[6/24, 10:49 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-1 _Hi Mutanena,mutanen amana,gani na dawo fa ku shirya ku gyara Zama._ 😻🤍 PLATEAU STATE, JOS NORTH. RingRoad. Dauke take da tulin daurin kaya akanta hannunta kuma tana rike da rake tana gatsa tamkar mayunwacin zaki. Tsohuwar dake gefenta suna tafiya ne ta ce, "Salame ai yau dai zan yi maganin Ilu duk iskancin da yake ji dashi da matar tashi sai na sauke masu shi kasa basu san cewa a zamanin ina daya daga cikin tantiran yan iskan kauye bane shiyasa suke mun wannan iskanci." Sai da Salma ta gatsi rakenta kafin ta ce, "Aradun Allah kuwa Inna kar ki raga masu sam sam kar ki raga masu gwanda ayi maganinsu ai." Ta karasa maganar suna tsaya daidai wani gida madaidaici baza ace da shi karami ba kuma ba za asa shi sahun manyan gidaje ba sai dai kam ba laifi ya tsaru wanda kallo guda za asama a tabbatar da cewa lallai mai gidan na da rufin asiri daidai gwargwado. Buga gate din suke dukansu su biyu tamkar wa inda suke dakan sakwara. Jiki na bari mai gadin ya bude yana, "Subhanallahi wasu gidahuman ne haka?" Inna ta kalleshi ita da Salma kafin ta ce, "gidahumai? Ni kake cewa gidahuma? Na ce ka ci gidanku ka ci gidan ku to nan gidan Ɗana ne nice nan uwar illu mai gidan nan ka kiyaye tun kafin inyi tamola da kai da shegen kai kamar kwallon mangoro." Mai gadi ya ce, "ehto ayi hakuri ranki yadade amman ni ba kan mangoro gareni ba." Inna ta bude baki kafin ta ce, "Au da ance ma raina ba zai dade bane? To ahir dinka dadewa kan munyi kuma muna kan yi sannan kuma kace kanka bana mangoro bane?" Ta fada tana maka masa rankwashi aka. Ita ko Salma me zata yi ban da dariya, "yawwa Inna wallahi ki kara masa har sai kan nasa ma ya koma irin na mangoron." Hayaniya ce ta kaure tsakanin mai gadi da Inna har sai dai Alhaji Ismail da Matarsa Hajiya Maryam suka fito. Kaka na ganinsu ta fashe da kuka tana faduwa kasa. Hawaye da majina shaɓe-shaɓe a fuska ta ce, "Ilu wai har kaine zaka dauko wanda zai dunga tozartani a gidan nan? Har kaine zaka dauko wanda zai ci mini mutunci." Durkusawa Salma ta yi tana share mata hawayen tare da fadin, "kiyi hakuri Inna mu koma kauye kawai tunda tun a kofa aka fara yi mana kora da hali kiyi hakuri ni ina sonki bana so ki mutu." Ta karasa maganar ita ma tana kakulo nata kukan. Da sauri Hajiya Maryam ta karasa tana rike Inna. Inna ta bangajeta tana , "Dalla cen guzumar munafuka ai gwamda kowa dake ni barni bana son munafurci." Alhaji Ismail ya kalli mai gadi ya ce, "kai ko me yasa zaka yi haka? Baka san cewa wannan din mahaifiyata ba ce?" Mai gadi zaiyi magana kenan Inna ta tunkure shi da kafarta sai da ya fadi a kasa ta ce, "munafiki ne ai kuma indai ina gidan nan sai na gyara masa zama." Karasawa Alhaji Ismail ya yi da kanshi ya daga Inna yana, "kiyi hakuri Inna In sha Allah ba zai kara ba." Tashi tayi tana tafiya dakyar kamar wacce aka ma duka. Suna tafiya Salma ta juya tayiwa mai gadi Gwalo, can ma sai ga Inna ta juyo da tsukeken bakinta ta masa gwalon. Sake baki ya yi yana mamaki A zahiri ya ce, "Ikon Allah gaskiya akwai matsala babba a gidannan." Suna shiga cikin gidan salma ta aje tulin kayanta ta fice. ★★ Ya fito daga wanka kenan daga shi sai towel dinsa a daure karasa ya yi daidai gun windown dakinsa yana budewa. Budewan da zaiyi fitsari ne ya fara sauka masa a fuska. A gigice ya daga kai suka yi ido biyu da Salma ce tsaye ta haye kan setin windown tana tsura fitsarinta hankali kwance a tsaye. Kallonshi ta yi tana murguda baki, "ji wani kasurgumin dan iska ina fitsari yana leƙena." Kasa hadiye yawu Abdul-Saheer ya yi kasancewar sa mutum mai zafin rai cikin sauri ya dauki belt ya fita ita kuwa Salma har lokacin tana zaune abunta tana, "gwanda ma da ka tafi don ni wallahi bana wasa da yara." Saukar Belt taji a gadon bayanta ta tsalla wani irin ihu. , "Ance miki nan gun fitsari ne da zaki zo kina yiwa mutane?" Ya daga zai kara mata tayi wani irin tsalle ta shige ciki da gudu tana, "kwarto jama'a kwarto yana dukana dan iska ne." Tsaki Saheer ya yi ya koma dakinsa kai tsaye toilet ya nufa zai kara yin wankan domin koda yace zai wanke iya gun ne yata tsarguwa. Salma na shiga ta birkitasu duka suka fito basu ga kowa ba. Inna ta ce, "daga zuwa birni har za a fyeɗe mun jika? Na ce har za a fyeɗe? To wallahi sai na dau mataki zan baku mamaki ga dukkan alamu dukanku yan gidannan sai na gyara zaman duwawunku domin a karkace suke duk." Haka Inna ta zauna Salma na jikinta ance su je suyi wanka fur sunƙi. Saheer ne ya fito cikin shirinsa zai fita dake weekend ne. Ko sallamar da ya fara bata bari ya karasa ba ta katse shi. ta fara nuna shi tana, "Inna wallahi wallahi shine kuma har lekani ya yi kuma ya dakeni." Tashi tsaye Inna tayi tana rike kwankwaso, "Iya ah lallai wato gadon uwarka ka yi Sahaaru? Gadon iskanci da fitsara Kodayake ai kasha a wancen tamulallen nonon uwar taka wacce ko nawa ya fita fasali to baka isa ba yadda ka fara gane mun ita sai ka aureta domin ka riga ka gama da ita ba zan bar gidan nan ba sai ka aureta e na ce sai ka auri salame." Daga Saheer har Iyayen nasa suman tsaye sukai sun gagara cewa komai. Salma ta..... 08103080717 Urs Xayyeesherthou [6/25, 11:07 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-2 Ta ce, "Aa fa Inna ni bana son auren dan iska yaje ya iskanta ni a banza a wofi." Tsaki Inna ta yi kafin ta ce, "Ya iskanta ki ban da tambadar da ya fara miki tun yanzu? Aure ba fashi." Ta ja kunnenta ta fada mata magana suka dago suna tafi da dariya kafin Inna ta gyara zama ta ce, "Yawwa ilu na san ka ji me na ce ai ko? Ko sai na maimaita ne? Ina so Sahaaru Ɗanka ya auri yar uwarsa salamatu." Kallon kallo suka fara yiwa juna. Momy,Daddy da Saheer. Dady ya ce, "To Inna In sha Allah za ayi hakan." Dauko garin goronta ta yi ta zuba a baki tana mamula domin tsabar tsufa gabadaya hakoran sun wawushe. Ta ce, "Ah to ka ma Musa mana bawai naga kuna kifi kifi da ido ba kai da matar ta ka mai baki kamar tsohuwar jaɓa ga hanci kamar agwagwa na magana, eheem so nake a daura masu aure gobe da safen nan." Wani irin mumman faduwa gaban Saheer ya yi take ya fice daga dakin cikin sauri, Momynsa ma ta fice. Dady ya ce, "To Inna amman kinsan ba a gaggawa a aure ki bari a shirya komai a tsanake tukunna kamar zai fi." Galla masa harara ta yi kafin ta ce, "ji mun wani salon rashin daraja da guntun iskanci, me za a shirya? Na ce me za a shirya? Ba abun da za a shirya kuma aure gobe nake so a daura, yoo Ɗan naka ma da rufa mai asiri za ayi ayi masa auren kafin ya gama tambaɗewa ,tunda ya fara leƙen duniya kuma ai gaba gaba sai yawo a ciki to ba dani ba na ce ma ba dani ba auren nan gobe gobe kafin ka dawo daga asuba ka tabbatar da cewa ka zo mun da albishir andaura auren sahaaru da Salamatu in ba haka ba kuwa kasani sarai zan iya zan iya daga maka nono ka bi duniya ka watangale ." Jiki a sanyaye ya amsata ba don yaso ba kuma ba don yasan ta ina zai bullowa lamarinta ba. Babban tashin hankalin ma bai san Dalilin zuwansu ba zato ba tsammani ita da bata son zaman birni. Kwatsam kuwa sai jin mai gadi ya yi yana sheda cewa ana sallama da shi. Bayan ya fita ya ga yaron fadar mai garin kauyesu ne. Bayan sun gaisa yake sheda masa cewa Mai gari ne ya aiko shi domin sheda masa cewa Salma da Inna sun yi laifi babba da ake nemansu ruwa a jallo domin kuwa sun kama matar mai garin duka su biyu sun mata dukan tsiya wanda har sai da ya kai ga ta suma sanadin kawai Don Salma ta kwacewa yaronta mangoro ta yi magana suka hadu suka dunga jibgarta kamar sun samu kayan wanki har sai da suka ga ta daina motsawa suka kwashe kayansu suka bar garin. Sallallami Alhaji Ismail ya fara ya bashi hakuri tare da sanar da shi cewa ya bawa mai gari ma hakuri kuma In sha Allah yana nan tafe zuwa kauyen shi ma. Jiki a mace ya koma cikin gidan ya nufi dakin Momy. Tagumi ya yi ya zauna ya yi shiru. Ta zauna gefen shi tana fadin, "Alhaji ba zama kayi tagumi bane mafita fa tunani zaka yi yadda za a bullowa lamarin domin kasan halin Inna inta kafe akan abu." Numfasawa Dady ya yi kafin ya ce, "Hmm abun ne na rasa da wanne zan ji, yanzu fa zuwa akai nemansu daga kauye na ce basa nan na bada hakuri ga wannan batun auren da ta taso da shi kuma sannan Saheer ma ko kadan ba zai iya rayuwa da Salma ba domin yarinyar an riga an gama sakaltata gyaruwarta da nutsuwarta zaiyi wahala sosai." Momy ta ce, "to ya za ayi karshen zancen dai kawai ka yi mata biyayya shi ma Saheer din ya yi hakuri." Dafe kai Dady ya yi ya ce, "abune mai wahala hakan ba zan so in cutar da Ɗana da hanuna ba dole zansan yadda zan bullowa lamarin." Ya fada yana tashi. "Bara in dan fita in dawo." Saheer kuwa yana fita a gidan kai tsaye School ya nufa duk da cewa weekend ne domin ya ji bai son zaman gidan sam kuma daman gashi ba mai son hayaniya ba hakan yasa yaje ya bude office dinsa kawai ya zauna. Saheer Namiji ne wanda ya amsa sunan namiji karfaffa domin kuwa wanda bai san shi ba zai iya alakanta da shi da jami'in tsaro kasancewar yanayinsa daya da nasu miskilanci,rashin son magana da rashin fara'a. Baya cikin sahun farare kuma ba asa shi cikin sahun bakake ba,yana da kyawun gani daidai gwargwado wanda kowacce mace zatai burin mallaka,saboda miskilancinsa yasa ko mata bai kulawa abokinsa ma guda ɗaya ne kadai wanda ya aminta da shi. Yana da tsafta da son gayu sosai daga nesa turaren jikinsa kan iya bayyanar da zuwansa waje sai dai yana da dabi'ar shan taba sigari wanda ta zame masa jiki musamman a lokutan da aka bata masa rai bai samun sukuni in bai zuƙa ba. Yana zaune Inya tuna da abun da Salma ta mai da maganar Inna sai yaji ranshi ya baci Sosai ban da tsaki babu abun da yake. Take ya kunna tabarsa yana sha. Salma kuwa ko a jikinta dadi take ji har cikin ranta Inna ta ce mata inta aure shi zata zama hajiya babba tayi kudi su koma kauye su kori mai gari da matansa. Salma irin yaran nan ne masu gaɓa-gaɓan jiki gata karamar yarinya da bata zarce sha uku ba amman girman jiki da kibarta ya kai na mai shekara Ashirin. Baƙace sosai amman irin bakin nan mai kyau da sheƙi. ★★★Salma da Inna zaune suke a filin gidan sun shinfida taburma sunyi kane-kane su ci wannan su ci wancen. Inna na ganin Saheer ya shigo da mota ta kalleta ta ce, "yawwa ga mijinki nan ya dawo maza tashi kije ki karbe shi ki mishi sannu da dawowa gwanda ki fara koya tun yanzu." Aikuwa tashi Salma tayi tinki tinki ta je gefen motar ta tsaya. Yana fitowa ta washe baki tana kokarin karban file hannunshi ta washe baki, "Barka da Zuwa Mijina." Wani takaicine ya sarƙafi zuciyar Saheer ya bita da wani gigitaccen kallo yana bisge hannunshi sai da ta fadi. Kafin Inna ta bude baki har salma ta tashi tana daga hannunta sai setin marar Saheer ta sauke masa. Bai san lokacin da ya saki wata kara ba,ta zura a guje. Ita kuwa Inna me zata yi ban da dariya. "Maddallah yoo daman Salma in baki rama ba ai ke ba jinina bace tunda shi ya yi gadon figaggiyar rashin daraja ke lukuta na koya miki." Mai gadi ne da sauri ya karaso ya rike Saheer..... 08103080717 Comments, Share and like Fisabilillah. Urs Xayyeesherthou 🤍🌾 [6/26, 10:16 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-3 Ganin yadda Saheer ya fara muradadawa lokaci guda kuma yanayinsa ya canja,hakan Yasa Inna da Salma tashi a guje. Suna tashi kuwa aka dauke wuta dake dare ya yi. Karo suka ci da juna karaf goshin Salma ana Inna. Wata irin kara ta yi jiki na rawa Inna ta ce, "Na shiga uku na lalace na shiga ukuna ni Shatou, Lawakiri ka yi mun rai aradun Allah bani na yi kisan ba Jikata ce, jikata Salame ce." Inna ta fada hannunta dauke a fuskarta ta rufe idanunta da daya,dayan kuma ta kankame goshinta da yaji bugu. Har an kunna Gen bata sani ba tana kankame a tsugune tana ta sambatu lawakiri ya yi hakuri ya mata rai lokacin baiyi ba tukunna da saura. Sautin dariyar Salma ta jiyo akanta tana, "Kai Inna Sarkin tsoro karo muka yi fa da goshi ba wani lawakiri." A hankali Inna ta bude ido tana kif-kif da ido kamar karamar munafuka ta ja dogon numfashi, "Allah na gode maka, yoo ko salame wai haka goshinki ke da azaba kamar an turo roka? Wannan ai sai ki kashe mutum amman dai goshin nan naki kwai rashin daraja ba don ni da kaina na mulmula miki maɗiga ba lokacin da aka haifeki da na ce anguwar zomanki bata iya karban haihuwa ba." Ita dai Salma dariya take harda shidewa. Inna ta ce, "Muguwa yar masara ni rikeni in tashi don ina ji ma har fitsari na gama yi a jikina aradun Allah, jina nake fa rabi a duniya rabi a lahira." Salma ta mika mata hannu ta tallafa mata ta tashi tana fadin , "Inna anji goshin manya ysn kin bani dariya yadda kika zauna dinnan nishadi kyauta." Da haka suka shige cikin gidan suka baje a falo domin sunki shiga daki. ★Saheer kuwa mai gadi ne ya tallafa masa ya shiga daki domin mararsa ciwo take yi masa sosai ta rike. Kwanciya ya yi na yan mintuna kafin ya tashi ya hada ruwan lipton ya sha. Aransa ya kudarci cewa duk yadda za ayi sai ya kama Salma ya hukuntata. A zahiri yake fadin, "wannan yarinyar sam bata da tarbiya babu shakka sai nayi maganinta na sa ta samu nutsuwa." Ko cikin gidan bai shiga ba ya kulle kanshi a daki hatta sallah ma a ciki ya yi. Salma da Inna na falo suna kuskus da tsoron cewa kar fa azo ace sun kashe Saheer. Salma ta ce, "ni gwanda ma ya mutun ai yana nan kamar wani dan kasar waje." Inna ta ce, "ke wawiyace matsalata dake salame gwanda ya rayun ai ki aure shi baza ki gane abun da nake nufi ba, ba don ba ba aure tsakaninki da uban shi ba ai da ubanshi zaki aura amman sai dai kash shi yasha Nono ya barwa Uwarki ta sha." Suna cikin magana sai ga Alhaji Ismail ya shigo falon. Durkusawa ya yi gaban Inna ya gaisheta sai ya yi shiru. Fara wura hanci Inna tayi tana dagawa ganin ya shigo da leda ga kuma kamshi na tashi. Ta ce, "Illu miye ne a ledar cen? Ji nake kamar kamshin gashasshiyar kaza miko min nan Salame." Jiki na rawa Salma ta tashi taje ta dauko ta baje a gaban Inna suka bude. Fara ci suka yi kamar sabin kamu musamman Inna da saidai ta mamula ba iya taunawan ma take ba. Alhaji Ismail ya yi gyaran murya kafin ya ciro wani dumin kudi a aljihunsa ya ajewa Inna a gefetan tukunna ya ce, "Inna Daman ina neman alfarma ne ban sani ba ko zaki amince." Inna na mamular nama ta ce, "ina jinka Illu illu dan albarka ina jinka ka yi gadon mahaifinta wajen sanin abun da nake so Illu nawa." Dady ya ce, "daman kan auren Saheer da Salma ne,na ce me zai hana ki bari ta kara girma tukunna sai nake ga kamar ai tayi karama a yanzu za a cutar da it..... Kafin ya karasa maganar ta fecar da kasar bakinta ta rike bango ta tashi tsaye ta kalli Salma ma ta ce, "ke salame tashi tsaye." Salma ta tashi tana jan cinyar kaza. Inna ta ce, "Yawwa juya gaba da baya." Salma ta juya. Ta ce, "to yi tafiya daga nan zuwa can." Salma ta taka daga farkon falon har karshe. Inna ta ce, "yawwa ince dai idanunka sun gani? Ko ta kara juyawa ne?" Alhaji Ismail ya girgiza kai alamar aa. Inna ta ce, "Yawwa batun aure ba fashi ka kalleta ka kara kallo." Ta nuna salma da hannu kafin ta ci gaba da fadin, "Diri iya diri gashi nan sassakar budurci iya sassaka gata nan,inma ƙirjin ne gashi nan a wadace dake gado tayi ba irin da shamulaliyar matarka ba,shi ma duwawun dai gashi nan kamar a dasa turmi ya zauna, mace iya mace son kowa kin wanda ya rasa salame ta kai,don haka ahir dunka da cewa tayi karama a aure ka cuceni ka kasheni da raina bayan danku ya fara leƙe mun ita,kai tsaya ma,wai kai bakasan diri ya gani ya furgice ba har yake kokarin fyedemun ita ? To ko yau na fadi na mutu indai Sahaaru bai auri salame ba ban yafe ma ba." Tana fada ta barke da kuka tana jan majina ta tattaro gefen zaninta tana gogewa. Salma ma zama tayi tana kukan tana kwanciya jikin Inna. Jiki na rawa Dady ya ce, "kiyi hakuri Don Allah Inna, kiyi shiru In sha Allah za ayi abin da kike so." Inna na sheƙan majina ta ce, "Illu Indai ba so kake in hadiye zuciya in mutu ba ka hada Sahaaru da Salame ." Murya na rawa ya ce, "e e In sha Allah Inna yanzu to kiyi shiru Don Allah." Share hawayen ta yi ta dauki kudin da aje mata gefe tana, "wa innan kudin da su zan yiwa salame hadin amare, kai ma kuma kaje a hada danka ehee." Salma ma ta share hawayen tana washe baki. Dady ya ce, "amman za a bari zuwa jibi ko Inna? Kinga yanzu ban tanadi su goron daurin auren ba." Inna ta ce, "e ba matsala Allah ya kaimu ai kamar yaune amman ka sani daga ranar ba dadi ba kari." ★★★Washegari. Da sassafe Salma ta fice tana zaune gefen motar Saheer tana wasa da kasa dake wajen akwai kasa ita har ma ta manta da abun da ya hada su jiya. Shi ko ya fito kenan ya shirya zai tafi school dake monday ne. Aiko yana ganinta ya koma da sauri ya ciro belt. Har ya fito sai kuma ya koma ya aje belt din tasa ya kara fitowa. Ji tayi kawai an dauketa cak. Ta fara wuntsili da kafa tana ihu hannunsa yasa ya rufe mata baki ya kaita dakin nasa yana shiga ya dauki tsimma ya rufe mata bakin ya daureta a jikin Window sannan ya dauko belt din ya...... 08103080717 Urs Xayyeesherthou [6/27, 9:54 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-4 Ya zabga mata a gadon baya, kara Salma take son yi amman babu hali saboda ya riga ya kulle bakin. Tana ta wutsil wutsil da jiki tana kokarin kunce daurin da ya mata. Cikin fushi Saheer ya kara sake mata Belt dinnan a jiki wanda don azaba sai da ta saki fitsari a gun ga wata irin zufar wahala da ta keto mata. Jin karar abu na zuba ya kalli kasa, aiko idanunsa suka ci karo da fitsari na tsiyaya kan tais dinsa kamar famfo. Wani takaicine ya kara sarƙafansa a zuciya. Ya ce, "Wai ke wacce irin bagidajiyar kazamiyar yarinya ce? Fitsari? Fitsari zaki mun anan? Aiko sai kin goge shi tas da kayan jikin ki, kafin nan ma zaki kara zuwa ki hau mun mota inyi magana ki mun rashin kunya har ki kai mun duka mara?" Ya fada yana murɗa mata kunne. A galabaice ta girgiza masa kai alamar e. Ya kara sake mata belt din kafin ya ce, "zan kunce ki kuma ki cire wannan zanin naki mai dauda ki kwashe fitsarin nan tas." Ya fada yana kunceta. Salma ido ya yi fiki-fiki anji azaba. Haka ya tasata a gaba ta cire zaninta tana kwashe fitsarin daga ita sai wani gajeran wando da dauda tasa ya canja launi domin yanayin fari garesa amman ya koma brown brown don azabar kazanta ga wani munafukin wari da ke tashi. Kasa jure tsayuwarta agun Saheer ya yi,tun yana toshe hanci har ya gagara ya ce, "Just Go." Yana kara rufe hancinsa. Ina Salma kam bata san me yake fada ba kara gogewa take. A fusace ya ce, "Ya isa ki fita na ce." Rungume Zaninta mai fitsarin ta yi ta fice da gudu sai da ta zaga daidai windown da yake tsaye ya yi tsuman tsaye ya tura kanta tana fadin, "Mugu azzalumi Dan Masara mai bakin Daddawa kan tafarnuwa aradun Allah sai na rama mai idon damusa kawai." Tana fada ta tattara yawo ta watsa masa daidai fuskarsa kafin ta arce a dari ta shige ciki. Rikicewa Saheer ya yi take kansa ya fara wani gigitaccen ciwo,idanunsa suka kada suka yi ja. Cikin sauri ya shiga toilet ya fara wanke fuskarsa yana wanken bakinsa. Karshe sai da ya kara brush ya kara yin wanka yasa kaya. Da sauri ya bar dakin domin gabadaya a tsarge yake da dakinma. Ciki ya shiga domin gaida iyayen nasa, ya shiga dakin Momy ya gaidata har zai fita ta ce, "Saheer." Ya juyo ya kalleta yana amsawa. Ta ce, "sai dai ka yi hakuri kuma ka sa aranka cewa babu Ɗan da zaiyiwa iyayensa biyayya ya taɓe biyayya bata taba zama a banza ka da kasa komai aranka ka ji cewa kawai duk abun da Ubangiji ya tabbatar shine daidai a garemu duka." Da mamaki ya kalli Momy domin sam bai gane inda ta nufa ba,don shi ya ma mance da wani batun auren shi da Salma. Ya ce, "Momy ban gane ba,me ya ke faru wa?" Momy ta ce, "magana nake akan aurenka da za a hada dana yar uwarka Salma." Momy na fada Saheer ya kara ji kanshi ya yi wani irin sarawa. Da sauri ya dafe kan. "ka karbi hakan a matsayin kaddara da biyayya kuma In sha Allah nan gaba zaka alfanun hakan." Momy ta fada. Kau da kanshi ya yi kawai bai ce komai ba ya fice. Momy ta kara fadin, "Dadynka na falo kaje ku gaisa kafin ka fita." Falon ya shiga kuwa ya tarar da shi zaune da Inna da Salma. Salma na ganin shi ta fara murguda mishi baki tana harara. "Inna kin ga wallahi duka na ya dunga yi da wani abu kamar wayar injin mugun ne." Gaishe da ita Saheer ya fara, "Inna an tashi lafiya?". Da harara ta bishi kafin ta ce, "Gidanku na ce ka ci gidanku da ban tashi lafiya ba zaka ganni hakane? Kodayake ai daman kai da Uwartaka fatan mutuwa kuke mun to ahir dinku na fiku tijjara da tashanci ni fa na gama fahimtar take taken yaron nan wato saboda kazo fyeɗeta baka samu galaba ba shine ka daura mata karan tsana da duka? Na ce to karbi nan gidanku gobe goben nan za a daura maku aure sai kaje can ya karata da maitarka." Ta kalli Dady kafin ta ce, "Illu ka ga abun da nake gudu ko? Wannan Ɗan naku tuzurun tuzure indai ba a gaggauta anyi abun nan ba akwai lukutar matsala kana ganin idanun sa ma ai ka ga mai bidar aure , gabadaya ya ga yarinya yar dumurmur ya birkice to ahir ayi abun da ya dace amman ban da duka." Dady ya ce, "In sha Allahu Inna." Saheer ya gaida Dady ya fice cikin sauri a dakin domin ya fara kasa gane kan shi. Bai nufi School ba,a kan hanya ya yi parking motarshi gefe ya kunna sigari yana sha. Aranshi yake fadin, "wai da gaske wannan bagidajiyar kazamiyar yarinyar za a aura mun? Aure ni kuma da wannan yarinyar? Mu zauna gida daya? Inuwa daya? Kai Never." Ya fada da karfi. Inna ta kalli Dady ta ce, "Yawwa Illu maza ka tashi ka je a tanadi goro da mintinan kan lokaci kuma kar a manta a kawo mun nawa yawwa, ke kuma Salame tashi mu shiga daki in baki wasu sirruka domin nan da gobe kin zama matar aure, kar waccer figaggiyar matar mai kirjin faranti ta ji ta karu maza mu shige ciki." [6/28, 12:39 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-5 Tashi Inna da Salma suka yi suka shiga cikin daki. Dukaninsu suka ɗare kan gado. Inna ta kalli Salma kafin ta ce, "Salame, ki jini da kyau ki saurareni yau zan baki sirrin da ya sa na mallake zuciyar Kakanki Malam Auduwana, kai Allah sarki Malam Auduwa na shatou mun diga soyayya fa kamar ba za a mutu ba mu fa tsabar soyayya har zuciyoyinmu magana suke da juna,haka inuwarmu in muna tafiya basa taba rabewa zaki gansu manne da juna, ina fada miki ka da ki kuskura ki bar mijinki shi kadai duk inda yake kina bibiyarsa sannan kina daukan wanka kina kashe kala wannan jagirar da kike ta kauye karki fasa." Salma ta ce, "Tom Inna ai nan ban da kayan kwalliyan fa." Inna ta ce, "Shi mijin naki ne ai zai siyo yoo ai shi zakiyi yiwa kwalliyar nidai ina fada miki, kuma ki dunga yi masa fari da idon nan." Inna ta karasa maganar tana wani irin juya ido. Kwaikwayonta Salma ta fara suka kyalkyale da dariya Inna ta ce, "Yawwa hakan kina ganinsa ki fara kina tande baki kina tsukewa wannan lamari ba karamin kara ɗankon soyayya yake ba,ko ya fita ke kawai zaina gani cikin idanunsa kamar ni da malam amadu shi fa ko kasuwa yaje in ba na bi bayansa ba ko ya dawo gida ya ganni mun hada ido nayi masa farin nan hankalinsa sam bai kwanciya." Salma ta gyara zama ta ce, "ai tare ma zamuna fita da shi duk inda zaije dinnan." Inna ta ce, "Yawware yar albarka haka nake son ji, in kuma baya nan ya dawo,yana dawowa ki rungumeshi irin rungumar da kike gani a talabijin din mudi mai balangu na yan indian nan." "Eee ee na gane inna har hada bakinsu suke fa suna wani abu wai shi kuss (kiss)" Salma ta fada tana tafi da hannunta tana dariya. Inna ta ce, "Tabbas kuss tsuke bakin ake sosai asa a ciki,yanzu ma kin ga kije kiyi wanka kisa kaya zanje in karbo miki kayan kwalliya gun waccer matar kafin ya dawo da dare ya ganki kin dau wanka." Hakan aka yi kuwa Inna taje ta titsiye Momy ta karbo kwalli da hoda salma na wanka ta mulka wata irin gira daga gishi har ido ta cika bakinta da baki tana juya ido. "Aradun Allah Inna na san inya kalleni suman dadi zaiyi domin na san na yi kyau na fitar hayyaci wooo ni Salame ." Inna tayi wani guntun murmushi ta ce, "ai Indai ina raye sai sahaaaru ya zame miki mijin kan ta ce ma." Mai Salma zata yi ban da dariya har cikin ranta wani dadi da shauki take ji. ★★Salman kuwa da ya fitan ma bai samu nutsuwa ba har sai da ya sha sigarinsa kamar yadda ya saba kafin ya shiga school. MARIA MEMORIAL PRIVATE SCHOOL. School ce mai kyan gani da kuma sanya son kasancewa a ciki ga dukkanin wasu yara masu tasowa domin cike take fal abubuwan wasaani da karatu. Saheer shine Headmaster a school din kuma yana koyarda Mathematics ga yan primary 4 da 5. Yana samun girmama matuka agun teacher din da students domin duk miskilancinsa yana da saukin kai da tausayi. ★★★Koda dare ya yi Saheer ya dawo bai shiga cikin gidan ba,domin aransa ji yake baya son ganin salma sam in ko ya ganta zai iya kasheta a yadda zuciyarsa take. Inna da ita nata faman jiran shigarsa sunji shiru. Inna ta ce, "maza ke tashi muje ki dauki mayafin ki muje kuyi zance ba zan iya da wannan lamarin naku ba dake shi din munafukine yana so yana kaiwa kasuwa Kodayake ai da kunya yaga asirinsa ya tonu na gano shi." Suka fita sunata bambami. Daidai kofar part dinsa suka je suka tsaya suna bugawa kamar zasu buga kofar. Inna na fadin, "kai sahaaru ka bude mune nan ." Tsaki ya yi ya bude kofar ba don ya so ba. Suna hada ido da Salma ta fara kada masa ido tana fari tana cuno masa baki kamar zatai mai kiss. Inna ta ce, "hira na kawota kuyi, ee hira zance zakuyi na masoya kafin gobe a daura maku aure." Saheer ya ce, "Inna kaina ciwo yake Don Allah ku barni in huta." Yana fada Inna tasa hannu aka ta kurma ihu tana, "na shiga uku na lalace Sahaaru har ni zan ce ma kayi abu ka ce baza ka yi ba? Har ni." Su Dady na fitowa ta kara daga murya tana kuka tana share hawayen da mayafinta. Shi kam Saheer ma ya rasa abun cewa binta da kallo kawai yake cike da mamaki ita kuma Salma na rarrashinta. Dady ya ce, "lafiya Inna?" Inna ta nuna saheer ta ce, "Yoo ina lafiya ilu ,na ce ina lafiya? Ummmm wai har nice zan sa sahaaru abu yaki? Wai daga na ce suyi zance da Salma tunda gobe za a daura masu aure wai shi aa kar mu dame shi,dole inyi kuka dole inyi kuka." Ta karasa maganar tana kara kakulo kukan . Dady ya ce, "ki yi haquri ki daina kukan Inna Don Allah." Ya kalli Saheer kafin ya ce, "kai kuma ka fito ku zauna kuyi zancen ai ko ba komai yar uwarka ce." Inna ta ce, "sosai ma kuma matarsa ba." Haka Inna ta tasa su a gaba suka zauna a falo . Salma ce kadai ke sambatunta Saheer kam takaici ya hanashi fadin komai. Karshe sai wayo ya musu yace zaije ya dawo ya yi ficewarsa. Washegari Dady na dawowa daga sallar asuba ya shedawa Inna an daura auren Saheer da Salma kamar yadda ta bukata. Inna ta ce, "Ma sha Allah Illu Allah yyi ma albarka ince dai wani gidan zasu tare ba nan ba ko? Suje can su ci amarcinsu ni zan zauna anan sai ta haihu sai inje can in mata wanka." Dady ya ce, "In sha Allah yanzu ma zan kira Saheer din muyi magana." Zuciyar Inna fara sol domin ta samu abunda take so. ★★Jiki a sanyaye Saheer yake durkushe gaban iyayen na shi. Dady ya ce, "na san cewa an wuce zamanin auren dole, don haka ina so kasa aranka cewa kai ba auren dole aka yi ma ba, auren biyayya da kuma sadaukar ne, sannan ina so ka mai da Salma makaranta ku dinga tafiya tare domin tamkar ceto rayuwarta zaka yi ,a cire ta daga duhun jahilci da kuma abubuwan da take wanda sam basu kamata ba dole sai ka yi hakuri amman ka sani akwai ranar yin murmushi da farinciki mara misaltawa da ikon Allah don haka zan baka keyn wancen gidan zaku tare acen an gyara anyi komai yau da dare In sha Allah acen zaku kwana." Saheer bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron iyayen nasa har suka gama yi masa nasiha ya yi godiya sannan ya tashi. Tun yamma Inna ta daurewa Salma tsimmokaranta a tsimma suka zauna suna jiran Saheer yazo ya dauketa. Harda kular dafaffen abinci. Ba yadda ya iya kuwa hakan aka yi ta shiga mota. Sai tabe tabe take tana yi masa sambatu shi kuwa aransa ji yake kamar ya jefar da ita ta windown. Suna shiga gidan ya shige daki ya barta a falo ta baje kular abincinta ta fara naƙa sai da ta ci ta koshi bayan nan kuma ta bige da kallo. Da taga ta fara jin barci ta bishi ciki. Tana shiga ta tarar shi kam Saheer ya jima a duniyar barci daga shi sai singlet da gajeren wando. Itama afkawa kan gadon tayi ta baje tana barci. Tana daga kafarta sai cikin bakin shi. Ga wani gwarti da take gabadaya ya mamaye dakin. Baki a bude duk ta wage jikinta kan gadon. Jin abun da ya yi a bakinsa yasa shi saurin bude ido...... 08103080717 [6/29, 11:12 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-6 Cikin bacin rai Saheer ya hular da kafarta gefe ya tashi ya daka mata duka abaya. A zabure ta farka tana, "wayyo wayyo Allah na." Ya daka mata tsawa, "ke dalla yi mun shiru, ke wai baki da hankali ne? Haka ake kwanciya? Wai ma waya baki damar kwanciya mun akan gado ne?" Sai da ta gama kare mishi kallo kafin ta Wage baki tana hamma tukun ta ce, "Mtsww aradun Allah ni na zata ma wani abun ne yake hwaruwa, gado kuma ai na mijina ne ko ance ma mata da miji na rabuwa ne? Inna ta ce a tare zamuna kwana kuma manne da juna ma kuwa muna shakar numfashi saboda yana kara dankon soyayya." Ta fada tana komawa ta kwanta daf da shi. Cikin zafin rai ya tureta gefe sai da ta fadi akan gadon. Ta tashi tana, "Kambala'i ashe za ayi ruwan bala'i da masifa cikin daren nan tureni ka yi fa har na fadi? To da na gurde fa? hmm ka ci sa'a barci nake ji amman ka sani bashi ka ci kuma sai na rama babu fashi." Ganin da gaske dai bazata bar gadon bane yasa Saheer daukan filo ya fita falo dake gidan karamine bed room dayane kadai. Ita ma filon ta dauka ta bi bayan shi. Yana kwanciya akan 3sita kawai ya ganta tsaye akanshi tana, "matsa mun to nima." Kallonta ya yi ya kara kallon inda yake kwancen A zuciyarsa ya ce, "ina ga dai wannan yarinya ta tabu." Ya rufe idonsa zai koma barci. Jinta ya yi kawai ta kwanta akan shi kamar an jibga kayan wanki. Ya hankadata ta fadi kasa ya tashi ya sake mata wani gigitaccen mari biyu ta kowanni bangare. Ihu ta fara tana birgima. Saheer ya ce, "ke wai wacce irin mayyace? To wallahi kika kara bina ko kika kara kuskura kika zo inda nake bare har ki taba jikina sai na baki mamaki." Rike hannunta tayi afuskarta tana, "na shiga uku wayyo ni wayyo Allah na,kuma wallahi sai na fadawa Inna ka ce kai baza kana kwana dani akan gado ba wallahi sai na fada." Saheer bai kara kulata ba har ta gama kukanta da sambatunta barci ya yi awun gaba da ita a falon. Asuba na yi ya tashi zaije ya yi sallah ya ganta yashe baki a wangale ga gwarti ga yawon barci ga kafofi duk a wangale. Tsaki ya yi ya wuce ta gefe yaje masallaci ya dawo . Ruwan sanyi yaje ya dibo ya watsa mata domin bai son ko hannunshi ya tabata. Aiko a firgice ta tashi. Ya ce, "maza ki tashi kije kiyi sallah kiyi wanka ki shirya zamu fita tare muje School." Da magagi take tana kokarin komawa amman tunda ta ji ya ce za su fita tare da sauri ta tashi tana washe baki tana , "To Miji... miji...mijinaaaa." Tana cewa mijin nan wani takaici ne ya kara tokaran saheer a kirji. Tsaki ya yi kawai ya nufi kitchen. Indomie ya dafa masu da kanshi ya zuba mata sannan shi ma ya zuba na shi. Ajiye mata ya yi,bayan tayi wanka tana sallah idonta na kan indomie tana yi mi shi gyaran murya. Ko kallon inda take bai ba bare ya kulata aiko da sauri ta dungura sallar nan ta tashi ta fara nakar indomie. Tana ci tana, "cab miji ashe ka iya girki, amman ko ni naji dadi ashe Inna ta iya zabe,ita tasan me ta hango tace sai munyi aure ji taliyar yaran nan kamar karta kare caii dadi iya dadi, aure dadi miji dadi." Ta na magana Saheer ji yake kamar ya tura ta cikin rami ya boye. Ta cinye tas sauran romon kuwa daga filet din ta yi tasa a baki ta shanye tas. Ko wanke hannu bata yi ba taje ta zumbula wata katotuwar rigarta duk da cewar tana da jiki amman yawo take a cikin kayan. Ya dauki hoda ta mulla ta kara kwaba farar hodar da ruwa tasa a bakinta. Gaban Saheer ta tsaya tana, "miji kalleni na yi kyau?" Daga kan da zaiyi sai da ya zabura domin ta koma kamar wata fatalwa. Rai baci cikin daga murya ya ce, "common jeki goge wannan shirme da haukan naki baza ki bini da wannan haukar ba." Da gudu taje ta wanke tana"cab yanzu haka kishi yake yi na yi kyau kar a kalle mai ni ,yoo da yaki fita dani ai gwanda inje in goge ,ysn kishi yake ya ga kyakkyawar mata." Saboda ta riga ya gama caba fuskar raguwa dai hodar tayi amman da sauran fari farin. Ta koma tana washe baki, "Mijin na goge." Bai ce komai ba ya tashi. Ita ma ta bi bayan shi. Suna shiga motan sai ga kiran Dady ya na cemai su biyo ta gida kafin su wuce zai bashi sako. Suna zuwa gidan Salma ta shige a guje ta rugume Inna. Inna ta ce, "ke wai har kin gama amarcin ne ya haka?" Sallamar Saheer ce ta katse su Da yake duka Momy har Dadyn ma suna falon. Dady ya ce, "e zasu je makaranta ne zata fara zuwa Inna kinga ba dadi abarta a gidan ita kadai." Inna ta ce , "Ah eeh kuma kam hakane ya yi kyau." Bayan duk sun gama gaisawa Dady ya bawa Saheer Files din da yace ma shi yazo ya karba. Zai tashi kenan Salma ta ce, "Yawwa Inna ba kin ce gado daya zamuna kwana ba?" Inna ta ce, "kwarai kuwa yo mene ne auren in ba kwana gado daya ba?" Salma ta ce , "aradun Allah cewa ya yi wai shi bazai kwana dani ba har da tureni a kasa kuma wai ko jikinshi kar in kara tabawa." Kuka Inna ta fashe da shi, "Oh Allah oh duniya yanzu Sahaaru abun da za ka mun kenan? Ka ce baza ku kwana gado daya ba? Sahaaru in baka kwana da matar ka ba dawa zaka kwana?bakin ciki kake mun da ganin yaran salame kafin in bar duniya? Sahaaru anya kana so ka ga Annabi kuwa? Wato da so kake ka ci bulus ka ci bati siddin anki an rufa ma asiri shine bari mu ka tona mana" Ta kara fashewa da kuka. Dafe kai Dady ya yi,ya kalli Saheer ya ce, "Ka bawa Inna hakuri kuma daga yau kar ka kara cewa ba za kwana da matarka ba kar in kara jin abu makamancin wannan." Saheer ya ce, "kiyi hakuri Inna in sha Allah hakan bazai kara faruwa ba." Share hawayen ta yi ta ce, "to too Allah yasa, ku tashi ku tafi." ★★Suna zuwa school din ta fara washe baki tana, "mijin nan ne makarantar da zaka sani?" Wani gigitaccen kallo ya bita da shi da yasata yin shirun dole. Office dinsa ya wuce da ita kai tsaye sannan ya kira wata teacher ya ce mata ta je ta mata interview kafin a bata class. Rike mata hannu tayi suka fita suka shiga wani office din. Ta mika mata takarda da biro ta ce, "Oya write ur name." Kallonta salma ta yi da mamaki tana, "namai? Namai kuma?" Teacher din ta yi murmushi ta ce, "Sorry rubuta mun sunanki." S din ta fara rubutawa tana kallon gabas kafin ta rubuta a na kallon yamma l din kuwa tun daga kasa har sama aka rubuta anan ta tsaya. Ta washe baki tana, "gashi nan malama." Teacher Hafsat ta ce, "mene ne sunan naki?" Salma ta kara washe baki kafin ta ce, "Salamatu amman Inna na ce mun salame amman yan garin nan gidan yan uwanmu ce mun suke salma." Teacher Hafsat ta jinjina kai kafin ta ce, "to zaki iya rubuta mun Abcd yanzu?" Salma ta girgiza kai, "cab aradun Allah ban iyawa duka na dai iya rerawa da waka duk." Bayan Teacher ta gama yi mata tare suka koma office din Saheer ta ce, "Sir gaskiya akwai matsala bata iya abubuwa ba da dama infact ma zan iya cewa tana bukatar sabin darusa ne indai ana son karatunta ya tashi da sauri." Saheer ya ce , "ok Teacher Hafsat amman me kike ganin ya dace a mata a yanzu?" Teacher Hafsat ta ce, "ehto ina ganin akaita primary four amman kuma a bawa iyayenta shawarar ana mata lesson a gida domin zamanta a primary 1 to 3 zai iya durkusar da ita maimakon so da ake ta tashi tunda duk yarana kananu sosai, in akace sa'a kuma ta maida hankali ina ganin za a iya samun abun da ake so." Saheer ya ce, "Ok to ki kaita class din yanzu sai kije ki duba ko za asamu uniform daidai nata da duk wasu materials ki hada ki kawo mun nan." "Ok sir." Ta amsa kafin su suka fice. Salma na shiga class kallon kallo take da yan ajin kusa da wani namiji da girman jikinsu ya kusan zuwa daya ta zauna. Ya daga mata hannu. Ta washe masa baki tana, "sunana salame kai fa." Ya ce , "Habib." Dariya ta yi ta ce, "Habibu." Kwanciya tayi akan desk ta fara barci har sai da lokacin break ya yi Habib ya tabata. Tana fita ta yi office din Saheer. Cike yake da mutane ya yi baƙi ko a jikinta ta bankada ta shige tana, "Mijin an fita tara,ka bani kudin tara...... Free pages na daf da karewa In sha Allah Saura two pages 500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank Evidence of payment to 08103080717 Luvs u all [6/30, 10:38 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-7 Saheer ya kau da kai kamar bai ji me take fada ba. Ya ci gaba da yi musu bayani. Karasawa gabansa ta yi ta ce, "Mijin na ce ma an fito tara ka bani kudi inje in siya abu nima in ci." Ganin hankalin kowa agun ya koma kanta yasa shi yin gyaran murya ya ce, "Sorry guys she's our new student and she comes from villege,so she may not be familiar with our way of behavior." Yana karasa maganar ya duba aljihunsa daga 500 sai 1000 , 500 din ya mika mata domin damuwarshi kawai ta fice daga office din ne a halin yanzu. Aiko yana mika mata ta fisge da sauri ,ta juya zata tafi Coke din ta gani gaban bakin ta koma ta kallesu sai da suka hada ido kafin ta dauka ta zura aguje. Sai da taje bakin kofar zata fita kafin ta juyo ta kallesu ta yi gwalo kafin ta ce, "in kana da karfi kazo ka kwata." Ta arce a dari. Dariya suka fara ban da Saheer da ya kulla. Ya yi gyaran murya ya ci gaba da maganarsa. Ita kuwa tana fita school shop din ta nufa inda ta ga yara na siyan abubuwa. Tana zuwa ta mika kudin tana abani, "fanke." Tsayawa kallon ta matar tayi domin ita bata fahimci me take fadi ba. Da salma ta ga haka ta ja robar fanken ta ce, "ki bani wannan fanken guda uku." Sai a lokacin ta gane ta zuba mata uku a leda sannan ta bata canjin dari biyu dake dari dari ne. Salma na karba ta baje school compound . Gabadaya ta wage jiki kamar an aje kayan dauda. Ta sa bakinta ta bude coke din, ta fara cin fanken tana hadawa da coke din hankalinta kwance tana waƙa. Sauran student din sai binta da kallo suke tamkar tv. Wata ta zo wucewa tana kallonta. Bakinta cike fal ta fara galla mata harara tana, "ke dilla ya da kallo? Na ci tuwon gidankune ban wanke kwano ba? To mijina ne ya bani kudin tara na siya ehee kwadayayya kawai." Ta kara galla mata harara. Tsayawa yarinyar tayi tana mata kallon tara saura kwata ta ce, "villege girl." Salma bata fahimta ba ta ci gaba da zakan coke da fankenta. Sauran kawayen yarinyar ne suka hadu su biyar suna kallonta suna dariya suna fadin villege girl. Daya a cikinsu ta ce, "She's not getting it, she only speaks hausa, so let's switch langauges." Suka fara fadin, " 'Yar Kauye kawai , katuwar banza ji beta ta wani baje tana shan coke." Salma na jin jawabansu ta tashi ta ajiye coke din da sauran fanken gefe ta cire karamin dankwalin dake kanta ta daura a ƙugunta ta ce, "ni kuke cewa yar kauye? Ni kuke cewa wawiya?" Nunata da hannu suka yi suna dariya, "e din wawiya yar kauye ka.... Kafin su karasa rufe baki Salma tayi kansu gabadaya dukansu take ta ko ina ba ji ba gani gasu su biyar ita daya amman ta gagare su. Da gudu sauran yaran dake gefe suka kira displine master din school din. Aiko dakyar ya kwacesu a hannun salma. Daga mai fasasshen baki sai masu kumburarren goshi duk ya yi ƙulu rudu rudu domin dukansu take ta ko ina harda wacce ta ciza kumatu. Sai numfarfashi take tana fadin, "ba ku kun iya raini ba? Iye ku kun iya raini? Ance muku ni sa'ar kuce? Mijine dani e mijine dani." Sai da displine master din ya zabga mata bulala kafin ta yi shiru tana cuno baki tana sosa baya. Kamar bakin ya mutu sai kuma ta ci gaba da sambatu, "gaba kwa kuma waya ce muku ni ana kawo mun wargi wallahi zan balballa yarane gida saba in ba tara, ni ba sa'ar wasanku bace ko a kauye ma ni ba saar yara bace bare nan." Kallonta displine master din ya yi ya ce, "After all this nonsense you've done, you should be ashamed to speak further. You ought to be more reflective,Oyaa get on your knees." Kura masa ido ta yi tana kallonsa, kafin ta ce , "ni kuma? ni na yi me? Su fa suka rainani ni ban kulasu ba cin kayan dadina nake kawai suka fara tsokanata." Dafe kai ya yi, ya ce, "ki durkusa akan gwiwarki yanzu nan zaki dauki hukunci." Salma ta zare ido , "cab hukunci? Hukunco aradun Allah ba mai dukana kuma naki dukawa kan gwiwar." Kara zabga mata dorinar hannunsa ya yi da ta saki wani sauti sai da ya karade School din. Jin hayaniya tayi yawa yasa Saheer saurin fitowa. Salma ya gani tsaye tana rike da baya tana bambami ga sauran student mata biyar jina jina sun bugu wata har bakinta ya kumbura mai kumatu ma ya yi combis haka ma goshi sai kyalle yake na azaba. Yana zuwa Salma da gudu ta koma bayan shi ta tsaya tana rike shi, "mijin wallahi su suka raina ni yaran can kuma ka ce musu ni matar aure ce,kuma kai ne mi...... Kafin ta karasa ya mata wata irin gigitacciyar tsawar da sai da ta razana. Ya ce..... Saura page daya free pages su kare maza hanzarta ki fara biyan naki domin har yanzu ba a fara asalin wasan ba😻 shagali na gaba. 500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank Evidence of payment to 08103080717 [7/1, 8:43 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-8 "Ki mun shiru kar in kara jin bakinki anan gurin." Salma ta cuna baki tana un uni kasa-kasa. Saheer ya ce, "Oya ka daukesu aje ayi ma wajen da suka ji ciwo dressing in an gama kuma su zo office su sameni." Salma dai tanata magana kasa-kasa , "aradun Allah yara suka ƙara rainani sai na ci musu mutunci marasa karfin banza da wofi kawai." Jan hannunta Saheer ya yi ya shiga da ita office dinsa sai da ya rufe kofar kafin ya rike bakinta da hannu, "kin ga wallahi in kika kara cemun wani mijin ko miji a cikin makarantar nan sai na yanke miki baki sai na farfasa miki shi ya yi caɓa-caɓa." Kokarin fara bude baki ta cijeshi tayi ya yi saurin sake mata bakin. Murgudawa ta yi kafin ta ce, "to karya na yi? Ai ba karya na yi ba kai mijina ne ko kaƙi ko kaso ehee kai mijina ne mijin Saheeru mijin Salma e." Ta fada tana juya jiki. Ganin ya ciro wata dorina yana fadin , "au ba za ki daina din ba kenan ko?" Da gudu ta bude kofar office din ta fice tana, "ai ba karya nake fada ba bare ace ba kyau indaina." Ta wuce class abunta. Tsaki Saheer ya yi ya koma ya zauna. Lokacin tashi kuwa na yi da gudu ta koma office din tana fadin, "an tashi,ka zo mu tafi gida mi...." Kallon da ya bita da shi ne yasata yin shirun dole ta tsaya tana murmurguda baki tana wurgi da hannu. Keyn motarshi ya dauka yana, "daga yau ba tare zamuna zuwa ba da kafafunki zakina zuwa school dinnan kuma kar ma ki kara nuna kin sanni." Taɓe baki ta yi , "unm oho ohon maka dai." Ta bi bayanshi ta shige motar ta zauna. Da sauri ya janye motar ya bar School din domin bai son kowa ya fahimci tare suke. Aiko suna zuwa gidan ta baje a falo zata yi kuka, "yunwa nake ji ni wallahi,yunwa nake ji." Ji ya yi kamar bai san me take fadi ba ya wuce cikin daki ya shiga toilet. Ta bi bayanshi tana zuwa ta bankada toilet din ya tuɓe wando kenan zaiyi fitsari. Idonta idon jikinsa. Wata kara ta sake tana rufe baki da hannu. "Na shiga uku na mutu na lalace kai kuma naka abun macijine zabgege ashe." Sambatu ta fara barkate kuma tana tsaye ta kura masa ido taki tafiya. Cikin fushi ya tura kofar sai da ya buga mata goshi. Ta rike goshin tana tsaye agun, "mugu kawai mai maciji aradun Allah sai na rama ji zaka fasa mun goshi." Gaban mirror taje tana kallon goshinta. Kwafa ta yi ta ce, "kyakkyawa dani yana son ya cuceni ya bata mun fuska,zan yi maganinka ysn." Man shafawa ta dauka taje daidai tais din dake bakin toilet din inda yana fitowa zai fara takawa a hankali ta shafa man. Sai da ta tabbatar ta shafa yadda mutum na takawa santsi zai ja shi ya fadi kafin simi simi ta fice a dakin ta tsaya a bakin kofar tana leƙe. Aiko yana fitowa da santsi ya ja shi ya yi wata irin sulewa sai ga kanshi a gefen gado ya bugu daram. Har cikin ranshi yaji wata irin azaba na ratsa shi yana sa hannunshi a goshi ya ji kamar an daura masa wani tulu. Salma mai zata yi ban da dariya harda rike ciki. Musamman da ya tashi ta ga goshin shi ya kumbura har tana birgima a kasa. "Wayyo ni da fatanya sunan wani abu, ji kai har wani sheƙi yake kamar naman akuya wayyo cikina,maganin mutum ai kenan in dai mutum ya ce shi mugu ne zai ga mugunta." Saheer bai kulata ba har sai da ya kalli kanshi a madubi. Lokaci gudu yanayin kamaninsa har ya canja goshi ya kumbura sintim. Yana kallonta ta kara shekewa da dariya. Binta ya yi a guje ita ma ta fara gudu...... *Da dai na so in tsaya da free pages 8 Dinnan amman yanzu saura 2 pages zamu kai page 10 In sha Allah a hanzarta a gama payment masoyan asali nice matar Hedimastan ga fa ko kun daina kaunata ne ban sani ba? Inga ruwan alert mussaman Xh Narrative Nest members*😻😂 MATAR HEDIMASTA 500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank Evidence of payment to 08103080717 [7/2, 12:57 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-9 Haka suka dunga zagaye gidan daga ciki har waje, ko a jikinta ganin tana kokarin mai da shi karamin mahaukaci karfi da ya ya kyaleta yana numfarfashi ya koma daki. Kwanciya ya yi akan gado ban da haki babu abun da yake yi,ga azaban da goshin sa ke yi masa, ga shi kuma sai ƙulu yake karawa kamar wanda ake sawa yeast. Ya rasa meke masa dadi,kwanciyar ma ya gagara,ya kwanta ya kifa kai, ya tashi ya juya yana kallon sama,ya koma gefe shi kadai dai yasan abun da yake ji ya rasa ina zai sa kanshi ya ji dadi. A karshe wani barcin azaba ne ya dibesa ba tare da ya ankare ba. Ita kuwa Salma kitchen ta shiga dake ta iya kunna gas caraf ta kunna Tana, "mutum na jin yunwa baza a bashi abinci ba,dadinta ma ai nima na iya girkin yi zan inci in koshi abuna." Ruwa ta fara zubawa a tukunyar sannan ta dibo shinkafa ta ko aunawa batai ba ta zuba. Sauran man gyadan da ya dafa indomie da shi ta kwashe ta zuba a ciki. Sauran magin indomie dinma ta dauka tana, "bara muji wannaan kuma mene ne." Ta zuba a hannunta kafin ta lashe a baki, dariya ta fara tana, "aradun Allah dandanon girki ne, ji kamar madara madara." Ta juyeshi kaf a cikin shinkafar ta dauki ludayi ta juya,ta juya shi sosai kafin ta rufe ta fita falo tana, "umm kafin abincin ya yi bara inyi kallona ma." Bai fi minti daya ba taje ta kara dubawa ta diba ruwan ta dandana , "umm da saura gaskiya amman shinkafar nan zata yi dadi sosai." Ta kara rufewa kafin ta koma falon ta ci gaba da kallo. Tana cikin kallo barci ya sace ta. Abinci tun yana yi a hankali har ruwa ya tsotse ya fara konewa. Har hayaki da ƙauri ya fara karade kitchen din da falon tana ta sharban barcinta ko a jikinta. Saheer na barci kamar ance ya farka ya fara jiyo wani irin hayaƙi. Da sauri ya tashi aiko yana zuwa har kitchen din ma ya gama karadewa da hayaki ya cika fal. Da sauri ya kashe gas din yana toshe hanci ban da tari babu abun da yake saboda ya riga ya shaƙi hayakin, Salma har lokacin bata san meke wakana ba barcinta take harda gwarti. Sai da ya daidaici daidai duwawunta ya maka mata duka, a zubure ta farka ta zata fara masifa kuma da ta kalleshi ta kalli goshinsa bata san lokacin da ta fashe da wata irin makirar dariyar mugunta ba. Ƙara kula ya yi ya ce, "wai ke duk bayan mintuna shashancin naki karuwa yake? Ki daura abinci ki zo nan ki wage baki kina barci? Da yanzu kin ja mana gobara fa." Sai a lokacin ta tuna da da abincinta. "Innalillahi wayyo abincina." Ta fada tana wucewa ta gefensa ba tare da ta kula shi ba. Tana zuwa ta sa hannu ta jefar da murfin tukunyar saboda zafi sannan tasa zaninta ta sauke tukunyar gabadaya ya kone yyi baki sai dan kadan a tsakiyan tukunyar da bazai wuce cokali goma ba. Bajewa ta yi a kasa kitchen din ta ja tukunyar gabanta tana kuka tana ci, "Ban da mugunta ace abar abincin mutum ya kone baza ana duba masa ba, wannan ai mugunta ne da son zuciya kuma aradun Allah sai na ci sai dai bakin ciki ya kashe mutum." Don takaici kasa kulata Saheer ya yi kawai ya zauna a falon ya yi tagumi. Shima wata azababbiyar yunwa ya fara ji gashi bazai iya shiga kitchen din ya yi girki ba. Tashi ya yi kawai ya fice masallaci ya fara zuwa ya yi sallah sannan ya wuce 3D Resturent ya ci abinci har ya fito kuma sai ya koma ya yi takeaway ya sa a mota. Bai koma gidan ba har sai da dare ya yi. Yana komawa yaga gidan da dakin kaca-kaca har wani hamamin wari ne yake tashi. Ita kuwa tana zaune gaban tv tana kallo tana ta sheƙa dariya ko a jikinta. Har ya shigo bata sani ba sai da ya kashe tv kafin ta juya tana , " wani dan iskan ne ya kashe mun kallona." Tana rufe baki suna hada ido. Ya ce , "Dan iska ko? Inaga dai duk ranar da na fasa miki bakin nan naki zaki setu ki rage rashin kunyar nan da fitsara kuma maza ki tashi ki gyara gidan nan tas domin ni ba dan aikin ki bane." Bin falon da kallo ta fara yi kafin ta kalleshi, "ina za a gyara me ye ya faru a gidan?" Saheer ya ce, "kin makance ne? Na ce ko kin makance ne ko kazantar taki ce ta shahara?" "Yoo shahara na nawa kuma? Ai ni sunana ma a kauye shahararriya salame." Salma ta fada tana murguda masa baki. Kasa hakuri ya yi ya cire belt dinsa zai maka mata cikin Muryar sauri ta ce, "zan yi wallahi zan gyara." Ya nuna mata kitchen da hannu. To maza muje ki fara da nan sai kin wanke komai kuma kinyi moping. A kanta ya tsaya da belt din a hannunsa ya na yi mata direction yadda zata yi tana yi tana kuka. Domin ba saba aiki tayi ba ta wanke ya ce bai wanku ba ta sake wankewa a haka har ta gama wanke wanken. Mopping din kuwa da rarrafe ta karasa tana yi tana zufa. Tana gama gyara kitchen din ya ce su dawo falo ma ta gyara, nan ma haka ya tsaya sai da ta gyara shi tsaf. Don dole bakinta ya mutu ta kasa magana bare motsawa a inda ta zauna. Ganin dare ya yi takeaway din da ya tawo da shi ya bata. Aiko tana karba ta fara ci hannu baka hannu kwarya. Tana gama ci ta baje agun sai barci. Saukar ruwa taji a fuskarta Saheer na fadin ta tashi taje tayi sallah. Tsaki tayi tana kokarin komawa. Ganin ya dauko belt ai tuni ta tashi aranta tana, "aradun Allah duk abun da ka mun yau sai na rama ai kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha." Sai da yyi sallar isha kafin ya dawo gidan ya kunna TV tana zaune a gefe yana zama ita ma taje kusa da shi ta zauna. Tsawa ya dakata mata yana, "wani irin iskanci ne wannan? Dallah nemi wajenki ki zauna." Bata kula shi ba kuwa ta zauna a gefe tana kallonshi. Can anjima ta kalleshi sai sun hada ido sai tayi kwafa sai ta kawar da kai haka ta dinga yi har sai da ya kashe tvn yaje ya kwanta ita kam tana zaune. Lakashi tayi sai da ta tabbatar ya yi barci sannan ta jura farar jallabiyarsa a jikinta ta shafa farar hodo a fuskarta ta bude kanta gashinta kamar hamtar yan iska a tsattsaye. Wutar dakin ta kashe sai na falon kadam kadan dake haska dakin. Ta shiga dakin tana Wata irin ƙatuwar muryar tana kiran sunan shi, "SAHEERUUUUUU SAHEEERUUUU SAHEERRUU." Kamar a mafarki Saheer yaji yana kiran shi aiko yana bude ido me zai gani..... *Gobe zamu gama free pages In sha Allah* 500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank Evidence of payment to 08103080717 [7/3, 9:53 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* ©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH* PAGE-10 *Last Free Page* Fararen kayan kawai yake ganin alama ana motsi kuma ana kiran sunan shi. "Innalillahi wa inna illaihir ra'ji'un,na shiga uku,na shiga uku." Ya fada yana ƙankame jikinsa yana janyewa zuwa karshen gadon. Ya gama tsorata. Ita kuwa Salma ƙara binshi take tana kiran sunan shi tana, "kar ka ƙara taɓa mana diyarmu salame kar ka kuskura ka kara dukanta ko yi mata kallon banza." Yana jin wannan maganar ya gane Salma ce. Cikin ɓacin rai ya tashi ya kunna wutar dakin idonta a rufe Bata san har ya tashi ba ci gaba da zaro zance take tana, "in ka kuskura ka kara taɓa mana diyarmu sai mun halakakaaa." Saukar marin da taji ne ya sata saurin bude ido. Saheer ya ce, "in ke baki hallaka ni ba ni na hallaka ki ai wawiya kawai." Da harara ta bi shi tana, "Oho dai Allah saka min mugu kawai mai kan agwagi." Ta karasa maganar tana ficewa da sauri. Tsaki ya yi ya ce, "idiot." ya koma ya kwanta abun shi. Sai da ta kara tabbatar da cewa ya koma barci kafin a hankali ta shige ta kwanta. Ta kwanta barci yaki zuwa ga baki ya saba da kwadayi. Haka ta tashi ta koma kitchen tana dube dube ta ci karo da gwangwan madarar gari. Washe baki tayi ta dauka ta dauki cokali ta je ta hau gadon ta Fara nakar madara kamar tuwo. Bakinta da fuskarta baja baja madara ta ko ina hatta zanin gadon ma duk ta fara batawa. Sautin yadda take shan madarar ne ya tada Saheer kamar mai jan ganda har wani gwaranci take. Yana tashi ta boye madarar a bayanta tana sude baki. Idanun nan kuwa sunyi kifi kifi na rashin gaskiya. ya ce, "me kike sha cikin daren nan?" "Umm umm ba komai." Ta fada tana kara boyewa . Kallon fuskarta ya yi da bakinta tana sudewa ya ce, "bani abun da kike sha." Salma ta ce, "ba komai fa ni ba wani abun da nake sha." "Na ce ki bani." Ya fada cikin tsawa. Da sauri ta mika masa gwangwanin madarar. Ya yi tsaki ya fita ya mayar ciki ne amman har ta kusa shanyewa saura kadan. Yana komawa dakin ya ce, "ke wai wace iri ce Don Allah? Hankali ne baki da ko yaya? Shin wannan ba madarar shan tea bane? Ko ke karamar yarinya ce?" Yana maganarsa ta juya masa baya abunta tana , "oho to waya sani ma." Saheer ya ce, "kar kimin shiru a wajen nan, kuma daga yau na kafa miki doka kullum kina tashi da sasafe kina gyara gidan nan kina dafawa kanki abun da zaki ci domin ni ba bawanki bane in ko hakan yaki samuwa zaki sha mamaki." Ya fada yana kwanciya. Kananun magana ta dunga yi ciki ciki har barci ya kwasheta ita ma. Wani irin kwanciya sukai gabadaya ta cinye gadon duk ta bararraje shiko ya tukura gefe guda gashi yana tsoron ba abun ya sauka kan gadon ba ta fadawa Inna ya shiga uku. Da asuba ya tasheta tana sallah ya sa ta fara gyaran gidan kamar yadda ya fada tana yi tana mita domin ita barci take ji. Yana gama shirinsa ya ajiye mata 200 kudin Break ya yi tafiyarsa. Binsa Salma ta yi tana, "Mijin mijin ba za ka jirani ba? Ban gama shiryawa ba fa." Wani mummunan kallo ya bita da shi ya ce, "kar ki tawo da kafafunki." Ya shige motarsa ya fice. "Mugu kawai mai kama da kashin awaki." Ta fada tana komawa ciki. Haka ta kwaba indomie ta dafa kamar an wanke kan mahaukaciya ta zauna ta naki abunta. Ta kwashe sauran madaran da ya kwace a gunta tasa a leda tasa cikin jaka. Uniform din tasa duk ya matse mata jiki ko ina ta motsa yana rawa . Irin guntuyen rigunan nan ne iya gwiwa da karamin hijabi. Hijabin nata kuwa ko kirjinta bai gama rufewa ba ga nonuwa a baje ba breziya duk inda tayi sai sun bi sun motsa. Rataya jakarta ta yi ta fice ita ma ta kama hanyar school din. Tana cikin tafiya ta tsaya bude jakar ta dauko kullin madararta tana tafiya tana sha. Ta ga wancen ta tsokana ta ga wannan ta tsokana har ta kai School din. Ta shige tun daga mai gadi har sauran student Binta ake da kallo. Zata shiga class ke nan Ta hango Saheer ya fito a office dinsa da kumburarren goshi ya kara tsini. Wage baki tayi tana dariya da karfi ta ce, "Mai ƙulu a goshi." Gabadaya student da sauran teacher din da ke wajen sai da suka juya suna kallonshi. Tana nuna shi tana dariya. Kunya kamar Saheer zai nutse haka ya koma office ba don ya so ba. Habib ne ya jata yana, "Ke Salma Headmaster ne fa ki daina." Ta ce "Shegemasta sunan shi?" Habib ya ce, "aa Headmaster shugaban makarantar nan." Tsaki ta yi, "yoo ina ruwana da wani Shegemasta gashi nan garin muguntarsa ai ya sha kulu." Suka shige class tare tana dariya. Bayan Kwana Uku. Kwance take a gado daga ita sai zani zanin ma ya fice babu komai a jikinta a dole tana jin zafi tayi daurin kirji ta kwanta barci shi kuma Saheer ya fita bai dawo gidan ba. Shigowar sa kenan da nufin zai shiga toilet ya yi wanka,har ya wuceta kawai ya dawo ya tsaya akanta wajen minti biyar yana ta sake sake a zuciyarsa can kuma kawai ya tsinci kanshi da fara cire kayan jikinsa ya haye kan gadon. Damkar da ya mata ne ya sata saurin farkawa tana kokarin kauce masa. Ina ya riga ya gama tafiya ihu ta fara ta tana "wayyo ni wayyo Allah inna ta aura mun mugu wayyo ni wayyo zai kasheni, shikenan zai kashe ni, mugu ne azzalumi mai fuskar agwagi, dan iskane maciji yake samun cikin jikina, mugu zai kasheni." Ta fada tana gantsara masa cizo. Tamkar zugashi take bai barta har sai da ya tabbatar da abun da yake bukata ya tabbatu. Washegari bata tashi ba har ya tafi School sai wajen karfe takwas da rabi ta tashi. Tana ganin agogo ta fara salati tana, "mugun cen, mugun cen ne ya ja mun." Ta tashi da sauri tayi wanka ta ci abinci duk da cewa bata jin dadin jikinta amman ta gammace taje school dinnan da ta zauna agidan. Haka ta fara nakan hanya tana yi tana hutawa. Tana zuwa kuwa shine a class dinsu. Ta shiga zata zauna ya ce, "wait yanzu ake zuwa school? Kin san karfe nawa ne yanzu?" Salma ta ce, "kai ka manta abun da ya faru jiyane da..... Kafin ta karasa ya yi saurin.... *To Ma Sha Allah wannan shine last free page duk wacce take son ci gaba zata biya domin ta shiga grp ta karanta, indai kun gama payment kan lokaci In sha Allah Monday zan ci gaba da posting😻🤍.* 500 ne kacal 8103080717 Aisha Abdullahi Sani Opay Or 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank Evidence of payment to 08103080717