SAKACIN WAYE? 2023 HAKKIN MALLAKAR LITTAFIN DA DUK ABINDA YA KUNSA NA MARUBUCIYAR SHI NE SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI). A GUJI KARANTAWA A YOUTUBE KO SARRAFA SHI TA KOWACCE HANYA BA TARE DA RUBUTACCEN IZNI NA BA. “GEMBU” (GARIN MU DA BABU KAMAR SA A SANYI A FADIN KASAR NAJERIYA)!!! G arin Gembu, kamar yadda na samu cikakken labari daga bakin Ummati, da sauran bincike na na ilmi a kan tarihin yankin namu, kasancewa ta wata irin mutum mai son sanin Tarihi da bin ussin salsalar ilmin abu, yankin Gembu wani babban birni ne ko kuwa in ce alkarya da ke a yankin Duwatsun “MAMBILLA” a jihar Taraba a Najeriya, shine babbar Hedkwatar karamar hukumar Sardauna wato (Sardauna Local Government) da aka fi sani da “Tsohuwar Mambilla” a jihar Taraba. Sunan Sardauna Local Government ya samo asali tun daga zuwan Alhaji (Sir) Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto yankin mu na Gembu a shekara ta (1956). Mutanen Mambila ko Mambilla suna zaune ne a Tudun Mambila (Mambilla Plateau). Garin yana kusa da Boda wato iyakar da ta raba kasar Najeriya da kasar Cameroon. A wasu lokutan masana tsaunin Mambila kan kira tudun na Mambila da ‘Heaven on Earth’ wato (Aljannah a duniya), wannan ya samo asali da kasancewar garin Gembu gari mafi kyawun yanayi na sanyi mai ban mamaki a arewa maso gabashin Najeriya. Masana ilmin labarin kasa (Geographers) sun tabbatar da cewa a kasar Najeriya bakidaya babu gari mai irin kyawun yanayi na sanyin Gembu. Sannan gari ne mai cike da albarkatun kasa wanda da gwamnati zata maida hankali wajen bunkasa shi da ta samu arzikin kudin shiga mai yawan gaske a kan sa, sakamakon yadda garin ya ja hankalin masu yawon bude ido na ciki da na waje. A Gembu akwai wasu manyan Dams guda biyu wato ‘Barup Dam’ da ‘Tunga Dam’ masu tsohon tarihi tun tana ancient town of (Bommi), garin Mambila na zaune a matsakaitan duwatsu tsayin kusan mita 1,348 (4,423 ft) sama da matakin Teku, yana daga cikin manyan biranen Najeriya. Gembu na da habakar kiwon shanu, tumaki, awakai da Buffalo. Tuntsayen gida kuwa Allah ya yi albarkar su a Gembu, wanda ya sanyawa garin albarkar nama da abinci mai lafiya, duk da cewa sun fi kiwon dabbobin su fiye da cin su. Abincin da ya fi yawa a Gembu shine kayan marmari (fruits) wanda ke taimakawa kwarai wajen kasancewar mutanen garin cikin koshin lafiya, yawan shan ‘Piya’ ya maida fatar mutanen Mambila wata irin danyar fata mai taushi da sulbi kamar larabawa. Gembu gari ne da Allah ya halicci kyawawan mata, in na ce kyau, to ina nufin tsurar kyau na halitta fiye da na sauran duka kabilun fulanin Najeriya. Akasarin ‘yan Gembu (musulman cikin mu) zaka gan mu dogaye haka sirara masu cikar zati da kamala, sirantakar dake kara mana kyau, matan Gembu masu asalin dogon hanci da doguwar fuska ne, masu sassanyan kyau da babu fulanin da suka mallaki irin sa a fadin kasar Najeriya. Wadannan din dana ambata ba dukkan su ne ‘yan kabilar Manbila ba, mutanen Gembu sun fito ne daga rukunin kabilu daban - daban wadanda suka hada da; Mambilla, Kaka, Kambu da Panso. Yaren garin Gembu shine fulatanci ziryan din sa, Hausa bata da tasiri sosai. Yaran da aka haifa a Gembu ko “zo in ka she ka” da hausa basu sani ba sai wadanda suke fita ko suke ta’ammali da bakin haure. Matan Gembu wasu irin kyawawan mata ne na bugawa a jarida kamar sun hada iri da larabawa, sabida tsananin sanyin garin basa ta’ammali da fanka ko A/C. Mutanen da aka haifa a Gembu basu taba ganin fanka ko A/C a zahiri ba sai a talbijin ko a littafi. Sabida karfin harshen fulatancin su hatta a Choci da fulatanci a ke sermon kasancewar kiristocin su kusan sun fi musulmai yawa. A wancan lokacin dana ke magana a kai mazan Gembu na fita cikin jihar Taraba don yin karatun boko amma matan Gembu basa karatun boko sai daidaiku, wadanda a wannan karnin da ake ciki ne ma suka dan fara karatun boko, shi yassa ake fadin cewa matan Gembu ‘yan kabilar Mambila basu da wayewar kai kamar na sauran fulanin Jalingo. Amma kuma suna bada karfin su a kan neman ilmin muhammadiyya wanda yasa bazaka taba kiran su jahilai ba. Sana’ar matan Gembu sakar kayan sanyi da zannuwan gado na rufuwa masu kauri, wadanda suke sakawa don amfanin kan su sabida yanayin garin su. Sai ko kiwo da noma. Sunan yaren garin ne “Mambila” sunan garin kuma shine “Gembu”. Kamar yadda na fada a sama Gembu shine birnin Mambilla wanda ke karkashin karamar hukumar Sardauna. Gabadayan garin da sauran kauyukan da ke makwabtaka da shi a kan Duwatsu suke tsugunne, wato (Mambilla Plateau). “Mambillah, the coolest wheather in Nigeria - (Wikipedia-Britannica)”. Mambilla ya zama tourist attraction na jihar Taraba sakamakon ni’imar sanyi da Allah ya yi wa garin da sauran albarkatun kasa da bazasu lissafu ba. Geographers da yawa sunyi rubutu a shafin wikipidia a kan tsaunin Mambila, haka masu binciken albarkatun kasa (soil scientists) sun tabbatar da cewa akwai Zinare da Shudin Yaqutu (Gold and Blue Sapphire) kwance a cikin kasar Mambilla Plateau, wasu marubutan ilmi kuma sun yi ittifaki a kan garin Mambila wanda sam gwamnati bata maida hankali akan albarkatun sa ba, da cewa; da gwamnatin Najeriya zata maida hankali a kan sa da ya tabbata “Heaven on Earth” din da ake kiran sa da shi ko kuwa ya zama tamkar kasar Dubai a Najeriya. Hanyar zuwa garin Mambilla kan shi a kan dutse yake, wanda ya taho daga garin Jalingo. Mambilawa wato ‘yan asalin Gembu basu cika ji ko yin yaren harshen hausa ba musulmin su da kiristocin su. They have a very strong Fulfulde accent wanda ya bambanta dana dukkan fulanin Najeriya. Kauyukan da ke yankin Gembu sun hada da; Tunga, Maisamari, Yelwa, Gurgu, Sabon gari da kuma Nguroje. Kafin zuwa garin Gembu sai ka fara isa Numan ta jihar Adamawa, sannan ka dauki hanyar Taraba, tafiyar awanni biyu a tsakani kafin ka iso Jalingo, daga nan ne zaka dauki hanyar da zata kai ka Gembu, tafiyar awanni takwas a tsakani kafin ka samu isa Gembu. Don haka tafiya daga Kano ko Kaduna zuwa Gembu tafiya ce mai nisa ta tsahon awanni 21-22, tafiyar kwana daya kenan cur, idan har ba mutum ya yi transit (matsaya) a garin Jalingo ba. Kasashen turawan yamma sun maida Gembu ‘tourist destination’ na Taraba, ba ka raba Gembu da bakin jar fata lokaci-lokaci suna daukar hotuna a cikin motocin su masu budadden sama. Ba turawa kadai ba duk ma wanda ya san ni’imomi da albarkatun da ke tattare da Gembu kuma ya ke da halin zuwa to kuwa zai so ya kai kan sa yawon bude ido wannan gari namu mai dimbin albarka, don hutawa da karin fadadar ilmi, musamman in ka kasance mai son karin ilmi a kan geographical setting na kasar Najeriya. Gembu na kusa da wata karamar hukuma mai suna Gashaka, inda a can ne ‘Gashaka Gumti National Park’ ya ke. - GEMBU; Garin da ya tara tsala-tsalan ‘yammata mafiya kyawu a Najeriya - (Saliadeen Sicey). Da zarar ka fara haurawa kan tsaunin Mambila daga wani tsauni da ake kira ‘Mayo Selbe’ da ke karamar hukumar Gashaka, zaka hangi Tsaunin Mambilla mai tudun gaske lullube da korran ciyayi da wasu irin dogayen bishiyoyi da yayyafin hazon kankara ya yi musu mayafi, don wasu lokutan kankara har zuba ta ke. Dalilai da yawa zasu sa ka son ziyartar Gembu; na farko zaka so ziyartar garin Gembu ko don ka ga tsala-tsalan matan da Allah ya halitta a can, in kai mai son zane-zane ne har ka so ka zana su da alkalamin ka, ka sha fruits nunannu iyaka shan ka (musamman Piya), ka sha danyar madara da nono kindirmo iyaka yunwar ka, ka ji ni’imar sanyia jikin ka da zuciyar ka iya ka jin ka, ka ji kamar ba a kasar Najeriya ka ke rayuwa ba, ka kuma amfana da tarin albarkatun kasar da ke tattare da garin, ka kara girmama girma da buwayar karfin ilmin halittar ubangiji. ***** UMMATIN MAMBILLAH! U mmati, sunan Kaka ta kenan wadda ta haifi mahaifi na. Sunan ta na asali Saudatu, ni na saka mata suna (Ummatin Mambila), kasancewar ita ta raine ni, daga madarar shanun ta mai dumi da gardi da ta zama makwafin nonon uwa a gare ni a wancan lokacin. Ban taba sanin dumin jikin mahaifiya ta ba sai na Ummati, na san fuskar ta dai a hoto kan wani tsohon farin hoto marar kala daukar zamanin da, da Ummati ta taba nuna min, sai naga ba maraba da tawa fuskar banda kuruciya dana fi ta, duk da cewa sanda aka yi hoton ma da tarin kuruciyar ta don bata cika shekaru ashirin ba. Kuma Ummati ta sha gaya min da kuruciyar ta ta rasu. Sunan Ummati da na lankaya mata tun ina koyon magana shi ya bi ta a bakin ‘ya’ya da jikokin ta, dama jama’ar garin Mambila baki daya, ita da kan ta ‘Ummati’ ta ke kiran kan ta da kanta, Saudatu ya dade da bacewa a bakin kowa. Ita da mijin ta mai rasuwa Malam Dalhatu ‘yan asalin garin Gembu ne, iyayen su da kakannin su sune tushen kabilar Mambila, wato wadanda sune ‘yan asalin garin Mambillan tun daga iyaye da kakannin su, aka kuma haife su a nan, suka girma suka yi aure suka rayu tsayin rayuwar su a nan. Malam Dalhatu Abdullahi Gembu, ya rasu ya bar matar sa Ummati da ‘ya’ya maza guda uku, Gidado da Mamman wadanda shekaru biyu ne kawai a tsakanin su sai suke tamkar tagwaye a idon mutane, sai kuma autan Ummati wato Baffa Adamu wanda suka baiwa ratar shekaru kusan bakwai. Wadannan zaratan ‘ya’ya maza guda uku na Ummati duka sun tashi sun girma tare karkashin kulawar ta da jajircewar ta a kan kiwo da sana’ar saka da ta ke yi don ta tallafi maraicin su a bayan ran mahaifin su. Ban taba ganin jarumar uwa irin Ummati ba. Wadda ta tsaya tsayin daka wajen hada kan ‘ya’yan ta da daukar dawainiyar su ta yadda basu taba kukan basu tashi tare da mahaifi ba. Lokacin da ta tashi yi wa Gidado da Mamman aure sai ta yi takakkiya ta tafi har makwabtan su garin da ake kira kauyen Gashaka, ta nemo musu auren Yaya da kanwa ‘yan asalin Gashaka masu nasaba mai girma sabida tsoron ta na kada mace ta raba mata kan su. Asshe da Hassu ‘ya’yan wani attajirin bafillace ne a Gashaka, in aka ce miki attajirin mutum a Mambila to fa ba tsabar kudi ko tarin dukiya ya bashi wannan sunan ba, a’ah; yawan dabbobin ka da gonakin ka na gado sune arzikin ka a Mambila. To ita kam Ummati ba ma wannan ta duba ba wajen aurawa Gidado da Mamman Aisha da ake kira (Asshe) da Hafsatu da ake kira (Hassu) illa duk fadin garin Gashaka su ne yaran da aka tabbatar sun sauke Al’qur ani sun kuma haddace shi kafin su cika shekaru goma-goma. Hassu da Asshe ‘yan biyu ne masu kamanni daya basu taba yin karatun boko ba sai na addini. Wanda ya sanya suka zama ‘yammata masu nutsuwa da tarbiyyah ababen rububi a wajen samarin Mambilla, kowanne uba da kowacce uwa fatan su a auro musu zuriyar Muhammadu Jauro, ga kuma kyawun sura da Allah ya basu. Gidado da Mamman ra’ayi ya banbanta a kan abinda suke so a rayuwa, yayin da ilmin boko ya kunno kai a Manbila wasu sun karbe shi da hannu bibbiyu musamman kiristocin cikin su, wasu kuwa musaman musulmi suna tababa a kan amsar shi, wasu da yawa sun yi hannun riga da shi ne da cewa sakon missionaries ne. Mamman dai ya karba da hannu bibbiyu ya shiga makaranta yayi firamare da sakandire yana kuma hadawa da kiwon shanun su na gado da noma duka bai bar Gidado da wahala shi kadai ba, Gidado ya yi wa kansa Allah ya kiyaye da boko ya maida hankali wajen kula da mahaifiyar su, daga noman da kiwon babu wanda ya dame shi ya fi gane ya tara yara a a zaure yana koya musu karatun Al’qur’ani, a kowanne karshen sati iyayen su su bashi sadakar kudin Laraba. Da haka ya zama malami sosai har manya yake karantarwa littafan addini a Alhamis da Juma’ah. Dan autan Ummati kuwa wato Baffa Adamu har ya fi Mamman son boko, Ummati kuma ta basu dama kan kowanne ya yi abinda yafi so in dai ba sabon Allah bane. Ta sadaukar da shanun gadon su masu yawa kafin a bawa Gidado da Mamman auren Asshe da Hassu. Gidado ya auri Hassu, Mamman ya auri Asshe. Gidado shi ya fara samun rabo shekara na zagayowa Hassu ta haifa masa Umarul-Faruq. Yaro tamkar khaki (photocopy) na mahaifin sa Gidado. Asshe kuwa shiru, tun ana saka rai har an hakura, da abin ya dame ta duk inda ta ji mai bada maganin haihuwa sai ta je a boye ta karbo sassake don idan ta bari Gidado ya sani zai sata a gaba ne yana mata wa’azin Allah kadai ke bada haihuwa, ta yarda Allah ke bada haihuwa amma shi ya ce tashi in taimake ka. Lura da damuwar Asshe da Ummati ta yi a kan haihuwa. Da Faruq ya isa yaye sai Ummati ta dauke shi ta baiwa Asshe. Don farin ciki Asshe saida tayi kuka a lokacin ita Hassu goyon ciki na biyu take yi. Asshe ta dauki Umar ta rike da dukkan kaunar duniya da kulawar data fi wadda yake samu a gun mahaifiyar sa. A wajen haihuwar na biyun ne sai ya zo da karar kwana Hassu ta rasu tare da abinda ke cikin ta. A wancan lokacin zautuwa ne kawai Malam Gidado bai yi ba sabida mutuwar matar sa uwar dan sa abokiyar rufin asiri, Hassu. To kuma ina ga ‘yar uwar ta da suka fito daga mahaifa guda suka yi yarinta da kuruciya da aure tare? Da kyar da kuma rokon Allah har da rubutun dangana Ummati ta samo kan sa, ya koma karantarwar sa kmar yadda ya saba. Malam Muhammadu Jauro wato mahaifin su Hassu ya ce “inama ina da wata diyar! Da na baiwa Gidado, domin ban taba yin surukin da ya san darajar mace kamar sa ba, amma duka na aurar da su”. Tun daga lokacin Baba Gidado ya dauki soyayyar duniya ya dora a kan Ya Umar, Inna Ashe kuma ta goya Umar - Faruq goyo na amana bata da lokacin kan ta sai na Faruq, bata da hidimar kowa sama da tasa ko mijin bata bashi lokacin da ta ke baiwa Faruq, koda yake ai dama Dan ta ne tunda kuwa shaqiqiyar ta ce ta haife shi. Wadda har ta rasu tana gaya mata a kullum “ke na haifawa Umaru dan ki ne halak malak”. Auren Asshe da Mamman ba jimawa gurbin karatun sa da ya nema a jami’ar Jos ya fito, ya tattara ya tafi Jos ya bar Asshe tana goyon Omar-Faruq a gaban mahaifiyar sa Ummati. Sai da Omar ya shekara bakwai cikin ikon Allah buwaya gagara misali rana daya (bayan ta riga ta fidda rai), sai gashi Allah ya dubi hakurin ta da zumuncin ta a kan maraya ya bata nata rabon, wato ta haife ni. Lokacin da na fara tasawa sai mutane ke cewa ai babu wanda nake kama da shi duk cikin iyayen mu, Ummati da ma dangin mu na wajen uwa dake Gashaka sai da Omar kadai. Dukkan mu kuma da iyayen mu mata muke kama don haka jama’a da yawa da basu san tarihin mu ba sun dauka uwa daya uba daya muke, musamman yadda Omar yake taya Asshe raino na tun ina mitsitsiya ta ya ke goya ni, yaje makaranta da ni goye a bayan sa. Tun ana korar sa kan ya mayar da ni gida ya dawo, sai malamin ya ga ya tsaya a bakin tagar ajin su ya ki tafiya yana leke yana sauraron karatun daga bakin taga, dole malamin su yake jin tausayin sa ya kyale shi yake zuwa karatu da ni. Don ya lura kaunar da Ya Omar yake min tana da yawa. Wannan ya faru ne a sanda na fara wayo. Wani abun jimami da ya biyo bayan murnar haihuwa ta shine tun bayan haihuwar Asshe ke fama da matsalar zubar jini, an yi yawon neman magani iri-iri har babban asibitin jihar Taraba inda likitoci suka tabbatar da cewa magunguna masu karfi data yi ta sha na gargajiya don neman haihuwa su suka lalata mahaifar ta, Allah ne ya rubuta zan shaki iskar duniya shiyasa har ta iya ta haife ni. Aka saka ranar da za’a yi mata aikin cire mahaifa don a samu zubar jinin ya tsaya ta huta ta samu lafiya gabadaya amma babu batun sake haihuwa. Da ranar ta zo aka yi komai lafiya aka gama lafiya, ana ta murna wahala ta kare, ashe kuwa da gaske babbar wahala ta kare domin kuwa Inna Asshe, bata farfado daga allurar anaesthesia ba. ****** MAMMAN “ Kina nufin Hassu da Asshe duka sun shigo rayuwar mu ne ni da Yaya Gidado halan don kawai su haifa mana marayun ‘ya’ya su bar mu da kananan marayu su koma? Me kike nufi da cewa ta zarce a cikin allura?? Kina nufin, nima ni kadai zan raini ‘dan nan/'yar nan kamar yadda Yaya Gidado yake rainon Omar Faruk shi kadai??? To shin da wanne nonon kike nufin zan raine shi/raine ta? Ai gara Umar ya sha nonon uwa har na tsayin shekaru biyu ko ba komai ya san dumin jikin uwar sa, ki ji tausayin halittar Allah baiwar Allah ki fada min gaskiya cewa wasa ki ke….. k ice min mata ta Asshe barci take yi a cikin allurar yanzunnan allurar za ta sake ta ta tashi mu tafi gida ta shayar da Dan ta”. Sai hawaye wasu na korar wasu suka biyo bayan maganganun da zaka tabbatar cikin fita hayyacin sa yake yin su. Abinda Baba na ya fadawa Nos din da ta gaya masa rasuwar mahaifiyata kenan kafin hawaye su cigaba da tsinke masa, ya kuma kasa karbar jaririn da take ta faman bashi kamar ya ce mata "ki musanya min shi da mata ta Asshe. Zata iya kara haifa min wani, amma ita bazan kara samun kamar ta ba!!!" Nos dai bata gane sambatun wannan mijin mai tsananin son matar sa me yake nufi ba, ta dai san zafin mutuwar matar sa ne ke bugun sa ya kuma fidda shi a hayyacin sa, sai hakuri take bashi. Tana tuna masa ayar Ubangiji da ta ce “Kullu Nafsin Za’ikatul Maut”. Ta kuma miko masa ni nannade cikin zanin atamfar mahaifiya ta tana fadin, “Yi hakuri ka karbi kyakkyawar kyautar ‘yar da Allah yayi maka ka ji! ‘Ya mace ce ba namiji ba. Idan ka yi mata kyakkyawan raino watarana zata ji kan ka kamar mahaifiyar ta”. Haka Abba ya karbe ni cikin yanayi na dimauta da yankewar buri gabadaya ya fito waje neman Ummati, can ya gano ta inda ya bar ta tana tahiyar sallame sallahr walha a inda ya bar ta tun safe kenan tana rokawa Ashe sauki a cikin tahiyar ta, ya karasa gabanta ya ajiye mata jaririyar a saman cinyar ta sannan ya koma gefe ya saka kai cikin kafafuwan sa ya saka kuka. Kukan da tun kafin ta san dalilin sa Ummati ta tabbatar itama Asshe maraya ta bar mata, marayun sun zame mata biyu, Ya ilahi, sai ta sallame sallahr ta ce masa “ka ce Innalillahiwa’innailaihiraji’oun Muhammadu, shine kawai abinda zaka yi Allah ya yi farin ciki da kai a wannan yanayin. Ka kuma karbi ‘yar ka ka yi mata huduba da sunan mahaifiyar ta. Ka yi fatan Allah ya baku tsahon rai ku ku raine su, ka je ka daukota mu tafi ka wanketa da hannun ka ka yi mata suttura ka kai ta makwancin ta da kan ka shine babbar soyayyar ka gare ta a yanzu, ka cigaba da nema mata aljannah”. D aga Jalingo kai tsaye suka yi shatar mota zuwa Manbila aka yi wa mahaifiyata sutturah. Mutuwar Inna Asshe ta fi taba Ya Omar fiye da kowa a gidan don shi bai san cewa ba ita ta haife shi bama. Omar bai san maraicin uwa ba sai da Inna Asshe ta rasu, kulawar mu ta koma hannun Ummati, duk da Ummati bata raga mana komai ba na kulawa da tarbiyyah amma Kakar mu ce kuma tsohuwa ce. Kulawar Kaka daban kulawar uwa-mahaifiya daban, idan ka hada duka biyun zaka fi kowa morewa, uwa ta kwabe ka har da bulala Kaka ta lallashe ka da tuwo da koko, tunda dai Kaka da sangarta jika aka san shi. Mafari kenan da raino na ya koma hannun Ummati, muka shaku wata irin shakuwa da Kakata Ummatin Mambila, kakkarfar dattijiya, doguwa fara mai kyawun surah wadda bata daukar kowanne irin wargi ko raini a kan jikokin ta, zaka yi mata komai ka kwana lafiya amma kada ka taba Aisha da Omar. Da ganin Ummati zaka san an zuba zamani kuma an zuba kyau an juya miji a lokacin kurucciya. Abu na farko da ya assasa shaquwar mu zuwa shakuwar da ta zarta ainahin wacce ke a tsakanin Kaka da jika ta zama ta mahaifiya da tilon ‘yar ta, ya sanya kuma ta dora min soyayyar duniya shine kasancewar ita bata taba haihuwar diya mace ba, na biyu ita ta shayar da ni daga madarar shanun ta, kuma na ci sunan mahaifiyata wadda tayi mata biyayya sosai. Baba Gidado yayi aure da jimawa da Jaru, matar wani marigayin abokin sa, bayan tsayin lokacin da ya dauka babu aure, don ya tabbata ba zai sake samun mace tamkar (Ummu-Faruqu) ba kamar yadda ya ke kiran Hassu har gobe, amma ko kadan baya jin dadin ta, haka dai ake zaman da dadi ba dadi. Ya riga ya saba da matar sa Hassu mai addini, mai hakuri da kuma godiya da duk abinda ya kawo mata, mai yakanah, wadda ko kara ya ajiye ya ce kada ta tsallaka bazata tsallaka ba, wadda in ya ce farin yadin nan baki ne zata ce da shi “bakikkirin kuwa”, amma Jaru? Akasin Hassu ce a komai. Ya yarda hakika Allah ba ya barin wani, don wani ya ji dadi. Da bai dauke masa Hassu ya hada shi da Jaru ba, da bai raba Mamman da Aishatu ba sabida wadannan matan guda biyu tamakar Hurul ‘eenin duniya suke ga mazajen da Allah ya baiwa su; Ga kyau ga kuma kyan hali. Ga addini da nasaba mai tsafta. A hakan dai suke zaune shi da Jaru; yau fari gobe tsumma, sabida ya yi alkawarin ba zai taba sakin mace a rayuwar sa ba, sai dai ta bizne shi ko ya bizne ta. Babbar damuwar sa da Jaru shine ta ki jinin Omar Faruq, ba dama ya zo sassan su goye da ni zata kora mu da tsawa da bulala, daga sanda ta fahimci Omar dan sa ne na cikin sa ba na kanin sa ba tsanar da ta ke ma Omar ta karu, sabida kanin nasa (wanda ta fahimci a Jos yake zaune zuwa yake yi ya koma), kullum ya zo tsarabar sa ta Omar-Faruq ce baya ko ta kan tashi ‘yar da ya haifa a cikin sa sai Omar, Omar dai Omar dai ko’ina ka shiga sunan sa ne a bakin jama’ar gidan alamar ya gama mamaye zukatan su. Ita kuma Jaru sai wata jarabta ta same ta; nan duniya babu namjin da yake burge ta irin Mamman sabida gayun sa, bokon sa da tsaftar sa, ya fita daban da mutanen garin Mambila domin a lokacin yana aikin koyarwa a jami’ar Jos matsayin Lecturer, a lokaci guda kuma yana hada digirin sa na ukku a can jami’ar Jos din. Lokaci - lokaci ya ke zuwa Gembu kuma in ya zo din baya jimawa bai fi yayi sati ko kwana uku ba ya koma, kasancewar dukkansu a gidan gadon su suke zaune har zuwa lokacin illa kowa da sassan sa, sassan Ummati da jikokin ta daban wanda yake daga can karshen gidan, nasu ita da Gidado daban a tsakiya sai na Mamman din a farkon shiga gidan wanda kullum yake a rufe sai idan ya zo garin Omar yake budewa ya share masa ya shigar da kayan sa. A babban zauren gidan kuma dakin Baffan mu Adamu ne wanda a wannan shekarar Abba (Mamman) sunan da na mayar masa kenan tunda na soma baki, shi kuma Baffa Gidado in ce masa Malam, Abba ya samar ma Baffa Adamu tagomashin tallafin karatu daga (federal scholarship board) zuwa kasar Algers inda zai yi karatun degree akan Diplomasiyya. A wancan lokacin su Abban mu sune manyan ‘yan bokon da kasar Najeriya yankin arewa maso gabas ke ji da su da kuma alfahari da su, yana daga cikin pioneers (sahun farko) na malaman tsangayar tsimi da tanadi ko kuwa tattalin arzikin kasa (department of economics) lokacin da aka fara darasin a jami’ar Jos, suna da damarmaki masu yawa a kan scholarships, ya baiwa samarin Mambila da dama tallafin karatu da scholarship zuwa Algers kasancewar a zamanin ba duka ne suka yarda suka karbi ilmin bokon ba a sanda ya kutso Taraba ya isko Manbila sai daidaiku irin su Abba, don haka su suka fi kowa cin gajiyar shi a zamanin da ake ciki yanzu sanda kai ya fara wayewa samarin Mambila na ta rububin shiga karatun. A kan Mamman Jaru ta raina Gidado take kuma ganin ta yi rashin dace da auren sa, da ta san da kanin da bazata auri wan ba, har fata take ya mutu don ta samu damar auren kanin sa. Ita kam dama ba ‘yar asalin Mambila bane bakin haure ne daga yankin kasar Kamaru, tsautsayi ya kai shi ga auren ta kasancewar tsohon mijin ta mai rasuwa Malam Jibo aminin sa ne kuma bata taba haihuwa ba, a tunanin sa rashin haihuwa da bata samu ba da Jibo, tsahon shekaru goma sha biyar da suka yi tare da shi zai sanya ta so tilon dan sa Faruku, ta taya Ummati kula da su shi da kanwar sa. Ba da jimawa ba ya fahimci ba wanda ta tsana a duniya irin Omar din. Abinda ke ran ta a kan kanin sa Mamman ne bai taba sani ba kuma tunanin sa bai taba bashi ba. To ta ina ma zai taba tunanin matar sa kanin sa take so? Har zuwa wannan lokacin da ya amsa sunan Dr. na ilmi, Mamman Gembu, bai yarda yayi aure ba, fada da nasiha da tsoratarwa babu irin wanda Ummati bata yi masa ba amma ya ki. A karshe Jaru ta ga babu mafita gareta ta samun damar auren Mamman in har Gidado na raye, sai ta soma tunanin hanyar da zata bi ta kawar da Gidado. Duk abinda ta yi tunanin yi, sai ta ga cewa za’a iya gane ta, a karshe ta nemi guba mai tsinka hanji ta saka mishi a cikin fura. Ta zauna jiran dawowar sa. Tun tana gadin dawowar sa, ta saka furar da abincin a gaba tana ta kiyasin gobe I yanzu tana cikin Takaba, wata uku masu zuwa sai ta maye gurbin wan da kanin, ko da tsiya ko da arziki (ko da ta asiri ne), tana nan zaune tana wannan saka da warwarar har wani mugun kashi ya zo ya matse ta. Da fari ta yi kokarin danne shi musamman da yake lokacin dawowar Gidado ya yi amma bayan gidan nan ya ki yarda da hakan, neman fitowa kawai yake yi ko ta halin kaka. Sai ta ga cewa zata iya zuwa tayi kashin ta dawo ba tare da ya dawo ba ko wani ya shigo. Ta ajiye masa a inda ta saba ajiye abincin sa ta koma sashen ta ta shiga bayan gida kenan Gidado ya shigo tare da wani saurayi. A nan falon sa suka zauna suna hira ya dauki furar ya baiwa bakon yana fadin. “Jira ta ta fito Bashari, na san ta zaga ne, ga nan fura ka sha, bari in dibo Asshe cikin gida na ji kukan ta yayi yawa, yanzu haka Faruqu ke cin zalin ta”. Ya saka takalmin sa ya nufi cikin gida da sauri babbar rigar sa na neman tadiye, shi don in da abinda yafi tsana a duniya to kukan Asshe ne. Bakon da ya kira da Bashari kuma ya kafa fura a kai yana kwankwada don a yunwace yake ainun a matsayin sa na matafiyi, ko ludayin kan faifai din bai saka ba kada ya bata masa lokaci a yunwar da ya kwaso tun daga kasar Kamaru. Yana sauke kwaryar daga fuskar sa suna hada ido da Yayar sa Jaru. Jaru ta kwalla kara tana fadin “na shiga uku na lalace Bashari furar Gidado ka sha??? Furar da na sakawa guba ce fa!” Yayi daidai da dawowar Gidado tsakar gidan tare da Ummati, ya na dauke da Asshe a kafadun sa. Omar na biye da su. Suna jin abinda Jaru ke fadi cikin yanayi na rashin hayyaci cewa ya ci gubar data sawa Gidado don ya mutu ta auri Mamman, abin nata kamar kaikayi ne ya koma mata, kasancewar Gidado Malami ne ya dade yana yi wa kan sa da ‘ya’yan sa tsari iri iri da ba dai mutum ba sai dai Allah. Ko kafin su farga Basharin ya fara shure shure kumfa na fita daga bakin sa, sai kuma jikin ya saki bakidaya alamar babu sauran rai a jikin sa. Wannan bakin al’amari da ya faru a gidan Malam Gidado babu wanda bai ji labarin sa a garin Gembu ba, aka saka Jaru a waka, hukuma tayi mata hukuncin da ya dace, Baba Gidado yayi alkawarin ba zai saki mace ba amma Ummati ta saka shi a gaba ta ce sai ya saki Jaru a take in yaso ya yi kaffara, wannan ba matar zama bace. Wannan shi ya kawo karshen auren Jaru (Hadiza) da Gidado Dalhatu Gembu. ****** MALLAMGIDADO DALHATU GEMBU H akika ya firgita da al’amarin mata wanda ya kai shi ga cewa babu shi babu kara aure har abada, wai a kan kanin sa ta yi niyyar kashe shi, wannan wane irin rikitaccen zamani ne na son zuciya da rashin tsoron Allah Allah ya kawo mu? Da yake Shi fa’aalun lima yuridu ne sai Ya juya abin a kan dan uwan ta. Shi kan sa Dr. Mamman Gembu da ya zo gari ya samu labarin ya firgita iya firgita, Allah ya tuba ko mata sun kare a duniya ai ba zai auri matar yaya Gidado ba koda mutuwar yayi ta Allah da Annabi. Shi kam! A lokacin ya kara jin tsoron duniya dana kaidin mata. Ya kama Omar - Faruq da Asshe dake zaune bisa cinyoyin sa ya rungume a jikin sa yana nema musu tsarin Ubangiji daga mugun ji da mugun gani da sharrin mutum da aljan. Ya roki Allah ya raya musu su har su aurar da su da hannun su shi da Yayan sa, ya yi alkawari tun a lokaci in har yana raye to Asshe bata da miji sai dan uwanta Omar, Omar baya da mata sai kanwar sa Aisha. Kada su je bare su cutar da su da sunan aure. Wannan abinda ya faru din ya kara nesanta shi daga kan turbar son sake aure shima, dan sauran hope din da ya fara samu na yin aure bayan kammala digirin sa na uku ya bi ruwa. A lokacin ya cika shekaru talatin da biyar a duniya, sabida kyawun surar sa na ‘yan Gembu da kamewar sa Allah kadai ya san iyakar matan da ke haukar ya aure su a can jami’ar Jos, inda yake aikin koyarwa. Lamarin Jaru ya taba Malam Gidado sosai ya kasa barin ran sa, tun daga lokacin kuma sai ya fara shiga ittikafi, yana nemawa ‘ya’yan sa tsari daga sharrin mutane. Ya fara fama da ciwon suga kadan kadan da hawan jini wanda a karshe ya kwantar da shi. Mamman ya dauke shi ya tafi da shi Jos don ya ga kwararrun likitoci, sun sha jelen asibiti kafin a samu saukin abin. Ina da shekaru uku Yaya Omar yana da shekaru goma Allah ya yi wa Baffa na malam Gidado Gembu rasuwa a cikin sujjadar sallahr asubahi. ****** R asuwar dan uwan sa Gidado ta kassara shi har fiye da rasuwar matar sa uwar ‘yar sa, Asshe. Na ci sunan mahaifiya ta ne wato Aishatu, Baban mu ke kira na SIYAMA kasancewar an haife ni ne a cikin watan azumin Ramadhana, Ummati kuwa Azumi take kira na. Yayin da a bakin Yaya na Omar nake ‘Boddo’. (Boddo na nufin kyakkyawa da harshen mu na Mambilla). Kowa kenan da sunan da yake kirana da shi a gidan mu. Wani ba ya taba aron na wani. Dr. Mamman Gembu a lokacin ya bar jami’ar Jos ya koma aiki da ‘Economic Communiy of West African States (ECOWAS), sai suka maida shi aiki a babbar hedquatar ECOWAS ta kasar Najeriya da ke Birnin Tarayyah. Still Abba ya na nan a gwauron shi. A ruwayar Ummati ta ce wai “aljana ce ta aure shi shiyasa ya ki aure, kuma da zaman sa a haka ai gara mata da ya auri jinsin jinnun”. A Duk ranar da tasa Abba a gaba tana gaya masa hakan mun yi ta sheka dariya kenan ni da Ya Omar, har sai Abba ya yi kwafa ya fita ya bar mata gidan zai huta da sharrin Ummati. Shi kuwa Uncle Adam (Young Abba) sunan da na ke kiran sa da shi kenan tun ina karama sabida dasawar mu, ya dade da gama karatun da yake yi a Algers, tun kafin ya dawo ya samu aiki duk ta sanadin Abba da U.S Diplomatic Mission. Ya auri wata abokiyar karatun sa mai suna Nasara Alkali ‘yar asalin garin Katsina, tushen unguwar Alkali, wadda suka yi karatu tare amma ba'a fanni guda ba, ita Nasara aikin jarida ta nazarta. Da yake sarkin raha ne autan na Ummati idan Ummati ta saka shi a gaba tana masa ciwon bakin ya rasa inda zai yi aure duk kyawun matan Manbila amma ya tsallake su ya je ya auro bakar bahaushiya sai ya yi maza ya daga mata hannu ya ce. “Allah sittiri bukui Ummati ba zan auri ‘yan Mambila ba tunda matan duniya basu kare ba, kada su mutu su bar ni da goyon 'ya'ya in kasa sake aure, ko in sake aure su saka min guba a abinci. A duk sanda Ummati ta yi masa korafin ya ki auren gida abinda yake gaya mata kenan ya kashe bakin ta, ita kuma sai ta ce “a'ah Adamu, kayi maza ka tuba tam, to dai ba’a yi wa Allah wayo kuma mutum ba ya tsallake kaddarar sa!”. Sai kuma ta tuno Gidado, sai ka ga ta sa habar zani ta rufe fuska ta yi ta shara kuka a gaban mu tana fadin. “Ya Ubangiji na binne mahaifin su, na binne babban su da hannuna, (tana yi tana daga tafin hannun ta), na bizne matayen su bakidaya, ina rokon ka Ya Allah, sauran biyun nan ka bar min su su binne ni da hannayen su ya Allah in samu masu yi min addu’a (Allah wadu ta mi meta irugo ‘bikkoi’am seni be irami). Wato (Allah ka sa kada in kara binne ‘ya’ya na sai dai su su binne ni)”. A yanzu haka shi Young Abba ( Baffa Adamu) da matar sa Anti Nasara a jihar Lagos suke zaune inda Diplomatic office na kasar Amurka ke tafiyar da ayyukan su tare da shi. ****** HERE COMES “WASILAH” (MY LIFESTYLE INFLUENCER). M asu iya magana kan ce “Rai dai… ba ya rabuwa da rabo sai dai idan ya kare”. Ko su ce "komai lokaci ne" musamman aure lokaci gare shi kuma kamar habo ya ke idan lokacin da aka kaddara ma dan adam yin sa ya zo. Abin mamaki a wannan zuwan da Abba ya yi Mambila ya zo ne da zancen da ya bai wa kowa mamaki, wato ya samu matar da zai aura a can Abuja, diyar shugaban wajen aikin su. Ummati ta bantari goro ta tauna kafin ta kura masa ido da son gane yana ciki hayyacin sa? Ko kuwa wannan matar asiri ta yi masa? Don an ce abinda matan barikin suka fi kwarewa a kai kenan in sun ga mazan da suka yi musu. Bata ga komai a tare da shi ba sai wata irin nutsuwa, da murmushi mai kwantar da rai, wanda ya nuna bayan cikin hayyacin sa yana cikin tantagaryar soyayyah kuma. “Matan Gembu da na kabilar Mambila sun kare ne?” Cikin izgili da tauna goro Ummati ta tambaya. Cikin lallashi da kwantar da murya Abba ya amsa mata da cewa. “Basu kare ba Ummatin Mambila, kuma har abada bazasu kare ba, wannan din ce dai kawai hankali na ya kwanta da ita. Ba ita ta ce tana so na ba ni na gan ta da kaina a gidan mahaifin ta, na yaba da hankalin ta, tarbiyyar ta da gidan da ta fito, na roki mahaifin ta cikin alfarma da ya bani ya kuma amince sabida kaunar da yake yi mun, ya ce in zo in turo magabata na”. Ko ba komai bayanan da yayin abun a duba ne, don haka Ummati ta rasa abin cewa, can kuma ta ce. “Ka ba ni kwanaki uku in yi istikhara”. Jiran kwanaki ukun a garin Mambilan da suka zamarwa Abba tamkar jiran shekaru uku, don hakika yana son Wasila. Bayan kwana ukun kuwa Ummati ta ce da Abba ya je ya samu waliyyan su wato aminan mahaifin su marigayi Malam Dalhatu su je su nema masa auren. Bata ga komai a tare da yarinyar ba sai alkhairi mai tarin yawa tattare da ita. Ta tambaye shi ko ‘yan asalin ina ne? Ya ce “Katsinawan Dikko ne. Aiki ne kawai ya kai mahaifin ta Abuja kamar yadda ya kai kowannen mu”. Ummati ta yi murmushi tana ta karantar farin cikin da yake ciki duk da yana kokarin dannewa ta ce, “kai da dan uwan ka duk Katsinan kuka gudu? Ina nan zaune kan shimfida ta zaku zo neman karin ta bibbiyu a Mambila, don matan mu basu da maraba da Hurul eenin aljannah”. Abba ya yi dariya sosai ya ce, “to babu laifi Ummati, bari sai mun karasa Aljannahr gaske, sai na kara da su”. Kowa ya na ta murna Abba zai yi aure ban da ni, karewa ma, bakin ciki nake yi sosai, ni bana son matar duk da zata auri Abba gaskiya haka kawai ta raba mu da shi. Ranar da na yi kuskuren fadin wannan maganar Ya Omar sai da ya buge min baki da tafin hannun sa, Ummati kuwa ta ce “irin ki kam, kishi zakuyi, har dana balbal wanda bai dace ba. Allah ya shirya masu kishin iyayen su, matar sa ai uwar ki ce in da tunani, kada in kara jin wannan maganar a bakin ki Azumi, shima in ya ji baki so ko bai fasa ba zaki sanyaya masa gwuiwa. Ke daban a wajen sa, matarsa ma daban, da wannan zaman da yayi shekara goma sha biyar cikin gwaurantaka ba gara masa auren ba koma wacece zai aura ai ta rufa masa asiri ta kuma taimake shi”. Wannan Magana ko kadan bata sanya na ji ina farin ciki da auren Abba ba, damuwa sosai na dauka na sakawa raina a kai babu gaira babu dalili har da kin cin abinci wuni guda, har Ya Omar ya gane fushi nake yi da dukkan su, tunda babu wanda ya bi bayan ra’ayi na. Na zo wucewa cikin gida daga islamiyya na gan shi zaune akan dakalin kofar gidan mu yana karatun jarida, wucewa nayi ba tare dana yi masa magana ba don har zuwa lokaci ina jin haushin buge min bakin da ya yi a kan matar Abba da bata kai ga zuwa bama. Omar ya bi ni da kallo ta kasan idanun sa har na wuce ciki ya ce, “Boddo am, kawomin buta a cikin gida zan yi alwallahr sallah, magriba ta yi” na zumbura baki na yi cikin gida ina cewa a raina zaka ga buta, tunda kana bayan auren Abba, kai ma idan ta zo raba mu zata yi don na fahimci ta fi ni farin jini yanzu a wurin ku, don ba abinda suke yi duk gidan yanzu sai shirye-shiryen tarbar matar Abba, an yi renovating gidan mu sosai ya koma na zamani, sabida a nan gidan mu zata fara zama na tsayin sati hudu. Na ji Ummati na fadin saura kwana uku daurin aure. Ya Omar ya na can yana ta jiran buta, har aka kira sallah, dole ya shigo cikin gidan ya dauka da kan sa yana mamakin share shin da na yi, sanda ya shigo nima alwallah nake yi a gindin famfo ya ce. "Boddo kin kyauta, ni kika share ko?" Kasa-kasa yadda Ummati bazata jiyo ni ba na ce "amaryar Abba ta dauko maka, tunda har zaka iya bugun baki na a kan ta" dariya yayi ya ce "to ni meye gami na da amaryar Abba? Ban san ta ba bata sanni ba, rashin kunya kika yi na hukunta ki, shin ma wai ke meye matsalar ki da auren Abba ne? Kada dai kina nufin kishin Baban ki kike yi?” Zaro ido na yi ina kallon Ya Omar, amma can a karkashin kasan idanun tabbacin hakan ke bayyana kansa baro-baro, wato tawa mahaifiyar na ke tayawa kishi wadda ke karkashin kasa har ta zama turbaya, a fili kuma nace. “Ba haka bane, zan gaya maka dalili na Ya Omar bayan sallahr isha". Ana idar da sallahr isha kuwa Ya Omar ya shigo gidan kamar yadda ya saba, Ummati na lazumi har zuwa lokacin, ban taba ganin mutum mai yawan jan tazbaha irin Ummati ba, abincin daren sa na fara dakko masa, gudun kurna ne da miyar taushe Ummati ta yi mana, yana budewa ya yamutsa fuska ya ce "Ummati, kin san bana son wannan abun" ta harare shi ta cikin hasken kwan lantarki da ya haske fararen fuskokin mu bata ce masa komai ba don bata gama lazimin ta ba. Ya mike tsaye yana karkade jikin sa yana fadin "da in ci wannan kulakulan naki ya sa ni bacin ciki gara na yi birki a teburin mai shayi an soya min lafcecen kwai da zazzafan shayi da ya ji madara creamler" ai jin haka yawu na ya tsinke na mike ina cewa "sai dai mu je tare baza ka ci kai kadai ba" wata harara ya sakar min ya ce "tebirin mai shayin zaki je? Kiyi zaman ki zan kullo miki" na ce, “ni ba teburin mai shayi zan hau na zauna ba, raka ka kawai zan yi muna tafe muna hirar mu kan abinda ya dame ni, na gaya maka Ya Omar ina da damuwa". Da wannan Ya Omar ya yarda muka tafi tare, don ya sanni wajen kafiya ko ya kara turzawa ba hakura zan yi ba. Ummati ko kula mu bata yi ba. Sararin samaniya yayi haske da hasken farin wata, babu wadatar haske a layin, muna tafe gefen hanya ni da Ya Omar a cikin layin mu, na ke gaya masa damuwa ta a kan auren Abba ba kishi bane na ke yi, na san in kowa bai fahimce ni ba shi Omar zai fahimce ni, mun yi nisa na ce da shi cikin sanyin murya, “Ya Omar ka san yadda nake son Abba na, na kuma ji an ce matan birni irin wadannan da Abba ya dauko zai aura azabtar da 'ya'yan miji suke yi, su raba shi da mahaifiyar shi da 'yan uwan shi, su cinye halayen sa na kirki ya koma wani sabon mutum mai sababbin halaye marassa kyau. Yau da a ce a nan Mambila Abba ya samu mata zai yi aure ba zan damu ba, kuma hankali na ba zai tashi ba". Na karasa maganata cikin damuwa tsantsa. Ganin haka Omar ya dube ni ciki mamaki ya ce "what is your business with this? Kina nan Mambila hannun Ummati suna can Abujan su me zai hada ki da su? Wannan rashin adalci ne ki ce duka matan birni haka suke, kina ina ta kauyen ta nemi kashe Baba Gidado? Boddo ki bari ta zo ki ga irin kamun ludayin ta kafin ki yanke mata hukunci. Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya Boddo na. Na hore ki da rashin daurawa kan ki matsalar wasu, abu ne da ba zai amfane ki ba". Daidai lokacin da muka iso wajen Garba mai shayi, ya biya aka soya mana Kwan, ina can gefe harde da hannaye a kirji aka zuba mishi a leda muka kamo hanyar gida Ya Omar ya ce. "Boddo abin kunya ne ace kina mace amma ko kwai baki iya soyawa ba, bana son wannan goyon jaki da kaya a kan da Ummati ke miki, don ke mace ce, uwa kuma matar aure, kika yi aure a gidan mijin da ke son abinci, na rantse wahala zaki sha a hnnun sa don ba zai jure ba". Na tura baki na yi gaba na bar shi ina kunkunin cewa "Ya Omar wa ya gaya maka zan yi aure? Ai sai Mutumin Mafarki na ya zo. Kuma har yanzu bai zo ba tukunna. Ai wato ni miji na duk duniya babu irin sa a halayya da dabi'a he’s simply special (na musamman ne) halin sa ba irin na sauran maza bane, ni na gaya maka bazai taba damuwa ba wai don ban iya girki ba, ni yake so ba girki na ba, ni kadai na san shi… A mafarki na kawai nake ganin sa….!!! Shi ba fari ba shi ba baki ba, gashinan dai Bakin dan Najeriya mai tsayi da cikar zati, dogo haka siriri, mai cikar gargasa da wadatar saje a zagayen fuskar shi, kullum sai na yi mafarkin sa Ya Omar ya na murmushin sa mai ratsa ni, yana gaya min cewa yana nan tafe, nan bada jimawa ba, na duba na hanga anan garin bakidaya babu shi babu mai kamar sa....". Ledar kwai da biredin hannun Ya Omar ta subuce ta fadi kasa, a lokacin he was like (ko Boddo ta yi gamo ne?) Ya sunkuya nima na sunkuya at the same time don daukar ledar da ta fadi, sai kawai hannnu na ya sauka a kan nasa. Ba zan taba mantawa da wannan glimpse din ba da ya faru cikin hasken farin wata. Hasken farin watan ya haska min cikin kwayan idanun Umar, sai na ga sun koma reddish-brown ba ainahin kalar su ta zahiri ba, kunshe da wani bakon al’amari da ya fi kama da kishi da ban taba gani cikin idanun sa ba, sakar min ledar yayi na dauka muka cigaba da tafiya bai tanka komai a kan shirmen da na fada ba. Ni kuma da gaske nake har ga Allah kullum sai na yi mafarki mijin Boddo, exactly yadda na suffantawa Ya Omar shi. Tun bana rike kamannin sa har na zo na rike, a da can bana iya rike kamannin sa banda cewa baki ne dogo mai cikar gargasa a fuska kuma ba dan Mambillah ba. Kwatakwata Ummati bata saka ni girki, ko tace in zo in gani in tana yi wai bata so in sha wahala, jikin nawa bashi da auki, don haka ni dinnan ko dafa indomie ban iya ba a shekaru na goma sha biyar a duniya, aji uku na karamar sakandire. Ga kiwa, ga son jiki kamar ‘yar mussa, inda duk wadannn abubuwan guda biyu suka hadu a waje guda ga mace to fa za’a samu boyayyar kazanta a tare da ita, bana son aiki ko kankani don tun farko ba’a sabar min da shi ba. Gashin kaina bai yi kama da na ‘yammata tsararraki na ba wadanda kullun cikin gyaran shi da yin ado da shi suke yana reto akan fararen fuskokin su, ni nawa kullum cunkushe ya ke cikin bakin dankwali babu wanki babu taza babu retouching, ga kwarkwata wadda na tabbata rashin kula irin nawa ne ta sabbaba zaman ta a kai na. Ni da Ya Omar wata irin mu’amala ce mai kyau kuma mai tsafta a tsakanin mu, ta fi karfin ta Yaya da kanwa don in da akwai alaqar da take sama da ta Yaya da kanwa a karfi da muhimmanci to ni da Ya Omar ce. Bamu da sama da junan mu a komai. Kuma bama hada lamarin da ya shafi dayan mu da komai a muhimmanci. Ya sanni kamar yadda ya san tafin hannun sa. Na san shi kamar yadda na san farcen hannu na. Omar mutum ne mai martaba iyaye da sanin darajar su, mai wani irin kawaici da alkunya, ma’abocin maida kai a kan duk abinda ya sa gaba tun a lokacin kuruciyar sa. Mai fifita ra’ayin wani sama da nasa. A fannnin karatu kuwa na rantse na sake rantsewa; ban taba katari da hazikin mutum a karatun boko dana addini irin Omar Faruq Gidado Gembu ba. Dalili na na fadin haka shine; Ya rubuce Al’qurani da hannun sa ya kai sau bakwai ya kuma haddace shi. Abba kan ce ko Alhuda-huda ba zai so hada gasar karatu da Omar ba. Wadannan qualities din ne Abba ke hange har yake ikirari shan alwashin hada mu aure, a tunanin Abba babu namijin da ya dace da auren Siyamar sa sai Dan sa Omar, Omar din da ya raina da kan sa, yake kuma fatan aure tsakanin mu ya dawwamar da zumuncin sa da marigayin dan uwan sa a bayan ran sa, ya kara yawan zuri’ar Ummati a igiya guda su zamo tamkar tsintsiya guda. Har ila yau, yake kuma fatan Ubangiji ya cika masa wannan burin nasa da ran sa da lafiyar sa. Abba kan ce “ba’a shaidar dan yau, amma ni na shaidi Da na Omar, shikadai zai rike min Boddo da irin rikon da nake so ta samu a gidan aure”. Amma kuma ni Siyaman, ina girma ne tare da mafarkai na da burika na (fantasies) wadanda daga ni sai Allah muka san su. Wato tunda ni fara ce farin da babu surki to miji baki (black) zan aura wannan na cikin mafarki na, har na kan hango ‘ya’yan da zamu haifa masu duhun kala da kyakkyawar suffa, idan ni suka dauko ko baban su wato mijin mafarki na zasu zama ne tamkar ruwa biyu. Ba ruwa na da abinda Abba ke hange, ba ruwa na da mafarkan Abba sai nawa mafarkan, ba ruwana da burin Abba, duk da ya dade yana fada yana maimaitawa a gaban mu ni da Omar din. Iyakaci Omar ya sunkuyar da kai amma bai taba tankawa a kan hakan ba, ni kuwa a duk lokacin da ya fada na kan zumbura baki ne in ce. “Abba! A ina ka taba ganin Yaya da kanwa sun yi aure?” Abba sai ya ce “daga kan ku za’a fara!”. Kuma daga wannan amsar da ya ke bani, ba na daukan zancen da nisa. A haka muke girma hankali na kara shigar mu, amma mafarki na da buri na na auren bakin mutumin cikin mafarki na bai taba canzawa ba, ta kai ta kawo har ina imagining din sa a idanu na na zahiri, I can feel his eyes all over me, da lamarin yayi gaba sai na fara jin muryar sa all over my earsyana kiran sunana in a unique way. A cikin mafarkin na kan gan shi tarr, ganin ido na, in ji shi sarai jin kunne na, in kuma rike kamannin sa amma da zarar na farka sai a shafe komai daga kwakwalwa ta. A wannan shekarar Ya Omar ya kammala karatun sakandire, da sakamakon su ya fito Abba ya ce ya cike jami’ar Abuja a JAMB form din sa don burin Abba kullum shine ya bude ido ya gan shi tare da Omar. Duk da ya san ba karamin yaki zai yi da Ummati ba kafin ta yarda Ni ko Omar wani ya bar gaban ta. Amma dole ne Omar ya shiga jami’a. ****** A n daura auren Abba da Anti Wasila a wata ranar Lahadi. Abba ya yi furnishing bangarensa na nan gidan mu ya tashi a matsayin apartment na zamani, ba can kadai ba har bangaren Ummati ya gyare tas babu maraba da nasa bangaren, ya min daki na mai kyau ya zuba min duk abin bukata. Duk garin Gembu yanzu babu gida kamar namu har wani lakabi akewa gidan wai gidan gilashi, sakamakon duk ta inda ka bi a gidan mu gilashin tagogin da na kofofin ke daukar idanun ka. Anti Wasila ta tare a gidan da tarin dukiya wadda ta kara kawata sassan nata kwarai. Ta tabbata ‘yar Ogan su Abba domin kuwa ni dai ban taba ganin duniya irin ta dakin Anti Wasila ba, ko kuwa don bani da exposure? Amma da na tuna Abba ya ce diyar shugaban sa ce sai ban yi mamaki ba. Anti Wasila na yawan gayamin cewa wai kira ta da suffata ta matan manya ne, wannan ya na kumbura kaina ya kara min burin auren mijin mafarki na, domin kuwa babban mutum ne ba yaro ba. Maganar da Abba na ke yi ba tun yau ba wai zaman Ya Umar nake ban taba daukan ta da wani muhimmanci ba. Can nake hango miji na bakin dan Najeriya, dan sardidi da shi na burgewa, ban taba addu’ar Allah ya bani miji nagari ba, nidai kullum addu’a ta Allah ya bani mijin cikin mafarki na, ya sada fuskokin mu nan ba da jimawa ba, domin jiki na ya gama bani yana raye cikin duniya, amma ba a Mambilah ba; shi ba fari bane yafi zama a rukunin bakake, dogo siriri mai yawan gargasa a fuska, mai wani kasaitaccen aji na musamman. Ranar da Ummati ta ji na furta wannan addu’ar bayan na idar da sallah taji nace Allah ya bayyana min mijin mafarki na haka, sai ta yi tsam, ta nutsu, tana sauraro na har na gama. Cikin nutsuwa Ummati ta ce. “Azumi, me na ji kin ce? A kul! Na kara jin wannan bahaguwar addu’a a bakin ki. Yau nake jin lalacewa wace irin addu’ar banza ce wannan?” Na kuwa cunno mata baki ina kunkunin cewa “ina ruwan ki da addu’a ta? Daga ranar sai nake addu’a ta a zuci kada wani ya kara ji ya yi min fatan rashin karbuwar ta. Ko sati biyu Anty Wasila bata rufa ba a gidan mu kasancewar ta caring a kan lamarin kowa na gidan ta gano wacece real Siyama; irin rayuwar tabarar da nake yi a gaban Kaka ta ta babu shan rana babu hantara sannan babu aikin wahala, domin ko firar dankali ta bani in yi mata zan fara amma tana kaucewa zan aje mata abinta in zura in gudu sassan Ummati. Gashi bata zo da mai aiki ba ayyuka suna mata yawa don bata rabo da girke girke kai kace (food and nutrition) ta karanta. Amma sam ko wankin cokali bana taya ta, ta lura ba ita kadai ba ko Ummatin ma bana tayawa kuma Ummatin bata damuwa, sannan bana son karatu ko kadan bana assignment bana homework iyakaci a dake ni in ban yi ba to jikina kam zuwa yanzu ya saba da dukan malaman makaranta har bana jin zafin sa, ya fi min sauki a kan wahalar karatu. Yadda nake ta munanawa Anti Wasila zato sai na samu akasin haka a dan zaman da tayi tare damu, bilhaqqi take son Abba da duk wanda ya dangance shi. Kullum sai ta zo ta sharewa Ummati daki ta wanke mata hijabanta ta shanya da yake Ummatin bata barin ayyuka su tarar mata kullum cikin aiki take shiyasa babu ayyuka da yawa a dakin nata. Da ta shiga daki na kuwa sai da ta toshe hanci, panties dina masu menses a jiki tun na wancan watan na cukuikuiye su na saka a wardrobe kana budewa wani hamami zai buge ka, babu shara babu mopping a dakin kaca-kaca da shi, ko ‘yar aikin gida bazata bar dakin ta haka ba, undies dina kamar tsummokara dukundukun dasu sai ‘yan dukununun uniform dina na boko da islamiyya duk sun ji jiki kasancewar bana goge su, littattafaina na makaranta kuwa da ta buda sai da ta kusa kuka. Shin ko wannan shine maraici na UWA-MAHAIFIYA A TARE DA DIYA MACEN DA TA BALAGA? Take neman uwar da zata ja ta a jiki ta nuna mata komai na tsaftar jikin 'ya'ya mataat puberty stage? Wasila ta tambayi kan ta cikin tausayin Siyama. Amma kuma bata cewa Ummati komai ba kan abubuwan data gani don ta lura da wani abu; ba’a fadar laifi na a gaban Ummati. Saidai daga wannan ranar Wasila ta dauki aniyar canza rayuwar diyar mijin ta Siyama. Rannan da gangan ta saka ni girki wai kanta ciwo yake. Ta shige daki kamar mai ciwon gaske ni kuma kamar abin arziki na tafasa ruwa daganan kuma na rasa me zan yi? Don wallahi ko dafa kwai ya dahu daidai ban iya ba sai ka samu ruwa-ruwa a cikin sa wato bai dahu gabadaya ba. Sai na ce tunda ta shige daki bari kawai in gudu iyakaci gobe ta ki kula ni, to sai me in ta ki kula nin? Na zo ficewa ashe-ashe ta kulle sassan da mukulli ta kuma zare mukullin ta tafi da shi dakin ta. Na rasa inda zan sa kaina don takaici na koma kicin na hau safah da marwah, a karshe nace bari kawai in mata wake da shinkafa ta ci da mai da yaji tunda shi ba sai an yi miya ba. Na hada waken da shinkafar na zuba a tukunya na antaya ruwan zafi a kai. Suna tsotsewa na kashe na hau kwashewa a sabuwar warmer dana taka island din kicin din na daukoa cikin kwalin ta, ni da kaina daga ganin abincin a ido na san tsoro kawai na bashi wato bai dahu ba. To amma yafi ta zo ta ga ban yi komai ba ta dauke ni wata bi ta can, in yaso in bai mata ba sai ta kara dafawa da kanta. Anti Wasila ta shigo tana hamma wai ta tashi daga baccin data samu, ta ce “Siyama na ji dadin kan nawa yanzu dana yi bacci kadan na sha paracetamol, zubo mana abincin nan muci a kan leda bana jin hawa tebir din nan ga shi yunwa nake ji sosai”. Iyakacin takurawa Anti Wasila ta takura min yau na rasa dalili, buri na kawai ta bude kofa in fece wajen Kakata amma ta ki, na zubo abincin a faranti mai fadi sai cin magani nake yi tayi kamar bata ganni ba, don kuwa cewa ta yi “sako cokula biyu yau tare zamu ci”, na bi umarnin ta, bayan na antaya mai da maggi da uban yaji na kawo kan ledar data shimfida, ta hau juya abincin da cokali amma ta ki kaiwa bakin ta, tana jira ni in fara kai loma. In kaga fuska ta a lokacin yadda ta yankwane kamar zan fashe da kuka don na gane Anti Wasila kamun kazar kuku tayi min yau, na dade ina guduwa in ta saka ni wani abu da ya shafi aikin gida ko na abinci. Ni kuma ba zan iya ce mata ban iya ba, na san a shekaru na goma sha biyar ba karamin abin kunya hakan zai haifar ba ko kuma ma ta raina ni. Dana ga ba sarki sai Allah dole na kai abincin baki na, na kuwa runtse ido na ki hadiyewa. Tsahon mintuna biyar Anti na bin karatun Qur’ani a wayar ta tana jujjuya cokali a abinci, cikin ginshira tace. “Yau sai kin cinye abincin nan Siyama, don ki tabbatarwa kan ki irin sa zaki dinga baiwa mijin ki Umar nan da shekaru biyu ko uku”. Ido na fal hawaye na furzo na baki na nace “Anti ki yiwa Allah da Annabi ki kyale ni haka” ta yi dariya ta ce “zan kyale ki ki fita in kin cinye, ko babu dadi ne?” Na fara hawaye na ce “wallahi Anti bai dahu ba, zai bata min ciki, ko taunuwa ba ya yi” “shi mijin ki da zaki dinga baiwa wannan ba zai bata masa ciki ba?” “Anti ai banda mijin tukunna ki bari sai nayi auren sai ki koya min” Anti ta ce “don tuwon gobe ake wanke tukunya ba sai an zo amfani da ita ba, zan kyale ki only in kin nuna min hammatar ki da cikin wandon ki don ban yarda bama kina yin shaving dasu wanke baki. Look at your teeth (kalli hakoran ki) yadda suka koma yellow kamar kin shekara baki basu maikilin ba”. Jin abinda tace wai in nuna mata hammata ta da cikin wando na na soma tababar ko matar nan bata da hankali ne? Ko kuma shaye shaye take yi? Ban furta ba amma kwayar idanuna sun gaya mata abinda nake tunani a kanta. Ko a jikin ta sai ma dora kafa daya da tayi kan daya, tana jiran in cika umarnin ta ko in kwana nan a dakin ta. Jin Anty Wasila ta yi rantsuwa sai na nuna mata hammata ta zata bude min kofa, na dinga kuka ina kankame jiki na. “Ummati ki zo ki cece ni, na shiga uku, kina ina ne za’a tube ni yau, Ummati!?” Anti na gintse dariyarta ta ce “tara kika shiga ba uku ba, sama tsami tsaka tsami matar Umar” sai na bar kiran Ummati don na tabbatar ta yi nisa bazata ji ni ba, na hau kiran Ya Umar shima, ta ce “ai gara ya zo don ya ganewa idon sa irin kazamar matar da Abban sa ke masa tanadi”. Ba shiri na yi shiru. Har da toshe bakin. Na hadiye gunjin kuka na don nima ba zan so ko kusa Ya Umar ya ga kasan hammata ta ba. Haka Anti ta tasa ni a gaba muka shiga toilet dinta ta aske ni tas da (shaving cream) mai santsi, ta ce kuma kaina ma askewa zata yi kwalkwal zata min idan har ban yarda ta wanke min shi da kanta da sheltox da kalkashi ba. Yau ni Siyama na ga ta kaina, har tara na shiga a wurin Anti Wasila hatta baki na sai da ta wanke min shi tas da maclean dinta mai karfi na Longrich sannan ta kyale ni. Na kuwa fice da gudu sai dakin Ummati ina nishi kamar wadda tayi gudun famfalaki. ****** N a bararraje na gwaggwafe kafafu a kasa ina baiwa Ummati labarin yadda na shiga uku hannun Antin Abba yau, na ce “wato Ummati Anti Wasilan nan ba karamar muguwa bace ta bugawa a jarida, kina ganin ta wata sumui-sumui muguntar da ke kunshe cikin bakin ta ta fi bakin ta girma. Ummati baki na yau har jini ya yi, sabida dirzar muguntar da ya sha a hannun ta…”. Sai na ji gyaran muryar ta tana tahowa ta ce “UMH! Sai kuma ta daga labule ta shigo kamar dama tana labe a kofar dakin, ta ce. “Ummati ke da kawar ki Siyama hira ake haka? To ga ‘meat balls’ kuna yi kuna taunawa, hira zata fi armashi”. Ta ajiye kyakkyawar roba a rufe a gaban Ummati, na faki idon ta na jefa mata harara, Ummati ta janyo akushin gaban ta ta bude ta dauki kosan naman kaza guda ta luntsuma a baki, dadin sa ya ratsa har kwanyar ta, bata san lokacin da ta ce. “Ai wato zaman nan da kika ga ta yi kamar Rakuma a gabana, ba abinda ta ke yi sai kwashe miki albarka!” Na zaro ido na ce “Ummati ki ji tsoron Allah ce miki fa kawai na yi na yi mata girki”. Sai kuka irin na borin kunya. Kunyar duniya ta lullube ni. Shiyasa na nannade ta da kuka. Ba abinda ya fi a kama ka kana gulma kiri-kiri, gulmar ma ta wanda ya kama ka red-handed. Anti Wasila tayi wani lallausar murmushi ta ce “ai kafa ta kafar ta zuwa Abuja Ummati, kawancen namu nida ita yanzu ya fara”. Ban san lokacin da na saka kukan da karfi ba ba ina fadin “idan wasa kike yi ki bari, in kin ga na bar Mambila to gidan bakinhadaddenmijin mafarki na zani a wani garin daban, amma ba zani gidan ki ba. Ba wanda zai raba ni da Ummati ita bata takura mun”. Anti ta wani dube ni shekeke! Tace “da wannan annakiyar kazantar taki da gashi fal hammata hadadden mijin zai zo? Lallai fa hadadden miji a mafarki! Ai sai a mafarkin kam! Allah tsinewa uwar mai karya, hatta Umar aka bashi ke a haka an takaice shi, kuma sai na gaya masa ya sayi shavingcream ya ajiye duk sati ya saka ki a toilet ya sullube ki da kan sa….”. Tashi na yi ina kumburi kamar kububuwa na bar mata dakin don na tsani Anty Wasila yanzu. Ummati na jin mu banda aika lomar ‘meat ball’ ba abinda take yi, na gama lura Anti ta gama saye Ummati da nau’in kayan dadin ta kala-kala kullum da abin dadin da zata sauya mata na makulashe ashe dama don ta raba mu ne don yanzu haka Ummati ta fi jin maganar Anti a kan tawa. Da daddare bayan sun gama cin abinci ita da Abba ta kwashe komai ta dawo ta same shi cikin kissa irin tata sai ta ce . “Baban Siyama amma dai da Siyama zamu koma Abuja ko? Tunda Umar ma komawa zai yi gara suna tare yadda suka taso nima kuma in ke jin motsin mutum a kusa da ni don wallahi bani da ra’ayin ‘yan aiki”. Abba kamar Anti ta shiga ran sa ta sosa masa inda ke masa kaikayi don ya gama yanke shawarar kai ni makaranta mai kyau don kamar bana koyon komai a makarantar mu ta nan Mambila, cikakken sentence wannan na turanci bazan iya hada maka daidai ba, kawai yana shayin rigimar Ummati ne. Anty bata fito fili ta gaya masa dalilin ta na son tafiya da ni ba amma shima Abba ya san wasu, musamman rashin kwaba ta da Ummati bata son yi, sannan Umar yana yawan kokan ta masa abubuwa da yawa da suke damun sa akan irin goyon Kaka da Ummati take min. Sai Abba ya ce “I thought as much. Amma Ummati bazata yarda ba”. Anti ta ce “ka bar komai a hannu na, I assure you zata yarda idan ni nayi mata magana. Tsakanina da Allah da kuma kaunar da nake maka Dr. nake son gyara rayuwar Siyama, hakika tana bukatar mentoring na uwa a wannan stage din na puberty da take ciki, ka saka a ranka tamkar Siyama na hannun mahaifiyar ta mai rasuwa a zaman da zamu yi tare ni da ita. Allah ya jikan ta da gafara”. Abba bai san sanda ya bude ma Wasila hannu ba ta yi azamar shigewa ciki ya rungume ta yana shi mata albarka. ***** “ Watakila dai matar nan har tsayuwar dare ta yi wa Ummati ta mallake ta!”. Haka na gayawa Ya Omar cikin kuka da ya tabbatar min Ummati ta amince gobe da Anti Wasila ta cika wata guda a Mambila zamu wuce Abuja tare bakidayan mu har da Abba da ita Antin. A kofar gida na dawo daga islamiyya ya tare ni yake gaya min wai maza in je in hada kaya na da sassafe zamu kama hanyar Abuja. Da kuka na wiwii na shiga gida domin kuwa a karo na biyu Ya Omar ya sake gwabje min baki wai na raina Anti Wasila da nace ta yi tsayuwar dare ta mallake Ummati. Kan Ummati na fada da kuka na “Ummati da gaske kin yarda a tafi da ni a raba mu? Ummati nice fa Azumin ki, Boodon ki, Asshenki, Siyamar ki”. Ummati tayi azamar ture ni daga kan kafafun ta tace “Allah yasa Sabira ce ba Siyama ba. In kin zauna wace tsiyar kike taimaka min da shi? Banda ki nade kafa a gado ki ci ki tashi hatta kwanon da kika ci abinci sai ni zan dauke miki, idan kuwa kashi kikayi sai dai in kora miki, hayya ratata Allah ya raka taki gona, Wasilar ce abin tausayi ba ke ba, sabida yadda zaki je ki maida mata daki matattarar kazantar ki. Faruqu kawai zan yi kewa”. Gefe na koma na saka kai cikin cinyoyi na na soma gunza kuka, na ki hada kayan na ki yin komai, maganganun Ummati sun bakanta min ba dan kadan ba, sai ga Antin ta yi sallama tana tambayar Ummati wai na kammala hada kayana? Abba ya na jera su a trunk din mota ne tun yanzu da daddare, don da assubah zamu kama hanya sabida sai mun kwana a hanya. Ummati ta ce “gata nan sai kuka take wai bazata bi ku ba” Anti ta karaso inda nake ta tsugunna cikin lallashi tana cewa “Oh ni Wasila bakin jinin nawa har ya kai haka gun Siyama?! To ki sha kurumin ki duk hutu da kaina zan kawo ki Mambila ki yi hutun ki tare da Ummati”. Na dago idanuna jajir, jagab dasu da hawaye na dube ta “kada ki kara tube min zani, babu kyau wani ya ga tsiraicin wani, in kin ce in yi ko menene zan yi, sannan don Allah kada ki kara saka ni girki” Anti tace “kece kika yi gardama in da kin yi salin alin ba zan yi miki da kai na ba, girki kuwa sunnar kowacce mace ne”. Na yi sharbe na ce “ai ba dole bane, tunda ni din bana so, kuma kada ki kai ni makaranta, bana so bana son karatu wallahi”. Anti ta yi dan jim! Kafin ta ce “ban yi wannan alkawarin ba, sabida ba ni ke iko da ke ba, alkawarin da zan yi shine ko iya sakandire kika yi zan roki Abba ya kyale ki ba lallai sai kin je jami’a ba, sai ku yi auren ku da Omar ki yi ta sullubowa Ummati kyawawan tattaba kunne”. Ummati mikewa tsaye ta yi don lallashin da Anti Wasila ke ta faman yimin ya fara bata haushi tace “da ke da mijin naki da tattaba kunnen naki da Antin naki duk ku tattara ku bar min daki kafin in miki tabon sallama da Mambila a kan farar fatar ki, ki koma birnin da dabbare-dabbare, kin san dai ban taba gwada kai hannu na jikin ki ba kada kisa mu yi sallama da shi yau (duka)”. Anti tace “yi hakuri Ummati, kukan sallama take miki, bari in hada mata kayan da kaina”. Anti ta shiga dakina tana hada min kaya amma ko nisa bata yi ba da ta ci karo da wanduna masu busashshen menses a jiki ta watsar ta fito tsigar jikin ta na tashi, tana ce da Ummati. “A tattara kayan Siyama duka a wanke a bada sadaqa Ummati” “to me zata saka in kuka tafi?” Ummati ta tambaya cikin mamaki, sai Anti tace “babu matsala zan diddinka mata wasu”. Shi kam Ya Omar sosai yake murnar komawar sa Abuja sabida jami’a da zai fara a can, nikadai nake bacin rai na da fama da kuncin zuciya. Da asubah muna idar da sallah muka kama hanyar barin Gembu, Gembun Mambila, Gembun da ta tattara duk wani dabdalar kuruciya ta. Zuwa birnin da ya bude sabon shafi na rayuwa a gareni, wanda mafarki na na shekara da shekaru ne yayi min sanadin sa. Da gaske Aunty Wasila has become my lifestyle influencer…. ta yi nasarar mai da ni MUTUM! Na farko ta raba ni da rayuwa mara ma’ana dana ke yi a baya. Amma da na san actualizing mafarkin dana ke faman yi shi ke jira na a birnin da ko kusa ban yarda na bi Wasila ba, gara na dauwama a dakin Ummati na, cikin kwarkwata da amosani da kirci, doyi da hamami na da gashin hammata ta. Hausawa suka ce wai zama lafiya ya fi zama dan sarki ta kowanne fanni. Abu daya nake tunani akan hanyar mu ta zuwa Abuja yake nutsar da bacin raina na rabo ni da Mambila da Wasila ta yi; watakila in hadu da shi…… Watakila silar haduwar mu kenan da mijin mafarki na, tunda na tabbata ba a Mambila yake ba, da a can yake, da tuni na ganshi a tsayin shekarun dana dauka ina mafarkin sa. Bai yi kama da Mambilawa ba ya fi kama da 'Black-Nigerians', don haka kila kaddara ta da shi ita ke sarrafa kanta a kaina. Na kuma tabbata kaddarar ce har ila yau ta sa Wasila fizgoni daga mahaifa ta zuwa birnin gamayyar ‘yan Najeriya. Domin na yi amanna da cewa Allah na nufin wani babban al’amari a tsakani na da shi wanda ba’a mafarki zai kare ba. Wanda kuma ban san farkon sa ban san karshen sa ba. Addu’a ta guda daya bazata taba canzawa a kan sa ba ta Allah ya bayyana min shi. Ya hada fuskokin mu ko da sau daya ne in gan shi a zahiri don cire kishirwar ganin sa da ke addabar idanu na dare da rana, in gaya masa tsahon shekarun dana dauka ina mafarkin sa…da mafarkin zamowar sa miji a gare ni. In kuma gaya masa cewa ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba. Hakika an halicci zuciyata sarqafe da tasa ta yadda na ke da assurance na cewa zukatan mu are undoubtedly connected, an yi min jarrabawa mai girma a kan sa tun kan in gan shi, tun kan in san shi, tun kan in mallaki hankalin kai na. ****** “TAFIYA MABUDIN ILMI” T un ina karama nake jin Ummati na yawan fadin wannan zancen na hausawa, "tafiya mabudin ilmi" ban taba yarda ba sai yau da na fito daga alkarya ta ta ainahi wadda ban taba barin ta ba tun haihuwa ta, na ke keta garuruwa da jihohin Arewa maso gabashin Najeriya cikin lafiyayyar motar Abba (4-Matic) baka wul. Sanyin A/C ya addabe ni sai da na roki Ya Umar da ke tukin motar akan ya rage, Abba ne zaune a gefen sa yana karatun Al’qur’ani ni da Anti muna kujerar baya. Anti na ramuwar barci ni kuwa idanuna tangaran ko son kiftawa bana yi kada a wuce wani garin ban tambayi Ya Umar sunan sa ba. Shikuma baya gajiya da gayamin har da karin bayanin karamar hukuma ce ko kuwa jiha. Da sunan gwamnan garin mai ci idan ya sani. Tafiya sosai ta kwana guda da yini guda kafin mu isa FCT Abuja. A hakan ma mun tsaya a Kano ne mun kwana a wani gidan saukar baki (Tahir Guest Palace) washegari da safe muka dauki hanya. Tunda aka haife ni ban taba fita daga garin Gembu ba sai wannan karon, hana rantsuwa na je Gashaka tare da Ummati wajen dangin mahaifiyata ba sau daya ba ba sau biyu ba dana yi wayo, don haka yau da na rinka ratsa jihohin arewa bude ido nayi kawai na yi ta shan kallo ina mamakin wasu gine ginen wadanda ban san da irin su a Najeriya ba. Da muka shigo Abuja kuwa manyan titunan ta masu fadi da gadojin sama da kasa su suka fi daukar hankali na domin cigaban dana tarar ya kai ya kawo. Sai yamma lis muka shiga wata kebantacciyar unguwa wai ita Jahi, inda anan gidan da Abba ya saya yake, gidan na mu ba wani babba bane kwatakwata (three bedrooms duplex) ne, dakuna uku kacal ke da gidan biyu a sama daya a kasa sai BQ inda anan Ya Umar zai zauna. Amma tsari da ilmin da aka zuba wajen tsara komai na gidan abin burgewa ne matuka. Ana kiran wadannan gidajen duplex, wadanda duk kusan iri daya ne cikin estate din, an kwaikwayo su ne daga gidajen kasar Sweden. Dakin kasa Anti ta bar min, inda a can babban falon gidan yake, da main kitchen, ita da Abba suna sama, Ya Umar na daga waje shikadai a BQ sai maigadi a nasa dakin can a jikin gate din shigowa. Kwana biyu kawai Anti ta bar ni na huta daga gajiyar mota daga ranar kuwa a gabanta nake wanka ina kuka ina komai ba ruwan ta, komai koya min take kamar ta samu katuwar jahila, tun daga alwallah har wankan tsarki, da wankan sabulu da yadda ake gyaran gashi, ta sayo min hand dryer ta koya min busar da gashi inna wanke, ta saya min shampoos ds conditioners samfurin Dr. Teal’s, komai na amfani na har man shafawa da bath foam dina samfurin (Dr. Teal’s) Anti ke zabar min, sati daya da zuwan mu ta kai ni H-MEDIX inda acan ta hada min set din su, daganan sai Grandsquare inda ta saya min undies farare sol sol da kayan barci kala biyar da dogayen riguna suma biyar biyar, Egyptian Jilbaabs kala-kala don zuwa islamiyya, maclean kuwa daga ni har ita dana Longrich muke amfani. Zuwa sati biyu na fara da rage kin shiga kitchen don kuwa Anti bata bari na in yi zaman banza irin wanda na saba a falon Ummati ina kallon talbijin, idan har zata shiga to dole ta biyo ta daki na ta sako ni a gaba, tare muke shiga safe, rana da yamma mu yi girki sau uku a rana. Aunty bata raga mini, ba ta sassauta min sai ta ga na yi komai daidai kamar yadda ta koya min shi a kicin. Haka da ta samu lokaci ta dauke ni muka je tayi min shopping kayayyaki na dinkawa kala kala atamfa, shadda, leshi da materials, ta bada a dinka min a gidan su bayan telan gidan su ya auna ni, sannan ta saya min kayan masarufi dana tsaftace jiki iri - iri, turaruka da deosprays masu dadin kamshi na Dolce&Gabbana, haka ta ke bata lokacin ta wajen nuna min yadda zan ke amfani da komai, yadda zan gyara fuskata, hatta shafa lipstick ita ta nuna min, kasancewar tana hutun aure bata zuwa aiki sai bayan wata daya. Amma duk da haka ni kullum cikin jin haushin Aunty Wasila nake. Gani nake ta takura rayuwa ta ta canza ta iyakar canzawa, ta matsa mini. "Me yasa ta damu da sai ta canza min tsarin rayuwa ta?" Idan ina yi ma Ya Umar wannan korafin sai ya girgiza kai ya ce “nan gaba kadan zaki gane babu mai son ki a duniya bayan iyayen ki sai Antin ki, Wasila”. Nace “au kai baka so na?” Yace “ni ba na cikin lissafin su, soyayyar miji daban ta iyaye daban. Aunty wasila da Abba iyayen ki ne”. Sai bayan ya fada yayi nadamar subutar bakin sa, yayi maza ya gyara da cewa “soyayyar Yaya daban take da ta kowa, kin ji? Ki daure ki daina korafi kan Antin ki, ki bata dukkan goyon baya da hadin kan ki. Bata nufin ki da komai sai tarin alkhairi. Ina tabbatar miki duk kudin da ta ke kashe miki ba Abba ne yake bata ba, hasali ma bai san tana yi ba. Don Abban namu Economist ne ba zai salwantar da kudi masu yawa har haka a kan ki wai don ki zama 'yar birni ba. Had you know how beautiful and radiant you have become now, da kin gode mata iyakar godewa. She is indeed your lifestyle influencer!” Murmushi nayi. Ban san takamaimai ma’anar kalmar da ya fada ta karshe a wancan lokacin ba, illa zuciya ta da ta fassara ta yadda ta ga dama, na san dai kawai Omar yana yabon kirkin Anti Wasila ne. Da hutun Anti ya kare ta koma aiki sai na samu saukin ayyukan gida, ni kadai nake wuni a gidan, kuma sai naji gidan ya yi min fadi babu dadi kamar da, kewar ta ta dame ni. Kasancewar har zuwa lokacin admission dina bai fito ba daga ‘Regent College’ inda Abba ya nema min. Ya Umar kuwa yanata zirga zirgar registration din sa tsakanin gida da Gwagwalada inda zai fara level 1 a tsangayar da Abban mu yayi nasa karatun wato tattalin arzikin kasa (economics). Don Abba so yake a komai Umar ya gaje shi tunda dai bai da dan da ya fi Umar din, amma shi a ra’ayin sa karatun likita ya so ya yi, likitan zuciya, amma tunda Abba yace ga abinda yake so ya karanta ya karba da hannu bibbiyu. Ko dama can shi mutum ne mai muhimmanta ra’ayin wanin sa a kan nasa, a haka kowa ya shaide shi. Kullum Anti ta fita aiki zaka same ni ne ina gyaran gidan mu ciki da bai din sa, bani kicin bani falo bani saman bene har sai naga ko’ina yayi kal-kal, tsaf-tsaf, yana daukar ido, sannan in dora mana abincin rana, zuwa yanzu kam ba laifi na iya girki daidai gwargwado na zamani amma banda na gargajiya wadanda Anti su tafi koya min. Direban ofis din su Abba na zuwa daukar masa abinci karfe biyu daidai na rana kasancewar Abba tunda ya auri Wasila bai iya cin abinci a waje. Ya Umar in ya tafi Gwagwalada tun safe sai yamma yake dawowa, motar haya yake hawa don Abba motar shi daya ce tal Anti ma haka, ina ji rannan yana masa alkawarin idan ya fito da (first class) mota sai wadda ya zaba zai saya masa. Amma a yanzu ya fi so ya koyi rayuwar gwagwarmaya irin ta kowanne dalibin public university a Najeriya. Ta hakan ne zai san muhimmancin wahalar neman ilmi. Ya iya tattalin abinda yake da shi. Sai a ka yi sa'a kusan duka halayen Abba irin na Umar ne, abin nufi anan Abba da Umar-Faruq ko kadan basu dauki rayuwar duniya da zafi ba, suna tafiyar da ita a saukake, a duk yadda ta riske su. Sun yarda jin dadi da daukaka basa zuwar ma mutum ta sauki a lokaci guda sai bayan ya sha gwagwarmaya a rayuwa. A tsayin watanni uku kacal na zama wata kasaitattar ‘yar hutu, budurwa ‘yar kwalisa mai aji da hankali na kwatance, mai nutsuwa mai kuma kyawun surar da yake samun gyara da attention din uwa, sannan da gani babu tambaya ka ga ‘yar gatan uwar riko da Abban ta. Rayuwa ta ta canza min baki daya positively, jiki na ma ya samu canji, ya nuna samun hutu da tsabta. Abu daya ne kawai har gobe bai canza a tare da ni ba wato (strong fulfulde accent) din Mambila bai bar baki na ya iya furta kalaman turanci dana hausa sosai ba. Ni kaina na san ina daga cikin ‘ya’ya masu sa’ar mahaifi a rayuwar su, wadanda basu taba neman wani abu daga mahaifi sun rasa ba. Wadanda maraicin uwa bai taba affecting walwalar su da jin dadin su ba, ko kuma don ban taba sanin ta bane? Farkon zuwa na sabida yadda Anti ke faman takuramin da aiyuka bana samun lokacin kaina balle har in samu lokacin tuna mijin mafarki na ko yin mafarkin sa. Kusan kullum sai na kira Ummati a wayar Anti mun sha hira, don ni Abba ya ce ba zai mallaka min waya ba sai na gama sakandire amma ya baiwa Faruq bayan dawowar mu nan, kullum na kira Ummati sai na bata labarin duk abinda nake ciki kamar kawata aminiya, rannan Anti bata nan ta bar wayar a hannu na nake ce da Ummati. “Oh! Ummati ban taba sanin haka tsafta yake da dadi ba, ashe da ba karamin cutar kaina na ke ba da nake zama cikin kazanta, ko'ina na tsami, yanzu fa Ummati da zan wuce ta gaban ki bazaki gane ni ba, gashi ke wayar ki Raka-ni-kashi ce (nokia) balle in yi hoto in turo miki ki ganni, ki ga yadda na koma, in kin ji irin kamshin dana ke yi kamar a kasar da ake sarrafa turare (Paris) din Faransa aka ahaife ni. Kai Allah dai ya yiwa Aunty Wasila albarka, ashe da can ni tantagaryar kazama ce ban sani ba Ummati? Ummati dai sai dariya take tana jin dadi a ranta. Na cigaba da fada mata. "Ashe Anti Wasila ba takura min take yi ba so na take yi da alkhairi kamar yadda Ya Umar ke yawan cewa? Ummati don Allah kullum kika yi sallah ki ke yi mata addu’a kin ji? Kice Allah ya bar ta da Abba na, Allah yasa ta haifa min kanne masu yawa”. Kafin Ummati ta samu zarafin amsa min na ji tafi raf-raf a kaina. Daga kan nan da zan yi sai nayi ido hudu da Anti da Abba a bakin kofar shigowa suna kallo na suna tafa hannayen su, da alama sun gama jin duk abinda na gama fadawa Ummati na. Kunya ta kama ni, nayi saurin rufe fuska da tafuka na. Nace. "Abba da Anti, Allah ya hana labe". Dariya suka yi su duka. Abba yace “mu bamu labe ba shigewa zamu yi muka ji ana ambatar mu. Sai in ce "Aamin to all your beautiful Du’as Siyama. Get ready for school tomorrow. Anti Waseelah zata sauke ki a Regent, kafin ta wuce nata aikin”. Na rasa murna zan yi yau ko bakin ciki, don dai na san a da can na ki jinin karatu kamar yadda na ki jinin mutuwa ta, amma wallahi yanzu ji nayi ina shawagi tsakanin farin ciki da doki, wadanda duka suka taru suka mamaye ni duka a lokaci guda. Na soma jerowa Anti tambayoyi. "Amma dai makarantar basa duka ko Anti?" Cikin rashin damuwa tace “in kin yi laifi me zai hana a duke ki?” Nace “ai ni matsala ta da makaranta Anti guda daya ce kin sani. Assignment/Homework da classwork, idan babu su to komai zai tafi lafiya kalau. Idan kuma kin yarda kullum na dawo gida zaki dinga yi mini da kan ki shike nan”. Anti ta dubi Abba tana fadin "saidai Abba yayi miki ya fi ni iyawa". Abba ya girgiza kai ya wuce sama yana fadin “Siyama har yanzu da sauran ki, bansan yaushe zaki girma ba”. Washegari Anti ce ta taimakamin na shirya tsaf cikin sabon uniform dina na daliban Regent, nayi matukar kyau kamar ba ni ba, na kawo mini hijab kalar uniform din na dora a kai, kai bazaka taba cewa nice wadda ta zo daga Mambilan nan firgai-firgai dani watanni ukku da suka wuce ba. Anti ta kai ni har makaranta ta karasa cike - ciken takardun da ya saura ba'ayi min ba, tukunna ta tafi ta bar ni cikin dalibai 'yan uwa na, wadanda duka 'ya'yan manyan ma'aikatan Abuja ne. Na lura daliban makarantar kabilu sun fi hausawa yawa, hausawan kuma wadanda sune (minority group) duk ‘yan girman kai ne, don babu wacce ta kula ni, basu san ni nafi son hakan ba, don dukkan su da lafiyayyen turanci suke magana, wanda ko come din su bana ganewa sabida yadda suke furtawa a gwanance, nikuwa ko sentence guda daya kwakkwara mai kyau bazan iya hada miki a wannan lokacin ba. A hakan kuma wai na gama juniorclass a garin Gembu, nan kuwa a aji biyu na sakandire aka barni wato an maida ni baya. Ana gab da tashi wata yarinya ta zo kaina ta tsaya tana min magana, da muryar ta mai sanyi, in zan girmeta to bazai fi da shekara daya ba. “Ke ya ba kya note?” Ta tambaye ni da Hausa, jin ta yi min husa sai naji dadi, na bata amsa da tawa hausar da ba fita take sosai ba, “shai gobe jan yi?” “Shaboda me? (Itama ta kwaikwayi baki na). Bata jira amsata ba ta cigaba da cewa "Idan Mr Kehinde yazo karbar Assignment gobe baki yi ba zai baki punishment”, “me ye kuma punishment?” Na tambaye ta, babu girman kai babu raini ta amsa min tace "horo, zai saki shara ko wankin toilet din sa, ba ruwan sa da ko ke 'yar waye a garin nan”. Ban san sanda nace “ai gara min punishment din da wannan uban rubutun, hannu na ciwo zai yi, baya na ma qagewa zai yi, na dade ban yi rubutu ba gaskiya” na bata dariya sosai ganin yadda nake magana da iyakar gaskiya ta, ta ce, “da alama ke 'yar auta ce” nace “ba wata auta fa, don kuwa Anti na tana da ciki yanzu haka. Kuma ta yi min alkawarin samun kanne duk shekara” na kara bata dariya tace “ya sunan ki don Allah? I like you” “sunana Aishatu Mamman Dalhatu Gembu” “ni kuma suna na “Azima Salim Ko’oje. Mu 'yan Sokoto ne. Kina iya kira na Ko'oje. Aisha can we be friends?” Ta fada tana miko min hannun ta, na mika mata nawa muka yi musabaha irin ta muslunci, ta samu wuri gefe na ta zauna tace. “Kawata dole ki cire kiwar rubutu da assignment if you really want to stay in Regent (idan da gaske kina so ki cigaba da zama a Regent) bazasu doke ki ba amma zasu sallame ki in kika ce haka zaki zauna ba kya rubutun class notes da yin assignment” cikin damuwa nace “to Azima kiyi min na yau don Allah, nayi miki alkawarin gobe zan fara da kai na, yanzu kam hutawa zan yi”. Tace to shikenan, kawo in miki”. Nan gefena ta zauna ta kwafar min aikin da aka yi duka tace in naje gida in tabbata na yi assignment din, wanda na darasin English ne akan darasin letterwriting (rubutun wasika)”. Tun daga ranar muka wani irin kulle ni da Ko’oje, tunda ta fahimci inada rauni take karfafani, idan na nemi sarewa ta ciccibe ni, tare da taimaka min kullum da rubutu har na fara sabawa da rubutun aji da kai na komin yawan sa da yin assignment. Idan na koma gida kuma Ya Umar shi yake zama malami na, duk abinda aka koya min a aji sai ya zauna ya tusa min shi da koyarwa mai nagarta ta juriya da repetition wato ayi ta maimaita karatu kamar ana koyar da karamin yaro mai lalurar LearningDisability, ba zai gaji ba har sai na gane. Ya bani aikin gwaji na yi a gaban sa. Idan ya ga na yi daidai sai ya tafa min sosai har wani lokacin ya bani kit-kat as a gift, shiyasa abin ya shiga raina farat daya na daina tsanar karatun makaranta sam a dalilin Yaya Faruq da Ko'oje. Ina cikin yaran da ke bukatar (special consideration) a yayin koyarwa don ban samu soundbackground wato tushen ilmin boko mai nagarta ba. Anan falon kasa muke zama a gefen su Abba kullum bayan salllahr isha'i, gefe daya zaka ga Anti bisa kujera da laptop din ta a cinya tana aikin office din ta. Anti ma'aikaciya ce karkashin Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development, Abba kuma yana sauraron labaran harshen Hausa a rediyon sa, ko ka same shi yana kallon labaran Aljazeera ko na CNN, amma ya fi karkata ga sauraron (VOA-Hausa) ban san meyasa ba, sai in ba su da labari wanda ya dauki hankalin sa ne yake murdo wata tashar daga cikin wadancan. Idan goma ta buga duk zamu tashi muyi sallama da juna kowa ya nufi makwancin sa. Wannan sabuwar rayuwar mai tsari da tarin abubuwan alfanu da abubuwan yi masu muhimmmanci ita ta kara kai ni FarAway daga mafarkan Dream Husband dina. Anti ta yi mana time - table ta kafe a kitchenkullum akwai abinda zamu dafa, bama taba maimaita abinci a sati sai satin ya zagayo. Aunty na son varities Abba na ganin tana masa almubazzaranci. Dole ta rage don Abba malamin tsimi da tanadi ne har gobe duk da ya bar jami'a. Sau biyu Ko’oje na zuwa gidan mu, har mun hada kawance tsakanin Maman ta da Anti, nice dai ban taba zuwa gidan su ba don Abba ba zai bar ni ba amma Anti ta san ta sosai yanzu, kuma ta yaba da ita har ma dai ranar da Maman ta ta kawo ta, su a Guzape suke zaune. Sabida Ko’oje yanzu bana shayin homework ko classwork duk wahalar sa, don sai ta tabbatar na gane na kuma gama nawa kafin ta yi nata, a gida kuma ga babban malami na can na bayan almuru yana jirana wato Professor Omar Faruq Gidado Gembu. Da ana bada ‘Professorial Chair’ daga matakin karatun dalibai a Jami'a tabbas da na dade da baiwa nawa mallamin; Mallam Omar Faruq Gidado Gembu, sabida koyarwar sa is in style da ko kai kafi kowa daqiqanci dole ka gane karatun da ya ke koya maka, ka kuma rungume shi da hannu bibbiyu sabida saukin koyarwar sa. ****** Y au Asabar a gidan iyayen Anti muka wuni, dake a unguwar Apo, Hajiyar su Anti mace karimiya mai son mutane, nan na tabbatar wa kaina Anti ba a kasa ta dauka ba, ita din 'yar na gada ce ba ‘yar na koya ba a karrama ‘yan adam kuma 'yar babban gida na tarbiyya da arziki sosai. Yau har Daddyn su Anti na gani, na kuma yi hira da shi inda ya tambaye ni abubuwa game da makaranta, don yana gida a yinin ranar bakidaya. Yadda kullum nake dada canzawa haka ma Omar ke girma yana dada murjewa, wani abin mamaki kwanannan na dade ban kara mafarkin 'Dream Husband' dina ba, sakamakon yadda na zama busy da karatu da ayyukan gida bani da lokacin kaina sam, balle in samu nutsuwar da zan yi mafarki ya zauna a cikin kai na. Koda muka samu hutu Abba yace ba zani Mambila ba sabida Tahfiz dana ke zuwa a nan kasan Estate dinmu kullum karfe hudu zuwa shidda, ba’a yi nasu hutun ba. Ya ce mu bari sai ya dauki annual leave (hutunkarshen shekara)Anti ma ta dauki nata in yasodukkan mu sai mu tattara mu tafi Gembun. Ummati dai kullum muna waya ko tuntube na yi a rana sai Ummati dake Mambila ta ji labarin sa. Shiyasa ban damu sosai da rashin zuwa na hutun ba kamar yadda aka riga aka yimin alkawari cewa duk hutun makaranta a Mambila zanyi. Nutsuwa ta shige ni sosai, ilmin addini dana zamani ya soma ratsa ni, ta ko’ina na zama cikakkar AISHATU-SIYAMA MAMMAN GEMBU na tashi daga (Boddon nan ta Mambila). Bani da abunda zan ce da Aunty Wasila sai Allah ya ja girman ta, ya kara hasken tauraruwar ta a zuciyar Dr. Mamman Dalhatu Gembu. Ya kuma sauke ta lafiya da abinda ke cikin ta, yasa ayi wa abinda zata haifa duk irin abinda ta yi min a bayan ran ta. Da ace duka matan uba irin Wasila ne tabbas da ‘ya’yan da wani dalili yasa suka rasa iyayen su bazasu taba koka maraicin uwa ba. She is really a MODEL! ***** H aka kwanaki suka yi ta shudewa a hankali suna mirginawa suna komawa watanni, har muka gangara wata na tara da komawa FCT, dukkan mu sai muka samu hutun kirsimeti Anti da Abba kuma suka dauki (Annual Leave) a lokaci daya don haka muka tattaro zuwa Mambila don yin hutun mu, dauke da tsarabar Ummati niki-niki iri-iri. Irin sukuwar dokin da na yi a jikin Ummati da shigar mu gidan sai da Abba ya daka min tsawa, "karasa min uwar zaki yi? Wannan wane irin rashin hankali ne? Ummatin kwari gareta har haka?" A can ne muka tarar dasu Young Abba (Adamu) da matarsa Anti Nasara suma sun zo hutun kirsimeti daga Lagos, familyn Ummati ya hadu ya batse waje daya abin sai masha Allah. A washegari aka yi (Get-together Party) na family, aka yi hotuna da vedio don tarihi aka yiwa mamatan mu Addua; Kakan mu Malam Dalhatu, Baba Gidado, iyayen mu Hassu da Asshe. Abba na yi wa Young Abba korafin bai taba zuwa gidan mu ba, in shi ba zai je ba ya dinga kai mana Nasara, Young Abba ya ce aikin shi sam bashi da lokacin tafiye tafiye amma ita Nasaran zai iya sako ta a jirgi ta zo insha Allahu idan sun koma sun samu dama. Young Abba dai dama rayuwar shi duka ta bakaken turawa ce, sai kuma ya zo ya samu aiki da US Diplomatic Mission tunanin sa ya kara sauyawa ya karkata kacokam kan rayuwar malam bature, bai wani damu da dangi ba, rayuwar sa ta 'yanci kawai yake yi da matar sa, yana dadewa bai zo gida ba. Kuma in ya zo ba ya jimawa. Hana rantsuwa ya san shi cikakken musulmi ne. Wato kowa ya bar gida gida ya bar shi kuma gaskiyar bature da ya ce “no place like home”. Mun ji dadin hutun mu a Mambila domin daga can mun je Gashaka ni da Ya Umar wajen dangin mahaifan mu na Uwa, Kakanmu Malam Muhammadu Jauro ya jima da rasuwa Amma akwai kanwar sa Goggo Halima da sauran dangin mu duk suna raye ba inda Goggo Halima bata sa a n kaimu ba, aka kuma rako mu da tsaraba rankatakaf ta fruits (Piya) kwan Zabbi da kwaryar Zuma, muka baro Gashaka cike da kaunar ‘yan uwa. Satin mu hudu cur a Mambila muka koma FCT don fara shirin komawa makaranta. ******* SHEKARU UKU A GABA A wannan lokacin ‘ya’yan Anti Wasila biyu; Maryam-Jamila yar shekara biyu da goyon Shukra-Nadiya 'yar watanni shidda. Anti haifar 'ya'yan kawai take amma ni ce komai din su, ma'ana ni nake musu komai amma dole dagabaya ta dauki Nanny sabida bana wuni a gida kullum ina makaranta har a Asabar da Lahadi muna yin Tahfiz. Ita kuma ga zuwa aikin ta.Ni da kaina “Azumi-Siyama” idan na dubi kaina a mudubi a wannan shekarar dana ke cika shekaru goma sha tara da haihuwa, ajin karshe na sakandire, bana saurin yarda cewa nice. Sabida girman da na kara da samun cigaban rayuwa ta kowannne fanni. Nafi yarda in aka ce wata bakuwar balarabiya ce daga UAE ba Boddo-Siyaman Ummati ba. Wannan Budurwa ce mai aji daidai nata, ba wannan kazamar Boddon ba. Kuma rainon ‘Regent College’. Ga nonuwa sun cika tantsan a kirjina har rinjaya ta suke yi. Wayewa ta, girman jiki na da exposure dina sun fi kama da na matakin 'yan Jami'a bana ‘secondary school level’ ba. A wannan shekarar da muke ciki zamu zana WAEC nan da watanni uku masu zuwa, kuma a cikin wannan shekarar ne abinda nake tunanin ya tafi har abada ya dawo min sabo; na koma mafarkan DREAM MAN dina. "Dream Man, ina murna ka tafi ka bani sarari ina karatu na yadda ya kamata don ginawa kaina future, sai gashi rana daya ka dawo, me yasa?" Na yi tambayar tamkar yana ji na, kodayake na tabbata yadda nake jin sa a ruhi da zuciyata shima yana jin hakan. Kamar dama yayi dan balaguro ne jira yake in gama da muhimman abubuwan da ke gabana, in mallaki hankali na sannan ya dawo ya cigaba da yi min babakere a zuciya. Burin Abba na shine in kammala sakandire lafiya, ya cika dadadden burin sa akan mu ni da Ya Umar. Hatta gidan da zamu zauna yasa Archititects sun zana masa an saka harsashin ginin a sabuwar unguwar Katampe. Tunda Abba ya fahimci bana so ana alakanta maganar aure tsakani na da Ya Umar ya shiga wani irin rudani, tsoron sa Allah tsoron sa abinda zai tada wannan alkawarin nasa, wanda yake son tabbatar da shi koda shine abu na karshe da zai aiwatar kafin Allah ya dau ran sa, don haka Abba ya dage wajen kyautata mini a dan tsukin nan da na ke gab da kammala makaranta, don samun damar cika kudurin sa a lokaci mafi dacewa, yana ja na a jiki sosai yana tambaya ta abubuwan da nake so ya saka min a gidan mu da yake gina mana. Yace hatta penti sai kalar dana zaba za'ayi. Rannan da abin ya ishe ni don na fara yarda Abba dai da gaske yake Ya Umar zai aura mini nan ba da jimawa ba, domin ya kawo taswirar zanen gidan da yake gina mana yana nuna min komai yana bayanin kowanne lungu da kowannne sako na gidan, ya ja layi a kan wani daki ya ce yana murmushi. "Ga nan dakin Grand-children dina, ba abinda baza’a saka a ciki ba tun daga kan feeder har keken koyon zama". Hankali na ya fara tashi kan maganganun Abba, don babu wasa yau a fuskar sa sabanin sauran lokuta da yake fadi cikin raha, idan ya ga na bata rai ya bar zancen, na yau din sounds extremely serious. Na sunkuyar da idanuna kasa daga barin kallon cikin idanun Abba na wadanda ke cike taf da kauna ta da fargaba as well; wato tsoro da fargabar kada na ce masa "a'ah", bazai yimin dole ba amma kuma ba zai iya tada alkawarin sa ba, nace, “shin Abba da gaske kake wai? Ni fa duk maganar auren Ya Omar da kake yi min tun ina karama na dauka wasa kake yi. Abba ba zan iya auren Yayan da na tashi a hannun sa kamar shi ya haife ni ba. Wallahi Abba ba zan iya ba (because i respect him). Kayi hakuri don Allah Abba inada wanda nake so tun ban san so ba!”. Daga Abba har Anti Wasila, zaro ido suka yi cikin kidima suna kallo na, Abba harda waiwayawa yana addu’ar Allah ya sa Omar baya falon, yayi ajiyar zuciya da ya tabbatar Omar bai ji ni ba. A wannan karon Abba ya nuna ni da dan yatsa idanun sa sun kada sun yi jajir ya ce. “Boddo kike ko Azumi ko Siyama ki kiyaye ni, mugun kiyayewa, wallahi bani da kyau, a fuska ne na ke da kyau, ban taba nuna miki other side dina ba sai na Uban da ke son ‘yar sa, sai dai ki sani wannan uban " ya fi son zumunci fiye da ‘ya’yan sa". Ni da dan uwa na Gidado bayan kasancewar mu ciki daya iyayen ku mata ma cikin su daya, ki gayamin akwai wanda zaki aura ya rike ki da daraja da ya kai Omar? Don haka ki duba wannan kusancin ya wuce duk yadda kike tunani, babu inda zan kai ki sai hannun Omar sai idan bana raye, zan tabbatar kuma kafin na mutu na barwa Ummati wasiyyar ko kin mutu a fara kai gawar ki gidan Omar kafin a zarce da ita makwancin gaskiya”. Daga haka ya tashi ya bar falon yana jin wani irin bakin ciki a ran sa, sakayyar da Siyama zata yi musu shi da Omar kenan? Lallai dan yau ba'a taba ci masa alwashi. ****** B a zan iya tantance how I reacted ga maganganun Abba na ba, bayan wucewar sa saman bene, abinda na sani kawai shine Abba da gaske yake yanzu kam, kan hada mu aure ni da Ya Umar, wanda ke garin Calabar a halin yanzu yana kammala hidimar kasa bayan kammala digirin sa da (first class result) kamar yadda Abba ke masa buri. Na tattara warning din Abba na jiye a gefe don ban dauke shi a matsayin abinda zai dame ni har ya hanani kwanciyar hankali ba, yadda nake da tabbacin Abba na so na kamar yadda yake son kan sa, na tabbata ba zai taba yi min auren dole ba. Idan na kafe akan ra’ayi na nan gaba inada yaqinin Abba zai janye nasa, musamman inna tsaya akan baka na na cewa ba son sa ne bana yi ba, girman sa da nake gani ne yasa bazan iya auren sa ba, ai Ya Omar bai yi kama da mazan da suka rasa matar aure ba, farin jinin sa kamar na Abba yake lokacin da yana jami’ar Jos, su ake cewa ana so ba su suke cewa suna son matan ba sabida kyawun surar da Allah yai mana. A gani na Ya Omar ya fi karfin ya auri matar da bata masa so na soyayya, wannan kwaruwa ce a gare shi ba kadan ba. I have ambitions, i have plans, na yin rayuwar soyayya da mijin aure na kamar ba abinda muka zo yi a duniyar sai bautar Allah da kuma SOYAYYAH! Kasancewar Allah ya halicce ni da zuciyar da bata son komai daga mijin auren ta sai soyayyah. Shakuwar mu da Omar tayi karfin da ba zan iya rayuwar aure da shi ba, meye bai sani ba nawa? Me zan yi ya burge shi? ‘There’s nothing special’ da zan yi in ja hankalin sa da sunan soyayya, haka shima. (A tunani na). Mutumin da ya gama goya ni a gadon bayan sa ya kuma gama yi min tsarkin kashi da fitsari! Na fara kirgan dangi da haila akan idanun sa. Ya sanni a sanda nake ‘yar sama tsami tsaka tsami na, wallahi ba zan yi kaffara ba in nace ban iya auren Ya Umar. Idan na yarda na aure shi zan kware shi kuma zan kwari kaina don ba zan iya hada shimfida da shi ba. A daren yau na yi mafarki da DREAM HUSBAND dina, irin mafarkin da ban taba yin irin sa ba tunda na fara mafarkai na a kansa; na gan mu ne a wata alkarya da tafi kama da korran ciyayin tsaunin Mambilla, cikin wata irin rayuwa ta soyayyahr da ke tsakanin mata da mijin ta kadai, wadda ma’aurata kadai ke tsintar kan su a cikin irin ta. Lamarin da ya tsorata ni ya firgita ni har ya saukar min da zazzabi-zazzabi. I can hear his voice clearly kuma yau na haddace ta kamar karatun sallah a cikin kai na. Koda na farka daga barci amon accent din sa wanda ban taba jin mai irin sa ba sakamakon tangardar harshe da yake da shi, kuma kamar harshen Hausa naji yana yi cikin 'yar sassarfa ta magana da yake fama da ita, amon muryar sa irin na Asians bai bar amsa-kuwwa a kunnuwa na ba, yana maimaita kiran suna na cikin shauki na soyayya wanda miji kadai zai iya yiwa matar sa magana cikin wannan yanayin da na gan mu cikin sa. Na kasa fita in taya Anty hada breakfast yau kamar yadda na saba a dalilin zazzabin da ya ci karfi na ya rafke ni a kan gado, na koma cikin duvet na cigaba da kwanciya ina kakkarwa. Na kuma tabbata a yanayin dana samu kaina wankan janaba ya kamani, janabar da na san ban aikata ba. Shin ko dai aljani ya aure ni ne wanda nake jin ana cewa haka suke auren bil adama? Sai gani yau ina kuka rurus ina neman agajin Ubangiji a kan wannan Jinnul Aashiq. Tsoro mai tsanani ya shige ni. Ina wankan ina jin kunyar hakan kamar na aikata zunubin da gaske. Maimakon in yi addu’ar Allah ya raba ni da shi sai na bige da addu’ar Allah ya bayyana min shi kawai muyi aure, ko aljanin ne INA SON SA HAKA! Da farko Anti ta kyale ni bata neme ni ba don itama a kule take da ni kan maganganun dana gayawa mahaifi na jiya wadanda ita kadai ta san cewa basu bar shi yayi barci ba. Yau din ta kasance Lahadi kuma ta kama rana ce ta hutun Ma'aikata (international worker's day) daga Abba har Anti duk suna gida, data ga shiru - shiru bata ji motsina ba har ta gama hada abin kari sai ta biyo bayana tana tambayar. "Lafiya dai ko Siyama?” Daga kwancen da nake dukunkune cikin Duvet na bata amsa. “Anti kai na ke ciwo da zazzabi” maimakon ta tausaya min kamar yadda na san ta da tausayi akan ciwo, sai ta kyabe baki ce “sabida an tuna miki maganar da tun haihuwar ki kin san da ita, tuna miki kawai aka yi ba sabuwa bace, shi ne kika sakawa kan naki damuwar data haifar miki da ciwo? To Allah ya sauwake, inda alkawari dai ruwa bazai dafa kifi ba!”. Tasa kai ta yi ficewar ta ta barni da tunanin ma’anar Karin maganar ta.. “In da halacci da amana ba za ki ki dan uwan ki Umar ba!" Ko "in da alkawari Abban ki bai cancanci wannan rashin biyayyar ba?” Dayan biyu, haka Anti take nufi ko me?. To ni na ce ina kin Ya Umar? Ai ina jin bayan wadda ta kawo ni duniya sai Abba sai shi a wadanda nake kauna, sai Ummati sannan kowa ma ya biyo baya. Ba zasu taba yarda da hujjoji na ba. Ko sun gane din ba zasu basu muhimmancin da ni na basu ba. Ba kowa ya san banbancin kauna ta 'yan uwantaka da kauna ta soyayyar aure ba. A sani na Namiji zai iya auren wadda baya so, ya zauna da ita for the satisfaction of his sexual desire kadai, mace kuwa ba zata iya auren wanda bata da sha'awa ta aure ko kankani a tare da shi ba, and that's exactly my point. Aure da Omar bazan iya ba gaskiya, ko duk duniya zata taru a kaina because i've no desire for him. A gareniSoyayya daban, kaunar ‘yan uwantaka daban. Omar can never be my choice of a husband, ban taba yaudarar Abba ba duk sanda yayi zancen nan ai gaskiya nake fada cewa Yaya na ne, bazan auri biologicalbrother na ba don babu banbanci kona haihuwa a tsakani na da Omar. Ban taba dai gaya masu ina da wanda zuciya ta ta afu gare shi ba sai jiya dana yi subutar baki. Sabida bani da tabbacin mutum ne ko aljan. Allah kadai ya san nufin Sa na sako shi cikin mafarkai na har na saba da shi har haka, na ke jin duk duniya bani da miji sai shi, wanda na tabbata ko bajima ko ba dade mafarkan nan zasu zama gaskiya... Mutumin nan baki, dogo siriri, mai tarin gargasa a fuska da giran ido, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana don junan mu aka halicce mu.... kuma yana gab da bayyana kan sa gare ni komai daren dadewa. ****** VOA - HAUSA S hirin su na safiyar yau Lahadi, wanda ya kasance (live-program) ne daga mita 0900 UTC (VOA-Muryar Amurka, Hausa). Shi Abba ya kunna a falon kasa ya kure sautin, yayi filo da hannayen sa bisa doguwar kujera yana sauraron labaran duniya daga bakin tauraruwar sa Grace Alheri Abdu. Tun bakwai na safe yake sauraren VOA har zuwa karfe tara lokacin da aka gama, kuma lokacin karya kumallon su yayi shi da iyalin sa. Grace Alheri Abdu na gama nata shirin, akayi taken VOA mai dadi, har Abba zai kashe rediyon sa shirin "HANTSI LEKA GIDAN KOWA" ya rufawa sallamar Grace baya, wato ya maye gurbin nata shirin. "Hantsi Leka Gidan Kowa" Sabon shiri ne daga gidan rediyon VOA wanda ya ta'allaqa kacokam ga zaqulo fitattun mutane na Afrika da suka shahara a fannin su wajen baiwa kasashen Afrika gudunmuwa a kafatanin fannonin rayuwar su ta bangarori daban-daban da suka hada da kiwon lafiya, tattalin arziki, ilmi, rubuce-rubuce (literature), tarihi, wasanni, siyasa ko zamantakewa. "A yau shirin mu na "hantsi leka gidan kowa" yana tafe ne tare da tsohon marubucin Najeriya Farfesa (Noble Laureate) Wole Soyinka, wato Shakespearn Najeriya, wanda muka fassara wa masu saurare zuwa harshen Hausa (live) daga gidan rediyon VOA-Amurka Hausa a safiyar yau Lahadi, Ashirin ga watan Aprilu, tare da ni …… HAMZAH....ALMUSTAPHA....MAWONMASE........!!! (Ya fadi sunan nasa dalla-dalla yana sama yana kasa da sautin sa kamar cikin rhyme). Tare da cewa; Ayi saurare lafiya......". Iyaka abinda ni Aisha-Siyama na ji kenan a safiyar yau, safiya mai dumbin tarihi, safiyar da ta juya ta kuma wulwula rayuwata bakidaya. Muryar ta fito ne kai tsaye daga radiyon Abba ina kokarin fitowa daga daki na don halartar tebirin karin kumallo. A karshe ya yi wa masu sauraren sa bankwana da cewa daga wannan lokacin, daga wannan hirar da zai yi da Soyinka, za’a jima ba’a ji shi ba don zai tafi karo kwas na wasu watanni kafin ya dawo. Nan take jiki na ya karbi wani irin quickreaction na extremeshock, kafin zuciya ta tayi tsalle ta fado kasa daga cikin kirji na ta karbi wani irin coolness duka a lokaci guda. Tamkar na narke a inda nake tsaye. Numfashi na yayi sama yana dambarwa a tsakanin kirji da hanci da kuma baki na. Tamkar mai fama da ciwon asthma sakamakon yadda shaqar numfashi ya koma cikin hunhu na ya gagare ni. Domin muryar da na gama ji ce a daren jiya a mafarki na nake jin ta yanzu a rediyon Abba, muryar mutumin da ya haifar min da zazzabi da wankan janaba na babu gaira babu dalili a safiyar yau. Ko ko ince; muryar da na girma na kuma rayu sama da shekaru bakwai ina jin ta cikin kunnuwa na, a cikin yanayin barci (mafarki) da yanayi na ido biyu (imagination) a wasu lokutan. Ta yaddda ta riga ta samu kyakkyawan matsuguni a kwanya ta; a koina na ji ta zan gane ta. Na sako kafa ta a falon kenan zan wuce diningroom don na san duk irin ciwon da nake fama da shi ban isa in ki fita cin abinci ba musamman da yake yau tare da Daddy ne a karshen mako, yana gida don haka tare muke cin three square meal, amma sai na dan dakata ina saurare, iya abinda na ji kenan a kan shirin amma na gama tantance muryar DREAM HUSBAND dina ce. Kawai kuma ba zato ba tsammani na Abba ya kashe rediyon sa domin Wasila ta zo ta tsaya a kan sa tana faman gaya masa "Breakfast is ready!". Su duka suka juya a tare jin Yiiipp! An fadi a bakin entrance na shigowa falon, Siyama ce dake shigowa ta zame ta fadi kasa, gabadaya suka yi kaina a guje suka daga ni suna faman kiran sunana amma ina! Sun nemi bakin 'eye balls' dake cikin idanun kowannne dan adam sun rasa a tare da nawa idon. Wasila na fadin Baban Siyama maza dauko mukullin mota" shi kuma yana fadin "ki nutsu, mu fara bata taimakon gaggawa tukunna, kawo min ruwa mai sanyi" kafin ya rufe bakin sa Anti ta fita da gudu neman ruwa Abba kuma ya hau karanta min addu'a yana tofawa, Maryam Jamila ta na gefe tana kuka tana cewa "Anty Siyama!" Abba na shafa min ruwan da mintuna biyu na yi ajiyar zuciya mai nauyi, kamin in lumshe idanuna bakin kwayar cikin su ya dawo. Hawaye ya gangaromin ta gefen ido, na soma sambatu ".... Abba na gaya maka dama yana raye, mutum ne ba aljani bane. Allah ne ke nufin mu da wani al'amari mai girma da ya shallake tunanin mu". Abba a kidime ya ce "Waye?" Na ce "Dream Husband dina, na rantse maka da Allah Abba yau na ji maganar shi a zahiri ba'a mafarki ba...... saura ganin sa ya rage min...." nayi - nayi in tuno sunan dana ji ya ambaci kan sa da shi kuma na kasa, tamkar anyi formatting memory dina mai alhakin tuna abubuwa, ko kuma don ban taba jin suna irin sa bane?. Abba sabida takaicin dana ba shi sai ya sakar wa anti Wasila ni yayi tafiyar sa dining ya zauna yayi jugum, sai kuma ya hada shayi amma ya kasa sha. Tsaki yayi can ya tashi ya dau mukullin mota ya bar gidan ya manta jallabiyya ce a jikin sa sai gajeren boxer daga kasan ta. Shi kansa bai san ina zai je ba". Anti Wasila ta ciccibe ni ta kai ni dakin ta, ta koma ta hado shayi mai kauri ta kawo min, a baki ta bani duk da zafin sa haka na bude baki na sha sosai don jiya ban ci abincin dare ba na kwanta. Saida Anti ta tabbatar na samu nutsuwa, barin da jiki na ke ta yi na yunwa da shock ya ragu, sai ta sanya tafukanta cikin nawa ta matsa a hankali. Tace "Yau dai sai an gaya min wanene wannan Lucky din da ke neman sheka min 'ya barzahu, ya hada ta da fushin mahaifin ta babu gaira babu dalili". Wani matsiyacin kuka ya zo min, na ce "Aunty Wasila kin san ba zan miki karya ba ko? Ba zan iya boye miki komai ba ko? To wallahi duk duniya shikadai nake so, Allah ya riga ya nuna min shi tun kafin ya bayyana min shi" cikin mamaki Anti tace "a ina ya nuna miki shi din?""A cikin mafarkai na Anti, rana dai dai ne bana kwana in tashi ban ganshi cikin barci na ba, har ta kai ta kawo zuwa yanzu na haddace kamannin sa da sautin muryar sa". Idanun Anty was like irin "Siyama ta yi gamo, aljani ya aure ta". Abinda na gani a cikin idanun Anti tsabaragen tsoro ne zallah. Ta ce "kwanta ki huta, in Abba ya dawo zan masa bayani abin ba na fushi bane Siyama kina bukatar taimako". Taimakon da ban gane wane iri take nufi ba. Da Abba ya dawo daga zagayen da yaje yayi a mota don neman nutsuwar yanke hukunci akan lamarin 'yar sa Siyama, sai da tayi kokari ya sha tea da chips kadan, sai ta karkace ta soma lallashi. "Baban Siyama fushi da Siyama ba naka bane, na fahimci gamo tayi". Abba ya dakata yana kallon matar sa Wasila da kankance ido da sakakken baki, ta ce "kwarai gamo ne, ina kyautata zaton namijin dare (jinnul aashiq) ya aure ta yana zuwa mata cikin mafarki, yau kuma ta ganshi maybe a cikin bangon falo ido da ido". Jikin Abba yayi sanyi ya ce "kin tabbata ba salon iskancin ta bane?" Anty ta yi rantsuwa akan abunda take zargi ta ce kuma idan aka samo malamai na gaske da suka iya rukiyyah zasu iya raba ni da shi, (a distant cousin of hers) ta yi fama da (similar problem) kuma da iyayen suka dage da neman magani an rabu lafiya yanzu har ta yi aure. Dole Abba ya yarda da Wasila amma wani bangare na zuciyar sa yana tababar yiwuwar hakan. A tsari da kafin da yasa aka yiwa gidan nan nashi kafin su tare wani shaidanin aljani bai isa ya shigo ba har ya samu matsugunni a jikin iyalin sa. Shima Gidado ne ya bashi wannan laqanin kafin rasuwar sa. Amma don kore shakku haka ya dauko malamai nagari masu fitar da jinnu daga jikin bil adama suka saka ni a gaba aka banka min turare sannan suka fara karatu. Baka jin komai sai tari na lokaci - lokaci sabida rashin dadin turaren nasu, amma har suka gama Suratul Baqarah ras nake, sai ma kafa danake canzawa position don karatun yana min dadi, na dade ban yi tilawar surah Baqarah ba sabida sakaci irin nawa. Ni na san bani da wani aljani amma na isa in yi jayayya? A je a hakan. Watarana da kan su zasu yarda da ni cewa, na san abinda basu sani ba. A karshe malaman suka gayawa Abba gaskiya babu shaidani a tare da ni, watakila dai na saka wani saurayi a raina ne shiyasa nake yawan mafarkin sa yake kuma yi min gizo a kunnuwa na. Abba ya kawo sadaqa ya sallame su. Bai ce komai ba ya bi matattakala zuwa saman bene Anti Wasila ta rufa masa baya. Tun kafin su karasa daki ya ce "kin ga abin da nake gaya miki ko. Salon iskanci ne kawai irin nata don ta gujewa auren dan uwanta, Omar bai ki Siyama sai ita ce zata ki shi har haka? Na rantse da Allah sai na aura mata Omar sai dai ta mutu da kiyayyar hakan..." Anti bata taba ganin fushin Abba a fili irin na yau ba. Tace "to tunda ta ce yana raye a duniya ka nemi ta kawo shi, in ta kasa sai kayi abinda ya dace" yace "babu wanda zan saurara akan Siyama, ni addini ya baiwa damar zaba mata miji kuma na zabar mata, ya rage nata tayi min biyayya ko ta bada min kasa a ido babu wani shirmen ta da zan kuma saurara". A daren ranar Anti ta sameni a daki dauke da indomie da dafaffen kwai guda biyu, ina kwance ne kawai ina fiskantar ceiling tunanin duniya ya addabe ni, kunnuwa na ba abinda suke son sake ji sai muryar sa da sunan sa, takamaimai bansan daga wane gidan radiyo bane don tsakiyar zancen na tsinta babu farkon sa. "Inaga zaki iya cin wannan tunda baida nauyi" ta fada tana zama a gefe na. "Bana jin yunwa Anti""nikuma bazamu yi magana ta fahimta ba sai kin ci abinci, tashi zaune a baki ma zan baki" ta debo abincin ta nufo bakina da shi, na kauda kai, sai ta hau yimin wakar da take yi wa Shukra-Nadiya idan ta ishe ta da rigima. "Hayya bina yaa Nadiaa, kam sa'atan laki na'imah!"(Tashi haka ‘ya ta Nadiya, awannin ki nawa kina barci?) Dariya ta bani sosai don wato nufin ta yau ni da Nadia yar watanni shidda bamu da maraba a wurin ta. Dole na karbi lomar abincin daga hannun ta, loma uku nayi nace don Allah ta kyale ni kada in yi amai. Da Anti ta fahimci na dan ware sai tace dani. "I want to see him!" Da alamar tambaya na dubeta ina juya hannu wato ina son sanin wa take son gani din? "I want to see our Dream Guy, in yi magana da shi ta gemu da gemu. Idan na gamsu dashi zanyi kokari in gamsar da Abba duk da na san ba karamin aiki bane mai sauki na daukowa kaina ba. Amma a matsayi na na 'yar uwa mace na san illar auren dole don haka zan taimaka miki, ki fada masa gobe ya zo ina son ganin sa a office dina" Sai na rasa abinda zan ce mata, anya idan na kara maimaita mata cewa nima ban san shi a zahiri ba, ban taba ganin sa ba, ban kuma san a ina yake ba zata manna min hauka ba? Tunda dai ta ce in kawo shi zata taimaka min to abinda zan yi yanzu shine in nemo shi, a duk inda yake, in kawo mata shi ta rarrasar min Abba ya karbe shi. Siyama kina da tabbacin shi yana son ki zai kuma iya auren ki? Haka ake soyayyar baka san mutum ba baka san halin sa ba baka san komai akan shi ba? Bai ce yana son ka ba sai ka je ka ce masa zo ka aure ni? Idan ma kin same shin kenan. Ko kuwa shi yace miki yadda kike mafarkin sa shima haka yake naki mafarkin? Lamarin is complicated amma ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare. I vowed to find him, a duka gidajen radiyon jiha dana tarayya. Kuma zan ke ta kasa kunne a duka gidajen radiyo da talbijin ma tunda na fahimci mijin mafarkin nawa Professional Radio Presenter ne. Ba zai min wuyar riska ba. Da Aunty ta ga nayi nisa a duniyar tunani sai ta mike tana fadin "sai ya zo. Ki fada masa daga karfe tara na safe zuwa sha biyu na rana zai iya gani na a HumanitarianAffairs". Daga haka ta fita, tana kara cewa "kinsan dai WAEC da NECO ne a gaban ki, ki ajiye komai ki fuskance su in kina son gina future din ki yadda ya kamata, idan zaki bari soyayya ta zama priority din ki a rayuwa kin kade har ganyen ki". Nisawa na yi bayan fitar Anty ina cewa ni kam ai har fadowa kasa warwas na riga na yi daga kan bishiyar karewar kadewar ganye indai a kan sa ne. A yadda nake jin karfin soyayyyar sa a raina zan iya bashi rayuwata, zan iya batawa da kowa in dai har zan tsira da shi. In na ce kowa ina nufin KOWA! ******* A unty ta fito daga matattakalar bene inda dakin barcin ta yake zuwa daki na rike da 'yan mukullan motar ta "Siyama na fita, zani Wuse Market kayan cefanen mu sun kare, da dai-dai kike da na nemi rakiyar ki, to duk kin bi kin susuta kan ki akan da namiji, kin susuta min Abban ki babu gaira babu sabar na kasa gane kan sa. Ga nan Nadia ki kula da ita kafin na dawo". Ta fada tana miko min ‘yar autar mu Nadia, babu kiwa ba komai yarinyar ta taho zuwa gare ni tana bangale baki, ta bani jakar jegonta mai dauke da abincin ta na frisco cream da kayan canjawa da su pampers din ta. "Sai kin dawo Anti, in kin ga radio please ki sayo min, latestone". "Radio kuma? Yaushe kika koyi sauraron radio naga dai da bata dame ki ba?" "Ina neman abinda zai ke debe min kewa ne ya hana ni tunanin auren dolen da ake son yi min". Aunty ta gyada kai kamar kadangaruwa ta sa kai ta fita tana mamaki. Ita bata ga aibun Omar ba, yaro saurayi matashi jazur da shi kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, ga tsafta ga addini, a irin shakuwa ta da shi bata taba zaton haka zata faru ba in aka fara maganar auren mu. Duk da na dade ina cewa ai Yaya na ne. Zata so kwarai ta ga wannan dream man din na Siyama, ta ga shin me ya taka har haka da ya narkar da zuciyar Boddo-Siyamah a murya da mafarki kadai? Ta san dai ba fin Omar kyau yayi ba yaro kamar Balaraben kasar Kuwait. Kuruciya ce kawai take damun Siyama ta ke neman kai ta ta baro, to wanda ya ki bin maganar mahaifin sa ai kuwa ya kai kan sa ya baro. Anti da ta tashi dawowa ta sawomin Radio mai quality kirar LG wadda babu inda bata kamowa gida da waje. Na yi mata godiya mai yawa sosai. Na ji kamar ma na hadu da shi na gama. Tamkar ta cikin radiyon nan zai bullo ya cimmani, ya wanke tsatsar kaunar sa da soyayyar sa da ke zuciyata. Tun daga ranar na yi mata saitin kamo tasoshin ko’ina, na dukufa sauraren tasoshin radio daban - daban na gida Najeriya, da ban kara jin muryar dana ke nema ba sai na karkata ga sauraren International Media masu magana da Harshen Hausa, nice kullum BBC ke har ma da VOA dana fi karfafa zaton a can naji shi, kuma ita ce major din Abba, da wuya ka ji yana sauraron wata tasha ba VOA ba, amma abun kamar delusion na samu a waccan ranar. Don kuwa ban kara jin waccan muryar ba ko mai kamar ta, ko sunan da ya ambaci kan sa da shi wanda na yi ta kokarin in tuna na kasa, sai a mafarki na kuma. Ni dai na tabbata na ji ta real a Radiyon Abba, saidai ban samu naji ko daga wace tasha bane, in na yi kamar in tambayeshi "Abba kwanaki wace tashar rediyo ka kunna ranar dana fadi dinnan ake maganar hantsi? Sai kuma in kwabi kaina da cewa zasu manna min hauka, zasu maida ni Psychiatry da zama, Abba likitan ilmi ne wadanda duk wani kankanin mental abnormality ba wuya zasu dangana shi da asibiti. Tunda an ce mai nema yana tare da samu, to zan ci gaba da nema da saurare har Allah yasa in kara jin sunan sa da muryar sa, ko da bazan gan shi a zahiri ba. An jarrabce ni da babbar jarrabawa mai girma a kan sa, wani iftila'i ne ya same ni wanda ban taba jin mai irin sa ba, na san ba zan fadi wannan jarrabawar a banza ba, yana can yana jira na ko ba dade ko bajima shima. To amma shin Siyama Abba (Dr. Mamman Gembu)", ya cancanci ya saka kara ki tsallaka a kan wani mutumin da baki da tabbacin a duniya yake? Ya cancanci butulcin da kike shirin yi masa na bada masa kasa a ido akan tsohon burin sa? Amsa ce mai nauyi da bana son baiwa kaina amsar ta. Shi kan sa Ya Faruq wani jigo ne a rayuwata da baya bukatar sai an tuna mini girman matsayin sa a gareni. Amma a fannin aure zuciyata bata zabi kasancewar sa abokin rayuwata ba. Sai kuma aka yi rashin sa'a ni mai sakarwa zuciya linzamin kanta ce. Idan a baya ina tababar wanzuwar sa da kasancewar sa dan Adam, to daga ranar da na ji muryar nan tasa a Radiyon Abba, ya fadi sunan sa da nasabar sa na tabbata Dream Husband dina is a Human Being... he’s somewhere far away from me, but he's in existence a tashi duniyar wadda nemo ta a yanzu shine babban kalubalen da ke a gabana. Wato nemo wanda zuciya da ruhi na suka afu a kan sa.... nemo shi ya zame min wajibi don shine kadai cikon farin ciki na, zan nemo shi a duk inda yake against all odds, sai na shiga rayuwar sa nima kamar yadda ya shigo tawa ya hana ta sukuni tun ban san so ba, sai na nemo shi da yardar Ubangijin da ya daura min son sa da kaunar sa.... Na rantse ba zai yiwu in sha wannan wahalar ni kadai ba, we must share the FEELINGS and all these emotions together… ina fatan har sai nasa ya fi nawa, insha Allahu. Ina da kyakkyawan hope (fata) da yaqinin (tabbacin) watarana Abba zai sauko har ya sa min albarka, idan ya dauki 'ya'yan mu a hannun sa, idan ya gan shi a zahiri zai karbe shi matsayin surukin sa. Zai yaba da zabi na. My dear Abba is not that harsh anymore (Abba na bashi da wannan tsananin), na fara zargin wannan ba Abba na bane wani ne dai mai tsananin kama da shi. Shi kam Ya Omar ina masa addu'a da fatan zai samu mata wadda ta fini son sa, wadda ta fi ni komai tun daga asali, nasaba, arziki da kyawun halitta. These are my wishes for him. Bai yi min komai ba sai alkhairi wanda yawun baki yayi kadan ya bayyana shi, zan saka masa alkhairin sa gare ni ta hanyoyi da dama musamman addu'a, amma ba ta hanyar aure ba, zai kasance cikin kowacce addu'ar sallahr farillah ta, har sai ranar da na daina numfashi. Domin hakika Ya Umar ya kaunace ni da kauna ta musamman wadda karfin ta da tasirin ta ya zarta ta ‘yan uwantakar da ke tsakanin mu. Wanda hakan ne yasa bazan iya rayuwar aure da shi ba. Ba zan aure shi in zo in kware shi ba, in na yi hakan ni kaina ba zan taba yafewa kaina ba. Ya Omar dina, bai cancanci irin wannan auren na rashin so ba. A cikin wannan yanayin na rashin nutsuwa na zana paper ta ta farko ta waec wadda ta kasance darasin Geography. An ce Juma'ar da zata yi kyau tun daga Laraba a ke gane ta, wannan jarrabawa da na ke zanawa kam tun daga Talata na gane sai wani ikon Allah zai sa in samu abin kirki. Tamkar an yi wiping duk wani ilmi da experience din dana ke tunanin na samu a Regent tsayin shekaru hudu an maye gurbin su da tunanin sa, babu komai a cikin kaina sai zallar tunanin (how would he look like a zahiri? Yadda yake a mafarki haka yake a fili? Ta yaya zan gane shi ranar da ya bayyana? Ko chimpanzee ne shi sabida muni haka nake son kaya na. A kullum da tunanin hanyar da zan bi wajen kaiwa gare shinake kwana nake tashi. Amma kullum bana samun wata idea in ba ta in dauko Radio in kunna ba in soma lalube daga wannan tasha zuwa waccan, sai ko in duniya zan shiga neman sa ba. Daga ranar dana bar gida kuma zuwa neman mutumin da ban taba gani a zahiri ba, kuma bani da tabbacin inda zan same shi (neman gaibu) nima kaina bana bukatar a kaini psychiatry zan mika kaina Dawanau ta jihar Kano dana ke jin labari, in basu damar kada su bar ni in fita ko'ina daga nan har illa masha Allahu. Zan tabbatar wa kaina hankali na ya gushe. ***** BAKON CALABAR M ota kirar Luxurious irin masu tasowa daga Kudu dinnan ta sauke Ya Omar a daya daga cikin tasoshin motar da suke tsayawa cikin Abuja wato tashar Jabi. Daga nan yayi Bolt zuwa gida. Ya fito sanye cikin kayan NYSC yayi kyau matuka don kudun ta karbe shi sosai, dauke da jakar kayan sa wadda bata cika girma ba. Mai Bolt din da ya sauke shi ko fita bai yi ba daga harabar gidan mu motar Abba ta shigo, suka yi ido hudu da dan sa Umar. Abba ya fito da azama ya rungume Umar suka karasa cikin gida yana yi masa barka da zuwa. Daga baya Anti ta fito daga kicin tare da su Maryam-Jamila da Nadia a hannun ta, itama bakin ta ya ki rufo da ganin bakon Calabar, yau watan sa shida rabon sa da gida sai da ya kammala gabadaya tun bayan sunan Nadiya ya tafi. Faruq Ya karbi Nadiya a hannun Anti yana fadin "yarinya kamar Boddo tana Baby". Anti tace ai Siyama da kai take kama, Nadiya ko da Abban ku take kama, don dai Siyamar ce a ranka shiyasa ka ga sun yi maka kama". Dariya yayi, wadda ta fiddo fararen jerarrun hakoransa kamar kankara dasu don haske, yace cikin jin nauyi. "Anti ni tana ina ne? Ban ji motsin ta ba" Anti ta ce " ka san sun fara WAEC tana can tana zanawa. Yanzu zaka gan ta". Bata rufe bakin ta ba nayi sallama a falon, rungume da takardu, sanye cikin uniform din Regent. Na rame sosai na kuma yi duhu. Ya Omar ya bi ni da kallo affectionately yana tambayar Anti dalilin wannan ramar tawa da duhun da ya ga na yi, ina ganin Abba ya harare ni cikin takaici. Anti ta ce cikin son kawar da zancen, "ka san jarrabawa take kuma kwana biyu dai bata ji dadi ba". Da haka ya bar zancen ba don ya gamsu ba sai don Abba na wurin, bay a son ya zurfafa nuna damuwar sa a kaina a kan idon Abba. A sanyaye na dube shi nace "ban san yau zaka dawo ba Ya Omar ban share dakin ka ba, amma bari in ajiye takardun nan in canza uniform ina zuwa yanzu zan gyara maka" da kulawa yace "na yafe Boddo, jikin ki babu kwari sam, zan share da kaina, da gajiyar jarrabawa zaki ji ko da gyaran daki?" A yadda yake min magana loving and romantic tamkar ba Ya Omar din ba yau,kamar ya maida ni cikin sa don so da kulawa, idanun sa na ta karakaina a kaina da duk wani motsi na, sai da yasa Abba da Anti jin kunya sosai suka soma kokarin barin wurin. Na wuce ban ce komai ba, don nima yau na ga sauyuka masu yawa a tare da Omar da suka sanyaya jiki na, shikuma Abba yace da shi da safe yana son ganin sa kafin ya fita ko'ina. Washegari ni da Anti muka shirya breakfast na musamman sabida dawowar Omar, yana gefen Abba ni ina gefen Anti da Maryam-Jamilah akan cinya ta ina bata dankali Anti kuma tana baiwa Nadiya abincin ta, Abba da Omar suka riga mu kammalawa sai Abba ya dauko mukullin mota 'Ranault' sabo dal ya ajiye ma Omar a tafin hannun sa. "Na cika alkawari kamar yadda ka cika alkawari ka fiddomin ‘first class degree’ Omar, Allah ya sanya albarka. Ka kammala hidimar kasa lafiya, gashi tuni na bada sunan ka a ECOWAS sabida na kusa yin retiring". Abba ya dakata yana duban mu dukkan mu, ganin duk mun nutsu muna sauraron sa sai ya samu karfin guiwar cigaba. Kafin ya ce da Umar. "Me ya saura maka yanzu? Ginin gidan ka na Katampe ya kammala, zaka bar gidan nan daga yau, don BQ ya maka kadan, ka koma gidan ka, ka riga ka zama babban mutum yanzu Umar, kafin ta karasa jarrabawar a daura muku aure ta tare. Na baku daga nan zuwa ta kammala jarrabawa ku fahimci juna ba irin waccan fahimtar ba, fahimta ta zama miji da mata. "Siyama!" Abba ya kira sunana da kakkausar murya kafin in dago in dube shi tuni na fara kakkarwa sabida ban zaci a gaban Ya Omar zai yi zancen nan ba, "har yanzu kina kan bakan ki na iskokai cewa wani kike so ba dan uwan ki ba, ko kuwa kin dawo cikin tunanin ki?" Ya ilahal alameen ka kawo min agaji, ko daren jiya na sake mafarki da shi ya kara yagalgala zuciyata da nau'ikan soyayyar sa. Bana ji bana kallon kowanne namiji da idanun soyayya sai shi. Kan Omar yana kasa bai iya yayi ko kwakkwaran motsi ba, Abba yace "na kashe wancan maganar taki ko bayan raina kada ki kara tada ita. Wannan shine mijin da addini yayi min umarni in zaba miki, shi na yarda ya zama uban 'ya'yan ki. Ina so daga yau in ga irin matsayi na a idanun ki Siyama, in ga kuma shin na isa da ke ko kuwa hoto nake a gare ki ba Uba ba?" Ya maida duban sa ga Omar yace "Faruqu I trust you beyond words, pls don't let me down. Su mata ka sani daga karkataccen kashin hakarkari aka halicce su kullum a karkace suke. Kwakwalwar su a baibai take. Sai ana yi ana mikar dasu, sai an yi hakuri ake cin gajiyar su, balle Siyama da har gobe yarinya ce shiyasa ma nake mata uzuri a wasu lokutan irin wanda nake so kaima ka koyi yi mata har komai ya daidaita a tsakanin ku. Allah yayi muku albarka zan fita, ina so yau ta zamo ranar da zaka fara zuwa zance gun kanwar ka officially". Abba yana gama fadin haka shi da Anti suka tashi suka hau sama. Ya zama daga ni sai Ya Omar don Maryam Jamila ma ta sauka daga jiki na ta bi bayan Anti, daga ni har shi kan mu na sunkuye don ji nayi kamar Abba ya dora min dutsen Uhudu a kai na, ya daddaure ni da kalaman sa. Umar kuwa tunanin sa daban ne da nawa wanda daga shi sai Ubangijin sa suka sani. Ba yau ya fara jin na ce ina son wani daban ba shi ba, karewa ma ya riga kowa ji tun ina fifteen years a Mambila ranar da muka je tebirin Garba mai shayi kuma tun a ranar yake jin ciwon abun a ran sa amma yau da Abba ya sake fade har yana rokon shi yayi hakuri da ni zamu daidaita a hankali kuma kaman by force zai aura masa ni sai ya ji kansa a mara sa'a, kuma mara abinda mace zata so. Dacin hakan da ya ji a ran sa ne ya sanya shi saurin dago kai ya dube ni da idanun da suka kada, ya ce "Boddo feel free with me, it's your Ya Omar, iknow you don't love me but please..... don't hate me because of him, I beg you. Ni na san I'm a loser, na sani amma ki kwantar da hankalin ki da yardar Allah in har ina raye ba zan bari Abba yayi miki auren dole ba". Ya karasa maganar cikin shakewar sauti, in ya tuna shi Boddo ta ke kiran auren sa na dole, kamar tana masa kallon matsala a rayuwar ta. Na wani irin dago cikin slow motion na dubi Ya Omar, jijiyoyin kan sa sun fito rada-rada abinki da farin mutum idanun sa sun kada, ban taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan yanayin ba. Sai na ji duk wani guilty conscience na duniya ya rufto a kaina ya danne ni, anya abinda nake shirin yiwa Abba da Omar a kan wani da ban sani ba, bani ma da tabbas a kan sa daidai ne? Anya ba zan yi SAKACIN da zan zo na kasa gyarawa ba?" "Ya Umar ban taba kin ka ba wallahi ka yarda da ni, ban taba alaqanta aure a tsakanin mu bane, ban taba baka matsayin ka mijin aure ba sabida na fi so kacigaba da zame min bango abin jingina, wanda in mijin ya bata min wajen ka zan zo. I only love you as a brother not as a husband, I'm sorry Ya Umar, i'm very sorry. I know it will hurt but you don't know how much it deeply hurts the culprit (na san abin da ciwo amma kada ka so tona yadda yafi zama ciwo ga wanda ta aikata), na sani Ya Omar ko da aure ko babu you will stand by me, ka taimaka min in nemo shi bani da idea. I may sound selfish but that is the bitter truth, my own fate, da iyakacin gaskiya ta nake magana. Babu gurbin kowa na soyayya a zuciya ta sai nasa. Ba lokaci daya na soma son sa ba, na so shi ne tun ban san son sa na ke ba. Dare da rana yana huntingdreams dina da duk wani sako na zuciya ta cikin shekaru bakwai, alhalin kuma ban san shi ba, ban san inda zan gan shi ba...... Yet i'm craving for him!". Na kifa kaina a kan teburin cin abincin na shiga rera kuka mai sauti. Jikin Umar har bari yake yi ya matso gabana ya dago ni, bansan ya aka yi ya aka yi ba, na samu kaina da fadawa jikin sa na rungume shi tsam-tsam, ina kuka ina kuma bashi hakuri. Omar suman zaune yayi don wannan ne karo na farko da hakan ta faru tsakanin sa da Boddo tun balagar su. Irin reaction din da jikin sa ya dauka ya tabbatar masa yana son Boddo, so na hakika pure and real, ba irin wanda ita take masa ba, yana kuma kaunar zamowar ta mata agare shi uwar 'ya'yan sa amma kash! Ga abinda ke fita daga bakin ta a kan wanin sa, Boddon da tun haihuwar ta ya ke son ta. Mun jima a haka kafin Ya Omar yayi ta maza ya raba ni da jikin sa, yasa hankicin sa yana share min fuska ya ce "Alright Boddo, na fahimta ki daina kuka ki kuma kwantar da hankalin ki bazan biyewa Abba in aure ki dole ba, zan sama mana solution wanda bazai yi fushi da ke ba. Amma lamarin naki is too complicated Boddo, ko ina son in taimaka miki din ban san ta ina zan fara ba, yau da ace kin san mutumin nan ne kuma kinsan inda yake, sannan kuma shima yana son ki it will be fine, but na kasa gane maganganun ki na baki san shi ba baki taba ganin shi ba sai a mafarki this is unblievable!. Ina so in taimaka miki amma ban san ta ina zan taimaka miki ba tunda bazan iya shiga cikin mafarkin ki in gan shi in yi magana da shi ba? I wish he's real (na yi fatan ace akwai shi a gaske) da sai inda karfi na ya kare wajen lallashin Abba.....". "Wallahi a raye ya ke Ya Omar, kuma mutum ne kamar kowa, ka bani lokaci zan nemo shi, in dai zaka cika alkawarin ka na rarrashin Abba, da kunnuwa na naji muryar sa a radio bayan na mafarki" "Radio?" Omar ya tambaya cikin kakabi na mamaki da tunanin Boddo soyayyar gaibu ta sa ta zare. "Kuma sai aka ce miki shine na cikin mafarkin ki? Wahayi aka yi miki ko me?" A wannan gejin na fara tunzura da tambayoyin da yake min masu son tabbatar da cikakken hankali na. Amma na san Omar yana nufin taimaka min da gaske, don haka na sassauta zuciyata na labarta masa abinda ya faru ranar, da Rukiyyar Aljanu da Anti tasa Abba yasa aka yi min". Duk halin da Ya Omar ke ciki saida yayi dariya yace "Boddo yanzu ta ina zamu fara neman Mr Radio?" Na harare shi don ganin shikuma hauka zai lankaya min, nace "in da gaske kake zaka taimake ni ne Ya Omar to mu fara zaga gidajen Radiyon Abuja, kuma ka tambayi Abba wace tasha yake saurare ranar da na fadi musu? Na rantse maka idan na ganshi daga ganin farko zan gane shi, da jin muryar sa zan shaida ta". Omar ya rufe fuska da tafukan sa yana murmushi mai ciwo, yace "a sa cewa mun same shi a gidajen rediyon da zamu je din, a sa cewa kin gane shi, sai mu ce masa me Boddo? Mr. Radio ka zo ka auri Boddo tana mafarkin ka tana son ka? Kin wuce nan Boddo, a matsayin ki na bafullatanar Mambillah. Ba kya tunanin hakan zubar da kimar ki ne ta diya mace mai darajar fulanin Mambilla, jikar Malam Dalhatu Gembu da Saudatu Ummatin Mambilla? Idan Ummati taji kin je nemowa kan ki miji a kan titin gidajen radiyo ba kya tunanin bafullatanar zuciyar ta zata iya bugawa da bakin cikin ki, don kuwa Ummati bata daukar abin kunya da zubda kima akan jinin ta. Idan zan baki shawara ki dauka kada ki taba attempting neman sa a ko'ina. Ki koyi hakuri a kan soyayya ki kuma koyi juriya. Don na fahimci your love for him is extremely hot. (Soyayya mai zafi kike masa). Kisa a ran ki idan mijin ki ne kina zaune Allah zai jefo miki shi daga duk inda yake, idan Allah ya nufa ba mijin ki bane Boddo soyayya bata kisa, why not ni ki aure ni give it a try, nawa son will be enoughfor all of us mu raba ni da ke, bana bukatar martanin soyayyah daga gare ki, ba kuma jikin ki nake so ba. I will only love you Boddo till eternity and actualize my love alone......!!!" Kuka na saka wiwi, na sa yatsuna hagu da dama na toshe kunnuwa na ina cewa "Ya Omar babu wannan maganar a tsakanin mu. Ba zan iya ba, ba zan iya yaudarar ka ba, in na aure ka na kware ka ba zan taba baka soyayyar da kake bukata daga gare ni ba". "Shine ni kuma nace miki bana bukatar taki soyayyar, tawa ta ishe ni. Ba zan aure ki don in huta da ke ba, zan aure ki don mu cigaba da rayuwar mu tare yadda Abban mu yake buri, har zuwa lokacin da tunanin ki a kaina zai sauya, ki sammini gurbi komai kankantar sa daga gurbin Mr Radio, i will be glad and grateful". Umar ya daina bani mamaki ya koma bani tu'ajjibi da tausayi, jin na kasa magana ya kara durkusawa a gabana, ya dora tafin hannun sa saman kafata ta dama yace, "kin amince ko Boddo?" Idanun sa na pleading, pink fatar bakin sa na motsawa a hankali kamar ba daga bakin sa maganar ke fita ba. "Zan yi kokari in sayawa kaina muhalli a zuciyar ki in muna tare, idan shi a mafarki yake nuna tasa soyayyar ni a zahiri zan nuna tawa. Shi matsoraci ne Boddo, raggo ne, tunda ya kasa bayyana kan sa, sai dai ya sadado ta cikin mafarki yana neman haukata ki. Boddo nine Omar dan Asshe da Hassu, Dan Gidado da Mamman jikan Ummati, shin wannan kakkarfar alaqa bata yi isar da zaki duba ki sadaukar da soyayyar bare a kan ta ba? Zan bar ki da wannan kiyi tunani a kai daga nan har zuwa ki gama jarrabawa, ba zan kara damun ki da wata magana da ta shafi wannan ba, don na fi so ki tara hankalin ki waje guda yanzu. Watanni uku sun ishe ki yanke mana hukunci, ni kuma duk abinda kika yanke insha Allah zan karba, zan kuma yi kokari Abba ma ya karba, zan yi amfani da karfin soyayyar da yake yi min wajen ganin kin samu duk abinda kike so". A wannan daren ko na minti goma ban iya na runtsa ba sai juyi a kan gado, ina tuna maganganun Ya Omar, hakika ina cikin rudani amma na kasa gane cewa mafita ta guda daya ce a daidai wannan gabar wato barwa Allah zabi. Na kasa tuna in tashi in gayawa Allah yayi min zabin alkhairi kada ya bar ni da dabarar kaina. Nafi karkata ga son Ubangiji yayi gaggawar bayyana min shi kawai, idan har ya bayyana komai zai zo da sauki don Umar ba ya magana biyu, tunda ya ce zai lallasar min Abba to kuwa zai yin. Ya Omar zai sa Abba ya aura min shi, Anti zata sa Abba yayi hakuri ya aura ma Ya Omar wata daban ko a cikin dangi, bana son tuno ko daya cikin kalaman Omar domin kuka suke saka ni, a daren ranar ma da kuka mai tsanani muka rabu, ban iya na bashi amsa ba. Washegari ban gan shi a gidan ba ban ji duriyar shi ba, haka na shirya na tafi makaranta duk jikina sukuku. Jarabawar ma ta yau na dai zana ta ne amma ni kaina nasan sunana loser. Har tsayin kwana uku ban kara ganin Umar ba, daga baya ne na ji Anti na waya da Anti Nasara wai ashe can ya tafi zai yi wata uku kafin ya dawo. Ko meye hikimar Umar na kauracewa gidan mu? Wata zuciyar ta ce don ya baki dama kiyi karatu. A fili nace Allah sarki Ya Omar, ko kana nan ko baka nan wannan jarabawar ta tashi a banza. Sunanta Fatima Tara (F9×9). Aka gama WAEC aka shiga NECO, a NECO ne kam Ko'oje ta ankarar da ni wai ina zana Radio akan answersheet dina na darasin lissafi. Da sauri na duba, kwarai Radio nake zanawa da sunayen gidajen Radio a Najeriya dana sani da manyan baki Bayan mun fita paper din Ko'oje ta kamo ni kamar ta fashe da kuka, "Aishatu Mamman Gembu me kika zamar da kan ki a kwanakin nan? Maths paper kike zanawa Radio? Meye gamin ki da Radio? Are you in your full senses? (Kina cikin cikakken hankalin ki)" Kai tsaye na sunkuyar da kai nace "I'm in LOVE Ko'oje, sincerely in love, unimportant love kuma!". Azima Salim Ko'oje ta kama hannaye na biyu ta rike gam cikin nata, ta ce "how did it become unimportant?""Sabida auren dole Abba na zai yi min da Ya Omar Azima, sun ki yarda mutum nake so dan Adamu da Hawwau, sun fi zaton na samu matsala ta aljanu ko ta kwakwalwa ne". "ni kuma na yarda da cewa kawata will never lose her sense because of a man, who is he? Who isthatLucky? Ki gayamin ko wanene? Shi din ya san kina son sa?" "Bai sani ba Ko'oje, nikadai nake kida na nake taka rawa ta karewa ma ban san a inda yake ba""to meye alaqar sa da Radio da kike zanawa a mathematics answersheet?""He's a Radio Presenter I guessed". Ko'oje ta ware manyan idanun ta akai na tana kallo na "kika ce baki san shi ba, yaya akai kika san hakan to?" "baiwar Allah ke lawyer ce ne?" Dariya ta yi tace "kwarai shi nake fatan zama,ke kuwa gaki nan a kan yardstick na ruining future din ki gabadaya". Bude idanu na yi na dube ta sosai, sai tace "ban taba jin wannan almarar ta ki ba, wallahi na dauka saurayin yana tare dake, ko a gida ne ba'a yarda da shi ba. Shiyasa na tsaya ina sauraron ki. Ashe ke you are just on delusions and illusions. Kafin ya zama worse zan gayawa Anti ta kai ki asibiti a dauki matakin gaggawa, sannan next year ki sake papers din ki". A fusace na tafi na bar ta tana kiran sunana amma ban ko juyo ba. Na yi tafiya mai dan nisa kafin in zauna akan wani kututturen icce in yi kuka na mai isata. Ko'oje is my last hope, amma kalla....itama yanzu tace delusion nake yi har ina ina hadawa da hallucinations. Ni na san kaina, kuma a dan ilmin da Allah ya bani na san lafiya ta kalau, kawai kalar tawa jarrabawar kenan, ko kuwa kaddarar rayuwata da ya barranta da na kowacce mace. Ni a mafarki da kuma imaginations nake tawa soyayyar. Our own love tragedy is unbelievable ga kowanne mai hankali. Ji nayi ana yimin horn, sai na daga idanuna jage - jage da hawaye na dubi inda motar ke tsaye, Anti ce ta zo dauka na da kanta yau don na gaya mata paper daya kawai zan yi. Tareda Ko'oje na gan su a tsaye can gefen motar suna magana, suna kuma kallo ni da tausayi a fuskokin su. Mikewa nayi na isa ga motar na shige Anti tayi sallama da Azima ta ja motar bayan ta dora min Nadia a cinya ta. Muka kama hanyar gida daga Mabushi. A hankali Anti ke jan motar kamar bata so mu isa gida, sai ta dauke kan motar ta yi wata hanyar daban, inda muka isa wani katafaren asibiti, ta dau jakarta tace in biyo ta, na gane asibiti ne na kwakwalwa daga karanta sunan. Wani bakin ciki ya tokare ni na ki fita, daga baya kawai sai na daura hannaye aka na saka mata kuka ina cewa "kema haukan zaki lankaya min?" Anti ta kidime, mutanen da ke wajen kuwa sun saba ganin iri na sai basu wani maida hankali a kan mu ba. Waya naga Anti ta dauko tana yi daga can gefe sai ga wani likita mai kamala ya fito tare da ma'aikatan jinya biyu karfafa da su. Ma'aikatan suka ce salin alin ki bimu mu shiga ofishin likita, in kika yi gardama mu saka ki a 'guard room' mu kulle". Ai jin haka na hadiye kuka na bakidayan sa ina kuma sakawa a raina gara fa in nutsu, idan gwajin su ya nuna lafiya ta kalau kowa zai shafa min lafiya. Likita ya bude firjin sa ya dauko ‘fresh milk’ mai sanyi ya bude ya tsiyaya min a tambulan ya miko min da murmushi, bayan ya bani kujerar da ke fuskantar sa na zauna, Anti na tsaye can gefe. Sai na kasa tankwabe wannan kulawar tasa, ko babu komai shi babu kallon mahaukaciya tattare dani cikin idanun sa. Dama a yunwace nake, na karba na shanye ya kara min na kuma shanyewa. Na lumshe ido nutsuwa ta ziyarce ni. Ya bani kujerar kusa da shi na zauna ina satar kallon Anti. Ya bude file yace "Yaya sunan kanwar tawa?" "Sunana Boddo" Na amsa a matukar gajarce. Fuska a gimtse. "Siyama dai ko? Meaning… Ramadan ko? Kyakkyawar yarinya dake haka ki ce sunan ki Boddo?" Sai ya bani dariyar data sa ni murmusawa, Anti ma ta murmusa cikin damuwa, tace masa Boddo yana nufin kyakkyawa, ni kuma nace "Aisha-Siyama sunana". Likita yace "koda na ji. Siyama Maman ki ta kawo ki a bisa zargin kin samu delusions, haka ne?""To ai ko na ce maka lafiya ta kalau ba lallai ka yarda ba, tunda an ce majority carries the vote". Dr. Amir yayi murmushi yace "wani lokacin majority din suna taruwa su duka su zabi wrong action da zaki ga ya zo ya dame su bakidayan su, wadanda suka zabi kalilan sai kiga sune on the right path. Don haka Aisha-Siyama saki jikin ki, i'm not among that majority na mutanen da ke miki kallon tabuwa, ina kan katanga ne ina kallon yadda rikicin zaben yake gudana, in an gama a matsayi na na likitan kwakwalwa, sai nayi alkalanci na gaskiya a tsakanin ki da su". Wani murmushi ya subuce min. Na ji kamar in gamsu da abunda ya ce mun. Wata zuciyar na cewa wayo ne kawai da hikima irin na likitoci in suna son sanin gaskiyar abu. Dr. Amir yace. "Aisha-Siyama menene damuwar ki har kike zana Radio akan NECO answersheet? Answersheet din ma ta mathematics?" "Duk abinda kayyi tunani a kaina, daidai ne" Na baiwa Dr. Amir amsa a gajarce. Don na daina kare kaina a kan haukan da suka riga suka lankaya min, saidai in karbi kowanne magani da za'a bani, amma ba zan sha ya yi min illa ba. Zubarwa zan yi. Duk dabarar likita naki cewa komai, a karshe ma sai na fashe masa da kuka nace "Dr. Na yarda da duk abinda suke ikirari na cewa na haukace, amma idan aka yi min auren dole zan kashe kaina". "An zo wurin!". In ji Anti. Wato irin har na iso critical stage na depression mai sanya wa mara lafiya suicidalthought. A tunanin Anti fa. Dr. Amir Yasa biro a gefen kunnen sa yana kallo na, "kin ki gaya min me ke damun ki, ni kuma na san lafiyar ki kalau koda kika yi maganan suicide. Amma kullum ki tuna ke din muslma ce wadda ta yarda Allah subhana ke bayarwa kuma shi ke hanawa, sannan shi yayi umarni da mu yi wa iyayen mu biyayya. Kina cikin soyayya, right?" Na daga ido na dube shi bance eh, ba ban kuma ce a'ah ba. Na yi alkawarin ba zan kara maganar Dream Husband dina da kowa ba, zan yi abinda zai bani kwanciyar hankali kawai; Nemansa. Dr. Ya ce "Aisha-Siyama forget him, face your exams, its your future, obey your parents, stop stressing your mental well being, face your reality. You are still young, yanzu ne damar da kike da shi na gina rayuwar ki kada ki bari damar ta wuce a banza cikin mafarkin da ba lallai ya koma gaskiya ba". Gyada masa kai nayi kawai, fatana ya sallame mu. Ya dubi Anti Wasila yace "yarinyar ki bata tare da delusions, bata tareda kowanne rashin lafiya na kwakwalwa, amma tana bukatar hutu sosai kamar barci mai tsaho don stress ya mata yawa sakamakon infatuations da ta sawa ran ta, in tayi barci sosai zata samu nutsuwar zuciya don haka zan mata allurar barci ne kawai in bata simple drugs that will relax her stress". Aunty Wasila tayi ajiyar zuciya tace Dr. Kana ji fa tana maganar suicide, kuma kana kira mata lafiya. Dr. Ya ce "then kada kuyi mata auren dole, tunda bata so, abinda yafi suicide ma mata suna yi akan auren dole, wasu su sanya kan su a prostitution ko barin gida. Don haka don Allah ku barta ta nutsu, ku bata dama ta manta da shi a hankali". Anti tace. "Dr. Tun zuwa na gidan mahaifinta take maganar mutumin nan da take so, ka taba jin an so gaibu? Ana neman shekaru biyar yanzu, bata taba dainawa ba, don haka bana jin zata daina din ko barcin kwana dubu zata yi". Dr. Amir Yace. "Siyama where is he? Have you ever meet him in person?" Hawaye suka cika idanuna suka soma digowa, sabida yadda yayi maganar cikin damuwa da damuwata da nuna concern. "I actually don't know Dr. I don't know." Dr. Ya ce ki bani izni in zama abokin shawarar ki a kan sa, wato komai kika ji ni zaki kira ki gayawa ba kowa ba, sannan kafin ki aiwatar da komai a kan sa ki fara shawara da ni, i'm with you Siyama. Lafiyar ki kalau, amma kina fama da infatuation wanda kika dade da sanyawa a ranki har ya zama kina mafarkin sa, a zahiri abinda muka saka a ran mu muka kwanta da shi, shi muke gani a cikin barcin mu. Amma babu wani mutum da yake zuwar miki a mafarki face imagination da kika dade da sanyawa a ran ki ya zamar miki (fantasies). Zaki iya raba kan ki da wannan fantasy da infatuation din ta hanyar treatment din fatar baki kadai da zan dora ki a kai (counselling) don kada ya zamo miki lahani ga kwakwalwa". "Gashi kuma Dr. Bana bukatar cire MAFARKAN nan nawa a raina sabida ina jin dadin su, na fi so in cigaba da rayuwa cikin mafarkai na, sun fi min komai dadi domin suna debe min kewar jiran sa. Na tabbata ko ba dade ko bajima jiki na na bani zai zo ne, mafarkan da kake son raba ni da su suna taya ni jiran sa, ba ni kadai nake wannan wahalar ba Likita, ka yarda da ni ba koshin wahala nake ba kamar yadda kuke zato. I believe that our hearts are jointly connected internally". Dr. Amir yayi murmushi ya mike yana hada allura, ya gama fahimtar duk abinda yake son fahimta, (she believed her fantasies and infatuations) na shekaru masu yawa raba ta da su farat daya zai yi wuya, har sai in ta samu actualizing din su. Ya gama hadawa ya dawo yace "bani hannun ki Siyama zan miki allurar da zata sa ki samu isashshen barci". Ai kuwa tunda muka shiga mota nake ta barci, Allah ya so ni gobe da jibi duka babu paper. Lallai barci Rahma ne kuma ni'ima ga dan adam, kuma yin sa da ban yi ba kwana biyu ya taimaka wajen birkita ni da ta'azzara infatuation dina. ****** A bba ya dubi Anti da ke ta kokarin shirya masa abinci "ina 'yar taki ne? Tun jiya ban gan ta ba""likita ya mata allura tana barci" bata da lafiya ne" ya tambaya yana yamutsa fuska. Anti tace "lafiyar ta kalau stress ne na jarrabawa kawai shine nasa aka mata allurar barci don ta huta sosai". Abba yace "but an fi son barci natural, yin allura don kawai ayi barci?""Likitan da yayi mata ya san abinda yake yi, wajen specialist (psychiatrist) na kaita, ko ba komai yanzu hankali na ya kwanta tunda na tabbatar Siyama bata da tabin hankali kuma bata da aljanin dare as well. Imagination ne data dade da sakawa a ranta yake zamar mata mafarki.”. "Sai tsabagen iya shege kuma ba!" Inji Abba cikin takaici. "Ni kuma nafi kowa iya shegantaka dani take zancen. Ko lefe bazan mata ba. Wai Umar ne Siyama bata so? Humm, duniya mai abin mamaki. Zuciya mugun nama mai kawace - kawacen banza. Allah ka shirya min Siyama, ka fidda rabon shaidan daga zuciyar ta". Anti ta amsa da "Amin, amma Abba don Allah likita ya roki a daga auren kada ayi a yanzu, a kara bata lokaci zai yi counselling din ta ta manta da wancan din" "Aikin banza aikin wofi, kada Allah yasa ta manta shi koma waye. Ta dauke shi su tafi gidan mijin ta tare. Bani da burin Siyama tayi zurfin ilmi a hannu na, gidan miji zan kaita a wannan watan da zamu shiga. Duk wani nauyi da Allah ya dora min nata na sauke, a yanzu aure kawai ya rage, kuma zan tabbatar a hannu nagari na damkata, ba ruwa na da shirmen ta. In ya so tayi tayi gunduwa-gunduwa da Umar din ta kawo mini, karewar rashin so kenan dai ko?" Anti kasa magana ta yi, don tsakanin uban da 'yar bata san wa ya fi wani taurin kai ba. Ba mamaki in ya kasance gadowa Siyaman tayi. Kwana uku ina bacci sai dai Anti ta tada ni ta bani ‘fresh milk’ in sha in koma, dama kuma cikin al'ada nake, wani zubin sai tazo da kanta ta kaini toilet ta taimakamin na canza Pad sabida nauyin barcin da ke kaina. Ranar da barcin ya sake ni na koma na karasa jarrabawoyi na. Wanda babu laifi na dan amsa wasu yanzu domin na samu nutsuwa sosai. ***** FAREWELL FROM REGENT COLLEGE A yau mun kammala Regent College Abuja, kowa ka gani cikin farin ciki marar misaltuwa yake sai hotuna ake dauka da 'yan uwa da iyaye da kawaye. Anti ce da su Nadia suka zo dauka na bayan mun yi sallama da Azima Ko'oje da sauran wadanda muke mutunci dasu, da alkawarin zan je gidan su Azima idan na huta, kai tsaye muka kama hanyar gida, amma sai Anti tace Dr. Amir yace mu biya ta wajen sa ya kara gani na. Ban ce komai ba, ko babu komai shine wanda ya wanke ni daga hauka a idanun ta. "Aisha Siyama an gama jarabawa lafiya ko, ina fatan akwai improvement?" "Alhmdulillah Dr., na dan tabuka ana karshe-karshen" "To wane course kike so zaki yi yanzu a jami’a?" "Babana ba zai barni ba" "Sai aure kenan" Na hadiyi miyau da kyar. Ji kake mukut. "Kin kara yin mafarkin sa?" Girgiza masa kai na yi alamar a'ah, "I only enjoyed my sleep" Masha Allahu Aisha, kin karbi maganar Baban ki da muhimmanci yanzu ko? Imean ta auren dan uwan ki?" Shiru nayi ban ce masa komai ba. Shi da kan sa sai y ace. "Prefer not to say?" Na gyada masa kai da sauri, yace “to ya yawan tunanin har yanzu yana nan?" Na ce a hankali "bana tunanin komai tunda na gama barcin nan, ni ina zargin ba allurar barci kayi min ba gaskiya, damuwar tayi nesa da zuciya ta sosai. Bana jin bacin bacin rai sam ko wata damuwa, sai an tada min maganar auren Ya Omar". Dr. Ya maida hankalin sa ga Aunty yace "Alhamdulillah, she has responded fully to the treatment made. Shawara ta karshe itace ku hakura da yi mata auren nan, if not, abinda ake gudu shi zai faru da Siyama wato, zata tabu". Aunty Wasila tayi zugum da ita, tace "Dr. Matsalar ba daga gare ni bane, ba kuma daga Umar bane, wallahi yafi kowa damuwa da farin cikin 'yar uwar sa, Baban su ne matsalar, ba zai taba yarda da wannan shawarar ba, iknowhim kamar tafin hannu na. In yace YES to da gaske yana nufin YES din, babu gudu babu ja da baya, baya waiwayen abinda zai je ya zo". ******* M una isowa gida Abba na dawowa, duk muka yi gare shi muna masa oyoyo, ya dube ni sai ya ga na rame ga idanu na sun zurma yace "jinya kika yi ne halan?” Girgiza kai nayi ban ce komai ba. Anti ce ta ce “na gaya maka ai, tayi jinyar baccin kwana uku", "to Allah ya kara lafiya, ya batun jarrabawa kuma sai yaushe za’a gama?""An gama yau". Ta fada da fargabar abinda zai biyo baya. Daidai sanda muka shiga cikin gidan duk muka zazzauna a leather seats na falon kasa. Abba ya bude ‘brief case’ dinsa ya fiddo (flight tickets) guda biyu ya mikowa Anti. "Ga nan, amshi, flighttickets din ku ne na tafiya Lagos gidan Adamu gobe, zaku hadu ke da matar Adamu ku yi sayayyar duk abinda ya dace na gidan Omar da Siyama, ku kuma hada mata lefe irin wanda duk take so. Da na ce bazan yi mata lefen ba amma Ummati ta ki. Rana ita yau da an sakko masallaci daurin auren su insha Allahu a Mambilah". Ya kawodaya daga cikin ‘credit cards’ din sa na bankin GT ya bata "abinda ke cikin nan nan ina ganin zai ishe ku sayayyar komai, ayi komai na hankali da kula bana son almubazzaranci". Hannu bibbiyu Anti tasa ta karba tana fadin. "A madadin Siyama Allah ya saka da alkhairi. Ni kuwa sai nayi kasa da kaina. Da daddare na bi Anti dakin ta na sameta tana canzawa Nadia Diaper, fuskata ba walwala nace "Anti nikam ba sai na biki Lagos dinnan ba, kuje kawai dik abinda kuka zabo zai min dai dai". Hawaye suka balle mini. Anti tace "sabida bakya farin ciki ko sabida baki godewa kokarin Baban ki ba ko??" "Anti....!" "Siyama ki shirya kayan ki zamu tashi Lagos gobe da safe insha Allahu, zamuyi kwanaki uku na san zasu ishe mu mu gama abinda ya kai mu. Kwana daya lefe, kwana daya furniture da kayan kitchen da labulaye. Nasara ta san ko'ina a Lagos da inda za'a samu komai mai kyau, zata raka mu". Juyawa nayi kawai na fita ba tareda na kara tankawa ba, don na san duk abinda zan fada din tirjiya ce kuma ta nuna min bazata karbi kowanne uzuri na ba. Na tashi da zazzafan zazzabi a safiyar washegari, zazzabi mai zafi sosai harda jijjiga, da kartar hakora, wanda yasa dole Anti ta barni a gida ta tafi sayayyar kayan aure a Lagos don bata isa keta umarnin Abba ba, ni kuma na shiga jinyar kaina da kaina don Abba ma ba ya gari daga ni sai Maryam Jamila. Ita take taimakamin da miko min duk abinda nake so ina daga kwance, ta bani paracetamol na sha naji dan dama-dam wajen azahar na dafa mana noodles muka ci nida ita. ******** N asara da Wasila ba inda basu shiga sun fita ba a kasuwannin garin Lagos suka hada lefe mai tsari, sannan kayan sakawa a gidan amarya. Kwanan Anti uku suka dawo. Ashe har da Ya Omar suka dawo gidan. Bai nemeni ba sai ana daurin aure saura kwana biyar muka hadu a kitchen yana shan ruwa daga firji, ni nasan na rame sosai amma dana dubi Ya Omar sai naga ya fi ni ramewa, ga kasumba ya bari a fuskarsa wadda a baya bashi da ita. Ya kara zama cikakken namji. A zuwan sa Lagos ma Young Abba ya yi masa tayin aiki da ofishin su, yace shi a'a a ofishin su Abba zai yi aiki sabida Abba ya kusa retire. Kaina a kasa na shiga kitchen din nayi kamar ban gan shi ba, har zai fita sai ya dakata yace. "Boddo ko gaisuwa babu?" Muryar sa kamar ta wanda ke fama da mura, na kasa kallon cikin idon sa don alkawarin da yayi min bai cika shi ba, ya ce zai lallashi Abba kada a yimin auren dole amma yayi hakan? Shirin angwancewa yake yi. Da ya ga ba zan gaishe shin ba kamar yadda na saba sai yace "kada ki damu fa Boddo ni ba bakon zafi bane, it's a promise bayan auren mu ba zan zo inda kike ba, I mean... I mean ba zamu hada shimfida ba don na fahimci damuwar ki kenan. Zan yi hakuri zan jure har sai ranar da kika karbe ni as a husband don radin kan ki. Ranar ne zaki banbance da banbancin da ke tsakanin Aya da tsakuwa; soyyayyar Yaya da ta wani bare da kike underestimating dina a kan sa. Zaki tabbatar soyayyar gaskiya ba a mafarki take gudana ba, a zahiri take; from theory to practice. Na tabbata Dream Man din naki, bai fi ni komai ba, haka bai fi sauran maza mazantaka ba, watakila ma.....watakila ma.....ya kyabe baki kafin yayi kasa da murya kada wani ya ji abinda zaya ce, kamar cikin rada ya ce, "watakila Boddo ko kwakkwarar sumba wannan (kissing) bai iya ba sai shegen tsayi kamar falwaya da bakar kalar sa dana fahimci sune abubuwan sa da ke rudar ki!". Hannaye na biyu na saka na toshe kunnuwa na na fita daga madafin ina mamakin sa. A baya in wani yace min Ya Umar zai iya irin wannan maganar ba zan taba yarda ba. Sabida kallon wani kasurgumin shaihin malami nake masa. A raina nayi murmushin tausayin sa, sabida ya gama amanna da ya same ni ya gama. Shi yasa bazai damu da abinda nake gudun auren sa a kan shi ba, tunda ya san ko ba dade ko bajima zai zama nasa ne. "Ya Omar da muguwar rawa gwanda kin tashi. Zamu ga wa za'a kai gidan ka balle har ayi batun hada shimfida ko akasin ta. Bana yin magana don yaudarar kowa amma tunda an zo wannan gejin zan yanke hukuncin da zuciyata ta fi amincewa da shi. Lokaci ya kure min da zan nemo ka Dream Husband, kamar komai ya kurace min muddin na bari aka daura min auren nan, suna maganar daurin aure nan da kwanaki uku. Omar ba zai taba saki na ba muddin igiyoyi na suka shiga hannun sa. Damuwa ta daya ce a ina zan nemo ka?" Anti ta gama shiryawa tsaf, shirin tafiya Mambila a washegari, inda za'a fara gudanar da bikin mu yadda Al'adar garin Gembu ta tsara. Na tabbatar muddin na saka kafa a Gembu, dakin Ummati aka shafa min lalle; aure na da Ya Omar ya gama tabbata, mai iya raba Omar Gidado Gembu da igiyar aure na kuwa sai dai mutuwa balle in yi fatan zan shiga ne in fito a sanda nake so, ko in Dream Husband ya bayyana kan sa, in bar Omar in koma masa, a halin yanzu kuwa bana bukatar auren kowa na fi so in bar duniyar bakidaya in huta da azabar soyayyar dana ke dandana, tunda bani da nasara a kan ta, da zai bayyana da ya bayyana haka kafin lokaci ya kure mana. Da in ganni a gidan Ya Omar matsayin matar auren sa gara in bi bayan mahaifiya ta, ko na samu cikar buri na a aljannah, ko mayi aure da wanda nake so a wata duniyar ba wannann tamun wadda muke ciki ba, tunda ya ki bayyana a duniya har gashi za'a yimin auren dole a dalilin (SAKACI) NEGLIGENCE irin nasa...... "FIYA-FIYA TANA TSINKA HANJI IDAN TA SHIGA JIKIN DAN ADAM. DON HAKA UMMATI KADA KI KARA AJIYE FIYA FIYA A DAKI SABIDA YARAN MAKWABTA DA NAKI JIKOKIN KANANA DAKE SHIGOWA SUNA DABDALA A TSAKAR DAKIN KI". Na tuno wata magana data taba gudana tsakanin Anti da Ummati a zuwan da muka yi mata yawon Arba'in din Nadiya, Maryam Jamila ta dauko wata kwalba akan talbijin tana tambayar Ummati ko turaren Dan Duala ne a ciki? Ummatin ta ce "a'ah fiya - fiya ce maganin sauro guba ce, maza ajiye ki je ki wanke hannun ki". Abbana ya ce wai ko gawata ce a kai gidan Umar, kafin a wuce da ita makabarta, to watakila ya fada da bakin mala'iku ne. Domin furucin iyaye karbabbe ne shi yasa ake so a kowanne lokaci su dinga tauna kalaman su a kan 'ya'yan su. Na zabi in sha fiya-fiya a kan dai na je zaman aure gidan wanda bana yiwa so na soyayya.....!!! (A wasu lokutan idan baka barwa Allah lamarin ka ba, idan ka zabi ya barka da dabarar ka sai ya barka din. Babban kuskure na ni Siyama, tunda na fara mafarkan nan da shi ban taba neman zabin Allah a kai ba, ban taba cewa idan soyayyar da nake yiwa wannan bawan Allah daidai ce da addini na, tarbiyya ta da lahira ta, kuma alkhairi ce a gare ni da addinin Allah, Allah ya sada ni da shi cikin hikima, buwaya, mulki da iyawar sa da tsarkin mulkin sa. Ni na san tun farko da ace wannan addu'ar na dukufa ina yi tsahon shekarun nan dana fara mafarkan sa, na tabbata da tuni na rabauta cikin zabin Allah. Amma a yanzu lamari na yana hannu na ne kacokam! Kuma shedan ya yi min kyakkyawar jagora yana gaya min rayuwa ba tare da shi da na kallafawa rai ba aikin banza ce, don ba zan taba jin dadin ta ba. Na daga kwalbar fiya-fiya na rufe ido sannan na yi kalmar shahada, ban sani ba ko Allah zai karbi shahadar nan tawa? Tunda ni nayi nufin yin ta da hannu na bata Allah da Annabi bace?? Ko kuma shan fiya fiya don gujewa auren dole daidai yake da kashe kai??? Gara in taimakawa Abba ya cika burin sa ya kai gawa ta dakin Ya Umar, sannan a zarce da ita makabarta. Shi kuwa Dream Husband dina bazan taba yafe masa ba, duk ranar da ya gama yangar sa ya ga damar bayyana kan sa gare ni, ya samu labarin na gaji da jiran sa na kashe kaina a kan sa he will then take it for granted.... I would love to see his reaction a lokacin da ya samu wannan labarin. Reaction din sa na samun labarin mutuwa ta a dalilin sa, shi zai nuna girman matsayi na a zuciyar sa..... shi zai bayyanawa mai karanta labari na cewa shima yana so na ko ni kadai nake koshin wahala a kan sa? Duk da 90% na zuciya ta na tabbatar min our hearts are jointly connected internally by the creator..... Ba ni kadai nake wannan suffering din ba. Na hango kaina Abba na binne ni yana kuka yana cewa da na sani na taimaka miki kin nemo shi Boddo, ba wanda ba zan iya nemowa a duniya ba idan na saka kaina, da na sani ban yi gaggawa ba wajen yanke hukuncin yi miki auren dole, da na sani ban ki bin shawarar likita ba da ya ce a tsahirta, da na sani Omar ya zabo duk macen da yake so da kan sa, in ya so na aura masa ko wacece koda zan rasa banten daurawa....Da na sani din da Abba zai yi a kan hukuncin da yayi wa rayuwata tana da yawa..... Amma me? Wani bangare mafi rinjaye na zuciya ta ya ki amincewa da hakan, cewa yake dani cikin amsa-kuwwa.... "Abba ba zai taba yin dana sani ba, don hukuncin sa bai sabawa Allah ba, ke ce zaki yi da kin sani, kece zaki dawwama cikin sa, kuma ki tabbata cikinsa daga nan har karshen rayuwar ki muddin kika aikata abinda zuciyar ki ke umartar ki a yanzu". Amma hakan bai sa ko kadan na fasa abinda nayi niyya ba, a ganina hanyar tsira daga auren dolen da Abbana zai min kawai kenan wanda zai zamo shinge/katanga ga tabbatuwar mafarkaina da wanda nake so. Da in rasa wadannan mafarkan nawa gara na rasa rayuwar dungurungum bakidayan ta. Love is real, kuma nawa baya karbar uzurin kowa face na samun wannan soyayyar gaibun dana ke so. Na soma tittila ruwan fiya-fiya a baki na ina hango DREAM HUSBAND dina, yau kam tar-tar nake ganin sa cikin idanu na ba kamar kullum da a fizge kawai nake iya ganin sa ba; those beautiful eyelashes sun kwanta sosai a saman lumsassun idanun sa, that cool man's pride da ke dimauta ni, wanda ya tafi ya zagaye habar sa ya kwanta lambam a kan kyakkyawar bakar fuskar sa sai sheki da salki gami da walkiya yake yi. Hakika Ubangijin halitta ya kyautata surar sa a cikin bakaken mutanen Africa, ya qawata min shi a zuciya da ruhi fiye da duk wani da namiji mai numfashi a duniya. Gani nake kamar ya bude min hannuwa yana min murmushin da ya lotsa gefen kumatunsa guda daya yana jiran isowa ta. Na amince Allah ne ya hada mu ba don komai ba sai don mu rayu tare, rayuwa ta har abada amma a wata duniyar daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba!!! ******** MAI RABON GANIN BADI....... A cewar Hausawa ko ana ga uzuru ana ga Shaho sai ya gani. Allah ne ya kawo Wasila a daidai wannan lokacin, wanda yayi dai-dai da zuke kwalbar fiya-fiya da nayi, idan Allah ya ce kwanan dan adam bai kare ba to babu abinda zai kashe shi sai kudura da iradar Ubangiji. Na yarda da hakan a yau a kaina domin tabbas na san na sha kwalbar fiya-fiya, daga nan sai shigowar Wasila da ihunta da na ji a kaina, bayan wannan ban kara tantance meke faruwa da ni a duniya ba. Na bude ido ne na ganni akan gadon asibitin Nizamiye, inda anan file din duka 'yan gidan mu yake, sauran abinda ya biyo baya mai ban tausayi ne domin kuwa Abba ba ta jinya ta da Wasila ke yi ya ke ba shi, bata tabbacin da likita ya bashi na nasha guba an samo ni da kyar da taimakon Ubangiji yake ba a'ah, ta shirin daurin aure na yake yi ko in mutu ko in yi rai. Koda na farfado na yi ido hudu da Abba ban iya kara yi masa kallo na biyu ba, sabida yadda fuskar sa ta koma ta tsantsar bacin rai ban taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan halin ba. A gefe Wasila na share hawaye, Umar na gefenta ya kura min ido harde da hannayen sa a kirji, gabadaya yayi wani zuru-zuru kamar wanda ya mutu ya dawo. Ina jin bai taba gamuwa da tashin hankali da bacin rai a rayuwarvsa irin na wannnan lokacin ba. Da Abba ya tabbatar na dawo cikin hayyaci na sai ya ja kujerar zaman 'yan dubiya gaba na ya zauna. Ya kura min ido yace "Siyama! Anya Siyamar dana sani na kuma haifa tareda Asshe ce wannan ko kuma dai Nos din data karbi haifuwar ki ta musanya min tawa Siyamar da wani jinin daban? Ina mamaki! Domin dai nawa sanin. Jinin malam Dalhatu Abdullahi Gembu ba zai taba aikata kisan kai ga kowa ba balle ga karan kan sa a bisa sani kuma, ba zai so ya zo duniya a banza ya koma a hofi ba. Haka ba zai so ya mutu kafiri ba. Akan wata kankanuwar bukata tasa ta duniya. A matsayi na na uba bazan ce ban so kika kubuta ba, amma na so ki cika burin ki kije lahira ki dandana azabar wuta kona wuni daya ne sannan ki dawo, watakila zaki fi sanin cewa iyaye ba abin wasa bane. Kuma duk wanda ya zabi son zuciya yayi SAKACI dasu yana tareda dawwamammiyar nadama. A karshe ina sanar dake cewa har yanzu ina nan akan baka na na cewa Omar na zaba miki, kuma jibin dana saka don daura muku aure ba zan fasa ba. Wannan karon sai ki sa wuka ki farke cikin ki don kifi mutuwa da sauri, a mika gawar ki gidan Omar kafin a wuce da ita makwanci.....". Abba ya fada cikin wani mashahurin bacin rai da ban taba gani a tare da shi ba. Daga bayan sa Ya Omar yayi gyaran murya cikin karaya ya soma rokon Abba "Abba don Allah.... na roke ka ka janye kudirin ka, ka bar Siyama ta nemo wanda take so ka aura mata. Abba rayuwar Siyama cikin farin ciki ta fiye min auren ta. Abba tunda har Siyama zata iya iya yunkurin kashe kanta a kaina Abba na hakura da Siyama na haramtawa kaina ita. Ina rokon ka kaima kayi hakurin musulunci kada ka yi fushi da ita, ka bata dama ta auri zabinta, don Allah Abba". Omar ya fada cikin despair da kuma karaya da al'amarina bakidaya. Anti tace Abba tunda har Umar ya hakura kaima kayi hakuri. Rayuwar Siyama gaba take da komai don Allah Abban Siyama..." Anti ta fada cikin hawaye, don hakika ta shiga tashin hankali irin wanda bata taba shiga a rayuwar ta ba, da tazo ta same ni ina shan fiya-fiya kuma babu jimawa na bi kwalbar muka zube a kasa, kumfa na fita daga baki na. Allah ne ya so Omar na falo a lokacin, da gudu ta fita tace "Siyama ta kashe kanta Omar, ta sha poison, ban san a ina ta samu ba". Irin zaburar da Omar yayi kamar ta fitar kibiya ya kuma daukoni a kafadar sa yasa a mota Anti ta shiga gaba basu zame ko’ina ba sai Nizamiye. An karbe ni a emergency likitoci suka rufu akaina don ceto raina. A lokacin ne Anti ta samu sukunin iya kiran Abba wanda bata san ina yayi ba a ranar. Hakika akwai kwararru ba na wasa ba a Nizamiye, watakila kwarewar su ce ko kuma ince Astagfirullah Allah bai yi kwanaki na sun kare ba kawai shi ya cece ni. Amma an kashe kudi ba na wasa ba. Sannan daga farfadowa ta Abba ya bi ni da wadannan muggan maganganun. Wanda suka nuna ko kadan suicidal attack dina bai sauko da shi daga kan dokin kudirin sa ba. Anti da Ya Omar suka dukufa roko, rokon Abba suke akan ya janye ya kyale ni in yaso duniya ta koya min hankali don wanda nake so din ma fa babu shi babu dalilin sa cikin duniya, imagination ne kawai nake yi. "Ai kuwa zata mutu cikin hasashe" inji Abba. Sannan ya juya ga Omar da ke durkushe a gaban sa, ya ce "Omar ba ka son Boddo?" A firgice Omar ya daga kai ya dubi Abba, Abba ya ce "amsa nake so eh ko a'ah ba wani dogon turanci ba". Omar ya rasa inda zai kansa, ya ce "it does not matter Abba son da nake yi wa Boddo tun tana zanin goyo, tunda ita bata so na na yafe soyayyar dana ke mata, na sadaukar da tawa soyayyar don farin cikin ta da kasancewar ta cikin kwanciyar hankali". Abba yace "magana ta kare Omar bana son jin karin komai. Ka tashi mu tafi, gobe zamu wuce Mambila ko sun sallameta ko basu sallameta ba a daura muku aure". Omar zai sake magiya Abba ya daka masa tsawar data gigita shi. Ya kuma sa kai ya fice a dakin asibitin. Dole Umar ya bi bayan sa don mukullin motar Abban na hannun sa. Yana fita yana waiwaye na. Gani yake kamar bazai dawo ya tadda ni a raye ba. A lokacin na lumshe idanuna bansan ya akayi ya akayi ba, kawai naji kwallar tausayin Umar sun wanke min fuska. Ni da Anty muka kwana duk wani motsi da zan yi a kan idanun ta nake yin sa, don tsoron ta na ko zan sake wani attempt din na salwantar da rayuwa ta. Akwai maganganu fal a bakin Anti amma ta adana su zuwa in samu lafiya. Bakin cikin abinda na aikata ya hana duk wani masoyi na sukuni a zuciyar sa kuma babu wanda na baiwa tausayi banda Ya Umar. Ita Anti da zata samu dama so take ta dan yi min shegen duka ko zata huce tashin hankalin dana jefa ta. Kwance kawai nake da ledar karin ruwa a jikin hannu na nida ita mun zama tamkar kurame ba mai ce da dan uwan sa uffan. Sai likitoci da ke ta shige da fice a kaina don tabbatar da aikin su na tafiya daidai. A daren Umar Faruq ya kasa barci, ya tabbata in har ya wayi gari jibi a gidan mu Abba ba zai fasa abinda zai zo yana nadama ba, idan a da yana ganin abin na Boddo wasa ne yanzu ya tabbata Boddo da gaske bata son sa, koda za'a dora mata wuka a makoshi bazata zauna da shi ba, tunda har Boddo zata iya kashe kanta a kansa shi kuwa meye ribar sa a cikin auren ta??? Wane farin ciki ko alheri zai tsinta a cikin auren matar da ke kin sa har haka? Matar data zabi shan guba fiye da hada shimfida da shi. Tausayin Abban mu kadai ya ishe shi amma ya yanke hukuncin da yake ganin yafi masa alkhairi. Ya kuma fi zama maslaha ga Abba sannan ya fi zama kyautatawa a gare ni. Washegari tunda safe likita ya sallame ni, Anty ta dauko ni muka taho gida jikina duka babu karfi. A falo muka cimma Abba yana saukowa daga matattakalar bene cikin shirin sa tsaf, da gani yayi shirin wucewa Mambila ne daurin aure na a gobe, don sun yi waya da Anti kafin mu taho ta gaya masa an sallame mu yace to yana jiran mu zamu wuce Gembu yanzu. Don haka muna shigowa Anti ta wuce dakin ta don dauko kayanta, nima na wuce nawa dakin kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ina hawaye, ganin irin kallon tsanar da Abba ya jefa min yau. Anti ta fito jaye da akwatin ta ta nufo daki na don ta hada min nawa kayan don ta san ba hadawa zan yi ba. Ita ta daukarmin komai ta hada cikin akwati sannan ta kama hannu na muka tadda Abba a falo, yana ta faman gwada layin Ya Omar ya ki shiga don shi zai ja mu a motar. Bayan tun daren jiya sun gama magana ya kuma gaya masa karfe goma na safe zamu kama hanya ko an sallame ni ko ba'a sallame ni ba, in ya so in karasa mutuwa a hanya. Amma gashi yanzu ana gaya masa layin Omar a rufe yake bakidaya. "Ban san ina Omar ya yi ba, ki duba min dakin sa ko bayan gida ya shiga" Abba yace da Anti. Anti Wasila tabi bayan Omar amma haka ta dawowa Abba tace bata gan shi ba, kuma bata ji motsi sa a bayan gida ba. Abba da kan sa ya tafi BQ neman Umar Anti ta rufa masa baya. Babu inda basu duba ba a dakin ba Umar babu mai kama da shi. Sai a lokacin ne ma suka lura babu kayan sa na sanyawa a dakin sai daidaiku. Akan chest-drawer Anti ta hango wata takarda da rubutun Umar ya dora biro a kai alamar bai jima da ajiye ta ba. Kawai sai ta dauka, ganin sunan Abba a jiki baro-baro yasa ta mika masa cikin kidimewa. -ABBAN MU Samun mutum irin wanda zumunci ne silar shigar su aljannah tamkar namu Abban na tabbata zai yi wuya a wannan zamanin da muke ciki. Hakika baka nufin komai a kan mu ni da Boddo sai zumuncin da kake so ya dore a zuri'ar Ummati har 'ya'ya da jikoki. Amma Abba ba kowanne mafarki da buri ne da muke da shi yake iya zama reality ba. Wasu mafarkan a mafarkai suke tabbata musamman idan Ubangiji ya san cewa ba alkhairi bane a gare mu. Hakika Abba ka yi duk iya kokarin ka na kulla wannan alkhairin a tare da mu, amma kaddara ta riga fata Boddo ta kamu da son wani na wanda take ganin zai hana ta yimin biyayyar aure, maimakon a nemi lahira da auren sai ya zame mata mujazar fadawa halaka. Na fahimci Boddo anan. Ba zan jagoranci ragamar wargajewar rayuwar ta ba sabida nawa farin cikin. Ni dan ka Omar ina bayan kanwata Boddo, and i will always stand by her, zan taya ta neman wanda take so cikin duniya kuma bazan aure ta bisa tirsasawa ba. A karshe ina baka hakuri Abban mu hakuri kan hakuri, na san na bata maka nima, akan hukuncin dana yanke. Bani da zabi ne Abba sai hakan don ka ki ka fahimce mu. Na bar gida Abba zuwa duk inda kaddara zata kai ni sai idan ka janye maganar aure tsakanina da Boddo ne zan dawo bayan shekaru uku masu zuwa in Allah ya kai mu. Idan har lokacin baka janye ba Abba zan ci gaba da zama a duk inda kaddara zata kai ni. Ni na san tunda inada kai to ni ba maraya bane Abba, amma idan na auri Boddo zan koma maraya idan na rasa soyayyar ta. Ina baka hakuri Abba, Abba Allah ya huci zuciyar ku. Ka yafewa Boddo ka kuma sa mata albarka ba don ni ba don Allah Abba. Daga Yayan Boddo Umar Gidado. Gumi, zufa, iri-iri suka ketowa Abba Dr. Mamman Gembu. Omar ya gudu! A dalilin Boddo bata son sa. Kuma yana ikirarin idan har Abba bai janye ba ko bayan shekara ukun da ya ambata ne ba zai dawo ba. Jikin Abba yayi mugun sanyi, ya saki takardar a kasa kawai sai ya juyo, da ni muka yi ido biyu idanuna a bubbude domin na fuskanci abinda ke faruwa Ya Omar ya zabi ya bar gidan mu akan dai Abba ya tursasa ni ga auren sa, kafin na ankara Abba ya yo kaina, ya soma duka na ta ko'ina da hannaye da kafafun sa iri dukan na huce bacin rai. Anti ta sa kuka ta rufu a kaina ta ce "gara kayi mana dukan tare. Yadda Omar ya ke Da a gare ka itama 'yar ka ce mai 'yanci. In shi maraya ne itama marainiya ce. Tana da damar ta auri wanda take so, tsaurin ka ne ya janyo komai, ka san Umar son da yakewa Boddo ba zai bari ya zabi nasa farin cikin akan nata ba. Abba yace "to kuwa bazata zauna min a gida ba, yadda Omar ya bar gidannan itama sai ta bar shi, bazan haifi dan da ban isa in tankwara ba". Kuka nake ina baiwa Abba hakuri na kuma ce zan nemo masa Ya Omar, zan kuma aure shi koda bana son sa..... Wannan kalma ita ta kara tunzura ran Abba, yace "kada Allah yasa ki so shi, ki sani daga yau nima na janye maganar aure a tsakanin ku, kije ki auri duk wanda kikeso Boddo, amma ki tabbata kafin na dawo gidannan kin bar min gida na." "Kada ka yi wa 'yar ka baki Mamman!" Anti ta tunasar da Abba cikin yanayi na rauni, Abba ya ce "ban yi mata baki ba ai, amma na janye nawa kudurin, na janye nawa burin don in samu Da na ya dawo gare ni. Ya fiye min ita sau dubu, kuma lallai -lallai yanzunnan ta bar min gida na". Anti zata kara magana Abba ya rufe idanun sa ruf, ya ce da ita. "Idan kika kara kare Boddo a ido na, ko kika kara nema mata alfarma ko afuwa daga gare ni a bakin auren ki". Wannan magana ba Anti kadai ta firgita ba har da ni. Ina jin sanda fitsari ya kwace min daga tsayen dana ke. Abba ya nuna min kofa da dan alin sa yace "kama hanya ki bar min gida na". A yanayin dana ga idanun Abba sai naji tsoron sake furta wata kalma, na tabbata in yi masa abinda ya bukata daga gare ni shine kawai mafita ta a wannan lokacin. In yaso daga baya idan ya huce na dawo na bashi hakuri. Ni kuka Anti kuka Jamila da Nadiya kuka haka na dau jakar kayan da Anti ta hada min na fito, babu ko sisi a jikina kuma bansan ina na nufa ba. A bakin gate maigadin mu ya biyo ni ganin ina tafe da jaka ina kuka wiwi, ya ce "uwardaki na kada kije ko'ina bada yardar iyayen ki ba, babu wata albarka a cikin sabawa iyaye kuma babu kwanciyar hankali cikin bijirewa umarnin su". "Abba shi yace in tafi Baba Dattijo, biyayya na yi masa zan tafi". "To kada kije da nisa, nemi wani waje mara nisa cikin gidajen yan uwa ki fake zuwa gobe idan zuciyar sa tayi sanyi ki dawo ki bashi hakuri ki kuma bi duk umarin da yayi miki". Na yarda da maganar Baba Dattijo amma ina zani? In ba gidan su Anti ba sai ko gidan su Ko'oje, wannan kuwa matsala ce ta cikin gida da bata bukatar third party, gara kawai in wuce Gembu gun Ummati ko kashe ni zata yi itama tayi, ita kadai ce zata iya shawo min kan Abba. Duk da yakinin dana ke da shi na cewa bazata taba bin bayana ba itama. "Ka taimaka min da kudin mota in tafi Mambila gun Ummati", Baba Dattijo ya sanya hannu a aljihun sa yana lalubawa yana cewa " anyi sa'a jiya Abban ya bani albashi na, gashi duka 'ya ta ki je kafin ya huce, ki kula da kan ki, nasan baki taba zuwa Gembu a motar haya ba, don haka muje in saka ki motar Numan". Shi ya daukar min akwatin ya tare mana drop wadda zata kai mu Jabi park, Baba Dattijo ya saka ni a motar Numan ya kuma gayawa direban ya saka ni a motar Jalingo in an je Numan. Sannan ya ce "daga Jalingo zaki hau motar Gembu amma ki nemi ko gidan mai unguwa ne ki kwana a Jalingo in yaso kiyi asubancin shiga motar Gembu". Nayi wa Baba Dattijo godiya kamar halshe na zai tsinke, kamar yawun baki na zai kafe. Sai yace "yar nan babu komai Ubanki mutumin kwarai ne babu abinda baya yi min nida iyali na tun da ya dauke ni aiki yake faranta min. Allah ya kai ku lafiya, Allah kuma ya huci zuciyar sa". Ya sayo kosai mai zafi da soyayyen dankalin hausa aka kumshe masa a leda da takarda ya miko min ta taga. Baba Dattijo bai bar wajen ba sai da ya ga tashin motar mu. Muna dagawa juna hannu hawaye sun ki tsayawa a idanu na. "Yau ga abinda ka janyo min Dream Husband, yau ga inda soyayyar gaibun ka tayi da ni; kora daga Abba". Ji nayi na tsani kaina iyakar tsana, na tsani soyayyar da nake masa amma shi din, nayi nayi in tsane shi na kasa. Na dauki alhakin komai na daurawa kaina. Tunda shi bai san ina yi ba. Ba kuma shi yace in ki zabin Abba na ba. Tafiya ta mika mana sosai muka naushi Arewa maso gabashin Najeriya. ****** S ai dare muka isa Numan, na rasa yadda zan yi ga gajiya ga yunwa, karo na farko dana shiga motar haya zuwa Gembu don ma dai Direban da Baba Dattijo ya baiwa amanata yayi ta kulada ni har muka iso Numan. Kuma da muka sauka daga motar sa saida ya tabbata na samu wajen da zan kai zuwa wayewar gari wato gidan sarkin Tasha, na kwana a dakin matar gidan, washegari Asubah na yi nayi sallah na yi harama tasa aka rakani na koma tasha aka sanya ni motar Mambila. Hankali na bai kwanta ba saida na fara jin sanyin yankinmu na Mambila a cikin jiki na, na hango tsaunin Mayo-Selbe, na tuna kuruciyata mai dadi a Mambila. Sai na ji rabin damuwata ya yaye ko ba komai watakila yadda na baro Abuja haka na baro duk wani memories dinsa a can. Sai kuma na tuna ai al'amari na da shi ya fara ne tun a Mambila ba a Abujar na samo ba. Wanda ke nufin watakila da soyayyar sa aka haife ni. Babbar damuwata Abba na yayi fushi dani ban san ranar da zai huce ba. Yaya Umar bani da haufi akan sa na san shi din namiji ne, wanda a ko'ina zai iya kula da kan sa kuma ba zai taba kai kan sa ga halaka ba. Ummati na kishingide a falonta tayi shimfidar siririyar katifar da take hutawa a kai, a gefe kwarya ce cike da kindirmo mai sanyi da radio a kunne tana saurare. Ko sallamar dana yi mata bata ji ba kasancewar murya ta ta dakushe iyakar dakushewa sabida yunwa da jigata. Sai gani na tayi a gabanta wurjanjan da ni. Tunda na zube a gabanta na shide na wasu mintoci sabida galabaita da yunwa, salati da sallallamin da Ummati ke yi hade da hamdala shi ya saka ni kara lumshe ido na. Ina ji tana shafa min ruwa a fuska kafin ta dago ni ta rike a jikin ta ta kafa min kofin danyar madara a baki. Kulawa iri - iri Ummati ta shiga yimin saida ta tabbatar na dawo hayyaci na. Ba jimawa kuma sai barci a gadon Ummati. Barcin da ba ni na farka ba sai safiyar washegari. A daren Ummati tayi waya da Abba ta gaya masa gani na zo mata hajaran majaran ko lafiya, budar bakin Abba sai cewa yayi "Ummati sallameta ta kara gaba, tunda ta yi sanadin salwantar min da Umar bata da sauran amfani a gabana itama". Ummati na iya jin irin numfarfashin da Abba ke yi domin a lokacin yana ta neman Umar sama da kasa cikin garin Abuja da wajen ta, ya kuma yi wa Wasila iyaka da magana ta yayi mata togaciya da igiyar auren ta don haka Wasila ta rasa abinda ya kamata ta yi tun bayan fita ta. Daga baya ne Baba dattijo ya kira ta a waya ya shaida mata cewa ya kai ni ya sakani a motar Numan ta yi min addu'ar sauka lafiya. A lokacin ne ta dan samu nutsuwa har ta so bugawa Ummati waya, amma data tuna gargadin Abba dole ta bari, ta koma addu'ar Allah ya kai ni lafiya. Ummati ta ce "ban gane ta zama silar salwantar da Faruku ba" Abba ya ce Ummati doguwar magana ce da bazata yiwu ta waya ba". Tace "to lallai-lallai gobe kuzo kai da Wasila ina neman ku". Sai dare na fara murmurewa, tambayar duniya Ummati ta yi min kan me ya hada ni da Abba ban ce komai ba. Ta tambayeni Ya Faruk da yadda aka yi suka barni na taho nikadai haka nan ma ban tsinka mata ba sai goge hawaye da nake yi lokaci-lokaci don nasan duk wannan kulawar data ke bani itama in taji abinda na aikata kuma na bijirema auren Omar sannan ya bar gida sabida ni, zallar kiyayya zata koma watakila har sai ta fi ta Abba. A haka muka kwana nida Ummati cikin dare ina kallon ta tana ta sallah tana addu'a kan Allah ya kare mata zuri'a ya albarkace su ya cire rabon shaidan daga zukatan mu, don ta fahimci al'amarin duk da ya rabo ni da Abba ba mai dadin ji bane, tunda yau har Abba ke fadin itama ta kore ni kamar yadda ya kore ni. Abba da Anti basu samu isowa Mambila ba sai bayan kwanaki biyu, lokacin har na ware damuwa ta yi min sauki. Na yarda kwanciyar hankali na shine in manta da shi, kamar yadda Omar ya fadawa Abba cikin wasikar sa, "Ba kowanne mafarki ne ya ke zama reality ba". (Dreams are conceived, but not all dreams are born alive). -Zainab Alkali. Abba da Anti Wasila shigowar dare suka yiwa Mambilla, tun da rana na gyara sashen nasu na share tsaf na saka turaren wuta don mukullin wajen Ummati yake ajiye. Ummati bata samu zama da su ba sai a safiyar washegari don sun gaji. Na tashi zan fita in basu wuri amma sai tace "in zauna ayi komai tare da ni kada in juya mata magana daga baya". Abba ya kwashe komai ya gaya wa Ummati. Da ya zo wajen shan fiya-fiya Ummati ta dora hannayen ta biyu a kan ta tana salati da sallallami. Ta dube ni tace "amma kuwa da kin mutu kafira.....". Sai ta saka kuka wiwi tana fadin wannan zamani ina zaka damu Boddo akan ki auri dan uwan ki da baki da ya shi a duniya kika zabi wannan hanyar, hakika kin yi kuskure, ina jiye miki yin sakacin da bazaki iya gyarawa ba a can gaba. Yanzu ina Omar din?" Abba ya ce "ban sani ba Ummati, koda ya zo nan kiyi gaggawar gaya masa ya dawo gare ni na janye aura masa Boddo, ko 'yar wa yake so sai inda karfina ya kare wajen aura masa. Nima na yi masa sakon hakan ta layin wayar sa na san duk ranar da ya bude zai gani". Anti Wasila bata iya magana saboda daga ni har Abban tausayi muke bata, kana iya ganin soyayyata a idanun sa wadda karfi da yaji so yake ya dakushe ta. A daren Ummati tsinemin ne kawai bata yi ba, na rasa inda zan saka kaina, washegari kuwa tunda assubah Abba da Wasila suka koma suka barni dakin Ummati don Abba ya ce ba zan kara taka masa gida ba. Na so tun a daren in je in bashi hakuri duk da ban san matakin dana daukarwa rayuwa ta ba, amma na san har yanzu ba wai ya huce bane, gara in dan kara bashi sarari zuwa ya huce. Tun kafin na tashi barci kuma suka dauki hanya sukayi tafiyar su. Zama na a gidan Ummati wannan karon sam babu armashi a cikin sa kamar da. Ummati ta fita hanya ta bata shiga sha'ani na kuma bata saka ni aikin komai illa idan ta gama abinci ta zuba min a wulakance, bata hirar komai dani, tayi kamar bata san ina existing a cikin gidanta ba. In ta tuna wai Boddo akan kada ta auri Umar ta sha fiya - fiya duk sai ta ji na fita a ranta. In ta tuna Umar ya bar gida akan Boddo basu san halin da yake ciki ba itama sai ta ji ta tsane ni kamar yadda Abba ya tsane ni, banbancin Ummati da Abba ita mace ce akwai zuciyar Uwa a tare da ita. Don haka bata hanani ci bata hanani sha, amma fa bata saka ni aiki sam kuma bata kula ni, harkokin ta kawai take yi cikin gidan ta, a mafi awancin lokuta kuma in ji ta tana yiwa Umar addu'a a fili, tana fadin duk inda yake Allah ya yi riko da hannayen sa. Allah ya saka shi a hannu na gari. Yasa fitarsa ta zamo masa silar daukaka a duniya. Haka muka cigaba da zama ni da kakata Ummatin Mambila cikin gidan kowa bai kula kowa ko kuwa in ce zaman kowa tasa ta fishsheshi. Tace tunda abinda na zaba kenan to in yi ta zama in karata amma fa kada in sake in shiga harkar ta idan ba jikan ta ne ya dawo lafiyar Allah ba daga inda nayi masa kurciya na tura mata shi don kar na aure shi. A haka na debi sati biyar a Mambila amma mu'amalar ta ki dadi tsakanin mu, ta ki komawa mai dadi kamar da, tsakani na da Ummati na yanzu sai kyara da hantara da tsana a fili. Hakan yasa na fara ramewa daga tsaye. Kullum ina tambayar kaina ta ina zan ga Mr Radio ko na samu sanyi daga gare shi? In gaya masa halin da soyayyar sa ta jefa ni a ciki tsakani na da kowa nawa, ya raba ni da Abba ya raba ni da Ummati ya raba ni da rabin jiki na Ya Faruq, yet shi din bai bayyana kansa ba har yanzu ya bar ni cikin tsammanin warabbuka. Above all ya raba ni da farin ciki da walwalata ta Siyaman Abba ya shiga tsakanina da iyaye na, ya jefa ni a sabuwar rayuwa mara focus, don kuwa bansan ina rayuwata ke dosa ba a yanzu, tunda a dalilin sa har karatu na ya lalace daga karshen kammala shi. "Dream Husband" dina isn't this enough? You are not fair to me at all. Ka kyale ni haka ka sakar min zuciya ta sarara, tayi rayuwa cikin walwala irin ta kowa, I think is high time da zaka tausaya min ka bayyana hakanan. Rayuwa ta juya min baya, Ya Omar ya guje ni, kowa ya yanke alaqa da ni, iyaye na duka sun ki ni a kan ka.......!". Nayi kuka mai yawa a wannan daren harna ba uku lada. A karshe na koma yin azumin tadawwi'i don bana iya cin abinci sam. Watarana na dauko Radio na wadda nayo guzurin ta daga gida na kunna don ta debe min kewa sai naji ana fadin sakamakon jarrabawar WAEC na wannan shekarar ya fito. Ummati na da talbijin amma sam bata kunnawa bansan me yasa ba, tafi sauraren radion jahar Taraba. Muna zaune a falo na juya na ga gyangyadi take, daga baya kuma ta bingire a shimfidar Donlop dinta tana barci, sai na lallaba na dauki wayar ta na fice can bayan dakin Anti Wasila na gidan. Numbar Ya Umar na shiga gwadawa hawaye fal idanu na, a kwanakin nan kewar sa nake ba 'yar kadan ba, rayuwar duka ta gundure ni ta zame mini boring, amma cikin rashin sa'a kwamfuta ke gayamin an ma daina amfani da layin. Anya ban yi wa rayuwa SAKACIN da bazan iya gyarawa ba? Na gwada kiran Anti Wasila ba jimawa wayar ta shiga ta kuma dauka. Jin muryar Anti kadai nayi duk raunin duniya ya ruftomin, na shiga kuka ba sassautawa. Duk matsalar dana fada na tabbata ni na jawa kaina ba wani ba, ina cikin rayuwata mai dadi ta gata da soyayyar iyaye da dan uwa na kinkimowa kaina rigimar da bazata bulle da ni ba; Son gaibu, ko in ce "son wanda bai san ma ina yi ba". Duka wadannan abubuwan marasa dadi dana ke gamuwa dasu kuma bai rage ko kankani daga soyayyar da zuciyata ke masa ba. Anti tace "komai ke kika jawowa kanki Siyama, mahaifin ki baya hada kaunarki data komai a duniya amma single biyayya kin kasa yi masa, shin menene laifin Omar a duniya da bazaki aure shi ba ki hutar da ranki daga takunkumin wahalar da kika jefa shi, ki hutar da mahaifin ki da dan uwanki walagigin da kika jefa su?" Da sauri nace cikin kuka "Anti wallahi na tuba na bi Allah na bi Abba na, ki gaya masa na yi nadamar abinda nayi masa, zan kuma nemo masa Omar. Abinda ya same ni ki dauka cewa jarrabawa ta ce ki tayani rokon Allah ya kawomin karshen ta da sakamakon da zan iya dauka. Na kasa manta shi, na kasa daina son sa!". Anti Wasila tace "duk ranar da kika daina zancen son mutumin nan na mafarkin ki, ranar ne Abba zai huce ya saurare ki, ranar da kika yarda zaki auri Omar akan radin kan ki, mahaifin ki yace zai manta da komai ki dawo gida ya nemo Omar duk inda yake yayi muku aure". Ko yaushe ce wannan ranar? Ko yaushe zata zo? Ranar da zan manta da Mr. Radio? Me yasa bazasu gane cewa ba ni na sakawa kaina ba, ba ni na dorawa kaina iftila'in da na ke ciki a kan sa ba? Balle in cirewa kaina a sanda suke so??? ***** KANIN UBA MAKWAFIN UBA! Y ammacin yau muka wayi gari da bakin Lagos, Young Abba (Baffa Adamu) da matar sa Anti Nasara. Sun kusa shekara basu zo Mambila ba sai wannan lokacin da suka zo yi wa Ummati sallama. Young Abba ya samu sauyin wajen aiki daga Lagos. Sai yau ne Ummati ta dan kula ni, albarkacin autan ta Young Abba, a daki ta same ni ina barci ta zabga min duka a cinya. "Ki tashi ki dafawa auta da matar sa abinda zasu ci, ni tuwo nayi kuma sunce duk basa so". "Ummati Young Abba ne ya zo? Da Anti Nasara don Allah?" Ban jira amsar ta ba nayi waje da gudu kasancewar ina shiri da Young Abba sosai, sannan ya auri wayayya "Nasara Alkali" wadda ta maida dangin sa tamkar nata, sosai Anti Nasara ke ji da ni ta kan ce wai sabida ina kama da Young Abba din ta. A falon Ummati na cimmasu, suna cikin shiga ta alfarma, ta karshen gayu, kai kace basu cikin damuwar da suke ciki ta rashin haihuwa har yanzu shekaru biyar da aure, fuskokin su banda annuri ba abinda suke fitarwa. Aunty Nasara ta bude min hannuwa na shige ta rungume ni, bansan ya akayi ba kawai naji na saka kuka kamar itace Wasila. Young Abba ya zare bakin gilashin Prada a idanun sa ya dubeni sosai yace "Siyama bata da lafiya ne Ummati? Wannan rama haka?" Ummati ta kyabe baki tace, "gata nan dai, itada Ubanta ne" "me ya faru?" Young Abba ya tambaya idanun sa na karakaina a kaina. "Idan ka ji abinda ta yi kaima sai ka daina jin tasayin ta, Azumi ta bata wayon ta, ta kuma batawa kanta don da ta mutu a irin mutuwar da ta so wa kanta da yanzu ta jima a wutar jahannama". "Ya Subhanallah" inji Young Abba da Nasara a tare, "me yayi zafi haka Ummati?" "Fiya-fiya ta sha don ta mutu kada ta auri Umar. Da kyar aka ceto ran ta. Sakamakon haka yanzu zancen dana ke maka Faruku ya bar mu, ya bar gida ba mu san inda ya fada ba, a cewar sa don kada Baban ta yayi mata auren dole dashi ya zabi ya bar gida, mu kuwa me zamu yi wa Boddo mu huce banda mu sallamata ta yi rayuwar ta yadda take son ta?" Young Abba sai jera "subhanallah" yake yi ba kakkautawa, yace "Boddo why? Kin san hukuncin suicide kuwa a wajen Ubangiji? Me yayi zafi a kan dan uwan ki?" Cikin kuka nace "Young Abba ba haka bane inada wanda nake so ne, sun kasa fahimta ta""ko kina da wanda kike so you shouldn't attempt this, sabida da kin mutu me zaki ce wa Ubangiji? Nima bana bayan a yi miki auren da bakya so, kuma bazan bari ba, amma maza-maza kiyi istigfari ga wannnan dingimmemen laifin da kika aikata". Nasara ta rungumo ni a jikin ta ganin yadda Young Abba ya bude min wuta sosai, ita sai take Magana cikin lallashi tana cewa "ina miki kallon mai hankali Boddon Omar, na san soyayya, i can relate with you amma ni kam kin ganni ko sigari bazan sha don na illata kaina akan namiji ba, ba zan kuma taba zabar sa akan rayuwa ta mai daraja ba balle iyayen da bani da kamar su. Maza kiyi istigfari". A fili na soma jero "ASTAGHFIRULLAH" suna taya ni. Kalmar da tunda na sha fiya fiya ban ambata ba. Young Abba ya miko min hannun sa na kama a hankali ya mikar da ni ya ja ni gefen sa ya zaunar dani a kwibin sa, yace, "Boddo do you want to stay with us? We don't have a child yet, and you know ina son ki tun kina karama ko?. An yi min relocation na wurin aiki na daga US Diplomatic Mission na garin Lagos zuwa babban reshen mu na birnin Washington D.C. Boddo zaki bi mu? Kin ga sai ki shiga makaranta ki zauna da Antin ki Nasara ki manta da wata soyayya kin ji Boddo? You are still a baby, baki kai ga cimma komai a rayuwa ba, tunda baki cika shekaru ashirin ba har yanzu, wannan rayuwar da kika jefa kan ki ta kuncin soyayya ba taki bace, ba kuma inda zata kai ki, kuma ko wanene ya sace min zuciyar diya ranar da Allah ya nuna min shi zan saka kafar wando daya da shi tunda ya hanata karatu sai soyayya". Kunya sosai naji na rufe fuska da tafuka na yace "Ummati dama sallama muka zo miki nida Nasara, to ga karin 'ya mun samu. Ku kwantar da hankalin ku Omar ba yaro bane ba zai kai kansa mahallaka ba. Ina tabbatar muku da cewa zai kula da kan sa a duk inda ya tafi. Kuma hukuncin da yayi ya burge ni, ya zabi farin cikin 'yar uwar sa akan nasa, wannan ya nuna shi mai kaunar ta ne kuma insha Allahu a hankali Boddo zata so Omar zata aure shi don radin kanta. Yanzu ki amince mana Ummati mu tafi tare da ita?". Ummati ta kyabe baki ta ce "ni ina ruwana abinda ba'a kaina take zaune ba, ku dai je can Abujar ku fara gaya musu in mahaifinta ya barta ni meye nawa a ciki? Na riga na sallama Boddo" "kiyi hakuri Ummati ki daina fadin haka a kanta". Inji Young Abba. Ummati tace "zan yafe mata kadai ranar dana ga Faruku a gabana ya dawo gida yayi aure tunda ba ita ce autar mata ba". Haka kawai naji hankali na ya nutsu da bin Young Abba da maidakin sa Nasara zuwa US. Ina fatan hakan ya zamo min hanyar samun kwanciyar hankali na har abada. Yasa ya zamo silar da zan manta da "Dream Man" dina nima in hutawa rai na. Ya sa kafin in dawo gida Ya Omar ya riga ni dawowa. Ya kuma sa tafiyata ta zama hanyar manta komai da ya faru dani a baya. (Bansan cewa wata kaddarar kana gudun ta tana bin ka bane. Ban san cewa mun riga mun saka kafar wando guda ni da kaddara ta ba. Kuma ita din tamkar Zanen Dutse take dan adam bai isa ya kankare ta ko ya tsallake ta ba). Tun a daren na hada komai nawa tsaf, da taimakon Aunty Nasara. Ummati sai cewa take "Allah raka taki gona". Ko don rashin mutuncin da ummati ke mini naji ina son tafiyar, idan da hali kada in sake dawo mata gida. Amma kuma bazan iya barin Najeriya ba tareda na je na nemi gafarar Abban mu ba koda kuwa zai koro ni ne da sanda. Aunty Nasara na zuge trolley dina taga ina sharar hawaye, tace "Dotty, ki kwantar da hankalin ki kin ji, na miki alkawarin zama makwafin Wasila insha Allahu. Sannan zan tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwar ki ta tafi daidai kamar ta kowacce mace 'yar musulmai jikar musulmai, da yardar Allah kuma zaki samu auren duk wanda kike so Young Abba ba zai taba bari a tauye ki ba". Nace "ba damuwata ba kenan Aunty Nasara, ina tunanin yadda zan cigaba da rayuwa alhalin Abba na ya koreni, yana cikin fushi dani, son samu mu fara biyawa ku tayani in bashi hakuri, ko bai bar ni na zauna ba ya yafe mini, ya yarda cewa tafiyar Ya Omar haka Allah ya tsara don babu kaddarar aure a tsakanin mu". Nasara tace "zan yi ma Adam magana mu fara tsayawa a Abuja". Muka kama hanya a washegari muka bar Gembu. Tafiya dasu Young Abba tafiya ce mai dadi kwarai, kana tare dasu kana daukar ilmin zamantakewar aure nagari, akwai kyakkyawar fahimta tsakanin sa da maidakinsa, ana tafe suna ta raha suna tsokanar juna cikin soyayya, wannan abu ya kara dasa min son aure na soyayya ya kuma sa nayi ta raya abubuwa da dama a raina inda ace nice tare da "Mr Radio" kamar yadda Ya Umar ya kira shi. A haka muka isa Kano muka kwana washegari muka karasa FCT. ****** ABUJA D aga Abba har Anty Wasila suna gida yau, kasancewar karshen mako ne, Maryam Jamila ce ta fara ganin fitowata daga mota ta kuwa kwaso da gudu tana ihun murna ta rungume ni. A haka muka karasa cikin main parlour kamar zata cinye ni don murna. Abba da Anty suka amsa sallamar Young Abba nidai sai rabewa nake a jikin bango. Anti ta taso ta bude min hannuwa ina hawaye na shige cikin jikin ta. Ina kallon Abba na satar kallon mu da harara amma ya maida hankalin sa kan dan uwan sa Adamu da ya kwana biyu bai gani ba yana "lale da mutan Legas". Nasara ta gaishe shi nima na zamo daga jikin Anti Wasila na durkusa a gabansa ina hawaye na ce. "Abba na ina wuni!" Sai kuka. 8 Kuka nake mai motsa zuciyar duk mai sauraro balle zuciyar Uba mahaifi. Ina kallon yadda fuskar Abba ke takunewa cikin yanayi na rashin jin dadi ga kunyar kanin sa da maidakin sa don baya so maganar ta hada mu a gaban su, bai san cewa Ummati ta riga ta gaya musu komai ba. Young Abba yace "Dr. Siyama tayi kuskure kuma ta karbi kuskuren ta ba zata sake ba, ka yafe mata". Abba yace "Adamu ka fita a maganar Siyama, bata da kirki bata da lissafi, tunda har Omar ya bar ni a dalilin ta itama bazata zauna min a gida ba, ta tafi Mambilan tayi ta zama idan zaman kauye dadi ne. Gatan dana nuna mata shi ya bata kwarin guiwar bijiremin da bijirewa umarni na, to na janye gatan ta je tayi rayuwar ta yadda take so". Young Abba yace "ni zan dauki Siyama ta zauna a hannu na ta cigaba da karatu, idan ta samu miji zan mata aure, auren dole bashi da ma'ana Yaya, na san kana son Omar kana kuma yi musu hange mai kyau ne amma dukkannin su suna da 'yancin su rayu ba ta hanyar auren juna ba, suna da damar su zabi abokin rayuwa wanda zuciyar su tafi kwantawa da shi". Abba ya ce "saidai ta bi ka din kuwa, ban haifi dan da saidai ni in bi shi ba, ba dai shi ya bi ni ba. Kullum na ganta a gaba na bacin rai zata dasa min na kore min Omar". Na gurfana gaban Abba na kama kafar sa nace "Abba na yi alkawarin nemo maka Omar, ko bajima ko ba dade, nayi alkawarin dawo dashi gida, ni dai fata na ka yafe min Abba, ka daina fushin nan da ni don Allah…". Na kama shi na kankame kamar bazan sake shi ba sai ya furta ya yafe min din. Abba ya ce afuwata daya ce gare ki Siyama in ga Umar ya dawo gida, na janye kalamai na kamar yadda yake so". Abba ya soma matsar kwallah wanda hakan ya kara gigita ni na rushe da kuka mai tsanani. Nace "alkawari ne zan dawo maka da Dan ka, amma ban yi alkawarin zan aure shi ba". Cikin mamakin taurin kaina Anti Wasila ta daka min tsawa tace "Boddo ke da kike neman afuwa kuma kike tada bara bana, Abba yana jin ciwo in kika ce bazaki auri Umar bane gara ki bar ra'ayin ki a ran ki tunda ya ce ya janye kudurin sa". Kowa ya hau yimin fada har Young Abba, yace tunda na karbi maganar kuma nace ban amince da auren dole ga kowannen ku ba, kada ki kara maimaita wannan maganar. Afuwar sa muke nema ba tada tsohon zance ba". Abba yace "in dai bazata zauna min a gida ba taje ko ina zata je bani da matsala da wannan" ".....wanda ke nufin Abba baka yafe min ba? Na tuba Abba na bi Allah na bi ka. Ka furta yafiya a gare ni don in ga albarka a rayuwa ta". Abba yace "zan yafe miki only ranar dana ga Da na Omar a cikin gidannan, na aura msa matar data fi ki" aka kada aka raya Abba ya ki canza maganar sa. Amma ya amince in bi su Young Abba duk ma inda zasu je ba matsalar sa bace. A hakan cikin rashin kwarin jiki kowa ya kwana a gidan. Don hukuncin Abba bai yi mana dadi ba, bai yi wa kowa dadi ba, bana so ina tafiya a duniya babu afuwar sa a jiki na, don haka na dauki aniyar nemo Ya Omar ko ta halin kaka. Washegari jirgin Azman muka bi zuwa jihar Ikko. Cikin sati biyu Young Abba ya gama yi min duk wani shiri na tafiya tare da su a cikin alfarmar iyalin sa. Ranar wata Litinin babbar rana muka sauka a birnin Washigton D.C din Amurka, inda acan ne headkwatar US Diplomatic Mission yake. Gidan Young Abba bashi da nisa da ofishin su. Tun saukar mu a kasar Amurka na samu nutsuwar data yi min karanci, Aunty Nasara kuma ta maida hankalinta kacokam kan zaryar asibiti akan matsalar haihuwar ta don ita ke da matsalar ba shi ba. Ta kan ce a kullum in yi mata addu'a Allah ya bata haihuwa ko guda daya ne, idan Young Abba yayi mata kishiya mutuwa zata yi sabida kishin sa. Kalaman ta na bani dariya a yawancin lokuta, sai kuma in ga in nice nima hakan ce zata faru dani, muddin wanda nake so na aura kamar ta. Sau tari ni kadai nake wuni a gidan, ba da jimawa ba Young Abba ya mallakamin wayar hannu, yace sabida su dinga jin halin dana ke ciki idan basa gida. Wato kadaici da kwanciyar hankalin dana samu sai ya dawo da bara bana. Na koma mafarkaina da shi, abin har yayi ta'azzarar da ya zarce na baya. Na kuma fi jin closeness dina da shi cikin zuciyata a garin Washington fiye da gida Najeriya. Saina koma nemawa kaina hanyoyin debe kewa da zasu rage min feelings din dana ke ji a kan sa, na abokantaki Talbijin a halin yanzu. Na zama mai bibiyar VOA TV: AMURKA. Kullum ranar Allah sai na kalli labaran VOA TV har Aunty ta canza min suna zuwa Siyama-VOA, don tace ta ga alama ina yin su sosai. Na sha kona mana girki akan kallon TV Programmes na VOA. Har ta kai ta kawo Aunty Nasara ta daina bar min girki yanzu, ban san abinda ke fizgata ga son sauraron su da kallon su ba. Face wani abu tamkar magnet dake jan zuciyata yake fizgata akan gidan talbijin da radio na VOA tunda na tabbata bana raba dayan biyun a can ne na fara jin real sautin sa a radion Abba na. ******* SILENT ENCOUNTER K imanin watanni takwas kenan da dawowar mu birnin Washington. Na gyagije na zama goyon 'yar gayu Aunty Nasara na yi tsaf da ni kwanciyar hankali ya wadace ni. Weather din birnin Washigton ya ratsa fatar jiki na. A yau shirin da VOA suka sako a safiyar yau is a Live TV Programme. Kwance nake a cikin sofa-bed ina cin gugguru, ina kuma kallo, a gefe ga hot coffee na hada sai turiri yake. Na mike zaune ina kurba ina cin gugguru kafin kuma na maida hankali na ga makekiyar talbijin din dake manne jikin bangon daki na na gidan Young Abba. Kimanin watannin mu takwas da zuwa Washington kenan. And there was where it all happened. Today I saw HIM!!! Bayan sallama ga masu saurare, tare da gabatar da kan sa a matsayin sa na Broadcastern VOA mai amsa sunan "Hamzah Almustapha Mawonmase". Sai ya fara gabatar da shirin sa LIVE na vedio tare da mara lafiya "Adam Toobin" mai fama da lalurar Celebral Palsy...... cikin harshen turanci daga sashen turanci na VOA. Hamzah ya cigaba da kwararo bayani kan lalurar Toobin..... "....... OVERCOMING OBSTACLES.....". Taken shirin sa kenan. -"LIVING WITH CELEBRAL PALSY.....!!!". Shine shirin da Hamzah yake gabatarwa kai tsaye (live) tare -da mara lafiya Adam G. Toobin wanda ke kwance cikin wheelchair mutumin kasar Amurka ta kudu, wanda ke rayuwa shekaru talatin cikin cutar 'Celebral Palsy' ba tare da motsi ba. Baya motsi (movement) kamar kowanne dan adam bai kuma taba sanin menene lafiya ba, amma yana magana daga cikin kujerar sa, yana kuma gayawa duniya yadda yake rayuwa cikin wannan larura, yake kuma tafiyar da al'amuran kamfanin sa a haka, tare da koyar da ma'aikatan kamfanin yadda zasu tafiyar da al'amuran kamfanin, yana gaya musu hanyoyin magance matsalolin da suka taso wa kamfanin in oral form. Hamzah na tattaunawa da shi yana bada feedback yana kuma daukar sa a hoto da vedio din sa. (Shi ba fari bane, baki ne cikakken dan Najeriya, dogo haka siriri mai zankadeden dogon karan hanci, wanda ya tafi ya dan rankwafa kadan a saman bakin sa sabida tsayin sa). Mutumin nan ne mai tarin gargasa a fuska da saman giran idon sa, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana, maimakon Hausar dana san shi da ita yau turanci yake yi zallah. Bashi da kauri kuma babu annuri a fuskar, a lokacin da yake gabatar da shirin "....... OVERCOMING OBSTACLES...., LIVING WITH CELEBRAL PALSY.... !". Tamkar yana taya client din sa Toobin alhini da juyayin halin lalurar rashin lafiya na har abada da yake ciki. Yana sanye da farin siririn gilashi na kara karfin gani. Wanda na tabbata yawan duban camera ne ya yi mujazar lalaurar idanun nan. Sanye a jikin sa 'Black - Grey Japanese Suit' ne, ya matse wuyan sa daga ciki da tsukakken neck-tie fari sol. Exactly yadda nake ganin sa cikin MAFARKI na, exactly yadda nake ganin sa a IDO BIYU na, wato inimaginations... haka exactly yadda nake picturing din kasancewar sa! Sannan muryar bata canza daga yadda na santa na kuma haddace ta ba. Wannan shine HAMZAH ALMUSTAPHA ........ da na dade ina baku labari, wanda na rayu shekaru rututu cikin mafarkan sa, wanda na taba tsinkayar muryar sa a kunnuwa na daga gidan rediyon VOA watanni masu yawa a baya. Yau dai ga Hamzah na gani cikin idanu na, Hamzah a kan screen din talbijin din daki na, a kan allon talbijin dina.... In reality ba'a mafarki ba, ba kuma a sautin murya ba. Yau na ganshi ne ganin idanu na. Ina kallon sa ina kuma jin sa. Kwarai sunan da ya ambaci kan sa da shi a wancan lokacin ma da na kasa tunawa kenan “HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE....!!!” Amma a wancan lokacin kidima da ikon Allah basu bani ikon rikewa ko tunawa ba!!! Wani abu tamkar zubar kankara ya bi ilahirin jikina ya sankarar da ni a inda nake kwance. Zuciya ta tamkar ta fito ta baki na. Yawun baki na ya kafe rayas. Nayi kokarin hadiyar miyau don jika makoshi na da ya bushe kamas, amma na gagara yin hakan saboda kidima. Sakamakon haka na jin numfashi na na shirin barin gangar jiki na. Ko wanene wannan shine 'dream man' dina, da ya hana rayuwata sukuni, ya rabo ni da gidan mu da iyaye na, ya raba ni da Ya Umar, ya jefa rayuwata cikin kaka-nikayi, shine mutumin da ke zuwa min kullum cikin MAFARKI KO A IDO BIYU! Shine wanda Ubangiji ke nufin al'amura da dama a tsakani na da shi tun ban san kai na ba, wadanda ban san farkon su balle karshen su ba. Iya abinda na iya tunawa kenan sai na shide cikin emotion, kowacce gaba ta sassan jikina na maimaita kiran sunan "Hamzah Mawonmase!" Don kada in kara mantawa ko ya kara bace min in sake shiga halin ha'u'la'i. To amma sanin da na yiwa Hamzah a yau bashi da wani amfani tunda dai ba zan dauki kafa a matsayi na na diya mace bafullatana mai daraja in tafi ofishin VOA neman sa ba, in ganshi in ce masa me? Ai sai kima da daraja ta na diya mace su fadi. In nayi haka na siyar da mata, na siyar da fulanin Mambilah wadanda ko a cikin fulani daban suke. A hakan dai zan cigaba da kwankwadar azabar soyayyata ni kadai, har zuwa ranar da numfashi na zai kare da sunan Hamzah Almustapha a cikin sa. Ko babu komai yanzu zuciyata ta samu sa'idah, na cewa Hamzah mutum ne bil adama, yana rayuwa ne a gidan radiyo da talbijin na VOA. Kuma muna cikin kasa daya. Kuma Allah ya nufa na gan shi in a silent way. Zuciya ta ta yarda shine mutumin mafarki na dana rayu da shi tsayin shekaru kusan goma a zuciya da kwakwalwata. Koda wannan kadai na tsira ya ishe ni kwanciyar hankali har karshen rayuwa ta; HAMZAH ALMUSTAPHA is a human, living in America. ******* EMOTIONS S ai ya kasance tun daga ranar dana gan shi a talbijin nake bibiyar sa, nake bibiyar komai nasa da wani irin emotion, yawanci na kan ga hotunan sa tare da sauran VOA TEAM na talbijin ko na radio, na kuma fahimci ba'a bangare daya yake broadcasting ba, yana yi a sashen hausa, yana kuma yi a sashen vedio na turanci. Wata irin walwala ta same ni a kwanakin nan, ba abinda ke bani nishadi irin kasancewar Hamzah mutum ne a raye ba aljani ba ba jinnul Aashiq ba, na koma bani da abin yi muhimmi irin na dinga bibiyar shirye-shiryen sa. Kullum da sabon shirin da zai kawo mai matukar muhimmanci da kayatarwa. Daga yadda yake gabatar da muhimman shirye-shirye a gidan radiyon da talbijin na VOA zaka fahimci dan gaban goshin su ne. Kusan duk wani shiri mai muhimmanci shi yake gabatar da shi. Watakila wannan ba zai rasa nasaba da zazzakar muryar da Allah yayi masa baiwar ta ba, mai wata irin sassarfar magana wadda ke karawa shirin sa armashi da jan attention din al'ummah, murya ce mai taushi da sanyawa dan adam nutsuwaka saurare shi koda baka ra'ayi, sassarfar ta kuma bata hana a gane me yake cewa cikin dadin rai. Sai take kara mata wani irin armashi. Hamzah na tafiya da zukata da dama ba tawa nikadai ba, na gane hakan ne ta hanyar comments da yake samu na miliyoyin mutane a shafin sa na Twitter da na Instagram a duk lokacin da VOA suka saki shirin sa. Babu cikakken bayani a kan sa a google amma akwai cikakken bayani na aiki da profession din sa a shafin sa na LinkedIN. Matakin Digiri dai-dai har guda uku reras yake rike dasu akan aikin Jarida daga Jami'ar 'Sussex'. He's a Chevening Scholar wato wanda yayi karatun sa na Masters daga tallafin 'Chevening', yayi Ph.D daga tallafin 'Commowealth Scholarship', cikakken dan Nigeria daga jihar Filato (Jos). Ya yi aiki na lokaci mai tsaho da British Broadcasting Corporation, yayi da Radiyon Jamani (Deustche Welle) kafin ya bari duka ya dawo uwar su VOA. Wadannan sune muhiman bayanan dana samu a kan Hamzahn da zuciyata ta ki hutawa a kan sa, daga shafin sa na professionalism wato LinkedIn. Suka zame min ababen taya hira, ababen debe kewa, ababen saka nishadi, hotunan sa kuma suka cika wayata fam. Wadanda nake sauke su daga shafukan sa na yanar gizo. Murmushin sa kadai mai kokarin narka zuciya ta ne, wanda ke tafiyar da numfashi na na wucin gadi. Na yarda ba abinda ya kai soyayya dadi a zuciya da ruhi. To ina ga inda take samun martani daga wannan masoyin?Gare ni dai, ni kadai nake ninkaya a koramar da zakin ta yafi na zuma, gardin ta yafi na madara. Koda Aunty Wasila ta aikowa da Young Abba sakamako na na WAEC da NECO babu wani abin a zo a gani a cikin su ban damu ba, a yanzu kam ko diyar Qaruna bana jin ta rufa bayana a kwanciyar hankali da samun contentment na rayuwa. I'm feeling myself on top of the world of happiness and excitedness. Tunda kullum idanuwa na na kallon abinda suke so, kunnuwa na na jin sautin mutumin da suka fi son ji a duniya bakidaya, wani abu wai shi karatu na rantse baya gabana idan ba yadda zan mallaki Hamzah ba. Uwar dakina Nasara Alkali, ta dade tana lura da sabuwar rayuwar dana fada, kamar bana cikin tamu duniyar, kamar a wata duniyar nake rayuwa nikadai, na zama addicted ga wayata ko bandaki zan shiga da wayar nake shiga, idan kuwa akan masai nake zaka sameta like ga kunnuwana ina sauraron Hamzah - Mawonmase. Duk abinda nake ciki ashe aunty Nasara na lura dani. Yau da Young Abba ya fita aiki sai ta shigo daki na cikin shiri, a daidai lokacin da Hamzah ya kammala shirin sa na safe wanda yayi akan janyewar yajin aikin jami'o'i na kasar Najeriya. “Mrs VOA, ko zan samu ki rakiyar ki zuwa Walmart Supermarket?" Nasara ta tambayeni tana kada mukullan motar hannun ta, tayi shigar ta islamically kamar kullum ta hanyar yin rolling da bakin mayafi akan doguwar riga samfurin kasar Oman ruwan kwaiduwar kwai data ke sanye da ita. Tunda Hamzah ya gama shirin dana ke saurare, ba matsala zan iya raka ta. Don haka nace Aunty bani mintuna biyu in dan watsa ruwa, nima ina son fita in motsa jiki na, yau kwana goma kenan ban je koina ba". "Sai sauraren Hamzah Mawonmase!". Anty ta fada cikin kirjin ta har sautin maganar ta ya dan fito. Na juyo daga kofar toilet bayan na zari towel daga ma'ajiyar sa, nace "na'am Aunty magana kike yi ne?" Ta girgiza kai tace "Oh! Ban ce komai ba fa. Yi maza ina jiran ki a mota". A gurguje nayi wankan na fito wani wajen ma kumfa bata fita ba, a haka na saka jacket wadda ta kai min har kasan guiwa da wandon Jeans baki. Na saka hijab wanda iyakacin sa kafaduna, na dauki wayata da 'yar karamar jakata 'Chanel' na bi bayan Anti zuwa mota. ***** "NASARA ALKALI" (MY SECOND LIFESTYLE INFLUENCER) M una kan hanyar mu ta zuwa ‘Walmart Supermarket' dake kan titin Riggs Road, South Dakota, inda a can Anti Nasara ke yin duk wani provision din kayan abincin mu dana amfanin ta. Anti ta dube ni da wutsiyar idon ta. Kafin ta maida hankalin ta kacokam kan tukin data ke yi cikin gwaninta. Sannan ta kira sunana cikin siga mai nuna muhimmiyar magana take son yi da ni. "Sai yanzu na gane dalilin da yasa Abban ki ya zabi yayi fushi da ke har ya kore ki Siyama. Nima kuma ina gab da yi; fushi da kora". Na zaro ido ina kallon Anti cikin tsoro da razanar maganar ta. Me nake shirin ji haka ni Siyama! Aunty Nasara bata damu da reaction dina ba kan maganar ta, ta cigaba da cewa. "As long as mace zata bari wani namiji da ba mijin ta na aure ba ya shiga zuciyar ta, ya shiga cikin rayuwar ta yayi kane-kane irin haka ya hana ta cigaba, ya hanata wani tunani bayan nasa, ya shiga tsakanin ta da iyayen ta, ya yi galaba a kan karatun ta, ya dauki ragamar zuciyar ta daga kan turba sahihiya, wannan mace macen sunan ta sorry domin mara hankali ce, kuma wadda bazata iya fighting da emotions din ta ba. Maimakon hakan, it's the emotions that drives her, not her own humble self, su suke jan ragamar ta tare da wannan namijin. Musamman wanda bata cikin rayuwar sa, ba kuma son ta ya ce yake yi ba". Anti ta dakata ta yi kwana ta dauki titin Walmart Supermarket, ta bar kalamanta na ragargaza ni, sannan ba tare da ta damu dani ba ko halin da ta jefa ni ta cigaba da cewa, "Siyama kin dauki hanya ta ruguza rayuwar ki, kin bar emotions suna driving din ki. Kin bar ALLAH Siyama tunda kin bar koyarwar AL'QUR'ANI, bayan cewa sune kadai abinda idan ka rike komi na rayuwa zai zo maka da sauki". Jiki na bakidaya ya saki, gwuiwoyi na sun yi sanyi kalau. Buri na kawai Aunty Nasara ta dauki hanya dodar kai tsaye ta gayamin me nake yi har haka da har take tunanin na bar ALLAH na dau hanyar rusa rayuwa ta. "Amsa ga tambayar da kike yiwa zuciyar ki a yanzu Siyama, yaushe rabon ki da karanta littafin Allah, yaushe rabon ki da yin sallahr dare don gayawa Allah bukatun ki da rokon sa a kan ya sassauta zuciyar mahaifin ki? Siyama kin fadi WAEC kin fadi NECO amma ba abinda ya dame ki sabida kin saka soyayya a zuciyar ki, soyayyar da bata da madafa don kuwa Hamzah Almustapha na gidan Rediyon VOA; BA MUSULMI BANE CHRISTIAN NE (Ahlil Kitabi) dake bin Addinin CHRISTIANITY." Don haka in zaki shiga hankalin ki ki shiga, in zaki dawo hayyacin ki ki dawo. Ki kama Allah ki kama iyayen ki. Ki maida hankali wajen gyara kuskuren da kika yiwa mahaifin ki, ya fiye miki alfanu duniya da lahira akan bibiyar shirye-shiryen Hamzah dare da rana, ya fiye miki alkhairi ga cigaban rayuwar ki, ya fiye miki maslaha da Ubangijin ki. Yara mata irin ki sun fi goma dana samu labarin sun yi RIDDAH a kan soyayyar wannan mushrikin a Najeriya. Don baiwar iya magana da ta halitta Allah yayi masa karshe, amma arne ne Siyama, ba addinin ku daya ba, ko kusa bai cancanci soyayyar ki ba. Siyama Gembu, 'yar musulmai ce rainon musulunci. Umar Faruq shine mijin da ya dace da rayuwar ki kamar yadda Abban ki ya hango miki, abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala da gwauron dutse ba zai hango ba. Shiyasa aka ce ta yaro kyau take amma bata taba yin karko. Don haka Siyama a matsayi na na UWA ba MARIKIYA ba nake baki shawarar ki kama abinda zai amfane ki ki manta da Hamzah, ki manta da Mawonmase, har yanzu ke yarinya ce da take kan gabar gina rayuwar ta. Baki kai ga cimma komi a rayuwar ki ba. You are still a Teen. Na sama miki islamiyyah school a New York na gama komai zan kai ki gobe, a tsayin watanni shidda kacal ake haddar Al'qurani, ta wasu musulman Canada ce Dr. Ismail Memon da dan sa Dr. Shaykh Ibrahim Memon Madani, su suka bude ta a birnin Buffalo, New York. Kafin watanni shidda nake son ganin Hafizah Siyama a gabana, in ga sabuwar Siyama mai Qira'ar Madani, wadda iyayen ta zasu yi alfahari da samun ta, kasancewar ta mahaddaciyar Al'qur'ani. Idan kin kammala wannan makarantar zan maida ke aji shidda na sakandire da sunan transfer daga Regent, ki sake zana jarrabawar kammmala sakandire sannan ki fara karatun Jami'a. Wannan shine tsarin da na yi miki nake kuma fatan ki bani hadin kai a kan sa, ko in mayar da ke Mambillah!!!". ****** MURFIN LITTAFI NA DAYA Ban iya tsayawa kallon yanayin da Siyamar mu ta fada ba na ajiye Biron, ba don komai ba sai don nafi Siyama kidimewa. Abinda ban sani ba; Shin SIYAMA zata bi tsarin uwardakin ta Nasara don a zauna lafiya da ita? Ko kuwa a'ah itama zata bi sahun masu yin RIDDAH ne kamar sauran matan da aka yi ittifakin sun yi RIDDAH a kan sa??? Tunda dai mun ga har fiya-fiya ta sha don ta tsira da shi da fantasie din ta a kan sa??? Sanin hakikanin wannan amsar sai ita kadai ‘yar mutanen Mambillah; Aisha-Siyama Mamman Gembu. Don haka mu biyo Boddon mu-Siyamar mu a littafi na biyu don jin yadda zata wakana tsakanin ta da ‘Dream Man' din ta. Shin da gaske Hamzah kafirin ne ko kuwa shaci-fadi ne irin na Nasara don ta samu hanyar raba Siyama da emotions din ta??? SAKACIN WAYE? 2 TARE SUKE DA LITTAFI NA DAYA. TAKU HAR ABADA SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI). In kinji tashin hankali, razani da kidimewar da suka sameni a wannan dan tsakanin da nasara ta dauka tana magana to guda daya kenan. Na shiga abinda ake kira bewilderment8 na zuciya da ƙwaƙwalwa. Na shiga coma ba dan na kwanta a kwance ba, sai don kasancewar ilahirin gaban jikina sun daina aiki na kame a kujerar da nake zaune.wani bangare na zuciya kuma yana Mai gasgata kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakin anti na. Na yarda iyakar gaskiyar da kowacce uwa zata fadamin kenan, iyakar mataki da kowacce uwa ta gari zata dauka kenan don tseratar da 'yarta daga fadawa halaka, shi nasara ta dauka take Kuma aiwatarwa a halin ynz. Ban tashi tare da mahaifiyarta ba amma Sai Allah ya hada Ni da wasu irin matan uba na gari wadanda irin su sun yi ƙaranci a wannan zamanin da muke ciki, wadanda Kullum burin su shine su dora ni akan hanya kuma turba sahihiya idan na karkace, in kasance yarinya ta gari abin koyi, abin alfahari gare su da mahaifina..iyakacin rudani na shige shi a wannan ranar, rudanin daya kusa fiddani a hankalina. Ba musulmi bane a ina ya samo sunan sahabin manzan Allah kuma baffansa sayyidina Hamza (A.S)? Ina ya samo sunan shugaban halitta (Almustapha) a surname din sa??? Duka wannan ma idan an bi salsala ai basu da wani amfani a wuri na, ba kuma zasu amfane Ni da komai ba.Tunda kuwa hamza bai taba sanin da wanzuwata a duniya ba,Hamza bai ce yana son siyama ba, Hamza bai Sanni ba....A takaice Ni kadai nake kida na, nake kuma taka rawa ta iri - iri akan sa, cikin wata duniya ta fantasy and imagination wadda ban taba jin mai irin taba sai ni. Amma kuma ina tababa hadi da waswasi a cikin al'amarina da wannan bawan Allah, tabbas akwai wani BOYAYYEN SIRRI wanda Allah kadai ya san shi, ya kuma ke nufi a kaina dashi hamzan, in ba haka ba ta ina ya kutso ya shigo cikin mafarkaina, na rayu shekara kusan goma ina mafarkinsa, na kuma Ganshi exactly a talabijin yanda nake ganinsa a mafarki da imaginations dina??? "Ya Allah taimakeni kafin na haukace!" Na fada a fili, cikin kama kaina dake neman rabuwa gida biyu saboda sarawar da yake min, ina girgizawa da karfi ina qara girgizawa da karfi ko hakan zai rage nauyin daya yimin. Anty tace mata dayawa sun yi RIDDAH wato sun bar addinin musulunci akan hamza, wanda ke nufin ta san shi farin sani, ta kuma san duk abinda nake ciki Akan sa, domin har zana shi nayi da pencil na kafe a cikin Frame din gefen gado na, sannan cikin wayata da laptop dina duka hotunan Hamza mawonmase ne,wanda nake saukewa daga cikin hotunan sa na shafukan social media, ga kuma kona mata girki da nake tayi akai akai tun daga lokacin da young Abba ya mallaka min waya, sannan a fili nake kunna Muryar tasa sautin na tashi daga Radio na, ko talabijin din gidan dake falo, in kura masa ido kamar tsohuwar mayya data ga Nana ko kuwa kamar mai shirin hadiye shi don so. A zahiri duk wata uwa indai mai kula ce akan al'amarin 'ya'yanta to tabbas zata yi saurin gano inda na dosa akan HAMZA VOA, ba wai labaran nasu nake kallo ko nake saurare ba, tunda kuwa in bashi yake labarai ba ai bana ko tsayawa in kalla ko in saurara