukai da Dr zaizo ya ganni jibi mu koma ban ma gaya mashi cewar ummi ta kara man kwanaki ba ,sai yazo inyi maganar gabanta don daker zai yarda amman idan tasa baki zai barni. Don nima ba son zaman nake ba don duk nima naji yasire man kamar yadda yace ya tsaeni yanzu,harma ni zaice ya tsana lallai ma koda yake kodacan ai haka yake nuna wa,ni baitab'a nuna man alamar yana sona ba inba ranar da zai bar garin ba. Ummi bata nan tun safe ta fita tace sai yamma zata dawo,bata son dr yazo bata nan kar ya daukeni yace zaigudu dani bamuyi bankwana ba daroya duk mukai nida mimi. Yah imran ne yakaita Nida mimi muka shiga kitchen muna hada ma Dr abunda zaici idan yazo,kasamcewar mimi badai iya girkiba don du itatyi wasu abubuwan,ina dai taya tane.........juice kurun na had'a na kai frig din karamin falonsu. Harda wani sweet cake tayi mashi,tace sairayinta Abukhalipa yana masifar sonsa wani irin cake ne yasha cream asamanshi,tace a frig take sashI sai yazo ma take fiddoshi don karyayi melting.....naji dadin sa sosai don saida naci miyauna kamar yayi tsartuwa.nasan kuma Dr zaiso shi duk na k'agu ya iso na yi kewarsa sosai. Shima ga frig din na kaishi sanan nawuce nayi wanka,yanu banson yin kwalliya don ko kadan bansonta, saboda cikin anan doguwar rigace mai kama da jallabiya Dr ya zabo mansu da mukaje saudiyya red ce sai kwalliyar golding tun daga sama har k'asa,ta fitar da shaf dina ga dan cikina yafito d'an wata biyar,zari ido nai ganin yadda rigar tayi masifar daukata,ta fiddoni sosai,don yanzu nayi wani irin haske ga hutu ga ciki,har wani daukar ido nake,daman bana saka komi ga fuskar sai farar power da liptis saboda bushewar baki,amman duk dahak nai kyau sai murmushi nake,sanan Dr idan yaganni kilan gaban ummin zai daukeni ya rungume.,don shi kunya ba isar sa tayi ba bana saka turare tunda na samu cikin nan saidai yar sure danake goga ma anfit dina da matse matsina saboda smeling. Fitowa nai da sauri don dauko wayata dake falo naji kamar sadam yana kwalan kira anan kirana, Sauri sauri haka nakeyi inje ga wayar nason Dr ne yaketa kira kilan ya iso aje adauko shi,,,,,jinai kaina da kirjina sunbugi abuu bansan nace washhh Allah na tsaki naja nawuce do k'amshinsa kadai ya isa yaga yan waye yashigo. Mikoman wayar yayi yana cewa "Number Dr ne sai kira ake." Ansa nai ina wucewa karamin falo don induba abunda nasaka ko yayi sanyi yadda nakeso,ina tafiya ina duba wayar kiransa nakeson inyi still yanzu ma karon mukai sosai,har wayar ta silale kasa ta fad'i...........wani kululu yazo ya tokare man wuya duk yadda na tsani kwayar idona ta kallai doke tasaka na zuba mai idanuna dasuka fito waje dukansu,,,,har wata ruwan kwallah naji suntaru acikin su bakina naji yana fada cikin jin haushi. "Wai meye hakane ehy d'azu kabanke ni na kyale nai hkr yanzu ma kuma haka gashi kafasan waya mijina sai kirana yake yaz..........."shut up stupid girl" Sake dalalo idona nai ina kallonsa tuni kwallah sun cika idon tab,nace"ni ......nice stupid.....ni...cikin tsawa yace "eh kedin! ba stupid din bace,kina tafiya kamar makauniya bakya kallon gabanki,,,comon ban waje nawuce nonsence....." WanI malolon kunci da bak'in ciki suka cika man zuciya.....kafin nayi magana ya janyeni gefe ya wurgar,bacin bango danai saurin dafewa da sai dai kan cikina zan fad'a.........durkushewa nai ina kuka bak'in ciki rabona da kuka bazan iya tuna waba.....mimi ta karaso cikin sauri. "Subhanallahi khairat lafiya,meyafaru mekikamai." "Mefa me zan mashi kawai zalincine da kuma daman jirana yake....banka ta fa yayi har saubiyu danme zanyi magana kina gani nan kadan ya hana bai turani k'asa ba da kan cikina zan fad'a......hakri taban taa tattara man wayata da ta tashi aiki,sim dina nacire na saka cikin wayar mimi nashiga kiran dr amman ban samu ba,kuka na kubce dashi yanzu haka akwai abunda zai ce man gashi nan yayi man sanadin rashin samunsa........koda ummi ta dawo banji ko dar ba na gaya mata ai kuwa ta hau balbalin bala,i kamar zata ari baki.....sadda ya dawo daddare har lokacin wayar Dr bansamu ba,,,duk nashiga halin damuwa ko yana ina ya iso bai iso ba ina ya taya oho.....ina kwance kan cinyarta idona saboda kuka har yayi fushi....koda ya shigo shida imran suna hirar kwallon k'afa ummi tabishi da harara baisan ma tanayi ba, Imran ya wuce dakinsu shikuma ya wuce karamin falo.....inanan kwance kamar ance dago ki kalli can dagowar dazanyi na hangoshi ya dauko wannan sweet cake d'in ya yanko kusan rabinshi kan plet,ga spoon dinsa yana yankowa yana saka wa baki.....kamar anzungura man Allura na tashi afirgice na nufi wajen da yake...... Tun kan na isa inda yake yasha mur kamar bai tab'a dariya ba,yace"ke..... kee.......karki sake ki iso maninan,wai bakida hankaline "ina zuwa na kab'ar da plet din ina hawaye nace"Wallahi da kacishi gara ya b'are ai bakai akaima wahalar ba,na rantse kuwa kozai tsutsa da hunhuna inhar wanda naimawa mijina baici ba kaima kuwa bazaka tab'acin sa ba......."keee............ni ....nikike gaya ma magana,don kinga ina ragar maki,zan daukeki da mari awajennan........"ummi tace da kuwa baka kara marin wata mace ba aduniya Ashe baka da hankali Areef,yarinyar da ciki kakeson kassarawa,oh abunda kayi mata d'azun bai ishekaba yanzu ma gabana kake kirarin zaka kwad'amata mari,to kafara dani kafin ka yi mata nata." Juyawa yai yashege b'angarensu cike da b'acin rai......lallashina taitayi tana ban baki,har nahkr daker nasha maltina da cake din na wuce daki nai sallar mangaruba na kwanta,wayar nake kallo inajin kirjina yana dukan tara tara hankalina ya gaza kwanciya ......me yafaru da Dr na hawaye suka silalo man,,,jinai kawai zuciyata tana karkarwa dandanan jikina yafar daukar wani fitinannan zafi.....mimice tashigo "Khairat ga wayar kisake jaraba kiransa ko za,adace saurin tashi nai don inaji ajikina zan sameshi insha Allah.....hannuna har wata karkarwa yake ina danna kiran,jinginanai inajin yadda zuciyata take duka jinai kurun kiran yashiga.........kafin bakina yaimagana naji wata murya bansanta ba tana cewa *MAI WAYAR GASHINAN ASIBITI SUNYI HAD'ARI KUYI SAURI KUZO YANA GAF DA RASUWA.* wata k'ara na fasa wadda tasani rugawa ni ma don kunnena fashewa zaiyyi......... Mrs Bb Ce Mom muhseen. 09034722970 [6/27, 9:41 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *_ABDOUL-NASSER (ALFAH) COMING SOON INSHA ALLAH,NASAN ZAKU NISHAD'ANTU DASHI KUCIGABA DA TSUMAYINSA SOON INSHA ALLAH.* KUYI HKR KWANA BIYU KUNJINI SHIRU WLH JIKINE BANJIN DADINSA FATAN ZAKUYI MAN UZIRI,ALLAH YAYI MAKU ALBARKA YA KUMA BIYA MAKI BUKATUNKU NA ALKAIRI AMEEN INA SONKU IRIN BABU IYAKAR NAN.😘😘😘💕💕💕💕🌹🌹🌹 Not edited 40. Wannan karar dana fasa yasaka gaba d'ayan su kuka runtumo aguje gareni,shashsheka nake ina dafe da cikina da ya wani irin juyawa............nishi kurun nake hawaye jage jage suna bin fuskata.......mimi ce a rikece ta d'agoni "kharat lfy maya faru ina Dr bai zo bane ina yasauka me yace maki." Cikin tashin hankali na dago nakaleta n kalli ummi nace"ummi........numfashina yayi sama kamar zai dauke daker nace......"yana asibiti hatsari sukai sunce muje da sauri yana gaf da rasuw.............ban k'arasa maganar ba numfashina ya fizga suduka duk sun gigice afirgice imran yashigo yana tambayar lafiya,,,,,,,"imran maza maza fiddo mota Dr yayi hatsari wane asibiti yace ankaishi khairat ki natsu mimi dauko mata ruwa tasha." Koda na sha ruwan daker ya wuce kuka kurun nake ina shashsheka........"ummi ban sani ba baigaya man ba,ummi kutai maka man kukaini inson ganinsa ummi banson rashi idan dr ya mutu yabarni nima mutuwar........"karki sake fad'an haka insha Allah zaitashi bani wayar maza maza imran sake kira kaji wane asibitine." Ansa yayi ya shiga kiran number ba jima wa aka dauka, "Don Allah wane asibitin aka kawo mai wannan wayar." Mutumen yace"kuyi kokari kuzo yana nan FMB HOSPITAL sai neman makusantanshi yake don aiki za,a shiga dashi ba lallai ai nasara ba,matarsa yaketa faman kira ita yake son gani kuyi kokari kuzo kafinan da minty talatin.......wyar ta yanke......tashin hankalin da na shiga bazan iya kwatan tashiba wani irin rawa jikina yake bansan ma me bakina yake furtawa ba,ga cikina da yadunkule waje guda ban iya mik'ewa tsaye aduke na isa motar......ummi ke rik'e dani muka shiga motar dagani sai ita da imran, Lallashina take sosai har muka isa,,,,,tunda muka doshi emergencybanda karkarwa babu abunda jikina yake.....yah imran ne yasake kiran wannan mutumen yagaya mashi inda zamu samai..........ba,a barin kowa shiga d'akin babu inda baya rwa jikina hawayen ma sun k'afe kaf. Mutumen yayi man iso cikin d'akin.........Idan kaga dr bazaka tab'a iya gane shiba......fuskarsa tayi kaca kaca babu inda babu rauni,jikinsa gab'a daya nannad'e yake da bandage...........idanunsa baka ganin komi cikinsu banda jini dake kwance......kuka ya kubceman "innalillahi wa inna ilaihir raju,un hazbunallahu wani imal wakil,,,,,,,nashiga ukuna wayyo Allahna dr na kaine haka dr na Allah yasa mafarki nake,Allah ka farka dani daga wannan mummunan mafarkin,,,,jinai yarik'o hannuna......muryara kanta ta canza ba kajinta yadda ya kama ta,saida na kanga kunnna saitin bakinsa wanda ansaka mashi oxygen........magana yake son yayi mni,shiyasa na cire mashi shi.......bakin kanshi babu kyan gani,,,,, "My love.......ki kula man da yarana,Allah baiyi zamu cigaba da rayuwa tare ba,naso in kasance dake iyakar rayuwarmu.....amman da alaman burina bazai cimmaba.......kikulaman da abunda ke cikinki banson hukuncin Allah ba da ya jarabemu da wannan kaddarar,Amman inaji ajikina zakoyi rayuwa mai kyau.......zaki samu mijin dazai kuka da ke fiye da yadda nakeyi maki,ina kuma kyautata zaton yadda zaisoki haka zaiso yarana,idan Allah yasaukeki my love in twins din danake fata kika samu,,,,ina rokon Alfarmar ckinsu kibarwa ummina guda,idan kuma dayane nabar wasoyyar arubuce nabarmakishi har abadan domin kisamu abun kallo kina tunawa dani,,,,,kiyi hkr kidaina kuka zakiyi farinciki nan gaba........tari yake kasa kasa kirjinsa yana d'agawa yacigaba"inarokon ki alfarmar da kidunga man Addua aduk sanda kika kai goshinki k'asa,my love zan tafi da tsananin kaunarki,zanso ko lahira kizama matata kiyi alkawarin bazakiyi man kukaba,,,,domin kinsan illar da yakewa mamaci karkiyi man alkawarin haka........kuka nake ina shashsheka bakina karkarwa yake "Aa Aa Dr na kabar fd'ar haka na rokeka kadaina cewa zaka mutu,bazaka mutu kabarni ba inhar katafi nima binka zanyi,yazanyi da kewarka ina zan saka kaunar ka,kataimaka katashi mutai gida kaganifa yaranka najinka tab'akajisu takai hannunsa saman cikinta.......idanunsa ke kakkafewa yayinda wani uban tari ya tirnik'eshi babu kakkautawa.....dandanan jini yaringa anbaliya ta hanci tabaki.....afirgice nake kallonsa yafice daga hayyacinsa likitocin dake kulawa dashi suka iso cikin gaggawa,fita dani suke ina rizgar kuka,,,,ni subarni naga mijina subarni muyi hirar bankwana......su ummi suka mik'amani kuka kurun nake ina kiran dr......suna can aka shiga dashi operation don tunda dama aka kawo masu accident din shine wanda yarayu zuwa yanzu sauran duk babu wanda yarayu. Don kafarsa guda jijiya kurun ke rik'e da ita dole suka cire ta don bazata tab'a gyaruwaba,,,,,,akwai wani karfe daya soki hunhunsa sunyi nasarar ciresa tun sadda aka kawoshi, yanzu aikin cikin zasuyi mashi,aikin yana da had'ari sosai don sai maitsawancin kwana da rabo yake rayuwa,amman dayawan mutane sun rasa ransu wajen irin wannan aikin. Nayi kuka har muryata bata fita,su kansu su ummi kukan suke suna share hawaye,,,,,, tun yamma har dare suna nan suna jiran tsammani har baccin wahala ya daukeni.........su ummi ne sukajira anfito aikin susan wace akeciki.......tsoranta daya kar dr ya mutu in yamutu ba karamin tashin hankali khairat zata shigaba,ga cikinta zai iya samun matsala.........likito cin basu fito ba said wajen karfe d'aya........sunce sukara hkr zuwa safe aga yadda jikin zaiyyi,sun kwantar masu da hankali sosai sukace suje gida da safe su dawo lokacin ya farka. Haka mima koma gida har lokacin bacci naked,van farka ba saida mukaje gida.......anan dadynsu yake tambayar me yafaru nan take sanar dashi halin da ake ciki...........ban iyayin bacci ba wannan dare tun bayan wanda nafara asibitin,yanzu kuwa ko alamarsa banji saboda tashin dake kaina......waya mukai da umminsu tace sunana isowa da safe yanzu jirgin zatashi zuwa shidda na suba sun so.......lallashina take sosai tana kwantarmun da hankali wanda nima nasan itama tana cikin wanda yafi nawa,saboda ita d'anta ne bata iya sake haihuwar kamarsa,nikuwa zan iya sake wani mijin.........kuka shine yatayani hira kafin gari yawaye.....saboda kerma har raui aji aman ba dauba daker nayi sallar asuba na k'agu muje ko naganshi insamu natsuwa.......zuciyata karkarwa take sadda nafito zamutai jikina kamar ansakani cikin frig k'arara.......bayadda ummi batai dani ba akan inci wani abu amman nace bazan iya cin komi ba dole ta rabu dani hada dady muka tai wannan karon a harda Areef. Wanda nakejin wata iri tsanar sa saboda duk shine yayi silar faruwar komi,,,,,,alokacin dabai bankeniba nasan zan samu dr ya gaya man inda yake aje adaukosa......amman dayake mugune shi azzalumi gashinan tasilarsa Dr na yasamu mummunan illar dako yarayu balallai ya zama yadda yake daba........muna isowa kofar asibitin naji wani mummunan fad'uwar gaba ta riskeni......cikna yawani motsa har saida na dafe marar. Kamoni ummi tayi na rungumeta inajin jiina amar ansakaman electric.........banda rawa babu abunda yakeyi.....idona kuwa banda hawaye babu abunda yake fitarwa......ina hango umminsu da su jalila harda Abbansu durkushewa nai kusadasu ina rizgar kuka........mai tsuma zuciya d'agoni tayi ta rungume duk da cikina daya turo sosai.......itama hawaue take gogewa su jalila kam kuka suke sosai itada fati.........adaddafe dai aka gaisa kafin likitan yazo yace "mutun uku kurun zasu shiga don baison hayaniya..........nida umminsu da Abbansu muka shiga kafafuna kerma suke hangoshi danai, kuka kurun nake inajin zuciyata tana kakkaryewa........idonsa kurun yake waje yanzun ma Izzy ne hancinsa da bakinsa........hannu ya mik'oma mu duk muka karasa gareshi....umminsa kuka tafashe dashi tana cewa, "Muhd,kaine haka muhd garin yaya innalillahi ya Allah katashi kafad'ar wannan bawan naka wayyo Allahana idan narasa ka muhd yazamuyi ina zamu saka ran mu muji dadi.......kuka taitayi Shikanshi Abban kasa magana yayi saidai hawaye dayake sharara daga idonsa.......hannunsa yasaka daker ya cire oxygen din......muryarsa adishe ta shak'e yace"kudaina kuka ummi,,,,,,,don Allah ko na mutu karkuyi man kuka hakan zai cutar dani.........ummi koda na mutu nabar wasiyya arubuce tana dakina cikin drowar na komi na rubuta don Allah ayiman......sannan ina rokon ku dakuyita yiman Addua,,,,,,,,,kallona yayi yasakarmu wani murmushi zan iya cewa tunda nake dashi ban tab'a ganin yayi manshi ba,yace"inasonki matata,inasonki zanbarki badan raina yaso ba,ummi Abba kuyi hkr inata fadan maganganu gabanku,ban da yadda ina iyane idan ban fad'a yanzu ba banda sauran lokaci dazan sake ganawa da ita........rike hannunshi nai gagam ina rusa kukana muna cikin haka yafara wata irin shak'uwa.........dandanan na rikice ina rik'e da hannunsa har lokacin.......aguje likitocin suka shigo,suka roki su Abba dasu fita amman nace babu inda zanje,,,,,sai dai su dubashi gabana daker da sidin goshi akajani waje kuka nake kamar raina zaifice.........kowa hankalin sa yayi kololuwar tashi ganin andauki awa guda babu alamar zasu fito......ina jikin ummina likitan yafito sai uban gumi yake......Abbansu dr ya fara nufa yajashi gefe amma bama jin mesuke fad'a......Abban mukaga ya silale kasa yadafe kai nana take naji wani irin duka ga zuciyata.......kaf kaf kaf kawai jikina yake dadunsu yah imran ne naji yana cewa ma su umminsu dr. *"sai hkr Allah yayi masa rasuwa......* Saidai sukajini nazube kasa timmm.......... Mrs bb Mom muhseen. Love u my All fans 😘😘😘🌹🌹🌹💕💕💕 [6/28, 2:12 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. Not edited. 41 Gaba d'aya hankalinsu yayo kaina sadda zasu dagata jinine male male yakebin kafafunta...........hankulansu suka kara tashi ko kagani wajen kuka yake share share da hawaye,har su dady hawayen suke........dandanan aka anshita akai emergency da ita........dady da Abba suka fita don zuwa fara hidimar shirya dr akaishi gidansa na gaskiya............Areef ke lallashin ummi yana bata baki don shikanshi lokaci lokaci yana share hawayensa,shikenan Abokinsa ya tafi bai tab'ajin mutuwar data ratsashi irin wannan ba,tausayin khairat ya lullub'eshi yarinya karama ta zama zajawara,,,ga karamin ciki wane irin ciwo takeji cikin ranta,ai komi tayi bai wadatar da kuncin da rad'ad'in da zuciyarta kemata,dole zata yake jiki tafad'i............likitoci uku ne kanta kowa yana aikinsa,domin samun ceto abunda ke cikinta don jinin dake fita idan yacigaba da fita ba tantama za,a rasa cikin.iyakar kokarinsu suke har Allah ya tai makesu cikin yadaidaita.....sannan suka shiga nemo numfashinta Amman abun yaci tura,abu guda zai nuna masu cewar ta da rai shine bugun zuciyarta,inbashi ba babu wata kafa ta jikinta dake nuna tana da rai.........sunyi mata iyakar abunda zasuyi mata suka kyaleta zuwa wani lokacin. Koda suka fito daya daga cikinsu yake ma ummi bayani cewar,ansamu nasarar daidaitar cikin saidai har yanzu numfashinta bai dawo ba,munyi mata allurai insha Allah zuwa gobe ko anjima da dare numfashin zai iya daidaita,karku damu zata samu lfy shikuma Allah yajikansa." Areef kurun ya iya ansawa saboda daga unmin dr har ummin yahAreed kuka suke sosai.........tsawon lokaci sunanan zaune kowa da abunda yake sakawa,,,,,,sun hkr sunbar kukan saboda yadda yarok'esu kar suyi mashi kuka.........su dady sunzo sun dauki gawar antai anyi mashi suturra ankaishi gidanshi na gaskiya,sunkira gida sun sanar da rasuwar zuwa safe zasu juya zuwa nigeria..........jin haka yasa suma su ummi sua koma gida don shirya kayan su,Areef da imran sun tafi ummin dr da dadynsu sun wuce masauki,ummina ce kurun akabari tabada sakon asanar da mimi manyan akwatunan su zata shirya masu kayansu,don ita tana saka ran bama zata dawoba daman don Abbansu yana aiki nan ne shiyasa,to yaringa zuwacan karshen wata.....kasuwamcinta kuma zata san yadda tai tamayar dashi Abujar....tafison zamakusada yar uwarta da kuma khairat. Can cikin dare na farka gaba d'aya nayi losing abunda ya faru,kallon dakin nake ina son tunawa amman nakasa,idona ya sauka kan ummi dake ta bacci ban tasheta ba na koma na kwanta,nasan dai na fad'i amman miye dalilin faduwar tawa shine nakasa tunawa........abunda yasa kuwa shine likitan sukai shawara da Areef kan cewar idan sunyarda zasuyi mata allurar mantuwa na wucin gadi,yadda za,asamu daidaituwar abundanke cikinta,don muddin ta tatashi mutuwar zata sake dawo mata sabuwa,kuma cikin yana bukatar hutu da natsuwarta,kuma hakan zaiyyi wuya karshe arasa cikin,amman idan akai allurar zata manta har zuwa kwana biyu sannan cikin ya samu sauki don yanzu baida isassar lfy idan tayi abu mai karfi zai iya fita.........hakan yaa Areef yace suyi mata kawai,yaje yayiwa ummin bayni itama tace ayi hakan shine samun natsuwarsu,don sun tabbatar tashin hankalin da zata shiga shine nasu tashin hankalin........kai jama,a mutuwa babban tashin hankalice ubangiji ya kyautata makwancinmu Amee. Washe gari ummi ce ta tai maka man nayi sallar asubah,sai dai ta fakaici idona ta share hawayenta,bayan nayi break da youghout shikadai nasha sannan nayi wanka,riga kawai na zira kwanta don jikina kwata kwata babu karfi,hakanan nakejin zuciya ta tana kareyewa,,,hawaye suka ziraromun ina kan cinyar ummin kuka nake can k'asa k'asa.... Batace mun komi ba don bazasu iya hanani kuka ba. tabbas sadda na farka adaren nan banzan iya tuna komi ba,aman gari na wayewa komi ydwo ma sabo,jin abunda ummi ke sanar wa da maaah da suke waya tana gaya mata allurar da akaiman,shiyasa nai iyakar kokarina wajen ganin ban tadawa kowa hankaliba,kuma ahalin yanzu babu abunda nakejin ina mutuwar so sama da abuna ke cikina,inajinsa tamkar fitar nufashina shiadaine abunda zan gani inaji sanyi cikin raina,domin kuwa dr mutunne harda rabi,yayi soni ya nuna man kauna da gata tsawon watannin da mukai dashi. Yanzu babu shi doran k'asa saidai yaransa idan Allah yasaukeni lfy,zanyi fatan nima na haifi twins din domin inbawa ummi itama ta ringa ganin photocopy din d'anta.........gobarar dake ci cikin zuciyata kad'ai ta isan,basaina na bayyana wata afiliba,inajin rad'ad'i da zafin rashin dr jinake abun kamar ba gaskeba jinake kamar mafarki nake ko labarine akebadawa ba gaskiyaba...........tun shekaran jiya da wannan malolon ya tokare makoshina da kirjina har yau bai wuce ba,banajin zaitaba wucewa domin ganin dr kad'ai shine maganinsa,,,,,tokuwa ina zanganshi yana can kabarinsa wasu hawayen masu zafi suka ringa sauka kan cinyar ummina,shikenan katafi bazan sake ganinkaba ina rokon Allah ya hadamu a lahira,gidan Aljanna ina maka fatan samun rabo mai albarka acikin kabarinka,ubangiji yakai rahma gareka drna zancigaba da maka addua har sai ranar da nabar numfashi adoran kasa...........jin abunda nake cewa yasa su ummi gane cewar nasan abunda nake ciki,allurar tasakan,jinina maikarfine bzata dauki lokaci tare daniba. Karge goma duk mun wuce airport akwatuna na nakalla,ina girgiza kai komi kecikinsu tare mukaje mukasiya,muna cikin farinciki lokacin da tsananin soyayyar juna.......daga jiya zuwa yau wani sabon son Dr yake kwarara cikin zuciyata,jinake bazan tab'a son wani mahaluki irin yadda nakejinsa ahalin yanzuba,,,,,,,haka rashi yake haka d'acin mutuwa yake ashe haka takeda rad'ad'i......ya Allah karka sake nuna man irin wannan mutuwar,ya Allah duk wanda zai mutu kasanya inrigashi,bazan iya cigaba da jurewa ba domin xuciyata bugawa zatai.........(😭😭😭 Allah sarki ta alkairin Abbu,hakika kinacikin radadin rashi,tabbas duk abunda kikaji yadace kijinshin,domin rashin miji,uba,uwa,d'a su shagaban duk wani tashin hankali,na tausaya maki Alah yabki ion jurewa.) Vaccine yasake saceni cikin jirgin,don har lokacin allurar baccin bata sakeni ba,mune bamu isa Abuja ba sai karfe bakwain dare,don mun tsaya ta london jirgin ya sauke fasinja ya huta sannan muka karaso. Sadda idona yasauka kan Abbuna sannan naji wani irin kuka ya kubceman.......rungumeshi nai ina rusa kukana ina sauke ajiyar zuciya. "Abbuna dr yatafi,dr yatafi yabarni Abbu ina zan saka rayuwata Abbu bazan iya rayuwa mai dadi babu shiba,yabarni lokacin danake tsananin bukatarsa,yabarni Abbu Dr ya barni yatafiyarsa..........shikanshi hawayen suka sauko mashi tausayinta maitsanani ya cika zuciyarsa....maah da ke kusada su kuka ta kamayi tanajin tsananin tausayin kharat d'in........kasa kallonta tai don zuciyarta karyewa zata suhadu suyita kukan,,,,anan filin jirgin su Abbu sukaiwa dadynsu dr gaisuwa tareda jajanta masu,kafin aka shiga mota kowa ya wuce gida. Wannan rana kamar lokacinne dr ya rasu don gidanmu haduwa mukai dani da yah meenah,mimi,Salma da tazo don inajin ansasatan ta koma sai husna itama tazo,kuka muka raba dare munayi karshe dole Annie tazo tatafi dani bangarenta,lallashi da ban baki shine taitayi man,tana man nasiha akan addua ce kurun yadace naringa mashi ba kuka ba,mamaci baison kuka duk yadda kikejin d'aci da ciwon hakan daurewa zakiyi kizama jaruma,shikadai zakiyi yaji dadi a inda yake,zaikumayi alfahari ake. Mrs bb ce Bazanniya cigaba badomin nikainaninajin abun kamar gaske hawaye sun cika idona,zan bari inhuta zuwa gobe ina alfahari dakasancewata daku masoyana😘😘😘💕💕💕💋💋 [7/1, 8:01 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *_Coming soon insha Allah ABDOUL-NASEER (ALFAH) BY TAKU MAI SAKAKU NISHAD'I MOM MUHSEEN OR MRS BB,LOVE U ALL MY FAN'S I REALLY LOVE U_* 😘😘😘💋💋💕💕😉 *kuyi hkr kwana biyu kunji shiru wlh abubuwa ne sunsha kaina,fatan zakuyi mun uziri,im very sorry*. Not edited. 42. Cikin kwanakin nan biyu da dawowarmu,ko kusa bana iya kai lomar abinci bakina,dama kuma ga kwaikwai ya tasoni gaba,kamar jira yake dr ya mutu ban iya ko d'aga yatsana. Yanxu ko ice cream din nasha saiyafito,balle wani youghout ko wani abucan,xuciyata banda kuka babu abunda take kullum ganin abun nake kamar za,a tasheni daga nannauyen baccin dana fad'a......amman ina it's the reality babu abunda ke canzawa,tun hawayena suna zuba har suka zo suka kare. To karewa mana tunda bayadda banyi don suzuba ko zan samu saukin zuciyata amman kemadagus basu fitowa,saidai fitinennen zafi da zuciyata keyi,inji kamar ankunna wata gagarumar wuta cikinta. Lallashi da ban baki kuwa ba abbuna na ba ummi ba ba Annie ba ba maah ba,kowa yi yake bakin kokarinshi,shiyasa nake iyakar yina don nima na karfafa kaina. Yan school dinmu sunzo man gaisuwa sosai ranar ban iya sanin inda kaina yake ba,saboda banson abunda zai tuna man mutuwar,duk da ba mancewa da ita naiba. Shiyasa idan anzo mana gaisuwar bama su isowa inda nake,saidai ayiwa su maah da su ummi,don yanzu ummi fat guda ake gyare masu suma danasu b'angaren,da cewa tai gida zasu siya suzauna Abbu yace aa gadai isasshe waje dazai wadacesu, basai sun wani sayi gidaba. Bedroom uku ne bangaren,amman kowane akwai tazara tsakaninsa da d'an uwanshi,guda na Abbansu idan yazo aka gyaremashi shi fesss,daya kuma na ummin sai gudan na sadam,don mimi tana nan bangaren maah shidama oga kwatakwata da bangarensu shida jahid. Akwana atashi babu wuya wajen ubangiji har anyi wata guda da rasuwar Dr,har su yah meenah sun koma makaranta,yayin da ni dole zan ajosting semester har sai na gama takaba,watau na haihu kenan,gashi IT zamu tafi da mu dawo sai muyi exam daganan zamu shiga final year........amman gashi ni zanyi westing one year saboda rasuwar mijina dole zan mashi takaba,inda Allah ya taimakeni ma baiwuce nayi ta wata hudu ba na haihu,tunda gashi har anyi one month........an daga bikin su yah jahid dasu yah meena har saina haihu. Lokacin nafita takaba abun zaifi armashi, Tunda muka dawo gida magana bata shiga tsakanina da shiba,domin kallonsa ban sonyi wata irin tsanarsa nakeji sunan sa ma banson inji wani dake kusadani ya anbata,inda zan ganshi ma bana kallo don jinake banda mak'iyi irinsa,duk sanda natuna shine dalilin rushewar farincikina shine silar da har dr ya rasa ranshi,akanme bzanji haushinsa ba kari da cewar tunda akai rasuwar baimun gaisuwaba,ko kallona baiyi balle ya tausayama halin danake ciki. Sannan ga wani bakin cikin naji kishin kishin aurensa tareda nasu yah jahid........zaniya cewa inajin haushi zan iya cewa banaji,bazan iya yankewa kaina hukuncin abunda nakejiba kan maganar aurensa dana faraji kasa kasa,zuwa yanzu babu laifi nafara sakin jikina magamace dai har yanzu bakajin inayi sosai,inba da Abbuna ba. Yau husna tazo itada momin su sake dubani,kasancewar yanzu zmunci ake sosai tunda za,a hada zuria. Ganin husna yasa nasaki jikina muka sha hira ,take bani labarin IT dinsu yadda yake kasancewa,sainaji inama nima inayin nau amman kaddara tariga fata,ga mimi gabyah meena sai ynin ranar yayi mun dadi,sai bayan sallar magruba suka tai.bayan tafiyarsu Na wuce wajen ummi don yau tace mun tayi sinasir miyar zallar hanta tasha Alayyahu sai k'amshi take,don yanzu babu laifi cin abinci nake kamar jakadon cikin dandanan yake sani jin yunwa. Kasancewar yafara nauyi don yashiga wata shida, baje baje nayi falonta nida ita inaci tana karaman,muna hira rabon danaci abinci mai yawa irin wannan zan iyacewa tun kafin nasamu cikin nan,ita kanta ummin dadi takeji yadda nasaki jiki yau sai labari muke. Kamar daga sama ya shigo falon cikin wata irin kyakkyawar shiga tatashin hankalin duk wacce ta ganshi,wata dankareriyar gizner ce brwon tasha wani arnen aiki jigunanne ya hadu iya hadu wa,har naka sa gane wane yafi mun haduwa shi da shaddar........baki da hanci kai har dama ido da kunne na saki ina kallon shi waya yake fuskarsa cike da tsananin murmushi,har kyawawan hakoransa suka bayyana,dumful d'insa guda d'aya ya fito sosai.......juya hannuna kurun nake cikin kwanon miyar dake gabana,yayinda ummi ta zage sai zuba man labari take. Jin nayi shiru yasata d'agowa tana kallona bansan ma tana kallon nau ba,inda taga ina kallo tabi da kallo itama. "Okay I'm sorry yau ai bazan ce haka ba,yanzu ma i'm on my way insha Allah......dariya yayi yana sauke wayar daga kan kunnensa. Sai lokacin nai saurin kawar da kaina ina sauke wani wahalellen numfashi, ga kirjina da yake dukan tara tara. Ummi ta kalleshi tace"wannan gayun fa Areef,kamar wanda zashi d'aurin aure,yaushe rabon daka saka manyan kaya kaga yadda suka maidaka babban mutun." Murmushin yake har lokacin ya zauna yana d'aura agogo yace"wlh ummi nima sai yanzu nagane hakan, don jahid da maah haka suka fad'a suma,zan cigaba da sawa insha Allah." "Allah yasa,yanzu ina zaka haka gaf da isha,i." Ya gama saka agigon kenan ya d'ago daidai idona yana kanshi,karaf sai cikin najuna kallon secon biyu mukaima juna yajaye idonsa,yana cewa"wlh ummi wajen *zulfa,a* zanje kullum dana saka ranar zuwan sai wani abu yashigo,kuma tana ta mun complain akan hakan,shiyasa nace yau bari naje kafin sadda zan koma Spain." Sinasir d'in dake cikin bakina ina kokowar had'iyeshi shine ya kwareni,,,,wani irin tari ya tirnik'eni babu k'ak'k'autawa gaba d'aya hankalin ummi ta yo kaina tana bubbuga bayana ahankali amman hakan bai hanantarin ba,sosai nake tarin don bakaramar kwarewa nai ba,yana zaune yana kallonmu sai bubbuga bayan take......mik'ewa zai fita aikuwa yabata haushi tace, "Ubanka nace gidan ubanwa zaka maza bani ruwa marar sanyai kitchen." Fuskarsa babu alamun wani haushi ko bacin rai yajuya yaje ya kawo cikin cup,ta ansa taban kirba biyu nai na ajiye ina sauke numfashi..........jinai yace"zan iya tafiya yanzu." Harararsa tayi yayi dariya yajuya yanabtafy ayana cewa. "Wallahi ummi ke kowa mai laifine indai akan wannan kundubar yarinyarne." Afusace ta mik'e tabishi da jifa da filo tana cewa, "Ubanka nace ja,iri zaka dawo kasaman." Sannu take ta faman yiman tana cewa"muje cikin gida cikin mutane rabu dashi don kundun ubanshi,zaisan da wanda yake magana." Daker nake taka k'afafuna muka fita,banda duka babu abunda nakeji cikin zuciyata,wata babbaka nakeji kirjina namun.......wacece *zulfa,a* meke tsakaninsu wata zuciyar tace mun "toke miye naki kiji da rashi mijinki ma,koma meke tsakaninsu babu ruwanki." Afiki kuma nace "hakane kuma," D'akinmu nawuce nabarta wajen su Annie suna hira. Mimi nat waya yah meena na ta seaching ga system,na zube gefe ina sauke numfashi hira muke da ita amman kwata kwata hankalina baya kanta,bazan iya cewa ga kalma guda danake fahimta cikin zamcen da take man ba,ashe hawaye nake ni bama saniba saina naji tace. "Subhanallahi!khairat kuka kuma meyafaru,badai har yanzu bazaki sakama zuciyarki hkr ba." Share fuskata nai nace "sorry nadaina bari nayi wanka inxo na kwanta nagaji sosai." Mrs bb Mom muhseen 09934722970. Follow me on wattpad *Humaira7531* and pls share it somes grps. *_Abdoul-nasser (Alfah) is very nice and sweet story,don't miss it,very soon zaifara uwa maku karki bari abaki labari ABDOUL-NASSER (ALFAH)_* [7/3, 10:26 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. Not edited. 43. Koda na fito shirin kwanciya nakeyi muna magada yah meenah,kayan nake bincika wa wadanda zasu shigeni,amman abun haushi duk sun man kad'an,saboda wannan cikin yayi girma kamar dan wata tara dariya yah meena keyi man,duk naji haushi ya kamani ficewa nai nabarta..........maah naje naiwa saida safe sannan na wuce wajen Annie don yau tare zamu kwana dady yayi tafiya shida Abbu Germany,sai nan da kwana uku zasu dawo. "Maah don Allah ki araman rigar dazan kwanta,wlh nau duk basu shigata." "Dama ya za,ai su shigeki khairat inbada rigima,jibekifa yadda kika koma sunbukekiya." B'ata fuska nai "haba maah kema haka zakice man,kowa sai yce man haka ni wlh nagaji da cikinnan wai yaushe zan haihune." Murmushi maah tayi tace"kinda sauran 3month gaba" "Nashiga UKu na maah nidai wlh yayi yawa." Bata fuska tayi tace"banson sakarci,kintab'a ganin an haihu wata takwas ko shidda,kiyi fatan ki haihu lfy shine kawai,anshi nan ni ki wuce kije ki kwanta kinata yawo kowa ya natsu bandake." Ansa nai nafita ina jin babu dadi,cikin nan ya isan hakanan,wahala nakesha ba yar karama ba. Allah yasa dai haihuwar saidai inji ance tashi kin haihu,don wannan wuyar mankad'ai ta isa. (😂😂🤣lallai ta alkairi to bari mujira mugani) Rigar na saka duk da cikin ne yacikata nikaina saida naima kaina dariya,saboda yadda rigar tayi man kamar buhu........kaina yana kan cinyar Anni muna kan gadonta,shafa kaina kurun take na lumshe idona ina tunanin rayuwata,daidai da second dr yana cikin raina,komi nake komi zanyi he still in my mind. Hawaye suka gangaro man,nashare na tuna abunda ya faru daxun falon ummi. Bansan ma naja wani dakikin tsakiba,jinai Annie tace"subhanallahi khairat,kina lafiya kuwa." Gyara kwanciyata nai nace"nothing." "Karya kike,kinsan karya dai ko to ita kike khairat don haka gaya man mekedamun ki." Kwallah suka cika man ido,bazan iya boyewa Annie damuwata ba,don koda can itace kawar shawarata,duk da ga yah meenah. "Inajinki kishare wannan kwallar kisanar dani." Ajiyar zuciya na sauke inajin tarin haushinsa cikin zuciyata, "Annie wacece *zulfa,a*." "Zulfa,a!"ta sake kiran sunan kafin tace"ina kikaji wannan sunan." "Annie nidai wacece." Shiru tayina wani lokaci kafin tace" *MATAR DA AREEF ZAI AURA CE.*" Lumshe idona nai inajin yadda kirjina yake duka,ganin na ki cewa komi yasa tace"ya akai kika tambayeni." Numfashi na sauke nace"d'azu ina wajen ummi naji yace zaije wajenta." "Toke miye naki aciki,kina fama da takabarki,kisamu ma kisauka lafya shine burinmu,kifita sabgarsa ko har yanzu kina nan kina dakon sonsa." Runtse ido na nayi inajin maganarta ta karshe ta sokan,"Aa Annie nima ban saniba,amman tsanarsa tafi karfi cikin zuciyata,duk da cewar idan nace banson yah nayi karya Annie,Amman wlh tun da yai sanadin mutuwar mijina naji natsaneshi,banson ganinsa ko kadan sannan kuma gashi baimun gaisuwaba." "To kishin me kike dajin zai aure" "Ni ma bansani ba amman insha allah annie zanfita harkarshi." "Stop da dai yafi,don sonake yadda ya baki wuya kema kirama,munanan zaizo ya sameki." Munjima muna hira da Annie tana ban shawarri masu ma,ana har mukai bacci. 💕💕💕💕💕💕💕💕 "Wai kana lfy kuwa Areef,ni bantab'a ganinka cikin irin wannan condition dinba,tunda ka dawo na lura baka da wata walwala,ni amatsayin dan uwanka kuma abokinka bazaka iya sharing problems dinka dani ba,atleast ai nabaka shawara,inkuma lallasheka koda banyi maka maganin abunda yake damunka ba." Kwance yake kasa yayi filo da hannunwansa,kafarsa kan daya,yana girgizata ko sawu cikin da yake sanye dasu bai cireba,idonsa akulle yanajin duk kalaman jahid. Mezaice mashi dawane idon zai kalli jahid yace yabashi shawara kan abunda ada suka samu sab'ani dashi,sukai kaca kaca ina it can't. "Shikenan Zan kyaleka kuma wallahi kaji rantsuwar dan musulmi muddin kasake nayi promise akan ka zakasha mamakina,don bazan sake damuwa da damuwark ba,tunda bankai matsayin da zaka fad'aman matsalarka ba." Yajuya ya haye gadon yaja bargo. Aranshi yake ta magana"kayi hkr jahid inajin kunyar kallon idonkanin gaya maka, ABIN CIKIN RUHINA ce ke azabtar da ruhina,akullum kaunarta sake azabtat dani take,bansan har sai yaushe zan huta da masifar so ba,nikuwa soyayya bata sona,na girma da kaunarki azuciyata tun banson kaina ba,gashi na azabtar dake atare a daliliba duk don in nuna ma waana ke tunin ina sonki cewar ni baki gabana,shin kema kina cikin masu ganin cewa baki gaba,kiyi hkr kiyafewa yayanki masoyinki baida kamarki duk cikin zuciyarsa,da sonki nake kwana nake tashi,koda wannan kika barni kadai ya isheni,insha Allah bazan sake rasa kiba karo na biyu,nine mijinki nine wanda zamu kare rayuwarmu tare,Allah yaga Abunda ke raina shiyasa ya dauke mijinki,don yasan bazan iya cigaba da rayuwa ba batare dakeba,duk wani abu danake borene amman bagaskiyar lamarin kenan ba,kiyafe man inasonki ina sonki inasonki,wlh nai ma kaina alkawarin mallakarki koda mutanen duniya zasu taru kaina don hanawa...................wannan dare Areef ya b'atashi ne yana kua da idonsa,akan son ABIN CIKIN RUHINSA ganin kuka da sabbatu basuyi,yasa yatashi yaringa jero salloli yana gaya ma ubangiji......duk abunda yake Jahid yana jinsa,dariya kurin yake cikin duvet don yasan tatsiniyar gizo bata wuce ta k'ok'i. *********** Yau salma tazo tana kuka duk ta tada mana hankali,kuka take sosai kamar ranta zaifice duk mun tusata gaba sai tambayarta ake ta kiyin magana,ummi daman har yanzu haushinta takeji,ganin takiyin shiru kuma taki fad'an abunda yafaru,yasa tatashi cikin fushi tafita tana cewa, "Yau ga yalbura uba,do ubanki ana tambayarki kina yiwa mutane shiru,to ki kwana dubu kinyin kuka ni kunga tafiyata inada abunyi." Ummi badai fad'a ba ba,atab'ota ba ma wace Allah cika bakle antab'ota,kukanta taitayi har lokacin da su yah jahid suka shigo sun dawo daga office. Yah jahid yace"lafiya me ya sameta haka take kuka." Maah tace"kilan kai ta fad'a maka mukan ai har mungaji da tambaya." Ni daman ina gefe zaune k'asa na baje ina cin gyad'a,cikinnan ya fito kamar wata randa,duk tambayar da yake mata tai ki bashi ansa yace"to Allah yabaki sa,a bari na wuce nai wanka." Wata tsawa da yah Aref ya daka mata saida na firgita zan ruga,saboda tsananin karfin ta. "Ubanwa zaki tusa gaba kina wa kuka ana tambayarki kuma kinwa mutane shiru,zan b'ab'b'allaki wlh anan wajen idan nasake jin shashshekarki saina farfasa bakinki sakarai kawai common tell them what's ur problem." Runtse ido nai saboda yadda yake magana kamar zai haukace,du yagigitani wlh. Saiga salma tayi tsit kamar ruwa yacita muryarta bata fita sosai tafara magana. "Maah,Ameer ne."sai hawaye sharrrr kamar ankunna famfo.......cikin dakakkar murya yace"meyasami Ameer din,mutuwa yai koko baida lafiya." Tana gunjin kuka tace"Aa,dukana yayi shida matarsa." (kasancewar bayan tafiyar su khairat yawon shakatawa Abbu yakirashi andaidaita ,amman yace shifa aure babu fashi sai ya auri raihana Haka dai aka samu aka sasanta ta koma akakuma yi auren sada raihana) "Mekika masu suka dakeki." Cewar yah Areef tace"yah kullum yana d'akinta sai yayi sati biyu bai dawo wajena ba,kuma banda damar dazan ce meyasa. sai yahau dukana,kuma duk abunda tace mashi dashi yake aiki bai yin bincike kawai sai yahau bala,I yana cewa shifa sai yasakei idan iskanci zanmar,ban girmama matarshi inko har ban girmamata to shibazai iya zama dani ba...........tasake rushewa da kuka ta cigaba da cewa kuma banda lafiya yaki kaini asibiti,amma kan idona zai daueta sutai yawo,yanzu jiya inajin yunwa kwana wajen goma sha batayin abinci dani saidai inroko makota,shine nace bazan iyaba nashiga kitchen na dafa taliya naci shine da ya dawo tagaya mai,yahau mun masifa harda marina nikuma narama shinefa yace intaho gida akoya man tarbiyya." Taciga ba da kukanta bansan sadda nimanidonanyacika da kwallah ab,na matsan kusada ita ina kuka nima ina lallashinta. Shiru yayi baice komi ba Annie kuwa sai fad'a take kamar zata ari baki, Maah tace"ni wannan aure naki salma yafita raina kwata kwata wlh,kullum babu zaman lfy kodayaushe ke yar yin yaji saiyace kitaho gida sabda baidaukeki da daraja ba,zai zaizo kau ya same mu muba iyaye banza bame,bakuma don bamu sonkiba,don haka tashi kiwuce ciki nasan abunyi,jibi duk yadda kika lalace kokadan aurensa bai anfaneki da komi ba sai azaba." Ciki ta wuce tana share kwallah,nima ina shashshekar kukana don har cikin raina taban tausayi......du tashi sukai kowa yawuce bangarenshi inanan ina matsar kwallah, Kallona yai ni nama mance yana wajen jinai yace cikin sanyin murya. "Ai saikibar kukan haka ko ruwa ruwa." Wata harara dabansan naniyaba na banka mai naja dogon tsaki namike daker nace"ina ruwan mutun dani kowa yayi harkarsa banson intermingling." Na wuce ina tura uba cikina gaba(😂😂) Mrs bb ce Mom muhseen. [7/3, 8:33 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *Abdoul-nasser (Alfah)* *coming soon* 44. Yau aka kai kayan saka ranar yah Areef da zulfa,ar sa.,ni yini nai ma ina bacci bansan wainar dasuke toya waba,kasanewar iyaye aza sukaje Abbu daya dawo yaga salma akai mai bayani,bai sake cewa komiba maah kuwa tsaye take don ganin ta karya asirin da raihana tayiwa Ameer,don muddin ba akarya shiba wataran ma sakinta zai. Hangar da tabi wajen karya wanda sukaiwa khairat da Areef,yanzu ma ita tabi ta saka ayi saukar qur,ani sau bakwak,tace da iznin Allah da kanshi zai biyota har gida. Don saubiyu Dady yana aikawa kiran ameer din yace zaizo in yasamu lokaci,wannan shine yakara b'atawa Abbu rai maah ce ke kwantar mashi da hankali cewa akyaleshi zai kawo kanshi. Zuwa yanzu yah Areef so yake muna magana,amman kallon mutunci ma bai isan ba,sautari idan yana falon zajani da magana,idan na ansa to kujerar da nake zaune ta ansa itama,babu irin fad'an da maah batai mani ba naruntse idona cewa banda makiyi saishi,don shine yayi silar kashe man miji......wannan maganar tafi komi kona mashi rai shida maah. Har rannan take cewa"wai don ubanki ke bakisan kaddaraba,eh akwai wanda ya isa ya kashe wani inhar kwanansa basu kareba,koda bai bankeki wayar ta fad'iba sai yabar duniyar alokacin da Aka rubuta barinsa,amman dayake bakida tawakkali kin kasa hakuri ki mance." Kuka na saka mata nace"wlh maah baki tausayina,mai makon kigoyi bayana shine zakice man haka.......dalla rufe man baki tashi kiban waje." Duk yana wajen ake wannan dramer jikinsa yayi sanyi,ganin irin kukan danake yace"kiyi hkr maah kidaina mata tsawa kingani ba ita kadai bace,sorry khairat kiyi hkr i don't mean 2 hot u.......wata harara na banka mai na mike nace"banyin hkr bazanyi ba,hankalinka dai ya kwanta dr yabarmaka duniyar kadauki duk abunda kake so cikin t...........jikake tass tasss maaah ta dauketa da mari mai tananin zafida d'i maucewa.........saurin tashi yayi ganin jiri zai kadani ya rikoni.......idona har duhu nake gani saboda tsananin yadda marin ya ratsani, Fizgewa nai nafice dafe da kuncina,dayan hannun kuma dafe da marata da ta daure man,zuwa yanzu cikina yaki wata takwas. daker na isa dakinmu na kwanta naita kuka kamar raina zaifita duk tambayar duniya mimi da Antu sida sunman amman bance msu komiba. Ranar ban sake lekowa faloba,washegari naishigewata shashen Annie.......inajin ana cigiyata naki fita saida Abbu yakirani sannan naje. Yana falon shi shida yah Areef din na samesu suna hira harda dariya,shiga nai da sallama daker nake d'aga kafata saboda nauyin cikin,daker na zauna ina gaidashi. "Ta alkairin Abbu sannu kinjiko." D'aga kai kurun nai kwallah na cika man idona, Shafa kaina yake yana cewa"sorry don't cry,gaya man me yayanku yayi maki har bakya gaidashi,baruwanki dashi imfact ance har zaginsa kike." Dagowa nai idona hawaye share share naceciki rawar murya"Abbu shine silar da dr ya rasu kuma ni wlh ban zagaiba."sai kuka ya barkemun bai hanani ba naitayi ina shashsheka. "Sorry my dear,daina kuka muyi magana."sha fa kaina kurun yake yana lallashina daker nai shiru. Yace"kiyi hkr ta Alkairina,Areef baiyi haka don wani abu yasamu dr kiba,kidauka daman haka Allah ya rubuta,dr bazai rayudake ba kiyi hkr kibar dora laifin kan shi,kingani babu kyau duk wanda kwanansa yakare babu tsumi babu dubara sai yatafi.don hk kibar zagin yayanki kuma kina ringa gaidashi,oky." Ina kuka nace"Abbu nace maka ni ban zaginsa ni kawai yafita harkata sabodashi fa maah dazun ta maran gashinan ma cikina ciwo yake."na sake rushewa da kuka. "Subhanallahi,itaa dakanta aikuwa bata kyauta bazan mata magana,yanzu yayanki yakaiki asibiti." "Ni Abbu banson ya kaini ciwonma yadaina." Suduka murmushi sukai aranshi yace"rigimamma kawai." "To shikenan daga yau kun shirya din haka yanzu ma yimashi magana." Ido nad'ago na hararai dariya yayi yashgwabe fuska yace"kagani ko Abbu hararata take,kuma damun fita zata cigaba da daureman fuska." Murmushi Abbun yayi yaa kallonsu sai hararashi take shikuma yana mata gwalo. Yace cikin dan bata fuska"ta alkairina kinga tun kafin ajimu yiwa yayanki magana,kibashi hkr akan abunda kikaimai.daganan komi yawuce." Kai na kasa ina hawaye"kayi hkr bazan sake ba." Tashinai nafito nabarsu wajen. Ranar yini nai inakunci duk wanda yamun magana sai kuka jnta masifa,ga ciki ya addaban abinci ma yanzu ban iya ci sosai gashi bana samun bacci isashshe,ayita halbina acikin......infalka inyita kuka. Salma kusan watanta guda gida ta murmure ta saki jikinta sosai,kuma duk wasu d'abiu nadacan ta barsu kowa girmamawa take,ga son aiki yanzu kusan itada mai aikinmu yare suke aikin gidan,maah tayi tayi tabari tace ai zaman isarta yake. Hajiyar su dr sunzo sunkawo kayan haihuwa duk abunda mai haihuwa take bukata sunkawo,harda kayan damukasiyo daga saudiya da kuma turkey,,,,,duk sun kawoman. Ranar mutuwar dr ta dawo man sabuwa banson iyakar lokacin dazan dauka ina missing dinsa ba,abunda sani kwai shine har abadan bazan mance dashiba bakina bazai gajiya wajen yi masa addua ba. Cikina yashiga watan haihuwa,ummi ma tayi siyayya kamar hauka,har mamaki nake narasa waye yafi kaunata da hajiyar dr da ummi da kuma Annie,don kowa yayi shirinsa tsaf don tarbar baby. Maah kuwa ganin fushi nake da ita yasa ta kirani tayi man nasiha sosai har muka shirya. Ina wajen ummi mimi na mammatsamun kafafuna dake ciwo, kasancewar bamu jima da dawo daga awo ba yah jahid da yah Arref suka kaimu,nida mimi wai saina kara sati biyu kozan haihu,jinai kamar nadunga cin ubansu don basu san yadda na k'agara na juye wannan nauyina ba wlh,ina zaune k'asa jingine da kujera salma ma tashigo anata hira,yah meenahnkuwa bata dawo daga wajen IT ba,anty shida kuwa daman bata faye shiga cikinmu ba. Ummi tana d'akin Abban su mimi don yaune zai iso daga dubai,fitowarta kenan shikua yashigo ri'eda leda ga hannunsa babba,zama yai yana cewa "washhh,salma ban ruwa pls." Tatashi tatafi ta kawo mashi mimi tace"yah sannu da dawowa." Jinjin mata kai yayi baiyi magana ba,,,,,satar kallona yayi nai kamar ban ganiba,daker na danne zuciyata nace mashi "ina wuni." Kamar jira yake yayi zak'al yace"lafiya lau uwar biyu." Shiru nai bansake cewa komiba mimi tacigaba daban labarin wasu masoya ina dariya. Ummi tashigo takallai "kaikuma fa?,daga ina haka da uwar leda meye aciki" ta jawo tana dubawa. Kayan jariraine rigunan mata hadaddu,kai da kagansu kasan zasuyi masifar kud'i,santinsu kurun ummi keyi dasu salma. Ni kaina kamar na tanka amman banson inyi dariya gabanshi,tunda na kalla sau d'aya ban sake kallonsu ba. "Areef ina kasamu wadannan kayan,sunyi kyau sosai ina zaka dasu." Mik'a yayi yana cewa"gata nan gabanki ta wani baje kamar kayan da ba,aso." Dandanan raina ya b'aci ganin duk dariya ma suke,aikuwa kamar yasan ba shiru zanba,yamike zawuce yana dariya. Naita sababi kamar me suma bawanda ya kulani don sunsan halina idan akatab'oni. Saida na huce nashiga yaba kyan kayan tace ai naune shi yasiyo man,nace tace ina godiya. Ina mamakin yadda ya kwaso duk na mata,to kdan namijine fa saidai yamayar abashi kudinsa. Lokaci nata ja har nashanye sati biyunan ban haihuba,duk nashiga damuwa hankalina duk yatashi,Su ummi ke kwantar mun da hankali don wata sa,in sai ince ma ummi,"ummi wai don Allah haihuwa akwai zafi,inkinsan akwai zafi kawai mune acire manshi banson inwahala." Satace ina ai babu wata wahala,kina zaunema zakiji kin haihu taita kwantar mun da hankali da wannan na sakankance cewar kilanma ina bacci zan haihun. Amma sai me cikin dare ciwo ya tasoni gaba kamar zan mutu. Mrs bb ce Mom muhseen. Plss share it and follow me on wattpad Humaira7531. 09034722970[7/4, 8:26 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 45. Tunda uwar data haifani ban tab'a jin ciwo irin wannan ba,tashi nai nashiga toilet inyo fitsari da rarrafe na isa,amman ko kad'an yaki fitowa bansan sadda na kwalawa Annie kiraba,don ina bangarenta dakin yah meena,ita asibiti ta kwana. Kankace me ciwo yayi kaca kaca dani,nifita hayyacina,duk wanda ke gidan yasan yau ina cikin tashin hankali,Abbu yace babu bukatar azauna gida atai asibiti kurun. Kankace me yah Areef yafiddo mota jikinsa babu inda bai rawa,duk yafirgice zan iya cewa yafi kowa firgicewa,,,,,,,yah jahid yazauna mazaunin driver sai Annie da ummi baya nidasu shikuma yah Areef yashiga gaba,gudu yah jahid keyi amman Yah Aref cewa yake. "Dalla malam kataka mota,baka ganin halin da take ciki inbaka iya bani waje."duk ya gigice yafita natsuwarsa ummi tace"banson hauka Areef duk wannan gudun baima ka ba,to sama kakeson ya tashi kome." Hkr Annie tabaketa badawa "haba banson wutar ciki,ko anbaka motar awannan yanyin naka iya janmu kake kaje ka jefamu rami duk mu mutu." Duk da halin da suke ciki saida suka dara,nikuwa banda ihu da kiran Abbu da maah babu abunda nake,Annie tace "yi hkr khairat insha Allah zaki sauka lfy." Cikin azaba nace"banyin hkrn wlh bazanba aikunsan da wannan azabar kuka ki gayaman ko Wayyo Abbu nashiga ukuna bayana ummi marata zata fashe." Me jahid zai ba dariya ba wani uban bugu Areef ya kaimashi yace"baka da imani dariya ma yakake ko." Ummi ma dariyar tayi tace"barshi yayi wlh don ubanki ai kinji yadda take ko,tukunna ma bakina tunanin kina bacci zata zo ba,aikidauka ma baccin kike." Annie tace"daurewa ake kiringa kiran hazbunannallhu wani imal wakil,yahayyu ya qayyumu birahmatika astagisu aslihli sha,ani kulluhu wala taqilni ila nafsi d'arfata ainin,ko kuma Allahumma la sahla illa ma ja,altahu sahlan wa,anta taja alul hazna iza shi,ita sahlan." Amman bud'ar bakin khairat tace"banyi wlh ban iyawa nabani zan mutu wlh kilan mutuwa zan,kuncuceni kun kasheni kucire man cikin nashiga ukuna ihu kurun nake ina kuka don ni kadai nasan azabar danakeji. Ummi kuwa mezatai ba dariya ba tace"yo dan ubanki sadda kikai cikin mun sanine." Jahid kunya kamar ta kasheshi Areef kuwa sai kunci yake don ganiyake duk basu damu da halin da take ciki ba cikin rashin jin dadin abunda tace yace"haba ummi waibaki tausaya mata ne kiga fa yadda take murd'e murd'e." "Inkasake magana saina ci ubanka zaka sauka yanzu wlh,ni ban san ma uwar data sa kabiyo muba,kokaine zaka anshi haihuwar." Shiru yayi yajin yadda khairat take sauke nishi da kakarin amai........sun isa asibitin cikin gaggawa aka ansheta,wata likitar matace ta dubani tace"ke wannan ai duka 3cm,ku koma kawai bama yanzu zaki haihuba sai kinkai yamma........ai ban bari ta k'arasaba na shak'o wuyanta cikin azaba nace"karya kike wlh,muguwa Azzaluma wlh baki isaba saikin cireman wannan cikin,kicireman shi ko in kasheki muguwa Macuciya....." Ba karamar shak'a tayiwa wannan likitarba cikin wuya tace"ke sakeni kicikani yoni naimaki cikin,sadda kike shan dadinki ni saninai,shine zaki huce haushin kaina......sake fizgota nai duk su annie sun rik'eni amman kamar mai hanun doki sunkasa kwatar ta wani uban nishi na saki nace, "Don uwarki ni ban sha dadiba,ubanwa yace nasha dadi,zaki cireman kokuwa saina cire kanki.........duk yadda kake tausayinta sai kayi dariya,yadda duk ta haukace gashinan ya warwartse,ta had'a wata uwar zufa ta masifa......ganin duk sun kasa ansheta yasa ya isa wajen yace"ku aketa pls,,,,,,,likitar zaro ido tai jin ance su ummi su saki khairat,kallonsa take da idonta daya fito sosai kwallah ta cika,tace"haba kaikuwa idan aka saketa sokake ta kashini." Shikanshi dariyar yayi don wannan dramer dole tabaka dariya. Yace"bazata kasheki ba ku saketa Annie kuga." Sakinta sukai matar tasake zaro ido jin yadda khairat tasake shaketa tana nishi,da huttai tana wani irin gurnani. Cikin sanyin jiki ya riko hannunta yana goge mata uwar zufar da takeyi,yace"sorry saketa kinjiko janki take,ko minty biyu bazaki k'araba zaki haihu,saketa tsokanarki take." Kamar magic sukaga ta saki hannunta dake kan wuyar matar,tana dalalo ido takalli Areef tace cikin nishi da shashsheka"pls kace masu sufitar mun da cikinan wlh kashenj zaiyi plsss.........tafad'a hawaye na silalowa jiyai shima kwallah sun cika idonsa don tausayi,da yanada ikon ciremata ciwon da takeji ya mayar kanshi da bazata sha wannan wahalar ba. Cikin lallashi da lalama da babu wanda yasan Areed ya iya yace"sorry my angel,zasu cire maki yanzu bada jimawa ba,kiyi hkr kedai kibar gardama komi nace kiyi karkiyi gardama kiyi kinko,inkikayi gardama bazasu cire maki shiba." Duk da yadda nakejin wani irin masifar ciwo hakan bai hana ni cewa to ba,........su ummi kallonsu kurun suke suna mamakin yadda yake lallashinta,bayan su sunyi kamar ma zugata suke. Kamani yayi muka sauko daga kan gadon. Ummi tace"inazaku kuma." Baice mata komiba toilet suka shiga alwallah yayi man,sosai nidai banda wash da innalillahi danake kira ban komi,itama innalillahin shiyace inyita kiranta,don bakina dimaucewa yake inkasa yin adduar. Fitowa mukai yashimfid'a kallabina k'asa yayi ya d'auko hijab d'ina yasaman,duk suna kallona. Zaunar dani zai nace daker"zan iyayi atsaye." "OK good daure kinjiko insha Allah kina gamawa zasu cire maki wannan cikin." Sallar naeyi daer na runtse ido,ban tab'a sanin haihuwa zaune tada d'uwawunta ba sai yanzu. Raka,a hud'u nai adaddafe daker na sallame,nafashe da kuka ina cewa. "Kuwa girman Allah kurabani da cikin nan wallahi kasheni zai........hannu ya d'ora kan lips dina yagirgiza man kai,idonsa duk kwallah sun cika su,yasha fa kaina yace"karki sake cewa haka,maza kiyi addua kuma duk adduar da Annie ta karanto maki cikin mota suzakiyita nanatawa,nasan kinsansu kinkuma iya.oya maza kiyi kowace sau uku uku kiroki allah duk abunda kikeso daure wa zakiyi kinjiko,ina murd'e-murd'e da hawaye nace to.likitar tace ma su ummi "wannan yaron akwai dubara,hakan da yai shine daidai,don bazamu iya control d'inta ba gaskiya ya iya kula da marar lafy." Su kansu su ummi abun ya burgesu,ganin suduka babu wanda ya iyayi mta wannan. Inayi ina kuka da murje murje, idan ta katsa saina mamuk'eshi gadagam duk shaddarsa nayi mata sqeuzing,ba damuba lallashina kawai yake mun dauki almost one hour sannan dr tace bari tasake dubani,kasamcewar dana gamar sallar ba zaune nakeba,yawo nake cikin d'akin,inta motsa idan na kamashi shikanshi sai yaji ajikinsa.amman ba damuba,sannu kurin yake mun. Tana dubani tace"wow it's 7cm insha Allah yanzu zaki haihu kedai sake dagewa kina yawon,daure kinjiko insha Allah yanzu zaki haihu." Zuwa lokacin jikina yafara galabaita duk karfina yafara karewa,durk'ushewa nai ina murzarshi sai hkr yakeban bansan ma yanayi ba,can wajen karfe shad'aya na safe data dubani tace aiga head nan ma,yah yafita shida su ummi. Duk inda hankalina yake ya tashi nishi nake sosai ina rikea wuyar rigara ga,nace wlh baifita babu inda zaije........atakaice danai maishi wani irin rik'o saiga kukan jinjira,wata irin damk'a nai mashi wata jinjirai tasake sillob'owa........haba tuni na some.nanfa duk hankula suka tashi,tun lokacin ake nemo numfashina har azahar abun ya faskara,Areef kuwa kuka yake kamar Allah ya aikosa,rirs haka yake kuka,duk su Abbu sunzo,da su maah kowa yazo jin khairat ta haihu yan biyu amman daya ta rasu,sannan tunda ta suma bata farkaba tunda .........cikin ikon Allah gaf da la,asar tafarfad'o wata nannauyar ajiyar zuciya yasauke,baibi ta kan jaririyarba don gudar har anbinnota,gwanin ban tausayi,kowa baiso rasuwar taba amman ya suka iya,sungodema Allah ma da yasa uwar ita tafarka. Kuka na nasha jikin Abbu jin cewar jaririyar daya takoma,sosai nake kuka har saida akaiman allaurar bacci sannan baccin ya saceni ina sauke ajiyar xuciya. Tunda yaga tafarka yabar asibitin. Gida yaje yasha kukansa kamar karamin yaro,don wani irin kishine maizafi ya turnekeshi,wai yau *ABIN CIKIN RUHINA* ce tahaihu da waninsa,shikenan yarasa abunda yake kwad'ayi,dukda badanshi yake sonta ba,Allahne kadai yasan yadda yake kaunar ta,amman baisan taya zai mallake taba,yanajin kunyar sake tunkarar Abbu da maganar ta,don kuwa yasan wancen karon bai kyautaba maiba. Amman ya ya iya da azabar da soyyyarta ke ga namai,ga wannan kaddareren auren da ummi ta takura saiya aureta,saboda tana diyar qawarta. baisake komawa ba wanka yayi yafice office don yana da aiki sosai,hankalinsa kwata kwata yana kan khairat,don ya tsorata sosai ganin halin da take ciki dazun. Duk da irin yadda jikinsa ke tsananin ciwo kuwa,don yasha damk'a bakad'anba kafad'unsa kamar yaji targad'e da cinyoyinsa,daker ya iya tuka kanshi ga bacci cike da idonsa amman sanin ayyukan dole yayisu yau yasa ya hkr ya tafi. ********* Kwanana biyu asibitin,sabida jinina daya hau don mutuwar jaririyar ta kasa barina,nasha kuka sosai saida naga b'acin ran Abbu sannan nayi shiru na hkr nabar kukan gaban mutane amman dana kadaice sainayi,saboda yadda naso ace naci kawa dr alkawarinsa na mallaka ma umminsa guda,yanzu ya zataji babu dai kokadan. Nai mamakin rashin dawowar yah Areef,saibaza ido nake inga yazo har aka sallame mu baizoba,sanda mukazo gida angyara mana d'aki guda nida babyna,salma kamar ta had'iyae babyn,itadasu mimi sai nan nan suke da ita,yah meenah kuwa tani take sai sannu takeman. Ranar umminsu tazo kasancewar batanan randa na haihu,rungumeta nai ina kuka nace"ummi kiyi hkr naso ace baby ta rayu nabaki ita,kiringa ganin jinin dr kina tunawa dashi,saidai kashh Bansan meyasa ubangiji ya ansheta ba .........kiyi hkr plssss." Lallashina take itama tana goge kwallah tace babu komi wannan ma Ta wadatar uabngiji yayi mata albarka,yakuma rayata yasaka tayo halin mahaifinta. Ranar nayi kuka saboda tunawa da mijina nai mashi addua sosai tare da abunda nahaifa,wata irin kaunace nakemata nan take Abbu yayi mata huduba da sunan ummin dr watau *maryam* aikuwa ba karamin dadi tajiba don hada kwallarta taita sunbatar babyn tana hawaye,kafin tatai nace saita fadi nickname din daza ringa fadamata daker da sidin goshi nasata tafada tace akirata da *Airah* sunan yayi matukar dadi saidare tatafi. Ina tunanin ganinsa da daddare amman har wayewar gari baizoba,annie keman wankan jego intayi mata shagwaba. Airah kuwa ummi ke mata kusan kwana hudu kenan,duk wanda yakamata yasan anyi haihuwar angaya mashi,husna kullum tanan saidare yah shahid ya maidata. Ina zaune falo inata kuka saboda ummi ta tsareni sananba Airah nono,nikuma zafin danakeji yasa nace nidai aa,shine ta ulaman bulala dole nabata ina hawaye itakuwa tsotsa kirun take kamar Allah ya aikota.......kamar ance na kalli kcofar shigowa naganshi yana murmushi,bayansa wata budurwace fara tas kamar zabaya,tasha gayu kamar zata zab'en sarauniyar kyau,babu karya akwai kyau jinai kirjina yabuga. Pls share it. Mrs bb ce Mom muhseen. Follow me on watt pad Humaira7531. And my what's app no 09034722970 [7/5, 7:12 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 46. Wani kullutune ya tsaya man ga mak'oshi,daker nake had'iye miyau,banma lura ba ga hanci na keta gwagwad'a mata nono,saida ummi ta kaimin duka ga baya"don ubanki kasheta zakiyi ki kalli gabanki." Sai sannan naja numfashi sannan na maida hankalina kan Airah,amman badan ina cikin natsuwata ba. gaishe da mutanen wajen tayi,tana gaida su ummi cike da kunya. Annie saijanta take wai amarya bata yawo,kartayi bak'i,basusan wadannan kalaman jinsu nake kamar wuta.mimi ce ta kawo mata lemu da snacks,suna ta janta da hira harda salma,kmar na kamasu da duka haka nakeji. Kusadani yazo ya zauna yana danna waya,dama tuni su ummi sun koma ciki,Airah baci tayi ysa na maida nono na ina rik'e da ita ga hannun. "Oum Airah ga zulfa,a tazo ganin baby baku gaisaba,saida nayi daker na fizgo murmushin da iyakarshi kan lab'b'ana,nace. "Sannu da zuwa." Tana murmushi itama tace"barka khairat Allah ya raya Airah." Daker nake magana "ngd sosai ga tanan,na mik'ama shi ita yabata sai kokarin ganin yasaka idonsa anau yake nak'iya,.ansarta tayi tana yabawa da kyanta don Airah abun biyu ya hade mata,don dr kyakkyawane sosai haka nima badon yaban kaiba,nasan im beautiful more. Hirar su suke kamar sun saba da ita,salma damar gwanar surutu. Husna ta fito daga ciki tayo sallar laasar suka gaisa ta zauna gefena tana mun rad'a. "Waccen ce kishiyar taki." Tureta nai ina banka mata harara nace"banson iskanci,karki sake mun haka don't like." Dari ya tayi tana rufe baki duk yana kallonmu yace mata, "Husna gulma ko,mekuke cewa." Sanin danai husna ba karamin aikinta bane ta fadi abunda tace yasa na tashi zanbar wajen,naji bakuwar nacewa"ansheta khairat wucewa ma zanyi wlh inason zuwa saloon,saimun dawo suna." Cikin rashin walwala nace"bawa mimi ta goyata zanje na kwanta inajin bacci,kigaida gida mungode." Nayi wucewa ta shiya tashi ya rakata tayiwa su ummi sallama,sannan suka fita ya maidata. Gaba d'aya hankalinsa yana kanta sauri kawai yake ya dawo yaje gareta,duk da baisan me zaice mata ba,amman yanada bukatar magana da ita yayi tsananin missing ganinta kwana biyar,sadda yashigo get di n anata kiran sallar isha,i dole tafito yadauki buta wajen maigdi yayi Alwallah yashige masallaci. Yau wankan magaruba mukai,don fitowa ta kenan ba adora ruwan da wuri bane shiyasa. Ina daure da towel ina goge jikina da wani,ummi kuma nayiwa Airah wanka sai kuka take,ummi na mata tsiya wai raguwa.....dariya nake masu na zauna ina shafa mai harta gama mata sannan ta mik'omun ita. "Anshinan kinji ko mijina nacan najirana kina iya shiryata." Shagwabe fuska nai nace"wayyo ummi wlh ni ban iyaba kar nakarya mata hannu,plss ki idasa ladarki shima dadyn ai bazai ce komi ba inkikace Amaryarsa kika yiwa shiri." Hararar wasa tayi man tace"zan makeki wlh nikadaice ga mijina har abadan,don haka inma baki iyaba ki koya,kinjama daga yau kece mai shiryata,nan gaba ma wankan ke zaki ringa mata."ficewa tayi tabarmu murmushi nai ina daukota inajin wata irin kaunarta cikin raina, "Kinji wai sweetie,ummi kishi take da ke karki anshe mata miji,kyaleta haushi takeji kinfita kyau." Na sunbaci goshinta ina dariya kamar almara itama tayi dariyar,nanfa naita dariya ina biye mata kamar zararrah. Riga na dauko ta bacci na zira sannan na dawo ina shafa mata mai,kamar ina tsoranta haka nake shafa mata shi. Bayan dawowar sa masallaci ya zube falo duk hira ake,ana kallo dan zauna wa yayi ya lumshe idonsa yana sauraren bugun xuciyarsa,yunwa yakeji amman son ganinsu itada baby ya danne yunwar.........Annie tace "kana lafiya kuwa Areef." Idona ya danyi ja yace "ba komi kaina ke ciwo." "Ayya sannu kaci abinci kasha magani." Tashi yayi nufi cikin gidan karo sukai da salma tace"sorry yah ban ganiba," "Ba komi ina khairat." "Suna daki tana shirya baby Airah." Wucewa yai itama ta wuce sadda ya tsaya bakin kofar jiyai numfashinsa yana d'agawa,runtse ido yayi ya bude sannan ya shiga da sallama. Tun d'azu nake son saka mata kayan na kasa,daker nasa mata pant. Waigowa nai jin motsi wajen kofa.........wani irin dokawa gabana yayi dandanan nad'an sha mur kadan,na ansa ciki ciki. Isowa yayi ya tsaya bayana yana kallon mu sai jagwalgwala ta nake,me zatai ba kuka ba ni duk na rikice tunda yashigo,nama rasa me zanmata. Jinai kurun ya sunkuyo ta bayana ya anshi rigar,sannan ya dawo gabanmu ya zauna daukarta yayi yana cewa"sorry my angel,ur mom she do not know yadda zata saka maki kaya gashinan duk ta karairaya maki hannuwa badole kiyi kuka ba." Kirjina ya bada rass jin yace na karyata,cikin rudewa nace"dagaske najimata ciwo,wlh ban saniba ummi ce tace dole saina saka mata,wlh kuma ban iyaba."sai hawaye sharrrrr "donAllah mukaita asibiti,aduba karta mutu itama." Ina kukana ina kallon yadda take shashsheka. Murmushi yayi yace"ruwa ruwa to wasa nake,saiki goge hawayen." Wata ajiyar xuciya nayi nace"ina sonta banson ta mutune kamar dayar." Rigar yasaka mata yana cewa"dont worry insha Allah keda ita ever and ever." Maganarsa tamun dadi rirrigata yake yana kallon fuskarta yacigaba da cewa. "Inama zaki ban ita idan anyi bikina ta zauna wajena,zulfa,a zata kula da ita fiyeda tunaninki because she love her so much,kamar yadda nakeson Airah itama tana sonta,pls inason Airah inaji kamar cikin jinina take,zaki ban ita oum Airah.? Tunda yafara maganar naji zuciyata tana amsawa saboda dukan da take,kalamansa jinake kamar ni yake fad'a masu,saidai jin cewar inbashi ita zulfa,a zata kula da ita duk ya wargaza man mood dina........bansani ba bansan yadda zan fasalta yadda nakejin kishin wannan matar ba,banson ko sunanta ana kira man.taya ma yake tunanin zan iya bashi y'ata ta zauna karkashin ikon wata,watarma wadda nakejinta tafita daban daga cikin mutanen da suke haska farincikina.......jinaima kwallah tacika idona,ban bari tafitoba tunda daman kaina k'asa yake......jinai ya sunbaci kuncinta yace"kinji inason Airah zakiban ita." Still kaina kasa nace cikin sanyin murya ina control din mood dina "kayi hkr bazan iya mallakawa kowa sweetie ba saboda nafi kowa bukatarta,kayi hkr sadda akai auren naku Allah zai baku taku kuma." Shiru yayi yana rik'e da ita har tayi bacci kafin ya mik'e ya isa ga gadonmu ya sakata cikin net dinta,bayan yasake sunbatar ta yace"sleep tight my angel." K'ofa ya nufa baice komi ba har ya b'ude kofar nace batare dana daagoba"tnx for helping me during labour." Idasa ficewa yayi bayan yagama jin abunda zance. Kwata kwata ranar ban iya samun bacci mai dadiba,kawai ina imagining ne yadda yakeji lokacin dazanyi aure,daman haka yakeji haka kishin yake wannan zafin duk na kishinne,da ker da taimakon kaina nayi bacci. Areef wannan daren yasha kuka,don duk sadda ya kusanci inda take kamar karamai wutar sonta ake,shiyazayyi da wannan auren bazai iya yin rayuwar aure mai dadi ba alhalin zuciyarsa daruhinsa gabaki daya suna gawata,bazai iyayimata adalciba zai tauyeta zai cutar da ita,taya zai ganar da ummi cewa bason zulfa,a khairat yakeso. Taya zai fahimtar dasu cewar itace farincikinsa,itace burinsa tsawon shekara aru aru.ina zai saka ransa soyayyar da yake mata shikanshi tana bashi tsoro,Amman sanin halin ummi shike tada mashi hankali,don ko duniyar zata tsaya bayanshi akan bazai auren nan ba babu wanda ya isa ya canza mata ra,ayi saidai idan itace taga dama. Jahid najinsa yana sabbatu yayi kamar baijiba,don yayi alkawarin bazai ce mashi uffan ba,ai kukama yanzu kafara Areef indai akan khairat ne badai ka wulakanta ta ba abaya tukunna ma dai. ********* Anyi sunan baby Airah taro yayi kyau,maijego da yarta sunsha kyaututtuka kamar hauka,don kudi masu sunan kudi khairat bazata iya lissafa yawansu ba,daga mai dubu biyar sai abunda yakai sama. Sunsha kyau kamar kasace su karuga,masha Allah Airah tasha gayu kowa sai saka Albarka yake,gidan yacika sosai yan uwa nanesa dana kisa kowanyazo sai daidaiku da basu samu zuwa ba. Haka dangin dr sun zo kuma sunyi bajinta sosai,ranar ma nasha kukan rashin dr don yadda yaci burin sunan lokacinan komi yace ai za,ai sunan da babu irinsa duk abuja.Ashe baida rabon gani Allah kakai rahma kabarinsa,itace adduata akodayaushe. Taro ya watse saidai muce Allah ya raya maryam (Airah). Bayan suna da sati biyu Areef ya shirya zai koma spain,saboda bai idasa aikin sa ba zaiyo wata guda,ga biki nata gaba towa baifi wata biyu ba,Abbu yaita fad'a cewar ba zaije ba ya tura yaronsa na office yatattaro mashi duk wasu ayyukan,amman taya zai tafi ga hidima anayi. Haka dadynsa ma yace dadynsu yah meenah kurun yabashi goyon baya,yace ayi hkr yaje har yadawo abunda duk ya kamata ayi za,ai mashi sadda ya dawo saiyaji da sauran. Kana dole suka hkr suka barshi ummi kiwa sai fada take, "To wlh bazaka tai ba saika bada kudin da za,a idasa hada lefe,aibani zan maka lefenba." Muna falo take fadarhaka nidai ina gefe inashayar da Airah,maah tace"haba yaya,don Allah kibarshi haka mana tun safe kike mashi fad'a ko abincin kirki baici gidan nan ba,kin tasoshi gaba sai bambami kike,kwana nawane idan Allah yakaimu,indai donta lefe ki kwantar da hankalinki wlh ni nagama hada komi." Duk kallon mamaki sukwa maah,Annie xtace yaushe duk kikai bau sani ba,Amma gaskiya kin shaacemu." Dariya tayi tace"kallonku kurin nake nariga nagama da wannan babin wlh,nabar maku nasu mujahid da Shahid." Ummi tace"ai haka abun yake kinso danki ko zamugani dana shin danasu nawa zaifi kyau." Nan sukabhau hirar kayan,already ni nagansu nasan kuma daman nashine. Kallona yayi nai saurin kauda kai,don tun wannan maganar bamu sake maganaba illa gaisuwa, Miko hannu yayi yadauki baby Airah data gama shan nono,bance komi ba ya shige ciki da ita. Nasan meyake nufi idan na matsu inbishi in ansota, ya samu damar yimun magana,buris nai dashi banma motsaba nake ma Su maa maganar makaranta tata,don su yah meena final exams suke yanzu. Tace na bari Abbu ya dawo inmai magana tasan shima cewai zai inbari Airah tayi kwari. Tashi nai nazuba abinci naci har karfe goma bai dawo da itaba,babu kuma wanda ya lura balle yace ina take.gajiya nai nanufi daki nayi shirin kwanciya wauata dake gefena naji tayi kara alamar tex massege,dubawa nai naga yace _Come and take Angel_ tsaki naja najefawayar can gefe inacewa"wlh banzuwa inka gaji kakawota d'an rainin wayau,baka ga komi ba wlh saika gane baka da wayau." Mimi ta shigo ta zauna gefena tace"oum Airah shawara nazo muyi." Tashi nai ina kallonta nace"inajinki mekefaruwa." Murmushi tayi tace"babu batun b'oye b'oye,kinason yah hargobe,shima kuma bama sainace maki yana sonki ba,kinsani.........enough mimi bansani ba,bansan komi yake ciki ba."........Aa oum Airah karkiyo saurin katseni,wlh duk wanda ke gidannan yasan halin dakuke ciki,kuma nayi imanin anyi shiru ne don aga iyakar gudun ruwanku,bawai ba asan halin da kuke cikiba." Cikin fushi nace"mimi pls kibari banson in nuna maki fushina shin waima meye naki ciki nacemaki ni zan sake aurene,nida aure saina gidan aljannah insha Allah.,and pls idan wannan maganar ta kawoki workout." Babu alamar fushi ko jin haushi kan fuskatar ta tace"shikenan,zaki gane menake nufi ni mai son farincikin kuce wlh i wish inganku kun mallaki juna..........oh may God,wai mimi nace maki knason mallakarsa ne..........kofar da aka bude yasa nai shiru,amman naso injuye haushina tsaye yake sab'e da Airah da alamar tayi bacci. Mikewa tayi tace"saida safe"banza nai na kyaleta tazo zata wuce yawurga mata wani kallo,tab'e fuska tayi tace"wlh nifa banyi komiba........common get out yaceda ita." Fita tayi sanna ya tura k'ofar da kafarsa,jallabiyace maroom da wani zanen kwalliya gaban ta,tayi masifar fiddo kyansa,haskensa ya sake bayhan cikin rigar,kauna kai nayi ina zaune fefn gadon ya k'araso yasaka Airah cikin net ya rufe sannan ya tsaya gabana idonsa akaina,aijinai kamar na kurma ihu azo afita dashi. Tsaye yai rungume da hannunsa perfume dinsa sai bugarmun hanci yake,duk yayiman gigirin bisa kai. "Nakiraki kin nunaman ban isa ba ko." Sai lokacin nad'ago kaina na kallai,saidai nai nadamar kallon don jinai zuciyata tana man wata irin rawa,sadda kai nayi nace. "I'm sorry banji kiranba shiyasa." Stool yajawo ya zauna gabana sosai kamar zai shige cikina,yace"ban kirakiba text nai maki." Banyarda nasake kallon saba nace"Ayya ban ma san inda wayar take ba banganiba,sorry again." Numfashi yafesar har kan fuskata runtse ido nai na wani lokaci na bude yace, "What mimi said." Jinaigabana ya tsinke yafad'i,nashiga uku mezance mashi. "She telling about me and u." Nabani karfa ace yaji. "What she tell." "Nifa babu komi kawai tana maganar.........karkiyi karya naji komi,don haka kikwantar da hankalinki indai nine kinsamu,inhar dai zaki iya zama da kishiya ba damuwa zan hada dake." Wani irin haushi da bakinciki suka cikaman zuciya cikin fushi da masifa nace, "Ni bance komi akanka ba,hasalima ni babu wanda ke gabana inbanda Airah,bazan sake aure ba balle nayi ma mijina butulci,ni bazan iya mashi reable ba,don allah karka bata man mood dina nimezan dakai plstkatai dakinka kwanciya zan.............fizgo hannuna yayi idonsa cikin nau dasuka cika da kwallah yace, "karya kike,u are lie kina sona kifito fili kifurta man tunkan lokaci yankure maki,karki damu zan soki ayadda kike i will manage u..............wata irin fizga naima hannuna na kwce n tureshi daga gabana,hawaye tuni sun wanke fuskata cikin fushi da kuka nace. *"bansonka! I hate u too."* "Ko maza sun kare bazan aure kaba,duk wanda yace maka ina sonka ya yaudareka,yes before bikina am sure Ilove u love u too,amman after and now Am sure 100% sure I HATE U I HATE U YAH AREEF,NA TSANEKA BANSONKA kadaina tunanin akwai tsarin sake yin aure cikin rayuwata,zaka yaudari makaryaciyar zucoyarka ne abanza don wlh bazan aurekaba ko duniya zata tashi ahalin yanzu ................idonsa kamar anzuba garwashi fuskarsa tayi jajawur,ya fizgoni ya rike kafaduna yana girgizani,cikin daga murya yace, "Karya kike khairat,u still love me ever and ever,kuma sai in aureni nine nan mijinki babu wani duk fadin duniyar nan saini.........kofar dakin aka turo nafizge daga gareshi ina koma wa gefe ina cigaba da kukana. Ummi ce da Annie sai su yah jahid da anty shida sai salma da yah meenah,shigowa sukai annie ketambayar lafiya. Dagani harshi babu mai iya bada ansa,kukan danake yasa ummi ta sake tunzura ta daka mashi tsawa tace, "Karkasake in sake tambayarka ,mekayiwa khairat kukan me take hayaniyar mekuke,dakai nake don ubanka.............mahana zaiyi ta daga hannu cicin karfinta ta kwasa mashi zazzafan mari......har cikin kokon raina naji marin,har saida na dago ina kallonta. Kaina tayo tana masifa, "daki ka dago rama mashi zakiyi don ubaki,nace rama mashi zakiyi ana tambayarku kin maida mu shashashu,........." Kukana naciga dayi Annie tace"kiyi hkr inajin can tsakaninsu ne,ki kyalesu." Ummi tankamana harara sannan tafita kowa yafita,Annie ce kirin bata fitaba tura kofar tayi taiso inda nake tana bubbuga bayana. Tsawkn lokaci tana lallashina har nayi shiru. "Wannan kad'ai ya isa ya nuna mana cewar abunda muke tunani haka yake,kowanenku yana son d'an uwansa.........saurin katseta nai nace"Aa Annie banson sa,ban kaunarsa pls kice yafita rayuwata,bazan iya wa dr kishiyaba......"shima cikin fushin yace"kinjiko Annie abunda take cewa,taya kunnena zai juri sauraren wadannan kalaman nata masu d'aci." Annie tace"ya isa haka ban son sakejin maganar kowa,yarage naku ku sasanta kanku,yarage naku karku sasanta kunaji kuna gani zaku sake rasa junama wannan karon,don haka bawanda zan hana duk abunda yaga dama,don haka shawara tarage gamai shiga rijiya,don ingaya maku iyayaenku maza babu wnda baisan wainar dakuke toyawa ba,hakan kuma bai hana aurenka kai Areef,don haka kunga tafiyata." Tafita tabarsu nan shima daga baya yajuya yafita cikin tsananin fushi.........zan iya cewa wannan darw babu wanda ya rintsa cikinsu,gashi gobe zai wuce spain early morning. Share it pls. Mrs bb ce Mom muhseen. [7/6, 7:25 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 47. Washe gari tun asuba da mukai wanka nida Airah bamu tashiba sai eleven,sadda na fito ina sab'e da ita zanyi break naji gidan ya rage hayaniya. Lami mai aiki na tambaya ina mutan gidan tace"maah dai tana ciki itada su shahida,salma da mimi sunje rakiyar Areef,.........tundaga sannan naji jina gaba daya ya dauke bansan me take sake cewa ba. Zamanai da Airah ga hannu kamar kwai ya fashe man ga ciki. Kamar marar lafiya haka na koma,kukan airah ya dawo dani daga duniyar tunanina.har cikin raina banso tafiyar ba,duk da haushinsa dana kwana dashi,hakan bai hana ni jin kewarsa ba. Dayanzu ya dauki baby bai maido man ita sai tafara kuka kokuma tayi bacci,hawaye naji sun cika idona nai saurin sharewa saboda mutsin danaji bayana. Maah ce da anty shida suka shigo falo,ina kan dining nayi tagumi ga Airah sai kuka take bam jin kukan,saboda halin da zuciyata take ciki. Jinai kurun Anty ta dauketa tana rirrigata,maah ta banka man harara. "Wahalalla,kicigaba da yi kar Allah yasa kidaina,." Idona cike da kwallah nace"maah menayi menamaki kuma." Tsaki taja ba wuce warta ta cigaba da huddodinta,kuka na rushe dashi saboda banson abunda kuma nayi ba,meyasa maah keyin haka duk dan sabida ita nake treating yah Areef haka,Amma Ku ma still ban yi daidaiba............Anty shida tace"ansheta kibata tasha sai kicigaba." Ansarta nai natashi na koma dakina abincin da banci ba kenan,yini nai daki duk mai son ganina can yake samuna. Babu wanda yadamu da damuwata,abun ya hademan biyu koma ince uku. Ga soyayyar wanda nasan har abadan bazan samesa ba,ga canjin hali daga maah sai hantara ta take,.........ga kewa da tsananin begen Dr sai tunaninsa ya dawo man sabo. Ganin abun ya isan naje na samu Abbu da safe kafin yafita. Duk nayi zuru zuru cikin kwana biyu ita kanta airah,don Annie na shigowa tana ansarta da wuyar da xata sha tana da yawa,don ma tafara wayau yanxu. Break yakeyi keyi na samu Maah tana saving dinsa,harara ta watsa man naji kwallah sun cika idona. "Ta alkairin abbu iso mana." Shiga nai ina rakub'ewa jikin kunera nesa dashi,ina goge kwallata, "Zomu Karya nasan baki kaiga yin nakiba," Girgiza kai nai cikin sanyin murya nace"Aa kaci naka Abbu idan nafita zanyi nawa,dama nazo ne kan batun makaranta anshiga sabon session." Kunun gyadarsa ya kurb'a ya saka tsokar nama baki sannan yace"nasan da haka,zan tura jahid sai yayi maki duk abunda yadace.,sai mekuma." Sadda kai nayi nace "bakomi" Na zo tashi yace "zauna ban sallameki ba." Zama nai ina wasa da yatsuna........duk gudan yafita kaina ummi kanta duk ta canza to wai menayi masu haka. "Meke damunki kwana biyu,bakida walwala kina yini dki bki shiga cikin y'an uwanki...........meke damunta daya wuce wahala,yarinya tana son kunyatani tadauki son duniya ta dorawa mashi,kamar shikadaine autan maza........"duk maah ke wannan maganar. Tuni hawaye sun wanke fuskata shashshekar kuka nake kasa kasa,saboda jin abunda maah tace,ni yaushe nayi wani abu har da zai nuna masu cewar har yanzu inason sa,to banyi karya ba inasonsa har gobe amman me wlh yadda ta nuna bata sona dashi nima shiyasa nake mashi duk abunda nai,shine zata ce haka. "Badake nake maganaba saudah karna sake jin bakinki." Ta banko man harara nasadda kai ina cigaba da kukana. "Bakiban ansa ba ta Alkairi." Ina sharben majina nafara magana cikin rawar murya. "Abbu maah ce..........sai kuka ya kubceman na tayin sa ina jan numfashi bai hananiba don daman kukan shine nakeyi nasamu sauki, Saida nagaji nayi shiru nacigaba da cewa, "Abbu bansan menayi mata ba,tun ranar da yah yatafi take daureman abu kadan taita hanta rata,kuma taki fitowa fili ta gaya man laifin danayi mata,inma don yah Areef ne wlh tallahi Abbu bana kulashi,ban shiga sabgarsa,shine yake damuna saboda ita ko maganar arziki bamuyi dashi.inbanda gaisuwa amman shine tace haka,wlh niban karya dokarkiba........na karashe ina kukana." Ajiyar zuciya Abbu ya sauke yana kallonta cikin kallon tuhuma alamun ransa ya baci, "Kin kyau ta saudah,yanzu da kanki zaki jefa wannan baiwar Allah kuka kijefata cikin kunci da damuwa,bacin wadda take ciki.shin kokin mance lalurarta ne saboda wani dalili can naki nabanza zaki ta kura ta,shin haramunne don ta so Areef,koko shi haramunne don y sota.kinsan dalilin ubangiji daya d'auke mijinta,kikasan hikimarsa nayi imanin saboda khairat rabon Areef ce shiyasa ya dauke mijinta,don shi yasameta. Kifita sabgar Allah kifita lamarin ubangiji,kebaki isa kihana ba haka baki isa kisaba,don sai Allah yanuna maki ikonsa,babu ruwanki daga yau namaki hani da shiga tsakaninsu." Maah cikin b'acin rai tace"yallab'ai ni ban isa shiga tsakaninsu ba,akwai abunda ya tunzurani har nake mata haka don tasama ranta babu ita babushi" Wani kallo yayi mata yace"mekike nufi inajinki." "Tun ranar dasukai hayaniya ita dashi Areef din,yaya ranta ya b'aci don tazo har d'aki ta sameni,cewa wai me khairat take nufi tana nufin har gobe tana kan bakata na son Areef,to ingar gad'eta don anriga angama komi kan batun auresa,kuma babu mai hana wannan auren na Areef,don tunda zulfa,a taga areef a UK take ma sonsa,kasancewar mahaifiyarta tasan ummin,sai tayi mta waya kancewar aikuwa yarta taga Areef ta haukace kanshi,babu wani jayayya tace insha Allah saiya aureta,mafarin taita taimakawa wajen ganin khairat bata auri Areef ba tun wancen karon. Saboda taja mashi kunne kuma nima ta kalailameni da kalamanta har nayarda da ita.to shinefa ta sake jaddadaman cewar mai hana aurensa da zulfa,a sai Allah inmata magana ta rike jawarcinta.........wannan abun shine yafi komi yiman ciwo yallabai,ashe har yaya hafsa zata ki jinina saboda wani abun duniya,ciki daya muka fito amman ta ki diyata da d'anta,taya kake ganin zanji dadi hawaye suka cika idonta tab........sharewa tayi yayinda nima nawa kukan ya k'aru tace"wlh zanyi farincikin aurensu domin dukansu nice na renesu nasan halin kowa,amman taya kake tunanin zan yarda khairat ta cigaba da nacewa kan haka,dole tasa nayi mata haka badan komiba,kayi hkr banyi nufin b'ata ranka ba." Rarrafowa nai na rike kafafunta ina kuka sosai nace"maah kiyi hkr don Allah kiyi hkr wlh tallahi zan goyi bayanki,nima na janye daga kan maganarsa,dama kuma ba kulasa nakeba bazan taba aurensa ba,inacin mutuwa mai tonan asiri taya zan kasance haka,,,,,,nacigaba da kukana. Shiru yayi yana auna maganganun da ta gaya mashi,tabbas baiga laifinta ba domin kuwa ba neman kai suke da khairat ba,abune na gida wnda idan akayi kowa ziyyi farinciki,amman tunda hakane abarshi ahakan........ "Ta Alkairina,kinji duk bayanan mahaifiyarki,don haka banda abun cewa daya wuce kiyi hkr kibar komi hannun Allah,insha Allah zai kawo maki wani wnda zakiyi farinciki fiyeda tunaninki,fatana kiyi man Alkawarin kiyaue dokokin Allah,kifita sabgarsa tunda daman kince baki kulasa,to atai ahaka inso samuna ne kitai waje ki idasa karatunki." "Aa abbu zanso in zauna kusada ku,nai maka alkawarin kiyaye duk abunda kace." "Masha Allah haka akeso,Allah yayi maki Albarka." Nace"Ameen Abbu ngd,maah kiyi hkr kiyafe man don Allah banajin dadin yadda kike man kihi hkr pls." "Babu komi ya wuce kidai kiyaye,don zamu sab'a inhar nasake ganin wata hudda ta hadaki dashi,kina iya tafiya." Natashi na dawo cikin gida ina wondering halin ummi,lallai mutun ba abun yarda bane,taban mamaki banyi tunanin haka daga gareta ba. ********* Shirye shiryen biki ake bakama hannun yaro,don ankai lefen yah shahid gidan su husna,ankuma anshi na yah meenah itada yah harun,dayake bayan da wowarmu daga dubai ya koma saboda aikinsa,amman tare zasu dawo da yah Areef. Hidima ta nake kamar babu wani abu cikin raina,nan kuwa karkaso ka bincika karfin haline kurin da juriya. Shima ankai nashi lefen amman saboda basusan darajar mutane ba suka wulakanta y'ankai lefen,har kuka maah tayi saboda yadda aka anshi kayan cikin renuwa da wulakanci,wai ai yarsu tafi karfin wannan yame yamen. KO zinari babu balle gwal,saikace ba yar minister kudiba,,,,,,,bayan akwati goma sha biyu haka aka cika da kaya,wanda maah saida ta cika akwati bakwai biyar ne kurin ummi tayi mashi,ita kanta ummin ta tsargu sabida yadda taga maah tayi masifar canza mata,ba kamar da suka dawo daga kai lefen taje har falonsu ta sameta tace. "Munkai lefe yaya hafsa,ankuma wulakanta mu kamar yadda kikazata an watsamana kudin tukuici a fuska,ance gashinan suba mata lauta bane da arzikinsu idan da munsan bamuda arxikin yi mata lefen,da munfad'a bazasuji komi ba don sun ranta mana,ummi ta kadu dajin irin abunda yafaru,tana kermar murya tace"wlh saudah bansan haka sukeba..........kinsani yah hafsa,wlh kinsani aibatun yau kike tare da hajiya safara,un ba,i think tun bakiyi aureba.shine kike son ansar yarsu matsayin surikarki gidan da ba,asan drajarmu ba ba,sa kimrmuba basusa mutunci da karamciba,no problem gashinan ayi mugani,amman kisani bazan sake shiga cikin wannan hidimarba wlh tallahi kau." Ta juya ta fito tabarota. Jikin ummi yayi masifar sanyi sosai,don kuwa maah tayi buris da lamarinta,duk zafin ummi da fadanta ta koma kamar ruwa yacita,maah kuwa tayi fushi sosai abunka ga wanda bai saba irin wannan fushinba.......gidan duk yazama babu dadi wajen annie kurun nakejin dadi,duk da maah din ta sauko tabar fushin dani,amman kodayaushe bata da walwala don Abunda ummi yayi mata yayi bala,in daure mata kai. Airah tayi wayau sosai don watanta uku yanzu,dariya kamar gonar auduga wadda kuwa halin mahaifinfa,tana girma kyanta yana karuwa. Tuni muka gama wanka Annie ce kegyarani kamar wata amarya,har kunya nakeji tace aiba dole saika tashi aureba,dole kazama cikin kulawa don kowane lokaci mijin na iya zuwa. Jinta kurin nake don ni bawani aure dazan sake,rainon diyata ya isan da karatuna,don tuni nakoma yanzu ma IT muke nan wani private ne,wani lokacin gida nake barin Airah,don bata barina aiki idan anyi sallar azahar indawo inbata nono tasha,naba yah meenah ita don sun kammala nasu tuni,don ma tanashan priso tayi wata irin kiba gwanin sha,awa kyanta sai sake bayyana yake kowa yaganta yayita santi,gata da shiga rai,kuma bata rigima sai idan yunwa takeji ko kuma bacci. Tunda ya tafi na sauke layin sayasanni dashi,don ma karya kirani balle wani sakonsa na banza,bawai har cikin zuciyata inajin dadin abunda nake ba,banda wani solution daya wuce haka,babu anfanin inta saurarensa inasaka kaina cikin shaukinsa,soyayyarsa mai girmace cikin zuciyata inhar inajin muryarsa,bazan iya control din mind dinaba shiyasa mafi a,ala in nisanceshi. Agajiye na dawo yau Airah naga nina taita mik'o hannnu,hararata nai ina cewa"acici ko hutawa baki barina inyi to kwalelenki yarinya,nai mata gwalo." Kamar tasan menake cewa ta fashe da kuka,dariya nai zanruga mimi ta rikeni, Annie face"wlh bakishiga saikin bata,muguwa kibar yarinyar tun safe yau ko dawowar dakike bakiyi ba,shine kuma bazaki bata hakkinta bakini tsoran Allah." Dariya nai ina harararta itako sai miko hannu take, Ansarta nai mimi nacewa"Allah zai saka maki babynah." Yinai kamar zan maketa taisaurin matsaw. Saida nabata sannan na mikata ga mimin nashige ciki,don tafi yarda dasu itada yah meenah da Annie.ko salma bata son taje wajenta. Wanka nashiga najiyo wayata nata ihu bafitoba saida nagama,lokaci kuma ta tsinke kaya nasa nayi sallar la,asar ina sallamewa aka sake kira. Dauko wayar nai babu suna aman da alamun daga wajene,harga Allah ban tunanin shi bane na d'auka nace. "Assalamu alaikum." Shirune yabiyo baya nasake maimaita sallamar, Sai sannan akai magana cewa, "Baki tausayina khairat...........daskarewa nai inda nake don kuwa tunin duniya na gane shi......so nake na yanke wayar amman hannuna ya kasa,zuciyata dokawa take kurin inajiyo numfashinsa ahankali kamar wanda baida lafiya......jinai yace"pls dr ka sallameni wlh nagaji da asibitinnan haka." Silalewa nai bakin gado nazauna kasa,inajin kwallah na cika idona......cikin rawar murya nace"yah .......bak....bakada lfy ne." Mrs bb ce Mom muhseen. 0934722970. Share it plss [7/7, 6:36 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 48. Hawaye share share fuskata kamar ankunna famfo,numfashi ya sauke baice mun komi ba duk hankalina inyayi dubu yatashi, "Don Allah kayi mgn bakada lfy ne,meyasa baka sanar agidaba plsss kadawo gida hakanan,anan babu mai kulawa dakai........" "Idan ma nadawo karaman wani ciwon zakuyi,no need for that Zan zauna anan inmutu kinga kowa yahuta." Kuka nake sosai nace"Aa yah kabar cewa zaka mutu,don Allah kadawo gida akula dakai sosai insha Allah yadda kake tunanin abun bazai faruba." Lumshe idonsa yayi yanajin wutar kaunarta na sake ruruwa cikin zuciyarsa,dafe xuciyar yayi yace cikin low voice dinsa,datai sanyi kamar kankara. "Kina so indawo." Ina share kwallah na silale kasa na kwanta ina kuka k'asa k'asa daker na fizgo maganar nace, "Eh" Sassanyar ajiyar xuciya yaja yace"ki ansa man abunda zan tambayeki." Numfashi kurun nake ja saboda yadda nakejin kaina,banson meyasa zuciyta take man haka ba,inhar akanshine bana iya dogon fushi duk yadda nake son nisanta kaina,dana ganshi ko naji muryarsa dandanan zuciyata zata koma kamar ruwa.............daker nace "uhh" Shiru yayi tsayin lokaci banda numfashinsa bakajin komi,lumshe idona nai ina sairaren yadda yake sauka cikin kunnena,hawaye na silaloman inajin sabbin feelings akansa..... .......... *"sweetheart!"* Jinai duk tsikar dake jikina tana tashi,muryarsa tana ratsa duk wani lungu da sako na jikina still hawayen basu bar zuba ba,na kasa ansa kiransa saidai ajiyar zuciya da fizgar numfashi nake..............jinai ya sake cewa. *"sweetheart are u on d line!!!"* Wayyo Allahna duk'unk'unewa nai waje guda ina shashsheka,jikina yayi masifar canzawa kadaddabe wayar nayi ina murtsike-murtsike.............bakina yana rawa nasake cewa "uh" Numfashi ya fesar wanda yasani runtse idona ina jan numfashi,iskar dakin jinake taimun kad'an. *"did you love me?"* Cikin wani irin yanayi na cire wayar daga kunnena na kasheta duka nai switching dinta off. Wurgata nai kan gado nazauna nadunga gurzar kuka kamar Allah ya aikoni,can lungun bayan gado nashige kamar wata mage,nai mamakin yadda har na shige wajen. Sosai nake kuka don uku biyu ya hayeman,ga haushin kaina da tsanar halina nara shin zuciya da banayi akansa,ga soyayyarsa kaunarsa shauk'insa sunmun taron dangi,ga gargad'in maah yana amsa kuwwa cikin kunnena kamar yanxu take yiman shi,,,,,,,shin yazanyi da raina ina akeson insaka rayuwata ne wai,yazanyi.........yazanyi ya akeson inyi.............ne.........na fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciya......kamar wata zararra nikad'ai naketa magana ta.........waini na dorama kaina ne ehy,Meyasa har yanxu nakaa samun farin ciki dorarre,wannan masifa ta isan nagaji nagaji nagaji...........mimice tashigo da Airah nata kuka rage sautin nawa nai inajan ajiyar zuciya......."subhanallahi,khairat lafiya kukan me kike kinga yada fuskar ki takoma?ansarta bata tasha garin rarrafe ta k'umeka da table." Ansarta nai na ciro nonon nabata ina tsane fuskata da kallabina,zama tai gefen gadona tana cewa"komi yayi zafi maganinsa Allah,kibar dorama kanki damuwa karta zo ta haifar maki da wani abun nada ban." Cikin kunan rai nace"mimi wallahi zuciyata ta fara gajiya da daukar k'unci,inajin kirjina yana mun nauyi,narasa ta inda zan kama duk inda naje babu sauki,yanzu yayanku yakirani baida lfy banyi niyar saurarensa ba amman wlh mimi jin muryarsa duk ya ruguza man komi,tabbas duk wani kwane kwane da nuk'u nuk'u nawa,insonsa banda wani burin daya wuce mallakarsa,amman mimi akwai katanga tsakanina dashi,katangar mai tsayice bazamu iya ganin juna ba sai ankaudata,kinsan komi ya faru kinsan kuma sharad'in maah gareni,cewar muddin nacigaba da kulashi inta kamani inkuka da kaina.karma intunanin zata saurareni,shikuma ya huraman wuta yace bazai dawo ba saidai ciwon ya kasheshi acan,niban tab'a ganin bala,in *SO* irin namu ba taurin kai ya hanashi ya furtayana sona kuma bazai iya cewa yafasa wannan aurenba,shin ki fad'i man yazanyi.............duk yadda nakai ga sonsa da kaunar kasancewa dashi wlh mimi abun yafi karfina,bazan iyaba..........nafashe da kuka. Iyakar tausayi khairat tabawa mimi don ita kanta saida taji hawaye sun zubo mata,wai meyasa ummi tacika son ranta,yanzu ko tausayi basu bata,shi yanacan rai hannun Allah ita gatanan bak'in ciki zai kassarata cikin d'aki duk wannan bai isa yakai ta dakayar da auren ba,Dady baida wata damuwa inhar tace abarshi zaiyi mirna,don shima baso yake ba miye aibun khairat duk wanda yaganta idam ba yaga Airah bazaice iyace uwarta ba,don babu abundan ya canza daga gareta. Lallashina mimi keyi tana ban hkr tare da karfafaman guiwa,dayin addua hakanan naji koba komi nafadi damuwata nasamu relif. Biki yataho yau yah imran ya iso kowa yayi mamakin rashin ganin Areef,wanda ni nasan daman bazai biyo shidinba,tunda shima yagaji taurin kai irin na uwatai. Ita ummin aitasan bai lafiya amman sabkda karma ace afasa auren yasa bata sanar da dadynsu ba,saida yah imran d'in yadawo yake gaya masu cewar ai yana can satinsa biyu kwance bakda lfy,yace kua bazai dawo ba har sai idan na amunce aurensa..........kowa yashiga shock jin cewa. Baida lfy kuma serous serious sick ne. Dadyn su yaita fada yana cewa audaman Areef nason khairat baitab'a saniba,nan maah ta bashi labarin komi yadda ya faru abaya,da kuma abunda ya faru cikin wannan kwanakin..........kamar zai ari baki yaketa banbami ummi tayi sukuti kai k'asa,ansar no din dayake anfani da ita yayi wajen imran yashiga kiransa.......saida yakira sau uku sannan ya dauka baibari yace komi ba yahau fad'a, "Don ubanka karka bari jirgin karfe goma ya taso baka biyoshiba jibi,ashe kai sakaran banza ne loton banza,da wofi kana sonta baka tab'a gaya man ba,kabiyewa sakarar uwarka to karfe biyu na rana ina tsumayinka gidannan dolon banza,har kake kwance sharaf kan mace maimakon katsaya kai fighting love d'inka katsaya dolanci." Lumshe idonsa yai yanjin abunda mahaifinsa ke cewa,kokadan zagin bai damunsa wani dadi ma yaji yana kwarara cikin ransa,yau zaiga ABIN CIKIN RUHINSA ganinta ma kadai ya isa ya kwantar da gobarar dake ci cikin zuciyata. Daker ya lalubo kalmar cewa"insha Allah dady kafinan ma zan iso zan biyo jirgin Abudabi zaisauka abuja karfe daya." Tsakiyaja yakashe wayar yana cigaba da fada Abbu da dadyn yah meena keta bashi hkr,nidai daman anafara maganar nabar wajen naga yada za,ai atursasani kuma yanxu don wallahi duk da nake jawara babu wanda zai sani auren mai mata. Yau biki saura sati daya duk munyo dinkunan mu anko kala biyar,less guda biyu atamfa daya sai material da shadda kamfala gizner..........inda naji dadi ummin su dr tazo tatai da Airah,sana waje aikina IT anbani hutun sati biyu,nasaki jikina munata shige da fice gyaran jiki muke zuwa nida amaren,hada salma don itama maah tace taje aimata ai kwatsam tana iya koma gidan mijinta,wanda har yau baizoba babu kuma wanda yasake bi takanshi ma balle yadamu,dukda ita dole tadamu tuna tana sonsa. Dawowar mukenan daga gidan k'unshi,nida su mimi,yah meenah.anty shida can itadasu kawayenta suke hidimarsu,bama nan gida suka zaunaba sunacan gidan wata kawarta. Husna kuwa tanan amman b'angaren Annie,anshirya event dinner da kamu sai bridal shower. Inkagannni zakai tunanin nima ina cikin amaren,sabkda yadda na murje nakoma wata yar 18 yr harabar gidan cike da motocin bakin biki,saidai zagaye mukai tacan baya,don akwai hanyoyi dayawa cikin gidan,dariya muke saboda mimi datai sabon saurayi wani kamar almajiri,sai dariya muke mata. Ita kuwa sai fad'a tana cewa"wai kinga hakoransa wlh kalarsu kalar yellow din shaddarsa yar dubu biyar,shiko kunya ma baijiba wai nagankine miyauna yaguda,don uwarsa kamar yaga tsire ko balango." Dariya kurun nake harda rik'e ciki jinai kawai nabanki mutun, cikin sauri nad'ago idonsa cikin nau..........mimi tace"laaa yah yaushe ka iso,sannu da zuwa." Kai kawai yad'aga mata suma duk suka gaidashi suka shige,bansan tsayuwar uban da nakeba, naja dogon tsaki narab'ashi zan wuce,wata irin fizga yamun yajinginani da bango.......idonsa har ya kad'a yayi jaa. "Rainin har yakai haka,nizaki kallah kiyiwa tsaki." Banyarda nasake kallonsa ba naketa kokowar kwayar kaina, "Kasakan man hannu zakajiman ciwo fah." Yatsansa yasa ya d'illi bakina "bazan sakiba kin rainani ko,bama ki mjrnan nadawo kodan ..........saikuma yayi shiru na dallabmai harara nafizge hannuna saida nakai kofa nace"meya hana kazauna can har mala,ika azara,ilu yasameka." Rugawa nai ahuje ina nishi don karya kamoni don yadda yanade hannun riga inya kamani bazanji dadi ba. Dariya yayi yana jin wani dadi cikin ransa atleast dai yaganta kuma zaita ganinta har agama biki,wsta xuciyar tace to in angamafa kaida kayi aure............tsaki yaja ya wuce don yana da baki waje zaije ya kama masu hotel. Yaune za,ai bridal shower,kawayenmu duk sunzo anata hidima da shirin fita ,don duk anan zasu shirya ni busy ma nake saboda yah imran ya sani aikin take away na bak'insa,inacan dakina nida mimi tana tayani,waya uke da ummin dr taa ban lbrn Airah,sai dariya nake tace ai gobe daren biki tare zasu zo,mungama wayar na ajiye ganin munkusa gamawa nace ma mimi. "Bari nayi wanka sandda zan fito kingama saina shiryasu cikin wannan babbar ledar,don waccen bata daukewa kema saiki je kiyi arfe biyar zasu zo daukar amarensu,muda bamuda mazan kinga saimukai kanmu." Dariya tayi yace"karki damu Muma very soon zamu shige daga ciki tsaki naja ina cire kayana nadaura towel,nace"saidai ke ko,tunda naga wannan hamdanan agaske yake.nafad'a ina dariya ita tasan wanda nake nufi aikiwa tab'ata fuska. "Wlh inajin nauyinki oum Airah,kodan arzikin haihuwar babyna dakikai." Dariya nai nace "sorry mu k'anwa nadaina nima d'anawa naibari nashiga saina fito." Wankan nashiga nayi kasancewar ina da dadewar wanka nakusa awa sannan na wanke jikina dayake da shawer nayi kaina yajike nasaka towel din dana shiga dashi natsane kaina,nadan bud'e k'ofar namik'o hannuna nace, "Mimi akwai towel din Sweetie nanan kan net dinta banshi indauro wannan yajike wlh,........mik'omun akai na ansa na daura ko cinyata bai rufeba don daker ma ya rutsai,mistakenly na duka tsaf zai kunce fitowa nai ina cewa"yaudai ban jimaba karkiyiman complan plsss.....................ido hudu mukai dashi yana zaune kan stool din miroow.........idonsa ker kaina baki na rufe ina zaro ido,,,,,,,,,,,, _*ABDOUL-NASSER (ALFAH) COMING SOON INSHA ALLAH LABARI DAYA SHA BANBAN DA SAURA,KARKIBARI ABAKI LBR*_ Mrs Bb ce Mom muhssen. [7/8, 2:10 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 49. "Haba don Allah wannan badai dai bane,yazaka shigo babu neman izni." Ganin ya m'ike yana tunkaro inda nake yasa naja baya,ina sake rik'e towel din sosai k'wak'wk'aran motsi idan nayi fit towel din zai fice,. "Kayi hkr,karka matso nasan banyi daidai ba d'azu bazan sakeba wlh bazan k'araba........gaba ya tsaya kikam kasancewar yafini tsayi iyakar kirjinsa na tsaya,runtse ido nai inajiran inji saukar mari ta ko ina. Dan sunkuyo wa yayi saitin kunnena har lips dinsa suna tab'a fatar kunnena...........wani irin tsauwwww naji ga jikina,magana yayi wanda ko ni don dai kan kunnena yayi da bazanjiba.........."suger khairat,biyoki nai nasake maki tambayar rannan." Turesa nafara yi ba arziki na daina jin towel din zaiman zigidir. Runtse ido nai nace"na rokeka kabar d'akin nan,banson ganin ka wlh plssssss live me wai ana dole nace ban.............yatsansa ya dora kan bakina yana kallon cikin idona,bansan dalilin dayasa naka sa kauda idonba,jinai ruwa yataru cikin idon sun fara silalowa...........dukowa yai yasaka halshensa yana lashewa dandanan jikina yadauki kerma.........hannuna rike gam da towel dina.......hancinsa yake gogawa ga kuncina ya lumshe idonsa yana cewa, "Bkison ganina *sweetheart*? Banyar daba kuma ba gaskiya bane,karki biyewa su ummi ki cutar da zuciyarki sannan nima ki cutar dani." Banda rawa babu abunda jikina yake duk yabi ya harmutsa man lissafi,bakina kerma yake inason inyi magana .........ina tsoron inbude bakin yacafkeshi hannuna d'aya na dora kan bakina nace, "Wlh kafata bata iya daukata,pls katafi kabarni nashirya na rokeka......jinai kurun ya sabeni kamar wata Airah kadan ya hana ban kurma ihuba.......ka ajiyeni ba kyau irin haka wai miye hakane wlh saina gaya wa maah kana tab'ani,kabari banso wayyo maaah...........lips d'insa masu tsananin taushi da k'amshi ya saman bisa bakina idonsa ker cikin nau yace"naga alamar dai sokike nayi kissing d'in wannan d'an baki." Kauda kai nai ina guntse bakina.........kwantar dani yayi kan gadona,ya zauna gefena yana canza salon kallona gareni.........wani irin shu,umin kallo yake bina dashi wanda dandanan naji duka jikina yayi masifar canzawa.........mai ya d'auko lotion dina dana ke shafawa ya bude ya matso ga hannunsa ya murza. Daga k'afafuna yafara shafaman tudaga yatsuna har zuwa saman cinyoyina dake waje,,,,,,,,,,wani irin numfashi nafizga,ina runtse ido yadda yake shafa man yasa gabaki d'aya nayi losing control d'ina...........inda Allah ya taimakeni tun a toilet na saka pant d'ina........abunda nakeji bazai kwatantuba tunda uwar data haifemi maah ban tab'ajin wannan feeling d'inba,damke hannunsa nai dake kokarin kwance towel d'ina........numfashina yana sama da k'asa nace"plssssss am begging u kabarni kafitarmu d'aki babu kyau na rokeka kabarni haka,banso bana so wlh."nafada idona yana cika da kwallah. Ajiyar zuciya yasauke yana karkata kai idanunsa akaina. "Menake maki,maifa ne zan shafa maki shine ba kyan,kin mance sadda nake maku wanka nashirya ku,harfa powder da janbaki nake shafa maku,uhmm inkinga nabar d'akinnan yau to kin cemun ILove u." Tattare k'afafuna nai na rungeme ga kirjina nace"wancen lokacin daban muna yarane,yanzu kuma........." Sadda kai nai ina murtsike hannuna wanda nakejin har yanzu hannunsa yanaman yawo cikin cinyoyina. "Idasa mana,yanzu kuma kin girma harkin haihu koba haka kikeson cewa ba." Shagwabe fuska nai na hade hannuna alamun rok'o nace"kayiwa girman Allah kabarni haka katafi wani zai iya shigowa wlh,nidai plssss don Allah." Matsowa yai sosai inda na takure runtse ido nai ina sake k'ank'ame jikina, "Babu Mai shigowa duk sunfita bacinan ma na rufe k'ofar da key kingan shi nan,yafiddoshi daga aljihun wandonsa." Dalalo ido nai ina sake zarosu. Bansan sadda kuka ya kubceman ba ina cewa"wayyo maah nabani wai menatare makane don Allah,kabarni nashirya nafita husna nacan najirana,kuma ma kaida amaryarka nacan najiranka mezanma ka ni,katashi kabarmun d'aki ko in maka ihu." Ai bama jira mezan sake cewa ba ya sunkuceni ya dora kan cinyarsa,dukansa nake ina hawaye amman kama ina dukan bango,ban sake shiga shock ba saida naji ya fixge wannan d'an towel d'in ya yarda k'asa........wata kara na fasa yayi saurin rufe man baki da tafin hannunsa......na daddage na gartsa mashi cizo. "Lalalala kika cijeni." Murmushi yayi mai kyau ya zauna sosai ya matso man yafara shafowa daga bayana,ba arziki na gantsare saboda wani irin abu danakeji...........b'oye kirjina nai ta hanyar rungeme shi gam,,,,,,,,kunnena ya kamo yad'an ciza kadan yace cikin wata irin murya maitsananin kashe jiki "suger nah,kiyi ihun mana,i wish kiyi azo aganmu haka kinga dolensu subanke,nafi kowa ne namiji bukatarki,donke akayini haka kema don ni akayiki,so plsss stop this mu fuskance su cewar muna son juna......ko ke bakya sona." Yadda na matsesa jikina kadai ya isa yagane cewar abunda yake man bazai barni nayi magana ba. Cikin wayau da salonsa da dubararsa ya cironi daga jikinsa ya kwantar dani plat banda hawaye babu abunda nake,don wannan bakinciki ne yadda ya gama kalle man jiki..........man ta shiga shafaman ga sauran jikina,wata irin m'ika nake ina kankame zanne gadon,still kwallah basu bar zubaba.........babu inda babi ya shafe da maiba sannan ya shiga clothes d'ina ya duba ga kayan dazan saka nayau,ya dauko ya nemo bra yazo ya saman ita,bakinciki danake ciki shiyasa hawayena fita,wannan iskancin da yake man har cikin raina i don't like. Less ruwan coffee da milkne,zanen flwers masu kyau manya ajikinsa riga da siket ne nayi,dakashi ya saman kayan ina turjewa ina komi yasaman. Zaunar dani yayi kan stool d'in ya mik'omun powder, "Shafa ko na idasa ladata." Wata harara na wurgamai idona yayi ja saboda kuka.fizga nai ina nuna mashi k'ofa...........dariya yake wadda ban tab'a ganin yanayi ba,tunda nake dashi ban tabaginin dariyar sa irin wannan ba. "Oh na gama wahalar shine zaki koran,kinsan Allah bazan barki ba yau d'inan har saikince man i love u,duk inda kika shiga inabiye dake don haka kishirya...........zanfita ina wajen get cikin mota am waiting for u idan ba haka ba har cikin gidan zanshigo wlh indaukeki kamar yadda nake daukar sweetie Airah,nasaki mota kinsan ba karamin aikina bane yadda kuma gidannan yae cike da mutane.kika tsaya sake da baki kina kallona zanzo na shanyeshi ba ayena bane." Guntse bakina nai ina magana k'asa k'asa cewa"bansan sadda ya koma marar kunya ba,don allah jebeshi ko kunya baiji." "Mekike cewa suger,maganata kike gulamata kike ko dawowa yake wajena naruga zan shige toilet ya cafkoni ya matse,mekike cewa fad'a man kokuma...........ya fara zuge zif din rigata wayyo zan fad'a wlh zan fad'a. "Cewa nai fah bakajin kunya kazama marar ........uhm nazama marar kunya. "Indai akankine komi zaki kirani ban zuciya kirani komekiso........kuma wlh yau saikince man i lov u kinjima na rantse inba haka ba nikadai nasan me zanmaki.........ya sunbaci wuyana da goshina yajuya yafita sai kuma yadawo, "Ina waje zanje na shirya wlh inbaki zo ba........basai na idaba." Ya fice zubewa nai kasa ina dafe da zuciyata inajin wani irin happiness yana ratsani,hakika inasonsa amman ya makomar soyayyarmu shin yadda maah tayi dogon fushinan zata iya hkr muyi aure,inaa i don't think so maah akwai taurin kai don zance hakinsune suduka itada ummi,bcos idan ban manta ba haka mahaifinsu yake da taurin kai don da ba dadynsu yah zata auraba,wanine takeso amman saboda shi gawanda yakeso dadynsu mimi yace ko mutuwa zatai saidai ta mutun amman bazata auri wanda takeson ba,ra,ayinsa ne shizai zab'amasu mijin aure. Ajiyar zuciya nai nadaga hannu sama ina hawaye nace, "YahAllah kai kace murokeka zaka biyamana bukatunmu,ya rabbi solve my problems..........hawaye suka zubo inajin kaunar sa tana karuwa duk bayan second ko awa." Tashinai na isa shirya wa nayi simple make up nasaka turare saisa saisa,sannan na dauko milk gyalena da milk jikkata da takalmi na saka,kallon kaina nai ina murmushi bazakace nai aure ba balle haihuwa. Allah sarki sweetie i missing so much wlh,wayata na cire a caji na nufi kofa..........gidan cike anata hidima wajen maah naje suna d'akin Annie itadasu yan uwan Annie nagaidasu suna tambaya ta sweetie nace tana wajen ummin dr sai gobe zata dawo. Nace"Maah zan wuce wajen event." Wani kallo tamun kamar na mara gaskiya tace"tun d'azu ina kika shiga,naje d'akinki na tadda kulle." Gabana yayi wata irin fad'uwa ban bari hakan ya nuna ga face dina ba,ina yak'e nace"ina shashen ummi munyi aikine dasu mimi shiyasa." "OK saikun dawo,kikula dakanki kuma." Nace"i will insha Allah,naima su annie sallana na fito ina sauke Abbu nahad'u dashi muka gaisa yace"ina ki ka shiga maah dinki taita nemanki." Karyar da naiwa maah ita naimashi. Yace"ga mukullin motarshi yaban sabuwa dal batai sati biyuba,yace"kihau wannan nasan kince napep zaki hau." Bazan iya cewa aa ba don karramani yayi yaban don yanata yaa kwalliyata wai kamar budurwa,dariya nai nasaka hannnu na ansa ina godiya........bansan yazanyi da shi ba hi wancan,ni bason ma had'a ido dashi kunyarsa nakejin,yadda yaganeman jiki abaza.....text namai cewa _Abbu yaban new car dinsa intai da ita yazanyi_ Yana ma cikin gida yaje kiran umminshi akan zasu gaisa da yan uwan dadynsu dasuka zo,yana kan hanyar fitowa yatsaya yadauki lemo frige saimurmushi yake yanajin wani irin farinciki wanda baisan yaushe rabonsa dashi ba,exotic ya d'auko karamin kwali yana sha yana nishad'i,reply ya mata da cewar. _suger nah where a u_ Bansan smile ya kubceman ba waiyau ni yah areef yake cewa suger dinsa,maida mashi nai da cewa. _niba suger ka bane,na dr na ne,kuma ina opposite da wajen exercise dinku._ Maimakon yaji haushi dariya yayi ya zagaya ta baya inda zai sameta,hangota yayi tana waige waige baisan sda yace "wow my suger." Ta ba yanta ya zagaya yarungumeta ta baya.......afirgice na juyo zanyi ihu don na tsorata ainun,dariya yayi yana cewa "matsoraciya kawai." Turo baki nai ina kallonsa ta gefen ido saboda masifar kyan dayayi man,maganarsa ta katseni yace"inaga muje cikin ta Abbun don karya ji badadi bari nabar tau bakin get,muje to ko bakya iya daga kafar ma yanzu sai andaukeki...........wayyo jinai kamar na nitse cikin k'asa. Gaba nai wsjen motar ina turo baki,mik'mashi key d'in nayi nashiga gaba......yau jina nake nafita daban. Kallonsa kurin nake asace don wlh yayi man kyau wata zuciyar tace"kin manta ango yake." Ras naji kirjina ya buga dandanan naji kwallah sun cika idona kauda kai nayi ina kallon window,hanky na fiddo cikin jikata afakaice ina gogewa..........Rufe duka glass din yayi ya kunne AC,tafiya yake kamar baiso hannu d'aya yana shan lemon sa,daya yana sarrafa sikiyarin motar........duk farincikin danake ciki naji cikin minty daya yabarni......."kuka kike suger?,kukan namiye kuma." Share kwallata nai nace batare dana juyoba "ba kuka nake ba mura nake." Murmushi yayi yace"sorry suger anshi nan to,ga maganin mura." D'an juyowa nai naga lemun hannunsa yake mik'omun kallonsa nai nace"akwai sanyi fah." Juyowa yai tunkanma muhada ido na kauda idona dariya yayi yace"tsoron kallona kike,koma kice nai kyau ko." Wani haushi ya turnikeni na kauda kai nace"inkayi hkr ita wadda kaima wa aizata gani inkaje." Farking yayi ya maido duk hankalinsa kaina yana kallona,kamar zai cinyeni. "Kallon ya isa fah." Ajiyar zuciya yaja sannan yace"sorry suger nah,kishiko im sorry karkidamu i'm your own inhar kinbani dama kuma kin amunce dani,babu wacce zata iya mallakata bayanke,amman inkinyi sake gobene karfe biyu za,a daureni." Kuka na fashe dashi mai cin zuciya baice komiba,don yayi alkawarin yau saiya tun zurata ta fira abunda take dannewa,idan har yasamu wannan damar to ya kashe boss din,sauran matsalar kuma yasan yadda zai shawo kan lamarin,bazai yi sake yasake rasata basai yau yasake tabbatar ma kanshi dacewar bazai tab'a yarda ta kubce mashiba.....jan motar yayi suka kara wajen event d'in,abunda yafiba ni mamaki babu dangin amaryar yah areef,itama babu ita,ban tambayeshiba na kucce na wuce wajensu husna dasu Yah meenah.........duk inda na gifta idonsa akaina,duk ya takureni da kallonsa,Hidima muke da abokanmu bajimawa akafara gabatar da shirin yadda yakamata,amare sun sha kyau kamar kasace su haka angwayen yah jahid baki har kunne,yah areef baima zaunab sosai ta abokansu yake......wani abokinsa da suke shige da fice tare damun hada ido saidai ya sakar mun murmushi,,,,,,,gabana yafad'i meyake nufi nashiga uku........mimi ce muke tare waje guda tace"Antyna da alamun fa kinyi babban kamu wajen nan." Wata uwar harara na banka mata nace"banson iskanci wlh karma kisake yah yajiki." Mezatai ba dariya ba don nima kaina saida nafad'a sanan naji naba kaina haushi. "Antyna kin amunce kenan,daman yadda naga yashigo duk yaburkice,nace aikuwa yau yah akwai rigima,harara ya bankaman yace intashi infita kuma in naji ana nemanki karna sake nace kina daki,mafarinma nagudu wajen Anty husna." Murmushi nai nace"uhmm wlh yayanku baida kunya.".dariya tayi tace"inaso irin haka gashinan yasa har kikara mai matsayi." Shashantar da maganar nayi........anyi party yadda yakamata don sunsha lik'o 100k yah yabani wai nayiwa amare lik'o,aikuwa sunsha shi,ba,a tashiba sai kusan shabiyu sanna akatashi..........text dinsa ya shigo wayata _Kisaman mota,karkisake inganki cikin motar wani wlh_ Murmushi nai yaufa nabani wlh ni bazan iya furta abunda yake soba,muddin maah bata amunce da aurenba,on bazan iya juyamata baya ba,don nasan akan y'ancina da mutuncina take yi ba dan itama bata so ba. Mrs bb ce Mom muhseen. Share it pls [7/8, 6:25 PM] Mom Muhseen: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️ ♥️♥️♥️♥️♥️ ♥️♥️♥️♥️ ♥️♥️♥️ ♥️♥️ ♥️ *_ABDOUL-NASSER_* _*{ALFAH}*_ WRITING BY 👇🏻 Mom muhseen. Mrs Bb. Wattpad name: Humairah7531. *_HELLO MASOYA TO DAY I'M BACK,GANI CIKIN WANI SABON SALO KONACE SABON SHASHE KONACE SABUWAR GWAGWARMAYA ACIKIN WANAN TAFIYA,KARKI BARI MUBARKI ABAYA KI MATSO KUSA DON KAR AMANTA DAKE,MOM MUHSEEN CE KUMA MRS BB,KUNSANTA TASANKU ITA GWANACE KUMA HAZIKA AFAGEN NISHADANTAR DAKU DA FADAKAD DAKU,KUNUNA MATA KAUNA TA WANNAN SHASHEN NGD SOSAI DA KAUNARKU GAMU CIKIN ABDOUL-NASSER KOYA TAFIYAR ZATA KAYA?KEDAI KIGYARA ZAMA,DOMIN ALFAH ZAI NISHAD'ANTAR DAKE YAKUMA FADAKAR DAKE_* *MOM MUHSEEN NAKE KUMA MRS BB,GYARA ZAMA DOMIN YANANAN TAFE* ♥️ *ABDOUL-NASEER(ALFAH)*♥️ *drinker guy* _mutunne shida baya hudda da kowa,ba ruwansa da kowa abokinsa guda,bai magana bai shiga sabgar kowa,ya tsani mace idan da akwai abunda ya tsana bayan *MATA* suke,sannan babu abunda yake masifar so kamar *MUTUWA* shiyasa yakeyin duk abunda zai saka tayi gaggawar daukarsa._ _Kwatsam!!_ _saiga wata yarinya the most beautiful lady and hot *SOFIYYA* wacce akafi kira da *FIYAH* tashiga rayuwarsa,bata da burin daya wuce ganin ta dawo dashi cikin rayuwa mai kyau.shin meye dalilin shigarsa duk wadannan halayen?baida iyaye ne?shin ko talauci ne yayi mashi illah?wace irin rayuwa yayi abaya har da yatsani abu mafi daraja watau *mace*_ _sai mun nitsa cikin wannan labari mai tsananin tsaya wa garai,karkugaji yanan tafe bada jima waba. Takuce akoda yaushe masonku da son farin cikinku watau *MOM MUHSEEN KUMA MRS BB* saina jiku. 09034722970 its my what's app no.💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 50. "Yah kace infito mutai kuma naga kusan ten minute baka tada motarba, plss bacci akeji wlh." Shanyayyun idanunsa ya zuba man kamar maijin bacci,yana wani juyasu duk sun rikita man lissafi,dauriya kurun nake wlh yau yaya duk ya susutani don nikadai nasan menakeji wanda ban tab'ajin saba............"suger nah babu inda zamu har sai kinfurta man abunda nakeso,inba haka ba daga nan kinsan inda zan kaiki.?" D'an shagwab'e fuskata nai ina dan juya kai nace cikin shagwabar da bansan inayiba"nidai gaskiya aa,kamaidani gida kuma niba suger dinka bace." Wani irin yanayi yatsinci kanshi ciki,lumshe ido yayi yanajin kamar yakamota yasa cikin kirjinsa,daurewa yayi murya can ciki kamar yn tsoron yi tace"ta waye idan ba tauba,koshi wanda kike kiran tashice ke bakiga da yake Allah yasa ke rabona bace ya daukeshi,don haka kibar wani cewa keba suger na bace ur my honey sweet and suger for me." Juyowa yayi sosai yana fuakanta ta duka hannayena yarik'o yana d'an mammatsasu kad'an,wanda jinake kamar nayita kuka saboda hanayin danake ciki,wani feeling ne da ban tab'a jinsa ba,sabone agareni wata irin kasala da mutuwar jiki sun lullub'eni..........cikin taushin murya da lauya harshe,yada zai idasa kashe man sauran d'an kuzarin daya rage man.......... *INA SONKI UMMULKHAIRAT,INASON MALLAKARKI KIZAMO ABOKIYAR RAYUWATA,INASON KI ZAMO UWAR Y'AY'ANA KISANI TSAWON SHEKARA ASHIRIN DA BIYU INA DAKON KAUNARKI,KECE _ABIN CIKIN RUHINA_* Tuni hawaye suka wanke man fuska kukana nake kasa kasa,inajin kaunarsa shaukinsa suna sake mamaye man dukan nin gangar jikina........shashshekar kuka nake na matse hannunsa sosai nafara magana cikin kuka da bayyana duk wani shaukin kaunta. "Yah kayi hkr........kayi hkr bazan iya bujire umurnin mahaifiyata ba,idan na bujire mata na zama diya marar sanin ciwon kan ta dana uwarta,kuka ya sake kubceman nacigaba da cewa. Aduk duniya bacin iyayena yah kaine mutun daya danake ma wani irin so wanda ni kaina bazan iya sanin iyakar saba,insonka yah Areef ina kaunarka tundaga farkon zuciyata har karshenta,amman bazan iya butulcewa mahaifiyata ba,koda hakan nanufin rasa raina.......wani kukan ya sake kubceman mai cin rai......tuni hankalinsa yayi masifar tashi,sake matsowa yayi kusadani duk ya rikice jikinsa anshi rawa yake,yace"oh my god sorry sweetheart,karkice aka karkiyi kokarin ganin kin janye dag gareni,ke kadaice hope dina insonki wlh khairat ina kaunarki,bazan iya yin waa rayuma mai dadi inbabu ke ba,wlh na tabbatar maki da cewa awannan karon muddin kika yi saken auren wani wlh wlh mutuwa zan hawayensa naji suna sauka kan hannuna,idonsa yayi wani irin jajawur bakinsa banda rawa babu abunda yake,bakinsa yasa yana sumbatar hannuna kamar zararrare,duk ya susuce. "Plss babyna karki bari arabamu,zanje in samu maah inroketa tabarmu da juna,nasan Abbu bazai zama matsala ba kamar ta ba,na rokeki karki gujeni inada heart attack kuskure kadan zai iya jefa rayuwata cikin hadari,kece kadai zaki iya cetona plssss baby sweetheart wlh ina sonki kiyafe man laifina danayi abaya zafin sonki ne da kishinki,,,,,,,,kamar karamin yaro haka yayita kuka yana kissing hannu na ni kaina kukan nake saboda na tabbatar shim din mutuwa zai ya barni,shikenan ni rayuwata haka zata cigaba da kasancewa,duk wanda na kwallafa raina dashi saiya barni........kukana yayi karfi sosai ya tallabo fuskata idonsa har lokacin kwallah na zuba,fuskarnan tayi jaa gefen kuncin sa yasa yana gogeman hawayena,yayinda nashi basu dakata daga zubarba..........kamar yadda ya tallabo fuskata nima hannuna dake rawan nasa na rik'o nashi muka k'urawa juna ido kowane yanajin zazzafan son d'an uwansa...........ban yi auneba naji tattausan lips d'insa kan nawa saida na sauke nannauyen numfashi,saboda yadda naji wani irin shock ya kamani. Cikin natsuwa yake tsotsar bakina har lokacin nidashi kukan muke,tsawon five minute ya d'auka yana sarrafa harshena.........kafin ya janye bakinsa muryarsa ta dishe sosai yace"kisani duk randa namutu cikin wannan halin kece da kaso sittin da alhakin hakan,zan kyaleki bazan sake maki wanan maganar,tunda har bazaki tayani yak'in da nakeyi ba,sannan har kice kina sona kindamu da halin da muke ciki,haba baby kinmun adalci kenan shikenan muje gida" Abunda yace kenan ya tada motar,zan iya cewa har muka iso gida nidashi babu wanda yasake cewa komi,jikina yayi masifar sanyi da kalaman sa,bakin get yayi parking ya bude zai fita nai saurin rik'o hannu sa kwallah share share cikin idona. "Don Allah karkaga laifina,wlh yah maah zata dauki mummunan mataki kaina muddin na kware mata baya,ka fahimceni,wlh na damu nadamu sosai akan wannan halin,karka yiman bahaguwar fahimata,wlh inasonka banda burin daya wuce kasancewa dakai tsawon rayuwata karka ce zaka hukuntani ahaka zuciyata bazata iya daukaba,wlh inajin ka tamkar fitar numfashina karkayi man haka don Allah..........na fashe da kuka ina shashsheka......zare hannunsa yayi yace "idan da kinsan kalamin dani ummi ta yiman akan gujewa wannan auren ke bazakice haka ba,amma kasancewar ina ganin idan na biyeta abanza zan illata rayuwata,dole tasa nadage wajen ganin nasamo kanki,amman shine zakice ke bazaki iya ja da umurin maah ba,yes hakan na da kyau bance kija da umurnin taba,amman ai saikisan hanyar da kika bi don ganin ta gane cewar kinson kasancewa dani,inba dai kema kin gwammace mutuwar tawa da rayuwata ba." Sake rik'e hannunsa nai ina kuka sosai "yah karka gujeni wlh ina sonka zuciyata takai limit d'in da bazata cigaba da daukaba amman kasani daraja da kima sun wuce komi,gara ka rasa komi daka rasa su.........cikin wani irin yanayi ya juyo afusace wanda ya tsoratani,,,,,,,har jijiyar kansa ta fito sosai.......idonsa yayi jaa sosai kwallah sun kwanta ciki muryarsa ta dishe sosai yace jinjina"is ok hakan ma ya isan." Ya fizge hanunsa ya shige cikin gida yabani zaune ina kuka mai tsananin tafasa zuciya,daker na tada motar bayan nadawo inda yake na shiga cikin harabar gidan. Parking nayi lokacin sha biyu na dare,ta baya na shige cikin gidan dakin yah meena nayi masauki........bacci suke don dagani sun gaji don duk dakin na same su salma ma k'asa tayi shimfid'a ta kwanta...........silalewa nai kasa bakin kofa naita rusa kuka na,yazanyi da maah ne wai meyake son nace mata,wai ko yamance irin zafin zuciyarta idan ranta yab'i da abu,ba ayenta bane tayi man mugun duka wlh,wata shawara tazo man nai saurin amuncewa da ita don idan ba haka ba banda wani hanya,kewaye na shiga nayi wanka nazo nai sallar isha,i na kwanta duk da ba baccin nakeji ba duniyar tunani natafi wai yau yah Areef ne yafurya man kalaman da nashekara aru aru ina tsumayinsu daga gareshi.yau iyae man kuka da idon sa akan yana sona,wannan kadai ya isan farinciki haka na lalalce ina tunaninsa bansan sadda bacci yayi awon gaba dani bah. ********** Washe gari daurin aure ant hidima nikuwa bacci kurun nake har wajen sha d'aya saboda ban samu nayishi da wuri ba jiya,kukan Airah ya tadani. afigice natashi ganinta nai ita kad'ai tashi nai naisaurin daukota ina dariya. "Oh my sweetie,I miss u so much muuaahhh naringa kissing dinta babu k'ak'k'autawa itama ganin sai dariya nake ina kiss dinta,itama saita bangala dariya tana mamuk'eni mukaita dariyar naji anturo k'ofar Anty shida ce tasha gayu na fitar shari,a tayi masifar kyau saidai kuma fuskarta hawaye nagani,dariyar tau tab'ace tashi nai na dauki zanen goyon Airah na goyeta nace"anty lafiya kuka kike fah don Allah kibari yaufa ranar farin cikin kuce." Rungumeni tayi tana shashshekar kuka tace"kinanan anacen ana tashin hankali cikin gida,wai maah da ummi suke fad'a cikin taron mutame khairat,kawai saboda keda Areef,gashican dangin zulfa,a sun maido lefe suna wulakanci da cin fuska,wai ummi ce ta roki alfarmar hadin auren saboda anata alkawarin kujerar minister of communication,yanzu wannan dacewa ne har k'asa yah Areef yake rokonta ta barshi ya aureki amman tasa k'afa ta halbeshi,gashi can anfita dashi asbiti.......mafarin kenan maah takai karshe wajen zuciya take aya ma ummi magana cewa,ta saida mutuncinta da darajarta wajen mutanen da basu da mutunci da kirki,gashinan sun watsa mata kasa ga ido ranar auren sun maido komi sunce basuyi........ta gwammace d'anta ya mutu bacin tanada halin taimakonsa......shinefa taji haushin maganganun ta mari maah,itama maah ta rama wlh khairat abun babu kyan gani dole akakira su Abbu awaje,yanzu haka ummi ta yi oarking kayanta wai barin gidan zatai.........ga mutane kahirat cikin taro wace irin masifa ce wannan wlh duk naji natsani ma auren....." Kina kasa zuwarmun yayi saboda wani irin abu daya kulleman ga zuciyata,wani yanayine nakejina da ban tab'ajin zuciyata ciki ba,saidai gani na tayi na zube kan gadon ga Airah ga bayana......wata k'ara ta fasa wadda ta janyo utanen dake falon Annie,kuka take sosai ta sauke Airah dake kukan itama,umminu dr ce ta ansheta Annie ta shiga shafa mata ruwa amman ina ko sake motsawa batai ba,aguje aka kira Dadyn su yah meenah shima ya rud'e daukar ta yayi annie biye dashi yasata mota, Daman maah da su mimi duk sunacan wajen areef da Abbu, Dadyn su mimi yaga sadda aka dauko khairat lokacin ya na tama ummj balbalin masifa,ya ce "wlh wani au yasamu yaran nan saint kinyi danasani wlh." Mota shima yashiga yabi bayan dadyn su yah meenah........inda aka kai yah can aka kaini cikin k'an kanen lokaci aka ansheta,........likitan ta nana lokacin wanda ke dubata lokaci lokaci,dashi aka shiga don ceto ranta......kuka maah keyi kamar ranta zaifita,Annie keta bata hkr itama Annie kukan take abbu ko ya dafe kai da duk hannayensa. Dadyn su mimi ya iso yana tambayarko ansau ka d'aya daga cikinsu,girgiza kai kurin Abbu yayi. Dadynsu yah meenah yace"inaga dole ai sanarwa andakatar da daurin auren sai zuwa sadda hankali yakwanta ko inaga hakan zaifi don dukan mu bamada kwanciyar hankali." Abbune ya d'ago idonsa yad'an canza yajasu gefe yace"aa jafar(dadynsu yah meenah kenan)baza,ai haka ba amuje ad'aura aure tunda akwai sauran lokaci nanda karfe biyune bazamu iya dakatar da mutanen dasuka taso daga wata uwa duniya ba don halartar daurin auren ba,sai sunzo kuma ace anfasa hakan baidace ba.abunda za,ai kawai kai kamal(dadyn su mimi kenan)ka zauna anan u zamuje muji da mutane kahid da ya iso da imran sai shahid dadyn su mimi yace "Aa muje duka wani cikinsu sai ya tsaya." Likitan da ke kula da yah Areef ya karaso yace"ku kwantar da hankalinku munankan kokarin cetoshi,insha Alkah cikin kankanen lokaci zai tashi,kuje ga hidimarku harkun gama kudawo insha Allah zasu sama very save." Jinjina kai sukai sannan suka bar angwayen sukatai,lallashin su maah sukaitayi yayinda sukansu suna cikin damuwa,kamar daga sama suka ga ummi taniso wajen tana kuka,babu wanda ya kulata cikin su maah harda su Shahid. Sai jahid ne yaketa bata baki rungumeshi tayi tana kuka tace"nayi dana sani mujahid nayi nadama,wlh son zuciya da kwadayi suka kaini ga haka amman duk duniya banda kamar ku yarannan,wlh bank'i Areef da khairat don inso ba,shedanne yyi nasara cikin xuciyata.........kaje kace wa iyayenku don Allah suyi hkr su daura masu aure yau hakan shine zai dawo dasu sucikin hayyacinsu." Agigice maah tatashi daga duken dabtake tana kuka,share kwallar ta tayi tace cikin tsananin fushi da bacin rai. "Hafsa!" Zaro ido tayi ummi tana kallon maah da mamaki bama ummin kadai ba har su dake wajen abun ya basu mamaki,don basu tab'ajin ta kirata haka ba saidai yaya koda yaushe. "Ehy hafsa,koba sunanki bane to idanma mafarki kike kifarka hakan bazai tab'a yuwuwa ba,khairat bazata auri d'ankiba kije kibashi duk wacce kike ganin itace ta cancanta,." Ummi kuka take tace"haba saudah,Areef fa nakine kece uwarsa...............ada ba ada nasan nice uwarsa amman ayanzu nabar maki kayanki saboda kin nuna man ikonki akashi,kibashi budurwa sabuwa dal aleda,ba dai jawara ba wacce ta haihu." Annie tai saurin rufewa maah baki tana cewa"haba saudah! yazaki koma kamar yarinya,duk wannan bai dace ba kufa y'an uwane ciki daya kuka fito yazaku bari aganku arana,kidufa yadda mutane suka gaye mu,acan gida kunyi yanzu ma nan bazaku hkr ba." Maah kuka ta fashe dashi ta rungume Annie tace"wlh gara munke saudbu miliyan akan hafsa,ta nuna man ni bakowanta bace ta tozartani cikin tarona ta wulakanta yarana danice na tarbiyantar dasu ta anshi d'anta da itace taban da hannunta,duk saboda abun duniya sabida mulki shege abun banza da wofi da zai kaika jahannama..........ta jefa rayuwar yara cikin garari gasunan kwance cikin halin mutuwa da rayuwa.mezanyi danita wlh tfita raina tafita daga cikin raina narantse da wandake busa man numfshi babuni babu.................aguje ummi ta rugo ta rufe bakin maah tana kuka sosai,duk tafice hayya cinta har numfashinta yi yake kamar zaifita,........"karkice haka narokeki karkice haka ni takice ke tawa ce saudah bazan iya rabuwa dakeba,kekadai garan sai jabir taya kikeson nayi rsyuwa babu ke..........Annie ta janye daga maah umi ta samu damar rungume maah kamar zata maidata ciki......kuka suke suduka idan kagansu saikayi masu kwallah........duk wanda ke wajen kukanyake masu shahid da imran barin asibitin sukai mujahid ne kurin ya tsaya shima kukan yake,daker yake basu hkr durkushewa kasa sukai rungume da juna kowace tana jin son yar uwarta ya ratsata........ba wacce ta sake cewa komi sai kuka da ajiyar zuciya. Mrs bb ce Mom muhseen.😘😂[7/10, 3:04 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 51. Suna nan durk'ushe suna kukan likitan Areef ya iso wajen,saurin sakin juna sukai suka mik'e jahid ne ya taresa yana tambayar ko yafarka. "Cikin ikon Allah mun samu mun daidaita matsalar,amman gaskiya kozai farka sai nan da gobe ko cikin dare,don muna son zuciyarsa ta huce daga zafin data d'auka,don waje guda yafara kunbura." Zaro ido duk sukai cikin kuka ummi tace"don Allah likita katai makemu ka ceto mana shi,karya mutu donAllah karka bari yamutu." Annie ce tarik'ota tana cewa"haba yaya,raida mutuwa suna hannun Allah shi zamu roka ya bashi lfy,kibar cewa haka." Jahid yace"yanzu zamu iya ganinsa don Allah kodan musamu natsuwar zuciya." Jinjina kai yayi yace b komi kushiga ku ganshi amma don Allah karkuyi Abunda zai tasheshi,idan kunsan kuka zakuyi plsss karkuje." Ummi tai saurin share hawayenta,tace"mun daina bazauyi ba insha Allah." Hanyar d'akin suka nufa kowa yana saurin shiga don ganinsa........kwance yake kan gadon,cikin awannin da basukai biyar ba ya yi wata irin rama kamar wanda ya kwana goma yana gudawa. Ganin ummi zata fashe da kuka yasa jahid fiddata........suma bajima suka fito maah hankalinta duk yana kan khairat,zaman zuru suka cigaba dayi har zuwa sadda su dady suka dawo daga wajen d'aurin aure. Masha Allah an daura aure saidai muce Allah yaba ma,auratan zaman lfy cewar Abbu dake sanar dasu maah. Likitan khairat ne yafito yace insha Allah anjima kadan zata tashi,tashiga shock ne amman dasauki jikin. Jin haka yasa Abbu yace duk su wuce gida,abar annie wajensu kawai itada salma..ke mimi kije ki kula da Airah tunda tafi sakewa dake........badan sun so ba duk suka juya zuwa gidan,yadda nazaci bikin zai watse sai ba haka ba gidan acike suka samai da bak'i. Dole maah da ummi suka saka fara,ar dole kan fuskokinsu aka shiga hidima ba kama hannun yaro. Amman duk hankulansu suna tare da yaran nasu,bayan sallar la,asar aka kawo Husna wajen ummi aka sauketa,don daman duk gidaje guda zasu zauna. Abbu ya fidda manya kudi masu kauri ya narka masu gini na gani nafad'a,Areef ya saka yazana masu gidan kasancewar yasan hardashi yasa yafidda k'yuya yazana tsantsarere,tunda akagama gidan Kowa yaje saiyayi masifar burgeshi,an narkar da kudi don ma Areef ya kama ma Abbun aka idasashi,50/50 sukai shima daker Abbun ya amunce. Kowace amarya cikinsu anmata jere na gani na fad'a kowace set din gado da kujeru uku uku,komidai anyishi cikin wadata iyakar karfinsu sunyiwa yaransu hidima sosai. Wajen karfe shida na yama nafarka daga dogo baccin dana tafi,dakin nake kallo cikin dimuwa don na mance mema ya kawoni nan.......runtse idona nai ina son tunowa.........jinai kaina ya sara dandanan naji wasu kalamai suna amsa kuwaa cikin kunnena. _har k'asa yah Areef ya duka yana rokonta tabarshi ya aureki amman tasa kafa ta halbeshi,gashi can anfita dashi rai hannun Allah_ Cikin tsananin kara na kwala kiran yah Areef,kuka nake ina fizge drip d'in da aka saman,dirowa nai daga kan gadon daidai fitowar salma daga kewaye.........da sauri ta rikoni,tana cewa"khairat ina zaki bakida lfiya fa don allah kidawo jiba fa hannunki jini yake,kincire drip d'in,nashiga uku na don allah kidawo." Fizgewa nai ina kuka "kibarni ki kyaleni wajen yah zanje wajensa zani zoki rakani,wlh bazan dawo ba saikin kaini wajen yah karya mutu ban ganshiba haka ma dr ya mutu bamu wani gana ba kibarni nace kibarni." Ita kanta salmar kuka take ganin irin wannan kauna maizafi,akullum tana mai danasanin shiga tsakaninsu da yanzu sun mance da sunyi aure,tunda itace musabbabin duk wad'annan matsalolin.likiane yashigo jin ihu sa kururuwar marar lafiar.......salma tana sha re hawaye tace"Doctor yawa gata nan wai saitaje wajen yayanmu d'ayan marar lfiyar,gashi nan har tafizge drip din hannun yana ta jini." "Saketa." Saki na tayi na ruga zan fice yyi saurin tareni yace"kinsan inda yake ne zomuje in kaiki amman ki natsu inba haka ba bazan kaiki ba." Share hawayena nai ina sauke numfashi yajani har d'akin dake gaba danau......baka k'ofar nai har lokacin bai farkaba Annie ce ta gama sallar mangaruba ta ganni..........ban tsaya ko inaba sai bakin gadonsa kuka ya sake kubceman,ganin yadda duk yasake lalacewa na tuna hirar mu dashi jiya. _plss babyna karki bari arabamu,zanje in samu maah in bata hkr tabarmu da juna nasan Abbu bazai zama matsala ba kamar ita,na rokeki karki gujeni inada heart attack kuskure kadan zai iya jefa rayuwata cikin hadari,kece kadai zaki iya cetona plss babyna_ Wani kuka na rushe dashi ina faduwa jikin annie, "Annie kice yatashi wlh bazan iya rabuwa dashiba,kice mai yafarka nidashi mutu karaba wlh yah inasonka bazan bari arabamu ba kaine farincikina..........."banda lallashi babu abunda annie keyi.......tashinai daga jikinta na isa wajensa na rik'e hannunsa ina hawaye,duk jini ya wanke jikina wanda kefita daga hannuna.likitan yazo ya cire nashi wanda aka sama yah Areef din yamaida shi jikina..........yace"nan kikeso ko." Daga kai nai ina kuka yace"to sha zamanki gaki ga shi babu mai rabaku sai allah." Yacewa Annie akyaleni har sadda zai tashi hakan zai taimaka wajen samun saukar jinina,don yace jinina yahau gaskiya. Jinginanai da bangon d'akin bacci yasace ni. Ajiyar zuciya annie tayi itada salma, Annie tace"wannan masifa Allah yaka wo mana karshenta,yara saikace kansu farau soyayya,kijifa yadda tabi ta haukace Allah naga Abunda ya isan,wlh gara azo ayi auren nan kowa yahuta haba wannan masifa dame tai kama." Salma ta share hawaye tace"wlh Annie tausayi suke ban,har gobe ban daina ganin laifina inajin zafin kaina sosai akan hakan,nayi nadamar duk abunda yafaru wlh,daba danni ba duk daba haka ba dayanzu anwuce wajen." Jawota tayi jikinta tana lallashi tace"koda badan keba salma dama haka kaddararsu take,dole sai rabon Airah ya shiga tsakaninta da Dr muhd,gashi ko shakara basuyi ba Allah ya anshe dr don hakan ne kurin zaisaka Areef yasameta.saboda rabonsa ce,shiyasa ba,ason kayi shishshigi cikin lamarin aure,don sai Allah ya kasheka kuma ayi abun,Alkah dai yasa abun yazo karshe don fitinar ta isa haka." Karfe goma daidai Areef ya bude idonsa,jin wani kusa dashi yasashi idasa bude idon,khairat ya gani tana ta bacci jingine da bango........duk da rashin karfin jiki da yake ciki haka ya tashi zaune ita ya kwantar da ita........kallon fuskarta kurun yake ko keftawa baiyi,yana runanin meya sameta ita kuma,don yini guda itama duk ta fita hayyacinta. Jin motsin kofa baisa yadaina kallonta ba,Abbune da dadynshi Annie na biye dasu sai salma. Ko kadan baiwaiga yaga ko waye ba,idonsa ker akanta jiyake kamar daya kauda ido zaiga gizo take mar ba ita bace........saida yaji Abbu yace "Areef kafarka yajikin naka." Hannu ya d'aga mai yace"Abbu kayi shiru karta gudu,kallonta nake idan na kauda ido zanga ba ita bace." Kadan yahana basu kece da dariya ba.sai dai murmushi dasukai,yace"babu inda zata ka juyo ka hutar da kanka da waige." Juyowar yayi yana sauke ajiyar zuciya,kallonsu yayi yace"Abbu meya samu khairat kagani harda drip akasa mata." Dady yace"abunda kayi itama shine yasameta duk kunbi kun tada hankalin mutane don ubanku." Salma dariya take ita da Annie shima murmushi yayi yana kallon khairat d'in yace"Abbu a sallamemu haka mun warke." Wannan karon saida Abbu yayi dariya yace"inkai ka warke ita tawarke ne." Annie tace ga alama kagani Alhaji,tunda har tabaro dakinta kamar mahaukaciya tataho nan,bacinma dr ya kamota ai kila bakin titi zata yi." Duk dariyar suke sai lokacin Areef yaji duk kunyar duniya ta kamashi,sai soke kai yake k'asa. Dady yace"ai anwuce wajen kuma." Bari akira dr ya baku sallama kun idasa warkewar can gida. Idona nake budewa daker don hayaniyar ce tatasheni.............ganinsu nai tsaye cirko cirko sai raba ido nake,kallon inda nake nai na zaro ido nashiga uku badai nan suka tadda niba. Ashe afili nai maganar ida naji salma tace ga zhiri ma kingani.ba arziki na diro ina boyewa bayan Annie duk suka saka man dariya,likitan yashigo ana hira dashi yace ai wadannan Kawai alhaji ku aura masu juna,inba haka ba wataran guduwa xasuyi suje suyi aure baku saniba,dariya aketayi nidai tuna na boye bayan Annie ban sak fitowaba.......ruguda mukai sai gida,salma sai tsokanata take ina hawaye,don wlh sai yanzu duk nakejin kunyar abunda nai,don bihakki banson nayi ba,nidai kawai zuciyata nagaya man ai yah ya mutu mafarin nai wannan rikicewar. Saida salma ta kamani muka karasa cikin gidan don jikina babu karfi sosai. Aigabaki dayansu suka rungumeni.abunda ma yafi ban mamaki harda ummi,don hawaye take sadda ta rungumeni........ban fita wani na shiga wani mamakin naji tace "kiyafe man diyata kiyafeman,naso kaina najefa ku cikin halin k'ak'ani kaye..........rufe mata baki nai kawai na janye na isa ga mahaifiyata. Kuka nasa mata inajin kaunar ta duk wanda yarasa uwa yayi kuka wlh,itama hawayen take ina share mata. *wlh ngaji pls kuyi hkr mu hdu gobe idan allah yasa munkai,inkunga typing error sorry wlh ina sauri ne* Mrs bb ce Mom muhseen😘😘 [7/12, 2:38 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 52. Abbune yace kowa yaje ya kwanta zuwa safe kowa ya hallar falonsa yana son magana damu,haka akai kuwa duk muka tai d'akunan mu,duk da har lokacin akwai tsirarun yan biki,amman yan uwane suka rage. Na tambayi mimi ina Airah tace ai ummi ta wuce da ita,don tunda kika suma take kuka taki yarda dakowa,daker ummi ta shawo kanta.dazata tai kuma nace aikuwa saidai sutai tare,inkin dawo hayyacinki sai amaidota." Harara na banka mata nace"au da hauka nafara kenan banson uskanci fah." Dariya tayi tace"to kema Antyna dagajin yah yana asibiti shikenan kema sai ki wane sheme." Duka na kaimata ina cire kayan jikina zanyi wanka,don tun na baccin jiyane sai tsami suke da warin asibitin. Nace"kinsan wlh yanzu zuciyata bata iya cigaba da boye kaunata akan yah,dacen ma kawai karfin haline amman nikadai nasan yadda nakeji." Kwanciya mimi tayi tanajin dadin abunda khairat tace tayi dariya tace"to da ya mutu fah." Zaro ido nai na watsa mata dak'uwa nace"Ba bakinki ba muguwa,insha Allah mutu karaba sai munga jikokinmu,Allah natuba daya sheka kina tunanin nima bazan bisa ba.....uhmmmm kedai kawai kigode Allah bai dora maki irin wannan zazzafar kaunar ba,amman wlh mutun bakar azaba yake sha ba yar karamaba." Dariya mimi keyi nikuma nashige Bathroom don in gyara jiki. Washe gari ban tashi da wuri ba,sai wajen karfe sha daya,saboda ni ma yasa Abbu yace abar meeting d'in sa dare,yau akai walima amaren kamar wasu amaren indiyawa,kunsan insukai kwalliya kamar ka sacesu. Naita tsokanar husna dake kuka itada yah meenah,dariya mukai ta masu nida mimi har saida maah da Annie suka ci k'aniyarmu sannan...........Anty shida tama fi kowa kuka ni mamaki ma suka ban,suda zasuyi aure kusada gida kuma duk sirikan nasu agida suke to meye na tashin hankali,bacin sun san basuda wata damuwa da su kamar yadda ake da haka za,acigaba. Tun da aka sallamomu ban ganshiba har wajen sallar la,asar duk kewarsa nakeji. Mimi na tambaya tace"suna gidan amare wasu abubuwan ake idasa wa,"dalalo ido nai nace"har yasamu karfin fita lallai daman pretending yake,don ya samu abunda yakeso." Dariya mukai nida ita sai dare za,a sada amare da gidajensu shiyasa duk muna tare,sai tsokanar su nake bakamar husna,don yah meenah mur tasha irin bata son wasa, Na lura daga juya zuwa yau ummi ba karamin canza wa tayi ba,duk tayi sanyi sosai,maah kuwa ta dauke wuta ko inda take bata kallo,sai naji taban tausayi.naje har d'aki nasamu mahh,duk da gaba na faduwa yake,haka na daure na tunkareta d'akin ba mutane ita kadai tana ta shirya kayanta da aka kawo daga wajen guga. Sallama nai ta juyo tare da ansawa,inda take na isa na anshi kayan ina cewa, "Maah sannu da aiki,bari na k'arasa maki." Barmun tayi tana koma wa ta zauna tana kallona,fuskarta har yau babu walwala,don tunda abubuwan nan suke faruwa bata da sakewar fuska,don abunda ummi tayi yayi matukar tsaya mata ga rai,don tana ganin cewar y'ar uwarta ce ta jini wacce suka yi tsananin shakuwa da juna,bata cancanci haka daga gareta ba. Ina ganin tashare hawaye afakaice bance mata komiba nabata damar kukanta a6oye,nagama shirya mata kayan tsaf cikin wadrop sannan nace"maah da akwai abunda zan maki yanzu." Jawoni tayi tarungume tana hawaye,sainaji duk jikina yayi sanyi sosai,hawayen nima suka cika idona nace"maah don Allah kiyi hkr kimance da komi,tunda kinga tayi dana sanin abunda tayi,wlh na tabbata ummi ko duniya da abunda ke cikinta za,a bata yanzu ace tayi maki haka wlh baza tayi ba,tayi nadama ba yar kadan ba pls kimance da komi ki sauko hakan zai saka keda ita duk kusamu natsuwa " Share hawayenta take tace"khairat Allah yayi maki albarka,Allah ya dawwamar farinciki cikin rayuwarku keda duk sauran yan uwanki,hakika kune farincikina kune gatana. nagane cewa duk wani maisona bayanku yake,saboda kan abunda yaya tayi man." Share mata kwallah nake ina cewa"haba maah kiyi hkr don Allah kishare ummi ta yi nadama wlh,kimanta komi ya wuce insha Allah bagashi wadanta ta ke gani da mutuncin ba sun wulakantata......tagane cewa kedin ce dai tatan wadda zata rufa mata asiri kuma ta sota duk wuya duk rintsi,kishare komi ki jata a jiki komi ya wuce,banjin dadin ganinki haka wlh duk sai naji banda walwalah." Murmushi ta sakarmun tana jaman hanci tace"ta Alkairin maah." Dariya nayi inajin dadin yadda ta sake nace"saina gaya wa Abbu kin mashi k'wacen ta Alkairinsa." Dariya tayi itama mukaji an bude kofa an shigo duk kallon k'ofar mukai nida ita. Tsaye yake yasha kaanun kaya,bakin jeans da blue and white color......kunneya rik'e alamun ban hkr yana kallon maah, Hararar sa tayi tana juya baya kallonsa nake inajin wani irin farinciki cikin zuciyata,yayi mun kyau matuka k'amshinsa duk yacika dakin isowa yayi har gabanta ya durkusa yana sake rike kunnensa yace"sorry my sweet maah,bazan sakeba wlh kunyarki nakeji nakasa bin umurninki i'm very sorry ." Juyowa tayi tana d'an murmushi kadan tace"aa karka yaudareni malamin love,ga sweet dinka nan bayanka zaka wani ce man wani wai sweet maah,bacin akanta har asibiti ka kwanta." Kunya bata barni na tsaya cikin d'akinba nafice ina dariya haka maah ta iya tsokana uhmmm sainaji ni cikin wani irin farinciki don samun walwalarta da kalaman ta dasuka nuna cewar ta amunce mana dari bisa dari. "Kin gani kin korar man ita ko maah." Dungurinsa tayi tace"tadai kori kanta ni nace khairat tafi." Shagwabe fuska yayi yace"bake kika bata kunya da kalaman kiba." "To karya nai ba itace sweet din taka ba,koba kaida ita hargadon asibiti ba saboda tsananin kauna,ita gamai Areef shine itama bari tabika inma mutuwa zakai kutai tare." Shikanshi jiyai kamar ya nitse tashi yayi yana sosa keya yace"nikam nima guduwar zanyi wlh maah,ni kibar fadar haka wlh kunya zaki ringa ban indaina zuwa gunki." Dariya tayi tace"kunji dashi marasa kunya kawai,ficewa yai yanajin wani dadi cikin ranshi,yasan kamar yaamu suger d'insa yagama. Wajen karfe takwas da rabi angama sallar isha,i Abbu yakira meeting falonsa,muduka harda amaren kowa ya hallara daga iyayen mata har mu yaran tunda kan yah Areef har zuwa kan salma. Anyi addua da Abbu ya umurci yah yayi,har zaifara magana kenan maigadinmu yayi sallama. Kallonsa duk mukai yadurkusa gaban Abbu yace"Yallabai ga yaron nan da kace kar yasake tako gidanan,gashinan tun d'axu sai kokowa muke dashi akan sai yashigo,nikuma nace bazai shigoba yallabai kaban dama in koya mai hankali." Shiru yayi nadan lokaci kafin yace"Aa kamalu,kashigo dashi har nan." Jinjina kai yayi yace"to rankayadade." Tashi yayi yafita maah ta kallai tace "waye haka kuma abbun su." Jingina yayi yana kallon salma kafin yace.................... *wlh daker nayi wannan kuyi hkr zuwa gobe wlh mura ta tasoni gaba.* Mrs bb ce Mom muhseen. Ina alfahari daku masoyana😘 [7/13, 12:45 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 53. "Ameer ne mijin salma,yakai sati biyu na zarya gidan nan yana son ganina nace kar abarshi ya shigo gidan koda wasa,don inason yadda ya wahalar mun da diya shima saina wahalar dashi." Dariya maah tayi ita dasu Annie,don wani sanyi taji cikin ranta alamun dai asirin ya karye,cikin jin dadi maah tace ma salma. "To abar kukan b'oye ga shinan yaxo biko da ban hkr." Dariya duka asa mata taita sunne kai tana dariya tace"nifa maah banayin kuka Allah kuwa." Murmushi kurun tayi don tasha kamata tana kukan,kuma bai wuce na rashin zuwan mijin nata. Sallama yayi bakin kofa cikin ladabi da biyayya duk ya rame ya lalace,yama canza kamanni gabaki daya,bakin k'ofar ya zauna yana gaida su Abbu da su dady cikin lumana. Dadyn yah meenah yace"iso ciki mana Ameer shigo kaima ai d'an gidane." Shigowa yayi yana satar kallon wajen da salma take,ita kuwa boyewa tayi bayan khairat tana jan tsaki kasa kasa. Dariya nai mata nace"keda habibinki sweetheart,kidan kashe mai ido mana." Duka ta kaimun ina dariya tace"banson wulakanci wlh,ki kyaleni sai ya gane kurensa." Abbune ya fara magana da cewa"Alhamdulillah ala kulli hali,godiya ta tabbata ga Allah mai daukakin sarki daya daidaita mana al,amurranmu,hakika ance komi yayi zafi maganinsa Allah,kuma in akai hkr komi mai wucewa ne,yaudai Allah ya tabbatar mana da ganin dukkaninku ya mallakin hankalinsa,ya zama babban mutun domin yanzu kowane zai je yazauna da abokin rayuwarsa,abunda nakeson nusar daku shine hakuri da rayuwa,duk wanda Allah ya hadaka dashi kayi hkrin zama dashi,domin hakuri shine maganin zaman duniya,kowa yayi hkr da abokin rayuwarsa. Sannan magana ta gaba itace kan Areef da khairat." Ummi ya kallai zai magana tai saurin cewa"Aa Abbun khairat,karkace komi don Allah wlh nasan duk abunda yafaru ban kyautaba,nayi danasani kuma insha Allah hakan bazai sake faruwaba,Areef na kairat ne haka kuma khairat ta Areef ce,ban isa in rabasu ba,domin Allah ne yaha da wannan kaunar inhar wani yayi kokarin shiga tsakani zaiga badaidai ba,ubangiji yabarsu tare ya kawar da shaidan,ina sake ba y'aruwata hkf abisa abunda yafaru,kiyi hkr saudah kiyafe man nayi kuskure." Girgiza kai maah tayi tace"komi ya wuce yaya,Allah ya yafe mana gaba d'aya." Dadyn su mimi yace"Alhandulillah angode Allah,daman koda hakan bata faruba mu munriga mun yanke hukunci tun ranar daurin aure,don aranar ba tashi taron daurin aureba saida aka daura nasu,munyi shirune don ganin yadda zaku sasanta kanku,to Alhamdulillah komi yayi kyau sai fatan Allah ya dawwamar da farinciki cikin wannan family.".kowa yace ameen amman ni nakasa don bakina nauyi yayi,duk najini wani iri,nice yau nazama matar yah Areef,abun yazo mun abazata kasa kallon kowa nayi,salma sai tsinkuloni take tana mun dariyar mugunta,da tsokana"Amarya yar shagali,hankali ya kwanta yaudai buri ya cika sai ayiwa Allah godiya." Bugeta nai bance komiba Abbu yace"sai maganar salma da Amer,gashinan yana jinmu,kozaka gaya mana dalilin dayasa ka korota,sannan aka aika kiranka kace bazaka zoba." Hawaye yake zubarwa ya tank'washe k'afa yace"Abbu don girman Allah kayi hkr,wlh banson nayi ba,Abbu ban cikin hayyacina hakika sakaci da ibada dakuma wasa da lokacin sallah yasa duk abunda yafaru dani ya faru,domin raihana qawar salma tayi anfani da qawancen dake tsakaninsu ta wargaza zamanmu,itace tasaka man magani cikin abinci na naci tundaga sannan ban sake ganin salma da kimaba,banson ma ganinta ko muryarta naji jinake kamar nayita dukanta,raihana kurin nake gani da mutunci,har iyayena ban ragawa ba,nasha zaginsu idan suka gaya man abunda baimun ba.......wlh Abbu raihana azzalumar macece shu,uma tarabani da komi har gidana tayi anshe,saboda tayi anfani da damar ta ta anshe tardun gida har hannu nasa mata,yanzu haka wajen aikina sun koran,saboda wasu kudi data sani na sato mata........kuka yake sosai kamar karamin yaro,wlh Abbu banyi da niyyaba bansan inayiba,saida asirinta yatonu,kwatsam saiga qawarta tazo rannan suna hirar,tana gaya mta cewa ai takora salma gida,kuma kwanan nanzata sani in saketa,alokacin naji kamar anbuga man guduma ga kai tunda na suma ban sake sanin inda kaina yakeba sai gadon asibiti............har nadawo hayyacina banga raihana ba,ashe tanacan ta kwashi abunda zata kwasa ta soyar da gidan tabar garin..........sai lokacin nadawo hayyacina nagane cewar raihana bata sona tazone daman ta wargaza mana zaman mu." Shiru falon yayi kowa ya tausaya mashi,salma kuka take kasa kasa don kuwa du laifinta ne,data kula alaka da ita,gashinan ta jawo abunda yawargaza farincikin su itada mijinta.............lallashinsa Yah jahid keyi yana bashi hkr, Abbu yace"Allah ya kyauta,saikayi kokarin gyara kuskurenka kakuma yi istigfari ka rik'e ibada,domin kuwa Allah yace duk wanda yabarni yana tare da 6ata,bazai ta6a ganin dai dai ba.Allah ya bamu ikon rike ibadarmu yakuma rike mana imanin mu,salma kinji bayanin mijinki don haka saiki yafe mashi,don bai cikin hayyacinsa kuma insha Allah zuwa gobe zaki koma d'akinki,zan baku gida halak malak,kuzauna sannan zan samar maka wani aikin,saika kiyaye gaba kasan me kake ciki." Godiya maah tayi mashi tare da yi masu nasiha itama mai ratsa jiki,duk iyayen kowa ya tofa albarkacin bakinsa,yaja hankulansu daidai yadda zasu zauna da junansu. Sannan tarewar Areef da khairat saita gama IT d'inta sun zana exams dinsu sannan,zuwa lokacin Airah ta k'ara k'wari ana ma iya yayeta lokacin." Kowa ya dauki atarsa kuwuce gida jenku Allah ya bada zaman lafiya.Ameer kaje zuwa gobe saikazo kuwuce saudah dauko mashi mukullin gidan nan na unguwar gwarumfa,yana nan cikin drower bedsed dina." Taje ta kawo mashi ya bashi yaita godiya yana mishi Addua,maah tace ma salma taje ta rakashi,akunyace tatashi Annie da ummi suna mata dariya. Fitowa duk mukai don rakiyar amaren,ina rike da hannun husna ina mata rad'a dukana fake tana kuka,bilhakki dagaskoya kukan take ummi ke lallashinta tacemun inje indauko hijab na rakasu nida mimi. Aguje ko muka koma muka dauko abayu don rakiyar amare don daman banje gidan ba zanso inganshi yadda aketa zuzutashi. Yah Imran da Amaryarsa yah meenah itama kukan take me zamuyi masu banda dariya,sai kace ba su sukace sunji sun gani ba,Anty shida ma kukan take jikin maah,sainaji sun ban tsausayi rabuwa da iyaye babu dadi kokadan,nima sai naji kwallar ta cika idona.hadesu maah tayi yana lallashi da nasiha tare da cewa inbanda abunku ba muna tareba ina nan ina maitama,kuyi shiru kunjiko." Daker sukai shiru suna ajiyar zuciya,ummi ma rungumesu tayi tana goge kwallarta itama........Annie kau kasa tsayawa tayi ta shige gida,Allah sarki abun gwanin ban tausayi saida Abbu dasu dady sukazo suka kai kowace cikin motar mijinta sannan fah yacewa su maah sukoma gida inkuma binsu zasuyi to." Murmushi sukai suka shiga gida nida mimi kuma motar yah Areef muka shiga. *muhadu gidan amaren pls aiki nake wlh* 😂 Mrs bb Mom muhseen.😘😘😘lov u my fans [7/14, 3:25 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 54. Sun isa gidan amaren lafiya tunda ga get din farko zaka gane cewar wannan gidan ba na wasa bane,get din kansa kamar ka k'wal k'waleshi ka gudu, get din farko zaka tarar da wani tsalelen gini hawa biyu,daga fuskar gidan zaka gane cewar gaskiya kudi sunyi kuka bama kadan ba,wannan gida na farko shine na yah jahid,shida amaryarsa Anty shida. Shiga sukai ciki tundaga waiting falo khairat da mimi harma dasu amareb suka fara santi,komi yaji don tsayawa fayyace tsarinsa sai mukwana mu wuni. (Zanso kuga wannan gidan y'an zauren mrs bb.kashh kallo yabar ku baya) Babu inda basu shiga ba suna yabawa har dakin amarya suka kaita,sannan suka fito don zuwa yah Imran. Areef ne ya jawo khairat baya ya matse jikinsa yamata rad'a. "Ki kwantar da hankalinki naki yafi na kowa kyau,don maigidan ki anan duk ya juye fasahar da Allah yai masa,kin san ko ai dole namu yafi na saura." Dariya nayi ina kokarin kwace hannuna rik'esa yayi gam yana bina da wani irin kallon kauna,daker na fizge na ruga wajen su mimi. Wanda ke bayan na yah jahid aka wuce mimi tace "yo yah ya zaku wuce nan bayan ga amaryar nan basai mu ajiyeta ba kurun." Dungure mata kai yah Areef yayi yace"ankiya tun yanzu ku gane mana gida sai randa zamu tare ko suger nah." Harararsa nayi ina bin bayan husna dake kusada yah meenah. Shima gidan yah imran ya had'u matuka don a iri daya bane,kowane da tsarin nasa nanma muka kara lalacewa muna zagayen gidan,daker muka fito muka kai su husna nasu,shima dai abun ba acewa komi saidai fatan alkairi ga dukkan masoyan,haka muka kai kowace tare da yimasu fatan alkairi,muma muka nufo hanyar gida. Yana yin parking mimi ta arce don daman ina kallonsu suna magana ta madubi,fitowa mukai duk naji yanayi na yayi bala,in canza wa duk tsoron yah yakama ni,saida ya rufe kofar falon yace"muje na rakaki d'akinki." Marairaice fuska nai idona dan danan ya kawo ruwa nace"pls katai ai inagani zanje dakaina." Dariya yayi mun yana kahe glup din falon gaba daya. Sand'o nake ina bin hanyar korido d'in da zai kaini d'akina.........caraf ya rik'eni har saida na sauke wani gauron numfashi,kan na akare yayi sama dani kamar yar baby,runtse ido nai don jin yadda naji duk jikina yayi sanyi,wlh nidai banson komi yashiga tsakaninmu har sai na tare,don ni wlh ban san ma yadda zamu kare dashiba wannan rawar kafar da yake. Da kafar sa ya tura kofar dakin,tunani na zanga mimi naga wayem,na jinjina kai tabbas abunda yake gaya mata kenan cikin mota,duk na tsure bai saboda jin yayi filingin da hijab dina. direni ko ina ba sai cikin bathroom durk'ushewa nai na kudun dune jikina ina saman wani table da nake jera kayan wanka na irinsu turaren wanka man wankin kai,makilin,man goge kafata da lotion din tsarkina. Tsura man ido yayi yana kallona kamar yasamu wani film,duk ya idasa kashemun jiki da wannan shu,umin kallon. Cikin sanyin murya nace"yah.......katseni yayi da cewa. shiiiiiiiitt lumshe idona nai don nasan wlh ba saurarata zai ba,idona duk ya raina fata kasa yin shiru nai nace"wlh ban shirya ba kuma idan maah ta sani ko ummi wlh fada zasuyi mun." D'an durkusa wa yayi gabana idonsa akan bakina,araina nace nashiga ukuna fah ba a daura auren ba ma wace Allah cika balle yasan andaura. "Ni bansan ma haka bakinki yake da bala,in kyauba sai yau,kinga yadda yake shek'i." Kauda kai yayi nayi inajin kalaman sa kadai suna rikita mun lissafi. Hannunsa naji saman kaina ya jare hular dana saka d'azun,cikin wata irin sweet voice d'insa dake narkar da duk wani kuzari nawa yace"wow I love it."yana shafa gashina dan danan naji kaina ya ansa,jin yatsunsa suna yawo cikin kaina,jujjuya kai nake don yanayin da nakeji bazan iya misalta shi ba. Tashi yayi yakunna ruwa cikin bathtub ya sirka shida mai d'umi,turaren wankana ya dauko idonsa akaina yana wani killer smile,zubawa yayi sannan ya motsa ruwan,ya maida inda ya ke ya dauko sabulun wankan cream ne,inka zuba ga hannunka zaka ringa bin jikinka dashi.......ajiyeshi yayi gefe wajen komin wankan,ya sake dauko lotion dina na tsarki yana karanta rubutun dake jikinsa,ya kallan yana sake k'awata fuskarsa da smile yace"suger nah meye wannan." Dagowa naiina kallon rubar jinai gabana ya fad'i naisaurin anshewa nace"shampo ne na wanke kai." Dariyarsa har saida tafito fili yace"ok ai dayake ma zamu wanke kan bari mu ajiyesa gefe." Zaro idonai don natabata ya gane kona meye nace kamar zanyi kuka"yah kaina baida datti da bikinnan fa naje saloon." Baice mun komi ba ya gama hada komi sannan ya nufi inda nake,zaro idonai nace"don Allah karkayi man irin na rannan plsss kabarni nayi shirin baccina,wlh ni dai nagode kayi tafiyarka." Uffan baice man ba ya daukoni ya dire kasa kan kafafuna,rungumeni yayi yana zaga yawa da hannunsa ta baya yana zuge zif din rigata.......runtse ido nai ina k'ank'ameshi don nasan babu abunda zance ya ya dakatar dashi. Zare rigar yayi dagani sai pant da bra don bansa undey ba d'anja baya yayi yana kallona from head to toy. Ajiyar zuciya yayi yace"i thank god daya bani mata irin wadda nake so,hannu ya mikomun taho kiji my suger." Banda wani zab'i dole na mik'a mashi hannun ya idasa jana jikinsa,fuskar sa ga wuyana yana shin shinani,hannunsa kuma yana 6alle mun bra d'in,numfashi naja ina jin kamar yana zare mun duk wata lakka ta jikina,saida yayi nasarar rabani da komina,sannan ya daukan ya saka ciin ruwannan daya gama had'awa,d'umi garai mai ratsa jiki. Idona lumshe inajin ruwan yana ratsani,hakika yanayin da nake ciki ko rabinsa ban tab'a tsintar kaina acikiba lokacin da nake tare da Dr,shidai barshi da yan tabe taben sa ya samu ya tadama kanshi tsumi,tofa da zaran ya dau caji babu ruwansa dani zauhau aikinsa baji babu gani,da ya kawo zai tsallakeni yana samun albarka,zan iya cewa tunda nai aure bansan dadin jima,i ba saida na samu ciki shima bawai don kaina ba saboda abunda ke cikina,dr baya romance dani babu ruwansa da wasu yan wasanni shidai yajishi tsundum shine burinsa. Tunanina ya tsaya lokacin danaji hannunsa saman wuyana yana yawo,zabura nai kamar an tsira man allura........yawo yake dashi zuwa kunnena zuwa saman fuskata,wani tsirin abune nakejin yana bin jikina banda sauke numfashi babu abunda nake,sabulun ya tsiyaya ga hannunsa yana bin sak'o da lungu na jikana,kua very slowly gently yana ba ko ina muhimmanci,kan kace me nafita duk wata natsawata shima nafitar dashi,bansan sadda najishi cikin ruwan ba,jikina da nashi suka game waje guda,nidashi idonmu duk rufe sai mulkar jikan yake yadda yakeso,nishi kurun nake fiddawa sai faman mik'a nake ina bank'arewa...........minfi karfin minty talatin sannan ya bude magunar ruwan yafita yasake tara wani,ina jikinasa na lafe kamar yar mage,dago habata yayi idonsa akan fuskata,duk sun canza launi cikin wata voice mai laushi da shiga jiki yace"suger open ur eyes and look at me." Wani irin numfashi naja ina jan ajiyar zuciya daker na lalubo maganar don muryata b'at bacewa tayi. "Bazan........baz....bazan iya..ba." Wannan maganar tayi masifar rikita mashi mashi tunani,lumshe idinsa yayi ya bude yace"ohh my suger pls mana,i want see my love In ur eyes,pls open it now." Jinai kamar yana zarar raina da wannan maganar,ba kamar da naji hannunsa saman nipple d'ina yana d'an murmmurzawa......bansan sadda nace"ohhhhhshhh." Muryar sa can kasan makoshi yace"oya open." Ahankali nake bude idon ina jin yanayina yana kara hauhawa,har na budesu tas cikin nasa na tabbata yadda idonsa ya canza haka nau yayi,kallonsa danake sai nakejin kamar zan mutu saboda yadda wasu irin mahaukatan feelings dake taso mun from now where......matso da fuskarsa yake haf da tawa yana cewa don't cloth it pls."kamar wata sakara haka na d'aga mashi kai,ahankali yake sake nufo face dina,har yazo gaf da bakina bansan sadda nazo zan lumshe su ba yayi saurin cewa"no don't do it." Daker na sake budesu bakina yake kallon yana goga hancinsa saman nawa,da gefe da gefen kuncina kafin yayi masauki saman bakina........wani dogon nishi muka saki nidashi,dandanan kamar wani mayunwaci yashiga kissing din bakina,bansan ma ina taya sa ba saboda har ga Allah nakai makura,wani irin zazzafan kiss mukewa juna,miyan sa yake jalalamun ina shanyewa,ina bashi nau yana sha munfi awa cikin bandakin nan,mun b'ta ruwa yakai kala uku. Wanan sabulun na tsarki ya dauko ban ma sani ba,saidai naji hannunsa can kasana wata irin zabura nai ina k'ankameshi,daker nake jawo numfashi matse kafata nai ina girgiza kai nakasa magana. Ahankali yake mun rad'a ga kunne. "I'm ur husband,duk abunda nai maki suger is not haram karki manta lada fa zaki samu kuma nima zan samu,plss karki hanani gonata ce Allah yaban damar shigarta aduk sanda naga dama plssss suger." Maganar yake yana dora kafata daya kan tasa yasake dora dayar ga dayar kafar,sake matso sabulun yayi yakai hanunsa wurin yana shafawa,nidashi saida mukaja wani irin numfashi,hade fuskokinmu yayi still yana shafawa ahankali,yana murzawa yadda zai shiga cikina daker nake numfashin yanxu,nidashi bazan banbance wanda yake gaf da suma ba,amman inajin nizan rigashi don bazan iya jure wanna feelings dinba.baiga alamar yah zai bar shafa niba,don sabulun ya hade da ruwan gabana yana bada wani irin sulb'i..........saida na fashe mashi da kuka sannan fa ya daina,ya kora ruwan yatara mana wani yadauraye mana jikinmu ya nadoni cikin towel,banda ajiyar zuciya babu abunda nake ja. Har kan gado ya direni ya shafa man mai yasa man kayan bacci,sanna ya shirya kansa saida naringa rera mashi kukan shagwaba sannan yatai yabarni,wannan rana ban samu bacci ba murje murje naitayi sai gaf asuba baccin ya sureni,ban samu sallar asuba ba sai wajen shidda da rabi,sannan nayi nakoma don idona har rufewa yake. *yaudai nayi rashin kunya,kunja kunyar ma hada ido nake daku*🙈😂🤭 Muhadu second to the last page 😄laifin dadi kare wa Mrs bb Mom muhseen😘😘 [7/16, 12:20 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. 55. Not edited (inkunga typing error kuyi hkr ina saurine) Ban tashi ba sai kusan karfe sha biyu,banyi mamaki ba saboda jiya naji bacci idona sosai. Wanka na shiga na fito ina shafa mai,ahankali inabin fata ta datayi wani irin fresh,don duk gyaran da akayiwa amare muma nida sweetheart dina sai da akai mana,shiyasa jikinmu gashinan kamar na jarirai,don wacce tayi aikin gwanace sosai annie ta daukota daga maiduguri.aikuwa munsha gyara don inajin shiyasa sha,awata kara karfi. Nai mamakin abunda ke fita daga kasana jiya na manta ashe fa nasha kaya da yawa,murmushi nai ina tuno moment dinmu najiya,lumshe ido nai inajin wani irin farin ciki yana cika zuciyata. Yanzu zan san nayi aure,yanzu zanji dadin dake cikin marking love.........Allah sarki dr Allah yajikan ka yayi maka rahma,Allah baisa zamu yi rayuwa maitsayi ba,ina maka fatan samun rahmar ubangiji. Shaf shaf na shirya don inje in gaida Abbu naji yace zaije unguwa yau. Riga da siket ne cikin kayan bikin da ban gama sawa ba nasa.sai na ganni na canza sosai fuskata sai annuri take,dariya nayiwa kaina ina fesa turare nafito daga d'akin. Saida na gaido Annie da sauran yan uwanta da zasu tai yau,sannan na wuce wajen Abbu muka gaisa yake jana wai harna yi kiba daga jiya zuwa yau,don jin nasamu abunda nakeso. Gudowa nai saboda kunyar da yabani,mimi ce mukai karo tana goye da Airah. Zaro ido nai ina kallon babynah "yaushe kikazo sweetie nayi kewarki wlh,zo taho ga mominki kima kinyi kewarta ko." Na sunbaci goshinta aikuwa ta hau b'angale dariya,duk ta kara man girma nagani ansar ta nai ina cewa"sweetie me ummi ke banka maki kikai wannan girman,wlh kinyi kyau muaaahhh." Dariya taitayi tana k'yalk'yalawa.mimi dai kallonmu take kafin tace"Amarya kinsha k'amshi to ya amarcin." Harara na banka mata ina wucewa b'angaren ummi biyoni tai tana dariya"daga ganinki ma wlh na samu ansata,kinga yadda kika yi jawur sai daukar ido kike dagani wlh kinsha madara jiya." Zaro dara daran idona nai in rufe bakina nace"innalillahi,mimi ubanwa ya koya maki iskanci,aikuwa kamar gaban ummi kikai saina gaya mata,shegiya marar kunya kuma zamu gauraya wlh nidai kika yaudara ko." Dariya kawai take tana rik'e ciki tasan ta hada rigima. jiya anyi kam tasan anyi shagali. Koma wa tai tabarsu suka shiga b'angaren ummin. Tana ta yiwa mai aikinta fad'a a kitchen suka sameta.tana ganinsu ta washe baki tana mik'o wa airah hannu amman ta mak'ale kafad'a Ummi tace"kinga ja ira,au kishinne ya tashi tokuwa saidai ki mutu yarinya,mijina yafi karfinki."tafada tana hararar Airah. Me khairat zatai ba dariya ba,hartana dukawa tace"kai ummi,itafa ba haka taje nufi ba." Hararata tayi tace"gashinan tana mun kallon uku saura kwata,kice ba haka take nufi ba to wlh koma mekike nufi yarinya nan gani nan bari wlh." Dariya nake har da hawaye don wlh ummi taban dariya ganin zan yadda Airah yasa itama tayi dariyar tana ansheta daga hannuna. Muka fito falonta ina gaidata ta ansa cikin walwalah ummi ta canza sosai,ferfesun yan shila ta kawo mun tace"maza cinyesu kishanye roman,karki tauna kashin don wlh wancen mayen idan bakiyi dagaske ba zakisha wuya,don naga rawar k'afarsa tayi yawa." Na shiga uku na kunya kamar ta kasheni sai soke kai nake k'asa,jinai ta dungure man kai tace"dallah can,wakike jima kunyar zan makeki wlh ja ira saki jiki kicinye ko sai na sab'a maki,kafin infito daki kin cinye shi.kekuma kishiyata zomuje d'aki badan halinki ba." Fita sukai suka barni ina cinsu,wlh babu dadin gaba balle na baya inaci ina ya mutsa fuska,daker na cinye su romon kuwa kasa shanye shi nayi duka na je kitchen na zubar na wanke kwanon. Ficewa nai don wlh bazan iya had'a ido da itaba wajen maah naje,itama da nata abun nida salma tatusa gaba saida taga ina shirin amai ta kyaleni,wasu abubuwane taringa durka mana,can nabaro salma,don indan natsaya saina amayar da duk abunda naci. Mimi kau yini tayi tana jana kamar zan mata kuka nace"plsss karki sake irin abunda kikai jiya wlh kadan yarage.........plsss kibari kingani cikin gida muke shikuma ba kunya ce ta isheshi ba baijin komi nizai bari da soke kai kasa." Tana dariya tace"sorry my Anty nabari bazan sake ba." Airah yini tay wajen ummi saboda ta tusa mata kayan wasa da chocolate,saudaya tasha nono abunda ma nalura dashi nonon bai dameta ba yanzu,sai dai koko ko costand. Karfe shidda Ameer yazo yasha gayunsa kamar dai sabon ango,sai zuba k'amshi yake dariya kamar ta kasheni saboda tsokanar ta danake,saida tayi kamar zatayi kuka nadaina har bakin mota muka rakota ta rungume maah tana hawaye. Maah tace"mezangani haka salma,kema sabuwar amaryarce bason sakarci fah." Cikin kuka tace"maah wancen karon banyi kuka ba,saboda ina murnan zanbarku ina ganin kun takura rayuwata ne baku sona shiyasa,amman saidaga baya nagane cewar banda masoya kamarku,dangin mamana da suka ringa zigani aranar,tundaga sannan ban sake ganinsu ba,babu wanda ke daukar kirana idan nakirashi,amman ku nadawo gidan kun ansheni hannu biyu,babu nuna damuwa ko zagi balle hantara,banda bakin da zan iya gode maki maah,saidai zan dawwama ina maki adduar gamawa da duniya lafiya,ke uwace tagari mai tsayuwa kan lamarin kowa,kiyafe mun maah kiyafe mun kisaman Albarka wannan karon,don nasan hakkinkine yabini wancen lokacin naimaki alkawarin yin biyayya gareshi da kuma hakuri da zama gidana,don kuwa shine zaisaka ki farincki,kiyafe mun maah." Babu wanda bata ba tausayiba lokacin don nida mimi kuka muke taya ta ,ita kanta maah din hawayen take gogewa tace"haba salma aike diyata ce har abadan,kuma na tabbata nono na dakika sha baki zubarba,kawaidai wani lamarine na ubangiji dakuma kaddara,na yafe maki duniya da lahira salma Allah kuma yayi maki Albarka ya azurtaku da zuria dayyiba,kibi mijinki sauda kafa koi ya umurceki inhar bai sab'a ma sharia ba kiyi,sannan zuwa yanzu kinyi hankali kindauki darasi,saikisan wanda zakiyi qawance dashi." Tana goge kwallarta tace "maah nida qwa har abadan,y'an uwana gasunan sun isheni rayuwa wlh." Dariya taba mu itama tanayi sannan ta shiga motar yayiwa kowa bankwana sukatai muna daga masu hannu. Sauna muguwar kewarta Allah sarki naka nakane koda kai mezai maka. Haka gidan ya koma daga ni sai mimi dasu maah,saifa sweetie na Airah,wsan b'uya muka komayi nida yah Areef,danaji zaishigo zan boye duk yadda yaso ganina nahana don yadda nakejin canjin jikina wlh ya tab'ani akwai damuwa.hutuna ya kare na koma IT dina daman sati uku yarage man na zage bakin kokarina inayin duk abunda ya kamata,saidai yah yabini har can yaganni amman ba gida,wata irin soyayya yake man maisanyi mairaysa ruhi,ina tsananin kewarsa nikaina yadda nakejin kaina ina bukatar shi,don umi da Annie da maah kamar zsu kshine da kayan gyara,musamman annie ta ke kirana tana mun darasin kwanciyar aure,ranar data fara kamar zan nitse harta gama bance kala ba,kaina yana kasa tace mun dukkansu yan uwanki babu wacce ban mawanba,saike shiyasa naga yadace na ganar dake na nusar dake,don mahaifiyarki bazata iya ba,ita kuma ummi tace kunyar ta da kike ji bazata barki kigane ba,gara dai ni na maki,don haka ki kula kikuma yi aiki dashi don wlh Areef dole saida kulawa,ina lura dashi duk yafi sauran rawar kafa." Haka annie tazage tun inajin kunyar harta rage,wani zubin idan inada tambaya zan mata kuma taban ansa,zuwa lokacin nikaina amatse nake wlh daker nake bacci saboda d'an banzan feelings dake hanani bacci. Hardai Allah yasa nakare IT dina muna exams din final lokacin ummin dr tace na yaye Airah tunda ma ba shan nonon take ba,da nayi gardama saboda inajin tausayin sweetie,amman da maah ta lallasheni ta kuma nuna man hakan shine daidai saina hakura na cireta,bayan kwana biyu ummin dr tazo ta tai da ita wajenta da kuka muka rabu kwana nai ina kukan rashin sweetie,Allah ya sani ina son Airah ban san ma ina sonta har haka ba saida akarabani da ita,ganin duk nashiga halin damuwa yasa ummin taki rani tace inyi hkr idan natare da sati biyu zata kawo mun ita. Wannan bayanin yasani na samu natsuwa har nasaki jiki aka cigaba da yimun gyaran jiki,inka nni ak ganeni,saboda canzawar danayi mimi sai santi take wai kosu Anty shida ba aiwa wanan gatan ba saini,Annie tace "kinsan ai ita tadaban ce kema ki hanzarta dai Abukhalipa yadawo atsayar da lokaci wanda yafi wannan ma yimaki za,ai." *MU HADU FINAL PAGE INSHA ALLAH.* INA MATUKAR ALFAHARI DAKU MASOYANA HAKIKA BANDA KAMARKU ALLAHBYABARMU TARE,YA KAWAR DA IDON MAKIYA KANMU KARKU MANTA COMMENT DINKU SHINE KWARIN GUIWATA,KUCIGABA DA YADDA KUKE MAMAN MUHSEEN TAMUCE INSHA ALLAH. MRS BB CE MOM MUHSEEN. [7/19, 6:24 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 🌹 *ABIN CIKIN RUHINA* Writing by mrs bb Mom muhseen. Wattpad name Humaira7531. DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB. *FINAL* *LAIFIN DADI KAREWA,BAKINA BAZAI IYA BIYANKU IRIN GODIYAR DA ZAN MAKU BA,KUN NUNA MAN KAUNA KUN SONI KUNSO BOOK DINA,ALLAH YA BARMU KU YASAKA DA ALAKIRI.* *WANNAN LAST PAGE DIN SADAUKARWA NE GAREKU MASOYAN ABIN CIKIN RUHINA.KUYI DUK YADDA KUKE SO DASHI.* Rana bata karya saidai uwar d'iya taji kunya,Allah yayarda lokaci yayi akawarin Allah ya tabbata khairat agidan *Abin cikin ruhinta* bayan tsawon shekaru dasuka gaba,bayan duk wata gwagwarmaya da akasha,bayan duk wasu kalubale dasuka fuskanta,bayan sallar magaruba Annie da Mimi da ummin dr suka rakata har gidanta,a can suka tada amaren anty shida husna Yah meenah.sai salma data zo itama Airah nai nai tazo ta k'iya tana lik'e jikin ummin. Suna kawo ni sukai sallar mangaruba suka wuce. Nanfa aka bude chapter hira nida nazo Ina risgar kuka saigashi na bige da dariya Anty shidah kuwa tashi tayi don jin maganar damuke husna kecewa. "Hum wlh khairat na tantance abunda kikaji lokacin da naje na sameki gidan dr.alokacin fah ganin bekenki nake,akan baki hkr da lalurar mijinki." Dariya nake Ina rik'e ciki yah meenah tace"uhm ai in ana salla ba,a magana duk yan gidanmmu kaf babu Wanda ban kiraba saboda azaba,banyi tunanin yah imran zai tab'aniba ranar nan,saboda yi yayi kamar bai damuba,ashe cewa yake gama bacin." Dariya harda kwalah nace"yah meenah baki kirani ba,aida dagudu zanzo na kawo maki d'auki." Hararata tayi tace"wlh sunanki yafi na kowa ya wan kira don har gobe dashi yake Jana." Dariya suke abunsu salma tace"wlh konidai da ba sabuwa ba randa na koma Ameer baimun da sauki ba,naji jiki don haka kibar dariya kilan duk area nan saikun jiyo ta yah meenah." Jinai gabana ya fad'i nai zuru ina zare ido. Anty shida dake cangefe tana danna waya ta kallan murmushi tayi tace"kuma wlh bamu zuwa muma." Me zasuyi ba dariya ba idona yayi kwalkwal dariya suka dunga mun,husna tace"kyalesu ta alkairin Abbu,babu wani abu dazai sameki abunda ma yayan naki ne sai yadda kikai dashifa." Nan dai sukaringa kwantar mata da hankali har sadda su Areef sua shigo anyi sallar isha,i zuwa lokacin khairat tayi wanka tasaka riga da siket,sai tsananin kamshi take,su husna sunbud'e gidan da k'amshi na turaren wuta da freshener. Yah jahid ne yafara shigowa idonsa akan anty shida dataje tayo wanka tayi gayu sosai,sakin baki yayi yana kallona,batama San yanayi ba sai fesa freshner,wjenta ya isa ya rungumo bayanta yana cewa"my dear u look so beautiful I love u." Salma dake kusada su takauda Kai tana dariya,husna tace"nidai saina tanka,yah ko ganin ido bakayi." Murmushi yake yana rik'eda hannun ta yace"Wankan makaho,Wanda yagani shiyaji kunya.ko ba haka ba dear." Dariya tayi tana janye wa daga gareshi,Shahid ne yashigo yana cewa"kifito muwuce gida wlh,don ango yace sai duk kunfita zaishigo,gara mufece kafin yakai ga samana bulala." Dariya sukai shida yah jahid,salma tace"wai dagase kake yah shahid." Yana rik'eda husna yace"wlh yana waje yamaki fitowa daga cikin motar." Jinjina Kai sukai itada yah meenah,suka kalli khairat suna dariya. "To amarya Mudai bari mufece Allah yasa Alkairi,ayita hkr." Dariya suke duk suka dauki gyaluluwasu sukafice,kuka nake sosai saboda a bun yaban haushi,donme zai korar Mani su,duk salon zakewa da rawar kafa aisai yazo yaci uwarda zaici. (Lol khairat kenan harkin gama kewartasa.) Salma ameer daman yana kan hanya,suka wuce gidan su don yanzu kauna suke zubaw kamar zasu cinye juna,yaje har gidansu Raihana ya kaimata takardar sakinta. Hakan yayiwa salman dadi ba kadan ba,don yanxu gudun b'acin ranta yake,Abbu ya Samar masa aiki sabon company daya bud'e shi yaba MD din wajen. Sallar isha i nai na fito falon komi need sai k'amshi ketashi,zanso kuga yadda falon yake babbane yasha manyan labulale different color's,ga kujerunta royal set biyu ga wasu can a karamin falon. Bedroom dinta kuwa gadajeni na Gan na fad'a,kuma Duk Areef ne da wannan aikin,sauran kayanta na gidan dr kuma yace salma ta dauka. Aikuwa ba karamin dadi yayi mata ba,don daman raihana ta kwashe mata kujeru ta siyar.gadon kuma ya lalace. Komi sabo haka ta Alkairin abbu akai Mata,kayan kitchen ne kurun dadyn yah meenah ya ba Annie kudi tasake mun. Gaskiya ban San irin godiyar dazan wa iyayena ba,don kuwa ta KO ina nasamu gata da jin dadi.iyaka dai addua da gama wa da duniya lafiya shine zamuyi tayI masu. Tana zaune falon ya shigo,shan mur tayi duk da yadda gaban ta yake mugun faduwa,ta mance rabon data ganshi kwayar idonta so take ta kalleshi Amman ta hana ta. Tunda ya shigo wani irin fitinennan kamshinsa ya bud'e Mata hanci,lumshe ido tayi tanajin kabanta yana sake faduwa. Wani glub ya kunna wanda ya karama falon kyau da haske. Green da red sai purple ne hasken,yana walwali. Kamar nariga haka naji Amman na kasa motsawa har sadda ya idasa isowa wajena. Kallabina ya ture yakaranta mun wasu adduoi. Yana gama wa ya sunkuceni yayi bedroom dina dani,zazzare ido na keyi shikuma yayi nasarar tura idonsa Viki nau,wani Shu,umin kallo yake jifata dashi,Wanda bansan sadda naji wata irin kasala ta rufeni ba,toilet ya ajiyeni yana kunna mun famfo. Cikin wata lallausar murya da bantab'a jinshi Da ita ba. "Kiyi alwallah in mai daki." Kallonsa nake kamar yau nafara ganinsa sun kuyowa yayi ya sunbaci goshina yace"oya do it now." Kamar yar koyo nafara alwallar,har nagama yana tsaye kaina. Sake d'aukata yayi yamaida cikin bedroom din sannan ya dauko mun hijab cikin wadrop ya Samun. Ya shimfida praymate ya mikardani ya lalubo kunnena yace "zamu godewa ubangijinmu daya zab'ama mana buna has nun da Rabin mallakar junanmu," Lumshe ido nai najinjina kai naka sa magana. Jammu jam,I yayi mukai raka a hud'u sannan muka sallame,yajima yana her adduoi masu tsayi ina amsawa da Amen. Duk na Neman Alkairin Ne da juria ta gari da kuma kariya daga shedanin mutun dana Aljan. Tashi yayi yaciro mun kayan baccina masu masifar lays da taushi,kamar gashin mage,yasamun banyi yukurin yimashi gardama ba,har yah samunkuma babu abunda ya tsayayi min kayan kurin ya Saman. Fita yayi yabarni nai zuru Ina zare ido,Anya yah Aref zaibarni awannan daren. Tunani Kala Kala babu Wanda banba kafin naji alamun shigowarsa. Tire ne yake dauke dashi kazace sai tiri take ma,ga wata d'anyar madara Mai shegen sanyi,sai lemo na kwali ga cups guda hud'u masu tsananin kyau da tsari. Dire shi yayi gabana yasha mur Lamar bashine yake murmushi mai kyau na yace"oya banson gardama banson kuma inji kince nakoshi." Daga Kai Kurun nai debowa yake yana Kai wa bakina wani zubin saiyajani yayi kamar zaiban sai yajanye saikuma yaban,saida naji kamar zanyi amai sannan yakyaleni. Yace inbashi shima dole na Saki jiki ina bashi yana Jana da labari,har nadaina wannan d'ari darin dashi......saigani ina dariya har saida shima yaci ya koshi sannan ya kauda kwanonin yawuce d'akinsa ya shirya. Brush nashiga nayo na dawo sadda zai shigo har bacci ya saceni ban sani ba gyara mata kwanciya yayi sannan shima ya kwanta. Abunda nai zargin bai yimun ba saidai yasani cikin jikinsa kamar zai mayar da cikinsa,saida asuba bayan mun gama salla labarin yaso can za wa,lamarin yazo mun a bazata don kuwa Kai na ya kunce nayi losing control d'ina domin yah wani salo yazo mun dashi da tunda maah ta haifeni ban tab'a jinsa ba,saboda yadda nakejin salon sa jinake kamar zan mutu,kuka nake harda hawayena saboda yadda nakejin salon yafi karfina,saida yakaini makura sannan ya nemi hanyarsa. Ashe kukan baizo ba tukun dazun kukan dadi nayi yanzu kuwa Kukan azaba nake,tun Ina gane karatun har nazo bangane komi IBU da neman dauki kuwa nayishi Karsh dad'emun baki yayi harsaida Allah yasa ya Kai linta.daidai da Dan yatsa ban iya dagawa kamar wadda ta mutu haka nakeji.nasha why ba karama ba saidai kokisa ban kai wuyar da tasha gidan dr ba don kuwa banbancin abayyane yake,duk da lokacin ina budurwa ne amman yah yabini salo salo daki daki,dalla dallah banda ajiyar zuciya babu abunda nake,shima sai albarka da addua yake samun. Yah kamar mahaukaci haka yakoma man kuka harda kururwa har yaban tsoro. Wanka yajani mukai sai riritani yake kamar d'anyen kwai,nikuwa sai shagwabe mashi nake haka muka samu muka koma baccin safe. Agurguje. Rayuwa maidadi suka shiga cikinsu kowa ji yake Da mayarsa din Areef idan kagansa gaban khairat saika daukar bawan tane,nan kiwa zallar kaunace da tsananin so. Salma ta haihu ta samu saurayi yaci sunan mahaifin Ameer suna kiransa salman. Mimi anyi bikinta da Abu khalipa ya dauketa sun wuce London,banji dadi ba don naso mimi ta zauna cikin mu. Anty shidah yan biyu mace da namiji sunan maah da na Abbu Iman da Ayman,saida sukayi wata biyar sannan yah meenah ta haihu itama mace sunan Annie Ameerah ake kiranta.husna kuma saida muka shekara biyu da Aure muka haihu tare don kwana ukune tsakaninmu ta rigani haihuwa ta samu saurayi sunan mahaifin ta sultan ake kiranshi. Nikuma nahaifi twins duk maza Dadynsu Yah Areef aka maka maida da sunan sunan Abbu again *shareef da shurem.* ake kiransu Bacin su ma na sake haihuwar wasu twins din DJ mata kuma *HANAN DA AFNAN* daga nan kuma haihuwar tsaya. Anty shida ma bata sake haihuwar ba mimi ce ta haihu say daya ta Sam u Mac itama suhaila. Yah meena ta sake haihuwa itama ta samu Ameer. Husan ma ta kara namini Khalil. haka rayuwar ta cigaba da tafiya gwanin sha,awa yaransu suna son junan su soyayya tsakanin khairat da Areef a bun ga jinin su yake,don baya jin kunyar nuna mata kauna kogaban waye. Abun sai sambarka kowanen su budi sai sake zuwa yake saboda saka albarkar iyaye. Salma yaronta ya rasu ta sake samun wu yaran,Aleeya da laila. *ALHMDULILLAH TAMMAT* ALLAH KABAN IKON GAMA ABDUL-NASSER LFY KAMAR YADDA KABAN LFY DA RAI HAR NAGAMA ABIN CIKIN RUHINA,INSHA IDAN NA HUTA ZAN YI CONTINUATION DINSA INSHA Allah By by masoyana love u soo much.